BUDURWAN SIRRI Littafin Shuraih Usman l Page 1 . Gargadi:- wannan littafi mallakar shafin hausaebooks ne don Allah kada wani ko wata ya juya wani bangare ko barin littafin na batare da iznin wannan shafi ba . Na fito daga gida ina sauri zan karasa wajen wani abokina domin na karbi wayata , nan na tsaya a bakin hanya ina neman lift, ban dade da tsayawa ba kuwa na samu wani dan anguwarmu yazo wucewa na tsayar da shi . "Abasu kala, dan Allah kabani wayana mana ya kanamin irin haka ne kaifa kasan in babu wannan waya toh fa abubuwa da yawa zasu rikirkice domin kuwa akwai document dina da yawa aciki . Kuma mutae da yawa suna jirana" Na fada a lokacin dana ke tsaye a shagon su umar shagon hada takalmane wanda wani dan cirani yazo ya bude cikin ikon Allah sai kuwa jama'a sukai ta saka yaransu cikin wannan shagon har takai yanzu wannan shago ta shahara wajen hada takalma . Umar wanda fuskarsa ya baci da dusar takalmi ya dubeni yace cikin muryar wasa " 99% wallahi wayanka tana gida , kuma yanzu dai kaga ina gugan takalma ne , babu yadda zanyi na saki gugan nan na je gida yanzu" . Kwafa kawai nayi cikin bacin rai na fice daga shagon sannan nayi natafiyata , don kuwa ba karamin haushi yabani ba, Nan na tuna yadda ya dauki wayar ina barci da safe , inda idanuwana biyu ne a lokacin toh da babu abunda zaisa na barshi ya dauki wayar . Gida na nufa cikin takaici da jimamin wannan abu da umar yayi mani, kamar daga sama sai naji wata zazzakan murya tana kiran sunana "Shuraih shuraih!! Shuraih!!!" . Cikin sauri na juyo don naga wacce take kirana amma cikin mamaki da zunzurutun al'ajabi sai banga kowa ba hakan ba karamin kidimani yayi ba amma sai na dauka tamkar kunnena ke yaudarana . Hakan na cigaba da tafiya ina isowa gida na wuce zuwa daki na , ina shiga naje na kwanta don kuwa yanzu lokacin hutu ne babu abun da nakeyi agida hakan yasa na ke dan rubutu da gajerun labarai na littatafan hausa na ringa post na su a social media, . Toh gashi dan iskannan ya dauke wayar kuma ya hanani,sai yawo da hankali yake yimini,kwanciya nayi bisa wata lallausar kujera dake girke a dakina, nan na kumshe idanuwa na domin kuwa barci nake bukata da nayi . . . . . . . . "INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UNN" Na fada alokacin dana farka na tsinci kaina cikin dokar daji babu gida baya babu gida gaba, . Na mike tsaye cikin tu'ajjibin wannan lamari ina mai tsananin mamaki da Al'ajabi don a tunani na ma mutuwa nayi, . Toh amma da mutuwa nayi ai dole, naga mala'iku hakan ya tabbatar mani. Ba mutuwa nayi ba , . Tayaya ni da na kwanta acikin dakina bisa kan shimfidata sannan na farka na ganni cikin dokar daji ai dole wannan abu ya rikita ni, . Babu abunda ya sake rikitani game da wannan daji face gani danayi wannan dajin sam bai yi kama da irin dajin dana saba gani ba, Don kuwa yanayin irin wannan daji a talabijin na saba gani cikin finanan kasashen waje . Ni shuraihu inkiya 99% sai dana firgita ainun da yanayin wannan daji na nemi waje na zauna ina ta tunani kala kala acikin zuciyata, can sai nayi karfin hali na tashi na tunkari gabas donni a tunanina, wai kodai barayi suka shigo gidanmu suka kamani suka zo suka ajjiye anan, . Sai wata zuciyar tace dani yo imma barayinne suka kama ni mene ne dalilin da yasanya suka kawoni wannan waje, nan dai na cigaba da tafiya ina ganin ababen mamaki, dogayen bishiyoyine suka cika wannan daji bishiyoyin kuma zaka gansu sai kamshi suke tamkar itatunan sandal, . Su kansu ganyayen wannan bishiyoyin korayene ababen sha'awa, sannan kasan wannan daji wasu irin ciyayi ne wayanda ban taba ganinsu ba , su wayannan ciyayi sun kasance jajaye, kuma koda na taka su sun durkushe take zasu sake dagowa . Koda na kara gaba sai na hadu da wani abun mamaki wanda yai matukar tayarmun da hankali Ba komaine na gani ba illa wata korama, wadda ruwanta yake zubowa daga saman wani katon dutse , shi wannan korama ruwansa garai garai ne dun kuwa koda na matso kusa da ruwan sai na ga hoton fuskata ya bayyana acikin ruwan tamkar an dauki hotona ne aka manna ajikin ruwan . Tsaban tashin hankalin dana tsinci akaina aciki a wannan lokacin yasa na kurma ihu, domin kuwa dauka nayi ko mafarki nake hakan yasa na cizi hannuna, a bisa mamaki sai naji zafi ya ziyarci hannanuna hakan ya tabbatar mani da cewa ba mafarki nake ba . Irin wannan koramar sam babu shi a kasar hausa, kuma na riga dana san a irin garuruwan da ake samun wayannan koramun, don kuwa na kanga hotunansu a jikin gorunan swan water da talabijin . Motsi naji daga bayana hakan ya tabbatar mani da a akwai wani halitta a bayana koda na waiga sai naga daga cikin wani surkukin ciyayi mitsin yake fitowa, nadai takure na matse sannan nayi na maza na daure don ganin mene ne ya ke fitowan . Abubuwan dana ga suna fitowa daga cikin wannan surkuki su suka saka naji cikina ya tsure, idan da ba dun ina da karfin haliba toh da babu abunda zai hana ban saki gudawa a wandona ba, amma duk da haka sai dana tsiyayo fitsari wanda ni ban ma san na tsiyayo ba . . Kai friends ku taimaka ina cikin firgici Shin ko kunsan mena gani alokacin toh ku jirani sati mai zuwa a cigaban wannan labari wanda zai runga zuwa maku duk sati Ranar Asabar da safe tare dani Shuraih Usman inkiya Shuraih 99% . Wannan kirkirarren labarine daga 99% Ku tsumayeni a page 2 Daga:- hausaebooks wepsite Da keffians News Teller BUDURWAN SIRRI Gajeran labari Marubuci Shuraih Usman @hausaebooks.cf @shuraih 99% Page 2 . Gargadi:- wannan littafi mallakar shafin hausaebooks ne don Allah kada wani ko wata ya juya wani bangare ko barin littafin na batare da iznin wannan shafi ba . Ba komai nagani ba face namun daji danginsu su Alfadari, Giwa, barewa,Zaki,maciji,damisa,kura kai duk dai wani dabba da kuka san yana rayuwa acikin daji, cikin gungunsu suka nufo ni ai koda ganin haka sai na juya da nufin na fada cikin wannan kogi dayake gabana . Amma me zan gani wasu kyawawan kananan kifaye na gani masu zakwa zakwan hakora lokaci lokaci zakaga suna kikkirta hakwaransu, abun yabani mamaki wai ace kifaye da hakwara amma sai na tuna wani american film din dana kalla mai suna PIRANHA . Koda naga haka sai nayi wani gefe da gudu don na tsere ma wayannan dabbobi da suka biyo ni da mugun nufi, gudu nake iya karfina don na ceci rayuwata daga hannanun wayannan dabbobin sai dana kai wajen mintin arba'in ina tsala gudu acikin wannan jeji amma wayannan dabbobin sai bina suke duk inda na shige, abunda zai baka mamaki da wayannan dabbobin shine . Su ba gudu suke ba don kuwa tafiya suke amma yadda kasan suna gudu domin kuwa duk lokacin dana waigo yayinda nake tsala gudu sai na hango su a kusa dani, Acikin wannan gudun danake yine, nazo gaban wani katon kogon dutse, batare da wani nazari ko shawaraba na afka cikin wannan kogon, . Ai koda shigata cikin kogon sai wani narkeken dutse ya mirgino da kanshi ya kulle bakin kogon ta yadda ko digon haske baya iya shigowa cikin wannan kogo, . Take duhu mai tsanani ya mamaye wannan kogon don kuwa ko tafin hannuna bana iya gani nan nacigaba da karanto addu'o'I kala kala duk wacce tazo bakina karantawa nake, har saida na karance gabadayan addu'o'in dana iya haka na runga jawo ayoyin kur'ani maigirma har zuwa wani dan lokaci . Koda naga an dauki dan lokaci banga komai ya faru ba sai na dan fara tafiya amma bakina babu abun daya ke furtawa face karatun kur'ani, . Tafiya nake ban san inda nake nufa ba, nidai nasan ina tafiya domin kuwa duhun daya mamaye wannan kogo baya bari naga maine ne agabana, na tsinci kaina tamkar wani makaho . Ni dai babu abunda nake furtawa face karatun kur'ani mai girma, koda na cigaba da tafiya acikin wannan kogon ina cin karo da duwatsu akalla na fadi yafi sau goma . Don kawai sai ina kan tafiya sai naji nayi karo da dutsi take zakaga na fadi gefe, a haka sai da hannuna na dama ya samu targade, Kukan zuci nake sosai ina tunanin lokacin da akeyimana wa'azi a islamiya zaka ji ana cemana muyi aiki mai kyau don kuwa akwai lokacin da mutuwa zata riskemu, . Sam sam bana son na mutu yanzu amma kuma gani nake tamkar tsakanina da mutuwata banfi zira'I daya ba zuciyata tana ta karantomin abubuwa da yawa na cutarwa da ka iya wanzuwa a cikin wannan kogon . ni ma'abocin karanta littatafan yakine nasha jin labarin yadda kogo take, kuma a yadda naga dutsin nan ya mirgino da kanshi yazo ya rufe kofar fita daga wannan kogo hakan ya tabbatar mani da cewa wannan al'amari akwai TSAFI acikin sa . Amma haka na dake na cigaba da addu'a da karatun kur'ani a zuciyana, kai in takai takawo ma har hadisai ma karantowa nake . Haka na kasance a cikin wannan kogon har na tsawon wajen sa'a daya wato awa daya sannan na fara tafiya, babu abunda yake zuwa zuciyana face tunanin ALJANNU . Don nasan inba lamari na Aljani ba babu ta yadda za'ayi na kwanta a gida cikin dakina bisa kujera mai laushi sannan na farka na ganni cikin kungurmin daji sannan ga wasu halittu na neman su halakani . Haka naci gaba da tafiya kwatsam ba zato ba tsammani sai cikin kogonnan ya gauraye da wani haske wanda koda Allura ne yafadi akasa toh za'a iya ganinsa . Hamdala nayi sannnan na gode ma Allah daya rabani da sharrin Duhu ya Allah karemu daga sharrin DUHU, . Toh sai a sannan naga ashema kogon nan cikinsa tamkar wani gidan hamshakin attajiri ne ko kuma mashahurin sarki , domin kuwa ganin kogon nayi a kawace da tsarin gida, . Shi dai wannan kogo dana afka sam daga ciki baiyi kama da kogo ba sai dai akirashi da fada domin kuwa wani kayataccen fada ne a ciki, nan na zama dan kallo nama daina mamakin yadda akayi na zo wannan daji na koma mamakin wannan fadar wanda tafi min kama da ALjannar duniya, sai a sannan ne na lura da komai dake cikin fadar fadan ya kawatu iya kawatuwa don kuwa tun da nake a duniya ban taba ganin wani fadan dayai rabin wannan kawatuwa, . Duk da na kasance masoyin kallon fina finan kasa shen waje irin na su yaki, toh ko a fina finan ban taba ganin irin wannan fada ba . Babbar fadace katuwa wacce zata iyacin wani karamin gari akarshen fadar wata kujerace ta zinare a girke wannan kujerar an kawata ta ainun don kuwa wasu irin takubba masu tsananin walkiya da kashe idanuwa aka sossoka su ajikin kujerar . A saitin kujerar daga gaba wata shimfida na gani itama kalarta kalar zinari an shimfidata takai har karken fadar, kai nan dai na tsaya ina ta kalle kalle , . Wani abun mamakin kuwa shine babu kowa acikin wannan fada sannan kuma ga a kowanne kusurwa na fadar an ajjiye wasu irin gumaka masu siffar mutane cikin shigan yaki, Koda na kare masu kallo dakyau sai na gane ashe wayannan kaman sojoji suke, . Nayi ta yawata wa acikin fadar har kafafuwana suka fara kuka, nan na zube kasa ina mai dafe da kafafuwana, sai a sannan idanuwa na suka kai ga wata, kofa wacce sam ban lura da ita ba yayin dana shigo cikin wannan fada, . Koda na ga haka sai na daure na mike tsaye na tunkari wannan kofa, ina isa bakin kofar na sanya hannu na bude , ko musu kofar baiyiba yabata wata kara "kikkir kikkirrrrrr" alamar ana bude kofar, kofa kofar ta gama wangamewa ta budu nan take nai arba da abun da ya tashi tayar mani da hankali ainun,kwakkwalwata ta kusan daina aiki,idanuwa na sukafara lumshewa a hankali tamkar me gyangyadi,gaba dayan lakar jikina ya mutu,!!! . Zazzakar muryace ta biyo baya "shuraih! Shuraih!! Shuraih!!! . SHIN A TUNANIN KU wai me nai arba da shine da har na rikice haka BUDURWAN SIRRI Gajeran labari Marubuci Shuraih Usman @hausaebooks.cf @shuraih 99% Page 3 . Gargadi:- wannan littafi mallakar shafin hausaebooks ne don Allah kada wani ko wata ya juya wani bangare ko barin littafin nan batare da iznin wannan shafi ba karkashin jagorancin Shuraih Usman . na daure na mike tsaye na tunkari wannan kofa, ina isa bakin kofar na sanya hannu na bude , ko musu kofar baiyiba yabata wata kara "kikkir kikkirrrrrr" alamar ana bude kofar, kofa kofar ta gama wangamewa ta budu nan take nai arba da abun da ya tashi tayar mani da hankali ainun,kwakkwalwata ta kusan daina aiki,idanuwa na sukafara lumshewa a hankali tamkar me gyangyadi,gaba dayan lakar jikina ya