An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels  BIRNIN SARAUNIYA... VISIT www.aihausanovels.com.ng For More Novel. AIHAUSANOVELS is website consists of hausa novels note, the reason of launching this site is to Entetaint, Motivate and Educate our readers. We provided hausa novels of many type, Such Adventure, love, romance, fiction, non-fiction, mystry, fantasy, action e.t.c from hausa Authors We provided a new and old novels both softcopy and hardcopy from our Author with thier permission. AIHAUSANOVELS shafin yanar gizo ne wanda yake ɗauke da littattafan hausa, dalilin bude wannan shafin shine domin Kayatar masu karatu da kuma ilimantar da su. Mun samar da littattafan hausa na nau'uka daban-daban, kama daga littafin, soyayya, tatsuniya, almara, Hikayoyi, gyara kayanki (yadda mata zasu kula da kansu a gidan mijinsu) da dai sauransu, daga Marubutan hausa. TABA KA LASHE KWANA DAYA MILIYAN DAYA! Kwana Uku kawai take bukata ya aure ta saiya sake ta takoma gidan tsohon mijinta na da. Ko wane kwana daya miliyan daya zan baka tace dashi. Farisu bai yarda da auren kisan wuta ba to amma kuma can cikin zuciyarsa naira miliyan uku na nan tana linkaya..... BIRNIN SARAUNIYA NAZIR ADAM SALIH [3/16, 4:50 PM] Abubakar Saleh AlQuyraeme: BIRNIN SARAUNIYA - 01 Kinsan fa auren da zamuyi auren kisan wuta haramun ne kuma mutumin da kike son ki sake aura bayan kin aure ni amanarsa zakici kina tsammanin da yasan abunda yake zuciyar ki yanzu zai yarda ya baki koda kwandala ce? Abin duniya fa ba abakin komai yake ba kiji tsoron ubangiji SALMA kada duniya ta...... "Amincewar ka nake bukata ba wa'azin ka ba idan ka yarda kowanne kwana daya zan baka naira miliyan daya. Miliyan uku kenan kwana uku saika sake ni.... Zo nan ka gani Ta bude but din motar buhuna biyu cike suke da yan wazobiya sababbi fil. Zanyi shawara nace da ita duk fa da wa'azin danayi mata abaya yanzu Na manta dashi...... BIRNIN SARAUNIYA Copyright © Nazir Adam Salih - 1998 Hakkin mallaka (M) Nazir Adam Salih - 1998 KAMNAS PUBLISHERS - 1998 An Buga shi a JET AGE PRINTERS TARIHIN BUGUNSA. An fara buga shi a Jet Age - 1998 A KULA Wannan littafi kagagge ne an rubuta shine badon cin zarafin kowa ba sai don nishadi dakuma gargadi ga al'ummar da ke jin yaren hausa akan irin yadda zamani ya rikice arayuwa. Tsarin rubutu a na'ura mai kwakwalwa: URGENT COMPUTERS NO=497 KASUWAR KURMI BIA YAN GURASA JAKARA KANO. Wanda ya shirya. TIJJANI IBRAHIM KURAWA - BAHAGOH RUWA BIRNIN SARAUNIYA NA NAZIRU ADAMU SALIHU (NAS) (NAS 98) BABI NA DAYA Acikin yammacin wata ranar Asabar ne nafara haduwa da ita yammaci ne mai dauke da ni'imtacciyar iska mai ratsa jiki tareda kamshin damina dake nuni da cewa akowane lokaci daga yanzu ruwa na iya samuwa. Aduk lokacin da iskar ta busa sai kaji dadi da nishadi maras misaltuwa sun rufe ka hakika muna bukatar sauyi musamman ma idan akayi la'akari da irin zafin da aka zabga a iya kwanakin da suka shude........ YARIMA A. GANGARIYA (jikan sidi mai jaka) [3/16, 4:51 PM] Abubakar Saleh AlQuyraeme: BIRNIN SARAUNIYA - 02 Hakika muna bukatar sauyi musamman ma idan akayi la'akari da irin zafin da aka zabga a iya kwanakin da suka shude. Duk da yake daddadar iskar na busawa ko ina cikin babban titi ne hakan bai hanani gumi ba kodayake ba abin mamaki bane idan akayi la'akari da irin rashin sa'ar data sameni aranar na dubi kayan Marmarin da nake sayarwa wadanda ke gefen titi a gindin bishiya sainaji bakin ciki ya sake rufe ni gumi kuma ya cigaba da keto mini kamar ruwa duk rabin kayan sun lalace musamman ma ayaba duk ta latse ta zama kamar teba sai wani ruwa ruwa ne ke fita ajikinta sannan ne abunda yafaru safiyar ranar yafado mini. A safiyar ranar an tashi da iska mai karfi wanda a sakamakon haka ne wani katon reshen bishiya ya karye abin tsautsayi saiya fado akan teburin kayan gaba daya ya tintsire wasu daga cikin lemukan suka watsu kan titi motocin suka tattake ayabar kuma ta lallatse daga karshe na tattaro kayan na sake wankewa na shanya ragowar masu kyaun a gefe su kuma lamutsatstsun gefe guda. Abinda yafi damuna a yanzu shine tun tun safiya har zuwa yanzu banyi cinikin koda naira arba'in ba abin kamar hau innalillahi Wa'inna Ilaihi raji'un abinda na cigaba da cewa kenan acikin zuciyata lokacin dana duba agogona naga karfe hudu na yamma. Tsoro da fargaba su ka kamani domin bansan abunda zan cewa mai kayan ba idan nakoma wajen sari gobe daman kayan bashi muke dauka idan mun sayar mu biya mu dauki wani to ga shi kuma abinda yafaru ni kuwa nasan ko yanka ni zaiyi saidai ya yanka ni din domin bani da abin biya saidai ko....... Tunanina ya katse adaidai lokacin dana hango shi ya nufo inda nake ba zato ba tsammani kamar an jefo shi shine mutum na karshe danake tsammanin zan gani agurin. Ya nufo ni yana murmushi mai kayan ne dake bamu bashi. Assalamu Alaikum Amin Wa'alaikumussalam..... Bakina ya kasa amsa sallamar abunda ya hanani amsa sallamar shine irin kallon danaga Yayiwa teburin kayan ta yamutse sannan ya dubeni yace ya samu kayan na gansu haka a ratattake kamar garken shanu ya bita kai? Wal..wallahi reshen bishiya ne ya yafado musu nace dashi ina in ina wannan wani abune da bai shafe ni ba yace dani. Inafatan ka hada min kudin kayana sannan yaci gaba da cewa daman karbar kudina ne yakawo ni saboda an kawo mini wasu kayan masu araha inason sayen su don haka ka ganni anan yanzu ma daga wurin su SALLAU Nake duk sun bani nasu. Yayi shiru yana duba na nasan abunda yake nufi don haka saina zato cinikin naira arba'in din danayi na tura masa gabansa na juya kaina gefe guda na bata rai. Menene wannan? Ya tambaye ni. Cinikin danayi ne nace dashi saika jira zuwa gobe idan na sayar na cika maka kudin ka ni na dogara da Allah ya mayar mini da asarar danayi domin nasan babu mamaki sainayi maka ciko. YA dubeni a fusace sannan yace cikin irin muryar da zaka iya kira bambaro Ai bamuyi haka dakai ba babu kuma abinda ya shafe ni da asarar dakayi ko kusa bata dameni ba daman ai sai dana gindiya maka sharudda kafin nabaka kayan kasan kuwa acikin sharuddan harda asara ko da faduwa kayi saika biyani kudina. Yayi shiru na dan lokaci yana mai da numfashinsa fuskarsa ta hada gumi sharkaf kamar ruwa....... [3/16, 4:52 PM] Abubakar Saleh AlQuyraeme: BIRNIN SARAUNIYA-03 Fuskarsa ta hada gumi sharkaf kamar ruwa. Dana san haka zata faru da ban baka kayana ba daman saida nace bazan bada kayana ba amma sallau ya takura min nabaka na amince dana baka amma ni daman da ganinka nasan zakayi sakarci in banda shashanci ina kai ina..... Kada ka zageni na katse masa hanzari domin nafara ggajiya da surutan banza dayake mini idan kudkinsa ne kakeyiwa wannan ihun to ka ceci numfashinka kar ciwon zuciya ya kama ka abanza zan biyaka amma idan na sayar... Baka isa ba yace dani ko sallau da muka dade dashi muna yin harkar bai isa yayi mini haka ba ban damu asararka ba ni kawai abinda na damu dashi shine kudina. Yayi shiru na dan wani lokaci muna duban juna yan mitsi mitsin idanunsa sunyi jawur katuwar faddadar fuskarsa mai kama da faifan garmaho ta hadu da gumi har naso takeyi kamar waina dan gajerene kakkaura baki bashida gashin baki bashi kuma da gemu sai dan tsurut din hana karya dayayiwa kansa hanya tsakanin habarsa dakuma fatar bakinsa kamar jela tsatstsewala hancinsa ya hade da fuskarsa amma ya dan bude daga karshe hancin yafi kama da usur fiyeda hancin mutum bakinsa wangameme kamar an datsa masa da gatari idan ba ganin kusa kayi masa ba saika rantse da Allah bashida kunne domin duka girmansa bai wuce fadin kwankwalati ba rigar dake jikinsa ruwan tsanwa-tsanwa ce wandonsa kuma launin fatar jakine takalminsa kamar kwale kwale tsohuwar hular dake kansa ita ta tuna mini da wani tsohon kakana daya rasu shekaru kadan kafin al'amarin yafaru zaren dake dinkin hular ya ratattake ya kode yakuma jeme har wahalar duniya tasa shi yafara zazzarewa da kansa. Ahaka mutumin ya tsaya agabana yana dubana da mummunanr fuskarsa. FARISA ya kira sunana akaro na farko nikuwa ko sunansa ban iya tunawa saboda yau kwana goma kenan da fara karbar kaya agurinsa. Kasan duk yanda za'ayi ka hada mini kudina daga nan zuwa gobe yaci gaba da cewa idan kuma kaki to Wallahi hukuma ta karbar mini abu guda ne baka gane ba farisu shine banida mutunci akan harkar kudi zan jiraka gobe karfe bakwai na safe idan bakazo mini da kudina ba to karfe takwas a folis siteshon zatayi maka yace dani ta hanyar amfani da wangamemen bakinsa kafin na sami abin cewa tuni yayi gaba yabar ni sororo agurin zuciyata cike da tunanin hanyar da zanbi na samo masa kudinsa. . Zuwansa gurin shiyasa sani manta da duk abinda yafaru abakin titin. Domin dodon kunnena baya sauraron komai sai maganarsa. Na daga kaina ahankali lokacin da rugugin motocin dake ta famar safa da marwa akan titin yaci gaba d adukan dodon kunnena. Lokacin dana dago kaina saina fahimci ashe har yara sun taru agindin teburin nawa suna sauraron bambanin fadan mutumin. Dago kaina keda wuya sai duk yaran suka watse wadanda mafi yawansu almajiraine. Motoci suka ci gaba da safa da marwarsu launi daban daban nikuma ina kallonsu ina mafarkin mallakarsu idan nace wannan azuciyata idan wata tazo saina fasa. Karfe hudu da minti arba'in da biyu tayi lokacin tashina ya kusa kenan don haka sai gabana yacigaba da faduwa domin nasan tabbas gobe a ofishin yansanda zan kwana domin banida hanyar da zan sami kudin da zan biyashi. Ahaka na tsaya gindin teburin inata karanta duk addu'ar da tazo bakina sannan zuciyata ta koma baya tun sa'ar dana gama karatuna na makarantar gaba da firamare wato sakandire aduk shekararmu babu wanda ya samu sakamako fiyeda nawa sakamakona yayi matukar kyau a jiharmu nine na daya wato dalibin dayafi kowa samun sakamako mai kyau amma abin bakin ciki saigashi rashin kudi ya hana ni cigaba da karatuna saboda karatun ya zama na kudi duk kyawun sakamakaonka idan bakada kudi to ya zama shirme domin baiyi ma amfani saidai ka saka sakamakon agaba kayita kallo. Mahaifana basuda karfin da zasu nauyina dama sakandiren ma wani makwabcinmune aminin mahaifina ya dauki nauyin karatun ina shekarar karshe a makarantar Allah yayi masa rasuwa ina da kanne biyu mace da namiji amma duk acikinsu ni kadaine nayi karatu saboda karamin karfin da mahaifinmu sukeda shi mahaifina lebura ne a wani kamfanin kwarori dan albashin da ake bashi bai isar mu saye abinci balle ayi zancen cigaba da karatuna ganin haka shiyasa na yanke shawarar samun sana'ar yi domin tara kudin da zan cigaba da karatu to ga irin sana'ar nan nafara kwana goma kacal da farawa saigashi har ana hsirin kaini ofishin yan sanda da farko aikin kamfani nafara to abin ka da dan boko ko kuma ince malalacin mutum irina saboda inada lalaci danaga bazan iya ba saina hakura shine to daga karshe na sami sallau wani mutum ne na kirki a nan unguwar mu nayi masa bayanin halin da nake ciki shine yaji tausayina ya hadani da...... Tuunanina ya katse hankalina yakoma bakin titin. Malam ko bakajine inata faman kira wata zazzakar muryace mai kamar sarewa take cewa dani haka. Nayi firgigit na fuskanci bakin titin kamar a mafarki sainaga zungureriyar mota a dab da inda teburina yake banji lokacin da ta tsaya ba don haka sai abin yabani mamaki motar ruwan tokace tana sheki kirar marsandi ce sannan ajikin fale falen lambar motar an rubuta kamar haka SALMA ONE.... [3/16, 4:53 PM] Abubakar Saleh AlQuyraeme: BIRNIN SARAUNIYA-04 Ajikin fale falen lambar motar an rubuta kamar haka SALMA ONE. Santala santalan kyawawan kafafuwanta ne suka fara taba kasa sanye suke cikin bakin takalmi wanda ke lullube da tattausan gashi mai sheki in dai kuma har ba idona ne yake nuna min karya ba arubuce ajikin dan wani karfe dake lilo ajikin takalmin kalma ce kamar haka GOLDEN HEART. Tun kafin jikinta yagama fitowa daga cikin motar kamshin turare ya hade gurin tunda nake ban taba shakar wani abu mai dadin turaren jikinta ba. Tunani kakeyi ne? Tace dani tana dan murmushi lokacinda ta matso kusa dani sai kamshin turaren dake jikinta ya dada rudani jikina ya dauki rawa na kasa yi mata magana abinka da farin shiga ni ko acikin abokaina matsoracin matane murmushin daya ci gaba da bayyana fuskarta shi ya tabbatar mini data gane halin danake ciki Yaya naga duk lemon naka ya lalace tace dani haryanzu murmushin bai bar fuskarta ba. Nayi karfin hali na daga kaina muka hada ido da ita akaro na farko tun zuwanta nayi matukar mamaki domin fahimtar ashe kallona take bata dauke ido. Reshen bishiya ne ya fado musu hajiya..... Nace da ita ina in-ina na dubi kayan dake jikinta masu sheki alokacin data karkatar da kanta zuwa kan teburin kayan marmarin da nake sayarwa tana sanye da doguwar riga siliki launin sararin samaniya kanta lullube da jan gyale mai shara shara Ta juya da fararen manyan idanunta kan fuskata muka sake ido hudu a karo na biyu kwarjininta shiyasa na fara kawar da fuskata atunanina zatayi min kimanin shekaru ashirin da biyar zuwa da takwas sannan indai ta shekara za'a bi to yayata ce. Dan samari ban ko san sunanka ba? Tace dani tana murmushi mamaki ya rufe ni bangane abinda take nufi ba yaya daga sayen lemo za'a tambayi sunana. Na dubeta sannan nace da ita menene dalilin sanin sunana? Laifi ne don an tambayi sunanka? Tace dani tana murmushi sannan taci gaba da cewa daman lemon da ayaba nake son saya saidai kuma gashi nayi rashin sa'a duk lemon kanana ne gashi kuma mafi yawansu sun lalace. Nayi shiru inajinta da kunnen sauraron tazo-mu-ji-ta domin nasan duk maganar da take fadi karya take a iya tsawon kwanakin danayi gurin na fahimci abu guda ba irin sune suke sayen lemona ba. Mafi yawancin masu sayen lemona leburori ne da kananan ma'aikata to amma wannan da duk jikinta ke cewa NAIRA yaushe.... Ta katse tunanina don Allah idan bazaka damu ba kuma kaga babu takurawa ga kudina zan baka gobe idan kaje gurin sayo kayan ka sayi mini manya manyan lemo da ayaba din zan aiko direba gobe da rana ya daukar mini ga mamakina sainaga ta bude jaka ta dauko damin kudi na wazobiya ta miko min na bude baki zanyi magana saita daga hannu har yanzu murmushin nan bai bar fuskarta ba kada ka damu idan ka saya ka rike guntun kudin ka rage asarar dakayi. Zan tafi tunda kaki fada min sunan naka. Tace dani tana murmushi sannan ta nufi motar nikuma nabita abaya ta shiga ta zauna sannan ta leko kanta ta tagar motar azatona wani abu take son fada don haka saina matsa kusa na dafa tagar motar da hannuna muka sake hada ido da ita sannan ta kanne idonta daya. Murmushinta yafadada ta dafa hannuna da tattausan hannunta mai sanyi sannan ta zaro wani dan karamin kati daga cikin jakarta ta miko mini adireshin gidana ne me yiwuwa direban nawa bazai sami damar zuwa ba kaga saika kawo mini kayan da kanka kenan. Ban ko duba katin ba saina tura shi a aljihun dana zuba kudin data bani haryanzu hannunta adafe yake da hannuna. Tattausan hannunta ya sake matse hannuna sannan tayi kasa kasa da murya tace dani. Bazaka fada min sunan naka ba? Nayi murmushi akaro na farko sannan nace ita sunana FARISU Alokaci guda kuma na janye hannuna dake karkashin nata hannun. Tayi sauri ta sake rike hannuna sannan tace dani Haba Farisu yaya zaka tafi muna yar hira na dubeta sainaji kunya ma ta rufe ni. Sunkuyo nan kaji tace dani na tura kaina ahankali cikin tagar motar cikin mamaki sannan kamar da wasa sai siraran kyawawan yan yatsunta suka shafi fuskata sannan tace dani Sunana...... Bata karasa ba sainaji dirin mota abayana ban juya ba saboda ganin yanayin dake fuskarta ta bude baki kamar zatayi ihu idonta na kallon motar dake bayana ta tsaya.. Wani abu mai kama da kofaton doki ya mari fuskata ta baya naji anyi sama dani an buga da kasa sannan akasa kafa aka take wuyana wani kuma ya rufe bakina sannan aka jefani bayan kujerar motar ta baya aka rufe karti uku suka danne ni sannan duka abin yafaru ne cikin abinda baifi dakika talatin ba aka fizgi motar da gudu nikuma suka cigaba da luguiguita ni kamar lemon yara suka dora wata zungureriyar wuka a makogwarona sannan dayansu yace dani. Zaka iya yin ihun idan kaso amma kada ka zargi wukar idan ta zarce kai tsaye ta rabaka kanka da gangar jikinka sannan yaci gaba da cewa. Abinda yafi maka sauki shine kayi shiru kawai mai yiwuwa idan kayi hakan ka tsira da ranka amma fa dole ne mu dan sassama ka mu dan karya kafarka da hannuwanka. Suka fashe da dariya sannan ne to motar taja ta tsaya suka jefoni waje tun kafin na gama fadowa wani daga cikinsu yasa kafarsa ya daki bayana sannan....... [3/16, 4:54 PM] Abubakar Saleh AlQuyraeme: BIRNIN SARAUNIYA-05 Tun kafin nagama fadowa wani daga cikinsu ya daki bayana na fado da fuska agefen titi. Na yunkura na tashi zaune fuskata duk ta kukkuje samarin hudu suka zagayeni duk kusan shekarunmu daya dasu guda uku daga cikinsu kansu daya sunada matsakaicin tsaho na ukunsu shine dogo fari mai dogon gemu kamar burushi kansa a aske yake tas dukkansu suna sanye da yankakken wando jeans dakuma bakar suwaita agaban kuma rigar babban nasu an rubuta cikin manyan haruffa kamar haka IJAKALA. Menene hadinka da ita? Babban nasu ya tambayeni na buda baki zan amsa saiya cigaba da cewa ba kai ba ita daga yau abinda tace mu ce dakai kenan idan kuma ka sake muka sake ganinta da ita toh sunanka Gawa. Banga lokacin daya daga hannunsa ba amma naji lokacin da naushin ya sauka a fuskata babu abinda zan iyayi akai. Na fadi anan sumamme lokacinda na farka sainaji ni lullube cikin wani abu kamar buhun algarara abin haushi koda na tashi sainaga ashe gurin sayar da lemona suka dawo dani suka kuma sakani a karkashin teburin lemon sannan suka rufeni da buhun algarara. Na tashi tsaye kaina nata buguwa kamar ana wasa da guduma aciki har yanzu kayana suna nan kamar yadda nabarsu ban ko damu da in dauke su ba sai na nufi gida. Misalin karfe goma na dare na bude dakina na shiga. Mutanen gida sunyi barci in ka dake muryar babana dake karatun alkur'ani mai girma fitilar kwan da na manta da safe ban kashe ba haryanzu tana ci na lalubi aljihuna na zaro katin data bani sannan na duba abinda ke rubuce a jiki BIRNIN SARAUNIYA NO-007 TITIN LUMFA.. Nayi ajiyar zuciya gamida godiya ga Allah daya sa katin bai fadi ba akalla dai nasan inda zan sameta. Birnin sarauniya.... Na nanata sunan cikin zuciyata ban taba zuwa unguwar ba saboda ba ajina bace. Amma duk da haka gobe zan gwada..... TOH MASU KARATU SAIKU BIYO NI ZUWA GOBEN DON GANIN YADDA ZATA KAYA [3/16, 4:54 PM] Abubakar Saleh AlQuyraeme: BIRNIN SARAUNIYA-06 Na lalubi aljihuna na zaro katin data bani sannan na duba abinda ke rubuce a jiki BIRNIN SARAUNIYA NO-007 TITIN LUMFA.. Nayi ajiyar zuciya gamida godiya ga Allah daya sa katin bai fadi ba akalla dai nasan inda zan sameta. Birnin sarauniya.... Na nanata sunan cikin zuciyata ban taba zuwa unguwar ba saboda ba ajina bace. Amma duk da haka gobe zan gwada..... BABI NA BIYU Yau bazakaje sarin lemon