_BINTUN BATUUL_ 001 _Ayshatuuu_ Top-notch season 3 *Somewhere around the Globe!* 1980s and there about! Tamkar me tafiya akan iska Haka ta fito daga dakin baccin nasu, kamar kiftawar idanu har ta isa wani daki dake can gefe da Wanda ta fito, tana zuwa ta murda door knob din, Wanda a take dakin ya bude, babu haske kasancewar tsakiyar dare ne, Kuma ta san da hannun ta ta kashe wutar, so hakan bai Bata mamaki ba, tana shiga ba tare da ta kunna wutar dakin ba ta karasa gaban gadon inda yaron yake kwance lullube da duvet, ta karasa har kafafun ta na hardewa gaban gadon, ko data yaye duvet din se ta samu Babu kowa a gadon illa pillows da aka jera, yayi kamar yaron ne a kwance, tayi saurin ja da baya tamkar wadda taga wani abu me tsoratar wa, sede hakan ne dai yaron baya Kan gadon da tayi coaxing din shi not long ago, tayi saurin bude wata kofar Dake dakin, tunanin ta ko toilet ya shiga, Amma wayam Babu kowa, abun ya Soma firgita ta, tunanin ta ya Fara Zama gaske, ta fito daga dakin cikin wani yanayi me firgitar wa, sede ko Ina idan ta duba Babu trace ko daya na yaron balle na uban yaro, ta tsugunna a tsakiyar parlon wani kuka Yana kubce mata, ta Fara yin shi Babu kakkautawa, tana Yi tana shesheka kamar zuciyar ta zata fito, wani irin tsoro take ji Yana shigar ta... Kada fa ace sun dauke Mata Babyn ta? Se Kuma ta tuna ai kuka ma ba maslaha bane ba, ya kamata tayi making report ASAP Dan duk inda Imam yake to tabbas baiyi nisa ba, ta Mike zuwa inda wayar gidan ta landline take, ta dialing number cops, cikin mintuna se ga shi an Fara Mata magana cikin harshen larabci, itama cikin harshen larabcin tayi filing complaint din bacewar yaron nata, Suka tambaye ta address nan ma ta fada musu, Suka tabbatar Mata zuwan su ba da jimawa ba! Ko da ta sauke wayar se ta Kuma sakin kuka, abin da Imam ya kulla kenan shiyasa yazo out of nowhere? Dama zuwa yayi ya tafi da yaron shi da ya manta shekara da shekaru? Ta Kara fashewa da kuka lokacin da ta daga idanun ta ta sauke Kan katon hoton shi Dake manne jikin bangon parlon, yaro ne kyakyawa, yayi kiba irin ta yaran da suke samun kulawa, ya daga hannun shi guda Yana sakin dariya, bakin  babu hakori ko daya amma dukda Haka idan ka kalla hoton zaka samu Kan ka da yin dariya ko Kuma murmushi! Har anan a durkushe cops suka same ta, bayan ta zauna sun Dan Yi bincike cikin gidan suka tabbatar da Babu shi fa yaron se Suka dawo Dan daukar statement din ta! Da farko dai ita din Yar Qatar ce, sunan ta Zainab, iyayen ta sun kasance musulmai Kuma larabawa kamar yadda muka San asalin Qatars! Ita din ma wanke hannu ka taba ce, kyakyawa Fara balarabiya, mahaifiyar ta ta rasu tun tana yarinya Kuma ta kasance ya daya tilo a wajen su, mahaifim ta shima ya rasu bayan ma ta Gama O level din ta. Ma'aikaci ne  a wani babban company cikin kasar, ranar da rasuwar tashi ta kasance,  Zainab ta fada Masa tana son cin abincin dare tare da shi, hakan yasa yayi ta kokarin kammalla aikin office dan cika Mata alkawari Amma aiki se ya Sha Kan shi, ya kasa fitowa sallar maghrib,  se a office yayi, ita Kuma tun da yace ta zaba masu top restaurant, ta riga da ta isa wajen har ta bada order kafin mahaifin nata ya karaso, a banagaren shi ya kammalla komai ya Mike tare da daukar wasu takaddu Dan zuwa ya samu tilon diyar tashi, Amma yana zuwa kofar da zai bude ya fita se kawai ya yanke jikin shi ya fadi, daga wannan faduwar bai sake shurawa ba Rai yayi halin shi! Shiru shiru har karfe Tara da wani abu Zainab na jiran mahaifin ta amma bai dawo ba, a lokacin ta tabbatar Babu lafiya, Dan Haka ta Mike ta fice zuwa wani nearby phone booth, ta Kira number office din shi sede Babu Wanda ya dauka, hakan ya sake tayar mata da hankali, kawai se ta kashe wayar ta nufi office din shi a mota, tana zuwa an fito da shi daga main building din company din akan stretcher, ga ma'aikatan da Basu tafi ba dukka suna alhinin abin da ya faru da Mr. Fahad!                               *** "Bintu! Bintu!!" Na Dan mikar da hannu na tare da kwankwasa kofar bayin Wai dan na fada musu Ina toilet, Amma hakan da nayi se ji nayi " Ke Bintu wai dama tuntuni kina toilet? Kina ji Ina ta babatu akan ki, to Mamaa ke Kiran ki se ki fito" Ban ce komai ba, na cigaba da abin da nake, ni nasan ko Ina nake zaayi min uzuri tunda a toilet nake, seda na kammalla na fito na tarar dakin Babu kowa sannan na fita zuwa dakin Mamaa, tana zaune saman gado ta baza atamfofi Wanda take siyarwa, inaga tana sorting din su according to kudin su ne. Nayi sallama a hankali na shiga, ba tare da ta dago ba tace " Bintu Ina kike tuntuni nake neman ki?" Nace " Mamaa Ina toilet!" Ta dago ta kalle ni na Dan lokaci kafin tace " Suleiman na parlor, ki gyara shigar ki kije ki Kai musu ruwa!" Nayi shiru Ina kallon Mamaa, Ina Kuma son tabbatar da abin da take fada, ya zanyi Wai nayi hakan? Ya zaayi Rana tsaka ace wai na Fara soyayya da Suleiman? Ya ma zaayi Haka? " Baki ji abin da nace ba ne ba?" Ta fada muryar ta na Dan dagawa, ban ce komai ba na juya a hankali na koma dakin da na fito daga ciki! Na tsaya gaban mirror Ina kallon Kai na, wani boubou style material ne a jiki na, color din shi me duhu ne Wanda ya sake saka fata ta tayi duhu, fuska ta duk kuraje ne saman ta wanda tun da na Kai puberty nake fama dasu, ni ko kadan bani cikin sahun Mata masu kyau, shiyasa nake da low self-esteem, bana son shiga cikin mutane ko kadan, bani da confidence, a kusan komai na rayuwa ni ce karshe. Ba tare da nayi adjusting shigar tawa ba, na dakko katon hijab na kima akan boubou din, Wanda ya sake fito da kibar da nake da ita, ban ko damu ba na nufi kofa Dan fita, se mukai kicibis da Batuul Dake kokarin shigowa, nasan an turo ta taga me nake har yanzun ban fito ba, ta kalle ni tana bude Baki in exclamation " Bintu! Ba dai a Haka Zaki je wajen shi ba? Kin ganki kuwa?" Na kalle ta Ina Kara Shan kunu, Amma cikin zuciya ta da jiki na tamkar an sassare min gwiwa Haka naji, " Ki koma ki danyi touching fuskar ki, ki canja Kaya. Amma wannan ai se yaga kamar..." Kafin ta karasa na bude Baki na nace " Se yaga kamar me? Kamar giwa? Ko kamar bull?" Se tayi shiru ta kasa fadin komai, ganin har idanu na sun Fara cikowa da kwalla, na gyada Kai in annoyance na bi gefen ta na wuce, wani irin radadi nake ji cikin zuciya ta, Wanda ba lallai wani ya fahimci yadda nake ji ba, ko da naje kitchen se da na danyi kuka kafin na samu zuciya ta ta huce! "Wai Kai Suleiman zaman me muke har yanzun anan?" Wannan shi ne abin da na Fara jiyowa lokacin da na nufi parlon, na ja na tsaya Ina kokarin daidai ta yanayi na kafin na shiga "Nima dai abin da na gani kenan, since ba zasu baka Batuul ba, to me kake jira" Dan kada su Fadi wani abun yasa nayi saurin summoning courage na shiga, da sallama a Baki na, dukkan su Suka dago idanu Suka zuba min Wanda yasa naji kamar na koma da baya, Amma Babu yadda zanyi na riga da na shiga. Na aje tray din hannu na sannan cikin rashin kuzari da kasa da murya na gaishe su, Suka amsa Amma ko kadan na kasa daga idanu na na kalle su, saboda gani nake dukkan su suna iya hango munin fuskata! Shiru na wajen mintina hudu kafin na Mike na dubi Suleiman a Karo na farko tun shigowa ta wajen, Sanye yake da men lace coffee da zare milk, Kan shi da hula wadda ta Kara fito da shigar ta shi, na Dan Yi ajiyar zuciya nace " Allah ya kiyaye hanya!" Ba tare da na jira sun amsa ba na Kama hanya ta Dan komawa daki, sede Ina barin wajen naji daya daga ciki yace " Sule! Wai wannan golf din zaka aura?" Yadda yake dariya, yadda dariyar take shiga kunnuwa na tana sauka a zuciya ta tare da piercing zuciyar, ba Wai nayi niyyar tsayawa bane ba, kawai dai kafafu na ne Suka tsaya Dan Kan su, "Ba kada kirki Fahad, Wai golf?!" Shima dariyar shakiyancin yake irin ta abokin shi, wannan karon se naji zuciya ta tamkar yayyaga ta ake in pieces, kafin a Kara fadin abin da zanyi shekaru Yana hunting zuciya ta, Naga gwara naja kafafu na kawai na tafi. Aikuwa Ina zuwa daki na fada gado Ina sakin kuka.... Taku har kullum Ayshatuuu Shin kina da labarin wannan karon ma tafiyar ta top-notch ce? Season 3 ake magana na shatuuu, me dambu da Kuma Aziza! Me kike jira 'yar uwa? N1300 kacal Zaki mallaki NAZNEEN, BINTUN BATUUL  da Kuma GEN. NASIR ZAKI! [1/3, 20:27] Maman: _BINTUN BATUUL_ Top-notch season 3 Ayshatuuu 003 Ban Kara sanin me yake faruwa ba, ko waye a kaina ba, I loss consciousness abin da ban taba Yi ba a rayuwar, gaba daya ajin har shi Dr Akram din Suka taho Kai na, gashi Ni kadai ce mace duk ajin, tun a shekarar farkon mu wasu suka canja department, wasu aka tilasta musu, a Haka nayi surviving ni daya, dama bamu da yawa da muka fara, dukkan mu matan mu shida ne kawai. Yana karasowa inda nake kwance, Wanda suke kusa dani a zaune, already sun baibaye ni, Yana zuwa Babu hesitation kawai ya taba fuskata da hannuwa na, gumin ya daina se sanyi da jiki na yayi kamar mataciyya, flashlight din wayar shi yasa ya haska kwayar idanu na, ganin ta yi dilating, wato ta Kara budewa ya saki ajiyar zuciya, tare da kallon sauran Yan class yace " Who's the class president?" Alamin ya daga hannun shi, cikin sauri ya wulla Masa key din motar shi ya fada Masa model din ta sannan yace " Idan ka bude ta, a backseat akwai wata bakar jaka, in 30 seconds nake so ka kawo min" A guje ya fita, Ema ya bi bayan shi, Basu Sha wahala ba se gashi Ema ya dawo da Jakar shi Kuma Alamin ya tsaya locking motar, wata na'ura Yar karama ya Ciro, ya zura wani strip a ciki, sannan yasa allura ya caka hannu na, a take jini ya bayyana, ya disa a strip din sannan ya jira har na'urar tayi reading, kowa se kallon shi yake in amazement, kadan ne Suka fahimci abin da yake yi, Wanda ko ni da idanu na biyu bana tunanin Zan gane me akeyi. " 1.8?!" Ya fada bayan numbers din sun watso a jikin screen din na'urar, fadar da yayi kamar me tambaya kamar me mamaki, suna tsaye ya saka min ruwa Wanda kafin 50mls su Shiga jiki na, na Fara kokarin bude idanu na, tare da kokarin tashi na zauna amma ya dakatar dani ta hanyar fadin " Be calming down! Ki Kara hutawa!" Ya fada Yana mikewa tare da komawa gaban podium, Wanda hakan ya tilasta ma sauran colleagues di na komawa wajen su. Cikin kwarewa da iya koyarwa ya cigaba da exploring din mu cikin course din, yana bayani Yana rubutawa akan farin allon Dake gaban shi, Sanin jiki na ba shi da kwarin da Zan iya rubutu se kawai na kunna recorder din waya ta dan ta nadar min bayanai. Bayan kamar awa ruwan da yake Shiga jiki na ya kare, kafin nayi Masa magana yazo ya cire min, Bai Kara minti na talatin ba ya Mana sallama ya fice! " Bintu azumi kike Yi?" Alamin ya tambaye ni, na girgiza Kai na nace " Ko daya! Abinci ne ban ci ba" Ya Bata Rai tare da tambayar " Me yasa? Me Zaki ci?" Nayi murmushi Ina gyara Zama na nace " Kawai bana Jin cin komai ne!" Yayi shiru Yana kallo na na Dan lokaci, Wanda yasa na takura nace " Alamin!" Yayi murmushi tare da mikewa ya fita, se ya zamana ni daya kawai na rage a cikin ajin. Nayi shiru deep in thought Ina ayyana dalilin halin da na Shiga dazun, ni dai a rayuwa ta ban taba Suma ba, ban taba fita a hayyaci na but what happened? Se Kuma na Zama curious akan lecturer da ya fita, waye shi? Is he a Doctor and an architect a lokaci daya? Kai hakan ba Mai yiwuwa bane ba... Shigowar Alamin tasa nayi snapping daga tunanin da nake, in da ya tashi nan ya koma ya zauna tare da aje ledar hannun shi a gaba na, " Nasan abinci ne Baki ci ba, Haka Dr Akram yace, Wai glucose din jikin ki ne yayi dropping!" Na kwalalo manyan idanu na waje nace " Likita ne? Amma me yasa yake koyar da mu?" Yayi dariya Yana bude min ledar da ya kawo, alala ce se coke me sanyi "Ko daya, kawai dai yasan abunne, PhD yake yanzun shiyasa Kika ji Dr Akram!' Na gyada Kai tare da Yi Masa godiya, ya tashi ya tafi Dan bari na naci abinci, na bude Coke din na Kai Baki na Ina ayyana to yaushe ne Zan rage kibar, gashi Ina son Fara slimming Kuma Haka kawai na Fara suma. A gajiye na fito daga faculty din mu, ni daya kamar kullum, na duba screen din wayata, biyar ta wuce sosae hakan yasa na hanzarta Fara tafiya Dan wucewa gida. Waya ta ta Fara ringing, na Dan dakata a gefen hanya, na dauka kiran " Maman Anum Ina wuni?" Daga dayan barin tace " Lafiya Lau Bintu, kin tashi a school?" Nasan wani aikin zata saka ni, nace " Eh yanzun nake fitowa!" "Yawwa, kinaji ki biya school din su Anum ki dakko su, ki wuce gida da su. Zan biyo na dauke su!" Na Kara Jin wata gajiya ta sakko min Amma Babu yadda Zan Yi nace " To!" Ban jira abin da zata ce min ba kawai na kashe wayar, Babu yadda zanyi Haka na tari me napep ya Kai ni school din yaran, kusan su kadai suka rage baa dauke su ba, suna gani na Ahlam yace " Ina Mama? Me yasa Kika zo?' Ko kula shi banyi ba, nayi signing sannan na dube su nace " Baku iya gaisuwa ba ko?" Anum ta gaishe ni Amma Ahlam se Bata fuska yake, na tafi da su gida, Muna Shiga suka wuce wajen Mamaa ni Kuma na wuce daki na. Ban Kara saka su a idanu na na se da naji muryar Maman su a parlor, na fito Ina sanye da hijab, tana zaune da su Mamaa har da Adda ma, yaran duk sun baibaye ta, daga shigar Dake jikin ta ya tabbatar min biki taje, na zauna na gaishe ta Amma maimakon ta amsa se ta Fara fadin " Dan Allah Bintu yaran nan kiga ko Kaya baa canja musu ba, haba Bintu ke kuwa!" Na kallo yaran sannan na kalle ta Amma bance uffan ba, maimakon tayi min godiya Akan wahalar dakko su day nayi, shi ne tazo take korafi, to Haka kusan dukka Yan gidan mu suke, in dai aikin wahala ne to Ni zasu saka, Amma babu godiya da Kuma zarar an Dan kuskure shikenan se korafi. Adda da se lokacin tayi magana tace " Suleiman zai zo anjima ki shirya!' Na kalle ta Ina marairaice fuska nace " Ayya Adda wallahi na gaji, banyi karatu ba yau dukka, Kuma na karba order shawarma. Beside Ni gaskiya bana son shi" Maman Anum ta dube ni tace " Ban gane Baki son shi ba, ke har option ne dake dama?" Se na kalle ta da rashin fahimtar abin da take fada, nace " Kowa ai Yana da option din ya kawo Wanda yake so, ni me yasa ake denying min wannan right din?" "Tun da kike waye ya taba zuwa gidannan da sunan Yana son ki?..." Kafin ta karasa kawai se na Mike Dan komawa daki, bansan meye amfanin Adda ba Dake wajen, na rasa gane dalilin da yasa iyayen mu ke kasa depending din mu irin wannan. Ko Dana koma daki se naji na Kara tsanar Kai na da rayuwa ta, na duba mudubi Wanda a kullum nakan kalli Kai na kamar sau goma Naga ta inda Zan Fara rage wannan fat din Dake jiki na, kilan shi ne dalilin da yasa kowa baya so na, shi yasa kowa yake kallo na kamar wata kasakantaciyya. Har karfe biyu na dare idanu na Basu runtsa ba, Ina zaune saman gado na wayata a hannu na Ina duba online methods na rage kiba,  da farko Naga akwai dieting, akwai pills akwai Kuma tea, na kudiri aniyar da gaske wannan karon ko zam mutu se na rame, no matter what! Na zata abun me sauki ne, na zata idan na rame na Zama Yar caras Zan tsira daga bakin mutane, Ashe ko Mai kayi ba zaka taba tsira daga bakin mutane ba, ba zaka taba burge su ba Kuma ba zasu fasa magana ba! To be continued... Top-notch season 3! Kun Yi subscribing kuwa? Ko har yanzun? To ku tuntube mu ta wannan number 09063467258 [1/3, 20:27] Maman: _BINTUN BATUUL_ Top-notch season 3 Ayshatuuu 002 Na Jima akan gadon Ina Jin amsa kuwwar Kira na da golf da abokin shi yayi, me yasa mutane suke min haka? Why am I being criticized akan abin da bani da power Akan shi? Shigowar Batuul yasa na dawo daga tunanin da nake, ta zauna gefe na tana bi na da kallo, Batuul kyakyawa ce, kamar ta daya da Adda akasin ni da zakuyi mistaken dina for Yar riko. "Bintu ya kikai da Suleiman?" Ta tambaya tana bani dukkan attention din ta, na kalle ta da kyau amma bance Mata komai ba, " Matsala ta Dake kenan, Ina Miki magana kiyi min banza!" "Ki Kira shi ki tambaye shi Mana!" Na fada Ina kokarin janyo handouts dita ta intro to landscape design, tana ganin Haka tayi saurin dauke shi saboda tafi kusa da bedside table din akai na, haushi ya Kama ni Akan Wanda already nake ji " Ai nasan da shi nake tambayar ki, Kinga Bintu kowa na kokari akan ki, duk abin da ake yi Dan ke akeyi..." Na daga Mata hannu Ina fadin " Batuul Dan Allah ki tafi, ki rabu da ni, ki kyale ni" Ina fadin Haka na warci handout din da ke hannun ta na bude na Fara karantawa, wani Abu Dani inada determination, idan na dage akan Abu mussamman karatu, to zaku ga nasara ta same ni cikin hukuncin Allah! Asali bani da kokari ko kadan, I'm always last a ajin mu, saboda yadda suke min akan rashin kokarin hakan yasa na dage na Kuma daura damara, se gashi nayi succeeding, dukda hakan Bai saka anyi acknowledging di na da kyau ba. Ba Wanda ya sake bi ta Kai na, se bayan maghrib, na idar da sallah na wuce kitchen Dan zuba abinci, rabo na da na ci tun breakfast din safe, anan mukai kicibis da Adda, ban masan ta dawo ba. Na gaishe ta Ina fadin " Adda sannu da zuwa!" "Yawwa Bintu, tun dazun kina Ina?" Na gyara tsayuwa ta Ina karbar yoghurt din hannun ta nace " Ina daki!" Aikuwa se ta Fara sababi " Ke kam kullum kina daki? Baki da gurin Zama se daki? Wai ke wacce irin yarinya ce?" Nayi shiru Ina tunanin to menene laifi na anan? Yawo ake so na tafi ko mene? " Karatu nake Adda! Kiyi hakuri" Na fada Ina Ciro Mata tumbler daga inda ake adana su, ta amsa ba tace min komai ba tayi ficewar ta. Ban koma ta kanta ba na zuba abinci dai dai yadda zai ishe ni cikin plate, Amma kafin na dakko spoon town crier gidan, wato Batula Fatima Hamisu Ginsau ta Fara kwala min Kira "Bintu Fatima Hamisu Ginsau!" Na aje plate din hannu na Ina kokarin fitowa, Alawiyya me Mana aiki ta shigo tana fadin "Wani yazo karbar cake a waje uwar daki na!" Tana daya daga cikin Wanda ban hada komai da su na jini ba, Amma suna mutunta ni. " Wayyo na manta, Kuma tun dazun ya Kira ni! Bari na Baki Dan Allah ki Mika Masa!" Ta amsa ni da to, ni Kuma na wuce nayi packaging eight inches fondant cake, se da ta fita kafin na tafi Kiran da ake yimin. A parlon Adda na same su dukka, na gaishe su sannan na zauna bayan Mamaa tace min na zauna " Ya kukai da Suleiman?" Kuma Kan ku nasan Kun gaji da karanta sunan Suleiman dinnan, balle ni Kuma da ake tambaya, for God sake magana Bata karewa a gidan nan ko menene? " Wanne tambaya kike Mata haka Mamaa? Bayan shi Suleiman ya riga da ya fada Mana abin da tayi Masa!" Adda ta fada kamar zata Kai min duka, na sunkuyar da Kai na, Ina ayyana ko wanne irin sharri yayi min a wajen su? Allah masani " Duk abin da ake yi ba Dan ke akeyi ba, ba kokari ake aga yadda kuka tashi tare da Batuul ba tayi aure ta barki ba, shi ne Zaki musu rashin arzikin naki ko?" Nanma bance uffan ba, hakan ya Kara hasala ta, ta cigaba da yimin fada kamar zata ari baki, se da ta gama sannan nace " Adda, Mamaa kuyi hakuri. Bana son shi, saboda Bai dace ace tsohon saurayin Batuul ni Kuma na koma Kan shi ba." " Ke Zaki ce ga abin da ya dace, idan an barki wa zai ce Yana son ki, fuska fal kuraje da munin ki a gurin, ke ba jiki me kyau ba!!" Wani irin dagowa nayi unconsciously, na tsira Mata idanuna da Suka kada lokaci daya sukai ja, wani irin Abu nake ji cikin zuciya ta Yana taso min, a hankali naji trickle din hawaye akan kunci na, kawai se Naga ta cije bakin ta, alamar subul da baka tayi, but who even cares? Mamaa tayi shiru tare da sunkuyar da kanta, " Na tafi?" Na fada in between sobs, Kai kawai ta gyada min, na Mike na wuce daki na, na fada Kan gado, na Fara tambayar Kai na " Menene laifi na? Me yasa ake criticizing di na akan abin da bani da iko akai? Menene kyau? Menene Muni? Ko dai akwai wata alfarma da kyawawa daa Kuma farare masu kyan jiki da suke samu, yayin da muke rasawa?" Na Jima a kwance Ina tunani kafin Kuma nayi sallar ishai na koma Kan karatu. Washegari na tashi kamar mayunwa ciya, Amma saboda wani Abu da na darsawa zuciya ta cewar ni fa se nayi slimming ko da Zan dai na cin abinci ne gaba daya, ban nema abinci ba nayi wanka na shirya cikin atamfa zani da Riga, na dakko hijab na saka sannan na dauki jaka ta na fita dakin kawu! Yana zaune Yana sauraren radio freedom nayi sallama, ya amsa Yana Dan adjusting volume din radio, muka gaisa yace " Se makaranta?" Na amsa da eh, yayi min addua kamar kullum sannan na tafi wajen Adda, ta gama shirin tafiya office, tun abun jiya da ya faru bamu sake haduwa ba, dukda ba karon farko da ta Fadi hakan ba, wani lokacin you can mistaken her for ruko na takeyi! "Adda Ina kwana?" " Lafiya Lau Bintu? How was your night?" Na amsa da alhamdulillah, sannan na juya Zan fita se tace min " Jira na sauke ki a makaranta" Kamar zanyi musu se Kuma nace Mata to Amma Bari na gaida Mamaa, na wuce dakin ta tana zaune tana karatun qurani, gani na yasa ta rufe tare da min murmushi tace " Bintu an shirya?" Na zauna sannan na amsa ta, na gaishe ta ta amsa tayi min adduar kullum kafin tace " Nasan Suleiman Karya yake abin da ya fada, ki rabu da shi, kina zaune Allah zai kawo Miki naki mijin" Hakan da ta fada se ya dada min Rai na, naji sanyi cikin zuciya ta, har bansan nayi murmushi ba, daidai shigowar Adda, suka gaisa da Mamaa sannan sukai sallama na mike na bi bayanta, se da tayi warming motar sannan Muka tafi, da farko tafiyar shiru Babu wanda yake magana cikin mu, se can ta Dan rage volume din speakers din motar, " Bintu akwai abin da yake damun ki?" Na Dan kalle ta kafin na girgiza Kai na bance komai ba, " Kinsan bana son shiru ko? Idan nayi magana Nafi son ki min magana" Nayi saurin bata hakuri Dan Adda na da temper, nace " Ba komai Adda!" " Then me yasa Baki sakin jiki da kowa a gida? Kin maida kanki kamar wata bare" To me Zan ce mata? bayan su Suka maida ni hakan, su suka Fara nuna min kamar I doesn't belong to them, dole na janye jiki na. Jin nayi shiru se Bata Kara cewa komai ba, se da ta sauke ni gaban faculty sannan ta ciro kudi cikin Jakarta ta miko min, na girgiza Kai na nace " Kawu ya bani kudi" " Na kawu daban nawa daban, karba joor!" Haka na saka hannu na karba, tayi murmushi mukai sallama, a hankali na sauka zuwa class dina mu, kamar kullum Ina cikin biyar din farko da suke zuwa da wuri. Na samu seat na zauna na dakko waya ta Ina sake duba timetable din ranar saboda semester Bata Jima da farawa ba, ban Gama haddace yadda schedules din suke ba! A hankali ya aje pen din hannun shi bayan ya duba agogon dake hannun shi, karfe takwas saura mintina goma, yasan Yana da class dole ya bar aikin dake gaban shi, wannan ne karon farko da zai Shiga ajin, hakan ya faru saboda sati biyu baya gari, ya dauka suit din Shi ya daura saman sky blue long sleeve din rigar shi, Ya dauki takardun shi sannan ya fita, mintina biyar Suka kawo shi class din mu, Yana shigowa ya tsaya Kan podium tare da gyara zaman glasses idanun shi, dukkan mu muka bada hankali Dan fahimtar abin da zai koyar. " I'm Akram Imam, I'll be guiding you on design process in Architecture!" Dukka Muka bada hankali, cikin turanci yake magana, Amma Haka kurum se nake Jim kamar a nesa nake Jin muryar ta shi, idan na dago na kalle shi se na ga Yana yin dishi dishi, na runtse idanu na Ina ayyana abin da yake faruwa da ni all of a sudden, se kawai na daina ji gaba daya, idanuna Suka Fara daukewa duk yadda nake kokarin bude su, wani irin yanayi ne me wuyar na fada muku, gumu ya jika ni sharkaf, kwace ruwa aka zuba min. Inata battling da idanu na, Naga alamar sakkowar shi Yana tahowa, na Fara kokarin composing Kai na Amma Abu yaci tura.... BINTUN BATUUL ba kyauta bane ba, na kudi. Tafiyar ba Ni kadai bace ba, tafiyar top-notch ce a Karo na uku, wannan karon Aziza tana tafe da GENERAL NASEER ZAKI, yayin da Anty Ramla ta kawo muku NAZNEEN duk akan N1500 kacal. Ki biyo mu ki Sha labari [1/3, 20:27] Maman: _BINTUN BATUUL_ 004 Ayshatuuu Top-notch season 3 Da farko dai sunana Bintu, a gidan mu na Zama tamkar wata shadow ce, wato idan nace shadow Ina nufin Inuwa, shi ne dalilin da Kai tsaye baa Kira na Bintu, sede ace BINTUN BATUUL. Da farko ban gane hakan ba se daga baya da nayi wayo na gane dalilin Kira na da hakan. Kamar yadda kuka sani, a kasar mu ta gado, wato kasar Nigeria mu nada arewaci da Kuma kudancin kasar, mu din Yan arewa ne Kuma arewar ma north west, wato arewa maso yamma. Da bana gane wannan intersection din se a hankali na Fara fahimtar yadda suke da Kuma me suke nufi. A jahar jigawa akwai wani daddaden gari me tarin tarihi, wanda ake tunanin suna daya daga cikin Hausa bakwai, wannan gari masarauta ce cikin daya daga cikin masarautu biyar da suke a garin na jigawa. Wannan garin kuwa shi ne Hadejia ginsau birnin Doki.  Kamar yadda kowanne gari zaka ga Allah ya hallitta musu irin mutane, yaren su da Kuma abincin su, ways of living, norms din su day values din su, to Suma a Hadejia suna da wannan! Na farko dai idan ka fiye Baki a jigawa we consider you Bahadeje (No offense, this is the reality) Yan garin bakake ne, saboda suna da asali da barebari, Amma Kuma akwai farare tunda ana samun auratayya tana hada su day wasu! Akwai Kuma miyar kuka, ban sani ba ko sune founders din miyar kuka, Amma mu a jigawa kirarin da ake ma kuka is always "Bahadejiya kin fi giya tsiya" Wai kuka fa ake cewa Haka, gaskiya justice for miyar kuka....lol Suna da ruwa,  shiyasa suke da kifi, garin Hadejia akwai kifi akwai Kuma ruwa, I remembered duk shekara Kawu zai ce ya tafi Yi musu jaje, either flooding ko Kuma garin is about to flood. Haka dai maganar take. Mahaifi na Dan asalin Hadejia na, tun daga mahaifiyar shi har mahaifin shi, tun mahaifi na Yana karami Allah yayi Masa son fararen mata, hajja tana yawan fada Mana ko bakuwa akai in dai Fara ce, to ko an aike shi sai saa zai je, da ya Fara girma kuwa kusan duk wadda ya gani Fara se yasan yadda yayi yayi Mata magana, se Kuma yasan yadda yayi ta kula shi ya Fara zuwa gidan su. Wannan shi ne mahaifi na!! Bansan me yasa maimakon Baba ko Kuma Abba ko ka Daddy, da ywanacin ake Kiran iyaye mu a gidan mu Kawu muke cewa, Haka muka tashi muka hi sauran yayin mu na Kiran shi muma Kuma muka dauka. Asalin sunan mahaifi na Hamisu, mutum ne dogo da Kuma jiki, irin mutanen nan da ake Kira da giant, Kuma Baki ne sosae, Dan kuwa Bai bar gida ba. Labarin da na Baku na rashin son bakaken Mata yasa yake da nacin nema, tun da mahaifiyar shi tace Masa ai fararen Mata masu kyau tsada ne da su, shikenan ta birkita wannan bawan Allah, karatu yayi na primary anan cikin Hadejia, kafin da ya Gama ya taho minjibir yayi makarantar maza ta karamar secondary! Da ya kammalla se ya dawo nan tsohuwar makaranta me cike da tarihi wato Rumfa college da ke cikin birnin na Kano. Anan Yana zaune gidan wani kanin mahaifin shi Kawu Sabaru, daga can yake Hawa Keke yaje makaranta, idan aka tashi ya cire uniform ya kulle a Leda ya tafi kasuwa inda nan ne yake yaron shago cikin kasuwar kwari, idan yamma tayi Kuma ya tuko Keke ya dawo gida. Yana ta fama har Allah ya nufe shi da kammalla secondary School, kamar ba zai cigaba ba Amma uban shagon ya nuna masa muhimmanci da yake gani a tattare da karatun Boko, cikin saa da kullum yake fada, Yana Kuma alfahari da shi din me sa'a ne a rayuwar shi. Ya samu gurbin karatu nan cikin bayero University, dukda Haka Yana kasuwancin shi, Yana Kuma yin taro yadda Baku tunani, a kwana a tashi , karatun shi yayi nisa haka ma kasuwan cin shi, mahaifin shi ya aike Masa da sakon komawa gida Dan an zaba Masa Mata. Kunsan dai ya Riga da yayi alkawarin mace in dai baka ce to Bata da gurbi a cikin gidan shi, Bai Yi musu ba ya tafi Hadejia Dan ganin Mata, Yana zuwa ya tarar da Yar kanin baban shi ce Salamatu, shi yarinyar saboda bakin ta ko magana ba yayi Mata, kuji fa gwano baijin warin jikin shi, shi ma da bakin ne. Ya nunawa mahaifin shi rashin son auren Amma mahaifin shi yace Babu fashi, shikuwa ya tattara na shi ya nashi ya dawo Kano ya cigaba da sabgar shi, aka daura aure kamar yadda aka saka rana, Amma ango har amarya tayi wata guda Babu shi Babu dalilin shi, Haka mahaifin shi ya dakko Salamatu ya taho da ita Kano, ya aje Masa ita dakin shi na zaure Dake gidan Kawu Sabaru. Se dare ya dawo kamar kullum, da bredi na kullum da yake tahowa da shi da Kuma alawa saboda Yara. Yana zuwa ya shiga dakin shi Kamar yadda ya saba, ya cire Kaya ya fito zuwa wani shago Dake makwabtan su yayi wanka sannan ya dawo, se da ya saka Kaya sannan ya lura da dankwali an kulle Kaya da shi, ya saka kafa ya shura dankwalin se Kuma ya dauki biredi da sauran kayan shi yayi cikin gida, Jin sallamar shi yaran Suka taho da gudu, dukda ba kula su yake can sosae ba, Amma dai Yana Basu alawa, shi Kuma alkhairi Yana saka mutum ya Shiga ran Wanda yake bawa, shiyasa kayi kokarin ganin ka kyautatawa mutane. Ya Mika musu ledar alawar su, sannan ya bawa babbar biredi Dan ta kaiwa mahaifiyar su, anan zaune yayi Ido hudu da Salamatu,  da taimakon aci balbal din Dake gaban ta wadda aka kunna Dan ta haska gidan, ya Bata fuska Yana ayyana wannan mayyar har nan ta biyo shi ko ko me? Suna gaisawa da Inna talatu matar Kawu Sabaru, se ga Kawu Sabarun ya shigo, Suka gaisa da Kawu Dake kokarin juyawa Amma Kawu Sabaru ya dakatar da shi, tabarma Salamatu ta shimfida musu Suka wanke hannu Suka ci tuwo tare, wannan cin tuwon tare implies alot, ya tabbatar akwai gagarumar magana a kasa Yana Kuma fata Bata danganci auren Salamatu ba, Dan kuwa ba zai aure ta ba, ba zai zauna da bakar mace marar wayewa irin ta ba. Idan Kuma suka matsa to gaskiya ba zai jure ba, zai bijire duk abin da zai faru ya faru, wannan shi ne  tunanin da yake yawo a cikin kwakwalwar Kawu. Bayan sun Gama cin tuwo an wanke hannu, Bayan Gama sude sude saboda Inna talatu ba dai girki ba, matar nan da ace a wannan zamanin take, to tabbas zata buge food content Creators da yawa! Cikin lallami, da Kuma tsara kalamai Kawu Sabaru yayi wa Kawu bayanin halin da ake ciki, na an Riga da fa an daura Masa aure da Salamatu, shi ne dalilin dawowar ta nan, ya kada Baki da fadin Kuma Yana son yayi hakuri ya zauna da matar shi lafiya su samu zuri'a dayyiba. Kawu da yake ta auna kalaman cikin Kan shi, like for real shi akaiwa auren Dole? Ko Kuma bashi Hamisun ba? To su wanne digimi ne ya kaisu entrusting Yar su gare shi, bayan he clearly said it, baya so, baya son ta ba Kuma zai aure ta ba. To fa cikin Abu biyu Dole zaayi daya, ko dai ayi Abu cikin lumana ko Kuma hatsaniya ta biyo baya domin shi dai Bata da space cikin rayuwar shi! " Kawu Sabaru, gaskiya maganar Allah bana son yarinyar can, bana kaunar ta ba Kuma Zan zauna da ita ba!" Kawu yayi saroro Yana kallon shi da mamaki a fuskar shi yace " To Hamisu waye yayi auren soyayya? Ai dukka Hadi akai Mana Kuma gashi mun manta cewa ba soyayya mukai ba! Ka da kake neman albarka..." "Wannan fa ya wuce Kawu! Ni na fadawa malam (mahaifin shi) ni ba Zan aure ta ba, saboda ni matar da Zan aura ba irin wannan suffar nake so ba" Mamaki ya Kara kama Kawu Sabaru, ai se ya Fara fada, ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, Amma wannan fadan Bai saka ya janye kalaman shi ba, Haka suka rabu baran baran, ya koma daki Yana ta pacing cikin tsukakkaen dakin Yana Kuma nemawa Kan shi mafita, a karshe se ji yayi an turo kofar an shigo, ya dago idanun shi Yana tunanin wanne isashen ne? Se gata a tsaye ta Sha lullubi Wanda ya Bata Masa Rai, maimakon Barin ta ta shigo se ya maida kofar ya barta a nan tsaye. A takaice kowa baccin bacin Rai yayi, kowa jira yake safiya tayi ya dauki mataki. Asuba nayi ya hade kayan shi tas saboda yasan idan ya aiwatar da abin da yayi niyya to tabbas zaman shi gidan Kawu Sabaru yazo karshe,shi Kuma saboda gurin Zama ba zai cuci rayuwar shi ba. Ana idar da sallah yayiwa Tasha tsinke ya hau mota se Hadejia, shima Kawu Sabaru Yana idar da sallah wanka ya dawo yayi a gida sannan ya dauki hanya se Hadejia! Ko da yaje gidan su ya wuce, ya samu mahaifin shi ya dawo daga su, wato kamun kifi saboda sanaar shi kenan, Bayan sun gaisa aka kawo Masa tuwon buski da miyar kuka, ya zauna yaci yayi hani'an kafin mahaifiyar shi ta Fara tambayar shi wajen su Inna talatu da Kuma amaryar ta shi? Lafiya kawai yace Mata sannan ya fice zuwa wajen baban shi, ya samu har Kawu Sabaru ya iso Kuma an Kira Kawu Mamman wato mahaifin Salamatu, dukka suna zaune suna sauraron abin da Kawu Sabaru yake fada musu. Ko dar baiji ba yaje ya zauna, malam ya Fara fada se Kawu Mamman ya dakatar da shi yace " Hamisu baka son Salamatu ko?" Ya gyada Kan shi, ba tare da yaji ounce of rashin dacewar abin da yayi ba "Bana son ta Baba, ban shirya aure ba. Ku gafarce ni, bana son zumunci ya lalace, ba Kuma nasan Bata muku, ko Kuma na zalunce ta shiyasa nazo nace muku ni na sawwake Mata igiyar aure na daya dake kanta idan ta samu miji tayi aure" Kun Yi subscribing top-notch season 3? To kada ku Bari NAZNEEN, BINTUN BATUUL da Kuma GEN NASIR ZAKI ya wuce ku. Wannan tafiyar daban take, labaran daban suke. N1300 for 3, N1000 for 2 and N500 for 1. [1/3, 20:27] Maman: BINTUN BATUUL Ayshatuuu Top-notch season 3 006 Ni fa ban yadda ace Wai wannan matar ba tada kishi ba, kowacce mace tana da kishi, Kuma tana da nata salon yadda take bayyana shi. Dan namiji yace zaiyi aure ba Wai Yana nufin ya gaji da ke ba, ko ya tsane ki ko Kuma irin kin kasa ta wani bangaren, it's a call they answer, raayi ne Haka Kuma yiwa mace kishiya a nawa ganin ba laifi bane ba, Amma dai a dinga kokarin yin adalci da Kuma gane concept din polygamy! A gani na laifi da akw shi ne path din da ake bi wajen auren da Kuma bayan auren, yadda wasu mazan ke muzgunawa matan gidan ko su wofantar da su, wannan shi ne laifi, Kuma Ina ganin abin da yawancin mu Mata muke tsoro kenan, kishiya Adda ta Kan ce tayi Dana sani tada hankali da dukkan abubuwan da tayi, idan da har tasan Mamaa ce kishiyar. Ni fa a gidan mu nake kasa banbance iyayen mu, su Adda suna da wani exceptional relationship tsakanin ta da Mamaa, shiyasa har zuciya ta bana ganin polygamy as a problem, rather wadan da suke cikin polygamy dinne masu matsala! Bari na fada muku Adda tayi balai, ta tada hankalin ta yadda Baku tunani, a ganinta wannan shi ne karshe, ta Yaya ma zaace Bata shekara biyar ba ayi Mata kishiya, akwai Rights din Kawu da ta daina saukewa, Wai ita tana fushi. A irin wannan lokacin, it's a crucial moment saboda aure zai iya mutuwa, idan namiji baiyi da gaske ba se kaga aure ya mutu. Lokacin da zaa yiwa Adda Sajida kishiya, akwai wani Abu da ta yiwa mijin ta Wanda se da ta dawo gida tayi zaman wata data, daga yace zaiyi aure Adda aka Fara throwing tantrums, zagi ta uwa ta uba, kishi dai na hauka, mutuminnan ya dauke idanun shi, lokacin harvest yayi ya kawo amfanin gona gida, mutuniyar ku tace to ita fa anan zatai ramuwa, ta dauki dawa ta hada da alkama, ridi da shinkafa, Kai Adda Sajida Bata da kirki, Dole se da ta dawo gida Amma Kuma mijin Bai sake ta ba, cewa yayi ta fitar Masa a gida ya daina ganin ta har se ya huce, to se da akai biki da sati uku amaryar har ta Zama Yar gari kafin uwargida Adda Sajida ta koma. To kunga hakan Bai Hana shi auren ba, se ma darajar ta da ya rage, Saboda maza basa uzuri akan kishi ko kada. Abin da ya karya lagon Adda shi ne zuwan Alhajin KT da Kuma Iya wato mahaifiyar ta, kunsan yadda iyayen da suke, mutane ne masu Kara da Kuma dattako, dukda a yanzun Ina ganin abin odd na goyawa mijin yata baya bayan nasan shi ne bashi da gaskiya, gaskiya bazan iya ba, dukda ance Wai hakan shi ne siya ma Dan naka daraja a gidan aure, this is all by the way! Alhajin KT da Iya sun Yi kokari matuka wajen tausar Adda, har ta samu ta Dan dangana Amma cikin zuciyar ta Bata tunanin rift din da aka samu tsakanin ta da Kawu Abu ne da zai cike, dadin dadawar bacin ran ta se Alhajin KT yayi uwa ya Kuma Yi makarbiya wajen ganin aurennan ya tafi, a karshe ma dai Wai shi ne walliyin Mamaa, ciwo goma da ashirin kenan! Aka kawo amarya dakin ta, kowa tausar Adda yake, tare da nuna Mata yadda zatai ta kwaci Kan ta, Amma da se idan ta rike wannan girman nata, idan ta Bari kuwa to zata kwace ita Kuma ta Zama Yar kallo, wasu Suka ce Mata duk namiji se yayi daukin amarya, se yayi rawar Kai se Kuma yayi falli, Amma idan uwargida tayi hakuri da zarar gishiri ya ishi Kan kaza to fa ungulu zata koma gidan ta na tsamiya, ai dama ance tsohuwar Zuma ita ke magani. (A soothing message to uwargidas' I'm rooting for you!) Dama bacci Kam dai rabi da rabi akai, kusan kwana tayi tana karatu Dan ya debe Mata kewa, Amma dukda haka amidst karatun zata kwanta tayi kuka ta godewa Allah, a Haka safiya tayi ta Mike jiki a sanyaye tayi wanka tayi sallah sannan kuma ta wuce kitchen ta daura sassaukan abinci kamar yadda Iya ta Nanata mata, tace Mata lallai lallai ta daure tayi girki ta Bata, shi ne girman, tana kammallawa ta koma daki ta zura fararen uniform din ta da suka Sha guga suka daukar idanu, a karshen hannun akwai lanyard na nuna ita din student ce, ta daura katon hijab akai da ya rufe Mata uniform din sannan ta dauki jakar ta Dan ficewa, sede tana kokarin kulle kofar parlon ta se ga Kawu ya nufo ta, da ta kalle shi se taga kamar Yana murmushi, kamar wani annuri ne ke exuding daga fuskar ta shi, taji kamar ta shake wuyan shi kowa ya huta, Amma se ta Fara Nanata auziyya Dan korar shaidan, ya karaso tare da karbar makullin da kulle Mata saboda battling da take tayi da shi ta kasa kullewa, saboda hankalin ta da Kuma tunanin ta dukka baya gurin, bayan ya rufe dakin ya Mika Mata makullin tare da amsa gaisuwar da ta Masa ciki ciki. Duk yadda Taki se da ya Kai ta har makaranta kamar yadda ya saba, sannan da ta tashi yaje ya dakko ta, lokacin da ta dawo Mamaa ta kammalla abinci, ta gyare gidan tsaf, tana daki tana sake sake. Se dare suka hadu yayi musu nasiha sosae tare da Yi musu alkawarin adalci. Da farko Adda Bata Shiga harkar Mamaa, ko abinci tayi se taki ci, Amma hakan Bai Hana Mamaa cigaba da kyautata Mata ba, a Haka har Adda bayan wajen watanni hudu ta fahimci sincerity din ta Kuma ga laulayi da ta Fara me ban wahala, Haka Adda ta yada makaman ta ta rungume ta, shikenan zaman lafiya se ya wanzu a gidan. Bayan watanni Adda ta Gama makaranta ta Kuma samu aiki cikin asibitin murtala Muhammad dake cikin kano, Fara zuwan ta Babu jimawa itama se ga ciki ya bayyana a jikin ta, lokacin na Mamaa wata wajen takwas. Kawu yayi murna kamar zai zauce, Mamaa ta Haifa mace aka saka Mata suna Fatima ana Kiran ta Haka, Bayan watanni Adda ma ta haihu aka saka Mata Fadima. Kunsan yadda Kawu ya dinga saka Mana suna Fatima se Dana Fara tunanin Anya kuwa bamu Hadi da shi'a? Yo Ina dalili mu kusan takwas suna daya, Fatima, Fadima, Sajida, Adawiyya, Zuhriyya, Zuhra, Zahra, Batuul da Kuma ni Bintu! Mu Tara kenan fa! To Haka sunan mu suke se maza guda uku Wanda yasa Auwal, Sani da Kuma Salis. Gidan mu kamar su kusan daya, farare Kuma kyawawa, sirara, dogaye. Yadda iyayen su Mata suke Haka Suma suke, kunsan it can't be a coincidence Dan akwai gidan da zakaje kaga kowa ya nada kyau, to gidan mu kenan, har alfahari suke da wannan kyan nasu! Bayan set din su Fatima da Fadima, se Kuma Mamaa ta Haifa Adda Sajida ita Kuma Adda ta haifa Yaya wato Auwal, tana aikin ta yayinda Mamaa ita ke zaune a gida, tamkar ministan cikin gida, komai indai na cikin gida ne to kada ma kaje wajen Adda kawai Mamaa ce komai. Mamaa ta sake haifan Yaya Adawiyya, ta sake haifan Yaya Zuhriyya se lokacin ita Kuma Adda ta haifa Yaya Sani, Mamaa ta haifi Zuhra, se Kuma sukai goyon Yaya Salis Wanda shi ne namiji kadai wajen Mamaa, Adda Kuma ta Haifa Zahra. Shikenan se haihuwan ya tsaya kamar daukewar ruwa, har su Yaya Zahra sukai shekara biyar abin da baa taba Yi ba a gidan, a yi shekara biyar Babu sabon jariri gidan. Lokacin Adda ta Gama BNSc din ta tana kokarin Fara masters se kawai ciki ya bullo a jikin ta, ta kance wannan cikin ba karamin katsalandan yayi Mata ba, saboda tana kokarin pursuing dream din ta se ga ciki ya fito, to ya zatayi? Haka ta hakura ta jira zuwa lokacin da zata haife abin da ke ciki. Ita Bata faye Shan wuya idan tana da ciki ba, Amma wannan karon Kam se cikin yazo da sabon salo, tun kafin first trimester ya wuce se ga bump ya fito Dan Haka kowa ya Fara tunanin kilan twin gestation ne, wato Yan biyu amma duk lokacin da taje hoton cikin se ya nuna guda daya ake gani, Dan Haka komai da aka siya na Batuul ne, Babu Wanda yasan da zuwa na saboda tun a ciki Batuul ta danne ni, ita kadai ake iya visualizing. Se da ta Fara nakuda aka kaita asibiti, tuntuni sunyi da Kawu wannan karon ma Fatima ce Babu fashi, se Yaya Fatima ta ce to dama bamu da Batuul Dan Haka se ace Mata Batuul. Wannan shi ne Shirin su, Bayan an haife ta Kuma se wani ciwo ya turnuke, ko da aka zo examination se akaji alamar wani Babyn Amma Kuma presenting part din ba Kai bane ba, maimakon a barta ta haihu se aka bada shawarar kawai ayi CS, Har a yanzun akwai Wanda suke ganin CS mutuwa ce balle a shekaru da dama da Suka gabata, hankulan kowa a tashe yake, Danna ita din nurse ce Amma Kuma family din ta fa? Haihuwa hudu kayi su lafiya har da wannan ta biyar Amma se a ta shida Abu ya gagara! Haka aka tafi da ita, Babu jimawa aka fito da ni sede baa Basu ba saboda Wai na sha ruwa banyi kuka ba, I've to go for another resuscitation, cikin hukuncin Allah kuwa se gashi Ina jin zafin heater na Fara kuka, Kuma jiki na ya koma pink yadda ake so. Su 'Yan biyu farin jini ne dasu sosae, musamman idan ba Kai ka Haifa ba, se kaji sun burge ka kana son ace naka ne, to Haka muma muke da wannan farin jinin, Amma yawanci Batuul ke da shi bani ba, Ni na kasance kamar wata shadow din ta! [1/3, 20:27] Maman: _BINTUN BATUUL_ 005 Top-notch season 3 Ayshatuuu Gaba daya sukai shiru suna jin abinda dan na su yake Yi, a ganin su diban albarka ce kawai wannan, a ganin su bokon da yake yi ita ce ta saka yake dukkan wannan abun, Amma a ciki Kawu Mamman ya fahimce shi, har ran shi ya Kuma ji Dadi,ban sani ba ko Dan kasancewar shi mahaifi ne ga Salamatu? Allah masani "Nagode sosae Hamisu, nagode da baka wulakanta min Diya ba ka dawo da ita da martabar ta, Ina maka fatan alkhairi a cikin rayuwar ka!" Kun fahimci abin da nake so ku fahimta? Shi Kawu Mamman he's grateful saboda lokacin da Kawu yaji Bai son Salamatu baiyi kasa a gwiwa ba yazo ya sanar musu, Bai wulakanta ta ba balle cutar da ita ba, da yake Yana da wayayyen Kai se gashi Bai ja maganar ba yazo ya dawo da auren. To bashi kadai bane ba, hatta malam mahaifin shi ya fahimce shi, Kawu Sabaru ne dai yake ta banbanmi, har da fada Masa kada ya sake taka kafar shi zuwa gidan shi, Wanda dama ko Bai fada ba Kawu Kam ya bar wannan dakin zauren. Bayam duk sun tafi, Malam yayi Masa fada sosae da sosae, ya nuna masa rashin dacewar abin da yayi, ya nuna masa illar rashin hakuri, a karshe ya Masa fatan alkhairi tare da bashi shawara akan rayuwa, ba tare da ko Innar shi yayiwa sallama ba, kawai ya dauki hanya ya koma Kano, Yana zuwa yayi sallama da Inna talatu ya tafi Dan Kama haya da Fara sabuwar rayuwa! Salamatu taji dacin mutuwar auren ta, tayi kuka marar iyaka Amma da taji zata cigaba da Zama Kano se hankalin ta ya kwanta, saboda tsoron komawa Hadejia ayi ta Yayata maganar. Shekara daya ta wuce da faruwar hakan, tun ana maganar ana kwashewa Hamisu albarka har aka manta, kunsan Haka Rai yake da mantuwa, itama Kuma se tayi aure nan a Kano shikenan se maganar ta sake mutuwa. Yayinda Kawu ke ta Fadi tashi wajen ganin ya nema na Kan shi, da adduar iyaye da yake yawan ziyarta Yana musu alkhairi dan ya goge laifin shi, ya kammalla karatun shi tas a BUK, ko aiki Bai tsaya nema ba ya cigaba da zuwa kasuwa, Allah ya nufe shi da siyar rumfa cikin kwari, ya Kuma Fara sayo Kaya Yana siyarwa, kwatsam se alkhairi da budi Suka ta ninkuwa se Kawu ya Zama Alhaji. Da fari ya saya fili da ake yankawa anan Yan kaba Dake Kan babban titin Hadejia road dake cikin Kano, a ganin shi nan din zaiyi kusa da daukar Hanya zuwa Hadejia, Ashe akwai ranar da zaa wayi gari a samu su sauna, dakata and the rest! A hankali yake ginin saboda shi mutum ne da ku kunsan Yana da high taste, komai Yana son ace nashi yafi na kowa, komai so yake ace nashi is outstanding. Karku manta fa da halayen shi nasan farar mace, Yana nan ba Wai ya canja bane ba, shi ne dalilin da ya Hana shi aure, Yana ta zuba idanu yaga kyakyawa Kuma Fara sannan siririya. Haka abokan da makwabtan shi na Rumfa a kasuwa zasui ta tsokanar shi Fara ko mayya ce! Sede yayi dariya kawai yace musu shi fa Abu me kyau yake so Bai wani zurfafa ba. Akwai wadanda ko me suke so se kaga Allah ya Basu akasin hakan, akwai Kuma wadanda Allah ke Basu dukkan abin da zuciyar su ta kwadaita masu. In that case Kawu na daya daga ciki, shiyasa yake ganin shi Mai sa'a ne shi. To mahaifiya mutuniyar jahar katsina ce, Amma idan Kika zauna da ita Zaki fahimci ba Yan asalin katsinar bane ba, in fact bama asalin Yan Nigeria bane ba, kawai dai sun hauro Kuma sun Jima har suka Fara aure da hayyayafa. Haduwar Kawu da Adda kamar yadda muke Kiran ta, a kasuwa ne, Bayan an idar da sallar azahar ya dawo shago, Yana fadawa daya daga cikin yaran sun je su siya Masa abinci gidan abincin da yake ci yunwa yake ji, Dan shi baya ma cin abincin da ake kawowa kasuwa, standard din shi ya wuce haka. Yana nan zaune kamar ance ya dago idanun shi, Yana daga idanu se cikin na Adda wadda take tare da iyayenta da Kuma kanwar ta Anty hajara, ganin Yana kallon ta ya Kuma ki dauke idanun shi se ta dauke Kan ta tana nunawa Anty hajara shi da Baki tana Mata kus din se kallon ta yake, shi kuwa a lokacin ganin ta ya tafi da komai na shi, Jin shi, ganin shi hatta da sense of stimuli din shi Adda tayi nasarar tafiya da shi! " Kai halilu" Wanda ya Kira da halilu ya dube shi Yana amsawa tare da jiran umarni, ya nuna masa inda su Adda suke yace Masa ya tabbatar da ya dakko hankalin su sun shigo shagon nan siyayya! Aikuwa halilu yayi nasara, ku kunsan bakin Yan kasuwa, kusan sun iya kalami, Haka kuwa Suka shiga ya tarbe su cikin mutunci da Kuma girmamawa, aka nuna musu kaya, ita dai Adda se Bata Rai take, saboda idan zata dago idanun ta sau Gama kuwa zata Kama Kawu Yana satar kallon ta, hakan yasa ta takurawa su Alhajin KT akan suje wani shagon su duba, su kuwa sun ga kaya, unique ga Kuma shimfidar fuska har da ta tabarma, Dan kafin su Fara saya ya bayar an sayowa kowanne zundumemen lemon kwalba 50cl dinnan. Bayan sun Gama ciniki yayi musu massive discount suka Masa sallama dan tafiya, hade da sake mishi godiya bisa karamcin shi, tare Kuma da Yi masa alkawarin dawowa wani lokacin idan bukatar hakan ta tashi! Ita dai Adda Babu bakin magana, daga harara se cone