mutu,!!! . Ba komai nai arba da shi ba face wata tsaleliyar kyakkyawar budurwa wacce saboda tsananin kyawunta ne nama kasa sarrafa kaina, . TABA RAKALLAHU AHSANUL KHALIQEEN, lallai Allah yayi halitta , ita dai wannan kyakkyawar mace wacce ta kasance bantaba ganin ta ba sai ayau, shekarunta ba za su wuce goma sha tara ba, tsananin tsabar kyawunta nema yasa har wasu dausayin fararen haskene ke bibiye da ita, . Na tabbata ko da cikin duhu ne mai tsanani wannan budurwa ta miko hannunta toh take duhun zai bace haske ya maye gurbinsa, "Shuraih! " Zazzakar muryarta wadda tafi na komai dadi aduniya ta katse mani tunanina , a irin salon yadda take kiran suna na, ji nake babu wanda ya iya kiran suna na face ita, koda wannan zazzakar muryar tata kawai mutum zai saurara toh da sai ya gwammaci ya saurara fiye da abashi kyautar makudan dukiya . Firgigit na dawo cikin hayyacina tamkar wanda ya farka daga barci na dubeta baki na sai kakkarwa yake amma na kasa fadan komai dakyar da sidin goshi na iya fadin "nnnna - m" . Murmushi tayi wanda ya kusa zautar dani don kuwa alokacin da gefen kuncinta suka lotse sai naga tama fi kyawu bisa kan da, . Koda taga halinda na shiga adalilin wannan murmushinn da tayi sai ta kyalkyale da dariya, ai saboda dadin sautin wannan dariya nata ban san lokacin dana sulale a kasa sumamme ba, Iya abin da masarrafin kwalkwata ya iya dauka shine daukewar dariyar wannan budurwa daga nan kuma ban sake sanin meke faruwa ba *** . A hankali nafara bude idanuwana, mutane ne nafara ganinsu dishi dishi akaina, na mike na zauna sai a sannan ne kwalkwalwata ta dawo aiki hankalina ya dawo jikina . Na dubi mutanen da suke gefena suna yimini sannu, sai naga ashe ma yan mata ne kyawawa, sanye da fararen dogayen kaya, sai a sannan na lura da dakin danake ciki . Karamin dakine an kawata shi da kayan ado na mutanen da, zaune nake a kan wani luntsumemen katifa, wadda yake bisa wani katakon gado, na budi baki na ce wa yan matannan "su waye ku, a ina nake sannan waya kauni nan?" Wata daga cikinsu tace ainan kana gaban birnin sin ne cikin garin LAJUJ . "Ina ne kuma garin lajuj, na tambayesu" na tambayesu cikin mamaki Wacce ta bani amsa da farko ta sake cewa "ai garin lajuj garine na Aljanu don kowa daka gani anan garin aljanine, mutum dayace kawai ba aljana ba, amma itama ba mutum ba ce, kuma itace ta kawoka wannan birni namu, " . Cikin rudewa na mike a firgice ina neman hanyar gudu don kuwa na riga dana gama firgita da maganarsu, Na nufi kofar fita daga dakin cikin gudu na kama mabudin kofan na murda take kofan ya bude . Ban jira komai ba na nausa a guje, wata doguwar hanya na gani ta mike santa wannan hanyar na zura a guje, ko waigowa baya bana yi, ban dade da fara bin hanyarba sai na hangi wata kofa karshen hanyar, wannan kofa abude take, . Turus naja na tsaya a yayin dana shige cikin wannnan daki da yake da wannan kofa, . Zaune take akan wata luntsumemiyar kujera haryanzu wannan murmushin nata yana nan a fuskarta, Ta dubeni tai mani nuni da wani kujera tace na zauna . Babu musu naje na zauna akan wannan luntsumemen kujera wanda saboda tsabar laushinsa sai danayi tsammanin ko bulalliyar kujerace, . Zamana keda wuya sai na cigaba da kallon kyakkyawar fuskarta wadda banki nayi shekaru talatin ina zaune ina kallo ba, karar budewan kofar dakin shine yaja hankalina inda na maida dubana ga wajen . Daya daga cikin matannan ne ta shigo tana dauke da wani faranti a hannunta mai dauke da akushi sai wani tambulan na zinare, tazo ta ajjiye a gabana . Tana ajjiyewa tayi ficewarta kyakkyawar budurwan ta dubeni tace "ga abunci nan kaci in kama sai muyi magana, " Ba musu na bude akushin wanda yake rufe sai nayi arba da dafaffiyar kaza, sai a sannan ne ma cikina ya fara kuka na tuna cewa wunin ranar ban ci komai ba , kuma banji yunwa ba sai yanzu . Toh dama ina cikin wannan hali ina zanji yunwa, cikin kankanin lokaci na gama da wannan kaza banbar komai a cikin akushin ba sai kasusuwa, nan na kora wani lemu mai tsananin zakin gaske sannan nayi hamdala ga Allah . Koda ta fahimci na iddar da abuncin sai ta fara magana da daddadan sautin muryanta wanda kan iya zauta mutum, "shuraih ka sani cewa ni sunana haseena tun ranar dana fara ganinka shekaru biyar baya naji zuciyata ta kamu da tsananin sonka, naji babu wanda nake so aduniya sama da kai, Tun a wancan lokacin na so na sanar dakai irin zunzurutun son dana ke maka Amma naji tsoron Abu daya, Wato naji tsoron SALMAN" Haseena tayi shiru ga barin magana llokacin data sadda kanta kasa, . Na tsinci kaina acikin wani irin Ni'ima wanda tunda nazo wannan duniya ban taba tsintar kaina a ciki ba, wai ni take so tabbas abun da Al'ajabi Cikin dakewa irin ta maza na dubeta bakina sai rawa takeyi nace HAS-sss Ena ta dago da kanta ta dubeni fuskarta na murmushi a gareni in ka ganta tamkar wata ran daren goma sha biyu . Nan da nan naji na samu kaina ina mai cemata "lallai babu mutumin da zaiyi arba dake baiji cewa yana sonki ba, tun dana fara ganinki nima zuciyata take bugawa ban taba gani ko jin labarin wata mai kyau irin nakinnan ba,, I na sssoosssonki Haseena" . Tayi murmushi sa'annan ta kama hannuna ta mike tsaye tace zo muje na gabatar dakai a wajen mahaifana, naji abun banbarakwai amma na dake nace mata masoyiya kafin muje mai yasa ba za kidan bani labarin wannan birni naku ba mai matukan ban Al'ajabi . Haseena ta dubeni da wani kayataccen kallo sa'annan Tace "habibina mai zai hana" Muka koma muka zauna akan luntsuma luntsuman kujerun dake makare a cikin dakin . Haseena ta dubeni tace "shuraih sunan wannan birni namu LAJUJ kuma wannan birni bayana kan Duniyarku bace ta mutane Wannan birni na Lajuj birnin Aljanu ne amma mun kasance musulmai kamar kai, mahaifina sunansa Nasaruddin kuma shine sarkin wannan gari namu..... ..Rayuwa haka take wakana yau lafiya gobe akasinta, dazu-dazu lafiya yanzu-yanzu rashinta Allah ka baiwa dukkan musulmi marasa lafiya masu lafiya kuwa Allah ka kara masu ,,,, Its 99% awakening from three 3 days sickness Yo sai mun Hadu MAKO mai zuwa Daga - www.facebook.com/hausaebooks . Marubuci:- Shuraih Usman Typing:- Shuraih 99% Hakkin mallaka (m) hausaebooks page BUDURWAN SIRRI Gajeran labari Marubuci Shuraih Usman @hausaebooks.cf @shuraih 99% Page 4 . Gargadi:- wannan littafi mallakar shafin hausaebooks ne don Allah kada wani ko wata ya juya wani bangare ko barin littafin nan batare da iznin wannan shafi ba . Haseena ta dubeni tace "shuraih sunan wannan birni namu LAJUJ kuma wannan birni bayana kan Duniyarku bace ta mutane Wannan birni na Lajuj birnin Aljanu ne amma mun kasance musulmai kamar kai, mahaifina sunansa Nasaruddin kuma shine sarkin wannan garin namu, . Mahaifina ya kasance jinsin aljanu ne , amma kuma daya tashi aure sai ya tafi naku duniyar ya auro jinsin bil'adama wacce ta kasance itace mahaifiyata, sai da mahaifi na ya yai shekaru biyu a duniyar mutane sannan Allah ya baiwa mahaifiyata haihuwa, amma cikin rashin sa'a data haifeni sai ta koma ga mahaliccinta . Mahaifina yayi kuka sosai akan rashinta, domin kuwa a kullum da dare baya samun bacci sai tunaninta yake sakamakon irin zunzurutun shakuwan dake tsakaninsu, da kuma matsanancin soyayyar da suke wa junansu . Tun daga wannan lokaci gaba dayan son da mahaifina yake yi wa mahaifiyata sai ya dawo kaina, ya dauko ni muka dawo wannan duniyar, amma lokaci lokaci yakan daukeni muje duniyar mutane na dan wani lokaci sannan mu dawo wannan duniyar . Abum Al'ajabin daya kasance dani shine ni ba Aljana bace haka nan ni ba mutum bace, kuma ni Aljana ce Ni mutum ce,.." Har zan yi magana sai ta daga mani hannu alamar nayi shiru, ta dora da "tsananin kyawuna ne ya sanya aljanu da yawa ke muradin suga sun aureni, amma sam mahaifina ni baya son na auri Aljan , , Daga cikin masu son su aureni akwai Salman salman shine sarkin yakin wannan birni namu Gaba daya mutanen wannan birni namu sona matukar tsoronshi da shakkar shi, saboda duk birnin nan babu wanda yakai shi jarumta , wannan nema yasa da yawa daga cikin masu neman aurena suka janye sakamakon tsoron salman da sukeyi . a Al'adar wannan kasa tamu itace duk wayanda suka hada neman wani abu tare da wani, ko suke neman mace tare toh akwai wata gasa da zasuyi wanda duk wanda ya cinye wannan gasa toh shine yayi nasarar mallakar wannan abu da suke rigima akai wannan gasa muna kiranshi da GASAR FIDDA GWANI" . Haseena tayi mani murmushi Wanda ke sanyaya min zuciyata, taci gaba "Toh Masoyi kaji tarihin birnin namu mai matukkar Al'ajabi," Wani shauki naji ya dirga min a zuciya sakamakon yadda naji sunan da haseena ta kirani da shi, ta matso kusa dani ta kama hannuna , ai bansan lokacin dana kurma wani dan karamin ihu ba sakamakon wani shocking dana ji ya ziyarci hannuna,murmushi kawai haseena tayi sannan ta dago ni, abun ya bani mamaki domin kuwa yadda ta daga ni sai kace ba katon gardi ta daga, yadda kasan fallen takarda, har naso na tambayeta game da hakan amma sai nayi shiru da bakina, muka fice daga cikin dakin atare . Tafiya muke a jere yayinda hannuna yake cikin nata fuskarta kuwa yana kan fuskana ko gabanta bata kallo sosai, wani zunzurutun wutar kaunarta ne yake ci a zuciyata, Ban yi aune ba sai gani nayi mun iso wani kayataccen fada wanda aka kawata da kayan ado irinsu, zinare,zubarjadi,lu'u lu'u da yakutu domin kuwa daben wajen ma da yakutu akayi shi, Ga bayi da hadimai sai zirga zirga suke tayi amma da zarar sun ganmu sai su russuna su kwashi gaisuwa sa'annan su wuce, Mun danyi tafiya mai dan nisa kafin mu iso bakin wata kofa wacce aka sana'antata da zallar farin zinare sannan akai mata ado da lu'u lu'u sai dai wani abun daya daure mani kai da kofar shine ganin wasu macizai danayi guda biyu nan na de da juna a jikin kofan, . Cikin mamaki naga haseena takai hannu jikin kofan ta kama macizan nan duka ta murde musu kayika, sai gashi kofan ta bude, nan muka shiga ciki har hanzu hannuna na cikin na haseena, dakin da muka shiga ya fi kowanne daki kayatuwa a cikin fadan don ni dai tun da na shigo banga wajen daya kai nan kayatuwa ba, . Sai a sannan na lura da wasu kirda kirdan mutani sanye da kayan karfe, suna rike da makamai a hannunsu, kallo daya nai masu na gane cewa Dakarune masu tsaron gidan, nakai dubana ga gabanmu inda muka dosa toh a nan ne naga tarin mutane suna zaune bisa wani dogon kujera wanda ya kusan kaini tsayi, . Wayannan kujerun suna jere ne, layi biyu kowanne kujera yana fuskantar daya, mutanen sunyi shiga ta alfarma wanda da gani kasan ba kananan mutane bane, mai karatu kar kaji nace mutane ka dauka ko bil'adama ne wayannan mutanen , a'a dukkansu Aljannune amma a siffar mutane suke rayuwa, sai kuma wayansu fuka fukai dake bayansu, . Wani dattijon aljani na gani kyakkyawa da shi, yana sanye da fararen kaya masu daraja, zaune yake akan wata karaga ta sarauta, wacce aka sana'antata da zallar lu'u lu'u aka kuma yi mata ado da takubba na farin yakutu, a gefen karagar sa wayansu sadaukan samudawan aljanu ne su goma cikin shirin kota, fuskarsu a murtuke tamkar wayanda aka aiko ma sakon mutuwa, ko motsi basa yi sai kace Gumaka kwana kallo daya nai ma samudawan aljanun nan na kau da kai don kuwa muddin na cigaba da kallonsu toh zan iya Sumewa wajen wayannan aljanu muka nufa ni da haseena muna zuwa gabansu haseena ta durkusa sannan ta kalleni tai min Alama dana durkusa ba musu nima na durkusa, kawai sai ji nayi haseena tana magana da wani irin yare wanda ni ban taba jin sa ba, bayan ta gama maganar ne wani daga cikin Aljanun nan yace mar habanki dake da wannan bako, yake gimbiya daga nan sai haseena ta mike tsaye ta karasa gaban wannan dattijon mai fararen kaya ta rungumeshi sannan ta tsaya a gefensa, dattijon aljanin ya dubeni har yanzu ina durkushe ban dago ba, . Yafara magana yakai wannan bako kuma masoyi ga yata kai sani cewa muna marhaban da zuwanka, kuma a sannu zamu sanar da kai dalilin daya sa muka kiraka izuwa wannan duniya tamu amma kafin nan yanzu za mu bari ka huta tukunna, aljanin yana zuwa nan a zancensa sai ya dubi wani wani bafaden aljani yace mai