bane? Mahaifina ya tambayeni lokacin danaje gaidashe awashegarin ranar da abin yafaru. BIRNIN SARAUNIYA nake son zuwa nace dashi ya dubeni na dan lokaci sannan yace dani me zakaje yi acan? Kaifa baka rabuwa shiririta daga farawa har zaka fara kawo matsala ko? Nayi shiru na dan lokaci sannan nace dashi wani aiki ne za'a samar mini acan ina tsammanin kuma yafi sayar da kayan marmarin riba. Har zaiyi magana sainaga yayi shiru yana duban fuskata me ya sameka haka a fuska? Tuni daman na shiryawa wannan tambayar Babur ne ya bugeni jiya zan tsallaka titi yayi shiru na dan lokaci yana jan tasbaha sannan daga karshe yace dani. Tashi ka tafi Allah ya taimaka idan ka sami aiki shikenan idan ma baka samu ba to gobe kaje sarin lemonka domin ni dai abinda nake so da kai shine kayi kokarin ganin kacigaba da karatun ka ni kuma sainaji da Wahalhalun gida. To baba. Nace dashi lokaci guda na tashi tsaye sannan na nufi dakina tun da asuba daman nayi wanka. Tun daren jiya na lissafa kudin data bani Naira dubi biyar ne acikin kudin ne na ware dubu daya sauran kuma na boye su ina fitowa daga cikin gida saina nufi kasuwa wajen da muke saro lemo. Karfe bakwai da rabi na isa kasuwar rabin awa kenan ya rage ya turo mini da yansanda tun daga nesa na hango wangamemen bakinsa mummunar fuskarsa ta yamutse lokacin da ya hange ni jama'a sun fara cika rumfar kowa na harkar gabansa masu sara da kudinsu nayi masu karbar bashi ma irin namu nayi sannan agefe guda almajirai na ta tsintar rubabbun lemo. Assalamu Alaikum na yi sallama sauran suka amsa amma shi bai amsa ba. INA KUDINA? Yace dani cikin rawar murya mutane sukayi shiru suna sauraren mu na zaro naira dari biyar da ashirin daga cikin naira dubun data bani sannan na tura masa kudin cikin aljihun babban rigarsa na juya ban ko ce masa sai anjima ba ina barin gurin sainaji hayaniya ta sake barkewa adaidai lokacin ne na hango Sallau ya nufo gurin nayi sauri na sauya hanya saboda banason bata lokaci tuni daman na gama shirin tafiyata tun jiya da daddare don haka saina wuce kai tsaye zuwa bakin titi ban dade ba wani dan tasi ya bullo na daga masa hannu ya tsaya. Ina zuwa? Ya tambayeni cikin rubabbiyar hausarsa na zaro katin na tura masa shi cikin tagar motar yayi nazarin katin na dan dakiku sannan ya girgiza kansa yace. Birnin sarauniya ko? Nace masa Eh yayi murmushi sannan yace SHIGO. Na bude gidan gaba na shiga sannan direban ya fizgi motar aguje kamar wanda ya sato ta. Ya dubeni sannan yayi murmushi adaidai lokacin da muka hau babban titin BAROON. direban dogo ne siriri bayerabe doguwar fuskarsa kamar anja ta da rula kowanne kunci an tsaga shi taya-taya kamar kwarya sanye yake da riga da wando na atamfa doguwar hularsa kamar husumiyar masallaci. Birnin sarauniya tab unguwar manya bayeraben yace dani. Naji ance duk fadin kasar nan babu tsararriyar unguwa data kai koda rabinta. Kafadawa kowa nace dashi lokacin dana muskuta sannan nace dashi naji ance wai babu gidan kasa da naira miliyan goma a unguwar gaskiya ne? Direban yayi wana gaba da shi ham sannan ya dauke kan motar muka hau kan titin TANIM ai sai abinda ka gani ma in dai birnin sarauniya ne domin ayadda naji ana jita-jita ance wai kana shiga unguwar zakaji tana kukan NAIRA NAIRA NAIRA direban ya fashe da dariya nayi sauri na toshe dodon kunnena banajin dariyar tasa zatafi kukan jaki dadin sauraro. Shi azatonsa wai ai yayi abin dariya ne jita jita zancen banza. Nace dashi gamida dan murmushin yake don dai karya gane cewa banji dadin dariyar da yayi ba. Kafin nacigaba da labarin danake shirin baka bari na baka hoton birnin sarauniya. Lokacin da muka shiga unguwar saina lura da duk kusan ginin unguwar irinsu daya tun da nake bantaba ganin unguwa mai tsafta irin ta ba kyawawan tituna na sheki sun mamaye ko ina cikin unguwar kofar gidan kowa a unguwar korayen ciyayi ne lif lif lif kamar ka yaga ka ci inda kuwa kaga babu ciyawa to tayil ne a shimfide unguwanninmu namasu karamin karfi sai suka fado mini azuciya lokacin dana tuna ko ina ka duba takardu ne da yayi marasa amfani ga bola ko ina. Wani abin bakin ciki kuma shine wadanda alhakin kwashewar ya rataya a wuyansu basu damu dasu kwashe ba. Kallo daya nayiwa gidan na tabbata shima ba wani babban gida bane amma tsarin gidan ya firgita ni hakan shiyasa ni tunanin ashe mu a kango muke kwana Direban ya taka burki sannan yajuyo yace dani Munzo nagani nace dashi ai komawa zakayi dani inda ka dauko ni. Direban ya dubeni cikin mamaki sannan yace EH. Bai sake cewa komai ba. Na dubi gidan a zagaye yake da yar madaidaiciyar katanga mai launin ruwan madara kyawawan furanni masu yado sun mamaye jikin katangar ko ina abin dai sai wanda ya gani kofar gidan ta farin kyaure ce ruwan azurfa amakale ajikin kofar wani dan karfe mai launin gwal an rubuta cikin kananan Haruffa kamar haka LUMFA STREET NO 007. Yanzu kam na tabbatar da gidan ne. Mu tafi nace da direban adaidai lokacin dana dubi karamin masallacin dake kofar gidan wanda kuma na tabbata baifi yaci........ [3/16, 4:55 PM] Abubakar Saleh AlQuyraeme: BIRNIN SARAUNIYA-07 Wanda na tabbata baifi yaci mutum tara ba har da liman nayi mamakin masallaci ne ko kuwa dakin kiwon kaji daga karshe dai na yardarwa kaina masallaci ne nayi kokarin hangen tsakiyar gidan amma dogwayen bishiyoyin turaren da suka zagaye gidan su sukace basu yarda dana hango aljannar duniyar dake boye abayansu ba. Abin da kawai nake iya hange shine shekin karfen da akayiwa tagar wani daki dake saman benen ado. Aduk lokacin da hasken hantsin ranar ya fada kansa saiya haske mini ido ta cikin tagar motar. Kafin na rufe bakina direban ya fizgi motar mukayi gaba nagama ganin abunda nake son gani. Na farko naso na sauka kasa nayi nazarin gidan amma abu biyu suka hanani na farko shine kayan da suke jikina basuyi daidai da yanayin unguwar ba domin naji jita jita cewa idan ka shiga Birnin sarauniya da wulakantaccen kaya ajikinka yansanda na iya cafke ka amatsayin barawo don haka duk wanda ka gani a unguwar tsaf tsaf yake sai su 'ya su wadanda suka isa sannan naira ta daure musu gindi abu biyu kuma shine tun lokacin da dan taksi din nan ya daukeni na lura da bakar motar nan da aka jefani cikinta ajiya na binmu abaya idan har ba idona ne yake fada min karya ba to na so na hango mutumin nan mai dogon kai kamar shantu acikin motar wannan shine abinda ya hanani fitowa daga cikin motar bankuma bari dan taksi din yagane cewa ana bin mu abaya ba. Abin ya wuce sanina koda yake nayi alkawarin sainaga yarinyar nan saikuma ta fada min dalilin dayasa ta janyo min duka haka kawai ba gaira ba dalili sannan kuma saina rama dukan da akayi min amma da farko bari na fara ganin yarinyar. Nayi murmushi lokacin dana juya na hango bakar motar na binmu abaya motoci biyu ne atsakaninmu da muka sake hawan titin Baron. ****** ****** ****** ***** ********** ***** ****** Na dubi kaina ajikin dogon mudubin dake dakina nayi murmushi sannan abinda yake jikin mudubin shima yayi murmushi. Sannan na tabbata nine. Tunda nake ban taba sa kaya masu tsada kamar wadannan ba kusan duk rabin kudin data bani awajen kayan yatafi farin kambas din da kuma bakin wandon jeans sunyi matukar dacewa da farar suwaitar dake jikina don daurewa karya gindi harda hula hana sallah baka sannan na rataya katuwar jaka abayana kamar dai irin yadda yaran masu hannu da shunin dake birnin sarauniya suke shiga haka nima nayi. Hakika irin yadda na ganni a mudubi abin ya burgeni sannan na rufe fuskata da bakin tabarau shiri yagamu sai BIRNIN SARAUNIYA. Karfe goma sha daya da minti uku na isa birnin sarauniya tun dana shiga unguwar babu wanda yayi miki koda kyakykyawan kallo domin na saje da sauran samarin dake unguwar tun daga nesa na hango mai gadin gidan yana alwala azatona kiyamulaili zaiyi don haka saina make saida nabashi kusan minti uku bayan na tabbata yafara sallar saina nufi kofar gidan nayi sa'a kasan takalmana na roba ne don haka basa wani kwakkwaran sauti da takun nawa yake bayarwa acan cikin zuciyata wani abu na ta kururuwar kira na a'a'a'a'a!!! Farisu ka dawo ka koma gida kada ka jefa kanka cikin abinda yafi karfinka amma duk kururuwar bata sa ni nayi koda gezau ba. Na tura kofar gidan kai tsaye kamar wanda yasan inda zashi ga mamakina sainaga kofar ta bude nayi sauri na rufo kofar bayana sannan na nufi cikin gidan ahankali koda yake banko damu na boye takun sawuna ba na nufi dan karamin benen dake tsakiyar gidan rabin gidan ahaske yake kamar rana da kwayayen lantarki amma daya bangaren cikin duhu yake abin yabani mamaki sannan kuma yabani damar lallabawa ta cikin duhun ta hanyar boye jikina cikin bishiyoyin turare dana dorawar turawan dake ko'ina cikin farfajiyar gidan. Ina cikin tafiya saina hangi kafar benen daga bangaren kudu batareda na sake tunani ba saina tasamma kafar benen..... Bako babu sallama wata siririyar murya tace dani lokaci guda kuma naji wani sassanyar hannu mai taushin gaske ya dafa kafadata tsigar jikina ta tashi naji kamar wayar lantarki ta tabani sannan kamar nayi fitsari a wando domin razana na juya ahankali cikin rawar jiki azatona zanyi ido hudu da mai kan shantu nayi ajiyar zuciya alokacin datayi maza ta kama hannuna muka tafi saman benen ta danna wani abu kofar ta bude sannan muka shiga dakin. Kamar sauran dakin masu hannu da shuni shima mamaye yake da kilishi gamida manya manyan kujeru na alfarma wadanda ke barazanar hadiye duk wanda ya zauna cikinsu. Dakin ya tsaru iya tsaruwa abinda yafi kuma daukar hankalina fiyeda komai shine wani hoto dake makale ajikin bangon dakin. Hotonta ne ita da wani mutum gajere mai dogon sanko kamar titin mota hancinsa kamar gutsurarran nakiya idanunsa can ciki kamar na kififiya nayi mamakin ko wanene mutumin. Na zabi kujera daya na nutsu aciki sannan na bude jakar danazo da ita na dauko lemo da aya acikin jakar leda na ajiye a tsakar dakin sannan nace da ita GA SAKON KI NA KAWO. Tayi murmushi sannan tace nasan yanzu ka daukeni makaryaciya kuma mayaudariya amma inason don Allah ka saurareni da kunnen basira. Inajinki nace da ita. Da farko dai kamar yadda nasan tuni ka fahimta shine duk maganar da.......... [3/16, 4:56 PM] Abubakar Saleh AlQuyraeme: BIRNIN SARAUNIYA-08 Da farko dai kamar yadda nasan tuni ka fahimta shine duk maganar da mukayi jiya zancen sayen lemo duk bogi ne sannan ba gaskiya bane. Nayi murmushi sannan nace da ita kice kawai karya kike yi ko kunyar fada kikeyi? Bata amsa ba saitaci gaba da cewa Farisu ni dai sunana SALMA kuma na kasance marar sa'a da rabo shine nake son don Allah ka taimakeni. Na dubeta kamar wanda yake tunanin ba kanta daya ba sannan nace bangane inda kikasa gaba ba. Shekaru biyar da suka wuce akayi mini auren fari nida wani hamshakin mai kudi taci gaba da cewa sannnan watanni uku da suka wuce wani sabani ya shiga tsakaninmu dashi amma laifina ne ni na uzura masa har yayi fushi dani cikin bacin rai yayi min SAKI UKU Tayi shiru tana tunani sannan ta tashi tsaye ta leka waje ta cikin tagar dakin bayan ta danyi dan lokaci tana tsaye awajen saita dawo ta zauna inafatan kana fahimta tace dani. Ina dan fahimta amma zancen ya gundureni domin kuwa bai shafeni ba abinda kawai nazo naji shine menene hadinki da mutanen da suka casa ni jiya da daddare tayi banza dani bata amsa ba sannan taci gaba da cewa yana da 'ya daya amma uwarta ta rasu bayan rasuwarta ya aureni yana mutuwar sona saidai kuma idan da wani abinda yarsa taki jinin ta gani aduniyar nan nice ta tsaneni matukar tsana saboda ganin ya manyata kuma muna tsammanin da kyar zai kara shekara biyu aduniya duk da yake dai sanin gawar fari sai Allah amma kasan anfi baiwa mara lafiya da tsoho mutuwa tayi murmushi sannan taci gaba da cewa yana da tarin dukiya kamar dan karuna kuma inada labarin cewa duk kusan rabin dukiyar ni zai baiwa tun kafin ya mutu saikuma gashi acikin rashin sa'a da tsautsayi yayi mini saki uku to amma kuma yanzu yadawo yana mutuwar sona saidai babu damar sake aure tsakaninmu dashi har sai na auri wani idan na fito saina koma gidansa tayi shiru tana maida numfashinta sannan tace dani... Watanni biyu da suka wuce nayi kokarin samun yaro matashi wanda zai aureni idan munyi sati guda kuma saiya sakeni na koma gidan mijina. Shikuma na biya shi. Tayi kwafa sannan tace Farisu Wallahi samari uku nayi kokarin aura amma duk shegiyar yarinyar nan tasa yan ta'addar mahaifinta sun tsorata su kai akwai wanda tasa suka..... Kofar ta bude kamar iska ta doko ta sannan ta fado cikin dakin kamar aljannu kowannensu rike da katon kulki babbansu na da dogon gemu kamar burushi sannan agaban rigarsa an rubuta cikin manyan haruffa IJAKALA. BABI NA UKU Nayi tsalle na tashi daga cikin kujerar sannan cikin hanzari na shiga gaban salma wacce ke zaune akan kujerar kamar ruwa ya cinyeta alamun razana karara a fuskarta. Bakaji kashedinmu ba ko? Mai kan shantu da dogon gemun ne ke magana yanzu ne zakaga amfanin taurin kai babu mamaki daga yau bazaka sake amfanuwa ba. Sannan katon ya juya ya kalli sauran ukun masu jajayen idanu kowannen su ya daga kulkinsa sama sannan suka fara matsoni idanunsu akan gangar jikina atsammanina kowa na auna inda zai dukeni ne adaidai lokacin ne salma ta tashi tsaye sannan tayi sauri ta shiga gabana tareda kareni. Kuyi min duk abinda kuke so amma kada ku sake ku taba shi. Tace dasu cikin rawar murya inason sa don haka babu wanda ya isa ya taba min shi kuma baku isa ku hanani aurensa ba ku koma kuce da SHEGIYAR data aiko ku na hana adake shi mai dogon gemun ya fashe da dariya yar tsakuwa mun ji ki ba sau daya ba ba sau biyu ba kin sha fadar haka akan guntun samarin da kika son kiyi auren kisan wuta dasu shin kina tsammanin kurinki zai hana mu aikata shi? Ba'a bamu iznin tabaki ba don haka ki kauce ki bamu guri sauri muke mu aika ta shi. Bazan kauce ba tace dashi saidai ku kashe ni mai dogon gemun banza tace dashi a fusace. Hakan data fada shi ya kawo karshen hakurinsa yayi taku biyu gaba ya kifa mata mari karfin marin shiya jefota baya ta maku ajikina nayi sauri na riketa ta kwalla kara alokacin daya sake kawo wani marin tsakaninmu dashi babu nisa domin ina iya jin hucin numfashinsa a fuskata hankalinsa gaba daya ya koma kanta hakan shi ya bani damar dunkule hannuna na kirba masa naushi a kahon zuciya naji kamar na naushi dutse hannuna ya sage babu mamaki kirjin karfe ne dashi naushin bazatan danayi masa shi yasa shi yayi taga taga kamar zai fadi sannan fuskarsa ta zama ruwan toka toka wata kumfa tafara fitowa daga bakinsa ya yiyo kaina da gudu kamar mahaukacin kare. Na ture salma gefe guda lokaci guda kuma na tsugunna kasa mahaukaci naushin daya kawo ya wuce ta saman kaina shuuu... Kamar iskar damina sannan yayi tuntube ya wuntsula bayan dakin ya girgiza saboda karfin faduwarsa.. Salma ta nufi kofar dakin dake fuskantar wanda muke ciki da gudu ta bude dakin sannan tayi sauri ta kulle kanta ciki. Naji saukar kulki abayana daya bayan daya kamar zubar ruwan sama na fadi rub da ciki sannan nayi kokarin tashi tuni mai kan shantu ya mike tsaye ya daga kulkinsa sama ya sake tika min shi abaya nakoma na kwanta jagwaff atsakar dakin kamar kayan wanki. Mai dogon gemun yasa kafa ya daki ruwan cikina dukan da yayi min shi ya sani aman ruwan dana sha kafin nafito daga gida MU CI GABA KO MU DAKATA ANAN SAI JANGO ?? [3/16, 4:57 PM] Abubakar Saleh AlQuyraeme: BIRNIN SARAUNIYA-09 Mai kan shantu ya mike tsaye yadaga kulkinsa sama ya sake tika min shi abaya nakoma na kwanta jagwaf tsakar dakin kamar kayan wanki. Mai dogon gemun ya daki ruwan cikina dukan dayayi min shiyasani aman ruwan dana sha kafin nabar gida sannan ya cakumi kwalata ya dagani sama yayi murmushi afuskata sannan yace dani Dan samari taurin kai babu dadi ka hakura ka rabu da yarinyar nan in ba so kake mu kashe ka abanza ba idan mun kashe ka mun kashe banza kamar kisan kurciya ne babu mai ita idan ka kasheta babu mai cewa yaya haka Sannan yayi jifa dani gaban sauran ukun tun kafin na taba kasa yasa kafa yayi Ball dani sannan ya take kirjina da takalminsa naji kamar duniyace aka doramin a tsakiyar kirjina hanjin cikina yafara barazanar fitowa ta bakina. Haryanzu kafarsa na kirjina ya jawo kwalin taba daga aljihunsa ya zari guda daya sannan ya kunna mata wuta ya busa hayakin sama ya sunkuya kasa kansa dab da fuskata kan nasa mai kamar shantu na kyalli kamar mudubi dogon gemunsa na barazanar tsokane min idona. Idan har muna raye toh bazaka taba cimma nasara ba gurin aurenta wannan shine kashedi na karshe idan ka sake muka sake hada hanya dakai to lallai kam badi kamar haka ana sadakar cika shekararka daya a kiyama. Ya tashi tsaye daga durkuson dayayi akaina sannan yace dani kodon gaba in mun hadu dakai ahanya zaka iya kirana da IJAKALA ya kyalkyale da dariya wadda a sanadiyar hakan har saida sauran yaransa sukaja da baya alokacin ne to na lura cewa ashe hakoransa biyu na gaba sun zube hakan shiya kara mai dashi dodo abin tsoratarwa adaidai lokacin ne mukaji takun sawu ga dukkan alamu kuma saman benen aka nufo da gudu mai dogon gemun ya nufi tagar dakin ya leka kamanninsa suka canza cikin zafin nama saiya juyo da gudu yace da sauran yana dariyar yake YANSANDA Yayi sauri yasa sakata ababbar kofar da yake tsammanin ita kadaice hanyar da yansanda zasu shigo cikin dakin sannan ya nufi tagar bangaren arewa yayi kokarin bude tagar amma yakasa saboda kasancewar mabudin kofar na zamani ne ya juyo da gudu zuwa tsakar dakin yana dube dube tuni har an fara kwankwasa kofar sauran kattin na tsaye sololo suna kallonsa kuji wani abin mamaki yace dasu cikin karaji kafin kiftawa da Bisimillah sai daya daga cikinsu ya nufo tagar dakin taki budewa ya kama da karfin tsiya yana jijjigata amma abin yaci tura abin ban haushi kuma kofar ta gilas ce amma duk fadin tsakar dakin babu wani kyakkyawan madoki da zai iya fasa gilashin kartin sukayi ta nauhsin gilashin amma abanza ba irin gilashin da suka saba fasawa bane. Akaci gaba da dukan kofar ayayinda kartin ukun suka cigaba da kokawa da tagar dakin amma ko motsi batayi ba nikuwa numfashina sama sama da kyar nake iya ganin abinda ke faruwa sabodan duk idanuna sun kukkumbure. Ga mamakina sainaga mai dogon gemun wanda ya kira kansa Ijakala ya kyalkyale da dariyar rashin tsoro dakuma ko in kula din da ya nuna yayi matukar sani kaduwa na raa abinda yakeyiwa dariya amma daga baya saina fahimci ashe kartin dake kokawa da tagar dakin yakewa dariya dukan kofar ya kara tsananta ina tsammanin yansandan dake kwankwasa kofar sun gaji sun fara kokarin karya kofar ta hanyar yin amfani da karfin tsiya. Ijakala yayi murmushi sannan ya kunna doguwar tabar dake bakinsa ya kashe ashanar gamida shafar dogon kansa mai kyalli kamar shantu sannan alokaci guda kuma ya shafa dogon gemunsa mai kamar burushi yace ku saurara haka ku sakarkarun banza suka yi tsaye cak kamar ruwa ya cinye su kowannensu ya hada gumi sai haki sukeyi kamar