baki. Kawu yaga da gaske tafiya zasuyi, Kuma tafiyar su na nufin sede yayi tunanin wannan kyakyawar budurwa dukda ma yasan sunan ta, yaji Maman ta na fadin " Asiya ga shadda irin wadda Kika ce kina so, ba Zaki dauka ba?" "Kalla kiga lace dinnan yayi kyau Asiya?" A Haka ya fahimci sunan ta, Dan Haka yayi ta maza ya tari Alhajin KT ya durkusa har kasa tare da fada Masa abinda yake zuciyar shi " Baba Naga daya daga cikin yaran ka,  Asiya Kuma naji Ina son ta, idan ka amince ka bani dama Ina son na aureta idan ta amince idan Kuma bakai Mata miji ba" Kafin wani a cikin su yayi magana tuni Adda tace "Ni gaskiya a'a, bana son shi!" Aikuwa iyayen duka biyu sukai kanta da fada, Ina ruwanta zata saka Baki a maganar manya, waye waye! Haka dai tayi shiru tana Kara hade fuska,  Anty hajara nata murmushi a gefe. Alhajin KT ya dubi Kawu yace " Zan Yi shawara duk yadda ake ciki zaka ji aike na!" Idan Allah yayi wannan da wannan zasu kasance karkashin Inuwar aure to lallai lallai, duk kiyayya, duk tashin hankali sannan duk wani abu se wannan auren anyi! Haka suka tafi bayan yayi kokarin sake musu alkhairi Amma Alhajin KT ya dakatar da shi, a'a ranar yaran shagon Suka ta Masa tsiya suna zolayar shi, tare da zuzuta how much ya iya zabe, fada suke suna karawa Adda fa tayi karshe ce, shi Kuma Yana murmushi Yana Jin Babu ya shi. A bangaren su Adda sun koma katsina lafiya, mahaifin ta bayan kwana biyu ya tada mutane har biyu daya yaje Hadejia ya gano Masa su waye dangin da Yar shi zata shiga, dayan Kuma ya tsaya a Kano cikin kasuwa Dan kuwa anan Kawu yafi Zama Kuma nan ce Hulda da mutane. Sede mu ce madalla da iyaye na gari, Allahu ya saka musu da mafificin alkhairi! Sati daya ya samu kyakyawan feedback Akan komai da ya danganci Kawu, hakan yasa yayi naam da shi ya Kuma samu babbar diyar ta shi da mahaifiyar ta, bayan addu'oi yace " Kisa a ran ki bazan Miki Dole ba, Amma musulinci ya bani damar Yi Miki zabi, to Ni na zaba Miki Hamisu ki aure shi, idan Kuma baiyi Miki ba har bayan Kun Yi magana, ko ki fahimci wani nakasu a addinin shi ko zamantakewar shi, Ina fata ki sanar Dani se a fasa..." Wannan fasawar da yace ta dadawa Adda, zuciyar ta tayi haske Dan a ganin ta so ake a cusa Mata auren da Bata so. Haka Alhajin KT ya sake aike ma Kawu sakon Fara nema through wani abokin shi dake nan sabon gari market. Zuwan farko yadda ta tarbe shi duk se yaji Babu dadi, Amma yadda yake son ta se ya kasa hakura, zuwa biyu, zuwa uku zuwa hudu, Adda se ta amince saboda yadda ya damu da ita, yadda yake kuka da ita, yawan kyauta da nagartattun halayen shi yasa ta amince. Wata bakwai daga lokacin se ga Adda a dakin Kawu. Anyi sure cikin mutunci da kyautata wa juna. Dukda Kawu ya kasance Dan kasuwa ne, to Amma wannan bokon da yayi har zuwa master's level ya saka yake shaawar ganin mace tayi Boko. Shiyasa bayan auren Adda da wata biyar wani abokin kasuwancin shi Dake matsayin Nurse a asibitin murtala yake fada masa, ai school of nursing Kano sun Fara Saida form, idan Yana da candidate ya kawo, bayan dogon tunani kawu ya samu Adda ya fada Mata ta kawo ssce din ta zai nema Mata makaranta. Lokacin da ta san school of nursing ne kamar zata maida Kawu ciki saboda murna, ita dai suna birgeta idan ta gan su a asibiti, wannan abun da Kawu yayi Mata ya sake zurfafa son shi cikin zuciyar ta. Ko da ta Fara zuwa makaranta, Bayan wata shida akai intro cikin hukuncin Allah ta samu nasara, lokacin da Suka Zama cikakkun student nurses se ta Fara wani tunani cikin zuciyar ta, school of nursing ba wajen wasan yaro bace ba, idan tayi Wasa ta samu ciki shikenan zaa kore ta, Dan Haka a boye da little knowledge din ta na family health ta saya pills take Sha, kusan shi ne kuskuren farko da tayi, Amma wani lokacin ta kance hakan ba kuskure bane ba. Babu haihuwa Babu labarin ta, shi Kuma Kawu Yana son Yara, lokacin ta Yi shekara uku suna Shirin yin hospital final, a wannan lokacin ya hadu da Mama! Idan aka hada maka Mama da Kuma Adda you'll be confused to who's more beautiful, dukkan su farare ne Kuma kyawawa, sirara masu diri me kyau. Mama Yar Yola ce, ita din I'm not sure of yadda Suka hadu da Kawu Amma dai yazo yace da Adda zaiyi aure, lokacin tana Shirin yin final nursing qualifying exams. BINTUN BATUUL na kudi me... [1/3, 20:27] Maman: _BINTUN BATUUL_ Ayshatuuu Top-notch season 3 007 Da farko dai bansan me mutane suke ji ba idan sun tanka hallitar ka, bansan pleasure din da suke driving ko kuma wani satisfaction da suke samu daga hakan ba, na Kan Dade Ina tunanin Ina ruwan mutane da hallitar mu, those shape, complexion, figure matters? Akwai wani alfarma da kyawawa suke samu a rayuwa? Akwai wani favor ko afuwa da rayuwa take bawa kyakyawawa? Nayi tunanin Allah cewa yayi Yana amfani da zuciya da Kuma ayyuka, Amma baya la'akari da suffar bawan shi! To me yasa mutane Basu iya dauke idanun su akan hakan? Me yasa se sunce Kinga yadda kikai kiba? Kai wannan kiba ce da ita! Wannan siririya ce! Tab Kinga kumatun ki? Ina ruwan ku? Meye matsalar ku? Jikin ku ne? Kunsan yadda muke ji kuwa? Nasan zuwa yanzun Kun fahimci wacece ni ko da kuwa kadan ne daga ciki, na rayu cikin tsoro, fargaba da kuma tantama da kokonto Haka na rayu, nasan da dama akwai Wanda suke fuskantar abun da nake fuskanta ko Wanda ya fi hakan . Bayan haihuwar mu, jikin Adda yayi sauki aka sallamo mu, kamar kowa Nima aka rada min Fatima Amma ana Kira na da Bintu, sati daya da haihuwar mu Adda ta dubi Mamaa dake min wanka tace " Nikam Mamaa kunnen Bintu kamar baya fita, kullum se kiga yayi duhu!" Ta sake gogar sabulu ta goga a wajen tace " Wallahi fa Adda, Nima na lura Amma na dirza yaki fita!" Wata kanwar Kawu, Anty zainab tace " Ai baka ce, ba datti bane ba!" "Me?" Suka hada Baki wajen fada tare da Kuma kallo na da nayi lamo cikin ruwan dumi, Anty zainab ta kalle su da mamakin wannan exclamation tace "Eh! Baka ce shiyasa kunnen ta yayi duhu, ai da nan ake gane bakin yaro" Duka sukai shiru suna bi na da kallo, kowanne cikin su Yana ayyana abubuwa daban. Kafin a rufa wata daya da haihuwar mu nayi wani irin baki Kai ka rantse da Allah kace ni ba jaririya bace ba, wannan kyan da suke da shi, ko daya ban Kama kafa ba, kamanni na daban suke da na kowa a gidan Amma Kuma da Kawu nake Kama, saboda su din na Kama da iyayen mu Mata yasa na fita daban kamar ba Yar gidan ba. Batuul ta kasance me kuka, kuka ne da ita sosai, se ya zamana idan Adda zata je makaranta da ita take tafiya ni Kuma kullum Ina gida ana dirka min madara, se idan ta dawo ta karbe ni tayi breastfeeding di na, Amma kusan lokuta da dama ko da tana gida to tana tare da Batuul ni Kuma Ina hannun Nanny. Kafin lokacin yaye na yaye Kai na, ko ta bani nono bana kamawa se kawai ta yaye ni ta cigaba da rainon Batuul abun ta! Muka Fara girma na Fara kiba, ga Baki ga Kuma kiba Wanda nake ganin ba laifi bane ba, Haka halitta ta take Amma Yan gidan mu kullum suna cikin zuzuta yadda nake, idan tafiya anguwa ya tashi, to Haka zasu dauki Batuul su tafi da ita leaving me behind, kawai saboda ni baka ce ba yanayin su ba! Lokacin da zaa saka mu makaranta yayi, aka saka mu a makaranta, ko a aji Batuul ce me kokari Amma ni bani da kokari, so ko a aji Batuul ake so Amma ban dani, Babu Wanda yake lura da ni, Babu Wanda yake ta tawa, kowa sede yace min sister Batuul as though ni din shadow din ta ce, tun Ina yarjnya na Fara Jin kamar I don't belong to inda nake, na Fara Jin haushin ita Batuul din da ake fifita ni akan ta. Idan akai classes ban iya ba se Anty din mu Miss Vivy tace naje wajen Batuul ta koya min, ita Kuma anan wulakancin ta yake tashi. Ni fa na yadda kowa da kake gani halin shi Yana farawa ne tun daga lokacin da aka haife shi, nasan akwai abubuwa na zamantakewa ta rayuwa da muke koya later in life, Amma na yadda sosae halayen mu start with us! Yadda muke ba identical ba Haka ma halayen kowa da nashi, tun muna primary take kamar Jin kunyar ace ni din Yar uwar ta ce saboda abin da take gani a gida kenan! Har Muka Fara girma Bata canza zani ba, a Haka muke rayuwa kowa da hanyar da yake bi. Lokacin da muka Kai shekara goma, na fara gane abubuwa da dama, dukda ban kasance bright child ba Amma Kuma I'm not too dull. Mun dawo daga makaranta dukkan mu a gajiye, driver dake Kai mu ya sauke mu kofar gida Bai Shiga ciki ba, a cewar shi min Yi Masa rashin kunya sede mu taka da kafafun mu, ranar yunwa nake ji saboda abincin da aka zuba min a flask di na kadan ne, na kasa gane me yasa kullum abinci na haka, ko kadan baya isata, tun da mu idan muka tashi da safe bamu cin abinci se mun he school lokacin break se mu ci Wanda aka zuba Mana. Sajida na samu a kitchen ita da Mamaa suna karasa abinci, na shiga ba tare da nayi sallama ba, " Mamaa yunwa nake ji" Ko kallo na Bata Yi ba, se sajida tace " Baki iya sallama ba ko? Fita kiyi sallama Yar baka kawai!" Cikin rashin Jin Dadi na fita, kamar ba Zan dawo ba Amma saboda yunwar da nake ji, nayi sallamar sannan na Shiga bayan sun amsa, nace " Mamaa sannu da aiki!" "Yawwa Bintu!" Ta fada tana kwashe abincin daga tukunya zuwa cooler, yawun Baki na har tsinkewa yake nace " Mamaa yunwa nake ji" " Idan an Gama zaa zuba Miki acici!" Sajida ta fada ko kallo na Bata Yi ba, se na fita tunda aka bani wannan amsar, Ina nan tsaye ko minti uku baayi ba se ga Batuul tazo ta wuce ni, within minutes se gafa ta fito da bowl cike da shinkafa, mamaki ya Kama ni nace " Batuul waye ya zuba Miki?" "Mamaa ce!" Ta bani amsa shortly tare da wucewar  ta, se na sake komawa kitchen din, banyi magana ba na tsaya, wannan karon har Adawiyya da Zahra na nan suna dibar abinci. Gani na tsaye yasa Zahra daukar plate ta zuba min tare da miko min, Amma kafin na amsa Mamaa ta amshe daga hannun ta, " Baban ku yace ta Fara tsallake abincin Rana saboda kibar ta tayi yawa!" Ban da sajida dukka Suka kalle ta sannan Suka kalle ni, Adawiyya tace " Mamaa! Se a Hana ta abinci saboda kiba? Ai kiba hallitta ce fa" Mamaa tace " Ai nasan da Haka, baban ku Zaki fadawa bani ba" Zahra Dake mamaki har lokacin tace " Idan Kuma tana Jin yunwa fa? " "Ni dai na fada muku, idan Kuma Kuna son samun matsala da baban ki se ki bata taci" Kafin ta gama fada ma na fahimci bazaa bani abincin ba, Dan Haka na juya na tafi dakin Adda, Bata nan nasan Bata dawo a aiki ba, Kuma ko tana nan zata goya baya akan Hana ni abincin da akai, tunda they all believed cewar idan na rage cin abinci Zan rame, ko sun manta kiba Babu ruwan ta da abinci ko tashin hankali, wani lokacin da yake cikin damuwa lokacin yake kiba, wani lokacin da ya daina cin abinci ba zai rame ba. Jakar school Dita na dauka, na laluba ciki with the hope Zan ga guntayen biscuits a ciki, cikin saa na samu pieces Wanda idan aka tada su to zasu iya tashin guda biyu, wani Dadi naji a zuciya ta, na dauki ruwa daya na jefa cikin jakar, tare da rufe fridge din na fita can wani guri a gidan mu, inda duk lokacin da nake son kadaicewa wajen nake tafiya, na zauna tare da Ciro pieces din biscuits din Ina ci a hankali har lumshe idanu na nake saboda dadin da nake ji. Bayan na cinye na Sha ruwa se na Ciro quantitative reasoning di na na Fara Yi, na kusa awa Ina Yi kafin na kammalla na maida cikin jaka ta, na cigaba da Zama har bayan laasar, dama Babu wani zancen sallah, se lokacin da nayi niyya nakeyi, ba Wanda ke takura Mana muyi sallah kowa is busy a gidan mu, wasu irin mutane ne gidan mu. Se yamma lis na koma ciki, shima yunwar ce ta Fara kwakula ta, straight na tafi kitchen, Ina zuwa na tarar hatta spoon an wanke an kife alamar abincin ya Kare, na bude freezer nasan akwai masu ajiya, Ina dubawa Naga Babu komai a ciki se su nama da kifi da Suka Zama block, hawaye kawai se ya Fara sakko min, wanne irin rayuwa ne wannan nake Yi a gidan mu, dukda bani da wayo can sosae Amma abun Yana damu na. Ko kinsan har yanzun muna tare a tafiyar top-notch kuwa? Wannan karon ba Abinda ya baka tsoro bane ba, a'a NAZNEEN, Gen Nasir Zaki da Kuma BINTUN BATUUL. Me kike jira Yar uwa? [1/3, 20:27] Maman: BINTUN BATUUL Ayshatuuu 009 Top-notch season 3 Haka na cigaba da Zama da yunwa a jiki na, idan na ci abincin safe a school to se bayan maghrib kafin Zan Kuma cin wani abu, duk yadda suke son na rame ban rame din ba, sede ni a jiki na nake Jin yunwar. Gaba daya gidan ya fita min a kaina, na Kara tsangwamar Kai na ta hanya Zama a daki in dai Ina gida, da zarar anyi Baki ko me nake Yi to se na gudu zuwa daki, idan baayi da gaske ba kuwa har su tafi ba Zan fito ba, se dai idan Yan Hadejia ne ko Yan katsina ko Kuma Yan uwan Mamaa, amma bayan wadannan Babu Wanda nake shiga shirgin shi. To a bangaren makarantar ma Haka ce take faruwa, duk da ban kasance me shiga mutane ba, Amma bana tsallake critics da Kuma tsokanar Yara Yan ajin mu, bana mantawa Anty din mu Haka take ce min Fatibombom, so Haka kusan dukka Yan ajin mu Haka suke fada min, wasu Kuma Babu ruwan su da tsokana ta, se ma Jana da suke a jikin su, Amma kasancewar kowa a idanu na is a monster yasa bana sakin jiki da su, ko Batuul da zarar mun shiga makaranta to tamkar bamu San juna ba Haka muke komawa, se idan Abu ya faru dole da zai hada mu! Bangaren islamiyya kamar mutanen cikin ta daban Haka suke, bana tunanin I ever heard someone talking about my size or face, Kai idan hakan ta faru ma gaskiya ba Zan iya tunawa ba, shiyasa the only place I find joy and solace shi ne islamiyyar. So bana jiran wani yazo muje islamiyya, Ina shiryawa nake tafiya, har bana son alhamis tazo saboda ba zanje islamiyya ba. Suleiman yaron abokin kawu ne, ba muda nisa da gidan su, zaman unguwa ya hada mahaifin shi abota da kawu, da ke su Adda wasu irin mutane ne yasa zumuncin su day maman Suleiman se idan Abu ya faru, ko haihuwa, ko jaje ko gaisuwa, itama tun tana zuwa har ta watsar da su. To shi Suleiman Yana yawan zuwa duk da ba shi da sa'a a gidan mu wato ba shi da age mate Amma bansan me yasa yake zuwa ba. Tun kowa Bai sakin jiki da shi har suka Fara sabawa da su, dama ni mujiyar gida se kazo ka tafi baka ma San Ina gidan ba. If I can remember shi ne ya Fara saka min BINTUN BATUUL, Bai taba Kira na Bintu sak ba se ya hada da Batuul dinnan! Ranar da muka fara haduwa, was a day na dawo daga islamiyya, na gaji matuka abinci kawai nake son na ci, na shigo da sallama a Baki na, Yana zaune Yana cin abinci, na gaishe shi se yace " Idan kin Shiga ciki kawo min ruwa!' Na gyada Kai na, Ina Shiga ko hijabi ban cire ba na tafi kitchen na dakko masa ruwa me sanyi na koma inda yake zaune, nan na samu Batuul na zaune suna cin abinci da shi har da zuhra ma. Na aje Masa ruwan yace min ya gode, na juya Zan tafi Batuul tace min " Bintu shi ne Kika tafi Baki tsaya nu ba, Kuma nasan an Kara karatu" Na juyo Ina harar ta nace " Dama Ina jiran ki ne? Anyi" Na fada Ina tafiya ta, zuhra Dake gefe tace " Bintu Allah ya shirya ki" Ko Amin bance ba balle ma na juya, se Suleiman yace " Itama a gidannan take?" Batuul tayi saurin fadin "Eh Mana, ka ganta baka ko? Haka take ita ce daban da kowa a gidannan, Kuma har a school ba ta da kokari!" Haka Batuul take, Haka halinta yake, ba'a sirri da ita, ko kadan Bata iya file bakin ta ba, Haka take sakin Baki tayi ta surutu kamar tababbiya, Suleiman da ke kwasar abinci yayi dariya yace " Ai kinfi ta kyau!" Batuul tayi murmushin Jin dadi, Suka cigaba da hirar su ni Kuma ban masan me suka fada ba. A hankali Suleiman ya fahimci ni twin din Batuul ce, shikenan ya lakana min BINTUN BATUUL. Idan yazo ya dinga tambayar Batuul Ina BINTUN ta, se tace Masa Ina daki. A Haka Suka shaku wani lokacin na Kan jiyo Mamaa nace masa ko dai ta bashi Batuul ne? Shikuma se yayi ta murna Yana washe baki Yana fadin " Wallahi kuwa Mamaa nagode sosae, Dan Allah Ina kamu" Shikenan kamar wasa se gashi sun Fara soyayya shi da ita, duka duka lokacin shekarar mu Sha uku there about, bana mantawa muna js3. Wannan soyayyar da Batuul ta Fara da Suleiman ya sake bude Mata idanun ta. Ta sake Jin Kan ta ita wata abar ce, yadda Kuma siblings din mu suke mata, ko biki zasu je ko wata unguwa ta fita kunya to zaga ka sun Aiko Batuul tazo su tafi unguwa, ko dinki zasu yi zaku ga Batuul zasu yiwa. I remembered a day, sallah ta kusa, kamar yadda aka Saba ministan harkokin cikin gida wato Mamaa, ta karbo Kaya daga shagon kawu, da daddare Ina daki da Yar karamar wayar da nake da ita Ina Facebook, zuhra ta shigo tace naje parlor, na tashi na tafi na tarar suna ta dagawa kowa se zaba yake, na zauna ni ma na Fara kokarin janyo wata coffee atamfa, se Naga duka suna dariya, na kalle su Mamaa tace " Ke Bintu wannan kayan idan kin saka ai ki fuskar ki ba zaa gani ba!" Suka Kara kwashewa da dariya, Batuul ta miko min wata ledar tace " Ga naki fa!" Tsabar abin da naji, se na kasa bude nawan balle ma naga wasu iri ne a ciki, kada fa kuce wani Baki ne da ni irin na kuzo ku gani dinnan! Ana Haka se gashi an aiko da lace na Batuul daga gidan Yaya Adawiyya, lace din yayi kyau se murna take, Ni kuwa inata kallon su Adda ta kalle ni Dan taga yanayin da nake ciki, " Ke Adawiyya Ina na Bintu Kuma!" "Whoa! Kinsan Adda zabar ma Baki Kaya wallahi wahala ne da shi, niyya ta na Bata kudin kawai ko powder ne ta siya!" Ana jimawa kuwa ta dakko kudi ta Mika min wai na saya wani abun, na girgiza Kai da wannan murmushin nawa nace " A'a nagode, ki bar shi!" Ta kasa ta raya Amma fur naki karba, karshe Mamaa ta bawa, na koma daki na tsaya gaban madubi Ina kallon Kai na, a hankali hawaye ya Fara sakko min daga idanu na, a lokacin nayi ta kallon fuskata da Kuma jiki na, na juya na Kara juyawa, se na Fara Jin to me yasa na kasance daban cikin gidannan? Me yasa na Zama baka? Me yasa ni banyi kyan su ba? Me yasa... Muna Gama junior secondary din mu, Batuul ta takurawa kawu Kan lallai se ya cire ta daga school din da muke ya maida ita wata, a cewar ta Wai dukka kawayen ta cire su zaayi. Kawu ya Kira mu tare a Kuma gaban iyayen mu mata, ya tambaye ta wadda take so ta fada Masa, ya kalle ni yadda na zauna kamar na gaji da zaman, yace " Bintu ta! Zo man Bintu ya akai?" Na karasa gefen shi na zauna amma a dadare, saboda Ni na tsani gathering, bana kaunar shi saboda in dai an hadu to se an Fadi abin da zai Bata min Rai na. " Ya Haka take kamar tsoro na?" Ya tambayi Adda, ta tabe Baki tace " Ai Haka take, Bata kaunar shiga cikin mutane ko kadan, kullum tana daki". Ya dube ni da kulawa yace "BINTU fada min menene? Akwai abin da kike so?" Na gyada Kai lokaci daya se hawaye ya Fara sakko min zuwa kunci na, kunsan kukan me nake? Dan kula ni da yayi, for unknown reason I felt warm inside me, har naji rush of emotion "Kawu boarding school nake so?" A lokaci daya Suka hada bakin fadin boarding Kuma? Na gyada Kai na in affirmation. Kawu yace " A'a Bintu boarding da wahala fa, ba Zaki dinga gani na ko moms din ki baz ga Batuul ma ba Zaki dinga ganin ta ba" Exactly why I want to leave kenan, na fada cikin zuciya ta, Amma a zahiri se na goge hawayen da yake saukar min nace " Eh na yadda kawu" Haka kuwa Babu yadda aka iya aka Fara processing makaranta, tun Adda da Mamaa da kowa a gidan suna ganin kamar wasa ne, se da aka kawo admission letter ta hade da dukkan needs din makaranta kafin Adda ta Kira ni daki wani dare, na zauna bayan ta bani umarni " Bintu kije ki samu baban ki kice masa kin fasa boarding dinnan! Kinsan wahalar boarding kuwa? Idan Kika tuna ni kuka zakiyi fa!" Na Dan Yi murmushi nace " Adda Ina so a hakan". Tayi shiru, thinking of a way to convince me, Amma fur naki yadda har ce mini tayi akwai mayu da aljanu a boarding, Ni kuwa nayi fatan idan naje can din Allah ya sa su cinye ni😁 BINTUN BATUUL, Gen Nasir Zaki and NAZNEEN. Wato Shatuuu, Azizat da Kuma me dambu akan farashin N1300. [1/3, 20:27] Maman: _BINTUN BATUUL_ Top-notch season 3 Ayshatuuu 008 Rasuwar iyaye Rashi ne da duk abin da zaka samu a duniya ba zai maye maka gurbin su ba, idan ka rasa iyaye hakika ka rasa wani bngare na rayuwar ka, Haka babu Wanda zai fahimci ciwon da yake a rashin iyaye se Wanda ta faru akan shi! Ina adduar Allah ya jikan iyayen mu da Wanda suka rasu da Wanda suke da Rai, yasa aljanna ce makomar su, ya Kuma kyautata namu zuwan! Amin Rasuwar Mr Fahad, ba karamin girgiza dukka kasar tayi ba Amma Kuma mussamman tilon diyar shi Zainab, wadda da farko kasa amincewa tayi da cewar Wai mahaifin nata ya rasu, ta dinga fadawa kakarta da ta haifi mahaifiyar ta cewar tace a duba shi fa, dogon Suma yayi saboda Bai ci abinci ba, wannan maganar da tayi ta Kara dagula lissafin kakar, tare da saka ta kuka sosae " Jadda! Bai mutu ba, jadda ki fada musu Bai mutu ba" Haka tayi ta maimaitawa har safiya lokacin da zaa tafi da shi makwancin shi, tunda aka fito da gawar Zainab ta yanke jikin ta ta Fadi, Wanda baa samu ta dawo hayyacin ta ba se da aka Kai ta asibiti, lokacin da ta farka taga kanwar mahaifiyar ta Raziya se ta sake fashe wa da kuka, ta dinga Yi Babu kakkautawa har se da aka Mata allura da ta saka ta bacci kafin Kuma dakin yayi shiru! A takaice Zainab ta rayu cikin maraici na rashin uwa da uba, se wannan jadda wato kakar ta, da tun rasuwar mahaifiyar ta, Mr Fahad ya role ta Kan ta dawo gidan ta zauna da Zainab, shi din bashi da kowa,na shi iyayen sun Jima da rasuwa, to yanzun ma jadda kawai ta rage Mata. Kunsan mutum yayi coping da irin wannan rashin Abu ne ba Mai sauki ba. Kafin rasuwar mahaifin ta, ta samu gurbin karatu a daya daga cikin manyan jami'oi dake kasar America, wannan rasuwar ce ta kawo tsaikon tafiyar tata, bayan wajen wata da rasuwar jadda ta lallaba ta ta wuce America. Zuwan ta America, se taji sabuwar rayuwa, taji ta daban cikin wata duniya wadda ba irin wadda ta tashi a ciki ba, Amma yau da gobe se ta Fara coping, har ma tayi kawa da wadda suke aji daya da ita wadda baturiya ce daga kasar America, course daya suke shi ne ya kawo shakuwa a tare da su. Zainab ta kasance nutsatsiya wadda ko a tafiyar ta zaka san wannan halitta a nutse take, maganar ta, al'amuran ta da komai nata, she's too gentle and beautiful! Shekaran farko Babu Wanda ya lura da ita, kamar yadda Bata shiga harkar kowa ban da Lily, ko da akai hutu na session se tace da jadda ba zata koma Qatar ba saboda tana tunanin yadda zata koma ba tare da taga mahaifin ta ba. Wani lokaci ta fito daga class a matukar gajiye, ga yunwa ga Kuma zafi da ake yi dukda baa Jima da dauke ruwan sama ba, Wanda ya samu ya kwanta a wasu wurare cikin makarantar, tafiya take Yi a hankali zuwa gate din makaranta Dan ta tsallaka ta Shiga taci abinci a eatery din da ta saba. Tana tafe sanye cikin bakar Abaya wadda tayi Mata kyau, ta yane Kan ta da mayafin abayar Baki, Wanda ya sake fito da asalin fatar larabawan da take da shi, tafiya take a nutse, Wanda ga masu wucewa gani suke yanga take, Amma a zahiri Haka tafiyar tata take, wani lokacin Alan tsayar da mota tare da yi Mata tayin free ride, Amma se ta girgiza Kan ta tare da godiya, ta kusa zuwa gate wata bakar sport car ta taho da mahaukacin gudu tamkar zai buge ta, har se da ta tsorata, Amma kafin ta matsa daga wajen se ji tayi ruwa tun daga Kan ta har cikin brown leather loafers din kafarta, cak ta tsaya tana kallon motar da ta wuce kamar me tukin Bai San ya watsa Mata ruwa ba, tayi shiru tana kallon jikin ta, kawai se taji hawaye ya Fara sauka saman kuncin ta, ta juyar da kanta tana kuka me ciwo, dama me neman kuka ne aka jefe shi da kashin awaki! Cikin motar wani bature ne me suna Charles, a gefen shi wani bakin African ne me suna Imam, kana kallon shi kasan Dan Africa ne, idan kayi bincike da yawa zaka iya fahimtar shi din Dan Nigeria ne, idan kana neman yaran da basa Jin magana cikin entire campus dinnan to idan ka samu clique din su Imam ka gama, kowa ya San su saboda yawan su, da Kuma sun hadu ne daga various departments. Tun da suka taho idanun shi ke Kan Zainab, tafiyar ta kawai ita ce abar da ta Fara daukar hankalin shi, na biyu Kuma shigar ta, cikin Kamala da mutunci Wanda ba kowa ke daurawa daga tarbiyar da iyayen shi Suka bashi ba, Yana wannan tunanin tare da begen ganin fuskar ta kawai se gani yayi Charles yayi Mata feshin ruwan saman da ya kwanta, wani duka ya Kai Masa unconsciously tare da fadin " Do you want to die? Are you crazy?" Charles ya kalle shi Baki bude da Kuma mamaki, Dan kuwa ba karon farko da suka Fara yiwa Yan Mata Haka ba. Shima yace w " What's wrong? Is just for fun" Ya kara dukan shi a keya Wanda ya kusa saka steerer kwacewa daga hannun shi, yayi saurin dafewa tare da gritting hankoran shi in annoyance, cikin turanci Imam yace Masa se sun koma ya Bata hakuri, wannan shi ne karon farko da suka taba yin hakan tun haduwar su, Babu yadda Charles zaiyi ya koma cikin school inda Zainab ke tsaye tana sharbar kuka, yayin da Imam ya Fara Jin wani nervousness hade da uneasiness Yana addabar shi tun kafin ma yayi idanu biyu da ita.... Tirkashi *** Na Jima a kitchen din kafin na fito na koma daki, Babu kowa duk sun tafi parlor kallon ka'ida, na kwanta nayi shiru Ina Jin ciki na yadda yake yi min ciwo, amma saboda Hali irin nawa se na hakura har aka Kira maghrib na tashi nayi sallah, sannan Batuul ta shigo da kwanon abinci, ta aje min a gaba na, kamar mayuwaciyar zakanya da ta ga nama Haka na dumfafi abincinnan Babu sadsauci, ban ma damu da zafin dake ciki ba, buri na na jishi a Baki na ya Kuma sauka a ciki na, se da na kona makogaro na kafin na sarara ya Dan Sha iska na cigaba da ci, Ina gamawa nayi gyatsa, Haka kurum naji ya kamata nace alhamdulillah! Na furta tare da Shiga toilet na wanke hannu na, na Tara Baki na a sink na Sha ruwa, Ina fadawa gado ko minti uku banyi ba bacci ya dauke ni, bansan me ya sake faruwa ba a gidan Dan lokacin da na tashi tsakiyar dare ne, kowa yayi bacci, Nima nayi juyi na cigaba da bacci. Da safe Dana tashi nayi wanka na saka uniform, dakin Mamaa naje na gaishe ta, sannan na wuce na Adda, ta Gama shiryawa cikin fararen Kaya na nurses, ni dai babban buri na a rayuwa ta a wannan lokacin idan na girma na Zama nurse, ba karamin burge ni suke ba, ban sani ba ko Dan kasancewar Adda nurse shi yasa nake son su? "Adda Ina kwana?" Ta kalle ni da kyau kafin tace " Ni wallahi mantawa nake Dake a gidannan Bintu, jiya Ina Kika je har dare ban gan ki ba?" Kun ga fa tun laasar ta dawo Bata ganni ba Amma Bata bada cigiya ta ba, nayi murmushi nace " Adda idan na girma Zan Zama nurse kamar ki!" Na fada Ina murmushi, ta tabe Baki tare da fadin " Da wani brain din? Times table ma ana yaki dake balle Nursing, ke ai sede education!" Lokacin naji kamar an sare min gwiwa ta, I began to think meye education? Nasan dai karatu ko ilimi I dunno how to put it, Amma su marasa kokari ne kenan? Se naji wani haushi ya Kama ni, ba tare da nace komai ba na juya Dan tafiya school. Ko Dana dawo daga school nan ma dai kamar jiya ne babu abinci, yau ko biscuits din ma ban rago ba se kawai na Sha ruwa na Yi assignment di na, idanu na kadai idan ka kalla kasan yunwa nake ji, Amma babu Wanda ya maida Kan shi Kai na, karshe ma a gaba na Batuul tazo da kwanon abincin ta taci, na dinga hadiyar yawu Amma ko mhmmm bance Mata ba, Dan nasan da gayya tayi hakan, idan nace Zan ci ta Hana ni yadda zanji haushi. Anyi sati ana haka, na Fara galabaita Dan Haka na samu Adda a daki na fada Mata abin da yake faruwa, dukda nasan ba Wai zata canja bane ba, amma dai gwadawa ce na gani me zata ce. Ile kuwa se tace Wai decision din kawu ne nayi hakuri, Ni bana Jin jiki na yayi nauyi? The top-notch writers are back again, wannan karon Gen Nasir Zaki ne na Azizat Hamza, NAZNEEN na Me Dambu da Kuma BINTUN BATUUL na Shatuuu, duk Akan farashi me sauki, N1300 [1/3, 20:27] Maman: BINTUN BATUUL Ayshatuuu Top-notch season 3 010 Ban taba sanin, Kai har cikin zuciya ta da gaske na dauka Adda Bata so na, na dauka idan aka ce a cikin yaran ta waye zata iya bayarwa a bata awara ni zata bayar. Amma dai daya a rayuwa tayi min wani abu da ya nuna min cewa ita uwata ce, Kuma babu uwar da take kin Dan ta, halayen ta akai na bansan me yasa take aibata ni ba, ban sani ba ki Bata San illar da hakan yake ma zuciya ta ba! Na Kuma yadda confidence, self esteem gaba daya ana Fara gino shi daga gida, tun a lokacin yarinta, Amma ni tun a gida na rasa wannan saboda yadda aka muzanta ni, aka nuna min cewar kiba laifi ce, eh mana it's absurd Amma abin da Suka nuna min kenan, nayi laifi tunda na Zama me kiba, to Amma me yasa Adda zata biye su matsayin ta na uwa ta? Instead ace ita ke goya min baya da nuna min kiba, fari, tsayi, gajarta, Baki da dukkan wata suffa ta Dan Adam doesn't count, wannan wani hikmar Allah ce ta banbanta mu da Kuma sakawa mu gane races din mu! Lokacin da kawu ya kawo Mata admission stuffs di na, ya Kuma dankawa Mamaa kudi me yawa Kan tayi min siyayya a Fara Shirin makaranta. Adda ta kalla makarantar wani Abu ya tsaya Mata a zuciya, ta kalla kawu da dukkan hankalain shi ke Kan business report da ake karantawa a labarai, tace " Yallabai!" Duk lokacin da ta Kira shi da hakan, to Mamaa zata basu guri tasan maganar su ta shafa, ya dago shima da idanun shi daga Kan TV din ya Bata dukkan hankalain shi, hakan da yayi ba se yayi magana ba, answer yake Bata Wai Ina jinki gimbiya ta! " Yanzun yallabai duk makarantun Dake Kano da jigawa da katsina, se Niger state zaka aika Bintu! Kasan Bata son Shiga mutane fa!' "Ita ta zaba tace boarding school Kuma kowacce ce tana so, a gaban ki na tambaye ta!" Cikin wani irin yanayi tace " Bintu yarinya ce yallabai, we can't let her make her own decision yet, she's slow Bata tunanin aftermath din hakan plus kasan Bata son Shiga mutane ko kadan" Shi dai kawu ya dage lallai New horizon can zanje, ya Riga da ya Gama komai, so sede tayi hakuri. Ta damu sosae, har Kira Ni tayi wata safiya da weekend, na same ta a daki, Ina Zama tace "Bintu Niger state Kawu zai kaiki fa!" Na Dan Yi murmushi a hankali nace " Na sani Adda! Ba Kya son school dinne?" Na tambaye ta a hankali, ta girgiza tace " Bintu yayi nisa, Wai tukunna ma menene dalilin da Kika nace se kin je boarding, Ni na son Baki son shiga mutane ko kadan! Wani Abu ake Miki da Baki so cikin gidannan?" Cikin zuciya ta nace, to wannan amsar tambayar ai is justified, ni mecece a gidannan ban da cikin gida, waye yake kallo na a matsayin mutum a gidannan? Babu Wanda ke regarding di na, ba Wanda yake kallo na matsayin I fit in illa kallon wata alien suke min.  Ni da Kai na nakan Yi tunanin yadda Zan iya coping a boarding school, how can I? Bayan bana son shiga mutane saboda Ina ganin kowa kallo na yake, I don't fit in, to Amma se Naga kawai gwara na gwada Naga yadda abun zai kasance! kwanakin da suka biyo baya har yaranta masu aure ta Kira akan su zo su roki kawu ya fasa maganar, Yaya Auwal yayi ta Mata dariya Wai dama Haka take Sona Bai sani ba, Ni kuwa se shiri na nake a hankali ni da Mamaa. Adda a karshe ta hakura ganin Babu Wanda yake Jin abin da take ki, ita dama mutum ce me so yaranta, dannewa take saboda Mamaa, Kuma yadda Mamaa ke wahala da mu ko ita Bata Yi rabin hakan ba. Kafin na tafi Adda da kanta ta kaini katsina, muka kwana nayi musu sallama, kowa na ya yimin fadan nayi karatu banda wasa ban da kuma abokan banza, daga nan se gidan su Mamaa Muka wuni sannan Muka wuce Hadejia muka kwana. Bayan mun dawo yasa Yaya Auwal ya kaini gidan Yaya Fatima da Fadima, Adawiyya da Zuhriyya. A fateful Monday, shi ne ranar da na bar Kano na tafi Niger, Mamaa da kawu da Batuul da sajida sukai min rakiya, ban masan ko murna nake ba ko kuma akasin hakan, na dai San kafin na dawo Yan gidan mu sun manta da ni tunda dama can ba Wai suna so na bane ba a tunani na kenan! Se da aka Gama komai na tafi hostel kafin suka tafi, tun da Muka shiga makarantar aka Fara checking Kaya na ko akwai contrabands Batuul ta Fara kuka, ai da na Fara Jan  akwati na se ta biyo ni ta rungume ni tana kuka, Amma naji wai I made a bad decision ko daya banji ba, in fact ji nake Dan Allah su tafi su barni! Ina shiga hostel aka raka ni daki na, aka nuna min gado na, room captain tace " Menene sunan ki?" Cikin turanci nace " Fatima Bintu Ginsau! From jigawa" Tayi min murmushi tare da sake min barka da zuwa, se naji Dadi har cikin zuciya ta, kunsan ance shimfidar fuska tafi ta tabarma. Da Kan ta ta nuna min inda Zan jera kaya na da komai, tace nayi sauri nan da 30 minutes sauran student zasu dawo daga games, itama zata wuce wajen su. Na Mata godiya ta tafi na gyara komai nayi wanka na saka sabon house wears di na sannan na zauna akan gadon da na dame da sabon bedspread,ba jimawa na Fara Jin hayaniya alamar sun dawo. Dakin mu mu biyar ne, biyu ajin mu daya, biyu SS2 suke se room captain da take SS3. Babu laifi dukkan su sunyi min magana tare da min barka da zuwa. Washegari na Fara zuwa class, Kuma a ranar na Fara period, ga bani da pad tun da shine karon farko da na Fara period din, rashin Sanin yadda zanyi yasa na tafi wajen Senior Aisha, tana zaune a class na same ta, ta dago tare da min murmushi, na mayar mata a hankali se ta tambaye ni ko akwai wani Abu? Nayi shiru kafin can na kakaro courage na fada Mata, da sauri ta Mike tace na biyo ta, mukaje clinic ta karbo min da kanta ta gwada min yadda Zan saka kafin na tafi. Zama na a school din Bai canja min halaye na ba, I was still Bintu da kowa ya sani marar son shiga mutane da Kuma hayaniya, wadda take tsoron wanne kallo mutane suke mata, to still Haka nake. A ajin mu Babu me tsokana ta Wai ko nayi kiba ko Kuma nayi Baki, saboda na samu Wanda Suka fini kiba da tsayi, suka fi ni Muni so Babu ma Wanda yake maida hankali Kai na, hakan yayi min dadi Amma Kuma dukda Haka bana iya sakin jiki a cikin mutane. A bangaren karatu naci da nake yasa Kai na ya Fara budewa, na Fara fahimtar abin da ake yi har na Fara ganewa, idan aka zo prep bana hira karatu kawai nake, saboda Haka Yan class din mu suke cemin Bintu nerd! Amma abun da zai Baku mamaki ko a class ake tambaya wallahi ba Zan bada amsa ba, I don't want anyone to notice my existence, gani nake da zarar anyi noticing di na kowa zai Fara aibata min jiki na Yana body shaming di na. Duk ranar kuwa da aka takira se nayi magana a class to kilan se nayi kuka, I lack the confidence da zanyi magana a cikin mutane! Wata na daya a school, visiting day tazo, dukka Yan dakin mu Bata shiri suna ta buga waya gida suna fadar abin da suke so akawo musu Amma ban dani, Ni ranar visiting din ma bayan nayi wanka se na kwanta Akan gado as though bana expecting zuwan kowa, Ina nan kwance se room captain ta saka a Kira ni, na tashi na fita, ai se na hango Batuul tsaye, mamaki ya Kama ni na ganin su, a hankali na cigaba da tafiya Ina Jin wani Dadi cikin zuciya ta marar misaltuwa ashe nayi missing din su. Tana gani na ta taho da gudu ta rungume ni, Ina murmushi na rungume ta, se na zauna kowa se tambaya ta yake ya school? Dukda ba dukkan su Suka zo ba, Adda da Mamaa da sajida se Batuul da zuhra, Suma anan suka kwana yau Suka zo. Na tambayi Kawu da sauran. Sajida tace " Bintu kiba Kika kara, ke yanzun makaranta yafi gida kenan!" Ban ce Mata komai ba, Amma a Rai na gani nake to ba dole nayi kiba ba hankali na a kwance Babu me takura min ko me body shaming di na! Haka ranar ta Kare min cikin farin ciki, da zasu tafi Adda ta Jani gefe tana tambaya ta ko akwai wani damuwa? Na girgiza Kai nace " Babu komai! I'm happy living here" Ta gyada Kai tana murmushi tace " Naji Dadi! You've improved a lot!" Daga Haka Suka tafi akan zasu sake kwana se washegari su wuce Kano, ni Kam Haka na cigaba da rayuwa ta cikin makaranta har akai hutun farko! Subscribe for top-notch season 3, @ N1300 only and have access to our beautiful and fascinating stories! [1/3, 20:27] Maman: BINTUN BATUUL Top-notch season 3 Ayshatuuu 011 Haka na cigaba da rayuwa ta, dukda tayi afuwa Amma dai ba kamar yadda kowa yake rayuwa ba, akwai tabon da idan akai ma rayuwan ka to idan ba Kai da gaske ba wannan abun zai ta hunting rayuwar ka har abada! Hutun farko da na koma kano, precisely ma dai satin farko kowa ji yake da ni kamar wani lallaba ni ake, to saboda ban Saba ba, se nake kallon abun odd na kasa sakin jiki na da kowa a gidan, na cigaba da Zama na daki. Bayan na kammalla session di na na farko, ma sake dawowa hutu, anan na cewa Kawu Ina son naje na koya snacks " Me yasa? Me zakiyi da shi? Ba akwai kayan girki ba ki koya a gida Mana!" Na Dan Yi shiru Ina tunanin yadda Zan tsara Masa words din not to sound some how! " Kawu Ina son na dinga yin snacks din siyarwa ne, shiyasa! Ya girgiza Kai yace " Ke Bintu me yasa kin Faye kawo bidi'a cikin al'amuran ki! Karatu zakiyi ko kuwa snacks Zaki dinga siyarwa?" Nayi shiru Dan bansan me zance ba, se kawai nace " Kayi hakuri kawu my mistake!" Yayi tsaki Yana canja channel yace " Ehhh ai gashi kullum shiyasa ba Zaki daina kiba ba, saboda son ci shiyasa idea Saida snacks ya zo Miki Rai!" Wani Abu ya sake zuwa min wuya na, na juya na fita mukai kicibis da Batuul zata shigo, tace " Kawu na parlor?" Kafin na Bata amsa tayi saurin fadin " Zanje nace Ina son naje koyon mota, Suleiman can be my couch!" Na gyada Kai ba tare da nace Mata uffan ba, Amma a Rai na , na tabbatar dole zai barta, aikuwa Bai kunya ta ni ba, zuwa yamma se gata ta ci kwalliyya da key din motar kawu a hannun ta, na dube ta lokacin da nake Zane akan plain sheet din Dake gaba na, nace " Ya yadda?" Tayi murmushi tana wulwula key din tace " Har wani yaji ma, ya yadda nake fada Miki!" Na gyada Kai na Ina Jin wani kunci cikin zuciyata, is not like ta Kai shekara goma Sha takwas, is not like ni bare ce a gidannan? Then me yasa ake treating di na equally? Ni ba bakin ciki nake ma Batuul ba Amma Dan me yasa ake yin hakan? Menene dalilin wannan partiality din? Na kwanta na Fara kuka wani irin bakin ciki da nake ji, naji na tsani rayuwa ta, na tsani komai, kowa baya so na. Akwai wani feeling na hopelessness, helplessness da Kuma worthlessness, to wadannan abubuwan guda uku su nayi taji, Haka zuciya ta ta dinga yimin wani irin zafi, na dinga Jin kunci. Har hutu ya Kare baa sake maganar ba, se ana gobe zan koma school naje dakin Mamaa Ina sake crosschecking abubuwan da aka siyo min, na karasa dubawa sannan na fada Mata abin da nake son a Kara min tace " To Bintu! Kawun ki yace Wai kwanaki kin ce kina son kiyi joining classes na snacks?" Na tabe Baki nace " Ai maganar ya wuce!" Ta kalle ni tace " Ke kinsan matsalar ki? Zuciya, baka zuciya da abin da baka da shi" Cikin kosawa da maganar nace " To Mamaa me zance? Komai na tambaya a gidannan baa yarda , kamar baa so na, kamar nayi laifi..." " Bintu!!!" Ta fada cikin karaji, kamar maganar batai Mata Dadi ba, Amma yau daya dai Ina son na fada abin da ke cikin zuciya ta, Ina son naji how it feels when one voice out "Mamaa Dan Ina da kiba ne ko Kuma Dan ni baka ce" "Zan mareki Bintu idan na sake Jin maganar ki? Waye yace Miki baa son ki? Waye ya takura Miki a gidannan?" Nima se nayi shiru, bance komai ba, a fusace tace na fitar Mata a dakin ta kafin na Sha Mari, Haka kuwan na tashi na fice, ko awa baayi ba se ga Adda a dakin mu, I'm sure Mamaa ta fada Mata abin da nace me shiyasa tazo. Bayan ta zauna tace min " So boarding din da kikaje fitsara da tsaurin idanu kuka koyo kenan?" Nayi saurin fadin " Kiyi hakuri Adda!" Se tayi shiru, nasan fada tazo tayi Amma wannan hakurin da na Bata se yasa tayi shiru tana kallon na Ina karasa saka ironed house wears di na. Can kafin ta fita tace " Har yanzun kina son cooking classes din?" Na gyada Kai na a hankali, daga Haka ta Mike ta tafi na tare da ta sake magana ba, washegari very early Muka wuce makaranta, bana mantawa a wannan term din na Fara yin kawa, sunan ta Samiha, Samiha yar katsina ce, kyakyawa ce sosae, gata fara Dan wani lokacin se tana magana ka dinga ganin jijiyoyin ta koraye na fitowa. Mutum ce me ibada, me kirki me Kuma ilimin addini. Zaman mu da ita is a form of symbiotic relation, Ina couching din ta abubuwan da akai class ita kuma tana koya min Qur'an da yadda ake gyara ibada. A hankali na Fara Jin dadin kawancen mu da ita, na fara amfanuwa da ita, duk da tana yawan complain din bana sakin jiki sosae da ita but to me shi ne Abu na karshe da Zan iya Yi! Da akai hutu maimakon na tafi Kano kamar yadda aka Saba, se na tafi Lagos gidan sajida, Wai Bata da lafiya laulayin ciki take, Haka naje na same ta duk ta firgice ta fita a hayyacin ta. Wannan zaman da nayi anan nayi joining classes din, naci da nake da shi yasa nayi wani irin succeeding, aka bani certificate na tafi, a Haka na koma school nan ma bayan anyi hutun na koma gidan ta na cigaba da Zama da ita. Zaman shiru yasa na bude Facebook da wayar ta, nake ganin yadda duniya ke ciki da Kuma gaisawa da mutane. Samiha ta bude min 2go da username dina BinGin wato Bintu Ginsau. Wannan lokacin na daya daga cikin lokaci da nayi farin ciki a rayuwa ta na gaske, Amma se Bai daure ba, Dan Haka se Kuma rayuwar ta sake kwabewa! Na manta ko 2go shi ma friend request ake turawa, ban dai San yadda nayi coming across wannan gayen ba, nasan dai kawai mun Fara " Hello" da Kuma "hi" shi ne abin da muka fara exchanging ni da shi, daga baya bacci ya Fara dauka ta, ban manta ba na saka ta a away saboda saboda star di ta ta bar Novice zuwa step na gaba, Wanda nasan ba professional bane ba Amma na manta wanne ne yanzun. Ko da safe Ina tashi bayan nayi shara da su gayaran gida ma sajida, na hadawa Yaya Saif breakfast, ya fito Muka gaisa Yana ta yimin godiyar dawainiya sannan yaci ya fita, Bayan ya fita n samu sajida a dakin shi tana kwance nace Mata " Sajida me Zaki ci yau?" Ta jiya tana kallo na tace " Alala!" Na bude Ido nace " Da safennan?" Ta tashi ta zauna tace " Ke Baki San meye ciki ba" Nayi murmushi na fita zuwa kitchen, na wanke wake, na hada markade na bawa yaron da ke Zama a compound din su Yana matsayin errand boy, na bashi ya Kai yadawo. Cikin lokaci kalilan na kammalla wannan alalar nayi serving din ta sannan na tafi nayi wanka, lokacin da na fito na zauna Kan gado wani Dadi naji cikin zuciya ta saboda gajiyar da nayi. Kullum Haka nake fama wani lokacin idan na gaji se naji kawai Ina ma a koma makaranta. Bayan na Gama shiryawa na dakko wayar Ina logging cikin 2go di na, anan na tarar da messages da yawa har da na BashPrince00 na share ba tare da nayi kokarin dubawa ba, se can da ya sake turo min magana kafin na bude Dan ganin content din messages din BashPrince00: hello BashPrince00: are you there BashPrince00: have you slept off? BashPrince00: I guess kin Yi bacci, goodnight then and I wish you the sweetest of dreams! Wannan su ne sakon shi na dare, se na samu Kai na da Sakin murmushi tare da sake rike wayar a hannu na, kamar wadda zaa zo a kwace ta, na maida hankali wajen karanta na safen BashPrince00: hello princess! Ina fata kin tashi yanzun? BashPrince00: haba Mana kiyi min reply naji Dadi! Whoa! Na furta Ina Jin wani irin waves of happiness Yana radiating cikin zuciya ta, awnnnn har princess yace min ya Kira ni da shi, na fada ina Jin kamar nayi winning medal a rayuwa ta. Na Jima da wayar a hannu na Ina tunanin me zance Masa? Se can nace BinGin: I slept off ne Amma na tashi alhamdulillah! Tuni se ga reply din shi BashPrince00: that's a relief princess! Ya Kika tashi? Kinci abinci Ni Bintu Naga ta Kai na, ai kamar wata wawiya na Shiga girgiza Kai kamar kadangaruwa nayi replying back da BinGin: a'a tukunna dai BashPrince00: ki hanzar ta kici kada ki bar Kan ki da yunwa bazan hi dadin hakan ba! OMG! BINTUN BATUUL na kudi ne, a daure ayi subscribing N1300 a samu damar accessing NAZNEEN, Gen Nasir Zaki da wannan labarin na Bintu⊂((・▽・))⊃ [1/3, 20:27] Maman: BINTUN BATUUL Ayshatuuu Top-notch season 3 012 A hankali ya karasa in da take tsaye, Amma ko da ya tsaya, tamkar ba naughty Imam ba se dukkan wasu kalamai da suke bakin shi Suka kafe, wata irin nutsuwa out of nowhere ta shige shi, kada ma da ta juyo yaga yadda fuskar ta tayi jawur, hawaye ya wanke Mata fuskar se yaji shima kamar ya fashe da kukan, wannan din ba halayen shi bane ba, in fact Bai ma taba jin Wai ya kalla wata mace yaji wani Abu game da ita ba, but who the hell is this girl? "I'm so sorry! I'm sorry please my Dear!" Ya fada muryar shi a tausashe, Jakar ta da ta Riga da ta Fadi a kasa ya tsugunna ya dakko Mata, tare da ma Charles signal din matsowa da motar, se da ya bude Mata owner's corner ya saka Mata Jakar a ciki kafin kuma, ya karaso ya Fara fada Mata tazo su sauke ta gida, Amma mirsisi Zainab taki yadda, se da kyar sannan ta Shiga ciki, yayin da Charles yake Jin kamar yayi bindiga saboda haushi, wanne Abu ne Imam ke Yi haka, se wani rokar yarinya yake kamar wani Wanda knots din Kan shi ya kunce! Gefen ta ya zauna, tare da bawa Charles umarnin Fara tukawa, cikin kunci Charles yace "Boss what are you doing?" "Me ye damuwar ka?" Ya tambaya yana talle Masa keyar shi, Zainab ta dauke Kai tare da murmushi a hankali, ita kawai dariya yake bata, tun da suka taho bayan ya tambaye ta address din ta fada masa wani close by off campus hostel ne. Kafin su karasa ta dubi Imam tare da fadin " Zan sauka anan, thank you for the lift!" Ya girgiza Kai yace " Ai se na Kai ki har hostel, be comfortable!" Ya fada Yana sakar Mata wani tattausan murmushi, ba tare da ta mayar masa martani ba ta dauke Kan ta, but yunwa take ji, so take taci abinci kamar ba gobe Amma Kuma ba zata iya fada Masa ba, se da suka Isa gaban hostel din sannan ya dube ta lokacin da take kokarin bude kofar da already aka saka ta a central lock. Yace " Dan Allah just wait a few second please" Daga Haka ya five ta Dan ja karamin tsaki saboda gajiyar da tayi, Kuma ta kasa fita, Bayan wajen mintina goma se ga shi ya dawo da leda, like a gentleman ya bude Mata motar, ta fito sannan ya Mika Mata ledar yace " Ban San menene favorite din ki ba, but I was able to buy my favorite for you!" Kamar ba zata amsa ba, Kuma se ta tuna abin da Mr Fahad yake yawan fada mata, kada ta rinka maida hannun kyauta baya, hakan halayen shedanu ne. Ta saka hannun ta ta amsa tare da fadin " Shukhran jazeelan!" Kada ku manta Zainab fa balarabiya ce, so karku Sha mamakin wata Rana kuji Imam ma ya Fara larabci...lol A wannan Daren Imam ya saka wani Dan Qatar, Murad wan da shi ma daya daga cikin yaran shi ne ko nace abokan shi, shi ne yayi bincike ya Kuma bashi feedback Akan Zainab, hatta da timetable din ta na lecture a hannun Imam ya kwana! Abu ne da Bai taba Yi ba, yasan baya Jin magana ko kadan hasalima dalilin da yasa aka Aiko shi kasar waje. Ya kwanta yayi.shiru a lokaci daya picture din Zainab ya cigaba da haskuwa cikin idanun shi, ya lumshe idanun shi tare da sakin murmushi wnda zaiyi melting zuciyar Wanda akai wa. Sede Yana son tafiyar da komai a hankali kada ya zake...                                 *** Cikin kankanin lokaci wata shakuwa ta Fara Shiga tsakani na da BashPrince00 babu wani abu da na sani bayan username din shi, Amma yadda yake nan da ni da yadda ya damu da ni yasa zuciya ta ta Fara fada Masa Nima. Akwai lokacin da attention kake bukata, akwai lokacin da matsalar is just for someone to care about you, yadda na koma cikin walwala da farin ciki se na fahimci kawai abin da nake bukata ba Wai ace ni kyakyawa bace ba, Ashe dai attention nake bukata, I need wajen da Zan samu solace! Tun sajida Bata fahimta ba, har ta fahimci yadda nake yawaita murmushi, yadda nake sakin fuska Wanda da can ba Hali na bane ba ko kadan, hasalima kunsan nafi son Zama a daki. Duk da har yanzun Ina zaman daki amma dai akwai sauyi cikin rayuwata! "Bintu wai nikam soyayya Kika Fara ne? Naga kina ta murmushi kamar wawuya" Na Dan kalle ta Ina murmushi da duk kokarin da nake na maida shi na kasa, se tayi dariya tace "Inyeeee! Yan soyayya. Ai shikenan Bintu, muna tunanin zakuyi karatu Amma ke da Batuul kun dage da soyayya! Ita Suleiman na can ya firgita Mata lissafi!' Na Kara murmushi nace " Ni fa bance Miki ba, karatu zanyi, ni da nake son Zama Architect!" Ta zaro idanu tare da fadin " To fa da wanne Kan zakiyi architecture din?" Nayi Mata shiru tare da maida Kai na Kan wayar da ke hannu na. A Haka hutun mi ya Kare zamu koma makaranta, tun saura sati daya muna chatting wani dare nace BinGin: Prince Cikin abin da Bai wuce minti daya ba se gashi yayi replying sako na da fadin BashPrince00: My princess! A take wani murmushi ya fita a fuska ta, har cikin zuciya ta nake Jin wannan sunan princess da yake Kira na da shi BinGin: next week Zan koma makaranta fa! Ai tuni Naga typing, se nayi relaxing baya na akan pillow na Fara jiran amsar shi, Babu jimawa se ga sakon BashPrince00: wacce makaranta Kuma? Baki Gama secondary ba? Ina murmushi ganin how curious he's nace BinGin: ban Gama ba Ina SS2. BashPrince00: wacce school ce? A take na fada masa, ya Fara mitar how badly he's going to miss me, to shi ya zaiyi ma dai da farko Babu ni. Se nace masa kada ya damu Samiha na zuwa da waya, we'll try to be in touch! A Haka ya roki na bashi number ta, Ni kuwa yadda yake on and off akaina Babu musu na tura masa, wa yaga farin shiga. Daga Haka muka Fara waya da shi, kafin wani lokaci shakuwa da Kuma soyayya me karfi ta shige ni, shima Ina da yakinin Yana so na sede abin da ya faru a karshe baiyi min dadi ba. Kafin wannan lokacin nasan na samu kulawa da Kuma farin ciki Wanda ba shi da algus babu mix ko kadan. Har na koma makaranta da wayar Samiha muke chatting da shi, Amma duk da yadda muke communicating ban Bari ya taba karatu na ba, shi ma kuma he make sure Bai Shiga lokacin da ya kamata ace na Yi karatu ba. Amma duk wannan abun da kuke gani Bayan sunan shi Bashir, kasancewar shi dan kaduna sannan Kuma Yana karatu a Abuja Babu wani Abu Dana sani, not even his picture, Haka shima Bai San komai a tare da Ni ba ban da abun da ya fada min a kanshi. Na manta cewar I can be criticized over my figure and looks, Amma gani nake mutanen da suke narrow minded su ne Suka damu da irin wannan abubuwan. Muna ta soyayya, Muna ta zuba kaina har akai hutu, wannan karon Kano naje, unlike sauran hutum. Tun da nayi wanka na tafi wajen Mamaa, Bayan mun gaisa naci abinci na karba wayar ta nayi logging 2go account di na. Kamar kullum kamar Kuma ko da yaushe Yana jira na online ya Kuma bar min offline message. BashPrince00: princess kinje gida lafiya? BinGin: nazo lafiya! Na Kuma samu kowa lafiya Ya turo min emoji me zuciya tare da fada min irin yadda yayi kewa ta daga lokacin da mukai magana karshe zuwa yanzun. "Ke Bintu murmushin me kike Yi?" Nayi saurin dagowa Ina tamke fuska nace "Ba komai!" Tace "Kije ki kwanta kiyi bacci!" Na Mike Bayan na amsa ta ba, na fice ba tare da na Bata wayar ba. I'm very busy with some stuffs here, I'm sorry for the late post [1/3, 20:27] Maman: BINTUN BATUUL Top-notch season 3 Ayshatuuu 013 Hakika soyayya wata aba ce me Dadi, duk yadda zuciya da baki zasu Kai ga kwatanta ta yadda feeling din yake bana tunanin zasu iya succeeding wajen yin hakan. Soyayya zata saka kayi duk abin da ka gama cika bakin ba zakai ba, kayi shi Kuma ka kasa gane dalilin da yasa kayi shi. A rayuwa ta nasan ban ji Dadi ba, nasan ni I was an example of mutanen da suka samu tabo cikin zuciyar su, Amma Kuma soyayya da nayi na Dan lokaci ta kasance wani likaci ne da naji dadin rayuwa, nayi cherishing kasancewar ta mutum Kuma mace. So, fast forward rayuwar na tafiya, Kun San wani lokacin idan ka Fara girma akwai abubuwan da zaka ga Yana raguwa, to Haka tsangwamar da ake min, caba min magana, punishing di na akan laifin da ba nawa ba. Abubuwan sun Dan lafa se yadda suke takura min akan kurajen fuskata, Adda ta kawo min wani magani na tube akan na dinga shafawa, na Fara shafawa Amma tamkar an sake watso min su akan fuska ta Haka sukai, da naje na fada Mata se tace min " Ba Kya using din shi correctly Bintu, idan kinsan munin da fuskar ki take karawa day by day da ba zakiyi Wasa ba" Jiki a sanyaye na dauki tube din na tafi Abu na, daga nan Kuma kullum se ta kwaba min nescafe da kwai da Kuma kurkum, kullum se naje na shafa kafin ta fita aiki, na yamma Kuma naje wajen Mamaa, kamar ibada Haka wannan mulke mulke da shafe shafen nake. Amma Kuma ko kadan Basu bar fuska ta ba, in fact Kara fesowa suke yi. Wani yammaci Ina kwance a daki, hutun mu ya kusa karewa. Ina ganin yadda ake Italian frosting dan already na Fara Saida cake da snacks duk da babu customers Amma dai a Haka nake Yi Dan hannu na ya fada. Tun safe ban ga Batuul ba, so duk tunani na taje gidan daya daga cikin siblings din mu. Se gata ta shigo kamar an jefo ta, na dago na kalle ta nace " Ban gan ki ba yau" Ta samu guri ta zauna gefe na, se Kuma ta Mike Wanda yasa na kalle ta Ina karantar yanayin da take ciki, she looks obviously nervous, ta tura kofar dakin sannan ta dawo ta sake Zama tare da Ciro wata Leda da ta kudundune a veil din ta. Ta Miki min, na saka hannu na amsa kwalin waya ne sealed ko bare shi baayi ba, na jujjuya ta Ina kallon ta, ban taba ganin wayar ba, ban ma taba jin sunan ba. Naga dai a jiki an rubuta iPhone 4S. Na dube ta Ina jiran Karin bayani Amma se Naga hannun ta kamar Yana tawa, cikin kwamtar mata da hankali na Kama hannun nata nace " Menene Batuul? Me ya faru?" Ta sake mikewa ta rufe window sannan ta Kara volume din food Network din da nake kallo tace " Bintu ki fada min abin da nayi is wrong ko?" Na kalle ta confused nace " Ki kwantar da hankalin ki, idan kina ganin Baki son disclosing maganar, Zaki iya rufe bakin ki" Ta girgiza min Kai tana sake ruke hannu na, tunda nake da Batuul ban taba ganin ta tsorata Haka ba, ita mutum ce me dakiya da karfin zuciya, akasin yau se Naga kamar an canja ta " Twin!" Kun taba Jin Batuul tace min twin? I can't remember idan ta taba fada gaskiya, na Kara Bata dukkan hankali na tace " I did a mistake! I was so stupid Bintu. Ya zanyi?" Na Fara kosawa, Nafi son ta fada min menene saboda zuciya ta wani irin bugawa take " To tsaya kiji Bintu, wannan wayar tayi wajen N200k..." "N200..?” Na katse ta Ina kwalalo idanu na waje, se Kuma na kalla kwalin wayar, wannan bitten Apple da na gani se ya tuna min I some how heard about wayar. "Waye ya Baki ? Suleiman ne?" Ta girgiza Kai ta Fara fada min Sunan shi Mahfuz, Bata San ko shi Dan waye ba, kamar yadda bansan Bashir Dan waye ba. Sun hadu through social media, if I can mention Facebook precisely. So suna tare duk da a gida tasan kowa Suleiman ya sani Kuma Suleiman zaa Bata, Amma wani lokacin mu Kan Yi wani Abu Wai shi black market, mu hada maza fiye da biyu ba tare da wani ya San da zaman wani ba. Suna ta soyayya se kwatsam jiya yace Mata Yana son ganin ta, kunsan dai Suleiman a gidan mu yake kusan dukkan al'amuram shi. Se ta nuna Masa hakan ba me yiwuwa bane ba, shi Kuma se ya nuna Mata ai haduwa da mace a gidan su old fashion ne, beside Yana son ta kawo Masa bedspread da Kuma snacks. Da farko ta nuna tsoro take ji Amma daga baya se ya yaudare ta da kalaman shi har ta dauki sabon bedspread din Adda, ta duba freezer ta kwashi snacks din da nayi ta soya sannan ba tare da kowa ya sani ba ta wuce ta same shi a wani top hotel a Kano. Shi ya fita ya Shiga da ita har dakin shi, sannan ya Fara Jan ta da hira har ta saki jiki, ya Bata juice Wanda tace min daga shan shi bacci ya dauke ta, Bata San me ya faru ba se Bayan azahar ta tashi, ta samu Kan ta Babu ko dankwali shi ne fa hankalin ta yayi mugim tashi ta Fara tuhumar shi da ko yayi Mata wani abu, yace shi ban da caressing gashin ta babu abin da yayi Mata, ta dinga shafa jikin ta to make sure cewar Babu wani Abu da ya cire a jikin ta, in fact shi Batuul tayi Masa kankanta. Tayi saurin gyara jikin ta, ta dakko dankwalin ta ta daura, shi ne ya Bata kyautar wannan sabuwar iPhone 4S. Na saki ajiyar zuciya me nauyin gaske nace " Batula Fatima Hamisu Ginsau! Wannan abin da kikai kuskure ne babba, kiyi kokari kada ki kara. Ina hankalin ki yake da yace kije hotel ki same shi?" Ta Kara kallona worriedly tace " Bazan Kara ba Bintu, nayi alkawarin ba Zan sake ba, Amma ya zanyi da wayar nan?" Anan fa ake yin ta, na rasa yadda Zan fada mata saboda nasan duk yadda muka Kai da boye boye akan wayar se gaskiya ta bayyana. A karshe dai bansan yadda akai ba har Batuul ta Fara amfani da ita ba, kawai Naga tana ta harkar ta da sabuwar wayar ta abin ta, Suleiman kadai ya tambayi yadda ta samu wayar se tace Masa mijin sajida ya aiki mata daga Lagos, shi kenan magana ta wuce kamar daukewar ruwa. Bayan na koma makaranta, Muka Shiga final year din mu, a wannan karon Bayan mun sake komawa gida na samu Kawu saboda career guide nace Masa " Kawu zanyi registering jamb, shi ne nazo nace maka wanne course Zan saka?" Ya Dan rage volume din radio din shi yayi kadan sannan yace " Ki zaba abin da Kika San Kan ki zai iya dauka, kinsan bana son failure a gida na" Na gyada Masa Kai sannan nace " Na saka architecture?" Yayi dariya yace " Waye zai iya architecture Bintu? Amma ba ke ba ko?" Na Dan Bata fuska nace " Zan iya Kawu!" Ya gyada Kai tare da fadin " Then carry on' Na fita zuwa dakin Yaya Auwal na fada Masa architecture zai cika min, da Kuma makarantar da nake so, ya danyi dariya yace " Bintu kin San menene architecture kuwa? Ke din ce Zaki iya wani architecture? To Ni Adda cewa tayi na saka Miki education na biology Kuma na Riga har na coke" Na dube shi wani Abu ya kawo min wuya nace " Biology education Kuma? Ni me yasa ba zaa ji raayi na ba? Haba Yaya" Ya shige ya barni a wajen, na koma daki kawai na Fara kuka, nayi me isata sannan na wanke fuska ta na karbo wayar Mamaa nayi dialing number BashPrince00 Wanda na Riga na haddace a Kai na. Ina magana yace "Princess me ya same ki? Kuka kikai?' Na gyada Kai na nace Ina Kara sakin wani kukan, ai se ya rikice gaba daya ya Fara tambaya ta abinnda ya faru, aikuwa Ina kuka na fada Masa duk abin da ya faru, se da nayi shiru yace " Are you sure zai iya architecture din?" Na gyada Kai na kamar Yana gaba na nace " I'm determined!" Se yace " To Ni Zan turo Miki kudi kije ki sake registration a nearby jamb office!" Nayi shiru Ina tunanin Anya kuwa na karba kudin shi? Ai Bai kamata ba, se na girgiza Kai na nace "A'a ka bar shi, I can't accept it!" "Saboda kin Raina ko? Me yasa kike min Haka ne Bintu? Baki dauke ni yadda na dauke ki ba ko? Kinsan yadda nake son ki kuwa? Ina Jin kamar akan ki I can move the mountain for you and I can melt the snow for you!" A take fuska ta ta cika da wani annuri me kayatarwa, bansan menene love language din ku ba, Amma nawa love language din is "words of affirmation" Ina son mutum constantly ya din ga tuna min Yana fadin how much I mean to him, yadda yake ji na cikin zuciyar shi, tamkar kuwa Bashir ya sani ko fahimta yayi he always does yadda nake so!!! Ta_kwalam ce BINTUN BATUUL, NAZNEEN da Kuma GEN NASIR ZAKI rubutu ne na kudi, Wanda N1300 kawai ta ishe ka subscribing... [1/3, 20:27] Maman: BINTUN BATUUL Top-notch season 3 015...Last free page Ayshatuuu *Kece me kallon mutane kice musu sun Yi kiba ko? Kece me kallon su kice ke Kinga ranar da kikai? Kun San illar bakin ku kuwa? Kunsan me maganar ki take jawowa?* "I finally got to see my BinGin" Ya fada Yana sake matsawa gefen da Samiha take, yayin da ko second glance Bai bani ba balle na saka ran zaiyi min magana. Wani irin Abu naji ya zamo min wuya na ya tsaya min tamkar an samo katon dutse an saka a gurin. Nayi shiru Ina kallon Samiha dake murmushi from ear to ear, na kalle shi ya lumshe idanun shi duk lokacin da wannan jijiyar ta goshin ta ta bayyana, there and then naji, I've lost this battle, wannan ba fadan da zanyi nasara bane ba, Amma se zuciya ta ke cemin " Bintu tafiya zakiyi? Ina Zaki je Baki fada Masa kece ba?" Se na tsaya saboda har lokacin Samiha taki tace ita ce BinGin, ta Kuma taki denying hakan, na cigaba da kallon yadda suke ma juna killer smile Kai ka rantse da Allah kace dama can sun San juna, kamar Zan Yi hakuri Naga gudun ruwan su, Amma a yau se hakuri na ya kare, na gagara yin hakan, Babu shiri nace Masa " Habiebie na!" Se ya juyo da sauri, I'm sure ya Gane murnar da Kuma salon da nake amfani da shi duk lokacin da Zan Kira shi da hakan, se Kuma ta juya ya kalla Samiha da murmushin fuskar ta ya Fara daukewa, ya kalle ni wani irin kallo na kada kice kece BinGin, na gyada Kai na nace " Nice Bintu Ginsau wato BinGin" "Kece?! How?" Ya fada cikin wata murya me wani irin amo, nayi shiru na rasa me zance masa, shima se yayi shiru yayun da nakan ga Yana stealing glance din Samiha wadda tayi shiru kamar ruwa ya cinye ta, ko kadan ban taba kawowa Samiha zata iya yin abin da tayi min ba, ko da Wasa ban taba kawowa hakan ba. A hankali yace " I'm sorry Bintu but..." Se yayi shiru ya kasa karasawa, Kun taba Jin bugun zuciyar ku ya karu har Kuna tunanin Anya wannan zuciyar tawa ba kokarin balls kirji na take ta fito ba? To Haka naji, I was so scared da zuciya ta ta kasa controlling bugun da take, nayi kokarin rike kirjina Wai duk kokari na, na kada zuciya ta ta fito " Bansan Haka kike ba, kiyi hakuri but you're not my type, bana son Mata masu *KIBA* " Ya fada idanun shi na Kan Samiha da lokaci daya murmushi ya Kara bayyana akan kumatun ta da fuskar ta. Na kalle shi sosae, na Kara kallon shi a Karo na biyu kafin Kuma na samu brain Dita ta Gama processing maganar da yayi min. Se na fahimci Yana nufin ni Bintu by type din shi bace ba, type din shi Samiha ce, beside baya ma son mace me kiba. Ai ina Gama tantance hakan ban jira wata magana ba, na juya na Fara wulla kafata, a wannan lokacin wallahi na manta cewar visiting akeyi, ko kadan na manta Wai hall din a cike yake da mutane, idanu na ba abinda suke gani, idan kuka dauke memory cells Dake taimakawa kowanne Dan Adam wajen tuna abin da ya Riga da ya sani, to bana tunanin Zan iya Kai kaina hostel. Na manta Wai bana son mutane, na manta wai bana sakewa idan mutane na guri, all that matters shi ne na kadaice. Ina zuwa hostel na Fara cire kayan jiki na, se da na cire tas na bar towel Dake daure a kirji na sannan na zumbula hijab na fita, Ina zuwa waje na samu drum ana Kone kone, a take na zuba dukkan kayan a ciki sannan na dawo, ba Wai Ina cikin hayyaci na ba ne ba, a lokacin I've completely lost my sense, bana cikin hayyaci na ko kadan. Ina zuwa toilet na tsaya gaban katon mirror Dake corridor kafin ka Shiga cikin toilet, nayi ta kallon Kai na, Ina juya Ina kallon tun daga fuskata down to my feet, Ina dadewa ban ga Muni na ba, Amma a wannan lokacin se Naga duk duniya Babu mummuna, Babu wadda batai dacen figure ba iri n, gani nake Babu wani Dan Adam da yafi Ni Bintu kiba a duniya, na wuce toilet na zauna saman toilet seat na Fara wani irin kuka Wanda har yau bana son na tuna wannan ranar " Shike nan? Ya Kare? Shike nan har an gama? Yanzun da gaske na barwa Samiha BashPrince00 kenan?" Kai a cikin zuciya ta nace Samiha ba zata taba yimin hakan ba, ba zata taba son abin da nake so ba...lol! I was too innocent, I was too softhearted, I was too kind-hearted also! Ban kawo ko wildest dreams dina Samiha zata iya son habiebie ba. To Amma se na ayyana ya akai har yanzun Bata biyo ni ba, kenan itama ta yadda ta Kuma karbe shi a matsayin saurayi To dai na Jima Ina kuka, kukan da yasa hanci na Fara zuba, kunne na ya toshe kamar kurma, sannan Kai na yayi wani irin nauyi kamr idan na tashi Zan Fadi. Ban dai na kuka ba se da naji hawaye ya daina zuba daga idanu na kafin na sakarwa Kai na ruwa na wajen minti na ashirin kafin na Mike zuwa daki, Ina zuwa na Fara karkarwa saboda sanyi da ke ratsa jiki na, hakora na suka Fara karkarwa kamar an saka ni cikin kankara. Haka na kudundune cikin blanket Ina wani irin karkarwar sanyi, ku tuna I was only sixteen years old, Kuma dama duk rayuwa ta na kasance bakin ciki kawai nake kunsa, Samiha da BashPrince00 su ne mutanen farko da na Fara samun solace wajen su, se gashi Ashe su ne zasuyi betraying di na, Kuna ganin kuwa Zan iya sake trusting mutane easily? Ai Abu ne me wuya. Ina nan kwance bansan har lokacin da na Kai a kwance ba, rufin asiri na period nake shiyasa har lokaci yayi nisa bansan karfe nawa bane ba. Ina nan a kwance inata kuka Ina Kuma karkarwar zazzabi. Se da hidaya room mate di ta ta shigo sannan ta ganni a Haka, cikin tashin hankali ta nufe ni tana tambaya ta abin da ya faru, Amma ganin halin da nake ciki kawai se taje ta Kira matron din hostel din mu, Suka dawo tare, sannan Suka taimaka min na saka Kaya suka kaini sickbay, ban ma dai San abin da ya faru ba na samu bacci me nauyin gaske ya tafi dani. Bani na farka ba se yamma can sannan akai discharging di na na dawo hostel Amma ko duriyar Samiha Babu a wannan clinic din har na tashi. Mamaki sosae nake yadda ta iya karkade idanun ta, but can kasan Rai na Ina Bata benefit of doubt, Ina ganin kamar abin da nake gani ba hakan bane ba, a Haka na karasa hostel Amma dakin su na Fara zuwa, na same ta da Yan dakin su sun baje Kaya suna kalla, it's down on me cewar kayan da ya kawo min ne. Da sallama na shiga Wanda yasa ta Mike tana kallo na tace " Ance Baki da lafiya?" Ban Bata wannan amsar ba nace " Ina son magana da ke please, can you step out?" Ina ganin yadda jikin ta yayi sanyi, se ta biyo ni bayan ta tattare kayan cikin Leda, se mamakin ta nake Baki bude, mamakin karfin halin ta da Kuma karshen rashin kunyar ta kawai nake gani, Amma Kuma har lokacin Ina ganin ba Haka bane ba. "Samiha..." Tayi saurin katse ni hade da fadin " Kinga Bintu, nasan Zaki ce ko na yudare ki, ko Kuma na Miki snatching Amma Kinga ba Haka bane ba..." "Menene Samiha? Ina kallon yadda kike mishi murmushi fa" Ta saki wani murmushin da ya sake Kona min zuciya tace "He chose me Bintu, a gaban ki yace ni ce type din shi ba ke ba, Kinga idan akwai me laifi Bashir ne bani ba. Ni kawai dama na samu Kuma na bi, so I'm not at fault!' "Dukka friendship din da mukai karya ne kenan? Samiha dama Haka zakiyi min, kinsan yadda nake son shi ko?" Se kawai ta girgiza Kai tace " Don't push yourself hard Bintu, kije ki aura daidai dake!" Wannan maganar ita ce tafi duka na a kaf abin da Samiha ta fada min, na juya a hankali na koma daki na lalubo waya ta na Fara Kiran shi, se da na Kira sau biyu ana uku sannan ya dauka, "Kaje gida lafiya?" Shi ne abin da na Fara tambayar shi, haushi Kuma na Fara ji bayan maganar ta fita daga Baki na. To Amma ya zanyi? Son shi nake Kuma bana tunanin akwai abin da zai canja wannan son, a hauka na fa! "Naje lafiya Bintu, kiyi hakuri abin da ya faru, I know I did a mistake da ban tambaye ki picture din ki ba, amma kiyi hakuri I can't continue with you!" "Ka Manta kace min fuskata doesn't matter, what matters is kyakyawar zuciyar da nake da ita, so it was all a lie..." "Ba Karya bane ba Bintu, I loved you wholeheartedly!..." "Then me kake Yi yanzun?" Yayi shiru ya kasa ce min komai se kawai na saki wayar ta fadi akan terrazzo flooring din dake wajen, nasan ta fashe, waya ta C2 ce da kawu ya siya min, na tafi na dakko katon Dutse tun karfi na na fasa wayar tare da taune sim din, meye ya rage? Meye Kuma amfanin wayar? Dama Dan shi nazo da ita, to it's all over then what's the essence? Ina nan tsaye Ina rike da kirji na dake zafi na hango Samiha ta fito da waya a kunnen ta, yadda kuka najr na shake ta Haka nake ji, Amma se kawai na juya zuwa daki. A wannan Daren kwana nayi banyi bacci ba, ga shi ni daya ce cikin dakin, wani irin dare ne na bakin ciki a gaba dayan rayuwa ta, bana fata wani ya dandana abin da na dandana a wannan Daren. Se komai na rayuwa ta ya Fara dawo min, tun daga Kan yadda Yan gidan mu suka ta tsangwamar ta Akan kiba ta, da yadda kowa ma idan na fita yake kallo na kamar wadda nayi laifi, se naga to ai bani da amfani, meye amfanin rayuwa ta gaba daya? Idan na cigaba da numfashi Haka Zan ta kullar bakin ciki, Dan Haka na mike zuwa locker ta na bude Dan lokacin shida na safe, Ina bude locker se ga kwalbar Dettol, a hankali dukda wasi wasi da nake Yi Amma na dauka Ina bude murfin...a Raina Fadi nake " Bari na mutu ko Zan huta da wannan rayuwar!!!" Har yanzun Wai bakiyi subscribing tafiyar top-notch season 3 ba? Kinsan kuwa irin fascinating stories din da Muka zo dasu? Wannan karon fa ba TSINTUWA bace ba, ba Kuma ASHRAF bane ba balle SANIN GAIBU! Magana ake ta GEN NASIR ZAKI, NAZNEEN da BINTUN BATUUL. N1300 kacal jama'a [1/3, 20:27] Maman: BINTUN BATUUL Top-notch season 3 Ayshatuuu 014 *Kina da kiba? Ko ke gajeriya ce? Ke siririya ce? Doguwa ce ko Kuma ke siririya ce? Are you being criticized saboda hallitar ki? To tsaya kiji wannan halittar, wannan kamanin uniqueness naki ne Wanda Allah ya Baki kyauta! Don't ever look down on yourself, it's your pride, don't body shame yourself* Shi ya biya min kudin sake registering jamb, zuwa yamma na shirya tare da saka Kaya na na fita, Ina zuwa aka ce min na makara sede na dawo washegari, Haka na dawo Babu yadda Zan yi Haka nan na dawo gida Rai na Babu dadi, washe gari da wuri na fita, kunsan mu a gidan mu muna da a bit of freedom, zaka iya fita ko baka tambaya ba, wannan shi ne kuskure na farko da iyaye ke Yi, Bai kamata ace yaro Yana da so much freedom ba, hakan zai Bata Masa tarbiyya sosae da sosae. Ko da naje wajen nayi generating remita da komai na biya, sannan na dawo da taimakon su a cafe din na cike komai nayi finger prints, Suka bani wasu books da zasu fito a English part. Ina kammalla na fito Ina kokarin tarar napep Dan komawa gida, wasu samari dake tsaye bakin titi, suna ta Hira, tun da na taho suke kallo na, kunsan Ni bana fita idan ba dole ba, bana kuma Shiga cikin mutane, ko yanzun da Zan fito Babu yadda Zan Yi shi yasa na fito. Ina tahowa daya daga cikin su yace " Kaga wata tana tahowa, kalli wata uwar kiba!" Har Wanda ma ba dasu yake ba dukka Suka juyo suna kallo na, a take na Fara Jin wani irin yanayi, kamar kasa ta tsage na shige, ko Kuma na ruga a guje na buya Amma Babu halin hakan tun da na riga da na taho. "Yanzun fa se tace ita budurwa ce, Ina salis shi ne me son masu kiba" Ina tunanin wannan shi ne salis din yace " Kaiiii! Barta dai yau waye zai aura wannan abun, ruguzaza!" Kunsan wani lokacin kana ji Amma se kaki ji, ka gani kaki gani. Akwai wani human instinct da mutum yake da shi, ability mutum ya saurari abin da yayi niyya. Haka nan na blocking kunnuwa na daga sauraran munanan kalaman su. Bayan na koma gida na tsaya a gaban madubi, Ina kallon Kai na, ta Ina Zan Fara rage wannan kibar? Ta Ina Zan Fara gyara wannan fuskar tawa? Me yasa nake muzanta cikin mutane. Kawai s na Fara kuka a gaban mudubin, nasan Ina da kiba, idan ka kalle ni dukka kiba ce amma to ya zanyi? Ta Ina Zan Fara? Rashin Sanin yadda zanyi yasa kawai na hakura na cigaba da muamula ta da BashPrince00. Ana Haka Muka koma makaranta mukai jamb, Kuma cikin hukuncin Allah se gani da over 200 score. Nayi murna na Kuma godewa Allah babu iyaka. A Haka dai Muka Fara waec Wanda yasa Muka Fara zaman extension. Wani dare mun Yi chatting da BashPrince00 yayi min albishir din zuwa ya ganni da weekend. Murna da na dinga Yi na kasa tsayawa har safiya tayi na bawa Samiha labari me dadi, a Daren na wuce dakin su na samu tana kwance tana waya, na zauna gefen ta Ina sakin murmushi Wanda tana gani tasan it's something to do with BashPrince00, Dan tasan shi kadai ke sani irin wannan farin cikin. "Bani labari! Me ya faru?" Cikin murna da zakwadi nace " He's coming on Saturday!" Na fada Ina jujjuya Kai na cikin farin ciki, tayi murmushi tace " Finally wata zata ga habiebie dinta" Nace " Wallahi! I'm so excited Amma Kuma tsoro nke ji" Na fada har tsoron Yana bayyana a fuskata. Ta Kara gyara zaman ta tace " Tsoron me kike ji? Why are you afraid?" Nace "Mhmmm! Idan yace ban Yi Masa ba fa? Idan yace nayi kiba da yawa fa?" Tayi murmushi tace " Ba zai ce ba, ai ke yake so ba wai jikin ki ba, Kuma ya yadda Yana son ki irrespective of kamar ki ko jikin ki. Kullum ina fada Miki BinGin you've a good heart, duk Wanda ya aure ki yayi nasara, your soul is beautiful kumma wallahi fuskar ki Bata da Muni, jikin ki baiyi Muni ba, kullum Ina fada Miki cherish what you have, shi wannan jikin da wannan fuskar kyauta ce Allah ya Baki. Kiyi alfahari da jikin ki, feel proud about it ki daina sunkuyar da Kan ki, kiba ba laifi bace ba!" Ina ma ace kowa yana tunanin da Samiha take, inama ace kowa mind din shi irin nata ne, Ina ma kowa idea din shi da view din shi akan kiba irin na Samiha ne. Kilan da ire ire na bamu ji rayuwa tayi Mana zafi ba. Har wajen daya Kuna ta shirye shirye da ita, a Karo na farko naji confidence a cikin rayuwa ta, naji cewar Nima mace ce Kuma I can stand out gaban kowa. Muna ta shiru har Saturday tayi wadda ta kasance ranar visiting, dama nace dasu Adda ba se sun zo ba duk wahala ne, Dan su akwai kokarin zuwa visiting, sun dauke shi kamar wani Abu daban. Nayi wanka wajen karfe goma, na shirya cikin goggen house wears di na, na shafa powder na saka khol tare da saka lip balm a lebe na, wannan Shirin da nayi is once in my life, bana saka powder saboda Ina ganin powder daban fuskata daban. Balle Azo zancen su foundation ko wani concealer, Tun ranar dana taba saka foundation zamu je biki Hadejia, na saka skirt da Riga na yafa veil irin yadda suke yafawa, Ina fitowa Zahra ta kalle ni ta tuntsure da dariya, dariyar ta ta janyo hankalin Adawiyya da tazo Dan mu tafi tare, itama ta Fara kyakyatawa " Wai Bintu waya ce Miki kiyi wannan kwalliyar? Kin taba ganin mutum yasa foundation ba irin skin tone din shi ba" Zuhriyya da ta gama waya lokacin tace " Ku bar ta dai ai, ita Abu ba kadan ba kiga wani yafen mayafi da tayi!" Gaba daya naji am humiliated, naji na kasakanta na Kuma wulakanta. Nayi shiru rooted to the ground na kasa moving an inch, suka cigaba da hirar su Akan kiba da yadda Basu son ko kadan suyi gaining weight. Kun San ranar wallahi Hadejia da banje ba kenan. Kuma tun daga wannan ranar ban sake ko da wasa shafa powder ba, ko da kuskure in fact wallahi make up stuffs di na dukka na tattara na bayar da su! A ranar saboda rashin confidence, kasa kallon madubi nayi, saboda kada Naga abin da zai saka na wanke fuska ta. Ina nan tsaye Samiha ta shigo da gogaggen house wears din ta, ba wani Abu ta shafa ba Amma tayi kyau sosae, se naji Ina tsoron kada muje fa ta kwace min habiebie. Se Kuma na kawar da wannan tunanin daga Rai na, a duk duniya Samiha ita ce wadda na Fara trusting, nake Kuma tsamannin ba zata taba ha'inta ta taba, aikuwa muka fita tare Bayan ta Gama "Ma shaaa Allah! Whoa! Wow! Kin gan ki kuwa BinGin, shiyasa nake cewa kiyi kwalliyya, Baki ga yadda fuskar ki tayi ba" Nayi murmushi Ina Jin Dadi tare da Jin wani nervousness na yadda haduwa ta da BashPrince00 zai kasance. A Haka dai muka tafi bayan ya Kira ya tabbatar min da zuwan shi. Muna tafe Ina haduwa da colleagues di na suna fada min nayi kyau ko dai BashPrince00 zai zo ne. Duk da ban Faye magana ba, ban Kuma faye shiga mutane ba Amma Ina yawan maganar shi har ta kasance Yan class din mu sun San shi, sun Kuma San yadda nake ji a tattare da shi. Visiting din mu a katon visiting hall ne wan da school ta ware domin hakan. Na Shiga ciki tare da Samiha Ina Jin wani irin yanayi saboda cikar mutane a gurin. Amma da ke kusa da Samiha nake I felt a lot relieved. Na wuce ciki Ina wuwwula idanun Inga ta inda Zan hango shi, ku kwace na San shi, wayar dake hannu na ta Fara vib, Cikin salo yadda wani ba zai gani ba na Kara a kunne na nace "Ban ganka ba" A hankali na hango wani can extreme a zaune, Yana waving hannun shi. A take naji dukkan jiki na yayi sanyi kamar an datse min gwiwoyi na Haka naji. Kunsan kalmar "elite?" Kunsan kalmar "butter?" To wadannan biyun su ne kawai kalmomi da zaa iya describing BashPrince00. Samiha ta saki murmushi tana rada min " Kai ba dai wancan shi ne BashPrince00 din ba?" Ni dai na kasa magana, har Muka karasa in da yake zaune, fuskar shi dauke da wani murmushi da kullum nake mafarkin gani, Ni kuwa na taba ganin namiji me dimple a rayuwa ta? Kai Anya kuwa? Inaga ban taba gani ba se Akan shi. Dimple din fa sosae fa Kuma both side, ba fari bane ba Amma kunsan caramel? Kunsan abin da ake cewa wancan caramel skin ne da shi? To Bari na fada muku caramel consist of butter, honey and sugar! Ku tuna irin sheki da shining din da caramel zaiyi, to kamar Haka skin din guy dinnan yake, ga wata gargasa da ta kayata wannan shiny skin din, ya zanyi na kwatanta muku BashPrince00 ni kuwa? Kawai jikin shi, kayan shi da komai nashi speaks of handsomeness, he's beautiful jama'a, ku manta ance beautiful is meant for girls, a'a fa yau fa shi ne kadai word din da zanyi muku kwatancen BashPrince00 da shi. Se murmushi yake da nake kallowa kasa kasa yayin da yake narkar min da zuciya ta. To Bari kuji kamannin Samiha, a'a ai na tuna na fada muku kammanin ta ai a other chapters, ta tunkuda ni Wanda yasa na Isa gaban shi babu shiri, na tsaya gaban shi Amma to my utmost disappointment hankalin shi da wannan murmushin Yana Kan Samiha... Wayyo ni BinGin! Kamar kullum kada ki Bari labarin BINTUN BATUUL, NAZNEEN da kuma GENERAL NASEER ZAKI ya wuce ki, kunsan dai tafiyar ba yau aka Fara ba, wannan season 3 ne! [1/3, 20:28] Maman: 016 Amma Kun San da gaske idan zaka aikata babban zunubi da gaske imanin ka tafiya yake, a lokacin da nake zaune gaban locker da Kuma kwalbar Dettol a hannu na, gaba daya bana ji bana Kuma gani, kawai abin da subconscious mind di na ke fada min, Bintu Ginsau kisha, kada ki tsaya, gwara ki kashe Kan ki ki huta da wannan bakin cikin, idan kin mutu ma Babu Wanda zai damu, Babu wan da zaiji wani Abu. Wannan zuga da zuciyata tayi min yasa hannu na na rawa na balle murfin, without any second thought na bude Baki na na Fara kwankwada, se da na Sha wajen rabi sannan na Fara Jin wani hautsinawa da ciki na ya Fara, na yarda kwalbar a kasa na sulale Ina wani Abu kamar me fitting. Ban San minti na nawa na dauka Ina Jin wannan azabar da Kuma ciwo ba, Amma saboda yadda zuciya ta tayi tauri ko neman taimako banyi ba, cikin hukuncin Allah se ga lubna wato roommate Dita ta shigo daga dakin kawar ta in da take zuwa kwana, wani irin salati ta saki lokacin idanuna rufewa suke Amma Ina kokarin bude su, ta karaso waje na tana fadin " Bintu! Bintu!! Bintu!!!" Ina Jin ta Amma na kasa dagowa balle na amsa, ta fita da gudu, only God knows minti na nawa ta dauka suka dawo ita da Senior prefect, house captain, Matron da Kuma Hall admin da ta shigo coincidentally. Ni dai bana ce ga abin da ya faru ba, Ashe suna.zuwa Hall admin ta Kira senior master Akan lallai a turo bus akwai emergency a hostel, Suka kalla kwalbar Dettol din dake gefe na anan suka tabbatar abin da na Sha kenan. Lubna ta dakko cup ta zazzago madara ta kada ta taho Dan bani, Amma se aka hanata akace ta Bari asibiti zaa je Dan na Riga da nayi loosing consciousness di na. Haka muka tafi asibit ko sick bay baa tsaya ba, cikin gaggawa aka karbe ni a emergency unit din su, cikin lokaci principal da vice suka karaso asibitin lokacin har an saka min tube ta hanci na zuwa Baki na zaayi draining Dettol Dake barazanar dauke min rauyuwa, se da aka kwashe tsaf kafin akai min abin da ake cewa daurayar ciki, Bayan an Gama sannan suka zauna da principal wadda hankalin ta a mugun tashe yake har lokacin. " Wannan ya nuna she wanted to commit suicide!" "Suicide doctor?! Suicide fa? Innanlillahi wa inna ilaihil rajiun!!" Ta fada hankalin ta a mugun tashe, Doctor din yace " So Kun fahimci ko tana da wani problem mentally? We need to invite her parents" Principal tayi shiru tana kallon Doctor din, ku kwayi tunanin amsar tambayar akan fuskar shi take a rubuce, se can tace " Ban San ta sosae ba, Amma room mate din ta tace dama Bata Shiga mutane since js1, she's always alone and lonely!' Doctor din ya sake rubutu sannan ya kalla principal yace " Ya kamata tuntuni ki gane me yake damun ta da har Bata shiga mutane, dukda banyi concluding ba tun da banyi magana da ita ba, Amma Ina tunanin yarinyar nan na fama da depression" "Depression again? To Doctor aside this. Tambayar da nake so batu maka shi ne ya jikin nata, Dettol din Bai bar Mata matsala ba?" Yayi dogon numfashi sannan yace " Eh daga yadda kukai saurin kawo ta, bana tunanin complications din me yawa ne, zamu jira zuwa ta farka sannan tayi hoto mu gani" Haka Suka Jima suna tattaunawa kafin principal ta fito ta samu vice tare da ce Masa ya Kira guardians di na da sauri. Haka ya koma school lokacin kusan kowa yasan abin da ya faru, Samiha dake bacci tashin ta akai aka fada Mata, wani irin zabura tayi tace "Dettol? Dettol fa? Bintun?" Ba karamin tsorata tayi ba, da Kuma gigita ba, tayi shiru tana pouncing akan gadon ta, tare da tunanin possible abin da zai saka ni Nasha Dettol, ita Baki daya ma ta manta what transpired tsakanin ni da ita da Kuma Bashir. Amma ni ta Ina Zan taba manta abin da sukai min. Kira sosae akai yiwa Kawu amma bai dauka ba, se kawai suka samu contact din Adda, suna Kira Babu jimawa ta dauka, a lokacin tana garin Abuja tazo wani conference da Nursing and midwifery council of Nigeria ta hada musu a matsayin ta na director school of nursing Kano. Sun Gama suna kokarin tafiya airport zuwa Kano, wayarta dake cikin jaka ta Fara kara, dole ta tsaya ta fito da ita tare da karawa a kunnen ta, bayan sun gaida tayi inquiring me magana, yayi saurin bata hakurin rashin gabatar da Kan shi da yayi tun farko kafin yayi Mata bayani hadi da cewa "Daga school din su Fatima Bintu Ginsau ne, Bata da lafiya sosae, Muna bukatar one of her Guardian to be in school please!" " Me ya samu Bintu? Me yake damun ta? Is she conscious? Subhannallah!!!" Ta fada ta Fara rikicewa, ni ba mutum bace ba me jinya, Dan Ni kowa yasan bana rashin lafiya, ko nayi ma sede ka gani Amma ba Zan fada ba, so Adda tasan duk abin da ya kayar da Ni lallai abun kallo ne. " Ki kwantar da hankalin ki Hajiya, tana da Rai Amma dai ya kamata ki samu kizo ko zuwa gobe ne!" Ta duba golden wrist watch din da ke daure a hannun ta na dama, se lokacin ma goma na safe tayi, Dan Haka tace " Yanzunnan Zan Yi catching next flight to Niger" Daga Haka ta sauke wayar ta nufi sauran directors din ta fada musu zataj canceling flight din ta zuwa Kano saboda rashin lafiya ta, dukkan su sukai Mata addua tare da tambayar ta ko tana bukatar taimakon su, ta girgiza Kai tare da musu sallama ta tafi yankan ticket, Allah ya taimaka ta samu, bayan ta zauna a lounge ta Fara Kiran Kawu amma bai dauka ba, se ta Kira Yaya Auwal da suke tare da kawu a kasuwa, shi ya kaiwa kawu wayar bayan sun gaida ya tambaye ta lafiya? Saboda yadda yaji muryar ta, cikin rashin Jin Dadi tace " Bintu ba tada lafiya sun Kira Ni daga makaranta, yanzun Haka ma can Zan wuce!" "Me ya same ta?" Ya tambaya Haka kurum yaji gaban shi ya fada "Ban sani ba yallabai, Amma dai jiki na na bani she's definitely in critical condition! Daga yadda vice din su ke magana!" Ya Kara sakin salati Yana tambayar ta ko ta samu tickets din? Tace ta samu amma duk yadda suke ciki zata Kira shi a waya! I was so busy wallahi yau dinnan, so nace Bari dai muyi taba ka lashe! [1/3, 20:28] Maman: 017 Tunda Adda take bata taba ganin doguwar tafiya irij daga Abuja zuwa Niger ba, duk da a zahiri tafiyar ba wata bace ba Amma saboda how anxious and eager she was taje taga halin da Bintu ke ciki yasa duk ta gaji ta koma kosa tare da ganin kamar a mota take tafe ba jirgi ba. Addua kala kala Babu wadda batai ba akan Allah yasa Bintu kada ta mutu, Allah Kuma yasa ba wani mummunan abun bane ba ya samu diyar tata ba, tayi hasashen duk wani possible rashin lafiya da Bintu zata iya Yi cikin kankanin lokaci, Amma ko kadan Bata kawo Bintu zata iya Shan Dettol ba Dan ta dauki rayuwar ta. Ko da ta isa cab ta samu Wanda ya Kai ya har asibitin bayan tayi communicating da vice ya bata address din asibitin da suke. Tana sauka gaban katon building din da aka rubuta Accident and emergency department! Ta sake Kiran shi tare da sanar Masa isowar ta, Babu jimawa se ga shi yazo, ba wani gaisawar kirki sukai sosae ba, saboda kana kallon ta kasan ba a nutse take ba. Suna shiga an fita da ni zuwa hoton makogaro da Kuma na ciki saboda a duba ko an samu chemical erosion a wuraren da Dettol din ya taba. Kafin na dawo Suka samu Zama ita da principal din " Mun taso ki ko?" Adda ta girgiza Kai cikin damuwa tace " Ai ba yadda zaayi, Amma me ya same ta" Principal ta gyara zaman ta, ta Fara ma Adda bayanin dukkan abin da ya faru, Adda tayi shiru in a total and complete shock. Se da tayi wajen minti na hudu bakin ta a rufe da hannun ta sannan ta sauke hannun tace da principal " How's she? Ya jikin nata?" Kafin ma principal din ta Bata amsa aka sake turo ni akan wannan gadon na asibiti Mai Kama da stretcher, tayi saurin mikewa tare da nufo ni, tana zuwa ta rike hannaye na, lokaci daya fuskata ta zabge nayi wani kuyas da Ni. A hankali na bude Baki nace " Adda sannu da zuwa!" Ta kasa magana kawai Naga tana kuka, se na lumshe idanu na Ina Jin wani irin radadi cikin zuciya ta, ya akai ban samu na mutu ba, ya akai Haka? Hawaye ya gangaro min daga rufaffun idanu na zuwa kunci na, abun bakin cikin bayan ban mutu ba, ban Kuma Yi nasarar cutar da ki na ba, Dan tun a radiology department din, radiographer yace da Doctor di na babu matsala, Dan mild erosion ne Wanda in no time zai warke da magunguna. Bayan na koma gado ya rage daga ni se Adda a daki, wadda ta Gama waya da kawu tana fada Masa jikin nawa da sauki " Bintu fada min me ya ke damun ki da har kikai kokarin kashe Kan ki" Nayi shiru bance komai ba, why is she even asking Bayan Bata taba tambayata ko Ina lafiya ba, ko Kuma tace min kibar dake jiki na ba komai bace ba, it's Allah's way of making me unique and different, Amma se ta Bari ake musguna min akan laifin da bani da shi, laifin da ba nawa ba, tana kallo Bata Hana ba, in fact kamar kunyar nuna ni take matsayin diyar ta. "Bintu talk to me! Kina da uwar da ta wuce ni? Ki fada min abin da yake damun ki" Nanma ko bude idanu na banyi ba, zuciya ta tayi nisa wajen hasaso min wata rayuwa ta daban, da duk bani da kiba, da duk ba mummuna bace ba da BashPrince00 Bai guje ni ba, da Samiha batayi betraying di na ba. Har Adda ta Gama zamanta likitan ya shigo, Ina Jin shi Yana Mata bayanin depression ke damu na, ya Kuma kamata su nema min therapy session idan ba Haka ba to watarana zasu ga na kashe Kai na tun da na Fara gwadawa kuwa! Hankalin Adda ya sake tashi, tayi ta kuka kunsan dama nace muku ita saurin kuka ne da ita, Amma kunsan menene, zuciya ta ko gezau na tausayin Adda ba tai ba, Ni buri na ma ta fita a dakin na hango wani syringe da Zan bula jijiya ta da shi, nasan da zarar jini ya fita da yawa a jiki na to Zan mutu kowa ya huta, Nima na huta da bakin cikin da nake ciki. Zuwa la'asar kawu ya karaso, anyi anyi na karba ruwa ko wani Abu Amma fur naki, bana ma magana balle wani ya saka ran Zan saurare shi, tun Adda na lallaba ni har katsinancin nata ya Mike ta Fara min masifa, nan ma dai Babu mafita, se kawai ta samu guri can gefe ta zauna ta zubawa sarautar Allah idanu, ta barni nayi duk abin da nake ganin daidai ne. Zuwan kawu ya saka ta Jin dadi a zuciyar ta, tare da ganin idan ita na Raina ta ai shi zanyi magana. Amma shima shiru me da ya takura ni kawai se na Fara kuka. Duk me ya janyo hakan? Duk me yasa na Zama hakan saboda bakin mutane, saboda mutane Basu gajiya da fadar abin da Bai kamata su fada ba, saboda mutane suna Shiga sabgar da Bata su ba! A Haka nayi kwana biyu, cikin hukuncin Allah na samu sauki, Kuma a ranar na ke paper ta ta karshe ta waec, Dan Haka daga asibiti naje na rubuta, na koma hostel hada Kaya na. Babu Wanda na kula se de amsa da sauki, Ina Gama hada Kaya ko graduation ban tsaya ba muka tafi Kano. Muna zuwa na yiwa Adda da kawu sannu sannan na shige daki na kulle! *** Komai da ya daganci Zainab se da ya kasance a tafin hannun Imam, Yana da network of information a cikin campus yadda Baku tunani, Amma saa daya da akai shi ne Yana da kokari, a ajin su bashi da na biyu, shiyasa ake overlooking rashin Jin shi. Zainab ta tashi da wurwuri saboda tana son wucewa school, tayi wanka ta samu noodle da tea taci sannan ta shirya cikin olive green Abaya me adon Baki a jiki, ta hada books din ta tsaf sannan ta dauki Jakar ta fito, tana tafe tana waya da jaddar ta wadda ke fada Mata yadda tayi kewar ta, da Kuma tambayar ta har wani lokaci ta dauka Zama a wannan kasar turawan. Zuciyar ta fes saboda a watan da ya gaba ta ba karamin takura Mata Imam yayi ba, har karamin hauka ta so tayi Amma shi ko a jikin shi, jiya dai tayi Masa warning akan idan ya sake biyo ta zata Kai shi Kara student affairs, to a tunanin ta yau ba zata gan shi ba. Zainab tayi murmushi daidai fitowar ta da ta daga gate din apartment din nasu, wannan murmushin da tayi a daidai Kan idanun Imam dake zaune cikin mota Yana kallon kofar da zata shigar da Kai in anticipation of her. Yayi saurin balle murfin motar ya fito, lokacin ta Fara takowa Dan fita Amma Kuma hankalin ta baya Kan shi, Bata ma lura da wanzuwar wani bawa a wajen ba, magana kawai take da jaddar ta wadda ke saka ta dariya da ba kasafai take ba se idan suna wayar da jadda. Dariyar da take ya saka shi shagala Yana kallon ta tare da kiyasto abubuwan da dama Wanda Baki ba zai iya fada ba se zuciya. Tana sauke wayar ta Fara kokarin tafiya, anan be yayi saurin Shan gaban ta Yana sakar Mata wani killer smile, ta dauke kan ta, tare da kokarin rabewa ta gefen shi ta wuce Amma Bai Bata wannan damar ba yace " Haba Zainab, tun 6am nake zaune Ina jiran ki sannan kizo ki wuce. At least ko hi Kya cemin" Ta kalle shi ya girgiza Kai tana kokarin sake wucewa Amma Dake Imam Imam ne se da yasan yadda akai yayi Mata magana har Kuma karshe ta shiga motar shi. Har department din ta, Kai har lecture hall ya Kai ta, se da ta zauna gurin ta ya samu wani yaron shi ya bashi Amana kafin ya tafi bayan ya Gaya Mata zaiyi missing din ta sosae. Kawai se ta samu kanta da dariya, saboda da gaske kawai kallon me tabin hankali take mishi. Tana Gama lecture ta fita Dan zuwa library kamar yadda ta saba Amma ga tsananin mamakin Zainab, Imam na kofar aji Yana jiran ta, wani irin yanayi taji har tace Masa " Baka da lecture ne?" Ya girgiza Kai yace " Ina da akwai of course.." "Then why are you here?" Ta tambaya curiously tare da kallon shi da idanun ta masu sheki. Se kawai ya duburburce ya fara stammering. Ganin Haka ta wuce abin ta ta bar shi tsaye, Amma kafin ta karasa ya samu shortcut ya karasa Yana tsaye kofar library Yana jiran karasowar ta, tana isowa taja ta tsaya tace " Kai aljani ne? You're stalking me I'll report you!" Maimamkon ya Bata amsa ko ya Bata hakuri se gani kawai tayi ya tsugunna ya Kuma Ciro wani Dan karamin box ya bude a take wani glittering ring ya bayyana a ciki, zainab ta bude idanun ta tana Jin wani tingles a cikin zuciyar ta, ya Kuma Miki Mata bunch of white roses tare da fadin " Zainab, please be my life partner! Marry me zainab!" Aka Fara ihu saboda taruwar student a wajen, se tafi suke suna hailing Imam, wasu Kuma na fada Mata tace yes! Ta kalle shi, ta Kuma kalli abubuwan dake hannun shi, he looks so sincere and cute. Tana murmushi a hankali Wanda Imam ke matukar kauna tace kamar whisper "Yes!" Bintun Batuul is not free! Contact me for payments. [1/3, 20:28] Maman: 018 Wani lokacin bamu Sanin yadda ake zuciyar mu Kan Fara son mutum, wani lokacin se mun gama cika Baki akan " Ni kike tunanin zanyi soyayya da wane? Allah ya kiyaye, Allah ya rufa min asiri" wannan shi ne yawancin abin da muke fada, Bayan min Mata Allah yake controlling zukatan mu, shike saka so a lokacin da yayi niyya. Beside wannan ita zuciya wata shu'umar halitta ce, munsan kwakwalwa ke controlling duk wani sassa na jikin Dan Adam, kowanne organ na functioning ne da izinin brain, Amma akan soyayya se kuga zuciya ta aiwatar da Abu ba tare da kwakwalwa ta ankare ba. Wani lokacin kiyayya ta Kan rikide ta koma kiyayya, yayin da mafi Muni shi ne ganin masoya sun Zama Makita, wannan Abu ba karamin tada hankalin mutane yake Yi ba. Zainab ta kasance Bata fiye kaunar duk wani Abu da ya shafa Imam ba, saboda yadda yake rayuwa ya banbanta da yadda take tata, Amma ku kalla how much yadda ya dinga kula da ita yasa ta karkato har ta bashi damar Shiga cikin zuciyar ta. She was so excited da ganin wannan zoben, ga roses, gashi Kuma a tsugunne a gaban ta Yana tambayar ta ko zata iya auren shi? Ta kalla fuskar shi me dauke da wani irin kasaitaccen murmushi da zaiyi wahala ka kalla baka ji zuciyar ka ta narke ba, Abu ne me wahalar gaske. A take taji ko Ina na zuciyar ta ya amsa, taji wani irin blood rush cikin jikin ta Baki daya, har Bata san ta Fara yelling " Yes! Yes!!" Ba, a take kowa dake gurin suka Soma tafi, da yawa abun ya burge su, yayin da ya Zama akasin Haka ga wasu,, suna ganin how foolish she's ta Fara kula wannan spoilt and rotten brat din! koma dai menene zainab bata damu ba, abin da ya dame ta shi ne Allah ya amince tayi rayuwa tare da Imam. Kowanne labari akwai farkon shi Kuma da karshen shi, karshen labari farkon wani labarin ne. Haka yake a dukkan rayuwar mu. Fatin ciki marar misaltuwa ne ya bayyana a Kan fuskar Imam, duk irin kyautatawa da stalking din