zirwanu ka kaishi masaukinsa dun ya huta nasan ya debo gajiya, wanda aka kira da zirwanu ya russuna angama ranka shi dade, ********** Ina zaune a cikin dakin da zirwanu ya kawo ni , nayi tagumi bana tunanin komai sai na gida, Yanzu a wani hali iyayena suke nasan dole su shiga wani irin hali izan har ya kaasance basu ganni ba, . Nan take naji bana marmarin komai sai gida dun kuwa nima ina so na gansu ko hankalina ya kwanta, sai de ba anan gizo ke sakar ba, aduk lokacin dana tuna cewa ina da zukekiyar budurwa kamar haseena sai inji zanma iya yin shekaru hamsin muddin zan zauna da haseena . Tunane tunane kala kala suna ta zuwanma kwakwalwata, ina cikin wannan hali ne sai na fara jin wata zazzakar waka tana tashi daga bayan dakin danake, cikin zumudi na nufi taga na bude don naga wacce keda wannan zazzakar muryar, Wani kayataccen lambu ne yaiwa idanuna maraba acikin wannan lambu kuwa yan mata ne su ashirin, suna rike da kayan kida sai kidi sukeyi, dukkan matan nan kyawawane na gaban kwatance domin kuwa in ka dauke haseena har yau banga macen da ta kaisu kyawu ba, A tsakiyar wayannan yan mata wata mace ce ta lullube kanta da mayafi zazzakar muryarta ne kawai yake tashi, ...... . . Kuyi hakuri da rashin post nawa akan lokaci rashin wadatuwan lokaci shi ya janyo haka , Ni dinne dai Shuraih Usman Inkiya 99% Daga:- www.facebook.com/hausaebooks BUDURWAN SIRRI Marubuci:- Shuraih Usman @hausaebooks.cf @shuraih 99% Page 5 . A tsakiyar wayannan yan mata wata mace ce ta lullube kanta da mayafi zazzakar muryarta ne kawai yake tashi, Zuciyata ce ke fisgata irin fisgar da ruwan kashe gobara yakeyi yayin fitowa daga cikin bututun ruwan . Ni kaina ban san lokacin dana je na bude kofar dakina ba da nufin nayo waje naga ko wacece wannan mai wakar, har na saka kafa na fita kuma sai nai wani tunani , Ayanda nake jin ana labarta min cewa nan duniyar aljanu ce , na tashi na nufi wajen wayannan kyawawan matan, kila ma aljanu ne ban sani ba, Wannan tunanin dana yi shi yasa na dawo da baya nai kwanciyata cikin dakina, Dakyar na samu nasarar yin bacci sakamakon wannan zazzakar wakar dake tashi daga waje, aduk lokacin dana runtse idanuwana domin nai bacci sai na wannan zazzakar murya ya farkar dani, Har takai da saida na samu wasu yanki na toshe kunnuwana da su sannan na dena jin wannan waka . Washe gari na farka a gajiye na tashi na nufi dan wani kofa dana gani a cikin dakin wanda tunanina ya bani cewa bayi ne, kama yadda na zata dun haka yake dun kuwaina budewa na shiga na samu ruwa cikin wata randa na zinare batare da bata lokaci ba nayi wanka da wannan ruwan sai de abun daya daure shine a duk lokacin dana debi wannan ruwa sai naga ya karu Har na iddar da wankan na fito daga bandakin na nufi kan gadona domin na saka kayan dana cire ajje , Amma kayan sai sukace daukanmu inda ka ajje, na neme su sama da kasa na rasa, can na bayan na gaji da nema sai na dawo kan gadon na zauna nayi tagumi, wani haske naga dan kashe mani idanu, na kai dubana ga wajenda hasken ke fitowa sai naga ashe ma a gefena ne, nakai hannu don ganin menene wannan yake wannan haske, cikin mamaki sai gani nayi hannuna ya tabo wasu lallausan abu duk da ban ko menene ba sai na daga abun sama toh anan ne aka samu mishkila abun ya kubuce daga hannuna ya fadi a kasa ai yana faduwa sai naga ashe ma kayane riga da wando irin na sarautar mutanen garin Cikin tu'ajjibi na dauki kayan na sanyasu a jikina sannan na nufi wajen madubin dayake dakin nayi mamaki ainun alokacin dana irin zunzurutun kyan danayi, kai alokacin sai dana koda kaina nace ashema ni kyakkyawane haka, , Karar Kofan dakin ne ya katse ni, lokacin da ake kwankwasawa, na nufi kofan nabude su ukune kamar yadda na fara ganinsu, har yanzu babu wani sauyi atare da su, yan matan jiya ne daya daga cikinsu ta dubeni tace "ran ka ya dade gimbiyace ta turomu mu tafi dakai wajenta don kuyi kalaci" "Wacece kuma gimbiya" na tambaya "Wacce ta kawo ka nan garin" "Wai HASEENA ki ke nufi" Na lura da cewa wannan kalma danayi na karshe yasa dukkansu sun tsorata duk da bansan dalilinsu na tsoratan ba, "Eh itace , amma yallabai kasani duk fadin kasarnan babu wadda yake kiran ta da sunanta hatta mahaifinta ma, " "Saboda me ba'a kiranta da sunanta" "Wannan kuma wani sirrine na gidan sarauta" Na jinjina kai sannan nace masu "Toh muje " Suka juya suka fara tafiya ni kuma na take masu baa . Mun danyi tafiya mai dan nisa sa wacce takaimu izuwa wani kayataccen lambu wanda ya yalwatu da yayan itatuwa, su kansu bishiyoyin dake cikin lambun ababen sha'awane, domin kuwa bishiyoyin dukkansu yana yinsu daya ne, tsayinsu da komai na su, Furannin lambun kuwa sun kasance a duk bayan dakika daya suna dunkule wa waje guda, Muka nufi wani waje daban a inda muka bi ta kan gada, wannan gadan de an kerashi ne da zallar itace da igiyoyi aduk lokacin da muka taka gadan sai kaji wani kara na tashi . Tun daga nisa na hango kyakkyawar fuskarnan nata sai sheki yakeyi, farace kyakkyawa gata da dirarriyar jiki domin kuwa shape dinta na kwalbar cokacola ne, Ta mallaki tsastsaikan fuska wadda ke dauke da dara daran idanu, wayanda jure kallonsu, dan mitstsin bakinta wanda idan ka lura da kyau alokacin data ke magana zakaga tamkar baya so ya bude, . Ayau tana sanye ne da irin kayan duniyanmu kuma irin na kasarmu, riga Atamfa da sikert, abun ya bani mamaki ainun, ni danake zaton babu irin wannan kaya a wannan garin, sai de dana tuna da abu guda sai nama dena mamaki . Ayau tafi kowanne lokaci kyau fuskarta sai sakin tausasan murmushi yake a gareni, ai ban san lokacin dana kura mata idanu ko kiftawa bana yi ba, Muka kariso wajen yan matan nan sukayi saurin russunawa akasa zasuyi magana kenan ta dakatar da su ta hanyar daga masu hannu sannan ta sallamesu, sukai tafiyarsu . Ta dubeni tai wani murmushi wanda yake zuzuta wutar kaunarta a zzuciyata, "ka kwana lafiya" "Lafiya lau" Ta riko hannuna , awannan lokacinma sai da naji shocking ya ziyarci kwakwalwata, har nayi dan kara karami, ta jani muka karisa gindin wata bishiya, inda naga an shimfide gaba dayan wajen da wani babbar tabarma, a tsakiyar ta barmar ga abubuwan ci da sha nan birjik, Takalmi na cire alokacin da nake shirin hawan tabarmar, Wani laushine ya ziyarci tafin kafafuwana ,ko kadan wannan baiyi kama da tabarmar dana sani ba mai uban gurza-gurza Haseena ta zaunar dani itama ta zauna kusa dani yanda muna iya jin numfashin juna "Shuraih tun da nake a duniya ban taba ganin dan Adam lokaci daya naji sonsa ba saikai, hakan nema yasa yau dinnan zan fada maka sirrin dake tattare dani ina sonka shuraih so ,kuma ina muradin zama abokiyyar zamarka na duniya da lahira, Jina nake tamkar wanda akaiwa kyautar Aljanna domin kuwa a wannan lokaci na tabbata babu wanda yakaini farin ciki "Haseena kiyi sani cewa nima ina sonki , kuma babu abunda bazan ma don na mallakeki, nasan cewa kina shakkun wannan gasa ta fidda gwani ne, toh ki sani muddin akan ki ne sai de na mutu awannan gasa don kuwa bazan bari wani daban ya sameki ba, ki kudurta a zuciyanki nine mijinki" Hannu ta saka ta dauki wani tuffa ta mai gaza daya, har zata kai na biyu sai nayi sauri na karbi tuffan daga hannunta ina mai yimata wani irin murmushi na zolaya, sannan nima na gaza daidai wajen da ta gaza Anan muka luluka izuwa duniyar soyayya domin kuwa hira muka shiga yi sosai yadda take bani labarin garinsu, sosai naji dadin wannan lokaci . Muna tsaka da hiran ne wani lokacin izan ta fadi abun dariya sai mu dara , wata kakkausar murya ce ta katse mu da fadin "BUDURWAN SIRRI bata bil'adama bace, . Dukkanmu muka juya don ganin mamallakin wannan murya,,,,,, . www.facebook.com/hausaebooks BUDURWAN SIRRI Gajeran labari Marubuci Shuraih Usman @hausaebooks page @shuraih 99% Page 6 . Gabjejen katone mai kirar mutanen farko yana da tsayi wanda na tabbata yayi ni Uku a tsayi don sai dana daga wuyana sannan nai nasarar ganin Fuskarsa a turbune fuskar yake babu alaman murmushi ko kadan a tare da shi, kwayan idanunsa jane, gashin kasumba ya rufe mai baki yayin da ya hade da gashin gemunsa wanda ya zura ma wani zobe ya kulle . Yana sanye da riga falmara mara hannu hakan yasa na samu nasarar ganin kwanjinshi, gaba daya jikinsa a mummurde yake, ga jijiyoyin jikinsa sun tashi sunyi burdum burdum kai kace igiyace . Hannunsa na dama yana rike da gashin gemunsa wanda ya rike daidai wajen da ya zura zoben yana dan liliyawa ,fuskarsa na yatsinewa wanda shi a zatonsa murmushi yake, Shi ba mummuna ba haka kuma shi ba kyakyawa ba, amma kallo daya kadai nai masa na gane cewa wannan dakare ne, domin kuwa akuibin cinyoyinsa hagu da dama akwai wasu takubba manya manya cikin kufensu , wayanda na tabbata in aka ce na daga daya cikinsu bazan iyaba . Cikin firgita da tsoro na saki baki galala ina kallonshi har ya kariso garemu, Abun daya daure mani kai shine sam babu alamun firgici a fuskar haseena A zuciyata nace yo ta ina zata firgita bayan itama yar uwarsu ce, na sake maimaita wannan suna da naji ya kira haseena da shi a cikin zuciyata BUDURWAN SIRRI . Yana tafiya takubban dake jikinsa suna dan kara sakamakon yadda yake tafiyar din . Ya kariso wajen da muke zaune Neman waje yayi ya zauna sannan ya harde kafafuwa irin zaman da yayi sai ya tuna mani da lokacin da nake makarantan Allo, fuska cikin fuska ya dubeni sannan ya takarkare da mahaukacin dariya mai matukar amo, ba shiri na sanya yan yatsuna na toshe kunnuwana sakamakon yadda naji dodon kunena na neman agaji . Sai da yayi dariya mai isarsa sannan ya dubi haseena yace "Budurwan sirri, wai dama wannan dan tsakon ki ka je kika samo, ai nayi mai girma ina laifin ki samo dai dani, " Ya nuna ni da yatsa batare daya kalleni ba sannan yacigab da magana da muryansa mai kama dana jaki "Ina mai tabbatar maki da cewa nine zan aureki ,kuma nine nan zan lashe wannan gasa wacce zamu kara wata mai zuwa ni da wannan dan kwaron " . Duk da cewa ina jin tsoron wannan basamuden aljani wanda bansan sunansa ba , ai koda naji irin kalaman dayake furtawa ga haseena sai na fahimci cewa shine SALMAN, nan take na nemi tsoron dana ke mai na rasa cikin kunan rai na daka masa tsawa "Kai Aljan mutun bisa kanka, girman jiki bashi bane ke nuna cewa mutun yana da karfi, to kayi sani nidin dai daka raina da yardar Allah sai na baka mamaki" ai sai dana gama furta maganar sannan nayi nadamar furtawa Domin kuwa alokacin fuskar aljani salman ta yamutse , yadda kasan an aiko masa da sakon mutuwa, . Badon ina da dauriya ba da babu abunda zai hana ban tsiyayo fitsari ba kasancewar irin kallon danaga yana yimin Cikin kunan zuciya ya daga girjejen hannunsa mai kama da tabarya da nufin ya zabga min mari, rufe idanuwa na nayi don kuwa nasan babu makawa zai aikata, ko kadan banyi kokarin kare kaina ba ta hanyar rufe fuskata don nasan muddin hannunsa ya taba jikina to take zan baje a kasa sumamme ko matacce . Cikin sauri haseena ta daka masa tsawa wanda ya sanya shi tsayawa cak tace "salman izan ba kana son kaaga fushina bane toh ka gaggauta barin wajennan , in kuwa ba haka toh zakayi daana sani wanda ba zai maka Amafani ba, " cike nake da tsoro kamar ace kyat na ruga na dubeshi a yayin da ya dunqule hannunsa ya naushi kasa , a hassale ya tashi sa'annan a dubeni yace "ka shirya nan da wata daya bil'adama maza bisa kanka," yana gama fadin hakan sai naga manyan fuka fukai guda biyu sun fito daga bayansa cikin kankanin lokaci ya tashi sama ya luluka cikin gajimare Na dawo da dubana ga haseena tambayoyi fal bakina . Murmushi tai min wanda shine ya mantar da ni dukkan wannan tambayoyi dana ke shirin jera mata su Tace "nasan ka tsorata da Al'amarin Salman amma karkadamu akwai wanda zan kaika wajensa ya koyar dakai fada da kuma yaki" . "Toh" kawai bakina ya samu fadi a yayin da muka cigaba da hirarmu in ka ganmu sai ka rantse mun yi shekaru da ita, na saki jiki sai zuba zance nake ****** . Washe gari tunda sassafe wayannan yan mata uku suka sake zuwa kirana sai de yau dukkansu sun canja kayan dake jikunsu irin kayan dana sanya jiya shi na sake sakawa duk da ban san wanda yake kawo mani kayan