wadanda suka hau bene hawa dari. Ijakala ya busa hayaki sama ya tashi dan karamin gajimaren da bana tsammanin zaiyi ruwa sannan lokaci guda ya nufo tagar dakin da gudu kamar an harbo shi ya sa dogon kansa mai kamar shantu ya daki gilashin tagar atake anan ya tarwatse sannan ya juyo yace dasu maza kuyi ta kanku karku bari wankin hula ya kaiku dare yan samari ya kyalkyale dariya sannan ya juyo gareni tuni sauran kartin uku sun sulale ta cikin tagar dakin nayi mamakin hanyar da sukabi suka sauka kasa Dan karamin sautin motsin reshinan bishiyoyin turaren dake daf da tagar dakin suka bani amsar tambayata Ya shafi dogon gemunsa sannan ya shafi kansa mai kyalli kamar mudubi abinda yayi matukar kara sani tsurewa lokacin dana dubi kan ijakala sainaga ko karcewa baiyi ba lallai to in ba kan karfe ne dashi ba to aljani ne nace cikin zuciyata domin na tabbata in da ni na daki tagar dakin da kaina babu abinda zai hana kaina rabewa gida biyu. Wannan shine kashedin karshe farisu yace dani adaidai lokacin da kofar dakin da yansandan suke kokarin karyawa ta fara motsi alamu ne dake nuni da cewa sun ci karfinta na cigaba da addu'ar Allah yasa su bude cikin gaggawa saboda ko kusa bana son zama tareda wannan naman dajin Ijakala wani mummunan tunani ya ratsa zuciyata yanzu idan mai dogon gemun nan yayi niyyar kasheni zai iya dukan kirjina ko kaina da dogon kansa. Nayi ajiyar zuciya sannan jikina ya dauki rawa lokacin dana tuna da irin dukan da yayiwa gilashin tagar dakin da dogon kansa. KUNA KARANTA WANNAN LITTAFIN NE MAI SUNA BIRNIN SARAUNIYA Wanda Nazir Adam Salih ya rubuta Nikuma Yarima A Gangariya Nake kwafowa daga littafin nake muku posting dinsa YARIMA A GANGARIYA (jikan sidi mai jaka) [3/16, 4:58 PM] Abubakar Saleh AlQuyraeme: BIRNIN SARAUNIYA-10 Nayi ajiyar zuciya sannan jikina ya dauki rawa lokacin dana tuna da irin dukan da yayiwa gilashin tagar dakin da gogon kansa. Ba karamin sakarci bane idan har kaci gaba da kudurar aniyarka ta auran salma kama godewa Allah dayasa ba a bani damar kashe ka ba kai tsaye. Amma ina tabbatar maka da cewa nasan wacce tasamu aikin zatayi farin ciki idan akace baka raye fiyeda ace ka auri salma. Ina fada maka duk wannan ne saboda na lura da irin kamanninka bana mutanen banza bane kuma duk halin daka tsinci kanka yanzu aciki ba laifinka bane jefaka akayi ko kuma nace kayi rashin sa'a da har salma ta zabe ka amatsayin saurayi na hudu da take shirin yin auren kisan wuta dashi. Munga bayan ukun farisu. Yace dani saikayi hankali kada mu ga bayan ka sannan kuma dadin dadawa ina tsammanin wannan karon zamuga bayan ka gaba daya sabanin sauran samarin da muka raunata abaya kai batar dakai zamuyi ma'ana KASHE KA ZATA SA MUYI Ina baka shawarar daka janye ka hakura ko mai zata baka kada ka sake ka nuna alamar aurenta. Kai daga yau ma kada ka sake mu kara ganin ku tare wanda baiji bari ba yaji hoho. Yace dani cikin karaji na gargadeka cikin abota lokaci na gaba bazamu zama abokai ba. Kafin na farga shi ma ya sulale ta cikin tagar dakin yabi duhun dare ya bace kamar aljani Kofar dakin ta karye ta fado gamida karar data girgiza dakin sannan lokaci guda itama salma ta fito daga cikin dakin data kulle kanta sannan tace da yansandan sun gudu ta taga me kukeyi da har kuka bari suka shigo mini gida. Kalli yadda suka lakadawa kanina duka nima dakyar na tsira na kulle kaina cikin dakin. Daya daga cikin yansandan wanda nake tsammanin igiyarsa biyu yace da ita kiyi hakuri hajiya wallahi munga shigowarsu amma damukaga motarsu mai tsada ce kuma tayi daidai da irin ajin motocin da suke shigowa gidan sai muka dauka bakinki ne. Salma ta harare shi sannan tace bakina ne mana tunda sun lakadawa kanina dukan tsiya saiku taimaka mini na kaishi asibiti. Yansandan sukayi mini cali cali ita kuma tana binsu a baya nayi mamakin abinda yasa taki fadawa yansandan gaskiyar al'amarin. ****** ****** ******* ******* ******* ****** ***** Cikin sa'a bayan danayi kwanaki biyu asibiti aka sallameni salma ce ta daukeni a motar ta itace kuma ta dauki nauyin duk dawainiyar jinyata abin mamaki ita kuma ke kwana gurin jinyata hakan kuma shiya bata damar lallabani tun tana bani baki ina kin kulata har ta yaudareni da daddadan kalamanta na soma sauraronta. Farisu ta kira sunana aranar da aka sallameni da safe bayan mun shiga motarta zata kaini gida nasan dai yanzu duk ka san abinda ake ciki don Allah ka taimakni ka aureni koda na kwana uku ne ka sakeni kuma kaga taimakon da zakayi bani kadai zaka taimakawa ba kaima zaka taimaki kanka domin zan biya ka ko naira miliyan biyu ne don ganin ka cika min burina Numfashina ya dauke gamida wani sassanyan gumi dake kwararowa akan fuskata na dubeta adaidai lokacin dana tuno muryar Ijakala yana cewa MUN GA BAYAN WADANCAN UKUN SAURA KAI. Na girgiza kaina sannan nace da ita kin cika son kanki salma na kira sunanta akaro na farko bakya tunanin irin halakar da zan fada idan na aureki ko kuma idan aka cigaba da ganinmu tare? Abinda kawai kika damu dashi shine dukiyar mutumin da zaki aura shin kuwa ko kina sane da cewa auren da zamuyi dake haramun ne? Kuma mutumin da zaki aura amanarsa zakici domin shi azatonsa kina kaunarsa kamar yadda yake kaunar ki kina tsammanin daya san abinda ke cikin zuciyarki yanzu zai yarda yabaki rabin dukiyar tasa kamar yanda yayi alkawari? Kiji tsoron Allah salma abin duniya ba'a bakin komai yake ba Ubangiji fa ba zai barki haka ba........ Nasan da wannan ta katseni abinda kawai nake so naji daga bakinka shine amincewarka Bawani zance ba. Zo nan... Tace dani lokacin data bude kofar motar ta nufi but dinta duba nan tace dani. Na leka abinda na gani aciki yaso yasani hauhawar jini buhuna ne guda biyu kowannensu cike yake da wazobiya sababbi fil. Naira miliyan uku ne idan ka amince zaka aureni KOWANNE KWANA DAYA DAIDAI YAKE DA MILIYAN DAYA. Gumi ya rufeni naji kafata gaba daya tana rawa ga koshi ga kwanan yunwa idan na amince arabani da rayuwata idan kuwa na tsallake to na zama miloniya. Zanyi shawara nace da ita bakina na rawa duk wa'azin danayi mata abaya na manta dashi. BABI NA HUDU Idan ka aureni kowane kwana daya amatsayin naira miliyan guda yake kwana uku naira miliyan uku kenan..... Maganganun da salma tayi min ne suka ci gaba da yawo cikin zuciyata zaman danayi yanzu akofar gidanmu bai hana ni cigaba da tunanin kudin datace zata bani ba idan na aureta nayi sa'a ranar data dawo dani gida gabana na faduwa saboda bansan abinda zance da mahaifina ba idan ya tambaya ina naje kwana biyu nasan zan iya yin karyar da zaata fitar dani amma karyace banason nayiwa mahaifina saboda wancan karon danayi masa karya banji dadi ba musamman dana lura da cewa jina kawai yayi amma bai yarda ba sauda yawa mukanyi tunanin zamuyi wa iyayenmu wayo amma karya ne duk abinda muka fada sun san gaskiyarsa da karyar sa...... (jikan sidi mai jaka) YARIMA A. GANGARIYA [3/16, 4:59 PM] Abubakar Saleh AlQuyraeme: BIRNIN SARAUNIYA-11 Sau dayawa mukanyi tunanin zamuyiwa iyayenmu wayo amma karya ne duk abinda muka fada sunsan gaskiyarsa ko karyarsa saidai kawai su kyale mu kurum tunanin hakan shiyasa ni faduwar gaba cikin sa'a saina tarar ashe tun ranar da mukayi sallama dashi na tafi birnin sarauniya shima sai tafiya ta same shi ta gaggawa zuwa wani garin nan dake kusa damu baifi kilomita talatin ba daga garinmu ayadda naji bazai dawo ba sai yayi kwana biyar yau kwanansa uku kenan acan. Miliyan uku!!! Na muskuta akan kujerar da nake zaune sannan na mike tsaye na fara safa da marwa daga kofar gidanmu zuwa karkashin bishiyar da nake ajiye kujerata hannayena biyu acikin aljihuna. Hakika salma ta shuka wani IRI acikin zuciyata sannan wasu sassa na zuciyata suna cewa dani me zai hana naci gaba da baiwa irin ruwa domin shima yaji dadi yaci gaba da yado? Ba wani IRI nake magana ba daya wuce irin naira miliyan uku don taci gaba da yado cikin zuciyata nasan kam yanzu rayuwata tana tsakanin abu uku ko halaka ko arziki kokuma talauci idan na amince zan auri salma to daya daga cikin abubuwan dana ambata na baya zasu iya kasancewa akaina kodai halaka kokuma mutuwa. Munga bayan samari uku sai kayi hankali kar kaima muga bayanka..... Gargadin Ijakala yaci gaba da kururuwa cikin zuciyata hakika idan naki amincewwa dana aureta to na tserar da kaina daga halaka saidai kuma me?.... Ma'ana zancigaba da zama cikin talauci har sai randa Allah yakawo karshensa. To amma anya kuwa zan iya barin miliyan uku abanza ta wuce ni saboda gargadin wani me dogon gemu....? Na juya maganar cikin zuciyata nakuma yi tunanin wahalar dana sha tun bayan gama karatuna na tuna irin wahalar da iyayena ke ciki na tuna irin wulakancin da mahaifina yace KWARORI nayi a kamfanin dayake aiki. Ba zan taba manta ranar da mahaifina yayi kwana hudu ba akulle a ofishin yansanda mudai bamu san abinda ya faru ba saiji mukayi wai an rufe mahaifina lokacin daya fitone nake tambayarsa dalilin anan ne yake cewa dani cikin sassanyar murya saboda ya manyanta yau shekaruna ashirin da uku ina aiki a kamfanin farisu tun ma ba'a haifeka ba amma saiga shi wai saboda galan din SINADARI daya tak ya bata a sashen mu shine aka rufemu wai mu ake zargi mun sace shi sai daga baya aka ganoshi a ofishin wani babban ofisa dake kamfanin. Kabar aikin to mana baba dole ne saikayi aiki a kamfanin? Idan to nabar aikin a kamfanin ina zasu daukeni. Samari majiya karfi ma suna wahala da neman aiki ballantana ni.. Yayi murmushin karfin hali sannan yace dani Farisu kome na duniya yanada karshe.... Tunanin hakan shiyasani yanke shawarar auren nata kai tsaye cikin zuciyata mai rabon ganin badi sai ya gani koda ana ruwan masu. Barazana da gargadin Ijakala basu isa su karkade mafarkin dake zuciyata ba ahalin yanzu ba kuma wani mafarki ne daya wuce na dora ahannuna akan naira miliyan uku ba Kwana Uku kawai na saketa saki ukiu shikenan miliyan uku ta zama tawa? KWANA UKU SAKI UKU MIILIYAN UKU naci gaba da nanata su cikin zuciyata babu wanda ya isa ya hanani saka hannuna akan kudin koda ijakala ne wannan ai wata dama ce Allah yabani nace cikin zuciyata na tabbata wahalar da zan sha ahannun su Ijakala bazatayi koda daya bisa hudun wacce mahaifina yasha abaya ba rashin kudin ne ya hanani cigaba da karatuna naci gaba da kawo dalilan da zasusa dole na halartawa kaina dora hannuna akan naira miliyan uku. Acan kuma wani bangare na cikin zuciyata nasan ba daidai bane na yanke hukuncin son zuciyata ba kawai nabi amma wanda yayi nisa baya jin kira tuni har nafara tunanin wai ganinan acikin wata dankareriyar mota na kama hanyar zuwa jami'a abokaina na ta dago min hannu suna adawo lafiya. ***** ****** ******* ****** ****** ****** ******** Naci gaba da safa da marwa duk minti biyu saina duba agogo domin munyi da ita zata zo a asirce ta sameni domin jin shawarar dana yanke kodai ban fada maka ba kasan abinda ke zuciyata ka kuma san shawarar dana yanke. Ayadda mukayi da ita in har na amince zan aureta din to gobe ne za'a daura auren tace wai ko iyayena bata son su sani domin abin a asirce za'ayi shi babu wanda ake son ya sani daga ni sai ita saikuma tsohon mijinta. Miliyan uku saki uku kwana uku na dubi tsohon ginin gidanmu wanda a tsammanina ya girmi kakana tuni har nafara kwatanta inda za'a ruguje asake sabon gini gobe warhaka na zama miloniya. Ayadda tace dani ana daura auren zata bani kudin gumi ya lillibeni dana tuna da cewa gobe wai zan zama miloniya alokacin ne wani tunani yafado min wanne irin bayani zanyiwa mutanen unguwa idan sukaga na fara wasa da kudi...? Na tambayi kaina na farko dai kowa a unguwar yasan mu ma su karamin karafine bana jin kuma ko mu aka sayar zamu kai naira miliyan uku yau da'ace inada wani kwakkwaran aiki ne irin aikin da mutane keyiwa kallon kudi to da da sauki ina iya fakewa dashi kowa ya ganni ina facaka da kudi zaiyi tsammanin harkoki ne suka bude wannan itace matsalar data cigaba da addabar zuciyata nayi iya tunanina don gano maganin matsalar amma abin yaci tura. Bari ita matsalar ta magance kanta zuwan......... [3/16, 4:59 PM] Abubakar Saleh AlQuyraeme: BIRNIN SARAUNIYA-12 Bari matsalar ta magance kanta zuwan miliyan uku din yafi wuya idan ina da miliyan uku wa ya isa yayi min tsurku nace da kaina sannan na dada da cewa waya isa yafada kan uwar sarki da kaho? Na sake duban agogona karfe biyar da minti arba'in da biyu adaidai lokacin ne abu biyu suka faru lokaci guda naji tsayawar mota sannan lokacin dana juya na fuskanci motar kamshin turare yayiwa hancina sallama. Assalamu Alaikum wata zazzakar murya tace dani daga cikin tagar motar data tsaya ne muryar take kwararowa sannan lokaci guda kuma naji an sake sallama akaro na biyu saidai wannan karon muryar namiji ce. Abokina sagir ne banji dadin zuwansa awannan lokacin ba saboda atsammanina hajiya salma ce a acikin motar data tsaya gabana. Sannu da zuwa sagir kwana biyu nace dashi bai sami damar bani amsa ba lokacin da duk hankalin mu yatafi kan motar dake gabanmu kofar motar ta bude santala-santalan kafafunta ne suka fara fitowa wadanda ke sanye da bakin takalmi mai dabbare-dabbare kamar fatar kada sannan ta fito gaba dayanta. Tana sanye ne da riga da wando na yadin makaranta ruwan kwai agaban bajon dake gaban rigar an rubuta EL-BASIR GIRLS SENIOR SECONDARY SCHOOL nayi mamakin ganinta da kayan makaranta sannan kuma wacce irin makaranta ce haka har kusan magariba tun safe? Na tambayi kaina. Bari na zana maka hotonta acikin zuciyarka ko ban fada maka ba nasan zaka canki irin haduwar datayi saboda zuwan wannan yarinya adaidai lokacin danake sauraron wacce zata zo min da kamshin naira miliyan uku tuni har ta gundureni. Zakayi mamaki idan nace maka HINDU elbasir kyakkyawa ce ta karshe ajin farko duk fadin unguwar mu babu saurayin da bai san labarin kyawunta ba sannan kuma babu wanda baisan girman kanta ba dakuma rashin mutuncinta ta wulakanta samari da dama takuma sa wasu sun zautu don kawai masifar sonta samari da dama sun kamu da ciwon sonta tun kafin ma su ganta a zahiri daga kawai kallon hotonta atarihi ba'a taba samun saurayin dayaci nasarar tsayawa da ita ba domin ita wai bata dauki bakin mutum da daraja ba kasancewar mahaifiyarta balarabiya ce sannan ubanta baki ne kamar mu. Ganinta agabana yanzu yayi matukar bani mamaki abin kawai daya rage min jin dadin zuwanta shine tunanin naira miliyan uku ba karamin daga aji bane azo wucewa aganni tare da ita nace cikin zuciyata. Doguwa ce ba can ba tana da dan kauri daidai misali idanunta dara dara sannan fari tas kamar takarda cikakkun labban bakinta dakuma jerin fararen hakoranta masu kyalli da walkiya wadanda idan tayi dariya saikaga fuskarka ciki su suka hadu da dan siririn dogon hancinta mai kamar biro suka bata kyawun daya zamanto wani maganadisu azuciyar duk wanda ya hada ido da ita shikuma yasa samari da dama sukance wai fuskarta har kyalli take kamar Diamond hindu kenan Elbasir wannan ma ya isheka hoton kyawunta. Tayi murmushi adaidai lokacin data matso kusa damu sannan tace sannun ku tana murmushi a gabanmu hannunta rike da alkalamin rubutu (Roller Pen) tana wasa dashi sannan ta rike gudunta tace damu. Don Allah Farisu nake tambaya har yanzu murmushin na fuskarta na dubi abokina sagir wanda ke tsaye kerere kamar an dasa shi sannan mukayi murmushi mu duka biyun sannan na juya na sake dubanta akaro na biyu NINE FARISU nace da ita tayi far da fararen idanunta sannan ta lumshe su lokaci guda kuma ta bude su kamar idon yar tsana kallon da takeyimin awannan karon akwai alamar mamaki afuskarta kaine Farisu? Ta sake neman tabbaci abinda nace na gyada kai sannan muka sake duban juna akwai alamar na tsayu a fuskarta don haka sainayi shiru ina sauraronta. Don Allah wani taimako nake son kayi min idan zan samu... Wane irin taimako? Na tambaye ta cikin mamaki nasan zakayi mamaki amma ba abin mamaki bane idan akayi la'akari da irin sakamakon daka samu a jarrabawarka ta karshe a sakandire tayi murmushi duk unguwarmu wane ne baisan da labarin sakamakon ka ba? Farisu da'ace ni Allah ya baiwa basirarka danaji dadi amma yanzu ma Alhamdulillahi tun da gaka na sameka daman roko nake don Allah ko zaka samu damar zuwa gidanmu domin kana koya min wasu abubuwan da suka shige min duhu Wallahi farisu munada malamai masu hazaka saidai ina tsammanin zanfi fahimtar taka laccar domin naji ance lokacin kana makaranta kasha cin gyaran malamanka. Banda dai zuga nace da ita muka kyalkyale da dariya. Dariyarta datafi komai dadin sauraro acan kuma cikin zuciyata ina tunanin lallai na samu maganin matsalar data addabeni yan sa'o'in da suka wuce duk wanda yaji labarin ina koyar da yar gidan elbasir zaiyi tsammanin lallai kam ni kakata ta yanke saka domin an san dolene na sami albashi mai tsoka zan iya fakewa da aikin nacigaba da badda naira miliyan ukuna batareda mutane sun zargeni akan ina nake samun kudi ba atake agurin na amince dana fara koyar da ita. Zanso na taimake ki din saidai kuma banajin zan iya zuwa gidanku batareda sanin mahaifinki ba. Karka damu da wannan tace dani idan kazo gobe saiku tattauna da mahaifin nawa tayi murmushi sannan tace aishi yabani damar daukar duk wanda NAKE SO YA KOYAR DANI AMMA FA........ [3/16, 5:00 PM] Abubakar Saleh AlQuyraeme: BIRNIN SARAUNIYA-13 Karka damu da wannan tace dani idan kazo gobe sai ku tattauna da mahaifin nawa. Tayi murmushi sannan tace ai shi yabani damar daukar duk wanda nake so ya koyar dani. Can cikin zuciyata wani abu na cewa dani duk maganar da take fada karya ce domin akwai kwazazzabai acikinta. karfe nawa zanzo na tambayeta...... Wannan shine kuskuren farko dana aikata Lokacin da ta tafi sai abokina sagir ya dubeni yace dani ban yarda da tatsuniyar datayi maka ba kanajin mahaifinta bazai iya daukar furofesa yazo har gida ya koya mata ba? Zai iya nace dashi amma kasan ra'ayi. Ra'ayi kukan jaki yace dani kai dai kayi ahankali farisu sharrin mata na da yawa musamman ma ita hindu kasan fa rashin mutuncinta ba sai na fada maka ba. Hakane nace dashi tuni na kosa yabar gurin saboda kowane lokaci daga yanzu salma na iya zuwa Ahaka muka rabu da abokina sagir lokacin da zamu rabu dashi saiyace kasan fa tace zubar da ajine ta tsaya da bakin mutum kana tsammani kai don fari ne ta bukaci dakaje har gida ka koya mata karatu? ***** ***** ***** ****** **** *** ***** ***** ***** Da farko bangane ta ba sai bayan data matso kusa dani tayi sallama sannan na shaida muryarta salma ce. Na idar da sallar magariba kenan ina jan tasbaha tazo ga mamakina sai naga tazo kusa dani ta zauna tana fuskantar gabas bayanta a rakabe da jikin bangon gidanmu babu wanda zai iya ganeta ahaka babu wanda kuma zai iya tantancewa shin matar aure ce ko budurwa saboda alokacin datazo sainayi sa'a duk fadin unguwarmu an dauke wuta don haka sai ko'ina ya gauraye da duhu musamman ma kofar gidanmu wacce ke lillibe da katuwar bishiyar darbejiya. Nasan duk mutumin dayazo wucewa zai gane ni amma bana tsammanin akwai mai iya ganeta koda kuwa dan ta'addan nan Ijakala ne. Wacce shawara ka yanke? Tace dani cikin sanyin murya da karayar zuciya tuni gurin ya gauraye da kamshin jikinta. Zan iya aurenki nace da ita kai tsaye banko yarda mun hada ido da ita ba. Haryanzu gabas muke fuskanta ita a tsugunne ajikin bango nikuma azaune akan dardumar danayi sallah. Tayi ajiyar zuciya sannan ta dafa kadafata tace Farisu na....gode kunya da mamaki suka rufeni don jin wai har godiya akeyi min don zanyi auren kwana uku kuma abiyani naira miliyan uku. Bansan daga inda ta zaro salular ba ko daman tana makale ne ahannunta Allah masani ta daddana yan lambobi sannan tace dani yanzu yakamata ka gana dashi tunda ka amince. Na dubeta cikin mamaki sannan nace wanene? Tsohon mijina mana nayi shiru na dan lokaci sannan taci gaba da cewa kudin dana nuna maka rannan ma shi ya bani su domin biyan duk wanda zai iya aurena daga baya ya sakeni akwai maganganun dayake son ya sanar dakaine. Sannan kuma zakuyi yarjejeniya. Akan me na tambayeta. Tayi murmushi sannan tace haryanzu gani yake wai idan ka aureni bazaka sakeni ba. tayi murmushi na fada maka yana masifar sona abinda yasa kenan yarsa ta tsane ni bata kaunar taga na koma gidan. Amma yanzu nafi karfinta tunda ka amince zaka aureni sannan ta turo min salular tace dani yi magana dashi yana jiranka. Na karbi salular hannuna na rawa wannan shine karo na farko da zan fara magana da SALULA FARISU NE? Wata sasasanyar murya tace dani nine nace dashi muryata na rawa toh farisu ina fatan duk tayi maka bayani abinda kawai da nake so dakai atakaice shine bayan kwana uku ka saketa ka kama gabanka ita ma ta kama gabanta daga rannan babu ruwanka da ita ka gane ko eh! Nace dashi muryata na rawa gobe za'a daura auren da yamma misalin karfe biyar amma kafin nan zamu hadu dakai agidanta domin sake tattaunawa. Hudu tayi maka agidanta daga nan ne zaku wuce inda za'a daura auren aboye bayan mun gama tattaunawa. Shirun danaji ita ta tabbatar min daya kashe tasa salular sannan ne nima namika mata tata salular gumi duk ya rufe ni adaidai lokacin ne ta mike tsaye tace dani zo mu je can yanzu zaka dawo. Nabita abaya nayi sa'a bamu hadu da koda mutum daya ba wanda ya sanni har muka tsallaka titi inda ta ajje motarta ta bude bayan motar sannan tace dani dauki naka ne dankakreriyar akwati mai taya ce bansan ko menene aciki ba nidai kawai na dauka ne. Kada ka manta zan jiraka gobe kamar yadda ya sanar dakai karfe hudu Nagode farisu tayi murmushi sannan ta rufe but din motar ta shiga ta tada Ita. me zanyi da akwatin? Na tambayeta. Kabari idan kaje daki ka buda ita zata fadama abinda ke cikinta. Taja motar tayi tafiyarta tabarni nan tsaye da kinkimemiyar akwati. Na sunkuya na kinkimi akwatin na dora akafadata da kyar sannan na tsallaka titi na nufi gida ina numfashi dakyar akan hanyata ta zuwa gida na hadu da mutum biyu dana sani daya abokina ne daya kuma makwabcin mu ne wanda yayi min sannu da zuwa saboda ganina dayayi da akwati amma daya abokin nawa mai suna ALIYU cewa yayi dani Lallai mutumin ka taki sa'a muka kyalkyale da dariya yayi gaba daman akan keke yake don haka bai tsaya tsurku ba saiya wuce Kai tsaye yana zolayata. Lokacin dana shiga cikin gida babu kowa abangaren da dakina yake yan gidanmu suna cikin bangarensu daban hakan shiyabani damar shiga da akwatin batareda kowa ya ganni ba. Saidai kuma Ashe.......... [3/16, 5:01 PM] Abubakar Saleh AlQuyraeme: BIRNIN SARAUNIYA-14 Hakan shi ya bani damar shiga da akwatin batareda kowa ya ganni ba. Na lalubi ashana na kunna fitilar kwai sannan na buda akwatin sannan naga abinda ya sani daukewar numfashi akwatin a dankare yake da wazobiyoyi sababbi fil. Kodai ban fada ma ba kasan na zama miloniya mafarkina ya zama gaskiya hakika salma tabani mamaki bantaba tsammanin zata biyani kudin haka da gaggawa ba azatona sai gobe idan an daura auren. Na fara kasafta yadda zan kashe kudin. Abinda bansani ba shine na aikata kuskure akaro na biyu na manta ban baiwa salma labarin yarinyar data nemi da inje har gida na koya mata karatu ba dana fada mata to da abinda yafaru akaina washegarin ranar bai faru ba. BABI NA BIYAR Aranar banyi cikakken barci ba duk sa'adda na rufe idona saina ci gaba da ganin damin damin wazobiya ajere reras acikin akwatin data bani banyi barci ba har saida na tabbata na samarwa akwatin kyakkyawan maboyi acikin daren na samo wani abin cire kusa da guduma na cire daya daga cikin rubabben silin din dake saman dakina na ciccibi akwatin da karfin tsiya na taka kujera na tura ta cikin silin din sannan na mai da silin din dana barke gurin zamansu na gyara babu wanda zai iya tsammanin akwai naira miliyan uku aboye a saman dakin. Sai bayan dana karbi kudin ne sannan naji matsaloli sun fara damuna na farko bansan yadda zanyi na sanar da mahaifina bayanin kudin ba domin na tabbata inna fadawa mahaifina gaskiyar lamarin bazai goyi bayana ba nasan sai raina yayi matukar baci kuma nasan dole ne saiya sani na maida kudin. Har gari ya waye ban cimma wata kwakkwaran shawarar abinda zanyi da kudin ba. Yau da ace iyayena zasu bani hadin kai to da da sauki to amma nasan wannan wani abune marar yiwuwa na san muddin na nuna musu kudin sai sun bukaci sauran bayani haka nayita saka ina warwarewa awashegarin ranar har kusan karfe dayan rana sannan na tashi na nufi gidan bayan na yi wanka saina sauya tufafin dake jikina da wasu wankakku sannan na dauki yan litattafaina na turanci dana lissafi don daurewa karya gindi har da karan alli guda uku na nufi gidan su Hindu El- bashir ayadda na tsara shine bayan na gama abinda zanyi agidansu Hindu daga nan saina wuce kai tsaye zuwa gidan Salma inda zamu gana da tsohon mijinta to amma abubuwa basu kasance yadda nake tsammani ba. Unguwarsu Hindu el'bashir tana makwabtaka ne da unguwarmu ta bangaren yamma sannan dankakareren gidan el'bashir shiya mamaye kusan rabin unguwar bari na zana maka hoton gidan el'bashir azuciyarka domin ka fahimci irin tsaruwar da kuma makudan kwandalolin daya hadiye. Lokacin daka dubi kofar gidan zakuyi ido hudu da tangamemen lambu wanda ke boye abayan doguwar farar katanga wacce keda katuwar kofa kamar kofar gari. Ga mamakina sainaga asaman katuwar kofar lambun wacce nake tsammanin ita zata kai ka har gidan an rubuta cikin hanyan haruffa launin gwal kamar haka SALMA GARDEN Nayi mamaki saboda ganin sunan salma ajikin kofar gidan amma daga baya saina daina mamaki ai masu suna salma na da yawa agarin nan nace cikin zuciyata. Kamshin furanni da kayan marmari ya bugi hancina lokacin dana jera koda lambun na shiga gabana nata dar dar sassanyat iskar tsabtatacciya ta bugi fuskata gamida kamshin ganyen bishiyar lemon zaki da kashu (yazawa) sannan ne fa na fara hango tangama tangaman gine ginen alfarmar dake boye abayan shuke shuken lambun. Wani dan siririn mai gadi fari sanye da bakaken kaya da farin rawani daya ziraro tun daga kansa har bayansa ya bayyana a gabana kamar an jefo shi. Kai kazami ina zaka ba sallama.. Ya buga min tsawa na dubi bakin zaren ulun dake daure adan siririn wuyansa mai kamar lilo nace. Dankerere shin mamanka hindu tana nan? Fuskarsa ta canza launi sanan idanunsa suka kada sukayi ja kafin ya yanke shawarar abinda zaiyi dani sainayi sauri nace dashi nine sabon malamin da zaike koya mata karatu shin ko kanada labarina? Ya dubeni a yatsine yana hadiyar zuciya nayi zaton zai kawo min duka amma maimakon hakan sainga fuskarsa ta washe kaine Farisu? Ya tambayeni kwarai kwarai nace dashi yayi murmushi kayi sa'a kazami ai bangane ka bane tace idan kazo ka jirata anan zatazo ta sameka.... Kodai kaje kafada mata nazo?... Ya girgiza kai abinda tace dani kenan kazami to dankere nace dashi wannan karon baiyi fushi ba maimakon hakan ma sai ya kyalkyale da dariya sannan yace nayi mamakin ganinka da farko datace min wani sabon malaminta zaizo nayi zaton zanga abu tsaf tsaf amma saina katse. Ya isa haka in ba so kake yanzu na murde maka dankereren wuyanka ba yayi murmushi sannan ya nuna min wata kujerar katako dake karkashin bishiyar yazawa Jeka can kajirata. Na nufi kujerar da nufin na zauna sannan sainaji kamar an sokeni da kibiya su hudune daya da manjagara yana sharar matattun ganyayyakin da suke zubowa na itatuwan kayan marmari ne biyu kuma dauke da fatanya suna saran kasar gindin kananan bishiyoyin da ake reno suna gina ramin da ruwa ke taruwa dayan kuma dauke da abin ban ruwa na hudunsu dauke da katon kwando yana tsintar kayan marmari yana tarawa aciki shine yafi daukar hankalina acan cikin lambun na hango su amma kayan dake jikinsu shi yayi min tarnaki na kasa tsaye na kasa zaune kowannen su sanye yake da yankakkun wando jeans kafi shanu wuya iya gwiwa sannan kuma da bakar suwaita gumi ya lullube ni sunyi kama dasu...... Lokacin daya dago kansa sama saina gane shi lokaci guda tun kafin ma ya gama juyowa mu hada ido dashi dogon kansa mai kamar shantu ma kawai ya isa na gane shi kansa sai kyalli yake acikin hasken ranar kamar madubi dogon gemun sa mai kamar burushi ya hada gumi sharkaf muka hada ido dashi kafata na rawa sannan sainaga ya ajiye kwandon kayan Marmarin akasa ya laluba aljihunsa ya zaro karan taba sannan ya kunna mata wuta ya fesa hayakin sama yayi min murmushi da bai kai har idonsa ba sannan ya juya kan aikin sa na tsintar kayan marmari yana zubawa a kwandon a gaban rigar sa an rubuta IJAKALA ****** ******* ****** ******* ******* ******* **** NA SHARE GUMIN DAKE KWARAROWA KAN GOSHINA... [3/16, 5:02 PM] Abubakar Saleh AlQuyraeme: BININ SARAUNIYA-15 Sannan ya juya kan aikinsa na tsintar kayan marmari yana zubawa a kwando agaban rigarsa an rubuta IJAKALA ***** ****** ****** ***** ******** ******* ******* Na share gumin dake kwararowa kan goshina sannan jikina na rawa na juya na yafuto dan siririn maigadin nan. Yau kam sai abinda hali yayi nace cikin zuciyata nasan na kawo kaina ga halaka. Menene kuma nace kayi jiranta yanzu zatazo yaushe wadancan suka fara aiki agidan nan? Na katse shi maigadin yayi shiru sannan bayan ya danyi yan waige waige ya tabbata aikinsu suke ba kallonmu suke ba saiya matso kusa dani yace cikin rada jiya suka fara aiki agidan nan ita ta kori wadancan masu gadin na shekaran jiya. Wallahi nima bana farin ciki da zuwansu ni tsoro suke bani kaganta dai kyakkyawar yarinya amma halinta mummuna ne kullum saita zageni gata da shegiyar rowa bata tabayi min kyauta ba kaima ina mamakin........ Yayi shiru lokacin daya lura cewa bashi nake kallo ba daga can cikin gidan hindu ce ita da wani mutum wanda nake tunanin shine mahaifin nata suka nufo inda nake. Koda maigadin ya fahimci abinda nake kallo sai yayi sauri ya sulale yabarni nan tsaye kamar nayi fitsari awandon don tsoro yanzu na fara gane abinda ke shirin faruwa abinda yafi sani kaduwar fiyeda komai shine lokacin danaga fuskar wanda nake tsammanin mahaifinta ne ko shakka babu shine mutumin danaga hotonsa shi da salma amakale ajikin bangon dakinta yanzu na tabbata yarinyar data nemi na koyar da ita karatu ba wata bace data wuce yarinyar datake son a hallakani don ganin ban auri matar ubanta ba wato salma. Tun daga nesa ta nuna ni da dan yatsa tace Baba gashi can sune irin barayin nan masu mana sata. Tace cikin karaji kamar da gaske. Inajin ma sune suka sace maka na'u'rorinka masu kwakwalwa na kwanakin nan sannan ta kwalla ihu kai masu gadi ku tare barawo. Yanzu ne na fahimci abinda take nufi so take tayimin kamun barawo idan yan ta'addar da ta dauko amatsayin masu aiki sun kasheni to sun kashe barawo kenan. Na zubar da litattafaina da karan allina guda biyu na zura aguje domin tserar da kaina na tabbata babu abinda zai fitar dani daga sharrin datayi min idan na tsaya kuma nasan sakamakon abinda zai faru. Ijakala ne yafara fitowa ya biyo ni da adda tsirara ahannunsa sannan sauran suka rufo masa baya da gudu yakawo min sara da adda amma bai sameni ba sannan muka cigaba da gudu duk kokarin da nake shine nakarasa kofa nasan indai na fita daga gidan shikenan banajin zasu iya biyoni waje. Ku tare barawo hindu ta sake kwalla ihu adaidai lokacin dana kusan karasa kofar gidan ba zato ba tsammani sai ga dan kereren mai gadin nan yashiga gabana alokacin ina kokarin kaiwa ga kofar nayi kan maigadin da gudu ashirye nake na banke shi domin tserar da rayuwata. Na runtse idanuna na banke maigadin adaidai lokacin da Ijakala ya kawo min sara da addarsa. Banke maigadin danayi shiyasa ni tuntube dashi na fadi fuskata ta daki kofar gidan ji kake gau gau naji wani radadadi ya soki kaina har wani kara nakeji a kunnena wur wur wur abin tsautsayi faduwar danayi ita ta cece ni cikin nufin Allah sai addar ijakala ta sauka awuyan maigadin nan take anan maigadin yafadi kasa yana shure shure tuni jini yayiwa rigarsa wanka. Ganin abinda yafaru shiyasani mantawa da nawa ciwon nayi zumbur na tashi sannan Ijakala yakawo min sara da addar na sunkuya ya sari kofar gidan sannan yayi sauri ya tsare kofar da adda a hannunsa tsirara tana walkiya ku gama dashi mana ya bugawa yaran tsawa daya daga cikinsu ya daga manjagaran dake hannunsa sama da niyyar ya sauke min shi a tsakiyar kai ganin cewa sauran basu karaso ba sai nayi amfani da damar na shige shi kafin ya sauke min manjagaran na daki ruwan cikinsa abinka da wanda yake gudun ceton rai dukan danayi masa shiyasa ya jefar da manjagaran gefe guda shi kuma ya durkusa nan rike da cikinsa nayi sauri na rarumi manjagaran daya yar. Ijakala ya sake kawo min sara nasa manjagaran na kare ji kake kal! Hakora uku na manjagaran suka balle adaidai lokacin dayake shirin sare min kafata ne naji an tika min wani abu abaya dam nafadi agurin ina murkususu azatona kashin bayana ne ya karye daya daga cikin yaron Ijakala na tsaye akaina hannunsa rike da dankareren icen bishiya yayi yani atsaye azatona irin icen da ake tashen zan buge dashi ne. Mai dogon gemun ya sake kawo min sara wannan karon kuwa saina sa hannu na kare saboda radadin dukan da akayi min bazaisa na kauce ba. Addar tasa ta tsarga min hannu jini yayi tsartuwa sannan ya sake daga addar nayi zumbur na mike adaidai lokacin daya sake sauke min ita agadon baya nayi sa'a bata sameni ba adaidai amma ta tsarga min riga nayi taga taga kamar zan fadi amma na cije domin nasan idan na sake na sake kaiwa ga faduwa kasa to ni shikenan tawa ta kare. Suka rufa min baya don tsabar sharri irin na mace su suna kokarin halakani ita kuma tana faman kururuwa wai barawo barawo nasan nufinta so take ta janyo hankalin sauran mutanen unguwa suzo su karasa ni. Nayi cikin shuke shuken gidan da gudu ina cikin gudu sai kayar bishiyar lemon tsami ta rike min riga nayi nayi na kwace amma...... [3/16, 5:02 PM] Abubakar Saleh AlQuyraeme: BIRNIN SARAUNIYA-16 Nayi cikin shuke shuken da gudu ina cikin gudu sai kayar bishiyar lemon tsami ta rike min riga nayi-nayi na kwace amma abin yaci tura gashi kuma Ijakala na biye dani ko wannen su dauke da makami. Shi da adda wani da manjagara dayan kuma da katon itace shikuma na cikon hudun dauke yake da dagi na hakar kasa. Ku rike shi na soke shi!! Yace dasu ijakala cikin karaji. BABI NA SHIDA Na fizge rigata da karfi daga jikin kayar anan nabar rabin rigar ajikin kayar nayi gaba da gudu duk kokarina bai wuce na kai wa ga katangar gidan ba gashi kuma lambun yanada fadin gaske abinda yafi damuna kuma shine kayoyin bishiyar lemon tsami da suke yayyagata duk sun kekketa min riga. Ga saran da sukayi min da adda yana zubar da jini duk kaina ya daure yayi wani dum.. Idona yakai ga wani katon sungumi dake jingine ajikin itaciyar goba nan da nan na dauke shi na rike ahannuna su kuma suna biye dani. Nafisu gudu nesa ba kusa ba don haka sainaga abinda yadace nayi shine na tsere musu na buya saboda na fuskanci sun fara gajiya. Nasha wata kwana sannan na zagaya bayan wata katuwar bishiyar mangwaro wacce keda yawan ganye lif lif har kasa na shige cikin ganyen namakale ina sauraron sautin takun kafafunsu suna ta gudu adaidai lokacin ne kuma naji shiru kamar an dauke ruwa nayi mamakin abinda ya tsaida su nasan kodai rashin ganina ne ya tsaida su kokuma wani abu yafaru.... Kuzo nan shashashan banza gabana yafadi danaji muryar Hindu ce. Ki bari mu karasa shi mana.... Ijakala yace da ita yana haki. Yadda addar dake hannunka shashashan banza tace dashi to hajiya ya jefar da addar. Babane yakirawo yan sanda tace dasu abinda nake so daku shine kowa ya koma kan aikinsa ku manta dashi babu ta inda zaifita domin yansanda na nan ako ina abayan gidan abinda nake so daku shine idan yansanda sun tambaye ku inason ku bada shaidar cewa kunga lokacin da barawon ya sari maigadi da adda wannan ma kawai ya isa kuma barshi da yansanda tunda dai Allah yasa maigadin ya mutu sai mubar laifin kisan akansa wannan ya ishe shi.... Ya mutu? Naji muryar ijakala na rawa lokacin daya tambayeta ko bai mutu ba nasan asibiti zai karasa sannan taci gaba da cewa idan kuwa yansanda basuci nasarar kama shi ba kodayake da wahala ma amma dai in hakan ta faru to kuna iya nemansa da kanku duk inda yake ku karasa shi yan sanda na iya tsammanin dukan da akayi masa ne ya kashe shi amma wannan babu wani abu nasan baba na iya kwantar da maganar musamman idan muka tsaya masa laifin kisan mai gadin....... **** ***** ***** ****** ******* ***** ****** ****** Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'una abinda naci gaba da cewa kenan lokacin danaji sun bar gurin yanzu kam nasan banida mafita nasan mabiyota a yanzu bazata hana yansanda ganina ba. Nayi karfin hali nafito daga karkashin ganyayyakin bishiyar mangwaron adaidai lokacin ne fa na hango ginin daya zagaye katon injin dake baiwa gidan wuta acan kuryar gidan yake aboye abayan shuke shuken itacen ayaba. Nan da nan nufo gurin dakyar nake tafiya juwa na daukata saboda karancin jinin daya zuba ajikina. Ajere abayan ginin wasu manya manyan durarruka ne na mai guda hudu biyu afafe suke amma sauran ba'a fafe su ba wata dabara ta fado min amma ni kaina nasan caca zanyi domin banida wata hanyar tsira data wuce wannan. Na daga daya daga cikin faffun durarrukan na rude kaina ciki idan baka sani ba saikayi zaton kawai kife duron din akayi. Banfi minti biyar da shiga ba naji takun sawun yansanda suna zazzagaya lambun suna nemana. Ba'a dade ba naji sunzo inda nake boye zamu duba nan naji daya daga cikinsu yace. Kana tsammanin zai buya anan ne kaima dai da wasa kake shima yasan ai dole ne mu duba nan na fada muku wahala kawai zamuyi domin ina tsammanin ya sulala tun kafin muzo. Abin kawai dayafi shine muyi sauri mu fita farautarsa tun kafin yayi nisa kamata yayi dai mu duba mu tabbatar baka sani ba kome na iya faruwa. Idan baku gaji da batawa kanku lokaci ba ni kunga tafiyata naji takun samunsa yabar gurin ba'a dade ba naji daya dansandan daya nace sai an duba ko ina cikin harabar mashin din shima ya hakura yabar gurin. Bansan iya tsawon lokacin danayi acikin