ta da komai da yayi gani yake she's too good and too decent for him, Amma ga mamakin shi se Allah cikin sauki ya karkato Masa da zuciyar ta har ta karba soyayyar shi, mikewa yayi tare da kokarin Kama slender but long fingers din ta Dan zura Mata ring din dake hannun shi Amma Taki hakan tare da karba daga hannun shi tana murmushi ta zura a index finger din ta tana sakin kayataccen murmushi me kwantar da hankalin Wanda ake yiwa. Daga Haka ta fasa Shiga library din sannan tabi Bayan shi kamar yadda ya bukata, Suka cigaba da tafiya zukatan su fari Kal Babu wani diso na bacin Rai, se da suka samu wani shade sannan suka zauna, bayan sun zauna ya dube ta har lokacin ya kasa cewa komai, he's so short of words! "Zainab! Ina son ki, bansan wanne irin so nake Miki ba, Amma zuciya ta yearns for you!" Tana murmushi cike da Jin kunya ta fur ta a hankali kasan numfashi tace " I love you too!" Hakan ba karamin Dadi yayi masa ba, anan ya dube ta Yana tambayar asalin labarin ta, duk da yasan da yawa daga cikin labarin daga bakin Murad, Amma dai zai so ace yaji daga bakin ta. Cikin nutsuwar ta ta Fara fada masa labarin ta kaf da dalilin zuwan ta kasar nan Dan karatu. Se da ta gama sannan yace " Kina ganin Zaki iya convincing jadda har muyi aure?" Se ta Ciro wayar ta ba tare da ta amsa ba, bugu biyu jadda ta dauka tana amsa gaisuwar ta cikin larabci, ta danyi shiru tana Wasa da yatsun ta kafin can dai saboda tambayar da jadda take Mata na fatan dai lafiya take, ta amsa eh Amma tana son gabatar Mata da wani, Jin wanin da ta fada jadda ta saki murmushi tana godewa Allah wannan kyakyawan labarin da taji daga bakin jikar tata. Ta so kwarai ta dawo gida ta samu wani Dan Qatar tayi aure, ba Wai ta samu a UK ba, but does that even matters? It doesn't as far as ita din tana son shi to magana Kam ta Kare. A wannan lokacin Bata kashe wayar ba se da sukai magana da Imam duk da an samu tangarda sosae, wato communication barrier. Shi Yana Jin turanci Amma babu larabci yayin da take jin larabci Babu turanci, karshe dai se zainab ce ta zame musu interpreter! Suka gausa tayi Masa tambaya sosae akan shi da kasar shi, Jin shi Dan Nigeria yasa ta Fara tambayar shi ko iyayen shi zasu amince ya aura zainab din? Se ya nuna Mata bashi da matsala da parent din shi,duk da a kasan ran shi yasan ba Haka bane ba, yasan iyayen shi mutane ne masu kabilanci, mahaifin shi ya fada Masa duk lokacin da zaiyi aure zai Nemo bafulatana yar uwar shi ya aura, to fa se gashi balarabiya ya samu wadda ba Yar kasar su ba, ba Kuma yaren su daya ba. Haka rayuwar su ta cigaba da tafiya gwanin ban shaawa, soyayyar su zata saka kaji kaina kana son ka samu me son ka, yadda yake Mata yadda yake kula da ita da yadda kokarin canja salon rayuwar shi duk saboda ita, Abu ne da kowa ke fatan samu Kuma zainab ta samu. Shudewar wasu watanni, jadda ta sake tuntubar su ko suna tare har lokacin zainab ta tabbatar Mata se abun da yayi gaba ma, wannan yasa jadda tace Mata " Na yarda Dake zainab, na Kuna yarda da tarbiyyar da mukai Miki, sede baka shaidar zuciyar da ta Fara soyayya, Ina ganin idan iyayen shi sun yadda ko zakuyi aure kawai, hankali na zaifi kwamciya" Imam Dake karanta translation din wayar da zainab ke yi, ya saki murmushi tare da mikewa ya daka tsalle, zainab ta Harare shi tana fadawa jadda zata ji daga bakin shi. Ko kunsan a yammacin wannan rana Suka Isa masallaci aka daura musu aure? Shike nan Imam ya Zama miji ga zainab, zainab ta Zama matar Imam! Sede duk wannan abun da sukai Babu wani mutum daya daga bangaren Imam da yasan abin da yake faruwa!!! *** Yadda daga Adda har Bintu, har Kawu kowa ya shige dakun shi ba tare da ya ce wani Abu ba ya bawa Mamaa tsoro, saboda ya kamata suyi bayani akan abin da ya faru, ta fito saboda tasan hankalin ta a tashe yake, ta shiga dakin Adda ta samu tana kokarin Shiga wanka, tana ganin ta ta Dan saki fuska tace " Sannu da gida Mamaa, na shigo a gajiye zanyi wanka ne!" Yadda Addan ke dauke yasa Mamaa Sanin tana bukatar kadaici se tayi Mata sannu da zuwa kawai ta wuce wajen Kawu, tana fita Adda ta kulle dakin tare da komawa ta zauna ta dakko wayar ta, ta Fara Kiran Fadima, kamar yadda kuka sani Yaya Fadima ita ce babba a wajen Adda, Kuma tana aure a sokoto da yaranta. Bayan ta dauka suka gaisa da Adda wadda muryar ta har rawa take Yi, tace " Adda Abu ya same ki ne? Ko wani abun ke faruwa a gidan bani da masaniya?" Adda se ta Fara kuka tana fadin " Fadima Bintu ce! Bintu..." Hankalin Yaya Fadima ya tashi, duk da tana kokarin dannar kanta Dan ta samu ta kwantarwa da Adda hankali " Me ya faru da BINTUN? Ina ce tana makaranta" Wannan karon kukan na Adda karuwa yake tace " Bansan me ya faru ba a makaranta, har ta Sha Dettol zata kashe kanta, se da ta..." " Ita BINTUN? Innanlillahi wa inna ilaihil rajiun! Ya rabbul alamin" "Ita dai fa Fadima, ya zanyi yanzun anyi ruling depression!" Shiru ya biyo baya saboda Tsabar yadda Yaya Fadima ta kadu, se Kuma tace " Ki daina kuka Adda, Amma kiyi hakuri laifin ki ne! Tun farko Baki dauki Bintu kamar Yar ki ba, kin Bari kowa Yana cin Kashi a kanta ko wannan kadai ya Isa Bintu ta samu depression har ta Kuma samu suicidal thoughts!" "Na sani, nasan nayi kuskure Fadima amma bansan ya zanyi na gyara ba, bansan yadda Zan Fara shawo Kan matsalar Bintu ba!" Cikin rashin Jin dadi yaya Fadima tace " ki nutsu tukunna, sannan ki huta, zuwa dare ko safe se muyi magana, Amma kiyi ta Mata addua" Daga Haka sukai sallama sannan ta Shiga wankan saboda kanta Dake ciwo. Kawu Yana kwance can cikin bedroom lokacin da Mamaa ta shig, ya juyawa kofa baya tare da yin likimo tamkar me yin bacci, Amma ba baccin yake ba ko kadan tunanin Bintu kawai yake, tausayin ta da Kuma Jin haushin Kan shi Akan halin da yarinyar take ciki, wanne irin sakaci yayi har yarinyar ta Shiga mawuyacin Hali take Kuma kokarin saukar rayuwar ta? Haka ta fito jikin ta a mugun sanyeye, se ta wuce waje na. Ina zaune akan gado da wata sabuwar Reza a hannu na Ina kallon hannu na ta wajen da na San radial artery di ta na nan! Ta-kwalam BINTUN BATUUL, NAZNEEN da Kuma GEN NASIR ZAKI is not free, do contact us for payment details! [1/3, 20:28] Maman: 020 BAYAN WATANNI UKU! Cikin karamin apartment din su dake dad da makaranta, Wanda tun bayan shaida auren su day Kuma shagulgula da colleagues din Imam suka hada masa na taya shi murnar auren burin zuciyar shi, se Kuma yaran shi da sukai raising makudan kudi Suka Kama Masa wannan apartment din da ya zauna da zainab din shi. To fa duk wannan halin da ake ciki Imam ko da Wasa, ko da subul da baka, Bai taba fadawa wani makusancin shi a Nigeria ba, duk abin shi Yana shakkar kakan shi Wanda shi din baya Wasa, duk da tsufa da girma Amma Bai Bari wani ya taka authority din shi ba, har a wannan lokacin shi ke da ragamar komai na family business din su. Imam na daga cikin kalilan din jikokin da Alhaji Gidado ke so, tun Yana jariri yake son shi, Salma Kuma cousin din shi ce wadda iyayen su maza suke immediate. Alhaji Gidado nasan Salma kamar yadda yake son Imam, ko da zai taho nan UK karatu se da Alhaji Gidado ya tabbatar masa idan ya dawo bashi da wata matar aure da ta wuce Salma, to ya zaiyi ko dai yayi naam cikin dadin Rai ko Kuma yayi cikin bacin rai. Amma ganin zainab se da ya ruguza Masa dukkan wani lissafi da wani tsoron Alhaji Gidado da ke zuciyar shi. Kwance zainab take akan gado, idan ka kalle t se kayi tunanin she's lifeless saboda uban aman da tayi da ya saka jikin ta saki kamar mataciyya! Ya shigo daga waje bayan ya dawo daga makaranta, da mamakin ganin Bata living room kamar yadda ta Saba idan ta riga shi dawowa, zata zauna ta jira shi har lokacin da zai dawo ta tarbe shi. Wani lokacin Kuma zata zauna gaban class din su har se ya kammalla lecture din shi kafin ya fito suyi trekking zuwa gida, soyayya iya soyayya, kauna iya kauna shi ne kawai abinda ke fitowa daga gurin su, ko minti uku kayi tare da su se ka fahimci yadda suke ji game da junan su, tun zainab tana kunyar yadda yake Mata ko a gaban mutane ne, har ta dawo Bata damuwa, itama ta Fara nuna mishi yadda take ji game da shi. Karasawa yayi ciki, cikin sauri ganin yadda take kokarin tashi ta zauna Amma Abu yaci tura, ta Fara kokarin tashin se taga idanun ta sun rufe se ta koma jagwab Kan gado. Wannan ya tayar masa da hankali balle da ya karasa inda take kwance ya ganta kamar mataciyya se hankalin shi yayi mugun tashi, ya Fara kiran Charles akan yayi saurin kawo Masa mota, ko veil Bai yafa Mata ba Haka ya dauke ta cilak yayi waje da ita, suna zuwa asibiti aka Fara bata taimakon gaggawa, a kankanin lokaci Suka tabbatar masa ciki ne a jikin ta na kimanin wata daya, yayi murna kwarai da gaske Dan dama abin da yake ta jira kenan ya samu weapon din yakar kakan shi ya amince da zainab a matsayin matar shi, yasan auren Salma Babu makawa zai aure ta Amma fa zainab kadai zuciyr shi ke so. Ganin yadda take Shan wahala se duk jikin shi yayi sanyi ya fara Jin Anya zai iya barin ta ta cigaba da Shan wannan wahalar? Haka dai ya bar ta har zuwa lokacin da ta Dan samu karfin jiki wato da daddare, ya zauna Yana yanka Mata apple da tace tana son ci, a hankali take taunawa kamar Bata so saboda bakin ta babu Dadi " Solace!" Ta dago ta kalle shi tana taunawa kamar Bata so, ya sake rike hannun ta yace " Solace mun samu Baby, you're pregnant! Are you happy?" Ta tsira Masa idanun ta masu haske da Suka Dan rine saboda wahalar da ta Sha, kamar so take ta gaskata abin da yake cewa, ita din da gaske take da ciki? Ita din ce baby yake kwance a cikin ta, Kuma Babyn ma na Imam, farin cikin rayuwar ta? Se hawaye a hankali ya Fara trickling Mata Kan kuncin ta, she was so happy, she was so elated har Bata san tana kuka ba. Amma kallon da yake Yi Mata yasa tace "Ba wani Abu bane ba, I'm just overwhelmed ne!" Se ya saki murmushi Yana rungume ta a jikin shi yace " Nayi tunanin Baki son cikin ne, har na tsorata" Ta girgiza Kai ba tare da tayi kokarin dauke hawayen ba, in fact se ma bari da tayi suka cigaba da zuba daga idanun ta, a hankali kamar whisper tace " Chum! Ina cikin farin ciki, Wanda ba Zan iya misalta maka shi ba, I'll be able to carry the fruit of our love" Yayi murmushi na Jin Dadi tare da shafa Kan ta. A Haka wannan masoyan Suka cigaba da rayuwa tare da rainon cikin su, sede cikin wahalar da zainab yake sosae, duk yadda take kokarin dannewa Amma hakan ya fito kowa ya ga irin wahalar da take Sha. Imam ya tada hankalin shi ganin wani lokacin se tayi kwana biyu ko ruwa ta saka a bakin ta se ya dawo, wannan dalilin yasa ya samu Murad Dake shi medical student ne, yace Masa ya kawo Masa abortion pills. Murad ya dube shi da tantamar abin da yace, " Wa zaka bawa boss? Kada dai sister in law zaka bawa?" Imam ya gyada Kai cikin alhini tare da fadin "Bata da lafiya, bana son ta mutu, gwara na hakura da wannan cikin akan na Rasa solace di ta" Murad kamar yayi dariya saboda ko da Wasa akace zaiyi wannan abun akan mace tabbas zaka Musa, shi baya ma son Abu ya dinga hada shi da Mata sosai, lallai zainab must be born with a great luck " Boss! Kana ji, it's normal during pregnancy, duk wannan abun zasu wuce after 3 months!" Wani mugun kallo yayi ma Murad Wanda yasa yasan shawarar shi Bata karbu ba, Kuma ba zata taba karbuwa ba. Instead se yace zai je ya kawo Masa. Only God knows how Murad ya samu pills dinnan ya kawowa Imam da ke zaune zuciyar shi kamar zata fito saboda jiran da yake yiwa Murad, ya kagu ya kawo masa maganin yaje ya saka Mata ko ta huta. Haka kuwa Murad ya kawo Masa, ko Kiran yaji directives din maganin baiyi ba ya karba ya wuce , yasan how much she likes apple drink, take yayi blending ya Kuma tace sannan ya jefa pills biyu ciki ya Bari ya narke, ya juya kafin ya wuce daki ya Kai Mata, tana kwance tayi lamo kamar wadda aka mawa duka Amma Tsabar rashin kuzari ne. Yana zuwa ta dago tana kallon shi duk ta rame kamar ba zainab din shi ba, hakan ya Kara bashi karfin gwiwar aiwatar da abin da yayi niyya. Ya dago ta jikin shi Yana mayar mata faint smile din da tayi masa, ya shafa Kan ta tare da furta " Ya kike ji yanzun" Ta Dan Yi murmushi tace "Alhamdulillah! Marhaba ya Chum!" Kamar yadda take Dan tsintar Hausa har ma da fullanci daga bakin shi, Haka shima yake tsintar larabci daga nata bakin. Ya Mika Mata tumbler hannun shi, Babu musu ta Soma Sha a hankali, a Haka ta shanye tas, a take wani bacci ya Fara kokarin daukar ta. A jikin shi tayi baccin, se da yaga tayi bacci sosae sannan ya gyara Mata kwanciya ya fita zuwa parlor. Ta_kwalam A Kara hakuri, jiki da Jini. Thanks for understanding [1/3, 20:28] Maman: 019 Ban San dalilin da yasa nake Jin urge din daukar rayuwa ta ba, na San dai kawai gaba daya mind di na is blank, Babu wani Abu da nake tunani bayan wani irin kunci da nake ji cikin zuciya ta. Na lumshe idanu na bayan na fito da rezar daga cikin gidan ta, sabuwa ce dal da alama Batuul ta siyo ta ta bar ta a wajen, saboda Batuul ko kadan Bata San menene Adana Abu ba, komai darajar shi zata iya tashi ta bar shi a wajen. Ina ta kallon hannun nawa Ina tunanin na yanka ko Kuma na tsaya? Amma zuciyar da take zuga ni Akan na yanka din se ta rinjaye ni, na daura Ina Jin hawaye suna min zarya akan kumatu na, sede kafin na dadara a hannun naji Mamaa na fadin "Bintu! Bintu!!" Na lumshe idanu na, ba tare da na dago ba, balle na kalle ta ko kallon zai saka na fasa, instead se na Yi kamar da dai duniya bansan tana yu ba, na saita rezar a hannuna ta karaso in da nake tare da tankwabar da hannu na, duk da Haka nayi nasarar yanka hannun sede sama sama Wanda ganin jini Yana fitowa daga hannun yasa Mamaa wanka min mari, wannan Marin did awaken my soul, na dago Ina kallon ta, ta Kara kwada min mari a dayan kuncin nawa, ta Fara fadin " Kashe Kan ki zakiyi? Ba kids hankali? Ke mahaukaciya ce Bintu? Me ya faru da ke da kike kokarin kashe Kan ki? Me ya same ki? Ina Kika bar imanin ki? So kike ki mutu kafira? Iyeee?" Wannan ihun da take yasa Batuul shigowa da sauri da take sanye cikin jeans da customized rigar su ta graduation, idan ka kalla Batuul zaka rantse ba Yar musulmai bace ba saboda shigar da tayi, ta dame jikin ta, an Sha fixed hair da lashes, ga uban artificial nail da akai polishing din shi aka Kuma je extra miles aka jera stones akai. Wani bingilin veil ne ta yafa Wanda ko kirjin ta Bai rufe ba, Ashe fada sukai kaca kaca ita da Suleiman Akan wannan shigar da tayi, tayi fushi ta sauka daga motar ta shiga napep ya kawo ta gida, tazo dan ta kawo karar shi wajen Mamaa Kuma se me Mana aiki ta sanar Mata ai Mamaa na dakin mu shi ne ta shigo. Juyawa tayi da sauri ta Kira Adda, Kawu dake tsaye window yaga gudun da Batuul ke yi, shima Babu shiri ya zura jallabiyya ya fito, suna zuwa Suka samu Mamaa na daure min hannu na, se kuka nake yayin da ko uffan Bata Kara ce min ba. Adda tana ganin wannan abun kawai ta Fara kuka, se da ta gama daure min hannun kafin ta dubi Batuul Dake tsaye tace " Ki zauna da ita kafin mu gama magana" A sanyaye Batuul ta gyada kai, yayin da Mamaa tayi waje, da kawu da Adda Suka bi bayanta, se da suka zauna parlon kawu sannan Mamaa ta dube su dukkan su hanklain su a tashe yake tace " Me yake faruwa da Bintu? Ko kunsan Reza ta dauka ta yanki kanta? Inda ban zo ba bansan wanne irin yanka zatai yiwa kanta ba" Kawu ya dafe Kan shi Yana ambaton sunan Allah! Wannan wacce irin siririyar masifa ce ta kunno Kai gidan shi " Ban sani ba, ban Kuma San me suka fada muku daga makarantar su Bintu ba, Amma koma menene yanzun Bintu tana bukatar a saka Mata idanu, ba a barta ita kadai ba, na fahimci kamar dukkan ku Kuna cikin damuwa, to Amma damuwa zata bayar da sahihin maslaha? Bana tunani..." "Ina ga Zan aika ta wajen Fadima a sokoto!" Adda ta fada tana Jin wani irin rashin Dadi cikin zuciyar ta. Kawu ya girgiza Kai yace " A'a Asiya, gwara ta zauna anan akan mu tura ta wani gurin taje ta zame musu burden.." "Gwara ta zauna nan, Ni Zan kula da ita, Zan Yi magana da ita, idan tana bukatar likita se muje" Adda ta dinga Yi Mata godiya kafin Mamaa ta Mike Dan komawa daki ta ganni, Ina zaune na kurawa pillow na idanu, Amma a zahiri ban masan a wacce duniyar nake ba, Batuul tayi jugum se kallo na take, ta Kuma rasa abin da zata ce min, Wanda hakan yayi min dadi Dan bana son hayaniya ko kadan. Haka ta shigo ta same mu, muryar Batuul da ke amsa maganar Mamaa yasa na dawo hayyaci na, na Dan kalle ta, itama sashen nawa take kallo, idanuna da fuskata sun rame kana kallo na kasan akwai abin da yake damu na, ko dai rashin lafiya ko wani abun. " Tashi muje Bintu!" Babu musu na mike a sanyaye na bi bayanta, har cikin bedroom Muka je, ta nuna min gefen gadon ta akan na zauna Babu musu na zauna, ta fita se can ta dawo da abinci ta aje min tare da kura min idanu da ya saka ni Babu yadda Zan yi na dauki spoon na Kai Baki na, wani irin daci naji rice din tana Yi, Amma kallon da take min yasa na cigaba da taunawa Ina Jin rashin Dadi a Baki na, se da naci da Dan yawa har naji Dadi a ciki na kafin na Sha ruwa Mamaa ta Fara yimin magana cikin tausashen murya. "Bintu kinsan hukuncin Wanda ya kashe Kan shi kuwa?" Ta fada tana ruko hannaye na cikin nata, ganin ba zanyi magana ba tace " Idan Kika mutu a Haka to kin mutu kafira, duk sallar da kikai, duk azumin da kikai, duk dokar Allah da Kika bi ta tashi a banza. Yaushe Bintu? Yaushe zakiyi wannan danyen hukuncin. Duk abin da rayuwa ta yi ai karki manta Allah Yana tare dake" Har lokacin ban ce komai ba, tasan maganar ta Bata shige ni ba, hakan yasa ta kyale ni. Wajen yamma ta shirya tace Nima na shirya mu fita, se lokacin nace " Ina son Zama a gida" Tace " Eh ba jimawa zamuyi ba!" Haka na shirya muka fita, Babu inda Muka je se zagaya unguwa, a hankali naji abin da yake cikin zuciya ta Yana Dan raguwa musamman da Banga wani yayi min wani irin kallon kalla wannan katuwar! Muna Shiga gida ana Kiran maghrib, tare mukai sallah tace na daga hannu na roki Allah gafara Dan tana da tabbacin Allah fushi yake Dani, wannan abin da ta fada se kawai na Fara kuka Jin wannan abun, dama abin da take so kawai taga nayi kenan. Kilan idan nayi kuka akwai tendency nayi magana, magana ta kuwa zai rage min radadi cikin zuciya ta! A kalla se da Muka dauki sati tare da Mamaa, kullum tana Kan yimin nasiha da nuna min babban laifi na aikata, Adda kullum se ta shigo ta ganni, Haka kawu ma, wannan dan abin da nayi se yasa na samu attention daga gurin iyaye na, na manta da jin wani yace min wai nayi kiba ko wani abu. Hankali na se ya Fara kwamciya har zuciya ta sanyaya na Fara Jin loved and belong! Sai da akai sati sannan da safe bayan mun kammalla breakfast ta Fara tambaya ta " Bintu bani labari, fada min me yasa Kika Sha Dettol a school?" Nayi shiru Ina kokarin battling da zuciya ta Akan na fada ko kada na fada a karshe na bude Baki na, na Fara fada mata "Mamaa bakwa so na, Babu Wanda yake so na a cikin gidannan, kowa blaming di na yake saboda Ina da kiba Mamaa, Amma Kun manta ai ba laifi na bane ba, Nima da an bani zabi bazan Zama me kiba ba...." Tayi shiru Allah kadai yasan yadda zuciyar ta take wani irin tafasa, tamkar zata fito Haka take ji, ko itama ta tuna watarana da na taba tambayar ta me yasa basa so na, Amma amsar da ta bani ba me Dadi bace ba " Laifi na ne Mamaa? Shiyasa Naga rayuwa ta Bata da amfani naga gwara na kashe Kai na kowa ya huta, kunga Kuma ba zaku damu da ganin mummuna a gidan ku ba!" Wannan karon rungume ni tayi, hakan yasa na Fara kuka ita Kuma tayi shiru Amma dai Bata ce komai ba. A washegari da Kuma nasihun da take Yi min yasa na Fara neman gafarar ubangiji, Ni kaina se naji kunyar Kai na nake, balle Allah, na tabbatar Allah yayi fushi Dani . Na dage Babu dare Babu Rana na dukufa neman gafarar shi, yadda nake rokon Allah se zuciya ta ke washewa, nake Jin kamar ni din wata sabuwar halitta ce. Na Fara mantawa da wani BashPrince00 da Samiha, dukda wani lokacin se naji I'm crazily missing him, Amma idan na tuna abinda sukai min se naji babu wani Abu da ya rage da Zan zauna Ina neman shi. Cikin iyayen nawa su uku kowa kokarin kyautata min yake. Wasu lokutan har Adda idan zata je office se ta tafi Dani dukda ba son hakan nake Yi ba Dan kunsan bana son shiga cikin mutane. Shikuma kawu se ya sake biya min naje na sake advance cake training, to wannan yafi komai yimin Dadi. I got to understand how much flour means to me, I find solace duk lokacin da na Fara kwabi. Cikin hukuncin Allah na Fara karbuwa hadi da naci da nake. Ina yin cake na sako su meat pie da wasu cikin assorted snacks! Ta_kwalam ce BINTUN BATUUL, NAZNEEN and GEN NASIR ZAKI is not free! [1/3, 20:28] Maman: 021 Peacefully zainab tayi bacci har wajen tsakiyar dare se wajen uku na daren sannan ta Fara Jin kamar ana mintsinin ta cikin marar ta, cikin rashin Jin dadi ta Yi juyi tare da Kara stretching kafarta, Amma a hankali se ciwon ya tashi daga mintsini ya koma ciwo sosae, Wanda Babu shiri zainab ta bude idanun ta tangararau, anan ta tabbatar da cewar ciwon da gaske ne. Ta tashi ta zauna a daddafe, taree da kallon gefen ta inda Imam ke baccin shi hankalin shi a kwance, Dan kada motsin ta ya tashe shi se ta Mike zuwa can living room ta Fara safa da marwa, wani lokacin ta durkushe a wajen ta saki siririyar Kara, ciwo yayi ta gaba, har tazo ta kasa ko da daga kafafun ta, gaba dayan su are numb. A hankali taji kamar Abu Yana sauka daga jiikin ta, tana Kai hannun ta Kan wandon sleeping wear din Dake jikin ta se taji danshi, ta saka hannun ta ta shafo kasan a take taji ruwa, ai kawai ta saki wata Kara Dan.tasan definitely jini ne. A gigice Imam ya hantsilo daga gadon, har Yana a dungure ya kunna fitilar bedroom din, sede Babu kowa hakan ya tabbatar Masa tana linving room, cikin hanzari ya nufo in da take durkushe tana kuka Kuma ta damke marar ta. Yayi saurin karasawaya tsugunna gaban ta Yana fadin " Solace! Me ya faru?" Ta Fara kuka a hankali tana fadin "Chum Mara ta, I'm bleeding, I'm losing my baby!" Ya rungume ta sosae cikin jikin shi wani irin guilt Yana addabar zuciyar shi, dama Haka ake barin? Shi yayi tunanin silently cikin zai fita Babu wani ciwo, Amma me yasa zainab din shi ke wannan irin ciwon hakan? Tsoron kada fa ta mutu yasa ya koma daki ya canja kaya, itama ya samo Mata wasu kayan sannan suka tafi asibiti, cikin gaggawa aka karbe ta a gynae, bayan hoto da akai Mata aka tabbatar da cewar ciki ya lalace, Dan da yawa ma ya fita, suka fito bayan sun daura Mata ruwa hade da Mata allura wadda zata easing Mata pains din da take ji. Imam na zaune a waiting area kamar yadda aka umarce shi da ya zauna ya jira, Yana ganin fitowar mutumin ya Mike tare da nufar shi Yana tambayar yadda jikin ta yake yanzun, se ya tabbatar Masa Babu yadda zasuyi su saving cikin sedd ya saka hannu idan ya yadda ayi Mata wankin mahaifa. Cikin sauri yace " Will she be ok? Kana ganin Babu complications da zai biyo baya?" Gaba daya Yana cikin tarin da na sani da guilt, da yaji shawarar Murad ya batta tun da ya tabbatar Masa duk inda ta Kai wata uku zata daina at most ta Kai wata biyar. Me yasa tausayin ta ta rinjaye shi har ya kara saka ta cikin pains haka? " Complications din kadan ne wani lokacin ma babu gaba daya, just sign the consent form, muyi mu Gama" Haka kuwan yayi seda yayi signing sannan ya shiga inda har lokacin zainab bata daina murkususu ba, yaje ya zauna ya ruko hannun ta, idanun shi sun kada sunyi jawur saboda tsananin tashin hankali da kaduwar da yake ciki. " I'm sorry solace! I've caused you a lot of pains!" Ta cije bakin ta cikin azabar ciwo, da azabar ciwon zuciya na fitar yaron da ta kwallafawa Rai akai, tace " Chum I'm sorry, I failed to protect our child!" Duk mazantaka irin ta Imam se gani yayi hawaye kawai suna sauka Masa daga kuncin shi, me yasa yayi Haka? Me yasa ya raba ta da abin da kullum yasan se tayi zancen shi, se yake Jin kunyar hada idanun shi da nata. A ranar akai komai, Wanda Bayan an Gama Mata wankin marar baccin da Bata samu tayi ba ya dauke ta ba tare da ta shirya ba. Shima se lokacin ya samu ya runtsa, a hankali ta Fara dawowa daidai duk da kullum se tayi kuka tare da bashi hakurin bata kula Masa da yaron sa ba, duk lokacin da tayi hakan se yaji Babu dadi cikin zuciyar shi, se yaji kamar bai cika masoyin ta na gaske ba, a Haka yayi deciding fada Mata gaskiya, aikuwa tayi ta kuka, tayi fushi da shi Wanda ya zamana shi ne na farko a zaman su, dukka sun wahala kafin ban Baki da Kuma shishigi da yake Mata yasa ta hakura! *** Fast forward, na cigaba da rayuwa ta, yadda na dukufa da istigfar da Kuma yin abubuwan da zasu saka na dauna yawan tunani yasa na daina kawo suicidal thoughts cikin zuciya ta, duk lokacin da na tuna ma ai na taba attempting kashe Kai na se na ji kunyar Allah nake ji, gani nake na kasance butulu akan tarin ni'imomin da yayi min. A gidan mu duka sun shiga hankalin su, tun daga kan iyayena har siblings di na ma. Mamaa wuta ta bude musu sosae, akwai ranar da bana mantawa na karba order mocktail na wasu masu bridal shower, Wanda Suka turo zai karba musu ko kadan bana Jin shi, Dan Haka na fito da 500 di ta Dan a siyo min airtime na Kira shi tunda lokacin event din ya kusa, ban samu ko matazu me Mana wanki ba, kawai se na wuce dakin Mamaa na samu sani a zaune Yana kallo, Ina Shiga ana Gama haska series din, na dube shi na marairaice fuska nace " Dan Allah Yaya airtime zaka karbo min Dan Allah, kaga maghrib yayi bazan iya fita ba!" Yayi kamar bai jini ba, na sake narke murya nace " Kaji Yaya" Yayi tsaki Yana karbar kudin yace " Uban me zakiyi da Kati da Daren nan? Kede nasan ba saurayi gare ki ba, yau yadda kike dinnan kamar wata giwa ai sede sugar daddy!" Wannan abun kawai Mamaa taji, aikuwa ta rufe shi da fada kamar zata Kai Masa hannu, " Baka da hankali zaka fada Mata Haka, idan sugar daddy ne ma Ina ruwan ka, Kai kayi kanka da zaka tanka halittar wani? Wawa kawai!" Se Kuma ta dawo Kai na tana tambayar me ya hada ni da shi in the first place, nace " Kawai tsokana ce Mamaa, ba se kinyi fada ba. Yaya Dan Allah siyo min Mana suna jira na" Ya wullo min dari biyar din Bayan ya maka min harara ya fice, Ina ganin lokacin da bakin shi ya motsa yace "Shegiya kurbusu kawai!" Naji wani Abu ya Dakar min zuciya ta, Amma ban kula shi ba kamar yadda kuka sani, se ma Zama da nayi na karba wayar Mamaa na Fara Kiran mutumin, aikuwa ya dauka na bashi hakuri sannan na bashi address din. Wannan tsayawa da Mamaa tayi min, yayi min dadi cikin rayuwa ta ya Kuma bani karfin gwiwar yin Hira da ita, na Kan fada Mata labarin fitar da nayi idan har na fita, hakan ya rage min yawan kadaicewar da nake Yi, Amma har yanzun ban daina kin shiga mutane ba, ban Kuma daina jin yadda zanyi na rage kibar jiki na ba. Ana Haka aka Fara bada admission, cikin hukuncin Allah na fito cikin Wanda Suka samu gurbin karatu cikin BUK, Architecture din da na cike shi din aka bani, farin ciki ranar kowa a gida se da ya fahimci hakan, naje na fadawa Adda bayan ta dawo daga office, tayi murmushi tace " Bintu kin tabbatar Zaki iya kuwa? Kinga University da secondary ba daya bane ba. Nasan Dan kin Dan samu luck kin ci exams shiyasa kike ganin kamar architecture din Wasa ne bko?" Adda ba zata daina muzanta ni Akan da ban kasance me kokari ba, Amma ni dai nasan yanzun kowanne course aka bani bana tunanin Zan Fadi, Dan kuwa I'm determined sosae da sosae! Duk jiki na yayi sanyi, saboda akwai abin da nayi lacking a rayuwa ta, toshe kunne na daga abin da mutane ke fada, ko Kuma kada na bar maganar su ta dame ni tunda mutane ba a iya musu, Amma bana iya hakan ko nayi niyyar hakan se na gagara, shiyasa Abu kadan zaa fada se ya tayar min da hanklai na, yaci ace zuwa yanzun na sike na Kuma Dake Amma ko kadan bana iya hakan. Kawu ya bani duk kudin da ake bukata na Yi registration da komai, da farko nace Ni hostel Zan zauna Amma Kuma se na fasa tuna cewar yanzun hostel din akwai mutane da dama a cikin shi, Kuma zaa din ga criticizing di na anyhow Wanda ba Zan iya jurewa ba, ba Kuma Zan iya bada amsa ba, se kawai na yadda na bari akan na dinga day, dukda Nisan Dake tsakanin mu. Na Fara karatu cikin hukuncin Allah, da farko it was hard to adjust Amma dana Yi wata daya se na Fara daidaita yanayi na. Bana iya fitowa daga aji duk lokacin da Naga mutane sun yawaita, bana shiga harkar kowa saboda gani nake kowa kallo na yake Yi Kuma babu Wanda zai so yin kawa dani. Ko da nazo da wuri to can baya nake zama Abu na, kullum fuska ta dauke da mask, sannan kayan jiki na ma kadai Kara min kiba suke. Idan Babu kowa a class to Zan saka earpiece kunne na Dan kada ma naji wani Abu da zai Bata min Rai na. Ranar Ina zaune Babu kowa cikin aji, Ina nufin lecturer, se mu kadai suna ta hayaniya, nayi shiru Ina rufe idanu na cikin tunanin duniya, se naji an taba ni, nayi firgigit na bude idanuna, wata Mata ce zatayi wajen shekaru ashirin da biyar zuwa sama, ta zauna kusa dani tana fadin " Sannu baiwar Allah!" Nace "Yawwa!" Se tace min "Ina kike Kai Babyn ki raino kuwa?" Se naji wani banbarakwai wani namiji da suna...nace " Bani da Baby, banyi aure ba" Kunsan wasu ba suda hankali ko kadan, instead ta tashi ta tafi se cewa tayi " Ke din? Tabdi me Kika tsaya Yi har yanzun bakiyi aure ba?" Nayi Mata banza ban Bata amsa ba, maimakon ta tafi se ta dauki ID card dina na school Dake makale jikin lanyard, a jiki akwai date of birth, a take tayi wani exclamation " Ke din ce shekarar ki Sha shida? Tabdi kina da girman jiki wannan ai we can mistaken you for someone of fourty years!!!" Kunsan menene? gaba daya idan kuka duba harshe bana tunanin anatomically akwai inda Kashi ya tokare shi, shi din tsoka ce amma Kuma tafi mashi kaifi, harshe masifa ne saboda shi yake magana, akwai lokutan da yawa da connection din da harshe ke dashi da kwakwalwa yakan tsinke, harshe ya ta fadan abin da Bai kamata ba. Kunga wannan abin da ta fada min, Wai nayi Kama da Yar shekara arbain se naji gaba daya zaman ajin ya gundure ni, tana ta surutu na Mike tare da daukar jaka ta na fita, Ina tafe Ina ayyana how old am I looking? Shiyasa Ashe idan naje submitting Abu se Naga ana cemin Hajiya? Hawaye ya Shiga sakko min, ta Yaya ma zaa hada budurwa Yar shekara Sha shida da shekara arbain? Wannan cin mutunci bashi da na biyu. Na karasa gida na cigaba da tsayuwa gaban mirror din dakin mu, na kalla fuskata, bani da kibar fuska in fact hallitar fuska ta irin ta Yara ce, idan ka dauke Baki da kurajen ta bana tunanin akwai wani abun assha a fuskar, na duba jiki na, a take na Fara kuka Ina ganin nayi kiba da yawa, a ranar se Naga kibar tafi ta kouaushe fitowa ma... Ta_kwalam ce BINTUN BATUUL, NAZNEEN da Kuma GEN NASIR ZAKI is not free! Contact the writers to make payment. [1/3, 20:28] Maman: 022 Lokuta da dama na kanyi mamakin me yasa bakin mutane baya shiru?  Me yasa suke Jin dole se sun Yi magana akan abin da bai shafe su ba, ni dai nasan ance idan zaayi magana a dinga taunawa kafin a fito da ita, saboda wani lokacin baka San how powerful your words are. Akwai wata Pakistan woman wadda ta kasance motivational speaker, muniba mazari ta taba wani video da na taba kalla take cewa " Be careful with your words, because words are so powerful that they can break you, deform you and destroy you..." Ma'ana tace kowa yayi hankali da kalaman shi saboda ita magana tana da karfin da zata iya kassara mutum. To kunga idan Haka ne ya kamata mu kasance Muna tantance abin da bakin mu zai furta. Bayan abinn da ya faru a class na fito na nufo gida, ba tare da na jira next lectures ba, nasan Hali na ko da ace na zauna to bazan iya Kara concentrating ba. Na shigo gida jiki na a matukar sanyaye, parlon Mamaa na Fara shiga Dan sanar Mata dawowa ta, Amma se na same ta ita da Suleiman a zaune, yanayin su dukka ya nuna they're in a serious conversation. Na dube ta na gaishe ta har Shi din ma sannan nace Mata na dawo, ta dube ni closely kamar wadda ke son fahimtar wani abu, na juya da sauri Ina fadin " Kai na na ciwo Bari naje daki!" Kafin ta bani amsa na wuce daki tare da yin sallama dukda bana tunanin Zan samu wani cikin dakin, tun da Batuul Kam tana makaranta, Ina shiga na karasa gaban dressing mirror na tsaya, kamar yadda na Saba a kullum kullum. Na juya na sake juyawa sannan na zauna Ina karewa fuskata kallo, idanu na suna cikowa da kwalla ta Ina ne nayi Kama da mutane masu shekara arbain, duk yadda nake ganin munin Kai na Amma nasan wannan abun is just a hearsay, Amma Kuma na kasa sakawa zuciya ta kada hakan ya dame ni. Ina nan zaune se naji sallamar Mamaa, na dago Ina kallon ta Bayan na amsa, ta zauna saman gadon tana bin gadon da kallo yadda na baza handouts anma fuskata da Kuma damuwar da take ciki ya tabbatar Mata ba karatun nake ba, kawai dai Ina zaune ne ina tunanin abubuwan da Bai kamata ace nayi dwelling akai ba. " Wani abun ya faru a makaranta ne?" Nayi saurin giegia Kai na nace " Ba komai!" Tayi murmushi tace " BINTU fada min me ya faru? Wani yace Miki wani abunne?" Se kawai hawaye Suka shammace ni Suka Fara tsirtuwa akan kunci na, wannan kadai da nayi se ya sake tabbatar mata akwai wani abun. Cikin kukan da nake son dakewa bana Kuma San Yi na Fara tambayar ta " Mamaa ki kalle ni, ki kalli fuskata Wai tana kama da ta Yan shekara araba'in?" Mamaa dariya ce kawai batai ba saboda Bata son ta Kara Bata mood din, tace " Kuma kin yadda Bintu? Duk yadda kike kallon madubi Baki taba lura ke din daban Allah ya hallitta ba? Har yaushe ma Bintu Zaki dinga barin maganar mutane na.shiga kunnen ki, Kinga ko ramewa kikai mutane se sun Yi magana. In dai kina son zaman lafiya, to abin da ya kamata ki toshe kunnen ki daga zantukan mutane" Inama Zan iya toshe kunnuwan nawa, inama Zan iya ji na share Amma ba Zan iya ba, bani da wannan karfin zuciyar. Idan da ace Ina Jin nasihar ta da tuni na wuce bacin Rai, Amma bana iya yin abin da take cewa. Wannan dalilin yasa na kusa kwana biyu ban je school ba, Ina gida Abu na, Mamaa ma bata kula ni ba balle taji dalilin da ya hanani zuwa, balle Adda da Kawu kuma da Suka koma nuna halin ko in kula a kaina. Wani yammaci na dawo daga school, a matukar gajiye nake, Bayan abin da ya faru sosae nayi kokarin ganin na sake rage cudanya ta da mutane. A kofar gida na hadu da Suleiman shi da wani abokin shi suna tsaye, ni kunsan ba wani shiri muke ba sosae, so briefly na gaishe su, Suleiman ya amsa Yana fadin "BINTUN BATUUL!" Na juyo ba tare da nace komai ba, yace " Do me a favor, ki turo Mana Batuul please!" Na gyada Kai na, Ina wucewa abokin yace " Ga ga Yar Duma Duma Naz!" Naz da yayi folding hannun shi tun da nazo yake kallo na yace Yana Yar dariya "Wannan rindinar itama gidan take?" Suleiman ya kwashe da dariya Yana maimaita rindinar da Naz yace, wani Abu me zafin gaske ya tsaya min a makogaro na, idanuna suka cika da kwalla Amma se nayi kokarin maida su na wuce ciki, straight daki na wuce na samu Batuul tana gyara zaman cajin sabuwar wayar ta. Na zauna Kan gado na Ina sakawa a Rai na akan ba Zan fada Mata sakon shi ba tun da ya Raina min hanklai. Amma se Naga to meye a ciki? Where's the lie? Ai ba Karya yayi ba da yace ni rindina ce. " Batuul Suleiman na Kiran ki!" Ta wani kalle ni wani irin, kafin ta tura Baki tare da fadin " Wallahi ba inda Zan je, Dan rainin hankali" Zakuyi tunanin Zan tambaye ta abin da ya faru ko? Tabdi ko uffan ban ce ba na cigaba da fito da books di na daga cikin jakar da na fita da ita, se Jin karar buga kudi da akeyi, na dago idanuna Ina kallon Batuul da ta gama rufe kofa Kuma take bubbuga wrapper new N500 notes tana stretching din su. Ta aje gefen gadon sannan ta zaro ta N200 notes mint din su ta hada su waje guda tana taunar gum, mamaki sosae ya Kama ni inda Batuul ta samu wannan uban kudin, Amma dai se bance Mata komai ba kawai na wuce toilet. Ko Dana fito ta Kara dakko wasu sabbi dal na N1000 mints da Kuma wata N500 din. Na tada sallah har na idar Bata kwashe ba, na mike Ina fadin " Batuul ajiya aka baki" Tayi murmushi tana adana su cikin jerin kayan ta Dake wardrobe tace " Ko daya, nawa ne!" "Naki?!" Na tambaya Ina sake yin kasa da muray ta kada wani ya jiyo abin da muke fada, tayi dariya tace " Shiyasa na yanke hukuncin ba Zan aura Suleiman ba" "Batuul!" "Bintu" Itama ta amsa min da same murya da Kuma yanayin maganar da na yi, " Ba Zan aure shi ba da gaske, shiyasa nake fada Miki kudi a gaban komai suke, har yanzun Suleiman wani matsiyacin aikin banki yake, Ina Zan iya? Mutumin da a probation yake, ko yaushe idan baiyi meeting requirements ba kora ce!" Na zauna dabas akan gado, na manta order akai ta 12pcs meat bread Baki daya, Kuma tashin da nayi niyya ta na wuce kitchen na Fara aikin. Amma wannan maganar ta Batuul ta girgiza ni. "Batuul Suleiman din? Akan kudi Zaki guje shi ? Tun kafin ki San kanki yake kula da ke Amma sakayyar kenan?" Ta zauna gefe na tace " Bintu, Baki waye ba. Kilan Baki da saurayi ma har yanzun. Kada ki damu Zan bar Miki Suleiman din se ki daura daga inda na tsaya!" Ayi hakuri a Kuma Kara hakuri, Dan Allah I'm sorry for ghosting, for typing little. I've a strong reason, I hope you can pray for me and understand me. [1/3, 20:28] Maman: 024 Shiru shiru akace Wai malam yaci shirwa, Imam nata Kira yaga ta inda ciki zai bullo daga jikin zainab Amma babu amo balle labari, Babu ciki Babu dalilin shi, itama tana ta saka ran zata Yi conceiving Amma shiru kake ji. Dukda hakan suna rayuwar su cikin aminci da alkhairi, suna zaman su cikin soyayya da kauna. Anan Imam ya kammalla karatun shi, ya Fara tunanin tafiya Nigeria, sede Allah is always the kindest, se Alhaji Gidado ya dakatar da shi da fada Masa akwai course akan administration da Kuma planning, Budget and implementation da yake son jikan na shi ya koya, saboda big plan da yake da shi ga rayuwar Imam din. Fatin ciki ba ga zainab ba Kuma ga Imam ba. Shekara daya ta Kara zuwa ta wuce, wannan lokacin tuni zainab ta kammalla makarantar ta, shima shekara ya rage, tare suka he Qatar aka zagaya da shi dangin ta. Ya gansu Suka gan shi sukai kwanaki sannan Suka koma inda suka fito, tunda Suka dawo Imam ya Zama wani irin mutum da zainab ta kasa gane Kan shi gaba daya. Wani yammaci ya dawo daga lecture a gajiye, ga Kuma yawan tunani da yake yi duk yabi ya rame. Bayan ta yi Masa serving wani local dish din su na kasar su ya zauna ya Fara ci cikin kwanciyar hanklai, tana ninke inners din shi tana Kuma karantar yanayin shi. Se da ya Gama ya Mike Dan Kai kwanon kitchen kamar yadda ya Saba, in dai yaci abinci to da Kan shi zai Kai kitchen ya wanke, to ka'idar shi ma idan ta tashi kafin ya tafi lecture zai tabbatar yayi Mata wanke wanke, idan ya dawo har girki yake mata. Yana dauraye hannun Shi Bayan ya kammalla wanke plates biyu da Kuma sauce pan da ya gani a cikin sink din. Bayan ya kammalla ya juyo se ganin ta yayi a tsaye ta kura masa idanun ta masu kaifi tana kallon shi. Ya Sha jinin jikin shi tare da matsowa inda take Yana dan sunnar da Kai yace " Solace what's up?" Ya fada Yana daga Mata hannu, maimakon ta mayar Masa murmushin da yake Mata se kawai ta ja hannun shi zuwa Kan sofa, bayan sun zauna yace " Solace menene?" Tace " Kai Zan tambaya, ka fada min menene yake damun ka?" Ya dauke Kan shi yace " Ba komai, na gaji ne" Ta Bata fuska saboda da gaske tasan akwai abin da yake damun shi, akwai abinda ya saka a ran shi yake Kuma damun shi, Kuma kowacce irin rantsuwa zaiyi Mata ba zata yarda cewar Wai Babu abin da yake damun shi ba. Yadda tayi da fuska ta Kuma sunkuyar da kanta tana fidgeting fingers din ta yasa shi fadin " Solace menene?" Tace cikin murya me rauni " Ka gaji da ni saboda ban haihu ba ko? Saboda har yanzun..." Yayi saurin rike ta wan da yasa maganar tata komawa cikin ta, idanun shi yayi jawur kamar zaiyi kuka, it's pains him so much idan yaji tana maganar haihuwar da Bata samu ba, saboda yasan ko menene ya faru to shi ne sanadi, duk wani Abu da akai yasan laifin shi ne. Ya gyara zaman shi Yana fadin " That will never be solace, ba Zan taba juy miki baya ba saboda Baki haihu ba, bazan tana ba, I assure you" Ta Fara kokarin bambare jikin ta da nashi, Amma se ya hanata se kawai ta kwantar da Kan nata tace " Then tell me, me yake damun ka? Wani Abu ya faru a Qatar ne? Naga tunda muka dawo you've not been yourself!" Yayi shiru ya kasa Yi Mata magana, Amma kuma dole zai fada Mata makomar su Dan abunnan ko yace maganar nan sooner or later zata fito. Ya danyi shiru sannan yace " Solace Ina son Miki bayani Akan family di na" Tace " What about them! Ba zasuyi accepting di na ba?" Ta tambaya har zuciyar ta tana Jin Babu dadi hade da tsoro Yana kamata, ya rike hannun ta Yana zana Mata soothing circles a jiki Dan ya Dan kwantar Mata da hankali. Bayan sun yaga alamar ta Dan daidaita ya Fara fada Mata " Family na basu yadda su karba wani ta auratayya other than mu aura na dangi. Se yanzun nake Jin tsoron yadda Zan Yi na kaiki wajen su" Tayi shiru tana assimilating abubuwan da ya fada, dama tana tunanin hakan saboda a shekaru uku zuwa hudu da sukai aure ko da mutum daya daga dangin shi Bata taba magana da shi ba, ko da ta tambaya zai Nemo wani excuse din Dan ya Kare Kan shi. Amma se ta dauka ai Babu komai tunda sun ruga da sunyi aure. "To me yasa ka aure ni in the first place? Me yasa?" Ya Kara matse ta a jikin shi yace " Saboda Ina son ki, saboda bana son losing din ki" "Then what if your family refuse to accept me? Ya zakai?" Yace cikin narkar da murya har se da tsikar jikin ta ta tashi yace "Shiyasa na aure ki, ko ba komai idan muka je nasan ba zasu raba mu ba" Ta Fara kuka a hankali me cin Rai Amma ta kasa fadar komai, gaba daya hankalin shi yayi masifar tashi, ya dinga lallashin ta with all the sweetest words da yasan zai iya sakawa tayi shiru Amma abun mamaki se hakan ta gagara, ta dauki lokaci sosae tana kuka sannan tayi shiru, Amma taki tace komai se ajiyar zuciya da take saukewa. Shima se ya Dan kyaleta amma duk da Haka ya kasa zuwa ko Ina duk kuwa da Kiran dasu Charles suke masa. Har ya dawo daga sallar maghrib Bata canja yanayi ba, tana zaune ta idar da sallah Amma kuka take tana Jin tausayin rayuwar ta, tana ganin watan lalacewar rayuwar ta ya tsaya, ita ba wani ta sani ba, all these years Imam ya kasance uwa da uba a gare ta, aboki da Kuma kawa, Babu wani wanda take kulawa ko ta saki jiki da shi idan ba Imam ba, hatta acan Qatar din jadda ce kawai, bayan jadda Kuma Bata da wasu shakikan Yan uwa makusanta. To ya Kuma ba zata tada hankalin ta ba, Bayan tasan rabuwar ta da Imam kamar rugujewar rayuwar ta ne! "Solace! Dan girman Allah, Dan Allah ki daina kuka kiyi hakuri, I promise you zanyi duk yadda zanyi Naga na tsaya Miki, ke kanki kinsan Zan iya ja da kowa akan ki ko?" Ta gyada kai tana rungume shi, Haka dai yayi ta bata Baki kafin kuma suka fita Dan Yana son iskar Dake kadawa ta tafiyar Mata da dukkan wani kunci Dake ranta. Idan Kuna Jin ana zancen Sharukh a soyayya, Romeo a fagen kauna to I assure you (inji Baba buhari 🤣) to Imam ne. Cikin darennan he made sure ya goge kaso me yawa na daga cikin abin da take ji akan wannan maganar da sukai. A kwana biyu se da ya tabbatar Mata shi din ba wani ba zai iya protecting din ta tare da yin fito na fito koma da waye. Kwanci tashi asarar me rai, se gashi har lokacin kammalla course din Imam yayi, Kuma ko suna so ko basa so dole ne su koma gida, a lokacin kullum adduar shi Allah ya daura shi akan Alhaji Gidado, ya Fara shiga tashin hankali duk da kokarin boyewa da yakeyi Dan kada zainab ta fahimta, Amma ita dinma anata bangaren abin da ke faruwa da itan kenan, tsoro ne da tashin hankali fal zuciyar ta, yayin da yake bawa Alhaji Gidado benefits of doubt kamar yadda itama take bashi wato shi Imam din. Zuciyar shi nada yakinin Allah will do the miracle ita Kuma ta sakawa zuciyar ta cewar kome zai faru Imam ba zai rabu da ita ba. Da wannan tunanin Suka baro kasar masu jajayen kunnuwa zuwa gida Nigeria. A Abuja Suka sauka kafin washegari Suka sake bin wani flight din zuwa Kano, sede a wani irin tsorace yake shi Imam, hakan har ya fito zainab ta gani se itama ta Kara rikicewa, karshe ta shawarce shi Akan yayi Mata booking hotel yaje ya sanar da iyayen shi a gida, idan komai yayi daidai yazo su tafi. Se yaji kamar tayi Masa bushara da aljanna, farin cikin shi ya fadada yaji Babu yadda zaayi ya daina son ta a cikin rayuwar shi. Saukar su ke da wuya ya kammalla dukkan abin da zaiyi, Yana fitowa ya hango Malam magaji, yayi saurin janyo baseball cap din shi Dan yayi disguising Kan shi, shi yasan Alhaji Gidado dole se ya turo a tafi dashi musamman matsayin shi na shalele. Haka suka tare taxi Suka tafi, se da ya Kai ta har hotel yayi Mata booking daki under his name kafin ya jira tayi settling, tana zaune tana kallon shi da idanun ta da suke nuna rauni, ya dawo kusa da ita tare da rungume ta a jikin shi yace " I assure you! I'll do everything in my power Naga ban rabu da ke ba, zainab ki sani kece farin cikin rayuwa ta, Babu wani wanda zai raba ni dake sede wani Abu daga Allah!" Wannan maganar ta saka zuciyar ta dan haskawa, ta sassauta rungumar da tayi masa tace " Don't abandon me please Chum Chum, kasan Kai kadai nake da shi ko?" Ya gyada Kan shi tare da pecking goshin ta sannan ya fita jiki a mace. Wucewa yayi straight gida ba tare da ya koma airport ba wajen Malam magaji. Tun da yaje kofar gidan yaga gaban shi Yana mugun faduwa saboda taron mutane da ya gani! What's happening?! Ta_kwalam ce! [1/3, 20:28] Maman: 025 Kowanne taro a yanayin fuskokin mutane ake gane na farin ciki ne ko kuwa akasin hakan, yanayin zirga zirga da Kuma walwalar jama'ar wajen yasa yaji hanklain shi yayi matukar kwanciya, yasan tabbas abun farin ciki ne ya faru, Kuma kafin yayi wani yunkurin wucewa se gani yayi ana fitowa da manyan silver tray shake da shinkafa da Mana, ga Kuma silver deep bowls masu girman gaske an hado tiwo da Miya, gidan su kenan, Haka suke biki shiyasa mutane ke son taron su saboda zaka ci me kyau ka Kuma Sha ka Kuma bar shi, Dan a wadace yake. Cikin kwarin gwiwa da Kuma tunanin yanayin da zainab take a wannan halin ya nufi gida, se de Yana shiga wangalelen iron gate din na su, yaga mutane nan ma da dama, Haka yayi ta bin gefe Yana wucewa saboda he's not ready for wani ya ganshi a tsaya ana ta gaishe gaishe plus ba kowa bane ba zai gane shi, se makusanta sosae, saboda shekarar shi wajen takwas a UK ko hutu bai taba zuwa ba. Se da ya kusa daf da gidan su sannan ne Suka hadu da mujahid, Ramadan da Sadiq, wadannan din duk cousins din shi ne kusan sa'anni ma suke da shi. Ai suna hada idanu da Sadiq tamkar wata mace se ya saki guda Yana fadin " Lallai yau take juma'a, shiyasa akace jumaatu babbar Rana. Ango ya karaso" Mujahid ya Kama hannun shi Yana fadin "My English bro! Anya kaso dawowa daga UK dinnan kuwa!" Ramadan Kam rungume shi kawai yayi Yana Masa barka da zuwa, shi dai tun da yaji zancen ango a bakin Sadiq, se ya ji kamar an watsa masa ruwan sanyi, shifa a wani dangin ana ganin nothing is possible ko, to ban da a Basu dangin, matsawar numfashim Alhaji Gidado ba ceasing yayi ba, Kuma kannen shi biyu da manyan yayan suna raye, to zasu cigaba da upholding duk wani policies din shi. Kafin wani lokaci Kam sauran cousins din shi dake kusa da Kuma Suka San shi duk sun yanyanbe shi, ga iyayen su acan Suma da abokan shi, mahaifin shi ya hango Yana murmushi, a take yaji duk wata nutsuwa ta sake shigar shi, da kyar ya samu suka sake shi ya tafi wajen baffanin na shi, kafin ya karasa wajen na su ya hango kakan shi da abokan shi shima, mahaifin shi da idanun shi yayi Masa alamar ya Fara zuwa wajen Alhaji Gidado, Babu shiri ya juya wajen Alhaji Gidadon dake kwasar gaisuwar mutane dake Masa Allah ya Sanya alkhairi, wani katon carpet ne da Kuma tumtum da ya samu ya shigida da shi, tamkar basarake Haka mutumin yake, Yana ji da kudi, mulki da Kuma izza. Yana hada idanu da jikan nashi se ya muke Yana bude hakoran shi alamar farin cikin isowar shi, ya cire sneakers din kafafun shi tare da karasawa ya rusuna cikin girmamawa Yana gaishe da kakan, Amma se ya rungume shi Yana jadadda Masa farin cikin ganin shi, anan ya umarci Sadiq da ya karbo Masa abinci a cikin gida, sannan ya dubi mujahid yace ya raka Imam ya gaida baffanin shi sannan su dawo , Yana jiran su suci abinci, Haka yaje cikin su ya gaishe su, suna ta murnar dawowar shi, mahaifin shi yayi Masa murmushin Yana shafa Kan shi kafin Suka koma wajen Alhaji Gidado, anan suka ci abinci kafin yace " Ango se kaje kayi wanka ka canja Kaya, ka dawo ku gaisa da mutane!" Haka ya mike jikin shi a matukar sanyaye Yana tunanin makomar shi shi da zainab, ko me take yanzun? Shi ne abin da ya Zama Yana Masa yawo cikin ran shi. Duk yadda su Sadiq suke zuzuta Masa amaryar ta shi da ya riga yasan Rukayya wadda ya San da alkawarin auren ta a kanshi tun kafin ya tafi UK, se Suka ga he's not excited at all, Sadiq cikin zolaya yace " Wai Imam baka murnar dawowar ka ne da Kuma sabuwar amrya da zaka hadu da ita?" Ya kalli Sadiq Yana wani fake smile Amma shi dai zuciyar shi ko kadan ba a nutse take ba. Se yanzun yake sake ganin wani tashin hankalin dake jiran shi. A gidan Baffa lamido Suma amaren dukka suna zazzaune da kawayen su, wasu kana kallon su zaka fahimci suna cikin farin ciki kada Rukayya da Safiyya suji labari Amma Fatima da Boddo gasu nan dai gasu nan. Haka sauran ma. Kanwar Imam wadda ya tafi ya barta tana da shekara shida, yanzun Haka ta Kai shekaru Sha hudu me suna Anisa ta rugo parlon da suke ciki tana kwala Kiran Adda Safiyya, Safiyya ta Mike tana gyara zaman veil din ta tace " Ya akai Anisa?" Tana panting saboda gudun da tayi tace " Adda! Hamma Imam ya dawo daga UK!" Wani karamin ihu Safiyya ta saki tana fadin " Da gaske Anisa? Oh Allah alhamdulillah!! Kin gan shi? Yana Ina?" Ta fada tana kokarin fita, Anisa tayi saurin rike ta tana girgiza Mata Kai alamar kada ta fita ta Kuma tsaya ta saurare ta. Hakan tayi ta tsaya amma she's so excited and eager to see him. " Ban gan shi ba Adda, naji Hamma mujahid na fadawa Innan su Boddo" Ta sake sakin murmushi tana juyawa alamar fita, wannan karon ma Anisa ta sake rike ta tace " Ke Adda Safiyya so kike wancan old hag din ya kashe ki? Kin manta ke amarya ce? I assure you Hamma da zarar yaji kece amaryar shi zai rugo wajen ki" Wannan abun ya sake sanyaya zuciyar Safiyya ta koma ta zauna sede ta kasa nutsuwa, ta dinga murmushi upon murmushi idan ta tuna mutumin nata ya dawo bayan shekara da shekaru! Duk yadda Imam yaso ya zille ya koma hotel wajen zainab Abu ya gagara, Haka ya cigaba da Zama cikin cousins din shi da abokan su. Se wajen goma ya samu ganin Ummiey wato mahaifiyar shi, farin cikin ganin shi sosae ta kasa boyewa, murnar ganin shi sosae tayi. Se da ya shiga zai kwanta zuciyar shi nayi Masa nauyin rashin ganin zainab, rashin ji daga gare ta aka turo kofa, Bilal brother din shi ya shigo ya zauna Yana Masa sannu da zuwa, har lokacin Imam Bai ma San wacece amaryar ta shi ba, shi dai Yana kyautata zaton Rukayya ce. " Hamma old hag yace gobe akwai meeting karfe Tara, ka huta before then!" Ya gyada Kan shi daga Haka Bilal ya fita shi Kuma ya kwanta Yana planning yadda given shi zata kasance. Washegari Yana dawowa daga sallar asuba, yayi wanka karfe shida ya fita daga gidan bayan ya kulle dakin shi yadda kowa idan yazo zaiyi assuming baya nan. Taxi ya samu har hotel din, kamar yayi tsintuwa zuwa ciki Haka ya dinga ji, so yake kawai ya ganta yaga lafiya take, Yana knocking Babu jimawa tazo ta bude, tana ganin shi ta fada jikin shi tana farin cikin ganin shi. Suka zauna saman cushion din dake dakin, ya Fara binta da soothing touches Wanda yasa ta Fara melting a jikin shi. Bayan sun nutsu ya tambaye ta yadda Daren ta ya kasance, tace Masa missing din shi badly da kyar tayi bacci, yanzun Kuma se ta Fara tambayar shi yadda ya samu Ummiey da Baffa kamar yadda taji Yana Kiran sunan su. Se ya zauna suka Karya sannan ya Fara Mata bayanin tayi hakuri ta Kuma Kara hakuri he'll take her home soon, yanzun yazo ya samu anyi Masa aure ne! Waji irin dagowa tayi... Ta_kwalam ce Good morning lovelies! [1/3, 20:28] Maman: 023 Mamaki kamar zai kashe ni a tsaye, nace " Batuul kiji tsoron Allah! Kada abun duniya da zai Kare ya saka ki bata tarbiyyar da akai Miki a gidannan..." Tayi saurin katse ni da fadin " A'a tsaya Bintu, wallahi banyi wani abun ba. Kar ma zuciyar ki ta zarge ni, I only used the beauty of my face nothing more!" Ta fada tana wani irin murmushi tare da shafa fuskar ta, na girgiza Kai nace " Ki dai ji tsoron Allah!" Daga Haka na fice zuwa kitchen Dan yin meat bread din da aka saka ni. Awa daya na kammalla sannan nayi packaging, se da na jira aka karba kafin na dauki zobo da pieces biyun da suka rage na wuce daki na Fara ci Ina tunanin maganganun Batuul, yanzun da gaske take zata iya rabuwa da Suleiman? Duk yadda yayi dawainiya da ita da Kuma shakuwa da sukai Amma zata iya Haka? Se naji kawai al'amuran Batuul ya Fara bani tsoro. Ina nan zaune Ina ci Ina Kuma karatu se gata ta sake shigowa, ta zauna bayan ta gutsiri Rabin meat bread din tace " Dan Allah idan kin Yi ki dinga sammin!" Ta kusa saka ni dariya, nace " Ki saka order, kici ki barshi!" Ta tabe Baki tace " Matsalar business people kenan, you guys don't care about relation at all!" Nayi Mata banza Ina cigaba da duba book di na, kafin na Kai ga dauka ta dauke ta cinye tana dariya. Nima se nayi murmushi nace " Batuul!" Ta kalle ni nonchalantly tace " Bintu! Ya akai?" Nace " Zancen Suleiman ne, ba zakiyi reconsidering ba, ki tuna years of relation da kuka dauka ke da shi, to ma tsaya tukunna, ya Zaki Fara samun Kawu da wannan maganar?" Tayi dariya tace "Kudi da kike gani Bintu Babu ruwan su da wani years of relation, what matters is na samu abin da nake so. Na Dade da gane Suleiman ba class di na bane ba, zancen su Kawu da kike bani Zan same su ba su zasu same ni. Ke dai ki zaba idanu ki gani. Ni dinnan ta Honorable Kura ce da yardar ubangiji" Nayi wani sneering nace " A'a Honorable Zaki ba kura ba. Ke Kika sani" Ina kwanciya Bayan na Jima Ina karatu sannan na kunna data, wani lokacin tsautsayi ke saka kayi wani abun. Ina kunnawa na tafi nayi uploading story akan washegari zanyi glazed pancake for breakfast me so yayi order. Har Zan kashe data din bansan me yasa ba se kawai na koma bangaren chat di na. Ina Fara scrolling se Naga wani message yayi popping, hannu na ya Kai Kan number, Ina shiga Naga image ne aka turon. Na bude na kurawa invitation card din da aka turo min. Abin da ya Fara daukar idanuna shi ne sunan Wanda zasuyi auren, wani irin mikewa nayi na zauna, na sake bude idanu na Dan na tabbatar sunan Samiha Suraj nake gani da Kuma sunan Bashir Garba Me yaki! Auren gaba daya sati biyu kawai ya rage, idanuna Suka ciko da kwalla Ina kallon sunan BashPrince00 da Samiha, so Haka sukai deciding, so a karshe dai aure zasuyi abin su, ikon Allah na sake ayyanawa a cikin zuciya ta. A take se Kuma naji kwallar da ta cika idanuna ta Fara sakkowa a hankali, na cigaba da sheshekar kuka a hankali Ina ayyana ni Kam akwai ranar da take zuwa take wucewa ba tare da hawaye ya fita a idanuna ba? Ko nace bazan Yi ba se wani abun ya gifta da zai saka naji kirji na yayi nauyi, Kuma the only solution is for me to cry! Duk yadda na dinga lallashin Kai Na se da na Jima Ina kuka kafin Kuma na Fara tuhumar Kai na dalilin Bata lokaci na Ina kuka dan kawai zasui aure? Kenan har yanzun Ina son BashPrince00 nake nufi Koko me? Se naji hawayen sun dauke daga idanuna, naji it's ok suyi auren su Nima watarana rabo na duk inda yake zai zo. Se na goge idanuna na kwanta Ina adduar Allah ya Kara min hakuri! Fast forward, rayuwa ta cigaba da tafiya, na cigaba da zuwa makaranta da Kuma neman kudi Abu na, na Zama expert a bangaren snacks har da abinci ma, wani lokacin har order seminar nake samu ko na daurin aure. Dan wasu su samu yasa na samu ma'aikatan da duk lokacin da Muka samu massive order to Zan Kira suzo muyi tare na Kuma biya su. Wannan sanaar ta zame min madogara da abin da nake Jin Dadi. Yayinda Yan gidan mu Suka rage abin da suke min. A bangaren Batuul tana ta soyayyar ta da Honorable Kura ne ko Zaki ? Oho Mata! Suleiman a Yan watannin nan bana so mu hadu, saboda idan muka Hadi se ya tsayara da Ni yayi tayi min korafi bisa canjawar Batuul da yadda take wulakanta shi, Ni dai kullum amsa ta ta kasance guda daya wato yayi hakuri yayi Mata uzuri, Amma na kasa fitowa na fada Masa gaskiyar Batuul ta Riga ta canja shi, Dan Batuul har Mota ce da ita, wadda Babu Wanda ya sani se ni da komai nata se ta fada min Koda Zan Mata menene, har tambayar ta nayi inda take packing ta fada can ne wani underground public parking lot, nan take Kai motar ta Kuma je ta dauka. A ranar se nace Mata "Yanzun ke Batuul Karya Kika koma Yi kenan? Ina ke Ina wata mota a age din ki?" " Ke a ganin ki nayi kankanta da mota?" Tayi dariya ta buga cinya tana sake applying sunscreen a fuskar ta tace " Ke Yar kauye ce Bintu ba Zaki waye ba Wallahi, kike kiga Yara less than age din mu suna fantamawa da motar su!" To me zance Mata? Se kawai naje na samu Adda wadda suke tare da Mamaa suna Hira, na fada musu abin da yake faruwa, na boye kudi da Kuma motar da take da shi. Nace " Ni ba gulma nake Yi ba, Amma kunga Suleiman ya Jima Dan Allah kada ku bari tayi haka!" Mamaa ta Fara ce min " To ai Bintu Suleiman ne yace ya fasa ba Batuul ba, Nima banji Dadi ba musamman shekara da shekarun da suka dauka tare" Wato abin da Batuul ta shirya kenan dama, shiyasa take yawan ce mini da kafafun shi zai gudu da Kuma bakin shi zai ce baya Yi, kenan abin da ta dinga yi shi ne halin ko in kula da Kuma Yi Masa wulakanci shiyasa ta tunkuda shi ya fasa, surely Batuul is wise and smart. Ga Kuma iyayen ta a zaune Amma dukka sun Goya Mata Bayan abin da take Yi, to me zance Kuma se na tashi na tafi, aikuwa Ina tafiya Adda tace " Ni Kam Mamaa to abun da nauyi ace yaronnan an bar shi ya tafi Haka, ko hooking din shi zakiyi da Bintu Yar dakin ki. Naga kamar Bata da saurayi ko daya Kuma Kawu ke ya fadawa Yana son aurar da su ko?" Mamaa tayi murmushi tace " Idan mu Kai Haka min wanke Kan mu kuwa, Dan yaron yayi jira sosae mutane se su zage mu ai" Anan suka kulla wannan abun without even considering anyone of us, wato ni da Suleiman din. Ko da suka fadawa kawu se yace ai hakan yayi indai yayi musu. Daga Haka aka bawa Honorable Aliyu Kura yazo akan ayi magana. Ranar Naga Abu, ni aka saka nayi girki kala kala, Batuul tun safe akw yiwa jiki spa, se kallon yadda kowa jikin shi yake rawa nake, hatta wasu daga cikin siblings din mu a gidan aure se da suka zo. Ina gamawa na fice na bar gidan zuwa makaranta Dan nayi karatu, bazan zauna Naga wannan abun bakin cikin ba, Yaya Fadima ta sokoto ita kada da sajida suka nuna rashin goyon Bayan su, Amma kowa Fadi yake ai dama can Suleiman ba tsarar ta bane ba, Ashe suna ta cewa a hada shi da Bintu ita ce daidai shi. Kuji fa Dan Allah. Ban dawo gida na se bayan maghrib saboda naje gidan Zuhriyya na zauna da yaranta tunda tana gida, se da ta taho sannan Nima na taho gida nazo na samu ana ta bude kayayyaki, I was so annoyed Amma Dan kada a ce bakin ciki nake se na zauna Muka kalla nayi Mata barka na wuce daki abu na. Inata makakin kokarin Yan gidan mu, ko kunya basa ji se wani zazzakewa suke yi kamar Basu taba Jin dadin kudi ba se yanzun. Duk abin da ake kullawa wallahi ban sani ba, abin da na saka gaba na shi ne shiga ta level 3 Ina kokarin ganin nayi scaling na Zama architect. Su Yan gidan mu sunyi focussing akan Batuul yayinda takurar da suke min ta ragu Amma a waje Kuma cikin mutane ban huta ba, kusan kullum se na hadu da me ce min " Kinyi kiba da yawa! Ki daure kiyi shedding a bit of weight." Haka dai suke fada duk da kowa is entitled to his or her own opinion, ya kamata mu din ga considering feelings din mutane, kunga yadda nake battling da mutane to Bai Kai Rabin abin da wasu su ka fuskanta ba, people are losing their minds silently saboda critics din mutane, kullum Ina fada a Rai na why must you talk? Dole ne se ka tanka halittar mutum? Idan ba dole bane ba ya kamata ki bar mu Haka nan muyi numfashi... To be continued In shaaa Allah! Ta_kwalam ce [1/3, 20:28] Maman: 027 Gaba daya na kasa gane Kan Batuul balle inda ta dosa, ta Zama wata iri magana ma da kyar take yi, Ni mamaki take bani kamar ba Batuul din da na sani ba. Sati biyu da faruwar abun yazo ya wuce, ranar Saturday da yamma Ina kitchen na kammalla shawarma Ina packaging, se naji sallama a kofar kitchen din, na Yi saurin juyowa anan Naga mahaifiyar Suleiman, da Dan murmushi saman fuska ta na gaishe ta, itama se Naga ta saki fuska ta amsa min da kulawar ta. Na fito Baki daya nace mata "Na fadawa Mamaa kinzo?" Tace "Eh har Asiya ma ki fada mata Ina jiran su" Wannan abun da ta fada se ya tabbatar min ba wani abun kirki ya kawo ta ba. Amma ni Ina ruwa na da abun su, ni ai tayi kokari sosae a gani na da ta iya hakuri ake juya Dan ta kamar waina a cikin kasko, he was devoted Dan abin da Suleiman yake Yi da Kuma errands din da yake wallahi ko daya daga Yaya Auwal ko sani basa ma kwatantawa. Mamaa Bata daki da naje se habiba yarinyar kanwar ta da tazo hutu gidan mu, na tambaye ta Mamaa tace min tana wajen Adda, na juya zuwa wajen Adda nan ma basa nan se kawai na tafi oarlon Kawu tun da Sunday ce I'm sure baije kasuwa ba. Aikuwa suna zaune dukkan su, da wani kudi a gaban su suna kasfatawa, na Shiga da sallama a baki na, dukka suna dago suna kallo na, na karasa Shiga Bayan nayi musu sannu nace " Adda Maman Suleiman din Batuul ce tazo?" Ta dalla min harara tana fadin " Wacce Batuul Kuma? Bayan ga kudin auren ta an kawo" Na Kara kallon kudin dake gaban su, a gidan mu dai nasan Muna da rufin asiri daidai gwargwado to Amma me yake saka su kwadayun abun duniya Haka? Na tabe Baki ko Allah ya Sanya alkhairi bance musu ba, na fito suka biyo baya na. Mamaa tace da Adda "Ni fa Adda bana son haduwa da matar nan, bansan da me tazo ba!" Adda ta tabe Baki tace " Tsoron me kike ji? Kina da Baki tana da Baki ta fada mu mayar Mata. Ya zamuyi tun da Batuul tace Bata son shi?" Ni fa wani lokacin iyaye na bani mamaki, ta Yaya zaka Haifa da a cikin ka, ka Sha wahalar shi, kayi Masa komai sannan ya kasa bin ka se Kaine zaka bishi? Kalla dai gidan mu, ya zaayi Batuul tace Bata son shi rana tsaka har Kawu su biye Mata kamar ita ta haife su Basu suka haife ta ba, wannan Abu na bani mamaki kwarai da gaske. Ko da na sanar mata suna tafe se kawai na koma kitchen wajen sanaa ta, Ina zuwa na tarar Alamin ya Kira ni, class rep din mu ne, Wanda shi ma Yana daya daga cikin mutanen da suka fita zakka a wadanda nake haduwa da su. Alamin mutum ne me kirkin gaske, a bakin shi ban taba Jin wani aibu na halitta ta ya furta ba, se ma idan yaga Ina damuwa yayi ta zolaya ta har se na Dan wartsake sannan zai bar ni. Na Fara kokarin Kiran shi se gashi ya sake Kira hakan yasa na dauka tare da karawa a kunnen na Muka gaisa, ya Dan zolaye ni kadan sannan ya sanar min akwai fixed class washegari karfe takwas na safe, kada na Bari nayi missing, nayi Masa godiya sannan mu Kai sallama. Ina aje wayar na jiyo muryar Maman Suleiman tana fadin " Ai idan ance mutum kwadayayye ne to an Gama magana, magana ta kare. Meye Suleiman Bai Yi muku ba, wacce bauta ce baiyiwa yarku ba Amma sakayyar da zakuyi Masa kenan? Da izinin Allah se Yar ku Batuul ta dandani makamancin abin da ya dandana na bacin Rai ..." "A'a tsaya malama, karki ma yarinyar mu baki, Dan kawai ta samu Wanda yafi shi, kinsan Fadi tashin da muke na ganin yadda zamuyi compensating din shi? Amma abin naki Babu arziki balle girma!" Fada sosae Adda da maman Suleiman sukai, kafin ta Mike ta fita, wani irin rashin Jin Dadi nake ji har cikin zuciya ta, ya ma zaayi iyayen mu su Zama so shameless Haka? Bayan ta fita suka ta mita a parlon har bansan yaushe kowacce ta tafi ba. Ko da dare yayi Ina kwance daki Batuul ta dawo, she looks tired, ta cire Kaya ko magana ba tayi min ba ta wuce toilet, Babu jimawa ta fito Ina zaune inda ta barni. Hijab di na ta dauka tayi sallah ae da ta idar sannan tace min "Bintu Dan Allah wanne irin perfume kike using, me Dadi Haka?" Ba tare da na kalle ta ba mace " SCENTMANIA nake amfani da shi" Se ta Mike tana fadin " A Ina Zan samu? Turaren nan duniya ne wallahi saboda yayi kamshi me kwantar da zuciya." Daga zaune na Fara Mata bayanin su, nace " Ai matar ta san lakanin turare Batuul, oils ta ke yi Kuma tana iya maida maka oil zuwa spray, Kuma idan Zaki siya, se kinyi Mata bayanin yadda kike son turare kafin tayi Miki recommending. Batuul ki gwada shi kawai..." Shigowar habiba ta dakatar da Ni daga bayanin SCENTMANIA, Nima bansan yadda akai na San shi ba, ba Zan iya tunawa ba, Amma fa yanzun bana tunanin akwai turaren da Zan iya amfani da shi Bayan SCENTMANIA. " Adda Bintu kizo in ji Mamaa" Na Mike Bayan na.amsa ta nabi Bayan ta zuwa dakin Mamaa, tana zaune da bowl a hannun ta na kwadon salad a ciki, na zauna bayan ta yimin tayi nayi murmushi nace " Pizza akai order, nayi ta Dan so tayi.yawa shi ne na cinye aba ta" "Ke dai Bintu ba Zaki rabu da wadannan fast food din ba, ke ba exercise kike ba, shiyasa jikin ki jiya I yau" Na tabbatar Mamaa ba zata taba fadar Haka ba, Amma Adda ai ba zata fasa ba, Koda kuwa zata ga na rataye Kai na ne Dan takaici. Bance komai ba se kicin kicin da fuska ta da nayi, shikenan saboda kana da kiba you can't eat abin da kake so? Ni dai Ina Zan saka Rai na ne naji Dadi? " Kinsan an kawo kudin Batuul ko?" Na gayda Mata Kai na Ina fadin " En! Allah ya Sanya alkhairi Suka amsa Amin baki dayan su, kafin Adda tace "Kawun ku ya tambayi ko kina da saurayi a hannu, mun fada Masa Babu kowa dake zuwa wajen ki, ya yanke hukuncin zai aura Miki Suleiman tun da,.." Ai ban Gama saurara ba, tunda sunan Suleiman da Kuma nawa hade da kalmar aure suka shigo sentence daya naji na daina gane me ake fada tukunna! Ta_kwalam [1/3, 20:28] Maman: 026 "Did I heard you well? Aure Kuma?" Ta fada da wata irin murya da zata tabbatar maka a raunane  take, ya sake ruko ta zuwa jikin shi saboda Yana iya ganin kishi karara akan fuskar ta, kafin yayi magana ta Fara kuka a hankali tana fadin " Tsoro nake ji, tsoron family din ka nake, you already have a wife how will they accept me Chum Chum?" Yayi shiru Yana Jin tashin hankali hade da tsoro Yana shigar shi, duk wata hanya da yake ganin lallashin ta zaiyi sauki yabi Amma se yaga abin na zainab kamar gaba yake sakewa. Kuka take sosae kamar yau aka sanar mata mutuwar Fahad, ya duba agogon dake kafe a hotel room din yaga karfe takwas da mintina goma , ya Kamata yayi haramar komawa amma Kuma idan ya kalle ta se yaji ta Ina zai bar ta a halin da take ciki, duk yadda Imam take sahibul Kalam yau gashi kalamai sun gagari bakin shi, abin da kawai yayi was hugged her and patted her back. Anan suke ta zaune har yaji alamar tayi bacci, cikin sauri ya kwantar da ita ba tare da yayi wani abu ba ya fice daga dakin. Dakin shi ya koma baifi minti na goma ya rage Tara tayi ba jikin shi ya gyara ya canja zuwa manyan Kaya da Bilal ya kawo masa, da saura mintina biyar ya Shiga wajen Ummiey, ya gaishe ta a gaggauce kafin ya wuce inda yake da tabbacin anan zaayi taron. Yana tafe Yana kallon gidajen da ke mallakin su, kowanne da idan aka haife shi ya isa sure anan zaa Gina Masa gida ayi Masa sure, a tarihin Gidado close Babu wani bare a cikin wannan waje, Haka zalika bai taba Jin labarin in da akace Wai yau a tarihin dangin su dake nan wani ya taba auren bare, shi ne na farko shiyasa yake Jin tension Yana building a jikin shi. Alhaji Gidado na zaune ya mikar da kafafun shi akan tumtum, dalilin hakan kuwa saboda kumburin kafafun da yake fama da shi kwana biyunnan. In dai taro zaayi to Alhaji Gidado yakan kasance mutum na farko da yake fara zuwa wajen taron, ba dai ka Riga shi ba sede ya jiraka. Gefen shi Amarya Safiyya ce wadda tun tana yarinya ita ke serving din shi tea, to ko jiya bayan anyi auren ma yau seda ta dafa Masa tea ta kawo Masa, tana zubawa taji deep voice din da tayi shekara takwas ba taji ba yayi sallama, a hankali ta juyo da wide grin saman fuskar ta, tace "Hamma Imam! Ashe ka dawo? Ashe da gaske ne!" Shima Yana murmushi Wanda kowa yasan Safiyya da Imam yadda suke, tun tana yarinya mutuniyar shi ce, saboda a cewar ta shi ya Fara kawo Mata cartoon din Sofia the first, wannan shi ne dalilin da yake ce Mata Sofia. Bayan ya zauna yace "Sofia the first!" Ya fada da murmushi saman fuskar shi, ta gyara Zama Bayan ta jira ya gaida Alhaji Gidado, sannan Suka gaisa tayi Masa murnar Gama makaranta da Kuma dawowa gidan cikin aminci da alkhairi, yayi murmushi Yana Mata godiya, a hankali daya biyu Kuma se ga iyayen su suna zuwa, dukka Suka gaishe su, Amma ganin Safiyya bata tafi ba se ya tabbatar wa da Kan shi taron har da ita, shi Bai maga tashi matar ba, tun da yazo Bai ga Rukayya ba, baisan Rukayya na dakin Mujahid ba, shi ta aura ba shi ba. Ganin lokaci ya cika se kawai akai proceeding da tattaunawar da zaayi, anan ya gabatar musu sabon construction company da ya bude Wanda ya damka shi kacokam hannun Imam, sannan ya tabbatar wa Imam Safiyya ce matar shi, a hankali ya dago Yana kallon ta Haka itama tana tayi Masa murmushin nan Mata me kwantar da hankalin, Haka kawai se yaji kaso me tsoka na damuwar da take ciki ta tafi, idan har Safiyya ce then komai zai zo da sauki. Bayan an Gama suka fito Bayan dogayen adduoi da Kuma nasiha da akai musu, suna tafe kowannen su yayi shiru zukatan su na tunani mabanbanta. A Haka Suka karasa wajen Ummiey shi, ta saka musu albarka, a ranar Bai samu damar komawa wajen zainab ba, se ya zauna a dakin shi yana tattaro bakin zaren, Yana ayyana yadda zai Fara, saboda kukan da zainab tayi yau da safe ba zai iya cigaba da ganin shi ba, ba zai iya boyewa ba saboda shi din ba Haka yake ba. Da daddare aka raka shi well furnished gidan shi, gidan da akai Masa shi da Safiyya, Bayan dukkan abin da sunna ta tanada se Suka Fara Hira like the old friends they were. Ya tambaye ta dalilin fasa bikin shi da Rukayya? Se ta fada Masa ai ganewa akai suna soyayya ita da Mujahid shi ne yasa aka fasa akace gwara ta aura Mujahid tun da dai har sun Riga da sun shirya Kan su. A bangaren shi se yace " Safiyya! Ban taba kawowa cewar Zan aure ki ba, though I've been eyeing you akan auren Ashe ke rabo na ce" Tayi murmushi tana sunkuyar da kanta kasa irin kunyar fulanin nan, yace "Ina son ki saurare ni, Ina son ki nutsu nayi Miki bayani Safiyya" Ta dago ta kalle shi taga fuskar shi Babu alamar Wasa, hakan ya tabbatar Mata da gaske yake maganar me muhimmanci ce, "Ina da aure Sofia! Yes da gaske nake nayi aure shekaru wajen hudu Sofia, I can't tell anyone Sofia, kinsan yadda muke rayuwa a gidannan, I'm scared!" Tabbas tayi mamaki, matuka ma kuwa Amma Kuma ba abin mamaki bane ba Dan dama kowa yasan Hamma Imam daban yake tun Yana yaro, duk wani abun Jan magana to ya iya dakko shi. Tasan tana son shi, tana son shi sosae, ko ranar da aka ce Mata zata aure shi, kusan murna hanata bacci tayi, har se da Dada wato mahaifiyar ta ta fahimta, anan ta Fara Bata dabarun yadda zata karkato hankalin shi gare ta tun kafin ma ya dawo, Kuma ko Ummiey ma Haka tayi ta Zama da ita tana nusar da ita dabarun sace zuciya tun da suka Haka akai musu aure ba tare da son rayukan su ba. Dole ka danne halin da kake ciki Dan ka faranta Masa Rai. "Tana Ina? A Ina ka barta? Tana can UK din?" Ya Kama hannun ta for the first time saboda abin da yake gani cikin idanun ta, she's trying hard to suppress kishin dake taso Mata, yace " Nazo da ita..." A hankali ya kwashe komai da komai ya fada Mata, tun daga soyayyar su day komai da komai, labarin soyayyar tasu se ta kayatar da ita ta Fara murmushi tana Jin Bai kamata su rabu ba, se da ya Gama yace " Bansan ya zanyi ba Sofia, Kai na ya kulle na Rasa yadda Zan fadawa wani cewar bake kadai bace Mata ta ba!" Ta saki nannauyar ajiyar zuciya tace "Ina son na ganta please, zaka kaini?" Yayi murmushi Yana matsa hannun ta yace " Of course Dear! Ya zanyi? Ki bani shawara" "Take it easy and slow, kasan gidannan ko bango na da idanu da kunnuwa!" Wannan abun da tayi Masa ya Bata kaso me girma cikin zuciyar shi, washegari ta shirya suka fita, Basu zame ko Ina ba se hotel din da zainab take. Baiwar Allah tana zaune yau ko breakfast din da aka kawo Mata Bata bude ba, tayi kuka cikin dare har ya hakura Dan kuwa tasan ta rigada ta shiga one chance, tana ganin rayuwar ta ta lalace, sede she's already stuck in this mess, soyayya a ganin ta batyi Mata adalci ba, Dan kuwa ta kawo ta kushewar ta, ta Ina zata Fara wannan yakin? Ina zata Fara wannan fadan da mutanen da bata San su ba, Bata San yaren su ba balle wani Abu nasu. Hawaye ya cigaba da sakko mata a kuncin ta, ta kalla lokaci past 10am Amma har yanzun Bai zo ba. Kawai se taji knocking a kofar dakin, cikin sauri ta Mike jikinta har wani rawa yake ta fita, tana zuwa ta bude ba tare da ta tambaya ba balle taji ko waye. Sofia tsaye da wani murmushi da yake saka mutane suji kaunar ta a zuciyar su, a Bayan ta Imam ne tsaye Yana Mata murmushi shi ma, da sauri taji wata nutsuwa tana saukar Mata, sede ta Kara kallon Safiyya tana ayyana wacece ita? Amma se taga suna Kama shi da ita, banbancin su kasancewar Safiyya tana da haske shi Kuma Imam duhu ne da shi. Ta sake sakin ajiyar zuciya sannan ta Basu hanya suka shigo, at least taga wani Dan uwan Imam hankalin ta a bit ya dan kwanta. Ta bawa Safiyya guri ta zauna, cikin sauri ta wuce t hado musu coffee cikin kananun mugs ta kawo musu sannan ta zauna. Suka gaisa, ta tamabye shi cikin simple larabcin da ta koya Masa Akan wacece wannan kyakyawar da batta gajiya da murmushi? Cikin turanci ya Bata amsa yadda Safiyya ba zata tsargu ba, yace matar shi ce ta jiya kuma cousin din shi, tayi shiru ba tare da tace komai ba, Safiyya ta matsa gefen ta a hankali tare da rungume ta tana murmushi tace " Jiya dare muka raba Yana bani labarin ki, se gashi da na ganki se naji you were underestimated!" Zainab ta Dan saki murmushin Jin dadi na maganar da Safiyya ta fada, Amma dai Bata ce komai ba, se da Safiyya tace "Naji labarin soyayyar ku, tayi min Dadi I'm mesmerized by the story, sede Zan taimaka muku iya bakin kokari na wajen ganin Baku rabu ba. But be patient zai Dan dauki lokaci" Wannan abun da tayi gaba daya ta jefa musu yardar ta cikin zukatan su. A karshe ta dan nema izinin shi Dan fita ta Basu waje su zanta. Tana fita zainab tana murmushi tace "I like her!" Sun Jima suna Hira kafin ya Mata sallama Suka tafi, to shikenan se ya zamana Haka suke kusan kullum zasu zo tare tun da Bai Fara zuwa aikin ba saboda company baa gama wasu touch ups ba. Wannan ya Sanya shakuwa me karfi tsakanin zainab da Safiyya, Suka Zama tamkar siblings, har lokacin mutum daya kaf wannan family Suka fadawa wato Ummiey, ta tsorata sosae, ta dinga yiwa Imam fada Amma se Safiyya ta nuna Mata tayi musu addua Dan tana ganin zainab zata ji soyayyar ta. A Haka wata guda yazo ya wuce, kamar Wasa Haka Imam yake gani, Wai duk mazantaka da tsaurin idanu da rashin tsoro ya kasa bayyana wannan maganar. Hatta Safiyya ta fishi jarumta Dan ita tayi yunkurin fadawa old Man kamar yadda suke Kiran shi, Imam ke hanata saboda tsoron makomar zainab, idan Dan ta shi ne zai iya jurar komai da zaayi masa. Wani dare Suka dawo daga wajen ta, sun samu Bata da lafiya, sun Kai Mata duk abinda take bukata kafin Suka rabu Dan da farko Safiyya ta yarje Masa kwana wajen ta, se zainab Taki amincewa kada a zargi wani Abu. A yadda Safiyya ke Bata labarin family din su ta fahimci she's trapped in a lion's Den. So itama hankalin ta yafi kwanciya zamanta anan Kuma a hakan. A wata na biyu Ummiey taga zainab, bisa rakiyar Safiyya, tabbas taji kauna da Kuma tausayin ta sun lullube ta Amma Yaya zatayi? Babu yadda ta iya, Dan Haka a wannan Daren cikin siyasa ta fadawa mijin ta wato mahaifin Imam abin da yake faruwa, Tsabar girgiza da yayi se da ya tashi ya zauna daga kwanciyar da yake, yace Mata cikin kasa da murya "Fatima wacce irin magana ce wannan? Imamu na da hankali kuwa? Bazai daina ja min magana a wajen Baffa ba?" Ta Kara kasa da murya tace " Me faruwa ta faru, kawai ka fada Mana yadda zamuyi, ya kamata yarinyar nan a bayyana ta Haka.." Ya girgiza Kai saboda ya kasance me tsoron mahaifin shi ne yace " Ba Zan iya ba, bana son bacin ran Baffa, bana son tashin hankali kinfi kowa Sanin hakan ko?" Tayi shiru tana tunanin mafita, wadda har safiya tayi Basu comma matsaya ba. Duk movement din su Ashe Alhaji Gidado ya sani, Malam magaji driver ya sanar Masa inda suke zuwa shi da Imam da Safiyya. Da yammaci zainab da ta dandana tuwo taji Dadi ta fadawa Safiyya tana son ta kawo Mata irin shi, Dan Haka Safiyya ta dage ta tuka tuwo tayi miyar da ta wadatu da nama sannan ta juye cikin kwanuka masu kyau, har zobo tayi Mata ya Kuma shirya tana jiran dawowar Imam... To be continued Ta_kwalam ce [1/3, 20:28] Maman: 028 "Baki ji ba? Baki ji abin da nace Miki ba?" Na dubi Adda confusingly nace " Adda Suleiman fa? Kai! Dan Allah kiyi hakuri, Dan Allah ku bawa Kawu hakuri Nima Zan samu miji na ko ba dade ko bajima!" Tace cikin Bata fuska " Waye yace miki opinion din ki ake nema? Waye yace miki option aka Baki, to Bintu ban da abunki waye zai zo kina shekara ashirin da biyu har yanzun Babu Wanda ya taba zuwa wajen ki, sannan kice Zaki samu mijin ki?" Kunsan kullum Ina fada muku shi harshe mugun Abu ne, gashi dai tsoka ce amma kaifi ne da ita, zata iya yanka har zuciyar mutum, be wary of abin da kuke furtawa. I'm so sorry to say abubuwan da dama laifin iyayen mu ne, saboda yawancin wannan body shaming din Yana faruwa ne daga gidajen mu, yawancin iyayen mu su suke Fara aibata mu Wanda yake saka Mana shakku cikin zukatan mu, ni na zame muku misali a rayuwa, ya kamata ace mu iya bakin mu " Adda me yasa kuke min Haka a gidannan? Wani laifi nayi da kullum bani da say a cikin rayuwa ta se abin da Batuul ta rage shi Zan dauka..." Mari naji akan kunci na Wanda yasa nayi saurin rufe Baki na, nasan Nima tabbas Bai kamata na Fadi Haka ba, to Amma Kuma zuciya ta ta kekeshe, wanne irin Abu ne wannan? Ya zaayi a hada ni da Suleiman! Zuciya ta kamar zata fito Haka nayi taji, na mike kamar jiri zai fadar Dani nayi daki, Ina zuwa na samu Batuul a kwance tana waya " To Hubby kwana nawa ne munyi aure? Why not ka jira ayi sealing deal kafin muma muyi sealing namu deal din" Wannan shi ne abin da na Fara jiyowa da na shigo dakin, na fada Kan gado na Fara wani irin kuka har jiki na Yana wani irin rawa, tayi saurin sallama da shi ta taho waje na a rude tace " Bintu me ya same ki? Bintu ya kike irin wannan kukan?" Yadda take fada a muryar ta ta tabbatar min how much she cares, Amma Karo na farko se naji wata irin tsanar Batuul ta Shiga zuciyata, naji komai da yake faruwa saboda ita ne, why am I cleaning after her mess?! Kuka kawai nake, da Naga zata takura min se na mike na wuce toilet na rufo kofar da karfin gaske, na sunkuyar da Kai na akan sink Ina wani irin kuka Wanda har addua nake dama ace numfashi na ya yanke na Fadi na mutu, nayi kukan har na gaji, Haka Batuul ta buga kofar kamar zata balla ta gaji, se ta Fara fada min " Bntu kiyi hakuri koma menene? Bintu Dan Allah ki fito wannan wanne irin kuka kike? Me ya faru?" Nayi Mata banza, se kawai ta fita taje ta samu Adda ta sanar da ita abin da yake faruwa, ta cigaba da kurbar tea din ta tace " Tayi duk abin da zatayi, auren Suleiman dai babu fashi Kuma ta sani, kiyi kwanciyar ki ki rabu da ita!" "To ai bazan iya bacci ba tana wannan kukan" Se tace Mata " Yi kwanciyar ki anan, taje ta Gama ihunta ita kadai!" Wannan Daren banyi bacci ba, kuka nayi shi na Kara, na sake Yi na Kuma to addua shi ne abin da yasa na dan samu saukin abin da ke zuciya ta. Washegari da wurwuri na shirya na tafi school, bayan na Gama lecture ma ban dawo ba se na tafi wani guri can gefen wani faculty na shimfida sallayar da bana rabuwa da ita, na dauki waya ta na Fara neman tips na yadda mutum zaiyi shading kibar shi, abin da ya Fara popping a gurin shi ne dieting, se na kudura aniyar daina cin abinci ko na samu na rage kiba, walaallah a daina musguna min, na Kuma samu mijin da Zan aura ba Suleiman ba. Present day! A hankali na Fara kokarin ganin ko ta wanne Hali na samu na zabge wannan kibar dake jiki na, ko Zan samu na samu afuwar rayuwa, na daina Jin Kai na kamar wata alien wadda tazo daga wata duniyar ba Earth ba, na saki ajiyar zuciya Ina gwada nauyi na akan bathroom weighing scale din da na siyo, 85kg shi ne abin da na gani, na Fara duba jiki na tun daga fuskata da kurajen da suke mutuwa Kuma suke sake dawowa, na kalla fuskar da kyau Ina ayyana I need a tangible skin care products na fara amfani da shi ( for visibility and advert send in your product). Na lumashe idanu na wannan shi ne first step din da na Fara dauka. Na karewa jiki na kallo da kyau sannan na Yi wanka na fito na duba wardrobe di na , duk yawancin Kaya na boubou style ne bana son wani style Kuma saboda tun Ina yarinya idan nace Ina son style din da Batuul ta zaba se ace min, ai ba na masu kiba bane ba. Shiyasa nake karbar duk abin da aka Dinka min. Na shirya fes sannan na murtsika Addictive Ambergris, shi ma daya daga cikin turarruka na SCENTMANIA ne, Yana da kamshi Yana da Dadi very affordable, wadda batai amfani da shi ba tabbas kamshi ya barta. Na wuce kitchen na dauki packages slice cake din da nayi saboda na kaiwa su Alamin, Bayan taimakon da sukai min da na Fadi a class ai they deserve more. Ina gamawa na kalla Irish da kwai da aka kammalla cikin warmer, ciki na yayi Kara Amma na dauke idanu na akan abincin I need to do it, I need to shed my weight ko na samu Abu yayi kyau, na samu mutane suyi accepting di na. Ban sani ba shirme nake Yi ko a daidai. Bansan akwai zancen test ba se da na karasa school, na samu me building construction and materials Yana kokarin yin test, na zauna na karba question paper nayi scanning da idanuna, Haka nan na karba ba Wai Dan inada tabbacin Zan iya ba, tunda ban taba bude littafin ba. A hankali na samu na amsa Wanda Zan iya na Yi ticking abin da zuciya ta ta Raya min. Muna kammallawa naji kaina ya Fara juyawa Yana Kuma ciwo, na daure na ji lecture din, Bayan ya fita na bawa Alamin sakon da na kawo yayi min godiya sosae na dawo na zauna. Lecture din karshe ta Akram ce, lokacin na gaji Kuma Ina da tabbacin yunwa nake ji, carrot din dake jaka ta na dauka naci sannan na Sha ruwa se naji saukin abin da nake ji. Babu jimawa se gashi ya shigo, kamar kullum fes da shi Dan gayu, ya Sha farin yadi me layi layi, Amma na kasa gane wanne color ne layin, Kan ya hau podium yazo Kai na ya tsaya, hakan yasa na gaishe shi a hankali, ya amsa ba tare da ya kalle ni ba, " Have you ate?" Se na Dan ji kamar I'm embarrassed, na gyada Kai na yace " Better! Bana son a dinga interrupting class di na" Bai jira amsa ta ba yayi gaba, na Dan daga murya yadda zaiji nace " Sir thank you! Sakallahu khairan!" Se naga ya Dan tsaya a hankali kafin Kuma ya juyo ya gyada min Kan shi ya koma Kan podium, cikin turanci shi me tsafta ya Fara binmu cikin course din, Ina ta fahimta se can na Fara hango shi bibbiyu, na kasa bude idanu na da kyau, se gumi me yawan gaske ya wanke min fuska a take na Fara wani irin numfashi, daga nan bannsan Kuma me ya faru ba.... *** Da murmushi Imam ya shigo, wani irin kallon kauna yake bin Safiyya da shi, tabbas a zaman su da farko bai sonta ko kadan amma wannan kauna da take yiwa zainab yasa zuciyar shi ta Fara karkatowa gare ta, cikin saa Kuma se ya Fara son ta, ya Fara Jin ya damu da ita albarkacin son da take yiwa zainab. Ko wannan basket din da yake aje se ya Kara sawa yaji kaunar ta a zuciyar shi. Ita dai tayi nasara dan kuwa zuciyar ta me kyau ta saka ta samu matsugunni me kyau a zuciyar da Imam yake ganin ta zainab ce kawai. Tare suka fita suna ta hirar su cikin soyayya, tana ta murmushi na Jin dadi, mahaifin ta Baffa Nasiru Yana zaune ya dube su bayan yayi musu izinin su tashi daga tsugunnon da sukai, yace " Wai imamu Ina kuke zuwa kullum ne Kai da Safiyya?" Ya Sosa Kan shi yace " Aboki na ne bashi da lafiya zamu je duniya!" Ya shi musu albarka sannan suka shiga mota inda driver ke jiran su. Kamar kullum kofar hotel ya sauke su suka shiga shi Kuma yayi parking karkashin bishiya. Zainab tana ta murna mussamman da taga abincin nan, ta zauna dukka suka hadu suna ci suna hira cikin Jin dadi. Knocking da Suka ji yasa dukka Suka tsaya da dariyar da suke, Imam ya dubi zainab yace " Solace waye?" Ta girgiza Kai tace " Ya Zan sani, I dunno!" Safiyya da Haka kurum taji gaban ta ya fadi tace " Bari na duba na gani" Ya dakatar da ita ya mike, yaje Yana budewa yayi mummunan gani, to mummunan gani Mana tun da kuwa Alhaji Gidado ne a tsaye da Kuma Alhaji Mamuda Wanda ya kasance kakan Safiyya na wajen uba, kakan Imam na uwa. Imam ya tsaya ya tokare kofar ba tare da ya matsa ba, Amma jinin shi kadai ma tafasa yake saboda ya firgita ba kadan ba har firgicin yayi nasarar bayyana saman fuskar shi. Jin shiru yasa zainab tace " Chum Chum waye?" A lokacin ya saki kofar Alhaji Gidado da Alhaji Mamuda da Kuma biyu daga cikin uncles din su Suka shigo Baki daya. Safiyya a firgice ta Mike Allah yasa ta hadiye abin da ta saka da babu yadda zaayi Bata kware ba. A take jikin ta ya Fara rawa kamar ana kada Mata mazari, ta dubi zainab da take tambayar ta su waye? Kafin ta Bata amsa taji saukar Mari a saman kuncin ta, wani dummm taji a kunnen ta, kafin marar ta ta tsikare ta, Amma zafin Marin yafi zafin ciwon da take ji a marar ta. Da sauri Imam ya taho ya tsugunna gwiwa kasa gaban Alhaji Gidado Yana fadin " Matata ce! Auren ta nayi daga UK, don't get the wrong idea!" Ta_kwalam ce [1/3, 20:28] Maman: 030 _Ni me laifi ne, bani da Kuma bakin da Zan Baki hakuri solace. I've hurt you ever since da na tafi Dake Nigeria, nasan ni coward ne, Ni matsoraci ne but wallahi zainab wannan shi ne kadai abin da Zan iya Yi nayi protecting din ki ke da Akram, thank you for raising this child alone. Thank you zainab, I never wanted to be a source of pain in your life, but this is the path we must cross. I'm so sorry, na sake ki saki daya to free you from this shackle..._ Kuka sosae zainab take tana kankame takardar, ta kasance mace ce me uzurin gaske, amma a yau zuciyar ta ta kasa yiwa Imam uzuri. Me yasa da yazo ba zai ce mata yazo tafiya da yaron shi be, must he stoop this low just to take away what belongs to him. Tasan shekaru bakwai da suka gabata tayi Masa uzurin zaman shi helpless, tasan Babu yadda zaiyi aka raba su, Haka tasan wannan tsohon kakan nashi ya saka shi shafe shekaru bakwai ba tare da ya waiwaye ta ba balle har yasan ta Haifa Masa Dan shi. Se wannan lokacin, out of nowhere yazo Kuma yayi sati Bayan tana ganin kamar komai ya warware se kawai ta bude idanu cikin dare taga babu Akram danta Kuma babu Imam, dukkan laifukan shi na baya ta yafe Masa Amma tana tantamar idan zata iya yafe Masa wannan, ga Kuma wani saki da yayi mata, ya sake ta! Hawaye ya cigaba da saukar Mata a kuncin ta, har yaushe zata ji dadi ita kuwa? Shima yaron se da suka samu labarin haihuwar shi Suka dauke shi, wanda shi ne kadai abin da ya rage Mata na Jin Dadi a rayuwar ta. Dawowar police officers din se ta nuna musu tasan Wanda ya dauka yaran sunyi communicating, police din sukai shiru alamar basu yadda ba Amma yadda ta dinga convincing din su dole suka tafi. Daga Haka ta Fara tunanin yadda zatayi da rayuwar ta, ta San a duniya in dai Safiyya na raye, Ummiey na duniya to tana da tabbacin Akram ya samu uwa mussamman da yace Safiyyar bata haihu ba har wannan lokacin. Ta Shiga dakin Akram tana Kara kallon kayan shi a barbaje na.wasa, hawaye ya zubo Mata tana Kuma adduar ya kasance kada Akram yayi kewar ta, sannan Allah ya Bata ikon cigaba da rayuwa yadda ya kamata. Da Rana tsaka Suka iso kasar Nigeria, cikin birnin kano, driver na jiran su tun safe Dan Basu ma Fadi karfe nawa ne zasu dawo din ba. Bayan driver har da mujahid a masu tarban su. Tunda suka Shiga jirgi Akram ya lafe a jikin Imam, saboda adan kwana biyun da sukai tare ba karamin sabo sukai ba, har suka kwana a Abuja baya zuwa ko Ina se gurin shi, ko kallon Alhaji Gidado da lokaci daya yaji so da kaunar yaron ta tsarga masa cikin zuciyar shi Amma ko kadan Akram yaki ya yarda ya raba jikin tsohon kamar yasan shi ne Wanda yayi destroying rayuwar mahaifiyar shi. Imam dai Yana zaune ne Amma zuciyar shi se tuhumar shi take akan dalilin abin da yayi, he needs his freedom ya sani, Amma Kuma neman freedom ba shi bane ba abin da zai saka yayiwa zuciyar da ta so shi, ta kaunace shi, ta kyautata Masa Haka ba. Yasan Alhaji Gidado yayi Masa barazana da dakko Akram ya samu yancin zuwa kowacce kasa da yake so hakan yayi amfani da shi, sede Kuma ya kasa nutsuwa Yana ayyana a wanne halin zainab din take, ga rashin Akram ga Kuma mutuwar aure, Abu goma da ashirin! Fast forward, Suka fito daga departure hall, Suka fito farfajiyar airport in da suka hangi driver na jiran su, Haka Suka karasa Yana sabe da Akram duk da girma da yayi. Mujahid da murna ya Fara kokarin karbar Akram tare da Yi Masa marhaba da Dan guntun larabcin da ya Dan tsinta only God knows where? Amma fur Akram yaki zuwa, dole Haka Suka tafi. A gida Safiyya ta kasa zaune ta kasa tsaye, shiri take sosae na tarbar mijin ta, ko kadan Bata da masaniyar zaa dakko Akram ne, ita tunanin ta ma wani abun Suka tafi. A gajiye ya shigo parlon Akram na biye da shi da katuwar beach ball a hannun shi, Safiyya ta taho tarar shi amma tana ganin yaro taja ta tsaya tana kallon yaron tana Kuma kallon Imam questioningly, ya Dan zauna Yana fadin " Daga Qatar muke, Akram ga Ummaah ka go to her!" Das das ya nufi Safiyya da take ta kallon yaron idanun ta sun ciko da kwalla, gashi dai yaron Kama yake da Imam sosae amma Kuma akwai features din shi da suke nuna shi din Dan zainab ne. Ta tsugunna daidai tsawon Akram ta bude Masa hannun ta, abun mamaki ya karasa ta rungume shi tana kuka, ga ikon Allah, kenan zainab da ciki ta tafi kenan? Shiyasa take ce Mata ta dafa Mata zobo da tuwa miyar taushe. Kankame shi tayi sosae a jikin ta . Imam ya dube su ganin Akram ya shagwabe fuska zaiyi kuka yace "Wife zaiyi kuka fa!" Tayi saurin sakin shi tana dariya hade da share hawayen fuskar ta, yau Kam tana cikin tsananin murna ta dago ta Fara tambayar shi inda maman shi take, yace cikin turancin shi da larabcin Qatar ya gurbatar yace " She's home!" Ta dubi Imam tace " Ba tare kuka zo ba? Acan ka barta? Me yasa ka barta baka taho da ita ba" Yayi shiru Kan shi ciwo yake, Bai son magana a wannan lokacin, gaba daya Kan shi a cunkushe yake. Yace " Wife Zan yi Miki bayani, na gaji I need to rest!" Tayi saurin bashi hakuri sannan ta ja hannun Akram ciki, tayi Masa wanka ta bashi abinci sannan tace ya kwanta ya huta. Se dare suka samu magana da Imam, yayi Mata bayanin abin da ya faru, a Karo na farko yaga fushin Safiyya tace " Ka bani mamaki, har yaushe zaka biyewa wancan tsohon kuyi Haka? Ya zaka raba uwa da danta ba tare da Sanin ta ba, iko da takamar ka danka ne ko? To baka kyauta ba, bakai Mata adalci ba ko kadan" "Na sani wife bansan ya zanyi ba, nima hankali na ba'a kwance yake ba, I'm guilty tension" Fushi ma babu abin da zaiyi ko kadan, Dan Akram da shi kan shi Imam abun tausayi ne. Haka Safiyya ta zame ma dukkan su sanyin idanuya, a hankali tun Akram Yana tambayar imam yaushe zasu je gurin Amma har ya daina. Imam ya koma Qatar din a zuciyar shi wannan karon zai gyara dukkan kurakuren da yayi a baya, dole ne ya dawo da zainab rayuwar shi, Amma kaddara wata abace da baka da say akan ta, baka San ya zakai ba. Yana zuwa ya tarar zainab bata nan, Babu Kuma Wanda yasan inda ta tafi, a wannan kasar da Bai San kowa ba Kuma ba shi da kowa Ina zai Fara neman zainab shi kuwa? Haka yayi sati Yana garari inda ya samu labarin family business din su da take kula da shi tayi hiring sabon manager dan ya kular Mata da komai, Amma su dunma since Basu San inda ta tafi ba. Akram Yana girma Yana Kuma rayuwa cikin Jin dadi, har lokacin Bai sakin jiki da mutane sosae, shiyasa ko school Imam ke kaishi ya dakko shi ko Safiyya, baya bin bus din family da take sauran yaran. I'm fact makarantar shi daban Imam ya saka shi da sauran, gani yake tunda yaran Bai son relating da kowa da yawa gwara ya nisan ta shi. Dukda hakan a cikin yaran gidan akwai Wanda suke zuwa gurin shi kuma yake kula su shima Yana Wasa dasu. A Haka yayi ta girma Yana ta karatu cikin hukuncin Allah ya shekara goma Sha hudu Wanda anan ne ya Fara rashin lafiya da aka kasa gane abin da yake faruwa saboda poor health system a lokacin. Bangaren Safiyya, rukon da tayiwa Akram irin rukon da uwa zatai wa danta ne, se ya zamana yafi sabawa da ita akan mahaifin shi ma, komai nashi ita ce itama Kuma yadda ta rike shi se Bata damu Dan Bata samu haihuwa ba. A shekarar shi ta goma Sha biyar Safiyya ta Haifa Yar ta mace aka saka