ba hakan bai hanani sakawa ba . Wannan karon ba yalwataccen lambunnan muka nufa ba wani bangare ne daban wanda kallo daya naiwa bangaren nagane cewa mutane ba su cika shiga wajen ba duba da yadda naga wajen yayi kura, kuma yanan gizo gizo duk ya gauraye rufin wajen, . Muka iso bakin wata kofa mai kauri wacce aka sana'antata da zallan bakin karfe daya daga cikin matannan ce ta ciro wata tsohuwar kubba daga jikinta ta zura a cikin dan siririn ramin dake jikin kofan sannan ta murda Dan karamin dakine mai dauke da kayan tarkace iri iri , a karshen bangon dakin muka hango ta naayi mamaki kwarai da ganinta anan . Na kariso ni kadai a yayin da yan mata ukunnan suka tsaya a bakin kofan dakin rufe kofar dakin sukai Na budi baki zanyi magana haseena ta dora yatsanta a kan lebbana alamar nayi shiru ta nufi wani kusurwan dakin daban wata tsohuwar tayan keken doki naga ta daga, ta kama wani katako ta murda shi . Nan take jiri ya fara dibana sakamakon yadda naga dakin yana juyawa da sauri haseena ta ruko hannuna sannan itama ta rike wani karfe , kafin kace kwabo sai dakin ya runga juyawa dukkan tarkacen nan suka fara tashi sama suna haduwa da junansu, baki kawai na saki ina kallon ikon rabbi, sai da gaba dayan tarkacennan suka gama hadewa waje guda suka dunkule kaman dunkulin magi . Sai da suka gama dulkulewa tukunna sai kuma dunkulin ya fara fitarda yar karamar kofa, kan kace kwabo har wannan dunkulin ya canja siffa izuwa na Kofa, Babu abunda zai baka mamaki ma kaman yadda kofan ta kasance sai haske take tana daukan idanu . Adai dai lokacinne dakin ya daina juyawa komai ya tsaya cak sai a sannan haseena ta ce "wannan shine babul hajir, ta cikin wannan kofa zaka iya tafiya ko ina a doron kasa, tun daga kan duniyarku har zuwa wasu duniyoyinma," . Shiru kawai nayi na saki baki ina kallonta ni yanzu ma har na saba da abubuwan mamakinsu koda na gani ma banayin mamaki sosai kamar yadda nake a baya . Ta ja hannuna wanda hakan yasa nima nabi bayanta bakin kofan muka zo muka tsaya ta sanya lallausan hannunta ta bude kofan sai a sannan dukkan wani mamakina ya karu domin kuwa babu komai a gaban kofan banda hazo daya ke gittawa lokaci lokaci, banga alaman wani abun ba . Haseena ta jani muka shiga cikin kofan ai sai dukkanmu muka ji kamar mun fado daga saman wani katon tsauni ne, saboda tsaban firgici kulle idanuwana nayi yayin da muke fadawa kasa iska sai gittani yake ta ko ina hakan yasa na saki wata kara . Kamar daukewan wutan nepa sai mukaji mun fado a cikin wani rami, abun da ya kara dauremin kai shine da kafafuwanmu muka fado kuma ko dan zogi banji kafata tayi min ba . Haseena tai murmushi "tace haka ka iya ihu dama ban sani ba, ai kuwa sai ka tanadi wani ihun da yafi wanda kayi a baya, domin kuwa yanzu ne za'afara ainahin tafiya" cikin sigar zolaya ta fada Na sosa keyana "ai ni kaina ban san lokacin da na saki ihun b....." Wani kara ne ya katse mani maganata karan kuma daga kasan inda muke yake fitowa sai a sannan na daga kaina na kalli sama Gani nai tamkar mun fada cikin rijiya gaba dubu ne Ban gama wannan tunanin ba kasan wajen ya wawake take muka fada ciki amma wannan karon a tsaye muka fada kuma ahankali muke sauka kasa, Cikin wani daji mai yawan guntayen bishiyu muka sauka , sosai yanayin dajin ya burgeni dukkan wasu ganye na dajin jane maimakon kore mun danyi gajeriyar tafiya da kafafunmu sannan muka riski wani Bukka irin na mutanen da shi kansa bukkan da jajayen itace aka sana'anta shi, bakin bukkar muka tsaya sannan haseena tai sallama, wata tsakurarriyar muryace ta amsa sallamar, daga bisani sai wani dattijon Aljani ya fito daga bukkar yana sanye da dogon yar shara har kasa sam sam fuskarsa bata nuna alamar tsufa ba ,zai yin kama da saurayi mai jini a jika Har kasa ya zube yayi gaisuwa wajen haseena ta durkusa ta dagoshi tace "baba zaikid nasan dai basai na maka bayanin abunda ya kawoni wajenka ba, amma duk da haka zan sake maimaitawa, wannan shine Mijin nawa In Allah ya yarda ina so a cire masa dukkan wani tsoro na jinsun mu kuma ka koya masa dukkan wasu dabaru da salon yaki, nan da wata daya zan dawo na daukeshi" Murmushi tsoho zaikid yayi "an gama ranki shi dade" Ni dai na cika da mamaki ainun jin cewa wai ni za a cire ma tsoro sannan kuma wai za a koya min yaki da dabarun fada Haseena ta dubeni a lokacin da fuskarta ....... Kwana biyu kun jini shiru Bani da lafiya ne shi isa BUDURWAN SIRRI Marubuci Shuraih Usman @hausaebooks.cf @shuraih 99% Page 7 . Haseena ta dubeni a lokacin da yanayin fuskarta ya sauya , ta kankame hannuna sosai tace" shuraih muddin muna son mu rayu har abada amatsayin mata da miji toh dolene ka koyi wasu abubuwa na yaki, da kuma ka kuma cire tsoro a zuciyarka, ina matukar sonka irin son da baki ba zai iya fasaltashi ba, hannu ba zai iya rubutashi ba ko na dakika daya bana son rabuwa dakai, amma dole na na barka anan domin ka koyi yadda zaka kare kanka daga sharrin Salman" . Har na budi baki zanyi magana sai ta sanya yatsanta a akan lebena alamar nayi shiru ba musu nayi shirun duk da irin tarin tambayoyin dana ke shirin jefamata Ta dan ja baya kadan sannan ta soma tafiya har tayi nisa idanunawana suna kanta ta juyo muka hada idanu ta sakarmin murmushi daga haka ta cigaba da tafiyarta har ta bacemin da gani ina nan tsaye a gun . Tsono zaikid ya dubeni da kyau yace "yaro shin meye sunanka" "Shuraih" na bashi amsa batare dana kallesa ba haryanzu idanuwana na kan hanyar da haseena ta bi Tsoho zaikid ya sha gabana sannan ya turbune fuska yace "shuraih kake ko wa to bari kaji Abunda kazo yi nan shi za kamai da hankalinka gareshi , domin kuwa in kai wasa toh kana ji kana gani ta rabu da kai kenan" Sosai hankalina ya tashi da maganganun wannan tsohon Batare daya jira amsana ba ya juya ya shige cikin bukkarsa yana cemin" ka dai shirya don kuwa daga gobe zamu fara atisaye " .... Har magriba ta gabato banga alamar tsohon nan zai fito ba hakan ya sani ta shi na kwankwasa kofan bukkar daga ciki muryan tsohon naji yace "ya akayi ne" "Yun wa nake ji ,kuma gashi dare ya fara yi baka bani makwanci ba" na fada Sautin dariyarsa naji alamar dariya yakeyi "In tambayeka mana" ya fada "Ina jinka "na bashi amsa "A rana sau nawa kake cin abunci" "Sau uku" "Toh daga yau ka sanya a ranka kuma a jikinka baza ka sake cin abinci ba sai bayan kwana daya,kuma ka sani baka da abunci sai yayan itace" Sosai na girgiza da jin batun tsohonnan "To shi kuma makwanci fa" "A nan zaka runga kwana kuma ka tabbata asubar fari ka farka yanzu dai ga ruwa kayi alwala kai sallah," ya jefo min wani batta na ruwa Na karba nai alwala nai sallah daga nan na zube wajen durkushe duk da yanayin wajen yana da kyau kuma ko kadan babu kwari ko wasu muggan dabbobi masu cutarwa a cikin dajin domin kuwa tunda muka shigo dajin kawo izuwa yanzu bamuyi gamo da wani abu mai rai ba . Haka na kwanta akasa kan ciyayin dajin masu tsananin laushi duk da ya kasance ina rawar dari saboda sanyi da nake ji, bai hana bacci daukata Ba . A fiirgice na farka sakamakon jin an kwara min ruwa da nayi waige waige na fara yi don ganin mahalukin daya kwara min ruwa dan tsakurkurin tsohon ne dai a gabana ya bata rai yana rike da wasu mayan mangala guda biyu Ya ce"shin jiya ban sanar dakai cewa asuban farko taimaka a farke ba, shine ka shagala har asuba ta biyu baka tashi ba" Bai jira cewana ba ya jefo mani mangalolin nan masu dan karen nauyi da kyar na iya cafe guda daga cikinsu Yacigaba "maza maza ka tashi ka tafi wancan kogin yai nuni da hannunsa zuwa wani gefe dabam, ka debo ruwa ka runga zubawa anan ya nuna mani wata katuwar rijiya wadda tun zuwana wajen ban lura da ita ba . A kasale na tashi na rarumi mangalalolin na nufi inda ya nuna mani nayi tafiya mai dan karen nisa kafin na iso bakin koramar na zauna kan daya daga cikin mangalolin nan ina hutawa bayan nagama hutun ne na cika mangala daya da ruwa sannan na kinkimeta da kyar da sidin goshi na dorata akaina irin nauyin danaji akaina yafi kama da na Mota ko wani katon dutse a daddafe da kuma ikon Allah har nakai bakin rijiyar na zuba ruwan na sake komawa rafin kai in takaice maku sai wajejen la'asar na idda kai ashirin din daya ce na zuba, na samu waje na baje a kasa ina numfashi sama sama alamar na jikkata naji karar budewan bukkar tsohon ya zo ya tsaya daidai gabana sannan ya bushe da dariya yace "kai amma bil'adama da ragwanta suke yanzu wai dan wannan aikin shine har da numfarfashi sai kace wanda yai aikin azo a gani, maza ka mike tsaye" A daddafe na mike tsaye don kuwa tun da nake a rayuwata ban taba yin wani aiki mai wahala daya kai wannan ba . Yanzu kam da sauki tunda dai na dan rage nishin da nake tsoho zaikid ya shige cikin bukkarsa yadan dau lokaci kafin ya fito rike da sanduna guda biyu, sandunan dogayene sosai don kuwa sunyi tsayina biyu Ya jefo mani guda daya duk yanda naso na cafe ta amma na gagara saboda irin saurin zuwan da tayi sai gashi sandan ta wuce ni tamkar walkiya , ta sauka nisa dani tsoho zaikid yayi murmushi " Maza kaje ka daukota" Ba musu na nufi wajen da sandar take ina zuwa na sanya hannuna da nufin na rabata da kasa amma sai wani nauyi ya ziyarci hannuna ji nai tamkar na ina kokarin daga katon dutsene na daddage na tara karfina har ina nishi na daga sandan daga kasa na kafata tsaye , sai nishi nake haka na fara jan sandan a kasa har na kawota wajen tsoho zaikid, "Da alama wannan tayi ma nauyi toh bani ita ka amshi tawa" Ya karfi wannan daya bani ya kuma mika mani nashi da sauri na karfa don dama ni nasan kuskure yayi wanda ya kamata ya bani shike hannunsa , ai mugun nauyin danaji shi yasa na saki sandar ta fadi a kasa don kuwa hartafi waccan dinma nauyi tsoho zaikid yai kasake yana kallona kafin yace "muddin zaka runga yimasu irin wannan daukan toh baza ka taba iya rike koda daya daga cikinsu ba" "Yaya kake so na dauka toh" "Kasanya a ranka cewa zaka iya , sannan kana nan ne kawai don BUDURWAN SIRRI, haka kuma ka cire tunanin duniyarku daga ranka ka dauka tamkar a gidanka kake, sannan ka tausasa zuciyarka, a natse zaka ji mamaki ainun don kuwa ba wannan sandan ba hatta wancan tsaunin zaka iya yin gamo a dora maka shi" Nai kasake ina kallonsa yayin da na kalli tsaunin daya ke nuna mani a zuciyana nace "toh ko nine ILYA DAN MAI KARFI sai haka" . Na nufi sandan nayi tamkar yadda yafada na rufe idanuwana na shafi sandan da hannuna na kama na daga cikin matukar mamaki sai naji tamkar na dau fallen takarda don kuwa ko kadan sandan bata da nauyi yanzu na juya na dube shi yai mani murmushi yace "shin yanzu ka yarda da magana ta" "Shakka babu na yarda" Daga nan ya fuskanceni yace "daga yau zamu fara darasin mu na koyan fada , da kuma yadda zaka kare kanka, . Ya koyar dani abubuwa da dama a wannan rana don kuwa in ba sallah ba babu abunda yake tsaida mu, da shike ina da saurin daukan abubuwa , har magariba tayi ya ce mani "je kai sallah ka kwanta kuma gobe ka tabbatar kafin safiya ka gama diba ruwanka nai godiya sannan nai wucewata izuwa inda na kwanta jiya ******* Kwanaki suna ta wucewa tamkar yadda takarda ke zukar ruwan biro yau saura kwana daya wata daya ta cika, A cikin wayannan kwanakin na koyi a bubuwa da dama, dun kuwa ji nake babu wanda ba zan iya tunkara ba yanzu batun tsoro kuwa babu ita , Tunda kuwa ni da kaina nake fada da manyan zakuna da kadoji kuma na kai su kar . Shi kansa tsoho zaikid yana mamaki ainun da saurin daukan fada na, kaman kullum yauma muna filin koyon fadanmu ni da tsoho zaikid sai fafatawa muke in ka ganmu a lokacin sai ka rantse wasu a bokan gaba ne domin kuwa kowannenmu burinsa shine yaga ya cutar da dan uwansa, ni dai na dage sai kare hare haren tsoho zaikid nake wanda shi kuma ya kufula ainun ganin sam bana kawo hari, sai da muka shafe wasu sa'o'I kafin ya samu nasarar buguna da sanda akafa nan take kafana ta gurde amma saboda juriya irin nawa sai na dake na kama kafar na murda ta sai ta dawo dai,a lokacinne na fusata na fara kaimai hari ba kakkautawa kan kace kwabo sai ga tsoho zaikid a kasa wanwar sakamakon bugunsa da nayi da sanda akansa . A gigice na nufeshi na tallabo kansa ina mai bashi hakuri yayi murmushi sannan yace "lallai na yarda yanzu kam ka kawo karfi ina son ka shiryaa don kuwa gobe BUDURWaN SIRRI zata zo ta dauke ka" Na gyada mai kai ina susa keyana ******* Washe gari tunda sassafe na iddar da debo ruwana don kuwa yanzu ji naake tamkar zan iya diba kai dubu ma, Nai sallah sannan na taho kofan bukkan tsoho zaikid na tsaya ina nan tsaye a wajen har gari ya waye, Tsoho zaikid ya fito daga bukkar hannunsa rike da sanda guda, na dubesa da mamaki don kuwa a kullum da sanduna biyu yake fitowa ya zauna kusa dani yace "shuraih ka tashi lafiya" "Lafiya lau" Daga haka ban sake magana ba Kaman a mafarki sai naji muryan haseena tana gaida tsoho zaikid na dago kai na dubeta da mamaki don kuwa shi kansa zaikid bai san lokacin da ta zo ba iyaka dai jin muryanta yai har kasa ya rissina ya gaiisheta sannan ya nuna ni da hannu yace "ranki shi dade yanzu matsoraci kuma ragon bakon ki ya juya izuwa jarumin saudauki wanda sam baya jin tsoron komai gaba dayan tsoronsa sun juya izuwa naciya da juriya" Tai murmushi wanda ya sake fitta kyawunta ta matso kusa dani ta kama hannuna da mamaki sai naga hawaye akan idanunta "Shuraih kayi hakri nasan cewa na cuci rayuwarka na sanyaka a kunci sakamakon son zuciya da sonkaina, kana zaman zamanka a duniyarku na daukoka na kawo ka nan gashi yau a kaina ka...." Na yi sauri na dora hannuna na rufe mata baki sannan nace "yana daga cikin rukunan imani yadda da kaddara mai kyau da mara kyau, wannan mukaddari ne bayin ki bane kuma ki sani muddin ina numfashi a doron kasa ba makawa sai na aureki bana tsoron mutum bare Aljan, ni kawai abunda nake bukata dake yanzu shine mu tafi izuwa filin wannan gasa domin na nuna ma salman cewa DAN ADAM HATSABIBI NE, Babu abunda baya sarrafawa komai girmanta koya takai da cutarwa" ********* Zaune naake bisa wata lallausan kujera yayinda haseena take fuskanta ta Kura mani idanu tayi bata ko kiftawa nim dai idanuwana akan nata suke, cikin kwayan idanunta babu digon baki sai wani digon jaja ja, haka nan naji ina matukar farin ciki tun ma bamuyi gasan ba Tace "shurai nasan cewa kana da tarin tambayoyin da kake son kai mani musamman ma akan wannan suna daka ji ana kirana wato BUDURWAN SIRRI, toh yau zan baka amsar dukkan tambayoyinka . Toh fa Nasan ku kanku kuna son jin labarin budurwan sirri kui kasake da kunnuwanku BUDURWAN SIRRI Marubuci Shuraih Usman @hausaebooks.cf @shuraih 99% Page 8 . "shurai nasan cewa kana da tarin tambayoyin da kake son kai mani musamman ma akan wannan suna daka ji ana kirana wato BUDURWAN SIRRI, toh yau zan baka amsar dukkan tambayoyinka" Nai murmushi "ni tambayata guda ce itace wannan suna dana ji ana kiran ki da ita BUDURWAN SIRRI, shin meye ma'anarta" , Haseena tai murmushi sa'annan tace "kaman yadda na baka labari a baya cewa mahaifina acan duniyarku yai aure kuma bil adama ya aura, nasan cewa kana mamaki inda har Aljani ya auri Bil'adama toh kama daina don kuwa jinsi ne kadai ba daya ba, domin kuwa a zamanin da Aljanu da yawa sun auri bil'adama haka suma Bil'adama da dama sun auri Aljanu sannan suka hayayyafa, Hakance ta kasance da mahaifina bayan an haifeni na kasance kyakkyawa wacce babu kamarta a duk fadin wannan duniya tamu , hakan yasa yayan saraku da Attajirai sukai ca akaina kowannensu yana so aureni ni kuma duk cikinsu babu wanda ya kwanta min arai hakan ce tasanya na ki amince masu, A kudancin duniyarmu a akwai wata babbar birni na Aljanu ana kiranta da BULZUM sai de su Aljanun sun kasance kafirai ne kuma matsafa, sarkin birnin azzalumine sunansa RAVA yana da 'da daya tilo daya haifa mai suna bishmalu, sarki rava yana son bishmalu sosai hakan ce tasa duk wata bukata da bishmalu ya nema duk wahalarta duk tsaurinta sai sarki rava ya biya masa ita wannan tasa shima bishmalu yake son mahaifin nasa sosai, Bansan tayadda akayi har bishmalu yaga fuskata ba, sai ganin dan aiken sarki rava mukayi yazo har fada da mummunar wasika wasikan da ta zama sanadiyan mutuwan rabin Aljanun wannan gari namu, "tana zuwa daidai nan ta fashe da kuka Banyi yunkurin hanata kukan ba cikin sheshsheka ta cigaba "mahaifina ya karbi wasikan ya bude shakka babu daya san abunda yake cikin wasikan nan toh da bazai bude ba, yana budewa sai wani farin hayaki yai fitar burgu daga cikin wasikar da ganin haka sai dan aiken daya kawo wasikan ya bace bat, ba afi minti daya ba sai gaba dayan fadan yadauka da dariya bakajin komai sai sautin dariyar sai da akayi dariyar sosai sannan wata kakkausar murya tafara magana "yakai wannan sarki kai sani cewa nine sarki Rava na birnin BULZUM musabbabin isowata wannan birni naka shine na nema wa Dana bishmalu auren zukekiyar yar nan taaka, bijirewa umarnina zai janyo da mugun tashin hankali ga Al'ummanka, don haka ina umartarka da ka gaggawar fitowa da ita don na kaita ga dana" . Hankalin mahaifina ya tashi , ya dugunzuma cikin muryan fada "kai kana ganin wanene kai da har zaka zo har birnina kuma cikin fadata sannan ka dau yata ,toh kai sani cewa mu ga Allah muka dogara, babu abunda ka isa kai mana ," Muryan ya bushee da dariya "dama an sanar dani cewa kana da girman kai, kuma sam ba zakai mani biyayya a bisa kudirina ba, kuma tun fil azal dama ina da muradin na murkushe wannan birni naka da dukkan wasu aljanun da suke ciki Amma bokana ya haneni ga aikata hakan Toh yau kai sani sai Rabin mutanen wannan birni sun ziyarci lahira,ziyarar da baza su taba dawo wa ba" . Kamar daukewan ruwan sama sai muryan ta dauke dif tamkar bata taba wanzuwa ba, Mahaifina yaa koma kan karagarsa ya zauna yai tagumi yana tunani Bayan dakika dari da hamsin sai ga wani badakare ya sukwano a guje akan dokinsa Badakaren bai tsaya a ko'ina ba sai gaban sarki gaba daya jikinsa ya baci da jini, kallo daya zaka mai kasancewa a firgice yake Wani dogari ya daka masa tsawa "kai meyafaru ne muka ganka haka, shin ina sauran abokan aikinka masu tsaron gari" "Wata muguwar masiface ta afku a cikin gari ranka shi dade , rayuka da yawa sun hallaka gidaje da dama sun ruguje, kana nun yara,mata,samari da tsofaffi dukkansu sun rasa rayukansu" Badakaren ya fada ayayin da yake numfarfashi Sarki ya mike tsaye cikin firgita da dimaucewa ya ce "menene ya faru da su" "Muna aikin bada tsaro a cikin babban kasuwa , mutane sai cinikaiya suke , yara,maza,mata,tsofaffi suna ta zirga zirga cikin yanayin nishadi Kwatsam sai mukaji wata kara daga karkashin kasa hakan yasa mutane sukai saurin barin wajen da karar yake fitowa mu kuma muka durfafi wajen cikin shiri, Kasan wajenne ya tsage tamkar an saka wukane aka tsargeta, wani mummunan halitta ne ya fito daga cikin kasan halittan babbane don kuwa tsayinsa yafi na gidajenmu sau goma, halittan yana da kaho guda akan goshinsa sai ido daya rankwalele daya ke gefen hancinsa Hannunsa na rike da wata katuwar Al'amudi wacce inda mutum dari zasu taru baza su iya rabata da kasa ba, Ai nan take sai wannan halitta ya hau ruguza gida jen mu duk abunda ya duka da al'amudin dake hannunsa sai de kaga ya ruguje hakan yasa muka cire tsoro muka far masa muka runga sara da sukan sassan jikinsa, Sam ko yasan munayi, cikin kankanin lokaci ya gama rushe rabin godajen birnin nan sannan ya hau Aljanu , duk aljanin daya taba da Al'amudin hannunsa sai kaga ya zama toka mun tsorata ainun da lamarin wannan halitta, gaba dayan Askar din daka hadani da su sun halaka ni kadai ne kawai na tsira" Askar din ya karasa maganarsa yana aman jini Hankalin mahaifina ya tashi ainun Hakan yasa sukai sauri suka garzaya cikin gari domin ganin barnan da halittan tayi, . Abun da suka gani ya basu tausayi sosai Gidaje sama da Dubu sun rushe, Aljanu sama da dubu sun halaka, sama da dari biyar sun ji munanan Raunuka, kowa sai neman taimako yake Anan take mahaifina ya fashe da kuka ,yana cikin kukan ne akaji wata kakkausar murya ta bushe da dariya sai tai mai isarta sa'annan tai shiru askarawa da yan majalisu sai waige waige suke ko zasu ga ta wajen da muryan ke futa, Muryan ta cigaba da fadin "ayanzu ina amfanin Gardama, Ayanzu ina Amfanin girman kai, da a ce ka yarje da bukatata da duk wannan abu bai faru ba, na rantse da karfin mulkina muddin ka ce baza ka aurawa dana yarka ba, toh nan da shekara mai zuwa sai irin wannan bala'I ta kara samunku, kuma kai sani cewa na gaba ba gidaje da jama'a kadai zai kashe ba 'a'a gaba dayan birnin ne zai Kone ta ta koma Toka, Gargadi na karshe da zan maka, ka daukesa a matsayin Doka ko umarni duk wani Talikin daya sake Kiran HASEENA da sunanta sai de wani ba shiba , da ga yau saide ku runga kiranta da BUDURWAN SIRRI, don kuwa ita ta kasance mai matukar rabo da sa'a da har zata auri dana,na baka nan da shekara daya muddin baka aiko da yarka zuwa marautata ba toh duk abunda ya faru daku, kui kuka da kanku" Muryan na gama fadin hakan sai ta dauke dif tamkar an zabga ruwan sama an dauke . Gaba dayan yan majalisan suka hau mahaifina suka suna cewa akan mace daya jal, an rasa dubban rayuka anyi asaran Arziki mai yawa mai zaisa ba za a bashi ita ba ko dan a kare bala'in da ke tunkararmu, shi de mahaifina shiru yayi yaki tanka masu . Yana dawowa gida ya shige turakarsa babu wanda yasan me yake a cikin turakansa din, Washe gari da sassafe na nufi turakar mahaifina ko kwankwasa kofan ban yi ba nasa kai, Na sameshi a zaune bisa kan sallaya alaman ya iddar da sallah kenan , Koda mahaifina ya ganni sai na ga kwalla suna gangarowa akan kuncinsa nai sauri naje na runugmesa ina mai fashewa da matsanancin kuka , Cikin shishshikan kuka nace "Abba ni na yarda na amince zan auri bishimalu , muddin hakan zai tsaida wannan masifa data ke tunkaromu, nasan cewa in na auri bishmalu Al'umma dayawa zasu tsira da rayukansu, da dukiyoyinsu" "A'a yata kada kiyi saurin yanke hukunci, shi rayuwa da mutuwa dukka Allah ne yake yankesu, ki tashi yanzu kije ki kwanta, ayau dinnan zanyi istahara naga abunda Allah ya zaba mana" Mahaifina ya fada cikin dakewa , Sum sum na tashi na fice daga turakar naje dakina na kwanta ************ Shin kuna biye dani kuwa fans , Alkalamin Shuraih Usman ne inkiya 99% BUDURWAN SIRRI Marubuci Shuraih Usman @hausaebooks.cf @shuraih 99% Page 9 . Washe gari da safiya naje na iske mahaifina a turakarsa domin jin abunda ya samu daga istaharan da yayi , Da sallamata na shiga cikin turakar na sameshi a zaune a wajen dana iskeshi jiya, Ya dago kai daga kallon kasa dayakeyi yana mai amsa sallamata, Na samu waje na zauna, Mahaifina yayi gyaran murya sannan ya fara bayani "haseena hakika Allah ba azzalumin bawansa bane, Jiya nayi istahara domin neman zabin Allah akan wannan mugun al'amari dayake tunkaro mu, An nuna mani a mafarkina cewa wani Dan Adam ne kadai zai iya tseratar da mu daga sharrin sarki Rava, dolenmu muje duniyar mutane mu dauko wani yaro wanda bansan sunansa ba, sannan zamu dukufa wajen sana'anta wata makami wacce ba'ataba yin irinta ba a doron kasa, da taimakon wannan makami ne zamu samu nasaran murkushe Garin Bulzum, an nuna mani dukkan wani abun da zamu bukata wajen sana'anta wannan makami a cikin mafarkina, " Yayi shiru yana mai dubana domin jin abunda zance Cikin doki nace "toh Abba waye wannan shi Dan Adam din da zai kubutar damu " "Bansan ko waye ba amma an nuna mani alomin da zan iya ganeshi, kuma kece da kanki zaki futa nemansa," Cikin tantama nace mai "toh amma Abba da wasu alamomine zan iya gane sa, ?" "Alama na farko shine a lokacin da kuka hadu da shi hadari zai hadu, kuma zaiyi hatsari a babur har ya karye a kafansa na dama, a lama na biyu shine yana da makaken tabo a tafin hannunsa na dama, wayannan sune alamomin da zaki iya ganeshi da su, " , Daga nan mahaifina ya tsara mani dukkan wani shiri da kuma tsari na yadda zanyi na daukoka daga duniyarku, harda irin shirin da zamu shirya maka" Haseena tayi shiru tana dubana a lokacin da mamaki da Al'ajabi suka dabaibayeni, nama rasa tacewa Haseena ta cigaba "Inhar bazaka mantaba shuraih akwai wani lokacin da ka taba yin hatsari har ka karye a kafarka ta dama, tun daga wannan lokacin na lura da tabon dake tafin hannunka, wannan yasa na daukoka tundaga duniyarku na kawoka nan dun ka taimakemu , shi kansa SALMAN shirine muka hada amma babu wani burbushin soyayya a tsakaninmu , " Sai ayanzu na gane dukkan manofofi da inda maganar haseena BUDURWAN SIRRI ya nufa iyayena,abokaina,kasata,mahaifana duk na rabu da su akan mace guda wacce a tunanina tana Sona da gaskiyane, tabbas na kamu da kaunarta irin kaunar da bazan iyya rayuwa imbabu ita ba, Irin kaunar da zan iya sadaukar da duk abun dana mallaka don ita Irin kaunar da zan iya bayar da rayuwata don ceto nata amma ashe ita ba kaunata take ba, Bansan lokacin da kwalla suka fara zarya akan kumatuna ba, haseena ta budi baki da niyyar ta sake furta wata kalma Cikin gaggawa na daga mata hannu alaman bana son sake jin wata magana daga bakinta na tashi tsaye fuskata ta sauya lokaci guda numfashina ya fara fita da sauri, zuciyata na tafasa nace da ita "Babu komai haseena NAJI NA GANI zan taimaki Al'ummanku da duk wata taimako da kuka nema daga wajena, amman bai kamata ......" Sai kuma nai shiru ga barin maganar duk da naso na furta wata magana amma na fasa kwalla ne suka kara gangarowa daga idanuwana , Na lura da haseena sai kallona takeyi tana son tai mani magana amma ganin irin yanayin dana ke ciki yasa taja bakinta tai gum . Jiki ba kwari ta fice daga dakin, Wani tsatsauran ciwon kaine ya fara ziyartar kwalkwata , na dafe kaina ina mai runtse idanuwa , babu abun da idanuwana suke hango mani face kyakkyawan suran nan na haseena , madaidaicin bakinta wanda baya rabo da murmushi , suke ta zarya a cikin kwalkwata, . A haka bacci yai awon gaba dani Bani da farkawa ba sai cikin dare koda na tashi na bude kofa na fice daga dakina, iyanzu kam na gane cewa haseena ba kaunata take ba, na gane cewa haseena ba sona take ba duk wasu abubuwa da suka wanzu a baya duk yaudarace don na biya mata bukatarta, nai murmushin takaici bisa ganin irin wasa da hankalina da tunanina da haseena tayi , Na mike wata hanya wacce zata sadani da babban falon fadan, cikin yan mintuna na isa falon kaman yadda na zata hakan take Al'umman aljanu ne cikin shigar mutane suna ta harkokinsu, na nufi wata kofa na bude Hasken rana yai wa idanuna maraba, Na fice daga falon na nufi farfajiyan masarautan ina mai kallon irin salon da akai amfani da shi wajen ginin gidan, Kai tsaye babbar kofar fita daga Gidan na nufa bansha wahala ba wajen tuhuma ta da masu gadi sukai, daga baya suka bani hanya na fice daga gidan sarautar gaba daya, Ni kaina bansan me ya futo dani ba kuma bansan dalilin fitana ba ni dai na tsinci kaina ina mai Tafiya nake ina mamakin irin ginin gidajen Garin, kwata kwata tsawon ginin bazai wuce kamu goma ba , kuma da zallar zinare suka sana'anta gidajen, Gaba dayan gidajen suna kamanceceniya da juna Sa'I sa'I nakan cimma jama'a suna harkokinsu baki kawai nake saki ina kallonsu duk daya kasance Aljanu ne amma ba zaka taba iya banabacesu da mutane ba , Ina cikin tafiya ban aune ba sai jin wata kakkausar murya nayi ta kwala mani kira Shakka babu na taba jin wannan murya, na juyo don ganin mai kiran nawa Salman ne na gani yana falfala a zabababben gudu a bayansa akwai wasu askarawa su hudu dukkansu suna masu falfala gudu don cimmini Cikim yam dakikoki suka iso gabana salman ya dubeni murmushi dauke a kan fuskarsa yace "Shuraih! Fitarka daga masarauta yana da hatsari sosai, don kuwa akowane lokaci sarki rava zai iya kawo ma ziyara don ya dade da jin labarinka" ************************************** . Ina zaune a gaban mahaifin haseena kaina ya na kallon kasa , yan majalisan sarki suna kewaye da shi kaman kullum "Shuraih kai hakuri bisa rabaka da mukayi da iyayenka da kasarku, sannan muna rokonka daka taimakemu daga masifan dake tunkararmu" Maganganunsa ne suka sanya na dago kaina ina mai dubansa, acikin zuciyata nace toh waishin ni da ban kwarance wajen fada ba tayaya har zan iya taimakonsu, "Nasan kana mamaki da jin cewa da mukai kaine zaka iya taimakonmu ka tserartar damu daga halaka da iznin Allah SWT" Salman ya fadi sannan yaci gaba "kamar yadda budurwan sirri tai maka bayani, ajiyane muka karashe aikin sana'anta wata makami wacce ba'ataba sana'anta makamanciyarta ba a doron kasa, wannan makamin tamkar nakiya take saide ita tana aikine kawai akan jinsin Aljanu , Gobe da safe zakaayi shiri mu baka wannan makami ka nufi garin Bulzum ka dasa ta " , ******** Shuraih ! Shuraih !! Shuraih!!! Muryan mahaifiyata na tsinkaya da sauri na futo daga cikin dakina na A tsaye na taras da ita a kofan dakin "Kazo wata ce tazo wajenka" "Toh mama" Amsar dana iya bata kenan Na mike na nufi kofan dakina Turus nayi ina kallonta murmushin dake fisgo zuciyata gareta dauke a kan lebbanta, "Haseena !" Firgigit na farka daga nannauyan baccin dayai awon gaba dani dazu, nan take dukkan abubuwan da suka faru dani suka fara dawowa cikin kwalkwata sai ayanzu naji ina matukar kewan gida, na tuna da mahaifiyata inna mairo, "Kwab kwab kwab" Karan bugun kofa ya katse mani tunanina , Na tashi naje na bude kofan Tsaye a gabana cikin kayan daana saba ganinsa , Fuskarsa sai murmushi take tamkar wanda aka mai kyautan Aljanna, "Kayi sauri ka shirya, maimartaba na nemanka " "Toh "kawai na iya cewa Cikin yan mintuna nai wanka na shirya cikin wasu kayan dana taras da su akan katifa , Nayi mamaki ainun da ganin kayan, bakin suite ne mai dauke da dan ciki, hade da wando damamme , ' ******* Zaune nake a gaban maimartaba , salman yana gefen damana yayinda haseena take gefen haguna, BUDURWAN SIRRI Marubuci Shuraih Usman @hausaebooks.cf @shuraih 99% Page 10 . Sanye nake cikin bakaken suite din dana iske cikin dakin da aka saukeni a ciki , Lokaci lokaci nakan kallaci gefen da haseena take, aduk lokacin dana kai dubana gareta sai mun hada idanu, cikin sauri nake kawar da dubana gareta don alokacin ni kadai nasan irin wutar tarzomar dake ruruwa a zuciyata, duka a sanadin haseena , "Shuraih dafatan ka gama duk wani shiri naka da zakai don zuwa garin bulzum" Na gyada kai alaman eh Maimartaba ya dubi wani ba'askare ya daga mai hannu, Ba'askaren na ganin haka sai ya dauko wani jaka dake bayansa yazo ya aje a gaban sarki , Nasarudin ya kai hannu kan jakan ya bude yaa fiddo da wani bakin mulmulallen dutse, , Ya mikawa salman mulmulallen dutsen yace "kayi masa bayanin duk yadda zaiyi ya dasa makamin da yadda zaiyi ya tasheta" , Salman ya karbi mulmulallen dutsen sannan ya dubeni yace "shuraih" Na amsa yayinda gabadaya hankalina ke ga mulmulallen dutsen wanda babu ko kwarzane a jikinsa sai yanzu na fahimci ashe dutsen din shine makamin da zanje na dasa a birnin Bulzum , "Izan ka isa birnin bulzum, sai ka samu wani waje ka dasa makamin, yadda zaka dasa kuwa shine izan ka fiddo makamin sai ka ajjiyeta a kasa ka hada mata wuta toh cikin dakika daya zata fashe, dukkan wani aljani dake wajen zai zama hayaki yabi iska, gidajen su kuwa da dukiyoyinsu zasu baje su zama Ruwa ********** Ina tsaye cikin kwale kwale wacce zata sadani da birnin Bulzum , Wani aljani ne ya hakimce sai tuka kwale kwalen yake, Akalla yanzu nakai sa'a daya da barin garin Lujaj Na nufi garin bulzum Shakka babu da nasan abun dake shirin faruwa dani toh da babu abunda zai sanya na bar garin lujaj Wannan tafiyan da nayi itace Tafiyar da ta wargaza mani farin ciki na, , Bana tunanin komai sai na haseena , yanzu kam na tabbata da gaske ne haseena bata kaunata duba ga yadda har na bar garin lujaj batayi mani magana ba, , "Bako mun iso" na tsinkayi muryan matukin kwalelen cikin kunnuwana Sai asannan na lura da daina motsin da kwale kwalen tayi, ashe wai har mun iso bakin gaba Na sauka daga cikin kwale kwalen ina mai kallon cikin dajin dake gabana, "Kayi sauri ka dasa makamin ina nan ina jiranka" ,, Na nufi cikin dajin gadan gadan batare dana bashi amsa ba, Na yi tafiya mai dan karen nisa kafin na fara hango ganuwar birnin Bulzum, da taimakon Taswiran da Salman ya bani , Har na kariso birnin ban ci karo da wani Aljani ba, Abun daya bani mamaki shine ganin babu wata kofa ko wani hanyar da za'a shiga birnin ta ciki, , nan fa na fara zagaye birnin ina neman hanayar shiga, sai da na zagayeta kaf banga wata hanyar shiga ba hakan ne yasa nayi kudirin in kwana a bakin birnin kafin gobe da safe na sake neman hanyar shiga , Waje kawai na share nayi kwanciyata batare da fargabar komai ba, har dare ya tsala, toh a sannan ne naji saukan wani abu a jikina, Cikin sauri na farka don ganin menene wannan Anan na tsinci kaina a cikin RAGA, an nanna deni, wasu munanan askar na Aljanu suna jana a kas, Banyi wani yunkurin kwatan kaina daga hannunsu ba ina kallo suna zuwa dani sai wani abun mamaki ya faru don kuwa wani banagarene daga katangan garin ya tsage da kanshi, nan suka jani muka shiga cikin garin din, muna wuce wa katangar ya hade kansa tamkar bai taba tsagewa ba, , Gaba daya Aljanun garin sai bina da kallo sukeyi yayinda nima nake kare masu kallo sama da kasa, tun danake ban taba arba da munanan Aljanu irin wayannan ba, domin kuwa ko acan birnin Lajuj a siffan mutane aljanu suke rayuwa, Sai da muka zo wani fankacecen fili, wanda girmansa yakai eka dubu, Sannan wayannan samudawan aljanun suka saki igiyoyin dake tattare da ragan dana ke ciki, sannan sukai tafiyansu, Toh a sannan ne Rana ya fara gasani irin gashin da wuta yakewa dankali, Kaina yafara amsawa, gaba dayan jikina ya jike sharkaf da gumi, sai a sannan na lalubo harshena daga cikin bakina na fara karanta ayoyin Alqur'ani mai girma , Ina fara karatunne naji jikina yayi sanyi tamkar wanda aka sanyashi cikin kankara, gaba daya ji nai na daina jin zafin ranan dayake damuna Sai a sannan na tuna da wata guntuwar Wuka da salman ya bani lokacin da zan hawa kwale kwale , Na zaro wukan daga kubenta cikin zafin nama na hau ragar da yanka Cikin kankanin lokaci nayi kaca kaca da ragar na fito na tsaya akan kafafuna, Na lalubi aljihun wandona don jin haryanzu makamin da nasaruddin yabani yana nan, Jin hannuna ya tabo wani kululun abu shi ya tabbatar mun da haryanzu makamin yana nan , Na falfala da azababben gudu domin na isa wani waje da muka wuce dazu naga ana kera takubba Har na iso wajen kiran askarawan birnin basu ankare dani ba, Aljanun dake kera takubban suka daga kawunansu suna kallona mamaki dauke akan fuskokinsu, kafin wani daga cikinsu ya mike tsaye, ya nufoni hannunsa rike da makekiyan barandami na tsaya ina kallonsa cikin kota kwana, Yana isowa dab dani ya kawo mani sara da barandamin dake hannunsa duk yadda nayi don na kaucewa saran nayi, amma sai da ya samu nasaran yankana a dantse wajen ya dare jini ya fara kwarara, Ina ganin haka na daka tsalle na dira akan wuyansa kafin yayi kokarin bambareni har na murda mashi kai nan take ya fadi akasa matacce , Yanuwansa suka tashi kowannensu yana rike da takobi a hannunsa, Nan fa suka far mani, suna masu kawo mani sara da suka , ni kuma na wanzu ina mai zullewa da gocewa kaifin takubbansu, a na hakane na hango wasu askarawa masu tsananin yawa sun dumfaro inda muke wannan artabu, Nan hankalina ya tashi, na ga muddin askarawannan suka kariso toh kashina ya buushe, ina gama ayyana haka a zuciyata sai nayi sauri na fidda makaminnan daga aljihuna, na falfala da gudu, izuwa cikin makeran Ina zuwa bakin wani murhu inda naga garwashin wuta sai na jefa makamin a ciki, Da jefawata sai makamin ya bada wata kara Fus alaman fashewansa, . Wani hayakine ya ziyarci idanuwana wanda ya sanya na fara gani dishi dishi, Bansan me ke faruwa ba sai tsintar kaina nayi a cikin wani kungurmun daji, na dubi dajin dakyau sai naga ashe dai wajennan ne da haseena ta kawoni aka koyamin fada, , Na nufi wani bangare da zai sada ni da sansanin tsoho zaikid, Haryanzu hannuna yana yimin zogi da tsananin zafi, na daiyi nasaran tsaida zuban jinin ta hanyar daure wajen Ina cikin tafiyanne sai naji kaman wani abu nayimin yawo cikin aljihun wando, na zura hannuna cikin aljihun cikin mamaki sai ji nai hannuna ya tabo mani wani takarda , Na damki takardan sannan na ciro hannuna don ganin takardar menene , Abun da naci karo da shi a rubuce a bayan takardan shi ya haddasa wani girgizan kasa cikin zuciyata Daga Haseena Masoyiyarka , Zuciyata na zumudi na bude takardar na fara karantawa kamar haka "Assalam masoyina shuraih kuma gwarzona, Nasan cewa kallon mayaudariya kake yimin, gani kake tamkar yaudaranka nayi Kasani cewa tunda nake a doron duniya babu wani namijin dana taba jin sonsa in banda kai, Alokacin dana fara ganinka, sai da zuciyata ta buga, ina matukar farin ciki da nishadi aduk lokacin dana ke tare da kai, duk da nasan na bata maka amma kayi hakuri ina sonka so na gaskiya Allah yabaka sa'a a wannan tafiya da zakayi yakuma dawo dakai gareni lafiya" Tsaban dadin danaji ya ziyarci zuciyana yasa na kurma ihu, ina fadin alhamdulillah, A haka har na iso bakin bukkar tsoho zaikid, Na sameshi a zaune kan wasu itatukan da muka sassaka a tare a matsayin kujeran zama, , Sam baiyi mamaki da ganina ba sai ma gani nake tamkar ya san da zuwana, Nayi masa sallama ya amsa cikin tausasa murya Cikin farin ciki na dubeshi nace "baba " sunan dana ke kiransa da shi kenan "So nake ka maidani garinsu haseena " Ina fadin haka sai naga kwalla ta gangaro daga fuskan tsohon ganin hakan ya rikita ni ainun Na matso ina mai tambayarsa" me ya faru ne baba" , "Haseena,nasaruddin da dukkan ilahirin Aljanun da suke birnin lajuj sun HALAKA" Abunda bakin tsohon ya furta kenan , Kirjina ya buga dumm gabana ya fadi Na dubeshi cikin rashin fahimtar inda zancensa ya nufa nace "kaman yaya sun halaka baba, nifa ban gane zancenkannan ba" , "Shuraih su Nasaruddin sunyi kuskure babba, wajen amfani da wannan makamin don hallaka birnin Bulzum, tabbas da sun san illan da makamin zaiyi masu toh da basu kwatanta amfani da shi ba gashi yanzu dukkansu sun hallaka birninsu ruwa ya mamayeshi" Tsoho zaikid ya fada yana mai tashi tsaye kafin ya cigaba "A ka'idan wannan makamin guda daya ake sana'antawa, in angama amfani da shi sai a sake sana'anta wani, Amma su nasaruddin sun sana'anta guda uku daga cikin ukunne suka baka daya kaje ka tayar a birnin bulzum abunda basu sani ba shine, muddin aka tayar da makamin ya gama aikinsa sai hayakinsa ya bazu a duniya a duk inda yaci karo da irin makamin sai ya tayar da shi, toh hakanne ya faru bayan ka tayar da daya a birnin Bulzum daya gama hallaka mutanen birnin sai hayakinsa yabi iska ya je har birnin lujaj ya kuma ci karo da irin makamin hakanne yasa ya taada su, toh kaji kuskuren da su nasarudden sukayi, sai ka shirya na mayar dakai duniyarku" Ya karashe maganar yana mai nufan bukkansa , Daskare nake a tsaye tamkar gunki, numfashina ya tsaya cak, inbanda bugun da zuciyata take sai ka rantse gunki ne ni , Tsaban rudewa ne ko tsaban firgici, BUDURWAN SIRRI Marubuci Shuraih Usman @hausaebooks.cf @shuraih 99% Page 11 . , Dukkan wani na'uran sadarwa na jikina ya dena aiki, ahankali a hankali, kwalkwata tafara kawo wuta, Tunanina ya fara dawowa, "INna lillahi wa inna ilaihir raji'unn" shine kalman da bakina keta faman furtawa, Na durkushe a kasa, yayinda kaina ke tsananin sara min, "Haseena! Haseena!!" Sunan da nake ambato kenan har na bingire a wajen a sume, ********* "Shuraih ina sonka ba zan taba Rabuwa dakai ba, me rabani da kai sai mutu...." Nayi sauri na sanya tafin hannuna na rufe mata baki "Ina fatan ko a Rayuwana bayan mutuwa na kasance dake, haseena" , Haseena kwance akan kafadana yayinda ni kuma nake shafa gashin kanta, Ta janye jikinta daga nawa sannan ta mike tsaye, ahankali ta fara tafiya tana miko mani hannu alaman na riketa, cikin zafin nama na mike na nufeta da dukkan kuzarina domin na riqe hannunta, Murmushi kawai take mani tana tafiya da baya, fuskarta na dubana, Hankalina bai sake tashi ba sai a lokacin da na hangi a bun dake gabanta, Wawakeken Rami ne, a gaban haseena wanda muddin ta kara gaba kadan toh zata fada, , Na sake kara karfin guduna domin na cimmata na rike mata hannu don kada ta fada cikin Ramin, Amma sai naji kaman ana rikeni ta baya gudu nake sosai amma gani nake tamkar ina gudu ne a cikin Kogi, , kamu daya kacal ya rage na cafke hannun haseena, hakan yasa na daka salle nayi sufa , Alokacin ne kafarta daya ta fada cikin ramin nayi nasara hannuna ya taba nata kafin gaba dayan jikinta su dulmuya cikin wawakeken Ramin , "Haseena!haseena" Firgigit na farka , ina mai sake kiran sunan nata a fili "haseena" "Inna lillahi wa inna ilaihirrajiun" na fada a fili yayinda nayi arba da abun da ya kusan zauta ni, Kwance nake a kan tangamemen lallausan kujeran dake girke a cikin daki . Dube dube da kalle kallen dakin dana tsinci kaina a ciki nake, . Kamar yadda dakin yake a baya kuma yadda na barsa, babu abunda ya canja Ina kwance akan dogon kujeran dake girke a cikin dakin, Dakina ne dana kwanta kwanakin baya, na farka na ganni a cikin dokar daji, , Karin tarin mamakina bai karu ba saida na kai dubana ga kayan dake sanye a jikina, kayan dana kwanta da su ne, a lokacin da na fito wajen Abasu kala don ya bani wayata, , Tunanika da yawa suka antayo mani a lokaci daya, anya ba mafarki nayi ba kuwa, kai tabbas wannan mafarkine , yo Im ba mafarki ba dama nasan babu ta yadda za'ayi wannan abu yafaru da gaske, ace wai daga kwanciyata a dakina na farka na tsinci kaina cikin dokan daji, . Nayi murmushi sannan nayi hamdala, yayin da dukkan tunanina ya raja'a akan dukkan wani labarin BUDURWAN SIRRI mafarki ne, addu'a na fara karaantawa lokacin dana mike na nufi kofan fita daga dakin , Na kama mabudin kofan na murza na yunkura da nufin na janyo kofan, Jinayi an turo kofan da karfi, hakan yasa na dan ja baya don ganin mahalukin dayake shirin shigowa cikin dakin, , Tunanina ya hasko min Ganina na farko da haseena acikin mafarkina dana yi, bansan lokacin da lebbana suka saki tausasan murmushi ba, , Abasu kala ne ya shigo cikin dakin, Yana sanye da bakar riga, wanda ake kira da jagaban, sai blue din jeans wandda aka yayyanka wani sashe na jikinta , da sunan Crazy, sabon style , "99%" ya fada yayin daya bani hannu muka tafa Cikin dariyan shekiyanci ya miko mani wayana, na sanya hannu zan karfa kenan sai naga ya zabura yayi baya, Walwala da annurin da fuskarsa ke dauke da ita ta juye izuwa tsoro da tsaban firgici Yayi nuni da hannunsa izuwa jikina yana cemin"99 menene haka ya ji maka rauni a dantse, dubi yadda jini ya bata maka riga" Nima cikin mamakin maganarsa na dubi dantsen haguna saide banga komai ba, Na sake juyo da dubana ga dantsen damana toh a sannan ne hankalina ya tashi, sakamakon abunda idanuna yaci karo da shi , In har ban manta ba, wannan rauni anyi mani shine a garin Bulzum, kuma wannan al'amari ya farune cikin mafarki, Toh wai dama in har abu ya faru dakai a mafarki, kuma ka farka wannan abu zai kasance a jikinka?? Na tambayi kaina Tambayar da bansan amsarta ba, , Na kai hannuna na taba wajen, Ihu mai karfi na saki sakamakon wani radadi daya ziyarci hannun , Karar ihun ne ya ankarar da mutanen Gidanmu akan halin dana ke ciki, Cikin sauri suka shigo dakin, Dukkansu sun firgita da halin da suka tsince ni a ciki, na yi kokari da taimakon Abasu kala na cire doguwar rigan dake jikina, Cire rigan keda wuya sai naji mutanen da suka shigo dakin suna salati suna salallami , Ban san akan me suke salatin ba amma tunanina yabani kodai suna mamakin yadda akayi har naji wannan babban rauni ne, "Shuraihu wayannan tabon da suke bayanka na menene, yaya akayi har kaji wayannan tabobin??" Na tsinkayi muryan mahaifiyana tana tambayana , Salati nayi kafin mahangar tunanina ya hango mani ta yadda akayi har na samu wayannan tabon, Alokacin da tsoho zaikid yake koya mani fada yakan ji mani rauni a jikina, "Inna lillahi wa inna ilaihirraji'un" na fada a fili Mafarki na neman ya zama gaskiya akaina Abun daya faru dani a mafarki na farka na ganshi a jikina, Anya kuwa wannan mafarkine, tun da nake a rayuwata ban taba jin wani labari makamanciyar nawa ba, wai ace kayi mafarki kaji rauni, kuma ka farka ka ganka dauke da raunin, Anya mafarkine nayi kuwa,???? . Tambaya Mafarkine ko Gaske . Rayuwa haka take wakana yau lafiya gobe akasinta, dazu-dazu lafiya yanzu-yanzu rashinta Allah ka baiwa dukkan musulmi marasa lafiya masu lafiya kuwa Allah ka kara masu ,,,, Its 99% awakening from three 3 days sickness BUDURWAN SIRRI Marubuci Shuraih Usman @hausaebooks.cf @shuraih 99% Page 12 . ........ Bayan Wata Uku * "Shuraih!! Shuraih!!! Ka tashi dare yayi fa" Na tsinkayi muryan abokina Abdulhamid a cikin kunnuwana, Na mike cikin magagin bacci nace "karfe nawa yanzu" "Goma da rabi ne yanzu" Ya bani amsa Da saauri na mike tsaye, cikin kankanin lokaci na wartsake daga magagin baccin dake dibana, Na zuri takalmina na fice daga dakin Abdulhamid ya bini da gudu yana mai kiran sunana, "Shuraih ka tsaya mana baka ga garin akwai hadari bane, kuma kafin ka kai gida ruwa ya tsinke," Na danyi nazari kadan kafin na jijjiga kaina nace "Ai gwara ruwan ya tareni a hanya akan na tsaya har shabiyun dare yai mun anan angwan naku" "Toh Allah ya kiyaye hanya" "Ameen " nace sannan na cigaba da tafiyana , Darene mai dauke nannauyan hadari wanda akowani lokaci ruwan dake tattare dashi na iya zubowa, in banda hayaniyan mutani, da karan wucewan iska, babu abunda kake ji a angwan, Karar aradu ne ya ziyarci kunnuwana wanda hakan ya sanya na kwararo addu'o'i , Ina tafiyanne sauri sauri gudu gudu, na matsu na ganni a kofan gidanmu, sabida bana son wannan ruwa ya riskeni akan hanya, duba ga yadda naga ban dade da dawowa daga asibiti ba, ' Tunanin abubuwan da suka faru a baya ne suka fara dawo min cikin kwalkwata tamkar a majigi (video), nayi murmushi a sa'an da hoton surar haseena suka baiyana cikin kwalkwata, Yau watanni uku kenan, tun bayan lokacin dana hadu da haseena a cikin wata rayuwa wadda na kira da mafarki, hakan ya janyo mani abubuwa da yawa, ciki kuwa har da daukana da akai a matsayin mahaukaci, sakamakon labarin dana sanar ma iyayena, Wannan yasa suka tarkatani sukai asibitin kwalkwalwa dani, watanni na uku acan ina karban magani da Allurai, babu yadda banyi ba dun na ganar da iyayena cewa ina cikin hankalina amma abu ya faskara, , A shekaran jiya ne aka sallamoni daga asibitin kwalkwalwa, Na saki murmushin kuna lokacin dana tuna wanda ya makala mani hauka, "Shuraih anya kana cikin hankalinka kuwa, taya za'a yi wannan abu ya faru a rayuwan zaahiri,sai kace wani wasan kwaikwayo (film)" Na tuna lokacin da mujahid ke fadin haka a gaban iyayena yayin dana basu labarin duk abunda ya faru dani da yadda akayi har naji ciwo a dantsena "Da gaske nake wallahi babu karya a cikin labarin dana baku" nafada ina kokarin baiyana masu gaskiyana "Baba ya kamata mukaisa asibitin kwalkwalwa su dubasa bana tunanin yana cikin hayyacinsa" Mujahid ya fadi yana duban mahaifina "Toh naji amma kafinnan bari mudan fara dana gargajiya tukun,ko ya kuka gani" mahaifina ya fadi yana dubansu , In gajarce maku sanda aka gaiyato malamai sunkai Goma sukai saukan qur'ani a gidanmu, maganin gargajiya kuwa babu iriyar wacce ba'a dankara mani ba, tun ina bi a hankali inayi masu bayanin cewa nifa lafiyana kalau, har takai sun tunzurani wata rana na kama wani mai magani da aka kawosa wai ya bani magani na lakada masa dukan tsiya, , Toh a sannan ne aka wuce dani asibitin kwalkwalwa, ko kuma ince asibitin mahaukata ,,, Barkewan da ruwaan saman yayi tamkar da bakin kwarya shi ya sanya na fara gudu, ina neman mafaka, cikin wani lungu nake wanda ma ban gama sanin hanyan ba, , Gani da nayi ruwan na neman ya kara karfi bisa kan na da, ya sa na fara tikan gudu, banyi nisa da gudun ba Ruwan saman ya fara saukowa da karfi, , Nayi tunanin muddin na cigaba da tafiya cikin ruwannan zan iya kamuwa da mura, ko zazzabi Sai a sannan nayi dana sanin zuwana angwan Tofa wajen Abdulhamid, , Na fara waige waige ko zanga wani mafaka don in samu in fake har sai an iddar da ruwan , sannan inyi tafiyata , Wani Zaure na hango daga nisa kadan da ni, Batare da na tsaya yanke wani shawara ba na afka cikin zauren da gudu, Shakka babu da nasan abun da zai biyo bayan shigana cikin zauren da banyi, kwadayin shiga ba Shakka babu da nasan cewa shiga na cikin zauren zai tono wani babban rauni a zuciyata ya kuma sake bude wani sabon babin Rayuwan mafarki a rayuwata, da banyi gangancin shiga ba , Ina tsaye a cikin zauren yayin da ruwa keta kwarowa a waje,sautin karan zuban ruwa a rufin gidajen jama'a shi kadai ne abun da jama'a ke iya saurara, , Zauren yana hadene da Gida saide kofan gidan a kulle yake ta ciki saboda yadda naga babu kwado a jikin kofan, , Na dau lokaci a tsaye a cikin zauren, yanzu kam an dan sarara da ruwan, sai de dan yayyafi da ake yi, wannan yasa na fara himman wucewa gida, Har na yuunkura da niyyar in mike daga tsugunon danayi, sai naji ana kiciniyar bude kofan Gidan , Na tattara hankalina gaba daya ga kofan don ganin wanda zai fito, Duk da darene amma ina ganin komai shar shar da taimakon hasken farin watan daya ke sararin sama , Kofan gidan ya bbude a lokaci daya, dishi dishin mutum idanuwana suka fara hangowa saide ban iya banbance namiji ne ko mace ba, Mutum din ya nufoni wannan karon kuwa na gane cewa macece, duba da yadda naga tana tafiya, da kuma yanayin surar jikinta, Sai da tazo daf dani sannan Numfashina ya tsaya cak, kwalkwata ta tafi hutun rabin lokaci Zuciyata ta dawo bugawa sau hudu a second daya,miyaun bakina ya kafe, da kyar na samu na sassaita kaina, Cikin dakewa na lalubo harshena na furta "BUDURWAN SIRRI" a rude na furta kalman , Tana tsaye a gabana, kamar yadda nasanta komai nata nanan, babu wani canji daya ziyarceta, Kayan dake jikinta sun jike da ruwa kuma bata sanye da hijab, hakan ya taimaka wajen baiyano da kiran jikinta, , Wani kallo ta makamin mai taken daga ina kake????? ,,,, Kai fans anya ba mafarkin na sake yi ba BUDURWAN SIRRI Marubuci Shuraih Usman @hausaebooks.cf @shuraih 99% Page 13 . "Malam daga ina ??" Ta harbeni da tammbaya fuskarta na nuna alamun bata taba ganina ba, , Karin mamaki ne ya mamayeni a sa'ilin data jefo mani wannan tambayar, , Maimakon na bata amsar tambayarta Sai natsaya ina kallonta kawai, kafin daga bisani na furta "Haseena shin baki gane ni ba"? , "To ta yaya kuwa za'ayi na gane ka, wai shin ma a ina na sanka, da har zan ganeka, naji ma har sunana ka sani?a ina kasan sunana" Bakinta kawai nake kallo yayinda take maganar sam na manta da duk wani kalubale na rayuwa dayake shirin tunkarata a sanadin wannan yarinyar, na manta irin tarin wahalan da nasha don kawai naga na mallaki budurwan sirri, , Karar tafin hannunta sune suka dawo dani cikin hayyacina , Kamar wanda ya farka daga barci, na girgiza kai ina mai cewa "Sam haseena bai kamata ace kin manta da wanda yake shirin sadaukar da rayuwarsa akan ki ba,kece..." Magana ta ya katse a lokacin da gaba dayan cikin zauren ya gauraye da hasken wutan NEPA, Kunnuwana suka daukomani muryan yara suna cewa NEPA, Minal jinnati wannas, abun danake furtawa cikin zuciyata kenan, kafin na furta "tabarakallahu ahsanul khaliqeen" , Duk ganin dana kewa haseena ban taba yi mata kallo irin na yau ba, ayau ne nasan cewa haseena tauraruwar matace, Na lura da yadda jikinta yayi sanyi ba kaman da ba, lokaci daya dukkan wani tsiwanta suka lafa, ita kanta ta zargu da irin kallon dana ke mata, Daga kai tayi sama, alaman tana son ta tuno da wani abu, Ihu mai karfi ta saki sa'annan ta sulale a kasa sumammiya, , Hankalina ya tashi da sauri na fadi a kasa kusa da ita ina mai tallabo kanta hade da kiran sunanta Da karfi nake kiran sunan nata, Karar bangaje kofa naji daga bayana da sauri na duba gefen da naji karar , Wata tsohuwace naga ta nufoni da gudunta, kallo daya nai wa tsohuwar na ga suna dan kaman ceceniya da haseena Tsohuwar wacce ban san ko wacece ita ba tana isowa ta kama hannun haseena kodubana batai ba, ta tallafo wuyanta da kafafunta ta daga ta sama cak, tayi cikin gidan da ita, , Tarin mamakinn da wannan al'amari ya bani shi ya sanya na fara jin jiri na dibana, don babu ta yadda za'ayi yar fingilar tsohuwar nan ta iya ciccibar budurwar mace kamar haseena, Na tabbata ko kosasshen akuya wannan tsohuwar ba zata iya dauka ba amma sai gashi ta ciccibi budurwa . Na yunkura da nufin na tashi nima nabi bayan tsohuwar cikin gidan, Toh alokacinne wani babban al'amari ya afku al'amarin daya sanya ni farinciki gaya, , Yun kura wata keda wuya na dumfari kofar shiga cikin gidan, Batare da wani shakku ko fargaba ba na bangaje kofan da kafata sannan na antaya ciki, 'Lahaula wala kuwwata illa billahil azizul hakeem" Na fada a bayyane yayin da idanuwana sukai arba da abunda ya kusan zautani, Shakka babu yanzu kam na yadda cewa Rayuwata a cikin mafarki gaskiyane, labarin budurwan sirri ma gaskiyane, sai de kuma kar ya kasance shima wannan karon mafarkin nakeyi, Tsintar kaina nayi cikin dajin da aka koya mani fada, a gaban bukkar tsoho zaikid, Nadai daure na isa gaban bukkan koda na tabbata bukkarne sai na nufi cikinta sai de tun kafin na kai ga shiga, naga ana kokarin futowa daaga cikin bukkar Tsoho zaikid ne ya fito fuskarsa tana mai yimani murmushi, abayan tsoho zaikid wannan tsohuwarce data dauki haseena Na saki baki cikin firgici ina kallonsu, anan take na fara tunanin shikenan na sake jefa kaina gidan jiya, "Dan saurayi Shuraihu! Taho ka zauna ba mafarki kake ba " Muryan tsoho zaikid ne ya ankarar dani daga dogon tunanin da na fada Ba musu kuwa na zo na zauna agabansu yadda kasan wani mai daukan darasi, su kuma suna zaune akan wata itace, Tsohuwar nan ta bude baki ta fara magana "Yaro hakika mun yarda da soyayyarka ga haseena, duk munga irin halin daka shiga sakamakon ta, shakka babu ka cancanci auran budurwan sirri," Tacigaba bayan taja gauron numfashi "Kai sani cewa Haseena ita kadai ce ta tsira da rayuwarta a yayin da ka dasa makaminnan, a garin bulzum ita kanta haseena abu daya ne ya taimaketa, Ta kasance a cikin kwayoyin halittar jikinta , rabin kwayoyin halittar na Aljanu ne rabi kuma na Bil'adama ne, Toh a yayin da wannan makami ya fashe, sai ya kasance kwayoyin jikinta na Aljanu sun mutu, da shike ALlah yasa tana da sauran kwana sai kwayoyin bil'adama suka maye gurbin wajen kwayoyin halittan, Yanzu kam haseena ta zamo bil'adama sak irinka Hakan ne ma yasa Zaikid ya dauketa daga duniyar nan ya kaita duniyarku ta bil'adama domin ta samu kyakyawawan kulawa," , Bakina bude nake dubansu na kasa bambance shin farin ciki zanyi na kasancewar haseena a matsayin bil'adama ko kuma bakin ciki zanyi na komo wata duniyar da babu Bil'adama, , Tsoho zaikid yayi murmushi a karo na farko yace "ina sane na sanar dakai cewa haseena ta halaka, na kuma koma da kai izuwa duniyarku, saide yanzu da kwai matsala daya" "Wata matsala kenan" Na tambaya Tsoho zaikid yace "matsalar shine haseena ta manta dukkan wani abun daya faru da ita lokacin da take duniyar nan, shi yasa ma da kuka hadu kaga bata shaida ka ba" , "Amma mai yasata faduwa dazunnan" Na tambaya ina kallon tsohuwar nan "Dogon tunani ko kuma son tunano abun daya faru lokkacin daya wuce" , "Ban fahimta ba" "Aduk lokacin da haseena tayi yunkurin tunano rayuwarta na baya toh hakane zai runga afkuwa da ita, zata iya Suma, izan kuma abun ya yawaita zai iya shafan lafiyanta, sai ka kiyayi yi mata duk wani abun da zai sanya tayi kokarin tunano rayuwarta na baya" Tsoho zaikid ya bani amsa Tsohuwar nan ta dubeni da kyau tace "Nasan kana tunanin koni wacece? Toh nice kakar haseena, dun kuwa ni na haifi mahaifiyarta Kafin Nuridden ya aureta alokacin mahaifinta ya rasu, kuma ni bansan cewa nuriddeen Aljani bane, har ya auri yata, suka samu karuwa da juna biyu, saide a yayin haihuwar yata ta koma ga mahaliccinta, Tun daga wannan lokaci ban sake ganin nuriddeen ba bare har na gana da haseena, sai a kwanakin baya wannan aljanin ya kawota wajena ina ganinta na ga fuskar yata a tattare da ita , shine yayi mani bayanin dukkan abun da ya faru " Ta karisa zancen tana mai duban tsoho zaikid 'Baba yanzu a ina haseenan take" 'Tana cikin bukkata" , Na mike tsaye na dumfari bukkar wacce tun dana fara zuwa Dajin har wa yau ban taba shiga ciki ba , Batarre da fargabar komai ba na tura kai cikin bukkar Yadda nai tsammani hakan take babu komai cikin bukkar sai wata tabarmar karau, sai wasu tarin tarkace a wani saqo, Idanuwana suka kai ga inda haseena take kwance a saman tabarmar karau dinnan tana barci , Kallonta nake bana ko kiftawa har na kariso inda take nakai hannu da zummar na taba saman goshinta cikin mamaki sai gani nayi ta bude idanunta, Da sauri na kauda hannuna , ta mike zaune tana dubana sama da kasa tace "Wanene kai ? Yanzu a ina nake" "Zaki iya kirana da masoyi yake abar qaunata," "Masoyi!" Ta nanata sunan a bakinta "Amma ina ji tamkar na taba ganin ka a wani waje daban" , Ta fadi tana kallona Nayi murmushi nace "eh tabbas kin sanni domin kuwa mun sha haduwa dake cikin mafarki a matsayin Masoya, masu begen juna, bazan taba mantawa da ranar da kika furta cewa kina Sona ba, " , A dan firgice ta zazzaro idanuwa tace "da gaske ni na fadi hakan" ' "Eh kin fadi haka kuma har ma kika bani zobe a matsayin Alkawarin aure a tsakaninmu, tun daga lokacin danai arba dake a cikin mafarkina rayuwata ta sauya, a kullum bana da buri sai na in sake yin mafarkinki, nakan raba dare ina mai tunano da kyakkyawann fuskarki , abun dayafi jamin hankali dangane dake shine murmushinki, aduk lokacin dana tunaki sai inji farin ciki ya baibayeni, duk irin kuncin dana ke ciki da zarar na tunaki sai ya yaye, Akullum addu'ata shine ubangiji ya bayyana min ke a zahiri, da shike Allah maji roqon bawansane, sai gashi Allah ya hadamu," Haseena tayi shiru tana kallona ga dukkan alamu kalamaina sun ratsa jikinta, Cikin sanyin jiki ta kwantar da kanta kas "Haseena" na kira sunanta Ta dago kai a hankali batare data amsa ba "Ina sonki, ina kaunarki, shin kina Sona" Bakintane ya fara kokarin motsi alamar tana son furta wani abun sai kuma ta fasa , Ta mike tsaye tsam ta fara tafiya cikin sanyin jiki , har ta isa bakin kofan bukkar sannan ta juyo muka hada idanuwa da ita Duk da bana iya jure kallon cikin kwayan idon haseena, a wannan lokaci sai na tsinci kaina ina mai kallonta batare da kiftawa , , Murmushi tayi yayin da gefen kumatunta suka lotse wushiryarta suka fito, hakan yayi matukar kara fidda kyawunta, daga nan sai ta fice daga bukkar a guje , Koda naga haka sai nima na tashi na fice daga cikin bukkar........ ALHAMDULILLAH Anan na kawo karshen Littafin BUDURWAN SIRRI Sai kun jini cikin sabon littafi , Duk wani kuskure dana tafka Allah ya yafeni Gefen ADABI kuwa, Ashirye nake don karbar gyararraki, shakka babu ni kaina nasan da kwai kurakurai da dama dana tafka, A kullum burina shine na ga na kware wajen rubutun hausa na adabi, DAlibi nake ba gwani ba , Dan koyo nake ba dan iya ba Wannan shine takena , (c) Shuraih 99% 2018 BUDURWAN SIRRI Publisher : (c) Shuraih 99% Author : Shuraih Usman Year : 2018 . Wannan littafin na BUDURWAN SIRRI an fara kasuwancinsa Okadabooks akan #300 , Wayanda suke son karantawa sai su duba facebook ko kuma su duba shafin Shuraih 99% , Masu neman Ebook sai suyi marmaza su garzaya shafinmu na ebook mai taken Hausaebooks.cf . Nagode wa Allah mai kowa mai komai daya bani dama na kammala littafinnan , Matukar godiya da jinjina ga ahalin ; _____ PAGE _____ Shuraih 99% Triple Abubakar Hausa Books Littattafan Hausa Dandalin Abduluk hausa books Zauran Labarai Home of Littafan Yaki And Hausa Novels Hikayoyin Yaki Hausa ebooks - pdf,txt and doc _______ GROUP _______ KINGBOY ISAH HAUSA NOVELS FILIN LITTAFAN HAUSA NEW TSANGAYAR MARUBUTA "TASKAR GIDAN LITTAFI" HAUSA BOOKS HAUSA NOVELS Chakwakiyar Soyayya Hausawa DA Pulani Donated By www.Hausazone.Com KUZO MUYI NISHADI Samee khairah novels group DANDALIN HAUSA NOVEL DUNIYAR MAKARANTA LITTATAFAN HAUS 360 Hausa Novel Books FEENAT JA'AFAR NOVEL'S HAUSA BOOKS NOVELS Just Hausa Novels kingarticle novels of abdul$bafferh Zumunci Hausa NoveLs [ÝäzèèÐ] HAUSA NOVELS ONLY *FATIMA ZARAH NOVEL GRP(HAUSA)* Hausa Novels by ASK (GREAT HAUSA NOVELS BOOKS) SOYAYYA RAYUWA CE ZAINAB MUHAMMAD AND NUHU ALIYU GUSAU NOVEL GROUP Nagode sosai da yadda kuka nuna kulawarku gareni da kuma bibiyar littafin budurwan sirri Allah ya barmu tare Nine dai nakunnan shuraih Usman inkiya 99%