duron a takura ba nidai azatona rashin isashshen jinine ya sumar dani na yunkura da duron na turar dashi gefe guda sannan nima na fadi gefe guda duhun dare yafara shigowa kaina yace me zaiyi ba ciwo ba na jingina ajikin ginin daya zagaye injin bada wutar na lumshe idona iskar hadarin daya fara hadowa ta fara kadawa sauran tsummar rigar dake jikina fal fal. Na bude idona na dubi farin gajimaren daya mamaye sararin samaniya adaidai lokacin ne na hango wata tsuntsuwa dauke da wani kyalle wanda nake tsammanin launin ja da shudi ne tsuntsuwar nata kokawa da dan karamin kyallen dake bakinta taki saki ita kuma karfin iskar ya hanata tafiya yarda take so iskar sai maida ita baya takeyi. Nayi mamakin abinda ya hana tsuntsuwar sakin tsumman kyallen wai shin ina amfani badi ba rai na tambayi kaina. Yanzu kam mafarkina na zama miloniya yabi iska ga kudin can na boye adaki nikuma gani nan ina shirin halaka shin dana hakura da yadda da Allah ya ajiyeni amatsayina na talaka da wannan zata faru akaina? Na tambayi kaina dana rabu da salma tun farko da yanzu ina gida zaune lafiya amma yanzu fa na sami kudin saidai kuma kudin bazasuyi mini amfani ba. Haryanzu tsuntsuwar na kokowa da tsumman dake bakinta me zai hana ta saki tsumman da kanta ta tserewa halaka? Na tambayi kaina saidai kuma can cikin zuciyata wani bangare na cewa abinda ya hanaka rabuwa da salma harka samu kanka ahalaka shine ya hana tsuntsuwar sakin tsumman. Hadama da rashin godiya ga Ubangiji..... Naji kaina yayi dum idanunwa sun fara rufewa ina shirin suma. Adaidai lokacin ne naji an take kafata da wani katon takalmi aka fara ci gaba da rugugi na bude idona don ganin wanda ya take kafar tawa gabana ya yafadi tsigar jikina tayi yar!!! Yanzu kam nasan ni rashin godiya ga ubangiji yakaini ga halaka yana tsaye akaina da kafceciyar adda ahannunsa dogon gemunsa kamar burushi dogon kansa mai kamar shantu na sheki kamar madubi IJAKALA NE. Ya daga addar sama sannan yace WANNAN SHINE KARSHEN MAI TAURIN KAI NAYI KALMAR SHAHADA NA RUFE IDONA INA JIRAN JIN SAUKAR ADDA. KADA KA RABA SHI GIDA BIYU WATA SASSANYAR MURYA TACE DAGA BAYA... ZAN CIGABA A LITTAFI NA BIYU Nazir Adam Salih. Saiku biyo ni a littafi na biyu don jin yanda zata kasance YARIMA A GANGARIYA (jikan sidi mai jaka) VISIT www.aihausanovels.com.ng For More Novel. AIHAUSANOVELS is website consists of hausa novels note, the reason of launching this site is to Entetaint, Motivate and Educate our readers. We provided hausa novels of many type, Such Adventure, love, romance, fiction, non-fiction, mystry, fantasy, action e.t.c from hausa Authors We provided a new and old novels both softcopy and hardcopy from our Author with thier permission. AIHAUSANOVELS shafin yanar gizo ne wanda yake ɗauke da littattafan hausa, dalilin bude wannan shafin shine domin Kayatar masu karatu da kuma ilimantar da su. Mun samar da littattafan hausa na nau'uka daban-daban, kama daga littafin, soyayya, tatsuniya, almara, Hikayoyi, gyara kayanki (yadda mata zasu kula da kansu a gidan mijinsu) da dai sauransu, daga Marubutan hausa. DANDANO DAGA LITTAFIN VISIT www.aihausanovels.com.ng For More Novel. AIHAUSANOVELS is website consists of hausa novels note, the reason of launching this site is to Entetaint, Motivate and Educate our readers. We provided hausa novels of many type, Such Adventure, love, romance, fiction, non-fiction, mystry, fantasy, action e.t.c from hausa Authors We provided a new and old novels both softcopy and hardcopy from our Author with thier permission. AIHAUSANOVELS shafin yanar gizo ne wanda yake ɗauke da littattafan hausa, dalilin bude wannan shafin shine domin Kayatar masu karatu da kuma ilimantar da su. Mun samar da littattafan hausa na nau'uka daban-daban, kama daga littafin, soyayya, tatsuniya, almara, Hikayoyi, gyara kayanki (yadda mata zasu kula da kansu a gidan mijinsu) da dai sauransu, daga Marubutan hausa. BIRNIN SARAUNIYA ( NA BIYU 2 ) Na Dallara hasken cocilar acikin dakin ga mamakina sai naga haryanzu dakin yana nan kamar yadda yake tun shekaru uku da suka wuce. Na bude akwatin ahankali sannan na haska cikinta kudin na nan kamar yadda na barsu, na dauki damin wazobiyoyi daya ina jujjuyawa ahannuna asannan ne naji gabana yafadi rassss Domin kudin dake kasan wanda na dauka duk ba kudi bane Damin yankakkun takardu ne farare sol ba kudi bane........ [3/16, 5:04 PM] Abubakar Saleh AlQuyraeme: BIRNIN SARAUNIYA 17 BOOK 2 LITTATTAFAN NAZIR ADAM SALIH *KIBIYAR AJALI *ME YAFI KUDI *TALEKO TA KOMA *BIRNIN SARAUNIYA *NAIRA DA KWABO *ALJANI YA TAKA WUTA *MUTUWAR KASKO SADAUKARWA NE GA. Kannena Mustapha Adam Salih Harisu Adam Salih. Mas'ud Adam Salih Shafa'atu Adam Salih Binta Adam Salih Dakuma Lamira Adam Salih Tukwuici ne ga Abokaina kamar su Bala Magnet(Hamilton) Nasir Asir Guy(warrios) Aminu Siba (Warrios) Abba United (Boys) Audu Madda (Strangers) Hamisu Manya. TUKWUICI NE GA Ma'awuya Yusuf Adam Sagir Fancy (Strangers) Musbahu (Abey) Barrister Mijin Hajiya (France) KYAUTATAWA NE GA MALAMAINA KAMAR. Malam Mustapha Abubakar Sadiq Islamiyya Malam Ussaini Malam Danladi Malam Danbaba Malam Musa BIRNIN SARAUNIYA (2) Copy Right (c) Nazir Adam Salih 'nas' 1998 Hakkin Mallaka (c) Nazir Adam Salih 'nas' 1998 Tarihin Bugawa 1998 AKULA Wannan Littafin Kagagge ne ba'ayi shi ba dan cin zarafain wani ko kuma bata masa suna ba sai dan gargadi dakuma nishadi ga al'umma Allah yasa mu amfana daga darasin da Littafin ke koyarwa kuskuren dake ciki kuma Jama'a a Gafarceni Allah yayi mana jagora Ameen. NINE NAKU Nazir Adam Salih(Nas) P.O Box 4792 Abubakar Saddiq Islamiyya Dakata. BIRNIN SARAUNIYA (2) Na Nazir Adam Salihu (NAS) Kada ka raba shi biyu wata sassanyar murya tace daga baya... Tuni na yanke kauna da rayuwa amma jin sassanyar muryar ta daki dodon kunnena sai naji farin ciki ya dan lillibeni. Idanuwana sunyi nauyi basa buduwa saboda jinin daya zuba daga jikina. Amma jin sassanyar muryar shi ya sani kunan bakin wake na dan bude idona kadan tuni daman sassanyar muryar ta bani hasken wanda ke maganar. Tana tsaye abayan Ijakala kanta lullube da farin gyale sanye take da doguwar riga shudiya babu alamar jin tausayi ko kuma razana afuskarta. Hannun ijakala wanda ke rike da addar yayi sororo sannan addar ta kwace ta fado daga hannunsa ya juya a sanyaye ya kalleta itama ta kalle shi sannan ya shafi dogon gemunsa sukayiwa juna kuruu na dan lokaci shine yafara kawar da idonsa. Wa yasa ka raba shi biyu? Yayi kimanin dakiku takwas baiko daga kai ya dubeta ba. Sannan ahankali saiya dago idonsa suka sake kallon juna akaro na biyu awannan karon ma shine yafara kawar da idonsa sannan ya shafi dogon gemunsa yace KI TAMBAYI HINDU Idan kina son sanin wanda ya sani na raba shi biyu bai ko sake dubanta ba saiya juya ahankali yakoma ta inda yafito yar sassanyar iskar dake kadawa ko ina cikin lambun taci gaba da karkada rigata. SALMA na tsaye tana kallonsa har ya kule acikin korayen bishiyoyin lambun sannu farisu tace dani adaidai lokacin data durkusa da gwiwowinta akasa sannan ta dafa hannun da aka sareni ahankali kamar wacce ke dafa maciji dafa hannun nawa datayi shiya sani cije baki tayi sauri ta dauke hannunta sannu Farisu kaji ta sake cewa dani akaro na biyu muryarta na rawa kamar zatayi kuka. Kaina yayi nauyi jikina yayi zafi sannan naji radadi marar misaltuwa ya soki jikina salma tayi sauri ta matso kusa dani ta dafa goshina sannan ne to naji tafara sheshshekar kuka hawaye suka fara kwararowa daga kumatunta. Farisu.... Farisu shi.... Shi... Yayi ma haka? Sautin kukanta yafara fitowa fili cikin murya mai ban tausayi ta sunkuyar da kanta kasa kamar zata dorashi akan ruwan cikina amma batayi hakan ba sai kawai ta tsaya ahaka taci gaba da kuka cikin yar siririyar murya. Ta dau kimanin mintuna uku tana kuka hawayen dake zuba daga idanunta yafara jika gaban rigata adaidai lokacin ne to wani dan kwakkwaran motsi abayanta yasa ta juya ahankali ta dubi bayanta. Atsaye abayanta sanye da doguwar riga sankon sa na kyalli kamar mudubi arana EL-MAHDI ne yansandan hudu ne abayansa kowannensu rike da bindiga harbi ka ruga suna zazzare idanu kamar saci babu El-mahdi ya daga kakkauran dan yatsansa ya nuna ni yace shine wannan kafin kiftawa da Bismillah sun cakume ni kamar buhu sukayi sama dani sakayau kamar gadon kara sannan suka sakeni na fadi tim akasa wani haske ya gifta ta kwayar idanuna sannan wani duhu ya maye hasken abu na karshe danaji shine kukan salma kada kabari su kashe shi Alhaji shine Farisun da nake Fadama......... Iska ta dauke maganar adaidai lokacin dana daina jin komai da komai wani duhu mai tsanani ya rufe zuciyata. **** **** ***** **** **** ****** **** **** ******* Abu na farko daya fara zuwa zuciyata yakuma sa kwakwalwata juyawa shine maganganun mutane dana keji sama sama sannan daga can wani bangaren danake nakanji sautin dakikar agogo tik tik kamar ana dukan kwarya da sillen kara. Da farko na dauka mafarki nakeyi ne nayi mamaki cikin zuciyata kai Amma fa wannan mafarki daban mamaki yake domin idan har ba kwakwalwata ce ke fada min karya ba naso naji muryar salma na kiran sunana. Farisu naji wata sanyayyar murya ta doki dodon kunnena Farisu kana jina? Haba hajiya dakin dan kyale shi ya huta kinsan da wahala ya tashi yanzu tunda allurar baccin da akayi masa tanada karfi dayawa. Wannan muryar dake magana bakuwace akunnuwana irin yadda sautin muryar ke fita da shashshake shiya sani nafara tsammanin kowanene mai muryar dole ne ya kasance....... (jikan sidi mai jaka) [3/16, 5:05 PM] Abubakar Saleh AlQuyraeme: BIRNIN SARAUNIYA 18 BOOK 2 Wannan muryar dake magana bakuwace a kunnuwana. Irin yadda sautin muryar ke fita shakakke shi ya sani nafara tsammanin kowanene mai muryar dole ya kasance babban mutum a tunina lukuti sannan alokaci guda nafara kokonto anya kuwa mafarki nake. Sannan kamar amsar tambayata sainaji wani lallausan hannu ya dafa fuskata kamshin turaren dake hannun ya doki hancina. Duk da yake ina tsammanin mafarki nake hakan bai hanani bude ido don ganin wanda ke dafa min fuskar ba. Banyi mamakin ganinta ba tana tsaye akaina sanye da doguwar riga shudiya wacce akayiwa ado da maballai tun daga samanta har kasanta kanta lullube yake da farin gyale sannan iskar fankar dake kadawa asaman dakin ita ta dan turar da lillibin dake kanta hakan kuma shiya haifar da sanadiyyar da siraran gashin kanta masu sheki da walkiya suka sami yancin fitowa suna kadawa gwanin sha'awa kamar gemun masara yayin iskar damina. Hajiya kiyi hakuri har zuwa lokacin da zai farka da zarar yatashi zanzo na sanar dake da kaina. Ai ya farka Salma tace da mai maganar a sanyaye. Na dan kara bude idona don ganin wacce ke maganar ga mamakina sainaga bakamar yadda nake tsammanin ganinta ba sabanin yadda zuciyata ta fasaltamin ita yar siririya ce doguwa ta dan tankwara kadan daga sama baza kuma ka iya sanyata acikin ajujuwan launin fatar jiki da muka sani yau da kullum ba domin kuwa baza ka iya kiranta fara bako ko kuma wankan tarwada ba kasancewarta zabiya kwayar idanunta launin ruwan kasane. Sannan gashin kanta launin ruwan kasane wanda suka so suyi kama da gashin masara tana sanye da doguwar riga fara iya kwauri irin kayan dai daka saba gani yau da kullum ajikin malaman asibiti sannan amanne asaman aljihun rigarta daga bangaren hagu wata yar roba ce shudiya dauke da sunanta TURAI SARAKI duk wannan abun na lakancesu ne akallo daya. Salma ta buda baki zatayi magana kenan sai kofar dakin ta bude ahankali atsammanina dan karamin yaro ne ke turota gabana yafadi alokacin dana ga sun shigo dakin ahankali kamar wadanda ke tafiya akan bawon kwai dayan saurayi ne kamar ni dan kyakkyawan wanda fatar bakinsa ta sama ke dauke da gashin bakin dake nuni da cewa dan sanda ne. Mutumin dan gajere ne fari kakkaura rigarsa hularsa da kuma komai dake jikinsa yadace dashi inka dauke wandonsa wanda ya dan dage kadan daga kasa kamar wanda ke shirin shiga ruwa. Dansandan na biyu magidanci ne shekarunsa zasu iya zama talatin ko arba'in kokuma hamsin Allah dai masani bakine dogo bakinsa dauke da tarin gashin baki kamar ciyawar bakin ruwa fatar bakinsa da hannayensa sun dafe baki-kirin da hayakin taba saman robar dake makale ajihun rigarsa an rubuta ABDUL S. Salamun Alaikum . Abdul din yace damu lokacin da suka shigo dakin yana murmushi hakoransa sun dafe sun koma launin zuma jajayen idanunsa akan fuskata tuni zuciyata tafara yi min gargadin cewa kada ka yarda dashi mayaudarine. Hajiya mu yakamata mu fara ganawa dashi kafin kowa ina fatan zaki gafarceni ranki ya dade. Yana yin aiki ne yazo da haka ga mamakina sai naga salma ta nufi kofar dakin tana kuka zazzafan hawaye na zuba akan kyawawan kumatunta. Tafice daga dakin lokacin data fice sainaji kamar wanda aka yiwa tsirara hankalina yatashi sannan jikina ya dauki rawa naji wani kadaici ya lullubeni kamar jaririn da aka dauke daga kirjin mahaifiyarsa ni kaina nayi mamaki ban kuma san menene dalilin hakan ba. Kada ku wuce minti biyar yar siririyar malamar asibirin tace dasu sannan ta dada dacewa kada ku takura masa da yawan tambayoyi domin yana bukatar hutu. Kada ki damu dansandan yace da ita sannan itama ahankali saita nufi kofar dakin dingyal-dingyal kamar mai tafiya akan tako tako lokacin data fice daga dakin sai naga kamar sun tsere sun barni ne acikin garken zakuna. Abdul ya kyasta ashana sannan ya kunnawa tabar dake bakinsa wuta ya zuki tabar sannan ya fesa hayakin afuskata. Menene sunanka dan samari yace dani yana zazzaee idanu sannan ya dada da cewa in zaka fadi fadi gaskiya yaro! Komai taja maka ka biya. Sannan ya kyalkyale da dariya gashin bakinsa ya baje akan fatar bakinsa muzu muzu kamar ciyawar bakin kogi. ***** ****** ***** ***** ***** **** **** ***** **** Saurayin dan sandan ya matso daf dani ya zauna abakin gadon. Alokacin ne na lakanci ashe sunansa IBRAHIM. Yansandan biyu suka dubeni ido da ido na dan tsawon lokaci sannan abdul ya sake maimaita tambayar sunana. Na motsa lebban bakina dakyar sannan nace dashi cikin rada Aikafini sani. Dansandan ya dubeni a yatsine sannan ya dauke idanunsa daga kan fuskata ya maida su kan bangon dakin kamar mai tunanin wani abu. Kusan tsawon dakiku talatin cif sai yajuyo ya dubeni sannan yayi murmushi. Farisu ko? Ya tambayeni kaji shi yana magana alokacin saika rantse da Allah da gaske ne bai san sunan nawa ba. Ya muskuta ahankali sannan ya zaro wata farar ambulan daga aljihunsa anutse saiya zaro wani abu daga cikin ambulan din mai kamar hoto ya dan daga abin sama yana dubansa kamar wanda ke kokarin gane komenene sannan saiya miko abin gaban fuskata daidai yadda zan iya gani yace KO KASAN WANNAN ?? [3/16, 5:06 PM] Abubakar Saleh AlQuyraeme: BIRNIN SARAUNIYA 19 BOOK 2 Ko kasan wannan? Nayi shiru na dan lokaci ina nazarin hoton sannan ne to naji wani abu ya soki hantar cikina bana ko shakka shine abinda kuma yasani kaduwa sannan yasa kwakwalwata tafarfasa shine abin dake hoton an dauke shine a irin wanda nake kwance idonsa ajujjuye bakinsa abude hangam-gam kamar wanda ke kokarin zuke iskar duniya gaba dayanta. Idan badon dan siririn wuyansa mai kamar lilo ba to da bazan taba gane shi ba dan siririn mai gadin nan ne wanda Ijakala ya sara awuya wajen kokarin sarana. Yanzu ne na fahimci abinda dansandan yake nufi yana nufin yace nine na kashe shi? Sannan dansanda ya dubeni sannan yayi murmushi sannan ya dada dacewa. Nasan daman zaka gane shi Farisu duk da yake dai nasan me yiwuwa baka yiwa fuskarsa kyakkyawan kallo ba lokacin da kake kokarin sararsa amma nasan hakan bazata hanaka gane shi ba. Me kake nufi na tambaya cikin kaduwa na dan dago daga kan gadon danake kwance jikina na rawa. Abinda nake nufi shne ana tuhumarka da laifin kisan maigadin gidan El-Mahdi wanda Allah yayiwa rasuwa jiya da daddare. Abdul ya zuki sigarinsa sannan ya karawa sama hazo ina fatan yanzu ka gane hausata ko haryanzu turanci nakeyi? Ya tambayeni yana zazzare idanu. Fitarsu keda wuya sai kofar dakin ta sake budewa ahankali yar siririyar malamar asibitin nan zabiya ta shigo wata yar gajeriyar malamar asibitin baka na biye da ita dauke da dan karamin faranti launin azurfa wanda ke dauke da sirinji da kuma ruwan Allura. Malamar asibitin ta dubeni sannan tayi murmushi tace. Ina fatan dai basu dameka sosai ba? Saidai kar akara nace cikin zuciyata na girgiza mata kai ahankali zuciyata cike da zulumin halin dana tsinci kaina. Malamar asibitin ta dafa kafakata ahankali sannan tayimin allura ahannu ba'a dade ba sai wani duhu mai tsanani ya rufe idanuna dakuma dukkan tunanin dake zuciyata na tsunduma barci kafin na farka nayi mafarkin dan siririn maigadin nan zaune gabana yana yi min dariya. Lokacin dana farka babu kowa adakin dagani sai gadon danake kwance akai gamida fankar dake juyawa asaman kaina wacce duk lokacin dana dubeta sainaji kaina yana juyawa nakanyi kuma addu'ar Allah yasa karta kwace ta fadomin akai. Agogon dake jikin bangon dakin yayi nuni da karfe goma sha dbiyu na rana saura kwata adaidai lokacin ne kofar dakin ta bude sannan ta shigo SALMA CE. Haryanzu sanye take da rigar da tazo da ita awancan lokaci saidai wani abin mamaki kuma daban idanuwanta duk a kukkumbure suke sun kada sunyi ja ko shakka banayi yawan kukan da tayine ya haifar mata da hakan ta matso kusa dani ahankali sannan ta zauna abakin gadon idanuwanta akan fuskata bata ko kiftawa alamun tausayi da kuma nadamar halin data jefani karara suke a fuskarta. Sannu farisu tace a sanyaye muryarta na rawa. Kofar dakin ta sake budewa akaro na biyu atsammanina zan sake ido hudu da yansanda amma sabanin hakan sai wata yar siririyar yarinya ta shgio ciki dauke da kurtun zuba abinci fara ce sanye da doguwar riga baka mai farin aiki agaba bugu da kari ta lillibe kanta da dan siririn gyale fari mai digo digon baki shekarun yarinyar zasu iya zama komai tsakanin goma zuwa sha biyar. Ta ajje abincin agaban salma sannan ta juyo fararen idanunta kan fuskata tace Sannu yaya jiki? Da sauki nace da ita sannan ta juya ahankali ta fice daga dakin simi simi kamar yadda ta shigo nayi mamakin cewa basu ko damu da suyi musayen kalma ba tsakaninta da salma. Na dubi salma itama ta dubeni mukayiwa juna kuri da ido na dan lokaci munyi kimanin tsawon dakiku talatin da wani abu batareda muncewa juna uffan ba. Salma ce tafara yiwa shirun karantsaye da cewa. Farisu.... tace bakinta na rawa don Allah kayi hakuri ka yafeni duk ni na jawo maka kana zaman zamanka ni kaina ban taba tsammanin azzaluman nan zasuyi maka haka ba Wallahi dana sani farisu da ban jefaka ciki ba dan Allah farisu ka.... Kada ki bata yawun bakin ki salma na katse maganar da takeyi kada kuma ki sake imani da cewa zan sake amincewa da tatsuniyarki nima hadama ce da rashin godiya ga Allah shiya jawomin. Amma inason ki sani har bayan rayuwata salma bazan taba mantawa da abinda kikayi min ba sanin kankine tuni kinyi sanadiyyar nakasa dakuma halakar mutane uku abaya wannan yafarune kafin haduwata dake amma saboda son kai da son abin duniya kika yaudareni ta hanyar nuna min dukiya saboda ganina da kikayi talaka kikayi sa'a kuma kika sameni marar wadatar zuci hadamamme kamar sauran talakawan da kika yaudara abayana maganina kenan salma dana godewa Allah nayi zamana ahalin dana kasance ada to da wannan bata faru akaina ba kinsan yan magana sunce Talauci da kwanciyar hankali yafi arziki da tashin hankali.. Sheshshekar kukan da salma keyi shiya katse kalaman dake fitowa daga bakina. Dan Allah farisu ka yafeni Wallahi farisu idan baka yafeni ba Farisu na shiga uku da rayuwata dan.... Dan Allah kayi hakuri....ta sake fashewa da kuka har hawayenta yafara zuba akan kirjina nayi sauri na kawar da fuskata amma hakan baiyi maganin komai ba kukan da take ya karyar da zuciyata. Taci gaba da sharbar hawaye nikuma idanuna na kallon bangon dakin zuciyata cike da tunani dakuma fargabar abinda zai faru Akaina nan gaba ko da........ (jikan sidi mai jaka) [3/16, 5:07 PM] Abubakar Saleh AlQuyraeme: BIRNIN SARAUNIYA 20 BOOK 2 Ni kuma idanuna na kallon bangon dakin zuciyata cike da tunani dakuma fargabar abinda zai faru akaina nan gaba ko kadan bana yaudarar kaina nasan kam ni tawa ta kare babu abinda Elmahdi bazaiyi ba don ganin an rataya min laifin kisan maigadinsa akaina kudine yana dasu zai iya daukar duk lauyoyin dake birnin sarauniya don ganin an bataddani tunda abin da yarsa ke so kenan to amma..... Salma ta katse tunanina Farisu takira sunana dan Allah farisu ka dubeni ka kuma yafemin kona ji sanyi azuciyata domin Allah ne yasan irin radadin dake cikinta. Na juyo fuskata ahankali muka dubi juna akaro na biyu ita tafara dauke idanunta. Tausayinta ya sake lillibe zuciyata na dubeta ahankali muryata na gargada nace. Salma. ta juyo ahankali ta dubeni sanan tace na'am farisu. Tausayinta ya dada lillibeni sannan nace da ita. Kiyimin alkawarin abu daya salma zakiyi min? Fadi mana farisu ni mai yi maka komaice ayanzu raina ma ni mai iya sallama maka ce in dai har inada iko inason ki taimakeni salma ki sanar da iyayena duk abinda ke faruwa ki kuma rokamin gafara agurinsu domin ni tawa takare babu wani abu da zan iya yi sai ko abinda Allah ya yi.... Ka daina fadar haka farisu salma tace dani babu abinda zai faru dakai kaidai kabani hadin kai zan turo maka lauyan da zai kareka idan kunje kotu zaizo yayi maka tambayoyi ina fatan zaka bashi hadin kai kwararre ne nakuma tabbata duk lauyoyin da Elmahdi kedasu basu isa su kayar dashi ba sai munyi narasa farisu karka damu kaji ko? Tace dani tana dubana abinda na gani a idonta shi ya tabbatar min da cewa tana nufin abinda tace har cikin zuciyarta. Ka yafeni farisu sannan taci gaba da cewa nasan yanzu ka tsaneni farisu amma inason kasan da abu daya farisu. Na yi shiru ina dubanta taci gaba da cewa. Wallahi farisu tunda nake bantaba sanin wani abu wai shi so ba har zuwa lokacin dana hadu dakai kai kanka farisu bana kaunarka alokacin da muka fara haduwa ina dai kawai son cimma wani buri nawa ne tayi shiru tana dubana sannan tace Farisu zakayi mamaki idan nace maka duk duniyar nan ayanzu banida abin kauna kamar Ka. Kwalla tafara cika mata idanu tasa gyalenta ta share sannan taci gaba da cewa nasan ka tsaneni farisu amma inason ka sani banida abinso aduniyar nan kamar ka babu yadda na iya da raina haka kawai na farka rana guda na tsinci kaina ina begenka ayanzu kam farisu na gane cewa so yafi komai dadi na gwammace Ace ina tare dakai har abada da ace ina tare da Elmahdi Tayi shiru na dan lokaci sannan tace kada ka damu farisu zamuyi nasara in Allah ya yarda ta dubeni tayi murmushi ga mamakina saina tsinci kaina ina mai yi mata murmushi akaro na farko tun bayan zuwan yansandan sai yanzu ne naji hankalina ya dan kwanta. Atunanina salma zata iya tserar dani wannan shine kuskurena na biyu. Salma ta dafa hanuna da lallausan tafukan hannunta sannan tace ya kamata kadan ci wani abu dafa hannun nawa datayi shiya tuno min da haduwar mu ta farko inda take cewa bazaka fada min sunan naka ba? **** ***** ***** ***** ********* ***** *********** Kafin mu rabu da salma sai da ta tabbatar min da cewa kada na damu domin wai tunda tana sona to babu yadda za'ayi tabarni na halaka. Na kuma yarda da duk abinda tace nakuma sami kwarin gwiwa ayadda tace dani jibine za'a fara sauraron shariar tamu. Bazan taba mantawa da lokuta biyu da al'amuran biyu suka faru kusan lokaci guda ba. Lokaci na farko karfe hudu saura minti biyu ne kofar dakin ta bude mai ziyara na gaba ya shigo ya dan mayanta yana sanye da bakar kwat da wando bakake dakuma bakin takalmi wankan tarwada ne mai matsaikacin tsawo idanunsa kanana bakinsa daidai misali dogon hancinsa yayi matukar dacewa da farin tabaran dake shakatawa a samansa sannan ahannunsa na hagu yana rike da bakar jaka. Dabi'un mutumin suna da ban mamaki kallo daya nayi masa na tabbata nutsatstse mai hankali da kuma kaifin basira da kwakwalwa lokaci guda kuma naji zuciyata ta kwanta dashi tabbas zuciyata na son mutumin. Farisu ya kira suna LAUYA MUKHTAT ABBAS ina fatan salma tayi maka zancena banyi mamakin ji cewa shine lauyana ba amma kasancewarsa agabana yabani mamaki saboda ban taba tsammanin zuwansa da gaggawa haka ba atsammanina sai gobe ne zata turoshi to amma tunda bata sanar dani lokacin zuwan nasa ba sai na saki jikina dashi. Ta sanar dani nace. BARKA DA ZUWA. Kwananka nawa asibitin nan? Ya tambayeni nayi shiru ina tunani ni kaina bazan iya cewa ga iya adadin kwanakina ba domin lokacin da aka kawoni hankalina baya jikina abinda kawai zan iya tunawa shine abin yafaru ne ranar shida ga watan bakwai. Yau nawa ga wata? Na tambaye shi ya dubeni anutse sannan yace yau sha biyu ga wata nayi shiru ina dubansa cikin mamaki indai hakane to yau kwanana shida kenan anan. M. Abbas ya zaro wasu takardu daga cikin jakarsa sannan yafara yan rubuce rubuce bayan dan lokaci ya juyo ya dubeni sannan yace Farisu saidai fa ka dan yi hakuri domin inada yar matsala akunne inason kayimin bayanin abinda yafaru tun daga farko amma ka dan daga murya Na amaryarsa masa da duk abinda na sani tun.......... [3/16, 5:08 PM] Abubakar Saleh AlQuyraeme: BIRNIN SARAUNIYA 21 BOOK 2 Na amayarsa masa da duk abinda nasani tun daga ranar da muka fara haduwa da salma har zuwa yanzu nayi shiru ina dubansa yana yan rubuce rubuce sannan ya dago kai ya dubeni akaro na biyu. Kaine ka kashe shi farisu? Tambayar tazo min abazata don haka sai naji kamar an karamin wayar lantarki agadon baya saboda tsabar kaduwa na dubeshi galala atsammanina ya dan tabune. Da hankalina farisu yace dani yana murmushi kamar wanda ke kallon abinda ke zuciyata yanayin aikin ne haka farisu don haka yanada matukar muhimmanci ka amsa duk tambayar da akayi maka. Ai.... Ai... Na dauka kafini sanin haka nace dashi muryata na rawa shin kai ka kashe shi? Ya sake maimaita tambayar na dubeshi duban ido da ido sannan nace bani na kashe shi ba. Me yasa ka tsammanin ba kai ka kashe shi ba? Me kake nufi? Na tambayeshi. Abinda nake nufi shine ka amsa duk tambayar danayi maka batareda kayimin taka tambayar ba dolene kuma kayi duk abinda nace kayi wannan umarni ne daga SALMA yace dani haryanzu dan gajeren murmushin na nan afuskarsa. Goyon bayanka yaci gaba da cewa dakuma amsar da zaka bani ita zata taimaka wajen cin nasararmu idan munje dakin shari'a to ai ni ban gane tambayar da kake yi min bane nace dashi ina dubansa ya dubeni sannan yace kasan wani lokaci dan adam yakan rasa kwakwalwarsa na dan lokaci saikaga ya aikata abu batareda ya sani ba ina fatan kagane abinda nake nufi yace dani yana dubana ido da ido. Ni kam da hankalina domin naga lokacin da Ijakala ya daga addar ya kawomin sara da addar na kauce gefe guda shine ya sari maigadin awuya. Ko zaka iya tunawa lokacin da ya kawo saran ko dabarar ka tura maigadin gabansa bata zo maka ba kasan wani lokaci dan adam yakan tura duk abinda ke kusa dashi amatsayin garkuwa idan wani abu ko wani bala'i yana shirin fada masa. Na girgiza kaina ko kusa hakan bata faru ba. Lauyan da yakira kansa da Mukhtar Abbas ya dago kansa ahankali ya dubeni sannan ya cire gilashin dake idonsa ya goge shi da farin kyallen dake hannunsa sannan ya maida gilashin daraf bisa hancinsa kamar daman anan Allah ya halicce shi. Mukhtar Abbas ya mike tsaye sannan ya hada yan takardunsa ya maidasu cikin jaka yace me yiwuwa zan sake ganawa dakai gobe kada ka damu zamuci nasara sannan ya dada dacewa sai goben ya nufi kofar dakin ahankali. Irin yadda yace zamuci nasara dakuma kallon karshe dayayimin shiyasa jikina ya dauki rawa kamar mazari ni kaina bansan abinda ke damuna ba amma acan cikin zuciyata wani abu nata yi min kururuwar cewa kayi kuskure farisu me yasa salma bata fada maka sunan lauyan ba in har ita ta aiko shi kofar ta sake budewa kamar kowanne lokaci sannan shima ya shigo dogo ne fari yana da dan siririn gashin baki shima sanye yake da bakar kwat da wando irin na wacan hancinsa dogone saidai ya dan lankwasa kadan daga can karshen karan hancin shaho babu alamar farin ciki ko bakin ciki a fuskarsa ya nufo inda nake yana takawa daidai kamar mai tafiya akan igiya. Sannu farisu yaya jikin yace dani fuskarsa ta washe da murmushi bana ko shakka lauyan farko ba salma ce ta aiko shi ba. Lauya IDRIS ABUBAKAR shine sunana yace dani ina fatan salma ta sanar dakai cewa ina nan tafe nayi shiru ina dubansa makoshina abushe yawu ya karanta abakina nasan na fada babban tarko. Tunda sassafe yan sanda bakwai suka shigo suna muzurai acikinsu harda Abdul shiya fara zaro ankwa daga aljihunsa sannan ya buga min ita ahannu baiko damu daya samin ita ahankali ba saboda ciwon dake hannuna inda ijakala ya sareni bai gama warkewa sosai ba. Wani dansanda gajere mai tarin gashin baki kamar shekar kurciya ya aza keyata gaba su kuma sauran suka dafa mana baya. Wanan shine karo na farko tun ranar da aka kawoni asibitin dana fito farfajiyarsa nayi mamakin ganin asibitin saboda babu wani abin azo agani cikinsa shima dai kamar su daya da sauran asibitocin daka saba gani yau da kullum na masu rufin asiri. Tun daga kofar dakin farko da aka fita na fara ganin irin tsatstsauran tsaron da akeyimin ashe danayi niyyar gudu ma to da iya kata kofar dakina abin mamaki kusan yansanda biyar ne. Ke gadin kofar dakin danake na lakanci hakane alokacin da ake fitowa dani. Tun kafin mukaraso kofar shiga asibitin na hango bakar motar baki kirin da ita har sheki take dan baki. Yansanda biyar ne atsaye abakin kofar shiga motar suna muzurai hancin bindigoginsu asaitin gangar jikina ko da aka matso dani daf da motar sai duk yansandan suka ja kunamar bindigarsu kyat kyat. Wani dogon dan sanda kakkaura ya bude bayan motar shiga ba biya. Budewarsa keda wuya sai yansandan suka kasu gida biyu wasu bindigarsu na saitina sauran kuma suka juya hancin bindigoginsu saitin bakin kofar alokacinne to na gane cewa ashe bani kadai za'a sa acikin motar ba tuni daman akwai wasu aciki. Lokacin da aka karaso dani bakin motar sainaji kamar ance dani daga kanka. Na juya ahankali tuni mutane sun hada yan kungiyoyi daga can nesa suna baiwa idonsu abinci yawancin majinyatan dake asibitin duk sun lelleko suna kallona wasu akasa wasu kuma ta saman bene idan kuma har ba kunnena ne ke fada min karya ba naso Naji wata siririyar murya nacewa TAURIN RAI IRIN NA ƁARAWO KINGA KO AJIKINSA MA OH!!!! Zuciyata tayi kuna bakin ciki mai tsanani Yayiwa zuciyata mayafi babu abinda yafi bata min rai fiyeda komai irin yadda sunana zai baci nasan tuni labari ya sami iyayena dakuma sauran mutanen unguwar mu tausayin kaina ya kamani sannan tunanin sallau ya fado min arai ko ina mutamin nan mai bamu bashin lemo? Na tambayi kaina ko me zaice idan yaji labarin? Na sake tambayar kaina me yiwuwa ya fashe da dariya na amsawa kaina cikin NADAMA. ****** ****** ***** ****** ****** ***** ********** [3/16, 5:09 PM] Abubakar Saleh AlQuyraeme: BIRNIN SARAUNIYA 22 BOOK 2 Na tambayi kaina ko me zaice idan yaji labarin? Na sake tambayar kaina me yiwuwa ya fashe da dariya na amsawa kaina cikin NADAMA. ***** ***** ***** **** **** ****** **** *********** Yansanda biyu suka kafa hancin bindigarsu agadon bayana yayinda wasu uku ke kokarin turani cikin shiga ba biya alokacin ne to na hangota. Tana tsaye daf da motar daga can nesa nisan dake tsakaninmu zaikai taku hamsin na gajeren mutum. babu alamar bakin ciki a fuskarta tana sanye da doguwar riga ruwan hoda takalminta baki ne (Cover shoe) mai dauke da ado na sarka ruwan gwal bata ko damu data lillibe gashin kanta ba maimakon hakan saita hada gashin kan nata abaya ta daure shi da ribon launin fari wanda akayiwa shan fure. Mukayi ido hudu da ita sannan wani faffadan murmushin nasara ya bayyana akyawawan labban bakinta burinta ya cika tayi min kallon kaje can ka karata sannan ta juya ta nufi motarta bakin tabaran dake idonta bai hanani gane ta ba HINDU ELMAHDI ce. Wannan shine gani na karshe danayi mata ban kuma sake ganin taba sai bayan shekaru uku. Yan sandan suka angizani cikin motar kamar wani buhu sannan suka garkame kofar mu uku ne acikin motar mutum biyu din dana tarar duk sun ji jiki tsammanina sun dade agidan tuhuma kafin ayi niyyar kaisu ga shari'a. Dayan yaro ne kamar ni amma na biyun ya dan tsere mana da yan shekaru kamar biyar. Mutanen biyu suka dago kai suka dubeni suna muzurai dayan wanda nake tsammanin kusan shekarunmu daya farine dogo siriri daga dogon hancinsa har zuwa bakinsa babu wani abin aibu a tattare dasu amma idan ka dubi idonsa anan ne zaka iya cankar dabi'unsa idanunsa sun fi kama dana maciji fiye dana mutum. Mutum na biyu bawani abun ku gani bane irin dai mutanen daka saba gani yau da kullum kan titunan birnin sarauniya suna yawo ne babu sabon al'amari ko siffa atattare dashi in ka dauke katon cikinsa mai kamar salka nayi mamakin ganin cikin nasa bai sace ba duk kuwa da irin azabar da nake tsammanin ana gana musu. Kayi sa'a dogon yace dani yana kifkifta idanu sa'ar ka daya itace da za'a yanke maka hukunci haka da gaggawa batareda an ajjeka lokaci mai tsawo agidan tuhuma ba. Na dubeshi cikin fushi sannan nace menene abin sa'a ga wanda ke fuskantar hukuncin kisa? Ba kai kadai ke fuskantar hukuncin kisa ba akalla dai bakaci dukan tsiya ba yace dani nayi shiru ina mai mamakin abinda sukayi har suka sami kansu airin wanan mummunan matsayi irin nawa. Adaidai lokacine mukaji motar ta fara tafiya bakin ciki ya sake lillibeni kowannen mu na tare da masaniyar cewa mutuwa muke fuskanta ga mamakina sainaji ni ko mutuwar bana tsoro na rufe idona kammanin salma suka bayyana karara a zuciyata alokacin data dafa hannuna farkon haduwarmu da ita tace min Bazaka fada min sunan naka ba? Nayi tsammanin sassanyar muryarta cikin zuciyata. **** ***** **** **** **** ********* ***** ********* Abinda yabiyo bayan shari'ar abin bakin ciki da takaici ne gareni dakuma duk mai kaunata. Abin yazomin abazata ban kuma taba tunanin bazamuyi nasara ba yaudarar da lauyan farko yayi min ita ta basu damar cin nasara akanmu ashe lauyan dayafara ziyartata asibitin ba salma ce ta aikoshi ba bansan yadda akayi suka san cewa salma zatayi tunanin lauya ba amma atsammanina su Elmahdi ne suk hada baki da malaman asibiti don yi musu leken asiri. Me yiwuwa kayi tunanin zan baka labarin abinda yafaru a kotun to ko kusa kada kafara tunanin haka domin bazan iya ba saboda fadin abinda yafaru akotun bashi da amfani tunda bamuyi nasara ba abubuwan da suka faru na bakin ciki aranar basa misaltuwa abinda ya faru ya riga ya faru babu irin kokarin da lauyana baiyi ba aranar don ganin ya cece ni amma ina mun makara domin su elmahdi sun shiryawa komai sun kuma zo da shaidu na karya wadanda suka rantse tsakanin karya da gaskiya wai sun ga lokacin dana sari mai gadin da adda awuya. An kuma kawo shaidun ne amatsayin masu hidima agidan elmahdi kuma acewarsu wai lokacin da akayi ihu barawo su suka fara kawo agaji kuma akan idon su na sari mai gadin lauyan yayi ta kokarin kareni bazan taba mantawa da ranakun shari'ar ba zama uku kotu tayi abinda yafaru kuma adan tsakanin kwanakin babu dadin ji. Inaji ina gani saboda banida gata akan laifin da banawa ba aka yanke min hukunci. Aranar da aka yanke min hukuncin karshe ne naji abinda ban taba jiba arayuwata abinda yafaru aranar shine nake tsammanin zan iya sanar dakai. Bayan lauyana yayita babatu kamar ransa zaifita amma hakan baisa ya cimma nasarar komai ba nasara daya kawai ya samu itace anyimin afuwa baza'a kashe ni ba amma za'ayimin daurin rai da rai lokacin da mai shari'a ya zartar da hukuncin sai duk kotun akayi ajiyar zuciya sanan hayaniya ta barke. Salma wacce ke cikin yan kallo ta fashe da kuka wiwi kamar karamar yarinya ta nufoni da gudu zata rungumeni amma yansanda suka maida ita tana ta kurururwa. Farisu Farisu Farisu na shiga uku Farisu wallahi ni a janyo maka wayyo Allah farisu nima mutuwa zanyi banga amfanin rayuwata ba amsa kuwwar kuka da kalamanta suka daki dodon kunena abin babu dadin ji dakyar aka fitar da ita waje. Ana cikin hargitsin ne sai kawai....... [3/16, 5:10 PM] Abubakar Saleh AlQuyraeme: BIRNIN SARAUNIYA 23 BOOK 2 Amsa kuwwar kukan da kalamanta suka daki dodon kunnena abin babu dadin ji dakyar aka fitar da ita. Ana cikin hargitsin ne to na hango mahaifina shida babata sun nufo inda yansanda suka zagayeni da bindigogi idanuwan babata duk sun kukkunbura saboda kuka shakaru sun karu akan nata nada saboda tsananin bacin rai wasu yan sanda biyu suka yi musu jagora har zuwa inda nake. Mahaifiyata tayi wuf ta kankameni tana kuka yan sandan dake zagaye dani suka dan dare domin su baiwa mahaifina damar karasowa kusa dani idonsu akaina basa kiftawa a tunanina suna tsammanin zan iya gudu ne. Dannan mahaifiyata tace dani tana kuka kamar ranta zaifita sunan kenan data saba kirana dashi shi kenan kuma dannan mun rabu dakai wayyo Allah!! Allah ka saka masa Allah kayi sakay... Kukan ya shake mata makwogoro ta kasa karasa abinda take son fada. Ku yafeni nace dasu cikin kuka kukan da suke ita da mahaifina sharaf sharaf shiyafi komai bata min rai fiyeda komai shine kuma ya karyar da kwarin zuciyata harna fara kuka. Mun yafe maka farisu sukace gaba daya mahaifina ya matso kusa dani ya dafa kaina sannan ya matso kusa da bakinsa daf da kunnena cikin rada yace Farisu kada ka damu mun yafe maka abu na karshe danake son ka sani shine ka yarda da kaddara haka Allah ya kaddara zata faru akanka kaci kuma gaba da addu'a aduk inda suka kaika Allah yana taimakon wanda ya rokeshi kada ka yanke kauna farisu nasan bazaka dauwama har iya rayuwarka acan ba domin Allah zai bukutar dakai da yardarsa nasan duk abinda kayi da wanda bakayi ba duk kayi shine saboda tunanin irin halin da muke ciki na talauci da matsi...zuciyarsa ta karye yafara shashshekar kuka akunena Allah na tare dakai Farisu sai... Sai... Wata.. Rana.... Wani