Mata zainab kamar yadda kowa yayi expecting. Duk da nema da suke yiwa zainab din Amma har lokacin ba su samu nasarar samun ta ba. Shekarar Ihsan wato zainab biyu Safiyya ta sake haihuwa aka saka ma yarinyar suna Iman daga nan Bata sake haihuwa ba. Akram Yana ta rashin lafiya sede Babu Wanda ya fahimci menene matsalar shi. Lokacin da ya Gama secondary School se Imam ya shawarci Safiyya akan kasar da take ganin su Kai Dan nasu karatu. Ta danyi little research kafin ta shawarce shi Akan ya Kai shi Qatar with the hope ko zai hadu da zainab, Haka ya tafi yana kewar mahaifiyar shi! Ta_kwalam [1/3, 20:28] Maman: 029 Maimakon ya saurari abin da Imam din ke fada Masa se baiyi hakan ba, hasalima wuce shi yayi ya nufi zainab, da har ta Fara kuka, ta Kan tuna labaran da Safiyya take ba ta na wannan tsohon, da dukkan alamu tasan shi ne ta Kuma San ta Kade har ganyen ta. Ta rasa yaren da zatayi amfani da shi tayi Masa magana, se da taji yayi Mata larabci, kunsan idan ka samu Wanda a dubban jama'a shi kadai ke Jin yaren da kake ji, zaka ji kwanciyar hankali ko? To Banda zainab saboda kawai kallon ma da Alhaji Gidado yake Mata is never pleasing, ta sunkuyar da kanta tana amsa Masa tambayar da yayi Mata na ita balarabiyar wacce kasa ce? A hankali cikin kuka tace " Qatar!" Yayi wani smirk yace " Shi ne kika taho tun daga can har nan saboda ki zubar da mutuncin ki?" Tayi saurin dagowa, a lokacin ba tashin hankali bane ba akan fuskar ta, se bacin ran abin da ya fada, sede Alhaji Gidado mutum ne da Allah ya hallice shi da kwarjini na gaske wannan yasa Babu Wanda yake iya ja dashi, ko ita zainab Banda ta kalla fuskar shi kilan zagin shi zatayi Amma suna hada idanu ta shanye bacin ran ta, sede Bata bashi amsa ba, hakan yasa yace ta dakko masa passport din ta, a lokacin kukan ta ya tsanan ta, ta Fara kallon Imam da idanun shi sukai jawur tamkar garwashi, wata irin wuta ce take ci cikin zuciyar shi, ya nufo Alhaji Gidado Yana fada Masa matar shi ce, ya tambaya a school din su kowa ya sani, Amma se ya daka masa tsawa yace " Karka kaini bango yaro, kada ka Bata min Rai ban zo kanka ba, ka Adana kalaman ka tukunna!" Duk da Haka baiyi shiru ba ya Fara fadin " Kai Allah ne? Ko Dan Allah ya baka dama shiyasa..." Mari yaji a kuncin shi Wanda uncle din shi ya saukar masa har yayi nasarar toshe bakin shi, jiki na rawa zainab tana Kuma kuka ta bashi dukka travel documents din ta, Bayan ya karba yace ta janyo suitcase din shi ta biyo, ta kalli Safiyya da se lokacin ya fito daga shock din marin, kuka take itama Amma bakin ta ya kasa magana, ta kalli Imam da yayi kukan Kura ya rike ta Yana fadin , matar shi ce babu inda zata je, Alhaji Gidado ya tsaya Yana kallon Imam da mamaki, Babu wani da a gidannan da ya taba mayar Masa magana se wannan tsageran yaron. Ya dubi zainab da take kuka har muryar ta ta daina fitowa yace ta zaba ko silently ta bishi ko Kuma yayi ma Imam abin da ba zai taba mantawa ba. Ta kalle su sannan ta rike hannun Imam kamar wadda take rada tace "Chum Chum! Kayi shiru, lemme go. I'll wait for you ko da nan da ten decades ne..." Daga Haka ta bambare hannun ta daga nashi tabi Bayan Alhaji Gidado da dayan daga cikin uncles din su Safiyya! Tana kuka ta wuce tana ta waigen shi a tsaye yayi shiru ya dunkule hannun shi, idanun shi looks dangerous at the same time Kuma he looks pitiful, Yana kallo Haka zainab tabi Bayan Alhaji Suka tafi, a hankali Safiyya ta sulale tayi zaman dabaro a kasa, Alhaji Mamuda da sauran Suka fice suka bar su su biyu Babu me cewa da Dan uwan shi wani abu. Se da awa daya ta wuce kafin Safiyya tayi yunkurin karaswa inda yake zaune ta ruko hannun shi, tana rike shi kawai se ya rungume ta ya Fara kuka " She has left me Safiyya! Ya zanyi? Ina Zan saka rayuwa ta?" Itama kuka take dukda suna da yakinin kakan nasu ba zai citar da ita ba Amma Kuma me yasa baiyi bincike ba? Me yasa Bai Basu dama suyi magana ba? Ta Fara patting bayan shi saboda tasan lokaci ne da ya kamata ta kasance jaruma Dan kuwa Imam na bukatar ta. Fast forward, Haka suka tafi gida kowannen su idanu sun Yi jawur kamar gauta, magana ta Riga da ta baza family akan Imam ya kawo karuwa tun daga UK Kuma Safiyya ta Goya Masa baya. Mahaifin Imam na Jin Haka ya Shiga wajen Ummiey Dan Jin kanin bayani, anan tana kuka tayi Masa bayani, ta Kara da fadin " Ni nasan Imam ba zai taba kawowa macen da Bata hallata a gare shi ba, Kuma inada shaida akan Safiyya ba zata goya masa baya hakanan ba. Kuskure tabbas yayi da ya boye bai fada ba, Amma nasan tsoron abin da zaije ya dawo yakeyi" Abba ya gyada Kai cikin gamsuwa da bayanin Ummiey yace " Na yadda, Amma Ina son duk yadda Alhaji zaiyi kada kice kinsan zancen Dan Allah!" Ta gyada Kan ta tare da tura Anisa taje taga yadda suke, sede tana zuwa.suna kokarin fitowa saboda ciwon Mara da Kuma bleeding da Safiyya ta Fara tun dawowar su. Da sauri ta koma ta sanar da Ummiey, Ummiey hankalin ta ya tashi tace tayi maza taje ta fadawa yakumbo halima wadda ta kasance kanwa ga mahaifin su Imam, cikin sauri ta sanar Mata aikuwa ta zaro mayafi ta same su har sun Shiga mota, tare suka tafi Bayan an tafi sanarwa Dadan Safiyya abin da yake faruwa. Suna zuwa asibiti aka tabbatar tana da ciki Kuma ya lalace, akai Mata wankin ciki Suka dawo washegari. Yan dubiya da masu tsegumi Haka suka ta zuwa, yayun da Imam ya zauna tsayin daka kula da Safiyya duk kuwa yadda yake cikin damuwa me yawan gaske. Bayan sati da maganar basu Kara haduwa da Alhaji Gidado ba, maganar ma cikin community din tasu ta lafa, da daddare suna zaune sun Gama cin abinci, kowannen su yayi shiru Yana tunanin zainab, Amma kowa ya kasa furtawa Dan uwan shi Dan gani suke zasuyi hurting feelings din juna musamman shi Imam din. Sallamar mahaifin shi da yaji a kofar parlon yasa shi mikewa da sauri ya nufi wajen, aikuwa Abba ne da Kuma baffan Safiyya, suka shigo suka zauna, a lokacin Safiyya ta fito da mayafi, ta tsugunna ta gaishe su sannan ta kawo musu ruwa. " Imamu me ya faru?" Shi ne tambayar da baffan Safiyya ya fara Yi masa, aikuwa a take Safiyya ta fara kuka, Imam ya dube ta da kulawa yace "Kiyi shiru kiyi hakuri" Imam cikin kwantar da Kai ya Fara bayani yace " Nasan nayi laifi Abba, nayi aure Babu Wanda ya sani ..." A hankali ya Fara Basu labari komai da ya faru har karshe, Bayan ya Gama baffan Safiyya yace " Me yasa baka fada Mana ba? Kana ganin muna Jin dadin abin da mahaifin mu yakeyi? Bamu Jin Dadi amma mu yaran shi ne ba yadda zamuyi, we want one of you to challenge him. You should have informed daya daga cikin mu da Haka Bai faru ba" Imam yayi shiru me faruwa ai ta faru, Ina zai San iyayen shi zasu goye Bayan shi. "Bamu San inda ya kaita ba, Kuma baice Mana komai ba" Abba yace " Ya maida ta Qatar, Ina ce baka sake ta ba?" Ya gyada kai, se Suka ce ya Basu lokaci. Haka suka cigaba da rayuwa kamar Imam ba zai Kai ba saboda kullum dare idan ya tashi sallah se yaji kewar zainab a cikin jikin shi, kullum faking yake Amma rashin zainab, tunanin halin da take ciki na saka zuciyar shi cikin kunci. Safiyya tayi kokari dukda wani lokacin tna Jin zafin zainab tun da kishi gaskiya ne Amma Kuma tana kokarin danne shi. A hankali shekara tazo ta wuce Babu wani labari Haka shima Alhaji Gidado baice komai ba, sede duk kokarin barin kasar da Imam yake Yi ya gagara saboda strings da Alhajin yayi pulling. Safiyya Bata sake samun ciki ba har shekara bakwai tazo ta wuce. A wannan shekarar Kuma Alhaji Dake da sauran karfin shi ya saka Imam a gaba akan su tafi Qatar dakko yaron shi! Somewhere in Qatar Da yammaci jirgin da ya dakko ta ya Isa kasar tata, kuka har ta gaji da yin shi musamman idan ta tuna yanayin da ta bar shi a ciki, ta kalla ko Ina ko a mafarki batai tunanin zata dawo kwana kusa ba,. Se gashi ta dawo ba tare da ta fahimta ba. Gidan jadda ta wuce wadda zuwan zainab din ya daga Mata hankali Amma ganin ta kamar hankalin ta baa kwance yake ba se kawai ta kyale ta, se da ta saka tayi wanka ta kawo Mata abinci Wanda tana cin shi ya dawo ta barta ta huta. Se Bayan kwana biyu zuciyar ta ya danyi sanyi kafin ta sanar ma jaddar abin da ya faru a Nigeria, ba karamin gudunmawa ta bawa daidaituwar zainab ba, wadda Suka fahimci ciki ne da ita. Ana ta raino har ta haifi Dan ta namiji ta kuma saka mishi Akram Bayan dogon deliberation. Kullum idan ta kalle shi mahaifin shi take gani a tare da shi, tana Kuma kewar Imam da Safiyya, lokuta da dama Haka zata shuga daki ko cikin dare tayi kuka ta godewa Allah, tayi tunanin wanne halin suke ciki Bayan tafiyar ta. A Haka shekaru sukai ta tafiya, Babu means din da zatai communicating da shi. Kullum jiran ta inda Imam zai zo take amma Babu Imam Babu dalilin shi, har Akram yayi shekara uku, a shakarar jadda ta rasu, zainab ta rasa kowa se ita se Akram, she's strong even for the sake of Akram. Se Bayan shekara bakwai, Akram ya Fara girma se ga Imam out of nowhere yazo gurin ta. Ku kaddara irin farin cikin da zuciyar ta zata kasance a ciki! Refer to page 1 Ta_kwalam ce [1/3, 20:28] Maman: 033 Bayan na fito daga office din na tsaya can nesa da gurin, na Fara tuhumar Kai na akan dalilin da zai saka na bude Masa ciki na, menene tsakanin mu? Yaushe ma na san shi da har Zan zauna Ina amsa tambayar shi kamar Wanda yayi bewitching dina irin dinnan! Se Kuma wata zuciyar tace ke kuwa Kika San shi tunda kuwa he saved your life ba sau daya ba, duk da bai san ke din wacece ba, gashi yayi kokarin Sanin matsalar ki Dan nema Miki magani. Se na tuna lokacin da nayi attempting suicide a Niger, I remembered Doctor din ya fadawa iyaye na akan lallai lallai su kaini wajen therapist, Amma kalla sun Kai ni? Bayan na dawo ma baa sake tuna maganar ba Tasha ruwa. Kuma tsangwamar da suke yimin ba dainawa sukai ba. Dan har yanzun zancen auren Suleiman bai gama mutuwa ba Dan ko shekaran jiya se da Adda tayi min maganar Shi, shi ba Kira na yake ba ba komai ba Amma sede yace musu yana ta Kira na naki dauka, na kasa gane abin da gayen yake nufi Dani. Ban sake komawa class saboda nasan we've closed for the day, na Gama dukkan lecture din da nake da shi a timetable. Gida na wuce kamar yadda na saba, na Shiga dakin Mamaa na sanar mata dawowa ta sannan na wuce dakin mu Bayan na tabbatar Adda Bata dawo ba. Ina zuwa na tarar da dakin a kulle which is odd, Ni nasan bama kulle daki no matter what, kitchen na Shiga na dauki ruwa sannan na tambayi Alawiyya ko tasan Wanda ya kulle dakin. Se tace min ai Batuul ce, tun dazun ta dawo Kuma ta rufe Kan ta a ciki. Se da na shanye ruwan na yadda sachet kafin na wuce dakin, na Fara knocking a hankali, na kusa minti na biyar a tsaye kafin tazo ta bude min kofar. Idanun ta sunyi jawur sannan sun tashi, ko baa fada ba kasan kuka tayi ta godewa Allah. Na Shiga ciki na Fara cire kayana sannan na wuce toilet nayi wanka, anan na Fara kallon ciki na, I can swear Naga yayi kasa ba kamar ko yaushe ba. Tabbas slimming pills dinnan da lemun tsami suna aiki. Har karamar rawa nayi a toilet din kafin na fito, har lokacin Batuul na kwance akan gado tayi rub da ciki se sheshekar kuka take yi, se da na Gama saka kayana sannan na dawo na zauna a gefen gado na yadda Ina iya kallon ta, se Kuma na mike na rufo dakin hade da saka lock a kofar sannan na dawo na sake Zama nace " Batuul me ya same ki? Me ya faru?" Ina ga dama neman Wanda zata fadawa take Yi, Dan kuwa Ina Mata magana tayi saurin tashi ta zauna, se da na kwalalo idanu da naga yadda fuskar ta tayi, tayi jawur ga swollen eye na alamar ta dade tana kuka, hancin ta Kan shi diga yake mura har ta Kama ta, na duba kasan daki yadda ya baci da used tissue paper, alamar ta kusa bata roll daya saboda fatar hanci. Rungume ni tayi ta sake fashewa da kuka, a'a se na saki Baki Ina mamakin ruwan da ta sake ballowa, saboda a gaskiya tarbiyya dai Batuul tayi lacking, an sakar Mata da yawa, iyayen ta suna kallo tana abubuwa Amma sun kasa Hana ta. Ni na raaa ma Ina suka saka gaba, idan kudi ne ai Babu laifi muma muna da daidai rufin asiri to me yasa suka barta take hakan "Batuul me ya faru? Fada min" Saki na tayi tana kukam tace " Honorable ne!" Na saki Baki Dan Ni ban ma gane waye honorable din ba. Kamar ta fahimci abin da nake tunani se tace " Wanda Zan aura fa! Could you imagine Bintu wai hotel ya kaini Kuma Wai he wants to have..." Se ta kasa fada min sauran maganar, ni Kuma se yayi Popping Kai na, ance hotel anzo Kuma ance have, ai karshen magana sex ake nufi. Ban wani kidimu ba saboda nasan mutane ba kowa ke tsoron Allah ba, yadda ya dinga Mata ruwan kudi abun zai Baku mamaki amma ba kowa ke hakan saboda Allah ba, wasu suna yi Dan Allah saboda son da suke wa mutum yayinda wasu su Kan yi Dan wani manufar su. I dunno tun ranar da na fara ganin shi, wani dare da yazo zance, irin kallon da yake Mata kawai naji ban yadda da shi ba. To Amma wa Zan cewa hakan Nima da ba yancin kaina na samu ba. " Me kike tunanin Yi yanzun?" "Ni bansani ba Bintu, bansan ya zanyi.ba!" Nace " Ki fadawa Kawu kawai!" A take kukam ya dauke tace " Kawu kuma? Idan na fada musu ai zasu ce a fasa auren." " To ke meye damuwar ki Dan kin rabu da shi. Hakan Bai Isa gaya Miki jikin ki yake so ba?" Na fada Ina gyara Zama na, ta girgiza Kai tace " Ba zan fada ba, kema Dan Allah kada ki fadawa kowa Dan Allah." Bance Mata komai ba kawai na janyo lottafi na dan nayi karatu, to dai Batuul ba shawara take nema ba, gwara na barta tayi abin da take so. Ina nan zaune se naji wayar ta na ringing da farko taki dauka se a Karo na biyu ta dauka. Na kalle ta ta Kara Bata fuska kamar a gaban shi take, " Tohm!" Daga Haka ta tashi ta Shiga toilet ta wanke fuskar ta, ta sake fitowa ta canja Kaya zuwa wata embroidered Abaya color baka, ta Ciro Addictive Ambergris daya daga cikin collection din SCENTMANIA. Turaren nan duniya ne, indai nice, cool and soft scent kake so ka nema SCENTMANIA. Ta fice Babu jimawa se gata ta dawo da wata katuwar leda a hannun ta, mamaki sosae ya Kama ni, ta zauna sannan ta dauki wayar ta ta Kira shi, Babu jimawa se ta Fara fadin " Bribe ne wannan din?" Bansan me yace Mata ba se Naga tayi dariya, a'a se na sake Baki Ina kallon matar da tuntuni take kuka. Bayan ta dauki wajen mintina ashirin tana waya sannan ta kashe ta dube Ni " Kinga hakuri ya bani, Wai Bai San me ya hau Kan shi ba" Na gyada Kai nace " Batuul kenan!" Ta Fara Ciro kayan Dake cikin ledar, wani zungureren roasted fish ta ciro, ta baje shi hade da juice ta Fara ce min " Nasan Baki ci abinci ba, kizo muci" Na girgiza Kai nace " Thank you!" Ta zauna taci abin ta sannan wannan ya wuce. Bamu sake haduwa da Dr Akram ba se da wani sabon satin ya kama, a class Muka hadu zuwa lokacin na Fara ramewa, wani.pills na samu nake Sha, ranar farko da na Sha ko gado na a durkushe nake sakkowa daga kan gado naje toilet, cikina kamar zai fita Dan ciwon da yake min, Amma zuwa dare se da naji jiki na ya Fara saki. Da nasha na biyu ya bani side effects din Amma Kuma Bai Kai ranar farko ba, a hankali Ina sha side effects din na tafiya shikenan se Kuma na Fara ramewa a hankali. Anan naga wata me yawan siyan cake waje na tana tallar wani herbal slimming tea, na saya ta Aiko min na tafasa nake sha, a hankali abunnan Yana bin jiki na Ina Kuma Dan ramewa. Bayan na Gama lecture di na na ranar ya rage se tashi kawai, na Ciro slice cake din da na taho da shi a jaka ta na cinye sannan na Sha ruwa, Babu jimawa se gashi ya shigo, a Karo na biyu ya karaso inda nake zaune fuskar shi da murmushi yace " Fatima howwa u?" Nace " I'm fine sir!" Ya gyada Kai sannan ya aje min meat pie da Schweppes, nayi saurin fadin " Sir naci abinci!" Yace " Mhmm it's an add more!" Daga Haka ya juya ya tafi, Alamin da Sadiq Suka juyo suna min dariya, se da yayi gyaran murya kafin dukka muka sake maida hankalin mu Kan shi. Cikin nutsuwa ya gama lecture din mu sannan ya tabbatar Mana akwai possiblity din zaiyi Mana test mu Zama cikin shiri. Yana gamawa ya dake yace " Fatima ki same ni a office di na!" Nayi saurin kallon shi sannan Kuma na kalle saura Yan class din mu da wasu ke murmushi, kamar nayi ihu Haka naji, Wai shi baya tsoron bakin mutane? Shi baya tunanin zaace ko wani abun ne tsakanin mu, shi baya wannan tunanin. Har ya tafi ban fara kokarin bin shi ba se da Alamin ya sake yimin magana kafin na tashi na tafi. A zaune na same shi wannan karon Yana cin danwake, har na juya Zan koma ya dawo dani ta hanyar Kiran sunana, na kalle shi yace " Dawo ki zauna na Gama!" Ya rufe kyakyawar warmer ya aje gefen table, magani ya ballo ya hada da bottled water ya Sha kafin yayi excusing din Kan shi zuwa toilet ya kuskure bakin shi sannan ya dawo ya zauna tare da ce min " A Ina muka tsaya Fatima?" Na danyi kasa da Kai na nace "Na manta!" "Ni ban manta ba" Ya bani amsa Yana sake gyara zaman shi yace " Me yasa kike son rage kiba, Zaki iya bani labari!" Wani lokacin wata tambayar se ta dawo.maka da dukkan wasu past and painful memories, a lokaci daya dukkan rayuwa ta tayi flashing ta idanu na. Amma na kasa magana saboda Ina ganin idan na fada Masa zai ga iyayen na Basu da hanklai. Kafin nayi magana se naji yace " Were you body shamed? Shi ne dalilin da yasa?" Na gyada Kai na a hankali, idanu na suna cikowa da kwalla wadda kafin nayi kokarin maida ita har ta Fara zubo min a saman kuncin na, se yayi shiru Yana Jin Babu dadi cikin zuciyar shi, dama ya sani baiyi min magana ba, if at all yasan hakan zai Zama sanadin kuka na. " I'm sorry Fatima, kiyi hakuri bansan zai saka ki kuka ba" Tashi yayi ya bude backpack din shi ya Miko min handkerchiefs yace " Share hawayen ki kinji! I'm so sorry Yi hakuri" Kunsan wani lokacin idan ana baka hakuri kawai se ka Fara sakalci, Nima kawai se naji kamar Yana ce min I should open up to him. Cikin kuka nace " Ba Wanda yake so na, kowa criticising di na yakeyi akan inada kiba, a gidan mu ba Wanda yake so na..." Kuka yaci karfi na, yayi shiru Yana kallo na Wai Bai masan actual abin da ya faru ba kenan... Ta_kwalam ce [1/3, 20:28] Maman: 032 Ta zauna tana Masa sannu da zuwa, ya zauna Yana amsawa. Tace "Ya patient din naka? Ta tashi?" Ya shafa kan shi yace "She eventually regain consciousness, na Kai ta gida" Safiyya ta gyada kai tace "Abinci fa? Ko kaci?" "A'a Ummaah! Daddy bai dawo ba?" A lokacin tayi mishi bayanin Daddy wato Imam ya tafi gaida Ummiey, ta sanar Masa Ummiey har Dada ma na cigiyar shi. Yayi murmushi yace " Ni fa laifi sukai min Ummaah, Wai naje gaida Ummiey na samu Dada na wajen ta, Nausaiban Uncle Ali taje wajen su kawai suka Fara ce min Wai sunyi min Mata!" Safiyya tayi dariya tace " To Banda abinka ai is high time kayi aure, you're turning thirty two in few days Akram, ya kamata zuwa yanzun ka Fara tunanin aure ko?" Yayi murmushi yace "Ummaah nace Miki lokaci ne fa, Ni na fada Miki gaskiya ba zanyi aure cikin gidannan ba beside waye zai aure ni na zame Masa burden Ummaah? Ki Bari a hankali Zan samu wadda zata karbe ni regardless of ciwon da ke jiki na" Ya Dade da fada Mata hakan, dama ai Haka ne barewa ba zatayi gudu a jeji ba sannan ayi tunanin danta zaiyi rarrafe ba. Har yanzun a cikin gidan abin da ake yi kenan, mutane baifi uku Bayan Imam suka auro bare ba, yawancin ma Kuma auren mutuwa yake shiyasa da yawa Basu son aurar bare, Amma shi dai Akram ya kudiri niyyar shi na ba zai aura wata cousin ba, a waje zaije ya samo matar shi ya aura. Beside bashi da lafiya, kullum Safiyya tana Masa adduar ya samu wadda zata kula da shi, ta jure dukkan wata al'alar shi, amma idan ta duba se taga to wacece? Yanzun Mata are lazy kafin Kuma Azo ga extra burden. " Allah ya kaimu, adduar mu ba zata Fadi ba. I'm sure daughter in law Dita tana wani wajen a boye!" Yayi murmushi, Haka suke tamkar kawa da aboki Haka Akram yake da Safiyya, relationship din su is very healthy unlike na sauran matar uba da dan miji. Da kanta ta Mike ta kawo Masa abinci, Yana budewa ya saki murmushi tare da dago kai ya dubi uwar tashi yace " Ummaah Allah ya saka Miki da aljanna!" Ta amsa da Amin tana Zama inda ta tashi. Iman ta fito da spoon hannun ta, Wanda yasa Akram yace " To zaa Fara parasitism kenan? Zo mu ci" Tare suka ci dashishin da ya Yi washar ya Kuma samu wadataciyya Miya ta taushe, sosae Akram yaci Yana ta Mata santi kafin ya kammalla, tare da Iman suka kwashe komai, sallama yayi Mata akan zaije wajen mahaifin shi, a hankali suke tafiya shi da Iman, tana ta bashi labarin birthday din Anwar da akai school, ta Fara lissafa Masa abubuwan da Anty ta raba musu, Yana ta sauraren ta. Lokaci lokaci yana gaida uncles din shi da suke haduwa da Kuma wani lokacin cousins din shi. A Haka suka karasa bangaren Abba da Ummiey inda mahaifin shi da Kuma uncles din shi biyi ke nan. Suka gaisa suna tambayar shi aiki da Kuma jikin shi, ya Basu amsa da Yana lura da kyau. Daga Haka Imam ya mike yayi musu sallama Suka tafi gida. Yana zuwa yayiwa iyayen shi sallama ya wuce wani daki dake jikin na shi, machines ne Wanda suke a gym, daya ya hau bayan ya cire kayan shi ya rage daga shi se singlet da short, timer yayi setting na mintina talatin. Yana kammallawa ya sakko ya dauki ruwa ya.sha sannan ya wuce dakin shi yayi wanka, ya fito sanye da robe. Se da ya kammalla Sanya pyjamas kafin ya dakko wani Dan karamin bakin jaka, wata karamar na'ura ya Ciro ya zura Mata wani stick kafin ya dauki karamar allura yayi pricking Kan shi, Dan drop din jinin da ya fito ya samu ya saka jikin stick din dake jone jikin na'urar. Babu jimawa wasu figures Suka bayyana a jikin na'urar 6.8... ajiyar zuciya ya sauke sannan ya maida ya rufe ya dawo ya runtse idanun shi Dan yin baccin. It has been a long day actually with all Bintus' issues. Se ya Fara tuannin me yake damun ta, from the looks of gidan da ya kaita jiya Babu alamar rashin abinci to Amma me yake faruwa. Haka kawai se zuciyar shi take fada Masa he needs to know the girl ko zai iya gane matsalar ta! Washegari da wurwuri na tashi, Bayan na Shiga kitchen na kammalla aikin da zanyi, noodles na dafa naci sannan na matse lemon tsami guda hudu cikin karamin cup sannan na zuba tafasasshen ruwan zafi kadan na runtse idanu na na kafa Kai na na shanye tas. Sannan na koma daki na karasa shiryawa Dan tafiya makaranta, Babu Wanda nayiwa sallama na fita, saboda naji haushin abin da sukai min jiya, na wuni a waje Amma Aki Kira aji me ya faru. Ina zuwa class na wuce wajen khalifa Ina tambayar shi abun da nayi missing jiya. Ya dakko ya bani sannan na koma inda nake na zauna. Bai shigo class din ba se karfe biyu, kafin lokacin bayan nayi sallah na fita na Nemo Coke na Sha sannan na dawo na zauna, I can't take this embarrassment anymore, ya kamata nayi wani abun Kuma. Yana shigowa ya dube ni bayan yazo daf Dani yace "Have you ate?" Nayi saurin gyada Kai na nace " Yes sir!" Ya Miko min sandwich me dumi da Kuma gwangwanin coke me sanyi yace " Eat it silently, don't disrupt my class!" Innalillahi wa inna ilaihil rajiun! Shi ne kawai abin da na furta, kunya kamar na nutse a wajen, kafin nayi wani Abu se kawai na gan shi har ya isa gaban system din shi Yana adjusting glasses din idanun shi, cikin turancin shi sassauka me Kuma saka tsikar jikin mutum ta tashi ya Fara bayanin topic din da ya Riga ya rubuta jikin white board. A hankali Ina jotting Ina Kuma munching sandwich din, a gani na dole naci kada jiki na ya sake betraying di na. Har aka kammalla class din garau nake ji na. Bayan ya fita se ga Alamin yazo ya zauna gefe na yace " Da kinsan yunwa ce take saki Haka me yasa Baki cin abinci?" Bance komai ba se Dan murmushin Jin kunya da nayi, yace " Shikenan! Kije Dr Akram Yana Kiran ki" Nayi saurin kallon Shi nace " Ni Kuma? Me yasa?" Shi ma se ya kalle ni irin yadda na kalle shi yace " A'a ya Zan sani? Malamin ke ne akwai dalilin Kiran ki Bayan karatu?" Se na Mike tare da sake Jin na kwafsa, tunanin me nakeyi da? Tunani nake zai ce Yana so na ko me? Nayi wani dariyar Bintu Baki da sense ko kadan. Irin wannan gaye me zaiyi da Ni? Jibgegiya da ni, kilan nayi size din mahaifiyar shi. Se naji Kuma wani irin rashin karfin gwiwa ya Kara maimaye ni. Haka na wuce zuwa office din da se da akai min kwatamce. A hankali nayi knocking kamar wadda take jin tsoro, nayi mamaki da naji an bude kofar, na Dan ja da baya har Ina neman zamewa, yace " Come in!" Yana fadar hakan ya shige ciki, a hankali na rufa Masa baya, ya zauna Kan kujerar shi, ya nuna min daya na zauna sannan ya amsa gaisuwar da nake Masa. Bayan ya cire glasses din idanun shi yace " Bintu ko?" Na gyada Kai yace " Fatima kenan! Yaushe Kika Fara wannan fainting din?" Kunsan wani lokacin akwai abubuwan da suke faruwa kaima baka San me yasa hakan yake faruwa ba. Ko Kuma se kaga a single soul ya shigo rayuwar ka ya canja maka komai, ko kuwa kaga ka daina wasu halaye ka kirkiri sabon Hali to someone particular. Kunsan duk wanda yayi min irin wannan tambayar ba lalali na kalle shi ba balle ya saka ran Zan bashi amsa. A hakan a Kan shi se naji I just want to open up. " Last week!" Ya gyada kai yace " Episodes nawa kikai kenan?" Nace " Uku!" Ya danyi shiru kafin yace " Fatima!" Na dago a hankali na dube shi, kallo na yake kamar akwai wani Abu a fuskata, yace " Ina son Miki tambaya, amma idan kinga akwai takura ba se kin amsa Ni ba! I just feel obliged to know your problem. Meye matsalar ki Fatima? Me yake hanaki cin abinci" Nayi shiru Ina Wasa da hannu na, na Rasa ta Ina Zan Fara bashi amsa, abun da nauyi Amma ya kamata ace shi daya duk duniya da ya taba damuwa da Sanin matsala ta ya kamata na fada masa. " Ina son rage kiba ne!" Na fada more of a whisper Amma Kuma se nayi mamakin yadda akai yaji, se yace " Kiba kike so ki rage? Me yasa can you share with me?" Kafin na.bashi amsa akai knocking a kofar Wanda yasa banyi magana ba, messenger Dean ne yazo ya sanar Masa Dean na neman shi da sauri, hakan yasa yace " Fatima I'm sorry, session din mu zai Kare daga nan, I hope we meet some other time!" Ta_kwalam ce [1/3, 20:28] Maman: 031 Dr. Akram ya Kara kallon wrist watch din hannun shi a Karo na babu adadi, ya sake duban Alamin Dake can gefe akan kujera hannun shi rike da wayata a hannun shi, wannan lokacin awa wajen uku kenan da na Fadi a cikin class, tun da ya hango fuska ta ya Fara tattakowa daga Kan podium Dan zuwa seat Dina Amma kafin ya karaso already nayi losing consciousness, a cikin tashin hankali dukka suka rufu akai na, ya sake wullawa Alamin mukullin motar shi ba tare da yayi magana ba, Alamin ya cafe ya Kuma fice a guje Dan dakko wannan set din da ya dakko.jiya, sede yau din glucose di na ya sauka sosae. Yana ganin Haka ya daura min ruwa a hannu na sannan yace su Kama ni mu tafi asibiti, na Dan motsa kadan Amma ban bude idanu na ba. Se da suka Shiga mota suka tuna baa dauki waya ta ba, Haka ya aika Alamin ya dakko Amma wayar is coded, Kuma an duba Emergency contact di na babu ko mutum daya a ciki. "Kuma ka tabbatar Doctor ba diabetes take da ita ba, wannan Karo na biyu kenan cikin satinnan fa tana Yi!" Likitan ya dubi Dr Akram yace " Bana tunanin diabetes ne, nafi kawo tana Wasa da abinci ne. Ka Dan Yi hakuri ta farka se muji abin da ya faru daga gurin ta!" Akram ya gyada Kan shi kawai tare da sake yiwa likitan godiya ya fito, ya samu Alamin da Sadiq Dake zaune da Ni. Ya dubi Alamin Bayan ya duba agogon hannun shi yace " Har yanzun Babu Wanda ya Kira daga family dinta? It's after maghrib fa!" Ya fada cikin kosawa dan so yake ya tafi gida, Yana Kuma ayyana dalilin da zai sa har yanzun a gidan mu Basu Kira ba, bugi da Kari Alamin ya tabbatar Masa a gida nake zaune ba hostel ba. Alamin yace " Har yanzun Sir!" Ya danyi tsaki yace " She doesn't have a friend? Ko da daga wani faculty ne?" Sadiq wannan karon ya bashi amsa da fadin " Babu fa sir! Kullum Bintu ita kadai take rayuwar ta, idan an Gama lecture ta tafi gida!" "Then she's not normal kenan" Akram ya fada Yana sake duba na, ban tashi ba Amma Kuma Doctor din ya tabbatar musu kawai stress ke damuna shi ne dalilin da yasa ban tashi ba, Amma dukka abubuwan da zasu nuna akwai damuwa a jiki na, are ok so Shi ya dauka hakan a matsayin brain Dita ke hutawa. Ya Kara kallon fuskata Yana ayyana ko ni wacece? Wayar shi ta katse Masa tunani Wanda hakan yasa shi cirowa daga pocket din shi, da murmushi a saman fuskar shi ya dauka Yana fadin " Ummaah! Ina wuni?" Daga dayan bangaren tace " Alhamdulillah! Me ya faru yau baka dawo gida ba, baka Kuma Kira ni ba. We're all worried here!" Ya dube ni da na Dan Yi juyi kadan alamar na Fara regaining ya sauke ajiyar zuciya yace " Kiyi hakuri Ummaah, wallahi wata student Dita ce ta fadi a class di na. Mun kawo ta asibiti Kuma har yanzun mun rasa family dinta" Kafin tayi magana na Fara bude idanu na a hankali, se yayi saurin yu Mata sallama akan Bari yaga ni gashi na tashi, a hankali na tashi na zauna Ina rarraba idanu Dan na fahimci a Ina ma nake in the first place, me Kuma ya faru, Amma muryar shi da naji tazo daf da Ni yasa na sake bude idanu na, wannan karon Sadiq da Alamin har shi ma suna tsaye a kaina. Kawai se na rufe idanu na saboda wata irin kunya ce ta rufe ni, da ace kasa zata tsage I'm very sure I'll gladly jump in ta hadiye Dani. Wannan wanne irin embarrassment ne na yiwa kaina. Na tuna vividly har tamabya ta yayi ko naci abinci saboda a cewar shi baya so nayi distracting class din shi. Amma kalli abun da ya faru. Kamar na kwala ihun da nake Yi cikin Kai na, suji ko zasu San cewa I'm embarrassed to the core! Shi ya fahimci halin da nake ciki se ya bar su Sadiq akan Bari ya Kira doctor yazo ya dubani, Ina Jin ya fita na bude idanu na Ina kallon su Alamin da tsanain kunya nace " Fainting na Kara Yi?" Yayi dariya yace "Eh mana, gashi kin dade yau Baki farka ba" Na daura hannu na akai na nace " Na shiga uku. Alamin, Sadiq thank you. Ya Zan kalla fuskar shi?" Sadiq ya Fara dariya kafin yace " Wai me yake Hana ki cin abinci ne? Kinsan wannan abun kuwa na barazana ga rayuwar ki?" Na Dan marairaice fuska bance komai ba, su barni da kunyar da nake ji kadai ta ishe ni. Babu jimawa se gasu sun shigo, nayi saurin runtse idanu na dan kada mu hada idanu da shi Amma se yace " I've caught you! Tashi a duba ki" Haka na tashi Ina ta sunkuyar da Kai na, doctor ya dududduba ni yace I'm fit zamu iya tafiya, nayi Masa godiya sannan Akram ya bishi Bayan ya jadadda min akan lallai lallai na dinga cin abinci idan ba Haka ba Kuma Zan iya mutuwa. To ai ni da Zan mutu inaga it will be for the best, wannan a wani sashe na zuciya ta ne, se Kuma nayi saurin istigfar, anything but Banda kashe kai, saboda Allah ya bani chance wancan karan wannan Karan ba lallai nayi surviving ba, Kuma na tabbatar idan na kashe Kai na, jahannama ta tabbata akai na! Shigowar shi ya dubeni bayan yazo daf da gadon yace " Ya jikin naki?" Nace " Alhamdulillah!" Ya gyada Kai sannan ya dube mu suka yace, kuzo mu tafi. Dukka Suka tashi Nima Haka a sanyaye na sakko daga gadon tun da nasan har Dani yake nufi, musamman da ya iya jira tun laasar har yanzun Bai tafi ba, yanzun ma nasan ba zai barni anan ba. Muka fita zuwa hadaddiyar motar shi, irin tafkekiyar motar nan ce katuwa. Ya bude sannan yace min na Shiga gaba su Kuma su shiga baya. Muna tafe Bai ce min komai ba har mukaje BUK lokacin ana ta Kiran sallar ishai, ya sauke su sannan yace na jira yayi sallah. Nayi saurin kallon shi nace " Sir Zan iya zuwa gida daga nan. Nagode Allah ya saka da alkhairi!" Ba tare da ya amsa godiyar da nake Masa ba yace "Idan kin fita Ina Zaki samu abin Hawa. Come on stay still nayi sallah nayi dropping din ki!" Babu abin da zance Kuma se kawai nayi shiru Ina ayyana yanzun dai ya kamata na aje dieting a gefe, is not for me gwara na Nemo natural hearbs da Kuma slimming tea da veniger na din ga Sha. Wani taimakon Allah bana sallah balle nayi ramuwa, shima Kuma bai tambaye ni ba, Babu jimawa se gashi ya dawo su Sadiq sun wuce hostel daga nan, ko sallama ba muyi ba. Ya Miko min waya ta bayan ya tada motar yace "Ki duba wayar ki muna sallah an Kira ki" Ya fada Yana kokarin yiwa motar key, nayi saurin dubawa se Naga Mamaa ce ta Kira da Batuul, na sake going through log din babu Wanda ya kira ni tun dazun. Kenan hakan na nufin Babu Wanda ya lura ban dawo gida ba se yanzun kenan? Se naji ban ju haushi ba tunda dama se an damu da Kai ake kulawa da rashin ka. Na Kira Mamaa Amma wayara Bata Shiga ba, instead se na Kira Batuul lokacin har mun fita daga gate din BUK. Na Kara kunne na saboda tata ta shiga "Ke Bintu Ina Kika je har yanzun Baki dawo ba?" Rai na ya baci saboda na tsani abubuwan da Batuul take yimin, tana magana da wata irin gadara, banyi tunanin volume din is that loud ba har Yana iya jiyo maganar Batuul din nace " Gani nan na taho ai" " Se kizo kiyi bayanin inda Kika je, tun dazun se neman ki ake, kin tayarwa da mutane hankali!" Ban Bata amsa ba na sauke wayar daga kunne na tare da hanging up, bansan amsar da Zan Bata ba ma. Ya dube Ni yace " Wacce unguwar kike?" Na bashi amsa da Badawa layout sannan ya cigaba da tukin shi. Babu jimawa wani Kiran ya sake shigowa waya ta, ya kalle ni ganin na Bata Rai se Kuma ya sake maida Kan shi ga titi, wannan karon Mamaa ce " Mamaa gani nan na taho!" "Ina Kika tsaya Bintu?" Nace " Na taho ai na kusa zuwa" Se ta kashe wayar kawai, can Muna tafe se yace " Me yasa ba Zaki fada musu inda kike ba" Meye amfanin fada musu? Ai bashi da amfani tun da ba damuwa zasui Dani ba. Allah ya sani duk wannan a zuciya ta nake fada Amma bansan yadda akai na samu betrayal daga inner mind di na har abun ya fito waje ba. Ya dube ni yace " Ba a gidan ku kike zaune ba?" Na kalle shi da Dan sauri nace " Gidan mu ne, they're my parents" Se ya gyada Kai kawai Bai sake magana ba har Muka shigo unguwar, se na Fara nuna Masa turns din da zai dauka har ya kawo ni kofar gidan mu. Dama Ina ta adduar Allah yasa Babu kowa, cikin saa har na sauka nayi Masa godiya sosae ba Wanda ya fito, na juya Zan Shiga ciki se ya Dan Kira Ni da muryar da ya tabbatar zanji "Fatima!" Wasu na Kira na Haka Amma Basu da yawa ko kadan, na juya a hankali na same shi, yace " Kici abinci, Kuma gobe I've your class don't come and faint again!" Na Dan sunkuyar da kaina in embarrassment nace " Nagode sir" Yaja motar ya tafi ni Kuma na shige gida, Ina shiga wajen Mamaa na wuce, na samu tana zaune ita da Adda, na gaishe su sannan na Fara yiwa Mamaa bayanin inda na tsaya, cikin tashin hankali tace " Allah ya sawwake. Ni bansan Baki dawo ba wallahi se da Alawiyya tazo ta fada min Baki dawo ba" Alawaiyyar fa Yar aikin mu ce, ita ce kadai ta fahimci bana gidan, ikon Allah! Adda Dake kallon mu tace "To Ina zaa gane Bata nan bayan kullum kina daki kamar daddawa. Kije Kan dressing mirror di na akwai wani skin product Dana gani ko zai sa wannan kurajen su tafi!" Nayi Mata godiya sannan na tafi. Ina dauka na zauna akan gadon ta Ina going through labels din Dake jiki, se na fahimci Bayan kuraje da yake kashewa Yana fading skin, so se na sakawa Rai na bazan Yi amfani da shi ba! A bangaren Akram ya karasa gida, kamar kullum Bayan yayi parking ya hanga Alhaji Gidado can a zaune yana cin abinci, ya tsufa sosae Amma har yanzun da guntun karfin shi. Ya dauke Kan shi ya nufi cikin gidan su, kafin ya shiga se ga Aiken Wai Alhaji Gidado yace yazo suci abinci, yace aje a fada Masa da Ummaah shi zaici, ya gode da tayi. Daga Haka ya wuce ciki, shi dai Bai son mutumin dan kuwa yaji labarin irin mulki da Kuma izza da yayi. Yasan Safiyya ba mahaifiyar shi bace ba, yasan fuskar mahaifiyar shi, Yana iya tuna kadan daga cikin rayuwar da sukai tare, har zuwa lokacin da Daddy wato Imam ya taho da shi, da farkon haduwar shi da Safiyya, Amma daga wannan ba zai tuna wani ya fada Masa ita din ba mahaifiyar shi bace ba, ko Kuma a fada Masa ga inda mahaifiyar shi take, lokuta da dama Yana son yasan rasuwa tayi ko me ya faru Amma baya son ya daga maganar saboda a duniyar shi, Safiyya ita ce uwa kowacce mace a bayanta take. Idan ya tuna ba ita ta haife shi ba ko Yana son Sanin inda asalin tashi uwar take se yaji kunyar Kan shi da Kan shi take, a ganin shi Safiyya ta wuce ya tuna ba ita ta haife shi ba. A hankali ya shiga parlon bakin shi dauke da sallama, ko Ina tas se kamshim turare Dake tashi in da ya hango burner na aiki, wannan wani Abu ne cikin zuciyar shi, Yana son kamshi Yana Kuma fatan aurar macen da zata kula da bama shi kanshi ba har da gidan shi. Rike shin da akai yasa ya dubi Iman dake da shekaru wajen goma yace " Imani" Bata fiye son Yana Kiran ta da Imani ba, a cewar ta ba Haka bane ba sunan ta. Ta Bata Rai tace " Ummaah Kinga Hamma ko?" Safiyya da ta shigo sanye da lace green da adon milk a jiki tana murmushi kamar yadda take a shkearun ta na baya tace " Hamma sannu da zuwa" Ya saki hannun shi daga wajen Iman ya nufi mahaifiyar shi da murmushi saman fuskar shi shima... Gobe in shaaa Allah, Zan danyi Abu and I'll not be able to post, idan Kuma na samu sarari zaku ganni Ta_kwalam ce [1/3, 20:28] Maman: 034 Akwai lokacin da baka fahimtar me kake ji a tattare da mutum, baka gane yadda zakai bayanin how that person meant to you, ko da duka ko da menene ba zaka iya gane meye matsayin wane a waje na ba. To wannan ma Haka take wajen Akram. Da farko da ya Fara ganin Bintu, yaji ta burge shi yadda akai ta iya surviving ita daya cikin wannan mazan, he respected her saboda yasan ba karamin efforts tayi putting ba, a tunanin shi ma ita din matar aure ce. Amma lokacin da ya kalle ta sosae se ya fahimci jikin ne kawai ba lallai akwai shekarun ba. Bai sake maida hankalin shi Kan ta ba se ranar da tayi wannan hypoglycemic episode na farko, a ranar yaji tausayin ta Amma Bai Bari ya wani dame shi ba se da tayi na biyu, sannan ya tabbatar akwai wani abu dake damun yarinyar. Kafin ta farfado ya tambayi Alamin, some few things game da ita Amma amsar da Alamin ya bashi cewar shi dai Yana ganin ta kawai, Bai San komai a tattare da ita ba, yasan bata kula mutane bata yawan magana, Bata Kuma San a gane tana waje. Ya Kara da cewar lokuta da dama idan an Gama classes ta leka taga an taru mutane da yawa, ta kwammata ta koma class ta zauna zuwa lokacin da zaa baje ta tafi, abin da Alamin ya fada da Kuma abin da yayi observing shi ne Bata da confidence Haka bata da self esteem ko kadan, tana Jin kanta kamar ita ce center of attention din mutane. Se Kuma gata a gaban shi tana kuka, irin kukan da babu wani mutum da ya taba Yi a gaban shi, saboda shi din Bai kasance me yawan Shiga sabgar mutane ba, Bayan gaisuwa babu wani Abu da ya ke Kara Shiga, sede idan abun aiki ne ko Kuma wani important abu. To Amma fa Bintu zaune tana kuka, kukan da yake jin shi har cikin zuciyar shi, yake Jin kamar dama she has been holding for long Kuma yau ta samu yadda zata fito da hakan. Se yaji dukka hankalin shi ya tashi, yaji ya rasa words din da zaiyi amfani da shi wajen comforting din ta, Haka Kuma Bai San me yasa yake Jin wani irin rashin hankali Yana shigar shi ba. Sosae nayi kuka, ni kaina so nake na daina kukan ganin yadda Dr Akram yake ta cemin he's sorry, kilan tunanin shi na bashi ko laifin shi ne Dan yayi magana, unknowing to him Ina kuka ne saboda komai na rayuwa ta da ya shude Yana dawo min, tamkar anyi min fami Haka nake ji. "Babu Wanda yake so na a gidan mu, a waje kowa fada min yake ni mummuna ce, suna ce min nayi kiba da yawa nayi shedding fat din jiki na. Sir ya zanyi? Ya mutane suke so nayi tunda bani da power over yadda nake son jiki na ya kasance" Yayi shiru Yana Jin abin da nake fada, se da na Gama yace " I understand abin da kike nufi Bintu. I'm so sorry that you went through all this alone. Kiyi shiru yanzun muje nayi dropping din ki a gida" Naji dadin wannan maganar Dan kuwa gani nake bazan iya cigaba da magana ba, idan na cigaba Kara kuka zanyi saboda Ina iya hango tausayi na cikin idanun shi and that happens to be my weakness! Na Mike sannan na dauki jaka ta, ya dauki keys din Shi yayi gaba, se da na Fara fita sannan ya biyo baya na. Motar shi ko a faculty daban take dukda wancan karon da daddare naga motar Amma yadda take daukar idanu dole na gane ta, kafin ya karaso ya bude min yayi min alamar na shiga, na bude na shiga baifi minti na biyar ba se gashi yazo, ya bude gefe na ya shiga, ya dube Ni hannun shi rike da ruwa da kuma Apple juice da ake siyarwa can baya, natural fruit extract ne. Ya Miko min yace " Ki Sha!" Haka na amsa ba tare da musu ba dan bazan ma iya musun ba. The drive was absolute silent har ya kaini kofar gida, yayi parking na juyo na kalle shi da kodaddun idanu na nace " Sir nagode! Nagode sosae Allah ya saka maka da alkhairi." Yayi min murmushi yace " Kada ki manta gobe muna da test, kiyi karatu sosae, I want you to emerge at the top!" Na gyada Masa Kai na Ina fadin in shaaa Allah, daga Haka na fito na wuce cikin gida. Se naji Dadi yau daya cikin zuciya ta, naji Nima akwai mutum daya da yayi honoring du na, har ya damu Dani ya Kuma ke son yaji abin da yake damu na! Dukda Nima mamakin yadda akai na sake jiki da shi nake, na Rasa me yasa Amma koma dai menene Ina Jin shi din wani me daban cikin rayuwa ta! Bayan ya zauna yaga shiga ta gida sannan ya juyar da Kan shi da nufin tafiya gida, se yaga wani dattijo ya fito.daga gidan, Kuma yanayin shi irin nawa ne, har ya Fara kokarin bude motar Dan yaje ya gaishe shi se Kuma wata zuciyar ta tuhume shi da dalilin hakan? Da ya kasa Kare Kan shi se kawai ya ja motar shi ya tafi gida. Yana zuwa kamar kullum yayi parking sede yau community din tasu kamar akwai damuwa, Bayan ya Shiga ciki ya tarar da Safiyya na kokarin fita, ya tambaye ta me yake faruwa tace Masa Alhaji Gidado ne bashi da lafiya Yana asibiti, ci abinci kazo muje idan baka gaji ba. "Muje na kaiki, Allah ya Kara sauki!" *** "Ni Mami na gaji, ko kadan ace mijin ka baya ganin mutucin ka, kullum cikin rigima da tashin hankali ake. Kuma idan mun zauna mu kasa gane abin da yake faruwa tsakanin mu" Daga dayan bangaren wayar Mamin tace " To Samiha Nima kullum na gaji da Jin korafin gidan ki, bake kadai bace ba 'Ya ta, na aurar da yawa. Idan akwai abin da kike Masa da baya so kiyi kokari ki daina" Kafin Samiha ta bawa mahaifiyar ta amsa se jiyo muryar Bashir tayi Yana kwala Mata Kira tamkar zai cire makogaron shi, cikin kosawa tace "Mami kin jishi ko? Kinji yadda yake Kira na kamar wadda tayi Masa sata ko? Mami na gaji" Ita kanta tana mamaki tasan bayan rabuwar su da Bintu soyayya sukai sosae ita da BashPrince00, soyayya wadda kowa ya tashi kwatance se anyi dasu Amma bayan sun Yi aure ko wata biyu basui ba tamkar an dauke musu nutsuwa Haka suke, Babu kwanciyar hankali ko kadan ya Kuma Rasa gane dalilin da yasa zaman nasu ya koma Haka. Ba zai iya tantancewa ba, idan Kuma ya zauna yayi tunanin shi dai yasan har cikin zuciyar shi Yana son ta, Amma ya rasa me yasa da ya dawo gida ya ganta se yaji she's getting on his nerve. Ya Sani ba halin shi bane ba fada, itama Kuma Haka Bata da fada Amma Kuma dukkan su sun canja sun Zama mafadata kamar wasu karnuka. Karasawa yayi ciki tana tsaye ta saka hannun ta a kugunta, har wani jijjiga jiki take irin kana cemin kule zance cas! Da ya taho niyyar shi yayi Mata magana a hankali Amma da yaga wannan abun se yaji ya sake fusata har wata zuciyar na fada Masa ya faffalla Mata Mari tunda Bata da kunya. Amma se yayi saurin girgiza Kai, anything Amma Banda duka, " Ke mahaukaciya ko ke kurma ce da kina ji na Ina kiranki kinyi min banza!" Wani lokacin abubuwan rayuwa se ana hakuri, Babu yadda zaayi ace Kuna zuane Kuma tare daya ba zaiyi hakuri da.daya ba, wannan ba hanya bace me bullewa ba. "Wuta ka taka da zaka dinga yimin irin wannan Kiran, na gaji na gaji da Zama da Kai, auren ka Babu abin da ya tsinana min ban da tashin hankali da musifa..." "Ni kike cewa Haka? To shikenan tunda Haka Kika ce kije na sake ki saki daya!" Tayi dariya tace "Alhamdulillah tafi nono fari, Nima na huta" Daga Haka kowannen su ya bar corridor din ya nufi dakin shi, kunsan yaran masu kudi, kowa ya Fara hada suitcase din shi Dan tafiya gidan su. Amma se Samiha ta Fara ayyana Wai fa auren ta ya mutu, auren ta da Bashir fa ya mutu, ai se ta bare Baki ta Fara kuka kamar zata tsaga dakin, shima a nashi bangaren bayam ya Gama rubuta takardar se ya zura ma takardar idanu Yana mamakin Kan shi, da hannun shi zai saki Samiha, me yake faruwa da shi? Ina dukkan son da yake Mata ya tafi? Ikirarin forever is the deal ya wargatse kenan? Se ya lalubi wayar shi ya Fara Kiran mahaifiyar shi da yake Kira Ammiey. Bugu daya ta dauka " Ya akai naji muryar ka Haka? Ita Kuma Samiha ta Kira Ni tana kuka. Me yake faruwa daku?" Shima da zai samu kukan zaiyi, idan da zai iya tabbas kuka zaiyi Amma shi bashi da saurin kuka ko kadan. "Ammiey na saki Samiha..." "Saboda me? Me ya faru? Me tayi maka?" Helplessly yace "Na gaji Ammiey, auren ta ya fita a raina, shekaru kusan biyu da auren mu Ammiey na kasa samun nutsuwa, kullum gidan mu kamar Tasha Haka yake, saboda fadan da muke. I need to take a break. " Ammiey ta saki ajiyar zuciya cikin rashin Jin Dadi tace " Ba zaku zauna kuyi sulhu ba? Gani kuke kashe auren naku shi ne mafita ubana? Ka jira ni Zan zo gidan yanzun!" Haka ya zauna da waya a hannun shi yayi shiru, idan ka kalla yadda suke rayuwa zaka rantse da Allah cewar wani ne yayi musu Allah ya Isa! [1/3, 20:28] Maman: 035 Dukkan su a zaune a parlor itama Kuma Ammiey shigowar ta kenan, da kanta ta shiga ta Kira surikar tata wato Samiha Santa samu tana ta kuka gwanin ban tausayi, fuskar ta tayi ja saboda kukan da take, tana ta lallashin ta har Suka fito sannan ta dauki wayar ta ta Kira Bashir, Babu jimawa ya fito, yazo gaban ta ya durkusa ya gaishe ta cikin ladabi da biyayya. Ta amsa cikin kulawa sannan ta bashi damar Zama kujerar Dake fuskantar ta Kuma take kusa da wadda Samiha ke zaune akai. " Me yake faruwa a cikin gidan ku? Da har ba zaku iya daidaita Kan ku ba se Kun kashe auren ku? Kun bani mamaki, nayi mamaki kwarai da naji Bashir ka saki Samiha, Ina kaunar da kuke yiwa junan ku? Ina yadda kuke kula da junan ku da har kowa yake shaawar ku?" Dukka sukai shiru tamkar ruwa ya cinye su, kowa a cikin su is reflecting Akan misdeed din shi, Amma kowa Kuma gani yake laifin Dan uwan shi ne! " Shi ne Ammiey!" " Ita ce Ammiey!" Suka fada kusan a tare, se Kuma dukkan su sukai shiru, hakan yasa Ammiey girgiza Kai tace " Ni bana zo fault finding bane ba, nazo naji matsalarku na Kuma baku shawarar yadda zaku maganace ta, idan har zaku cigaba da ganin laifin juna abubuwan ku bazasu tafi daidai ba. Kai na Sanka da hakuri ke na San ki da tarbiyya to duk Ina Suka tafi? Watsar dasu kukai?" Tayi musu fada sosae sannan ta bar su ba tare da ta tilasta musu su maida auren su ba, hakan da tayi musu tana son taga gudun ruwan su ne. Bayan fitar ta ya dube Samiha da tayi shiru maganganun sirikar tata na sinking cikin Kanta, itama ba Haka taso ba, ba Haka ta tsara rayuwar auren ta ya kasance ba, sede Bata da tsimi balle Kuma dubara. A hankali ta Mike Dan tafiya dakin ta, Bashir yayi saurin bin Bayan ta yace "Na janye sakin da nayi Miki! Ina fatan mu zauna lafiya!" Ta sauke wata nannauyar ajiyar zuciya ba tare da ta juyo ba ta wuce dakin ta. Wayar ta ta dauka ta Kira aminiyar ta Hafsatou Bala, Bayan sun gaisa Hafsatou tace " Me ya samu muryar ki naji duk a shake?" "Hafsatou could you believe Bashir yau ya bude bakin shi yace Wai naje gidan mu ya sake bi!" "Ke Bari Dan Allah Samiha! Wannan tatsuniya kike karanta min ba dai Bashir ba" Hafsatou mamakin wannan magana take har cikin ranta " Nima da ya fada Hafsatou ban yadda ba Amma wallahi da gaske ne!" Se ta Fara salati kafin Kuma ta nutsu tace "Kina Ina yanzun? Kada dai har kin tafi gidan Mami?" Ta girgiza Kai tana kallon suitcase din ta wadda tayi dam da kaya, tace " Ammin shi tazo, Bayan ta tafi ya dawo Dani. Amma nasan tunda aka Fara haka wata Rana zaa sake yi. So ya zanyi? Ki bani shawara" Tayi shiru tana tunani kullum tana so tayi Mata magana Amma ta rasa ta inda zata Fara , Amma yau tace to bari ta gwada saar ta "Ki saurare ni Samiha, nasan kina tunanin why is your matrimonial home always in dispute. Baki tunanin hakkin Bintu Ginsau ne?" Samiha tayi shiru tana son ta tuna wacece Bintu Ginsau ma? Se kuwan ta tuna a take komai da ya faru yayi clicking kanta tace " Sure BinGin! To Amma Hafsatou nayi Mata laifi ne?" "Kinyi mana, Zaki ga kamar ba laifi kikai ba but morally abin da kike Bai kamata ba" *** A tare suka tafi asibiti shi da Safiyya da Kuma Iman ita zeeyzeey tana makaranta. Tunda suka dauki hanya yake bawa Ummaah labarin Bintu, tunda take da shi, Bai taba ko da Wasa ya Bata labarin wata mace ba, Wai da sunan kawa ko wani abu se yau. Hakan yasa ta bashi dukkan hankalin ta tana sauraren shi " Ummaah ta Yaya kawai Dan danka Yana da kiba, body figure din shi ko Kuma yayi Baki se ka tsane Shi Ummaah, what's beauty idan ba trial ba" Safiyya na murmushi tace " Amma banji Dadi ba, a Ina ka santa? What's her name?" Ba tare da ya fahimci yanayin yadda uwar tashi ta fassara zancen shi ba yace " Student di na ce, sunan ta Fatima Bintu!" Ta gyada Kai tace " Allah sarki!" Haka ya cigaba da bata labarin Bintu ba tare da ya ma fahimci yanayin hakan ba. A zuciyar Safiyya tamkar an haska saboda dadi, yau danta ne take zancen wata yarinya. Alhaji Gidado na kwance a gadon da aka bashi na asibiti, Dan ma ance a Dan fita a bashi waje Amma yadda yaran shi da Kuma yaran Yan uwan shi Suka cika gurin. A hankali Suka tako Yana rike da Jakar mahaifiyar ta shi, dayan hannun shi Kuma Iman ta kankame hannun. Kowa da ke asibitin yasan tabbas an kwantar da babban mutum saboda yadda wannan family din suka taru Babu kakkautawa. Aunties din shi ya gaggaisar sannan ya wuce can inda mazan suke ya zauna suka gagaggaisa, Bayan wajen awa Suka shiga suka duba shi sannan suka fito. Zasu tafi Minal wata cousin din shi ta karaso da sauri tana fadin " Hamma Akram Dan Allah nazo mu tafi ka sauke ni zanyi shopping!" Ya tsaya sannan ya dube ta yace " Bata nan zamu wuce ba!" Daga Haka ya cigaba da tafiya shi da Iman da ke tsalle tsalle, yayin da ita kuma Safiyya se lokacin zata taho ta tsaya gaisawa da wadanda suka kwana biyu Basu gaisa ba. Suna zuwa gida abinci ya Fara ci sannan yayi sallah, kamar kullum ya Yi dukkan routine din Shi kafin kwanciya sannan ya zo kwanciyar. Se Kuma Bintu ta Fado masa, ko me take Yi a yanzun?ya ayyana cikin ran shi, ya cigaba da Dan tunanin how much of pains da yake tunanin tayi enduring ita kadai cikin rayuwar ta. A bangaren na nayi karatu sosae, dukda na kasance Haka nake Amma wannan karatun se nake ji kamar I owe it to someone, naji Ina son na fidda shi kunya ta hanyar cinye test dinnan. Dan Haka babu Wasa na dukufa ni ce har dayan dare kafin na je kitchen na tafasa slimming tea di na na zubo cikin mug, Ina karatu Ina Sha har na shanye tas kafin na kuskuro Baki na sannan na kwanta, Babu jimawa Bayan na Gama duk tunanin peace din da ya Fara ziyartar rayuwa ta kwana biyu, Ina ayyana dalilin hakan se Kuma na tuna irin gudunmawar da Akram ya bawa rayuwa ta, for unknown reason se kawai na Fara murmushi Ina Jin wani nishadi me dadi Yana shiga ta. Mamaki sosae ya Kama ni na yadda lokaci daya nake Jin kamar rayuwa ta tana canjawa. A hankali dai bacci ya tafi dani. Washegari na tashi da wani irin kuzari, for the first time naji na tashi da annashuwa da Kuma walwalar. What has gotten into you Bintu? Haka na dinga tambayar Kai na lokacin da nake kitchen Ina hada meaty spaghetti da akai order. Bayan na kammalla nayi wanka naci abinci kamar kullum na Sha abubuwan da nake ganin zasu saka kiba ta ta ragu na Zama yadda nake so. Bayan na shirya na sako wani atamfa me kyau da Mamaa ta Dinka Mana, normally duk kayan zuwa makaranta ta materials ne Amma yau se naji Ina son na saka wani kayan daban. Bayan na saka na Fara kokarin daura Dan kwali se na kasa, Batuul dake shafa Mai akan gado tace " Haka saurayi kikai Naga har wani rawar Kai kike" Ban ce Mata komai ba balle na Bata amsa, a karshe na samu na daura dankwalin na dakko wani veil da ya shiga da atamfar na yafa se naji dukka I'm uncomfortable. Nan ma Batuul ta Fara dariya tana fadin " Wallahi gwara ki saka hijabin ki kinfi kyau, Kinga yadda tumbin ki ya fito kuwa?" Na juya a fusace Ina kallon ta, ta karasa yafa karamin veil din ta ta fice ta barni tsaye Ina harar ta, se Kuma naji I'm demoralized bani da confidence din fita da shi, kilan idan na fita da shi mutane suyi tayi min dariya nayi wani irin, cikin sauri na maida shi wardrobe sannan na dauki hijab na saka na dauki jaka ta na fita, dakin Mamaa naje nayi Mata sallama sannan naje dakin Adda wadda ta Gama shiryawa alamar fita zatai, tace " Muje na sauke ki. Kin dai ki Suleiman ko? Naga Wanda Zaki aura ai. Har ni zance Miki kiyi Abu ki kiyi" Wani irin yanayi naji marar Dadi nace " Adda ya zanyi? Kema kin San Suleiman baya so na, so kike na dinga cusa Kai na wajen shi?" Ta fusata zata Kai min hannu nayi saurin matsawa Wai na Yi Mata rashin kunya, har Ina mayar Mata magana. Na Bata hakuri sannan nabi Bayan ta zuciya ta kamar zata fito. Batuul na gaba ni Kuma Ina baya muna tafe suna Hira wadda kusan dukka labarin saurayin ta take bawa Addar ita Kuma tana ta saurare tare da murmushi. A school suka sauke ni, na Mata godiya sannan na tafi class, gaba daya mood di na ya baci, yadda na tashi da safe cikin farin ciki ne da zumudin zuaa makaranta amma a yanzun se naji duk Raina ya baci. Bayan zuhr aka zo yin test din, yau Bai zo inda nake ba Wanda yasa naji rashin Dadi, bai Kuma tambaye nu ko naci abinci ba kamar yadda ya saba, duk se naji kamar an kukkunce min knots din Kai na. Fuskar shi Babu annuri ko kadan ni Kuma saboda zakewa Wai se nake Jin Babu dadi, guys imagine my audacity! Haka ya rarraba question papers din ko kallo na baiyi ba da yazo wajen bani, duk se naji idanuna sun cicciko da kwalla, ko dai shima ya gaji Dani he find me boring and unattractive again? Me yasa bani da sa'a ne cikin rayuwa ta? BashPrince00 ma da ya Fara so na he chose Samiha over me! Kuma a take se na tuna samihan, I'm sure tana can tana farin ciki a rayuwar ta, wannan tunanin sun da nayi se kawai na Fara kuka a hankali Wanda ko mutum na kusa dani ba lallai ya fahimci hakan ba. Duk abinda nake Ashe Yana kallona, ban gaya muku how observant gayen nan yake ba ko? To shi mutum ne me kula da Kuma lura. Har aka kammalla test dinnan banyi cikin dadin Rai ba Bai Kuma kula ni ba, sannan na kasa fahimtar ma abin da yake tunani daga fuskar shi, Dan kuwa expression din shi was very blank! Ayi hakuri a Kuma Kara hakuri... we're almost there. Thank you for hanging around 😊❤️😘 Ta_kwalam ce [1/3, 20:28] Maman: 036 Ko da Muka kammalla test din nayi tunanin kamar yadda aka Saba zai bimu ne one on one ya karba, Amma se yace Mana duk wanda ya Gama kawai ya kife sheet din ya fita, the class is over. Haka kuwan nayi na goge fuska ta sannan na sake dage hijab di na ya rufe kusan rabin fuskata kafin na fita, duk tunani na zaice na tsaya Amma shiru kake ji baice min ba, hakan ya sake tunzura ni naji kamar irin I'm worthless dinnan, na Fara tunanin ko dai shima he finds me boring kamar yadda kowa yake gani. Ina fita napep na.sauke wata Dan Haka na tare Dan tafiya gida, sede kafin na Kai ga Shiga sajida ta fara Kira na. Se da na shiga sannan na dauki Kiran, Muka gaisa ta tambayi ko na gama lecture nace Mata na gama se tace tana son nazo gidan ta na zauna da yaran ita Kuma zata je biki da Batuul! Wato Ni na Zama Nanny kenan? Kowa idan ya dakko wahalar yaran shi se ya Kira Ni nayi babysitting ko? For the first time nace " Na karba order cake yanzun zanje nayi suna jira na" Na fada Ina sake tamke fuska ta, tace " To kizo ki tafi dasu gida idan yaso idan na dawo se na biyo na dauke su!" Nan ma nace " Ai na kusa zuwa gida, sede ki biyo ki kawo su" Nasan yau zatai mamaki saboda ko kadan ban taba Yi musu musu ba, duk wani abu da zasu saka ni Ina Yi dukda ba godiya ake yi min ba. Haka na kashe wayar Ina jiyo ta tana cewa Batuul ai nace na wuce ita Bata San yadda zatai da yaran ba. Ina zuwa gida na wuce daki kamar yadda na saba, kwamciya nayi zuciya ta ko kadan Babu dadi. Kawai hango dull fuskar shi nake da yadda ko kula ni baiyi ba, zuciya ta se ta Fara tuhuma ta da Wai me yasa na damu tun da kuwa nasan ni da shi Babu wani Abu da ya hada mu, he's just my lecturer, whereas I'm his only female student. To se menene Dan Bai kula ni ba, Naga Yan gidan mu karewa da muke related by blood ba kula ni suke ba shi ne Zan damu Kai na. Maimakon wannan tunanin yasa naji Dan Dadi ko na watsar da tunanin shi, a'a se ma wani bangare na zuciya ta ya Fara kokarin Kare muradin ta da nuna min, shi fa Akram mutum ne me muhimmanci cikin rayuwa ta shi din therapist di na ne, ta Yaya zaai naji Dadi idan therapist di na ya daina kula ni? Shi fa ya Dan Fara boosting confidence di na ya nuna min Nima mutum ce like all other person. Ina nan kwance se sallah kawai ke tashi na har na Fara jiyo muryar hajja, kamar an tsikare ni Haka na mike, ita hajja mahaifiyar Mamaa ce, da gudu na fita na fada jikin ta Ina dariya, ta rungume ni tana fadin " Ja'ira! Karya ni kike so kiyi?" Nayi dariya Ina Zama kusa da ita nace " Hajja Baki ce min Zaki zo ba Kuma? Sannu da zuwa! Me Zaki ci?" I find comfort and love a wajen wannan tsohuwar, Mamaa da Adda se murmushi suke ganin yadda muke da ita, ita dinma sosae take sakin jiki da Ni ko jikokim ta albarka. Na tashi naje kitchen cikin zobon da nayi na kawo Mata, na dauki Jakar kayanta zuwa dakin mu. Cikin hour daya nayi Mata grilling kifi na kawo Mata hade da abincin da akai a gida. Se da Naga taci sosae kafin na bar ta ta tafi wajen Mamaa sannan na dawo daki Ina Jin dadin zuwan ta, ko ba komai zuwan nata ya saka hankali na ya dauke daga tunanin Akram. Bayan maghrib hajja ta dawo daki na Muna ta hira har na kasa karatu, Babu jimawa Kuma se ga Iyan KT, ban sani ba ko Kun tuna ta? Idan ba ku tuna ta ba to mahaifiyar Adda kenan. Ai murnar da nake se da ta bawa kowa mamaki, ita ko dakin su Adda da Mamaa Bata je ba, yadda na karbo kayan ta dakin mu na wuce da su, na hada Mata ruwa tayi wanka sannan na hada musu abinci ita da hajja suna ta yabon girkina, Wai ko iayye na albarka. Abin da nayi zai tabbatar maka how lonely my soul is, I'm yearning for love and attention. Su Adda har Kawu anan Suka zo suka gaishe su. Wajen Tara na Gama musu shimfida anan nake Jin ai kudin Batuul zaa kawo shi ne dalilin zuwan nasu. Adda Dake zaune Bata tafi ba, hajja tace " Asiya Ina Batula Kuma?" Se Kuma Adda ta dube Ni tace " Bintu Ina 'yar uwar ki? Me ya faru Bata dawo ba?" Na dubi Adda da mamakin tambaya ta Inda shalelen ta take nace " Tana gidan sajida!" Se kuwa Iyan KT ta Fara fada " Yanzun Asiya har Baki San inda budurwar Yar ki ta tafi ba, karfe nawa yanzun? Har yanzun Baki daina sakar ma yarannan suyi abin da suke ba. Ki wasu irin iyaye ne? Ke kawata.." Ta fada Wanda nasan dani take, dama kokarin fita nake tace " Wuce kije ki Kira min kawun ku da Maman ku" Ita fa Haka Iya take, matsawar idan tazo gidannan to se kowa ya koma hankalin shi, bana mantawa akwai wani zuwa da tayi ta samu ana ta zabar kayan sallah Ina daki a zaune, ta Fara tambayar Mamaa ni Kuma fa? Se tace ai Ni bana zaba saboda Kaya na daban kawu yake kawowa tunda ni baka ce. Ta bude idanun ta, Ina Gaya muku katsinancin nata ya motsa. Ta Fara fada tana tambayar su ko sun bawa Allah wani Abu ne da yayi su farare, dama har wani dadi ne ko afuwa ne Akan zaman ka fari. Kusan ranar yini tayi tana fada har kayan da aka kawo min se da aka mayar kasuwa aka canjo min, danma dai shagon Kawu ne. To daga hajja har Iyan KT dukka basu shiri da Batuul, dukda tafi zuwa inda suke Amma Basu shiri saboda wani dalili da ban sani ba. Haka naje na Kira Mamaa da Kawu, suna tare ma tayi Masa serving abinci. Tunda suka Shiga suka zauna take fada akan Batuul saboda dukkan su sunsan ta tafi makaranta Amma Basu ma San ta tafi gidan sajida ba. Karshe da lallami kawu ya Kira sajida wadda ta tabbatar Masa tun maghrib Suka rabu da Batuul ta taho gida " Kun bani kunya, har yaushe yarinya daya ku kasa kula da ita, wannan ya tabbatar min cewar Haka take kullum, Kuma Baku ma sani ba. Yaushe lalacewar ku ta Kai haka Hamisu, Asiya da Rukayya! Batular nawa take da zata gagare ku?" Dake hajja Bata da fada, shiyasa maganganun ta ko fada take to kamar nasiha take, Kawu da kowa dukka sukai shiru ga shi sun kasa samun ta a waya, Nima Kuma Ina parlor se Kiran dayar number ta da duk gidan Ni kadai nake da ita, Nima wani birthday party zaayi na friend dinta shi ne ta Kira Ni da shi da suna min kwatancen in da zaa Kai musu cake shi ne Dana gane contact din ta ne nayi saving. "Wai menene kike damu na" Shi ne abin da ta Fara fada da ta dauka, kawai Dan bani da saurin fushi, Kuma Ina da hakuri bacin Haka da tuni gaba ce tsakani na da wannan marar mutuncin. Nace " Batuul kina kallon lokaci kuwa? Ina kike?" Daga yadda take maganar nasan ranta a bace yake tace " Ina gidan sajida Mana yanzun Zan taho" Ban Karya ta ta ba saboda ni bansan an Kira sajida ba, nace Mata tayi sauri ta dawo saboda Kawu na neman ta, ai shi Bata Gama Raina shi ba. in no time zakuga ta dawo! " Sannan me yasa auren Batula kawai zaayi Banda Bintu?" Hajja ta tambaya, Adda tace " Batuul ce kawai ta samu miji, ita kawar taku ko saurayi Bata da shi, sannan wannan yaron Suleiman muka so hada ta da shi Amma tayi ta Masa wulakanci..." Ai kuwa Adda Bata San ta ballo ruwa ba, Iyan KT tace " Ita din BINTUN ba Yar ku bace ba? Tsinto ta kukai? Dan me zata Yi soyayya da abin da Yar uwar ta ta Bari? Wai ku a gidannan kanku daya kuwa? Wanne irin rayuwa kuke? Kun bani kunya, ta Yaya zaku fifita wasu daga cikin yaran ku Akan wasu wannan ba daidai bane ba. Itama kawar tawa tana zaune mijin ta tsalale na idon duniya zai fito, Kuma ba Baki nayi muku ba Allah ya sakawa Bintu kada kuga Kun haife ta, akwai hisabi tsakanin iyaye da yaran su. Ku fita ku bamu waje!" Dukka suka Mike suka fita jiki a sanyaye, har lokacin Ina parlor Ina jiran Batuul wadda ta sake Kira na Akan Ina Kawu, nace Yana daki tayi sauri ta shigo. Cikin rashin saa tana shigowa suna fitowa su kuma, sukai kicibis akace Wai kicibis mugun gamo! Ran shi dama a mugun bace yake, Ina fata Baku manta kawu da zuciya ba dukda ba sosae yake nuna hakan ba, Yana zuwa ya dauke ta da mari Yana fadin " Daga gidan uban wa kike? Ina Kika je se goma kike dawowa?" Marin ya girgiza ta ba kadan ba, Dan har Jakarta da Bata Gama rufewa ba Bayan ta karba kudi hannun honorable ta Fadi a kasa, a take kudin Suka fito, dukka Mamaa da Adda Suka bude bakin su suna fadin wannan wanne irin tozarci ne cikin dare. Kafin ta Kai hannu ta dauka har ya dauka, mint ne na 1k wrapper guda biyu, ai Ina Gaya muku wannan Daren kusan kashe Batuul yayi, duka dai seda hajja da iya da Kuma wani makwabcin mu suka so kafin aka kwaci Batuul hannun shi, kawu Bai hakura ba ya shigo dakin mu Dan ita se rusa kuka take ta gudu dakin Auwal, Ina tsaye Ina kuka saboda hankali na ya tashi na Kuma tsorota da dukan yace " Ina ne wajen kayan ta!" Hannu na rawa na nuna Masa, aikuwa ya bude ya dinga watso da kayan kasa, kudi Nadi Nadi Haka Suka din ga fadowa, kunsan se da aka hada kudin sun Kai 900k, ai Adda se ta Fara kuka, ana bude Jakar ta se ga mukulin wata Benz ya Fado, innalillahi wa inna ilaihil rajiun! Munga tashin hankali wannan Daren Wai Saar mu saya sirikan kawu na nan, se da suka ji inama Basu ce Ina Batula ba da kilan hakan Bai faru ba. Tun da yaga key din motar ya ciri igiyar shanya ya nufi dakin Yaya Auwal ya fito da ita, tana ihu ga lokacin gari yayi shiru Bayan dare Kuma layout ce, kunga kowa na gidan shi, anan tsakar gida yace a gaban kowa ta Fadi motar waye? Da farko tace ta kawar tace, da ya zuba Mata wannan igiyar guys se tace " Kawu wallahi tawa ce, tawa ce !" Yace " Uban waye ya siya Miki?" Tana ihu Yana tafkar ta tace " Honorable ne!" Lokacin dukan yayi yawa har ya samu fuskar ta, nayi ta maza ganin kowa tsoron magana yake masa, na rike bulalar na tsugunna har kasa nace " Kawu Dan Allah kayi hakuri, Dan Allah!" Kilan shima jira yake wani ya Hana shi, kunsan dai yadda kawu yake son Batuul, Dan da amincewar shi Batuul ta ruguza maganar Suleiman Dan abokin shi. Ya yarda bulalar sannan ya wuce dakin shi, Nima naja hannun kawaye na muka tafi, kowa jikin shi a sanyaye yake. Muna zuwa har sun kwanta se ga Batuul ta shigo har lokacin kuka take, tana shigowa Ina tattare Mata kayanta, warcewa tayi daga hannu na tace min " Munafuka kawai!" Sannan ta nufi gadon ta kafin ta hau ta hangi iya da Kuma hajja a gado na dake nawa na da girma tace " Anan zasu kwana! Aikin banza uwar shishigi duk se kin da dakin mu yayi warin tsofi!" Tana fadin Haka ta fice ta barni da Jin kunya, hajja tace " Wannan yarinya iyayenta sun lalata ta da yawa!" Ta_kwalam ce Be reminded that BINTUN BATUUL is not free, NAZNEEN and GEN NASIR ZAKI! They're still ongoing with as low as N1300. [1/3, 20:28] Maman: 037 A wannan Daren bana tunanin a cikin gidannan akwai Wanda yayi bacci me Dadi kowa bacci dai se barawo Wanda sukai Kuma cikin dare da sun farka abin da ya faru zai Fado musu. Washegari da wurwuri nayi ma kawaye na breakfast, ba tare da na jira kowa ya tashi ba nayiwa su hajja sallama na tafi makaranta, ranar ta Kama Friday amma Zan fita saboda akwai lecture daya da nake da ita. Se Bayan na fita sannan na duba waya ta Naga message din Alamin Akan the class will not hold so it will be a free day! Wani rashin Dadi naji saboda bayan na fita abubuwan da Suka faru a class din Dr Akram se Suka dawo min, rudanin jiya da yasa na manta komai se gashi ya lafa yanzun se Kuma asalin damuwa ta ta dawo! Haka na koma gida badan na so ba. Na samu Kawu Bai fita ba, Haka Adda ma, dukkan su suna parlor an rutsa Batuul ta Fadi inda motar take, could you imagine motar tana gidan zuhra, Ashe can ta maida ta. Nan kawu ya Kira mijin zuhra akan su zo Yana neman su, Haka shima honorable din Kawu ya Kira shi sede baya gari yabi earliest flight to Lagos, Dan Haka Kawu yace Masa to ya fadawa masu kawo kudi su wuce Hadejia Kuma biki ya fasa saka watanni shida kamar yadda Honorable din ta nema, ya maida shi wata biyu. Ita Kuma Batuul hatta school din ta sede Auwal ya Kai ta ya dakko ta, duk wani Wanda zata hadu da shi ya kasance a gida ne. Har lokacin kuka take yi, ta bani tausayi sosae da sosae yadda Baku tunani, Koda dai ta kasance a wayward child Amma ai ba laifin ta bane ba ita kadai, laifi har da iyayen mu Dana yayin mu. Ai kamar yadda hajja tace ne, wani lokacin idan yaranka sukai aure sukan canja, sukan Zama dafi ga yaranka da basui ba. Ku kalla dai yadda zuhra ta yadda Batula tayi ajiyar motar ta a gidan ta, for only God knows when, Allah kadai ya San tsahon lokacin. Kuma yawan fitar da suke da ita da yadda suke nuna Mata ita me kyau ce tayi amfani da kyanta na daya daga cikin abin da ya sake hatgitsa tunanin ta! Bangaren Akram, bayan shi da Alamin sun kammalla tattare dukka answer sheets din mu, ya dube shi yace Kai min office di na, messenger ya bude maka, Zan karaso Jima yanzun. Alamin yayi yadda akace sannan shi Kuma Akram ya fita Dan duba ni, Amma cikin rashin saa ko wata me mustard yellow din hijab bai gani ba, yafi mintina biyar a tsaye kafin yayi concluding na tafi, shima se ya wuce zuwa office din shi, inda ya tarar dukkan papers din mu aje akan desk din shi. Ya zauna Yana ayyana dalilin da yasa na tafi da wurwuri Haka, he thought that we're friends Amma se yaga au shi ne Bai kula ni ba. Kam shi ya shafa daidai shigowar Kiran Ummaan shi wayar shi, ya gyara Zama ya dauka bayan sun gaida ta sanar Masa ai Alhaji Gidado ya samu sauki an dawo da shi gida, yayi musu murna sannan ta tambayi yaushe zai dawo, yace ai se dare saboda Yana son marking test, se ta sanar Masa zata Aiko Masa abincin shi kawai! Har ya kashe se gashi ta sake kira, Bayan ya dauka tace masa "Ina Bintu Fatima?" Yayi murmushi yace "Baki manta sunan ta ba? Ban Jima da barin class dinnsu ba" Tayi murmushi tace "Ya Zan manta Bayan ita ce mace ta farko da ka taba bani labarin. She must be sweet tunda har idanun yaro na ya sauka Akan ta!" Yayi murmushi, baisan dalilin wannan dadin da yake ji ba yace "Ummaah, Zaki so Fatima idan Kika ganta, idan Kika zauna da ita Zaki ga how pure her heart is!" "Yaushe zaa kawo min ita? Na ganta mu gaisa!" Ya bude Baki Yana murmushi yace " Kai ba zata yarda ba Ummaah, na dai hada ku a waya watarana" Uwar tashi tayi murmushi ba tare da ta Kara cewa komai ba, sukai sallama Akan se sun hadu anjima. Aikuwa Babu jimawa se ga driver ya kawo Masa abinci, ya karba Yana me Yi Masa godiya, kafin ya Fara ci seda yayi wa Kan Shai gwajin jini, bayan results din ya fita saman Dan censor din se ya bude madaidaiciyar warmer din, alala ce hadadiya , wani karamin flask Kuma anyi Masa vegetable soup wadda zata tafi da alalar, ga jug shake da kunun Aya. Sosae yaci sannan ya bawa messenger din wajen ya Kuma Fara marking. Yana ta tunanin menene reg. No dina Amma ya kasa tunawa tunda dama ba sani yayi ba. Se ya dauki wayar shi ya Fara kokarin Kira na, yayi ta scrolling Amma ya rasa me yake yi ko Kuma dalilin hakan. Then it down on him cewar bashi da contact di na gaba daya. Se ya Fara dariyar abin da ya faru, instead kawai se ya Kira Alamin da niyyar yace masa ya tura Masa contact dina Amma Yana dauka se hankalin shi ya dawo jikin shi, ya kasa tambayar sa contact din instead se cewa yayi ya Kira yaji ko Yana school akwai aikin da zai saka shi, se yace Masa ai ya tafi tun dazun, Amma zai dawo yanzun, se yace Masa " Nooo... Ma hadu Monday. Thank you!" Daga Haka sukai sallama ya aje wayar tare da dafe Kan shi Yana tunanin what has gotten into him shi kuwan? Why is he so desperate Akan son Jin muryar Bintu ne, a ran shi ya ayyana ai shi therapist din ta ne, Dan Haka ko Yaya ya fahimci slight change a mood din ta, ya kamata ace ya tambayi dalilin hakan. Har ya koma gida Bai samu wani kwakwaran dalilin neman number ta ba, se kawai ya wuce gida ba tare da Jin Dadi ba. Yana shiga abinci kawai Suka ci Safiyya ta saka shi a gaba Suka tafi side din Alhaji Gidado Dan duba shi, tasan tabbas idan ta bar shi ba lallai yaje ba, Kuma hakan Bai kamata ba. Suna zuwa suka tarar yana cin abinci, suka zauna har ya Gama saboda ba Wai ta daina mulki bane ba, dukda mulkin na shi yaran shi da jikokin shi yake yiwa kawai, Ina wannan Yan bana bakwai din zasu amince da wannan mulkin mallakar, wasu ma daga ciki ko aure sukai Basu Zama a apartment din Gidado community, waje suke fita su Zama independent, wasu ma Adamawar duk suke komawa. Bayan ya kammalla ya amsa gaisuwar su sannan ya dubi Safiyya Dake kokarin fita Dan bin Bayan Akram da ya Riga ya fita, cikin fullanci yace " Kun shafa min bakin penti a fuska, yaron ku Kiri Kiri yake nuna ko ganina Bai son Yi" Tayi murmushin Jin kunya tace " Ba Haka bane ba Grandpa, kasan Akram yadda yake ko da sauran cousins din shi!" Ya tabe Baki yace " Ai nasan Yana fushi Dani Akan abin da ya faru da uwar shi zainab ne ko? Amma ai ba wani laifi nayi ba..." Tayi saurin juyawa Dan ganin ko Akram Yana nan ko ya tafi, ta saki ajiyar zuciya ganin baya nan tace " Ayya Bai masan komai akan mahaifiyar shi ba, kamar yadda Bai taba tambayar wadda ta haife shi ba, dukda nasan yasan bani na haife shi ba" Shigowar Uncle Ali yasa tayi.masa sallama ta tafi, Akram na tsaye Yana jiran ta se gata ta fito Suka wuce. Washegari Friday, very early ya fito Dan zuwa office, slice of wheat bread kadai yaci da wani spread din su na masu condition irin na shi, Amma sede ajin na su babu kowa, se ya Kira Alamin ya tabbatar Masa ai ba su day class ne. Washegari ya gaji da wannan wasan Dan Haka kawai ya rufe idanu ya saka Sadiq ya tura Masa contact Dina. Ina tsaka da aiki a daki Dan zaman lafiya a gidan ya Dan wanzu har kawaye na sun tafi, nasan mun kusa Fara exams dole na dage da karatu. Unexpectedly se kawai Naga Kiran shi, bansan waye ba kamar yadda kuke tunani, Ina dagawa yace " Fatima!" Yana fada nasan shi ne saboda shi kadai ke Kira na da Fatima ba Bintu ba. Nayi saurin aje gum din hannu na nace " Sir Ina wuni?" Yayi murmushi yace " I'm good fatima!" Wai Kuma dukka se mukai shiru se shi ne yace " Kina ji na?" Nace Masa Ina Jin shi, ya gyara zaman shi yace " Kawai Ina son naji yaushe zamu Gama session din mu? Ko you're busy!" Nayi saurin ture kayan da nake hada delivery box da shi nace " No Babu abinda nake sir! Mu cigaba" Kunsan dai yawanci Wanda sukje zuwa therapy session Basu kaunar session din Amma ban dani, I was excited ma da zaa cigaba. Ya sake rike wayar a kunnen shi Yana gyara zaman shi saman couch yace "Ina jinki" Yau ko musu Babu nayi relaxing baya na a pillow na Fara bashi labari na tun daga abin da Zan iya tunawa har zuwa yanzun! Kunsan se banyi kuka ba, da alama dai zuciya ta ta kekeshe, nayi shiru Ina maida ajiyar zuciya me nauyin gaske nace " This is all I went through sir! Ban sani ba ko inada laifin discriminating di na da akai a gidan mu, mutanen gari da suke criticizing dina Akan abin da bani da laifi" Yace " I'm sorry!..." Kawai haka yake fada saboda gaba daya zuciyar shi wani irin yanayi yake ji da ba zai iya misalta shi ba... Ta_kwalam [1/3, 20:28] Maman: 38 Somewhere in Nigeria Gloves din hannun shi yayi saurin cirewa tare da tashi daga Kan cadaver da yake examining, wayar shi ya dakko da take ringing a Karo na biyu, Yana dubawa yaga Babu number se de anyi hiding din caller ID din, ba tare da damuwa ba yayi swiping green ya dauka tare da karawa a kunnen shi Amma baiyi magana ba, daga dayan bangaren cikin harshen turanci Wanda kana Fara sauraro zaka San turancin second language, saboda yadda take fitar da kalaman zaka fahimci akwai wani yaren da ya riga yayi staining harshen ta. "Sadik Garba?" Ta tambaya a hankali, yayi murmushi dan a take ya fahimci wacece, wannan kusan shekaru uku rabon da ta Kira shi, Bata taba barin ID din ta a bude ba, so idan ba ita ta neme shi ba, Babu yadda zaayi ya neme ta. "Ma'am kwana biyu!" Tayi murmushin Jin har ya Gane ta tace " Ina lafiya! Ya Akram yake? Ya jikin shi? Yayi aure? Ya Gama makaranta?" Yayi murmushi Yana zama nesa da examination table din da cadaver yake Kai yace " Akram Yana lafiya, Babu wani episode da ya samu a shekara biyu da Suka gabata. Ya samu aiki Yana lecturing a wata prestigious University!" Wani farin ciki ya saukar Mata tace " Baiyi aure ba?" Ya girgiza Kai yace " Har yanzun dai babu wannan maganar a kasa!" Ta gyada Kai tace " Nagode! Bank details din ka sune har yanzun?" Ya gyada Kai, kafin yayi Mata sallama har ta kashe wayar!!! *** "Fatima!" Ya fada a tausashe, na Dan ja numfashi kadan nace " Sir!" "Yana cikin abin da mu Dan Adam mukai lacking, da farko se kin so kanki kafin wani ya soki, you've to accept yourself before others accept you! Fatima Mata nawa ne suka fiki kiba, Suka fiki baki Amma suna rayuwa cikin farin ciki? Kinsan me yasa? To saboda sun rufe kunnuwan su Kuma suna alfahari da yadda jikin su yake, kema da haka kikai bana tunanin abin da mutane suka fada zai dame ki. Shi Dan Adam da Kika gani ko ubangiji da ya hallice shi baya iya Masa, Dan Adam bawa ne marar godiya, baa iya masa komai se yayi magana. So you can never impress people just impress yourself kiga yadda mutane zasu manta da sunyi criticizing din ki!" Maganganun shi sun shiga kunnuwa na, Kuma sunyi sinking cikin Kai na, Kuma Haka ne tabbas idan Kai baka so kanka ba, kayi alfahari da kanka ba to duk duniya Babu me yi maka hakan, for the world to recognize you, you have to accept yourself. To Amma ta Ina Zan Fara ganin Kai na a matsayin Nima na Isa? " Sir it's hard!" Yace " Na sani Fatima, shi ne next abin da zamuyi. So yanzun Naga an kusa daura lunch, don't just stay in your room. Go and help out!" Nayi murmushi Wanda I'm sure yaji sautin shi nace " Sir nagode! Sir nagode!! Allah ya saka maka da mafificin alkhairi, thank you so much sir, I'm very grateful ! Nagode..." "A'a tun kafin session din ya Kare, kada ki damu anything for you. Just make sure you saved my contact kinji!" "Right away sir!" Na fada Ina Jin wani Abu a kirji na, da wani farin ciki me sakawa kaji kamar a gajumare kake... Bayan na kashe wayar se na Fara kokarin saving contact din nashi, Amma bana son saka sunan shi, nayi ta kawo sunaye cikin Kai na Amma a karshe se nayi Masa saving da *Noor* kunsan me yasa? Saboda a rayuwa ta Akram haske ne da ya haska tawa rayuwar , ya Kuma haska min hanyar da nake takawa. A bangaren shi kamar wani Wawa Haka bakin shi ya kasa rufuwa, dukda tausayi na na gaske da yake ji Amma se yake Jin zuciyar shi is light like a feather, yake Jin kamar yayi ihu saboda murna Amma se yake kokarin suppressing hakan ta hanyar murmushi kawai. Sallamar Safiyya tasa yayi saurin aje wayar tare da mikewa har lokacin curve din da labbansa sukai saboda murmushi ya kasa gushewa, bayan ta aje tray din data shigo da shi ta zauna, shima ya zauna Yana gaishe ta, ta amsa tana fadin " Menene labari, saboda fuskar ka ta nuna akwai abin da ake so a fada min!" Yayi dariya yace " Ummaah ya ake Gane idan ana son mutum?" Ta dan bude idanun ta da kyau tana kallon shi, da farko mamakin tambayar tayi Amma a karshe adduar ta Allah yasa ya samu wata Yana son ta ne! "Mhmmm! Ya danganta da me kake ji. Can you share with me?" Ya gyara zaman shi, Dan Yana daukar Safiyya tamkar kawarshi ba mahaifiyar shi ba, saboda itama kamar aboki ta dauke shi ba dan ta ba. " Ummaah Ina kin tausayin ta sosae da farko, ko na rabu da ita lokauta da dama se naji Ina son sanin me take Yi? Ko Kuma me yake faruwa da ita a wannan lokacin? Ummaah idan Ina magana da ita I feel the happiest a rayuwa ta and I cherish every moment da mukai magana da ita. Idan bata kula ni ba, Ummaah hankali na tashi yake. Kwana biyunnan I've checked har Google ko Zan ga da gaske son Fatima nake Yi" Safiyya har lokacin Bata dai na murmushi ba, Dan ita din sarauniyar hakan ce Kuma hakan weapon din ta ne, tace " Son ta kake, wannan shi ne feeling din soyayya Akram" Se taga murmushin fuskar shi ya dauke, kamar tsoro ta gani saman fuskar shi Wanda ya Bata mamaki tace " Are you scared? Why" Yace cikin rauni "Ummaah ta Yaya zata aure ni Bayan Ni bani da lafiya?" Tace cikin kwantar da murya " Kayi Mata bayani? Kace Mata kana da diabetes?" Ya girgiza Kai yace " I'm scared Ummaah! Kar tace ba zata iya daukar wannan burden din ba" "Ba zata ce ba, Kai fa kace min she's very good,she has a pure heart ko? To kayi kokarin winning tata zuciyar. Ai nasan ba se na koya maka ba ko?" Yayi murmushi a kunyace, Yana son Safiyya yadda take Kara karfafa Masa gwiwa. Gaba daya ranar Haka ya karasa ta cikin walwala da annashuwa, ji yake kamar ya tsinci hakori... 🎵🎶 _So idan ya Kai so, abin da baka zato kake yi_ _Baka gane haske balle duhu se ka sauka layi_ _Al'ajab na so ko da wanne lokaci ya kanyi sauyi_ _Bai da tausayi, Dan kuwa Bai barin gangar jiki cikin sauki_ 🎶 "Abbaa" Safiyya ta Kira sunan Imam a hankali lokacin da ya Gama Shan tea din shi na kullum kafin ya kwanta, ya dago ya kalle ta Yana kokarin plugging system din shi jikin socket, ya juyo yace " Akwai magana ne?" Ta gyada Kai, hakan yasa ya koma ya zauna tare da Bata dukkan hankalin shi, tace " Akram dazun munyi magana da shi, da alamar ya samu yarinyar da yake so..." " Yar wacece?" Tun da ya Fadi hakan ta fahimci yayi tunanin a nan community din su yake nufi, tayi murmushi tace " Amma kasan barewa ba zatayi gudu Dan ta yayi rarrafe ba ko?" "Me kike nufi" "Eh Ina nufin outsider ya samu, Kuma nayi Masa alkawarin nu da Kai zamu Goya Masa baya dari bisa dari. We need cross breeding!" Imam yayi murmushin cross breeding din da tace, yace " Shi kenan, idan ya Baki details din yarinyar se na saka ai launching bincike akan ta ko?" Se ta saki ajiyar zuciya tace " Duk ba wannan ba, yaushe zamu fada masa shi din Yana da wata uwar bayan ni. Nasan yasan bani na haife shi ba, Amma Akram yayi min Kara da Bai taba nunawa yasan bani na haife shi ba. So Dan Allah Abba Ina son muyi Masa bayani, he owes her addua ko da Bata Raye" In dai maganar Zainab ce to har yanzun ita ce weakness din Imam, cikin wani irin yanayi yace "Tsoron yadda zai fahimce ni nake shiyasa duk wannan lokacin na kasa sanar da shi saboda nasan zai kalle ni a matsayin Wanda ya Gaza ya Kuma kasa protecting Babar shi" "Bana tunanin hakan Abba, Akram is an understanding person, na tabbatar da kwakwalwa zai saurare ka ba da zuciya ba. So Allah ya kaimu goben." Wannan Daren Imam Haka yayi ta juyi, yasan Babu ranar da tazo ta wuce baiyi adduar bayyanar zainab ba, saboda kullum Yana blaming kanshi a matsayin Wanda ya lalata Mata rayuwar ta, saboda yasan ita soyayyar shi Babu abin da ta samar Mata Banda tsananin tashin hankali, hargitsi da Kuma lalacewar rayuwa! Amma yasan lokaci yayi da ya kamata ya sanarwa Imam wacece zainab! Washegari da wurwuri Safiyya ta kammalla breakfast, dukka a tare suka ci abinci dukda Akram nashi daban ne da Wanda sauran ke ci. Bayan sun Gama Safiyya ta dakatar da Akram daga komawa dakin shi, saurin da yake yaje ya Kira ni kamar yadda yayi min alkawarin. Sauran yaran ta tura su daki. Safiyya ta dubi Imam da ya Zama kamar anyi Masa mutuwa, tace " Abba let's get started! Akram Abban ka Yana son magana da Kai me muhimmanci, Ina son ka bashi aron hankalin ka kaji?" Ya gyada Kan shi, a lokacin ta Mike zata tafi, Amma duka suka tsayar da ita saboda ita ce strength din kowannen su. Haka ta koma ta zauna. A hankali shi Kuma ya Fara bawa Akram labarin shi da zainab, har ya Gama sannan yace " Kayi hakuri na rufe maka all this while, inata kokarin ganin na ganta before you come up age wannan shi ne dalilin na" Akram da idanun shi yayi jawur Yana ta furta innalillahi wa inna ilaihil rajiun! Wani irin mawuyacin yanayi zuciyar shi take ciki, shiyasa ko sau daya Bai taba Jin wannan community din ta burge shi ba, shiyasa ya tsani Alhaji Gidado da wasu daga cikin kakkanin iayyen shi, Ashe abin da sukai ma mahaifiyar shi kenan? Ya rasa abin da zai fada se shiru kawai da yayi! Ta_kwalam [1/3, 20:28] Maman: 039 Dakin shi ya koma a hankali, yayi tsaye Yana kallon dakin ba tare da Sanin abinnda ya kamata yayi ba, tuntuni yasan Safiyya tabbas ba ita ta haife shi ba amma Bai taba tunanin wannan shi ne abin da wannan mutanen da suke Kiran Kan su family sukai yiwa mahaifiyar shi ba. Bayn maida ta kasar ta, Bayan zaman shekaru bakwai da aure a Kanta Kuma babu miji, an barta da ciki ba tare da mahaifin cikin ya ma San da zaman cikin ba. Allah kadai yasan the hell she went through while raising him alone. Se Kuma dare daya, Rana daya, lokaci daya bayan ta hakura ya Kuma Saba da rashin kowa a ryuwar ta, da Zama ita kadai a rayuwa. Se Imam ya sake lallabowa ya dawo Mata da dukkan wasu memories da sukai fading, memories da ta Riga ta aje a gefe ya dawo dasu, he conspired and took him away ba tare da ta sani ba. Ya wannan abun zai je ma mutum? Duk da memories din na shi akan ta fragments ne, Amma dai zai iya tuna har lokacin da take murnar zuwan Imam, da Bayan ya dawo daga school take fada Masa Imam ne mahaifin shi, se Kuma tafiyar da sukai me tsawo daga kasar Qatar din wadda da bai masan ya sunan kasar ba se yau. Ya dunkule hannun shi Yana sakin numfashi dai daya, zuciyar shi Banda zafi Babu abin da take Yi,duk wani kokarin Kare Imam da yake, da kokarin Yi Masa uzuri ya kasa Yi a yau, yama zaka dauki responsibility din abin da kasan ba zaka iya ba, ya zaka Fara wannan? And he shamelessly tell him Wai Yana son ta? Wannan shi ne so? Idan har wannan shi ne so to shi nashi abinda yake ji akam Bintu ba so bane ba, saboda ya saka Bintu a matsayin zainab, idan shi ne se de ya bar duk wani wealth and fame ya zauna da Bintu, Amma mahaifin shi ya zaba company over his mother that sacrificed everything for him! A Dan kwana biyun da Muka kasance very close ni da Akram, na gane mutum ne shi me cika alkawarin, zaiyi wahala yace I'll call you back, Kuma Bai Kira ba. So kamar yau da safe Muna cikin waya Yana Karan boosting confidence di na ta hanyar nuna min I'm beautiful the way I'm, shi ya yadda idan na danyi shading few kilos for the sake of my health, Amma Bai yadda Dan Wai muatne na zauna na dinga Shan abubuwan da zasu kashe min jiki in no time ba. Duk maganar da ya fada min, zuciyata da kwakwalwa ta kawai amsa take, Bata ma wani tsayawa yin musu balle ta nuna ba zata yadda ba, komai ya fada se naji kawai ya zauna cikin Kai na Kuma kamar wajibin dole ne na se nayi amfani da hakan. Nayi kusan awa Ina kallon waya ta Ina jiran Kiran shi Amma Bayan wajen awa da wani Abu se ga message din shi ya shigo _Zan Kira ki anjima in the evening, I'm a bit busy please_ Na saki ajiyar zuciya har Ina mamakin irin wannan damuwa da nayi da shi, but Kuma ai Noor Dina ne, Wanda ya sama min farin cikin da nake ganin na Rasa Shi a duniya, confidence din da bani da shi se gashi na Fara Dan jin a bit of Nima fa dan ina da kiba I can stand out cikin mutane Kuma har babu damuwa. Karfe hudu nake ganin shi ne evening, so kafin hudu komai da komai da zanyi har karatu, girki da komai na gama kawai nazo na zauna na saka wayar a gaba in anticipation for his call, Amma har isha Babu Kira Babu dalilin shi, there and then na tabbatar Babu lafiya, duk inda Noor yake bashi da lafiya. Wajen takwas na dare na kasa jurewa se kawai na dauki waya na Kira shi dukda zuciya ta na tuhuma ta Akan zakewa da nake, Amma abin da nayi se nace ka gaida me gaishe ka ko bazai amsa ba, Kuma mutum ya damu da Kai dole ka nuna mishi kulawa. Da wannan na samu na Kare kai na daga tuhumar da zuciya ta take min. Wayar shi bata shiga, har nayi bacci Ina trying Amma ban samu wayar ta shiga ba. Nayi ta mafarkin shi Wanda ma da na tashi na kasa gane me mafarkin ya kunsa, kawai dai nasan saboda he has been in my thoughts the whole day shi ne dalilin mafarkin na shi da nayi. Wannan ranar ma Haka ta wuce the whole day ban samu munyi magana ba, idan na Kira shi bana samun shi, gashi public holiday aieyi balle ace Zan iya zuwa makaranta na gan shi. Gaba daya na damu, nutsuwa ta ta ragu, bani da wani kwanciyar hankali ko kallo na kayi kasan akwai abin da yake damuna sosae, a kwana na biyu na tashi da kamar zazzabi zazzabi saboda damuwa, nayi ta Kiran shi a waya har wajen Sha biyu na Rana, wannan karon tana shiga dauka be baayi, zuciya ta ta gama tsinkewa na Kuma Fara gane zuciya ta ta zarme wajen son shi, wata kan Bata manta abin da ya faru ba da BashPrince00, ta Kara zuwa ta Fara son wani Kuma, but Amma a yanzun duk ba wannan me damuwar ba, damuwa ta shi ne yadda zaa Yi nasan me yake faruwa da shi. Ina zaune Bayan na idar da sallah Ina ta adduar Allah yasa lafiya yake, Allah yasa ba wani Abu bane ba marar Dadi ya faru da shi ba. Wayata na sake janyowa a Karo na babu adadi na sake Kiran shi, cikin hukuncin Allah se gashi an dauka, ban tsaya nayi comprehending muryar da tayi min magana ba kawai cewa nayi " Sir! Me ya faru? Are you ok?" Safiyya ta lumshe idanun ta, hannun ta Yana cikin hannun Akram da har lokacin Bai farfado ba, kallon fuskar shi take wadda tayi kamar an zabge ta saboda ramar da yayi lokaci daya kamar Wanda ya jima Yana jinya, Dana sani ta kasa dainawa, Bata taba tunanin ko da Wasa wannan maganar zatai affecting din shi haka, da tuntuni sun fada mishi ko Kuma sun bar maganar. Tun ranar da ta fada Masa shekaran jiya da ya shige dakin shi Bai sake fitowa ba se sallah kawai yake fitowa yayi ya dawo, Yana dawowa Kuma zai kulle dakin shi deep in thought, ya rasa ta Ina zai Fara kamo zaren balle yasan ta inda zai Fara neman mahaifiyar shi, Haka Kuma ya kasa yiwa mahaifin shi uzuuri saboda Yana ganin duk abin da ya faru sakacin shi ne ba wani abun ba. Safiyya da Imam har na da yaran.dukka hankalin su ya tashi musamman da yaki yaci abinci Kuma sunsan hakan zai iya leading to babbar matsala, Safiyya Babu ban Baki da batayi ba Amma sede ya Sha ruwa kawai, a Rana na uku wato yau din shi ne ya fito dan zuwa suyi magana da Safiyya ya yanke jikin shi ya fadi a kasa. Suna zuwa asibiti an Riga da an San condition din shi tun da nan yake ganin likita dama aka Fara bashi taimakon gaggawa, saboda abinci da baici ba glucose din Dake jinin shi ya sauka Wanda ko me lafiya ya sauka haka to tabbas jikin shi ba zai amfanu ba balle shi da dama yake.da issues. "Fatima ce?" Shi ne abin da Safiyya ta tambaya, saboda sunan da ya saka ta kasa gane maanar shi, duba kuma da yawan zance na da yakeyi, da maganar da sukai yasa ta fahimci nice me Kiran. Kamar zance a'a se nayi saurin fadin " Ni ce" Ko Bata ce komai ba nasan Babu lafiya, tunda da lafiya he supposed to pick up his phone himself, ba Wai a daga Masa ba, Amma Jin muryar ta se naji nauyin tambayar ta yadda yake, kamar tasan abinda nake tunani tace " Fatima, Akram bashi da lafiya! Muna asibiti Bai masan inda Kan shi yake ba!" Wani irin duummmmm naji cikin kunne na Kai na har da Kai na, na Yi shiru Ina assimilating abin da ta fada, "Kina ji na?" Nayi saurin girgiza Kai hankali na ya Riga da ya Kai kololuwar tashi nace " Me ya same shi? Wanne asibitin kuke?" Ita ta fada min komai, na mike ba tare da nace komai ba na canja Kaya na, na zura gogaggen hijab sannan na fito zuwa dakin Mamaa idanuna sunyi jawur, kana kallo na kasan bana cikin nutsuwa balle kwanciyar hankali, Mamaa na zaune ita da Zuhriyya da tazo da bansan yaushe ba, na shiga nace Mata zanje dubiya, ko amsarta ban jira ba na fice Ina Jin kamar nayi tsuntsuwa naje gare shi. Mintina ashirin da wani abua suka kaini asibitin, ta Riga ta fada min bangaren da suke hakan yasa na tafi Kai na tsaye, har lokacin zuciya ta ce kawai take tafiyar da ni Amma ko kadan kwakwalwa ta Bata ankare da abin da yake faruwa ba. Se da naje kofar dakin inda na Dan ga mutane, se na Fara tunanin me yasa nazo? A matsayin wa nazo? Nayi shiru na kasa motsawa har seda wayata ta Fara ringing kafin na dawo daga dogon tunani hade da wasiwasin na shiga ko na juya da nakeyi " Kina ina?" Ta fada Bayan na dauka, a hankali nace " Ina kofar dakin da yake!" Se tace na jira gata nan zuwa, Babu jimawa se gata ta fito, dukda yanayin damuwa da fuskar ta ke ciki, Bai hanata yimin murmushi ba, na tsugunna har kasa Zan gaishe ta ta dakatar dani ta hanyar Kama kafadu na tace " Muje, nagode sosae da Kika zo!" Haka muka shiga ciki, Yana kwance ruwa na shiga jikin shi, bakin shi ya bushe yayi fari Haka jikin shi baya wannan shekin da yake a Koda yaushe. Noor ne a kwance Haka? Kawai se na Fara kuka a hankali, zuciya ta gaba daya ta karye ji nake kamar na tashe shi ni Kuma na kwanta madadin shi, to Babu halin hakan. Mahaifiyar shi wato Safiyya wadda naji suna Kira Ummaah ita tayi ta lallashi na dukda wani lokacin se ta goge hawayen da yake zubo Mata, kowa yazo dubiya se ya tambaye ta ni wacece? Bata ma fiye bada amsa ba. Anan na lura yadda suke Kama sosae da junan su day fullanci da suke tayi gwanin shaawa, Nima naso ace na iya wani yaren Bayan Hausa da turanci! Ta_kwalam [1/3, 20:30] Maman: 041 Ban yanke hukuncin abin da Zan fada Masa ba har dare yayi, zuwa lokacin I was very anxious na San zai bukaci Sanin amsar request din shi, na zauna nayi tunani na Kuma Kara tuanani, abin da yafi komai Dadi da sauki a rayuwa shi ne nayi kokarin bawa wannan bawan Allahn chance. Se Kuma naji tsoro nake, what if idan tarihi ya sake maimaita Kan shi? To saboda me ma zanyi wannan tunanin? Kuma saboda me zai maimaita kanshi, tunda dama relationship di na dana BashPrince00 was a blind relationship, ko kadan bamu taba haduwa ba, Kuma a ranar da ya ganni yaji baya so na, se ya zaba wadda yake ganin ta dace da rayuwar shi! Wajen karfe takwas na idar da sallar ishai, Ina zaune saman sallayar na bude littafin Ina dubawa saboda kada naje gobe ayi Mana test wadda zata hautsina ni. Ina yin karatun Amma fin Rabin hankali na Yana kan wayata, Kiran shi kawai nake anticipating a wannan lokacin. Bayan kamar mintina hudu se ga Batuul ta shigo, duk tayi wani cool da ita, tun wannan abun da ya faru, dukda tana Dan barin lecture ta tafi inda take son zuwa, Wai me Hali ance ba fa ya fasa halin na shi ko Yaya ne. Zama tayi gefen gado tana shafa wani sunscreen a fuskar ta, waya ta ta Fara ringing, gaba na ya fadi saboda ganin sunan nashi ne, wannan alama ce ta shima jira na yake. Nayi saurin daukar wayar tare da mikewa na fita, Ina zuwa parlor Babu kowa na zauna sannan ma Kara wayar a kunne na Ina Masa sallama, a hankali naji ya saki ajiyar zuciya sannan yace " Kinje gida lafiya? Thank you so much, abincin yayi Dadi thank you!" Nayi murmushi cikin Jin Dadi nace " I'm glad! Ya jikin naka? Yaushe zaa sallame ka?" Yace " Ina gida yanzun! Na Kira nayi godiya for your kind gesture and na fada miki da gaske banyi zaben tumin dare ba. From day one nasan zabi na bana Wasa bane ba!" Nayi murmushi Ina Jin Dadi, dama Haka words suke, Haka nauyin kalamai masu dadi suke? Kunsan fa dama ni I'm a word of affirmative. Bana gajiya da a dinga fada min how worthy I'm sannan Kuma yadda mutum yake so na, bana gajiya, banki ace kullum a sake maimaita min ba, inaga I'll never be bored. "To ka kwanta ka huta, kaga I'm sure ka gaji ko?" Yayi murmushi yace " Na gaji sosae Amma Kuma Ina son ma Dan ji yadda kike. Wait wai nikam ma how far da maganar mu? Kin amince Zaki aure ni?" Nayi shiru Ina Jin yadda ake wani race cikin kirji na nace " Ammm! Zan iya yin tunani?" Yace " Come on Fatima bazan zalunce ki ba fa, ba Zan Bari wani ya musguna Miki ba, I'll never be a source of pain to you. Give me chance kinji Fatima ta!" Oh Allah Wai Fatimar shi, ai duka se kunya ta lullube ni, Amma Kuma naji dadin hakan da ya fada. To wa yaga farin Shiga. Lallaba shi nayi ya kwanta sannan Muka rabu akan se da safe zamuyi magana kafin na fita school. Na dawo daki fuskata dauke da wani madaukakin murmushi, zuciya ta kamar anyi min albishir da hajji ko Kuma aljanna ma gaba daya. Tunda na zauna akan gadon Batuul ke kallo na, ta dube Ni tace "Saurayi Kika Yi? Naga kina ta murmushi kamar kin tsinci hakori" Bance Mata komai ba se sake fadada murmushi na da nayi, har na kwanta tace "Bintu!" Na dago na kalle ta nace " Ya akai?" Tace " Kinga bikin mu ya kusa Bintu, Amma kawu yace Wai ba zaayi.event ba" Nace "Me yasa?" Se ta Fara kuka tana fadin "Haba Mana Bintu ya zanyi aure lami Babu wani shagali kamar auren Hadi, ta Yaya ma kawu zaiyi hakan? Haka yace fa Wai indai biki ne ma a Hadejia zaayi" Na saki ajiyar zuciya nace " To kiyi hakuri ki yadda da hakan mana..." "Ya zanyi na hakura? Kinsan yadda na gama fadawa kowa zancen bikin nan, na gama zuzuta mijin da Zan aura Kuma kawai ace a Haka Zan Kara!" To Ni dai na Rasa me zance na Bata hakuri saboda nasan ko menene kawu ya yanke akan Batuul laifin ta, she break their trust. Da ace lafiya Lau suke batai wannan abun ba, na tabbatar kawu ba zaiyi hakan ba! Washegari, na tashi da wurwuri na Kama hanyar school, tun asuba ya Kira Ni Bayan na.idar da sallah, Ina toilet Ina wanka ma, naji Batuul tana fadin " Kaga farin shiga, wato sunan shi Noor kenan!" Ina daga toilet nace " Batuul kada kiyi picking call dinnan kina ji ko?" Tayi dariya ta aje wayar tana fadin " Aaaa lallai, Babu damuwa idan tayi wari zamu ji" Ina fitowa na dauki wayar ko ruwan jiki na ban gama tsanewa ba, na Fara Kiran shi tare da Zama gefen gado na, Bai dauka ba se gashi yayi returning call din nawa cikin hanzari. " I'm sorry, wanka nake" Yayi murmushi yace " Ina kwana Fatima ta!" Na Dan sunkuyar da Kai na Ina murmushi a hankali nace " Sir an tashi lafiya? Ya saukin jiki?" Yace " Alhamdulillah! So how far? Kin yadda na turo Abba ya nema min auren ki?" Kamar na danyi tsalle saboda yadda yai twisting tongue din shi nace cikin kasa da murya kamar wadda nake whispering nace " Na amince and I'll be glad" Wani karamin ihu yayi yace " Alhamdulillah! I promise you the world and beyond. I'll keep you happy no matter what!" Nayi murmushi da na kasa gane dalilin wannan murmushi da nake sosae da sosae, gaba daya na Zama kamar wata sakarya ma. Mun Dan taba Hira sannan ya barni na shirya na tafi school. Haka nayi lecture din cikeda Jin Dadi da annashuwa, so this is the feeling of being loved? Lokacin da na Gama lecture na wuce masallaci nayi sallah, Ina idarwa Kiran shi ya shigo cikin waya ta na dauka, Bayan mun gaisa yace nazo bayan faculty Yana jira na. Se na samu Kai na da tsayawa gyara fuska ta, abin da ko kadan bana Yi, in fact banma damu da hakan ba, to me gani nake ko me Zan shafa bazan taba kyau ba. Amma Bayan na samu skin care products masu kyau da tsada , jiki na ma se da ya canja, balle fuska ta da 80% na kurajen sun fita se Wanda ba zaa rasa ba. Na gyara zaman hijab di na sannan na nufe shi. Yana cikin mota, Nima na bude na shiga na zauna Ina kallon shi a hankali, shi Kuma waya yake so dukka hankalin shi Yana Kan wayar da yake. Se da ya Gama kafin ya juyo yace "I'm sorry! Ya lecture?" Na kalle Shi da kulawa, Babu laifi fuskar shi ta ciko ba kamar jiya ba, Haka Kuma ya Dan fi kyan gani akan jiya. Na amsa da alhamdulillah sannan ya taka accelerator Muka Fara tafiya a hankali. Muna tafe ya Fara fada min asalin shi Wanda ko kadan banyi tunanin shi din ruwa biyu bane ba, saboda kasancewar shi ya Zama complete Hausa fulani, saboda shi Bai ma son Yana fullanci ko a gida akai Masa to zai mayar da Hausa balle Kuma yanzun da yasan abinda sukai ma mahaifiyar shi kenan! Se da ya Gama Bata labarin shi tsaf ko Rabin tafiyar bamu Yi ba, saboda yadda yake tafiya a hankali kamar Wanda muke riding Keke. Na ji tausayin shi, na Kuma ji cewar kowa da nashi labarin Kuma kowa Yana da nashi dark story din. Na bashi shawarar neman ta duk inda take, se yace shiyasa yake son ya aure ni soon se mu wuce tare! Ta_kwalam [1/3, 20:30] Maman: 042 Tunani dai baya taba karewa, Bayan dogon nazari da nayi akan labarin mahaifiyar shi da ya bani se na Fara tunanin, should I ko Kuma shouldn't I. Saboda gaskiya Ina Jin tsoro sosae, kada ya Zama na Nima se munyi aure family din su su Kore ni ko wani Abu marar kyau ya faru da Ni ya zanyi kenan! Nima haka.zan tafi na bar yaro na a hannun only God knows who? Se naji duk jiki na yayi sanyi naji Anya Zan iya Zama cikin wannan family din. Ina son Akram, so na gaskiya Wanda bana tuannin rabuwa da shi a yanzun zai Zama Abu me sauki, na kuma.tuna yadda yake min alkawarin protecting di na. Se naji Dan kwarin gwiwa har na Kira eldest sister din mu ta sokoto. Babu laifi Muna Dan Yi da ita, plus ni kawai Ina son wani ya bani shawara. Bayan ta dauka tace " Bintu tunawa kikai da ni yau?" Nayi murmushi Ina fadin "Kai Yaya ko daya, ya su Khalilo?" Tace " Lafiya su kalau. Ai mun kusa zuwa muma in shaaa Allah" Nace " Bikin Batuul ko?" Tace " Eh!" Se nace " To Nima Yaya akwai wani lecturer din mu Yana so na, dukda baifi sati daya mukai tare da shi ba. Amma na Kira na fada Miki ki bani shawara!" Tace cikin muryar farin ciki "Alhamdulillah! Ai dama na sani, komai lokaci ne. Ko jiya se da na fadawa Adda nace ta daina damuwa akan ki mijin ki zai zo. Yana da Mata? Kina son shi?" Na girgiza Kai nace " Ina son shi, Kuma Bai taba aure ba!" Tace " To daidai kenan ai. Se yaje yayi magana da kawu ko Kuma akwai abin da kike son fada min?" Na sauke ajiyar zuciya cike da shakku nace " Yaya Kinga su gidan su basa auren bare, dukkan su family daya ne fulani. Shi mahaifiyar shi Yar Qatar ce balarabiya ce, so tun shekaru talatin da wani Abu baban shi da ya aure ta yaje karatu london, da ya dawo da ita family din shi Suka ki karbar shi karshe ta bar kasar fa! Tsoro nake ji kada Nima hakan ya faru a kaina!" Ta numfasa da karfi tace " Eh abun tunani kam hakan Bintu, you've a good foresight Kam. To tambayar anan Bayan mahaifin shi akwai Wanda Suka sake auren wani daga waje ko Kuma se Akan ki?" Nace " Yace wasu sun aura sede wasu sun rabu, very few suke tare!" Ta danyi shiru kafin tace " To kiyi addua kinji? Ki dage ki fadawa Allah ya zaba Miki mafi alkhairi. Duk hukuncin da Allah ya yanke ki karba a Haka. For now keep following your heart!" Sosae nayi Mata godiya, na Kuma ji dadin adduar da tace min nayi, Dan kuwa idan kun fahimci Abu a tattare da ni, I'm not much of a prayer type, nasan Ina addua Amma Nima a karon Kai na Ina Jin I'm not totally devoted, kilan shiyasa abubuwa suke cushe min. Daga ranar na Fara addua sosae, ko da Ina zaune, ko Ina cin abinci ko me nake Sai se nayi addua, wallahi se na Fara jin wani irin peace of mind, duk wannan tsoron da nake ji wallahi se ya ragu, se nake Jin Babu wani da ya Isa yayi min wani abun ba tare da Allah ya nufa ba, Dan Haka I cleared my mind nayi devoting ma soyayyar Akram sosae. Shi dinma baya bada wani space da har zanji tantama ko shakku a cikin zuciya ta. Wani dare na dawo daga school na gaji sosae da sosae, wanka nayi sannan na dakko abinci zanci, na bude drawer se naga tarin herbs, tea bags da nayi amfani da su Akan slimming, na tsaya a wajen Ina kallon su da mamakin Kai na, Wai nice da Kai na na daina shaye shayen nan da nake, yadda na Zama determined Akan shading weight di na ban taba tunanin akwai abin da zai hanani ba, Amma kalla abun mamaki Wai na daina Sha. Na tuna ko a nasihar Akram da yake yimin Bai taba ko da Wasa yace na daina Shan abin da nake sha ba, in fact shi kawai ya nuna min there are lots of healthy ways da mutum zaiyi maintaining jikin shi ba tare da ya Zama obese ba. Da Kai na na hango wannan hanyar Kuma na Fara amfani da ita. Lokaci kenan, tabbas komai Yana da lokacin shi, yanzun nawa yazo na accepting Kai na da Kai na. Nayi murmushi sannan na zauna Ina kallon kwanon nawa, vegetable yafi yawa a cikin kwanon, na zauna naci sannan na shanye oranges din da na bare, Mamaa ta shigo dakin da sallama tana kallo na, na gyara Zama Ina amsawa, bayan ta zauna tace " Bintu karatun ke sakawa kike rama ko Yaya ne?" Nayi saurin kallon Kai na a madubi, ban wani rame ba, bayan idanuna da suka fada kadan, Suma tunani nake hakan na da nasaba da gajiyar da nayi, malaman sun sako mu gaba da test da sauran su. "Ba komai!" Ta gyada Kai tace " Kizo kawun ku yana kiranki" Nace Mata to Zan zo Ina kuskure Baki na. Ta fita na Shiga toilet na kuskure bakin sannan na fito se ga Kiran Noor Yana shigowa, da murmushi na dauka na Kuma Kara kunne na nace " Tun dazun ka manta da ni!" Yace " Ni na Isa? I was busy ne kiyi hakuri!" Na Bata Rai Ina sulking nace " So har akwai abin da zai hanaka Kira na kenan! Shikenan" Yayi dariya Amma kafin yayi magana nace " Shikenan se anjima" Kafin ya Kai ga magana na Riga da na kashe wayar Baki daya, na tsaya kallon ta Ina murmushi sannan na Masa message Kawu na neman na. Bayan nan nayi plugging wayar a caji na tafi parlon shi. Suna zaune da Batuul, Mamaa da shi Kawu da Kuma Adda. Na zauna bayan na gaishe su, kawu yace " Na fada Masa gobe yazo kuje kuyi test a asibiti saboda Hadejia zaa daura auren ki Kuma jigawa dokar su se ka kawo result na HIV test" Ta gyada Kan ta, idanun ta duk sunyi jawur, Ina tunanin ya fada Mata wani abun da yayi Mata zafi, itama Adda ranta a bace yake Dana kalle ta. Bayan ya sallami Batuul ta tafi ya dubeni yace " Bintu! Wani yaro Akram ya same ni dazun a shago ya sanar min ya ganki Yana son ki, Kuma idan na bashi dama zai turo iyayen shi! Kinsan maganar ko ? Tunda yace Kun Fara magana da shi already ko?" Na gyada Kai na a hankali, dukka iyayen nawa Mata Suka zuba min idanun na mamaki, Adda tace " Shi ne Baki gaya Mana ba!" Kawu yace " Ki Bari na gama da ita tukunna!" "Kina son shi? Nayi bincike ko Kuma kada na bata lokaci na, saboda bazan Yi tolerating abin da kikai min akan Suleiman ba" Na Bata Rai Jin Wai har yanzun zancen Suleiman Bai kau ba. Ko kunya banji ba nace " Ina son shi!" Aikuwa Adda tace " Jimin fitsararriyar yarinya marar kunya. Da bakin ki Zaki ce kina son shi" Ga mamaki na se kawu yace " Asiya Ina ruwan ki? Se yaushe Bintu zatai Abu ta burge ki? Ki kyale ta Mana" Tayi shiru tana juyar da Kai, ita dai Mamaa ba tace komai ba, kawu yace na sani Babu canji yadda nace Ina son shi Haka magana zata Kai har karshe. Na amince da hakan na tafi, Ina zuwa daki na samu calls din shi da nayi missing, nayi dariya nasan yayi tunanin ko fushi nayi irin dinnan. Kiran shi nayi Yana dauka yace " Kin bani tsoro, nayi tunanin da gaske fushin Kika Yi!" Nayi murmushi nace " Banyi ba, Wasa nake maka. Ni bani da saurin fushi ai" Yace "Shiyasa nayi mamaki ai. So kunyi magana da kawun?" "Munyi! Ashe kaje ka same shi? Baka ji tsoro ba?" Yayi dariya yace "Da Abba Zan tura mishi ma, na dai je neman izini ne and soon su Abba zasu same shi. Ko yau da safe se da yace yaushe nake son aje ayimin tambaya. Ita Kam Ummaah har ta Fara siyayya!" Nayi dariya wa yaga zumudi, Nima jiya ta Kira Ni tana tambaya ta abin da nake so na lefe, I was so surprised irin wannan zumudi da Ummaah takeyi ai se kayi dariya. So washegari na tafi makaranta, Batuul tayi wanka tayi kwalliyya ta saka wata fitted gown ta atamfa, anyi fleeting kasan ta, dukka curves din ta da Kuma shape din ta sun bayyana. Tayi kyau Amma shigar Bai kamata ace an fita da ita ba. Wani siririn Chantilly veil ta yafa a saman daurin da tayi, ko kirjin ta Bai sauka ba, ta dauki Jakar ta ta rataya sannan ta dauki dalleliyar wayar ta ta rike a hannu. Tana cikin saka takalmin kawarta Nafi lamido ta kira, ta dauka suka danyi rudu yadda suka Saba sannan tace " Ke Batuul Ginsau nayi contracting Fatima garo akan sourvenirs din da zamu raba a biki!" Batuul tace " Kayan suna da kyau!" Ai tuni Nafi ta Fara fada Mata yadda kayan suke. "Kin gane Adudum ne wannan local basket na kaba, akwai kayan kamu a ciki, ki Kuma ki fada Mata content din da kike so se a saka Miki. Amma ga contact dinta Zan turo Miki da IG handle din ta ki duba" Batuul ta amsa da to sannan ta koma ta zauna daidai lokacin message din ya shigo _Fgees_collection_ _08067802846_ Tuni Batuul ta gyara Zama se taga ai har home decor take siyarwa, Jewelry, bedsheets da Kuma sourvenirs na biki. Kayan sun hadu babu karya, a take ta tura mata DM sannan ta fita Dan message din honorable ya Riga da ya shigo wayar ta akan ya karaso. Babu Wanda ya yiwa sallama a gidan ta wuce. Yana zaune a Bayan mota ya Sha kananan kaya, hannun shi rike da wayar shi Yana going through! Ta_kwalam 043 Bayan watanni biyu Ban dauka komai zai zo.da sauki ba kamar yadda yazo da sauki Haka. Na dauka dangin Shi da yake cewa ai Yan kauye ne tun da har yanzun sun ki karbar canjin zamani, su gani suke old norms din su da values shi ne komai. Idan ya fadi hakan na kance Masa ba Haka bane ba, suna kokarin preserving bloodline din su ne. Se yace ba wani nan kauyanci ne da racism da hauka. Ban sani ba ko dan sun ga abin da ya faru da mahaifiyar shi yasa Babu Wanda yaja da maganar kowa se yace Allah ya Sanya alkhairi, dama Kuma yadda Imam yayi Bai ma bada damar ko cikin Uncles din shi ko brothers ko cousins wani ya Fadi opinion din shi. Safiyya ta fada masa matsawar Yana son wanke laifin shi a wajen Akram to dole ya Kare Akram From critics dun family, ko Kuma wani yaga fuskar yace ya nema a cikin dangi, hakan yasa Imam yin tunani Kuma yaga tabbas Haka ne, dole ya tsayawa Dan shi tun da shi shekaru talatin da suka gabata Bai samu wannan goyon Bayan ba. Dukda Haka akwai Wanda basu iya rufe Baki ba se da suka samu Imam suka nuna Masa abin da yake Shirin aikatawa Bai kamata ba, wasu Kuma matan Safiyya suke fadawa akan yanzun duk Yara matan da suke da shi cikin wannan katon community din Amma har se yaje waje ya dakko wata. Safiyya se tayi murmushi tace, zabin shi ne Dan Haka dole mu bar shi yayi abin da yake so. To dai a Haka suka turo aka saka Rana Wanda watanni biyu kacal aka saka, zuwa lokacin na kammalla exams di ta ta session din. Wani lokacin haduwa da mutane yakan Zama kamar wani turning point ne a rayuwar ka. Shiyasa bana taba Dana Sanin haduwa da mutane, saboda Allah kadai yasan wanne Abu wannan mutumin ya shigo da shi cikin rayuwar ka. A bangaren mu, wato a gidan mu tamkar ba wani biki zaayi ba, Banga irin wannan a tafi kasuwa a dinga siyayya ba, da farko sun Fara da Mamaa da Adda Amma tun da akace biki na kawai zaayi se naga duk sunyi slacking, mamaki sosae nake na har yanzun sun kasa daina banbanci tsakanin mu. Ban ma damu ba saboda kunsan dai ina sanaa, Kuma kudin Babu abin da nake da shi, profit di na kawai aje su nake, Dan Haka a hankali nake siyan abin da Naga ya kamata Ina ajewa. Shigowa ta kenan daga last paper da Zan rubuta a wannan semester, Kuma exams din ta Noor ce. Tun dare ya tashe ni karfe biyu yace na dakko reading materials di na, Babu musu nace ya jira na wanke fuska ta na dawo, Haka na kunna bulb na zauna muka Fara karatu ni da shi, Bayan awa daya yace naje kitchen na hada tea saboda karatun da nayi, he's sure glucose di na ya Kone. Haka na tashi saboda shi mutum ne da baya son musu ko kadan, nima Kuma Ina kokarin ganin bana Masa musu. Na hado Ina sha har muka Kara 30 minutes, se yace mu Yi sallah da addua na mintina goma, Bayan min idar yace na kwanta Dan brain di na ta huta, nayi Masa sallama hade da godiya na kwanta, Babu jimawa bacci ya dauke ni. Se asuba ya tashe ni , nayi sallah Bayan na idar na Yi wanka, kamar kullum muna cin abinci muna waya saboda yace Bai yadda Dani ba Akan skipping meals. Bai sani ba ko kadan rage kiba, saboda abin da mutane suke fada ya daina damu na, Kuma wani Abu Dana fahimta yanzun mutane Basu fiya ce min kina da kiba, ke ki rage kiba. Wato dai it's all about accepting yourself, that's when mutane zasuyi accepting din ka. Idan na zauna nayi tunanin rayuwar da nayi ta baya, se naji har kunya nake ji, idan Kuma na kalli Kai na se Naga to wai Ina kibar take da na damu Kai na akan ta, idan na duba se Naga ai akwai Wanda suka fini kiba sosae da sosae Amma suna rayuwar su cikin farin ciki Babu tsangwamar Babu Kuma takurawa Kai. Shiyasa nake fada muku kullum kusan irin maganar da zaku fadawa mutane, Baku San irin battle din da mutane suke ciki ba internally, kowa da ka gan shi bashi yaso ya Zama me kiba ba, ko siriri ko mummuna ba, se me idan Yana da kiba rayuwar ku ce? Ko Kuma jikin ku ne, kunsan how much critics din ku ke halaka mutane? Ina fatan Bayan karanta labari na, ba ruwanku da tanka jikin mutane. That's by the way! Na shirya cikin Abaya olive, anyi Mata embroidery da bakin zare, na saka sannan na saka bakar hula, na dakko daya daga cikin turaren SCENTMANIA na murtsika a hannu na na shafe jiki na da shi sannan na yafa veil din, na kalla Kai na a mirror dakin mu Naga yadda nayi kyau, jiki na Bai dame ba Kuma nayi kyau. Zama na da Akram ya nuna min akwai gayu da zakai kayi kyau ba tare da kayi exposing jikin ka ba, shi yayi ta siya min Abaya sannan ya dinga encouraging di na na saka Naga yadda zanyi, ranar farko da na saka kunya nayi ta ji, shi Kuma yayi ta min dariya Yana cemin Wai no Yar kauye ce, a hankali Kuma na fahimci Yana son mace da Abaya se na dage har ya Zama jiki na, na daina Jin komai idan na saka. Jaka ta na dauka na fice zuwa dakin Adda, Bata nan hakan ya tabbatar min suna tare da Mamaa ko da Kawu, aikuwa dukka suna tare a parlon Mamaa, na gaishe su sannan na mike, Mamaa tace " Yau shi ne ranar karshe ko?" Na gyada Kai Ina gyara zaman veil di na nace " Eh" Dukka Suka hada Baki wajen yimin adduar nasara, naji Dadi sannan na tafi Abu na. Banyi expecting ganin shi a exam Hall din ba Amma ana farawa se gashi ya shigo shi da Dean, yayi kyau cikin kaftan maroon da ta kawata yanayin shi, Dake na saka mask a fuska ta hakan ya bani damar kallon shi da kyau, shima kallo na yake lovingly, nayi murmushi na cigaba da rubutu na. Ban sake dagowa ba se da naji kamshin turaren addictive ambergris na wajen SCENTMANIA tawa, birthday gift na bashi lokacin da ya cika shekara talatin da biyu, da yayi amfani da shi ranar yini yayi Yana Koda turaren nata, fada min yake it's the best gift da aka taba bashi a matsayin birthday gift. Ina dagowa idanun mu Suka Shiga na juna, na sauke ajiyar zuciya Ina Dan murmushi softly, yayinda ya danyi min wink da yasa naji wasu butterflies a ciki na. Kai na na mayar akan abin da nake rubutawa, shikuma se ya cigaba da karanta abin da na rubuta. " Dr. Akram zaka zauna na tafi?" Mukaji muryar Dean, hakan yasa ya girgiza Kai sannan ya Fara kokarin janye idanun shi daga Kai na yace " Idan kin fito, call me I want to drop you home!" Daga Haka ya fita Nima Babu jimawa na kammalla nayi submitting Muka fito tare da Sadiq, ya tambaye ni exams nace Masa alhamdulillah Dan kuwa Allah shi ne abin godiya. Yace " Ina Jin ki?" Na dube shi da rashin fahimta nace " Menene fa?" Ya bude backpack din shi ya Ciro wata envelope me kyau ta IV yace " Sir Akram gave me! Ashe aure zakuyi Amma shi ne Baki fada min ba. Akwai aminci kuwa?" Nayi dariya cikeda Jin kunya nace " Kayi hakuri, nayi tunanin Alamin ya fada maka, saboda na fada Masa shi!" Yayi murmushi yace " Alhamdulillah! I'm happy for you! Allah ya sanyar muku da alkhairi, farin cikin ki shi ne namu!" Nayi murmushi Ina Masa godiya, waya ta ta Fara Ringing se na tuna ban Kira shi ba, cikin sauri na dauka nace " Yanzun Zan Kira ka fa!" Yace "Shiyasa Naga kina tsaye da Sadiq Kuna dariya!" Nayi saurin juyawa Ina waiwayen Ina Zan gan shi, Sadiq da ya fahimci aabin da yake faruwa ya nuna min motar tashi, nayi saurin kashe wayar na ma Sadiq sallama tun da hutun session zamu tafi Kuma kowa yasan irin dadewar da ake. Tun da na shiga yake cona Baki Wai shi yayi fushi, nayi murmushi Ina connecting wayata da Bluetooth din motar shi ba tare da na kula shi ba, se Dan Kan shi yace " Fushi nake fa! Baki gani ba?" "Na gani Mana!" Na fada Ina murmushi, shima se ya Fara murmushin yace " Ba Zaki kula ki ba Kuma? Ko lallashi babu?" Na Kara fadada murmushin fuskata Wanda in dai Muna tare fuskata Bata dauke wa da smiles, har mamakin Kai na nake, am I that grumpy Bintu kuwa ko dai wata ce daban. But this is all in the past, Kuma all credit goes to Noor di na! "Noor!" Na fada softly, ya Dan kalle ni sannan yace " Naam Noor!" Shima Noor din yake cemin, nace " Kasan duk mazan duniya Kai kadai nake so ko?" Ya gyada Kai da sauri, nace " Kuma Kai kadai na zaba ko?" Nan ma yayi saurin gyada Kan shi, nace " So, Ina son na Kara tabbatar maka no matter what I'll choose you over all the Men in the world! Kaji Noor di na?" Ya saki ajiyar zuciya, kayataccen murmushi a fuskar shi yace " Thank you Noor! Na Miki alkawarin farin ciki na har abada! See" Se na kalle shi anan yake fada min, shi fa ba zai zauna a community din su ba, na tambayi dalilin se yace kawai saboda Yana son privacy, Kuma Bai son wani ya takura min, Yana son nayi rayuwa me yanci kamar kowacce matar aure! Noor di na bashi da na biyu, you can argue with your keyboard...lol. Asibiti mukaje mukai gwajin da ya kamata sannan ya kaini gida, a gajiye matuka na shiga, se Dana fadawa Adda dawowa ta sannan na Kuma Bata result din mu ni da shi kafin na leka wajen Mamaa, da ta baje kayan kitchen, Ina shiga tace nazo na zaba, na girgiza Kai nace " Kawai ki zabar min duk abin da Kika ga ya dace!" Bansan me yasa ba har yanzun wasu abubuwan.basu bar zuciya ta ba, dukda lokaci ya Dan tafi Amma har yanzun bana iya zaben Abu in dai a gida na, gani nake why should I choose. Daki na wuce dukda tace min gida na ne fa, nazo na gani, Ni dai na tabbatar Mata Babu damuwa. Ashe bayan na fita Yaya Fadima ta Kira su tace musu gwara su fitar da kudi Dan kuwa ga irin gidan da Zan shiga, se kawu yace ma Adda ta fito da kayan Batuul da yayi ta bata kudi dama ai shiyasa har yanzun Bai bada kudin siyayya ba saboda he believes kayan da aka siyawa Batuul sun Isa kitchen di na. Da farko tace ai da sunan Batuul aka siya Dan Haka se de a siya wasu. Adda nada abun mamaki, kowa se yayi mamakin da gaske ita ta haife ni kuwa? Wannan raayin ta ne. Wuta Kawu ya bude Mata yace ya ishe shi banbancin da take nunawa, da waya ce ta kawo kayan? Yanzun dole ta kawo kayan tunda Ni kadai zaa yuwa biki! Ina Shiga daki na samu Batuul a kwance tayi ruf da ciki, dake ta Saba kwamciya a Haka so se nayi tunanin ko bacci take, nayi sallama sannan na rage kayan jiki na, na zauna Ina tattare books di na waje daya, Ina hakan se Naga ta juyo da fuskar ta kamar nunnanen tumatur, fuskar tayi jawur kada idon ta da hancin ta suji labari. Nace " Batuul are you ok? Me ya same ki?" Tun watanni biyu da Suka wuce, tun da aka fasa auren ta gaba daya ta Zama wata iri, Bata Shiga mutane Bata fita, makaranta ma daina zuwa tayi Kuma kamar Babu Wanda ya damu a gidan, Dan kawu cewa yayi gwara tayi zaman ta kawai yafi sauki da ta dakko musu magana. " Ke ma kin daina so na ko Bintu, Baki taba tambayar abin da yake damuna ba. Duk Kun tsanenu ko?" Nayi saurin komawa kusa da ita nace " Haba dai Batuul! Kiyi hakuri Naga idan na tamabye ki kuka kike shiyasa na barki tace!" Tana kukan ma sannan tace " Bintu kinji dadi, rayuwar ki gwanin shaawa! Har burge ni kike Yi, you lead a silent life Amma a karshe kinyi achieving Abu. Ki yafe min" Na danyi murmushi nace " Ke ma kinyi achieving wasu abubuwan ai. Dan an fasa auren ki ai wasu na zuwa, Kuma life always offers a second chance!" Ta danyi tsaki tace " Bintu I've messed up! Kinga Honorable Allah kadai zai saka min abubuwan da yayi min! Allah ya Isa tsakani na dashi!" Bari muji me ya faru da Batuul tukunna! Bayan fitar Batuul da shigar ta motar Honorable, straight wani first class hotel Suka tafi, yadda Batuul take lokacin da suka Shiga ta underground kawai zai tabbatar maka wannan ba Karo na farko bane ba, ba Kuma na biyu ba balle na uku. Suna shiga Presidential suite din shi ta Fara bashi abin da ya kawo su. Ba wani Ina nufin just a common smooch ba, a'a Ina nufin having an affair shi ne abin da Suka Yi. Shi baiji kunyar kawo yarinya wadda autar shi ta girme ta ba, ita Bata ji kunyar stripping kayanta gaban wanna tsohon dattijon ba, Bata Kuma ji komai na cin amanar iyayen ta da tayi ba. Ita dai Abu daya ne a zuciyar ta, she can go to any length ta samu kudi sannan ta aure shi. Barin ta yayi tana bacci ya nufi asibitin da ya kamata suje test, se da ya tabbatar babu me Gane fuskar shi saboda yadda yayi disguising Kan shi. Ciki ya shiga, ya samu daya daga cikin clinicians din yace Yana son Sanin status din shi, Babu jimawa kuwa aka dakko kayan test a cikin Lab din dake jikin building din, anayi se ga HIV nan positive Rado Rado! Bayan an Shiga counselling ya fadawa clinician din shi yasan status din shi Kuma Yana Kan magani, Amma akwai yarinyar da yake son ya aura to Yana son kawo ta suyi test tunda Yan gidan su sun matsa, Amma Yana son a boye status din shi su Zama dukkan su negative. Clinician din se kallon shi yake with a plain face wadda take emotionless, ba lallai ka fahimci abin da yake tuanani ba. Kafin yayi wani Abu har honorable ya fito da bandit din N1000 notes bandir biyu, 200k kenan a matsayin toshiyar Baki! Ina fatan na wanke laifi na! Thank you guys for the call, wasu da yawa sun dauka bani da lafiya, not at all abubuwa ne beyond my control. Thank you for hanging around 😊 Ta_kwalam ce 044 Bayan Nan ya koma yaje ya dakko Batuul da ta kammalla shiryawa shi take jira. Suna tafe suna Hira gwanin shaawa, Kai kace gaske ne. Har Suka Isa asibitin Batuul bata kawo komai ba, saboda duk wayon ta mutum ce me yadda da mutane, shiyasa ni da ita muka banbanta. Bayan sunje gaban clinician dinnan, kamar yadda tsaurin yake kafin a dauka jinin ka zaa Yi maka bayanin gwajin da zaayi maka, ruwanka ne ka amince ko lace a'a, to Batuul ta amince Bayan an Gama pre test counselling, a tare aka dauki jinin su tamkar Babu abin da ya faru tsakanin clinician din da Kuma Honorable, kowa a cikin su ya basar tamkar haduwar su ce ta farko. Suna ta Dan Hira har se gashi result ya fito na su dukka biyun, as expected Honorable positive ita Kuma Batuul luckily for her nata negative. Ya dubi result din sannan ya dubesu ganin dukkan su sun bashi hankalin su. Yace " Fatima Batuul na Fadi result din ki yaji?" A take taji gaban ta yayi wani mugun faduwa ta dubi Honorable da yake ma clinician wani irin kallo, tace " Akwai matsala ne?" Ya girgiza Kan shi ganin yadda har idanun ta sun Fara Tara ruwa alamar zatayi kuka, se Kuma ya dubi Honorable yace "Honorable na fada Mata result din ka?" A take ya Bata Rai yayi kicin kicin da fuska Yana muzurai yace "Fada mata!" A wannan lokacin Batuul was confused, musamman da clinician ya bude drawer ya Ciro wannan wrapper kudin ya aje gaban Honorable Wanda yake kallon shi da wani irin yanayi yace " I'm sorry sir! Ba Zan iya boye mata ba, abinda yasa na amince saboda nasan ko na ki zaka kaita wani wajen kilan ka samu masu son zuciya su karba" Ya juyo Kai na yayinda ya bar Honorable cikin wasiwasin ya tashi ko Kuma ya tsaya ya gama ganin karshen iskancin yaron nan "Batuul gwajin ya nuna Baki da matsala, Amma shi nashi akwai matsala!" Idanun Batuul kamar zasu Fado a kasa, tun da akace akwai matsala ai Yana nufin he's HIV positive, tamkar an kwara mata ruwa Haka tayi tsumu tsumu. Yayinda Honorable ya dauki kudin shi ran shi a bace ya fice. Batuul Kam tana nan zaune tayi shiru Dan ta Riga ta fahimci boyewar da yayi mata, ta fahimci ha'intar ta yaso yayi ya rufe Mata. Clinician din yace " Ki tafi Baki da matsala!" Se ta Mike ta dauki Jakar ta tana Jin wani irin yanayi na rashin kuzari da karfi tace " Nagode! Nagode sosae!! Nagode Allah ya saka maka da mafificin alkhairi. Nagode sosae. Allah ya biyaka. Nagode!" Mutumin yayi murmushi sannan yace ta zauna kafin ta zauna ya fara fadin " Muna samun irin wannan cases din kala kala Amma shiyasa ake bamu kudi, kada kudin irin wannan mutumin su dauke Mana hankali. Kaddara na bari kin aure shi, se Kuma ya mutu, bayan nan kije ki auri kilan me Mata uku ki Kara yadawa, Kinga banyi Miki adalci ba ko kadan" Ta saki ajiyar zuciya tana sake Masa godiya, har ta tashi zata tafi bayan exchanging numbers da sukai se ta dawo ta tambaye shi hanyoyin da ake dauka, anan ya fada Mata hanyoyi uku da ake dauka, tun da taji sexual intercourse se ta Fara kuka tana fadin " Aikin Gama ya Gama! Na Shiga uku" Wata sabuwa inji Yan caca, nan fa clinician yayi Mata nasiha sosae sannan ya dakko magani ya Bata yace ta dinga Sha kullum Bayan watanni uku ta dawo a sake gwaji in dai babu to ya tabbatar babun da gaske! Haka ta dakko ta taho gida kamar mahaukaciya saboda yadda take a gigice. Tana shigowa ta tarar da Kuma labarin ya Kira kawu yace ya fasa auren ta ya janye, wannan Bai ma dame ta ba saboda komai yace ya bari shi dai asirin shi ya rufu kawai. Amma har zuciyar shi yaso auren Batuul, yaso ya aure ta saboda Yana son ta kuskure daya na rashin hakuri da yayi har ya lalata ta. Dukka gidan wato su Mamaa suka ta tambayar ta ko wani abun ya hadasu Amma ta kasa magana se kuka kawai da suke, shi Kawu tun anan yayi sensing rashin gaskiyar ta Dan haka ya tattara ya kyale. Duk yadda kowa yaso yaji abin da ya faru Batuul Taki magana ta kulle bakin ta. To me zata ce? Itama abin zai dawo kanta, tun daga wannan kuwa ta nutsu ta daina yawo se zaman daki ko dakin Adda, ko gidan sisters din mu ta daina zuwa. Adda ba karamin damuwa tayi ba saboda yadda ta Riga ta saka buri akan wannan bikin, da auren ma Baki daya. Shiyasa idan Suka kebe da Batuul se tace Mata ta Kira honorable ta bashi hakuri Amma ita tsoron ta cikar wannan watanni ukun! Dabas Haka na zauna bayan ta gama kora min bayani, jiki na kamar an watsa min kankara Haka naji, na kasa cewa komai se kallon ta kawai nake, se kuka take, no wonder kullum Batuul na daki, Batuul har sallar tsakar dare take, magana ma ba sosae take Yi ba, wayar ta ma ba sosae zaka ganta a hannun ta ba, gaba daya tayi la'asar ta nutsu ta Shiga taitayin ta. Nace " Sannu Batuul! Allah ma Yana son ki shiyasa ya dawo Dake Kan tafarkin daidai. Kiyi kokari kiyi amfani da wannan damar ki tuba, tuba na gaskiya, Ina me tabbatar Miki Allah zai amsa, Allah Yana son bawa me tuba!" Hawaye ya sake gangaro Mata tace " Ina Yi Batuul, shi ne abin da yasa har yanzun banyi loosing sanity di na ba. Kuma Ina jin sauki cikin zuciya ta. Amma Batuul idan na kamu da HIV fa?" Na rike hannun ta dukda Nima a kasan zuciya ta tsoron nake ji, Amma ya zanyi dole nayi concealing nawa na Bata shawara " In shaaa Allah Babu abin da zai faru, ki cigaba da addua, Allah ba zai tona Miki asiri ba" Mun Jima tare da ita, har se da ta daina kuka sannan na zuba Mana abinci muka ci, gaba daya shekarun mu ashirin ne fa, Amma kalla yadda Batuul ta lalace Wanda Ni dai kullum laifin iyayen mu ne. Kuma na yadda da abin da tace wallahi wani lokacin kyau Yana daya daga cikin musiba da kuma trial na rayuwa, saboda Wanda suke da kyau gani suke wata alfarma ce daban Allah yayi musu, suna amfani da wannan kyawun suna yin abin da bai dace ba, ban ce kowa ba amma ku tuna yadda Batuul tayi, wani lokacin masu kyau har wani girman Kai suke ji, na menene? Da zasu dinga criticizing wanda basu Kai su ba. A hankali na shiga sabga na Fara shirin biki, gashi bani da kawa ko daya, ko cikin cousins dina ba wata kwaya daya da zaka ga Wai I'm very close da ita, Dan Haka komai da Kai na kawai nake, se Kuma abun mamaki Batuul ta ware kusan komai da ta hada na bikin ta ta fito da shi ta bani, tun daga Kan make-up, Mai kunshi da Kuma gyaran jiki dukka ta barmin. Da farko naki yadda se ta nuna min sede idan fushi nake na abubuwan da tayi min, se Adda da ta sakko itama tace " Ba refunding zasui ba, gwara ayi amfani da shi kada ya Zama waste" Se na shawarci Noor se yace min Babu damuwa na karba kada suga kamar fushi nayi, Haka na amince daga nan kuwa kowa ya zage damtse aka Fara Shirin biki. Sati daya ya rage biki Akram yazo ya samu Kawu akan Yana son zai tafi dani Qatar har ma yayi applying Mana visa. Kawu yayi murmushi yace " Banda abin ka Akram idan ka aura Bintu ai ta Zama karkashin ikon ka, so ni Dana baka auren ta, bani da matsala da duk inda zaka kaita. Allah ya Baku zaman lafiya me daurewa!" Akram yayi godiya sannan ya shiga ya gaida Adda da Mamaa da Kuma siblings di na wanda se lokacin Suka fara ganin shi ma. Bayan ya tafi Suka ji labarin tafiya ta Qatar, kowa Baki da magana Amma anyi kum, to dama Haka Allah yake abin shi, Ina Suka taba tunanin cewar Zan yi aure kwana kusa, I still remembered irin maganganun da suka fada da naki yadda da maganar Suleiman, har cewa sukai Ina tunanin Zan samu anything better than him? To se gashi na samu Wanda yafi shi komai da komai. Da na dawo da yamma ni da Batuul da take kaini ta jira ni a Gama gyaran jiki naji labarin zuwan shi, Dan Ni Bai fada min yazo ba. Kuma Babu kunya se gasu suna fadin wai nayi dace miji na kyakyawa gashi me kudi. Kinji wani Abu Kuma, I hate it when people capitalize over money! Kafin wani lokacin ko nace kafin mu ankare se gashi biki har yazo, imagine the simplest wedding ever to shi nayi. Kamu ma Ina zaune a parlor akai min, Babu kawa ko daya se Batuul da cousins di na. Washegari juma'a aka daura Mana aure ni da Akram. Wata super atamfa na saka red da brown tayi min kyau sosae da sosae, sannan Mamaa ta daura min lafaya me ado irin na atamfar jiki na. Nayi kyau ga kamshin turaren nan na SCENTMANIA duniyar kamshi, ko a lefe na shi Akram ya saka min. Har kyaututtuka ta bamu ni dashi na appreciation. Da ya shigo Bayan an daura aure muka danyi pictures, shima ba wasu abokai ke gare shi ba se tarin Yan uwa. Zuwa yamma aka kaini family community din su, ba Wai da son ran shi aka kaini ba, so yayi kawai a wuce da ni gida Amma se Safiyya ta nuna Masa yayi hakuri ayi wannan formalities din idan ba Haka ba kuwa zai barta da surutun mutane. Hakan yasa ya amince se gashi ya Kira Ni, na Gama canja kaya kenan an lullube ni ana yimin turare, Batuul ta miko min wayar tana fada min "Noor din ki ya Kira!" I've to smile fa, saboda farin cikin da nake shiga, Ina Kuma adduar Allahu yasa wannan farin cikin, soyayyar mu ta daure har abada! Na karba bayan nayi sliding nace "Noor!" Maimakon ya Kira Ni da Noor se yace " Wife! Ya kike?" Nayi murmushi nace " I'm fine!" "Zaa kawo ki gida, I mean community din mu. Ban so ba Amma Ummaah tace wai formalities ne. I'm sorry!" Nayi murmushi nace " Ba komai Noor, ba damuwa" Yace " Kinsan dai I chose you over many ladies ko a family din mu ko? So nasan idan kikaje people will talk. Dan Allah wife kada ya Dame ki, ki sani I love you and you only no compromise." Nima tun da aka fada min can zaa Kai Ni jiki na yayi sanyi, Amma Kuma wannan maganar se yasa zuciya ta tayi sanyi, nace " I promise you!" Ile kuwa, ko da mukaje, nasan na shiga gidan yawa, saboda ko ta Ina mutane ne, gidaje sosae da sosae masu kyau. Dukda Kai na a sunkuye yake Amma Ina iya ganin inda muke wucewa. Se da na canja Kaya sannan aka kaini wajen da zaayi budar Kai. Bayan an yaye min lullubin fuskata ta bayyana, se naji duk na takura, Batuul tazo ta tsaya kusa da ni, akai pictures da sauran su sannan aka Fara kokarin tashi. Lokacin da na mike Zan tafi wasu yanmata dake gefen can suna dariya tace " Ikon Allah ! Su Hamma Akram Kuma duk yadda aka tsallake mu akan wannan ya kare!" Dayar tayi dariya tace " Kede bari, wannan ai se ta goya shi!" Naji komai da suke fada, Batuul ta juya nayi saurin rike hannun ta, a hankali nace " Dan Allah kada kice komai, wannan opinion din su ne Kuma kowa is entitled to his own opinion. Karki kula su" Ba Wai ban ji haushi ba, naji wani irin rashin karfin gwiwa kamar zai shige ni, da na tuna abin da Noor ya fada min se naji zuciya ta tayi sanyi, naji kwarin gwiwa ya Kama ni! Ta_kwalam ce Finale A hankali wayar ta shi ya Fara Kara, yayi saurin barin tarin mutanen da yake ciki Yana sakin murmushi, he has been anticipating for her call da jimawa, Amma yau yasan account din sa se sunyi kukan farin ciki, Dan shi tuni yasan yau labarin da zai bayar zai dada Mata zuciya! Bayan sun gaisa kamar yadda suka Saba yace " Akwai labari me dadi. Yau Akram yayi aure" Cikin wani irin excitement zainab tace " Ma shaaa Allah! Alhamdulillah!! A family din su yayi aure?" "A'a fa, shima kamar mahaifin shi wata ya auro daban a wani family!" Tayi murmushi tana Jin kamar tayi tsuntsuwa tazo ta gan shi, hakika tayi kokari, ba kadan ba tayi namijin kokari wajen kauda idanun ta akan Dan ta na tsawon wannan shekarun, dukda bege da zuciya takeyi na son kasancewar da shi Amma ta Bari yazo ya neme ta da Kan shi. " Ma'am! Yanzun Haka Yana kokarin zuwa Qatar shi da amaryar ta shi Dan su neme ki, should I divert their attention away ko na bar su..." Cikin sauri ta katse Shi da fadin " Don't do that, allow them to meet me! Zan tura maka mail di na da zarar sun shirya tahowa please notify me!" Daga Haka sukai sallama da shi ta kashe wayar, kujerar da take zaune irin ta executives dinnan ce, to ita din ma ai executive ce a wannan company, tunda kuwa ita ce chairwoman ta company. Tana nan a yadda kuka santa kyakyawar nan ta gaske, se alamar ta Dan manyanta da Kuma Kuma kwanciyar hankali da ya sake bayyana a jikin ta da fuskar ta. Dukda har yau zuciyar ta me naci tana son Imam wani lokacin ta kanji Bata Dana Sanin tarayyar ta da shi, yayin da wani lokacin ta Kan ji if she will start all over, she wouldn't have chosen him! To Amma Kuma ai a tarayyar ta da shi Imam ya sota da dukkan ruhi, zuciya, Rai, gangar jiki da komai. Sede duk abinda ya faru ta kasance ita din me Yi Masa uzuri ce, Abu daya ta gagara mantawa shi ne Dan ta da ya dauke Bayan ya yaudare ta, har wannan lokacin idan ta tuna se zuciyar t tayi kamar zata fito Amma dai ya wanke laifin shi da irin rayuwar da ya bawa Akram, tana da labarin komai na Akram Kuma she's forever grateful to Imam! *** Se dare sannan aka Mika ni daki na, ko nace gida na, gidan aure na. Yawancin mutane kafin muzo sukaje suka ga daki kamar yadda yake a al'ada. Siblings di na sukai wa gidan final touch kafin sukai min sallama har da Batuul Wanda wannan Dan satittikan da mukai tare da ita wani kyakyawan bond me karfi ya kara shuga tsakanin mu. Zasu tafi kowa yayi min Dan nasihar shi sannan suka tafi Suka barni ni daya zuru cikin wata sabuwar rayuwa. Amma dai ko kuka banyi ba, hasalima farin ciki nake Zan bude sabon babi cikin kundin rayuwa ta, tare da Wanda ya bani karfin gwiwa na Zama abin da nake a yau dinnan. Ban Jima ba se gashi ya shigo, shi kadai ba tare da rakiyar kowa ba, wannan Hadi namu ko zamu din ga samun mutane ma kuwa? Na ayyana cikin zuciyata. Bayan ya karaso tare da ruko hannu na cikin na shi bayan ya zauna gefe na, not minding kujerar ma tayi Mana matsi, shi dai abin da ya Dame shi ya samu wannan closeness din Dani. Shiru dukkan mu min kasa furtawa juna komai Amma zukatan mu Allah kadai yasan me ke wanzuwa a cikin su. Se can ya dubeni cikin saa Nima na karkata kaina Zan kalle shi yace " Muje muyi sallah!" Tare Muka tafi daki nayi alwala bayan na fito ya Shiga yayi sannan ya jamu sallah, Bayan min idar yayi Mana addua doguwa ganin na Dan Fara hamma yace muci abinci, kowa na shi daban Haka mukaci. Sannan ya zauna saman gado yace " I need to work out, saboda na samu abincin ya zagaye jiki na. Shirya ki kwanta nasan kin gaji!" Babu musu na shirya sannan na kwanta ya lulluba min duvet ya daidaita sanyin dakin kafin yayi pecking di na a goshi ya fita, nayi murmushi Ina saka hannu na a wajen da yayi min peck din, a Haka dai baccin gajiya me nauyin gaske yayi gaba da Ni. Bayan wajen awa biyu se gshi ya shigo ya saka wasu lallausan pyjamas, ya Jima a Kai na Yana kallon fuskata da yadda nake bacci hanklai a kwance se yaji ba zai iya tashi na ba, karshen gadon yaje ya kwanta Babu jimawa bacci ya dauke shi. Bamu farka ba se asuba mukai sallah sannan na hada Masa oats na kawo Masa, ya amsa sannan ya koma ya dakko wani spoon din muka Sha tare, daga haka muka gaisa yace " Muje mu huta ko Noor!" Muka wuce zuwa daki, Muka kwanta duk da naso na Fara gyara gidan Amma banyi hakan ba, na bishi na kwanta, a wannan kwanciyar ne we became so intimate har akai deflowering di na, pains ne da bana son na tuna, ba Kuma Zan iya bada labarin yadda naji ba. Dan Haka baccin wahala ne ya tafi dani na barshi shi.kadai Yana caressing gashin Kai na. A washegari da daddare muka je community din su, bayan munyi sallar maghrib muka je, kafin muje gida Ummaah tace mu bibbiya inda tayi Masa lissafi Kuma kada ya tsallake ko daya a ciki, Dan ta San halin shi. God suna da yawa Haka muka ta yawo Allah yasa saukakken Kaya na saka da Kuma takalmi da bansan irin gajiyar da zanyi ba. Yawancin Yan matan ke mun kallon banza Ni kuwa ban bi ta kansu ba se da Muka Isa wajen Ummaah kafin na saki ajiyar zuciya, ta zauna Bayan min gaisa tace " Kin gaji ko?" Nayi murmushi kawai, ta cigaba da Jana da Hira har na warware mukai Dan Yi Hira da Abban ya dawo suka hadu sukai mana nasiha me ratsa jiki, kafin ta nuna min yadda Zan dinga calculating calories din dake cikin each meal da zanyiwa Akram, ta bani tips da Kuma abubuwa da dama da zasu taimaka min wajen kula da lafiyar shi. A karshe sukai tayi min godiya har naji kunya. Washegari Muka je gidan mu, Suma Suka tarbe mu da kyau bamu Jima ba muka tafi yayi ta yawo Dani Dan naji dadi, a cewar shi zaman will be boring idan bama fita. Daga Haka se Muka maida hankali Kuma akan junan mu, yadda zaman mu yake tafiya kwanciyar hankali ce kawai da farin ciki a ciki, shiyasa duk lokacin da naji ance aure ya mutu within first month se na kasa fahimtar what actually went wrong? Like nasan har lokacin kowa Bai Gama fitowa da true colors din shi ba, har lokacin zaman dauki ake kowa Bai Saba da kowa ba. That's by the way! Bayan wata daya sannan visa din mu ta fito, mukai sallama da kowa se Qatar. Muna jirgi ne nake tambayar shi ko yasan inda Maman take? Se yace shima dai kawai Zai duba company mahaifin ta yasan zasu San inda take ko da mutum daya ne. A Haka Muka Isa kasar. Se da mukai kwana biyu Wai muna hutawa, Wanda Ni dai ba wani hutu Banda Tsabar soyayya da yake nuna min, wani lokacin na Kan ga rayuwa ta kamar mafarki komai yake faruwa, ku tuna irin kuncin da na kwasa a ryuwar ta, ku tuna how much criticism akai min a rayuwa ta Amma Wai ya wuce shiyasa nake adduar wannan labarin nawa yasa ya Zama solace to mutane iri na, Ina fatan zamu samu sauki cikin zukatan mu, za Kuma mu karba rayuwar mu yadda tazo Mana ba tare da mun kushe Kan mu kamar yadda mutane suke Mana ba! A kwana na uku shi ne mukaje company, Amma tun daga waje aka Hana mu Shiga saboda mu ba ma'aikata bane ba, gashi daga ni har shi Babu mai Jin larabci balle muyi ma securities din bayanin abin da ya kawo mu, shi Kuma ba turanci yake ji ba. Kunga akwai language barrier kenan! Noor yace min mu tafi Amma naki instead se nayi downloading translator, na fada Mata da turanci se ta fassara Masa da yaren da yake ganewa, karshe yace shi ba zamu ga chairwoman ba se Muna da appointment, sannan Kuma ba zaiyi disclosing address din ta ba. Karshe dai Haka Muka tafi duk jikin shi yayi sanyi, dukda kokarin rufe hakan da yake. Ko da mukai waya da Ummaan Haka na fada Mata se tace washegari muje da wurwuri tasan zainab is always punctual. Shi kin zuwa ma yayi ni ce na shirya cikin fuschia pink din abaya, na yane Kai na da veil din ta sannan na tafi, shi Kam shi security din se da ya jadadda naci na. Ina nan tsaye se gashi wata dalleliyar mota ta kawo kai, kamar ance ta tsaya se ta tsaya wajen security tana tambayar me nake a tsaye se da ya dubeni kafin ya Fara Yi Mata bayanin tun jiya muke nemanta , aikuwa.ta Fara Masa fada sannan ta fito cikin sauri ta nufo ni, tunda ta taho na gaskata miracle din Allah, sure baya Kama da ita Akram ko kadan but I can see him in her! " Kece BINTUN Akram?" Na gyada Kai na se ta rungume ni ta Fara tamabayr Akram nace Mata na barshi a suite din mu, ai tuni ta bude mota ta shiga bayan na shuga muka dauki hanya, Yana zaune Muka same shi, yayi Dana Sanin Bari na na tafi Ni daya yafi a irga se kawai yaji swiping card, aikuwa ya mike se gani ga Ummiey. Allah suka se da suka bani tausayi musamman ita, yadda take Masa ta rungume shi, ta shafa fuskan shi tana kuka tana fadin " My baby is all grown up!" Lallai akwai zalinci a raba uwa da danta. A wannan ranar muka bita gida, ban manta na Kira Ummaah na fada Mata ba. Aikuwa tayi ta murna. Sati na zagayowa se gata da Abba, mukai ta rokonta Dan sosae Muka Saba, musamman Dani da nake Jin ta kamar uwar da ta haife ni Akan Dan Allah ta komawa auren Abba Amma se ta kalle ni da Ummaah tayi ta dariya tace ai wannan ya wuce ba dai ita zainab din ba. Watan mu biyu Ni da shi sannan mukai Mata sallama Muka bar kasar , with the hope zata canja raayin ta ta komawa Abba, Amma dai nasan yaudarar Kan mu muke saboda she's so adamant Akan ta Gama wannan auren. Bayan min koma Adda da Mamaa suka.zo min, naji Dadi dukda Basu Jima ba suka bar Batuul da ta tabbatar min Bata da matsala anyi test har sau uku, wannan labarin ba karamin dadi ya yiwa kunnuwa na ba, na Bata shawarwari ta wuce se Kuma na Fara laulayi Wanda yasa ni wata irin Rama. Ranar dai da nake nema se a karshe tazo, Kuma se Naga nayi Muni, Naga duk banyi kyau ba musamman idan nasa Kaya Naga yayi min wani iri se naji Babu dadi. Tohm wannan shi ne labarin BINTUN BATUUL! Nasan akwai korafin nayi saurin rufe labarin, kowa yyai hakuri. Nagode sosae da sosae da dukkan mabiya na Wanda Basu gajiyawa ko kadan wajen gingering dina da nuna min rubuta na na da muhimmanci, nagode sosae da sosae Ina muku fatan alkhairi and hugs to each and everyone of you! Kada ku manta Dan Allah a dinga yimin addua, just pray for me. Ina fata Allah yasa na Kara samun damar yin wani rubutun nan gaba! Thank you so much lovelies. Allah ya bar zumunci. Ta_kwalam ce