dan sanda dogo ya dan taba mahaifina abaya sannan yayi masa nuni da cewa dan lokacin da aka basu don ganawa dani ta karshe ya wuce har akayi waje dasu babata bata daina kukaba amma mahaifina ya dan saurara lokacin dayazo fita sai ya juyo maka hada ido yan sandan na tsaye suna kallon mu babu wanda yace uffan munyi kimanin dakiku goma sha biyu babu wanda yace uffan sannan ga mamakina sai naga yayi murmushi nasan murmushin karfin hali ne irin na namiji amma hakika murmushin ya karamin kwarin gwiwa. Mintuna biyar da faruwar hakan sai suka iza kyeyata zuwa inda motar take shiga ba biya wacce ke tsaye bakikirin tana sheki acikin hantsi suka turani ciki sannan suka nufi babban gidan yarin dake birnin sarauniya dani motar tana tafiya nikuma ina leken waje ta yan kofofin da aka bari domin iska ta sami gurin shiga kallon karshe nakeyiwa birnin a tsammanina nida sake dawowa nan saidai ko a makara idan na mutu. To amma abubuwa basu faru kamar yadda nake tsammani ba. Wasu yara na wasa akofar gida suka dago mana hannu duk da yake kuwa basa ganin wanda ke cikin motar na danyi murmushin karfin hali sannan nace Allah ya shiryeku yara na lumshe idona ina sauraron shiga sabuwar rayuwar da bai kamata ace ta zama tawa ba. Wani kakkauran hannu mai kama da bayan kada ya mari wuyana nayi firgigit na bude idanuna tun kafin na gama mutsutstsuke idanuna nagane wanda ke dukan nawa. Wannan bashine karo na farko ba bakuma na biyu ba kai bama na dari kona dari biyu ba wannan shine kusan dubu daya da chasa'in da biyar 1095 da kakkausan hannunsa ya mari wuyana shekara kamar kwana indai har lissafinda nake daidai ne to yau kusan shekaruna uku kenan agidan maza. Aduk kuma iya kwanakin danayi wannan kakkausan hannun shine ke tashina barci. Kamar kullum saina bude idanuna ina dubansa ahankali ina duban mai tashin nawa. Dan siriri ne mai kamar langa langa saidai kuma zuciyarsa irin ta manyan mutane ce masifa da mugunta kuwa ko sauro ya rufa masa asiri dogone baki koda yake ayanzu ya rikide ya koma launin shudi shudi saboda tsabar wahala mukuma farare fararen mun koma launin kunun kwankwa kasuma duk ta cika mana fuska duguzum-zum babu kyan gani da ace zamu fito cikin mutanen dake cikin gari to da babu abinda zai hana musa kananan yara mafarki. Barcin ya isa hakanan yace dani yana zazzare idanunsa kamar wani ubana karka tona kaga yadda nake tsoronsa badan komai ba kuwa sai don azabarsa mu uku ne adakin duk da yake kuwa dakin bai ishi dan karamin yaro ya kwanta ciki ba indai har ana zancen duniyar mutanen kirkine to amma anan haka muke zaune a dankare guri guda kamar kifayen gwangwani. Dauke hannunka yace dani na dauke hannuna sannan yafara sharamin mari saida ya mareni sau goma sha biyu sannan yasa kafa ya daki kirjina gyaran kenan yace dani yana muzurai. Wannan shine ka'idarsa akullum idan ya rigamu tashi daga barci saiya mammare mu sau goma sha bibbiyu idan kuma kai ka rigashi tashi saiyace saika mare shi sau biyar to idan ka mare shi din saiyace ko wanne mari amatsayin mari goma yake hamsin kenan yau shekara uku kullum haka muke babu yadda zamuyi tunda yafi karfinmu domin idan ka biye masa yana iya hallaka ka baki daya. Na dubeshi cikin takaici dan lange-lange dashi kamar lilo amma sai karfin tsiya kamar shari'a na dubi siraran hannunsa. Sai naga...... [3/16, 5:10 PM] Abubakar Saleh AlQuyraeme: BIRNIN SARAUNIYA 24 Nadubeshi cikin takaici dan lange lage dashi kamar lilo amma sai karfin tsiya kamar shari'a na dubi siraran hannunsa masu kama da alkalamin rubutun sha. amma karfin dake jikinsu na mamakine daga haka kamar na kama na karya amma idan ya rikeka dasu saikaji kamar hakorin kada ne ya damkeka. Gama marina keda wuya saiya matsa kusa dan uwan zaman mu ya mareshi afuska yayi firgigit ya tashi zaune shima ya hada kai da gwiwa. Kamar ni shima ya riga ya saba da azabar dan kereren mutumin nan. Daga hannunka yace da mutumin ba'a dade ba shima yagama sharara masa nasa marin sannan ya juyo yace damu. Ina fatan kun wartsake muka gyada kai gaba daya domin idan muka ki to karamana zaiyi yace bamu wartsake ba. Aka'ida duk lokacin daya gama marin mu saiya juya mana baya yaci gaba da al'amuransa tunani yake? Me yake? Allah masani bazai sake koda daga kai ya kallemu ba sai kuma gobe idan Allah ya kaimu in zamu fasa dakin da surutu mu biyu bazaice mana cikan ku ba shekaru uku kenan bamu ko tabajin sunansa ba domin shi kullum kalmarsa daya yake amfani ita akanmu itace DAGA HANNUNKA Amma abin mamaki sabanin hakan yau saiya kalleni yace cikin murmushin mugunta dan samari hira nake so muyi dakai kabani labarinka nima nabaka nawa ko kanaso ko baka so yace dani sannan ya juya kan dayan yace toshe kunenka idan ka sake ka saurari hirarmu saika dandana kudarka yace dashi yana muzurai. **** ***** **** ***** ***** ****** ***** ********** Sunana ACI BULUS yace dani yana yayyake hakora zaka iya kirana haka domin shine sunan da abokaina suka saba kirana dashi. Ya dan matso daf dani warin da jikinsa keyi ya bugi hancina dakyar nake shakar numfashi nima jikina na wari amma hakan bai hana nasa jikin ya ninka nawa wari ba kasancewarsa daddade agidan yarin bansan iya shekarun dayayi aciki ba to amma nagane cewa ya dade aciki tun ranar da aka kawoni gidan yarin. Rigar dake jikinsa dakuma irin warin dake fita daga jikinsa sun isa su nusar dakai dadewarsa aciki. Menene sunanka dan samari? Ya tambayeni. FARISU nace dashi ya bude idona cikin mamaki farisu? Akaro na farko cikin shekara uku sai naga bakinsa ya fadada izuwa tattausan murmushi sunanku daya da kanina yace dani kakkausan hannunsa ya bugi bayana daga yau ka zama kanina kaji ko yace dani. Bance dashi komai ba saiyaci gaba da cewa Tarihina ba wani mai tsawo bane kanina nidai tsohon ma'aikacin wani kamfani ne amma badashi na dogara ba lokaci lokaci nakansa hannu idan za'a aiwatar da fashi da makami kusan shekaruna goma sha daya ina aiki a kamfanin amma duk abinda nake samu ta hanyar aikina dakuma fashi da makamin da muke basu isheni ba yayi shiru yana dubana sannan yace. Farisu kasan wani abu kuwa? Allah ya doramin masifaffen son kashe kudi irin yadda nake kashe kudi ko gobara batacin takarda haka kudi basu taba isa taba farisu yace dani a tunanina yafara tabuwa ne kasancewarsa dadadde agidan maza. Watarana farisu yaci gaba da cewa saina yanke shawarar nayi mai dungurungum ma'ana shine mu fashe kamfanin danake aiki ciki mu kwashe duk wani abu mai daraja dake kamfanin. Wannan yabiyo bayan wata yar tarzoma ce tsakanina da wani kwara dake kamfanin. Wannan shine karshen tarihina farisu baka bukatar sanin komai akarshe babu wanda yakai labari acikinmu wasu daga cikinmu tuni an harbe su yayi dariya yace dani yau shekaru goma kenan cif cif suna karkashin kasa suna baiwa kwari da tsutsotsi abin kalaci ni nafisu sa'a aka yanke min hukuncin daurin rai da rai amatsayina na wanda yake da hannu cikin fashin menene labarinka farisu? Ya tambayeni yana tauna farcen dan yatsansa na hagu. Na dubeshi shima ya dubeni akwai wani abu dake tattare da idonsa wanda yasa naji jikina yayi sanyi. Asanyaye saina fara bashi labarina lokacin dana kawo inda salma tabani kudin sainaga ya daga min hannu yayi zumbur ya mike tsaye. Yafara safa da marwa cikin dan kankanin dakin mai kamar akurki. Kana nufin kace yanzu kudin suna nan asaman dakin ka? Ya tambayeni kwarai kuwa nace dashi. Baka fadawa kowa ba? Ya sake tambayata tabbas sunanan nace dashi irin masifar dana shiga ce ta fitar da duk tunanin kudin daga cikin zuciyata naso na sanar da iyayena maganar kudin amma sam sam na manta saboda bacin rai domin ni alokacin kudin basune agabana ba. Nayi shiru sannan naci gaba da ce masa sai bayan da mukayi ganawar karshe da iyayena ne sannan boyayyan kudin suka fadomin arai kaico nace dashi inama ace na sanar dasu. Gara da baka sanar dasu ba farisu yace dani yana dubana ido da ido haryanzu bai daina safa da marwa ba. Hannuwansa biyu amakale da bayansa. Wannan itace babbar damar mu ta karshe Farisu. damar me fa? Na tambaye shi ina dubansa ido da ido. Damar da zatayi sanadiyyar tsirarmu daga wannan masifa indai har yadda kafada gaskiyane to naira miliyan uku ta isa ta buda mana hanya tun daga nan har zuwa kasashen ketare. Yayi shiru yana dubana. Amsa kuwwar kalamansa sukaci gaba da ruri cikin kwakwalwata lallai kuwa yafadi gaskiya tabbas domin babu masifar data wuce ace mutum yayi ta zama cikin irin wannan mummunan yanayi har... [3/16, 5:11 PM] Abubakar Saleh AlQuyraeme: BIRNIN SARAUNIYA 25 Damar da zatayi sanadiyyar tsiranmu daga wannan mafisa indai har yadda ka fada gaskiyane to naira miliyan uku ta isa ta buda mana hanya tun daga nan har zuwa kasashen ketare. Yayi shiru yana dubana amsar kuwwar kalamansa sukaci gaba da ruri cikin kwakwalwata lallai kuwa yafadi gaskiya tabbas domin babu mafisar data wuce ace mutum yayita zama cikin irin wannan mummunan yanyi har iya rayuwarsa da ace haka ta faru akaina gara na mutu na huta to amma ina mafita kamar wanda ke karantar zuciyata saiya dubeni yace. Nasan abinda kake tunani kada ka damu da wannan matsalar tuni na sami maganinta tun sa'adda na shigo gidan nan nake ta tunanin hanyar tsira to amma ba tsiran ba idan na gudu ina zani nasan idan nayi nisa nafita daga birnin nan amma daga nan ban ko kara riskar wani birnin zasu cimmani tunda banida kudi. Yayi shiru na dan lokaci sannan yace. Naira miliyan uku daka bani labari ita ta kawo karshen shirin guduwar danake kasan in ba mahaukaci ba babu wanda zai yarda ya kare rayuwarsa anan ka tuna fa farisu tuni nayi shekara goma anan. Ya matso daf dani sannan ya daga hannuna yace ka amince? Batare dana sake tunani ba saina sami kaina ina cewa na NA AMINCE dakyau namiji yace dani gobe warhaka muna kan hanyar zuwa matsera. Na dubeshi cikin mamaki nace dashi tayaya zamu tsere daga nan.? Yayi murmushi yakuma dubi daya mutumin dake can kuryar dakin kwance ya toshe kunnuwansa sannan ya matso kusa dani yafara yi min bayani cikin rada. **** ****** ****** ***** ********** ************** Irin abincin da ake bamu agidan yarin banko san sunansa ba acikin leda ake tura mana shi ta tsakanin karafunan kofar kejin da muke ciki kamar kullum yauma duk sai muka marmatso kusa da karfen kofar muka daddafa da hannunmu muna jiran mai rabon abincin ya karaso kanmu tuni har wasu dakunan sun sami nasu kason gidan yarin ya dauki hayaniya. Lokacin da gandiroban mai rabon abincin ya karaso sai na kara gaskata labarin da aci bulus yabani dazu sunyi kama sosai ban kuma taba kula da hakan ba sai bayan daya gama bani labarin. Nafara tunanin magangamun da mukayi dashi kanin babata ne yace dani yana kuma masifar sona saboda wani lokaci dacan babata ta taimaka masa sosai tun zamanin yana makaranta. Na dubi mutumin dakyau sainaci gaba da tunanin in da aci bulu yake cewa dani. Ko shakka karkayi farisu na tabbata zai iya yin hanyar da zamu tsere kasan duk iya zamana anan shine mai kula da bangaren mu aduk safiyar duniya karfe uku na rana yake tashi wani yazo ya karbe shi kaidai ka barni dashi farisu yace dani nasan abinda zanyi masa. Gandiroban ya matsa dakinmu sannan ya miko min abincin acikin leda shi kadaine ya rage akan farantin dan haka sai yace dashi ina zuwa aci bulus yafito shi sannan ya rada masa wani abu duk abin yafaru ne cikin abinda bai wuce dakika bakwai ba. Gandiroban ya juya yafita ba'a jima ba saigashi yadawo da wasu kulli kullin abincin akan faranti ya dauki babban cikin su ya mikowa aci bulus sannan yawuce gaba yaci gaba da rabawa sauran fursunonin abincin wannan shine tsarin wannan gidan fursunan. Aci bulus ya bude kunshin abincin sa amma bayan abincin akwai wata yar guntuwar takarda da biro aciki. Aci bulus yayi kamar abincin yake ci amma azahiri rubutu yake a takardar bai dade da gama Rubutun ba sai ga gandiroban nan ya dawo zai wuce aci bulus ya yafito shi kamar zaice dashi wani abu sai ya tura masa takardar daya rubuta. Misalin karfe daya na rana saiga gandiroban yadawo rabon abinci kamar dai dazu acikin abincin aci bulus akwai farar takarda mai dauke da rubutu aci bulus ya fara karantawa sannan ya dago kai ya kalleni yayi murmushi. An gama farisu gobe warhaka mun sami yancin kanmu karfe biyu da rabi zai dawo. Na dubeshi sororo amma ban yarda da abinda yake fadiba. Cikin talatainin daren ranar ina kwance koda yake ba wani cikakkken barci nakeyi ba sainaji Aci bulus yatabani tashi Farisu yace dani lokacin tafiya yayi. Nayi shiru ina dubansa ban gaskata abinda kunnuwana suka jiye min ba. Nayi zumbur na mike tsaye. Tuni aci bulus yakai ga kofar dakin da muke. Gandiroban na tsaye ajikin karafunan kofar sanye da bakaken kaya komai nasa bakine hatta takalmin dake kafarsa bakine. Kun shirya ? Ya tambayi aci bulus mun shirya aci bulus yace dashi cikin rada amma jirani ina zuwa anan ne naga rashin Imani. Aci bulus ya makure dayan mutumin dake kwance yayi masa kamshin mutuwa mutumin yayita wutsul wutsul da kafafunsa daga karshe sai yayi laushi tubus jikinsa yayi lakwas bai kara motsi ba azatona suma yayi. Tun kafin aci bulus yagama da mutumin tuni gandiroban ya bude kofar da irin gwanintar wanda yasan aikinsa ga mamakina sainaga yashigo cikin dakin ya maida kofar ya rufe sannan ne fa na lura da bakar jakar dake hannunsa yana shigowa sai ya jefar da jakar adaben dakin adaidai lokacin ne to mukaji motsin wani ya nufo dakin. Ku kwankwanta yace damu cikin rada kafin ya rufa bakinsa aci bulus yakai kasa ba'a dade ba nima nayi wanwar a kasa hadi da munshari wai barci nake. Gandiroban ya zauna a takure aguri guda baya ko motsi tsananin duhu dake dakin bazai bari a ganshi ba muma fararen kayan fursunan dake jikin mu su suke nuna alamar mu. Baka jin motsin komai sai kawai...... [3/16, 5:12 PM] Abubakar Saleh AlQuyraeme: BIRNIN SARAUNIYA 26 BOOK 2 Muma fararen kayan fursunan dake jikinmu su suke nuna alamar mu. Bakajin motsin komai sai kukan gyare dana wasu daga cikin tsuntsayen dake bishiyoyin gidan yarin. Kwaf kwaf kwaf karar takun sawun mai sunturin ne wani gandiroba ne dan gajere mai babban kai bindiga harbi ka ruga ta sami mazauni daraf abayansa. Lokacin dayazo daf da dakin mu baiko damu daya daga kai yadubi dakinba a tunaninsa duk yan yari sunyi barci. Bayan dan lokaci sai muka daina jin takumn sawun nasa to daman wannan itace al'adarsa akullum yakanyi sintiri agurin akalla sau goma sha hudu duk bayan mintuna ashirin saiya zagayo shine mai kula da sashen mu idan dare yayi wato dai shine yake chanjin gandiroban nan da aci bulus yace kanin babarsa ne. Gandiroban ne yafara tashi sannan muka mike tsaye ya buda jakar da yazo da ita sannan ya tsamo wasu riguna guda biyu da wanduna hadda takalmi sau ciki. Kuyi sauri kusa kayan yace damu karfe ukun dare yanzu ina kuka nufa idan mun fita daga nan? Ya tambayemu aci bulus yayi kasa kasa da muryarsa sannan yace. Kai dai ka fitar damu din mu munsan inda zamu. Ku saurara dakyau yace damu cikin sauri idan mun fita yaci gaba da cewa. Kada ku yiwa kowa magana ni zan fara fita ku kuma ku biyoni abaya zamu fice ta kofar yamma kada kuma kuyiwa duk wanda kuka hadu dashi magana ku tuna kuma fa kamar masu gadi kuke kuma kuna suntiri ne daga kofar gidan yarin zuwa ciki yayi murmushi sannan yace Inafatan kun fahimci hoton danake kokarin nuna muku? Muka gyada kai gaba dayanmu. Ya bude kofar ahankali sannan ya leka yana duddubawa yayi kimanin tsawon dakiku arba'in yana dudduba cikin duhun daren sannan ahankali saiyace Ku dan bani lokaci saiku biyoni. Aci bulus shiya fara bin bayansa yana tattakawa dai dai kamar da gaske sannan kuma saini jikina na rawa kamar mazari nabi bayansa anan ne to nayi babban kuskuren da duk ya bata lamarin mantawa nayi ban rufe kofar ba. Banko juya ba sai nabi bayansu ina sassarfa. Gandiroban cikin bakaken kaya kamar aljani ya karkata yabi wani dan siririn lungu baki kirin babu alamar haske alungun bamuyi wata wata sai muka rufa masa baya dakyar nake ganin gabana ga kuma hanyar da kwazazzabai. Atsammanina hanyar da ruwa ke bice idan anyi ruwan sama. Hanyar da muke bi bayan ginin dakunan fursunoni take kokarin kaimu nayi mamakin yadda akabar hanyar haka a gururrube. Bayan munyi kusan tafiyar mintuna biyu. Sai hanyar ta fara karkacewa tanayin bangaren yamma tuni mun bar gine ginenan dakunan kwanan yan fursunan haryanzu bamu hadu da ko mai gadi daya ba bakajin motsin komai agidan sai jefi jefin kukan tsuntsaye nan da can wasu lokutan kuma idan ka saurara da kyau zaka iyajin amsa kuwwar sautin takun masu gadin dake sintiri acan cikin yankin dakunan fursunoni. Bamuyi aune ba muna cikin tafiya sai kawai muka ganmu a bakin wasu shuke shuke atsammanina kayan lambune aka shuka agurin kasancewar mu alokacin damina. Gandiroban dake yi mana jagora ya tsaya sannan ya yafuto mu da hannunsa muka nufi inda yake tsaye. Ku jirani anan yace damu bai jira munce wani abu ba saiya nufi bakin wata rijiya wacce ke daf damu abakin rijiyar akwai guga da igiyarsa sannan aboye acikin ciyawa daf da gugan wani dogon tsanine na katako. Nayi mamakin basira irin ta wannan gandiroba ina kyautata zaton tunda rana ya tanadi tsanin agurin. Gandiroban ya dauki tsanin ya nufi zungureriyar katangar data zagaye gidan ba'a dade ba yagama jingina tsanin ajiki ya dawo ya samemu a inda ya barmu haryanzu jikina bai daina rawa ba. Gandiroban ya dubi aci bulus sannan yace USMAN wannan shine karo na farko dana san sunansa na gaskiya gandiroban yaci gaba da cewa. Duk abinda zan iya yi nayi ma. Yace da aci bulus ba karamin hadari nasa kaina aciki ba wajen taimakon ku amman duk wannan ba wani abu bane in har akayi la'akari da abinda mahaifiyarka tayimin tayi matukar taimakona wani lokaci da can daya wuce abinda bazan taba mantawa dashi bane. Yayi shiru na dan lokaci sannan yace. Mutumiyar kirki kenan. Ya girgia kansa yana duban can nesa damu kamar mai tunanin wani abu. Ya juyo ahankali ya dubemu sannan yamikawa aci bulus hannu sukayi musabiha sai watarana. Yace dashi Allah ya bada sa'a ga tsani can ka fara tsallakawa sai abokinka ya biyo ka sannan ya juyo kaina ya mikomin hannu yace. Abokina sai watarana ko? Ya jijjiga hannuna hakan da yayi shiyasa tausayinsa yakamani nayi mamakin irin rayuwa da yayi abaya ko wacce iri ce ? Na tambayi kaina. Gandiroban ya dan daki bayan aci bulus sannan yace sai anjima aci bulus ya juyo ya dubeni sannan yace sai kayi sauri ina jiranka abaya. To na amsa masa da sauri bakina na rawa. Aci bulus yanufi katangar da sauri sauri sannan ne to kuskuren danayi ya bata shirin gaba daya babu zato babu tsammani sai mukaji wani sautin usir mai karar tsiya ya ratsa sararin samaniya sannan ya gauraye ko ina cikin gidan yarin sannan sautin gudun sawun masu gadi ya biyo baya. Aci bulus yayi turus ya tsaya cak kamar wanda aka soka agadon baya. Gandiroban ya dubeni nima na dube shi cikin rudewa sannan ne fa......... [3/16, 5:13 PM] Abubakar Saleh AlQuyraeme: BIRNIN SARAUNIYA 27 BOOK 2 Gandiroban ya dubeni nima na dubeshi cikin rudewa sannan yace dani. KA RUFE KOFAR DAKIN KUWA? Nayi Galala ina dubansa hakan shiya tabbatar masa da cewa ban rufe ba irin kallon da gandiroban yayi min alokacin bansan da abinda zan fassara shi ba. ***** ***** ***** ***** ******** ****** ********** Dawo da baya gandiroban yace da aci bulus bai ko damu daya tausasa muryarsa ba. Har aci bulus ya juyo zai dawo sai kuma ya fasa har zuwa yanzu danake baka labarin nan na kasa gane abinda ya hana aci bulus bin umarnin gandiroban nan. Aci bulus ya nufi gindin katangar da gudu tsanin yake kokarin kaiwa tun kafin yayi kwararan taku hudu wasu masu gadi gandirobobi uku suka fito daga cikin duhun daren suka rufa masa baya kayan dake jikinsa basuyi masa amfanin komai ba saboda gandirobobin sunga kokarin tserewa yakeyi. Biyu daga cikinsu suka kaiwa kugunsa cafka yajuyo afusace yasa hannunsa mai kamar kafar ya naushi daya gandiroban afuska anan take yabaje akasa koda daya gandiroban yaga abinda yafaru saiya ja da baya yaja kunamar bindigarsa kyatkyat aci bulus baiga abinda yake ba don haka sai ya zaci ko tsorata yayi sai kawai ya nufi tsanin yafara takawa cikin sauri baiko damu daya duba abinda ke faruwa abayansa ba. Karan bindiga ya cika ko ina cikin gidan yarin mukayi tsalle gefe guda muka kwanta cikin ciyawa hannayena a toshe da kunnena wannan shine karo na farko da aka taba harba bindiga agabana. Aci bulus ya sandare ajikin tsanin sannan yafado da baya baiko shura ba. Kafin kiftawa da Bisimillah gandirobibi sama da ashirin sun zagaye shi suna jujjuya shi kamar waina sannan ne to wani daga cikinsu ya bada izinin su warwatsu cikin gidan yarin domin su nemoni. Sannan yabada izinin wasu daga cikinsu su haura katangar tayin amfani da tsanin atunaninsu ni tuni na haura. Duk wannan akan idonmu yafaru kuma duhun dare dakuma bakin hadarin dake haduwa asararin samanniya su suka dakushe hasken farin watan da zai iya tona mana asiri. Tashi ka bisu gandiroban yace dani bakinsa na rawa da farko bangane abinda yake nufi ba sai bayan dana dan nutsu sannan kwakwalwata ta ganar dani abinda yake nufi. Haryanzu wasu gandirobin na bullowa daga cikin duhun daren suna warwatsuwa da sauran wasu mutum biyu sukazo wucewa ta daf damu suna wucewa sai nayi zumbur na mike sannan nace da gandiroban dake kwance rub da ciki nagode sai watarana. Kada ka damu dani kaidai kayi ta kanka na girgiza kaina sannan batareda dana dubeshi ba saina rufawa mutane biyun baya muna zuwa sainaga sun kama tsanin suna tsallaka katangar jikina na rawa nima na kama tsanin kowane lokaci tsammami nake zanji an cakumi kuguna amma hakan bata faru ba sa'a tafi manyan kaya. Mu takwas ne muka haura katangar batareda bata lokaci ba sai naga kowa yayi nasa guri agurguje suna ta lalube lalubena cikin duhu ina cikin gudu sai Allah yakawoni daidai wani gidan bariki nayi ajiyar zuciya sannan na duba bayana babu alamar gandirobobin. Ban bata lokaci ba saina nufi gidan barikin saman benen an rubuta cikin manyan Harrufa SARAUNIYA HOTEL. Kidan zamani na tashi daga cikin wasu manya manyan lasifikoki guda hudu mutum tara ne aciki babban dakin shagalin otel din biyar mata ne cikakkun yan bariki hudu kuma mazane sun sha giya sunyi tatul dakyar wasu daga cikinsu suka daga ido suka dubeni uku daga cikinsu suna rawa biyu kuma suna hira acan gefe kuma mutum uku ne suna daga kwalbar barasa daga can kuryar dakin kuma wani mutum ne dogo mai tarin gashin baki yana karatun jarida karan sigari ahannunsa na hagu ganin mutumin shiyasa jikina rawa tabbas nasan mutumin. Na matsa kusa dashi sannan nace SAGIR ya dago kai ya dubeni cikin mamaki banyi kuskure ba tabbas na sanshi makwabcinmune tsakanin gidanmu da nasa gidaje uku ne tsakani farisu yakira sunana. Sagir ya girgiza kansa cikin mamaki atunanina yana shakkar abinda ya ganine dogon gemun dake fuskata bai hanashi gane ni ba. Ba mafarki kake ba sagir nace dashi nine kake gani ba wani ba ya dubi kayan dake jikina zai magana saina daga masa hannu kazo da motarka na tambayeshi ya gyada kai nayi ajiyar zuciya. Kaini gida nace dashi baiyi min musu ba nakumayi mamaki saboda duk zamansa a unguwarmu babu wata kwakkwaran mu'amala data taba shiga tsakaninmu kasancewarsa mai kaurin suna a unguwar babu wanda ke shiga harkarsa saboda tsabar fasikancinsa to amma ga mamakina sai gashi yau zai taimakeni wani lokaci dacan daya wuce ina daya daga cikin masu zaginsa. Muka nufi wajen fakin din motoci dake otal din muna zuwa saiya bude kofar motar fijo ce 504 fara nayi wuf na fada cikin motar ina zazzare idanu kowane lokaci tsammani nake za'a daka min tsawa amma har yasa wa motar giya muka fara tafiya babu abinda yafaru. Ina zan kai ka ya tambayeni yana yanayi yimin huci afuska na yi sauri na dauke hancina saboda warin giyar dake fita daga hucinsa. Gida zaka kaini nace dashi sannan naci gaba da cewa amma zaka jirani akofa akwai kayan da nake son daukowa idan na dauko su zaka taimakeni ka karasa dani tashar jirgin kasa. Ina fatan ba takurawa? Na tambaye shi. Sagir ya gyada kai batareda ya dubeni ba lokaci lokaci kan motar kan dan kwace daga hannunsa dakyar yake dawo da ita kan titi na rufe idona ina addu'a Allah saukemu lafiya. Haryanzu unguwarmu tana nan kamar yadda na barta shekaru uku da suka wuce amma saidai.... [3/16, 5:13 PM] Abubakar Saleh AlQuyraeme: BIRNIN SARAUNIYA 28 BOOK 2 Haryanzu unguwar mu tana nan kamar yadda na barta shekara uku da suka wuce babu wani kwakkwaran sauyi a tattare da ita inka dauke wasu yan gyararraki da akeyiwa wasu gidajen dake layin amma gidanmu baya cikin gidajen da aka yiwa gyara saidai na lura da tulin yashi da kuma tarin bulallukan simitin masu yawan gaske daga bangaren arewa na gidan. Ina zuwa nace dashi da sagir ban jira yace wani abu ba saina bude kofar motar sannan na nufi kofar gidanmu. Na tura kofar ga mamakina saita bude. Adaidai lokacin ne to naji babban ladanin unguwarmu ya kwala kiran sallar asuba saina daina mamakin ganin kofar abude nasan babana ne ya budeta a ka'ida akullum karfe uku na dare yake tafiya masallaci. Dakina yana nan kamar yadda na barshi babu ko dan makulli abude dakin sai wata waya akayi amfani da ita aka daure na kunce wayar sannan na shiga dakin ahankali ina yan dube dube bayan dan lokaci idona ya saba da duhun dakin na janyo wata tsohuwar kujera dake kuryar dakin bansan da zaman ta ba atsammanina bayan tafiyata aka kawota. Amma in ka dauke bakuwar kujerar dake dakin komai na nan yadda yake. Na taka kujerar sannan cikin hanzari nakama saman silin din na jijjiga da karfi tuni daman duk gara ta cinye silin din. Don haka jijjigawata hudu sai silin din ya barke na zura hannuna sannan nayi ajiyar zuciya. Haryanzu akwatin na gurin. Na janyo ta cikin hanzari na ajjeta a tsakar dakin sannan nayi waje da sauri haryanzu sagir na nan cikin motar zaune ya dora kansa akan matukin motar. Sagir na kira sunansa dan Allah bani aron cocila ko kuma ashana baiyi magana ba saiya bude wani dan akwati dake gaban motar ya dauko wata yar siririyar cocila mai kamar biro amma tafi biro kauri da kadan ya mikomin. Na juya da sauri na nufi cikin dakina ina zuwa saina bude akwatin na dallara hasken cocilar cikin akwatin kudin suna nan damin wazobiya wazobiya wani zazzafan gumi ya lullubeni gabana na dakan uku uku saina dauki dami daya na wazobiya ina juyawa ahannuna. GABANA YAFADI RASSSSS. Dana lura da cewa damin kudin dake kasan wanda na dauke ba kudi bane fararen takardune ashirye an yi musu yanka irin na kudi. Cikin rawar jiki saina daddauke damin wazobiyoyin dake saman akwatin. Ga mamakina sainaga ashe duk kasan akwatin dami damin yankakkun takardune farare sol sannan kuma suma dami damin kudin dake saman akwatin takarde ne dake sama su kadaine na gaskiya amma sauran duk fararen takardu ne. Wani abu yataho tun daga tsakiyar kaina har zuwa babban dan yatsana na kafa naji juwa tafara daukata yawun bakina ya kafe bugun zuciyata yakara sauri nayi gaggawa na zauna jagwaff adaben dakin na jingina bayana da jikin karfen gadona. Nagama yawo nace acikin zuciyata tuni rigata tagama jikewa sharkaf da gumi kamar ana zubamin ruwa.... ***** ***** ****** ***** ****** ****** *********** Bansan iya tsawon lokacin danayi agurin ajingine ba. Na yunkura na tashi tsaye duk kwakwalwata ta rikice bata tunanin komai sai shirme na nufi kofar dakin sannan na karkata na nufi kofar gida da niyyar naga halin da sagiru yake ciki. Idanuwana duk sun rufe dishi dishi nake gani. Lokacin dana isa kofar gida saina taradda sagiru ajingine ajikin motar na matsa kusa dashi ban lura da sauran wadanke ke tare dashi ba sai bayan danazo daf dashi ne to mukayi ido hudu dasu. Su shida ne yansandan kowannan su rike da bindiga. Tun kafin nagama kare musu kallo naji karfen ankwa ya rutsa hannuna sannan kowanen daga cikinsu ya caf cafki inda yake so ajikina. Adaidai lokacin ne to bakar motar shiga ba biya ta shigo cikin layin hasken fitilar motar ya haskake sauran duhun dake layin tuni har mutane sun fara dawowa daga masallaci. Tun daga cikin motar suka fara ligwigwita ni abinda yafaru aranar wani abune da bazan taba mantawa dashi ba hakika na wahala aranar abin babu dadin ji ungulu takoma gidanta na tsamiya. ***** ***** ***** ***** ******* ****** *********** Na takura adan karamin dakin mai kama da gwangwanin kifi sadin ko kafafuna bana mikewa sau daya kuma ake bani abinci arana na rame na zama kamar tabarya yau watana daya kenan babu kwana biyu adakin. Aranar da aka kawoni babu irin azabar da ba'a gallaza min ba daga karshe na basu labarin gandiroban daya taimaka mana muka tsere to amma yadda na sami labari daga baya ba'a ko sami labarin wanda yakara ganinsa ba daga ranar. Ina nan atakure acikin akurkin dakin na gwammace mutuwa da rayuwa. Asafiyar wata litinin ne naji duk hayaniya ta cika ko ina cikin gidan yarin wata daya kenan da dawowata. Nayi shiru ina sauraron hayaniyar sainaji kamar sowar murna akeyi nidai banida ko damar motsawa ballanta in tabuka wani abu. Misalin karfe goma sha daya na rana wasu gandirobobi samari guda hudu suka nufi inda nake ga mamakina sainaga sun bude akurkin sannan sauka umarceni dana biyosu na tashi da kyar na fara tafiya saina fadi. Sukazo da sauri suka tasheni sannan suka rirrikeni suka nufi wani makeken daki mai kama da dakin taro. Fursunoni kamata sun kai kimanin dari biyu acikin dakin aka umarcemu damu zazzauna. Sannan ne to wani mutum dogo kakkaura wanda nake tsammanin........ [3/16, 5:15 PM] Abubakar Saleh AlQuyraeme: BIRNIN SARAUNIYA 29 BOOK 2 Sannan ne to wani mutum dogo kakkaura wanda nake tsammanin shine shugaban gidan yarin yafara bayani. Da farko inason na sanar daku cewa anyi sauyin sabuwar gwabnati akasar nan mukayi shiru muna saurarensa amman abin mamaki sai naga wasu daga cikin fursunonin har dariya suke nikuwa agurina canjin sabuwar gwamnati shirme ne ina ni ina murna dan ansami sauyin sabuwar gwabnati. Ya katse tunanina lokacin dayaci gaba da cewa. Mai girma da adalci sabon shugaban kasa yabada izinin ayiwa duk wanda yayi shekara uku agidannan afuwa koda kuwa daurin rai da rai aka yanke masa. Ba'a bari ya karasa ba sai sowa da kukan murna suka cika gurin wasu suka fadi sumammu dan dadi wasu kuma suka rungume junansu suna kukan yiwa juna barka. Gobene ranar da aka bamu izinin mu sake ku saboda haka kowa saiya kwana cikin shiri. Na lumshe idanuna ina mai godiya ga Allah daya tserar dani daga wannan masifa na kasa gaskata abinda kunnuwana suka jiyemin. Gobe ....ne.... Ranar.... Da aka bamu izinin mu sake ku naji amsa kuwwar muryar mai jawabin tana ruri cikin kunnena shin anya kuwa hakan zai iya zama gaskiya? Na tambayi kaina. Ga mamakina sainaji babu abinda yafara fadomin azuciya sai SALMA wannan haukane nace da kaina itace matar datayi sanadiyyar fadawarka halin da kake ciki ayanzu fa wata zuciya tace dani...... ****** ****** ****** ***** ******** ************** Ranar Talata ranar farin ciki ce agaremu. Tun da asussuba yan fursuna keta hargowa nikuwa zuciyata cike da tunanin irin sabuwar rayuwar da zan ginawa kaina. Gabana ya danyi ras. Haryanzu dai bata sauya zani ba. Ana nan dai gidan jiya. Koda yake zama da talauci dai yafi kwanciyar hankali fiyeda zamana anan. Abinda yafi damuna ayanzu shine koda nafita sabuwar duniyar da nake shirin komawa ayau toda wahala na kasance cikin jin dadin rayuwa domin nasan ko aiki na nema da wahala na samu amatsayina na gwanjon fursuna. Ban karasa tunanin ba sai akayi kiran mu sannan aka bamu izinin yin wanka ga duk wanda ke so. Nan da nan wasu daga cikin yan fursunan suka tube atake anan sararin subhanahu wata'ala suna wankansu basu ko damu da su boye tsaraicinsu ba. Karfe bakwai na safe daidai aka bude wani tangamemen daki wanda ke dauke da tulin tsummokaran fursunonin dake gidan sannan aka bada izinin kowa yashiga ya duba nasa. Wasu da dama sukayi ta daukar kayan wasu suna sawa. Nayi sororo atsaye zuciyata nata wasi wasi nasan koda naga nawa kayan bazasuyi min wani amfani ba domin duk sun kekkece tun lokacin da muka fafata dasu Ijakala. Adai lokacin ne wani gandiroba saurayi ya nufoni da farko gabana yafadi atsammanina za'ace an fasa afuwar da akayimin amma sabanin hakan sai naga yayi murmushi sannan yamiko min wata shudiyar jakar leda. Na karba cikin mamaki sannan gandiroban ya karkace ya zaro wata guntuwar takarda daga aljihunsa ya mikomin. Ajikinta anyi rubutu cikin siraran haruffa kamar haka. NAGODEWA ALLAH DAYA DAWO MIN DAKAI MASOYINA DUK DA YAKE NASAN KA TSANENI HAR YANZU NI INA NAN INA SONKA CIKIN ZUCIYATA. (SALMA) Jikina na rawa na bude jakar wando da rigane aciki dinkin shadda shudiya mai dogon ciki agabanta atake agurin na warware su sannan na dan boye abayan wani gini nasa kayan kamar ta auna ni sunyi min daidai. Bakwai da rabi daidai aka salllame mu saida na bari duk sun gama ficewa sannan na nufi kofar ahankali wani daga cikin dattijawan dake gadi a tangamemen kofar firsunan ya dubeni sannan yace ALLAH YA BADA SA'A KAJI DAN SAMARI. Allah ya kiyaye gaba na dube shi nace Amin Baba. Hasken ranar dake kokarin tasowa tsakiyar samaniya ya dan dallare min idona na daga tafukan hannuna ina kokarin kare idanuna adaidai lokacin ne to na hangota tana dagomin hannu da farko da nayi niyyar shareta amma sai wata zuciya tace dani tunda babu wanda yazo ya tareka me zai hana kaje? Tun kafin na karasa inda take ta nufo ni da sauri muka hadu ahanya sannan ta kama hannuna muka nufi zungureriyar motar dake gindin katuwar bishiryar dake daf da kofar gidan yarin. Ta budemin gidan gaba na shiga sannan ta zagaya ta hau kujerar direba ta tada motar sannan ta tuka muka fice daga farfajiyar gidan firsunan ahankali kamar masu tafiya akan hayaki. Farisu salma ta kira sunana a sanyaye haryanzu baka daina fushi dani ba ko? Ta tambayeni tambayar taso ta bani haushi. Na dago kai ahankali na dubeta itama ta dubeni naji zuciyata ta buga har yanzu tana nan da kyawunta kamar yadda nasanta shekara uku da suka shude atunanina har tafi da kyau. Na dauke kaina ina duban waje ta cikin tagar motar bayan yan mintuna sai salma ta dauke kan motar sannan tayi kwana muka bi dogon lungu sannan muka bulle akwanar da zata shiga har layin gidanmu nan salma ta tsaida motar. Tajuyo ahankali ta dubeni sannan tace Farisu ina son ka gane wani abu Wallahi idan baka daina fushi dani ba bansan yadda zanyi da rayuwata ba nayi shiru ina duban cikin layin mu daga inda muke ina iya hangen gidanmu ga mamakina sainaga an ruguje gidan ana sake masa fasali har an kusan kammalawa na kuma yi mamakin ganin cewa tuni leburori sun fito aiki duk da........ [3/16, 5:16 PM] Abubakar Saleh AlQuyraeme: BIRNIN SARAUNIYA 30 BOOK 2 KARSHE Nakuma yi mamakin ganin cewa tuni leburori sun fito aiki duk dayake kuwa sanyin safiya ce. Salma ta lura da kallon mamakin danakewa gidan sai naga tayi murmushi wannan shi ya tabbatar min da cewa ita tasa ake gyaran gidan. Salma ta dubeni sannan tace Dan Allah Farisu kayimin magana kona danji sanyi azuciyata wallahi farisu in ba aurena kayi ba banajin zan iya rayuwa begenka ya kamani awuya babu damar kwacewa. Ta danyi shiru na dan lokaci sannan taci gaba da cewa. Ka ceci rayuwata farisu idan kaki aurena karshen rayuwata yazo kenan nasan begenka ne zai kasheni. Idanunta sukayi rau rau sannan kwalla ta fara zuba akan kyawawan kumatun ta. Na dubeta kallo irin na ido da ido sannan nace da ita akaro na farko. NAWA ZAKI BIYANI? Ta dubeni cikin kaduwa sannan tace me kake nufi farisu? Abinda nake nufi shine miliyan nawa zaki biyani kafin na aureki na tambayeta haba farisu yanzu saina baka kudi zaka aureni baka kaunata ne? Nayi mata kallon hadarin kaji sannan nace kwarai kuwa sai kin biyani zan aureki in har kin damu dana aureki din to ki cikamin alkawarin da mukayi dake na miliyan uku kinsan fa haryanzu baki cika alkawarin ba ko kin cika nayi wuf na bude kofar motar kafin nagama fita saita rike hannuna. Kayi min rai Farisu dan Allah ka saurareni. Na fincike hannuna sannan nafice daga motar na nufi gida zuciyata na radadi. Farisu...... Ta kira sunana muryarta na rawa na juyo na dubeta ta kifa kanta akan mutukin motar tana kuka. Ban koma ba saina nufi gida bansake juyowa ba koda nake shiga saina tuna farkon haduwarmu da ita inda ta dafa hannuna da lallausan tafukan hannanunta sannan sautin sassanyar muryarta mai ratsa kashi da bargo ya sake dawowa zuciyata inda take cewa. BAZAKA FADA MIN SUNAN NAKA BA? Na kama kofar gidanmu zan shige amma ban iya hakan ba saidana juya na dubi inda Salma take. Adaidai lokacin ne naga ta tashi motar koda muka hada ido da ita saita dago min hannu taja motar ahankali ta fice daga layin ahankali. Na girgiza kaina cikin takaici ni kaina ba'a son raina nayi mata haka ba ga mamakina sai naji kwalla ta cika idona. SALMA na kira sunanta cikin zuciyata asanyaye. KARSHE... Nazir Adam Salih GA MAI SON CIGABAN LABARIN RAYUWAR MUTUM HUDU WATO * EL-MAHDI * HINDU * SALMA DAKUMA FARISU SAI YA NEMI.............. MUTUWAR KASKO. Nagode (NAS) VISIT www.aihausanovels.com.ng For More Novel. AIHAUSANOVELS is website consists of hausa novels note, the reason of launching this site is to Entetaint, Motivate and Educate our readers. We provided hausa novels of many type, Such Adventure, love, romance, fiction, non-fiction, mystry, fantasy, action e.t.c from hausa Authors We provided a new and old novels both softcopy and hardcopy from our Author with thier permission. AIHAUSANOVELS shafin yanar gizo ne wanda yake ɗauke da littattafan hausa, dalilin bude wannan shafin shine domin Kayatar masu karatu da kuma ilimantar da su. Mun samar da littattafan hausa na nau'uka daban-daban, kama daga littafin, soyayya, tatsuniya, almara, Hikayoyi, gyara kayanki (yadda mata zasu kula da kansu a gidan mijinsu) da dai sauransu, daga Marubutan hausa. An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels