[20/9/2022, 12:32 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE* 💕 ( 'Yata ce) *By* *Salmerh MD* 🅿️....1 .........Duban farko idan kai mata zaka fahimci cewa matashiya ce mai karancin shekaru kasa da ashirin, sanye take da zanin atampan wanda daurin ya tsaya mata saman siraran kafafuwan ta sai hijab din ta na roba mai zanen blue da fari wanda shima dududu bai wuce tsayin hannun ta ba. Tafiya take cike da sassarfa rungume da 'kullin kaya cikin wani ko'da'd'den zanin da ba se ka sha wahala wajen fahimtar cewa zanin ya jima yana shan ruwa ruwa ba musamman saboda kodewar da yayi. Duk da cewa tana cikin yanayin tafiya ne na sauri amma hakan bazai hana ka fahimtar nutsuwar da Allah yayi mata ba. Akai akai zaka ga ta kai bayan hannun ta daya tana share 'kwallar da ke zuba daga idanun ta babu 'kakkautawa. Tayi tafiya me dan nisa sosai domin daga inda take tsayen sam ko kusa ko alama bazaka iya hango alamun gari ko makamancin hakan ba. Abu daya dake sata waigawa shine idan taji dirin tahowar mota daga bayan ta takan waiga wani sa'in har tsayuwa take yi ta tsurawa motar idanu har sai ta wuce inda take ga dukkan alamu kage take wajen ganin ta samu abin hawan amma hakan be yiyu ba. Zuwa wannan lokacin tuni hawayen nata sun tsagaita sai dai har yanzun fuskar ta daure take babu wani alamun fara'a tattare da ita. Bayan kamar shudewan rabin sa'a tana tafiyar batare da ta samu abin hawan ba, wata doguwar farar Bus ce ta taho wanda mutanen cikin ta basu haura mutane biyar ba. Ban yi mamakin tsayuwar da tayi ba bayan jin tahowar motar saboda na jima da fahimtar motar da zai tsaya ta hau tun dazun take dako. Cak kuwa ta tsaya tabi motar da idanu, bansan dalilin da yasa har yanzun takasa budan baki tayi magana ko nuna alamu da hannun ta wajen tsaida abin hawan ba duk da cewa alamu sun bayyana asalin matsuwar ta da son ganin ta samu abin hawan amma hakan bai sa ta iya furtawa ko nuna alamun hakan ga matukan motocin dake faman zuwa suna wuce ta ba...sai dai bana raba dayan biyu cewa ta kasance bakuwa ce a wannan harkar shiyasa. Kadan Bus din ta gitta ta cikin sa'a kuwa sai tsaya daga gabanta kadan take drivern Bus din ya sauko. Cikin ranta ta saki hamdala gami da ajiyan zuciya afili. "Uwargida ina zaki..?" Drivern ya fada yana me bude mata bayan motar. "..Inda kuka nufa.." Tace dashi tana me kokarin taka motar ta haye. Bai sake magana ba kawai ya ja marfin ya rufe ya koma mazaunin sa tare da jan mota suka yi gaba. Karo na farko kenan a rayuwar ta da ta ta6a sanya kafa ta bar mahaifar ta, a iya sanin ta tunda mahaifiyar ta ta haife ta bata ta6a zuwa ko'ina ba...ta girma ta budi ido tayi wayo duk cikin garin su...sai gashi ayau kaddara ta rabata da mahaifar ta da kowa da ya kasance ahalin ta ne. Duk da cewa kwanakin nan din wajajen nasu bai fiya lafiya ba amma sam bata ji hakan ya dame ta ba musamman da ta ga cikin motar akwai wasu mata guda uku da maza biyu...ta riga ta tsaida zuciyar ta akan kudurin ta na barin garin dan haka aranta take ji koma ina ne suka nufa a shirye take itama. Rintse idanu tayi gami da dafe kanta. Yayin da dayan hannun nata kuma ta kai bayan ta ta dafe abinda ke goye abayan ta dashi bata sake daga kanta ba har sai da kunnuwan ta suka fara jiyo mata tashin hayaniyar mutane...amma baza ta ce ga tsawon lokacin da suka dauka suna wannan tafiyar ba. Sai a lokacin ne ta dago kanta ga mamakin ta sai tayi arba da mutane, titina da kuma gine gine ba irin wanda ta saba gani a garin su ba..." _Duniya sabuwa_ ". Ta furta cikin ranta tana mai gyara rikon da ta yiwa kunshin kayanta tare da daidaita zamanta da kyau dan kar ta takurawa abinda take goye da shi...duk dama tun farkon shigar ta zuwa zaman da tayi a motar ankare take ko da wasa hankalin ta bai bar kan abinda ke goye a bayan tan ba. Motar bata zame ko'ina ba sai cikin tasha wanda ya kasance tasha ne babba shake da al'umma da kuma motoci kala kala ana ta hada hada. Gani tayi an tsaya kowa na shirin sauka...itama sai tabi sahu ta sauka kamar yadda taga sauran sunyi...biyan kudin motar tayi adadin yanda matukin motar ya fada mata. Mace daya cikin motar da tun duba na farko da ta mata ta fahimci sun hada alaka da ita 6angaren yare ita tabi abaya batare ma da matar ta ankare da ita ba...cikin rashin sa'a sai taga matar wani motan take kokarin shiga. Inda taji wani da take kyautata zaton sune masu kula da hada hadan wurin yana fadin.." Hajiya mutun biyu daga nan har Azaren Bauchi...". Bata yi kasa a gwiwa ba wurin shiga motar kamar yadda taga matar ta shiga duk da cewa kuwa bata san inda tafiyar zata tsaya mata ba kamar yadda bata san mafarin ta ba...amma hakan bai sa ta fasa tafiyar ba. Fatan ta kawai shine Allah yasa wannan kaddararriyar tafiyar ta sada ta ga Alkhairi ba Sharri ba...nan ma haka ta biya kudin motar adadin da akace mata ta biya. Sunyi tafiya kusan ta sa'o'i uku kafin taga an sake tsayawa kowa na nemawa kansa hanyar barin motar..itama hakan tayi sai dai wannan karan bata yi yunkurin sake bin matar ba tana tsaye a wurin taga duk wadanda suka zo a motar kowa ya kama gaban sa...wasu da kafafun su suka yi gaba yayinda wasunsu suka hau adaidaita kamar dai matar nan da ta biyo wanda hakan ya kasance nan ne karshen ganin ta da matar. A fili ta saki ajiyan zuciya, Gabas, yamma kudu da arewa ta waiga bata ga ta inda zata fara ba. Duk da hakan a wannan lokacin da take tsaye gefen titin tana da tabbacin tayi tafiya, tafiya mai nisan gaske nisab da ko ba'a fada mata ba ita kanta tasan tayi nisa da gida, sam takasa jin farin ciki cikin zuciyar ta duk da cewa ita da kanta ta za6a wa kanta hakan amma ji take tamkar ta raba rayuwar ta ne gida biyu. Safayau taje jin kanta sam ba nawi..yayin da cikin zuciyar ta take jin ta cunkushe da nawin da bata hango ranar warwarewar ta kwana kusa ba. Jiri taji yana shirin diban ta idanun ta duhu duhu yake gani yayin da taga komai na kokarin canza mata yanayi...dai dai lokacin kuma da abinda ke goye a bayan ta yayi mutsumutsu akaro na barkatai da ita kanta bata san ko na sau nawa bane sai dai wannan din da alamu hakurin ta ya gaza ne. Tuni ta dawo da tunanin ta daidai ta riga tasan matsalar, tasan me ke damun su daga ita har abinda ke bayan tan...bakomai bace face yunwa..dan tasan rabon su da saka wani abu a cikin tun kafin barowar su gida. Dube dube ta fara can ta hango wata bishiyar dalbejiya yalwatacciya, batare da tunanin komai ba ta nufi karkashin bishiyar ta yada zango...Kullin kayan ta fara ajiyewa kafin ta kai ga zama kuma sai ta sa hannu ta kunce abinda ke bayan ta ta dawo da shi ta gaba sannan ta dage hijabin ta gaban tana zama, nan idanu na suka ci karo da wata kyakkyawar halitta, wanda duba na farko ba sai ka kara ba zaka fahimci cewa yarinyar kyakkyawa ce, yarinya ce 'yar karama wadda akalla bazata wuce sati uku zuwa hudu da haihuwa ba. " Sarkin bacci kenan..." Ta fada tana murmushi tare da gyara rikon yarinyar. Matukar mamaki ne ya kama ni da ganin murmushin ta akaro na farko, domin yinin yau din kaf ban ga murmushi ko sakin fuska dai dai kwayar zarra kan fuskar ta ba, sai yanzu da ta yi arba da fuskar 'yar yarinyar nan dake hannun ta. Ga mamaki na sai naga ta kunce kullin kayan ta ciro gongonin madara ta yara, Pure watern da tun kafin ta sauka a mota ta siya da niyyan sha amma bata sha din ba da shi ta dama madarar ta bawa yarinyar nan tasha abinta yayin da ita kuma ta tsaida mai awarar da ta ga na wucewa ta gefen ta shi ta siya taci tare da korawa da guntun ruwan pure watern nan. Sake maida goyon ta tayi abayan ta ta dauki kayan ta ta cigaba da tafiya a hankali duk da yake bata san inda ta nufa ba amma dole ne tayi tafiyar. Karshe wata bishiyar ta sake yada zango sai sai wannan din ba bakin titi take kamar wacce ta baro ba. Ruwa ta sake siya tayi alwala da shi tayi sallah batare da cire goyon ta ba. Wannan bishiyar nan ta maida wajen zaman ta, sai idan dare yy kuma ta koma wani lungu ko wata runfa ta kwana rungume da yar ta ajikin ta baccin kirki ma bata iyawa hankalin ta duk akan yarinyar ne tana gadin ta har gari ya waye da rana kuma ta dan kara kekkewayawa idan taji yunwa ta siyi abinci taci..da haka har ta saba da wata mai sai da abinci kusa da wurin kadan. Rashin baccin da ta ke fuskanta yaso ya sa mata ciwon kai mai tsanani amma sam bata sashi aka ba da haka har ya gaji yayi nasa wuri. Wannan mai sai da abincin ta fara magana da ita tun zuwan ta garin kwana biyu kenan yanzu, inda ta roke ta cewa ko zata bata aiki a wajen tana yi mata, matar da farko kin amincewa tayi tace babu wani aiki sai dai daga baya kuma sai ta tuna ashe me mata wanke wanke wata me kamawan nan ne za'ayi bikin ta. Hakan yasa tayi saurin dakatar da ita tai mata bayani akwai aikin wanke wanke in zata yi amma zata fara aikin ne bayan kwanaki ashirin da takwas masu zuwa inda ya kama kusan sati uku kenan kafin zuwan ranar. Ba karamin farin ciki jin hakan ya sata ba bata kuma yi kasa a gwiwa ba wajen nuna amincewa da godiyar ta a fili. Nan ta sake rokan matar akan ta taimaka mata da neman inda zata zauna na haya in zata samu nan kusa saboda itan bakuwa ce bata da wurin zama. Wani banzan kallo matar tayi mata cike da rainin hankali ta sake binta da kallo daga sama har kasa sannan ta tsaida idanun ta kan fuskar ta..." Ya sunan ki...?" " Zaituna"! Ta bata amsa tana me hadiyar yawun tsoron irin kallon da matar nan tai mata. Ita ba saba irin rayuwar nan tayi ba...bata saba neman alfarmar kowa ba. Ko da take gida bata daukan rainin hankali, bata roko bata kallon abin wani taji ya birge ta bata ta6a neman komai a wajen kowa ba illah mutun daya tak kuma shi din gudan jinin ta ne. Sai dai ayau kam tana jin dole na ta jure komai, dole ne ta jure kowani irin hali da ta tsinci kanta tunda har ta kai wannan ga6ar dole ne ta kaskantar da kanta ta nemi alfarma badan kanta ba, badan jin dadin ta ba badan farin cikin ta ba sai dan yarinyar da ke goye abayan ta. "...Akwai wajen zama nan kusa sai dai bana tunanin zaki iya biya, ni kuma ba aiki na bane 6atawa kaina lokaci wajen nemawa mutane muhallin zama musamman dan zaki yi min aiki ba...kije kawai zan sa a duba min wata daban dama already na yi magana..." Ba karamin bugu zuciyar zaituna yayi ba jin kalaman matar nan da adan kwana biyu da tayi tana rayuwa kusa da wajen ta fahimci suna da ake kiran matar da shi shine Hajia Talatu...Hajia Talatu mai abinci. Da rawar murya ta fara fadin "...Hajia ki fada min kudin Insha Allahu idan bai fi karfi na ba zan biya..." "...Yama fi karfin ki, kama gaban ki kawai bana son shirme.." Hajia ta fada a tsawace. Dan ta fara gajiya da magana da yarinyar. Sosai jikin Zaituna ya fara rawa, tunani take idan tabar nan sai kuma ina zata nufa...? " Dan Allah Hajia ki saurare ni, ni dai in zan samu wajen zama inda bazai takuramu ba wlh zan iya biya koda hakan na nufin in rasa na sakawa abaki na ne, ki fada min nawa ake biya Hajia Insha Allahu zan biya kuma..." " Dubu ashirin da biyar ne daki ne daya..." " Zan biya Hajia..."! Zaituna tayi saurin bada amsa tana me sauko da kullin kayan ta gaban Hajiyan. Wani banzan kallo Hajiyan tayi mata gami da fadin kin kuwa ji me na fada ko..?" " erh Hajiya zan iya biya ko yanzu ma..." Kai Hajiyan ta girgiza gami da fadin sam sam ban yadda da ke ba baiwar Allah...zan mafi kyautata zaton sata kika yi daga inda kike cewa kin fito...maza ki 6ace min da gani kafin in tara miki mutane ai miki bugun 6arayi yanzun nan.." Ta karashe maganar tana me bada umarni ga wata mai mata girkin abincin daga can wajen dafa abincin, dan ita bata aikin komai sai bada Umarni kawai ga ma'aikatan ta. Kukan da Zaituna ta sanya ya dawo da hankalin ta gareta take tayi kicin kicin da fuska tana duban ta. " Mayya ce ke kam hala?" kai Zaituna ta girgiza da sauri alamun a a . " Toh tashi ki bar wajen nan nace..." Sum sum ta tashi ta tafi tana share kwalla...jikin ta duk yayi sanyi. ta rasa dalilin hajiya nakin amincewa da ita kan batun hayar nan, shin ba ita tace zata biya dakanta bane, ko de Hajiya naganin kamar bazata iya biya bane. Ta san hakan ne babu tantama ita da kanta tasan hakan, dan kafin wannan lokacin ita kanta bata taba tunanin zat iya rike kudi kwatankwacin jaka biyar bama amma kaddara ta fi karfin komai. Ba karamin matsuwa tayi da son samun wajen zaman nan ba musamman ma dan ta samu ta watsawa jikin ta ruwa, a matukar takure take ainun da zaman wajen bishiyar nan. Ga yarinyar ta ma da rashin wankan da take fuskan ta yake sata kananun kuka yanzun sosai hakan ke damin ta. Karo na farko kenan da taji tayi nadamar barin gida. Take kuma sai wata zuciyar tace mata toh ko kina gidan ma a ina zaki zauna da yarinyar nan. " Innalillahi wa inna ilaihiraji'un..." Allah ka sassauta min, yah Allah ka bayyana min abinda yafi dacewa dani. Kuka sosai tayi tana tuno abubuwa da dama, masu dadi da akasin hakan, sosai take jin rauni tattare da ita. Ranar kwanan Rumfan mai kayan miya ta sake yi...washe gari kuwa da sassafe ta sake yiwa Hajiya Talatuwa sammako. Duk ta rame ta fita hayyacin ta kamar ba ita ba. Gaishe da Hajiyan tayi tana me silalo da siraran kwalla. Gani tayi Hajiyan ta tsaya kallon ta duk da bata san meke cikin zuciyar ta ba amma ga dukkan alamu rahamar da ke kan fuskar Hajiyan na yau ya 'dara na jiya sau adadin da bazata iya kididdigewa ba. Cike da marairaita ta fara fadin "...Hajiya dan Allah kiji tausayi na, wlh tun da nake ban ta6a satan ko gudan Naira na wani ba haka wannan kudin ma da nace zan biya hayan da shi ba kudin sata bane Hajiya wlh kaddara ce ta sa na bar inda nake inaso in dan sarara ne kafin wani dan lokaci in koma gida..wallahi ke kadai naji zuciya ta yadda da ita..dan Allah Hajia ki taimaka min na miki alkwarin bazan ta6a baki kunya ba..." "..Baiwar Allah ya ma kika ce sunan ki...?'" Hajiyan ta tare ta tun ma kafin takai karshen maganar ta. Cike da zakuwa ta amsa Hajiyan da fadin. " Sunana Zaituna Hajia". Kinga bawai kin nema miki nayi ba gani nayi kinyi karama gaskiya Zaituna, kinyi karama sosai ace kin kama daki kina zaune ke kadai kamar ydda nake tunanin bazaki iya biyan hayan ba amma in zaki iya ni ai ba ruwa na..kasuwanci ne kawai kuma babu daga kafa .." " Insha Allahu Hajia zan iya biya ni dai dan Allah ki taimaka min.." Bata sake ce da Zaituna komai ba kawai ta dago wayar ta kira wani wanda sai bayan ya isi ne Zaituna ta fahimci cewa shine wanda zai mata jagora zuwa inda zata zauna din. Tare da shi suka je ya bude dakin dakansa sannan yayi mata bayanin gidan da ya kasance bayan layin inda Hajia ke saida abincin ta ne... Sake jajjada mata kudin hayar mutumin yayi take kuwa cikin kayan ta ta ciro kudin ta biya hayan zuciyar ta cike da farin cikin samun matsuguni. Sosai kuwa gidan yayi mata tsab da shi...daki ne daga farkon gidan sai wasu dakunan daga can ciki wanda ta fuskanci da mutane ma a cikin su...sai bayin su guda biyu na wanka daban na bahaya daban. _Salmerh_ 😘 [20/9/2022, 12:32 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE* 💕 *( 'Yata ce)* *Salmerh MD* 🅿️....2 .......Cike da zumudi ta shiga dakin can kasan zuciyar ta take jin wani irin kwanciyan hankali, sai dai fayau da taga dakin bayan shigan ta ya sanya mata tsinkan zuciya, ashe da sauran rina a kaba, ta zaci komai ya kammala kenan tunda ta sami dakin, shaf ta mance da cewa bata da komai na amfanin yau da kullun. Take gadon ta dake a can gida ya fado ranta sai tayi saurin girgiza kai cike da karayar zuciya. Duk da tasan cewa shima din ba wani gado ne na kirki har na azo agani b amma ko ba komai yayi mata amfani tsawon shekaru wanda ko a yanzun haka da take tsaye cikin wangamemen dakin nan da zata budi ido tagan sa anan gaban ta sai tafi kowa jindadi. Dakin malale yake da lafiyyan siminti, ga kofa ma mai kyau haka ma windown dakin babu penti kam amma hakan bai sa taga rashin kyan dakin ba musamman da tasan cewa ya dinka nata na can gida. Matsalar ta daya ne da taji yafi damin ta bata da komai na amfani ko kuma wanda zata rika yiwa yarinyar ta shinfida da shi kuma bazata iya kwantar da yarinyar haka nan kan simintin dakin ba musamman ma dayake a yanzun ana cikin yanayi ne na damina. Bata ta6a zaton abin zai iya kaiwa har haka ba, sai yanzun idanun ta suka fara raina fata, yanzu ne ma tafara ji aranta cewa meyasa ta aikata hakan. Ban dama Allah ya dube ta ya tsaida ruwa a iya kwanakin da tayi tana kwanan layi da bata san ya zata yi a wancan lokacin ba, amma da ikon Allah ko digon ruwa dis bai sauka ba sai ma zafi da take kyautata zaton na nunan gero ne. Jakan tan kawai ta ajiye ta sake fitowa harabar gidan da ya kasance matsakaici, zai yi wahala ace mutun yayi uzurin sa cikin gidan har ya gama batare da gani ko jin motsin kowa ba saboda rashin wadataccen fili da gidan ke dashi sai dai in ya kasance masu rayuwa cikin gidan basa kusa ne. Cikin kankanin lokaci ta karewa gidan kallo babu laifi yana da kyau da kuma tsabta dai dai gwargwado dan kuwa ko kusa ba ta isa ta hada wannan gidan da can gida da ta baro ba. Wata kofa dake gefe da nata dakin kadan tabi da kallo ganin sa garkame da katoton kwado bata yi wani dogon nazari ba wajen fahimtar cewa mamallakan dakin basa sa nanne ko kuma shima din layin haya yake da ba a riga an shiga ba tukunna duba da cewa nata dakin ma sai da ta zo kafin aka bude shi gami da bata makullin. Sallama tayi cikin sassanyan muryar ta daga bakin 6angaren da tun dazun take dan jiyo motsin mutun amma sai taji shiru ba'a amsa mata ba. Sallaman ta sake rerawa wannan karan da dan sauti tayi shi..can ciki taji an amsa mata bayan wasu dakiku kuma wata mata mai matsakaicin tsayi ta fito. " a a bakuwa ce ma..barka da zuwa ga gurin zama nan zauna." Tayi maganar tana daidaitawa Zaituna kujera daga gefe kadan sai kuma ta koma bakin kofar dakin ta ta zauna. Zama Zaitun tayi itama sannan ta gaida matar dan sakin fuska musamman da ta lura matar kamar bata da matsala ta wajen sakin fuskar ta ga ko wanda ma bata sanshi ba. " Sai dai ban gane ki ba wallahi.." Matar ta fada tana 'yar dariya. Zaituna ma murmushin tayi " Bakuwa ce, amma ta gida...wancan dakin na hanyan waje nake dazun na shigo..." "...a a Masha Allahu...gaskiya nayi farin ciki sosai kice zan samu abokan hira, gashi kamar ma bayan ki da goyo..." Takai karshen maganar ne tare da mikewa ta taho ga Zaitun da alamu abinda ke goye abayan Zaitun din take da niyyan karba. Fahimtar hakan da Zaitun tayi ne ya sanya ta ware goyon ta sauko da ita ta bawa matar idanun ta kur akan yarinyar tana sassanyan murmushi. "..Tabarakallah masha Allah...ai kuwa ga yarinya...ya sunan ta...?" Tana duban fuskar yarinyar ta fadi hakan tare da gyara mata rigar jikin ta da duk ya tattare zuwa sama. "..Aisha sunan ta...." Cewar Zaitun wanda tun kafin takai ga karshen abinda tayi niyyan fada ta jiyo sallama da hayaniyar raya na tunkaro su. Gaba daya sai suka kai duban su ga yaran domin hayaniyar tasu ya dauki hankalin su gaba daya. Da gudu 'daya ya taho ga matar nan yana fadin "Mama!..Mama kinsan abinda Siyama tayi?" Kai ta girgiza masa alamar a a " Wlh mama gidan su Fatima 'yar ajin su ta shiga wancan na farkon layin wai anjima zasu je Partyn suna dan ance sunan Babyn Mufeeda shine itama wai daga yau sunan Teddyn ta Mufeeda....kuma Mama ba da cewa tayi sunan Teddyn nata Aisha bane..?" Yayi maganar ne cike da zafin kai tamkar wanda akai masa ba dai dai ba. Dududu yaron bai wuce shekaru uku zuwa hudu ba sai dayar da ya kira da Siyaman wacce bazata haura biyar ba itama. Siyaman kuwa hade rai tayi sosai tana duban kanin nata da ke kokarin shigar da gulma ga maman nasu. " Toh kai ina ruwan ka ne Abdul ai naga Teddyn ba naka bane ko...kuma ma mama ai zan iya kiranta da suna biyu kamar irin nawa ko...?" " Hakane mama na...daga yau sunan Teddyn ki Aishatul Mufeeda". Tsalle Siyama ta buga cike da farin ciki take maimaita sunan cike da jin dadi. Ya isa hakan nan toh...sai kace baku ga bakuwa ba bazaku gaida ta ba".. Da sauri yaran suka risina suna gaida Zaitun sai taji sun birge ta sosai suka shiga ranta. Haka ta amsa musu cike da murmushi sannan suka gaida maman sun ma wanda sai a lokacin suka lura da Babyn dake hannun mahaifiyar tasu..atare suka zubar da basket din makarantan dake hannayen su suka nufo jikin ta sosai kowa na fadin abinda yazo bakin sa. " Laaa mama Babyn waye..?" "..Mama ki bani na dauka na iya rikewa". "Kai Siyama me yasa kun cika hayaniya ne da wai? da kyar na samu Ahmad yayi bacci gashi ihun ku zai sa ku tasar min da shi tun yanzu..." Shiru yaran suka yi suna duban Babyn da ke hannun tan. " Maza ku wuce ku cire uniform dinnan azo a watsa ruwa aci abinci ayi sallah saura inji wata sabuwar fitinar kuma..." " Mama idan nayo wankan zaki bani Babyn in rike ko?" Cewar Siyama cikin marairaita tana daukan baske din ta. " Wannan kam ai tana nan daga yanzu har sai kin gaji da daukan ta ma maza je a yi wankan a fito tukunna kar ayi lattin Islamiya" " Toh mama miye sunan ta ?" Ta sake fada cike da murna jin cewa suna nan. " Sunan ta daya da Teddyn ki..."! Farin ciki sosai ya bayyana kan fuskar Siyama har da dan tsallen ta ta shige ciki tana yiwa Abdul albishir din sunan Babyn daya kasance daya ne da Teddyn ta. Sai a sannan hankalin su ya dawo kan juna " kai yaran nan ba dai hayaniya ba." Cewar Maman Abdul tana murmushi. Zaitun kam mikewa tayi itan ma tana murmushin ta sa hannu ta kar6i Yarinyar ta suka koma nasu dakin. Zama kawai tayi bisa takalman ta da sune kadai makwafin abin zama a dakin, da hannun ta daya tayi tagumi zuciyar ta cike fal da tunanin ta ina ma zata fara ne...? Lissafin abubuwan da take bukata a yanzu haka tana ganin 6ata lokaci ne, babban damuwar a yanzun shine murdawar yunwa da take ji cikin ta nayi, idan bata manta ba yau din tun safe bata sanya komai acikin nata ba. " Dole in nemo wani abin yanzu". Tayi maganar ne gami da mikewa dai dai lokacin da Siyama ta bayyana bakin kofar da 'yar sallaman ta, amsa Zaitun tayi tana bin yarinyar da idanu cike da mamaki ganin ta dauke da flask din abinci. " Ashe gefen dakin Hajjan mu ma kuke..?" Siyama ta fada tana me ajiye abinda ke hannun ta. " Ki bani in dauke ta na iya nima, na iya daukan Teddy na ma har goya ta nake yi a bayana.." Duk da Zaitun bata san mene Teddy din ba amma tana kyautata zaton Teddyn bai kai darajar yarinyar ta ba..dan haka bazata iya bawa Siyama yarinyar ta dan ta rike ba. " Ki bari bacci take yi yanzu idan ta tashi sai kizo ki dauke tan ko.." " Uhum..Maman Mufeeda ai ma zaki goya min ita ko...?" "Insha Allah" Ta fada tana kara waro idanun ta kan Siyaman jin sunan da ta kira ta da shi.. " Maman Mufeeda!"..Maman Mufeeda wai!! Ita din wai..yau din..?" Lallai..ta fada a fili tana 'yar murmushi. Har siyama ta juya zata fita Zaituna tayi saurin dakatar da ita da fadin wannan fa .." " mamana tace in kawo" "Kai kuma har haka da wahala..bama fa na jin yunwa ki kai muku kawai kuci kinji" " Ai namu da yawa ne Maman Mufeeda ki ajiye anjima idan kinji yunwa sai kici". Siyama na kokarin sanya silifas dinta ta tafadi hakan da alamu bata da niyyan komawa dashi. Wannan yarinya ba dai surutu ba..ta fada cikin ranta a fili kuwa cewa tayi " Kice angode.."! Abinda kadai taga zata iya furtawa sannan ta dawo da duban ta kan madaidaicin flask din. Duk da cewa a yanzun babu wani abinda tafi bukata sama da abincin amma sai taji wani iri cikin zuciyar ta, gani tayi tamkar ta dorawa matar nawi. Kasa ko bude flask din tayi balle ma akai ga zancen cin abinda ke ciki kawai ta zauna shiru, tana ji cikin ranta dole ta nemo mafita, ita da kanta ta yanke shawarar da taga ya fi mata dan haka ba kuma zata zo ta dora nawin ta akan kowa ba...dole ne tasan abin yi. Duk da uban yunwan da take ji yake addabar ta kuwa hakan bai sa taji sha'awar cin abincin ba. Gefe ta ajiye flask din ta cigaba da tunanin abinda yake damin ta arai. Kokadan bata so tunanin gida yazo ranta, shiyasa da taji kamar kewan gidan zai shigo tunanin sai tai saurin kawar da shi. 'Yar yarinyar dake bacci saman cinyar ta ta tsurawa idanu tana ayyana yawan bacci irin nata kusan koda wani lokaci bacci yarinyar take daga taji cikin ta ya dan dauka shikenan sai bacci, sau da dama ma sai Zaitun ta tashe ta ta kara mata madaran da kanta in bahaka bazata yanke baccin cikin lokaci kalilan ba. Ta lura yarinyar sam bata da fitina irin wacce yara ke yi din nan. Jiyo tashin kiran sallah ya sanya ta daidaita zaman kayan sun ta kwantar da yarinyar akai, bakin Pampon da ta ga su Maman Abdul na diban ruwa taje ta dauro alwala itama ta dawo, bata yi mamaki ko jin dar din amfani da famfon ba dan kuwa akwai a masallacin dake can garin su da yawa na alwala da gwabnati tayi musu. Kayan ta ta janyo bayan ta idar da sallahn ta warware kayan gaba daya. Ragowar kudin da ya rage mata ta ciro ta irga dubu sha daya ne da dari biyar da naira hamsin..idan ta hada da wanda ta kashe tun a gida da na mota da ta biya abincin da ta ci har zuwa kudin hayar da ta biya akalla kudin sun tasamma dubu sittin da 'yan kai. 'Dif taji kirjin ta ya buga lokaci guda...tsoro ne taji ya mamaye ta, sosai ta jinjina yawan kudin da tun farko bata lissafa su ba sai yanzun. Hakan ma ba dan Ya Bukar da ke dan siya mata wasu abubuwan da kudin sa ba da kila zuwa yanzu ma babu wannan kudin sun kare gaba daya. " Toh yanzu idan suka kare ya zanyi"? Wata zuciyar ta ta jefa mata wannan tambayar kuma sosai tambayar tayi tasiri cikin ranta. Lallai dole ne in nemi mafita ko dan yarinyar nan..yanzu haka kam bata da matsala kan madaran yarinyar dan akwai ragowa me dan dama sosai amma sam bata so ya yanke musu. Lissafi tayi ta ga cewa cikin kudin zata iya siyan madaran kimanin gongoni uku gudun kar ya kare dacwuri inyaso sauran kudin sai tasan yadda zata yi da shi. Gashi bata da abinda zata na yiwa yarinyar shinfida dashi illa zanbuwan ta kadai kuma tana gudun sanyi ya kama mata yarinyar. Aranta ta yanke cewar idan tayi sallah zata koma wajen Maman Abdul ko zata samu inda zata siyawa yarinyar abin shinfida da sauran kudin dake hannun ta. Sai dai kuma bata so matar taji kamar ta takurata ne da yawa shiyasa ko da ta idar da sallahn kasa komawa tayi. Abincin ta hanyo da ya kasance jallop ce ta shinkafa, haka ta dan tsatstsakura ta toshe inda take jin yunwar ta mayar ta rufe shi...ita kadai acikin dakin amma jin ta take a tsarke tamkar wacce ke aikata ba dai dai ba. Bata kuma kara fitowa ba duk da kuwa abubuwa da yawa tana da bukatan su a lokacin. Roban da zata rika yiwa yarinyar wanka, abinda zata shimfida mata dan tana matukar son taga tayi mata shinfida itama tayi bacci asake kamar ko wani yaro, kwana biyun nan duk akan cikin ta take kifa ta suyi bacci a hakan, sai kuma take ga tamkar tana takurawa yarinyar ne da hana ta sakewa tamkar batai mata adalci ba, gefe guda kuma ga abincin yarinyar da shi yafi komai daga mata hankali idan yai kasa. Bata kara fitowa ba har kusan karfe biyar na yamma...tana zaune tana ta sake sake banda sallah babu abinda ke tada ta. Maman Abdul dince da kanta tazo wajen ta ganin tun dazun bata sake jiyo motsin ta ba, sai tayi tunanin ko aikin shirya kaya ne ya rike ta, tausayin Zaituna tun dazun ya kasa barin zuciyar ta ganin cewa yarinya ce karama da akalla zata iya yin kanwa da ita kusan na hudu amma jibi yadda haihuwa tai mata sammako ya riske ta tun a karancin shekarun ta, raino baya da sauki kokadan musamman ga yara irin su Zaitunan. Wannan tunanin ne ya sanya ta nufi dakin tan da zummar kama mata wasu ayyukan su kammala da wuri. Sai dai me ba karamin mamaki tayi ba lokacin da ta riski dakin ba a yanayin da tayi tsammani ba...turus ta tsaya ta karewa dakin kallo. Da sallama ta shigo Ahmad da bazai haura shekara guda ba tafe abayan ta, fuskar ta cike da alamun mamakin da har yakasa boyuwa mata idanun ta kur akan Zaitun din domin daga ita babu wani 6angare da zaka 6atawa kanka lokaci wajen duban sa a dakin dan tas yake babu komai. Kakalo murmushi tayi tace " Na jiku shiru ne gashi har yanzu baki kwance yarinyar nan kin huta ba Zaituna.." " Zan kwance ta am..am" Sai kuma ta kasa karawasa. " Da kyar ma idan kin yi mata wanka..." da sauri Zaitun ta girgiza kanta... " Ai kuwa naga alama bari akwai ruwan wankan su Siyama dana dora musu na dare sai ayi mata wankan da shi inyaso sai in sake sanya musu wani kafin a dauke wutar". Bata ma jirayi amsar Zaitun din ba ta fice da sauri. Da yake ma a kettle ne ruwan tana juyewa ta sake sanya wani ta taho da wannan cikin baho hadda sabulu mai kamshi ta dauko. Da kanta ta karbi Yarinyar dan yi mata wanka yayin da Zaitun ta juya ga kullin kayan su ta ciro riga wanda ya kasance shine karshe cikin kayan sawan yarinyar da bai yi datti ba...dama ba wani yawa gare su ba ga kuma yanayi na rashin matsuguni da ta shiga kwanaki biyun da suka gaba ta hakan sai ya hana ta samun sukunin wanke mata kayan hakan kuma bai hana ta cancanza mata kayan ba..a lokacin jiga dankwalin ta take ta goge mata jiki da kyau sannan ta sa mata kaya. " Dole sai nayi wanki kenan a yau ko gobe" Zaitun ta fada cikin zuciyar ta lokacin da take kokarin dauko rigar. Maman Abdul bata sake tambayar Zaitun komai ba dan ta gama fahimtar ko wani irin taimako ma Zaitunan tana bukatar shi a yanzu. Kuka sosai Yarinyar tai ta tsanyarawa lokacin da ake gasa mata jikin ta da ruwan dumin da yake ta kwan biyu bata samu hakan ba. Ai kuwa Maman Abdul na gama wankan ta sata cikin zanin goyon ta mikawa Zaitun ita tare da fadin " wannan me sassanyan muryan ta iya kuka...bata tasha kafin a karasa shiryata." Zaitun kam da tunanin bai gama bata ma'anar maganan Maman Abdul ba cigaba kawai tayi da lallaba yarinyar dan tayi shiru. Murmushi Maman Abdul tayi" ai inaga in ba nonon ta kama ba bazata taba yin shiru ba wannan..." 'Dif zuciyar Zaitun ya buga da karfi...bata so ta sake maimaita abinda kunnuwan ta suka jiye mata Maman Abdul ta fada. Jikin ta har rawa ya fara ta kasa daga idanu ta kalle ta..sam sam bata so ta fallasa asirin zuciyar ta a yanzu...amma meyasa babu wanda ya ta6a cewa ta shayar da yarinyar sai Maman Abdul. Maman Abdul kam jinjinawa kunya irin na Zaitunan tayi shiyasa ma kuma bata ga laifin ta ba...domin ita Kunya adon mace ce. Kokarin dauko madarar yarinyar Zaitun tayi da dayan hannun ta...wanda yasa maman Abdul dake kokarin mikewa da niyyar barin dakin dan bata damar sakewa gudun kar ta takura ta bin hannun nata da kallo... " Wannan za'a bata..." Zaitun ta fada batare da ta iya daga ido ta dubi Maman Abdul din ba. Ba karamin mamaki maman Abdul ta shiga ba sai dai bata tsawaita tunanin ba ta karbi gongonin ta ajiye...Zaitun kam idanu ta zuvawa yarinyar sai ma lallashin ya gagare ta..gaba daya rasa abinyi tayi, abu daya da tasani kawau shine tana matukar kaunar yarinyar nan irin kaunar da a kowani irin lokaci hauhawa yake yi baya raguwa. Maman Abdul komawa tayi 6anagren ta dawo da ruwan dumi a kofi ta dama madarar ta karbi yarinyar da kanta ta bata ga mamakin ta kuwa sai taga yarinyar bata nuna alamun kin sha ko wani abu ba ga dukkan alamu ma ta riga ta saba da shan abinta...ai kuwa shikenan kuka ya kare sai bacci. Rigar maman Abdul ta dauka tana sanyawa yarinyar a fakaice take duban Zaitun din abubuwa da yawa na mata yawo aka. Cike da kulawa fa fara fadin "...amma Zaitun me yasa kuka yi shawaran bata madara tun a yanzun ta ai tayi karama sosai ina ma laifun abari tadan kara watanni kafin, ko mahaifin ta ne ya bada umarnin ayi hakan..?" Shiru Zaitun tayi tana duban Maman Abdul ido cikin ido bama tasan tayi hakan ba kuma...kalmar mahaifi da Maman Abdul ta ambata shi ke yawo tsakanin kwakwalwa da zuciyar Zaitun. "mahaifin ta...Mahaifin ta...toh ma shi din waye kenan mahaifin nata...?" Ta tambayi kanta. Tsinkayan muryar maman Abdul ta yi tana sake tausan ta duk dai akan maganar madaran nan wanda hakan shi ya sata dawowa daga tunanin da ta lula. Kai ta girgiza tare da yin kasa da kanta tace " Kaddara ce kawai ta za6a mana hakan daga ni har ita, Maman Siyama ba nice nayi ra'ayin hakan ba haka kuma babu wanda ya tilasta ni...". "Amma ai da ba tun yanzu ba Zaitun yarinyar tayi karama Nonon mahaifiyar ta shi tafi bukata a wannan lokacin ba wai madara ba". Bata sake cewa komai ba illah siraran hawaye da ya gangaro mata ta kuma kasa tsaida su, kamar yadda bakin ta ya kasa buduwa ya ce wani abu, kasa kawai tayi da kanta bata sake dagowa ba. Ganin hakan da Maman Abdul tayi ya sanya jikin ta yin sanyi..sai kuma taji matsanan cin tausayin ta ya kara shigan ta. " kiyi hakuri idan magana ta ta 6ata miki rai ne Zaitun ba nufi na kenan ba" Daga hakan taja bakin ta tayi shiru sai dai ta gaza hana zuciya ta yin sake sake kan lamarin. Da kanta ta sake zuwa ta hado wani ruwan zafin ta kawo wa Zaituna tace itama taje ta yi wankan bari ta goye mata yarinyar kafin ta fito. Sosai karamci da mutuncin matar ya tsayawa Zaitun aranta...hakan yasa ko musu batayi mata ba ta dauki ruwan ta shiga wankan duk da cewa kuwa kaf din hankalin ta naga 'yar yarinta dake bayan matar ne..amma haka kawai sai taji tana jin nawin matar nan...kauna ta zahiri ta nuna musu ita da 'yar ta a haduwar su ta yau kadai...rana guda daya tal...dole ta jinjinawa karamcin wannan baiwar Allah. Fitowar ta daga wankan kuwa ta sake ta tarar da wani abin mamakin domin tabarma ta tadda shimfide a dakin hadda wani bargo akai mai kauri an shinfida shima sai kuma bargon yara daga gefe ajiye ga dukkan alamu dan 'yar yarinyar ta aka ajiye sa. Bata tadda Maman Abdul cikin dakin ba dan haka sosai farin cikin ta ya kasa 6oyuwa haka ma hawayen ta. Ayau taga karin mutun cikin wadanda suka nuna kauna ta hakika ga Yarinyar ta..wadanda daidai da rana guda basu taba nuna kyama ga yarinyar ba. Wannan wankan da tayin ba karamin dadin sa taji ba haka ta shirya cikin wata atampan ta daban duk da yake itan ma ba wata mai kyau ba ce amma dai baza a kira ta kai tsaye da kazantacce ba. Maman Abdul ce ta sake dawowa goye da yarinyar bayan ta su Siyama ne da Abdul sai Ahmad, " 'yan Islamiya ashe andawo.." Ta fada tana duban su Siyama fuskar ta wadace da murmushi. Bata jira yi amsar yaran ba ta maida duban ta izuwa ga Maman sun...da niyyar mika mata tsantsan godiyar ta. Sai dai kafin ma tayi magana Maman Abdul ta kunto yarinyar daga bayan ta tana fadin..." simintin akwai sanyi sosai shiyasa na sanya muku tabarmar zai dan rage koda kadan ne ma". " Nagode sosai Maman Abdul, Ubangiji Allah ya saka miki da mafificin alkhairi, dama inaso in tambaye ki inda zan samu bargon yaran in siya mata sai kuma...." " ai bama sai kin siya ba Zaitun wannan ta Ahmad ce dayake yanzu ya girme shi kawai ai mata amfani da shi...akwai kayan sanyi ma da Net din sa zuwa gobe Insha Allahu duk zan duba muku tunda mun daina amfani da shi..." Bata bari Zaitunan ta kara ko kalma guda ba ta tisa keyar yaran ta suka bar dakin suna mata sai da safe domin da kyar ne sake haduwar su a yau din kofar gidan ma tuni sun garkame shi tunda basake fita wani cikin su zai yi ba. Duk da yake Maman Abdul taki bata daman nuna godiyar ta amma dole ne ko da bayan idanun ta ne ta gode ta kuma yi mata fatan alkhairi da ita da zuri'ar ta gaba daya. Dan ko kafin Mmn Adul ta rufe kofan gidan sai da ta tambayi bakin Zaitun saboda hakkin zaman tare...Zaitun din ce tace mata ai babu inda zata kuma fita ayau din Maman Abdul ai kin gama wadata mu da komai. _Salmerh_ 😘 [20/9/2022, 12:32 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE* 💕 *( ' Yata ce)* *Salmerh MD* 🅿️...3 Sosai taji dadin ganin yadda yarinyar tayi bacci sake a ranar, sau daya tak ta farka kamar yadda ta saba tun farko tun ma a gida kafin suzo nan dan haka bai zamewa Zaitun wani sabon abu ba, haka ta tashi ta bata madarar ta ba'a jima ba kuwa ta koma baccin har wayewar gari. Gari na karasa wayewa yau din ta kuduri aniyar fita ta nemo abinda zata karya da shi da 'dan canjin dake hannun ta dan bata so ta daurawa Maman Abdul nawi da yawa kocdaren jiya ma ragowar abincin da Maman Abdul din ta aiko mata shi taci tayi bacci. Waina ta siyo ta naira dari sannan ta fara laluben inda zata ga shago, ba karamin wahala tayi ba kafin ta gano inda shagon yake anan ta sai sabulu da omo anan shagon taga ana saida tsintsiya dan haka shima ta siya guda daya...hatta baho anan ta siya dan madaidaici ta hada hadda bokiti ta siya karami da yake shagon na yorubawa ne kusan komai suna saidawa. Kafin ma ta samu ta dawo gida har rana ta hau kadan shiyasa ko lokacin da ta dawo gidan shiru ta jisa da alamu su Siyama har an wuce makaranta. Gidan basu da matsalar ruwa sam sam dan haka tana gama cinye wainar ta ta tattaro kayan yarinyar kaf da nata da suka yi datti ta fito da su. Wajen Maman Abdul tayi tunanin zuwa ta gaida ta dan ko bakomai matar nan ta nuna mata halacci da kauna daga ita har yarinyar ta. Bayan sun gaisa din ne Maman Abdul take mata tayin abinci tace a a taci abinci ai. Maman Abdul bata takura ta kan hakan ba sai cewa da tayi toh ga ruwan wanka nan tun dazun ma ya tafasa na leka naga bakwa nan. Ahmad dake shan Mama a cinyar Maman Abdul Zaitun ta 'dan yiwa wasa cikin ranta take jinjina tsabta irin na matar nan yaron tsab da shi alamun har an mai wanka, tun zuwan ta gidan bata ga alamun datti ko kazanta tattare da yaranta ba"..an gode sosai Maman Siyama, dama inaso nayi dauraya ne yanzun inyaso idan na kammala sai muyi wankan daga baya" " a a ke de kije kiyi wankin naki ita yarinyar kawo ta in mata wankan zata fi jin dadin jikin ta idan an mata da wuri". Zaitun bata yi musu ba ta kwanto yarinyar daga bayan ta ta mikawa Maman Abdul ita. Cikin kwanaki kalilan shakuwa ta shiga tsakanin Zaitun da Maman Abdul, 'dan ragowar kudin da ya rage mata tuni ta tanadarwa Yarinyar ta madara da shi. Ta siya omo wadatacce wanda tasan bazai zo ya kare mata cikin kasa da sati biyu ba ko dan saboda wankin yarinyar ma. Tuni kuwa Maman Abdul ta kawo mata wasu kayayyakin kamar yadda ta fada ranar Zaitun har kuka sai da ta yi saboda farin ciki. Net irin na yara wanda zai hana sauro cizan mata yarinya, kayan sanyi masu kyau wadanda take da tabbacin basu wani dade ana amfani da su ba, ragowar kayan Ahmad na jegon sa kananun rigunan da suka gaza mai hadda washin Pampers Maman Abdul ta bata. Shiyasa matar ta gama shiga ranta ta zauna daram domin ta saukaka mata abubuwa da dama. Wannan washin Pampers din shi take sawa yarinyar da dare shiyasa yanxu ta huta wankin kayan fitsari da ta shi tai wanka tai wa yarinyar sai ta kayan da ta cire mata da Pampers din ta shanya kafin ta dawo MamanvAbdul ta kwashe mata kayan ta adana ta mata su. Yanzu kam bata da tashin hankali tunda yarinyar ta wadace take da komai sai dan abinda ba a rasa ba. Dawowar Sirkar Maman Abdul gidan daga tafiyan da tayi shine babban tashin hankalin Zaitun a yanzu dan ko kadan matar bata da dadi, sosai take ciwa Zaitun mutunci ita da 'yar ta dan tun abin ba ya damin ta har yazo yana ci mata zuciya musamman da ta lura abin bana kare bane. Gashi sai ta hana jikokin ta ra6ar Zaitun din sai dai suzo asace in dai tana gida in kuwa bata nan toh tamkar dangi suke da yaran. Sosai suke kaunar yarinyar tata, dan haka tuni ta yada makaman ta na hana Siyama daukan yarinyar yanzu kam bata hana ta. Sukan kira yarinyar da Mufeeda, wani lokacin kuma Muphy...yayin da Ahmad da be iya magana sosai ba yakan kira ta da Feefy ne shi bisa ga rashin kwarin harshen sa. Sukan yi dariya sosai idan ya fadi sunan amma wasa wasa da tsokana da 'yar raha har sunan da Ahmad din ke fada ya bi bakin duk su Siyaman. Hajja itace kakar su Siyaman wadda ta kasance mahaifiya ce ga Baban su Maman Abdul ke fada min cewa zaman su tare ya samo asali ne tun lokacin da ta haifi Ahmad saboda gargadar da haihuwar tazo da shi har sai da akai mata aiki tun lokacin da Hajja ta dawo zama da su bata sake komawa ba sai dai taje ta ziyar ci dangin nata ta dawo kamar dai wannan tafiyar da tayin kafin zuwan Zaitun gidan. Baban Abdul mota yake ja daga gari zuwa wani gari har kudu yakan kai kaya dayake babbar mota ce yake ja, kuma mutun ne shi mai zuciya ga kokari, dan ya kan wadata gidan sa da komai da komai na bukatan rayuwa duk da yake ba zaman wuri daya ya cika yi ba amma hakan bai sa ya rage abinda yake musu ba, dan tun zuwan Zaitun gidan bata ta6a ganin sa ba, kamar yadda bata ta6a ji ko ganin Maman Abdul sun nemi wani abu sun rasa ba. Gudun kar ta zame musu tamkar karin nawi ta 6angare guda ya sanya ta ma rage zaman gidan gaba daya. Sati guda ya rage ta fara fita aikin ta dan haka ta shirya taje wajen Hajiya Talatu gudun kar ta manta da batun ta. Ai kuwa batayi mamaki ba lokacin da Hajiya Talatu ke sake tambayar ta wacece ita sai da ta yi mata bayani dalla dalla kafin ta gane ta. "...ai kuwa na ma manta dake...amma dai babu damuwa tunda kika dawo da kanki da alamu shirte kike, Allah de yasa zaki min aiki yadda ya kamata dan ni bana daukan wargi...wanke wanke ne amma duk lokacin da Customers suka ci abinci atake ake wanke min su babu 6ata lokaci dan banason kazanta...fatan kin fahimta?..aikin ki zai fara ne daga safe har zuwa lokacin da za'a rufe wannan wurin...sannan kudin aikin ki dubu shida ne duk bayan wata guda". Sosai Zaitun taji dadin yadda Hajiyan ta kar6e ta cikin sauki take ta nuna godiyar ta a fili duk da kuwa cikin zuciyar ta lissafi take na yadda kudin zai ishe ta dawainiyar yarinyar ta. Tana shirin juyawa ta tafi bayan Hajiyan ta sanar da ita lokacin da ya kamata ta fara zuwa aikin Mufeeda dake bayan ta ta dan yi yunkuri gami da sakin kuka kadan irin na jirajirai. Ido Hajiya ta waro akan Zaituna gami da fadin" Zaitun wannan fa..me nake ji haka?" Murmushi Zaituna tayi tana girgiza Mufeedan tace.." Hajiya 'YATA CE". " Wai dama kina da goyo?" Cike da mamaki hajiya ta tambaye ta tana me bin ta da idanu. Da kai Zaitun ta bata amsa..yayin da mamakin Hajiya ya kasa 6oyuwa. "...kuma da ita zaki yi aikin..?" " Hajiya saboda ita ma na nemi aikin ai...". Shiru Hajiyan tayi illah idanun ta dake yawo jikin Zaitun din tana kissima abubuwa da dama, hakika zamani ya gama lalacewa, baya ga haka ace kamar wannan yarinyar har ace tana da goyo. Ita fa bata mata kallon wata aba ba, kuma ko ranar can sam bata kula da cewa Zaitun din dauke da goyo take ba shiyasa ma ta rage asalin kudin da take biyan masu wanke wanken nata dashi ganin yarintar Zaitun din ashe ta wuce ma tunanin ta. Daga shagon nan Zaitun bata koma gida ba kamar yadda ta saba...gida gida take bi tana tambayar in suna da bukatan ai musu wanki, wanke wanke, shara ko wani abin daban sai tayi a biya ta, da kudin take samu take siyan abinda take ci kullun gefe guda kuma take ajiye wani abu kalilan daga ciki dan kula da yarinyar ta, da yake har yau din nan Zaitun bata ta6a hura wuta ba..toh ina ma taga tukunyar da zata dora din bata da shi, dawainiyar da zata yi kafin fara dora girki kuwa a gida ta kwammaci kullun kawai ta rika siyan abincin tana ci yafi mata sauqi. Babu abinda ya dame ta yanzu tunda asirin ta a rufe yake yanzun a ganin ta. Damuwar ta bai wuce zagin da Hajja ke yawan yi mata ba ita da yarinyar ta, ta tsani kalmar nan da Hajja ke jifan ta da shi ta kuma kira yarinyar ta da shegiya...Hajjan na cin darajar Maman Abdul ne da kuma yawan shekarun ta baya ga haka da sam bazata iya cigaba da barin ta tana aibanta mata yarinya ba. Dalilin kenan da ya sanya zuciyar ta za6a mata daina zama a gidan tana fita yawon neman aiki yafiye mata...Hajja bata gansu bama balle ta bisu da kalami mummuna. Sai daga baya ma ta fahimci rashin zaman nata ba karamin taimakon ta yayi ba domin ta koyi abubuwa da dama daga cikin halayyar mutane wadanda ada sam bata san su ba. Cikin ikon Allah kwanakin fara fita aikin ta yayi ta fara zuwa tana aikin kamar yadda Hajiya ta tsara mata. Sai dai me ita Hajiyar a kullun gani take kamar muhimmancin da ta bawa yarinyar ya fi wanda ta bawa aikin ta, shiyasa ta kafa mata dokar sai dai fa ta nemi wurin saka yarinyar in har aikin zata yi dagaske in kuwa ba haka ba ta hakura da aikin ita zata iya neman wata daban... ba karamin tashi hankalin Zaitun yayi ba, tana matukar kaunar 'yar ta kamar yadda take tsananin son aikin nan na ta domin shine rufin asirin ta, wannan dalilin ya sanya ta nemi shawarar Maman Abdul kan batun, nan take kuwa Maman Abdul tace mata kar ta damu ita zata rika kula mata da yarinyar har taje ta dawo. "..um um Maman Siyama abin ai sai yayi miki yawa, ga yaran ki ga kuma Muphy? Kuma ma ai kinga yini nake yi kullun.." " kar ki damu Zaitun Insha Allahu hakan bazai zaman min matsala ba.." Maman Abdul bata kai ga rufe bakin ta ba suka tsinkayi muryar Hajja na fadin.." Allah ya sawwaka a cakuda min jikoki na da irin layi..." Maman Abdul ce tayi saurin cewa " Haba Hajja wallahi abin nan da kike yi babu dadi sam..." "..Toh ba sai ki fada min abinda ya kamata inyin ba Rahama..." Tayi maganar tana bankawa Maman Abdul uwar harara...Dukkan su shiru sukayi illah Zaitun dake dan sheshsheka a hankali, dan zuwa yanzun tunanin.ya fara cunkushewa, tana tsoron ta isa ga6ar da shekarun ta zasu gaza cigaba da daukan wasu abubuwan. Gyara tsayuwa Hajja tayi tana cigaba da fadin..." Ni dai na gama magana babu wanda ya isa ya caku'da min jikoki da 'ya'yan shegu in rainon take so ta kawo ni nan zan mata ta rika biya na..." Ta kai karshen maganar ne tana me ballan goron dake hannun ta. Ido sosai Mmn Abdul ta bude tana duban Hajjan da kyau wai ita zata yi raino a biya ta..bacin ko kadan bata taba nuna fuskar rahama ga yarinyar ba dai dai da rana guda, taya Zaitun zata iya sakin ranta ta bar mata rainon 'yar ta...tana cikin tunanin ta tsinkayi muryar Zaitun cikin kuka tana fadin "....Ni dai Hajjah dan girman Allah ki daina sheganta min yarinya, wlh yarinya ta 'yar halak ce ba shegiya ba...zan fi jin dadi ni ki dinga zagina akan yarinyar nan...". " Wannan kuma sai ki fadawa wanda bai san dan yau ba, ni din Zaituna ba ta yau bace halin 'ya 'yan zamani kuwa jimla jimla babu wanda ban sani ba, ban mayi shahada bane dana ce zan miki rainon inda ke wata ce gode min ya kamata kiyi ba kuka ba...mthew ta karashe da jan tsaki tana komawa dakin ta. Maman Abdul ce ta kwantar mata da hankali tare da nuna mata cewa kar ta wani damu tunda tana gida ga kuma Siyama tunda anyi hutun makaranta tayi mata alkawarin bada dukkan kulawar ta ga yarinyar koda kuwa tana wajen Hajjan kamar tana wajen tane. Da kyar Zaitun ta yadda ta amince da batun sai dai tana ji cikin ranta cewa daidai da rana guda idan taga rainon bai mata ba zata bar aikin ne kawau gaba daya ta cigaba da kula da 'yar ta inyaso tai ta yawon neman aikatau din goye da 'yar ta duk da tasan hakan yafi wahala amma gwamma hakan da ta zuba idanu tana gani ana cin zarafin yarinyar nan. Maman Abdul ce tace mata kuma kar ta daga hankalin ita Hajjan yawan kudi bai damin ta ko dubu guda ta bata idan lokaci yayi bazata raina ba. Sai da ta koma daki tayi zaman lissafi, kenan idan ta bada dubu daya na rainon Mufeeda dubu biyar ne zai rage mata sam bata damu ba duk da raguwar adadin kudin dan matukar zai ishe ta hidimar yarinyar aganin ta shikenan ita kam me zata saie nema, Mufee ne kadai damuwar ta kuma ta tabbatar dubu biyar zai ishe ta tayi mata duk abinda ya dace da shi kowani wata. Da haka ta amince ta fara barin Mufee a gida, amma tana wajen aikin hankalin ta a rarrabe da kyar ta fara sabawa da rashin Mufee kusa da ita...kullum idan ta dawo da dare sai tayi wanki saboda kayan ta ba yawa ne da su ba...itama Mufeen tana so ta kara mata wasu kayan sawan amma bata da sukunin yin hakan saboda karancin kudaden ta. Fara barin Mufee a gida da kwanaki goma sha daya Baban su Siyama ya dawo daga tafiyar da yayi ya dawo ne cikin dare bayan har Zaitun sun yi bacci, dan ita har ga Allah bama tasan da dawowar shin ba kasantuwar bacci da yake mata nawi musamman saboda gajiyar take yini kwasowa wajen aiki kuma Alhamdulillah tunda ta fara barin yarinyar bata ta6a zuwa ta same ta cikin yanayin da zai sosa ranta ba kamar dai yadda Maman Abdul tai mata alkawari. Tun wayewar gari da taci karo da mutumin ta fahimci cewa ba mutumin kirki bane shi musamman saboda yadda yake binta da wani irin kallo. ..Shi kuwa ta 6angaren ta tun ganin sa da ita na farko yaji yarinyar tai masa a ransa, sai dai da yake tun da safe da yaje gaida Hajja tayi masa bayanin Zaitun din a yadda ita ta fahimta yasa tunanin sa canza wa...kamar an tambayi Hajjan ko kuma ance tai masa bayanin ta. ...Ashe matsala guda tak da Maman Abdul din ke fuskanta daga maigidan nata kenan saboda muguwar halayyar sa ta neman mata, wanda akansa ne kadai suke yawan samun matsala da shi. Ko lokacin zuwan Zaitun gidan ashe Maman Abdul bata dade da dawowa daga gidan su ba in da ta tafi ta barwa Hajja yaran saboda takaicin halayyar Mijin nata, kwanaki kalilan da dawowar ta Hajja ma tace zata je wajen 'yan uwan ta huta saboda bar mata yaran da Maman Abdul tayi ba karamin jinjiki tayi ba kafin ta dawo acewar ta dole itama taje ta huta, shiyasa ko lokacin zuwan Zaitun din ta samo kofan Hajjan a garkame, bayan tafiyar Hajja washe gari shima Baban Abdul ya tafi shine sai jiya ya dawo. Sosai Maman su Abdul ta tsani wannan halayyar tasa gefe guda kuma tana tsoron ya debo mata wata cuta...duba da irin zamanin da ake ciki yanzu. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya wa Zaitun wani iri, sosai mutumin nan ya matsa mata ya sa ta gaba da kallo da shishshgi wataran har dakin ta yake shiga wai ya siyowa Feefy biskit Zaitun kamar tayi ihu take ji dan haushi amma haka ta basar. Sam mutumin bai mata ba, sosai ta tsani ganin sa har Allah Allah take yi ta bar gidan saboda shi. ...Mufee na shan wahala a wurin su Siyama dan karfi da yaji rainon ta ya dawo hannun su musamman da yake yanzun su ke yini da ita a gida. Kwatsam sai aka wayi gari kanin Maman Abdul ya rasu ta shirya ta tafi gidan nasu...bata dawo ba kuwa har kusan kimanin sati uku...aka barwa Hajja su Abdul da Siyama ga kuma yarinyar Zaitun itama. Yarinyar har 'yar rama tayi dan bata samun kula yanda ya dace kamar yadda take samu a baya, Ceralac din ma sai lokacin da aka ga dama ake bata...a hakan ma wani sa'in sai su Abdul suzo su shanye mata sai daga baya ne Hajjan tayi dabarar ajiyewa saman wardrop ganin kamar Zaitun din bata jin dadin yanda yake karewa cikin kwanaki kalilan. Har targade su Siyama suka yiwa hannun Mufee ranar Zaitun tasha kuka kamar ranta zai fita, ranar Hajjan da kanta ta kai ta wajen gyarawa bisa jagorancin Baban Abdul Zaitun sai da tai kwana uku bata leka wajen aikin ta ba, ranar da ta tashi komawan ma da Feefyn taje goye abayan ta nan matar ta tuhume ta, Zaitun dalili ta sanar da ita sai tace ai shikenan amma yanzun ma har ta riga ta nemi wata mai wanke wanken ita kuma sai dai ta koma kitchen sannan aikin cikin kitchen bazai yiyu tana tare da yarinya ba. Haka dole washegari ta baro Feefyn agida jikin ta sanyi qalau, sai da ma tayi mata addu'o'i kafin ta baro ta. Hankalin ta baya ta6a kwanciya kuwa har sai taga ta dawo gida. Amma daga ranar da Maman Abdul ta dawo gidan ne fargaban Zaitun ya kare kaf. Sai dai kuma wata sabuwar fitina da Baban Abdul din ya tsiro da shi ne yake damin ta, ko kunya baya ji ballantana tsoron Allah, dan har wajen aikin ta yake binta idan ya daidaici lokacin tashin su ya kusa sai ya jira har ta fito dan komawa gida anan ne zai ta mata maganganun banza...har zuwa inda suka rabu sai ya dau wata hanyar ita kuma tayi gida, bata ta6a tanka masa ba, kamar yadda bata ta6a gigin sanar da kowa ba, dan Maman Abdul tai mata halacci arayuwar ta, halaccin da bai kamata ace taji wannan irin maganar daga gareta ba. Kuma wani sa'in bata ganin laifin sa domin ba shine mutun na farko da ya fara yi mata kallon marar kamun kai ba amma tuntuni ta kar6i hakan ta kuma shiryawa wanda zai biyo bayan wannan din ma ko da ace munin sa ya zarta hakan ne, in dai akan Mufeeda ne zata iya juran komai da za'a mata a shirye take ta fuskanci koma wani irin kalubale matukar abin ita kadai zai shafa batare da yarinyar ba. Zuwa yanzun ta gama fahimtar inda mutumin ya dosa amma bata ta6a tankashi ba, in dama Allah ya taimake ta ba yinin gida take yi ba in kuwa ta dawo gidan bata ta6a gangancin barin kofar ta abude gudun kar ya shigo mata..komin zafi haka zata rufe musu kofa kirib gashi su ba fanka ne da su ba..haka zata hana idanun ta bacci tayi ta wa yarinyar fifita da wani dan kwali da ta yago kwanaki. Farin ciki take ji idan taga yarinyar ma bacci cikin kwanciyar hankali. Burin ta a yanzu bai wuce taga Baban su Abdul ya koma inda ya fito ba. Zuwa yanzun Mufeeda nada watanni hudu cif ne da haihuwa tuni ma tafara koyon zama haka tsab ta gama gane Zaituna duk da bata kiyuya amma kaunar da take nunawa ga Zaitun ta musamman ce...kuma a yanzun ne Zaitun ta fara shawarar canza mata abinci a karo na uku. Dan bayan Madara da ta fara bata Maman Abdul ce ta fara bata shawaran ta hada mata da ceralac daga lokacin da ta cika watanni biyu zuwa yanzun da take da wata hudu. A yanzun kuwa tayi tunanin fara bata kila shima zai taimaka wa yarinyar, dan har ga Allah yadda taga yarinyar tata 'yar fiyot babu girman jiki abin baya mata dadi..shiyasa ta dage take aiki tukuru dan ganin ta kula da ita sosai amma duk kokarin ta a kullun gani take tamkar ta gaza. 😘 [20/9/2022, 12:32 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE* 💕 *( 'Yata ce)* *Salmerh MD* 🅿️...5 ....Adam shi ya fara koyawa Mufee kiran sa da Daddy dan acewar sa da izinin Allah karkashin inuwar gidan sa Mufeeda zata taso shiyasa gwamma ta saba tun yanzu. Ya jima da fallasawa Zaitun asirin zuciyar sa sai dai har yau din nan bai samu gamsashshiyar amsa daga wurin ta ba, yayin da Zaitun ke tsananin mamakin Adam, kokadan bata ga dacewar su ba, Adam kyakykyawan matashi ne 'dan gayu ga ilimi ta kowani fanni yana da shi. Sau da dama ma takanyi mamakin yadda yake cinye musu lokacin sa wajen ganin ya faranta musu ita da yarinyar ta dan farko ma kokadan bata sake masa fuska sai da Maman Abdul ta dage kafin ta dan fara sakewa sai gashi Adam ya shigar da haske cikin rayuwar su sosai suka canza ita da 'yar ta batare da tasan takamamman lokacin ba. Adam shike dora mata karatu da kansa kullin idan yazo yakan bata hadda kuma Alhamdulillah tana kokarin ganin ta kawo haddan ta adaidai. Yaso ta shiga Islamiya tun yanzun amma yace baya so ya dakatar mata da aikin ta tunda yini take amma da zarar sunyi aure dole ne ya sata a amakarantar Islamiya hadda boko. Ba karamar rawa Adam ya taka cikin rayuwar Zaitun ba shiyasa a yanzun take matukar girmama al'amarin sa. Hajja tasha yada musu habaici bayan ta ta6a binsa har kofar gida watarana da ya zo bayan Zaitun sun shigo gida. Zaitun dai bata san me Hajjan tace da shi ba amma tasan ba magana me dadi bace..abin mamaki Adam ko dis maganganun Hajjan basu dadashi ba ganin hakan yasa Hajja ringa sakin habaici idan ta ganshi bai ta6a daga ido ya dube ta ba..." Sau 'daya tak ya ta6a bata amsa inda yace"..Mama ai ita kaddara babu kan wanda bata iya sauka kuma in ma abinda kike tunani kan Zaitun hakan yake ai ni ne da kaina nace naji na gani babu wanda ya tilasta ni.." Daga ranar bai sake tanka Hajjan ba har ta gaji da ganta ta sarara masa. Ita kuwa da tasan halin Hajjan tasan ba sabon abu bane indai akan ita da 'yar ta ne. Adam ya nuna musu zallar kauna ya fito musu da martabar su ya kuma nuna wa duniya cewa su din wasu ne masu daraja, su din mutane ne masu matukar muhimmanci a idanun sa. Ita kuwa a ganin ta me zatayi ta sakawa wannan bawan Allah da ya wuce ta bashi dama wajen ganin ya cimma muradin sa. Baban su Abdul kadai ne damuwar ta a yanzu, kuma ko da wasa ko cikin mafarki bata tunanin zata iya aikata abinda yake nufin ta da shi, gashi da zarar ya tafi kamar tsungulin sa ake acan din yake sake dawowa gida, ada kafin zuwan ta gidan kamar yadda Mmn Abdul ta ta6a bata labari tace yakan shafe akalla watanni uku, hudu zuwa biyar bai zo gida ba amma ta lura tun zuwan da yayi ya ganta a gidan sai komai ya canza daga 6angaren sa, dawowa yake duk bayan wata guda, tsaraba kuwa daga ita har Mufee baya wuce su. Yayin da ta 6angaren Zaitun gwanin tan nasa bai ta6a birge ta ba, bata san dalili ba kam amma har cikin zuciyar ta ta tsani taga yayi musu wani abu makamancin kyauta ko wani abu ta tsani komai da zai fito daga hannun sa. Baban Abdul shine mutun na farko a tarihin rayuwar Zaitun da ya nuna kaunar sa ga Mufee wanda hakan bai birge Zaitun ba, bata kuma sanya shi cikin layin masoyan ta ba. Maman Abdul kuwa da ta riga ta gama fahimtar inda mijin nata ya dosa sosai take mamakin sa ganin cewa abin nasa har na cikin gida bai bari ba. Sau da dama ya kan siyo abu dangin sitira, kayan wasa ko kuma kayan tea ya bata yace ta kaiwa Zaitun din kuma bata ta6a jin haushin hakan ba duk da cewa ta san dalilin sa nayin hakan, amma kuma bata ta6a jin haushin Zaitun kan lamarin ba saboda ta riga da ta san da wa take zaune. Tsoron ta daya kar wannan mugun halin nasa ya kai shi ga janyo musu abin kunya watarana, dallilin kenan da ya sanya kawai saboda ta canza tunanin sa yasa da kanta ta bashi shawaran auren Zaitun din duk da tasan abu ne mai matukar wahala Zaitun ta amince da shi, ko Adam ma da yaya ta amince masa ballantana Bbn Abdul, gefe guda kuma ga Hajjah ma tasan ko sama da kasa zasu hade bazata ta6a barin sa ya auri Zaitun din ba domin ita datake zaune dasu itace tasan adadin irin kiyayyar da Hajjan ke musu. Maman Abdul bata yi mamakin irin tsantsan farin ciki da mijin nata ya nuna ba sakamakon wannan shawara da ta bashi...sosai ya kasa 6oye farin cikin sa. Ido kawai ta rika binsa da shi cike da mamakin sa, da farko wasa ta dauki lamarin amma ganin yanda ya kar6i zancen ya sanya itama dole tunanin ta ya canza nan take...aganin ta bata da wata hanya ko mafitar da ya fi mata wannan din a yanzu, domin Allah ya riga ya hada su hadda rabon haihuwar 'ya'ya..baya ga addu'a da kullun take faman yi tana mika kukan ta ga mahalicci dole ne kuma ta tallafo shi ta wani 6angaren in har hakan ba zai zame musu matsala ba baki 'dayan su..idan auren sa da Zaitun alkhairi ne tana fatan Allah ya tabbatar musu da shi in kuwa sa6anin hakan ne Allah ubangiji ya canza musu da mafi alkhairi. Ta riga da ta gama fahimtar waye Zaitun, ba tun yau tasan halin ta ba ta kuma fahimci asalin dangantakar dake tsakanin ta da Mufeeda, Zaitun ba ta da wani mugun halayya da zai sa aki ra6ar ta saboda shi dan haka bata da matsala da ita matukar zai kula ya daidaita adalcin sa tsakanin su ita me goya masa bayane cikin ko wani irin hali. Baban Abdul bai yi kasa a gwiwa ba wajen bayyanawa Zaitun kudurin sa da soyayyar da yake yi mata da kwarin gwiwar sa musamman da yake ya gama samin license din ne daga wajen Matar sa Rahama ( Mmn Abdul)..Zaitun kam maganar tasa ya matukar tada mata hankali. Ta yama karamar kwakwalwar Baban Abdul take tunanin ita zata iya auren mijin Matar nan? Mace mafi karamci agare ta mace mafi kyautatawa sai a wayi gari kuma ita Zaituna ta tashi daga matsayin makwabciyar ta ta koma Kishiya...inaa bata fatan faruwar hakan har abada. Daren ranar kaf bacci kaurace wa idanun ta yayi, bayan kukan da ta sha da tunani ta karasa wayan garin ji take komai ma a baibai yake zuwa mata ita. Da yake Baban Abdul kamar a matse yake wajen ganin ya auri Zaitun din hakan yasa bai 6ata lokaci wajen sanar da mahaifiyar sa ba wato Hajja duk da cewa bai ji koda furuci guda daga bakin Zaitun din ba bai kuma san inda zuciyar ta ta fuskan ta ba amma zumudin da yake ciki ya kara bashi kwarin gwiwa da kyautata zaton zata amince dan shi duk zuwan da Adam ke yi ma basu ta6a haduwa ba balle yayai tunanin yana da wani rival. Ranar kuwa yaga tijara wajen Hajja, da asuban fari lokacin da yaje gaida ta ya sanar da ita kudirin nasa wanda a lokacin kowa na gida babu wanda ya fita ciki kuwa hadda Zaitun. 'Karan hargagin Hajja ne ya maida hankalin Zaitun ga wajen kawai sai ta dafe kanta dai dai lokacin da kunnuwan ta suka tsinkayi muryar Hajjan na fadin..." sai kace da suna Saratu aka yanka min ragon suna, wlh koda mata sun kare a duniyan nan bazan ta6a amincewa ka auri Zaituna ba...kai ko da bayan raina ne ma ban amince ka aure ta ba, kai baka da hankali ne shin? baka ganin abinda ke tare da ita ne ko kuwa kasan dalilin da ya sa ta tsamo jiki daga cikin 'yan uwan ta zuwa nan...wlh ka kiyaye ni Ibrahim tun wuri ka dakatar da wannan zancen kafin in ci maka mutunci a gidan nan...". Bata ji me Baban Abdul din ya fada ba illah muryar Hajjan da take sake jiyowa kasa kasa" Banda lalacewa ta zamani dubi 'yar yarinyar nan da har a yanzun tan ma bai wuci ace tana jikin mahaifiyar ta ba amma shine hadda goyon shege..ni an gaya maka da ace ina da dama da tuni ban jima da sallaman ta daga gidan nan bane, kawai dan bani da damar hakan ne amma ina dalili mutun ya gama biye biyen titi da kwararo kai kuma kazo ka zauna da shi salon ya gur6ata maka zuri'a in ba lalura bama me zai sa in amince da hakan, kai kuma dayake gaula ne shine wai har ka abin aura anan, toh ahir dinka wallahi Ibrahim har abada bada yawuna ba...". Duk da cewa har cikin zuciyar ta kalaman Hajjan suka soke ta kokadan basu mata dadi ba amma ta wani 6angaren na zuciyar ta ji tayi kalaman sun faranta mata. Tun kuwa da taji kalaman Hajjan sai ta dan ji natsuwa, ko ba komai yanzu tasan maganar auren zai sha ruwa tunda Hajja mahaifiya ce dole kuma ya bi maganar ta. Duk yadda yayi da Hajja kuwa kin amince masa tayi karshe ma tace da kudin da zai yi auren gwamma yaje ya karasa ginin gidan sa su koma can ta rabu da alakakai in kuma ba zai yi hakan ba toh ya biya mata kudin jirgi ta koma ta sake sauke farali dama ta dade da zuwa tun mahaifin ta na da 'dan abin hannun sa lokacin ya biya musu ita da mahifiyar ta suka je farkon auren ta da mahaifin Baban Abdul din tunkan ta san zata haife shi ma. Kwana biyu kwarara Baban Abdul bai kara yi cikin gidan ba ya kara gaba saboda haushin Hajja ta hana sa cika burin sa na auren Zaitun. Ita kuwa daga lokacin rayuwa ta kara yi mata dadi dan babu me takura mata yanzu, Hajja ce kadai taga ta sake ninka tsanar da tayi mata abaya amma dayake tasan dalilin sam hakan bai dame ta ba. Daga karshe ma daina ganin Hajja tayi a gidan bata san ina ta tafi ba bata kuma tambayi Mmn Abdul ba dan itan tun asali ba gwana bace wajen cusa kai in da ba hurumin ta ba. Zuwa lokacin kuwa tuni Maman Abdul ta yaye Ahmad shiyasa Mufeedan ta ke samun cikakkiyar kulawa. _Salmerh_ 😘 [20/9/2022, 12:32 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE* 💕 *( 'Yata ce)* *Salmerh MD* 🅿️...4 ......Bata yi kasa a gwiwa wajen fara bawa yarinyar kunun ba sai dai me kokadan Feefy bata son shi, idan ta bata ma ta rinka amai kenan sam ta rasa dalilin hakan..gefe guda kuma tsananin tashin hankali take shiga idan taji ko ta ga yarinyar cikin wani irin yanayi. Maman Abdul ce ta bata shawaran cigaba da bata a hakan inda a hankali zata saba da shi tunda watannin ta sun riga sun kai gejin da zata iya sha din. Inda tace ai ba dan ma shakkan zuciyar Zaitun da take ji ba da tuni yarinyar ta jima da fara cin abinci dan ko ba ita ba hatta su Siyama sun so su fara bata abinci idan suna ci amma Maman sun ke hana su. Ido Zaitun ta waro kan Maman Abdul din.." bakya ganin tayi karama ne Maman Siyama watannin ta hudu ne fa kacal ko zama me kyau ma yaushe ta fara shi, ni da cewa ma fa sai ta kai watanni takwas kafin in fara bata abinci". "..ahh haba har watanni takwas be yi yawa ba Zaitun, wai ni tausaya miki nake ne duba da yadda kike ta fadi tashin nan.." "...saboda ita duk nake yi ai Maman Siyama" "Nafi kowa sanin hakan Zaitun shiyasa nake so ki dan sassauta afara bata kunun yanzu muga yadda hali zaiyi.." Zaitun bata sake musu wa Mmn Abdul din ba, dan tasan duk abinda matar ke dora ta akai bai ta6a cutar da ita ba, bata ta6a dana sanin bin shawaran Mmn Abdul ba dan haka wannan din ma tana da yakinin Insha Allahu bazata yi ba. Kudi kawai ta bawa Mmn Abdul din ita ta aika aka siyo gyada ta gyara aka marka'da mata dashi ake yiwa Feefyn kunu amma ba'a saka mata tsamiya shiyasa duk ranar da Zaitun ta samu sukuni ta kan kara mata garin madara akai. Cikin rashin sa'a Mufeeda sam bata son kunun nan in an bata dawo dashi take yi in an matsa akai mata dura kuwa..haka zata harar da shi gashi ta rika kuka kenan taki yin shiru. Hankalin Zaitun tashi yake idan taga hakan, cike da marairaita idanu ruwa ruwa ta dubi Mmn Abdul tace" dan Allah a daina bata haka nan Mmn Siyama ki ga fa yadda take kuka.." " Ki bari a hankali zata saba ne, ba'a biye ta yara Zaitun in ba ke bama har tsawon wani lokaci zaki dauka kina wannan hidima da celarac da madaran bacin ina da tabbaci ko cikin ki baki bashi kula yadda ya dace kwatankwacin yadda kike bawa yarinyar nan, dubi kanki fa Zaitun sittirar kirki baki sawa baki damu da duk wani farin ciki ko jin dadi naki na kanki ba, takalmi idan kika siya kika fara amfani dashi ke da canza sa har sai ya daina amfanuwa a kullun ke dai Mufeeda! Mufeeda!!..babu abinda Mufee ta rasa a yanzu, kema ki ringa yiwa kanki adalci dan Allah Zaitun". Jikin Zaitun sanyi yayi sosai..tarasa meyasa a kullun Mmn Abdul ke gani kamar ta zurfafa a kaunar da take yiwa Mufee ne, bata san cewa ita din ita ce jigon farin cikin ta ba ne, baya ga hakama alkawari ta daukan ma kanta cewar zata zame mata Garkuwa, ta kula da ita gami da bata kariya ta ko wani irin fanni matukar hakan bazai sa ta sa6awa mahaliccin ta ba. Kalaman Mmn Abdul sosai ya sanyatar mata da jiki, hakan yasa bata kara magana ba ta jure kawai aka cigaba da bawa Mufee kunun nan ahakan kuwa tun bata so har tazo ta saba da shansa. Watannin su shida a gidan fitinar Baban su Siyama ya ishe ta sosai, dan har kara ramewa tayi saboda damuwa, tuntuni ta fara tunanin barin gidan amma zuciyar ta ta kasa tsaida mata inda ya kamata bayan nan din, kuma ma takan tambayi kanta da wani kudin zata sake neman hayar, ko nan din ma albarkacin wancan kudin dake hannun ta ne kuma tuntuni da jimawa labarin su ya shude, 'dan wanda ake biyan ta wajen aiki kuma hidimar kanta da ta Mufee ba barin kudin yake sukai wani lokacin ba, dan ma ahakan Mufeeda kadai take siyawa abinci ita kam lissafin cin abincin ta a cikin kudin duk babu shi. Da gari ya waye idan ta tashi ta dama kunun Mufee ta juye cikin 'yar teaflask din da Mmn Abdul ta bata shawaran siya ta kuma bata shawaran siyan karamin kettle tunda ba girki take yi ba duk wani hidimar ta ta ruwan zafi ce. Wankan ta da na Mufee sai 'yan wankin kayan da Mufeen ta kwana da shi da yake koda wasa bata yadda ta rabu da omo a dakin ta da sabulu sai dai in abin yafi karfin ta ne. Da zarar ta gama da yarinyar shikenan sai ta shirya ta wuce wajen aikin ta tuni ta cire batun yin breakfast a tsarin rayuwar ta..abincin da ake basu na rana a wajen aikin shine kullun mahadin breakfast da lunch dinta, ta jima da sabawa cikin ta da hakan. Sai kuma in ragowar na siyarwar ya rage zuwa lokacin tashin su Hajiya Talatu nada halaccin bar musu su raba tsakanin su duk da irin hakan ba kullun yake faruwa ba amma duk ranar da hakan ya farun ba karamin faranta ran Zaitun yake ba. Duk iya zaman ta a wurin kuwa mutun guda daya tak ta saba da shi wato _Adam_. Adam ya kasance 'da ne ga kanwar Hajiya Talatu da ta rasu shekaru ashirin da biyar baya wanda bayan rasuwar mahaifiyar sa rikon sa sai ya dawo hannun Hajiya Talatu kuma shi kadai gare ta Allah bai ta6a bata haihuwa ba, tayi aure har mazaje uku amma bata samu rabo da ko guda daga cikin su ba, shiyasa gaba daya ta hakura da maganar aure ta kama sana'ar ta wanda aganin ta yafiye mata yawon auren duba da cewa shekarun ta sun riga sun ja me kuma zata sake nema bayan taga ta inganta rayuwar marayan danta guda 'daya tilo da Allah ya bata. Dalili kenan da ya sanya ta dauki son duniya ta daura akan Adam. Farkon zuwan Zaitun wajen bata ta6a ganin sa ba ashe baya gari ne lokacin yana can kudancin kasar nan wajen bautar kasa..dan Hajiya Talatu ta tsaya tsayin daka wajen ganin ta bashi ilimi ingantacce. Bayan dawowar sa ne Zaitun ta lura da shi da kusan kullun sai yazo wajen musamman da rana yakan zo yaci abinci ya kara gaba. Kuma sau tari idan Hajiya na bukatan wani abin shi take kira ya siyo mata na kayan abincin da ake amfani da shi a wurin ko wani abu daban...sosai Zaitun ta lura da sauqin kan da Adam ke da shi da kuma haba haba da jama'ah dan duk lokacin da yazo wurin sai yayi musu sannu da aiki bai ta6a binsu da mummunan kallo ba duba da cewa karkashin mahaifiyar sa suke aiki. Zaitun bata ta6a zaton Adam ya san da zaman ta a wurin ba sai ranar da ya kasance bata zo wajen aiki ba sakamakon zazza6in hakori da Mufeeda ta tashi da shi. Daga chemist da ta kai yarinyar ta yanke shawaran zuwa wajen aikin ta tai bayani dan kar Hajiyan taga shiru kuma ba wani bayani. Bayan ta gama da Hajiyar ta fito ne kan hanya suka ci karo da Adam inda ya bita da kallo..." wannan ba Zaitun bace..?" Yayi tambayar yana me juyowa ya dube ta cike da mamaki yake sake yawo da idanun sa kan Zaitun din. Tsayawa tayi tace nice tana kakalo murmushin da iya fuska kawai ya tsaya mata dan ita kadai tasan irin halin da take ciki hakan ma dan mai Chemist din da taje dazun ya kwantar mata da hankali da faddin ai ba wani abu bane zazza6in fitan hakori ne kuma shike sata gudawan da ta kwana tana tsula tsulawa, shine ya tashi hanakalin Zaitun gari na karasa wayewa ko Mmn Abdul bata san da fitar ta ba balle tasan abinda ke faruwa. " Ina kwana" tace da shi tana mai kawar da duban ta daga gare shi dan ba saba magana tayi da shi irin hakan ba sam- sam ma bata san cewa har sunan ta ya sani ba inba yanzu da ya ambata taji ba. Adam bai bi takan gaisuwar da tayi masan ba illah tambaya da ya sake jifan ta da shi.." Ina zuwa haka ko yau din babu aikin ne...?" " a a akwai ni din ce dai bazan samu daman yini wajen aikin ba..." Bata ma kai ga rufe baki ba yace " saboda me..hala matsala aka samu tsakanin ki da Hajiyar ko..?' " Da alamu wannan ya kware wajen zayyano tambayoyi." Wannan maganar cikin zuciyar ta ne tana me yatsina fuskar ta. A fili kuwa kai ta girgiza masa.." ba haka bane...'YATA CE bata jin dadi shiyasa". Cike da karin mamaki ya zaro idanu " 'Yar ki..? ya tambaya yana me jin tamkar mashi ta caka masa a kahon zuciya.." dama kina da 'ya ne ban ta6a sani ba Zaitun?" "Da yake bada ita nake zuwa wajen aikin ba shiyasa ba kowa ya santa ba.." " Ya subhanallahi!" Ya furta a fili gami da kasa 6oye mamakin sa. Sam bai zaci Zaitun tana da yarinya ba, bai ta6a kawowa aransa hakan ba duba da irin karancin shekarun ta, amma me yasa jikin ta bai nuna alamun hakan ba, duba daya zaka mata ka fahimci zallar kuruciya tattare da ita, ko yanzun ma da ya lura bayan ta da goyo bai kawo aransa cewa goyon nata bane...me kenan? me hakan ke nufi wai?" Yayi wa kansa wannan tambayar yana me shafo gashin gansa daga keya har mafitan gashin. Ba ya san yarda da irin amsar da zuciyar sa take shirin basa akan yarinyar...ji yayi jikin sa duk yayi sanyi. Sake 'daga idanu yayi ya bi bayan ta da kallo duk da cewa tayi nisa da inda yake tsaye yanzun amma bai daina hango bayan ta. Haka ya juya zuwa inda ya tunkara yana 'daga kafafu da kyar, dama wajen Hajiyar sa zashi da yake basu hadu da safiyar yau din kwata- kwata ba bisa ga rashin kwana da bai yi a gidan ba. Washe gari da yamma kamar wasa sai taji ana sallama daga mashigar gidan da yake itace ke farko zata fi kowa saurin jiyo duk wani motsi da ya tunkaro gidan nasu. Ko da ta leko sai taga yaro ne" ka karasa ciki mana ai daga nan masu gidan baza su jiyo ka ba..." Tayi maganar tana mai shirin mai da kanta data leko cikin dakin ta. Yaro kam da ya san wajen wa aka aiko sa sai cewa yayi " Wai ana magana da Zaitun a waje.." Abinda taji yaron ya fada kenan da ya sanya ta tsayawa cak, ba ita kadai ba hatta tunanin ta sai da ya tsaya na wasu sakanni illah bugun zuciyar ta da ya kara sauri, lokaci guda tunanin ta ya dawo sai kuma ta lula can baya can a wancan lokacin da Abbale kadai ke aikawa ayi kiran ta kamar hakan dai. Da sauri ta sake dawo da kanta sai dai madadin lekawan wannan karan gaba dayan ta ta fito dai dai lokacin da yaron ya juya zai maida aikan ganin bai samu gamsashshiyar ansa daga wajen ta ba. "..Baka ji ba..?" Da sauri yaron ya waigo...sai lokacin ma ta lura ashe dan makwabtan su ne duk da ba wata shakuwa ce tsakanin ta da gidajen ba amma yau da gobe tasa tana iya gane su. " Wa ke magana da Zaitunan..?" Ta tambaye shi tana mai kure shi da idanu. " Wani ne..nima ban sanshi ba". " Je ka tambaya sai kazo ka fada min kaji.." Kai ya yaron ya dage mata gami da juyawa. Ita kam tsaye tayi tama kasa 'daga kafafuwan ta..tunanin ta ya kasa bata shin waye zai zo neman ta...kar dai!...kar dai!!...kai um um bana tunanin hakan, amma ai shi kadai ne nake da yakinin zai iya nemo inda nake a duk fadin duniyar nan domin shi kadai ne ya damu dani shi kadai yake min kauna da dukkan zuciyar sa...amma taya YA BUKAR zai gano inda nake...a tunani na nayi tafiya me nisan da ni kaina bazan iya kiyastawa ba. " Wai yace Adam ne daga inda kike aiki...". Wata shegiyar ajiyar zuciya Zaitun ta sauke da ita kanta bata san ta menene ba sai dai tana da tabbacin cewa na jin cewa ba Yah Bukar ne me neman nata ba kamar yadda tayi hasashe, 'dan takaitaccen bayanin da yaron yayi ya sanya batare da dogon nazari ba ta fahimci waye ne..kuma tana da yakinin shima din yayi hakan ne saboda tayi saurin ganewa. " Ba mamaki Hajiya ta aiko sa". Ta fada a fili gami da komawa ciki. Babban Hijabin ta da tun iya zaman ta shine kadai yalwataccen Hijab data mallaka kuma take matukar ji da shi shi ta sanya kalar Navy Blue sosai ya fito mata da kalar madaidaicin hasken ta ras. Sai da ta gyarawa Feefy kwanciyar ta ta sake lullu6e ta saboda yanayi na sanyi da ake ciki sannan ta fita cikin natsuwa take takun ta kokadan Zaitun ba rawar kai tattare da ita. Sallama tayi da 'yar muryar ta da baya fita da hayaniya. Saurin waigowa Adam yayi yana me sakin kayataccen murmushi.." Barka da zuwa..fatan anyini lafia?" Ta hada duk lokaci guda dan rasa ma yadda zata tarbe shi tayi, gefe guda kuma zuciyar ta na taraddadin abinda ya kawo sa..tsoron ta daya kar Hajiya Talatu ta aiko sa da mummunan sako, sam bata so ta rasa aikin ta musamman saboda rufin asirin su ma itada Feefyn ta. Bai amsa gaisuwar da tayi ma san ba sai ma gyara tsayuwar sa da ya sake yi karo kusan na uku kenan" Sai naga wai kamar ba'a yi maraba da zuwan nawa ba, kar dai in takura ki Zaitun dan ni har abada bana da burin shiga hakkin rayuwar ki...." Duban ta takai gare shi a karo na farko suka hada idanu take sai kuma ta kawar da idanun ta amma hakan bai hana Adam fahimtar me ke cikin zuciyar ta ba a lokacin dan kai tsaye ya fahimci kallo ne me cike da tarin tambayoyin da ba lalle nexta iya furta su ba dan haka sai cewa yayi" Gani nayi kamar a 'darare kike irin ba a son ranki na fito da ke a irin lokacin nan ba". " Ni..ba haka bane..me Hajiya tace ka fa'da...min?" Tayi maganar muryar ta na rawa sosai shiyasa duk maganar tata ya kasance a rarrabe. Sai yanzun ya fahimci damuwar Zaitun din 'karara sai ya saki murmushin sa me burgewa, wani 'dan madaidaicin bishiyar Nyim dake gaba da su kadan ya kaiwa duba cikin daddadar muryar sa yace..." Nifa ba Hajiya ta aiko ni ba, ki kwantar da hankalin ki..yarinyar ki nazo dubawa ya jikin nata yanzu..?" Tsabar jin dadin cewa zuwan nasa bai shafi aikin ta ba ya sanya ta lumshe idanu cike da jindadin da ita kadai tasan abinta ta bashi amsa"..auu Mufeeda, jikin ta da sauqi Alhamdulillah dama zazza6i ne na hakori kuma na bata magani..." " Masha Allahu..Ubangiji Allah ya kara sauqi.." " Nagode sosai ka gaida gida". Ta fada tana kokarin juyawa cikin gida. "...Zaitun kenan!..dukkan alamu dai sun bayyana cewa bani da damar ganin Mufeeda ko..?" Dakatawa tayi daga tafiyar da tayi niyyan yi din, sai ta girgiza kanta.." Ba haka bane ba fa wallahi bacci take yi ne yanzun shiyasa.." "Babu damuwa in da rai ai wani lokacin zan ganta duk dama na fahimci 6oye abarki kike yi shiyasa tuntuni ban ta6a ganin ki tare da ita ba". Wannan karan kam bata ce da shi kala ba sai sallama da take sake kokarin yi masa. " Zan ma tafi ba sai an kore ni ba ai". Ya ce yana murmushi tare mika mata ledan hannun sa.." saura kice min Mufeeda bata bukatar su ni kuma inyi saurin fahimtar kadan suka yi.." " Yah Adam...!" " Dan girman Allah Zaitun ki ansa banason jan magana". Yadda yayi maganar ne ya sanya Zaitun 'daga hannu ta kar6a ba wai dan ranta naso ba sai dan ganin yadda yayi kicin kicin da fuskar sa. " Allah ya bata lafiya.." Ya fada yana me juyawa yayi tafiyar sa. Zaitun kam kasa motsawa tayi daga wurin zuciyar ta cike da wasi- wasi. Wannan shine farkon sabon ta da Adam da kuma dalilin sa wanda a hankali batare da ita kanta ta farga ba Adam ya shige jikin ta. Sau da dama yakan sayi abu idan ta taso wajen aiki ya bata yace na Mufeeda ne kuma tun lokacin da yazo gaishe ta da bata da lafiya bai sake zuwa gidan su ba sai bayan wani lokaci sannan ya sake yi mata bazata, ranar kam bai yadda ya bar kofan gidan ba har sai da Zaitun ta kawo Mufeeda ya ganta, bai 6oye yabawar sa kan yarinyar ba dan ko yaro karami ya dubi Mufeeda yasan yarinyar kyakykyawa ce ajin farko. Tun daga ranar Mufeeda ta shige ransa...hidima kuwa sai abinda ya karu, da kansa yakan siyo mata riguna masu kyau wadanda Zaitun tasan sai ta hada kudaden aikin ta na wata biyu ma kafin ta iya siyan irin rigar guda daya..takalma da komai na amfanin yara da zai fito da martaba da kyawun su Adam baya gajiya da siyawa Mufeeda su, in Zaitun tayi magana yace " Wannan yarinyar taki kalar 'yan gayu ce Zaitun barni in fito da ita, kuma ma baki so ne nima in samu ladan marainiyar Allahn nan" Dole Zaitun take jan bakin ta tayi shiru da yake da kanta ta sanar dashi cewa mahaifin Mufeeda rasuwa yayi tun yarinyar na jinjira ta kuma kara da fadin bata san kuma ina zata samu dangin sa ba shiyasa bata neme su ba. Ko da ya nuna mata rashin kama da yaga basa yi da yarinyar sai cewa tayi" Kamar mahaifin ta sak ta dauko har hasken sa shiyasa banbamcin kamannin su da ita ya fito fili. Adam kam batare da wani dogon nazari ba ya yadda da batun na Zaitun domin shi tun a kallon farko da ya yiwa Zaitun yaji ta shiga ransa, ko da yazo ya fahimci ta ta6a aure har da yarinya ma kaunar da yaji yake mata kokadan bai girgiza ba sai ma karuwa da yayi. Yasan a yadda yaga ta riki aikin nan dole tana cikin matsalar rayuwa ne shiyasa yake dan rage mata wasu abubuwan duk da kuwa kusan kullun sai ya dage kafin take kar6an duk abinda ya kawo mata. Ya jima da fahimtar yadda ta riga ta sadaukar da lokaci, 'karfi da jin dadin ta ga yarinyar shiyasa yake tsananin tausayin ta gami da tayata kulawa da yarinyar a fakaice. Ita kanta Zaitunan bai bar ta abaya ba..domin lura kawai yake da ita ya fahimci abinda take da karancin sa kawai sai taga ya kawo mata a bazata in taki ansa kuma ya nuna 6acin ransa shima. _Salmerh_ 😘 [20/9/2022, 12:32 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE* 💕 *( ' Yata ce)* *Salmerh MD* 🅿️...6 .....Wasa-wasa Bbn Abdul da ya tafi sai da ya shafe watanni uku cif bai waiwayo gida ba wanda yayi dai dai da cikan Feefy watan bakwai da haihuwa, Bbn Abdul sai dai aike kawai da ya saba yi musu ya cigaba...Mmn Abdul kadai abin ke damu domin tasan shirun nasa ba alkhairi yake shukawa acan din ba yayin da Hajja tayi mirsisi ko ajikin ta tamkar ba shi ne kadai kyautar da Allah ya bata na haihuwa ba. Tuni Mufeedah ma ta fara takawa kadan kadan ba karami dadi hakan yayi wa Zaitun ba ji tayi tamkar zata hadiye ta saboda farin ciki, hatta Adam sai da tai masa albishir washegari cewa Mufeeda ta fara taka kafar ta, bai boye farin cikin sa ba shima in da kara da alkawarin zuwa yaga tafiyar Mufee a ranar da yamma hadda guzurin dandasheshen takalmi. Matakin kaunar da Zaitun ke wa yarinyar bai ta6a yin kasa cikin zuciyar ta ba sai ma karuwa, zaku yi mamaki idan kuka a yadda Zaitun ke kwana da yarinyar bata ta6a bari Mufee tai juyi ba'a cikin jikin ta ba, kullun kan cikin ta take kwantar da yarinyar ta bata ta6a gajiya da hakan ba sai dai in gari ya waye lokacin in zata yi sallah sannan take kwantar da ita zuwa wayewar gari, shiyasa ko baccin rana mai kyau Mufeeda bata iyawa saboda sabo da jikin Zaitun da tayi. Zuwa yanzun kuwa tuni Mufee ta gama sakin jikin ta da kowa na gidan banda Hajja kadai da kullun kyara da tsangwama ce tsakanin su hakan yasa Mufee kokadan bata kaunar zama inda Hajjan take, yarinya ce amma tana da tsananin wayo da takatsantsan sosai tasan me kaunar ta da me kyarar ta. Su Siyama kadai ne abokan wasan ta sai su yini suna wasa bata damu ba in kuwa suna makaranta da Ahmad take wasan ta. In ka jiyo tashin dariyar Feefy toh kuwa da Siyama ne ko kuma Zaitun. Takan ci ko wani irin abinci yanzu shiyasa tuni Zaitun ta huta siyan madara sai dai dan hada mata shayi, dan kullun dare Mufee sai ta tashe ta tasha shayin nan. Duk lokacin da Zaitun ta dawo gida daga wajen aikin ta farin cikin Mufee bai ta6a 6oyuwa haka zata zo da gudu tana " Mammi!..Mammi..!!" Tana daga hannuwa sama tana dariya. Kamar dai yau ma hakan ne ya faru Zaitun na dariya ta dago ta sama " Oyoyo Mamana...oyoyo 'yan mata na.". 'Dago Mufeen da tayi idanun ta sak ya sauka kan gashin Mufee ta kalla ta sake kalla take sai ta dan dama fuskar ta tana duban Maman Abdul dake zaune tana jifan su da kayataccen murmushi da yake tasan me hakan da Zaitun tayi yake nufi. " Kwantar da hankalin ki Hajjaju ba ma tayi kuka ba...ke baki ga yanayin kitson bane bafa sosai na kama mata ba.." Murnushi Zaitun tayi itama tana lakutan kumatun Mufee tace" Kinyi kyau Feefy na, kin yi kyau sosai 'yar albarka.." Ta karashe da fadin" kuma fa kitson ya haska ta sosai, Mmn Siyama dole abaki tukuici tunda yake bata yi kuka ba...yarinya ta tayi kyau wlh.." Ta karashe maganar tana saukar da Mufee ta dago Ahmad da shima yake 'dago hannayen sa yana fadin.." Feefy.." Da son shima a daga sa. " Ahmadi na Feefyn ka yau an sha kitso an zama 'yan mata kyakykyawa..". " Dama asali mai kyau ce ita, ki ringa bari ana mata kitso kiga yadda yarinyar nan zata dawo, yau ma din kawai gashin ne naga kamar idan aka biye ta taki ahaka zai ta lalacewa shiyasa na kama mata kuma ma in ba a yi mata ai bazata saba da kitson da wuri ba..". Bata bi takan wannan zancen na Mmn Abdul ba kawai ta gaida Maman Abdul din tare da yi mata barka da gida da kuma ban gajiyar kula mata da yarinya da take yi kullun...yau din haka kawai take jin zuciyar ta wasai..shiyasa murmushi ya kasa barin fuskar ta. Biskuit, sweet da cheese balls da ta saba siyowa yaran yauma shi ta raba musu kowa ya ansa cike da annashuwa. " Bari in dan watsa ruwa yau din wlh duk na gaji sosai. Ko bayan shigewar ta Maman Abdul tunani kawai ta lula tana duban fuskar Mufee da kullun asalin kyawun yarinyar ke kara fitowa, musamman yanzu da yake Maman Abdul din na kulawa da ita sosai tamkar daga cikin ta ta haife ta...idan baka san Mufee tun farko da Zaitun ba bazaka ta6a tunanin yarinyar ta bace sam. Duba ma da yadda kalar hasken fatan su ya banbamta, hanci da idanun su kadai ne da suka zo iri daya baya ga haka babu abinda Mufee ta kwaso daga Zaitun din, sosai hasken ya kere na Zaitun nesa ba kusa ba. Tsananin soyayyar da Zaitun ke nunawa yarinyar ne yake matukar tsaya mata a zuciya, sosai abin ke sanya. Mmn Abdul tunani, da ace bata ta6a haihuwa ba kila da zata ce dan bata da 'da ne shiyasa bata san zafin su ko dadin su ba amma abin sam ba haka bane, soyayya ce zallah da ko da wasa bata hada shi da komai ba, ta jima da fahimtar irin sadaukar da farin cikin ta da take yi saboda yarinyar, kitso wannan sai da aka kai ruwa rana kafin Zaitun ta amince ta fara yiwa Mufee shi dan har ta kai watanni bakwai da haihuwa ba'a ta6a saka hannu cikin kanta ba dan yin kitso ba kuma gashin ba laifi tana da shi amma Zaitun sai dai ta taje shi in Maman Abdul ta matsa ne sai ta sa rubber band ta daure shi manya in ta ga dama uku in yayi yawa ne guda biyar, kuma taki yadda kowa ya sa hannun sa kan yarinyar, hatta Adam ya mata complain kan barin kan Mufeen ba kitso amma Zaitun sai ce masa tayi kuka zata yi idan aka kama kan. Babu yadda ya iya dole ya kyale ta. Watarana da tadawo tazo ta tadda an wa Mufee kitso shuku mai kyau ibra akalla zasu kai kwaya sha takwas bakaramin zaro idanu tayi ba cike da tashin hankali, dan kallo daya ta yiwa yarinyar ta fahimci tasha kuka wanda take kyautata zaton na kitson ne...yayi kyau kam ya kuma kara fito mata da kyau da hasken 'yar ta amma ita duk wannan ba shine gaban ta ba, the fact that Mufeeda tayi kuka shine kadai damuwar ta. Amma tayi kokari wajen ganin ta danne hakan saboda karamcin Maman Abdul agare ta yafi karfin wannan, a fili nuna jindadin ta da ganin kitson tayi inda ta yabawa Maman Abdul din sosai... Sai dai duk Maman Abdul na lura da ita, sarai tasan kukan yarinyar ya tsaya mata arai kawai basarwa tayi domin duk wani takun Zaitun din baya mata wahalar ganewa kawai itama sai tayi murmushi. Da sati ya zago kuwa Zaitun da kanta ta tsefe kitson nan tunda rana da yake asabar bata zuwa aiki dan haka da dare ta hana idanun ta bacci haka ta ringa lalla6a kan tamkar me lalla6a kwan da be gama kwari ba, da zarar ta motsa kuwa sai ta bari da haka har ta kammala mata kitson, kuma fa ba wai iyawa ta yi ba kawai dai bata san ganin an takurawa yarinyar ne sam shiyasa ta lalla6a tayi da kanta. Washe gari da Maman Abdul taga kitson dariya sosai tayi. " Wlh Zaitun baki da dama, yanzun wato rigakafi akayi mana shine kika yi wannan din ko? da ki bari ai mata mai kyau gara ki mata hana kuka da kanki.." Murmushi kawai Zaitun tayi tana shafa kan yarinyar tace"...Toh ba gashi ba asirin mu arufe babu wanda yaji kukan mu.." " Gara kuyi zuciya ai dan ni kam yanzu na fara indai bazaki mata da kanki ba toh kuwa kin ringa tarar da mu da jajayen idanu sai dai kiyi hakuri kawai" " Kai Mmn Abdul baki tausayin ta ne dan Allah..?" " Ba rashin tausayi bane ai ke ma din so nake ki rage ki na dinga sassautawa, kaunar da kike nuna mata sai inga kamar yana zarta iyaka, baki ji ba ne da hausawa kan ce kazo naka duniya ta 'kishi..." Bata yi magana a fili ba cikin ranta tace" Ko kowa ya ki ta ni ina son kayana" A fili kuwa daidaita zaman fuskar ta tayi da ta Mufeeda dake wasa da wani Balloon a hannun ta. Hannayen tasa gefe da gefen fuskar yarinyar ta lumshe idanu..." Kauna bata ta6a yin yawa Maman Siyama, ni gani nake ma tamkar da saurana cikin irin tarin kaunar da nake yiwa yarinyar nan, wannan halittar da kike gani itace bugun zuciya ta Mmn Abdul, itace farin ciki na, Mufeedah wata 6angare ce daga cikin rayuwa ta, ji nake daga ranar da tayi nesa dani tamkar anan rayuwa ta zata tsaya..'digan hawayen Mufeeda jin sa nake tamkar garwashin wuta cikin kirji na..." Cike da mamaki Maman Abdul ke duban ta cikin ranta ta furta " Allah mai iko.." "...Zaitun ni kam har kullun cike nake da son jin tarihin rayuwar ki ina so in san wace ke, meyasa ke baki ta6a tunanin bani labarin ki ba duk iya tsawon zaman nan da muka yi..." Sai lokacin Zaitun ta dago ta dubi Mmn Abdul ido cikin ido yayin da nata idanun ke cike taf da ruwan hawaye da ya tsatstsafo sakanni kalilan bayan maganar Mmn Abdul na karshe. Kafin hawayen ya gangaro ne tayi saurin maida duban ta ga fuskar Mufeeda wanda yayi daidai da gangarowan hawayen nata suka hada idanu da yarinyar, tuno abubuwa da dama take yi, abubuwa ne da bata jin har abada zata iya mancewa da su. Mufeeda kam cikin idanun Zaitun din ta tsaya kalla ganin yana ruwa...daga ita Zaitun din har Mmn Abdul sun yi matukar mamakin ganin yadda Mufee ta saki Balloon din da take wasa da shi tayi saurin kai hannun ta ga fuskar Zaitun..." Mam..mi..!" Ta fada tana me shafo hawayen dake gangarowa. Tsaye cak Zaitun ta mike tare da sake rungumo yarinyar sosai bisa kirjin ta tana jin tamkar zuciyar ta zata fado saboda bugu, bata jin a duniya kaf akwai wata halitta baya ga mahaifan ta da zata so kwatankwacin yarinyar nan, dan a ganin ta idan kwana zata yi tana yiwa Mmn Abdul bayanin irin tarin kaunar da take yiwa Mufee ba zata fahimce ta ba, kuma bakomai ne cikin labarin rayuwar ta ba illah Mufeedah kadai, dan haka gara kawai abar wasu abubuwan a yadda idanu kadai ne ke iya ganin su. _Salmerh_😘 [20/9/2022, 12:32 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE* 💕 *(' Yata ce)* *Salmerh MD* 🅿️ *...7* ....Sai da ta koma daki sai taji kuka ya kufce mata, kukan da ita kanta bata san dalilin yin sa ba, sai kuma taji nawin da zuciyar ta yayi mata ya dan sauka, bayan wani dan lokaci da ta nutsu sannan sai ta ji kamar kuma bata yiwa Mmn Abdul adalci ba, baiwar Allahn bata san wace ita ba amma ta kar6e ta hakanan, bata san daga inda ta fito bata san meke 6oye cikin rayuwar ta ba amma a hakan ta nuna mata kauna ita da 'yar ta, tai musu halacci ta bada gudunmmawa cikin rayuwar su gwargwadon iyawar ta, bata ta6a kyarar su ba bata ta6a kyamatar su ba iya zaman su, meyasa kuma ita bazata bude mata zuciyar ta ba. A daren ranar ta yanke shawaran washe gari zata bawa Mmn Abdul amsan tambayar da tai mata game da tarihin rayuwar ta, sai dai kuma kaf din daren kasa tsaida hawayen ta tayi haka ta kwana kuka bacci ma kauracewa idanun ta yayi, Mufeeda na kwance kan cikin ta tana shafa bayan ta duk wani motsin yarinyar tana lura da shi. Abubuwa ne masu yawa suke yawo cikin zuciyar ta da ta jima tana danne su, ba karamin kokari tayi ba iya tsawon lokacin nan tana hana kanta tuno su, karfi da yaji ta hana kanta samun lokacin da zata ware domin tunawa da su. Amma a yau hakan ya gagare ta, yau din ji take tamkar zuciyar ta zata fashe ne, sosai take jin kewa, tana jin dana sani na son taso mata, zafi take ji cikin kirjin ta sosai...zafi na rashin madafa rashin sanin tudun dafawa. Washegari cikin rashin sa'a sai ta tashi da zazzafan zazza6in da take kyautata zaton matsantawa kanta da tayi da tunani ne ya haifar da shi. Da kyar ta lalla6a ta yi wanka ta yiwa Mufee ma, Tea ta hada musu suka sha da guntun bread din da Adam ya kawo musu tun shekaran jiya da yazo, wanda a jiya da safe wata 'yar tafiya ta kama shi da take kyautata zaton har a yanzu ma bai dawo ba. Kayan Mufeeda set biyu da suka yi datti tayi zaman wankewa su cike da karfin hali, dan gabobin ta duk ba karfi take jin su, hatta hannun ta ma ji take nan da wani dan lokaci tamkar bazasu iya amfanuwa ba saboda zafin zazza6in. So take tayi ta kammala ta lalla6a wajen Mmn Abdul ta bata hakurin abinda tai mata jiya...dan tasan dole ne zata ji babu dadi. _"...Salam Alaikum..."!_ Tajiyo tashin sallamar da tun ma kafin me rero sallamar ta bayyana Zaitun ta fahimci wace ita. Amsa sallamar tayi tana mai kakalo murmushi ta dorawa fuskar ta na karfin hali. "...Yau Anty Rauda ce da sassafe haka..." "...ai dai ba yawon bariki naje ba balle ace na aikata ba daidai ba.." Ta fada tana wani yatsina cike da kallon raini take watsawa Zaitun da ke Zaune har yanzun bakin kofar ta. Sanye take da dan Hijab din ta da ta riga ta sabawa kanta dashi matukar zata fito harabar gidan. "...Barka da zuwa Anty Rauda fatan an iso lpy..." Ta sake fada duk da tasan cewa abu ne mai wahala ta samu kyakykyawar amsa daga Raudan..ga mamakin ta kuwa hakan ne. " Da ba lafiyar ba ai baza'a ganni gidan 'yar uwa ta ba a wannan lokacin...kuma zikau aka ganni babu 'yar jagora balle tukuicin bariki..." Wannan karon kam Zaitun bata sake tanka ta ba dan batun yau ba in da sabo yaci ace ta saba da halayyar Raudan da a kullun indai tazo gidan sai ta yada mata magana makamancin wannan, wani bin sosai take mamakin Raudan, yadda take daukan zafi akan Zaitunan kai kace akwai wata mummunar gaba da ya ta6a hada su, amma ba komai ne ya kawo hakan ba face zaman Mufee tare da su Siyama da suka kasance 'ya'yan yar ta kasantuwar ita din kanwa ce ga Mmn Abdul uwa daya uba daya sai dai akwai banbancin halayya karara. Tun da jimawa farkon zuwan Zaitun gidan da Rauda tazo Hajja ta fesa mata karya da gaskiya shikenan tun daga ranar ta dauki karan tsana ta dora musu. Mmn Abdul ke taka mata birki wani bin dan matukar taji ko ganin Raudan tayi mata ba dai dai ba takan tsawatar mata..wana Zaitun din ke kyautata zaton ko na yau din ma da ace taji bazata ta6a yin shiru ba. Zaitun bata sake bi ta kansu ba bayan ta shanya kayan wankin nata daki ta koma ta cigaba da kwanciya zazza6in kuwa kamar jira yake yace Salamu Alaikum, dan sosai take rawar sanyi, Mufee dake can gefe tana ta wasa da kayan wasan da Adam ya siya mata Zaitun ita Zaitun ta kurawa idanu, yanzu idan Allah ya kar6i rayuwar ta cikin wannan halin waye zai maye gurbin ta wajen Mufeen?, waye zai kala da ita? meyasa ma ta baro gida ne? Anya kuwa ta yiwa kanta adalci, ta yiwa mahaifa da 'yan uwan ta adalci..?" Ta jima da fara tunanin waiwayar gida amma tsoro take ji dan zaman ta da Mufee ba zai ta6a yiyuwa a gidan mahaifin ta ba haka ma ga mahaifiyar ta..shiyasa ta yanke shawaran bari idan Mufeedan ta dan kara wayo sannan su koma aga yadda hali zai yi ko zasu kar6e su su yadda da tata salon kaddarar rayuwar. Kara karaf-karaf dake tasowa daga 6bangaren Mmn Abdul shine ya maida hankalin Zaitun a can, tasan dai a wannan lokacin Abdul da Siyama na makaranta balle tace sune suke yi, sai daga ma fahimci ashe _kwalema_ su Mmn Abdul din keyi wanda shine ma dalilin zuwan Raudan gidan da farar safiya. Taso ta fita ko zata iya saka musu hannu amma ko data gwada mikewa sai taji jiri na shirin kayar da ita dole ba dan taso ba ta hakura kawai ta cigaba da kwanciyar ta har kusan sallar azahar sannan da Mmn Abdul taji shirun yayi yawa ne ta lekota nan taga ashe Zaitun din bata ji dadi bane shiyasa. " Subhanallahi.." Ta furta cike da kulawa. " Toh kin sha magani ne..?" Ta tambayi Zaitun din tana me ta6a wuyan ta. " a a zansha anjima kadan" " Ki daure kisha dai Zaitun inda hali ma da chemist kika leka a duba ki acan, ni kwa dai nayi mamaki, tun dazun naji shiru nake tambayar kaina ko me ya faru ashe zazzai ne ya rike ki anan, toh Allah ya sawwaka ya sa kaffara ne, bari Siyama ta karaso sai ta rakaki kuje chemist din ko.?" " Toh Mmn Abdul nagode sosai.." " 'yan mata yau Mammi na gida an mance da ni ko.?..". Ta karasar da maganar tana mai sauke idanun ta kan Mufee dake kwance gefe da Zaitun din ta wani rungume mata hannu. Yinin ranar kaf babu inda ta je ban da wajen mai chemist da Mmn Abdul ta matsa akan sai taje aka duba ta gami da bata magani ta biya kudin. Da yake yanzu tana dan ajiye canji cikin albashin ta saboda nawin abubuwa da dama da Adam ya dauke mata. A hanyar su ta dawowa ne suka hadu da Hajja ta sauka adaidaita tun a farkon layi. Ganin ta da Siyama tayi yasa ta tafi da gudu tana murnar ganin ta ta rungume ta.(Siyaman ce ta raka Zaitun chemist din.) Zaitun bata san meyasa ba amma sam ganin Hajjan be mata dadi ba har a zuciyar ta, tun barin Hajja gidan tashin hankalin ta ya ragu, damuwar ta ta zabge, yawan tunani yai mata kaura dan dama sau tari maganganun Hajja ke sawa tana yawan tuna baya...tuna bayan kuma shi ke yawan sata zubda kwallan da bata iya hana su sauka. Kawar da duk wannan tunanin Zaitun tayi cike da karfin hali ta nufi Hajjan itama tana mata barka da zuwa gami da mika hannu da niyyar kar6a buhun bagco da Hajjan tazo da shi amma ga mamakin ta sai Hajjan tayi saurin janye abinta alamu karara na nuni ga cewa bata bukatan tallafi daga Zaitun din sai ma tayi gaba batare da ko sannun da Zaitun tayi mata ta ansa ba. A hankali Zaitun ta bisu abaya gudun kar jiri ya kwashe ta dama ba wani karfin dauka ke gareta ba kawai itama dauriya tayi sai kuma aka yi sa'a Hajja tai bore. A yanayin da take tafiyar ne ya sanya kunnuwan ta jiyo hirar wasu matasa dake zaman majalisar bayan azahar. "...Rayuwa wallahi yanzu duk ta lalace Sabi'u, dubi wancan 'yar yarinyar idan akace maka zaman kanta take zaka yadda...?" " ahh haba dai ni da zan ma ce maka tayi min ka binciko min gidan su tunda kai dan unguwa ne..." "...Allah ya tsare ka da wannan...in gaya maka har shegiyar yarinya take da shi mara uba...'yar iska ce wannan ta karshe...." Maganar tasa dakatawa yayi ganin yadda Zaitun ta waigo tana duban sa duba irin na tuhuma dama kadan ta gita su so taku kadan tayi ta dawo baya gaban su. Cikin idon mai bayanin ta duba tace" Waye yace maka yarinya ta shegiya ce marar uba..?" Tayi tambayar ne cikin tsare su da idanun ta kai kace in aka barta zata iya tsinana wani abin kirki ne. Tuni tama nemi hawaye ta rasa a idanun ta, hakika mutane abin tsoro ne a wannan zamani, yaushe ma aka santaa unguwar har da labarin ta zai fito ta wannan sigar. Mai bada dogon bayanin na shirin tankata wanda aka kira da Sabi'un yai saurin dakatar da shi, sai duk suka zuba mata idanu. Ganin bazai tanka ba yasa Zaitun cigaba da fa'din..." Daga yau ko da abayan idanu ne ka sake aibanta min yarinya da suna shegiya wlh bazan ta6a yafe maka ba kuma sai Allah ya mata hisabi da kai da ita...ka guji daukan hakkin marayan da bai ji ba gani ba...". Daga haka ta juya ta fara tafiya da dan sassarfa tana ganin gaban ta da kyar, har tama manta da wani zazza6i ballantana jiri da take ji. Jikin matasan nan sanyi yayi sosai kusan shafewan wasu dakiku kafin mai suna Sabi'u ya saki ajiyar Zuciya..." Babu mamaki kallon kitse kuka tsaya yiwa rogo dan ni wlh kalaman yarinyar sunyi tasiri a zuciya ta tuni naji na yadda da ita dari dari bisa" " Ka dalla can...ashe karamin kwakwalce da kai, wannan kuma wani sabon abu ne Sabi'u? Ni nan da kake gani burga baya tasiri a zuciya ta waye ma bai san zaman kanta take cikin unguwar nan ba..". Ajiyar zuciya kawai Sabi'u ya sauke da fadin" Allah ya kyauta". Hajja da Siyama sun riga Zaitun kaiwa gida dan haka ko da ta karasa dakin ta ta shige bata kuma bi ta kansu ba dan ita kadai tasan yanayin da take jin kanta a yanzu...sai da ta tsinci kanta cikin dakin ta tama kafin taji wani kuka mai karfi yazo mata cike da kunar zuciya...Da hannun ta daya ta toshe bakin ta gami da kife kanta tasha kukan ta batare da kowa ya jiyo ta ba. Mmn Abdul ke tambayar Siyama ina ta baro Zaitun din bayan ta gama gaisuwa da Hajja tana mai kokarin diban mata ruwan da zata sha take yiwa Siyama tambayar. Amsa ta Siyaman tayi da fadin. " Tana tahowa abayan mu...tace jiri take ji idan tayi sauri faduwa zata yi...". " Kai Allah dai ya sawwaka ni kam wannan irin ciwo lokaci guda haka.." Tayi maganar nan ne tana mai ajiye ruwan gaban Hajja tana sake zama bakin tabarma gefe da Hajjan kadan. Sai da Hajja ta sha ruwa ta sauke kofin sannan cike da gatse tace" Ita waccan din me ya same ta..?" " Wallahi zazza6i ne kawai Hajja amma kar kiga yadda ta zabge rana guda tak abinki da me kazar kazar duk sai kaji wani iri babu dadi..itama yarinyar kamar ta san uwar ta ba lafiya yau din yini tayi sukuku duk ba wata walwala sai da na goya ta ma kafin aka samu ta danyi bacci..". Baki Hajja ta kyabe tana duban Mmn Abdul.." Wato dai Rahma har yanzu baki bar wannan bautar da kika daurawa kanki ba ko..?, Allah yasa ma ba wani abin kunyar ta kuma karo muku ba tunda taga kuna kar6a mata hannu bibbiyu hadda tayin raino..." " Um um Hajja na tabbata Zaitun bazata aikata wancan danyan aikin ba.." " Sai kuma kiyi, lokacin da tayi na farkon ta nemi shawarar ki ne...?" Rauda dake gefe da Hajjan saurin jefa nata tayi itama. " Bar Anty Rahma dai Hajja da ba'a aje shaida mun gani bane sai muce ba haka abin yake ba amma ga zahiri nan..." Wani dan banzan harara da Mmn Abdul ta zabga mata yasa taja baki batare da ta karasa fadin abinda tayi niyya ba ta karashe da kawar da kai tana kunkuni. Mmn Abdul kokadan bata ji dadin wannan magana ta Hajja da 'yar uwar ta ba, amma babu yadda ta iya da ita dole taja baki tayi shiru, wani lokacin bata ganin laifin su ma duk laifin Zaitun ne, da ace ta bude zuciyar ta ta bayyana al'amarin a yadda yake asali tasan da duk hakan bazai faru ba. Kamar Mmn Abdul tasan abinda ke zuciyar Zaitun kenan adaidai wannan lokacin dan itama tashin farko ta dauki laifin karankataf ta daurawa kanta, sai dai tasan koma me zata fada musu ba lallai ne ya canza zuciyar su ba, ba kowa ne zai amince da batun da zata fada din ba kamar yadda tun a gida akai mata tawaye aka ki fahimtar ta shiyasa a kullun take ganin babu anfanin sake bayyanawa dan duk mutane iri daya suke kusan kowani lokaci. A nan kwancen da take tana iya jiyo duk abinda suke tattaunawa dan bakin dakin Hajja suke zaune kuma shine daf makwabcin dakin ta. Hannu ta kai ta dafe kirjin ta dashi saitin zuciyar ta, har ga Allah tana cutuwa a mabanbantan lokuta kuma sanadin mabanbantan mutane, bata so akai gandun da raunin dake zuciyar ta yin tasiri akanta da wanne zata ji, meyasa kowa yake aibantata sanadin Mufeeda, meyasa kowa bai kunar yarinyar ne?" Zuciyar ta taji nayi mata suka tamkar wacce aka cake ta a kirjin da mashi..." Hajja dai bazata ta6a canzawa ba itama.." Dakyar ta samu ta daidaita hawayen ta sannan ta lalla6a ta fito har yanzun kuma basu tashi inda suke zaune ba illa Mmn Abdul da bata gani ba tana can tana karasa gyaran da aka yiwa dakin nata a yau din. Gaishe da Hajjan tayi bayan ta zaune gefe kadan da ita. Sai ga mamakin ta daga Hajjan har Rauda kowa kawar da kansa yayi bacin tana da tabbacin sunji gaisuwar da tayi, sake maimaitawa tayi sai dai har yanzun Hajja bata amsa ba. Cak Zaitun ta mike tare da kwashe rigunan yarinyar ta dake kan igiya ta koma ciki. Dama hakkin makwabtaka da kuma girma da take bawa Hajjan dalilin Mmn Abdul ya sanya ta fitowa bayaga haka me zai sa ta 6ata lokacin ta wajen wacce kokadan bata kaunar ta balle yarinyar ta. *****....... Kamar hadin baki washegarin dawowar Hajja sai ga Bbn Abdul ma inda yai musu diran safiya. Wani sabon tashin hankalin da Zaitun ta jima da mancewa da shi ne ya diran mata da ganin Bbn Abdul din. Sai yanzu ma ta fahimci dalilin dawowar Hajja da kwalema da su Mmn Abdul suka yi a jiyan kenan dan Bbn Abdul zai dawo ne, meyasa kwatakwata kwakwalwar ta bata kai can din ba. Toh banda abin Zaitun yaushe ma damuwar da take ciki tun jiyan ya barta ta yiwa abubuwa duban fahimta..? Tun a jiyan bata wani nutsu ba gata nan dai kawai tunanin ta duk yana ga neman mafita ne sai ga kuma wata sabuwa. Da ace Bbn Abdul bai nuna mata halin sa daga isowar ta shi bama da zata yi tunanin tuni labarin wancan lamarin ya shude amma daga isowan shi suna hada idanu ya wani dage mata yana mata wani kallo kasa kasa da ita kadai take fahimta sbd ba yanzu ne farko da ya mata hakan ba. Duk tsarabar da ya kawo Mmn Abdul ta so diban ma Zaitun ko wanne daga ciki, dangin Manja, doya, irish Potato, kwakwa, doya, garin kwaki hadda tulin tsintsiyan kwakwa dadai sauran su..amma Hajja ta tsaya tsayin daka ta hana a cewar ta ma daidai kwayar tsintsiya idan aka bawa Zaitun din bata yafe masa ba. Wannan lamari sosai ya ta6a ran Mmn Abdul yayin da 6angaren Zaitun dadi ma ya mata, dama bata ta6a jin kwadayin wani abu na Bbn Abdul din ba ko min girman abin kuwa. Mmn Abdul tsabar kunya kasa hada idanu tayi da Zaitun ganin yadda ake ta raba tsaraba wa makwabta amma ita an hana abata. Daga karshe dole ta daure taje har daki ta bawa Zaitun hakuri...Zaitun kam ko ajikin ta, abu ma ko an baka sai an biyo bayan sa da gori ina amfanin sa, tunda bata rasa ci da sha ba Alhamdulillah ta godewa Ubangijin ta. Hatta Mufee Zaitun bata kara barin ta taje kofan Mmn Abdul ba gudun abinda zai iya zuwa ya dawo...Mmn Abdul ce tayi saurin lura da hakan har taso nuna 6acin ranta wa Zaitun din da fadin ko dai fushi takeyi da su gaba daya. Zaitun rasa ma abin cewa tayi, erh mana rasa abin cewa domin idan har tace zata wanke kanta game da hakan toh sai ta hada da rantse- rantse kafin ta iya wanke kanta, yawan rantsuwa kuwa ba halin ta bane ba kuma tasan jan zance. Wannan dalilin ne ya sa ranar da zata koma bakin aikin ta dole ta bar Mufeeda a gida badan komai ba sai dan Mmn Abdul kada ta fassara ta sigar da ba haka abin yake ba. Bayan kwana biyu da dawowan Bbn Abdul ne ta koma aikin kuma har zuwa lokacin bata sake haduwa da shi a gidan ba, bata sanin lokacin fitan sa balle shigan sa da sauran al'amura ashe doka mai karfi Hajjan ta kafa masa game da Zaitun din bata sani ba. Ranar da takoma ya bita wajen aikin lokacin tana daf da isa ya sha gaban ta. " Zaitun tawa ni kadai!..da fatan kina sane da cewar har yanzu ban hakura ba?" " Ko da yake ban biyo ki nan dan in ji wata kalma daga bakin ki ba nazo ne kawai dan in tunatar da ke cewa a kowani lokaci dare ko rana a shirye nake matukar kika amsa tayi na...in kinga na hakura kuwa toh na cimma muradi na akan ki ne in hakan bai samu ba toh ganin ki karkashin iko na, bi ma'ana matsayin matata ko da na sati guda shine kadai kwanciyar hankali na...". Daga haka ya juya da niyyar barin wajen. Zaitun da tayi suman tsaye bata san lokacin da ta dakatar da shi ba..." Bbn Abdul..!" Waigowa yayi fuskar sa cike da murmushin jin dadi a zaton sa nasara ce ta tunkaro sa, dan yau ne karon farko da Zaitun din ta ta6a tankashi a duk bibiyar da yake mata. " Meyasa ka za6i lallai- lallai sai ka shiga rayuwa ta ne?" " Saboda kauna Zaitun da kuma son kasancewa tare da ke.." " Koda mahaifiyar ka bata kaunar hakan...?" "Manta da Hajja rikicin tsufa ke ta6a ta..." yace yana mai gyara tsayuwan sa. " Kuma ko da hakan yana nufin ta hanyar sa6on Allah ne...?" " Jin dadin rayuwa dai Zaitun!, wai me yasa kike wani waskewa ne kamar akai na zaki fara...?" Zata yi magana yayi saurin dakatar da ita da fadin.." ki bari mu karasa wannan maganar a gida ki karasa wajen aikin ki kar kiyi latti." Yana gama fadin hakan ya juya ya tafi batare da ya ko sake waigowa ba. " Mutun har mutun amma zuciya na shirin lalacewa.." Zaitun da ke tsaye har a lokacin ta fada bayan doguwar tazara ta shiga tsakanin su. " Zaitun..!" Taji an kirayi sunan ta da muryar da ko cikin mayen bacci tasan waye ne.." Saurin juyawa tayi ta dube shi tsaye gefe kadan da inda suka tsaya da Bbn Abdul. Bata san iya tsawon lokacin da ya dauka a wurin ba amma daga yanayin fuskar sa ta fahimci yaji wani abu cikin maganar su koma yaji gaba daya. 'Dan washe baki tayi tana kawar da wancan damuwar tace" Laa Yah Adam..yaushe ka dawo..?" Madadin ya amsa ta a a tambaya ya jefe da shi da fadin" Waye wannan da ya tafin..?" Yayi maganar ne fuskar sa daure tamau ko alamun fara'a babu ga dukkan alamu dai baya cikin yanayi mai dadi. Hanyar da Bbn Abdul yabi ta sake bi da kallo sai kuma ta rasa takamamman amsar da zata bashi. Sai da ya sake maimaita mata tambayar karo na biyu sai dai wannan karon a 'dan tsawace yayi ta wanda hakan yasa Zaitun dawo da hankslin ta jikin ta da rawar murya ta fara harhada amsar da zata bashi..." Mutu...min gidan..mu ne..Bbn su....Siyama" " and what is he doing here ?" Kallon sa Zaitun tayi a afakaice dan kokadan bata san me yafada da wannan yaren ba...ba mamaki ya manta cewar bata san komai akan yaren ba. Tunowa da Adam yayi bata ji ya sashi jan tsaki da yin 'kwafa kawai yayi tafiyar sa ya ma fasa shiga wurin Hajiyan. ( _Su Adam kishi_ 🙄 ) Salmerh 😘 [20/9/2022, 12:32 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE* 💕 *(' Yata ce)* *Salmerh MD* 🅿️ *...8* Sai da ta taso wajen aikin a hanyar ta na zuwa gida ne maganganun Bbn Abdul suka fara dawo mata 'daya bayan 'daya, sai a lokacin kuma ta fara jin tashin hankali na shigan ta na gaske. Da yace zasu karasa maganar a ina kenan yake nufi?. Kuma da wani lokaci?. Lokaci guda Bbn Abdul yasa taji zaman gidan nasu gaba daya ya fice mata aka, kudin shekara ta biya amma bata jin zata iya cike shekaran a gidan matukar Bbn Abdul bazai bar shiga sabgar ta ba. Da komawar ta gida ta shiga lalu6o 'yan kudaden da take tarawa a hankali, wasu daga cikin kudin hakkin ta ne na wajen aikin yayin da wasu Adam ke bata lokaci zuwa lokaci, ko da ta irga sai taga sun kai kimanin Naira dubu goma sha shida cif. Tunani ta fara na inda zata samu daki koda kudin rabin shekara ne ta biya a hnkl sai ta bada sauran daga baya. Toh a ina zata samu? Ta tambayi kanta. Ko de Adam zata yiwa magana ya bincika mata. Sai dai fa shima Adam din yanzu haduwar su ta kan dan yi wahala sakamakon aikin matsa mai da ya samu a wata Filling Station. Karshe da ta kewaya kuma dai kan Adam din tunanin ta ya tsaya, dole sai shi zata yiwa maganar tunda shi kadai ne me iya zama ya saurari kukan ta. Murmushi tayi kayatacce lokacin da take gyara musu shimfida bisa sabuwar katifar su da dududu bata wuce sati uku da siyan ta ba. Mufee dake a goye a bayan ta wacce tuni tai bacci ta kwanto ta shimfidar da ita bisa katifar. Dan yanzu tana 'dan barin ta kwanta ba'a jikin ta ba saboda samuwar katifar Mufeedan ce ma bata saba da kwanciya ita kadai ba dole ko da tayi bacci sai ta farka cikin dare in dai ba'a jikin Zaitun tayi bacci ba dole dai karshe akan cikin zata dora ta su karasa baccin. A hankali ta fara tariyo yadda aka yi kafin siyan katifar wani lokaci da ciwon mura yai wa Mufee kamun karfi...abin ya damu Zaitun sosai dan hatta itama a lokacin lafiyar bata ishe ta ba amma na Mufeedan yafi tsaya mata a rai fiye da komai. Ko da Adam yake tambayar ta garin yaya duk suka kamu lokaci guda haka ai bata ma san lokacin da tace" Ina ga sanyin siminti ne fa Yah Adam Allah kar kaga yadda kullun dare atishawa ke hana ta sakewa a hakan ma saman ciki na nake kwantar da ita da kullun" " Babu gado ne ko irin katifa haka..?" Da kai ta bashi amsa gami da fadin" a a tabarma ce kawai shiyasa.." Adam bai sake yin magana akan hakan ba bayan kwana biyu kawai taga katifa ya kawo. Da ta rasa bakin yi mai godiya sai kawai ta fara hawaye" Dan Allah Yah Adam ka daina wahal da kanka saboda mu..ni fa ban fada dan wani dalili ba a lokacin rikicewa nayi..dan Allah ka koma da shi sai inga kamar bana maka adalci duba da yadda na dora maka nawin abubuwa da dama da ba hakki ne akan ka ba..." " Zaitun kenan.." Ya fada yana me zuba hannayen sa cikin aljihun wandon jumpan da ke jikin sa. "..in ban yi muku ba toh ma wa zan yiwa?...daga Hajiya ta sai ku kadai gare ni fa a yanzu, ba dole in kula da duk wata damuwar ku ba in dai ina da damar hakan..." "Yah Adam..." " Ni dai kinga tafiya ta idan kin ga dama ki kyasta ashana ki 'kona ko kuma ki qi kwanciya akai saboda ni ne na kawo.." Daga haka yayi gaba abin sa bai ko sake waigowa ba. " Wannan bawan Allah akwai tausayi, Ubangiji Allah ya saka maka da mafificin alkhairi ya kuma kara arziki" Addu'ar da kullun take yiwa Adam din kenan ko gaban sa ko a bayan idanun sa ne. Tunowa da tayi a safiyar yau din kamar da 6acin rai suka rabu ya sanya ta kara jin zafin Bbn Abdul har cikin zuciyar ta. In dama ta gode Allah har dare yayi sukai shirin bacci bata ji ko duriyar sa ba. Har ta fara karanto musu Addu'an bacci sai kuma taji fitsarin da tasan matukar bata yi shi ba sai ya tada ita cikin dare. Dole ta tashi ta fita fitsarin wanda a lokacin gari yayi duhu sosai kuma babu wuta an dauke. Bbn Abdul da shigowar sa gidan kenan wajen karfe goma saura har zai gitta dakin Zaitun sai kuma yaga kamar bude yake hakan yasa batare da tunanin komai ba kawai ya afka dakin duk da takalmin sa bai cire ba gudun kar Hajja ko Mmn Abdul su gani, zuciyar sa cike fal da farin ciki da tunanin bacci ne ya dauke Zaitun har ta manta bata rufe kofar tata ba. Shi kansa bai san me yasa ya shigo mata dakin ba abu guda da ya sani kawai shine ya na matukar muradin kasancewa da ita. Da hasken da ke fuskan wayar sa ya haska madadin yaga su biyu suna bacci sai yaga Mufee kadaice kwance tana baccin ta cikin kwanciyar hankali..jikin ta fes babu wani datti da alamun sai da akai mata wanka kafin tayi baccin. Kafin yayi wani yunkurin kirki sai jin alamun tahowar mutun yayi, cikin rashin madafa kawai ya shige bayan labilen jikin windown dakin da yake har kasa ya sauka. Zaitun kam da dawowar ta sake garkame sakata tayi tana sakin nannauyan ajiyan numfashi gami da jinjina duhu irin na daren ranar ga wata ma ta shige duhu sosai. Komawa tayi kusa da Mufee ta dan haska fuskar ta tana shafo kanta tayi murmushi..." Feefy na sarkin bacci". Hasken ta ajiye ta fara cigaba da karanto musu addu'ar bacci. Kamar da wasa sai taji motsi wajen windown ta da sauri ta waiga dan dama Zaitun matsoraciya ce ta ajin karshe. Ganin mutun tayi ya bayyana ta bayan labilen dakin ta..." Yah Subhanallahi.." Da sauri ta yunkura gami da bude baki da niyyan sakin ihun neman agaji, kafin ta gai ga hakan ne Bbn Abdul da ya gama fahimtar abinda take shirin yi taku daya tak yayi sai gashi gaban ta ya rufe mata baki ruf da hannun sa daya..." Haba Zaitun ya zakimin haka? " ba daman nace miki zamu yi magana ba..?" Kici kicin kwatan jikin ta take yi yayin da ko'ina na jikin ta duk ya dauki rawa. Duk iya tattaro karfin ta da tayi hakan be sa Bbn Abdul yayi ko gezau ba dan karfin ba 'daya bane. "..Ki nutsu dan Allah babu abinda zan miki...ni dai dan Allah Zaitun ki taimaka ki amince muyi aure tun kafin shaukin sonki ya kaini ga aikata ba daidai ba tsab sai inyi aika-aika.." Fadan hakan da taji yayi ya kara mata kaimi wajen son ganin ta kwaci kanta amma inaa..ta kasa cire hannun Bbn Abdul daga bakin ta. "..Wai ke baki jin tausayi na ne Zaitun?..wlh ina son ki kuma na miki alkawari zan kula Mufeeda tamkar 'yar ciki na, duk abinda zanwa su Siyama nai mk alkawari shi zanwa Mufeeda dan Allah ki amshi soyayya ta..." Duk maganar nan yayi ta ne batare da ya bawa Zaitun damar kwatan kanta daga hannun sa ba. Takaicin ta daya ma ko Hijab babu ajikin ta dankwalin ta ma tuni yayi nasa waje sai tsefaffen gashin ta da duk ya barbaje saboda kiciniyar da take yi. "...Ki nutsu nace ba abinda zan miki...amma kina yin wani kuskuren da ya janyo hankalin mutane har aka shigo cewa zanyi ke ce kika gayyato ni dan ban miki abinda kike so bane kuma yasa kike min ihu..." Daga fadin hakan ya sake mata baki ya mike tsaye batare da wani 6ata lokaci ba. Kuka kawai Zaitun ta saki mai cike da takaici, kuka mai tsuma zuciyan duk wanda ya ji. Jifan sa ta fara yi da duk abinda hannun ta yaci karo da shi.." Mugu! macuci,..wlh ban yafe ta6a jiki na da kayi ba..kuma ka kuskura ka sake shigo min daki sai na illata ka..baza'a aure kan ba, bazan aure ka ba mara imani kawai...". Ta jero duk wadannan batare da ita kanta tasan me take fadi ba,ta karashe da durkusawa kasa kan gwiwoyin ta kukan takaici na sake kubce mata. Irin kukan nan da kake yi idan a cuce ka kuma an hanaka daukan fansa. Shi kansa jikin sa yayi sanyi but he have to do all this ko hakan zai sa ya same ta yadda yake so. Bbn Abdul bai ce da ita komai ba sai ma hanyar fita da ya dauka bayan gama jin kalaman nata. Sai da ya sa kai zai fita sannan ya waigo..." Ki sani, bazan sake 6ata lokaci na wajen nuna mk soyayya ta ko kuma rokon ki akan ki aure ni ba daga yau, amma ki shirya tarata daga gobe zuwa kowani lokaci.." Daga haka ya fice abin sa ya tafi, da gudu Zaitun ta tashi taje ta isa ga kofan sakatan ta saka tana wani irin kuka gwanin tausayi. Jikin kofan tabi ta sulale ta cigaba da kukan ta, sai da tayi mai isan ta kafin ta tashi ta koma gefen Mufeeda ta kwanta..bacci sam kaurace mata yayi tana ta tunani, meyasa abubuwa ke neman fin karfin ta ne. Shin cikin kaf din rayuwar ta akwai inda ta kuskure ne da Allah ke hukunta da shi. Bata da amsoshin duk tambayoyin da ke makare cikin zuciyar ta dan haka dole ta hakura. Bacci 6arawo ne ya sace ta batare da ta sani ba. washegari bata bi ta kan kowa na gidan ba tana kammala hidimomin da ke gaban ta ta goye Mufee suka wuce wajen aiki dan aranar ko mutun guda daga cikin gidan ji tayi idanun ta basa kaunar gani. Idanun ta sam basa ko ganin inda take jefa kafafun ta kadan ya rage ma bata afka wani ramin soak away da aka fara tona bada jimawa ba har sai da wasu 'yan mata biyu dake bayan ta suka ankarar da ita. Da haka ta samu ta isa wajen aikin, sai ya kasance yau din babu wanda ya riga ta isa cikin ma'aikatan gaba daya….sai dai me? tun kafin ma ta gama shigowa balle akai ga batun gaisuwa Hajia ta fara surfa mata ruwan bala'in tazo mata da goyo bacin ba haka suka yi da ita ba. Hawaye kawai Zaitun ke sauqewa, ta rasa me ke damun kwakwalwar Hajiyan, shin Mufee kadai take yiwa wannan kiyayyar ko kuma duk har itan take wa kora da hali. Ta riga da ta saba da duk ayyukan da take yi a wajan kuma tana da tabbacin Mufee baza ta6a yi mata sha maki da ayyukan ta ba...toh ta ina matsalar take? A tun zuwan da takeyi da Mufee bata ta6a kuskuren da yarinyar tayi ko da 6arna bane balle ace dalilin kena...toh me Hajiya ke nufi da ita?" Bata tanka Hajiyan ba a zahiri amma gaba daya taji aranta aikin ma ya isheta kwatakwata. Sai da Hajiyab tayi mata tatas tayi mai isar ta kafin ta barta ta kama aikin ta...abu guda ke mata yawo cikin zuciya kashedin Hajiyan na cewa alfarmar yau kawai tayi mata daga yau din kuma bazata sake tolerating irin hakan ba...toh in ba aikin take so ta bari me take so? bata jin zata sake iya barin yarinyar ta wajen koma waye ne. Tayi aikin ranar ne duk cikin rashin natsuwa sai dai ko kadan bata yadda tayi kuskuren da za'a kamata da laifin sa ba balle a 'dora alhakin kan zuwan da tayi da Mufee. Da misalin karfe uku ya tashi a aiki, sai da ya wuce gida yayi wanka ya fito fes da shi. Masallaci ya tsaya ya sallaci sallar la'asar kafin ya karasa wajen Hajiyar tasa. Tun isowan shi wajen idanun sa ya sauka akanta, wanda kallo 'daya yai mata ya fahimci akwai abinda ke damun ta. Gaishe da Hajiyan yayi yana me 'dan yatsina fuskar sa. Hajiyan da tasan halin kayan ta sai cewa tayi bari a ha'do maka abinci nasan matsalar kenan ai" Inda tayi maganar tana murmushi da yake tasan Adam ba me wasa da cikin sa bane. "..Yanzu Adam wannan aikin kake ganin yafi dacewa kayi da gatan ka da komai?" " Hajiya nafi san in nemi halak dina ne da kaina..dan Allah ki samin albarka kawai shi nafi bukata". " Toh Allah yasa hakan shine mafi alkhairi". Hajiya Talatu ta fada tana me bada umarnin a ha'do masa abinci, cikin sa'a kuwa sai abin ya fada kan Zaitun. Shamsiyya da a kullun Adam din ke kara tafiya da imanin ta ta idan yazo ta dinga binsa da kallo kenan a 6oye. " 'Karasa aikin ki bari ni zan ha'da masa" Tace da Zaitun tana mai basarwa tamkar babu wani abu cikin ranta. Zaitun kam bata kawo komai aranta ba ta bar mata ta cigaba da sabgar ta. 'Bangaren Adam kuwa gani da yayi Hajiyan wa Zaitun ta bawa umarnin kawo masa abincin yasa shi neman hanyar komawa gefe dan nesa kadan da Hajiyan ta inda baza ta hangoshi ba koda zai yi magana da Zaitun din. Dan tunda yaga yanayin fuskar ta lokacin da ya shigo gaba daya ya rasa natsuwar sa, ji yayi hankalin sa bai kwanta ba, 'kage yake da son jin damuwar ta a yanzun. Unfortunately sai kuma yaga ba Zaitun ce ta kawo abincin ba, sai dai bai yi azar6a6in tambayan Shamsiyya dalili ba dan har yau babu wanda yasan alakar da ke tsakanin sa da Zaitun din kaf shagon Hajiyan, sosai suka iya takun su dan duk din su daga shi har Zaitun din ba masu rawar kai bane sam. Duk da yunwan dake kwakulan ma ciki amma haka yaji abincin ya kasa yi masa dadi, dagaske fa damuwar Zaitun din kawai ke gaban sa a yanzu. Gudun kar Hajiya ta zargi wani abu yasa shi daurewa ya dan ci abincin kafin ya tashi. " Ga Hajiyan ya dawo yana me yawo da idanun sa cikin babban shagon yake fadin Hajiya zan dan fita yanzun akwai wani uzuri dake gabana amma ba mamaki kafin maghrib in dawo ko zuwa bayan Isha". " Sai ka dawo Allah ya tsare min kai..." " Ameen Ameeen Hajiya ta ni kadai..." " Yauwa mun yi magana da Alhajin ku dazun yace idan akwai wata damuwa ayi masa magana". Bai ma juyo ya dubi Hajiyar ba yace..." Ni bani da damuwar komai Hajiya.". Daga haka ya kama hanya ya fice a wajen zuciyar sa taf wasi wasi. Ko da ya fita ji yayi tamkar bazai iya barin wajen ba har sai yaji menene matsalar tan, cak ya tsaya ya waigo da tunanin ko zai hango ta amma bai ganta ba. Kai tsaye zuciyar sa ta bashi umarnin toh shin wa kake tsoro ka koma mana ka tambaye ta ko dan kwanciyar hankalin ka ma har zai bi umarnin zuciyar tasa amma sai wani 6arin zuciyar ya hana shi. " Kai Adam..kabi a hankali dai sannu sannu bata hana zuwa sai dai a dade ba'a je ba...". Da wannan shawarar ya samu kwarin gwiwar barin wajen sai dai bai iya yaje inda asali yayi niyya ba wajen wani abokin sa dake can wajen gari shima wani gidan mai yake aiki wanda shine ma yayi wa Adam hanyar samin nasa aikin a inda yake. Adam Hustler ne baya zama sam, dan bayan gidan mai da yake aiki yana da wajen san'ar sa nashi na kashin kansa inda yake saida su Kerosine, Petrol, da engine oil kuma Alhamdulillah ba karamin alkhairi yake samu ba, hakan ma ba shike zama da kansa ba saboda aikin da yake zuwa ya sanya shi dora yaro akan wannan sai dai ya kan kai masa ziyara duk lokacin da yake da lokaci watarana ma yakan zauna ya ringa siyar da mai din da kansa ba tare da girman kai ba. Kamar dai yau din da be samu zuwa wajen abokin nasa ba kawai ya tsaya wajen sana'ar tasa sai dai duk ilahirin hankalin sa baya tare da shi, shi bai ma san wani irin so Allah ya jarabce shi da shi ba, ya riga yasan abu ne mai wahala su Hajiya su amince masa batun auren Zaitunan amma a shirye yake ya fuskanci ko wani irin kalubale matukar hakan zai kai shi ga nasarar da ya jima yana sakawa. Zaman sa ba da jimawa ba arean wajen ya fara dinkewa saboda tahowar wasu shegun motoci bakake masu masifar daukan hankali. Da gudu suka ringa wucewa 'daya bayan daya kimanin su shida cif. Yaron dake kula masa da kayan ne ya saki murmushi yana duban motocin da fadin" Yau 'Dan maliki yazo gari kenan ina yin ka mutumi na.". Ya fada yana me bayyanar da tsantsan farin cikin sa a fili. Wata guntuwar tsaki Adam ya saki da shi kadai yasan ma'anar kayan sa da alamu dai zancen da yaron yayi ne bai samu shiga wajen Adam din ba. Karshe ma tashi yayi yai tafiyar sa baiko yi masa Sallama ba. Daga masallacin da yayi sallar Maghrib bai zame ko'ina ba sai kofan gidan su Zaitun ya aika yaro aka yi masa kiran ta. Dama tasan dole yau din sai yazo shiyasa ta kasance a shirye dan farin sani ta yiwa halayyar Adam, tasan yadda yake damuwa da duk wani damuwar ta canjin fuska idan yaga tayi sai ya nemi ba'asi. Tasan abu ne mai wahala idan bai zo yau din ba, dole sai yazo yaji matsalar da take ciki tun bayan ganin da yai mata a shago da safe. Tun faruwar lamarin nan jiya bata sake kuskuren barin kofar ta a bude ba, ko bathroom zata sai ta kulle kirib. Ko yanzun ma da zata fita wajen Adam sai da ta kulle shi kafin ta fita. Kanta a kasa ta isa wurin sa daga sallama kuwa ko gaisuwa bai bari sun yi ba yasa hannu ya kar6i Mufeeda dake hannun ta yana fadin.." Yau duk baki barni na yini cikin natsuwa ba sosai kika tada min hankali Zaitun.." Ido ya tsura mata jin bata ce da shi komai ba illa wasa da yatsun hannun ta da take faman yi tsawon wani lokaci, ganin da gaske ba fa zata yi maganan bane ya sanya shi a hankali cikin sanyin muryar sa mai dadin sauraro yace" Pls Zaitun ki fa'da min me ke damun ki?" Salmerh😘 [20/9/2022, 12:32 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE* 💕 *( 'Yata ce)* *Salmerh MD* 🅿️ *...9* " Zaitun dan Allah ki amsa ni, u don't have idea about yadda nake jin zuciya ta..ko har yanzu bani da wannan matsayin da zan iya sanin matsalar ki..?" Shiru Zaitun tayi illa kai da ta girgiza masa kwalla na sauko mata, ba karamin kokari take cikin ranta wajen har hado amsar da zata bashi ba. Adam da bai fahimci hakan ba ajiyan numfashi ya sauke mai nauyi..." Well!..bazan tilasta ki fadin abinda baki yi niyya ba Zaitun ki rike damuwar ki tunda hakan kika ga yafi miki, amma ki sani ni Adam ina tsananin kaunar ki, ban damu da sai nasan kullin da ke cikin rayuwar ki ba tunda baki yi ra'ayin sanar da ni ba, abinda kadai na sani shine _INA SON KI!.._ I love u Zaitun with all my heart, a shirye nake da kar6ar ko wacce irin kaddara dake tare dake cikin ko wani irin yanayi ina tare da ke". Duban sa ya maida kan Mufee da ke wasa da agogon hannun sa wani choculate ya ciro cikin aljihun sa ya sa mata a hannu. Bai dubi inda Zaitun take ba ya cigaba da fadin" Zaitun bana fata zuwa na ya zam miki tamkar takura ne duba da yanayin dana sameki.." Sai yanzun ya juya ya kalli fuskar ta dake kallon kasa illah hawayen da ke sauko mata" Damuwar ki a zuciya ta nake jin sa Zaitun, kuncin ki, farin cikin ki, walwalar ki ko akasin hakan duk tafiyar su dai dai yake da nawa in baki sani ba yau in fada miki...zan wuce yanzu amma duk lokacin da kika shirya sanar dani damuwar nima a shirye nake in saurare ki.." Daga haka ya juya ya fara tafiya da takun sa mai birgewa. Taku uku yayi bai kai ga yin na hudu ba Zaitun ta mike tsaye daga dakalin dake shinfide a kofan gidan. " Yah Adam.." Ta kira sunan shi da raunin murya mai raunin amo, bai yi kasa a gwiwa ba ya waigo.." Dan Allah kayi hakuri Yah Adam, ba nufi na in 6ata ranka ba..." " Na san hakan Zaitun karki damu" Ya fada yana mai kokarin cigaba da tafiyar sa.." Yah Adam!!". Ta sake kiran sa a karo na biyu. Tsayawa ya sake yi amma bai waigo ba" Kar kayi fushi da ni dan Allah". Maganar tata ma dariya ta bashi amma da yake baya cikin yanayi mai dadi madadin dariyar sai yayi murmushi kawau...sai da ya juyo sosai ya dube ta kafin yace" Me kuma zai sa inyi fushi da abar kaunata..baki min laifin komai ba ai da zai sa inyi fushi da ke". Mufee dake rungume da kafafun ta tun ganin mikewar Zaitun din tasa hannu ta dago ta sama ta rungume ta sosai. " Zan fada maka abinda ya faru". .......***** " Kika ce shine wanda jiya na ganki tare da shi..?" Adam yayi tambayar bayan Zaitun ta gama bashi labarin kaf yadda lamarin ya faru tun a farkon zuwan ta gidan. Da kai Zaitun ta amsa shi tana duban gefen sa lokaci lokaci take sa hannu ta share hawaye yayin da Mufee tayi luf cikin jikin ta kamar me fahimtar abinda suke tattaunawa. " Meyasa baki ta6a sanar dani hakan ba toh..?" Shiru tayi..." Yanzu da wani mugun abin ya faru dake fa? a tunanin ki zan iya dauka ne? kinsan halin da zan iya shiga ne...?" " Kayi hakuri..!" " Mtheew..." Ya fada yana sake mikewa tsaye dafe da kansa. Kai kawo ya fara daga gabas zuwa yamma yana tunanin mafita. Dole ne sai yayi wani abu a wannan ga6ar gudun abinda kan iya zuwa ya dawo...ajiyar zuciya ya sauke mai sanyi, ga dukkan alamu ya samo mafita ne. Gaban ta ya dawo ya duka kamar me shirin neman tuba. " Kinsan yadda za'ayi Zaitun? dole ne sai kin bar gidan nan, bana so ki kara cikakken sati guda a cikin sa in so samu ne ma kafin satin ki kasance karkashin ikona amma duk hakan ba zai faru ba sai da amincewar ki kinsan hakan ko...?" Da kai Zaitun ta bashi amsa tunanin ta na rarrabewa sashi zuwa sashi. " Zan yi magana da Hajiya amma kafin hakan dan Allah banaso ki sake komawa wajen aikin kin nan ki zauna a gida, kuma ki kula da kofar ki duk inda zaki ki ringa kulleshi hatta bathroom bana son kiyi kuskuren sake barin kofa a bude in zaki shiga, dama ni tun farko mutanen gidan kun ba kwanta min suka yi ba amma zan san abinyi, dole zan yi magana da Hajiya ta..tashi ki koma gida...". Ya karasa maganar da mikewa tsaye hadi da matsawa baya kadan daga gaban ta. Ko da ya koma gida bacci kaurace masa yayi throughout daren, sake sake yake ta inda zai fara fuskantar Hajiya da maganar. Shi da ake shirin turashi cigaba da karatu matakin masters shine kuma zai zo musu da wannan sabon batun..yasan sai sun sha drama da Hajiya kafin ta amince. 'Bangaren Mmn Abdul kuwa tsananin kunyar Zaitun ne ya hana ta sakewa, ji tayi sam bazata iya hada idanu da ita ba sai aka yi sa'a ita ma Zaitun din aranar ko bi ta kansu bata yi cikin gidan ba. Mmn Abdul kadaice tasan duk abinda ya faru daren jiyan domin taji duk maganganun mijin nata da Zaitun. Dama ita bata ta6a zargin Zaitun ko makamancin hakan ba dayake tasan shaidanin, sai ma tsananin kunyar ta da ya cika ta a yanzun. Rabon da magana ta hada ta da Bbn Abdul tun jiya kafin faruwar lamarin duk ta dauke masa wuta har da kansa ya fara zargin ko dai tasan abinda ya faru tsakanin sa da Zaitun ne..kai anya kuwa? taya ma hakan Zai faru bacin time din daya dawo tuni baccin ta yy nisa. Wannan tunanin duk yayi su ne bayan dawowar shi gida daga sabgogin sa ya tadda gidan bb kowa, Mmn Abdul ta tattara yaranta kaf sun bar masa gidan..ga Hajja ma bata nan kishiyar Mahaifiyar marigayin Maigidan ta ta rasu tana can, in bai manta ba ko a safiyar yau din gaisuwa wannan bai shiga tsakanin sa da Mmn Abdul ba. Zaitun kuwa da bata san wainar da ake toyawa cikin gidan ba dakin ta ta shige bayan rabuwar ta da Adam, duk da taji gidan shiru tun dawowar ta daga aiki zuwa yanzun amma bata wani sa akanta ba da yake ba sune gaban ta ba a yanzu... Cikin rashin sani daga ita sai Bbn Abdul ranar suka kwana cikin gidan Zaitun duk bata san hakan ba..bcuz da tasani hankalin ta ba zai kwanta ba. Sai da ta kwashe kimanin kwanaki uku ras bata leka ko kofan gida ba haka kuma bata sake jin 'duriyar Adam ba wanda zuwa lokacin ta jima da fahimtar Mmn Abdul bata a gidan amma abinda yadan kwantar mata da hankali shine ganin Hajja ta dawo. ******* Zama yayi kasan Carpet gefen Hajiya da ke zaune bisa kujera mai zaman mutun biyu tana duban sa da mamaki tace.." Miye hakan Shahid naga ka wani Zauna kasa tamkar wani ba'ko ko me neman gafara". " Hajiya mgana nake so muyi.." " Shine sai ka zauna a 'kasa.." " Zan fi jin dadin neman alfarmar ta hakan ne Hajiya..". Gyara zama tayi tana me maida dukkan hankalin ta gareshi.." Ina jin ka toh meyafaru?". Shiru ne ya dan biyo baya fargaba yake shin Hajiya zata kar6i maganar da hannu bibbiyu ko akasin hakan, yasan abu ne mai wahala ta kar6a masa cikin sauqi shi kuma amincewar ta kadai yake bukata...gyara zama yi tamkar wani abu na tsungulin sa yayin da Hajiya Talatu ta kasa dauke idanun ta akan sa tana jira taji mecece alfarmar dayake nema din. Da kyar yayi gathering courage wajen fara harhado abinda ke mintsinan zuciyar sa. " Hajiya kin kasance min ne tamkar haske a cikin rayuwa ta, kin so ni kin kaunace ni kika nuna min gata, kika zame min mahaifiya a lokacin da na rasa tawa, bani da bakin gode miki illa inta miki addu'a muddin raina..." Ajiyan numfashi nannauya Hajiya ta sauke ga dukkan alamu maganganun nasa sun ta6o ranta ne. " Allah ya gafartawa Mahaifiyar ka ya jikan dukkan muslumi". " Amin "yace a hankali. " Ban fahimci me kake shirin fada min ba Shahid kayi min bayani dalla dalla..Insha Allahu ni mai tsaya maka ce akan komai matukar be fi karfi na ba dan bana da burin da ya wuce ganin ka cikin farin ciki". " Nagode sosai Hajiya, a yanzu amincewar ki kadai nake bukata ina so a daura min aure ne karshen satin nan..." " Aure !" Ta fada cike da mamakin sa. " Aure Shahid cikin sati guda kamar ta wasan yara..?" " Hajiya abin ne yazo min nima a bazata, ban ta6a kawo hakan cikin lokacin nan ba.." Sake gyara zama Hajiya tayi idanun ta kur akan sa, haka kawai sai taji tsoro ya tsarga mata. Tsoron abinda zuciyar ta ta darsa mata game da maganganun Shahid din taji. Kuma in ba dai hakan bane dagaske menene dalilin da zai sa ya nemi a daura masa aure cikin kwanakin da suka gaza sati daya tak. " Dan Allah kai min bayani sosai Shahid kar ka barni cikin duhu na kasa jin kwanciyar hankali, shin iyayen yarinyar ne suka matsa akan sai an yi hakan..?" " a a Hajiya..?" " Toh me yasa? Me kake tunani ko tsoro da zai ka tunanin yin aure cikin gaggawa haka? aure fa ba wasa bane Shahid Su waye iyayen yarinyar ina ne gidan su?" _Tirkashi!..inda gizo ke sakar kenan._ Cewar Adam cikin zuciyar sa, domin bashi da amsoshin dukkan tambayoyin Hajiyan ko 'kwara daya. Sai dai yana ga a wannan bigiren 6oye-6oye bashi da wani amfani dole ne ya fito fili ya bayyanawa Hajiyan koma menene. Cikin kwantar da murya cike da fargaban yadda Hajiya zata kar6i zancen ya fara fadin" Hajiya ita bakowa bace ba kuma wata ba, kuma batada wani da zata fito ta nuna da sunan nata ne a yanzu haka...ni dai kawai na tsinci zuciya ta ne cikin tsananin so da kaunar ta..dan Allah Hajiya kar kice a a kar ki hanani damar mallakan ta..." Bata jira ya karasa maganar ba ma cike da kaguwa tace.." Wacece haka ne Shahid kar ka zauce akan mace har haka mana...fada min wacece?" " ZAITOON ce!..." "Zaitun?..wace Zaitun kake nufi?" Hajiya ta maimaita sunan gami da sake tambayar sa cike da son kore shakkun ta. " Wacce ke aiki a shagon ki..." _Tas...tass...tasss_ karan saukar marin da Hajiya ta sauke kan fuskar sa kenan batare ma da ta jira taji karshen zancen nasa ba, a karo na farko tun tasowar sa yau Hajiya ta maresa har mari uku lokaci gada..ko da wasa Hajiya bata ta6a daga masa ko murya ba balle ta kai hannu da sunan dukan sa, sai gashi dalilin soyayyar sa yau ta mare shi. "..Baka da hankali..!" Fadin Hajiyar tana me sauke huci da alamu ranta yakai kololuwa ne wajen 6aci. " Ashe baka da wayo Shaheed bansani ba?..ko kunya ta baka ji? ka dubi tsabar idanu na ka wani ce min Zaitoon? duk duniyan nan baka ga 'yan mata bane sai Zaitun?" Adam dake zaune har yanzun motsin kirki ya kasa iyawa hatta marin da Hajiya ta sauqe masa bai ko daga hannu yakai wajen ba balle ya nuna alamun sun ratsa shi. Ciwo da tsoron da suka taru suka haifar wa zuciyar sa gudu mai cike da razani shine agaban sa..tsoron sa daya kar Hajiya ta kafe kan bakan ta na kin auren sa da Zaitun, bai ta6a tunani ko jin tsoron rasa abu a duniya ba sai yanzu akan Zaitun yake kuma zaune gaban Hajiya tana sauke masa ruwan bala'i..da gaske Hajiya bazata bar sa ya auri Zaitun ba kenan duba da irin muggan kalaman da take furtawa. Bai 'dago ya kalle ta ba dan baya kaunar ganin 6acin ran Hajiya dai-dai da kwayar zarra, amma dole ne a yau ya nuna mata tsananin bukatar sa ga auren yarinyar. "..Haji..ya dan girman Allah kar ki ce a a wlh ina kaunar Zaitun ina kuma tausaya mata, Hajiya kowa fa da kalan tashi kaddarar kowa da hanyar da Allah yake jarabtan sa, Zaitun a zahiri kamilalliya ce ba ta da wani aibu ko mummunan halin da zaisa ki qi kar6an ta matsayin matar 'danki, wlh Hajiya ban duban wata mace da suna soyayya ba sai Zaitun ita kadai nake so nake kuma da burin karasa rayuwa ta da ita...." " Kayi min shiru dan Allah, kayi min shiru Shahid..." Ta daka masa tsawan da ya tilasta shi yin shiru batare da ya shirya ba kamar yadda Hajiya ta bukata. " Zaitun dai! Zaitun dai!!, ko ba Zaitun dana sani me min aiki ba? Zaitun wacce ke goyon yarinyar da babu wanda yasan waye ubanta, Zaitun da kowa ya riga yasan ba yarinyar kirki ba ce? Zaitun da ke rayuwa ita kadai babu dangin iya babu na baba duk kuwa da karancin shekarun ta? Zaitun da ta shafe kwanaki da dama tana kwanan layi tamkar mahaukaciya, Zaitun dai da tazo min shago kamar almajira..saboda tausayin ta na bata aiki?..ita ce Shahid? Itace kai Shahid Adam Jibrin 'dana dana raina da hannu na zaka dube ni batare da ko 'dar ba kace min ita kake so in aura maka? Mata sun kare ne a duniya Shahid?" Hajiya ta karasa maganar tana kwalalo idanu akan Adam dake zaune gaban ta. Shikan sa jikin sanyi ya karayi, ta ya zai iya kare Zaitun wajen Hajiyan bayan duk wadannan bayan da suka kasance akan ta daba bakin Hajiyar. Hannun ta duka biyu takai bayan ta tana sakin huci me zafi gami da juya masa baya tana girgiza kai tace..." bana tunanin haka nan ta barka Shahid bazan ga laifin ka ba, tashi ka ban wuri". " Hajiya...!" " tashi ka fice min nace". Ta daka masa tsawan da yasa gaba daya 'dakin amsawa. Haka nan ya tashi ya fice yana jin kafafun sa tamkar bazasu iya daukan sa ba. Ranar haka ya yini ya kwana bai ko sake leko waje ba wanda hakan yayi daidai da cikan kwanaki hudu kenan rabon da Zaitun ta sashi a idanun ta. _Salmerh_ 😘 [20/9/2022, 12:32 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE* 💕 *( 'Yata ce)* *Salmerh MD* 🅿️ *...10* _"...Assalamu Alaikum"_ Zaitun dake zaune tana kokarin juye musu taliyar da ta tafasa a kettle kunnuwan ta suka jiyo tashin sallamar da ya taho mata da bugun zuciya...dan tana jiyo sallamar gaban ta ya fa'di sai kuma ta kasa amsawa duk da bata san da wacce Hajiyan tazo ba da yake gidan mallakin ta ne, gashi kuma itan ma'aikaciyar ta ne, duk da haka sai taji ta kasa natsuwa da zuwan Hajiyan tuni ma cire batun aiki a lissafin ta mafitar da Adam yace zai nemo musu shine kullun cikin zuciyar ta dama. Hajja ce ta fito jin sallamar Hajiyan inda ta amsa cike da fara'a mai tafe da fadanci tana kokarin bawa Hajiyan wajen zama. Kokadan bazaka dubi fuskan Hajiyan kayi tunanin akwai wani abu cikin ranta ba...ganin da tayi Hajja na shirin bata wajen zama ne yasa tai saurin dakatar da ita da fadin " a a Hajja dama nazo wajen Zaitun ne". " aww inajin tana ciki ai ki shiga mana..." Cewar Hajja tana me kokarin komawa dakin ta da fatan Allah yasa kudin haya Zaitun ta kasa biya aka kawo mata Notice har gida. _" Salamu Alaikum"_ !! Saukar tashin Sallamar Hajiyan akaro na biyu sai dai wannan karon tayi sallaman ne gami da tura kofan dakin Zaitun dake a kare ta shigo ciki wanda yayi daidai da dawowan Zaitun cikin hayyacin ta. Hijab din ta tayi saurin lalu6owa tana sakawa take amsa sallamar Hajiyan. "..Hajiya sannu da isowa... ke da kanki kuma Hajiya haka..?" " Dole ce ta sani zuwan nima ba'a son raina ba". Hajiya tayi maganar tana mai samawa kanta wajen zama bisa karamar daddumar da ta gani shinfide a dakin. Zama Zaitun tayi itama tana gaida Hajiyan a 'darare tamkar wacce tayi wa sarki karya. " Zauna me kyau Zaitun magana nazo muyi da ke". Cewar Hajiya Talatu bayan ta amsa gaisuwar Zaitunan. Gyara zama Zaitun tayi jin cewa magana zasu yi. " Zaituna kinsan Shahid Adam ko...?" Kallon Hajiya tayi tana me girgiza mata kai..." Shaa..hid Adam Hajiya kina nufin...Adam din ki..?" " Shi 'din dai, shi nake nufi..dama yana zuwa gidan nan ne..?" " erh...Hajiya yana..zuwa amma ba...sosai ba..." Tayi maganar ne a rarrabe sbd bugun da zuciyarta da ya kara tsanan ta. " Yana dai zuwan kuma wajen ki yake zuwan ko...?" Shiru Zaitun tayi bata bawa Hajiyan amsa ba...sbd ta fara hasaso dalilin zuwan Hajiyan. Bata damu da rashin amsawar ba sai ma wata tambayar da ta sake jefa wa Zaituna. " wace iriyar ala'ka ce tsakanin ke da shi..?" 'Kasa Zaitun tayi da kanta tana mai jin wani nauyi da kunyar Hajiyan na taso mata wanda sai yau din kadai ne taji haka game da Hajiyan. " Zaitun ki fada min gaskiya..." Haka kawai sai ta tsinci kanta da furta" Hajiya babu komai". Shiru ne ya ratsa dakin na 'dan wani lokaci, kowa abinda yake sa'kawa cikin zuciyar sa daban, ita Zaitun rudani ta shiga yayin da Hajiyar ke kissima abubuwa da dama sam bata ga wata dacewa tsakanin Zaitun da Adam ba, bata san me ya jashi har ya birge shi game da yarinyar ba, baza'a kira Zaitun mummuna ba kam dan kyau tana da kyanta daidai gwargwado amma ita ai a ganin ta kyan dan maciji tayi. Sai da Hajiya ta saki huci abinka da masu dan qiba sannan ta cigaba..." kikace babu komai?" Kai Zaitun ta daga cikin taraddadin abinda ya dace tace da Hajiyan. " Amma me yasa ya same ni da batun yana san auren ki..? Nasan kinsan komai gaula kawai kike son maishe dani" " Toh kiji in fada miki wani abinda baki sani ba Zaituna". Kadan ta dago ta dubi Hajiyan ta kuma 'dauke kanta da sauri" nasan a iya matsayin shekarun ki bazaki rasa sanin waye tsohon Sanata Jibrin Adam 'Dan maliki ba ko..?" Shiru Zaitun tayi tana tunano inda tasan sunan, 'dagowa tayi ta kalli Hajiya lokacin da ta tuno wani dan siyasa ne me irin wannan sunan..." Kamar tasan abinda ke ran Zaitun sai cewa tayi" 'Dan Maliki da kika sani wannan 'dan siyasan shine asalin mahaifin Adam Shaheed" Hajiya ta fadi cike da tabbatarwa. Idanu Zaitun ta zaro cike da mamaki...yayin da Hajiya ta cigaba da fadin. " Adam da kike gani ba sa'an auren ki bane, bar ganin sa haka nan Adam mutun ne shi mai matukar kima da daraja uwa uba kamilallan yaro ne da kowa zai yi alfaharin kasancewar sa 'da agareshi, bar ma natun wannan, ta ya ma ke da shi din 'karamar kwakwalwar ku take muku tunanin ni Talatu zan amince 'da na, yaro irin Adam ya auri mace wulakantacciya irin ki? Mace mai zaman kanta? Mace marar ilimi? Macen da bata san kanta ba? Macen dana tabbatar ba kamilalliya bace, macen da ta bar gaban iyayen ta ta za6i tai zaman kanta..? haba baiwar Allah ki yiwa kanki adalci mana...bana raba 'dayan biyu ma korar ki iyayen ki suka yi saboda abin kunyar dakika jajibowa kanki..? kuma ni sai in zuba idanu ina ji ina gani in bar 'dana ya kwashe ki?..me ne suna na kenan?" Shiru babu amsa tuni hawaye ya 6allewa Zaitun hakika in dai hakane ta zurma da yawa, amma me yasa sai Hajiya ta sata a gaba da wannan irin zagin cin da cin mutuncin dan kawai tana so ta rabu mata da 'dan ta...'daya bayan 'daya zagin da Hajiyan tai mata suke shiga kwakwalwar ta suke samun wuri..ji take ba'a ta6a ci mata mutunci irin hakan ba kaf din rayuwar ta. Mufee dake zaune gefe ma tuni ta taso izuwa jikin Zaitun din ta jingina daga gefen ta tamkar tasan cin mutunci akewa uwar ta haka ta tsura idanu wa Hajiyan tana kallon ta. " Dubi kanki fa? dube ki? dubi inda kike rayuwa? inda ta fadi hakan tana me rarraba idanu a dakin Zaitunan...ita kam bata bukatar sai ta kalla ko Hajiyan bata fada ba tasan cewa ita din kaskantacciya ce batun yau ba..."Ko kusa Zaitun ko alama kai ko a wasan yara sam baki dace da auren 'daa na ba, kuma matukar ina raye matukar ina numfashi bazan ta6a kuskuren barin hakan ya faru ba har abada..." " Dan haka daga yau daga yanzu..mintina ashirin ban amince ki sake karawa cikin gidan nan ba ki bar min kaya na..ki tafi duk inda zaki je, duk inda ya miki, akwai gidajen bariki da dama wadanda suka dace da zaman mace irin ki amma ba gidan Shaheed 'dina ba, gidan auren tsarkakke ne bai kuma dace da zaman mace watsatstsiya irin ki ba, ki tafi dan Allah kiyi ne sa da rayuwar yaro na.." Numfashi Hajiya ta sauke sbd dogon maganar da tayi kuma ya kasance a zuciye take yin sa dole sai da ta sauke numfashi kafin ta cigaba. " Na hada ki da Allah ne saboda in tabbatar miki cewa da gaske nake, in kuwa kika qi, kika bijirewa magana ta bisa son zuciyar ki da kwadayin da ke ranki wallahi Zaitun duk abinda na aikata agareki ki zargi kanki da kanki...". Daga haka Hajiya ta mike tsaye ta kama hanyar barin dakin jakar ta rataye a dantsen hannun ta...sai kuma ta tsaya tace.." Karki manta mintina ashirin kacal na baki ki bar min gidana kashedi na na karshe da ke kenan...". Daga haka Hajiyan bata sake waigowa ba sai jin karar kofan gida Zaitun tayi da alamu ta fice kenan. Idanun ta ta sauke kan abincin da take shirin hada musu kafin shigowan Hajiyan sai kuma ta juyo ga Mufee data kwantar da kanta bisa kafadar Zaitun din. Hannu takai ta shafi fuskar yarinyar cike da karfin hali tace" Mamana zaki ci abincin..? bari in sa miki.." Tayi maganar ne tana jan jiki zuwa ga abincin duba daya idan kayi mata sai ka tausaya mata sbd yadda yanayin ta ya nuna tsantsan tashin hankalin da take ciki..da ace tana da dama da hannu zata sa aka tayi ta zabga ihu har sai numfashin ta ya kare gana daya...amma sbd Mufeeda..ita kai saboda ita kadai dole zata so cigaba da rayuwa, zata rayu domin ta ne kadai. Duk abin da take yi kwalla bai bar sauka mata ba...hawaye ne kawai ke sauqo mata dan shidin bazata iya dakatar da shi ba...maganganun Hajiyan sun sosa ranta fiye da zaton mai karatu amma da yake tasan ta cancanci hakan sai bata ga laifin Hajiyar ba. Zaunar da Mufee tayi ta aje mata abincin a gabanta tunda ta iya dan ci dakanta kadan kadan...duk da dai tasan ba sosai take iya ci da kan nata ba amma dai tana kyautata zaton kafin ta kammala abinda ke gaban ta Mufeedan zata ci yadda ya kamata. Da yake ta riga ta sallaci azahar dama sallayar kenan da Hajiya ta samo shimfide ta yada zango akai. Shi Zaitun ta fara ninkewa har a lokacin kuma hawayen ta na zuba...cikin mintina kalilan ta gama hade musu kayan sawan su cikin wata karamar Ghana must go wanda daga iya kayan sawan bata yadda ta dauki komai ba ta dai juye guntun taliyar a bakar leda saboda Mufeeda sai kuma takalman su da bai fi kala bibbiyu ba..Mufee ce ma ke da kusan kala hudu saboda Adam na yawan siya mata. Zama tayi ta karasa bawa Mufee abincin da kanta wanda bata ma jima da fara batan ta ta nuna ta koshi sai da ta bata ruwa tasha kafin ta goge mata baki tas ta goye ta abaya tare da zum6ula Hijabi akanta. Haka ta fito daga ita sai jakan kayan su tana sake bawa kanta kwarin gwiwa, jan kofan kawai tayi ta juya ta yiwa gidan kallon 'karshe, bata so tafiya batare da ta yi magana da maman Abdul ba, ga shi ita ba waya ce gare ta ba balle ta kira ta, a irin zaman da suka yi da Mmn Abdul be kamata suyi irin rabuwar nan ba, sai gashi bazata sun rabu a lokacin da kowannen su bai yi tsammani ba, rabuwar da bata tunanin akwai ranar sake haduwar su. Hajja ce tayi saurin fitowa jin motsin Zaitun din, da yake duk abinda suka tattauna a kunnen ta ne, Hajja bata yadda ta zauna adaki ba tun bayan shigowan Hajiyan...sai gashi kunnuwan ta sun yi mata kyakykyawan ji abin faranta zuciya, ba karamin farin ciki taji ba da Hajiya tace Zaitun ta bar mata gidan ta..itama zata huta da alakakai daga yau. " a a har tafiyar kenan...?" Hajja tace da Zaitun bayan ta leko babu ko kunya balle nuna alhini. Zaitun bata ce da Hajjan komai ba baya ga juyawa da tayi, kallon ido cikin ido tai wa Hajjan batare da tayi niyyar furta komai ba. Tana shirin dauke idanun ta Hajjan tayi saurin fadin. " abu bai yi dadi ba, sai naji babu dadi kin san sabo.." Tayi maganr tana kya6e baki wanda duba 'daya idan kai mata kasan iya fuska maganar ta tsaya. " amma ni kam 'yar nan.. me ze hana ki koma ga iyayen ki ki nemi gafarar su ba fi miki wannan gantalin ba...?" Kallon Hajja tayi da farko bata yi niyyan tanka ta ba amma jin cewa shawara yau din Hajjan take bata amma me kama da cin mutunci data tabbatar kuma gaskiya Hajjan ta fa'da yasa ta bude baki da kyar muryar ta duk bata fita tace" Ni ba gantali nake ba Hajja meyasa kowa bazai fahimce ni ba?, ko can gidan na koma babu wanda zai karbe ni matukar ina tare da yarinyar nan...". " Toh ke meyasa bazaki yi irin yadda 'ya'yan zamanin keyi ba, ki jefar da ita kiyi tafiyar ki mana ko kuma ki maishe da rikon ta gidan marayu..." " Bazan iya ba..bazan iya rabuwa da ita ba.." Ta bawa Hajja amsa cike da tabbatarwa. Da yasa Hajjan bude idanu akanta sosai " aw toh...Allah shi kyauta.." Cewat Hajja kenan tana me gyara daurin zanin ta. Zaitun sake duban ta tayi daidai tana gyar rikon da ta yiwa jakar kayan su..." ni na wuce Hajja, idan Mmn Siyama ta dawo kice mata injini dan Allah ta yafe min..." Tana gama fadin hakan ta tunkari kofa bata sake waiwayar gidan ba hatta dakin da ta zauna ciki wanda ragowar kayan ta ke ciki ma bata waiwaya ba balle Hajja dake mata Allah ya bada sa'ar tafiya. Tayi tafiya me nisan gaske da ita kanta bata san inda take nufa ba, dan a har yanzun bawai sanin garin tayi gaba daya ba, mafi yawan unguwanni da wurare duk bata san su ba. Ba ita ta dakata da tafiyar ba har sai da taji tamkar kafafun ta zasu tsinke sbd gajiya, banda numfashin ta dake fita sama sama yana kokarin ankarar da ita cewar bata ci wani abin ba tun ruwan lipton da ta sha da safe, 'dan guntun madarar data rage musu Mufee ta hadawa tasha dashi ita tasha ba'kin lipton din ba ko isashshen Sugar balle mahadi makamancin bread. Bakin wani makaranta ta zauna tana dan ajiyan numfashin gajiya gashi ko sallar la'asar bata yi ba ga maghrib nan ta gabato. Gani tayi zaman nata baya da wani amfani dan haka tashi tayi ta dauki jakan kayan nasu ta cigaba da tafiyar ta, duk da bata san inda zata ba, bata san inda ta nufa ba amma gwara tayi ta tafiyar kamar yadda Hajiya ta bukaci cewa tayi nesa da shi...ita kanta a yanzu zuciyar ta tafi bukatar yin nesa da su din ko hankalin ta zai kwanta. Tun farkon alakar tasu da kanta ta ji aranta kamar Adam din ba sa'an yin ta bane amma shine duk ya kawar mata da wannan tunanin ganin yadda a kullun yake kokarin nuna musu zallar kauna yake nuna mata cewar ita din mutun ce mai daraja ashe hasashen Adam ne kawai, har yanzu darajar ta bai kai ko bakin farce ba wanda bata farga da hakan da kanta ba har sai da lamarin ta dangana da Hajiya ta tunatar da ita. Wani gida da Zaitun ta gani kawai tayi shawaran shiga inda ta roke yarinyar da ta gani akan tana so ta yi fitsari, sallah take so tayi amma tafi son ta fara yin fitsarin sannan. Batare da ko 'dar ba yarinyar ta bata buta gami da nuna mata bayin. Jaka kawai Zaitun ta ajiye ta ansa butan gami da godiya. " Da goyon zaki shiga kuma? ai da kin kawo ma na rike miki..." Yarinyar ta fada cike da kulawa..Zaitun da ke kokarin shiga sai cewa tayi. " a a bakomai nagode ." Sai daga baya ma Zaitun ta fahimci ashe yarinyar itace matar gidan, yarinya da abu mai wahala ne in zata wuce sa'ar ta, da alamu ma amarya ce duba da ganin komai na gidan sabo ne..tunani take yi itama da zuwa wannan lokacin tana nata gidan a dakin mijin ta. Alwala tayi ta fito tana shirin shimfida dan kwalin ta matar tace a a haba bari mana abaki abin sallah. Godiya tayi wa matar bayan ta ansa abin sallar. Addu'a tayi sosai takai kukan ta wajen Ubnagiji wanda har bata ankara tana yi da kwalla ba sai da taje shafa addu'ar kafin taji kwalla a idanun ta..bata tashi ba ko da ta sallame sallar la'asar din data tsaya mata tun dazun tana nan kan abin sallar ta tajiyo kiran maghrib bata yi kasa a gwiwa ba shima ta gabatar da shi, kuma duk tana yin komai ne da yarinyar ta daure dam abayan ta, dan akan yarinyar sam bata yadda da kowa. Da yake Mufeen ta tashi already hakan yasa ta sauko da ita guntun abincin su data juyo shi ta bude suka ci ita da Mufee bayan ta yiwa matar gidan tayi duk da tasan ba ci zatayi ba amma hakkin ganin ido, a baki ta ringa bawa Mufeedan har suka kammala..ta bata ruwan da matar ta basu itama tasha sannan ta sake goye 'yar ta matar gidan na murmushi tace" 'yarinyar ki kyakykyawa..." Itama Zaitun murmushi kawai tayi mata...tana ninke mata abin sallar ta bata gami da mika mata dodiyar ta, cikin ranta take ayyana kila da itama tasan labarin su da bazata karbe su har ta sakan mata fuska ba. Tafiya ta cigaba da yi yayin da duhun dare ke 'kara shigowa...bata san ina take nufa ba har ta tsinci kanta cikin wata unguwa. Yawaitar hasken kwan lantarki dake unguwar shi ya hana duhun daren tasirin bayyana kansa, Zaitun gani tayi unguwar sam bata yi kama da tasu da ta baro abaya ba. Irin Pampo da masu hali ke sawa ta wajen gidajen su saboda bukatun jama'ah da shi Zaitun tayi amfani ta samu ta sallaci Isha'in ta gefen wani gida data ta samu da 'yar lungu kuma anan ta yanke shawaran yada zango kafin gobe ta cigaba da tafiya. Tausayin kansu ya kamata musamman ma Mufeeda da take 'yar karama sai taji sharr hawaye na zuba mata na tausayin rayuwar data shigar dasu, sake rungume Mufee tayi dake lullu6e kirib cikin hijab din ta, jin yarinyar take daga jini har a zuciyar ta, yanda take kaffa kaffa da yarinyar kuwa abin har zai baka mamaki kamar zata maida ta cikin ta take jin ta...cikin zuciyar ta take fa'din" Kowa ma ya kini zan iya jurewa Mufee na, kowa ya guje ni bazan damu ba amma nayi alqawarin bazan ta6a rabuwa da ke ba har abada..Insha Allahu". Da yake unguwar ba irin me yawan mutane din nan bace shiyasa babu wanda ya lura da wanzuwar ta a wurin har safiya, itama bata damu ba balle taji tsoro dan a ganin ta ai inda sabo yaci ace ta saba haka nan da kwanan titi. Washe gari tun asubar fari tayi sallah bata huta ba ta cigaba da tafiyar ta har zuwa bakin titin da take iya hangowa. Nan ta samu inda ake kunu da kosai ta siya musu suka karya ita da Mufee tafiya kadan tayi ta ganta bakin babban titi sai ta tsaya tsam tana nazartar wurin, gefe can ta hango musakai masu neman sadaka kawai sai ta nufi wajen su tamkar ana ingiza ta. Kamar wasa sai ga Zaitun ta shiga sahun mabarata...sukan jeru ne kawai wasu na dan wa'ke irin na bara yayin da wasu ke fadin..." Allah ya baku mu samu." Wasu kuwa shiru kawai suke su tsaya da kwanonin barar su a hannu. Irin ta da bata san me zata ce ba kawai ta ajiye jakar kayan su ta zauna akai tana bin titi da motocin dake wucewa da kallo, ita kadai ta san me ke addabar zuciyar ta a lokacin, kokari take ta yaki zuciyar ta, so take ta kori dukkan kewa dake san taso mata. _".....bama wannan ba, ta ya ma ke da shi din 'karamar kwakwalwar ku take muku tunanin ni Talatu zan amince 'da na, yaro irin Adam ya auri mace wulakantacciya irin ki?_ " .......'daya daga cikin maganganun Hajiya ya dawo mata.." Tabbas ni din wulakatacciya ce...amma ba irin wanda ke kike tunani ba Hajiya Talatu...Insha Allah kuma zan tabbatar miki da hakan. Wannan maganar ne ya kara mata karsashi da kwarin gwiwan sakan jiki a bakin titin ta amsa suna mabaraciya. *Salmerh😘* [20/9/2022, 12:32 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE* 💕 *( 'Yata ce)* *Salmerh MD* 🅿️ *...11* 'Bangaren Adam Shaheed kuwa sai da ya shafe kwanaki biyu ras idanun sa basu ga hasken rana ba, sai da abokin sa Hafeez ya azazzale shi da mita kafin ya shirya ya fito, sai dai kafin ya je wajen Hafeez 'din ya yanke shawarar fara zuwa wajen Zaitun bfore ya wuce wajen Hafeez 'din dan ba karamin kewar ta yayi ba, gashi ya hana ta fita ya hana ta zuwa aiki yace kar taje ko'ina, kuma yana da tabbacin matu'kar ya hana 'din toh Zaitun bazata je ko'ina din ba kamar yadda ya bukata...in haka ne kuwa yasan jin shiru daga gare shi bai kamata ba sam domin haka na iya haifar mata da wasiwasi akan sa. Haka ya isa kofar gidan da niyyar 'kara mata 'kwarin gwiwa dan har yanzu bai cire rai da samun ta ba yana ji aransa da iznin Allah Zaitun tashi ce. Ba yau yasan halin Hajiyar sa ba, lokaci guda take hawa tamkar kumfa in kuwa ta sauka shikenan komai yake wucewa a wurin ta...yana kyautata zaton nan da 'dan wani lokaci Hajiyar zata sauko daga dokin na'kin da ta hau za kuma ta amince da kudurin sa na auren Zaitun, tunda batun aure ne ya 'dauko ba sa6on Allah ba. Komai da yake yi cikin sanyi yake yin sa, dan shi ka'dai yasan irin halin da yake jin zuciyar sa ciki...kamar kaine ace rana guda za'a raba ka da wani abu mafi soyuwa a wajenka a zuciar ka..abin ba sauqi, balle Zaitun da ya dauki duk buri da farin cikin rayuwar sa ya 'daura a kanta, be ta6a kallon kowace mace da sunan soyayya ba sai Zaitun, akan ta ya sanin zafin so akan ta yasan 'kauna ta asali da ta boge, amma rana tsaka Hajiya na neman tarwatsa duk tubalin da ya fara ginawa. Yaro ya aika kamar yadda ya saba kullun amma sai bai fahimci amsar da yaron ke san sanar da shi ba..." an ce wai bata gidan tun jiya...." Abinda yaron ya sanar da shi kenan matsayin amsar aiken da yai masa. Take yaji bugun zuciya mai tsanani.." tun jiya kuma...?" Ya sake tambayar yaron yana mai kankance idanu cike da rashin yadda da maganar. " Erh Hajja ce tace a fa'da maka...". Guntuwar tsaki yaja jin cewa Hajja ce duk ji yayi ma bai yadda da zancen ba gaba 'daya, ai duk yana da lbrn yadda Hajjan ta tsani Zaitun, baya raba 'dayan biyu wani makircin Hajja ta shirya kuma. " Amma kai kaga alamun tana gidan ne...?" Ya sake tambayar yaron. Sai cewa yayi.." a a ni dai Hajja ka'dai na gani kuma ita ta fa'da min..." " Toh fa..! Kaga dan Allah koma kace wai afa'da maka inda taje..sai kazo ka fa'da min kaji?...". Haka yaron ya koma cikin gidan, can sai gashi ya sake fitowa Hajja tafe a bayan sa da guntun mayafin ta aka... Hango Hajja bayan yaron ya sanya Adam maida hankalin sa gareta batare da ya sake bi takan yaron ba..." aww kaine ashe...yaro ai mutuniyar taka bata nan tun jiya Hajiyar gidan tazo da kanta ta sallame ta babu kuma wanda yasan inda ta nufa..." " Innalillahi wa inna ilaihi raji'un..sallama kuma kamar yaya?...ban fahimce ki ba wlh Mama..." " Koranta Hajiya tayi daga gidan inajin dai wani laifi tayi mata.." " Subhanallahi...wai kina nufin Hajiyata ce tazo har gidan nan..kuma ta kori Zaitun..?" " Tabbas...". Kansa ya dafe da hannun 'daya. " Hajiya kin kashe ni..."! bai san lokacin da hakan ma ya fito bakin sa ba saboda tsabar ka'duwan da yayi.. dafe kirjin sa yayi gami da zama bisa dakalin kofar gidan yana jin kamar ya fasa ihu ko zai sami sauqin zuciyar sa. Hajja kam ciki ta koma tana mita 'kasa 'kasa" Jimin kinbabbe, santalelen yaro da kai ka tsaya lalacewa karkashin waccan banzar..." Itakam Hajja ai barka tayi ma da faruwar wannan lamarin, dan a cewar ta an yada kwallon mangoro menene abin damuwa ban da kayi farin ciki 'kuda sun bar ka...yarinya duk tabi ta hana kowa zaman lafiya. Shi kan sa Bbn Abdul ba karamin tashin hankali ya shiga ba da Hajjan ke sanar masa yadda abin ya kasance..." ke kuma Hajja sai kika barta ta tafi batare da kin bincika kinsan inda zata je ba?" Yayi maganar ne cike da alhini gami da haushin rabuwa da Zaitun din adaidai lokacin yake tsaka da kaunar kasancewa tare da ita. Wani zabura Hajja tayi tayo kansa da masifar ya yake so tayi da ita ne bacin masu gida ne da kansu suka sallame ta...ana me zata tsaida ta. Bbn Abdul bai ko sake tanka Hajjan ba ya tafi 6angaren su yana me fatan Allah ya sake nuna mishi Zaituna a lokacin ne zai fito fili ya nunawa Hajjan cewa shifa dagaske yake son ta ba wasa ba. Wannan shine yadda suka yi da Bbn Abdul akan Zaitunan....wanda duk Hajjan tana kan hanyar komawa gida take sake tariyowa, ai kuwa sai jan wata doguwar tsaki tayi ta fara magana a fili ita kadai..." Yarinya sai kace 'kanwar ifiritu". Sam ta rasa itan wace iriyar yarinya ce, bayaga haka ace duk wadannan zabga- zabgan mazajen na shiga rudu saboda rashin ta?...( Adam da Bbn Abdul). Adam sai da ya shafe kimanin rabin sa'a zaune a wajen batare da ya motsa ba hannuwan sa daya dafe da saitin zuciyar sa bai sauke ba, shi kadai yasan abinda yake ya kuma san damuwar da hakan ya haifar masa...bai ta6a kawowa aransa Hajiya zata aikata hakan ba. Iya tunanin sa ya kure na inda Zaitunan zata shiga a fa'din garin amma bai tunano komai ba bai tuna kowa da yasan ta sani ba, gashi bata da waya taki yadda ya sai mata wayan dan acewar ta ita wa take da da har zata yi magana da shi a waya...yau ga ranar wayar ai. Daga nan bai zame ko'ina ba sai gidan Hajiya wajen Hafez 'din ma fasa zuwa yayi gaba 'daya, 'dakin sa ya shige ya kwanta, tun yana tunani har tunanin nasa ya toshe baki 'daya..sallah ka'dai ke iya tada shi. Ko da Hajiya ta dawo ma bai iya ya tanka ta ba, toh me zai ce mata? Abinda ya faru ya riga ya faru bazai iya dawo da lamarin baya ba, kuma yasan duk Hajiya na yin hakan ne a tunanin ta sbd ta tseratar masa da mutuncin sa..dan haka bai 'kara tada maganar ba kawai yake jinyar zuciyar sa a tsaye ko abinci ba iya ci sosai yake ba...kafin wasu kwanaki har ya zabge ya rame sosai. Hajiya da fari share sa tayi ta fita sabgar sa a cewar ta yayi ya gama fushin da kansa ma ze sauko ne, sai daga baya kuma da kanta ta fuskanci abin fa ba fushi ne kadai da alamu hatta lafiyar sa ma da ta jima tana tattali ya samu gi6i, sai kuma taji ta damu. _Salmerh_ 😘 [20/9/2022, 12:32 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE* 💕 *( 'yata ce)* *Salmerh MD* 🅿️ *...12* ......Kimanin sati guda kenan Zaitun na zama cikin mabaratan bakin titi kuma har a lokacin magana be ta6a ha'da ta da ko guda daga cikin masu baran ba. Ba burin ta tayi bara dan ta samu kudi ko wani abin ba a a kawai ta za6i zama cikin masu baran ne sbd tana ganin nan ne kawai ya dace da ita haka zuciyar ta yafi natsuwa da su... Cikin wani kango take kwana gefe ka'dan da titin anan take rayuwar ta ita da yarinyar ta, sai dai babu batun wanka yanzun, babu batun wanki ba kuma wajen kwanciya mai da'di, baccin ma ba samu take tayi sa cikin natsuwa ba sbd tsoron kar tayi bacci wani abin ya saman mata Mufeeda ba karamin kaffa kaffa take da yarinyar ba. Duk Zaitun ta lalace ta 'kara duhu ta zam tamkar wata zararriya, abinci kam bata rasawa sbd tana da 'dan guntun ku'da'den ta da ta6a bada hankali ta tara shi da niyyan canza musu muhalli, da shi take ta amfani yanzun duk dama ta cinye fiye da rabin sa daga zuwan ta waken zuwa yanzun. Ta kanzo bakin titin ne ta zauna kan jakan kayan ta gefe kadan da su, bata iya barin jakan ta a gefe ne sbd tsoron kar a raba ta da kayan nata domin akwai abu muhimmi da bata san ta rabu da shi sam aciki, sau 'daya wata mata ta ta6a bata sadaka har ta Naira dari biyu wanda daga nan bata sake samin wata sadakan ba..domin a yadda ta lura ma hatta su masu baran ba sosai suke samin sadakan ba. Ko yau din ma daga inda take zaune take iya hango wata yarinya daga can tsallake suna fuskantar inda take zaune, yarinyar 'karama ce da bazata haura shekara goma ba wacce ta kasance 'yar jagora ce ga wata mata wacce dukkan alamu suka bayyana cewar idanun ta ne basa gani duba da yadda take tsaye rike da wata sanda, lokaci lokaci yarinyar ke share hawaye. Duk da Zaitun bata san mene dalilin kukan yarinyar ba amma haka kawai sai taji ta bata tausayi, da farko tayi niyyar basar da ita amma sai taji sam bazata iya ba..rashin nuna jin 'kai da tausayi ba halayyar ta bane ba. Haka ta tashi rike da jakar kayan nata ta tsallaka inda suke..." 'yan mata me ya same ki ne naga kina share hawaye..." Ta tambayi yarinyar tana duban ta cike da kulawa. "...yunwa...nake ji..Yawuro kuma tace bata da ku'din da zanci abinci yanzu...". Yarinyar ta bata amsa cikin shashshekan kuka. Wannan mata me sandan ne ta zaburo da niyyan masife yarinyar nan...Zaitun da ta lura da hakan sai tayi saurin dakatar da ita..." Yi hakuri Baaba abin ai bai kai nan ba, kinsan yunwa ba kara ce da ita ba..." " Nasani Hajiya amma cewa nayi ta'dan dakata mu samu sadaka sannan nima din ai ba wani abin naci ba kawai dauriya ce..." Zaitun kam kalmar _Hajiya_ da akai mata la'kabi da shi shine yafi tsaya mata take ya ya dauki hankalin ta gaba daya, wai " _Hajiya_ "ta tabbata dan matar bata gani ne shiyasa, bayaga haka da ko kusanta ta da wannan kalmar bazata yi ba. ....Maganar ta ta karshe ce kadai ta shiga kunnuwan Zaitun..."... _nima 'din ai ba wani abin naci ba kawai dauriya ce..."_ Hakan ne yasa ta fa'din " ayi hakuri dai Baaba, itan ai yarinya ce...ga wannan ta sama muku abinda zaku ci kafin zuwa anjiman za'a rage kaifin yunwar ai.." Zaitun ta 'karashe da mika musu Naira dari biyu da aka bata sadakar sa rannan har lokacin bata kashe ba ba kuma ta canza ta ba. " Allahu Akbar..'yata angode..Allah yashi albarka ya 'kara arziki, Yah Allah ya daukaki darajar ki ya kare ki da dukkan sharri..Allah Ubangiji yayi miki abinda kikai mana, Allah ya saka miki da mafificin Alkhairi." Cikin zuciyar ta ta amsa da Amin tana mai jin dadin addu'ar...batun yau tasan irin dadin da mutun ke tsintan kansa idan akai masa taimako musamman sa'in da yake cikin halin bukata ba, tabbas itan ganao ce ba jiyau ba. Goyon dake bayan ta ta gyarawa zama 'dam sannan ta dauki jakar kayan ta da zuwa yanzun ko nauyin sa ma daina ji tayi, domin ya kasance mata ne tamkar abokin tafiya...duk motsin da zata yi yana nan a hannun ta. Sake nufan kan titin tayi da niyyan komawa can 6angaren da ta taso cikin rashin sa'a sai mota tayi ciki da ita...inda Allah ya takaita ma aka yi saurin take birki motar bata wani bige ta sosai ba kawai ta fa'di gaban motar a hankali ta sulale 'kasa sumammiya. Cikin sauri mai jan motar ta fito ashe ma mace ce wanda yayi daidai da sakin kukan da Mufee tayi saboda buguwar da kanta yayi bayan fa'duwan Zaitun. Nan take wurin ya hargitse da mutane aka kewaye Zaitun tamkar dama jiran faruwar lamarin ake. Kwance Mufeeda akayi da ke faman kuka tana fadin...Mam..mi..Mammi" da irin nata harshen. Wani mutun ne da shima yake kokarin wucewa lamarin ya afku a gaban sa, shine yayi saurin tambayar ko akwai wani nata ko wanda ya santa a kusa. Babu wanda ya bada cikakkiyar amsa game da Zaitun din dan dagaske bata san kowa ba kamar yadda suma basu san ta ba, ba ta saba da kowa a wurin ba kasancewar ta bakuwa sabon zuwa kuma mai sake jiki sosai da mutane ba. Haka aka tattara ta da ita da kayan ta Mufee dake ta faman kuka akai asbiti da su. Emergency aka shiga da ita inda likitoci suka tsaya sosai akanta dan da alama Hajiyan da ta kade ta sananna ce ba karamar mace bace ba, bayan dogon bincike ne likitocin suka gano ba wani mummunan abu bane ya same ta, amma an bari zuwa lokacin da zata farka tayi musu bayani da kanta zai fi. Zuwa karfe hudu na yamma ta farka cikin sa'a bata jin komai illa kanta da yai mata nauyi. Ko data juya gefen ta sai taga Mufeeda kwance bisa wani single gadon dake dakin itama din baccin ta takeyi cikin kwanciyar hankali. Hamdala Zaitun tayi ganin babu abinda ya samu yarinyar ta. _Dr Rasheed_ shine likitan da alhakin kula da ita yake hannun sa, ko da yazo ya duba ta bayan yai mata 'yan tambayoyi ya tabbatar ba wata matsala bai sake ce da ita komai ba sai juyawa da yayi day niyyar barin 'dakin. " Likita..?" Zaitun ta kirayi sunan shi wanda hakan ne ya dakatar da shi daga fitar da yayi niyyan yi. Waigawa tayi ta dubi Mufeeda gami da komarcda idanun ta kansa kallon...fahimtar abinda take nufi da yayi ya sanya shi fadin" ba abinda ya same ta.." " Alhamdulillah..". Zaitun ta furta a fili gami da lumshe idanun jin dadi, wani natsuwa taji ya saukar mata sai yanzun taji hankalin ta ya kwanta sosai fiye ma da 'dazu. Wasa- wasa taga har dare ba'a basu izinin tafiya ba gashi kuma ita takure take kasantuwar bata yi wasu salloli da suka hau kanta ba..gashi babu wanda ya sake bi ta kansu har sai bayan maghrib kafin taga wata mata kyakykyawa me girman jiki ga gayu wacce da ganin ta kasan Naira sun zauna dai dai gwargwardo. Ita ta fara shigowa bayan ta kuwa wata budurwa ce da zata girmewa Zaitun da kusan shekaru hudu ko biyar sai dai kana ganin yarinyar kasan tarbiya bata samu muhalli anan ba sai taunan chewing gum take tamkar ba sansanin masu karancin lafiya take ba. " Hajjaju dama akan wannan abin kika tashi hankalin ki har haka..?" Tayi maganar cike da rainin hankali tana jifan Zaitun da kallon kaskanci. " Ki min shiru Shaheeda bana san irin haka fa". Matar nan da aka kira da Hajjaju ta fadi tana mai karasawa gaban Zaitun dake kwance tana kallon ikon Allah. Wacce aka kira da Shaheeda kam baki ta kyabe gami da ajiya ledan da dake hannun ta. " Sannu baiwar Allah.." Cewan babban matar da kulawa. " Da kai Zaitun ta amsa ta tana mai kare mata kallo. " Ya jikin naki ?" " Alhamdulillah da sauqi sosai...". Zaituna ta fadi tana mai kokari tashi ta zauna. " Masha Allahu, zuwa safiya ma insha Allahu inajin za'a baki sallama tunda jikin ba wata matsala". Shiru ya 'dan biyo baya sai karan taunar chewing gum din Shaheeda kadai da ya cika dakin. Can Hajiyar ta nisa tamkar ta tuna wani abu ganin yadda Zaitun ke yawo da idanun ta kansu..." kinga baiwar Allah saki jikin ki kinji, nasan baki san mu ba amma nice wadda na kade ki da mota wanda hakan ya faru ne bisa rikicewa da nayi ganin bazata na ganki gabana...ki gafarce ni..." " Bakomai Hajiya haka dama Allah ya tsara.." Cewan Zaitun cikin sanyin murya mai cike da rauni...dan duk sunyi laushi daga ita har Mufeeda kuma ta tabbatar duk yunwa ce ke cin cikin nasu. " Wannan fa...?" Hajiyar ta tambaya tana duban Mufee dake gaban Zaitun tayi luf cikin.jikin ta. Itama maida idanun ta tayi kan Mufeen haka ma Shaheeda dake can gefe tana jifan su da kallon kaskanci... " 'YATA CE.." Cewar Zaitun cike da tabbatar wa. " Masha Allahu...kyakykyawa abinta.." Cewar Hajiyan tana sakin murmushi. " Hajiya ina so nayi sallah dan Allah.." "Ahhh..ai ga bayi nan, ki shiga ki yo alwala kiyi sallah sai kuci abinci...Shaheeda miko abincin nan.." Ta karashe maganar da waigowa tana duban inda Shaheedar ke tsaye. Wani farin ciki ne ya lullu6e zuciyar Zaitun dama duk tunanin ta inda zata sama musu abinda zasu ci ne musamman ma Mufee da tafi tausayawa..gashi kuma kaf dakin bata ga alamun jakam kayan ta suke ba balle ta yi tunanin amfani da 'yan kudin ta wajen sama musu abincin. " Hajiya angode.." Shine kadai abinda Zaitun ta fa'di. Kafin Hajiya tace wani abu Shaheeda cikin tata kalar shagwa6a tayi saurin fa'din.." Hajjaju dan Allah ki tashi mu wuce..kin manta akwai inda zamu biya ne...?" Murmushi kawai Hajjajun tayi sannan ta mike..." Bari mu wuce zuwa safiya Insha Allahu zan dawo kinji, Allah ya kara afuwa.." Daga haka suka fice batare da sun kara ko waiwayan su ba. Zaitun kam dama ba sabo tayi da kashe jikin ta ba dan suna fita ta mike bata jin komai a jikin ta illah kanta da ke sara mata sosai bayin ta leka sai taga ba mai wahalar amfani bane shiga tayi tayo alwala ta dawo dakin, sai da ta jero sallolin ta kaf sannan ta mike, ledan nan da suka ce abinci ta bude sai taga abinci ne a takeaway har guda uku, ba tare da 6ata lokaci ba suka far wa abincin nan tana ci tana bawa yarinyar har suka jisu full kafin suka sarara bayan sun dage takeaway biyu daya ya rage suka sha ruwan roba da ta gani a ledan shima guda biyu. Take taji natsuwa ta shige ta jin ta dam Mufee ma a koshe, rungumo Mufee tayi abu daya ne yanzu matsalar ta shine sanyi da suke ji, amma bai wani 'daga mata hankali sosai ba, dan ta jima da lura da Mufeeda duk irin sanyin da ake da zarar ta shigar da ita jikin ta ta lullu6a mata Hijabi shikenan bata sake motsin kirki, dan haka wannan damuwar sanyi bata wani dame ta sosai dan tana da yadda zatayi da Mufee. Haka kawai sai take jin tamkar su tabbata a haka a dakin asbitin...amma tasan hakan ba me yiyuwa bane. Washe gari kuwa kamar yadda Hajiyan ta fadi aka basu sallama bayan Dr Rasheed ya sake duba ta haka sun 'dunguma motar Hajiyan batare da tasan inda za'a kai su ba, kuma bata ga fuska daga wurin kowa da zata iya tambaya ba dan yau din Hajiyar ma a 'dime take. Gida ne tsararre daya sha kyau har ya gaji, Zaitun tun da take bata shiga gida irin wannan ba, kenan yau din shine karonta farko data'' shiga irin hakan, wanda kafin yau din sai dai ta hango su daga nesa ko kuma ta wuce ta kofar irin gidajen batare da tunanin itama akwai ranar da zata zo har ta iya tsintan kanta a irin gidajen ba. Parlour suka yada zango wanda suna shiga Hajiya ta fara kwala kiran wata me suna _Na'eema_ bakin ta uku kafin Na'eeman ta amsa gami da fitowa dan kwalin ta a hannu tana kokarin daurawa a kanta. " Ina kuka shiga ne haka da bakwa jin kira.?" Tayi maganar tana me zama bisa daya daga cikin kujerun parlour. " Wallahi Hajjaju bacci ke shirin dauka na..." cewar Na'eeman da itama ta zauna daura da Hajiyar. " Ga dai aiki na samo miki amma kafin nan bari inga ko ta gida ce" Tayi maganar tana me maida duban ta Zaituna. " Baiwar Allah sai gaki a gida na ko?" 'Murmushi kawai Zaitun tai mata. " Ni suna na Hajiya Mardiya..amma anfi sani na da Hajjaju kamar dai yadda kika ji 'yan matana na kira na da shi...nasan bazaki gane ni ba amma ni nasan ki...kwanaki kalilan da suka gabata na ganki a wurin can har na baki sadaka kafin na wuce kuma ko ajiyan ma wallahi dan ke kadai na bi wancan titin cikin rashin sa'a kuma sai ga abinda ya faru...". Cike da mamaki Zaitun ta dago kanta ta dubi Hajiyar tabbas ta tuna wata mace ta bata sadakan gudan Naira 'dari biyu sai dai a lokacin bata da cikakkiyar natsuwan da zata tsaya gani balle har ta tuna wacce ta bata sadakan. Jin shiru daga 6angaren Zaitun ya sanya Hajjaju cigaba da fa'din.." Nasan abu ne mai wahala ki iya tunawa amma babu wani abu, tun inda aka kade ki mun bincika ko dakwai 'yan uwan ki amma bamu samu kowa ko wanda ya sanki a wurin ba, fatan zama tare damu bazai zame miki matsala ba..?" Ta 'karashe da sigar tambaya. Kai Zaitun ta girgiza mata alamar a a. " Da kyau...kin taimaki kanki yarinya.." Cewar Na'eema kenan tana murmusawa...yayin da Hajjaju ta cigaba da fadin " Zaki zauna tare da mu ki zam 'daya daga cikin ahalin gidan nan...?" " erh Hajiya Insha Allahu." " Ki 'kirani Hajjaju nafi jin dadin sunan haka..". " Ni nice shugabar gidan nan akwai kuma sabbin tsaruka namu na 'yan gidan nan da zasu biyo baya amma kafin bayyana su gare ki sai naga kin saki ciki damu tukunna, a yanzu dai ina so naga walwala a fuskar ki kamar yadda zaki gani ga sauran 'yan uwan ki fatan kin fahimce ni..?" Da kai Zaitun ta bata amsa. " Wannan da kike gani sunan ta Na'eema, kuma daga yanzu har zuwa lokacin da naga sauyi itace zata kasance shugabar ki mai kula da duk al'amuran ki, ita zata koyar da ke salo da tsarin kasancewa cikin ahalin Hajjaju...Na'eema ga wannan sabuwar 'daliba ce..ya ma sunan ki...?" Ta karashe maganar da tambayan sunan ta... A hankali da sanyin murya tace..." Suna na Zaitoona.." " Toh Zaituna..mu dai Zaitoon zamu kira ki.." Cewar Hajiyan tana murmushi..." Na'eema ki shiga da ita ciki akwai jakan ta a nan dakin ki nuna nasan zata bukata....in kin shigan ki turo min Muhibba.." " Toh Hajjaju..". Salmerh😘 [20/9/2022, 12:32 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE* 💕 *( 'Yata ce)* *Salmerh MD* 🅿️ *...13* Wani 'daki aka kai ta babu komai a dakin sai katifa da walldraw din bango sai wata kofa data ke kyautata zaton bayi ne kamar na asbitin da ta baro da safiyar yau din. Suna shiga Na'eema ta wuce ciki murafen waldraw din ta bude gaba daya ta wangale a gaban Zaitun tace" ga Ghanar ki anan ga kuma can bayi.." Tayi maganar da nuna kofan bayin sannan ta cigaba..." Ko ba'a fada miki ba ai kinsan jikin ki na bukatan ruwa ko..? Zan je in dawo yanzun nan..". Daga haka tayi waje abinta. Daga nan sakon Hajjaju ta mika na kiran Muhibba sannan ta dawo wajen Hajjajun tana me dan 6ata rai. Hajjaju da tasan kwanan zancen sai murmushi kawai take yi tana duban fuskar Na'eeman..." Wlh Hajjaju wannan tayi local da yawa...baki na har tara yawu fa yake idan na je kusa da ita..." " Na'eema kenan...bazaku gane bane, wannan da kike gani ba karamar kadara bace bari ta wanku zaki sha mamaki...". 'Karamar tsaki Na'eeman ta saki kawai ta kawar da kai gefe. 'Bangaren Zaitun kuwa wanka tayi ta kuma yiwa Mufee wanda cikin sa'a da bude pampo ga mamakin ta ruwan dumi taji yake zubowa hakan ba 'karamin farin ciki ya sanya ta ba, take tai wanka ta kuma yiwa Mufee ta wanke musu kawunan su duk, dan dama sosai ya ishe ta hakuri kawai take da dauriya saboda rashin sukuni kuma babu yadda zata yi. Ko da ta fito wankan jakan kayan sun kaf ta zazzage bisa wannan katifar, rigan Mufee guda 'daya tak ta rage mara datti sai kuma pant dinta guda biyu amma sauran kayan duk masu datti ne ita kan ma bata ga na sawa cikin nata kayan ba dole suna bukatan wanki. Man shafan su ta ciro suka shafa wanda tun ranar da ta bar gidan Hajiya Talatu jikin su bai sake ganin mai ba sai yau...shiyasa suka kokkode. Sai da ta gama shirya Mufeedan sannan ta tattari kayan su masu dattin ta shiga bayin dakin da yake tana da ragowar sabulun ta da omo da ta taho da shi daga gidan Hajiya da su tayi amfani ta wanke musu kayan su kaf wanda tana cikin wankin ne Na'eema ta dawo ganin hakan yasa tace.." aww dauraya kike toh in kin kammala akwai igiya ta bayan kitchen, ta cikin Kitchen din zaki fita.." " ai ban san kitchen din ba..." " Ina Parlour idan kin gama.." Cewar Na'eeman kenan ta sake ficewa. Zaitun sai ta rasa wannan su wasu irin mutane ne da basa bawa mutun abinci..tunanin yarinyar ta take damma tayi bacci yanzun amma ai inta tashi dole bukaci cin abinci. Koda ta kammala wankin bata je wajen shanyan ba zama tayi wajen Mufee cike da lalla6i ta bi ta kitse mata gashin kanta, ba wani iya kitson tayi ba amma da yake gashin yarinyar mai kyau ne kuma ya hadu da hasken fatar ta sai kitson ya dan fito yarr ya kuma yi mata kyau...murmushi tayi cikin ranta tace _" Ya dai fi babu.."_ . Sai lokacin ta dauko bucket din da ta tara kayan shanyar ta fito...Na'eeman ce ta nuna mata hanyar kitchen ta bi ta kofar baya ta shanya kayan tas. ***** Wasa wasa yau ga Zaitun tana cikin kwanaki na sha uku a gidan Hajjaju...tuni sunyi fes da su daga ita har Mufeeda dan basu da matsalar komai. Na'eema kuwa bakomai yass aka hada ta da Zaitunan ba illa ganin shige da ficen ta, yanayin rayuwar ta da yarinyar ta, gefe guda kuma kula da tsabta da cimar su...jikin su duk yayi kyau yanzu bazama kace Zaitunan nan bace ta wajen Mabarata. Abu guda da ta lura da shi kuma yake yawan faruwa a gidan shine yawan shige da fitar maza, wanda lokuta da dama idan sunzo din sukan fita da wata daga cikin 'yan matan Hajjajun ne wadanda suka tasamma goma sha 'daya. Itama ba rana guda ta fahimci hakan ba sai a hankali, kuma ta fahimci Hajjajun ba ita ce ta haifi 'yan matan nan ba kawai ita ta kasance ne tamkar shugabar su. Ita dai har yau din bata samu matsala da kowa daga cikin su ba har gara ma Shaheeda itace sam ta tsani ganin su bata kuma san dalili ba. Bata da lokacin saka damuwar kowa aranta a yanzu dan haka itama banza ta bawa ajiyar ta..damuwar ta yanzu daya ce tuno gida da take yawan yi tana kewar su sosai tana kuma san ganin ahalin ta..abu guda dake taka mata birki shine kasancewar Mufeeda tare da ita. Gefe guda kuma ga Adam..bawan Allah mai kyakkyawar zuciya, bata san ya zai ji idan yazo ya tarar Hajiyar sa ta kore su ba..irin yadda ya nuna yana tausayin su tsawon zaman su da shi ya sanya a kullun sai ta tuna da shi...gefe guda kuma Mmn Abdul...kullun fatan alkhairi take binta da shi ita da zuri'ar ta. _Bayan kwanaki ashirin da biyar._ Yanayin yadda rayuwar gidan ke guda na sai yazo ya fara bawa Zaitun tsoro dan zuwa yanzun ta gama fahimtar su wanene Hajjaju da kuma manufar ajiye ta tare da su. Sosai abin ya razana ta dan haka sai ta fara tunanin yadda zata yi ta rabu da su tun kafin wankin hula ya kaita ga dare...ita ba kalan rayuwar da take da burin aikatawa ba kenan...ba shine a gaban ta ba. Tana cikin tunanin mafita kwatsam da wani dare sai ga 'yan fashi sun shigo musu gidan aka tattaro su gaba daya zuwa babban parlourn gidan inda 'aka ritsa Hajjaju da bindiga saitin kanta...daren ba wai ya raba bane dan dududu bai wuce karfe sha 'daya bane. na dare, kuma a yanayin da 6arayin suka zo sun zo musu da sigar bakin da ke zuwa musu, har Hajiya na murnar tayi manyan bakin kwana bisa ga yadda taga shigar su babu karanta a ciki sai kuma akayi rashin dace ashe sa6anin tunanin Hajiyan ne. Ita kanta Zaitun da ace bata ga bindiga ganin idanun ta ba da bazata ta6a yadda cewa 'yan fashi bane, sai dai tace abokan huldar su Hajjajun ne kawai suka zo, amma ganin bindiga ya sa jikin ta tsuma ta rungume Mufeeda sosai idanun ta kuwa ko bude su bata sake iyawa ba saboda tsoro. Bata san me ya faru ba kuma, ta dai farka ta ganta kwance a dakin ta na gidan ga Mufeeda rungume da jikin ta kadan..suna baccin su. Saurin mikewa tayi zaune tuno abinda ya faru sai dai kuma bata ga alamun 6arayin nan a gidan ba hakan ya sa ta gyarawa Mufee kwanciya ta tashi, hutun sallah takeyi shiyasa koda ta shiga bayi ta fito bata nemi abin sallah ba kawai tayi waje. Can babban Parlour ta hango su Hajjaju zaune sun yi jigum- jigum. Nan take jin labarin yadda abin ya kasance daga abikin su, anan ne ma ta fahimci cewar ita din doguwar suma tayi. Gwala- gwalan Hajjaju duk suka kar6e inda suka kuma bawa Hajjajun sati biyu kacal ta nemi wurin shiga ta bar musu unguwar su in bahaka 'kone gidan za suyi gaba daya kowa ma ya huta. Babu wanda bai shiga tashin hankali bisa ga bayanan 'yan fashin ba gashi duk sun rasa dalilin wannan lamari. Dole bayan kwana biyu da abin ya dan bar jikin su Hajjaju ta fara tunanin mafita yadda zatayi da 'yan matan ta...a fizge Zaitun take jin sabon tsarin da Hajjajun ta yanke musu dole sai ta rarraba su ga kawayen ta magajiyoyi irin ta kafin tayi settling sabon waje ko garin da zai fi dacewa da su. Bayan shu'dewan kwanaki biyu Hajjaju na ta hada- hadan rarraba 'yan matan ta, duk kuma abinda suke yi basu saka Zaitun cikin sabgar su dan a har lokacin bata gama sakan jiki da su ba amma Hajjaju ba karamin tattalin ta take ba, duk wani abu na jin dadin rayuwa takan wadata Zaitun da shi saboda ta kwantar mata da hankali hadda Mufee take hadawa. Ranar wata Juma'a ne Zaitun na a 'daki ita da Mufee tana yanke mata farcen ta sai da ta gama na Mufee kafin ta fara yanke nata ma. Sanye take da wata doguwar rigar abaya peach colour wanda Hajiyar ta sai mata sai mayafin rigar data yafa a kanta, yayin da Mufee ke sanye da wata riga irin ta yara armless iya gwiwan ta sai takalmin ta baki mai igiya har baya. Cak ta tashi da irin tafiyar ta da har yanzun bai gama warwarewa ba ta dauko goran ruwa da yake emty tana jijjigawa..." Mam..mi..u..wa..". Ta fadi hakan tana tahowa wajen Zaitun... Zaitun bata sha wahalar fahimtar abinda yarinyar ke bukata ba dan haka take ta mike ta 'dauke ta suka nufi hanyar kitchen dan nema ruwan da take bukata. Kadan ya rage su karasa babban Parlour kunnuwan ta suka jiyo mata abinda ya 'dugunzuma hankalin ta baki daya. Muryar Shaheeda ta tsinkaya cike da tsiwa mai tafe da rainin hankali tana fadin..." Kai Hajjaju Zaitunar...amma dai sai an....... Salmerh😘 [20/9/2022, 12:32 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Salmerh MD* 🅿️ *...14* "..Kai Hajjaju Zaitunar..?...amma dai sai an raba ta da yarinyar nan ko, dan kinsan Hajiya Kameela bazata yadda ta kar6e ta da yarinya ba.." Nisawa Hajjaju tayi kana tace " Nima nayi wannan tunanin wlh Shaheeda na kuma samo mafita tuntuni, akwai wata Hajiyar Bangis da kwanaki muka je wajen tannan can Hayi kin tuna ni ko ba dake muka je bane? Mubeena kamar da ke ne ko...?" Ta kai karshen zancen da juyawa ta dubi mai suna Mubeenar. "...erh Hajjaju da ni ne ban manta ba kuma..." Amsar Mubeenar kenan dake daga can gefe tana faman latsa waya da taunar cingum lokaci guda. " Toh ita ai tana amsar kananun yara, can take kaisu Lagos ake dillancin su ina ga itama wannan din hakan za'ayi kinga ba kare bin damo dole ta saki ranta damu in ta wayi gari taga babu 'yar...." " Ho Hajjaju...Ho Hajjaju uwar 'yan mata, Hajjaju maganin kukan mu...." 'Yan matan nata da basu fi uku a wajen ba suka saki shewan da zai baka mamaki. Murmushi Hajjaju tayi cike da jin dadin yadda 'yan matan ke fasa mata kai...tace" ni ina Sa'eeda ne mutumin ta fa ya shigo gari is better ta zam cikin shiri kunsan 'Dan maliki babu sauqi.." " Wlh Hajjajun mu baki da kyau..". Cewar 'daya daga cikin su tana me sakin dariya gami da mikewa..." Bari kuwa inje in tunatar da ita dan nasan mu ma zamu 'dan ji'ku albarkacin masu albarka..." Tayi maganar tana me nufan 6angaren da 'dakin Sa'eeda yake. Daya ke ko ina 'dakuna ne birjik zagaye da babban Parlourn gidan. Zaitun kam da ta ji wani fa'duwar gaba bata san lokacin da ta juya ta koma dakin ta ba harda sa lock a kofar, ba ta ma tsaya ta saurin sauran surutan nasu ba dan bashi ne gaban ta ba, sunan ta da taji da kuma na Mufeeda shine kadai damuwar, the fact that za'a rabata da Mufee shi yafi dugunzuma hankalin ta, tsoro da fargaba duk suka diran mata lokaci guda..banda 'kwalla babu abinda ke mata zarya...dukkanin ilahirin jikin ta rawa yake...ko nan da can ta kasa matsawa sai da tayi kuka mai isan ta kafin ta fara tambayar kanta. " Wai me yasa kowa bai san ganin ta tare da Mufee ne? Meyasa kowa be son ta..? Shin 'yar yarinyar nan akwai abinda take tare musu ne ko me...?" Tashin hankali da damuwar da Zaitunar ta shiga sosai ya kasa 6oyuwa agare ta...tun lokacin da taji zancen kuka bai bar idanun ta ba...karshe sai a bayi ta tarawa Mufee ruwan tasha ba ta iya ta sake fita cikin ahalin gidan ba ko kaunar ganin guda daga cikin su ma bata yi...cikin kayan kwalam da Hajjaju ke 'dan siya mata ta samawa Mufee biskuits ta ci tasha ruwa akai..dama yarinyar ba wani cin abincin azo agani take ba shiyasa bata dame ta ba tai baccin ta. Can kusan la'asar taji ana nocking 'kofar kamar bazata bude ba amma kuma sai ta tashi ta bude jin muryar Na'eema...tana budewa kuwa Na'eeman ta gani hannun ta rike da plate din abinci suka ha'da idanu...kowa tsayawa yiwa 'dan uwan sa kallon tuhuma yayi...yayin da Na'eema ta zaro idanu kan fuskar Zaitun din tace..." Kai Maman Mufee kin ga idanun ki kuwa..hala ciwo suke miki..?" Kawar da kai Zaitun tayi gudun kar Na'eemar ta dago damuwar ta tana duban gefe ta bata amsa da fadin " Zogi suke min..koda nayi bacci kuma sai duk suka kumbura..". " Kai sannu..dama abinci na kawo miki, yau fa duk ma baki fito ba Hajjaju ma da kanta na cigiyan ki ". " Zan fito bari na 'dan watsa ruwa kafin.." Zaitun ta fada tana me ansan abincin daga hannun Na'eema, kamar tace bazata ciba Na'eemar ta koma da shi amma gudun kar ta gano manufar ta yasa ta ansa kawai. " Da dai yafi gaskiya..ki 'dan fito ko 'yar hiran nan ma ai tana 'debe kewa". Na'eema ta fada tana juyawa cikin tafiyar rausaya da a kullun ake kokarin koyawa Zaitun shi...Sai da ta sake rufe kofar kafin ta koma cikin dakin. Ruwan ta shiga ta watsa kamar yadda ta fada dan koba komai ita kanta tana so taji dadin jikin ta sosai ta wanke fuskar ta da ruwa me 'dan 'dumi sbd kumburin fuskar ya sake. Tana fitowa kuma sai ta ci karo da Mufee ta tashi daga baccin tana rarraba idanun neman ta dama baccin da take yi yin ne ya sa Zaitun barin ta bayan ta rufe ko'ina ta tabbatar da babu hanya ko kafar da wani zai iya shigowa..." Yauwa Mama na zo in miki wanka kema dan dukkan alamu sun nuna wata kaddarar ke son sake tunkaro mu.." Ta karasa maganar tana 'dago Mufee gami da cire mata kayan jikin ta. Mai take shafa mata amma idanun Mufee na kan Plate din abincin nan da ke ajiye can gefe wanda ita Zaitun ma tuni ta manta da shi. Ko da Zaitun ta lura da hakan sai ta 'dago ta sama.." Feefy na abincin kk so..?" Tayi tambayar cike da kulawa, duk tasan ba amsa zata samu daga yarinyar ba amma yanayin ta kadai ya bayyana mata amsar da take bukata. Ita kadai take magana..." Ban so ta6a abincin nan ba Feefy amma babu yadda zanyi tunda kina jin yunwa..dole zamu ci, tare zamu ci shi in ma abin mutuwa ne a ciki na 'kwammaci mutuwar ta riske mu a tare, da in barki ko ki barni cikin wannan duniyar..." ( Hala Zaitun ta manta cewar kowa na da rana da kuma silar ajalin sa). Hakan kuwa akayi tare suka ci abincin suka sha ruwa. Zugum Zaitun ta zauna tare da yarinyar saman cinyar ta ita nan wai tana jiran taga me ya zai faru da su bayan sun ci abincin, daga 'karshe har ta gaji ta watsar da batun abincin...amma ta gama yankewa cikin ranta cewar ayau din nan ba sai gobe ba zata bar gidan...dole ne ta bar shi kafin su rabata da 'yar ta...domin bata da tasirin da ta isa dakatar da su daga abinda suka yi niyya bata kuma san ta ina zasu farmake su ba balle ta dau mataki, shiyasa gara ta yunkura kafin su su riga ta, a yanzu ta gama fahimtar cewa mutun a duniyan nan ba abin yadda ba ne. A lokacin da ka saki jiki da shi ka bashi amanar kanka a lokacin shi kuma zai fara yunkurin cutar da kai, wani ma burin sa ganin bayan ka ne gaba daya. Tun kafin maghrib ta zazzage kayan sawan su kaf, ta dauki duk abinda take da bukata abinda tasan bata kaunar rabuwa da shi iya su ta dauka sai Panties din Mufee da Pampers da Hajjaju ta sai mata da wasu rigunan ta guda uku, sai nata na kanta itama dogin riguna ta dauka ta atampa 'daya da kuma abaya da duk Adam ne ya sai mata, sai wata rigar material da tun tana gidan Hajiya Talatun shima ta 'dinka, cikin wata leda mai kyau na kayan shopping ta zuba kayan. Shiga mai kyau ta yiwa yarinyar complete set na kayan sanyi hadda socks da hula akanta dan cikin zuciyar ta take da tabbacin yau ma za suyi kwanan layi, riga ta saka ta atampa a jikin ta da skirt, sukam sabbi ne cikin wanda Hajjaju ta dinka mata, Babban Hijabin ta ta 'dauka ta sanya shima har 'kasa. Sai da ta maida kayan kaf ta maida su ma'ajiyar su, abin goyo ta 'dauka ta goya Mufeeda 'dam abayan ta sannan ta gyara ko'ina a 'dakin ta yadda babu wanda zai yi saurin fahimtar bata 'dakin. Ta gama fahimtar duk yanayin rayuwar gidan daga yamma zuwa maghrib duk shiru zakaji gidan kowa na nasa 'dakin sai kuma bayan maghrib hada hadar gidan ke tashi, ba'kin gidan ma sai a lokacin suke 'kara yawaita hakan yasa ta zauna zaman jiran jin kiran sallah. Mintina ka'dan kunnuwan ta suka fara jiyo mata tashin kiran sallah, ta window dinta ta leka Baba Habu mai gadi, tasan halin sa Baba Habu mutun ne shi mai matukar kula da lokutan sallah baya ta6a bari jam'i ya shige masa dan haka tana nan tsaye take hango bakin gate. Bata ga Baba Habu ba bata kuma ga alamar yana nan a kusa ba, tsoro ne taji ya tsarga mata, tsoron kar sai ta fita kuma taci karo da shi, bata so kowa ya ganta tafi son kafin su farga bata gidan sai ta yi musu nisa sosai. Tana daga tsayen taji an shiga sallah a masallacin dake kusa da gidan nasu wanda yake ta hannun dama daga gidan makwabtan gidan Hajjaju. Jin an shiga sallah ya sata tsaida tunanin ta a yanda tasan halin Baba Habu matukar yana kusa da gidan nan toh a yanzu haka yana masallaci, in ma baya kusa da gidan a duk inda yake tasan masallaci yake. Wannan tunanin ne ya bata kwarin gwiwar fitowa ta tasamma tsakar gidan bata so ta yi ko waiwaye ko wani motsin da zai sa su fahimci rashin gaskiyar ta..dan haka tunda ta tunkari kofar bata juyo ba har ta fice...wani sassanyar ajiyar zuciya ta sauke gami da hamdala batare da ko waiwaye ba ta fuskanci hannun hagun ta wanda ta yi hakan ne saboda tayi hannun riga da masallacin da take tunanin Baba Habu yake. Sai da ta fito ne ma taci karo da kujerar zaman sa wajen kofar da alamu daman tun yammaci anan ya yada zango. Zaitun bata ji zuciyar ta ta sake ba har sai da ta tsinci kanta a bakin layin da ya kasance shine gaba da na Hajjaju, tayi hakan ne kuma saboda ta jirkita tunanin duk wanda ya fito da niyyar neman ta, tayi tafiya me nisan gaske da har duhun maghriba ya riga ya gauraye ko'ina sai hasken farin wata, tabbaci da taji cikin zuciyar ta cewa ta yiwa Hajjaju nisa ya sata sakin ajiyar zuciya, kuma sai a sannan taji natsuwa ta 'dan shige ta, ko ba komai ta rabu da masifa, ta rabu da mugun iri ita da 'yar ta, ta rabu da makasan farin cikin ta...domin aganin ta duk me niyyar raba ta da Mufee toh shine babban makashin farin cikin ta a duniya, _marar 'kaunar Mufeeda kuwa bata jin har duniya ta na'de itama zata kaunace sa_ . Da yake tana hutun sallah hakan yasa bata yada zango ko'ina ba tafiya take batare da waiwaye ko 'dar ba har akayi sallahr isha'i tana kan tafiya, tun tana ji da ganin hayaniyar mutane har ya fara tsagaita, gari ya fara yin shiru, bataji tsoro ko 'dar ba wannan karan ma, dan tasan itace 'kwarin gwiwar duk su biyun, idan ta karaya tun yanzun bata jin zasu iya cimma nasara, amma har sai yaushe zata bar wannan guje gujen?, har sai yaushe natsuwa zata same su itada Mufee..?" wannan abin na cimata rai ba 'dan kadan ba. Bata so Mufeeda ta taso ta tarar da su cikin wannan halin, bata so rayuwar yarinyar ta 'kuntata...bata so sam taci amanar da Allah ya bata. Ba Zaitun ta dakata da tafiyar ba har sai da taji ta gaji da tafiyar, taji 'kafafun ta sun gaza tafiyar kafin ta sarara karkashin wata rumfa da ta kasance majalisa ce ta wasu manyan mutane amma da rana suke zaman majalisar ba dare ba..nan rumfar take gefe daf da titi..kuma anan Zaitun ta yanke shawaran kwana dan aganin ta yafi mata musamman da taga tabarmi ninke ajiye a gefe..zuciyar ta taji tafi kwanciya mata da nan din, dan zuwa yanzu ta gaji da halin mutane, bazata sake neman alfarma wajen kowa ba matukar ba ya zam mata dole bane, mutane 'daya suke duk karshe tsagwaron butulci suke nuna mata..gara tayi rayuwar ta, zata nema da duk karfin ta, da lafiyar ta da lokacin ta, zata yi duk wani aiki ko min wuyar sa dan tseratar da rayuwar ta data 'yar ta. 'Bangaren su Oganniya Hajjaju da 'yan matan ta kuwa, duk wani shirye shirye sun kammala dan Hajjaju ta riga tayi magana da Hajiyar Bangis, ta kuma amince zata kar6i yarinyar, dan haka a yau din nan ba sai gobe ba zasu kai mata Mufeeda. Maganin bacci aka shirya cikin abincin Zaitun wanda da zaran taci babu 6ata lokaci bacci mai nauyi zai 'dauke su daga ita har yarinyar matukar abincin ya ziyarci cikin su, koda 'dan ka'lilan ne kuwa sai ya bugar da su, a fa'dar su hatta ita yarinyar sai dai ta budi taga babu uwarta haka ma Zaitun zuwa lokacin da maganin zai sake ta Mufeeda tai mata nisa...shikenan an musu farraqu. Duk da Na'eema na jin babu dadi cikin ranta na yadda duk yinin yau din ita ke ta hidimar abincin Zaitun tamkar wata baiwar ta sai dai na yanzun bata ji wancan damuwar tayi tasiri cikin ranta ba musamman sbd yadda take ganin nasara ga cikar burin su, ba 'karamin 'kaguwa tayi taga wannan Zaitunar ta dulmiya cikin harka irin tasu ba, duk da kwanaki data kwankwasata ta fahimci kamar ba'kuwa ce a harkar sai dai ta kasa yadda sam da hakan musamman kuwa data ke ganin ta hadda yarinya. Daga baya ta fara zaton ba mamaki ta haifi yarinyar ne ta hanyar aure tunda ba wata wayayya bace kila auren kauye ne ko kuma dai wani abu haka har 'kaddara ta jefo ta cikin su. Koda Na'eema ta 'karasa bakin 'kofar ta turawa tayi gami da 'yar sallama, baki ta kya6e ganin babu kowa a dakin ba da alamu suna bayi ne, dan ba tun yau ta fahimci wannan 'dabi'a ta Zaitun ba, ko wanka zata bata barin yarinyar da ita take shiga abin ta, ta kuma rasa wannan dalili sai kace akan ta aka fara haihuwar kyawawa, inda ta 'karashe tunanin nata da sakin gajeruwar tsaki..(cKowa da abinda ya dame sa kenan... Ita kuma Na'eema kyawun yarinyar ya dame ta..) Baki ta kya6e a fili ta furta" Yau dai zamu ga 'karyar soyayya..." Ajiye abincin tayi da nufin anjima zata dawo bayan ta tabbatar sun gama ci, da yake ita ce mai kula da al'amuran Zaitun din ya sanya ba'a saka kowa ba sai ita gudun kar Zaitun ta gano wani abu..a yanda suka shirya sai in Na'eema ta koma ta tabbatar sunci kuma sunyi baccin kafin ta. kai rahoto wajen Hajjaju...wanda a lokacin ne komai zai kammala. Cikin rashin sani basu san cewa Zaitun tai musu nisa ba zuwa wannan lokacin. Bayan kusan mintina ashirin kafin Na'eema ta dawo, ga mamakin ta babu abinda ya canza, kofar 'dakin nan nan a yadda ta bar shi, kofan bayi ma haka, uwa uba abincin da ta ajiye shima haka. Idanu ta waro ta tafi ga abincin ta bu'de ko 'dis baiyi ciwon kai ba, 'kofan bayin ta 'dan buga.."Zaitoon..!" Shiru ba amsa..."..Zaitoona!!" Ta dan 'kara karfin sauti...." Maman Mufeedah....." Ta 'kara 'kiran sunan ta akaro na uku. Still shiru babu amsa, dan haka sai ta tura 'kofan bayin...wayam taga bama alamun an shige sa awanni ka'dan baya..duba da yadda yake a bushe kamas. Cikin 'dakin ta dawo da kallon ta...tabi kwantacciyar katifan da kallo gyare tsab yake babu ko alamun an a hausa mintina kadan baya.." .toh ina suke...?" Ta tambayi kanta. Baya kadan ta matsa sai taji 'kafar ta take abu a 'kasa da sauri ta kai duban ta wajen abin, sai taga wata 'karamar takadda ce, saurin kaiwa hannu tayi ta 'dago shi sai a sannan ta fahimci katin receipt ne na wata Pharmacy "..Zaitun Ahmad...". Ta karanta a fili sai kuma address 'din inda Pharmacyn yake. " Ina suka shiga ne..?" Ta sake tambayar kanta karo na biyu. Komawa tayi gaban waldrop din kayan su ta bu'de...sai taga jakan kayan su nan kamar yadda yake a kullun. Tuno Pampers din Mufee dake nan gefen jakar 'dazu da safe da ta ganshi yasa takai duban ta wajen wayam tagani babu shi babu alamun sa...." Zaitun ta gudu..."! Ta furta a fili tare da maida kofan waldrop din da karfi ta rufe. Dole yadda tayin da ace da wani cikin 'dakin sai ya firgita amma da yake babu kowa ita kadai ce hakan yasa bata damu ba, Sameera da dakin ta ya kasance daura dana Zaitun din itace ta farga da tashin karan da tajiyo wanda hakan yasa ta lekowa. Na'eema waje tayo da gudu tana kwala kiran sunan Hajjaju.... Salmerh 😘 [20/9/2022, 12:32 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Salmerh MD* 🅿️ *...15* "...Hajjaju Zaitun ta gudu..." Shine abinda take fa'di tun ma kafin ta isa ga Hajjajun... Sameera da ta leko bayan ta tabi da kallo cike da rashin fahimta... Yanayin yadda Na'eema ke maganan da karfi ya sanya duk wani dake cikin gidan ankarewa lokaci guda duk akayi haduwar kaska a babban parlourn Hajajjun..kowa na son jiyewa kunnuwan sa rahoto...." Wlh bata 'dakin kaf na bincika Hajjaju.."! Cewar Na'eema tana duban Hajjaju. " Kamar ya bata dakin?...kin tabbatar bata bathroom...?" " Hajjaju duk na duba da alamu ma ta dade da barin dakin dan hadda wasu kayan amfanin su ma babu...". 'Dunguma duk suka yi tamkar umarni ne ya riske su kowa so yake ya gani da idanun sa ba sai an bashi labari ba. .....Wayam suka ga 'dakin kamar dai yadda Na'eema ta labarta musu..." Zonan ina Sa'eeda? je kira min Baba Habu da Allah...yaushe yarinyar nan ta bar gidan nan fisabilillahi babu wanda ya sani...wannan wani irin asara take shirin janyo min...?" Tayi tambayar tana duban 'yan matan ta yayin da Sa'eeda tayi hanyar waje zauwa wajen mai gadi dan cika umarnin Hajjaju. Tare suka dawo da Sa'eeda yana bayan ta inda ya same su tsatststaye kan kafafuwan su illah Hajjaju da tsayuwan ya gagare ta ta zauna bakin katifa. Tun kafin ya kara sa isowa gaban su Hajjaju ta jefa masa tambaya," Baba Habu an samu matsala, ya akayi ka bar yarinya ta bar gidan nan batare da ni na sani ba..?" " Yarinya kuwa Hajiya...wlh bansan anyi hakan ba.." " Ga shi dai an duba bata nan Baba Habu, kuma dole nasan ta 'kofan gate ta fita tunda ba wata 6oyayyar hanya bace ta daban a gidan". " Hajiya wlh ni dai ban ga fitan yarinya ba, ban san kuma yadda akayi hakan ya faru ba, amma ki kwantar da hankalin ki Hajiya bari a dubo ko batayi nisa ba....." " Daga haka ya juya ya fita abinsa dan baya so maganar tayi tsayi da shi, cikin ransa yake mitar kun kawo yarinya taga bazata iya irin hallayar ku ba badole ta gudu ba, babu wani inda zani neman ta Allah ya kara rufa miki asiri yarinya..." Ya fada cikin ransa yana me nufar bakin gate, shima kansa zaman dole yake saboda rashin madafa amma me za sa ya tsaya zaman gadin karuwai 'yan iska...shi be san yarinyar da Hajiyan ke magana akai ba dan bai san an kawo ta bama sauran 'yan matan Hajiyan ne duk ya san fuskar su kuma sukan fita koda su kadai ne su kuma dawo abinsu....koda ya fita yawata wan sa yaje yayi ya dawo yace bai fa ganta ba shi kam. .." Wlh Baba Habu yarinyar asara zata ja min, da yake ban fara saka ta cikin harkoki na ba kafin yau din yanzu ne na gama komai akanta har an shigar da sunan ta alayi amma ta gudu yaushe ma na maida gurbin asarar da 'yan fashin nan suka jaza min sai ga wani kuma...?" Hajiya ta fada da raunin murya. " Sai hakuri Hajiya Insha Allahu za aganta ". Daga haka ya juya ya fice abinsa. Yana Allah wadaran halin su. .......Zaitun zama tayi kan tabarmin nan bayan ta kwantar da su batare da ta warware su ba ta zubawa ttitin idanu wanda zuwa lokacin daidaikun motoci ke wucewa har suka zo suka daina wucewan ma gari yayi 'dib, ko'ina shiru kake ji, tana nan tana tunanin duniya tana tunanin irin tata kalar rayuwar, ada kafin Mufee ta shigo rayuwar ta ba haka komai yake tafiya mata ba, amma tun daga ranar da 'kaddarar Mufee ta same ta shikenan rayuwar ta ta canza salo...amma har yau 'din nan har yanzu da take zaune bakin titin bata ji tana danasanin kasancewa da yarinyar ba, bata sani ba, bata kuma san dalili ba amma tana ji har cikin ranta cewa duk rintsi duk tsananin wuya tana tare da yarinyar...tasan jarrabawa ce ta yiwu kuma alhaki ce ta wata fannin, amma Insha Allahu zata jure zata daure komai da zai sameta, tasan dole inda rai watarana Allah zai dube su, Allah zai yaye musu wannan kuncin suma suyi farin ciki. A kullun adduar ta shine ko da allah yasa rayuwar ta gajera ce to ya sada Mufeeda da ingantacciyar rayuwa inda zatai farin ciki inda za'a kula mata da ita tunda ita ta gaza sama mata farin cikin. Sosai ta zurfafa a tunani har bata san tana 'kwalla ba, bata kuma san da wanzuwar wasu matasan samari har guda uku ba tsaye a kanta, irin street boys din nan ne fitsararru marasa imani. Tsaye suke kowa na kallon ta ta hasken da farin watan ke haskawa. Motsin da Mufeeda tayi ne ya dawo da ita hayyacin ta, hannu ta kai ta share hawayen fuskar ta da ta fahimci ya jike, yayin da 'daya hannun ta kai bayan ta tana bubbuga bayan Mufee alamar rarrashi. Cire hannun da ke kan idanun nata ke da wuya sai taga tamkar tsayuwar mutun a gaban ta sake goge idanun tayi gami da waro su dan tabbatar da abinda idanun suka gani tabbas mutun ne rungume da hannun sa a kirjin sa tsaye jingine da Pillarn Varandar ya kwantar da kansa jikin pillar. Da gaske Mutun ne ba ma 'daya ba har su uku jere suna kallon ta. Zabura tayi kamar zata tashi amma yadda tsoro ya riga ya karya mata zuciya haka taji kafafun ta ma sun karye sunyi sanyi sun gaza daukan nauyin ta. Dur'kushewa tayi kan gwiwoyin ta ta saki kuka mai tsuma zuciya hannayen ta duk biyu ta kai kan bakin ta tana kuka wanda duk rashin imanin ka daka ji sa kasan cewa abin a tausaya wa ce a lokacin, domin cike da rauni take kukan gami shashsheka duk zaton ta mutanen Hajjaju ne suka biyo bayan ta, dan haka cikin kukan ta fara rokon su..." dan Allah kuji kaina bayin Allah, ku dubi girman Allah da manzon sa ku rabu da mu, wlh yarinyar nan marainiya ce, in kuka rabani da ita bazan taba jin dadi ba dan Allah ku bar mu muyi tafiyar mu, na muku alkawari Insha Allahu bazan sake waiwayar gidan Hajjaju ba har abada.." Babu wanda yace mata ko _'kala_ cikin samarin nan uku illah 'daya cikin su da ya 'daga siraran 'kafafun sa ya matso gaban ta, ya tsaya a saitin kanta, tsabar tsoro Zaitun rintse idanu tayi da karfi take fadin" Dan Allah kar ku rabani da ita, dan Allah ku bar min yarinya ta, kuji tausayin mu bayin Allah..." Dukkanin ilahirin jikin Zaitun rawa yake. _Fiiit.._ taji an fizge mata Hijab a bazata daga kanta...wani zabura ta sake yi da niyyar yin baya take ta bude idanun ta...nan taga ashe har duk su ukun sun matso kusa da ita sun gewaye ta..." BK bayan ta goyo fa...?" Karo na faro da 'daya daga cikin su yayi magana. Wanda aka kira da BK 'din ne da wata kalar murya irin ta 'yan 'kwaya yace " ta kwance mana...in kuma bazata iya ba a kwance mata...". Jin hakan yasa Zaitun tayi wani kukan kura ta zabura zata gudu ta tsakanin su, da sauri wanda ke daga bayan ta ya rike mata hannaye duk biyu wanda hakan yasa ta kasa guduwan kamar yadda tayi niyya, 'daya mai suna BK 'din ne ya sa hannu ya kwance goyon ta gaban ta, jin Mufeeda na shirin fa'di ne ya sanya ta 'dan gwada yunkurin fizgan jikin ta daga hannun mutumin amma ta kasa, zuwa lokacin kuwa tsab kukan ta ya tsaya hawayen ma tuni ta neme su ta rasa tuni zuciyar ta bushe, bata kuma sake yunkurin rokon su ba dan ta lura ba fahimtar rokon nata suke ba. Ganin da suka yi tana musu fizge- fizge ya sa 'daya daga cikin su rike mata 'kafafu yayin da Bk da ke tsaye kanta ya sauke mata wata lafiyayyar mari, sosai marin ya shige dan har jini sai da yan 'dan fito daga hancin ta amma duk da hakan bata bar fizge- fizgen ba, so take ta gwada iya iyawar ta ko Allah ze taimake ta ta iya tseratar da su dan har yanzu a tunanin ta mutanen Hajjaju ne. Fizgo Mufee wanda ke bayan tan yayi wanda hakan ya firgita yarinyar har yasa ta sakin kuka mai karfi a razane. Kukan Feefy shi ya dawo wa Zaitun da nata hawayen, dagaske ta tsorata cin sun cire mata yarinyar a bayan ta, bata fatan wannan ya kasance shine karshen ganin ta da Mufeeda. Take ya dangwarar da yarinyar gefe ya kuma sa hannu ya farke bayan rigar Zaitun 'din daga sama har 'kasa batare da yayi la'akari da Zip da rigar ke dauke da shi ba.. nan take kuwa ya raba rigar biyu wanda jin haka ne yasa Zaitun dawo da hankalin ta waje ta guda sa6anin da data raba dan kula da yadda zasu yi mata da yarinya. Fahimtar abinda mutanen nan ke nufi ya sanya ta jin mafi girman tsoro ya shige ta, yau ka'dai taga illar kwanan titi. Iya kokari tayi wajen ganin ta kwaci kanta amma abin ya gagara kawai sai ta saki kuka, irin kukan nan mai cin zuciya, kuka na rashin mafita, cikin ranta take rokon Allah tseratar da ita ya tseratar da su baki 'daya... Wanda ke tsaye daga bayan tan ne ya fisgi hannayen ta baya da nufin kwantar da ita sai akayi rashin sa'a 'kafar sa ta bige Mufeeda take ta 'karawa kukan ta volume lokaci guda tamkar wanda a gutsiri wani sashe daga jikin ta, karan da ya ratsa kaf kewayan wajen baki 'daya, dai-dai tahowan wata ba'kar mota da gudu ta wuce musamman da yake babu kowa sai su kadai so babu wata mota da zatai musu shamaki da gudun da suke shararawa....har motar ta gota sai kuma ya tsaya cak.... _Salmerh_ 😘 [20/9/2022, 12:32 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Salmerh MD* 🅿️ *...16* _Shiiit_ ...shine abin da ya bayyana daga sautin muryar sa at same time yana me bugan sitiyarin motar da hannun sa 'daya...da alamu bai so tsayawan ba...amma kunnen sa sun jiye masa kukan yarinya 'karama. Baya ya dawo da motar ya bu'de ya fito, sai a sannan ma yaji ashe ba yarinya kadai ke kuka ba har da wata mace sakamakon jiyo sauti bibbiyu da yayi. Da hanzari ya nufi inda suke domin yana iya hangosu daga inda yake tsayen, dai dai lokacin ne kuma wadannan matasan suka tarwatse kowa yayi hanyar sa, bai bi ta kansu ba hankalin sa na ga mata da yarinyar da ya gani durkushe a wurin ne yake kuma jiyo kukan su, lokaci 'daya 'kwa'kwalwar sa ta basa abinda ke shirin faruwa a wurin duba ya yadda yaga duk sun hargitse riga a rabe, wanda ga dukkan alamu kiris ya rage mai afkuwa ta afku in ba dan ikon Allah da ya kawo su ba. Baya baya ta fara ja tana me sake sakin kuka sbd a halin nan da take ciki bata iya banbance mugu da wanda yake sa6anin haka. "....Dan Allah!... dan Allah..." Take ta fadi batare da ta iya karasa abinda take da niyyan furtawa ba. Ganin kamar shima tsoron sa take yasa shi daka mata tsawa" _Nutsu da Allah..._ "! 'Dif Zaitun ta shanye kukan ta tare da rintse idanu da karfin gaske. Batare da yasan wace ba ya jefa mata tambaya yana me kokarin kare ma fuskar ta kallo"..Me kk yi waje da wannan uban daren..?" Shiru ba amsa illa baya da ta kara saurin matsawa sakamakon tsawar da ya sake mata, gaba 'daya ta firgice. Jin ta iso kusa da Mufee yasa tai saurin rarumo ta ta gurme ta tamkar zata maida ta cikin ta... Ido ya tsura mata cike da mamaki wanda sai alokacin ma ya fahimci wace ita gami da tunano inda ya santa, in bai manta ba ya ga wannan fuskar tare da wannan 'yar yarinyar a mabanbantan wurare har sau biyu. ...Ido ya 'dan zaro cike da mamaki yana nuna ta yatsa"...You!..what ar u doing here?..ina zaki je da wannan lokacin?" Zaitun dai ba fahimtar sa take ba dan har a lkcn bata dawo hayyacin ta ba, d fact that za'a raba ta da Feefy da kuma fyaden da aka so yi mata shine ka'dai ya tsaye mata. Hijab 'din ta dake yashe gefen kafarcsa ya dauka ya jefe mata.." sa mayafin ki..". Ya fa'da da murya mai 'dan sanyi..hakan ne ya sa ta lalu6i abinda taji ya jefa matan ta suturta jikin ta da shi, ita kanta tafi son hakan duk da yake tana cikin yanayi na rudu amma data suturta jikin nata sai ta dan ji dama..kuma har a wannan lokacin bata bude ido ba balle ta ga wanda ke mata maganar. Fatan ta kawai shine taji yayi tafiyar sa shima batare da ya cutar da ita ko Mufeeda ba. Muryar da take ji nayi mata maganr yai mata kama da wata murya da ta ta6a ji sai dai a a wannan halin bata da nutsuwar iya tuna inda ta san muryar bazata iya tunawa ba. Kokari tayi ta 'dan bude ido kadan jin shiru na wasu sakanni ne ce komai ba kuma bata ji alamun ya tafi ba, hakan yasa ta 'dan 'dago dan duban fuskar sa cikin rashin sa'a idanun ta suka sauka akan hannun sa na dama dake ri'ke da 'karamar bindiga.." Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un abinda Zaitun ta furta kenan cike da kidima gami da sake rintse idanu ta kame jikin ta kamkam Mufee kanta dake rungume da ita sai da ta saki dan kara bayan tuni ta bar kukan tana sakin ajiyan zuciya. Komai sai ya tsaya mata cak. Sauran mutane uku da ke zaune cikin motar ne sukai saurin fitowa, dama duk hnkulan su na gareshi gudun kar wani abu ya sami shugaban nasu. Yana jin fitowar su, kuma yasan da fitowar tasu me zasu yi next bindigogi zasu ciro dan attacking koma miye, sanin hakan da yayi ya sanya shi saurin 'daga musu hannu dan dakatar da su ba tare da ya bari ta gani ba, amma ina ba mamaki mantuwa yayi da cewar shima akwai a hannun sa. Ita kam hankalin ta duk ya bar jikin ta banda 'kyarma babu abinda jikin ta keyi, tunanin ta kaf ya tafi ne ga tunano amfanin bindiga...abu biyu kacal ke dawo mata...ranar da aka harbe Nadia, da kuma daren da 'yan fashi suka shigo gidan Hajjaju wannan ma ta gansu da bindigogi a hannayen su. Kafin ya sake yun'kurin yi mata wata tambayar tuni Zaitun ta sume a zaune. Tsaye yaran san suke cirko cirko yayin da shi kuma ya durkushe gaban Zaitun yana sake kare mata kallo dan tabbatarwa idanun sa cewa ita din ce dai ba wata ba. Bayan fahimtar suman da tayi ne sai ya saurin dafe kansa cike da 'yar damuwa. Tsaye ya mi'ke daga durkuson da yayi gami da 'daukan bindigar sa...ya koma mota da 'dan sauri, yayin da yaran sa suka take mar baya duk suka shige batare da kowa ya furta ko kalma ba. Key ya yiwa motar ya tada da niyyar barin wajen amma sai yaji zuciyar sa ta kasa amincewa da hakan...Birki ya taka gami da bawa yaran sa umarnin a shigar da su da kayan su... Kafin cikar mintina biyar har sun 6ace daga wurin. Zaitun duk bata san anyi hakan ba sai bu'de idanu tayi ta ganta kwance kan wani gado lafiyayye. Ta gane hakan ne kuma saboda yanayin yanda taji laushin sa da kuma yanayin yadda dakin yake...motsi tayi da hannun ta da niyyar tashi ta zauna nan ta fahimci ruwa da bata san na menene ba da ake kara mata hakan yasa ta koma ta kwanta tana mai dafe goshin ta da 'dayan hannun ta, Hijab din ta da taji akanta yasa ta gode wa Allah domin tasan shine rufin asirin ta, tunowa da tayi cewar rigar ta a yage take..bata san ya akayi tazo nan din ba kam amma duk da hakan ta gode Allah da ya tseratar da ita...tsintar kanta tayi da fa'din _Alhamdulillahi_ wannan maganar ta tsaya mata iya kan la66an ta ne. Gefe da gefen ta ta kalla sai taga babu Feefy babu me ko me kama da ita sai wani kyakykyawan mutun zaune nesa kadan da ita ya zuba mata idanu. Tashin farko ba tare da wani dogon tunani ba ta fahimci waye shi ta kuma tuno inda ta sanshi..." Dr Rasheed..!" Ta fa'da 'kasan ma'koshi. Gira ya ha'de ba tare da ya furta ko kalma ba kawai ya mike tsaye bayan ya tabbatar da tashin nata..nan Parlour ya koma zauna ya cigaba da latse- latsen sa cikin laptop..."..ina 'ya ta..? Ta tambayi kanta tana me kokarin tashi zaune. " kar dai dagaske sun raba ni da ita?" Ta tambayi kanta. Sai kuma ta rushe da kuka...dan ita gani take duk bakin su 'daya ne da Hajjaju, bazata manta ba ko acan asbitin da kwanaki aka kwantar da ita tare ta gansu. Ko 'kala Dr Rasheed bai ce da ita ba bai kuma dawo 'dakin dan yi mata magana ba har tayi kukan, tayi surutan ta koma ajiyan zuciya..ta kuma sake sakin wani kukan daga baya wanda ya fahimci tana yin kukan ne cike da kewa da kuma damuwa gami da nadama. Fahimtar da yy idan ba dakatar da ita yy ba har illah zata iya yiwa zuciyar ta yasa shi dawowa 'dakin gami da fa'din"...ya isa hakan nan mana, kukan ya ishe ni haka..." Cikin kukan ta furta.. " Yarinya ta banganta ba fa ina kuka kai min yarinya...?" Sai yanzu ya fahimci dalilin tsananta kukan, shi abin ma dariya ya bashi ganin 'yar yarinya da ita da yake da tabbaci 16yrs ma bata haura ba amma wai har yarinya gareta, tun a wancan lokacin yayi mamaki. Sai da ya dawo ya zauna bisa drawer inda ya tashi dazun kafin cike da kulawa cikin kwantar da murya yace " Ki kwantar da hankalin ki yarinyar ki tana nan..kuma zaki ganta amma sai kin daina kukan nan...." Jin hakan yasa ta saurin goge hawayen tana duban fuskar sa. " Ina ke mk ciwo yanzun?" Ya sake jefa mata tambaya cike da kulawa. "...Ni...ba komai.." ta bashi amsa cikin sauri tana 'dan turo bakin ta irin ita ba wannan ce damuwar ta ba..kanta na tsananin ciwo amma bata shi take ba. " So..zaki iya tafiya yanzu kenan?" kai ta 'daga masa alamar "ehh.." Waya ya 'daga yy kira inda yayi magana da harshen turancin da Zaitun ko ka'dan bata jin sa. Nan take ba a wani dade ba taga wani ya shigo hannun sa rike da Mufee. Mufeeda na ganin Zaitun ta fara 'daga hannuwa da nuna alamun son isa gareta. Dan haka ya matso ya kawo mata yarinyar, ai da ganin Mufee jikin ta ta washe baki gami da rungume ta har ta ma mance da karin ruwan da ke hannun ta...itama Mufee sai ajiyan zuciya take sauqewa da alamu tasha kuka sosai. Jikin fess an mata wanka an canza mata riga tayi kyau abinta...zuwa yanzu ta gama fahimtar cewa Dr Rasheed shine ya taimake ta bata manta sautin muryar ba sam sai dai wani abu guda daya tsaye mata. In bata manta ba taga bindiga a hannun sa jiyan, kuma ta san shi likita ne, toh menene hadin ma'aikacin asbiti da rike bindiga...ko duk cikin ceton lafitar mutanan ne tamkar dai yadda ya faru da ita. Dole Dr Rasheed ya cire mata karin ruwan kafin ta karkata bakin allura ta janyo wani abin daban, yana murmushi yake jinjina kaunar juna da suke yi ita da 'diyar tata. "..Zan turo driver sai ki fa'da masa gidan ku ya kaiki kafin a fara neman ki". Ya fa'di hakan bayan ya mike tsaye da niyyar barin 'dakin... Bata tanka shi ba har sai da ya kusan fita daga 'dakin kafin kamar bata son yin magana tace"..mu ba wani gida da muke da shi, kuma babu wanda zai neme mu, kawai ka barshi da kaina ma zan tafi...nagode sosai da taimakon ku". Cak ya tsaya ba tare da ya jiyo ba...tunani yake cikin zuciyar sa..." me yarinyar ke nufi da wannan maganar? Baya ya dawo ya tsaya a kanta. " Me kika ce?" Ya sake jefa mata tambayar yana mata kallon tuhuma. Zaitun sake maimaita masa tayi tana gyara rigan dake jikin Mufeedah. Hannun sa duk biyu yasa cikin aljihun wandon bakin jeans dake jikin sa, sannan yana gyara tsayuwa yace " Dama can a ina kike rayuwa kafin ha'duwar ki da Hajiya Mardiyya?" Shiru tayi bata ce da shi komai ba...tunanin amsar ma da ya kamata ta bashi take, in hasashen ta yazo daidai yana tambaya ne akan Hajjaju domin tare tasan ya ta6a ganin su lkcn da ta kaita asbitin su amma ita bata san asalin sunan Hajjajun ba, in kuwa akanta yake magana bata da wani dangantaka da ita Hajjajun kade ta kawai tayi da mota har ta kai ta asbiti daga nan kuma gidan ta. In kuwa itan ce ai tasan yasan duk wannan tunda shine likitan da ya duba ta a lokacin...toh me kuma yake son sani bayan wannan. " Tambayar ki nake yi ko...dama menene alakar ki da Hajiya Mardiyyan...?" Salmerh😘 [20/9/2022, 12:32 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Salmerh MD* 🅿️ *...17* Jin canza salo da tambayar tasa tayi ne ya sanya Zaitun 'dago idanun ta ta dube shi suka hada idanu, saurin kawar da kanta tayi gefe...kawai sai taji zuciyar ta ta aminta da shi 'dari bisa bari, take damuwar ta fara rage nauyi a zuciyar ta, haka kawai sai take jin sa tamkar wani garkuwa ne a garesu baki 'daya. Wani sabon hawaye ne ya 6alle mata na tausayin kansu, amma sai tai saurin share hawayen, a hankali ta bu'di baki tace" Ni ban san su ba...Hajiyar ce ta kaini gidan bayan mun baro asbiti a wancan lokacin, ita ta taimaka mana ba tare da nasan su din wa'danne irin mutane bane, lokacin da nazo na farga da hakan na fara tunanin rabuwa da su a lokacin su kuma suka shirya raba ni da 'yata shiyasa na gudu, jiya na bar gidan da dare saboda in tseratar da yarinya ta garin hakan Allah ya hada mu da wadancan a bakin titi...yanzu bani da kowa bani da inda zanje, kawai zan tafi ne, ina so inyi nesa da su inda bazasu sake gani na ba". Tana gama fadin hakan hawayen ta ya kara karfin kwaranya. Bai ce mata komai ba illa kallon ta da ya tsaya yi sosai yaji ya tausayawa mata, domin shi yasan wace Hajiya Mardiyya, farin sani yai mata tun ba yau ba, kusan mintina biyu yana tsaye a wajen kamar ba zai sake magana ba sai kuma can ya furta" Kafin ha'duwar ki da Hajiya Mardiyya...?" Bata ma bari ya kai karshe ba tayi saurin tarar sa da fa'din..." Bara nake bamu da kowa kuma a haka muke rayuwar mu..." Tayi saurin fadin haka ne gudun kar yace zai tambaye ta asalin garinta da kuma dangin ta balle yayi tunanin mayar da su... Kallon sakanni Dr Rasheed yai mata sai kuma ya juya ya fita yana me ciro wayar sa dake aljihun sa. Parlour ya koma yy kira wanda Zaitun sam ba fahimtar abinda yake fada take yi ba sai dai ko kadan hakan bai sa taji shakka ko tsoron kasancewar ta anan din ba. Mahaifiyar sa ya 'kira yayi mata bayani bayani a takaice ta kuma fahimce shi dan macece mai saukin kai sam bata da matsala. "…Ba komai Abbah..indai kaga hakan ba zai zama wata matsala ba kayi yanda ya dace kawai, Ni dama tunani na Hameeda ce kar taki amincewa.." " erh dama zanyi magana da ita Hameedan tukunna.." Ya fadi hakanne kuma saboda ya kwantarwa da mahifiyar tasa hankali amma ba wai dan ya damu da amincewar ita Hameedan ba. "..Toh shikenan Ubangiji Allah ya 'kara rufa asiri..." Da Ameen Ya amsa gami da ajiye wayar. Tunani yayi na 'yan mintina sannan ya tashi kawai yayi waje. Fitar sa da kusan mintina talatin kenan yanzu...Zaitun na zaune tana ta zuba ido, jira take taga ta inda shi kuma zai 6ullo da nasa lamarin amma shiru...tana so ta shiga bayi ma amma sam ta kasa tashi daga inda take zaunen. Allah ya sota ma tana hutun sallah ne amma sosai take da bukatan rsaftace jikin ta. Haka ta cigaba da zama ba wai dan bata san ta inda zata fara ba ko kuma bata fahimci inda bathroom din yake bane kawai dai fargabar abinda ke jiran ta agaba ne ya hanata tashin. Shahada kawai tayi ta yunkura ta sauko cikin sa'a kuwa tana saukowa sai taga ledan kayan ta a kasan gadon wanda ta sako musu 'yan kayan su a ciki. Hamdala ta saki cikin zuciyar ta gami da daukan ledan tana me gyara rikon Mufeeda da kyau. Bathroom ta shiga da be wani yi mata wahalar ganewa ba, dan ta koyi wannan tun a asbiti da kuma gidan Hajjaju, duk da yake na nan din haduwar sa daban ne amma bai bata matsala ba. Da yake taga Mufeeda Fes da ita so bata yi tunanin sake yi mata wanka ba tunda taga har sabuwar riga aka sanya mata da bata san takamamme wanda yayi hakan ba..sai dai tasan koma menene an yishi ne bisa umarnin Dr Rasheed. Sai da ta tsaftace jikin ta ta canza Pad din da Na'eema ta koya mata amfani da shi, canza shiga tayi zuwa doguwar rigar abaya sannan suka fito..sai ma da idanun ta suka yi arba da yagaggiyar rigar ta kafin ta kare godewa mahalicci daya tseratar da ita ya kawo mata wannan mutumin, ko bakomai iya taimakon da yayi matan ba karamin tallafawa bace kuma yaci ace ta girmama shi..domin badan zuwan sa ba bata san iya abinda ze afku gareta ba, da kila ba wannan zancen ake yi ba yanzu. Ba'a jima ba aka kawo musu abinci har 'daki wanda ta fahimci siyo shi aka yi daga wurin masu sayar da abinci, nan suka ci suka yi 'kat ba tare da fargabar komai ba. Suna nan zaune har zuwa dare babu wanda ya sake leko su..sai dai ta kan jiyo tashin muryoyin mutane cikin gidan kuma har zuwa lokacin kunnuwan ta basu jiyo mata muryar mace ko guda ba haka kuma itama bata damu ta leka ko fita daga dakin ba. Bata sake ganin Dr Rashed ba amma duk lkcn da ya kama na cin abinci ne kawai sai taga an kawo mata. Tana nan har akayi, Asr, Maghrib ga Isha'i da yake jerowa a daidai wannan lokacin. Zaitun ban da tunani babu abinda take, sosai yau din Adam ya dawo ranta, tana tuna kyautatawar da yayi mata, Adam ya nuna musu kauna irin kaunar da har ta mutu bazata iya mancewa ba, ga kuma Mmn Abdul mace me kyakykyawan zuciya, wa'dannan bayin Allahn bazata ta6a mancewa da su cikin tarihin rayuwar ta ba, sun zauna da ita sun rayu da ita ba tare da sun san wace ita ba, ba kuma.su damu da sanin hakan ba suka aminta da ita, ba tare da ta gutsira musu ko kwayar zarra cikin tarihin rayuwar ta ba. Kwalla ta share bayan tunawa da 'dan uwan ta abin alfaharin ta wato Yah Bukar, tana da tabbaci da zai san inda take tabbas sai yazo gare ta, uwa uba mahaifiyar ta, yau kam tana jin dole ne ta bawa kanta lkcn tunawa da su, tana matukar kewar su, tana kewar ahalin ta amma akwai wani shamaki, akwai babban dalilin da bazai ta6a bari taje gare su ba a yanzun. Ta dauki tsawon lkc tana wannan sakar zucin, hannu ta kai tana share kwallan da ke zubo mata dai dai kunnuwan da jiyo tsayuwar mota da kunnuwan ta suka yi, wanda ya kasance mintina kamar arba'in ne bayan sallar Isha taji harabar gidan, sosai taji faduwar gaba, bakomai ta tuna ba face ranar da 'yan fashi suka dira gidan Hajjaju. Tsam ta tsaida tunanin ta gami da daidai ta zaman ta ta tsurawa kofar dakin manyan idanun ta, kallo daya zakai mata kasan cewa a tsorace take. Sai yanzun ma tunanin ina matar gidan ya fado mata, dan tun farkawar ta bata ji motsi ko tashin muryar mace ba. Mufeedah dake bacci kan cikin ta ta sake gyarawa kwanciya still idanun ta na ga kofan dakin. Tsawon wasu mintina bata sake jiyo motsin komai ba, amma dai hnkln ta taji bai kwanta ba sam. Tashi tayi rungume da yarinyar sa'daf sa'daf ta taji jikin kofan, kadan ta bude ta leka, wani karamin parpour taci karo da shi amma babu kowa a 'dakin. Bata san dalili ba sai kawai taji tamkar ana ingiza ta ne, daf da zata wuce gaban wani 'daki dake kusa da wani corridor ta jiyo tashin muryan mace 'kasa'kasa tana kuka cike da sheshsheka. Sake zaro idanu tayi tana kokarin tura kofar ganin a dan bude yake ta jiyo muryar Dr Rasheed kuma, hakan ne yasa ta daka ta da tunanin ba hurumin ta bane. Duk da hakan bata ji zuciyar ta ta aminta da yanayin kukan yarinyar da tajiyo ba tana so ta tilasta wa kantan cewa iyalin ta sace dagaske amma ina, ta gaza. Tasan kukan iri daban daban, tasan yanayin kuka kala kala sbd ta tsinci kanta cikin mabanbantan yanayi da ita kadai ta sansu ta kuma san zafin su. Wannan kukan ya banbanta da kukan dackai tsaye zata ce normal kuka ne. Kuka ne me tsayuwa a zuci kukan neman agaji abin a tausaya. Bata gama tantance abinda ya kamata tayi ba ta fara jiyo maganar Dr Rasheed.... " Alhajin Allah bar rokona ka saurare ni, dokokina uku ne kacal, babu hukuma cikin aikina, idan kayi abinda aka kamamin yaro mintina biyu kacal bayan kamashin ka tabbatar sunan 'yar ka gawa, ciwon farce yaro na yy bayan karbo kudin ina tabbatar maka da cewa sunan 'yarka matacciya...idan kuma kabi dokokina kamar yadda suke zaka saurari zuwan 'yar ka kwana biyu bayan na tabbatar baka yi abinda ya sosa min zuciya wurin kar6ar kudin ba...fatan ka fahimta..?". " Shawara mai kyau..". " Baka da matsala da wannan". Tattaunawar Dr kenan kan waya sai dai bata iya jiyo ko guda daga can 'daya 6angaren wayar ba. Bata fahimci komai da maganganun ke nufi ba amma kalmar _gawa_ da kuma _matacciya_ da ji su suka matukar 'dimautata, take jikin ta ya fara kyarma, tsoro da fargaba suka cikata, juyawa tayi da niyyar barin wajen cikin rashin sa'a Dr Rasheed ya bayyana bakin 'kofar da alamu ya gama abinda ya kaishi dakin ne. Jin karar bude kofan ne ya sata juyowa a firgice idanun su suka sarke cikin na juna...Zaitun tuni hawaye ya cika mata idanu suna gangarowa. 'Dayan hannu ta kai ta rufe bakin ta da shi dan kar sheshshekan ta ya fito at same time ta zube bisa gwiwowin ta da alamun roko. Dr Rasheed har a lkcn kallon ta yake da mamaki, sam bai ta6a zaton zata fito daga dakin da take ba, bai ta6a zaton zata iya kawo kanta har nan ba. 'Daya cikin yaran sa ne ya bayyana a wajen da 'dan sassarfa wanda da isowar sa ya fara kokarin mikawa Dr Rasheed wani abu amma bai bi takan abin ba. " ..lock the door.." Ya fada masa yana me matsawa daga bakin kofar towards inda Zaitun ke durkushe, daga gaban ta ya tsaya sai tai saurin yin kasa da kanta still bakin ta a toshe dayan hannun kuma na rungume da Mufee. " Me ya kawo ki nan..?" Bata iya budan baki ta bashi amsa ba sai kai data fara girgizawa da alamun roko. "...Me ya fito da ke, me kunnuwan ki suka ji...?" Yayi maganar da buga mata tsawan da yasa ta sakin guntun fitsari. Duk kammanin sa sun canza sun koma wani abu daban, ashe duk kallon da take masa da fuskar rahamar sa take ganin sa. Baya kadan taja sbd yanda ta tsure, cikin tsananin kuka da nadamar fitowar tan tafara fadin".. wlh ni babu abinda naji,dan girman Allah kayi hakuri...". A fusace yayo kanta ya sauke mata wani marin da ya sake gigita"...Don't sorry me...fada min abinda ya fito dake..". Zaman dirshan Zaitun tayi tana me sakin wani wahalallen kuka tama kasa furta komai. Bata yi aune ba sai ji tayi ya sa mata abu akai akai wanda tashin farko ta fahimci cewa bindiga ne. Cak kukan ta ya tsaya ta fara gani taratara yau ita ce bindiga akanta innalillahi...tama kasa karasawa. " wa ya baki iznin fitowa...?" Ya sake jefa mata wata tambayar wanda da kaji kasan ransa ya kai kololuwa wajen 6aci. "...Wlh...bakowa...tsoro, tsoro naji shiyasa na fito...amma wlh ban ji komai da kace...". Yaron da ke tsaye daga bayan sa ne kadai yayi murmushi fahimtar da yayi cewa rudewa ce ta sa ta fadin hakan. Yanavso ya bawa Dr hakuri amma yafi so yaga karshen game din. "...Tsoro ko..?" Dr ya tambaye ta. Da sauri ta dage kanta alamar erh jikin ta na kyarma. "...Yanzu kika fara rayuwa cikin tsoro har sai ranar da abinda kk ji ya bar kwanyar ki...a feel like in fasa mk kwakwalwa yanzun nan but kinci albarkacin Babyn nan..". Ido ya kara warawa akanta ya cigaba da fadin.." Daga yau duk abinda kikaji ko kk gani ya zam a cikin cikin ki...furta wata kalma ko ishara game dani daidai yake da daukewar numfashin ki daga ke har wannan da hannu na zan fasa mk kai...kina jina...?" Da sauri take dage kai hawaye na sake gangaro mata fatan ta daya shine ya ingiza keyar ta wajen gidan sa, ya korata, ta gwammaci rayuwa kan titi da wannan rayuwar tare da Dr...ashe dagaske bindiga ta gani a hannun sa jiya, ashe ba mafakar natsuwa ta sama musu ita da ita Mufee ba. "...Oya back to ur room...". Yayi maganar yana juyawa cike da sassarfa ya bar wajen illah wancan dayan da yazo. Shine ya sake maimaita mata ganin bata motsa ba.." tashi ki koma 'dakin ki..". Kasa motsawa Zaitun tayi illa ido take kara warewa. " Daki kuma...?" Ta tambayi zuciyar ta..meyasa bazasu fitar da ni ba. 'Dagowa tayi ta kalle shi yana sanye ne cikin ba'ka'ken kaya fuskar sa ma rufe take da face mask, kamar dai yadda Dr Rasheed yake shima. "...Dan Allah bawan Allah ku kore ni, ku ce in bar muku gidan ku dan Allah..." Bai ma bari ta kai karshe ba ya 'dago mata bindiga ya saita kanta, tuni tai tsit ta fara kokarin mikewa amma ta kasa da rarrafe ta fara jan jikin ta har zuwa dakin. Wancan me zai yi in ba dariya ba bayan ta bar wajen a fili yace" ga kau'di ga tsoro..". Da kyar ma ta gane dakin sbd tsabr rudewa..in dai hakane ko bakin kofa bazata sake zuwa ba Insha Allahu, ba karamin nadamar fita tayi ba. " Wannan wace iriyar ukuba ce haka...?" " Gaba kura baya siyaki...haka kenan zai ta kasancewa da ita a ko wani lkc...?" Yau kadai take ji cikin ranta da zata sami hanya ba abinda zai hanata komawa can gida inyaso ko kashe ta ne ta kwammaci suyi yafi mata wannan tashe tashen hankulan. Ranar ko rintsawa batai ba har akayi asubah...Mufee kadai ta iya dorawa saman gadon ita kam kafafun ta ma nauyi sukai mata, haka anan kasan tiles ta sulale..kafin safiya wani zazzafan zazza6i ya kamata. Me kawo musu breakfast ne ya fara fahimtar halin da take ciki..amma bai tanka ba. Ita kam ma tashin hankalin da take ciki be bari tabi ta kan zazzabin ba. Mufee ta bawa abincin taci itama ta tuttura sbd bata san ta bawa Mufeedah abu batare da itama ta ci ba gudun abinda zai cutar da yarinyar. A daddafe ta kai su bayi ta watsawa Mufee ruwa itama tayi. Haka tazo ta zauna gami da rungume Mufee, duk ta zare ta fita hayyacin ta tai tsumu da ita tamkar yakuwan da yaji ruwan zafi. Mufeeda kam da bata san me duniya take ciki ba sai surutan ta take irin na yara tana lafe a jikin ta. Salmerh😘 [20/9/2022, 12:32 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Salmerh MD* _Wattpad@ Salmerh-md_ 🅿️ *...18* Dr Rasheed ya kasance likita ne a zahirin rayuwa da kuma fahimtar kowa ciki kuwa hadda mahaifan sa da sauran dangin sa, Dr Rasheed ya kasance shine yaro na farko kuma 'da namiji tilo wajen iyayen sa inda yaci sunan kakan sa wato mahaifin baban sa Abdulrasheed, dalili kenan da ya sanya mahaifiyar sa ke kiran sa da Abbah yayin da suke tsananin so da kaunar sa tamkar shi daya Allah ya basu, duk kuwa da kasancewar su masu karancin dukiya hkn bai sa sun gaza wajen samar masa ingantaccen ilimin zamani har ma da na addini ba hkn kuma ya cigaba da wakana har ga sauran kannan sa, sun tsaya tsayin daka wajen ganin sun daidaita tarbiyar yaransu yadda ya kamata kuma Alhamdulillahi basu samu tsaiko game da hkn ba, sai dai wasu lokutan rubutacciyar kaddara ta kan yi tasiri ga rayuwar mutun ne sa6anin yadda ake zaton, duk kokarin ka baka isa gyarawa mutun zuciya ba sai abinda Allah mahaliccin sarki ya tsara kuma yaso gani game da bayin sa, san zuciya da kuma babban buri na son tara abun duniya su suka yi tasiri a zuciyar Rasheed hkn kuma ya sanya shi karkacewa daga tubar da iayen sa suk 'dora shi batare da sun sani ba, lokaci guda ya fada mummunar harka ta fashi da kuma garkuwa da yaran manyan mutane ana biyan sa makudan kudade. Yana da yaran da yk aiki da su guda biyar kacal wadanda su kadai ya aminta da su, kuma da su kadai yake aiki, su kadai ne suka san cewa yana wannan harkar a zahiri bayaga wasu manya da suka kasance masa jagora. Rasheed yana da wani tanfatsetsen gida da ko mahifiyar sa sai da tayi mamaki lkcn da ya mallaki wannan gida duba da cewa aikin likitan ci kawai yk, kuma mahaifin sa me karamin karfi ne su kansu gidan da suke ciki shine ya canza musu kafin ma ya siya nasa na kansa, domin ada wani dan madaidaicin gida ne suke zaune kuma ya taso a cikin sa wanda yake mallakin mahaifin sa ne, daga baya ya canza musu muhalli wanda ya matukar basu mmk, da 'kyar ma mahaifin nasa ya amince ya koma gidan bawai dan yana zargin dan nasa ba a lkcn kawai dai acewar sa shi ya saka iyalin sa a ciki su inda suke ma Alhamdulillahi ya ishe su rayuwa, sai dai Rasheed sam yace a a daga karshe dai bayan an kai ruwa rana dole mahaifin nasa ya amince suka koma bayan Rasheed ya hada da wasu manya cikin ahalin su da kuma abokan mahaifin nasa. Bayan komai ya daidaita ne sai yaje ga mahaifan nasa da batun kasuwanci da yake yi ta kasa da kasa na kayan masarufi ya kuma bayyana musu cewa ya dade da fara wannan harkar, ba laifi sun ji dadi sun kuma saka masa albarka.inda daga karshe sukai masa nasiha sosai akan kiyaye haram cikin lamuran sa. Dr Rasheed yana da matar aure kwaya 'daya mai suna Hameedah yana kuma da yaran sa biyu mace da namiji...Wildan shine babba wanda ya kasance yaro 'dan shekara hudu da haihuwa sai kuma Naina wacce ba ta ajiye shekara biyu kwarara ba. Ya kanyi duk wani 6oyayyun harkokin sa ne a gefe kuma babu wanda ya ankare da shi har a yanzu, hatta Hameeda bata san da wannan harkar ba. Ko da ya kasance yana yawan fitan dare a gidan bata ta6a damuwa da hkn ko bin diddigi ba sbd tasan yanayin aikin sa ta kuma san hkn na iya faruwa duk da yk itama din ba wani karatu me zrfi ke gareta ba, a yanzun ne take makarantar kuma yajin aiki da jami'oin gwabnatin tarayya ke yi dole ya dakatar da ita, tsananin kaunar da take yi masa kuma ya sanya a mafi yawan lokuta Hameeda bata ganin laifin sa balle ta tahume shi ta kan yawaita yi masa uzuri. Dr Rasheed shine ya jagoranci harin da aka kai gidan Hajjaju a wancan lkcn, kuma bakin wani abokin aikin sa yaji komai akan Hajjajun, kuma kawai sunyi zancen ne as in hira dan yana yawaita ganin ta cikin asbitin kusan ma nanne kadai asbitin da tafi mu'amala da su, ya kan ganta amma be san wace ita ba sai lokacin da ta kai Zaitun sannan sai kuma yaga dacewar ziyartar gidan badan komai ba sai dan kawai ji da yy ance tana matukar murza Naira iya son ranta sbd da manyan alhazai take harkokin ta. Sai akayi rashin sa'a kuma gidan ya fado cikin unguwar da yake 6oyayyar harkar sa shima dan hk suka shiga gidan nan ya tabbatar dagaske ne Hajjajun bata wasa ba ce, sun kar6i abinda ya kaisu karshe kuma da kansa ya kafa mata dokar tashi a unguwar bisa dole cikin wasu kididdigaggun kwanaki...ba dan komai yy hakan ba kuma kawai sbd shi ya tsani harka irin wannan, duk da yk shi laifi laifi ne, hk kuma zakunci zalunci ne ba'a raina shi amma ta wannan 6angaren kam ya kiyaye, duk abubuwan da yake aikatawa bai ta6a keta haddin kowacce mace ba, baya cin zarafin su bai kuma bari yaran sa ma sun aikata hkn ba. Duk yaran nasa sun kasance fasihai ne ta 6angarori daban daban, kamar su sanin na'ura, sani da kutsawa cikin manya da sauran su. Duk da hakan Dr Rasheed baya ta6a saka rayuwar su cikin hatsari komai ya kan yi kokarin cusa kansa ne da kansa ba tare da victims 'din sun san cewa shine da kansa zuciyar 'kungiyar ba, ya kance shine yy burin tara arziki dan hk dole shine da kansa zai farauci abinsa da kansa, ko kar6an kudin fansa mafiya yawa da kansa yk zuwa dan baya so ya saka rayuwar kowa cikin ha'dari sai dai bisa dole. Lokacin da ya sace yarinyar Alhaji Modu asbitin su aka kai shi jinya sakamakon hawa da jinin sa yy, hawa mummuna, kuma shine likita me kula da shi, ta fannin aikin sa ya kan nuna tsatsan kula da tausayi. Tsayuwa yy sosai kan Alh Modu duk da kuwa yasan shi din wanene ya kuma san menene ma'kasudin ciwon, amma hkn bai hana shi sakin rai yy aikin sa yadda ya kamata ba. Haka ya dinga bashi treatment tsakanin sa Allah sai dai ya kan ce da iyalan sa ya kamata a daina daga masa hnkl haka nan, duk wani abu da suka san yana tada hnkln sa su sarara masa sbd kiyaye lafiyar sa, domin in jinin sa ya 'kara hawa makamancin hakan yana iya rasa lafiyar sa koma ransa gaba daya. Matar sa da sauran yaran sa kam sai kuka...da kyar mahaifiyar ta iya bu'dan baki tace " Dr. wlh yarinyar mu ce ta 6ata yau kwana biyar kenan bamu san inda take ba" Ido Rasheed ya zaro cike da tashin hnkl kamar gaske yace" Subhanallahi... har kwana biyar bb wani lbr kuma?" "..mun barwa Allah dai mun kuma kai report ga hukuma amma har yanzu bb wani labarin komai..." " Innalillahi....ya kai har karshe, wannan kam dole hnklin sa ya tashi Allah buwayi ya bayyana ta..". Dr Rasheed baya wulakanci kuma ya tsani mutum mai wulaqanci..sannan yana tausayi da kuma kyautatawa. Da rana idan ka ganshi a office zaka yi tunanin duk duniya bb wanda ya kaishi hankali da natsuwa amma idan kasan abinda yk aikatawa a 6oye zaka yi matukar mamaki. Ya kan yi anfani da beard, face mask ga glass, bakaken kaya, bakaken jackets da handglove sosai kamannin sa suke canzawa ko ka san shi da wuya ne ka iya gane shi cikin wannan shigar idan yayi. Salmerh😘 [20/9/2022, 12:32 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Wattpad@* *Serlmerh-md* 🅿️ *...19* Haka Zaitoon ta cigaba da rayuwa cikin wannan gidan cikin kuncin zuciya bakin ciki da damuwa, ko bakin kofa bata sake gigin takawa ba, gaba 'daya komai ma na duniyan ya fice mata aka, abinci ne dai ba'a fasa kawo musu ba kamar yadda aka saba ko wani yini sau uku, tun ma bata iya cin abincin har tazo ta fara sakin ranta tana dan ta6awa sbd karfin jikinta, shima zazza6in tuni yy nashi waje, tun ranar bata sake ganin Dr Rasheed ba, bata sake jiyo ko tashin muryar sa ba haka kuma bata san me ke faruwa a gidan ba tun bayan waccan ranar. Kwanan ta biyar a haka duk ta sake ramewa tayi duhu sai idanuwan ta da suka kara fitowa, Mufee kanta sai da yanayin ta ya canza sbd rashin natsuwa da Zaitun din ke ciki dole ya shafe ta. Da wani dare bayan ta idar da sallahr isha'i sun gama cin abinci taga an turo kofan, ta tsorata sosai sbd bb wanda ya ta6a shigo mata a irin wannan lkcn dan haka tai zuru zuru. Wani daban ta gani ba wanda ya saba zuwa ba sbd bambancin tsawo da ta fahimci akwai tsakanin sa da wancan din. Gaban ta ya iso ya tsaya daga muryar sa ta fahimci fuskar babu alamun rahama balle wasa tattare da shi" Ku tattara ku biyo ni". Haka kawai yace da ita yaja baya kadan, bazata iya mai musu ba dan hk a hankali cikin sanyin jiki rauni da tunani ta sauko, yanzu a yanda ma take jin jikin ta ko magana ta kirki ba iya wa zata yi yadda za'a fahimce ta ba balle ta iya tanka shi, ta riga ta barwa Allah komai nata yanzu sai yadda kawai ya yi da ita a cewar ta...yanda kawai taji muryar mutumin da ko idanun sa bata iya gani sakamakon bakin gilashin daya rufe masa idanun banda tsoron su ma ba abinda ya karu mata, dama tsoron kowa na gidan ya riga ya mamaye ta tun kwanaki biyar baya. Bayan sa tabi a hnkl rungume da Mufeeda da kayan su, dan ji take tamkar kafafun ta zasu karye saboda rashin karfin jiki. Har gaban mota yaje ya tsaya ya bu'de mata baya, shiga tayi tana zazzare idanuwa tamkar mage amma bazata iya tambayar sa inda zasu ba, ita fatan ta kawai su bar ta, Allah yasa kar su rabata da Mufee koma me zasu yi mata suyi amma su barta ta rayu da yarinyar ta, in da Allah zai bata ikon rokon su da zatayi kawai tace su barta tayi tafiyar ta amma bazata iya ba, tun kashedin da Dr Rasheed yai mata sai take jin harshen ta yy mata nauyi. Bata kara sanin komai ba tun shigar ta motar sai bude idanu tayi ta ganta a wani katafaren 'dakin da yaso firgitata, ga kuma Mufee na bacci gefen ta. Kasa motsawa Zaitun tayi sbd tsoro, Allah gani gareka ta furta cikin zuciyar ta..wasu kwalla masu zafi na gangaro mata. Bata tashi daga kwancen ba har zuwa lkcn da kunnuwan ta suka jiyo mata kiran assalatu. Bata yi kasa a gwiwa ba ta tashi ta nufi bayi. Ta da'de kan Carpet 'din da tai sallahn tana hawaye tana rokon Allah ya sassauta mata ya kuma yafe mata laifukan ta manya da kananu, ta mika masa lamuran ta yy mata jagora ya raya mata yarinyar ta ya kuma kawo musu mafita. Gefen Mufee ta koma ta kwanta tana sake rufa mata Hijab din jikin ta, tunani take yadda rayuwa ke ta gargara ta..zuwa yanzun duk ta saduda tsoron Allah da shakkan mutanen dunia ya gama cika ta. Da safe misalin karfe bakwai taji an turo kofar gami da sallama, Dr Rasheed ne bayan sa kuma wata mace ce doguwa 'yar kyakkyawa sai dai fuskar ta tamau babu ko alamun fara'a. Wani faduwan gaba Zaitoon taji me tsanani da ganin Rasheed, duk da yk bata yi mmkn ganin nasa ba amma sosai ta tsorata, rabon da ta gansa tun ranar da ya kafa mata warning sai yau kuma, sosai jikin ta ya fara rawa amma tashin farko bazaka fahimci hkn ba sai in ka dubi cikin idanhn ta, hk kuwa ta bude idanu ta zuba akan su zuciyar ta cike fal da tsoro da fargaban me kuma ya kawo su gareta...fahimtar hakn yasa shi sakin 6oyayyar murmushi idanun sa fess akanta. "...Kuntun ubancan!..lalle ma Rasheed, yana nufin wannan ce matar? 'yar yarinyar nan, rainin hankali" " Erh lallai! salon ta zauna da ita bayan ta waye tazo ta aure mata miji...bazata sa6u ba sam wlh.." Zancen zucin Hameedah kenan wanda tayi sa ne tana daga inda take tsaye bayan Rasheed itama tana duban Zaitun da wani mugun kallo. Da rawar murya ta gaida su, babu wanda ya amsa gaisuwar daga cikin su sai ma " Ya jikin naki..?" Da taji Dr Rasheed ya fa'di. Rarraba idanu ta fara da tunanin wani jikin kuma? bata san dalilin tambayar ba dan hk kawai ta amsa masa" Alham..dulillah..da sauki..". Gaba 'daya ya gama rikitar da ita, " dama bani da lpy ne..?" Ta tambayi kanta tana me yin tsam da tunanin ta gami da hasaso inda ke mata ciwo cikin jikin ta..bata ji komai ba. Waigawa yayi ga Hameeda yana 'yar murmushi yace" Hameeda meet Zaitoon...my Patient.." " Na ganta.." Ta amsa a sanyaye tana kya6e baki da kawar da kanta. " Zaitoon wannan matata ce sunan ta Hameeda..nan kuma gida na ne..zaki zauna tare da mu zuwa lkcn da zaki dan kara samin sauki sai aga yadda hali zai yi ko..?" Ya fa'da cike da kulawa, sai dai hkn duk ba shi Zaitoon ke son ji ko samu daga gareshi ba, ba wannan kalmar take son ji ba, sam ta kasa fahimtar inda maganganun nasa ma suka dosa, yana nufin zama zata cigaba da yi dasu, tayi musu me? amma bata da bakin tankawa koma me yace mata dole ta amsa shi dan bata ta6a mance haduwar ta ta karshe da shi. Shi kansa ma yasan hkn shiyasa bai wani damu da sake jaddada mata wani kashedin ko tilasta ta amsa maganar sa ba. " Amma wai sai anan gidan dole zata yi jinyan ne Abban Naina? why not can asbiti inda kowa ke zuwa kuma yafi dacewa.....". " Anan nayi ra'ayi Hameeda pls, bana san dogon magana". Dole taja baki tayi shiru badan hnkln ta ya kwanta akan zaman ta da Zaitoon din ba sai dan gudun 6acin ransa. Tare suka sake ficewa a dakin suka bar Zaitun cikin zullumi da toshewar tunani. Duk ta rasa meke shirin faruwa da ita ne. In tunanin ta ya bata daidai kenan an canza musu muhalli zuwa gidan sa inda iyalan sa suke kuma an kawo ta ne da sunan marar lafiya..kenan bashi da niyyar barin ta tafi ne ko me hkn ke nufi..Yah Subhanallahi, wannan wani irin tarko ne? kenan ta bar bakin kare ne ta fa'da bakin kura. A hanya Hameeda ke sake tambayar sa amma ba da'dewa zatayi anan din ba ko? Yace" Ni kaina ban sani ba, ma mmk su dade 'din. Turus tayi cike da takaici batayi kasa a gwaiwa ba ta sake jefa masa wata tambayar.. zata na fitowa tayata aiki yace sam ita ba me aiki bace majinyaciya ce. Wannan karon sosai ya hassala ta duk wani zafin da ke zuciyar sai da ya bayyana kan fuskar ta ta kasa danne shi. " Amma Abban Naina sai nk ganin kamar ka zake da yawa akan yarinyar nan...taya za'ai ka kawo min gantsamemiyar yarinya irin wannan hk kawai kuma kace in Zauna da ita ba muharramar ka ba ba tawa ba ba komai ba..." " Thought gidan nawa ne..?" Ya tare ta da tsawa yana waigowa gareta muryar sa da alamun fushi, ji yy ya gaji da maganar gaba 'daya, tun daren jiya yk kokarin fahimtar da ita amma ta kasa fahimtar sa. Hameeda saroro tayi tana duban sa cike da mamakin sa. " Anya Abban Naina cikin hnkalin ka kk kuwa...?" Ta tambaya cikin wani sanyi da raunin tsoron yadda ya buga mata tsawa sbd waccan yarinyar. " What ever..abinda na sani kawai shine ke da duk wani abinda ke cikin gidan nan mai rai ko sa6anin hkn mallaki na ne, kuma karkashin iko na, dan hk ba lalle sai nayi tarayya da wani wajen zartas da hukunci cikin gidan nan ba...Zaitun zata zauna tare da mu daga yanzu har zuwa lkcn da nayi ra'ayi nd that's final...."! Salmerh😘 [20/9/2022, 12:32 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Salmerh MD* 🅿️ *...20* Yana gama fa'din hakan yy gaba abin sa batare da sake jiran wata kalma tata ba, da kallo kawai Hameeda ta bishi cike da tsananin mamakin sa..." is this real...?" Ta tambayi zuciyar ta. Dr Rasheed ne ke mata irin wannan surutan akanta..me kenan hkn ke nufi?..kenan...kenan laifi ne dan ta nuna bazata iya zama da yarinyar ba? Kasa ko 'daga kafafun ta tayi a wajen tana jin wata karaya na tsirga mata cikin dukkan ga6o6in ta. Ji take tamkar ta sanya hannu aka tayi ihu ko zata ji saukin zuciyar ta. Gaba 'daya ji tayi ya 'karawa zuciyar ta zafi..sosai taji tsanar Zaitoon har can kasan zuciyar ta fiye ma da farko, akanta ne Rasheed ke buga mata irin wannan tsawar da rabon da ta ji yamata irin sa baza ma ta iya tunawa ba? Da gudu ta koma dakin ta hawaye na zuba mata babu kakkautawa. Waya ta lalu6o ta dannawa mahaifiyar sa kira nan ta zayyano mata komai har ma da kari, ga mamakin ta hakuri kawai ta bata tare da kalaman da zasu kwantar mata da hnkl. Inda ta kara da fadin in kuma taga zuciyar ta bazai kwanta da zaman yarinyar acan ba zatai masa magana ya kawo ta nan wajen ta. Godiya kawai Hameeda tayi mata ta kashe wayar, tana nufin itama tasan da batun kenan? Kenan kalaman ta ta fahimci tamkar lbrn ba sabo yk agare ba, baki suka hada ko kuma mene...tun yaushe Rasheed ya shirya wannan lamarin bata da masaniya. In kuwa har mahaifiyar sa ma tasan da batun dole itama ta nuna nata ikon in ba hk ba zasu kaita kasa. Dole akwai wani boyayyen abu da ita bata sanshi ba..zata bincika za kuma ta 'dauki mataki. Ta jima tana tunanin yadda abubuwan zasu iya wakana, ita zama da yarinyar tare da su din bata bukatar sa sam sam kuma shi tafi tsana sannan abinda zai iya biyo bayan zaman, ko da tace akai ta can gidan ta din ma Hameeda sai taji bata aminta da hakan ba, da aje can ana hada kullin da bata sani ba gwamma ayi agaban idanun ta yafi, koba komai zata san shirin su. Kai anya ba baki aka jada za'a mata sakiyar da ba ruwa ba..tunanin ta ya kasa tsayawa waje guda. Wannan yarinyar in ta wanku ai ko bakin farcen ta ba ta isa ta kama a kyauba, in kuwa akace yau ta zama kishiyar ta ta gama kadewa har ganyen ta. Kuma in dai bb wata akasa me yasa shi aminta da ita yarinyar har da kawo ta gidan sa. me yasa Rasheed dagewa akan ta, shi da ko 'yan aiki bai yadda da ko guda cikin gidan sa ba, duk girman gidan ita kadai ke kula da abinta..ita kadai ke shawagi cikin sa sai 'ya'yan ta, sai kuma me sharar haraban gidan sai duk bayan kwana biyu shima yake zuwa yayi sharan sa ya kama gaban sa..gateman kadai ne yk nan. Karshe dai dole ta yanke shawarar zaman Zaitun din tare da su a gidan taga gudun ruwan su kafin kuma ta 'dau nata matakin. Dr Rasheed bai sake bi takan Hameeda ba har ya gama shirin office ya fice abinsa shi da Wildan ya ajiye sa a schl. Shi kansa yana mamakin kansa, dan bai san dalilin da ya sa yake jin yarinyar ba, yake kuma son su zauna tare da shi, yana ganin dukkan motsin ta, ya san dai tun washe garin ranar da ya taimaka mata yk jin zuciyar sa nayi masa nauyi game da ita ya kuma ji baya son tai masa nisa..amma bai ta6a zaton zai iya tsawatar wa Hameeda akan ta har hakan ba. Idanu ya lumshe gami da shafo kansa da kansa yasan bai kyauta mata ba amma baiga laifin sa wani cancan ba, batun yau yasan Hameeda da tsananin kishi ba, sarai yasan ta, sai dai abu guda da take birge shi kokadan bata da mummunan zargi akansa sai wanda ta gani da idanun ta, shiyasa duk irin zirga zirgar da yake yi bata ta6a tanka masa ko nuna zargi kan hakan ba. Kuma sarai yasan ta fisa gaskia akan Zaitun, amma ba yanzu ya shirya barin ta tafiya ba, bai ma yi niyyan kawo ta ba bayaga gudun kar Hajiya ta gano ba'a gidan take ba ta dasa masa wata ayar tambayar da yake tun farko ya riga ya sanar da ita batun Zaitunar. Kuma jiya kannen sa sun ce masa zasu zo gidan nashi yini kwanan nan...shiyasa ya kawo ta. Ranar Zaitun taga rayuwa, tun safe bata sake jin motsin kowa ba balle idanun ta suga abinci tun na karyawa da aka basu, damuwar ta ma Mufeedah ce bata ta kanta, da rana ma ragowar bread din su na safe tai ta hankara mata ta kuma yi bacci gashi har yamma babu motsin kowa ita kuma tsoron fita take dan ta lura matar gidan bata yi na'am da su ba tun ganin yanayin fuskar ta safe. Kafin dare duk sunyi laushi..shi Dr Rasheed ma kwata kwata ya mance da lamarin su sai da yazo ya tarar da Hameeda a 'dime kafin ya tuna sanadin fushin. Da kansa ya 'diba abinci ya kai musu Hameeda nata binsa da kallo, dan kuwa iya abincin kenan da ya rage nashi ne iya su da ta sabawa yiwa girkin iya su taiwa, dan tuni ita da yaran ta sun ci nasu dan ba karamin fushi take da shi ba akan Zaitunar. Taya ma za'ayi ace ita zata rika dawainiya da ita bacin itama mace ce kamar ta. Bata tashi tsinkewa da lamarin na Rasheed ba har sai bayan Isha'i da yasa ta bisa dole sai ta sama masa abinda zai ci. Bakin ciki kamar zai karta, haka ta nufi kitchen din tana 'kwalla, taya ma za'ayi ta kaunaci yarinyar nan...yini 'daya tak ta birkita mata lissafin miji ta hana ta farin ciki da sukuni ta dauke mata walwala duk ta birkita mata cikin gidan ta. Bama wannan ba, wacce irin rashin lafiya ce wannan da sai a gidan ta za'a yi jinyar ta? da me tafi sauran marasa lafiyar? kai anya kuwa..?...anya..?. Karon farko cikin rayuwar ta da ta dasa zargin Dr Rasheed din cikin zuciyar ta. Ranar kowa 6angaren sa ya kwana, bai neme ta ba haka ita ma bata kusanci ko hanyar nashi 6angaren ba. Shi kam bai wani damu ba, aransa yake ayyana zaama ta sauko ne, shikenan dan kana da mata a gida baka isa kayi taimako ba, baka isa kayi wani abin alkhairi ba sai ya zam laifi. Washegari haka banda gaisuwa babu abinda ya ha'da su, shi 'din ma cikin 'daurewar fuska tayi shi, yayi kokarin fahimtar da ita dalilin zaman Zaitun din amma ta gaza fahimtar sa, sai ma sake jaddada masa da tayi cewar bazata zauna tare da ita ba gaskiya, ita bata ma ga alamar jinya ko rashin lafiya tattare da ita ba, dan haka ya tattarata su bar mata gidan ta in dai yana son kwanciyan hankali ya cigaba da gudana cikin gidan sa, in kuma ba so yake ta fara zargin wani abu daban ba. Wannan bayani da Hameeda tayi shiyasa Dr Rasheed fito mata a mutun shima ya sake kafa nashi dokar inda yace zama da ita yanzu ta fara matukar zata cigaba da zama matsayin mata agare shi bb inda zai kai Zaitunan, in kuma ta gaji da cigaba da amsa sunan matar sa ne bai hanata ba zata iya aikata duk abinda taso. Wannan dalili ya sake tada hankalin Hameeda sosai ta rikice masa ta hana kanta sukuni. Bai bi takan ta ba yy ficewar sa office sai dai duk hankalin sa na nan gidan. Sarai yasan halin Hameeda da kyar ne idan zata sake waiwayar su shiyasa ma tun kafin ya tafi ya mika musu breakfast da kansa, 12 na yi kuwa da kansa yabi ya 'dauko Wildan a shcl ya zarto gidan, da kansa ya tura Wildan yai kiran Zaitun 'din suka ci abinci su duk a dinning zuciyar Hameeda kamar zai fashe sbd bakin ciki, ita har Zaitun din basu wani ci abin kirki ba, kowa abinda ke ransa daban, Zaitun jin ta tayi a takure sosai, Mufeeda tai ta bawa abincin sai da ta tabbatar ta koshi sannan ta mike ta koma inda ta fito. Dr Rasheed duk na lura da su amma bai cewa kowa kanzil ba, a ganin sa ai duk ba yara bane su. Zaitun kam kusan tafi Hameedar ma rashin sukuni da damuwa..bayan duk abinda ya faru a wancan gidan taya yake tunanin zata iya sake jiki ta cigaba da zama da shi? ba cikin iyalan sa ya kawo ta ba ko da gaban mahaifan sa ya kaita wlh bata jin zata iya sakewa da su, bindiga fa! da bindiga ta ganshi. Da ace zata iya bude baki ta roke shi ma da tuni ta aikata hakan, amma bazata iya ba, yanzu hanya take nema, so take kawau ta bar musu gidan su, kwatakwata ta gaji da kallon fuskar sa a rayuwar ta, ko me kama da shi bata kaunar gani a yanzu balle shi, gashi anyi sa'a ma matar gidan bata kar6i ba'kuncin nasu ba sai take fatan Allah yasa hakan ya zam sanadin da zasu nar gidan, ita ta kowace hanya ma, ta kowace siga fatan ta kawai ace bata gidan ne. Ita ko ka'dan bata ganin laifin Hameedan ba, abu ne mawuyaci ace miji da kansa ya d'auko wata mace, mace budurwa kamar ta ya kawo cikin gidan sa wajen matar sa ace kuma ta samu tarba yadda ya kamata batare da an samu matsala ba, balle ita da ya kasance zama ne bama ziyaran zuwa a koma na dan mintina ba, tabbas ba za'a rasa masu kawaici ba amma da kamar wuya samun macen da zata jure hkn sai dai in ya kasance matar mai fahimta ce ko kuma me karancin kishi. Kamar Dr Rasheed yasan me take da burin yi cikin zuciyar ta washegari ya kafa mata dokar ko babban parlourn gidan be amince ta wuce ba balle tayi tunanin fita harabar gidan, yace daga kitchen bai amince ta wuce nan ba, shima kitshen din sai inya zam dole, tana iya shiga dan sama musu abinda zasu ci bayaga haka matukar ta kuskura ta sa6a dokar sa toh kuwa ta tabbatar zata bakunci lahira ne daga ita har Mufeeda bazai bari ba, domin da hannun sa zai sa bindiga ya tarwatsa mata kwakwalwa, Dr Rasheed kuma yy wannan bayani ne da tunanin ko da Zaitun din zata ce zata na fita dan kama wani aikin ko wani abin daban uwa uba kuma kar tayi tunanin barin gidan, a yadda ya fahimce hakan kadai ne ya rusunar da ita waje guda batare da ta sa6a dokar sa ba. Banda Innalillahi bb abinda take jerawa cikin zuciyar ta, sosai maganganun sa suka sake tarwatsa dan guntun kwarin gwiwar da ta samu, sosai komai ya sake kwance mata, meyasa duk shirin da tayi yk rusa mata?..ba haka taso tayi rayuwa da yarinyar ta ba, ba haka ta tsara musu ba. Haka take kwana kuka, ta yini zubda kwalla, yayin da Mufeeda ke kura mata idanu kawai tana kallon ta dan bata baki, amma a yanda take kallon nata da ace tana da bakin magana da zata taushe ta ne, ta kuma lallashe ta, ta jima da yin nadamar barowar ta gida, ta kwammaci dama tayi zaman ta a garin nasu ko Allah zai sa su fahimce ta su tausaya mata su rike ta ita da Mufeedan. A yanzun ma ji take da zata samu hanyar barin wannan bakin gidan babu abinda zai hanata komawa can gida. Banda rashin walwala da tarin damuwa gefe guda kuma a tsanake ake hukunta su da yunwa cikin lumana batare da zafafawa ba. Domin ita bazata iya yadda Dr Rasheed din yace tayi ba, taya ma za' ai ta iya taka kafar ta ta fita zuwa kitchen din gidan dan sama musu abinda zasu ci in ba'a basu ba...taya zata iya hakan bacin tun farko bata ga fuska wajen matar gidan ba, tsaurin idon ta ma bai kai wannan ga6ar ba, ai koba komai ta san abinda ya dace da wanda bai dace ba. Ranar da kannan sa suka kawo musu ziyara gidan ne ta 'dan ji dama dama, domin da kansu su ka binciki dakunan gidan suka binciko inda take, anan kam taga zallar kauna, yara ne 'yan mata guda biyu, 'daya zata girme mata sai 'dayar kuma bazata wuce sa'ar ta ba. Sosai suka ja ta ajiki sukai ta yaba kyawun ita har Mufeedahn...duk da kasa sakin jikin ta da su da tayi amma su basu damu ba, su zaton har lokacin batada koshin lpy ne...sun dauki kimanin awa guda tare da ita sannan suka koma can babban parlourn, karshen ta abinci ma cewa sukai tare da ita zasu ci ko kyankyamin ta basa yi ko kadan. Nan ne ma tadan samu taci abincin me dan dama sbd yadda suke damuwa da ita da ganin taci abincin. Cikin zuciyar ta sai suke bata tausayi, yadda suka damu da yayan nasu magana ka'dan Yah Rasheed, ta fahimci suna matukar ji da shi ga dukkan alamu basu san shi din tamkar dafin maciji yake ba. Kamar wasa sai gashi sun yini da Zabba'u da Zaleeha, yayin da Hameeda ko kallo su duk basu ishe ta ba, dama ba wani kwakkwaran shakuwa ke a tsakanin su ba, sai kuma taga sun zo sun wani nane wajen Zaitun abin sai ya sake 'kona ta. Dagaske Zaitun taji su Zaleeha sun shiga ranta musamman yadda taga sun ja yarinyar ta ajiki, da farko tare da Naina suka taho dakin nata sai dai ba'a jima ba Hameeda tazo ta dauke yarinyar ta wai baza'a hada mata yarinya da irin titi ba. Duk din su basu ji dadin maganar ba amma bb wanda yabi takan zancen sai ma hira da suka dasa sabuwa. Sosai Hameeda ta zurfafa tunani, mafita take nema, at any cost ita dai burinta qce Zaitun bata tare da su. Bata yi maganar da mahaifiyar ta ba dan tasan zata bata rashin gaskiya, yayar ta wacce take bi mata ita ta kira ta zayyane mata komai bayan tafiyar su Zabba'u da yini biyu. "...Shine baki sanar dani tuntuni ba?...". Cewar yayar Hameedan me suna Anty Saleeha. "...Wlh duk bani da natsuwa ne Anty, gaba 'daya hankali na ba a kwance yake ba, kin kuwa ga yarinyar ne Anty taya ma zan iya zama tare da ita cikin gidan nan hnkl na ya kasance a kwance...". Hameeda ta fada da dukkan gaskiyar ta. " Ki bari gobe zamuyi magana, zan kira ki...". Salmerh...😘 [20/9/2022, 12:34 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* _Wattpad@_ _Serlmerh-md_ 🅿️ *...21* ......" Ba'kin talauci, fatara, damuwa da matsalolin rayuwa ne suka da'kushe komai da ya dangance ta suka kuma 6oye duk wani sirrin kyawun da Allah ya bata, dan bana jin ko ita kanta tasan ta mallaki wannan sirrin, amma wlh da zarar duk wa'dannan sun kau abu ne mawuyaci Dr Rasheed ya sake yimin duba irin na 'ya mace cikakkiya da daraja matukar yana ganin yarinyar nan gaban idanun sa kuma yasa ta a zuciya...tsoro nk ji kar abin yazo yafi karfi na watarana Anty...". Bayanin Hameeda kenan da ke zaune kan 'daya daga cikin kujera mai zaman mutun 'daya dake madaidaicin Parlon da ya kasance maha'di ga bedroom din ta, kuma tayi duk wannan bayanin ne ga 'yar uwar ta Anty Saleeha wacce ta cika alkawarin kiran da tace zatai wa Hameedan washegari bayan ta samu isasshen lkcn da zata iya ganawa da ita. " Ki kwantar da hnkalin ki nace, amma tuntuni kin kasa yin hakan kan wani abu da bai taka kara ya karya ba ki ke ragewa kanki daraja da baiwar da Allah ya baki, abu mai tsananin saukin da ke da kanki ma zaki iya samawa kanki mafita idan kin nutsu kk bi a hankali.." " Kar kice haka wlh Anty Saleeha dan baki ga yarinyar bane kk ganin kamar abin ba na kirki ba, ki dai na ganin abin kamar me sauki, ni nasan halin da zuciya ta take ciki a yanzu, wani baiwar kyau Allah yy mata da duba 'daya zakai mata ba sai ka 'kara ba za ka fahimta matukar kana da kula, taya zan iya zama da ita cikin gida na Anty na kuma kasance cikin natsuwa da kwanciyar hnakalin da kk fada alhali nasan shi kansa Rasheed 'din abinda nk gani game da yarinyar shima hkn ya fahimta ne yasa shi ajiyan ta zuwa wani lkc, abin takaicin ma fa har yarinya gare ta Anty, kuma na tabbata garin biye- biyen tituna da kwararo ta samo cikin har ta haife, sai ma kin ga yarinyar...wlh duk lkcn da na tuno da su bama na gansu ba sai gaba na ya fadi bazan iya jure yawan ganin suna wulgawa gaba na ba wlh, ina kishin miji na sosai....". "...Shin ke Hameeda kyanta ne ka'dai ya dame ki..?, baki tunanin makomar ki bayan abubuwan da ake gudu sun gudana, bakin tunanin cushewar al'amura da canzawar su? baki tunanin me ze biyo baya? da bakin ki fa kk ce har yarinya gareta bakya tunanin cewa ta fiki sanin dunia da budewar ido? ba mmk lamfo kawai take mk amma da zarar ta saita komai zaki yi mmk, irin su bada wasa ake bin su ba, domin su 'din tamkar maciji suke, dole sai an musu tashin wuf lokaci guda, cire batun kyawun ta a lissafin ki, kiyi tunanin makomar ki da ta yaran ki anan gaba...a lokacin nasan zaki fi fahimtar duk wasu bayanan da zan mk..." Da gama fa'din hakan ta fara kokarin datse kiran, fahimtar hakan da Hameeda tayi ne yasa ta zabura ta dakatar da ita da sauri " wlh Anty yanzu ma a shirye nk zan fahimce ki, me zan tsaya jira da har sai nayi tunani?.." " Naga kamar inda tunanin ki ya tafi daban da inda nawa yk...". Cewar Anty Saleehan cike da gatsali..cikin ranta kuwa ayyana irin tagomashin Nairori da zata samu take matukar Hameeda ta amince da batun ta. "...Na dawo daidai nima yanzu, fada min koma menene..." Cewar Hameeda tana gyara zama cikin 'kaguwa da son jin mafita me 6illewa daga yayar tata. Murmushi Saleeha tayi sannan ta 'dora da fa'din " Nan kusa da ni ne ba nisa da gidan nan, kisan yadda zaki yi kawai ki taho da ita gida na, chamber ce da ake tara irin su ake mi'ka su aikatau ko wani abin daban ga masu bukata amma za'a yi komai ne bisa tsari da kuma sirrantawa kar ta fahimta kar kowa ma ya fahimta sbd rufin asirin ki, da zarar ta shiga hannun su an dam'kata gare su shikenan bata kuma da wata mafita, dan suna da tsaro sosai, chamber ce da wani attajiri ke jagoranta kuma be 'dauki abin da wasa ba...da zaran ta shiga hannun su shikenan tunanin ta zai canza sai yadda suka yi da ita, sai abinda suka ce da ita zata yi, wannan shine ka'dai mafita agareki in kinga zaki iya amma..." Sosai Hameeda tayi na'am da zancen sbd a ganin ta yama fiye mata sau'ki akan shawarar da zuciyar ta ta fara yanke mata na yiwa Zaitun korar kare a gidan, sbd in korar tata tayi gateman zai iya fallasa ta ga maigidan, kuma bata da ikon aiken sa ko'ina domin Rasheed bai yadda ya matsa ko nan da can ba daga jikin gate din, da yake ma ba sallah zai yi ba dan ba musulmi bane..baya ga haka ma in korar tata tayi ba mamaki ta sake komawa can asbitin wajen sa ya kara dawo da ita aikin banza kenan tayi, amma in tabi shawarar Anty Saleeha zata kashe maciji ne tare da sare kansa duk lkc guda dan haka sosai shawarar tayi mata. Tun daga lkcn kaso mafi rinjaye daga cikin damuwar ta ya kau, tana jin cewa matsalar ta tazo karshe ne baki 'daya. Sai ma taga waitar ta da har tayi zancen da kawar ta Nabeela tuno yadda tattaunawar ta su ta kasance, sunyi sec. schl ne tare da ita acan Kano dan itama daga can aiki ya dawo da mahaifin su nan, kuma shine abinda ya raba su da kawar tata sai dai sukan yi waya lkc zuwa lkc, duk da yk ita kawar tata Allah bai mata mijin aure ba har yanzun amma ya bata tarin nagarta, ilimi da sanin ya kamata bata da banzan hali da kai tsaye zaka nuna game da ita. "...Dan Allah Hameeda ki kwantar da hankalin ki, me yasa wata can zata dame ki? kin manta mijin ki ne shi? Ke ce fa kk da damar sarrafa tunanin sa duk ta yadda kika ga dama matukar zaki bi komai a sannu, ki daina bari damuwar da bata kai a 'kira ta damuwa ba tana hana ki sukuni da yin abinda ya dace, yanda kk ganin tana kyau ba mmk ma kin fita kowa nada nashi kyawun ai a yadda Allah ya halicce shi, kuma nasan ba za'a rasa abubuwa da yawa ba da kk fita da su a fili da 6oye kyawun ta da ya mk karan tsaye shine zai hana ki fahimtar hkn, ki nutsu ki daina damuwa da batun kyawun yarinyar zai iya yiyuwa hassada ta kamu da zuciyar ki batare da kin fargaba karshe har kizo ki kasa aiwatar da abinda ya dace...ki nutsu kiyi ta addu'a kibi komai a sannu Insha Allahu bb abinda zai faru sai Alkhairi, kamar yadda ya kawo ta hk zai kara dauke mk ita gaban idanun ki ki huta ganin ta har abada dan Allah ki daina damuwa kinji...." Kwata-kwata shawarar kawarta ta bai mata ba, abu guda ma da ta fi ri'kewa a ciki shine kalmar hassada da ta anbata..ta nisa ta zurfafa tunani amma ita bata ga abinda za'a ce take wa hassada game da Zaitunan ba, hakan ne yasa ta kasa tankawa kawarta ta ko da ta gama bayanin ma..." Nagode Nabeela..". Shine kadai abinda ta iya furtawa, tasan cewa Nabeela bata san zafin kishi bane shiyasa, ko kuma dan bata da aure shiyasa bata san yadda ake ji game da faruwar irin hakan ba. Sai ma taga wautar ta da tun farko ta nemi shawarar Nabeelan...karshe da zazzafar kalma kwara daya ta bar zuciyar ta abin kokawa. Ta yi alkawarin bazata sake tunkaran Nabeelan da duk wata shawara tata ko neman mafita ba, tunda ba fahimtar ta kwakwalwar Nabeelan take ba. Duk da 'dimbin farin cikin cikin da zuciyar ta cika da shi, hakan bai sa ko alama ta nunawa Rasheed ba, hk ta cigaba da 6oye farin cikin ta dan kar ya zargi wani abu har zuwa lokacin da zai dawo gidan bai tarar da Zaitun ba, dan sarai ta sanshi, ba 'karamin jaa kwakwalwar sa take ba, cikin sauki zai iya gane shirin ta. Washe garin ranar kafin ya wuce wajen aiki da kansa ya dubo su Zaitun 'din cikin 'daki dan tabbatar da lafiyar su, karshe sai gashi ya fito da Mufee a hannun sa yanai mata wasa, Hameeda bakin ciki duk yabi ya baibaye ta kawai ta kawar da kai gefe, bata so abin nasu ya ringa girmama fiye da na baya. Haka Wildan da Naina suka baibaye Rasheed ganin sa da yarinya kowa na fa'din ra'ayin sa, Wildan ne yace laa Abbah tazo wajen ka..? ranar da ka aike ni wajen maman ta kin zuwa waje na tayi dana ce zan dauke ta ta makalewa maman ta, itama maman nata ta hanani ta6a ta...". Gajeruwar murmushi Rasheed yy bai kuma yi mmk ba dan ya san hatta shi da tana da iko bazata barshi ya ta6a yarinyar ba talkmore of ya dauke ta gaban idanun ta ya fito da ita, wani dalili ya sa take barin sa take kuma shakkan hanasa ta6a yarinyar da tankasa akan komai. " Bata sanka bane shiyasa, amma idan ta saba da kanta ma zata zo wajen ka.." Rasheed ya fa'da wa Wildan yana shafa kansa cike da kulawa yana 'yar dariya. Naina kam hannun Mufee ta kamo cikin hannun ta tana makale jikin Rasheed din tana wasu surutai da bakowa ke gane mata ba kasantuwar nauyin harshe da take da shi. Wildan ne yana tura baki yace" Toh Abba yaushe zamu saba? " " A hankali ka ringa ka na mata wasa wataran ko ka dauke ta bazata ki ba har ka kawo ta wajen Naina kuyi wasa..". " Abba ai in na ce zanje wajen su Mummy ke hana ni shiyasa bata sanni ba har yanzu...". A fakaice ya harari Hameedar tai kamar bata ji tattaunawar ta su sai ma ta kara 'dimewa cikin ranta take ayyana cin uwa da zata yiwa Wildan din in Rasheed ya fita. Mufeeda kam rarraba musu ido kawai take tana kallon su. Sosai Dr Rasheed yake jinjina tsabta da kullun yake ganin yarinyar a ciki duk da ba suturun kirki gare su ba amma bai ta6a ganin yarinyar cikin wani yanayi na rashin tsabta ko kula ba, shiyasa sam baya jin ko dar yk iya daukar ta. Cikin ransa ya ayyana zai kokarta ya sama musu suturu ko da ba masu yawa ba. Ranar haka suka yi breakfast anan kasan parlor shi da duk yaran, da kansa ya ringa bawa Naina da Mufee a baki. Hameeda kamar zata fashe sbd bakin cikin an hargitsa mata yara. Taya ma za'ayi yy hakan, taya zai rinka caku'da mata 'ya'ya da yarinyar. Zaitun na can 'daki hnkln ta duk ya tashi ganin ya fita da Mufeeda, tsoro da fargaba sun gama cikata har bata san lkcn da kwalla ya fara bin idanun ta ba. Ko breakfast 'din da ke gaban ta bata kalla ba balle ya samu arzikin ta ta6a shi, hnkln ta duk naga yarinyar ne...gashi ita yanzu tsoron Dr Rasheed take sosai baya ga hk bb abinda zai hana ta bi sawun su, so ta kagu ta bar gidan nan, so take ta bar shi cikin ko wani irin hali, a kullun jin ta take tamkar tana kan 'kaya ne. Tana cikin zulumi sai ta fara jiyo hayaniyar yaran na kusanto ta, da wuri ta mike tsaye ta jirayi isowar su tana me kurawa 'kofan dakin idanu. Wildan ne ya fara shigowa da 'dan tsallen sa jikin sa sanuye da uniform sai Dr Rasheed hannun sa rike da Naina yayin da kuma Mufeeda da ke rungume saman hannun sa 'dayan. Wani 6oyayyen ajiyan zuciya ta sauke, ganin yarinyar tata garau babu abinda ya same ta. Mi'ka mata yarinyar yai yana fa'din.." Ba a cinye ta ba dai ga tanan ta dawo.." Yayi maganar yana 'yar murmushi a kokarin sa na ganin ta 'dan saki jiki da su musamman ma shi. Bata ce komai ba kamar yadda bata nuna alamun ma ta jishi ba, hankalin ta duk ta mayar kan Mufeeda tamkar iya su ka'dai ne a dakin har zuwa lkcn da sautin muryar Rasheed ya sake dokan kunnuwan ta. " Wildan yace kina hana shi daukan Mufeeda, bakya so su saba ne? ai yayan ta shi kamar yadda yk yayan Naina ko..?" Ya karashe maganar da tambayar Wildan wanda da da hanzari ya dage kansa alamun " erh..". Ko guda cikin maganganun nasu bata ji na tankawa ba sai kallo da tai masa na mmk kenan bb ranar tafiyar ta. Haka suka juya suka fita dukkan su Wildan na kokarin cewa" Anty idan na dawo daga schl zanzo in dauke ta ai bazaki hana ni ita ba ko, Naina tayi nauyi yanzu bana iya daukan ta ne....". Yayi maganar ne ya duban idanun ta wanda dole hkn ya tilasta mata amsashi da fa'din "..toh sai ka dawo.." Wannan ta fada ne kawai dan ganin idon Dr Rasheed baya ga hk da ko kula yaron ma bazata yi ba. Ba wani bashi Mufeeda da zata yi. A ranar da haushi ya cika zuciyar Hameeda ko fita zuwa gidan Anty Saleehan bata iya ta tambaye shi ba dan tana so ne ta kawo karshen matsalar cikin kankanin lokaci, tun kafin 'dan zaki ya girma yafi karfin dabarar ta, sai da aka kwana biyu wanda yayi daidai da cikar Zaitun kwanaki takwas cif a cikin gidan. Tuni Dr Rasheed ya kawo wa Mufeeda kaya har kala biyar Zaitun kuma dogin riguna guda biyu...sai wasu 'yan abubuwa na amfanin yau da kullun wanda yasan zasu iya bukata. Ita kam yanzu duk irin wadan nan abubuwan basu ne gaban ta ba, taimakon kowa ma bata bukata a halin yanzu, kawai bb yadda ta iya da shi ne, amma kullun addu'a take Allah ya kawo mata mafita ta rabu da wannan zaman takurar. Kokadan bata sakewa agidan, motsin kirki bata iyawa sai taga kamar komai idan tayi masu gidan zasu ce laifi ne tayi, gashi sarai tasan matar gidan bata kaunar su bata kaunar zama tare da su, fuskar ta bai ta6a nuna alamun sakewa a garesu ba, taya zata iya cigaba da zama cikin irin wannan yanayin tasyin lkcn da ita kanta bata sanshi ba. Bata da wata mafita da zata iya tseraratar da kanta shiyasa kawai ta mika lamuran ta gaba daya ga Allah..tasan shine ka'dai zai iya tseratar da ita. Hameeda da kanta ta sassauta fishin ta ranar hadda zuwa 6angaren Dr Rasheed kwana, shi dama ba fishi yk da ita ba kawai ya bita ne dan ganin iya gudun ruwan ta, bai yi kasa a gwaiwa ba kuwa ya kar6e ta suka raya daren su cikin farin ciki da kaunar juna..wanda Hameeda tayi amfani da wannan damar ta nemi iznin zuwa gidan Antyn ta Saleeha, tun farko ma shine dalilin saukowar ta da kuma ziyartas sa da yi a daren, dan ta sanshi matukar tace da 6acin ran zata tambaye shi ko tanka ta ma ba yi zai yi ba balle ta samu izinin tafiyar...hakan kuwa da tayi tasan mafarin nasarar ta ce domin zata jefi tsuntsaye har uku ne da dutsi kwara 'daya tak. Dr Rasheed shima bai hana ta fitan ba dan yasan Saleehar 'yar uwar ta ce kuma a iya sanin sa ta jima bata ziyarci Saleehan ba. Hameeda ita kadai tasan farin cikin dake kasan zuciyar ta na samu wannan damar amma ta danne shi da tunanin daga yau dai duk wata damuwar ta kare ne. Comment Share Vote Salmerh😘 [20/9/2022, 12:34 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* Wattpad@ Serlmerh-md 🅿️ *...22* ........Daf da 'kofan Palor tai parking motar sannan ta koma ciki bayan ta bar Naina cikin motar. Bata zame ko'ina ba sai 'dakin Zaitun tana me 'kara 'daure fuska tamau, sosai take jin tsanar Zaitun 'din har cikin jinin ta, burin ta kawai ta budi ido taga bata tare da su, koma me zai biyo baya ta shirya tar6ar sa daga wajen Rasheed din indai bb idanun yarinyar. Kallon kallo suka tsaya yi Zaitun da Hameeda, Zaitun duba take mata na mamaki da firgicin abinda ya kawo ta, kallo 'daya idan kaiwa Zaitun zaka fahimci a tsorace take sosai, manyan idanun ta da suka kasance ruwa-ruwa su ta zubawa Hameedan yayin da ita Hameeda ke binta da kallon tsana da takaici, tsana irin marar mix din nan da ba'a iya 6oye shi. Sai da ta banka mata harara kafin cike da 'dacin rai tace " Ki shirya yanzun nan, Abban su Naina yace na kaiki wajen uwar'dakin sa..". A yanda tayi maganar a yatsine zaka 'dauka cewa tilastata yin hkn akayi bada niyyar ta bane, amma ga wanda yasani ya kuma san halinta da shirin ta tashi guda zai zaka fahimci tsagwaron tsana ce kawai da rashin kirki ke damin Hameeda. Zaitun bata yi musu ba ta tashi tsaye kan kafafun ta..." Ki tattaro duk da kayan ku..." Hameeda ta sake fa'da wanda ne hakan ya sanya Zaitun cikin wani yanayi marar misaltuwa, shin farin ciki zata yi ko kovbakin ciki, farin cikin zata bar gidan Dr Rasheed ko bakin cikin bata san inda za'a kuma jefa ta ba. Cikin wani babban ledan kayan shopping da Rasheed ya kawo musu kaya ta tattare musu kayan nasu duk aciki. Bata bar komai ba kamar yadda Hameeda ta bata umarni, ita dai lalla6a su take su rabu lpy sbd bindiga bama 'daya ba data tabbatar suna dashi da kuma kashedin Rasheed a gareta. Goye Mufee tayi ta dauko ledan suka fito..baya Hameeda ta bude mata ta shiga ta kuma rufe shi tana sakin nannauyan ajiyan zuciya, da 'karfi take jin fargaba wanda ya haddasa mata bugun zuciya amma sam bata bawa hkn dama ba ta ci gaba da aiwatar da niyyar ta. Kamar yadda ta tsara hkn ne ya faru, gateman bai ga shigar su motar ba illa Hameeda ya gani, kuma tinted ce mai duhu da motar, ita kanta ma motar ba'ka ce, sanin hakan kuma ya sa ta yanke shawarar amfani da motar gudun kar kowa yasan sun fita tare. Unfortunately kuma bata san cewa motar na 'daya daga cikin motocin mugayen fataucin mijin ta ba. Babu wanda ya tanka kowa cikin motar nan dan kowa nashi tunanin daban, burin Hameeda kawai taga ta isa inda take da buri wanda shine mabudin farin cikin ta ya rufu kwanaki kadan baya, yayin da Zaitun ke ta rarraba idanu da son ganin inda kuma za'a jefa ta. Dukkan su basu farga ba, basu lura da yadda wani Police bike ke ta bin bayan su ba, basu lura da yadda yk ta magana da wani abu dake makale kan kunnan sa ba har Hameeda ta bar babban titi ta hau by- pass din da zai kaita gidan Antyn ta Saleeha, kawai bazata kamar daga sama suka ga an musu kawanya an tare gaban su bakaken hilux da ya kasance na jami'an tsaro har guda biyu gaba da baya ga Bike din nan ta gefe saitin Hameeda dake tuki ya saita mata bindiga ga dukkan alamu so ake ta dakatar da driving 'din. Daga Zaitun har Hameeda bb wanda bai rikice ba, dama ko basu nemi ta tsaya ba dole ne sai ta tsaya 'din taji ba'asin bibiyar tata, balle ma sun nema. Da gudu 'yan sanda nan suka yi kan Hameeda da ta fara fitowa daga motar sannan suka bu'de da kansu suka fito da Zaitun da tuni har ta fara kwalla. Me yasa hakan ne wai? Me yasa kusan ko wani lokaci abubuwa ke mata shamaki ga duk wani cikan burin ta, me yasa bindiga ke yawan bibiyar rayuwar ta..? Tattara su duk akayi aka wuce da su ofishin 'yan sanda batare da an ba ko guda daga cikin su damar furta ko kalma guda ba...kamar yadda ba ba' sanar da su laifin da ake tuhumar su akai ba. Ranar haka office din ya kasance a rikice, ma'aikata kowa busy sbd kamo su Zaitun da akayi. Gashi basu san me suka aikata ba, sai da daga baya ne ma suka fahimci akan me ake tuhumar ta su bayan duk sun galabaita da kuka da tashin hnkl. Duk 'din su babu wanda zaka gani kace 'dan dama dama dan gaba 'dayan su ba cikin nutsuwa suke ba, har gara ma Zaitun ita da taji dalilin tuhumar bata yi mamaki ba, dan dama tana da 'dan sani akai kadan bata san komai ba kam amma ta dade da dasa ayar tambaya akan Dr Rasheed 'din. Anan nema ta fahimci Hameeda bata san komai akan lamarin ba. Motar da suka fita da ita kwanaki an sace 'diyar wani hamshaki da ita, sai shekaran jiya da yamma aka saki yarinyar bayan an biya kudin fansa da kwanaki hudu, toh inda aka samu akasi wajen da akai garkuwar gaban wata Plaza ne kuma akwai 6oyayyar cctv ita ta bayyana musu lambar motar bayan dogon bincike da akayi, sosai suke bin diddigin lamarin an baza numbern motar ga dukkan jami'an Jahar gaba 'daya...sai yau Allah ya bayyana musu motar...kuma ita din ce ba wata ba. Bayan 'yan bincike da akai musu nan aka gano Dr Rasheed shi ke da hannu dumu- dumu cikin lamarin. Ba'ayi 'kasa a gwiwa ba aka cafko shi, kafin wani 'dan lkc iyaye da dangin su Hameeda duk sun cika ofishin. Sun nemi abasu bailin su Hameeda amma bb wata kofa data bada damar hakan, abin tun daga sama ne, babu bailing har sai anje kotu. Sai dai an sanar da su baza'a dauki dogon lkc kan zuwa Kotun ba sbd case din ya hada ne da babban mutun. Dama ance rana dubu ta 6arawo....yau dai ga Dr Rasheed ga Hameedah ga kuma Zaitun garkame a bayan kanta. Ba 'karamin wahala suke sha a hannun jami'an tsaron ba musamman da yake Hameeda da Zaitun sunki amsa laifin sai kuka, ko abincin kirki basa iya ci, gefe guda kuma ga wari da uban sauron da cizon su kadai ma azaba ne. Zaitun ba karamin damuwa ta shiga ba, taci burin barin gidan Dr Rasheed cikin ko wani irin hali ba tare da tayi tunanin neman za6in Allah game da alkhairin kasancewar ta a gidan ko akasin hakan ba, yau ga shi Allah ya cika mata burin ta ta fita a gidan Dr Rasheed amma sai ta sake fadawa wani wurin da ta kwammaci rayuwa gidan Rasheed sau babu adadi akan nan 'din...duk lkcn da ta tuno hakan kwalla kawai take sharewa...ta sa aranta cewa bazata sake yin irin wancan fata da addu'an ba, zata roki Allah alkhairin abu kafin ta aiwatar da koma menene. Mahaifiyar Dr Rasheed ce ta roki a fitar mata da Naina da kuma Mufeeda wannan ma sai da aka kai ruwa rana kafin aka amince aka bata yaran ta tafi da su. 'Bangaren Zaitun ai 'karin kuka da tashin hankln ta kenan, ita kanta bata son zaman yarinyar a cikin Cell din sbd azabar sa amma rashin sanin inda za akai mata ita kuma shiyafi tada mata hankl. Dagasken gaske Zaitun ta shiga tashin hnkl, tun tana kuka har tazo zuciyar ta ta bushe, dukan su ake bada wasa ba karfi da yaji wai sai sun amsa laifin da basu san tushe da makamar sa ba. Ita har Hameedan kuwa sun ki amincewa kowa ya kafe kan ra'ayin sa...kusan sati biyu ana abu 'daya, tuni an gama baza hotunan su a media gidan Television da Redio duk labarin su ake...mafi yawan mutane in sun budi baki sai dai suce an kama gawurtaccen 'dan fashi da garkuwa da mutane shi da mukarraban sa, abin mamaki ma wai har da mata ne. Dan duk yadda aka ka'da Dr Rasheed bai yadda ya tona asirin yaran sa ko guda ba..yasan shine ya ja ra'ayin su har ya gur6ata musu tunanin su suka biye shi dan haka bai tozarta rayuwar su ba a wannan hali, yadda babu wanda yasan da su haka yk so su kasance 6oyayyu ga kowa. Dalili kenan da yasa ranar da aka fito da shi dan yimasa tambayoyi ya mi'ka musu sako cikin azanci da yasan su kadai ne zasu fahimta..ishara yy musu ga barin harkar da ya 'dora su akai din su nemi sana'a dan shine kwanciyar hnkl da zaman lpyr su, matukar kace ta mummunan hanya zaka nemi arziki to ka sanyawa ranka faruwar rana irin tasa, ranar tonon silili, ranar da kowa zai san me kake aikatawa, ranar irin wannan me tafe da tarin abin kunya tozarci da kuma dana sani marar amfani, ban da ma ranar da Allah da kansa zai yi ram da kai. Al'umma duk sun dauki maganar tasa ga cewa nadama ce yake kuma tunatar da mutane akan irin halayyar tasa amma su wanda yy dan su din fahimce shi sarai. Dr Rasheed bai yi wani dogon jayayya ba ya amsa laifin sa, shiyasa tuni asbitin da yake aiki ma suka buga stamp din dakatar da shi wajen aiki...abin bai musu dadi ba musamman da yake har cikin asbitin jami'ai suka zo suka kama shi sun dole hakan.sai ya ta6a mutunci da kimar asbitin su in suka yi sa'a ma gwabnati bata rufe asbitin ba kenan. Zaitun ta kafe ne kan iya abinda taga zata iya sanar da su game da dangantakar ta da Rasheed din daga ranar da ya taimake ta har ya kaita gidan sa zuwa ranar da aka kama su, kuma ko da wasa bata yadda ta canza magana ba. Haka ma Hameeda ita kam dama bata san komai ba illa kasancewa matsayin matar sa da Allah yasa ta yi. Duk da haka ba 'karamar wahala suka sha wajen Jami'an ba, duk sun fita hayyacin su sun rame sunyi baki sai tabon cizon 'kwari da sauro da kuma bugun da ake sa jami'ai mata ke musu lokaci zuwa lokaci already kuma an saka ranar da za'a fara gabatar da su gaban kotu dan ansan hukunci daidai da laifin su. ******* "...Shiyasa aka ce yaro yaro ne, yanzu ba ga irin ta nan ba, ka na dai sane da yadda duniya ta dauka an kama Zaitun cikin masu sata da garkuwa da mutane...kuma da ahakan kk so ni in barka ka aureta Shaheed? yarinyar da babu wanda yasan asalin ta balle tsuhen ta, ko kashe ka tayi ta gudu babu ta yadda zamu iya binciko ta har mu kamo ta tunda bamu san wace ita ba...yanzu da asalin wace ita ya bayyana ai sai ka saki ranka nima ka barni na nutsu, ka hana kanka farin ciki, ka toshe dukkan wata hanya ta walwalar ka, 'karshe ma karatu ma gagara tafiya kayi duk dan sbd ita, ni dama tun gani na da yarinyar wlh bata kwanta min ba...". Furucin Hajiya Talatu kenan ga Adam Shaheed dake kwance kan kujera yayin da yasa daya hannun sa ya dafe goshin sa da shi sakamakon sara da kansa ke faman yi masa, 'daya hannun kuma na rike da wayar sa da ya kife ta bisa kirjin sa tun wasu mintina baya. Sam zuciyar sa ta kasa yadda da wannan batun, shi yasan Zaitun, ya kuma san halin ta, duk da akan ce zuciya na gurbacewa amma yasan dai bata da mummunan tunanin da zai sata aikata irin wannan 'danyen aikin...taya ma zai yadda? taya zai amince? Zaitun da ko wani lkc damuwar ta 'diyar ta ce yaushe zata amince ta fa'da harkar da tasan a kowani lkc tashin hnkl na iya riskar su. Bai ce da Hajiyar tasa komai ba har ta 'karaci bambamin ta tayi shiru...ko fita baya kaunar yi waje, balle yaci karo da muggan kalamai ga Zaitunan. Shi dai Allah ne ya dasa masa kaunar ta, kuma ba wai ya kasa yadda da zancen sbd kaunar ta da yk yi ba ne, ya kasa yadda ne kawai sbd ya san nagartar ta da halayen ta...duk tashin hnkln da ya riski kansa abaya dalilin rabuwar su bakomai bane compared to tashin hnklin da yake ciki a yanzu. Dalilin kuma shine sani da yy cewar Zaitun bata da kowa babu wanda zai tsaya mata, gata yarinya ce 'karama me kuma 'karancin shekaru, dole tana bukatar wani nata kusa da ita, dole zata nemi tallafawa, agaji ko kuma kalaman kwantar da hankali daga wani makusancin ta. A yanda dunia ta gurbace ma tsoro yk kar rashin gata ya sanya shari'ar tasu juyewa kar a dorwa Zaitun laifin da yasan bazata iya aikatawa ba. Cikin ransa ya ayyana lokaci yayi, lokaci yazo dole a wannan ga6ar ya neni taimako, ya nemi tallafi da saka hannu a karo na farko kaf 'din rayuwar sa zai nemi taimakon wanda ya kasance mahaifi ne agare shi ba dan kansa ba, ba dan jin dadin sa ba, ba kuma dan farin cikin sa ba sai dan Zaitun. Wannan dalili ne ya sanya batare da sanin Hajiya Talatu ba ya tafi cikin babban birnin jahar tasu ya isa ga station 'din da aka rufe su Zaitunan amma duk yadda ya buga ba'a barshi ganin ta ba dole ya ha'kura bai kuma yi mmk ba dan irin tuhunar da ake musu dole tana bukatar tsatstsauran tsaro, ba mmk ha'duwar su yanzu sai kuma a kotu. Mmn Abdul da mijin ta hatta Hajja duk abin ya ta6a su sai dai dole damuwar na wani yafi na wani, Bbn Abdul hnkln sa ya tashi sosai dan har yau har gobe yana jin Zaitun cikin zuciyar sa, amma tashin hankalin da Mmn Abdul ta shiga har zai baka mamaki, abin kamar 'yar uwar ta jinin jikin ta ya shafa, yadda ta 'daga hnklin ta ma yasa Hajja da tausayin Zaitun din ya 'dar su mata tuni tai gefe da tausayin ta fara sirfawa Mmn Abdul ruwan masifa dan har zazza6i sai da tayi sbd kuka da damuwa. Ita kanta Hajja tasan mawuyaci ne Zaitun ta aikata abinda ake zargin, amma tsana da haushin yarinyar sun riga sun gama rinjayen zuciyar ta hakan yasa tayi fatali da duk wani tunanin cewa bazata iya din ba. Hajjaju da mukarraban ta kuwa da suka gani cewa sukai Allah shi kara dai dai kenan..sosai faruwar lamarin yai musu daidai. Cikin hakan kwanakin da aka tsara na shiga kotu suka cika aka kuma shiga kotun. Zaitun ko iya daga idanu bata iyawa ta dubi mutane, yadda ma kotun ya cika makil dan sauraren shari'ar ta ina zata fara kallon su, da wani idanun ma, wara su me kyau ma bata iyawa sbd tsananin kukan azabtar da su da aka ringa yi, sau 'daya ta iya 'daga idanu ta dubi jama'ar bata 'kara ba kuma. Baya da su alkali ne zaune, mutun ne wanda duba 'daya idan kai masa zaka fahimci nagarta da iya aikin sa. Gefe da su kuma lauyoyi ne masu kare wanda ke kara da wadanda ake 'karan, yayin da nasu ya kasance lauyoyin gwabnati ne kadai zasu gwabza, tama yi mmk ganin cikin lauyoyi masu bayyana kawunan sun hadda masu kare su wai, ita mmkin ta in laifin suka yi dagasken gasken miye anfanin kare su kuma? wacce hujja za'a kare? 'Daya gefen nasu ma wasu manyan Lauyoyin ne daban suma, wanda suka amsa sunan su na lauyoyi hamshakai...wa'danda mafiya yawan su sun zo ne kawai dan saurarar karar ba dan su tofa wani abu ba. Sannan da yawa sun koka da ganin yanayin Zaitun da karancin shekarun ta. Can gefe guda kuma ga jami'an tsaro ga kuma masu tsaron Prison da kuma masu kare hakkin 'yan Adam...sai dai ba'a bar 'dan jarida ko guda shiga cikin kotun ba haka kuma ba'a bawa kowa damar 'daukan hoto ko video ba ko da a waya ne kuwa. Adam Shaheed da ya kasance a sahun farko na masu sauraron karan tun zaman sa idanun sa na kan Zaitun kur...ji yake tamkar ya zubda mata 'kwalla ganin yadda ta koma, duk ta zama wata aba daban kamar ba Zaitun da ya sani ba, wannan yarinya sassanya me tarin hankali da natsuwa, duk wanda yayi mata irin wannan sharrin bai mata adalci ba, shi kansa ma baya jin har abada zai iya yafe wa mai shi...me tayi musu har haka..? Sosai yk jin mafi tsananin tausayin ta cikin zuciyar sa, wanda sai ma a yanzu daya ganta yaji komai ya kwance masa, sabuwar kauna zazzafa da tarin tausayin ta suka sake diram masa, yana jin dole ne ma yayai wani abu, dole ya tunkari mahaifin nasa game da ita wannan karon ba da yawun kowa ba, da kansa zai je ya nemi wannan alfarmar dan ganin an ceto rayuwar Zaitun din daga fadawa wani yanayi. Lokacin da Adam Shaheed ya zurfafa a tunani ga wasu mutane abin ba haka yk ba, da yawa na Allah wadai da halayya irin ta tasu Zaitun din ne gaba daya, yayin da wasu ke fatan ayi musu hukunci mai tsanani irin wanda zai sa na baya ma su kiyaye aikata laifi irinnasu, hukuncin da zai sa su raina kansu ko da agaba bazasu sake tunanin aikata irin hakan ba. Da yawa kuma hankalin su yafi tafiya ga Zaitun suna tunanin abinda yaja hankalin ta ga irin wannan muguwar ta'asar musamman da ya kasance shekarun tane mafi karanci daga cikin shekarun masu laifin. Daga kan Hameeda shari'ar ta fara inda aka sa ta rantse ta kuma tabbatar akan zata fa'di gaskiya akan duk wata tambayar da zata biyo bayan zaman kotun, Hameeda ta rantse cikin sanyi kamar yadda aka bukata, sunan ta shekarun ta da kuma sana'ar ta, duk ta fadi...tana da aure ko bata da, adadin yaran ta..duk ta basu amsa karshe aka tambaye ta dangatakar da ke tsakanin ta da Rasheed tace mijin ta ne...tana share kwalla daga karshe. Zata sake magana lauyan ya dakatar da ita....tambayoyin shari'a suka biyo baya. Daga kan Hameeda ga Zaitun tambayoyin suka koma...itama kuma sai da ta rantse, ta kuma basu tabbacin zata fa'di iya gaskiyar ta. " Kotu na bu'katar jin sunan ki..." " Suna na Zaitun Ahmad..." Ta bashi amsa muryar ta can 'kasa, ga wanda bai san ta ba zai dauka duk tsantsan wahalar da tasha ne, amma ga wa'danda suka santa sun san cewa asali tana da sanyin magana bugu da kari kuma ga abinda ya farun ya kara saukar da ita. "..Toh Zaitun Ahmad...shekarun ki nawa.?." " Goma sha bakwai.." " Kina da aure ne..?" " a a bani da aure.." " Toh mene dangantakar ki da Dr Rasheed kamar yadda kowa yk son ji..?" Sai da ta 'dago ta dubi fuskar lauyan kafin ta sake maida idanun ta kasa ta cigaba da magana. " Dr Rasheed taimako na yayi."....ta bashi takaitaccen bayanin taimakon da yayi mata. " Idan na fahimce ki kenan daga ranar da ya taimake kin kuka ha'da kai kuka cigaba da satan dukiya da 'ya'yan al'umma...". Da sauri ta 'dago kai ta dube shi kafin ma ta furta wata kalma wani daga cikin lauyoyin ya nemi alkali ya dakatar da shi daga irin wannan tambayar domin ya zama ne tamkar cusawa wanda ake kara ra'ayin amsa laifi bisa dole. Alkali yayi na'am ya kuma ce a kiyaye. Rigar da ke jikin sa ya gyara gami da sake duban Zaitun yace..." Kafin ha'duwar ki da Dr Rasheed din har zuwa daren ranar da ya taimake ki...a ina kike rayuwa kuma meya fito dake a daren ranar?" " Yawon bara nake kuma anan titi nk rayuwa nk kwana bamu da muhalli...". Zaitun cikin ranta ta yanke shawaran fa'din hakan sbd bata so sunan kowa ya fito balle har a shigo da wata ko wani cikin irin wannan azabar da su suka sha, dan taga a bakin Hameeda aka ji sunan Dr Rasheed shima aka kawo shi. "..kika ce baku da muhalli...ke da waye kenan kike nufi ...?" Taji ya sake tambayar ta. Shiru tayi dan ita har ga Allah tsananin son ganin Mufee take bata san inda aka kaimata yarinya ba, duk yadda taji zuciyar ta ta bushe haka tuno Mufee da da tayi ya sanya hawayen ta saurin saukowa. Sai da ya sake maimaita tambayar kafin ta bashi amsa .." Ni da 'yata ne..". Da mamaki yace " 'diyar ki, kuma kince baki da aure...?" "...Erh...'yata ce kawai...". Wancan lauyan ne ya sake mi'kewa da sauri yana wa alkali ishara da cewa lauya mai tambaya yana 'ko'karin shiga hurumin da ba nasa bane cikin tambayoyin sa. Alkali yace a kiyaye. Daga haka ya barta da tambayoyin yayin da kotu ta 'dauki 'kananun surutai jin cewa Zaitun 'din har nada yarinya...dan kowa yaga karancin shekarun ta, amma jin cewa a bakin titina take kwana ya hana da yawan mutanen mamaki sai dai jimantawa da alhinin irin zamanin mu ta yanzu. Daga Zaitun Dr Rasheed aka yiwa tambayoyin kuma Alhamdulillah duk abubuwan da su Zaitun suka fa'da shima 'din haka yace sai dai abinda ya 'dauki hankalin mutane cikin amsoshin tambayoyin da akai masa, tashin farko Dr Rasheed ya bayyana sunan...... Vote Comment Share Salmerh 😘 [20/9/2022, 12:34 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* Wattpad@ Serlmerh-md 🅿️ *...23* ...... _Alhaji Jibrin Adam 'Dan- maliki_ matsayin ubangidan sa kuma me 'daukan nauyin duk wasu makaman da yake amfani da shi. Sosai kowa yy mmk, take kotun ta 'dauki surutai da kananun maganganu da 'kyar aka samu komai ya daidaita, Adam dake zaune ta gaba- gaba kusan suman zaune yayi da jin wannan furucin, ba 'karamin shiga tashin hankali yayi ba, duk da cewa baya shiga harkar sa amma ai jini ba karya bace..kuma duk inda akaje aka dawo dole dai jini yafi ruwa kauri...baya ga haka ma burin shi fa? mutumin da yake da burin samin sa kan saka hannu cikin maganar dan ya taimaka wajen wanke laifin Zaitun sai kuma yaji sunan sa...Innalillahi wa inna ilaihi raji'un..kawai yk iya maimaitawa. Karshe dole aka 'dage shari'ar har sai zuwa nan da wasu kwanaki kimanin goma sha hudu, domin sake kaurara bincike game da sabon furucin na Dr Rasheed. Hankulan jama'ah duk ya dauku ga sunan da Rasheed ya ambata, kasancewar sa wani kusa ne a gwabnati bayyananne kuma sananne ga mafiya yawan al'ummar jahar, kuma da yawa ba'a yi masa kallon gur6attace shiyasa akai matukar mamaki. Tuni an mance da zancen su Zaitun an koma kan 'Dan- maliki, dama haka jama'ah suke, abu 'kalilan ke 'daukan hankulan su ga abu haka kuma wani 'kalilan 'din ke sake juyar da hankalin su zuwa wani waje. Wannan karan wata ma'ajiya aka maida su a Prison dake babbar karamar hukumar jahar tasu...wuri mafi tsamani da muni ga jikkunan su kuma illa ga numfashi da lafiyar su. Irin kukan da Zaitun tayi ranar baya ta6a misaltuwa, tayi kuka kuka me tsamanin gaske, ganin kwanakin shan wahalar tasu a kullun da'da yin gaba yake yi bbu kuma alamun sassautawa balle suyi tunanin 'dan lokaci ne. Kullun sassauci baya zuwan musu sai dai tsanani... Haka kawai in tana zaune sai kaji tana fa'din" Allah! Yah Allah!!, Yah Malikal mulk Yah Zuljalal wal ikhram...tsabar yadda damuwar ta takai ma'kura sai ta rasa mai ma zata furta ne, me zata roki ubangiji yayi mata a wannan halin, kawai sai ta saki kuka me karya zuciya mai azabtar da ruhi da gangar jiki, ita ka'dai tasan halin da zuciyar ta take ciki...wai ita ce yau a prison, itace tayi zaman cell tsawon kwanaki itace akai ta jiba bisa tuhuma akan laifin da ko cikin mafarki bata fatan ta tsinci kanta a ciki balle a zahori, itace yau dubban al'umma ke mata kallon mai laifi, itace ake shari'ah da ita a kotu da bata tunanin ya wanzu a doran 'kasa ba, itace itace abin da yawa fa...hakan kadai idan ta tuna yakan yi mata zafi matuka, zafi ma me kona zucia.... Abu biyu ke mata kai kawo, bata san inda Mufeeda take ba bata kuma san wa zata tambaya game da yarinyar ba, dan rashin ganin Mufeeda shine ya sake ta'azzara yanayin da take ciki. Kamar almara kamar a mafarki abubuwan ke ta faruwa mata daki- daki duk cikin kankanin lokaci. Cikin kalilan 'din watanni ta tsinci kanta a waurare da kuma yanayi daban- daban wa'danda ko cikin tarihi bata ta6a jin su ba iya tsawon shekarun ta na dunia, bata ta6a tunanin faruwar haka ga rayuwar ta ba, shekara 'daya tak baya in ance mata zata fuskanci wadannan abubuwa bugan kirji zata yi ta karya ta amma abin mamaki sai ga shi karshen ta ma yau ga inda kaddara ta jefo da ita. Ta kuma rasa shin waye me laifin, iyayen ta ne ko kuma ita? ko kuma Mufeeda. Shin Iyayen ta da suka kasa rike ta sbd kaddarar data same ta ne ke da laifin ko kuma ita da ta kar6i kaddarar tata ta rungume hannu biyu..?" Haka suka cigaba da kwana cikin prison 'din, basu da banbanci da dabbobi, domin kowa baya musu kallon arziki, kowa kallon su yake kamar ba 'yan Adam da Allah da kansa ya karrama su ba. Kafin cikar kwanaki Sha hudun nan Zaitun sun koma sai 'kashi idan ka dube su, banda katon kai babu komai, duhu sosai suka yi suka jeme, ba ma kamar Hameeda da ake 'dan 'kara gyara jikin da lafiyayyan mayuka da supplements tsadaddu, yanzu da ya kasance babu shi komawa tayi kamar wata Hameeda ta daban. Tuni ta mance da 'kiyayyar da take faman yiwa Zaitun 'din dan yanzu ta koma mata ne kamar 'yar uwa.. lokuta da dama Zaitun din ta fita kwarin zuciya da ma dauriya, domin ita tun asali Zaitun a wahala ta taso...sau kusan uky ana kai Hameeda asbiti ana dawo da ita sbd cutuka da suka tasammata haikan kamar bazasu barta ba, tuni jinin ta ya hau, Ulcer ga zazzafar Maleria sakamakon mummunan cizon sauro da suke sha, yayin da aka kai Zaitun sau daya tak dan itama malerian bai barta ba...dalilin ma kenan da ya kara lalata mata kamanni, in dai ba sanin Zaitun kayi ba bazaka ta6a gane ta ba, sosai ramar ta fito fili. Tun farko Zaitun yarinya ce kyakykyawa da duban farko idan kayi mata ba sai ka kara ba zaka san cewa ita din kyakykyawa ce. Wani kyau ne da ita mai sanyi da shiga zuciya, idan kuma kai mata duba na fahimta zaka fahimci cewa komai daya dangance ta me kyau ne, ga tarin nutsuwa da Allah ya bata, in badan muguwar 'kaddara data fa'da mata ba Zaitun mace ce har mace, ta kasance me matsaikacin tsawo, round face mai 'dauke da dara daran idanu, eye lashes mikakku gazar gazar haka suke, fuskar ta na dauke da karamin baki gwanin birgewa...tana da yalwar gashi daidai gwargwado wanda kana iya ganin yanda yake kwance luf saman goshin ta da..sai dai bata cika fari sosai ba. Yanzu duk ba wannan Zaitun 'din wata ce ta daban zaka gani, wata siririya me tsayi, sbd ramar da tayi fuskar ta dake round ta 'yar koma karama goshin ta ya 'kara fitowa kaitsaye zaka iya kiran ta da me baby face sai hancin ta daya kara fitowa sosai..sai dai ban da ramar a har yanzun ta me kyau ce ita. Ko a wannan jigila cikin 'yan sanda hare haren masu akuyancin halin da yawa ta tsallake cikin kariyar ubangiji kuma har kawo yau da take Prison 'din basu daina kawo mata hari ba. ***** Mufeeda kam na can wajen mahaifiyar Rasheed tare da sauran yaran sa, da kyar ta saba zama da su, da fari tasha kuka sosai, da kyar take cin abinci su Zabba'u da su Wildan ne sukai ta kokarin bata kulawa da jan ta a jiki har ta dan saki jiki da su sai dai ba sosai ba, abu guda dake kara ta azzara rashin sakewar ta ya hana ta sukuni shine mage da suke da ita a gidan, Mufeeda bata son mage, jikin ta baya so kuma har zuciyar ta, dan bayan firgici da take shiga idan taga magen, gashin jikin ta ma duk sai ya wani mimmike wani abu rudu- rudu ya fito kan fatar ta kamar gurbin cizon wasu kwari. Akwai ranar da magen tazo jikin ta Mufeeda ko kuka kasawa tai kawai ta sume a wajen. Fahimtar abinda ke sata cikin wannan yanayin da Hajiyar Rasheed tayi batare da tunanin komai ba tasa aka dauke magen aka killace ta, dan acewar ta ita ta kar6o yarinyar bai kuma kamata tayi watsi da lafiyar ta ba tunda zama ne na 'dan lokaci zasu yi, ranar da suka rabu sai su fito da abar su ta cigaba da rayuwa kamar da. Tun da aka killace magen kuwa Mufeeda bata sake shiga wani yanayi ba, sai dai kewar Zaitun da take faman yi duk da kuwa karancin wayo da take da shi hkn bai sa ta mance da ita ba...sau tari ko tana bacci takance" Mammi..!" Duk sun san wa take nufi dan hk kawai sai dai su tausaya mata, musamman Hajiyar Rasheed da tasan cewa 'dan tane silar koma menene..sosai take tausayawa rayuwar su gaba 'daya. ***** Ranar da akai komawa kotu ta biyu a ranar idanun Zaitun suka yi arba da Alhaji Jibrin 'dan Maliki, bata yi mamaki ba duk da yake bata wani tsaya kare masa kallo har na sosai ba, amma iya fuskar sa da ta yiwa kallo daya ta fahimci 'yar kama da suke yi da Adam duk da kamar ba wata sosai bace dan yafi 'daukan kamar mahaifiyar sa ne kamar yadda ya ta6a sanar da ita..amma a hakan ma jini ba wasa bane duk wanda ya san Adam ya kuma ga Alhajin zai ga 'yar kama...kenan dagaske mahaifin nasa ne kamar yadda Hajiya Talatu ta ta6a sanar da ita. Ranar kam Adam Shaheed bai je kotun ba dan bazai iya juran ganin mace mafi soyuwa aransa da wanda yake matsayin mahaifi agaresa bisa tuhuma iri guda ba...bayan duk wani shirin da yayi na taimakon ta ya rushe toh me zai je kotun kuma yy mata ban da karawa zuciyar sa nauyi. Haka akai ta fafata shari'ar amma ba'a karashe ta ba aka sake saka wata rana daban da za'a yanke hukunci wanda ya kama nan da kwana ki bakwai masu zuwa cewar alkali. Da yawan mutane basu so hakn ba, hakama wadanda ake shari'ar da su, in ka dauke 'Dan maliki da shi kam dama bai shirya kar6ar hukuncin sa aranar ba, gani yake kamar akwai mafita akwai yadda za'a yi ya zillewa shari'ar batare da hukunci ya hau kansa ba shiyasa yaji dadi sosai da aka dage shari'ar. Yayin da 6angaren alkali ya kasance yayi ne sbd wasu 'yan bincike da ya kamata a karasar da kuma tabbatar da kwarrarun shaidu. Da wannan damar Dr Rasheed yayi amfani ya bayyana wata 'dauka daya yi bada jimawa ba, shi kansa a lokacin bai san dalilin yin daukar ba amma haka kawai yaji zuciyar ta amince masa da yi awata zama da sukayi shi da 'Dan Malikin kwanaki kalilan baya...kuma sun yi zaman ne bisa kokarin fadada harkar tasu izuwa ga babban matsayi wanda zai fi kawo musu ku'di maku'dai yayin da ga al'umma kuma zai kasance ne mafi tsananin tashin hankli sai dai Allah cikin ikon sa basu kai ga ida nufin su ba asirin su ya tonu. Duk shaidar da Dr Rasheed ya bayar tabbatattu ne masu matukar tasiri, shiyasa ma ba awani sha wahalar bin ba'asi ba, dan hatta da sautin murya wadda yake 'dauka ta waya duk suna nan...sai ma wasu muggan halaye na 'Dan Malikin da suka sake bayyana karara wanda ba kowa ne ya sansu ba. Bakaramar nadama Rasheed yy ba, sosai yy nadamar mummunan zuciya da halayyar sa wadda suka riga suka bi jinin jikin sa batare da ya ta6a tunanin makomar sa ba, yau gashi wannan banzan halin yy sanadin mutuwar dukkan wani farin ciki nasa na rayuwa, ya kuma yi sanadin kashe duk wani walwala da farin cikin ahalin sa, uwa uba kisan mummuke da ya yiwa wata sabuwar ajiya da ya yiwa zuciyar sa da shikan sa bai gama tantance matsayin da yake kai ba. Ya ci buri ba 'karama ba kan sabuwar soyayyar da ya tabbatar yake yiwa Zaitun ashe duk zasu tashi ne tamkar tashin tsuntsaye ba tare da komai da ya ci buri sun kammala ba batare da guda cikin burin sa ya kai ga cika ba...gaba 'daya komai ya tsaya matsa cak, duk da yasan abu ne mawuyaci Zaitun din ta kar6e shi cikin sauki, but ya jima yana tsara yanda komai zai tafi masa yadda ya dace ashe saka yake yana warwarewa daga baya batare da ya sani ba. Kana naka ne Allah na nashi, a yanzu kam gaba 'daya ya saduda, ya kuma tabbatar Allah shike da ikon yin duk abinda yk so duk kuma abinda ya ga dama, sosai ya kara jin tausayin Zaitun bayan duk sun ji abinda Hameeda ta fada, domin bata 6oye duk nata shirin ba ta bayyanawa kotu, ita kanta Zaitun tayi mamaki sosai, ashe da hakan be faru bama wata ukubar akayi niyyan jefata a ciki, hakika Allah maji roko ne baya kuma zalunci sai gashi duk 'din su bau tsallake nasa shirin ba. Bata ji haushin Hameeda ba kamar yadda Rasheed ma bai ji haushin ta ba, wala Alah faruwar hakan shine mafi dacewa ga Zaotun, da badan faruwar abinda ya faru ba, dabadan shirin Hameeda na 6atar da ita 'din suka fito har aka kama su ba kila da tuni ta 6atar da Zaitunan, da tuni ta shafe babin ta a idanun sa, da tuni ta bar shi da tabon zucin da bai san ranar da zai goge agare shi ba. Da hakan ya faru kuwa wata dama Allah ya bashi, amma ba zai bi kowa da sharri ba, zai yi amfani da wannan damar da sakawa duk din su da alkhairi gwargwadon iyawar sa bazai yadda ya sake cutar da kowa ba...idan ya wanke laifukan su yasan kotu zata sallame su zaku tafi kowa zai yi hanyar sa ne, Zaitun zata rabu da Hameeda ta yadda babu wanda zai sake tunanin cutar da 'dan uwan sa cikin su, ba mamaki rabuwar su ma ta kasance rabuwa ce ta har abada. Yanzu kam bashi kuma da wani buri a rayuwar sa illah kawai yaga ya kar6i hikuncin sa daidai da abinda ya aikata. Ranar zaman kotun da ya kasance na karshe, kuma shari'ah ta karshe da za'a gabatar a ranar, a kuma ranar Dr Rasheed ya tabbatarwa kotun cewa Zaitun da Hameeda basu da hannu kuma basu san komai da ke faruwa kan lamarin ba, sai dai duk yadda kotu ta so bincike da gano sauran abokan harkar tasa Dr Rasheed bai bar kofa ba. Haka dole badan kotu taso ba ta yanke musu hukunci shi da 'Dan Malliki bisa tsari na na dokar kasa. Kafin atashi a zaman kotun ma aka sanar da dakatar da aikin asbiti da aka yiwa Dr Rasheed shima bisa tsatstsauran dokar takaddun sa bazasu sake yin aiki karkashin kowace ma'aikata ba daga ta gwabnati har wadda ma ba gwabnatin ba. Wannan shar'iar ta matukar daukar hankalin dubban mutane kowa na mamaki kan yadda zuciyoyi ya gur6ace kan tara dukiya kadai, inda Allah ya taimaki Dr Rasheed ma bai ta6a 'daukan ran kowa ba duk wasu furuci da yk yi duk burga ce kawai sbd ya tsoratar amma ba wai dan ya ta6a yin kisan ba, wannan dalilin ne ya sa kotu ta yanke masa shekaru ashirin gidan yari batare da aikin wahala ba dan bai wahal da shari'a ba, yayin da shi jagaban aka yanke masa shekaru ashirin da biyar. Daga 'karshe kotu ta sallami Zaitun da Hameeda ta kuma wanke su kan cewa basu da laifin komai, Dr Basheer ne ya nemi iznin kotu inda yayi amfani da wannan damar ya nemi yafiyar Zaitun da Hameeda bisa wahalhalun da suka sha sanadin sa ba tare da hakkin su ba. Sai a lokacin Zaitun taji wani 6angare na damuwar dake cikin zuciyar ta ya zagwanye...tsabar farin ciki ma sulalewa tayi a wajen kawai tana sakin kukan farin ciki me ta6a zuciya, bata da kowa, bata da wani da zai zo ya rungume ta kamar yadda taga an baibaye Hameeda ana ta koke koke da farin cikin wanke ta da kotu ta yi. Sosai take jin kewa na shigan ta ta kowani 6angare , tasan ba ahali ta rasa ba, ba masu kaunar ta ta rasa ba, ba kuma wa'danda zasu koka da al'amuran ta ta rasa ba, amma yau 'din sai take jin daban, haka kawai take so itama ta samu majingina, tana so taga me taya ta farin ciki da wannan rana. Yah Bukar! Tasan ya mata nisa. Mahaifiyar ta ma haka. Mahaifin ta tasan yafi karfin shirmen ta tun asali. Adam Shaheed...shine ya fado mata amma tasan bazai zo ba, bazai ta6a zuwa ya tayata farin ciki ba alhali ana kokarin kulle mahaifin sa a magar'kama. Comment Vote Share Salmerh😘 [20/9/2022, 12:34 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* Wattpad@ Serlmerh-md 🅿️ *...25* .....A hankali ya sau'ke labilen windon 'dakin nasa yana sakin 'karamar ajiyan numfashi wacce zahiri a hakan zaka iya kiran ta amma a badini shi ka'dai ya san zafin da hakan yake masa a kirji da cikin zuciya, rabon da yayi farin ciki da wahala tun rabuwar sa da Zaitun na farko, raban da aga cikakkiyar fara'a kan fuskar sa koda ta ya'ke ce tun ranar da yaji sunan wanda mahaifi yake gareshi a kotu matsayin shugaba kuma mai 'daukan nauyin ta'addanci, duk da yake ba wata kwakkwarar ala'ka ko shakuwa ke tsakanin su ba amma sosai abin ya dame sa ya kuma tsaye masa a zucia..wannan kalma ta iyaye mahaifi da mahaifiya ba 'karamin tasiri suke da shi azuciyar kowani halitta ba, duk yadda yakai ga tsanar halayyar mahaifin nasa amma deep down yana jin kauna da kewar rashin shakuwa dake tsakanin su, sai dai munanan halayen mahaifin nasa su suka han komai yin tasiri game da shi. Gaba 'daya sai ma ya kuma ji mutumin ya sake fice masa aka, musamman da ya kasance dalilin damuwar halayyar sa yasa ya sake rasa damar ganawa da Zaitun a karo na biyu, meyasa a ko wani lokaci da gi6i yake barin zuciyar sa ne? meyasa koda wani lokaci rashin nasara ke gilmawa tsakanin sa da mahaifin nasa? meyasa son zuciya da son kansa sukai masa yawa? meyasa sam bashi da tausayi cikin zuciyar sa? meyasa, meyasa abubuwa da dama? Idanu ya lumshe fahimtar da yayi cewa hawaye ke bin fuskar sa, aikin kenan, abinda a mafi yawan lokuta ke faruwa matukar haduwa ta hada shi da mahaifin nasa shine zubda kwalla, kusan a kaf 'din rayuwar sa mahaifin nasa shine mutun na farko da ya kasance me sashi zubar da kwalla, in dai kaga Adam na hawaye toh yaci karo ne da takaicin 'daya daga cikin halayyar mahaifin sa dalili kenan da ya sa a mafi yawan lokuta yake kalubalantar ha'duwa da shi. Akan mutun me irin wannan 'dabi'a shine Hajiya zata yi iya bu'dan baki har tayi tutiya da alfahari dan sun kasance makusantan sa?, shin mancewa Hajiya tayi ne da wuri haka? Xuciyar sa ke zayyano masa wannan tambayar yana dafe da kansa. Mutun irin wannan shine Hajiya take kafa hujja dashi cike da ya'kini ta shiga tsakanin sa da Zaitun a wani dalili...? Sam bai san ma miye ya canza Hajiyar tasa har haka ba, ba mamaki kwata- kwata ta mance ne da waye asalin Jibrin 'Dan Maliki a gareta, may be ta mance ba'kin cikin da ya dasawa zuciyar ta abaya. Da bayan yatsar hannun sa manuniya ya 'dauke 'kwallan da ke bin idanun sa yana me zama bakin gadon sa ha'de da lumshe idanu...tunanin rayuwar sa ta baya ya fara dawo masa cikin kwakwalwa. ~~~~Cikakken sunan sa shine _Adam Shaheed Jibrin 'Dan- Maliki_ , ya kasance 'da kwara 'daya tilo ga mahaifin sa da ake kira 'Dan Maliki tun zamanin kuruciya, shi kadai kuma ya mallaka a fa'din duniya baki 'daya, duk da yake bai taso gaban mahaifiyar sa ba amma bai ta6a kokawa saboda rashin gata ko kan wani abin ba, hasalima bai taso yaga mahaifiyar sa ba sai dai a photo, bai ta6a jin sautin muryar ta ba sanadiyyan rasuwa da tayi tun bayan da ta haife shi duniya tace ga garinku nan. Yana taso ne gaban makwafi agare ta, domin bayan dangataka ta jini akwai tarin kama 'kak'karfa tsakanin mahaifiyar sa da Hajiya Talatu. Hafsat macece mai tarin ilimi, hakuri, natsuwa da nagarta, ta kasance 'kanwa ga Hajiya Talatu wanda su biyu kacal iyayen su suka haifa kafin su bar dunia, sun kuma koma ga mahaliccin su sanadiyyar ambaliyar ruwa da ya afka da su a wasu shekaru can baya wanda a lokacin Hafsat da yayar ta sunje hutu wajen wani Baffan su ne wato 'kanin mahaifin su kafin dawowar su ne lamarin ya auku. Sun yi kuka sun kuma shiga damuwa gami da tsananin alhini saboda rashin mahaifan nasu amma daga baya duk suka dangana suka fawwalawa Allah komai, haka suka cigaba da rayuwa cikin maraicin uwa da uba, sun ga kalubale da dama wajen dangin su saboda mahaifin su asali ba wadata bane dashi sosai amma akwai cikakkiyar wadatar zuci, basu gaji komai daga mahaifin nasu ba sai gona guda 'daya sai dai tana da girma ba laifi. Basu tashi sanin basu da cikakkiyar gata ba sai da suka rasa mahaifan nasu aka kuma rasa cikakken wanda zai kar6e su da hannu bibbiyu ya rike su ya kuma basu gata da kulawa, 'karshe karatu ma gagarar su tayi saboda rashin wanda ze biya musu kudin makarantar, haka kuma batun gonar mahaifin su ma basu samu cikakken bayani akan ta ba. Lokacin da Hajiya Talatu tayi auren ta na farko tare da Hafsat ta fara zama domin a cewar ta hankalin ta zai fi kwanciya ne idan tana ganin Hafsat din tare da ita, ta bayyana hkn ne kawai amma ita ka'dai cikin zuciyar ta tasan dalilin ta, irin dabdalar da akayi wajen aurar da itan kadai yafi tsaya mata a zuciya, wadanda suke gani sune jigo agaresun da kyar suka hada suka sama mata kayan dakin da suka aurar da ita bayan an sha gwagwarmaya da kai kawo, har da su fa'dace fa'dace sbd rarrabuwar kai da aka samu, a lokacin wata zuciyar har na zuga ta kan kawai ta fasa auren ma gaba 'daya, Hafsat ce ta ringa tausan ta da ban baki har aka kammala komai aka mi'ka ta da'kin ta komai sai a hankali, a fili zaka fahimci cewa maraici da rashin gata na tattare da rayuwar ta karara, cikin sa'a kuma sai Allah ya bata miji me kaunar ta da fahimta bashi da tashin hankali. Wannan dalilin yasa taji sam bazata iya barin 'yar uwar ta cigaba da zama tare dasu ba zata rike ta gaban ta har zuwa lkcn da itama Allah zai bata mijin aure domin tozarcin da akayi mata ma ka'dai ya isa, bazata juri ganin na 'yar uwarta a nan gaba ba. Allah cikin ikon sa sai ba'a jima ba itama Hafsat batun auren ta ya taso dan already dama ta zama budurwa matashiya, ko lokacin auren kuwa Hajiya Talatu taso ta nuna kin amincewar ta sakamakon shaidar rashin halin kwarai da aka yiwa manemin nata Jibrin 'dan Maliki, amma Hafsat ta nuna tirjiya da zallar kaunar da take yi masa ga yayar tata, a lokacin kwata- kwata shekarun ta basu fi goma sha shida zuwa sha bakwai ba, amma hakan be sa ta zama me ragaggen tunani ba, ba tsananin so ba ne ba kuma kauna kakkarfa ba, ba wai ta 'kagu tayi aure bane, ba kuma gajiya tayi da zama da 'yar uwarta tata ba, kawai gani take kamar tsarin zaman nasu be mata ba, so take ta basu fili su sarara suma a gidan auren su, musamman ma shi mijin 'yar uwar ta ta, mutun ne mai tsananin sanyin halayya hakuri da kawaici, bai fiye nuna gajiyawar sa kan abu a zahiri ba, wannan dalili ya sanya take gani kamar koda tana takurashi bazai nuna ba, koda tana hana shi sakewa cikin gidan sa bazai ta6a nunawa ba, dan duk abinda 'yar uwar tan ke so shima mara mata baya yake, sosai yake tsananin tausayawa maraicin su so bata so su kure shi. Shiyasa ta yanke shawarar kawai zata yi auren, batare kuma da dogon nazari ko mikawa Allah za6i ba kawai ta kafe kai da fata tace ita dai sai shi, cikar burinta kawai ne agaban ta a lkcn ba komai ba. Ganin ta dage kamar yadda Talatu ta kafe kan dokin naki ne ya sa mijin nata da kansa sanya baki cikin lamarin, zama yayi dasu suka yi magana ta fahimta 'karshe dole yasa Hajiya Talatu amincewa da batun auren amma ba wai a son ranta ba dan baya ga halayyar sa da aka kushe haka kawai ma tana ganin cewar shi din ba sa'an auren Hafsat 'din bane sbd tazarar shekaru dake tsakanin su dan ko a lokacin shekarun sa zasu ninka na Hafsat 'din har sau biyu, bugu da kari wayewar sa ta banbanta da ta Hafsat, yafi ta wayewa da gogewar rayuwa nesa ba kusa ba, a ganin ta mace wayayya wacce tasan rayuwa sosai ita tafi dacewa da shi ba 'yar uwarta Hafsat ba, tsoro take ji kar 'yar uwarta ta cutu. Sai dai ba laifi shima Jibrin ya nuna mata kauna ya kuma nuna bajintar sa tun da aka fara batun auren har zuwa lokacin da aka sada Hafsat da 'dakin mijin ta ko sau 'daya bai nuna wani hali da za'a zage sa da shi ba, bai kuma bar 'kofar da wani zargi zai bayyana da za'a iya tuhumar sa da shi ba, ba laifi itama Talatu sai taji hankalin ta ya 'dan kwanta da auren Hafsat 'din. Sai dai abin mamaki Hafsat bata cika sati hudu 'kwarara a gidan sa ba ta fara fuskantar wasu 'kalubale, in da ta fara cin karo da wasu abubuwa da ta kasa fahimtar inda suka dosa, ya kan dawo gidan cike da maye ya zube mata a parlour, tana zuwa kusa dashi idan ya ganta sai yace ta bashi ruwa da zarar yasha ruwan kuma sai ya fara sheka amai daga nan bacci. Haka zata tsaftace wajen tana yi tana kuka, washegari idan ya tashi ya gansa a wajen kuma in bata yi sa'a ba sai tasha jigba ranar da ta taki sa'a ne yake tsayawa a mari ka'dai, duk wai dan me yasa bata tashe shi ba ta barshi ya kwana parlor ko 'saman tiles. Ita kam rasa abin cewa ma take yi sai kuka, toh me zatace dashi, da kansa yasan ba iya 'dagasa zata yi ba, sannan a wancan hali da yk ciki ko ta tashe shi ba lallai tashin zai yi ba. Hafsat ta juri abubuwa da dama tattare da Jibrin, haka zai zauna mata a Palor ya dinga zu'kan tabar sa sai yashaki iya son ransa sannan ya bar gidan ita zata tattare sauran tana kukan takaici, bata son warin taban amma bata isa tayi 'korafi ba sai tasha jibga. Sai yanzu ta fahimci abinda tun farko yayarta Talatu take mata ishara akan su amma zuciyar ta ta lullu6a ga cikar burin ta ta kasa gani. Tasani bata mai da hankali wajen za6en abokin rayuwa ba, haka kuma bata dace da samun nagartacce ba, wannan dalilin ya sanya ta fara kai kukan ta ga mahalicci akan ya shirya mata shi, bataso yaran da zata haifa su taso su tarar da shi da wannan halayyar balle har su tuhume ta da rashin za6a musu uba nagari da batayi ba, dan tasan koda basu tuhume ta da tambaya ba dole cikin zuciyar su suji bb dadi. Koda wasa bata ta6a sanar da yayarta wannan lamari ba a kullun tunanin ta shine zai canza wataran, dole zai san ba daidai yake aikatawa ba ya kuma yi nadamar komai. Wataran idan Jibrin ya bar gida tun safe in ya ga dama bazai dawo mata ba sai tsakiyar dare, wataran ma ba ya dawowa gidan kwata- kwata, ba zai kuma 'kira ya fa'da mata uzurin sa ba gudun kar ta tashi hankalin ta ba..ba ruwan sa da wannan, idan kuma ita ta kira 'din bazai 'daga wayar ba sai yaga dama, in taci sa'a ya 'daga ma masife ta yake da cewar tana damin sa aiki ne ya rike shi...hmm wai aiki har tsakiyar dare. Takaici baya barin ta yin bacci, in ta taki sa'a ya dawo gidan washegari ma ta kanci karo ne da abu biyu zuwa uku, inma yazo mata a buge tatul inma kuma yazo da budurwa su shige 'dakin sa har sai ta kwammaci dama bai dawo gidan ba yafi mata, haka zata 'kara kwana cikin wani zullumin tana kuka, in ta taki tsananin sa'a ne yake dawo mata normal batare da yasha komai ba, in kuwa ta nemi su tattauna zancen ya kan tsatstsare ta ko kuma a takaice ya ce aiki ne yake masa yawa shi kuma yake hanasa dawowa kan lokaci, dole bata da tacewa. A kuma 'dan tsakankanin ne ta fahimci Jibrin yana tu'ammali da wasu 6ata gari, hk zai kawo su gidan suyi mata 'da'd'daya a palor yasa tayi ta musu hidima ko kishinta ma baya nunawa sam. Hankalin Hafsat ba 'karamin tashi yayi ba data fahimci hakan gashi a lokacin Talatu sun tafi aikin Hajji da mijin ta. Haka tai ta rike damuwar ta bata ta6a fa'dawa kowa ba, haka ko makwabtan ta bata bari sun fahimci komai ba duk kuwa da zumuncin dake tsakanin su. Lokacin da Talatu suka dawo kafin nan kuwa duk Hafsat ta 'kare ta lalace sai haske ka'dai da ta 'kara, a lokacin da taje gaishe ta da barkan dawowar su a sannan ta sanar da ita bayan tambayar da Talatun tai mata na dalilin ramar ta, abin nema yake yafi karfin ta gaba 'daya tsabar 6acin rai bata ma san lokacin da ta kunce mata komai ba, duk wasu abubuwan da ta dade tana 6oyewa tsab ta sanar da ita, amma abin mamaki sai Talatu ta 'kara mata zafi, duk wasu takaicin ta na lokacin auren sai a nan ta samu ta huce su, duk bakin cikin da ta kunsa na dagewa da auren da Hafsat tayi tun a farko tsab ta zazzage su, tana yi tana kuka haka Hafsat ma na kuka, 'karshe suka rungume junan su suka cigaba da kukan a hk..amma har Hafsat ta koma bata iya ta tanka kan batun ba. Sai daga baya da ta huce gaba 'daya ta kuma fahimci damuwar Hafsat 'din kullun gaba yake ba raguwa ba sannan ta shiga lamarin sosai gashi ma laulayi ya sako Hafsat 'din gaba gadan gadan tsoron ta kar abin yazo yai mata yawa har ya kai ga illatata, duk da yake ba 'karamin farin ciki tayi da samun cikin Hafsat din ba amma tsanar da ta yiwa Jibrin yasha gaban komai. Bata da matsalar komai a gidan auren ta, irin nustuwa da kwanciyar hankalin da take ciki gidan mijin ta sau tari ta kanyi tunanin da ana rabawa da tabbas sai ta raba ta bawa 'yar uwar ta rabi da quartern sa, amma hakan ba me yiyuwa bane sam, abu 'daya da Allah ya hana ta cikin rayuwar auren ta shine haihuwa, kuma bata cire rai da samun sa ba shima 'din dan ita akaran kanta ma ta jima tana son ta samu ciki ban da maigidan ta da 'yan uwan sa da suka fita damuwa amma har a lokacin Allah bai basu ba, sai ga Hafsat daga yin auren ta lokaci kankani ya azurta da samun ciki bayan ko cikakkiyar nutsuwa bata samu gidan auren ba ma. A kan zuciyar ta take jin Hafsat dan ita ka'dai ce danginta take ji a kaf fa'din rayuwa, kauna da burin ganin farin cikin Hafsat shine mura'din ta a ko wani lokaci, ace kuma yau ga wannan Hafsat 'din 'dauke da ciki a jikin ta bata jin akwai wanda zai kaita kaunar cikin nan koda kuwa mahaifin cikin ne. Son dunia Hjy.Talatu ta 'dora wa cikin nan kamar a jikin ta yake, banda tausayin Hafsat din daya sake cika mata kirji, tana ji dole ne a wannan ga6ar tayi wani abu dole ne ta tsayawa Hafsat wajen ganin ta samu 'yan cin ta, bazata sake bari Jibrin ya cutar mata da 'yar uwa ta kyale ba, duk yadda taso 6oye kauna da farin cikin bayyanar cikin Hafsat din sbd tsanar halin Jibrin amma kasa jurewa tayi. Manya ta ha'da da maigidan ta da yake babban mutun ne shi mai kuma dattako ta ha'da da manya daga cikin dangin mahaifan su inda ta sanar da su halin da Hafsat take ciki. An zauna da Jibrin an yi masa fa'da an kuma nuna masa kuskuren sa ya amince tamkar gaske ya kuma basu haku'ri gaba 'daya, hatta ita Hafsat din sai da ya bata hakuri da kansa batare da wani yace ba, amma suna dawowa gida ya kama Hafsat ya jibga son ransa ya mata dukan tsiya, dukan da yasa hatta cikin jikin ta sai da ya fita duk wai sbd karar san da takai. Hajiya Talatu ba 'karamin bakin ciki tayi da faruwar lamarin ba taci alwashin sai ta kai 'karar sa ga hukuma a hukunta sa amma maigidan ta ya hana ta, acewar sa tsakanin mata da miji ba'a shiga, ciki kuma Allah ke bada shi idan yaso zai 'kara basu wani aduk lkcn da yaga dama, batun duka ne dai sai da aka sake masa magana dan sai da Hafsat tayi sati kwance a gadon asbiti kafin ta 'dan warware..kowa baiji da'din lamarin ba. Daga asbiti Hajiya Talatu gidan ta ta wuce da ita wasa-wasa sai da Hafsat ta shafe watanni hudu bata koma gidan ta ba, duk yadda Jibrin ya nuna damuwar sa Hajiya Talatu kallo bai ishe ta ba, karshe mijinta ne da Jibrin ya biyo ta hannun sa ya sa dole badan ta so ba ta maida Hafsat 'din 'dakin amma da 'kwakkwarar kashedi ga Jibrin ya kuma amince. Comment Share Vote Salmerh😘 [20/9/2022, 12:34 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* Wattpad@ Serlmerh-md 🅿️ *...24* .......Kafa'dar ta taji an dafe daga bayan ta tayi saurin 'daga kai sbd tsoro, nan tai arba da Mufeeda, Mufeedan ta rike a hannun wata babbar mace da bata san ko wace ita ba, murmushi take yi da ganin yarinyar amma idanun ta na zubda 'kwalla, yau ga ta ga Mufeeda suna yiwa juna kallon kallo, bayan tsawon wasu kwanaki wadanda suka kasnce mafi tsananin muni daga cikin rayuwar ta. Hannu Mufeeda ta mika mata tamkar wacce ta tuno wani abin tana fa'din"..Mammi...". Da sauri Zaitun ta 'dago nata hannayen ta amshi yarinyar da duka ta taho gare ta tana washe mata baki. Ita canzawar yarinyar ne ma ya bata mamaki sosai, kokadan bata ga abin da zata ce bai yi ba game da yarinyar. Garin kar6ar Mufeeda ne idanun ta suka yi arba da Zabba'u da Zaleeha tsaye abayan matar, Zaitun sai ta dan kalle su sannan ta dubi matar. Dukkan su kuka suke yi kuma tasan kukan bana komai bane face na tausayin 'dan uwan su, aikin shai'dan kenan da kuma sharrin biyewa son zuciya, baya ga haka ga shi da yan uwa masu tsananin kaunar sa, ga mahaifiyar sa mace nagartacciya ga innocent yaran sa masu so da kaunar sa amma ya lalata musu sunan ahali...ya barwa yaran sa tabon da har su mutu bazai goge a garesu ba. _Yah Ubangiji Allah ka raba mu da son zuciya...kasa mufi karfin zuciyar mu cikin dukkan wani tsanani na rayuwa._ Mahaifiyar Rasheed ta nemi su koma gidan su da Zaitun amma taki amincewa, dan ita yanzu ba wannan bane burin ta, taya ma za ai ta iya ra6ar wani daga cikin ahalin Rasheed, sosai ta yadda da kaddara amma bazata sake kuskuren jefa kanta cikin wata damuwar ba, bazata yadda ta bada gudummawar faruwan kuskure makamancin wanda ta tsallake da 'kyar ba. Dan hk sai tabawa Hajiyar Rasheed ha'kuri, ta bawa su Zabba'u ma ha'kuri dan tasan sune zasu sa Hajiyan cewa ta roke ta, tana san suna kaunar ta amma bazata iya sake rayuwa tare da duk wani abu daya dangance su ba, bazata iya bin su ba. Sun so takura mata amma mahaifiyar su ta dakatar da su, acewar ta su barta ba dadi tun bata ra'ayi ba dole bane sai ta zauna da su, ita aganin ta Zaitun din ma tayi tunani, domin zama tare da sun din bazai bar abin ya 6ace mata a zuciya cikin sau'ki ba, gara tayi nesa da su. Ita Zaitun din ma akaran kanta yanzu bata bu'katar taimakon kowa bata so ta sake ra6ar jikin kowa bata bukatar tallafin kowa cikin rayuwar ta, in kuwa ya kasance dole ne toh gara cikin biyu tayi abu da'ya.... Daga 'karshe kayan ta dake leda tun wanda ranar ta fito da su su ta gani sun mi'ka mata ba da son ran su ba, sosai tayi farin ciki da ganin kayan bayan duk gwagwarmayar da ta sha ashe kayan ta nan nan...daga haka sukai mata sallama suka yi gaba tana kuka suna kuka, kowa abinda ke zuciyar sa daban. Mufeeda dake hannun ta ta sake rungumewa tamkar wacce za'a 'kwace mata ita, dagaske tana jin kanta wata iri ne yanzu, tana jin kamar she is no more that Zaitun da ta sha gwagwarmaya abaya, dole ta canza musu salon rayuwa dole ne ta za6i abu guda cikin rayuwar ta, a yanzu tana jin zata iya fuskantar koma menene ya tunkaro ta, tana jin cikin ranta tamkar bata shakkar kowa..dan haka dole tabi za6in da zuciyar ta tai mata game da rayiwar su. Jin kamar tsayuwar na neman garar ta ne yasa ta koma ta zauna tana maida numfashi, tana tuno lkcn da irin wannan abin ya fara riskar ta tun bayan da aka kulle su bata iya doguwar tsayuwa sai ta fara jin jiri bata kuma san dalili ba. Ta kai tsawon mintina biyar a zaunen banda aikin kuka rungume da Mufeedan babu abinda yake yi, tun bayan tafiyar su Zabba'u bata sake 'dago kanta ba, wanda tana yin kukan cike da tausayin kansu, gida take son komawa, amma bata da ko sisi da zata iya 'daukar nauyin su da shi, bata da ko sisin da zata dauki 'dawainiyar su da shi ko da ta koma gidan, toh kuma idan taje gidan wajen wa ma zata nufa?, wajen Yah Bukar..kai ina tsinuwar Iyami fa da ta riga ta anbata...? Gaban mahaifiyar ta...?...toh auren ta fa?, bata so tayi sanadin kashewa mahaifiyar ta aure..daga karshe dole dai ta sake yanke wata shawara ta daban. Tana cikin kukan taji an sake dafa kafa'dar ta akaro na biyu, 'dago kai tayi da sauri tana tunanin yanzun kuma wanene kuma menene, tunda wancan dafawar da akai mata Mufeeda ta gani da ta 'dago yanzun kuma fa. Arba idanun ta suka yi da wata hamshakiyar mata, 'yar gayu da birgewa, babbar mace ce sanye cikin wani tsadaddan lace da mayafin da ya bi tsari da zubin lace din ya tafi da shi, duba 'daya Zaitun tai mata taji bugun zuciya sanadiyyan kwarjini da matar tai mata a idanun ta. A hankali ta bi hannun da ya dafatan da kallo banda jan lalle babu komai a hannun, sake maida idanun ta tayi kan kamilalliyar fuskar matar dake mata tsugunne gaban ta duk da irin tarin shekaru da gayun da Allah ya azirta ta da shi. Giran ta duk biyu ta 'dan 'dage zuwa sama..tana bin Zaitun 'din da kallo tace..." Kukan nan ya kasa 'karewa har yanzu...?" Zaitun bata bata amsa ba illa sake duban ta da take yi cike da mamakin ta, tana so tace ina ruwan ki da kuka na amma bakin ta ya kasa furtawa, bai dade ba take jin zuciyar ta tamkar bata tsoron kowa ashe karya take, sai gashi tun ba'aje ko'ina ba ta karyata kanta da kanta bata kuma san dalili ba, ba mamaki shelarun matar ne, ba mamaki kuma gayun ta, a a ba mamaki dai kwarjinin ta ne da ya cika mata idanu. Ita kadai take tufka da warwarar ta cikin zuciya, tuno a yanayin yanda matar tai maganar tamkar wacce sanayya ke tsakanin su kwakkwara ya saka ta sake dago idanu ta dube ta daidai lokacin da kai hannu ta kar6i Mufeeda take jikin Zaitun a lafe. Zaitun bata hana ta ba dan sosai matar tai mata tsananin kwarjini shiyasa ma ta kasa tanka ta. " Tashi mu tafi..."! Shine abinda kunnuwan Zaitun suka sake tsinkaya daga bakin matar wanda ta sake maimaitawa ne bayan ta amshi Mufeeda tama 'daukan ledan kayan Zaitun dake gaban ta. Zaro idanu sosai Zaitun tayi ganin matar ta fara tafiya mata da kaya da kuma yarinya dan ko amsar Zaitun bata jirayi ji ba ta fara takawa, dole Zaitun ta mi'ke ta take mata baya da 'dan sassarfa dan har ga Allah bata san wace ita ba, da sauri da 'dan gudu gudu ta sha gaban matar da niyyar kar6ar Mufee dake hannun ta ta kuma Jaddada mata tambayar inda zata kaisu...amma suna ha'da idanu sai ta ji bazata iya ba sosai nawin matar ya saukar mata ga6o6i har ta harshen ta yai mata nauyi. 'Kasa tayi da idanun nata amma bata bata matsa daga gaban ta ba, tsoro taji ya cika mata zuciya, meyasa ta kasa hanata? me yasa ta kasa tanka ta? anya kuwa, shin da wani irin shiri tazo haka?...murmushi matar da ta gama fahimtar Zaitun din tayi, ta fahimci manufar ta bata da ra'ayin binta ko'ina ne, dan haka sai da ta gyara rikon Mufeeda sannan tace " kina tsaida mu, akwai kuma doguwar tafiya agaban mu fa...". Sai lokacin Zaitun ta iya bu'dan baki tace.." Hajiya kiyi hakuri, mu ba tafiya zamuyi ba...". "...Na sani kar ki damu, ke de biyo ni muje sauri nake ina da wajen zuwa ayau 'din wannan shari'ar ce ta 'dauki hankalina musamman ma ke.. dole tasa na taho sbd ke ka'dai..." Tayi wannan maganar ne tana sake tafiyan da ya sake sanya Zaitun dole bin bayan su ba dan taso ba. Suna fita harabar kotun kuwa dandazon 'yan Jarida sukai mata caa tamkar dama jiran ta suke....kowa na mika mata tasa irin tambayar yayin da da yawa ke jef mata tambayar yanayin da ta tsinci kanta jin cewa kotu ta wanke su... Hajiyan nan ce ta yi ruwa tayi tsaki ta hana Zaitun furta komai har suka isa gaban motar ta, Drivern ta yyi saurin karbar ledan hannun ta sannan ya bude mata baya ta shiga tana nuna masa Zaitun da itama dole ta shiga ko dan gujewa tarin tambayoyin 'yan jaridar ma uwa uba kuma ga Mufeeda da aka riga aka shiga da ita. Mufeeda na ganin Zaitun gefen ta tayi saurin komawa jikin ta itama dake nata burin kenan sai ta rungume abarta da ta lafe luf a jikin ta. Hajiyar nan sai tayi murmushi ganin yadda duk suka rungume juna da sakin ajiyan numfashi lkc guda kamar wadanda suka dauki shekaru basu ga juna ba. Cikin wasu mintina suka 6acewa ganin kotun nan, 'karshe ma suka yiwa garin na Bauchi bankwana suka tasamma hanyar Kano, sosai Zaitun ta daina hango komai daya danganci kotun nan, ta rabu da duk jama'a da gwagwarmayar rayuwa da ta fuskanta cikin kotun, ta rabu da Dr Rasheed da kuma Hameeda, ta rabu da Hajjaju me son rabata da 'diyar ta, ta rabu da su Zabba'u da Zaleeha masu kaunar ta da zuciya 'daya, fatan ta shine ya kasance ta bar duk wa'dannan kenan bari na har abada barin nata kuma ya kasance shine mafi alkhairi kuma mabu'din alkhairi ga rayuwar su gaba 'daya. 'Kalilan daga cikin farin cikin ta ne ya 'karu duk da kuwa nauyin da take ji akan kirjin ta sosai ya ragu tunda kotu ta wanke ta, zama a iya cewa bakin cikin ta ya kau gaba daya, amma kasancewar ta da wannan dattijuwar matar ne bata san dalilin sa ba, bata kuma san me yake nufi ba bata san makamar ta balle tasan karshen ta, ba tasan kuma inda za'a jefa ta ba, musamman da taga sai tafiya ake bb kakkautawa, abinda ya tsaye mata kenan a zuci sai kuma wani tabo daya kasance cikin zuciyar ta da har abada bata jin zata iya mancewa da shi. Azaman cell da prison din nan idanun ta sunga abubuwa da dama...taga abubuwan da 'karamar kwakwalwar ta bazata iya mancewa da su cikin sauki ba, ta kuma koyi wasu abubuwan da kila su taimake ta ne a rayuwar ta ta nan gaba, ta koyi hakuri ta kuma koyi rashin sa, ta koyi kawar da kai sai dai ba akan komai ba. " Ina so ne in raba ki da yawon barar da kk ce shi kk yi shiyasa na dawo zan kuma nesanta ki da garin Bauchi ta yadda babu wanda zai kara tunawa da kema balle a tuna yawon bara kike uwa uba a tuna cewa an ta6a shari'a a kotu da me irin kama da ke, nafi son koda zaki dawo Bauchi ki dawo cikin wani yanayi na daban, ban dauke ki dan cutar da ke ba sai dan in tallafawa rayuwar ki sanadiyyan tausayin ki da ya shige ni tun a zaman kotu na farko, nima 'din Lauya ce ta kasa kuma ina aiki da kungiyar tallafawa mata gajiyayyu da kananun yara...fatan zaki bani goyon baya ki saki jikin ki dani...?" Shiru kawai Zaitun tayi tana mamakin furucin Matar nan, ita aganin ta ai wannan shishshigi ne ba komai ba, bayaga hk ina ruwan ta da su da wata rayuwar su..bata fa bukatar taimakon kowa ma a yanzu ita. Bakin ciki ma sai ya hanata furta komai kwata- kwata, inda taimakon zata yi mata ma dagaske da kudi ta bata ta nemi haya ta kama inyaso sai ta nemi wata sana'ar tayi...Kamar dai yadda tayi abaya farkon zuwan ta. Duk da tasan wancan lkcn da kuma yanzu da banbanci, a yanzu mawuyaci ne ma jama'ar garin su kar6e ta cikin sauki, ko abaya ma tasha wahala kafin a kar6e ta balle yanzu da ta kasance tana da mugun tabo a goshin ta. Duk da hakan batayi 'kasa a gwiwa ba ta bayyanawa Hajiyar ra'ayin ta...sai kawai tayi murmushi.." Kar ki damu can 'din ma in kinaso zakiyi aikin...ita kuma wannan fa...?" Hajiyar ta 'kare da tambaya tana nuna Mufeeda. Kallon Mufeedan tayi dake lumshe ido alamar son yin bacci a hnkl ta bata amsa da fa'din.." 'YATA CE". Jinjina kai tayi tace " Masha Allah, amma meyasa ban ta6a ganin wani naki ba a duk zaman kotun da ake yi...har yau 'din nan da ya kamata ace 'yan uwan ki na nan tare dake saboda murnar saukan hukuncin kotu akanki banga kowa tare dake ba..meyasa...?" Baki ta 'dan tura gaba tayi 'kasa da kanta sbd ba shine cikakkiyar maganar da taso ji daga bakin Hajiyan ba...tana so ne taji ina zata kaisu. " Sbd bamu da kowa ne Hajiya...". Amsar da ta bata kenan kawai tana gyara zaman Mufeeda a jikin ta. " Wa'danda naga sun kawo mk yarinyar nan 'dazu a..." Bata ma jira jin karshen tambayar Hajiyan ba tayi saurin bata amsa da fa'din..." Mahaifiyar Dr Rasheed ce da 'kannan sa, ta rike min ita ne tun lkcn da aka shigar da mu cell tun a farko..." Hajiyar kam sai ta jinjina kai tana 'dan murmushi jin yadda Zaitun ta bata ansa a fizge tana sake duban ta tace..." Ta kyauta gaskia ta kuma yi abinda ya dace, toh amma ina mijin ki fa, I mean mahaifin 'diyar taki...?" Zaitun bata ma san lkcn da ta zaro idanu tana kallon fuskar Hajiyan ba, dagaske wai amsa take jiran ji daga bakin ta? shiru motar ta 'dauka kamar bazata yi magana ba sai kawai taji 'kwalla na zubo mata, kenan kowa sai ya tambayi mahaifin yarinyar ne, kaddai itama Mufeeda watarana tayi mata wannan tambayar me zata ce da ita kenan?...cikin sanyi can ciki ta tsinci bakin ta da furta.." Marainiya ce....". Sosai Hajiyan ta tausaya mata inda tayi mata addu'a cike da alhini gami da tunanin mahaifin Mufeedan ne ya rasu...daga nan bata sake yi mata tambaya ba har suka tsinci kansu cikin garin Kano. Vote Share Salmerh😘 [20/9/2022, 12:34 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* Wattpad@ Serlmerh-md 🅿️ *...25* .....A hankali ya sau'ke labilen windon 'dakin nasa yana sakin 'karamar ajiyan numfashi wacce zahiri a hakan zaka iya kiran ta amma a badini shi ka'dai ya san zafin da hakan yake masa a kirji da cikin zuciya, rabon da yayi farin ciki da wahala tun rabuwar sa da Zaitun na farko, raban da aga cikakkiyar fara'a kan fuskar sa koda ta ya'ke ce tun ranar da yaji sunan wanda mahaifi yake gareshi a kotu matsayin shugaba kuma mai 'daukan nauyin ta'addanci, duk da yake ba wata kwakkwarar ala'ka ko shakuwa ke tsakanin su ba amma sosai abin ya dame sa ya kuma tsaye masa a zucia..wannan kalma ta iyaye mahaifi da mahaifiya ba 'karamin tasiri suke da shi azuciyar kowani halitta ba, duk yadda yakai ga tsanar halayyar mahaifin nasa amma deep down yana jin kauna da kewar rashin shakuwa dake tsakanin su, sai dai munanan halayen mahaifin nasa su suka han komai yin tasiri game da shi. Gaba 'daya sai ma ya kuma ji mutumin ya sake fice masa aka, musamman da ya kasance dalilin damuwar halayyar sa yasa ya sake rasa damar ganawa da Zaitun a karo na biyu, meyasa a ko wani lokaci da gi6i yake barin zuciyar sa ne? meyasa koda wani lokaci rashin nasara ke gilmawa tsakanin sa da mahaifin nasa? meyasa son zuciya da son kansa sukai masa yawa? meyasa sam bashi da tausayi cikin zuciyar sa? meyasa, meyasa abubuwa da dama? Idanu ya lumshe fahimtar da yayi cewa hawaye ke bin fuskar sa, aikin kenan, abinda a mafi yawan lokuta ke faruwa matukar haduwa ta hada shi da mahaifin nasa shine zubda kwalla, kusan a kaf 'din rayuwar sa mahaifin nasa shine mutun na farko da ya kasance me sashi zubar da kwalla, in dai kaga Adam na hawaye toh yaci karo ne da takaicin 'daya daga cikin halayyar mahaifin sa dalili kenan da ya sa a mafi yawan lokuta yake kalubalantar ha'duwa da shi. Akan mutun me irin wannan 'dabi'a shine Hajiya zata yi iya bu'dan baki har tayi tutiya da alfahari dan sun kasance makusantan sa?, shin mancewa Hajiya tayi ne da wuri haka? Xuciyar sa ke zayyano masa wannan tambayar yana dafe da kansa. Mutun irin wannan shine Hajiya take kafa hujja dashi cike da ya'kini ta shiga tsakanin sa da Zaitun a wani dalili...? Sam bai san ma miye ya canza Hajiyar tasa har haka ba, ba mamaki kwata- kwata ta mance ne da waye asalin Jibrin 'Dan Maliki a gareta, may be ta mance ba'kin cikin da ya dasawa zuciyar ta abaya. Da bayan yatsar hannun sa manuniya ya 'dauke 'kwallan da ke bin idanun sa yana me zama bakin gadon sa ha'de da lumshe idanu...tunanin rayuwar sa ta baya ya fara dawo masa cikin kwakwalwa. ~~~~Cikakken sunan sa shine _Adam Shaheed Jibrin 'Dan- Maliki_ , ya kasance 'da kwara 'daya tilo ga mahaifin sa da ake kira 'Dan Maliki tun zamanin kuruciya, shi kadai kuma ya mallaka a fa'din duniya baki 'daya, duk da yake bai taso gaban mahaifiyar sa ba amma bai ta6a kokawa saboda rashin gata ko kan wani abin ba, hasalima bai taso yaga mahaifiyar sa ba sai dai a photo, bai ta6a jin sautin muryar ta ba sanadiyyan rasuwa da tayi tun bayan da ta haife shi duniya tace ga garinku nan. Yana taso ne gaban makwafi agare ta, domin bayan dangataka ta jini akwai tarin kama 'kak'karfa tsakanin mahaifiyar sa da Hajiya Talatu. Hafsat macece mai tarin ilimi, hakuri, natsuwa da nagarta, ta kasance 'kanwa ga Hajiya Talatu wanda su biyu kacal iyayen su suka haifa kafin su bar dunia, sun kuma koma ga mahaliccin su sanadiyyar ambaliyar ruwa da ya afka da su a wasu shekaru can baya wanda a lokacin Hafsat da yayar ta sunje hutu wajen wani Baffan su ne wato 'kanin mahaifin su kafin dawowar su ne lamarin ya auku. Sun yi kuka sun kuma shiga damuwa gami da tsananin alhini saboda rashin mahaifan nasu amma daga baya duk suka dangana suka fawwalawa Allah komai, haka suka cigaba da rayuwa cikin maraicin uwa da uba, sun ga kalubale da dama wajen dangin su saboda mahaifin su asali ba wadata bane dashi sosai amma akwai cikakkiyar wadatar zuci, basu gaji komai daga mahaifin nasu ba sai gona guda 'daya sai dai tana da girma ba laifi. Basu tashi sanin basu da cikakkiyar gata ba sai da suka rasa mahaifan nasu aka kuma rasa cikakken wanda zai kar6e su da hannu bibbiyu ya rike su ya kuma basu gata da kulawa, 'karshe karatu ma gagarar su tayi saboda rashin wanda ze biya musu kudin makarantar, haka kuma batun gonar mahaifin su ma basu samu cikakken bayani akan ta ba. Lokacin da Hajiya Talatu tayi auren ta na farko tare da Hafsat ta fara zama domin a cewar ta hankalin ta zai fi kwanciya ne idan tana ganin Hafsat din tare da ita, ta bayyana hkn ne kawai amma ita ka'dai cikin zuciyar ta tasan dalilin ta, irin dabdalar da akayi wajen aurar da itan kadai yafi tsaya mata a zuciya, wadanda suke gani sune jigo agaresun da kyar suka hada suka sama mata kayan dakin da suka aurar da ita bayan an sha gwagwarmaya da kai kawo, har da su fa'dace fa'dace sbd rarrabuwar kai da aka samu, a lokacin wata zuciyar har na zuga ta kan kawai ta fasa auren ma gaba 'daya, Hafsat ce ta ringa tausan ta da ban baki har aka kammala komai aka mi'ka ta da'kin ta komai sai a hankali, a fili zaka fahimci cewa maraici da rashin gata na tattare da rayuwar ta karara, cikin sa'a kuma sai Allah ya bata miji me kaunar ta da fahimta bashi da tashin hankali. Wannan dalilin yasa taji sam bazata iya barin 'yar uwar ta cigaba da zama tare dasu ba zata rike ta gaban ta har zuwa lkcn da itama Allah zai bata mijin aure domin tozarcin da akayi mata ma ka'dai ya isa, bazata juri ganin na 'yar uwarta a nan gaba ba. Allah cikin ikon sa sai ba'a jima ba itama Hafsat batun auren ta ya taso dan already dama ta zama budurwa matashiya, ko lokacin auren kuwa Hajiya Talatu taso ta nuna kin amincewar ta sakamakon shaidar rashin halin kwarai da aka yiwa manemin nata Jibrin 'dan Maliki, amma Hafsat ta nuna tirjiya da zallar kaunar da take yi masa ga yayar tata, a lokacin kwata- kwata shekarun ta basu fi goma sha shida zuwa sha bakwai ba, amma hakan be sa ta zama me ragaggen tunani ba, ba tsananin so ba ne ba kuma kauna kakkarfa ba, ba wai ta 'kagu tayi aure bane, ba kuma gajiya tayi da zama da 'yar uwarta tata ba, kawai gani take kamar tsarin zaman nasu be mata ba, so take ta basu fili su sarara suma a gidan auren su, musamman ma shi mijin 'yar uwar ta ta, mutun ne mai tsananin sanyin halayya hakuri da kawaici, bai fiye nuna gajiyawar sa kan abu a zahiri ba, wannan dalili ya sanya take gani kamar koda tana takurashi bazai nuna ba, koda tana hana shi sakewa cikin gidan sa bazai ta6a nunawa ba, dan duk abinda 'yar uwar tan ke so shima mara mata baya yake, sosai yake tsananin tausayawa maraicin su so bata so su kure shi. Shiyasa ta yanke shawarar kawai zata yi auren, batare kuma da dogon nazari ko mikawa Allah za6i ba kawai ta kafe kai da fata tace ita dai sai shi, cikar burinta kawai ne agaban ta a lkcn ba komai ba. Ganin ta dage kamar yadda Talatu ta kafe kan dokin naki ne ya sa mijin nata da kansa sanya baki cikin lamarin, zama yayi dasu suka yi magana ta fahimta 'karshe dole yasa Hajiya Talatu amincewa da batun auren amma ba wai a son ranta ba dan baya ga halayyar sa da aka kushe haka kawai ma tana ganin cewar shi din ba sa'an auren Hafsat 'din bane sbd tazarar shekaru dake tsakanin su dan ko a lokacin shekarun sa zasu ninka na Hafsat 'din har sau biyu, bugu da kari wayewar sa ta banbanta da ta Hafsat, yafi ta wayewa da gogewar rayuwa nesa ba kusa ba, a ganin ta mace wayayya wacce tasan rayuwa sosai ita tafi dacewa da shi ba 'yar uwarta Hafsat ba, tsoro take ji kar 'yar uwarta ta cutu. Sai dai ba laifi shima Jibrin ya nuna mata kauna ya kuma nuna bajintar sa tun da aka fara batun auren har zuwa lokacin da aka sada Hafsat da 'dakin mijin ta ko sau 'daya bai nuna wani hali da za'a zage sa da shi ba, bai kuma bar 'kofar da wani zargi zai bayyana da za'a iya tuhumar sa da shi ba, ba laifi itama Talatu sai taji hankalin ta ya 'dan kwanta da auren Hafsat 'din. Sai dai abin mamaki Hafsat bata cika sati hudu 'kwarara a gidan sa ba ta fara fuskantar wasu 'kalubale, in da ta fara cin karo da wasu abubuwa da ta kasa fahimtar inda suka dosa, ya kan dawo gidan cike da maye ya zube mata a parlour, tana zuwa kusa dashi idan ya ganta sai yace ta bashi ruwa da zarar yasha ruwan kuma sai ya fara sheka amai daga nan bacci. Haka zata tsaftace wajen tana yi tana kuka, washegari idan ya tashi ya gansa a wajen kuma in bata yi sa'a ba sai tasha jigba ranar da ta taki sa'a ne yake tsayawa a mari ka'dai, duk wai dan me yasa bata tashe shi ba ta barshi ya kwana parlor ko 'saman tiles. Ita kam rasa abin cewa ma take yi sai kuka, toh me zatace dashi, da kansa yasan ba iya 'dagasa zata yi ba, sannan a wancan hali da yk ciki ko ta tashe shi ba lallai tashin zai yi ba. Hafsat ta juri abubuwa da dama tattare da Jibrin, haka zai zauna mata a Palor ya dinga zu'kan tabar sa sai yashaki iya son ransa sannan ya bar gidan ita zata tattare sauran tana kukan takaici, bata son warin taban amma bata isa tayi 'korafi ba sai tasha jibga. Sai yanzu ta fahimci abinda tun farko yayarta Talatu take mata ishara akan su amma zuciyar ta ta lullu6a ga cikar burin ta ta kasa gani. Tasani bata mai da hankali wajen za6en abokin rayuwa ba, haka kuma bata dace da samun nagartacce ba, wannan dalilin ya sanya ta fara kai kukan ta ga mahalicci akan ya shirya mata shi, bataso yaran da zata haifa su taso su tarar da shi da wannan halayyar balle har su tuhume ta da rashin za6a musu uba nagari da batayi ba, dan tasan koda basu tuhume ta da tambaya ba dole cikin zuciyar su suji bb dadi. Koda wasa bata ta6a sanar da yayarta wannan lamari ba a kullun tunanin ta shine zai canza wataran, dole zai san ba daidai yake aikatawa ba ya kuma yi nadamar komai. Wataran idan Jibrin ya bar gida tun safe in ya ga dama bazai dawo mata ba sai tsakiyar dare, wataran ma ba ya dawowa gidan kwata- kwata, ba zai kuma 'kira ya fa'da mata uzurin sa ba gudun kar ta tashi hankalin ta ba..ba ruwan sa da wannan, idan kuma ita ta kira 'din bazai 'daga wayar ba sai yaga dama, in taci sa'a ya 'daga ma masife ta yake da cewar tana damin sa aiki ne ya rike shi...hmm wai aiki har tsakiyar dare. Takaici baya barin ta yin bacci, in ta taki sa'a ya dawo gidan washegari ma ta kanci karo ne da abu biyu zuwa uku, inma yazo mata a buge tatul inma kuma yazo da budurwa su shige 'dakin sa har sai ta kwammaci dama bai dawo gidan ba yafi mata, haka zata 'kara kwana cikin wani zullumin tana kuka, in ta taki tsananin sa'a ne yake dawo mata normal batare da yasha komai ba, in kuwa ta nemi su tattauna zancen ya kan tsatstsare ta ko kuma a takaice ya ce aiki ne yake masa yawa shi kuma yake hanasa dawowa kan lokaci, dole bata da tacewa. A kuma 'dan tsakankanin ne ta fahimci Jibrin yana tu'ammali da wasu 6ata gari, hk zai kawo su gidan suyi mata 'da'd'daya a palor yasa tayi ta musu hidima ko kishinta ma baya nunawa sam. Hankalin Hafsat ba 'karamin tashi yayi ba data fahimci hakan gashi a lokacin Talatu sun tafi aikin Hajji da mijin ta. Haka tai ta rike damuwar ta bata ta6a fa'dawa kowa ba, haka ko makwabtan ta bata bari sun fahimci komai ba duk kuwa da zumuncin dake tsakanin su. Lokacin da Talatu suka dawo kafin nan kuwa duk Hafsat ta 'kare ta lalace sai haske ka'dai da ta 'kara, a lokacin da taje gaishe ta da barkan dawowar su a sannan ta sanar da ita bayan tambayar da Talatun tai mata na dalilin ramar ta, abin nema yake yafi karfin ta gaba 'daya tsabar 6acin rai bata ma san lokacin da ta kunce mata komai ba, duk wasu abubuwan da ta dade tana 6oyewa tsab ta sanar da ita, amma abin mamaki sai Talatu ta 'kara mata zafi, duk wasu takaicin ta na lokacin auren sai a nan ta samu ta huce su, duk bakin cikin da ta kunsa na dagewa da auren da Hafsat tayi tun a farko tsab ta zazzage su, tana yi tana kuka haka Hafsat ma na kuka, 'karshe suka rungume junan su suka cigaba da kukan a hk..amma har Hafsat ta koma bata iya ta tanka kan batun ba. Sai daga baya da ta huce gaba 'daya ta kuma fahimci damuwar Hafsat 'din kullun gaba yake ba raguwa ba sannan ta shiga lamarin sosai gashi ma laulayi ya sako Hafsat 'din gaba gadan gadan tsoron ta kar abin yazo yai mata yawa har ya kai ga illatata, duk da yake ba 'karamin farin ciki tayi da samun cikin Hafsat din ba amma tsanar da ta yiwa Jibrin yasha gaban komai. Bata da matsalar komai a gidan auren ta, irin nustuwa da kwanciyar hankalin da take ciki gidan mijin ta sau tari ta kanyi tunanin da ana rabawa da tabbas sai ta raba ta bawa 'yar uwar ta rabi da quartern sa, amma hakan ba me yiyuwa bane sam, abu 'daya da Allah ya hana ta cikin rayuwar auren ta shine haihuwa, kuma bata cire rai da samun sa ba shima 'din dan ita akaran kanta ma ta jima tana son ta samu ciki ban da maigidan ta da 'yan uwan sa da suka fita damuwa amma har a lokacin Allah bai basu ba, sai ga Hafsat daga yin auren ta lokaci kankani ya azurta da samun ciki bayan ko cikakkiyar nutsuwa bata samu gidan auren ba ma. A kan zuciyar ta take jin Hafsat dan ita ka'dai ce danginta take ji a kaf fa'din rayuwa, kauna da burin ganin farin cikin Hafsat shine mura'din ta a ko wani lokaci, ace kuma yau ga wannan Hafsat 'din 'dauke da ciki a jikin ta bata jin akwai wanda zai kaita kaunar cikin nan koda kuwa mahaifin cikin ne. Son dunia Hjy.Talatu ta 'dora wa cikin nan kamar a jikin ta yake, banda tausayin Hafsat din daya sake cika mata kirji, tana ji dole ne a wannan ga6ar tayi wani abu dole ne ta tsayawa Hafsat wajen ganin ta samu 'yan cin ta, bazata sake bari Jibrin ya cutar mata da 'yar uwa ta kyale ba, duk yadda taso 6oye kauna da farin cikin bayyanar cikin Hafsat din sbd tsanar halin Jibrin amma kasa jurewa tayi. Manya ta ha'da da maigidan ta da yake babban mutun ne shi mai kuma dattako ta ha'da da manya daga cikin dangin mahaifan su inda ta sanar da su halin da Hafsat take ciki. An zauna da Jibrin an yi masa fa'da an kuma nuna masa kuskuren sa ya amince tamkar gaske ya kuma basu haku'ri gaba 'daya, hatta ita Hafsat din sai da ya bata hakuri da kansa batare da wani yace ba, amma suna dawowa gida ya kama Hafsat ya jibga son ransa ya mata dukan tsiya, dukan da yasa hatta cikin jikin ta sai da ya fita duk wai sbd karar san da takai. Hajiya Talatu ba 'karamin bakin ciki tayi da faruwar lamarin ba taci alwashin sai ta kai 'karar sa ga hukuma a hukunta sa amma maigidan ta ya hana ta, acewar sa tsakanin mata da miji ba'a shiga, ciki kuma Allah ke bada shi idan yaso zai 'kara basu wani aduk lkcn da yaga dama, batun duka ne dai sai da aka sake masa magana dan sai da Hafsat tayi sati kwance a gadon asbiti kafin ta 'dan warware..kowa baiji da'din lamarin ba. Daga asbiti Hajiya Talatu gidan ta ta wuce da ita wasa-wasa sai da Hafsat ta shafe watanni hudu bata koma gidan ta ba, duk yadda Jibrin ya nuna damuwar sa Hajiya Talatu kallo bai ishe ta ba, karshe mijinta ne da Jibrin ya biyo ta hannun sa ya sa dole badan ta so ba ta maida Hafsat 'din 'dakin amma da 'kwakkwarar kashedi ga Jibrin ya kuma amince. Comment Share Vote Salmerh😘 [20/9/2022, 12:34 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* Wattpad@ Serlmerh-md 🅿️ *...26* .......Haka tayi ta lalla6awa, shima Jibrin 'din sai ya 'dan canza kamar gaske, ya kan 'dan bata kulawa ko da bana kirki bane ya dai fi baya da yake babu kulawar gaba 'daya, ya kuma daina kawo mata gida da 'yan mata ya rage tsawon dare da yk yi ya kuma sassauta time din da yk dawowa, taba ce dai bai daina zaman sha a parloun ba amma bata kulashi, haka in ya gama zata tattare tsab ta sanyawa 'dakin turare faman da ta tayi kenan har zuwa lokacin da Allah ya sake bata wani cikin watanni bakwai bayan fitan na farko. Wannan karon kam Hajiya Talatu sai ta tsaya tsayin daka tana kula da ita, kusan kullun sai ta zo gidan in ma bata zo ba takan kirata a waya taji ya take karshe ma data ga hankalin ta yaki kwanciya ta nemi Hafsat din ta dawo gidan ta har zuwa lkcn da zata haihu amma Jibrin bai amince ba dole ta hakura da batun domin bata da ikon tilasta shi. Lokacin da cikin Hafsat ya 'dauko tsufa a daidai lokacin harkokin Jibrin suka sha kansa, sanadiyar za6e da ya gabato, shi kuma yana 'daya daga cikin na hannun daman wani 'dan takarar ne a wancan lkcn, sam Hafsat ta rage yawan ganin sa, sai tayi wasu kwanaki ma bata sashi a idanun ta ba, kuma bata da bakin tanka shi. Ranar wata Laraba tatashi da nakuda cikin rashin sani ta cigaba da harkokin ta na cikin gida batare da bawa abin muhimmanci ba. Kafin fitar Jibrin a gidan ne sai abin yaso yai mata tsanani ta nemi ya kaita asbiti amma yace mata ta 'dan daure dai bari yaje wani 'dan taro ana jiran sa ne zai dawo. Da haka yasa kai ya fice a gidan batare da damuwar komai ba balle ya damu da halin da ya barta a ciki. Sosai abin ya damu Hafsat, gashi bata da ko sisi a hannun ta, wayar ta ma rabon ta da kati har ta mance balle ta kira yayar ta Talatu ta sanar da ita halin da take ciki. Cikin sa'a kuwa daidai lokacin da take gab da galabaita a dai- dai lokacin Hajiya Talatu tayi kiran ta kamar yadda ta saba a kullun dan jin lafiyar ta, da 'kyar ta iya amsa wayar maganar ma sai ta gagare ta yi sai nishi da take saukewa kasa kasa. Hajiya Talatu ma da jin yanayin da ta ke hankali tashe ta fara shirin tahowa. Cikin sa'a kafin isowar ta wata makwabciyar su ta shigo gidan dan duba ta dayake tana zaman mutunci da kowa, so kafin ma Hajiya Talatu ta iso har matar ta taimakawa Hafsat, ba daman zuwa asbiti a lokacin dan haihuwar ta riga ta taho gadangadan ne. Tare suka taimaka mata ta haifo 'dan ta namiji kyakykyawa dashi me kama da mahaifiyar sa sak har hasken ta bai bari ba. Ta galabaita sosai dan hk koda suka gyara ta suka ce asbiti zasu kaita a duba lafiyar su tukun na. Suna niyyar tafiya asbitin jini ya 6allewa Hafsat cikin lokaci kankani kuma ya galabaitar da ita ta fita hayyacin ta gaba 'daya, da gudu Talatu tayi waje ko zata sama musu abin hawa at same time tana kiran wayar Jibrin amma baya 'dagawa...ta 'kira numbern mijin ta shima ya bar wayar a mota ya shiga meeting. Da 'kyar ta samo mota ta dawo gidan da gudu-gudu sauri- sauri tana fa'din kamata mu tafi asbitin na samo abin hawa. Duk yadda makwabciyar Hafsat taso yi mata bayani kasa fahimta tayi tace sam suje asbiti ita dai bata ji ta ydda ba, taya zata wani bata numfashi sai dai in doguwar suma tayi dan haka ita dai su je asbitin. Abin yazo ne gaba daya cikin 'kan'kanin lokacin da duk cikin su babu wanda yy zato. Hajiya Talatu da ta kasa yadda sai da suka dangana da asbiti kafin, acan aka tabbatar musu da cewar already ma ta rasu, dan zuwan su asbitin ma ko ciro ta cikin motar ba ayi ba aka duba aka kuma sanar da su dan haka suka juyo gida, Talatu ji take kamar tayi ta ihu tana fada musu cewar Hafsat din ta tana nan a raye bata mutu ba amma tasan ko ta fada karya take, mutuwa dole ce akan kowa kuma kowa nada nashi lokacin..a karo na biyu ta sake rasa makusanciyar ta. Fa'din irin tashin hankalin da Hajiya Talatu ta shiga ma 6ata lokaci ne, ko kuka kasawa tayi, gaba 'daya jin ta take tamkar itama ba a duniyar take ba ido kawai ta kurawa gawar Hafsat 'din ta kasa ko kyaftawa, yayin da sabon jaririn dake hannun makwabciyar Hafsat din yake ta tsanyara kuka tamkar yasan meke faruwa. Karshe Jibrin sai zuwa yy ya tadda Hafsat sam6al a kwance amma wai babu rai tattare da ita. Ido ya kura mata kamar zai ce tashi amma bb dama, kokadan bazaka iya bayyana halin da yake ciki ba. Haka akai mata suttura aka kaita gidan ta na gaskia. Tun daga lokacin rikon Adam da Jibrin yai masa hu'duba da sunan mahaifin sa ya dawo hannun Hajiya Talatu, dan a cewar ta bazata sake yin sakaci karo na biyu ba, sosai ta 'kullaci Jibrin duk da tasan mutuwa dole ce amma a ganin ta da gudunmawar sa wajen rashin Hafsat da tayi. Sosai ta tattara so da kaunar da take yiwa Hafsat ta 'kara kan wanda take yiwa yaron ta ha'da masa gaba daya, kulawa take bashi tamkar kwai, gaba 'daya ta baibaye rayuwar sa da farin ciki da 'kauna. Sau tari ba 'karamin mamaki Jibrin ke bata ba, dan yana iya shafe watanni biyu 'kwarara koma fin hakan batare da yaji ko ganin yaron ba, bai damu da komai da ya dangance sa ba, ko maraicin da yaron ke ciki Jibrin baya dubawa, haka kuma 'daya daga cikin halayyar sa bai canza ko guda ba sai ma abinda ya karu tamkar dama fili yake jira ta bashi, duk abubuwan da yy abaya sharan fage za'a iya kiran su. Dama ba wasu dangin sa Hajiya Talatu ta sani ba mahaifiyar sa ce ka'dai kuma itama bayan auren sa da Hafsat Allah yy mata rasuwa, ko wajen rasuwar Hafsat basuga kowa nasa ba. Bata tsinke da al'amarin Jibrin ba har sai da taga ana neman shafe shekaru biyu Jibrin bai zo ganin 'dan sa gudan jinin sa ba bai kuma kira a waya yaji lafiyar sa ba..ba 'karamin mmk tayi da hkn ba, bata ta6a tsammanin abin nasa har zai iya shafan gudan jinin sa ba, tun daga lokacin ta tsinke da al'amarin Jibrin ta kuma 'daura aniyar kulawa da Adam muddin ranta. Adam bai ta6a sanin yana da wani uban ba baya ga maigidan Hajiya Talatu har ya cika shekaru biyar da haihuwa sannan watarana Jibrin 'din yazo tamkar daga sama ya fa'do. Ko kallo bai ishe ta ba, ba ta dai hana shi ganin 'dansa ba amma itakam bai ga idanun ta ba balle har ya samu sakin fuskar ta, dama maigidan ne ya shigo da shi, ko daga Adam din ma bai samu sakewa ba dan ba sanin sa yayi ba shima 'din ko a photo kuma bai ga laifin yaron ba. Ko da yy wannan zuwan kuwa bai kara zuwa ba har da aka 'dauki tsawon wani lokaci, sannan ya nemi inda suke, dan auren ta ya mutu tuntuni sakamakon matsawar dangin miji da tayi ta fuskanta kan rashin haihuwar da basu samu ba, ita har har mijin babu wanda ya tsira, afa'dar su kuma ta kawo musu bare 'dansu nata hidima dashi bazasu iya jure gani ba dole ya sake ta ya 'kara aure, yaso fahimtar da magabatan nasa cewar ko da bai saki Talatun ba zai iya auren sa kamar yadda suke so tunda Allah ya bashi abinda zai iya rike su da shi suka ce sam 'karshe dole sai da aka rabun hankalin kowa ya kwanta. So da 'kyar Jibrin ya samo inda take bisa jagorancin tsohon mijin nata a lokacin ma already tayi aure na biyu shekarar su biyu suka rabu tana shirye- shiryen yin wani auren ne karo na uku. Duk wata kulawa ta mahaifi Jibrin bai iya bawa Adam ba, bai iya jansa ajiki ba, idan yazo din ma banda gaisuwa bb abinda yk ha'da su, bb wata sha'kuwa ta 'da da mahaifi babu kyautatawa sam, bai san cin Adam ba balle sutturar sa, bai san lafiyar sa ba ina ya kwana ina ya tashi duk basu dame shi ba, bai san damuwar Adam ba, bai san ilimin sa ba bai san komai da ya danganci Adam ba. Duk da hk Hajiya Talatu bata ta6a shiga tsakanin sa da yaron ba amma tuni Adam yasan komai game da labarin mahaifiyar sa da irin zaman da tayi da mahaifin sa kuskuren da Hajiya Talatu tayi shine na rashin 6oye masa komai da tayi. Tun kuma lokacin da Adam yaji labarin mahaifiyar sa har zuwa lokacin da ta rasa ranta yk jin zafin mahaifin sa a ransa har yau kuma hakan bai canza ba. Jibrin yazo ya auri wata mata amma bata haihu da shiba kasantuwar babbar mace ce ta kuma riga ta gama haihuwar ta kafin suka yi aure. Ganin yadda yaranta ke zuwa gidan sa suna watayawa son ransu da dukiyar sa ne ya sanya shi fara sha'awar dawo da nasa 'dan shima gaban sa ya kula da shi a kokarin sa na ganin bai zama inuwar giginya ba, a time din kuma Adam har na aji na farko a Jami'a, ba 'karamin mamaki Jibrin yayi ba 'kwarai da gaske, da yaji sau'kar Alkur'anin Adam din har sau biyu har 'kwalla sai da ya zubar domin yaga kokarin Hajiyan sosai take yayi musu alkawarin kujerar Hajji ita har Adam 'din, koda ya bayyana 'kudurin sa Hajiya Talatu bata ce komai ba ta dai ce ya jirayi zuwan yaron yaji ta bakin sa dan ita bata da cewa. Taso tace wani abu kafin ma zuwan Adam 'din amma gudun yaga kamar tana ziga yaron ne ya sanya taja bakin ta tai shiru, tana kuma da yakinin Adam din da kansa shima bazai amince ba. Ilai kuwa hkn akayi, dan 'kin amincewa yayi, 'karshe jibrin dole ya koma inda ya fito bayan ya cika Hajiya Talatu da Alkhairi akaro na farko cikin rayuwar sa tun rike masa Adam 'din da tayi. Alkhairin da ko kallo basu ishi Adam ba, tun ma kafin Jibrin ya bar gidan Adam ya fara masifar ta mayar sa da kudin sa, su basu da bukata, ai ko abaya basu mutu sbd rashin kudin sa ba dan haka a yanzu ma kudin bazasu tare musu komai ba..kuma shi bai ce yana so abiya masa Hajji ba, da kudin sa yake so yaje halak 'din sa gumin sa bada wani ba. Jibrin murmushi kawai yayi ya juya ya fita yayin da Hajiya Talatu tai shiru tana duban kudin da tunanin yadda zata yi da su. Dan tasan taurin kai irin na Adam bazai ta6a yadda yy amfani da shi ba kamar kuma yadda yace bai amshi kyautar kujerar Hajjin ba haka 'din bai kar6an ba while a wannan ga6ar tasan yanada bukatan kudi kodan hidimar karatun sa ma...da kyar ta shawo kansa ya dan sauko daga fushin rike kudin da tayi ma amma duk yadda taso ya anshi kudin bai amince da hkn ba...suna cikin rashi a lokacin dan mijin da ta aura ba me karfi bane kamar na baya amma Adam yafi gane yaje yy ko wani irin aiki ne ya samo ku'din sa yy amfani da shi fiye da yayi amfani dana Mahaifin nasa Jibrin...Adam bai ta6a ambatar Jibrin da sunan da kai tsaye zaka fahimci cewa mahaifi yake agare shi ba _Alhaji_ yake kiran sa da shi shima 'din sakamakon arzikin zuwa saudi da ya san samu. Shi kansa Jibrin ya 'dauki abin wasa sai da lkcn fara shirye- shiryen tafiya yayi Adam ya tire sam shi babu inda zashi. P.An Jibrin cikin zuciyar sa yace " kaji marar rabo" har ga Allah shi bai ta6a gani ko jin tarihi makamancin wannan ba, abin mamaki...Hajji fa..?amma ana bin sa yana kaucewa. Jibrin kuwa cewa yayi shifa idan ya cire kyauta baya maida shi. Karshe Adam cewa yayi sai dai mijin Hajiyan da ita suje amma shi babu inda zashi. Aikin carwash, gareji, welding, capentary, leburancin gini, hatta kasadar gyaran wuta sai da yy, ha'kar Soakaway da borehole aikin painti da saka tiles, ha'da satelite bb irin aikin da Adam be yi ba a rayuwar sa, yayi aikin driver a wani gida ma, dan tun yana 6oyewa Hajiyan har tazo ta fahimta tayi masa fa'da amma 'karshe dole ta kyale shi, duk da irin tarin dukiyar da Jibrin ya tara ya kuma kafa tarihin da kowa ya san erh lallai yana da dukiyar amma sam basa gaban Adam tamkar ma bai san da wanzuwar sa ba. Tun daga lokacin kuma Jibrin yake shiga rayuwar Adam din a hnkl batare da ya sani ba, dan shima ganin shekaru sun tasammasa haikan bashi da wani da zai kira nashi illa Adam 'din yasa ya 'dan fara shiga taitayin sa, duk da yk dama can yana kaunar yaron kawai dai yafi bawa harkokin sa muhimmanci ne fiye da komai, kuma rashin damuwar sa ya ta'allaka ne da tabbaci da yk dashi na cewar Adam din yana hannun da yasan baza'a ta6a barin sa ya koka sbd damuwa ba, zai samu cikakkiyar kulawa tamkar yana hannun mahaifiyar sa shiyasa bai wani damu ba. Abin mmk duk inda Jibrin ya fahimci Adam na zuwa leburanci sai yaje ya sa an dakatar da shi ya kuma nuna musu cewa 'dan sa ne jinin sa, fushi yy dashi ne shiyasa kawai yake huce takaicin wajen aiki da su, 'karshe sai yy musu alkhairi ya tafi ya bar su da 'dimbin mamakin Adam. A ganin su taya me uba kamar Jibrin 'Dan Maliki zai na aikin sana'ar leburanci irin wanda su suke yi, bacin irin su tun kafin a haife su aka tara musu dukiya suka tashi cikin sa, wasu na ganin wautar Adam yayin da wasu ke ganin kawai saukin kansa ne yy yawa. Duk kuwa yadda Jibrin yaso yi masa bazata da aiki amma Adam yaki duban ko'ina, dan acewar sa bai nemi aiki da kowa ba dan hk koda an neme shi da appointment nunawa yk baya bukata dan sarai yasan aikin waye...infact ma shi be gama schl ba balle har ya kaiga neman aikin dan haka duk daraja da girman aikin baya masa gani.sau biyo acewar sa baya bukatar ko guda. Sosai hakan da yake yi yake 'kona ran Jibrin ya kuma rasa yadda zai yi da shi. Idan sun ha'du zai gaida shi a mutunce babu rashin da'a amma daga hakan babu wata magana kuma, kuma har yau yaki amincewa da duk wani abinda zai fito daga hannun sa ko ta dalilin sa gaba daya ya rasa me ke damun Adam din. Da kansa ya budi baki ya bashi hakuri da tunanin ko rashin kulawa da bai bashi bane abaya yk damun sa amma Adam yace hakurin na menene kuma shi bai masa laifin komai ba. Ba 'karamin azabtar da zuciyar Jibrin yk da irin wannan halayyar tasa ba cikin su kowa na ganin 'dan uwan san baya kyauta masa. Dan Adam zuciyar sa cike take da haushin abinda yayiwa mahaifiyar sa ne gashi yaki ya dube shi da sunan 'dan sa har sai da yaga ya tasamma shekarun girma sannan yazo yana tarwatsa masa duk wani shirin sa na sana'a da ke yi yayin da Jibrin ke ganin dansa yafi karfin yy irin wannan sana'ar while yana raye a doran 'kasa. A hk rayuwa ke tafiya musu tsakanin shi da mahaifin nasa, ko da Jibrin yayi fushi baya iya doguwar fushi da Adam 'din dole yake sakkowa amma still Adam ya kasa fahimtar sa. Time 'din daya gama schl ma kyautar mota ya bashi wacce ya tabbatar samari irin sa ke burin mallaka amma abin mamaki Adam ya ki ansa yace baya bukata, daga can makaranta ma aka bashi appointment da sunan sbd kyan da takaddun sa suka yi ne wannan ma Adam ya rufe idanu yace baya bukata kuma bai bari Hajiyar sa tasan da batun ba. Su biyu suke zaman su yanzu sakamakon rasuwa da mijin Hajiyar na karshe yayi bayan dawowar su daga Hajji, tun daga nan kuwa Hajiya Talatu ta ha'da duk kudaden wajen ta da mafi yawa daga 'Dan miliki suke ta bude wajen saida abinci, dan acewar ta ta gama aure yanzu, yayin da Adam ya tattara nashi da ya tara da gumin sa ya fara sana'ar sayar da kerosine, engine oil da sauran su a bakin titi, acewar sa ai wannan kam ba karkashin wani bane balle ai masa ma'kar'kashiya. Da zai tafi service sai da ya 'dora wani akai sannan ya tafi. Duk da yake Adam baya bada fuska amma sosai yadda 'Dan Malikin ke damuwa da lamarin Adam abin ke mata dadi, aganin ta ko ba komai dai dole Adam watarana za ya nemi uban nasa domin da uba ake ado, kuma ba laifi tana kokarin.yi masa fa'da kawai ya kasa fuskantar ta ne. Tsundum Jibrin ya fa'da harkar siyasa ya kuma yi nasarar da duk wani makusanta da masoyan sa suka taya shi farin ciki, yayin da 6angaren Adam abin ba haka yake ba dan ko a jikin sa ma, ko yaji cewa abin ya masa aran sa ma bai ji ba, aganin sa tunda ya kasa kula da lafiya da farin cikin mahaifiyar sa ya kuma kasa sauke hakkin sa dake kansa matsayin sa na uba toh meze dame sa da shi. Adam kyakkyawan saurayi ne fari mai matsakaicin tsayi, tsabta da nutsuwa kusan sune suka karbi gaba wajen bayyanar da asalin kyawun da yake da shi gashi da kyakkyawar mu'amala. Ba karamin buri Hajiya take ci akan saba kwatsam sai Zaitun ta fa'do cikin rayuwar sa batare da Hajiyan ta farga ba, bata yi kasa a gwaiba wajen shiga tsakanin su da nuna mata nisan tazara dake tsakanin Adam da ita, ta kuma yi nasara sakamakon sanin da Zaitun ta yiwa sunan 'Dan Maliki badan tasan shi a fuska ba amma tasan babba ne shi a 'kasan nan, ta kuma san waye mahaifin ta tasan gaskiyar Hajiyan ne akwai tazara tsakanin su duk da Adam bai ta6a gwada mata hakan ba. Kwatsam alhini da jimamin rashin Zaitun bai bar zuciyar sa ba labari ya isko shi cewar wata babbar mota tayi fatali da kayan sana'ar sa na bakin titi komai ya lalace, yaron ma Allah ka'dai ya sa ya tsira da kadan motar ta bi kansa, hankalin Adam ya tashi sosai dan har kwalla sai da ya zubar da jin wannan labari amma daga baya da ya tsaida tunanin sa sai zuciyar sa ta sanar da shi waye sanadi bai kuma yi mamaki ba dan yasan fiye da hakan ma zai iya aikatawa dan ganin ya durkusar da shi ta yadda dole sai ya ja hankalin sa ya fito duniya ya nuna cewar shi 'din 'da ne agare shi shi kuma bai ji zai iya hakan ba. Salmerh😘 [20/9/2022, 12:34 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Wattpad@* *Serlmerh-md* 🅿️ *...27* ......Haushin fatali da 6arnatar masa dukiya da akai batare da wata 'kwak'kwarar dalili ba ya sashi yanke shawarar zuwa ga 'Dan Maliki suyi magana ta fuska da fuska, yana so ya fito masa a mutun ya nuna masa gaskiyar cewa ya gaji ya kuma kai 'karshen bango, yana so a sarara masa haka nan, kuma inda hali baya so ya 'kara shiga sabgar rayuwar sa, shike da ikon za6arwa kansa duk irin sana'ar da yake so ya kuma ga ta kwanta masa dan haka ya 'kyale shi, ko kwasar kwata zai yi babu ruwan kowa da shi. Sun tattauna da Hafeez kan hakan lokacin da yazo yi masa jajen lamarin ya kuma so dakatar da Adam 'din kan cewa da yayi zai sami 'Dan Malikin tunda a zahiri babu wata alama da ta bayyana da sa hannun sa ciki. Amma Adam sam ya ki amincewa da batun Hafeez domin acewar sa shi ya san waye 'Dan Malikin da duk shirin sa, dan haka in zai raka shi toh bismillah in kuwa baza shi ba ma duk ba matsala bace agare shi zai iya zuwa shi ka'dai. Da wannan tunanin ya ringa kwana yana tashi har zuwa ranar da ya samu lkcn zuwa ga 'Dan Maliki domin ganawar bisa tursasawar sa ga Hafeez dole sai da ya raka shi. Unfortunately sai basu je kan sa'a ba sakamakon katari da mugun gani da suka yi shi har Hafeez 'din babu wanda bai tsinci kansa cikin tashin hankali ba. Duk wa'danda ke aiki tare da mahaifin nasa zuwa lokacin sun riga da sun san kakkarfar alaka da ke tsakanin sa da Adam dan haka koda ya nemi ganin sa bai samu wata matsala ba, sai dai cikin rashin sa'a sun same shi ne tare da wasu watsatstsun 'yan mata, ba sai an fa'da masa ba domin a yanayin da ya gansu amsar shi ta riga ta bayyana a fili karara, ya kuma san already matar da yake aure tana can Abuja da zama kuma ita babbar macece ba kamar 'yan matan da ya gani tare da shi ba, wa'danda yana da tabbaci ba dan ku'di da suke samu daga 'Dan Malikin ba da bb abinda zai sa su saurare shi ma sbd shekaru da suka bayyana gareshi 'karara. Fa'din halin da Adam ya tsinci zuciyar sa a wannan ranar ma 6ata lkc ne, abin ya matukar ka'da shi, sosai yayi masa ciwo a zuci, yayi ba'kin ciki irin wanda ya jima bai yi irin sa ba, haka ya fito batare da ya tsaya bi takan hatta Hafeez ba ma balle ya jira su yi maganar da ta kaishi da Alhajin, tafiyar ma yin ta kawai yk amma dishi dishi yk gani, baya so ya 'kara koda minti guda cikin gidan baya ga haka da babu abinda zai hana shi samawa kansa hutu, sai dai yafi bukatar barin gidan akan hutun da yake ji kamar yana da bukata saboda tsananin yadda bugun zuciyar ya karu yake kuma masa barazanar 'dauke masa numfashi. Yana jin yadda 'Dan Malikin ke kwala kiran sunan sa da nufin dakatar da shi amma bai ko waigo ba bai ma nuna alamun yaji kiran ba, kuma baya da niyyan tsayawa kamar yadda bashi da burin sake ganin fuskar 'Dan Malikin gaban idanun sa. Kallo 'daya zakai masa ka tabbatar ba cikin hayyacin sa yake ba, tafiya kawai yake bama ya sanin ina yk jefa kafar sa balle yasan inda ya dosa, haka kawai sai yaga kamar harabar gidan ya 'kara fa'di da tsayi ne, duk 'ko'karin da yake wajen ganin ya fitar da kansa cikin gidan amma abin ya faskara, bai ta6a fahimtar girman da gidan ke dashi ba sai a wannan lokaci. Gaba 'daya fuskar sa da idanun sa sun koma jajaye, jijiyoyin kansa da gashin jikin sa sun mimmike, banda wani dun'kulallen abu da ya tokare masa kirji yai masa nauyi sosai...cikin ransa yk ji tamkar ba zai yi tsawon rayuwa ba aduniyan nan, kuma shi akaran kansa ma yafi son hakan da ya cigaba da rayuwa yana cin karo da irin wagga lamari daga mahaifin sa gara ace bashi ma a duniyar yafi a ganin sa kenan. " Har sai yaushe? sai yaushe ne zai canza? Duk da wannan shekarun amma har yanzu bb abinda ya canza game da shi? Sai yaushe zai samu cikakken farin ciki daga mahaifin nasa? sai yaushe zai fuskanci rayuwa ya san cewa annabi ya kafu, sai yaushe tsoron Allah zai dasu masa a zuciya? sai da wani lokaci zai san cewa shi 'din yanzu ba yaro bane shekarun sa sun ja sosai, sai yaushe ne shi kansa zai samu cikakkiyar adalci daga mahaifin nasa? tun yana cikin mahaifiyar sa bai samu kula da adalci daga gareshi yadda ya kamata ba sai yaushe ne zai samu hakan wai? Yaushe wannan mutumin zai bari ta6on da ya dade cikin zuciyar sa ya warke gaba 'daya?" Duk yadda 'Dan Maliki yaso dakatar da shi 'kin tsayawa yayi za'a iya cewa ma bai san yanayi ba, tunani ne da tarin tambayoyi fal kirjin sa. Sai dai kafin ya kai ga isa gate 'din da zai fitar da shi daga gidan tuni 'Dan Maliki ya bada umarnin adawo masa da shi, haka securites 'din sa suka cicci6o Adam suka dawo dashi gaban sa bayan sun sha fama da shi, uku daga cikin su sai da suka amshi lafiyayyyun mari daga gareshi amma bai dame su ba, burin su kawai su cika umarnin shugaban su ne, da yake ance sarkin yawa yafi sarkin karfi haka badan yaso ba bisa dole suka dawo dashi gaban 'Dan Malikin suka juya suka fita. Kallon kallo suka tsaya yi tsakanin sa da 'Dan Malikin bai kuma sake ganin 'yan mata guda biyu daya gani 'dazun tare da shi suna yi masa tausa cikin mummunar shiga kuma mafi munin ma a nan palor ba, bai kuma ga Hafeez ba. Bai san takamamme me yk ji game da 'Dan Maliki ba amma daga jiki har zuciyar sa yk jin baya bu'katar ganin mutumin kwata- kwata, yana ji da ace yana da iko da tuni ya saka almakashi ya datse duk wata alakar dake tsakanin sa da shi, duk da baya so ya tabbatar wa zuciyar sa hakan amma can 'kasan ransa yake jin tsana mafi muni na ginuwa masa kan mutumin, ba 'karamin jinjinawa 'karfin hali irin nasa yayi ba da har ya iya tsayawa ya dubi cikin idanun sa ma bayan duk wannan abin da shi idanun sa suka gane masa...shi da kansa kunyar kansa da kansa Adam yake yi amma me yasa 'Dan Malikin bai ji kunyar abinda ya aikata ba? Idanun sa yayi 'ko'karin kawar wa ga barin duban mahaifin nasa a daidai kuma lokacin da sautin muryar sa ya kara'de kunnuwan Adam. " Dan Allah ka gafarce ni Adam, kayi hakuri..."! Shine abinda ya fito bakin 'Dan Maliki yana mai lumshe idanu gami da juyawa Adam baya. Bai tanka ba bai kuma yi niyyar tankawan ba dan bashi da kalma ko guda cikin kirjin sa da harshen sa zai iya furta ga 'Dan Maliki a wannan ga6ar. Fahimtar cewa bazai tankan bane ya sanya 'Dan Maliki cigaba da magana batare da ya sake duban idanun Adam 'din ba, ba 'karya tsananin kunya da nauyin yaron nasa yake ji ba tun yau ba ba kuma yanzu ba, kawai dannewa yake a 'ko'karin sa na ganin ya dake gudun kar ya raunata tunanin Adam 'din gaba 'daya, balle abinda ya faru yau din dole matsayin sa na uba yaji kunyar sa koda kuwa ace ba 'dan sa na cikin sa da ya haifa bane da kunya balle ya sani sarai shi din gudan jinin sa ne cikakken mahaifi yake agare shi da babu madadin sa a kaf fa'din duniyar nan. " Nasan ban kyauta maka ba kuma har a yanzun bana kyauta maka nasani dan girman Allah Adam kayi hakuri...". Kicin- kicin Adam yayi da fuska, taya ma zai yi saurin ha'da shi da Allah kan wani shirmen sa can, da can bai san da girman Allahn bane yake sheke ayar sa batare da tsoron sa ko sanin girman sa ba, ko ko bai ta6a tunanin akwai ranar da Allah da kansa zai yi ram da shi ba bane, shin jira yake a sanar dashi cewa ya girmi irin wannan abubuwan ko ko jira yake sai shekarun nasa da kansu sun sanar da shi? " In yi hakuri kace...? Laifin me kayi min ni kuma?" Adam ya tambaya cike da 'karfin hali, baya jin idan ya cigaba da tsayawa gaban mutumin nan da wani lokaci za'a iya samun numfashi tattare da shi a yadda yk jin 'kirjin sa.... " ba hurumi na bane ban kuma cancanci hakuri daga gareka ba ni ko kadan ma ni bani da alaka da hakan, meyasa kake bani hakuri...?". Adam ya 'karashe da fitar da huci mai zafi yana jin kansa na 'ko'karin juyawa. " Ni dai nace kayi hakuri.." Shima 'Dan maliki yayi saurin taran sa da fa'din hakan, bai kuma sarara ba yaci gaba da fa'din" nasha yi maka bayani abaya ba sai na sake maimaitawa yanzun ba Adam, dan hk akan abinda ya riga ya wuce nake baka ha'kuri ka yafe min, abinda idanun ka suka gani yau kuma shima zan iya cewa kayi hakuri, nasan bai kamata in budi baki in furta kalmar hakuri agare ka ba kamar yadda nasan ban cancanci zama uba ga mutun kamili irin ka ba saboda kalmar hakuri tayi ka'dan, amma dan Allah Adam ba dan niba, ba kuma dan halayyata kar ka dubi wannan ka gafarce ni, hakika na matukar jin kunya gami da nadamar abinda ya faru, nasan ban kyauta ba, ban kuma yi amfani da lokaci na ta hanyar da ta dace ba, ban yi ribaci arzikin rai da lafia da Allah ya azurta da su ta hanyoyin da suka dace ba sbd son zuciya ta, na manta da shekaru na, na manta cewa lokaci na nake kararwa a banza, na manta cewa watarana Allah zai iya kunyata ni dan mutuncin da jama'a ke gani na da shi zai iya tafiya, na manta cewa mutuwa na iya riskata a kowani lokaci, hakika nayi nadama Adam ban kuma ji dadin yadda ka tarar da ni ba..." " Hmm.." Adam yace yana gyara tsayuwar sa gami da kawar da kai gefe, daga shi har kalaman nasa babu wanda yake jin suna shigan shi bama ya jin cewa nadamar yayi dagaske kamar yadda yake zayyanawa... " Me kuma yayi saura...?a ganin sa komai ma ya kare ne, babu wani sauran mutuncin da ya rage musu..." Wani kallo Adam ke yi masa irin kallon nan na ka ma raina wa kanka hankali har ya kai 'karshen maganar sannan cike da bakin rai idanun sa jajir banda huci da yake ji na fito masa daga 'kirjin sa. "...ni duk ba wannan ne ya kawo ni ba, abinda ya kawo ni gare ka daban ne, tsarin rayuwar ka taka ce, mutunci naka ne...so ka zubda su ko kuma ka basu daraja wannan duk ra'ayin ka ne ba damuwa ta bane ba kuma sune a gabana ba, ka aikata duk son zuciyar ka rayuwar ka ce kai kadai..amma da irin wannan kake so ni in dawo gareka na rayu tare da kai..?" Kai ya girgiza yana fa'din" har abada! kamar yadda abaya ka horar da ni da rashin zama tare da kai ka koya min rashin shakuwa da kai da ma kowa naka toh akan hakan na ginu kuma har gobe, har jibi, satikai watanni, shekara shekaru ma bana jin hakan zai canza a zuciya ta" Ya 'karashe da fitar da numfashi me zafi, shikan sa fa'da kawai yake dan ya karasa jagula lissafin Alhajin ba wai dan dagaske abin bai dame sa ba kokari sosai yake wajen dannewa, 'dagowa yayi ya dubi gefen da 'Dan Maliki ke tsaye kallo 'daya yai masa ya 'dauke kansa, duk yadda yk jin kirjin sa na tsanan ta ciwo amma ya kudurta cikin ransa cewa a yau 'din sai ya isar da sakon da ya kawo shi, duk da ba da irin wannan niyyan yazo ba amma yanayi yasa manufar sa dole ya canza dan hk ya cigaba... " Alhaji bazan iya rayuwa da mutumin da son zuciyar sa ya rufe masa ido ya hana shi ganin dai dai ba, son zuciyar sa bai sa ya iya yakan zuciyar sa wajen ganin ya bar ko guda cikin halayyar sa ba, bayaga haka ma ni miye nawa? miye laifi na aciki? ko laifi ne zamtowa da nayi matsayin 'da awajen ka? Ko kuwa rashin kirkin da baka 'karasar kan mahaifiya ta tun a wancan shekarun bane kake 'kokarin 'karasa shi akaina? Me na maka da kowani lokaci baka da buri illah ka tozarta ni? Me nai maka da bazaka barni inyi rayuwa ta cikin salama irin wacce nayi abaya tun ina yaro ba? naace bana bu'katar tallafin ka bana bu'katar komai daga gareka, bana bukatar duk wani abu daya dangance ka meyasa bazaka barni ba? Meyasa sai ka shiga rayuwa ta a koda yaushe? Ban rayu da sanin inada mahaifi ba tun alokacin da na fi bukatar hakan meyasa sai yanzu?... sunan ka ka'dai da na kasance tare da shi illah ya yiwa rabin zuciya ta a karo na farko..." Ya fa'di hakan yana me 'daura hannun sa bisa kirjin sa saitin zuciyar sa, yana sake tuno yadda Hajiyar sa tayi amfani da sunan 'dan Maliki ta tarwatsa masa tsaftatacciyar soyayyar sa ta rushe duk wani burin sa kan Zaitun. " Kasantuwar ka tare da ni a kullun sake illata ni yake Alhaji so kake in bar maka duniyar ne ko gani na a duniyar gaba 'daya ne baka bukata?...in haka ne dan Allah kawai ka kashe ni Alhaji! kasa hannun ka ka rabani da numfashi na lokaci guda ba ka ringa kashe ni kowacce rana ba Alhaji, ka 'dauko makami ka kashe ni nima in huta a duniyar nan baki 'daya....." Ya karashe maganar a 'dan zafafe yana jin zafin zuciyar sa na karuwa dai-dai da sau'kar tagwayen mari da ya ziyarci gefe da gefen fuskar sa a lokaci guda. Bai damu yasan waye 'dayan da ya mare shin ba illah hannu 'daya da ya kai ya dafe gefen kuncin da ya tabbatar hannun 'Dan Maliki ne ya sau'ka a wajen, hawaye yaji ya cika masa idanu lokacin daya tsinkayi sautin muryar Hafeez yana fa'din" baka da hankali ne Adam..haba!..Haba dan Allah Shaheed ina ilimin ka da sanin yakamatan ka ya tafi? mahaifin ka ne fa kake furta masa irin wannan kalaman...?" Kan gwiwowin sa ya sulale ya sau'ka a hankali cike da raunin da dole idan ka dube shi sai ka tausaya masa, dai- dai lokacin da hawayen da suka cika masa idanu suka gangaro, sarai yaji abinda Hafeez ya fa'da amma bai bi takan zancen ba kamar yadda bai damu yasan iya tsawon lkcn da Hafeez ya 'dauka tare da su a Palorn ba, yana shafa gefen fuskar tasa hawaye masu zafi na sau'ko masa idanun sa kan 'kafafun 'dan Maliki yake fa'din. "....Ka mareni..? da hannun ka ka mari fuska ta yau Alhaji..? abinda na da'de ina mura'din gani? abinda na jima ina son ganin ya faru dani, abu guda da nake tsananin so nima inga mahaifina ya min watarana amma ban ta6a samu ba, ban ta6a yin arzikin samun hukunci daga mahaifi na bisa wani laifi ba ko daidai da rana guda ba...Hafeez yau Alhaji mari na yayi da hannun sa saman fuska ta...". Hawaye Hafeez ya share da sauri yana jin tausayin abokin nasa na sake cika shi, batun yau yake jin tausayin abokin nasa cikin ransa ba, batun yau yasan babbar damuwar sa ba a rayuwa dan kusan duk wata damuwar Shaheed da Hafeez yake tattauna ta, shiyasa shima yake matukar kaunar sa har cikin ransa yake kuma biye da duk wasu lamuran sa na rayuwa, yasan bai ta6a samun yadda yake so daga mahaifin sa ba, ya rayu cikin tsananin kewar abubuwa da dama cikin rayuwar sa, duk kuwa yadda yake 'kaunar ganin ya kasance tare da mahaifin nasa amma bai ta6a nuna hakan a fili ba. Yasha kama shi yana share 'kwalla a duk lokacin da ya ziyarci gidan su ya kuma ga yadda mahaifan sa ke nuna kulawa da yin nan nan da shi, sau tari idan mahaifin Hafeez ya zaunar da su yana musu fa'da kan wani abin ko kuma nasiha kawai game da halin rayuwa Adam da hawaye yake tashi a wajen dan shi bai ta6a samun irin haka daga nasa mahaifin ba, ko da fa'da mahaifin sa ya masa har ta kai ga hukunci hakan ba karamin birge Adam Shaheed yake ba har wani sa'in ba ya iya yin shiru ya kance " Hafeez kai kam kaji da'di..a kullun mahaifin ka burin sa shine gyara goben ka sa6anin ni da neman dukiya kadai ce agaban nawa mahaifin ba shi da damuwa da ni, irin 'dan hukuncin nan da ake samu wajen mahaifi ban ta6a samu ba, ba wai dan bana yin laifin ba kuma kawai dai bani da wannan gatan ne..." Sosai Hafeez ke tausaya masa duk da yake bashi da matsala wajen kulawar uwa dan Hajiya Talatu ta toshe duk wata kafa da zai iya sawa yaji cewa shi 'din maraya ne, amma ai dole ya ringa jin ba dadi idan ya tuna mahaifin sa na raye amma ba shi da damuwa da shi sam ba shine gaban sa ba yana nan ne yana rayuwa tamkar wanda mahaifiya da mahaifin sa suka bar duniya gaba 'daya, shi bai ma ta6a jin me irin makamanciyar tasa rayuwar ba. Duk da hakan a matsayin sa na aboki kuma me son ganin farin cikin sa yakan taushi zuciyar sa da furta masa kalaman kwantar da hankali sosai yake kokarin ganin ya nuna masa muhimmanci da kuma kaunar da mahaifin sa ke masa duk da bashi da tabbaci kan hakan amma mawuyaci ne ace mutun da 'dansa kuma ce babu kaunar dan nasa tattare da shi. Adam sam baya amincewa da zancen Hafeez, karara yake karya ta shi dan shi bai ta6a hango alamun kauna tattare da mahaifin san agare shi ba, yakan iya jero hujjoji kan hakan kwarara da shi kansa Hafeez 'din idan yaji bakin sa mutuwa yake yi dole yayi shiru, yasan ba laifin kowa bane face na 'Dan Maliki domin da ya kula da shi da duk hakan bai faru ba, duk da hakan baya fasa kwantar masa hankali da wasu kalaman duk da yasan ba wani tasiri suke yi ga Shaheed 'din ba amma hakan bai sa yy 'kasa a gwiwa ko daidai da rana guda ba tun ma basu kai hakan a shekaru ba har kawo lokacin da mahaifin nasa ya fara kokarin daidaita tsakanin sa da Shaheed 'din bai kyale shi haka nan ba, iya kokarin sa yana yi wajen ganin ya bada gudummuwar daidaituwar alaka tsakanin su amma har ayanzun Adam gani yake tamkar da wata manufa kawai mahaifin nasa ke neman su sasanta babu wata kauna da yake masa ta 'daa da mahaifi. Amma ba zai iya 'kyale shi ba, ba zai iya tsayawa yana ji yana kuma gani Adam 'din na furta muggan kalamai ga mahaifin nasa ya 'kyale shi ba, yasan cewa ya samu ilimi daidai gwargwado dan baya ga 6acin rai babu abinda zai sa Adam furta wasu kalaman sai dai ma yayi fa'da da nasiha ga wanda yaji ke 'ko'karin furta su. 'Dan Maliki dake tsaye shima hannun sa da ya mari Adam da shi ya ke bi da kallo ya kasa fahimtar me ma ya aikata ne? Me yasa ya mareshi ne...? did i suppose to slap him? Why should I...? " just because yace ka kashe shi da hannun ka ne kaji haushi har ka maresa. Wata zuciyar sa ta amsashi. Marin Adam yayi amma sai yake jin zafin hakan sosai cikin zuciyar sa, bisa dukkan alamu kuma sai ya lura tamkar farin ciki marin ya saka Adam ciki...abu ne da ya kamata ya sosa masa rai ganin tun da yake yaro bai bada wata gudummawa da ta dace agare shi ko kwara guds ba bai sauke hakkin sa da Allah ya dora masa ko guda ba amma sai gashi da girman sa tashin farko sai tsarabar mari ne ya biyo baya abin mamaki sai yaga abinda bai ta6a zato daga Adam 'din ba. Murmushi yake yana shafa wajen marin at same time kuma kwalla cike a idanun sa. Shin me hakan ke nufi? har haka Adam ke kaunar sa a zuciyar sa ne ko yaya? tsawon wani lokaci ya 'dauka yana cutar da zuciyar yaron bai sani ba, me yasa ya kasa fuskantar halin 'kunci da kewar da Adam ke ciki tsawon lokaci? shin me ma ya 'dauki hankalin sa ya manta da lamarin sa har haka ne...? Duk cikin zuciyar sa yake wannan tunanin yayin da a zahiri ko inda Adam yake dur'kushe bai iya ya yayi wa kyakykyawan kallo ba, nawi da kunya gami da tsananin haushin kansa ne suka cika shi. Salmerh😘 [20/9/2022, 12:34 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* Wattpad@ Serlmerh-md 🅿️ *...28* .......Idanu Adam ya lumshe wani zazzafan hawayen na sake 6ul6ulo masa, batare da ya bu'de idanun ba ya cigaba da fa'din..." tun ina saka rai akan watarana zaka zo gare ni ka nuna min kauna da kulawa kamar yadda naga ake bawa sauran mutane kamata har nazo na fara fahimtar so na ne kawai baka yi shiyasa baka ta6a damuwa da lamari na ba, baka ta6a tuna cewa ka bar marayan yaro a hannun wata mace ba, baka tunanin yaro na yana rayuwa cikin duniya ban san halin da yake ciki ba, baka damu da lafiya ta ba, ci na ko sha na duk ba sune gaban ka ba, baka damu da ilimi na ba baka damu da yanayin tarbiya da halin rayuwa da zan iya fuskanta ba, baka damu da amanar da Allah ya dam'ka maka akaina ba, dukiyar ka ka'dai ce agaban ka, burin ka kawai shine ka tara arziki, kayi rayuwar ka duk yadda kake so batare da tuna cewa Allah na ganin ka ba, shin baka jin kunyar duk abubuwan da kake aikatawa ne Alhaji? Meyasa ka za6i wannan hanyar wajen salwantar da ni dama dukiyar ka batare da tsoron Allah ba? batare da tuna cewa ni har dukiyar taka duk 'din mu amana Allah ya baka ba? Ka wofintar da ni ka barwa duniya ni ka za6i wa'dansu daban suka maye maka gurbi na, kuma na tabbata da mahaifiya ta na raye bazata ta6a yin watsi da ni da lamari na kamar yadda kai ka aikata ba, sau da dama na kan tuhumi kaina da zamtowa 'daa agare ka a mafi yawan lokuta na kan ce dama ba kai Allah ya za6a min matsayin mahaifi ba dan na tabbatar kai kanka baka shirya kar6a ta matsayin 'daa a lokacin da Allah ya azurta ka da samu na ba, sai da kaga na girma? Ciwo na ya ri'ka? 'Kunci ya gama mamaya ta? na gama gwagwarmayar rayuwa ta, na bar dukkan 'kalubale da na fuskanta abaya, karfi na ya fara kawowa na fara mantawa da damuwa da rashin ka kusa dani, lokacin da na fara burin gina rayuwa ta da halali na a lokacin ne zaka ce zaka tallafi rayuwa ta..? ka 'dauka ni 'din bani da zuciya cikin kirji na ne..? shin inada laifi ne idan nace bana bukatar komai daga gare ka? Alhaji ka bani amsar tambaya ta ina so in ji amsa ta daga bakin ka ne shin inada laifi ko guda anan....?". Ya 'karashe maganar yana jin 'karin nawi cikin kirjin sa saboda rarrabuwar numfashi daya fara fuskanta, maganar ma da 'kyar ya 'karasa ta amma dan 'karfin hali ya dage sai yayi, inda ya 'karashe da wara idanu kan Alhajin yana faman dafe 'kirji sakamakon tari da ya sarke shi. Hafeez da ya fahimci yana jin jiki da sauri ya iso gare shi yana kokarin kwantar masa da hankali, yasan dama lafiya ba isan Adam din sosai tayi ba amma taurin rai irin na Adam har na bashi tsoro wani lokaci, duk yadda yake da dauriya ji yadda yake dafe kirjin sa da gani kasan bisa dole yake hkn, ya da'de yana fama da ciwon zuciyar da babu wanda yasan farkon sa sai Allah mahalicci. Hannun sa da Hafeez ya kama yayi saurin fisgewa..." ka barni Hafeez, ka barni in tambaye shi abinda ya da'de yake damu na cikin zuciya ta, ban ta6a ganin halitta mafi tsananin son kai irin wannan mutumin ba ka bar ni in tambaye shi ya bani amsar tambaya ta.." " Haba Adam! haba dan Allah baka ganin halin da kake ciki ne baka ganin yanayin kane? kar fa ka manta condition da kake ciki fa..."Cewar Hafeez ga Adam cike da kulawa. " Ba wannan ne damuwa ta ba Hafeez, please let him answer my question, ya tsangwami rayuwa ta, ya hana ni fuskantar rayuwata, shi lokacin da ya fara tashi rayuwar waye ya taka masa birki, ko akwai wanda ya ce lallai lallai dole shi zai za6a masa sana'ar yi ?" Idon Hafeez cikin na Adam yake masa kallon rashin jin dadin kalaman sa, kai ya girgiza masa gami da lumshe ido yayi kasa da kansa. Sosai Adam ya fahimci Hafeez dan ba sanin yau ke tsakanin su ba, sani ce mai cike da fahimtar da juna ya kuma san Hafeez da zuciya 'daya yake 'kaunar sa. Shima 'din 'kasa yayi da nasa kan yana mai zazzafan numfashi yayin da Hafeez ya cigaba da fa'din.." Bana jin da'din kalaman naka Adam, please mu koma gida...". Ya 'karashe maganar ya tallafo hannun Adam da nufin mi'kar da dashi. 'Dan Maliki dake tsaye ne yayi saurin dakatar da shi da 'daga masa hannu gami da fa'din"...Kaga barshi yayi maganar sa, barshi ya amaryar da duk abinda ke ransa, na cancanci kowace irin magana ce daga gare shi a yanzun matukar zai sa ya fuskance ni, kuma shima na tabbatar hakan zai fi sama masa sauki a zuciya..". Shiru Hafeez yayi illa jinjina kai da yayi yana duban Adam 'din. Bai damu da duk irin maganganun da suka wanzu tsakanin Hafeez da 'Dan Malikin ba illah sake maida duban sa da yayi ga 'Dan Malikin ya cigaba da fa'din" Ina da ciwo a zuciya ta wanda na kamu da shi duk ta dalilin damuwar ka ka ta6a sanin hakan..? Tsam 'Dan Maliki yayi da ransa idanun sa kir kan Adam 'dun cike da al'jabin.jin furucin sa. Haka ma Hafeez duban abokin nasa yake babu ko kiftawa " Tsawon lokaci ina 6oyewa Hajiyata ciwo na gudun kar hankalin ta ya tashi saboda ita ka'dai gareni a duniyar nan da ace ka damu dani duk da na san kaddara ta kenan amma da ka nuna min kauna kana tunanin hakan zai faru da ni ne..? damuwa ta kullun 'kara yawaita take kamar yadda shekaru na suke karuwa kowacce rana, damar sanin dalilin ka na barwa dunia ni har yau na kasa sani, dan Allah Alhaji yau ka'dai gani agaban ka ka sanar da ni meyasa baka kauna ta? Laifin me nai maka a rayuwa da ka tsane ni ka tsani ganin farin ciki na? ka za6i gani na cikin kewa da 'kuncin zuciya da damuwa tsawon lokaci? Shin laifi ne dan na kasance 'daa agare ka ka sanar dani....". Kasa bashi amsa ko guda daga cikin tambayoyin nasa 'Dan Maliki yayi illa tahowa da yayi a hankali yana jin 'kafafun sa tamkar bazasu iya 'daukar sa ba, 'dago Adam yayi ya rungume sosai cikin jikin sa a karo na farkon kaf 'din rayuwar su, kowa 'kwalla yake zubdawa, rungumar da rabon da yayi masa tun ranar da aka haife shi yazo ya tadda mahaifiyar sa ta koma ga Allah bayan ta haifa masa shi, wani 'kauna da tausayin Adam ke ratsa masa dukkan ga6o6in jiki wanda bai ta6a zaton yana masa irin sa ba sai a yau 'din. Yasan Adam ya fishi gaskia, yasan ya fishi tarin hujjoji ya kuma ninkasa juriya da hakuri shiyasa bai ga laifin sa ko guda cikin duk irin kalaman da ya furta ba, amma me ya sha kansa ya mance da lamarin yaron sa har haka ne a rayuwa, meyasa be ta6a tunanin 'dansa zai rayu da kewar mahaifin sa ba, ina tunanin sa ya tafi ya mance da lamarin mafi soyuwar 'da guda 'daya tak da Allah ya bashi a fa'din duniyar nan? Me yasa bai ta6a mai da hankali ya fuskanci irin tarin kaunar da Adam ke masa ne yasa yake dukkan abubuwan da yake aikatawa ba, meyasa ya kasa fahimtar haushi yasa Adam ke ta guje masa da duk wani abu da ya shafe shi ba? gashi dai ya tara dukiyar ya kuma samu soyayyar mutane, ya yi suna fin yadda ma shi ya tsammaci zai iya yi, sai dai a yanzu baya jin duk yana da bukatar su sama da farin cikin gudan jinin sa, sosai yayi nadamar komai da ya aikata tun ma kafin a haifi Adam har zuwa yau 'din dayake rungume da shi cikin jikin sa nadama duk ta baibaye shi. Gaskiyar Adam ne, gaskiyar sa ce da ya ce yayi watsi da amanar da Allah ya bashi ya banzatar da shi. Dukiyar banza, neman sunan banza, banda tarin zunubbai ma me dukiyar ta tsinana masa...? Tsawon mintina biyar suna a hakan sannan ya ciro shi yana share masa hawaye shi har Adam 'din babu wanda ya iya kallon cikin idanun juna da hannuwan sa duk biyu ya dafe gefe da gefen kafadun Adam da wani taushin murya ya fara magana..." Ka daina kuka kaji, na baka dama idan kalaman da ke cikin zuciyar ka basu 'kare ba duk ka fitar da su, ka fa'da min dukkan laifi na har sai kaji zuciyar ka tayi sanyi sannan ka sarara.." Shiru dukkan su suka yi babu wanda ya sake furta komai, 'Dan Maliki na karantar yanayin fuskar Adam 'din ne yayin da Adam yake jin lamarin ba'ko agare shi shiyasa ya kasa tsaida zuciyar sa wuri guda balle har bakin sa ya iya furta wata kalma. "...Nasani ni'din mai laifi ne, amma hakan ba zai hanani sanar da kai abu guda zuwa biyu ba, duk da nasan ba lallai ne ka amince ba amma ina tabbatar maka iya gaskiya ta kenan, kar ka sake tunanin ni Jibrin 'Dan Maliki bana kaunar ka, sannan kar ka sake ji aranka cewa ban shirya kar6ar ka matsayin 'daa ba, wa nake da shi a duniyan kaf ban da kai Adam? Idan ban 'kaunace ka ba wa zan 'kauna ta? wallahi yadda nake kaunar ka ban ta6a jin abinda ya kai ka muhimmanci cikin zuciya ta ba, duk abinda kake tunani akaina ba haka bane Adam, taya ma zan iya wofintar da rayuwar yaro na guda a duniya, ta ya zan yi watsi da kai da duk abinda ya shafe ka gaba 'daya, wallahi Adam kullum kana zuciya ta, in samu lokacin da zan ware saboda kai ne abin ke gagarata ban kuma san dalili ba, sai da nasan dukkan bawa dama da kalan tashi jarrabawar, babu mamaki ni har kai 'din kalar jarrabawar da Allah yaso yi mana kenan, amma ka gafarce ni...duk abinda kake son ji game dani zan sanar da kai yanzun nan komai da kake bukata zaka jishi a yanzun, zauna anan ina zuwa..." Ya 'karashe maganar da zaunar da Adam bisa 'daya daga cikin hanshakan kujerun dake palorn. Tuni Hafeez ya fice abinsa ya basu waje, shi kansa gaba 'daya jikin sa yayi sanyi, yana matukar son yaga an samu cikakken sasanci da kyakkyawar fahimta tsakanin abokin nasa da mahaifin sa, amma bai so abin ya kasance ta wannan sigar ba, bai ta6a fatan ranar da zai ji ko ganin Adam na furta zafafan kalamai ga mahaifin nasa ba, yaso maslahar tazo cikin nastuwa sai dai wani 6arin zuciyar sa bai ga laifin sa ba, musamman idan yayi la'akari da cewa ayau 'din sun ci karo ne da abinda shi har Adam 'din basu ta6a tsammata ba haka kuma tunanin sa matsayin 'daa agare shi mawuyaci ne ya iya jurewa, bai ta6a sanin har yau mahaifin nasa na hul'da da matan banza ba amma ya gode Allah da ya ji Adam bai furta su ga Alhajin ba, bai tsammaci zai kawar da wancan batun ba dan yasan halin Adam da 'dan banzan zuciya..amma yadda yayin ya matukar birgeshi..can 'kasan ransa yake jin wani tarin farin ciki marar musaltuwa, fatan sa Allah ya tsayar da lamarin haka nan..Allah yasa wannan haduwar tasu ta zam silar shiryuwar 'Dan Maliki ta kuma zam silar samun sassauci wa zuciyar Adam. Yau 'din da kansa yaci alwashin yiwa Hajiya Talatu albishir 'din wannan lamari, yasan zata fi kowa jin dadin jin samun sasanci da fahimtar juna tsakanin Adam da mahaifin nasa...duk da ya lura dama mahaifin nasa ya 'dan kwana biyu yana neman sasancin Adam ne ke bijirewa, fatan sa ayau komai ya kammala tsakanin su shiyasa ya fito ya basu waje. Da goran ruwa 'Dan Maliki ya dawo da kuma glasscup a 'daya hannun sa, inda ya mikawa Adam cup 'din da nufin shi da kansa ya sa masa ruwan amma Adam bai bi takan cup din ba ya kar6i ruwan ya 6alle marfin ya kafa a baki bai cire ba sai da ya shanye tass. Yana cire goran yake sauke sassanyan ajiyan zuciya, kadan kadan yake jin zafin da zuciyar sa ya dade yake yi masa yadan sauka sai dai a tunanin sa hakan ya ta'allaka ne da ruwan da yasha kasancewar sa mai sanyi. Sau 'daya tak ya dubi fuskar 'Dan Maliki take ya kawar da kansa gefe cike da basarwa " Thanks". Yace batare da ya sake duban sa ba. Cak ya mike tsaye jin ya 'dan samu nutsuwa, kuma baya so 'yar natsuwar da ya samu ta barshi dan haka cikin ransa ya yanke shawarar barin gidan nan take. Juyawa mahaifin nasa baya yayi ya fuskanci 'kofar fita batare da ya sake duban sa ba, taku 'daya biyu yayi kafin ya kai gayin na uku 'Dan Maliki ya fahimci manufar sa hakan ya sa ya dakatar da shi da kiran sunan sa..." Adam..!" Cak ya tsaya amma bai juyo ba. " Shikenan haka zaka tafi? baka bukatar jin komai daga gare ni...?" Juyowa yayi ya dubi 'Dan Malikin kallon da bai fi na seconds biyu zuwa uku ba ya 'dauke idanun sa. " Zan tafi ne, I have a lots to do outside there...". " Har sun fi ni muhimmanci...? Sun fi tattaunawar da zaka zauna kayi dani muhimmanci...?" Kai ya girgiza masa gami da kankance idanu yace" Ko 'daya, kawai dai bana son 'karin fami ne bisa ciwon da ke zuciya ta, dan Allah kayi hakuri ina da burika da dama a rayuwa ta, matsalar dake tsakani na da kai a kullun shine farko sama da komai amma not this time..dama rokon ka ne ya kawo ni gidan nan, alfarmar ka nazo nema..." Hannun sa ya 'dago duk biyu ya ha'de waje guda alamar roko sannan ya cigaba da fadin..." Dan Allah ka barni nima na kafa sana'ata yadda ta dace ka daina rusa min hanyoyin samu na, zan 'kara tayar da wajen sana'ata a karo na biyu, ban ta6a neman alfarmar komai daga wajen ka ba a yau ina neman alfarma a karo na farko wannan karon ka bar min abu na, shekaru na na ja batare da na fuskanci inda na dosa ba kuma ina so nima inga na kula da Hajiya ta fiye da kulawar da ta bani a rayuwa ta, hakan kuma bazai ta6a faruwa ba sai ina da sana'a, na roke ka dan Allah Alhaji..." Daga haka ya juya batare da ya jira jin amsar komai daga mahaifin nasa ba yayi gaba. Kallon bayan sa 'Dan Maliki ya tsaya yi ya ma kasa fa'din komai. Wai dagaske yaron nan ya ke yi baya bu'katan dukiyar sa? baya bukatar komai daga gareshi, dagaske yake da kansa yake so sai ya kafa kansa bayan ya jima yana tara masa, toh miye amfanin neman da ya 'karashi ilahirin rayuwar sa yana yi...idanu ya lumshe cike da dakiya ya furta. " _...Adam Shaheed Jibrin Adam 'Dan- Maliki......."!_ *Comment nd Share to other groups* Salmerh😘 [20/9/2022, 12:34 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* Wattpad@ Serlmerh-md 🅿️ *...29* .........Cak ya tsaya yana jin zuciyar sa na harbawa da kai kawo jin yadda mahaifin nasa ya kira sunan sa abinda bai taba ji ba. " Kar ka manta da cikakken sunan ka da kuma waye mahaifin ka a duniyar nan..." "...Tun ina yaro ma ban ta6a mantawa ba balle yanzu.." ..." Well..kaje kayi sana'ar da duk kake ganin tayi maka bazan hana ka ba, amma ina sake jaddada maka cewa kai 'din jinin 'Dan Maliki ne kuma wani 6angare na rayuwar sa kar ka ta6a mancewa da wannan, ka kuma kula...". Adam bai ce da shi komai ba kawai ya fice daga palorn bayan ya juyo ya dube shi sau 'daya, da ace yana cikin mood mai kyau babu abinda zai hana shi murmushi da jin kalaman 'Dan Maliki amma baya cikin wannan yanayin a wannan lokaci, hanyar da yasan zata fitar da shi daga gidan ma gaba 'daya ya tunkara yana jinsa wani sakayau babu nauyi. A bakin gate ya tarar da Hafeez tare da gate man yayin da sauran securities 'din Alhajin ke gefe suna sha'anin su. Bai ce da Hafeez komai ba shima da ganin sa kawai ya taso suka fice yana wa gate man 'din sallama..daga haka suka bar gidan ma gaba 'daya inda suka bar 'Dan Maliki cike da zullumi da nadama matsananciya, sosai jikin sa yayi sanyi, raunin da bai ta6a fuskanta bace ta ke shigan sa a wannan lokaci, ji yake tamkar ya sulale ya 'dora hannu aka yayi ta ihun ta6argazar da yayi ta aikatawa, abu 'daya da a kullun yake gode Allah akai shine da bai tsaya duban halayyar sa ba ya bashi yaro nagartacce mai zuciya irin Adam. Babu ta yadda halayyar su tayi kama, shi'din tamkar kishiyar halayyar sa ya kwaso, babban abinda ya birge shi ga Adam 'din shine yadda koka'dan dukiyar sa basu dameshi ba, burin sa kawai ya tara nashi da gumin sa. Daga gidan Maliki basu zame ko'ina ba sai gidan su Adam Shaheed nan ma direct 6angaren sa. Hafeez ne yasa hannu ya bu'de 'dakin da suka shiga kuma ya maida ya rufe harda saka makulli. Adam kam kan kujera ya zauna yana dafe goshin sa, kadan kadan yake jin kwanciyar hankali na shigan sa, sai dai yasan mawuyaci ne ya samu kwanciyar hankalin gaba 'daya, wancan abin da ya gani ya kuma yi kokarin dannewa can kasan zuciyar sa bazai ta6a barin sa ya samu cikakken farin ciki ba. " Meyasa ne? " Why Alhaji? " Da wannan shekarun? " Kuma yaran cikin ka..? Hafeez ne da ya taho kanshi ya tsaya ya dakatar masa da tunanin da fadin..." kasan me nake ji kuwa...?" Dago idanu yayi gami da bude su akan Hafeez 'din tare da lumshewa ya kuma budewa nan take alamun ina jin ka. Hafeez da ya san ma'anar hakan sai cigaba yayi da fa'din..." Ji nake tamkar in ta dukan ka har sai ka suma"! Hafeez ya furta cike da jin haushi. Waro idanun yayi kan fuskar Hafeez da alamun tambaya amma bakin sa ya gaza furta wata kalma. "...ka bani haushi sosai, meyasa ka kasa tauna kalaman ka, ka kasa sassauta furuci da sautin muryar ka gare shi? Meyasa zaka sashi agaba kana furta duk abinda yazo bakin ka? Kaman ta mahaifi yake agare ka ne, ka manta cewar shine aljannar ka.." Ran Hafeez dagaske ya 6aci sosai da yatsa ya nuna Adam sannan ya cigaba da fadin" bari in fada maka wani abu Adam wallahi duk lalacewar masa tafi kashin shanu daraja, duk tsiya mahaifin ka ne, duk lalacewa da mugun halin sa mahaifi yake a wajen ka, nasan kuma kasan girma da darajar da iyaye suke da shi a wajen mu iyaye iyaye ne hara abada ba'a ta6a canzawa tuwo suna, kayi maza ka nemi yafiyan sa kafin lokaci ya kure maka ina fada maka". Ya karasar da daga murya. Adam Maida idanun sa yayi ya rufe sannan ya bude su kan fuskar Hafeez ganin yadda ya dauki zafi ne ya sashi bu'dan baki da 'kyar ya fara magana..." wai duk wannan zafin ran akan maganar nan ne? Hafeez harara ya banka masa batare da ya furta komai ba. murmushin gefen baki Adam yayi sannan cikin sigar lallashi yace" ka kwantar hankalin ka zanyi duk abinda kace amma ba yanzu ba, for now ka barshi nasan ban kyauta ba amma dole tasa nayi hakan, ya rayu ne kaf din rayuwar sa babu mai fada masa gaskia a yanzu kuma da nake da damar hakan bai kamata in yi wasa da wannan damar ba..." Shiru yayi na dan wani lokaci yana jin tukuki cikin ransa amma ya zai yi ya zam masa dole ne ya nema masa rufin asiri. Sai da ya kawar da kai gefe tamkar bazai yi magana ba sannan a hankali cike da rauni ya 'kira sunan Hafeez. Duban sa yayi gami da sauraron abinda yake son fada masa. " Hafeez nasan kai amini kake a wajena dan tabbas ka wuce aboki musamman a yanzu da muka yi tarayya wajen ganin abu guda, Hafeez ina rokon dan Allah abinda muka gani gidan Alhaji..." Bai ma jira ya karasa ba ya tare shi da fadin" kar ka damu kasa a ranka tamkar batare da ni kaje gidan ba, I promise u...u won't regrets trusting me..". Ajiyar zuciya Adam ya sauke ko ba komai matakin nutsuwar da ya 'dan samu ta kara hauhawa. Ya yadda da Hafeez kwatankwacin yardar da ya yiwa kansa, ya zame masa dole ne ya kare mutunci da martabar 'Dan Malikin duk da yasan ba lallai ne ya iya hakan ba, duba da cewar wanda ya gani ne kadai ya sani bai kuma san farkon lamarin ba balle karshen, baya shakka kan Hafeez dan ya masa farin sani, yasan shi din mutun ne mai kwatantata rikon amana iya iyawar sa..yasan indai ta wannan bangaren ne bazai samu matsala da Hafeez ba koda kuwa bai kara tada zancen ba amma da yake mutun akace shiyasa ya sake jaddadawa gami da rokon sa ya rufa wa mahaifin nasa asiri yadda dunia take ganin sa matsayin mutum mai mutunci da kyautatawa wanda hakan yasa jama'a kaunar sa lets it be.... ***** Tun daga wancan rana Jibrin 'Dan Maliki ya fara kokarin ganin ya gyara mu'amalar sa da ubangijin sa, ya kuma fara gyara dukkan wata 6araka dake cikin rayuwar sa gaba 'daya. 'Bangaren Adam kuwa tun da ya bar gidan Alhajin suka yi.magana da Hafeez bai sake tattauna al'amarin da kowa ba hatta da Hafeez 'din kuwa, sai ma killace kansa da yayi ya daina fita ko'ina, wannan karon ma jinyar zuciyar sa yake faman yi a 6oye batare da Hajiya Talatu ta sani ba. Hafeez ne kamar yadda yayi alwashi, shi ya labarta mata komai, ba 'karamin mamaki kuwa tayi ba ganin shi Adam 'din bai sanar da ita ba, hatta da shi kansa 'Dan Malikin bai ce da ita komai game da ha'duwar su da Adam Shaheed 'din ba. Tayi farin ciki sosai da fara wanzuwar shiri tsakanin Adam 'din da mahaifin sa. Ita kanta bazata so ganin Adam na fama da kewar mahaifin nasa ba bacin yana nan a raye. Sai dai itama bata ce da shi komai ba kawai ta zuba masa idanu dan ganin gudun ruwan sa. Shi da kansa ganin killace kan bazai masa ba kawai yasa ya sake harha'da 'yan ku'da'den sa ya tada wajen sana'ar tasa da zummar yin fito na fito wannan karon da duk wanda ya sake yun'kurin hana shi rawan gaban hantsi. Sosai ya sake ja baya da komai da ya shafi mahaifin nasa, hatta Hajiyar sa ma yanzu ba sosai suke samun zama tare ba, 'kunci ya yiwa zuciyar sa yawa, sau da dama ya kanji tamkar Jibrin 'Dan Malikin badluck yk ga rayuwar sa sai dai baya barin wannan tunanin yin tasiri a zuciyar sa, dan yasan koma ya yake dole mahaifin sane, koma me ya zama a duniyan nan dole ne ya kira shi da suna mahaifi, kuma yana 'kaunar sa bawai baya yi ba kawai rashin sha'kuwa da fahimta ne tsakanin su, in ya tuna hakan ma da wuri yake istighfari ya kawar da batun a ransa, yana kuma 'ko'karin yi musu addu'a shi har da mahaifiyar sa kowa da tashi kalar addu'ar...yana kuma fatan Allah ya bayyana masa Zaitun cikin kowacce sallar sa dan ita ka'dai ce macen da zuciyar sa ke tsananin muradi a kaf fa'din duniyar nan. Tsawon sati uku bai sake ji daga 'Dan Malikin ba, yayin da shirin sa na wajen sana'ar sa duk ya kammala har ma ya fara kasuwancin sa na Bunburutu, sai dai abin sai a hankali jarin bai kai wanda ya karye abaya karfi ba a hakan ma sai da Hajiya Talatu ta saka masa hannu kafin ya daidaita. Hankalin sa ya fara kwanciya damuwar sa ta fara raguwa yayin da 'kuncin dake zuciyar sa yake sulalewa a hankali, sosai yake jajircewa wajen tabbatarwa zuciyar sa cewa shi'din namiji ne, baya ga haka da tuni ya kwanta jinya a asbiti...amma Alhamdulillah duk wani nawi da yake ji a 'kirjin sa yanzu da sassauci sosai sai dai abinda ba'a rasa ba. 'Bangaren 'Dan Maliki ma yana ta 'ko'karin shirin sa a 6oye batare da shi Adam ya sani ba wanda yana yin komai ne da taimakon Hafeez daya fahimci amintacce ne ga Adam Shaheed 'din. Ashe duk ba wannan ne mugun ji da gani da zai kuma yi ga mahaifin nasa ba...kwatsam 'karar su Zaitun a kotu ta bayyana da bai ta6a zaton sake ganin ta cikin sauki haka nan ba, yana farin ciki da murnar ganin Zaitun yaje kotu da zummar ganawa da ita, domin ko kowa bai yadda ba shi dai yana da ya'kini 'kakkarfa cewa Zaitun bazata aikata abinda ake tuhumar ta dashi ba, yaushe ma tabar shi, yaushe ma ta rabu da shi da har za'a ce ta fa'da irin harkan nan sam bai ji ya yadda da mummunan zargin da ake mata ba. Zaitun batada burin tara dukiya, kudi sam basa gaban ta, yasan halin ta sarai burin ta a kullun Mufeeda ne, burin ta ta samawa yarinyar farin ciki, yasan mutun me 'karancin shekaru irin ta me kuma irin wancan burin mawuyaci ne ta sanya rayuwar ta cikin ha'dari saboda son dukia kawai, sosai ya ci burin sake magantuwa da mahaifin sa kan Zaitun 'din dan yasan yana da yadda zai yi kotu ta wanke ta. Kwatsam sai ga wani tashin hankalin kuma ya bayyana gareshi jin sunan mahaifin na sa ya fito cikin manyan masu 'daukar nawin laifiin a bazata. Tuni raunin sa ya bayyana 'karara, taya zuciyar sa zai iya 'daukan duk wannan nauyin? mutane biyu ne masu matukar muhimmanci da daraja a zuciyar sa sama da kowa, amma baya da ikon taimaka musu ta ko'ina, bashi da dama, banda nawi babu abinda zuciyar sa ya karu da shi...nawin da yake farin ciki da sulelalewar sa daga kirjin sa sai gashi tashin farko yayi dawowar lokaci guda tamkar saukar aradu. Duk yadda yaso ya cigaba da daurewa hakan ya gagare sa, duk yadda yaso nuna 'karfin hali sam yakasa aikata hakan, yaso sake ziyarar kotun ko sauraren shari'ar ma yayi amma ya kasa, taya zai iya zuwa ya zauna ya zuba musu idanu bacin bashi da hanyar basu kariya ko ta wacce hanya, sam bazai iya ba, fita ma ya kasa, ba zai iya shiga cikin mutane yana fuskantar zafafan kalaman su kan 'Dan Maliki ba, bazai iya jure ganin yaddar da ada yake gani a idanu da kalaman jama'ah game da mahaifin nasa na sulalewa ba. Ranar da za'a yanke hukuncin 'karshe ma yaso zuwa amma sam hakan be yiyuba, zama yayi gida amma natsuwa ta kasaa zuwan masa gaba 'daya tayi masa 'kaura. Lokacin da labari ya riske shi rasa ina zai sa kansa yayi, shin farin ciki zai yi ko ba'kin ciki. Kotu ta wanke Zaitun lallai hakan yai masa da'di ya kuma yi farin ciki amma mahaifin sa fa? kotu cewa tayi zata 'daure shi har na tsawon shekaru goma sha biyar ban da tara da zai biya masu matukar nauyi...taya zai ji kwanciyar hankali har farin cikin sa ya bayyana a duniyar nan. 'Karshe sai da aka dangana Adam da asbiti saboda tashin farat 'daya da ciwon sa yayi, hankalin Hajiya Talatu ba 'karamin tashi yayi ba ta yadda baki ma bazai iya fasaltawa ba, haka yake ga Hafeez ma dan bayan 'dimbin amanar da ya kar6a game da Adam Shaheed, shi 'din abokin sane kuma amintacce da ba zai so ganin gazawar sa kan komai ba, a hakan ma yasan yana matukar 'kokarin yin tawakkali da danne abubuwa da dama ya kuma san matsayin kaddara ga bawa. Amma irin yadda rayuwa take walagigi da rayuwar sa abin a tausaya masa ne, yadda jarrabawa ke ta riskar sa 'daya bayan 'daya yana ganin da shi ne ma da tuni raunannar zuciyarsa ta samu matsalar da baza'a so afkuwar ta ba. Ita kanta Hajiya Talatu sai a lokacin ta samu labarin ciwon zuciyar sa ta kuma yi mamaki 'kwarai da gaske, musamman da taji cewa ciwon ya dade yana damun sa har ya kai wani mataki, me Adam ya aikata haka? meyasa ya 6oye mata duk wannan? Lokacin da ta tuhumi Hafeez da maganar ta fahimci tamkar ya san da batun tuntuni batasan lokacin da ta sau'ke mishi zazzafan mari ba tana kuka take fa'din sun cuce ta shi har Adam 'din gaba 'daya, basu mata adalci ba me yasa zasu 6oye mata irin wannan lamari, taya zasu yi wasa da rayuwar Adam 'din. Duk yadda Hafeez yaso kwantar mata da hankali abin gagarar sa yayi, kuka wiwi Hajiya Talatu ta zauna tana yi tamkar ranta zai faso 'kirjin ta ya fito, ashe ta kusa kashe 'dan ta da hannun ta bata sani ba, ashe lokacin da ya 6oye kansa sbd raba shi da Zaitun da tayi har take ganin in ya gama fushin zai sauko ne ashe duk jinyar zuciyar sa yake bata sani ba sai yau da Hafeez yake sanar da ita. Danasani marar misaltuwa tayi 'kwarai da gaske, danasanin abubuwa da dama, ciki harda raba shi da Zaitun da tayi, ta 'kudurta kuma a ranta tunda kotu ta wanke laifin Zaitun 'din dole sai ta nemo masa ita, badan ta raba shi da ciwon gaba 'daya zata yi hakan ba dan tasan abu ne mawuyaci tunda ba dalilin ta ya kamu da ciwon ba dalilin mahaifin sa ne kuma bata da ikon samar masa da farin ciki ta wancan 6angaren duba da abinda ma ya riga ya faru, amma ko da duk abinda ta mallaka zai 'kara wajen neman Zaitun ne ta 'dauki alwashin nema masa ita dan ganin yayi farin ciki ko da 'kan'kani ne, tasan har gobe yana 'kaunar yarinyar dan ko bayan da aka kamata ma ta fahimci hakan musamman daga camzawar yanayi da walwalar sa, zata dawo masa da Zaitun cikin rayuwar sa ko hakan zai rage masa ra'da'din ciwon ta wani 6angare ya samu ragin damuwa dole ne ta bada gudunmuwa wajen farfado da soyayyar sa. *Toh fa masu karatu, ga Hajiya Talatu tayi alwashin neman Zaitun ga kuma can Zaitun a hanyar Kano...yaya kuke ganin zata kaya ne...?* _Ku cigaba da biyo ni dan jin dukkan amsoshin ku._ *Comment nd Share to other groups* Salmerh😘 [20/9/2022, 12:34 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* Wattpad@ Serlmerh-md 🅿️ *...30* .........Ido ta waro sosai ganin irin girma da kyan gidan da suka shigo bayan an bude gate din gidan, sosai jikin ta ya fara rawa saboda tsoro, sake rungume Mufee tayi tana me dawo da kallon ta ga Hajiyar da ke zaune gefen ta, magana take son yi amma yadda bugun zuciyar ta ya rinjayi duk wani 'kwarin gwiwa da take ikirarin tana da shi haka ya rinjayi harshen ta ma yayi mata nawi. Dagaske tsoro da fargaba ya tsarga mata nan take, tuni ta raina kanta ta jinjinawa rashin wayo irin nata, sai lokacin ta fara nadamar yadda da tayi ta biyo matar nan. Tsayawar motar yayi dai dai da tsayuwar wasu mutane har guda biyu sanye da kayan da take kyautata zaton na aiki ne..." Alhamdulillah"! Hajiyar ta furta a fili gami da sakin ajiyan zuciya ga dukkan alamu bata tare da wata damuwa sa6anin Zaitun da ta raku6e ta kasa ko da motsin kirki. Wa'dannan da suka zo tar6ar Hajiyan ne suka bu'de motar batare da 6ata lokaci ba matar nan ta fara kokarin sanya 'kafafun ta waje. Ganin haka yasa Zaitun tai saurin ri'ke mata hannu idanun ta da kullum suke nan ruwa- ruwa ta 'daga ta dube ta da shi wanda take wasu sabbin hawayen suka taru cikin idanun ta. Kai ta fara girgizawa batare da ta saki hannun matar ba yayin da 'daya hannun ta ke rike dam da Mufeeda tamkar za'a 'kwace ta. "...Dan Allah Hajiya ki sa a maida mu inda aka 'dauko mu, wlh tsoro nake ji sosai...". murmushi tayi tana duban hannun ta da Zaitun ta ri'ke sannan ta dubi fuskar ta " Karki damu daughter, kar kuma kiji tsoro nan gida na ne...sauko mu shiga ina sauri ne....". Hawayen Zaitun tuni ya gangaro, sau 'daya ta dubi matar sai ta mayar da duban ta ga sauran matasa dake tsaye wajen motar..ita dai haka kawai sai taji hankalin ta bai kwanta da gidan nan ba. Bu'de mata 6angaren da take akayi bata zaci hakan ba dan haka da sauri ta dubi wajen ganin wani ne sanye da bakaken kaya kamar sauran ya bude ya sa da sauri badan ta so ba ta bi bayan matar ta inda ta fita, dan ji take tamkar zasu kamata bata manta farkon haduwar ta da Dr Rasheed ba, haka ta gansu duk sanye da bakaken kaya. Da gudu- gudu sauri- sauri ta fara bin bayan ta har yanzun kuma hawayen ta bai daina sauka ba..." Easy madam.. kar ki fa'di..". Taji an fa'da daga bayan ta, hakan sai ya 'kara mata sauri, matar nan murmushi kawai tayi batare da ta sake duban Zaitun ba, bata damu bane dan tasan tana nan biye da bayan ta har suka ratso cikin tsakiyar 'dakin da duba 'daya Zaitun tai masa ta fahimci Palor ne irin ma wanda ya amsa sunan san nan. A iya yawon da ta yi ta san faluka iri- daban daban sai dai wannan 'din yasha bambam da kowanne, girma da tsarin sa na musamman ne, wani ni'imtaccen 'kamshi yake fiddawa da duk yadda kake jin zuciyar ka da ka ratsa palon nan sai kaji 'yar nutsuwa ta shige ka. Wata mata ce ta shigo tsab da ita sai dai, rissina tayi fuskar ta cike da fara'a take fa'din "..Barka da dawowa Ammi...an iso lafiya...?" " Lapia 'kalau Alhamdulillah Raleeya ina Hajja Ladi fa...?" " Tana kitchen". " Kice ta same ni dan Allah..." Hajiya tayi maganar tana me hawa saman stairs tare da bawa Zaitun umarnin samun wajen zama. Ita har wacce aka 'kira da suna Raleeyan bb wanda yayi ma 'dan uwan sa duba sau biyu. Zaitun banda bin parlon da kallo da tunanin makomar ta bb abinda take yi. Lokaci lokaci takan gyara rikon da ta yiwa Mufeeda da har yanzu ke bacci tamkar wacce wani abu ke tsikarin ta haka take yawan gyarata. Sau 'daya tak in ka kalle ta zaka fahimci cewa a matukar tsorace take. Haka kuma ta kasa bin umarnin matar na cewa da tayi ta zauna. Ta ina zata iya zama a wannan wajen, ta zauna ma tayi me..? Tana nan tsaye kallo mai kyau bata iya bin parlorn da shi ba sbd wasi wasin da zuciyar ta ke ciki... Wata mata ce ta sake bayyana da take kyautata zaton itace Hajja Ladi da Hajiya tace ta same ta dan bata yi kama da matar gidan ba ko a yanayi, ta fahimci hakan ne musamman dan ganin hanyar da Hajiyan tabi itama shi ta bi sannan cike da sassarfa ta bi hanya ga dukkan alamu kuma cikin zakuwa take wajen ganin ta cika umarnin Hajiyar. Tsawon wasu mintina sannan matar ta sake sakkowa, har a lokacin kuwa Zaitun na nan tsaye ledan kayan ta da wani ya shigo da shi na nan gefen ta. Da wani mugun kallon ta fara cin karo daga Hajja Ladi da sakkowar ta kenan daga sama, kuma tun kafin ta 'karasa sakkowar ta fara aika mata da kallon da ke nuni da zallar tsana da jin haushin ta. " Ki biyo ni...". Haka kawai ta ce ga Zaitun bayan ta 'karasa sakkowar tana me nufan wani 6angare daban daga kasan stairs din. Ke gezau Zaitun batayi ba, sai ma mamakin Hajja Ladin, tabi ta takaita ina kenan bacin ba 'kofan fita taga ta nufa ba. Wani tunani da ya zo ranta yasa tayi saurin duban Hajja Ladin da rawar murya tace..." Ina zamu...dan Allah ki fitar da ni daga gidan nan...". Turus Hajja Ladin tayi tana mata wani banzan kallo. " Hala da kafa ta kika shigo gidan..?" Shiru Zaitun tayi tana kallon fuskar ta, mamakin yadda Hajja Ladin ke mata kallon da ta tabbatar ba na arziki bane take da kuma take mata magana wani iri, hakan yasa bata iya bama Hajja Ladin amsar maganar ta ba sai ma wara idanuwa da tayi kan fuskar ta. "...'daddaure ki aka yi ne aka shigo dake dole?" Tsayuwar ta daidai ta da kyau sannan ta cigaba da fa'din " Ga hanya zaki iya tafiya ai tunda ke shashasha ce...mthew" Ta karashe da jan tsaki. Har ta fara tafia sai ta kuma ta waigo. " Ki sani ba'a ganganci a gidan nan gara in fada miki, Ammi tace in nuna miki 'dakin da zaki zauna kafin ta dawo sauri nake ina da ayyuka a gabana kar ki 6ata min lokaci..." Ta 'karashe da juyawa da nufin tafia inda zata nunawa Zaitun 'din. Ko alama bata yi na nuna cewa tana da niyyan bin Hajja Ladin ba, saima tsayuwa da ta sake gyarawa tana juya maganganun ta, ta kasa fahimtar manufar ta na cewa ba'a ganganci a gidan nan, menene manufar Hajja Ladin ta kasa fahimta. Hajja ladi da taga bata da alamun bin ta tsaki kawai tayi ta koma kitchen ta cigaba da ayyukan ta, ranta na sake suya da bakantuwa bata sake bi takan Zaitun ba. Tana nan tsaye har Matar da ta kawo ta gidan ta kuma saukowa cikin sabuwar kamilalliyar shiga hannun ta rike da hand bag 'dinta fuskar ta 'dauke da yalwatacciyar murmushi banda sassanyan kamshi da ke mata rakiya. " Ah ah Zaitun ya haka? Har yanzun baki zauna ba? Ina Hajja Ladin bana ce ta nuna miki 'dakin ki ba...?". 'Dan cunno baki tayi gaba gami da kawar da kai tana fadin " Hajiya ni gaskiya bana so dan Allah ki mayar dani ko kisa a maida ni.." Ta 'karashe hawaye na sakko mata. 'Yar dariya Hajiyan tayi marar sauti tana me 'karasowa gaban Zaitun tace, " ki dube ni matsayin uwa Zaitun bazan cutar da ke ba kinji, zanje Abuja yanzu idan na dawo zamu yi magana, amma ki kwantar da hankalin ki dan Allah bana so in dawo in samo ki cikin damuwar nan, ki saki jikin ki babu abinda zai same ku kinji...?" Shiru Zaitun tayi tana duban ta bata iya tace komai ba illa hawayen dai. Hajja Ladi Hajiyan ta sake kwalawa 'kira da sauri ta fito ta iso inda suke tsayen. " Kinji abinda na gaya miki ko Hajja Ladi, dan Allah a kula da ita kafin na dawo, dauki kayan ki taya ta ku je 'dakin ki nuna mata komai, ni na tafi..." Kai ta jinjina hankalin ta duk na kan Zaitun tana binta da wani kallo tace. " Toh Ammi a dawo lafiya...". Jakar ta 'dauka ta nufi wani hanya. Ita kuma Hajiyan tana kokarin fita da hanzari ga dukkan alamu dai saurin dagaske take kamar yadda ta fadi, 'kila tafiyar gaggawa ce ta same ta. A hankali ta 'daga 'kafa ta bi bayan Hajja Ladin bayan ta tabbatar da cewa wacce ake kira da Ammin ta fita..da alamu kuma su ka'dai suka rage cikin gidan dan shiru yk sosai bb alamun kowa. Cikin wani makeken 'daki da yaji komai na more rayuwa aka sauke ta, komai da yake 'dakin mai kyau ne me kuma bala'in birgewa. Kasa motsi Zaitun tayi saboda tsoro. " Anan zan zauna...?" Ta tambayi Hajja Ladin maganar ta na har'dewa tana sake bin 'dakin da kallo. " Haka Ammi tace!" "...Hmm..kema kinga abinda na gani kenan?" Tayi maganar ne tana duban Zaitun sannan ta cigaba. " Ni kaina naga rashin dacewar ki da wannan muhallin saboda sosai yafi 'karfin mutun irin ki...". Shiru Zaitun tayi tana mata kallon mamaki, bata zaci wannan kalmar ne zai fito daga bakin ta ba. Wai wannan matar me take nufi ne..? Har ta juya zata fita sai kuma ta waigo"..Ya sunan ki?" " Zaituna!". Ta bata amsa kai tsaye idanun su sarke cikin na juna kowa abinda ke cikin ransa daban. " Toh Malama Zaituna zaki cigaba da zama anan kafin masu gidan su dawo.." Ta 'karashe maganar da bankawa Zaitun muguwar harara sannan tayi gaba. Jikin ta sanyi qalau yayi haka ta cigaba da tsayuwa tana sake rungume Mufee da kyau, hakika ita kanta taga rashin dacewar ta da 'dakin, bama gidan Hajjaju ba, ko lokacin da take gidan Dr Rasheed 'dakin ta bai ko taka 'kafar wannan a kyau ba. Sai ma ta kasa ko da 'daga kafafuwan ta balle ta kai ga neman wajen zama illa sake karewa 'dakin kallo da take daga nan inda take tsayen, sai ta da ta ji 'karfin ta na 'ko'karin 'karewa ne sannan ta nemi wajen zama kan sofa ta zauna daidai da tashin mufee a bacci. Sassanyar ajiyar zuciya ta sauqe ganin tashin yarinyar, kaso guda daga cikin damuwar ta tuni taji yayi nasa waje..zaka yi mamakin ganin murmushi saman fuskar ta tana 'dago yarinyar suka fuskanci juna. "..'yan mata na an tashi a baccin ?". Shiru Mufeeda tayi tana duban fuskar Zaitun sosai tamkar wacce ke karantar wani abu. Fa'da'da fara'ar ta Zaitun ta yi tana kamo kumatun Mufee.."...Mamana kina mamakin gani na tare da ke ko..? na dawo gareki yanzu sai dai gamu cikin wata 'kaddarar da muka kuma fa'dawa, ban kuma san ta mecece ba ita...amma koma miye Insha Allah ina nan tare da ke babu wanda zai raba mu, a shirye nake da koma menene a yanzu, tunda muka tsallake shari'ar nan Insha Allahu babu abinda zai sha gaban mu da zai fi 'karfin mu kinjj, Allah na nan tare da mu..." Kusan za'a ce ita ka'dai ke sumbatun ta dan Mufee ba fahimtar ta take ba, kamar yadda ba magana take ba balle ta amsa ta, amma ga mamaki na a yadda Zaitun 'din ke mata maganar itama sai ta washe baki tana fara'a irin tasu ta yara. Wanda ya matukar faranta ran Zaitun, sosai ta fahimci Mufeedan tata, tana dariya ne saboda ganin ta da tayi, ba mamaki ta riga ta cire rai da hakan, duk da yake yarinya ce amma farin cikin ta kasa 6oyuwa yayi da ganin Zaitunan shiyasa tayi 'yar dariya. Can kitchen kuwa Hajja Ladi ce ke faman yanka albasa bisa chopping board da zafi zafi tamkar zata ha'da da yatsun hannun ta ne ta yanke su tare, ranta duk a jagule hatta da saman fuskar ta bai 6oye tsananin 6acin ran da take ciki ba...tun dawowar ta daga kai Zaitun 'daki bata sake yin wani abu cikin natsuwa a kitchen 'din ba...dan ma ba ita ka'dai ke aikin ba da tuni tayi kwa6a wajen girkin. Raleeya duk na lure da ita, ta kuma riga tasan ainahin matsalar Hajja Ladin, tasan meke saurin ba'kanta mata rai a cikin gidan nan, ta lura Hajja Ladi ta sani taga kowa matukar ba ahalin masu gidan bane ya 'dara ta ta wani fanni. 'Yar murmushi tayi ta gefen baki da ko da ace kallon ta kake bazaka fahimci abinda tayi ba balle baka duban fuskar ta. Bata kalli Hajja Ladin ba tace " Ni kam Hajja Ladi lafiya...? tun 'dazun naga kamar ranki a 6ace...". Shiru tayi bata tankawa Raleeya ba, sai da ta sake yi mata tambayar kafin ta saki tsaki sannan tace.."...Ni da ba'kuwar Ammi nan ce wlh, ta fiye taurin kai..." Ta 'karashe da jan wata guntuwar tsakin kuma. " Ayyah ai kinsan wasu mutane haka suke sai hakuri ba mamaki halayyarta ce.". "...Hmmm" Tace sai kuma tayi shiru. Bayan wasu 'yan sakanni ta sake fa'din..." Ammi ta wuce Abujan yau da alama tana sauri ne..tace taro zasu yi da yamma a yau 'din" " Allah ya dawo da ita lafiya, zata da'de ne..?" Cewar Raleeya. " Gaskia ban sani ba dan bamu yi maganar da ita ba.." " Ta ina zaku yi maganar bayan kin 'kunsa ba'kin rai a zuciyar ki ..." Cewar Raleeya cikin ranta. Yayin da Hajja Ladi ta cigaba da fadin. " Wai kuwa kinsan inda Ammi ta sa na sauke bakuwar nan...? abun mamaki.." Cewar Hajja Ladi da ta tattara hankalin ta gaba 'daya kan Raleeya da alamu ta shirya fidda komai dake ranta ne. Raleeya kam bin ta tai da idanu kawai tana sauraron jin 'karshen zancen cikin ranta take fa'din.." _Ai dama na sani, tatsuniyar gizo kenan_ ..". "...'Dakin 'diyar ta da ta rasu fa, kinsan kyan 'dakin kuwa amma a rasa wa za'a bu'dewa 'dakin sai wannan yarinyar...". " Hajja Ladi su da gidan su, ai su ke da ikon saukar da duk wanda suka ga dama a kuma duk inda suka so, mu miye namu...a hakan ma ai muna samun bakin rabon mu..". "...Hmmm..." Hajja ladi tace bata 'kara wata kalma a zahiri ba, cikin ranta take ayyana da alamu Raleeya bata fahimtar inda tunanin ta ya dosa, dan haka bata 'kara maganar da ita ba taja bakin ta tai shiru. Tunowa da Zaitun tayi bata yi sallah ba yasa ta mi'ke sai da ta tabbatar ta rufe 'kofa da kyau sannan ta shiga, wanka tayi mai kyau da ta jima rabon da tayi irin sa, ruwa mai 'dumi sosai ta ha'da ta tayi wankan da shi ta wanke kanta sannan ta 'dauro alwala ta fito. Tsab ta shirya cikin kayan ta da ke shirye a leda tun ranar da suka fito da Hameeda aka kama su. Salmerh 😘 [20/9/2022, 12:34 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* _Wattpad@_ _Serlmerh-md_ 🅿️ *...31* ......Koda ta idar da sallar bata tashi a wajen ba, komawa tayi ta kwanta bisa daddumar ta lumshe idanu, tunanin rayuwar ta ne yake dawo mata daki daki, 'kwalla ne suka fara gangaro mata tayi saurin goge su. " Ya isa haka nan!, kukan nan ya isa" Ta furta cikin ranta cike da bawa kanta 'kwarin gwiwa. " Mene ma ribar shi?" Ta sake tambayar zuciyar ta. Bude idanu tayi ta sauke su kan Mufee dake wasa da 'dan 'karamin kwalin waya da bata san ko wacce iri ba ce ba ta dai tabbatar da kwalin waya ne duba da ganin hoton wayar da tayi a jiki, daga hannayen yarinyar fuskar ta maida duban ta har kullum kaunar ta sake ninkuwa mata yake a zuciya ita da kanta tana mamakin kanta lokuta da dama. Daidai da rana guda bata ta6a ji yarinyar ta ishe ta ba, bata san meyasa ba, duk da irin tarin qalubale da ta fuskanta amma bata ta6a jin sa6anin 'kauna game da yarinyar ba..ko meyasa? Wani 6ari na zuciyar ta ne ya bata amsa da fa'din.." Saboda ita 'din marainiya ce.." " Tabbas hakane! Ta tabbatarwa kanta. " Mufee na marainiya ce..ni kuma uwa ce zan kuma zame mata uba da kowa data rasa a duniyan nan...". kusan kowani lokaci alwashin da Zaitun ke ci kenan ko bata furta a fili ba takan ayyana cikin ranta ta kuma tabbatarwa ranta cewar tabbas zata iya. Kwanan ta biyu cikin gidan bata samu matsala ta kowani fanni ba, babu wanda ya takura ta ko ya shiga rayuwar ta, babu wanda take hira da shi sai Mufee duk da yake dama ita ba gwanar surutu ba ce amma haka kawai sai taji zaman shirun ya ishe ta, bata da matsala wajen abinci sbd sau uku ukun nan kullun ake bata abinci Hajja Ladi ke wannan hidimar wanda ta tabbatar bisa umarnin Hajiyar gidan ne. 'Bangaren Mufee ma bata samu matsala da ita ba dan tana cin duk abinda ta bata yanzu ko da babu yawa, dan har ayanzun Mufee ba cin abincin kirki take ba, 'dan banzan za6e ne da yarinyar, kuma in abu bai mata ba bata ta6a cin sa shiyasa a cewar Zaitun har yanzu bata da kumari tana nan 'karama da ita amma matukar zata ga yarinyar cikin walwala da kuzari hankalin ta kwanciya yake ta mance da duk damuwar da take ciki, sam ita bata ta kanta ma. Sai dai kuma tana jin bazata iya zaman gidan nan ba, bata son takura ko damuwa yanzu a rayuwar su bata son karin wata matsala makamanciyar wadda ta fito cikin ta kwanaki 'kalilan baya...aiki take so tayi burin ta taga ta fara tara ku'din mota dan hankalin ta ya fara komawa gida, burinta kafin cikar lokacin da ta 'debar musu na komawa ga ahalin nata ya zaman ace tana da isashshiyar ku'din motar da zata kaisu ba tare da wata gargada ba. Duk da yake har cikin zuciyar ta taji ta yadda da matar da ta dauko tan amma ai tun ranar da ta kawo ta ta fita bata sake ganin ta ba balle tasan matsayin zaman ta tare da su. Shiyasa wasi- wasi ya kasa barin zuciyar ta, ta riga ta yanke cikin ranta cewar barin gidan shine maslaha a gare ta da ma rayuwar ta. Sai dai wani 6ari na zuciyar ta na jin shakka, wancan daren tsoron faruwar makamanciyar sa take, tana tsoron mummunar 'kaddarar da zata iya fa'da mata tunda ta jima da lura rayuwar ta cike take da 'kaddarori masu matukar yawa, amma duk da haka tana matukar so da 'kaunar mutuncin ta, tana kuma iya 'ko'karin ta wajen kare shi..a kullum fatan ta shine Allah ya bata kariya ta wannan fannin, ya basu ikon cinye dukkan jarabawar su batare da sun cutar da wata halitta tasa ba, ba kuma tare da sa6a wa umarnin sa ko keta haddin islama ta kowacce fanni ba. Ko cikin dare bacci na yanke mata dalilin tunani da damuwar makomar ta da kuma kaddarar ta ta gaba, fatan ta kawai shine Allah ya sassauta mata koda wata kaddarace yasa komai yazo mata da sauqi..bacci 6arawo ne yayi gaba da ita batare da ta sani ba sakamakon 'karancin bacci da take fuskanta a kwanakin shiyasa kusan duk lokacin da ta samu natsuwa ta zauna shiru bacci ke kawo mata hari. Duk launin idanun ta sun canza, har kuma a yanzun ramar ta na nan sai manyan idanuwan ta da suke farare tas, tsawon mintina da basu haura bakwai ba da baccin nata taji Mufee na kokarin shiga jikin ta dole ta bude idanu tana jin baccin cike a idanun ta, gyara kwanciyar yarinyar tayi cikin jikin ta ta rungume..." _Bacci cikin natsuwa 'yan mata na_ ...". Ta ra'dawa Mufee cikin kunne a sanyaye tana sake rufe idanun ta dan baccin sosai take ji. Da irin wannan lokacin kawai ta ke samu ta yi bacci wanda dududu baya wuce na awa 'daya baccin yake sakin ta gaba 'daya sai kuma dare in tayi sa'a ko kuma washegari da irin wannan lokacin..misalin karfe goma ne na safia zuwa sha daya dai ko sha biyu na rana zuwa bayan Azahar. Kamar dai yau 'din daya kasance bayan azahar 'din ne. Bata aikin komai, illa hidimar kanta da ta 'diyar ta da ta riga ta saba da su, sai muhallin su da a koda yaushe yake tsabtace bata ta6a barin aga datti ko min 'kalilan 'din sa a inda take zaune. Wannan kuwa asalin dabi'ar ta ce tun ma tana gidan mahaifinta ta tsani datti. Ko da ta tashi a baccin sallah taji ake 'kira wanda ta tabbatar na la'asar ne, ba 'karamin mamaki tayi ba ganin yau 'din baccin ta yayi nisa sosai. Koda tayi sallar tunani ta fara na ko tabi shawarar Raleeya ne da tace ta ringa fita tana shan iska, sosai taji yau 'din dai bari ta gwada, hakan yasa tayi zaman jiran Mufeeda har ta tashi a baccin sannan ta watsa mata ruwa suka fito tana jikin ta. A hankali suke tafiyar kamar bazata taka 'kasa ba, bata san meyasa take jin ragaggiyar fargaba cikin gidan nan ba sa6anin gidajen da ta zauna abaya, in ka 'dauke gidan Hajiya Talatu da tasan zaman ku'din hayar da ta biya tayi babu inda ta zauna babu fargaba sosai cikin ranta sai wannan gidan. Tasan kuma bakomai bane face kamala, sakin fuska da karamcin da ta lura mamallakiyar gidan ke da shi. Can ta samo su Raleeya zaune a babban Parlon gidan suna sauraran maimaicin labarai da ake yi 'karde hu'du na kowacce yammaci, har a yanzu babu wata sakin fuska da take samu daga Hajja Ladi sai dai ga Raleeya abin ba haka yake ba. Dan haka barka da hutawa tai musu a jimlace sannan itama ta zauna 'diyar ta rungume da jikin ta. Raleeya ce ta yi kokarin kar6ar Mufee amma ta noke sai ma sake rungume Zaitun da tayi. 'Yar dariya Raleeya tayi tana mata tsiyan kyiyuya da take har Mufee ta fara dariyan itama saboda wasan da Raleeya ke mata. Ganin haka yasa dukkan su sakin fuskar su illah Hajja Ladi da ko kallo ma basu ishe ta ba. Ji ma take da tana da iko da tada su a parlorn zata yi tace su koma inda suka fito amma tasan Ammi bata lamuntar abu irin hakan matukar taji labari kuma bazata kyaleta ba..bata ta6a ganin mutun mai karrama 'dan Adam irin baiwar Allahn nan Ammi ba. Tuna hakan yasa ta ja karamar tsaki ta tashi a parlon ta bar su da Raleeya, sosai take jin tsanar Zaitun haka kawai har cikin zuciyar ta. Kallon suka cigaba da yi ana ta bada kanun labarai sai dai da turanci ake labaran Zaitun ba fahimta take ba, amma jin sunan garin su ya fa'do cikin labaran yasa ta bada hankalin ta sosai har aka lula cikin labaran. Bata iya fahimtar komai ba sai dai lura da Raleeya tayi ta bada hankali ga labaran yasa take 'dan tofa nata itama, bawai dan tana tunanin Zaitun 'din bata fahimta ba ne a a kawai dai dan 'karawa zaman shirun nasu armashi. Sosai jikin Zaitun yayi sanyi kur ta kurawa Tv 'din idanu..har Raleeya na iya hango hoton Tvn cikin idanun ta saboda yadda suka cika taf da ruwan da ta hana su sau'ka, sai walwali da suka 'karawa idanun. Duk 'kwa'kwar ka bazaka ta6a fahimtar inda hankali da tunanin ta ya dosa ba, amma ita ka'dai tasan halin da ta shiga a wannan zaman. Sosai take jin gudun jinin ta na 'kara sauri akan nada, haka ma bugun zuciyar ta, tayi 'ko'karin ri'ke hawayen ta gudun kar Raleeya ta gani amma bata san tuntuni sau'ka suke ba sai da taji Raleeya na fa'din..." Subhanallah...Zaitun kuka kuma...?" Firgigi tayi tana duban Raleeya tamkar wacce zata gano wani abu daya danganci garin nasu akan fuskar ta. " ...Da tausayi kam ni kaina naji babu dadi amma ya zamu yi? Addu'a kawai zamu cigaba da musu Allah ya saka musu ya bi musu hakkin su, wa'danda aka kwasan kuma Allah ya ku6utar da su...yankin Borno ai suna cikin tashin hankali sosai, dole a tausaya musu". Cewar Raleeya cikin raunin murya tana dauke 'yar 'kwallar da ya sakko mata da yatsan ta. _(Allah Ubangiji ka 'kara bada kariya da tsaron ka duk jihohin mu da ke fuskantar tashin hankali da barazanar 'yan ta'adda Allah ka kare mana dukkanin al'ummar mu..Ameeen)_ Kawar da idanu Zaitun tayi zuwa wani 6arin. " Kenan dagaske abinda take tunanin ya farun shi ya faru...?" " Yah Allah...Ya rabbil Izzati, ya Zul arshil majeed Yah Raheemu Yah Rahman ka kare min mahaifa na, 'yan uwana da ma dukkan musulmi..." Tunanin ta tsayawa yayi jin cigaba da maganar da Raleeya tayi...." Haka ma fa kwanaki a kan hanya aka ringa yiwa mutane kisan gilla, wlh wai yankan rago an zubda jinin musulmi sosai ko labari bana son inji anayi saboda yadda abin ya munana, shiyasa yanzu da yawa ke fargabar tunkarar hanyar Borno abun bb dadi sam..." " Innalillahi wa inna ilaihi raji'un.." Ta maimaita yakai sau uku. Tana so ta bu'di baki ta tambayi Raleeya yaushe akayi hakan amma bakin ta duk taji ya mata nauyi. Ido kawai ta waro kan fuskar Raleeya. Ga me fahimta zai iya fahimtar inda tunanin ta ya tafi da abinda take son ji sa6anin Raleeya da itama alhini ya cikata bata lura da hakan ba, sai ma cigaba da tayi da bawa Zaitun iya abinda ta sani game da Jihar ta Borno. Zaitun banda salati cikin ranta babu abinda take yi, wai duk tana ina hakan ya faru..? Meyasa bata da labari sai yanzu?. Tashi tayi tana toshe bakin ta da hannu dan yadda take ji kuka na shirin kwace mata. Raleeya da idanu ta bita cike da tausayi da kuma jinjina halin tausayi irin na Zaitun 'din, not knowing that kanta take wa kukan, mahaifan ta, 'yan uwan ta, dangin ta, da kowa nata take tunawa. Da sassarfa ta isa 'dakin ta, tana shiga ta maida 'kofan ta rufe, jingina tayi da jikin 'kofan ta sulale 'kasa tana sakin kuka, kuka mai tattare da ma'anoni da dama. Ita kanta bata san tsawon wani lokaci ta 'dauka yashe a wajen take kuka ba, Mufeeda zuba mata idanu tai itama duk jikin ta yayi laushi tamkar tasan abinda ke faruwa. Ashe rabon taji mummunan labari yasa ta fita ayau 'din, ashe dama kuka bai kare mata ba kwarin gwiwar da take tunanin ta bawa zuciyar ta duk ba nisa zasuyi ba ashe. Tayi kukan da tun barowar ta gida bata ta6a yin irin sa ba, tsoro da fargabar ta cikin kowani seconds hauhawa yake da'da yi, dama can Zaitun muguwar matsoraciya ce, da jin wannan labari kuma tsoron nata sai ya 'kara tsananta, tasani ba sai an bata labari ba itq 'din shaida ce game da illar da 'yan ta'addan ke yiwa yankin su. Gashi in tayi duba da labarin da Raleeya ta bata sai taji tsoron tunkaran hanyar, tana so taje taga ahalin ta amma in ba ta sama zata bi ta ina zata iya riskar su? Idan itama taje aka yanka wuyan ta fa? Kuka sosai ta 'karasa yinin ranar da shi har sai da taji kanta ya fara sara mata kafin ta sarara. Bata 'kara iya fita cikin 'dakin ba har washegari, hatta abinci bata iya taci ba ta dai bawa Mufeeda gudun shiga hakkin ta. Sosai taji jikin ta yayi sanyi, dukkan wani 6oyayyen raunin ta ya fito fili, shirun ta ya ninka na baya. Kasa ma yanke takamamman shawarar da ya dace ta yi, shin taje ne ko kuwa ta dakata tukunna. Idan taje aka kashe ta a hanya fa? Ko kuma sai ta isa garin itama su 'dauke ta tamkar yadda Raleeya tai mata bayanin yadda suka 'dauke 'yan mata da matasan yara da dama a 'kauyen nasu. Wannan wace iriyar musiba ce haka, sai yaushe ne zasu samu zaman lafia da kwanciyar hankali. Gaba 'daya ta rasa mafitar 6illewa, 'karshe dole ta yanke shawarar bada tazara kafin zuwan ta, amma dole zata koma gida...ta tabbatarwa zuciyar ta. Tun daga lokacin Zaitun bata sake walwalar kirki ba, in ma anga tayi walwalar to da Mufeeda ne, sosai ta shiga wani yanayi na tsananin tashin hankali da damuwa, ta ya ma zata ji farin ciki ne bayan jin labarin abinda ya faru. Bata sake tattauna maganar da kowa ba, sai dai a kullum addu'ah take ubangiji Allah ya kare mata ahalin ta ya kuma kawo musu saukin lamarin. Wa'danda aka tafi da su kuma tana nema musu sassauci wajen ubangiji ya kare su ya kuma ku6utar da su izuwa ga iyayen su lami lafia...bata yi 'kasa a gwiwa ba kuma wajen rokon Allah in har zuwan ta shine mafi alkhairi Allah ya bata yadda zata yi ya kuma bata daman zuwa nan kusa. Tun daga wancan ranar bata 'kara fitowa koda wajen corridor bane balle har ta 'karasa can main Palor. Cikin 'daki take zama tana kuma mamakin yadda har yau 'din da take 'ko'karin cike kwanaki hu'du cikin gidan bata sake ji ko ganin Hajiyar gidan ba...bata ma sake jin 'duriyar kowa da ya dangance ta ba, mamaki take dama wai haka Hajiyar ke rayuwa ita ka'dai bata da kowa. Koda yake ita da take 'daki koda ace akwai wani na Hajiyan ai ba lallai ta gansu ba tunda ba fita take ba. Zaitun akaran kanta 'karshe taga cewa zama gidan nan bazai yi mata ba, dan tun zuwan ta babu wanda ya bi ta kanta, babu wanda ya damu da lamuran ta, babu wanda ya damu da sanin halin da ta take ciki, hatta abinci tana ji ba dan albarkacin Raleeya ba ba lallai ne ta ringa samu yadda ya kamata ba. Tsoron ta 'daya ma kar a kuma maimaita 'yar gidan jiya, bata da 'karfin zuciyar da zata sake jure irin wancan badakala da wahalwalun rayuwar da har abada bata jin zata iya mancewa da su. Ha'duwar ta da Dr Rasheed ya kansance 'daya daga mummunan babi cikin rayuwar ta wanda ya tsaya mata a zuciya. Tasan taimakon ta yy, amma daga karshe taimakon juye mata yy izuwa ga wani abu daban abin bakanta ruhi da zuciya, wadda bai tsaya iya nan ba hatta da gangar jikin ta sai da ya bayyana hakan 'karara, illah gagaruma yayi wa rayuwar ta illah kuwa ta har abada. Kuka take haiqan irin kukan da ke nuna zallar tashin hankali da shiga taskun rayuwa, fuskar ta kife da 'daya daga cikin pillown da ke 'dakin yayin da Mufee ke kwance kan bayan ta tamkar goyo amma babu zani, duk tayi laushi itama ganin Zaitun cikin wani yanayi a kwanakin dole ya affecting nata itama. A yau'din ji take tamkar ana shirin zare ranta ne gaba 'daya, meyasa tun farko bata tuna hakan ba sai yanzu, meyasa sai yanzu take jin bata da 'karfin gwiwa, ba tun yau tasan irin tashin hankalin dake faruwa a yankin nasu ba, ba tun yau tasan halin da suke yawan tsintan kansu aciki ba, amma meyasa a yanzun abin yafi shigan ta, sosai take hasashen halin da ahalin ta zasu iya fadawa, bata san wani iri bane sannan babu wani tartibin sani game da yanayin da suke a yanzu, taya ma hankalin ta zai kwanta ne...bazata iya ba. A yanzu da take da burin ganin ta waiwayi gida ko da ba kwana kusan nan ba taya ma zata iya zaman gidan nan ba tare da aikin komai da zai kawo mata ku'di ba, banda bu'katun ta da na Mufee, ya zam mata dole ne ta nemi ku'din motar da zai kaita garin nasu...dan haka bazata iya zaman gidan nan ba da batasan me ke tattare da shi ba, bata san wace kaddarar ke 'kunshe cikin sa ba dole ne ta nemi mafita dan a yanzu tsoro take ji sosai, tsoron ranar da raunin ta zai dur'kusar da ita gaba 'daya. Kafin faruwar hakan take so ta cimma wani buri nata koda guda ne tal. *Comment, vote nd Share to other groups* . Salmerh😘 [20/9/2022, 12:34 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* Wattpad@ _Serlmerh-md_ 🅿️ *...32* .......Washegari misalin 9:13pm. Kwance take tana maida numfashi 'kasa 'kasa fuskar ta yalwace da murmushin da ya 'kawata ilahirin fuskar ta, lullu6e take da wani babban duvet da ya mamaye dukkanin jikin ta illah kanta dake waje, ba 'karamin gajiya tayi ba, gaba 'daya ta jikkata, bata jin 'karfi cikin jikin ta kona miskala zarratin, hakan yasa ta kasa yin wani kyakkyawan yun'kuri balle ace ta mi'ke tsaye. Tunani da shau'kin abinda ya wakana tsakanin su bada jimawa ba ya sanya murmushi kasa barin fuskar ta...sosai take so da kaunar sa take kuma girmama lamuran sa. Tsawon mintina goma sha takwas tana ahakan sannan 'kofan bathroom da take fuskanta ya bu'du. Tun daga 'kafafun sa ta fara bi da kallo har zuwa saman fuskar sa. 'Kugun sa 'daure yake da towel fari 'kal yayin da hannun sa ke rike da wani 'karamin towel 'din yana tsane ruwan jikin sa da shi. Gargasar jikin sa ya kwanta luf sakamakon jikuwa da jikin nasa ke da ruwa har kana iya ganin 'digan su tun daga sumar kanshi har izuwa 'kafafuwan sa. Kallo 'daya zakai masa kasam yana 'daga 'karfe sakamakon irin 'kirar da zaka fuskanta game da shi, ba fari yake can ba skin 'din sa choculate color ne sai idanun sa da suke da 'dan fa'di, sumar kansa kwance take luf gwanin birgewa, murmushi tayi tuno yadda suka sha drama da mahaifiyar sa kwanakin.baya kan ya rage gashin amma ya ki dole ta kyale shi. Yana da dogon hanci da madaidaicin baki da ya taimaka wajen 'kayatuwar kyan fuskar sa. Babban abinda yafi birgeta da shi shine jarumtar sa. Sau 'daya ya dube ta ya 'dauke kansa. Gaban mirror ya isa ya tsaya, 'kurawa mirrorn idanu yayi yana ganin kansa aciki tamkar wanda akace masa an canza masa kalar fuska ne, idanun sa yake gani da suke ja har yanzun basu washe ba. Ciki ciki ya saki tsaki sannan ya waiga gami da tahowa cikin wani irin yanayi kamar zai nufi kan gadon sai kuma yayi turus ya tsaya batare da ya 'karasa ba, ko me ya tuno oho. "...Amrah je ki tsabtace jikin ki kafin kiyi baccin pls..." Ya fa'di a sanyaye a kuma dake sai dai kana jin muryar sa kasan farinciki bai gama wadatar sa ba. Mi'ka tayi da ilahirin jikin ta tana daga kwancen..da wata muryar shagwa6a tace.." Baby ban gama hutawa ba fa...". Ta 'karashe da turo bakin ta gaba. Ido ya waro yana duban inda take da hannuwan da duk biyu ya kama kugunsa cike da mamakin ta yace " Amrah....." " Baby Pleeease..". Ta tare shi da fa'din hakan tana sake narkewa. Yana shirin sake magana 'karan wayar sa ya dakatar da shi, duban sa ya kai ga wayar dake ajiye kan side drawer yamma da hadadden gadon dake 'dakin. A hankali ya isa ga wayar... _Mum_ da ya ga ke yawo kan fuskar wayar da alamun hoton zuciya ya sanya shi saurin 'dagawa ya kai kunnen sa. Sallama yayi gami da gaishe da ita ta amsa cike da nuna kulawa gami da bashi uzurin rashin responding call 'din sa da batai ba 'dazun da yammaci da yai kiran ta. " Hope kiran nawa bai takura ka ba ganin dare ya 'dan yi..". "..oh no bakomai Ammi...ban yi bacci ba ai ina wani aiki ne...abubuwa sun cushe min a company ga Sultan ya'ki dawowa..." "..Sorry son zan mai magana ya dawo, Allah ya yi muku albarka ya kare min ku.." " Ameen Ammi...". " Ya Amrah fa..?" "...Tana nan lafia, thought tayi bacci ma.." Ya fa'di maganar yana duban inda take idanun su kafar suka ha'de da juna. " Alright my regards...". "..Insha Allah Ammi..." " Ba wata matsala ko..?" " Nop, bakomai Ammi..." " Masha Allah..". Ya fa'di yana shafo kansa da ruwa har yanzun ke bin bayan sa yana murmushin 'karyar da ya yiwa Ammi na cewar Amrah na bacci. 'Kiran sunan sa da Ammi ta sake yi ne yasa shi natsuwa dan ba.kasafai zakaji ta kira shi da sunan sa ba. " Akwai ba'ki a gidan fa hope ana kula min da su yadda ya kamata...?" " Baki kuma Ammi?...Raihana tazo ne...?" " A a ba ita ba ce...kar kace min baka ma san da zaman kowa a gidan ba Rayyaan...?" Ammi ta fa'di cike da son jin amsar sa. Kai ya girgiza tamkar yana gaban ta...sai kuma yace"...Anty Madeena ce...?" " Madeenan ce zata zo gidan batare da ta nemeka ba...". " Toh naga Marwa ai basu dawo ba...ko dai wasu family ne suka zo mana ziyara Ammi bani da labari?" " Yayi kyau sosai Rayyaan.." Ta bashi amsa a 'dan kufule. " Sorry Ammi, Allah kinsan ban zauna bane shiyasa.." " Sai ka tashi kaje ka duba min su ai yanzun nan, nima abubuwa suka sha kaina shiyasa ban tuna na tambayi ya suke ba sai yanzun kwata kwata ma na mance da cewar na bar baki kuma na kira layin Hajja ladi baya tafia, kaje can 'dakin Safaa anan aka sauke su ka duba min ko suna lafia pls.." " Kuma yanzu Ammi..? Why not tomorrow?" " um um yanzun dai Rayyan gobe ta Allah ce, kuma nasan goben ma cemin zakai ka manta, kaje ina kan layin ina jiran ka ko kuma ka ha'da mu awayar idan kaje. " Ok " Yace sannan ya 'dora da" When ar u coming back...? " Very soon " Tace gami da tsinke kiran. Uwa dai uwace bayaga haka in ba Ammin ba waye ya isa sashi wannan aikin da uban daren nan... sai dai koka'dan fuskar sa bata nuna alamun rashin jin dadin aikin da Ammin ta sashi ba, domin yasan Ammi ta wuce hakan agare shi, ba 'karamin girmama matsayin ta yake a zuciyar sa ba. Sai da ya ajiye wayar kafin kuma ya fara tunanin wani irin muhimman baki ne ga Ammin haka da har ilahirin 'dakunan gidan basu ishe su sau'ka ba sai 'dakin sistern shi? Juyowa ga Amrah yayi ya dube ta sannan yace.." Amrah wasu ba'ki ne a side 'din Ammi..?" " Wlh baby ban sani ba.." Manyan idanuwan sa ya zaro yana duban inda take kwancen cike da mamaki yace " Don't tell me tun tafiyar Ammi baki je can 6angaren ba..?". Baki ta tura gaba tana gyara kwanciya tace. " toh Baby me zanje nayi? Ammi bata nan Marwa bata nan wajen wa zanje a can 'din..?" " amma aikin me kike da bazaki iya zuwa ki duba ko da sau 'daya ne a rana ba..?" " Kullun Raleeya tazo aiki anan na kan tambaye ta ya suke ko kuma da wata matsala duk abinda ke tafia ta na sanar dani shiyasa naga ai ba sai naje ba kuma ma ni bata ta6a ce min akwai ba'ki ba ". Ta 'karashe 'kasa- 'kasa. " Ya miki kyau..." Ya fa'di hakan ne bawai dan yaga laifin ta wajen rashin sanin zaman ba'kin da batayi ba, ya fa'di hakan ne sbd rashin jin maganar sa da batayi, yasha gaya mata koda Ammi bata nan ta ringa zuwa tana duba yanayin zaman ma'aikatan gidan tunda ita ba wani aiki take ba, makarnta ce ka'dai kuma ITF take yanzu, so babu inda take zuwa sai dan banzan yawo da rashin jin maganar sa. Tunanin sa koda wani abin zai taso 6angaren Ammin ba lallai ya sani ba amma ita zata iya sani tunda duk mata ne 'yan uwan ta a 6angaren. Aiki yasha kansa ita kuma rashin ji ya hana ta nutsuwa ta duba abubuwa, yana sane da cewa ko da Ammin nasa na gari ma ba kullun Amrah ke zuwa gaida ta ba sai ranar da ta ga dama ko kuma shi ya nuna 6acin ransa, ko kuma ya sata agaba suje tare kafin take zuwa, wataran ma sai Ammin da kanta tayi cikiyan ta kafin take zuwa 6angaren, sam ya rasa taurin kai irin na Amrah, bata jin magana sam, sai dai yana iya 'daukan duk shashancin ta rashin girmama masa mahaifiya ne ka'dai bazai iya 'dauka ba. " Baby fushi kayi...?" Ta tsinkayi muryar ta tana tambayar sa gami da yun'kurin tashi ta zauna ta bashi dukkan hankalin ta. Bai dube ta ba yace " Meyasa zanyi...?" Yanayin muryar sa ka'dai ya tabbatar mata da zargin ta. " I'm so sorry Baby ban sakewa, daga gobe Insha Allah kullum zan ringa zuwa ". " Ruwan ki..." Haka kawai ya furta 'kasa 'kasa batare da ya dubi inda take ba yana me cigaba da shirin sa cikin 'kayatattun kayan bacci kalan sararin samaniya ya feshe jikin sa da turarukan sa masu sanyaya zucia sannan ya fito daga 6angaren nasa ya durfafi 6angaren Ammi. Da yake gidan ba bakon sa bane, in ma akwai wanda ya yiwa gidan sanin tsab to bazai wuce Rayyan ba, dan haka bai sha wahalar neman inda 'dakin Safaa yake ba, taya ma zai iya mantawa bacin a kullum kewar ta na nan dan'kare cikin zuciya da ruhin sa. 'Kage ma yake da son zuwa dan yaga wasu irin baki ne wa'dannan da har Ammi ta martaba da basu 'dakin beloved late sistern shi zu zauna a ciki. Wannan tunanin ne ya sake zafafa ransa yasa shi 'karin azama haka ya tura kofar 'dakin da karfi batare da tunanin komai ba, batare da tunanin ba'kin zasu iya kasancewa manya da ya kamata ya girmama ba. Ko sallama bai yi ba duk da kuwa yasan muhimman cin sallama a muslunce gaba 'daya ransa a ha'de hatta fuskar sa sai da ta bayyana hakan. Wani 'kakkarfan bugu ne ya ziyarci zuciyar sa da baya raba 'dayan biyu tuno sistern shi da rayuwar ta ne ya sanya hakan. Bai ga kowa 'dakin ba sai wata 'yar yarinya kwance tana bacci lullu6e da mayafi sai kuma wata da yake iya hango bayan ta zaune kan dadduma wanda a kiyasin da idanuwan sa suka yi duba da yanayin jikin ta bazata wuce sa'ar su Safaa 'din sa ba. Kallon bayan nata ya tsaya yi tsawon mintina biyu hannuwan ta 'dage a sama ga dukkan alamu dai addu'a take yi, sak yadda yasan halin Safaa 'din sa haka itama take da yawan kusanta kanta ga mahalicci a hankali ya sake maida duban sa ga 'yar yarinyar dake kwance, jiyake bugun da zuciyar sa keyi na 'kara hauhauwa. Sautin muryar ta da ya fara tsinkayowa ne ya rinjayi hankalin sa wajen ta. Tsam yayi yana sauraron abinda take fada. " Yaa Allah ka bu'de 'kofofin alkhairan ka da albarkokin ka gare mu, ka kiyaye mu daga sharrin shai'dan da shai'danun mutane, Yah Allah ka kare mu daga sharrin aljanu..ka bamu cikakkiyar kariya daga mummunan tanadin magauta da mugayen mutane. Ya Allah ka ji6anci dukkan lamarin mu da na 'yan uwan mu da 'ya'yan mu da dukkanin ahalin mu, Yah Allah ka tsarkake mana zukatan mu ka kare mu daga dukkan sharri, gare ka muka dogara kuma wajen ka muke nema Yah Zuljali wal ikraam, Yah Allah kamar yadda na 'daura aniyar kulawa da 'diya ta Yah Allah ka dafa min ka bani yadda zanyi..Yah Allah bamu da wani sai kai bamu da wani abin dogwaro face kai, Yah Allah ka bu'de mana kofofin Rahamar ka ka sanya mana albarka cikin rayuwar mu..kaine mafi karamci, mafi kyauta da kyautatawa, mafi girman baiwa, mafi jin'kan masu jin 'kai...Yah Allah ka kare min iyaye na kaji 'kan su kamar yadda suka ji 'kaina tun ban san kaina ba, Yah Allah ka basu wadata ka sanya su cikin aljannar ka ma'daukakiya.... Bai jira yaji 'karshen doguwar addu'ar tata ba ya ja musu 'kofan a hankali ba kamar yadda ya turo da farko ba..tsintsn harshen sa yayi yana amsawa da " Ameeen.." Haka ya tafi yana jin wani nawi a zuciyar sa yana mamayar sa har kuma a lokacin haushin ganin su baje 'dakin sistern shi bai barshi ba. Bai zame ko'ina ba sai 6angaren sa, nan ya samu Amrah still na kwance a gadon sa har a lokacin kuma bai ga alamun ta tashi ba tun fitan sa. Gaba 'daya ji yayi 6acin rai ya sake mamayan zuciyar sa. A tsawace yace ta tashi ta bar masa 'daki in ba zata tsarkake jikin ta ba. Menene amfanin zama da najasa ajiki batare da wani dalili kwakkwara ba. Baki ta tura, dama tasan halin masifar sa, sai dai a yanzun bata san me ya 6ata masa rai da ya sauke fushin akanta ba. Tashi tayi ta lalu6i towel ta fa'da bathroom 'din 'dakin nasa inda ya rakata da 'karamar tsaki. Tana fitowa ko inda yake bata kalla ba tabi hanyar fita zuwa 'dakin ta. Turare kawai ta feshe jikin ta da shi ta sanya rigar bacci tabi lafiyar gado. Wayar ta ta 'dauka jin babu bacci a idanun ta, ta bu'de Data, nan ta fara jiran sakonni su gama shigowa. Sai da suka gama shigowa sannan ta lulu6i wata number duk da mamallakin numbern baya online amma haka bai sa tayi 'kasa a gwiwa ba, farko emojin 6acin rai ta tura daga 'kasa kuma ta rubuta" _yau an 6ata min raina dear_ ..." *Comment, Vote and Share* *Salmerh* 😘 [20/9/2022, 12:34 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Wattpad@ Serlmerh-md* 🅿️ *...33* .......Cigaba tayi da duba sauran sakonnin da suka gama tururuwar shigowa cikin wayar tata. Wata me suna Ameera ce ta tura mata" _Mrs RM baki yi bacci ba_ ...?" Bata kula ba sai da ta 'dan 'dauki lokaci cikin wani group bayan ta gama nazartan duk abonda ke wakana cikin group 'din kafin ta fito. Amsa ta turawa Ameeran da fa'din ".. _Wlh Ameera ban yi ba..ina dai niyya, ya labari_ ..?" " _Shiru ne fa 'kawata, ya Babyn ki_ ..?" " _Yana 'kalau, yana can 'dakin sa..."_ Ta bata amsar in I don't care manner. Idanu Ameerah ta zaro a zahiri ta kuma tura mata emoji exactly yadda tayi da idanun ta sannan ta 'kara da rubuta " ' _kawata 'dakin sa fa kika ce, ke kuma fa_ ..?" 'Dan ha'de rai Amrah tayi tana bawa Ameeran amsa da fa'din.." _Nima nawa 'dakin nake..mun yi fa'da ne..."!_ Dariya Ameeran tayi har a fili daga inda take. " Shegiya tawan, wayon dai har yau babu, ko waye yace mata ana haka a wannan zamanin oho ...ta furta a fili. Sai kuma ta tura mata emojin daria.." 😂... _fa'da da Babyn naki mrs Rayyan_ ....?". " _Ki bari kawai Ameera 'dan yawa ne wlh kina ganin sa, sai uban fushi, rashin ha'kuri da zafin rai..."_ " _Kai.._ 😱 _" Allah kuwa, masife ni yayi fa dan kawai ban yi wanka akan kari ba ko ina ruwan sa oho..._ " Ta 'karashe da 'kya6e baki. " _Kai 'kawata ke ma dai yawar gareki wani lokacin yasin.."_ Cewar Ameerah inda ta turo mata tana murmushi. Tiryan- tiryan ta labarta mata yadda suka yi kaf da Rayyan hadda wanda ba ma ranar ya faru ba, da abinda ma bai kamata ta sani ba duk ta sanar da ita, Ameera nata mata daria da ganin wautar ta, ita bata wani ga abin fushi anan ba ma 'karshe dai haka suka rabu ba tare da wata 'kwakkwarar magana ba a tsakanin su. Ameera ita har ga Allah abin dadi yai mata...ta jima tana so da begen Rayyan 'din amma ta rasa ko wata iriyar damar ganin sa ma balle magana da shi, ita kuma a yadda take jin zuciyar ta bata da kwarin gwiwar iya fitowa fili ta bayyana masa kudurin ta, baya ga haka ma Amran babbar kawarta ce, kawancen su kuma yafara ne tun suna da 'kananun shekaru bazata iya cin amanar ta ba shiyasa ta hakura kawai ta barwa Allah komai, sai dai daidai da rana guda bata ta6a bata shawara game da zamantakewar auren ta ba, duk da tasan iriyar tarin ta6ara da Amran ke tafkawa amma hakan bai sa ta 'dora ta da hanya ko sau 'daya ba. Tun fitar Amrah ya ja wata doguwar tsaki kuma har a lokacin bugun zuciyar sa bai dai dai ta ba, Safaa is his lovely sister which atimes take iya zame mishi tamkar aboki, ya shaku da ita fiye da duk sauran sisters 'din sa duk da yake ba mai sakewa bane shi, amma hakan bai hana Safaa shiga jikin sa har suka saba ba, hatta Sultan da yake namiji basu shaku da shi kamar da Safaa ba, she is very friendly with a genuine personality, tana da hakuri sosai gata da fara'a ga mugun 'kaunar ahalin ta da Allah ya 'daura mata nd that's what makes her leave her footprint still in his heart...he adore nd missed her alots... A fili ya furta Allah ya gafarta miki ya 'kara haskaka kabarin ki...Ameeen..." Wayar sa ya 'dago ya 'kira Ammi ya sanar da ita yaje ya kuma tarar da su lafiya. Murmushi Ammi tayi ba tare da wani jin nauyi ba tace da shi " Thank u..." Bata tsawaita ba, domin daga jin yanayin muryar sa tasan a dame yake duk da bata san dalili ba amma tana kyautata zaton akan aikan da tai mishi ne...ko ma ba itan bace kuwa tasan ba lallai ne ya fa'da mata ba ko da ta tambaye shi dan tasan halin sa sarai da za6an ri'ke komin sa a zuciyar sa, bai fiye son yana tarayya kan wani abu nasa da ya shafe shi da wani ba, mugun son privacy ne da shi hatta ita da ta haife shi bakomai yake iya tattaunawa da ita ba, abubuwa da yawa sai dai ya aikata abinsa batare da tasani ba, wanda Allah yasa taji labari shi take ji wanda bata ji ba kuwa ya wuce ta kenan, tasan wannan halayyar a wajen ta da ma mahaifin sa ya 'debo shiyasa abin ya.kama.zuciyar sa sosai, domin ita har mahaifinsa kusan duk suna da wannan 'dabi'ar amma zuwa yanzu ta fahimci Rayyan ya ninka nata halayyar sau babu adadi. Yayin da daga 6angaren Rayyan har ga Allah aiken Ammi bai 6ata ransa kamar yadda Amrah ta 6ata masa ba... Ita kanta Ammi tasan tsakanin su dama bb wata doguwar hira shiyasa bata tsawaita ba, ranar da yaso da kansa yake mata hirar ranar da kuwa bai ga dama ba maganar bakin sa ma sai yaso ake ji. Sai dai duk da haka sosai yake son mahaifiyar sa da duk 'yan uwan sa sbd sune ka'dai yake da su...ko miye kuwa da Ammi ta bashi umarni tace masa abu kaza zakayi koda baya son abin bazaka ta6a ji ko ganin yayi musu ba, in ya ga dama ko a fuska bazaka ga alamun rashin amincewar zuciyar sa ga abin ba, sai dai wani lokaci yabi Ammin da kallo bacin hkn kuma amincewar sa ne zai biyo baya. Bai ta6a yi mata musu ba, da kanta take fahimtar komin sa daga cikin idanun sa, wanda idan ta fahimci kamar zata cutar da shine ma sai ita ta janye nata kudurin in kuwa tasan ba ze cutar da shi ba hk take barin sa kawai daga 'karshe kuma alfanun abin zai gani da farin ciki yake 'karewa. Ko lokacin da zai fara Degree 'din sa, ABU Zaria ya so yi har ransa amma Ammi tace sam karatun likitanci take so yayi kuma ma a wajen 'kasar nan, har ga Allah baya ra'ayi, ya so ya karanci fannin business ne kawai tunda a ciki suka taso suka ga mahaifin su har ya bar dunia kuma sana'ar sa kenan. Sau 'daya kawai Rayyan ya dube ta ba tare da musun komai ba kawai ya amince...amma cikin wannan kallon ta fahimci ba ya ra'ayi basarwa tayi amma sarai tasan ba ra'ayin sa kenan ba biyayya ce kawai yy mata, ba burinta ta kuntatawa 'diyoyin ta ba, bata fatan dai dai da rana guda ta tauye hakkin wani daga cikin su amma wannan karan bata jin zata iya janyewa daga kudurin ta, sai tayi fatan Allah yasa ya kasance shine hanyar alkhairin sa a rayuwa. Da wannan tunanin tayi ta sa masa albarka tare da nuna tsantsar farin cikin ta da amincewar san gami da alfahari da shi...ta kuma gode Allah dan tasan ba kowa ke dacen samun 'da irin sa ba...' da mai biyayya da juriya da jajircewa wanda baya ta6a son ganin 6acin rai saman fuskar mahaifan sa. Cikin sa'a kuma tunda ya fara karatun bai samu matsalar komai ba, ya kuma bada hankali yayi karatun sa fiye ma da yadda ita tayi tsammani, daga 'karashe da riba biyu ya fita kowa na taya sa farin ciki..shikan sa farin cikin yayi. Tsaki yaja a bayyane ganin yadda Amrah ta bar masa gadon sa a hargitse tayi ficewar ta, ya rasa wace iriyar mutun ce Amrah a duniyan nan. Ace komai ita sai an mata shi, ko an saka tayi sannan zata yi. Da kansa ya gyara komai sannan ya koma bathroom ya 'dauro alwala bayan ya gama uzurin sa ya fito sai da yayi shafa'i da wutri kafin yabi lafiyar gado, zuciyar sa cike taf da tunani kala- kala. 'Bangaren Zaitun ma kusan haka ne, tamkar dai Rayyan, tunani ne fal a zuciyar ta, bata kuma san cewa an shigo 'dakin bama balle tayi tunanin waye wanda ya shigo, da nisa can ta bayar da hankali ga mahalicci dan neman cikar burin ta, sai da ta idar ta shafa addu'ar ta kafin ta fahimci ba'kon 'kamshi ya gama mamayar 'dakin. Dube- dube ta 'danyi cike da firgici lokaci guda abinda ya ta6a faruwa tsakanin ta baban Abdul ya dawo mata, sa6anin wancan wannan karan bata ga alamun tunanin ta zai.iya zama.gaskia ba, musamman da yake wannan labilen a sakale yake jikin wani karfe ba ta yadda za'a yi mutun ya 6oye batare da ta ga mai shi ba, sannan 'kofa a rufe yake.kamar yadda ta bar shi. Bata tsawaita tunanin ba kawai ta basar da tunanin ba mamaki hancin tane kawai ya jiyo mata kamshin. Mufee ta gyarawa kwanciya sannan tayi mata addu'a ta shafe ta daga baya tayi nata ta shafa itama ta kwanta da niyyan bacci amma sam baccin ya gagare ta. Tunani kala- kala ke dawo mata, a shekara guda 'daya baya idan ance mata zata tsinci kanta cikin irin rayuwar da take yanzu tsab zata karyata, sai gashi kamar wasa kamar cikin mafarki ta shiga yanayi mabanbanta da bata ta6a tsammanin tsintan kanta cikin su ba, fatan ta Allah ya bata ikon jurewa, ya kara mata karfin gwiwa. Sai bayan kwanaki biyar da zuwan su gidan kafin hajiyar gidan ta dawo daga Abuja wajen taron da taje, Zaitun bata ma sani ba ni..dan bata fitowa daga 'dakin su tsabar yadda take shiga damuwa da son kusanta kanta ga Allah har sallar walaha ta fara cikin 'yan kwanakin,..ko ruwa take so a bathroom take dibar musu susha sam bata damu da fita cikin gidan ba. Tana so ta fita ta danyi wani aikin amma rasa 'kwarin gwiwar hakan take yi kusan kowani lokaci. Tana zaune kan daddumar da take salla akai sai taji ana kwankwasa kofa ta tasan bb mmk Raleeya ce ta miko musu abinci hakan yasa tayi saurin mikewa ta bude kofar...sa6anin Raleeya yau Hajja ladi na gani tsaye amma babu komai a hannun ga dukkan alamu ba abincin ta kawo ba sannan fuskar ta kamar kullun babu wata walwala. "...Ammi na kiran ki a babban parlour...". Daga haka ta juya sai kuma ta dawo da baya" kiyi maza in raka ki". Muphy ta koma ta 'dauko a inda take zaune gefen da tayi sallah tabi bayan Hajja Ladi zuwa wani sashe mai girma...ashe wancan parloun da ta gani ba komai ba ne wannan shine asalin jindadin rayuwa...Hajia ce zaune ta hakimce gefen ta kuma wani ne da bata ta6a gani ba sai dai yanayin jini da ya bayyana kamanni tsakanin sa da Ammi yasa ta fahimci yana da ala'ka da ita. Zama tayi ta 'dora Muphy saman cinyar ta tana fuskantar gefeyayin da Zaitun ke fuskar su Ammi ta fara gaisar wa cike da murnar ganin ta, ta kuwa amsa cike da fara'ar da nuna kulawar ta gare su. Su uku ne zaune a parlorn dan haka shima na da ke zaune gafen Ammin ta gaida shi.. A takaice ya amsa mata tamkar mai ciwon baki yana duba tsadadden agogo dake 'daure a tsintsiyar hannun sa...bata iya ta sake kallon inda yake ba duk da tana jin zuciyar ta na muradin.m sake duban fuskar sa, badan komai ba sai dan kawai son tantance tsakanin shi da Ammi shin wayafi wani kyau ne, amma masifaffen kwarjini ne da shi da ya hana ta sake duban nasa, gaba 'daya ji take kamar ya cika ilahirin 'dakin shi ka'dai. Kallon sa Ammi tayi tana murmushi tace" Saurin me kake haka ne naga kana wani duba agogo..?" 'Yar murmsuhi yy batare da ya bata amsa ba. Ammi bata damu da amsar tashi ba sai ta dawo da duban ta ga Zaitun tace" Hajja Ladi ta gaya min abinda ya faru, tace tun tafia ta baki fito kin sha iska ba, meyasa kika za6i killace kanki cikin 'daki bacin na fa'da miki ki saki jikin ki a gidan nan..?" Shiru Zaitun tayi tana wasa da igiyar rigar Muphy dake kan cinyar ta. " Ganin hakan yasa Ammi gyara zama ta tana mai cigaba da fa'din" Shikenan..wannan ya wuce, in dai bazaki takura ba duk 'daya ai, amma ina so dan Allah in dai babu wata matsala ki bani labarin ki wala Allah ko akwai taimakon da zamu iya yi miki matsayin mu na 'yan uwanki musulmai." Shiru Zaitun tayi kawai ta sunkuyar da kanta tana kallon 'kafar muphy gami da wasa da yatsun ta. " Ina jin ki kinyi shiru Zaitun..?" 'Yar 'karamar tsaki Rayyan yaja yana kawar da kansa gefe haushin ma yarinyar yake ji sosai taya zata wani ringa bata musu lokaci angaya mata su din kamar ita ne da bata bawa lokutan ta muhimmanci ba. Ammi ce ta banka masa harara sannan ta cigaba da tambayar Zaitun.." ina fatan ba wulaqancin namiji bane ya sa kk baro gida da yarinya?" A hankali ta 'dago kai ta kalli Ammi sai kuma ta girgiza kanta...alamar a a tana mai saukar da idanu. Iya zaman ta a gidan ta fahimci kowa Ammi yake kiranta dan haka itama da wannan sunan tayi amfani " Ammi ni bansan me zance mk game da labari na ba..iya abinda na sani shine ni bani da kowa bani da gida sannan bani da iyaye ko yan uwa anan kusa, mun kasance ne tamkar marayu, Mufeedah ka'dai ce yan uwa na ita ka'dai nake da shi a yanzu, lokacin da Allah ya bani mufeedah kusan kowa baya son ta, kowa gudun ta yake yi harda ni ma, kalilan ke nuna mana kauna..amma mafi yawa sunce bazasu iya zama da ni da Mufeedah ba ni kuma ina son 'yata...dalilin haka yasa yanzu.bamu da kowa, nayi 'yan sana'o'i a baya wanda da shine ya taimaka mana babu tagaiyara ba har zuwa lokacin da abubuwa suka gagara muka koma bara a bakin titi...nan ta cigaba da bata labari a ta'kaice na yanda abubuwa suka kasance mta har zuwa ranar da suka hadu a kotu da Ammin. Ajiyar zuciya hajia ta sauqe gami da furta " Allah sarki…gaskiya kin sha wahalar rayuwa, kuma banga laifin ki ba da kk matukar son 'diyar ki har kika sadaukar da dukkanin farin cikin ki saboda ita…'ya 'ya Rahama ne kuma ga wanda Allah yaso ka'dai yake bada su...muma da kika ganmu babu abinda muka fi so da kishirwa irin muga yara agidan nan amma Allah cikin ikon sa bai nufe mu da samu ba so ni banga laifin ki ba. "...Ammi.."! Rayyan ya kira sunan ta cike da kufula jin kamar Ammi na son ta tona mata sirrin ahalin su ne bacin bama gama sanin takamman wace ita tayi ba. Tun farkon fara labarin nata matsayin sa na mai shari'a ya fahimci ta 6oye abubuwa da dama bai kuma san manufar ta kan hakan ba, toh meyasa ita zata ji nasu. Hararan sa Ammi tayi saying.." I know what I'm doing.." A yadda tayi maganar ba lallai Zaitun ta fahimci warning ta bashi ba tamkar sako ta isar haka tayi maganar, musamman da ta cigaba da fa'din" Allah ya raya mk ita yasa mata albarka ya baki ikon tarbiyantar da ita..." 'Kasa- 'kasa ta amsa da " Amin ngd Ammi..." " Bakomai Zaitun...sai dai kuma ina da shawara da zan iya baki idan zaki amince, dan agani na shi yafi dacewa akan zaman ki haka nan, duba da irin ha'darurrukan da kika tsallake a baya, gudun faruwar makamanciyar su da ba'a san da wacce siga zasu iya zuwa ba, me zai hana ki koma ga iyayen ki ki basu hakuri ko zasu amince su kar6e ki da yarinyar taki..." 'Dago idanu tayi ta na duban Ammin idanun ta fal tsoro wanda yake har zuciyar ta. " Kar kiji nace haka kiyi tunanin koran ki nake so nayi daga gida na, sam ba nufi na kenan ba, fatana in kwadaita miki hanyar tsira ne, duk yadda kike tunanin iyaye sun wuce nan Zaitun..kuma dolen mu muyi musu biyayya har mu.rabu da su lafia, kema wannan nake kwadaita mk, kuma kar ki damu ni nan zan miki jagora zuwa garesu insha Allahu kuma ba zasu ki amincewa da zaman ki tare da su ba". Kai Zaitun take girgizawa a hankali sosai maganar Ammi ta shige ta, wasu sanyayyun.hawaue suka kwaranyo mata...inama inama, inama zata iya hakan, ita oanta bata burin da ya wuce ta ganta cikin halin ta kamar baya amma wani dalili yai mata cikas da hakan. Abu guda ne zae taka mata birki shine tsoro, a hankali Zaitun tayi 'kasa da idanun ta da suke cike tafi da kwallan da ke sauko mata tace.." Ammi zan koma, ni kaina zan fi son hakan amma dole ba yanzu ba, kiyi hakuri Ammi kar kice na bijirewa shawarar ki, hakika maganar ki ta faranta raina, na kuma gode sosai Ammi, kece mutun ta farko da kika bu'de min zuciyar ki har haka, kece kadai kika nuna zaki iya min jagora zuwa ga iyaye na, amma a yanzu bani da damar hakan Ammi, ko da nace zanyi, rayuwa ta ne da ta Mufeeda zasu iya shiga garari ba mamaki ma mu iya rasa ran mu har ma da wanda zai mana jagoran, bazan so kuma wani abu ya faru dake ba Ammi ta dalili na..kuma kona koma gida a yanzu babu wanda zai fahimce ni babu inda zan samu sauki balle muhallin da zan zauna da yarinyar nan sun riga sun 'kalubalance mu, zasu gani kuma kamar na 'kisu ne saboda yarinyar zasu ga na za6i yarinyar sama da su dan haka tsanar da akai mata bazai ragu ba sai dai ya karu amma na tabbata akwai lokacin da su da kansu zasu fahimce ni, a lokacin da na tabbatar ko da na koma gare su takuran da zasu yiwa Mufeeda bazai iya tasiri ba dan zata iya 'dauka, Ammi nafi so sai shekarun Mufeeda sun kai wani matsayi kafin zan koma, a lokacin da na tabbatar da ita kanta zata iya bawa kanta kulawa, koda bata tare dani, amma a yanzu ni.kadai ta sani, ni kadai ta budi ido ta sani, mufeeda bata saba da kowa ba sai ni zuciya ta bazata iya 'daukan rabuwa da ita ba". " Shikenan Zaitun, bazan takuraki ba..duk shawara da kika yanke.bi mai goye mk baya ce, fatana kawai shine ki.kasance yarinya mai.biyayya ga mahaifan.ki, kar ki kuskura wasu abubuwa dake cikin.duniyar su ra'de ki ga barinvhanyar tsira..." " Insha Allah Ammi...". Ajiyar zuciya Ammi ta saki tana mai fadin. " Allah ubangiji yayi mana jagora..." "Ameen ". Zaitun tace yayin da Rayyan kamar ba shi cikin 'dakin, banda danna wayar sa babu abinda yake yi..kokadan bai sake duban daya cikin su ba amma duk tattaunar sun akan kunnen sa ne, haushi ji yake tamkar zuciyar sa zata yi bindiga. Meyasa Ammi.ta kasa fuskanta, yarinya karama ta zauna sai ninke take a baibai, dama taya ma za'ayi ta koma ga iyayen ta tasan ta tafka abun kunya in tama da kunya ai dole ta nisance su. Zaitun kam sake rungume Mufee tayi tana jin ninkin 'kaunar yarinyar cikin zuciyar ta, wani irin so take wa yarinyar, wani irin zazzafan kauna da soyayya, a yanzun ne ma take jin zuciyar ta na sake 'daura sabuwar aniyar bata kulawa. Tun daga ranar kuma ta fara aiki da sauran ma'aikatan gidan, kullun tare suke aiki a kitchen 'din da su Hajja Ladi duk da ba wani sakin fuska take samu daga wurin ta ba amma da yake akwai Raleeya sai bata damuwa sosai. Amma ko aiki take yi a kitchen ba ta nutsuwa ta ringa raba hnkl kenan musamman idan tasan ta bar Mufee na bacci a 'daki ta ringa zarya kenan tana zuwa duba ta tana dawowa, wai dan kar ta tashi taga bata nan tayi kuka, a ba'dini kuwa ba manufar ta ka'dai kenan ba, tsabar rashin yadda ne, dan har alokacin zuciyar ta bai sake a gidan ba, gani take kamar zasu cutar mata da yarinyar watarana. Raleeya na shan mata dariya, wani bin kuma kawai goye abinta take abaya tayi aikin da ita a haka amma sai in tana bacci, in ba haka ba matukar idanun Mufee biyu bata yadda da goyo ta ringa 'kananun kuka kenan har sai ta sau'ke ta. Ammi tun bata lura ba har tazo ta fahimci Zaitun 'din, ta kuma jinjinawa irin wannan 'kauna, da gangan watarana ta tambaye ta zaryar me take yi sai cewa tayi Mufee na nake dubawa Ammi kar ta tashi bata ganni ba tayi kuka. Murmushi kawai Ammin tayi mata sannan tace ki kwantar da hankalin ki da ta tashi zan kira ki ba gani nan akusa ba. Ita kuwa sam hankalin ta bai kwanta ba domin bata manta halin mugunta da son zuciya irin ta mutane ba...akan Mufee sam bata yadda kowa a duniyar nan. Duk aikin da take yi tana yi ne saboda yarinyar dan bata so taga komai nata yayi 'kasa sam bata damu da kanta ba shiyasa a kullum take jajircewa wurin ganin tayi aiki ta kula da rayuwar 'diyar ta..tasan 'diyarta mai albarka ce shiyasa ma abubuwa da dama ke zuwa musu da sauki. Wannan dalilin shiyasa Ammi cire ta a aikin kitchen ta maida ita 6angaren ta, dan acewar aikin zai fi mata sauki tunda akwai nawin kulawa da 'diyar ta akanta kar abubuwan su mata yawa zata fi natsuwa idan gyara da sharan 'dakine ka'dai, sai mopping aikin ta. Itama sosai taji dadi da wannan canjin ta kuma nuna tsantsar farin cikin ta ga Ammi. Zuwa lokacin tagama fahimtar cewa ba Ammi ka'dai ke zaune cikin gidan ba akwai matar 'dan ta sai dai da yake gidan nada girma yasa tsakanin su akwai tazara sosai, kuma daga nan Ammi ke tura mai aiki can 6angaren kullun safia, kuma ba kowa Ammi ke turawa ba face Raleeya da ta kasance asali dama dan wancan 6angaren aka 'dauke ta. Komai kuma daya shafi wancan 6angaren a hannun Raleeya yake, hatta da hidimar abincin su. Kimanin sati biyu kenan amma kwata-kwata sau biyu kacal Zaitun taga matar da ta kasance itace matar 'dan Ammin mai suna Amrah kamar yadda taji Ammi na kiran ta da shi. Shima zuwan nata ko kyakkyawan kallo bata samu daga wajen ta ba ita har Mufee, bata damu ba kuwa, hakan ma tasan kaddarar haduwar sun dan dai Ammi ta dawo da ita aikin 6angaren ta me baya ga haka da ace a kitchen take aiki inama zata ganta. Sau biyu tazo 6angaren Ammin cikin kwanaki kusan goma sha biyar duk da yake cewa cikin gida 'daya suke. Amma koka'dan Ammi bata ta6a complaint ko nuna rashin jin dadin ta game da hakan ba...Ammi macece mai matukar girmama zamantakewa da kyautata mu'amala, babu ruwanta da shiga sabgar da bata sahfe ta ba, abinda yake gaban ta kawai ne bata damuwa da lamarin wani, ga ta kawaici da nuna kauna ga kowa. Yayin da Amrah ta kasance yarinya ba wata babba ba, dan shekarun ta ashirin ne da uku zuwa da hu'du, sai dai bata da girman jiki, komai nata 'dan daidai ne, ga ta kyakkyawa mai hasken fata. Amrah 'yar 'kwalisa ta 'karshe ta iya gayu ga ilimi. Abu 'daya da Zaitun zata ce bai mata ba game da Amrah shine 'dagawa rashin sakewar ta gare su sannan ta fiya zafin kai da raina mutane. Wannan dalili kuma shi ya rage kaso mafi rinjaye daga dukkan wani kyawun ta da suke gani a zahiri, dole ta 'darsa musu jin haushin ta musamman Raleeya da tafi kowa sanin halin Amrahn ta kuma fi kowa shan hantara da masifa a wajen ta musamman da yake ita ce ke zuwa yi mata komai, ta kan iya sata yin girki sau uku lokaci guda da sunan duk wadanda akayin basu mata ba, ko kuma tace ba yanda take so akayi ba, ita kuma bazata tashi tayi da kanta dan kwanciyar hankalin ta ba. _Share to other groups..._ _Salmerh_ 😘 [20/9/2022, 9:29 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* Wattpad@ Serlmerh-md 🅿️ *...34* .......Satin Adam biyu a asbiti kafin aka sallamo shi, duk ya rame ya zam tamkar ba shi ba, abu 'daya kadaivne bai canza game da shi ba shine gayun sa, shima 'din ba kamar baya ba dan a har yanzun ba cikin natsuwa yake jin kansa sosai ba. Duk yadda Hafeez da Hajiyar sa suka so ya kara samun nutsuwa ki yayi, Hajiya da kanta tai masa alkawarin nema masa Zaitun ita dai burin ta ya samu natsuwa amma ya kiya. Adam yasha bakar wahala wajen neman Zaitun amma sam ya gaza cimma burin sa, bai kuma ji ko da wanda ya ganta bane balle lbrn inda suke...sai da Adam ya koma tamkar mahaukaci sbd neman Zaitun amma ya rasa ta, gefe guda ga damuwar abinda mahaifin sa ya aikata ya kasa barin zuciyar sa. Daga baya ya nemi gidan mahaifiyar Dr Rashed da tunanin ko tana tare dasu amma suka ce basa tare da ita, sun nemi ta biyo su amma taki amincewa hkn kuma basu san ina take ba a halin yanzu. Da 'kyar Adam ya saduda ganin kamar Zaitun tayi masa nisan zango ne nisan da baya jin zai iya samo ta anan kusa..dole badan yaso ba ya hakura amma bai cire rai da samun ta ba watarana. Sai da aka sake shafe wasu kwanaki kafin da ban baki Hafeez ya sa shi agaba suka kaiwa Alhaji Jibrin ziyara a prison, a hakan ma da 'kyar aka barsu ganin sa, dan killace yake a wuri na musamman. Hakika 'dan Adam ba'a bakin komai yake ba, idan kaga yadda 'Dan Maliki duk yayi sanyi bazaka ta6a 'dauka wannan mutumi mai izan nan bane, bazaka zaci cewa wannan mai tunkaho da dukia da karfin mulkin siyasan nan bane wanda jama'a ke matukar martabawa...rayuwa kenan. " Al..ha...ji"! Adam ya furta sunan sa a mamakance gami da mi'kewa tsaye ganin cikin 'yan kalilan din satikai gaba 'daya kamanin sa sun sauya zuwa wani daban, zama yayi bisa kujerar da ya mike yana jin idanuwan sa na tara ruwa...Innalillahi wa inna ilaihiraji'un... Ya furta a fili 'kasa 'kasa yana jin wani abu mai kama da tashin hankali yana shigan sa. Shi har 'Dan Malikin da ya zaune kujerar dake zaune facing da Adam 'din kasantuwar baya iya jure doguwar tsayuwa a yanzu jiri ke 'diban sa, dukkan su kwalla suke zubdawa, babu wanda ya iya furta komai daga cikin su Abu guda da yafi damun 'Dan Maliki ya kuma fi tsaye masa a zuciya bakomai bane face tunanin yadda Adam zai kar6i maganar, dama tun ma kafin faruwar lamarin ya riga yayi nadamar komai ya kuma zanta da Hafeez ya sanar masa duk niyyar sa, sai dai bai san ta yadda 'adn nasa zai kar6i zancen bane, tuni kuma ya fara neman gafarar ubangijin sa yana.fatan kuma ya yafe masa duk kuraransa kafin.lokaci ya 'kure masa. Yasan kuma.wannan duk shirin ubangiji ne, ya riga ya tsara masa sai ya kar6i wani hukunci tun anan dunia kafin haduwar su aganin sa shiyasa har maganar ma ta bayyana bai kuma yi bakin ciki sosai da hakan ba, a iya sanin sa abinda ya shuka ne zai girba amma tunanin sa Adam ne, musamman da yasan cewa yana da ciwo sanadin damuwar sa sai ga wannan kuma...wani hali zai shiga, ya zaiji idan wannan labari ya riske shi...kullun tunanin sa kenan. A yau kuma da Adam ke zaune gaban sa banda tsananin kunyar sa babu abinda yake masa kai kawo, sosai yake jin babu dadi idan ya tuna makomar da Adam din zai iya fadawa, sai gashi ayau 'din daya gansa ma duban farko ya fahimci Adam din ba karamar wahala yasha ba duba da yadda duk ya rame ya zam sai 'kashi duk wata kumari tasa babu ita...wai sai yaushe ne zai daina azabtar da zuciyar bawan Allahn nan. 'Bangaren Adam kuwa rasa ta inda zai fara ma yayi, bai san me ze ce da mahaifin nasa ba, shin jaje zai masa ko kuma gaisuwa game da faruwar lamarin?, bazai iya ko guda daga ciki ba, gaba 'daya ji yayi komai ya kwance masa, wata zazzafar 'kauna da tausayin mahaifin nasa suka diram masa lokaci guda fin ma kaunar da yake yi masa abaya, meyasa ya za6i wannan hanyar wajen tara dukiyar sa..? Meyasa bai yi tunanin makomar da hakan zai iya jefa shi ba da duk masoyan sa...? Sosai yake zubda 'kwalla kansa a kasa, ya ma kasa duban 'Dan Maliki sau biyu tun duban farko da yayi masa bai iya ya 'kara ba, gashi wannan karon Hafeez bai biyo shi sun shigo ciki ba cewa yayi zai jira shi awaje balle ya 'kara masa 'kwarin gwiwa. 'Dan Malikin ne yayi 'karfin halin magana ganin lokacin sa na tafia kamar yadda aka bashi. 'Yar murmushi ya 'ka'kalo wacce ta tsaya masa iya saman fuskar sa, yana duban Adam yace..." wannan karon ma hakuri zan baka 'dana, koda wani lokaci kalmar kenan, sai dai ina fatan ya tsaya hakanan, hakika na kasance mai tsananin san zuciya ta batare da tunanin baya na ba, batare da tunanin me gobe na zai iya haifarwa ba...Na san na sanya zuciyar ka cikin 'kunci duba da yadda naga duk ka rame ba kamar yadda na san ka abaya ba.." Dan Allah kayi hakuri kaji, Hafeez ya sanar da ni komai har da batun rabuwar ka da waccen yarinyar...Zai...Zaitoona ko?...ni kaina banji da'di ba ina kuma ji araina da ina da dama da duk lungun da ta shiga a fadin duniyar nan sai na binciko maka ita, amma ina fatan ni ka'dai 'dinnan na kasance iya mugayen kaddararorin da zazu faru da kai anan dunia, Allah yasa iya 'kuncin da zan sakaka kenan a duniyar nan, Allah yasa sun 'kare kenan.." " nayi maka alkawarin daga iya abinda ya faru bazaka sake jin wani mummunan abu daga gareni ba har abada 'daana ." Kai ya girgiza da zummar maida 'kwallar sa amma hakan ya kasa yiyuwa, sosai ya bawa zuciyar sa dakiya wajen ganin sheshshe'kan sa bai bayyana a fili ba gami da rarraba kalaman Mahaifin nasa cikin ransa"...me kuma zan sake gani ya tambayi zuciyar sa aganin sa duk abin da zai sake biyo baya ba zai kai abinda duk ya riga ya faru ba game da mahaifin nasa..." Cikin zuciyar sa duk yayi wannan tunanin yayin da a fili kuwa bai iya ya furta masa komai ba.... Hannun sa 'Dan Maliki ya kamo duk biyu ya rike cikin nasa hannun ya cigaba da magana...Adam na jin yadda hannun ke rawa sosai amma bai janye hannun sa ba. " Naji da'di sosai da ka tuna dani har ka ziyarce ni ba tare da ka yi duba izuwa ga tarin kurakuraina ba, ban ta6a zaton zaka zo gare ni ba ko cikin mafarki..hakika kai 'din 'dan halak ne, Allah yayi maka albarka ya yiwa rayuwar ka albarka ya kara haskaka imanin ka, amma ina mai sake rokon ka Adam ko bazaka yafe min ba, ko da bazaka sake ziyarta ta ba, dan Allah ko da sau 'daya ne cikin rayuwar ka, ka dube ni kai min duba irin na uba a zuciyar ka ko nima zanji da'di, na maka alkawarin zama nagartaccen uba daga rana irin wannan har 'karshen rayuwa ta, mahaifiyar ka ta riga ta koma ga mahaliccin ta, na sani Hafsat mace ce nagartacciya wacce har ta bar duniya babu wani abu guda da zan fito in nuna ko ince tai min na 6acin rai, duk abubuwan da suka ta faruwa nasan son zuciya ta ne kadai ke kawo su, kuma bazan 6oye maka ba na shiga tsananin tashin hankali da rudani game da rashin Hafsat na kuma yi nadamar duk abubuwan da nai mata abaya wanda ban kai ga neman yafiyar ta ba Allah ya kar6i rayuwar ta, bana son in sake wannan kuskuren a yanzu ga ni ga ka tun numfashi bai 'kare min ba da harshe na idanuwa na kallon ka nake rokon ka Adam ka yafe min kaji ka yafewa wannan mahaifin da ya rayu da tsananin son zuciyar sa shikadai batare da damuwa na na 'kasan sa ba..." Hannun Adam dake cikin nasa yaji rikon ya bambanta, sosai Adam ya tamke hannun sa cikin na mahaifin nasa yana jin wani nutsuwa na shigan sa da bai ta6a jin makamanciyar sa ba..ba 'karamin mamaki 'Dan Maliki yayi ba da jin hakan sosai ya tsurawa hannayen nasu idanu cike da mamaki, a hankali Adam ya fara magana. " Ni ban ri'ke ka cikin zuciya ta ba, nasan komai mukaddari ne, na kuma san akwai son zucia akwai jarrabawa, sannan akwai 'kaddara, na rasa Zaitun yes nasan nayi rashi but rashin Zaitun ba shine 'karshen rayuwa ta ba, ba shine karshen farin ciki na ba, tunda ina daku ina da kai, ina da Hajiya sannan ga Hafeez ku ka'dai kun ishe ni rayuwa amma komai ya wuce ban isa in canza komai ba, kamar yadda nima 'din ban fi karfin Allah ya jarrabce ni da daya daga cikin duk abubuwan nan ba...". Da sauri 'Dan Maliki da farin ciki ya gama mamayar sa yana girgiza kai ya furta" Insha Allah babu ko guda da zai same ka, daga yanzu har karshen rayuwa ta addu'a zan ta rokon Allah ne ya kare min kai....". Murmushi kawai yayi 'yar kadan sannan ya cigaba da fa'din..." A yau nazo gareka ne, ba dan neman alfarma ba, badan in maka jaje ba, ba nazo ne musamman dan wani abu ba nazo ne kawai a matsayi na na 'daa izuwa ga mahaifi na...." 'Dan Maliki da ya kasa hakurin jin 'karshen kalamin Adam sake rungume hannayen sa yayi yana fadin.. _Alhamdulillah_ nagode, nagode, nagode 'daana ubangiji Allah ya yiwa rayuwar ka albarka, ya baka 'yayan da zasu yi bika suyi maka biyayya Allah ya cigaba da haskaka rayuwar ka ya haska gaban ka da bayan ka, Allah ya jikan mahaifiyar ka ya kai haske 'kabarin ta....". Addu'a kawai yake ta jerowa harshen har na sarkewa. "...Thank u Abbah...Amin Nagode sosai nima ka yafe min..." Adam ya fada yana duban sa cike da rauni. " Bakai min komai ba, baka ta6a min laifin komai ba Adam..kuma har abada bazaka ta6a zama mai laifi a waje na ba da iznin Allah...". Murmushi Adam yayi sannan ya mi'ke a hankali ya zare hannun sa cikin na mahaifin nasa sannan yace " Zan tafi..."! " Thank u son..Allah yai maka albarka.." " Amin Abbah.." Har ya juya sai kuma ya tuno wani abu hakan yasa ya juyo " Baka bani labarin kowa naka ba, I mean labarin familyn ka gaba 'daya..." Ka samu abokin ka Hafeez akwai komai tare da shi bani da isasshen lokacin da zan ma bayani da baki shiyasa na takaita komai.... Daga haka aka zo aka fice da 'Dan Maliki Adam na kallo amma bashi da ikon dakawatar da su, haka ya fita yana mai jin babu da'di but deep down yana jin sanyi cikin zuciyar sa, shi kansa 'Dan Malikin yanzu nutsuwa yake ji tana shigar sa, tamkar wanda akace masa freedom za'a bashi a yau din, bai ta6a zaton duk damuwar sa akan Adam take ba sai yanzun, hakika 'ya'ya Rahama ne, a yanzu wasai yake jin zuciyar sa ba kamar kwanakin da suka shu'de ba. Adam na fita suka ci karo da Hafeez da ke ta kai kawo a inda yake zaman jiran sa. Yana ganin sa ya taho da saurin sa fuskar sa da alamun damuwa yace..." Ya akayi ka dade haka, ka fa bani tsoro.."! Murmushi Adam yai masa gami da fa'din " Worry not ba gani ba...". Ido Hafeez ya zaro yana fa'din" kai din..? Da mamaki, domin rabon da yaga fara'a kan fuskar abokin nasa har ya manta. Tafiya suka fara izuwa ga tashar da zasu samu motar da zata maida su gida dan dukkanin su har yanzu babu wani da ya mallaki motar hawan kansa. Hamdala kawai Hafeez ke yi cikin zuciyar sa gami da nuna jin dadin sa a fili. " Hakika yau 'din farar tafia suka yi...basu yi tafiyar banza ba domin ga dukkan alama ta janyo gagarumar nasara tsakanin Adam da mahaifin sa. Kasa jurewa yayi yana duban Adam yace.." Kamar ba kai ba..." " Da akayi yaya...?" " Ka fini sani ai 'dan air, yau ni Hafeez zanyi bacci har da minshari". Ya fa'da da 'karfi yana duban sama gami da dafe 'kirji da hannun sa 'daya. Duka Adam ya kai masa sai ya goce yana fa'din" Kai kyale ni in nuna wa Allah godiya ta..fatan kasa mi Alhajin lafiya...."." Turus Adam yaja ya tsaya, " Wani Alhajin kenan? kana nufin Abba na..?" " Toh fa , sabon salo, nasan ban da ni ai, naka ne kai kadai duk duniyan nan babu wanda ya fi dacewa ya furta hakan sama da kai, amma ai ka amsa min tambaya ta dai ko..? Daria dukkan su suka sanya sannan Adam ya fara fa'din " yana nan 'kalau ya mace in gaida ka da Hajiya ta..". " Masha Allah abu dai yayi kyau...". " Ya fa'da maka wani abu ne..?" " Kamar me fa..?" Shima ya maida masa amsar tambaya madadin amsar da yake bukata. " Kaifa 'dan yawa ne wlh...wani abu dai haka bai fada maka ba...". " Abubuwa da dama ya fada min..har ma yai ta samin albarka ni har zuri'ar da zan haifa gaba 'daya...". Comment nd share to other groups please. Salmerh😘 [23/9/2022, 10:51 am] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* Wattpad@ Serlmerh-md 🅿️ *...35* ........." Ba wannan nake son ji ba Malam...kana nufin Alhaji bai sanar da kai komai ba? bai ambaci suna na ko sau 'daya cikin maganar sa ba...?". Cewar Hafeez cike da nuna rashin jin dadin sa a fili. Adam na dariyar shakiyan ci yace" Ji wani zance kai kuma, meyasa zai ambace ka bayan gani kuma gaban sa....?" Wannan karon cike da jin haushi Hafeez ya kai masa naushi ya goce yana dariya sosai. " Ka dallah malam sakar min mara...ba dai so kake kaji ba? Toh ya sanar da ni ya baka ajiyar kundin tarihin ahalin sa...kaga nima zan samu dangi nan kusa". Murmushi Hafeez yayi yana hararan sa yace.." Shine sai ka wahal da ni..?" Ba 'karamin dadi Hafeez yayi da wannan annuri da farin cikin da ga abokin sa a ciki...fuskar sa cike da fara'a yace" Toh bayan haka fa...?" " Babu komai" Inji Adam yana tafiya Hafeez ma kokarin jerawa da shi ya sake fadin" Ka tuna dai...". " Ka manta asali ni ba gwanin mantuwa bane...?" "Ai shikenan, amma dai ba kundin tarihi ka'dai Alhaji ya bani ajiya ba, har da kundin tattalin arzikin sa gaba 'daya ma'ana dukiyar sa wacce ya mika ta kacokam ga 'dan sa 'kwaya 'daya tilo wato _Adam Shaheed Jibrin 'Dan Maliki.._ ." " Wasa kake ". Adam ya fadi cike da nuna rashin kulawa ga maganar. Ganin hakan yasa Hafeez fizgo hannun sa cike da kufula yace" meyasa kake maida komai wasa ne Adam? wannan batun fa ba na 'kananun ku'di nake maka magana ba, ina maka magana ne akan 'dimbin dukiyar mahaifin ka da ya tara ya kuma mallaka ta gareka...". Ganin kamar Hafeez 'din dagaske yake ya sa Adam 'dan 6ata rai yana dakatawa da tafiyar ya fuskanci Hafeez 'din da kyau. " Kafi kowa sanin bana bukata meyasa ka kar6i ajiyar sa..? ka maida masa abinsa". Ya bashi amsa da iya gaskiyar sa sannan ya cigaba da takawa, wannan karam da 'dan saurin sa. Cike da jin haushi Hafeez ya fara fa'din" Ba za'a maida ba Adam, bazan maida masa komai ba, wai anya kana cikin hankalin ka kuwa..?" " Kafi.kowa sanin matakin da hankali na yake ba sai na maimaita ba maka ba, kamar yadda kafi kowa sanin ba dukiyar sa ta kawo ni gareshi ba?" " Shi kansa ma yasan wannan ba ma ni ba, amma duk da hakan bai sa ya kasa mallaka maka ba...". Fuska Adam ya had'e sosai ya wani 'kankance idanu yana duban Hafeez yace" wai dagaske kake ne...?" Kai Hafeez ya jinjina masa alamun tabbatar wa. " Ka mayar masa dukiyar sa Hafeez kwandalar sa bana bukata, ka manta ire- iren hanyoyin da yabi wajen tara dukiyar ne...?" " ban manta ba, amma ai da ka nutsu ka saurare ni bazaka furta hakan ba..." " Ni dai dan girman Allah Hafeez ka maida masa kayan sa, burina a duniyar in samu yardar Allah mahalicci na na rabu da duniyar lafiya, na kuma san hakan bazai ta6a yiyuwa ba har sai na bi mahaifana, bana da mahaifiya sai mahaifi, na kuma yi kokarin wajen ganin na gyara mu'amala ta da shi ko a yanzu na mutu bazan ji bakin ciki ba, domin nasan tsakani na da Abbah na babu wata matsala...ban ta6a kwa'dayin dukiyar sa ba tun abaya ma, so mai yasa zanyi kwadayin rike ta a yanzu....wlh Hafeez bana bukatar komai daga cikin dukiyar sa, ka maida masa abinsa ba mamaki lokacin da Allah yayi fitowar sa suyi masa amfani...". " Ta ya zan mayar bayan ba hannu na suke ba...?" " Toh mecece damuwar ka kuma..tun da ba hannun ka suke ba? ka 'kyale ni da maganar hakan nan dan Allah Hafeez, ka mance kawai.." " Tamkar amana ya bani Adam, sannan ni Alhaji ya wakilta matsayin jagoran da zan isar da ita gare ka saboda yadda dani da yayi da kuma sanin kusancin da ke tsakani na da kai amma komai na wajen Lauyan sa....nan ya zayyane wa Adam duk yadda suka yi da 'Dan Maliki, yadda ya kasafta dukiyar sa kashi kusan biyar, kaso hudu duk ya mallakawa gidajen marayu da sunan Adam kaso guda kacal ya rage yace na Adam 'din ne, ya kuma tabbatar musu da cewar babu haramun cikin wannan kaso gudan dai- dai da 'kwayar zarra. " Duk da yake munanan harkoki masu yawa Alhaji ke yi amma bai yadda ya sirka dukiyar sa da ta haramun din ba, kowacce da ma'ajiyar ta ka yadda da ni Adam..". Hafeez ya karasar da taushin murya. " Toh me ze hana duk a ha'da akai gidan marayun...?" Adam ya tambayi Hafeez da iya gaskiyar sa. " Baza'a kai ba Adam, wannan mallakin ka ne, ka daina yankewa mutum hukunci bisa halayyar sa ta baya domin lokaci yana koyar da su darasi kuma ya kan canza su, ina tabbatar maka da cewa matukar ka sake bijire wa wannan lamarin zaka zo kayi dana sani watarana, dana sani ma marar amfani". Cike da jin haushi Adam yace..." Fata kake min ko me ne hakan Hafeez?". Hannaye ya 'daga sama" ohh no..gaskiya kawai na fa'da maka...". Tafiya suka cigaba da yi babu wanda ya sake furta wani abu. Hafeez 'kasa- 'kasa yace" mutum sai shegen taurin kan tsiya ana baka kana 'kin kar6a". Abinda kawai ya bawa Hafeez mamaki shine yadda kaso guda cikin dukiyar Alhajin yaso bashi tsoro dukiya ce bata wasa ba da ya tabbatar matu'kar abokin sa ya mallaka ya gama da babin talauci a rayuwar sa, duk wani fadi tashin neman sa sun 'kare hatta jikokin sa sai sun an tara musu, dan shi kansa Alhaji Jibrin sai da ya bashi kyautar 1ml matsayin nasa tukuicin na zama da 'dan sa da yayi da zuciya 'daya, ya bawa Lauyan sa ma tasa kyautar haka ma Hajia Talatu. Kwanciyar jinya da Adam ya da'de yana yi yasa suk bai san da wannan labarin ba balle yasan anyi haka. Har suka isa gida babu wanda ya sake tankawa 'dan uwan sa, ko cikin mota magana bata ha'da su ba, kowa abinda yake cikin ransa daban. Duk yadda Adam yaso ya zame hakan faskara yayi, domin wanan karan Hafeez nuna masa yayi cewa erh shima fa ba baya ne wajen tirjiya da taurin kai, ya kuma nuna masa erh lallai ya isa da shi, da gudummuwar Hajiya Talatu komai ya kammala, dan itama ta tsaya tsayin daka wajen ganin bai bijirewa sakon da mahaifin sa ya bari a basa ba. Adam dagewa yayi akan aha'de duk a mi'ka gidan marayu kamar yadda ya bada sauran amma suka ce sam baza'ayi haka ba...Hajiya Talatu da dama babban burin ta a duniyan nan bai wuce ace taga Adam 'din ta ya zam wani abu shima a fadin duniyan nan ba hakan yasa ta dage sosai kan lamarin, haka Lauyan Alhaji Jibrin 'din shima har ransa sai da ya sosu da taurin kan Adam 'din gashi yana so ya mika masa komai ne zai bar kasar zuwa wani taro...'karshe dole Adam ya sa hannu ya kar6a badan ransa yaso ba. Aganin sun kasa fahimtar sa ne kawai, amma ai Allah da kansa yace mu gujewa haramun, kuma yace duk jikin da aka gina shi da haramun makamashin wutan jahannama yake kasancewa, abinda yake tsoro kenan dan shi yasan waye 'Dan Maliki. Sai da Lauyan 'Dan Malikin ya sake tabbatar masa da cewa asali Alhaji bai ha'da dukiyar kasuwancin sa da ta siyasar sa waje guda ba, haka ma dukiyar da yasan ba ta hanyan halal ya same ta ba baya shigar da shi cikin kundin dukiyoyin sa, daban yake ajiyar su..kamar dai yadda Hafeez ya sanar da shi. Anan ne ma Adam ya fahimci cewa already 'Dan Maliki ya riga ya canza sunayen kan komai daya dangancesa izuwa ga shi Adam 'din yayi mamaki kwarai da dagaske. Duk da tunanin sa zai kula masa da komai ne kafin lokacin da Allah zai yi fitowar sa daga gidan maza amma shi 'Dan Maliki da alamu ba 'kudurin sa kenan ba, sa hannun Adam kawai ya rage a duk tarin takaddun dake hannun Lauyan Alhajin shikenan komai ya sauya..daga ranar da 'dora hannun sa kan takaddun da sunan signing daga lokacin ya tashi daga Adam ya koma attajiri Adam. Haka ya bi duk ya sa hannu, yana jin wani iri, something that bai ta6a zaton faruwar sa ba yau shi yake faruwa da shi, transfering all the assets of that Famous Politician former senate Jibrin Adam 'Dan- Maliki izuwa ga shi 'Dan bunburutu mai aiki a fuel station...abin akwai ta6a zuciya sosai. Basu rabu da Lauya ba kusan sati suna abu 'daya yana nuna masa komai da ya danganci takardun, sati gudan nan kaf Adam bai samu ya nutsu ba sam bai zauna ba, tun yana danne gajiya da jin haushin abubuwa cikin ransa 'karshe har ya fara ba'kin rai yana ciccin magani. Sai da suka kammala komai kafin shi da Lauyan suka koma wajen 'Dan Maliki inda ya kama sati uku kenan bayan waccen ziyarar da suka je da Hafeez. Da wannan damar Alhaji yayi amfani ya sake yi masa bayanin komai, duk da yake zuwa wannan lokacin jikin Alhajin sai a hankali amma yana kokarin dannewa kar su fahimci baya jin dadi, hawan jini da Diabetes 'din sa suka motsa lokaci guda. Shi ya sake yiwa Adam bayanin asalin waye shi da kauyen su dake can jihar yobe 'kar'kashin 'karamar hukumar Gujba mai suna _Katarko_ mafiya yawan al'ummar garin fulani ne, sai tsirarun wasu kabilun daban amma Fulanin sun rinjayi garin kamar dai yadda 'Dan Maliki ma ya kasance bafulatanin usul shima. Duk bayanin da yake Adam duk bai tanka masa ba, Lauya ka'dai ke 'dan rubuce rubuce yana 'dan tanka maganar Alhajin, yayin da Adam ya tsurawa 'Dan Malikin idanu har sai da ya fara tsarguwa da kallon amma bai tanka ba...ya cigaba da bayanan sa. Sai daya kai aya yana jira Adam yace wani abu kafin amma yaji Adam shiru. Dukkan su duban su suka mayar gareshi...amma abinda ya fito bakin sa sai ya basu mamaki, domin ba amsar da suke son ji bace daga bakin sa. " Abbah baka da lafia sosai shine kake 6oyewa ko?" Idanu ya fitar da zummar karyata batun da Adam yazo da shi din amma bai.saurare shi ba. " Sun kaika asbiti ne ko kuwa kawai magani suke baka anan?" Shiru Lauya yayi yana duban Alhajin shi kansa ya fahimci ba lafia yake ba karfin hali ce kawai yake sashi dannewa. Yayin da 'Dan Maliki ya zaro idanu baki.ya bude zai ce wani abu sai kuma take tari ya sarke shi tankar dama jira yake ayi maganar, masu tsaron sa ne suka yo kanshi da sauri suna tambayar lafia, Adam ne yayi musu bayanin cewa baya da lafiya ne sukai shi asbiti ko kuma su basu shi zasu kaisa. Basu yadda su bashi Alhajin ba amma cikin 'kalilan 'din lokaci angama shirya komai na tafiya asbitin, dan ciwon Alhajin kamar dama jira yake lokaci guda duk ya galabaitar da shi. Can babban asbitin gwabnati dake jihar aka kaisa bayan 'yan gwaje gwaje dole aka bashi gado, 'daki na mussaman suka kaishi inda suka 'daure hannun sa da handcuffs suka ha'da da karfen jikin gadon banda tsaro da suka sanya a kowani kusurwa dake asbitin gaba da bayan 'dakin da yake duk jami'an tsaro ne ke gadin shige da fice. Duk yadda Adam yaso a barshi ganin sa hanawa sukai, dole ya hakura ya koma gida har sai an koma da shi prison kafin zasu iya ganin sa. _Sai dai muce fatan samun lafia Alhaji Jibrin 'Dan Maliki._ Hankalin Adam ba 'karamin tashi yayi ba da ciwon Abban nasa, gaba daya yaji ma komai ya fice masa aka, duk wani zumudin sa da son ganin dangin sa da yake duk yaji sun gushe lokaci guda, mahaifi ba wasa bane yanzu ya sake tabbatarwa zuciyar sa, yanzu ya sake tabbatar da irin 'kaunar da yake wa Abban nasa. Duk da ba'a bari ya isa wajen sa har ya gansa amma hakan bai sa ya gaji da zuwa asbitin ba ko daidai da rana guda ba, kusan kullum anan yake yini, kwanan sa biyar a asbitin sannan aka sallamo shi suka koma koma da shi prison anan Adam ya samu damar ganin shi, sosai jikin sa yayi sanyi, duk 'Dan Maliki ya canza masa rama sosai yayi ko wani jijiya dake karkashin.fatar sa ta bayyana kanta a fili. Gam ya rike hannun Adam cikin nasa sai wasu kalamai yake faman jera masa kamar ba cikin hayyacin sa yake ba. Adam kasa jurewa yayi saida yayi 'kwalla sbd tsananin tausayin halin da mahaifin nasa yake ciki. Daren ranar bai iya ya yi.m baccin kirki ba, duk ya karar da daren wajen nemawa mahaifin sa sassauci wurin mahalicci, yana nema masa gafara da fatan samun sauki, ya kuma yiwa mahaifiyar sa ma addu'ar dacewa da Rahamar Allah. Kwana biyu da sallamo 'Dan Maliki yace ga garin ku nan, sai kiran Adam akayi aka sanar da shi yana tsaka da tunanin ta yadda zai dau mataki kan ciwon mahaifin nasa. Sosai ya rikice ya fita hayyacin sa, bai ta6a zaton Alhajin zai tafi cikin kwanaki kalilan ya bar shi a duniyar nan ba...amma ba yiwa Allah gyara. Shi kenan yanzu ya zam cikakken maraya ba uwa ba uba duk Allah da ya fisa sonsu ya dauke su. Duk abinda ake so Adam ne yayi wajen dawo da Alhaji gida dan yi masa suttura da sallah Adam kasawa yayi sam ya kasa bawa kansa wannan kwarin gwiwar, da 'kyar da taimakon Hafeez komai ya kammala aka sada Alhaji 'Dan Maliki da gidan sa na gaskia. Shikenan littafi ya rufu, Rakib da Atid sun gama aikin su, fa'di tashin duniya duk sun 'kare, numfashi ya tsaya cak, bugun zuciya ya tsaya, wahalhalu, jindadin dunia da walwala duk babu su, rayuwa kenan. *( Allah Ubangiji ka ji'kan dukkan musulmai da suka riga mu gidan gaskia, Ya Rabbi ka kai haske 'kabarin su, Yah Allah kasa mu da muke rayen karshen mu yayi kyau, Allah ka bamu dacewa dunia da lahira, Yah Allah kasa mu cika da kyau da imani, kasa mu mutu muna jero kalmar Shahada Amin Yah Rabbal Alamin...)* 👏 _Salmerh_ 😰 [23/9/2022, 1:35 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* Wattpad@ Serlmerh-md 🅿️ *...36* .......Bayan da aka gama komai, zaman makoki ya kare kafin Adam ya 'dan sake, domin ranar da akai addua'n bakwai an yi nasiha sosai musamman ga Adam kan tawakkali da imani da kaddara. Ya kuma fahimta ya rike ta hannu bibbiyu, yasan cewa kowa lokaci daman yake jira, mutuwan nan dole ce. Abu guda dake sanyaya masa zuciya ma shine rabuwa lafiya da suka yi da mahaifin nasa, domin har ya koma ga Allah yana sakawa rayuwar sa albarka da fatan dacewa. Wannan kadai idan ya tuna yakan kara masa karfin gwiwar cigaba da walwalar sa kamar baya, addu'a ce dai bazai fasa yi masa ba har 'karshen nasa numfashin, duk da bai da tabbacin yana da tsawon rayuwa shima. Washe garin da akayi bakwai ya shirya shi da Hajiya Talatu da Hafeez da a cewar sa shima baza'a barshi a baya ba da shi za'a yi wannan tafiyar, haka suka yiwa Jahar Yobe dirar mikiya, ba'a kwan da su ba aka tashi dasu, ba'a san da zuwan su ba sai ga su, ba'a san da wanzuwar su ba ma a duniyar suka bayyana gare su kamar shigar mashi. Farko gidan sarkin garin suka nufa da da bincike da komai aka gano dangin mahaifin nasa da ba laifi suna da yawa ga kuma karamci irin na dattawa. Anan suka samu lbr ashe 'Dan Maliki tun yana yaro ya gudu ya bar garin, karatun almajiranci aka sanya shi sai kuma ya kasance malamin na da saurin hannu ga zafin duka kusan duk dukan da zai musu in dai da dorina ce toh sai ya fasa mk jiki. Abin yana kona rana 'dan Maliki gashi kullun duk dole ne musamman idan baka kawo hadda daidai. Da wani dare bayan sun tashi karatun dare 'Dan Maliki yasha dorina har sai da ta masa shati biyu ya damtsen hannun sa, 'daya ya fashe hadda jini 'daya kuwa bai fashe ba duk akan aya 'dayan karshe suratul Taghabun da bai kawo ba. A zuciye ya bi bayan malam har turakar sa ya kwada masa dutsi aka ya gudu abinsa ya bar garin ya bar malam cikin azaba da tsiyayar jini har sai da akai masa dinki aka. Cike da azaba yana dafe goshin sa yake fadin" Kai Jibrila ramuwa kazo kayi, ni ban isa in hukunta ka ba kenan, 'dan iskan yaro shaidanin banza, insha Allahu sai ka gani ai, sai ka bi dunia ka lalace...". Sosai wannan lamari ya sosa ran Malami har ya yiwa 'Dan Malaki mugun baki kasantuwar sa mai kanbun baka sai kuwa bakin sa ya kama 'Dan Maliki. Duk da duk da wani mai imani yasan cewa komai sai da nufin Allah, amma mun kuma san cewa littafi ko hdithi bai 'karya ta Kambun baka ba, ha'ki'ka Kambun baka gaskiya ne. Koda aka nuna wa Adam Malamin murmushi kawai yayi suka gaisa a mutun ce dan Malamin ya tsufa jigif amma still tabon na nan a goshin sa bai 6ace ba. Tun kuma fitar 'Dan Maliki wancan lokacin bai sake dawowa ba har sai da ya 'dauki shekaru masu yawa sannan ya waiwayo gida, a lokacin tuni mahaifin sa ya rasu saura mahaifiyar sa da kishiyoyin ta, su uku ta haifa 'daya ta rasu 'dayar kuma tayi aure cikin fulanin tashi sun kuwa tashi da ita har yau ba ita babu labarin ta, sai shi ka'dai, hakan yasa ya 'dauke mahaifiyar sa ya tafi da ita. Tunda kuwa da ya 'dauke ta bai sake waiwayen kauyen ba har ya koma ga mahaliccin sa. Duk yadda zan misalta muku yanayin tarin farin cikin da Adam ya tsinci zuciyar sa a ciki bazaku fahimta ku misalta da kanku. Abu ne da ya jima yana muradi sai a yanzun Allah ya nufe shi da shi. ***** Tun shigowar Rayyan gidan ta fahimci a yanayin da yake amma ta basar, tana kitchen taje daukan ruwan sha ta hangi.bayan sa ya shigo sai da ya zauna a parlour ya'dan huta kafin ya tashi ya 'karasa bedroom 'din sa. Baki ta kya6e sam bata jin yau zata iya yi masa komai da yake da bukata, gaba 'daya ma jinta take tamkar wata marar lafiya tsabar wahalan da Sultan ya gana mata ayau din. Tarasa mecece matsalar sa da Rayyan a rayuwa, abinda ya mata yau din ta fahimci kamar duk huce takaicin sa yake yi akanta da bashi da wata hanyar sai ita, ba yau tasan halin sa ba, duk lokacin da ransa ya 6aci da Rayyan akan ta yake sauke duk fushin sa sai ya tabbatar ta jikkatu kafin yake barin ta. Kamar dai yau ma haushin sa ya sauke mata yana kananun surutai bata kuma san mene ya hada shi da Rayyan din ba. Ga kuma Rayyan cikin yanayin da sam bazata iya da shi ba kuma. Dan shima din ba sauqi ne da shi ba har yama fi Sultan, matukar tace zata jarraba kusanta kanta gare shi kuwa tana jin sai dai a 'dauki gawar ta a yau ba sai gobe ba. Tuno yadda Sultan ya lalata mata aikin gyaran da ta kwana biyu tana kaffa kaffa ya sata jan tsaki hadda 'yar 'kwallar ta, ta tabbatar ba zallan jarumtar sa da ta sani bace, dole akwai abinda yasha da gangan dan kawai ya wahal da ita. Hawayen nata kuma sai ya kasa tsayawa. Sai data tabbatar ya shige 'dakin.sa ya rufo sannan ta fito ta koma 'dakin ta itama. Rayyan da tun shigowar sa ya ji gidan shiru ya sa direct ya wuce 6angaren sa, sai da ya watsa ruwa ya huta kafin ya tashi hannun sa rike da wayar sa ya nufi dakin Amrah...gajiye sosai yau yake jin kansa hutu sosai yake bukata bana wasa ba. Luf take kan gado lullu6e da bargo har kanta, ganin hakan ya sa shi 'karasawa wajen ta cike da mamaki dan yasan ba lafiya ce zata sa Amran cikin wannan yanayin ba. Musamman ma dan ganin bata zo ta rungume shi kamar yadda ta saba duk sanda ya dawo gidan ba, a hankali ya 'karasa gare ta dan tabbatar da lafiyar ta. " Amrah lafia..?" Ya tamabaya yana tabbata saman wuyan ta zuwa fuskar ta cike da kulawa. Kuka kawai ta tsinke masa da shi tana mai mayar da kanta bisa cinyar sa da ya lankwasa ya zauna bakin gwadon 'kafar sa 'daya akasa. " Baby zazza6i ciwon kai, ko ina ma ciwo yake min ajiki na..." Ta 'karasa da rungume shi sosai ajikin ta tana sake sakin wani kukan shagwa6an. Dagaske Rayyan yaji jikin ta da zafin zazza6in. Amma bai iya yace komai ba. Sai da ta gama kukan taja ajiyan zuciya kafin yana shafa bayan ta yace" Very sorry..". 'Dan lumshe idanu tayi ta dube shi tana gyara kwanciyar ta ajikin sa. "...Tun yaushe ya fara miki?". " Tun safe fa Baby".! Ta bashi.amsa cike da shagwaba. " nd baki kira kin sanar da ni ba, kuma ai munyi waya 'dazun baki sanar da ni ba why..?" " I'm so sorry Baby, ban san ina tayar ma da hankali ne fa...". " Come on, wani tashin hankali kuma Amrah? akwai tashin hankalin da ya wuce zaman ki cikin ciwo ne..pls kar ki sake irin hakan kinji..?" Kai ta gyada masa ana mai sake narkewa a jikin sa. " Alright..let me get some drugs...ko Clinic zamu.?" Da sauri ta girgiza kanta alamar a a. Bai ce da ita komai ba kawai ya fara kokarin mi'kewa yana cire hannun ta dake cikin nasa itama ta 'daga kanta data aza bisa cinyar sa. Har yaje 6angaren sa ya samo mata maganin da ruwa bata yi motsin kirki ba tsoro take kar ya gano ta. Koda ya kawo da kansa ya bata tasha sannan yace zai je sallah itama kar ta koma sbd maghrib ta gabato zai je ya dawo. Fitar sa yasa fargaban Amrah 'karuwa, ta rasa ma wani tunani zata yi ayau in ta bari Rayyan ya ra6e ta ai bata jin zata tashi araye ayadda take jin jikin ta. Wlh sultan ya cuce ta ba 'dan kadan ba. Ta raya a zuciyar ta cike da jin haushin sa. Sai ma bayan fitar Rayyan da ta gwada tashi zuwa bathroom ta fahimci illar da yai mata, tafiya wannan da kyar taka ta yi. Sosai ta sake gasa jikin ta fin wanda tayi 'dazu, sai kace yau tafara sanin 'da namiji..." Ta 'karashe da jan tsaki. Kafin ya dawo tayi sallah sharp- sharp ta koma ta kwanta kar ma ya dawo yagan ta da 'kafafunta yayi zaton ta samu sauki dan haka ta sake komawa tayi luf. Shi kam daga masallaci 6angaren Ammi ya nufa..sai da ya shafe kusan mintina talatin acan kafin ya dawo 6angaren nasa. Abinci ya tambayi Amrah taci tace erh..dan bama tajin cin komai ayau 'din in ba yazam mata dole ba. Bai bi takan zancen ta ba ya tafi izuwa ga fridge ya dauko mata fresh milk mara sanyi ya tsiyaya mata gami da mika mata dole ta tashi ta dan zauna tasha ka'dan ta mika masa cup din. Bai yi magana ba kamar yadda bai tilasta ta sha bisa dole ba, haka ya mayar bayan wani dan lokaci ya sake dawowa cikin shirin bacci dakin da tarkacen laptop din sa da wayoyi. Da ta ji dadowar sa sai da zuciyar ta ya tsinke da karfi, haka fargaban ta duk ya karu. Ita kanta kasa bacci tayi kamar yadda shima bai yi bacci ba ya zauna sai da ya kammala ayyukan duk dake gaban sa kusan sha 'daya na dare kafin ya tattare komai. Amrah duk na binsa da idanu, sosai take jin ciwon jiki amma bata san ta ina zata furta masa ba balle ya bata maganin ciwon jikin. Alwala ya dauro yazo yayi shafa'i da wutr yayi addu'o'in sa kamar yadda ya saba kafin ya hawo gadon. Jikin ta ya koma gami da janyo ta ya rungume sosai, jin kamar har a lokacin zazza6in nata bai sau'ka ba ya sanya shi fara rabata da kayan jikin ta. Da jin hakan tayi saurain dakatar da shi..." Baby sanyi nake ji sosai fa..." Tayi maganar a shagwabe sosai tana mai 'kara lan'kwasa wuya a dole ya tausaya mata. " Shiii.." Yace a hankali. " Ba abinda zan mk.." Tasan bazai yin ba tunda ya furta dan haka bata hana shi karasar da abinda yayi niyya ba. Haka ya raba ta da duk kayan jikin ta ya shigar da ita cikin jikin sa ya rungume. Abu guda yake jin sha'awar yi amma sam baya samun natsuwa da 'kwarin gwiwar aikatawa ga Amrah, sosai yake jin haushin yadda ta bar jikin ta ya lalace, sam baya jin dadi har cikin zuciyar sa game da hakan. Kuma ya kwana da sanin a haka Amrah tazo gidan shi, bai nuna damuwa bane sbd yasan mata kowa da nata kalar halittar da Allah ya mata. Sai daga baya kuma ya fahimci hadda fa rashin gyara shiyasa yaje wajen Anty Madeena bai bayyana mata komai ba ya dai ce mata zai turo Amrah ayi mata gyaran jiki itama dan yasan Anty Madeenan gwana ce ta wannan fannin sbd sana'ar ta kenan... Manyan mata take wa gyaran jiki shi kansa shaida ne tun shekaru 'kalilan baya. Amrah bata warware ba har sai da aka kwana biyu, kuma cikin duk kwanaki biyun bata kunna wayar ta ba, tsoron 'kira daga Sultan ta ke yi, tasan halin sa muddin ya dawo gari baya ta6a 'daga mata 'kafa dai dai da rana guda, ita kuma bata jin zata iya masa cikin wannan halin shiyasa ta toshe duk wata kafar da ta san zai iya samun ta. Cikin rashin sa'a kwana uku da yin hakan sai ga sallamar shi, lokacin tana kan dinning Raleeya ta gama mata komai ta koma side din Ammi, shima Rayyan ya fice office sai ita ka'dai tana kokarin kaiwa Cup a ba'kin ta kawai ta tsinkayi tashin sallamar sa da bayyanar sa duk lokaci guda. Yana shigowa kuma ya maida kofar ya rufe har da sanya makulli. Jikinta rawa ya fara, har tea din dake hannun ta sai da zube mata a jiki kasancewar yana da zafi hakan yasa ta mi'ke cike da firgici biyu lokaci guda. Idanun ta kan Sultan tayi kicin kicin da fuska yayin da shima ya zuba mata idanu yana wani killer smile. " Kin mance nan 'din gidan mu ne ko?...bani da shamaki da ko'ina da ma kowa da ke rayuwa cikin gidan fa...". Ya 'karashe maganar da bude hannuwan sa duk biyu yana duban ta fuskar sa dauke da murmushin mugunta. Bata tankashi ba illah banzan kallo da ta watsa masa. A hankali ya tako gaban ta ya fara kewaye ta yana dariyar shakiyan ci, bashin kwana biyu kika ci dear..ni kuma bana 'daga kafa bana barin bashina hope kin kwana da sanin haka ko?" Ya 'karashe maganar nan ne da tsayuwa a gaban ta yana 'kare mata kallo...kai ya girgiza..." Kin 'dan rame dear tell me meya faru..?" Yanavyawo da idanun sa a jikin ta yake fadin hakan. " Oshh kin jike jikin ki fa dear muje in taya ki wankewa.." Yayi wannan maganar ne yana cafko hannun ta ya jata izuwa 'dakin da ya jima da sanin shine nata yana mai cigaba da fa'din " daga dawowa ta duk kin 6ata raina Amrah, bacin kinsan irin missing dinki da nayi sai kuma ki gujeni..?" Wani 'karfi ne taji yazo mata nan take, hannun ta ta wafce daga cikin nasa tamkar zata yi wani abin kirki tana hararar sa tace.." Ni ban gudan ka nayi ba...". " Roh me kika yi, bayan tun ranar da kika dawo nake neman wayar ki bata tafia". " Ai ban da lafiya ne..". Jikin ta ya matso sosai ya rungume ta ta baya, a kunne ya ra'da mata" Shine har da rufe wayar ki..?" Shiru tayi bata amsa shi ba tsoron Sultan take ji yanzu kar yace zai sake maimaita mata irin wahalar da ya bata kwanaki uku baya bacin ko shi Rayyan har yau zaman mara lafiya take a wajen sa bata yadda ya ra6e ta ba. Jin tayi shiru ya sanya shi cire ta daga jikin sa ya juyo da ita suna fuskantar juna. Ha6arta ya tallafo sama kasancewar ya fita tsayi idanun sa cikin nata ya ce" Shine ko?..Shine ya rufe wayar taki da kansa ko?" Kai ta girgiza alamar a a. Shima din bai sake magana illah kusanta bakin sa da ya fara da nata..fahimtar hakan yasata fizge jikin ta ta 'dan ja baya tana fa'din" Sultan dan Allah ka bari, wallahi ban da lafiya ranar fa kusan kashe ni kayi, har yau ban koma normal ba". "...Ohh really...kusa kika ce ai ban kashe kin ba, kuma idan na kashe ki ai na yiwa kaina nima tun da gaki kuwa me za'a fasa...?" " Wlh bana jin dadi meyasa baka da tausayi ne kai...?" Rai ya hade shima " Amma ai hakan bai hanaki bawa Rayyan kanki ba sai ni ne zaki cemin a a hadda min bore?". " Wallahi ko shima babu abinda ya min tun ranar da muka fita har yau 'din nan..." " Shi yaga zai iya Amrah, kuma tunda har kika ganni cikin dakin nan ai kinsan bazan bar nan ba har sai na samu abinda nake so ko..". Tasan halin sa sarai dan haka ta fara ro'kon sa da al'kawarin gobe da kanta zata same sa a duk inda ya za6ar musu yace sam. Dole sai da ta biye shi tana fa'din" amma wlh kadai ji kunya..." " Naji " " Toh amma kadan fa...". Ya sake fadin" Naji.." yana rabata da kayan jikin ta. Wahalar da ta guda tun farkon nan sai da ya tasha sho a hannun Sultan, tana kuka take kai masa bugu a kirji tana fa'din.." Wlh dear baka da tausayi..mugu kawai.." Dariyar mugunta yake mata yana kokarin kamo hannun ta da take bugun sa da shi din tana zamewa. 'Karshe yayi nasarar kama hannun rumfa ya koma yayi mata ya ha'de fuskar su waje guda yana sakin wata killer smile cikin ra'da yace" Ko in 'kara?" Da sauri ta girgiza kanta alamar a a. " Ka'dan fa..?" " Ni dai pls a a...wlh na gaji...". Hancin ta yaja yana fa'din" Lazy girl, matata ta fiki jarumta..". " Kasan hakan ai ka barta ka taho gare ni...". Ta bashi amsa cike da jin haushin furucin sa. " Rage zafi ne, kuma hausawa sunce raba arne da makami ko...?" " Karasa min mana na manta...". Hararar sa tayi. " Sai kaje ka samo arnen naka ai kuma yanzu". " Kanki akeji yarinya kuma nima yanzu ko kince in 'kara ba 'karin zanyi ba ina da wajen zuwa amma gobe ki shirya karki manta da alkawarin da kika yi min...". " Bayan wanda ka yi yanzun..?" " Shima na goben babu fashi dear..". " Haba Sultan ka bari na gama samun 'karfi mana so kake ke kashe ni ne...". " Babu wannan maganar, kin yi alkawari kawai ki cika, da kika yi sa'a ma bance anjima ba?". Shiru tayi kawai tana duban sa har ya shige bathroom dinta ya watso ruwa ya fito. A gaban ta ya shirya sannan ya nufi gaban dressing mirror, turaren da ya kasance dan shi kadai aka ajiye duk da yake ba gidan sa bane kuma shi ka'dai ke amfani da shi batare da kowa ya san manufar ajiye turaren ba ya fesa yana shirin fita yace" wai wannan gayen bai baki ku'din gyaran jiki bane?" " Lastweek fa ya bani kuma nayi amma da dawowar ka duk ka wargaza komai hatta shi bai masan nayi ko ban yi ba har yanzun.." Ta 'karashe da turo baki gaba. Wata dariyar mugunta sosai Sultan ya saki yana fa'din " Dai- dai kenan, zai baki wani ai inya jiki salaf na sani, sai ki bada himma...." Daga haka ya fice ba tare da damuwar komai ba. Amrah da har yanzun ke kwance kan gadon da idanu ta raka shi har ta daina hango shi sannan ta saki ajiyar zuciya. A fili ta furta" babu abinda ya iya sai mugunta da cin zali kuma 'karshe yayi gaba abinsa ya barka babu ruwan sa da halin da ya barka aciki. Comment nd Share Salmerh😘 [24/9/2022, 1:53 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* Wattpad@ Serlmerh-md 🅿️ *...37* ........Kamar yadda ya bu'kata haka Amrah ta shirya washegari suka sake ha'dewa, dan ita kanta bata san dalili ba bata iya bijirewa maganar sa. Komai Sultan yace ko bata ra'ayin abin haka sai taji zuciyar ta ta tilasta mata yin sa. Ko Rayyan bai san ta fita ba dan ko daren jiya daya dawo ya tarar zazza6in nata ya dawo da kansa yayi mata treatment ganin yanda duk tayi laushi, har ya fara zargin ko shigan ciki ne amma bai sawa ransa ba dan gudun kar azo kuma ba hakan bane. Duk da haka washegari sai daya ja jinin ta ya mi'ka asbitin da yake aiki a take aka gwada masa aka tabbatar masa da cewa babu komai sai 'yar maleria. Baiyi mamaki ba dan shima yafi kyautata zaton malerian ne kuma treatment 'din sa yake mata. Haka yake yini 'kiran wayar ta dan tabbatar da lafiyar ta da kuma shan maganin ta akan lokaci. Yayin da duk amsa wayar da Amrah ke yi bata a gidan, tana can tare da Sultan a wani tsadadden hotel. Shiri sosai tayi kafin ta fita, harda socks da ni'kabi ga dogon hijabi da ta sanya, in ba dai wanda yai mata farin sani ba ba lallai ne a gane ta ba. Kwanaki kusan shida kenan tana yiwa Rayyan 'karyar ciwo yayin da gefe guda babu ranar da bata ha'duwa da Sultan kuma duk abinda yake so yake yi da ita...gajiyar ha'duwar ta da Sultan take bayyanawa ga Rayyan matsayin bata da lafia, hatta Ammi sai da tazo duba ta har side 'din ta, haka ma Marwa musamman tazo gaida ta. Bata samu lokacin Rayyan ba har sai da Sultan ya sarara mata akaran kansa bisa shiryawar ta, dan tasan yanayin ta ita, jikin ta irin jikin nan dake son gyara akai- akai a koda yaushe yakan bu'kaci gyara, matu'kar ta 'dan 'dauki lokaci bata yi amfani da kayan gyaran jiki ba ita kanta ta kan fahimci wasu canze- canze, ganin yadda Sultan ya ri'ke mata wuta kuma ya sanya ta'ki yarda tayi amfani da komai dan matukar tayi toh bazai fasa neman ta ko na rana guda ba, tana.shan azaba kam amma haka take jurewa har sai da ya 'kure da kansa...ai kuwa shirin ta yayi aiki dan Sultan da kansa ya sarara ya kyale ta yana sake jaddada mata cewar ta tambayi Rayyan ku'di tayi gyaran jikin ta. Baki ta tura tana kukkuni 'kasa- 'kasa da ta tabbatar zai ji ta. " Shi ina ruwan sa, ba cin duk kaine ka lalata komai shi yaushe ma ya bani ku'din, kuma idan ya bani ku'din bakai ke amshewa ba. " Kar ki damu wannan karan wlh bazan amsa ba, ai dani za'a kwashi garar, dole in bari kiyi dan kina bukatar hakan sosai, Matata ba haka take ba kuma ban ta6a bata ku'din gyaran jiki ba...". Fa'dan hakan da yayi ne ya sanya suka yi rabuwar baran baran, tana masifar yana ha'da ta da matar sa bacin shi ne yafi nace mata. Yana mata daria yace " Kema ai kinaso kinga sabon jini kin li'ke min shiyasa da nace hy kike cewa Yesss..." Fuu ta tashi ta nufi bayi cike da haushin maganar sa tace " Zan kuwa baka mamaki. " Babu yadda kika iya dani 'yan mata..". Ya 'karashe yana dariyan mugunta. Abinda ya faru kenan tsakanin Amrah da Sultan aranar ha'duwar su ta 'karshe da shi. Tasan gaskia ya fa'da mata tana bukatar gyaran ita kanta ta sani amma ko giyar wake tashe bata isa taje ga Rayyan da wannan batun a yanzu ba sai dai ta nema tayi da kanta, shi kuma Sultan tasan bazai ta6a bata ku'di ba, dole ta yanke shawarar neman ku'di wajen mahaifiyar ta. Cikin rashin sa'a kuma a daren ranar Rayyan ya nemi hakkin sa wajen ta ta sigar da yasan bata ta6a iya bijirewa bukatar sa. Ba 'karamin mamaki yayi ba da jin Amrahn tasa ba kamar yadda ya tsammata ba, bayan duk ku'da'den da ya ajiye mata kwanaki tara baya, kuma yana da tabbacin tun ranar bai sake kusanta kansa gareta ba sai yau 'din, kenan bata yi komai ba, amma ai Anty Madeena ta sanar da shi cewa ta ha'da mata komai ya akayi haka. Ko dai bata yi amfani da su bane. Gefe ya koma dafe da kansa yana sakin numfashi mai zafi. Cikin muryar da yasan ita ka'dai zata jishi yace" Amrah baki son farin ciki na ko..?" Baki ta 'dan tura gaba ta riga tasan laifin ta amma hakan bai hana ta basarwa ba tana yatsine fuska tace " Baby ni me nayi kuma..., bayan duk kokarin da nayi?" 'Karamin tsaki yaja" Sau nawa zance miki ki daina wasa da amfani da abubuwan da Anty Madeena ke ha'da miki..?" " Ai nayi..". Ta fa'da tana turo baki. " Shut up da Allah.." Ya dakatar da ita a tsawace yana 'dan waigo wa. " Ni kike cewa kinyi Amrah? karya zan mk kenan ko me?" Shiru tayi ta kawar da kai tana jinjina hali irin na Rayyan, sam baya 'daga 'kafa indai akan abinda ya shafi shimfi'dar sa ne baya wasa da lamarin. " Sau nawa ni da kaina ma nake kawo mk abubuwan da nasan zasu miki amfani Amrah amma banga alamun kina kusantar su ba, duk wani abinda zan shigo miki dashi gidan nan sai na tabbatar da cewa zai anfane ki nake shigo da shi, amma dan ki nuna min baki son farin ciki na shiyasa kika za6i yin watsi da komai ko...." Tashi tayi daga kwancen tana jan mayafi dan sitirce cikin ta ta zauna da kyau kan gadon tana kara turo baki gaba. " Wait ma kafin tafiya ta ban baki ku'di ba da kika ce zaki gyara jikin ki meyasa kika fi son 6atan rai ne Amrah.." " Toh Baby ba bani da lafiya bane kuma ma fa nayi kawai dai wlh dan ka kwan biyu ne shiyasa kaji kamar ban yi ba.." Tsaki yaja kawai ya tashi ya wuce bathroom ya sakarwa kansa ruwa. Sosai taji tausayin sa tasan yana matukar kokari wajen kulawa da ita, baya shayin kashe mata kudi ko nawa ta bukata indai wajen ganin ta gyara jikin ta ne musamman boobs din ta, ko da 'karya tai masa kan gyaran jiki baya shayin tura mata kudi, wataran tana yi kamar yadda yake so but wataran Sultan ke hana ta ya amshe ku'din. Wani lokaci kuma da gayya zai bari har sai tayi gyaran jikin ya rike mata wuta har sai ya lalata komai. Tana so da 'kaunar Rayyan sosai but tana jin dadin mu'amala da Sultan bata kuma son rabuwa da shi bata san me yasa ba. Amma yadda ayau 'din taga yadda Rayyan ya 'dau fushi ya sanya ta yanke shawarar neman mafita sai dai bazata tunkari Anty Madeena kai tsaye ba, dan a ganin ta ai ma sai ta raina ta ganin koda yaushe sai ta nemi kayan gyara zata iya gano lagon ta. Ko bayan ya fito bai ko dubi inda take ba ya gama shirin baccin sa itama ta fa'da bathroom 'din ta watso ruwa ta fito. Rigar baccinta ta maida ta feshe jikin ta da turare mai sanyin 'kamshi sannan ta 'dauki wayar ta da niyyar barin 'dakin ganin Rayyan ya'ki ko duban inda take ne da alamu fushi yy da ita...gaba 'daya ji tayi itama tayi sanyi. Fahimtar hakan da yayi ya sashi cafko hannun ta ya janyo ta ta fa'da jikin sa, kamar jira take kuma kawai sai ta saki kuka. Shi kansa yasan bai kyauta ba masifar da yayi mata, tunda yasan ba ita ta halicci kanta ba Allah yayi ta haka, amma ai ba laifin sa bane itama ta sani, out of anger yayi wa'dancan maganganun, bai tashi sanin bai kyauta ba kuma har sai da ya samu natsuwa bayan ya gama wankan sa tukunna. Shafa bayan ta yake a hankali yana 'ko'karin cusa kansa tsakankanin wuyan ta. " I'm so sorry Babyn Baby...I didn't mean to...". Sau 'daya ya fa'di hakan bai sake magana ba illah shafa bayan ta da yake faman yi alamar lallashi. Tasan dama ba hana ta kuka yake ba, in dai abin kuka ya same ta fili yake bata tayi kukan ta son ran ta batare da ya hana ta ba sai ta gama kukan kafin yake lallashin ta. Kamar yanzun ma dai, sai da ta gama kukan kafin ya bata ha'kuri ya kuma yi al'kawarin sake tura mata ku'di ta sake gyaran jikin domin dagaske yaji ta canza sosai irin canjin da ya gaza samun natsuwa da ita...dan yafi so koda wani lokaci yajita zam- zam. Haka suka kwana tana rungume cikin jikin sa tana sakin ajiyar zuciyan kukan da tayi. Washe gari bayan ta tabbatar ya tafi office sannan ta fara lalubo mafita, dan ta gama yanke bazata tunkari Anty Madeena ba ai da kunya. Ameera ta yanke shawarar tambaya sai ta tuna ai Ameerar da 'kyar ne ma ta sani balle ta fahimce ta musamman da yake ba aure ne da ita ba. Cikin wani group 'din su na whatsapp mai suna matan Aljannah ta tura tambayar tata kan cewa _urgent please a bani list 'din kayan gyaran jiki ni'ima dana Boobs._ Take kuwa aka watso mata su kala- Kala har sai da ta gaji da dubawa. Da 'kyar ta ware wasu da suka fi kwanta mata kamar haka. HA'DIN KAYAN ITATUWA Yana 'kara ni'ima sosai ga mace. Kankana Cucumber Tumatir Mazar'kwaila Dabino Madara peak. Gani tayi duk abubuwan nan babu wanda Rayyan bai yawan kawo mata acikin su amma bai ta6a fa'da mata amfanin shansu ba itama bata basu muhimmanci sam, Anty Madeena ce dai ta ta6a fa'da mata amfanin wasu daga ciki...dan haka su ta yanke shawarar nema. Sai da tabi procedures 'din duk da aka fa'da ta sake duba wani ha'din Hulba wanda ake yin sa shima da abubuwa kamar haka. Gya'da Aya Mazarkwaila Hulba Nono ko madara. Akwai kuma HADIN 'BAWON RUMAN Wanda ake yin sa da Zuma da 'Bawon Ruman wanda akace Larabawan Dubai suka fi amfani da shi domin sanin muhimmancin sa, wannan ha'din yana matsi sosai. Wa'dannan suka fi kwanta mata arai, dan haka Raleeya ta nemo ta tura kasuwa dan siyo mata abubuwan da ta tabbatar babu cikin gidan. Da kanta ta ha'da komai da taimakon Raleeya ta kuma fara amfani da shi tun a lokacin dan ya kasance ne shan safiya da yammaci. Kwanaki biyu bayan hakan Sultan ya 'kirata yake tambayar ta ko Rayyan ya bata ku'din, tace masa ya ki bata yace ne wai sai ya samu ku'di. " Ji munafuki, ku'din da zai bakin ne har zai ce sai ya samu?" " Haka yace amma Insha Allahu idan ya dawo yau 'din zan sake mai maganar". " Ya dai kamata kam dan kina da bukatan canji gaskia." cewar Sultan yana kashe wayar sa. Haushi sosai na cika sa. Yayin da Amra ta saki wani makirin murmushi bayan ya kashe wayar, bata jin wannan karon zata iya sadaukar da wannan gyaran ga Sultan kadai, sosai take so ta farantawa Rayyan rai da gyaran da ta sha fama wajen haTda sa da hannayen ta... Sun 'dauki tsawon lokaci tana dojewa Rayyan da Sultan dan ganin ha'din nata ya tsuma jikin ta sosai tukunna. Ta kuwa yi nasara, dan sosai Rayyan ya zauce lokacin da ya tarar da Amrah kamar yadda yake so ya kuma samu gamsuwa da ita da ya jima bai samu irin sa ba. Albarka kam tasha shi ranar har bata san adadin su ba. _Salmerh_ 😘 [24/9/2022, 3:41 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* Wattpad@ Serlmerh-md 🅿️ *...38* .........Tun dawowar Sultan da Marwa kusan kullum sai ta shigo gidan Ammi, da yake ba wata tazara ce tsakanin su ba, hakan yasa ta maida gidan tamkar wajen yinin ta, dan Sultan in ya fita bada wuri yake dawowa gida ba kamar dai Rayyan, duk lokacin da ya dawo kuma ya kan 'karaso ya 'dauke ta su wuce ko kuma ya sanar da ita dawowar tasa a waya sai ta koma da kanta. Cikin sati biyu kacal Marwa ta saba da Zaitun sosai musamman saboda Mufeeda da farat 'daya yarinyar ta shige ranta, ta kan kuma 6ata lokaci sosai wajen yarinyar tanai mata wasa tun bata saba da ita ba har ta fara sakewa da ita. Sau tari kuma indai ranar da zata koma gidan ta da kanta ne Zaitun ke rakata sbd tazarar ba mai yawa bace gidaje basu fi biyar bane tsakanin su. Sunyi sabo da Marwa kasantuwar ta surutacciya wanda awajen Marwa ta tsinci wasu abubuwa daya shafi ahalin su. Cikin hirar Marwa take sanar da Zaitun cewa ai mijinta ma 'dan gidan nan ne Zaitun bata yi mamaki musamman duba da yadda hankali kwance Amrah ke lamuran ta cikin gidan, bata ta6a damuwa da komawa gidan ta on time dan acewar ta matukar ta yini anan babu abinda take tsinanawa a gidan ta in yunwa yake jima ya kanzo nan yaci abincin sai su wuce nasu gidan batare da damuwa ba. Tace in kuwa baya gari gida take tarkatowa har sai ya dawo. Hajja Ladi ce mai zuba ma yan aiki magani ko su gudu da kansu ko kuma kowa gidan yaji bai sansu 'karshe dole su rabu da su, da 'dai'dai ta ringa koran duk wa'danda ake kawowa aiki saboda hassada kawai da kanta, ita a dole sai ta zama shugaba kuma tafi so duk abinda za'ayi ya zam ita ake wakiltawa ba wata ba. Ta gwammaci ta kwashe ayyukan gidan kaf akanta da ta bari wata ta shigo dan taimaka mata..dayake in ita kadai ne dinne akan ninka mata albashin ta banda wasu kyaututtuka datale samu daga Ammi musamman sbd yabawa kwazo da kokarin ta. Ko Raleeya da ta bari suke zama dan 6angare daban take aiki ne shiyasa. Haka take yi kowani lokaci shiyasa take ita ka'dai har zuwa kan Zaitun da Sultan ya yakama tana barba'de kan abincin ta tana surutsi 'kasa 'kasa, bai ci abinda take fadi ba amma kallo 'daya yai mata yasan ba ta da gaskiya. Sultan bai tanka mata ba har sai da ta gama ta kuma maida maganin bakin zanin ta sam bata damu ba ko damuwar wani zanta dan tasan ita ka'dai ke da lokacin shiga kitchen da wannan lokacin so bata yi tunanin wani zai zo ba tana juyowa tana yatsina fuska sai tayi arba da shi tsaye hannayen sa har'de bisa kirjin sa yayi crossing kafafuwa yana 'kare mata kallo. Take jikin ta ya fara kyarma ta fara waige-waigen da ya tabbatar da cewa bata da gaskiya. A hankali Sultan ya 'karaso ciki yana mata kallon kin yiwa kanki duk da bai san mai ta aikata ba bai kuma san manufar ta ba amma hk kawai yaji bai yadda da ita bai. Duk girma da shekarun Hajja ladi hakan bai hana Sultan tsare ta akan sai taci abincin ba...duk yadda Ammi ta so hana shi wannan hukuncin amma fir Sultan ya rufe idanu ya'ki sauraron kowa dan shima gwani ne wajen rikici da kafiya da rashin mutunci. Tana kuka tana ro'kon sa amma hk ya murje idanu ya ce sai taci, ita kuwa bata son taci itama gudun kar maganin yayi aiki akanta ne dan idan ta bar gidan bata san kuma inda zata kai kanta kwatankwacin wannan gidan ba a wannan zamanin. 'Karshe su Jessy da Yussy ya 'kira 6oyayyun securities 'din shi da Rayyan ne da ba kowa ya san da zaman su ba sbd tsaro, mutun biyu ne da bindigogin su a hannu suka tsaya akanta dolen ta sai da ta ci abincin nan da ganin bindigu saitin kanta....Hajja Ladi tana ci tana kukan bakin ciki kuma Sultan yace duk abincin zata cinye ba ragi. Ammi 'dakin ta ta koma tana tunanin wannan lamari, ta rasa duk menene ma silar sa... Zaitoon kam duk bata san abinda ke faruwa ba tana 'daki 'diyar ta kwance kan cikin ta tana shafa bayan ta cikin salon son tayi bacci amma yarinyar nan taqi sai gunguni take ta jefa yatsa a baki da kananun kuka irin na yara. Sai da ya ga ta cinye tass sannan ya tsare ta da tambayar maganin na menene ta da tasaka cikin abincin? 'Kin fa'da Hajja Ladi tayi sai da taga ya bawa wa'dannan masu bindigar damar kwa'deta kafin ta saki ihu" zan fa'da, zan fa'da wlh dan Allah kuyi ha'kuri"...Ihun nata ne ya sake fito da Ammi wacce tun daga sama ta fara fa'din" Haba, haba Sulty..babbar mace haka kk shirin wulaqantawa, ba nace abar maganar ba... " Bai ko kula Ammin ba har ta 'karasa sau'kowa, Zaitun ma da sauri ta fito rungume da 'diyar ta ko hijab din yau bata tuna sawa ba sakamakon jiyo ihun Hajja Ladi, daga bakin corridor tayi turus, amma tana hango su cike da mamalin abinda ke wakana a parlourn...ga kuma wasu tsaye da bindigu a hannu. Kallon fuskar Mufee tayi cikin rai tace" Na kawo mu wata rayuwa kuma Mufee na..." Domin ganin bindigogin sosai ya tsinka min zuciya tuno abinda ya faru abaya. Ammi ce ta sake bu'dan baki zata yi magana Sultan yy saurin dakatar da ita da fa'din" Rabu da ita Ammi wani take so ta cutar ai da ganin ta gaskia bai wadace ta ba..." Gyara zaman sa yy 'kafa 'daya kan 'daya tamkar wani basarake fuskar sa taf da alamun rashin mutunci..yace oya tayi bayani yanzu. Tiryan-tiryan Hajja Ladi tayi musu bayanin komai tana share 'kwalla har da wanda ta zubawa magani a yau din, mamaki sosai ya cika shi haka ma Ammi, wato shi 'dan adam a kullum bashi da godiar Allah duk yanda ka samu wuri sai kuma ka fara tunanin zarta nan sbd buri, mutum bata tsare mk komai ba bata hana a biyaki hakkin ki yadda aka saba ba amma ita kk kokarin cutar wa..wacece ma hk ban san ta ba?" Ya 'karashe maganar da tambayar Ammi" Wace Zaituna...?" Bugu taji kirjin ta yayi jin sunan ta da ya shiga cikin maganar su...take idanun ta ya cika da 'kwalla...har ga Allah ita tsoron bindiga take yi ko kallon ta bata 'kaunar yi..." me na musu zasu saka ni cikin maganar su, me me ya fito da ni..?" Ta jerawa kanta tambayoyi. Sunan ta da taji Ammi ta anbata ne ya sanya guntun hawayen nata karasa saukowa. Jiki na 6ari ta karasa inda suke kafafunta na sarkewa, kanta ko 'dan kwali babu saboda firgici kuma bata tuna hakan ba. Taa 'karasawa parlourn ta zube bisa gwiwyoyin ta Feefy ta zaunar kan cinyarta tana fuskan tar ta ita kuwa ta sake rungume ta da kyau dan har yanzun idanun ta da birbishin bacci. Kusan kowa dake wurin da idanu ya bita dalilin ji da ganin kukan da take yi mai sauti...Bata bari sun warware daga mamakin su ba ta ha'de hannayen ta waje guda ta fara fa'din" Dan Allah kuyi ha'kuri Ammi, yalla6ai kayi ha'kuri wallahi bansan laifi na ba". Ta koma ga Sultan tana kuka ta cigaba da fa'din" Ni ban san me nayi ba amma dan Allah ko zaku kashe ni ku bar 'ya ta ta rayu dan Allah Ammi kinji..." Bata kai 'karshe ba Ammi tayi murmushi" Kwantar da hankali babu mai kashe ki Zaitun.." Sultan ta kalla tace" Ga Zaitun nan dududu ma bata dade a gidan nan ba takamammen aiki ma ba ware mata ba tukunna saboda tun zuwan ta ban zauna ba amma kaga har hassada ta shigo, ban ta6a zaton haka ba ga Hajja Ladi, nayi mamaki 'kwarai da gaske..." Kusan duk mazan da ke parlourn hankalin su akan ta yake musamman sbd kayan da ke jikin ta, rigar bacci ce riga da dogon wando kuma ko da wasa bata ta6a gigin fitowa da su ba yau 'din ma a rikice take shiyasa ta manta kuma har yanzu bata ankare da irin kallon da suke mata ba sbd ta riga ta shiga ru'dani...hatta Sultan shashancewa yy wurin kallon ta, sai daga baya ya 'dan basar bayan ya girgiza kansa, kawar da kai yayi ya maidar izuwa ga Hajja ladi dake kukan takaici, tasan da kyar ne wannan 'dan iskan ya bar ta sake zama a gidan nan dan shi sam baya da mutunci ba kamar yayan sa ba da sam baya shiga harkar kowa, bai damu da komai zaka aikata ba ko ya ganka ma sai dai ya kawar da kansa babu ruwan sa ba zai nuna ya gani ba balle ya tashi hankalin sa a banza. ***** Marwa da Ammi na matukar nuna musu 'kauna sai Sultan da shima bai ta6a yi musu duban 'kaskanci ba, na hu'dun su itace Raleeya, amma daga Hajja Ladi, Matar Rayyan da shi kansa Rayyan 'din basu ta6a nuna sun ma san da zaman Zaitun cikin gidan ba, hatta da Mufee kuwa bata tsira daga rashin mutuncin su ba. Ranar da Mufeeda ta cike shekara guda da haihuwa ya kama cikin watan Ramadan ne, wanda yayi dai- dai da cikar su sati tara kenan agidan Ammi, biki gagarumi Marwa tayi niyyan shiryawa amma sbd 'dimbin falala irin ta Ramadan yasa ta 'daga zuwa bayan sallah. Aikuwa ana yin sallah da kwana biyu ta shirya mata biki a harabar gidan Ammi, Zaitun sai da ta zubda 'kwalla ganin yadda Marwa ke nunawa 'diyar ta zallar 'kauna... Yadda aka gyara Mufee kai kace 'diyar wani hamsha'kin ne ba 'diyar Zaitun ba. Ta sani ba 'kananun kudade Marwa ta kashe wajen wannan hidimar ba, haka aka ra'kashe aka yanka cake, Marwa ta sanyawa Mufee a baki ita kuwa Mufeeda data yanko kawai ta nufi bakin Zaitoon da shi tana washe ha'kora, sosai abin ya kayatar da kowa. Aka sanya shewa ana jinjina kauna irin ta uwa da 'diya, Marwa ma daria take tace" ji ja'ira wato dai har kin san muhimmancin Mamin ki fiye da kowa ko..?" Lokacin da aka sanya wa'kar Sarkin waka na cikin shirin labari na Marwa tashi tayi tana takawa cikin wani salo mai birgewa ta kama hannun Mufee duk biyu cikin nata suna takawa tana bin bakin wakar a hankali Mufee kanta daria ta ringa 'kyalkyalewa sbd abin ya birge ta. Bikin ya kayatar da Zaitun sosai, wuri na musamman ta ware ta sanya Marwa har take jin ta tamkar wata 'yar uwarta ce ta jini. Kyaututuka kuwa Mufee ta shasu na ban mamaki dan Marwa kaf 'kawayen ta sai da ta gayyato, gift 'din Marwa na musamman ne, dan kayan sawa ta siyawa Mufee har kal goma cif kaya kuma da suka amsa sunan su kaya wandanda tasan sun fi karfin sawarc 'diyar ta sai dai dayake na Allah baya karewa kuma ya kan iya azurta ka da abinda baka ta6a zato ba a duk lokacin da yaso. A ganinta in bama irin su Marwan ba a ina Mufee zata samu irin kayayyakin nan..tasan har abada abu mawuyaci a garesu. Kamar ha'din baki Ammi ma kayan sawan ta bata sai sauran gifts din da suka hada hadda ku'da'de takalma da sauran tarkace hadda abubuwan wasan yara. Zaitun tunda aka fara taron kuka take, duk wata kwalliyar da Marwa tasa musamman aka zo har gida akai musu duk ta lalata shi da kukan farin ciki. Ana tsaka da shagali Rayyan yazo ya tarwatsa komai yana masifar an maida musu gida kamar gidan 'koroso. Hatta Ammi bata iya dakatar da shi ba sbd dokin zuciya daya hau, dole yasa aka tashi haka nan cike da kyaututtuka na ban mamaki. Dama tasan ba kaunar su yake ba, dan ko gaiduwar ta ba amsawa yake ba duk ranar da suka ha'du a 6angaren Ammi, haka ma Mufee baya kulata, sai dai tasha kama sa yana bin Mufeedan da kallo bata kuma san ma'anar kallon ba. Ta kance aniyar ka ta bika inma maye ne kai. Ita ma yarinyar kamar tasan baya son su haka kawai itama tsoron sa take ji shiyasa take gudun sa. Ko inda yake bata yadda taje. Shi da kansa yasan ba 'dabi'ar sa bace yawan kallo amma akan yarinyar nan dabi'ar da shi kansa ya yiwa kansa shaidar ta na neman canzawa, bai san mai yake kallo game da yarinyar ba haka kawai tsintan kansa yake da son ganin fuskar ta, ji yake tamkar ganin yarinyar na 'debe masa kewar abubuwa da dama bai kuma san dalili ba. Sai daga baya da yaga abin na neman fin 'karfin dakiyar sa ya sanya shi yakice lamarin 'karfi da yaji wajen 'dorawa zuciyar sa mummunan tsana, da zarar ya tuno wani abu game da su sai yayi kokarin tuno wani abu mummuna kuma daya 'darsawa ransa game da su musamman ma a yadda ya fahimci labarin su da yaji take baiwa Ammi farkon zuwan su. Ka'dan da ka'dan tsanar tayi tasiri ya rinjayi komai aransa, dan yafi bawa tsanar muhimmanci fiye da sakewa yarinyar. Da zarar yazo 6angaren Ammin sai ya wani hade rai abu ka'dan ke tunzura shi laifi kadan zaka yi ya maidasa babba... Baya sakewa Mufee fuska sam, kar Zaitun ma taji labari dan duk 'din su baya son harkar da zata hada sa dasu, ko a kuskure Mufee ta ta6a jikin sa tsawa yake daka mata batare da tunanin 'karamar yarinya bace, duk yadda Ammi taso saita masa tunani akan su abin ya faskara. Yanda yake hantara da rashin fara'a ga Mufy yasa da zarar ta gansa sai ta 6oye fuskar ta ko kuma ta tsanyara kuka ta nemi wajen shiga. Idan hakan ya faru da sauri zaki ga Zaitun ta zo ta 'dauki abinta ta rungume dan sam bata son kukan ta ko da wasa karya mata zuciya yake. Dalili kenan da ya sanya har yau 'din nan bata damun kanta da yiwa Mufy kitso dan yarinyar bata so da an ta6a kanta take sakin kuka. Sau tari sai dai in taga lallai lallai kannata na bukatar kitson sai ta hana idanun ta bacci cikin dare lokacin da ta tabbatar baccin yarinyar yayi nisa sannan zata dinga yi mata da 'daya da 'daya kuma a hankali sama- sama dan kar yayi mata zafi gashi yarinyar akwai suma sosai akanta wani lokacin har mamaki take yi dan ko ita bazata nuna mata 'kyan gashi ba...sai dai ta nuna mata tsawo da cika amma gashin Mufee mai kyau ne kuma gashi bakikirin amma duk da tarin baiwar nan da Allah yai mata bazaka ta6a ganin kitso mai kyau akanta bacsai dai in Marwa na nan, tun na ranar da akai mata birthday kuwa bata sake yadda an mata kitso ba sbd kukan da take sha wajen yin kitson. Zaitun bata barin Mufee zama a duk inda tasan zasu hadu da duk wanda bai sake mata ma balle ganin sa ya sanya ta kuka, kullum yarinyar ta na rungume da ita a goye ne ko kuma a hannun ta basu cika rabuwa ba. Ta 'kwammaci ta goye abinta suyi aikin a haka da ta barta wani banza na firgita mata ita a cewar ta hakan ya fi mata...bazata ta6a gajiya da rainon abinta ba ...a yanzu Feefy ce farin cikin ta itace ka'dai abinda zata gani taji farin ciki ya lullu6e ta tasan cewa itama tana da wani nata kusa da ita...a kullum fuskar mahifiyar ta take gani yake sake bayyana kan fuskar yarinyar, hasken su ma 'daya ne da ita...tasan ba dan wancan 'kaddarar ba da yanzu tana nan cikin dangin ta da 'yan uwanta tana walwala kamar kowa...amma Allah ya 'kaddaro musu wancan 'kaddarar ya za6e ta ya dam'ka mata amanar sa da ya kasanceckaddarar rayuwa ta ne, ta kuma kar6i 'kaddarar ta da hannu bibbiyu kuma tayi al'kawarin bata tarbiya, kulawa da komai da ya shafe ta muddin ranta. Mufee ka'dai ta ishe ta rayuwa, koda ace zata rayu babu aure babu 'dan kanta matu'kar zata kasance da Mufee a ganin ta bata da damuwar komai, 'kaunar Mufee acikin jinin ta take jinsa, tasan abu ne me wahala ta iya raba zuciyar ta da 'kaunar yarinyar, sun shaqu irin shaquwar da ko wace uwa take iya yiwa abinda ta haifa. _Ni kam a gani na 6angaren Zaitun ta zake da yawa ma fa.._ 😂 Domin akan Mufee ta sadaukar da duk wani farin cikin ta, ta sadaukar da dangin ta domin ko a lokacin da suka nuna 'kyama ga abin bai mata dadi ba, aganinta kaddara tana kan kowa kuma tana iya samun duk wanda Allah yaso cikin kowacce irin siga. Amma sun kasa fahimtar ta. Ba wai dan ta kisu bane tayi musu nisa sai dan bawa kowa dama da kuma hucewar zuciya. Dan haka ba taga wani 'kato da sama taka zai zo ya ringa firgita mata yarinya abanza ta bari ba, tun daga lokacin ta 'dauri aniyar yin fito na fito da duk wani wanda zai ta6a musu farin cikin su...duk me 'kaunar Mufeeda itama tana son shi ma'kiyin Mufee kuwa matsayin babban ma'kiyi itama yake a wurin ta. Bata nemi taimakon kowa wurin kula da yarinyar ta ba, balle wataran ai mata gorin hkn, tayi kuma alwashin zata yi kowani irin aiki ne dan ganin kawai yarinyar ta ta samu rayuwa mai kyau kuma Alhamdulillah ta wannan 6angaren yanzu bata da matsalar komai. Tun lokacin da Allah ya ha'da ta da Ammi kaso mafi yawa daga cikin damuwar ta ya kau...domin Ammi 'yar halak ce, Ammi mutun ce har mutun, ta kula da ita ta kuma bata 'kwarin gwiwa wurin kulawa da yarinyar ta. Bata ta6a nuna 'kyamar ta ga yarinyar ba hakan kuwa shine sanadin da ya ja mata babban matsayi a zuciyar Zaitun har ya sata sakin ranta da zummar yin aiki karkashin ta har zuwa lokacin data 'dibar ma ranta. Ammi ta wadata Mufee da sutura mafi tsada da 'daukan hankali, sutura mafi birgewa daga cikin duk suturun da ta ta6a sanyawa yarinyar tsawon rayuwar su, ta wadata da duk wani abu na more rayuwa wanda tasan ko cikin 'yan gayu 'diyar ta ta shiga zata 6ace acikin su 6at. Zaitun sam bata damu da kanta ba, burin ta taga Feefy na dariya tana wasa tana walwala hakan kawai shine farin cikin rayuwar ta, sai ta zauna ta zuba mata idanu tana murmushi tana tuno abubuwa da dama, atimes kuma in hakan ya kasance sai kaga tana share 'kwalla. Shekaran Feefy 'daya ne da wasu watanni amma saboda kyakkyawar rayuwa da ta samu idan ka ganta sam bazaka yi zaton ta gaza 2yrs ba, abinda ta jima tana buri bata samu hakan ba sai gashi a gidan Ammi ta same shi. Ta jima tana burin ganin Mufeen ta ta yi kiba ta murmure amma haka ya kasa samuwa mata sai gashi a yanzu ta samu wannan cikar burin, sai yanzu ma asalin kyan yarinyar da hasken ta suka sake bayyana a fili. Wani lokacin idan Rayyan na magana zuba masa idanu take yi har sai taji murmushi ya kubce mata, cikin zuciyar ta sai ta ayyana" ka tsani 'yata sai kuma gashi bakin ku ya juye ya koma sak iri 'daya, bakin 'dan cukul mai kyau zagaye da bakin layi da ya kasance dishi dishi sai ya 'kara gyara musu bakin ya koma mai 'daukan hankali. Zaitun ta kance duk zaman mu baki 'dauki komai nawa ba sai na wannan masifaffen da ko kallon arzki bai ta6a yi mk ba..haba 'yan matana...wannan rashin adalci har ne gaskia. Ta 'karashe da jan kumatun Mufee tana murmushi. Ammi kam daga baya ma wata mai aikin ta sa aka nema mata dan taya Zaitun aiki dan ganin kamar Zaitun 'din yanzu aikin yawa yake mata ga kuma kula da yarinya da a koda yaushe zaka gansu tare. Kuma ko wani irin aiki take yi ko ma wa take yiwa aiki to kuwa da zarar taji kukan Mufee zaki ga ta bari ta tafi da sauri...Ammi kam inda sabo da riga ta saba da wannan 'dabia na Zaitun hakan yasa ta daina damuwa da komai dazata gani daga gareta ta game da yarinyar ta. Salmerh 😘 [26/9/2022, 8:05 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* Wattpad@ Serlmerh-md 🅿️ *...39* ........Hawowa yake cikin takun sa mai matukar birgewa da tafiya da hankalin duk mai kallon sa, tafiyar sa cikin natsuwa yake yin ta, tun da ya fara haurowa ya lura da yarinyar da bama tasan da tahowar sa ba, ba 'karamin mamaki yayi ba ganin ta bakin stairs ita ka'dai ayau 'din, iya sanin sa da 'yar gwal 'din nan ba kasafai zaka ganta ita daya batare da uwarta ba, da wuya ne ma idan uwar tasan cewa ta iso har nan dan ya lura tafi bawa yarinyar muhimmanci fiye ma da kowa da cikin rayuwar ta, sai dai tunda ya ganta saman Ammin yasan cewa uwartata ma na nan kusa da ita dan a yadda ya fahimce ta bata iya yin nisa da yarinyar sosai, shi kam kallon ta yake yana jinjina kyau irin na yarinyar, sai kuma akayi dace ta yi sa'ar uwa mai son farin cikin ta da son gyara mata jiki, domin tun da yake ganin yarinyar be ta6a ganin ta cikin yanayin da ba shine ba..kullum tsab zaka ganta cikin kayan ta masu 'daukan hankali..... Bai ma gama wannan tunanin ba Mufee ta 'dago ta kalle shi bayan ankarewa da tayi da mutum na tahowa kusa da ita sanadiyyan 'karan takun sa da taji. Ai kuwa take ta gigice ta fara kyabe baki tana 'daga hannuwa sama kamar mai 'daukan nata na a kusa da ita ne da alamun 'kage take sosai ta bar wurin kafin ya cimmata, cikin rashin sa'a sai ta zame tayo baya, step biyu ya rage masa ya hauro amma ganin yarinyar na shirin gangarawa yasa shi take su a taki 'daya caraf ya riqo hannun ta hakan ya taimaka wajen hanata fa'duwa. Hakan ma gaba 'daya ya faru ne cikin sakannin da a'kalla baza fi biyu zuwa uku ba, shikan sa bazata abin yai masa, bai zaci faruwar hakan ba, yayin da Moopy ta sake razana jin ta ya riketa fin ma razanar da tayi abaya da ganin sa, hakan ne ya sanya ta sakin kuka mai 'karfi. Rintse idanu yy yana jin ihun nata na neman hargitsa masa kwalkwalwa...yau ka'dai yaji tashin hankali har ransa saboda kukan yarinyar nan...lokaci guda tunanin yadda zai lallasheta tayi shiru yazo ransa amma ya rasa me zai mata. A hankali ya sau'ke idanun sa a kan fuskar ta yayinda yake jin bugun zuciyar sa na 'kara tsanantawa..wanda yayi dai-dai da fitowar Zaitun da gudu daga bedroom 'din Ammi.... Turus taja ta tsaya ganin 'diyar ta a hannun sa cike da mamaki ta zuba masa idanu tama kasa kasa 'karasawa inda suke. Ganin yadda ta ritsa shi da idanu ya sa shima 'din kallon ta, fuskar sa babu yabo babu fallasa bazaka ta6a fassara yanayin da yake ciki ba. Ido cikin ido suke kallon juna kowa da abinda yake sa'kawa cikin ransa gefe guda kuma kukan Mufeedah na tashi har yanzu bata da alamun tsagaitawa...tuni idanun Zaitun sun cika da 'kwalla har bibbiyu take ganin sa banda tu'ku'ki da zuciyar ta ke yi, dama ta sani tunda taji kukan Mufee tasan bakowa bane sai shi. Tsawon mintina biyu suna kallon kallo da shi ko zuciyar sai lokacin ma Moopy dake ta faman zillewa tana son barin hannun sa ta lura da Zaitun dake tsaye can nesa ka'dan dasu, hakan sai ya 'kara mata kaimi wajen son barin jikin nasa tare da fa'din Mam...my..., Mam...my cikin kuka sosai tana mi'ka hannayen ta ga Zaitun. Shi kam bai wani damu ba sai ya 'dage gira 'daya ya 'daga 'kafa ya taho a hankali zuwa gaban ta yana fa'din" Kin wani tsaya kallo na..so kike sai ta toshe min kunnuwa da ihunta kafin ki kar6e ta dan mugunta ko?" Bata ce dashi 'kala har yanzun kallon sa take tana mamakin abinda yai wa yarinyar. Mi'ka mata Mufeedahn yy gaba yana sake fa'din " amshe ta ko in sake ta ta fa'di.." Da sauri Moopy ta bar jikin sa ta cakume jikin Zaitun 'din tana rage sautin kukan ta itama tana duban Rayyan. Zaitun ma sai ta rungume ta 'kam tana sake bin shi da kallon tuhuma har da waigawa, kamar bazai yi magana ba amma ganin irin kallon da take binsan da shi yasa shi batare da ya jiyo ba ya furta" Dan Allah kar ki cinye ni....zamewa zatayi na tare ta". Daga haka ya tura 'dakin Ammi da sallama ya shiga. Ita kam rintse idanu tayi sai lokacin kuma hawayen ta suka gangaro...tana tsaye a wurin yazo ya sake giftata ganin Ammi bata 'dakin ya kuma ji motsin ruwa a bayi dole yasan kuma zata bu'kacy privacy idan ta fito shiyasa kawai ya fito da niyyar jiran ta a parlourn 'kasa. Sau 'daya kawai ya kalle ta ya 'dauke kansa, baki ya kya6e ganin yanda ta rungume 'yar yarinyar tamkar zata maida ta cikin ta " Wannan kam ina jin tafi kowa sanin zafin haihuwa". Abinda ya fa'da kenan cikin ransa dai-dai lokacin da ya isa bakin matakalar benen yana kya6e baki. Wannan karon kam da 'dan hanzarin sa ya sau'ka ba kamar yadda ya hawo ba. Zaitun cire Moopy tayi daga jikin ta itama dur'kusawa tayi gaban ta tana bin jikin yarinyar da kallo wai ko zata ga gurbin ciwo a jikin ta amma bata ga komai ba. Har rigar ta sai da ta 'daddaga amma bata ga komai ba, hannun ta ta kama duka biyu tana 'dan ja baya Moopy na biyo ta nan ma taga tafiyar yarinyar normal ne ba wata matsala ta tabbatar kafar ta bata ji ciwo ba, haka kuma ba marin ta yayi ba bata kuma ga alamun bugu kan skin 'din yarinyar ba. Sassanyar ajiyar zuciya ta sau'ke mai 'kunshe da jin da'din ganin ba cutar mata da yarinyar yayi ba...'kwafa tayi cikin zuciya ta furta" Allah ya taimake ka wallahi da kaga yanda ake ramuwa". (Su Zaituna manya, ni kwa nace me zaki iya yiwa Mr Rayyan ne). Dama tun ba yau ba tayi alwashin duk ranar da ya sake sa mata yarinya kuka to kuwa sai ta rama mata duk abinda yai mata babu ruwan ta da wani girma da mulkin sa, tunda bai san tausayi ba bai san yaro ba itama haka bazata 'daga masa 'kafa ba..ya maida mata yarinya tamkar tsarar sa abokiyar gaban sa haka kawai. Dan ta sake tabbatar da babu abinda ya samu yarinyar madadin ta 'daga ta sai ta kama hannun ta suka koma 'dakin Ammi tana mai sake lura da yanayin tafiyar ta. Suna shiga Ammi da fitowar ta kenan daga bayi ta saki murmushi tace" Kishiya ta ya ido da hawaye kuma?" dan ita Ammi bata ji kukan Moopyn ba sam kasantuwar tana bathroom ne. Amsa Zaitun ta bata da fa'din" Wallahi Ammi Fa'duwa tayi". " Ayyah fatan bata ji ciwo ba?" " Ina ga dai kamar bakomai". " Toh Masha Allah..Allah ya rufa asiri..ya kare min kishiya ta farin cikin Mamin ta". Murmushi Zaitun tayi gami da fa'din" Ameen Ammi". har cikin zuciyar ta taji da'din wannan addu'ah ta Ammi shiyasa take bata daraja tamkar ta mahaifiyar ta. A duk lokacin da ta shiga firgici musamman akan Moopy to yanayin ta gaba 'daya ke sauyawa, sai tayi kyau, idanun ta su zama wasu lumsassu kafin hawayen ta ya sau'ko gashin idanun ta ne ke fara ji'ka da ruwan hawayen ta a hakan zaki ga tana zaro idanun musamman idan tana zargin wani da ta6a mata 'yar ta haka zata ritsa ka da ji'ka'k'ku kuma lumsassun idanun ta tana binka da kallon tuhuma, ko da bata tanka ba toh wannan kallon ka'dai ya kan isar da sa'kon zuciyar ta. Yanayin ta a wannan lokacin sosai yake tafiya da imanin sa, har ya kan gaza 'dauke idanu akan ta...ya ringa jin bugun zuciyar sa na da'da 'karuwa kenan akanta nd bai san dalilin hakan ba, shi dai kawai tsintan kansa yake da shiga wani yanayi akan yarinyar. Shiyasa sau da dama ya kan firgita mata yarinya batare da sanin cewa da gangan yayi ba sai ta saki kuka, ita kuwa uawar son 'ya ko a ina take ko me take yi da zaran ta ji muryar Moopy zata taho a gigice dan ganin abinda ya same ta. Haka zata zo ta ritsa shi da idanu shi kuma yana enjoying kallon ta bata sani ba, bazata yi magana ba haka shima ba zai yi ba, cikin zuciyar ta kawai take jin tsanar sa na 'kara ninkuwa cikin kowani dakika musamman da ya sako mata 'ya agaba kamar abokiyar gaban sa. Shi da kansa daga baya yazo ya fara jin haushin kansa kan hakan sai ya fara kwa6an kansa yama daina shiga sabgar su kwata kwata. Ya ma manta da wanzuwar su cikin gidan gaba 'daya balle har wani abu ya ha'da su. Wasa- wasa watannin Zaitun kusan hu'du yanzu suna a gidan Ammi, ba ta da matsalar komai yanzu duk da yake Marwa sun sake yin wata doguwar tafiya da mijin ta sati shida kenan yanzu bata da wata abokiyar hira bayaga Raleeya, sai ko wani lokacin Ammi, amma hakan bai rage ta da komai ba dan bata da wata matsala a yanzu babu shiga sabgar su. A bakin Raleeya take ma jin ceea ashe tun auren Sultan da Marwan basu yi zaman watanni uku mai kyau a Kano ba, yawon 'kasashe suke tafiyar su suna hutawa. Kwata- kwata Sultan baya bawa ma'aikatar ta su muhimmanci sai dai duk da hakan salaryn sa bai samu tangar'da dai- dai da rana guda ba. Sosai abin yake bawa Rayyan haushi, ya mai magana amma kuma 'karshe Sultan daina 'daukan wayar sa ma yayi kwata kwata, shine ya yanke shawarar samun Ammi suyi maganar. Yana so ne su dakatar da Sultan daga wannan yawon banzan da yake 'daukan Marwa suke tafia da ba wata amfani gareta ba, ya dawo gida su ha'da 'karfi su kula da ma'aikatar su. Dan shi abin yawa yake masa, yana zuwa hospital lokaci zuwa lokaci as a consultant duk da ma tuni ya ajiye wannan aikin amma sun 'ki sakin sa, dole suka ro'ki yake aiki da su as in contract abin yawa yake yi masa. Yana ganin matukar babar sallah ta wuce Sultan bai tattaro ya dawo gida gaba 'daya ba sosai zai 6ata masa rai dole zai nuna masa asali waye waye Rayyan Sa'ad Auta dan sakarcin yayi yawa. ***** " Zaitoon!...Zaitoon!!" Muryar Ammi ke 'kwala 'kiran sunan Zaitun tana nufar 'dakin da suke. Amma kasantuwar tana bathroom sai bata amsa ba. Ammi na tura 'kofan 'dakin ita kuma tana bu'de na bathroom sai suka yi hudu ido. Ido Zaitun ta kwalalo tana fa'di " Ahh Ammi da kanki, yanzu ma fa nake niyyan zuwa can 'din". Tayi maganar tana 'karasowa tsakiyar 'dakin. 'Yar daria Ammi tayi tana kallon Moopy dake wasan ta da kayan wasa na yara da aka wadata ta da shi tace.." Haba bakomai, duk 'daya ai..". " Wannan kishiyar tawa bata amsa sallama ne..?". Ta 'karasa maganar tana mikawa Moopy hannun ta gami da zama bakin gadon Zaitun 'din at same time tana ajiye wata babbar ba'kar ledar da ta shigo da shi hannun ta. Atampopi ne masu kyau aciki guda hudu da ku'di 20k na 'dinki kasantuwar latti da akayi saboda karatowar kwanakin sallar yasa gudun kar ta basu wahala ya sa ta ha'da da kudin wala'Allah ko zasu samu inda za'ai musu 'dinkin express, amma babu wanda yasan hakan fa sai ita ka'dai. Moopy bata ki zuwa wajen Ammin ba dan zuwa yanzu sun saba sosai, sai dai duk sabon su ba kasafai ta ke sake jiki da Ammin ba matukar babu Zaitun a wajen. 'Dan wasa Ammi tai mata, ta fara daria wanda hakan yasa Zaitun murmusawa cike da jin da'di har 'kasan zuciyar ta take duban su. Sai da Ammi ta gama da Moopy kafin ta dawo da kallon ta ga Zaitun tace.." Wai dai sa'ko ne wallahi shap na mance ne gashi lokaci ya kure duk da hakan dai ba wani abu tunda mantuwa ce...". Duk da Zaitun bata san inda maganar Ammi ta dosa ba dan ta kara mata kwarin gwiwa yasa ta fa'din" Allah ma yakan yi uzuri ga ma'abocin mantuwa Ammi ba laifin ki bane ai..". " Hakane Zaitun, nagode..". Murmushi kawai tayi yayin da Ammi ta cigaba da magana tana kuma nuni da hannun ta" Nan ma'kwabta yamma da mu haka ina jin gida na uku ko hu'du zaki ga gidan dai da brown gate dan Allah ki mika musu, suyi hakuri dan Allah mantuwa ta same ni wlh...". " Toh Ammi ba wani abu, kamar ma fa na gane, ba gidan da Raleeya tace min na marayun nan da suke zaune da kakar su ba..?" Da sauri Ammi ta jinjina kai tana fa'din" Allah yai mk albarka nan 'din ne dai 'yata ". Sosai Zaitun ta jinjina karamci irin na wannan matar dan tasan Ammi ba baya ba wajen kyautatawa, ko su da suke aiki a karkashinta sai dai suce masha Allah, sutturun da aka 'dinka musu a sallah abin ba acewa komai kuma ko sallar azumi hakan akayi musu. Kayan Zaitun ta 'dauka" Barin je in dawo Ammi..." Sam batayi niyyan zuwa da Moopy ba a tunanin ta zata barta da Ammi ta mi'ka sa'kon ta dawo tunda ba da'dewa zatayi ba. Amma Moopy na ganin ta da hijab kuma tana kokarin barin 'dakin kawai ta fara kuka tana mika mata hannu. " Ja'ira bazamu zauna ta dawo yanzun ba..?" Kamar jira take sai ta 'kara sautin kukan ta. " Dawo ki kar6i abarki wannn ba zama zata yi ba Zaitoon..". Cewar Ammi tan mikewa tsaye ta bata yarinyar duk suna 'yar daria. A hannu ta rike ta suka tafi a haka.... Sosai jikin Zaitun yayi sanyi da ganin yadda tsohuwar nan ke share 'kwalla da jin cewa Ammi ce ta aiko ta..." Allah sarki Aseeya.." Ta ringa jero mata addu'i'o tana share 'kwalla sosai. Nan.ta bawa Zaitun labarin cewa 'dan ta 'daya ne kuma Allah bai bata shi da wuri ba har sai da ta cire rai da samun rabo kafin ta same shi, tun kuma kafin ta haife shi mahaifin sa ya rasu ita kadai ta rain shi har girma yayi aure ya dauko ta suna zama tare dukkan su da matar sa mai kirki yaran sa uku duk mata kuma ba wasu manya bane dan babbar ce ma ke da shekaru shida, rana guda ciwon ajali ya kama shi yini guda a asbiti Allah ya kar6i ransa.... Sun shiga tashin.hankali sosai gami alhini da rashin sa, sunyi zaman shekaru biyu da matar sa kafin 'yan uwan ta suka nemi ta koma gida tayi wani auren. Yanzu haka tana aure a Zamfara ita kuma tsohuwa ta cigaba da zama da yaran. Kusan Ammi tafi kowa 'dauke musu bu'katun su batare da kowa ya sani ba, abincin su suttutarar su hidimar makarantar su duk Ammi ke musu. Akwai kuma wasu 'yan.unguea da abokan.arziki da ke tallafa musu dan ko lokacin da yake raye ba wani mai karfi sosai ba ne rufin asiri ne kawai na ubangiji har ya jefo shi cikin unguwar da suke da suke. Sosai Zaitun ta jinjinawa Ammi ta kuma 'kara bata wani babban matsayi cikin zuciyar ta saboda halin kwarai da take da shi. Ita kanta sai da ta taya tsohuwar nan share 'kwalla, hakika rayuwa iri iri ce, duk yadda kake zaton tsananin dake cikin rayuwar ka ya kai wani matsayi idan kaji na wasu sai ka raina naka, Zaitun da batayi tunanin 6ata ko mintina biyu a gidan ba sai gashi ta sahfe sama da awa guda suna tattaunawa da tsohuwar, tace jikokin nata duk basa nan suna makaranta shiyasa gidan ya kasance shiru babu kowa. Suna tsaka da hirar sai ga wata brown magen ta 'yar kyakykyawa da ita ta taho sa'daf- sa'daf cikin irin tafiyar su da babu tashin hankali a ciki, bata zame ko'ina ba sai jikin tsohuwar nan ta lafe ta fara goga mata kanta. Zaitun sam bata lura da tahowar magen ba sbd yanda duk hankalin ta ya 'dauku ga labaran da tsohuwar nan ke bata. Duk 'din su babu wanda ya lura, suna tsaka da magana Zaitun ta 'dan kalli fuskar Moopy jin yanda jikin ta ke daukan 'dumi. Ido ta 'kwalalo waje tana furta kalmar Innalillahi...ganin yadda skin 'din yarinyar ya wani koma jajajir da wasu kananun kuraje kamar na zafi da duk bata san lokacin da hakan ya faru ba, zabura tayi tana sake duban jikin yarinyar, sai lokacin tsohuwar nan ta lura da abinda ya razana Zaitun 'din. " 'yar nan me yasa kika 'dauko musu 'diya zuwa gidan nan? ai dama saboda sun san bana rabuwa da mage yaran Aseeyah da jikokin ta basa shigowa nan gidan...wannan 'din ma inajin mancewa akai aka barki tahowa da ita, maza kai musu 'diyar su gida akwai abinda suke shafawa zai washe...". Cewar tsohuwar tana mi'kewa tsaye da kokarin mi'kar da Zaitun ganin ta kasa ta6uka komai. Zaitun da duk bata fahimci kan maganar tsohuwar ba tuni ta fara ziraro 'kwalla tana jijjiga Mufeeda da jikin ta duk ya saki..." Innalillahi wa inna wa inna ilaohi raji'un...dan Allah Mamana karki mutu ki barni, Moopy, Moopy na..." Ina yarinya kam idanun ta duk sunyi luhu luhu tamkar mai jin bacci yayin da jikin ta ke ra daukan 'dumi yana kuma 'kara yin jaa. Lami lafia suka zo ta sani toh me ke faruwa kuma? Me ya samu Mufeedan haka? Me ya samu yarinyar ta? Tuni kuka ya riga yaci 'karfin ta da 'kyar tsohuwar nan ta tashe ta ta kama hanyar gida rungune da Moopy gudu- gudu sauri sauri ko kulawa da inda take takwa bata yi. _Salmerh_ 😘 [26/9/2022, 10:19 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* Wattpad@ Serlmerh-md 🅿️ *...40* .......A rikice ta shigo gidan tana nufan babban part 'din dake gaban ta...bata zame ko'ina ba sai saman Ammi dan ba ai mata shamaki da ko'ina na gidan ba musamman 6angaren Ammin da ya kasance nan ne wajen aikin ta. "...Ammi, Ammi...kalli jikin Mufeeda." Ammi da ke zaune a parlourn saman nesa kadan da ita Rayyan me suna kan tattauna batun dadoear Sultan gida kawai suka tsinkayi muryar Zaitun da yau ko sallama bata tuna yi ba. Ba'karamin tashi hankali Ammi yayi ba ganin tahowar Zaitun a hakan da ko ba'a fa'da ba tasan ba lafiya ba, tun kan ta 'karasu tasan cike da tashin hankali ta tunkaro ta. Tsam Ammi tayi ta zubawa inda tasan Zaitun 'din zata 6ullo idanu tama kasa ta6uka komai jira kawai take taji meke faruwa da fatan Allah yasa ba wani abun bane babba, amma 'kasan ranta take jin kamar ba 'karamin abu ne fa zai tayar da hankalin Zaitun har haka ba. " Ammi, dan Allah ki taimake ni Ammi dubi jikin Moopy abinda yayi, Ammi dan Allah kice kar ta mutu ta barni wallahi ina son ta..." Abinda take cewa kenan tana zubda 'kwalla ta zube gaban Ammi. Sai lokacin ta saki asalin kuka tana kifa kanta saman cinyoyin ta gaba 'daya nutauwar ta tafi. Da mamaki ya 'dago ya kalle ta, take kuma ya sake kawar da kansa yana tsakin tsaki kasa kasa, haushin tsayar musu tattaunar da suke nema yafi cika shi..'karshe wayar sa ya ciro ya fara danne dannen da shi ka'dai ya san meke yake yi cikin wayar. Ammi zubawa Moooy idanu tayi bayan ta kar6e ta tana tambayar Zaitun abinda ya same ta, sai dai ganin yadda jikin yarinyar yayi yasa mamaki cika ta banda zafi da jikin ya 'dauka... Cikin kuka Zaitun ta fara yi mata bayanin " Wallahi Ammi ban san komai ba, muna cikin magana da Dada ( haka ake cewa tsohuwar) kawai naga jikin ta ya koma haka ga shi ya 'dauki zafi, kuma fa Ammi ko iya tsaida idanun ta ta kalle ni bata yi 'karshe ma idanun rufewa sukai"... Ta 'karashe da sakin kuka sosai mai ta6a zuciya, gani take tamkar yarinyar ta mutu ne Ammi ke 6oye mata. Ammi rasa ma abin fa'da tayi har yanzun duban jikin yarinyar take, sosai yanayin abun yai mata kama da na yaranta, wanda tasha fama abaya kuma har a yanzun basu daina samun irin wannan attack 'din ba, sai dai da yake sun manyanta sukan kiyaye shiga inda suka san zai dame su balle irin hakan ya faru da su..tuno wani abu yasa ta 'dan so ta sa a fahimci abinda ke faruwa..zazza6i ne ya shige ta mai 'karfi Zaitun dole sai an kaita clinic, amma gidan Dada har yanzu akwai mage ne dama..?" " Erh akwai naga wata 'yar fara fara haka ajikin Dadan". Zaitun ta bata amsa tana mai jin haushin shigo da wannan tambayar bacin ga damuwar da yake gaban ta. Ammi bata sake fa'din komai ba illah mamakin samun me irin jinin yaran ta a dunia da take.... "...Toh ya isa, daina kukan haka nan bari a kaita hospital ko...". Ga Rayyan ta maida duban ta tana fa'din" Rayyan abin mamaki, kalli yarinyar nan, she is also allergic to...". Bai bar Ammin.ta 'karasar bama ya tare da fa'din" Kai Ammi..da ganin abu, kika san ko 'kazanta ce ta kawo mata hakan..". Yayi maganar yana maida wayar sa aljihu dan tun farkon maganar ta su bai sanya musu baki ba sai yanzun da Ammi ta gayyato shi. Hararar sa Ammin tayi tana gayara zaman yarinyar da kyau a jikin ta. A fakaice ya saci kallon Zaitun ganin turereniyar da hawayen ta ke yi...shi kam sosai yake jinjina irin wannan soyayyar, bai ta6a ganin irin wannan 'kaunar ba, shin hauka ne ma ko kuwa dai 'kaunar ce dagaske? sai kace akan ta aka fara haihuwa..to in mutuwa tazo ta isa hana yarinyar tafiya ne...? Kya6e baki yayi yana kawar da kansa. " Rayyan akwai abinda za'a iya mata a gida ne ko sai an kaita hospital? her condition is as exactly as you people more especially Raihana, Safaa nd u Rayyan... tun kuna yara haka jikin ku ke yi sak matukar kuka kusanci mage kuma har girman ku...i wonder why itama takeyin irin naku..?" Ta 'karashe tana duban Rayyan fuskar ta cike da tsantsan mamaki. Cike da haushin wannan dogon sharhi na Ammi yace" Toh Ammi duk mu ba halittun Allah bane? shi ya haliccemu ya kuma raba mu jinsi- jinsi, ya raba mu kala daban daban, ya bamu kamanni mabanbanta, haka ya raba mu wasu lafiyayyu wasu masu 'karancin lafiya, wasu masu hankali wasu akasin hakan, duk tsananin yanayin da kake ciki dole a wani wajen daban inma kusa da kai ne ko kuma nesa da kai dole sai ka samu me yanayi makamancin naka, bazaka ta6a cewa kai ka'dai ke fama da abu kaza duk duniya ba dole akwai irin ka a wani wajen..kar kiyi mamaki Ammu, buwayar Ubangiji ta wuce misali...". Kai Ammi ta jinjina tana sakin.ajiyar zuciya tace " Hakane Rayyan, Ubangiji Allah yasa mu dace da Rahamar sa ya bamu dacewa duniya da Lahira". " Ya amsa da " Ameen". Yayin da Zaitun ke share 'kwalla kawai, tuni ta daina sheshshekan kukan amma hawayen ta ya kasa tsayawa. Yasan ba son ta bane ace shi yakai yarinyar asbiti, bazata ta6a son hakan ba, amma ko dan sbd ya sake 'kona ranta sai ya mi'ke, rigar sa ya gyara sannan ya sa hannu ya karbi yarinyar daga hannun Ammi. Zaitun kam kafewa tayi wuri guda ta zuba masa idanu, ji take kamar tace ya bata 'diyar ta dan tasan halin muguntar sa amma sai ta kasa furta komai illa 'kure shi da kallo da tayi. Tana son 'diyar ta ta samu lafiya amma me yasa sai shi. Gira Rayyan ya 'daga mata alamar. " Ya dai"...murmushin mugunta can 6oye saman fuskar sa. Bai jira jin abinda zata ce da shi hatta Ammin kawai yy waje rungume da yarinyar, tsabar yadda ta kasa kunnuwa hatta takun steps da yake tamkar a tsakar kanta yake yi, har ya sau'ka 'kasa ne ta daina jiyo takun sawayen sa...tanajin tamkar zai dawo yace ta tashi su tafi amma shiru..har bayan wasu mintina babu shi babu alamun sa. Ammin kam da ke ta jimamin lamarin shiru tayi tana nazari. Haushin bai ce suje tare ba ya sanya ta tashi ta sauka da gudu ta koma 'dakin ta, a hanya ta ha'du da sabuwar mai aikin Ammin tana tambayar lafiya ko kula ta ma batai ba tayi wucewar ta 'daki ta saki wani sabon kuka zuciyar ta a hargitse...dan sam bata ji zuciyar ta ta nutsu da fitar ta su ba. Shi kam dama ba wani hospital da zai kaita, yana da ragowar maganin da yashafa kwanaki da yake shima bai jima da samun attack 'din ba, kawai 'kin bayyana hakan yayi ga Ammi. Kuma attack 'din na sa ma ba kowa ya sani ba sai Amrah ka'dai. Daf da zai shiga 6angaren sa ya dubi fuskar yarinyar. Murmushi yy 'kasan zuciyar sa yace..." 'yar gold, 'yar gatan Maman ta...yau dai gaki a hannu na ni 'din da dai ake gudu na...". Ko da ya shafa mata maganin, wani 'daki ya kaita gefe bedroom 'dinsa ya kwantar da ita. Alluran bacci yayi mata wanda zai sa ta baccin awanni biyu zuwa uku ya gyara mata kwanciya ya kashe A'c ya koma bedroom 'din sa. Lokaci- lokaci ya kan shiga ya duba ta, Bai tashi kai yarinyar ba har aka yi azahar har kusan la'asar da yayi shirin fita sannan ya mi'ka ta, ranar ma Amrah taje bikin wata friend 'din ta. Shi kuma yau hutu yake dama baije aiki ba. Lokacin da ya kai yarinyar tuni Zaitun tayi laushi, idanun ta ko bu'duwa da kyau ba sayi tsabar kuka. Ammi ma tayi ta 'kiran wayoyin sa duk akashe shiyasa hankalin Zaitun ya tashi sosai. A palorn 'kasa yaci karo da ita, ta zubawa kofa idanu da alamu dawowar su take tsumayi, bai yi mamaki ba da ganin yadda Zaitun duk ta firgice yini guda kacal amma har 'yar rama tayi, ji yayi daria na shirin 'kwace masa." _firituwa kenan_ ". Ya ma san da 'kyar ne yau idan anci abinci sbd ba'aga 'yar gold ba... Da ganin sa ta mi'ke tsaye amma sai yayi tamkar bai ganta ba. Direct saman Ammi ya wuce, da sassarfa Zaitun ta mara musu baya. Da sallama ya shiga ya yiwa Ammi barka gida sannan mi'ka mata yarinyar yana fa'din" gata Ammi kurajen duk sun koma, zafin jikin ma ya sau'ka, za ta dawo to her normal condition da zarar ta farka...". " Amma ya akayi wayoyin ka duk basa tafiya Rayyan..? Yini nayi ina 'kiran numbers din ka duk akashe". Tayi maganar tana duban fuskar sa while tana gyara ri'kon yarinyar. " Ammi mota na mance su gaba 'daya..". "..and they ar all switchoff a motar ko..?" Murmushi yayi tuno karyar sa bata hau kan seti ba dayake ba saba yin ta yai ba. Yana shafa kansa yace.. " i'm sorry mum...zan 'dan fita gari..." " Adawo lafiya..ka kyauta ai.." _Salmerh_ 😘 [29/9/2022, 4:18 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* Wattpad@ Serlmerh-md 🅿️ *...41* _Washe gari_ Tana cikin bathroom 'din Ammi tana wankewa, daga cikin bedroom 'din kuma Ammi ce ke waya da 'diyar ta Raihana yayin da Moopy ke gefe tana wasan ta tamkar ba ita ce ta kusa shekawa jiya ba. " Erh baza dai su wuce this week ba, kinsan 'dan uwan naku sai a hankali...Rayyan ne ya matsa akan su dawo gida..". Da fitowar Zaitun abinda kunnuwan ta suka fara tsainkaya daga wayar Ammin kenan, kuma shi ta tsaya tunani har Ammi ta kammala wayar bata 'kara fahimtar komai da ta fa'di ba. Tunani take toh su waye zasu dawo Allah yasa Marwa ce, dan wlh sosai tayi kewar ta, tayi kewar abokiyar hira, duk da yake wasu lokutan Marwa kalaman Marwa sai a hankali, takan iya furta kalma marar dadi sai ita a wajen ta bada wata manufa take hakan ba, fahimtar halayyarta da Zaitun ta yi yasa take yi mata uzuri, ba mamaki ta saba da hakan ne shiyasa. Maganar Ammi ce ta dawo da ita"..Mutumiyar ki an kusa dawowa..dama kullum muka yi waya mita take wai ita ta gaji tana so ta dawo Sultan ya ki..". Murmushin jindadi ne ya wadaci fuskar Zaitun.." Masha Allah....Allah ya dawo da su lafiya..". A fahimtar ta ita kanta Ammi annurin fuskar ta yafi na kulluma ga dukkan alamu itama ba son zaman su can wata kasar take ba kawai ba yadda zata yi ne shiyasa. Koda ta gama aikin ta koma 'daki tunanin moments 'din su da Marwa ke 'dan zuwa mata, har mamakin kanta take yi, bata ta6a sanin tayi kewar Marwa har hakan ba sai yanzun. Akwai halittu da dama cikin zuciyar ta da take tsananin kewar su fin ma Marwa amma bata fiya bawa zuciyar ta isashshen damar tunowa da su ba. Abu ne me sauki tayi ta zubda kwalla matukar tace zata bada 'kofar da kewar su zai shiga jikin ta, amma taya zata yi ta ta iya manta karamci irin na ma'kwabciyar Mmn Abdul, taya zata iya mancewa da Adam a rayuwar ta, taya zata iya mance rayuwar ta ta baya. Hatta Hajja da sauran mutanen da suka munana mata ma bata iya mancewa da su balle wa'danda sukai mata halacci. Marwa kuwa abokiyar hirar ta ce kuma 'kaunar da take nuna wa 'diyar ta ya sanya ta bata babban matsayi. A hankali tunanin ta ya gangara ranar da Hajja Ladi ta bar gidan.... Maganar Sultan ne ta dawo da Hajja Ladi daga 'dan guntun tunanin da ta lula" Yanzu akan wannan 'yar yarinyar kk wannan hassadar Hajja Ladi...?" Shiru tayi ta sunkuyar da kanta, sai da ya sake maimaitawa da tsawa kafin ta ce" Ranka shi da'de dan Allah kayi min rai kayi ha'kuri nayi alkwari bazan sake ba wannan 'din ma kuskure ne.." " Ri'ke al'kawarin ki Hajja, idan wannan ya zam kuskure sauran na baya fa..?" Shiru tayi kanta na kallon 'kasa. " Kice kin zama shai'dan kawai, salon na bar ki watarana muma ki sam6a'da mana magani mu fice mu bar miki gidan...?". " Sultan miye haka...?" " Jin muryar Ammi yasa Hajja Ladi maida hankalin ta ga Ammin da alamun ro'ko. " Kalli nan...". Sultan yace da nufin maido da hankalin ta gare shi. " nima albishir zan miki yanzun nan..." Nuno Zaitun yayi yace" kinga wannan da kk shirin koran ko..to ita zata maye gurbin ki, ke kuma daga yanzu 15mints bana so ki kara sakewa cikin gidan nan kije ki cewa bokan ki asirin ki yau ya tonu sultan ya kamaki..dan bazan iya barin ki zama tare da mu ba, in dai har zaki iya cutar da masu aikin da kuke tare to ko mutanen gidan ma basu tsira daga sharrin ki ba wa ya sani ma ko da ke aka ha'da baki...". " Um um Sultan please..". Ammi ta dakatar da maganar da yayi niyyan furtawa tana girgiza masa kai. "...dan haka ki bar mana gida kawai yanzun nan, ko kuma in sa afasa min kwakwalwarki da harsashi...". Da fa'din haka ya tashi yayi hanyar waje bai ko sake waigowa ba. Ni kam da sauri na matsa ganin ta inda nake zai wuce ni kuka Hajja ladi kuka su Yusee kam gaba suka saka Hajja ladi ta tattaro kayan ta cikin lokaci kan'kani ta fito. Ammi ma saman ta ta koma ta 'dauko ku'din aikin Hajja Ladi ta bata, dan ko ita dama hukuncin da zatai mata kenan ko da Sultan bai yi hakan ba, bata zama da azzalumi kuma ta tsane sa, duk wani wanda zai iya cutar da wata halitta bata 'kaunar ko ha'da inuwa ne da shi. Ha'kuri zata bawa Ammin..Ammi tayi saurin dakatar da ita.." Kar ki damu Hajja Ladi Allah ya ha'da fuskokin mu da alkhairi. Daga haka tana ji tana gani akayi waje da ita. Ni kam gaban Ammi na koma ina sake bata ha'kuri ina kuka sai tayi murmushi tace" Haba Zaitun baki yi laifin komai ba fa, baki fahimci abinda ke faruwa bane..?" Sarai na fahimci komai, sannan ganin bindigu ya sake hargitsa min tunani na, sosai abin ya dami zucia ta, ga batun Hajja Ladin ma ya tsaye min musamman da yake sanadi na hakan ya faru sai nake ga kamar nice na cutar da ita, da banzo gidan ba 'kila da duk hakan bazai faru ba, da yanzu tana bakin aikin ta tana neman halalin ta. Dan haka shiru nayi ban yi magana ba sai kuka, kukan da ke taso min tunda 'kasan zuciya ta, tunanin abubuwa da dama nake, tun da na ga bindigar nan tunani na ya koma can baya..tsoro da fargaba ke 'kara tsananta gare ni cikin kowani giftawar da'ki'ka. " Ki daina kuka, mu ai mun saba ganin hakan, sharrin mutane nada yawa Zaitun, ke ma in kina son ki rayu cikin gidan nan sai kin zama mai takatsantsan akan komai, yanayin sultan da kk gani kuma dole ce ta sashi zamtowa hakan saboda wan sa da aka so cutarwa ta irin hanyar, kuma har yau mun kasa kamo bakin zaren sai muka barwa Allah kawai, kuma shi muke roko ya raba mu da duk wanda ya lura babu tsoron Allah cikin zuciyar sa..." " Ameen..". " Bazan 6oye miki ba Zaitun, ni tun zuwan ki gidan nan naji kin kwanta min, kuma naji zuciya ta ta nutsu dake, amanar ahali na zan baki dan ni ba mazauniya bace sosai, akwai harkoki masu yawa a gaba na, amma na barwa Allah komai ne kuma na tabbata zai mana jagora domin yace matu'kar ka dogara da shi toh ya isar maka..babu mai cutar da kai sai da amincewar sa amma da Allah Zaitun mu kokari mu rike amana kinki..?". Da kai na amsa Ammi ina mai share 'kwalla.. har lokacin hankali na bai wani kwanta ba na kuma kasa fahimtar manufar maganar Ammi. Cigaba da magana tayi. "...Gobe ina so zan je Maiduguri amma insha Allahu ma ba dadewa zan yi ba..". Ina share hawaye nace" To Ammi Allah ya kaiki lafiya ki kuma dawo cikin koshin lafiya da kariyar mahallici.." Tana murmushi tace nagode sosai Zaitun zaki iya tafiya...kuma da Allah ki kwantar da hankalin ki Insha Allahu babu abinda zai faru..". Marwa da Ammi na matukar nuna mana 'kauna sai Sultan da shima bai ta6a yi mana duban 'kaskanci ba, na hu'dun su itace Raleeya, amma daga Hajja Ladi, Matar Rayyan da shi kansa Rayyan 'din basu ta6a nuna sun ma san mecece kyauyatatawa cikin gidan ba, hatta da Mufee kuwa bata tsira daga rashin mutuncin su ba. Har ranar da Allah ya raba su da Hajja Ladi. Tun daga wannan ranar kuwa Sultan ya rike Zaitoon daram cikin ransa, sau tari sai yaji kawai bari yazo ya ganta, tun ranar da ya ganta cikin kayan bacci bako 'dan kwali..idan ya tuna sai yaji tsikar jikin sa na tashi. Sai dai sau tari ya kan zo gidan kawai dan ya ganta kafin su bar 'kasar kuma har tafiyar ta su Zaitun bata san da wannan batun ba. Shima 'din sai da suka tafi kafin lamarin ya bar zuciyar sa. Numfashi Zaitun ta sau'ke baya tuno faruwar abubuwan, ha'kika 'dan Adam abin tsoro ne, kuma zata so dawowar Marwa dan sosai take 'debe mata kewa. ***** Kwatsam itama Raleeya mahaifin ta yazo daga Niger ya tafi da ita can. Da yake dama rabuwa suka yi da mahaifiyar ta ta taho da ita shine ya biyo sahu. Hakan ne yasa dole Ammi tasa sabbin masu aikin ta suka ri6anya ayyukan su ita kuma Zaitun aka replacing nata da Raleeya ita zata ke zuwa 6angaren Rayyan tana masu wasu ayyukan. Sam bata so hakan ba, amma babu yadda zata yi, saboda Ammi da kanta ta yanke wannan hukuncin..ba dan komai ba kuma sai dan gudun abinda ka iya zuwa ya dawo, sai ta yadda da mutun sosai kafin take barin sa aiki 6angaren Rayyan gudun kar a cutar mata da rayuwar su. Amma Zaitun sam wannan canjin bai mata ba, yadda tasan cewa daga Rayyan har matar sa ba 'kaunar ganin su suke ba taya zata iya sakin jiki tai musu aiki. Haka dai ba dan taso ba take zuwa aikin tana.kuma takatsantsan da duk abinda tasan zai ja mata magana, da ta kammala kuwa take komawar ta can babban 6angaren na Ammi. Marwa ma ta dawo sai dai wannan karon ba sosai suke samun zama ba sakamakon canjin aiki da akai mata. Ranar wata lahadi ne Rayyan na zaune a parlorn sa yana hutawa da yake weekend ce babu aiki, yayin da Amrah ke 'daki yau kanta gaba 'daya ya 'dau zafi Sultan ke nema su ha'du ta tambayi Rayyan fita kuma ya hanata acewar sa yau weekend ce ranar hutun sa kuma yana bu'katar ta kusa da shi, taya zata ce zata fita, duk working days din da suka shu'de meyasa bata fita ba sai yau din. Yace ta bari zuwa yamma da kansa zai kaita duk inda take son zuwan Amrah taki amincewa tace ita in ba yanzu ba ta yafe, mamaki ne ya kama shi. Ko ta nemi marairaice masa ji yayi ransa ma na 6aci..aganin sa Amran na neman raina masa hankali ne ma. Hakan yasa ya daka mata tsawar ta bar gaban sa babu inda zata ce. Kai kawo take yi cikin 'dakin ta sam tarasa mafita, gashi ya ki fita ko'ina balle ta samu hanya itama..can kuma shima Sultan ya matsa mata cewar sai sun ha'du ayau din duk ta rasa yadda zata yi da ranta ma. Tarin warmers da suka yi breakfast da shi take zaryar kwashewa daga dinning zuwa Kitchen Mufee na goye a bayan ta, haushin wannAn lamari duk ya bi ya isheta ace wai ita wannan matar gidan komai sai an mata ne. Jin zuciyar sa na mai 'daci ne ya sanya shi tashi ya bu'de 'kofa ya fito dan samun sassanyan abinda zai ji'ka ma'koshin sa da shi, yana fitowa yaga wulagawar " Kinga..". Maganar Rayyan ne ya dakatar da ita da nufan dinninga da tayi. Abinda yake so ya sanar da ita yana me komawa saman kujerun Parlourn ya kishingi'da. Umarnin sa ta cika ta dauko masa da cup akan wani 'karamin tray 'dan madaidaici. Da yake ba yau tasan ka'idar sa ba hakan yasa koda ta ajiye bata wuce ba sai da ta tsiyaya masa. Zata mika masa kenan zai ta ji kamar Moopy na zamewa zata fa'di dayake da 'dan kwalinta yau tayi goyon so bai zauna da kyau ba, take hankalin ta ya koma gareta, shaf ta manta da abinda ke hannun ta kawai ta sake ta tallafi Moopy da ke shirin fa'duwa da duk hannuwan ta biyu. Sai da ma ta ji 'karar parantin da kuma sanyin juice 'din kan 'kafar ta kafin ta ankara da abinda ta aikata. Shi kam Rayyan tsaye ya mi'ke jin rashin hankalin da tayi masa, cike da takaici ya mi'ke tsaye yana duba jikin sa fara sol 'din shirt 'din sa duk ta 6aci da stain na juice 'din ya zam tamkar kampala. Wani mugun kallo ya bita da shi ransa a ha'de ganin ko ta kansa ma bata bi ba sai 'diyar ta abin sai ya sake 'kona ran sa dama kuma cike yake da haushin Amra. A zafafe ya 'daga hannu da niyyar sau'ke mata marin da zai dawo da hankalin ta ga abinda ta aikata sai dai cikin rashin sa'a yana 'daga hannun ita kuma ta sulale 'kasa dan bashi ha'kuri ganin kan 'kafafun sa ya parantin ya fa'di sannan ya gangara amma still idanun ta na akan Moopy bata ma lura mikewar sa ba balle tasan da batun mari tana sulalewa mari na tahowa suka buga sa6ani. Sai kan iska ya sau'ke shi. 'Baci ransa ya sake yi ganin ta kaucewa wannan bai bari 'karfin marin sa ya tafi abanza ba cike da hassala kawai ya kai mata hambari da kafarsa, rashin sa'a duk yanda yy balance ya kai harbin sai ya sau'ka a gefen cinyar Mufeedah. Wani gigitaccen kuka ta sanya da ya kusan hautsinawa Zaitun hanjin cikin ta. Tsaye ta mi'ke nan take kamar an tsunkule ta tana rungumar Mufeedan tana bin shi da wani kallon tsana wanda ke fita tun daga zuciyar ta...ido cikin ido suke kallon juna kowa ransa a matukar 6ace. Tsawa ya buga mata da fa'din"...Daina kallona ni mayya..kurwata tafi 'karfin manyan ki ma balle ke..useless kawai..". Ita dai bata yi magana ba banda hankalin ta da ya 'kara kakkasuwa kashi-kashi, kukan Moopy da ke ratsa ta ga kuma takaicin babu damar ramawa Moopy wannan zaluncin da akai mata, hakan yasa ta kasa 'dauke idanun ta da suka cika da ruwan hawaye akan sa.... Kallon fuskar Moopy ta sake yi tana shafa mata gefen cinyar tata sai gani tayi fuskar tayi ja da alamu cike da azaba take kukan. Bata ko sake kallon shi ba ta juya ta fice abinta tana sake rungumar Mufeedah ajikin ta hawayen idanun ta gangarowa. Daf da zata bar 'dakin ta tsinkayo muryar sa yana fa'din"...wani uban ne zai gyara mk nan 'din?" " ....Uban da ya dakar min ''diya ta.." Amsar da ta bashi kenan daga haka tayi waje bata ko.sake waigowa ba, kuma bata yi tunanin wannan maganar me ze iya janyowa ba...ji kawai tayi cikin ranta ta maida masa martani koba komai shima zai ji zafi cikin ransa koda bai kai zafin da Moopy taji cikin jikin ta ba. Bata ko shiga part 'din Ammi ba baya ta koma wajen lambu anan ta samu da 'kyar ta lallashi Moopy tana kuka itama. Sai da taga yarinyar tayi bacci tana sau'ke ajiyan zuciya kafin ta samu natsuwa amma har a lokacin bata daina jin zafin wannan bugun ba da yai wa Moopy ba...yarinyar ya buga amma ita taji zafin a zuciya, dan babu mamaki na yarinyar ya washe cikin kankanin lokaci amma itace ciwon da ya ji mata a zuci game da hakan ba me warkewa ba ne har abada. Shi kam Raina hannu ya cusa cikin gashin kansa gami da kama kunkumi da da 'dayan hannun, alamun mamaki 'karara ya bayyana kan fuskar sa. Iska ya furzar daga bakin sa yana sake maimaita abinda kunnuwan sa suka jiye masa ta fa'da. Baya so zuciyar sa ta shirya masa 'karya kan abinda yaji amma ai in dai ba yaudarar zuciyar sa zai yi ba babu shakku kan abinda kunnuwan sa suka ji daga sautin muryar ta. Wannan yarinyar da alamu hankalin ta barin jikin ta yake yi akan wannan 'diyar tata, har ni zata mayar wa magana..ni ta zage ni..? Wata zuciyar ne tace da shi ai laifin kane malam da baka ta6a 'diyar ta ba da bazata ta6a iya yi maka ko da tari bane akan ka balle abu irin hakan. "..to ai ni ba niyya ta in bugi yarinyar ba yar ta ba ido na ne ya rufe da takaicin abinda tayi min shiyasa ban ko lura ba 'kafar yarinyar ba, amma ai komiyene nafi 'karfin ta mayar min magana da zagi tunda ni ba sa'an ta bane, wannan yarinyar yarinyar da bata fi karfin ace na haifa ba, ko su Safaa da Marwa fa sun girme ta nesa ba kusa ba. Jikin sa yabi da kallo yana aiyana tsadar sittirar da ke jikin sa..ya tabbata zai iya 'dauke cimar gidan su na kwana biyar lafiyayyu.... Wayar sa ya lalu6o ya danna sunan Ammi daf da zai tsinke ta 'daga, bai jira tace komai ba ya fara fa'din" Wallahi Ammi duk masu aikin kinnan basu da tarbiya kokadan...". " Me kuma suka yi maka Rayyan a ringa hakuri dai dan Allah haba Ammi...Ammi.." Sai kuma yayi shiru rolling idanu yayi cike da rashin madafa. Ammi dake can 6angaren yanayin muryar sa ka'dai ya tabbatar mata da cewar ya gama 'kulewa yau 'din..ta kuma san halin fushin sa hukuncin sa ba ya yin kyau matukar aka kai sa ma'kura. " Bana son fushin nan naka fa Rayyan..Kwantar da hankalin ka kai min bayanin komai insha Allah zan yi wa tufkar hanci." Hannu ya 'daga ya nuna mata 6angaren stained tiles 'din hadda jikin kujerar sa da kuma carpet in dake 'kasan 'dakin tamkar Ammin na gaban sa ne. " Kalli abinda tayi min Ammi duk da bata min parlour da lemo sannan akan wata shegiya banzar 'diyar ta zata gane ni...ni fa Ammi nayi mata magana sai ta zage ni.." Tsaye ya mi'ke yana zaro jajayen idanun sa ya sake maimaita " Ta zagi ubana Ammi..ni Muhammad Rayyan". Ya 'karashe da nuna 'kirjin sa...." Wallahi Ammi na kama yarinyar nan sai ma canza mata kamanni.." Ammi kam yanke wayar tayi gaba 'daya jin yadda yaje buga mata tsawa ba mamaki ya mance da ita ce tai masa laifin ba. Dole ta 'dau mayafi ta nufi 6angaren da rabon ta da shi bama zata iya tunawa ba, ba kasafai take zuwa ba sai da dalili kwakkwara. Da idanu kawai take bin sa bayan ta shigo parlorn da 'yar sallamar ta, bata ga Amra ba, kuma bata yi mamaki dama dan tafi zaton cewa bata a gidan. Duba 'daya zaka yi masa ka tabbatar da cewa har can zuciyar sa yake jin haushi...kuma zuwa yanzun Ammi ta gama fahimtar da Zaitun suka samu matsala, amma ita ta yadda da yarinyar da kuma yadda da tarbiyar ta, abu 'daya kawai zaka mata ka fahimci 'daya bangaren halayyar ta shine ka ta6a mata yarinyar ta tana kuma da yi'kinin shima ya ta6o yarinyar ne tunda har ta shigo cikin zancen, akan Moopy ka'dai ne Zaitun bata iya sarrafa 6acin ranta kuma ita kam bata ga laifin ta ba tayi mata uzuri akan hakan domin duk wata uwa burin ta bai wuce ta kare martaba da asalin yayan ta ba..... Bata gama wannan tunanin ba ta tsinkayo muryar sa yana fa'din" Ammi tell her to leave this house in ba haka ba wlh zan illatata who d hell is she? akan wata shegiyar ''diyar ta? Akan ta aka fara haihuwa ne ko me?..nima nan badan ikon Allah ba ai da ina da 'diya ko yaro na agabana, yaushe ma 'ya'yan gaba da fatiha suka samu license na zama daidai da kowa? Ko kuma tsabar ta nuna wa mutane cewa itan cukakkaiyar mara tarbiya ce shiyasa zata budi baki zage ni bayan ta gama yawon barikin ta? Ni da ita waye abin zagi Ammi..? Wama ya bata wannan damar a gidan nan..?" Saurin matsawa kusa da shi Ammi tayi ta kamo hannun sa, ta zaunar da shi sannan ta mi'ke frigde 'din nasu ba komai a ciki sai madara da kuma ruwa...ba mamaki 'karewa duk sukayi kuma ba'a saka wasu ba amma tana da tabbacin akwai a store. Ruwan ta 'dakko masa mai sanyi ta bashi ya kuwa kafa kai ya shanye tas. Baya yy ya jingina bayan sa da jikin kujera ya lumshe idanu. " Allah ya huci zuciyar Baba na..". Ta fa'da tana murmushi gami da duban fuskar sa. Bai tanka Ammin ba haka kuma baiyi alamun zai tanka 'din ba. " Ayi hakuri a kuma nutsu, kar fushi ya gusar maka da tunani Rayyan har ka dinga fa'din wasu maganganun da basu dace ba musamman wa'danda baka da tabbas akan su, shaidar zina girma ne da ita, ni kaina da kk gani haka na ganta da 'diyar ta kuma dana tambaye ta sai naga kamar bata shirya bayyana asalin labarin ta gareni ba shiyasa kawai na share amma duk da haka bamu da hujjar sheganta mata 'diyar ta, domin idan kayi mata duban natsuwa zaka fahimci Zaitun nada wani abu 6oyayyen cikin zuciyar ta wanda yake yi mata ciwo, walwalar ta fa ka'dai Mafeedah ce, idan kaga tayi murmushi to Mufeedah ce, idan kaji tashin dariyar ta to tare suke, ni da kaina na fahimci hakan, domin duk zaman mu da ita ban ta6a ganin asalin farin ciki me fita tun daga zuciyar ta ba sai ranar da na siyowa Mufeedah kaya anan na fahimci lalle farin cikin ta na manne ne da na Mufeedah, bata damu da komai ba na jin da'din kanta burin ta a kullum Mufeedah tayi farin ciki...akan yarinyar sai ta hana idanun ta bacci ko kuma wani abu muhimmi da ya danganci tata rayuwar. Tana da hakuri, tana da tausayi sai dai Zaitun sam bata 'daukan wulakanci a wajen koma waye ne..uwa uba bata da kawaici ga duk wanda ya ta6a mata yarinyar ta, ko da bazata iya 'daukan mataki ba sai ta nuna 6acin ranta a zahiri...ko kaima 'din na tabbata ka ta6o mata 'diyar ta ne shiyasa har kaga tayi maka rasar kunya hakane ko ba haka ba.? Shiru yy bai tanka ba kar yadda kuma bai bu'de idanun sa ba. Banda juya kalaman Ammi babu abinda zuciyar sa ke yi. Dama haka uwaye suke? Sadaukar da farin cikin su suke yi saboda yayan su? amma ai ita wannan natan har yy yawa. Ammi ce ta cigaba da fa'din " yanzu dai kayi ha'kuri, irin wannan fushin ba naka bane sam bana 'kaunar sa, kayi 'ko'karin kore shi dan Allah Rayyan kaji, kuma ka manta da batun yarinyar zanyi mata magana insha Allahu hakan ba zai sake faruwa ba..." Bata gama rufe bakin ta ba ya bu'de idanu ya kalle ta da alamun tambaya amma bai furat ba. Cikin zuciyar sa ya ayyana kina nufin haka zan barta taci bulus bayan ubana da ta zaga Ammi..? Ammi da ke ta gane ma'anar kallon sai tayi saurin fa'din" Kayi ha'kuri nace..da kaina fa na baka ha'kuri Muhammad". Sake lumshe idanu yayi ita kuma sai ta mi'ke tsaye. " Allah ya yi maka albarka ya kuma hutar min da zuciyar Baba na...yanzun zan turo a gyara maka wurin ka daina tashin hankalin nan ka kaji". Kai kawai ya 'daga mata a hankali la66an sa suka motsa ya furta" Thanks Ammi". Salmerh😘 [29/9/2022, 4:19 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* Wattpad@ Serlmerh-md 🅿️ *...42* Kamar yadda Ammi ta fa'da wata ta tura ta gyara masa inda yake kunfar baki akai 'din tamkar dama can shi ke aikin da kansa. Amra duk bata san me ake ba sai bayan da aka gyara wajen dan 'karshe ma bacci ne me nauyi yayi gaba da ita ta batare da ta shirya masa ba. Ko da ta fito bata tarar da kowa ba Rayyan ya riga yayi ficewar sa..haushi sosai Amra taji da ganin baya gidan, acewar ta taya zai hana ta fita shi kuma yayi ficewar sa batare ma da ta sani ba. Ta mance cewar fushi tayi ta shige dakin ta ta barshi shi. Jin wani jiri jiri yasa ta koma ta zauna tana sakin numfashi 'kasa- 'kasa. Ammi bata tankawa Zaitun kan maganar ba har sai washegari, nan Zaitun tai mata bayanin komai da ya faru, Ammi bata ga laifin ta ba, sai ma laifin Rayyan da ta gani dan shi ya mayar da abin babba, ta kuma san ba wai laifin Zaitun 'din ne asali damuwar sa ba da alamu dama da 6acin ransa yake tafe Zaitun ta taka sahun 6arawo ne, laifin ta 'daya ta gani martani da zagin da tai masa, ta kuma yi mata fada sosai kan hakan domin tamkar 'diya take ganin ta fadan da zata yiwa su Marwa shi zata yiwa Zaitun, kuma ko ba komai Rayyan ya girme mata bai dace ace ta zage shi ta wannan sigar ba. Itama Zaitun sai a lokacin da ga kuskuren ta, nan tayi nadamar zagin ta kuma bawa Ammi hakuri da alkawarin Insha Allahu bazata sake maimaita irin hakan ba. Sosai Ammi taji dadi dan haka nasiha ta 'kara yi mata gami da sake bata damar cigaba da komawa bakin aikin ta. Duk da Zaitun bata so komawa can 6angaren ba amma Ammin ta wuce haka awajen ta...ta koma amma da takatsantsan fin wanda take yi abaya...duk wata hanyar da zata hda ta da Rayyan a gidan bata binta, aikin ta kuma tana yi yadda yakamata amma tafi sakewa tayi aikin idan ta tabbatar ya fita, hatta 'dakin sa ita ke gyarawa ta sharo ada amma daga baya ya hana yace baya so dole ya tilasta Amra take yi masa iya nashi 'dakin ta sharo kullum wataran ma bata yi sai ya kusa dawowa. A wannan karon an samu sauye- sauye sosai daga Amra, musamman wajen abinci, Zaitun ta rasa dalili, sam bata san mugunta ke sata yi mata hakan ko kuwa menene ba, amma sai ta hada musu abinci Amra zata ce sam ba shi take so ga wanda take so, wani sa'in ma ko tayi wanin kuma ba kula shi zata yi ba. Ba 'karamin haushi ke kama Zaitun ba, ta kuma rasa yadda zata 6ullo mata. Ranar kawai ta yanke shawarar yi musu abincin gargajiya, duk da Raleeya ta ta6a bata labarin yadda suka kwashe da ta ta6a yi musu, mai gidan kadai yaci amma Amra bala'i ta ringa surfa mata kuma bata ci abincin ba. Amma ganin tsirfar da Amra ta tsiro da shi cikin kwanaki yasa ta yanke shawarar gwada sa'ar ta. Cikin sauki ta ha'de komai ta kammala ta jera musu kan dinning tana dariyar mugunta ta koma 6angaren Ammi. Cikin ranta take ayyana ita da su ganta sai kuma gobe, in sun so suci in sun so su kwan da yunwa amma ita babu ma mai ganin idanun ta balle tasha kananun surutai. Ko lokacin da suka zo cin nasu abincin da dare data tuna da su Amra daria taji na shirin 'kwace mata, bata ta6a sanin ita muguwa bace sai yau. Tuwon semo ta tu'ka musu da miyar kuka, kukan ma da 'kyar ta samu sai da ta zo kitchen 'din Ammi ta 'dauka. Ga mamakin ta washegari da taje taga dishes 'din bata ga6a ganin sun ci abinci mai yawan na ranar ba. Shi kansa Rayyan sai da yayi mamakin Amra dan yafi kowa sanin bata son tuwo amma yau ci na musamman tayi masa. Har sai da yayi mata daria yana tsokanan ta ko de tuwon Zaitun yafi na kowa dadi ne shiyasa take ci hadda 'kari. 'Yar daria tayi masa sannan tace.." Kai Baby bafa wani dadi, kawai danna taimaka mata naci shine yazam wani abu...". " Ke de fa'di gaskia...". " Allah ba wani da'di..ji nayi kawai ina son ci..". " Hmm" Yace yana mai cigab da cin tuwon sa. Zaitun data shirya mugunta sai gashi ta kare da mamakin su. Bata san shi Rayyan dama asali ma'abocin son tuwo bane samu ne da baya yi ya sa shi hakura, in kuwa ya samu baya yi mata da wasa. Tun daga ranar da an kwana biyu Amra zata ce da Zaitun tuwo, abun har ya fara isan Zaitun kuma, tace dama bata fara na _daga nuna wa mutum hanya shikenan sai yace ya ga wajen zuwa_ . Kamar wasa tsirfar Amra sai 'kara yawaita suke yi Rayyan kansa sai da yasa ayar tambaya akanta. Dama yakai 3weeks da zargin wani abu game da ita, gani yake tana 'kara haske ga boobs 'dinta sun cicciko kuma yasan ita kanta bata lura da hakan ba. Cigaba yayi da nazarin ta batare da ya sawa ransa sosai ba kawai dai yana fatan Allah yasa hasashen sa ya zam gaskia. Abinda ma ya 'dauke masa hankali shine shirshiryen tafia Lagos da yake yi, wannan abun yazo masa cikin lokaci guda kuma tafiyar ta gaggawa ce kayane da aka kawo musu ba'a sauke ba aka kama shine zai bi sahu amma ya bari a ransa da zaran ya dawo zai yi mai yiyuwa dan tabbatar da hasashen sa. Tun daren ranar ya tashi zuwa Lagos bai dawo ba kuma sai da yayi kwana biyar. Cikin kwanaki biyar 'din nan sosai Amra da Sultan suka samu kansu, sheke ayar su suke bada wasa ba, shi da aka matsa ya dawo sbd kula da ma'aikatar su sai gashi ba wannan ne gaban sa ba, dunduniyar Rayyan yake ci batare da shi ya sani ba. Kamar kullum yau ma wani dan'kareren 'dakin hotel suke kwance bayan sun gama masha'ar su. Hannun Sultan kan cikin Amra yana yawo da shi yace " Allah yarinyar nan ban yadda dake ba..kinga canzawar da kika yi Amra..anya kuwa..?r " Anya me...?" Ta tambaye shi tana ha'de gira...tayi kokarin cire hannun sa a jikin ta ta mike amma yaki bata wannan damar ki tsaya mana in tabbatar tukunna. " Wai mene Sultan yake damun ka..?" Bai daina yawo da hannun nasa ba yace" abubuwa da dama Amra...ke bazaki ta6a ganewa ba..". Dan ya 'dauke hankalin ta yasa shi yin sama da hannun nasa zuwa saman boobs 'dinta yana sake nazartar ta. " Ke baki ga yadda wannan abin ya canza ba..?" " Na gani mana, haka ya gadama..." " A ganin ko Amrah...?" " Hakan nema ai." Ta bashi amsa tana sakin nishin gami da ban'karo 'kirjin ta. Ganin kamar ta fara daukan wani layi yasa shi komawa yayi mata rumfa yayin da ya maye hannun sa dake kan boobs dinta da bakin sa. Hannun kuma ya cigaba da shafa shi akan ruwan cikin ta har zuwa kan marar ta. Yana isar da hannun sa wajen ya danna da 'karfin sa nan yaji tauri awajen. Wani ihu Amra ta saki tana ture sa...bai yi musu ba ya kyaleta dan ya riga ya cika burin sa. Sai dai tun 'dauke hannun sa kan cikin Amra tamkar tare da farin cikin sa ya 'dauke hannun. Nan take yanayin sa ya 'dan sauya. Bai sake 6ata lokaci mai tsayi ba ya watsa ruwa yayi ficewar sa ya barta a 'dakin. Sai da ta gama hucin numfashin danna mata mara da yayi kafin ta mi'ke tana dafa bango ta shiga bathroom itama, ba 'karamin mamaki ya kamata ba da jin wannan canjin a marar ta. Koda ta koma gida kwanciya kawai tayi, banda waya da Rayyan babu abinda ta tsinana shima 'din gaisuwa kawai sukayi tace da shi bata jin dadi yace" shikenan Allah ya 'kara afuwa". Daga can inda yaken murmushi ne ya su6ce masa. Har ya kashe sai kuma ya sake 'kira Amra da 'kyar ta 'daga dan haushi bacci take son yi. Rayyan wata tambaya ya jefa mata.." Banda ciwon kai 'din kina jin zazza6i ne?". Tace " A ah bakomai". " Bacci fa..?" " Ina ji yanzu haka ma sosai.." " Abinci fa..?". Murmushi tayi tana lumshe idanu tace " Baby wai yau me ke damun ka ne haka, in na fada maka abincin da nike so zaka kawo min ne kai da kake can wata uwa dunia..?". Murmushi yayi daga inda 'din da gaskiyar ta kuma fa amma jindadi kawai ya sahi tambayar. " Babu ruwan ki Babyn Baby ke de fa'da min kika sani ko zan iya tura mk daga zuciya ta...". Yayi maganar cike da shauki cikin wata kasalalliyar murya. Sosai maganar tasa ta sata jin dadi. " Baby..when ar u coming back..?" " Sai jibi my dear..fa'da min abinda duk kike so 'din zan sa Sultan ya kawo miki yanzun nan..". Idanu ta lumshe cike da jin dadin furucin sa. " Bakomai Baby..alele naji nake so kuma zan wa Zaitun magana ta dafa min.." " Sai kuma me...?" Ya sake tambaya cike da kulawa. " Babu..". Tace Tuno kafin tafiyar sa abinda tafi son sha yasa yace... " Berries....?" Da sauri tace " Mai tsami...". Daria Rayyan ya kwashe da shi jin yadda ta responding kamar dama jira take...yace " Na kamo ki..yanzun Sultan zai kawo miki, Zaitun kuma kice tayi mk abun mai da'di fa...ya ma sunan sa...?" Tace " Alele..." Yace " Good..ayi bacci lafia my dear.." Daga haka ya yanke kiran cike da jin dadi, fatan sa Allah ya tabbatar masa da zargin sa gaba 'daya ya 'kagu ya bar wannan garin amma abu ya faskara sun rike shi dayawa. Kamar yadda ya fa'da kuwa Sultan ya kawo mata sa'kon har a lokacin kuma fuskar sa babu walwalar kirki.bai ma zauna wajen ta ba ya tafi 6angaren Ammi nan ma gaishe ta kawai yayi ya fito tana tambayar abinda ke damun sa yace bakomai gajiya ce kawai. Ammi tace " Ai dole ". Addu'ah ta bisa da shi tare da fatan alkhairi. Ranar ko takan Marwa bai bi ba ya koma gida sai Zaitun ta raka ta daga baya. Sai da aka 'kara kwanaki biyu kafin Rayyan ya dawo, da dawowar sa kuwa washe gari yasa Amra tayi gwajin fitsari idanun sa suka gane masa abinda ya jima yana muradi dan tabbatar da zargin sa ya sanya shi daukan ta zuwa asbitin su, Fawwaz abokin sa ya sa yayi masa gwajin da kansa aka.kuma tabbatar. Rayyan ji yayi tamkar zai maida Amra cikin sa sbd farin ciki. Cikin sati guda da bayyanar cikin hatta Raihana da bata kusa sai da ta samu labarin cikin nan..kowa yayi murna musamman ma Marwa da itace gwanar 'kiraye kiraye da labartawa. Duk yadda bata shiri da Amra sanadin cikin nan sai da suka fara magana sama sama, Anty Madeena da Ammi kam har 'kwalla sai da suka zubda sbd farin ciki. Tako ina kaffa kaffa ake da Amra, ita kanta Amran mamaki take, bata ta6a zaton 'kaunar su da samun jika har ya kai haka ba sai yanzun, ji tayi ai da tasan hkn da duk shekara tayi ta hahife musu jikoki, amma da yake masu tawakkali ne basu ta6a nuna damuwar su ba suka barwa mahalicci. ***** Tun fara aikin Zaitun 6angaren Amrah ta fuskanci wasu abubuwa, dama can ba shiri suke ba, haka itama Zaitun yarinyar batai mata ba sam, yanzu kuwa da suke kusan yini a 6angaren ta sakamakon bayyanar cikin ta da hidimar ta 'karu fin na baya, sai rashin shirin nasu ya fito 'karara tamkar masu ganin hanjin juna, hantara kyara dungurin kan Moopy kusan kullum sai Amra tayi su. Yayin da Zaitun take jin haushin ta badan komai ba sai dan abubuwan da take yiwa yarinyar ta sosai ta tsane ta, bata ko 'kaunar ganin ta sbd bata son 'yar ta, ko da yaushe idan hakan ya faru sai dai ta bita da mugun kallo ta rungume 'diyar ta dake kuka sosai dan babu yadda zata yi...sbd kowa yanzu Amra ce gaban sa, ita kanta ta taya su farin ciki har zuciyar ta abu guda ne yasa Amran ke bata haushi shine yadda ta tsani Moopy..amma cikin jikin ta har zuciyar ta taji tana 'kaunar sa. Kamar dai yau ma, Amra kunun tsamiya tace take so, Zaitun ta ha'do mata lafiyyan kunun tsamiya da yaji kayan yaji ta kawo mata. Ta ha'da tasa sugar da komai ta gauraya tana shirin mikewa amra ta sake fa'din ta 'dauko mata zuma a kitchen na kan dinning ya kare. Dole Zaitun ta bar Moopy ta tafi 'dauko mata, kafin ta dawo ne yarinyar ta fara bin bayan ta. Amra wani tsawa ta bugawa yarinyar " Toh makalemata dallah can dawo ki jira ta nan cinyeki zanyi ne..?" Tsawar ce ta firgita Moopy ta saki kuka harda fa'duwa, duk maganar Amran kan kunnen Zaitun ne, hakan yasa ko da tazo yarinyar ta 'dago tana ajiye mata robar zuman. " Malama bude min zaki yi ba cewa nayi ki ajiye min ba.."! Cewar Amra tana sake juya kunun ta a cup. Kallon ta Zaitun ke yi shi bata kuma yi niyyar bude Zuman ba, kallon sai ya hassala Amra ta mike tsaye tana nunata da yatsa take masifar wai Zaitun ta gama raina ta akan me ne..hadda zata harareta. Tace " Bafa na son iskanci da rainin hankali, da alamu jin kanki kike dan kinga an taimaka an wayar da ke ko, to wlh ki kiyaye ni in ba haka ba sai nayi sanadin da zaki koma bin kwaroro kina tara yara tunda haka kika fi so..a bu'de min zuma nace ba a tsaya a kaina ba...Moopy da ta tsura mata idanu ta 'karashe da buga mata tsawa bayan ta sauqe idanu akanta..." Daina kallo na ni banza Shegiya dangin 'yan titi...". " Kar ki kuskura...'yarinya ta ba shegiya bace daraja ce da ita na musamman in baki sani ba ni nasan abu na". Tsayuwa Amrah ta gyara tana tafa hannuwa tace" Hehehehe...yau naga rasar kunya ta zahiri, wato an fara yiwa shegu lasisi a 'kasanan nan ne ban sani ba har haka...ke ko kunya bakiji kike neman kare wannan abar.."? ta 'karashe da nuna Moopy. Zaitun kam bata kula ta ba sai ma gyara rikon da ta yiwa Mufeedah da tayi izuwa gefen ta na hagu. Bata tankawa Amrah ba illa juyawa da tayi tana 'daukan wani al'kawari cikin ranta...yayin da ta bar Amrah na ta sababi da kunfar baki. Kafin su bar Parlorn sai ga Rayyan ya fito yana 'daura bottle 'din hannun longslip shirt dake jikin sa. Gaban Amra ya dawo ya tsaya batare da ya furta komai ba. Da ganin sa ne sai ta 'dan sassauta ihun da yake tasan baya son hayaniya kuma itama ya hane ta. Shi kam baki ya kya6e sam ko da wasa bai ta6a yin tunanin dakatar da Amrah daga cin zarafin da take yiwa wannan mai aikin ba, dan shi baya saka kansa abinda bb ruwan sa. Labari Amra ta 'dan fara bashi bayan sun zauna bisa kujerar tana 'karasa sanya masa botiran da yake da magana a bakin ta sai ta saki ranta tana bashi labarin duk abinda ya faru" To ke ma ina ruwan ki da rayuwar su Amrah plz ki daina shiga sabgar su kinji...". Ya 'karashe yana 'dan ha'de rai gami da saukaka muryar sa. " Bazaka gane bane Baby yarinyar ce 'yar rainin hankali wlh". Bai sake magana ba har ta gama masa ta 'daure masa sannan ya mi'ke yana ayyana yau yaci sa'a kenan an masa babu tura baki. " Tashi muje ki gaida Ammi...har cikiyar ki take yi fa...ke har yanzu baki jin magana ta ko...?" " Kai Baby, toh jira in shirya sai muje..". Ido ya 'dan fitar.." Wani shiri kuma again...". " Ni dai please Baby..." Ta fada cike da shagwa6a tana bubbuga 'kafafu. " Toh kawai same ni acan..". Ya fa'da yana ficewa daga gidan ya nufi 6angaren Ammi anan yaci karo da ita a hanya ta jingina kanta da bangon da zai shigar da kai parlorn Ammi ga dukkan alamu wani abu ke cin zuciyar ta, kawai da kai yayi tamkar bai ganta ba kawai ya shigewar sa ciki. Har Amra ta fito Zaitun na nan, abin dunia duk yabi ya isheta bata kuma san ta ina zata 6ullo musu ba. Amrah cikin takun ta na isa da birgewa take tafiya bayan shigewar sa da ka kamar mintina sha biyar sannan ta fito tana wucewa tana taunar cingam 'kas 'kas musamman da ganin Zaitun tsaye daga waje tasan damuwa ce ta cika ta, tana tafiya tana ha'de hanya 'kamshin ta na mara mata baya. Sai da tazo dai dai Zaitun ta wani tauna cingam ya bada 'karacsosai da tasan dole hankalin Zaitun zai dauku gareta sannan tace" Waya fa'dawa yarinya ana ja da isashshiya matar Rayyan ne?" Salmerh😘 [2/10/2022, 11:28 am] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* Wattpad@ Serlmerh-md 🅿️ *...43* .....Ta 'kofan kitchen Zaitun tabi ta wuce 'dakin ta bata kuma san lokacin da suka bar 6angaren ba. Babu wanda ya san abinda ya faru tsakanin ku hatta da Marwa Zaitun bata bawa labari ba..haka kuma bata fasa zuwa dan yin aiki ba. Bayan kwana Biyu Ammi ta tafi Abuja Marwa taje Zaria yin clearance na makarantar ta. Zaitun sam sai taji gidan yayi mata fili sosai sbd bata ganin Marwa yanzu, sanyin ta ma sai ya 'karu, yanzu duk abinda Amra zatai mata bata ko 'daga idanu ta dube ta ma balle mayar da martani. A hankali Mufeeda ta fara er zazza6i, tun abin bai yi zafi ba har zazza6in ya shiga jikin ta sosai, Zaitun ta rasa yadda zata yi da yarinyar. 'Daya cikin sabbin masu aikin gidan ne ta bata shawarar bata paracetamol amma still jikin sai a hankali. Zaitun kuka sosai take zaunawa tayi haka duk dare ita kanta sai da tayi 'yar rama. Ko 6angaren Amra ba zuwa take yi ba yanzu ita kadai tasan damuwar da take ciki. Gashi har yanzu Ammi bata dawo ba haka Marwa ma...Sultan ma yanzu ba sosai yake shigowa ba. Tana kwance a 'daki da wani yammaci da bama tasan wace rana bace ma tana sharar kwalla da tunanin mafita sai ji tayi ana mata sallama wai ana kiranta a Parlor. Tayi niyyan barin yarinyar amma sai taji tsoron barin ta ita ka'dai, gani take kafin taje ta dawo Moopyn zata iya tafia ta barta saboda yadda zafin jikin ta yayi tsanani. Jikin ta na 6ari ta fito idanun ta duk sun fito sbd yawan damuwar da take ciki. Tana fitowa Rayyan bai ma bari ta gama 'karasowa ba ya fara fa'din" kin kuwa san aikin ki anya a gidan nan?" Da jin hakan tasan mene laifin ta hakan yasa taja ta tsaya tayi 'kasa da idanun ta tana addu'ar Allah yasa yayi mata uzuri. Cike da marairaita tace" Dan Allah kayi ha'kuri wallahi yarinya ta ce bata ....." Bai bari takai aya ba ya tare ta da 'daga mata hannu, dama yasan a kullum excuse dinta kenan. Ya gaji da wannan kalmar akoda yaushe, komai yarinyar ta yarinyar ta yarinyar ta, shi me ruwan sa da wani batun yarinyar ta, aiki aka 'dauke ta kuma ta yadda zata yi meyasa zata bar masa muhalli da kazanta kusan kwanaki uku yanzu, ko ina yayi 'kura babu kyan gani. Kici kicin yayi da fuska yace " Akan wata 'diyar ki ne bazaki je ki tsabtace min muhalli ba...?" Yatsa ya 'daga ya nuna mata yana daga tsayen yace.." Wallahi idan kk kuskura kk kaini bango bazaki ji dadin hukunci na ba, bana son iskanci da rainin wayo, kullum da an ta6a ki yarinya, yarinya, ke ko kunyar fa'di bakiji? akanki aka fara haihuwa ne ko me...?" Ammi ce da ke tsaye bakin 'kofar shigowa tayi saurin dakatar da shi da fa'din " Rayyaan...?" Ransa a matu'kar 6ace ya waigo jin muryar mahaifiyar sa da be yi zato ba...'dan lumshe idanu yayi sannan ya juya ya isa gareta cikin natsuwa. Handbag dake hannun ta ya kai hannu ya kar6a batare da ya yadda sun ha'de ido ba yace" Welcome Ammi". Duk yadda Ammi ke kallon sa da 'ko'karin son ganin 'kwayar idanun sa sam ya'ki amincewa...ko wlcm da yy mata ma 'kin amsawa tayi. Ganin hakan ya sashi fahimtar ranta ya 6aci ne da kalaman sa. Bai yi mamaki ba bcuz shi da kansa ba ze iya fa'din tsawon lokacin da take tsaye a wurin ba. Zaitun kam goge hawayen ta tayi da tun 'dazun ke gangaro mata tana sake ta6a fuskar Moopy dake rungune saman kafa'dar ta tana mai jin 'dumin jikin ta na sake ratsa nata jikin..tsananin tausayin Moopy ne ya cika mata zuciya banda wannan ba'kin suna da ake bi mata yarinya da shi, duk duniya zata iya ha'kuri da komai amma bazata ta6a iya jure zagin Moopy da sunan shege ba..domin ta fahimci duk kalaman sa jurwaye yai mata, bai fito fili ya fadi kalmar ba amma duk dai hakan yake nufi while ita 'diyar ta ba shegiya bace kamar yadda suke tunani. Hannun sa da hannun Ammi duk ri'ke da jakar amma ta'ki sake masa sai ma sake ha'de rai da tayi...a hankali ya 'dago nasa jajayen idanun ya zuba kan fuskar ta suka ha'de idanu.." am so sorry Ammi...ban sakewa". Yayi maganar ta yadda ita ka'dai dake kusa da shi ne zata iya jin sa. Sake masa jakar tayi da jin abinda ya fa'di sannan ta kawar da idanun ta daga gare shi. Murmushi ta sakar mata tana me takowa izuwa cikin parlorn idanun ta na kan Moopy da taga ya langa6e a jikin Zaitun. Zaitun murmushin 'karfin hali ta 'kakalo tana duban Ammi tace" Ammi barka da hanya.." " Yauwa Zaitun...fatan kuna lafiya". Ammi ta fa'di tana me 'ko'karin zama bisa kujera tare da cire gilashin idanun ta. Zaitun na amsa mata tana shirin kwantar da Moopy kan 'daya daga cikin kujerun domin kawo wa Ammi ruwa. Ammin ce tayi saurin fa'din bani ita nagan ta ne ma wata iri..." Bata tanka ba kawai ta juya bayan mikawa Ammin ita sakamakon jiyo takun haurawar Rayyan da tayi zuwa saman Ammi wanda ya kai handbag da 'dan trolley na kayan Ammin da aka shigo da shi ne sama. Kitchen ta wuce ta ha'dowa Ammi abubuwan sha masu sau'kin sanyi ta fito dai- dai lokacin da shima yake saukowa daga stairs 'din stairs ta gefen sa ta wuce batare da ta dubi ko inda yake ba ta isa gaban Ammi wanda tun ma kafin ta kai ga ajiye abin hannun ta Ammi dake rungume da Moopy ta jefa mata tambayar abinda ke damun yarinyar. Jin hakan ya sanya ta zama gefen Ammin tayi rau-rau da idanu gami da fa'din" Zazza6i ne Ammi, tun shekaran jiya yafara mata jikin sai dau zafi sosai kuma bata iya cin abinci kwata- kwata..." Tana kaiwa nan sai hawayen ta take ta rikewa ya 'karasa gangarowa... Rayyan dake tsaye ciki-ciki yayi tsaki ganin akan wata 'diyar ta ne take yiwa Ammi kuka..." who cares?" Waje yayi kawai ya ma fasa zama ko gaisuwa ba suyi da Ammin ba..bai ko sake kallon inda suke ba dan sosai ta bashi haushi yau din...ko Ammin ma bai tanka mata ba yayi wucewar sa ya bar part 'din kawai sai ta bishi da idanu har ya fice bata hana shi tafiya ba. " Kin bata magani ne toh?" Ammi ta jefa mata tambayar bayan ta 'dauke idanun ta daga hanyar da Rayyan ya bi. Kai ta 'daga mata alamar " Erh...sannan ta 'karasa da na bata panadol syrup ma amma jikin har yanzu da zafi". " Rayyan bai duba ta ba?" Ammi ta tambaya tana duban Zaitun. Yadda Zaitun tayi da fuska cike da mamakin jin furucin Ammin yasa Ammin cigaba da fa'din" Ai da kin fa'da masa ma da ko bai duba ta ba zai mika ku asbiti a duba ta sbd asbitin zai fi amma dubi yadda yarinya duk tayi laushi haka kina gani Zaitun...?" Hawayen ta share batare da furta komai ba kawai ta janyo tiren da ta kawo, glass cup ta tsayar ta cika shi da juice 'din exotic me sanyi ta mi'kawa Ammin gami da fa'din" kisha ruwa Ammi". Cikin zuciyar ta tace" Allah ya sawwake..salon ya 'karasamin yarinya a banza.." 'Dan yatsina fuska Ammi tayi tace" bani ruwa kawai Zaitun.." Maida shi ta ijiye sannan ta sake 'daga wani cup ta cika shi da ruwa ta mika mata. Ammi ko hutawa bata yi ba tace suje asbiti aduba Moopy. Ran Zaitun fari tas domin kuwa babu abinda yafi mata hakan farin ciki..lafiyar 'yar ta shine farin cikin ta a duniyar nan...amma koda yake hakan shine mura'din ta bata 'kaunar ya kasance ta hannun Rayyan ne. Zazza6in ya riga ya shiga jikin ta dan haka sai da aka basu gado aka 'daura mata drip sannan...Zaitun ce ta ro'ki Ammi da ta koma gida ta huta kawai ita ka'dai ma zata iya kulawa da ita. Ammi bata yi musu ba dan 'karfin hali kawai take sbd ganin yanayin yarinyar da kuma damuwa da ta fahimci ita Zaitun 'din ta shiga amma da kanta ma tasan tana bu'katar hutun. Da yake ma an tabbatar mata da cewa drip 'din be kawai kuma da zarar ya 'kare zasu koma gida so tasan ba wata matsala ba jimawa zasu yi ba. Sallama tayi mata da al'kawarin zata turo a maida su gida. 'Karfe biyar da 'yan mintina ya shigo part 'din har a lokacin fuskar sa a ha'de take..yana shigowa sai yaci karo da Ammi zaune a parlorn ta na sama, a hankali ya 'karaso gareta ya zauna ganin ita ka'daice babu wa'dancan tarkacen. Zama yayi gefen Ammin yana sakin ajiyan zuciyan numfashi ya jingina kansa da kafa'dun ta yana lumshe idanu. Murmushi Ammi tayi itam ta dube shi sannan tace" Ka daina fushi da ni 'din ne tun yanzu?" Idanu ya bu'de batare da ya tanka mata ba sai da yayi baya ya gyara zaman sa ya jingina da jikin kujrea sannan ya gaida ta gami da yi mata ya gajiyar tafiya...Ammi ta amsa cikin sakin fuska. Duban ta ya sake yi yana me baza kunnuwan sa sosai domin tsintan zuciyar sa yayi da son jin motsin su kamar yadda ya saba ji amma har yanzun shiru, kawar da wancan tunanin yayi yace da ita" Ammi da alamu yanzu kin daina son ganin farin ciki na gaba 'daya?" Ido ta zuba masa da alamar tambaya saman fuskar ta, duk dama tasan zancen ba zai wuce na batun dawowar ta bane..amma sai bata nuna masa cewa tasan abinda yake nufi ba...shiru tayi kawai tana sauraran sa yayin da Rayyan a hankali ya cigaba da magana cikin nuna rashin jinda'din sa 'karara yake fa'din" Ammi bana so wallahi...kullum idan kinyi tafiya baki son sanar dani in zaki dawo sam na rasa dalilin hakan...Ammi bazan ta6a yafewa kaina ba idan wani abu ya same ki batare da na sani ba kin sani, dan Allah Ammi ki tausaya min ki daina sanya zuciya ta cikin ru'dani, kuma da dawowar ki ma ko gaisuwan kirki bamu yi ba na dawo ban same ki gidan ba Ammi me yasa baki son hutu ne plss....". Ya 'karashe maganar fuskar sa cike da tsananin damuwa yana duban ta. Hannun sa ta kamo ta ri'ke cikin nata sannan da sanyin murya tace" Haba Rayyan yanzu akan hakan shine ka wani damu kanka?" " Dole in damu Ammi..a yanzu ke ka'dai nake da shi, ke ka'dai ce zan gani in ji da'di cikin zuciya ta kece ka'dai sanyin raina Ammi taya bazan damu da yanda kike nuna halin ko in kula agare ni ba". Idanu ta 'dan zaro tana duban sa tace" Rayyan...yanzu har wannan maganar ta kai ka ce ni ina nuna halin ko'in kula agare ka, idan ban kula da ku ba wa zan kula da shi Rayyan.. ?" " Nace aikin nan ma ki barshi Ammi kin 'ki ji na, kullum gani nake tamkar dukiya ta ta gaza 'dauke dukkan 'dawainiyar kine Ammi yasa kike aikin nan....." " Koka'dan ba dan ku'di nake aikin ba Rayyan...nasha fada mk hakan ko...?" " Toh ki barshi Ammi...dan Allah..ki zauna waje guda, ki zauna damu...". Don son kawar da wancan batun sai tayi saurin fa'din" Ba wannan ba yanzu..'dazun fa asbiti muka je da Zaitun yarinyar ta ba lafiya amma meyasa baku lura ba har abin ya shiga jikin yarinyar haka...?" Rai ya ha'de sosai yana kawar da kai yace" Bata fa'da ba ai shiyasa..." " Ta bani tausayi wallahi, an ma 'daura mata drip zuwa anjima ka'dan dan Allah kaje ka taho min da su gida". Ha'de rai yayi sosai bai ce da ita komai ba...tasan kuma ba zai ce 'din ba domin an ta6o 6angaren da baya so ne amma tasan koma me tace da shi Rayyan baya ta6a yi mata musu dan haka bata wani 'daga hankalin ta ba tasan for sure zai je shi. Shiru ya 'dan biyo sai itace ta sake tambayar sa Amrah fa? Ya take da jikin ta" Kai ya girgiza mata sannan yace" Tana gidan su tuntuni tace tana bukatar hutu ne kuma a gida..". " Amma dai ba wata matsala dai ko..". " Babu komai Ammi in akwai zata sanar da ni..". Idanun sa ya maida ya lumshe yana tunanin hanyar da ya kamata ya bi domin raba Ammin sa da wa'dannan halittun..sun dame shi sun takura shi..sam baya son ganin su yanzu, barin ma yarinyar da kullum ya ganta sai yaji bugun zuciya sam ya rasa dalili sai dai yasan hakan baya rasa nasaba da tsanar da yy mata ne tun lokacin da ya fahimci 'dakin Safaa 'din sa aka saukar da ita sannan kuma ya fahimci ga ta hanyar da aka samu yarinyar. 'Karfe hu'du da mintina arba'in ya bar wajen Ammi, bai ce da ita 'kala ba haka itama bata sake tuna masa batun zuwa asbitin ba kawai ta bishi da murmushi cikin zuciyar ta take yi masa kyakkyawar addu'ah...kaf cikin yaranta tafi 'kaunar Rayyan tana kuma 'kaunar farin cikin sa...sosai ta zurfafa tunani bayan fitar sa har zuwa lokacin da 'karan wayar ta ya katse mata tunanin. Idanun ta ta sau'ke kan fuskar wayar gami da sakin ajiyan numfashi.. Recieve taja gami da sada wayar da kunnan ta. Daga 'dayan 6angaren yace" Ammi sunan asbitin..?" Saurin sanar da shi tayi hadda room no. Sai dai har a lokacin shake taji muryar sa ba kamar yadda ta saba ba. Salmerh😘 [2/10/2022, 11:28 am] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* Wattpad@ Serlmerh-md 🅿️ *...44* .......Marwa da driver ya tafi 'daukowa a Zaria da har yasa Ammi tura Rayyan dauko Zaituna hispital tuni sun dawo gida, ko lokacin da Zaitun ta samu labarin dawowar Marwa ba 'karamin farin ciki tayi ba, ko ba komai Marwa mai kaunar ta ce kuma dole ta kaunace ta itama. Bazata manta yadda suka sha dramma da Rayyan ba kan dauko su daga asbitin dan cewa bazata biyo sa ba dakanta zata iya komawa gida, ma'aikaciyar da ke tare da su tana ta mamakin kalaman Zaitun har tana dan tausan ta da bata baki dan duk zaton ta iyalansa ne din musamman idan ta dubi 'yar kama dake tsakanin sa da Mufee amma Zaitun sam fuskar ta babu sauki. Fushi yayi ya fice da nufin yin tafiyar sa ya barta amma tuno cewa Ammi ce ta saka shi ya sanya shi kasa tafiya cikin motar sa ya koma ya zauna yana maida numfashin takaici. Bayan fitar sa ne ma'aikaciyar ta cigaba da tausan Zaitun tana nuna mata rashin dacewar taurin kai wa miji anan ne Zaitun ta fahimci me wannan ma'aikaciyar ke nufi a zabure ta mike tana zaro idanuwa. " Bafa komin sa bane mu ki rufa mana asiri dan Allah...ba matar sa bace ni..". Cike da mamaki ma'aikaciyar nan ke duban Zaitun. Sai kuma a hankali ta sauke idanun ta kan Mufee da ke kwance kan gadon asbitin fuskar ta da alamun tambaya. Sai kuma ta 'kara duban fuskar Zaitun. Tana so tayi tambaya amma sai ta ma rasa mai zata ce da Zaitun din. Cikin.zuciyar ta ta gama yanke cewa toh indai dagaske ita ba matar sa bace toh yarinyar nan fa..bata yadda za'a yi ace wannan gayen bai ha'da jini da yarinyar nan ba.." Ita kanta Zaitun ganin irin duban da ma'aikaciyar nan ke yiwa Mufee ya sa jikin ta yin sanyi. Ashe ba ita kadai bace ke ganin wannan abin, ashe ba ita kadai ke ganin 'yar kama tsakanin iyalan Ammi da Mufeen ta ba, musamman ma Rayyan da Raihana da Marwa ta ta6a nuna mata pic din ta cikin waya. Kafin suyi wani yunkuri sai gani sukayi an sake turo kofan, bai yi wata wata ba kawai da shigowar sa direct ga Mufee ya isa ya sa hannu ya dauke ta ya rungume a kirjin sa yayi waje da ita. Sam baya ta6a shayin daukan yarunyar sbd koda wani lokaci jikinta tsabtace yake sannan yakanji nutsuwa a zuciyar sa matukar ya kasance tare da yarinyar waje guda, rashin sanin takamamme abinda ke sashi hakan yake sashi birkicewa da san neman dalili har hakan ke sashi ya hantare ta a lokuta da dama. Kafin Zaitun tayi wani yunkuri sai gani tayi ya fice mata da yarinya batare da ya tanka ta ba, da gudu ta bishi abaya, shima da gangan ya yanke wannan wannan shawarar dan ya riga yasan lagon ta tun da jimawa. Sauran tarkacen su ma sai ma'aikaciyar nan ta biyo su da shi abaya tana murmushi da ganin wannan dramma ta su. Duk da bata san tsakanin su ba amma sosai taji sun matu'kar birgeta. Da zuwa mota ya shige da Mufee ya gyara zama, ya rufe motar yana shirin tadawa Zaitun ta karaso da gudu tana huci ta bude motan ta shige itama tana masa duban tuhuma amma bata iya tayi magana ba. Mika mata yarinyar yayi fuskar sa babu yabo babu fallasa. Daria ke cin sa ta ciki yadda yaga tayi zuru zuru amma bashi da hujjan darawa agaban Zaitun dan babu hakan tsakanin su sam. " Rike abarki ba cinye ta zanyi ba malama...". Da sauri ta kar6e ta tana gyara mata kwanciya ajikin ta zuwa lokacin jikin nata da sauki sosai. yYana shirin tada motar ma'aikaciyar nan ta iso da dan sassarfa...ta mika masa kayan su tana fadin. " Haba Daddy, haka ake yi? da ga dauko 'diyar ka shikenan sai a manta da uwa da kuma kayan amfani...?". Hannu yasa ya amshi kayan yana fa'din " Thanks" da 'yar murmushi saman fuskar sa ganin kamar bazai kara fadin komai bane ya sanya ta maida duban ta ga Zaitun ta cigaba.." Toh Madam Allah ya 'kara afuwa ya kuma tsare na gaba..". Da kai Zaitun ta bata amsa tana daga mata hannu. Har suka iso gida babu wanda ya jara tankawa kowa..daga compound kuma suka rabu kowa yayi hanyar sa. Bayan kwana biyu da dawowar Amrah sannan ta shigo gidan Ammi. Ta jima tare da Ammi kafin suka samu zama da Zaitun dan yi mata ya jikin Mufee da yake Ammi ta sanar da ita. Zaune a 'dakin Zaitun suke da Marwa suna 'yar hira, Marwa ke fadin" Gani nayi duk kin rame ga Mufeeda ma ba kamar yadda na santa ba duk tayi sanyi ashe rashin lafiya kuka yi..Ammi ke sanar dani wlh dazun" . " Mufee tayi dai amma ni lafiya ta kalau..". " Nima Ammi bata ce min da ke ba amma yadda na gankin tuni na karyata zuciyata...har ma fa kinfi yarinyar lalacewa". 'Yar daria Zaitun tayi tana sunkuyar da kai. Tasan rama dole ce dan yadda nutsuwa taso barinta da jinyar Mufeedan amma ita bata san ramar tata har ta kai wani matsayi da wani daban ma zai gane ba. Hira sosai suka cigaba da yi, Marwa ke bata labarin makaranta da yadda abubuwa ke tafia mata, a hankali hankali har labarin ya gangaro na cikin gida, nan take labarta mata yadda Sultan ya damu sosai da rashin haihuwar ta, tace kwata- kwata 1yr 3mnths ne fa da auren mu amma yadda Yah Sultan ya damu zaki 'dauka kamar mun shafe shekarune, bansan miye matsalar sa da haihuwa ba, abu Allah ke bada shi. Kai Zaitun ta jinjina tana fadin" HakaNe kam Marwa, kuma in anyi hakuri komai ai mai wucewa ne.." " Abinda nake ta so in fahimtar da shi kenan amma Yah Sultan da alamu he is not ready yet ya fahimci abubuwa, yanzu in na yadda Ammi tasan damuwar san nan Allah ita kanta hankalin ta tashi zaiyi...bata san damuwar kowa cikin mu gaba daya..". " Allah dai ya rufa asiri ya kawo rabon nan kusa mai albarka.." " Ameen Zaitun, Ameen Yah Rabbi...shine ma dai da ya kasa fahimta amma ai rayuwar ma gaba daya 'yar hakuri ce, musamman idan ya lura da Yah Rayyan, da yayi hakuri ba gashi ba cikin ikon Allah Allah ya sake azurta shi da wani cikin bayan wanda ya rasa abaya..." Cewar Marwa. Sai kuma tayi 'yar dariya tana duban Zaitun tace" Haka fa raywar nan take, wani na nema wani na gudun sa, wani kuma bai shirya kar6a bama Allah ke bashi, kamar dai ke ba gashi ya baki baby kyakkyawa ba a lokacin da nasan ke kanki baki shirya kar6anta ba, kamar ki bani kyautar ta wlh, hk kawai nake jin ta a zuciya ta...idan na zauna fa wani lokaci Allah tunanin ki ke zuwa raina ko lokacin da nake school, sai inga gaskia kamar anyi asarar tarbiya anan...." Kallon ta Zaitun tayi cike da mamaki tana duban ta. Ba wai yau tasan kalaman Marwa ba, haka take wani lokaci kalaman ta na mata kamanceceniya da ta Amrah, babu dadin ji sam amma da yake azahiri bata nuna musu 'kyama shiyasa bata fiya damuwa da munin kalaman nata ba. Balle wannan bata zaton ma da ita take yi...cigaba da magana Marwa tayi. " Allah wani lokaci ina mamaki, Zaitun kema 'yar 'karama da ke har kin iya kiyi cikin shege kuma ki haife....." Ta 'karasar da kya6e bakin ta amma still there is smile on her face. " Dan ma banga laifin ki ba, kamar kinsan cute baby zaki haifa shiyasa kika haife abarki" Shiru Zaitun tayi yau Marwa ta ta6o mata inda a rayuwa ta tsani jin sa, bata ta6a zaton Marwa zata iya furta hakan a gareta ba, iya zaman su da rashin dadin kalamanta da suke zuwa mata lokaci zuwa lokaci Marwa bata ta6a furta irin wannan maganar a gareta ba. Murmushi mai ciwo Zaitun tayi gami da tsurawa Mufee idanun ta da tuni sun kawo ruwa amma tayi kokarin danne su...bata san me yasamu Marwa yau din ba. " Wato ashe har a 'kauye ma ana tsula tsiya, sai dai sakamakon duk 'daya ne ai tunda gashi yanzu kema kin gani, ke da kika biyewa banzan yanzu kece aciki tunda gashi yanzu baki ga tsuntsu baki ga tarko, baki ga shi uban 'yar baki kuma ga iyayen ki kin rabu da kowa naki, shi kuwa yana can yana shanawan sa, in yana da sa'ar rayuwa ma ko 'yar sarkin garin sai kiga ya aura ya kuma zauna lami lafia, shiyasa fa ni sam ban yadda da ko wani banzan saurayi balle har a kaiga wannan shashancin...Yah Rayyan ma yaji labari ai kashe ni zaiyi ko kuma ya binne ni da raina...". Da kyar ta iya budan baki ta tare dogon sharhin da Marwa ta gingimo dan sosai ta gaji da jin su. Batare da ta dubi fuskar Marwa ba tace" Ke de kawai Marwa kiyi ta addu'a kawai kar kiyi alfahari, kiyi fatan Allah ya baki kariya, ya kuma rabaki da mummunan kaddara domin ita kaddara idan taka ce wlh ko kin binne kanki cikin 'kasane matukar mala'ikan mutuwa bai ziyarce ki ba toh kuwa binki zatayi kuma sai ta same ki addu'a kadai ke iya canza ta, ni kuma da kike gani ba wai kula na rasa ba da har yasa na haifi Mufeeda, ba tsayayye akaina na rasa ba, ba kuma rashin tarbiya ya sani samun Mufeeda ta ba, kaddara ta ce ita kuma na kar6eta, a kullum kuma fatan shine in kwatanta sama mata kula da tarbiya kwatankwaci koma fin wanda ni aka bani, kaddara ta Mufeeda ba yadda duk kike zato bane, 'diya ta 'yar halak ce Marwa, maraici ne kaddarar mu bayaga haka haka babu komai..." Ajiyar zuciya Marwa tayi tana mai jin kunyar kalamanta ga Zaitun da ta kasance tamkar kawa agareta...ita kanta bata san me ya shiga kanta ayau ba...sai yanzu kuma taga rashin kyautawar ta. " Gaskia ne Zaitun, Allah dai ya 'kara rufa mana asiri ya bamu ikon kar6an 'kaddarorin mu ya kuma bamu da sau'ki..kiyi ha'kuri kuma idan na 6ata ranki.." Ko tankawa Zaitun batai mata ba cikin ranta ta amsa da" Ameen". Yayin da Marwa itama cikin ranta take tunanin rashin kyautawar ta, yayin da wani 6arin zuciyar ta ke ganin tamkar rainin hankali kawai Zaitun ke son nuna mata baya ga haka ai yanayin su da tarihin su da ta bayar bai 6oye irin rayuwar su ba, gani na farko da su zaka fahimci inda matsalar take wato cikin shege tayi iyayen ta suka kore ta daga gidan su. Irin hakan ba ba'kon lamari bane a wannan 'kasar ba kuma ba'kon abu ba, bata san meyasa Zaitun ta ke wani 6oye lamarin ba, hala kunya take ji, koma menene ita dai haka kawai Allah ya jarrabce ta da kaunar su musamman ma 'diyar ta. " Nima fa wlh ina son baby, amma dai ban kai Yah Sultan ba gaskia kuma ma yadda nake jin ake fadin labarin wahalar haihuwa yasa nake dan ji tsoro..ki fa'damin ya kk ji lokacin da zaki haifi Moofy" Kallon ta Zaitun tayi da mamaki take kuma sai ta kawar da kanta...komai idan Marwa ta riga ta furta shi ya wuce kenan a wajenta, ba yau tasan wannan halayya tata ba, bata da riko bata da jan magana, so gani take tamkar kowa ma irinta ne, yaushe ma ta gama cire wancan batun da tai mata arai da har zata kara mata da wata kuma, gaba 'daya ji Zaitun tayi hirar tasu ta ishe ta ma yau din. Batacgama tunanin ba taji Marwa na tsakanin ta da Allah na cigaba da ro'kon ta. " Dan Allah ki bani labari inji Zaitun nifa kullum tsoro ke kamani idan Ya Sultan yayi batun haihuwar nan". Zaitun idanu ta lumshe a hankali hawayen ta suka gangaro da tun dazu take danne su..sake rungume Mufy tayi cikin jikin ta tace" Bazaki ta6a ganwa ba duk yadda zan yi miki bayani Marwa amma kowa da kalar tashi haihuwar, wasu na zuwa musu cikin sauki wasu ko akasin hakan, wata zata ce miki da wahala yayin da wata zata ce mk haihuwa babu wata wahala amma duk da hakan har gobe ba'a fasa haihuwar 'ya'ya ba, toh me ze sa kiji tsoro bacin ke baki ma san wani nau'i zaizo mk yayin haihuwar..ni dai abinda kawai na sani haihuwa akwai wahala Marwa babu sauki sam ba wani gayan hakan ba kuma da kaina na fahimta...kiyi fatan Allah ya baki yara masu albarka wa'danda wahalar haihuwar ki akan su bazai tafi abanza ba..." Cikin sanyin murya ta cigaba da fa'din" Shiyasa na ke son mufy na na kuma sadaukar da abubuwa da dama domin ta, dan ni ka'dai nasan wahala da kalubalen da suka faru yayin haihuwar ta, ni da na gani ni nasan ciwon hakan shiyasa nake iya 'kokari na wajen ganin na kwatan ta abinda nasan ko da tare take da mahaifin ta bazai ta6a bari ayi mata su ba wato cin zarafi da rashin samun kulawa, bansani ba ko haka ya kamata nayi ko kuma na gaza...". " Wallahi baki gaza ba, tab a hakan Zaitun, ke ko mu nan da muka jima muna muradin ganin jikoki a gidannan iya sadaukarwar da zamu iya yi kenan balle ke...aikin yi kokari...ki dube mu nan kiga mun rasa, mahaifin mu da babban yayan mu,mun rasa matan yayun mu da 'diyar sa amma hakan bai sa mun sadaukar da farin cikin mu ga wasun mu ba...hakan bai hana Ammin mu fita wajen aikin ta ba, bai hana mu walwala da cigaban al'amuran rayuwar mu ba, kuma a hakan mun isa muce mahaifiyar mu ta gaza akan mu ne wallahi bata gaza ba ta ko ina..balle ke da kika sha fa'di tashi cikin rayuwar ki, kika yi ta sadaukarwar da ke kanki baki san karshen su ba..kike fadin hakan...Zaitun kenan mamaki ma kika bani wallahi..". Da yamma lis da Marwa zata koma gidan ta Zaitun dauke da 'diyar ta suka fito dan yi mata rakiya, a daidai gaban part din Ammi suci karo da Rayyan shi kuma zai shiga. Cike da 'kauna Marwa ta gaida shi" Yah barka da yamma.." " Yauwa Marwa ya schl 'din..? kin kammala komai ko..?" " Erh Yayah.." " Toh Masha Allah..Allah ya bada sa'a ". " Ameen Yayah..". Yana cigaba da tafiya yace" Ammi fa..?" " Tana ciki ". " Ok" yace yana mai nufan mashigar da zata sadaka da babban Parlor. Da sauri Marwa ta waigo tana duban Zaitun..." Baki gaida Yah Rayyan ba.."! Shiru Zaitun tayi tana mai cigaba da tafiya. Da 'dan hanzari Marwa ta daidaita tafiyar su tana maimaita mata tambayar. Turus Zaitun taja ta tsaya tana duban ta.." Wai in rakiyar ne baki so ki sanar da ni mana kawai..". 'Yar dariya Marwa tayi " Ni kuma yaushe nace hakan abinda nake tambayar ki daban da batun rakiya...ko de wani abin yai mk kike 6oye min...?" Marwa ta 'karasa tana yawo da idanun ta kan fuskar Zaitun da son karantar yanayin ta amma ta gaza gano komai. Kai Zaitun ta girgiza. " a a kam babu komai, kawai dai shi in aka gaida shi baya amsawa ne shiyasa na daina...". Dariya Marwa tayi. " lallai, dan baki san waye Yah Rayyan ba ne yarinya, haka fa yake, ko nima haka yake min har gara yanzu amma da nima har bansan gaida shi baya magana, baya doguwar magana, ko ada da Safaa ka'dai yake doguwar magana kafin rasuwar ta bayan rasuwar ta kuma shike nan, sai ko Yah Sultan da Ammi amma yanzu Alhamdulillah ai ya canza, kawai ke ce da baki fahimce shi ba..amma yana amsawa ko da da kai ne ko ido..." Cike da mamaki Zaitun ta dube ta.." Da kai ko ido..?" " Yess..." " Toh sai kace ban da abinyi sai in tsaya gaida shi yana amsawa da ido da kai bacin ga ayyuka nan cunkus a 6angaren Ammi da suka isa in 6ata lokaci wajen yin su...?" Dariya sosai Marwa tayi tana fa'din..." Ke Yayana ne fa, my one nd only brother haka yake, shifa da kike gani ba kamar kowa yake ba, komin sa na daban ne..." Baki Zaitun ta kya6e tana kawar da kai.." Ke dai ke ganin hakan.." " Kema watarana zaki fahimta, baki san tarihin gidan mu ba ko, baki san asalin labarin ahalin Late Alhaji Sa'ad Muhammad Auta ba ko..?" Salmerh😘 [10/10/2022, 10:12 am] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* Wattpad@ Serlmerh-md 🅿️ *...45* ........" Baki sani ba shiyasa kike fadin haka...". " Toh Marwa taya zan sani bacin ba'a sanar da ni ba..?" " Hakane...amma Insha Allahu in na samu dama zan baki labarin gidan mu, labarin ahalin mu ma gaba daya". " Allah ya bada iko, nima zanso ji Marwa.." 'Yar daria Marwan tayi tace" Sai.na samu isaahshen lokaci". Da haka suka 'karasa rakiyar Marwan suka juyo gida. ***** Hutu sosai Zaitun ke samu a yanzu da yake Amrah bata gari tayi tafia, aikin ta ba wani mai yawa bane, Rayyan ma 6angaren Ammi yake zuwa cin abinci...shiyasa suke samun zama susha hirar su sosai duk ranar da Marwa ta samu shigowa. Kusan za'a iya cewa yanzu bata da wata matsala a gidan nan, babu abinda aka tsawwala mata a kansa. Ko Rayyan ma ba shiga sabgar ta yake ba, koda wani aikin ya kai ta 6angaren sa sai dai bisa kuskure abu yake hada su, kuma yawanci ma akan Mufeeda ne, ta jima da fahimtar cewa asali shi ba me shiga sabgar mutum bane kawai dai itan ma rashin fahimta ke sawa suke samin sa6ani. Rayuwar sa yake yi batare da ya shiga sabgar kowa ba haka shima baya bari a shiga tashi sabgar da garaje. Ko doguwar magana ba koda yaushe yinta ba sai ta kama, da Ammin sa ko 'yan uwan sa ne idan kaga yanayi, sai ko matar sa Amrah. Tun zuwan ta gidan ta fahimci halayyar sa wanda daga baya ya dan kara wasu abubuwa kadan sa6anin.na bayan har yake iya doguwar magama musamman idan akan su ne, ada tasan mugun sanyi ne da shi, baya da hayaniya...ko magana ze yi da 'kyar yake harha'dawa..(baki ji ba..) idan kina kusa da shi kika kuma ji ya furta hakan to ki san cewa da ke yake magana wataran kuma ( Ji mana) shine abinda yk furtawa ko kuma...(nace ba)...duk sanda hakan ta ha'da ku toh abinda ze biyo baya shima takaitacce ne..coffee, ruwa, ina Ammi? Amrah fa? Marwa ta shigo ne..? Sune abinda ze iya tambaya wurin mutum baya ga hk komin sa da kansa yake baya jira ya saurari kowa ko kuma jiran ayi masa. Baya da fa'da koka'dan, amma idan ka 'kure shi abin ba ze ma kyau ba, baya shiga sabgar da ba ta ha'da hul'da da shi ba...ita dai tsawon lokacin zaman ta a gidan su bata ta6a ganin yayi doguwar magana ta tsayin mintina ba...sai dai in akan su ne. Likita ne shi, kuma Barrister ne, CEO ne a companyn mahaifin sa da ya mutu ya bari...farko kafin girman sa Rayyan bashi da burin da ya wuce ya zama 'daya daga cikin manya manyan Alkalan 'kasar Nigeria tamkar dai mahaifiyar sa, burin.ya shahara ta fannin alkalanci, hakan yasa da gama secondary school 'dinsa a lokacin shekarun sa goma sha shida ne ya nemi cigaba da karatun sa fannin LAW amma hakan bai samu gare shi ba, mahaifiyar sa da kanta ta za6a masa karatu 6angaren likitanci, mahaifin sa ne yayi jagora wajen nema masa gurbin karatu a India kafin cikar sa shekara ashirin da ashirin da 'daya kuwa har ya kammala inda ya fito da sakamako mai matukar kyau, mahaifin sa be yi 'kasa a gwiwa ba wurin sake fa'da masa ilimin likitancin sa inda ya sake nema masa gurbin karatu sai dai wannan karon a anan 'kasa Nigeria yayi karatun..yana matashi mai 'karancin shekaru ya zam cikakken likita wanda ke da matu'kar kwazo da 'kwarewa bisa aikin sa. Rasuwar mahaifin sa ya sashi sha'awar dawo da muradin sa aikin Lawyer bai yi 'kasa a gwiwa ba kuwa ya fara aiwatar da 'kudurin sa, dai- dai lokacin da aka fara shirye shiryen auren sa gadan gadan. Matar sa ta kasance likita ce itama dan tare suka yi karatu a India da ita, bambancin kawai ita ta samu fita Indian ne ta hanyar scholarship yayin da shi kuma 6angaren sa ba hakan bane ba. Tare suke aiki da wani abokin sa mai suna Fawwaz kasancewar sa 'dan abokin mahaifin sa ne kuma asbitin ta mahaifin Fawwaz ne. Nan ya fara aiki kafin yazo ya 'dan ja baya yayin da kuma ya cigaba da gudanar da karatun sa a gefe guda. Ya ha'da karatun sa na aikin Lawyer yana da shekaru 29 da haihuwa ya kuma zama cikakken Lawyer kamar yadda yake da muradi...wanda sai lokacin da yake tsaka da karatun kafin Ammin sa tasan batun ta kuwa yi masa fa'da sosai amma ya kwantar da kai ya bata hakuri bai kuma sanar da ita dalilin karatun nasa ba. A time 'din da yake cigaba da karatun nasa already babban yayan su Kabeer ya cigaba da gudanar da kasuwancin mahaifin su kuma komai na tafia dai dai da yake dama shi harkar kasuwancin ya za6a kamar dai Sultan da shima yafi so ya karanci fannin kasuwancin. Amma wani dalili ya sanya Sultan tafiya training na soja da yake an tsaya masa bai yi wahalar samu ba sai dai tun ba'a yi nisa ba shima ya ajiye aikin suka cigaba da gudanar da kasuwancin su tare, duk da Sultan 'din ba sosai yake bawa harkar muhimmanci ba amma ahakan sosai Rayyan ke.jin dadin ganin sun hade kansu sun kula da komai nasu atare. Wani lokacin Rayyan is nice amma wani lokacin kam ba'a gane kansa Haka yake tamkar wani mai aljannu. Komai na Rayyan me kyau ne kama daga halittar sa zuwa tsarin rayuwar sa, tamkar shi da kansa yake za6awa kansa komai cikin rayuwa. Haka abubuwa suka cigaba da tafiya har zuwa wani 'dan lokaci. ***** " Haba 'diyar albarka, kibari in kama mk ko biyu ne mana, nima ba kin yi min ba ko so kike ki sake yi min wani?" kai ta daga sama alamar erh. " amma fa kan nawa ya fara ciwo Moopy baza'a barni in huta haka ba.."? Kafa'da Moopy ta no'ke Zaitun sai tayi murmushi toh shikenan zo kiyi min in kin gama sai in 'karasa miki naki kema". Tayi maganar tana gyara kwanciya gaban yarinyar Cikin ranta take ayyana" Moopy na rigimar ki yawa ne da ita wallahi". Haka suke shashancewa lokuta da dama wajen yin kitso, dan sam Moopy bata 'kaunar kitso a rayuwar ta har yanzun, amma idan Zaitun zata zauna gaban ta tace _yi min kitso_ toh shikenan ta gama siye mata zuciya an ringa jagwalgwala kan kenan, da haka da 'kyar da dabara take samu tayi mata nata kitson da a kullum baya haura guda hudu zuwa shida in yayi yawa takwas zuwa goma ne, sai dai ta kanyi 'ko'kari wajen ganin ta canza masa style wanda ze birge duk wanda ya kalla. Ammi kam da ta kasa ha'kuri sai da ta tambaye ta me yasa kitson Moopy kullum baya wuce haka dan indai ba Marwa ce ta sa akai mata kitso mai kyau ba toh kuwa kullum haka kan nata yake, ita kanta ma ba kitson take so ba balle ta damu da na 'diyar ta. Zaitun sai ta yi murmushi tace" Ammi ai hakan ma da 'kyar da dabara muke yi fa..yarinyar nan bata 'kaunar a ta6a mata kai sam..." " Ke kuma bakya iya yi mata abinda bata kauna ko?" Murmushin ta 'karayi tana fa'din" Ba haka bane fa Ammi..kawai dai kukan ne bana so...." " Haba Zaitun ai tsakanin ki da Moopy kam sai dai ni in bada labari ma wasu amma babu abinda ban sani ba...". " Hakane Ammi..". " Kamar dai wata 'diya ta da ta rasu shekarun baya, tun tana 'yar 'karama itama haka take bata 'kaunar ata6a mata kanta sa6anin 'yar uwar ta Marwa da ita kuma ko sau nawa zaki ware ki kitse mata bazata yi kuka ba, har suka girma haka suke da bambanci ta wannan 6angaren amma hakan bai sa daidai da rana guda na biye mata ba, har ciwo Safaa take 'kir'kira duk lokacin da ta tabbatar ranar zuwa Saloon 'din su ne, amma ahakan zan tura ta wani lokaci ko bayan anyi kitson sai tayi zazza6i, Yayan su ne ya roki adaina yi mata kawai ana gyara kan sbd bata so amma dan tani ahakan zata saba...ai mace sai da ado, mace 'yar kwalliya ce kuma hakan bai samuwa sai da gyara". " Hakane Ammi, Allah ya ji kan su da Rahama, Allah ya gafartawa dukkan musulmi..". " Ameen Yah Rabbir raheem..Amin 'diya ta...". Cewar Ammi sannan ta cigaba da fadin" Ni inaso inga anyiwa Mufeeda kitso irin me kyau da ake yiwa yaran nan idan babu damuwa, kinga akwai wajen da Marwa ke kaita sai a kaita ayi mata mai kyau acan..." Ido Zaitun ta zaro tana duban Ammi... Itama kallon ta tayi suka ha'da idanu take sai ta yi kasa da idanun ta kan fuskar Moopy ta sau'ke idanun, take taji wani tausayi, 'kauna da kuma soyayyar ta ya 'kara kama ta. A nutse ta sake duban Ammi ta 'dan shafa goshin ta sannan ta bu'di baki tace" Ammi kuka fa take yi sosai idan an kaita, bazata ta6a yadda ba wancan ma da kyar aka yishi, kuma, kuma..ni..." Sai tayi shiru tayi 'kasa da kanta. Duk abinda take yi Ammin na kallon ta kuma tsab ta karanci yanayin da take ciki, ganin ta kasa furta abinda ke ranta ne yasa ta 'karasar mata da fadin" ....ke kuma bazaki iya juran ganin kukan ta ba ko?" Murmushi tayi tayi kasa sosai da kanta tana sake rungumar Moopy a jiki. Ammi ma murmushin tayi tace" gashi tun ba'ayi nisa ba ai na kama ki". Nasan ai wannan dalilin yasa tun farko baki saba mata da kitson ba dan bata so kema sai baki bada hankali wajen yi mata ba". 'Yar dariya tayi me birgewa wanda take jimawa kafin tayi irin sa, sai ma in taga farin cikin Moopy kafin kaga tayi irin wannan dariyar, Ammi kanta sai da tayi murumushi ganin dariyar Zaitoon din. Tana dariyar tace " yau dai Ammi nima zan daure raina ai mata kitson nan Allah yasa kar yayi mata zafi.." Insha Allah ba zai mata ba Zaitoon". "Amma Ammi ai ba yau ba kam ko...kinga yau akayi wannan..." kar ki damu sai nextweek idan an ware wannan za ai mata..." " shikenan Ammi Allah ya nuna mana". Dama tun bayan tafiyar su Marwa ba' a sake yi mata kitso me kyau ba. Da yammacin ranar Rayyan ya shigo 6angaren Ammi, kasantuwar ya 'kira wayar ta baya tafiya sai da ya 'kira ta landline dake Bedroom 'dinta kafin ya same ta nan ta sanar da shi dama tana so suyi magana yazo ya tana jiran sa. Shima yace yunwa tace ba matsala yazo yanzu ma ake ha'da abincin. Ko da ya shigo bai tarar da kowa palorn saman Ammin ba, dan haka sai ya koma ya mi'ke kan 3sitter yasan Ammin zata fito yunwa da gajiya duk bi sun kashe masa jiki duk yau bai samu lokaci yasa komai a cikin sa ba. Sabo da yiwa Zaitun kitso da Moopy tayi ne yasa da ta ga mutum kwance kuma gashin sa luf luf kawai ta nufi wajen sa, hannun ta ta cusa cikin gashin kansa shima tana jagwalgwalawa tamkar dai yadda take yiwa Zaitun da sunan kitso. Cikin 'dan baccin da ya fara daukan sa yaji ana masa 'kaikaiyi akansa, bai bu'de ido ba ya tsaya idanun sa a lumshe yana sauraran abinda ake yi masa, sosai yake jin natsuwa na shigan sa duk da bai san gwanin da ke yi masa hakan ba zuciyar sa fal da mamaki, a hankali ya bu'de lumsassun idanun sa batare da ya waigo ba, domin tun kafin ya waigo din ya fahimci hannun waye akan nasa haka kawai sai yayi murmushi. _He wish 'diyar sa ce wannan halittar_ Karo na farko cikin rayuwar sa da wannan tunanin ya 'darsu masa a zuci. 'Dan waigowa yayi ka'dan ya sauke idanun sa akan fuskar Moopy kamar dai yadda yayi zato ita 'din ce. Wani bugu zuciyar sa tayi da ganin fuskar yarinyar, ido ya tsura mata yana jin zuciyar sa na tsananin bugu da 'karfi, bai san me yasa shi bugun zuciyar ba kuma bai kuma san matakin dauka kan hakan ba. Moopy kam da hankalin ta ya 'dauku ga kitson bama tasan yana kallon ta ba bata kuma san kan waye take wasa da shi 'din ba har a lokacin. Sai da ya gama 'karewa fuskar ta kallo sannan ya sake juuawa da kyau ya koma rub da ciki, fuskar sa ya tallafe cikin tafukan hannun sa sai ya kasance gaba daya hankali da idanuwan sa na gareta ne. Kallon kallo suka tsaya yi da Moopy, tamkar masu karantan juna. Lokaci guda kuma ta 'dan ja baya tamkar wacce ta tuno wani abu, da sauri take matsawa baya sbd tuno waye shi, tsoron shi take ji sosai, kwana biyu da bata ganin sa yasa ta 'dan mance shi kadan, da sauri ta fara yin baya baya, hakan sam be yi mata ba dan gani take kamar zai kamata ta bayan ta hakan ya sanya kawai ta sanya kuka tana nufar hanyar da tasan ta baro Zaitoon. Zaitun na tsaka da gugan kayan Ammi kawai taji muryar gudan jinin ta na 'kiran _Mammy_ cikin kuka ai da sauri ta ajiye iron 'din ta fito da hanzari tama mance da cewar kan mayafi tabar iron 'din...tana isowa bakin kofar taci karo da ita duk ta rikice, sama da 'daga ta idanun ta na kan sa da yake Zaune dafe da kansa sbd hayaniyan kukan Moopy da ya cika masa kunne yake neman rabashi da nutsuwar sa. Wani kallo na mugun tsana, haushi da takaici Zaitun ke binsa da shi tana kwantar da kan Moopyn kan 'kirjin ta. Sam ta kasa dauke idanun ta akansa, ga kuma takaicin rashin sanin abinda yayi ma yarinyar da ya addabi zuciyar ta. Tana jin da ace tana da dama da babu abinda zai hana ta ramawa Moopy duk muguntar da yk yi mata. Dadin da'dawa ma ga yarinyar ta kasa yin shiru, dama 'dan banzan zuciya gareta da idan ta riga ta fara kuka to lallashin ta da kyar take iya yi. Tana tsaye a wurin Ammi ta fito jin 'karan kukan Moopyn, da zuwan ta kuwa kallo 'daya tayi musu ta fahimci me yake faruwa dan kuwa har a lokacin idanun Zaitun na kansa ne tana yi masa mugun kallo yayin da shi kuma ke dafe da kansa da duk hannuwan sa biyu be masan da zuwan Ammi wurin ba. 'Karamin tsaki ya ja ya mi'ke ya nufi hanyar barin palorn, ganin hakan yasa Ammi saurin dakatar da shi da tambayar" Me ka yiwa yarinyar nan Muhammad?" Cak ya tsaya da jin furucin Ammin amma bai waigo ba. " Me Ammi take tunanin.zan mata..?" Ya tambayi zuciyar sa. Sai da Ammi ta sake maimaita tambayar tata da alamun 6acin rai sosai cikin muryar ta wanda ya bayyana har kan fuskar ta kafin ya waigo, kan zaitun ya fara sau'ke idanun sa kana yayi hanzarin maida su kan fuskar Ammi, sosai yayi kici- kicin da fuska, shi kansa ransa 6ace yake yanzu ganin yarinya 'karama na neman ha'da sa da mahaifiyar sa, kan abinda ko hauka yake bazai iya aikatawa ba... ya riga yasan duk zargin sa suke da dukan yarinyar while shi ko da wasa be ga abin bugu a wajen ta ba me ma tayi masa da har zai 'daga hannu yi buge ta...ko wancan ma daya ta6a faruwa bisa kuskure ne amma ba niyyar sa ya bige ta ba. Ha'da idanu da suka yi da Ammin ya fahimci tsananin bacin rai da ta shiga. A hankali ya lumshe idanun sa sannan ya 'daga 'kafafu ya yi waje be ko sake kallon inda suke ba. Zuwa lokacin ma Moopy tayi shiru jikin Zaitun sai ajiyan zuciya da take saukewa. Ammi ma sassautawa ranta tayi tunda ta ha'da idanu da Rayyan din...domin kuwa ita tasan abinda ta haifa, tasan duk rashin hankalin Rayyan ba zai iya 'daga hannu ya bigi Mufeeda ba. Hakan yasa ta juya ga Zaitun tace ba mamaki tsorata tayi da ganin sa shiyasa take kuka kinsan ba wani sabo ne tsakanin su ba...mi'ka min ita ki duba aikin da kike yi, ina jiyo 'kauri." Ammi ta 'karashe maganar da mika hannuwa dan kar6ar Zaitun 'din. Mi'ka mata yarinyar Zaitun tayi tare da komawa 'dakin nan taga 6arnar da tafka, ashe bata tsaida iron din ba kan mayafin Ammi ta barshi gashi ya kwashe mayafin ya kone sa. Cike da firgici take kallon wajen tana mamakin yadda ma akayi ta manta. Ami dake bayan ta ma kallon mayafin tayi sai kuma ta dubi Moopy dake hannun na tana murmushi irin nasu na manya. Juyawa tayi da niyyar fita bata yi niyyan tankawa ba. Jin motsin ta ne yasa ta waigo da wuri ganin.Ammi yasa ta mikewa da hanzari. Tasan ta riga ta gani. " Ammi..." Tace sai kuma ta kasa 'karasawa, tasan bata kyauta mata ba. " Ammi dan Allah kiyi hakuri..." Wannan karan tayi kokarin furtawa " Kar ki damu..." Ammi ta bata amsa batare da ta waigo ba, ta kuma cigaba da tafiya har ta bar 'dakin. Wata nannauyar ajiyar zuciya Zaitoon ta sauke, ganin alamun Ammi bata damu ba duk da yake tsaddaden mayafi ta kone mata, shiyasa har kullum darajar Ammin kara hauhawa yake mata a zuciyar ta. Gaba 'daya laifin kacokam ta tattara sa akan Rayyan tamkar shi da hannun sa ya 'kone mayafin. Aikin ta ta cigaba da yi tana jin 'kwalla na ganagaro mata amma bata iya ta share sa ba. Har sai yaushe mutane zasu fahimci wace Moopy ne, har su tausayawa maraicin ta, su tausaya wa rayuwar ta su daina yi mata mugunta.... Wani sabuwar tsanar Rayyan take ji na taso mata, meyasa ya za6e su ne, meyasa ya za6i ya maida su abokan gaban sa bayan yasan tako ina yayi musu zarra ya musu fintinkau, me suka tsone masa a duniyan nan...ko zaman gidan ne baya kauna suke yi..? Tambayoyi ne cunkus cikin ranta amma bata da me amsa mata su. Haka rayuwar su ta cigaba da tafiya har zuwa lokacin da Amrah ta dawo. Ita kam gaba 'daya sai a hankali ta ko ina bata da sauki, ita kanta bata san meyasa ta tsani Zaitun ba, balle ita kanta Zaitoon din ta sani, sai da bari aranata cewar kawai rashin jituwa ne. Komai tayi laifi ne a wajen Amrah, abu ka'dan sai tace Zaitoon ta raina ta ne shiyasa take yi mata rashin kunya, ko kuma tace Ammi ce ta daure mata gindi yasa har ta raina ta. Salmerh😘 [10/10/2022, 10:12 am] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Wattpad@* _Serlmerh-md_ 🅿️ *...46* ......Duk yadda Zaitoon ke kokarin kauce mata Amrah dole sai ta shiga sabgar ta, sau tari takan gama aikin ta tayi mopping ta tsabtace ko'ina amma Amrah sai tace sam bai yi ba sai ta sake, ko kuma idan Zaitoon ta saka freshner Amrah tace bata son kamshin sa ta san yadda zata yi ta raba mata daki da warin freshner din dan iskanci wai wari bacin Rayyan da kansa ke siyo su masu shegen kamshin da ko ita kanta Zaitoon suna birgeta haka Amrah zata ce turaren wuta take so, sosai take gara Zaitoon da wannan cikin nata da ya 'dan fara bayyana kansa, ga Moopy ma bata tsira a wajen ta duk da 'karantar yarinyar sam Amrah bata gani. Akwai ranar da Amrah ta kai ta bango akan Moopy ranar ne ta nuna mata cewa ba zata iya 'daukan wasu maganganun akan Moopy ba, Amrah na cikin sanba'do zagi kawai taji sau'kan mari lafiyayye saman kuncin ta...zaro idanu tayi ta dafe gurin, nuna mufeeda tayi tace" akan wannan banzan wai kk mare ni?" Sau'kan wani marin taji abinki da ba'a saba ba har 'kasa ta dur'kushe tuni hawaye ya fara fito mata. Kasa magana tayi dan har kunnuwan ta ji take tamkar sun bar jikin ta banda ra'da'di babu abinda take ji ilahirin jikin ta duk yabi jini zafin marin. Nuna ta da yatsa Zaitun tayi tace" Kashedi na dake na 'karshe kenan akan yarinya ta, wlh idan kika sake aibanta min yarinya sai na sa6a miki kamannin ki..zan jure komai amma banda wulan'kanta min yarinya...ke kika haifa min ita ne ko kuwa kinsan matsayin ta gare ni...akan Mufeeda na 'kwammaci na rabu da kowa nawa dan haka bana tsoron kowa akan ta, kuma bazan laumci cin fuska a wajen koma waye ba, alkwari na 'daukar wa kaina cewar zan kare mata mutunci da darajar ta akanki kuma bazan karya alkwari na ba, in kin so ki sa a kore ni..." Wani 'kwarin gwiwa Amrah taji dan ta sosa mata inda yake mata kaikayi, a zafafe ta mi'ke da jajayen idanu tace" Ke har kina gani shegu na da wata daraja ne da har zaki kare mata? 'yar zinar? Dangin fasikai...wallahi kin ji kunya da ko kunyar Allah bakiji balle na mutane kk furta irin wannan magangun..." bata kai 'karshe ba Zaitun ta nuna ta yatsa tace" Kar ki sake ai banta min 'ya.." " An aibanta miki 'yar me zakiyi?" " Bazan yi komai ba, amma nasan duk wanda ya 'kira min 'diya ta da sunan 'yar zina to shine babban 'dan zinan.." Jin haka yasa Amrah ta manta da zafin marin ta ta taho da sauri wajenta wuyan rigar ta takama tana fa'din" Ni kike so kice wa 'yar zina kome..ke har kin isa kina matsayin 'yar aiki na kice zaki min wannan iskancin, wallahi yau ko ubanki da ya 'daure miki gindi kika je kika yo cikin shege be isa ya hanani korar ki daga gidan nan ba..." " Sakar ni to" tayi maganan tana bin hannun Amrah da kallo.. a hargitse Amrah ta furta " Baza'a sake ba me zakiyi...?" Saukan mari kawai ta sake ji saman fuskar ta da ya sa ta sakin rigar Zaitun tayi baya...matsawa Zaitun ta sake yi kusa da ita dan ta riga ta hassala..amma kafin ta 'karasa gaban Amrah ta ganshi kamar daga sama agaban ta, daga shi sai dogon wando ba'ki da alamu bacci yake yi hayaniyar su ta tashe shi. Amrah na ganin sa ta dafe ciki ta saki wani sautin wani wahalallen kuka tana fadin " cikina, wayyo cikina zata kashe ni.." ta durkushe a wajen dafe da cikin ta. Da sauri Rayyan ya maida duban sa gareta cike da mamaki ya nufe ta yana tallafo ta zuwa jikin sa tare da cusa hannun sa 'daya cikin rigar ta yana shafo cikin nata yake mata sannu cike da kulawa. Sai da ya kaita kan kujerar ya zaunar da ita da kyau gami da daidaita mata zaman yadda zata fi jin dadi kafin ya dawo da duban sa ga Zaitoon da tuni tayi mutuwar tsaye jin sharrin da Amrah ta kirkiro. Ganin irin kallon da yake bin ta da shi ne ya sanya ta kawar da kanta gefe zuciyar ta na harbawa...kan Moopy dake ma'kale da 'kafafun ta ya sau'ke idanun sa. Kallon rainin hankali ya 'dago yayi mata bata damu ba ta 'dago Moopy saman jikin ta...tana niyyan juyawa ta tsinkayi muryar sa yana fa'din" 'Ya'ya da dukiya halaka ne ga 'yan Adam, ban tabbatar ba sai yanzu da na ga misali akanki, Matata kk duka akan 'diyar ki? 'yar kin ma mara asali mara gata irin wannan..? Mata ta dake 'dauke da cikin gudan jini na..?" Waigowa tayi bata kalle shi ba idanun ta ta sau'ke akan Amrah dake kuka harda sheshsheka..da gudu itama hawayen ta suka gangaro...wannan kalmar ta ishe ta haka, wace iriyar rayuwa ce wannan da son kai ya yiwa kowa 'kawanya? duk babu 'kaunar Moopy cikin zu'katan su, duk zuciyoyin su babu gaskiya, duk gidan nan Ammi ka'dai ke son Moopy sai Marwa in basu ba kowa tsana yake nuna mata, dan haka a yau ba sai gobe ba dole zata bar gidan nan, zata bar musu gidan su taje inda zata samawa Moopy farin ciki da walwala. " Bakya tunanin irin 'daurin da zan iya miki dalilin dakar min iyali da kika yi acikin gidana, baki tunanin hanyar halaka kika dauko wa kanki bayan na baya da kika aikata akan 'diyar ki...Baki tunanin zan iya halakaki idan wani abu ya samu cikin dake jikin ta sanadin ki? iyali nace fa Amrah ko kin mance ne..?" Duban inda Amrah take tayi suka sake ha'da idanu, bata kalle shi ba kamar yadda koka'dan bata ji tsoron sa ba ko tsoron abinda zai iya biyo baya ba...cikin maganganun sa abu guda kawai tafi ri'kewa kuma shine yake ta mata yawo a 'kwa'kwalwa har ya dasa ayar maganar sa. " 'Diya ta ba shegiya bace ku sani, kuma nasan duk abinda ya faru dani kaddara ce kowa kuma baifi karfin ta faru gareshi ba...". Daga hakan bata ce da shi komai ba kawai ta juya tayi gaba abinta. Shi kam rintse idanu yayi yana jin zuciyar sa na 'daukan zafi, shifa ba nufin sa ya zagi 'diyar ta ba, sam bai yi niyyan zagin ta ko 'yar ta ba amma haushin ganin dukan da tayiwa Amrah ne ya 'dan ta6a ransa duk da yasan ba cikin Amrah ta buga ba kamar yadda idanun sa suka gane masa yasan kawai Amrah tayi hakan ne sbdcwata manufa kuma ko maganar da yayin yayi ne kawai dan Amrah taji dadi aranta, ko ba komai Amrah iyalin sa ne kuma shi ke da alhakin kare dukkan hakkokin ta... " Wallahi Baby ka kora ta agidan nan mari na fa tayi dan kawai nace da 'yar ta shegiya kuma ai shegiyar ce Baby ba 'karya nayi ba". Muryar Amrah ya tsinkaya tana fa'din hakan. ko juyowa ya kalle ta bai yi ba kawai ya koma 'dakin sa, yasan itama Amrahn da laifin ta, ta fiye shiga sbgar su yana lura da ita batun yau ba kawai magana ce bai ta6a yi mata kan hakan ba bai kuma san dalilin shirun sa ba kamar yadda bai san matsayin abinda Amrahn ke aikatawa cikin ransa ba musamman idan yayi duba da rashin jituwar da ke tsakanin Zaitoon din da shi sai ya rasa shin abinda Amrahn ke yi da'da'da masa yake yi ko kuma ba'kanta masa sam ya rasa takamammiyar amsa shiyasa bai ta6a tankawa ba. Amma lokuta da dama ya kanji babu dadi idan yaga ko jin faruwar wani abu tsakanin ta Amrah, sai yaji yafi so shi da kansa yayi ta ba'kanta musu amma kar wani ya kwatanta irin hakan sai shi ka'dai, atimes kuma sai yaji bai damu ba koda an ci zarafin nasu. Ita kam Amrah zama tayi nan kan kujera tana 'karasa kukan ta da bata 'karasa ba cike da takaici. Ba haka ta so ba, taso da Rayyan ya fito ya rama mata dukan ta...amma be yi hakan ba, dama can ta san shi ba gwanin bugun mutum bane especially mace baya so yaga ana cin zarafin 'ya mace amma ai wannan kamar cin zarafin ta akayi itama kuma yayi biris da al'amarin. Wayar ta 'dauko tana kuka ta irgawa mahaifiyar ta tas hadda 'kari ma, da 'kyar ta lallashe ta tayi shiru da alkwarin zata 'kira Ammin nasu idan ta dawo ma zata zo da kanta su yi magana. Tace bazai yiwu yar aiki ta samu wannan babbar damar ba bacin asali 'diyar ta da gatanta, ba gidan aure ne ya bata gata ba balle a dinga karya mata darajar ta, baya ga hakama ciki take dauke da shi ita da yakamata a ririta kuma ace itace zata zam abin banza bazai yiyu ba ..." Shin ko Ammi zata amince da hukuncin mahaifiyar Amrah...? Salmerh😘 [11/10/2022, 6:10 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Wattpad@* _Serlmerh-md_ 🅿️ *...47* .......Koda Mummyn Amrah ta yiwa Ammi magana, Ammi bata ce da ita komai ba illah hakuri da ta bata, sai dai jin tana cewa mai aiki- mai aiki cikin maganar ta yasa Ammin tabbatar mata da cewar yarinyar ba wai mai aiki ce kawai kamar kowa ba, tace 'yantacciya ce a wurin ta tamkar 'diyar cikin ta take kawai ta bari ne tana taimakawa Amrah da wasu ayyukan na cikin gida dan haka itama Amrah bata da damar da zata ringa wulakanta tata son ranta. Haushi sosai mahaifiyar Amrah taji hakan yasa ta kashe wayar batare da ta sake tankawa Ammi ba. Bayan kwana biyu da faruwar wannan lamarin babu wani abu da ya sake shiga tsakanin ta da Amrah, hasalima daina ganin ta tayi, ko ta shigo aikin ta basu haduwa da Amrah har ta kammala ta bar sashen ita kamma sai tafi sakewa da hakan, saboda ba kaunar tashin hankalin nan take yi ba sam a dole take biye mata...baya ga haka ma Ammi ta sake bata hakuri gami da garga'dan ta kan biyewa Amrahn, ta kuma fahimci Ammi, musamman sbd cikin da suke matukar tattali da Amrahn ke 'dauke dashi, kusan kaf ahalin ta lura duk wata kauna da soyayyar su kan cikin suka mika ta, ita kuwa bazata so tayi ta mata musu rai a banza ba, dan ta lura indai akam cikin nan ne toh kuwa ba sauki zata samu daga gare su ba duk kuwa da irin 'daga mata 'kafa da Ammi take bazata iya kawar da kai kan gudan jinin jikan ta da suke daukin zuwan sa duniya ba...hakan yasa ta yanke shawarar kiyaye komai da zai iya hada ta da Amrah kuma Alhamdulillah itama Amrah kamar tasan nufin ta sai ta ja baya. Bayan kwanaki biyu... Zaitun na kitchen tana ha'da musu abincin su na dinner ta fara jiyo hayaniyar Amrah, da sauri ta waiga ta ga Moopy na nan kitchen tana wasan ta kasan ta tiles, hakan ya tabbatar mata da cewa ba da ita take yi ba. Ajiyar zuciya ta sauke gami da hamdala a fili. Ka'dan da ka'dan ta fara jiyo hayaniyan na kusanto wa kitchen inda take. Bata fahimci komai cikin maganar Amrah kasantuwar amsa kuwwa da maganar ke yi kuma ba cikin natsuwa Amrah ke maganar ba. Har sai da Amrah ta iso bakin kitchen tana masifar wai Zaitoon ta fito mata da sarkar ta data sace mata in ba haka ba wallahi sai ta sa an mata 'daurin da babu uban da ya isa fitar da ita. Sosai Zaitun tayi mamaki jin wai ita Amrah ke tuhuma da sata satan ma na sarkar Zinare ita kam me zata yi da wani abu wai shi sarka a rayuwar ta. Duk kuma yadda taso fahimtar da Amrah abin ya faskara kokadan bata bata damar hakan ba sai ma sake azalzalar ta da take tana kumfar baki. Abin takaici ko da mai gidan yaji hayaniyar su ya sakko ma ko tankawa Amrah bai yi ba balle ya tsawatar mata kan sharrin da take shirin kullawa Zaitun. Kokarin ficewa ma yayi daga 6angaren Amrah ce tayi saurin dakatar da shi da fadin" Baby kace ta fito min da sarka ta in ba haka ba wlh sai na sa an 'daure ta..." Ta karashe maganar tana wani jijjiga kamar wata jaruma. Kallon Amrah yayi cikin ido sosai, bai ga alamun gaskia ko 'yar ka'dan tattare da ita ba, yasan ba mmk huce takaicin ta yasa ta biyowa ta wannan sigar...ba yau yasan Amrah ba, ba tun yau ya karanci yanayin ta ba. Ga Zaitun ya maida duban sa da take tsaye wuri wuri da idanu waje, kallo 'daya yai mata ya 'dauke kansa ganin yadda idanun ta suka cicciko..." Ki bata abinta in ke kika 'dauka pls bana son wannan hayaniyar...". Tamkar zatayi aman wuta haka take jin zuciyar ta, wai yau ita Zaitun Ahmad Kyari ake tuhuma da sata? sharrin sata fa..? Shin shi talaucin hauka ne? Ko kuwa rashin galihu ne haukar? Koko rashin gata kawai yasa akai mata wannan sharrin? Saboda rasa abin fa'da kawai sai ta ringa bin su da kallo 'daya bayan 'daya hawayen ma ya kasa gangarowa. Ba abinda yafi tsaya mata arai irin furucin Rayyan, a tunanin ta shi din yafi Amrah hankali, a tunanin ta zai dakatar da 'kudurin Amrah ne, amma sa6anin hakan sai ma biye mata da yayi..kenan sun taru sun ha'de mata baki ne, ko dai dama bakin su 'daya, ba mamaki tare suka yi shawarar hakan dan su tozarta ta dama tasan duk ba kaunar zaman ta gidan suke ba...baya ga haka meyasa daga fadin magana har ya hau ya yadda. M Toh ita a zaman tan nan idan ta saci sar'ka mai zata yi da shi? ina zata kai sar'ka cikin duniyar nan, in satan zata yi meyasa bata yi tun abaya ba sai yanzu..? Meyasa basa ta6a fahimtar ne wai?, kan abubuwa da dama sai sun 'kalubalance ta?. Shin zama da su dole ne ko kuwa 'daure ta akayi tare da su. Amrah da kanta ta daga waya ta 'kira Ammi ta sanar da ita abinda ke faruwa tana cika tana batsewa. Allah ma yasa Ammin na gari, cikin lokaci 'kan'kani ta bayyana 6angaren Rayyan cikin tashin hankali, rabon ta 6angaren Amrah har ta mance. " Wai me yake faruwa ne...?" Ammi da shigowar ta kenan ta jefa musu tambayar tana duban Rayyan dake zaune bisa kujera yana duban dramar tasu dan tun dazun ya rasa me ma zai ce ne. 'Yar takaitacciyar kalma zata raba husumar amma yasan Amrah zata birkice masa ne idan yayi hakan, dalili kenan da ya sanya shi komawa gefe yana duban su dan ganin karshen yadda abin zai kaya, kuma ma ko ba komai yau zai morewa kallon yadda Zaitun zata shiga taitayin ta duk da ma ya fahimci tuni tayi sanyi tun farkon maganar. Gira ya dage sama yana fadin" haka na gansu Ammi wai Sar'kar Amrah aka sace...". " Shine sai aka yi yaya...?" Ta sake tambaya tana ha'de ranta gami da dawo da duban ta ga Amrah. " Kar ace min zargin Zaitun ake da satan sarkar...?" Shiru suka yi dukkan su yayin da Zaitun tayi 'kasa da idanun ta Amrah kuwa kawar da kai tayi tana wani girgiza jiki. " Tambayar ku nake fa kun min shiru". Ta sake fadi a dan zafafe. Amrah ce ta bu'di cike da zafin kai tace.." ai wacce tayi satan ta san kanta in dai ba goye mata baya za'a yi ba kam..." Ta 'karasa maganar tana kyabe baki gami da 'yan harare-harare. Rayyan daga inda yake ya tsura mata idanu sosai yayi mamakin da yadda ta amsa maganar Ammi...bai ta6a ganin hakan da idanun sa ba sai yanzu. Duk wasu abubuwa da Amrahn ke yi na kaucewa mu'amala tsakanin ta da Ammi yana sane amma wannan ba'kone a gare shi. Tsaye ya mi'ke ya taho kusa da su da nufin kashe mata warning kan mahaifiyar sa. Daidai lokacin da Ammi.ke sake fa'din..." Amrah ban san rigima fa, kin duba sarkar taki da kyau ne da kai tsaye zaki ce ga wanda kike tuhuma da rashin ta...?" " Da ban duba ba ai bazan ce ita bace, ni dai kawai a fito min da sarka ta wlh ko na yi maganin mutum cikin gidan nan, dama nasan ba kauna ta ake yi ba tunda ake fifita wasu karere akai....." Lafiyayyan marin da ya sauka saman kuncin ta ne ya hana ta dakatar da maganar da ta dauko... Ba kowa bane kuwa face Rayyan da tuni ya hassala ganin yadda take bawa Ammi amsa tamkar sa'ar ta. Sai dai yana shirin kara mata wani.marin Ammi tayi saurin rike masa hannu ramta 6ace" Haba Rayyaan, miye hakan kuma...baka da hankali ne mace zaka yiwa irin wannan bugun, kuma ma a gabana...?" Bai bi takan maganar Ammin ba, tuni idanuwan sa sun koma jajajir kuma still Amrah yake kallo duk wani mutsa mutsan 6acin ransa sun gama bayyana saman fuskar sa..da 'daya hannun sa da Ammi bata rike ba ya nuna Amrah" Ke har iskancin naki yakai haka Amrah...Ammi ce fa, mahaifiya ta....?". Ya ma kasa magana illah dafe kansa da yayi da hannu 'dayan tsabar yadda ransa yakai kololuwa wajen 6aci har kansa na mai sara. Ammi bata bi ta kan shi ba kamar yadda bata bi takan abinda ya furta ga Amrah ba..abu biyu kawai ke gaban ta a yanzu...shine bugun Amrah da yayi sai kuma maganar da asali ya kawo ta 6angaren. " Bana son shashancin banza Rayyan, I always says ka koyi sarrafa fushin ka ko ban san isa na hana ka abu ba..?" Da sauri ya 'dago ya kalle ta yana mai dauke hannun sa da ke kansa. Da kyar bakin sa ya iya furta " Haba Ammi..." " Daga yau..duk hukuncin da zaka yi kar ka sake ka sake 'daga hannun ka dan bugun mace kana jina...?" Kai ya 'daga mata alamar yaji..." Shin ka mace waye Amrah ne? Mancewa kayi da yanayin da take ciki ne...?" Shiru bai ce komai ba illah Amrah da ya juya ya kalla da ke dafe da kuncin ta har yanzun hawaye kawai ke mata zarya. Kan cikin ta ya sauke idanun sa take yaji mugun tausayin ta ya tsirga masa," uwar 'ya'yana ce..." Zuciyar sa ta furta masa take ya lumshe idanu yana jin gaba 'daya tamkar wani ne bashi ba" Ammi tafi kowa kauna da burin ganin 'ya'yan su a duniyan nan bazai so ya ringa 6ata mata ba." ...a fili ya furta" I'm so sorry Ammi...". Yayi.maganar ne yadda shi da ita kadai zasu ji musaman sbd kusancin dake tsakain su sai ko Amrah dake daura da su amma zurfafa tunani da tayi ma bai bari taji abinda ya fadan ba sai dai na Ammi da ta dan yi da sauti kadan tana duban sa. " Oya je ka sha ruwa yanzun nan..". Ammi ta bashi umarni inda tayi maganar tana mai sakin masa hannu. Ga Zaitoon ta maida duban da tuni ta durkushe saman gwiwar ta tana kuka 'diyar ta na jikin ta ta lafe itama...tun lokacin da Rayyan ya saukewa Amrah mari Zaitoon ta durkushe dan gaba daya tsoro da fargaba ne suka shige ta, sai a lokacin kuma hawayen ta suka 6alle gaba 'daya, abinda bata ta6a gani ba, abinda bata ta6a zaton zai faru tsakanin su ba musamman sbd irin kaunar da ta tabbatar suke yiwa juna, yau ita kam tata ta kare, akan ta Rayyan ya daga hannu ya mari Amrah?, duk akanta suke wannan 6acin ran, hatta Ammi da ta shigo fuskar ta babu alamun walwala koka'dan.... Gani.take tamkar zasu yi gunduwa gunduwa da naman ta ne yau din nan, dalili kenan daya sanya ta sake matse 'diyar ta ajiki sosai tana fadin" Yau Zaitoon ina kika kawo ku...?" Sunan ta da Ammi ta ambata yasa da sauri ta 'dago da kanta, tuni idanun ya rine jajajir..." Zaitoon zan tambaye ki ki tabbatar kin sanar dani gaskia, dan ko baki fada min ba Allah ya gani kuma kinsan sai ya miki hukunci kan hakan..." " Kin dau ki sarkar Amrah ko.baki dauka ba...?" Kai ta fara girgizawa" Wallahi Ammi ban ta6a sha'awar 'daukan abin.kowa ba, ban ta6a ganin abinda ba nawa ba ne nayi sha'awar 'dauka kuma har abada bana fatan hakan ya faru dani, sarkar ta kuma ban ma san ya kalar ta take ba balle in dauka...." Tana maganar ne hawaye na sauko mata da gudun su. Ammi bata jira taji karshen maganar Zaitun ba ta maida duban ta ga Amrah domin ta riga ta samu amsar da take bu'kata..." duk zaman da zakiyi da mutum Amrah ki tabbatar baki zalunce shi daidai da 'kwayar zarra cikin zaman ku ba domin Allah baya barin azzalumi da maha'inci, sannan ki tabbatar kina da hujja kwakkwara kafin ki yanke hukunci gudun abinda zai je ya dawo, dukkan ku tamkar 'ya'yana nake jinku so bazan bari 'daya ya cutar da wanin sa ba...ba kuma nufi na in 6atawa kowa daga cikin ku ba amma gaskia ce a duk yanayin da tazo dole zan fade ta hakan shine dai-dai... " Kafin Zaitun ta fara yi miki aiki ta min aiki na tsawon lokaci kuma nasha bar mata bedroom 'dina ta gyara ta share min lungu da sa'ko na dakin, ko wani 6angare ban mata shamaki da shi ba..daidai da allura ban ta6a nema na rasa ba har kawo yau 'din nan kuma bata fasa ba, me yasa sai a wajen ki zata 'dauki abu? Me Zaitun zata yi da sarkar ki...? Ku ji tsoron Allah ku kyautatawa 'yan uwan ku zato ku kuma kyautata mu'amala da kowa da ke rayuwa kusa da ku 'daya daga cikin halayyar mutumin kirki kenan...." " Zaitoon zo mu wuce ". Ta fa'da tana duban 6angaren da Zaitun take. Sai kuma ta sake dawowa ga Amrah" In kuma aikin da take yi mk ne baki so daga yau an daina kiji dadin ki, sai ku nemo mai muku hidimar sashen ku daga yanzu, sarkar taki kuma idan baki samu ba ki rubuto min adadin kudin ta zan bayar aka kawo miki sai ki sayi wata..." Daga haka Ammi ta ja hannun Zaitun suka yi gaba. Amrah kuka kawai ta sanya ta zube a kasa tana fa'din an ci mata mutunci, an muzantata, yau an wulakantata gaban 'yar aikin ta. Rayyan kuwa ficewa yayi ya bar gidan kawai bai dawo ba kuwa sai yamma. Shikan sa yana bayan maganar Ammi, dan bai ta6a jin anyi complain da 6atan komai a wancan 6angaren ba...kawai dai Amrah wani abin take nufi ko kuma inma gaskiya ne bata ga sar'kar ba to ba mamaki Amran manta inda ta ajiye sarkar tayi ko kuma bata nutsu ta duba da kyau ba...amma bari idan ya koma zai tayata su sake dubawa ko za'a dace. Ko da ya koma gidan bai tarar da Amrah ba, bai kuma neme ta ba dan yana kyautata zaton gidan su tai tafiyar ta. Har washegari Amrah bata dawo ba, bai sanar da Ammi bata nan ba haka kuma har a lokacin bai nemi numbern wayar ta ba. 'Bangaren Zaitun kuwa daren ranar kuka tasha sosai ta 'koshi, ji take tun da take aduniya ba'a ta6a ci mata mutunci irin ranar nan ba, sata fa, tayi me da kayan sata...?" Tun daren ta yanke shawarar barin gidan, ta sha yanke irin shawarar nan akaro babu adadi amma wannan karon tana jin babu abinda zai dakatar da ita. Washegari da ya tashi wajen aiki gidan su Amrah ya nufa ya nemi ganin ta amma mahaifiyar ta taki bashi dama, haka ta 'dime ta zayyana masa sharu'd'da kafin ta sake bashi dama akan Amran, ranshi ya 6aci sosai da jin kalaman mahaifiyar Amrah. Tun anan yaga gazawar ta wajen mutuntaka, kuma ya tabbatar dan mahaifin ta baya gari ne amma da baza'ayi hakan ba. Taya zata ce sai an sallami mai aiki a gidan kafin Amrah ta dawo, ba fa shi ya kawo yarinyar ba..mahaifiyar sa ce, so take ya yi iko da Ammin nasa ko kuwa me take nufi...?" Duk yadda yaso fahimtar da Mummyn Amrah gagara fahimtar sa tayi. Cike da haushi ya bar gidan cikin ransa yake fa'din ta ji'ka Amran ta shanye idan wata tsiya ce..". *Drop ur Comment pls* Salmerh😘 [11/10/2022, 6:10 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Wattpad@* _Serlmerh-md_ 🅿️ *...48* .......A hanyar sa ta komawa gida ne ya fara hango wata kamar Zaitun kamar kuma ba ita ba...hakan yasa ya rage speed ya fara tafiyar a hankali sosai tamkar bai so yayi. Tafiya take tunani kala- kala na zuwan mata. A yanzu babu abinda tafi tsoro irin masu hannu da shunin nan, duk kan su kusan iri 'daya suke, kowa da nashi kalar sharrin yake tafe, bazata ta6a mantawa da zancen Hajia Talatu ba, a maganganun ta 'karara ta nuna mata bayyanannar tazara dake tsakanin ta da su, a yanzu kuwa ta sake tabbatar da hakan, ta sake tabbatar da cewa su 'din rayuwar su kal dabn take da ita koda kuwa aiki kake karkashin su kawai dole sai sun nuna maka bambanci. Shiyasa Hajiya Talatu ta tabbtar mata da bambancin dake tsakanin ta da Adam Shaheed abaya, ta nuna mata cewa Adam ba sa'anta bane ta kowace fanni, a lokacin bata yi mamaki ba, sai ma mamakin yadda Adam bai ta6a sanar da ita hakan ba da tayi, bai ta6a nuna mata wata alama da zata sa ta gane cewa mahaifin sa wani babba ne a'kasar nan ba. Sai dai maganganun Hajiya Talatu ba 'karamin tasiri sukai mata a zuciya ba, dagaske har zuciyar ta ba taji son Adam ba, bata ji tana 'kaunar sa ba, bata kuma ji cewa ta shirya aure a lokacin ba, ko dan bata taba yin so bane oho, dan dama tun asali ita zancen so baya gaban ta kokadan...kyautatawar sa dama agareta ne kadai yasa taji erh zata iya amincewa ta aure shin, ko ba komai shidin me 'kaunar ta ne tunda yana 'kaunar Moopy gami da bata kulawa, kuma ance zuciya na son me kyautata mata ne. Sai dai bisa shara'di da kashedin Hajiya Talatu dole ta barshi, kuma bata yi ba'kin ciki da hakan ba ba balle ta matsawa zuciyar ta da tunani, jin babu da'di ko tausayin sa, dan tasan ita din ba kowan kowa bace, ba komai bace cikin tarin kyawawan mata da Allah ya azurta duniya da su, mata masu aji da ilimi da tunkaho da dukiya da karfin mulkin iyayen su wadanda suka fi dacewa da shi tamkar yadda Hajiyar sa tafiso, tasan Cikin lkc kalilin Adam zai samu wacce ta fita ta maye masa gurbin ta, shiyasa bata damu ba sam, musamman da tasani kuma ta aminta da cewa lalle dagaske ita din ba tsarar sa ba ce..dama can ta saba da wahalar rayuwar ta, ta saba da fadi tashin ta ita ka'dai, so ba sabon abu bane yanzu gareta...hakan yasa ta saki ranta ta cigaba da rayuwar ta tamkar yadda ta saba can baya kafin zuwan kaddarar ha'duwa da Dr Rasheed ta same ta. Sai dai daga ranar da ta ji sunan mahaifin sa cikin case 'din su, komai ya kwance mata, tausayin Adam ya tsarga mata sosai, tasan zaiji babu da'di, zai kuma ji nawin cigaba da walwalar sa kamar baya yadda ya saba. Zaitun tayi duk wannan tunanin ne lkcn da take tafiya bayan ta bar gidan Ammi...gidan da taji fit ya fice mata aka, bazata ta6a iya rayuwa a inda ake binta da sharrin sata ba...yinin ranar kaf jin ta take tamkar akan 'kaya take, ko lkcn da take kulle a prison bata ji matsuwar barin sa kamar wannan gidan ba, kuma tana fita daga cikin sa taji wata natsuwa ta sau'kar mata..har da sakin ajiyar zuciya. Tun kafin ta bar layin gidan ta fara hango mota na tahowa ya kuma haske ta sosai duk da duhun ba mamayi garin sosai ba amma sai aka wani haske ta da fitilar motar, bata san waye haka cikin motar ba amma yadda ya rage gudun motar ya kuma haske ta ya sanya tsoro sake tsirga mata, Cikin ko wani da'ki'ka rayuwar ta na baya ke sake dawo mata. Tsoro da fargaba cika mata zuciya suke akai akai...tsoron abinda ya ta6a faruwa da ita ya sake maimaita kansa. Tun ba ta yi nisa ba taji jikin ta yayi sanyi. Bata ta6a sanin zama cikin gidan babban garkuwa ne agareta ba sai yanzun da ta tsinci kanta bisa titi ga hasken da ya dallare ta. Bata san inda zata nufa a cikin gari irin kano ba, bata san gabas ba balle yamma. Tun fitowar ta taji kanta gaba 'daya ya juye mata wani 6angare na daban. Daf da ita motar tazo ta faka sai dai ba'a bude ba, sai anan ma ta fahimci ashe 'daya daga cikin motocin gidan Ammi ne sai dai bata san waye a ciki ba duk da tasan waye ya fiye amfani da wannan motar kasantuwar windown 'dakin ta dake saitin babban wajen parking din gidan. Tana iya jin yadda idanu ke mata yawo ajiki ta tabbata ita ake 'karewa kallo hakan ne yasa tsoron ta 'kara karfi, shirin gudu ta fara sai kuma akayi rashin sa'a dai dai zata gota motar taga anbude ta. Taku baifi hudu yayi ba ya cimma ta yana dawo da ita baya fuskar sa babu yabo babu fallasa yace" Sai ina kuma? Ko dai yawon bai 'kare bane har yanzu...?" Ya tambaya yana duban 'kwayar idanun ta. " Cika min hannu na malam". Ta fa'da cike da karfin gwiwa da zafin masifa da ya taso mata nan take, dukkan su ahalin gidan haushin su take ji in ka 'dauke Ammi ka'dai. Gire ya 'dage yana kallon fuskar ta yace " Toh fa..wannan irin masifa haka, ko dai nima marin zansha kamar yadda aka yiwa Amrah kwanaki..?" Bata amsa shi ba illa kokawa da hannun sa da take a kokarin ta na son 'kwatar nata hannun. Tsayuwar sa ya gayaa jikin mota, daga nesa idan ka hango su sai ka zaci maganar arziki suke yi tsakanin su. Gashin kansa ya shafo da 'dayan hannun sa yayin da 'daya hannun yake ri'ke da tsintsiyar hannun Zaitun har a lokacin bai saki ba. " Wai ina zaki je ne?...kin gaji da zama waje 'dayan ne za'a 'dora? ko kuwa guduwa kike son yi bayan daf kike da kashe min aure na..? Hararar sa tayi Sai ya yi kamar bai gani ba. " Ai in kinga kin bar gidan nan toh aure na bai daina lilo ba, Toh ma Ammi tasan kin fito ko kuwa..?" Cike da haushi tace " Wallahi idan baka cika ni ba sai na maka ihun kwarto...". Idanu ya zaro sosai..." ohh really...mene ma kwarto?...ohh na gane, ki gwada mana, kowa yasan ni ba kwarto bane akaf unguwar nan kuma ko zanyin ma ba dai da irin ki zanyi ba..baya ga haka ma ni da ke waye mai shaidar da zata bayyana kwartancin?". Ya 'karashe maganar yana sakin wata 'yar dariyar mugunta. Wani fizga ta yiwa hannun nata dake hannun sa tana fa'din" Ni dai wlh ba 'yar iska bace sai dai ko kai da ka rike min hannu..." wannan maganar ya sanya ya 'daga 'daya hannun sa kamar zai mareta sai kuma ya fasa..kan hannun nata dake hannun sa ya sauke idanu. Shi da kansa mamakin kansa yake yau din da har ya biye mata har haka, me me ruwan sa da ita? Amma haka kawai yaji zuciyar sa bai yadda ya barta ta tafi da wannan lokacin ba. Ba 'karamin girgiza Zaitoon tai ba da ganin ya 'daga hannun sa da nufin marin ta, gashi ya tsare ta idanuwan sa masu mugun shigar da ita taitayin ta...bata manta marin da ya saukewa Amrah ba...ita bata taso ta saba ganin ana bugun mutum ba haka kuma itama baza tace ga ranar da aka mare ta irin hakan ba shiyasa take jin tsoron ranar da hakan zai faru gareta amma duk da hakan bata yadda ta bayyana firgicin ta gare shi ba. " Shiga mota mu koma gida..." 'Karfin halin magana tayi tana sake ha'de rai " Wani gidan..kenan..? Babu inda zan koma ni, gidan da bashi da maraba da bakin kura, gidan da banda zalunci da 'karairayi babu abinda aka iya a cikin sa, ka cika min hannu nayi tafiya ta, nagaji da azabtar min da 'diya da cutar da mu da kuke yi a gidan ku..kuma ka fa'da wa matar ka ni kaf gidan banga abin sata ba balle har nayi sha'awar daukan sa, nafi 'karfin in 'dauki abinta wallahi koma menene shi..." Kallon cikin idanun ta ya tsaya yi har ta dasa aya, duk da duhun maghrib da ya fara shigowa amma hakan bai hana shi ganin fuskar ta da kyau ba, mamakin kalaman ta yake da ya tabbatar tsantsar gaskiyar abinda yake zuciyar ta take furtawa.... Kansa ya kawar gefe yana 'yar daria da kokadan bata bayyana saman fuskar sa ba , bai kuma bari Zaitun ta fahimta ba. " Kika ce babu abin sata a gidan?" " Ban ta6a ganin sa ba...". Ta bashi amsa ranta a 6ace itama. " Na yadda babu 'din, amma ina jiye mk ranar da zan kamki da satan wani abu kuwa..tsaya ma tukun na kin tabbatar baki sato komai yanzun bama ko...sai na tabbatar sannan zan yadda dake, har kuma yanzu na.kasa tabbatarwa musamman saboda yadda naga kike tirjewa da son kika ga kin wuce..kodai sarkar matartawa za'a je a siyar...?" Bata bashi amsa ba illah harara da ta banak masa sai lokacin taji hawaye. Shima da ganin hakan sai ya 'daule kansa. Ji yake tamkar yayi ta sheka daria amma bazai iya gaban yarinyar ba. Wayar sa ya ciro agaban rigar sa ya danna 'kiran Ammi. Ko da ta 'daga sunan sa ta fara ambata yace.." Na'am Ammi barka da Yamma, ina wannan maid 'din taki, mamar yarinyar nan...?" " Ohh Zaitoon...?" Wlh nima cigiyar ta nake yanzu ina tunanin can 6angaren naka take ma dan bata nan..". " Ok shikenan...". Idanun sa akan ta ya cire wayar daga kunnen sa..." Ammi bata san kin fito ba, oya shiga mota mu koma gida...." Kuka mai sauti ta sanya tana fa'din" wallahi ni babu inda zani dole ne sai an zauna tare da ku...?" " Ba dole ba ne...amma waye ya kawo ki Kano ne...?" " Ina ruwan ka ai dai bakai bane toh...?" Wani killer smile yayi, sannan yace" Wanda ya kawo ki kano shine mamallakin ki a yanzu dan haka shiga muje, in ma bazaki fa'da ba ai ni sani...". Zata sake magana ya cicci6e ta ita har yarinyar bayan ta ya santa su abayan motar sa yana fadin mutun sai shegen nauyi da taurin kan tsiya...". Watsa hannuwa yayi yana fa'din wash hannu na da gangan duk da yasan ba gaskia yake fa'da ba, ita har 'yar tata da ya 'daga weight din su bai taka kara ya karya ba. 'Kofar motar ya mayar ya rufe da karfi shima ya shiga gaba. Kuka sosai Zaitun take ta kifar da kanta bisa cinyoyin ta. " Aimin shiru ko nayi bugu bana son hayaniya..dan ma kin samu na saki a motata.". " Ni na ro'ki a sani cikin mota ne toh..?" Kin kulata yayi kawai yayi murmushi itama bata sake tanka saba yaja motar yayi gaba, tafiya ka'dan yayi suka iso 'kofar gate gidan su ya danna horn Mai gadi yaja gate ya fara tura hancin motar ciki dai-dai saitin maigadi ya ja ya tsaya yana ya fito sa da hannu. " Ranka ya da'de barka da dawowa". " Yauwa Emma ya akayi ka bar wannan yarinyar tafita batare da binciken komai akanta ba...kasani ko sata tayi zata gudu...?" " I'm so sorry Oga, she said she ll buy rechard card nd come back now...". " Ok..kar ka sake wannan gangancin kaji, duk wanda kaji.baka yadda da shiga ko fitan sa ba ka kira ka sanar dani before letting every body out kana ji na ko...?" " Yes Oga..Thank u...". Gaba yaja motar ya isa wajen Parking sannan ya bu'de ya fito itama fitowa tayi. " Allah sai ya sakamin sharrin satan da akai min...". Bai tanka ta ba sai ma gira da ya dage kawai ya nufi 6angaren sa. Ita kuma jikin ta sanyi 'kalau ta nufi 6angaren Ammi. *Drop ur Comment pls* Salmerh😘 [12/10/2022, 12:27 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Wattpad@* _Serlmerh-md_ 🅿️ *...49* ........Fa'da sosai Ammi tai mata kan yanke shawarar tafiya da tayi batare da ta sanar da ita ba, ita Ammi a sonta daga nan gidan Zaitun bazata sake zuwa ko'ina ba sai gaban iyayen ta, tafi so ta damkata a hannun su kamar yadda ta yiwa kanta alkwari tun farko. Meyasa Zaitun din bazata yi hakuri ba, ita kanta tasan ba gaskia Amrah ke fadi ba kuma ko awajen bata goyi bayan ta ba meyasa daga baya Zaitun din zata yi fushi ta tafi. Tana ganin kamar batai mata adalci bane ko me take nufi. Hakuri Zaitun ta bawa Ammin sannan ta sake komawa dakin su da ta baro. Ta 'dauki tsawon kwanaki kafin walwalar ta ta dan dawo dai- dai, ba komai yafi tsaye mata ba face zancen satan nan, Ammi kuwa bata tashi sanin cewa Amrah bata gidan ba har sai da aka shafe tsawon sati guda. Rayyan ne da ya shigo 6angaren ta take tambayar sa Amrah fa tace har yanzu fushin take yi dani ne naga bata leko nan ba, ka sanar da ita nace tayi hakuri ba nufi na in 6ata ranta ba ne. " Ammi ai Amrah tun ranar can bata kwana gidan nan ba.." Ya bata amsa a ta'kaice Yana shirin mi'kewa. Gira sosai Ammi ta ha'de tana duban sa" Me kake nufi Rayyaan..?" " Ta tafi gida naje bayan kwanaki biyu da tafiyar tata amma ban samu ganin ta ba.." Shima fa'da sosai Ammi tayi masa na rashin sanar da ita da wuri da bai yi ba ta inda take shiga bata nan take fita ba, tace meyasa zai yi kan irin wannan maganar bacin yasan yanayin da Amrahn ke ciki, kai ko 'dar ma bakaji, taya zaka bari har sati guda bata tare da kai bayan kasan da 'karamin ciki ajikin ta, idan wani abu ya samu cikin fa..." " Ammi ni bazan iya zarya ana cimin zarafi haka nan kawai ba, 'karshe ma nayi magana Amaran yanzu haka bata Kano tana Kaduna nayi bincike kuma na tabbatar da hakan ne dagaske...babu yadda zanyi ne Ammi, umarnin mahaifiyar ta take bi itama." " Kuma da aure da cikin duk take wannan yawon..?" Ammi ta tambaya cike da 6acin rai. " Rabu da su Ammi..in hauka suke ji na 'dara su, na riga na sanar da ita, ko kwarzanen abu ya samu cikina I would not hesitate in 'daure mutum babu ruwa na, nd tasan zan aikata.." Tsaki Ammi tayi ta wuce sama. Washe gari tana da tafiya agaban amma ta soke shi zuwa rana ta gaba. Da kanta taje gidan su Amrah dan ganawa da mahaifan ta kan batun amma kamar yadda mahaifiyar Amrah ta shaidawa Rayyan haka ta shaida ga Ammi. Sosai ran Ammi ya 6aci, sai taga ma kamar raina musu hankali kawai suke son yi, bayaga haka taya za ace sai su ne zasu bata dokar yadda rayuwar gidan ta zai kasance, kamar dai yadda Rayyan ya bar gidan cike da 6acin rai haka ma Ammi, inda duk suke yin tafiyar su batare da an tsaida magana guda muhimmiya ba. Tun faruwar lamarin can Zaitoon bata sake aikin komai cikin gidan ba, wannan karon koda Marwa ta dawo gidan Ammi ta tare gaba daya, dan Sultan yayi wata doguwar tafiya zuwa kasar senegal. Sosai suke samun time susha hira yadda ya kamata da Marwa. Sosai take zuzuta girman da Moopy ta kara a idanun ta, round face ne da ita da manyan idanuwa da hasken fata dan Mufee fara ce tas ba kamar Zaitun ba take choculate ba fara sosai ba, yanayin shape din fuska da yanayin jikin su iri daya ne haske ne dai ya bambanta su hakan yasa tace ko batace ba ba kasafai ake tantama wurin bayyana Mufeeda 'diyar tace ko ba tata ba. Wannan zuwa na Marwa shi ya 'karo sha'kuwa mai 'karfi tsakanin su da Zaitun dan Marwa har ta fara zancen zasu shiga Islamiya tare. Bacci ka'dai ke raba su da Zaitun, hatta abinci tare suke ci da Marwa adakin ta, kokadan bata nuna musu kyama. Suttura kuwa yanzu Zaitun sai dai ta bada ga wasu, duk wani nauyin kayan 'kawa na rayuwa itama yanzu kewaye take da su. Sosai ta kara samun wayewar rayuwa, ta murje ita da Moopy tamkar basu ba. Tare suke komin su da Marwa hatta unguwa tare suke zuwa har gidan Anty Madeena da ta kasance kanwa ga mahaifin su. Aikin da yaka ma su suyi tare suke yi, in an gama abinci ma suci cikin plate guda hatta Moopy yanzu sun kara sha'kuwa da Marwa sosai, yarinya ta fito tsab ta juye kalar 'yan gayu. ***** Misalin sha 'daya ne safia, cikin 'dakin Ammi suke suna canza masa fasali, kasantuwar a ranar zata dawo daga tafiyar da tayi zuwa Abuja wajen kaddamar da wani tallafi da suka wallafa na kungiyar su ta taimakawa gajiyayyu a Abuja. Aikin suke amma komai cikin sanyi Zaitun ke yin sa, Marwa duk na lure da ita amma ta saka mata ido, ganin kamar yanayin kara shigan ta yake ne ya sanya Marwa jefa mata tambayar abinda ke damun ta da wannan lokacin. Kai ta girgiza tana duban Marwa" Me kika gani..?" " Babu abinda ma ban gani ba ai, ni dai dan Allah fada min meke damun ki, bana son muna zaune da mutum inga yanayin sa ya canza wlh sai inji babu dadi...". Ajiyar zuciya Zaitoon ta sauke kana ta tabbatar wa Marwa cewa babu komai banu abinda ke damun ta. Shiru Marwa tayi tana duban ta ga dukkan alamu bata ji dadin amsar Zaitoon din a gareta ba. Kawar da kai tayi ta cigaba da aiki itama, babu wanda ya sake tanka kowa tsakanin su sai dai Zaitoon da ta fahimci tamkar itama Marwa yayanin ya canza zuwa sabon yanayi duba da yadda taja baki ta gimtse sa6anin yadda suka saba tayi ta mata hira, wannan karon sbd ta kawar da shirun sai ta ringa 'ka'kalo 'yar hira amma Marwa ta'ki tankata ta karshe ma ficewa tayi ta koma dakin ta ta bar Zaitoon bayan ta tabbatar sun kammala aikin. Bayan ta Zaitoon tabi da kallo...saman la66a ta furta" Fushi kenan...?". Sai da ta tabbatar ta kammala komai kafin ta nufi wajen Marwa dake kwance saman gadon ta rike da wayar ta a hannu. Tura 'kofan tayi ta shiga da sallama amma Marwa tamkar ma bata ganta ba balle ta nuna taji abinta ta fa'di. Daf da ita ta isa ta tsaya tana duban fuskar ta da bakin ta dake bin wa'kar Mr Meddy da ke tashi cikin wayar ta. " Marwa wai fushi kike dani kome...?" " Me yasa zan yi fushi da ke kuma..?" Ta bata amsa batare da ta dube ta ba. 'Yar daria Zaitoon tayi.." Baki saba ba shiyasa sam bai kar6e ki ba yanayin..." " Ai ko ban saba dole zanyi tunda iya zaman mu baki yadda dani ba balle ki iya sanar da ni damuwar ki duk da cewa kuwa da kaina na tambaya..." Ta 'karashe maganar gami da mi'kewa zaune. " Kai Marwa ta, kaddai akan maganar 'dazun ce, indai itane kiyi ha'kuri zan sanar dake komai.. amma kafin nan dan Allah ki sanar dani ya asalin rayuwar gidan ku ke gudana...?" Idanu Marwa ta fitar sosai..." Rayuwar gidan mu?, tamkar na kowa take mana..meyasa kika min wannan tambayar...?" " Ina mamaki ne kawai" Zaitoon tace tana shirin zama bakin bed din kusa da Marwa...sannan ta cigaba... " _Kinsan jiya da dare da wuri muka yi bacci, toh ni dai ban san me ke faruwa ba, cikin daren Moopy na ta dame ni da 'kananun kuka, ba kasafai take min irin wannan rigimar ba dan haka sai naji hankali na duk ya tashi, saboda bansan abinda ke damun ta ba gashi ba baki ke gareta ba ballantana ta sanar da ni matsalar ta._ _Cikin wannan daren dole sai da na goya ta, a lokacin idan ban yi 'karya ba 'karfe biyu ne da 'yan mintina na dare, jikin window na tafi ina kan jijjiga ta sai nayi tunanin da ace zata koma ma da na dan yi nafilfili sai dai tuno cewa fashin sallah nake yasa na watsar da wancan batun._ _Daga inda nake tsaye ina iya hango harabar gidan har zuwa wurin parking motoci da yake dama kinsan direct saitin windown 'dakin da nake yake._ _Ga mamaki na sai na hango kamar motsin mutum 'kar'kashin motar yayan ki..."_ Da hanzari Marwa ta mi'ke tsaye dafe da 'kirji tace" Innalillahi wa inna ilaihiraji'un..wani Yayan nawa kenan...kardai Yah Rayyaan?" " Ki kwantar da hankalin ki Marwa ba...." " Babu wannan maganar Zaitoon ke de 'karasa bani labarin kawai baki san yadda naji zuciya ta ba ne..." Cewar Marwa bakin ta har na sarkewa ta wani dam'ko hannuwan Zaitoon cikin tafukan hannun ta ta rike dam tamkar ance mata zata gudu ne batare da ta karasa mata labarin ba. Kafin Zaitoon ta fara magana suka tsinkayi 'karar wayar Marwa dukkan su duban wayar suka yi..." _Yah Sulty_ " Suka ga an rubuta da tambarin heart ajiki. " _Kyale shi zan kira shi daga baya cigaba da ban labarin abinda kika gani kawai_ ". " _Nima mamaki ne ya kama ni sosai, ban san me hakan ke nufi ba amma har zuciya ta sai naji na kasa samun natsuwa, kafe wajen da idanu nayi ai kuwa sai ganin mutum nayi ya fito daga wurin yana 'yan dube- dube irin na marassa gaskia...Can ya nufa wurin hanyar gate daga nan ban san kuma ina ya kuma yi ba, ban da ba'ka'ken kayan sa da hasken wutar lantarkin harabar gidan ya taimaka min wajen gani ban fahimci komai game da shi ba..._ " " _Jiki na sosai ya fara rawa zucia ta ta cika da wasi- wasin abinda hakan ke nufi, a zahiri nasan shirin ba na alkhairi bane shiyasa aka bi dare sai dai ban san manufar wanda na gani ba, ban kuma san ta ina ya kamata in fara bayyana abinda na gani ba, nasan bani da shaidar da zan fahimtar da masu gidan tunda bansan nufin koma waye bane nagani ya aikata hakan...shiru nayi, amma zuciya ta ta kasa saituwa, nutsuwa ta ta kasa dawowa jiki na._ _Zuwa lokacin tuni Moopy na ta jima da komawa bacci amma ni na kasa barin wurin har 'karfe uku ta gota da wasu mintina...Ajiyar zuciya na sau'ke bayan wani 'dan guntun tunani da nayi..'kila gyara suke yi wa motar..wani 6arin zuciyar tawa kuma tace min..gyara da wannan tsohon daren, meyasa sai tsakiyar dare?...to ke Zaitoona ina ruwan ki ne?_ _Nima dai haka na gani shiyasa na saki ajiyar zuciya...amma duk na kasa jina dai- dai._ _Da hakan na koma na kwantar da Moopy sannan nima na kwanta..duk 'ko'karin da nake dan ganin na cire abin a zuciya ta abin ya faskara._ _Sam bacci sai ya gagara 'dauka ta har sai da akai sallah sannan bacci ya 'dauke ni batare da na sani ba._ _'Karfe bakwai na tashi a bacci kasancewar Moopy na ta riga ni farkawa sai ta ringa min mutsutstsuku a jiki na tana 'kiran Mammi dole na tashi badan na soba...amma da tashi na wancan lamarin ya fara zuwan min kwanya ta...Sai kuma nake jin tamkar idan nayi shiru ban kyauta ba musamman idan na tuno irin karamcin Ammi gare ni, kuma wannan lamarin ya shafi ahalin ta ne, ya shafi farin cikin ta ne domin nasan ahalin ta suna farin cikin ta a halin yanzu, dan nayi shiru kuma bani da tabbacin daidai na aikata, ban san ina ne karshen lamarin gaba daya ba, ta iya yiyuwa shirun nawa ya kawo babbar matsala ta iya yiyuwa akasin hakan amma dai dole sai an yun'kura kafin ake kaiwa gaci, bai kamata inyi shiru in zubawa lamarin idanu har sai ya faru ba._ _Da wannan tunanin na samu 'kwarin gwiwar mi'kewa, bayi na shiga nayi wanka sannan na yiwa Moopy na ma"._ _Shi kansa ba sosai nake ganin sa ba yanzu, na kan mance ma da lamarin sa a rayuwa ta har naji muryar ko ganin sa, wannan ma sai dai in Ammi na gida ne kawai in bata nan ba kasafai ake ganin sa ba kinsan, abinda na guda in fada miki shine kar ki kasa fahimta ta shiyasa naji zuciya ta tafi bani in fara sanar da shi tukunna, ta iya yiyuwa idan na fada mk kafin zancen ya samu isa gare shi wani abin ya faru duk ba'a fata, amma dai ganin mutum karkashin motar wani haka siddan da tsakiyar dare ansan ba lafia bane, ta iya yiyuwa kuma ba abinda nake zargi bane amma nasan shi idan nai masa bayani zai fi fahimta ta ko da ace ba hakan bane, kuma ina da tabbacin zancen bazai yi yawo ba_ . _Haka kawai yau na yanke shawarar zuwa aiki na da nake yi a 6angaren Amrah duk da kuwa har yau 'din nasan bata dawo gidan ba, kuma rabo na da yi musu aiki tun batun satan nan da akayi kwanaki, idan ban manta ba kwanaki goma sha tara kenan yanzu, amma zan yi hakan ne kawai dan in samu damar ganawa da Rayyan ba dan komai ba, duk da nasan mawuyaci ne ma ya saurare ni._ _Duk da nasan dai matukar Allah ya riga ya tsara wa bawa abu toh kuwa wani bawa bai isa ya dakatar da faruwar lamarin ba, amma muna fatan faruwar alkhairi ne kowace wayewar safia wala alla yun'kurin mu su kasance mana garkuwa idan Allah yaso...._ _Da wannan tunanin na sake samun 'kwarin gwiwar 'kaddamar da nufi na, Knocking bakin parlorn nayi amma shiru ba'azo an bu'de min ba, tsawon mintina ina tsaye ji nake tamkar in koma amma kuma 'kafafuna sai suka kasa motsawa duk da kuwa zuciya ta ta riga ta bani umarnin in ha'kura kawai nayi tafiya ta._ _A hankali na sake 'daga hannu na danna bell din ina lumshe idanu da fatan nasara._ _Bayan kamar da'ki'ku hamsin sai kawai na yanke shawarar juyawa, wannan karan 'kafa ta batayi min nawi ba, amma daga yadda nake tafiyan zaki fahimci ba a son raina nake tafiyar ba...kawai dai naga alamun ba lallai ne a bu'de min kofar ba...bazan samu ganin sa ba kenan..ba mamaki ma baya 'dakin kilan yana wajen motsa jikin sa kamar yadda ya saba duk safiya, amma ai lokacin barin sa wajen tuni ya gota...duk wannan tunanin ina yinta ne cikin zuciya ta yayin da idanuwa na ke kafe kan motar da na tabbatar akayi abu 'kar'kashin ta._ _Ka'dan ya rage nayi nisa da bakin 'kofan naji alamun an bu'de ta, haka kawai na saki ajiyan numfashi._ _Waigowa nayi muka ha'de idanu, sanye yake da dogon wando mai kauri na ba'kin jeans da singileti fari, fuskar sa babu yabo babu fallasa...sai kuma naji kwarin gwiwar da suka yo min rakiya duk sun zagwanye..Allah ya bawa Rayyan kwarjini, kyau da cikar kamala gashi mutum ne mai matukar natsuwa._ " _Kin tsaya kallo na bake ke sallamar bane..._ ?" _Ban bashi amsa ba illa takowa da nayi na dawo baya step uku dake nan wajen tamkar dakali da zaka fara takewa kafin isa ga barandar Parlorn nasa kafa na fara takowa a hankali idanu na na 'kasa._ ' _Kofar ya saki ya koma ciki batare da ya rufe ta ba_ . Cikin ransa ya furta..." " _Tamkar wata mumina_ " _A hankali na tura na shiga, ban wani yi yawo da idanu na sosai a palorn ba kasantuwar yana a ciki shima can gefe bisa kujerar dinning da yake 6angaren ba wani babba sosai bane ba so daga inda nake ina iya hango shi kuma shima yana kallo na._ _6angaren sa ne tun na zamanin samartakar sar sa kuma ko lokacin da aka daow da Amrah gidan ba ai masa gyaran komai ba._ _Sau 'daya dana dubi parlon na tabbatar baya samun isasshen gyara yadda ya kamata dan babu takamman mai zuwa ya kula da tsabtar sa._ _Shi da kansa Rayyan yake komin sa tun bayan tafiyar Amrah dayaga Zaitoon bata zo aikin ba bai sake gayyatan wata dan yi masa aiki ba, haka kuma itama bai neme ta ba sbd yasan dole ne taji babu da'di bayan sharrin sata da Amrah tayi mata...sannan itama Ammi fushi tayi ta ki sake tura musu mai aiki domin acewar ta bazata ringa mika yaran mutane ana binsu da sharri ba._ _Ban iya 'daga idanu na dube shi ba kawai nace" Yayan Marwa Barka da safia"_ _Bakin sa kawai ya motsa sai numfashin sa da ya fito da sautin murmushi, dan har ga Allah furucin nata ya basa daria, bata ta6a yi masa suna ba tun zaman ta gidan sai yau kadai yau din ma..." Wai Yayan Marwa.."._ Ya sake nanatawa cikin ransa. _Dama nasan bazai amsa ba..ba yau ya saba min irin hakan ba._ _Kitchen kawai na wuce dan fara aiki na duk da nasan ba shine ainahin abinda ya kawo ni ba, amma yadda naga 6angaren ya canza ya zam min dole in canza masa yanayi..." An aiko ki ne hala..?"_ _Ya jefa min tambayar yana sipping ruwan tea dake cikin wata mug a hannun sa._ _" Aiki nazo yi kawai"._ _" Fa'di gaskia ke dai, ai kin me zakiyi bacin kin riga kin korar min mata..?"_ _Ya yi mata tambayar yana kawar da kansa gefe a kokarin sa na 6oye murmushin da ke saman fuskar sa domin yasan dole zata waigo._ _Ai kuwa da sauri na waigo._ _" Ni kuma na koreta...?"_ _Na tambaya da idanu na waje sosai._ Kai ya jinjina min kawai ya mike ya nufi dakin sa. _Kalaman san nan sai suka 'kara sanyatar min da jiki na..kaddai dagaske gani yake ni 'dince na korar masa mata, bazan manta ba haka kwanaki ya ta6a furta min ranar da ya dawo dani gida._ Idan da gaske ni din ce ya _zanyi yi..Allah ma bazai barni ba fa._ _Sosai na sake tsorata...haka na fara aikin cike da rashin natsuwa amma dai hakan bai sa nayi abinda ba shine ba._ _Ina tsaka da aikin har ma na mance batun da ya kawo ni ina ta tunanin Amrah da tausayin ta sosai musamman da nasan cewa tana da juna, kamata yayi ace tana tare da mijin ta a wannan halin amma hakan bai samu gareta ba._ _Ina tsaka da tunani kawai naji alamun anbude bude kofa...nasan lokacin fitar sa office ne yayi._ _Take komai ya dawo min lokaci guda._ _Da sauri na dawo bakin kitchen 'din na tsaya ina gani yana nufar 'kofar da zata fitar da shi amma sai na rasa 'kwarin gwiwar tunkarar sa, ta ina zan fara yi mai bayani ne ban sani ba._ Shima daf da zai fita ya kamar yasan ina kallon sa sai ya waigo...ga mamakin sa Zaitoon ce, kuma shi take kallo. Gira ya 'dage mata duk biyu da alamun tambaya cikin idanun sa. " _Wani abun kike so ne_ ...?" Na tsinkayi muryar sa yana fa'din hakan. Da sauri na girgiza kaina ina maida dubana izuwa 'kasan tiles. " Ko nii...?" Ya sake fa'da yana nuna 'kirjin sa da hannun sa 'daya. Take sai kuma ya juya gaba daya ya fuskance ta. " Ohh na gane...kin korar min mata sai kuma kizo kina kalle mata miji ko, ya miki ne ki fa'da...?" " _Ko ka'dan, banga abinda zai min ko ya birge ni tattare da shi ba..."_ Na bashi amsa cike da kwarin gwiwar da nasan iya baki ya tsaya, duk da inajin fargaba, rashin ha'duwar mu kwanakin da suka gabatan nan yasa nake ganin sa daban da baya a yadda nake ganin sa da kuma yadda mu'amalar mu take kasancewa. " Kin tabbatar...?" " Fiye da zaton ka...". 'Yar murmushi yayi kawai ya juya batare da sake fa'din komai ba..taku biyu yayi uku naga alamun kamar dagaske tafiyan zai yi hakan yasa na budi baki da 'kyar nace..." In baka shawara...?" *Drop ur comment* *From the writter of CAPTAIN ABBAS & NOORUL (Haske na)* _Salmerh_ 😘 [16/10/2022, 9:03 am] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Wattpad@* _Serlmerh-md_ 🅿️ *...50* ......" In baka shawara?" Cak ya tsaya da tafiyar duk da kuwa naga alamun cikin hanzari yake kasantuwar shigan lokacin da ya riske shi ya kuma haifar masa da makara, yana da ba'kin da zasu gana da wannan safiyar ne shiyasa kuma hanzarin nasa ya sake ta'azzara. Ban jira ya juyo ba na 'dora da fa'din " Kar ka hau motar nan taka yau ka fara bincika ta tukunna...". Cikin tsanaki ya juyo ya dube ni cike da tsananin mamakin jin kalaman baki na, yayin da zuciyar sa ke sake shiga ru'dani amma ya basar. Yayin da ni kuma nayi 'kasa da kaina dan bana san 'kwarin gwiwa ta ta barni. " Hakan shawara ce...?" Da kai na bashi amsa alamar" erh". ".. _Bisa wani dalili kenan?_ Sai kuma ya girgiza kansa ya canza maganar da fa'din" _I mean hujja_ ...?" Shiru nayi, na rasa ma me zance masa ne. Da gaske ya kamata ace ina da hujja kafin bashi shawarar saboda gudun abinda ka iya zuwa ya dawo amma..amma ai hujja ta tanadaddiya ce, tabbbas ina da hujja amma shin idan na fada zai fahimce ni ko kuwa..?" Na tambayi kaina. Toh ma idan bai fahimce ni ba rayuwar waye take cikin ha'dari..? shine! Idan bai 'dauki shawara ta bama kansa ya yiwa ba bani ba. Wata 6arin zuciyar tawa ta ayyana hakan. Sai dai bazan so faruwar hakan ba sam, ko bakomai shi jinin Ammi ce, bazan so ganin ta cikin 'kunci dai- dai da 'kwayar zarra ba, kuma na tabbatar duk ranar da akace babu shi na tabbatar Ammi sai ta shiga wani hali. " Ni dai dan Allah.."! Na tsinci la66ana na motsawa wajen furta hakan cike da marairai ta batare da na shirya ba. Kallo na ya tsaya yi batare da ya furta wata kalma ba. A hankali kamar bansan maganar nace" ka canza masu kulawa da ku.." Bansan meyasa ba amma haka kawai naji zuciya ta bata amince da su ba, duk da bansan inda 'karshen maganar zai tsaya ba amma ni dai inaji araina in fa'da masa koda hakan zai iya sanadin tawa rayuwar ne, zan yi ne saboda Allah da kuma Ammi. 'Dan ha'de rai Rayyan yayi da alamun wani sabon mamakin kuma, sai dai maganar tata ya hana mamakin nasa bayyanuwa. Wai.. _masu kula da kai..._ me yarinyar nan ke nufi? Tana nufin su Huzaifa zan canza ko me?.. Ya tambayi kansa. Yaushe ma na basu damar bibiya ta, yaran da a yini bai fi mu hadu sau biyu ba, gidan ma yaushe suke shigowa sam bai amince da cewar su bayyana kansu matsayin masu bashi kariya ba, a ganin sa babu kariyar da tafi ta mahallici, amma duk da hakan bazai watsawa Ammi kasa a idanu ba kamar yadda ta bukata, hakan yasa ya barsu a matsayin da suke kai ake kuma biyan su. Kawar da kansa gefe yayi batare da ya sake furta komai ba. Hannun sa ya 'dago ya dubi agogon sa sai kuma ya saka yayi waje. Nayi tsayuwar fin mintina ashirin bayan fitar ban iya na sake motsawa ba, tunani na ma sai ya hargitse gaba 'daya. " Me ma na fa'da ne?" Na tambayi kaina a fili. A hankali duk abinda na fa'da masa suka fara dawo min. Ro'kon Allah nake Allah yasa ban furta abinda zai zame min matsala anan gaba ba. Tsabar shiga ru'du ban ma san lokacin da ya bar gidan ba, sai uban sara da kaina yake. Tuno wani abun ya sani fita da sauri na fito harabar gidan...wajen ajiyan motoci na duba ga mamaki na motar bata nan. Wani sara naji kirjina ya min. Kar dai bawan Allahn nan bai 'dauki shawara ta ba..?" Wata zuciyar tawa ce ta amsani da fadin..." baki fa'di abu da 'kwakkwaran hujja ba taya zai 'dauki shawarar ki..?" Innalillahi amma ai ni na gani da ido na, naga mutum 'karkashin motar sa sannan kuma ya fito yayi 'yan dube dube kafin ya 6acewa gani na. Sai da safiyan nan ne ma dana zurfafa tunani naga yanayi da zubin sa kamar 'daya daga cikin ma'aikatan sa ne, duk da bawai sanin tsab nai musu ba amma yau da gobe ta wuce wasa. Ciki na koma jiki na sanyi 'kalau, ba 'karamin haushi ya bani ba, amma hakan bai hana ni nema masa kariya wajen Ubangiji ba. Sai da na kammala aikina tsaf kafin na baro sashen da tunanin makomata. " Shiyasa kika ga duk jiki na yayi sanyi, Wallahi Marwa inajin tsoro sosai sam hankali na ya kasa kwanciya ban kuma san dalilin ba...". Ga mamakin ta sai taga Marwa tayi dariya sannan tace" Ba mamaki tsoron hukuncin da Yah Rayyan zai miki ke jefa ki cikin fargaba...". Idanu na bu'de ina duban ta. " Ban ga fa kin tsorata ba Marwa? Bakya tsoron abinda zai iya samun yayan ki...?" " Ni kuwa nake ji Zaitoon, ba ma ka'dan ba..sai dai nasan a kowani lokaci Allah yakan bamu kariya ne saboda isar sa ya kan kuma sawa wani abu ya riske mu wanda zamu koka da shi wannan ma saboda isar sa ne.." Sosai na gamsu da bayanin ta duk da hakan sai naji ina son tunatar da ita sharri irin na 'dan Adam da kuma amfanin kiyaye wasu abubuwa kafin faruwar su baya ga haka ma ina jin shakka kan zancen da muka yi da shi, kar ya fassara ni ta wani 6angaren ko kuma ya tuhume ni akan sa. " Amma Marwa....." Da sauri ta tare ni. " Kar ki wani ji kin damu, ina dai kin sanar da shi kuma kin tabbatar ya jiki..?" Da kai na amsa ta. Kuma kin tabbatar ya saurari abinda kika fada...?" Wannan karan ma da kai na bata amsa. " Zai kiyaye..Insha Allahu babu abinda zai samu Yah Rayyan...". Cikin zuciya ta na amsa da Allah yasa. Yayin da a fili kuwa na jefa mata tambayar..." Amma dama kuna da makiya ne da suke yi muku zagon kasa a rayuwa..?" Kai Marwa ta jinjina gami da fa'din sosai ma, baki da labari ko...?" " a a...ban sani ba wlh amma daga abinda ya faru jiyan nan na fara zargin wani abu, kuma tsoro ya cika min zuciya..." Murmushi Marwa tayi...idanun ta na cikowa da 'kwalla. Da sauri ta dafe kanta da duk hannuwan ta biyu a 'ko'karin ta na son 6oye yanayin da ta shiga. " Kiyi hakuri idan tambaya ta ta bata ranki ne Marwa, ba nufi na in 'kona miki ba..". Na fa'da cike da sanyi bayan fahimtar halin da Marwa ta shiga. Tsawon mintina biyu muna ahakan duk 'din mu babu wanda ya sake fa'din komai kowa abinda ke cikin zuciyar sa daban. Bangare na ni kam mamaki da da nadamar tambayar da nayi mata nake, yayin da Marwa ke alhini da tunano abubuwa masu dama da suka shu'de cikin rayuwar su. 'Bangaren Rayyan kuwa, da fitar sa wajen motar ya tunkara ya 6ata tsawon minti guda yana 'karewa motar kallo. Jiya da yamman aka wanke masa ita gata fess da ita kamar yadda ya barta. Mamakin abinda Zaitoon ta fa'da masa yake sam ya kasa tantance manufar ta balle yasan gaskiya take fa'da ko a a. Shiga yayi ya dudduba cikin motar bai ga wani ba'kon lamari da zai sa mishi zargi ba. Ya kunna ta ya gwada komai da yasan rashin su na iya kawo barazana ga rayuwar sa amma bai ci karo da komai da ya dangancin hakan ba, dalili kenan da yasa shi tabbatar wa kansa cewar may be mafarki tayi ba gaskiya bane abinda take fa'da, ko kuma idanun ta basu gane mata da kyau ba. Batare da damuwar komai ba ya tada motar ya yi gaba abinsa. Ko da ya isa ga mai gadi tsayawa yai yayi masa tambayar ko akwai abinda yake zargin faruwar sa daga daren jiya zuwa wayewar safiyar yau ya tabbatar wa Rayyan cewa babu komai. Ya sake tambayar su Huzaifa aka tabbatar masa da cewar basu shigo ba rabon su da gidan tun jiya da yamma. Kansa ya jinjina gami da harba motar yayi gaba. Tuni ya watsar da al'amarin cikin ransa ya sawa ransa cewar shirme ne kawai na mata ba komai ba..ko kuma gani take fadin irin wannan maganar zai sa ta samu fada a wajen sa ne oho.. Ba 'karamin gudu yake shararawa bisa titin ba Allah Allah yake yaga ya isa ma'aikatar saboda shigewar lokaci ya tabbata yanzu haka ana nan dakon isowar sa. Yana cikin sharara gudun kwatsam sai ya hangi wani dattijo agaban sa yana dogara sanda da nufin tsallaka titi a cikin gari irin kano da wannan safiyar da jama'ah duk ke tururuwar tafiya bakin ayyuka da wajajen sana'ar su, ya tabbata ba 'karamin kuskure bane barin wannan dattijon ya tsallaka shi ka'dai. Sai da ma ya iso ya fahimci ashe ba tsufa bace tasa mutumin nan dogara sanda ba face rashin isashshen lafiya ta ciwon 'kafar sa ta dama. Yana isowa kusa da shi ya taka motar ya tsaya sannan ya fito da 'dan hanzari ya kama hannun sa yana fa'din Baba, ina zaka je haka da safiyar nan? titinnan yayi girma ka tsallake bayan ga yawaitar ababen hawa". " 'dan nan Magani zan kar6owa 'diyata a wancan 6angaren yau ta tashi da masassara ne ga shi dama lafiyar ba ta ishe ta ba shiyasa na yanke shawar zuwa da kaina". " Subhanallahi Allah ya rufa asiri baba". Yace cike da tausayin mutumin nan. Shi ya ya yiwa masa jagora suka tsallaka sannan ya ciri 5k ya bashi yace ya 'kara akan ku'din maganin. Yana kawar da idanun sa daga kan tsohon zuwa bakin titin da nufin samun damar tsallakawa idanun sa suka sau'ka akan wani abin al'ajabi. Motar sa ke fidda wani bakin haya'ki sosai kamar wacce ake 'kona taya ajiki abin mamaki kuma ta 'kar'kashin motar hayakin ke fitowa. Har hankalin mutane ya fara dawowa kan motar, kafin yayi wani yun'kuri kuma lokaci guda wuta ta tashi da motar tamkar dai tashin Bomb. " Innalillahi wa inna ilaihi raji'un..." Ya furta a fili yana duban motar da cikin 'kan'kanin lokaci da faruwar lamarin amma tuni ta fita a kammanin ta ta yadda bazata iya 'kara amfanuwa ba. Abin kamar al'amara kamar cikin mafarki. Lokaci guda maganar Zaitoon ya dawo masa. Kansa ya dafe yana komawa baya ya jingina da jikin wata motar da ta parking daura dashi sakamokon abinda ke faruwa. Duk yadda aka so tsaida wutar da ke ci cikin motar abin ya faskara ana ji ana gani motar nan tayi 'kurmus. Abinda ya fara zuwa masa shine " da fa yanzu da shi cikin motar nan...Yah Subhanallahi.." Dattijon nan da shi ka'dai ya san cewa motar tashi ce shine ke ta bashi 'kwarin gwiwa a tunanin sa Rayyan ya shiga ru'du ne sbd asarar motar da yayi. Sa6anin tunanin Rayyan da ya tafi gurin tantance faruwar lamarin da ma'kasudin sa. Baya so ya zargi kowa duk da yake har gobe bashi da wanda zai zarga 'din kuma har zuciyar sa baya so ya amince da zancen Zaitoon a ganin sa zai zama ne tamkar rashin tawakkali. Abin dole cikin biyu 'daya ne. Amma yafi bawa zuciyar sa tabbacin duk faruwar lamarin shirin ubangiji ne. Hatta zancen Zaitoon bai yadda ya kama zuciyar sa sama da hakan ba. Allah ne ya 'kaddaro ya kuma tseratar dani na ku6uta batare da nasan hakan zai faru ba. Abinda ya tilastawa zuciyar sa rikicewa kenan. Ko lokacin da 'yan kwana- kwana suka iso tuni mota kam ta gama 'konewa. Bai 'kira kowa dan ya tallafa masa ba kamar yadda bai 'kira kowa ya sanar wa faruwar lamarin ba...hatta Ammi kuwa. Yana shirin taran adaidaita yaga gilmawar mota ta gaban sa a slow sakamakon 'dai'daikun mutane dake wajen har yanzu duk da kuwa yawa sun riga sunyi nasu waje amma still da mutane. Baya ka'dan motar da dawo bayan har ya shiga Adaidaitan suka ji 'karar horn da 'karfi, duk 'din su duban su suka kai wajen. " Fawwaz " Ya furta saman la66an sa. Fitowa Fawwaz yayi da sauri shima Rayyan ya fito daga adaidaita. Fawwaz 'din ne ya mi'kawa mai adaidaitan Naira 'dari biyu..hankalin sa na ga Rayyan da bai ma tanka sa ba sai motar Fawwaz 'din daya nufa. A hanya yake bawa Fawwaz labarin duk abinda ya faru a wajen ba 'karamin mamaki Fawwaz yayi ba..sai dai 'karshe hamdala kawai yake ta zubawa ga mahalicci da ya ku6utar masa da aboki. Sai da ya sau'ke shi a office 'din su kafin ya wuce asbiti wajen aikin sa. Duk da yake ba'a nitse yake ba sannan ya makara sosai amma duk hakan bai hana shi shiga meeting 'din dan zantawa da bakin nasa ba. Ya kuma yi 'ko'karin yin komai bisa tsari da natsuwa yadda ya kamata. Ammi na can Abuja labari ya riske ta na abinda ke faruwa wanda ta samu labari daga bakin wani abokin 'dan ta marigayi Muhammad Kabeer. Sosai ta shiga tashin hankali. Abinda ya 'kara 'daga hankalin nata kuwa shine rashin samun Rayyan da bata yi ba, wayoyin sa duk na cikin motar lokacin da ya fita ga wannan dattijon shiyasa ta kasa samun sa. Sau'kin ta 'daya a ranar ta yi niyyan dawowa gida dama, ai kuwa batare da 6ata lokaci ba ta tattara ta nufi filin tashi da saukan jiragen sama. Ita ka'dai tasan halin da zuciyar ta ke ciki a wannan lokacin. 'Bangaren su Zaitoon kuwa..'karar wayar Marwa akaro na biyu shi ya sake 'daukan hankalin su gaba 'daya. Har ila yau 'din dai Sultan ne. Sai dai wannan karan batare da 6ata lokaci ba ta 'daga 'kiran...kawai sai ta sanya mishi kuka. Kukan da tun 'dazun take faman dannewa. Da kyar Sultan ya lallasheta tayi shiru, ita kanta Zaitoon dake Zaune gefe sai da taji 'kwalla ya zubo mata, duk da bata san dalili ba amma haka kawai sai taji rauni gaba 'daya ya mamaye ta. Ko da Sultan ya tambayi Marwa abinda ya sata kukan bata 6oye masa ba, a zahiri hankalin Sultan ma ba 'karamin tashi yayi ba har Marwa sai data fahimta 'karshe kwantar mata da hankali yayi yace bari ya nemi Rayyan din yaji meke faruwa. Haka Marwa ta share hawaye kamar yadda ya bu'kata ta kuma sawa ranta ruwan sanyi, dan sosai taji ta gamsu da kalaman Sultan 'din. Yayin da 6angaren Sultan murmushi yayi, 'dayan wayar sa dake hannun sa ya 'dago yana sake kallo akaro na babu adadi, abin mamaki Rayyan ne, da motar sa lokacin da take 'konewa, an 'dauki takaitaccen video ne na abinda ya faru har zuwa lokacin da Rayyan ya bar wajen cikin motar Fawwaz. Da sauri Sultan ya kife wayar yana lumshe idanu gami da 'daga kansa sama ya fitar da wani zazzafan huci a fili ya furta" Shegen ya tsallake...wannan karan ma bai fa'da ba...sam na gaji, na gaji da ganin ka kana shawagi agabana, na gaji da ganin ka kana tauye ni da hana ni fantamawa...."! 'Dayan wayar sa ya 'dago yy 'kiran wata number yana mi'kewa tsaye. Bakomai ya sanar ba face " zan shigo, dole a yau zan dawo ko zuwa gobe...ka shirya sabon shiri zamu 'dauko...". Haka ya furta cikin wayar sannan ya rabata da kunnen sa. Gaba 'daya kamannin Sultan ya canza ba kamar yadda yake ba. Marwa na ajiye wayar tata kafin ta sake wata magana wani 'kiran ya sake shigowa. Wannan karan Anty Raihana ce ta 'kira, itama ba komai ta sanar da Marwan ba face ta nemi wayar Ammi bai tafi ba. Marwa tace ai kuwa da safen nan munyi magana da ita amma da yake yau zata dawo ba mamaki sun taso ne shiyasa wayar ta daina tafiya. " Toh Allah ya iso da ita lafiya..." Cewar Raihana cike da gamsuwa. Inda ta 'kara da fa'din" Sai naji muryar ki wani iri Marwa ina fatan dai lafiya..?" Gyaran murya Marwa tayi da sauri tana fa'din" babu komai fa Anty Raihana kawai dai 'yar mura ke damuna kuma already ma nasha magani..." " Allah ya 'kara afuwa toh nima zuwa nextweek zamu dawo north 'din hutun karshen shekara na matsu in dawo wallahi, I so much missed u guys..." Wani ihu da Marwa tayi na farin ciki har saida Anty Raihana ta cire wayar a kunnen ta tana dariya da shirmen Marwa 'karshe ma tsinke wayar tayi gaba 'daya. Wannan albishir 'din na Anty Raihana shi ya faranta ran Marwa har ya sa ta saki ranta murmushi ya wadaci fuskar ta. " Na kasa 6oye farin ciki na, kinsan rabo na da Anty Raihana, tun bayan bikin mu da tazo ban kara ganin ta ba". Tayi maganar tana duban Zaitoon. Kai Zaitoon ta jinjina tana fadin " Lallai, dole kiyi murna, itama 'diyar Ammi ce ko...?" " erh mana ita ke bin Yah Rayyan fa..." " Na kasa ganewa, shi kuma mijin ki fa, ina nufin Yah Sultan..?" " Ohh..shi..?" Marwa ta tambayi Zaitoon tana 'yar daria. " Wannan ma 'dan Ammi ne amma ba ita haife shi ba shiyasa ma kika ga har munyi aure da shi..a yadda muka samu labari wai Abbah ya fito sallar asuba ya tsince sa a 'kofar gida tun yana jinjiri, muma bamu san wannan labarin ba har sai lokacin da ya nuna yana son aure na kafin maganar ta fito dan har girman mahaifan mu basu bari munsan da wannan batun ba duk da kuwa akwai bambamcin kamanni ta zahiri tsakanin mu da shi...tausayi da kuma kaunar da bansan ina masa ta sa na amince da auren sa duk da yake da farko ba ni ya fara so ba 'yar uwata Safaa ya fara nunawa 'kauna kafin rasuwar ta...." Ba 'karamin mamaki Zaitoon tayi da jin wannan labarin ba, domin in ba sani kayi ba abu ne mawuyaci ka iya fahimtar cewa babu wata ala'ka ta jini tsakanin Sultan da Ammi sbd yadda ta ha'de kansu duk da juye mata izuwa sirki amma in ba fa'da maka akai ba bazaka ta6a kawo wa cikin ranka cewar Sultan 'dan tsintuwa ne agidan ba. ****** Asalin Sunan Mahaifin mu Alhaji Sa'ad Auta, 'dan asalin nan garin Kano ne....sun ha'du da Ammi Aseeya ne wajen wani taron musaba'ka da akayi na jahohi su Ammi ne aka turo daga jihar Borno inda akayi musaba'kar a Kano, nan Abbah yaga Ammi daga baya ya bibiye ta ya nemi mahaifin ta suka gana 'karshe har suka yi aure bisa ga umarnin iyayen ta kuma Alhamdulillah lafiya lau suke zaune agidan sa ta cigaba da karatun ta dan sunyi aure ne tun tana cikin shekarun 'kuruciya shi kuma ya girme mata sosai amma hakan bai sa yayi amfani da shekarun sa ya tauye ta ta kowani fanni ba. Kannen Abbahn mu ne Kawu Sufyan sai 'karama Anty Madeena, kuma tuni tayi aure ma sai dai Allah bai bata rabon haihuwa ba, haka ma Kawu Sufyan bashi da 'da ko guda amma duk sun mika lamuran su ga mahallici dan sun san shike badawa kuma shike hanawa. Yayin da Ammi take ita 'kwara 'daya tal a gaban mahaifan ta daga sai 'yar mage da ta kasance mata abokiyar hira. Tun tasowar ta ta tarar da mahaifiyar ta na kiwon mage kuma ko wani abu ya samu wacce take dashi din ta kan dauko wata amma bata ajiye fiye da 'daya. Hakan yasa Ammi sha'kuwa da mage sosai ko lokacin da tayi aure taso ta 'dauko a gidan ta sbd kaunar ta da su amma Abbah yace sam baya so, ta 'dauki abin wasa inda ta nemo wata 'yar kyakyawa 'karama ta kawo da tunanin ai idan yazo ya ga ta riga ta kawo zai hakura ya barta da abinta. Bata ta6a sanin cewa jinin sa ne baya son abin ba har sai da ya dawo gida taga halin da ya shiga abin ya ru'da ta sosai fatan jikin sa yayi rudu rudu idanun sa suka firfito da gaba 'daya ta rude ta fara kuka da 'kyar yayi mata bayanin abinda ya kawo hakan, tun daga ranar da ta cire a gidan ta bata 'kara kawo ta gidan ta har yau 'karshe itama sai taji ta daina birgeta dan ko wajen mahaifiyar ta taje da tuni sunan ta ya juye izuwa maman Mage bata sakewa da abin sai taji ta takura ta sai ta baro gidan tukunna. Daga baya ta fahimci ba Abbah kadai bane, hatta su Kawu Sufyan da Anty Madeena ma hakan ke faruwa dasu matukar suka hada muhalli daya da mage kuma haka yaranta ma dan Kabeer da Rayyan sun tama fuskantar irin matsalan nan. Sai kuma Su Safaa suma a gidan Dada dake daura da su... Da farko Anty Madeena can Gombe take zama farkon auren ta, sun kuma zauna a Bauchi daga baya suka dawo nan Kano da zama gaba daya, ganin basu samu rabon haihuwa bane ya sanya maigidan ta sake wani aure bisa ga amincewar Anty Madeenan cikin sa'a kuma sai Allah ya azurta shi da samun 'diya mace shekara guda bayan auren nasa, yarinya ta ci suna Badi'a shekara hudu bayanta aka sake haifan Imran...yadda Anty Madeena ke nuna 'kauna ga yaran ya sanya a hankali rikon Badi'a ya dawo hannun ta duk da yake gidan su ba 'daya ne da abokiyar zaman tata ba kuma akwai fahimta sosai a tsakanin su. Sa6anin Anty Madeena kuwa 'dan uwan ta sosai ya samu yalwar 'ya'ya dan yaran sa biyar ya haifa, Muhammad Kabeer shine babba sai Muhammad Rayyan, Muhammad Sultan da aka tsince sa lokacin da Ammi ke da 'karamin cikin Raihana, tsintar sa da watanni bakwai kafin Ammi ta haifi Raihana sai Marwa da Safaa da ta rigamu gidan gaskiya. Dalili kenan da ya sanya yaran sa suka kasance shida sa6anin biyar da ya haifa. Su Marwa sun kasance sune auta a wajen mahaifan su, kamar yadda suka kasance 'yan biyu ka'dai da Ammin su ta haifa. Wani aiki ne ya kai Abban su 'kasar saudiya tsawon watanni takwas wanda tafiyar ta ha'da hadda Ammi a lkcn tace bata san ma tana da cikin su ba har sai da suka isa can...kafin hakan ta jima da cire rai da samun wani haihuwa arayuwar ta dan Raihana har na da shekaru bakwai da haihuwa tuni an barta zaman autar Ammi kwatsam sai ciki ya sake bayyana mata. Sun yi ma'tukar farin ciki da kyautar da Allah ya basu haka aka cigaba da rainon cikin su acan Saudia cikin kwanciyar hankali, Ammi ta haife su ne washegarin da aka fara aikin hajji a wancan shekarar dalili kenan da ya sanya suka yanke shawarar sanya musu suna Safaa da Marwa. Sun taso cikin gata da 'kaunar yayye da mahaifan su, wanda Allah cikin ikon sa daga kansu Ammi bata sake haihuwa ba. Kabeer yayi auren sa na fari a lokacin da suke Jss3 ita da Safaa...tun farkon auren sa ya so ya 'dauki 'daya daga cikin su amma Ammi bata amince masa ba, sai dai daga baya Safaa da suka sha'ku da matar sa sai take yawan zuwa musu, watarana ma har kwana take acan, 'karshe ma taso tarewa gidan na sa gaba 'daya saboda ita Allah ya zuba mata tsananin ma'kon 'yan uwan ta sosai tai wa Marwa zarra ta wannan 6angaren. Sai da Ammi ta tsaya tsayin daka kafin ta samu daidaituwar zaman Safaa waje guda a hakan ma duk weekend can take yini abinta. A wancan lokacin Rayyan na karatu a wajen 'kasar nan wanda Ammi ta tura shi badan yana so ba. Da safaa ya tattauna batun tun kafin tafiyar sa har itama Marwa ta samu labari daga bakin Safaa anan nema tasan ra'ayin sa sun kuma tausaya masa, domin duk cikin su babu wacce yafi sha'kuwa da ita irin Safaa sosai yake zama yayi hira da ita ba kamar Marwa ba da tun asali gaisuwa ka'dai ke ha'da su amma duk da haka ba 'karamin 'kauna ke tsakanin su ba. Salmerh😘 [16/10/2022, 9:06 am] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Wattpad@* _Serlmerh-md_ 🅿️ *...51* .......Shekara biyu da auren Yah Kabeer Allah ya azurta shi da samun 'karuwar yarinya 'diya mace 'kyakkyawa da ita. Ranar suna yarinya taci sunan Ammi Wato Aseeya amma muna 'kiran ta da _Zamrud_ ... Tun haihuwar Zamrud duk wata 'kauna da soyayyar mu muka tattara muka 'daura akanta, hatta Rayyan da ba 'kasar yake ba ba'a barshi abaya ba, ya kan kira Kabeer lokacin da ya tabbatar yana gida suyi videocall kawai yai ta surutu da Zamrud tana sashi daria. A lokacin ka'dan ya rage mana mu kammala secondary ni da Safaa domin Yah Kabeer cewa yayi baza muyi SS3 ba har ma mun yi registration na Jamb saura mu rubuta..tun wajen cike Jamb 'din kuma muka samu bambamcin ra'ayi...ni na kasance babban burina shine na karanci accounting yayin da ita kuma Safaa take son karantar fannin journalist. Duk cikin mu babu wanda aka tauyewa ra'ayin sa...duk din mu ra'ayoyin mu muka bi sai dai still an samu bambamcin samun makaranta. Safaa nan Kano ta samu BUK yayin da ni kuma nasamu admission a jami'ar ABU dake Zaria. Ammi taso hana mu rabuwa da juna amma Abban mu yace a a ta bari ai kowa da nashi kaddarar yake tafe, kasancewar mu 'yan biyu bashi zai sa komai na rayuwar mu ya zam iri 'daya ba. Shi in a ra'ayin sa ne ma aure zai mana kamar yadda ya yiwa Anty Raihana da gama secondary ya aurar da ita acan gidan ta ta yi karatun ta ta gama kamar dai yadda ya kasance da Ammi kuma ba gashi tana aikin ta cikin kwanciyan hankali ba, sai dai ganin zamani ke 'kara bu'dewa ya sa mu 'din ya bamu dama. Da wannan kalma ta mahaifin mu suka samu damar tafiya makaranta amma zuciyoyin mu cike da alhinin rabuwa da juna. A lokacin Sultan ma na 'ko'karin ha'de degree 'din sa fannin Computer engineering shima anan BUK yake...dan ko da Abban yai masa tayin fita 'kasar waje kamar dai Rayyan amma Sultan 'kin amincewa yayi, acewar sa gwara ya zauna yana ringa sanin halin da ahalin sa ke ciki. Sosai Abba yayi na'am ya kuma yi farin ciki da wannan batu na Sultan dan sosai yaga hankali da hangen nesan sa ba wai dan sauran yayyen nasa sun gaza ba a a kawai dai ganin sa na 'karami cikin su amma yasan abinda yafi dacewa...kuma dole dama a matsayin sa na 'dan kasuwa ya nemi matallafi. Ammi ce ma taso nuna 'kin amincewar ta kan karatun Sultan a BUK 'din amma Abbah ya taka mata birki dan ba laifi Ammi akwai bragging tana so komai nata ya zam first class ne ita a rayuwa. Koda ya gama Degree 'din nasa a can Sokoto yayi serving 'kasar sa a lokacin dududu shekarun sa ashirin ne da biyu shi da Anty Raihanan mu dake aure a garin Kaduna shekarun su kusan na tafiya dai- dai ne, yayin da Rayyan yake ashirin da biyar zuwa da shida. yah Kabeer kuwa ya kai Talatin. Safaa da Marwa kuma suna 'yan sha shida ne kacal. Zaman Safaa a BUK tare da Sultan ya sa suka 'kara shakuwa sosai, kamar yadda zaman ta a gida ya 'kara sha'kuwar ta da sauran yayyen mu fiye da ni da sai nazo hutu. Hutun kawai ke kawo ni gida, wani sa'i hutun ma ba nan Kano nake dawowa ba kawai sai na wucewa ta Kaduna gidan Anty Raihana nayi hutu na acan. Muna shekara ta biyu a Jami'ah Yah Rayyan ya gama karatun sa ya dawo gida, yayin da Sultan ya kammala bautar 'kasar sa har ma ya fara aiki da Abban mu 'kar'kashin companyn su kamar Yadda Kabeer yake fama dan shi dama gaba 'daya fannin kasuwanci ya karanta ba dan komai ba saboda tallafawa kasuwancin mahaifin sa acewar sa. Shekarar da Rayyan yah kammalo karatun sa da 'yan watanni a shekarar Raihanan Mu ta haihu inda ta haifi yaro namiji mai kama da baban sa sak, misalta irin farin cikin da wannan family suka tsinci kan su aciki ma 6ata lokaci ne, ranar suna yaro yaci sunan Muhammad (kakan sa mahaifin Baban sa) amma ana 'kiran sa da Bassam. Yah Rayyan na dawowa da shedar kammala karatun sa Abbah yace sam bazai cigaba ba sai yayi aure shima tukunna, dan baya so suyi irin nashi ne kasantuwar Abbah bai ajiye iyali da wuri ba har da shekarun sa suka dan jaa kafin, so yafi so 'ya'yan sa su yi aure da wuri kafin shekarun su tasa, yana duba kansa ne dan tuni girma ya gama kamashi ahalin yanzu. Duk yadda Rayyan yaso zame wa batun abin ya gagara, dan Abbah be zo da wasa ba wannan karan tsaye yake kan batun sa babu ja da baya. Toh shi a lokacin ma takamammiyar budurwa baya da shi, yarinya 'daya yake kulawa wata course mate 'dinsa kuma itama saboda yabawa da hankalin ta da yayi ne har ya yadda suke abota. Ta hanyar schoolarship ta samu fita India karatu iyayen ta ba masu 'karfi bane akwai dai rufin asiri na Allah. Sunan ta Nadia 'yar asalin jahar Borno ce ta kasance daga cikin 'kabilar Barebari...tana da nagartattun halayen da ya tabbatar bazai yi da nasani ba ko da ya za6e ta a matsayin uwa ga 'ya 'yan sa ba. Ta kasance tamkar 'kawa ce gare shi lokacin suna school amma da jin batun Abban su ya nemi canzawa dangantakar tasu salo duk da yasan dama ita Nadia ta jima tana 'kaunar sa shine kawai bai bata fuskar bayyana masa hakan ba. Cikin lokaci 'kankani ya samu cikakkiyar kar6uwa, soyayya zazzafa 'kauna da kulawa daga Anty Nadia, sosai ya yaba mata ta wannan 6angaren bai 6ata lokaci ba wajen yi mata batun aure. Ta kuwa nuna amincewar ta dari bisa dari. Kafin ya bayyana ta ga mahaifan mu ne, su kuma suka fara yi masa zancen Amrah, dan itama a lokacin tana Jam'i a ne sai dai ita ba nan kusa take karatun nata ba ita a Maleysia take yi..Amrah ta kasance 'diyar abokin Abban mu ne kuma Ammi bata ki batun ba koda Abban ya sanar da ita kan cewa ya nemawa Rayyan auren Amrah farin ciki tayi sosai. Rayyan bai 'ki batun su Abbah ba kamar yadda bai fasa bayyana musu Nadia ba matsayin wacce ya riga ya za6awa kansa ba har ma ya yi mata batun aure, dan kokadan a rayuwa ba abu 'kalilan ke karya 'kwarin gwiwar Rayyan ba. Abbah ne yace duk za'a yi, batare kuma da matsala ba da iznin Allah, tunda ya riga yayi mata batun aure haka kuma itama Amrah Abba ya riga yayi magana da Mahaifin ta. Duk babu wanda za'a karyawa alkawari daga ciki acewar Abbahn mu. Inda ya shirya komai akan cewa za'a fara auren sa da Nadia kafin na Amrah ya biyo baya tunda ma ita yanzu take karatu mahaifin ta yafi so sai ta gama a yadda Abba ya fahimce shi. Su Abbah sun kai ku'din gaisuwan Rayyan a Maiduguri, su hu'du Abbah, da 'dan uwan sa Kawu Sufyan sai wani abokin sa Alhaji Rufa'i sai kuma Sultan da ya tu'ka su. A hanyar su ta dawowa ne 'yan fashi suka tare su anan nan gaba ka'dan da Wudil dan sunyi tafiyar dare ne basu yadda sun kwana acan Maidugurin ba...kuma tafiyar mota ce suka yi. Harbe Abban mu aka yi a cikin sa yayin da 'kanin sa Kawu Sufyan suka harbeshi saitin zuciya nan take ma yace ga garin ku nan. Sultan kuwa duka sukai masa sosai yayin da 'daya abokin Abban tun tsaida su da akayi ya suma hakan yasa basu bi takan shi ba sai bayan da komai ya lafa sannan ya farfa'do. Abban mu da 'kyar yake numfashi cikin azabtuwa da neman agaji...numfashin sa bai tsaya ba har sai da aka dangana shi da asbitin su Yah Rayyan da tun ganin sa da shi yanda ya jikkata ya rikice...duk wata jarumtar sa neman ta yayi ya rasa ta. Rayyan kasa ri'ke kukan sa yayi, yana kuka yana fa'din sai ya kashe duk wanda yy wa mahaifin sa haka..shi kam Abbahn mu murmushi kawai yake yi masa da haka fuskar sa da murmushi ransa ya bar gangan jikin sa gaba daya. Kwalla Marwa ta share da dan yatsanta yayin da wani hawayen ke sake biyo bayan yatsun ta. Ita kanta Zaitoon sai taji babu da'di, daga bakin su ta san cewa mahaifin su rasuwa yayi amma bata ta6a sanin cewa harbe shi aka yi ba. Bata san me ke damun mutanen mu na yanzu ba da 'daukan rai bai zama abin tsoro a gare su ba. Cikin ranta ta furta" Allah ya ji'kan Abbah ya gafarta masa.." Tana 'dauke hawayen idanun ta ta furta hakan itama. Moopy na kwance abayan Marwa a yadda take zaune bakin bed din ta ta 'dan ran'kwafo ahakan take bawa Zaitoon labarin ita kuma Mufeeda ta kwanta daga bayan ta tana 'yan surutan su na yara har bacci yayi gaba da ita. Ganin tayi baccin ne yasa Zaitun mi'kewa ta 'dauke ta abayan Marwa gami da kwantar da ita sannan ta koma gurbin da ta taso. Yayin da Marwa ta cigaba da raira kukan ta cike jimamin mahaifin su, hakika mutuwar iyaye ba 'karamin ta6a zuciya yake ba, kasa ma magana tayi illah kukan, Zaitoon ma hawayen take tana mai tausayawa halin da Marwa ta shiga. ***** Watannin Rayyan shida ne kacal da fara aikin likitancin sa kaddaran nan ta fa'dawa mahaifin su, Rayyan dake rungume da shi idanu ya tsura masa, sam ya kasa tantance abinda ke faruwa. Sai da likitoci suka yi aikin su dan shi kasawa yayi nan suka tabbatar da cewa Alhajin baya tare da numfashin sa. " Irin kukan da Yah Rayyan yayi bazan iya misalta miki shi ba kada ma Safaa taji labari, Sultan kuka kai subhanallah abin babu da'di gaskia...Allah ya ji'kan Abban mu...wlh Zaitun mun yi rashi sosai cikin rayuwar mu da bana jin zamu sake makamancin sa a duniyan nan". " Yah Rayyan yafi kowa shiga ru'dani domin kaf ya ajiye duk wani mazantakar sa ya bu'de zuciyar sa yasha kuka da rashin mahaifin sa. Tun a lokacin ya qalubalanci aikin sa na likitanci sbd a ganin sa bashi da wani amfani tunda har bai iya ya ceci ran mahaifin sa ba. Babu yadda Ammi batayi da shi kan hakan ba amma yaki amincewa, duk yadda ta so fahimtar da shi 'kaddara da kuma 'karar kwana, tace lokacin mahaifin sa ne ya riga yy bawai gazawar sa ba amma Yah Rayyan kasa fahimtar ta yy, 'karshe kauracewa tsaddaden asbitin da yake aiki yy, har bayan rasuwar mahaifin mu da kusan watanni biyu bai je aiki ba. Ammi da kanta daga baya tazo ta fahimci bawai kaddarar bace bae yadda da ita ba kawai dai aikin ne ya fice masa aka bugu da 'kari dama ba wai ra'ayin sa bane aikin duk da hakan bata gajiya da nasiha da nusashshemu akan rayuwa, tsoron Allah da kuma kyautata mu'amalar mu. Unfortunately kuma sai Yah Kabeer yazo masa da wani batu, domin shi ya fara gano wani boyayyen sirri game da mutuwar Abban mu, abin kamar shiryayyan al'amari ne ba haka kawai ya afku ba, sai da suka zurfafa sosai sannan suka fahimci tun da da'dewa akwai abinda mahaifin mu ke kokarin 6oye musu, sai dai duk iya binciken su sun kasa gano asalin menene kuma suwaye makasan mahaifin namu. Ranar Yah Sultan ya sha kuka, kuka fa ba kuka irin wanda ake yi na zahiri ba, kuka ne yy kamar ransa zai fita, kukan zuci mai sanya karaya da nakasta kwarin gwiwa, ya kuma yi da hawayen sa hatta wanda bai sanshi ba idan ya dube shi zai fuskanci yana cikin halin tsananin 'kunci. Wannan lamarin shi ya sake wargaza natsuwar Yah Rayyan da ma sauran. Babban damuwan su shine basu san ta inda zasu fuskanci lamarin ba...Sultan baiyi 'kasa agwiwa ba wurin bayyana abinda ya fuskanta ga Ammin mu duk da kuwa ba komai ne ya sani ba shima din suna dan 6oye masa wasu abubuwan, ita kam bata wani yi mamaki ba, domin ta jima da sanin akwai wani sirri da Abban mu ya jima yana 6oye musu wanda su basu san menene shi ba, tasha kama shi yana wayar sirri wanda galibi da ya ji motsin ta yake zabura ya kashe wayar, sau da dama tana kama shi cikin yanayi na damuwa, tagumi da kuma hawaye wasu lokutan, amma Abban mu bai ta6a bu'dan baki ya sanar da ita komai ba, 'karshe shawara ta bashi akan ya kai lamarin sa wurin ubangiji, tunda daga ranar bai 'kara 6ata daren sa yana bacci ba, zai yi sallah, ya 'daga hannu sama yana addu'ah yana hawaye, Ammi sosai take tausaya masa hakan yasa itama ta daina bacci, kullum takan taya shi raya daren sa wurin kaiwa kukan su ga mahallici, duk da bata san meke faruwa ba amma tasan zahiri akwai abinda ke damun sa kuma shi Allah maji ro'ko ne....abinda ka'dai zata iya tuna yana yawan ambata shine yarana, Yah Allah ka tsare min yara na, Aseeyah dan Allah ko bana raye ki kula min da yara na...." 'Karan wayar Marwa shi ya katse ta daga labarin da take bawa Zaitoon inda duk 'din su ga wayar suka kai duban su. Ganin cewa Ammi ce kiran yasa Marwa saurin 'dagawa. Dawowar ta kawai ta sanar da Marwa ta katse watar dama abinda ya sa ta kiran kenan. Batare da 6ata wani dogon lokaci ba Marwa ta mike musamman ma yadda tajiyo muryar Ammi wani iri. Tana nufar kofa take sanar da Zaitoon cewa ina zuwa Ammi har ta iso gida. Masha Allah kawai Zaitoon tace batare da tayi niyyar mikewa, domin a irin wannan lokacin bata cusa kanta inda suke, zata je yiwa Ammin barka da isowa amma sai ta dan huta tukunna zuwa anjima kadan sai taje...hakan ne yasa ko yun'kurin bin bayan Marwa batayi ba. " Ammi barka da isowa..." Marwa ta fada gami da zama gefen Ammin. Bayan gaisuwa da shiga tsakanin su abu na gaba da Ammi ta furta shine 'kira min wayar yayan ku ina kiran sa baya tafiya tun 'dazun. " Ai kuwa haka Yah Sultan ma yace layukan sa duk basu tafiya...amma bari in dauko wayar mu gwada muyi comfirming..". Ko da koma 'dakin ta dan 'dauko wayar bata tara da Zaitoon ba hatta Mufee da tasan bacci take ma Zaitoon.bata barta ba 'daukan abinta tayi suka koma 'dakin su. Batare da wani dogon tunani ba Marwa ta 'dau wayar ta koma ga Ammi. Koda suka kira din kuwa still numbers din sa basu tafiya. Hankalin ta ba 'karamin tasho yayi ba. Ga Landline ta koma ta kira numbern office 'din sa direct nan ma ba'a 'daga ba, ta kira kusan sau uku sannan aka sanar da ita baya kusa tambaya tayi amma yana lafiya akace mata erh. Tace dan Allah anemo mata shi yanzun nan tana son magana da shi. Tsawon mintina talatin taji shiru kawai sai securities 'din sa suka zo ranta, take ta lalubo Huzaifa a waya abin takaici wai ai shima kwata- kwata yau 'din basu ma hadu ba bai fito aiki ba...bacin duk karshen wata ko kwana guda ba'a 'karawa ake biyan su albashin su. Umarmi ta bashi ma duk inda yake yazo gida ya dauki mota ya je office din su Rayyan ya dauko shi zuwa gida ko kuma daga can inda yaken ya wuce sai su dawo tare. _( ~Mu dai babu ruwan mu, Ko Marwa bata cigaba da bamu labarin ba zamu binciko da kanmu mu cigaba....~ 🤪)_ *A cigaba da gashi....* 👇🫶 Salmerh 😘 [16/10/2022, 9:06 am] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Wattpad@* _Serlmerh-md_ 🅿️ *...52* _.......Cigaban labarin._ Abban su na da zurfin ciki, taurin kai da kuma kafiya akan abu shiyasa itama Ammi bata tsanantawa kan tambayar sa abu domin tasan in ba niyya yayi ba he won't tell her anything. Abinda kawai bata sani ba shine takamammen dalilin da ya sa aka kashe shi, wannan kuwa bata 'dorawa kowa laifi ba...amma batun da Sultan yazo mata da shi ya matu'kar jijjiga ta ashe da dagaske akwai abinda Alhaji ke 6oye mata ba hasashen ta bane kawai ba. Sai gashi Sultan ya fara bincikowa domin haka ya nuna mata tamkar shi kadai yake binciken as in shi yafi damuwa da lamarin Abbah fiye da sauran. Kai Ammi ta fara juyawa tana kuka sosai, Sultan bai ma san ya bu'de baki cike da mamakin Ammi ba sam bai san yayi hakan ba, cikin ransa ya ayyana shi kam ya gama kuka ai tun daren ranar da ya ci karo da lamarin da yake zaton suke 6oye masa har Ammi, ba 'karamin aiki ke gaban sa ba a halin yanzu bayada lokacin 6atawa wajen kuka. Duk da ba shi da cikakken labari kan binciken da yayyen nasa ke yi amma dole sai ya san inda suka dosa, shin dagaske binciken suka fara ko kuwa, shin sun samo wata alama ko kuwa, son sanin hakan yasa yazo ga Ammi da tunanin ko zaiji wani abu daga bakin ta, dan shi 6oye masa suke da tunanin shi yaro ne, yayin da shi kuma yake gani kamar suna 6oye masa ne sbd kasancewar sa bare a cikin su. Kuma ko wayar Abbahn nasu already tana hannun Rayyan ne, duk da Sultan yaso ya riga kowa samun wayar sbd wani dalili nashi amma hakan bai samu gare shi ba. Shigowar sa kenan ya tadda Sultan da Ammi na tattaunawa a palorn ta dake sama. Sosai jikin sa yayi sanyi, musamman da ganin yadda hawayen Ammi ke zuba 'kasa abanza. Nan take jijiyoyin kansa suka fito sosai, sai idanun sa da suka yi ja, a hakan ya zubawa Ammi idanun sa, yana kallon hawayen ta dake 'diga, fatan sa Allah yasa ba gaskiya bane abinda yake zargi, in kuwa hakane yayi al'kawarin koma waye ke da hannu cikin mutuwar mahaifin sa bazai barsa ba. Da sanyin murya Sultan dake gaban ta yace" Please mana Ammi ki daina kukan haka nan...ni ya kike so inji idan ke da kanki kina shiga irin wannan halin a yanzu..." Ya 'karashe maganar yana sunkuyar da kansa gami da shafo kan nasa da duk hannayen sa biyu, duba 'daya zaka yi masa ka fahimci cewa yana da babban damuwa a zuciya. "..Sultan" Ammi ta 'kira sunan sa cikin tsananin karayar zuciya. Bai amsa ba illa kai daya 'dago yana duban ta. "...Dan Allah Sultan yadda ka fara binciko abin nan kai ka'dai ka rufa min asiri ka binne shi kai ka'dai kar 'yan uwan ka suji, Sultan mahaifin ku ya shafe shekaru a 'kalla uku yana jaddada min amanar ku..dan Allah kar ku saka kanku cikin abinda zai zo ya dame mu har in kasa ri'ke amanar da Alhaji ya bar min..." Shi kam Sultan ido ya tsura mata na tsawon mintina biyu...a hankali da sanyin murya yace " Ammi..!" " Na'am Sultan dan Allah ba dan ni ba ka bar wannan zancen kaji.." " Kai Ammi don't tell me kinsan komai dama kike 6oye mana tun ba yanzu ba...." Kai tayi saurin girgizawa sannan tace" Koka'dan Sultan ban san komai ba, amma na jima da fahimtar mahaifin ku na cikin tsananin damuwa amma kasan halin sa, bai ta6a ko kwatanta sanar da ni damuwar sa ba...sai dai nasan babu abinda Mutum ya isa yayi wa wata halitta matu'kar ba Allah ne ya tsara masa ba, bansan tasa kalar matsalar ba, ban kuma san ta ina ta taso ba dan haka Sultan bisa umarni na..ka rufe wannan batun ka fuskanci rayuwar ka kaji 'dana dan Allah..." Shiru Sultan yy ya tsurawa guri guda idanu. Rayyan kam fasa shigowa ma yayi kawai ya juya ya koma da baya, bazai iya jure ganin mahaifiyar sa cikin wannan yanayin ba sam. Bayan kamar mintina hu'du 'dakin bb komai sai ajiyan zuciyan Ammi, tashi Sultan yayi batare da ya furta komai ba ya sa kai ya bar saman sitting room 'din. Ammi kam tashin hankali ne sosai ya ziyarce ta, ta riga tasan halin abinda ta haifa, yaran ta duk babu mai sau'kin hali indai an ta6a su, nd bata so su saka kansu cikin abinda zai sa ta rasa ko da 'daya daga cikin su, ba Sultan ko Kabeer ne damuwar ta ba, babban damuwar tata dama Rayyan ne, tasan in dai ya riga yaji komai to kuwa kwanciyar hankali ya bar shi kenan. Tun daga ranar bata sake saka Sultan a idanu ba har akayi kwana biyu. Shima Rayyan gaba 'daya damuwar sa 'kara yawaita tayi har bai kula da rashin ganin wulgawar Sultan cikin gidan ba. Abubuwa ne suka kulle kansa, bai so tun farko Sultan ya samu labari ba, amma kwatsam sai ji yayi suna zantawa da Ammi kan batun da suke faman 6oyewa tsakanin su. Ina Sultan ya samu labari har ya isar ga Ammi..bai sani ba. Tsawon kwanakin abinda yake tunani kenan amma ya rasa amsar sa. Dole ya nemi ganawa da 'dan uwan sa wato Kabeer kafin ya zauna da Sultan din ma. Da yake shima Kabeer 'din kwana biyu shiru babu labarin sa sai dai suyi waya kawai, yayin da yake can yana sake zurfafa bincike kan lamarin da iya zuciyar sa hatta Rayyan bai shigar cikin binciken sa ba. Dan haka Rayyan ya shirya ha'duwa da shi, bayaga haka ma yanda Ammi ke damun kanta sosai akan rashin ganin sun shi har Sultan ne ya 'kara masa 'kwarin gwiwar neman sa da dan Sultan kam hatta wayar sa ma bata shiga. Anan ya tarar da wan nasa cikin tsananin tashin hankali wanda da ganin Rayyan ya saki hamdala dama yayi kewar su sosai. Ashe baya jin da'di ne kuma jikin yayi tsanani sosai kuma ya hana matar sa sanar da kowa. Rayyan da kansa ya duba sa inda ya tarar da damuwa ce da kuma hawan jini suka kamasa. Da kansa ya harha'do masa mugunguna kafin ya bar gidan 'karshe zancen da yakai shin ma bai samu damar tattauna wa akanta ba. Shine ya kawo labarin rashin lafiyar dan uwan nasa ga Ammi. Nan hankalin ta ya 'kara ta shi dukkan su har Anty Raihana suka je duba shi. Yayin da shi kuma daga nan ya wuce can wani ke6antaccen gidan Abban su ya tabbatar zai samu Sultan acan, domin a mafi yawan lokuta nan ne wajen zaman sa indai har yana a yanayi marar da'di. Yayin da 6angaren Sultan ya ke6e kansa ne da gangan sbd ya cigaba da gudanar da ayyukan sirrin sa cikin sauki da kuma sirrintaka. Kabeer kam damuwar sa ce tai tsanani sosai, tun ranar da suka fara bincike da Rayyan ya fahimci abin kamar ba daga nesa bane kusa da yake tasowa, ansha yiwa Abbah barazana akan abubuwa da dama da ya tabbatar wanda yasan sirrin su sosai ne ka'dai zai aikata...'karshe ma hallaka Abban aka yi. Sosai ya abin ya 'daure masa kai har ya haddasa damuwar da ta kaishi ga kwanciya musamnan saboda tsanantawa wajen gano wa zai iya aikata hakan gare su cikin makusantan su, amma ya kasa ganowa, wannan karan hatta da Rayyan 6oye masa yayi ya ta aikin sa shi ka'dai, sai da ya ga numfashin sa na neman barin sa ne kafin ya fara tunanin sanar da Rayyan cikin sa'a sai gashi yazo duba shi duk da hakan basu samu tattaunawa ba ya bari zuwa ha'duwa ta gaba, amma dole ne suyi zaman sirri da juna. Yaso ya ha'kura da binciken amma zuciyar sa ta kasa amincewa da hakan, babban abinda ya hana shi ha'kuran shine barazanar da akai ta wa Abban su har akan su 'ya'yan sa, tunanin sa idan suka yi shiru kan al'amarin har abin ya dawo kansu fa, ta ina zasu iya 'daukan mataki..kafin a cimmasu a kassara su. Bai san waye ne ba, bai kuma san dalilin da yasa su ka kashe masa mahaifi ba amma guarantee yasan their must be a reason but bai sani ba, bai san waye kuma zai sanar da shi ba. Yayi bincike iya iyawar sa batare ma da Rayyan ya sani ba har zuwa lokacin da ya san zai samu wani evidence amma abanza, ba 'karamin iya taku suka yi ba...duk sun rufe hanyar da ya kamata yasan abinda yasa suka kashe masa mahaifi. To ya zaiyi, da kansa yaji ma ya tsani kansa dama duniyar baki 'daya, yana tsoron ranar da za'a sake ta6a masa 'daya daga cikin 'yan uwan sa. Babban burin sa shine yin ram da koma waye yake da hannu dan ya fahimci ba mahaifin su ka'dai suke hari ba, yana so ya 'daukan masa fansar abinda aka yi masa burin sa ya du'kufar da makasan agaban kuliya...amma..how can he do all this..? bai sani ba. Ya 'dauki a'kalla tsawon sati biyu kafin ya sami mafita dan zuciyar sa ta kasa ha'kura balle ya yafe ma koma waye yy hakan. Aganin sa ta inda aka hau ta nan ake sau'ka...bazai ta6a ragawa koma waye ba, bashi da burin kisa ko kuma ganin ankashe amma hakan bazai hana shi 'daukan fansa ba. 'Bangaren Rayyan kuwa tunanin sa bai bashi karya ba, nan inda yake tunanin zai samu Sultan anan ya tadda shi, Sultan na ganin Rayyan ya taho ya rungume shi, tamkar 'karamin yaro haka ya ringa kuka yana fa'din basu kyauta masa ba da suka 6oye masa cewa kisan Abbah akwai hannu aciki, sosai jikin Rayyan yayi sanyi, da 'kyar Rayyan ya shawo kansa bayan sun zauna bisa kujera, anan ya sanar da shi cewa basu tabbatar bane shiyasa basu bayyana ba amma suna kan bincike Insha Allahu da zarar sun tabbatar zasu 'dauki mataki. Tare da Sultan suka dawo gidan bayan ya ce da Rayyan su zo su sake bincika 'dakin Abbahn ko zasu dace da samun wani clue 'din.. sai dai a ba'dini duk cikin shirin sa ne. Ai kuwa hakan akayi, kafin Ammi ma tasan da batun dawowar su gidan 6angaren Abbah suka yiwa tsinke, bincike sosai suka yi amma basu samu komai ba duk da dama already Rayyan sun riga sun yi duk abinda ya dace tare da wansa Kabeer amma tunda Sultan ya nemi ayi hakan bazai iya musa masa ba dan kar yaji babu da'di, hatta motar Abbahn sai da suka duba amma babu komai babu wani abinda zai bayyana wannan sirrin..amma kuma cikin wayar sa ga zahiri akwai matsala kama daga text messages da baya gogewa a wayar sa system 'din sa ma basu samu komai ba sai kuma 'kira da wasu numbobi, kuma duk numbobin Rayyan ya gwada 'kira tun ba yau ba amma ko 'daya basu shiga...yayi binciken duk da yakamata akan numbers 'din amma da alamu mai amfani da layukan yana da matukar wayo. Guda 'daya ne aka samu har aka iya tressing inda yake 'karshe a wata unguwa can rijiyar lemo cikin magudanar ruwa suka gano shi, wannan binciken Rayyan da Kaberr duk suka yishi batare da sanin kowa ba...iya hangen su kuma basu tuna kowa da suka sani a Rijiyar lemo ba. Anan ne Rayyan ke 'dan bawa Sultan labari a zahiri ya nuna hankalin sa ya tashi sosai. Dukkan su tagumi suka yi a palorn Mahaifin nasu, sun rasa ta ina zasu fuskanci lamarin kwata- kwata daga 'karshe Rayyan ne ya fito da sharwarar kawai su share tunda basu san ta inda zasu fuskanci lamarin ba ya kuma nemi Sultan ma daya kwantar da hankalin sa ya cire komai aransa ya daina damuwa, ya nuna masa yawan damuwar su kan iya sawa sauran matan ma walwalar su ta kasa komawa dai- dai. Sultan yaro ne amma sam baya giving up da wuri, dan ko wannan lokacin ma kai ya girgiza yace be iyawa, yace ba zai iya rayuwa cikin farin ciki ba kamar yadda Rayyan ya bukaci yayi bayan yasan mahaifin sa na da muggan ma'kiyan da har suka kaishi 'kasa kuma ace bai sansu ba, bai san ta inda zai fara kamo su ba amma yasan duk da'dewa komai zai bayyana, dan haka yace zai tari lamarin da babban makami... Duban Rayyan yayi yace " Ya Rayyan aikin soja nake son shiga domin bana so idan na kama ma'kiyin Daddy in yi masa da sau'ki kuma bana so case 'din ya shiga hannun kowa dan duniya ba gaskiya yanzu, bazan fa'dawa Ammi ba haka ma Yah Kabeer hanani zaiyi, ya Rayyan kai ka'dai nake neman amincewar ka nasan idan ka amince babu mai cewa a a.." Kan gwiwoyin sa ya zube gami da 'dago hannayen sa duk biyu ya rike hannuwan Rayyan din sannan ya cigaba.." idan kana son ganin farin ciki na yaya ka amince min dan Allah wannan shine buri na a halin yanzu...." Ya 'karashe cikin yanayi na ro'ko mai tafe da tsantsan rauni da damuwa. Rayyan idanu kawai ya lumshe gami da jingina kansa da jikin kujera, 'kauna da begen 'yan uwan sa na 'kara shigan sa ta kowani kafa na gashin jikin sa suna yi ha'de masa a zuciya..babu wanda ya sake magana a cikin su illah aikin zuciya da 'kwa'kwalwa sai 'karar fan dake aiki...asali ya tsani aikin force shi a rayuwar sa amma baya jin zai iya ture wannan muradi na Sultan kwata- kwata. Sultan kam zuciyar sa sai bugawa take da tsoron kar Rayyan 'din ya'ki amincewa, sbd yasan halin sa da kafiya, dalili kenan ma da ya sanya shi shigar da batun a wannan ga6ar da yasan mawuyaci ne ya'ki amincewa. Tun zaman a wancan gidan tunanin mafita da dacewar lokacin yake tunani sai gashi cikin sauki Allah ya bashi dama, ba burin sa yayi aikin soja dan kare ahalin gidan ko dan fansa ga Abbah ba, burin sa na ganin ya shiga aikin soja manufa ce tashi ta kashin kansa ta yadda zai kawar da duk zargin da zai iya biyowa ta kansa ne. Tsawon mintina takwas suna a haka, Sultan yafi Rayyan shiga 'dimuwa dan yasan kalma guda ta Rayyan na iya ruguza duk shirin sane gaba 'daya, tsoron abinda zai fito bakin sa yake yi...a hankali Rayyan ya saki ajiyar numfashi. Idanun sa ya bu'de ya sau'ke su kan fuskar Sultan da ya tsura masa idanu yana jiran amsar sa..a hankali cike da mazantaka yace" Kaje kaga Ammi..." ***** .....Daga wajen Ammin Sultan bai zame ko'ina ba sai 'dakin sa, a zahiri bama ya son ha'duwa da kowa, bayan haushin dramar da yayi a wajen Ammi na nuna mata damuwar sa da yake 'karara kan lamarin, babban damuwar sa itace rashin jin gamsashshiyar amsa daga bakin Rayyan ne, hatta Ammi bayaso taji 'kudurin sa har sai ya tabbatar ya samu amincewar Rayyan 'dari bisa 'dari dan yasan shine 'kwarin gwiwar sa, idan Ammi ka'dai ya tunkara yasan bazata ta6a amincewa masa ba dan a halin yanzu bata kaunar guda cikin su yayi mata nisa. Wannan dalilin ya saka shi sake killace kansa domin kawai ya nuna wa Rayyan damuwar sa akan zancen da suka yi...baya ga shi da Ammi cikin gidan babu wanda yasan ya dawo. 'Bangaren Rayyan kuwa tun fitar Sultan tunani yake to in dai har Sultan dake 'kasa gare shi kuma bare a cikin su yake da wannan shau'kin har yayi tunanin nan saboda mahaifin su shi kuma mecece tashi gudummuwar kenan?" Wata zuciyar sa ta bashi amsa da fa'din" addu'ah..." Tabbas hakane..yana wa mahaifan su addu'a sai ma abinda ya 'karu a halin yanzu, kuma Insha Allah zai 'kara kaimi sosai wajen ganin ya ninka akan wanda yake yi abaya. Har ga Allah shi bai ta6a zargin wani ko wata kan mutuwar mahaifin su ba, haka kuma ko a baya ma bai taba tunanin akwai wanda ke bibiyar mahaifin sa ba, domin Abbah bai ta6a barin wata kafa da zasu zargi faruwar wani abu daban ba...'karshe sai gashi a hannun sa Mahaifin sa ya cika batare da ya iya dakatar da makiyan sa ganin bayan sa ba..". Wata zuciyar ce ta tuna masa cewa..." _Ai mutuwa daga Allah ne, kuma dolen kowa ce...in lokacin mutum yy kuma babu mai iya hana shi tafiya..._ " Yasan tabbas hakane Amma yanzu fa? Bayan mai afkuwa ta afku, bayan sanin cewa mahaifin sa na da magauta sai kuma ya na'de hannu ya zuba musu idanu su cigaba da aikata munanan ayyukan su?" " _Bazai yiyu ba_ " Yace a fili. Bana so duk wani ma'kiyin Abbah na especially wa'danda suka yi sanadin mutuwar sa su samu sassauci ko ka'dan... " _Zaka mutu_ ". Shine ta'kaitaccen text na 'karshe da ya gani cikin wayar Abbahn wanda ya shigo wayar sa mintina 'kalilan kafin rasuwar sa..ya kuma kasa samun numbern bai kuma ga suna a jiki ba. Idanuwan sa ya bu'de da suka rine izuwa jajaye, sai kuma ya sake lumshewa nan take. " U definately win, mahaifi na ya mutu amma ya bar baya...Bazan ta6a sarara muku ba..bazan ta6a bari ku rayu cikin salama ba...but how? ya tambayi kansa. waye? ina yake? me yasa suke yi masa barazana akan 'ya'yan sa? me yasa basu zo ga mu 'y'ayan kai tsaye ba sai shi? menene dalilin su na kashe mahaifina? Me ya musu? wa'dannan tambayoyin duk amsoshin su na ga mutum biyu ne tak, Abbah da kuma makasan nasa. ta Abbah ta 'kare domin ya riga ya tafi..kai kuma ina kake? ina zan ganka? Ina zan ganka ka sanar da ni ala'kar ka da mahaifina da har yasa ka kashe min shi? Ya fa'di hakan ne tare da dun'kule hannu ya buga inda hannun sa ke ajiye wato gefen kujerar...sam bai ji zafin hakan ba domin zafin da yake ji cikin zuciyar sa ya ninka wannan da yaji a zahiri. Haka kuma bai fasa yin gaba da baya da kujerar ba.." Sam bazan bar duk mai hannu cikin lamarin nan ya tsira ba, da hannu na zan 'dauki fansa, da ilimi na, da dukiya ta nayi al'kawari sai na tozarta duk wani wanda ke da hannu wajen kisan mahaifina...zan gurfanar da ku irin gurfanar da babu wanda ya isa ya tseratar da ku...wannan al'kawarin Rayyan ne..". Cikin kwanaki biyu duk Ammi ta kasa gane kan yaranta, ganin su ma na neman yafi 'karfin ta domin kowa cikin damuwa yake sosai, ita kanta bata da walwala tun ranar da Sultan yazo mata da waccan maganar kuma ya tafi har ya dawo 'din bata dawo da walwalar ta dai- dai ba, tana matu'kar son yaran ta tana son farin cikin su amma ta rasa hanyar da zata bi dan raba su da damuwar da suke ciki, ga Kabeer can kwance babu lafiya. Ga Anty Madeena ma ta koma gidan ta tunda akayi 40days sai dai in ta samu lokaci tazo ta leka su ta koma gida Ko lokacin da Sultan ya dawo fa'da sosai ta yi masa tana yi idanun ta na 'kwalla, domin ta fahimci kamar Sultan ya sanar da Rayyan komai ne bayan sai da ta garga'de shi..sam bata so hakan ba amma ganin Rayyan cikin kwanakin ya kasa natsuwa ya sata ta zargi hakan. Batasan cewa asalin binciken ma shine da Kabeer ne mafarin ta ba. Bata son yaran ta su cusa kansu cikin wani abu daban shiyasa ta damu, nd tsoron kafiyar su take yi tasan da wuya ne ta iya tan'kwara su domin ita tasan me ta haifa. Safaah ce ka'dai ke da sanyin zuciya na biyun ta itace Marwa sai dai itama Marwan ba cikakken lafiya gareta ba, kullum tana nan ne jiya i yau sbd matsalar sanyi da take fama da shi..wato Pneunomornia. Kuma itace ka'dai a gidan bata san komai dake faruwa ba, sai dai 'karancin walwala da ta fuskanta game da sauran 'yan uwanta sosai itama yake ta6a ta. Ga Raihana ma an 'kira ta saboda Bassam 'din ta babu lafiya da yake dama bata taho da shi ba yana can wajen kakannin sa ne a Kaduna dole ta shirya ta tafi. Safaa data fuskanci damuwar Ammi kullum 'kara gaba yake yi sai itama ta rasa sukunin zuciya, dan ma a hakan sosai Ammi ke 'ko'karin 6oye mata. Sultan sake zurfafa bincike yake da kulla sabon shiri bayan killace kansan da yayi dama gashi masanin na'ura ne shi, yayin da Rayyan kullum indai yana gida zaka same shi kan kujeran sa yana juyawa da idanuwa lumshe yana tunanin mafita, dama al'adar sa kenan tun a baya matukar yana cikin farin ciki ko akasin hakan zaka same shi bisa kujerar sa yana juyawa da idanuwa lumshe bambamcin kawai shine idan yana a yanayi na farin ciki zaka tsinci murmushi saman fuskar sa ne. Sa6anin yanayin sa na yanzu da sam babu walwala saman fuskar sa, kullum burin sa shine 'daukan fansa..amma ya rasa ta ina zai fara, likita ne shi yanzu, ba hukumar bincike yake aiki ba, bai masan komai game da aikin bincike ba dan babu abinda ya ta6a ha'da shi da hakan, shi ba jami'in tsaro ba ba kuma alkali ba...to ta ina zai fara? _Zaka iya yin komai idan kazama lawyer mai zaman kansa_ Wannan shawara ce daga wani 6angare na zuciyar sa, take kuwa ya bu'de idanu sai kuma ya sake lumshewa. Lawyer...! Lawyer....!! Lawyer......!!! Dama tun asali wannan burin sa ne, amma a wannan ga6ar hakan na da wata fa'ida ne? Ya sake tambayar kansa... Bai kai ga kaiwa 'karshen tunanin ba sallamar Safaah ya dakatar da shi. A hankali ya bu'de idanu, ciki- ciki ya amsa ta. Duba 'daya yayi mata ya fahimci damuwa ce ke tafe da ita. Gaban sa tazo ta zauna inda ya daina lila kujerar ya zuba mata idanu. Kanta ta kwantar saman gwiwoyin sa kawai ta fara rera kuka mai sauti ko magana ba ta iyawa. Shi kam kanta ya zubawa idanu yana tunanin me ya sata kuka haka kuma? Tunanin sa ya tafi ne ga Yayan sa Kabeer da kuma 'dan 'kanwar sa Bassam da Marwa da duk basu da lafiya suke kwance. Lokaci guda sai yaji jikin sa yayi sanyi sosai...duk da yake ko ayau ma sai da ya dubo jikin Kabeer din kuma Alhamdulillah da sauki sosai sai dai still zuciyar sa babu natsuwa..kuma ba abin mamaki bane a wajen ubangiji daukan ran duk wanda ya so. Tsawon mintina suna a hakan yama kasa dakatar da ita a hankali ya 'kira sunan ta gami da 'dora hannun sa bisa kanta alamar rarrashi. " Me ya faru ?" Bata amsa shi ba ta cigaba da kukan ta dan ta jima tana tarawa. Sakanni talatin ya 'kara mata sannan ya sake tambayar ta " Safaah me ya faru ne wai?" " Yaya..Ammi ce". Ta fa'di da muryar kuka tana 'dago idanu jin yanayin da yy magana tasan gaf take da kaishi wani ma'kura in batai saurin bashi amsa ba. Ido ya 'dan bu'de yana duban ta yace" Ammi kuma, me ya faru da Ammin?" " Nima ban sani ba Yaya, but kullum bata magana sosai, sai ta yi ta kuka kuma bata so mu gani, idan na tambaye ta kuma sai tace min bakomai kuma wallahi yaya akwai abinda ke damun ta please kaje ka tambaye ta ko ta zata fa'da maka, Yah Sultan ma bana ganin shi yanzu..kuma yana part din sa amma ko naje baya bu'de min 'kofa ban san meke damun sa ba..." Shiru Rayyan yy yana duban 'kasan tiles da alamu walwalar gidan su na shirin barin su ne... jin kukan Safaah da ya cigaba ne ya sashi sake duban ta yace " Ki daina kuka..tashi kije nima zan shigo yanzu, but kar ki sake damun Ammi da tambaya kinji sister?" kai ta 'daga masa alamar taji. Daga nan 'dakin ta ta nufa ta cigaba da kukan ta dan gani take tamkar babu wani sauran farin cikin da yayi mata saura. Shi kam ko bayan fitar ta ya shafe sama da mintina talatin yana tunani, har tsawon wani lokaci zai zauna yana ganin wannan tashin hankalin cikin zuciyar kowa dake gidan su? sai yaushe ahalin sa zasu samu nutsuwa, kowa burin sa a duniya yaga iyayen sa cikin farin ciki da walwala..to shi na shi mahaifin kashe sa akayi, mahaifiyar su da ta rage ita kuma bata cikin farin ciki kullum, Sultan ma haka ga Safaa ma da ya tabbatar baza ta iya juran ganin Ammi cikin damuwa ba, Yah Kabeer na kwance, ga Marwa ma shikenan gidan su na shirin tarwatsewa kenan,...sam bazan iya zuba idanu in ga faruwar hakan ba. Tsaye ya mi'ke ya fa'da bathroom 'din sa ya watso ruwa. 'Kananun kaya ya sanya ya 'dauki wayar sa ya nufi part 'din Sultan. Salmerh😘 [16/10/2022, 12:19 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Wattpad@* _Serlmerh-md_ 🅿️ *...53* .......Bai zame ko'ina ba sai part din Sultan zuciyar sa cike fal da tunanin me ya sake jefa Sultan cikin wannan yanayin kuma. Bell ya ta dannawa amma shiru kamar ciki ba kowa. 'Karshe kai Kawaicya girgiza ya wuce babban part 'din..a hankali yake tafiyar sa cikin natsuwa, jin kansa yake tamkar ba shi ba da kansa yake jin weight 'din sa ya ragu sosai, gaba 'daya ya zabge ramar sa ta fito fili cikin kwanaki 'kalilan....Bai tadda Ammi a parlorn 'kasa ba dan haka sai yayi zaman sa bisa kujera, Hajja Ladi mai aiki ce tafi to ta ganshi tana niyyan komawa ta kawo masa abin sha sai yy saurin yafi to ta da hannu. Da sauri ta 'karaso tana risinawa take fa'din" Ranka ya da'de barka da yamma..." Bai bi ta kan gaisuwar ba kawai yace" Kira min Safaah". Da sauri ta wuce 'dakin Safaah tai 'kiran ta. Mintina hu'du basu cika ba sai ga ta fito, tun bata 'karaso ba yace" duba min Ammi pls kice mata ina 'kasa..". Zama ya cigaba da yi ya 'kurawa wayar sa idanu..bansan me yake dubawa cikin wayar ba har lokacin da yaji sautin tafiya daga matakalar bene. Bai 'daga kai ba ban sani ba ko bai san da tahowar Ammin ba. Fuskan ta wasai babu alamun damuwa, sosai tayi 'ko'kari wajen 6oye musu damuwar ta har 'yar powder ta shafawa fuskar ta ta ramba'da kwalli cikin idanun ta inda ya fito ras da shi, idan ba sani kayi ba bazaka ta6a tunanin akwai wani abinda ke damun ta a rai ba. " Rayyaan..shine kuma ka zauna anan kamar wani ba'ko me ya hana ka hawo wa saman yau kuma?" Idanu ya lumshe ya kuma bu'de su tare da ajiye wayar hannun sa gefe da shi. Sai da ya saki ajiyan zuciya kafin ya dubi Ammi yace " Haka nan kawai Ammi". Zama tayi tana sake duban sa dan ko 'dazu da ya shigo suka gaisa bata kula da yayanin sa ba kamar yanzun ba, ramar da yy ne ya matu'kar bata mamaki sosai. " Anya Rayyan kana ganin kankacikin madubi kuwa? wannan ramar tayi yawa ko baka jin da'di ne kake 6oye min kaima...?" Murmushi yy yana gyara zama yace" Safaah ta fini shiga damuwa Ammi..dan Allah ki tausayawa yarinyar nan ki rage damun kanki kar damuwa ta yiwa zuciyar ta illah, abinda ya faru ya riga ya faru..in kuma tunanin ki mu ne to ki kwantar da hankalin ki babu abinda zai faru insha Allahu Rabbi..." Shiru tayi tana kallon cikin idanun sa..sai ya sake yin murmushi yana 'dan lumshe idanu dan ta yarda da shi.." Rayyan..!" Na'am Ammi. " Bana son ku sake saka kanku cikin wani ha'darin ne daban, dan Allah ka bawa 'kanin ka ha'kuri ku barwa Allah komai na tabbata shi yasan da mu da duk abinda ke faruwa damu, kuma zai yi mana sakayya dan baya barin zalunci, amma bazan iya juran rashin 'daya daga cikin ku ba, i wish ni in mutu kafin in ga ranar da 'dayan ku zai barni, kai da kanka kasan saka baki ciki irin wannan lamarin dai- dai yake da saka kai tsakanin mutuwa da rayuwa...dan Allah ku rufa min asiri..mu fawwalawa Allah komai.." " Ki kwantar da hankalin ki Ammi insha Allah babu abinda zai faru, kuma ma mu ina muka ga damar saka kai cikin lamarin? ba fa musan kowa bama balle musan ma'kasudin faruwar lamarin balle akai ga batun tuhumar sa, so kinga kuwa bamu da hanyar saka kanmu, in kuma Sultan ne ki kwantar da hankalin ki zan masa magana...". Sosai yayi ta kwantar wa da Ammi hankali har ta saki ranta sannan suka cigaba da hira. Dan shima kokari sosai yy wajen danne abinda yake ji cikin zuciyar sa kawai dai baya son Ammi tasan shirin su ne. Annan Ammi ke sanar da shi cewa tayi magana da Kabeer anjima zata tura adaeo da su gida tunda akwai isahsshen wajen zama kuma zai fu samun kula idan yana kusa da su. Rayyan kansa yayi wannan tunanin dama dan haka yace mata..." hakan ma yayi, Allah ya kawo su lafiya..". Wancan part dake gefen nawan inaga zaifi ko?" " Erh ai har ma nasa an gyare shi" Cewar Ammi. Kai Rayyan ya jinjina yana fadin" masha Allah". ***** .....Daga wurin Ammin 6angaren Sultan ya nufa sai dai ko yanzun ma bai bu'de 'kofar ba. Bai matsan ta da bugun 'kofar ba kawai ya wuce motar sa ya bar gidan. Bai ha'du da Sultan ba sai da dare dan ko wayar sa ka 'kira baya 'dauka sam...abin ya fara damun sa sosai, sai da ya matsa da 'kiran wayar kafin Sultan ya 'daga" Ba ka da hankali ko?" "..Sorry Yaya...." " Yi min shiru my friend tun yaushe nake faman bugun 'kofar ka, ko door bell 'din ma kana nufin baka ji 'karan sa ba...?" " Yah dan Allah kayi ha'kuru". "...just open d door ina 'kofar part 'din ka yanzu..." Daga haka ya yanke wayar ya jefa ta cikin aljihu. Bayan kamar mintina uku sai ga Sultan yazo ya bu'de 'kofan, yana wani sunkuyar da idanu. Jikin sa blue 3quarter jeans ne sai farar singlete. Haka Rayyan ya bishi da idanu..sannan ya dire duban sa kan fuskar sa yana masa kallon tuhuma. " Me ke nan kk yi haka Sultan..?" Bai yi magana ba sai hanya da ya bawa yayan nasa ya shigo ciki. Zama yy shima Sultan ya zauna da hannayen sa kan kan gwiwoyin sa. " Kayi ha'kuri Yaya wallahi na kasa sarrafa zuciya ta ne abin na damu na sosai..." " nd who tell u hakan da kk yi is d best solution to dat issue..?" Shiru yy bai kuma kalli Rayyan ba. " Kasan tashin hankalin da ka sanya Ammi ciki ne, ace kana cikin gidan nan amma kusan 2days babu wanda yaga idanun ka Sultan...dai-dai ne kenan? Safaah kanta da kuka ta same ni akanka, try to control ur anger plz Sultan banaso Ammi ta fahimci komai yanzu. Ko so kake in fasa yadda da millitary force 'din na ka? Da sauri ya girgiza kansa. "...then better change ka dawo Sultan da muka sani ka kori wannan sabon sultan din kaji, ni nasan yanda kk ji amma ya zamuyi, dole ne mu ringa dannewa kar kowa ya fahimta, don't forget that har yanzu fa bamu san who is behind d issue ba..to idan kana bayyana halin da kk ciki ai 6oye kansa zai cigaba dayi ta yadda bazamu iya gano ko su waye ba tunda sun fahimci mun san da su kuma muna bincike akan su...ka nutsu ka kwantar da hankalin ka, nayi magana da aboki na Rilwaan yace insha Allah next year burin ka zai cika kaga kafin lokacin ka gama tattara duk takaddun ka ma..." Kai ya jinjina cike da farin ciki jin cewa burin sa na gab da cika. Shima Rayyan murmushi yy sannan ya koma baya ya jingina sosai yace nima zan koma school, but pls ban so Ammi ta sani, ce mata zanyi asbitin mu suka tura ni..kaga idan na tafi sai ta ganni kuma. Dukkan su murmushi suka yi. Sultan ya mika masa hannu suka sha irin ta mazaje gami da jinjinawa junan su. Kamar yadda Ammi ta fa'da kuma Kaberr sun dawo gida da zama. A hankali yake samun sau'ki cikin kwanaki 'kalilan. Ganin hakan yasa hankalin Sultan tashi dan baya so ya warke tun yanzu saboda ha'de hannuwan su da Rayyan shine kwarin gwiwar su...baya so.su kassara masa shirin sa. Poison ya nemo yazo ya faki idanu ya zuba masa cikin maganin sa da yake na ruwa ne hadin itatuwa na Islamic chemist ne na 'kara 'karfin jiki da zuciya Sultan sai da ya karka'da sosai sannan yayi tafiyar sa a lokacin Kabeer na bathroom ne. Lokacin shan maganin sa na yammaci nayi ya 'dauka ya sha cikin mintina 'kalilan ya fara fita hayyacin sa dan ma matar sa na tare da shi ne a lokacin ita tayi alerting cikin gida aka fara lalu6o Rayyan da shima daiwar sa kenan aiki amma yadda yaga wannasa yas dole sai da aka dangana shi da asbiti. Anan aka tabbatar musu da cewar guba yasha sai dai ba mai 'karfi sosai bace. Sultan ne ya aikata amma saboda karfin hali shine yake so ya dangana lamarin da ma'aikatan gidan musamman Hajja Ladi da kwanaki ya koreta. A wancan lokacin kuwa har Kabeer ya samu sauki suka dawo gida ba'a san wanda ya aikata hkan ba. Sultan ne ma daga baya ya fara cusa musu tunani da zargin Alhaji Rufa'i da suka yi tafiya zuwa Maiduguri atare, musamman da yaji ya fra batun auren Rayyan kan cewa ya kamata magana ta cigaba a cigaba da yiwa Abbah addu'a kawai. Duk 'din su sun fara amince wa da zargin Alhaji Rufa'in musamman da Sultan ya fara rattabo musu sabon bayanin da tun bayan rasuwar Abbah babu wanda ya sake bi ta kan sa. Rashin.ta6a Alhaji Rufa'i da makasan basu yi ba, acewar Sultan yana da tabbacin suman 'karya yayi ma ko a wancan lokacin daga baya ya farfa'do da gangan. Kuma acewar Sultan in ba shi 'din da suke tare bama waye yasan cewa suna kan hanya a wancan daren tunda iya sune suka yi tafiyar shine kadai bare acikin su. Sosai ya basu gamsassun shaidu da suka sanya su fara dasa zargi akansa. Gaba 'daya hankulan su sai ya koma gare shi da bincikar duk wani motsin sa...Kuma hakan bai sanya shamaki garesu wajen son cika burikan su ba. ***** Batare da shawarar kowa ba Rayyan ya nemi gurbin karatu ya kuma samu a Uk...cikin lokaci 'kankani ya fara shirye- shiryen tafia a 6oye. Damuwar rashin mahaifin sa gaba 'daya ya 'dauke hankalin sa daga kan kowacce mace ma ciki hadda Nadia, sai dai takan 'kira shi da kanta su gaisa lokaci zuwa lokaci dan shi har mancewa ma yake da ita a rayuwar sa. Yana cikin shirye- shiryen tafiyar sa ne Alhaji Rufa'i ya samu Ammi da maganar auren su, dan aganin sa alhakin auren yanzu bisa wuyan sa ya rataya tunda da shi aka faro. Cikin rashin sani bai san cewa duk kallon biri suke yi masa ba idan ka 'dauke Ammi ka'dai. Ha'kika ba 'karamin so tayi ta manta da zancen auren ba in ba dan Alhaji Rufa'in ya tunasar da ita ba. Ta kuwa yi masa godia sosai tace zata yi magana da wan sa duk abinda ake ciki zata sanar da shi. Da 'kyar Ammi ta sashi amincewa da batun auren dan bai so zancen ya taso a wannan ga6ar ba da yake shirte shiryen barin 'kasar. Ya so ya dakatar da batun sbd wannan dalilin amma Ammi ta dakatar da shi da cewar sai suyi tafiyar su tare tunda ba wai bazai iya 'dakuna nauyin su bane. Wannan dalilin ya 'kara masa jin haushin Alhaji Rufa'i cikin ransa dama Nadian ita kanta. Ganin yadda Ammi ta matsa ne yasa ya basu dama, Alhaji Rufa'i abokin mahaifin sa ne sosai kuma ko bayan rasuwar Alhajin basu ka'dai suka shiga tashin hankali ba hadda shi amma duk basu sani ba, shine ya tsaya tsayin daka wajen ganin anyi komai.bisa tsari cikin satikai shida aka 'daura masa aure da Nadia bisa sadakin da bai ma san nawa bane sai a wajen 'daurin aure yaji yawan su. Dolen sa haka ba dan yaso ba ya tattara Nadia suka tafi tare. Kabeer ne ya fara dasa ayar tambaya akan Sultan dan haka kawai sai yaji zuciyar sa bata yadda da shi ba, tun bayan bikin Rayyan abubuwa suka 'dan sarara musu har suka tattara suka koma gidan sa wannan karan hadda Safaa suka koma inda ta cigaba da zuwa makarantar ta acan. Gidan babu kowa yanzu, Ammi ma sun bude wata kungiya a Abuja so ba sosai take samun zama ba, Marwa na school Raihana kuma ta koma gidan mijin ta. Tuni soyayyar dake tsakanin Sultan da Safaah ta riga ta fito fili, Ammi dai kam tayi na'am da hakan yayin da Kabeer yaji abun mai masa tsari ba, sam bai ga dacewar aure tsakanin Sultan da Safaah ba haka kawai yaji bai amince da ha'din ba ba wai dan yana da wani dalili ba. Sun zauna da Sultan sunyi magana da yake Sultan nada kaifin 'kwa'kwalwa hakan yasa duk da Kaberr bai fito fili ya bayyana ba amma sosai ya fahimci manufar sa sai dai bai nuna masa ba shima. Sai dai level 'din haushin Kabeer da ya 'kara hauhawa masa a zuciya. Ji yake matu'kar aka hana wannan ha'din toh an gama da shi ne a duniyan nan, kenan duk wahalar sa ta tsawon shekaru ya tafi abanza. Cikin kwanaki biyu rak ya samowa kansa mafita. Bai yi 'kasa a gwiwa ba ya sake shiri da wani 'karamin kwali ya nufi gidan Kaberr da shi. Ashe mage ce aciki. Bayan motar Kabeer yaje ya ajye kwalin sannan ya fita batare da ya 'karasa ciki ba dan ban da mai gadi babu wanda yasan da zuwan sa. Yana fita ya 'daga wayar sa ya 'kira Kabeer 'din yacevda shi Ammi na neman su gaba 'dayan su wai yanzun nan akwai maganar da take so su tattauna. Kabeer yayi 'ko'kari wajen ganin ya 'kira Ammi domin ya tabbatar amma wayar Ammin na shiga ba'a 'dagawa, ashe already wayar na tare da Sultan ne. Sai da ya tabbatar ya 6ata wani abu a jikin wayar ta kuma bashi ya duba mata matsalar sannan ya aikata duk shirin sa. Ganin Ammi bata 'daga wayar ne ya sashi dole badan yaso ba suka fito, shi da Safaah matar sa da kuma Zamrud 'diyar sa duk basu bar kowa ba, dayake bayan maghrib ne babu wanda ya yadda ya zauna shikadai a gida...ashe ajali ke kiran su. Da shigan su motar Safaah. kabeer da Zamrud suka fara jin wani iri ajikin su amma basu bi takan yanayin ba. Sun fara tafiya har sun hau babban titi kawai yanayin.ya ta'azzara gare su har idanun Kabeer suka fara juyawa bayan rikidewa ja da suka yi, ga uban atishawa da suke jerawa, ya fara zargin wani abu kawai suka fara jiyo kukan mage daga bayan booth 'din motar kamar wasa. Wani uban birki da ya taka tsakiyar titi cike da mamakin yadda akayi mage ta shigo masa motar da wannan lokacin har ma ya mance da cewar tsakiyar titi suke. Kafin yayi wani yun'kuri cikin abinda bai fi seconds shida ba abin ya faru, wata babbar motar da ke tafe abayan su ta haura musu babu sassauci koka'dan tamkar matu'kin motar baya gani. Daga shi har sauran babu wanda ya sake jan dogon numfashi illah Kabeer da Zamrud ita ka'dai. Kafin jama'a su gama tururuwar neman agaji Sultan ne kan gaba wajen basu taimakon karya. Zaku sha mamakin cewa da shi cikin wannan babbar motar da ta bibiyi bayan su batare da sun san cewa su take bi ba. A zahiri ba taimakon su yake ba so yake yaga wanda bai 'karasa cikin su ba ya 'karasar da su. Zamrud ya fara fahimtar tana numfashi sai Kabeer da ko 'dan yatsan sa baya iya 'dagawa. Cikin nuna rashin imani da tausayi a 6oye garin fito da Zamrud cikin motar ya mur'de wuyan ta. Hakan ya faru ne akan idanun Kabeer amma bashi da damar motsawa balle ya dakatar da shi. Idanu ya lumshe ya kuma bu'dewa yana jin yadda hawayen sa ke gangarawa gefe da gefen fuskar sa. Sultan ne ya mur'de wuyan 'yar..gudan jinin sa bayan duk soyayyar da yake nuna mata....ashe soyayyar 'dan kada Sultan ke yiwa Zamrud. wannan wani irin butulci ne? Ha'kika yau yaga cin amana ganin idon sa, bai ta6a zaton haka halin Sultan yake ba, bai ta6a zaton suna rayuwa ne tare da makashin su ba, shakka babu Sultan ne... Sultan ne ya kashe musu mahaifi...ya kuma dasa musu zargin Alhaji Rufa'i da gangan, badan ma Allah ya rufa asiri ba da ba 'karamin tafka abin kunya zasu yi ba. Sai da ya ciro Zamrud ya shimfi'de bayan ya tabbatar bata numfashi sannan ya koma kan Kabeer ya fara kukan 'karya. Kan Kabeer ya 'dora saman cinyar sa yana kiran sunan sa yana faman jijjiga shi. " Yah Dan Allah kar ka tafi ka barmu ya zaka yi mana haka Yayah..?" Kabeer idanun sa 'kyam akan fuskar Sultan yana ji inama...inama, inama da ba acikin wannan halin ya gano waye Sultan ba. Ji yake da yana da hali da babu abinda zai hana shi bayyana sa ga 'yan sanda koda hakan shine abu na 'karshe da zai aikata kafin numfashin sa ya barshi amma babu dama...ji yake da yana da dama idan bai ga bayan Sultan ba bai haifu cikin Ammin sa ba. Jikin sa kaca- kaca da jini ta ko'ina saboda rashin wasu sassa na jikin sa amma ahakan Sultan ya rungume shi kai kace duk dunia babu mai 'kaunar sa sai shi ka'dai. Cikin hakan batare da kowa ya farga ba ya danne ma'kogoron Kabeer yana kan kukan 'karyan bai 'daga ba sai da ya tabbatar 'dan numfashin da ya yi masa saura ya tafi. Bazan iya misalta muku irin tashin hankalin da wannan ahali suka sake samun kansu ba...rayuka ne 'dai 'dai har guda hu'du. Rayyan kansa wannan karan sai da ya kusan kwantawa asbiti saboda tsananin tashin hankali. Sultan ya shirya kashe shi ne kawai saboda alamu da yagani na cewar bazai yadda abashi auren Safaah ba...duk da ma akwai wannan 'kudurin a ramsa, cikin lissafin wa'damda zasu tafi harda shi amma alamu da ya nuna cewa kamar baya ra'ayin ha'din auren su ya sanya dole mutuwar sa ta matso kusa cikin jadawalin lissafin Sultan. Duk dama bawai soyayya tasa yake son auren Safaah 'din ba kawai saboda wata manufa ce tashi ta daban ne. Wannan karan ma ankai ruwa rana kafin gidan nan suka dawo dai- dai, sai dai dole a halin yanzu basu da walwala. Bayan rasuwar da kusan watanni hu'du sannan Rayyan ya koma Uk amma bai koma tre da Nadia ba. Ta zauna ne tare da su Ammi acikin gida. Ita ta maye gurbin Rayyan a asbitin da yake aiki ta 'dan fita saboda Ammi tace zama waje 'dayan babu da'di sam. Bayan auren sa da Nadia da shekara biyu mahaifin Amrah ya fara yiwa Alhaji Rufa'i zancen auren Rayyan da Nadia, dayake duk sun san da zancen dan anyi sane tun Alhaji Sa'ad Auta na raye wato mahaifin Rayyan. Shima Alhaji Rufa'i bai yi 'kasa a gwiwa ba yace tabbas shima ya fara tunanin hakan, domin zama da al'kawari aka babu da'di gwamma a sau'ke shi. Musamman a yanzu da ya tabbatar Ammi sun damu da rashin haihuwar sa duk da sun san Allah ke badawa amma suma yun'kurin su ba laifi bane acewar sa. Ko da aka sanar da Rayyan sam bai wani damu, cikin ransa ya ce su suka sani, komai ma suyi shi yanzu bashi da bakin tankawa, ya riga yasan ba kowacce mace bace zata iya zama da shi in bama irin Nadian ba, yasan ba 'karamin ha'kurin zama take yi da shi ba, tana son shi shiyasa take jure duk wani rashin kirki na sa, yasan ana aure ne saboda kiyaye iyakokin ubangiji amma gundarin zaman auren ba shine gaban sa ba a yanzu. Itama Nadian ba samun kansa take ba balle kuma wata Amra da ko sanin ya kamannin ta yake ma bai yi ba. Menene amfanin tara mata bayan ba iya kulawa dasu yake ba sai dai yasan ko kwana zai yi yana fa'da babu wanda zai saurare shi. Bayaga haka ma shi da kansa zai so a saukewa Abban sa nauyin al'kawarin da ya 'dauka tun yana raye. Baya ga haka da sam bazai amince ba, ba iya damuwa yake da sau'ke hakkokin dake kansa yake ba, sbd sam shi mace bata gaban sa a yanzu a, ba 'karamin dauriya yake yi yake bata lokacin sa ba idan ta bu'kaci hakan, duk da yasan ada can baya ba haka yake ba, 'kuncin zuciya ce da damuwa duk suka canza shi. Sai yaga kamar ta fara shiga damuwa kafin yake bata lokacin sa, a hakan ma sau da dama kwanciyar sa yake yi yace ya gaji, bata nuna ta damu sai dai yaga tana ta sallah tana addu'o'i atimes har sai yaga tana kuka...zata 'daga hannu ta jima tana addu'oi kuma yasan hadda cikin addu'o'in nata tana matu'kar bashi tausayi amma ya kasa canzawa. Ya jima da sanin halin Nadia, ba 'karamin ri'ko tayiwa addinin ta ba, gata kamilalliya natsuwa da ilimin ta take komai. Ganin yawan damuwar da ta keyi yasa shi ya 'dan sassauta mata yana 'dan bata lokacin sa babu laifi. Ada idan ta shine zai 'dauki a'kalla watanni biyu ma bai waiwaye ta ba amma yanzu yakan bata hakkin ta babu laifi. Hakan ma dan ita ne saboda yasan tana 'kaunar shi sosai kuma tana da natsuwa. Amma tun bayan da aka aura masa Amrah da akayi sai ya koma halin sa na baya, bai damu da ita ba balle ya damu da hakkin da Allah ya 'dora masa. Sai ya shafe tsawon wata ko fiye da hakan ma batare da ya kusance ta ba, hakan shiya jefa Amrah cikin wani hali, gashi bazai ta6a zama suyi hira ba balle ya fahimci damuwar ta. Cikin rashin sa'a shai'dan ya rinjaye ta ta fa'da harkar maza, dama can ta saba abinta kuma tun tarayyar sa da ita na farko ya fahimta amma bai tanka mata ba, me ma zai ce da ita toh. Duk abinda yayi tamkar ya bayyana sirrin auren sa ne, Auren ta ne ya sa ta sarara wancan halayyar har ma tayi alwashin dainawa, but rashin samun kula daga gareshi yasa ta komawa ruwa. Tun lokacin da za'ayi auren sa da Amrah dole Nadia ta bar gidan Ammi ya ha'da su a can wani gidan sa da yake babba wadattace, tare suke a gida 'daya amma babu wanda zaman 'dan uwan zai takurasa. Ko da ya tashi komawa bai yadda ya koma da ko 'dayan su ba, haka yayi bankwana da gida bayan ya barwa Sultan babban garga'di kan kulawa da kuma takatsan-tsan da komai nasu. Haka kuma bai tafi ba sai da ya tabbatar ya zuba securites wadattu cikin gidan nasu saboda Ammin sa da sistern shi ya kuma zuba a nashi gidan a lokacin ma already Sultan ya bar aikin sojan da aka sanya ku'di wajen sama masa dan acewar bazai iya ba akwai wahala. Haka rayuwa ta cigaba da gurgurawa, yau da'di gobe akasin haka tun Ammi na saka ran dawowar sa har ta ha'kura sai dai kawai suyi waya da shi suyi video call yana kuma tambayar wani matsala idan akwai... Cikin hakan Ammi ta sanar da shi Sultan zai koma running ma'aikatar su ta Lagos dan tun rasuwar mahaifin su Kabeer ne kan 'dan kulawa da su yanzu kuma babu kowa da ke kula da su. Sam Rayyan bai ji da'di ba amma babu yadda zai yi, ko da yy mata maganar ya za'a bar gida ba kowa sai su ka'dai ga Marwa ma idan Sultan ya koma Lagos Ammi taje Abuja ya Marwa zata yi, sai cewa tayi ai Marwan na makaranta dan badan differing da tayi bama da yanzu ba wannan labarin ake ba da tuni ta 'kare, amma a'kalla ta shafe 2 yrs batare da je makarantar saboda rashin lafiya da kuma abubuwan da suka yi ta faruwa abaya. Dan haka tace da shi bakomai ai zata iya zama tunda aikin ma ba kullum bane kuma akwai Hajja Ladi ma babbar mace ce suna tare a gidan.. " Um-um fa Ammi kinsan mutane..." " kar ka damu ba komai na yaba sosai da matar ne shiyasa kaga ban damu ba...kuma ma baga can gidan ka ba in tana so zata iya zama acan.." Shi dai dama sam ba ya son wannan aiki na Ammi tunda da'dewa ya kuma yi iya yin sa akan ta barshi ta 'ki. Ko Sultan 'din ma Rayyan cewa yayi ina ma laifi yayi aikin a companyn su na nan Kano tunda duk Alhaji Rufa'i aka bari da nawi..amma Ammi tace ya barshi tunda can 'din ya za6a. Cikin rashin sani basu san cewa Sultan ya hari can 'din bane saboda wancan na Lagos 'din yafi girma da tsari. Ko da ya koma can 'din kuwa sai da ya tabbatar da cewa ya sa6unta abubuwa masu dama bisa tsarin sa hatta ma'aikatan sai da ya tabbatr ya zuba nashi kafin ya baro ya sake dawowa na nan Kano din..bayan ya tabbatar duk wani share na riba da company zai cire yana da kaso guda daga ciki batare da sun sani ba direct account 'din sa ku'din ke shiga. Shekarar Rayyan biyar da fara makarantar sa kafin ya kammala inda ya dawo gida matsayin cikakken lawyer mai zaman kansa....Ammi ta sha mamaki sosai ta kuma rasa dalilin wannan canjin nasa...shrmekaru biyar kenan da auren sa da Nadia yayin da auren sa da Amrah yake da shekaru uku...yayin da shi dududu yake da Shekara talatin da 'daya da haihuwa...Sultan kuma ashirin da Bakwai. Yakan yawan ziyartar matan sa duk bayan watanni shida, duk da nisan waje amma dayake shi ya 'daurawa kansa sam baya gani...sai dai wani abinda Allah ya 'dora masa duk cikin matan sa ko 6atan wata babu wacce tayi acikin su. Tun fahimtar halayyar Amrha da Sultan yayi shima sai ya saka kansa ya fara bibiyar ta bai sha wani wahala ba kuwa ya amince, dama ya jima yana neman hanyar da zai dur'kusar da Rayyan sai ya gashi ya samu cikin sau'ki...Tun fara harkar su da Sultan sai Amrah ta daina fita da kowa sai shi ka'dai dan ya tare ko'ina ya kuma yi mata kashe din ya sake ganin ta da wani zai tona ta wajen mijin ta ne babu ruwan sa, yace mata shi yasan ko sha'rai za'ayi iyaka ai masa bulala ne tunda ba aure shi ba amma ita hukuncin kisa ne nata, hadda kwatanta mata yadda ake kisan mazinaci abinda ya kara tsorata Amrah kenan yasa take biye masa batare da ta sa6a dokar sa daidai da rana guda ba. Salmerh😘 [19/10/2022, 6:11 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Wattpad@* _Serlmerh-md_ 🅿️ *...54* .......Amrah bata da wayo sam shiyasa duk umarnin da Sultan ya 'dora akai bi take yi, a hankali ta fara jin tamkar tana son shi kuma tana jin dadin mu'amala da shi, duk da cewa kuwa a wannan daowa ta Rayyan shima ya canza, walwalar sa ta dawo sosai, kula da tattalin da yake basu ya bambanta dana baya...amma duk da haka bazata iya sa6a umarnin Sultan ba ko dan saboda rufin asirin ta ma. Tun dawowar Rayyan daga Uk ya fara samun offer na aiki a wajeje da dama manya da kananun office, bisa shawarar Ammi ya za6i guda ciki ya fara gwada aiki da su. Gefe guda kuma yana running business 'din mahaifin sa domin tun dawowar tasa ya tarar Alhaji Rufa'i Diabetes ya kwantar da shi jikin sai a hankali, dole ya 'dauki komai na dukiyar su ya dam'ka a hannun Rayyan dama daowar sa yake jira domin bai ya damka a hannun Sultan ba dan ya lura dan nanaye ne shi natsuwar ka'dan ce. Shima Rayyan bai yi 'kasa a gwiwa ba ya bada gudunmawa iya iyawar sa wajen kula da lafiyar Alhaji Rufa'in...sau'ki ne dai daga Allah dama yake zuwa kuma sai a hankali. A ta'kaice yanzu Rayyan Dr ne shi, kuma Barrister ne, CEO ne a companyn mahaifin sa da ya mutu ya bari wato INFINITY GLOBAL COMPANY...kuma duk cikin wa'dannan babu wanda bai 'kware a fannin ba. Yayin da 6angaren Sultan.wannan abinda Alhaji Rafa'in yayi ya sake 'kon masa zuciya, tsanar Rayyan ta dasu aransa sosai haka ma ta Alh Rufa'i da bai bashi komai kafin dawowar Rayyan ba. Abinda ma ya 'dan.sanyaya masa zuciya shine gani da yayi Rayyan ya jawo shi ajiki komai da shi ake, koka'dan Rayyan bai bar 'kofar da har wani zai iya zargin shi 'din ba jinin su 'daya bane da juna musamman ma da yake tun tasowar su ba'a nuna musu hakan ba. Dawowar Rayyan da kusan watanni biyar aka wayi gari Nadia na da juna. Misalta muku irin farin cikin da wannan ahali suka tsinci kansu ciki musamman ma Rayyan 6ata lokaci ne. Rayyan ji yake tamkar ya goya ta saboda da'di, ji yayi kamar babu wani sauran bakin ciki da ya rage masa...tunani yake ashe shima yana da rabon ganin 'kwansa a duniya...duk da yake dama ba wai ya cire rai da samu bane a kullum yana kyautatawa Allah zato saboda yasan shi ke badawa ga duk wanda yaso, amma atimes idan ya tuna Anty Madeena da har yau Allah bai nufe ta da haihuwan ba ga Kawu Sufyan har ya bar dunia bashi da magaji sai jikin sa yayi sanyi. Amma tuna cewa Raihana ma ta haihu hakan yakan yakan bashi 'kwarin gwiwa da tunanin shima zai haihu da iznin Ubangiji sai gashi Allah ya cika masa burin sa. Yayin da 6angaren Sultan sam abin ba haka yake ba, kwata-kwata bai tsara hakan cikin jadawalin sa ba, haihuwa daga Rayyan babban nakasu zai kawo ga cikar burin sa, ya jima da 'daukan mataki daga 6angaren Amrah domin da kansa yake 'dirka mata magungunan hana 'daukan ciki har ma ba bisa ka'ida ba. Amrah bata ta6a taka masa birki ba dan sosai kaoaman sa suka yi tasiri cikin zuciyar ta, acewar sa na hana 'daukan cikin sa kawai yake mata a wautar ta kuma sai ta amince da batun sa bata ta6a musun sha ba kamar yadda bata ta6a nuna damuwa ga rashin haihuwar ta ba. Sultan ya jima yana kitsa mata illolin haihuwa agareta, zakayi mamaki idan kaji irin kalaman da Sultan ke sanar da ita tamkar shi har itan ba haifan su aka yi ba, inda ya tabbatar mata da cewar haihuwa jirkita mata halitta zai yi kawai kuma ahakan ta tafi kowacce mace a duniya kyau da tsari, kar ta yadda ta haihu tun yanzu batare da ta mori 'kuruciyar ta ba. ***** Akwana a tashi babu wuya a wajen Allah, sai gashi cikin Nadia nada watanni takwas cif sosai ya gama fitowa, da yake itama ma'akaciyar lafia ce tuni tayi scanning kusan sau uku ana tabbatar mata da cewa cikin 'yan biyu take 'dauke da shi. Ranar da aka 'kara tabbatar mata da hakan kusan kwana tayi tana yiwa Allah godia duk da nawin da cikin ke da shi amma hakan bai sa tayi kasalar yin nafililin nuna godiyar ta ga ubangiji ba. Kuma bata labarta wa Rayyan ba dan tafi so wannan ya kasance suprise mafi soyuwa cikin zuciyar sa da za'ai masa a rayuwar sa. Tafi kowa sanin halin sa da irin tsananin farin cikin da zai shiga idan yaji labarin amma tafi so ya gani kawai da idanun sa ba wai jin labari kawai da kunnuwan sa ba. Da ace Rayyan ma'abocin tambaya ne da sai ya tuhume ta akan kwana sallar da tayi amma da yake shi ba gwani bane wayen shiga rayuwar mutum ya sanya tunda ya lura ta tashin nata shima kawai ya tashi ya jonata, haka ya ringa tayata raya daren dan yasan dama ita ma'abociyar tsayuwar dare ne...sai dai ga mamakin sa har ya kammala yayi addu'o'in sa ya kwanta Nadia bata kammala nata ba, sam sai bacci ya kasa 'daukan sa ma, haka ya ringa juye- juye yana lura da ita har kusan sallar asubah, nan ma bata yi bacci ba har sai da ta dangana da sallar asubah kafin ta koma ta kwanta. Bai yadda tayi bacci ba sai da ya tabbatar ya ha'da mata tea mai zafi tasha kafin a hankali ya ringa matsa mata 'kafar ta yana tsokanar ta. Inda yace " Allah yasa dai nima an nema min gafara da albarkar dan nasan duk wannan dogon daren saboda abin cikin ki ne ka'dai ba ni ba..." Murmushi tayi tana gyara kwanciya tace" Wa yace maka idan ana sallah ana mancewa da alwala...?". " Babu wanda yace...wama ya isa..." Ya bata amsa cike da 'kauna. " Toh kaga, dole shine tushen ibada, taya za'a yi a manta da shi...". Ta 'karashe maganar da hasaso irin farin cikin da zai shiga duk ranar da Allah ya bata ikon sau'ke masa 'ya'yan sa har guda biyu da bai san da zaman cewa su biyu bane acikin ta..... " Ke de fadi gaskia nasan siyasa za'ai min kawai anan...". " Haba yalla6ai...wace ni da yi maka siyasa sai dai in ta maka biyayya har 'karshen rayuwa ta...yauwa ma dan Allah inje Maiduguri mana in duba Umma ta, ni ko kwana 'daya ne ma idan ka amince bazan 'kara ba dan Allah...." Ta fa'di maganar tana mai 'ko'karin sake mi'kewa zaune domin fuskantar sa. " Ai ma bazan amince 'din ba madam balle har ki samu damar 'karawa...". " Haba yalla6ai...dan Allah fa, ni haka kawai kwanan nan nake so in ganta tana yawan zuwa mafarki na...". " Ki bari sai kin haihu..." Ido ta zaro sosai tace " Haihuwa kuma...wannan dogon zangon ai na me nisan kwana ne dan Allah fa kayi ha'kuri..." " Sleep my dear ba wani tafiya da zakiyi ina.tabbatar miki...." Dole tayi shiru amma ba wai dan ta ha'kura ba, ta 'dauki a'kalla tsawon kwanaki uku tana lalla6a shi kafin ta samu ya amince bayan ankai ruwa rana...ya kuma ce ma bisa shara'di ne kwana biyu rak ya bata ta dawo...kuma dole tafiyar jirgi zata yi tace ta amince. Tunda Sultan ya samu labarin wannan tafia ta Amrah ya fara Jin da'di da tunanin babbar dama ta sake zuwa masa bayan tsawon lokacin da ya 'dauka Yana dakon zuwan irin ranan nan. Duk da 'karancin shekarun Sultan amma yawan sharrukan da ke cikin zuciyar sa sun zarta yawan kwanakin sa a dunia. Sultan bashi da burin da ya wuce ace yau shi ne shi ka'dai ke da mallakin INFINITY GLOBAL COMPANY Kano da kuma ( IGC Ikeja.) da wannan burin ya girma aran sa tun Alhaji Sa'ad na raye kuma har yau wannan burin ke sake ginuwa bai ta6a rushewa aransa ba. Burin Sultan ace duk wasu ba'ki ko masu san ha'din gwiwa da companyn Infinity ace da shi suke zama ba da Rayyan ba, babban dalilin da ya sanya ba ya iya zama a Kano sosai ya 'kwammaci yayi ta tafiye- tafiyen izuea 'kasashen 'ketare kenan ko kuma idan ana bu'katar kaya ya tafi shi ya jagoranci tafiyar acewar sa hakan yafi masa da ya zauna yana ganin kayan takaici, kuma ma ai hakan duk 'karuwan sa ne domin zai 'kara samun experience ne sosai kan harkar kasuwancin 'kasashe har lokacin da komai ya dawo hannun sa bashi da fargaba. Saboda Companyn Infinity ya 'kwammaci ya karanci computer engineering badan komai ba sai dan son cika kwantattun burikan da suke ransa. Sultan yakan yi duk shirin sa cike tsari da iyawa, zai yi wahala tashin farko a zarge shi, ko Kabeer ma ya fara zargin Sultan ne sbd zurfafa bincike da yayi, sai dai bai kai ga tabbatar da zargin sa ba Sultan yayi sanadin mutuwar sa. Ko cikin mafarki, ko kusa ko alama Sultan baya 'kaunar yaga ahalin Alhaji Sa'ad na kara hayayyafa a duniya balle har suyi yawan da zasu fi 'karfin shirin sa, domin ba burin sa yayi ta rayuwa 'kar'kashin su ba, burin sa ya kafa kansa ne shima ta yadda dunia zata san da zaman sa, dunia ta dama da shi...duk damuwa da suke da rashin haihuwar su Sultan kawai taya su yake abaki bawai dan yana jimantawa ko 'kaunar haihuwar ta su da gaske bane, musamman Rayyan ya tsani yaji Rayyan ya haihu. Samun cikin Nadia kowa yayi farin ciki da shi illah Sultan da cikin ya kusan zame masa babbar barazana ga shirin sa da 'kyar ya saita kanshi, abu guda daya 'kara masa 'kwarin gwiwa shine tabbatarwa kansa da yayi ko ta halin 'ka'ka ne, ko bayan an haife cikin sai ya halaka abinda aka haifa ya kuma tabbatar wa ransa hakan shiyasa ya watsar da batun kawai ya cigaba da rayuwar sa kamar kowa. Ba dan komai Sultan ya nuna 'kauna ga Marwa har ya aure ta ba sai dan kawai ya ga ya haihu da ita ta yadda kota halin 'ka'ka ne shima ya kasance yana da share acikin Infinity Company. Infinity Global Service babban company ne da ake sarrafa 'karafuna, kuma suke sau'ke motoci manya da 'kanana..kuma Alhamdulillah ya samu kar6uwa, gefe guda kuma ana kasuwancin any kind of computer, typewriting machine, photocopier, scanner, wayoyi da sauran su, duk dai nau'i kan elctronics da ake amfani dashi a 'kasar nan sukan sau'ke shi babban waje ne sosai, kuma Alhamdulillah ba 'karamin samun 'karuwa da Ma'aikatar suke ba kuma. Sannan sukan sau'ke Spare parts na motoci a Infinity dake Lagos dama motocin kansu, Rayyan sun zauna da Ammi akan irin ribar da companyn ke kawowa kwanaki abin har na basu tsoro amma a sirrince suka yi shawarar suka.kuma yanke shawarar bayan zakka da suke cirewa zasu ringa tura wasu ku'da'den cikin asusun kungiyar tallafi ta su Ammi batare da ansan su ke aikawa da ku'din ba, kamar yadda suka saba saka kudi cikin asusun Gidan Marayu batare da ansan su ke turawa ba. Sai dai Rayyan ya ro'ki Ammi akan ta bar aikin ta wakilta wasu Ammi tace sam zata yi abinta da kanta...dole Rayyan ya ha'kura ya 'kyale ta sai dai har gobe baya 'kaunar tafiyen tafiyen Ammi kawai babu yadda ya iya da ita ne ya sashi ha'kuri. Shirye- shiryen tafia Nadia ta fara kamar wacce zata je Saudia, abin har sai ma ya fara bawa Rayyan haushi, ita ma Marwa shige da ficen Nadian sai ya fara 'kona ranta amma bata tanka ba. Rayyan kasa ha'kuri yayi yana tsaye kanta tana zuge zip 'din akwati ya wani 'daure hannayen sa duk biyu a 'kirji yana duban ta har ta kammala sannan yace" Wai duk wannan na menene haka...?" 'Yar daria tayi tana matsar da akwatin tace" tafiya mana..." " Kin mance kwana nawa zakiyi ne...?" " Ban mance ba...amma kasan abu da ikon Allah ne..". Kicin- kicin yayi da fuska " me kike nufi..?" " Kai Yalla6ai...toh in haihuwa ta kamani acan kuma fa..ba dole a bu'kaci wasu kayayyakin ba shiyasa kawai na 'diba zan tafi da kayana..." " Kar kisa in soke tafiyar nan Allah, har hakama zaki ce kenan baki da niyyan dawiwa ma yanzu tunda nasan dai a lissafi haihuwa ma da sauran lokaci..." Ido ta dan fitar..." Haba dai rufa min asiri kar afasa dan Allah, ni wasa nake maka ma, abin bai kai nan ba fa..Kayayyakin ma wasu zan bada ne akwai masu bukata acan shiyasa na 'diba...". " Yanzu na ji zanje...". Yace yana gyara tsayuwa. Yanzu dai kiyi sallah barin je masallaci in dawo sai muje ki yiwa Ammin sallama ko.?" " aha..adawo lpy..". Ta fa'di hakan ne tana 'ko'karin mi'kewa. Daga gidan Ammin Shoprite suka wuce ya sake yi mata siyayyan kayan amfani nata na kanta da ya san cewa zata bu'kata sannan suka dawo gida. Da kansa ya 'karasa ha'da mata sauran kayan ta hadda shirgin handbag da zata ri'ke a hannun ta, ya kuma zuba mata ku'di cikin jakar da bama tasan nawa bane. Yana shirin jefa mata IDCard 'din ta wajen aiki tace" Wannan kam amfanin me ma zai min acan bar min shi agida kawai yafi.." " Gani nayi kin kwashi su handgloves da sauran su na sani ne ko wani sabon asbiti zaki bu'de acan shiyasa zan saka mk Card 'din naki ai may be ki iya bu'katar sa..." Ya bata amsa yana 'yar dariya. Murmushi tayi itama..." Toh ban da abinka dear sabon asbiti ai sai da sabon IDcard..wa zai bu'kaci tsoho kuma..." " Haka ma zaki ce ko...toh sai ince an fasa tafiyar..." " Waiyo Allah na, yalla6ai aimin afuwa ni wallahi wasa nake fa...". " Tashi toh mu wuce ko inzo in 'daga ki..?" " Zan iya da kaina ma..." Ta fa'di hakan tana 'ko'karin mi'kewa dan tasan ka'dan ga aikin Rayyan ne idan yaga kamar sai da taimakon sa ta mi'ke yace ya fasa tafiyar. Har sun fara tafia tana bin bayan sa, sai kuma ta juyo, takaddar last scan da akai mata dake ninke cikin drawer ta dauko ta jefa cikin jaka, bataso ya gani ko da bayam tafiyar ta ne dan duk sauran ta 6oye su shine na 'karshen bata kai ga 6oye shi ba shiyasa ta dauke abinta. Waigowa yayi..." Ya akayi kuma..?" " Mantuwa nayi kuma na 'dauka ma..". " Hmm.." Yace sannan suka cigaba da tafiya. Sai da suka je ta yiwa Amrah sallama kafin suka fito, koka'dan babu wata sha'kuwa tsakanin ta da Amrah amma kuma babu raini tsakanin su sam, dan sosai Nadia ke kama girman ta bata bar kowacce kafa da Amrah zata ga lagon ta har ta raina ta akai ba. Jirgin yamma Nadia ta bi zuwa Maiduguri yayin da Rayyan ya kasa barin filin jirgin har bayan da jirgin da Nadia ta hau ya riga ya tashi. Haka kawai sai yake jin tamkar ta tafi masa ne da wani 6ari na farin cikin sa. Bai bar filin jirgin ba har sai da yaji wayar sa na ringing sannan ya saki nannauyan ajiyan zuciya, ko duba mai 'kiran nasa bai yi ba kawai ya tada mota ya dawo gida. Sai da yayi parking kafin ya 'dago wayar tasa ya duba nan ya tarar da missedcalls har biyar, sai yaga ashe ma Amrah ce ke 'kiran nasa sai Sultan da kuma wani abokin sa Fawwaz amma duk bai bi bayan 'kiran kowa cikin su ba sai na Sultan. " Big bro barka da yamma...ina ta 'kira ne inji ko Anty Nadia ta wuce wlh na shiga gari ne wasu uzururruka shiyasa banzo munyi sallama ba..." " Bakomai Sultan kar ka damu, ta wuce already yanzu ma nake dawowa daga airport 'din.." " Masha Allah...Allah ya dawo da ita lafiya..." Yana 'yar daria yace" Shine ta wuce bata ko yi cigiya ta ba ko dan ma kar na rakata in gano sirrin Kanurai....". Shima Rayyan murmushi yayi sannan ya fara fa'din" Toh 'dan nema, ka mance Ammin ka ma kanurin ce...kaje wajen ta duk wani sirri da kake nema zaka samu a wajen ta ai...". Hannu Sultan ya toshe bakin sa yana daria 'kasa 'kasa..." Yace ai Ammi na ta musamman ce ta riga ta sanar da ni wanda ta sani sauran Anty Nadia aka barwa" Shima Rayyan dariya kawai yayi daga 'karshe cewa yayi..." Indai Nadia ce ai zata 'kira ka indai ta sau'ka.." Daga haka ya yanke wayar yana 'ko'karin fitowa cikin motar. Sultan dake kwance a wani tsadajjan 'dakin hotel tun bayan fitar Amrah da ya sallame ta bai iya ya tashi ya shirya ba ma balle yayi niyyar barin hotel 'din. Duk tunanin sa ya tattara ne izuwa ga Nadia da abinda zata haifa, sosai yake marmarin ganin ya salwantar da koma menene..ko bayan da suka yi waya da Rayyan cikin zuciyar sa fata yake ace jirgin nasu ya 'kone a sama, inama gobe da sassafe yana bu'de Television cikin kanun labarai ya tsinci cewa anyi plain crash daga Kano zuwa Maiduguri. Mi'ka yayi sosai akan bed 'din hotel 'din, a hankali tuno moments din su da Amrah sai yasa shi sakin murmushi, ya tabbatar zuwa yanzu ta isa gida, sosai yake enjoying kasancewa da ita badan komai ba sai dan kawai yaji aransa cewa ta wannan 6angaren Rayyan bai zarta shi ba. Inda yake tutiya da alfaharin yan shiga shima tuni ya ratsa shi, Nadia ce ka'dai ya kasa samun wannan damar daga gare ta bai ma ga fuska ta wannan 6angaren ba. Sannan ya riga yayi maganin matsalar sa ta 6angaren ta dan yasan abu ne mawuyaci Amrah ta samu ciki inma ta samu 'din zai yi wahala ace har cikin ya bayyana batare da ya sani ba. Abu 'kalilan suka rage masa a yanzu da suka hana shi cimma burikan sa sai dai sun kasance ne kuma sune tsani mafi girma da ha'dari a gare sa, kuskure ka'dan zai yi ya tona asirin kansa shiyasa yake bi a hankali. Dole zai auri Marwa ta kasance 'kar'kashin ikon sa, inda hali wajen haihuwa yake son Nadia ko abinda zata haifa daya ya tafi abin zai fi zuwa masa da sauki bayan wani 'dan lokaci sai ya sa 'dayan ma yabi bayan 'dan uwan sa, in ma Nadian ce ko kuma abinda zata haifa shikenan labarin su ya shu'de. Wannan duk mai sauki ne a ganin sa, domin yana da hanyoyin da zai bi kuma yana da ku'din da zai iya sawa duk shirin sa su tafi bisa tsari kamar yadda ya shirya. Raihana ba damuwar sa bace balle 'dan ta 'kwaya 'daya tilo da take da shi wato Bassam, domi ko da ace ya bar ta a raye yasan ba ta da iko da kuma sani akan wasu abubuwan na gidan su da dukiyar su kamar sa. 'Dan ta kuwa da gidan uban sa zai yi tutiya ba gidan mahaifan uwar sa ba. Babban abin harin nasa dama Rayyan ne, amma dole sai yabi komai a hankali. ***** Nadia sosai taji dadin zuwan ta gida dan ta tarar da Umman ta lafia 'kalau, mahaifin ta ne ma yake 'dan fama da hawan jini amma bai kwantar da shi ba. Akwai wata kanwar Umman ta dake aure acan Damaturun jihar yobe kuma tana fama da ciwon Cancer tsawon watanni ko da Umman ta ke bata labari cewa tayi zata je ta duba ta kafin ta wuce. Umman ta taso hanata musamman sbd yanayin da take ciki Nadia 'kin amincewa tayi, tace" Umma ai babu dadi taji cewa nazo kuma banje na gaishe ta ba, ba wani abu ai Umma, shi nauyin jiki kam ai ba sabon abu bane, na taso tun daga Kano ma balle nan Damaturu mintina nawa ne naje na dawo..". Kai Umma ta ka'da" Toh shikenan Nadia amma ki fara sanar da shi mai gidan naki tukunna idan ya amince sai a samu driver ya kaiki a motar Abban ku a abiyashi tunda ba da mota kika zo ba..." " Bari dai in yi magana da shi tukunna Ummah ka'dan ga aikin sa ne ma yace bai yadda ba...". Ta fa'di hakan tana barin 'dakin ta nufi masau'kin ta. Ringing biyu Rayyan ya 'daga..." Mrs Rayyan ya akayi..? Mantuwa aka yi ne da ba'a fada 'dazun ba sai yanzu...?" " Kamar ka sani..." Ta bashi amsa tana gyara zaman ta dan irin wannan magana ga Rayyan sai ta nutsu sosai sbd sanin halin sa da tayi. " Uhum inaji Mrs Rayyan bani labari..". Murmushi tayi..." Kasan Aunty na na Damaturun nan ko, ina nufin 'kanwar Umma ta...?" " Yes..Anty Yakura...". " Yauwa Dear, dan Allah inaso inje in gaishe ta ne, wallahi wai bata da lafiya serious kuma babu da'di ace nazo har nan na koma ban duba ta ba..kuma kaga bansan ramar dawowa ta....pls my dear...". Zaune yake saman kujerar sa na office amma da jin furucin Nadia sai da mi'ke tsaye ya isa wajen window ya tsaya, tun ma kafin ta kai aya sai ma ya kasa cewa da ita komai har ta dasa aya. Jikin sa rawa yake tsabar takaici. Shin manta yanayin da take ciki tayi ne ko kuwa. A hankali ya 'kira sunan ta..." Nadia...."! Abinda ta da'de rabon da taji ya fito bakin sa kenan. Sosai taji bakin ta ma ya mutu da 'kyar la66an ta suka iya motsawa ta amsa da na'am Hubby...". " Don't pls..don't Hubby me..." Ya fa'da har yana 'daga hannu kai kace tsaye take gaban sa yana duban ta. " Dan kin samu kin tafi shine zaki tsiro min da wani abu ko...?" " I'm sorry..in baka amince ba shikenan..". " Yes ban amince ba nd ki shirya gobe da sassafe ki dawo Kano.." " Ok..." Ta tace tana yanke wayar. Basu sake magana ba. Ita kanta Umman ta da taji shiru bata 'kara bi takan ta ba dan tana da ya'kinin bata samu damar tafiyan ba shiyasa taji ta shiru bata fito 'dakin ba. Haka 'yan uwa na kusa suka rinka zuwa gaishe ta sakamakon yanayin ta suka ce bazai yiyu tayi ta zirga zrigar zuwa gidajen su ba acikin kwanaki biyu kacal da zatayi bayan ta riga da tayi nawi. Da yawa ma fa'dan tahowar tata suke yi idan suka ji cewa tafiyar ta kwana biyu ce, bayan sunyi zaton haihuwa ta dawo yi a gida kamar yadda wasu ke yi amma sai tace a a..yanzu laifi ne da na zo aka sada zumunchi. " ba laifi bane amma ai da kin bari idan Allah ya sauke ki lafia sai ki zo ziyarar ki ki sada zumunchi yadda ya kamata babu mai cewa a a". " Wannan ai lissafin Gaibu ne, mu da bamu san 'karshen yinin yau bama ballantana na gobe talkmore of bayan haihuwa yaushe zamu ringa dogon lissafi...". Amsar da Nadia ke basu kenan kuma sosai take gamsar da su dan maganar tata tafe take da hujja 'kwakkwara. Zuwa azahar Rayyan ya sake 'kiran wayarxta kamar yadda ya saba ko da tana gida indai shi baya nan yana office ne ko wani wajen daban yakan kira matan sa yaji lafiyar su akai- akai. Yana fitowa daga masallaci Amrah ya fara 'kira kafin Nadia sai dai bata yi picking call fin ba sakamakon hayaniyar ba'kin da take cikin su suna ta shan hira. Sai da yayi mata missedcall biyu kafin ya bari. Ganin bata daukan ba dai domin shi ba gwanin jerawa mutane kira bane daya yake mai hujja ya bari. Amma wannan karon sai yaji ya kasa samun natsuwa da Nadian bata 'dauki 'kiran ba. Yana shiga office 'din sa ya sake gwada 'kiran layin nata yana kuma tunanin ayyukan da ke gaban sa, domin akwai wasu jerin takaddun da suke jiran saka hannun sa kuma zuwa yammaci ake bu'katar su...amma ji yake mutukar bai gana da Nadia ba bazai iya aikin ba. Cikin sa'a wannan karon sai tayi piciking. Tsaye yake ya kama jikin kujerar tasa cike da fargaba amma da jin ta 'dauka ya sa shi sakin boyayyiyar ajiyan numafashi yana zama bisa kujerar ya wani yi baya da ta ita ya 'dora 'kafa 'daya bisa 'daya saman Desk din dake gaban sa na office." Mrs Rayyan fushi...?" " a a " Ta bashi amsa atakaice. " Toh menene...Na 'kira tun 'dazun but u didnt pick d call har kin sani cikin fargaba..". " Bakomai, ina cikin ba'ki ne..". " Kuma kina fushi..."! Sai tayi shiru. " Right...?" " a a kam". " Fa'da min gaskia dear." Sai tayi shiru. " Na sani ai, I heard ur voice ba haka na saba ji ba..ke bazaki gane abinda nake nufi bane, sam bakya tausayin kanki naga alamu..." " Bakomai fa babu abinda ke damu na ko da na taho ma ba wata gajiyar da naji.." " Really..?" " Yes har aiki nake taya Umma fa..". " Da kyau, amma ai da bambamci, that's airjourney nd this tafiyar mota ce, dole gajiyar ta bambanta, nasan dole ne zaki gaji because its 2 to 3 hrs journey kuma ki dawo aranar akwai gajiya fa dear...kuma ma kuma ma who ll massage ur legs idan kika dawo..?" " Zan tara idan na dawo duk ka fanshe min abu na..." " Ba ruwana, ni na saka mutun yawo ne...?" Murmushi tayi cike da jindadi, tasan zai barta tafiyar a yadda ta fahimci kalaman sa. " Kinsan mene..?" " Sai ka fa'da " " Ki tura min numbern Auwal ko kuma ki ha'da ni da shi( Kanin ta..), zan mai magana ne ya samu mota mai kyau sai akai ki zan tura miki ku'di sai ki mata siyayya amma pls ki kula kinji...?" " Insha Allah, thanks my dear Allah ya bar min kai, Allah ya kare min kai, Allah ya baka zuri'a masu albarka ya kuma baka ikon kulawa da su" " Ameen Ameen...Ameen Yah Rabbi..". Ya ce cike da jin dadin addu'ar ta. " Amma ina da sauran kudi a hannu na, kuma akwai ATM a waje na I think ba sai ka 'kara tura ku'di ba zan yi duk abinda ya dace..." " Ban dai isa ba kike nufi..." " Haba dai..kai kuwa ka isa har ka fi ma.." " Toh abar ni, nima ladan nake so nasamu ai..". " Shikenan..Allah ya 'kara arziki mai albarka.." " Amin...thank u.." Yana shirin yanke wayar tace" Maganar Mota kuma...?" " Uhum ina jin ki. " Dama nace ko za a sama min 'karamar mota a tasha sai muyi tafiyar kaga wanda ya kainin shi zai dawo dani har gida..." " Ok ba matsala dama magabar da zanyi da Auwal kenan..Amma dai ki ha'da ni da shi'din in mai bayani da kaina nafi so sai ya tabbatar yana da sani akan driver din sosai tukunna" Da hk suka yi sallama ta kuma tura masa numbern Auwal din sun yi magana 'karshe da kansa ya 'kara mata kwana 'daya akan wanda ya bata da farko...tayi murna sosai da jin hakan kuwa dan zata fi sakewa. Washe gari da safe suka yi tafiyar cikin sa'a suka isa lafiya, ba 'karamin tausayawa halin da Anty Yakura ta ke ciki tayi ba, duk da suna da 'karfi amma jikin ne sai a hankali kuma ba laifi ana 'ko'kari sosai kan kulawa da ita. Ita kanta Anty yakuran da taga yanayin cikin Nadia sai da tai mata fa'da sosai akan wannan ganganci nata duk da koka'dan cikin ba mai wahal da ita bane amma girman sa ke sawa suke gani kamar 'karfin hali take ita kuwa rass take jin kanta sai dan abinda ba'a rasa ba. Kwanan ta guda a wajen Anty Yakura washe gari da safe suka yi musu sallama da nufin komawa Maiduguri daga nan kuma idan ta huta d following day ta kama hanyar Kano. Salmerh 😘 [19/10/2022, 6:11 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Wattpad@* _Serlmerh-md_ 🅿️ *...55* .......Tun kafin azahar yake faman neman layin ta amma wayar bata tafiya, sosai yake jin hankalin sa a tashe, ranar ko office ha'kura yayi da shi ya dawo gida musamman yadda yake ji zuciyar sa na mai zafi, fargaba ya gama cika masa zuciya, duk wani 'kwarin gwiwa tasa tuni ta bar shi. Kwance yake a 'dakin sa har wani zazza6i zazza6i yake ji na shigan sa yayin da Amrah ke gefen sa tana 'ko'karin kwantar masa da hankali sai dai koka'dan bata ga alamun nasara ba. 'Karshe shafa kansa ta koma yi a hankali tana taya shi jimantawa. Bayan yawan Dialled call dake wayar sa na numbern Nadia ita kanta Amrah ajiye batun kishi tayi sbd yadda taga ya koma ta gwada kiran layin Nadia fin sau goma sha biyar amma duk basu same ta ba. Akai- akai yake 'kiran Auwal yana tambayar sa ta iso gida ne Auwal nace masa "a a" shima cab tuni hankalin sa yake atashe musamaman da yake da labarin harin da akai yau a garin na Damaturu sun kuma tuntu6i Anty Yakura ta tabbatar musu da cewar Nadia takwas ma bata same ta a gida ba. Innalillahi wa inna ilaihi raji'un kawai Auwal da Abbahn su ke nanatawa. Umman Nadia kam tuni ta fara kuka. Abban su ne ke kokarin kwantar musu da hankali duk da shima 'karfin hali kawai yake amma tuni lamarin ya sanya shi cikin fargaba. Numbern drivern da Auwal ya kar6a ma yayi ta gwadawa bata tafiya. Rayyan kam mutuwar jiki bata tashi kama shi ba har sai bayan da Sultan ya 'kira shi yake tambayar Nadia ta iso gidane.." " Rayyan yace a a atakaice ya masa bayanin halin da suke ciki ma yanzu haka...na rashin samun ta har ya fara tunanin bin bayan ta. Ashe Sultan na tare da Ammi ne alokacin sakamakon labarin da suka ji ayanzu nan yasa ta saka shi nemo Rayyan 'din a waya. Sai dai jin amsar da ya bawa Sultan ya saka ta amshe wayar tace kul kar ma ya fara batun tafia, Maiduguri har Damaturun yau ba su tashi cikin yanayi mai da'di ba, ya bari a cigaba da neman ta awaya a kuma cigaba da addu'a Insha Allah babu abinda zai samu Nadia. Duk Rayyan bai da wannan labarin sai yanzu domin tuni ya na gida kuma basu kunna television ba. Amma jin wannan labari shi ya sake ta'azzara yanayin sa dan hatta Auwal da yake 'kira balbale shi yayi na 6oye masa da yake tuntuni bai sanar da shi ga abinda ke faruwa ba. Wasa- wasa har yamma babu Nadia babu labarin ta. Kamar wasa kamar gaske sai ga labarin na neman girmama izuwa wani abu daban har wayewar safia. Rayyan da ya kasa hakuri dole sai da Ammi ta hakura ta barshi ya tafi. Tuni ma an riga an saka doka 48hrs a garin so bashi da damar isa har bayan wannan awannin. Tare da Sultan zasu kuma yaso suyi tafiyar mota amma Rayyan yace sam mota 6ata musu lokaci zata yi...dole badan Sultan yaso ba sai da suka yi bi jirgi bayan cikar awanni arba'in da takwas wanda yake dai dai da cikar Nadia kwanaki uku kenan ba asan inda take ba. A cikin tsawon kwanakin nan irin ramar da Rayyan yayi har sai ya baka mamaki, domin lokaci guda ya zabge tamkar bashi ba, bai ta6a zaton yana yiwa Nadia irin wannan 'kaunar ba sai yanzu...ji yake inama inama, inama tun farko bai amince mata tayi tafiyar ba...da yasan wannan tashin hankalin ne zai biyo ba da bazai ta6a amince mata tafiyar ba...sai dai komai nufin Allah ne..komai Allah ke tsarawa. Kwata- kwata ma mancewa da cikin da take dauke da shi yayi saboda tashin hankalin rashin ta yafiye masa wannan, sai dai lokacin da cikin ya fa'do ransa ma da wuri ya kawar da tunanin sa domin yasan matu'kar ana raye inda rabon sa Allah zai sake bashi wani amma Nadia fa, baya jin zai iya samun mace a duniyar nan kamar ta, mace mai sau'kin yanayi, fahimta, juriya, hakuri da da'din zama. Mace ce da ya san indai har da gaske damar shiga aljannar ta a hannun sa take toh indai ya kasa bata wannan damar toh bai yiwa kansa da ita kanta adalci ba, babu ta inda ta rage shi sai dai abinda ba'a rasa na daga ajizanci irin na Adam. Tun ba yau ba ya jima da mata la'kabi da suna mar'atussaliha. Ko da ya isa Maidugurin babu abinda ya canza sai 'karin tashin hankali daya riska, ayadda yaga yanayin su Umma da su Auwal sosai shima ya 'kara shiga cikin ru'dani, bai tsinke da lamarin bama sai da suka yi masa cikakken bayanin abinda ke faruwa. Shikansa salati kawai.ya fara yasa hannuwa duk biyu yana shafo kansa. Baya so tun yanzu ya nuna karayar sa amma sosai yake jin tsoro. Sai dai babban tsoron nasa ya zarta wannan. Yana shakkan yadda da abinda zuciyar sa ke raya masa...baya fatan ace hakan ne ya kasance, bazai iya jure wannan lamarin ba sam. Idan akace 'yan ta'ddan nan ha'duwa suka yi da Nadia suka 'dauke maasa mata da ke dauke da cikin sa, kuma kashe masa mata suka yi...baya fatan cikin duk wa'dannan guda daga cikin su ya kasance gaskia. Da yake yana hul'da da manya haka ya sa batare da 6ata lokaci ba akayi masa bincike sosai amma Allah da ikon sa babu wani labari da ya shafi Nadia. Motoci 'konannu da gawarwakin mutane aka samu masu yawan gaske, wasu ma tuni har 'yan uwan su sun 'dauke su dan yi musu sittira yayin da wasun kuma abin sai a hankali sam babu kyan gani suna nan babu ma alamun za'a zo gare su...mutun dai, ran mutum dai haka tamkar ba 'dan Adam da Allah da kansa ya karrama ba...sosai ya ka'du da ganin abubuwan nan, kuma har a lokacin wasun su basu samu kula yadda ya dace ba hakan kuma shi yake sanadin wasu daga cikin victims 'din yayin da wasu ke cikin mawuyacin yanayi. Shi da kansa ma mancewa da damuwar sa yayi tuni ya sakala handglove ya taimakawa da dama daga cikin victims 'din da iya taimakaon da zai iya na daga ilimin likitanci dayake da shi cikakke. Zuwan su asbitocin nan soai ya 'kara sanyatar da jikin Rayyan da 'kyar kuma binciken su ya nuna musu motar da Nadia ta taho da shi ya kone 'kurmus, kuma bisa ga bincike jami'ai sun antabbatar da cewa tare da mutane fasinjoji acikin motar ta 'kone kuma tuni an binne su, kuskuren da suka yi shine basu fa'di mutane ko nawa bane aka cire a cikin motar abinda ya sake tada hankalin Rayyan kenan, dan yasan matar sa ba tafiya tayi ta cikin jam'in mutane ba, balle har a dangana ta da fasinjoji. Sosai abin ya 'daure kansa, sai dai ya kasa yadda da bayan nasu. Ko da suka nemi cikakken bayanai akan lamarin basu samu komai yadda ya dace ba. Yadda yake ji kansa ke juyawa ma ji yake ya tsani komai dama garin gaba 'daya, sauran abubuwan Sultan ne ya 'karasar da su da wasu cike ciken file na cikiya hadda photon Nadia suka bari wajen hukumar bincike ko da ko da za'a dace da ganin Nadian sai a sanar da su...dan sam Rayyan bai yadda da waccan bayanan ba, duk kuwa da cewa hukumar transport ta tabbatar musu da cewa lallai motar nan da aka samu konanniya kan hanya daura da wani 'karamin 'kauye akan hanyar Maidugurin lallai itace motar Haruna dirver da yakai Nadia Damaturu, domin kafin tafiyar sa sai da ya sanar da hakan, kuma iyalan sa ma sun tabbatar da cewa motar tasa kenan sakamakon numbern motar da suka iya ganewa, sai dai shima har a lokacin basu samu wani sahihin labarin inda yake ba. Daga Damaturu har Maidugurin aikin da suka yi kenan kusan kwanaki hu'du suna abu 'daya...da 'kyar suka samu suka dawo gida bayan duk sun fita hayyacin su sbd tsananin rashin. sukuni da tashin hankali. Ko da suka dawo gida koka'dan Rayyan ya kasa komawa dai- dai, a kullum damuwar sa 'kara yawaita take yi. Tsoro yake ji kar ace irin rabuwar da zaiyi da Nadiar sa kenan, kuma can 'kasan zuciyar sa yake jin wani abu na tabbatar masa da cewa mayuwaci ne idan Nadia tana raye, in kuwa tana rayen toh tana ina? tana ina ta barshi cikin mayuwacin halin rashin ta. Sultan kam duk lokacin da ya dubi Rayyan sai dai ya saki makirin murmushi sosai yake jin da'di da faruwar wannan al'amarin domin aganin sa 'yan ta'addan sun sau'ka'ka masa al'amura ne. An doshi sati har biyu kenan yanzu da rashin Nadia sosai zu'katan ahalin biyu ke cikin tsananin tashin hankali, kar ma Anty Yakura taji labari domin in ka 'dauke Umman Nadia da Rayyan toh Anty yakura tafi kowa shiga damuwa sbd tasan sanadin ta ne komai ya faru, ita ne tazo ita ta zo dubawa, duk da kuwa tasan girma da dajarar kaddara ga duk wani muslumi amma damuwar rashin Nadia da rashin samun cikakken bayani game da ita sai ya hana Anty Yakura samun sukuni kwata kwata. Dole suka sake bu'de wani babin binciken da taimakon mai gidan ta suke nasu daban domin ko ba komai zata so ace kowa yasan takamamman halin da Nadia take ciki, inma bata raye zata zo su san cewa erh bata rayen dagaske da kwakkwaran shaida da kuma Hujja tanadaddiya...sbd hankula zasu fi kwantawa. ***** Zaune yake gaban Ammi bayan ya shigo gidan gaishe ta da safia, amma yadda Ammi ta ganshi sai taji duk hankalin ta ya tashi sosai itama, kusan kowacce rana Rayyan sake zabgewa yake yi, yayin da Amrah kanta bata samun hankali da natsuwar sa cikin kwanakin kwata- kwata. Ita kanta Amrah rashin Nadia ya ta6a ta sosai amma da yake tana tare da shai'dani sai ya 'ki bawa hakan damar bayyanuwa a zahiri. Dai- dai da 'kwayar zarra Sultan bai canza daga yayayin sa ba sai dai na ganin ido wanda yake yin sa na 'dan lokaci, sai dai ko in yana tare da Ammi, Rayyan ko Marwa yake nuna cewa shima fa yana cikin damuwa da rashin Nadia, amma sa6anin wa'dannan rayuwar sa yake cike da walwala da jin da'din nasara da kesake tunkaro sa a ko wani lokaci. " Rayyan har sai yaushe zaka gane cewa mutuwa da rayuwa duk a hannun Allah suke ka daina damun kanka, kaga kuwa yadda ka dawo? so kake kace min ja da ikon Allah kake ko me Rayyan...?" " Ammi ba ja nake da ikon Allah ba, ni waye da zan ce ban yadda Allah ke kashewa da rayawa ba, kawai dai Ammi ni kaina bansan meke damuna ba, na kasa cire lamarin araina.." " Ammi..Nadia nada wata daraja ne a idanu na wanda zai yi wahala na iya mancewa da shi cikin lokaci 'kan'kani haka balle ace mancewa na har abada, damuwa ta a kullum bai wuce na in san inda take bane a yanzu, shin tana raye ne ko kuwa ta barni, wallahi a kullum jin zuciya ta nake tamkar zata fashe saboda ra'da'din rashin ta Ammi.." " Ha'kuri zaka yi mu kuma cigaba da Addu'ah, ni kaina wannan abin na tsananin 'daure min kai, gashi abin damuwar ma shine tsohon cikin da take tare da shi..fatan mu a kullum shine ubangiji Allah ya bata kariya ya bayyanar mana da ita a duk inda take cikin koshin lafia..". Sunkuyar da kansa kawai yayi yana jin wani 'kuna cikin zuciyar sa...a duk lokacin da ya tuno cikin da take tare da shi ji yake tamkar ransa zai bar jikin sa ne, sosai yake tsananin tausayin halin da Nadia zata shiga da tsohon ciki jikin ta...Yah Allah ka bayyana min iyalaina ka kare min su a duk inda suke". Wannan shine addu'ar da yake yi kusan kowa ni lokaci fili da zuciyar sa. Ya jima yana 'kaunar haihuwa ya jima yana son ganin gudan jinin sa a dunia amma Allah bai bashi wannan damar ba sai a wannan lokacin sai gashi kuma bayan ya gama saka rai da samun haihuwar sai Allah 6oye masa su cikin 'kudurar sa. Dalilin yawan damuwar Rayyan akan Nadia da har Amrah ta fara kawo mata 'korafi ya sanya Ammi zuwa gidan da kanta ta ciccire duk wasu photuna da duk abinda daya danganci Nadia cikin gidan tayi musu ajiya mai zurfin gaske ta inda kwata-kwata tunanin sa ba zai kai ba..hkn yasa ko wani irin bincike zaka yi cikin gidan bazaka ta6a cin karo da photon Nadia ba, tayi tayi da shi ya saki ransa amma abin ya gagara hkn yasa kawai take yi masa nasiha kullum gami da Addu'ar samun sassauci wurin mahalicci. Aganin ta zuwa yanzun kam ya kamata ace sun yadda cewa Nadia ta barsu kenan bari na har abada, kamar yadda aka bayyana musu tun farko ta 'kone cikin mota kamar kuma yadda mahaifan ta suka yadda suka kuma 'dauki dangana suka mi'kawa Allah sauran lamuran, to kuma su wenene da bazasu fawwalawa Allah ba, tunda sun riga da sun san haka..a ganin ta Addu'ah ce kawai yanzun zasu cigaba da yi mata bakomai ba. Ko jiya sai da suka yi waya da mahaifan Nadia su ka zanta da mahaifiyar ta ta kuma fahimce ta sosai domin mutanene su masu dattako gami da tawakkali, 'karshe ma ita Ammi daya kamata tai musu jaje ita Umman Nadia ke 'kara bawa ha'kuri gami da 'karfafa mata zuciya. Kwatsam bayan kwanaki ka'dan sai binciken Anty yakura yai tasiri har ya kai ta ga cin nasara inda ta binciko duk wani abinda ya faru da Nadia...acikin jerin wasu files da aka riga aka rufe babin su. Har da Photon Nadia da aka 'dauka da 'dan jaririn ta data haifa kafin rasuwar ta mai tsananin kama da Rayyan tamkar an tsaga kara, sai kuma bayanan kwanakin da abin ya faru wuri da kuma lokaci duk acikin file din, already ma an riga an binne su domin an gane cewa musulma ce ita da jan lalle da take 'dauke da shi bisa hannayen ta duk biyu. Wannan labari shi ya sake tada hankalin Rayyan jin cewa ta haifa masa cikin sa kafin barin ta dunia sun kuma koma ga mahalicci a lokaci guda, sai dai gefe guda kuma sai ya dan ji natsuwa sakamakon sahihin labari da ya samu harda photon su da aka 'dauka bayan rasuwar su aka yi amfani da shi cikin file 'din. Ya nemi abasu photon da dake cikin file 'din bai kuma samu matsala da hakan ba. Ranar da Rayyan ya dawo Kano yasha kuka da hawayen sa abinda bazai ta6a iya tuna rabon sa da yi ba. A duk lokacin da yaga photon Nadiar sa kwance cikin jini da marigayin jaririn sa abun sosai yake ta6a masa zuciya. Sai dai sanin da yayi cewa Allah shike kashewa yake kuma rayawa, yasa dole ya ha'kura ya cigaba da yi musu addu'ah da fatan Allah ya gafarta mata zunubanta da duk yan uwa musulmai. Tun bayan bayyanar mutuwar Nadia a zahiri Da suka dawo gidan Ammi suka dan yi kwanaki biyu har yau basu sake komawa gidan su ba zaman gidan ya zam na dindindin. Duk da ko ha'di babu da wannan na Ammi da kuma nashi daya ke kamar aljannar dunia amma hakan bai sa dai-dai da rana guda Rayyan yaji sha'awar komawa wancan gidan ba. Kuma har gobe bai manta da Nadia ba da duka ahalin sa da ya rasa a duniyan nan, yasan cewa wannan ma 'daya daga cikin jarrabawa ce ta ubangiji, a kullum fata da burin sa shine Allah ya bashi ikon cinye dukkan jarabawar sa a duniyar nan. Bayan rasuwar Nadia da wasu watanni aka wayi gari Amrah nada juna, sunyi farin ciki sosai sai dai 6angaren Rayyan bai ma san mai ze ce yake ji game da cikin ba, a zahiri da ba'dini yakan ji ne tamkar bashi begen cikin koka'dan. Kamar wasa bai fi sati guda da bayyanar zancen cikin ba aka wayi gari babu shi Sultan yasa an mata allura cikin da yake na satikan da basu fi bakwai ba babu shi an wanke shi. Rayyan bazai ce bai yi ba'kin ciki da lalacewar cikin ba, musamman da yake binciken likitoci ya nuna cewa cikin cire shi akayi amma ya kasa tuhumar Amrah akan sa sam. Ya dai 'dauke mata wuta na wani lokaci da tunanin 'danyan kan tane yasa ta cire cikin bakomai ba. Yasan Amrah akwai rashin wayo ita aganin ta har yanzu bata shirya hayayyafa ba ne bai san cewa duk bisa tsari da shirin Sultan take tafia ba. Sultan ya riga ya dasawa zuciyar sa cewa bazai ta6a bari Amrah ta haifawa Rayyan 'da a duniyan nan ba matu'kar yana raye. Sam ya mance da cewar Allah ke yin komai a duk inda yaso a kuma duk lokacin da yaso. Wani lokaci idan Sultan yayi wani abin sai ka rantse da Allah cewar bai ta6a zaman ajin islamiya ba nan kuwa har saukar alkur'ani sai da yayi kamar yadda duk 'ya'yan Alhaji Sa'ad Auta suka yi. An wadata su da ilimi boko da arabi shine kawai ya fita daban sakamakon zuciyar sa da ya riga ya gur6ata ta da son zuciya da tsananin butulci da son kansa. Ata'kaice Sultan ne munafukin gidan gaba 'daya, shi yasa aka kashe Abbah da Kawu Sufyan, ya kuma yi sanadin mutuwar Kabeer, Safaa da iyalan Kabeer din, 'karshe ya auri Marwa da burin kawai ta haifa masa 'ya'yan da zai yi tutiya su kuma zame masa tsani wajen mallakar dukkan dukiyar Familyn Alhaji Sa'ad Auta, yana kuma fita da Amrah wato matar RAYYAAN a 6oye sannan can 'kasar zuciyar sa ya 6oye soyayyar Zaitoon da ta kam shi tun ranar farko da ya ganta har zuwa lokacin da nasara zata cimmasa ta kasance tashi shi ka'dai, 'karshe yanzu ya zo ya nemi ran Rayyan bisa taimakon ma'akaitan sa sakamakon gani da yake kamar ya dace ace Rayyan ya bar dunia domin ya masa babakere bisa abubuwa da dama, kuma dole sai babu shi kafin ya samu damar mallakan komai da yk so ciki kuwa harda Zaitoona. Domin matu'kar suna raye da kunya ya dubi tsabar idanun su yace yana bukatar auren Zaitoon bayan 'diyar su Amrah yake aure. Wannan shine takaitaccen tarihin Alhaji Sa'ad Auta da iayalan sa, duk abinda kuka ga bai zo cikin labarin ba yana nan agaba ka'dan komai zai bayyana Insha Allah. ```~One love~``` 🫶 Back to labari........👇 ( Ammi tasa ta tura Huzaifa ya nemo mata Rayyan bayan 'konewar motar sa...) Salmerh😘 [21/10/2022, 3:25 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Wattpad@* _Serlmerh-md_ 🅿️ *...56* ........Ammi bata iya ta sake 'kwakkwaran motsi ba har sai da taji tashin sallama da shigowan Rayyan bayan sa kuma Huzaifa ne. Wani sassanyan ajiyan zuciya ta sau'ke da ganin Rayyan lafiya 'kalau. " Afternoon Madam.." Cewar Huzaifa yana 'dan rissinawa. Hannu kawai ta 'daga masa amma idanun ta na kan gudan jinin ta ne da ya koma gefe da ita ya zauna yana fitar da huci mai zafi. Huzaifa bai sake 6ata lokaci ba yayi gaba abin sa domin yasan ko ba'a fa'da masa ba da kansa yasan ba'a bukatar sa a wannan zaman. " Ammi barka da isowa..." Yace bayan fitan Huzaifa. Bata amsa shi ba illa duban sa kawai da take yi. Jin zuciyar ta take tamkar na tafarfasa ta ciki saboda taraddadi. Kallon 'kwayar idanun Rayyan ka'dai ya sake 'dimauta mata tunani, domin tasan shima 'din cikin yanayi na damuwa yake. Bata masan me zata ce ba a yanzun saboda rsananin.karaya da taji tayi, ashe tsugunne bata 'kare musu ba tsoro take kar labari ya sake maimaita kansa. Rayyan bai ankara ba sai gani yayi hawaye na sakkowa cikin idanun mahaifiyar sa. Da sauri ya gyara zama daga kishingi'dar da yayi. " Haba Ammi...haba dan Allah Ammi...idan ke da kanki zaki dinga zudfa hawaye akan irin wa'dannan 'kananun abubuwan ai 'kwarin gwiwar mu zaki kawar mana...ni banga abin damuwa ba tunda gashi Allah ya tseratar da ni...komai 'kaddara ne fa, kin manta ke ke tunatar da mu hakan, kuma kinsan 'karfen bature ba'a iya musu ai...." Da sauri Ammi ta tareshi. " Kaimin shiru Rayyan, bana san wannan rufa rufar...irin wannan abin ne kake 'kira da suna 'kananun abubuwa? a tunanin ka idan 'kananun abubuwan da kake ikirari suka cigaba da faruwa har akwai wani sauran 'kwarin gwiwa da zai mana saura ne? mu kam mu labarin mu.shudewa zaiyi talkmore of wani 'kwarin gwiwar mu...?" Sosai jikin Rayyan yayi sanyi, da duk hannuwan sa biyu da ri'ke kansa da yake ji na juya masa sam yama rasa ya zai yi da Ammi a wannan yanayin baya son wannan 'kwallar tata sam, a cikin 'kirjin sa yake jin ciwon su. Cike da raunin murya yace" Ammi pls..ki bar kukan haka nan dan Allah.." Bata kula da maganar sa ba illa cigaba da magana da tayi..." Tsoro nake ji Rayyan, kai kasan abubuwan da sukai ta faruwa a gidan nan bana so wani abu ya same ku, a yanzu ku ka'dai nake dashi kuma kune farin ciki na..taya kake tunanin zan iya kwantar da hankali na bayan irin wa'dannan abubuwan na cigaba da faruwa...?" Hannun ta yayi saurin kamawa" Ki kwantar da hankalin ki Ammi, Insha Allah babu abinda zai faru da mu, kin manta yaranki are kinda warriors? Insha Allah together we would succeed tare zamu rayu har 'karshen rayuwar mu..." Wannan kalmar ce ta sanyaya ranta har yasa ta murmushi.." Rayyan bani labarin abinda ya faru pls.." Shiru yayi ya kalle ta, a yadda yaga ta 'dan saki rantan nan baya 'kaunar abinda zai sake dama mata yanayi balle har ace shine da kansa ya furta mata da bakin sa. Tsaye ya mi'ke ya shiga kitchen Ammi ta bishi da idanu, nan ya kawo mata ruwa mai sanyi da cup ya tsiyaya mata ta sha, yana shirin 'karawa tace a a. Yana ajiyewa kan center table yake cewa" Ki kwanar da hankalin ki Ammi komai ya riga ya wuce ai, bagani zaune agaban ki lafia ba...?" " Hakane Rayyan but u must tell me saboda gaba, dole musan yadda zamu 6ullowa lamarin ba akan ka ka'dai ba har da sauran 'yan uwan ka, karka manta akwai Sultan, akwai Marwa akwai Raihana sannan ga ni kaina toh idan bamu san ta inda matsalar ke tasowa ba ta ya zamu magance ta...?" " Ammi ai kowa da kalar 'kaddarar sa..." Bata ma bari yakai aya ba ta dakatar da shi da 'kiran sunan sa. " I said u must tell me dole in san komai Rayyan..." Dole ba dan yaso ba ya bata labari beriefly kuma bai fa'da mata yadda suka yi da Zaitoon ba, domin in tasan cewa yes akwai hannu aciki dole hankalin ta zai 'kara tashi ne. Duk da 6oye matan da yayi sai da Ammi ta nuna damuwar ta 'karara sosai tayi mamakin faruwar lamarin, motar da abin ya faru sabuwa ce dal 7months mai kyau ma bata cika yana hawan ta ba, marcedes benz ce kuma ta tattabatar lafiyayya ce shi kansa ya sani domin ko da wasa Rayyan baya yadda ya hau motar da yasan bata cika lafia ba balle ta bashi matsala bayan fitar sa daga gida. Amma wannan 'din abin da mamaki ace kamawa tayi da wuta hakan kawai bisa titi. Ganin Ammi na 'kokarin zurfafa tunani ne ya sanya shi fa'din" Ba'a mamaki da ikon Allah Ammi right...?" Ajiyan zucia ta sau'ke sannan ta 'dora da" Hakane Rayyan, Allah ya kare min ku, ya tsare min ku, ya dawwamar da farin ciki cikin rayuwar ku ya kuma wadata ku da imani da tsoron sa...". " Ameen Ammi...muma Allah ya kare mana ke ya 'kara miki nisan kwana mai albarka ya kuma bamu ikon kyautata miki har 'karshen rayuwar mu..." Murmushi tayi kawai tana kawar da idanun ta shima haka murmushin yayi. Tun yana office 'yan sanda suke ta 'ko'karin takura masa kan bincike bisa 'konewar motar amma sam ya 'ki basu wata dama domin yasan wahalar da shi kawai zasu yi ta yi da zirga zirga, kuma shi bayi da wata hujja da makama bayaga zancen da Zaitun tai masa da safia wannan ma bai tabbatar ba duk da babu wasa tsakanin su balle yace wadsa take yi masa ya kuma san mawuyaci ne ta shirya 'karya haka nan kawai ta fa'da masa. Kuma matu'kar ya kuskura ya furta wannan kalmar ga 'yan sanda bazasu ta6a barin yarinyar ba an ringa bincike kenan hakan kuma bazai ta6a bari Ammin sa ta nutsu waje guda ba itama ayadda ya fahimce ta, matukar aka fara binciken batun yarinyar itama Ammi bazata nutsu ba kuma shima baya 'kaunar yaga Ammin sa cikin tashin hankali. Ai indai kere na yawo zabo na yawo dole wataran za'a ha'du...kuma ya riga yasan babu wanda ya isa ya yi musu abinda ba shine 'kaddarar su ba duk da hakan ya kanyi imagining duk ranar da Allah ya bashi ikon 'dam'ke makashin ahalin sa irin hukuncin da zai masa..fatan sa kawai shine Allah ya bashi tsawon rai ya kuma nufe shi da nasara a lokacin da ya fi dacewa, hatta su Huzaifan bazai dakatar da ko guda daga cikin su ba sai zai 'kara sanya idanuwa ga dukkan su...ya kuma sawa aransa dole sai ya kafa warning wa yarinyar can gudun kar tayi azar6a6in sanar da Ammi abinda ta gani ta bari kawai tsakanin su shi da kanshi zai 'dauki mataki akan koma wanene. Da wannan tunanin ya koma 6angaren sa dai- dai lokacin da Amrah tazo ta mamayi tunanin sa. Dagaske fa yayi kewar ta shi kansa yasan hakan, amma hauka da rashin hankalin ta yake so yaga iyakar su kawai shiyasa bai ta6a nuna damuwar sa ga kowa ba. Bai samu lokaci ya yayiwa Zaitoon warning akan fitar da batun ba kwatsam bayan kwana biyu Sultan ya kira yake jajanta masa abinda ya faru nan yake maimaita masa batun kamar yadda Zaitoon ta sanar da shi, ya so yayi mamakin inda Sultan ya samu labarin sai dai cikin sau'ki Sultan ya warware masa komai cewa shima wlh Marwa ke bashi labari inda ya jajanta masa sosai ya kuma nuna alhinin sa gami da tabbatarwa Rayyan 'din cewa dole cikin kwanakin nan zai dawo a san abinyi kan lamarin. Rayyan yayi saurin dakatar da shi da fa'din kar ya damu kuma da Allah ko yayi waya da Ammi kar ya kuskura ya sanar da ita gudun kar hankalin ta ya tashi inda ya tabbatar masa da cewa bazai fa'da mata ba kuma itama Marwa zai ja kunnen ta. Da haka suka yi sallama kowa abinda ke zuciyar sa daban..shi Sultan dama ba so yake ayi ta ririta maganar ba gudun tonuwar asiri, yayin da Rayyan yaso yayi mamakin yadda akayi Marwa tasan labarin sai dai tuna kusancin da ke tsakanin ta da Zaitoon ya sa mamakin sa yin nasa waje..haushi ya maye gurbin sa. Sosai yaji haushin Zaitoon da fa'dan ma Marwa maganar da tayi. ***** Kwanci tashi rayuwa nata mi'kawa, Sultan ya dawo ya kuma matsawa Rayyan da batun dawo da matar sa gida inda ya nuna masa cewa ba mutunci ne zaman sa haka nan 'din ba a matsayin sa na babba gare su kuma madadin uba, duk abinda tayi masa ha'kuri zai yi ya mance da shi dama da ha'kuri aka san babba balle matsayin sa na namiji bai kamata ace yana biyewa shirmen mata ba. Kallon sa Rayyan kawai ya tsaya yi yana murmushi da jin da'din kalaman dan uwan nasa, badan komai ba, bawai dan yana marmarin dawo da Amrah ba sai dan kawai ganin girma da mutuntaka da suka bayyana daga Sultan din. Yayin da Sultan ya 'dora da" Kuma ma Yayah ai ko bakomai sai ka duba babyn mu dake tare da ita, ko dan shima ya kamata ace ta dawo kusa damu 'kar'kashin kulawar mu..ni bama sai kaje ba inka amince kawai zanje in dawo da ita..." Duk da yaji da'din maganar Sultan din amma hakan bai hana shi fa'dan nashi ra'ayin ba. " Ban amince ba Sultan ka rabu da ita, duk lokacin da tayi ra'ayi sai ta dawo da kanta ai ba nine nace ta tafi ba, ra'syin da ya sata tafita shi zai sake sawa ta dawo" Ido Sultan ya 'kwalalo yana duban sa. " Haba Yah Rayyan, sai kace bamu san darajar Babyn mu ba, ai in muka yi hakan a fili muka nuna bamu damu da cikin dake jikin ta ba...." Karya wuya Sultan yayi ya cigaba" ni fa wallahi ba itan ce damuwa ta ba Yayah Unborn din mu ne, wai duk 'kauna da mura'din da muke yi akan haihuwa sai mu bar Amrah ta tafi can wata uwa dunia da ciki bacin muna nan araye da lafiyar mu kuma ba rasa abin da zamu kula da su muka yi ba...Ni nama yi mamaki wallahi yadda kayi biris ka share lamarin har tsawon lokacin nan...". " " Sannu sarkin surutu..". Rayyan ya fa'da yana mikewa tsaye batare da ya bashi amsa 'kwa'k'kwara ba. Sultan ya 'dauki kimanin yini biyu yana ro'ko da ban baki ga Rayyan game da dawowar Amrah amma ya'ki amincewa 'karshe sai da ya ha'da da Ammi cikin maganar kafin Rayyan ya amince masa zuwa dawo da itan ko za'a dace amma shi kam yace baya da lokacin zuwa. Sosai Sultan yaji da'di, badan komai ya damu ya dawo da Amrah ba sai dan abubuwa biyu, na farko saboda cika burin sa da ya jima da shiryawa akan cikin nata, na biyu kuma saboda kansa ne, dan sosai yayi missing dinta. Batun yau yasan cewa Amrah bata Kano ba tana can Kaduna, tunda kusan kullum sai sunyi waya da shi, ita kanta ma takan 'kira shi koda shi bai 'kira ta ba, kuma sosai take nuna masa irin kewar sa da tayi har ma hakan ya ta6a tunzura shi 'daura niyyar zuwa Kaduna wajen ta sai dai bai samu lokaci ba dan a dawowar san nan Rayyan ya ri'ke masa wuta da ayyukan office sosai. Kuma duk da takan tura masa hoton ta harma da na cikin ta amma sosai ya matsu yaga cikin a zahiri kafin ya aikata shirin sa. Tashin farko Sultan daga gida direct ya wuce Kaduna ko neman inda mahaifan Amrah yake kan batun bai yi ba. Ko da yaje ba 'karamin ka'duwa yayi ba da ganin girman cikin Amrah ba yayin da zuciyar sa ta sake 'dokantuwa izuwa ga salwantar da cikin tun kafin ya dawo, tun yana Kaduna ya fara shirya yadda zai yi da cikin, wasa- wasa sai ga Sultan ya shafe kwanaki uku a Kaduna batare da sun dawo ba, sai da suka gama she'ke ayar su a hotel kafin ya tattaro ta suka dawo Kano. Amrah sai 'kiran mahaifiyar ta tayi ta sanar da ita cewa Rayyan ya sa an dawo da ita gida. Haushi ne sosai ya turnu'ke ran MUmmyn Amrah, tace" yasa an dawo dake ko kuma yaje ya dawo dake..." Shiru Amrah tayi tana ta tunzura baki gaba, tasan dama mummyn ta sai tayi masifa ai, amma ita har yanzun bata san waye Rayyan bane shiyasa take fa'din irin wannan maganar. Tsaki Mummyn Amrah tayi tana fa'din " Ke kika sani ai, ni gata na nema miki, ta ya zaki zauna da mijin da sam bai san darajar ki ba, tuni ma wannan auren ya fice min aka wallahi badan wannan cikin da ke jikin ki ba Allah sai ya rabu da ke...". Da hanzari Amrah tace " Rabuwa kuma Mummy? nifa ina son miji na...". " Haka zaki ce min Amrah..? shiyasa kika biye yaudarar sa kika koma masa kenan batare da ko mu an tuntu6e mu ba ko? toh kiyi zaman ki tare da mijin ki amma wallahi ki sani..koma menene ya biyo baya kar ki kuskura ki sani aciki...mtheew" Ta 'karashe da jan tsaki gami da kashe wayar. Tsakanin mata da miji sai Allah, domin da farko Rayyan yaso share Amrah baiso ya nuna yama san da zaman ta agidan ba, sai dai tun bayan kwana biyu da dawowar ta da Ammi ta tara su tai musu nasiha game da zaman tare ya sa jikin sa yin sanyi, koda dare da Amrah tazo 'dakin nasa cikin kyakkyawar shiga kasa kawar da idanun sa daga kanta yayi, sosai cikin dake jikin ta ya 'kara fito da kyawu da tsarin ta, tun dawowar ta ya ke kaucewa ha'duwa da ita domin baya iya 'dauke idanun sa akan cikin, baya kuma so ta gano lagon sa, sosai ya ke so da muradin jin lafiyar babyn sa amma ya bar hakan cikin ran sa...bai ta6a sanin yana tsananin 'kauna da kewar Amrah da Babyn sa ba sai yanzun da take tsaye gaban idanun sa tana duban sa. Kallon sakan kusan sha biyar yayi mata sannan ya 'dauke kansa ya cigaba da abinda yake cikin system 'din sa. Ganin haka yasa da dan gudu gudu Amrah ta taho ta rungume shi daga bayan sa gami da sakin kuka. Cikin kukan take furta masa kalaman ban ha'kuri da kewa da nadamar abinda ta aikata. Rayyan bai hanata kukan ba kamar yadda bai tankawa kalamanta ko guda ba, sai dai shima kasa ta6uka komai yayi har zuwa lokacin da ya tabbatar wa ransa cewar kukan nata ya isa hakanan...kuma kalaman tan sosai suka yi tasiri aransa...hannun sa har rawa yake wajen 'ko'karin juyo da ita ta fuskance sa. Yana juyo da ita at same time kuma yake cusa hannu cikin rigar ta. Lokacin da yaji hannun sa ya sau'ka kan cikin ta ajiyar zuciyar zuciya ya sau'ke gami da sanya idanun sa cikin nata. Yana shirin tambayar ta lafiyar Babyn domin tabbatar wa, amma Amrah bata bashi wannan damar ba wajen saurin ha'de bakin ta da nashi waje guda. Shi kansa yayi kewar wannan scene 'din dan haka bata sha wahalar samun kansa ba tuni labari yasha bambam. Amrah bata cika sati guda a gidan ba komai ya daidaita tsakanin ta da mijinta, kuma ba laifi wannan karan ta kanyi 'ko'karin zuwa 6angaren Ammi sai dai Ammin da kanta ta dakatar da ita musamman saboda ganin cikin ta daya fara girma gudun karta wahal da ranta. Rayyan da kansa ya duba cikin ya kuma tabbatar da komai lafia hakan shi ya 'kara masa natsuwa da kwanciyar hankali. Haka rayuwa ta cigaba da gogawa, Marwa ma tuni ta tattara ta koma gidan ta tun dawowar Sultan daga Senegal sai dai ta shigo ziyara. Kuma har yau sha'kuwar su da Zaitoon tana nan sai dai abinda ya 'karu. Sultan ma na can na shiri babu abinda ya sauya daga 'kudurin sa, be it now or later abinda kawai ya sani kuma dasawa ransa shine dole sai ya kawar da abinda ke cikin Amra kafin hankalin sa ya kwanta. A cewar sa shine ya dace ya haihu ba Rayyan ba. Shine ya dace ya fantama ya kuma ji aransa cewa INFINITY tasa ce shi ka'dai bata kowa ba domin shine yasan darajar ku'di ba Rayyan da ko irin fita yawon 'kashashen dunia sam bai iyaba. Akwana a tashi har ga shi Mufeeda na neman cika shekaru biyu da haihuwa, yayin da cikin Amrah ke hararo watanni bakwai kuma ya fito ya yi mata 'das zuwa lokacin duk ahalin Sa'ad Auta hankalin su na kan cikin ne. 'Kauna da kulawa kam Amrah har ta gaji da shi sai dai tace Alhamdulillah, ita kanta tasan yanzu cikin gata da 'kauna take ta ko'ina. Wata sabuwar mai mata hidima Ammi ta samu sbd Amrah bayan fahimta da tayi cewar babu jituwa tsakanin ta da Zaitoon kwata- kwata, sai dai tun ba'ayi nisa ba, Mai aiki tace bazata iya da tsirfa da rashin kirkin Amrah ba, dole aka sake canza mata wata. Yanzu aikin Ammi ka'dai Zaitoon take yi shima 'din ba wai wani mai yawa bane, har ila yau dai 6angaren Ammi aikin yake ba'a canza mata ba. Sai dai in ta ji tana ra'ayi da kanta takan shiga kitchen ta taya su wasy ayyuka a hakan kuwa ba 'karamin 'karuwa take yi ba, ita kanta tasan ta 'karu da abubuwa masu dama da har abada zata yi alfahari da su. Salmerh😘 [21/10/2022, 3:26 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Wattpad@* _Serlmerh_md_ 🅿️ *...57* ........Sau da dama Ammi kam mamakin ta ma take yi, domin ta jima da fahimtar cewa ba ita ce ta haifi Moopy ba, domin ba ita ta shayar da yarinyar ba madara taba ta, amma ta gaza samun cikakken prove da zai tabbatar mata da hakan domin Zaitoon ta toshe dukkan wata kafa da zaka samu direct game da ko'kontan ka, 6angaren kula da yarinyar new ko kuwa 6angaren dangantaka, ko cikin labarin da Zaitun ta bata ta nuna mata ne cewar dalilin yarinyar ne ta bar gidan su kawai dama garin baki 'daya, amma bata sanar da ita tushe da asalin wace ita ba. Hakan yasa har yau ta kasa samun gaskiyar lamarin da zata riga game da Zaitoon. Yarinyar na da hankali uwa uba nutsuwa, kamilalliya ce a zahirin gaske, sannan kuma tsawon zaman su bata ta6a ganin wata alama da zai tabbatar mata da cewa bata da kamun kai ba har yau 'din. Sau da dama takan yi kwa'dayin kasancewar ta mata ga 'daya daga cikin 'ya'yan ta musamman ma Sultan da tasan cewa bazai ta6a yi mata gardama ba koda ta za6a masa Zaitun matsayin mata sai dai tasan hakan ba me yiyuwa bane domin Rayyan ma kansa ba ze ta6a amincewa da batun ba...baya ga hakan ahar yanzun bata san takamammai asalin Zaitun ba shiyasa ta kasa bawa kanta 'kwarin gwiwar aiwatar da shirin ba...'karshe ma kawai sai tayi watsi da batun gaba 'daya. Wata biyu ya rage Moopy ta cike shekara biyu wanda yayi dai- dai da cikar shekarun rasuwar Nadia itama shekaru biyu, ya kasance watan Ramadan ne da bata jin zata ta6a iya mancewa da shi, sosai Ammi ke jimantawa da rashin ta sai dai bata da yadda zata iya ba kuma wani gata da ya rage mata a yanzu illa addu'a da basa gajiya da yi mata shi. Yayin da Amrah kenan itama haihuwa yau ko gobe harma Ammi ta nemi Rayyan ya dawo da ita 6angaren ta Rayyan yace toh amma har yau bata ga suna da niyyar hakan ba, saboda cikin Amara nema kuma ya sa Ammi soke duk wata tafiya tata ta 'dauki hutu har sai bayan haihuwar Amra kafin nan ta cigaba, domin bata ji matu'kar tana numfashi zata daina wannan harka ta taimakawa da 'karfin ta dukiya dama zuciyar ta gaba 'daya. Ta koyi darussa masu dama cikin wannan harkar ta kuma koyi sanin darajar 'dan Adam, tasan bambancin tsakanin akwai da babu, wasu idan labaran su ya iso su kafin su bincika har sukan iya 'karyatawa ma sbd tsanani dake cikin labarin amma lokuta da dama idan suka bincika sai su tarar da erh ashe gaskia ne, koma da kuskuren toh shine mafi 'karanci. Hakika idan Allah yayi maka ni'ima kamata yyi ka gode masa, duk wani abin da Ubangiji ya baka ka raina idan ka shiga rayuwar wasu zaka tarar ne cewa 'kalilan daga cikin taka ni'imar daka raina idan aka basu sosai zasu karramashi har ma suji tamkar suma basu da wata damuwa. Allah yayi mana ni'imomi masu dama, Allah ya halicce mu musulmai ya bamu Rai ya bamu lafiya, ya bamu arziki, ya bamu ji da gani, yayi mana kyautar imani ya kuma wadata mu da ni'imomin sa da mu kanmu ba zamu 'kayyade yawan su ba...ba tare kuma da ya nemi komai daga gare mu ba so baya ga mu bauta masa me zamu yi in ba godia agare shi ba. A mafi yawan lokuta ta kan gode wa mahalicci da ni'imomin da ya yi mata har ma takan nutsar da 'ya'yan ta game da hakan, takan hane su raina halittar Allah ko ya take musamman 'dan Adam, ta hane su kaskantar da duk wanda suke tunanin su suna sama da shi..hakika Allah ke bawa bayin sa komai a kuma duk lokacin da ya ga dama, su da ya basu ba son su da yake ne fin na kowa ba ba kuma iyawar su ce ta sanya hakan ba, ba kaunar su yafi yi fiye da sauran ba face dan kawai ya jarabce su. Ammi ta hane su da almubazarranci da kuma 'dagawa, kyakkyawar mu'amala ta koya musu da zasu aiwatar a ko'ina suka tsinci kawunan su kuma tsakanin su da kowa. Ko Zaitoon Ammi ta 'dauko tane sbd tausayi da kuma ganin kamar tana da maganin matsalolin yarinyar, baya ga hakama tayi duba izuwa ga 'karancin shekarun ta bai kamata ce kamar ta tana gallafiri saman titi ba, tana da muhallin da tasan zata iya ajiye mutane fin 'dari batare da kowa ya takura 'dan uwan sa ba, sannan tana da abinda tasan ba yayan ta ba hatta da jikokin ta mawuyacu ne suyi rayuwar 'kunci da talauci ba in dai ba wani ikon Allah ba, toh miye yasa zata barta tana yawon bara akan titi bayan tana da damar tallafa mata. Babban dalilin da ya sanya ta taimakawa Zaitoon kenan, kuma sai bata ji sha'awar shigar da ita cikin list 'din kungiyar su ba kawai tabar komai nata a hannun ta ita ka'dai. ***** Zaune suke suna hira da Zaitoon nan suke lissafin shekarun Mufeeda da kuma watannin da ya rage ta cika shekara biyu...Ammi tace ai an kusa kai Mufee makaranta da zarar ta cike shekara biyun za'a fara sata wata Day care ta saba tunda wuri kafin ta fara gwangwan makarantar dan tuni Moopy ta murmure tayi 'kibar ta jikinta yayi kyau sosai kamar yadda Zaitoon take tsananin mura'din ganin ta. A lokacin da Ammi tayi maganar hankalin Zaitun tashi yayi domin gani take kamar rabata da Moopy kawai za'ayi bayaga haka nawa take da za'a wani kaita makaranta bayan su agarin su sai mutum ya girma yayi wayo wani sai yayi 'kanne har biyu ma kafin ake sashi makaranta. Ta ina mutun kamar Mufeeda za'a kaita makaranta, ai tayi 'ka'kanta da yawa me ma zata koya ? baya ga haka ma ai yarinyar bazata sake a makarantar ba, kuka kawai zata tayi musu, ita kanta tana da burin wadata yarinyar da ilimi boko da arabi dan tasan sune ka'dai gatan da zatai mata, gatan da koda a hannun iyayen ta take suma din hakan za suyi mata, daidai da 'kwayar zarra bata son ta tauye Moopy da shi amma duk da hkn ba yanzu ta shirya kaita makaranta ba, kamar wasa sai ga idanun Zaitoon sun kawo ruwa tuni ta fara yiwa Ammi kuka tana ro'kon ta akan abarta ta 'dan 'kara girma mana, dan Allah Ammi a bari ta 'kara wayo tukunna, duk yadda Ammi taso nuna mata dacewar sata makarantar tun yanzu sam Zaitun bata fahimce ta ba.. Yanda ta tashi hankalin tan har yasa Rayyan sanya baki domin yazo ya tarar da su suna kan maganar ne. Sosai ransa ya 6aci da jin yadda Zaitoon ke kuka sbd kawai ance za'a kai yarinya makaranta. Cike da haushi yace" Ammi to ana dole ne ki bar ta mana idan akanta aka fara haihuwa sai mu gani, duk kaunar ka da yaro gatan dakawai zakai masa a duniayn nan shine ka bashi ilimi shine wanda ko bayan ranka zai yi alfahari da shi... yara masu daraja da gata ma an kaisu makaranta balle taki dake da matsayin sheg....". " Mind ur tongue Rayyan bana son irin haka fa". Ammi tayi saurin dakatar da shi da fa'din hakan tana duban sa. Ganin ya yi shiru ya sanya ta 'dorawa da fa'din" idan bazaka fa'di alkhairi ba kayi min shiru babu ruwan ka cikin zancen mu". A fusace ya tashi ya fita yayin da Ammi ta cigaba da lalla6ata har ta amince. 'Bangaren Rayyan koda ya koma sashen sa kan kujera ya yada zango zuciyar sa na masa tu'ku'kin ba'kin ciki da takaicin Zaitun..a ransa yake jin haushin ta sosai kan yarinyar tata...bai cika shiga sabgar da bata shafe shi ba but akan yarinyar nan duk sun dulmiyar da shi cikin lamuran su bai kuma san yaushe hakan ya faru ba, haka kawai yake tsintan kansa cikin lamuran rayuwar su, ko yanzun ma kwafa yayi cikin ransa ya gama yanke hukuncin sai ya sa an kai yarinyar makaranta kodan ya ga yanda zatayi in ma mutuwa ne sai dai tayi sai kace 'diyar ta ce ka'dai 'ya a dunia. Washegari da safe da ya shigo gaida Ammi nan cikin natsuwa ta ringa nuna masa rashin dacewar abinda ya aikata jiyan inda Tace dashi kar wai kaga dan ta haihu ta hanyar da bata dace ba ka ringa aiban ta mata abinta, babu wanda zaka ga ya haifa kuma yace baya so balle ma ita da nake da ya'kinin zargi kawai muke har 'din nan bamu san gaskiyar lamarin ba, babu mamaki 'kaddara ce ta hau kanta har hakan ta kasance, iya zaman mu ban ta6a cin karo da wani abu da ya shafi rashin natsuwa tattare da ita ba, shiyasa idan ka zauna da mutun ba wai halayya ta zahori ce kawai abin dubawa ba, akwai halayyar ba'dini da wani lokaci kai da kanka ma baka san kana aikatasu ba kuma Alhamdulillah ban ta6a samun Zaitoon da halin da bai dace ko guda ba dan haka bamu da hujjar aiban tata ni dai har ga Allah ban ta6a yi mata kallon watsatsiya ba..." Baki ya kya6e gami da fa'din " Ammi ai ba gane su ake yi a fuska ba...domin munafukai ne". " Ba ka dai da hujja tunda baka san komai game da ita ba" " Munafuncin kenan ai Ammi bayaga haka meyasa zata 6oye miki asalin ta iya zaman nan..da tana da gaskia bazata ta6a yi hakan ba.." " Ba ni kadai bace, bama najin ta ta6a bawa kowa cikakken labarin asalin ta hakan ta za6a, ta za6i sirrinta tarihin ta ne kaga kuma bamu da hujjar tilastata. " Kuma Ammi haka zamu cigaba da zama da ita bayan bamu san wace ita ba...?" " Da me hakan zai rage mu..?" " Babu komai, kuma har azuciya ta naji na yadda da ita dan haka sanin asali kowace ita bashi ne gabana ba, duk lokacin da ta shirya sanar da ni nima a shirye nake inji..nasan halin 'yan Adam yanzu sai.a hankali sam baka sanin mai kaunar ka amma na jima da kyuatatawa yarinyar nan zato kuma Insha Allahu bazata bani kunya ba, kaima abinda nake so da kai shine please Rayyan ka tsarkake harshen ka bana jin da'di ace dan cikina ke yin irin hakan, abinda kk yi 'din sam baya mata da'di haka kuma nima idan bazaka tayata son 'diyar ta ba toh pls ka cire idanun ka akan su sam banso in sake ji ka aiban ta mata yarinya.. shiyasa fa ta wannan fannin Sultan yayi maka zarra, sam babu ruwan sa da rayuwar kowa, yanzu agidan nan ka ta6a ji ko ganin sa yana ma wani fa'da ne, babu ban ta6a ji ba..amma kai indai akaji ko ganin tashin hankali daga yarinyar nan in aka bibiya da sa hannun ka aciki, 'kaddara ai tana kan kowa kuma babu wanda ya san ta inda nasa 'kaddarar zata zo masa so ka daina 'kara mata zafi..." Shiru yayi ya sunkuyar da kansa. " wai zafi....hmm ai sai dai ta 'kone amma sai yaga 'kurewar iskancin ta... Ammi kuwa ta cigaba " Yanzu alal misali kai, matarka ba ciki ne da ita ba, Allah ya sauke ta lafiya ace wani ko wata ya sa ma 'dan agaba da zagi, cin mutunci ko aibantawa da sunan shege ya zakaji..?" A zabure ya dubi Ammi yana fa'din" Haba Ammi...haba dan Allah, da kanki kike fa'din irin wannan maganar kuma..?" " Misali na baka, ba gashi kaima kaji babu da'di ba, ai haihuwa duk haihuwa ce, 'da kuwa ko wani iri ne abin 'kaune yake ga mahaifan sa, 'kaddara kaine Zaitoon yanda zaka rinka ji idan ana kira ma 'da da suna shege kusan kowacce rana...?". " Insha Allahu ma babu wanda zai zagar min da, ai akwai bambamci..." " Hmm " Ammi tace Yayin da shi kuma ya shiru kawai ya kawar da kansa gami da lumshe idanu, imagining yake irin hukuncin da zai iya yiwa wanda ya aibanta masa 'da kamar yadda Ammi tace..sosai yaji babu da'di amma hakan bai sa ya mance da 'kudurin sa ba..A hankali la66an sa suka motsa wajen furta" Ammi tog batun makarantar fa..". inda yy maganar yana murmushin mugunta da shi ka'dai yasan ma'anar ta...ba abinda yafi 'kauna irin yaga ya 'kuntata zuciyar Zaitun yaga tana zubda 'kwalla sbd wannan 'diyar ta ta abin na sa shi nishadi matu'ka. Toj akan irin yarinyar nan ma ana 'kwalla ina ga in ya kansace ta hanyar halak Aka samu haihuwar? Ajiyan zuciya Ammi ta sauke sannan tace" Ranar monday Insha Allah za'a kai Mufeeda makaranta.." " Monday..ta amince kenan..? dan nasan dole sai da amincewar ta sannan zaki yanke hukunci.." " Ba dole ba Rayyan ita da 'diyar ta, ita ke da iko da abar ta ai.." " Lalle kuwa, ta kyautawa kanta ai, amma ni ko bata amince ba na riga na yanke hukunci domin haka kawai nake ji araina inada iko da yarinyar dan haka ta amince ko bata amince ba za'a kai yarinyar skul ba za'a biye shirmen ta ba". Da sauri Ammi ta kalle shi..." Did I heard u said ko bata amince ba..? thaugh yanzun nan muka gama magana da kai kace ka daina irin abin nan...?" Murmushi ne ya wadaci fuskar sa, yatsan sa 'karami na 'karshe ya 'dago yayin da saura ke kalmashe yace da Ammi" Wannan ka'dai ne kuma Insha Allah shine na 'karshe.." Yayi maganar yana 'ko'karin mi'kewa tsaye". " Baka tambayi wace makarantar bace naga kana shirin mi'kewa". Gira ya ha'de tare da fa'din " toh ni Ammi me ya shafe ni..wannan ba shirgina bane ai..ba dai ta amince ba ai shikenan". " Um-Um fa Rayyan me yake damun kane wai?" Kallon cikin idanun sa tayi daya zuba mata su tana 'dan ha'de rai tace..." kai nake so ka kai ta nd that's Final.." Fasa tashi yayi ya hade rai sosai yace" Gaskiya Ammi monday kinsan banda lokaci..." " Zan ma Huzaifa magana ko kuma James 'dayan su ya kaita ba shikenan ba.." " Ba shikenan ba kai din dai da nace kai din zaka nemo lokacin dole Rayyan kaje da kanka...ni friday zan tafi Abuja ka sani kuma sai Upper week zan dawo badan haka ba ai da kaina ma zanyi basai na nemi taimakon ka ba amma ganin na isa da kai ne yasa na wakilta ka in kuma bane ai shikenan, Alhamdulillah ma tunda ba kai ka'dai gareni ba". Ta 'karashe maganar tana kawar da kanta. Da sauri ya gayra zama jin furucin nata abinda bai saba ji daga bakin ta ba. " Yah Subhanallahi, Ammi maganar fa duk bata kai nan ba, indai makaranta ce wallahi zan kaita dan Allah kiyi ha'kuri" 'Yar murmushi tayi tana dawo da kallon ta gare shi. " ko kaifa, abinda nake so da kai kawai shine kayi ha'kuri kaji? ka daina biyewa zuciyar ka kana aikata abinda nasan ba halayyar ka bace dan nasan ba haka Babana yake ba amma na lura ka jima da bawa shai'dan damar sarrafa maka zucia". Kai kawai ya girgiza a hankali yace" ba haka bane Ammi na, amma Insha Allah zan yi kokari in ga ban cigaba da aikata abinda kike zaton na sauya ba.." " Masha Allah..ina ro'kon Allah ya albarka ci rayuwar ka da albarka, ya wadata zuciyar ka da tsoron sa.." " Ameen ya Rabbir raheem..thanks Ammi." Daga haka ya mi'ke gami da barin parlon Ammin a hankali yake taka stairs 'din...ransa yake jin duk babu da'di sbd kalaman Ammin na 'dazu, sam bai saba da jin irin wancan kalamin daga bakin ta ba. Yana zuwa gama sakkowa ya tunkari corridorn da zata kai shi uzuwa ga Parlorn downstairs anan parlorn ya tarar da ita suna wasa da Moofy tana 'dan guje mata Mufeedan kuma na binta tana son kamo ta suna dariya dukkan su...da alamun basu tare da wata damuwa. Duba 'daumya yai musu batare da ya dakata da tafiyar tasa ba ya ratso ta tsakanin su zai wuce Cikin rashin sa'a Moopy dake faman dariya ganin mutun kawai sai tayi saurin kama 'kafar sa 'daya ta ri'ke tana dariya mai matu'kar birgewa...shikan sa dariyar yarinyar ya matu'kar birge shi amma yadda yaji zuciyar ya amsa da fa'duwar gaba gami da bugu akai- akai ya sanya shi kawar da batun birgewar dariyar yarinyar ya bibiyi kadin zuciyar sa. Cak Zaitun ta tsaya da tata dariyar domin tasan ba alkhairi hakan zai haifar ba ta riga tayi masa shaidar mugunta kuma bai ta6a karyata tunanin ta ba daidai da 'kwayar zarra in dai akan su ne... A sukwane ta fara 'karasowa wurin da suke tsayen domin 'dauke 'diyar ta musamman ganin yanda Rayyan ya 'dime ya ha'de ransa sosai, cikin rashin sa'a kafin ta 'karasa tsakiyar 'dakin shi kuma Rayyan yy saurin janye 'kafar sa a hassale daga ri'kon da Moopy tai masa yayi gaba yana sakin 'karamar tsaki, take Moopy ta fa'di sanadin jan 'kafar da yayi ta buga bakin ta 'yan ha'koran dake bakin suka bugu da tiles suka datse mata la66anta sai jini. Razanannen kuka ta sanya daya maye gurbin dariyar ta, yayin da bugun da 'kirjin Zaitun ke yi ya sanya ta zaman dirshan a wurin ta janyo ta ta rungume a 'kirjin ta itama sai hawaye...cike da tausayin 'diyar ta azuciyar ta take shafa bayan ta amma babu alamun kukan ta zai tsagaita anan kusa. Rayyan kuwa ko waigowa bai yi ba ya fice abinsa tamkar ma bai ji kukan yarinyar ba, duk da can 'kasan zuciyar sa yana jin babu da'di, yana jin rashin natsuwa yana jin tamkar bai kyauta ba. Sam ta rasa shi wannan wani irin marar hankali ne shi? Wani irin mutun ne da bai da imani sam? amma Rayyan yanada zuciyar tausayi a kijrjin sa kuwa, Me yasa baya iya bambance tsakanin babba da yaro? yarinya kamar wannan har abin ka mayar abin gabar ka ce...miye ribar da zaka tsinta idan ka cutar da ita. Kukan Moopy da Ammi ta jiyo ne ya sanya ta saurin saukowa a rikice tana salati cikin zuciyar ta hakama ma'aikatan gidan duk suka fito domin abin ya faru ne a palon dake 'kasa kuma duk kukan Moopyn ya kara'de ko'ina. Sanin da Ammi tayi cewar kukan Moopy tafiya yake dana Zaitun ya sanya ta 'kara hanzari...cikin zuciyar ta take ayyana Allah yasa ba Rayyan bane sanadi. Tun kafin ta sau'ko kuwa ta hango su zaune 'kasan tiles. Zaitun rungume da yarinyar tana kuka itama...ga wata mai aikin tana 'ko'karin amsar yarinyar daga hannun ta amma Zaitoon ta kasa bata dama, ri'kon sosai ta yiwa yarinyar tana aikin kuka itama. A rikice Ammi ta 'karaso gaban su tana tambayar Zaitun abinda ya faru. Yanda take faman lumlumshe idanu hawayen ta masu kauri na sauka ka'dai idan ka duba ya isa ka fahimci cewa har cikin zuciyar ta take jin zafin wannan lamari. Da farko ma rasa amsar da zata bawa Ammi tayi da 'kyar ta harha'da kalamai a bakin ta furta" Fa'duwa tayi Ammi..." Wani hawayen mai 'kulle zuciya na sake sau'ko mata. 'Ko'karin kar6ar ta Ammi tayi dan har a lokacin Moopy kuka take yi sosai...ga mamakin ta sai ji tayi Zaitun ta sake matse ta jikin ta tana jin kukan na ratsa mata har 'kwa'kwalwa da jinin ta. Gani take kowa ma yanzu baya kaunar 'diyar ta ita ka'dai ke son abin ta shiyasa ta kasa bawa Ammin ita. Ji tayi ta tsani kowa ya ra6e su domin ta lura mutane bazasu ta6a canzawa ba..kowa mugu ne idan akan Moopy ne. Da 'kyar da lallami ta sakewa Ammi ita sai dai me ganin yanda bakin Moopyn ya kumbura sintim ga jini ya sanya bata ma san lokacin da ta saki shash- sheka ba. Da gudu ta tashi ta shige 'dakin su ta turo 'kofar bazata iya ganin yarinyar cikin wannan yanayin ba. Kuka take yi sosai na tausayin yarinyar ta...bata jin har abada zata iya yafewa wannan bawan Allahn da har ya iya sanadin da jini ya fita jikin yarinyar ta...wallahi na tsaneka a duniyan nan, mugu kawai, azzalumi, marar tsoron Allah.... Ta furta a fili. Sam bazan iya cigaba da zama da kuba, idan na zauna na san wataran gawar Feefy na zan tsinta ka kashe min ita. Cike da rauni take wannan kukan ta gama yanke shawarar bar musu gidan su, sam ta kasa fitowa ta sake ganin wannan jinin a jikin Mufeedah, bazata iya jurewa ba. Ammi kam da ganin yanayin fuskar yarinyar ta furta subhanallah...wannan irin fa'duwan haka..dole Zaitun tayi kuka. Wanda bai kai haka bama yasa Zaitun kuka balle wannan" Da 'kyar Ammi ta lallashi Moopy tayi shiru bayan ta goge jinin dake bakin ta sannan ta tashi ta koma 'dakin ta ita a kafa'dar ta, mayafi ta 'dauko da makullin mota ta fito. Bata ko bi ta kan Zaitun ba kawai tayi hanyar waje. Driver take da niyyan sawa ya kaisu asbiti cikin sa'a sai ga Rayyan ya fito daga part 'din sa. Ganin Ammin sa ya sa ya tunkari inda take yana sussunkuyar da kansa domin yasan dole yanzun ma zata yi masa fa'da tunda da kansa yasan abinda ya aikata ga yarinyar da yake gani kwance saman kafa'dar ta. Yana isowa bata ma bari yayi magana ba ta yi saurin fa'din" Yauwa Babana kaimu asbiti pls ko kuma ka kaita kawai..fa'duwa tayi bakin ta ya bugu da tiles..kaga yanda ya kumbura har zazzafan zazzabi ya shige ta, uwar ma na can tana kuka zanje in lalla6a ta..duk abinda ake ciki sai ka sanar dani now pls". Ta 'karasa maganar da mi'ka masa yarinyar ta juya batare da ta jira jin komai daga bakin sa ba. Shi kam mutuwar tsaye yayi yabi ta kawai da idanu, har sai da ya daina ganin ta, shifa natsuwar sa da ya nema ya rasa ne ya sashi fitowa da niyyan barin gidan sai gashi kuma abin ya juye ya koma masa...meyasa kullum sai shi Ammi ke jangwalawa yarinyar..? Jiyake tamkar ya yadata a 'kasan wajen yy tafiyar sa amma Ammi tafi 'karfin hakan agareshi. A hankali ya sau'ke idanun sa kan fuskar yarinyar sai yaji wani 'kif 'kirjin sa ya buga da 'karfi, babban abinda yasa yake 'kara tsanar ta kenan, kullum hakan yake ji daga sun ha'da idanu da ita ya tsani hakan kuma shi a rayuwar sa, ya tsani abinda zai takura shi ajiyan zuciyan sheshekan kuka da tayi take saukewa cike da rauni idanun ta a lumshe na bacci, fuskar gaba 'daya tayi ja ga bakin ta da ya kumbura sintim dashi har kamannin ta ya sauya. Yasan da ace idaun ta biyu da babu abinda zai sata amince da shi har yatafi da ita wani wurin...amma da yake tana bacci har damar kare mata kallo ya samu. A hankali ya kafe idanun sa wajen bakin ta take yaji jikin sa ya yi sanyi sosai da ganin yanda bakin yayi...yasan bai kyau ba, amma me ne yasha kanshi har haka? Jinin da ke gaban pitch rigar ta ya kalla a lokacin ji yayi tsigar jikin sa duk ya tashi..." Muhammadu baka kyauta ba...." Ya tabbatarwa kansa. 'Dan tattare goshi yayi ya juya da ita a hannun sa..Moopy kam tuni anyi baccin wahala bata masan hannun wa take ba da tuni ta tara masa jama'ah dan ta tsane shi itama balle ta ganta a 'kirjin sa. *Drop ur comment* Salmerh 😘 [22/10/2022, 6:27 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Wattpad@* _Serlmerh-md_ 🅿️ *...58* ......James ya yafito da hannun sa, ya kuwa taho da gudun sa dan cika umarnin ubangidan sa, Rayyan Key ya mi'ka..." muje Hospital plz..." Abinda kawai yace da shi kenan ya juya ya shiga motar James driver ya jasu suka bar gidan zuwa asbiti yayin da Rayyan ke rungume da Feefy tsab ajikin sa ko 'kyan'kyamin jinin da ya 6ata mata riga ma bai yi bai kuma san dalilin sa na jin hakan ba. Sai da suka hau titi kafin James yace" Sir which hospital...?" Kallon sa Rayyan yayi" Wanne kuwa James ban da YOUHEAL... YOUHEAL zamu, dama na kwana biyu ban le'ka su ba.." Kai kawai James ya ka'da ya tunkari Youheal Hospital. Direct wurin Fawwaz abokin sa yace a wuce da ita dan tun shigowar su aka amshe yarinyar a hannun sa ana ta mi'ka masa gaisuwa musamman likitocin da suka yi aiki 'kar'kashin sa. Kafin ma ya iso ga Fawwaz 'din tuni ya duba ta, tunda kuma yaji ance Rayyan da kansa ya kawo yarinyar yasa bai wakilta kowa ba da kansa ya duba ta zuciyar sa cike da tsantsan mamaki, domin banda tsagwaron kamanni babu abinda ya gani tattare da yarinyar da kuma Rayyan. Ko lokacin da Rayyan ya 'karaso ya tarar yana aikin bai 'akarsa gare su ba bayan sallama wurin zama ya nema yana fadin" likita bokan turai...sannu da aiki..." " Yauwa INFINITY CEO.." Wata isashshiyar daria Rayyan yayi yana gyara zaman sa yace" Ya aikin?" " Mun gode Allah, baka.'ki mu ba..muna nan muna ta fafatawa..." With smile on his face yace " da wanne zanji ne Fawwaz kai baka ganin kokari na ma kenan..?" " Wani 'ko'kari bayan sai bayan month kafin ake ganin ka YOUHEAL yau 'din ma nasan badan Babyn nan ba da bamu isa ganin ka ba..." " Hmm kai dai nutsu kayi aikin gaban ka nima wani waje zani yanzun..." Fawwaz bai furta komai ba kawai ya mi'ka masa yarinyar yana sake duban fuskar ta. Shiru ya ratsa office 'din har zuwa lokacin da Fawwaz ya kammalla ha'da injection zai mata...har a lokacin bacci take ganin allurar ne ya sanya Rayyan duban fuskar ta..for d first time yaji tausayin ta ya tsarga masa sosai har cikin jinin sa...lumshe idanu yayi a hankali ya kuma bu'de su nan take...cikin zuciyar sa ya ayyana rashin kyautawar sa. " Gyara ta ayi mata allurar ko malam". Fawwaz ya fa'di yana duban sa amma sam babu fara'a saman fuskar sa, a tunanin sa Rayyan 6oye masa cewa yana 'diya yayi shiyasa ya 'dan ji haushi kadan. Gyara ta yayi ta yanda za'ayi mata allurar batare da wata matsala ba ya kuma yi mata ri'ko mai kyau dan yasan da 'kyar idan tana iya jure injection dan yasan irin rainon da uwar ta ke mata ko 'kwai albarka...wannan kam itama uwar da kanta ya aka 'kare balle 'yar da ta kasance rainon ta. Ai kuwa ana sanya allurar sai ta yamutsa fuska ta saki 'karamin kuka tana rungume shi da fa'din Mammy...zuciyar sa yaji ta tsinke sosai, sai yaji babu da'di harda lumshe idanun sa. Sai da aka cire allurar kafin ya bu'de idanun sa yana jera mata" So sorry Baby ya isa ko?" Yana lalla6a ta gami da 'dan buga bayan ta har tayi shiru ta koma baccin ta, ga mamakin sa batare da ta damu ba. Yana duban Fawwaz yace" Da uwar ta na kusa kuwa da kun kwashi drama...bama najin an ta6a yi mata injection fa". Yana murmushi ya 'karashe maganar yana duban Fawwaz wanda shima murmushin yayi gami da yi masa duba irin mai cike da tarin tambayoyin nan. Gira 'daya Rayyan ya 'dage yana mai cigaba da fa'din" Ai inajin bazata ta6a yadda ka 6ula mata jikin yarinya a idanun ta har haka kuma ta iya jurewa ba...". 'Yar dariya Fawwaz yayi da son jan magana yace" kace kai dai Disney gaba 'daya ne a gidan ka kana shan drama abinka...ya sunan Babyn ta ka?" Ido ya 'dan zaro gami da kya6e baki yana duban gefe dan bai masan me ze ce da Fawwaz ba sam bai san takamamme sunan yarinyar ba har ga Allah. Fawwaz kam da abubuwa ke ransa da yawa manta waccan tambayar ma yayi ya sake jefa masa wani da fa'din" Wai dama kana da yarinya har haka Rayyan shine ban ta6a sani ba ko dai 'diyar Raihana ce?" Sai yanzun ya tsuke fuska tamau bayan fahimtar abinda Fawwaz 'din ke nufi..ganin haka yasa shi jinjina kansa yana cire hanglove a hannun sa yake fadin" Gakiya baka da kirki Rayyan abin ya ban mamaki sosai wallahi..da farko nayi tunanin ko Babyn Sistern ka ne ko wani relatives 'din ka sai kuma naga ai idan ya kasance hakan nasan da kanka bazaka jagoranci zuwa asbiti ba dan nasan halin ka sai dai ka turo hakan yasa na fahimci wannan 'din ta musamman ce..bayan fahimtar tsantsar kama da ke tsakanin ka da ita musamman ma tsohuwar matar ka...." Saurin duban sa Rayyan yayi yana 6ata fuska, bai ta6a jin mummunar magana irin wannan daga bakin Fawwaz ba sai yau 'din, har gani yake kamar ma Fawwaz 'din ba cikin hanakalin sa yayi maganar ba sai kace mai shafar aljanu, erh mana aljanu, baya ga haka mai yasa babu wanda ya ta6a ganin kammanin su sai shi, babu wanda ya ta6a fa'da hakan sai shi, meyasa shi ma da kansa bai ta6a ganin wani kama tsakanin su ba..a hankali ya zamo Moopy dake baccin ta peacefully ya kwantar saman cinyar sa wai ko zai ga kamannin amma bai ga ko 'dis 'din kama tsakanin sa da ita ba banda ma shirmen Fawwaz da wannan kumburarran fuskan har ya wani ga kama tsakanin su in banda kawai ya 6ata mai ransa abanza ba menene. " Wai ina kamar?" Ya tambaya yana duban Mufeeda. " Ga ta kuwa gaban ka, wlh Rayyan ko rantsuwa nayi nasan bazan yi kaffara ba akwai kama ta jini tsakanin ka da yarinyar nan. Baki ya kya6e a fili ya furta raba ni da Allah Fawwaz banson shirme ina wani kama anan in ba sharri ba, kasan wace ita kuwa..hmm ban da wata ala'ka da ita Ammi ce ta yimin aikan dole..." Kai Fawwaz ya jinjina cikin ransa ma jinjinawa 'karyar Rayyan yayi, dan kuwa ko makaho da idanun sa suka bu'du yau 'din nan idan yaga wannan yarinya ya kuma ga Rayyan take zai fahimci suna da ala'ka da juna, badan yasan ahalin Rayyan banda Bassam basu da wani 'karamin yaro ba cikin kannen sa kaf ba da zai ce kila yar 'dan uwan sace ko 'dan uwan sa domin kamar har ta 6aci ma. Amma da kansa yasan Sultan ne mijin Marwa kuma basu haihu ba, Safaa ta rasu haka ma Yah Kabeer da matar sa har ma da 'diyar sa Zamrud, Anty Madeena kuma Allah bai taba bata haihuwa ba..Raihana kadai ke da yaro Bassam duk yasan wannan, sannan matar Rayyan Nadia yanzu shekaru biyu ake nema da rasuwar ta da tsohon cikin ta bai manta komai ba domin kuwa dashi aka sha fama akan Rayyan kafin ya dawo rayuwar sa normal. Yayin da Amrah yasan yanzu hakane ma take da juna kuma na farko dan ko kwana biyu da ya wuce Rayyan ya kawo ta scanning. Sam tunanin sa ya kasa bashi amsar da ta dace da lamarin, dole cikin abu biyu 'daya ne daidai, inma ta kasance 'diyar 'yan uwan sa ko kuma 'kila Rayyan yana 6oye wanzuwar yarinyar ne saboda abubuwan da suka ta faruwa abaya, kila sbd magauta dake bibiyar rayuwar su ne, in hakane kuwa sam bai ga laifin sa ba, kuma ya bashi gaskia, sosai ya goyi bayan sa kan hakan, domin yafi kowa sanin halin da Rayyan ya shiga lokacin da aka akashe masa mahaifi anan asbitin nasu ya rasu a hannun Rayyan, ba 'karamin tashin hankali Rayyan ya shiga ba, haka na Yah Kabeer da Safaa sbd kiyayya, kuma har yau 'din nan an kasa samun wanda ke da hannu ko guda, tuno hakan yasa yaja bakin sa yy shiru...sai dai zuciyar sa cike fal da tunanin yaushe aka haifawa Rayyan yarinyar. Magunguna Fawwaz ya rubuta ya basa saboda zafin zazza6an da kuma kumburin fuskar ta, still zuciyar sa na kissima masa abubuwa da dama. Rayyan bai ce komai ba ya juya yana godiya yayi gaba abinsa, dan shi tuni ma ya watsar da batun cikin zuciyar sa bai wani bashi muhimmanci ba. Can gida kuwa Ammi da 'kyar ta lallashi Zaitoon tayi shiru domin kuka sosai take yi cikin zuciyar ta take 'kissima irin muguwar tsanar da Rayyan yayi wa Feefy da har zai iya yi mata irin wannan muguntar batare da ya dubi 'karancin shekarun ta ba, yarinya ce 'karama 'kasa da abinda zai iya haifa a cikin sa amma yake yi mata irin wannan muguntar, idan ganin su ne be so ai kamata yayi yace su bar musu gidan su amma ba wai ya dinga cutar mata da yarinya ba, yanzu kam ya kaita ma'kura sam bazata sake juran irin hakan daga wurin koma wanene ba. Sosai take ganin mutuncin Ammi domin ita a fili take bayyana 'kaunar ta gare su musamman ma irin kulawa da kaunar da take yiwa Mufeeda shiyasa ta bata wani matsayi babba, matsayi na daban cikin zuciyar ta wanda kaf 'din rayuwar ta mutun 'daya ne ya taka wannan matsayi kuma har abada tana jin babu wanda zai taddo sa cikin ranta, akwai mutum biyu bayan wancan amma tana jin duk sun biyo bayan Ammi ne sai na ukun su itace Marwa, hatta Rayyan albarkacin su yake ciki yasa har take iya 'dan 'daga masa lokuta da dama tana kawar da kai ga wasu abubuwan da shi da matar suke mata indai ba sun kure hakurinta bane bata tankasu. Amma badan hakan ba sam mancewa zatayi da taimako da suke mata ta fito masa a mutun ta nuna masa kuskuren sa na takurawa yarinyar ta da yake yi. Irin kukan da take yi har na bawa Ammi mamaki, aganin ta indai akan dan Mufeeda ta fa'di ne ai wannan normal yake ga yara, ko kuwa dan jini da ta gani ya fitowa yarinyar nan, ko dai wani abun daban ke damin ta sam Ammi ta rasa amsa guda da zata bawa tambayoyin ta. Gashi har a lokacin Zaitoon bata bayyana mata asalin yadda abin ya kasance ba ta 6oye mata cewa Rayyan ne silar komai. Sai da tayi kukan ta ta gaji da kanta sannan tayi shiru a hankali ta sau'ke numfashi tana goge hawayen ta ta mi'ke zaune Ammi kam sai binta da kallo ta kae cike da mamakin ta. Shin wannan 'din duk 'kaunace ko kuwa menene..?" Ammi ta sake tambayar kanta... Tun lokacin da ta gudo dakin ta tura kuka take har ta kai yarinyar ga Rayyan ta dawo bata daina kukan ba, ita kanta Ammin yanzu ta sahfe kusan rabin sa'a zaune tana lallashin ta amma ta kasa yin shiru 'karshe dole ta haukra da lallashin ta zubawa sarautar Allah idanu. Tana so ma ta bar dakin.zuwa saman ta dan 'kiran Rayyan taji halin da suke ciki amma mamakin Zaitun ya hana ta. Irin duban da taga Ammi na mata na tsantsan mamaki ne ya sa jikin ta yin sanyi, a hankali da sanyin murya tace" Kiyi ha'kuri Ammi na daina kukan...bari inje in bata ko Panadol ne ma kar zazza6i ya shige ta" Murmushi Ammi tayi sannan tana gyara zama tace" Kwantar da hankalin ki ai na tura su asbiti can za'a fi bata kulawar da ta fi dacewa..amma wai kukan duk na menene haka Zaitoon..?" Ammi ta 'karashe maganar da tambaya. Sam Zaitoon bata bi ta kan zancen Ammi na 'karshen ba tamkar ma bata ji abinda ta fada ba, maganar ta ta farkon ne yafi yi mata yawo aka, jin cewa har asbiti Ammi ta tura akaita yasa ta sau'ke ajiyan numfashi, gefen Ammin ta koma ta zauna tana mai sunkuyar da kanta sosai taji sanyi cikin ranta dan hk a hankali ta furta" Nagode sosai Ammi...Ubangiji Allah ya saka mk da mafificin Alkhairi..." Batun yau ta fahimci cewa Ammin zuciyar zinare gare ta ba sai gashi kusan kowani lokaci gaskata tunanin ta actions din Ammin keyi. " Ameen Zaitun...Ameen Ameen" Hannun ta kamo cikin nata sannan ta cigaba" amma daga yau bana son wannan doguwar godiyan kinji ko har yau baki 'dauke ni matsayin mahaifiya bane ?" " Matsayin ki kamar hakan take a waje na Ammi, domin ke ka'dai kk bani wannan gatan tun tasowa ta...". " Yauwa 'diya ta, so ki saki jikin ki kinji, ki saki ranki Insha Allabu Mufeedah zata samu lafiya babu abinda zai samu yarinyar ki kinji..." Kai ta jinjinawa Ammin cike da jin dadin kalaman ta. Bata ma bari Ammi ta kai 'karshen maganar tata ba ta tare ta da fa'din" Insha Allah Ammi, amma Ammi waye ya kaita asbitin..?" domin hankalin ta taji kamar bai kwanta ba daga can kasan zuciyar ta. Shiyasa tayi tambayar. Batare da wata damuwa ba Ammi tace" Rayyan ne ya kaita ina jin ma ba da'dewa zasu yi ba". Taso ta 6oye tashin hankalin ta amma sam hakan ya gagare ta...idanun ta da taji suna tara sabbin ruwa tayi saurin kawar wa kar Ammi ta gani. Baya ta juya mata ta koma ta kwanta ta 6oye fuskar ta a hankali idanun ta ya cigaba da tsiyayar da ruwa...itafa tsoro take, tsanar Feefy da take gani tattare da Rayyan gani take komai ma zai iya yiwa Moopy na cutarwa, a gida ma a gaban ta a kuma gaban Ammi ya aka 'kare ballantana inda babu idanun kowa. Ammi da bata san me ke faruwa ba ganin kamar hutu take bu'kata ya sanya ta tashi ta fita tana fa'din" barin inje in 'kira shi inji ko suna hanya. Ko 'kala zaitun bata ce da ita ba har ta 'karasa ficewa daga 'dakin...abu guda kawai ta sani ta kuma dasawa ranta shine matu'kar aka cutar mata da yarinyar ta bazata ta6a 'kyalewa ba...a lokacin ne kowa zai fahimci asalin wacece ita, ita kanta bata iya kissima abinda zata iya aikatawa idan aka cutar da yarinyar nan amma tasan abin bazai yi kyau bane kawai. Allah ya sani yanzu kam zuciyar ta bazata iya 'daukan wani mummunan abu da zai yiwa Zaitun ba..mutun da agaban idanun ta ma bai ji kunyar hantarar ta ba taya zata iya kwantar da hankalin ta alhali tasan 'diyar ta na tare da shi kuma ba imani ne da shi ba. 'kila ma ya kashe min yarinya..wannan tunanin da tayi ne yasa ta tashi a zabure ta zauna, kukan ta sai ya kasa tsayawa, tashi tayi ta koma bakin window ta tsaya ta na 'karewa harabar gidan kallo..tabbas babu motar sa, gate 'din gidan ta kurawa idanu tana addu'ar taga shigowar su cikin gidan yanzun nan. Ai kam bata bar bakin windown ba har lokacin da taji 'karar horn aka wangale gate ya bude, Motar Rayyan ta shigo...madadin taji sanyi a aranta a a. Saima sake zare idanu da ta yi tabi motar da idanu har zuwa inda yayi parking. 'Kur take kallon motar bb ko 'kyaftawa ganin fitowar Rayyan rungume da yarinyar ne ya sanya ta sakin ajiyar numfashi me sanyi...sai alokacin ta dan ji hankin ta ya kwanta. Rayyan kuwa daga asbiti be tsaya ko'ina ba sai Pharmacy ya sayo komai da aka rubuta masa sannan ya kamo hanyar gida har a lokacin kuma Feefy na kwance saman kafa'dar sa. Zaitoon na jin muryar sa ta taso da sauri ta fito ganin sa rungume da Feefy ya sanya ta kasa barin bakin 'kofar balle ta 'karaso..shi kam duba 'daya kawai yayi mata ya 'dauke kansa bai sake kallon inda take ba sai ma baki daya kya6e domin kallo 'daya idan kayi mata zaka fahimci tsananin damuwa da tashin hankalin da take ciki...cikin zuciyar sa ya furta" kamar akanta aka fara haihuwa. 'karamin tsaki ya saki wanda ya fito fili, maganin hannun sa ya fara sau'kewa hango Ammi na sau'kowa daga saman bene...a hankali taga ya sau'ko da Moopy ma dake saman kafa'dar sa ya kwantar da ita har da gyara mata kwanciyar cike da kulawa wanda hakan yayi dai- dai da isowar Ammi tsakiyar parlorn hango Ammin ya sanya itama Zaitoon jin 'kwarin gwiwar 'karasowa da sauri dan ganin fuskar 'diyar ta, ammavsaivtavkasa 'karasawa, sam ji tayi bata amince da shi ba har cikin zuciyar ta. Kuma duk wannan tattali da ya nuna wa yarinyar bata sa aka ba dan aganin ta duk na ganin ido ne...dama dai wani daban ne yai mata raunin da zata iya yadda da shi amma fa dakan sa ya fa'dar da Mufee har bakin ta sai da ya fashe taya zata yadda da shi. Shi kam maganin kawai ya mi'kawa Ammi ya juya ya fice abinsa batare da ya jira ko shi 'din ya furta wani abin ba. Ammi murmushi tayi kawai dan tasan dalilin sa na yin hakan be wuci yace ta shiga rayuwar sa ta tilasta shi yin abinda bai yi niyya bane kawai. Zaitoon na 'karasowa ta isa gaban Moopy ta rungume ta tana sakin ajiyan zuciya. A hankali ta sumbaci goshin ta tana shafa kwantaccan gashin dake goshin nata take murmushi ta furta " Ammi kinga bakin ma kumburin ya fara sau'ka kuma ba wani zazza6i da ya kamata...". Ta 'karasa maganar tana sakin murmushin da 'karara zaka fahimci na jin da'di ne. Ammi ma murmushin tayi kawai cikin ranta tace" ya sau'ka dai zazza6in" Yayin da a fili kuwa cewa tayi" ai ina ga an bata magani ko kuma allura suka yi mata sai Allah" Tana fa'din hakan ne da shirin zaunawa sai bayan ta zauna sannan ta ciro magungunan daga ledar su tace" Ki barta tayi baccin ta toh idan ta tashi sai kiyi mata wanka sai abata magungunan nata ko.." " Toh Ammi" Ta furta tana mi'kewa tsaye tace" bari in kaita ciki.." " A a barta anan kar kuma yawan jagwalgwalon ya yanke mata baccin ta.." Zaitun bata yi musu ba ta koma ta zauna tana sake gyara rigar dake jikin Zaitoon wanda yake 'ko'karin rufe mata fuska, duk rigar ta 6aci da jini da kuma yawun kukan ta tasha hatta jikin Rayyan ma taga yayi stained da jirwayin jinin wanda take kyautata zaton abinda ya sake hassala shi kenan ya fice da hanzari. Ita kam lokaci- lokaci take juyawa ta kalli Feefy, Allah- Allah take yarinyar ta tashi domin sam rigar dake jikin tan ya tsaye mata arai, bata barin yarinyar ta cikin datti ko 'kazanta ko da wasa shiyasa hankalin ta ya kasa barin kanta. Zaune take daga gefen ta zuba mata idanu Ammi kuwa hankalin ta na kan T.V komin 'kan'kantan abu ya zo jikin Moopyn da sauri zaki ga ta ka'de shi ko kuma ta hure shi... a kullum 'kaunar 'diyar ta sake ninkuwa mata yake cikin zuciyar ta...Allah ya sani dai- dai da 'kwayar zarra bata 'kaunar abinda zai raba ta da ita shiyasa ko a wancan lokacin ma bata bari rabuwar su ta ci galaba akanta ba, duk yadda aka so raba su sam Zaitoon taki bada damar haka. Tun a wancan lokacin ta hana wa'dannan mutanen ganin ta, lokacin da jami'an tsaro suka zo ma tana gefe can 6oye tana duban su amma sai ta kasa 'daga 'kafafun ta ta bayyana gaban su gani take tamkar 'kwace mata 'diyar da uwar ta tayi mata kyautan ta zasu yi...tana da komai da zai iya sada ta da asalin dangin Moopy amma tun ranar da mahifiyar ta ta bata abubuwan har yau bata ta6a ko tunanin 'dago su ta duba ba balle har ta yi wani yun'kuri akai...'ji take tamkar da 'kaunar Moopy aka 'dura mata jinin jikin ta..bata ta6a 'kaunar wani abu irin hakan ba...shiyasa duk wanda ya dube su baya ta6a yin tunanin ba itace mahaifiyar Feefyn ba ita kuwa ko ajikin ta..abu 'daya ne bata jura idan akace mata shegiya mara asali..takan yi iya yinta wurin 'kure masifar ta wajen 'kwatar wa 'diyar ta 'yanci ta kuma 'karyata duk wanda ya furta hakan. Tana kuka zaki ji tana fa'din " ni yarinya ta ba shegiya bace..tana da gatan ta. Hatta Rayyan dake aibanta ta da wannan sunan wasu lokutan ji take tamkar ta shake masa wuya sbd takaicin sa..a 'kira ta 'yar iska, mara tarbiya mai yawon banza, a 'kira 'diyar ta shegiya 'yar gaba da fatiha duk wa'dannan zagin ba ba'kinta bane in da sabo ma ta riga ta saba, sam nata zagin baya yi mata ciwo saboda tasan bata aikata ba, amma na Mufeedan idan akayi ji take tamkar ta ciro zuciyar ta daga 'kirjin ta saboda azalzalar da yake yi mata. Salmerh😘 [25/10/2022, 11:35 am] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* Wattpad@ Serlmerh-md 🅿️ *...59* ........Koda ranar Monday tayi ba'a samu damar mi'ka Mufeeda skul 'din ba kamar yadda suka tsara sbd yanayin jikin ta, hakan yasa Ammi tace abari sai ranar Tuesday kawai akaita that's washegari kenan. Ai kuwa washegarin gudun karya manta ma Ammi da kanta ta 'kira wayar shi da sassafe ta tunatas da shi. Sam ba haka yaso ba amma da yake Ammi ta dage sai shi da kansa zai kai yarinyar ya sanya shi amincewa domin bashi hujja ko ikon yin jayayya da ita. 7:02am ya fito cikin shirin sa, sai da ya duba Amrah ya tabbatar babu wata matsala kafin ya fito zuwa sashen Ammi. Shirye ya tadda su duk a Palorn 'kasa, Ammi da Mufee zaune gefen ta tasha wanka cikin wata ha'daddiyar shiga sai Zaitun dake daura da su fuskar ta babu yabo babu fallasa. Ammi ce ta amsa sallamar tashi yayin da Zaitoon ta amsa ciki- ciki ahakan ma sbd kawai sau'ke nauyin addini ne amma ko kallo bai ishe ta ba har a zuciyar ta. Taso kawar da kai daga kallon sa amma tuna cewa a yau shi ke da ragamar rayuwar su ya sanya ta dole maido da hankalin ta gare shi. Gaishe shi tayi a takaice Rayyan kam bai ma amsa ba illah kallon ta da yayi ya kuma 'dauke kansa, tasan amsar kenan matukar baiyi niyyan yin magana da bakin sa ba. " Shikenan kuje toh.. idan yaso duk abinda ake ciki naji labari daga bakin Zaitoon idan ta dawo..." Ammi ce ta fa'di hakan bayan sun gama gaisawa da shi. Har ya mi'ke sai kuma ya dubi Ammi cikin hanzari, yana ha'de gira yace..." Wace Zaitoon kuma Ammi...?" " ina nufin uwar Mufeeda, idan baka santa ba gata nan gefe na toh 'dan nema kawai...". Cewar Ammi a 'dan kufule. Sau 'daya ya kalle ta ya wani 'dauke kansa yana sake ha'de rai sosai" wai Ammi hadda ita za'a ne? Gaskia ni bazan kuma dawowa gida dan kawai in sau'ke ta ba tayi zaman ta tunda ba cinye mata 'diyar zanyi ba..." Ya fa'da ransa 6acin rai na son taso masa yana me kama hannun Mufeeda dake gaban Ammi. Mufeeda bata yi gardamar binsa ba dan Ammi ta gama lalla6an ta tun 'dazun akan zasu je da Mammyn ta da Uncle Rayyan skul a siya mata kayan wasa. Sai da Mufeeda taga suna shirin barin Palorn ne kafin ta dan waigo ganin Zaitoon a zaune yasa ta fara 'kiran sunan ta tana shirin kya6e baki. Fahimtar hakan da Rayyan yayi ya sashi 'dago ta cak zuwa gefen kafa'dar sa ya rungume ta yana fa'din " shiii"...suka cigaba da tafiyar. Zaitoon kam mutuwar zaune tayi, kamar wasa kamar gaske take ganin fitar Rayyan da Mufeeda su ka'dai daga gida, motsin kirki ma kasawa tayi sbd al'ajab 'din maganar sa. Rayyan kuwa bai zame ko'ina ba sai motar sa da aka ware masa zai fita da ita, ciki ya sanya Mufeeda sai dai yana ajiye ta tana sake 'kan'kame shi da sakin kukan da bai fito mata tun 'dazun ba...tana 'kiran" Mammi.." Rasa yadda zai yi da ita ma yayi. Da farko iska ya hura abakin sa yana jin tamkar ya maida musu yarinyar ciki, shi bazai iya raino haka nan kawai babu gaira ba dalili ba. Haushin wannan lamari duk ya tsaye masa a zuci, meyasa Ammi zata tilasta lallai sai shi bacin ga mutane da yawa da zasu iya sada yarinyar da skul ba lallai sai shi da kansa ba. Idan kuma tafiso na gida ya kaita ina laifin Sultan toh amma wai sai shi...abinda ko Marwa ma aka bawa dama zata iya mi'ka ta. Dabara ce ta fa'do masa dan har ga Allah bai san ta yadda zai lallashi yarinyar ba, shi ba gwanin lallashi bane balle yace zai ma gwada, wayar sa ya zaro yana sake gyara ri'kon da Mufeeda tayi masa. Youtube ya hau ya searching children Rhymes ya kunna mata...hadda 'kara sautin muryar ta yadda zai dauki hankalin ta sosai. Ya kuwa yi nasara domin a hankali ya 'dan zamo da ita yana nuna mata wayar idanun sa na kan fuskar ta dake ji'ke da ruwan hawaye. Wani bugawa da yaji zuciyar sa tayi masa har sai da ya sashi dafe 'kirjin sa yana lumshe idanu a hankali ya bu'de idanun ya sake sau'kewa saman fuskar ta haka kawai fa yaga fuskar Nadian sa ta wulga a kan fuskar yarinyar, abinda bai ta6a gani ko lura ba sai yau 'din ka'dai. Sai da ya zuba mata idanu kafin ya yadda da gaske fa yarinyar na 'dan shige da Nadian sa..." Allah mai iko..." ya furta cikin zuciya Yayin da sautin kukan Mufeeda ke raguwa a hankali tana bin wayar dake hannun sa da kallo. Sake mi'ka mata yayi bayan fahimtar ya samu nasaran janyo hankalin ta. Da 'kyar yayu dauriyan da harshen sa ya iya furta " Come on...take it and see your friends playing..hho..." A hankali ta sa hannu ta kar6a tana sakin wuyan sa da ta ri'ke, shi kuma ya sake bin fuskar ta da kallo a hankali, sosai tsabtar da ake mata yake matu'kar birge shi. Shiyasa baya shayin dau'kan yarinyar sam kuma ko can cikin zuciyar sa ya kanji tana shiga ranshi sbd wannan tsabtar...Marwa hadda 'karyar turaren yara duk take siya mata idan ta fita shopping kuma Zaitoon na mata amfani da shi, 'kamshin ta kullun mai sanyin dadi sosai Rayyan yake jin natsuwa a yadda suke zaune da yarinyar. Abu guda ne bai so game da ita yadda yake jin bugawar zuciya indai ya sanya idanun sa cikin nata sai kuma yau da acewar sa shai'dan ya shigar da fuskar Nadian sa kan tata alhalin yasan 'karya ne babu wata ala'ka da ta gifta tsakanin su, duk da bai san dangin Nadia kaf ba amma a iya sanin sa basu da mai suna Zaitoon balle wannan da Ammi ta tabbatar masa da cewa a garin Bauchi suka hadu har ta taho da su. Bayan shu'dewar wani 'dan lokaci data shagala da kallon Rhymes 'din daya sake duban fuskar ta ta sai kuma bai ga fuskar Nadian ba. Hakan ne ya sake tabbatar masa da zargin sa ma cewar shai'dan kawai ya raya masa ko 'dazun ma. Sai da ya 6ata tsawon mintina uku yana tayata kallon dan hankalin ta ya kwanta kafin ya zame a hankali ya zaga ya shiga motar ya tada ya durfafi hanyar gate. Mufeeda sam bata ma kula da hakan ba hankalin ta naga wayar dake hannun ta ne. Bai zame ko'ina ba sai bakin gate 'din CONCORD ACADEMY...yasan makarantar akwai tsada sosai amma tsarukan makarantar suna matu'kar birge shi ba tun yau ba, sannan professional teachers da suka san me suke yi suke aiki dasu, haka nan kawai ya tsinci zuciyar sa da bashi shawarar kawo ta CONCORD bai kuma san dalili ba, nan take kusa unguwar su Anty Madeena tsakanin su ba wata tazarar kirki bace. Sosai hankalin Mufeeda ya 'dauku ga kallon Rhymes 'din shi kansa sai yaji baya son ma ya yanke mata, musamman sbd gudun kar ya dawo mata da kukan ta baya. Ko da yayi parking 'din juyawa yayi yana duban ta ko 'daga kai bata yi ba ba balle tasan abinda yake yi illa ido data tsurawa wayar tana kallon tana tatta6a fuskar wayar. Fitowa yayi ya zaga ya bu'de 6angaren da take sai lokacin ta dube shi. Hannun sa 'daya ya mi'ka mata da nufin tazo su tafi ita kuwa sai ta kalli hannun sannan ta kalli wayar dake hannun ta. Mi'ka masa tayi da tunanin ko abarsa yake so tunda tasan cewa dai ba nasu bane. Bai 'ki ba ya amshi wayar sa sannan a hankali yace" Baby muje ko, we ar almost getting late..." Yana maganar ne gami da 'dago ta ya fito da ita. Yadda yake tsammanin tsadar makarantar ma har ya wuce tunanin sa, bai tabbatar da hakan ba sai da aka bashi list 'din expenses na skul 'din kafin ya sake tabbatarwa. Sai dai kuma baiga laifin tsadar tasu ba bayan karance list din expenses ya fahimci komai su ke badawa kama daga Lunch box na yaro sneekers hatta da socks zasu bada kala biyu sai dai in kanaso daga baya ka 'karo ma yaron ka but same sample. Sai da yayi sighing na acceptance kafin aka sake bashi form ya cike mata wanda shine shaidar zamtowar ta cikkiyar 'daliba a CONCORD ACADEMY. Wannan lamarin na faruwa ne duk Mufeeda na manne da jikin sa tayi luf kai baka ce ta ta6a yin kuka akan shi ko ta ta6a gudun sa ba . Sai da suka nemi yi mata passport kafin aka 'dan so yin daga da Mufeeda abin mamaki sai ta'ki bin kowa daga cikin su ta ma'kal'kale shi. Rayyan murmushi yayi da ganin hakan, sam bai ta6a zaton Mufeeda zata so shi akan wasu ba, har can cikin zuciyar sa yaji da'din haka, take sai yaji wata 'kaunar ta ta ta taso masa da bai san daga ina ba. Da kanshi ya kaita wajen passport din aka 'dauka da kalar background da suke so kafin suka dawo office din head of the school din dan cigaba da cike form 'din da ya fara. Sunan ta shine abu na farko da zai fara rubutawa kuma bai sani ba, kallon sa ya kai gareta amma yasan itama ba cikakkiyar amsa zai samu daga wajen ta ba ya sani. Sai da yabi sauran ya gama cikewa har wajen Guardian inda ba tare da tunani ko tantamar komai ba ya rubuta sunan sa, wajen signing na mahaifi shima ya buga signing dinsa. Sai da ya gama cike duk inda ya dace shi yayi kafin ya 'kira Ammi a waya yake tambayar ta sunan yarinyar. Ammi ta ce da shi sunan ta _Aisha..._ " Ammi Aisha ka'dai ai ba suna bane i mean her full name fa..." " Toh wannan ne dai ka bari in tambayo maka Zaitoon gaskia nima ba sani nayi ba...". 'Dan 'karamin tsaki ya sau'ke yana duba agogon hannun sa. Sosai ya shiga lokacin sa gashi yana da ayyuka masu dama agaban sa, akwai kayan da zasu yi exporting kuma bai gama saka hannu ba, gashi yau zasu yi voucher na biyan ma'aikatan su duk kuma sai ya sa hannu. Tuno hakan ya sanya shi fara rubuta Aisha dan rage aiki kafin Ammi ta 'kira ta sanar da shi sauran sunan, dan yana kyautata zaton daga haka ya kama komai, sai dai yana fara rubuta Aisha kafin ya ankara har Muhammad ya biyo baya. Ya ankara da hakan ne kafin ya rubuta Sa'ad ko Auta dan haka sai yayi saurin ajiye biron yana cika iska cikin bakin sa ya lumshe idanu. Dai-dai lokacin da aka taking excuse aka gabatar da passport 'din Mufeeda da aka 'dauke ta. Sake kallon sunan yayi _Aisha Muhammad_ ya maimaita saman la66an sa a hankali yakai hannu ya 'dago Form 'din yana mi'kawa PC da fatan Allah yasa sunan mahaifin nata da Ammi zata tambayo ya kasance Muhammad 'din ne kamar yadda ya rubuta. Mufee ta so yin rigima lokacin da zai tafi amma da yake suna da wajen wasan yara sai suka ja hankalin ta da wannan, dama Marwa ta saba kaita irin wuraren yawo dan haka basu sha wahalar 'dauke hankalin ta da wannan ba musamman ma data ga yara sa'oin ta nata wasan su tuni itama ta zage, da wannan time 'din Rayyan yayi amfani ya zame ya bar skul din ya nufi ma'aikatar su. Sha biyu da rabi ya ga 'kiran sabon number da yayi saving da PC wanda suka yi exchanging numbers kafin ya bar skul 'din bayan wanda ya ajiye wajen cike form. Shaf ya mance ma da batun yarinyar sai da yaga call 'din PC. Goshi ya dafe dagaske ya mance da ita....bai yi niyyar fita bama a lokacin dan niyyar sa sai time 'din sallar azahar kawai zai fita sbd ayyuka amma da ganin call din tuni ya mi'ke ya rusa waccan tsarin...gashi Sultam ma ya fita wai baya jin dadi da duk tara masa ayyukan duk zai yi. Da hanzari ya dauki abinda yasan yana da bukata ya fice kiran PC na sake shigo masa yayi saurin 'dagawa domin bai samu daman daukan kira na farkon ba. Batun yarinyar ya tunasar da shi kamar yadda ya tsammata take ya tabbatar musu da cewa yana hanya. " Innalillahi..." ya furta idanun sa na kan Mufeeda da tazo ta rungume shi...bayan kukan da tasha tuni tayi sanyi. Anan PC ke tunasar da shi mantuwar da yayi na rashin kawo mata abinci da bai yi ba ya dafe goshin sa, wallahi shaf ya mance ne amma bai yi niyyar barinta da yunwa ba, ayyukan dake gaban sa ne suka sha kansa..wani tausayin yarinyar ya tsarga masa ya mmayi ilahirin zuciyar sa, gaba 'daya sai yaji ya ma karaya. Bayani PC ya cigaba da yi masa cewar amma ya gafarce su sun bata biscuit da abinsha sbd kar ta galabaita duk da sunsan haka ya sa6awa dokar makaranta amma ba yadda zasu yi ne, Nannyn su ta kawo ta tana kuka kuma lokacin breakfast ma tace bata ga tana cin abinci ba shiyasa suka bata. Rayyan yace" bakomai.." 'Dago ta sama yayi yana sake rungume ta yake fa'din" So sorry Baby.. " Yayi maganar yana share mata fuska da sky blue hankicin sa. PC ne ya gabatar masa da Uniforms nata har guda biyu, ga game dress nata Blue house take, textbooks, takalmi, socks, lunch box da sauran duk tarkacen da skul zata bata...Duk sukai masa packaging. Haka ya tattaro ta da kayan suka fito zuwa mota. Lissafin time yayi yaga bashi da isashshsen lokaci, ga azahar ya riga ya gabato ba'a abin ya 'kira Huzaifa yazo ya kaita gidan ba amma zaman jiran sa ma ai aiki ne, toh ko office din zai wuce da ita yaga sam ina, itama ai yanzu haka tan bu'katar wanka, abinci, natsuwa or may be bacci da sauran su, da kulawa da ita zai ji ma ko da ayyukan sa... shawarar zuciyar sa yabi kawai ya mi'kata gidan Anty Madeena in yaso bayan tashin sa a aiki sai ya biya ya 'kara sa da ita gida ko kuma ya kuma tura kawai akaita can gidan. Karshe dai gidan Anty Madeenan ya kaita yace " Anty dan Allah ina da ayyukane, anjima da yamma ko gobe zan dawo in 'dauke ta amma kar a gayawa Ammi tana nan kar ma a sanar da kowa cewa Babyn ta nan..." Kai Antyn ta jinjina masa, shi kuwa ya fadi hkane badan komai ba sai dan kar Ammi taga kamar da gangan yayi hakan dan ya 'kuntatawa Zaitoon alhali ba haka bane. Fita yayi bayan kamar mintina ashirin har yayi salla kafin ya dawo da kayan ciye ciye da su pampers da komai da yasan Feefy zata bu'kata ya ajiye mata, hatta tarkacen skul 'din ta duk sai da ya shigo da su ya kuma ce idan ta fara kuka su 'diga mata maganin bacci. shima drop 'din da kanshi ya kai siyo shi. Wannan ne kadai Anty tayi magana akai inda tace " A a fa Rayyan kar ya cutar da ita..miye abin sai an bata drop an sata baccin dole..." " Babu abinda zai mata Anty bacci kawai zatayi banaso ta dame ku da kuka ne..." " Amma ai da shiga hakki...?" Cewar Anty. Kai ya girgiza yana shirin mi'kewa yace " Anty sai.kacr baki san yarinyar nan ba, Allah kuka zata tai muku abanza.." " Babu ruwan ka idan ma tayi kukan kai ina.kake...?" " Ai shikenan Anty nikam na wuce..." " Adawo lafia...". Daga haka ya bar gidan ya koma office. Kusan hauka Zaitoon tayi ganin har yamma babu su babu labarin su, hatta abinci yinin ranar kaf bata sa a bakin ba tun breakfast din safe, Sallah ka'dai ne take iyawa batare da jin bata da kwarin gwiwar yin ta ba, ko aiki ma ranar bata wani yi na kirki ba, da ace a hannun wani yarinyar take misali Ammi, Marwa ko Sultan da sam bazata damu ba kamar yanzu da ya kasance tare take da Rayyan, bata manta ba kwana biyu kacal da ya gabata shi yayi sanadin fitan jini a bakin yarinyar wanda har yanzun ma gurbin ciwon bai gama barin bakin ta ba, idan ta tuna hakan sai taji ta rasa natsuwar ta gaba 'daya yayin da haushin sa ke kara ninkuwa mata. Wankan jikin ta ma sai da Marwa ta shigo ta tilasta ta yinsa tana zolayar ta da fadin" Raguwar uwa maras dauriya...tace since from her day one in skul kin wani gigice haka kamar wacce akan ta aka fara, tace makarantar da an fara ta kenan har zuwa nan da shekaru masu yawa Allah ne kadai yasan iyakar yaushe karatun nata zai tsaya, ba mamaki daga nan har Phd...tace kuma ma Yah Rayyan 'din ne baki sani ba kome, ko kina tunanin zai 6atar miki da yarinyar ne...shi 'din fa kaf Kano ba 6oyayyen mutum ba ne miye abin tada hankali Zaitoon..ji yadda duk kika takura kanki....? Shiru tayi kawai bata tanka Marwa ba amma tunanin wancan ranar kawai take, babu mamaki ita Marwa ta mance ne da batun saboda ba'a idanun ta komai ya faru ba, amma ai ita bazata iya mancewa ba har abada, wancan ma gaban idanun kowa ne balle kuma baya tare da kowa sai ita sai shi ai Allah ne kadai yasan muguntar da zai mata. Marwa kamar ta shiga zuciyar ta sai cewa tayi" Ko abinda ya faru shekaran jiya ne kike tunani har kika ri'ke a ranki...?" Shiru Zaitoon tayi cikin zuciyar ta tace..." Ashe kin ma sani..." Yayin da Marwa ta cigaba da fa'din" wannan ma nasan bisa kuksure ne, amma Yah Rayyan din shi bayi da abinyi ne da zai tsaya mugunta wa Mufeeda? kema kinsan ba hka bane...duk tunanin da zaki yi akan sa Allah ba haka bane kawai dai jinin ku ne bai ha'du da shi ba shiyasa..amma ki kwantar da hankalin ki na tabbata ur daughter would surely come back home safely nd healthy Insha Allah I assure u this...". Bayan fitar sa ne Anty Madeena ta fara ragewa Mufeeda kayan jikin ta 'karshe da pant kawai ta barta tana 'kiran Nuwairah take harha'da kayayyakin da ta cire mata..." Nuwair....cak maganan nata ya tsaya sakamakon wani gani da idanun ta suka yi..fat fat fat...zuciyar ta ya fara ya fara harbawa ta tsura mata idanu. A hankali ta kai hannu jikin Mufeeda tana kama yatsun hannun ta, hannun Mufeedah tayi saurin sakewa tana mayar da nata hannun saman cikin Mufeeda, wani ba'kin abu tamkar tabo, ba'ki ne sosai tamkar an shafa ba'kin Paint, kwatankwacin girman sa kamar coin yana nan daga gefen cikin Mufeeda 6angaren dama, shine ya 'dauki hankalin Anty Madeena har Nuwaira da ta ke ta kwala 'kira tazo bata ma sani ba. Hakika wannan al'ajabi da yawa yake..toh me ya kawo hakan? menene sila, ta jima tana kallon kamannin yarinyar da ahalin wanta marigayi Sa'ad Auta a fizge, haka nan kuma bata ta6a bawa abin muhimmanci ba, but after seeing this bata jin zata iya yin shiru har sai ta ji me yake faruwa? Menene yake 6oye da bata sani ba? me su Ammi Aseeya ke 6oye mata tsawon lokacin nan..? Koka'dan ko da wasa bata manta da nasa ba lkcn yana 'karami kuma tana da ya'kinin har girman sa abin yana nan bai goge ba, ta tsinci zuciyar ta cikin tsananin mamaki da al'ajabin da bata jin zata iya 6ata tsawon lokaci batare da tayi binciken da ya kamata ba. Da gaske akwai ayar tambaya, tun a farkon fari meyasa suka zo gidan...? Amsa Ammi Aseeya ta sanar da ita komai cewa yawon bara suke har suka taka sahun 6arawo zance har kotu sai dai bincike ya nuna bata da laifi kotu ta wanke ta shine ita kuma ta taho da ita..." Ta yadda da wannan but on what Purpose? Ammi Aseeyah ta sanar mata da cewa zata na mata aiki ta biya ta saboda tafi san irin su wa'danda basu san ku'di ba balle su dasawa ransu ha'inci duba da yanayin rayuwar gidan su.... Tabbas ta yadda da wannan 'dari bisa 'dari. Amma a wani dalili Ammi Aseeyah ta basu masau'ki daban da na sauran ma'aikatan ta...? Babu amsa. Meyasa aka sau'ke ta a 'dakin Safaa...?" Bata sani ba. Meyasa Ammi Aseeya ta bata yaddan da har yasa ta sake mata ragamar komai na gidan batare da wani shamaki ba..?" wannan ma bata da amsa. Meyasa har aka sa ta aiki 6angaren Rayyan...? No answer... Meyasa Ammi Aseeya ta bata daraja fin sauran duk masu aiki da take yi...? Cikin maganganun Ammi Aseeya ta sanar mata da cewa haka nan kawai take jin tausayin ta tana kuma jin ta tamkar 'ya take a wurin ta da bazata iya mata rikon househelp kawai ba face 'yantacciyar 'ya a wajen ta. Tambayoyi ba ka'dan ba sun jima suna trending a brain din ta, meyasa sha'kuwar su da Marwa kullum 'karuwa take...hakika dole akwai wani abu da ita bata sani ba. Sai dai bata fatan ji ko ganin mummunan lamari game da ahalin wan nata, amma tana tsoron sakamakon da zata binciko game da wannan batu dan tabbas wannan daga jinin Sa'ad Auta ta fito bata tantamar haka. Salmerh😘 [25/10/2022, 1:09 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* Wattpad@ Serlmerh-md 🅿️ *...60* ......Wayar ta tasa a akawo mata ta k'ira shi sai dai bai samu zuwa akan lokaci ba sai bayan ya tashi a aiki. Anty Madeena cike da 6acin rai take duban sa har abin yaso bashi tsoro. Sai dai wannan kallon da take masa shafan mai akan tambayar da ta jefa masa wacce ya jita tamkar saukan ruwan zafi saman fatan jikin sa. erh mana ruwan zafi dan shine zafi da radain.sa ke rasawa direct izuwa ga zuciyar ka...amsa kuwa maganar tata ta fara yi masa har bai san lokacin da ya mike tsaye ba a firgice..." Wai Rayyan dama wannan yarinyar 'diyar kace shine kk 6oye mana ko kuwa ni ka'dai kake 6oyewa.....?" Da 'kyar ya iya sau'ke idanun sa kanta la66an sa na rawa ya furta"...Anty wace yarinyar kike magana akai...?" Harara ta buga masa " Wace kuwa banda Mufeeda..kar ka raina min hankali Rayyan...". Ido yazaro cike da firgici yace " Anty Mufeedah kuma...? Ni 'din...?" Kai ya girgiza yana sau'ke ajiyar zuciya yace" wlh kin bani tsoro Anty, ni har na isa in 6oye mk abinda na jima ina nema ne Anty?" " Maganar fahimta nk so muyi Rayyan kar ka 6oye min komai...wato dama munafurtar mu kayi ganin ta haifa ma yarinya shine ka shirya kawo ta gida ta hanyar Ammi Aseeya da sunan taimako mata ko...?" "...Innalillahi wa inna ilaihi raji'un..Haba Anty mana, haba dan Allah..sai kace baki sanni ba, Anty manta waye Muhammad Rayyan kika yi ne...ban san inda maganar ki ta nufa ba sam how I wish mafarki nake...". Ya 'akarsa da dafe kansa da duk hannuwan sa biyu, sosai yake jin babu da'di da kalaman Antyn tasa. Wani gatsau- gatsau yake jin suke sukar sa hatta kansa juya masa yake yi. Bata ce da shi komai ba sai ta fara kiran mai aikin ta..." Nuwairah!...Nuwairah!!... Nuwairah!!!.." " Na'am Hajia.." " Kawo min yarinyar nan". Rungume a jikin Nuwaira suka fito an sake mata wanka sai dai babu kayan da zata saka hakan yasa aka maida mata da nata bayan an wanke shi har ya bushe. Moopu kuwa na ganin sa sai ta 'kura masa idanu duk da bata shiri da shi sosai amma kunsan yaro wanda ya saba gani shine nasa sau da dama zaki ga yaro na 'kin mutum agida amma dazarar kun ke6e inda bb kowa da ya sani sai kaga ya za6e ka akan sauran.... Haka ma Moopy, dan tana ganin sa da ta gama 'kare masa kallo bayan ta tabbatar shine sai ta fara mi'ka masa hannu tana kya6e baki. Nuwairah kam Anty Madeena ta kalla sai ta ce da ita kaita wurin sa.." Tuni Moofy ta fara kuka ganin kamar Baza'a kaita wurin san ba, ana bata shi ta rungume shi tsam tana 'kara volume 'din kukan ta...shima rumgume ta yy sosai a jikin sa yana jin wani iri cikin zuciyar sa..." Mam..mie.! Mammie!! Ta fa'da da alamun son ganin ta kawai take yi. Jikin sa sanyi 'kalau yy cikin ransa ya jinjina irin wannan 'kaunar, lalle ya 'dauki alhakin bayin Allahn nan, Itama uwar ya tabbatar tana can ta fice hayyacin ta ita kuma wannan ta makalkale shi da tunanin zai kaita wurin Mammie... 'Yar murmushi yayi yace" Aiki Jaa..." Wannan fari ne, jan na zuwa daga baya... Kallon ta yayi da alamun tambaya sai ta 'dora da" Cire rigar jikin ta ka gani..." Kallan Antyn yayi amma ganin yanda ta saka serious face ya sanya shi yin kamar yadda tace. Rigar ya cire yana 'dan lalla6a ta da fa'din" Mamin ki kk so ko Baby...bari I wld take u to her...pls stop crying Mammies Angel..?" Ita kam sai ajiyar zuciya take saukewa. Yana gama cire rigar Anty Madeena tace" Kalli gefen cikin ta..." Dubawa yayi amma baiga komai ba..sai ya 'daga kai ya kalli Anty yace" me yake faruwa ne Anty banga komai bafa..hala ciwo taji...?" " Duba dai da kyau zaka gani..". Sai ya kalli 'dayan gefen nata...kasa 'daga idanun sa yy akan wurin a hankali ya kai hannu yana shafawa Muphy kam jikin sa ta kwanta har yanzu tana sau'kar da ajiyar zuciya..'kasan ma'koshi ya furta " Ikon Allah...". Ba wannan ka'dai ba Rayyan, yanzu kai baka lura da kamannin yarinyar nan da kai ba, dubi fuskar ta pls..bakin ta hancin ta hatta idanun ta irin naka ne..ni kaina ban ta6a lura da hakan ba sai yanzu..Rayyan kar ka 6oye min dan Allah ka gaya min gaskiya..". Kai ya girgiza yace" Wallahi Anty bb wata ala'ka ta jini tsakani na da wannan yarinyar baki ga mahaifiyar ta ba ban san taba, ban taba ganin ta ba wlh sai a gida kawai da Ammi ta kawo ta...". " Sam ban yarda ba Rayyan...dole akwai wani abu..ko kai ko Sultan...ba dan Kabeer ya jima da rasuwa ba da sai ince har da shi tunda kammnnin ku 'daya ne da gaba 'daya..." Shi kam ido ya zuba mata yana kallon ta bama fahimtar ta yake yi sosai ba, shi kansa yy mamakin wannan lamari...sak fa irin nasa wannan ba'kin abin..inba ikon Allah ba waye ya isa yy haka, da ace shi me neman mata ne da sai yace shine yy cikin yarinyar amma yasan ba haka bane sam bb mata a tsarin rayuwar sa, especially matan banza ya tsane su, ya tsani duk mai irin harkar ma, me zai yi da wasu mata can har ya 6ata lokacin sa wajen su bayan Allah ya hore masa abinda zai yi aure ya kuma kula da rayuwar su ya kuma bashi damar ajiye 'dai 'dai har guda hu'du me zai yi da wata mace daban a waje?...amma shi kansa yayi mamaki, meyasa yake dan ganin kamannin Nadia tattare da yarinyar? musamman dazu da zai fito da ita daga gida har sai da hakan ya doki zuciyar sa. ......Fawwaz da ya fa'do ransa ne ya sa komai ya tsaya masa cak, kardai dagAske shima abinda ya lura da shi kenan har yake zargin ko 'diyar sa ce ko ta 'yan uwan sa , babu shakka, amma ai shi yasan babu komai, kuma ma in dai hakan ne dagaske mecece ala'kar sa da su, shifa haka ya gansu tare da Ammin sa, da dantashi ne ma da tuni sun bar gidan tun farkon zuwan su, me ma zai sa ya haifi 'diya kuma ya bari ana yawon bara da ita, ko da ace bata hanyar aure ya haifa ba baya jin zai iya bari.... 'Dagowa yayi ya kalli Anty Madeena data tsura musu idanu, gani kawai take taMkar Mufeedan tsagin jikin sa ne, yadda yarinyar ta rungume shi ba kowa bane zai iya shakkar fa'din cewa shi'din mahaifi yake agare ta...muryar Rayyan ya dakatar da ita daga dogon tunanin data fa'da. " Anty ku fahimce ni mana, babu komai babu wata ala'ka tsakani na da su wlh Anty, kawai ikon Allah ne, kinsan yafi gaban hakan, fiye da hakan ma sai ya aikata ba abin mamaki bane, haka fa Fawwaz yaso ya 6atan rai lastweek...sai da na nuna masa 6acin raina kafin ya bar zancen..." " Kai kuma da yake kai sauna ne har abin alfahari kaek ganin ka aikata da nuna masa 6acin ran naka ko...?" Dagowa yayi ya kalle ta sai ta cigaba" Erh mana.. me ze hana daya fa'di hakan baka sa kai ka bincika ba, inma ka tabbatar da cewa kaine sarkin wawnnci ba, ai ko ba da kanka ba sauran 'yan uwan ka fa....?" .." Haba Anty...!" Ya zaki ce haka? wauta ce dan ban kula da maganar ba..?" " 'Kwarai kuwa ai inda ba 'kasa nan ake gaddamar kokawa, kuma in ba anga alamu ba za'a fara fadin hakan ne.." " Anty bayan nasan babu wata ala'ka da zai kawo hakan mai zai sa in damu kaina ko in takura kaina da wani bincikawa...ni 'din nan ne dai kuma nasan bamu da wata ala'ka, ban ta6a sanin yarinyar nan ba sai da nazo gida na tadda Ammi ta kawo ta...Allah ne shaida ta...." Shiru Anty Madeena tayi tana duban sa. Amma meyasa sam zuciyar tata kasa yadda cewa basu da ala'ka, dole akwai wani abin dai... Ta tabbatar wa kanta. Tuni Mufeeda tayi bacci ajikin sa, hakan yasa ya fahimci yinin ranar kaf batayi baccin ba. Ya kuma fahimci Anty Madeena basu bata drop din da zai sata baccin ba kamar yadda ya fa'da. A hankali ya kwantar da ita gudun kar ta farka ya tashi kawai yayi waje ko sallama bai yiwa Anty Madeenan ba. Ko da ya isa gida direct 6angaren sa ya wuce har akayi maghrib kuma bai shiga 6angaren Ammi ba. Da suka gaji da jira ne Marwa ta bawa Ammi shawarar ta6o shi a waya, ita kanta 'kage take da ganin yarinyar..." Can't wait to see this cute baby in her school uniform..." that's what Marwa keep saying throughout the day..duk damuwar da Zaitoon take ciki ita bashi ne gaban ta ba...dan tasan ko giyar wake kullum Rayyan kesha bazai kwatanta abinda Zaitoon ke zaton zai aikata ba, me akayi akayi Mufeeda da har zai zalin ta, babba ma Rayyan ba kowa yake da lokacin tankawa ba balle Mufeeda. Tasan duk abinda ke faruwa tsakanin su coincidence ne da kuma sakawa arai da Zaitoon tayi...Babban abinda ke damun zuciyar ta kuma shine rashin yadda da yake hana ta sakewa da mutane...ciki kuwa har da Rayyan...kuma babban abinda ya fara haifar musu da sa6ani kenan...sai dai zata yi 'ko'kari ta daidaita wannan kafar Insha Allah. 'Karan wayar sane ya yanke masa tunanin sa. Ammi ce, ya kuma san abinda zata tambaya, hakan yasa kawai ya shuri silifas 'din sa ya yayo 6angaren ta. Da sallamar sa ya shigo Ammi da Marwa suka amsa yayin da Zaitoon ta dube shi da jajayen idanuwa tana le'ko bayan sa, ji yayi daria na shirin 'kwace masa a yadda ya gantan tamkar ganyen paw- paw da ruwa ya gaza masa, yasan cewa an yini aikin kuka ne yau din. Zama yayi yana amsar gaisuwar Marwa, me kike a gidan nan har yanzu baki tafi gidan ki ba...?" Yace yana duban ta. " Yah Sultan nake jira.." Ta bashi amsa tana yin 'kasa da kanta. " Har yanzu bai dawo ba ne...?" Ya sake tambayar ta. " Erh Yayah...". " Anya kuwa, ki dai je ki duba, tun kusan 12 ya bar office fa wai baya jin da'di inaga ma yana can gida fa ke kuma kinyi zaman ki anan baki san wani hali yake ciki ba...." " A a fa Yayah munyi waya yace min zuwa 8 zai shigo mu wuce". Shiru Rayyan yayi da tunanin ko Sultan 'din bai sanar da ita bane gudun kar hankalin ta ya tashi. Ga Ammi ya maida hankalin sa ya gaida ta amsa ta kuma 'kara da fa'din.." Nace wai ko makarantar yini da kwana aka kai mana yarinyar...?" Kansa ya dan shafa ya na jin bai kyauta ba da bai zo ya sanar da su ba tun daowar sa gidan...shaf ya mance ne da hakan kwata- kwata bayan zafin da Anty Madeena ta 'kara masa..." abin mamaki yanzun ma sai naga baka shigo da ita ba ko wajen Amrah ka baro ta...?" Cewar Ammi tana masa kallon mamaki. " Ohh no tana can fa na mance ne, tana wajen Anty Madeena tun da azahar,...". Wani sassanyar ajiyar numfashi Zaitoon ta sau'ke da har sai da yasa duk suka kalle ta sannan Rayyan da Ammi suka 'dauke kansu suka cigaba da magana. " Toh haka muka yi da kai ne? duk kabi ka tayar mana da hankali a banza, kuma ma ai sai ka 'kira ka sanar da ni amma kayi shiru ina ta 'kiran wayar ka kuma baka responding...". "afwan Ammi ban kyauta ba na sani amma sharrin mantuwa ne, Insha Allah gobe zan sa adawo da ita gida immediately when they are off...." " Da dai yafi kam...ya batun makarantar toh...?" Ammi ta fada tana gyara zama dan sai yanzu taji hankalin ta ya kwanta. " An gama komai nd they offer her everything suna can gidan..." " Masha Allah...Allah ya saka da Alkhairi yayi maka albarka..ka jini shiru batun suna k, shirme tayi min ai caa tayi wai asaka Aisha Zaitoon Kyari...shirme fa shiyasa ma kaga ban kuma 'kiran naka ba..." Da mamaki yace Aisha Zaitoon kuma, mance sunan uban tayi ne ko me...?" " Wai ita hakan tafi so asaka mata.." Ammi ta 'karasa da duban Zaitoon da kanta ke 'kasa yayin da Marwa ke 'yar daria da jin yadda suka yi da Ammi dan a time 'din bata shigo ba shiyasa bata sani ba. Shima kallon ta yayi take kuma sai ya 'dauke kansa yana gyara zama yace " Yanzu dai na bata aron sunana cuz lokacin I'm in hurry zan yi late a office shiyasa nayi haka, duk time 'din data tuna sai ta sanar aje a canza mata..." Zaitoon kam tun lokacin da ta ji Mufeeda na tare da Anty Madeena taji hankalin ta ya kwanta, gaba 'daya damuwar ta ta kau, dan tasan Anty Madeena sosai ta kuma san halayyar ta, sosai take 'kaunar Mufeeda tasan zata samu kula yadda ya dace a hannunn ta. Washegari kuwa bai koma gidan Anty Madeena ba office ya wuce abin sa, yayin da Anty Madeena ta kwana da zullumi da tsanan ta tunani, sosai take ganin dacewar wasu abubuwa tsakanin Rayyan da Mufeeda, amma meyasa tun farko babu wanda ya lura da hakan sai ita, itan ma kuma sai yanzu, duk da ta jima tana kallon yanayi da zubin halittar Nadia da yaran yayan nata tattare da yarinyar amma bata sa aka ba sai da yau taga wannan ba'kin abin da ya kasance irin na Rayyan sak, domin tasan Rayyan tun yana tsumman goyon sa...ganin wannan ba'kin tambarin ya sanya duk tunanin ta hautsinewa. Bazata ta6a jin natsuwar zucia ba har sai ta tabbatar da cewa wannan yarinyar ba jinin ahalin yayan ta bane ko kuma tasu... Address 'din makarantar ya turawa Anty Madeena washegari tasa aka kai Mufeeda da komai da tasan zata bu'kata, yarinyar ma babu ruwan ta tana da saurin sabo dan har Mufeeda ta 'dan fara sakewa dasu ko da daren ma basu 'diga mata drop din baccin ba kuma bata basu matsala ba tayi baccin ta, sau 'daya kawai ta farka shima bata da'de ba ta koma. Badi'a ma da'di kamar ya sumar da ita yau gata ga Mufeeda cikin gida 'daya. Da safe ita taimata wanka duk da Nuwairah da Anty Madeena na 'ko'karin hanata amma ta turje. Ita ta shirya Mufeeda tsab suka kuma fito tare aka wuce da su bayan an 'dauko Imran acan gidan su. Abu wasa- wasa fa zuciyar Anty Madeena ya kasa barin batun, cikin ko wani da'ki'ka 'karin kusanci da kamanni take sake ji da gani game da Mufeeda. Hakan sai yaso ya ta6a daily routine dinta, yini tayi tana tunani har lokacin tashi yayi aka dawo da Mufeeda data tabbatar shine ya tura. Kasa hakuri tayi sai da ta kirashi awaya ta sanar da shi tana neman sa idan ya taso a aikin yace toh ba matsala. Saboda yanayin da yaji maganar ta ma yasa ya kasa samun sukuni tun la'asar daya fito sallah bai koma office ba ya nufi gidan nata. " Anty dan Allah ki bar wannan batun, na riga na san babu wata ala'ka tsakanin mu...meyasa kike takura kanki da tunani ne, Anty ko dai baki yadda dani bane dama tsawon lokacin nan..?" Ya fa'da bayan jin bayanan da ya fito bakin Anty Madeenan. Tace" Ko ka'dan Rayyan, abu guda da har Allah ya 'dauki raina bazan yi shaidar sa akanku ba kenan Insha Allahu, amma ni na kasa tantance wani tunani zanyi akai, hakika bazan ta6a samun natsuwar zuciya ba matukar ban tabbatar da cewa Mufeeda ba 'diyar kowa daga cikin ku bace, abinda ya fi 'daure min kai ma.shine yanayin kamannin ta da ya zo 'daya da Nadia kai da kuma Safaa...." Jim yayi shi kansa maganganun Antyn sun fara shigan sa, amma baya so su shiga kansa su zauna domin yasan indai ba wani Rayyan din na daban bane Antyn ke magana shi kam yasan babu wata alaka. Fawwaz ne ya sake zuwa masa tunani...sai kuma ya tuno kammanin Nadia da ya gani tattare da ita a safiyar jiya, ga kuma magangnun Anty Madeena. " Yah Subhanallah...me ke shirin faruwa da shi ne wai...?" Ya tambayi zuciyar sa yana mai cusa hannun sa cikin sumar kansa. " Anty yanzu ya kike so ayi toh, ni har ga Allah bansan yadda zan 6ullowa lamarin nan ba, haka 'dazu da safe dana fito da ita zan kaita skul wallahi Anty kamar 'kiftawa naga kamannin Nadia saman fuskar ta har yaso sani cikin ru'dani amma daga baya sai na lura ba hakan bane. Babu mamaki fa shai'dan ke son yi mana wasa da hankali dan ni nasan bani da alaka da su, kuma Sultan ban zargin sa sam bayaga haka ma ba yadda za'ayi Sultan ya haifi me kamanni da ahalin mu da yanayi da mu matukar ba da jinin ahalin mu suke tare ba nasan kin fini sani Anty...toh duk na rasa mai ma zance, kawai a watsar da batun, ki kwantar da hankalin ki dan Allah ki daina damun kanki da abinda Allah ne ka'dai ya tsara shi bamu san komai akai ba balle musan mafitar sa..." " Hakane Rayyan...Amma baka yadda cewa tun kafin Allah ya halicci cuta ya halicci magani ba, sannan ya halicci tsanani ya kuma kawo sau'ki..? Baka ganin cewa Allah da kansa ya bamu hanyoyin da zamu samawa kan mu mafita kan duk wani damuwar da ta dame mu...?" Shiru yayi yana duban ta...duk yadda ya kai ga raina lamarin abin nema yake yafi karfin sa, dagaske ba haka yaso ba, meyasa Anty Madeena zata tashi hankalin ta ta kuma tada mashi, baya ma 'kaunar su Ammi suji wannan labarin dan suma duk hankalin su kan batun zai koma suyi ta zargin sa alhali yasan shi bai aikata komai ba, bayaga hakama baya so hankalin su ya tashi kwatantacin yadda yake ganin Anty a halin yanzu...tuni ma yafara regretting kawo Mufeeda gidan ta, da yasan hakan ne zai faru da bai yi azar6a6in kawo ta ba, da yasani da office 'din san kawai ya wuce da ita yafi mashi. " Mafitar mu ba haramtacciya ce, ba kuma rashin yadda da hukuncin ubangiji bane face dan samun masalaha da natsuwar zuciya, kai Rayyan kana ganin akwai ranar da zanji kwanciyar hankali ne matukar ban tabbatar da wannan 'diyar bata da ala'ka da mu ba zahiri...?" " Toh Anty how, ni ne nace bani n bane, Sultan it's impossible, toh Anty Raihana ko Marwa kin san babu ko 'daya..bama zai yiwu ace su ba toh miye abin damuwa akai..?" " Abin damuwar yanayin Nadia da ke tattare da ita..". Shiru yayi ya zubawa Antyn idanu. " Idan kuma ance Nadia who next..? It's u Rayyan..." " Anty kin manta Nadia ta rasu ne..?" " Ban manta ba kamar yadda ban manta yanayi da halin da ta rasu ciki ba, Allah ka'dai ne yasan komai dan haka na riga na gama yanke shawarar asbiti zamu je, idan aka tabbatar min baku da ala'ka sannan hankali na ya kwanta fiye ma da yadda kake zato...". Salmerh 😘 [27/10/2022, 1:04 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Wattpad@* *Serlmerh-md* 🅿️ *...61* ........" Ina Marwa ta shiga ne? Marwa!..Marwa!!..." Ammi ke cigiyar ta tana 'yan dube- dube amma bata ganta ba. Bayan kamar mintina biyu sai ga Zaitoon ta hawo saman nata da sallama a bakin ta hannun ta 'dauke da wani kyakkyawan bowl da spoon bata dire shi ko'ina ba sai gaban Ammi. Sai da ta dai- dai ta zaman glass bowl 'din da kyau sannan ta koma gefe ta zauna daga gefen kujerar Ammi fuskar ta babu yabo babu fallasa. Ammi ma gyara zaman ta tayi gami da 'dago bowl din a hannun ta tana fa'din" banga Marwa ba hala itama tama can kitchen 'din ne ko..?" " A a Ammi inaga dai 'dakin ta take fa.." " Ok...wai da so nake taje ta duba min Amrah ya tashi, amma bari dai ta shigo tukunna...". " Ko dai in 'kira ta ne kawai Ammi..?" " a a barta zata shigo ai..." Shiru ne ya 'dan ratsa wajen na 'yan wasu da'ki'kai...kowa sakar zuci yake amma daban, Ammi tunanin Amrah take da yanayin girman cikin ta sosai take tausaya mata, yayin da Zaitoon kewar Mufeeda ke nu'ku'rkusar ta. A hankali Zaitoon ta 'dago tana duban gefen Ammi bakin har na 'dan rawa tace.." Amma Ammi yau in an tashi su Mufeeda gida za'a kawo ta ko...?" 'Yar murmushi Ammi tayi tana tauna fruits din bakin ta a hankali, sai da ta gama taunawa kafin tace..." Ha'kurin Zaitoon ya 'kare kenan...?" Murmushi tayi ta sunkuyar da kanta, yayin da Ammi ta cigaba da fa'din.." Nima nan bansani ba wannan hukunci duk na Rayyan ne, amma may be ya dawo da ita yau 'din jiyan ma ai kinji yace ayyukane sukai masa yawa shiyasa kawai ya barta acan ya koma office. " " Hakane Ammi...Allah ya taimaka ya bada sa'a..." " Ameen Ameen...ai naga ma kinyi 'ko'kari fa, tun jiya an yini an kuma kwana ana sake shirin wani yinin batare da kuma Mufeeda ba ai dole a jinjina miki...." Ammi ta fa'da tana 'yar dariyar zolaya...dayake dama ta saba jan mutane ajiki, bata da girman kai sam Ammi, da kowa ma zata zauna tasha hira abinta in taso tsokanar ka ma duk yi zatayi. Itama Zaitun murmushi tayi kana tayi 'kasa da kanta. " Zaitoon kenan tsananin son da kike wa yarinyar nan ya zarta kowa a zuciyar ki da alama fa..?" Murmushin ta kawai ne ya 'kara fa'da'da wanda kai tsaye ta aika shi ga Ammin cikin bayyana amsar tambayar ta yayin da Ammi ta cigaba da fa'din" na jima da fahimtar haka na kuma kasa ganewa, ko ince kin kasa sanar da ni sahihin labarin ki har yau balle in tabbatar da abinda zuciya ta ke raya min, amma tunani na yafi tsayawa akan cewa rasuwa mahaifin ta yayi shiyasa kk ninka 'kaunar da kike yi masa akan ta ko? Kai ta girgizawa Ammin ba tare da ta dube ta ba...da alamun a a. " Duk da yake ba yau na fara tambayar ki ko nuna miki manufata ba ta son sanin ainihin labarin ki ba amma bazan gaji da tambayar ki ba har gobe har kullum ma har sai zuwa lokacin da zanyi dacen samun amsar 'daya daga cikin tambayoyi na, Allah ya sani ban ta6a nufin ki da sharri ba balle diyarki zama nake da ke da zuciya ta daya, amma na lura ke har yanzu kin kasa fahimtar hakan balle ki iya bambance wanda ya dace da wanda bai dace yasan wace ke ba, duk da hakan zan baki shawara ko dan gaba, ba wai nufina in miki titsiye ba Zaitoon ba kuma dan zan iya tilasta ki ba, but matakin 'kaunar da kk nunawa Mufeedah ya kai matsayin da dole ne adasa ayar tambaya akai, na haifa Zaitun 'yan uwana sun haifa, 'ya 'yan ciki na sun haifa 'kawaye na, ma'kwabtana da kuma sauran mutane, amma ban ta6a ganin zahirin 'kauna da sha'kuwa kamar yanda na fuskanta game da ke da Mufeeda ba, hakan yasa bazan iya ha'kurin ri'ke wannan a zuciya ta ba domin ba tun yau na shiga tsananin kokonta da tunanin sanadin hakan ba, abaya hasashe na yana bani ne akan cewa..mahaifin Mufeedah mutuwa yy ya barki da ita shiyasa kk ha'da 'kaunar da kk yiwa mahaifin ta da nata duk kk nin ka mata su..amma kin ce ba haka ba ne, ni kaina wani sa'in kuma na kanga kamar ba hakan ka'dai ne zai saki yiwa Mufeeda irin wannan 'kauna da sadaukarwar ba..shin Zaitun bakya tunanin akwai mutuwa da zata iya raba ku watarana ne? Bakya tunanin akwai wata kaddarar ta daban da zata iya raba ki da ita..? ban miki fata Zaitun amma kiyi tunanin irin halin da 'dayan ku zai iya shiga idan mutuwa ta gitta tsakanin ku..." " Kuka sosai Zaitun ta fashe da shi a fili ta furta " " Ammi...!" Sai kuma tayi shiru illa kukan daya ci 'karfin ta, ji tayi gaba daya zuciyar ta ta cunkushe. " Idan na 6ata miki kiyi hakuri, but u need to no this bcuz ke yarinya ce 'karama, baki san me duniya take ciki ba baki san manyan 'kalubale da ke cikin rayuwa ba, matukar kika kasamce uwa dole ne ki koyi hakuri, juriya kawar da kai da kuma natsuwa...akoda yaushe ki rika ji aranki cewar wanda ya baki 'da ko 'yar zai iya raba ku duk lokacin da yaso, kuma ba lallai ne dama ku taso atare ba, baki duba marayun yaran da iyayen su ke barin su tun basu san kansu ba amma cikin ikon sa sai kiga sun taso cikin kulawa da gatan da ko iyaten su albarka, har kullum kisa aranki cewar dake ko ba ke dole ne watarana Mufeeda zata yi kuka, zata yi rashin lafiya, zata rayu inda babu ke tunda dole ne ki kaita makaranta, karshe dole ne 'dayan ku zai iya mutuwa ya bar 'daya a lokacin ya zaki ji bayan kin gama sawa aranki cewar kina tare da ita, kin manta cewar mutuwa zata iya giftawa ko kuma itama kin gama dasa mata hakan aranta ki 'kiyasta kiji yadda zaku tsinta zu'katan ku..." Kuka sosai take da hawaye "...Wallahi Ammi ban ta6a mantawa da mutuwa ba, taya ma zan iya mancewa da ita? ta yaya? mutuwar ce fa Ammi, mutuwar ce sanadin komai...." Ta fa'da ne tana me 'kara sakin kuka tare da du'kar da kanta ga dukkan alamu abubuwa take tunawa, abubuwa masu zafi masu tsayawa a zuciya.." Kai Ammi ta girgiza cike da alhini ta ce" na sani, dama nasan bazai wuce hakan ba Zaitun, da kaina na fahimci ciwo da zogin mutuwa ma'kare cikin zuciyar ki da yake saki zafafa abubuwa harma ya hana ki ganin wasu abubuwa ba'a daidai da yadda suke ba..sai dai yanayi da 6angaren mutuwar ne ban san daga wani kusurwa bane, duk da hakan zan ro'ke ki ki sassauta Zaitun ki sassautawa zuciyar ki abinda yake damun ta..ba ina nufin kar ki 'kaunaci 'diyar ki ba ne amma ki sassauta hakan kar watarana ya muku illah, mutuwa tana kan kowa kuma kowa zai 'dan'dane ta, kin ganni nan badan tawakkali da na sanyawa raina ba da yanzu ba wannan zancen ake mk ba Zaitun da sai dai abaki tarihina, domin ni.m naga mutuwa ganin idona, naga mutuwa daki daki da ba kowa Allah ke jarrabta da irin hakan ba amma dana fawwalawa Allah na mika masa kukana ba gashi yanzu nima ina rayuwa ta cikin farin ciki ba, ba abinda ya rage tsakanin mu da wadanda suka riga mu gidan gaskiya illah addu'a. ki sassautawa ranki kema ki kuma sassauta kaunar da kk yiwa yarinyar nan ki daina nuna ta a zahiri ba dan komai ba sai dan irin hakan, wani ma da wannan damar zai yi amfani ya cutar da dayan ku, yayin da wani haka siddan babu gaira babu dalili zai iya jin tsanar ki ko 'diyar kin cikin ransa, akwai masimu mu mgun baki, akwai masu kambun baka duk suna daga cikin mutane masu sharrin da a kullum muke neman tsari da su, sannan dole ne mu kiyaye faruwar wasu abubuwan gudun abinda ka iya zuwa ya dawo". ...Kuka sosai Zaitun ta ke yi mai ta6a zuciya, hakika ita ka'dai tasan inda kukan ta ya dosa, ta fahimci babu wanda zai iya fahimtar asalin zuciyar ta ko inda rayuwar ta ta dosa sai ita kadai, kamar dai Ammi, ta fahimci tunanin ta daban ne..tunanin kukan mutuwa take yi na mahaifin Mufeeda ko wani abu daban..." Ammi ni kam mutuwa kyauta tai min, kyauta mafi soyuwa a zucia, domin mutuwa ta bani yarinya, ta kuma bani ita ne a gabar da ni kaina ban tsammaci hakan ba, hakika ina jin ciwon mutuwarm har cikin zuciya ta ina kuma godewa Allah kullum bisa kyautar Mufeedah da ya bani wanda hakan shi ya rinjayi komai a zuciya ta cikin duniyan nan...." Cikin ranta ta ayyana hakan wanda a fili banda kwalla babu abinda zaka gani saman fuskar ta. Ammi kam idanu ta zuba mata tsawon wani lokaci. Sannan ta dafa kafa'dun ta a hankali ta 'kira sunan ta. Zaitoon..." 'Dagowa tayi ta dubi Ammi sabbin hawaye na sake gangaro mata. Ammi kai ta girgiza, sosai ta kwa'daitu da son jin labarin Zaitun...sosai ta 'kagu taji wani abu daga cikin labarin ta koda da yanki ka'dan ne...domin burin ta na gaba shine sada ta da mahaifan ta, cikin abinda ya gaza wata guda zuwa biyu take so ta sada Zaitoon da mahaifan ta, sai dai zata ro'ke su alfarma su bar mata ita ta cigaba da zama tare da su bayan ta tabbatar komai ya dai- daita tsakanin su...amma duk hakan bazai faru na har sai ta san menene dun'kule cikin rayuwar ta domin tasan ta inda zata fara tunkarar lamarin dama iyayen ta gaba daya. "..Shin laifi ne idan kk bu'de min zuciyar ki kk sanar da ni labarin ki Zaitun? zan so jin asalin tarihin rayuwar ki da kuma dalilin rabuwar ki da ahalin ki tsawon lokacin da ni kaina bazan iya 'kiyasta shi ba...nai mk alkawari zan kuma sake tabbatar mk, daga yau daga yanzu na mk alkwari bazan sake tambayar ki ba matukar baki sanar da ni ba..kuma ba zan ji haushin ki ba ko da baki sanar da ni din ba sai dai nasan sam bazan ji dadi bane kawai... " Shin rabuwa kuka yi da mahaifin Mufeeda...ina nufin saki ne ya shiga tsakanin ku ko mene..?" A hankali Zaitun ta 'dago idanu ta ta sau'ke su kan fuskar Ammi..idanun ta na cikowa da hawaye tace " Ammi ni fa ban ta6a aure ba kawai Allah ne ya bani ita batare da na tsamman ta ba..". ta 'karasa maganar tana mai 'kokarin shanye kukan ta dan kar ta tona asirin zuciyar ta. Shiru Ammi tayi tana duban ta da mamaki domin ta fahimci kamar bata son tunowa da incidence 'din ne..sai dai mamakin ta bai tsaya nan kusa ba can ya tafi wani wuri daban.. a fili ta fahimci manufar maganar tata, babu mamaki wani ne ya yaudare ta kenan ya ra6e ta har yy sanadin samun cikin ko kuma ta hanyar fya'de amma a zahiri da ka ga Zaitun kasan mutunci da kamala sun wadace ta, da wuya ta iya banzatar da rayuwar ta sai dai sanadin da yazam mata dole kamar yadda a kullum take gastata tunanin ta. Wannan dalilin ya sanya Ammi sake jin tausayin ta cikin ranta..sosai ta 'kudurtawa ranta binciko gaskiyar lamarin wanda take fatan ta jishi daga bakin Zaitun ka'dai domin zata fi yadda sosai ta yadda da ita. " ...Allah ya rufa asiri toh.." Shine kawai abinda Ammi ta furta bayan fahimtar Zaitoon bata shirya bata labarin ba. " tashi 'kira min Marwa ku dubo min Amrah da jikin ta, tun 'dazun tana raina wlh...." Ammi tayi maganar batare da ta dubi Zaitoon ba illa juya cokali da take cikin fruits salad 'dinta da har sanyin sa ya tafi. Sai da Zaitoon ta tashi kafin Ammi tabi bayan ta da idanu, bata san meyasa take kaunar Zaitoon 'din ba sam, haka nan kawai take jin ta aranta tamkar 'diyar da ta haifa amma yarinyar har yau ta kasa sake jikin ta da su. ***** Tsaye ya mi'ke yana cusa hannun sa cikin sumar kansa, gaba 'daya lissafi ma ya 'kwace masa, meyasa Anty Madeena ta matsa har haka ne...?" Kai kawo yake yana jin kansa na juya masa... Duban sa ya mayat gareta yace" Anty haka nan kawai sai mu 'dauki 'yar mutane mu kai hospital dan kawai muna zargin wani abu da ba lallai ne ya kasance gaskia ba...?" " Ka manta me nace ne Rayyan?...zamu yi ne domin tabbatar wa da kuma gudun kokonto, idan muka tabbatar da zargin mu ba gaskia bane ba shikenan hankali ya kwanta ba, amma for now ina tabbatar maka da cewa dole ne fa sai anyi gwajin nan...". Anty Madeena ta fa'da babu wasa saman fuskar ta. Kai kawon ya cigaba dayi yana tunanin wata mafitar bayan wannan...tuno wani abu ya sanya shi 'dage giran sa sama duk biyu. Da hanzari ya dawo ya zauna yana fuskantar ta...zamu je asbiti Anty Amma kafin nan muyi wani gwajin na gida tukunna, kwanaki in ban manta ba Ammi ta bani yarinyar nan cikin wani yanayi da nake kyautata zaton attack ta samu, she is allergic to something that really irritated her that way..tabbas bcuz ni nayi treating nata..." Ido Anty Madeena ta zuba masa tana masa wani irin kallo...gaba 'daya yasan da duk wannan amma yake zaune batare da ya 'kara bincikawa ba, sam ba haka tasan Rayyan abaya ba bata san me ya canza sa har haka ba yanzu... Mage ke irritating 'dinsu wannan abin cikin jinin ahalin su ne, in ka 'dauke Sultan ka'dai kaf ahalin su babu mai iya ha'da wajen zama da mage matukar jinin Dattijo Muhammad Auta na yawon cikin jikin ka wato kakan su, dan haka wannan shine matakin gwaji na farko da ya fara tunowa kuma shi ya kamata a jarraba domin sake tabbatarwa duk da kwanaki yagani da idanun sa yadda yarinyar tayi amma dole a yau zai sake gwadawa da ra'din kansa. Idanun sa ya maida kan fuskar Anty Madeena da ta tsaya kallon sa cike da mamakin sakaci da halin ko'in kulan sa da ya 'kara shahara har gashi yana son cutar da shi batare da ya sani ba..erh mana cutarwa..taya zaka rayu da abinda yake mallakin ka batare da ka sani ba sbd sakaci da rashin kular ka ..Kai Rayyan ya jinjina mata " Yes Anty ina kyautata zaton she is also allergic to cats...lets try this first...a ina zamu samu mage yanzu...?" Hannu ta 'daga tana kawar da kai tace.." Can bayan layin mu akwai gidan da akwai amma babu mai kawowa yanzu, Badi'a na skul kuma kaga sai 5 zata dawo suma yaran can gidan haka ne...". Wayar sa ya fara lalu6owa" Bari na nemi Sultan ko zai samo min...." Anty bata ce da shi 'kala ba dan gaba 'daya ma ji tayi jikin ta yayi sanyi..dukkan alamu sun gama bayyana agare ta cewar jinin da ke yawo jikin Mufeeda nada alaka da su amma meyasa sam basu fahimci hakan ba... Tunanin da take kenan har zuwa lokacin da sautin muryar Rayyan ya doki kunnuwan ta. " Wa alaikassalam..Sultan jikin naka...?" " Masha Allah haka ake so thought har yanzu ne naga baka fita aiki yau ba" " Bawani abu...Allah ya 'kara afuwa ya kuma kaimu goben..." " Kasan mene..? Mage nake so ka sama min dan Allah ko gidan Dadaa ne ka duba min the fourth house next to our house by the left I think tana da shi ka aro ka kace injini ne yanzu za'a maida mata" " Erh...ina gidan Anty Madeena aka wo min yanzu, in ma baka samu dama ba ko aikowa kayi akawo min.." " Aha..Thank u.." Daga haka ya kashe wayar suka cigaba da zaman zullumi, kamar dai Sultan da shima cikin zullumin ya bar shi...sosai mamaki ya kama shi 'kararara, iya sanin sa duniyan nan babu abinda ke ha'da Rayyan da irin wannan abin amma me yasa yau da kansa yake neman akawo masa...cikin satin kaf banda neman mafita da wasu tsare tsare babu abinda yake faman yi kuma shrin.sa na daf da kammaluwa a halin yanzu..sosai yake so yakai Rayyan kas wannan karan ya gaji da wannan ha'kurin kwata- kwata...fatan sa Allah yasa ba shirin sa Rayyan ke neman rusawa ba" Kai ya jinjina yana mai tabbatarwa kansa cewar Dole ne ma yaje gidan Anty Madeenan da kansa domin ya ganewa idanun sa koma menene. Salmerh 😘 [27/10/2022, 1:04 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Wattpad@* _Serlmerh-md_ 🅿️ *...62* .......Bai sha wani wahalar samun abinda Rayyan din ya bu'kata ba dayake akwai a gidan su wani abokin sa, dan haka batare da 6ata lokaci ba ya nufi gidan Anty Madeena da fatan Allah yasa ba shirin sa Rayyan ke son wargazawa ba, inko hakane tabbas nesan sa zata matso kusa kwanan nan. " Assalamu Alaikum..." Ya furta abakin 'kofan parlon yana shafa kan magen dake rungume gefen hagun sa yana 'yar murmushin da shi ka'dai ya san ta mecece. Sallamar ya sake gami da 'dan buga 'kofan hakan yasa Anty Madeena mi'kewa taje ta bu'de. Idanu ta runtse sosai da ganin abinda ke hannun san, kanta na fara sarawa, a hankali ta bu'de idanun tana fa'din " Sultan har ka iso...?" Tayi maganar gami da juyawa domin bazata iya jure yanayin da take jin jikin ta ba tuni ta fara jin sanyi can cikin jikin ta. Gaba tayi Sultan ya biyo bayan ta bayan ya tura 'kofar, yayin da Rayyan ke nan kishingi'de har a lokacin bai yadda ya kalli inda Sultan din yake ba. Sai da har ya iso gaban sa ya tsaya yana gaida shi kafin ya 'daga kai ya dube shi, cak idanun sa suka sauka akan magen sai ya 'dan bu'de idanu. " Sultan haka ka taho da shi a hannun ka...?" " Erh Yayah, ai babu wani abu thought yanzu zan sake komawa da shi". " Duk da hakan ai da ka sako shi cikin wani abu taya zan ri'ke shi haka nan bacin kasan meke faruwa..." Ya 'karasa maganar ne yana fitar da numfashi da 'kyar sbd yadda numfashin sa ke neman sarke shi... Sultan idanu ya zuba masa zuciyar sa cike da mamaki da kuma tunanin asalin dalilin da ya sanya shi sawa akawo magen bacin yasan jinin sa ba so yake ba. Yasan dole dai akwai babban dalili da ya sa aka kawo din amma tunanin sa ya kasa bashi komai. " Where is the ointment nd the drugs...?" Tambayar da Rayyan yayi masa kenan da ya dawo da shi hayyacin sa, tuni ma Rayyan kam ya fara sakin atishawa akai- akai idanun sa sun koma jajaye. Sultan da sauri ya matsa kusa da shi bayan ya saki magen..'ko'karin tallabo shi yake yana fa'din" Haba Yayah, dama me yasa zaka ce akawo mage bayan kasan irin hakan ne dama zai faru...?" Yayi maganar cike da nuna tsantsar kulawa kamar gaske. Rayyan 'ko'karin cire hannun sa yake daga jikin sa domin zafi hannun Sultan 'din ke masa tamkar wuta.." Kar ka damu Sultan, komai zai daidaita ai, yi maza kaje ka kawo min maganin ka dawo..." " Yayah taya zan tafi in barka acikin wannan halin...ai hankali na ma bazai kwanta ba...". Jajayen idanun sa ya sanya cikin na Sultan, nace kar ka damu ko...baka ganin jikina ne..." kalli kaga" ya nuna masa jikin sa gaba 'daya. " and the more u sit here d more the condition is worsening...pls kayi sauri ka dawo, Insha Allah babu abinda zai same ni..." Dole Sultan ba dan ya so ba ya mi'ke tsaye sau 'daya ya kalli magen ya kawar da kansa ya nufi 'kofa, 'ko'kari yake yaga yayi sauri kamar yadda Rayyan yace amma duk yadda 'kafafun sa ke son cika umarnin Rayyan 'din zuciyar sa taki mara masa baya, damuwar sa yasan asalin dalilin da ya sa akawo magen. Yanda ya juya baya yake tafiyar haka Nuwaira dake sakkowa take takowa rungume da Mufeeda a hannun sa. Wani sanyi Rayyan yayi da ganin nasara sa da ya samu na kora Sultan kafin suka fito, baya san kowa yasan wannan batu tunda bai tabbatar ba tukunna, kai koda ya tabbatar 'din ma in dai ba gaskiyar maganar ya tono ba bazai bari kowa nashi yaji ba illah Anty Madeena da aka faro da ita. Sultan na shirin bu'de 'kofa ya 'kara waigowa dan ganin Rayyan, sai dai kafin idanun sa sukai ga Rayyan kan Nuwaira suka fara sauka dake ri'ke da yarinya amma sam baiga fuskar yarinyar ba...a hankali ya 'daga 'kafar sa yayi waje yana sake jan 'kofar har da 'kara le'kowa amma still bai ga fuskar yarinyar ba ballantana ya fahimci manufar su. Tafia yake amma kokadan bashi tare da nutsuwar sa sbd tsananin takurawa kansa da yayi da tunani, shin me Rayyan zai yi da Mage? mai yasa aka kawo masa yarinya?...me ma yasa zai ce lallai lallai sai ya tafi ne...yaso da bai hana shi zaman ba shima ya ganewa idanun sa koma menene. But a wannan halin sam ba rashin zaman nasa bane ya dame sa ba wannan yarinyar da yaga an kawo masa itace tafi tsaya masa. " _Naga ya fita da 'karamar yarinyar nan..."_ Maganar Yusee ta dawo masa, cak ya tsaya yana sake waigawa, tabbas sun fita, sannan kuma ko jiya da yaje gidan bai ga yarinyar ba, haka ma yau da safe duk bai ganta ba amma yaga Zaitun, kuma yasan matukar yarinyar na nan kusa to tare zaka gansu. Da 'dan yatsan sa 'daya yake bubbuga gemun sa alamun nazari sai kuma ya juya ya kalli sashin Anty Madeena daya baro. Kai ya ka'da ya cigaba da tafiyar sa, sai dai har a lokacin puzzle din ya kasa ha'duwa masa, a birkice komai ke zuwa kwanyar sa. Rayyan, Mage, Mufeeda, gidan Anty Madeena...gaba 'daya ya kasa ha'de kan lamarin ta yadda zasu bashi ma'ana guda. Sai dai dole yasan there must be a reason behind all these...kuma dole zai binciko daga baya. 'Bangaren Rayyan kuwa da kawo masa Mufeeda yayi saurin kar6ar ta yana nunawa Nuwaira Magen da fa'din ta kamata ta sanya ta cikin wani abu Sultan zai zo ya tafi da shi. Tuni gashin jikin Mufeeda suka mimmi'ke jikin kuma ya 'dau zafi, jikin Rayyan tayi luf motsin kirki ma bata yi. Rayyan duk na lure da ita... a hankali yake bin skin din ta da idanu domin wasu kananun kumburi yake gani da ada babu su saman fatar ta. Atishawan da ta fara ne ya dauki hankalin sa sosai sai dai bashi da damar tallafata mata, tanayi ne shima yanayi. Can bayan kujeru magen ta 6oye da 'kyar Nuwaira ta iya cafko ta...yayin da wanzuwar magen cikin parlorn yk kara worsening yanayin su har wani wari warin ta Rayyan yake ji, kokari kawai yake yi yana dannewa amma har amai ke taso masa. Nuwaira bata zame ko'ina ba sai kitchen taje ta juye ragowar maggin su dake kwali ta sanya magen cikin kwalin maggin ta rufe ta...sannan ta dawo parloun. Waje Rayyan ya nuna mata yace ta kaita waje Sultan zai zo ya 'dauka. Hakan kuwa akayi waje ta mikata sannan ta dawo ciki. Idanun Rayyan rufe ruf suke 'dumin jikin Mufee na ratsa shi yana kuma jin sa a zuciyar sa. Tunani kala kala ke zuwan masa, hakika maganar Anty Madeena akwai 'kamshin gaskia aciki, dole akwai wani babban dalilin da ya kawo hakan, ba hk nan kawai Mufeeda zata yi kama da shi ta kuma kwaso yanayi da zubin matar sa ba, sannan the worse ma tayi kalar jinin su...yasan duk wannan amma ya kasa gano asalin ta inda dangantakar take. Tsoro yake kar ace wannan yarinyar tashi ce tsawon lokacin nan...tsoron ne kuma ya sanya da ya tuno Nadia sai yayi saurin girgiza kai..." ohh no...it can't be...". A dole yake tilastawa zuciyar sa kawar da Nadia cikin lamarin dan ma kar shi ya shigo ciki. Bai ma san da zaman Anty Madeena wurin ba tsabar yadda ya shiga halin ru'dani, yayin da tun fitowar ta zuba masa idanu bayan ta gama 'karewa dacewa ta jini tsakanin sa da Mufeeda. Kawar da kai tayi ganin alamun ya riga yayi nisa cikin nazari. " Nuwaira, Nuwaira...ta fara kwalawa kira wanda hakan shine ya maido da hankalin Rayyan gare ta. A hankali ya bude jajayen idanun sa ya sauke akan Anty Madeena. Ji yake tamkar 'kwalla zasu zubo mishi ne musamman sbd rashin takamammen madafa. Mintina 'kalilan da suka gabata Anty Madeena ce ke 'kage da son ji da gano dangantakar su, yayin da a halin yanzu yake jin nasa 'kaguwan ya ninka nata. " Bari Nuwaira tazo ta tafi da yarinyar kafin ka maida ta cikin cikin ka..." Cewar Anty Madeena tana duban sa. Sai a lokacin ma ya lura da yadda ya 'kwa'kume Mufeeda ajikin sa, bai ma kula da cewa jikin tan tuni ya saki ba. A hankali ya fiddo ta daga jikin sa yana shafa gurbin da ya kukkumburo a kan fatar ta da ya tabbatar kafin akawo masa ita babu shi... " Anty kina gani ko, itama attack din ta samu kamar ni, ina jin tsoron ace duk wannan ba kamanceceniya ce da Allah ya ha'da haka nan kawai ba...inajin tsoro ace yarinyar nan jinin mu ce Anty...amma abinda ya ke daure min kai na kasa fahimta shine..." Isowar Nuwaira ne ya sanya maganar tashi dakatawa. " Amshi yarinyar kije ki sake mata wankA da ruwa mai 'dumi sosai kisa lalle cikin ruwan zaki ga wani magani na ajiye saman mirror na ki shafe mata jiki da shi in tayi bacci shikenan..." Kai Nuwaira ta jinjina tana mai yin gaba dan cika umarnin Anty Madeenan. " Ina jinka..." Tace tana duban sa.. " Anty Zan je gida...kawai ina so in huta zuwa gobe sai muje asbitin...". " Bazaka jira dawowar Sultan din ba?". " A a Anty.. idan ya dawo kawai ya 'dauki magen sa ya tafi..." Yayi maganar yana mi'kewa. " Toh naga bamu 'karasa maganar ta mu ba kuma". " Ma yi daga baya Anty..." " Shikenan Allah ya tsare, amma dai ka tabbatar baka bawa kowa damar sanin komai kan wannan lamarin ba, idan nace kowa ina nufin hatta Ammi Aseeyah..biyo bayan ta kuwa babu wanda ya cancanci sani a halin yanzu, domin kasan har yanzu bincike ake bamu tabbatar da komai ba, baya ga haka ma kar ka mance akwai ma'kiya da nake da ya'kinin akusa suke, sirri nada matukar amfani a mafi yawan lokuta...ko Ammi ba yanzu ya kamata ta sani ba balle wasu daban...kar ka sake in kuma ji makamancin maganar ta fito..." " Insha Allah Anty...". Yace yana mai yin gaba. Tafiyar sa da kusan awa guda kafin Sultan ya dawo dan cewa yayi Rayyan ya more da magen kafin nan ya kawo maganin dan mugunta irin tasa. Cikin rashin sa'a kuma da ya dawo bai tarar da shi ba sunyi sa6ani, hakan ya sa ya 'dauki magen sa ya yiwa Anty Madeena sallama yayi gaba abin sa. Anty kam da idanu ta bishi har ya 6acewa ganin ta, ita dama tun can asali haka nan kawai jinin bai hadu da yaron ba, shiyasa ko lokacin da zai auri Marwa taso hanawa amma tasan duk abinda ta fa'da za a ga kamar dan shi dan tsuntuwa ne shiyasa take kin jinin sa. Baya ga haka ma bata da ikon sawa ko hana abu dangane da su, sai dai in ya zama dole ne ma tana iya bada shawara. Rayyan kam daga gidan Anty Madeena YOUHEAL ya wuce wajen Fawwaz. Shine yayi masa allura yana mitar dama yasan da yanayin sa meyasa zai je inda magen suke. Rayyan yace" arashin sani ne..." Fawwaz bai bar shi ya tafi ba har sai da ya tabbatar zazzafan yanayin ya sauka masa kafin ya barshi tafiya dan cewa yayi driving cikin wannan yanayin is very risk. A hankali yake 'dan jan sa da hira, hirar kuwa bata kowa bace face ta Mufeeda..." Inda ya fara da fa'din" Ya Babyn nan?..ya jikin ta...?" Hakan da ya fa'di ne ya sa Rayyan fahimtar wacce yake tambaya. Idanun sa ya lumshe domin wani karaya ne yaji ya ziyarce shi nan take...har ma ya sashi ji zaman asbitin ya gundure sa. Kusan kowani da'ki'ka tsoro ke sake shigan sa. Tsoron tabbatuwar alaka tsakanin sa da Mufeeda, tsawon lokacin nan batare da yasan cewa jinin sa bace ba. Ji yake bazai iya yafewa kansa ba, bazai iya yafewa kansa abubuwan da sukai ta faruwa abaya ba, ta ya zai iya sake duban idanun yarinyar nan banda tsananin kunyar ta da zai ji...duk da still yana kokonto, yafi bawa ikon Allah ne kawai ya kawo kamar su da yanayin jinin su, but yanayin ta da Nadiar sa ya kan sa yaji tsoro sosai ya kama shi...amma ai a pic din da jami'ai suka nuna masa yaga pic din Nadiya kwance cikin jini da jaririn da ta haifa masa kuma duk sun rasu..toh me yasa alakar su da Mufee ya ha'da da ita, sannan yadda yake jin zuciyar sa a duk lokacin da suke tare da yarinyar is something else. Bai bawa Fawwaz amsa ba dan shi a yanzu bama ya jin harshen sa zai iya dogon magana. Tashi kawai yayi yana 'dagawa Fawwaz hannu yayi gaba. Bai koma office ba kawai ya wuce gida. Nan ma tsaye ya same su kan 'kafafuwan su, mai gadi da sauran ma'aikatan gidan na compound suna jajanta wani batu, domin sa6ani suka yi, ana fita da Amrah zuwa asbiti shi kuma yana shigowa da motar sa. Ji yayi gaba 'daya hankalin sa ya tashi sosai, sharp- sharp ya shiga ya watso ruwa da nufin bin su amma 'kiran sallar maghrib da aka fara shi ya dakatar da shi. Alwala yayi ya fita zuwa masallaci. Sai bayan ya idar da sallah ya komo gida, tun abakin gate ya tambye su asbitin suka ce basu sani ba sai dai a tambayi sauran dake ciki, 6angaren sa ya koma ya 'dauki wayar sa, numbern Ammi yake ta faman 'kira har alokacin amma still bata 'dagawa haka ma na Amrah ba'a 'dagawa sai daga baya ya fahimci ai wayar Amrah ma na nan gida. Sunan asbitin da suke kawai yake so ya tambaya ba komai ba, amma ya rasa samun su, yasan ba lallai ne Ammi tasa akai su YOUHEAL ba indai taga condition din Amran ya haura sosai, bai san ma meyasa basu neme shi a waya ba kafin tafiyar su. Keyn motar sa ya 'dauka ya nufi 6angaren Ammi da zummar ko zai samu amsa daga wajen su. Sai dai nan ma bai tarar da kowa ba Marwa da Ammi duk sun wuce asbitin sai Zaitoon da sauran 'yan aikin gidan kawai. Wata mai aikin ne ta bashi wannan amsar har ya juya sai kuma ya dawo ya bata umarnin 'kira masa Zaitoon 'din. Tare suka dawo Zaitoon na bayan ta...duk jikin ta yayi sanyi da ganin halin da Amrah ta shiga, dama tun 'dazun da Ammi tasa su dubo ta suka fahimci bata jin dadi amma koda Marwa ta tambaye ta cewa tayi bakomai ita lafiyar ta 'kalau, kuma ta tabbata mijin nata ma kafin ya bar gida lafiya kalau ya barta, a hankali bakudar ta taso mata kafin yammacin kuwa har tayi tsanani. Sosai take jin babu da'di musamman da ta tuno abinda ya faru abaya. " Barka da dare Yah.." Ta fa'da da sanyin murya tana yin 'kasa da kanta. " Yauwa..barka dai, ya sunan hospital 'din da Ammi suka je...?" " Wallahi ban sani ba sai dai ka 'kira su..." Ta fa'da cike da ladabi dan bata jin 'kwarin gwiwa yanzun koka'dan. Haushi ma amsar tata ta basa hakan yasa ya juya yana sakin 'karamar tsaki da tunanin tama raina masa hankali, inma 'kiran wayar ne 'karamar 'kwa'kwalwar ta bai bata akan ya 'kira bai same su bane kafin yazo tambayar, ko kuwa tana tunanin ita ta fishi sani abinda ya dace ne. Daf da zai bar parlorn tace " Dan Allah yaushe za'a dawo min da yarinya ta..?" Ta tambaya yanzu ne dan tasan shine ka'dai damar da take da shi. Bayaga yaushe zata ma gansa, tsoro take ji kar tayi shiru ta kyale a kasa kawo mata yarinyar..babu mamaki kuma tana can tana kuka kullum. Cak ya tsaya yana jin wani abu na masa yawo a zuciya, sai lokacin ma ta tunasar da shi kan ga6ar dake gudana cikin rayuwar sa kafin tasowar batun Amrah. Kafar sa 'daya ya 'daga ya juya ta wanda hakan ya bashi damar juyowa ya fuskance ta. Hasken 'dakin dake tarwai shi ya bashi damar 'karewa fuskar ta kallo da kyau. Tsawon mintina biyu yana kallon ta yana kissima abubuwa da dama, sosai yake nazarin ta a zuciyar sa, bai ma ta6a tsayawa yayi mata kallon tsap irin na yau ba. Sosai yayi comparing Mufeeda da Zaitoon, sam kokadan ko alama babu kama ta zahiri da zai bayyana maka cewa akwai ha'din jini tsakanin su...babu shi, sannan yana ma tantamar in yarinyar nan ta kai haihuwa ma, yanayin jiki da zubin ta sam bai nuna alamun haihuwa ko shayarwa tattare da ita ba, ai shi likita ne, he suppose to understand this since from d very moment, amma me yasa be ta6a lura da hakan ko tsawaita tunani ba sai yanzun...me ma yasha kansa ne?. Ya tambayi kansa. A fili kuwa cewa yayi " Wace yarinya kike magana akai haka...?" Ido ta 'dan fitar ta kalle shi sai kuma ta kawar da kai. " Yarinya ta Mufeeda fa wacce ka kaita makaranta jiya ka mance?, kacewa Ammi tana gidan Anty Madeena..." Ta 'karashe maganar idanun ta na tsatstsafo da ruwan hawaye..dagaske fargaba take ji yana shigan ta, dan tambayar tasa ba 'karamin girgiza zuciyar ta yayi ba. " Itan 'diyar ki ce...?" Ya tambaya yana yatsina fuska. " Erh *'YATA CE* " " Waye ya haifa miki ita...?" Zaro idanu tayi tuni hawayen nata sun gangaro, a firgice take kallon sa, wannan wace iriyar tambaya ce haka. Rayyan kam zuba mata idanu kawai yayi yana duban ta da 'kara karantan wasu abubuwa, duk yadda yake jin da'din kallon ta idan tana kuka ko ta shiga ru'dani amma haka kawai yau 'din hankalin sa bai je wajen ba. Ji yake har gara itama, kukan da'di take...shi ji yake kamar yayi ta kwarara ihu ko zai ji saukin dake zuciyar sa, a yanzun hakan nan badan da abu agaban sa ba da babu abinda zai hana shi tsareta ayau 'din nan har sai ta sanar da shi inda ta samo yarinyar duk da har yanzu bashi da tabbacin daga ahalin su ta fito, amma tuni zuciyar sa ta karkata ga hakan...sai dai gaggawa ba nashi bane, dole ne yabi komai a tsanake har zuwa lokacin da zai fahimci gaskiyar lamarin..bayaga haka ma ga batun Amra da halin yanzun yafi komai tsaya masa, akwai lokaci ai in dai da rai kam...time ll reveal everything. Juyawa yayi ya cigaba da tafiyar sa, yayin da Zaitoon ke faman kuka, kuka take sosai ba na wasa ba, ba dan komai ba sai dan tambayar da yayi mata, wace amsa zata bashi toh, me ma yasa yayi mata wannan tambayar...wa yake tunanin zai haifa mata yarinyar, in ma haifa matan akayi ina ruwan sa. Rayyan kam saduda kawai yayi ya nufi YOUHEAL 'din cikin rashin sa'a kuwa basu nan, still yana ta faman gwada 'kiran wayar Ammin kuma ba'a dagawa, yafi zaton cewa wayar na gida ne, ilai kuwa hakan ne. Zaitoon ta shafe kimanin mintina sha biyar tana zaune a wajen tana risgar kuka mai tafe da tsantsan fargaba. Tsoro take ji kar Rayyan ya tono sirrin tane. Sultan ne ya shigo gidan da sallamar sa sai dai ganin Zaitun durkushe anan palor ya sa bai tsaya 'karashe sallamar ba balle ya jira amsawa kawai ya karaso gaban ta shima ya tsugunna. Kan ta a'kasa tana ajiyar zuciya da tunani taji kamar mutum kusa da ita. Da sauri ta 'dago sai kuma taja baya tana kawar da kanta. " Me ya same ki kika zauna anan..? Ina mutanen gidan suke..?" Ido ya dan fitar yana duban fuskar ta, a hankali ya kai hannu a 'ko'karin sa na son lakuto hawayen fuskar ta...da sauri ta kawar da kai tana sake yin baya. " Kuka kike?...ke da waye..? Rayyan ko...? Shiru tayi tana duban sa da mamakin sa. " Fa'da min wabda ya saki kuka koma uban waye zaki ga matakin da zan 'dauka akansa, ba Rayyan ba ko ma uban Rayyan ne da kansa zaki gani dan na lura shine kadai ciwon idanun ki cikin gidan nan na gaji da ganin hawayen ki kan wan banza can...?" Ido sosai Zaitoon ta fitar tuni ma ta nemi kukan ta ta rasa...bakin ta har na rawa tace da Sultan..." Yayan naka...?" Idanu ya rintse ya kuma bude su akanta yana mi'kewa tsaye..kansa ya 'dan jijjiga" I'm sorry raina ne ya 6aci, bana son kowa ya dinga takuraki ne.." Sosai ta gaji da wanzuwar sa a wurin banda ma damuwar Mufeeda dake damun ta ga ta Amrah ga kuma shima yana cikata da wasu maganganun da ba gane kansu take ba illa 'kara sata cikin ru'dani da yake. " Amrah na asbiti sun tafi da Ammi da Marwa..." Ta bashi amsa tana mikewa tsayen itama. A firgice ya dube ta..." Tun yaushe?" Tace" Kafin Maghrib...". " Shine babu wanda ya fa'da min...?" " Ina jin basu fa'dawa kowa ba ma dan shima mijin nata nan yazo yake tambayar inda suke...". Batare da sake fadin komai ba kawai Sultan ya juya ya fita da sauri. Motar sa ya shiga ya tada ta ya bar gidan da wani irin gudu tamkar mai amsa 'kiran shiga aljanna...bashi da lokacin 6atawa a yanzu..dan Rayyan, gudan jinin Rayyan na shirin fa'dowa dunia ina yaga natsuwa...in da hali a yau ba sai gobe ba yake so yaron ya koma inda ya fito. Wani asbiti dake nan kusa da unguwar su ya fara dubawa, cikin sa'a kuwa ya tarar nan suke sai dai koda yaje ya samu ne Amrah na cikin mawuyacin yanayi da suke tunanin sai ma an mata C.S, hankalin su duk tashi yayi, illa Sultan ne mai 'kara musu 'kwarin gwiwa. Ammi ce ta bawa Sultan umarnin 'kiran Rayyan ya sanar da shi nan yace dasu su tattaro su taho YOUHEAL shima yana can. Kafin isowar su an gama harha'da komai da za'a bu'kata na kar6ar haihuwa. Da isowar su aka 'doro Amrah kan gadon 'daukan marassa lafiya akayi 'dakin haihuwa da ita. Rayyan da kansa ya kar6i haihuwar duk da yake shima ba da'di yake ji ba amma he have to do this dan baiso ai mata wani C.S sam. Dai-dai fitowar yaron shima zafin jiki da ciwon kai suka so kayar da shi. Nurse 'din dake tare da shi ce ta ro'ki yaje ya huta kawai zata 'karasar da komai. Office 'dinsa dake hospital 'din yaje ya kishingida cikin kujera, gaba 'daya haka kawai yake jin zuciyar sa babu da'di, kamata yayi ace yau 'din cikin tsananin farin ciki yake da samun 'karuwar 'da da abinda ya dade yana muradi, kai ba ma shi kadai kaf zuri'ar su basu da burin da ya wuce wannan, amma sai gashi sa6anin hakan ta kasance gareshi..cunkushe yake jin zuciyar sa babu dadi. Rasa ma wani tunani ma zai yi ma yayi, Mufeeda, Zaitoon Amra ko kuma new Babyn sa..". Tsaf Nurse ta shirya Babyn sannan ta mi'kawa Amrah shi fuskar ta cike da yalwar fatin ciki, Amra kuwa duk tayi zuru zuru sbd tsananin na'kudar da tasha, sai dai duk da zafin na'kudar Babyn na fita taji kamar an cire mata 'kaya ne. Numfashi ta ringa sau'kewa karshe ma da aka gama komai zaune ta tashi har zuwa lokacin da Nurse ta mi'ka mata baby tana congratulating 'din ta.... Fuskar Amrah wadace da murmushi ta kar6i Babyn tana sau'ke idanu kan fuskar shi, tamkar yayewar iska haka fara'ar dake fuskar tata ta kau, ba 'karamin girgiza zuciyar ta tayi ba, ta rufe ido ta kuma bu'dewa fin sau ashirin domin sake tabbatarwa amma still abu 'daya take gani ya kasa canzawa...hawaye kawai taji ya zubo mata wanda direct ya 'diga bisa goshin yaron. hakan kuwa yashi motsawa..... A fili ta furta _Innalillahi wa inna ilaihiraji'un...._ *Masoyiyar Sultan how market....?*🥳 Salmerh😘 [30/10/2022, 1:39 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* Wattpad@ Serlmerh-md 🅿️ *...63* ........ _Innalillahi wa inna ilaihi raji'un...._ Sai da ta maimaita har sau uku kafin wani kuka ya 'kwace mata mai 'karfin gaske, hawayen Amrah kasa tsayawa yayi kawai ta kwantar da babyn kusa da ita, meyasa zai mata haka?, meyasa Sultan zai mata haka? Dama dakon cikin sa tayi batare da ta sani ba, dama dakon cikin 'dan da bana Rayyan ta yi ba? Kuka sosai take sai dai cikin kukan take fatan kamar yadda taga fuskar yaron nan ita ka'dai har ta fahimci bashi da ala'ka da Rayyan Allah yasa har abada ya kasance ita ka'dai 'din Allah zai bawa damar ganin kamannin sa, tun daga can cikin zuciyar ta kukan ke tasowa, sosai jikin Nurse yayi sanyi, kasa cigaba da aikin da ke gaban ta tayi ta tsurawa Amrah idanu, sai ma ta rasa da wani kalma zata fara yi mata magana. Kusa da ita ta matsa daf tasa hannu ta 'dauke yaron daga kusa da Amrah ta maida shi gefe can inda ake saka jarirai ta kwantar da shi sannan da mugun sanyin jiki ta dawo ga Amrah ta 'dan dafa kafa'dar ta..." Haba Hajia, wannan kukan naki zai iya kawo illa ga lafiyar ki fa, dan Allah kiyi hakuri ki bar kukan nan, ke da ya kamata ace kinfi kowa farin ciki da kyautar da Allah ya baki sannan ya baki dama kika haifo 'danki lafia, shi lafiya kema da lafiyar ki meyasa kuma kike 'ko'karin saka masa da butulci irin wannan....?" Kai Amrah ke faman juyawa hagu da dama, " Ki barni nayi kuka dan Allah, ki barni nayi kuka na, dan sam bani da mafita ban san yadda zanyi ba..." Hannu duk biyu ta ha'de tana kallon Nurse hawaye na bin fuskar ta ta fara fa'din..." Nurse dan Allah ki taimake ni, ki sanar da ni taya zan cire kaina, nasan babu wanda zai sake yadda dani a halin yanzu kafin hakan ma bansan ta yadda zan fuskanci kowa ba harda mijina, _wallahi yaron nan ba 'dan Rayyan bane na Sultan ne, ki fa'da min yanzu ya zanyi kenan kowa idan ya ga Babyn zai gane na waye ne...?"_ Ido Nurse ta zaro sosai tana duban Amrah..." Ban fahimce ki ba Madam..kina nufin wannan babyn ba na Dr Rayyan bane...shi waye Sultan kuma...?" " Kanin sa ne, kani yake a wajen sa..." Ta bata amsa da sauri. " Ohh 'kanin sa..? Lallai... _wannan shine matar me gida ta haifi 'dan maigadin gida_ Nurse ta furta cikin zuciyar ta ta jinjina kai..ji wani al'amari. "..to ke me ya kaiki wannan danyen aikin? Ko ba Sultan wannan daya kawo kun ba..? Haba 'yar uwa, dubi Dr Rayyan fisabilillahi, dubi kyan zubi da tsarin halittar sa banda baiwa kala kala da Allah ya bashi amma har wani namijin banza da be kama 'kafar sa a komai bane zai ru'de ki....?" " Wallahi nima sai yanzu naga rashin kyautawa ta, yanzu ne na fahimci kuskuren da nayi ta aikatawa abaya, for now mafita kawai nake bu'kata daga gareki ta yadda babu wanda zai gane kamar yaron tashin farko.." Baki Nurse ta kya6e" ni dai babu wata hanya da na sani..amma tunda 'yan uwa suke ai babu wata matsala, zai kasance ne tamkar kawai yaron ya 'dakko kamannin 'kanin mahaifin sa ne..." " Ke akwai fa matsala babba ma kuwa, that it'snt possible hakan ya faru.." " As in..?" " Babu wata ala'kar jini fa tsakanin su kawai sunan 'kani yake amsawa a wajen sa..." " Toh kawai ki masge karki nuna damuwar ki ma balle wani ya fahimci halin da kike ciki, idan babu wanda ke zargin ki dama can toh babu wanda zai fahimta...." " Ina jin tsoro...." " Kar ki damu babu abinda zai faru da iznin Allah, amma a ringa kiyaye dokokin Allah musamman in ya kasance da aure akanki hukuncin ba 'daya bane, kuma idan ka daure ranka nawa ma rayuwar take jindadin nan duniyar fa bai ko kama 'kafar can ba....." Duk maganganun da suka tattauna a kunnan Dr Fawwaz ne, dan yazo 'daukan yaron yaron dan kaishi ai masa kaciya yaji abinda yaso rikitar da shi, da 'kyar ya iya daurewa ya basar kamar bai ji komai ba. Bashi da tantama na neman Hujja ko wani abin daban tunda da kunnuwan sa yaji Amrah da bakin ta take fa'da 'karshen shaida kenan. Ji yayi ko 'kaunar ganin Amran bai yi hakan yasa yasa shi juyawa ya fita da niyyar fasa shiga dakin, amma tuno Rayyan abokin sa ya sanyashi dakatawa, yanzun nan rabuwar su a masallaci da shi ya kuma fahimci kwata- kwata ba cikin yanayi mai da'di yake ba, Rayyan wani sa'in na bashi tausayi matu'ka, sbd yadda abubuwa marasa da'di ke yawan yi masa 'kawanya, sai dai yasan duk jarrabawa ce ta ubangiji kuma bayin sa da yake so.yake jarabta masu hakuri kadai ke iya jurewa su cinye jarrabawar su. Shi ma bai ma san yau 'din me ya hana shi tafia gida ba, shi da yake aikin rana ashe rabon jin wannan zance ne.... Komawa baya yayi ya durfafi ke6antaccen 'dakin da Amran take, yayin da yake jin duk wani step da 'kafar sa ke yi yana tafiya ne da bugun zuciyar sa, sosai ya ji ya tsani Amrah ko kallon inda take baya 'kaunar yayi bisa ga cin amanar aure da ta yiwa abokin sa..me za'ayi da mace ballagaza irin wannan. Koda ya 'kwan'kwasa 'kofar bai shiga ba sai da Nurse ta bada iznin shigowa sannan ya shiga, duk da yake ba rufe 'kofar take ba amma hakan ya zam masa tamkar al'ada ne. Kamata yayi da shigan sa Amrah zai fara yiwa ya jiki amma gaba 'daya sai yaji harshan sa yayi masa nauyi. 'Dauko yaron yayi yana sake duban fuskar sa da kyau tabbas babu 'karya cikin abinda kunnuwan sa suka jiye masa..tunda har ita Amrah da ta aikata tasan cewa 'dan bana Rayyan bane toh wa ya isa ya 'karyata...ban dama kammanin Sultan da suka fito 6aro6aro a fuskar yaron. A hankali ya 'dago idanu ya dubi Amrah dan yadda yake ji idanuwa na masa yawo ajiki yasa dole sai ya 'dago din...caraf kuwa idanun su suka sar'ke da na Amra ta wani yi zuru- zuru da ita da yake tsarge take. Murmushin takaici ne ya 'kwace masa da ya bayyana kan fuskar sa. Amrah da bata fahimci na.m takaici bane sai itama ta 'dan saki ranta..." Madam ya jikin..Allah ya raya mana.Baby da imani..." Yayi 'karfin halin fa'da. Amrah tace" Amin Dr...jiki kuma Alhamdulillah..." Bai sake magana ba illah kai daya ka'da yayi gaba abinsa batare da ya sake duban inda take ba. Wani ajiyar zucia ta sau'ke mai sauti. Nurse ma wajen tayi. Dr Fawwaz ne yayi wa su Ammi bayanin abinda aka samu da kuma dacen lafiyar duk jaririn da mai jegon ya kuma ce zasu iya shiga su duba ta. Sun kuwa nuna tsantsan farin cikin su a fili. Barin ma Marwa da nata ya kasa 6oyuwa, Ammi ce dai cikin zuciyar ta kawai take nuna godiyar ta ga mahallici yayin da Sultan ya tsaya 'kyam zuciyar sa na yi masa tu'kuki tamkar wuta ke ci a 'kirjin.sa. Kuma sam ya rasa ta ina ma zai fara gudanar da shirin sa, ganin nan 'din duk abokan huldar Rayyan, ya sansu sun kuma sanshi so bayi da damar shigar da bu'katar sa garesu koda kuwa nawa zai ajiye musu. Bai ga alamunnasarar sa tattare da su ba dole ne sai dai ya sake.shiri. Idanu ya lumshe ya kuma bu'de su yana mai juya bayan sa. Hakika yau 'din ranar ba'kin cikin sane, ya ma rasa sam meya sha kansa da har ya bari cikin Amrah yayi 'kwari batare da ya salwantar da shi yabi rariya ba...gashi yana shirin zame masa barazana ga ayyukan sa. Tuni Marwa da Ammi sun shiga duba jikin Amrah kuma Alhamdulillah yadda suka ganta zaune tankarkar ya sanya su fahimtar zancen Dr Fawwaz gaskiya ne jikin nata da sauki. Kafin adawo da babyn sai da akai masa wankan sa tass haka itama Amrah tuni an kawo mata ruwan zafi tayi wanka, da yake dokar asbitin ce haka, mai jego bata komawa gida batare da an gama tsaftace su ba amma duk cikin ku'din aikin kane suke wannan hidimar, ire iren wa'dannan hidindimun ya sanya YOUHEAL yayi fice wajen tsada, duk wanda ya shirya zuwa asbitin toh sai yayi tanadin kudi. Basu koma gida ba har sai washegari kuma har zuwa lokacin banda su Ammi Rayyan kam bai samu lokacin ganin jaririn da kyau ba sbd rashin kuzari shima da ya ziyarce shi da tsinkan zuciya. Sultan kam da ganin yaron sosai zuciyar sa ta tsinke, ya 'dan ja baya" kama dani yake.." Ya fa'da cikin ransa. Wani kallo ya bugawa Amrah da shi da ita ka'dai suka san ma'anar sa ransa a matu'kar ha'de. Ta ya zata 'dauki cikin sa har ta haife batare da ya ma sani ba ne,, lallai Amra ta gama raina masa wayo, taya zata 6oye masa cewa cikin nasa ne ma, tonuwar asirin sa take son gani ko kuwa mene. Sultan ne ya dawo da su gida wanda daga ajiye su ya sake juyawa da motar ya koma gidan sa ko takan Marwa bai bi. Ammi da Marwa kam babu ruwan su sai hada- hada suke an haifa musu yaro babu wanda ma yabi ta kan kamannin sa dayake ba kowa ke gane kamannin jariri ba sai sa'idinawa...🤭 [ wasa nk 😜] Sai da aka shirya yaron tsab cikin kayan sa masu matukar kyau da 'daukan hankali kafin Marwa ta 'dauke shi a waya ta sanya shi a status. Rayyan ma sai a lokacin ya fito daga 'dakin sa, lokacin su mummyn Amra ma tuni sun iso sai dai kowa idan yazo ya ga yanayin Amrah dake komai cikin sanyi sai suji tausayin ta sosai, da yawa na tunanin ko zafin naku'da ne ya sata yin sanyi Mummyn ta kuwa cikin ranta tace indai wahalar da tasha ne ya maida ta hakan ba lallai ne ta sake haihuwar ba gaskia tunda ta samu 'daya, ai suma ita ka'dai suka haifa, da me hakan ya rage su? Tace akan haihuwa bazata zauna a maida mata 'diya so depressed tana kallo ba. Rayyan kam" masha Allah". kawai yace ko da ya amshi jaririn nasa, zuciyar sa cike da farin ciki ya ri'ke shi, nan yai masa duk abinda ya dace ya kuma yi masa 'kiran salla da suna a kunnen sa. 'Karshe addu'o'i yayi zabga masa cikin kunne fuska dama ilahirin jikin sa gaba 'daya. Amrah kuwa duk lokacin da ta ga Rayyan ta kuma kalli jaririn nata sai taji ga6o6in ta sun yi sanyi, bata ta6a nadamar abubuwan da tai ta aikatawa ba irin ranar nan. Ammi na can ta hakimce a palourn ta sai bin contact 'din ta take tana kiran 'yan uwa da abokan ar'ziki layi- layi tana sanar da su 'karuwar da suka samu. Su Zaitun ne ke ta hada- hadar ha'da abinci a 6angaren mai jegon amma har a lokacin basu samu ganin jaririn ba. Sai.da suka gam ha'da pepper soup na mai jego, Zaitoon ta 'dauka bayan an ha'da komai dan ta kai mata nan tarar da Marwa zaune gefe da jaririn Amrah kuma na bathroom. Tana murmushi ta matsa kusa da shi tana bu'de fuskar sa dake lullu6e cikin mayafin sa sky blue mai 'dankaren laushi. Sosai taji komai na Babyn ya birge ta, haka.l kawai sai taji 'kwalla na shirin zubo.mata tuno.tata 'diyar lokacin tana kamar hakan bata samu.wannan gatan ba. A hankali ta janye lullu6in yaron" Tabarakallah masha Allah..." Zaitoon tace tana murmushi a hankali banda Marwa ka'dai ma dake kusa da ita babu wanda zai ji me tace tamkar da jiririn take magana ko kuma ita ka'dai. Marwa da ke faman danna waya ne ta 'dan dube ta. " A a 'dauke shi mana kema ki sa masa albarka, kya wani tsaya tamkar me tsoron 'daga shi....." Ai kuwa kamar jira take ta 'dauke shi cak ajikin ta tana sake tuno wasu lokutan can baya da take mugun son 'daukan jinjiri. " Masha Allah...yaron nan ba dai haske ba kam kamar Mufee na lokacin tana 'karama itama sai kin ganta..." Murmushi Marwa tayi..." Ba dole ba, ya 'dauko uwar sa ce kinsan Matar Yayah ba dai haske ba ga shima Yah Rayyan 'din ba laifi...". Sake kallon fuskar sa Zaitoon tayi tace " Hakane...amma sai ya'ki 'dauko kamannin ko guda daga cikin su..." Marwa tana daria tace kamar taki 'diyar har lau...dan Mufeeda koka'dan itama bata 'dauko ki ba..." " ai kuwa...itama kam hakane...amma wannan da mijin ki yake kama wallahi..." " Wa wai? yah Sultan ko..ashe ba ni ka'dai nake 'dan ganin kamar ba, yaron nan ko kara ni bai min ba ya tsallake ni ya wani 'dauko Yah Sultan dan iyayi...". Dukkan su daria suka yi dai- dai lokacin da Amrah ta fito a bathroom. Harara ta bankawa Zaitoon sanin da tayi itace ta 'dauko zancen dan suna tare da Marwa tun jiya har yau bata kawo ko makamancin hakan ba sai yanzu da zuwan Zaitunan. " Malama da Allah ajiye min yaro kiyi gaba bana son munafurci..." Ido Marwa ta zaro" haba Anty Amrah...hira fa muke na me zaki kore ta...ai gara ki koramu tare yafi sai in san cewa baki son ana zuwa inda kike. " 'Kyaleta taje tayi aikin ta Marwa...nan taga akwai sa'an yin tane komene..ni bana son munafurci da kinbibi irin na 'yan aikin nan, garin haka har a cinye ma kurwar yaro..." " Ashe da muma bamu kawo wannan bigiren ba indai hakane kuwa.." Marwa ta bata amsa da 'dan 6acin rai saman fuksar ta Zaitoon kam ajiye yaron tayi ta tashi tayi waje zuciyar ta cike fal da mamakin Amra wani kinbibi ko munafurcin me tayi ita kuma..?" Kafin 'kiran Ammi ya isa kan Anty Madeena a whatsapp Status 'din Marwa Anty Madeena taga Pics 'din Baby, 'kasan pic 'din ta rubuta _it's a boy_ da blue hrt ajiki, 'dayan kuma tasa _Welcome to the world my luv_ ta kuwa tambayi Marwa Babyn waye...?" Marwa tace" Matar Yah Rayyan ce ta haihu jiya...nama tura miki ai." Anty tace " Erh ban duba private messages 'dina bane...inaga shiyasa ban gani ba..." " Amma Matar Rayyan Tta haihu ko kuma matar Sultan..?" " Anty Yah Sultan kuma? Kin mance ni ka'dai ce matar sa..?" "Gani nayi Babyn kammanin sa ne sak ai shiyasa..." 'Yar daria Marwa tayi tana fa'din" Yanzu ma muka gama maganar da Zaitoon ai, iyayi ya kaisa 'dauko kamannin Yah Sultan 'din ba komai ba kalan dangi ne..." Marwa na daria sosai ta fa'di haka. " Hmm..bari sai zuwa yamma zan shigo, Allah ya raya mana bisa tafarkin muslunci..." " Ameen Anty.." " Anty Dan Allah in zaki zo ki taho mana da Moopy mana, wlh we missed her ba 'dan ka'dan ba.." " a a ba yau ba kam gaskia." " Kai Anty pls mana, daga baki ajiya kawai sai a mallake mana ita kuma..." Emojin daria kawai Anty Madeena ta tura mata bata sake fa'din komai ba. Koda Anty Madeena tazo anan ta sake tabbartawa idanun ta kammanin yaron, suna ta dariya ita da Ammi suna zungurin kansa suke cewa" _dan nema....iyayi inji Marwa.."._ Sultan kam sosai ya 'dauke 'kafar sa a gidan sbd karma a yawaita ganin sa har a fara zargin wani abu, tuni kuma ya fara tunanin mafita. Ranar suna yaro yaci suna Muhammad amma suna 'kiran sa da [ Arfan..] Ansha Shagalin suna sosai dan ba 'kananun ku'di Rayyan ya kashe wajen sunan Arfan ba. Sosai ya bu'de bakin aljihu akasha shagali aka ci mai kyau komai san barka. Rayyan hana Amrah zuwa gida yayi yace babu inda za'aje mai da yaro, nan ma ai gida ne tunda ga Ammi ga su Marwa ga kuma ma'aikata duk wani kula da take bu'kata zata same shi. Duk yadda Amrah tayi ta samu damar tafia abin gagarar ta yayi. Dan Rayyan yace sam. Ita kuwa tafi so ta dan yi nesa da su sbd zata fi samun natsuwa, har a yanzun kawai gatan nan ne amma sam bata iya sakewa sai ta tajin fargaba kamar kowa yasan yaron bana Rayyan bane. Ma'aikatan office 'din Rayyan na Infinity sun zo sun gaida mai jego sun kuma taya Rayyan samun 'karuwa da ya samu da kyaututtukan su masu 'dumbin yawa ga jariri da mahaifiyar sa, haka ma abokan aikin sa na Youheal amma banda Dr Fawwaz, dan cewa yayi bashi da lokacin 6atawa wajen wannan shirmen. Takaici ke cika shi sosai da sosai a duk lokacin da maganganun Amrah suka dawo masa cikin tsananin 6acin yake tsintan kansa a duk lokacin da ya tuno wannan cin amana da Sultan da Amrah suka yi ma abokin sa...amma bai san ta ina zai fara yiwa Rayyan bayani ba ta yadda zai fahimce shi cikin sauki. Baya son ya bar abokin sa cikin duhu kan wannan lamari...kamar yadda baya so ya saka rai sosai akan yaron alhali ba mallakin sa bane..in kuwa hakane koda yanzu asirin ya rufu har yaro ya girma da sunan nashi dole watan watarana sai an tona, may be a lokacin da zai fi bu'katan yaron, may be a lokacin tonawar zata fi yi masa ciwo fiye da yanzu..tunda shi ya sani, Amrah ta sani, Nurse Muneera ta sani, shi kansa Sultan 'din yasan ya sani...zai yi wahala maganar ta rayu da sunan sirri. Sbd ya ankarar da shi Rayyan 'din ma ma somtimes idan suna waya sai ya tambaye shi" Ina mai kama da 'kanin baban shi..?" Amma Rayyan sai dai yayi daria kawai bai ta6a jin wani abu game da hakan ba wasa ya 'dau batun...dan shi zuciyar sa 'daya yake zaune da kowa...bai fiye kawo munanan abubuwa cikin tunanin sa tsakanin sa da makusantan sa ba. 'Karshe Rayyan tun baya bada hankali kan batun har wataran ya tambayi Fawwaz cewa wai dagaske da Sultan yaron nan ke kama?" " Kana nufin kai baka ga kamar ba dama..?" Fawwaz ya sake jefa masa wata tambayar. " Ina 'dan gani dai ka'dan amma kasan yara na canza kamanni time to time har sai sunyi wayo kake ganin standard kamannin da suka dauk..". " Toh kai da dawa yake ma kama..?" Baki ya kyabe..." Har yaushe zan tsaya wannan tunanin, ni dai ba Allah ya azurta ni da abinda na jima ina nema ba, banda gode masa me zan bata wa kaina lokaci ina yi kuma......" Fawwaz cikin ransa yace" Allah ya azurta masu shi da samun sa dai..."! Rayyan.kuwa cigaba yayi da fa'din...".Amrah dai tace da Yah Kabeer yake kama wai..." " Yah Kabeer kuma..wani Yah Kabeer 'din..?" Inji Fawwaz ya tambaya da mamaki. " Yah Kabeer dai daka sani Kabeer Sa'ad Auta.." Rayyan fa fa'da yana 'yar murmushi. Fawwaz yana jinjina kai yace " Lallai...wannan makirar ta iya ninke ka a baibai..." Bakin Fawwaz ya su6ce wajen fa'din hakan. A zuciyar sa yaso yin maganar amma sai da ta fito. " Rayyan yace me kace...?" " Babu, ni dai Allah ya sani bazan iya ri'kewa a raina ba, idan ka samu time mu ha'du dan Allah zamu yi wata magana." " Ok.." Salmerh😘 [31/10/2022, 7:48 am] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Wattpad@* *Serlmerh-md* 🅿️ *...64* .......Duk wannan bidiri kuwa da akayi ba'a kawowa Zaitoon yarinyar ta ba dan Anty Madeena cewa tayi sai sun gama bincike tukunna. Dole Zaitoon ta ke 'dan ya'ke bata bayyana damuwar ta sosai kan rashin Mufeen kusa da ita sai dai in sun ke6e da Marwa ta kan 'dan jajanta tayi tayi da Marwa suje gidan Anty ko gano yarinyar ne ma tayi amma Marwa sam taki, amma Ammi tuni ta gano damuwar da take faman 6oyewa. Ayyukan da suka sha kanta ne a 6angaren Amrah ya sanya ko zama bata fiya yi sosai ba balle su tattauna da Ammi. 'Bangaren babu kowa sai ita ka'dai, Rayyan office Amrah kuwa na 'daki da jaririn ta, wankin kayan yaron da ta tattaro bayan sun bushe ta ninke ta shigo da shi 6angaren Amran sai dai kafin shigar ta ta fara jiyo tashin hayaniya, idan kunnuwan ta basu yi mata 'karya ba kuwa sautin muryar Sultan ne..." Har kin isa ki mumafurce ni Amrah, ta ya ma zaki haifi 'dan da kika san nawa ne bana Rayyan ba salon kowa yasan sirrina dake 6oye ko me..ki fayda min manufar ki kan hakan..." Ya 'karasa tsawace. Cikin kwantar da murya Amrah tace " Toh kai ban da abinka Sulty taya zan san cikin naka ne ko nashi? tunda ba ke6e lokacin tarayya da ku duk biyun nayi ba, dan na fita da kai bani da hujjar da zan hana shi hakkin sa idan ya bu'kata, toh in hakane kuwa taya zan iya bambance lokacin da nasamu cikin da kuma mamallakin sa? kaga dan Allah ka daina min ihu aka, ka barni ma da damuwar da nake ciki, kullum cikin fargaba nake kwana nk kuma tashi tsorona in aka gano wannan dan bana Rayyan bane nasan na ka'de ne har ganye na aure na da kyar ne ya cigaba da wanzuwa dan.nasan halin Rayyan sannan Daddy na kashe ni zai yi...kai kuma fa, iyaka Rayyan yayi fushi da kaine kuma nasan zai sakko da zarar ka bashi ha'kuri kace masa sharrin shai'dan ne ko Ammi bana tunanin zata iya juya ma baya balle matar ka, yanzu waye kk ganin zai fi cutuwa tsakanin ni da kai? har gara kaima damuwar ka ka'dan ce wlh..bazaka ta6a fahimtar halin da nake ciki ba a yanzu..." " Ke ba dogon sharhi nazo ji a wajen ki ba, nazo ne in shaida miki cewar ba fa zan iya 'kyale yaron nan ya cigaba da rayuwa ba, ina son abuna amma rufuwar sirrina ya fiye min komai...dole ne a salwantar da rayuwar sa indai kina son zaman lafia..." Tsaye Amrah ta mi'ke tace" wannan ne kuma baka isa ba Sultan...duk yadda nake jina cikin damuwa amma wallahi ina 'kaunar yaro na, shin ka tayani rainon cikin sa ne ko kuwa kaine kai min na'kudar haihuwar sa, kasan irin wahalar da nasha taya za'ai kace wani a salwantar da shi ka sani ko har abada babu me ganewa hk kawai ka raba ni da yarona a banza...a a wlh...wa ma ya sani ko shi kadai ne haihuwar da zanyi a dunia..." " Zamu gani ai...". Ya fa'da gami da juyawa. Amrah tace " 'Dan Halak ka fasa..". Zaitoon ma saurin juyawa tayi ta 6uya abayan pillar dinning zuciyar ta na harbawa. Ban da salallami babu abinda take. In dai abinda kunnuwan ta suka jiye mata dai- dai ne kenan Muhammad Arfan ba 'dan Rayyan bane na Sultan ne. Amma abinda ta kasa fahimta shine shin Amrah da auren nata take ke6ewa da wani mijin ko kuwa ya lamari ya kene...Yah ilahi. Ashe idanun ta ba 'karya sukai mata ba da suke hango kamannin Sultan tattare da jaririn. Fata take abinda taji ya kasance mafarki ne ba gaskia ba...dan babu wanda zai ji wannan batu batare da girgiza ba. Babu wanda yasan taji hatta Marwa kuwa, dan cikin ranta ta ri'ke shi tana fatan ya kasance ba gaskiya bane. Tausayin Ammi take ji sosai, yadda take so da 'kaunar yaron nan, take kaffa- kaffa da shi ya zata ji duk ranar da ta san cewa ba jinin Rayyan 'din ta bane...tasan sai tafi kowa shiga tashin hankali. Yah Rabb Rayyan fa, ya zaiji idan zamcen ya riske shi, tsananin tausayin su take ji matu'ka. Anty Raihana ma fa sai shekaran jiya ta koma tun bayan haihuwa da tazo, kuma ta fahimci irin 'kauna da suke nuna wa yaron ko kuka sun tsani suji yana yi. Sau tari tsakanin Amrah da yaron sai dai shayarwa amma wajen su Ammi yake yini, koda kaje gidan yana 6angaren Ammi. Bassam 'din Anty Raihana kam ma cewa yayi shi dai bazai tafi ba lallai- lallai sai dai su koma da yaron da 'kyar aka shawo kanshi suka tafi yana kuka. Ranar da ya cika kwanaki tara da haihuwa Rayyan da kansa ya kaisu Youheal Allura da tunanin maganar da Fawwaz yace zasu yi, anan ne Fawwaz ya samu daman ke6ewa da shi..Ya so ya fito kai tsaye ya bayyana masa halin da ake ciki amma 6acin ransa yake gudu, bayaga haka ma bai san 'karshe yanayin da Rayyan zai kar6i zancen ba shiyasa bai yi hakan ba. Sai 'karya ya yiwa Rayyan da cewar an kawo sabon tsarin birth certificate yanzu kuma da shi suke amfani...kuma ba'a cirewa Arfan nasa ba dan haka ranar da suka shirya yi masa birth certificate din sai suzo shi da matar sa, akwai test akwai kuma sign da zasu yi. Da mamaki Rayyan yake duban sa..." yaushe aka samo wannan tsarin kuma..?" Inji Rayyan dake duban sa. Fwwaz yace " Just recently, bamu ma fara amfani da tsarin sosai ba but da yake tsari ne mai kyau that's why i prefer it than na baya, sai kuma naga dacewar mu fara a kanka..." " Amma bani da labari..." " ba lallai ka sani ba ai, tunda sai ka ga dama kake lekomu..." Fawwaz ya karasa yana murmushi. " Toh why not ayi yau 'din kawai, tunda gamu gaba 'daya.." " a a ba lallai sai yau ba if kun shirya kawai kai min magana...sai kuzo.." " a a ayi yau 'din tunda gamu zan iya.mantawa ma kasan aiki na min yawa yanzu..." " Hakane..toh bismillah...muke ko" Fawwaz ya fada yana mikewa tsaye. Cikin ransa yake fatan Allah yasa komai ya tafi masa a tsari kamar yadda ya faro. Lab Fawwaz ya kaisu aka ja jinin su da na yaron da Amrah da Fawwaz yayi basaja da ita kawai. Cikin gaggawa akayi aikin aka fitar da sakamako, a shirin Fawwaz cewa yayi da details 'din kan test result din za a cike birth certificate din. Rayyan kam tuni ya fara mitar shi fa ya gaji, wannan tsarin yayi tsauri da yawa. Ko da aka kawo result din hannun Rayyan aka damka su, Nurse da ta kawo bata wani 6ata lkc ba tayi waje abinta. Bi yayi ya karanta amma tamkar ba likita ba gaba 'daya sai ya kasa fahimtar komai, ya karanta duk biyu ya kai sau uku amma still kansa ya kasa bashi abinda yake dai- dai. Gani yake tamkar idanun sa ba daidai suke gane masa ba. " Fawwaz wai me nake gani haka ne..?" Yayi maganar yana mi'kawa Fawwaz papers din fuskar sa a yamutse. Kar6a Fawwaz yayi shima ya duba ya kuwa saki hamdala cikin zuciyar sa dama burin sa kawai shine ace komai ya zo 'karshe Rayyan ya fahimta..sai kuwa gashi cikin sauki abin ke tafia. " Toh ranka ya da'de aboki na Malam Rayyan, sakamakon fa nunawa yayi cewar babu ala'kar jini tsakanin ka da sabon jaririn ka....." " Ya isa da Allah Fawwaz, wannan wace iriyar magana ce....taya ma za'ai hkn ya kasance? su ma'aikatan lab din makafi ne ko kuwa menene da zasu canza mana sample da muka bayar...?" Baya Fawwaz yayi ya jingina da kujerar sa yana sakin huci mai zafi... " Amma dai kai kanka shaida ne bamu ta6a samun matsala irin wannan ba a wannan hospital 'din ko..?" " Shine a kaina za'a fara samu...? Yayi maganar yana mi'kewa tsaye cike da zafin rai. " Ina kuma zaka...?" Fawwaz ma dake mi'kewan ya tambaye sa da mamaki. " Lab din zanje inji dalilin su na yin haka..." Yayi maganar batare da ya dakata da tafiya ba. Bayan sa Fawwaz ya bi da hanzari yana ro'kon sa kan ya dakata amma Rayyan ko kula sa bai yi ba tamkar ba dashi yake magana ba. " Dr Rayyan kayi ha'kuri mana, in Test 'din ne baka yadda da shi ba sai mu sake yi da kan mu ni da kai ai zamu fi tabbatarwa...kuma zuciyar ka zata fita a wasi wasi. Hakan kuwa akayi sabon gwaji suka sake Fawwaz da kansa yaja jini shi da Rayyan sukayi aikin sai dai tuni akalar test din ya sauya salo daga birth certificate zuwa na DNA test 'karara. Koda sakamako ya fito ya zam exactly kamar na farkon ne babu kuskure ko guda. Tsaye Fawwaz ya mi'ke " Ai dama na fa'da maka, komin mu na tafia ne bisa tsari, ina tabbatar maka da cewar babu kuskure cikin wancan sakamakon tamkar dai yadda nasan baka ga alamun kuskure cikin wannan ba..." " Fawwaz kasan me kake fa'da kuwa, dubi fa kaga abinda sakamakon nan ke fa'di shine babu kuskuren?.. ana maganar Arfan ba jini ba ne kake cewa babu kuskure...? " Tabbas kuwa.." Fawwaz ya tabbatar masa. " Toh na waye...?" Rayyan ya tambaya cike da mamaki. " Mu koma office first..." Cewar Fawwaz yana juyawa. Amrah dake nan cikin sauran Nurses suna hira har ta gaji da zama bata kuma san me ya ri'ke Rayyan har haka ba...kaddai patient ya tsaya dubawa ya barsu yashe a reception sai faman 'diban jinin su ake babu 'kakkautawa. Ko dai yau aikin likitacin nasa ya tashi masa ne akan su...?" ( Mace ki jira dai madam zaki ga aikin likitanci). Koda suka koma office Fawwaz zama yayi bisa kujerar sa, haka ma Rayyan yana duban sa. " Fawwaz plz tell me me ka sani akaina kake 6oye min, I can see something in ur eyes that worth bcuz birth certificate kawai ake wannan abin but somthing else, which I did'nt know..pls tell me ka cire ni a duhun da ka sani...." Tsaye Fawwaz ya mi'ke ya nufi jikin window yana mai cusa hannayen sa duk biyu cikin aljihun wandon sa. " Yes Rayyan i owe u these...Hakika na san wani abu akan ka Rayyan, but nasan ba lallai ka fahimce ni ba, ba lallai ka yadda da zance na ba...ni kaina lamarin ya girgiza ni, ya kuma bani tsoro, da ace labari aka bani lallai bazan ta6a yadda ba but I heard it with my own ears, kuma ko ban fa'da maka yanzu ba ina tabbatar maka da cewar watarana dole sai na fa'da maka...amma hausawa sun ce da sassafe ake kamun fara...bana so ka rayu cikin duhun da tunanin ka bazai iya fiddaka kwana kusa ba...". " Ban fahimce ka ba fa me kake son fa ne wai..straight to the point plss..." " I heard ur wife saying....." Nan ya labarta masa duk abinda yaji da ranar da kuma lokacin da duk yaji abin, Rayyan mutuwar zaune yayi yana duban fawwaz, yama kasa bawa maganar matsuguni a zuciyar sa balle ya samu damar yin nazari akanta. Cunkushe yaji zuciyar sa gaba daya banda wani 'daci da juyawa da kansa ke yi. Da yaga alamun Rayyan kamar bai yadda ba Fawwaz sai ya 'daga wayar sa ya 'kira waccan Nurse 'din akan tazo bata aiki ma a lokacin amma da ganin 'kiran ogan nata batare da 6ata lokaci ba ta shirya ta taho. Rayyan na ganin ta ya gane ta tabbas tare da ita suka kar6i haihuwar Amrah ranar can, ita ce kuma tace ya tafi zata kimtsa su. Fawwaz ne ya tambaye ta tsakanin ta da Allah ta kuma tabbatar da cewa tabbas sun tattauna da Amrah kan hakan dan ta fa'da mata ne out of guiltiness neman mafita take a lkcn. Rayyan ji yayi jikin sa ya mai nawi, Salati kawai ya fara saki a zuciyar sa. Fawwaz ne ya sallami Nurse tayi gaba abinta tana tunanin toh wa ya kai masa zancen shi kuma, ita dai har ga Allah batayi niyyan tonawa ba amma da aka riga aka kai wannan level din bata da yadda zata yi domin 6oyewar ta kan iya zama wani abu daban...bata kuma san iya inda zancen zai tsaya ba, bata ta6a nufin kowa da sharri ba sannan bata cusa kanta cikin lamarin mutun ko dan gudun abinda zai iya zuwa ya dawo amma Amrah 'karfi da yaji ta cusa ta cikin lamarin da kan iya zame mata matsala watan wataran...fatan ya tsaya iya haka nan. " Fawwaz kasan babu irin wannan tsakanin mu, Pls ka fada min ba gaskiya bane wannan maganar, ba gaskia yarinyar nan take fada ba....". " Na fa'da maka iya abinda naji Rayyan na kuma baka haske ta 'kofofi biyu yanzu haka, kafin yau na bu'da maka hanyar da zaka taka kai dan gano manufata amma duk hakan bai samu ba, ka ga abinda Na'ura ya cire wannan ba ni na fa'da ko na rubuta ba, ba Nurse ta zo gaban ka ta baka labari ba, idan still baka yadda ba kuma zaka iya tsaurara bincike akai nasan ramin 'karya kurrarrae ne dole zaka fahimta watarana...kuma ba wani batun birth certificate dama tun farko kawai na fada ne sbd bani da damar da kai tsaye zan ce kayi gwaji tsakanin ka da yaron ka, ka kuma fahimce ni..this is the only simplest way da zan iya samun nasara kuma Alhamdulillah I did it...na fita hakkin ka, sauran kuma ya rage naka ne, ka yadda ko kar ka yadda duk za6i naka ne...kayi bincike ko ka kyale ra'ayin ka ne..." Tsaye Rayyan ya mi'ke ya nufi 'kofa kawai batare da ya tankawa Fawwaz ba, kalaman sa sake dawo masa cikin 'kwa'kwalwa suke suna masa amsa kuwwa. Sultan, Amrah, Arfan sunayen sa ke masa yawo aka idanun sa, ya ma rasa takamammai abinda ya kamata ya aikata. Reception ya nufa da zummar yiwa Amrah magana su wuce gida yayin da sauran kananun likitocin su ke gaida shi, hannu kawai yake 'daga musu batare da ya iya bu'de bakin sa ba. Tun fara doso reception da yayi ya hango Amrah na daria da alamu hirar da suke yi ne ya sata dariar, a hankali idanun sa ya sauka akan wata Likita dake 'dauke da jinjiri Arfan...while daga kasan kujerar da take wata farar mage ce irin wanda wani lokaci ake gani a asbitin nan kwance tana baccin ta...da alamu ma sun saba da Nurses din. Sake duban Arfan dake laps din likatar yayi bai ga alamun wani sauyi tattare da yaron ba, a hankali ya 'daga 'kafafun sa ya isa inda suke, bai kula kowa dake wajen ba hatta Amrah kuwa illah ga Arfan ya bu'de fuskar sa dake lullu6e. Bacci sa yake peacefully..bavtare davwata damuwa ba. Sai ya dubi jikin sa yayin da tuni gashin jikin san suka mimmi'ke sa6anin na Arfan da be masan me duniyar take ciki ba. Tsaye sauran suka mi'ke hadda Amrah tana duban sa yadda idanuwan sa suka yi jaa sosai..." Baby lafia, meke damun ka..?" Ta tambaya cike da kulawa tana matso shi. Atishawa ya fara saki wanda hakan ya hana shi amsa gaisuwar da likitoci matan ke masa. " Meet me outside..." Abinda ya iya cewa da ita yayi gaba yana sake jin tsanar Amrah cikin ransa. Da sauri tabi bayan sa ko ta kan Arfan bata yi ba sai biyo ta akayi da shi. Rayyan kam tuni ya isa cikin motar sa ya kwantar da kai yana sakin zafafan numfashi. " Yah Ilahi..." ya fa'da yana dafe goshin sa. Ko da Amrah ta shigo bai ko kalli inda take ba, duk tambayar da take yi masa kuma bai bata amsar ko guda cikin tambayoyin ta ba. Ko kallon inda fuskar Amrah take baya 'kaunar yi a halin yanzu balle jin muryar ta, dagaske Amrah cin amanar sa suke da Sultan, har kuma ta haifa masa 'daa da sunan nasa. " Da me ya ragi Amrah ne..? Ta ina ya gaza mata...? " Shin bashi da jarumta irinta 'da miji ne ko menene yasa har ta iya ha'da jiki da wani namiji, wanin Sultan 'kanin sa...? " Da me Sultan ya fishi..? " Amma me ma yasa Sultan zai masa haka..? Ya 'dauki tsawon mintina goma shiru cikin motar batare da ya tada ba haka kuma bai tanka Amrah ba 'karshe ma Huzaifa ya 'kira a waya akan yazo ya kaisu gida, yana sau'ke wayar a kunnen sa yake bata umarnin komawa baya. Salmerh😘 [2/11/2022, 9:28 am] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Wattpad@* _Serlmerh-md_ 🅿️ *...65* ........Shi da Huzaifa suka zauna agaba, motar shiru babu wanda ke motsin kirki balle doguwar magana, shi dama Huzaifa ba hira suke yi da Rayyan ba yayin da Amrah ke nan tana zullumin abinda ya samu Rayyan da duk zaton ta baya jin dadin jikin sa ne, tuni ma ta mance da batun 'danta ganin an 'dauki tsawon kwanakin nan babu wanda ya tanka akai sai ma wasa da aka maida lamarin ana tsokanar sa mai kama da kanin Daddyn sa. A tunanin ta a haka zancen zai wuce batare da kowa ya zarge ta ko Sultan ba. Rayyan kam gaba 'daya duniyar ce ma yake jin take juya masa, motsin kirki baya 'kaunar yi sam...bai tashi sanin sun iso gida bama sai da yaji karar horn sannan ya dan bude idanu. Suna isa wajen parking Sultan kuma na fitowa daga sashen Ammi shima ya nufo wajen parking din dan motar sa na wajen. Da alamu ya zo gaisar da Ammi ne. Tun tsayuwar su da Rayyan ya bu'de idanu akan Sultan suka fara sauka, take jiyoyin kansa suka motsa, suka 'kara 'karfi, idanun sa suka 'kara rinewa sosai, bai san mai ya sa ya kasa dauke idanu akan sa ba, be san meyasa yk jin yayi tackallon Sultan din ba, sa6anin Amrah da ko ji da ganin ta baya 'kaunar yi kwata kwata, sai dai can 'kasan ransa yake ji tamkar zai iya ganin wani abu da zai iya 'karyata duk wancan bayanan da ke cinsa a zuci...amma ko alamar hakan bai fara gani ba balle ya saka rai da gani, sai ma 'kara dulmiyar dashi suke da dawo masa da wasu abubuwa da abaya tunanin sa bai ta6a basa hakan ba. .....Kallon Sultan yake yana kissima abubuwa, tamkar tashin tsuntsaye haka abubuwa ke shawagi game da Sultan a kwanyar sa...mamaki, al'ajab, rashin yadda, tsana, da wasy abubuwan da bama zai iya lissafawa ba, ha'ki'ka in Allah ya baka zucia mai kyau toh tabbas ka du'kufa wajen gode masa dan yayi maka kyauta, kyauta mafi inganci da alfahari...me ya yiwa Sultan har haka? Me yasa Sultan zai ci masa amana, cin amana mafi muni irin wannan...baya so ya zafafa abinda yake ji kamar yadda baya so ya gina wani shinge tsakanin sa da Sultan shingen da ya tabbatar dukkan su bazasu ji dadin sa ba, har gobe yana 'kaunar sa domin ba'a koya musu ki ko nuna bambanci tsakanin su da shi ba, 'kaunar juna da mutuntawa aka koya musu shiyasa yake 'ko'karin danne ransa yake danne abubuwan da ke taso masa baya so su fashe, baya ga haka idan ya biyewa umarnin zuciyar sa hukuncin da zai yi musu bazai yi musu da'di dukkan su ba. Amrah ce ta fara fitowa a motar sai kuwa Sultan da ya riga ya kusa isowa kusa da su ya washe ha'kora. Huzaifa na hanzarin fita dan zuwa bu'de masa motar Rayyan ya dakatar da shi. Sultan kuwa wajen su ya nufa yana fa'din.." Maman Boy daga ina haka...?, Hope lafiya dai kam...?" Yayi maganar yana bu'de fuskan yaron dake hannun Amrah at same time yana kashe mata ido 'daya sai ta saki murmushi tana bin hannun sa da kallo, duk suka sauke idanun su kan fuskar Arfan atare. Duk faruwan hakan akan idanun Rayyan ne, zuwa yanzun sun daina ma bashi mamaki, sai dai baya jin duk cikin su akwai 'daya da zai iya nasarar illata masa zuciya sun yi kadan, bazai zauna abanza su nakaskta masa kwarin zuciyar sa ba. A hankali Amrah batare da ta dube shi ba tace" Tare muke da Baby fa..". " Wani Babyn..?" Ya tambaya yana 'dage gira. " Sorry...I mean Rayyan...". Ido ya 'dan fitar" Ohh...shine baki bani signal da wuri in je in kwashi gaisuwa ba..?" Ya 'karashe maganar da kar6an Arfan dake hannun ta ya nufi motar da Rayyan ke ciki, dai- dai shima ya sa hannu ya bu'de motar caraf idanun su suka sau'ka kan cikin na juna, kowa kallon da yayiwa 'dan uwan sa cikin zuciya daban yake. Yayin da fuskar kowa ke 'kokarin lullu6e wani abu da shi 'kadai yasan ma'anar ta. " Yah..Barka da war haka..." Kallon sa kawai Rayyan yake bakin sa ya ma kasa motsi balle ya amsashi, ji yake tamkar ya sha'ke shi amma har yanzu bashi da ikon yin hukunci bisa ga abinda bayi da hujja 'kwa'k'kwara ta zahiri a hannun sa da kai tsaye zai ce Sultan na fita da matar sa, zargi ne kawai, zargin ma da bai kai yayi tuhuma akansa ba tukunna, he still need more evidences. Amma har can cikin zuciyar sa yake jin erh lallai dagaske Arfan ba jinin sa bane, after all ma shi bazai ce yana jin yaron har cikin ransa ba that's the number reason da ke rage masa kuzari sannan the Cat..Yah Rabb the test...yasan wa'dannan manyan hujjoji ne but dole sai ya sake jarraba wasu akaran kansa. Dama tun farko yakan tuhumi kansa tun bayan haihuwar yaron meyasa baya jin sa a ransa ne. Baya ga haka ma kusanci da gyanayin sha'kuwar dake tsakanin Amra da Sultan ba yar 'karama bace wanda ya fahimci hakan ne mintina 'kalilan da isowar su wajen nan. " Yah Rayyan Sai ka bar wa Amrah Babyn bacin kasan rawar kai gareta, wannan sai fa ta kayar mana da Baby abanza...." Ya 'karashe yana 'yar daria da waigawa ya kallo Amrah sannan ya dawo da kallon sa kan Rayyan. Sam Sultan bai damu da rashin masar Rayyan ba dan yasan wannan ya zam tamkar dabi'ar sa ne, sai lkcn da so yake magana ko amsa gaisuwa, abu 'daya da ya lura da shi a yanzun shine canjin yanayin sa ba kamar sauran lokuta ba, sai dai bai dora hakan bisa mizanin da har zai iya shafar sa ba. Wannan maganar da Sultan yayi ita ta sake tunzura zuciyar Rayyan. Gira 'daya ya 'dage ya dubi Sultan 'din sama zuwa 'kasa 'karshe ya sau'ke idanun sa kan Arfan dake hannun sa yana mi'kawa Rayyan da alamu so yake ya amshi yaron. 'Karfi da yaji yake son ya sake karfafa bond 'din dake tsakanin su...fahimtar haka da Rayyan yayi ya sashi ha'de rai sosai, wani tukukin takaici ya taso masa, da 'kyar ya iya dannewa sai dai bai ma san lokacin da bakin sa ya furta..." Get out of my way..." a tsawace ba. Ya fa'da ne yana tsare Sultan din sosai. Ba shi Sultan ka'dai ba, hatta Amrah sai da tayi mamaki matuka, iya tsawon rayuwar da tayi tare da su, bata ta6a ji ko ganin abu makamancin irin haka daga Rayyan ba akan 'yan uwan sa, 'kaunace mikakkiya mai tushe yake nuna musu, amma yau din ta rasa mai ke damun sa kwata- kwata, sai kace wani mai aljanu...? Ta tambayi zuciyar ta. Rayyan kam da fa'din hakan yabi gefen Sultan da ya 'dan kauce agaban sa yayi gaba abinsa ya nufi 6angaren sa. Duk 'din su da idanu suka rakashi har ya kusa shigewa wato Amrah da Huzaifa sai dai banda Sultan da tuni kallon sa ya dawo kan fuskar Arfan. Fuskar sa babu yabo babu fallasa, kai baka ce ga yayanin da zuciyar sa take ciki ba. Amma he is burning inside da wannan tsawar da Rayyan ya buga masa...idanun sa akan Arfan yake tunanin...dole akwai wani abu, Rayyan bazai ta6a yi masa tsawa haka nan kawai ba..." Amrah ce ta matsa kusa da shi cike da damuwa tace " Sultan wai meke faruwa ne?...na kasa gane kansa tun bayan isar mu hospital ya canza gaba 'daya anya Baby bashi da aljanu kuwa...?" " Nima aljanun gare ni Amrah zan kuwa tabbatar muku da hakan..." Zaro ido tayi sosai tana bu'de baki. Sai ya girgiza kansa.." Kuma dayake ke 'kwa'kwalwar dusa gare ki ni kk tambaya abinda ke damun sa..? Matsayin ki na mata agare shi baki san meke damun sa ba taya kk tunanin ni kuma zan sani..?" " Haba Sultan bayan ba fa'da min yayi ba ya kake so nayi toh..." Ta bashi amsa cike da tsantsan damuwa. " Sam ke de na rasa wace iriyar macece, mijin ki ne fa amma tun ganin sa cikin wani yanayi ai sai ki matsa masa da tambaya ke ko irin kissar nan ta mata baki iya bane...?" Rai ta hade. " Kar ka fa'da min magana mana Sultan, Rayyan ne baka sani ba ko halin sa, naga kaima gashi ya maka yanzun nan, shi in ba niyyar yin abu yayi ba ana sashi ne...wannan aikin ai sai dai Ammin sa kasani.." " Dama daga ina kuke..?" " Asbiti" " Doing what..?" " Allura aka wa Arfan.." " Kin tabbatar abinda kawai kuka yi asbitin kenan..?" " Noo...anja jinin mu duka..." " Har Arfan...?" " Erh hadda shi..." Idanu ya lumshe cikin zuciyar sa yace" Tafaru ta 'kare..." Tsaki Sultan yaja a fili yana bugawa Amrah banzan kallo. " Allah ke jaka ce...tunanin ki sam baya aiki, ki zauna har lkcn da zai fito fili ya bayyana mk cewa ga damuwar sa nan, a time din zaki fi yadda da cewar ke din jakar ce dagaske kamar yadda na fadi...". Cikin ransa yace" Zan kuwa yi maganin Rayyan wallhi...da ni yake magana.." Amrah dake bin Sultan da banzan kallo cike da takaicin zagin da yayi mata ji take tamkar ta rufe shi da duka. Mi'ka mata 'dan ta yayi.." take ur Baby ku shiga ciki..." Daga 'karshe dukkan su babu wanda ya bar wajen cikin da'din rai.."Amrah ciki tayi tana ayyana" Wallahi kaci bashi Sultan..". Huzaifa kuwa dake daga daya can 'daya 6angaren shima cikin mota ya koma yana kya6e baki, dan Rayyan yace masa ya jira shi fita zasu sake yi, bai zago ta inda suke ba sai dai duk dramar tasu a kunnan sa ne...shima Sultan yasan duk yajin amma bai damu ba domin duk tamkar madubin sa suke...photo kawai suke ga Rayyan batare da ya sani ba. Yanda Sultan ya fizgi motar a zuciye har abin zai baka tsoro da mamaki ga wanda bai san abinda ya faru ba. Huzaifa kansa le'kowa yayi yabi bayan motar da kallo haka Amrah ma dake kan.m hanyar 6angaren ta, sai da ta waigo ta dubi bayan motar tana girgiza kai ta juya ta cigaba da tafiyar ta. " Ku dai Allah ya shirya, kowa zuciya akan abinda bana kirki ba...". Tana isa Palor shi kuma yana fitowa, ko kallon inda take bai yi ba yai waje abinsa da dukkan wayoyi da system dinsa dama wasu abubuwan da bata san komene ba. " Baby fita zaka sake yi kuma...?" Bai kulata ba yaci gaba da tafiyar sa. Tasan dama wannan halin sa ne amma still sai ta sake fa'din" Baby magana nake fa ina zaka je haka...?" " Inda kika aike ni" Inda yayi maganar yana me cigaba da tafiyar sa tamkar bashi yayi ba. Haka nan kawai ta tsinci zuciyar ta cikin rashin sukuni da fitar tasan karshe da idanu tabi sa har ya 6acewa ganin ta. " Allah ya kyauta." Tace a fili tana me zama bisa kujera mai zaman mutum biyu. Rayyan kam sake fita suka yi da Huzaifa da niyyar sa Huzaifa ya kaisa inda za shi amma tuno maganar ta kwanaki... _Ka canza masu Kula da kai._ da yayi ya sanya shi dakatar da Hauzaifan, dama driving yake tunanin kamar zai bashi wahala but dole zai daure yayi da kansa. A hanlin yanzu baya son kowa ma ya san inda yake balle a dame sa, sosai yake so ya samawa zuciyar sa hutu na wani lokaci. Ku'di kawai ya Huzaifa da sunan ya samu abin hawa ya koma shi zai 'karasa inda zashin kawai. Huzaifa ba 'karamin mamaki yayi ba da jin sauyin ra'ayi da ga Rayyan din sai sai dai sanin da yayi cewar hakan ba sabon abu bane a wajen sa ba ya sanya shi watsar da batun ya tari adaidaita yayi gaba abinsa. Rayyan haka kawai yanzu yake ji har cikin zuciyar sa bai yadda da kowa ba, kuma ya tsani duk wata mu'amala da zata ha'da shi da wani na daban. Bai zame ko'ina ba sai can gidan sa da ya bari tun bayan rasuwar Nadia, Nadia matar sa mafi karamci cikin matan sa, ya san dama yayi rashi tunda Nadia ta barshi yasan yayi rashi matuka, yayi rashin macen 'kwarai da baya jin har abada zai samu makanciyar ta, har abada kuwa bazai daina nema mata gafara wajen mahalicci ba, ya tabbata da Nadia ce mazaunin Amrah bazata ta6a iya cin amanar sa da wani namijin ba ballantana 'kani ma awajen sa irin Sultan. Cikin gidan nan yayi rayuwa da matan sa biyu bazai manta ba shekaru ne 'kalilan da suka wuce 'kasa da shekaru biyar amma yau da ya tsinci kansa cikin gidan cikin 'dakin ta ji yake tamkar ya shekara 'dari ne rabon sa da ita. Kewar Nadia da kuma cin amanar da akayi masa ya sanya shi jin duk ga6o6in sa sunyi sanyi. Gidan cike yake da 'kura dan ba sosai yake le'ko shi ba amma ahakan ko da ya samu ya yaye leda 'daya da aka rufe kujeru da shi yaga 'kurar wajen babu sakamakon ledar da ta musu shamaki da kurar ahaka ya zauna akai yana mai daga kansa sama dayake jin yana sara masa tamkar zai rane gida biyu. An jima ana munafurtar sa, anjima ana masa ha'inci a rayuwa, anjima ana cin amanar sa amma in ka 'dauke ta kashe Daddyn sa da akayi wannan shine cin amana mafi muni da ya tsaya masa arai sosai, in dai har Sultan da tun tasowar sa yake yiwa kallon 'dan uwa, kuma 'kani a wajen sa na jini zai masa haka me ze hana wani ma daban ha'intar sa? Indai har Amra da take matsayin matar sa ta iya masa haka toh waye bazai masa ba. Turaren Sultan da ke saman mirrorn ta da ya ta6a gani da jimawa...kuma yaci gaba da gani har zuwa lkcn da cikin Amrah sannan ya daina gani, bai ta6a damuwa ko zargin wani abu da ganin turaren ba, duk zaton sa itace take amfani da shi duk da bai ta6a jin 'kamshin sa ajikin ta ba. Ashe shi suka mayar sauna, ashe ala'kar su tayi 'karfin da ta zarta tunanin sa. Bai san tsawon wani lokaci suka 'dauka suna wannan rayuwar da Sultan ba amma shi abinda ya sani kawai shine daga yau din nan baya jin zai iya sake rayuwar aure da ita har abada. Har cikin zuciyar sa yake jin ta fita daga ransa ya kuma cire ta cikin tsarin rayuwar sa kwata- kwata. Hankalin Amrah bai sake tashi ba har sai da taga dare yayi babu Rayyan babu alamar sa, ta kira wayar sa fin a 'kirga amma duk numbers din sa basu tafiya...wasa- wasa har sha 'daya babu shi, bai ma ta6a yi mata irin hakan ba tun farkon auren ta da shi sai yau din..shiyasa hankalin ta ya tashi. Tuni ta 'kira Ammi ta sanar da ita, itama tayi ta 'kiran sa numbern sa bai tafiya. 'Karshe Sultan Ammi ta tambaya yace shi bai san inda yake ba amma zai bincika Insha Allah. Sultan baccin sa yasha haka ma Marwa da bata san meke faruwa ba dan lokacin da Ammi ta 'kirasa Marwa na bathroom ne, ko da ta fito kuwa bai sanar da ita ba, yayin da Ammi da Amrah suka yi kwanan fargaba. Zuwa lkcn Amrah ta gama fahimtar akwai wani abu, dole akwai abinda Rayyan ya sani musamman ma idan tayi fashin baki ga kalaman Sultan da tun jiyan bata yi nazarin komai akai ba lallai dagaske itan sauna ce bata san inda wayo da tunanin ta suka tafi ba. 'Bangaren Zaitoon kuwa da farin ciki ta kwanta da yasa har ta 'kagu gari ya waye sbd tsabar zumu'di. Tun kafin yammacin ranar ta roki Ammi adawo da Mufeeda haka, agaban ta Ammi ta 'kira Anty Madeena dan ta lura Rayyan bashi da niyyan dawo da yarinyar...Nan Ammi ta roki Anty Madeena kamar yadda Zaitoon itama ta roketa kan dawo da yarinyar. Anty Madeena tace abarta mana, yarinyar da tuni ta saba da su ta sake tana wasan ta, makarantar ma tuni ta saba da ita, tace Badi'a bazata ji dadi ba idan aka dauke ta wallahi. Ammi tace itama uwar dan baku san halin da take ciki bane...ai tayi hakuri ma. Anty Madeema tace kai Hajjaju..ku dai kuce kuna son adawo muku da 'diyar ku ne kawai amma nan din ma ai duk gida ne.." " Erh munji adawo da ita duk wannan hakurin baku gani ba?" Ammi tace tana murmushi. " Bari dai toh in gani in zai yiyu zuwa gobe sai asan ya za'ayi ko zuwa jibi ma..." " Allah ya nuna mana dan Allah a kokarta munyi kewar ta sosai..." Duk wayar a handsfree akayi shi, kuma wannan wayar da taji shi ya sanya zuciyar ta cikin walwala sosai har ma idan ka dube ta lokacin da take bacci murmushi zaka gani kwance saman fuskar ta. Tun bayan jin maganganun Amrah da Sultan, bata sake jin kanta cikin farin ciki kamar yau din ba. Tun cikin dare Anty Madeena ke neman layin san amma baya shiga, so take ta sanar da shi batun test din su danta lura tunda ya samu Arfan ya mance da batun Mufeeda... aganin Ammi fa.. Rayyan nan kan kujerar ya Kwana, tun tasowar sa har girman sa bai ta6a yin kwanan takura irin wannan rana ba, amma ji yake zuciyar sa tafi natsuwa fiye da ace yana gida 'kar'kashin inuwa guda da Amrah, baya so fushin sa ya haura level 'din da bazai iya controlling fushin sa ba dan zai iya illata both Amrah da Sultan din. Sallah kadai ke tada shi. Da dare kuwa kwana yayi sallah yana rokon Allah gafara, rayuwar tasa tsoro take basa ayanzu, ta ko'ina baya samun sassauci. Ta ko'ina illata masa zuciya ake. Baccin da bai yi da daren bane ya rinjaye sa da safe shiyasa sai da yakai har kusan sha daya sannan ya farka. Sai da ya watso ruwa sannan yazo ya zauna wayar sa 'daya da yasan yafi huldar family da shi ita ya kunna, Ammi yake son kira amma ga mamakin sa yana kunna wayar 'kiran Sultan ne ya fara shigowa, haushin hakan ya sanya shi sake rufe wayar ya kife ta ya tafi izuwa ga 'kananun kayan sa ya sanya a jikin sa. Bai sake bi takan wayar ba har sai daya dawo daga sallar azahar da ya fita masallaci, sannan bai dawo akan kari ba dan sai da ya wuce Shoprite ya siyo kayan da yasan zai bukata anan na 'yan kwanki... Anan nema daya ga hada- hadar mutane ta yawaita sosai ya tuna ashe fa daf ake da kama azumin ramadan...shaf ya mance. Ammin ce dai still acikin ransa. Hakan yasa da dawowar sa ya sake kunna wayar sa tasa, dan manufar ta karu masa. So yake ya sanar da ita inda yake gudun kar ta shiga damuwa, baya ga haka yana kuma so ya tunasar da ita adadin kudin da za'a fitar dan rabawa mabu'kata kayan abinci da suka saba kowace Ramadan. Wannan karan ma yana kunna wayar kiran Anty Madeena ya shigo masa. Sai dai bai 'ki 'daga nata 'kiran ba duk da ba hakan yaso ba. " Sannu isashshe..sai yanzu kaga damar bude wayar? meyasa kake son kashe dukkan wayoyin ka ne Rayyan sai ayi neman ka baza'a samu ba...?" " Wlh Anty bana jin dadi ne..." Ya bata amsa da sanyin murya. " Subhanallah...ya jikin..kuma fa gashi ina son ganin ka, kaga Ammi da Zaitoon sun matsa adawo musu da yarinyar nan gashi har yau ka kasa tsayar da lokacin da ya kamata muje asbitin, kuma nafi so ayi komai a kamamala cikin lkc 'kankani ta yadda babu wanda zai zargi wani abu...in da hali ka daure muje ko zuwa bayan la'asar dan Allah...". Hannun ya cusa cikin gashin kansa ya shafo wannan ha'da shi da Allahn da Anty Madeena tayi yasa shi amince mata bisa dolen sa. " Toh Anty Insha Allah zan yi kokari in zo sai muje..." Daga haka suka yi sallama...Ya kira Ammi...gaba daya hankalin ta tashe yake tun jiya take kiran sa har yau din amma shiru, dole hankalin ta ya tashi tana tsoron abinda ya faru abaya ya sake faruwa gare shi shiyasa duk ta shiga tashin hankali. Ga Marwa bata shigo gidan ranar ba balle ta taya ta jimantawa sai Zaitoon kadai, Amrah kuwa yaron ta kuka yake yawan damun ta da shi itama ba nutse take ba. Tana zaune zaman zullumin inda yake da abinda ya same shi taji wayar ta na 'kara, da sauri ta kai duban ta ganin shine ya sa ta 'daga da sauri. " Rayyan?..haba Rayyan..ina ka shiga haka ne...?" " I'm sorry Ammi...ina gidana ne..." " Shine bazaka fada min ba kuma ka kashe wayoyin ka Rayyan, hankalina ya tashi sosai wlh..." " I'm sorry Ammi kawai na bukaci hakan ne but zuwa dare zan shigo Insha Allahu..." " Ok...pls kar ka sake min irin hakan kaji duk inda zaka ko wani abu ka sanar dani dan Allah.." " Insha Allah Ammi...". Bai yi niyyar zuwa ba amma jin yadda Ammi ta rikice da jinsa ya sanya shi dole yayi skipping maganar kayan Ramadan har sai yaje, dan ya lura ganin sa ne kadai zai iya sanyaya zuciyar Ammin sa. Sultan kuwa tunda ya 'kira Rayyan ya kashe masa waya zuciyar sa ke tafarfasa, gaba action 'din Rayyan 'din sun dagula lissafin sa, dama yasan na'ura sosai, so kawai bin diddigin Rayyan din yayi ya kuma yi nasarar gano inda ya ke amma bai sanar da Ammi ba, haka shima bai je ba. Ko ta 'kira sai dai yace mata yana kan bincikawa. Shirin sa kawai ya cigaba da yi a 6oye batare da kowa ya sani ba daga shi sai Allahn sa sai kuma mataimakan sa. Rayyan kam kaya ya canza ya fita zuwa gidan Anty Madeena dan zuwa yanzun shi kansa yana so koma mene akai shi 'karshe ya gaji da walagigi da saka rai da ake masa akan yara...bai sani ba ko bashi da rabon samu ne alhali Allah ya daura masa kaunar su...basu wani 6ata lokaci ba suka fita zuwa hospital, tun kafin zuwan su ya kira Fawwaz ya sanar da shi ya tabbatar masa cewa yana hospital. Tun isowar su da yaga Anty Madeena ya kuma ga Mufeeda zuciyar sa ya bashi wani abu, ganin yanayin Rayyan bai bashi mamaki ba domin yasan dama fin haka ma za iya gani tun ranar da yaga yarinyar yaji cewa akwai wani abu. Salmerh😘 [3/11/2022, 9:16 am] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Wattpad@* _Serlmerh-md_ 🅿️ *...66* ........Bai manta dalili da kuma yanayin da suka rabu a jiya ba. Gaisar da Anty Madeena yayi yana me duban Rayyan dan sosai tausayin abokin nasa ya tsaya masa arai tun a jiya. Anty Madeena ce tayi masa takaitaccen bayanin abinda take so ayi. Ya kuwa kallo RAYYAN a firgice yana me mi'kewa, shi dama ya ta6a zargin hakan, ba kuma yaji aransa cewar zargin nasa ll totally go.in vein hakanan kawai ba, amma dayake Rayyan bai bashi 'kofa ba yasa dole ya watsar da batun. Rayyan daya san dole da jin maganar Fawwaz zai dube shi sai ya ki 'daga idanu ya kalle shi balle su ha'da idanu...ji yake tamkar Fawwaz din na 6ata mai lokaci, 'kage yake da son jin 'karshen sakamakon...ba dan ba zai iya ta6uka komai ba da ko sauraran wani ma bazai yi ba da kansa zai yi komai. Fawwaz da kansa ya ja jinin su duka yayin da Mufeeda dake rungume jikin Anty Madeena ta saki kuka jin yadda allura ya 6ula mata jiki. Sosai Anty Ta rungume ta yayin da Rayyan ya zuba musu idanu. Ji yake tamkar yaje ya kar6e ta ya lallashe ta sbd yadda kukan ke ratsa masa zuciya...amma baya so Anty taga kamar ya za'ke da yawa...amma da ace zai bi umarnin zuciyar sa da tabbas hakan zai yi. Fawwaz tsaye ya tsaya kan 'kafafaun sa a Lab 'din har aka yi komai aka gama, duk da yake sun zone kusan za'ace a 'kurraren lokaci amma yadda Rayyan ya shiga damuwa yana fatan wannan sakamakon ya wanke masa dukkanin bakin cikin dake cikin zuciyar sa. Tun da ya fito da sakamakon yake sakin hamdala gami da murmushi ya nufo office 'din sa da sassarfa, ji yake tamkar wani babban kyauta akai masa. Hakika Allah gwanin baiwa ne kuma sarkin sarakai, Allah mai kyauta da 'kari, ya hana ka wani abin ya kuma baka wani a lkcn da bak zato, sai gashi ya dawo ma Rayyan da farin cikin sa a lokacin da yake tunanin ya rasa ta. Da zuwa bai ko kalli inda Anty Madeena take ba ya nufi Rayyan ya mika masa Papers 'din fuskar sa kumshe da yalwataccen murmushi, yayin da ya tsurawa Rayyan idanu dan ganin nashi yanayin. Idanu Rayyan ya zuba akan Papers din tunda ya fara karantawa da ya fahimci abinda suka 'kunsa kawai sai ma ya kasa 'karasa karatun ya tsura musu idanu...sai ya ma rasa shin nazartar rubutun yake ko kuwa irga yawan su, bai ta shi sanin 'kwalla ke bin 'kuncin sa ba har sai da Fawwaz ya dafa shi. A lokacin ya 'dan motsa kansa sai kuma ya 'daga kai ya kalli Fawwaz dake tsaye kansa da rinannun idanuwan sa, Kai Fawwaz ya jijjiga masa..." Hamdala ya kamata kayi ba kuka ba Dr...ka godewa Allah da ya nufe ka da fahimtar haka tun kafin 'diyar ka ta dulmiya cikin dunia batare da ka san da zaman ta ba, baka ma gode Allah ba da ya sake dawo maka da ita gaban idanun ka ta rayu gaban ka, karkashin inuwar ka da dukiyar ka duk da kuwa baka san cewa jinin ka bace...?" Karo na farko tsayin ranar ya saki murmushi, murmushin da ya fito tun daga zuciyar sa ya kuma kore masa dukkan 'kuncin da yake jin sa ciki lokuta 'kalilan baya. A hankali ya sau'ke idanun sa kan cinyar Anty Madeena, Mufeeda ce, yarinyar Zaitoon, hakika ita din jini na nace, 'diyar ciki na.... Daga kan kujerar kawai gani suka yi Rayyan ya zame ya bi kasan tiles basu fahimci abinda yake shirin yi ba sai da suka ga ya sada goshin sa da 'kasan tiles suka fahimci sujudush shukr yayi..... Anty Madeena kallon sa take yi amma sam hankali da tunanin ta basu a wurin kwata kwata. Hakika dole a godewa Baiwa, buwaya da kuma cikan ikon ubangiji, bayaga shi wa zai iya wannan abin....Ita kanta 'kwalla take sharewa lkc zuwa lkc. Bata san kuma me ya rage mata a yanzu da zata yi cikin asbitin ba...hakan yasa ta mi'kewa rungume da Mufeeda suka fita. Can inda babu kowa ta ke6e ta zauna tana tunani gami da wassafa yadda abubuwan suka kasance...amma still idanuwan ta sun kasa daina tsiyaya. Rayyan ya da'de yana addu'a gami da nuna tsantsar godiyar sa kafin ya 'dago. Fawwaz da har lokacin yake tsaye kusa da shi ya rungume yana fa'din thank u so much Fawwaz... Bai jira cewar komai daga Fawwaz ba kawai yayi gaba. Parking lot yaje sai dai baiga Anty Madeena ba, dube dube ya fara da jajayen idanuwan sa sai can ya hango ta zaune ta rungume yarinyar sosai. Anty Madeena ba 'karamin 'kaunar sa take yi ba shi kansa shaida ne ba sai an fa'da masa ba, haka kuma 'kauna da soyayyar ta bata rage kan koda 'ya'yan da suka haifa ba, da kai tsaye za'a iya 'kiran su jikoki agare ta ba. Hankali ya daga 'kafafu ya taka zuwa inda suke..Anty bata san da tahowar sa ba har sai da ya dur'kusa gefe da ita ganin yanda hawayen ta ke gudu daya bayan daya...duk sai yaji jikin sa ya 'kara yin sanyi. " Anty Kema kuka kike...?" Da sauri ta dube shi tana 'ko'karin share fuskar ta. Tsaye ta mi'ke batare da ta tanka shi ba kawai tayi gaba ya biyo bayan ta. Ko da suka isa gidan ta bai yadda ya shiga ba, duk yadda Anty taso ya shigan ko dan yaci abinci ma Rayyan dan tasan mawuyaci ne idan yaci abu yinin ranar kaf amma sam kin shiga Rayyan yayi yace zai je ya dawo. Tace nasan da kyar ne ka dawo a yau Rayyan, dan haka gargadi zan baka, akan yarinyar nan dan Allah bana so kowa yaji batun nan for now, let it be safe har zuwa wani lokaci kaji? ina tsoron wani abu ne Rayyan sai yanzu nake ji a zuciya ta kamar akwai wasu abubuwa da ba dai- dai suke tafiya ba, ko kuma ince muna tafiya ne da su amma su bayan mu suke hange, dole sai munyi taka tsantsan.. gani nake kamar idan an bayyana ta za'a iya salwantar mana ita da ita, kuma har yanzu bamu san ta ina makiyan mu suke ba balle musan shirin su, baya ga haka ma har yanzu akwai sauran binciken da ba'a kammala ba ka sani..." " Erh Anty kuma Insha Allah zanyi iya kokari na naga na binciko komai hatta ita Zaitunan, da kaina zan bincike ta..." " Yauwa hakan yayi, dama dole ne a bincike amma kuma ka tabbatar baka yi shi azafafe ba dan na san halin ka, ko bakomai kuma Zaitun abar jinjina ce agare mu baki 'daya, sannan kayi komai cikin sirri, har ila ban ce kasa Ammi ciki ba tukunna...nafi so a lkcn da labari zai iske ta ya kasance cewa komai ya tabbata ne babu wani sauran kokonto..." " Insha Allahu Anty.." " Shikenan...take care.." Daga hak yaja motar ya sake fita. Direct gidan sa ya wuce, bai yada zango a ko'ina ba sai 'dakin Nadia, banda kayan gado babu komai, ya riga yasan hakan, dan da sanin sa Ammi ta tattare komai da ya shafi personal life din Nadia. Idanu ya lumshe ya kuma bu'de su yana duban gaban mirrorn ta, inda a kullum take zama bayan ta fito wanka" She has already gone far, very far...da yasan bazai ta6a sake ganin ta ba.." Da 'kyar yake iya 'daga 'kafafuwan sa sbdo nawi da suka yi masa. Idan har akace wannan 'diyar Nadia ce ya akayi kuma ya ganta da wani jinjiri a wancan hoton da ya samu wajen kundin mutuwar ta...? Me hakan ke nufi? Tun 'dazu abinda ke masa yawo aka kenan ya kuma rasa mai bashi amsa. Kar dai canza masa 'ya akayi aka sace yarinyar aka ajiye mata wanda aka tabbatar baya da rai bayan ansan ta riga da ta koma ga mahalllici? Wa kenan yayi wannan aika aikan...?" " Zaitoon! Wata zuciyar sa ta amsashi. Da sauri ya motsa kansa..." Ohh noo...bazata iya aikata hkn ba.." " Then who is behind all these?" Ko kuma dama karya ake a wancan lokacin ba dagaske bane 'diyar shi tana raye suka ce bata da rai, har suka yi mata hoto da Nadia cikin jini. Toh indai har hakan ya iya faruwa zai iya zargin matar sa ma tana raye kenan duk da kuwa cewa yasan mutuwa ya kuma san daga Allah ne, amma a zahiri zai iya cewa tana raye duba da wannan kwakkwarar hujja da ta bayyana, babu mmk itama 6atar masa da ita akayi kawai da 'karyar ta mutu. Amma yasan ba yadda za'ayi ace Nadia na raye tsawon shekaru biyu amma ace bata dawo gareshi ba. Kansa ya shafo a hankali yana jin 'kirjin sa na yi masa zafi sosai...sam ya mance ma ashe tun safe bai sa komai a cikin sa ba. Gaban drawern ta yaje ya bu'de yana tuno ranar da zata tafi, ranar da ya kasabce musu rana ta 'karshen ganawar su, kaita airport da yayi shine bankwana na 'karshe da yayi wa ganin ta...har sun fita ta dawo ta bu'de wannan drawer ta 'dauki wani Paper ninkakke ta jefa cikin jakar ta amma bai san ko takaddar menene ba. Da ya san haka zai faru da tun a lokacin yayi mata wayo yaga takaddar amma Allah bai nufe shi da yin hkn ba, kuma ya tabbata mai muhimmanci ce tunda har Nadia ta bata muhummanci. Janyo drawer yayi ya bu'de babu komai a ciki, haka na 'kasan sa ma ba komai, 'dayan ma bakomai. Wasa wasa sai ga Rayyan yabi duk drawers dake cikin bedroom din ya wangale su hatta saman sip 'din ta sai da ya hau abu ya duba amma babu komai da ya gani. Bai ga komai da ya danganci Nadia cikin gidan ba. Yasan Aikin Ammi ne, yasan ita ta tattare komai bai kuma san inda ta zuba su ba. Zama yayi yana maida numfashi. Shawaran da zuciyar sa ta bashi yabi dan haka ya ciro wayar sa ya kira Ammi. Tambayan ta yayi ina ta saka kayan Nadia ne yana so zai duba wani abu aciki, Ammi tace ya taho suna nan gida wajen ta. Dole badan yaso ba ya tashi ya fita zuwa gidan...Ammi kuwa hanyan haduwa da shi take nema dama, yace mata zai shigo tun 'dazun amma bata ga alamun yana da niyya ba, sai kuwa fa'duwa tazo dai- dai da zama. Kallo biyu bai yiwa 6angaren sa ba ya nufi baban sashen da yake na Ammi...Can saman ta ya same ta..Ammi duba 'daya tayi masa ta fahimci 'yar ramar da yayi"...Rayyan wai lafiyan ka kuwa...? Ka dubi yadda kake purnishing kanka abanza wai duk menene hakan wai? wani abin ke damun ka da har zai saka cikin wani hali batare da ni nasani ba Rayyan...?" " Ammi bakomai fa, ki kwantar da hankalin ki dan Allah...." Ya bata amsa yana zama gefen ta. " Idan da kasan yadda nake ganin ka bazaka budi baki kace in kwantar da hankali na ba, kar kace min har yanzu batun Nadia bai bar zuciyar ka ba, shin baka san 'kaddara bane kome kake so ka tabbatar min...?" " Dan Allah Ammi kiyi hakuri, ni duk ba wannan ne damuwa ta ba, taya bazan san 'kaddara ba bacin nima nasan zan mutu yanzu ko anjima..bani da damuwar komai..Nadia kuma da na miki magana abu ne ya taso min da zan duba cikin kayab ta dole...". " Naji...toh sai ka fa'da min at first place meyasa ka tafi ka bar matar ka da yaron ka tun jiya baka waiwaye su ba? baka san halin da suke ciki ba? ba ka kuma 'kira waya ba...kasan damuwar da ka sanya zu'katan mu a ciki kuwa Rayyan daga jiyan nan zuwa yau...?" " Ammi dan girman Allah kiyi hkr ku yafe min, abubuwa ne suka taso min da dole sai na gujewa hayaniya kafin zan samu natsuwar aiwatarwa...." Yayi maganar da rauni sosai ganin halin da yaso jefa mahaifiyar sa ciki. Ajiyar numfashi Ammi ta sau'ke bata sake magana ba. Shiru ne ya dan biyo sai ta gyara zaman ta tana jin sanyi cikin ranta. " Babu ma alamun ka sanya wa cikin ka abu tun safia.." " Erh Ammi hakane...zan ci abinci amma please bari in gama duba abinda zan duba sannan inyi zaman cin abincin..." " Wannan ne kuma bk isa ba...". Zaitoon Ammi ta fara kwallawa kira da gama fadin hkn, da yake nan saman nata take batasha wahalar kiran ba ta kuwa taho da saurin ta izuwa ga Ammin. Tun 6ullowar ta Rayyan ya kawar da kansa gefe, yana so yaga fuskar ta amma idan ya tuno Mufeeda sai yaji ya tsani komai, tunanin sa yadda ta samu yarinyar shi kadai ne damuwar sa a yanzu. Ya kuma san abu mai sauki ne gareta yanzu tace zata tambayi 'diyarta da ganin san shiyasa ya kawar da kansa karma taga fuska... " Barka da Yamma...Yah Rayyan..." Tace tana mai sunkuyar da kai ta kuma ce " Gani Ammi." Rayyan bai tanka ba, itama bata damu ba dama tasan hakan ne. " Ha'do masa abinci kinji ki ha'do da tea mai dan zafi ya fara sha tukunna koda kadan ne ma..." " Toh Ammi..." Ta fa'da tana mi'kewa. Ambatan abinci da Ammi tayi yaji duk shi fa ina bama zai iya cin wani abinci ba... har ta kusa isa bakin bene da zai sada ta da downstairs yace.." Kinga...!". A waigo..." idan akwai fruits kawai ki ha'do min ki bar abincin nan..." Kai ta 'daga masa sannan tayi gaba. Idanun sa ne ya sau'ka akan na Ammi dake kallon sa. " Ammi shi ka'dai ma fa ya ishe ni ban jin abinci ne yanzu...." " Hmm". tace tana daidaita zaman ta. " Sultan ma fa kwana biyun ganin sa yay min wuya duk kun je kun ha'de kanku kun hana kawunan ku sukuni saboda wai Company ko?...naga dai INFINITY da ku ko ba ku babu abinda zai dakatar da ayyukan sa indai har za'a biya ma'aikata hakkin su yadda ya kamat..." " Hakane Ammi but inda mu din ai kin san komai yafi tafia bisa tsari kuma babu danne hakkin wani, sa6anin haka nan da za'a barshi sai dai manager kawai ai kinga kowa zai yi abinda yaga dama ne..". " Da wannan ma, amma dai kuna dan sassautawa ko dan saboda iyalan ku suma ku dinga basu lokutan ku kuna zama da su, musamman kai ka ga ka fara tara iyali, dole ne abubuwa zasu bambanta da yadda suke a baya..." Sallamar Zaitoon ne ya hanashi magana kuma dama ba niyyar yin maganar yayi ba sbd bashi da amsar bawa Ammin. Da yake 'kage yake da son cigaba da abinda ya kawo shi hakan yasa batare da 6ata lokaci ba ya fara aika kayan ituwan zuwa cikin sa. Duk ba wani da'din su yake ji ba amma gudun kar Ammi ta sake complaining ya sanya shi daurewa ya cusa su a dole. Da gamawar sa ya sake tambayar Ammi kayan tace" Ka matsa Rayyan Allah yasa dai Alkhairi..." " Insha Allah Ammi.." " Suna can 'dakin Safaa..kaje ka duba.." " Tsaye ya mi'ke da hanzari sai dai tuno wani abu ya sanya shi sake duban Ammi..." Amma Ammi 'dakin Safaa ba shine wancan yarinyar take ciki ba..." " Shine ". " Ammi idan na tarar ta 6ata min kayan m..." " Kar ka damu babu abinda ya ta6a kayan ka, Zaitun bata da wannan rawar kan da 'kyar ne idan tasan da zaman su a 'dakin ma..kaje ka duba drawer 'karshe da zaka ga alamun ma ba'a bude shi kwata kwata, key din sa na can saman sa ka duba..." Tashi yayi ya fita..'Dakin gyare yake tsab sai 'kamshi dake tashi, bai wani tsaya dogon nazarin inda ta samu turare ba dan yasan Marwa ce, Ammi kanta tana siya mata turare ya sani. Sai da yabi drawers din duk ya bi ya bu'de bai kuma san dalilin.sa nayin hakan ba, Kayan Mufeeda ya gani wanke kuma a goge jere reras bisa tsari sosai suka birge shi hka ma ma'abociyar gyaran, ko ba komai bai ta6a samun ta da 'kin jinin sa ba, ta kuma kula da Mufeeda tamkar ranta..." Rufe drawers din yayi yana jin bugun da zuciyar sa ke masa. Hakan yasa shi jingina da jikin drawern Yana dafe saitin zuciyar tasa. Ganin kamar zai 6ata lokaci ya sanya shi.janyo side drawer ya hau ya dubo key din ya bude. Sai da ya barbaza kayan kaf a 'kasan tiles, yana bi yan kallo, photuna da takaddu da komai da ya shafi Nadia mai muhummanci da akasin sa. Takardar Anti- natal 'din ta da kuma kati da sauran Scan results 'din ta duk ya ware gefe ya duba su da kyau..zuciyar sa na harbawa. Gani yake tamkar ba dai- dai idanun sa suke game masa ba. Meyasa duk a baya bai ta6a tunanin duba cikin da kansa ba? Meyasa bai ta neman ganin takaddar Scanning d'in ta ba..?" Gaba 'daya ji yayi komai.ya kwance masa har wani jiri jiri yake gani hakan yasa shi zama bakin gado dan tabbas zai iya kaiwa kasa batare da ya farga ba. Ya bude ido ya rufe fin 'kirga, ya girgiza kansa yafi sau shuri masaki da tunanin ko de bacci yake har yake mafarki amma duk babu ko guda daga cikin tunanin sa da yake dai dai, abin nan dai da yake gani shidin ne. Ashe cikin 'yan biyu Nadian sa ke 'dauke da shi a lkcn batare da ya sani ba....? Harha'da komai yayi kawai ya cusa cikin jakar da suke ciki ya maida ya kulle drawwer yayi waje illah takaddar dake hannun sa. Ko sake bi ta saman Ammi bai yi ba balle sashen Amrah ya sake hawa motar sa yayi gaba abinsa bai zame ko'ina ba sai unguwar Anty Madeena. Kafin shigar sa gidan ya tsaya ya sallaci maghrib da ta 'dan 'kwace masa sannan yayi zaman azkar. Zaitoon ko da ta dawo 'dakin ta tarar kan tiles 'din kaca kaca da 'kura ba 'karamin mamaki ya kamata ba dan tasan ba haka tabar shi ba. Sai da tabi dakin da kallo sosai sannan ta fahimci anma shigo cikin sa. Sanin da tayi cewar ba ita kadai ke rayuwa cikin gidan ba uwa uba zaman alfarma take ba itace mamallakiyar dakin ba ya sata cire damuwa ta gyare tsab ya koma tamkar bashi ba. Ganin Isha'i ta gabato kawai ya tsaya har aka sallaci isha'in, bayan haka ma ya 'dan 6ata lokaci sosai wajen azkar gami da addu'o'i sannan ya fita ya 'karasa gidan Anty Madeena. Sai dai cikin rashin sa'a sa6ani suka buga, domin basu jima da fita zuwa Shoprite ba da Abbahn su Badi'a da Anty Madeena hadda Mufeeda. Bai ji da'din hakan ba Amma albishir 'din da yazo mata da shi baya jin zai iya tafiya batare da ya isar da shi gareta ba. Dan hka yayi zama sa a parlon ba'ki yana jiran dawowar su, nan yake ta sake- saken abubuwa, babu abinda bai zo kansa na duk abubuwan da ke faruwa gereshi ba, yasan dole Allah na jarabtan bayin sa da komai dake cikin duniyar nan fatan sa Allah ya bashi ikon cinye tashi jarrabawan batare da ya kuskure ba. Tsabar rashin natsuwar da ya shiga cikin 'yan kwanakin nan da baya samun bacci, zaman sa anan har bacci ya 'dan fara 'daukan sa..bacci kuma mai nauyin gaske. Sultan da dama yake bibiya da fakon duk motsin Rayyan cikin 'yan.kwanakin sai abin ya 'kara tasiri, tun bayan tsawar da Rayyan ya doka masa ranar nan. Sosai ya baza mutanen sa suke lura masa da shiga da fitar sa, a yadda labari yaje wa ya fahimci dole akwai wani abu, domin shiga da fitan da yake gidan Anty Madeena yafi yawa..hatta fitan su zuwa asbiti tare da yarinya sai da aka sanar masa sai dai babu wanda yasan abinda ya kaisu, wannan dalilin ya sanya shi 'daura ayar tambaya akan Yarinyar, ba kuma zai samu natsuwa ba har sai ya tabbatar da cewa bata numfashi, Abinda ka'dai Allah ya hana Sultan fahimta game da yarinyar shine kamannin ta shi be taba tsayawa ya 'karewa kammanin ta kallo ba balle ma ya fahimci wani abu. Sannan sun yi magana da Amrah ya kuma fahimce ta sosai, tun bayan zuwan su asbiti da Rayyan basu kara samun isashsen lkcn sa ba, gidan ma bari yayi gaba 'daya, tana kuka take masa bayani...tashin farko ya fahimci inda matsalar take, yasan babu mmk Rayyan ya gano cewa Arfan ba jinin sa bane shiyasa ya dauke musu wuta, in kuwa hakane asirin sa dab yake da tonuwa kenan, ayanzu Rayyan abinda ya sani kawai shine bashi da alaka da Arfan ya kuma yi reacting ina kuma ga cewar ya fahimci cewa yaron na sane...koma ya fahimta bazai bashi damar bayyana ta ga kowa ba. Masu bibiyan masa diddigin Rayyan basu san cewa Anty sun riga sun fita tare da sauran iyalan ta ba dan su Rayyan suke bi, tun shigar sa unguwar kuma bai fita ba haka suma basu fita ba basu ga wani ya fita gidan ba haka babu wanda fita tun shigar sa. Haka suka sanar da Sultan..dan haka yace kawai suyi kokari su haura gidan su banka wuta ta ko'ina ta yadda zai tashi lokaci guda kafin kowa ya farga yayi illar da suke bukata dan sam baya so Rayyan ko Anty Madeena 'dayan su ya fito araye...... Salmerh😘 [8/11/2022, 11:42 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Wattpad@* _Serlmerh-md_ 🅿️ *...67* .......Hakan kuwa akayi, lokaci guda kawai wuta ta kama ci a gidan, gateman kuwa dukan tsiya sukai masa sannan suka kulle shi cikin 'dakin sa ko motsin kirki bai iyawa. Daga Rayyan sai Nuwaira cikin gidan, itama tuni bacci ya fara 'daukan ta dan haka bata farga da wutan da wuri ba har sai da wutar ta mamayi ko'ina cikin gidan..Lokacin da jama'ar unguwa suka farga da wutan take suka fara kawo 'dauki, a dai- dai lokacin ma'aikatan Sultan suka dulmiya cikin su kamar masu kawo 'daukin suma. Ihun Nuwaira ne ya fargar da shi sai kuma salatin mutane da 'kauri da tiririn wuta dake ratso shi. A firgici ya mike zai leka window yaga babu hali sbd wutar tuni ta hauro Salati ya fara ya nufi kofa sai dai ina tuni wutar ta ratso parlorn ta kama kujeru babu ta inda zai iya tseratar da kansa ma balle wani ban da ihun Nuwaira da ya ke iya jiyowa. 'Kofofin ma munafukai da jin wutar duk suka 'kara kamewa....Jikin bango ya kalla yaga babu fire estinguisher anan 'kasa, Parlon saman Anty ne ka'dai dama yake ganin akwai basu sa a kasan ba sa6anin gidan su da yake kota ina an sanya shi ko wani 6angaren. Kuma wutar ta haura sosai abinda ma ya takaita saboda POP dake saman parlon ne shiyasa wutar ta tsaya iya 'kasan amma yasan idan wutar ta mai yawa shima 'din na iya tsagewa so yake ya samu damar haurawa saman stairs amma hakan ya gagare shi. Ihun Nuwaira da yake faman ji yana sake rage sauti ya fi 'daukan hankalin sa sosai. Kalle- kalle ya fara ko.zai samu abinda zai iya tallafa masa amma bai ga komai ba, 'Karfen labile da yagani ya jawo ya take da takalmin sa da yake labilen ya riga ya kama da wutar shima, da shi yayi amfani wajen kawar da abubuwan da ke cin wuta agaban sa ya tsallaka gefen da yake jiyo ihun Nuwaira. Bakin 'kofar ta take tsaye tana ihun, wutan ne ya hanata wucewa tuni kuma haya'kin ya gama ratsata duk ta fara yin sanyi...cikin sa'a sai yaga daga waje ana faman 6alle windown nata ma da yake suma awajen suna jiyo ihun nata. Ana gama 6allewa ya taimaka mata ta fita 'yan waje suka kar6e ta cikin sauri yayin da hankalin wasu ya koma kansa cike da hanzari ya fara yun'kurin fita shima amma kafin ya kaiga hakan window ya 6antaro ya fa'do masa kan hannun sa, cike da tsananin wahala ya wani saki ihun aza6a ya zube kasa numfashin sa na 'kokarin 'daukewa. Hankalin masu taimakon tashi yayi sosai, dayake ma kuma unguwar ta manya ce tuni sun yi magana da 'yan kwana kwana hakan ma basu tsaya jiran su ba ruwa suke 'debowa suna watsawa a kokarin su na ganin 'karfin wutar batai tasirin da zata iya illata wa'danda ke cikin ba cikin sa'a ma da fa'duwar Rayyan sai yan kwana kwanan suka iso har motoci biyu. Su Anty Madeena ma Neighbours din su sun 'kira su sun dawo, fahimtar cewar da Rayyan acikin gidan ya sa Anty Madeena fara kuka sosai tana fa'din ataimaka mata...yaron ta na ciki. Ganin abinda ya faru da shi kuwa ya sake 'dugunzuma hankalin ta..ta tashi hankalin ta ta kuma tada na sauram mutanen da ke wajen. Hakan ne yasa da isowar 'yan kwana kwanan aka fara kashe wutar daga inda Rayyan ya fa'di,....da mutuwar wutan kuwa wasu matasa suka fito da shi kawai aka wuce da shi hospital batare da wani.6ata lokaci ba...daga shi har Nuwaira da tuni take a sume. Babu wanda yasan mafarin wutan balle asan makasudin ta...babu wanda yasan dalilin ta. Amma ba 'karamin tada hankalin ahalin Sa'ad Auta wutar nan tayi ba. Daga Rayyan har Nuwaira jikin su bai kone ba but dole suna bu'katar kulawar likititoci...Musamman Rayyan da ya sha'ki hayakin sosai fiye da Nuwaira, an daiyi nasarar zu'ke haya'kin da ka'dan ya rage yayi masa illa ma dan tuni hayakin yayi masauki cikin zuciyar sa dalilin kenan da yasanya duk da an cire hayakin amma sai da sai da ya fa'da doguwar suma, domin kansa ya bugu sosai ga muguwar karayar da yayi a hannun sa na dama ga kuma zafin wuta da hayakin da ya sha'ka. Ammi kuka da hawaye take haka ma Marwa da Amrah hatta Zaitoon sai da zubda masa 'kwalla dan ita ta fara kuka ne ma tun daga lokacin da labarin 'konewar gidan Anty Madeenan ya riske ta sanin cewar 'diyar ta na gidan...har Ammi na bata bakin cewa tayi hakuri..ita kanta Ammi a lkcn bata san cewa da gudan jinin ta a ciki ba...hasalima dan shi aka tada wutar gaba 'daya batare da sun san da hakan ba. Sai da da suka je suka tarar da Mufee na nan zam a hannun Badi'a babau.abinda ya same ta sai dai Rayyan, anan zuciyar su ta karye gaba 'daya..Kukan da Zaitoon ke yi zaka rantse da Allah cewar Mufeedan ta ce aka ce ta rasu, ba 'karamin tausayi Rayyan ya bata da ganin yadda 'kasusuwan hannun sa suka sauka ba. Ammi kam ai ba labari ma, yah Ilahi tamkar zata shi'de idan ka ganta duk ta fice hankalin ta haka ma sauran, Sultan ne dai babu shi a wajen ba kuma dalilin sa. Rayyan ya sha ba'kar wahala wajen 'daure hannun nan inda aka yi sa'a ma yana cikin yanayin suma ne shiyasa sukayi at risk domin ta iya yiyuwa idan ya dawo hayyacin sa su tarar basu yi 'daurin bisa tsari ba sai sun sake amma dai basa fatan kasancewar hakan da iznin ubangiji. Rayyan ya kai kimanin kwanaki shida kwance a asbitin batare da ya san inda kansa yake ba duk wani kokari daya kamata suyi sun jarraba dan ganin ya dawo hayyacin sa amma abin ya faskara har su Ammi sun fara tunanin fita waje da shi amma Fawwaz yace a a, yace a barshi tukunna bama sai an fita ba, dan dole can 'din ma ko an je duk abinda suka yi anan shi din za'a maimaita acan, abinda kawai ake bukata yanzu farfa'dowar sa ne...da dole sai an yi hakurin hakan. Yace inda hali ma abinda yafi kawai a maida shi gida zai fi natsuwa, shi zai na zuwa duba shi inyaso duk ranar da aka samu nasarar farkowar sa sai a dawo asbitin a'karasa abinda ya kamata. Anty Madeena ta so tace a a amma Ammi tace ta bari ai aikin su ne shi yasan abinda yafi dacewa ai..ko ba komai tasan Fawwaz aminin Rayyan ne ba zai ta6a yin abinda yasan zai cutar da shi ba. Da wannan shawarar aka dawo da Rayyan gida sai dai kuma wani 'karin tashin hankali da suka fuskanta sine...kwanan sa 'daya agidan kwatsam sai mahaifiyar Amrah tazo gaida shi itama, dan tun faruwar lamarin sau 'daya tazo bayan nan suka yi wata 'yar tafia sai jiya ta dawo shine yau tace bari tazo duba shi. Lokacin da tazo 6angaren Ammi.ta fara zuwa bayan gaisuwa suka dan sake jajantawa sai suka tattaro izuwa ga sashen Rayyan 'din bisa rakiyar Ammi. Wannan karan dole sai da aka 'karawa Amrah masu tayata hidima sbd lalurar mijin ta, duk su Zaitoon sun dawo 6angaren ta, mai raino ma daban, ga su Anty Madeena da ta hana kanta sakat sai da ta dawo gidan itama sbd ciwon Rayyan din Raihana ma tazo tun washegarin faruwar lamarin kuma suna kokarin hudimtawa Rayyan da be masan inda yake ba, wani abin ne dai dole sai matar sa ko Sultan ya kamata suyi masa, hakan yasa suke barin wasu abubuwan ga Amrah. Shigowar Mummyn ta yayi dai- dai da lkcn da Amrah ke gogewa Rayyan jikin sa ga kuma Arfan ma nata kuka, duk sai Amrah ta rikice. Sauri take ta kammala hidimar Rayyan sannan ta dawo ga Arfan, cikin hakan aka sanar da ita Mummyn ta tazo. Zaman jiran Amrah tayi na kimanin mintinan da basu haura sha biyar ba yayin da Raihana ke ta lallashin Arfan da 'kyar yayi shiru, kafin cikar mintina sha biyar din tuni 6acin rai ya gauraye zuciyar Mummyn Amrah. Har ta shiga ta duba jikin Rayyan ranta bai saki ba, ta kuma riga ta kudurtawa ranta hukuncin da yai mata taga yafi dacewa. Ko da suka ke6e da Amrah abinda da ta fara furtawa shine" Daughter jaka kk maida kanki a gidan nan wai ko me Allah ya nuna min..?" Cike da mamaki Amrah ta dubi Mummyn ta. " Jaka kuma Mummy kamar yaya...?". Tayi maganar tana gyaran Arfan dake kan cinyar ta tana shayar da shi. " Ke baki ganin yadda duk kika 'kare ne Amrah..? ke ce kk haifa musu 'dan ne da zasu barki da jinyar sa ke ka'dai ga kuma 'dansa ma da kike fama da shi da wanne zaki ji..?" 'Yar murmushi Amrah tayi tana fadin..." Kai Mummy na sha wani abin ne ma wlh, bafa ni ke jinyar sa ba, Allah duk su ke yin komai ni nawa hidimar ka'dance, wannan da suke ji tamkar ya tashi 'dayan su ya kwanta a madadin nasa ne zasu barni da jinyar sa ni ka'dai...shi kuwa wannan 'dan banzan kuka dama gare shi da ni da Nannyn.nasa duk isar mu yake yi..." Ta 'karashe maganar da jan hancin Arfan tana duban fuskar sa... With serious tune Mummy Amrah cike da bakin rai tace. " Ni dai wallahi bazan barki zama jinyar wani 'kato can ba maza tattaro kayan ki mu wuce gida..". 'Dan 6ata rai Amrayi tana karkace wuya tace. " Haba Mummy...mijina ne fa kk ce wani 'kato bayan na fada mk ba wata hidima da nake ni dai babu inda zani wallahi..." " Wallahi Allah sai mun tafi Amrah ta ya ma hankali na zai kwanta bayan na tafi na barki alhali idona ya riga ya gane min? dole ma mu tafi in kinga ban tafi dake ba 'kaddara wata uwar kk canza bani ba..amma matsawar ina nan a matsayin mahaifiyar ki to bazan ta6a barin ki cikin wannan 'kuncin ba..yaso idan Allah ya tashi kafa'dun sa kya dawo ki cigaba da zama...amma irin wannan wahala haka ina zaki iya juran sa na tabbata kafin a ce ya samu sau'ki ke kuma duk kin 'kare nima jinyar ki za'a barni dashi..." Haka ta koma Parlor ta bar Amrah nata zum6ura baki tana ha'da kaya. Ko da suka fita babban Palor su Anty Madeena ne zaune da Raihana sai kuma Sultan da shigowar sa kenan. Cike da mamaki suke duban Amrah ganin ta da lullu6i da handbag tama kasa duban idanun su sbd nawin abinda Mummyn ta ta tsefe idanu take shirin aikatawa. " A ah lafia na ganku cikin shiri haka, hala unguwa zaku..?" Mummyn Amrah ta.bada amsa da fadin.." Ba wata unguwa, tafia zanyi da ita sbd ba ma'aikaciyar jinya na haifa ba..." Cike da mamaki duk suka dube ta hatta da Sultan kuwa. " Hajia Hafsat ban fahimta ba..me kk son fa'da ne...?" Anty Madeena tayi 'karfin halin tambayar ta. " Erh ina nufin bazan barta zaman jinya ba...tafia zanyi da 'diya ta...ku samu wanda zai muku jinyar 'danku amma ba Amrah ta ba..." Amrah ji tayi tamkar ta saki ihu sbd takaici. Taya ma Mummyn ta zata ce haka, a ganin ta ai hakan ma butulci ne, itafa tana 'kaunar mijin ta kuma bata ga wani abu da tayi masa da har za'a ce ya shiga layin 'kunci ko wahala ba..duk ma yawan mutanen gidan nan amma duk da haka ta wani ce sai sun tafi..abinda ma yafi tsaye mata arai shine cewar da Mummyn tayi wai da wanne zata ji a cikin su yanzu, da 'danta ko kuma da kulawa da majinyacin da babu ma tabbas 'din zai rayu...?" Kuma ta fa'di maganar ne fa ga Anty Madeena da Raihana ga kuma Sultan ma zaune..sannan ta tabbata wasu ma'akatan gidan ma sunji salon su rainata ta ko menene. Amrah ji tayi da tana da ikon bijirewa mahaifiyar tata da babu abinda zai hana ta bijirewa ta'ki binta. Amma tasan halin mahaifiyar ta da zafin rai sosai akan duk abinda ranta bai 'dauka ba. Wannan maganar sosai ya yiwa Anty Madeena ciwo haka ma Ammi da ta samu labari bayan tafiyar su..hatta Raihana itama abin ya 'kona ta. Salmerh 😘 [13/11/2022, 2:59 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Wattpad@* _Serlmerh-md_ 🅿️ *...68* ........Sosai Anty Madeena take masifa Raihana na tayata, duk da yake ita din ba mai magana bace amma yanayin da lamarin ya kasance sai da yasa fusata ta 'ka'kalo masifa 'karfi da yaji take.taya Anty Madeena dan sosai ransu ya 6aci a ganin su abinda mahaifiyar Amran tayi ba komai bane face cin zarafin su. Marwa dai na gefe bata ce komai ba. Da 'kyar Ammi ta samu da ban baki Anty Madeena ta sarara suka yi shiru amma maganar ta kasa barin ransu, wannan kam hatta da Ammin ma 6angaren ta abin haka ne. Da za'a tona ranta ma tafi su shiga tashin hankali sai dai kawai tana dannewa ne. Ko da dare kusan kwana tayi tana tunani bata yi bacci ba, musamman idan ta tuna Rayyan ta tuna yanayin rayuwar sa amma yau rana tsaka ake gudun sa sbd lalura ta same shi sosai abin ke yi mata ciwo. Rayyan dai Rayyan dai. Ganin baccin ba zuwa mata zai yi ba ya sa ta dauro alwala ta ringa sallah tana nema masa afuwa wurin mahalicci. Ha'ki'ka 'dan Adam ba'a bakin komai yake ba, duk yadda kake jin kanka kake ji cewa kai wani ne bisa tsari da yaddar ubangiji kake komai, cikin yan kalilan din sakanni zai iya canza maka rayuwa ta inda yaga dama. Bayan kwanaki biyu. Ammi ba 'karamin tausayin tilon 'dan nata take ji ba, sosai ta damu da wannan rashin lafiyar tasa, kwana take ta tashi cikin rashin sukuni da fargabar kar ta wayi gari ace mata shima babu shi. Bata san halin da zata iya shiga ba matukar ta rasa shi duka tasan kadan.ne daga hukuncin Ubangiji amma tasan dole rashin sa sai ya jijjiga ta, yanzu da yake kwance take ganin nasa ma ya takare, abinci wannan sai an tuna mata cin sa kafin take samu tayi aqueezing lkc taci shima ba wani ba mai yawa ba sbd tsantsan damuwa. Har a lkcn ko dan yatsansa bai motsa ba, yana nan ne tamkar gawa amma an tabbatar mata da cewa da rai tattare da shi....amma ace yana cikin irin wannan mawuyacin halin amma matar sa ta guje shi, duk da tasan yes ba laifin Amrah bane amma sam abin ya matukar bata mamaki, bata ta6a zaton hauka da rashin hankalin mahaifiyar Amrah ya kai har hakan ba. Sai dai duk ba wannan ne damuwar ta ayanzu ba, burinta Rayyan ne, burin ta taga ya tsaya da kafafun sa tamkar baya, bata da wani aiki a yanzu illa yi masa addu'a ba dare ba rana. Duk da kusan raba dare da tayi tana tunani hakan bai sa ta kasa tashi sallar asuba akan lkc kamar yadda ta saba ba...domin 'kage take ta taje taga Rayyan ko an samu wani cigaba a lafiyar sa. Baya ga haka akwai wani abu aranta data idda yanke shawarar aikatawa kuma da shi ta kwana cikin ranta. Tun kafin gari ya gama yin haske ta kira Fawwaz ta sanar da shi halin da ake ciki, ta kuma nemi shawarar sa kan hukuncin da ta yanke na cewar ko za'a mayar da Rayyan din karkashin kulawar asbiti hankalin ta zai fi kwantawa fiye da zaman sa a gidan alhali babu takamamman me kula mata da shi illah Fawwaz din...Fawwaz yace hakan ma ai karkashin kulawar tasu yake tunda 'dakin da yake a gidan baya da bambanci da na asbitin, duk wasu na'ura da ya kamata su tallafawa lafiyar sa an samar da su suna kuma amfani. Fawwaz yace tayi hakuri, ta kuma kara akan wanda take yi, dan yasan dole ne ta damu shi kansa karfin hali kawai yake amma sanin da yayi babu yadda zasu yi yasa shi dangana ya mi'kawa Allah komai. Batun Amrah ma duk ta cire shi a ranta yace a samu wani amintacce inma biyan sa ne a ri'ka yi Ammi sai yana kulawa da Rayyan din. Ammi da hanzari ta katse shi..dan sam bata jin ta yadda da kowa a wannan halin balle har ta iya bashi ragamar kulawa da Rayyan bazata iya ba. She wish da namiji ce ita da ta tabbatar babu abinda zai mata shamaki da kulawa da gudan jinin ta musamman a yanzu da yafi bu'katar taimakon wani nashi makusanchi. Fawwaz ne yace toh sai ayi magana da Sultan yana zuwa yana masa wani abin kafin aga yadda hali zai yi, idan anyi sa'a ma ya tashi nan kusa ai shikenan...dan a binciken su da suka gudanar sun fahimci cewa yana iya farkawa a ko wani lkc ma. Yadda Fawwaz ya bawa Ammi shawara haka tayi Sultan ne ya fara taimakawa Rayyan 'din da tsaftace jikin sa, a lokacin kuwa sosai 'yan uwa, Neighbours da abokan arziki dama ma'aikatan sa ke zuwa gaida shi, kowa yazo kuwa sai ya tausaya masa matu'ka, masu raunin zuciya kuwa har na zuvda kwalla, ana kuma yabawa sosai da 'ko'karin Sultan akansa shi kansa Sultan 'din yadda ake yaba masan na yi masa dadi dan babu wanda ko alama zai iya zargin sa akan lamarin, sai dai ba'ayi kwanaki uku cikakku ba ya fara jan baya har sai an 'kira shi a waya an tunasar da shi kafin yake tuna cewa ashe Rayyan na kwance. Anty Madeena da dama ba wani shiri ne sosai tsakanin su ba sai haushi duk ya 'kara cikata, dan ita indai akan alhalin yayantan nan ne toh bata saka kowa sama da su. Bata dai tanka ba but cikin ranat take jin bb dadi da halin ko'in kula da Sultan ya fara nunawa. Karyar yau daban ta gobe daban a duk lokacin da yasan bai kyauta ba, ko kuma aka kira shi kafin yazo...galibi ma Marwa ce, idan taji su Anty na mitar rashin zuwan nasa sai ta koma gefe batare da sanin su ta kira shi dan ita kanta bata jin dadin abinda yake yi din, ko bakomai Rayyan ai jinin ta ne, Company, kullum aka tuhume shi sai batun Company ko waye ya fa'da masa cewar Company ne ya dame su a halin yanzu? Babu wani abinda suke nema a halin yanzu illah lafiyar Rayyan kadai. Abin mamaki Sultan sai ma ya tsiri tafiya zuwa Lagos batare da sanin Ammi ko Marwa ba, har sai da ma ya sau'ka kafin ya kira ya sanar da Marwa anan su Ammi suka ji labarin tafitar tasa. Washegari da safe kuwa suka rasa yadda zasu yi da Rayyan. Dole Anty Madeena da Raihana sai da suka sake 'dago maganar Amrah duk da Ammi ta hana su amma a ganin su yazam dole ne su jimanta a wannan ga6ar sbd kowa na da ranar sa, kowa kagani cikin duniyar nan yana da amfanin da Allah kadai ne ya barwa kansa sanin sa kafin ya bayyana ta ga bayin sa. A yau ga ranar Amrah, ga bu'katar Amrah nan ya taso musu amma kuma tai musu nisa. A zahiri mahaifiyar Amrah ta nuna cewa ba 'kauna irin wacce Allah da manzon sa suka koyar da mu suke yiwa Rayyan ba, tunda sun guje shi ne a lokacin da larura ta same shi da har suke tunanin mawuyaci ne ma ya tashi kamar baya, ta mance cewa mutuwa da rayuwa duk na Allah ne. Ammi shiru tayi tama jinsu, ita kanta abin ya dame ta sosai, tasan ba wai rasa wa'danda zata biya kula mata da shi tayi ba, ba wai ku'din biyan ta rasa ba tsoron ta kawai kar ta 'dauko wanda zasu zame mata ajalin 'daa da kudin ta ne ...baya ga haka ma ga su Huzaifa dake nan kusa amma sam bata ji zata iya basu wannan yadda da amincewar a halin yanzu. Fawwaz ne da ya zo duba shi shi ya tsaftace masa jikin sa bayan yayi masa duk wani abinda ya san aikin sane hadda ma wanda ba nashin ba sannan ya tafi. Zugum suka yi a parlourn dake 6angaren Rayyan 'din hirar kirki ma rabon da suyi ta yadda ya kamata har sun manta. Kowa yayi shiru tunanin da ke kai kawo cikin zukatan su daban. " Ni wallahi Ammi dama nema masa wata matar akayi aka yi musu aure da sai hankalin mu yafi kwanciya..." Cike da mamaki gaba daya suke waigo suna duban Raihana da ta fadi maganar da iya gaskiyar ta... Ganin kallon da Ammi ke yi mata ne yasa ta cigaba da fadin..." Erh mana Ammi, ki duba kiga yadda duk kuka rame kuka canza duk sbd damuwa Ammi, kuma na tabbata rashin Amrah na daya daga cikin abinda ya sake zurfafa abin sbd muna ganin tamkar tunda Amrah ta juya masa baya kowa ma na iya juya masa duk na nasan ba haka bane, amma bazamu ta6a gane gaskiyar ba har sai mun gwada sa'ar mu...a samu wata a aura masa na tabbata baza'a rasa na Allah ba, dan ba duk aka hadu aka zam 'daya ba, a duk lkcn da wani ya kika ya guje ka ya nuna maka kai ba komai bane ma'ana baka da muhimmanci cikin rayuwar sa a daidai lkcn zaka samu wani kuma wutan kaunar ka ke sake ruruwa masa a zuciya...Insha Allah bazamu rasa wacce zata kaunaci Yah Rayyan ahakan sa ba, ta kuma zauna da shi ta kula mana da shi har zuwa lkcn da zai samu lafia, nasan kuma ko shi yaji abinda ya faru da yadda Amrah ta guje shi da kuma yadda matar ta kula da shi bazai ce a a ba, Anty Madeena ko ba gaskia na fada ba....." Ta karasar da maganar da waigawa ta dubi Anty Madeena. Wani banzan kallo Ammi ta jefa mata, Raihana da ta fahimci manufar Ammi sai ta kasa da idanu tana jin babu dadi cikin ranta. Yayin da Anty Madeena ta taji tamkar ta rungume ta sbd yadda shawarar tata ya shige ranta. Da sauri ta cafko hannun. Raihana cike da jin dadi gami da nuna tsantsan farin cikin ta a fili take fadin. " Allah yai miki albarka Raihana, wallahi tamkar kinsan menene acikin raina tsawon kwanakin nan, abinda kullum nk kwana nake tashi da shi kenan, amma gudun yadda za'a karbi zancen ya hana ni furtawa ga kowa sai gashi kema kinyi tunani irin nawa..." Wannan magana ta Anty Madeena ita tasa Raihana ta dan saki ranta jin cewar tana da partner...tasan babu mamaki shawarar tata ta iya samun kar6uwa... Ga Ammi Anty Madeena ta maida duban ta tana mai cigaba da fa'din..." Dan Allah Hajia Aseeyah a duba lamarin nan dai...magana ce muhimmiya, wallahi kuma na tabbata zata taimaka mana sosai wajen saukaka damuwoyin da muke ciki gami da tunanin mafita...." Cike da zafin rai Ammi tana duban Anty Madeena tace. " Lalle Madeena, ban ta6a tunanin shirmen ki na biyewa zancen yaran nan har ya kai hakan ba...taya kuke tunanin hakan zai faru ma? Kun ajiye matar ne, ko kuwa kun ajiye iyayen da zasu haifa maku yarinya haka nan kawai kuma su 'dauke ta su bawa majinyacin 'danku auren ta alhali kunsan halin da yake ciki, yana nan ne tsakanin rayuwa da mutuwa..babu wanda yasan mai gobe zata haifar...". " Ji wani magana dan Allah...Haba Hajia Aseeyah! da kanki ma kike fa'din hakan toh me.kike tunanin wasu kuma zasu ce ...?" Cewar Anty Madeena tana duban Ammi. Marwa dake gefe banda kwalla babu abinda take sharewa, wai yau Yah Rayyan din su ne ake duk wannan muhawarar akan sa...alhali gashi can kwance bai masan wace duniyar yake ba. Sosai take tausaya masa take tausayawa wannan hali da yake ciki. Anty Madeena ce ta cigaba da fa'din" Nasan samun matar zai fi mana wahala dama, amman Insha Allahu bazamu rasa ba, mu bincika, wallahi ko min talaucin gidan su indai mun yadda da tarbiyar ta da kuma tsoron Allahn ta zamu iya jarrabawa mugani..." " Madeena sai kace wata ba'kuwa cikin rayuwar nan, har yanzu baku saduda da sharrin mutane kun fita harkar mutane ba ashe Madeena?...bayan tabbatar da bayanin da gateman din gidan ki yayi har yanzu baki gama fahimtar cewa da shiri aka sa wuta a gidan ki ba ko sbd aga bayan ku duka? ...shin kinsan waye yayi ne..? Ko kuwa har kin mance kike si kice min...? Me kuke sake nema? Me wata matar zata sake yi mana agidan nan...?" " Hajia Aseeya ba haka nk nufi ba, taya ma zan iya mantawa, wannan abin ba abinda mutum zai iya mantawa cikin sauki hakan nan kawai bane but halin da Rayyan yake ciki abin dubawa ne, shine babban abin dubawa, wallahi tausayin shi a kullum karya min zuciya yake sai inga kamar muma da gudunmawar mu wajen guje masa bayan guje masa da Amrah tayi...yau idan ya tashi ya fahimci guje masa Amrah tayi ya kike tunanin zai ji a zuciyar sa Hajia Aseeyah? kina tunanin bazai ji zafin abin bane? Saukin da zamu samu shine kawai ya tara Amrah ta guje shi amma mun aura masa wata matar domin ta bashi kulawar da bai samu wajen Amrah ba..muma kanmu ai abin zai fi zuwa mana da sauki, in ba haka ba da wacce damuwar zamu ji?..ta rashin lafiyar sa ko kuwa ta rashin me kula mana da shi..". " Wannan duk na Allah..mu bar masa komai a hannun sa Insha Allah babu wani abu da zai faru...". Cewar Ammi. Raihana ce ta sake fadin..." Duk da hakan dai Ammi a duba lamarin...kinfi kowa sanin cewa Yah Rayyan na bukatar wani kusa da shi yanzu..." " Hmmm....." Ammi ta saki ajiyan zucia mai 'karfi, daga hakan kuwa bata sake fa'din komai ba. Washegari da safe ma babu wanda zai goge masa jiki ya shafa masa magani dan babu Sultan, dole Ammi ce tayi da kanta...Anty Raihana ta tayata. Ko lkcn da Fawwaz yazo ma tuni sun gama masa komai dan Ammi cewa tayi bazai yiwu su 'daura masa dukkan nawin kulawa da Rayyan din akansa ba. Har aka kwana biyu ita da kanta ke masa komai, ba kuma su sake tada zancen ba dan Ammi bata 'kara basu fuskar maganar ba. Sosai suke tausaya mata sbd sunsan ba dadin jikin ta take ba itama amma tsoro da fargabar halayyar mutane yasata saduda take ta hidima da shi...burinta a kullun taga ko da dan yatsansa ne yayi motsi amma yaci tura. Dole Anty Madeena ta sake tada batun Raihana ma ta tayata. Marwa dai bata ce komai ba da yake ba sa'annin ta bane su duk, kuma ba'a musu tarbiyar tsoma baki cikin maganar manya ba, tana nan dai ta buga tagumi a gefe tamkar yajin 'kosai. Ita kanta tana da tata shawarar cikin ranta amma bata san waya kamta ta tunkara ba hakan yasa ta rike abinta cikin ranta take binsu kawai da idanu. Cike da ginshira da zancen nasu Ammi da rabon ta da fara'a cikin gidan tun kafin kwamciyar Rayyan, ta dube ta sannan tace. " Hakane Madeena, amma please ku bar batun matar nan tukunna muyi ta lafiyar sa first, kowa tsoro yake bani a yanzu, ita kanta Amran ma ba sanin zuciyar ta muka yi ba, tunda ga 'karamin misali tun tafiyar ta su ko a waya ai bata kira taji ya jikin nasa ba balle muyi tunanin dama can bada san ranta tabi mahaifiyar tata ba, toh itama da take matar sa, suka yi zama da ita na wasu shekaru balle ace wata sabuwar matar daban da bata san waye shi ba, bata san ya halin sa yake ba kuna tunanin zata fi kaunar sa har ta kula da shi yadda muke so ne? bana tunanin wannan abin me yiyuwa ne Madeena bayaga haka ma zucia ta bazata ta6a iya jin yadda ko sakewa da ita ba matu'kar Rayyan 'dina na kwance bazan iya kwantar da hankali na in barshi da wata can daban wai matar sa ba...." Wani abu ne ya tsikari zuciyar Marwa da yasa ta dubi Ammi da sauri, sai yanzu ta fahimci Ammi, ba wai auren ne bata so ba kawai tsoron mutame take a halin yanzu...tsoron da bazai iya barinta amincewa da yi masa auren ba duk da yake tasan cewa auren ne kadai mafita a hakin yanzu. Bakin ta har na rawa wajen fa'din... ....." Ammi... Sai kuma tayi shiru zuciyarta ya gama cika da fargaba. Yayin da hankalin su da idanun su duk ya koma kanta. " Ammi har Zaitoon ma baki yadda da ita ba kamar sauran...?" Ta fa'da da sanyin sautin da ke tafe da tsananin fargabar maganar tata. Dukkan su duban su suka kai gare ta hatta Ammi da tama kasa fa'din komai. Ba ita ka'dai ba hatta Raihana da Anty Madeena ma basu ta6a kawo Zaitoon cikin ransu ba maganar Marwa duk sai ya ankarar da su. " Zaitoon..!" Ammi tace tana duban Marwa....yayin da su Raihana duk suka zuba mata idanu. " Erh Ammi...Zaitoon, kinsan ta Ammi, kinsan halin ta, kin kuma san wani irin tarbiya gare ta Ammi, kinsan abinda zata aikata da wanda bazata iya aikatawa ba, kuma na tabbata Zaitoon bata yi kama da maciya amana ba, Ammi tun zaman mu da ita bata ta6a aikata wani abin Allah wadai ba da kanki ke shaida ce kan haka Ammi, me zai hana a tuntu6e ta ko zata amince ta aure shi, ba wai dan mun gaza ba ko.itama ta gaza bisa ayyuka da hidimar da take yi mana a gidan dama wanda shikan sa take yi masa ba sai dai dan cike wasu ka'idoji ....". A zafafe Ammi tace " Baki da hankali ne Marwa? Kin san abinda kike fada kuwa...?" " A a Ammi, wallahi shawarar Marwa kan hanya take, koba komai duk munsan Zaitoon, kuma mun rayu da ita, nasan ko dan halacci bazata 'ki amincewa da maganar nan ba..." Anty Raihana ce ta kar6e maganar da fa'din haka. Ga Raihana Ammi ta maida duban ta da ta gama wannan maganar. Rai 6ace sosai tace " Kuma dan bamu da adalci sai mu tauye ta? sbd muna tunanin munyi mata halaccin da ya kamata ta saka mana sai mu ce ga abinda muke so tayi mana ko...?". " a a Ammi..."! " Yi min shiru da Allah...Ni ban ta6a tunanin Zaitoon watarana ta biyani abinda nai mata ba, ba ita kadai bama ban ta6a yiwa wani wani abinda da zan nemi sakayya a wurin sa ba kuma bana fatab hakan har abada, dan Allah ku kyale ni, ku sarara da wannan batun dan Allah ku cigaba da addu'a kuna nemawa dan uwan ku lafia yafiye min wannan maganar da kuke yi yanzu....". Anty Madeena de bata tanka ba, banda murmushi babu abinda take yi domin a sarari take hango mafita, mafita ma kuwa mai 6illewa. _Afuwan pls readers...nasan anyi hakuri sosai dani amma a 'kara..bani da time ne sosai shiyasa kukaji shiru amma amma Insha Allahu idan na samu time ko anjima zuwa dare ko gobe zaku sake jina._ *Thank u for your care and calls, Allah ya bar 'kauna, Allah bar zumunchi, Allah ya albarkaci zuri'a...nagode sosai 'yan uwa.*🤝💝 Salmerh😘 [15/11/2022, 10:06 am] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Wattpad@* _Serlmerh-md_ 🅿️ *...69* ........Yadda Ammi tayi kicin- kicin da fuska yasa babu wanda ya sake samun damar tada wancan maganar yayin da Anty Madeena tayi shiru dagangan ta dai fara shirin ta ta 'kasa- 'kasa ba tare da kowa ya fahimci manufar ta ba. Da wayo sai da tayi abinda sauran masu aikin 6angaren nasa duk suka bari illa Zaitoon, batare da sun farga ba kuwa Anty Madeena tayi nasarar fara saka ta yi masa wasu hidindimu a 'dakin da yake kwance. 'Karshe tayi magana da maigidan ta ta kuma fahimtar da shi game da halin da ake kici ta kuma bashi dalilai kwarara ya kuma.gamsu dari bisa dari, domin dama asali Anty Madeena Zara take awajen sa sam bai ha'da ta da kowa ba, da kansa yazo ya samu Ammi as in shawara ya bata bakomai ba, nan fa kan Ammi ya 'kara 'daukan zafi, gefe guda kuma sai taga a hankali hidimar Rayyan 'din na komawa hannun ita Zaitoonan bata kuma san dalili ba. Da dawowar Sultan bayan kwanaki biyar da tafiyar sa, Ammi ta zaunar da shi suka yi tattauna...shi kansa da farko yayi na'am da batun ko dan kar a dinga takura shi ma but jin wacce suke magana akai 'din yasa zuciyar Sultan luguden gudu, saurin canza baki yayi yace da Ammi sam Zaitoon bata dace ba, ama bar wani batun auren.gaba 'daya inda hali, taya ma za'a ce Zaitoon za'a aura masa alhali ba sanin asalin ta suka yi ba...cewar Sultan cike da bakin kishin dake ci masa zucia. Ammi tace ni kaina ina kokonto duk da kuwa na yadda da tarbiyar yarinyar dari bisa dari, amma tsoron kowa ma nk ni a yanzu..bana so in 'debo mana abinda zai zo ya dame mu watarana...." " Gaskia a dai dakata Ammi, inda hali ma a bar zancen gaba 'daya ni da zai fi, dama dai watace daban ba ita ba,.amma Zaitoon 'din nan sam hankali na bai 'dauke ta da auren 'dan uwa na ba...." Zancen Sultan 'din sai ya tsayewa Ammi a zucia, domin tun ganin yadda Zaitoon ke hidima da shi yasa ta fara sakkowa kan dokin na'kin da ta hau, amma batun Sultan ya sake rikita mata tunani ta yadda hatta su Raihana sai da suka fahimci canzawar yanayin ta karaf 'daya. Ranar ko magana batayi sosai ba...hakika Rayyan na bukatar matallafi, in dai kuma ba san zuciya zasuyi ba bai kamata suce Zaitoon tana yi masa wasu abubuwa fannin kulawa da jikin sa zuwa wasu abubuwan hakan kawai sbd yana kwance ba, bacin sun san ba muharrami 'yk agareta ba, gefe guda kuma tunanin ta yadda Zaitoon zata kar6i zancen take sai kuma ga maganar Sultan da ya wargaza mata komai. Ko da Raihana ta tambaye ta damuwar ta bata 6oye mata ba, nan dai Rainahan ta 'dan 'kara mata 'kwarin gwiwa daga baya takaiwa Anty Madeena Zancen suka sake tattaunawa, dan tuni raunin Ammi ya fito fili...dan haka dole ne suma su sake wani yunkuri. Dama ita Anty Madeena can Sultan haushi yake bata, bayaga haka ma yazo ya gudu Lagos alhali yana ganin Rayyan kwance rai a hannun Allah duk da haka bai damu ba yayi tafiyar sa afterall ai yasan shike yi masa komai amma yayi tafiyar sa. Saboda irin wa'dannan halayen nasa ya sanya tun farko baya birge ta...shine har zaizo ya wani sake zuge Ammi sbd munafunci...toh shi ina ruwan sa da koma menene hukuncin da suka yanke a junan sa ai bai sjafe shi ba. A ganin Anty Madeena kenan. Cikin ranta tace ai in kasan wata baka san wata ba. Ta 'karashe da jinjina kai tana mai cizon la66a. Maigidan ta taje ta samu da batun shima yaje ya samu Alhaji Rufa'i da yake ma yanzu jikin nasa da sauki sosai anan suka shirya yadda abin zai kasance. Anty Madeena da Raihana su biyu suka samu Zaitun har 'dakin ta suka zauna a'kasa tamkar basu ne sama da ita ta ta fannoni da dama na rayuwa da kuma shekaru ba. Cike da laushin murya suke ro'kan ta akan ta amince da auren Rayyan ko dan kula da lafiyar sa ma, ta taimake su, ita ka'dai suke ganin dacewa tattare da ita kuma ita din ce suka fi jin yadda da amincewar su har can 'kasan zukatan su. Hankalin Zaitoon ba 'karamin tashi yayi ba, tuni itama ta zube 'kasan tana kuka tama rasa mai zata ce da su. Meyasa zasu bijiro mata da wannan gingimemen lamarin bacin sunsan ba abinda take nema wajen su ba kenan, me yasa sai ita? Meyasa zasu ce ta aure shi bayan sun san ba wata shiri ke tsakanin su ba, me zai hana su tuntubi wata cikin sauran ma'akatan gidan ba ita ba, shin suna tunanin zata amince tayi aure ne bada sanin ko yaddar iyayen ta ba, toh kuma ma idan ta amince bayan ya samu lpy ya matsayin auren yake...? Ko ka'dan bata ta6a jin sha'awar hada inuwa 'daya da Rayyan ba ko cikin mafarki...meyasa yanzu..?" Ganin yadda hankalin ta ya tashi ne, yasa Anty Madeena kamo hannun ta tana mai kwantar mata da hankali, tace kar ta damu, auren ba wai aure ne na damuwa ba, taimakon su kawai zatayi tunda tasan komai akan idanun ta Amrah ta tafi ta barshi ba sai sun maimaita mata ba...so ko bayan ya farka taga cewa bata ra'ayin auren abu mai sau'ki ne kawai a sallama mata batare da kowa ma yasan anyi auren ba balle sakin illah shaidu..." Girgiza kanta kawai take yi..Raihana ne tace.." Yes zai zama ne kamar auren contract ko yarjejeniya kin gane, dan shi kanshi yayan ma ba'a san kar6an da zai wa auren ba but for now dan Allah ki taimaka mana, wallahi mun mk alkawarin babu wata matsala da zata kunno da har zai sa kiyi blaming auren da iznin Allah, amma zasu bata lkc nan zuwa dare tayi tunani. Da 'kyar bakin ta ya iya buduwa tana duban Anty Madeena tana girgiza kai hawaye na sakko mata tace..." Wallahi Anty idan Yah Rayyan ya san wannan maganar kashe ni zai yi...dan Allah ku rufa min asiri ku aura masa wata ba ni ba, Anty idan ya kashe ni Mufeeda fa...wa zai kula min da ita..." Kallon ta kawai Anty Madeena ke yi tana sake kissima abubuwa, har yau har gobe ta kasa gane wace iriyar 'kauna Zaituna ke wa Mufee ta kuma kasa gane dalilin 'kaunar. Bata da buri a yanzu illa ta samun lafiyar Rayyan, daga nan kuma ita ka'dai tasan shirin ta. A lokacin zata fasa duk wani 6oyayyen lamarin da suke 6oyewa ita da Rayyan, bata san wani irin yanayi Ammi Aseeya da iyalan ta zasu tsinci kansu ba in suka ji wannan labarin. Ganin kamar Anty Madeena bazata yi magana bane yasa Anty Raihana cije da kwantar da hankali ta cigaba da fadin " Kinga Zaitoon..ai mun waye Yaya Insha Allahu babu abinda zai faru ki kwantar da hankali kinji, ki nutsu kiyi tunani muna nan muna jiran shawarar da kk yanke..." Daga haka suka fita suka barta ita ka'dai Anty Madeena 'dauke da Mufeeda a hannun ta, Zaitoon kuka sosai take, bakomai ke zuwa ranta ba illa Ammi, shin da amincewar ta ne, ko kuwa ita ta turo su...? Indai hakane mai ya kamata tayi, ya kamata ta amince ne ko kuwa ta ce a a.. shin menene matsayain hallaccin su gareta, ya dace ta watsa musu kasa a ido ko kuwa bai dace ba, shin ya dace ta amince da auren nan ko kuwa bai da ce ba...? " Taimako ne kawai Zaitoona..kuma akwai tabbacin yana farkawa zai bijirewa auren kinga shikenan daga nan zai sallame ki..." Wata zuciyar ta ta bata shawaran haka. After all ma da kunya a ganin ta, akwai tsananin kunya ta dubi tsabar idanun mutanen nan tace musu bazata auri 'dansu ba bacin ita kanta tasan a halin yanzu yanada bukatar matallafi akusa da shi...sai dai abinda kai kawo cikin zuciyar ta shine..shin zata iya aikin da suke so suyi auren ko kuwa, sam bata ji zata iya kwata-kwata, Rayyan fa..? Rayyan 'din Ammi, Rayyan mijin Amrah Yayan Marwa, Rayyan me cikar kamala da izzan nan..wannan 'dan 'kwalisan nan me ji da kyau me murza Naira ganin daman san nan. Baya ga ciwo ina ita ina Rayyan a wannan duniyar? tasan har abada!...dan haka ko ka'dan ita kam bazata iya aikin da suke so tayi musun ba kuma zata fa'da musu gaskia...bazata iya auren Rayyan ba. Yinin ranar kaf bata samu sukunin zucia ba...Marwa ce ma da taje ta dubo Yayan nata ta dawo 6angaren Ammi still bata gan Zaitoon ba tunicsai ta nemi hanyar 'dakin ta. Hankalin ta yaso tashi da ganin yanayin Zaitoon din amma gano inda matsalar take ya sanya ta 6oyayyen murmushi. Ita dama taso hakan tuntuni kawai babu ta yadda zata iya hadawa ne yasa ta basar...dan tasan Rayyan ba abokin wasan ta ba ne, amma taso shi da Zaitoon sosai, shiyasa sau da dama dramar su ke sata nisha'di. Tuni Marwa tayi fuskar tausayi ta 'dora kan ro'kan da su Raihanan sukai mata, 'karshe sai ga su duk sun 'kare da kuka ba Marwan ba ba Zaitoonan ba, dan Marwa tsananin tausayin Rayyan ya kan hana hawayen ta tsayawa kusan ko wani lokaci idan har ta tuna da shi, but ganin wai yau gashi su ne suke rokon alfarmar wata mace akan ta amince ta auri Rayyan ya sa duk taji ta rasa 'kwarin gwiwar ta...Yayin da Zaitoon ke kukan ta mai sauti tana sakin ajiyar zuciya, abin yana ta6a ranta sosai...haka suka kasance kowa abinda yake sa'kawa cikin zuciyar sa daban. Sai da suka gama kukan suka nutsu kafin Zaitoon take tambayar Marwa cewar " Yanzu Marwa idan ban amince da wannan auren ba ya zakiji?" " babu dadi..." " Ammi fa...?" " Itama hakan ne, zaku ma taga cewar kin guji ha'da jini da ita ne a dai- dai lkcn da yake matukar bukatar taimakon ki..." " Marwa..."! " Sincerely speeking Zaitoon ai kinsan bazan mk 'karya ba...a halin yanzu amincewar ki ka'dai kowa ke jira, wallahi zaku ma mufi kowa farin ciki idan kk amince da auren Yayah, wannan kadai idan ki kai mana wallahi kin gama mana komai..." " Kina nufin Har Ammi..?" " Tabbas kuwa...sai ma tafi kowa, dan zai zamana ne bata da haufi akan mai bawa Yah Rayyan kulawa koda bata kusa tunda tasan kece...karkashin kulawar ki yake har zuwa lkcn da zai samu sauki...hankalin ta zai kwanta sosai.." " Baki san wani abu bama Zaitoon..a wannan halin fa abu na biyu da zai matukar farantawa Ammi shine auren Yayah na farkon shine ganin sa da lafiyar sa, so ki 'kiyasta cikin ranki ki bawa farin cikin nata matsayi zaki fahimci me nake nufi..." Tsaye Zaitoon ta mi'ke a hankali ta juyawa Marwa baya, ga can window ta tafi ta dafa karfen windown tana jin wani 'ka'kkarfan kuka na taso mata amma tana danne shi...wani sabon yanayi ke sake shiganta. Wai wannan wani irin dabaobayi rayuwa ke son yi mata batare da ta shirya ba. Cike da raunin murya ta fara magana ta yadda Marwa zata ji ta...." Ammi ta 'kaunace ni ta 'yanta ni, Ammi ta bani gata, ta bamu dangi tai mana sittira ta faranta mana ni da Mufee na, Ammi ta zame mana garkuwa ni har 'diyata a lkcn da bamu da duk wannan ni kuwa me nake da shi? me na mallaka da zan saka mata da shi baya ga in ganta cikin farin ciki..farin ciki me dorewa na. har abada, wallahi Marwa matu'kar Ammi tayi na'am za kuma tayi farin ciki toh nima na amince, sai dai bisa shara'di 'daya...." Marwa da gudu tazo ta rungume ta out of excitement hawayen farin ciki na sulalo mata ita kanta Zaitoon 'din ma hakan ne...tuni kukan ya 6alle mata...ba kowa take tunawa ba illah Yayan ta, tasan bata kyauta ba, a yau ta yankewa kanta hukunci batare da sanin sa ko amincewar sa ba. " Dan Allah fa'da min, fa'da min shara'din dan Allah Zaitoon..." " Hannu takai ta na share mata hawayen take cewa" dube ki sai kace wacce akace mk lafiya zan bawa yayan kin..." Da sauri Marwa ta kawar da kanta tana murmushin farin ciki tace " Bar min hawaye na, bar min su su sauka iya san ransu, a yau dadin su nake ji fiye da komai dan tafiya suke min da kullin dake cikin zucia ta, after all ma ai ke ma hawayen kike, ni dai fa'da min shara'din naki dan Allah yanzu..." " Da zarar ya samu sau'ki zai sallami auren dan inaso ko bayan sallah babba ne in koma gaban iyaye na kuma bana so su san da wani batun aure akaina...." Marwa bata ce komai ba sai sake rungume Zaitoon da tayi, lkc guda kuma ta sake ta tayi waje da gudu cike da tsantsan farin cikin da bazata iya misalta shi ba, dan farin ciki ne na cikar burika da dama dake ranta. Da Ammi ta fara cin karo itama rungume ta tayi har Ammi na firgita ta kuma ce..." Kai Marwa ke meyasa kullum baki sanin girma ne pls..?" " Ammi guest what...". Tayi maganar tana 'yar tsalle. " Toh fa..kede fa'da min kawai Allah yasa alkhairi ne dai, yanzu na baro wajen Rayyan da sai ince ko shine ya farfa'do da kike irin wannan murnar" Ammi ta 'karashe maganar da rauni. " Ammi shima Yayan da iznin Allah zai farfado ai muna masa addu'a ba dare ba rana..." " Toh menene fa'da min...". Ammi tayi maganar tana mai kokarin cire Marwa cikin jikin ta. " Zaitoon ta amince da auren Yayah, yanzun nan ta sanar da ni, tana ma can kuma tana kuka na barota...". Karaf a kunnen Raihana. Ta kuwa kasa 6oye farin cikin ta itama. Yayin da Ammi ta 'dan bu'de idanu akan Marwa.." Bangane ba Marwa, dama waya fa'da mata da har ta amince 'din...?" " Bansani ba wallahi Ammi, amma dai inaga su Anty ne.." " Toh ba dole tayi kuka ba, wama yace musu su sanar da ita, sun mata caa aka kam ba dole shakkan su yasata ta amince ba, ni na aiki wani daga cikin su ne ko kuwa nace musu na amince da batun auren..." " Ba haka bane fa Ammi, ni sai ita ne fa muka yi maganar kuma tun 'dazun nake wajen ta wallahi babu wanda ya tilastata ra'ayin ta ne na kanta, kuma tace sbd Allah da kuma ke, amma bisa shara'di..." Nan ta zayyano wa Ammin yadda sukayi. Ammi rasa abin cewa tayi...da baya da baya ta koma kan kujera ta zauna tana sakin ajiyar zuciya mai zafi da har wani jiri jiri yake sata ji. " Marwa 'kira min ita please..." " Ammi baki ga halin da take ciki bane, ki bari zuwa gobe sai kuyi magana da ita". Washegari a 6angaren Rayyan suka ha'du, kallo 'daya zaka yiwa Zaitoon ka fahimci bata kwana cikin yanayi mai dadi ba. Hakan yasa Ammi jin tausayin ta ba 'dan kadan ba...ta kuma kasa sakewa a a yau din dan sai take jin tamkar ta za'ke da yawa ne duk da yake su ne suka bu'kaci tallafin ta. Bayan ta kammala aikin ta tana niyyar tafia Ammi ta dakatar da ita. Ammi bata yi 'kauran baki ba ta tambaye ta ta kuwa amsa ta cike da dakiya. " Zaitoon kiyi hakuri kinji..nasan baki da ra'ayi kan maganar da su Raihana suka je mk da ita amma bazan 6oye mk ba nayi matu'kar mamaki da jin amincewar ki wanda nima naji abakin Marwa, Zaitoon in babu wata damuwa ko zan iya sanin dalili...?" _Salmerh_ 😘 [16/11/2022, 11:59 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Wattpad@* _Serlmerh-md_ 🅿️ *...70* ......." Saboda Allah na amince Ammi da kuma ke...."! Zaitoon ta bata amsa cike da dakiya domin in dai zata biyewa zuciyar ta, yadda take ji da banda kuka babu abinda zata sawa Ammi a wannan lkcn, sai dai dole ne ta bawa kanta 'kwarin gwiwa bisa abubuwa masu dama, ba dan komai ba sai dan kawai taga bata karya zu'katan wa'danda suka mutunta a rayuwa ba, taga cewar ta rama alkhairin da suka yi mata da wani alkhairin ko da bai kai wanda su suka yi mata ba. A ganin ta Ammi tafi 'karfin komai a wajen ta musamman ma a yanzu da ta tabbatar tana da bu'katar taimakon nata da gasken gaske. " Zaitoon kar ki biyewa su Raihana ki takurawa zuciyar ki akan abinda kika san ba ra'ayin ki bane, aure wa Rayyan ba wai dole bane kawai sbd wasu dalilai ne da na tabbatar akwai auren da babu shi babu abinda zai canza shi, sai dai kasancewar auren na iya sau'ka'ka al'amura ba ma ka'dan ba, kar ki tilastawa zuciyar ki dan nima ba wai na sa auren nasa araina sosai bane...". Kai Zaitoon ta girgiza tana kallon gefen Ammi tace.." Ammi in dai har su Anty Raihana da Anty Madeena da kansu zasu same ni har 'dakin da nake zaune kan wata magana toh na tabbata mai muhimmanci ne, kuma akwai dalili kwakkara da zai sa su nemi taimako na, Ammi ban manta ku 'din su waye agare ni ba balle na iya juyawa maganar ku baya, Ammi kiyi fatan alkhairi tsakanin yin sa ko barin sa Allah ne zai bayyana mana, nima din ta 6angare na hakan ne, bazan kuma gushe ina neman za6in Allah ba har sai naga abinda ya tabbatar min...". " Zaitoon ki fahimce ni, bana so a takura mk ko shiga hakkin ki akan wannan maganar koka'dan asan wace ke na kuma wasu daga cikin ra'ayoyin ki duk da ba kowanne ba amma ina da tabbacin baki da ra'ayin wani aure dai dai da 'kwayar zarra cikin ranki..toh mene amfanin sa...?" Shiru Zaitoon tayi tana duban gefe ban da sara babu abinda kan ta ke mata amma bata so tun yanzu Ammi ta gama fahimtar rikitar yanayin ta balle ta cigaba da tuhumar kanta bisa tursasawar da ta ganin sun mata bayan tasan Ammin sai tafi kowa farin ciki idan ta amince da auren Rayyan kawai 6oyewa take cikin ranta. Ammi ce ta cigaba da fa'din..." Ki 'kara zurfafa tunani kinji 'diya ta, idan kin tabbatar zuciyar ki tayi na'am da batun ina tabbatar miki da cewa sai na fi kowa farin ciki akasin hakan ma bazan ta6a ganin laifin ki ba Zaitoon..." Wasu siraran 'kwallan da suka zubo mata tayi saurin sharewa cikin ranta ta ayyana" _Anzo wurin_ !...dama tasan hakan ne kamar Ammi tasan menene cikin ranta adaidai lkcn. Tana mai 'kakalo murmushi a zahiri ta furta" Ammi na gama tunanin fa shiyasa ma na yanke shawara kuma har zuciya ta, ba wannan ba Ammi ko wani abin ne daban da ya fi wannan girma matu'kar bai sa6awa addini ba Insha Allahu zan iya mk shi Ammi indai har zai sa zakuyi farin ciki da faruwar shi, domin kun min fiye da yadda zan iya yi muku a duniyan nan...ba kuma zan yi sbd abinda kukai min bane kadai Ammi, ba kuma sbd kunyar kar in ce a a kuji babu da'di ba ne, zan yi ne kawai sbd Allah da manzon sa, baya ga haka ma Ammi kin manta na 'dan lokaci ne ba wai na har abada ba Insha Allah ba wata matsalar da za'a samu daga 6angare na na kuma yi mk al'kawari zan yi fiye da yadda kuke tsammani daga gareni da iznin Allah Ammi.....". Cike da farin cikin da ke fitowa tun daga zuciya Ammi take fa'din " Nagode..'diyata, nagode sosai Zaitoon Ubangiji Allah yayi mk albarka ya albarkaci rayuwar ki data zuri'ar ki, Insha Allah nima nai mk alkwari da zaran Rayyan ya samu lafiya hankula suka 'dan kwanta zan bincika mk iyayen ki zan kuma fahimtar da su su kar6e ki ke da 'diyar ki a yadda 'kaddara ta gina ku, Insha Allah za ki rayu cikin farin ciki tsakanin 'yan uwa da dangin ki tamkar kowa...". " Allah yasa..!Nagode Ammi..." Yadda Ammi tayi farin ciki da wannan lamari kar ku tona zuciyar Raihana, Marwa da Anty Madeena, banda sauran 'yan uwa da suka zo daga wasu garuruwan domin duba jikin Rayyan din, suma da zarar sunji labarin abinda mahaifiyar Amrah tayi sai suji babu dadi, gashi Raihana da Anty Madeena sam basa rufe maganar da gangan suke bayyana ta ga kowa sbd a 'kalubalanci lamarin a kuma yi saurin amincewa da batun Zaitoon. Kamar wasa sai magana ta tsaya akan ranar Friday bayan sallar Juma'ah za'a 'daura aure. Alhaji Rufa'i ne zai yi wakilcin Rayyan while mijin Anty Madeena shine ya bada auren ya kuma kar6i sadaki. Sultan jin zuciyar sa yake tamkar zata yi bindiga sbd takaici. A ganin sa sai ma da batun auren ya taso gadan- gadan yake ganin wani kula da kaffa- kaffa da akewa Zaitoon da 'diyar ta...abin sosai yake ta6a shi dan hatta Marwa daina ganin fara'ar sa tayi cikin kwanakin. Rabon da ya tako 'kafar sa gidan ganin Rayyan ko gaishe da Ammi awanni Arba'in da takwas kenan yanzu...banda zurfafa tunani da rashin sukuni babu abinda ke dawainiya da shi...wannan shine Fitsarin Fako, shi da ya shirya shiryayyen mugunta ga Rayyan dan kashe shi banda rashin nasarar da ta same shi sai gashi lokci guda ana shirin zabtare masa wani yanki na farin cikin sa ahakan ma Rayyan na kwance ne, kenan duk wancan shirin da ya jima yana tsarawa da lokaci, dukiya, tunani da ilimin sa duk Rayyan zasu amfana ba shi ba? Kenan nasarar ta Rayyan ce ba shi ba..? Erh mana...tunda gashi lokaci guda ana shirin aura masa yarinyar da 'kaunar ta ke neman halakashi, yarinyar da ta kasance bugun zuciyar sa, yarinyar da bayan ita ba ya iya yiwa sauran mata kallo mai muhimmanci ciki kuwa hadda matar sa Marwa, hakika kaunar ta ba 'karamin kamu ya yiwa zuciyar sa ba. Kenan abinda yayi masa wata nasara ya kara masa ba ci baya ba. Gashi su Raihana sun kane kane sun kasa bada wata damar da zai 'karasa shi abin na.masa ciwo a zucia. Duk kuma yadda yaso ha'duwa da Zaitoon abin ya faskara dan sam ya rasa damar hakan. Yayin da Zaitoon ke can tana 'kokari sosai wajen ganin ta danne damuwar da take jin zuciyar ta a ciki gudun kar su Ammi su fahimta suji kamar erh dagaske sun tilastata din ne. Amma sau tari idan ta ke6e ita kadai yanzu banda kuka bata da wani aikin yi, sai ta ringa gani tamkar ba dai- dai ta aikata ba da amincewa batun da tayi, wani sa'in kuma sai ta ji cewar ai ba wani abu bane dan ta amince tunda na lkc ne da zarar ya farka zai sallama mata, wannan 'dan tunanin ke 'kara mata 'kwarin gwiwa kusan ko wani lkc. Kamar wasa kamar gaske sai gashi an fara kasantuwar lissafin lokacin, tun daga ranar data amince musu basu sarara ba har zuwa ranar da ya kasance kwanaki biyu kacal suka rage a 'daura mata aure da Rayyan, ta kuma tabbatar bazasu sarara din ba har sai sun tabbatar an 'daura dagaske. Saidai batasan me yasa ba, a tsakanin kwanakin maganar tafi tsaye mata a zucia, bata san menene dalilin dayasa maganar ke ta6ata sosai har hakan ba, batasan meye dalilin da jiki ta da zuciyar ta suke sake shiga rudu da girgiza har haka ba, shin maganar sabo yake agare ta ne ko kuwa tunanin me goben ta zai haifar mata ne? Ga dai tanan amma Allah kadai yasan halin da take ciki. Meye matsayin ta? meye sakamakon rayuwar ta anan gaba? Duk bata sani ba, wanne sabon shafin zata sake bu'dewa? Shima bata sani ba...wace 'kaddarar ke sake tunkaro ta, wacce sabuwar kaddarar zata jefa su ita da 'diyar ta duk bata da masaniya. Sultan be samu daman ganin Zaitoon ba har sai da ana gobe 'daurin aure kafin ya faki ido har 'dakin ta ya same ta, a lkcn kwance take tana tunani, ita ka'dai a 'daki domin rabon ta da Mufee ma idan bata manta ba tun safia, tana can wajen su Anty Madeena dan tun su Raihana na dariyar yadda Anty Madeena ke bawa yarinyar kula har suka daina suma suka bi sahu, bisa alkwarin da ke tsakanin ta da Rayyan kuma basu yanke shawarar bayyana boyayyen maganar ta su ga kowa ba shiyasa su Raihana basu san dalilin sha'kuwar dake tsakanin ta da Mufeeda ba a tunanin su kawai dan sun yi zama tare ne shiyasa, kuma su kansu shaida ne akan yadda Mufeedan ke shigewa zukatan mutane lokaci guda sbd tsabta da kuma kulawar da take samu bayaga haka ma Allah ya zuba wa yarinyar tsantsan farin jinin mutane duk da yake ba magananniya bace sosai..amma tabbas a jinin ta ne tamkar dai na uwar ta. Sanin haian da sukayi yasa basu ta6a zargan komai ba ciki kuwa hadda Ammi. Sai dai 6angaren Sultan abin ba haka yake ba...shima da farko yayi tunanin ko da suna son hillatar Zaitoon din ne ta auri 'dan su shiyasa suka dauke mata nawin yarinyar ta, sai dai daga baya ya fahimci sam ba haka kadai bane domin yanayin kauna da shakuwar ya zarta tunanin sa ya kuma kasa hasaso komai. Anty Madeena kuwa babban abinda ke dakatar da ita bayyana matsayin yarinyar ga kowa shine cewar da Rayyan yayi bai gama binciken ba tukunna ta 6angaren sa...baya ga haka da tuni ta bayyana yarinyar tasan zasu yi matukar mamaki da jin hakan, ko batun auren Zaitoon ma ta karfafa shi ne sbd abubuwa biyu, farko batun Amrah burinta a 'kona zuciyar su kwatankwacin yadda suka 'kona tasu zuciyoyin, abu na biyu kuma sbd Rayyan, ta tabbatar idan Zaitoon ta kasance 'karkashin ikon sa binciken su zai fi zuwa masu da sauki...za samu duk abinda suke da bu'kata cikin sauki da iznin Allah. Zaitoon kam kwance take tana tunani, domin a wannan lokacin bata da wani abokin hira sai ita sai tunanin ta kadai, tama mance da duniyar da take ciki kawai taji motsi, a firgice ta mike zaune. Ga mamakin ta sai taga ashe Sultan ne. Idanu ta fitar waje sosai bakin ta na dan rawa tace..." Yah Sultan...lafia...?". " Bani da tabbaci Zaitoon domin daf ake da kaini 'kasa....!" Ya bata amsa yana me 'karasowa inda take yayin da tayi saurin mikewa tsaye ta sauka a gadon tana sake fuksantar sa gami da hade giran waje guda. Kallon ta ya tsaya yi cikin ido yana sake jin wata kaunar ta zazzafa na ratsashi, yana son Zaitoon har zuciyar sa, yana kuma tsananin kishin ta. Duk wani tsari da plan na rayuwar sa ta gaba da ita yake tsarawa...amma sai gashi kwatsam rana tsaka ana so a rushe duk wannan shirin nasa da ya jima yana tsarawa. " Yah Sultan meyafaru, wani abu kake nema ne..?" Ta sake tambayar sa muryar ta na rarrabewa sbd ganin irin kallon da yake mata. Idanu ya lumshe ya kuma bu'dewa akan fuskar ta..yana sakin huci mai zafi. " Babu komai...ba komai Zaitoon sai dai illar da ake so.a yiwa zuciya ta dalilin ki kadai....". Bata fahimci maganar tasa ba hakan yasa tayi shiru...sai kuma taga yin shirun nata sam bai dace ba, kamar yadda ke6ewar tasu bai kwanta mata a zucia ba. " Yah Sultan idan wani abu kake so dan.Allah ka fada min sai in kawo maka aima da ba sai ka taho har nan ba da aikawa kayi a kirani kawai sai inzo..." " Da Allah kimin shiru..." Ya buga mata tsawa yana jin hucin da zuciyar sa ke fiddawa. Tuni idanun sa sun rikide zuwa jajaye. Duk abubuwan da ya aikata abaya baya jin sun kai wani matsayi, baya jin sun kai. girman abinda zai iya aikatawa matukar aka yadda aka shiga tsakanin sa da yarinyar nan. Abinda zai aikata akan.Zaitoon zai iya bawa kowa mamaki amma ita kanta bata san hakan ba. Tsawar tashi tuni sake rikita ta..sai ta fara duban hanya ta gama yanke.shawarar ficewa ta bar dakin aganin ta yafiye mata fiye da kasancewa tare da shi a dakin tun kafin akai matsayin da zai make ta duk da yake bata san laifin ta ba har yanzun. Fahimtar da yayi cewa shirin gudu take ya sa shi saurin tare kofar yana sake bin ta da kallo sai tayi kasada idanun.ta. Tsawon sakanni masu yawa yana kallon ta gami da tausan zuciyar sa ya kuma sanyaya muryar sa. " Wai da hankalin ki? Zaitoon da wayon ki zaki amincewa auren wancan dutsen...?" Salmerh😘 [18/11/2022, 3:08 am] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Wattpad@* _Serlmerh-md_ 🅿️ *...71* .......'Kan'kance idanu Zaitoon tayi sosai tana duban sa da mamaki..." Yah Sultan Dutse kuma..? waye dutsen...?" Shima a zuciye ya bata amsa sbd yanayin 6acin ransa ke 'kara hauhawa musamman daya ga yau gashi ga ita wuri guda amma lkc kadan ya rage ta zama mallakin wani ba shi ba. Ji yake tamkar ya 'dauke ta gaba 'daya ya gudu da ita yaje ya killace akabar sa kowa ma ya daina ganin ta sai shi ka'dai. " Wancan dake kwance yake irga kwanakin mutuwar san nake nufi..! Yayi maganar tare da yin nuni da hannun sa idanun sa na sake rinewa ".....me kike tunanin zaki samu tattare da shi? Me kike tunanin zai amfanar miki da shi baya ga bauta da zaki yi ta masa har 'karshen rayuwar sa..." Baya kadan taja sbd yadda yake.fitar da maganar tasa tamkar zai hadiye ta 'danya. Tana 'dan yamutsa fuska gami da takure jikin ta waje guda tace. " Yah Sultan dama ai ba dan in samu wani abu na amince da auren ba face dan inyi bautar ka'dai...". Sultan ji yake tamkar ya make ta sbd takaicin ta, meyasa ta kasa fahimtar inda ya dosa ne? meyasa sam kwakwalwar ta bata ja koka'dan..shi aganin sa Zaitoon tafi 'karfin tayi wannan bautar har abada sbd itan mallakin sa ce, be san me ya hana Rayyan 'din mutuwa tun a ranar farko ba, bai san me ya tsaya jira ba da har za'a bautar masa da Zaitoon sbd shi. Ya 'karashe tunanin yana mai watsa hannu alamun dai takaici ke cin sa. Har ya juya sai kuma yy turus, still dai idanun sa na nan a rine. Babu komai...a yanzu damar tasa ce gaba 'daya, damar sa ne ya bar Rayyan ya cigaba da rayuwa, damar sa ne kuma ya 'karasar da shi ga hanyar barin.duniyar da ya kamk....amma tabbas bazai bari ba, dole ne sai yayi wani abu guda...wala alla hakan zai iya haifar masa da kwanciyar hankali mai 'dorewa. ***** Ha'ki'ka a wasu lokutan 'kaddara abu ne mai matu'kar ban mmk, mai rikitar da tunani sanya ru'dani da kuma haifar da kwanciyar hankali ga wasu yayin da ga wasu abin ba hk yk ba, sai dai a mafi yawan lokuta 'kaddara takan riski bawa ne cikin yanayi na bazata ko rashin shirya zuwan ta, kuma ta kan zo ne cikin siga guda biyu da suke mabambantan juna, inma kayi farin ciki da zuwan ta ko kuma akasin haka, sai dai ga Zaitoon sam abin ba haka yake ba, sam ko alama har a yanzun ta kasa hasaso yanayin 'kaddararta ta kasancewar ta gidan Ammi Aseeya, ta kasa hasaso karshen 'kaddarar tun daga farkon zuwan ta har zuwa yau 'din nan, har a yanzu da take amsa suna matar Rayyan bata san wani gurbi zata sanya wannan karkatacciyar 'kaddarar ba. Abin ya kasance mata ne tamkar wasa ko shirin drama, yayin da ta wani 6angaren take gani tamkar a gaske. Ga dai ta a yanzu tana nan na da wani gagarumin abu akanta mai suna aure, auren da ta kasa tantance matsayin sa wajen ta kamar yadda ta kasa tantance asalin dangantaka da kuma halayen ahalin gidan Ammi Aseeya. Tuni ta gama fahimtar mafiya yawan ahalin sun yi na'am sun kuma yi farin ciki da wanzuwar auren, yayin da 'kalilan daga cikin su a fili suka nuna 'kiyayyar su bata kuma san dalili ba. Abin kuma bai kasance abu mai saukin fahimta ba kwatankwacin yadda auren ta da Rayyan ya kasance mai sauki kuma ya faru cikin sauki, illa bride price da ya kasance mai nauyin da ya bata matu'kar mamaki. Da ace saukin fahimtar su ya kasance mai sau'ki kamar yadda sau'kin kasantuwar auren ta yake da sai tafi kowa farin ciki sbd cikin kalilan din lkc zata fahimci inda ra'ayin kowa cikin ahalin ya fuskanta....amma ina abin ba haka yake ba, shiyasa duk suka bar zuciyar ta cikin kokonto da wasi- wasi, banda tsoro da fargaba dake 'kara shiganta kusan kowani lokaci. Cikin lokaci 'kan'kani duk wasu hidindimun Rayyan a hankali kaf suka dawo hannun ta, ita ke masa komai, tun tana jin nawi har tazo ta dan saki jikin ta ganin babu wani mai bi takan kunyar ta. Baya ga haka ma ita da kanta tasan dalilin da yasa aka hada auren kenan dan haka itan tamkar baiwa ce ga shugaban ta, bata da iko, matsayi ko damar da zatace shi ya hanata aiwatar da aikin ta. Hatta da Fawwaz ma yanzu sun saba da shi sosai, domin wasu abubuwan ma da kanshi yake 'kara koya mata yadda zata yi da kuma bi da Rayyan 'din. 'Bangaren Ammi ma hakane, domin a yanzu ta kan 'dan ji natsuwa da kwanciyar hankali duk da ba wai na wani can can bane amma dai da sau'ki fiye da baya. Saboda kusan kowani lokaci gani take tamkar an takura Zaitoon ne, an kuma shiga hakkin ta, duk da Zaitunan ta tabbatar mata da cewa ba yadda take tunani bane amma ta kasa fitarwa cikin ranta. A halin yanzu ba Rayyan kadai ke bata tausayi ba hadda ma Zaituna, shiyasa itama take biye Anty Madeena gaba 'daya sun 'dauke mata hidima da kula da Mufeeda a wuyan ta, gudun wai kar abubuwan suyi mata yawa, wani sa'in ma hatta kwana Mufeeda batayi wajen Zaitoon kuma bata damu ba. Hakan shi ya sake haifar da wata sabuwar sha'kuwa tsakanin.su gaba 'daya. Wani 'bangaren kuma sanin da Ammi tayi cewar Zaitoon na matukar kokari wajen kulawa da Rayyan tana kuma nan tare da shi kusan kowani lokaci yasa kullum banda albarka babu abinda take sanyawa Zaitoon... domin aganin ta tai mata halaccin da ba kowa ne zai iya mata ba, ta mata abinda tasan har abada bata da abin saka mata da shi sai dai ta bata wani babban matsayi cikin zuciyar ta da tasan zai yi wahala ya bar mata zuciya, yadda da amanar ta duk ta dan'kata ga Zaitoon da ya'kinin bazata ta6a cutar mata da shi ko watsa musu 'kasa a idanu ba. Yawan godia da albarkar da Ammi ke sa mata ya sanya Zaitoon jin da'din ayyukan da take yiwa Rayyan. Bata ta6a jin cewa wahalar banza take yi ba saboda tasan tana faranta ran Ammi dama sauran 'yan uwan sa..hakan kuwa na sake tsunduma ta cikin farin ciki da walwala itama...ya kan kuma kara mata karsashin aiwatar da ayyukan ta gare shi. Shine dai bata da tabbacin zai yaba ko akasin haka, amma sam bata shi take ba, bata amincewar sa rashin sa take ba, burin ta tayi ta samu lada na biyu kuma ta farantawa mahaifan sa musamman sbd yadda taga itama suke kula mata da yarinya kamar ransu. Har wata Nanny gareta yanzu a gidan domin kulawa da ita ita ka'dai. Hakan kuwa da suka yi sosai ya 'kara musu daraja da kima a idanun ta. Fatan ta da addu'an da bata gajiya da yinsa a yanzu kawai shine Allah ya bashi lafiya ya tashi kafadun sa cikin aminci domin tasan da zarar ya samu sau'ki shikenan komai zai zo 'karshe. Aure da hidimar duk 'karshen su kenan. Bata sake saka Sultan a idanun ta ba sai da aka dauki tsawon wasu kwanaki sannan yazo duba jikin Rayyan fuskar murtuk babu fara'ah dai dai da 'yar ka'dan, hatta gaisuwar da Zaitoon take yi masa ma bai amsa ba itama kuma hakan bai dame ta inda sabo ai ta saba da irin hakan tunda 'dabi'ar Rayyan ce ga Sultan ne dai take sabuwa a yanzu bata kuma san dalili ba. Washe garin zuwan Sultan take jin labari a bakin Marwa wai a Amrah ta 'kira wayar Rayyan Anty Raihana ce kuma ta amsa, tsabar shiga rudu da zafin kishin dake cinta tama mance da cewar Rayyan fa ne kwance ba wani daban ba. Da jin an 'dauki waya bata tsaya bi ta kan waye kan layin ba kawai ta fara surutai cike da 6acin rai...tana fa'din..." Yanzu Baby dagaske aure kayi? Auren ma ka rasa wacce zaka aura sai 'yar aiki na dan kawai ka tozarta ni..?..'yar aiki fa Baby..? 'Yar aikin ma wai Zaitun fisabilillahi..?" " Hakan dai ne ya kasance kuma babu ja da baya Zaitoon da kika sani mai taya ki ayyuka abaya ba ita ce Zaitoon din mu ta yanzu ba domin wannan matar Rayyan ce..". Shiru Amrah tayi daga can 6angaren tana mai jin kukan takaici da bakin ciki na taso mata. Da hannun ta 'daya ta toshe baki gudun kar sautin kukan ta yafito fili tama kasa cewa komai. Anty Raihanan ce ta cigaba da magana. "...mene dama yafi dacewa da duk matar da ta tafi ta bar mijin ta cikin mugun yanayin da tasan cewa yanada bukatar ta kusa da shi? Ita matar ta mance ne cewar ba ita kadai ce mace cikin duniyar ba ko me? Ke anya ma Amrah kina da kunya kuwa, sai yanzun kika san ki 'kira sbd kinji batun auren sa daga bakin wasu amma da kanki kinsan halin da kika barshi ciki amma hakan bai sa kin 'kira ko da sau 'daya bane kiji lafiyar sa.....?" Da sauri Amrah ta kashe wayar batare da ta jira karshen maganar ba. Koda Marwa ta gama bawa Zaitoon labari ji tayi babu dadi, cike da sanyin rai tace da Marwa" ai da Anty Raihana bata ce mata haka ba...ayi mata uzuri mana, kinga fa itama biyayya ta yiwa mahaifiyar ta..." " Dalla can 'kyale ta, ni wlh an min dai dai, gara tasan cewa bata kyauta ba. Cewar Marwa tana barin 'dakin. Nan ta bar Zaitoon zugum tana tunani a zaune, gani take tamkar itace silar komai, kuma bata so taga ta kuntatawa wani sam a rayuwar ta, sosai ta 'kara kaimin addu'ar ta gareshi ba dare ba rana. Burin ta ya samu lafia ya sallame ta kowa ma ya huta. 'Bangaren Amrah kuwa sosai tasha kuka, taji aranta cewar bata kyauta ba sam bata kuma ankara tun farko ba sai yanzu da maganganun Raihana suka ankarar da ita. Tun zuwan ta gidan mahaifiyar ta ta mantar da ita komai, domin duk wani abu na jin dadi wanda zai kawo mata kwanciyar hankali shi ta ri'ka yi mata take kuma sawa ake mata...dan hatta Arfan tsakanin ta da shi shayarwa shima din sai ta ga dama. Fita ko'ina babu mai taka mata birki ko da yini zata yi kuwa. Hakan kuwa ya sa suka cigaba da holewar su da Sultan bayan ya shawo kanta da kyar domin tsoron sake jefa kanta cikin kuskure take tunda Allah ya taimake ta ta tsallake na Arfan babu wanda ya 'dago. Amma da yake Sultan shegen kaya ne tuni ya kalallame abar sa ya nuna mata cewar wancan ma kuksuren ta ne ya jawo, da ace tana bin maganar sa da ka'idar maganin da yake bata da duk hakan bai faru ba amma zasu kiyaye bazai sake bari a maimaita makamancin kuskuren ba. Amrah ta kuwa amince da shi, kusan kullun sai yazo ya dauke ta ko kuma su hada appointment na wajen haduwa kawai su ha'de acan...tun bayan komawar ta gida har zuwa ranar da ya sanar da ita batun auren Zaitoon da Rayyan da gangan dan ta taya shi ya'kin 'kwato abar 'kaunar sa...so yake ta koma gidan..ya kuma yi nasarar hakan. Domin Amrah ba karamin rigima ta yiwa mahaifiyar ta ba tana fadin ta cuce ta da ta dauko ta gashi ta ja an mata kishiya tana zaman zaman ta. Tasan Rayyan bayi da ra'ayin aure nan kusa amma sakaci da rashin wayon ta yasa gashi an mata kishiya, kishiyar ma abin takaici wai yar aikin ta. Duk yadda Mummyn ta taso kwantar mata da hankali abin ya faskara domin 6acin ran Ameah ya riga ya haura ta yadda take rasa control din zuciyar ta. Fadi take ta cuce ta da tasa ta dawo hida bayan tasan mijin ta na da bukatar kulawar ta, ita da take tsohuwa ma ba ai mata kishiya ba sai ita bayan tasan yadda take kaunar mijin ta. Amrah kanta bata ta6a sanin tana tsananin kishin Rayyan ba sai a wannan lkcn, Mummyn ta na mamakin ta itama. Dan lkcn Nadia bata yi irin kishin nan ba sam sai yanzu. Amrah tana kuka take ha'da musu kaya..da 'kyar Mummyn nata ta samu ta nutsu har akayi kwanaki biyu sannan tasaka driver ya maida ta gidan mijin ta ganin ta kasa kwantar da hankalin ta. Bayan ita a ganin ta gata take yi mata. Duk yadda taso fahimtar da ita rashin muhimmancin auren ga Rayyan Amrah bata fahimtar ta. Taso ta nuna mata manufar auren ta kuma bata tabbacin Rayyan fa bai san da batun auren ba kwata kwata, babu mamaki kuma da zarar ya samu lafia ma ya saki yarinyar tunda ba shi yace yana so ba, baya ga haka ma kin manta 'yar aiki ce kika ce? Ki tuno waye Rayyan ki sannan ki kiyasta ta yadda zai amincecda auren wata yar aikin gidan sa..." Duk Amrah bata nutsu ta fahimci Mummyn ba balle ta gane abinda take nufi. Tun dawowar ta gida kuwa Ammi ta owa6i kowa akan btankata ko sake maida abinda ya wuce. Hatta da Anty Madeena Ammi rokonta tayi akan dan Allah kar ta tanka Amrah, da kanta ta tafi da kanta ta kuma dawowa dan haka su zuba mata idanu kawai. Hakan kuwa akayi tsakanin su sai dai idanu da dauke kai dan kowa na jin haushin kowa cikin ransa. Sosai kumacsuka dauke kafafu a 6angaren Rayyan yanzu sbd gudun fitina inji Ammi musamman sbd ganin Amrah ta dawo. Sun kuma san baya da karancin samun kula a yanzu ballecsuji damuwa...dan Zaitoon na yin iya kokarin ta kamar yadda ta alkawarta abaya. Sukan je ne kawai su duba shi da safia da kuma kafin dare in angan su zaunevtare da shi yanzu sai dai in bukatar hakan ce ta taso. Arfan ne dai kam suka ce dama ai nasu ne, Anty Madeena ce dai kam yaron ko kallo bai ishe ta ba balle uwar sa. Salmerh😘 [23/11/2022, 4:32 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Wattpad@* _Serlmerh-md_ 🅿️ *...72* ........Tsakanin Amrah da Zaituna babu wani maganar kirki sai dai banzan kallo da harara dake tasowa daga 6angaren Amrah, zagi kuwa babu irin wanda bata sauke mata, sai dai Zaitun bata ta6a tankata ba, bata ta6a 'daga idanu tayi mata duba sau biyu ba sai ma 'karin kyautatawa da take yi mata dan har a yanzun Zaitun bata raba kanta da yiwa Amrah hidima ba. Ganin daman ta ta sararawa Zaitoon da yawan masifar domin bata kula ta, kuma tana jin shakkar ranar da zata kaita bango tasan abin bazai musu kyau ba sam..domin bata mance dukan da ta ta6a sha a wurin ta ba. Zaitun ba shiga sabgar ta take yi ba, illah ayyukan gaban ta kadai koda yaushe take kokarin sauke nawin su akanta, dama Amran ce ke takalo ta amma sanin da tayi cewar ita tai musu kutse cikin rayuwar su yasa bata ta6a tankata ba. Kuma har yau 'din nan Amrah bata yiwa Rayyan komai wai dan ta tallafawa Zaitoon da wani abin ko kuma dan samun lada bata ta6a ko kwatantawa ba. Takan dai yawaita jifan Zaitoon da habaicin dama aikin ta kenan, sbd kwa'dayi da shishshigi sai da tayi abinda yasa aka aura mata Rayyan, toh ta gama bautar da kanta duk a abanza ne domin tana da ya'kinin da Rayyan ya dawo hayyacin sa ubanta zai ci...aceawar Amrah Mmn Arfan kenan...lolz Zaitoon bata ta6a tankata ba, after all ita kanta tasan abinda Amran take fadi gaskia ne..kuma cikin shirin zuwan lkcn take kusan kowacce rana, tunda Allah ne ka'dai yasan lkcn da zai farka, yanzu ne, anjima, gobe ko rana ta gaba. Domin Dr Fawwaz ya 'kara tabbatar musu da cewa yana iya farkawa cikin ko wani lkc shiyasa maganganun Amra basu ta6a damun ta ba balle taji haushin su. Amrah bata da'de da dawowa gidan ba zirga-zrigar Sultan ta yawaita sosai a sashen, abin mamaki kuma a duk shigowar tasa ba lallai ne kaga ya isa ya duba jikin Rayyan ba...sabgogin gaban sa yake yayi ficewar sa kawai. Idan baka sani ba kuma sai ka 'dauka sbd Rayyan yake shigowa sashen, musamman yanzu da yake su Anty ba zama sosai suma suke a 6angaren ba yanzu, hakan yasan kowa ke aikata son ransa batare da tsoron Allah ba. Sukan yini basu shigo 6angaren ba...sbd Ammi ta hana su yawan zarya a sashen afadar ta cewar tunda ga matan sa har biyu tare da shi su din sai su dan sarara. Nan ma hakan bai yiwa Ammi ba, masifa ta fara wa Anty Raihana da kananun mita akan ta koma 'dakin ta, dole badan taso ba ta fara shirin tafia, dama kusan kullum suka yi waya da yaron ta Bassam sai yayi mata kukan taki dawowa...ita dama tana tunanin Rayyan ne, tsananin tausayin sa ke ninkuwa mata a zucia, gani take tamkar hankalin ta baxai kwanta ba idan tayi nisa da shi. Anty Madeena ma na shirin komawa gidan ta da suka canza dan wancan bazai zaunu ba dole sai an masa gyara sosai. Shiyasa yanzu ri'kon Mufee ya fara dawowa hannun ta, sau tari ma da ita ake mi'ka yarinyar makaranta..wani bin sukan kwana su kuma yini tare su da juna. Amrah rayuwar ta take son ranta duk ta mance da batun rashin lafiyar Rayyan ba 'karamin holewar su suke da Sultan ba..a hakan kuma ba 'karamin kishi take ji cikin zuciyar ta akan Zaitoon ba. Abu guda ke taka mata birki shine sanin manufar auren nasu shiyasa sau tari ta ke dan iya danne kishin nata tai ta dariuar mugunta cikin ranta. Zaitoon ma ranar da ta fahimci abinda ke faruwa ba 'karamin ka'data abin yayi ba. Sam bata ga aikin wayo ko dabarar Amra anan wajen ba. Sau tari bata sanin shigowar Sultan sai dai taga fitar sa kawai. Wani sa'in kuma ko taga shigan sa bata sanin lkcn da yake fita. Kuma tasha cin karo da shi yana 'dakin Amra tamkar shine mijin ta ba Rayyan da ke kwance. Ba tun yau ta fahimci kazamtacciyar ala'kar da ke tsakanin su ba tunda da kunnan ta ta ta6a ji suna magana akan Arfan cewa na Sultan ne ba Rayyan ba. Ta kuma fahimci hakan ya faru ne bisa kuskuren da su kansu basu san da shi ba, a zaton wannan kadai ya isa yasa Amra shiga taitayin ta ashe ita kam sake bu'de mata 'kofar holewa ma yayi. ( Yah Rabbis- samawati ka tsarkake mana zucia...Ameen). Kwanaki tana jin gwagwarmayar da suka.sha akan yaron domin lkc guda ya fara rashin lafia sosai suka rasa me ke damun sa, 'karshe da suka dangana da asbiti nan aka tabbatar musu da cewar yaron na dauke da cutar sickler ne. Sun sha wahala sosai har sai da aka 'kara masa jini..kuma Allah cikin ikon sa aka rasa jinin da yazo 'daya da nasa sai na Sultan. Hankulan su ya Ammi ya tashi sosai da jinuar yaron, banda rudani da suka shiga na.yadda aka yi yaron ya kasance mai cutar sickler domin a sanin su Rayyan jinin sa lafiyayye ne. Duk irin ru'danin da suka shiga Anty Madeena kallo ma basu ishe ta ba, sai ma inta lura da yadda Sultane ke rikicewa sai ta kya6e baki cikin ranta take ayyana ranar da zata tona sirrin su ga kowa. Sultan da Amra basu samu kwanciyar hankali ba har sai da yaron nan ya dawo dai-dai, a hakan wai duk Sultan na karyar sbd Rayyan yake komai...alhali tun bayan haihuwar yaron da ya tabbatar nasane kauna da soyayyar yaron suka yi masa ram da zuciya. Amra ce ta fara ziga Sultan akan 'kaunar da taga su Anty ke nunawa Mufeeda dan abin na mata ciwo sosai, musamman lkcn da Arfan bai da lafiya duk ta lura da Anty Madeena yadda ta nuna halin ko in kula da su, sa6anin yadda take yiwa Mufeeda, tari wannan idan yrinyar tayi sai ta tabbatar na lfia ne kafin take samun natsuwa. Wani gefen kuma haushin ganin yadda su Marwa suka ha'de kansu da yaron ta da yake 'dan gida alhali ita Mufee ba kowan kowa bace agare su face karere...'diyar 'yar aikin gidan su. Bata san cewa 'kaunar daga zuci take ba, 'kaunar daga indallahi ce, dole yadda zaka ji naka a zuciya sai yafi na wani daban nauyi. Tace sam ni ban yadda da su ba ma, da farko na 'dauka ko tayata rainon 'diyar ta take sbd itama na musu hidima da Rayyan...amma daga baya sai fahimci abin nasu fa ba haka yake ba, kauna ce ta gaskia wlh suke wa yarinyar, har wani 'yar kama naga yarinyar keyi da Marwa fa bansani ba ko dan na kwana biyu banganta bane oho...amma ada ban ta6a lura da kamannin nasu ba sai yanzu...haka nan kawai nk ji araina suna da alaka, kuma ma idan ka lura zaka iya tabbatar da magana ta, kaga har yau babu wanda yasan dangin Zaitoon balle asan uban 'diyarta ta.... Shiru Sultan yayi ya tsura mata idanu, zuciyar sa yake ji na fa'duwa sosai gami da luguden gudu. Ya jima da fara zargin wata ala'ka 'ka'k'karfa tsakanin su da yarinyar nan sai dai rashin 'kwakkwaran hujja bayaga kammannin bai ga komai ba, duk iya tsawaita tunanin da yy da hakan ya kasa hasaso ta inda hakan zai iya faruwa, sannan gefe guda yafi tsoron ace wannan yarinyar jinin Rayyan ce..duk yasan Rayyan farin sani, yasan matan banza basu ta6a birge Rayyan balle wata tarayya ta ha'da su...wannan dalilin yasa bai bawa zargin nasa muhimmanci ba duk da haka da gangan ya shirya harin gidan Anty Madeena domin ya 6atar da kowa, ya so ya 6atar hadda zargin sa gaba 'daya amma bai samu nasarar hakan ba. Sai kuma gashi yau Amrah na sake yi masa ishara akai. Sai yanzu yaga wautar sa da kansa..meyasa tun farko ma bai binciki wace ita da dalilin zuwan ta gidan ba har ya yadda ya bar zuciyar sa fadawa tsananin kaunar ta ta yadda bai san ta ina zai fara raba kansa da shi ba. Hakika shi sauna ne, akan hakan sam tunanin sa bai yi aiki ba. Tun bayan faruwar lamarin bai sake bi takan yarinyar ba but maganar Amrah yanzu ya sake ankarar da shi...dole ne kuwa sai ya binciki lamarin ya kuma dauki mataki in dai zargin su shi da Amrah ya kasance gaskia. Bai nuna wa Amrah komai ba kamar yadda bakin sa bai furta komai kan abinda tace 'din ba a zahiri sai ma kya6e baki da yayi. ***** 'Bangaren Zaitoon kuwa sam hankalin ta yanzu ba akan su yake bama dan ba su ne gaban ta ba. Kulawa da hakkin mutane biyu da nawin su ke rataye a wuyan ta shine ka'dai damuwar ta kusan ko wani lokaci. Ita kanta Amrah tasan cewa Zaitoon duk na ankare da su amma sanin halin ta na kawar da kai yasa bata ta6a damuwa ko jin shakka ba, ta riga tasan mawuyaci ne maganar ta fita ta 6angaren Zaitoon in dai ba wani ikon Allah ba, sai dai duk da hakan ta kan iya takun ta dan bata so ko da wasa maganar ya fita wurin su Ammi da wa'dannan fitanannun 'yan uwan nasa..acewar ta...domin tasan da zarar sun ji to ta ka'de ne har ganyen ta. Ita kam Zaitun wani.sa'in har na mamakin dalilin da yasa Amrah bata wani zama da mijin ta, duk kuwa da ba lafiya ce da shi ba amma duk wasu abubuwa da ya kamata ace ita ce a gurbin ko kuma suyi tarayya akan sa su biyu to bata bi takan su, duk ta barwa Zaitun sai dai tazo ta duba shi kawai tayi gaba tana kya6e baki. Wani lkc Sultan ko su Huzaifa na zuwa su wanke masa jiki, idan ko suka yi masan itace ke tsabtace muhallin nasa, idan sun fito daga wankan kuma zata fita ne idan sun gama shirya shi sai ta dawo ta tsabtace bayin da sauran abubuwa, abinci dama ba'a maganar sa, watarana ita da Ammi suke hidimar idan tana kusa idan kuwa bata gari ta kance ta bar shi amana a hannun Zaitun, duk da tana tausaya mata sosai sbd rainon Mufee ga kuma kula da shi amma hakan sam baya damun Zaitoon. Sau da dama ma har sai sun gama yi masa komai sun bashi maganin sa kafin Amrah ke zuwa ta zo wai duba shi, mama kam bata ta6a nuna mata 6acin ranta ba, may be dalilin ma kenan da ya sanya ta bada ragamar kula da shi a hannun Zaitun 'din gaba 'daya. Magungunan sa kuwa kaf mama ke ajiye su sbd gudun abinda kan iya zuwa ya dawo sai za'a bashi sannan take 'dauko su, idan zata yi tafiya kuma a hannun zaitun take bada su, duk dama yanzu komai ajiyewa tayi saboda jinyar Rayyan in bata fiye zuwa ko'ina ba in ba ya zam mata dole ba toh ba kasafai take yin ta ba. Watarana ne da sassafe aka yi mata 'kiran gaggawa akan wata goggon ta acan Jahar Maiduguri 'karamar hukumar Geidam, hakan yasa ta rikice ta hau shirin tafiya dan su ka'dai gare ta a yanzu dangin mahaifi da na mahaifiyar ta amma asalin mahaifan ta duk sun rasu. Goggon tata dama ta tsufa gashi babu isashshen lafia..hakan ya ru'da mata tunani sosai, har bata tuna bawa Zaitoon maganin Rayyan ba hankalin ta gaba 'daya yy gaba. Haka ta shirya ta fito, rashin sani ashe ma set up akayi mata babu abinda ya sami goggon ta tana nan dai- dai kamar kullum ba kamar yadda aka sanar da ita jikin yake ba. An dai je gida an sassace musu wayoyi amma kowa na nan lafiyar sa 'kalau, shiyasa ma koda Ammin ta 'kira layukan su duk basu tafi ba numbern da aka 'kira tan ma baya tafia. A gigice ta bar gidan bayan ta bawa Zaitun amanar Rayyan, ita kan ta Zaitun Kukan take yi sosai sbd tausayin Ammi, ta rasa wannan wacce iriyar 'kaddara ce, ta shiga halin 'dimuwa abaya wanda take tunanin bb ce ta sanya hakan sai dai zuwa yanzun ta fahimci masu halin ma idan suka tashi shiga damuwa bada wasa suke shigan ta ba...a yanzu ne Zaitoon ta fahimci ita rayuwa komai mukaddari ne..kuma jarrabawa, sannan Allah na jarabtan bayin sa ba wai dan baya sansu ba sai dan ya gwada imanin su...ya kan jarabci duk wanda yaso ne cikin bayin sa batare da ya za6i nasaba, arziki ko akasin hakan ba. Ammi bata jima da tafiya ba Sultan ya zo da kansa, fuskar sa babu yabo babu fallasa ya duba jikin Rayyan sannan ya fita, har ya fita kuma ya dawo ya dubi Zaitoon. " Magungunan sa fa...?" Tace" Ammi.bata bani ba, ina jin ta mance ne...". Kai ya jinjina wata 'yar murmushi ya subce masa. Sai yace.." Ok..bari a 'kira ta kafin su tashi sai ta fa'di inda suke ko kuma a siyo wasu a cigaba da bashi, bai kamata a yanke bashin ba dan bata nan..." Yayi maganar yana juyawa ya fita yana mai ciro wayar sa a aljihun dake gaban rigar sa. Zaitoon kam kai ta jinjina tana mai maida duban ta izuwa gare shi. Tausayi yake bata sosai, gashi nan kwance kamar kace wane tashi amma babu dama... _Allah gwanin baiwa...._ Ta jinjina cikin ranta. Bayan tafiyar Sultan bada jimawa ba sai ga sa'ko yazo ta hannun masu kula da shi wato su Huzaifa, a parlor suka tarar da ita, su biyu ne sun sha suit ba'ka'ke da ba'kin gilashi ko za'a kashe ta kuwa bazata iya yi musu kallo biyu 'kwa'k'kwara ba balle har ta iya gane su saboda yanda suka ha'de rai kamar masu kawo sakon mutuwa. Wasu sabbin magunguna taga sun bata da bazata iya tantance su ba, akwai na ruwa dake farin kwalba shi yafi 'daukan hankalin ta sai dai girman kwalbar ya gaza wanda take gani Ammi ke bawa Rayyan sosai, sannan an kwaye takaddar jikin kwalbar haka zaka hango kalar ruwan dake ciki, bata san dalilin kwaye takaddar kwalbar ba, tana son sani amma kuma bata iya ta bu'de baki ta tambaye su dalilin ba. Sai da ta kalli kwalbar kafin ta 'dan 'daga kai ta dubi 'daya da ya gaza 'dayan a tsayi ka'dan yana gyara gaban rigar shi ganin ta kalle shi sai yace" Inji Hajia ne wai a ringa bashi sau uku arana kafin ta dawo". 'Kasa tayi da kanta tana mai sake duban kwalbar dan shine a hannun ta tare da girgiza kai tana mai kimtsa bakin ta, a lokacin sam batayi wani tunani na daban ba, saboda tasan Ammi bata bar mata magungunan nasa ba 'kila shiyasa ta aiko da su yanzu. Motsin bu'de 'kofa suka ji sai taga sun yi saurin waigawa suna masu shirin ficewa cikin hanzari..Zaitoon kam bin su tayi da kallo har lokacin da Amrah ta 'karaso ta samo ta tsaye a wurin da take cikin takun nan nata mai birgewa...tana tafiyar take fa'din. " Ke kuma fa..kin wani yi tsaye tamkar wata dogari?..koda yake babu bambanci ma...tafiyar kusan 'daya ce..." Ta 'karashe maganar tana mai zama bisa 'daya daga cikin kujerun parlorn. Zaitoon bata kula ta ba kawai tayi 'kasa da kanta tana mai fa'din" Barka da safiya". Bata tanka ta ba sai ma kya6e baki da tayi tana sakin huci. " Ya jikin nasa? ashe Ammi ta wuce Borno?" " Erh" Ta bata amsa da fa'din haka a a takaice. Baki ta kuma kya6ewa batare da furta komai ba kawai ta 'dauki remote, kallon ta Zaitoon tayi a tsanake, cikin ranta take ayyana mamakin da Amrah ke bata, ga dukkan alamu ko jikin mijin nata bata je ta duba ba ta wuto nan wurin tana wani tambayar ta. Tana canza channel take sake tambayar..." Wai har yanzu ko motsi bai yi ba...?" " Kije ki duba shi da kanki zaki tabbatarwa ..." Zaitoon ta bata amsa batare da ta kalle ta. A fusace ta waigo gare ta tana kankance idanu. " Toh ban yi niyya ba...isashshiya, in kuma za'a sani dole ne sai inji...". " Hmm..." Tace a hankali, bata san ma meyasa ta bata amsar farkon ba, bata san ya akayi amsar ta shiryu cikin ranta har ta iya furta shi ga Amran ba. Sai daga baya ta fahimci haushin Amran ya bata kwarin gwiwar amsata...gashi kuwa taji zafin sa. Wani 6angare na zuciyar ta ke bata shawarar bata hakuri, yayin da wani 6arin zuciyar ke yi mata garga'din kar tayi. Kwalbar dake hannun ta ta dam'ke sosai sannan ta wuce 'daki inda Mufee ke bacci, ba yanzu zataje 'dakin nasa ba tunda ta riga ta gama yi masa duk abinda zata masa, yanzu kuma Dr Fawwaz ya rage yazo ya 'kara dubashi ko yanzun ma da su ka ganta palor aiki ta gama parlorn tana shirin wucewa suka tarar da ita. 'Karfe takwas zuwa tara baya wucewa batare da Dr Fawwaz ya iso gidan ba, tasan haka amma bata san mai ya dauki hankalin ta ba har kusan 'karfe goma sannan ta tuna da lokacin da ya kamata ta kasance a dakin nasa, da sauri ta tashi ta fito Moofy na biye abayan ta dan ta riga ta tashi a baccin kuma idan ta barta ita ka'dai kuka zata yi...hannun ta ri'ke da ledan magungunan da aka kawo mata cewa nasa ne...ita dai haka nan kawai taji zuciyar bata yi na'am da su ba koka'dan. Da sallama ta shiga 'dakin duk da tasan ba lallai ne ta samu amsar sallamar ta ba indai ba Dr Fawwaz ne ya iso ko su Sultan ba, shima Sultan yanzu haushi ta yake ji ko zai amsa sautin muryar sa da 'kyar yake fita...jin shiru babu amsa yasa ta fahimci babu wanda ya iso kamar yadda take tunani. A hankali ta 'karaso cikin 'dakin kanta na kallon 'kasa dan sau tari bata fiye son kallon inda yake karaf 'daya ba kasantuwar tsananin tausayin sa da kullum ke 'kara hauhawa mata a zucia...idan ta juri kallon sa a hakan abu na gaba da zata tsinci kanta ciki shine zubar hawaye da karayar zucia. Sai ji tayi an bu'de 'kofan bathroom dake 'dakin, tsaye ta mi'ke cikin ranta take ayyana suma sun makara kamar ni kenan..basu zo da wuri ba ne ko kuma aikin ne bai 'kare musu da wuri ba....duk zaton ta wani cikin masu zuwa duba shi ba ne. Salmerh😘 [23/11/2022, 7:04 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Wattpad@* _Serlmerh-md_ 🅿️ *...73* ......Tunanin Zaitoon ya tsaya ne dai- dai da tsayawar numfashin ta, tsaye ta mike cak numfashin ta na kokuwa da juna wajen fita sbd al'jab, cike da mamaki ta zaro idanun ta waje sosai, sake maido da duban ta tayi kan gadon ganin wayam babu kowa. Take ta sake kallon sa akaro na biyu domin tabbatarwa idanun ta, Rayyan ne ko kuwa wani mai kama da shi ne....? Tsam ta tsaida idanun ta akansa, yayin da yai mata duba 'daya kawai ya 'dauke idanun sa daga kanta. Rayyan ne ya fito daga bayin dagaske ba wani ba. Ta tabbatar wa zuciyar ta hakan. Cike da tsananin mamaki take duban sa, shi kam cigaba yayivda tafiyar sa da take da 'kyar kuma a dur'kushe tamkar wani dattijon da 'karfi da lafiya sukai masa 'karanci, hannun sa na hagu dafe a cikin sa yake tafiyar kuma a hankali. Jikin sa farar singlete ce da bakin dogon wando..kallo 'daya zakai masa ka fahimci irin muguwar ramar da yayi..tamkar ba Rayyan da tasani abaya ba. Cike da mamaki Zaitoon ta ringa binshi da idanu sam bata san har haka aka samu cigaba ba...kuma har zuciyar ta taji tana taya Ammi farin ciki da samun sauqin 'dan na ta ko ba komai alamu sun nuna cigaban lafiyar yafi na baya tunda gashi da 'kafafun sa...yayin da gefe guda kuma kanta take tayawa farin ciki, domin alamu sun nuna ta kusan samun 'yancin kanta itama. Sai ma ta rasa shin wazata gayyato yazo yaga abin da idanun ta ke gane mata, ko kuwa ihu zata yi dan bayyana farin cikin ta, Amrah..kai a a...Marwa...Marwa tana gidan ta yanzu haka, Anty Madeena ta tafi, haka ma Anty Raihana...sannan bata da waya balle ta kira wanin su...da ace ma tana da wayar da Ammi zata fara yiwa wannan albishir din ayanzu. Dan rasa abin yi kawai sai tsurawa maganin dake hannun ta idanu amma tunanin ta baya tare da shi sam, sau 'daya idan ka.kalli fuskar ta zaka hasko wannan kwantaccen farin ciki dake tasowa tun daga zuciyar ta...murmushi ya kasa barin fuskar kwata- kwata. Sai da ta rintse idanu ta bude su akan hannun ta tana mai sake kallan maganin domin bazata iya sake duban inda yake ba. Shima maganin bazata iya gane komai ba, amma data tsaida idanun ta akansa sai ta kasa tuno me irin kalar shi cikin magungunan da Ammi ke bashi, wannan kalar sa yellow ne, cikin wa'dancan kuma babu yellow, takaddar jiki kam bazata iya tantance su ba amma kalar maganin ba zai 6ace mata ba dan sau tari da ita ake basa...abu guda daya da har yau bata iya yi masa ita ka'dai shine goge masa jikin sa, inma zata yi toh sai dai in goge masa iya inda yake waje ne, misali kamar saman kafa'dun sa hannayen sa da 'kafafuwan sa. Shima 'din tun ranar da taga irin ba'kin tabon da Mufeedan ta ke da shi a jikin sa bata 'kara ba...dan da zarar ta gani sai taji zuciyar ta na tsinkewa da 'karfi gami da fargaba. Dr Fawwaz ke masa sauran. Bazata manta ba ko ranar ma Dr Fawwaz din yasa ta zama, inda yace lallai ta zauna taga yadda yake yi sbd ta koya da kanta ba sai sun ta jira azo a gyara masa jiki ba. Bata ce da shi komai ba kawai tayi murmushi. Hakan kuwa ta tsaya sai dai kusan rabin tsayuwar tata kaita a 'kasa yake...lkc lkc ta kan 'dago kai ta kalle su sai ta kuma sunkuyar da kanta, a lkcn cikin sa Dr Fawwaz ke goge masa da wiper dake hannun sa. Har ta sunkuyar da kanta sai kuma take ta sake 'dagowa dan tabbatar da abinda idanun ta suka gane mata. Madadin taji fargaba sai taji murmushi ya kubce mata. Cikin rai ta ayyana irin na Moopy na.." Har ila yau dai ga wani abin da kuka yi tarraya kansa kai da Moopy na bayan yanayin hallitar lips 'din ku. Ko bayan fitar Dr Fawwaz kasa nutsuwa tayi, sai da ta sake 'daga singlete 'din sa ta zubawa ba'kin circle dake gefen cikin sa idanu. A hankali ta kai hannu ta shafo shi..tana murmushin mugunta, har hasko yanayin fuskar sa take yadda zaiji idan ya ji cewar wannan abin ma Mufeedan ta nada irin sa. Kamar an tsikare ta kuma ta cire hannu gami da mikewa tsaye..sakamakon wani faduwar gaba da taji. A waNcan lkcn Mufeeda na can makaranta...sai lkcn tashi ya kusa take zuwa ta taho da ita gida...amma hakan nan ranar kasa zuwa tayi sai dawo mata da yarinyar driver yayi shi ka'dai. Tun kuma ranar bata 'kara yadda taga abin ba sbd fargaban dake ziyartar ta. Ko yanzun ma tuno wancan ranar da tayi yasa ta saki wata 6oyayyar ajiyar zuciya gami da murmushin mugunta ta cigaba da bin maganin da idanu. Zuciyar ta fal farin ciki ta shiga bayin da ya fito ta tsabtace shi, duk tasan ba wani datti gare shi ba dan ba kowa ke amfani da shi ba duk da hakan kusan kullum takan tsabtace shi. Tana yi tana tunanin ta yadda zata yiwa Ammi wannan kyakkyawan albishir 'din gashi ita ba waya ba bata kuma san ranar da zata dawo ba. Sai dai ko in sun hadu da Marwa tayi mata albishir din ita kuma ta tayata isarwa ga Ammi. Baiwar Allah kusan kullum sai ta sashi agaba tayi ta kuka da hawaye, sosai take son 'dan ta amma ma'kiya sun musu katanga. Lokacin da ta fito abayin sai taga ya koma ya kwanta kamar yadda ya saba kullum duk yadda akayi yanzun ma babban uzuri ne ya tashe shi, to ko tsawon wani lokaci ya 'dauka cikin wannan halin oho, tsawon wani lokaci ya 'dauka yana tashi da kansa yy wa kansa abu batare da ta sani ba, ko kuwa dai yau ne farko...duk bata da amsa. 'Kofar fita ta nufa fuskar ta cike da murmushi yayin da hannun ta ke rike da na Mufeeda. Rayyan tsurawa bayan yarinyar idanu yayi, yana jin wani sassanyan yanayi na shigan sa, sai ma ya rasa albarka zai sawa Zaitoon ko kuwa mai zai mata. Kamar tasan zai bukaci ganin 'diyar sa a yau din nan ta kuwa zo masa da ita...ji yake tamkar ya janyo yarinyar ya rike ta a wurin sa gudun kar wani abu ya saman masa ita. Sai dai hakan ma ya gode wa Allah daya 6oye wa kowa ita, ya gode Allah da bai yi azar6a6in bayyanata tun san da ya fahimci cewa jinin sa bace ita, da yanzu a zaman jinyar sannan bai san me zai faru gare ta ba,...Alhamdulillah, Alhamdulillah kawai yake ambata cikin ransa. Zaitoon har ta kusa fita sai kuma ta dawo da baya, gaban gadon nasa taje ta tsaya ganin ya sake maida idanun sa ya lumshe amma tasan ba bacci yake kamar na baya da basu da tabbacin ranar farkawar sa, sa6anin wancan yanzu da kansa ya kwanta ba kwantar da shi akayi ba, za kuma a iya tashin sa ya tashi ba kamar baya ba... kuma sarai yasan da wanzuwar ta a cikin 'dakin sai dai sam bai nuna alamun hakan ba. Magani ya kamata yasha first amma bata san ta yadda zata mai bayani ba..batasani ba ko zai bu'kaci wani abin daban bayan maganin. Take sai ta diririce tama rasa mai ya kamata tayi. Ashe dai dama 'karyar sakewa take a 'dakin nasa ashe dan baya cikin hayyacin sa ne yasa take sakewa. Gashi yau Dr Fawwaz ya makara dan bata ga alamun zuwan sa ba sam. Babu mamaki ma sai yamma zai shigo, 'kila wani uzuri ya ri'ke shi. Da 'kyar ta saisaita sautin muryar ta a hakan ma muryar na rawa kanta a'kasa tafara fa'din.." Kayi hakuri...dama an wa Ammi 'kiran gaggawa ne yau da sassafe ta wuce Maiduguri amma ga wannan magungunan ta aiko wai kasha...". A hankali ya bu'de idanun sa ya tsayar akan maganin da ta 'dago tana nuna masa...koda ace kullum idanun sa a lumshe suke amma hakan bazai hana shi gane kalan nashi maganin ba, balle ma tunda yaji tace wa'dansu sai ya ji bai yadda da maganin ba, ledar maganin ya kalla sannan ya sake bin hannun ta da kallo da ke rike da magungunan. Sai yaga kuma gashi an cire takaddar jikin wasu dan kar agane wani irin magani ne ma kenan. Shiru yy bai tanka mata ba illa maida idanun sa da yayi kan Mufeeda kallon sakan hudu yai mata ya sake maida idanun ya rufe su. Ji suka yi ana nocking 'kofar lkc guda... da mamaki ta kalli 'kofar dan tasan bayan shigowar ta bata kulle har da key ba. Kallon juna suka yi ita da shi lokaci guda, hakan yasa shi mi'ka mata hannu, maganin ta bashi da 'dan jan jiki ya tashi zaune dan har yanzu yana jin jiki ciwon jikin sosai File 'din sa dake kan side drawer ya bu'de da yake ciki da biro, amma babu damar ya yagi 'daya daga cikin takaddun domin duk bisa tsari suke. Zaitun kam binsa da idanu kawai take cike da tsananin mamakin sa, yayin da farin cikin da ke mamayar ta yake rinjayar mamakin a hankali. Kansa ya dafe sai kuma yayi saurin kamo hannun ta har ta firgita sai kuma taga bai bi ta kan firgicin nata ba, rubutu layi guda yy mata cikin tafin hannun ta while ana cigaba da bugun 'kofan daga waje. Yana gama rubutawa ya ajiye biron ya koma ya kwanta kamar ba shi ne ya tashi zaune yanzun ba. Zaitun sai da ta sake duban sa kafin ta dubi hannun ta inda yy rubutu da mamaki, me hakan ke nufi kenan? Ta tambayi zuciyar ta. Bugun 'kofar da aka sake yi gami da ambatar sunan ta ya sata saurin ankarewa domin idan kunnuwan ta basu yi mata karya ba sautin muryar Ammi taji ta 'kira yi sunan ta. Zuwa tayi ta bu'de tana sakin ajiyan zuciya tace.." Ammi har kin dawo? ina cikin bathroom ne ina aiki wlh banji bugun ba..." Ta 'karashe maganar da sakin ajiyan zuciya mai sanyi...gami da jinjina karyar da ta gamawa shirgawa. " Bakomai..." Ammi tace tana mai bin ta da kallo sama zuwa 'kasa. Fara'ar da ta karanta saman fuskar ta ya bata mamaki matuka. " Nadawo...ai hankali na ya kasa kwanciya sai da na 'kira wata 'kawata da muka yi secondary school tare acan Geidam 'din itama take aure, ita ta tabbatar min babu komai, karshe ma ta ha'dani waya dasu mukayi magana, andai sace musu wayoyi amma kowa yana nan lafia kalau duk mun yi magana da su... shiyasa na dawo kawai tunda nima marar lafiyr gare ni zuwa wani lkc naje in dubo su..." Ammi tayi duk wannan bayanin ne tana mai 'karasawa cikin 'dakin. " Masha Allah...Allah ya 'kara tsarewa.." Cewar Zaitoon itama tana mai bin bayan Ammi zuwa ciki. Kamar zata yi mata albishir 'din tashin san amma ganin yanda ya koma ya sake kwanatawa sai ya fahimtar da ita wani abu."...Ya jikin nasa ne Zaitoon...?" Ammi ta tambaya tana mai kama hannun sa. " Alhamdulillah da sauki sosai Ammi...". Zaitoon ta bata amsa tana murmushi. Ammi da yake ba duban fuskar ta take ba yasa bata fahimci hakan ba...sai ma.cigaba da tayi da fadin. " Ni abin ma yanzu ya fara bani tsoro, so nake mu sake magana da Fawwaz, 'dazun ya 'kirani wai zai shiga tiyata da safen nan bazai samu shigowa ba sai zuwa anjima may be zuwa yamma zai shigo, so nake a canza wannan tsarin, in ma asbitin ne gara mu koma abin yana ban tso....." Bata kai ga rufe baki ba Zaitoon dake cike da tsananin farin ciki ta ce " Ammi... !" Sai kuma tayi shiru tana zare idanu. Kallon inda Rayyan yake kwance tayi tana kikkif da idanu domin bata san me ya kamata tace da Ammin ba kuma. Duban ta Ammi tayi ta kuma bi inda take kallo da idanu. " Me ya same shi ne Zaitoon...? Me kike son sanar da ni...? Wani abu ya faru da shine...?" kai ta girgiza sannan ta 'dora da fa'din.." Ammi wallahi 'dazun naga kamar shi ya fito daga bathroom da 'kafafun sa kuma shi ka'dai..." A ru'de Ammi ta dube ta da kyau...Zaitoon da rawar muryar ta 'kara da fa'din" Kamar shi Ammi...wallahi shi na gani..." Inda tayi maganar a 'darare tamkar mai tsoron furtawa hadda 'dan ja baya ganin yadda Ammin ta fuskance ta. " Zaitoon kin tabbatar abinda kike fada min gaskia ne ko kuwa kina fada ne kawai dan naji dadi...?" Yanayin da Ammi tayi maganar Zaitoon sai taji ta bata tausayi sosai. Ita kanta zuciyar ta ya karaya...bata fatan ace ganin san da tayi ace ba gaskia bane...amma tana da tabbacin a zahiri ne ta ganshi bisa 'kafafun nasa tunda har ta6a hannun ta yayi. Da sauri ta 'dago hannun nata dan sake tabbatarwa sannan tace da Ammi. " Dagaske nake Ammi, kin ga ma har ya rubuta min abu a hannu na...". Ta 'karashe maganar da nuna mata hannun ta. Da sauri Ammi ta kamo hannun Zaitoon tana kallo gami da shafa rubutun, Zaitoon kin tabbatar shine ya rubuta wannan...?" Da kai ta bawa Ammi amsa tana duban fuskar ta da hawaye gami da murmushi suka lullu6e shi. Sai dai murmushin ya bayyana cewa na tsantsan farin ciki ne dake tasowa tun daga 'kasan zucia. Gaban gadon da yake kwance Ammi ta isa ta tsaya tana bin sa da idanu tama kasa fa'din komai. Zaitun bin su da idanu tayi daga shi har Ammin batare da ta 'daga 'kafafun ta ba. A hankali ya bu'de idanun sa ya sau'ke su akan fuskar Ammi ya sau'ke su, sai dai bai motsa ko da 'dan yatsan sa ba. Bai so bayyana kansa cikin gaggawa haka ba amma wannan dakikiyar yarinyar ta riga ta tona shi, sai kace bata ga rubutun da yayi mata ba....sai dai bisa ga rubutun da Zaitoon ta nuna wa Ammin nasa yasan itan zata fahimci manufar sa zaku ma ta rufe sirrin sa. 'Kasa Ammi ta dur'kushe tana sakin hamdala a bayyane...bayan haka ta fara jero masa tambayoyin inda ke masa ciwo Rayyan bai bata amsar ko guda da bakin sa ba...'karshe 'kokari kawai yayi ya mi'ke zaune. Hakan ya sake ruda hankali da farin cikin Ammi. Ganin hakan yasa Zaitoon kama hannun 'diyar ta kawai suka yi waje taja musu 'kofar tana sakin murmushi. Cikin ranta take masa fatan samun lpy ingantacciya. Salmerh😘 [25/11/2022, 9:25 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Wattpad@* _Serlmerh-md_ 🅿️ *...74* ........Zaitoon kam 'daki ta koma tana sake duban hannun ta...har a lokacin Amrah na zaune tana kallon Zee world...ko inda take bata ma kalla ba haka itama ta wucewar ta bata damu da wanzuwar ta cikin palorn ba.... Hannun ta nada saurin yin zufa hakan yasa tana shiga ta nemi abin rubutu da 'kyar ta samu 'yar takadda wacce ake zubo magani a ciki sai dai babu abin rubutu sam dan bata da shi ba amfani take da shi ba.... Hankalin ta taji ya fara tashi saboda ita kanta tana so ta san manufar rubutun da yai mata a hannun...kuma ita bata iya karatun hausa sosai ba ka'dan- ka'dan ta iya shima 'din Marwa ce ta koya mata duk da haka sai ta nutsu sosai take iya ha'dawa da 'kyar. Bincike ta hau yi hankalin ta atashe, kamar an ce mata wani abin tashin hankali ne ya rubuta mata, tasan ba hakan bane amma haka kawai taji zuciyar ta ta 'kagu da son sanin abinda ya rubuta 'din dan tasan a halin da yake ciki dole ne ya kasance abu mai muhimmanci ne. Da 'kyar ta ci karo da brown eyes pencil cikin drawer wanda ake zana gira da shi bata da mu ba ta koma ta zauna....Mufee na 'kananun kuka ma amma bata damu ba da yake tasan wanka take bukata ba komai ba, karo na farko kenan da taji wani abu daban ya 'dauki hankalin ta akan 'yarinyar ta akaf din rayuwar ta. Jikin ta ta jawo Mufee ta kwantar da kanta saman 'kafa'dar ta...da 'da'd'daya 'da'd'daya ta fara 'dauko rubutun nasa tana ajiye wa saman papern nan...wasu ma har suna fara gogewa saboda yawan zufan dake hannun ta. " K a r k i f a d i m a w a k!...." " Subahanallah 'karshen ya goge wallahi". Ta fa'da cikin ranta tana mai jin babu da'di. Sam ta kasa gane menene a wurin, duk iya kokarin da tayi wajen ganowa amma ta kasa ganewa haka ta ha'kura da wanda ta samu ganewa. Tana bubbuga bayan Mufee a hankali take nazartar rubutun...da manyan harruffa ne ma zata fi saurin gane su da kyau amma 'kananun haruffa na bata wahalar ganewa gaskiya, dan bata kai ga bambance su a makaranta ba har ta bar garin nasu...wannan ma bisa taimakon Marwa ne da take 'dan nuna mata wasu abubuwan yasa har ta iya ha'dawa. " _K...kar..kak...kar ki..fa' dima k..."_ Abin sai ya kasa bata ma'ana guda 'kwa'k'kwara. Ta maimaita fin sau bakwai kafin ta fahimci ka'dan ahakan ma " Kar ki fa'dima ko..." Shiru tayi ta shiga nazarin rubutun sosai..sam ta kasa 'karasawa, a cewar ta sai take ganin kamar sunan mutum ne ya rubuta amma duk gidan batasan wani da sunan shi ya fara da kalmar _ko_ ba. Har taje tayiwa Mufee wanka itama tayo nata ta fito abin na ranta kuma ta kasa fahimtar in da maganar ta dosa. Tana shirya Mufeeda tana sake duba rubutun nata. Ganin bata da masalaha yasa ta kawai ta 'karasa da kanta, in dai har zaice kar ta gayawa wani to ai akwai dalilin sa na fa'din hakan, dan haka kawai gara ta 'karasa da "kowa.." Kenan kawai inja baki na inyi shiru yake nufi in dai na fahimta dai- dai. Cikin.ranta take ta zancen zucin ita kadai...ta sa'ka wannan ta kwance wannan har dai ta gama yanke shawarar da taga shine mata dai- dai. Baki ta kya6e tana tura bakin ta gaba, a fili na furta ai na riga na fa'dawa Ammi toh kaima meyasa baka sanar da ni tunda wuri ba....." " Toh ai kuma Ammi ce, ya ma ya isa yace har ita kar in fa'dawa ne, bayan yasan tafi kowa damuwa da rashin lafiyar tasa. Yanke wannan hukuncin ne ya sani ta shi da rubutun nata ta wuce bayi, mitsi-mitsi tayi da shi ta kora shi a rariya. Luf kuwa taji hankalin ta ya kwanta, sai dai wani 6oyayyan farin cikin da ta san duk na taya Ammi murnar tashin 'dan ta ne...matar na matu'kar bata tausayi musamnan idan taga tana zubda hawaye akansa, haka take zama ta tayata kukan itama tana sake rungumar Mufeeda a kirjin ta da tunanin idan akace ita ce a wannan halin ni ya zanji. Duk lokacin da tayi wannan tunanin bugun zuciyar ta canzawa yake yi, har ga Allah bazata iya juran ganin Feefy cikin wani hali ba sam...ta kan furta a fili cewar..." _Yah Allah ka tsare min ita, Yah Allah ka kare mu, ka bamu kariya, Yah Allah ka jikan iyayena ka tsare min su a duk inda suke, Yah Allah 'daura mu akan makiyan mu ka rabamu da mummunan 'kaddara ka bamu dacewa dunia da lahira..._ " Addu'ar ta kenan kusan kowani lkc indai akan kanta ne. Parlor ta dawo dan lokacin ha'dawa Amrah breakfast yayi, tana fitowa tagan ta har yanzu ta maida hankali kan kallon ta tamkar ance mata nan aljannar ta take. Baki ta kya6e tana girgiza kanta a 6oye...wannan hala bata ga isowar Ammi bane ko mene, ko kuwa tsabar iskanci ne da nuna isa ke damun ta, tunda abu ne mawuyaci tasan mutun ya wuce ta nan parlorn batare da ka ganshi ba tunda ba girma ne da 6angaren wani na sosai ba. Da ganin Zaitoon Amra sai ta 'dan yi mi'ka tana gyara zama tace " Ke ha'do min tea dan Allah kafin kije gyaran dakin nasa bana so wannan series 'din ya wuce ni ne, sai na gama zan shiga na duba shi naga ma Ammin tasa ta fita..." Tayi duk wannan dogon bayanin ne batare da ta dubi inda Zaitoon take ba. Ni kam Mamaki sosai Amrah ke bani, mamakin yadda koka'dan ba ta jin kunyar abinda take yi, bata san sai yaushe zata canza ba, mutum gaban iyayen sa ki ringa nuna halin ko in kula da lafiyar sa har haka..ko albarkacin rashin lafiyar ta sama ai sai yaci. Tasan kawai haushi ke cinta haushin kuma bana komai bane face na wai an masa aure da ita, auren da ita kanta tasan ba zuwa ko'ina zai yi ba, auren da shi da babu duk 'daya ne duk 'din su sun sani....toh in kuwa haka ne menene abin damuwa kuma... Duk da yake har ga Allah bansan yadda ake zama da miji ba amma nasan yanayin zaman Amrah da majinyacin mijin ta akwai matsala aciki...sam ba bisa tsari abubuwa ke tafia ba, Amrah sam damu da shi ba...ni kuwa da kullum nake ji na tamkar matafiya me ze sa in saki jiki ko kuma a damu da wanzuwa ta. A hakan ma Amrah ta 'dan rage zafin kishin ta ne ganin Zaitoon bata ta6a nuna mata cewar dai- dai suke yanzu ba, aikin da take mata ada da tana matsayin 'yar aikin ta bata canza ko guda ba. Haka ta ha'do mata Tea ta kawo mata Amrah ta kar6a idanun ta na kan T.V..ganin Zaitoon zata koma 'daki ya sanya ta fa'din.." Yau 'din kuma ni kike so in gyara masa 'dakin ne ko me..?" " Na riga na yi ai". Shine amsar da ta bata atakaice batare da ta waigo ba, itama bata damu ba dan idanun ta na kan T.V ne. Anty Madeena da Anty Raihana sosai suka garga'de ta akan yiwa Amrah hidima dan acewar su matsayi 'daya suke da ita a yanzu agidan cikin abubuwa da dama kuwa ta kan fahimci abinda suka fa'da 'din shi suke nufi sai dai ita sam bazata iya ba, har kullum bata ganin sauyawar matsayin ta da na baya a gidan, shiyasa tace baza ta iya daina yiwa Amrah hidima ba kamar yadda bazata daina yiwa kanta kallon ma'aikaciya a gidan ba, abu guda ne baza ta 'dauka ba shine rainin hankali da cin fuska...banda su ma Anty da wata magana ita yaushe a ina ma ta isa ha'da kanta matsayi da iyalin Rayyan. ***** A 6angaren Rayyan kuwa 'kar'kashin pillow ya cusa magungunan da ya kar6a a hannun Zaitoon, yasan basu ha'da ala'ka da shi ta ko wacce siga ba, yasan ba maganin.da zasu amfani lafiyar sa bane sai dai su kassara shi, dan yasan magani farin sani. Sun yi magana da Ammin sa duk da shi dai bai bu'di baki ya tanka ta ba amma cikin magananun nata ya fahimci tsananin damuwar da take ciki akan sa. Baya ga haka ma duba 'daya yayi mata ya fahimci ramar da tayi sbd damuwa. Sai da ta gama fa'din duk abinda zata fa'da gami da jero masa tambayoyin da zata yi masa 'daya bayan 'daya yana bata amsa da kansa yana jin wani rauni gami da tausayin mahaifiyar tasa na ratsa shi matu'ka. Tambayoyin duk da tai masa game da lafiyar sa ne, me yake ji meke damun sa a yanzu. Ta so ta kira Dr Fawwaz ta sanar da shi amma Rayyan ya hana ta. Tace ta kira masa Sultan nan ma yace a a..'karshe fita tayi zuwa 'dauko maganin sa acewar ta, tana fita kuwa ya tashi ya sake sawa 'kofar key ya wuce bayi da maganin dan sam bai yadda da shi ba...barin ma da tace wai aikowa da shi akayi...bai ta6a zargin kowa kan komai na rayuwar sa kai tsaye ba amma wannan karan tashin farko abinda ya fara zuwa bakin sa shine _SULTAN_, batare da wani dogon nazari ba ya yanke hukuncin Sultan ya kawo shi.... Domin ya fahimci maganin ba daga Ammi bane yazo bata ma san da zaman sa ba, da farko yy tunanin ko ta bayar akawo ne aka canza shi amma dalilin sanar da shi da tayi cewar bari taje ta kawo masa maganin sa har tace mantawa tayi, yasa ya fahimta, ta kuma ce tama 'kira Sultan tace ya sa Marwa ta dubo maganin a 'dakin ta ta kawo su bashi bata san ko sun 'dauko ko kuwa sun manta ba...sunan Sultan da yaji cikin bayanin yasa ya tabbatar da zargin da zuciyar sa keyi akansa. Cikin sinc ya gwada zuba yawun sa ka'dan sai ya bu'de bakin kwalbar ya 'diga 'daya maganin ciki lokaci 'kan'kani yaga yawun nasa ya tsinke yana komawa kamar ruwa...shi dai haka kawai yaji maganin bai kwanta masa ba dan yasan Ammi bazata ta6a aikowa ta hannun wasu daban ba sa6anin ahalin ta. Ruwa ya sake ya kora wanda ya zuba 'din sannan ya fito, adana magungunan yayi ta yadda babu wanda zai san inda ya ajiye, sake bu'de 'kofan yayi sannan ya koma ya kwanta kamar yadda kowa yasan yadda yake kwance tun farko. Addu'ah yake cikin ransa Allah yasa kar yarinyar nan ta fa'da ta ganshi da 'kafafun sa, dan yasan ma'kiyan sa ba ha'kura suka yi ba, tunda a yana kwancen ma ba fasa kawo masa hari suka yi ba, yafi so ya gama tabbatar da zargin sa kafin zartas da hukuncin koma waye ke bibiyar rayuwar sa...dan hk fitar bazata yake so yy ma kowa bayan ya samu 'karfi sosai ajikin sa...Ko Amrah ma ba 'karamin mamakin ta yake ba, domin tun da yafara gane kansa ya fahimci bata damu da shi ba sam, a yini bai fi sau 'daya take zuwa inda yake ba, wataran ma sai dare take zuwa duba shi hakan kuwa bai ta6a damun sa ba illah mamakin ta, ya kan tuno soyayya da 'kaunar da Amrah ke yi masa kafin kwanciyar sa amma yanzu duk babu su. Hak'ika lafiya ni'ima ce lafiya jarice, duk halin da zaka shiga a duniyan nan idan ka tsinci kanka cikin masu lafiya kawai ka gode masa domin yayi maka baiwa, a hakan ma kwanciyar yayi babu abinda ya illatu a jikin sa illa hannun sa amma Amrah take yin banza da shi. A hakan fa zaka tarar wasu hankali suka rasa, wasu kafa wasu hannuwan suka rasa, wasu ji wasu gani,.amma shi duk Allah bai raba shi da ko guda ba, ciwom hannun sa kuma yasan da zarar an gyara shikenan...toh miye dalilin Amrah na guje masa...illa wannan yarinyar da kullum bata gajia da shigowa hidima da shi. Abinda ya lura ma har abinda bai dace ita tai masa bama ita a wurin, sosai abin ke 'daure masa kai, yakan kuma yawaita tuno masa da marigayiyar matar sa dan halin su da bambamci sosai da Amrah yasan da itace ba haka zata watsar da shi ba ga wata 'yar aikin ta ba...cikin ransa yai mata Addu'ar samun Rahama wurin mahalicci, ya sa abinda ta haifa suka kuma koma tare da ita ya kasance mai ceton ta ne...yin wannan addu'ar ya tuno masa da Mufeeda, hakan yasa shi dakatawa da addu'ar tasa yayi tsam da ransa...tun tashin sa sai biyu kawai yaga yarinyar, ji yayi tamkar ya tambaya akawo masa ita amma yasan kwatanta yin hakan koda sau guda ne dai dai yake da jefa rayuwar ta cikin ha'dari. Bayan kwanciyar sa da kusan awa biyu kafin Amrah ta shigo duba shi...ko zama bata yi bama lokacin kuwa bacci ya 'dauke shi me 'dan nawi so bai san da shigowar ta ba. Ko da Ammi ta dawo bata tashe shi ba, zama tayi tana jiran tashin sa a baccin yayin da zuciyar ta ke cike taf da farin ciki mara misaltuwa. A haka Zaitoon tazo ta tarar da ita. Nan ta sake gaida ta, Ammi sosai take yabawa 'ko'karin ta gami da yi mata godiyar kyakkyawan albishirin da tayi mata a yau 'din. Zaitoon na murmushi tace bakomai Ammi. Ammi tace yau kam kije ki huta wa ranki kema zan taya ki aikin kinji. Zaitoon tace" a a Ammi zanyi...ai aiki na ne..." Maganganun sun ne ya tada Rayyan a bacci ya kuwa zuba musu idanu yana kallon su gami da sauraran su. Zaitoon ce ka'dai ta lura da tashin sa domin sau biyu suna ha'de idanu Ammi ce dai bata lura ba, so ganin tashin nasa ne ya 'kara mata 'kwarin gwiwar barin dakin. Har ta 'karasa ficewa kuwa Rayyan bai motsa ba, sai bayan fitar sa ne da Ammi ta dawo da duban ta gare shi sannan ta ga yana kallon ta. " A a ashe ma ka tashi...sannu babana...zaka iya tashi ka zauna ne ko kuwa kwanciyar yafi maka...?" Tayi maganar gami da mi'kewa tsaye da niyyar tallafa masa. Bai tankata ba, dan bai san meyasa tun tashin sa yake jin harshen sa nayi masa nawi wajen furta kalmomi ba. Duk da hakan abinda ke mai kai kawo a zuci yake son fa'di a bayyane, so yake ya tambayi Ammi wani abu dake kulle masa tunani. " Ya jikin naka...?" Ammi ta tambaya di kulawa fuskar ta da annuri cikakke. Da kai ya bata amsa. Ammi ta ta6a jikin sa da wuyan sa, hannun sa da ta lura alamun baya motsa shi har yanzun bayan uban 'dauri da akai masa tun ranar farko...aka kuma yi tunanin ya ha'de aka kwance shi bai fi kwanaki goma baya ba. Hannun ta kamo a hankali ta 'dago ya rintse idanu gami da cije bakin sa yace.." Wash Ammi...". Tace" Har yanzu yana ciwo ne...?" Kai ya 'dage mata sama...alamar erh. tace " Ikon Allah...sannu, bari Fawwaz ya iso asan me za'a yi, ko kuwa dai asbitin zamu je kawai mu same shi..dama kasan dole a koma ai for check up. " a a Ammi..."! Ya bata amsa cikin sauri. Duban fuskar sa tayi da alamun tambaya. Sai ya wani yatsine fuska yana komawa baya ya kishingi'da yana gyara zaman hannun sa mai ciwon da hannun sa na hagu saman jikin sa. " Alhamdulilla jiki na da sauki sosai bana jin komai yanzu sai ciwon jiki..shima with time zai warware.." " Amma kasan dole ne sai an maka check up 'din ai ko...?" " Za'a yi daga baya Ammi.." Bata ce da shi 'kala ba illa" Hmm" da tace kawai ta mi'ke, tea ta ha'do masa mai zafi mai kuma kauri ta kawo masa. Bazai iya ri'kewa da hannun daman san ba hakan yasa ta ri'ke a hannun ta tana bashi abaki ka'dan- ka'dan yake sha ko rabin sa ma bai sha ba yace ya isa, duk yadda tso ya 'kara Rayyan 'ki yayi. Ammi sai tayi murmushi...dama tasan halin sa idan bai da lafiya sai a hankali...koma mata yake tamkar wani 'dan goye. Yana murza hannun sa mai ciwon da 'daya hannu mai lpyr yace " Ammi yarinyar nan..wai meyasa take yawan shigowa nan ne..ban so ni...i need privacy bana san ana yawan takura ni.." " Wace wai...kake magana akai ne..?" Ammi ta tambaye shi tana ajiye mug 'din dake hannun ta duk da ta fahimci wa yake nufi amma bata so ta nuna masa kai tsaye. " Wai Amrah kake nufi..?" " a a Ammi..wancan yarinyar...". " Wai Zaitoon..?" Ammi ta tambaye shi tana mai 'ko'karin saka idanun ta cikin nasa. Da kai ya amsa ta yana kawar da kansa gefe tamkar yasan mai Ammi ke da niyyar yi. " Toh in dai wannan ce ai a halin yanzu baka da privacyn da ya zarta ta..." Ta bashi amsa cikin nuna halin ko in kula da maganar. Kallon sa ya dawo da shi gareta Ammi tayi saurin jinjina masa kai domin tabbatarwa. Sannan ta 'kara da fa'din..." Ina nufin a halin yanzu Zaitoon mata take agare ka, an kuma aura maka ita ne sbd ita ka'dai na yadda ta kula min da kai, ita ka'dai zuciya ta ta yadda in barwa amanar ka na kuma yabawa 'ko'karin ta matuka...domin kyautatawar da tayi maka a lokacin da baka da lfy kake kwance abin a yaba mata ne..." Tun bata kai ga rufe baki ba ya zaro idanu yana duban Ammi. Kai ta sake jinjina masa sannan ta cigaba da fa'din" Burina kaima ka 'kauna ce ta ka kula da ita, buri na zaman ka tare da ita ya kasance na har abada ne, hakan ka'dai ne zai baka damar saka mata abinda tayi mk domin a yanzu ko kace zaka sallame ta ni bazan goyi bayan haka ba, idan kace ku'di kuma ba yadda ita zata yi ta kar6a ba..." " Ammi ko bazata kar6i kudi ba a dai nemi wata hanyar amma banda batun aure Pls.." " Me kk nufi wai Muhammad? kana ga kamar zanyi maka za6in da zai cutar da kai ne, ko kuwa kana gani kamar zan ha'de baki da ita in cuce ka ne...?" Idanu ya lumshe bai kalli Ammi ba bai kuma bata amsar komai ba, bai ma san ta yaya Ammin zata fahimce shi ba..hannu ya sa ya ringa shafa goshin sa da yatsun sa biyu. Jin Ammi ta saki 'karamin tsaki ne ya sanya shi saurin bu'de idanu ya kalle ta a tsaye ya ganta ya kuma fahimci shirin barin 'dakin take sai yy saurin fadin" Ammi dan Allah ki..." Hannu ta 'daga masa sannan tace" Kar kace min komai..daga tashin ka bazaka sani gaba da abin 6acin rai ba..kai baka da tunani ne hala...?" Shiru yayi yana jin babu dadi cikin ransa. Ammi ruwa ta kawo masa ajiye sannan ta matsar masa da magungunan sa tace" kasha magani. Daga haka ta fice ta bar masa dakin Rayyan ya bita da idanu. Ya rasa wani irin hukunci ne wannan. Wai ma shin wani irin hali ya shiga ne da har za'a 'daura masa aure batare da ya sani ba..ina Amrah da ita bazata kula da shi ba har sai an 'daura masa aure da yarinyar nan. Kimanin mintina sha biyar ya 6ata kafin ya tashi ya 6alle marfin ruwan sannan ya sha magungunan sa yana sha yana jinjina tsadar su. Gefe guda kuma damuwar dake cikin zuciyar sa daban. Sosai jikin sa yayi sanyi 'kalau..shi mamakin Ammin tasa ma yake yi..ita Ammi saurin yadda ne da ita baya ga haka me yasa zata yi haka? yarinyar nan fa haka kawai muka ganta, babu wanda yasan dangin ta yan uwan ta balle asan daga inda ta fito talk more of asalin hallayar ta, wace ita, duk babu wanda ya sani, abu mafi muni da ba ze taba barin shi yin zaman aure da ita bama shine rashin sanin hanyar da tabi har rikon 'diyar sa ya dawo hannun ta. Sai dai ya riga ya 'dauri aniyar bincikan ta tunda jimawa. Sosai yake da bukatar magantuwa da Anty Madeena amma yafi so abin ya kasance iya tsakanin su ne. Ajiyar zuciya ya sauqe mai karfi..wai Zaitoon yanzu matar sa ce kenan..? Ya tambayi kansa, ya sani 6angaren hallaya kam ta ciri tuta domin da kansa ma ya yadda da yarinyar 100%..yasan bata da wani mugun hali da za'a 'kita sbd shi...amma ai shi baya da ra'ayin aure ma kwata kwata ma a rayuwar sa balle ace auren ta. Salmerh😘 [30/11/2022, 2:22 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Wattpad@* _Serlmerh-md_ 🅿️ *...75* .......Baya ya koma ya kwantar da bayan sa jikin gado yana sake zurfafa tunani, shaf sai ya mance da cewar 6oye kansa yake, ya kuma manta cewar da Ammi ta fita bai kuma rufe 'kofar ba, bazata kawai yaji an turo 'kofar gami da sallama ciki- ciki. Da sauri ya 'dago kansa gami da bu'de idanun, duk da yake tun kafin ya 'dago idanun ya fahimci wanene, dirowar bazata da yai masan shiyasa shi 'dagowa a gaggauce, nan kuwa idanun sa sukayi arba da babban aboki kuma aminin sa wato Dr Fawwaz, 'dan 6ata rai yayi yana komawa dan daidaita kwanciyar sa. Yayin da Dr Fawwaz ya waro idanu sosai yana kallon sa gami da nuna shi da 'dan yatsa ya ma rasa kalmar da zai furta. Da 'kyar bakin sa ya iya tattaro abin fadi har ya furta sunan" Rayyan". " What..? Ya tambaya a dake batare da ya dube shi ba. " ....Wai kaine nake gani ahaka ko kuwa idanu na ke min 'karya....?" 'Karamin tsaki Rayyan yaja na neman magana ya kuma watsa masa harara yana mai juya mai baya yace..." A a ka manta...kanka kake gani haka ba Rayyan ba....!" " Yah Subhanallah..." Fawwaz yace out of excitement...ai da gudu ya tafi gare shi ya rungume shi sosai yana sakin hamdala gami da daria bayyananniya.... Ture shi Rayyan ya fara da hannun sa 'daya mai lafiyar yana fa'din" Kai...kai..wai miye haka ne, 'karasar dani kake so kayi kome...?" Fawwaz ko ta kansa bai bi ba balle ya ya fahimci abinda yk nufi, farin cikin da ke cin sa ya rinjaye komai a lkcm. Sai da ya gama bayyana farin cikin sa gami da godiyar sa ga ubangiji kafin ya fara zolayar Rayyan wai shegen kaya wannan irin nisan tafiyar da kayi duk kabi ka sa hankulan mu sun tashi fa, gaskia ka shirya sai mun ci tarar ka" " Wani karon in zan tafi ai tare zamu kwantar da hankalin ka...!" Hannaye Fawwaz ya 'daga da sauri yana fa'din " A a...a a bawan Allah rufa min asiri ban gama ha'de guzuri na ba tukunna...". " Matsorracin banza..." Cewar Rayyan...yana 'yar daria, Fawwaz yace" naji dai...ai da gaskia ta,...Ya jikin naka toh, yau dai an hutar da bayin Allah daga damuwar zucia da ta zahiri..." 'Ko'karin zama Rayyan ya yayi yana bawa Fawwaz umarnin rufo 'kofa da hannun sa yk fa'din" Ni kuma sai da na 'kwammaci ban ma tashin ba sbd damuwar da na tarar...". " Damuwa kuma...kamar wace iri..." Cewar Fawwaz da ke dawowa daga rufe kofar idanun sa akan Rayyan. " Kassarani da kuke son yi mana..dan na san komai gudunmawar ka ya faru...". 'Yar daria Faweaz yayi gano abinda yake nufi yana zama gefen sa yace" Kanka ake ji kuma yanzu..". Nan Rayyan yai masa takaitaccen bayani akan yadda yake jin hannun nasa. Atare suka yi aikin duba hannun atare da taimakon junan su, nan kuwa gano inda matsalar take sun kuma fahimci mafita 'daya gare su in dai ana so hannun ya dawo daidai kamar da toh sai an sake yi masa aikin gyara karayar dake a hannun. Rayyan yace sam shi dai ba yanzu ba tukunna, ya kuma ro'ki Fawwaz akan dan Allah ko Ammi ta bu'kaci su koma asbiti yasan 'karyar da zai mata ya waske, yasan da zarar anje asbiti sai an ri'ke shi shi kuma bai son zaman can dai- dai da ta yini guda ne wai da sunan jinya. Sun sha hira sosai da Fawwaz kafin suka rabu kowa zuciyar sa na masa da'di da ganin 'dan uwan sa..a bakin Fawwaz ma yaji wasu abubuwan da shi bai san da zaman su ba, kamar tsawon lkcn zaman da yayi a kwance, yanayin jinyar sa, auren su da aka 'daura da Zaitoon a masallacin Uthman bn Affan da ke nan cikin unguwar ta su da irin hidimar da ta yi ta faman yi masa..da dai sauran abubuwa. Sosai ya sake tsunduma cikin yanayin zurfafa tunani. Ko yaso hana kansa tunani abin gagarar sa yake, a yanzu babban damuwar sa 'diyar sa ne, yadda zai bayyana wanzuwar ta ga kowa shine damuwar sa, ko ciwon hannun sa bai dame sa kamar yadda lamarin Mufeeda ke damun sa ba...burin sa a kullum shine yaga ya 'yantar da 'diyar sa ta dawo 'diyar sa a zahiri, ta kuma rayu tamkar ko wani 'da a gidan mahaifin sa, yana so ya gatanta ta ya 'daga darajar ta fin wanda akayi mata abaya. Burin sa kenan a halin yanzu sai dai kafin hakan yasan dole ne sai ya tuntu6i Zaitoon yasan ta yadda akayi komai ya faru. Tuno kalmar zargin da yai ta jifan ta da shi abaya..yasashi jin babu dadi sosai cikin ransa, hakika bata cancanci wannan kalmar daga gareshi ba... _Astaghfirullah_ ... Ya furta saman la66an sa. Koda ya tuno sunan da yasha jifan Mufee da shi fili da zuciyar sa kuwa idanu yayi saurin rintsewa yana gyara kwanciyar sa. A hankali ya cigaba da kulawa da lafiyar sa da taimakon ragowar 'karfin da ya rage masa. domin a halin yanzu ko Zaitoon ta shigo duba shi ma ko kallon arziki bata samu daga gare shi balle har ta samu damar yi masa wani taimako...kuma da yake tasan ya farka sai bata sakewa kamar baya bata ta6a iya matsawa kusa da shi in dai ba shine ya bu'kaci hkn ba. Sa6anin hk kuwa ayyukan ta kawai take yi ta ficewar ta. Shima Rayyan haushin ta yake ji musamman idan ya tuno wai matar sa ce itama, amma duk cikin su ita har Amran babu mai iya yin zaman mintina talatin tare da shi. Abu guda 'daya ke sashi raga mata shine idan ya tuno Mufeeda. Mufeeda ta bayyana cewar ita din jinin sa ne, kuma Zaitoon ta kula da ita ta 'kauna ce ta da dukkan 'karfi da zuciyar ta, sannan ga shi shima yaji a bakin da yasan baza su yi masa 'karya ba Zaitoon ta kula da shi, toh idan yayi mata ba'kin rai ai da kansa yasan bai mata adalci ba, yarinyar ta 'karachi ilahirin rayuwar ta ne wajen bauta masa shi da 'diyar sa, bata san da'din rayuwa ba sam burin ta ta sama musu farin ciki ne a koda yaushe. Duk san da ya tuno wannan abin sai yaji bazai iya yi mata abinda yake jin zuciyar sa na ingiza sa ba, dan sosai yake ji cikin zuciyar sa cewar yayi mata koran kare daga sashin sa gaba 'daya. Amrah da ta fahimci farkowar sa 'korafi na farko data fara shigar masa shine na auren Zaitoon..Rayyan kasa ma tanka ta yayi. Tace taya ma Ammi da kanta zata amince ta aura maka wannan 'yar iskar yarinyar, Baby ka manta har yarinya ce da ita marar uba....?" A hankali idanun sa suka koma suka lumshe da jin wannan furuci na Amrah. A cikin zuciyar sa yake jin zafin kalmar ta kuma mamayi ilahirin jikin sa amma sam baya da wata kalmar furtawa ga Amrah. Sam baya 'kaunar ko da ganin fuskar ta ne, bayan cin mutuncin da sukai masa da yake kwance bashi da lafiya mai kuma take sake nema awajen sa...yana wannan tunanin ne daidai lkcn da ya tsinkayi sautin muryar Amrah na fadin" Dan Allah Baby ka sallame ta tun Kafin ta caku'da mana zuria da irin nata iskan yarana..." " Dan Allah Amrah go to ur room...plz leave me..." Ya fa'da a'dan tsawace ransa a 6ace sosai tun ma kafin ta dasa ayar maganar ta. Sum- sum ta fita tana 'ku'k'kunin mutun na jinya ma amma ba'kin hali na nan bai barsa ba. Amrah ko da ganin sa zaune hakan bai hana ta fita yawon ta yadda taga dama ba, dan tasan babu mai taka mata birki a halin da ake ciki. Hatta su Ammi sun san yawan fita da Amrah ke yi amma basu ta6a tanka ta ba... ala'kar ta Sultan ne dai basu da masaniya akansa illah Zaitoon kadai ta sani sai kuma shi uban gayyar, itama 'din albarkacin zaman ta sashen yasa ta fahimta...domin wani bin sukan shafe sama da awanni biyu cikin 'dakin Amrah...yayinda wani sa'in sukan shafe tsawon wasu kwanaki a hotel suna hutawa abinsu. In sun so kuma su shirya wajen ha'duwa ta fice ta tafi wurin sa, suyi yawo daga nan a wuce hotel asha sharholiya sannan a dawo gida..gaba 'daya Sultan ya gama lalata zuciyar Amrah bata gane kalaman kowa sai nasa. Su Ammi basu ta6a hana ta ko yi mata fa'dan yawan yawon da take yi ba sbd gudun fitina sai suka kyale ta...musamman Ammi da ta bawa abin cewa 'kilan uzuuri gareta dake sata yawan fitan. Hankalin su duk akan Rayyan ne, burin su suga ya waraware gaba 'daya ya tashi da 'kafafun sa tamkar baya. Tunda ita bata san ta yiwa kanta fa'da ba a matsayin ta na mata kuma matsayin uwa ba ai sai tayi. Ganin yadda yk fama da amfani da hannun hagun sa ka'dai dake aiki dole tasa Ammi rokon Zaitun cigaba da kulawa da shi kamar baya da yake kwance...ga kuma yadda matar sa ke nuna masa halin ko in kula da sha'anin sa...dan a lokacin ma ya samu sau'ki ba laifi sai dai hannun sa na dama dake da matsala baya aiki sam, gashi dai tsab zaki ganshi mutum har mutn amma hannun haggun sa ne ka'dai me amfani hakan yasa dole wasu abubuwan sai an taimaka masa, kama daga alwala, yin brush, cin abinci, dressing da sauran su. To Amrah babuvruwan ta yanzu a bayyane take nuna ita bata son wahala akansa, 'karshe ma Uk ta tafi da 'kawayen ta yawon sha'katawa, shi kuma a lkcn sam bai damu da Zaitoon ba bai 'dauke ta wai matar shi ce dagaske kamar ya samu lbr ba, a hankali kuma sai abubuwa suka fara fin 'karfin sa, gashi sultan baya gari yy masa nisa haka ma Amrah, cikin 'kunci yake jin zuciyar sa sosai amma bai bari kowa ya fahimta ba. Ranar da zasu koma asbiti da 'kyar ya shirya kansa yanayi yana tasbihi ga ubangiji da ya halicce shi.mutum cikakke, ha'kika nakasta jarabta ce. Duk yadda yayi 'kokarin shirya kansan amma saka ma6allai da 'daura necktied sun gagare shi...gashi ba'kin halin sa yasa ya hana Zaitoon sakewa a 6angaren nashi ma balle taimaka masa. Dole ya 'kira Ammi akan ta taya shi saka ma6allan. Ammi bata yi musu ba tazo ta 'daura masa amma tana yi tana masa fa'da ha'di da nasiha cikin natsuwa, ta yadda zai fahimce ta da kyau, nan ta nuna masa muhimman cin Zaitun a kusa da shi.. Rayyan shiru yayi bai ce uffan ba...kamar 'karamin yaro a gaban Ammin kawai ya 'dan ha'de ransa yana sauararen ta. Ammi bata yadda tabar gidan ba sai da ta tabbatar ta sake bawa Zaitoon hakuri gami da rokon ta alfarma akaro na kusan uku kenan yanzu akan sa, kuma ba akan komai ba sai dan ta ringa kulawa da shi kamar yadda ta saba dan ba komai ne yake iya yiwa kansa ba. Zaitoon bata ji shakkan sanar da Ammi cewa shine yace bai son taimakon ta ba... Ammi tace 'kyale shi, bazai sake fa'din hakan ba Insha Allahu. Zaitoon shiru tayi, bata so ta ringa jan musu da Ammin ko kuma 'karyata ta amma ita tasan ba'kin halin Rayyan a gidan nan, bacin da kansa yace ta daina zuwan masa 'daki. 'Karshe basu rabu rabu da Ammi ba sai da tasa Zaitoon yi mata al'kawarin zata bashi kulawa, tace mata yanzu ba Mufee bace ka'dai nauyin da Allah ya 'daura mata tace shine babban nauyin da ke kanta wanda har zai iya sadata da aljanna. Har Ammi ta bar 'dakin nata bata 'kara iya magana ko kallon inda take ba. Tunani take ta yadda Ammi zata fahimce ta amma bata ga alamun hakan ba. Yini tayi tunanin mafita amma bata hango ko guda ba. Bata kuma.samu damar zuwa 'bangaren ba har sai da yammaci lkcn da ta tabbatar duk inda yake ya dawo saboda Ammi ta jima da dawowa. Zaune ta same shi kan sofa da hannun sa 'daya mai cikakken lafiyar yake shafa saman dantsen hannun sa 'dayan da ke ciwo...da alamu sabon 'dauri akayi masa a hannun, jikin sa babu riga illa dogon wando ka'dai, kallo.'daya tayi masa ta 'dauke kanta. Yanayin da ya amsa sallamar ta tasan ko ta gaida shi abu ne me wahala ya amsa ta..ilai kuwa hakan ne sai dai sam bata damu ba, ai inda sabo ta riga ta saba da wannan halayyar tasa. " Ya jiki...?" Ta 'kara tambaya tana mai kawar da kanta izuwa gefen gadon sa. 'Dagowa yayi ya dubi bayan ta dayake already ta juya. Bai amsa ba kamar yadda bai sake kallon inda take ba, ya mike yayi kwanciyar sa yana lumshe idanu. Sai da ta gyara masa gadon da ta tabbatar yana da bukatan gyaran kafin ta nufi bayi ma ta tsabtace shi duk da babu wata alama ta kazanta dake bayin illa kayan sa da ya cire da safe sai da ta wanke su kafin ta fito..bata sake duban inda yake ba tayi waje abinta. Bayan maghrib ita ta gabatar masa da abinci amma bai ci ba yace Coffee mai zafi kawai yake so...Rayyan bai sake korar ta ko yi mata ba'kin rai ba sai dai babu wata doguwar magana tsakanin su. Duk kuma abinda tasan nawin sa yin sa na kanta ne takan yi 'kokarin aikata shi tun ma kafin ya bu'kaci hakan. Hutun ta ka'dai idan su Ammi ko Anty Madeena sunzo ne sai kuma Marwa da ke 'dan tallafa mata da sauran aikace- aikace. Wannan dalilin ne ya kawo 'yar kusanci tsakanin su, ya kan yi mata wayo ya hanata tafiya 'dakin ta da dare ko kuma idan tana yi masa addu'ah yayi ta kallon ta tun yana mamakin abinda take yi masa a hannun sa har yazo ya saba ma, ko magani zata shafa masa ya dinga kallon cikin idanun ta kenan, musamman idan tayi 'kasa da idanun ta sosai yake 'daukan hankalin sa. Haka in zata bashi abinci ko taya shi dressing amma maganar kirki babu a tsakanin su har lokacin sai dai ta idanu kadai. Sosai yake yawaita jin abinda bai saba ji ba akan sauran matan sa dan shi be kasance mutum mai tsananin bu'kata ba amma akan yarinyar sai yake ji daban. Haka kawai ganin idanun sa sai yaga ta rame masa bai kuma san dalili ba, amma da ya zurfafa tunani sai yga kamar hidimar sa ce tayi mata yawa ga kuma ta Mufeeda. Yaso ya ce da Anty Madeena ta 'dauke yarinyar a wurin ta amma shi kansa baya so tayi masa nisa. Kuma ko ya hana ta yin wasu aikin ba ji take ba, yayin da 6angaren ta take ganin idan bata yi ba wa zai musu toh..tunda alhakin komai na wuyan ta ne a yanzu. Har mantawa yake da wata wai Amrah sbd tuntuni halayyar ta yasa ta fita ransa kwata- kwata. Bata fiye zama wajen sa har yaci abinci ba indai ba Mufee na nan tare da su ba, yakan ce ta bar yarinyar suci abinci, haka zai lalace wajen Mufee yana bata abakin ta tun basu saba ita da Mufeedan ba har ya zam musu jiki, Zaitoon dai na mamakin wannan sabon sauyin daga gare shi, toh in dai ba dan yarinyar ba sau tari sai ya gama take dawowa ta kwashe warmers 'din...so bata san yanayin cin abincin san ba. Akwai ranar ta gama jera masa abinci ta harha'da duk abinda tasan zai bu'kata saman dinning ranar haka kawai taji ta tsaya har ya kallama kafin ta tafi...koda tayi serving nasa ya fara niyyar cin abincin ga mamakin ta sai taga left hand din sa ka'dai yake amfani da shi, tasan hakan yk yi idan tare suke da Mufeeda amma bata zaci ko da shi ka'dai ne hkan zai yi ba.Koda ya 'debo abincin gani tayi abin ya mata baibai sai taji zuciyar ta ya kasa sakewa. A hankali ya taune abincin kamar bai san cin sa, sai da ya 'debo wani yana niyyar kaiwa bakin sa da sauri ta yi 'karfin halin ri'ke mai hannu cike da tausayin sa a zuciyar ta ta girgiza masa kai idanun su sar'ke da na juna. Tausayin sa sosai ya kamata tuna kwanaki baya kadan ba hakan yake ba mutum ne shi lafiyayye amma Allah cikin ikon sa ji yadda ya canza shi, har wani ruwa taji idanun ta ke tarawa. Rayyan sake mata spoon 'din yayi yana sakin sassanyan ajiyar zuciya. Taso ta daburce kan shishshigin da tayi na ansan spoon 'din domin da farko rasa me ma zatayi da shi tayi, amma ganin yadda yake duban ta da sauraran dalilin ta na yin hakan yasa taji wani 'kwarin gwiwa ya shige ta da bata san daga ina ya taho ba. Kujera ta ja ta zauna batare da ta dubi fuskar sa, abincin ta 'debo ta nufi bakin sa da shi tana me sake ssau'kar da idanun ta. Rayyan sai yaki bude bakin sa ya tsaya bin ta da kallo. Jin shiru bai amsa ba yasa ta 'dagowa da tunanin ko hankalin sa baya kanta ne ta ankarar da shi. Sai dai tana 'dagowa suka yi ido hu'du. Abincin dake hannun ta ta kalla sannan ta kalle ahi. Gira ya 'dage yana duban ta batare da ya motsa ba. Sai ta sake kallon abincin nan ta fahimci manufar sa. Dagaske ba bakin sa ta nufa da spoon 'din ba wuyan sa ne. Kunya taji sosai sai ta sake 'dago hannun ta sama ka'dan ya kuwa bu'de bakin sa ya amsa. Dole take 'dagowa ta kalle shi badan komai ba sai dan ta saita inda bakin sa dan ko ta karkace mai mata gyara ya kan tsaya duban ta ne kawai. Amma duk wannan bata yadda ta sake ha'de ido da shi ba har ya 'kare cin abincin sbd kunyar abinda ke faruwa. Tun daga ranar kuwa sai ya zamana ita ta ke bashi abincin abaki, wanda hakan ya sake kawo kusanci a tsakanin su, sbd kullum tare suke zama tayi serving nasa ta kuma basa sai dai in Ammi na nan tare da su ne salon zaman ke canzawa ita ke bashi da kanta. Ranar da ta fara ganin yadda Ammi yadda Ammi ke bashi abincin tana kuma lalla6a shi suna 'yar hira zuciyar ta cika yayi taf da mamaki, sai kuma taji wani iri cikin ranta. Gatan da tun tasowar ta bata ta6a dacen samu ba kenan, gatan da yai mata fintinkau a rayuwa, bawai dan bata da mahaifiya ko mahaifi ba ne a a, sai dan kawai haka Allah 'kaddaro mata tata rayuwar. Ba wannan ranar ce ta kasance farko ko 'karshe ba kuma, domin ko Ammi bata nan idan Anty Madeena na nan kusa ta kan bashi abincin itama abaki tamkar yaro 'karami, sbd sun san hannun sa da ya dace yayi amfani da shi wajen cin abinci ba lafia gare shi ba. Bata san wani irin 'kauna da soyayya suke yiwa Rayyan ba ahalin gidan nan. Marwa ce dai bazata iya masa hakan ba amma duk wani abinda tasan zata iya batare da ta jawa kanta magana daga gare shi ba takan yi 'kokarin ta wajen yi itama, kuma har ila yau babu abinda ya canza daga sha'kuwar su. Suna 'kokari sosai wajen nuna kulawar su gare shi sai dai dole a hankali wasu abubuwan sai da suka dawo hannun zaitoon gaba 'daya. Sau tari in dai da Mufeeda tazo duk tare suke cin abincin illa na dare ka'dai da basa ha'da hira da Mufee sbd saurin bacci gareta hkn kuma shi na sanadin da ya sa basa yin dinner tare...Rayyan kansa bai so hkn ba amma yarinyar ta riga ta saba. Ranar har fa'da yaso yiwa Zaitoon out of confusion akan wai ta koya mata baccin wuri..hk kawai salon ta maida yarinyar wata kala. Zaitoon kam baki ta sake cike da mamakin sa tace " Ji wani 'karfin hali.." Rabon da taji sautin maganar sa a suna tare iya su biyu har ta mance amma wai yau shi ne ke mata mita akan 'diyar ta. Sai ta ga kamar dagaske fa yake fadan sannan ta tankashi da fadin..." Ai baccin shine mata dai dai, in bata yi bacci ba ma zai tayi a irin wannan lkcn...kuma ta riga ta saba babu abinda zai mata ai...". Babban ledan kayan za'ki da ya tahowa Mufeeda dashi ya cire ya tura gaban ta batare da ya furta komai ba. Tun ma kafin ta bude ta fahimci menene dan ba yau ya fara taho mata da abubuwa ba matukar ya fita a ranar, be it asbiti yaje company ko kuma wata sabgar shi ta daban. " An gode..Allah ya kara arziki da lfy" tace tana kawar da ledan gefe. Hararan ta yayi cikin ransa yake " ayyana sarkin za'kewa kawai..'karfi da yaji ta hana ni ganin yarinya ta...". Feefy bata ta6a wuce 'karfe 8 batare da tayi bacci ba...shi kuma sai bayan isha'i yake cin abinci...karfe 8:40 zuwa 'karfe 'karfe tara na dare yake cin abincin sa da wannan damar kuma yy amfani ya zuba mata maganin bacci cikin abin shan da yake zatan zata sha idan ya bata umarni. Shigan ta ciyar da Feefy ne kafin ta fito ya 'zuba mata maganin da Fawwaz ya bashi 'dazu da yaje wajen sa, cikin cup 'din da ya 'dan yi gaba ka'dan zuwa kusa da ita yasan idan har zata sha din dagaske toh hannun ta kansa zai fara sau'ka dan zuba abin sha 'din, dan haka yy fuska tamkar bb komai a ciki, da yake yau 'din ya riga ta fitowa kan dinning 'din sai ya kasance tamkar yunwa ce kawai ta ciwo shi..hakan da ta gani yasa ta yin komai cikin hanzari dan kar yunwan ta illata shi ta riga ta kuma san ba zai ta6a bu'dan baki ya sanar da ita a zahiri ba. Abincin ta zuba gami da ajiyewa gaban sa, kwalin abin sha 'din ta 'dago yana ganin ta a kishingi'den da yy ta 'kasan idanun sa, sai dai ita kanta ma bata san a yadda yaken duk wani motsin ta kan idanun sa bane ba. Shi dai cikin kwanakin nan yarinyar na matu'kar birge shi, ya so ya garga'di zuciyar sa akan abubuwa da dama game da ita amma sam ya kasa. Komin ta yake ji na tafiya dai- dai da tsarin sa, musamman yanda take yin komin ta cikin sanyi ba kamar yadda yaga wasu matan ke yin abu wufwuf kamar maza ba, yana matu'kar son mace mai sanyi shi a rayuwar sa. Ba tun yau yasan yanayin ta ba, inda sabo ya riga ya saba amma cikin kwanakin nan ya kan tsinco zuciyar sa cikin shauki da bukatawa mai tsanani ta yadda har ya kasa iya dakatar da kansa hukuncin da zuciyar sa ta yanke masa. " Ai matar ka ce...halalin ka..." Jimillar kalmomin da ke faman yi masa yawo aka kenan kuma suke 'kara masa 'kwarin gwiwa. Ganin ta cika cup 'din ta ajiye masa ne ya sashi 'dagowa daga kishingi'dar da yayi babu wata magana kawai ya 'dago ya gyara zaman sa fuskar babu yabo babu fallasa. Haka suke tamkar kurame dan duk ba gwanayen hayaniya bane su. Abincin ta fara bashi a baki a hankali kamar yadda ta saba, sai dai tayi mamaki da yau taga Rayyan bai tsaya 6ata lkc ba yake kar6am abincin..sai da ya amshi 'daya, biyu, uku amma na hu'dun sai ya tsare ta da idanu yana kallon cikin idanun ta, itama kallon sa tayi bata san me yk nufi da hakan ba yasa itama ta kalle shi, idanun sa ya rufe ya kuma bu'de su nan take tare 'dan dage gira da kansa atare, ita wannan yaren ba ba'kon ta bane dan ya jima da karantar da ita salo- salo, dan haka bata sha wahalar fahimtar abinda yake nufi ba, sai dai bayan fahimtar tasa 'kasa tayi da idanun ta gami da girgiza kanta alamar a a, dan ko da da take bashi abincin ma bata ta6a ci har sai ta tabbatar ya gama cin nashi sannan, domin baya tashi haka zai sata gaba dole wai sai taci ya gani shima..yakan yi mata alamun bashi da lafiyar hannu ne amma da shima zai ciyar da ita tamkar yadda take ciyar da shi..'karshe sai yy mata alamun ban ha'kuri, hakan yasa yake tsare ta agaban sa wai taci abincin...sai dai duk zai yi bata iyawa 'kar'kari ta 'dan kai bakin ta sai tasha ruwa shikenan. Sai dai in ya matsa dole haka zata ringa tsakura ka'dan ka'dan kamar mai shirin cin wuta, idan ta kai 'daya sai ta shafe mintina da yawa kafin take sakewa kafin ta kammala kuwa abincin yy sanyi sosai ko ka'dan kuwa Rayyan baya gajiya da zaman jiran cin abincin nata dan a ganin sa tunda shima ta juri ciyar da shi dole shima ya 'dan ware lkc cikin lokutan sa dan ita ka'dai matsayin ta na matar shi ta aure itama ya bata kulawa. Salmerh😘 [30/11/2022, 2:22 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Wattpad@* _Serlmerh-md_ 🅿️ *...76* .......Ko da ta fahimci nufin sa akan itama ta ci abincin ne sai taji sam bazata iya ba yau 'din, dan ba hk suka saba ba, ganin bazata cin ba take nufi ya sanya shima yin baya ya jingina da jikin kujera alamar shima kenan bazai ci ba sai ta ci. Tasan yana jin yunwa sosai tunda da kansa ya zo dinning 'din batare da an gayyato shi ba balle ya 6atawa mutane rai, har ma ya riga ta zuwa kuma gashi da rana bai ci abinci ba, hakan yasa taji hankalin ta ya kasa kwanciya, kallon 'yan da'ki'ku suka yiwa juna sannan ya lumshe idanun sa alamun" ba ruwa na ni..." Dan ya karanci ro'kon da tayi masa cikin idanun ta hadda ma karya wuya gefe. Abincin ta tsurawa idanu tana tunanin yadda zata yi da shi, ita har ga Allah ba wani son cin abinci da take a yanzu, a hankali ta kai hannu ta 'deba ta kai bakin ta...idanun sa a lumshe amma hakan bai hana shi 'kare mata kallo ba, yana matu'kar son natsuwa a rayuwar shi, shiyasa sau da dama yake shagala wajen kallon ta batare da yasan yana yi ba, yadda take taunan abincin ma wani salon yake badawa, wani kalan atsuwa ne tattare da yarinyar da ya tabbatar ba kowa ke da irin ta ba...wanda hakan ya kuma kara bada babban gudun muwa wajen ingiza sa ga son kusanta kansa gare ta...bai kuma yaushe ya fara jin hakan game da ita ba. Zuba mata idanu yy wanda bai masan lokacin da ya bu'de su tarwai akanta ba...ita kam bata kalle shi ba sai da ta tabbatar ta ha'diye abincin sannan ta 'dago suka ha'de idanu. Murmushin gefen baki yy sannan ya sake 'dagowa ya gyara zaman sa, da idanu yy mata alamar ta bashi shima, cike da natsuwa ta 'debo ta bashi abincin tana lura da yadda yau 'din ma yake ta faman tsare ta da manyan idanuwan sa, sai dai ita ko ka'dan bazata iya jurewa kallon sa ba, hakan yaso yasa ta daburce nan gaban sa but bata bari hakan yy tasiri gare ta ba, kawai ta riga kauda idanun ta daga ha'de idanu da shi, yasan dama bazata yi hakan ba, ko da da take iya 'kure shi da kallo ma yasan sbd yarinyar ta ne kuma takan yi haian ne out of 6acin rai, sbd zargin da take ne na ya cutar mata yarinya, wanda ya tabbatar a lokacin ji take da ita ce sama da shi ko kuma zata samu dama da ba 'karamin bugu zata yi masa ba amma bb damar haka. 'Daya ya kar6a ya kuma no'kewa, dole sai da ta sake ci sannan ya sake kar6a... tasan shi ma'abocin shan ruwa ne idan yana cin abinci kamar dai ita dan wannan ga6ar kam tarayya suka yi kan 'dabi'a guda. Cup 'din abin shan da ta 'dazun ta 'dago ta nufi bakin sa da shi amma sai ya rintse idanu gami da 'dan ja baya ka'dan cikin ransa yace" Idan kk shayar da ni wannan kuma ai kin yi dani 'yan mata". Bu'de idanun sa yy akan ta dan ita ma shi take kallo da mamakin sa, sai dai a fili ta fahimci cewa madarar ce baya ra'ayi... Hakan yasa ta 'dan kalle shi sai kuma tayi 'kasa da idanun ta zuwa kan lips 'din shi dake motsi.." Exotic zaki bani..". Yace a hankali kamar wanda bai son yin maganar. Tsaye ta mi'ke ta je ta 'dauko masa mai sanyi cikin 'dayan cup 'din ta tsiyaya sannan ta koma ta zauna, da kansa taso yasha amma yayi fuska dole ta 'daga ta kai bakin sa, ka'dan ya kur6a ta cire ta sake mayarwa ganin tana son sake cirewa ne ya sanya shi 'dago hannun sa na hagun ya 'daura saman nata wanda hakan ne tilasta mata tsayar da cup in abakin sa idanun sa na kallon nata idanun amma ta ki yadda su hade ido. Sanyin hannun sa da sanyin jikin cup 'din a hankali yake ratsa mata jiki har 'kwalwalwa..hannun nasa ta ritsa da idanun ta, ita dai wannan gargasar da ke jikin sa ba 'karamin tafiya da imanin ta yake ba...sosai yake birge ta ta yadda bata iya hana zuciyar ta bayyana 'kaunar sa. Shi kansa ma Rayyan ya riga ya gama 'dago ta tunda jimawa, cuz idan tana shafa masa magani ya kan lura da ita yanda take wasa da gashin hannun san wani bin har shagala take batare da ankare ba, balle wancan hannun da ba amfani yake da shi ba 'din shi nashi wani luf yy ya kwanta gwanin birgewa...Wani bin addu'an da take yi masa ma da biyu ne, idan ta na son ganin hannun san ne take zuwa ta janye rigar ta fara tofa masa addu'ah tana shafawa a hankali batare da ta yadda ta kalli fuskar sa ba, shikam har lumshe idanu yake yi domin ba'kon yanayi ke ziyartar sa. Sai da yasha rabin cup 'din kafin ya 'daga hannun ta gami da janye kansa baya, ita kam a lokacin gaba 'daya ta shagala cikin wani yanayi, 'karamin murmushi yy cikin zuciyar sa cike da jin da'din rikita mata tunani da yayi. A haka suka ci abincin wanda dole tasa Zaitun shanye hollandian da ta zuba masa tunda yau 'din ba ita ya shaba ya canza she'ka... Sai dai kuma bata san dalili ba tun tana tattare dinning 'din ta fara sakin 'kananun hamma, tana zuwa kitchen idanun ta na lumshewa. Rayyan kuwa tuni ya koma cikin parlourn yana binta da kallo a afakaice har ta gama tattare dinning 'din, zuwa lokacin gaba 'daya jikin ta ya saki bacci sosai ke damun ta har yana 'ko'karin cin 'karfin ta. Da gefen ido ya kalle ta dai- dai lokacin da tazo zata gifta shi a hankali kamar bai son magana ya ce" Ki canza min bedsheet bacci nake ji sosai..." Yayi maganar ne yana lumshe idanu wanda tun safe wannan shine maganar sauti da ta ji ya furta mata na biyu, dan ko gaisuwar ta ma da idanun sa yake amsa ta. Jin yadda yy maganar ya sanya ta zubo masa lumsassun idanun ta masu cike da yanayi na bacci amma haka dole ta juya ta koma 'dakin nasa dan cika umarnin sa. Sai dai me tun a awajen cire pillow case baccin ya ci 'karfin idanun ta bata san ma lokacin da ta sulale ta fara baccin ba da yake zaune bakin gadon take tana cire pillow cases dan canzawa sai ya ta koma ta jinginu da jikin gadon pillown na kan cinyar ta har ta cire rigar pillow 'daya saura 'daya baccin yy gaba da ita. Bayan shigan ta da kusan mintina arba'in sannan ya shigo a lokacin ya tabbatar baccin ta yy nisa dan tun shigar ta bai sake jin motsin ta ba bai kuma ga ta fito ta wuce ba. ***** Abu ne da bai ta6a tunanin zai faru gare shi ba ko cikin mafarkin sa, bai ta6a kawo akwai ranar da shi zai iya aikata irin hakan ba, sai dai 'kaddara, ya riga ya san komai.na.faruwa ne bisa yadda Allah 'kaddara wa bawan sa komai na rayuwar sa, sannan babban 'kwarin gwiwar sa ya samu ne daga sanin da yayi cewar ita 'din halaliyar sa ne a halin yanzu, mallakin sa take. Yasan bai kyauta ba sam, bai mata adalci ba kamar yadda yasan bai yiwa kansa ba, amma hakan aganin sa shine ka'dai mafita domin bazai iya cigaba da jure yanayin da yake jin kansa ba kamar yadda bazai iya fitowa fili ya bayyana mata bu'katar sa gareta ba. Sai dai ya kasa tantancewa shin hakan dai- dai ne ko kuwa kuskure ne gagarumi, duk wata natsuwar da yake so ya same ta amma can can 'kasan zuciyar sa yana jin babu da'di...gaba ya sata ya ma rasa me ya kamata ya aikata mata, wani taimakon ya kamata ya bata, shin taya zai sanar da ita akan ta tsarkake jikin ta batare da ta zarge shi ba. Rashin mafita yasa shi yanke shawarar ya maida ta 'dakin ta kawai. Hakan kuwa akayi, amma kafin ya maida tan sai da yayi mata allurar pain relif da yasan zai taimaka mata sosai wajen rage zafin jikin ta ko kuma ciwo. Yadda yasan tayi shigar ta ya maida mata sannan da hannun sa mai lafiyar da ya dauke ta ya maida ta 'dakin ta ya kwantar da ita hadda rufa mata abin rufa. Idanun sa ne suka sau'ka akan Mufeeda dake bacci tayi 'da'd'daya, gyara mata kwanciyar yayi yana mai zama bakin gadon ya sasu agaban sa, a hankali yake shafa kan Mufee yana jin wata 'kauna da soyayyar 'diyar tashi na taso masa sabuwa fil. Rigar ta ya 'dage yana sake duban wannan ba'kin abun da Anty Madeena ta nuna masa a jikin ta. Tabbas irin nashi ne sak, peck ya sauke mata a saman goshin ta sannan ya rufe ta itama yana tunanin yadda ya samu Zaitoon a 'danyar ta ya same ta, babu alamun ma tasan wani namijin balle har ta kai ta ga haihuwa. Sannan dukkan alamu sun gama bayyana masa cewar babu hadin jini tsakanin ta da Mufeeda dagaske, kauna ce kawai take wa yarinyar, kauna daga indallah. Koda ya koma 'dakin sa kasa bacci yayi, ya kuma rasa menene ya hana shi baccin, abu guda ka'dai dake masa kaikawo shine rashin sanin asali da farkon alakar Zaitoon da Mufeeda...he really want to know everything.... Bai ta6a 'dokantuwa da son jin dangantakar ta su sama da yau ba, bai ta6a jin 'kaguwa da son jin wani abu game da su sama da wannan ranar ba. Ba shine bacci ya 'dauke shi ba har sai tsakiyar dare, ko da safe kuwa da ya fito bai ji alamun motsin kowa ba, yasan babu mamaki basu tashi bane, ya kuma riga yasan koma menene shine silar komai. Idanun sa ne ya sau'ka akan 'kofan 'dakin Amrah sai ya kasa kawar da idanun sa. Tsam yayi da ransa tunanin sa na canza salo daga na Zaitoon zuwa na Amrah. " _Sultaan...Amrah..._" Ya furta 'kasan ransa. A hankali ya saki 'kofar sa ya nufi 'dakin Amrah bai tatar da shi da lock ba hakan ya sa ya wuce ciki kawai. Tsaye yayi yana 'karewa 'dakin kallo, sosai yayi 'kura, yasan kuma ba komai ya kawo hakan ba face da'dewar da yayi mamallakin sa bata nan. Gaban ya tafi ya tsaya yana 'karewa shirgin ta dake jere saman mirror 'din kallo yana jin wani bugun zucia akai akai na mamayar normal hrtbeat din sa. Baya so ya tuno komai, baya so ya tuno irin rainin hankali da cin amanar da bayin Allahn nan ke yi masa. Under his roof, kuma da igiyar auren sa...abin ya munana sosai kamar yadda yake kuntata masa zucia a duk lkcn da zai tuna cewar 'dan ma da yake tunanin ta haifa masa shima ba nashi bane na Sultan ne. " Sultaan fa, Sultan dake matsayin 'kani a wajen sa, Sultan mijin blood sistern sa, Sultyn Ammin su da take yi masa kirari da shi kafin abashi auren Marwa... Wani jiri- jiri ya fara ji na shirin 'diban sa hakan yasa ya dafe bango numfashi ya fara saukewa a hankali yana tunano da me ya ragi Amrah a duniyan nan...ta ina gaza mata. Sake 'dago idanu yayi ya sauke kan mirrorn nata, nan idanun sa suka sau'ka akan wani wristwatch. Wristwatch 'din da ko.ba'a fada masa ba yasan na wanene..domin da kansa ya siyo a Dubai wani zuwa da yayi. Sultan ne da ya gani yace masa yana so ya kuma bashi, ya gani a hannun sa ya kai sau uku bayan ya bashi 'din sai kuma yanzu gashi a 'dakin Amrah. Wani 'kwarin gwiwa ne yaji ya shige shi. Kan 'kafafun sa ya tsaya a har lkcn yana jin bugun zuciyar sa bai koma daidai ba. Gaban madubin.yaje ya tsaya ya tsurawa agogon idanu batare da ya ko gwada kaiwa hannun sa ba. Hannun sa mai lafiyar ya cusa cikin aljihun wandon sa 'kafafun sa a 'dan bu'de, yayin da idanun sa suka koma jajaye sosai jijiyan kansa suka fito. Tun daga yanayin tsayuwar sa zaka fahimci ba dai- dai yake ba balle idan kaga fuskar sa da ta riga ta gama bayyana yanayin sa. Wani kishi mai zafi yake jin na taso masa, tsawon wani lkc ya 'dauka yana tarayya da matar da bata san darajar kanta ba balle auren ta. Tsawon wani lkc ya 'dauka ana yaudarar sa da ha'intar sa. Rayyan ya da'de gaban madubin Amrah kafin ya bar 'dakin batare da hannun sa ya ta6a daidai da allura cikin 'dakin ba. 'Bangaren Zaitoon kuwa ko data farka sosai tayi mamakin irin baccin da tayi, domin har gari yayi haske kafin ta tashi ahaian ma still tana jin idanun ta da nawi. Mufeeda dake gefen ta kalla da alamu ta jima da farkawa tana ta wasan ta kawai batare da ta takura ta ba. 'Ko'karin tashi zaune tayi sai taji duk jikin ta nayi mata ciwo tamkar an mata dukan tsiya. Ba 'karamin mamaki tayi ba da jin hakan. Koda ta gwada yin yunkurin farat 'daya sosai taji babu dadi ajikin ta har tsayuwar na neman gagarar ta. Tayi mamakin abinda ya same ta kwarai da gaske, me ya kawo hakan meke faruwa duk bata sani ba. A daddafe ta samu ta shiga bathroom ta cire kayan jikin ta tsab sannan ta tsaya 'karewa jikin ta kallo a gaban madubi..sbd yadda take jin jikin tan har na neman zarta tunanin ta. Ko'ina ciwo yake mata hatta Boobs 'din ta. Tuno wani abu yasa ta komawa ta jingina tana me dafe kanta sai hawaye shar suka gangaro. " Wai har yanzu...?" Ta tambayi kanta tana mai toshe bakin ta da hannun ta 'daya. Kuka sosai Zaitoon tasha a bayin nan kafin ta ha'da ruwa mai zafi tayi wanka ta gasa jikin ta tana mai tunano rayuwar ta baya, sai dai ai dacan baya koda ta tashi ta tsinci kanta cikin irin yanayin nan bata jin ciwon jiki kamar wannan. Haka ta gama wankan ta kuma yi wankan tsarki kamar yadda aka koyar da ita tun a baya..sannan ta fita ta gabatar da sallah. Tana so ta tashi ta yiwa Mufee wanka ta shirya ta cikin shigar makaranta amma sam ta kasa yin hakan, jikin ta take ji babu 'karfi sosai. Asali tun abaya takan yawaita yin mafarki kuma ta tashi ta ganta cikin wani yanayi amma ai an da'de sosai da ta daina, meyasa yanzu kuma? Shin addu'o'in ta ta sun raunata ne ko kuwa mene..? Tunani take yi sosai tana mai share hawaye, ita kadai tasan takaicin da take ji, ita ka'dai tasan 'kuncin da irin wannan abin ke jefa ta. Ko abaya yayanta ka'dai ke sauraranta har ya kwantar mata da hankali, ayanzu kuwa wa ze maye mata gurbin sa, wa take da shi da zai saurari damuwar ta? Babu kowa. Taso koda ka'dan ne ta tunano mafarkin nata amma ta kasa, kwata'kwata jin 'kwa'kwalwar ta take acushe. Abu 'daya zuwa biyu kawai take iya tunowa. Tasan ta shiga gyarawa Rayyan gado amma batasan yaushe ta dawo nan ba...toh ma indai ba tunanin ta ya 6ace bane ai dai tasan bata baro 'dakin ba bacci ya 'dauke ta, in kuwa hakane ya akayi ta ganta a 'dakin ta kuma...sosai abin ya 'daure mata kai. Tana cikin wannan tunanin taji an turo 'kofa..da sauri ta 'daga idanun ta...nan tayi arba da Rayyan fuskar sa babu yabo babu fallasa, dan tuni ya kori duk wani 6acin rai da tunanin abinda ya shafi Amrah aransa, yace bashi da lkcn 6atawa wajen tunanin wa'danda basu san ma inda yake musu ciwo cikin jikin su ba balle su san na wani. Idanu ya tsura mata ya kasa kawar da kansa. Zaitoon kam kokarin mi'kewa tayi tana me share hawayen ta...amma jin zogi sosai yasa ta fasa mikewan ta koma ta zauna sai ga wasu sabbin hawaye. Gira Rayyan ya 'dage yana duban ta yace.." Kuka...?" Zuciyar sa na tsinkewa kar dai ta gane abinda yai mata. A hankali ya tako ya isa gefen gado ya zauna yayin da Zaitoon ke daga gefen sa sai tayi 'kasa da kanta sosai. Hawayen ta share tana me harha'do kalaman bakin ta ta furta masa" ina kwana, ya jiki..?" Rayyan bai amsa ba kawai ya zuba mata idanu. Ita kuma ta kasa kallon shi, gani take tamkar da ya ha'da idanu da ita zai fahimci damuwar ta. " Me ya faru wai? Me ya same ki..?" Ya tambaye ta a ha'de duk da bashi da tabbacin samun amsar ta yayin da ta wani 6angaren zai iya cewa ya ma fita sanin ainihin masar tambayoyin nasa. Shiru Zaitoon tayi bata ce komai ba illa sautin kukan ta da ta yakara karfi. Rayyan shiru yayi yana duban ta cikin ransa yake jin babu da'di, sosai yake ganin rashin kyautawar sa a fili, sai yanzun yake ji dama ya sani bai biyewa zuciyar sa ba, da yasani da be bi da ita da wannan hanyar ba. Bai ce tayi shiru ba kamar yadda bai rarrashe ta ba illah Mufeeda da ya tashi ya 'dauko ya 'daura saman cinyar sa. Sai da ta yi kukan ta son ranta ta fara tsagaitawa kafin ya sake maimaita mata tambayoyin. " Ban ..jin...dadi ne...". Ta bashi amsa a rarrabe. " Subhanallah sannu, ina ke mk ciwo...?" Tace" Ko'ina...". " Kamar...?" Sai tayi shiru tana me sake dukar da kanta. " Toh kin sha magani ne...?" Girgiza kai tayi alamar a a. 'Kasa ya 'dan yi da muryar sa tamkar wanda bai son wani ya jisa yace..." Wanka fa...? Kinyi...?" Ta 'dage kanta sama alamar" erh.." Yace" Wanka me kyau na tsarki...?" Da sauri tayi 'kasa da kanta cikin gwiwoyin ta tana me jin wani iri da tambayar tasa, hawayen ta kuwa tamkar 'kara tuttu'do su ake yi, sai dai can 'kasan ranta tana mamakin yadda akayi yasan matsalar ta da har yake tambayar ta akan tsarki...waya sanar da shi ta ya akayi ya Sani? Ai ko yayan ta Habu da ada yake sanin damuwar ta ba haka nan kawai bane, ita ce ke sanar da shi da kanta. " Baki ce komai ba..." Ya sake jefa mata wata tambayar. " Nayi..."! Ta bashi amsa da muryar kuka a kuma cike da 'kosawa da tambayoyin sa. Wani ajiyar zuciya ya sau'ke yana mai mayar da kallon sa ga Mufeeda, dama shi damuwar sa makomar ibadar ta ne, amma tunda ta fahimta har tayi wankan ai shikenan...sai dai shi kansa yayi mamakin yadda har akayi ta fahimci abinda ya faru cikin sauki hakanan, ba sai an bashi labari ba a halin yanzu ya san wace ita balle ya budi baki yace ta san hakan ne sbd ta saba aikatawa...in ma ya furta hakan yasan bai mata adalchi ba. Toh in ma ta fahimta 'din yaji but wa take zargi aranta...? Ya tambayi kansa. Sam bai so ta zarge shi, aganin sa ai girman sa fa'duwa zai yi a idanun ta in dai hakane. Toh kuma wa zata zarga in ba shi 'din ba, tunda tare suke su biyu a part din. Ai bama ita kadai ba kowa ma idan yaji labarin abinda ya faru daga bakin ta shi zai zarga. Amma a zahiri bai ga alamun tana zargin sa kan lamarin ba...toh wa take zargi aranta kenan..?" Kansa ya kulle sosai. Zaitoon ma kantan kullewan yayi da tunanin ta yadda ya san abinda ya faru da ita, sam ko kadan cikin ranta bata ji tana zargin kowa ba tunda tasan kanta batun yau ba...wannan tunanin.shine ya 'dan tsagaitar mata da kukan da take cike da mamaki a hankali batare da ta 'dago ba tace" Amma...." Sai kuma tayi shiru. " Amma me...?" Ya sake tambayar ta cike da kulawa. " Feel free to talk kar kiji kunya ta kinji...kin manta kece sama dani yanzu...I'm ur patient remember?...so amma me? tell me..." " Ya akayi kasan...kasan..." Sai kuma ta rasa kalmar da zata 'daura bayan hakan. Shine ya kar6e zancen da fa'din..." ...ya akayi nasan damuwar ki ko...? Ko ba shine abinda kike son tambaya ba. Sai tayi shiru...still zuciyar ta na sake cika da mamaki. Yana gyara zaman sa yace " Ai ni 'dan baiwa ne, ke baki ta6a sani ba? tambayi Ammi na zata fa'da mk ai...". Shiru Zaitoon tayi tana mai kissima kalar baiwar tasa sosai ta auna ta a mizani ko dagaske yake ko kuma wasa...tunanin ta ya kasa bata, amma bata ta6a ji ko ganin baiwar tasa ba meyasa sai a kanta. 'Dagowa tayi ta dubi fuskar shi da tunanin ko zata samu amsar tambayar ta saman fuskar amma ta gaza. Shi kam 'yar murmushi yayi da ganin hakan. " Wasa nake mk sarkin bin 'kwakwaf...kece da bakin ki kk ban labari fa idan kin nutsu zaki tuna lkcn da kanki..kuma kar ki damu Insha Allahu za'a 'dauki mataki akai bada jimawa ba" Yanzu kam rai ta ha'de sosai tana me kawar da kanta gefe... 'kasan ranta tace" Ni kuma? da yaushe toh..?" Sabon kuka ta fashe da shi na takaici da bakin ciki ta kuma jinjina wautar ta cikin ranta. Me ma yasa tayi hakan, meyasa zata sanar da shi, da yaushe tayi hakan ta kasa tunawa...a wani ma dalilin zata sanar da shi, ina hankalin ta ya tafi da har tayi hakan.? Tambayoyi ne birjik cikin ranta amma bata da me amsa mata su...hakan kuwa shi yasake tsawaita kukan tata kuma kasa rarrashin zuciyar ta balle tayi shiru. Rayyan ma bai ce da ita komai ba, dan be san me ze ce 'din ba dama...amma tsananin tausayin ta da haushin kansa yake ji na cikasa. Sai da tayi kukan me isan ta tayi shiru tana sakin ajiyar zuciya.." kiyi hakuri.." Itace kalmar da ya iya furta mata sau 'daya tak kuma be sake ba har tayi shirun. Takaici goma da ashirin ne suka yi mata yawa a zuciya. Jin tayi shiru ya sa shi sakin 6oyayyar ajiyan zuciya. Mufeeda ya 'dago yana gyara mata zama ajikin sa yace..." Kin yi wankan ki amma baki yiwa mama na ba...". Shiru tayi bata tanka shi ba sai jan numfashi da tayi. Tuno cewa yarinyar zata skull ne ya sanya ta bashi amsa da fa'din" Zan mata yanzu...". Tace tana mai 'kokarin yin dauriyar tashi. Hadda cije baki banda wani 'dan zazza6i da take ji ka'dan- ka'dan yana taso mata. A fakaice yake duban ta, yasan dauriya kawai take, shi kansa kuma yana so ta huta sosai a yau 'din. Kawar da kansa yayi yana yiwa Mufeeda data wani narke a jikin sa wasa, tamkar itama tasan waye shi agare ta yanzu, bata gudun sa kamar baya. Batare da ya dube ta ba... Yace" in tayaki...?" Sai ta waigo da sauri ta dube shi. Rayyan sai ya 'dan daburce da tunanin kar fa ya za'ke da yawa kuma..." I mean in taya ki yi mata wankan...?" Tana ninke daddumar da ta tashi akai da sanyin murya gami da mamakin jin furucin sa tace..." a a..ai bazaka iya ba..."! " Kina kokonto ne...?" " a a tabbacu nake da shi, kai da komai ma sai an tayaka yin sa shine har zaka iya yiwa Mufee wanka..." Tun tashin ta wannan shine doguwar magana da tayi na bai 'daya..ta kuma yi shi ne da sanyin sauti me cike da birgewa. Rayyan kansa jin da'din maganar ta yake dan haka sai yayi 'dan murmushi. " Zan baki mamaki kuwa..just wait nd see.." Tace.." Allah ka bari zan mata ma fa yanzu..." Tsaye ya mi'ke da Mufeedan ya nufi bathroom yana fa'din " ke de ki jira mu...." Zaitoon saroro tayi da mamakin sa tama kasa ta6uka komai har suka yi wankan suka fito. Bata san me yace da Mufeeda ba kawai taga sun fito duk suna dariya. Mamakin ta ya 'kara 'karuwa. Gaban ta yazo ya mi'ka mata Mufeeda domin iya abinda zai iya yi mata kenan. Bakin gadon ya koma ya zauna yana duba agogo yace" yau dai kinsa yarinya latti a banza". Shap shap ta shirya ta cikin uniform 'din ta, tuno ko breakfast bata shirya mata ba balle na lunch 'din ta...a ranta kuma tana tunanin dan bai san meke damun ta bane da har zai ce haka...amma ita kadai tasan ciwon da jikin ke yi mata. Duk abinda take Rayyan na lura da ita, ya kuma fahimci kawai dauriya take domin motsin kirki bata yadda tayi da jikin ta sai dai in ya kama na dole ne. Kawai ji tayi ana magana awaya...ya kuma saka wayar a speaker... " Na 'kira Ammi bata 'daga ba..." Muryar Marwa taji daga 'dayan 6angaren tace.. " May be tana 'kasa ne bari in duba ta..." Cewar Marwa tana mai ziraro 'kafafun ta daga saman gado. " No barta, breakfast nake so a shirya min yanzu da lunch 'din Mufeeda plz..maman ta bata jin da'di ne yau......" " Ok " Tace tana ajiye wayar. Zaitoon yau mamakin sa kasa barin ta yayi, wai dagaske Rayyan ne yau 'din ko kuwa wani daban ne aka canza shi. Yana cire wayar idanun sa akanta ganin yadda take masa kallon mamaki yasa shi 'dan ha'de rai yace..." What...?" Kawar da kai tayi bata ce da shi komai ba. Duk yadda ya fa'da 'din hakan akai masa, a cikin mintinan da basu haura ashirin ba aka gabatar da masa da komai da ya bu'kata. Gaba yasa Mufeeda da Zaitoon akan suyi breakfast Zaitoon sam ji tayi bata bukatar komai tea kawai ta sha yayin da yasa Mufee ta 'dan ci soyayyar irish da aka kawo da Tea 'din sannan ya 'dauki lunch box 'din ta gami da kama hannun ta suka yi waje. Ga James yaje ya dam'ka ta yace akaita skul, in time 'din tashin su yayi kuma a 'dauko masa ita. " Oya..Mamana bye bye...ayi karatu so kinji..?" Ya fa'di hakan yana sakin hannun ta gami da 'daga mata hannu sannan ya koma 'dakin sa. Bai sake dubo Zaitoon ba sai bayan kusan 2hrs kafin ya koma 'dakin nata dan duba jikin ta. Du'kun'kune ya same ta cikin bargo da alamu sanyi take ji sosai. Hannu yasa cikin abin rufan ya ta6o wuyan ta yaji yaji babu zafi, saman goshin ta ya sake shimfi'da tafin hannun sa sai dai jin yanayin zafin jikin nata yasa ya kasa 'dage hannun nasa har ta bu'de idanu ta sau'ke akan fuskar sa. Salmerh😘 [30/11/2022, 2:22 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Wattpad@* _Serlmerh-md_ 🅿️ *...77* ........" Sannu". yace mata yana shirin zama gefen ta. Da sauri ta matsar da jikin ta gefen ta tana kuma 'ko'karin cire hannun sa da ke kan goshin ta amma ta kasa 'dagewa, ya kuma 'ki bata damar da zata 'daga 'din. Sai da yaga ta matsa ne sannan yace.." What..."! Tayi shiru. " Ashe babu da'di...ni da kullum kike ta6a min jiki na fa...?" Yatsina fuska tayi tana kawar da kai gefe. Rayyan sai yayi 'yar murmushi...a hankali yace..." Ya jikin fa.." Da sar'kewar murya ta amsa shi..." Alhamdulillah...lafiya ta ma kalau....". " Kin tabbatar...?" Ta 'dage kanta. " Toh zafin jikin fa...?" " Haka nan kawai....". Yana shirin sake magana yaji 'karan wayar sa dake aljihun gaban rigar sa. Duban sa ya kai ga wayar kafin a hankali ya 'dauke hannun sa dake saman goshin ta ya ciro wayar Ammi ya gani... Yaje gaishe ta ya tarar bata nan sassafe yau ta fita. Gaishe ta yayi ta amsa sannan ta 'dora da fa'din" Ina 'diya ta?" " Wace...?" " Gidan ku Rayyan...". 'Yar dariya yayi" Toh Ammi ai Marwa na can part 'din yau bata zo nan ba...". " Aww toh...Zaitoon nake nufi, Marwa tace min wai bata ji da'di ba in jika...?". 'Dan kallan inda take yayi sannan ya amsata da fadin.." erh wlh Ammi, tana bacci ne amma da sauki dai Alhamdulillah...". " Dama me ya same ta?" 'Dan jim yy sai kuma yace" Bata da lafiya ne Ammi?" " Subhanallah, toh Rayyan a duba ta, in kuma bazaka iya ba, a 'kira Doctor ko kuma a kaita can a duba ta zaifi ko?" " Toh Ammi.." " Wanne za'ayi ?" Ta sake tambayar sa dan tabbatarwa sbd tasan halin.sa da 'kyar ne idan zai bawa maganar muhimmanci. " Ammi fa na duba ta kuma naga jikin ne da sauki yanzu sai dai zafin zazza6i" " Baka da hankali Rayyan, ai ba a raina ciwo, plz ka duba ta ko kuma kasa a duba ta, shi ciwo ba'a raina wanzuwar sa..." 'Kayataccen murmushi kawai yy bai ce komai ba, sai da ta sake magana sannan yace" Insha Allah Ammi za'a yi kamar yadda kika ce..". Ga Zaitoon ya maida duban sa yana fa'din har baccin ya ishe ki..? Shiru tayi masa bata bashi amsa ba. Shima bai damu da rashin masawar tata ba dan in da sabo ya riga ya saba da halin ta batun yau ba. Juyawa tayi 'daya 6angaren tana gyara kwanciyar ta. " Ba kiji ba...?" Sai ta 'dan waigo tana 'kan'kance idanu..ina ke miki ciwo yanzu?" da kai ta bashi amsa alamar bako ina ta hanyar girgiza masa kanta. " Ammi ta 'kira tace wai akaiki clinic a duba ki, kuma ai naga jikin da sau'ki ko?" kai ta sake 'daga masa tana 'ko'karin tashi zaune... " Ke ya kika gani, ko kema kin fiso aje can 'din...?" Har cikin ranta bata so 'din amma sbd kar Ammi taji babu da'di idan taji cewar ta 'kiya yasa ta fa'din Bai kai ga rufe baki ba tace" ai ma naji sau'ki, bana jin komai yanzu...." " Toh...kawai idan ta nemi magana da ke kice da ita anje kinji?" Shiru tayi bata bashi amsa ba...dan haka ya mi'ke ya fita a 'dakin Zaitoon bata ko sake kallon inda yake ba...damuwar da ke cin zuciyar ta yafi damun ta a yanzun. Ko dare sai da ya shigo duba ta kafin ya kwanta bacci, anan sai yag kamar ya bayyana damuwar sa akanta da yawa kar taga kamar wani abin ne daban. Harcya juya zai fita sai kuma ya waigo, bai yi mamakin kama ta da yayi tana kallon sa ba, yasan dole sai anyi hakan..." Kallo na kike..?" Yi tayi kamar bata jisa ba, me kuma yake so ta fada masa bayan ya ganta ta tana kallon nasa... Kar fa kiyi tunanin wani damuwa nayi dake kema kice zaki kwatanta musamman dan kinga ina ta zuwa duba ki, badan komai bane face dan naga baki da lafia ne, sannan ni ba mugu bane, na kuma san hakkin na kusa da ni, bayaga haka ma rama taimakon da kikai ta min nk mk ba komai ba...kin fahimta...?" Shiru tayi tana juya kanta gefe gami da kwantar da kan jikin gado. 'Kasa kasa tace.." Toh dama ni yaushe nace mk bani da lafia..." Sarai ya jita amma bai ce komai ba, baya son jan maganar ne, dan haka sai kawai yayi murmushi ya juya yana mata fatan samun lafia. Bata ce da shi uffan ba har ya fita ya ja mata 'kofar. Tunani take ta inda ta gaza, shin addu'o'in ta ne suka rauna ta ko kuwa ta kuskure ne..tasan bata wasa da yin addu'o'in ta tun bayan da Yayan ta ya koya mata su, bata ta6a yin sake akansu ba dai- dai da rana guda kuma Alhamdulillah ta ga fa'idar su... Kasa yin wani baccin tayi kawai tayi tsam da ranta tana tunani, rayuwar ta na can can baya ke dawo mata, tun da da jimawa irin wannan abun ke faruwa da ita ta sani, amma bata san meyasa na yau 'din yafi tsaya mata arai sosai ba, bata san meyasa yafi ba'kanta mata rai fiye da baya ba, shin ko dan ta jima ne, ko kuwa dan ta 'kara wayo fiye da baya ne, sosai taji zafin wannan lamarin musamman da yake ciwon da take ji a jikin ta ya matu'kar bambanta da na baya...har bata san tuna kalar mafarkan nata na baya, ada idan ta farka tana iya tuna komai da ya faru da ita, sa6anin yau da sam ta kasa tuna komai. Duk yadda ta zurfafa tunani ta kasa tuna daidai da 'kwayar zarra cikin mafarkin nata. Sanin da tayi cewar bata da mafita, bata da me zama ya fahimci matsala ko damuwar ta ya sa ta watsar da komai, ta cire komai a ranta ta cigaba da hul'do'din ta aganin ta hakan shine kawai mata mafita musamman da yake bayau ne ka'dai ya fara faruwa ba, inda ta sabo ta riga ta saba. Kawai shawarar da ta bawa kanta shine zata sake tsananta addu'a ta kuma barwa Allah komai, domin tasan duniyan Allahn shine gatan ta ta ko wani fanni. Ba'a da'de ba Marwa ta shigo gaishe ta nan ta tatar da ita tana aiki..tayi mamaki 'kwarai da gaske. " Wai mara lafiyar kenan...?" 'Yar murmushi tayi kawai ta fara gaida Marwa. " Na fa warke kawai dai karfin jiki ne bana da shi sosai..." " Toh...banda abinki Zaitoon ba sai ki samu ki huta ba, shi Yayan yace kiyi aiki...?" Da sauri ta girgiza kanta. " Allah ya ke de Allah ya shirya ki...sai kace dole...da lafiyar kinyi babu lafiyan ma bazaki huta ba, dan Allah muje waje..Fa'iza zata zo ta karasar da aikin..." Da haka Marwa ta jata suka koma 'daki...sun dade tare kafin Marwa ta tafi dan har Mufeeda ta dawo ma kafin tafiyar ta. Ammi ma da kanta ta shiga ta duba su ita har Rayyan din. Zaitoon duk sai take jin kanta a takure sosai, bata sake bari an yi mata kallon marar lafiya ba sbd san rufe sirrin rayuwar ta washe gari ta tashi tsab da ita, dan tayi magana da Marwa akan ciwon da jikin ta ke mata Marwa tace ki gasa jikin ki da ruwa me 'dumi zai rage mk zazza6i kuma zaki fi jin 'karfin jikin ki... Marwan ce ta 'kara da fa'din" ai ruwan zafi yayi yana da matukar amfani sosai..." Da kanta ta tsinta wani abu cikin kalaman Marwa kawai tayi ta amfani da ruwan zafi ta kuwa ji dama dama..da yamma ma Rayyan ya bata magani yace mata na zazza6i ne tasha so washe garin rass ta tashi kamar ba ita ba. Nan ta 'daura rayuwar ta ta mance komai duk da yana nan aranta amma bata yadda ta bashi wani 6angaren cikin lokutan rayuwar ta ba. _Bayan kwanaki biyar...._ Tana 'daki tana tunanin sai yaushe ne za'a tsinke igiyar auren da aka 'ka'kaba mata tunda kam ya samu sau'ki ba laifi, tasan shi da kansa ma a karin kanshi ba barin auren zai yi akan sa ba dile zai tsinke shi in dai Rayyan da ta sani ne, amma wace rana? yaushe ? Da kuma wani lokaci duk bata sani ba... Tana zaunen taji 'karar landline dake 'dakin..a hankali ta kai hannu ta duba babu abinda take fahimta, dan haka sai ta sada shi da kunnen ta kamar yadda taga ahalin gudan ke yi, da sanyin murya tace" Hello". " Ki sameni yanzu". Taji muryar sa yace hakan sai dai kafin tayi wata magana ya kashe wayar. Doguwar rigar ta sanya ta na'de mayafin rigar akanta sannan ta nufi 6angaren sa, zaune ta ganshi gaban mirror yana shafa mai a hankali kamar baya son yi, cikin ranta tace wannan fa dama da alamu mugun son jiki ne da shi, sai ya ringa wani lalla6a jikin sa tamkar mace...cikin ranta ra furta hakan tana daga inda take tsaye dan ko sallamar da tayi bata ji ya amsa ba. Tana nan tsaye har ya gama da mai 'din ya taso..bai ko kalli inda take ba ita kam ganin ya taso ya sata saurin fa'din" Ina kwana..". kallo 'daya yy mata kawai ya 'dauke kansa. Kayan da zai saka ya warware yana dubawa, su ma 'din da 'kyar ya waro su sbd yau hannun nasa ya matsa sosai, dama ita ke za6ar masa kayan kuma kusan sati kenan rabon ta da zuwa yi masa wani abin, Da can Amrah ke masa komai kuma yanzu bata nan. Ganin zai saka kaya ya sanya ta saurin 'dauke kanta tayi 'kasa da shi. Sai da ya sa dogon wandon sannan ya 'dau rigar ma ya sanya gaban mirror ya tafi ya ya zauna duk wannan batare da yace da ita uffan ba. Ta cikin madubin ya gama 'kare mata kallon da ya kwana biyu bai yi mata irin sa ba, sosai yaga ta canza masa shirun ta ya 'karu, 'yar sha'kuwar da ta shiga tsakanin su ma yanzu duk babu ita. Ta cikin madubin suka ha'da idanu sai yayi mata alamun tazo, a hankali ta 'karasa ta tsaya daga bayan sa. Comb ya mi'ka mata yana shafo kansa, ko bata tambaya ba tasan me yake nufi dan haka sai ta matsa a hankali ta fara taje masa gashin har ta gama tajewa bai yi motsin kirki ba, mayukan da yake shafawa akan nasa ya 'dauka ya mi'ka mata ta kar6a ta shafe masa a hankali cikin natsuwa kamar yadda taga yake yin abubuwan sa tun ba yau ba. Bata zaci har a yanzun hidimar sa bata 'kare ba sai da taga ya juyo mata gaban rigar sa da alamu botiran yake so ta sanya masa. Idanun sa ta kalla sai ya 'dan 'kan'kance nasa bashi kuma da niyyar furta kalma ko guda. Hannu ta kai ta 6alle masa botiran daga 'kasa zuwa sama, Turarunkan sa ta 'dauka tun ma kafin ya bata umarni dan tasan itan ce zata yi, bata ga alamun yau 'din yana da niyyar yiwa kansa komai ba. Haja ta ringa feshe shi da su kamar zasu 'kare ko zai ce wani abu amma bai yi magana ba illa ido da ya zubawa fuskar ta ita kuma ta'ki yadda ta ha'de ido da shi. Da kanta ta gaji da fesawan ta ajiye tana girgiza kai gami da jinjina al'amarin sa cikin ranta, mugun son 'kamshi ne da shi na masifa, shiyasa ko da yaushe idan ka ha'du da shi 'kamshin sa ke fara ziyartar hancin ka kafin kayi tozali da shi.... Bai 'kara komai daga shirin da tayi masa ba kawai ya sake duba jikin sa cikin madubi sai ya saki murmushin da bata san na menene ba..sai dai a zahiri yayi mata kama da na jin da'di. Kanta a 'kasa bata sake duban shi ba, ganin hakan yasa shi ha'de yatsan sa ya murza suka bada sautin 'kara. Da sauri ta 'dago ta dube shi, dama manufar sa kenan, so yake ya ja hankalin ta ta dube shi. Da hannun sa 'dayan ya yabi jikin sa...sannan a karo na farko tun shigowar ta ya bu'di baki ya tambaye ta..." How do i look..?" Murmushi ne ya kwace mata ganin yadda yayi 'din hadda gyara tsayuwa yayi. Babban yatsanta ta ha'da da na kusa da shi ta 'dago masa alamun Superb...ya kuwa ji da'di sosai hadda blowing mata kiss. Hakan sai ya sata ...Shirgin sa kawai ya 'diba yy waje abinsa ya bar ta da kwalbar turare a hannu. Mamakin sa sosai ya kamata, dama dalilin 'kiran kenan? Kuma ma ba sannu bare na gode kamar ya samu wata baiwar sa. Dan rage takaici itama sai fesa turaren sannan ta kama hanyar barin 'dakin sai kuma taga rashin kyautawar hakan, tunda dama can tasan aikin ta ne kafin ta 'dan janye da aikin, ta kuwa san Ammi bazata ta6a tanka ta kan hakan ba, ko da ace daina yin aikin tayi kwata- kwata, dan haka gara ta gyara tun bata 6ata gurbin daraja da 'dan mutuncin ta da ake gani ba. Baya ta dawo ta fara gyara masa gado dan a hargitse yake ko bakomai kuma aikin ta ne dama ta saba, balle yanzu da ya tasan cewa hadda guzurin lada zata samu ai ba laifi bane idan tayi hakan daga yanzu har zuwa lkcn da zai sallame ta. Sai da ta gyare 'dakin tsab ta tsabtace shi sannan ta fita bayan ta ja 'kofar. Cikin ranta take ayyana sai yau aka ga daman zuwa ganin likitan kenan... Da komawar ta bata ma zauna ba ta wuce sashen Ammi wajen Marwa, anan ta shashance har lokaci yaja sosai suna ta hira da Marwa anan suka sallaci azahar ma. Ko da Mufeeda ta dawo daga skul anan ta same su, Marwa ce tai mata wanka ta shirya ta tace fita yawo zasu yi, Zaitoon dai bata ce komai ba. Sai da Marwa taga bata da alamun tashi ta shirya sannan tace.." Banga kina niyya ba..." " Niyyan me ne, ni fa babu inda zani.." Turus Marwa ta ja ta tsaya tana duban ta..." Kamar Yaya, Allah baki isa ba, kin.san inda zamu je ne..?" " Ni dai dan Allah Marwa kuje abinku ni babu inda zani..." Marwa har zata yi magana sai kuma ta tuna wani abu. Murmushi tayi tana jinjina kai..." Na mance ai, kice izinin yaya kike bukata kafin ki fita...". Sosai Zaitoon ta zaro idanu tana toshe bakin ta cike da mamaki tace..." Marwa!" ...." Yes ai na fahimta...". " Ni yaushe nace mk haka Marwa?...wace ni ma da zan ce sai da izinin sa zan fita...". " Kin fini sanin koma mecece ke awajen sa ai yarinya..." Cewar Marwa tana dariya..." Yanzu dai fa'di gaskia, in tambaya mk shi ko abar shi...?" " a a ni dai bance ba dan Allah, kawai kuje abinku..." " Sai fa kinje, dan ya yini.a office nema da har 'daki zan raka ki ki tambaye shi...." Zaitoon kasa fa'din komai tayi kawai ta tsaya saroro tana duban Marwa..bata ankara ba kawai taji sautin muryar sa cikin wayar dake hannun Marwa. Ga mamakin su duk Rayyan cewa yayi suje amma banda Zaitoon. Duk basu yi zaton zai hana ba tunda ba wani daraja ya bawa auren nasu ba... " Toh fa sabon salo...". Cewar Marwa bayan ta kashe 'kiran. Bata bar Zaitoon ba ta ringa tsokanar ta har suka fita bayan sun 'dauki hotuna. Ba 'karamin kyau Mufeeda tayi cikin shigar da Marwa tai mata ba. Suna cikin mota ta turawa Sultan hotunan ganin yadda suka yi kyau suka fito rass da su...yayin da wasu kuma ta tura su status. Amrah ce ta uku cikin wa'danda suka fara bude status din take wani kullutun bakin ciki ya turnuke ta. Haka ta ringa mita tana fa'dan magana gami da kushesu wa Sultan. So take kawau ya raba matar sa da su ta ko wani fanni amma Sultan be ce komai ba, sai dai tuno maganar da suka yi da ita kwana ki da kuma ganin hotunan su Marwan da yayi ayau ya sake haddasa masa wani mugun abu cikin ransa. Sultan baya jira ba kuma ya tsaya 6atawa kansa lokaci kan duk wani abu da ya sa gaba. Idan yayi niyya baya ja.da baya ba kuma ya sararawa har sai ya zartass, dan haka tun daren ranar ya 'kira waya ya fara shirya abinda yake ganin shine mafi 6illewa agare shi ya kuma fara shirin komawa gida shi da Amrah, sun huta sosai, sun kuma yi yawon dunia, kowa ya gansu tare dauka yake mata ne da mijin ta hadda 'dansu, musamman da kamar yaron yake 'kara fitowa sosai da shi. Tun daren ya shirya tafuyar su Amrah dan ba jirgi guda yake so su koma Nja aciki ba. So yake kowa yayi tafiyar kansa da kansa. Washe gari sassafe jirgin su Amra ya tashi ko da suka isa kuwa Kaduna ta yada zango. Shi kuma Sultan ya shigo da yammacin ranar sai dai babu wanda ya san da sau'kar sa kaf cikin 'yan uwan sa, har ma da matar sa. Bayan kwana biyu...Zaitoon ta shirya Mufeeda zuwa skul ta kamo hannun ta suka fito harabar gidan sai dai babu kowa illah gate man. Ta kuma tambaye shi yace duk drivers din an aike su ne...bata yi mamaki ba domin ba yau aka fara irin hakan ba sai dai duk yadda za'a yi tasan Ammi bata ta6a bari drivers su watse gaba 'daya in dai ba taga an mika Mufee makaranta ba, gashi yau din gab take da makara ma, ji take tamkar ta bari sai washegari taje kawai amma sai taji kuma zuciyar ta bai nutsu da hakan ba. Cikin ranta ta yanke shawarar gara ko keke napep ne ta hau ya kaita ta sau'ke ta tunda tasan makarantar, ba komai ke bata kwarin gwiwar hakan ba face yadda take jin yarinyar ta na rairo karatu sosai yafi ya fara birge ta kadan kadan har ya shie ranta take jin dadi, ada bata so aka akai Mufeeda amma yanzu dai- dai da rana guda bata kaunar taga Mufee tayi fashin zuwa, dan haka zata kaita in yaso idan an tashi sai a 'dauko mata ita babu mamaki kafin lkcn sun dawo. Hakan kuwa akayi, lkcn har takwas kusan da rabi na shirin yi, ai da tasan drivers din zasu fita dukkan su ma da ta ro'ki Rayyan su wuce mata yarinyar su ajiye ta lkcn fitar sa. Sai da ta koma ciki ta 'dauko ku'di kafin ta sake fitowa, tana isa bakin titi ta samu adaidaita sahu tamkar dama jiran isowar ta yake yace" hajia sai ina...?". Tace" Concord dan Allah zaka ajiye mu, ka hanzarta, mun riga mun makara ma sosai..." Tayi maganar tana shiga cikin adaidaita sahun. yace" ai a babu wani abu, bani mintina sha biyar zaki gan mu bakin gate din makarantar. Yana fara tafia bai yi nisa ba taga ya tsaya wani matashi ya hau gefen sa. Mufeeda ce ta yi tari sai ta kalle ta gami da janyo ta zuwa jikin ta sosai tana mai yi mata sannu. Bata 'dago kai daga kallon yarinyar ba ta nemi hankalin ta ta ta rasa, bata kuma san dalili ba sai bu'de idanu tayi ta ganta a wani 'daki mai duhu baki 'kirin. Kuka ta sanya da 'karfi tana mai lalu6o Mufeeda nan ta tsinto ta yashe gefen ta tana baccin wahala itama dan Mufee har a lkcn bata san ma ina suke ba balle tasan me ke faruwa. Duk ihun da Zaitoon take da kuka babu wanda ya kawo mata agaji, babu kuma motsin wanda taji illa 'karan wani 'ka'k'karfan sauti da ke tashi na wa'ko'kin turanci. Sai yamma lis kafin wani mai rufaffen fuska yazo gare ta ya dur'kusa hannun sa da 'yar torchlight. Jajayen idanun sa ya zuba mata Zaitoon kam ko ganin sa da kyau ma bata yi har a lkcn kuma Mufeeda bata farka ba. " Kina jin yunwa...?" ya tambaye ta da wani bau'da'd'den muryar sa dake nan tamkar 'karan drum. Kallon sa kawai ta tsaya yi tama kasa bashi amsar komai..mamakin yadda akayi ta ganta anan 'din take, me take yi anan, wa kuma ya kawo ta. Sosai tsoro da fargaba suka cika mata zuciya amma taki bawa hakan damar bayyana a zahiri. Bata kuma san meyasa taji tsoro da fargaban ta ya iya dannuwa mata a rai ba. Abu 'daya kawai take tunawa a yanzu shine Dr Abdulrasheed...kamar hakan dai ne ya ta6a faruwa tsakanin ita da shi, sai dai shi ba sato ta yayi ba, ba kuma cutar da ita yayi ba, bambancin kawai shine wannan karan ba kowa take jin tana zargi ba illa Rayyan, shi ka'dai ne take jin kamar zai iya yi mata wannan abin, sai dai kuma ta kasa samo hujjar da zata rike da cewa shi dinne da dagaske, a kullum rasa gane kan Rayyan take, wani lkc he is nice wani lkcn kuma sai a hankali, amma idan ma.shi 'din nevfatan ta 'daya ne Allah yasa kar su cutar da ita ko diyar ta. Shirun da tayi masa ne ya sashi sake maimaita tambayar sa...ya kuma 'kara da fa'din..." amsar ki zata taimaka sosai wajen ku6utar ke har ma da 'diyar ki gaba 'daya, amma hkn bazai faru ba har sai kin bamu ha'din kai 'dari bisa 'dari...." Tambaya ta farko zan kuma maimaita mk" Shin kina jin yunwa...?" Da kai tayi saurin amsashi alamar a a. " Sallah fa kinaso kiyi. 'Daga kai tayi alamar "erh..." "Gud of u..". Ya fada gami da jinjina mata, ki bani amsoshin tambayoyin da zan mk cikin sauki cikin kuma lkc kankani indai dagaske kina so abarki kiyi ibadar ki...". Tambaya 'daya ce zuwa biyu..." Ta farko shin menene ala'kar 'diyar ki da Sa'ad Auta's family? Me kuma yasa suke 'kaunar ta sosai fiye da jikan su Arfan da matar Rayyan ta haifa...?" Salmerh😘 [7/12/2022, 12:14 am] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Wattpad@* _Serlmerh-md_ 🅿️ *...78* ........Shiru Zaitoon tayi tama amsar da ta dace ta bashi, cikin ranta take ayyana" wannan wace iriyar tambaya ce? 'kauna kam ai Allah ke dasa ta cikin zu'kata, kuma shine ya sanya musu 'kaunar Mufeeda ba wai ita ta sa ba, me yasa hakan zai zam abinda har sai an nemi hujjar da za'a kare shi da shi, shin laifi ne dan sun so Mufeeda ko kuwa wani abin daban suke nufi da ita bata sani ba. Shirun da tayi tana duban da tunani ba 'karamin 'kona ran sa yayi ba. Ganin kamar bazata amsa shi ba ne dan bai ga alamun tana da niyya ba, hakan ya sa ya fisgo Mufeeda dake jikin ta, wata irin fuzga ne.da ko kadan babu 'digon imani ko tausayawa tattare da shi. Mufeeda kuka ta sanya har tana kokarin shi'dewa, ai da sauri Zaitoon ta zabura ta koma kan gwiwoyin ta tana kuka ta fara ro'kon sa da ban baki. " Dan Allah kayi min rai ka bar min 'diya ta, wallahi dana san amsar tambayar ka babu abinda zai hana ni sanar da kai amma ban sani ba, tamkar kana tambaya na ilimin gaibu ne fa.." " In dai kina son cigaba da ganin ta araye toh amsamin tambayoyi na yanzun nan..." Yayi mata magama da wata bu'da'd'diyar muryar da babu alamun wasa a ciki, sautin ta kadai ma na iya hargitsa lissafin matsoraci. " Dan Allah kayi hkr, wallahi babu wata ala'ka tsakanin mu da su fa, kawai dai ha'duwar jini ya sa suke sonta amma na rantse maka babu komai...." " Toh ina mahaifinta yake...?" " Ya rasu! ya rasu tun ma kafin a haife ta...." Ta sake bashi amsa jiki na mazari idanun ta akan Mufeeda dake hannun sa tana kuka. Gefe ta karya wuyan ta tana jin babu dadi, kukan take itama cike da tausayin 'diyar ta, rikon da yayi mata kadai abin a tausaya ne, domin tamkar wani sa'an sa ko kuma wani abin cutar wa ya damko haka yayi, hala ya mance ne cewar 'yar yarinya Mufeeda ce a hannun sa ba wani daban ba. Tasan sarai yana sane tunda ba makaho bane shi ba kuma hauka yake ba cikin hankalin sa yake komai. Wannan wace iriyar rashin imani ne haka wai...?" Magana akayi masa cikin wata 'yar abin magana dake ma'kale jikin kunnen sa, hakan yasa ya ajiye mata 'diyar ta da ya fizgo ya fita. Tamkar jira take ta janyo yarinyar jikin ta ta rungume sosai suna sakin wani sabon kuka atare...Mufeeda na fadin..." Mammi..." Zaitoon na fadin Mufee na...Allah yana gani, kuma nasan zai saka mana tunda ba komai muka yi musu ba.." Can gida kuwa hankula duk sun tashi an rasa Zaitoon da 'diyar ta ba 'a san inda suka yi ba, 6at babu su sama ko 'kasa ba'a gansu ba. Babu wanda hankalin sa bai tashi ba kowa kuma tunanin da zuciyar sa ta basa daban, kowa tunanin 6acewar Zaitoon 'din fassara ya bashi na daban in ka 'dauke Ammi ka'dai da sam zuciyar ta ya kasa bata takamamman dalili guda da zai sa arasa su gaba 'daya. Kar ma ka tona zuciyar Rayyan da Anty Madeena da masu ra'ayin fassarar ya bambanta da na kowa, banda luguden gudu gami da fargaban abinda ke shirin tunkaro su da yai tsaya musu karan tsaye a 'kirji tamkar suyi bindiga haka suke ji cikin zuciyar su... _wannan shine ta leko ta koma._ Marwa kam kuka take sosai, bata ta6a sanin sha'kuwar su ta kai har hakan ba sai yanzun da aka rasa su. Gida yayi zugum gaba 'daya, hatta Raihana da sauran 'yan uwa tuni labari ya iske su, domin da yawan su sun san Zaitoon musamman lokacin rashin lafitar Rayyan da suka zo dubiya a wannan lkcn da yawan su suka santa...yanzu kuwa da akace babu ita babu wanda bai jimanta ba illa 'kalilan da suka kasance mahassada daga cikin su. Wani bin Ammi har na mamakin yadda damuwar Anty Madeena ya kasa 6oye kansa, bata san dalili ba amma yanayin damuwar ta ta sosai ya sa Ammi dasa ayar tambaya akan sa, ba zallan sha'kuwa take ganin alamun tasirantuwar sa akan fuskar Anty Madeena ba, zallan damuwa ce dake tasowa tun daga 'kasan zuciya, bata iya dannewa damuwar ta dai- dai da 'kwayar zarra ba, dan ko Marwa bata kai ta shiga tashin hankali a zahiri ba. Kamar dai yadda ta kasa gane kan Rayyan kwata- kwata, 'kunci ne ko damuwa ko kuwa fargabar rashi na har abada ya sa shi fita hayyacin sa bata sani ba, abu guda da ya bambanta yanayin su shine kawai kasamcewar sa 'da namiji, hakan kuma ya bashi damar dauko jarumta ya sanya wa zuciyar sa da in ba sanin kwaf kai masa ba bazaka ta6a fahimtar halin da yake ciki ba, ita ma 'din sanin sosai tai masa shiyasa tayi saurin fahimtar sa, abinda ta kasa fahimta daga gare shine, shin damuwar 6acewan matar sa ne ya dame shi ko kuwa damuwar sa dan sun 6ace ne 'karkashin inuwar su...? Ta kasa tantance makomar damuwar Rayyan sam kuma yaki bada 'kofar da za'a fahimta cikin sauki. Kuma shi har Anty Madeena har lkcn sun kasa fitar da abinda ke ransu, dan lkcn fa'dan ba shine mai muhimmanci ba a ganin su, samun su shine kan gaba a halin yanzu. Hatta baccin dare kuwa 'kalilan cikin gidan ne suke samun yin sa...sbd tsantsar damuwa. Rayyan abin yafi 'kona masa zuciya sosai, domin tunanin sake rasa 'diyar sa akaro na biyun nan bazai iya dauka ba gefe guda kuma ga auren sa, sai dai bai damu da auren nasa sosai kamar yadda diyar sa ta tsaye masa ba, abaubuwa da dama da yake shirin kammalawa game da ita bai samu yayi ba, karashen binciken tushen lamarin duk bai yi ba, a tunanin sa Zaitoon ta gudu masa da 'diya hakan yasa natsuwa tai masa nisan zango, burin sa kawai ta dawo masa da 'diyar sa ne. Fa'di yake cikin ransa" lallai wannan yarinya ta gama raina ni, wallahi sai na bata mamaki, sai na nuna mata asalin waye ni, dani take zancen. Tun dawowar sa daga fitar da yayi da ya shigo bai tarar da dasu a gida ba, da farko ya 'dauka suna can 6angaren Ammi ne shiyasa bai damu ba, yazo yayi tunanin ko sun 'dan fita ne amma still sshiru bayan lkc yaja sosai y fara binciken gateman nan ya samu labarin cewa tun fitar safe da da ta mika Mufeeda skul basu dawo ba. abin kamar wasa amma sai gashi wankin.hula na nemen.kai su izuwa dare. Wasa wasa ana neman cike kwanaki biyu cikin na uku babu su babu dalilin su. Rayyan sai da aka Ammi ta dage kafin yake 'dan samu ya sanyawa cikin sa wani abu, har ya fara komawa 'yar gidan jiya bayan murmurewar da ya samu yayi cikin kwana kin da suka gabata... Ganin fa dagaske lamarin ke shirin tabbata yasa fargaba da tashin hankalin sa 'kara hauhawa zuwa wani matsayi, har takai ta kawo motsa jikin sa bai isa yayi ba sbd tsantsan ciwon kai da 'dan hawa da jinin sa yayi ya haddasa masa. Kullum tunanin sa ta ina zai fara nemo inda Zaitoon ta shiga masa da yarinya ne. Sai a kwana na ukun kafin ya samu wani 'kira da wata numbern da bai da ita ma sam cikin wayar sa. Bai ta6a zaton wai sace su Zaitoon akayi ba hakan yasa ko bi takan wayar bai yi ba ba, aganin sa damuwar da yake ciki ta zarta zaman amsa wayar da zai yi da koma wanene a halin yanzu. Rayyan ko tuna cewa baya da isashshsen lpy bai yi, shaf ya mance da halin ciwon da yake ciki...ko da lkcn komawar sa asbiti yayi ma bisa ga ranar da aka basa bai tuna ba balle ya samu damar komawa. Tuni ya mi'ka cikiya kafafen sadarwa both gidan talabijin da redio stations ya kuma sake musu makudan ku'da'den da yasa suka isar masa da sakon sa da zafi zafi, haka kawai yake ji aransa cewar duk inda Zaitoon ta shiga masa da yarinya bai wuce nan cikin Kano ba, hakan yasa ya cigaba da gudanar da binciken sa ta gefe guda. A dai- dai lkcn ne kuma wata 'kira ta sake shigo masa...akaro na adadin da bazai iya kiyastawa ba. Wannan karon a zuciye ya kai hannu ya janyo wayar da niyyar masife mai 'kiran... Sai dai tun lkcn da sautin muryar mai 'kiran ya doki kunnen sa yaji komai ya kwance masa...tsaye ya mike yana takawa a hankali yana dawowa 'karshe zama ya koma yayi yana mai jin kansa na sarawa. Batare da wani 6ata lokaci ba suka sanar da shi cewa Zaitoon da Mufeeda na hannun su ne. Ya shiga firgici da tashin hankali fiye da zaton mai karatu domin bai ta6a kawowa cikin ransa cewar hakan ne zai faru ba kwatsam sai gashi sigar da abin ya koma, ya kuma rasa kalmar da zai fada musu su fahimce shi. Taya akayi haka? ya akayi suka san Zaitoon har suka 'dauke ta, ya akayi suka san da cewa akwai dangantaka tsakanin mu, a ina suka ganta? yarinyar da bama fita take agida ba, kuma waye ya basu family number 'din sa da har suka samu daman 'kiran sa da shi. Abinda ya tsaya tunani kenan bai samu damar basu amsar tambayar da sukai masa ba, infact bai ma ji 'karashen bayanan nasu ba balle ya amsa su. Ji kawai yayi wayar ta yanke, kuma ya bi 'kiran atake bayan furzar da numfashi da yayi amma sam baya tafia. Bayan kamar mintina talatin wani 'kiran ya sake shigo masa. Sai dai wannan karan 'kiran daga Anty Madeena ne, sun yi magana da ita ya kuma sanar mata bayanin da akai masa, ita ma mamakin ne ya kamata. Duk yadda Rayyan ya so bibiyar layin abin ya faskara domin sun toshe duk wata kafa da zai iya bayyana su, amfani 'daya suke da layi shikenan ya tashi a aiki, duk yadda kaso bibiya kuma bazaka ta6a tarar da abinda kk da buri ba, hakika ba 'karamin sani suka yiwa na'ura ba domin alamu sun nuna hakan 'karara, shikan sa Rayyan ya tabbatar da haka. Kusan za'ace babu wanda hankalin sa bai sake tashi akan na baya ba da jin cewa garkuwa da su akayi. Basu sake kiran sa ba har sai washegari bayan an fito sallar maghrib. Da sauri ya 'daga domin dama 'kage yake da son sake magantuwa da su duk da yake ba wancan numbern bane amma cikin lkcn tsammanin kiran su yake a kowani irin time dan yasan dole zasu sake 'kiran sa...ya riga ya gama yankewa cikin ransa cewar ko nawa suke da bu'kata a shirye yake ya basu matukar dukiyar sa zata kai indai zasu sako masa su. Sai dai ga mamakin sa a yadda ya tsammaci lamarin ba a hakan ya zo masa ba. Maganganun da sukai masa ba 'karamin tashin hankali suka sake sanya shi ba, gaba 'daya ma sai ji yayi 'kwa'kwalwar sa na neman tsayawa da aiki. Dagaske wa'dannan ba kidnappers bane ma'kiyan sa ne...cikin kalaman su ya fahimci hakan..ya kuma tabbatar tabbas ba hakanan kawai bane..dole akwai ha'din gwiwa ciki. Domin basu nemi ku'di ba kamar yadda ya tsammata, za6i kawai suka bashi na wanda za'a kashe acikin Zaitoon da Mufeeda ya za6i guda...a kuma kashe guda. Wannan batun ba 'karamin ta'azzara tunanin sa yayi ba, gaba 'daya komai ya kwance masa, babu abinda ke kaiwa da kawowa a jikin sa sai da yaji komai ya tsaya masa cak. Bai san lokacin da ma ya nemi waje ya zauna ba..." A wani dalili kenan...?" Ya jefa musu tambayar yana mai baiwa kansa 'kwarin gwiwa. " Umarni ne...na wa cikawa..."! Aka bashi amsar da ba ita yake da burin ji ba. Shiru Rayyan yayi ya rintse idanu..abin ya masa bazata ya kuma yi masa girma da yawa...sam bazai iya baude baki yace ya za6i daya daga cikin su ba. Dake wayar na handsfree ne yana iya jiyo tashin kukan Zaitoon ka'dan'dan kuma itama tana iya jin maganar sa dan zaune gaban ta wayar ga6a 'daya. Cikin ranta banda rokon Allah babu abinda take faman yi, tasbihi take ga mahalicci akan ya kawo musu mafita. Wani fizgowa da aka yiwa mufeedah yasa itama take ta tsanyara kuka tana fa'din" Mam..mi". Gami da mikawa Zaitoon hannu. Da 'karfi Rayyan ya sake dam'ke idanun sa bayan jin hakan, yayin da sautin kukan Zaitoon ma ya 'karu duk suna kokarin tarwatsa masa kwanya, kukan ko guda daga cikin su baya son ji a halin yanzu. Rokon su Zaitoon ta fara nan take tana fadin" dan girman Allah ku daina yi mata irin hakan wallahi amana ce a wurina kuma nasan sai Allah ya tambaye ni akanta, ku taimaka ku bar min yarinya ta kada ku raunata mu..." Yadda take maganar cikin kuka ko.da zuciyar ka babu imani dole sai kaji tausayin ta amma mutanen nan tamkar ma ba da su take ba. Ko bi takan maganar ta ta babu wanda yi, yayin da idanun Rayyan tuni suka bu'de ya waro su sosai, ji yake tamkar ya ga kansa agaban su a wannan lkc...amma yasan babu hali. Tsaye ya mi'ke kan 'kafafun sa dai- dai lokacin da kunnuwan sa suka jiyo masa magana ta cikin wayar"... tambaya ta 'karshe gare ka Dr Rayyan...ka za6a ka kuma sanar da mu wanda kk so ta rayu cikin su dan dole ne sai mun 'dauki ran 'daya sannan ka fanshi ran 'dayan da dukiyar ka kafin abin ya kewayo kanka kaima...". Tsayuwar da bai shirya yinta ba bace ta kama shi, amma jin jiri na son kayar da shi bayan tsayuwar ya sa shi ba komawa ya zauna yana jin bugun zuciyar sa na hauhawa, zuciyar sa yake jin tamkar zai faso kirjin sa ya fito. Kuka Zaituna ta cigaba da yi sosai bisa gwiwoyin ta, wanda yake iya jiyowa daga inda yake, tana kuma yin sa ne a tsananin galabaice gami da wahaltuwa, da 'kyar maganan ta ke iya fita take fa'din" Dan Allah ku bar min 'ya ta ta rayu, ku kaiwa Ammi ita, nasan ita ka'dai zata kula min da ita, na yadda ni ku kashe ni dan Allah..ku bar mufeedah ta ta rayu ..." Babu wanda ya kula da maganar ta sai" muna sauraron ka da suka fa'da da alamu ba maganar Zaitoon suke da bu'katar ji ba face ta Rayyan. Amsar sa ka'dai suke da bukata. Shi kansa Rayyan rasa amsar basu yayi, shin wannan wani irin iskanci ne. " Nawa kuke da bukata dan Allah ku sanar dani...zan baku ko nawa ne amma ku sakar min su gaba daya...". " Ba bu'kata Alhaji...ri'ke ku'din ka zasu yi mk amfani daga baya wajen fansan ran 'dayan daka za6a daga cikin su, ka daina 6ata mana lkc, mukan yi komai ne bisa tsari kuma ina tabbatar maka da cewar yanzun nan kana za6a zamu idasa aikin mu mu 'dora da abinda ke gaban mu, idan ka bada hadin kai a yau ma 'dayar da ka za6a zata iya dawowa gareka, idan kuwa kayi taurin kai zaka tsinci gawawwakin su ne gaba 'daya a saman babban titi a yashe..za6i naka ne Babban gaye...."! Ya 'karashe da muryar sha'kiyanci. Wani dake can gefe ne ya matso ya fizge wayar yace da Rayyan..." Starting from yanzu zuwa 10 mins...idan baka za6a ba toh ka tabbatar mun lashe wasan....". Yana gama fa'din hakan ya yanke 'kiran. Waje 'daya Rayyan ya 'kurawa idanu, meyasa tun farko bai yi tunanin zama ready kan bin diddigin yan iskan nan bane? meyasa hankalin sa ya 'dauke ga hakan. Gashi yanzu duk wani dogon jan lkc da zai yi babu wani amfani, lkc ya riga ya 'kure masa, yaushe ya bi diddigin su yaushe ya sa aka shirya masa troop yaushe aka je inda suke 'din duk cikin mintina goma? kuma ya tabbata ba tausayi ko tsoron Allah gare su ba a yadda yaji muryoyin su, daga yanayin da ya jisu ya tabbatar da cewar ri'ka'k'kun yan iskan gari aka tara. Cikin hanzari ya danna kira wata lamba, umarni ya bayar bayan an 'daga kiran kan layin da aka 'kira shi last... Har ya fara jero musu numbobin wayar sai kuma wani tunani ya fado masa, ta iya yiyuwa numbern bazai sake amfani a wajen su ba, a yanda ya fahimce su. Wannan tunanin yasa shi camza shawara kan cewar kawai a bibiyi nashi layin, duk wani kira da ya shiga ko ya fita har zuwa lkcn da zai basu umarnin dakatawa. Wata number ya sake 'kira yayi wasu takaitattun bayanai duk kan lamarin. Sam bai zauna ba, sai safa da Marwa yake yana faman danna waya hankali tashe. Kafin ya gama kiraye kirayen nasa sai gani yayi mintina biyu kacal suka rage cikin goman da suka basa. Video call ya 'kira amma kiran bai tafi ba, sai ya 'kira voice call nan ma haka bai tafi ba...cikin hakan yaga kira da wata sabuwar numbern batare da wani nazari ba ya 'daga ya sata a speaker. Sai ji yayi sun she'ke masa da wata iriyar dariyar mugunta. Tsabar takaici ma kawar da wayar yayi saitin fuskar sa yana mai jin ra'dadi a zuciyar sa... sa fuskar sa kuwa tamkar bakin ha'dari idan ka dube shi...ya so su ja wasan zuwa wani lkc amma tuno yadda duk ya rasa 'yan uwan sa da mahaifin sa cikin 'yan 'kalilan din lokuta ya sanya ji aransa cewar bazai sake wasa da wata dama da tazo masa a rayuwa...hakan yasa ya kawar da wannan tunanin...abu ne guda biyu da yasan dole indai ba wani ikon Allah ba dole zai daya ya faru gare shi...har can cikin ransa baya so ya rasa ko guda cikin Zaitoon ko Mufeeda amma bashi da lkc...sun shirya kafin suka tunkare shi sun kuma yanke lokacin ba wadatacce ba. Har ga baya so ya sake rasa wani nashi makusanci ta hanyar kisan gilla aganin sa hakan ya isa, baya so ya fara zargin kansa cikin lamarin da sam bai ta6a tunanin faruwar sa ko da cikin mafarki bane, amma sai gashi a halin yanzu bashi da iko ko damar sauya musu tunani kamar yadda bashi da damar dakatar da su, basu jin roko ya sani da wallahi ko ro'kon su zai yi akan su bar masa su duk araye ya famshe su da ko da kaf din dukiyar sa ne...bashi da damar dakatar da su sai dai ya mi'kawa Allah, yana ji kuma yana gani, yana kuma rokon sa akan ya ku6utar masa da su gaba 'daya. " Ya akayi ne 'karamin Alhaji?! Yaji muryar 'daya daga cikin su ya doki kunnen sa. Takawa ya fara ya nufi jikin window ya tsaya yana hangi harabar gidan sai dai ba anan zuciyar sa take ba, tana can wani wuri me daban da shi iansa bai san ina ne ba. He wish a gaban sa suke wannan isakanci da duk sai ya tabbatar yaji musu rauni da hannun sa. "...wa ka za6a..wa kuma za'a kashe...?" Hakan da yaji suka fa'da masa yasa shi tabbatar da cewa basu da niyyar sauya ra'ayi. Hannun sa mai.ciwon ya 'dago ya dafe kargen windown da shi bai san kuma lkcn da yayi hakan ba, kamar yadda sam bai tuna cewar hannun ciwo yake ba balle ma yaji zafin ciwon. " Sakanni talatin suka rage maka ka za6a..bayan wa'dannan sakannin kuma kawai ka tsumaye mu motsin mu na gaba..." Tambaya ta 'karshe Mr CEO wa ka za6a...?" Rayyan cike da sanyi da kuma rawar muryar da sautin ta ke fita masa da 'daci yace" Ku bar babbar kawai...". Dariya suka she'ke masa da ita gaba 'daya kamar dama jira suke ya furta hakan.. shi kuwa ya rintse idanu, wannan shine ga 'koshi ga kwanan yunwa, kenan yanzu ma ya sake rasa damar cigaba da gani gami da rayuwa da gudan jinin sa a duniya kenan..?" Zaitun kuwa na jin abinda ya fa'da ta zabura ta na nufo wanda ke ri'ke da wayar tace" Dan Allah ku rufa min asiri, kar ku biye shi ku bar min 'diyata araye, wallahi dama baya 'kaunar ta ko ka'dan, mugu ne azzalumi idan kasa aka kashe min 'yata wallahi bazan ta6a yafe mk ba kuma bazan barka ba sai na kashe ka kaima da hannu na...mugu kawai...." Ta 'karashe da sakin kuka tana mai dur'kushewa bisa gwiwoyin ta cikin yanayi mara dadin gani, gwanin ban tausayi sosai tunda Zaitoon take aryauwar ta duk da irin gwagwarmayar da tayi bata ta6a galabaita irin na wannan lkcn ba. Gwiwa ta fara ja tana 'kara ro'kon su tana kuka, dan Allah kar ku kashe ta, ni na yadda ku kashe ni, amma ku kaimin Mufeeda wajen Anty Madeena ko Ammi...dan Allah..." 'Daya cikin su ne ya doka mata tsawan tayi musu shiru. Amma Zaitoon taki bin umarnin sa. Bindiga ya 'dago take Zaitoon ta ha'diye wani mugun miyau tana duban cikin idanun sa da shi kadai take iya hangowa... kirjin ta take faman nunawa tana kuma kokarin harha'de kalaman ta da tuni suka watse a kwanyar ta... sake rungume Mufeeda da 'dayan hannun ta tayi yayin da 'dayan hannun take toshe bakin ta da shi. " Ni k..kashe ni..dan Allah kar ka ka kashe min yarinya ta ka ...barta... ta rayu...". Bata gama rufe baki kunnuwan ta suka ji 'karar fitar harsashin da bata san takamamme inda ya sau'ka ba. Hakan yasa ta sakin wani 'ka'k'karfan ihun da yayi amsa kuwa yabi iska take ta fadi a wajen sumammiya. 'Kit Rayyan shima ya kashe wayar yana mai mayar da idanun sa ya lumshe... Tunda kunnuwan sa suka jiye masa 'karan bindigar bai sake sanin ina tunanin sa suke ba, bakin sa bai sake iya furta komai ba ji yayi yayi masa nauyi, haka kwakwalwar sa bata sake fahimtar abinda ke faruwa da shi ba balle wayar da ke hannun sa, yana nan tsaye tamkar an dasa shi idanun sa na hango down stairs kamar me nazarin wani abu...amma tunanin sa na can wani wuri. Har wani 'kiran ya sake shigo masa ma duk bai lura ba da yake wayar ba 'kara take ba..wa'dancan da ya bawa umarnin bin diddigin sune suka 'kira sun sake 'kira still bai 'daga ba yana can yana tunani. Shikenan sun kashe min ita. Shikenan itama ta tafi ta barni. Abinda ya fara zuwa maza cikin brain kenan bayan ya dawo daga duniyar da ya lula. Baya yayi ya jingina bayan sa da jikin kujera yana tunani, jikin sa duk yy sanyi, shi kansa bai san meyasa ya za6i uwar ba...bai san yaushe kuma a wani dalili ya za6i Zaitoon kan gudan jinin sa ba. *Afuwan pls...nasan nayi laifi* 🙏 *Zagi is allowed but HAKURI da UZURI over everything please..* 👌 ~Ina son ku...~ 👍 Salmerh ce😘 [9/12/2022, 4:55 am] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Wattpad@* _Serlmerh-md_ 🅿️ *...79* ........" Anty Wlh hankali na ya kasa kwanciya da rashin Zaitoon a gidan nan, Anty tsoro nake ji kar a cutar da su..." Marwa ta fada tana mai 'ko'karin share hawaye. Duban ta Anty Madeena take cike da tausayin ta, a hakan ma dan bata san 'ka'k'karfar ala'kar da ke tsakanin ta da Mufeeda ba kenan.." Anty Madeena ta ayyana hakan cikin ranta. A fili kuwa ajiyar numfashi tayi tana mai gyara zama tace..." Nima kaina Marwa hankali na ba kwance yake ba, babu mamaki ma.yafi naki hankalin tashi, ina matu'kar fargaban abinda zai biyo bayan wannan tafiya ta Zaitoon...cikin rashin sani tayi tafiyar bayan ta riga ta bar cibiyar 'diyar ta anan ta kuma bar zuciyar ta ita kanta ma anan 'din...ina fargabar inda Zaitoon zata shiga da auren Rayyan akanta...amma babu komai, Insha Allah babu.abinda zai faru, zamu ji alkhairi madadin sharrin da muke gudu bi'iznillah..." " Allah yasa Anty, Allah yasa muji Alkhairi ba sharri ba..." " Ameen Ameen..." Cewar Anty Madeena tana mikewa dan komawa babban palor. Can 6angaren kuwa tunda suka ga yadda Zaitoon ta sume sai suka she'ke da dariyar mugunta gaba 'daya illah mutum 'daya, babban su ne yace" Ni dai ina da shawara..." Damar magana aka bashi ya kuwa furta abinda ke ransa. " A gani na bai kamata ace an kashe ko guda ba aciki ba, domin alamu sun nuna duk suna da muhimmanci a wajan sa, kunga shi uwar ya za6a ita kuma ta bada ranta wa 'yar da alamu ko nawa aka tatsi shegen zai fitar..." Da wannan shawarar suka rufe zancen nasu, nan suka bar Zaitoon da Mufee cikin mugun yanayi abin tausayi. Mufeeda kam kuka sosai take tana shiga jikin Zaitoon dake sume dan itama 'karar bindigan ya firgita ta sosai, wani ne ya dawo hannun sa dauke da goran ruwa nan ya bude ya she'ka mata ruwan mai azabar sanyi, a gigice ta farka zata saki kuka taji kukan Mufeeda gefen ta hakan yasa ta waiga gareta da sauri ta janyo ta rungume abar ta tana sakin kukan farin cikin ashe tana raye basu kashe mata ita itaba. Kuka take tamkar ranta zai fita...haka suka cigaba da zama cikin 'dakin har zuwa yammacin ranar, duk sanda taji an bu'de 'kofa razana take yi da tunanin lokacin raba ta da Feefy ne yazo dan ita bata san da wancan shawarar tasu ba...sai dai kuma ga mamakin ta abinci ka'dai suke basu da ruwa su koma har aka sake yin kwana biyu. Rayyan da tun da yaji karan harbin nan ya tabbatar na kisan diyar sa ne komai ya kwance masa, bai sake bi ta kan komai ba hatta wayar sa kuwa, da kiraye kiraye suka dame shi ma sai kaseh wayoyin sa yayi baki 'daya. Bai kuma sanar da kowa ba sai da Ammi ta matsa ne ma da ganin canjin nasa sannan yayi mata bayani atakaice. Hankalin Ammi tashi yayi sosai, nan ta fara yi masa fada meyasa yayi saurin bada za6in sa, atace ai da rokon su yayi su basu ku'di ko zasu sake su, amma yanzu idan Zaitoon ta tabbatar da cewar da bakin sa aka kashe mata 'diya tasan har abada bazata ta6a yafe masa ba balle ta kwantar da hankali tayi bautar auren ta. Rayyan dai bai ce da Ammi komai ba yayi shiru dafe da kansa. Cikin lokaci 'kankani yayi busu busu da shi ya tattara gashi a fuskar sa. Banda jinin sa dake shirin hawa sama. Akan wayoyin sa ma sai da Ammi tayi dagaske kafin ya bude su. Awanni ka'dan bayan bu'dewar wani abu ya fado ransa, da sauri ya janyo waya daya ya fara lalu6o wata number, nan ma yaga ashe sun tara masa missedcall tun ma kafin lkcn da ya kashe wayar. Bayanin da akai masa kan bin diddigin da ya sa ayi ba 'karamin tayar masa da hankali yayi ba. Sake jinjinawa yake cikin ransa..nan yasa aka shirya masa troop daga headquater...sai nan ne ma ya dan ji kwarin gwiwa sai dai wani tunani ke sake kashe masa gwiwar nan take. Har gida suka biyo suka dauke suka wuce. Traicer ke nuna musu hanyar da ya bada umarnin abi masa kiran da akai masa a wancan lkcn. Cikin kowani dakika fargabar sa karuwa take, sosai yake kokari wajen ganin ya 6oye abinda ke masa kai kawo a zuci...meyasa sai nan unguwar toh...?" Ya tambayi kansa. Bai sake tsinkewa da lamarin ba har sai da yaga motocin sun tsaya gaban wani guest house din Abban su. Ido ya lumshevya kuma bu'dewa domin tabbatarwa amma still nan din dai yake gani ba wani waje daban ba. Zaitoon na nan yashe duk ta galabaita, rabon ta da ganin wani halitta a gidan har awanni talatin da hu'du kenan yanzu. Ta gane hakan ne ta agogon bangon dake manne saman 'dakin da aka ajiye su. Bata san me ya faru ba, bata kuma san ya suka 'kare da shi ba balle tasan dalilin da yasa ta daina ganin su. Ashe ya fahimci kutsen da akai masa ne ya sa shi basu umarnin barin gidan cikin gaggawa, yaso su fito gaba 'daya har su Zaitoon amma sai yaran nasa suka yi kuskure basu fito da su Mufeedan ba sai ma sake kullesu da suka yi suka fice daga gidan. Lokacin da ya fahimci wautar da suka yi ba karamin haushi yaji ba bashi kuma da damar saka su su koma gudun kar ayi ram da su...dole ya hakura bai koma gidan ba kamar yadda bai bada umarnin wani ya koma ba. Sai dai yasan dole hakan sai yayi wa sirrin sa gi6i. Gudun kar a zarge shi ya sa cikin lkc kankani ya nemi ticket ya sake komawa can 'kasar da ya fito..can gidan su kuwa babu wanda ma yasan ya dawo Nja ciki kuwa hadda matar sa Marwa. Kamar cikin mafarki Rayyan ke ganin lamarin, fita suka duk 'karasa jikin gate din da kafafun su. Sai da aka 6alle gate din kafin suka samu damar shiga dan ko mai maigadin ma bayanan tuni an sallame shi batare da Rayyan yama sani ba, bai san tsawon wani lkc ya bar aikin ba kamar yadda ba'a fasa tura masa kudin albashin sa duk 'karshen wata tare da sayran ma'aikatan sa ba. Kallo 'daya yayi wa harabar gidan ya tabbatar 'kafa bai jima da 'daukewa cikin ta...sunan da yake ta so ya kawar din kasa tafiya yayi, dole batare da ya shirya ba yahi la66an sa sun motsa wajen furta sunan..." _SULTAAN_ ..."! Bincike sosai suka yi kafin suka gano dagaske su Zaitoon na cikin gidan nan, sai dai ko alama 'yan iskan basu bar wata kafa da za'a gane su da shi ba. Sun galabaita sosai dan hatta hannu babu mai iya 'dagawa tsakanin Zaitoon da Mufeeda, yunwa da ishirwa duk sun galabaitar da su. Wata kakkarfar ajiyar zuciya Rayyan ya sauke da ganin Mufeeda araye ba kamar yadda ya zata ba. Ganin tan kuma shi ya kara masa karsashi da kuzarin jikin sa. Zaitoon dai taga mutane amma koka'dan bata gane ko su waye bane balle tasan manufar zuwan su...domin dishi- dishi take gani..cikin zuciyar take iya ayyana abinda take so bakin ta ya furta amma tsabar galabaita bakin nata bazai iya furtawa ba...hakan yasa ta koma ta kwantar da kanta tana jiran 'karasowar mutuwar da ta tabbatar shine ya tunkaro ta a halin yanzu. 'Karshe sai bu'de idanu tayi taci karo da farin POP flat saman kanta sa6anin na can gidan da aka kaisu da yake designed ne. Rufe ido tayi ta sake budewa dai- dai da tsinkewar da zuciyar ta tayi..." Mufeedah.."! Ta furta a hankali dan muryar ta baya fita sosai. " Mufee na..!! Ta sake maimaitawa. 'Karfin halin mi'kewa zaune tayi duk da yanda take jin hannun ta a 'da'ddaure amma hajan bai rage komai daga niyyar ta ba...fahumtar da tayi cewar zata iya 'dage hannun ya sa ta 'dagowa ta kalla, nan ta fahimci ruwa ake 'kara mata. Zaune tayi kokarin mikewa tana mai jin ga6o6in jikin ta babu 'karfi sam. Da Shi ta ci karo zaune ya tsura mata idanu kawai yana duban ta amma bai ce da ita uffan ba....hannun nata ta kalla tana 'ko'karin fizge abin hannun nata, sai anan yayi magana inda yace..." Ki nutsu.." " Ba dai yanzu ba.." Ta bashi amsa batare da ta dube shi ba. " Kina hauka ne?" " Babu mama ki". " Baki ganin halin da kk ciki ne..?" Yayi maganar yana ri'ko hannun nata. Kuka ta sanya tana mai fizge hannun tace" Wannan ni bai dame ni ba..Yarinya ta ina kuka kaimin ita inaso in ganta yanzu...sake rushewa tayi da kuka tana fa'din wannan wani irin rashin imani ne fisabilillahi? me yarinya ta tai muku? me Mufeeda ta tsare muku ne duk a duniyan nan?..na zauna da ku tsakani na da Allah na na bauta muku batare da na nemi komai daga wajen ku ba amma sakayyar da zaku yi min kenan? Sai ku kashe min yarinya ta? Bacin baku san ta yadda na same ta ba, amana ce fa a waje na, amanar ta aka bani, yarinyar nan marainiya ce, me kuke so in fa'da wa Ubangiji na idan ya tambaye ni akanta...?" Kuka sosai ta rushe da shi tana mai kifa kanta da ga gwiwoyin ga. Rayyan kam shiru yayi yana duban ta gami da fasa maganganun ta dalla dallah ya kuma fahimci me take nufi tsab..... Shi dama ba gwanin lallashi bane dan haka yayi shiru yana duban ta sai dai tsananin tausayin ita har Mufeedan yake ji. " Wallahi bazan ta6a yafe muku ba, kuma bazaku ta6a yin 'karshe mai kyau ba Insha Allahu...duk.wanda yake da hannu cikin kisan 'diya ta sai yaga sakayya...." " Zaitoon...!".... Yayi saurin dakatar da ita da 'kiran sunan ta, sai dai ga mamakin sa jawabin ta da ya biyo baya kaushi gare shi...".karka kuskura ka 'kira suna na, ka 'kyale ni nayi kukana tunda haka kuka fi so ku ganni, burin ku ku tozarta ni, burin ku ku ganni cikin kunci shiyasa kuke ha'de bakin ku, macuta kawai maciya amana, marasa tsoron Allah, maha'inta kawai....". Ta fada batare da ko jin shakkar sa bane. Shi kam bai san kuma me zai 'kara fa'da mata ba illah ido daya tsura mata yana kallon yanda take kuka...wai dama dagaske haka iyaye suke ji ne akan 'ya'yan su..ko kuwa natan ne na daban hadda iskanci, shi bata ma ga jarumtar sa ba da ya iya sadaukar da ran 'diyar sa ya fanshi nata aranar ba dan son kai take fa'da masa irin wannan ba'ka'ken maganganun akan that same yarinyar...? ya tabbata da sunyi.niyyar kashe ta da gaske da sun kashe masa 'ya aranar amma Allah ya dube shi, amma shine zata sashi gaba da irin wannan tijarar..? Abinda ya tambayi kansa kenan yana sake waro idanu akanta cike da mamakin ta. Zaitoon kam ganin irin kallon da yake yi mata ne ya sanya taji fa'duwar gaba sosai, ko shakka bata yi ba balle tsoro ta 'dago hannu ta nuna shi da yatsa, cak kukan ta ya tsaya ta wani 'kan'kance idanu, idanun ta cikin nasa tace " Kar ka gaya min cewa kun kashe min yarinya ta dagaske ne..?" Shirun da taga yayi yana duban ta ne ya sanya ta fizge abin hannun ta gaba 'daya ta mi'ke, bata damu da jirin da ke 'diban ta ba ta tashi ta tsaya a tsawace tamkar itace sama da shi tace " Tambayar ka nake ina 'ya ta, wallahi matukar Mufee na ta rasa ranta ta dalilin ka wallahi kaima kashe ka zanyi da hannu na, dan akanta babu wanda bazan iya 'daukan mataki akan sa ba...." Sai kuma ta zube 'kasa saman gwiwoyin ta tana me sake rushewa da kuka ganin ko 'kala ya 'ki cewa da ita, kuka sosai ta saki tana bubbuga kanta tace" ita ka'dai fa gare ni, Mufee bata san kowa ba sai ni, babu wanda yake son ta sai ni, kunsa na ci amanar alkawarin da na 'dauka na cewa zan bata kariya, 'karshe kun kashe min ita kuka rabani da ita haka nan kawai batare da tai muku laifin komai ba..mecece ribar ku? wallahi bazan bar duk wanda ke da hannu akan kisan yata ya cigaba da farin ciki ba..." Tsaye ta mike a harzuke zata yi hanyar waje yy saurin ri'ko hannun ta da hannun hagun sa mai cikakken lfyr, ita ma da 'daya hannun ta take bubbuga na shin tana fa'din " Ka sake ni, mugu kawai azaalumi, masu 'daukan rayukan yara 'kanana wallahi Allah bazai barku ba sai ya mana sakayya..." Ganin taki natsuwa ne ya sanya shi bu'de murya ya 'kira near by Nurse. Shigowa tayi tana mai rusunawa. Yi min magana da doctor". Fita Fa'izan tayi tana mai jinjina kanta. Cikin sakanni 'kalilan likitan ya shigo. Da turanci yy masa magana wanda hakan ya sa Zaitoon banka masa uwar harara. Fita likitan ya sake bai da'de ba ya dawo shi da wata nurse abayan sa..Zaitoon nata fama da kokuwar 'kwace jikin ta amma ta kasa, kuka take amma da ganin likita na gyara Allura ya sanya ta zabura tana 'kara sautin kukan ta, ba wai dan tana tsoron alluran bane a a, sai dai dan takaicin rashin 'diyar ta a ganin ta bb wani ciwo dake damun ta illah ciwon rashin Mufee kuma allura ba zai mata maganin wannan ba, dan hk babu wanda ya isa ya sa ai mata allura.... Hannun ta take shirin fisgewa daga cikin nashi yay saurin gyara rikon yana duban fuskar ta. Matso da ita yy kusa da shi ya sar'ke ta da 'kafafun sa ganin hakan yasa ta fara fizga tana fa'din" Bana so.." " Ka kyale ni, mugaye kawai, azzalumai...wallahi sai nakai 'karar ku wajen hukuma dukkan ku...masu zuciyar fir'auna kawai, masu halakar da kananan yara, in ba zalunchi ba me yarinya tai muku....". Sam bai damu da zagin da take jerowa ba, da hannun sa 'daya mai cikakken lafiyr ya matse ta cikin jikin sa amma ko motsi kasa yi tayi dan sosai ya dabaibaye ta da 'kafafun sa. Hannun daman ta dake cikin nashi ya mi'kar wa likitan yana bashi umarnin yi mata allurar. Nurse din ce ta taimaka masa suka kwantar da ita..yana gyara mata mazaunin kanta bisa pillow tana 'dan lumshe idanu tace" Kai..ma mugu ne ashe...." Murmushi yy ta'kaitacciya, dan shi ka'dai yaji abinda tace dan lokacin bacci ya fara cin 'karfin ta. Sai da ya shafi fuskar ta kafin ya nufi hanyar fita yana amsa 'kiran da Ammi tayi masa. Tsawon time 'din da Zaitoon ya kamata ta 'dauka a baccin ko rabin sa bata yi ba ta farka, su kansu sun yi matu'kar mamaki, ta kuwa 'daga musu hankali, ga shi Rayyan bayanan, sai Marwa ka'dai, duk yadda taso kwantar mata da hankali sam Zaitoon ta 'kiya, dole sai da Marwa ta 'kira Rayyan a waya yazo, yana can yana kan 'karasa binciken abinda ya faru ya tsinkayi wayar Marwa hankalin sa ya tashi, sosai ransa kuma ya 6aci. Yarinyar na can gidan Anty Madeena mancewa ma yayi bai taho mata da ita ba da safen, dama niyyar sa sai ya tashi komawa ne zai tafi da ita. Jin tashin hankalin da take yi musu kuma ya sanya ransa 6aci yama fasa 'dauko yarinyar, haka ya nufi asbitin cike da zafin rai. Yana zuwa ya tarar ta birkita ko'ina tamkar mahaukaciya ta kasa sauraran kowa duk ta jiwa kanta ciwo banda kuka da take yi duk wai akan Mufeeda. Marwa kanta ma kukan take tana fa'din haba Zaitoon! Haba dan Allah, wai kina hauka ne?...ance miki Mufeeda na nan a raye bb abinda ya same ta meyasa bazaki kwantar da hankalin ki, ki bi komai a sannu ba...?" Idanu ta waro akan Marwa tana duban ta da mmk... " Marwa in kwantar da hankali na kika ce, bayan sun kashe min yarinya...?" " Babu wanda ya kashe ta ki kwantar da hankalin ki dan Allah ki nutsu..gaba 'daya kin.kasa saurarn kanki ma balle ki bawa kankin damar sauraran wani, Mufeedan ki tana raye ai kinsan bazan miki 'karya ba ko ba...?" " Karya ne.." ta fada da 'dan 'karfin sauti tana mai watsa hannuwa. " 'Karya ne kawai fada kike Marwa, in dai dagaske tana raye toh in ganta mana, a gabana fa, tana hannu na aka harba mata bindiga Marwa..." Sai kuma ta rushe da kuka tana mai juya kai side by side. Rayyan na isa daya 'kare wa 'dakin kallo direct ya nufi inda take idanun sa na kanta...da isar sa ya sa hannu zai kamo hannun ta ta fizge da 'karfi tana matsawa baya kadan. Juyowar da zai yi kawai ya sau'ke mata mari lafiyayye saman kuncin ta wanda yasa Zaitoon dafe wurin nan take, tana shirin zamewa 'kasa yayi saurin cafko hannun ta hakan ya hana ta zamewa. Idanun sa cikin nata idanun dake cike taf da ruwan hawaye suna shirin gangarowa yace..." Kina tunanin ke ka'dai ke 'kaunar Mufeeda ne? ko kuwa naki hauka da karamin 'kwa'kwalwan ne ya ninka na kowa..?..ke a tunanin zaki fi kowa jin zafi ne idan akace yau babu Mufeeda, ni kinsan yadda zanji, kinsan 'kuncin da zan fada ne sbd rashin ta, wallahi naki ba komai bane akan yadda ni zanji...?" Jin furucin sa yasa ta waro idanu sosai akansa ta fara jan baya tana girgiza kanta wani sabon kukan na zuwa mata...gani take kamar kawai ya fa'di son ransa ne, sai taga kamar kokari yake ya kwace mata matsayin da take da shi a wajen Mufeeda baya ga hakan meyasa zai ce haka...?" Ganin yadda ya sake rikita mata tunani gami da canzawar yanayin ta yasa Rayyan kama hannun ta yaja ta zuwa waje. Bai tsaya ko'ina ba sai cikin motar sa da wani 'dan banzan gudu yaja motar zuwa gidan Anty Madeena...batare da ya sake furta wata kalma ba ko duban inda take ma bai yi ba. Marwa kam cike da mamakin furucin sa tabi su da idanu har suka 6acewa ganin ta, jujjuya maganar take cikin ranta ta kuma kasa gano manufar su...a iya sanin ta dai ba hakan bane amma meyasa zai wa furtawa Zaitoon, rashin sanin takamammen dalili yasa tuni tayi watsi da su. Zaitoon kam kuka take tana jin maganganun nasa nayi mata yawo aka, bata ma san ina suka nufa ba balle tasan lkcn da suka iso sai ji tayi yayi parking. Koda yayi parking da kansa yazo ya bu'de mata motar ya kuma sake fizgan hannun ta zuwa sabon 6angaren Anty Madeena..abin mamaki da shigan su parlorn sai ganin Mufeeda tayi tana wasan ta cikin kwanciyar hankali. Zaitoon bata san lkcn da ta zame 'kasa saman gwiwoyin ta ba, gaban yarinyar ta tsaya tana bude mata hannu gami da washe baki, Mufeeda ma na ganin ta ta taho da gudu wajen ta cike da murna tana fa'din " Mammi.." Zaitoon janyo ta tayi ta rungume ta sosai tana sakin wani sabon kuka na farin cikin ganin Mufeedan ta na raye...yayin da cikin ranta banda hamdala bb abinda take yi. Mufeeda ma da sauri ta shige jikin ta tana daria ta sake fa'din..." Mammi..."! Rayyan bai ce da ita 'kala ba kawai ya samu waje ya zauna yana sakin zazaffan huci idanun sa a kansu, a hankali ya 'dage kansa sama yana dafewa da hannun sa 'daya. ".... _Sultaan_ !...ya sake furtawa saman la66an sa a karo biyu, tunani ya cigaba da yi a kansa, Sultan ya gama 'kure shi..ya gama kaishi ma'kura, Sultan ya riga ya kaishi gejin da sam ba zai iya rintse idanu ya cigaba da barin sa ba, ba zai iya cigaba da barin Sultan yana da'kusar masa da duk wata walwalar sa...ya ishe sa haka nan. Bai san mai Sultan ke shirin zama a dunia ba sam, bai san ina ya cusa ilimi da tsoran Allahn sa ba, a yanzu ya riga ya kaishi ga6ar da bazai iya barin sa ba, ba zai barin sa sake cin nasara akan sa ba sam sam.... Da fitowar Anty Madeena ta tarar da Zaitoon da Mufee rungume da juna...kallon.su ta dan yi na 'yan sakanni tana ayyana wani abu cikin ranta. Ba komai ke mata yawo aka ba kusan ko wani lkc face tasan yadda akayi Zaitoon ta samu Mufeeda, musamman idan ta dubi yarinyar taga yadda kusan kullun kamar ta ke 'kara bayyana 'karara sai taji ta sake 'kaguwa da son sanin mafari da tsushen komai...amma ta lura Rayyan kamar har yanzu bai bawa lamarin muhimmanci ba. A hankali ta dawo da kallon ta ga Rayyan dake dafe da kansa. Yanayin sa sai yafi 'daukan hankalin ta dan haka wajen sa ta nufa tana zama gefen sa take tambayar sa" ya akayi ne Rayyan...?" Bude jajayen idanun sa yayi ya sau'ke bisa fuskar Antyn tasa, sai dai madadin ya amsa ta kawai sai ya mi'ke tsaye sannan yace..." Bakomai Anty, bari muje kawai za muyi magana daga baya, akwai abinda ke gaba na yanzu wannan fitinanniyar ta rikita min hankali akan Mufeeda...". Duban inda suke Anty Madeena tayi sai tayi 'yar murmushi.." Ina laifin me son naka Rayyan...?" " Hmm"..kawai yace batare da ya 'kara wata kalma ba yayi gaba. " in kin gama koken sai ku taso mu wuce..." Yace da Zaitoon batare da ya dube ta ba sannan ya fita. Kallon Anty tayi tana girgiza kai tace "Anty kice ya barmu anan dan Allah...". " Kiyi hakuri ki bishi Zaitoon, baki ganin tashin hankalin da yake ciki ne, dole kinsan zai bu'kaci ganin ku kusa da shi ai..tashi kinji yi ha'kuri....". Tayi maganar tana mai tasowa ta 'dago Mufeeda daga jikin ta dole Zaitoon ta mike tana zum6ura baki. Cikin ranta take jin babu dadi, meyasa kowa son kansa ya fiye masa yawa ne, taya baza su fahimce ta ba sai kansu? Mutumin da da kunnuwan ta taji ya za6i akashe mata yarinya shine za'a ce zai bukaci ganin su toh suyi masa me kuma..? Gida Rayyan ya mayar da su sannan ya sake ficewa batare da ko cikin gidan ya 'karasa ba. Zaitoon wannan karan 'dakin ta dake can 6angaren Ammi ta koma tayi zaman ta. 'Bangaren Rayyan kuma dama ya jima da fara zargin Sultan tun bayan haihuwar Arfan ya fara dasa ayar tambaya akan sa, a hankali yake binciken sa kwanciyar sa jinya ya dakatar da komai, sai dai bayan hakan a yanzu ya gano abubuwa da dama da suka faru wanda Sultan ne da kansa ya jagoranta, ya gano da sa hannun Sultan bisa abubuwa masu dama kuma marasa da'di da suke faruwa a company da ma cikin gidan su gaba 'daya, sai dai he can't directly point a finger on each incidenced. Amma kidnapping Zaitoon da Mufeeda da akayi ya kuma revealing masa komai, domin ba 'karamin tsaurara bincike yayi kan lamarin ba tun bayan fahimtar da yayi cewa a 'daya daga cikin guest house din Abban su aka 6oye su. Wannan gidan ya kasance mallakin mahaifin su ne wato Sa'ad Auta...kuma su ka'dai ahalin gidan ke amfani da shi suma 'din banda matan cikin su, a atakaice yanzu kuwa daga shi ne sai Sultan araye kawai ke amfani da wannan gidan...kusan ma Sultan ya fishi dan shi ba kasafai yake zuwa ba sauran gidajen Abban nasu ba. Yaso yayi jayayya da zuciyar sa akan saurin sau'kar da zargin ta bisa kan Sultan duk da kuwa yana da hujjoji 'kwarara but hkan bai yi tasiri cikin ransa ba..dole ya tabbatar da shi 'din ne dai, babu wanda ke da access da wancan gidan bayan su, kuma basu bada hayar sa balle aro dole shine ko Sultan, in ba shine da kansa ba kuwa sai dai Sultan...da 'kyar ya harha'de Puzzle din, amma har gobe ya kasa gano manufar Sultan kan haka, kenan dai Sultan ne ya kidnapping 'din su ko kuma yasa ayi domin yasan baya 'kasar a halin yanzu, ya kuma razana shi akan kisan 'daya 'daga cikin su alhali bai kashe ko guda ba, me hakan ke nufi kenan...?" Sultan ya kar6i ku'di a hannun sa masu yawan gaske da sunan ku'din fansan ran Zaitoon bayan acewar sa ya sa an sanar da shi cewar an kashe Mufeeda....Sultan! Sultaan!! Sultaan!!!..what's the meaning of all these...wai duk wannan shirin Sultan din sa ne ya yisu...?". Ya tambayi kansa. Tuni ya sa an kamo wasu dake aiki da Sultan din ciki kuwa hadda su Yusee da su Huzaifa anan kuma ya 'kara samun cikakken bayani kan komai...ya kuma tabbatar da zargin sa. Cikin firgici yake tariyo 'kazamin aikin da Sultan ya aikata musu batare da sun san shi bane, batare da sun san kwana suke su tashi da makiyin su ba, Sultan ne ya kashe masa mahaifi da 'kanin mahaifin sa, Sultan ne ya kashe masa 'dan uwan sa da duk ahalin sa mata da 'diyar sa bayan ya tabbatar da cewar ya fara zargin makircin sa, Sultan ya kashe masa 'yar uwa duk a bakin yaran sa ya samu cikakkun bayanan da be ji kokonto akan su ba dai dai da kwayar zarra. Sultan ya gama 'kure shi gaba 'daya, bayan duk wannan kuma shine yake fita da matar sa Amrah ya ke kuma bata maganin hana haihuwa dan kar ta haifa masa 'dan da zai gaje shi...'karshe kuma shi ta haifawa 'dan suka kuma waske kamar 'dan Rayyan ne batare da sun san ya gano su ba. Sultan ya kan dauki Amrah suyi duk tafiyar da suka ga dama tamkar ba auran sa ne akan ta ba, tamkar ba zaman 'dan uwa Sultan yake a wajen sa ba. Hakika Sultan bai kasance 'dan uwa abin alfahari ba, Sultan ya nuna masa bambanci tsakanin jini da ruwa, hakika kaurin jini ya rinjayi ruwa nesa ba kusa ba, Sultan yayi masa gi6in da har karshen rayuwar sa bazai ta6a mantawa ba. Kallon 'dan uwa yake wa Sultan ta yadda koka'dan bai ta6a zargin sa kan komai ba, har gidan soja ya kaishi bisa neman cika masa burin sa na 'karya, erh mana na 'karya tunda burin shaho ne ba na gaskia bane tunda 'karshe Sultan ajiye aikin yayi duk fadi tashin da yayi kafin ya sama masa. Ta6a masa ahali a halin yanzu bazai iya jurewa ba, domin jin su yake tamkar ransa...duk ya fahimci shirin Sultan aka sacen sun da sa ayi, unfortunately kuma da aka 'kira aka bashi za6i sai ya za6i Zaitoon yace inma kisan ne su kashe yarinyar. Ba dan komai yy hkn ba kuma face dan rama khairan da khairan. Bai yiwa Zaitoon adalci ba aganin sa idan ya za6i 'diyar sa akanta bayan duk wahalhalun da tayi tayi su ne sbd Mufeedan yasani. Hakan kuma da yayi shi ya bawa Sultan tabbacin cewa basu da ala'ka da yarinyar, dalili kenan da yasa duk wani shiri nasa da hasashe ya korar da su...ya kar6i makudan ku'dade a hannun sa...ku'daden sa na halak da ya tara su da gumin sa amma Sultan yake can yana kashe su ta hanyar banza, da dukiyar sa Sultan yake amfani wajen ci masa dunduniya, da dukiyar sa yk amfani wajen yin duk shashancin da yaga dama ciki kuwa hadda matar sa ta sunna. Bazai ta6a iya barin Sultan yasha haka nan kawai ba...idan yabar shi yasan bazai ta6a barin sa yin abun kansa ba. Dole ne sai ya 'dauki tsatstsauran mataki a akan sa. Tun kafin Sultan ya dawo Rayyan yasa aka tsaida komai nasa, an dakatar da share da ake basa na company an kuma rufe account din ma gaba 'daya. Rayyan ya gama duk shirin sa ya tattatara hujjoji da bayanan sa gamsassu dawowar Sultan 'kasar kawai yake jira a yanzu sai kuma a lkcn yaji hankalin sa ya kwanta. 'Bangaren Sultan kuwa hankalin sa tashi yayi bayan fahimtar da yayi cewa asusun bankin sa duk an dakatar da su, ya tuntu6i bankuna kuma sun nemi da dole sai yazo ya ciccike wasu forms kafin komai ya daidaita, cikin rashin sani sai yi dogon nazari ba, sanin na'urar sa ya kasa yi mai amfani kan hkn. Sannan ko ya 'kira yaran sa da yake aiki da su baya samun su a waya. Yayi magana da Amrah kuma tace masa babu mamaki shirye- shiryen 'karshen shekara ne ya biyo takan asusun nasa. Dole ya fara shirye shiryen dawowa gida. Rayyan kam ciwon sa ne ya kusan sake kwantar da shi bayan da ya gama binciken sbd stress da yai masa yawa, domin tsananin damuwa da rashin sukuni ya dan sa jinin sa haurawa, sai da yasha treatment aka bashi hutu sosai kafin ya 'dan samu nutsuwa, sai kuma a lkcn ne Zaitoon ta je duba shi domin tun bayan dawowan su gida da Mufee bata 'kara yadda ta je inda yake ba bata sake sanyashi a idanu ba domin bata fita ko'ina koda yaushe tana dakin ta, hatta Marwa ita ke biyo ta 'dakin suyi hira gaishe da Ammi ka'dai ke fidda ta shima 'din ba kullum ba. Haka ma Mufeeda bata sake zuwa makaranta ba...shi kansa yana sane da hakn amma yana so sai ya gama shirin sa tukunnna. Tuni ma yaje yayi magana da makarantar akan yarinyar. Ko rashin lafiyar tasa a abakin Marwa taji, ta kuma ga yadda duk suke rawan jiki kan hkn...hakan yasa ta yanke shawarar zuwa gaida shi. Salmerh😘 [9/12/2022, 4:04 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Wattpad@* _Serlmerh-md_ 🅿️ *...80* ........" Sai yau aka ga daman zuwa duba ni...?" Yace yana duban fuskar ta bayan ya amsa sallamar da tayi. Zaitoon baki ta 'dan tura gaba tana mai kawar da kanta gefe. " even once Zaitoon..? ko mafarkin ki bai raya miki cewar kizo ki duba ya nake ba? kika mance da ni baki tunanin cewa akwai wani bawan Allah da ya dace ki san halin da yake ciki ba? ya nk ya na kwana? lpy ta ko babu duk ba shine gaban ki ba yarinyar kice kawai damuwar ki ko? Ni yadda nake ganin kk 'kaunar Mufeeda ma yana sa inji na rasa hope kwata kwata, sai inga kamar bb wani wanda zai iya sake samun gurbi cikin zuciyar ki makamanciyar ta Mufeedah...tunda gashi ina shirin mutuwa ma amma ba'a damu da ko zuwa gani na ba.." " Ba kaine kace baka son Mufee na akashe min ita ba.." Ta bashi amsa da dukkan gaskiyar ta da sanyin sauti. Rayyan yace "..akan hakan kk ta fushi dani dama..?" Ya tambaya yana 'dan waro idanu akan ta. Kanta ta 'dauke..cikin sanyin murya me cike da jin haushi tace" cewa fa kayi su kashe min ita, me yasa ba kace ni ba a lkcn? kasan yanda naji cikin zuciya ta ne a daka furta hakan? ji nayi tamkar kaina zai tsage gida biyu Allah kamar raina baya jiki na, da ace sun kashe min ita a wancan ranar da ban san halin da zan iya tsintan kaina ba..." Ta 'karashe maganar hawaye na gangaro mata sosai. Jikin sa sanyi 'kalau yayi, gaba 'daya yaji mutuwar jiki ta ziyarce shi da jin kalaman nata, domin ya fahimci da iya gaskiyar ta take maganar. Tasowa yayi ya zago ta bayan ta ya tsaya yana duban ta sosai. So yake ya janyo ta ya rungume amma baya so ta fassara manufar sa zuwa ga wani abu daban. Hannun sa ya 'dago ya janyo nata da shi zuwa bakin gadon da ya taso sai da ya koma ya zauna sannan a hankali ya shigar da ita cikin jikin sa ya zagaye ta da hannuwan sa. Jin ta cikin jikin sa ya sa ta fara 'ko'karin fita 'kwantan kanta amma ta kasa, a kunne ya ra'da mata " Shiiii...calm down please, u ar still my wife remember..?" Bata fahimci abinda yace 'din ba sam amma haka kawai sai ta ji ranta na raya mata tamkar garga'di yai mata, a fili ta saki ajiyar zuciya tana mai cigaba da 'kara sautin kukan ta. Tsawon mintina biyu suna a hakan tana a jikin sa yana ayyana irin wannan 'kaunar, ganin kamar bazata sarara bane ya sa da sigar rarrashi yace"...i'm sorry..ba nufi na kenan ba kinji...but nasan bazaki ta6a fahimta ta ba? amma in zaki min adalci ki kwatanta da kanki if akace ki za6a tsakanin ni da Mufeedah wa kk ganin zaki za6a..?" Wani kallo ta 'dago tayi masa da ita kanta bata san ma'anar ta ba... Bai damu ba ya 'dan yi guntun murmushi yana duban idanun ta da frawning nd crying face 'din ta yace" I know...na riga na sani...ni bani da wannan darajar in dai a wurin ki ne but yadda zaki ji a zuciyar ki idan za'a rabaki da Mufeedah nima hakan naji koma fiye da naki a lokacin, kuma akan kowanne daga cikin ku ba wai mutum 'daya ba, kawai nabi dacewa ne, na kuma cire son zuciya...i can't afford loosing u both sbd mabambantan matsayi da kuke da shi a wuri na, but a rayuwa akwai cancanta da halacci, sharri kansa ba'a mancewa da shi cikin sauki balle khairin da ka tabbatar domin Allah aka yisa, manufa ta rama khairan ne Zaitoon ba wai dan bana so ko kaunaf Mufeeda ba, nasan ko da na rasa ta Insha Allah watarana zaki haifa min wasu kamar ta...amma ke 'din idan na rasaki shikenan na rasa ki kenan har abada, na rasa wani 6angare ne na rayuwa ta, na kuma yiwa 'ya'ya na hasarar uwar da ta dace...ki fahimce ni ki fahimce ni...." Kawar da kai tayi tana mai share hawayen da ke sau'ko mata, sosai ya 'daure mata kai da kalaman nasa, yayin da ta wani 6angaren ta fahimce shi ta kuma fahimci girma da darajar da take da shi a wurin sa, wanda take kyautata zaton bakomai yasa hakan ba face bautar da tayi masa har yake ikirarin khairan ya kuma so maida mata da takuicin sa ta hanyar bata damar cigaba da rayuwa a dunia, ha'kika ta ji dadin hakan domin ta fahimci shi kansa yasan ta bautu akan sa, duk da domin Allah tayi, amma kayi a yaba maka ma wata sabuwar nasarar ce. Duk da hakan da ta tuno wacce ya za6i akashe hkn bai hana ta turo baki gaba ba, cikin shagwa6ar da bata san ta ina ta fito ba tace" ...ni dai ban ji da'di ba da kace su kashe min 'yata.." " I also felt very bad dana bada wannan za6in amma nasan ban yi kuskure ba.." " Ni dai bana son rasa ta..kar ka sake dan Allah..idan bakwa son ta ai ni ina 'kaunar abu na..." " nd i also luv u..". Yayi maganar yana 'dage gira da wani zazzafan sauti mai shiga zuciya. Da sauri ta sunkuyar da kai tana mai kokarin barin jikin sa amma Rayyan yaki bata dama. 'Karshe zamewa tayi ta kwantar da kanta saman 'kafar sa bata sake magana ba sai ma 6oye fuska da tayi da tafukan hannun ta domin bazata iya cigaba da duban fuskar sa ba. Murmushin mugunta Rayyan yayi, Yana duban fuskar ta a hankali yace" in tambaye ki wani abu....?" Shiru tayi babu amsa. Sai da ya sake maimaitawa kafin ta ce. " Allah yasa nasan amsar...." " Insha Allah ma kin sani idan kuma ke baki sani ba ai bb mai amsani kaf duniyan nan...." " uhumm ina jinka..." Sai da yaja numfashi kafin ya furta. " Ina mahaifin Mufeeda ne...?" " Ya rasu..." " Waye shi toh...?" Da sauri ta cire hannun ta dake kan fuskar ta cike da tsoro, fargaba gami da mamakin tambayar tasa...sau nawa suke so tayi ta amsa musu wannan tambayar ne? Ta tambayi zuciyar ta. Ganin tayi shiru ne yasa shi fadin" Ina jin ki..." " Ai baka san shi ba..."! Ta bashi amsa zuciyar ta na luguden gudu mai tsanani. " Mahaifiyar ta fa...?" Ya sake jefa mata wata tambayar. Shiru Zaitoon tayi tana wawware idanu, daga 'dayan 6angaren, bata san duk yana kallon idanun nata ba. Zaune tayi 'kokarin mi'kewa sai fuskar su ta kusan cin karo da juna... Ido suka tsurawa junan su kowa na kissima abu a aran sa. Rayyan ne ya sake magana inda a hankali ta yadda ita ka'dai dake kusa da shi zata jisa yace..." Baki bani amsar tambaya ta ba..." " Me ma kace...?" Ta sake tambaya tana kawar da idanun ta gami da mikewa zaune ta juya masa baya. " Mahaifiyar Mufeeda..." " Bata da uwar da ta wuce ni ai...". Bayan ta ya tsurawa idanu yana mamakin 'karfin hali irin nata. " Baki ji ba...?" Sai ta 'dan juyo ta kalle shi, tuni ya karanci wasu 6oyayyun abubuwa tun daga sautin muryar ta har zuwa kan fuskar ta. " What I mean is...waye ya haifi Mufeeda...?" 'Kan'kance idanu tayi sosai a 'kokarin ta na ganin ta hana hawayen ta saukowa. Sam yau bata san meke damun Rayyan ba...wannan wasu irin tambayoyi ne haka yake damun ta akan su. Duk yadda taso dai-daita sautin muryar ta abun yaci tura..dole da rawar murya ta amsa shi da fadin. " Gani...nice mana, Mufeeda bata da wata mahaifiyar ai baya ga ni...." Gira ya 'dage sama ya 'dan ja jikin sa baya.." Ohh really ...?" Ta jinjina kai alamun tabbatarwa. " Ni nasani..na san ba kece kika haife ta kuma ke kanki kinsani right..?" Tayi shiru. " Zaitoon...kalle ni.." Rintse idanu tayi da sauri. Taya ma zai wani ce ta kalle shi salon duk ya 'kure mata 'karyar ta ko mene? Me ma ruwan sa da 'diyar ta balle mahaifiyar ta..?" Fahimtar da yayi cewar bazata kalle shin ba ya sanya shi cigaba da magana. " Zaitoon..ina so a yau, kuma ayanzu ki sake fahimtar da ni...ki fa'da min duk wata gaskiyar da kika jima kina 6oyewa, rayuwa bata ta6a tafiya bisa tsarin da ke kika 'dora taki rayuwar akai..akwai kuskure babba bayan 'kalubale akwai kasada...idan kuma baki shirya fa'din komai ba ni nan shirye nake da in tunasar da ke omai, baki na bazai min ciwo ba, zuciya ta bazata 'kuntata ba kamar yadda na tabbatar bazata ta6a raunata dan na fadi abinda ke raina ba, sai dai za ta rayu cikin farin ciki, farin cikin da nake fatan ya kasance na har abada daga yanzu da zan sanar dake cewa Aishatul Mufeeda jini nace, nine mahaifin Mufeeda kamar yadda Matata ta kasance mahaifiya ta hakika awajen ta har zuwa lokacin da zan tabbatar miki da hakan a zahiri....."! A wani firgice Zaitoon ta mike hadda ja baya tana 'kare masa kallo gami da waro idanu tana nuna sa da yatsan ta...yadda tayin ga wanda bai sani ba zai 'dauka wani abin tsoro ta gani. Bakin ta na rawa sosai tama.kasa furta komai, tana so tayi magana amma harshen ta sai yayi mata nauyi...da 'kyar ta harha'da kalmomi 'kalilan ta iya bayyana su saman la66an ta...tace " Kai kuma...Mufeeda ta fa kace..?" " Yes..ni 'din dai..." Ya fadi yana mai sake jinjina mata kansa yana kum murmushi 'kasa 'kasa. Sosai ya karamci firgici da tsoron ta saman fuskar ta. Wani hawaye ne ya gangaro mata shar da gudun su. Da sauri ta juya baya tana mai 'dauke hawayen da 'dan yatsanta amma a banza kamar ana tunku'do su ne. Da muryar kuka batare da waigo ba ta fara fa'din. " Bana son irin wasan nan dan Allah....". " Ke kanki shaida ce Zaitoon wasa 'daya tak nake mk a kaf 'din zama na dake...wannan ba ya cikin jerin abubuwan da zan iya wasa akan su da gasken gaske nake miki magana, da kuma iya gaskia ta..." Shafo kanta tayi daga gaba zuwa baya, sai kuma.ta 'daura hannu aka take ta kuma sauke shi...a hankali ta girgiza kanta hakan bai mata, sai ta sake girgizawa da karfi wai ko zata farka daga baccin da take yi abanza,...sake mintsinin saman hannun ta tayi still Rayyan take gani yana kuma duban ta yake yana jiran amsar ta duk cikin yanayi guda, yanayin da ya kasance iri guda da wanda yake mata maganar, idan kuma ba 'karya idanuwa da kunnuwan ta ke mata ba, Rayyan ne! Rayyan ne ke cewa mufeedan ta 'diyar sa ce, mufeedan ta jinin sa ne, Mufeedan ta 'diyar sa ce da matar sa ta haifa masa...." Kusa da shi ta matso ta shafa fuskar sa nan ta tabbatar shi'din ne dai ba wai gizo ba ba kuma mafarki ba..." Mintsine ni dan Allah ko zan farka..." Tace da shi with serious tune tana mai mika masa hannun ta. Maganar ta sai ma ta bashi daria, gefe guda kuma tausayin ta bashi sosai, hakika dole abin yai mata bazata domin baya tunanin ta ta6a kawo faruwar hakan cikin ranta, dama ba yau yasan mashirmaciya bace Zaitoon..amma shirmen yau 'din tausayin ta ya dasa masa a zuciya. Bai yi yadda tace 'din ba sai ma ziro 'kafafun sa da yayi zuwa 'kasa. " Baki yadda ba ko..?" Shiru tayi tana duban sa sosai, ashe tayi wauta sosai, meyasa tun farkon fari bata hasaso faruwar irin ranar nan ba, tunani take yi cikin ranta, ta jima tana ganin kamannin wasu 'dai'daikun halittu tsakanin Mufeeda da shi sannan wannan ba'kin da take gani a gefen cikin sa tasan irin na Mufeeda ne, amma ai babu yadda Allah baya ikon sa, taya kai tsaye zai wani fito yace Mufee 'diyar sa ce batare da wata hujja ba, meyasa tun farko bai fadi hakan ba sai yanzu, sai da yaga 'diyar ta ta zama mutun sannan zai shigo da wani zance na daban, wa ma ya ce masa ba itace ta haifi Mufeeda ba da har zai ce 'diyar sace..?" Kar dai wayo zai mata ya 'kwace mata yarinya. Hawaye ne ya sakko mata...shar shar. Tana shirin share hawayen ya rike hannun ta. Kai ya girgiza mata idanun sa cikin nata. " Kiyi kuka kinji, kiyi kuka bazan hana ki ba kema bana so ki na hana kanki, kiyi kuka ki 'koshi har sai kokonto da tararradi ya bar ranki domin zance na babu gyara..magana ta hakikan ce...kuma yanzun nan zan tabbatar miki da hakan. Hannun ta da ya kama yaja yayi gaba dole ta bishi a baya can 'dakin ta suka koma dake nan 6angaren Ammi. Da shigar su 'dakin nata ya saki hannun ta. Wancan drawer da kayan Nadia ke ciki ya lalu6o key ya bu'de ya ciro duk kayan da ke ciki. Da6as ta zauna gaban tarin kayan sakamakon hango. wani hoton da tayi. Hannu tasa da rawar jiki ta ciro shi tana mai goge jikin sa ta 'kura masa idanu. A hankali hawayen ta ya cigaba da sakkowa tana shafa saman hoton... Rayyan idanu ya 'kura mata yana lura da yanayin ta sosai, akwai rudani rikici gami fargaba gami da tsoro duk tattare da ita a halin yanzu, hakan kuwa shi ke sake alamta masa dakwai wani abu da bata san tunowa da shi, sannan akwai wani abu da bata so kuma bata shirya faruwar sa ba a halin yanzu.... Kai Zaitoon ta fara girgizawa tana kuka take kallon sa. " Ya akayi...?" Rayyan ya tambaye ta yana mai matsowa kusa da ita. Kai tayi saurin girgizawa tana fa'din" ba Komai..." " Kukan fa...?" Baya ta 'kara ja da sauri tana fa'din..." Wannan matar..! Na santa fa...wallahi nasan matar jikin wannan hoton...?" Wani sanyi yaji har zuciyar sa. A fili ya saji ajiyar zuciya. Dad'in yarinta kenan babu 'karya a lamarin su. Yana duban fuskar ta yace " Mata tace ita..I mean itace matata ta farko....". Baki Zaitoon ta toshe da hannun ta 'daya tana duban fuskar sa sosai. Gani yayi tamkar bata yadda da zancen sa ba duk da kuwa ya fahimci ru'dani ta shiga. Hakan yasa ya lalu6o hotunan Nadia da yawa ya zube a gaban ta. Zaitoon kam banda hawaye babu abinda take yi tana ''da'd'daga hotunan a ru'de. Gani take tamkar cikin mafarki take ganin hoton Hajia a fa'dar ta. Ko da ya sake yin hakan ma gani yayi still bata yadda cewar matar sa ce ba, hoton sa dana matar ya sake nuna mata na lkcn auren su da bayan auren da kuma wanda suka yi su uku hadda Amrah, duk yaga alamun bata yadda ba har a lkcn, photunan su wanda tun suna makaranta yata nuna mata dake cikin wayar sa harda ma wanda yy ta mata lokacin da take da tsohon cikin ta kafin ta rasu, wasu pic din tare suka yi da shi, wani kuma a bedroom 'din sa ne bata gane kayan cikin dakin ba dan ba wannan gidan bane.. Kuka ta sanya sosai ta tana mai toshe bakin ta, da gudu ta tashi ta kama hanyar waje sai kuma ta sake dawowa ta kwashi pics 'din da gudu ta nufi wajen Ammi dake can saman ta da su tana kuka ta zube agaban ta, shima da ya biyo bayan ta tsayawa yy hankalin sa a matu'kar tashe domin da farko bai san ina ta nufa ba. Ita kanta Ammin sun bata tsoro a yanayin da suka shigo mata..." A a laifia nagan ku haka...?" Tayi maganar tana 'kare musu kallo. Rayyan bai ce komai ba illah takawa da yayi kusa da Ammi ya zauna yana sakin numfashi. " Ammi kalli ki gaya min dan Allah wacece wannan?" tana kuka ta tambayi Ammin tana nuna mata photon dake hannun ta, su biyu ne jikin photon ma enlergement mai kyau da aka yi, gefen ta Rayyan ne suna dariya aka dauki photon. Ammi kam jikin ta sanyi 'kalau yayi, kallon photon tayi ta 'dago shi sannan ta 'dago ta sau'ke idanun ta akan Rayyan da yake can tsaye. Jinjina mata kai yy alamun ta sanar da ita...Ammi ita duk zaton ta kishi ne ya sa Zaitoon irin wannan rikicewan...bata 'karasa tunanin ta ba taji muryar Zaitoon na sake fa'din" Ammi dan Allah kar ki 6oye min ki fada min komai..." Ta 'karashe da shasheqa. " Ki kwantar da hankalin ki Zaitoon, ki nutsu ki share hawayen ki sai na sanar dake duk abinda kk son ji yanzu". Kallon Rayyan tayi tace " Babana sam baka jin magana, me yasa zaka tunzura ta har batun Nadia ya shigo bacin kasan bama ta raye...shi kishi bb inda baya ratsawa ..." " Hannuwan sa duk biyu ya 'dagawa Ammin yace" Ba batun ba kenan fa Ammi ni babu ruwa na...gaskia kawai na fa'da mata, kuma ai ko hauka nk kinsan bazan aikata abinda kike tunani ba Ammi.." Ga Zaitoon Ammi ta dawo da kallon ta sannan tace" Kinga wannan da kike gani gefen san ko..matar sa ce.. wacce suka yi makaranta tare bayan sun gama sai suka yi aure, ita ta kasance za6in sa ne Amrah kuwa za6in mahaifin sa ne... Amma Nadia ta da'de da rasuwa kusan shakaru uku kenan yanzu..." Da sauri Zaitoon ta jefa mata tabayar " Ammi a ina ta rasu dan Allah..?" Hawaye Ammi ta share da ya ziraro mata tuno wace Nadia tace" Nadia ta rasu ne acan Jahar Borni can wani 'kauye da ni kaina bazan iya tuna sunan shi ba, ganin iyayen ta taje tsautsayi ya rutsa da ita har ta rasa ranta ita da abinda ta haifa..." Hawaye sosai Ammi ta share sannan ta cigaba da fa'din" Nadia mutunce harda 'kari Zaitoon, ni kaina na shaidi halin ta wanda sai daga bayan auren su ma naga rashin amfanin sashi ya auri Amrah da muka yi tun farko, domin Nadia ta cike duk wani gurbi da ya kamata ace mace ta gari ta cike shi a gidan mijin ta..Ina da tabbaci ko da ace tana raye ya aure ki Nadia bazata taba 'kalubalantar ki ko kishi da ke ba balle ace ma bata numfashi..." " hmm Allah sarki, Nadia ta tafi mana da duk wani buri da farin cikin mu, ta tafi da tsohon cikin ta da haihuwar sa zai iya kamawa a koda yaushe amma ajali ya riga ya 'kira ta hakan yasa duk yadda aka so fahimtar da ita abin bai yi tsari ba bata saurare mu ba, muna ji muna gani ta tafi tafiyar kwana 'daya tayi amma 'karshe hotunan gawar ta ne cikin mummunan yanayi ya dawo mana gare mu..." Kuka sosai Ammi ta sanya hk Zaitun ma da tuni ta ta rarrafo ta rungume 'kafar Ammin tana kuka. Cikin kukan tace" kiyi ha'kuri, ki bar kukan nan dan Allah ki warware min komai, wacce ta bani amanar Mufeeda sunan ta Nadia Ammi, tace min ita 'yar Kano amma ban san ina take nufi a Kano ba, Ammi kiyi saurin fahimtar dani cewa Feefy na babban matsayi ne da ita ban sani ba, Ammi ki gaya min menene silar mutuwan Nadian ku dan Allah..." " Harbi Zaitoon...Harbin ta akayi daga ita har yaron da ta haifa...nayi kuka sosai, nayi kuka fili da zucia domin Nadia ta kasance ne abin alfahari, dole ayi kukan rashin ta, bacin haka ma sosai gidan nan muke da kishirwar yara da Allah ya bata kuma sai ya kar6i abinsa nan take batare da mu ya nufe mu da ko da kallon abinda ta haifa ba..." Dukkan su kuka suke yi...sosai amma Banda Rayyan, sai shi kansa idan ka dube shi zaka fahimci baya cikin yanayi mai da'di, tuno abubuwa da dama yake yi, hawayen ma ji yayi yana shirin zubo masa sai dai bai bar hakan ya faru ba...gaban su ya 'karaso zai yi magana Zaitoon ta riga shi da fa'din. " Ammi ki kwantar da hankalin ki indai wannan ta jikin hoton ita ce Nadian ku to ina tabbatar miki da cewar har yanzu jinin Nadia na tare da ke Ammi... domin Mufee na 'diyar ta ce, itace ta bani amanar ta...."! Cak kukan Ammi ya tsaya ta 'dan ja baya ka'dan nan take wani mugun tunani ya 'dar su aranta..kar dai Zaitoon ma irin mutanen nan ne masu 'karya da sunan yaro dan kawai su ci dukiya...tasan akwai mazanbata da yawa akwai macuta, akwai maha'inta amma bata sako Zaitoon cikin su ba. Zaitoon kam ganin irin kallon da Ammi take yi mata ya sanya ta jinjina mata kai tana share hawaye tace" Ba batun wasa Ammi, kuma kinsan bazan yi mk 'karya ba..." Hannu Ammi tayi saurin 'daga mata tana.kawar da kai cikin zazzafan yanayi ta daka mata tsawa. " Ya ishe ni haka nan dan Allah, basai kin bayyana min ba nasan me kk so yanzu, yanzu ne na fahimci asali wacece ke, yanzu ne na fahimci manufar ki na zama tare da mu, yanzu ne na fahimci fuska biyu gare ki Zaitoon..." Rayyan ne yayi saurin zama gefen Ammi ya 'dan kwantar da kansa saman kafa'dar ta da alamun son kwantar mata da hankali. Ita kuwa Ammi nuna Zaitoon tayi da har yanzu take goge fuksar ta tace" Rayyan kana jin me wannan yarinyar take fa'da kuwa...". " Naji Ammi...ki kwantar da hankalin ki..zaki fahimci komai yanzu..." Zaitoon kam gyara zama tayi sosai tana duban Ammi tace" Ammi yau zan gaya mk abinda zai baki mamaki, yau zan gaya mk asali wace ce ni, yau zan sanar miki asalin labari na da na jima ina 6oye mk Ammi..... Salmerh😘 [11/12/2022, 4:28 am] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Wattpad@* _Serlmerh-md_ 🅿️ *...81* ........Shigowan Marwa da Anty Marwa ne ya dakatar da maganar da Zaitoon ke yi, sakamakon ji da tayi ko sallaman Marwan an rasa mai amsawa a cikin su sbd yadda suka bada dukkan hankalin su gareta. Saman la66a ta amsa sallamar tana mai waigawa ta dubi Marwa. Idanu Marwa ta waro ganin yanayin Zaitoon da hannuwa tayi mata alamun tambaya.." Lafiya..me ya faru kuma...?" Hankalin Both Ammi da Rayyan ma kanta suka koma sbd ganin Zaitoon ta mayar da hankali wajen ta. Kafin su 'dauke idanun su daga kan Marwa sai wata sallamar suka sake tsinkaya ciki- ciki da wata sautin muryar da suka tabbatar da cewa ba sabuwa take a wajen su ba. Kusan dukkan su atare suka raya sunan ta cikin zu'katan su amma ko 'daya babu wanda ya nuna alamun farin ciki da ganin ta har ta 'karaso ciki ta samu waje ta zauna. Sai lokacin Ammi ta budi baki tace..." Amrah..! daga ina haka...?" " Daga gida muke Ammi munzo..." Bata ma bari Amrah ta kai aya ba ta jinjina kai gami da fadin..." Sannun ku toh...ya wajen su Mummyn naki...?" " Suna nan lafia.." " Haka ake so...". Duk wannan maganar Rayyan ko sau 'daya bai dubi inda suke ba balle ya nuna alamun yasan da zuwan su, Marwa kuwa tuni ta 'karasa kusa da Zaitoon 'kasa 'kasa tayi mata ra'da a kunne.." Dan Allah me ya faru..naga fuskar ki da hawaye...?" Zaitoon bata ce da ita 'kala ba illah juya idanu da tayi ta dubi gaban ta hakan yasa Marwa ma ta kai duban ta wajen. Dabas ta zauna yanayin na sauyawa izuwa na alhini ta kai hannu ta 'dago hoto 'daya..saman la66a ta furta" Anty Nadia...!" Muryar Amrah ne ya hana Marwa cigaba da magana jin tana mi'kawa Rayyan gaisuwa hadda mikewa ta isa wajen sa tana mai mi'ka masa yaron dake hannun ta. Rayyan sam bai iya bude baki ya amsa gaisuwar da take yi masan ba sbd tsananin mamakin ta. Wai yau Amrah haka ko kuwa idanun sa ke yi masa gizo. Sai yanzu ne ta san da cewar yana da muhimman ci? Bayan sun gama lalaceqar su da Sultan hadda binsa tafia wata 'kasa ta barshi kwance cikin jinya..bata damu ba, bata damu da ko ya mutu ko ya rayu ba sai yanzun da ta tabbatar ya warke shine ya zama mutun ko...?" Kallon ta yayi ya kuma duban yaron, jikin su fresh sun yi kyau sosai amma kokadan bai ji dai dai da kwayar zarra na kewar su ko farin ciki da zuwan su ba. Kan yaron ya tsayar da duban sa take yaji wani murmushi na shirin 'kwace masa, bai kuma hana faruwar hakan ba, domin bai ga aibun sa ba idan yayin...cikin ransa ya jinjina wannan iko na rabbiz izzati, yaron bai bar komai na Sultan ba sai ma kamannin su da ya 'kara fitowa. Alamu yayi wa Amrah da cewar hannun sa baya aiki balle ya kar6e shi sai ta 'dan nuna jimami saman fuskar ta tana shirin magana tajiyo hayaniya na tunkaro palorn saman Ammin da 'dan gudu gudu. Badi'a ce ta shigo, bayan ta Mufeeda ce sai Imran daga 'karshe. Yayin da sautin muryar Anty Madeena daga bayan su tana tahowa take yi musu masifar rashin natsuwa.." Ke de Badi'a ban san lkcn da zaki girma ba wlh...". " Wallahi Anty itama rigima gareta wai fa sai na goya ta kuma nawi gare ta yanzu...". Badi'an ta fa'da tana mai 'kara hanzari zuwa saman...tace" Mutum sai shegen son jikin tsiya..." Anty Madeena ce tace" Daina zagar min ita..ai duk laifin ki ne, ba ke kk koya mata ba kuma sai yanzu ki wani ce zaki guje mata...?" Sallamar da Badi'a tayi ya hana ta sake tanka maganar kasantuwar itace a farko, Imran yayi jin haka yasa Mufeeda ma yin sallamar. Ba su dake zaune cikin 'dakin ba hatta da Anty Madeena dake bayan su sai da ta murmusa da jin muryar Mufeeda na sallama...in ka 'dauke Amra kadai da tun farko ta tsani yarinyar. Yanzu ma abinda ya dawo da ita gida shine kan batun auren su, so take ya sawwakewa Zaitoon tunda ya samu sau'ki domin ita bazata iya cigaba da ha'da miji da 'yar aikin ta ba. Murmushin Zaitoon yafi na kowa fa'da'da jin muryar sahibar ta da sauri ta waigo suka ha'de idanu. " Mammi...."! Mufeeda tace tana mai tahowa wajen ta da gudu. Zaitoon kuwa ta bu'de mata hannuwa tana murmushi hawayen da bata san na menene ba yana sakko mata. Da gudu Mufee ta fada jikin ta suka rungume juna. Dai dai da 'karasowar Anty Madeena ciki. Idanun ta cak akan su a fili ta furta" rai yaga rai kenan.." Sannan ta 'dora da sallama. Maganar farko da tayin da kuma sallamar da Mufeeda tayi 'dazun shi yasa fuskar kowa ta kasance cikin fara'a da annashuwa. Har aka gama gaishe gaishe...Anty Madeena ke zolayar Badi'a da fa'din" Kina mata rowar hawa bayan ki..toh yau ga ta ga wacce bata gajia da goya ta ko da kuwa yini zata yi bayan ta..." " Ta66in...da wannan nawin nata, ai banajin ko Anrmty Zaitoon din ma zata iya kamar da..yarinya duk ta zama 'katuwa da ita...". " Tabarakallah masha Allah..." Anty Madeena tace cike da jin da'di. Amrah dai sai rarraba idanuwa take, sai taji zaman ya gundure ta anan, ko da ta mike dan wucewa sashen ta kuwa Ammi ta dakatar da ita da fa'din ta zauna magana zasu yi. A kunne Zaitoon ta ra'dawa yarinyar.." Baki gaida Ammi da Abty Marwa ba, ga can Abba ma yana kallon ki wai gaida shi ba..." Duban Abban Mufee tayi suka ha'de idanu tana no'ke kafa'da gami da ha'de ranta. Duk da bai san dalili ba amma sai da yayi murmushi ya kuma kasa 'dauke idanu akanta, da gaske wannan 'diyar sa ce ko kuwa akwai sauran bayani agaba. Baya fatan jin wani bayani sa6anin wanda ya fara tararwa wajen binciken sa ya bayyana, abinda kawai yake son ji yanzu daga bakin Zaitoon ne ka'dai. Cikin ransa yake raya abinda Zaitoon tace da yarinyar da har ta dube shi...amma ya kasa samun abinda zai cike masa gurbin maganar ta su...kowanne ya kiyasta sai yaga bai hau dai dai ba. " Kishiya ta babu gaisuwa ne...?" Ammi tace tana mi'kawa Mufeeda hannuwa. Tayi kyau sosai cikin shigan ta akayi mata kamar wata 'diyar 'yan gayu..dama Mufee ba dai kyau ba aka kuma dace da samun kula sosai kyanta ya kara fitowa jikin ta ya murje sosai. Abin da yasa kenan Zaitoon bata ta6a bakin ciki ko.da Mufee zata yi fin sati gidan Anty Madeena domin tasan ana bata kula yadda ya dace, ba wani ke sanar da ita ba face tsabar saka idanu da kulawa da take bata ya sa take fahimta daga yanayin yarinyar idan ta dawo. Sai da Zaitoon ta lalla6a ta kafin ta tafi wajen Ammi dan ta ki barin jikin ta tunda suka shigo. Saman cinya Ammi ta 'daura ta tana yi mata wasa. Abin ya sosa ran Amra sosai, domin ita tun shigiwar ta babu wanda ya ko.nuna alamun yana son 'daukan Arfan balle har a 'dauke san..ban dama wata bakar harara kasa kasa da take fuskan ta daga wasun su da nuna halin ko in kula da akayi da su. Amma fa ji wannan, ko da yake ta san Arfan da jinin.su bane amma ai tunda ba sanin gaskiyar zancen suka yi ba bai kamata su yi banza da shi har haka. Shiyasa tun farko ta zige Rayyan dan ganin an kawar da su a gidan amma hakan bai samu ba, ta zige mahaifiyar ta ta kuma yi barazana da auren ta duk dan sun bar gidan amma a banza. 'Karshe Sultan ta hurawa wuta akan su, sai dai shima 'din bata ga abin kirki da ya tsinana ba tunda har yanzun dai gasu nan duk araye cikin gidan kuma cikin 'koshin lafiyar su. Baki ta tura ta wani ha'de rai sosai bata sake yadda ta dubi inda suke ba sbd takaici. Cikin.ranta ta ayyana cewar tunda sun kasa da kaina zan dauki mataki, bazai yiyu in zauna wata banza ta kwace matsayin da ya dace 'dana ne ya kasance akan ta ba sam. Sai da Ammi ta gama yiwa Mufeeda wasa tana 'yar daria ta mikawa Marwa ita tana mai mayar da duban ta ga Zaitoon tace..." Zaitoon bismillah muna sauraren ki..."! Wata ajiyar zuciya 'kakkarfa Rayyan ya sau'ke yana mai lumshe idanu tun 'dazun abinda yake jiran ji kenan baya ga haka mai zai zaunar da shi cikin hayaniyar nan tasu da tuni ya cikawa tayar sa iska yayi gaba, amma sam ji yayi bazai iya ba, ji yake idan ya tafi tamkar ya 6antari wani 6ari ne daga cikin abinda yake son ji daga bakin ta, yafi so da bukatar ayi komai kan idanun sa..da kunnuwan sa yake son jin komai ba maimaici ba, ba kuma a bashi labari ba. Kunnuwa ya baza yana fatan yaji kyakkyawa, yana fatan yaji komai kamar yadda yake tsammani, yana fatan abinda Zaitoon zata fa'da ya kasance masa tabbaci ne akan cewa Mufeeda 'diyar sa ce babu wani kokonto. Shiru 'dakin ya 'dauka jin abinda Ammi ta fa'da, idan ka 'dauke Marwa, Rayyan da Ammin babu wanda yasan kan maganar Ammin amma da jin sunan wanda ta ambata yasa duk hankalin su ya dawo gare ta. Zaitoon kam duban Mufeeda tayi dake kan cinyar Marwa ta tsura mata idanu tunanin can can baya na dawo mata daki daki, tamkar yau ne abin ya faru, tamkar yanzu ne yake ya faruwa...hakika badan da idabuwan ta taga hotunan Nadia tarecda su ba babu abinda zai sata fasa wannan sirimrin gare su, amma a yanzu bata da wani hujjar 6oyewa, bata da wani hujjar hana su jin abinda ya faru tunda ta sani sun kuma san ta sani 'din.. abinda kawai ta kasa raba ranta da shi shine tsananin mamaki, idan akace abinda ta fara sanar da Ammi 'dazun ya kasance hakan ne meyasa tun farko bata gane ba, meyasa duk cikin su babu wanda ya gane sai yanzu..? Tausayin kanta ne taji ya kamata, tausayin halin da zata iya shiga tun ma kafin ya riske ta, domin tasan ayau 'din nan wani abu babba, gagarumi na tunkaro ta ne, wani abu da bata san ta sigar da zai iya zuwa ba, ta iya yiyuwa bakin ta ya furta abinda zai zam mata hujja wajen hukunta ta kan abinda tayi, kan son zuciyar da ta yi abaya...sai dai sam bazata fasa ba, ayau ta riga ta 'dauri aniya, ta 'dauri aniyar bayyana musu sirrin dake tsakanin ta da Mufeeda domin tasan 'kage suke suji, tasan ayanzu basu da wata bukata sama da hakan. Idanu ta lumshe wani zazzafan hawaye ya gangaro mata..batare da ta bude idanun ba ta 'daura da fa'din..... Salmerh😘 [24/12/2022, 11:00 am] Zee Ingawa: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Wattpad@* _Serlmerh-md_ 🅿️ *...82* ......" Asalin suna na shine Zaitoon Ahmad Kyari, 'yar asalin jahar Borno ce ni cikin 'kabilar Barebari, mahaifi na kanuri ne na asali dake zaune a wani 'kauye ne dake 'kar'kashin wata 'karamar hukuma acan jahar ta Borno, yayin da mahaifiya ta ta kasance bafulatana ce usul sai dai bazan iya fa'din asalin 'yar wani yanki bace ita. Tun tasowa ta na budi ido da ganin mata biyu a gidan mu wato matan mahaifi na, Iyami itace babba sai mahaifiya ta da ta kasance biyu. Mu biyar ne a wajen mahaifin mu, Yah Bukar shine babba sai mai bi masa Yaagana ( Zahra) sai Muhammad ( Goni) sai ni Zaitoon, autar mu itace Khausar..Duk 'yan uwana guda hu'dun nan sun kasance 'ya'yan da Iyami ta haifa ne, ni kuwa tilo mahaifiya ta ta haife ni a gidan daka kaina Allah bai sake bata wani haihuwar ba. Yah Bukar yana da mata 'daya mai Azeema da yaran sa biyu Ummaru da Haneefa ( Aisha)..sai Yaaganan mu dake aure a nan cikin garin itama tana da yaran ta uku. Duk da yake ni kadaice gaban mahaifiya ta amma hakan bai sa na taso cikin kula da gata yadda ya dace ba sakamakon tsangwama, rashin sukuni da kwanciyar hankali da Innata ke fuskan ta a gidan har nima ya shafe ni. ***** Shesh- she'kan kukan da kunnuwan sa suka fara cin karo da shine ya 'dauki hankalin sa da shigowar sa gidan kenan, mahaifiyar sa yake gaidawa amma hankalin sa da idanuwan sa na ga 'kofar 'dakin da yake jiyo kukan duk ya 'kagu ya shiga yaji abinda ya sani kuka yau kuma da wannan farar safiyar. Tsaye ya mi'ke fuskar sa cike da alamun tsantsan damuwa yake fa'din" Iyami yau kuma me ya samu Zaituna da sassafen nan take kuka?" Baki Iyami ta kya6e gami da komawa tana fiffita wutan da take hurawa a tsakar gidan na abin karin safe...'kasa- 'kasa cike da jin haushi tace " Wannan kuma sai ka isa gare ta kunnan ka ya jiye maka ai...tunda ni banyi darajar a zo a sanar da ni abinda ke faruwa ba dan munafurci sai dai a zauna a kukan 'karya..." Bai damu da kalaman Iyamin ba sbd ba yau yasan halin ta ba, da hanzari ya juya ya nufi 'kofar dan duk hankalin sa tashe yake jin sa dan ma na tsagaita kukan tun lokacin da na tsinkayo muryar sa... Tsaye yake daga bakin 'kofan 'dakin ri'ke da labile yake duba na cike da tausayi da alamun tambaya saman fuskar sa. Ganin hakan yasa nayi 'kasa da kaina ina mai share hawayen dake bin kunci na suka kuma kasa tsayawa. " Hamma Bukar barka da safiya.." Bai amsa ba sai ma tambaya da ya jefe ni da shi" 'Kanwa ta me ya saki kuka kuma da safiyan nan haka..ko yunwa ce..?" Madadin in bashi amsar tambayar sa, a a sai ma wani kukan da ya kufce min mai karya zuciya. Sosai jikin sa yayi sanyi a hankali ya saki labilen gami da 'karasowa ciki bayan ya zame takalman 'kafafun sa. Gaba na ya 'karaso ya dur'kusa da sanyin murya mai tafe da kulawa cikin yaran kanuri yace dani" Baki da lafiya ne...?" Ina kukan na girgiza masa kaina alamar a a batare da na dubi idanun sa ba. " To menene?" Ya sake tambaya ta da kulawa sai de har yanzun ban iya na bashi amsar tamabayar sa ba kuka na kawai nake yi mai sanyin sauti gwanin ban tausayi...da Hijabin da ke kaina na rufe fuska ta nake kuma share hawayen da shi. Shiru yayi yana sauraron kukan nawa tsawon da'ki'ku sai yama rasa kalmar 'daurawa, har cikin zuciyar sa yake jin kukan nan domin na kasance mafi soyuwa a zuciyar sa duk cikin 'kannan sa gaba 'daya. Shakuwar ta daban ne, kamar yadda Yah Bukar ya kasance na daban cikin dukkan yayye na. Sam baya so ya sako sunan mahaifiyar sa cikin maganar duk da yana iya zargin makadmsudin kukan daga wajen ta ne, amma yana iya raba zargin nasa zuwa gida biyu musamman da yasan cewa da wannan safiyar mawuyaci ne ace wani abu ya ha'da mu domin rayuwar gidan kaf cikin tafin hannun sa yake...sanin hakan da yayi yasa shi tafiyar da zargin sa izuwa 6angaren zargin sa na biyu. Sosai ya rage sautin muryar sa ya 'kira suna na da sautin da ni kaina nasan cewa mai kauna da kulawa agare ka ne kadai yk da lkcn yi mk irin ta. Kaina na 'dago hawayen na sake gangarowa saman fuskar sa na sauke idanu na da fatan ya fahimci damuwa ta ba sai na kai ga furtawa ba. Cikin sa'a kuwa da ha'da idanun mu ya jefa min tambayar da ita nafi bukatar jin ya furta fiye da komai. " Yau ma kinyi mafarkin ne?" Ya tambaye ni da dukkan kulawa gami da tausayi na. Wannan karon da sauri na 'dage kaina alamar " Erh". Kai ya 'dan girgiza alamar damuwa domin sosai hakan ya bayyana kan fuskar sa. " Kin sanar da Iyami ne?" Kai na sake girgiza masa alamar a a. Ajiyar numafshi ya sauke yana mai dauke duban sa daga kaina yace. " Toh shikenan ki bar kukan nan haka, kuma bana so ki sake gayawa kowa idan kinyi mafarkin kin ji?" Da kaina na sake bashi amsa alamar to. Shi kuma ya cigaba " Abin nima ya fara bani tsoro amma Insha Allahu zan yi magana da Baffa Liman inji ko akwai wani dalilin hakan..in akwai nasan bazai rasa mafitar da zai bamu ba da iznin Allah zaki daina kinji...?" Kai na sake 'dagawa sama cike da gamsywa da bayanan sa, domin sarai nasan halin 'dan uwa na, afa'da ne a cika bai fiya magana biyu kan abu guda ba musamman kan abinda ya shafe ni baya sanya da shi. A wancan ga6ar kuma ni kaina na gaji so nake a sama min mafita bata komai ba kuma sai ta yadda zan daina wannan mafarkin mai rikitarwa. Magamar Yah Bukar ce ta dakatar da tunani na" to maza share hawayen ki fito kiyi abinda ya kamata kuma kar ki fa'dawa kowa kinji...wata'kila wani abin ne daban da bamu sani ba amma Insha Allahu Alkhairi ne zai biyo ba domin shi muke data ko wani lkc ko..'kanwa ta?" Da sauri na 'dage kaina ina mai jin dadin kalaman sa gami da goge fuska ta kamar yadda ya bukata. Tsaye ya mike..." Bari naje..zan dawo anjima watakila Yayi maganar yana mai barin 'dakin nawa. Mintina 'kalilan bayan fitar sa na 'dauka zaune a 'dakin ganin yawan tunanin ba zai min ba yawa kawai na fito cikin gida. Iyami dake tsakar gidan baki ta kya6e tana juya kanta tace" Ai na 'dauka jira na kike yi in shigo 'dakin in tuna miki ayyukan da zaki yi...banda shashanci sabon abu ne ko kuwa yau ne farau da zaki wani zauna kina rusawa mutane kuka a 'daki sai kace uwar ki ce akace ta mutu..?" Haka Iyami ta dinga sababi tana kan ayyukan ta. Ni dai ban ce komai ba na wuce na 'dauki tsintsiya na fara share tsakar gidan ina hawaye, lokaci- lokaci kuma nake kama bakin hijabi na nake dauke hawayen... Iyami kuwa har lkcn bata bar 'kananun mita ba zaune gaban murhu tana gyara itacen da ke cikin wuta. Haka na gama sharan na 'dauki bokiti na nufi rijiyan mu dake hanyar fita dan jan ruwa, duk jikina da rauni domin mafarkin nawa na matu'kar tsayawa arai na sosai idan na yishi, kuma yaki barin tunani na sosai yake bani tsoro. Ganin hakan yasa Iyami bina da kallo tana dubana da sakakken baki tace" Wai yau ma 'din da hijabin gadon naki zakiyi 'diban ruwan?" " Iyami zan tattare fa kuma ma ai bai takura ni ba....." Nayi maganar ina mai 'dan tura baki gami da sunkuyar da kaina dan cigaba da abinda ke gaba na. Juyawa Iyami tayi tana fifita wuta da mafici tace" Ke kika sani ai...kullum 'kunsun-'kunsun cikin hijabi kamar wata limamiya, ko matan wan ubanki da suke Matan limaman ma ba haka naga suke yi ba sai ke..." Ni dai ban 'kara fa'din komai ba kawai na cigaba da abinda ke gaba na. Jajayen randunan ruwa dake tsakar gidan wanda duk suka koma wasu kala sun kokko'de saboda jimawa, 'dayan ma bakin sa a 6algace ko wani irin marfi baya iya rufe shi a hakan duk sai da na cika su da ruwa dake yauvdin ba wani karfi nake jina sosai aciki ba ya sa duk aikin da sanyi nake yin sa. Bokitin na cika na ajiye a gefe inda naga an tara kwanikan wanke-wanke na fara wanke su har a lokacin kuma idanuna hawaye suke yi basu tsaya ba. Iyami kam ko kallo ban ishe ta ba balle in samu arzi'kin nuna tausayi ko kulawa. Sai da na kammala wanke- wanken kafin na wuce 'daki na taso su Khausar da Ummariri dake bacci cikin 'dakin Iyami. Nan na kama Ummariri na wanke masa idanu yana ta muzurai da alamu baccin bai gama barin idanun sa ba..sai da na wanke masa idanun da kyau sannan nace yy alwala. Khausar kam buta ta 'dauka ta wuce bayi tun Ina tsayuwar Kiran fitowar ta har na gani na kama wani aikin inayi Amma duk da hakan ta 'dan 'dauki lokaci kafin ta fito tana 'kwa'kule hancin ta. Ganin hakan yasa nayi kwafa gami da fara yi mata magana da fa'din" Ke Khausar baki ganin hasken rana ne kike yin abu kamar ba sallah zaki yi ba...?" Kafin Khausar tayi magana Iyami ta riga da fa'din" Kar ki ta kura ta da Allah, nawa ma take da zaki ringa matsa mata akan sallah...koda wani lokaci tayi abinta ai duk sallah sunan ta ba canza suna zata yi ba...ke wannan da Liman 'din ne da kansa ya haife ki ma da bansan me zaki maida kanki ba wallahi...kinbibin masifa haba....!ta 'karashe da jan guntuwar tsaki. Ni kam 'daki na na koma in mai girgiza kaina, sosai nake mamakin hali irin na Iyami tun ba yau ba... Gata ne zaka yi wa amma har sai ya zarce 'ka'idan da ya dace ka nuna masa, miye laifi na dan nayi mata fa'da akan daidaita lokutan sallah. Sai da na gama shan kokon da Iyami ta dama da ko wadattacen damu bai samu ba balle akai ga batun sugar duk na san Yah Bukar ya kawo Sugar jiya jiyan nan amma ni da Baba bamu ko ji alamun ta cikin namu abin 'karin ba, sai da na kammala kaf kafin na fito ma sake 'diban ruwa, shirin wanka nayi kaina sanye da hijabia na sai zani da ke 'daure daga saman 'kirji na..ina sanya takalma najiyo sallama daga hanyar shigowa. Baki na washe ina kallon wurin duk ban ga mai sallamar ba amma na riga nasan wacecec, cike da fara'ata nace" Dijeh kamar wacce ki kayi kwanan mafarki na?" Turus taja ta tsaya tana banko min harara tana fadin" da yake ni bana yin abin arzikin da za'a yaba min ko". Baki na nayi saurin kamawa ina girgiza kai nace" Haba tawan, wace ni da fa'din haka kawai fa nayi mmkin ganin ki ne.." " Barka na biyo mk mu wuce shiyasa nazo da wuri kafin in zo ban same ki ba" Ta fa'da tana mai 'karasowa ciki. Ga Iyami ta juya dake zaune bakin 'dakin ta tana sakace ha'kora..Khausar kuma ce kwance gefen ta ita kuma tana zane akan 'kasa. " Ina kwana Iyami.." Ta fada tana mai rusunawa cike da girmamawa. Iyamin ma ba yabo ba fallasa ta amsa da " Lafiya Dijeh...Ya Umman ki?" " Lafiyan 'kalau Iyami". " Naji kina cewa barka zaku ku da bakwa rasawa, wacece kuma ta haihu da zaku yi wannan sammakon?" 'dan murmushi Dije tayi sannan tace da Iyami" Marwa ce fa matar Bah Shehun mu..Jiya ta haihu da dare shine nace bari in biyawa Zaituna muje muga jinjiri.." " Aikin kenan..." Cewar Iyami tana mai kawar da kanta gefe...can kuma tace" Allah ya raya mata...ku ma 'din zuciya zaku yi kuyi auren ku haihu yafiye maku da wannan bibiye- bibiyen gidajen masu jego da kuke faman yi". Murmushi kawai dukkan su suka yi, yayin da nayi saurin kamo hannun Dijeh muka shige 'daki jna washe baki nake sake tambayar ta da gaske Marwanatu ta haihu Dijeh..me ta samu kuma?" " Yarinya ce aka samu, ni dai kiyi sauri muje..Ummata fa ta hanani wai sai de anjima muje da su Innani ni kuma zuciya ta ta kasa ha'kurin haka wallahi, ki hanzarta mu je mu 'dauki jinjira..." " To zauna ki jira ni da Allah...yanzu ma 'dauraye jiki na zani sai kawai mu wuce ko..." Nayi maganar ina mai nufan hanyar fita jikina har na rawa zabar zumudin da nake ciki, har na kusa fita sai kuma na juyo nace " amma fa ni ce zan fara 'daukan yarinyar idan munje ki Dije..." " Wallahi ban yarda ba ke idan kin 'dauka bakya bawa mutun da wuri yau ni zan fara 'daukar ta.. haka ma fa Jinjirin Azeeman Yah Bukar ma hanani 'daukan sa kike yi kullum sai de ke..ranar sai da na san'di hanya baki sani ba naje ni ka'dai kafin na samu na 'dauki jinjirin" Murmushi nayi na juya ina fa'din " Bari ke de in yi in zo muje yau dai bazan hana ki 'dauka ba Insha Allahu..." Duk yadda na ke jina cikin damuwa game da mafarkin da nayi yau 'din tuni damuwar ta kau sanadiyan jin labarin haihuwar da nayi, gaba 'daya hankali na ya tafi wajen gaba 'daya domin Allah yayi ni mai masifar son gani da 'daukar jinjiri, haka cikin hanzari na watso ruwan na fito na shirya cikin zani da riga na sake rufa hijabi na da ko gwiwa ba kai min yake ba amma dai nafi jin da'din sa akan sauran, sa6anin Dijeh da ke 'damare da 'dan gyalen ta yellow kanta 'daure da 'dan kwalin zanin jikin ta sai tshirt fara mara nauyi mai hoton keke a gaba. Kamar yadda na saba duk ranar da nayi mafarkin sai na bawa Dijeh labari, haka kawai sai na 'dauri aniyar sanar da ita..amma yau din haka nan kawai sai naji bana da ra'ayi kuma, duk wata niyya ta ta son bawa Dije labarin ya kau naja kamar yadda nayiwa Yah Bukar al'kawarin bazan sanar da kowa ba. _Shin wai wani irin mafarki ne wannan tayi ko kuma ince take yi ma?_ *Ku biyo ni dan jin me ke 'kunshe cikin labarin ZAITOON...taku ce mai 'kaunar ku da burin faranta ranku.....* 👇🏻 Salmerh ce😘 [24/12/2022, 11:00 am] Zee Ingawa: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Wattpad@* _Serlmerh-md_ 🅿️ *...83* ......Zaune yake gaban wani dattijon mutumi da ke lullu6e cikin babbar riga, fuskar sa cike take da kamala da kuma annurin ganin 'dan 'dan uwan nasa. " Allah yayi maka albarka Buba..Allah ya 'kara arziki ya kara rufa asiri, ai kai kam akwai 'ko'kari Buba...jiya ma nake gayawa mahaifin ka cewa wancan satin ka aiko mana da 'kashin miya yace ai bai ma sani ba...shima haka yaji miya daban da ya tambaya ake ce ai Buba ne ya kawo...Allah ya 'kara maka bu'di 'dan nan ai kai kam ba kamar su Muhammadu ba babu abinda suka iya sai shanshanci da rashin hankali.." Murmushi kawai Bukar yy yana sake sunkuyar da kansa yace" Addu'ah za'a 'kara yi mana Baffah suma 'din Insha Allahu wataran zasu yi fin hakan ma.." Kai Baffah Liman ya kawar yana fa'din " Ashsha...ai yaran nan kawai addu'ar dai da kace itan za'a cigaba amma ina wani batu mai da'di kuma wajen su Modu..kwata-kwata bansan yadda zan yi da su ba ni..." " Sai ha'kuri dai Baffah...Allah ya 'kara rufa asiri..." " To Amin Buba...Allah kuma ya muku albarka ya 'kara muku zuciya...". Murmushi yayi yana sake du'kar da kansa yace" Baffah dama Batun Zaituna ne nazo da shi...kwanaki na yiwa Baba magana sai ya nuna min ai bakomai, to abin dai da ya matsa shine na sake yi masa magana yace to zai same ka to kuma bansan yadda kuka yi ba..naga dai bai sake yin maganar ba....". Hankalin wan mahaifin nasa gaba 'daya kansa ya dawo yana masa kallo mai cike da tambayoyi har sai da ya ji ya dasa aya sannan yace " Wai wani batu kake nufi sam ban gane ba, Mahaifin ku bai zo min da wani batu kan Zaituna ba sam...ko batun auren dake tsakanin su da Babaji kake magana..?" Da sauri ya girgiza kansa sannan yace" a a Baffah wani batu ne de na daban.." " Au to ai kuwa ba muyi magana da shi kan yarinyar nan daban ba baya ga wancan...to ina jin ka Buba...me ne ya faru?" Yayi maganar yana gyara zaman sa gami da maida hankalin sa kacokam kan Yah Bukar. Nawi sosai yaji ya kama sa sai kuma ya rasa ta ina ma zai fara bayyana wannan batun, ya tabbata ko ita Zaitunar lokacin da ta fara bayyana masa abinda ke faruwa da ita wayo bai gama isan ta bane shiyasa, yasan da yanzu ne ba zata iya sanar da shi ba duk kuwa da irin kusancin da ke tsakanin su...shiyasa ma yanzu idan tayi mafarkin sai dai tayi ta kuka ga dukkan alamu ta fara fahimtar asalin me ke faruwa da ita ne shiyasa ba ta iya labartawa. Toh shi kuwa ta ina zai dauko bayanin kenan tun daga farko, da ace Baban su ya fara maganar nr shima zai 'daura nasa amma Abban su bai yi hakan ba. Kansa ya shafo yana sake 6oyayyan huci, du'kar da kansa ya sake yi sosai sannan yace " Baffah wallahi..ina jin shai'danu ke firgitata cikin bacci...tana yawan firgita sai ta yi ta kuka abin ya jima yana damun ta to na sanar da Baffah tun kwanaki nama yi zaton zai same ka da maganar ne bansan bai sanar da kai ba..." Kai Baffah ya jinjina da mamaki yace" Ita Zaitunar shai'danu ke firgitawa shine kuma yayi biris da maganar..?" Shiru Bukar yayi..sai shi Baffa Liman 'din ne ya cigaba da fa'din...Ni dai bansan wani irin mutum ne Ahmadu ba, yanzu ko wani abin ne daban haka zai yi shiru akai bazai sanar min ba har sai abu ya lalace ko...". " Ayi ha'kuri Baffah ina jin mantuwa ce yayi". Cewar Bukar da ke sake yin 'kasa da kansa, sam bai san cewa Abban nasu bai sanar da Baffah Liman ba da ba zai ma zo ba..dama da Baffan ya fa'da ne to da tuni kawai zai masa kan maganar amma yanzu kam sam bazai iya ba, sai dai ya koma ya sake tunawa mahaifin nasu 'kila zai zo ya masa bayanin dalla-dalla tunda shi yasan komai akai. Cikin zuciyar sa yake wannan tunanin da kansa a du'ke...amma sai yake ga kamar hajan kuma ba mai yiyuwa bane dan sarai yasan waye mahaifin sa yasan halin sa kamar yunwar cikin sa, abu ne mawuyaci ya iya zuwan musamman sbd ita. Mahaifin su bai wani damu da damuwar su ba, bai damu da 'kuncin su ko farin cikin su ba, bai damu da duk halin da zasu tsinci kansu aciki ba, shi dai bai san me yake damun Abban na su ba amma halin ko un kula da yake nuna musu abin na damun sa arai sosai, ace mutum tsakanin ka da iyalan ka daga abinci sai abinci baka damu da jin damuwar su ko kuma tsaya musu kan lamarin da ya taso musu ba, to ma bai damu ba balle idan ka sanar da shi yy maka maganin damuwar ka...kullum gari na wayewa ya bar gida sai kuma yamma zai dawo babu damuwar sa da sanin ya kuka kwana balle ya kuka tashi, shi kansa idan yana so ya ha'du da shi su gaisa sai dai idan sun fito daga masallaci idan kuma basu ha'du masallacin ba sai dai ya taho gidan sassafe tunda duru-duru. Shiyasa yake matu'kar tausayin 'kanwar tasa Zaituna, domin ita bata da kowa agidan, sai Allah, bata da wanda zai jata a jiki yaji damuwar ta sai shi kadai, bata da wanda zata zauna tayi hira da shi kaf cikin gidan sai shi ka'dai. Shiyasa shakuwar su ta ninka ta kowa. Dan ko can wajen mahaifiyar ta ma da take zuwa Iyami ta sa mahaifin su ya hana ta zuwa kwata-kwata da mummunar doka akan hakan kuma...in ba rashin imani da tausayi ba menene wannan haka, yarinya da mahaifiyar ta araye ace kuma an shiga tsakanin su kar su yi zumunci, wannan zamanin mace na da tsayayye akanta ma ya aka 'kare ballantana kuma babu wanda zai jata ajiki yaji damuwar ta.... Maganar Baffah Liman ce ta katse masa dogon tafiyar da yayi "...Kana jina ko Bukar..?" Saurin gya'da kansa yayi. Baffan ne ya cigaba da fa'din.." Ka turo min ita Zaitunar da kanta zaifi kasan sharri na shai'danu ai babu dadi...amma banda abu na irin na Ahmadu ai bai kamata yy shiru kan hakan ba...kai de ta shi kaje ka cigaba da hatkokin ka..Allah ya shi albarka ka turo min ita da Allah ko zuwa gobe ma..." " Insha Allah Baffah zan turo ta...Allah ya 'kara girma.." " Amin Amin Buba ka gayar min da mahaifiyar taku..ina wannan gagaren kuma sarkin surutu Ummaru?" Murmushi Bukar yayi yana saka takalma yace" yana nan duk lafiyar su kalau Baffah" " Toh madallah...Allah yai muku albarka ya tsare mana ku". Yana amsawa da Amin ya bar Baffah Liman 'din zuciyar sa cike da neman wata mafita. Ai ya riga yasan halin Zaituna ko tazo babu abinda zata iya cewa Baffahn nasu domin ko shima lokacin da ta gaya masan wayon ta da saura yanzu kam ko ya tambaye ta sai de kawai tace masa mafarkin nayi.." Kwanakin nan kam ma sai dai kawai tayi ta zabga uban kuka bata fadin komai, Iyami kuwa na jinta duk da yake ta riga tasan matsalar amma bata ta6a nuna damuwar ta akai ba sai de ta kya6e baki, bai san ko dan cewa ba ita ta haife ta bane oho. Allah ma ya taimaka babu wani bare da yasan labarin dan ko ita Zaitunar ya hana ta fa'diwa kowa baya ga hk da yanzu yasan ana can ana ta yama'di'di da su a gari bacin bb wanda ya fi karfin Allah ya jarrabce shi da makakamanciyar ta...cuta ce ya kuma san tabbas tana da magani, yasan addu'a ce kan gaba shiyasa ya fara koya mata addu'o'in tsari daga shaidanu tun a farko kuma Alhamdulillah yasan zuwa yanzu ta haddace su. Yana kan tafiyar ya yanke shawarar abinda yaga yafi masa arai...dan hk washe gari kashe ranar yayi gaba 'daya ya bar san'ar sa ya nufi cikin garin na Maiduguri dan niyyar neman mafita wa 'yar kanwar tasa...domin ba zai iya zuba idanu yana ganin ta cikin damuwa koda yaushe ba da wanne zata ji ma. Da yake Maidugurin ba ba'kon sa bane can ya saba harkokin sana'ar sa ba tun yau ba yana kuma da wani aboki shi yy masa jagora zuwa wajen wani babban malamin sunna...anan ya samu cikakken bayani kan abinda ke damun Zaituna wato namijin dare...sosai yayi masa bayani ya kuma fahimce shi, daga 'karshe ya bashi addu'o'i a rubuce masu yawa, ya hada masa hadin magani da musulunci ya bamu damar amfani da su duk yayi masa bayanin komai, 'karshe kuma wani 'kullin magani ya bashi wanda zata na shafawa a jikin ta idan zatayi bacci. Godiya sosai yayi wa malamin barin ma da yaki kar6ar ko sisin sa yace in sun sake haduwa zai ansa, haka ya dawo gida jikin sa sanyi kalau sakamakon jiyo sirrin mafarkin kanwar tasa da yayi. Sosai lamarin ya karya masa zuciya, Zaituna nawa take da har hakan zai ringa faruwa da ita, suma aljanun basu mata adalci ba sam aganin sa, Zaituna yarinya ce mai natsuwa da kuma kamala, sam bata da rawar kai uwa uba ma'abociyar suturta jiki ce ita, bacci wannan da haijabin ta take yinsa kuma ko cikin gidan bazaka ta6a ganin kanta bb hijabi ba...Sallah ma baya ta6a wuce ta duk da yasan ba wani karatun addini mai zurfi ne da ita ba amma ko a ina zai yi shaidar Zaituna kan riko da addinin ta....karatun allo dukkan su suka yi wajen wan mahaifin su wato Baffah Liman, amma babu laifi yasan sun san kan addinin su. Shidai Bukar yayi sau'ka har sau biyu amma Zaituna bata yi da nisa ba dan kwata- kwata bata fi izu biyar ba..amma Alhamdllh duk da hakan yasan tana sau'ke hakkin addinin ta dai dai gwargwado, to me ya kawo mata wannan matsalar kuma? gashi sam shi bai da sani akan hakan, shiyasa tun da shekaru biyu kenan da suka wuce ta sanar da shi irin mafarkin da take cewa wani mutum yana danne ta a bacci tayi masa bayanin abinda yk yi mata, ta kuma ce ita tsoro yake bata sosai, a yanzu kuma sai salon abin ya canza domin tace masa idan mutumin ya danne ta kuma da safe sai taga wani abu a jikin ta. A lokacin yayi mamaki sosai..amma hakan bai sa ya 'daga hankali ba domin ba akai akai take yin irin mafarkin ba, wani lokaci har sai ya manta ma sannan take ce masa tayi...da kansa ya ringa koya mata addu'o'in da zata ringa yi..kuma Alhmdllh duk wadanda ya koya mata ta iya su. To da abin ya dame shi shine ya samu Iyami da zancen ita kam sai ta kya6e baki tace to ita ina ruwan ta ita tasan inda ta yayibo aljanun ai.. jin kalmar aljannun da Iyami ta furta ne yasa abin ya tsaya masa aransa hakan yasa ya tunkari mahaifin sa da maganar inda yayi masa bayani dalla-dallah, abin mamaki sai yy biris da maganar tamkar ba abin damuwa bane aka sanar da shi.. Shima kansa har ya fara mantawa da batun sai gashi kwanaki bai fi wata biyu ba ya same ta tana kuka ko da ya nemi jin abinda ke faruwa sai tace masa mafarki tayi. Ido ya zaro sosai yace mafarkin kike wa kuka 'kanwata?" " Yaah ni dai bana so bansan yadda zanyi ba" Yace baki yi addu'a kafin ki kwanta ba ko. .?" Tun ma kafin ya rufe baki ta bashi amsa da fadin" Wallahi Yaah nayi ban ta6a mancewa ba ko sau 'daya, kuma ina yin alwala kullum..." " Masha Allah, toh kar ki damu kinji kanwata, Insha Allah watarana duk zaki daina su tun da muna addu'a babu fashi..zamu yi ta rokon Allah ya yaye miki yasa ki daina yi kinji.." Ranar da kyar ya samu ya kwantar mata da hankali...shiru shiru kuma abin ya lafa sai jiya ya sake samun ta kuma still Mafarkin ne...so abin ya dame shi gaskiya kuma yasan Zaituna bata da wanda zai tsaya mata sama da shi, tunda an riga an shiga tsakanin ta da mahaifiyar ta dole shi'din ne dai.... Da dawowar sa ko gidan sa bai shiga ba ya wuce gidan mahaifin sa dan yiwa Zaituna albishir 'din ya samo mafita sai dai ko da yazo bai same ta gida ba wai sunje barka da ganin wajen jinjiri gidan Babaji... Bukar baiyi mamaki ba sam dan sarai yasan halin 'kanwar tasa da tsananin son yara musamman 'yan jirajirai... Gidan sa ya koma ya yi wanka ya ci abinci ya huta sai dare ya dawo bayan yy sallar maghrib ya shigo, kan wata yagaggiyar dadduma ta ya same ni na sallame sallah ina zaune shiru kamar me tunani... Ya kuma san bai wuci batun mafarkin ne ke raina ba har yanzun. Da sallama ya shigo wanda yasa ni waigawa da sauri na dube sa, tsaye na mi'ke ina fa'din" Yaah Bukar kaine da wannan lokacin?" Murmushi yayi yace nine 'kanwata 'dazu nazo ai akace wai kunje gidan Babaji kallon Jinjiri..." Murmushi nayi nima gami da fa'din" Yaah ai ma bamu da'de ba fa muka dawo gida..." " Da alamu fa kin ma fi mai jegon farin ciki ko 'kanwata ..?" 'Yar dariya nayi sai yace" eeh mana ai na fahimta, yadda naga wannan fara'ar saman fuskar ki nasan duk ta ganin sabon jinjirin ne, jiya ma fa Ummaru yace min kunje da shi, sai gashi yauma kun koma..." " Ni dai ina son yaran ne kawai Yaah amma ai gobe bazan je ba..wata'kila ma sai ranar suna..." Nayi maganar ina murmushi shima yana murmushin yayi" anya kuwa! banga alamar zaki iya ba, munyi sa'a ma da baki tare gidan ba gaba 'daya ai..." Wannan karon kam dukkan mu dariya muka yi sannan ya zauna daga bakin 'dan gado na na kwangwala dake 'dakin. Sosai ya dube ni ya kuma.mayar da hankalin.sa kacokam akaina. Ganin hakan ya sa nayi kasa da idanu na ina wasa da yatsun hannu na. " Magana fa nazo muyi 'kanwata..." Ya fa'da yana mai gyara zaman sa. A hankali na 'dago na dube shi " Toh Yaah ina jin ka..." Daga haka na kuma mayar da kaina 'kasa. " Kinga duk yinin yau 'dina ke kadai na barwa shi kamwa ta..har Yerwa na shiga sbd ke kadai, ba dan komai ba kuma sai dan kawai domin neman maki magani..." Sallayan dake hannu na na ajiye gefe da inda yake zaune daga 'kasa na zauna ina duban sa cikin sanyin yanayin da ya riske ni lkc guda. Maganin ya fara mi'ka min sannan ya 'daura da fa'din" na samo miki magani da wasu addu'o'i kuma ina da yakinin insha Allahu zaki daina mafarkin nan da kike yi kinji..?" Kai na 'daga masa da sauri alamar naji ina mai sunkuyar da kaina, dan ni kaina na gaji da wannan mafarkin, sosai na gaji da yinsa. Bai fito fili ya bayyana min asalin abinda malamin ya sanar da shi ba amma yace da ni...malamin yace duk lokacin da na farka na kuma ga sauyi a jikina ko kuma ba'kon abu kawai nayi wanka saboda gudun kokonto...ai kin iya wankan tsarki ko 'kanwa ta?" Kai na 'dage masa alamar erh ina mai yin 'kasa da idanu na. Sai yace" yauwa kanwa ta, to zaki yi amma da niyya daban, niyyan janaba zakiyi ba irin wanda kk saba ba kinji, da iznin Allah komai zai daidaita ki daina ganin kowa a mafarki...akwai wasu addu'o'in da ya bani kuma suma duk zan koya miki su amma kafin nan, ai kin iya su kulhuwallahu ko?" Kai na 'dage masa alamar erh" karanto min dai inji ko kin iya da gasken babu kuskure". Yayi maganar yana 'dan murmushi, nima murmushin nayi sannan na fara karanta masa. Bai ci karo da gyara na ko guda ba, dan haka yace na karanto masa Ayatul kursiyyu..jinjina min yayi fuskar sa yalwace da annuri bayan na karanto yace " addu'an bacci shima kin iya ko?" Da kai na bashi amsa domin dama gwanace ni wurin 'dinke baki ta zanta da mutum da sassan jiki na. Bai damu ba sai cewa da yayi" Karanta shima inji..." " Masha Allah ashe 'kanwar tawa hafiza ce bansani ba" Haka ya rinka min tambayoyi ina amsa shi wanda ban iya ba kuma ince masa ban iya ba, haka wanda nayi kuskure sai ya gyara min shi, ya kuma ringa maimaita min har kusan sau bakwai kafin idan yaji baki na ya iya ras sai muyi gaba. 'Karshe jinjina min yayi yana mai cika da tsantsan farin ciki yace " Yauwa 'yar kanwata...daga yanzu ki daina damun kanki kinji, matukar mutum ya ri'ke addu'o'i to insha Allahu babu abinda zai sha masa kai a rayuwa, ya kuma ya dingi ganin dai dai kenan cikin rayuwar sa har illa masha Allah. Wannan 'din ma ina fatan daga wannan lokacin ya 'kare kenan har g.." Bai kaiga rufe baki ba muka ga an 'dage 'dan yamutsatatten labilen dake bakin 'kofar 'dakin. A tare muka kai duban mu wajen nan muka yi arba da Iyami...ranta a ha'de sosai tace" tun 'dazu naji sallamar ka Buba amma shine baka san ka zo ni ka fara gaida ni kaga ya nake ba ka wani zo ka rashe anan ko? Wace uwar take tsinana mk banda shirmen banza da na wofi, kar ka fita hanyar yarinyar nan kaga, wallahi duk mutuncin ku zanci daga kai har ita, uwar ta ma da ya na 'kare da ita anan gidan da 'kyar wallahi na yakice ta ajiki na gashi kaima an 'dauko hanyar hk...ka fito yanzun nan ka wuce gida..." Daga hk ta saki labilen tana mai cigaba da mitar" Mutane munafukai, dangin azzalumai, wama yasan tushen su wani iri ne, duk ta bi ta mallake min gida yanzu kuma an dawo kan dan ciki na, ni kuwa bazan lamunta ba dan naga abin yana neman yafara zarce iyaka, ina gidan nan amma Bukar ya fara mancewa da ni sai wata banza can dangin mayu..." Ni dai 'kasa nayi da kaina ban 'kara kallon ta ba, fa'dan Iyami ai inda sabo ya kamata ace na saba shi, dan duk ranar da fa'dan ta ya cika ta sosai take sau'ke min buhunan bala'i akaina har sai ta gaji dan kanta take kyale ni...mahaifiyar tawa ma da a lkcn ba gidan take ba amma bata tsira ba. Tsaye Buba ya mi'ke da sauri ya bi bayan Iyami yace"..na zata fa kina sallah ne dana shigo shine kawai nayo nan 'din kuma addu'ah ma nake karanta mata saboda matsalar mafarkin da take fama da shi ba komai ba Iyami dan Allah kiyi hakuri...." " Kai da Allah rufa min baki...wani addu'ah kai 'din ka iya da har zaka koya mata...in kayi wasa ma karshe sai sun zo sun ce kaine mai danne ta cikin daren ai..." Da sauri ya 'dage kansa ya kalle ta ransa duk babu da'di yace " Haba Iyami, Zaituna ce fa, dan Allah ki ringa gyara kalaman ki kafin ki furta su, ki daina fa'din abu irin wannan ba da haka aka san babba ba..." " Sai ka koya min ai tunda ni bansan me nake ba, banza shanyayye kawai, ana nuna maka gaskiya kana bau'dewa ni dai wallahi bansan wani iri na haifa ba, ga Khausar nan 'yar yarinya da ita amma tasan ta faranta min tayi min biyayya amma banda kai..ka fice min anan ne ko sai na make ka...". Ta kai 'karshen maganar da kauce masa ta bashi hanyar barin 'dakin. Kai ya girgiza sannan ya fara tafiya da sanyin murya yace" Sai da safe 'kanwata kuma kar ki manta sau uku- uku duk zaki karanta kafin ki kwanta kuma ki ringa yin alwala..sauran addu'o'in a hankali zan koya mk daga baya.". Shiru nayi ban ce masa komai ba illa kaina da na sake du'karwa... Sai da Iymai taga fitar sa kafin ta dawo kaina tace" Aikin banza..wama yasan ko da kanki kike gayyato abinki kina ta wahal min da yaro abanza...mthhew" Ta 'karashe da jan tsaki tayi gaba. Ina cikin wata matsala 'yan uwa, dan girman Allah ku sani cikin addu'o'in ku ko da sau 'daya ne tak.😭 UBANGIJI ALLAH YA KAWO MIN MAFITA CIKIN AL 'AMURA NA, YA YAYE MIN DAMUWA TA🙏 Salmerh😘 [25/12/2022, 11:19 am] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Wattpad@* _Serlmerh-md_ 🅿️ *...84* .......Ban iya na sake motsawa a wurin ba har akayi sallar isha'i sannan na tashi na kunna 'yar tocilar da Yaah Bukar ya siya min kwanaki ganin 'dakin nawa babu wadataccen haske...to ma gashi batirin duk yy sanyi..yau kuwa ban yini a gida ba balle na tuna na sa su arana su 'dan farfa'do. A haka na lalla6a na gabatar da sallan ta hasken tocilar na kara sau'ka, 'karshe ma 'daukewa yayi gaba 'daya. Idanu na lumshe ina ta sake maimaita karatun da ya yi min 'dazun dan kar in manta, a haka na gama dukkan addu'o'in da zan yi na shafa daga haka na hau kan gadon kwangwala ta da babu komai akai face wata 'yar tsohuwar tabarma. Da hannu na nayi pillow idanu na tsam a wuri guda ina tunanin rayuwa ta gaba 'daya, kwata- kwata bana jin da'din zaman gidan namu a halin yanzu, domin bana samun walwala da sakewa yadda ya kamata, idan an ganni da fara'a cikin gidan nan toh ni da Ummaru me ko Yayana, amma ni da damun sakewa sai dai in bana cikin gidan amma matukar ina gida komai a takure nake yin sa, a hakan ma abin da 'dan sau'ki domin kwana biyu Iyami bata tura ni jeji ba. Ajiyar zuciya na sau'ke tuno abinda ya faru da ni watanni 'kalilan baya da suka wuce. Hannu na na kai cikin riga ta kan saman ciki na nake shafawa, bazan ta6a mantawa da 'dan karen wahalar da nasha ba a lokacin da naji ciwon nan..wannan ma Iyamj ce ta tura ni 'debo mata kara a jeji wai na hura wuta, ranar sai na taki sa'a Ummaru yace zai rakani, haka muka tafi muna 'yar hirar mu ni da shi sama...tare muka harha'da karan na 'daura ina shirin 'dagawa sama kafin na 'daga har na kai hannu kenan sai naji Ummaru ya kwalla min 'kara da iya 'karfin sa a lokaci guda kuma yake 'dan jan baya idanuwan sa warwaje yace" Yaah Zaituna maciji...maciji ki matsa..." Yayi maganar yana mai yi min nuni da inda ya hango macijin. Da sauri na saki karan na mi'ke tsaye ina mai kai dubana wajen da yake nuna min 'din... ido hudu nayi da macijin nima nan na tabbatar da gaske yake, take nayi baya jiki na na daukan rawa..hannun Ummaru na kama muka fara gudu gudu sosai tamkar ance min bayan mu macijin ke bi, ko ganin inda nake sanya 'kafata ban yi, bamu kuma bi ta kan karan da muka daura 'din ba. Muna cikin gudun ne nayi tuntu6e da wani abu da ban san ko menene shi ba, ai kafin nayi wani yunkuri ko dabara tuni na fa'di da ciki na cikin rashin sa'a kuma sai na fa'di akan wani gurbin karan dawar da ake yanke amma ba'a gama cire shi gaba 'daya ba, kuma ta sai tin ciki na.... Sau 'daya nayi ihu mai cike da azaba daga nan ban sake sanin inda kaina yake ba, sai bu'de ido nayi na ganni kwance a wani babban asbiti dake cikin garin Maiduguri, wanda kusan zan iya cewa wannan shine shiga na cikin garin na farko. Ashe Ummaru ne yaje gida da gudu arikice ya sanar da su wai Zaituna ta mutu da jini a jini .." Jin hakan yasa mutane suka yi saurin kawo min 'dauki nan aka tarar da ni sume na kuma zubda jini ba 'dan ka'dan ba. Yaah Bukar shine ya 'dauki nawin komai da akayi min a asbitin har suka dawo gida, kama daga kudin jinya 'karin jini da akai min har zuwa 'dinkin da akai min a wurin nan 'kasan cibiya ta ka'dan, kafin ya warke kuwa ba 'karamin wuya na ci ba sbd rashin samun cikakken kulawa. A wannan kwanciyar tawa ma sake tabbatar da cewa ni din marar galihu ce, mutun 'daya ke tausayi na kuma shine ke min dukkan 'dawainiya sai 'kawa ta Dije da muke kusan yini tare da ita. A lokacin na sake tabbatar da cewa babu 'kauna ta ciki kuwa hadda mahaifiya ta. Domin har nayi ciwon na gama na cigaba da harkoki na ko da sau 'daya mahaifiya ta bata ta6a shigowa gidan mu da sunan duba ni ba...sosai abin ya bani haushi amma bani da matakin 'dauka...domin bani da ikon yin komai face illar da hakan ke sake yi min a zucia ta. Ga gurbin ciwon nan har yau idan na ta6o shi na kan ji abin na dawo min sabo dal cikin raina. Ashe ita ma Abban mu cewa yayi da ita ko da a cikin mafarki ta yadda ta taka 'kafar ta wuri na sai yaji dalili balle a zahiri sai ya daure ta, ni kuma idan ni naje wajen ta bai yafe min ba...ni sam ban san wace iriyar 'kiyayya bace wannan, a yanzun kuwa da nake fama da wannan ciwon sosai nake bu'katar mahaifiyar ta a kusa da ni, ina matu'kar bu'katan kasancewa tare da ita, ada har fushi nayi amma daga baya sai na fahimci ba laifin ta bane kawai tana jiye min mummunan bakin mahaifi na a gare ni ne, amma so da burin samun mace makusanciya abokiyar shawara kusa da ni wacce zata kula da ni ina ji araina tamkar da wannan burin rayuwa ta zata 'kare, ba 'karamin ka'daici ke 'dawainiya da rayuwa ta ba. Bana son yawan fa'dan da Iyami ke yiwa Yayana saboda ni, abin na min ciwo sosai, ni kaina ina so ya huta haka nan, baya ga haka ma yau da gobe ya wuce ya wuce wasa, bana so watarana bakin Iyami yayi tasiri akansa tunda mahaifiya ce ita agare shi dolen sa yi mata biyayya ya kuma guji 6acin ranta, Yaah Bukar yana matukar kiyaye komai da 6ata mata amma a kaina hakan baya tasiri sam. Ba kuma na so akai bigiren da hakurin Iyami zai kai ma'kura har ta furta wata kalmar da zata iya zame masa dafi mummuna cikin rayuwar sa, a koda yaushe alkhairi nake wa Yayana buri ba sharri ba. Ba tun yau na fahimci cewa shima 'din iyami so take ta raba mu ba, na fahimci bata 'kaunar wannan shakuwar ta mu sam Iyami bata so ta ganni da kowa ma balle 'dan ta na cikin ta...hatta Dije ma dan kawai Allah ya hada jinin mu ne, kuma mahaifiyar ta ba mai jin ziga bace, amma Iyami ta so shiga tsakanin mu ta hanyar gayawa mahaifiyar Dijen matsalar da ke damuna na mafarki a tunanin ta hakan zai sa su gaje ni ne sai taga sa6anin haka. Afa'dar Iyami wai idan mahaifiyar Dije bata raba Dije da ni ba to kuwa itama watarana sai ta kwaso musu abinda yafi 'karfin su domin mutanen 6oye ne dani kuma kullum lalu6a ta suke yi cikin dare..." Ita kam bata wani bawa zancen muhimmanci ba shiyasa maganar bata je ko'ina ba, kuma ma ai tasan a da na kan sanar da Dijen abinda ke faruwa da ni wani sa'in ma itama Dijen na sanar da ita idan abin.ya damu zciyar ta shiyasa bata ji shi matsayin bakon lamari ba balle har ta kai ga daukan kalan matakin da Iyami ke fata. Bayan wannan Iyami ta 'kara da wasu 'karairayin amma duk basu yi wani tasiri ba hakan ne yasa ta ha'kura ta fita hanyar su. Juyi na sake yi ina jin tausayin kaina sosai yana 'kara kamani. Tuno wancan maganin da Yayana ya kawo min ne ya sani ta shi nayi kamar yadda yace nayi duk na shafe jiki na da shi bayan na ji'ka da ruwa. Addu'o'im da ya koya min shi nayi sau uku uku batare da na gaji da maimaita su ba sannan shima na shafe ajiki na... sai sannan na kwanta ban da'de ba kuwa bacci yayi awon gaba da ni. Juyi mai kyau ban yi ba har garin Allah ya waye bayan anyi sallah an fito daga masallaci sannan na farka, zuciya ta fes na jita ba kamar yadda nake jin ta cunkushe abaya ba...bansan lkcn da na saki murmushi ba, har ga Allah sosai naji da'din baccin yau 'din, sosai naji da'din sabon canjin da na tsinci zucia a ciki wanda nasan ka'dan ne daga cikin falalar addu'an da nayi. Da yake dama fa ni ba wani tuna nake da yin addu'an bacci ba har sai da na fara fahimtar wannan lalurar da nake fama sannan na fara tunawa da yin adduar duk da ko abayan ma na 'dan iya wasu amma sam baya zuwa kaina idan zan yi bacci, hakan yasa ban wani bashi muhimmanci ba, amma yau ka'dai da nayi addua'ah cikakkiya sai na ji da'din baccin sosai, ko mafarkin wannan uban ruwan ma da nake yi yau sam ban yi shi ba haka kawai sai nake jin kaina tamkar ba ni ba..." Allah yayi maka albarka ya 'karo maka farin ciki daumammiya Yaya na...". Abinda na furta kenan a fili tare da mi'kewa na nufi hanyar fita dan 'dauri alwala. Bayan kwana biyu Yah Bukar ya fara koya min adduo'in, amanar rasulu ya fara koya min sannan sauran addu'o'in wa'danda muka 'dan sha wahala kafin na koye su, amma dai Alhamdulillah yanzu duk na iya su sun zama tamkar wa'ka a baki na, kuma tunda na fara addu'oin ma sau 'daya kawai tayi mafarkin mutumin ya danne ni, da safe da na tashi naga sabon abu a jikina sam hakan bai min da'di ba amma ban sanar da Yayana ba gudun kar ya raina 'ko'karin sa akaina. Haka naje nayi wannan wankan da Yah Bukar yace na ringa yi kafin nayi sallah idan na fuskanci canjin yanayi tattare da ni. A hankali damuwar abin ya fara barin raina, har nazo na mance da shi ma kwata kwata, domin a 'kalla na 'dauki sama da kusan watanni shida ban sake ganin mutumin cikin bacci na ba, kuma nima ban yi sanya da addu'oi na dai dai da rana guda ba...sosai na dage da akan su kamar yadda Yayana ya koyar da ni... Haka kuma babu abinda na fasa daga halayya ta na zuwa ganin duk wani sabon jinjiri da aka haifa saima abinda ya 'karu, wannan kam ya riga ya zame min tamkar jinin jiki kusan kowa ya sanni da wannan 'dabi'ar. ***** Muhammad Babagana...shine wanda akai mana Baiko da shi, duk iyaye kowa ya riga ya san da zancen lokaci kawai ake jira a 'daura mana aure, shi 'din 'dan gidan wan mahaifin mu ne wato Baffa Liman, an mana baiko da shi tun bansan kaina ba, domin shekara ta goma sha 'daya a lokacin aka bada aure na ga Babagana...yanzu kuwa shekaru na goma sha biyar..'yan watanni kawai ya rage ayi auren sai kuma wani dalili na daban da ya kutso kai ya dan yi tsaiko ga taso batun, shiyasa a duk lokacin da muka je ganin jinjiri idan an haifa sai a dinga yi mana tsiya wai ai muma zamu haihun ne mu daina gaggawa tunda lokaci 'kalilan ya rage ayi mana aure su huta.... Tun bana damuwa da maganar har nazo na fara jin kunya a duk lkcn da aka fadi hakan. Baya ga haka ma ya kan sani jin 'kaguwa da son ganin hakan ya tabbata zahiri. Ada sam ban wani damu da auren ba, shi kansa Babagana idan ance min na tuna ranar da na gansa ma bazan iya tunawa ba, amma tunda mutanen nan suka ankarar da ni cewa da zarar na yi aure zan haifi mawa 'dan nima shikenan sai nake 'daukin ranar auren nawa yayi, badan komai ba sai dan kawai nima in ga na samu jinjiri kamar yadda wasu ke fada. Idan a tuna hakan fa ni ka'dai sai na ringa sakin sassanyan murmushi. Ba 'karamin 'kauna ce tsakani na da 'yan jinjiraye ba...sosai Allah ya jarabce ni da 'kaunar yara. Kwanaki na tafiya, komai na rayuwa na sauyawa, yanzu bama zam iya tuna rabon da nayi mafarki da wannan mutumin na bacci na ba, da alamu dai nasara ta samu gare mu ni da Yayana.... Bam manta ba lokacin da Baffah Liman ya 'kira mi kan nayi masa 'karin bayani kan maganar da Yah Bukar yaje ya sanar da shi acewar sa, haka na ringa yi masa kuka na kasa fa'din komai...abin ya min wani irin bambara'kawai ne kawai, taya ma zan iya duban idanun sa na gaya masa ga abinda ke faruwa ni, Yayana ka'dai ne ya san komai kuma nasan shi kamar makullin sirrina yake kuma ban damu ba dan yasan hakan game da ni domin shi 'din mutum ne na daban a waje na, zaman mahaifi yake a gare ni da mahaifiya, yaya yake wani sa'in kuma ya kan kasance tamkar 'kawata. Yah Bukar wani tsagi ne na jikina, sosai nake jin sa a zuciya ta nake kuma alfahari da kasancewar sa 'dan uwa agare ni...bana haufi dan yasan abu makamancin hakan bazan kuma damu ba idan da bakin sa ya sanar da wani dan nasan yana da dalili kwakkwara, amma ni sam bazan iya labartawa ba. Ban ji haushin sa ko wani abu na daban ba domin nasan bazai ta6a yin wani abu da yasan zai cutar da ni ba. Ina son shi da duk zu'riar sa, duk dama matar sa Azeema sam ba 'kauna ta ko guda a zuciyar ta, soaai take biyewa Iyami take nuna min tsana da 'kyama a fili. Har na bar wajen wan mahaifin nawa ban iya furta komai ba domin daga 'karshe da kansa ya sallame ni ganin bani da niyyar magana illa kuka da nake masa. Ban kuma san manufar zuciyar sa kan hakan ba domin bai furta min komai ba. Yah Bukar bai ta6a sanin 'kiyayyar da Azeema ke nuna min ba haka nima ban ta6a sanar da shi ba dan bana son na tarwatsa masa farin cikin gidan sa, domin nasan halin Yayana, abune mai sau'ki yaci mutuncin Azeema akaina. Ummaru kam da ya kasamce 'dan Yah Bukar na farko Allah ya ha'da jinin sa da ni, kuma nima ina 'kaunar yaron sosai...sau da dama da shi nake zuwa unguwa...ko Khausar bai damu da ita kamar yadda ya damu da ni ba. Sun kasance su hudu ne Iyami ta haifa, Yah Abubakar shine Babba, sai Yaagana, Goni da kuma Khausar, ni kuwa ni ka'dai mahaifiya ta ta haifa kuma tun ina da shekaru ta shida suka rabu da mahaifi na...nayi zaman zawarci na shekara kusan hu'du kafin ta auri mijin ta na yanzu, wanda shi kam duk matan sa 'kin zama suka yi da shi saboda fitinar sa ga kuma rashin haihuwa, duk da ma Alhamdulillah yana da rufin asirin sa ba laifi amma rashin haihuwar san kan hana mata zama da shi, 'diya 'daya tak Allah ya bashi kuma daga ita bai sake samun rabon haihuwa ba, ita ma 'diyar tasa mahaifiyar ta rasuwa tayi tuni kuma ya aurar da ita. Yana da uban fitina irin wanda idan ya ha'du da maras ha'kuri sati guda baza su iya yi atare wuri guda ba. Da haka mahaifiya ta ke ha'kurin zama da shi...bashi da kowa agarin domin kasuwanci ya kawo shi garin har ya zama 'dan gari ya fara fita fatauci zuwa wasu garuruwa, har can kudu ba'a bar shi abaya ba, yana zuwa ko'ina harkar sana'ar sa ta saida Shanu, kuma ba laifi yana samu gaskiya dan mahaifiya ta bata nemi komai ta rasa ba na dai- dai bu'katan ma'abocin rayuwar karkara, bansani ba ko gani da sanin hakan ne yasa Iyami ha'da tuggun da aka hana ni zuwa gare ta gudun kar ta 'dauke min wasu 'dawainiya ta. Nikam bai wani dame ni sosai ba domin tun dama can ba wani sha'kuwa ne tsakani na da ita ba...da farko ma Abba na bai hana ni zuwa wurin ta ba, har kusan bayan auren ta da shekaru uku, har ma wani lokacin na kan kwana acan, amma tun daga lokacin da aka bada aure na ga Babagana shikenan aka kuma yi min katanga da mahaifiya ta shekaru hu'du kenan yanzu sai dai mu ha'du a wani wuri idan ana taro ko wani abin daban, gashi 'karin abin haushi bansan ko mutun guda daga cikin dangin ta ba..na jima da fahimtar cewa ba wani damuwa da ita suka yi ba shiyasa babu wanda ya ta6a zuwa wajen ta dan ganin ya take ko kuma ya rayuwa ke juya mata, hakan yasa nima na cire su cikin sabgar rayuwa ta. Rayuwa ta kawai nake yi yanda Allah ya 'daura min na.kuma taso a cikin ta, sam ban saka damuwar komai arai na...a yanzu na gama fahimtar sam ba na gaban mahaifina, ba na cikin lissafin sa sam, na 'kara fahimtar hakan ne a lkcn da na ji ciwo a ciki na..sai gashi yanzu ma kusan kwanaki shida kenan ni da shi bamu ga juna ba, kuma ko da wasa bai damu ya nemi inda nake ba balle sanin halin da nake ciki, ni kaina na damu sosai da rashin haduwar ta mu, ko ba.komai mahaifi yake a waje na da nake matu'kar bu'katar albarkar sa, duk yadda na so ko da safiya ce mu hadu in gaida shi abin ya faskara domin kafin na tashi a bacci ya bar gida. Kuma ko da mun hadun na gaida shi amsawa ka'dai yake yi ya kawar da kansa abin na min ciwo sosai. Sai fa idan abin kafa doka ya taso sannan yake za'kal'kawalewa ya rattafo min shara'di da dokokin sa ha'di da mummunar kalmar sa ta Allah ya isa da na fahimci ni ka'dai yake yiwa ita...sai dai ban damu ba, mahaifi na kuma dole na ne na yi masa uzuri. Dije ce ta sanar da ni ai mutane cewa suke wai Iyami mallake Abban mu tayi da asiri...ni dai a lkcn ban fahimci kan zancen sosai ba balle in san manufar ta, baya ga haka itama a bakin mutane ta ji, kuma na tabbatar hasashe ne ba gaskia ba...sai dai yau da gobe ya wuce wasa, da farko ban sa zancen a raina ba amma yadda lokaci guda naga Abba na mantawa da ni cikin gidan, sannan abubuwa na sauyawa zuwa wani yanayin da ba shi na saba gani ba ya sani na fara kokonto a zucia ta, da kaina na fara zargin wancan maganar, a hankali kuma na fara tabbatar wa zuciya ta ita...duk da yake bani da tabbaci amma dukkan alamu sun bayyana hakan. Dalili kenan da ya sanya na lafta masa uziri har cikin zucia ta, ina kuma yi masa addu'a da fatan lkcn da zai tuna wacece ni da matsayin da Allah ya bani na zamowa 'ya agare shi yayi saurin zuwa, wallahi badan Yayana ba da bansan yanda zanyi da rayuwa ta ba, Allah kadai nake da shi sai kuma Yayana, shine fa suttura ta takalmi na idan ya mutu shine, sabulun wanki na shi, shike tunawa da cewa muhalli na babu fitila ya kawo tocila, haka idan ya fahimci babu batiri da kansa zai siya ya kawo min dan yasan ni ba tambayar sa zanyi ba, Yayana shike zama ya binciki matsayin ilimi na ya kuma 'daura min.akan wanda nake da shi.. duk dama ba boko nake yi ba tuni na barshi, amma Yayana bai bari na batare da ya tunatar da ni muhimmancin ilimi ba musamman karatun Alkur'ani mai girma ba, shine ka'dai me zama yaji damuwa ta shine farin ciki na wanda zan gani inji cewa erh ina da 'dan uwa a dunia, shine ya sa nake jin kaina erh nima.wata abace a duniyan nan, duk sauran 'kannan sa da suke uwa 'daya basu sona basu 'kaunar gani na sam hakan bai sa ya zuna idanu yana gani a wulakantani cikin gidan ba, Yah Bukar bai ta6a yi min wani abu dan ya cutar da ni ba sai dai ya 'kare ni da shi...'yan uwa na kuwa nima ban damu da shiga cikin su ba sbd basa kaunar gani na tare da su. Lokacin da labarin cewa Yah Bukar zai fara sana'ar sai da dabbobi zuwa Maiduguri da sauran jihohi ya riske ni, ba 'karamin tashin hankali na shiga ba, Allah ya sani bana so yai nesa da ni domin shi ka'dai ne mai kulawa da ni da damuwa ta...nasan idan baya kusa da ni ba 'karamin gararin rayuwa zan shiga ba. Sai da ya zauna dani sosai ya lalla6ani ya taushi zucia ta da kalaman kwantar da hankali sbd sam na kasa daina zubda kwalla sbd tafiyar tasa. Daga 'karshe mun rabu da ina mai yi masa addua da fatan nasara a ko'ina. Haka zai je yayi kusan sati ko sati biyu sannan ya dawo...nasara ta farko da ya fara samu gaba na yazo ya baje ta ya nuna min cike da farin cikin sa nima ina taya shi, yace insha Allahu sai ya bawa kowa mamaki a lokacin aure na tunda yanzu sana'a ta kar6e shi, shi dama a yanzu baya da burin da wuce yaga ya aurar da ni lafiya 'kalau..ya kuma fitar da ni kunya ya bawa mara'dda kunya...Alhamdulillah kuma da alamu Allah nason shi da Alkhairi yana kuma son ya cika al'kawarin da ya 'daukan ma kansa. A cewar sa. Ni kam ban iya nace masa komai ba illa murmushi..zo kaga zuciya ta fal murna Zaituna zata yi aure ta haifi jinjiri itama...burina fa ka'dai kenan ni, sai dai wannan burin ban bari koda wasa na ya san da shi ba..daga 'karshe addu'ar cigaba da samun nasara na ringa zuba masa, da ya tashi tafiya kuwa har yimin kyautar Naira 'dari hudu cikin ku'din da ya samo. Ido na zaro sosai ina kallon ku'din nace" Yaa me zan yi da wannan ku'din har haka?" Yace ki ajiye a wurin ki idan bana nan ki ringa siyan abu da shi. Nace a a Yace" zaki 6ata min rai 'kanwa ta..ni 'din ne ban isa nayi miki abu ba ko kuwa me kk nufi...?" Hakuri na bashi gami da yi masa godiya sosai sannan ya tafi...sai dai me...wallahi ni ban 'kara sanin inda ku'din nan suka yi ba cikin 'dakin, sama ko 'kasa sam ban ga ni ba, ranar ma sugar nayi niyyan siya Iyami ta bani koko ba sugar shine na tuna da ku'din na duba ai kuwa ku'di yace ba dai ni ba.... Ban zargi kowa ba haka kuma ban saka damuwar ku'din araina ba da yake dama ba saba ri'ke su nayi a hannu na ba. Salmerh 😘 [25/12/2022, 11:19 am] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Wattpad@* _Serlmerh-md_ 🅿️ *...85* .......Kwanaki na ta tafiya lokaci na shu'dewa, amma an dauki tsawon lkc ba'a saka ranar auren mu da Babagana ba, Baffah Liman cewa yayi ko ma shekaru nawa ne za'a 'dauka suna nan bazai ta6a bawa bawa Babagana aure batare da ya ri'ki kwakwarar sana'ar yi ba, sbd har alkcn Allah bai nufe shi da dacen sana'a ba, yayin da Baffa Liman ke ganin kamar da gayya yake yaki.mayar da hankali ya samu sana'a tunda ga sa'o'in sa nan duk suna da abinyi sai shi. Ni kuwa zuwa lokacin sosai na 'kagu inga anyi auren duk dama ban furta hakan ga kowa ba hatta Dije bata sani ba, amma ina da dalilai na da ni ka'dai na barwa kaina sanin su...ba wai dan ina 'kaunar sa ba ba kuma wai dan sbd bu'katar kaina ba..amma sosai na 'kagara inga na bar gaban Iyami ko dan in samu 'yancin kaina da kaina. Gashi yanzu Babagana ya fara zuwa zance, Iyami sai ta tayi min habaici wai sai dai muta bin bango ni da shi kullum amma bata ga ranar auren ba, ni fa bansan me hakan ke nufi ba a zahiri amma har ga Allah maganganun nata na matu'kar 'kona zucia ta. Shi kansa Bbgana idan yazo ro'ka na yake akan in taimake sa in sanar da Baffah cewa ko babu sana'ar ma zamu iya zama tunda yana nema kullum kuma baya rasa na rufin asirin da yasan zai iya rike mu da shi. Yace shi bai san meyasa Baffa ya zafafa da yawa ba, ba dan.shine ya haife shi.ba da ya sai yace Ni 'din.ce Baffah baya son bashi, amma mahaifi yake agare shi da ya tabbatar bazai cutar da shi ba. Ni kaina nasan hakan, na kuma san gata Baffah ke son masa ba komai ba, a yadda yake a yanzu idan aka cigaba a haka har aka yi kasadan bashi aka kuma fara ciyar masa da ita to kuwa zuciyar sa mutuwa zata yi bazai ta6a yun'kurin neman na kansan da gaske ba, amma ya kasa ganewa. Ni dai idan ya fa'di cewa in samu Baffan kallon sa kawai nake yi da mamakin sa, taya yake yake tunanin zan iya hakan, wace iriyar rashin kunya kenan zan ce na aikata? Wani sa'in idanu nake 'kwalalowa sai in girgiza masa kaina. Wani sa'in kuwa ce masa nake ni gaskiya bazan iya ba, sai yace wai in fadawa Yaa Bukar to...sanin da nayi cewa shi ka'dai zan iya samu da maganar ne ya sani amince masa a tunani na zan iya shi 'din sai dai koka'dan da ya dawo naji bama zan ta6a iyawa ba, shine ma ke min mitar hukuncin da Baffah ya yanke kan batun auren namu dan shi a fa'dar sa wai duk shirin sa ya kankama Baffa kadai ke son mayar da shi baya, sam a ganin sa bai kyauta ba, shi aure ai haske ne, yace ko muma lokacin da mukayi auren ai babu wani abin arziki, kusan kullum ma agida muke cin abinci musamnan idan damina ta tsaya dan a lokacin ko'ina babu sau'ki, to da ikon Allah ba gashi tun ba aje ko'ina komai ya daidaita ba har muma zamu iya aurar da wasu..." Yayi maganar yana kallona ni dai ban iya na kalle shi ba illa murmushi cikin raina nake ayyana da alamu dai Yah Bukar bu'di ya samu. Bana yawan shiga gidan sa amma a bakin Ummaru nake yawan jin zancen.." Sun ci abu kaza da kaza nakan ji da'di har raina da jin cewa rayuwar 'dan uwa na ta fara sauyawa, ko muma agida ba laifi abincin mu ya 'dan sauya salo ba kamar baya ba gaskiya, hatta Yaaganan mu ma idan taji labarin yazo ta kanzo yayi mata ihsani ta koma gidan ta cikin jin da'di..Iyami kam ai ba'a cewa komai, ni kuwa duk lokacin da ya bani ku'di idan na ajiye bana sake ganin su koda kuwa na canza wurin ajiye ne, to ma ina ne lungu da zan wani iya ajiye ku'di a 'dakin, daga gadon kwangwalar da ke 'dakin da 'yar tabar ma akai shike nan sai jakar kayan sawa na...daga haka 'dakin babu komai to a ina zan ajiye da baza'a gani ba. Sittira wannan idan sabuwa ce ya siyomin da kasafai ake bar min nema nake na rasa ta, shiyasa kullum nake nan.cikin tsummokarai, idan ya lura da haka ya tambaye ni inda kayana suke kuwa sai ince masa suna nan kawai. Ban ta6a damuwa da rashin ku'din ba dan dama ni saba kashe su nayi ba, amma rashin kayan na matukar kona zuciya ta, duk yawancin zuwan sa kuwa sai ya kawo mana kaya ni da Khausar da Ummaru a hakan dai nake 'dan samun nasawa. Bansani ba ko ya lura da hakan ne yasa yanzu idan yazo da kaya zama yake cikin gida yace kowa yayi wanka ya sanyo kayan yana so ya tantance wanda bai iya kwalliya ba. Hakan kuwa ake yi duk sai mu shiryo cikin sabbin kayan mu dan ya gani, yakan kuwa yaba mana baya yadda a kushe kowa sai dai zai gyara maka inda ka kuskure. Kayan nan kuwa idan an saka shi sai na kwana biyu nake cirewa, na kance ko da na rasa ma ai dai na mori abu na. Cikin ikon Allah kuwa sai na lura idan na sanya kayan bana rasa shi ni ke kashe abina...anan na fahimci manufa da dabarar Yayan nawa. Da wannan dubararcta Yaah Bukar na 'dan fara saka kaya mai kyau nima. Matar sa ce ma naga tana 'kara wani shan 'kamshi idan tazo gidan namu sai ta ta wani harha'de rai tamkar dole aka sanya ta zuwan bansani ba, a ahakan kuma Iyami tai ta ji da ita tana jan ta a jiki ana nan nan da ita, ni dai kya6e baki kawai nake yi idan yaron ta yazo kusa da ni in 'dauke shi in yi masa wasa idan kuwa bai zo ba nima ban zuwa in 'dauke shi saboda nasan masifa za'a min idan ma naje dan 'daukar sa. Hamma Bukar bai sake samun damar jimawa a gida ba sai da lokacin damina tayi, lokacin kam ya dawo ya zauna saboda noma amma jefi-jefi sukan je su yo kwana biyu su dawo. ***** ......Lokacin damina lokaci ne mai matu'kar ni'ima da haka kuma mafi yawancin mazauna karkara kan ji da'din yanayi na damina, musamman saboda sukan wadatu da kayan ganye su sarrafa zuwa nau'ika daban- daban...sukan sarrafa su a duk nau'in da suke bu'kata suci su sha ruwa. Kusan kowa na jin da'din wannan yanayi...sa6anin ni ka'dai, domin mu a gidan mu da zarar damina ta kama to fa babu wani abinci da Iyami zata ri'ka da ya wuce dambu...ni kuma har ga Allah bana so, bana 'kaunar cin dambu sam kuma duk.wanda ya sanyi ya san hakan...amma ita ko ajikin ta sam bata damu ba, inci ko kar inci ba damuwar ta bane ban sani ba mugunta ce ko ra'ayin ta ne hakan kawai. 'Karin abin takaici kuma nice mai 'debo mata ganyen a gonar Abban mu, kusan kullum da na kammala ayyuka na na gida zata tura ni jejin, yakuwa, kalkashi ko kuma zogale in ciro in kawo mata ta shanya wasu wasu kuma ta sarrafa su zuwa wani abin da ciki zai iya 'dauka aci ayi bacci, ba wai dan bamu da abincin da zamu ci ba sai dan iko da isar da Iyami ke da shi a gidan...Yah Bukar yayi yayi da ita akan ta daina tura ni jejin nan musamman saboda abinda ya faru dani shekarar da ta gaba ta amma abanza Iyami kam babu ruwan ta, haka zanje in ciro mata ganyen kullum ta shanya wanda zata shanya wasu kuma ta bawa sirkar ta Azeema yayin da wani kuma ta kanyi amfani da shi a cikin gida. Abin har ya fara zame min jiki, ba na ma damuwa yanzu, ba kuma sai ta maimaita min ba tuni na saka shi cikin jerin ayyukana na kowace rana. Shima Yah Bukar gajiya yayi da magana ya 'kyale ta..hakan ma gara shi akan Abban mu, dan shi tamkar ma babu shi cikin gidan namu yanzu, abin nasa ma sai na lura kamar gaba gaba yake 'karawa, yanzu fa komai ma sai abinda Iyami tayi a gidan ta kafa doka ta kuma shimfi'da shara'din ta yadda taso, shi dai nashi ido ne na amsawa yace to ko kuma ya sake jaddadawa. ***** ......Kwance nake rub da ciki saman gado na da shikan sa zan iya cewa 'kara min ciwon jiki yake, wata shekararriya kuma yamutsatstsiyar tabarma ce akai sai wani bargon da ni kaina bazan iya fa'din shekarun sa ba, sam 'dakin babu komai da zaka gani na jin da'din rayuwa amma hakan bai sa 'dakin ya kasance 'kazantacce ba, kullum tsab zaka gansa a share hatta samintin 'kasan 'dakin bazaka ta6a yin shayin zama akai ba saboda yadda nake 'ko'karin goge shi..babban abinda yasa Hamma Bukar ke ji da ni kenan, saboda tsabtar da yake ce ina da ita, har fa'da yake da alfahari akan sam Zaituna bata da 'kazanta shiyasa ko ka'dan bai jin shayin siya mata ko wani irin kaya, baya shakkan wadata ta da sabulai dan yasan ba asarar ku'din sa yake yi ba..idan na tashi wanki kuwa agidan hatta kayan Iyami da su Khausar bana bari kaf nake wanke musu da na Ummaru dake gidan, shima Yayan nakan sha damun sa akan ya kawo kayan sa na wanke masa mana sai yace a a na bari ai Azeema na wanke masa kuma shima 'din duk ranar da ya samu zama da kansa yake wankewa...ni dai ban ta6a yin kwanaki biyar batare da nayi wanki ba sam bana barin kayana su zauna da datti. Zani ne da riga ajiki na sai kuma wani hijabi na na roba mai ratsin ba'ki- ba'ki, idanuna lumshe suke yayin da fuska ta ke fuskantar 6angaren gefen bango, cikina ke matsanancin ciwo amma saboda karfin hali yasa ko ka'dan a duba na farko bazaka ta6a fahimtar halin da nake ciki ba, ta 'kar'kashin ciki na na cusa hannu ina mammatsa cikin da shi wai ko zan 'dan ji sassauci amma ko gezau, yanzun nan fa shigowa ta 'dakin bayan na samu na kammala ayyukan cikin gidan a daddafe, barka na ma yau Ummaru bai kwana gidan namu ba, yau Khausar ma azumi take yi sa6anin jiya da batayi ba, hakan yasa yau 'din babu batun karin safiya tunda ma Ummaru baya nan, jan ruwa shine abu na 'karshe da nayi wanda kuma shine ya haddasa min jin jiri sosai har yawun bakina na nake jin na ka'fewa, da 'kyar na samu na lalla6a na kammala ina yi ina hutawa har na samu na shigo 'dakin. Tun daga 'kirji na nake ji a tokare, zuciya ta kuma na min 'kuna, ga ciki na da ya kumbura sosai rabon da na iya sanyawa cikina wani abin tun jiya da akayi bu'da baki, ko da aka tashi sahur ma kasa cin komai nayi. .....Ina daga kwancen nake iya tsinkayo muryar Iyami dake zaune gefen Khausar daga ba'kin 'kofar ta, daga nan 'din take karantowa min abinda zan yi na gaba wato na tashi na tafi jeji na 'debo mata ganye. " Tun wuri ki tashi ki wuce kafin anjima azumin ya fara ratsaki kije baki 'debo min abin kirki ba...". Abinda Iyami ta fa'di kenan wanda yasa ni lumshe idanu, cikin zuciya ta nake jin wani turnu'kin ba'kin ciki da takaici na taso min, banda tsoro da fargaba da ya cika min zuciya tun cikin dare ban kuma san na menene...wasu hawaye ne suka cika min cikin idanu ina jin zuciya ta na tsananta bugawa a fili na furta" Har abada Iyami bazata canza ba...". Haka na furta batare da nayi yun'kurin motsawa ko kuma tunanin wani zai ji ni ba dan nasan ni ka'dai ke rayuwa cikin akurkin 'dakin nawa Wannan zuwa jejin gaba 'daya ya ishe ni wallahi, kullum ina zuwa meyasa yau ka'dai bazata yimin uzuri ba, shin da wanne zanji? Da ciwo da nake ji ko kuma da fargabar dake damun zucia ta. Ga tabon da hakan ya jaza min har yau 'din nan bashi da alamun 6acewa, ko jiya mafa da naje jejin sai da naci karo da wani al'ajabin mai ban tsoro, shi kansa ya kasa barin raina, tsoron saoe komawa nake har zuciya ta. Gaba 'daya sai naji duniyar ma ta ishe ni gaba 'daya, mafita nake nema amma na rasa ta, ban ta6a sanin cewa gata abin nema bane sai yau din ka'dai, ban ta6a sanin cewar rashin gata babban 'kalubale bane sai yanzu. Juyi na sake yi ina mai tunano abinda ya faru jiya a jeji da ya matukar tsaye min zuciya....da yake Ummaru ya raka ni jiyan hakan ya sa da ya hango tsuntsu a 'kasa yana fikim-fikim ya tafi da gudu yana murna da fa'din" Yaah Zaituna kizo ki kamamin shi..." Da murmushi na 'karaso inda yake hannu na ri'ke da buhun da muka taho da shi dan 'debo ciyawan dabbobi da kuma ganye a ciki. Gefe na ajiye buhun ina mai tsintan zuciya ta na cika da tsananin fargaba, kallon tsuntsun nayi na kuma kalli Ummaru da ke ta washe ha'kora yau ya samu tsuntsu. Yana shirin 'dago wa ya mi'ka min nayi saurin dakatar da shi da fa'din" Kai!..kyale shi, kar ka ta6a shi baka ga bashi da lafiya ba ne?" Na fa'di hakan ne dan in hana Ummaru ta6awa amma a zahiri ba hakan ya sani hana shi 'dago tsuntsun ba, jikin sa da na gani duk layu shine ya bani tsoro. Ummaru kam kuka ya fara min wai shi sai ya 'dauka jin hakan yasani fa'din" To duba abu ko ma 'dan kwalba idan ka gani mu cire masa wannan abin in yaso sai ka 'dauke shi...". Nayi maganar ina 'dan dube-dube ina wara idanuna a 'kasan wurin..." Yauwa ga can wani fasashshen kwalba 'dauko". Na nuna masa in da na hango kwalbar, da 'dan gudu ya tafi ya kawo min sannan na maida kallo na izuwa ga tsuntsun da ke kwance a 'kasa har yanzun yana ta bori da alamu ma mutuwa zai yi. Tausayin sa sosai naji ya kamani, hakan yasa cike da tausayawa na 'dauke shi a hannu na, durkuso nayi na ajiye shi gaba na, la66ana duk na shigar cikin baki na ina tunanin ta inda zan fara yanke masa wannan sar'kewar dake jikin sa, zuciya ta cike da mamakin inda ya har'de har haka shi da ke tafiya a sararin samaniya me ya ha'da shi da shrigin layu? gashi har yana neman rasa ransa abanza. Cikin natsuwa da takatsantsan nabi duk na yan-yanke masa layun dake jikin san, Allah cikin ikon sa kuwa duk da hakan be yi rai ba, dan ina gama cirewa shima yayi 'dif. Na jima dur'kushe a wurin ina jimami, a hankali na kai duba na wurin shirgin da na cire masa, sai a lkcn kuma na ji fargaba ganin tulin layun dake jiki, gashi kyakykywan 'dauri aka yi masa ga dukkan alamu ba da kansa yayi hakan ba. Ummaru na kalla da shima ya zuba min idanu duk muka yi tsam da ran mu kowa abinda ke cikin zuciyar sa daban. 'Dan karkata kai nayi gami da kamo hannun sa na dama nace" Ka ga ma fa ya mutu ka bari zan kamo maka wani kwanan kaji yaro na..?" Shi dai bai ji da'di ba amma sai ya 'dage min kansa alamar yaji. Sakin hannun sa nayi na maida duba na izuwa tsuntsun sannan na koma kallon shirgin dake gaba na. Cike da rigima na fara yayyanka layun 'daya bayan 'daya..wani bana ganin komai a ciki sai farar takadda, sai na ukun da na wawware ciki naga wani abu kamar gashin kan mutum abin ya bani tsoro sosai. Cikin hannu na na hagu na tattaro su, buhun nawa na tsugunna na 'dauka sannan na fito bakin hanya da su, gefe can naga wata 'yar 'karamar bola na tashin haya'ki ga dukkan alamu an tattare wurin ne kasancewar gobe ranar kasuwa ce. Cikin wutar naje na je fa su daga haka na kakka6e hannu na na sake kama hannun Ummaru muka muce wuce jejin. Sai da muka koma gida ne ina bawa Hamma na labari dan nasan shi ka'dai ne zai iya zama ya saurari labarai na, a hakan ma Iyami sai hararar mu take yi tana kya6e baki. Shi kam mamaki yayi kwarai da gaske domin ya kasa 6oye hakan cikin zuciyar sa har sai da ya furta" Allah sarki" muryar sa cike da yanayin tausayawa yace" Allah ya sakawa mai shi...". Jin hakan yasa na 'kwalalo ido da mamaki nace" Hamma ba fa nice na kashe Tsuntsun ba, Allah ka tambayi Ummaru ma kaji.." Na 'karashe maganar idanu na na tara ruwan hawaye. Sai yayi murmushi mai sanyi yana kallo na yace " Ni fa bance kiyi min kuka ba ai nasan 'kanwa ta ba zata iya kisan ko da 6era bane balle tsuntsu..ki kwantar da hankalin ki ba da ke nake yi ba...ai da alamu wani aka shilla duniya da wannan tsuntsun da kk gani..." Da ido kawai nake kallon sa domin bangane manufar sa ba sam fahimtar hakan da yayi ne ya sashi yi min bayani filla-filla. Hankali na tashi yayi sosai har ina hawaye domin ni Allah yyi ni da uban tausayi na masifa, har kamar zan yi sashshe'ka duk da ban san wanda abin ya faru da shi ba....amma na taya mai shi bakin ciki gaskiya, ayanda na fahimci zancen kenan an raba shi ne da gida da duk 'yan uwan sa...to duk saboda mene hakan wai?" Kai na grigiza cikin zucia ta nake fa'din" Yah Allah ka shiryi mutane ka kuma rufa mana asiri ka raba mu da mugaye daga cikin bayin ka....Ameen.." Iyami ce ta azazzali Hamma da fa'din" ka wani zauna kana ta surutan banza kar ka tashi ka wuce in da zaka, in dai wannan ce sai ta yini bata gaji da jero maka tambayoyi ba...mthew." ta 'karashe da jan tsaki, ni kam murmushi nayi daga haka na tashi na shiga 'daki zuciya ta cike da tausayi tsoro fargaba gami da jimamin zalunci irin na mutane. Salmerh😘 [27/12/2022, 8:53 am] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Wattpad@* _Serlmerh-md_ 🅿️ *...86* .......Ban gama watsar da wancan al'amarin cikin raina ba sai gashi yau ma Iyami na shirin turani jejin, wani lokaci sai in ga kamar da gangan kawai take yi min hakan saboda mugunta ko kuma wani abin daban. " Zaituna!" Na sake jiyo muryar ta a akaro na biyu. Ko.nace zan amsa sautin murya ta bazai fito fili har ta ji sakamakon zazzafan yaanayin da nake ciki. " Ke Zaituna!! N sake tsinkayo muryar Iyami dake furta sunan nawa cike da izza da masifar da ya cika mata zucia. Hakan kuwa shi ya ankarar da ni cewa ashe fa tun 'dazun take faman 'kira na ina can ina shirin zurfafa tunani. Wani abu ne me 'daci naji ya tokare min zuciya, 'kirji na ne ya cigaba da bugawa da 'karfi yayin da sautin muryar Iyami ya cigaba ta kara'de gidan namu, masifa take da iya karfin ta tana faman aibatani. Tsawon wani lkc tana abu guda, yayin da nake sake ji jiki na na min nawi sosai, bansan lkcn da 'kwalla ya fara kwaranyo min ba, kalma guda ce da kusan kullum sai na ambace ta har yau din kuma na rasa amsar ta. " Shin da wanne zanji...?" Kusan kowace rana sai abubuwa sun ca6e min na rasa mafita guda. " Yah Allah ka dube ni, ka saukaka min al'amura na...Yah Allah idan bari na duniya shine min alkhairi kuma sau'ki ga zazzafar rayuwar da nake ciki Yah Allah ka 'dauki raina badan na gaji da yi maka bauta ko gajia da jarabtar da ka 'daura min ba, Yah Allah ka 'dauki raina kana mai yarje min cikin aminci da salama ka sani cikin bayin ka salihai..." Duk yadda naso katange kaina da kunnuwa na daga sauraren masifar da Iyami ke sauke min abin ya faskara. Da 'kyar na bawa kaina 'kwarin gwiwar da har na iya sakko da kafafu na na zauna da 'kyar ina me sakin wahalallen numfashi. Na 6ata kimanin mintina uku kafin na iya mi'kewa tsaye saboda yanda nake jin 'kirji na, banda jiri da nake ji na shirin 'diba na. Gyara zaman hijabin da ke kaina nayi idanu na kokarin lumshewa..bango na dafe na fara takawa a hankali, amma bazan iya mi'kewa tsaye tsaf kamar yadda na saba ba. Sam bana so, bana so bana 'kaunar wannan dambun da Iyami ta nacewa yin sa kullum, watan azumi fa muke amma dan mugunta irin ta Iyami sai dai ta dafawa mutane dambu shi kuma Abbah ba zai ce komai ba. Hamma na ne ma idan ya sani zai yi magana amma shima gidan sa yake bu'de baki sai dai ya aiko mana 'dan abinda ya sauwa'ka wanda ni kam ma ban ta6a gani da idanu na ba sai dai in ji 'kamshi ko kuma Ummaru ya bani labari ko ka'dan kuwa ban ta6a sawa raina damuwa ba, ni Hamma na ya wanke min komai, dalilin sa nake yiwa Iyami uzuri bisa abubuwa da dama ban fiya ganin laifin ta ba. Shi da kansa yanzu ya hana ni wanke-wanke yace sai dai Khausar ta ringa yi ai itama ba yarinya bace tunda shekarun ta goma sha biyu yanzu..dole badan sun so ba Khausar 'din ke yi amma 6angaren Iyami da Khausar 'din kuwa tsanata ne ya 'kara ninkuwa musu a zuciya. A hakan ma ba bari nake kullum tana yi ba na kan kar6a in tayata kusan kowacce rana amma maganar kirki bata hada ni da ita. Haka na tabbata da Hamma na ya san ba'a bani abin da yake aikowa da zai ringa kawo min nawa ne daban, amma ban damu ba, ban kuma ta6a 'daura aniyar sanar da shi ba, na riga nasan komai da lokacin da Allah ke 'debar masa, ko babu aure akwai mutuwa ai, watarana sai labari...dole sai dai wani ne zai tuna da wani, ni kuwa ko da wani lokaci fata na shine a ko'ina a tuna da Alkhairi na ba sharri ba. Kaina a 'kasa na tako da 'kyar 'kafafuna na har'dewa, wallahi lokuta da dama har fargaban shigowar yanayi na damina nake yi saboda irin wannan lamari. Ga shi ni a rayuwa ta babu abinda nafi tsana cikin abinci sama da dambu, ban sani ba ko sanin hakan da Iyami ta yi ne ya sanya ta nacewa yin sa kullum ta kuma tilasatwa kowa cinsa domin daga shi bata sake dafa wani abin sai ta ga dama....kowa ma agidan yanzu ya saba hatta Abba cin abin sa yake yi ya sha ruwa hankali kwance. Ni ka'dai ce wacce ciki na ya kasa sabawa da shi, ban kuma san ta yadda zan 6ullowa Iyami ta fahimce ni ba, ban kasance ma'abociyar cin abincin gidan mutane ba duk kuwa da irin shige-shige da muke yi ban fiya shan ko da ruwa ba har sai na dawo gida...ba tun yau Iyami ta fahimci bana so ba amma ta kawar da kai ta cigaba da yin abin ta duk lokacin da ta ga dama, kafin watan azumi ya tsaya ma sam bana kulawa idan tayi da rana to bazan ma kalli inda yake ba kawai sai injira abincin dare inci in kuwa da rana tayi sa to haka nake kwana banci abinci ba..yanzu kuwa da ya kasance yanayi na azumi dole ne sai ka ci abinci shiyasa nake tilastawa kaina cin sa duk da kuwa nasan illar da yake wa ciki na. Kaina a 'kasa na fito ina jina tamkar zan fa'di idanu na na zuvar da hawaye, da ganin fitowa ta Iyami sai taja tsaki....inda ta cigaba da masifa" Shashancin banza da wofi, ina fatan dai kin ji abinda nace kika wani zo kaina kina 'kif'kifta min idanu iwa mage...da shegen munafukin hijabin ki na gadon tsiya kamar sanin Allah kika fi mutane...." Yaa Bukar da shigowar sa kenan turus yayi yana duba na sannan ya dubi Iyami...a hankali ya 'karaso yana daga tsaye yake tambayar Iyami me ke faruwa kuma da safen nan Iyami?" Ya 'karashe maganar yana me sau'ke idanun sa akaina, 'kasa na sake yi da kaina daidai lokacin da naji wani suka a 'kirji na amma ko motsin kirki ban yi ba balle in nuna alamun jin hakan da nayi ko kuma yin yunkurin dafe 'kirjin nawa, hawaye na kawai ya gangaro da gudun gaske sanadiyyan rintse idanu da nayi. Iyami maimaita abinda ta fa'damin tayi na zuwa mata jeji amma bata maimaita zagin da tai min ba, da yake sarai tasan halin Hamma Bukar yanzun sai yace sam bazani ba, hakan yasa ta canza salon sautin ta izuwa ga lafazi mai sanyi ta kuma 'karashe maganar tana mai kawar da kanta. Da jin abinda ta fa'di kuwa take ya ha'de fuska sosai yana duban ta yace" Haba Iyami..." " Sannu Uba na...". Ta furta a fusace ranta a matukar 6ace...batare ma da ta bari ya kai karshe ba, domin ta riga tasan karashen zancen indai Hamma Bukar akan Zaituna ne. Saurin rage sautin muryar sa yayi yace " Kiyi ha'kuri Iyami, ba haka nake nufi ba, amma ki tausaya mata mana, da bakin ki fa 'dazu kike ce min ko sahur bata tashi tayi yau 'din ba kuma kinsan ba haka nan kawai a banza taki tashin ba sai dan rashin jin da'di da take yi, yanzun ma ita na shigo dubawa kafin in wuce, kuma fisabilillahi ahakan zaki sake tura ta jeji Iyami?..ki duba lamarin dai...". " Ke kinsan Zaituna bata da son jiki, yau ka'dai ayi mata uzuri mana dan Allah Iyami..." " Yo ai gani nayi jinyar ba kwantar da ita tayi ba kawai fa tsirfa ce da shegen langwami da ke damunta..". " Ko ma dai menene Iyami zuwa jejin nan kiyi ha'kuri da shi, ki barshi zuwa gobe idan ta samu sauki ba sai taje miki ba, amma yau kam gaskiya babu inda zata je, yarinyar nan idan tana da lafiya bata yi miki musu kullum na yau ka'dai kam ba zai zama abin damuwa ba...dan Allah Iyami kiyi mata uzuri ki barta na yau ka'dai...". Yana gama fa'din hakan bai ma jira amsar ta ba ya dawo da kallon sa gare ni yace" Ki koma 'daki ki kwanta idan na fita zan aiko miki da magani sai kisha kinji.. ba dai cikin ki ke ciwo ba?" Ya tambaye ni cike da kulawa. Kaina na 'dage masa batare da na kalli ko da 'daya daga cikin su ba. Daga haka ya sa kai yayi waje Iyami ta raka shi da doguwar harara, ni kam raina fes dan nasan ba zuwan kuma zanyi ba tunda ya hana nasan ya hanu...tsaki ta saki bayan ya 'karasa ficewa sannan ta dawo gare ni ta bankamin wata uwar hararar da ya sanya ni jin 'kafafuna na rawar mazari. .'kasa na sake yi da kaina sosai wannan karan hawaye na bai sakko ba jin bazan je jejin ba. " Dama me ke damun ki?" Ta tambaya a matu'kar hassale, dan ji take tamkar ta make ni. " Ciki na ne ke ciwo Iyami". Na bata amsa da sanyin murya ta batare da na kalli inda take ba. Sake hassala tayi ta hayyako kaina wanda ya sani takure kaina waje guda yayin da ta cigaba da fa'din. " Shegiya munafuka, in ma mene ke damun ki ke kika sani, mutum kullum 'kun'kunsun cikin hijabi kamar wata mutuniyar arzi'ki, saura kuma goben ma ki tsirfo min wata 'karyar kiga maganin ki da zanyi, dambun da kika raina kike yangar ci 'din wataran fin 'karfin ki zai yi matukar ina numfashi, ba dai Babagana kike 'kwa'kwa ba.. muna nan ai...". Ta 'karashe da yin 'kwafa gami da juyawa tayi gaba. " Ki yi ha'kuri Iyami...". Na furta cike da sanyin jiki da marairaita dan har ga Allah banji dadin furucin ta ba, kuma kalmar ha'kuri da na furta ya taso min ne tun daga can 'kasan zucia ta. Sai dai ban san takamamman dalilin da ya sani furta shi gare ta ba. Ban kai ga rufe baki bama Iyami tayi saurin waigowa a hassale ta tare ni da fa'din" Uwar ki zanyi munafuka...bazan yi ha'kurin ba 'yar iska kawai...annamimiya". Ni dai ban damu ba na juya na koma cikin 'daki na ina mai jin farin ciki da hana fita ta da Hamma yayi, dan nasan ko da ma na fita yau 'din da 'kyar ne in iya yi mata abinda ranta ke so dan sosai nake jin babu da'di a jiki na Ba dan ba zai yiwu ace kayi azumi baka ci abinci ba ai da banga abinda zai sani cin wannan abin ba, sai ma naga na yau 'din yafi wahal da ni fiye da kullum kasantuwar rashin be ta6a yi min irin hakan ba, kuma fa har a lokacin banji mur'dawar ciki ba balle inyi gudawa, 'kirji na kawai naji ya tokare ni sai ciki na da ya kumbura sosai gashi idan zan yi tafiya jiri ke 'diba na. Lumshe idanu na nayi bayan nazo na mi'ke a 'kasan 'dakin nawa sanyin simintin na ratsa ni, tuno cewa jiya dambun Iyami ya samu kuskure da nayi shine ya sani bu'de idanu na, sam jiya dambun Iyami bai tiraru da kyau ba, sanadin ruwan sama da ya sakko da maraicen jiyan bayan har ta hura wuta, sosai kuwa aka shirga ruwa haka da 'kyar a daddafe ta kammala. Ina da ya'kinin rashin dahuwar dambun ne ya haddasa min wannan ciwon da ya kasance min na daban kuma zazzafa. Ummaru Hamma ya aiko da maganin ya kawo min amma sai naji sam bazan iya karya azumi na sbd wannan ciwon ba, hakan yasa na ajiye sai ansha ruwa sai na sha. Ranar a 'daki na yini bana fitowa sai in alwala zanyi, karo na farko kenan a rayuwa ta da Dije tazo min da labarin anyi haihuwa a makwabtan su amma ban samu damar zuwa ba nace da ita bana jin da'di bazan iya doguwar tafiya ba. Zuwa lokacin na jima da fara jin zuciya ta na tashi hararwa nake son yi amma ya gagare ni gaba 'daya bana jin da'din komai tattare da jiki na. Kusan ko 'ina na ciwo yake min ji nake kamar a bu'de ciki na akwashe min abinda ke ciki ko zanji da'din jiki na. Idanu na duk sun yi luhu- luhu ba 'karamin galabaita nayi ba amma hakan bai hana ni fitowa ba lokacin da na tsinkayo muryar Addah ta tazo gidan ba. Haka na fito cike da 'karfin hali ina 'ka'kalo murmushi na sanyawa fuska ta. Shigowan ta kenan ko zama bata yi ba na fito lokacin suna tsokanan juna da Azeemah matar Hamma Bukar dake zaune kan tabarma gefen 'dakin Iyami. Maraba nayi mata sannan na zaga bayan ta ina 'ko'karin kar6ar goyon yaron dake bayan ta duk a kokari na na gudun kar nayi wani laifi. " Dama nasan abinda ya fito dake kenan". Tayi maganar tana kunce 'daurin goyon da tayi fuskar ta babu yabo ba fallasa. 'Yar murmsuhi nayi ban kuma fasa kar6ar goyon ba. Azeemah ce ta kya6e baki sannan taja 'kafar ta ta gyara tace" Ai kuwa dai..ku masu abinda za'a fito domin sa ba, kinga ni ai duk jimawa ta azaune anan banga idanun ta ba saboda bani da jinjiri a hannu na da za'a kar6a...". " Kema kinsan halin Zaituna ai..sai a hankali in dai akan yara ne.." Cewar Yaagana. Daga haka Yaagana bata sake bi ta kan zancen ba zama kawai tayi suka cigaba da hira har Iyami ma tafito suka gaisa tana banka min uwar harara...da alamu tun abinda ya faru da safen nan bai bar zuciyar ta. Ni kam ban damu ba nayi 'kasa da kaina ina gyarawa yaron rigar jikin sa, watannin sa fa hu'du ne da wasu kwanaki amma idan ka ganshi sai kayi zaton watan sa biyu ne kacan saboda rashin girman jiki. Yaagana ce ke faman fifita da maficin dake hannun ta ta waigo inda nake tace" gaskiya yau garin 'daure yake akwai zafi, Zaituna cire masa rigar jikin sa ya sha iska da Allah.." " Toh..." Kawai nace mata sai ta cigaba da fa'din" Ke kam da alamu baki jin zafin nan, cikin gidan ma bazaki daina zama da hijabin nan ba sai kace wata matar limami..ai ni bazan iya ba wallahi?" Ta 'karashe maganar tana kya6e bakin ta gefe. Iyami ce tayi saurin kar6e maganar da fa'din" ai in dai wannan ce ko cikin 'dakin ma ba cire hijabi take ba yadda kika san haihuwar ta akayi da su..." Azeema kuwa cewa tayi Allah dai yasa na gaskiya ne bana munafurci ba..." Tayi maganar tana kawar da kanta gefe. Daga nan suka cigaba da hirar su...ni kaina 'karfin hali kawai nayi na zauna a wurin amma wani uban gumi nake ji yana karyo min cikin jiki na, wanda na tabbatar na abu biyu ne, na ciwon dake damu na da kuma zafin da ake zabgawa ni kuma gani da hijabi amma sam banji zan iya cirewa ba sbd sabo. Salmerh😘 [29/12/2022, 7:48 am] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Wattpad@* _Serlmerh-md_ 🅿️ *...87* .......Cikin sa'a zuwa yammaci ma sai naji 'kirjin nawa ya sake ni sai dai ciki na dake min mur'da haka kuma na kwana ina fama da shi, da 'kyar ma na 'dan samu na saka wani abu a baki na lokacin sahur sanin da nayi cewar banci wani abin kirki lokacin bu'de baki ba gudun kar azumin ya wahal da ni. Kusan kwana nayi idanu na biyu, ina jin babu da'di sosai cikin raina, na kan kuma yawaita jin fa'duwar gaba duk da dama ba yau na fara fuskantar irin hakan ba, da jimawa na ta6a yiwa Hamma na maganar yace in rin'ka maimaita _La'ilaha illalallahu wahdahu laa sharikalahu yuhyi wa yumit, wa huwa ala kulli shai'in qadeer.._ a lokacin ban ta6a mantawa ba na kan yawaita yin sa kuma Alhamdulillah na samu sassaucin jin yawan fargabar at times ma sai inji kamar ana bin bayana idan ina tafiya amma yanzu duk hakan babu su, sai dai a yau 'din a yadda na lura fargabar tawa kusan duk bayan wasu mintina 'kara tsanani take yi. Sosai jiki nake jin raina babu dadi, gashi har a lkcn banajin dadin yanayin ciki na dan bai sake ni gaba 'daya ba.... Ban 'dora duk wannan matsalolin kan komai ba face Dambu da naci, na kuma 'dauki al'kawari cikin zucia ta kan cewa da iznin Allah.. bazan 'kara cin dambu ba koda kuwa shine ka'dai abinda ya rage da zanci a gidan matu'kar ba shine abu na 'karshe da zanci ya min sanadin aljanna ba, ya wahal da ni kuma yana kan wahal da ni 'din ba da wasa ba. Komin kadan din sa naci baya bari na yin rayuwa cikin natsuwa ta. Yanzu haka fa zawo nake yi zaryar yi, daga lokacin sahur zuwa yanzu na shiga bayi fin sau hu'du...ka'dan-ka'dan nake ji kamar zazza6i na shirin kamani, ga uban fargaba ga mur'dawar ciki dake 'karuwa min, gefe guda kuma zaryar zuwa bayi gashi banda wani da zai tsaya akaina ya kula ni ko in samu arzikin samun magani sai dai Hamma Bukar ka'dai. A hakan a daddafe ina yi ina hutawa na samu na kammala ayyuka na na cikin gida da wuri dan nasan yau kam ciro ganyen Iyami babu fashi ne sai dai in gangan jiki na baya tare da numfashi. Sai dai na kammala komai kafin rana yayi zafi na shirya tafiya jejin da 'yar ledan buhu na da na saba 'debo mata a ciki. Ina ninke ledar nake ce da Iyami " Iyami na tafi jejin..". " Adawo lafiya...kuma a tsinko min masu yawa dan kinga ko dabbobi na ma tun jiyan basu samu ciyawa sun ci ba..kuma ki dawo da wuri babu mamaki Goni shigar safia zai yi..." Da sauri na waigo..." Iyami Goni zai dawo ne dama yau...". Na tambaya cike da jin dadi duk da cewa ba wani shirin kirki ke tsakani na da shi ba...amma 'dan uwa yafi gaban wasa..kuma ba shakka nayi kewar 'dan uwa na sosai...tunda yasa kai ya tafi can kudancin 'kasa ban 'kara jin ko da labarin sa ba sai yanzun da Iyami tace zai dawo. Iyami harara ta 6alla min batare da ta bani amsa ba. Ina 'karasa ninke ledan hannu nake fadin" Allah ya dawo da shi lafia..Allah ya sa ya kawo mana tsarabar kankana..." " Da yake 'kanin ubanki ne ai dole kice haka..." Yadda naji suka da 'dacin wannan zagi na Iyami bazan iya kwatantashi ba. Sosai abin ya min ciwo. Shin menene laifin magana ta..? Ko kuwa laifi ne dan furta hakan ga 'dan uwa na jini na wanda muke uba 'daya da shi. Bansan meyasa naji ciki na ya mur'da daidai da wanzuwar 6acin da naji zucia ta tayi ba. Ledar nayi saurin ajiyewa na 'dauki buta da sauri na nufi bayi domin hakan nafi bukata a dai- dai wannan lokaci. Inaso ina kuka, amma sam ya kasa samuwa gare ni, hawaye nake so in fidda ko zai tafi min da ba'kin cikin da ke cikin zucia ta amma ya gagare ni. Hakan yasa nake jin wani 'daci da bugawar zucia na daban ba irin wanda nake ji a safiyar ranar ba. Bayan wani 'dan lokaci na fito daga bayin...Iyami baki ta kya6e ta kawar da kanta gefe tamkar bata fahimci halin da nake ciki ba. Gaban ta na nufa ina 'dan ciccije baki na saboda mur'dawar da ciki na ke min...yau ko Hamma bamu gaisa ba saboda har yanzun bai shigo gidan namu ba, Abban mu kuwa tuni ya bar gida... " Iyami dan Allah ko Flagyl babu a dakin ki ne insha wlh ciki na yaki daina ciwo har yanzu, wanda Hamma ya sai min jiyan kuma duk na shanye..." " Nima bani da shi..." Ta bani amsar da bazan iya ce ga gaskiyar ta. Tsaye na mike ina yamitsa fuska ta nace..." Toh shi kenan zan wuce jejin.." " Ki dai tabbatar kin ciro min mai kyau kuma da yawa nake so dan nasan halin muguntar ki yanzu sai ki kwaso 'dan ka'dan..dayawa zaki 'debo ina sake gaya miki" " Toh Iyami" nace ina juyawa. Khausar dake can tana wasa na kalla nace" Khausar dan Allah ki 'dan raka ni mana...?" Kafa'da ta noke tana mai cigaba da wasan ta tamkar wata 'yar goye. Yayin da Iyami ta banka min uwar harara sannan tace " Bata zuwa!..salon kije ki mammake min ita ko...munafuka ai duk nasan halin muguntar ki...maza kama hanya ki wuce kafin in sa6a mk..shegiya dangin mayu..". 'Kasa nayi da kaina na kama hanyar fita zucia ta cike da wasi- wasi, wani abu nace min inje jejin yayin da wata zuciyar nace min kawai inje in 'debo mata rayuwa ce ai. Tafiya nake amma sai nake ji kamar ana 'da'd'daure ni, hatta 'kafafuna rawa suke min saboda tsananin fargabar dana ke ciki ga kuma ciki na da ya 'ki sarara min. A haka na tunkari jejin..idan na 'dan yi tafiya sai in samu wuri in zauna dan hutawa, a hankali nake sau'ke numfashi, da ace inada gata nasan da baza'a ta6a tura ni jejin nan ba musamman saboda halin da nake ciki, kulawa nake da bu'kata amma nasan banda Hamma na babu mai bani wannan kulawar a yanzu, sosai nake ji da ganin 'kokarin sa kuwa, shiyasa ma ba ko wani lokaci nake kai masa 'korafin damuwa ta ba saboda kar 'dawainiyar tayi masa yawa, ga ta gidan sa ga ta Iyami ga kuma tawa, Hamma na ba 'karamin 'kokari yake yi ba wajen sau'ke nauyin ahalin sa ba...dan haka akan wannan ciwon cikin bazan 'daga hankalin sa ba. Lokaci sosai na 6ata a hanya domin kafin ma na isa rana ya fito sosai ya haske ko'ina...da yake lokaci ne na Ramadan hakan yasa harkoki da dama suka ragu musamman da safiya ko kasuwanci ma sai da rana aka fiye fara shi zuwa yammaci har izuwa dare...dalilin kenan da ya sanya 'dai'daikun mutane ne zaka ga gani suke gilmawa, garin shiru babu wani hayaniya da zai 'daga maka hankali. Duk da haka fa fargabar da nake ciki koka'dan bai ragu min ba sai ma karuwa har abin na ban mamaki, sai kuma na fara tunanin 'kilan mutuwa zanyi ne shiyasa nake jin hakan, dan ko ciwon cikina 'kara tsanani yayi ba raguwa ba, a hakan nabi jejin na 'debowa Iyami ganyen duk da nasan take so na kamo hanyar dawowa gida, still ina tafiya ina hutawa ga gajiya, ga ciwo ga zafin rana fa nauyin abinda na 'debo banda jiri dake son kayar da ni..tafiya ka'dan ce ta rage in hawo bakin titi sai na ji 'kara garam mai firgitarwa, tsam na tsaya daga inda nake jiki na ya fara rawa bana iya hango bakin titin saboda yawan bishiyoyi amma daga inda nake kunnuwa na na iya jiyo abinda ke faruwa. Ri'kon ledar na gyara a kaina na fara taku a hankali zucia ta cike da mamakin abinda ke faruwa..dan har takun gudu nake ji sai dai ba dayawa bane dan mutane ka'dan ne ke zirga-zirga cikin garin...ban kuma san me janyo gudun ba. Tsoro ne fal zuciya ta amma nasan hankali na zai kwanta ne kawai idan na tsinci kaina cikin gidan mu shiyasa ban yi yunkurin dakatar da tafiyar tawa ba.... Cak na tsaya take ledar da ke kaina tayi 'kasa sakamakon rage 'karfin riko da hannu na yayi mata, 'dif-'dif na ringa jin zuciya ta na harbawa tana dukan tara-tara, daga inda nake ina iya sake jiyo yanda motoci dake wucewa suke gudu tamkar na neman tseratar da ransu, ga dukkan alamu kuma ba cikin natsuwa suke gudun ba. Sake rirkicewa nayi gashi dama ba kuzarin kirki gareni ba, take ciki na ya sake hautsinewa da ciwo, cikin na dafe hawayen da tuntuni naso jin saukowar su suka ki yanzun ban ma san lkcn da suka fara min zarya ba, take na dur'kushe a wurin ina furta kalmar _innalillahi wa inna ilaihi raji'un...Allahumma ajirni fii musibati wa aklifni khairan minha..._ ...na shiga uku ni Zatituna yau me ke faruwa ne agarin kuma?" Cikin kuka na furta hakan a fili yayin da tsoro na ke 'kara tsanani. Ban kai ga dawowa hayyaci na bisa ga tsoron da ya sarke ni ba na fara tsinkayo nishin mutum na kusanto inda nake amma ban ganin kowa. A firgice nayi baya ina zare idanu amma na kasa 'dauke idanu na daga inda nake jiyo nishin a hakan kuma nake yin baya- baya alamun tsoro 'karara ya bayyana sosai kan fuska ta. Jin nishin na sake tunkaro ni ne ya sanya ni yin baya da sauri ina sake rarraba idanu na. Tsoro ya riga ya kashe min gwiwoyi na dan nasan abu guda mu 'yan wannan yankin ke fama da shi, matukar muka ji irin wannan guje- gujen to tashin hankali ne ya faru na 6ullowar 'yan ta'addah. Ji nayi nishin na sake tunkaro ni sosai, take nayi baya gami da mikewa na ware 'kafa na fara gudu a rikice, cikin jejin na koma ina 'kiran sunan Allah a fili da zucia ta. Sai da na 'dan yi nisa ka'dan da wurin kafin na tsaya na lafe bayan wasu gajerun bishiyu da suka ha'du sukayi duhuwar da na san zai iya 6oye ni. A hankli nake sau'ke numfashi sbd tsoro, hannu na bisa 'kirji na ciwon cikin ma tuni na rasa inda ya shiga, ta tsakanin ganyen bishiyun nake le'ken hanyar da ke gaba na inda na biyo a lokacin jin zuciya ta nake tamkar zata fito kan hannu na, jiki na nasan da za'a tsaga mawuyaci ne a samu jinin kirki a ciki, wuri- wuri nayi da idanu cikin bishiyun tamkarr wata 6era...sai kakkarwa da ilahirin jiki na keyi. Daga 'dan nesa ka'dan na fara hango wata mace na tahowa da 'kyar tana tafiyar hannun ta 'daya nakan tulelen cikin ta, 'dayan hannun kuma ta ri'ke zani da jakar ta da shi. Dur'kuso tayi kan gwiwoyin ta ta ringa maida numfashi da 'kyar da 'kyar, yayin da gumi ke tsatsafo mata ta ko ina. Ba bukatar tambaya, domin da ganin ta kasan ba 'karamin galabaita tayi tashin farko za kuma ka fahimci cewar cikin wahala take wanda bata saba shiga irin sa a zahiri ba. Sai a lokacin na fahimci hawaye na gangaro min sosai bayan na tsura mata idanu sosai, bazan yi 'karya ba har ga Allah ta bani tausayi domin wani gaban yafi gaban wani, ko kusa ko alama ciwon ta ya bambanta da nawa...tuni kuma ganin ta yasa nawa ciwon tafiya sbd tsananin tausayin ta da naji. Tsakani na da matar akwai 'dan tazara amma hakan bai hanani 'kare mata kallo gaba 'daya ba...da alamu ta gaji ne da gudun dan sosai ta galabaita ta fita hayyacin ta gaba 'daya. Ni kam banda kuka babu abinda nake yi cikin bishiyun tsoron fitowa nake yi dan har yanzun ban daina jiyo guje- gujen motoci da mutane ba. A hankali naga ta sake mi'kewa cike da 'karfin hali, a 'ko'karin ta na ganin ta tseratar da ranta daga abinda yasa ta gudun tun a farkon fari. Ganin yadda matar ke tafiya da 'kyar tana dafe cikin ta ne ya sanya ni jin tausayin ta sosai ya 'kara kamani, musamman da na tuno yadda nima nasha wahala da ciwon ciki jiya duk nasan nata yafi nawa, amma nasan babu sau'ki kuma da alama ita ma wannan 'din ciwon cikin ke damun ta tunda cikin take dafewa. Yadda na tsura mata idanu kai kace wani abin nake son karanta a jikin ta, anan na fahimci ciki ne babba jikin matar kuma shike galabaitar da ita. Wannan karon kam danne tsoro na nayi na fito cikin bishiyun na tsaya na zubawa matar idanu. Ganin kamar 'karfin ta na yin 'kasa sosai ne ya sanya nayi saurin isa gare ta da sassarfa, ina jin tsoro amma tausayin ta sai ya danne komai dake zucia ta. Ji kawai nayi baki na ya furta " sannu kina ambaton sunan Allah ko da cikin zuciyar ki ne..." Na fadi hakan ne bayan na kamo hannun ta da ni kaina naga karfin halina a wannan wajen. 'Daga hannun ta nayi anan na tabbatar ko gani mai kayu bata yi dan har na kama hannun nata na kaita gefe bata san waye ba..banda hawaye babu abinda nake ganin yake fitowa daga idanun ta, da alamu ta riga ta cire rai da sake rayuwa a duniya ma. 'Karkashin wata babbar bishiyar gamji muka zauna kowa na sau'ke numfashi sama- sama amma na matar cike yake da zafin ciwon da ita kadai tasan yanayin sa..har a lkcn kuma hannun ta na dafe da cikin ta ne. Ganin yadda nishin matar yaki 'karewa ne ya sanya ni matsawa kusa da ita gami da sake furta" Sannu Hajiya..."! Inda na furta hakan cikin sanyin murya me tafe da fargaba. Jin magana ta ya sanya wani hawayen sake gangaro mata, ahankali kuma ta kamo hannu na sannan ta bu'de idanun ta ta kalle ni, sai a lokacin muka ha'da idanu, duba 'daya nayi mata na fahimci rayuwar mu da ita da bambamci bayyananne...akwai tazara sosai tsakanin rayuwar mu da ita, tazarar nisan da zan iya 'kiyasta shi da nisa kwatankwacin tafiyar da ke tsakanin Borno da Lagos...sam babu maha'da. Ban sake tabbatar da hakan ba sai da na sanya idanu na cikin nata. A hankali na lumshe idanu na kuma bu'de su jin yadda take sake ri'ke min hannu na, taushin hannun matar na musamnan ne, hutu sosai ke jikin ta hutu, hutu irin wanda ya amsa sunan sa hutu.... Da kyar nayi gathering courage wajen furta" Hajia dan Allah ki daina kukan haka nan...ni bansan me ya faru ba har yanzun, kawai nima.. tsorata nayi jin motsin ki kuma ya sake firgita ni...me yasa ake gudu bakin titi dan Allah ki sanar da ni...". Na 'karashe maganar murya ta na rarrabewa. Kai ta girgiza min da sauri tana sake maida idanun ta ta rufe ruf, da alamu wani abu ke cin zuciyar ta wanda ni banda masaniya akai sam. Banyi zaton zanji muryar ta ba dan har a lkcn banga alamun zatayi magana ba. Ga mamaki na sai naji ta kara ri'ke min hannu na da kyau..cikin sanyin murya wanda ke fita da kyar ta fara fa'din" Ya hanani, sai da ya hanani tafiyar nan fa amma na nace masa.." Bakin ta rawa ya fara da alamu tana danasanin kin bin maganar wanda take maganar akai din ne...." " Ni nace sai nazo naga Ummah ta..ashe rabon wahala ya kawo ni..." Daga haka ta rushe da kuka sosai, nima hawaye ya fara sakko min saboda tausayin matar duk da har yanzu ban gama fahimtar me take nufi da maganganun ta ba. Cikin kukan nace da ita.." Hajia ki kwantar da hankalin ki bawa baya ta6a wuce 'kaddarar sa..." Cak naji kukan ta ya tsaya sai hannu na da ta sake rikewa cikin nata tana sakin nishi mai 'karfi idanun ta a rintse. Ba 'karamin firgita ni tayi da wannan yanayin ba, take na sake rikicewa dan bansan me hakan ke nufi ba, tunowa da nayi anacewa hadda mata cikin 'yan ta'addan kuma sai ya sani marairaicewa hawaye na na sake sau'kowa a guje, rintsattstun idanun ta na kalla da fuskar ta da ta ke ta faman yamutsewa tana cije baki. Sake tsorata nayi ganin yanda ta 'kwakumo ni jikin ta ko motsin kirki ban iyawa...cikin kuka na fara ro'kon ta" Hajia dan Allah kiyi ha'kuri kar ki cutar da ni, wallahi banda kowa bani da komi...Hamma na bazai ji dadi ba idan kk kashe ni, kinga ni tausayin ki ya sani zuwa inda kike, dan Allah ki rufa min asiri kar ki cutar da ni.....". Me kuke tunanin zai faru? Share ur views pls...ina so inji inda tunanin ku ya nufa.... Salmerh😘 [2/1/2023, 10:23 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Wattpad@* _Serlmerh-md_ 🅿️ *...88* ........Ban kai ga rufe baki na ba kunnuwa na suka jiyo min abinda ya sake firgita ta 'yar natsuwar dake tare da ni, wato kukan jinjiri, wanda zuwa lokacin garin yayi tsit da alamu kowa ya nemi mafakar da zata zame masa garkuwa, banda sautin kukan babu abinda ke ratsa ilahirin dajin dama wani sashi na garin na mu gaba 'daya. Ido na zaro sosai ina kallon ikon Allah wato ruwan dake bin inda matar ke kwance da kuma jinjirin dake kuka a 'kar'kashin ta. Baya nayi kokarin ja amma hakan ya kasa samuwa gare ni, fizgar hannu na naso nayi da niyyar gudu amma matar nan sam bata da niyyan sake min hannu. Ba 'karamin tsorata nayi ba, hakika wani tashin hankalin yafi gaban wani, dama haka ake haihuwa ? Na tambayi kaina da kaina. Ko kuwa dai ita wannan 'din ce nata yazo ta wannan sigar..ma'ana daban da saura..? Ina cikin tunani da son tantance gaskiyar lamarin da nake da da bu'katar sani, ji nayi matar nan na sakin hamdala a fili gami da saukar da ajiyar numfashi mai zafi, hakan ma ya sake bani tsoro, still tashi na sake niyyar yi amma dole na koma na zauna sakamakon hannu na da naji cikin na matar har yanzu bata sake ni ba. Numfashi kawai take sau'kewa sai dai zuwa yanzun ya koma a hankali, banda kallon matar nan da mamaki babu abinda nake yi tunanin nawa ma tuni ya tsaya cak, idan na kalli Babyn sai na kalli matar da har yanzu ta kasa saki na. Babu wanda ya sake yin wata magana a cikin mu illa ni da ke ta muzurai. Tsawon mintina sama da biyar muna ahaka sannan naga matar ta fara sake yin wani nishin amma wannan karon babu abinda ya fito...salati ta fara tana kiran sunan Allah da alamu ba 'karamin ciwo take ji ba a yadda naga yanayin ta... Mun 'dauki tsawon lokaci a hakan sai kuma na rasa takamammai abinda ya kamata na aikata. Zuwa lokacin na gama fahimtar haihuwa matar tayi, na kuma fahimci irin ciwo da zafin dake cikin haihuwa, ashe mu ganin yara kawai muke muyi farin ciki bamu san wahalar da ake sha kafin a haife su ba, hakika dole mu jinjinawa iyayen mu, dole mu yi musu biyayya muddin ran mu, bamu da komai bamu da wani abinda zamu iya yi ko mu biya su da shi face mu yi biyayya ga duk wani abinda muka san zai sanya su farin ciki. Na tausaya mata sosai, domin tuni na fara kuka wanda har zuwa lokacin wannan babyn na kwance inda uwar ta haifo ta babu wanda ya ta6a ta har ta yi kukan ta ta gaji tayi shiru. Da kyar Allah ya taimake ta ta sake haifo wani Babyn wanda hakan shi ya dakatar da nishin da take yi ya kuma dakatar da zafin ciwon da take ciki ta koma sauke wani numfashin tana sakin hamdala cike da galabaita a zahiri. Shi kam na biyun bai ko motsa ba, kwancen sa yake yadda ya fito kuma ko idanun sa basu motsa ba balle yayi kuka kamar na farkon. Kallon ta na sake yi na kuma dubi yaran duk biyu ina jan hannu na domin zogi yake min sosai. Sai da ta dube ni sannan ta saki hannun nawa tana murmushi, da alamu ma mantawa tayi da cewa ta rike min hannu. " Da na sake ki da tuni kin gudu kin bar ni ko...?" Matar ta fa'da tana duban fuska ta muryar ta na rarrabewa kuma cike da sanyi. Sam ban bi ta kan maganar tata ba sai ma idanu na da suka 'kara fitowa waje ina yarfe hannun idanu na akan yaran nace...." Sannu hajiya....". Inda ta ri'ke 'din har sai daya koma ja saboda ba 'karamin riko tayi min ba. " Na haifi yaran ka Doctor, sai dai ka yafe min a jeji na haife maka su..." Abinda naji ta furta kenan madadin amsar sannun da nai mata. Ido ta lumshe sannan ta sake furta"...Abinda na so yi maka suprise akan su sai gashi Allah bai nufa in haife su a hannun ka ba, Allah bai nufe ka da fara ganin jinin ka a dunia ba, Allah bai sa kaine zaka amshi haihuwar yaran ka da kanka ba...ka yafe min miji na, hkn sam ba daga cikin shirina bane, shirin Allah ne...". Tayi maganar hawaye na gangaro mata ta gefe da gefen idanun ta. Ni kam tuni hankali na ya bar kan matar ya koma kan yaran dake gaba na, so nake na 'dauki ko da 'daya ne daga cikin su amma yanayin da naga suke ne ya hana ni..ko ka'dan ban saurari ko kalma guda cikin maganganun matar ba balle na fahimci manufar ta. Yun'kuri tayi ta tashi zaune, ganin ta zauna ne ya sa hankali na komawa gareta, ina nuna yaran da zararren idanu nace" Hajia har guda biyu fa?" Murmushi matar tayi min kawai batare da ta bani amsa ba. Sai na cigaba. " Hajia na tsorata sosai...dama haka ake haihuwa da wahala..?" Murmushi kawai tayi min bata furta komai ba har a lokacin....dube dube naga ta fara ni kuwa ban wani kula da hakan ba sai faman rarraba idanu da nake akan yaran wanda 'daya ke motsi 'daya kuma tun fitowar sa bai motsa ba. Hannu na ta kamo sai na kalle ta da sauri dama a 'darare nake, can inda ta yada jakar ta inda na kamo ta zuwa nan ta nuna min. Nima sai na kalli wurin da sauri na mi'ke na 'dauko mata. Razor blade naga ta ciro cikin 'yar purse 'din ta ta fara 'ko'karin yanka cibin yaran, da sauri na rintse idanu. Tsananin kamar da ke gare su ne ya sanya cibiyar su ya kasance a ha'de...a fa'dar ta. Sai da na tabbatar ta gama yankewa kafin na bu'de idanu na..." Dama haka ake yi...?" Na tambaya ina kallon su, kai kawai ta 'daga min bata ce komai ba har ta kammala abinda zatayi, 'dan kwalin ta ta warware sai kuma ta tsaya kallon yarinyar tana murmushi tace" Allah sarki" Inda tayi maganar tana shafa cikin yarinyar, da muka ha'da ido sai tayi min murmushi. A karo na biyu na sake jin sautin muryar ta dake fita da wani salon birgewa. Cikin raina na ayyana tabbas wannan matar 'yar gayu ce ta 'karshe. Komai nata gwanin birgewa. 'Dan janye, hannun ta dake kan cikin yarinyar tayi sai lokacin ma na lura da wani ba'kin abu dake a cikin yarinyar, girman sa kamar sulalla kuma ba'ki ne si'dik kamar an sanya gawayi. Ni kaina nayi mamakin ganin abin dan ban ta6a ganin irin shi jikin duk yaran da nake ,dauka na mutane ba, yayin da na lura ita matar ganin abin farin ciki ya sanya ta. Nuna min shi tayi tace" Kinga wannan? sak irin na mahaifin ta ne..yarinya ta iya gado" Ta 'karashe tana murmushin dana tabbatar tun daga zuciyar ta ne. Duk da nakan lura lkc zuwa lkc takan dan rintse idanu da alamu wani ciwon na dan tsinkulin ta amma bata bayyana shi a fili ba. Nima murmushi nayi mata dan ban fahimci zancen da kyau ba, hankali na duk na kan yarinyar ne. Na'de jinjirar tayi tana ta motsi da bakin ta g dukkan alamu abu take so ya shiga bakin ta...sosai naji sun shiga raina, lokaci guda wani so da kaunar su ya ratsa cikin zucia ta gami da tsananin tausayin su gaba 'daya har da mahaifiyar ta su ma, dan yau ne rana na farko a rayuwa ta da naga yanda mata ke shan wahala wurin haihuwa ganin ido na.... " Allah ya baki aljanna Innata". Shine abinda na fa'da cikin zuciya ta sai dai ga mamakina matar nan 'daga kai tayi ta kalle bi gami da fa'din" Ameen Ameen." Wannan furucin ne ya sani fahimtar cewa a fili nayi maganar ba a zucia ba. Ganin tana shirin na'de 'dayan yaron da bai motsi cikin mayafin ta ne ya sanya ni saurin ciro 'dan kwalin da ke kaina na mi'ka mata... Bata yi musu ba ta amsa bayan ta bini da 'kayataccen murmushi mai nuna alamun godiya. Kan cinya ta 'dora mai motsin ita kuma ta rungume 'dayan bisa 'kirjin ta...ban sha wahalar daidaita rikon yarinyar ba dan kuwa wannan ba sabon abu bane a wuri na rike jirajirai abu ne da na riga na sabarwa kaina da shi tun ba yau ba. Hawaye ne ya sau'ko mata a hankali na tausayin yaran ta, baya ga haka ma dauriya kawai take yi amma tsananin ciwon ciki ke damun ta, cikin sanyi ta furta" 'kanwa ta ya sunan ki?" " Zaituna". Na bata amsa a takaice ina sake duban fuskar babyn dake hannu na, koka'dan ban ji 'kyankyami ko wani abin ba, sai ma wani 'kaunar babyn dake ratsa ni kusan kowacce da'kika na shiga da fitan numfashi na. Murmushi matar tayi min tana kallo na tace " ni kuma sunana Nadia...Kano nake zama da miji..." Shiru tayi batare da ta 'karasa abinda tayi niyyan fa'di ba sai tayi 'kasa da kanta tana cihe la66an ta. Ita ka'dai tasan me ta ke ji da yasa ta yin hakan amma hakan bai hana ni fahimtar hakin da take ciki ba. " Sannu Hajiya" Na furta cike da tausayin matar nan mai suna Nadia. Indai haka haihuwa yake ai dole aji tausayin mata, balle ita da ta haifi har guda biyu, Ni fa tunda nake 'kwa'kwar zuwa gidan masu jego sau 'daya na ta6a ganin wacce ta haifi biyu lokaci guda shima 'din 'dayan kwanan sa 'daya ya rasu ya bar 'dayan, ban sani ba ko Allah ne kawai bai so nuna min hakan kafin yau 'din ba. Ina cikin tunanin naji matar na fa'din" Daga Damaturu nake zamu wuce maiduguri daga can kuma zan hau jirgin da zai kaini zuwa kano sai kuma cikin rashin sa'a muka yi katari da tashin hankalin nan....". Shiru ta sake yi tayi 'kasa da kanta, yayin da na tsura mata ido zucia ta cike fal da tausayin ta, gami da mamakin ta, ashe har jirgi ma take hawa...na ayyana cikin raina. Yaron dake 'kirjin ta ta rungume da 'karfi hatta hannayen ta ma da na lura sai naga rawa suke tamkar mai jin sanyi. Hakan sai yaso bani tsoro, baya ga haka ma fa da kyar take ta rattafo min wannan bayanin muryar ta na rarrabewa. Tausayin ta sosai ya kamani, cikin natsuwa ta yadda zata fi fahimta ta na furta" Hajiya ki daina maganar idan yana damun ki, ni ba sai kin sanar da ni komai ba, ba bukata ta in san wace ke ba ko ban san ki bama zan iya taimaka miki iya iyawa ta balle ke da nake da yakinin cikin wannan halin ko maikyin ki ne bazai ki taimakon ki ba indai yana da tausayi aran sa.." Kai matar ta girgiza min sannan cike da 'karfin hali ta 'dago kai tana murmushi tace" Ai dole ne in baki labari na 'kanwa ta, baki so idan mun ha'du a wani wuri ki yi saurin tunawa da ni..?" " Wallahi ko iya haka ma bazan ta6a iya mantawa da ke ba, na koyi wani ilimi tare da ke sannan na fahimci abinda ban san haka yake ba tsawon rayuwar da nayi a dunia, sannan kin mallaki abinda ko cikin bacci na na gansu da farin ciki nake farkawa balle kuma a zahiri kinga kuwa babu ta yadda zan iya mantawa da ke a rayuwa ta...". Na bata amsa cike da yakinin da na tabbatar hkn yk har a zucia ta. Tace " Hakane amma duk da haka ya kamata kisan ni wacece da kuma inda na fito, sannab nima ina so in san ke wacece domin kin yi min taimako sosai, kinga rikicewa driver yy sakamakon 'karan harbe harbe da muka jiyo ta ko ina harma bamu san takamammam 6angaren da abin ke fitowa ba. Tafiya kawai yake batare da sanin inda ya nufa ba sai dai da yake a rikice yake shiyasa tu'kin be yi wahalar 'kwace masa ba muka gangara gefen hanya bai kai ga saita tu'kin ba ma muka ci karo da wata bishiya can bakin titi, shikam ma bansan wani yanayi yk ba a halin yanzu..nima 'din nasan kila Allah yy niyyan ha'da ni da ke ne shiyasa ya tseratar da ni..." Hawaye ta goge gami da ajiyan numfashi idanun ta ta sau'ke kan babyn dake hannun ta sai ta girgiza kanta, a hankali ta sake 'dago kanta sannan ta cigaba da fa'din" Kin ga ikon Allah..ciki na bai ko kai lokacin haihuwa ba amma wuya ta sani haihuwar dole..ina da saura kusan sati uku fa agaba...amma Alhamdulillah zan ce, tunda cikin kudurar sa gashi ya raba ni da su lpy. Ban ce da ita komai ba banda kallon fuskar ta da nk. Allah ya yiwa matar wani baiwa ne na kyau da cikar kamala, kyau irin mai matu'kar birgewan nan...komai na matar mai kyau ne..duba 'daya zaka yi mata ka fahimci cewa 'yar gayu ce ta gaske banda hutu da karara ya bayyana kansa a zahiri. Kai ta jinjina sannan ta maida idanun ta kan jakar ta tace" Ban san inda wayata take ba...amma bani jakata zan rubuta miki wani abu". Ta fada da wani irin sanyin muryar da ni da kaina sai da jikina yy sanyi kalau, mi'ka mata jakar ta nayi ina jin babu da'di cikin raina. "....Yanzu kam amanar mu duk a hannun ki yake ni da abinda na haifa, daga yanzu har zuwa lokacin rabuwar mu kinji...." Ta fada tana mai lalu6a cikin jakar fuskar ta da murmushi. Nima murmushin nayi mata mai sanyi sannan ta cigaba" Insha Allahu ko na tafi zan dawo saboda ke ka'dai Zaitoon...kin min halacci kin taimaka min a lokacin da nafi bukatar taimako, baki 'kyamace ni ba duk da nasan ni din a yanzu abin 'kyama ce...nagode kinji, nagode sosai 'kanwa ta...miji na kansa idan yaji labarin ki zai so yi miki tukuici da duk abinda yasan zai faranta miki, domin bashi da wani buri a duniyar nan fiye da yaga na haife masa abinda ke ciki na, shi mahaifiyar sa da duk familyn sa sun 'dokantu da son ganin abinda zan haifa musu..suma nasan zasu so ganin wacce ta taimaka har jikokin su suka samu second chance na sake rayuwa a duniya...ban san me zan baki ba bani da komai yanzu amma ga wannan dan Allah kar kice min a a, nagode sosai da taimakamin da kika yi..ina miki fatan alkhairi, Allah ya baki miji na gari ya raba ki da iyayen ki lpy..." Tayi maganar tana mika min ku'di da bazan iya cewa ga adadin su ba. Baki na na furta" Ameen sbd jin dadin addu'ar da tayi min nake kuma girgiza mata kaina da sauri nace" Hajia ni kam me zan yi da ku'di ki bar abinki zasu yi miki amfani ai..kinga nima Hamma na ya na bani idan bani da shi...nima nagode da kk yadda da ni Ubangiji Allah ya raya miki ya ranki ya sa musu albarka". In sun girma kice musu ina kaunar su..kuma zan cigaba da kaunar su har karshen numfashi na...". Murmushi matar tayi min kana tace" 'daya ce ai ta rage Zaitoon, shi wannan bai ma zo da rai ba" Ta yi maganar tana kallon wanda ke ri'ke a hannun ta wanda ta ha'da shi da duk mabiyan su ta lullu6e shi tare da su. Kai na girgiza cike da alhini ina duban yaron nima. Hawaye naji yana gangaro min..a hankali nace" Kenan shi bashi da rai ko?" Kai ta jinjina min tana kallon fuskar yaron tace" Kamar mahaifin su ne da shi na san da zai fi kowa farin ciki idan ya gansa, amma Allah bai tsara ya rayu tare da shi ba.." Ta 'karashe maganar tana mai 'dagowa ta dube ni, dai dai ina share kwallan da ke sauko min. Cike da mamaki na tace" Kuka kuma 'kanwa ta, baga little princess 'din ki tare da ke ba..kar ki damu kinji, Allah yafi mu sanin dalilin da yasa ya 'dauke shi.." Da kai na amsa ta. " Share hawayen toh in baki wani lbr...". Yadda tace din nayi amma hawayen sun kasa tsayawa. Ita kuma ta cigaba" Auren mu ya dauki wasu shekaru yanzu amma sai wannan shekarar Allah ya nufe ni da samun haihuwa wanda ya kasance babban abin farin ciki ga duk familyn da nake aure, ma'aikaciyar lafiya ce ni hakan yasa ban sha wahala wajen gano yara biyu ne a ciki na ba, sai dai na 6oyewa miji na hakan da burin yi masa bazata sai kuma kinga yadda ta kasance...." Tace" Ya hana ni wannan tafiyar amma na nace sai nayi...ido ta lumshe tana mai saukar da hawaye... Nima ina hawayen nace" Ki tashi muje gidan Innah ta toh kuyi wanka in yaso sai in kar6o miki wayar Hamma Bukar ki 'kira mijin naki ki sanar da shi in da kuke.." Na fada ina mai yunkurin mi'kewa. " Ya sunan garin naku?" Ta jefa min tambaya. Da sunan garin na mu na amsa ta duk jiki na yayi sanyi. Jinjina kanta tayi amma sai naga tamkar bata da niyyyan mi'kewa kamar yadda ni na yunkura duk da ni din ma ban kai ga mikewan ba. Ganin hakan yasa na sake fa'din" Hajia ki tashi mu tafi ko.. naga kuna bu'katar kulawa sosai, Inna ta zata kula da ku har zuwa lokacin da za'a zo a tafi da ku". Jinjina kai tayi tana murmushi tace" Haka kawai fa yau 'din ina jin da'din hira dake, babu wanda ya min shaidar surutu daga dangi na har gidan miji na amma nasan ke kam zaki ce matar nan surutu ne da ita ko?" 'Yar daria nayi, domin ji nayi matar nan ta gama kamo tasha ta. Kamar tasan abinda ke raina. So nake ta tashi mu wuce gidan Inna ta amma ita ta tsaya surutu ni kuma ba shine damuwa ta ba a wannan lkcn. " Bari dai in tashi muje din..kar na 'kure hakurin 'kanwa ta.." Ta 'karashe maganar tana yunkurin mi'kewa tsaye...nima sai na mike. Ganin yadda zanin jikin ta ya 6aci sosai ne ya sanya saurin cire Hijabin kaina na mi'ka mata nace" Hajia ki cire mayafin na ki 'daura shi kan zanin jikin ki sai ki rufa wannan..bai dace mu ratsa cikin mutane kina a wannan yanayin ba..". Nayi maganar batare da na dubi fuskar ta ba. Kallo mai kyau tayi min sai kuma ta girgiza kanta alamar a a. Da sauri nace " Dan Allah ki rufa kin ga fa zanin ya lalace kuma sai mun bi cikin gari kafin muje gida...". " To ke haka zaki tafi?" " Kar ki damu da ni Hajia ai ni garin mu ne bakomai..." " Yanayin jikin ki da ke kanki bai nuna alamun kin saba cire hijab din kanki a ko'ina ba...bana so in shiga hakkin ki kanwa ta..." " Hajia ba komai, yau ka'dai dai nasan bazai zame min damuwa a zuciya ba, baya ga haka ma ai a yanzu kam nasan kin fini bukatar sa...". " Nagode sosai...." Tace tana amsar hijabin. Kamar yadda nace mata haka tayi sai ya kasance daga jinjirar dake rungume jikina babu komai...fayau nake ji iska na shiga na ta ko'ina ba. Da gaske fa naji wani iri kasamtuwar ban saba hakan ba. Amma karo na farko kenan a rayuwa ta da naji har a raina zan iya ratsa cikin garin namu batare da hijabi na ajiki na kamar yadda na saba ba, koma 'dan kwali babu akai na sai 'kananun kitson da suka sakko min saman kafa'da ta. Bana jin da'din yanayin amma haka ta daure saboda rufa sirrin matar agani na yafi min kwanciyar hankali...tausayin ta tare da yaranta shi yafi komai tsaye min ya mamayi zuciya ta a wancan lokacin. Nice ke ri'ke da jaririya mai numfashin yayin da matar ta rungumi 'dayan da tace bai zo da rai ba. A hankali muke tafiyar dan matar 'ko'kari kawai take yi amma da kyar take 'daga 'kafafun ta take takawa. A can gida kuwa hankalin Hamma Bukar in yayi dubu ya tashi, kowa na gida Goni ma tuni ya iso, gari shau kamar ba'a yi halitta ko guda a ciki ba kowa ya nemi ma6oya sbd tsoro illa Yaah Bukar da sam ya kasa samun natsuwa kasantuwar har yanzu ban koma gida ba, sosai yayiwa Iyami mita akan tura ni jejin da tayi bayan tasan ma baisashshiyar lafia gare ni ba, daga duba 'daya idan ka yi masa zaka fahimci tsananin tashin hankalin da yake ciki. Duk da yasan gari ba lafia amma ya kasa ha'kura ya zauna a gida, baya iya yin mintina ashirin batare da ya fito ya duba wai ko Zaituna ta dawo ba. Hankalin sa duk ya gama tashi haushin iyami yake ji sosai bata ta6a yin abinda ta matu'kar bashi haushi irin na yau 'din ba. Daga 'karshe kasa ha'kuri yayi ya kamo hanya da niyyan zuwa duba ni, Goni ma da ganin hakan ya biyo bayan sa duk da ba wani hutawan kirki yayi ba, ya riga ya sawa ransa cewa zai dubo ni so bai damu da duk wani abinda zai biyo naya ba. Tun daga nesa muka fara jiyo karan tahowar motoci sai dai hakan bai sa mun dakata da tafiyar ba kasancewar tun farko ma motoci na wucewa da dugu dan mamallakan motocin na gudun ceton ransu ne, kamar dai ita wannan matar da nake tare da ita, duk tunanin mu ya raja'a ne akan masu gudun ceton ransu ne shiyasa bamu yi yun'kurin dakatawa da tafiyar ba. Muna daf da hawa saman titin muka 'dan dakata dan motocin su wuce da yake da gudun su suke tahowa..sam bamu fahimci ko su waye ke cikin motocin ba kamar yadda bamu san manufar fitar su ta ranar ba, ashe 'yan ta addar ne suka dawo dan komawa ma6oyar su..amma tun daga inda suka fara tafiyar basu barin duk wanda suka ci karo da shi, harbi suke saki da sun hango mutum, namiji ne ko mace yara ko manya babu ruwan su. Salmerh😘 [2/1/2023, 10:23 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Wattpad@* _Serlmerh-md_ 🅿️ *...89* .......Cak numfashin mu ya tsaya dukkan mu muka yi suman tsaye sakamakon 'karar harbi da muka jiyo tun kafin su 'karaso inda muke. Duk cikin mu kuwa babu wanda ya iya 'daga koda 'dan yatsan sa ne balle muyi yukurin guduwa, tsayuwa kawai muka cigaba da yi idanuwan na bin titin da kallo..idan ka ganmu zaka yi zaton an shanye jinin jikin mu ne tsaye nan inda muke. Mota ta farko Bus ce ta wuce, sai wata golf, ta ukun ma golf ce daga nan sai helux fara kuma duk muna ganin mutanen dake cikin motar, motar da ta 'kara kunno kai ita ma helux ce amma ba'ka, ta bayan ta ma bakar helux ce mutanen ciki tsaitsaiye da bindiga a hannuwan su, nan muka yi ido hu'du da mutum biyu dake cikin motar suna fuskantar mu da bindiga a hannun su, kusan ko wani 6angare akwai wa'danda idanun su ke kallon wurin kuma suke ankare da duk wanda zasu gani. 'Karar harbi muka ji daga 'daya 'bangaren wanda muka tabbatar mutum suka gani suka harba, ni kam idanu na 'kyam na ware su ina duban masu bindigan illah bugun zuciya ta da ya 'kara tsanani ji nake kamar zai faso 'kirjina ya fito. Matar ce dai ta rintse idanu da 'karfi hawaye masu zafi suka gangaro mata, da sauri ta kuma bu'de idanun ta sai taga already wannan farar helux 'din ta wuce ba'ka ce yanzu saitin mu ita kuwa ba gudu take yi kamar sauran ba. Kafin muyi wani yun'kuri sai gani muka yi 'daya daga cikin su ya saito mu da bindiga, wani bushshshen yawu na ha'diye, wanda na tabbatar ko ma'kogorana bai wuce ba. Matar ce ganin ana shirin harbin mu tayi 'karfin halin tura ni bayan ta ita kuma ta kasance a gaba tana sake rungume 'danta a 'kirji. Bazata batare da mun shiryawa hakan ba kawai muka ji 'karab harbi, 'karan harbin da ya gigita min kwanya yasa na daina jin komai na wucin gadi. Harbi na farko ta kan jaririn dake hannun Nadia ya shiga ya kuma fita ya ratsa ha'karkarin ta sai dai bai shige can ciki ba. Idanu tayi saurin rintsewa tana karanto Innalillahi wa inna ialihi raji'un a fili..cike da galabaita, ban san abinda ya faru ba, ban san cewa harbin gare mu ya taho ba amma jin tana innalillahi yasa da sauri na ri'ke ta musamman ma jin yadda ta kame wuri guda, ina kokarin fitowa daga bayan ta tayi saurin rike min riga ta baya da 'daya hannun ta..da karfi ta rike ni ta kuma tokare ni ta yadda motsi ka'dan idan nayi 'kasa zata yi duk bansan meke faruwa ba, ajiyan numfashi na sauke wanda yayi daidai da sake jin saukan wani harbin a gefen cikin ta, wannan karon kam gaba 'daya tayo baya ta kwanto jikina, bani da karfin iya 'daukan nawin matar da kuma kaina hakan yasa muka yi baya nuka fa'di 'kasa gaba 'daya...Nadia na salati, jaririya kam na jin yanda muka fa'do sai ta tsanyara kuka dan ita ba haka ta saba jin tana rayuwa cikin mahaifiyar ta a gigice ba, sai kuma akayi rashin dace ta fito dunia ne adai dai ga6ar da kowa ke neman tsira da ransa Yanda matar ta danne ni ne ya sa na kasa cire kaina daga 'kar'kashin ta da wuri ga kuma kukan jaririyar dake ratsa min ko'ina a jikina...kukan take yi kamar ranta zai bar jikin ta, ni kuma gaba 'daya sai hankali na ya tashi ganin abubuwa na neman tsarwatsa min kwakwalwata, me ke faruwa ne har alkcn ban sani ba. A gigice kawai na tashi zaune daidai lokacin da motocin 'yan ta addan suka 'karasa wucewa da alamu sun 'kare kenan..kan matar sai ya zama na akan cinya ta yake hakan yasa na zuba mata idanu a rikice nake tambayar ta ko lpy. Dafe cikin ta kawai tayi da 'dayan hannun ta wanda 'dazu take rike ni da shi, a hankali idanun ta ke lumshewa hawaye masu sanyi na gangarowa ta gefe da gefen idanu, har yanzun kuma jinjirin na rungume da ita bata sake shi ba. Jini da na gani yake malala daga jikin ta ne ya matu'kar gigita ni, take na kai hannu bakina na saki kuka jikina ya fara rawa sosai...da rawar murya nake ro'kon ta akan ta taimake ni ta ta shi dan ni ban san yadda zan yi da su ba. A hankali matar ta 'dage hannun ta kan cikin wanda duk ya 6aci da jinin harbin da aka yi mata. Hannu na ta kamo ta rike cikin nata hannun tana duban fuska ta take murmushin 'karfin hali. Sai da ta lashe la66an ta kafin tace"...Zaitoon"! Ban iya na amsa ta ba sai idanu na dake turereniyar hawaye na zuba mata na ma kasa fadin komai " Nasan ke 'yar halak ce, kamar yadda yarana suke 'ya'yan halak..." Ido ta lumshe cike da galabaita tace" Na baki ita kinji, na baki Aisha halak malak ki kula min da ita ki bata tarbiya mai kyau kamar yadda akayi maki kinji...daga yau Aisha 'diyar ki ce... Cikin jakata akwai ku'di sai dai ba yawa akwai katin banki na aciki zaki iya amfani da shi..kiyi ha'kuri dan Allah, ni ba niyya ta in saki cikin matsala ba, ba niyya ta in shiga rayuwar ki in cutar da ke ba amma Allah yafimu sanin kowani sirri, nasan Allah ne ya ga daman ha'da ni dake, ko bayan bani kimin wannan uzurin kinji 'kanwata, duk halin da zaki tsinci kanki a ciki karkiyi tunanin dan mugunta na saki..bani da yadda zanyi ne..amma babu mamaki ki ha'du da..." bata 'karasa ba sai kuma tayi shiru. Ni kam banda kuka babu abinda nake yi, kuka nk hadda sheshsheka sosai jikina yayi sanyi. Idanun ta ta lumshe sannan tace" Ina jin zafi sosai.., 'kirji na yana min zafi sosai Zaitoon..". A hankali sosai tayi maganar amma dayake kanta na kan cinya ta ne hakan yasa naji abinda ta fa'da. Hijabin kanta ta nayi saurin cire mata dan dama ba wani sauka mata yayi sosai ba kasantuwar bashi da girma. Kalle-kalle na fara da nufin samun abinda zan yi mata fifita tunda tace zafi take ji, sai dai ban ga komai ba a kusa da mu ba, Allah ma ya taimake ni zuwa lokacin yarinyar ta tsagaita da kukan da take yi tayi shiru. Dogon numfashi Nadia taja cike da 'karfin hali ta juya ta kalli 'diyar tan dake hannu na sai kuma ta kalle ni da tun 'dazun nake tsiyayar da hawaye. " Ki bar kukan mana.." Ta fa'da da sanyin sauti mai cike da rauni. Hatta idanun ta bazaka yi zaton tana iya ganin abu ahakan da su ba yadda duk suka zama lumsassu. Cikin 'karfin hali ta sake bu'de baki ta furta" Tashi..ki kaita Inna tayi mata wanka sai ki kawo min ita in ganta kinji?" "...toh..toh..mutafi tare mana". Nace da rawar murya ina kokarin 'dago mata kanta. Tace " A a kije ki dawo tukunna..ina nan ina jiran ku baki ga naji ciwo a ciki na ba, sai na huta tukunna zan iya tafia..kuje ku dawo...". " Ba ciwo ba ne..sune suka ji miki ciwon da bindigar su...kuma Insha Allah baza suyi 'karshe mai kyau ba, Insha Allahu su ma sai anyi musu fiye da yadda sukai mk..." Baki na ta toshe min sai na 'karashe maganar da kukan tausayin Nadia. " Mance da su...kiyi ta yiwa 'diyar ki addu'a yafi kin ji...nima idan ta girma kice mata ina son ta ina 'kaunar ta..." Kai na fara juyawa da sauri..." Bani ce zan fada mata hk ba ai ke ce Hajia, kece zaki fada mata ina kaunar ta sosai...". Murmushi tayi, murmushin da sai daga baya na fahimci cewa na 'karfin hali ne. " In hkn toh yi sauri kuje ku dawo ina jiran ku ...." Da jin hakan sai na fara yun'kurin mi'kewa a hankali na sau'ke kan ta daga jikina ban mike ba sai da na 'dauki jinjirar na kuma rungume ta sosai a jiki na, ina shirin mi'kewa sai naji Nadia ta riko hannu na da idanu ta mika min karamin jakan ta ban yi musu ba na amsa na gyara rikon yarinyar da kyau ta yadda babu wanda zai ganta a hannu na. Haka na wuce ina tafiya ina sake waigowa domin itama Nadia idanun ta akan mu yake, ta zuba mana idanu tayi tana kallon su har muka 'dan yi mata nisa da inda take sannan ta maida idanu ta lumshe tana kallon sama. Da sassarfa na isa gidan Innah ta duk da Abbab mu ya hana ni zuwa amma inaji cikin raina cewa na yau ka'dai kam bazai zame min matsala ba, kuma ko bazai saurare ni ba zan bashi ha'kuri duk da ban san takamammai dalilin hana ni zuwan ba sai dai inaji araina cewa wannan taimakon Inna ce ka'dai zata iya yi min shi cikin salama har na mayar wa Nadia diyar ta batare da an samu matsalar komai ba, dan sarai nasan halin Iyami bazata ta6a yi wa yarinyar wankan ba 'karshe ma 'kila ta tara min jama'a ne akaina kawai. Ita kanta Inna ta da ta ganni haka sai ta rikice musamman da yake tasan gari babu lafiya ga kuma jikin hijabina da hannayen na duk jini. Lokacin da ta lura da jaririyar dake 'dauke ahannun na kuwa sake rikicewa tayi tana tambaya ta inda ta samo. Sama- sama nayi mata bayani tare da sanar da ita abinda nake so ayiwa yarinyar nace mahaifiyar ta na can tana jira na maida ta...dama tare zamu zo amma an harbe ta a cikin ta". Sam ban 6oye wa Inna ta komai ba, kamar yadda ban fada mata 'karya dai dai da kalma guda ba. Salati Inna kawai ta fara jerowa zuciyar ta cike da tsoro da fargaba tace" Ke kuma ina kuka ha'du da ita?" " Iyami ce ta aike ni jeji ciro ganye na ma barshi a can jejin idan nayi zan 'dauka in kai mata..Innani har yara biyu fa ta haifa amma tace 'dayan wai bashi da rai yana can tare da ita.". " Allah sarki..." Inji Inna ta cike da tausayawa. Hakan sai ya kara min kwarin gwiwa...nace " Sai ma kin ganta Innani, wallahi 'yar gayu ce fa jikin ta 'kamshi mai da'di". Nayi maganar ina cire lully6in jikina, take na ja ruwa na wanke shi kafin ma ruwan da innani ta dora yayi zafi ni har na gama wanke kayan da suka 6acin na shanya..gefen Innani nazo na zauna..ina fa'din" Ayi mata da wuri Innani tace in koma zamu zo tare...". Innani dai bata ce komai ba ta tashi ta ha'da ruwa ta wanki yarinyar. Wanda ya rage bisa wutan ta saka na 'debo ta 'dan sanyatar da shi dai-dai ta bawa yarinyar tasha..ko kukan kirki kuwa batayi ba ana wankan ma tana 'ko'karin yin bacci. Sai da ta gama bata ruwan kafin ta dube ni tace" Sai dai babu riga kuma da za'a sanya mata". Kai na dafe da alamun tunani wanda ganin hakan yasa Innani kawar da kallon ta daga gare ni tace" Akwai rigar salisu jikan maigidan nan da jiya suka zo suka yini anan sai suka manta.." Ban ma bari Innani ta kai 'karshe ba na saki fuska nace" Yauwa Innani a sanya mata dan Allah, idan mahaifiyar ta ta ganta da rigar zata ji da'di..." Koda aka gama shirya ta nice na sake rungume ta bayan na saka 'daya daga cikin hijaban Innani dayake yawanci hijaban ba wasu manya bane su, so ko wannan 'din ma bai fi wanda ni nake sanyawa ba. A hanya ne nake 'dan bawa Innani labarin yanda muka yi da matar hadda kyauta da amanar yarinyar da uwar ta bani kamar almara. Ita dai Innani kallo na kawai take yi amma tasan in ba wani ikon.Allah ba da kyar ne in har yanzu matar nan na raye..maganganun nata duk sun yi mata kama ne da wasiyya. Ai kuwa muna zuwa muka ci karo da wasu motocin da tun daga nesa muka fara hango su a wurin, su uku na jami'an tsaro guda biyu da na asbiti guda 'daya(Ambulance). Bamu san takamamman meke faruwa ba, mun dai fito muka ga mutane tsatstsaye amma da nisa basu isa kusa da jami'an tsaron ba. Bazan iya bambance tsakanin jam'in tsaro da kuma 'yan ta'addan ba saboda kamanceceniya da suke da shi, sai dai daga yanayin tsabtar motoci da kayan dake jikin su na fahimci wa'dannan daban da suke da wa'dancan..hadda wata mota blue wanda nake kyuatata zaton ta ma'aikatan Road Safety ne, balle kuma da maga har mutane na tsaye suna kallon su daga 'dan nisa sai na fahimta dagaske cewa ba makasa bane jami'an gwammati ne...tunda wa'dancan idan an gansu ko jin labarin su guduwa ake yi. Tsayuwa muma muka yi kamar yadda kowa dake wurin yayi..in ba kasani ba bazaka ta6a fahimtar cewa da mutum a hannuna ba. Babu wanda yayi gigin zuwa kusa da mu dan duk sun tsatstsaya da bindigu muna rarraba idanu. Daga inda muke tsaye ina iya hango yadda aka ciro gawar wani drivern da sai a lkcn ma na tuno abinda matar nan ta sanar da ni game nata drivern, babu mamaki shi din me. Gaba 'daya ya koma bakikirin ashe ma motar 'konewa tayi bayan tafiyar ta. Rintse idanu mayi sosai, take naji zuciya ta ta bushe gaba 'daya, Innani kanta bata san lokacin da ma bar gefen ta ba dan baki ta sake tana ganin ikon Allah. Zagawa mayi bayan na 'dan yi tafiya mai 'dan tsayi, ina rungume da jinjirar har yanzu, burina bai wuce na ga na sada ta mahaifiyar ta ba kamar yadda ma yi al'kawari. Can nesa sosai da jami'an tsoron na ratsa na shiga jejin, haka ta ringa ratsawa har na kusan isa inda na bar Nadia kwance cikin jini da jaririn ta. Har a lkcn kuwa kwance take sai kamar yadda na barta sai hijabina da aka sake rufe mata jiki da shi. Hango wani jami'in da nayi tsaye kanta ya sanya ni dakatawa na lafe bayan kananun bishiyu ina sakin ajiyar zuciya. Sam bana jin wani tsoro ko fargaba cikin zuciya ta, cikin sa'a ma babu wanda ya lura da ni hakan ya sa na sake baro bayan bishiyar na fito fili, haka na ringa lalla6awa cikin dogon ciyayi dake wurin ina sake matsawa kusa da su. 'Buya nayi cikin ciyawan na dur'kusar da kaina ina hango Nadia da har yanzun take kwance yadda na narta babu wata alamun motsi tattare da ita. Jami'ai biyu ne tsaye kanta ..ban san me ya faru ba kam amma haka kawai sai naji karaya ta ziyarci zuciya ta lkc guda.... hawaye ne na ya gangaro min, dan ko ba'a fa'da ba nasan da 'kyar ne idan matar nan tana numfashi. Nasan banda 'kaddara babu abinda zai ha'da ni da matan nan, nasan ayadda take din nan ko a hanya ta ganni ba lallai ne idan ko kallon arziki zan iya samu daga gare ta na balle har muyi magana na tsawon lokaci..amma ji inda kaddara ya kawo ta, gata can yashe tamkar marar gata..." _Aisha 'diyar ki ce, na baki ita halak malak, ki kula min da ita ki bata tarbiya kamar yadda aka baki..."_ Kalaman matar da na tuna kenan wanda suke tai min yawo a kwanya ta...sai nayi saurin share hawaye. Ban gama tunanin ba naji muryar wani dake tahowa ya tambaya " wannan fa? Inda yayi maganar yana Nadia. " She is dead". 'daya ya amsa shi yayin da 'dayan ya furta" Oga gawa ce ta riga ta rasu". Kuka ne naji zai kwace min da karfi kuma lic guda, sai nayi saurin toshe bakina, hawaye na na zuba kan jikin yarinyar dake hannuna Daga wajen da nake 6oyen ina iya hango duk abinda suke yi amma duhun ciyayin ya hana su su hango ni. Yarinyar da ke rungume da 'kirji na na sake rungumewa wasu hawaye masu zafi suna gangaro min..." Yah Allah ka bayyana min abinda ya dace na aikata.." Abinda na furta kenan ina kallon sama sai na sake sau'ke idanu na akan jami'an tsaron ganin an taho da wani abu kamar gado wani daga cikin su na shirin 'dauke gawan Nadia da 'dayan jinjirin ta. Sosai ta rungume ta 'kirjina ina jin 'kaunar ta na tsarga min a zuciya. Fuskar ta na duba cikin zuciya ta na furta" Hajia ta bani ke, tace ta bani ke halak malak, idan na bayyana musu ke ma 'kwace min ke zasu yi har abada kuma bazan sake ganin ki ba, da waki rayu da wa zako tashu ban sani ba tunda ance ita ta rasu...da muryar kuka nake fa'din..." Bana so in rasa ki, wallahi bana so kiyi nesa da ni daidai da rana guda, bana so in yi butulci bisa amanar ki da na kar6a, na ba Kano bane balle in ce ga mahaifin ki za'a kaiki, kuma bani da tabbacin haduwar ki da shi..." Yah Allah ka bu'de min 'kofar da zata 6ille mana gaba 'daya ni da yarinyar....". Kuka nake sosai, kukan da ni kaina bazan iya na menene ba, kusan tun haduwa ta da Nadia idanu na basu bushe babu hawaye ba. Ina nan ina le'ken su har suka gama duk abinda zasu yi suka kwashe gawawwakin suka sanya cikin mota. Wa'dannan biyun dake tsaye kan gawar Nadia ne kafin a 'dauke ta naga sun tsaya 'yan dube-dube...kamar babyn da ke hannu na ta sani sai ji nayi kawai ta 'dan yi motsi sai kuma ta fara mutsu- mutsu sosai da alamu kuka take da niyyar sakewa, ai kuwa take nayi saurin 'dago ta na sanya mata le6en baki na na 'kasa cikin bakin ta ta fara tsotso. Bugun tara- tara zuciya ta keyi ina hango su da gefen idanuna ina kuma Addu'ah cikin zuciya ta Allah yasa kar su gano ni. Daa zararren idanu 'dan 'dan sandan nan ya dubi 'daya da niyyar tambayar sa ko kunnuwan sa sun jiyo masa abinda shi ya jiyo sai dai bai kai ga furta abinda yayi niyya ba wani Inspecta ya basu umarnin barin wajen....kowa yasan jami'in tsaro suna matukar biyayya ga duk manyan su mawuyaci ne kaji sun yi musu ga duk umarnin da aka basu. Hakan ne ya sasu watsar da batun suka juya duk suka isa inda shugaban nasu ke tsaye. Da ganin hakan sai na sau'ke ajiyar zuciya mai sanyi...a fili nake sakin murmushin jinda'di. Sai kuma naji hankali na ya tashi sosai..tambayar kaina nayi ina mai duban fuskar yarinyar" _Shin yanzu sata nayi ko kuma taimako?"_ Bani da hujjar da zan rika dan kare kaina akan rike yarinyar nan da nayi amma can kasan zuciya ta nake jin ban aikata kuskure ba, ban sani ba ko 'kwarin gwiwar da nake ji daga wani 6angaren dai dai ne ko kuwa son zucia ta ne kawai ba. Jijjiga kai nayi hawaye na gangaro min...da baya da baya na fara barin wurin wani tunani na 'darsuwa min cikin zuciya..ko ganin gabana da kyau bana yi saboda yadda hawayen ke min turereniya. " Kowa yanzu da 6arauniyar yarinya zai ganni...zan kai musu ita su ha'da ta da dangin ta indai suna da damar hakan.....". Tafiya nafara ina jin zuciya ta babu da'di, rabuwa da yarinyar idan na tuno shine ke tunkaro ni sai naji kwata- kwata bani da wani kuzari, kan gwiwoyi na na zube na ringa kuka ina sake rungume yarinyar"...kiyi ha'kuri Hajia wallahi bazan iya ri'ke yarinyar nan ba, bazan iya rike mk wannan amanar mai gagarumin girma ba, sam bazan iya ba, tafi 'karfi na, Iyami, Abban mu, Hamma na, mahaifiya ta da 'yan uwa na duk babu wanda zai goyi bayana. Kuka nake sosai wanda ya 'dauke ni tswon lokacin da ni kaina ban sani ba...kuma wai duk kukan zan rabu da yarinyar ne. 'Karfin hali nayi na mi'ke na sake bin hanya har na fito bakin titin da niyyan kaiwa jami'an tsaron yarinyar su tafi da ita sai dai kan titi shau na ganshi tamkar an yi ruwa an 'dauke, babu kowa, babu jami'ai babu motocin su, dagaske bangan su ba babu su babu alamar su. " Innalillahi". Na furta cike da ka'duwa. Waige- waige na fara sai ma naga babu kowa ba jami'an tsaro kadai ba hatta wa'danda suka tsaya kallon ma babu su. Tsakiyan titin na sake hawowa wai na gani da kyau amma abu 'daya idanu na ke gani babu kowa. Wannan karan ma kan kwaltar na zube na saki wani kukan da tasomin tun daga can kasan zuciya ta yake fita...a fili nake fadin" dan Allah ku dawo, ku dawo zan baku ita wallahi ku tafi da ita...ko bama tare zan yi mata addu'a, zan yi mata fatan alkhairi muddin raina. Babu wanda ya bi ta kaina balle asan manufata, babu wanda yasan halin da nake ciki balle asan matsala ta ko damuwa ta, babu kowa...hatta cikin garin ma ba mutane ne sosai ba sakamakon rashin natsuwa da aka wayi garin dashi. Da 'kyar na samu na lalla6a na koma gefen titi na sha kukana son raina kafin na tashi na kama hanyar gidan Inna ta. Kamar daga sama naji wata murya daga gefe na ta can nesa ka'dan da ni an 'kira suna na. waigawa nayi na kallo wurin da jajayen idanu na. Salele ne mai chemist.." Bai da'de ba Bukar ya bar nan duk hankalin sa tashe yake yana neman ki ashe kina nan?". Yayi maganar yana nufowa inda nake. Turus yayi kuma yana bi na da kallo sama da 'kasa yace" me ya same ki kuma kike kuka haka Zaituna .?" Kai nayi saurin kawarwa gefe sannan nace babu komai, kaina kawai ke min ciwo". Ina shirin yin gaba sai yayi saurin dakatar da ni ta hanyar shan gaba na yace" Haba Zaituna da gani wani abu na damun ki, dan Allah ki sanar dani, ai ni kamar yayan ki ne" Kuka na rushe masa da shi nayi 'kasa da kaina...yanda nake kukan har yasa babyn dake hannu na motsawa gami da yin mi'ka irin tasu ta yara. Salele cike da mamaki yake bi na da kallo, idanun sa duk waje yace" Wai me nake gani ne haka kamar mutum a hannun ki Zaitoon?" Wannan karan da yaren kanuri yayi min wanna tambayar inda ya 'karashe yana mai 'daga hibajin jiki na. Baya ka'dan yaja da ganin yana kare min kallo sama zuwa 'kasa. " Subhanallah" yace cike da firgici. " Zaituna na waye a ina kk samo kuma?" Cikin kuka nayi masa bayanin komai har niyya ta na basu yarinyar amma na tarar sun tafi. Kai ya girgiza yace" ikon Allah baya karewa, yanzu ina zaki?" " Gidan Inna ta". " To kije insha Allahu anjima zanzo 'kila ma Muzo da Habu yanzu kinga lokacin sallah yayi idan mun fito daga masallaci zaki ganmu, ki kwantar da hankalin ki kinji?" Kai na na 'daga masa sannan nayi gaba. Inna ta kam bata ce da ni 'kala ba har na 'karashi kuka na nayi bacci. Tashin hankalin ta 'daya ne kawai yadda za'ayi da yarinyar na dan tasan halin tsohon mijin ta kamar yadda tasan halin mijin ta na yanzu. Ita bata san gangancin da ya hana ni 'kin bada yarinyar ba. Su Hamma na sai la'asar suka shigo shi da Saleh, duk hankalin sa a tashe dan yau yinin nemana yayi amma bai same ni ba...banda wani tashin hankalin da ya same shi ganin idon sa. Ko da ya ganni ma tsayawa kawai yayi yana kallo na dan duk Salele ya gama sanar da shi komai. Bai kula ni ba sai ya tafi ga Innata suka gaishe ta sannan cikin kalami na fahimta yace" Inna naji duk abinda ya faru, kuma naga kuskuren Zaituna sannan sam sam bazan iya barin ta zama tare da yarinyar nan ba mayar da ita za'ayi?" Salmerh ce😘 [4/1/2023, 12:03 am] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Wattpad@* _Serlmerh-md_ 🅿️ *...90* ......Kuka sosai na sanya daga cikin 'dakin Inna ta..harga Allah ni banaso kowa ya rabani da ita, yini 'daya tak da nayi da yarinyar sai naji ta 'kara shiga raina sosai. Bansan ya 'karshen tattaunawar tasu ta 'kare ba saboda kukan da nake yi. Hamma na nagani tsaye daga bakin 'kofa yana fa'din" Tashi mu wuce gida kafin gobe a maida ta inda yafi dacewa da ita". Simi- simi na tashi na nufo 'kofar batare da na 'dauki yarinyar ba, sai yace" 'dauko ta mana..ai bazaki barwa Inna wahalar ta ba tunda ke ce kika jaji6o ta". Ni dama hakan yafi min har a zucia ta, nafi so in tafi da itan..hakan yasa naji dadin kalamin sa wani sanyi ya ratsa zucia ta. 'Dauko ta nayi na rungume ta cikin hijabi na kamar 'dazun na bishi abaya har muka je gida. Yau kam kowa na gida Baffah ma tuni ya dawo saboda tashin hankalin da ake ciki..ga Goni ma da ya auna sa'a duk bani da labari sai yanzu da na dawo gidan. Garin nemana da kadan ya rage a harbe sa badan suna tare da Yah Bukar da yy saurin ankarar da shi suka zube 'kasa hakan yasa harbin yabi iska ya wuce, basu mike ba kuwa har sai da 'yan ta'addan suka karasa wucewa. Kaina 'akasa dama na shiga gidan a bayan Hamma Bukar shi da Salele...a hanya naji suke tattauna batun su biyu. Tsoro ya sake kamani, sbd jin auna sa'ar da 'yan uwana suka suka yi..yau da ace an harbi dayan su ta dalili na da bansan inda zan tsoma rayuwa ta, banda ma Iyami da sai ta kusan yin dambu da namana. Gefen tabarmar Abban mu suka zauna inda ya tashi daga kihsingidan da yayi yace" Aww Bukar ka samo ta ne?" Sam banyi mamaki ba, dan na jima da fahimtar irin mahaifin da Allah ya bani, yafa san bana gidan tun safe amma amadadin a fita da shi a duba ni sai ma zama da yyi a gida ya mi'ke 'kafafu ko alamr damuwa babu tattare da shi, na dawo ko kar na dawo ruwa na, in mutu ko in dawo a raye duk ba damuwar sa bace. Hamma Bukar ka'dai ya damu dani a gidan na kuma shika'dai ne ya damu da rashin ganin nawa sai Goni da shima isowar sa kenan da safiyar ranar. Shima din na tabbata da bai dade da dawowa bane da ko kallo ban ishe shi ba, shi dama haka yake, babu ruwan sa da duk wata sabgar da ya san bazata kare shi ba, baya shiga sabgar kowa balle kace ga abinda yayi maka na 6acin rai..'kyaliya ce da shi na masifa. Ban yi mamakin jin furucin mahaifi na ba sai lokacin da Iyami ta fito daga 'dakin ta tana 'ko'karin 'daura zani naga ta bini da wani mugun kallo..." Ashe zaki dawo na 'dauka ai gawar ki za'a kawo min tunda ke hankali bai gama isan ki ba har yanzun, kina ji gari bb lafiya amma dan iya shege bazaki dawo gida ba sai kin bawa mutane wahala...?" Ta 'karashe da yanayi na tambaya. " Wato gawa ta?..to gani ai na dawo da 'kafafu na". Abinda na fa'di cikin zuciya ta kenan..a zahiri kuma gyara ri'kon yarinyar hannu na kawai nayi. " Wlh da kin kuskura sanadin ki lafiyar 'ya'ya na ya samu gi6i da sai kin sha mamakin abinda zan aikata agare ki...a ina kk tsaya tun safiyar da baki dawo gida ba....?" Shiru nayi na ma rasa amsar bata... " Da kika yi shiru kina jin mutane 'din kuma fa, ba dake ake magana ba ne...banza munafu....". Maganar Iyami tsayawa daidai yy lokacin da taga na gyara ri'kon yarinyar hannu na akaro na biyu. Baki ta bu'de tana bina da kallo sai a sannan ta lura da yanayi na, a hankali cike da mamaki tace" Zaituna"!. " Na'am Iyami..." Na amsa ta cikin sanyi nima batare da na dubi fuskar ta ba. " Me nake gani haka wai?..menene a hannun ki...?" Kafin nayi magana..Hamma Bukar ya riga ni da fa'din" Ki 'karaso ki zauna mana Iyami dama maganar da zamuyi kenan..." Ai kam kujera tayi saurin 'dakkowa ta zauna tana sake bina da kallo me cike da tambayoyi da ma'anonin da ni kaina bansan iyakar su ba. Gyaran murya Hammah yayi sannan ya kora musu bayanin duk abinda Salele ya sanar masa yana yi yana kallo na, ni kam 'kasa nayi da kaina dan ko ka'dan babu 'karya a cikin maganar salale bai canza komai cikin duk abinda na sanar da shi ba. Iyami kam tun kan Hamma ya dasa aya tayi saurin mi'kewa tsaye tana shewa tace" Zancen banza, ni za'a rainawa hankali? Abubakar ni fa na haife ka, itama 'din gabana akayi rainon cikin ta zuwa na'kudar ta, har kun isa, a tunanin ku kun girma kenan..? Kunyi girman da zaku shirya munafurcin da 'karamin kwakwalwar ku ta sanar da ku cewa ni Hajara zan yadda da ita....? Yarinya taje tayi cikin ta haife sannan ku wani zo min da wani batu, ita matar jakar ina ce da zata 'dauki 'yata sukutum tace ta bawa Zaituna, bata da dangi ne kome?" " Haba..Haba Iyami, maganar nan fa gaba 'dayan ta bata tashin hankali bace...magana ce da za'a yi ta ta fahimta ba komai ba, ta ya ma zaki ce Zaituna ta haifa bayan kullum yarinyar nan gaban ki take sabgogin rayuwar ta? " Kayi min shiru Habu, kayi min shiru banason munafunci..da alamu kaima an koya maka yadda zaka juya ni ne ko...to 'karya kuke? An gaya ma na manta halin da take ciki ne? yarinya ce amma kullum safiya sai ta yi wankan buta agidan nan in banda shashanci miye hakan ke nufi?" Sosai ran Hamma Bukar ya fara 6aci, amma da yake yasan da wacce yake maganar dole ya danne fushin sa...yace " Iyami wannan ai tsohon zance ne tun yaushe rabon ta da hakan kuma ai kinsan lalurar da take 'dauke da shi da yasa ta ke wankan...". Da hannu tayi saurin dakatar da shi... " Raba ni da gaibu, raba ni da shaidar da ban san farkon ta ba, ni babu abinda na sani ni..bansan komai ba, kuma da zakace tun yaushe rabon ta da wankan to ta riga tayi abinda ranta ke so tasan tana da ciki ba dole ta daina bin mazan da take gi din ba..abin nema ne ya samu shiyasa ta daina..kuma da yake tasan gab take da haifo nata ca nake ba'a da'de ba da Dija tazo su je barka ta 'kiya.. ." " Innalillahi...haba Iyami, meyasa kike furta irin wannan kalamin fisabilillahi...ke fa tamkar mahifiya kike a wurin ta ...". " Allah sittira, Allah ya tsari gatari na da saran shuka, wallahi ban haifi irin mayu dangin karuwai ba, dan haka baza'a lika min na kale ba, kaima kar ka yi hankali kaga ni, watan watarana muna nan da kai sai an ce kaine uban 'diyar ai.." " Ya ilahi..." Ya fa'di yana dafe goshin sa. Duk wannan tijarar da Iyami ke yi Abban mu na zaune ko uhum bai ce ba, balle yy yunkurin tankawa, Salale ma sai yanzun yayi magana inda ya ce" Haba Iyami sai kace baki san wace Zaituna ba, muma fa da ba gidan muke rayuwa ba zamu iya shaidar halin ta balle kuma ke da kullum kuke tare, wallahi ni har a zuciya ta banji cewa 'karya Zaituna tayi min ba, bata yi kama da mai karya ba balle wannan gagarumin abinda kk tunanin ta aikata, baya ga ma ni a gabana aka kwashi gawar matar da 'dayan jinjirin nata..dan Allah ki sassauta mata iyami, yarinyar nan taimako tayi abin kuma sai ya juye haka nan..." Kanta ta kawar gefe tana girgiza 'kafafu...Nasiha Salale yayi mata kafin ya bar gidan amma babu 'daya da ya shiga zuciyar ta, sai dai abu guda da ya sa danji kwanciyar hankali shine duk cikin su babu wanda yayi zancen zai raba ni da Yarinyar, babban abinda ya wanki zuciya ta kenan har yasa fa'dan Iyami sam bai wani dame ni ba. Duk da kuwa hayaniyan da tayi 'dazun ya sanya ma'kwabtan mu na kusa le'kowa hadda masu le'kowa ta saman katanga, matar Hamma Bukar da ke can gidan ta ma tuni labari ya isa mata, haka ta zaro mayafi ta taho cikin gidan, kusan komai gaban idanun ta aka yishi. Kowa kallon mara gaskiya yake min, kowa na min kallon mai fuska biyu...musamman bayan fitan Salele da Iyami ta cigaba da sababi tana fa'din" Wannan jarabar hijabin dama ai kowa yasan ba zai kasance na alkhairi ba, yarinya ace kullum sai dai ta tashi ta kuma kwanta da hijabi kamar haihuwar cikin limamai? ashe duk na munafurci ne ciki kike 6oyewa a ciki, an dai yi hasara wallahi tallahi, mu kam abin arziki muka gada ba na sharri ba, dama ina za'a irin kirki wajen gantalallu, ace mutane basu da takamamman wajen zama sai cin arziki a zauna a tashi, mu dai gidan nan bamu da makwancin shege sai ki nemi inda dare yai miki tun da wuri ki san yadda zaki yi da kazantar 'diyar ki..." Wannan maganar ya 'kona min zucia sosai, ban kuma sha wani wahalar fahimtar zagin da take min, zagin asalin mahaifiya ta take, duk da masan kusan abinda ta fada gaskia ne amma hakan ba shine yake nuni da cewar asalin ta ba mai kyau ba ne, mahaifan ta fulani ne kuma na tashi...dalilin rabuwar ta da su kenan bayan auren ta Abban mu har kuma yau din nan bata san inda suke ba suma basu zo gare ta ba dayake suna jin haushin ta na auren barebari da ta za6i yi ta 'ki bafulatani 'dan uwan ta. Iyami zata sake magana Yaah Bukar yy saurin dakatar da ita. " Haba dan Allah Iyami, gaskiya baki kyautawa yarinyar nan, saka hijabin nata laifi ya zama dan yau ta gamu da 'kaddara? dan Allah kar kiyi amfani da wasu abubuwa na rayuwar ta ki 6ata mata suna dan Allah Iyami, yanzun aka gama yi miki bayani amma kina sake 'kwakulo wata maganar daban saboda menene dan Allah...?" " Saboda Ubanka ne Modu Kyari..nace sbd uban ka ne kaji Habu...wallahi bana son shashanci idan ka ishe ni zan zazzabga maka mari yanzun nan babu ruwa na ka kiyaye ni..." " To kiyi ha'kuri ni dai Iyami, indai dan yarinyar nan ne insha Allahu zuwa gobe za'a san yadda za'ayi da ita ki iwantar da hankalin ki". Ya fada yana mai sunkuyar da kansa cikin tsananin damuwa. Ni kam dama tuni kuka nake, rabon da idanuwa na su bushe har na manta lkcn. Jira nake Abban mu ya furta wata kalma ko.zan samu sassauci daga wajen sa amma babu alamun hakan. Iyami ce ta kawar da kai tace" Da yafi muku dan wallahi, dan ni babu wanda ya isa ya zauna min agida da shegen iri". Hamma na kai ya girgiza kawai ya tashi ya nufi 'kofa...haka ma Goni da tun zaman sa bai furta ko da kalma guda bane shima 'dakin sa ya wuce. Azeemah kuwa tsaye take hannun ta ri'ke da yaron ta tana bina da wani shegen kallon da na tabbatar na tsana ne. Har Hamma ya fita sai kuma sai ya dawo daga bakin 'kofa ya tsaya yace" Ke Azeemah zo ki wuce gida". Inda yayi maganar babu wasa balle fara'a saman fuskar sa. Sum-sum naga tabi bayan sa ta fita itama tana 'kara hade ranta. Ni kam banda kuka babu abinda nake yi har a lkcn. Iyami ma 'dakin ta ta shige Khausar bata nan haka ma Ummaru suna gidan Hamma Bukar tun 'dazun. Ganin kowa ya barni ne ya sani kallon inda Abban mu yake zaune, wani uban harara ya banka min da muka hada idanu wanda yasa take na mi'ke na shige 'daki na ina sake rusa kukan rashin madafa. Shikenan fa kafin ace sallar maghrib maganar Iyami tayi tasiri ta kuma yi nisan zango, inda tayi tafiyar da ni kaina bansan iayakr ta ba, tafia ce da zata bawa kowa mamaki. Kowa cewa yake ashe dama Zaituna 'yar iska ce, gashi ta haifi 'yar da ba'asan waye ubanta ba....ashe.. ashe...ashe..ashe dai maganganu dai kala- kala. Dayawan mutane fa sun san me yafaru yau agarin, an kuma san cewa an zo an kwashi gawawwakin mutane, sannan ko cikin garin namu akwai wa'danda abin ya ritsa da su ya kuma yi sanadin rayukan su, kuma sunga lokacin da aka tafi da gawar matar da 'dayan jinjirin amma saboda son zuciya kowa 'karyatani yake, wai sharri kawai nayi mata dan naga itama ta haihu...kuma dan naga bata raye ne shiyasa, amma ai tare take da jinjirin ta..babu wanda ya yadda cewar matar ce ta haifi 'yan biyun ta kuma ban 'daya a hannu na illa Salele mai Chemist da Hamma Bukar. Iyami kam kafin dare yayi duk ta cire abinda ke 'kunshe a ranta game da ni, ciki hadda zaryar shiga bayi da nata yi da safiyar ranar, kwana da nayi da ciwon ciki da tafiyar dur'kuso da nayi sbd ciwo wai duk ashe na'kuda nake bata kula ba...ni kuma na 6oye sbd munafurci. Sai bayan maghrib Hamma ya dawo, lokacin kuwa yarinyar na ta kuka nima ina taya ta dan na rasa yadda zanyi da ita...da kansa ya 'dauki yarinyar ya bata zam- zam da ya shigo da shi ya kuma tauna dabino mai yawa ya bata Allah cikin ikon sa kuwa sai tayi bacci. kwantar da ita yayi sannan ya kalle ni" Kukan ya isa haka nan to". Ya fa'di yana kallo na. Hawayen fuska ta na fara sharewa yayin da Hamma ya cigaba da fa'din" Kin dai ji abinda Iyami tace ko? nasan abu ne me wahala ta bari ki zauna da yarinyar nan cikin gidan nan, kin kuwa sani ba sai na maimaita mk akan Abbah ma ba zai ta6a tankawa ba..Baffah Liman kam na tabbatar har gwamma kowa akan sa dan 'dazu na same da shi da batun sai ya nuna min cewa ai tun 'dazu ma yaji labari yace kuma shi babu ruwan sa be ce kije ki kwashi ciki ba balle a rataya masa wani nawi, duk yadda naso fahimtar da shi abin ya faskara sai ma wasu hujjoji da yake bani kwatankwacin na Iyami, dole na hakura na baro wajen sa...koma fa ya tsaya ya saurareni bai yi ba, shima yayi amfani da zancen mutane na cewa kece kika haifi Yarinyar". Kuka na sanya mai sauti ina toshe baki na nace" Hamma wallahi ni bani na haife ta ba...". Bai bari ba kai aya ba yace" Na sani..ni na sani 'kanwata, na san ba ke kk haifi yarinyar ba rashin fahimta ne kawai irin na mutane ya sanya kowa yk fa'din ke ce kika haife ta...amma ni nasan halin 'kanwata...taimakon da kika yi ubangiji Allah ya baki ladan sa, Allah yasa ya kasance mk alkhairi, Allah ya ji6inci lamuran ki ya haska mk rayuwar ki...ita kuma uwar Allah ya ji'kan ta yayi mata Rahama..". Cikin zuciya ta nake amsawa da Ameen... Shi kuma ya cigaba da fa'din" Na riga ya yanke shawarar maida yarinyar nan hannun hukuma..sbd a gani na...." a firgice na 'dago kaina na kalle shi. Sai ya jinjina min kai sannan ya cigaba da fa'din" Umm...dole zan maida ta Zaituna duk da nasan hakan ma wani batun daban zai tayar, amma dai dole wata mafitar ta 'dara wata, 'kila mutane su ce dagangan aka salwantar da yarinyar dan asirin ki ya rufu amma ban damu ba dole hakan za'ayi, dan bana so ki cigaba da rayuwa kullum cikin 'kunci da rashin sukuni, zaman ki da yarinyar nan kuwa dai- dai yake da 'kauracewar farin ciki a rayuwar ki gaba 'daya...." Shiru nayi illa hawayen da ke bin kunci na ka'dan- ka'dan. Ba najin tsawon rayuwa ta na baya na ta6a shiga tashin hankali sama da wancan ranar, tunani na ya toshe, ji na da gani na neman dusashewa suke, ji nk kowace kalma ba na fahimtar ta sosai indai akan rabani da yarinyar ne, ina 'kaunar ta, kuma har 'kasan zucia ta bana so arabani da ita, yini gudan da nayi da ita sai nake ji tamkar shakera muka yi, wallahi banajin fargabar faruwar komai ko kuma tasirin 'kunci cikin rayuwa ta matu'kar zan bu'di idanu in ganta kusa dani. Hamma ne ya cigaba da magana da sanyin murya yake fa'din"....Ko da an barki da ita bazaki iya rainon ta ba Zatuna, raino da kk gani bashi da sau'ki ko ka'dan, balle ke tuna iya shekarun ki, har yanzun ke yarinya ce, ba na fa'di hakn dan kinyi 'kan'kan da ki raini yarinyar ba ne duba da cewar da ace taki ce ta kanki bani da damar furta hkn, dan nasan kin isa kiyi shi, amma 'kanwata raino na bukatar matallafi inma ya kasance miji ne, mahaifiya ko kuma 'yan uwanki, sannan ya kasance babu tsangwama, da duk akwai wannan bazan hanaki ba 'kanwa ta, amma nasan kin fini sanin wace ke da kuma inda kk rayuwa, kin fini sanin su waye kewaye dake kk rayuwa da su, zaki fahimci me nk nufi idan kin zurfafa cikin magana ta, babban dalili ma Zaituna kinga baki da abincin da ya dace ki bata wahala kawai zaku sha daga ke har ita...". Dagaske Hamma yy maganar da ya kamata in fahimce shi amma kwakwalwata toshe take, kaunar yarinyar ya riga ya rufe min idanu na. Cikin kuka na dube shi " Ni dai dan..Allah Hamma... ka barmin ita..wallahi zan iya kulawa da ita, amanar ta mahaifiyar ta bani, kuma tace halak malak ta ta bani ita..idan na kai ta wani wajen ai naci amanar ta Hamma, kuma har abada bazan ji salama cikin zucia ta ba...dan Allah Hamma ka bar min ita...wlh ina son ta...". Baki bu'de Hamma yake kallo na da alamun mamaki...bai 6oye cikin ransa ba sai da ya furta..." Kina nufin duk kunyi wannan doguwar maganar da ita..amma meyasa ta kasa sanar dake asalin ta...". " Hamma bb mamaki Allah ne bai sa tunanin ta ya tafi wurin ba..." Cikin sa'a naji wannan amsar tazo baki na. Yace" Ke kuma meyasa baki tambaye ta ba?" " Hamma nima ban tuna ba ne..amma tace min Kano take mahaifiyar ta kuma na nan Maiduguri ta fa'da min sunan unguwar da take amma na manta sunan...". " Zaituna...!" " Wallahi Hamma dagaske nk..." Kallo na ya tsaya yi na tsawon mintina sannan ya girgiza kansa kawai ya tashi ya fita. " Ke de ki shirya insha Allah zuwa jibi idan an bu'de gari zamu maida ta hannun jami'an tsaro su zasu iya sada ta da dangin ta..." Ya fa'da yana mai barin 'dakin. Ni kam kuka sosai nake yi haka kuma na kwana tunani, cikin dare babu irin tunanin da banyi ba, nasan da wuya ne jami'an tsaron su iya gano inda asalin yarinyar yake, ba lallai ne ma su gane wace ita ba tunda mutane da yawa aka kwashi gawarwakin sun ba wai nan garin ka'dai bane.. 'karshe ma gidan marayu zasu je su jefa ta ta taso acan..ni kam bazan yadda akai mata yarinya gidan marayu ba bayan ta gama bayyana min tsananin 'kaunar ta da suke yi ita har dangin mijin na ta..baya ga hk ma ai itan yanzu amana ta ce, idan nayi hkn ban yi mata adalci ba ace 'diyar su ta taso cikin gidan marayu, duk da hutu da gayun da na fahimta tattare da ita, na kuma tabbata attajirai ne tunda cikin magabar ta naji tace min da jirgi ma tazo Maiduguri...idan na yadda na mayar da yarinyar aka siyar da ita wa 'yan yankan kai ai ban musu adalci ba...". Ire iren wannan tunanin ne ya hanani bacci daren ranar..ko da safe da na tashi zazza6i sosai na tashi da shi saboda yini da kwanan da nayi inayin kuka, ranar ko azumi ban iya 'dauka ba...a hakan ma da Iyami taga ina alwala dogon tsaki taja tana mitar duk dai munafurci ne sai kace ba'a san me ke faruwa da ni ba. Ni dai ban damu ba na wuce na yi sallah na....ina idarwa sai ga Hamma na ya shigo da ruwan zafin sa ka'dan akofi...da kansa ya 'dauki yarinyar ya bata tasha bayan na gaishe shi. Yau kam Iyami bata wani jira nayi mata aiki ba dan afa'dar ta wai baza'a ta6a mata kwanuka da hannu mai najasa ba inje can inyi ta fama da shegiyar 'diya ta, kuma ita wallahi baza'a zauna mata agida haka nan ba sai dai in ita ta bar gidan. " Hammah Bukar". Na 'kira sunan shi cikin sanyin murya ta daga kwancen da nike sai ya 'dago a hankali ya dube ni..ido na 'dan lumshe dan kunyar sa ma nake ji yanzu " Inajin ki..'kan wata" Ya fa'da fuskar sa bb alamun fara'a koka'dan, domin ni har shi munji duk abinda Iyami ta fa'da. " Hammah dan Allah kar ka raba ni ita..'yar 'karama ce fa, bata da baki, bata da wayon da zata gane su waye asalin iyayen ta, suma jami'an tsaron fa bamu da tabbacin inda zasu kaita 'kila ma jefar da ita zasu yi, dan Allah Hamma ka barmin ita zan bawa Iyami ha'kuri..ta barmu mu zauna ko da zamu na fita nema ne da kanmu dan muci...". " Zaitun ke fa guntun tunani gare ki ko..?" Ya bani amsa a kufule, baki san illar yin hakan ga rayuwar ki ba ko, baki tunanin 'kalubalen da yk tunkaro rayuwar ki ba, baki ma sani ba mutum ce ko aljan, musulma ko kafira kawai ke de abarki ki zauna da ita...". " Wallahi Hamma musulma ce...sunan ta Nadia...". Shiru yayi yana bina da kallon mmk. Sai na karya wuya na gefe nayi 'kasa da idanu na sannan nace. " Ni dai ina son ta Hamma amanar ta aka bani kuma idan aka rabamu bansan yadda zanyi da raina ba.." Na 'karashe maganar cikin kuka mai sauti da ko fita murya ta bata yi sosai. " Nifa Zaituna ina jiye miki abinda zai je ya dawo ne, kuma ma kinga ba nutsuwa zaki samu ba idan kina tare da ita...sannan me ma zaki bata matsayin abinci...?" " Hammah da yawa fa iyayen su na haifar su kuma su rasu su barsu a hakan kuma suke rayuwa har su girma, na tabbata itama wannan 'din zata rayu da izinin Allah tunda ga koko..." Wannan karan murmushi yayi sannan ya girgiza kansa yace" Bata kai shan koka ba tukunna sai dai abata madara". 'Kayattacen murmushi ne ya 'kwace min duk da yk fuska ta da ruwan hawaye, da sanyin murya nace" Hammanm kenan ka yadda zata zauna da ni..?" " Sai nayi shawara tukunna kuma sai Iyami ta amince..". Duk da ya fa'di hakan amma sam ban damu ba, dan ni amincewar Hamma Bukar ce damuwa ta nasan da ya amince min shikenan. Haka ya fita ya barni ina jin da'di sosai, da fitar sa daga 'dakin yaci karo da matan ma'kwabtan mu har su hu'du wai sun zo gaida masu jego.... Zaitoon mai jego🤪 Salmerh😘 [6/1/2023, 8:07 am] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Wattpad@* _Serlmerh-md_ 🅿️ *...91* .......Wani tu'kukin takaici ne yaji ya ziyarce zuciyar shi a lkc guda..da irr-iren wadan nan mutanen kewaye da su ma ta ya ze iya barin Zaituna zama da yarinyar nan...? ya tambayi kansa. Da gangan sai ya'ki matsawa daga bakin 'kofar har suka gama gaisawa da shi..." Masu jegon na ciki?" 'Daya daga cikin matan ta tambaya cike da azar6a6i. " A a bacci suke yi". Shine amsar da ya basu da yana mai banka musu wata muguwar harara da 'kasa-'kasa. " Aww to amma ai za'a iya ganin 'diyar ko?" " Bata da ishasshiyar lafiya an kuma hana jagwalgwala ta". Amsar da ya basu kenan a tsare ya kuma kawar da kansa gefe sam bayi da niyyan matsawa daga 'kofar. Haka badan sun so ba suka yi waje suna mita 'kasa 'kasa wai irin wannan abin, dan ma 'yar gaba da fatiha ce, ake wani 'da'd'daurewa ana 'kafafa, waye uban sai Allah?" Shi kam kasa barin gidan yayi saboda takaici...ya 'dauki a 'kalla tsawon mintina sama da talatin tsaye a wurin kafin ya fara yun'kurin sanya takalman sa..ni kam tuntuni bacci yy gaba da ni, baccin da ban samu yin sa da kyau tsakanin kwanakin ba..musamman ma daren jiya da zazzafan ciwon da kai ya taso ni gaba. Har ya kusa barin gidan sai Abban mu ya fito daga 'dakin sa, nan ya zauna bisa kujerar sa da yake zama irin ta dattawa...yayin da Hamma ya isa ya tsugunna gaban sa daga 'kasa kan 'kafafuwan sa... " Abbah barka da yamma, fatan ansha ruwa lpy ..?" " Kira min Zaituna". Abbahn mu ya fa'da batare da ya bi ta kan gaisuwar Hamman ba. Hamma Bukar ne yaje ya tashe ni daga baccin da nake muka fito tare da shi..jiri sosai nake yake shirin 'diba na saboda zafin ciwon kai 'din da nake son takurani. Amma ganin inda Hamma ya tunkara wato wajen Abban mu da ko alamun fara'a babu saman fuskar sa yasa take na nemi ciwon na rasa har na isa gaban sa nima nayi zaman dirshan zucia ta na harbawa da 'karfin da bana jin na ta6a fuskantar irinta. Lokacin da kunnuwa na suka jiye min kalamin mahaifi na agare ni ba ciwon kai ba natsuwa ta ma gaba 'daya rasa ta nayi na fara rarraba idanu. Addu'a nk Allah yasa ba dai-dai kunnuwa na suka jiye min ba, Allah yasa ba Abbah na bane ya furta. Amma duk yadda naso 'karya sautin muryar ban samu canji ko guda ba..abin nan dai da najin shi yace..wanda tashin farko na fahimci cewa yana tafiya ne bisa ra'ayin matar sa Iyani. " Mahaifiyar ku tace bazata zauna da shege a gida ba, dan haka kafin yamma bana so in dawo in same ki cikin gidana..ki tattara ki san inda zaki saka wannan abin kunyar da kk kwaso ko kuma ki kaiwa ubanta ya ri'ke abinsa tunda na tabbata kinsan waye ubanta, ni ke ka'dai na haifa ban kuma haifi shege ba balle in raini na wasu, dan haka baza'a tayar min da hankalin gida ina zaman zama na ba..". Hamma Bukar shiru yayi yana tunanin ta inda zai 6ullowa lamarin. Ni kuwa kuka ne kawai ya 'kwace min bayan tabbatar da cewa mahaifi na da gaske yake...ina girgiza kaina nake fa'din" Abban mu wallahi ni bani na haifi yarinyar ba, kuma ina zan ga ubanta balle in sanshi har in bashi 'diyar shi, Abbah uwar ce fa kawai muka ha'du da ita kuma bata yi min bayani cikakke kan asalin su ba, dan Allah Abbah kayi min rai kar ka kore ni da 'yar yarinyar nan, idan ka kore ni ina zan saka rayuwa ta..wallahi Abbah ka tambayi Hamma Bukar kaji.. shi ya sani ba nice na haifi yarinyar nan ba Abbah..dan Allah kayi ha'kuri..." Na 'karashe ina mai komawa bisa gwiwoyi na. Kafin Abbah ko Hamma 'dayan su yayi magana sai ji muka yi Iyami na tafa hannuwa tana fa'din "...wallahi Zaituna bazaki zauna min agida da ''diyar shege ba, ban gaji hakan ba dan haka bazan zauna gida 'daya da mai shi a gur6ata min zuri'ah ba, kina nan kullum 'kunsun-'kunsun cikin hijabi ashe na munafurci ne sai ga sakamakon hijabin ya bayyana 'karara...kima san yadda zakiyi tun wuri da shegen abin nan matu'kar kina son zama agidan nan sa6anin hakan kuwa wallahi terere zan cigaba da yi miki kowa sai yaji me kika aikata da kuma sakamakon da kk samo, kema da kanki kin san sauran kin kuma san iya fin hakan ma..." Rintse idanu nayi ina jin wani suka a cikin zuciya ta, nasan babu abinda zan iya fa'da a wannan halin wanda zai yi tasiri akan Iyami har yasa ta canza ra'ayi, dama Hamma Bukar ne 'dan gaban goshin ta shima 'din yanzu idanun ta sun rufe akan sa, Abbahn mu kansa maganar ta yake bi kuma abu ne me wuya ya canza maganar sa shima. Idanu Hamma ya zuba mata har takai 'karshen maganar ta a hankali ya furta " Dan Allah Iyami kiyi ha'kuri....". " kar ma ka fara..." Iyami tayi saurin dakatar da shi ta hanyar fa'din hkn gami da 'daga masa hannu. sannan ta cigaba da fa'din" ai na riga na bata za6i..sai ki za6a ko shegen abin nan ko kuma zama a cikin gidan uban ki.." Sunkuyar da kai nayi hawaye na na sau'ko min sosai, Abban mu, na kalla naga yadda shima ya tsura min idanu yana kallo na bansan tunanin me yake yi ba, ban kuma san damuwar da ta dame shi cikin ransa ba. A hankali na kalli Hamma da naga ya shiga alamu na rashin mafita" IYami ni dai ina son ta dan Allah ki barni in zauna da ita.." Baki Iyami ta kya6e gami da karkata kanta tana fa'din" asararriya kawai, kin dai cuci hijabi wlh...kuma ba dai a gidan nan ba in sake nanata mk, sau 'dari idan zance wani abu kan zancen nan toh kuwa abu guda zan yi ta nanatawa ..". Hamma na kalla na lumshe idanu na kuma bu'dewa sannan na kalli mahaifi na a hankali na furta" Shikenan Iyami, zan tafi, zan bar gidan nan Insha Allahu bazan zauna da ita anan ba...". Yadda na 'kurawa mahifina ido nake maganar ya sani fahimtar wani 6oyayyen abu cikin idanun sa, domin da jin zan bar gidan naga ya lumshe idanun sa da 'karfi ya juyar da kai gefe. Nasan bai ji da'din magana ta ba, sannan da za'a tona zuciyar sa ba son ransa bane hakan ya faru amma sam bashi da damar dakatar da komai, biyayya yake yi tamkar yadda mu 'ya'ya muke yi. Ga Hamma Bukar na dawo da duba na da tuni ya mi'ke tsaye ban ma kula ba sai a lkcn. Nima tsayen na mi'ke nace" Hamma na zan tafi....zan bar gidan nan, zan tafi wajen...." Bai kai ga rufe baki na ba naji ya saukar mari gefen kunci na, kafin in yi kyakykwan motsi na sake ji ya sharara min wani marin nan na tashi da mari har guda biyu. Da duk hannuwa na na dafe kunci na hawaye na sakko min nk binsa da kallo. Shi kansa idanuwan sa hawaye ne a cike taf... amma ko 'diss bai bari ya sauko ba. Zuciyar sa ke yi masa tafarfasa da jin kalaman Iyami da kuma furuci na na cewar zan bar gidan, amma ya kasa furta komai a zahiri.... Hannu ya kuma 'dagowa ya nuna ni da 'dan yatsa yana kallon cikin idanu na. Jikin sa rawa yake domin ko hannun nasa ka duba zaka fahimci hakan. Yarfar da hannun yayi gami da juyar da kansa gefe cike da tashin hnkl. Da gudu na juya na wuce 'daki na na 'dauko yarinyar da jakar kayan sawa na, dama su ka'dai ne suka kasance mallaki na a gidan...ina dawowa tsakar gidan na tarar da Hamma gaban Abban mu ya dur'kusa bisa gwiwoyin sa yana rusa kuka tamkar wanda akayi masa mutuwa gagaruma...cikin kukan yake fa'din" Abbah kana ganin abinda ke faruwa da idanun ka? Abbah kana ji kana gani mai yasa bazaka bu'di baki kayi magana ba Abbah, wallahi Abbah ba Zaituna ce ta haifi yarinyar nan ba na sani, dan Allah kuyi mata uzuri mana, me yasa bazaku fahimci irin yarinyar da kuka haifa kuka kuma raina agaban ku ba....?" Kuka yake sosai kamar ransa zai fita irin kukan dake fita da takaici tun daga can cikin zucia, kukan da gaba 'daya ya tsinka min jiyoyin jiki na kaf, kukan da duk ya karya min duk wani 'kwarin gwiwa ta. Ban ta6a ganin Yayana cikin irin wannan yanayin ba..sai yau ka'dai, yau 'din ma a sanadi na. Abin mamaki ko 'kala Abbah bai ce ba tamkar bada shi ake yi ba. Nima tuni na zube bisa sbd ganin yanayin Hamma na yake yi ya sanya ni dur'kushewa bisa gwiwoyi na ina kuka nake fa'din" Abbah ka yafe min dan Allah, ba nufi na in guje ku ko 6ata ranku ba, amana na kar6a kuma ina so in cika al'kawari na ne Abbah, Hammah dan Allah ka tsayar da hawayen ka haka nan, ciwon su nake ji a zucia ta, Hamma wlh har abada bazan ta6a yafewa kaina ba wannan hawayen da ka zubda sbd ni, dan Allah Hamma ka yafe min, duk tsawon rayuwa ta ban ta6a tunanin akwai irin wannan ranar ba, ban ta6a tunanin akwai ranar da ni zan zamo sanadin kukan ka ba...." Kuka ya 'kwace min sosai har na kasa 'karasa abinda nayi niyyan fa'da. A hankali na mi'ke tsaye rungume da yarinyar na sa6i jaka ta da 'dayan hannu na da 'kyar na 'daga 'kafa ta nayi gaba ban ko sake waigowa ba. Ganin ina fita shima Hamma Bukar ya mike yabi baya na da sauri. Kafin ya fita Iyami ta 'kira sunan sa cikin Izza da nuna ikon ta.. Cak ya tsaya amma bai waigo ba" Wallahi Abubakar idan kuskura ka kai yarinyar nan gidan ka bani ba kai har abada na fa'da maka...". Ji yayi tamkar an 'da'd'daure shi, wani zafi yaji tamkar an zuba masa ruwan zafi saman 'kirjin sa. Cikin ransa ya furta " wannan wani irin son zucia ne haka? Wannan wani irin shiga hakki ne..?" Da 'kyar ya samu damar waigowa ya kalle ta da kyau yaga yanayin ta erh da gaske take yi sannan ya yi waje yana goge ragowar 'kwallan da ya zubo masa. Taku ka'dan yayi ya cimmani sai ganin sa nayi agaba na idanun sa duk sun firfito waje sun koma jajaye. " Hakan yafi maki ko 'kanwa ta?" Ya fa'da yana 'kure ni da kallo. Kuka na fara tare da sakin jakar hannu na ina shirin sulalewa 'kasa yayi saurin dakatar da ni da fa'din..." Ban ce ki tara min mutane ba, kije gidan Innani zan zo an jima na same...". Daga haka ya bar gaba na ya kama hanyar gidan sa. Ni kam waigowa nayi nabi bayan sa da kallo..." 'dan uwa na, abin alfahari na, sosai nake ji da Hamma na, sosai nake 'kaunar sa, amma yau ni da kaina nasan na 6ata masa ransa.... " To Hamma ya zanyi, tun jiya nake ro'kon Allah ya bayyana min abinda ya kamata inyi amma har yanzu zucia ta toshe take na rasa mafita...bani da za6i illah in barwa Iyami gidan ta kamar yadda naga tafi raja'a kansa...." Na furta hakan cikjn zucia ta, ina hawaye na kama hanyar gidan Inna ta. Na kan lura da kallon da mutane ke min a hanya ta amma sam kallon bai dame ni ba, abinda suke furtawa biyo bayan kallon shima sam bai bai dame ni ba, in motsa hannu na inji yarinyar na nan tare da ni shine ka'dai buri na, ban sani ba hukunci na kuskure ne ko kuma akan dai- dai nake ba. Kwance na samu Inna ta tana hutawa, da zuwa na kuwa na dur'kushe bisa gwiwoyi na na ringa mata kuka..bata ce da ni 'kala ba wanda cikkn kukan nake fa'din" Iyami tace bazan zauna mata a gida da yarinyar ba Inna, Innani ni dai ina son ta dan Allah kar ku raba ni da ita..." Kuka nake sosai, ina jin yadda kaina ke min sara sbd yawan kukan da nayi amma sam ban bi ta kansa ba. Inna ta ma bata ce da ni uffan ba illah yarinyar da ta amsa daga hannu na amma a yanayin ta na fahimci bata ji dadin maganar ba. Bari na tayi a 'dakin ta fita ta hura wuta tayi mata wanka, ruwan 'dumin ta bata ta sha take kuwa cikin sa'a sai tayi bacci...sai lokacin Innani ta dawo da ita ta kwantar da ita bisa katifa sannan ta sake fita waje, rigar da ta cirewa yarinyar shi taje ta wanke ta kuma dawowa ta zauna gefe na. " In kin gama kukan sai kije kiyi wanka kiji da'din jikin ki ke ma, ni kam bansan me zan ce da ke ba yanzu tunda kin riga kin za6awa kanki abinda kikaga yafi maki...amma ki sani duk abinda zai biyo baya ni babu ruwa na, kinga wannan ma somin ta6i ne matukar kk cc ke a kullum sai abinda kk niyya ko ra'ayi zakiyi to kuwa ki shirya tar6ar 'kalubale iri daban daban...". " Innani ki daina min mugun fata dan Allah..." Kai ta girgiza sannan tace" Kema kinsan har abada bazan ta6a yi miki mugun fata ba, magana ce dai ta gaskiya nake fada miki, kuma ya zam min dole ne in fada miki 'din tunda a yanzu idanun ki rufe suke, wala alla ko zaku bu'da su ka'dan ki fahimci abinda ake hango mk..." " Inna..."! Na fada da niyyar magana sai tayi saurin dakatar da ni da 'daga hannun ta 'daya. "..Ba maganar ki nake bu'katan ji ba, so nake ki gane ki kuma lura.. tun ba'aje ko'ina ba gidan mahaifin ki na neman yafi 'karfin ki sbd rigimar ki...jiya yaron nan Habu yazo ya same ni kan yadda kuka yi da shi..kan kin 'ki amincewa a maida yarinyar nan..." Kuka nake sosai sbd ko a maganar Inna ta ma fahimci ita kanta ba so na take da yarinyar ba...duk da hakan sai da naso fahimtar da ita cewa ba bu fa wanda yasan inda dangin ta suke toh in haka ne wajen waye za'a maida ta dan Allah in dai ba salwantar da ita ba....?" " Sannu mai imani sarkin masu tausayi, yanzu kam za6i ya rage naki ai ni babu abinda zance miki..tunda gashi har kin sa magana ta cika gari ta fannin da ba hakan yake ba, kuma ina tabbatar miki da cewa mawuyaci ne jama'a su fahimce ki kamar yadda kk tunani.....". Ban sake ce da ita uffan ba haka itama bata bar inda nake ba. Sai da nayi kuka na na gaji nayi shiru dan kaina kafin Inna ta ta fara lalla6ani...." Ba wai nufi na in raba ki da yarinyar bane so nake ki fahimci kalar gagarumin aikin da zaki kwasowa kanki, kinsani na sani ba gata ne da mu cikin garin nan ba balle muyi tunanin akwai mai tsaya mana..Yayan ki ne ka'dai, kuma yana iya bakin 'ko'karin sa, bai kamata sbd tsananin rigima ki sake kwaso masa wani nauyin na daban ba..." Cike da shagwa6a gami da son kawar da zancen nace da Innani ni dai yunwa nake ji...". " Baki 'dauki azumin bane"? Ta tambaye ni da kulawa tana dubana. Kaina na girgiza mata gami da fa'din" Ciwon kai da zazza6i ke damu na kuma tun jiya banci abuncin kirki ba..". " To kije dai kiyi wankan sai ki zo ga can kunu kisha kafin in sama miki wani abin mai kauri ki sanya a cikin naki". Sai bayan la'asar liss Hamma Bukar yazo gidan har 'yar rama naga yayi saboda tashin hankalin da na santa shi ciki. Sai da suka gaisa da Innani kafin ya wuto 'daki wuri na inda ya same ni zaune na tasa yarinyar gaba ina kallon ta. Kaina 'kasa na gaida shi saboda kunyar abinda nake shirin saka shi. " Ya yarinyar ina fatan tana lafiya..?". Da" erh "na masa shi ina mai wasa da yatsun hannu na. Shiru ne ya 'dan biyo baya sannan yayi gyaran murya gami da 'kiran suna na. Kai na 'daga na 'dan kalle shi sai yace" Sam ni ban so rayuwar ki ta kasance hakan ba 'kanwa ta, kin dai riga da kin san buri na, amma da alamu wannan abinda ya farun duk yana shirin rushe min komai, bazan ta6a jin da'di ace yau bakya gidan mahaifin ki saboda wani dalili na daban ba, amma babu yadda zanyi na riga na sashi a mizanin 'kaddara kuma na amsa fatana Allah ya bamu ikon cinye shi...ni dai duk abinda zan yi ina yin shine ta fannin da nasan bazai cutar da ke ba..saboda farin cikin ki da kwanciyar hankalin ki nake yin wasu abubuwan, haka kuma dalilin kenan da ya sanya ni cewa amaida yarinyar amma kika 'ki amincewa, babu yadda zanyi Zaituna, na barki da ita amma ki san wani abu..'dazun Baffah Liman da kansa yayi min bayanin cewa shi daga yanzu babu wani batun aure tsakanin ki da Baabagana, a fa'dar sa wai bazai ha'da zuri'a da mutane masu biyewa son zuciya ba, kin dai san me hakan ke nufi ko...?" Shiru nayi masa kaina a 'kasa. Yayin da ya cigaba " Ko baki gane yanzu ba nasan wataran zaki fahimta tunda a yanzu kusan duk jama'ar gari irin kallon da suke yiwa al'amrin kenan, bana fatan inga an tozarta min ke amma babu yadda zanyi..buri na kawai kiyi farin ciki kinji.. zan yi magana da Innani ki cigaba da zama anan kafin in shawo kan lamarin acan gida...Allah ya taya ki rainon 'diyar ki ya baki ikon kulawa da ita, haka kike so ince ko...". Ya 'karashe da sigar zolaya. Duk da jiki na yayi sanyi 'kalau amma hakan bai sa na kasa murmusawa ba, na sake sunkuyar da kaina. Kalaman Hamma na sun fi komai sanya ni cikin natsuwa, idan yana fushi ji nake tamkar an tafi min da nawa walwalar ne, yanzu kuwa da na fahimci ya sakko ya kuma yarje min in zauna da yarinyar sai naji natsuwa sosai ya shige ni kamar bani da wata damuwa...abu guda da yafi tsaye min shine kalmar _rigima_ da mahaifiya ta ta furta gare ni, ban tashi sanin da gaske rigimar nayi ba sai lkcn da abubuwa suka kusa tafia min da natsuwa ta. 'Daukan yarinyar Yah Bukar yayi yayi mata addu'a sannan ya ajiye ta ya mi'ke yayi mana sallama ya fita. Dabino ya bani yace idan ansha ruwa in tauna in bata abaki...da yake bai san cewa bana azmi yau 'din ba. Da fitar sa ni kuwa na tauna na ringa bata dan dama tausayin ta ya fara kamani tun da mahaifiyar ta ta haife ta ruwan 'dumi kawai ake bata sai ruwan Zam- zam. Daren ranar ne ma Innani taje ta nemo madarar shanu ta bata tasha ranar kuwa tasha baccin ta sosai bata koyi mutsu-mutsun kirki ba kamar tasan halin da ake ciki. Innani babu ruwan ta haka zata wanki yarinyar ta kuma wanke mata rigar ta da take sanya mata guda 'daya jal da yake har a lkcn babu wata, idan an cire an wanke sai ya bushe sannan ake sake sanya mata...daga ruwa sai madarar shanu idan an samu an siya ake bata in kuwa ba'a samu ba haka nan take zama da ruwan ka'dai, abin ya fara damu na, in bama ikon Allah ba ai yarinyar ba 'karamin wahala zata sha ba, amma Allah ya yassare min abubuwa da dama, ya kare min ita, ya ciyar min da ita a lkcn da ni kaina ban sani ba, ya kuma wadata da lpy ingantacce har zuwa girman ta..... Mun shafe kwanaki biyu a gidan Innani amma banga Dijeh ba banga alamar ta ba, haka kuma banga aboki na Ummaru ko sau 'daya balle su Khausar, Goni kam dama tuni ya koma, nasan kuma babu mamaki iyayen su ne suka hana su zuwa inda nake sai dai wani abu da basu sani ba shine ni duk hakan bai dame ni ba in dai zan bu'de idanu inga yarinyar nan kusa dani toh banda damuwar komai. Salmerh😘 [6/1/2023, 8:07 am] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Wattpad@* _Serlmerh-md_ 🅿️ *...92* ......Tun da handbag in matar ya kasance a wuri na ban ta6a dubawa ba, sai da rashin takamamman abinda yarinyar zata ci ya dame ni kafin na 'dauko jakar na duba da yake ko lokacin da zan tafi gidan Abban mu ban tafi da jakar ba nan na barta gidan inna ta. Ku'di na gani masu 'dan yawa a ciki, nasan akwai su domin tun a wancan ranar Nadia taso yi min kyautar su amma na'ki amsa. Sam banji wani iri ba dan ba sune a gaba na ba, damuwa ta kawai yarinyar ne. Guda biyu na zaro daga ciki 'yan dubu dubu na 'dauki hijabi na na fita wurin salele mai Chemist. Gaishe ni nayi ya masa da sakin fuska sai nace" Dan Allah ko ana iya samun wani magani da za'a ringa bawa yara matsayin abincin su?" Ko 'dar ban ji game da yi masa tambayar ba domin nasan ya riga da yasan komai. 'Yar dariya yayi yace" Ya Baby...?" " Tana nan..." " Lpy..." na rarrabe amsar ina mai kawar da kaina daga kallon sa. Sai yy 'yar murmushi sannan ya 'dora da fa'din" a gaskiya ni dai banda shi irin wanda kk so 'din, amma kuma munyi magana da Habu ma ai ya bani sa'kon madarar yaran, rashin samun hanya ne kawai ya hana sa'kon isowa amma tuni..ku'din yana can na tura...". Da jin hakan na washe ha'kora, godiya sosai nayi masa tamkar wacce ya bani wani gagarumin kyauta. Shi kanshi yaji da'din godiyar da nai masa domin a saman fuskar sa na fahimci hakan. Sai yace" Kafin isowar wancan 'din ina ga zaki iya bata wannan glucose 'din.. yana 'dan 'karawa yara kuzari sai adinga sanyawa cikin ruwan da ake bata zuwa yammaci ma idan sa'a kayan zasu iso"...godiya sosai nayi masa tare da mi'ka masa ku'din hanni na yace a a na barshi kawai in koma gida. Haka na koma zuciya ta fal farin ciki da 'kaguwa sa'kon salele ya iso. Sale kam ko bayan tafiya ta ma kai ya girgiza cike da tausaya wa. Wani da yazo siyan magani bayan na bar wajen shine ya bi baya na da kallo har na 6acewa ganin sa. Dogon tsaki yaja yana mi'kawa Salele ku'din hannun sa yake fa'din" Dunia ta zam abinda ta zama wlh yanzu" Salele yace" Sai Addu'a kawai". " Badole ba! Ai dole ma mu tsananta addu'a in ba hk ba dubi 'yar yarinyar nan amma har tasan tayo ciki ta haife babu ko kunyar Allah balle ta mutane har da fitowa cikin gari yawo tamkar wacce ta aikata wani abin aba mata?". Ransa 6ace sosai yk maganar nan yana kuma yin ta ne cikin harshen Kanuri. Kai Salele ya girgiza yana duban sa yace" Kana da hujjar da zai tabbatar da cewa itan ce ta haife 'diyar...?" A hassale yace da shi" Wace hujja kuma Sale kk nema bayan wanda ya riga ya bayyana..?" " Wannan ba hujja ba ce sam, ku sake tsananta tunani mana, yaushe tayi cikin yaushs ta raine shi kuma duk bb wanda ya ta6a lura har sai da haife? Ku ringa shaida akan abinda kuke da tabbaci dan Allah, ina tabbatar mk cewa yadda wasu suka 'dauki abin ba haka yake ba, na tabbata da Zaituna ta haifi yarinyar nan dagaske da babu abinda zai sata fitowa ina cigiyar abinda zan bata matsayin abinci alhali abincin ta na nan tare da ita kasani nasani, indai zata iya haifewa toh menene kuma shayarwa ai bazai bata wahala ba, sannan kowa yasan halin ta fannin, natsuwa, hankali da sanin ya kamata ta riga ta ci tuta ta wannan fannin, bai jima bama fa muka yi musu akan 'yan matan garin nan kaf amajalisar mu kan wacce tafi hankali da natsuwa kowa Zaituna yake yaba sai gashi jiya- jiya kuwa baki ya sauya hatta Modu da shi zai aure ta ma zagin ta yake yi da sunan da bai dace ba, dama dunia da mutanen cikin ta sam basu da tabbas, da bakin sa yake cewa shi dama da jimawa ya kasa gane kan yarinyar kuma fa 'karya ce kawai, wai kullum tana 'kunshe cikin hijabi ashe ba abin arziki take kunshewa ba, jifa kayan takaici irin ta Modu, jiya baki na kamar zai yi tsayi, a gani na ai ko bata ci darajar matar auren sa ta gaba ba ya kamata taci darajar matsayin 'kanwa da take da shi a wurin sa..." Shiri yayi yana duban gefe tsawon wasu mintina, sannan ya saki ajiyar numfashi. Abinda yk so ya sanar da Sale ya bashi ya juya yana fadin" Allah ya kyauta..." Ameen" Inji Sale. Da gaske shi bb ruwan sa dan hatta Hamma Bukar shi ya kai masa lbrin kuma bai canza komai ba cikin abinda na fa'da masa. Ya kan yawaita yin musu da mutane kuma akan hkn. Yace" _ni kaga yarinyar nan bazan ta6a yi mata mummunan shaida ba, domin da bakin ta bani labarin duk abinda yake faruwa tun ranar da abin ya faru, kuma ni banga alamar 'karya tattare da ita ba har ga Allah.._ " Ko da yaji cewa mahaifina ya kore ni ma ba 'karamin tausayi ne ya kama shi ba, sosai abin ya tsaye masa a zuciya har sai da ya yiwa Hamma Bukar maganar inda yace masa yana bibiyan lamarin dai a hankali tukunna Insha Allah zai shawo kan Abbahn, sai da yaji hkn sannan hankalin sa ya kwanta. Kafin yammaci Hamma Bukar yazo ya kawo madarar da kansa, farin cikin da naji kamar in rungume shi, bayanin yadda za'ayi amfani da shi yayi mana sannan ya 'dauki yarinyar yana kallo na yace" wani suna zaki saka wa 'diyar ta ki ne 'kanwa ta..?" 'Dan murmushi nayi ina yin 'kasa da kaina nace" naji Mahaifiyar ta ambace ta da suna Aishatu ". Murmushin shima yayi yana gyara ri'kon yarinyar a hannun sa. Ba 'karamin da'di nake ji ba da yadda Yayana baya nunawa yarinya ta 'kyama, hakan yasa yake 'kara samun wata gurbi cikin zucia ta gagaruma. A wannan ranar da akayi mata huduba da suna Aishatu...kwana nayi banyi bacci ba sbd tsananin farin ciku, tana rungume da jiki na, idan na kalli fuksar ta sai inji sanyi a zucia ta, in gaji da rikon ta sai in kwantar da ita saman ciki na, gani nake tamkar idan na ajiye ta wani abin zai zo ya 'dauke min ita...balle yadda nasan kowa 'kaunar ta yasa dole nake kaffa- kaffa da abuna...kuma tsayin daren kaf murmushi bai bar saman fuska ta ba. Kafin gari ya waye babu tunanin da banyi ba game da sunan ta, na kasa tantance wani suna ya kamata in kira ta da shi, cewa nake yadda take da kyau din nan toh suna mai kyau mai dadi nake so na 'kaira ta da shi amma na rasa wanne yafi dacewa ..'karshe dole na hakura domin da gaske ni ba sanin sunaye nayi ba sai dai irin namu. Kullymum addu'a ta shine..Allah ya taimake ni ya bani ikon kulawa da ita, yah Allah ka hana kowa raba ni da ita, Yah Allah ka sada mu da alkhairin dake tattare da junan mu tsakanin ni da ita. Ko cikin sallata addu'a ga Mufeeda shine abu na biyu da ke biyo bayan addu'a ta farko...bayan na yiwa iyaye na Yayana da kaina Mufeeda nake 6ata lkc wajen yiwa addu'a...babu kalan addu'ar da bana mata, Allah ya raya ta, Allah ya sa kar idan ta girma ta 'kini, Yah Allah yadda ya kawo kaddarar da ta ha'da ni da ita a lokacin da bana zato Yah Allah ya 'daura ni kan hanyar da ta dace da mu koda ban zaci hakan ba...Allah ya kawar da duk sharrin dake tattare da ita.... Washe gari ranar kasuwar garin mu ne, haka na 'dauki wannan dubu biyun da na fitar cikin jakar Nadia na nufi kasuwa. A hanya na ha'du da Dije 'kawata amma ta kawar da kai tamkar bata sanni ba, turus naja na tsaya ina duban gefen fuskar ta, ga mamaki na idanun Dije hawaye suka fiddawa. A hankali na isa bayan ta na tsaya. Sai kuma na kasa fadin komai..baki na naji yai min nauyi. Sam banga laifin Dijeh ba domin nasan ba ra'din kanta ne ta yanke 'kin kula ni ba babu mamaki umarni take bi kamar yadda nasan dole sai an gindaya mata akan tarayya da ni. Da kanta ta juyo ta kalle ni idanun ta na zubda 'kwalla sosai jiki na yayi sanyi. " Zaitoon kina nan? Ina yarinyar ki...?" Ta tambaye ni da muryar kuka amma cikin sautin muryar ta na fahimci alamun farin gani na tattare da shi. " Abinda ya dace ki fara tambaya ta kenan kema Dije...?" Wani hawayen ne ya sake biyo kuncin ta masu gudu. Sai ta daburce, na riga na gama fahimtar ta rashin sanin abinda zata fada ne ya sata furta hakan. " Kiyi hakuri, ki yafe min kinji Zaituna, ni ban guje ki ba, kuma har abada bazan ta6a guje ki ba musamman akan abinda nasan bazaki ta6a aikatawa ba, shaidar da nayi mk cikin zucia ta ina da yakinin da shi zan mutu babu abinda zai canza shi.. nasan 'kaddara ce ta ha'da ku, sai dai wannan 'kaddara ce zazzafa Zaituna tunda gashi tayi nasarar shiga tsakanin mu...ki rike amana kuma tsananta addu'a ta Insha Allah 'diyar ki alkhairi ce agare ki, da iznin Allah kuma bazaki ta6a yin danasanin kasancewa da ita ba...". Daga haka ta juya bata 'kara waigiwa ta dube ni ba. Dije na kenan, itama mun rabu kenan...?" Na tambayi kaina. Kafin in dawo daga 'dan guntun tunanin da na fa'da Dije har tayi nisa. Bansan lkcn da na kwasa a guje nabi bayan ta ba. " Dijeh..!" Na 'kira sunan ta da 'karfi. Cak ta tsaya amma bata waigi ba, 'ko'kari take ta cika umarnin mahaifan ta amma abin na neman gagarar ta. " Dije nagode sosai...!" Kawai na furta bayan fahimtae da nayi cewa ba tsawaita zance take da bu'katar yi da ni ba. Sai a licn ta waigo, hawayen idanun ta sun bushe, ni kuma a lkcn nawa suka sakko. Hannu ta 'daga min alamun bankwana, amma ni na kasa maida mata martani. Kai na juya mata kawai alamun amsawa. Daga haka tayi tafiyar ta, shikenan Dije na ta barni kenan, daga ranar ban sake saka ta a idanu na ba. Na jima tsaye a wurin ina zubda 'kwalla har na daina hangen Dije kafin na 'daga 'kafafu na da 'kyar na shiga kasuwar da na fito da niyyar zuwa. Riguna na siyowa Aishatu kala uku sai Panties guda hu'du, farin Powder da man shafan ta, kwalli da safa 'kafa uku da huluna guda biyu..sai omo da sabulu na wankin kayan ta. Salmerh😘 [17/1/2023, 10:38 am] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Wattpad@* _Serlmerh-md_ 🅿️ *...93* .......Bani da matsalar komai yanzu sai damuwar rashin makusanta na. Kuma akai- akai Hamma ke kawo magunguna, madara da Glucose 'din yarinyar, ko baya gari kuma ba'a fasa kawowa domin ya riga yayi magana da Mai Chemist abokin sa. Hatta kayan sallahn mu ni da Aishatu duk ya tanadar mana tuntuni. Kewa guda ta ke damuna a hlin yanzu shine kewar gidan mahaifi na, su 'din dole na ne, bani da tamkar su, ko da su basu nemi inda nk ba tunda ni ina nan da lafia ta dole zan neme su. Hakan yasa na yanke shawarar ziyartar gidan mahaifi na da wata safia sbd kawai in hadu da Abbahn mu yasa na fita da sassafe. Da sallama ta na shiga..Iyami ce 'tsakar gidan " Wa alaik..." Sai kuma tayi shiru ta ha'de rai ba'ki'kirin tana bina da wani mugun kallo. " Lafia ..?" Ta jefa min tambaya. " Nazo gaishe ku ne Iyami" Na bata amsa ina 'daga 'kafata zuwa ciki. " Wa yace miki yana bukatan gaisuwar ki anan gidan...? Gayyar 'kasantar..gantalallu mabiya lunguna...?" Sam zagin Iyami na yau 'din bai shiga zucia ta balle ya dame ni, burina kawai in ida nufi na inyi gaba. Kujera da na gani gefe nayi 'kokarin zaunawa ina mai bin cikin gidan namu da kallo yadda duk 'kazance...ko irin gyaran shirye- shiryen sallah da ake yi din nan banga alamun ana da niyyar yi cikin gidan ba. " Iyami Abban mu na nan kuwa..?" " Kin bada ajiyar sa ne..ko kuwa dan kin tmraina ni kk tambaya ta shi, ai naga alamun yanzu raini ke 'dawainiya dake tunda kin riga kinsan waye 'da namiji ba dole ki fitsare idanun ki ba..." Ban bi ta kan maganar tata ba kawai na mike na nfi inda tsintsiya yake na 'dauko domin tsaftace gidan kamar yadda na saba kafin barina gidan. Da sauri Iyani ta hayyako min tana masifa ta kwace tsintsiyar ta.." ai da in bari ki share min ki zazzaga min burbudin karuwanci na kwammaci datti ya hadiye mu ni da yara na, maza kama hanya ki bar gidan nan, bukatar ganin ki ma babu mai yi balle marmarin aikin ki..." Wannan hayagaga ta Iyami ita ta fito da Khausar da ke 'daki ita da Ummaru hk ma Abban mu. A hnkli nace " Haba Iyami...wai dan Allah mance matsayi na cikin gidan kk yi ne...ni 'din fa 'diyar ku ce kuma a tunani na ba'a ta6a canzawa tuwo suna..." Da gudu naji an rungume min 'kafafu..ko da na kalla sai naga Ummaru ne..." Yaa Zaituna..." Ya furta cike da farin cikin sa. Ina kakalo murmushi na dube shi. " Yah Zaituna Iyami tace wai bazaki sake dawowa ba sbd kin zama karuwa nayi ta neman ki banganki ba...ashe zaki dawo, Yah Zaituna kar ki koma kinji...?" Kai na 'daga masa ina mai shafa kansa daidai lkcn da wani zazzafan hawaye ya sakko min. Sam ba aimin adalci ba, kokadan ba'a kyauta min ba a gidan nan..indai har za'a zauna a tsarawa yaro 'karami irin Umar wannan maganar toh me ne kuma za'a aikata da zan bani mmk. Iyami na kalla sai ta kya6e baki ta kawar da kanta...bani da wata kalma da zan fadiwa Ummaru domin wanke kaina amma nasan watan wataran zai fahimta. Khausar na duba ta banko min wata uwar harara dai dai lkcn da sautin muryar Abban mu ta doki kunnuwa na. " Sakar min yaro da Allah...me ma ya kawo gidan nan...?" " Abbah" Na furta ina zubewa bisa gwiwoyina na rushe da kuka. " Abban mu nice fa Zaituna...!" " Sai akayi yaya...bani da wata ala'ka da mutun irin ki balle mai irin sunan ki, na riga na cire ki cikin yaran gidan nan tun daga ranar da kk kwasowa kanki abin kunya, kuma daga yau 'din nan ko a hanya kk ha'du da jinina kk yadda magana ta hada ku wlh ban yafe mk ba, kije can da 'diyar ki..kije ta zame mk dangi amma ba ahali na ba...kin zame mana abin kyamata domin haihuwar irin ku bata da wani riba..." " _Innalillahi wa inna ilaihi raji'un...haba Abbah! Dan Allah ka sassauta min Abban mu, wlh bani da alaka da yarinyar nan indai kuma akan ta ne kk kokarin cire ni daga cikin yaranka Abbah na hakura da yarinyar a mayar da ita gidan marayun na amince amma Abbah kar kai min mugun baki akanta, wlh bani ce na haife ta ba kaddara ce kawai ta hada mu..Abba tausayin ta nk ji sosai agabana aka harbi mahaifiyar ta..._!.. Dakatar da ni yayi da hannun sa. " Wannan duk damuwar ki ce Zaituna...kin haifa baki haifa ba sam bai dame ni ba, amma kasantuwar kin hada jiki da yarinyar kin kuma 'kaunace ta aranki hakn kadai bazai sa in barki cikin zuri'a ta ba...mun riga mun haramta gareki, kije ki rayu da 'diyar ki..inkin ga dama ji zama uwar karuwan duk dunia ma bai dame ni ba Zaituna...tashi ki bar min gida na, kuma daga yau ban yafe ba idan kk sake ko kallon 'kofar gidan nan...". Daga hk ya sa kai yy waje abin sa hnkl kwance. Anya wannan Abban mu ne kuwa, anya shi ya haife ni? Babu abinda nk sai salati fili da zucia ta, yau shine rana na farko da nayi dana sanin duk rayuwa ta, nayi danasanin duk wani taimako da na aikata, ji nayi duniyar tai min zafi gaba 'daya, da wanne zanji, kalaman Abba na sun matu'kar yi min nauyi a zucia ta, meyasa zai ce ko da na batare da yarinyar bazai barni da matsayi na na 'diyar shi ba, dama jiran faruwar lamarin ake ko me? meyasa zai yi saurin yanke hukunci? Riba guda na samu cikin maganganun sa..domin cikin maganar sa na fahimci yaddar da yai min...juya masa kwakwalwa akwai akayi amma da kansa yasan ni ba mazinaci ya bace, sarai yasan ba ni na haifi yarinyar ba amma sbd ya yiwa matar sa biyayya ya sa shi kawar da kai ga hakan. " Ki tashi ki bar mana gida ko 'kira matasa su fitar min dake da duka....". Na tsnkayi muryar Iyami ta fadi hakan. Kai na 'daga na ganta tsaye akaina fuskar ta tamkar ba'kin hadari. Tsab nasan zata iya amma duk da hakan ban yi yun'kurin mi'kewa ba. 'Kasa nayi da kaina ina jin wata 'kwarin gwiwa cak kuka na ya tsaya. Tsaye na mi'ke ina goge fuska ta idanu na a cikin nata nace..." Iyami kiji tsoron Allah, ki sani cewa kowa zai mutu..sannan kafin mutuwar akwai jerin kaddarorin da bau wanda ya san iyakar su balle asan 'karshen su..." " Dan ubanki bazan ji tsoron Allahn ba, idan kinji zafi ki sa Allahn ya 'mayar da abin kaina in kin isa..." Kai na juya gefe da gefe. " Bani da damar sawa ki haifi 'dan da za'a muzanta ki sbd shi kamar yadda bani da damar canza 'kaddarar ki..amma kuma ban isa nace bazaki iya cin karo da 'kaddarar da zata iya sha mk kai ki kasa samun mafita ba koda ace baki da ala'ka da abun..misali kamar dai ni...abu guda da bazan iya gajiya da furtawa agare ki ba shine...kiji tsoron Allah Iyami ki guji hakkin 'dan Adam..." Daga haka na juya na fita na bar Iyami na ta sababi. Ni kaina naga 'ko'kari na, domin ban ta6a tsayawa na mayrawa Iyami magana irin ta yau 'din ba tun tasowa ta. Ko ma'kwabta dake bina da kallon mamaki, tuhuma, zargi, da sauran su duk ban nuna alamun na san suna yi ba kawai na wuce gidan Innata. Tun daga ranar ban sake tako ko hanyar gidan mu ba, na basu lkc nasan da iznin Allah wataran zasu fahimci gaskia. Har akayi sallah 'karama aka yi bikin Sallah aka gama cikin farin ciki illa ni da har a lkcn ban san inda nawa farin cikin ya shige ba. Bayan Sallah da sati Yayana ya koma harkar kasuwancin sa gadan- gadan..kafin hakan kuwa kullum yakan bani baki akan inyi hakuri. Dama ban 6oye masa komai ba, duk na fa'da masa kalaman Abban namu domin sune suka fi yimin zafi, na ce da Hamma Bukar na hakura a mayar da yarinyar tunda Abba ya kasa fahimta ta yace sam baza'a yi haka ba, ai kalaman sa masu reshe ne, nufin da yarinyar ko ba yarinyar basu sake bukatar ki tunda kin riga kin shafe ta, abari kawai ana addua a hankl wataran Abban zai sakko. Yace kuma mayar da yarinyar a halin yanzu zai iya zame mana matsala dukkan mu, musamman idan aka tsaurara bincike za'a iya kama mu da laifin rashin bayyana ta tun a farkon fari...shi yana tsoron abinda zai iya zuwa ya dawo tunda mu ba ishashen ilimi ba, ba dukia ba ba karfin mulki gare mu ba..yace abinda ya guda tun farko kenan amma nakiya, amma bakonai ita kaddara dama rubutacciya ce, Allah ya riga ya tsara hakan inyi hakuri mu cigaba da zama da ita shi ya san yadda zai 6ullowa lamarin, amma a halin yanzu abar Abban ya huce tukunna..." Sosai na gamsu da bayanan sa, na kuma fahimci kuskuren da nayi tun farko da ban san zai iya faruwa ba, tun da gashi komai na neman kwance min, mahaifi na na neman guje min sbd wannan dalilin. Duk wannan maganar mun yi ta ranar da yazo yi mana sallama zai tafi kudu harkar kasuwanci. Ranar ma nasha kuka, kawai nake jin tamkar zan yi kewa idan ya tafi. Duk wannan abinda ke faruwa kuwa daidai ko 'kwayar zarra ban ji yaragu daga cikin 'kaunar da nakewa Aishatu ba sai ma 'karuwa. Ko cewa da nayi a mayar da ita na fa'da ne kawai dan samun sulhu tsakanin ni da mahaifana ba wai dan na gaji da ita ko na daina 'kaunar ta ba. Ko da an mayar da itan da kaina nasan sai nayi kuka da rashin ta, zan kuma yi kewar ta sosai...idan na tuna hakan sai in jinjinawa kaina kawai domin nasan Allah ne ya tsara mana komai, ya kuma sanya min 'kaunar ta mai tsanani a zucia ta.. na gama yadda yanzu 'kauna ta da Aishatu daga Allah ne...! Duk da yadda mutane ke tururuwar zuwa gaida mu a gidan Innani abin bai ta6a damu na ba domin nasan yadda su suka 'daukan ba hakan yake ba kuma ni bani da ikon canza musu tunani akaina. Wanda ya yadda da ni ya yadda ni wanda kuwa akasin hakan yake a zuciyar sa shima bazan tuhume shi game da hukuncin da zuciyar sa ta riga ta yanke masa domin akwai hujja ta zahiri yadda hujjar ta tafiyu ne kawai bambanci. Fatana kawai shine Allah ya bamu dacewa. Na kan yawaita tuno kalaman Dije agare ni na 'karshe, ina matukar kaunar Dije domin itan aminiya ta ce ta gaske, Mun rayu da Dije ne tamkar 'yan uwan jini, nasan ba dan bin umarni ba Dije bazata ta6a juya min baya ba. Bazan manta ba kwanaki ta aikowa da Aishatu hula a 6oye kuma na tabbata babu wanda ya sani, na kuma matukar jin dadi da wannan sako na Dije domin hakan shi ya sake alamta min da cewa tana nan tare da ni, ganin juna ne dai ya haramta gare mu amma muna nan cikin zu'katan juna. Ina yawan kuka idan na tuna lkcn da Nadia ta barni, idan na zauna tariyo tun farkon ha'duwar mu zuwa 'karshen rabuwar mu kuwa da shashshe'kan kuka nake 'karasar da tunanin, na rasa wannan wace iriyar 'kaddara ce tamkar a shirin drama. Gashi abin tamkar danni ya faru duk yazo ya cushe min ni ka'dai, wanda ya tafi kam ya riga ya tafi ai sai dai addu'a ta rage tsakanin mu, kuma har yau 'din nan bana gajia da yiwa Nadia shi cikin kowacce sallah ta. **** Kwanaki biyar kacal da tafiyar Yayana kasuwancin sa mijin Inna ta ya dawo daga doguwar tafiyar da yayi, dama yaso yazo kafin sallah amma Allah bai yi ba sai yanzun, tun da yadawo gidan babu fara'a a fuskar sa domin ko gaisuwar da nai masa bai amsa min ba...haka ma ta Innata. Ko da ya fita ya dawo kuwa bansan me yaji ko ince aka sanar da shi ba amma cikin hassala ya fara masifa 'karshe ya kore ni daga gidan sa. Yace sam shima gidan sa babu makwancin shege wanda ya haife ni ma ya kasa zama da ni a gidan sa sai shi ne da aka rainawa wayo za'a zo a tare masa agida..sam bazai yadda ba, yace wanda muka yi da bai sani bama bai yafe ba...yace shi ba 'dan iska bane da zai tafi yawon nema ana nan ana ciyar da karuwai daga cikin dukiyar sa..badan wani abu bama kotu zai kaimu sai an biya sa, ran Innata ya 6aci sosai amma ya zam min dole na bar masa gidan sa. Ni kaina hankali na tashe nake jin sa amma ganin yanayin Innata ya sa dole na danne nawa na kwantar mata da hankali...sannan na 'dora da fa'din zan koma wurin Abban mu in sake bashi ha'kuri ko zai ha'kura duk da nasan mawuyaci ne ma ya ha'kuran, ni da aka haramta min ko kallon 'kofar gidan toj da wani 'kafafun kuma zan iya sa kaina a cikin sa...? Haka na tattare kayana kaf cikin jakar da Inna ta ta bani zucia ta fal da tunanin inda zan saka rayuwa ta...Allah ka dube ni...ka kawo min mafita mai 'dorewa. dama kayan nawa ba wasu masu yawa bane dan haka basu wani bani wahalar 'dauka ba, 'karamin jakan Nadia dake wuri na ma ban barshi ba na sanya shi can 'kasan kayan nawa...goye Mufeedah nayi a bayana na lullu6e ta da hijabin dake kaina, cikin ko wani da'ki'ka 'kaunar ta nake ji yana sake ratsa ni har cikin jini na...tausayin ta nake ji sosai sbd maraicin ta, sannan kaunar da nake yi mata na tabbata sbd an haife ta kan idanu na ne, nasani a yanzu Mufeeda bata da wani dangi sama da ni toh idan na guje ta hanun wa zata fa'da?. Ni har ita a yanzu Allah kadai ne gatan mu. Dama a rayuwa dole sai an ha'kura da wasu abubuwan sannan ake samun daidaituwar wasu...fatana a kullun Allah ya bamu dacewa dunia da kiyama. Ko hauka nake bazan ta6a iya taka 'kafata gidan Abbah na ba dan nasan halin sa da kafiya..hakan yasa na nufi gidan Yayana da tunanin zan sami muhalli a can tunda nasan tun farko duk cikin yaran Iyami shine yafi 'kauna ta, ko tafiyar nan da zaiyi ma sai da yaje ya bani ku'di yace in ri'ke a hannu na kafin ya dawo. Naso naki amsa sbd hidimar da yake yi akan mu ni da Mufeeda bazai fadu ba amma ya nuna min 6acin ran sa...hakan yasa dole na ansa. Sam banyi mamakin irin tijjarar da Azeemah tayi min tayi min a wannan ranar ba, dan nasan tun farko dama ba shiri muke yi da ita ba balle da batun yarinyar nan ya bayyana sune kan gaba wurin nuna min kyara da tsana. Buga kirji tayi tace min babu wanda ya isa ya zauna mata da 'dan shege cikin gida ganin yanda take hargagi take 'ko'kari tara min jama'ah yasa hawayen da tuntuni nake dannewa suka fara bulbulowa. Gyara goyo na nayi da kyau sannan na 'dauki jaka ta ina hawaye na fita daga gidan ko ganin gabana da kyau bana yi..sam a lokacin ban yi tunanin sake zuwa wurin kowa ba dan nasan bakowa ne zai kar6e ni da wannan 'kaddarar ba domin ko wurin su Yaaganan mu naje nasan dole sai an samu bambancin ra'ayi ta iya yiyuwa ita zaman ta na yar uwa ta ta kar6e ni amma 6angaren mijin ta kuwa bani da tabbaci babu mmk shima ya min kwatankwacin na mijin Inna ta ko ma fin haka..Baffa Liman kuwa dama inada labarin yafi kowa 'daukan zafi kan batun, kusan ra'ayin su 'daya ne da Iyami tamkar a takadda guda suka karanta abinda ke cikin zu'katan su. Kausasan kalamai naji su babu iyaka, anci min zarafi sau ba adadi an kuma muzanta ni sau da dama amma ban ta6a jin sun cire ni cikin natsuwa ta irin na yau ka'dai da nake neman rasa inda zan tsoma rayuwa ta ba. Ban kuma mance tsauraran kalaman Abbah akaina ba, Abbah na Allah ya isa ya min ga koda kallon gidan sa ne balle kusanta kaina ga dukkan wanda ya kasance jinin sa ne..badan komai ba sai dan kawai na shafi yarinyar, toh ya zanyi? Bani da ikon mayar da 'kaddara ta baya da wlh na mayar da ita ta yadda bazan je jejin bama balle har na hadu da Nadia balle akai ga batun Mufeeda. Amma Abbah ya kasa fahimta ta..kuskure ne da ya riga ya faru, da ace kafin ha'duwa ta da Nadia Abbah ya fa'di hakan da ko hauka nake bazan ta6a ha'da jiki na da ita ba, amma meyasa sai da abinda ya faru ya riga ya faru Abban zai gina doguwar katanga tsakanin mu, bayan yasan ban isa na maida 'kaddara ta baya ba, meyasa zai ce hatta ni baya da bu'kata bayan ni 'din jinin sa ce.. ina Abban mu yake so naje a wannan duniyar da ke da matu'kar girma da fa'di. Muurmushi mai ciwo nayi..tuno matsayin Abbah na a wuri na, mahaifi na yake, kuma abin alfahari na ne shi, hawaye ne masu zafi ya 6ul6ulo min tare da tuno Inna ta...inna ta bata ta6a nuna min kyara ko tsangwama ba akan yarinyar nan, domin da idanun ta taga gawar mahaifiyar yarinyar, tun a lokacin taso mu bayar da ita amma nace a a dan ban manta batun uwar Mufeedah ba da tace min ta iya yiyuwa ko yarinyar ta shiga hannun hukuma 'kila baza'a sada ta da asalin dangin ta ba, babu mamaki ta fa'da mugun hannu ko kuma ta rayu cikin gidan marayu alhali nasan tana da asali ni kaina bazan so faruwar hakan ba tunda nasan tana da dangin ta can wani wuri masu matu'kar so da 'kaunar ta tun kafin a haife ta. Haka kawai Nadia taji ta yadda da ni, sam bata ji 'dar ba wurin barmin amanar 'diyar ta ba, duk kuwa da cewa bata san ko ni 'din wacece ba, to ni kuma me yasa bazan kar6a mata ba, sam bazan iya bari a a tozarta 'diyar ta ba tunda hakan mahaifiyar ta ta guje mata tun farko...da bayan hannu na goge hawaye na ina mai sunkuyar da kaina tare da gyara ri'kon da nayiwa jakar kayan mu. Daidai da motsin da mufeedah tayi a baya na, 'dayan hannu na na kai 'kar'kashin ta ina jijjiga ta..cikin raina" Na 'dauka mata al'kawarin kulawa da ita, nayi al'kawarin sadaukar da duk farin ciki na saboda ita...daga yanzu zan 'dauka ta ne tamkar bani da kowa a duniyan nan sai ita, itace jina da gani na, itace sanyin idanu na..itace tsagin jiki na kuma jigo na...Hamma na ka yafe min ban yi hakan saboda ka kasa ba, ban yi hakan saboda farin cikin kaina ba face dan farin cikin wannan baiwar Allah marainiya da ke bayana, zan jure komai daga yanzun nan, zan iya komai da 'karfi na saboda kawai inga na gyara rayuwar Aishatu na. A yanzu na gama yadda cewa in aka 'dauke mahaifa na bani da wani masoyi sama da Yayana...Bazan ta6a gajia da maimaita cewawa gami da jinjinawa Yah Bukar ba, domin shine madadin uwata a gidan mahaifi na, shine malami na, shine yayana kuma garkuwa ta...shi ya koya min dukkan add'uo'in da na iya saboda in ringa bawa kaina kariya da su, ya min al'kawarin nema min maganin matsalar da ke damu na tun kafin faruwar wannan lamarin kuma Alhamdulillah burin sa ya cika...duk safiyar da yazo ya tarar da ni ina kuka ya kan zauna ya saurari damuwa ta zai ji matsala ta kuma ya fahimce ni...daga nan sai ya jero min kalaman kwantar da hankali ya kuma 'karamin 'kwarin gwiwar cewa insha Allahu watarana zan daina, matu'kar zan ri'ki tsoron Allah da ta'kawa da gaskiya, in kiyaye dokokin sa, in kuma ringa yin ibadu na yadda ya kamata da kanshi zai kawo min sau'ki.. Hamma na shiya koya min addu'ar safiya da maraice...ya kuma koya min wacce kafin nayi bacci zanyi, shiga ban 'daki da fitowa da kuma idan zan sanya tufafi na...sai gashi a yau kwatsam 'kaddara mai girma tana neman raba ni da kai jigo na, ina 'kaunar ka Hamma na Insha Allahu watarana zan dawo, zan dawo sbd kai ka'dai da mahaifiya ta. Fuskar Innata yazo min sai na girgiza kaina, ni ka'dai Allah ya bawa Inna ta, ban san dangin ta ba, bansan kiwa nata ba, kuma daga ni bata sake haihuwa ba har rabuwar su tazo da mahaifi na... Da wannan tunanin na isa bakin titi inda motoci ke wucewa.... " Inna ta ki yafe min, bani da muhalli cikin gidan mahaifi na dan hk bazan koma ba, hk kema bazan dawo wurin ki in kashe mk aure ba tunda baki da kowa agarin nan..ku yafe min dan Allah, nasan ku kunsan ni ba cikin shege ne ya kawo min mufeedah ba, kyautar ta Allah ya bani kuma na kar6a...kuyi min fatan dacewa, fatana Allah ya bani ikon kulawa da ita. Tafiya nake ina share hawaye na...gaba 'daya ji nai duniyar tai min zafi...bansan inda zan nufa ba amma haka kawai na tsinci 'kafafuna da nufar bakin titi. Salmerh😘 [17/1/2023, 10:39 am] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Wattpad@* _Serlmerh-md_ 🅿️ *...94* .......Cikin zucia ta na furta Allah ka yafe min, yah Allah ka sa kowa ma ya yafe min bisa son zuciyar da na aikata, wallahi ba da mugun nufi nayi hakan ba, 'kaunar ta nake har jikin jini na, Yah Allah ka taimake ni ka bani ikon kulawa da ita, yah Allah ka hana kowa raba ni da ita har abada, Yah Allah ka raya min ita, kasa mata albarka, Yah Allah ka sanya mana nutsuwa a zukatan mu ni da ita, Yah Allah kasa itama ta soni kamar yadda nake kaunar ta Yah Allah...". Jero Addu'ar kawai nake bansan me nake fada ba domin hankali na sam baya tare da ni a lkcn. Kallo guda zakai min ka fahimci ba cikin natsuwa ta nake ba. Bazata kawai naji jakar dake hannu na ta yage, dama tuni ta nuna alamun babu 'karfi isashshe tattare da ita ban kuma ta6a zaton zai min irin wannan butulcin ba...irin Ghana must go 'din nan ce kuma ta jima ana amfani da ita. Ban damu da yagaewar tata ba kawai na tsugunna cikin hanzari domin ji nake tamkar za'a zo a 'kwace ta ne a waje na, da sauri na baza kayan gaba 'daya, cikin wani zani na mayar da su na 'daure sannan na cigaba da tafiya ta. Nayi tafia mai nisan gaske domin tuntuni na bawa mahaifata baya kuma har a lkcn ban tsagaita da tafiyar ba, har a lkcn kuma idanu na basu daina zunar da 'kwalla ba. Lokaci- lokaci nake sa bayan hannu in 'dauke hawayen na kuma waiga idan naji tahowar mota amma da alamu duk babu mai shirin 'dauka ta. Har na fara gajia da tafiyar amma ban yi yun'kurin tsagaita tafiyar ba. Koka'dan ban ji araina na damu da kaina ba ko kuma abinda zai biyo bayan tafiya ta ba..ni dai damuwa ta yarinyar ne kawai..burina in ga na bata gata, ta bata farin ciki, domin nasan hkn ka'dai ne zanyi ya kasance na kwatanta cika al'kawarin da na daukan ma mahaifiyar ta...na kuma san ko da tana a wajen su gatan zata samu fiye ma da wanda nake da niyyar wadata ta da shi. Da 'kyar na samu abin hawa na tare na kuma shiga, sau 'daya na juya na yiwa mahaifata kallon 'karshe, nasan tuni na yiwa jama'ar ta nisa amma akwai wa'danda duk nisan da nayi su suna nan ne kusa kusa da zucia ta. Bansan inda tafiyar su ta faro ba balle insan inda suka dosa amma sam banji karaya a cikin zucia ta ba...abu guda da nake da tabbaci akai shine sun taso ne daga garin Maiduguri tabbas nasan bazai wuce nan ba sai dai ban san inda suka nausa ba kuma amma hakan ba hana ni shiga cikin motar in zauna ba. Haka ta cigaba da basu lbrn barin ta mahaifar ta garin iyaye da kakannin ta har zuwa sa'in ha'duwar ta hajia Talatu, zaman su da mwakbciyar kirki Maman Abdul, ba kowa ke dacen samun makwabci irin ta ba, duk da yk zaman haya ya ha'da su amma Mmn Abdul bata rike ta da wannan matsayin ba, sun yi zama ne matsayin Yaa da 'kanwa, rayuwar su gwanin birgewa kafin bayyanar halin Bbn Abdul da yaso tarwatsa mata zucia, irin 'kalubalen da ta fuskanta daga ma'kwabta da 'yan unguwa har ma Tsohuwa mahaifiyar Bbn Abdul da sauran su, irin gwagwarmayar da tasha da mutane akan aibanta mata yarinya domin tana da tabbaci akan cewa yarinyar ta 'diyar halak ce akan hakan kuma ta tsaya ta kuma hana kanta shakkar kowa indai akan kare martabar 'diyar ta ne..sannan Adam bawan Allah, Adam Jibrin 'Dan Maliki masoyin gaskia da take yawan maimaita cewa har ta mutu bazata iya mancewa da shi ba, wanda sanadiyar tarayyar su aka koreta a gidan da dake haya, ta kuma san zai yi ba'kin ciki da tafiyar ta bata kuma sake waiwaiyan inda yake ba har yau 'din nan, yawon titi da yawon bara da duk tayi da Mufeeda, ha'duwar ta Hajjaju uwar 'yan mata, rayuwar ta tare da su har zuwa lokacin da ta gudu ta bar gudan Hajjaju wanda shine sanadin ha'duwar ta da Dr Rasheed da matar sa wa'danda suka kasance mata ba'kin 'kaddara da ya gitta rayuwar ta akaro na farko, a kuma licn da bata ta6a zata ba balle ta shiryawa zuwan ta, tayi kuka sosai, tayi bakin ciki da takaici, a lkcn babu irin tunanin da bata yi ba, ta kuma yi nadaman barin ta gida a wannan lkcn yafi sau shurin masaki, ha'kika Dr Rasheed ya bar mata ta6o a zucia, irin tabon da bata jin yana iya 'ko'kewa har abadan, ko tunowa da lamarin bata fiye 'kaunar yi ba domin yana matukar karya mata zucia, Dr Rasheed dai har abada bata fatan Allah ya sake ha'data da makamancin mutum irin sa ma balle irin 'kaddarar sa. Sai dai mahaifiyar sa da 'kannan sa masu kirki ne, sun kasance masu matukar kirki da son mutane, domin hatta Mufeeda basu ta6a nuna 'kyamar su garera ba. Ansha gwagwarmaya sosai, Allah cikin ikon sa 'karshe akayi rabuwar da tayi sanadin haduwar su da Ammi Aseeyah...The Most Famous and adorable Woman Hajia Aseeya Muhammad ( Ammi)...( from page one)... Wacce ta kasance silar kauracewan duk wani 'kunci da Zaitoon ta fuskanta abaya, ta kasance musu silar farin ciki da jin da'din rayuwa, ta wanke zuciyar su da kyautatawa da alkhairin ta, ta rike mu tamkar 'ya yan cikin ta. Hakika Ammi da zuri'ar ta sun taka rawar gani sosai cikin rayuwar Zaitoon not knowing that ba ha'duwar jini ce kawai ba, akwai wani bond 'ka'kkarfa da kusan shine ya 'kara musu armashin 'kauna da son zama da su. Ta 'karashe basu labarin tana kuka sosai, tace sam.ban ta6a tunanin haka.ba, ban ta6a kawo maiamncin hakan cikin raina ba, abu guda da na sani shine nasan watarana dole a rabu, nasan zanyi kewar ku sosai Ammi, zanyi kewar Marwa ta fiye da yadda nake jin kewar Mmn Abdul cikin zucia ta, amma duk da hakan ban ta6a yin tunanin irin wannan ala'kar na iya ratsowa ba ko da a cikin mafarki na ne kuwa..Ammi kar ku ga laifi na dan Allah kuyi min uzuri, ban sani ba a lkcn rawar kai ne ko kuwa son zucia na bi ba, ni dai kawai nasan ina 'kaunar yarinyar nan kuma sai bazan iya barin ta yin nisa da ni ba, ku yafe min Ammi dan Allah, ku yafe min bisa halin kewa da na sanya zukatan ku tsawon lkc...kuka take sosai hk duk wa'danda ke parlorn ma hawaye suke sharewa amma babu wanda ya tankata ki.ya bata amsar maganar ta. In ka 'dauke Imran da yake yaro ne sai Amrah da banda wata ba'kar harara babu abinda take jefawa Zaitoon, na ukun su shine Rayyan da ya tsura mata idanu shi kansa bai san tunanin me yake cikin ransa ba, but jin zuciyar sa yk tamkar zata yi tarwatse, wasu abubuwa ke yi masa yawo a 'kwa'kwalwa amma bazai iya siffanta su...wai duk wannan gantali da wahalhalun rayuwa da gudan jinin sa akayi su...? Abin ya tsaye masa sosai. He can't just point a finger on what he is feeling but yana jin haushin kansa sosai, haushin kansa da kansa yake ji sosai, after all this wahalhalun shima da kansa yazo ya ringa 'kara musu zafi, ya hana ta natsuwa ya hana su kwanciyar hankali dukkan su, kuma sarai da gayya yake yin wasu abubuwan, not knowing that kansa yake yi masa, 6arin jikin sa maha'din rayuwar sa suke dukkan su, bai tabbatar da hakan ba sai lkcn da akayi nasarar sace su. Bazai iya kwatanata tashin hankalin da ya shiga ba a wancan lkcn, amma sai da ya kusan yin 'karamin hauka. Ina tunanin sa ya tsaya ne tun farko? Ina hankalin ya tafi da ya kasa tsaurara bincike akan lamarin tun bayan da lbrn mutuwar Nadia ya riske shi? Meyasa ya bar su suka sha wannan wahalar bacin yana raye a doron 'kasa...? Meyasa wai? Wata zuciar tasa ne ta basa amsa da fa'din" ' _kaddara ce_ " Tabbas ita ce, kalmar 'kaddara na da matu'kar girma da bawa bai isa ya ja da ita..hakika wannan bakomai bane face 'Kaddara da kuma jarrabawa daga ubangijin sa. Bai san wani irin yabo da godia zai yiwa yarinyar nan ba, domin a ganin sa ta cancanci duk wani irin nau'i na yabo, ta 'kaunaci gudan jinin sa irin 'kaunar da ya tabbatar fitacce ne ko a cikin dubu, shi kansa shaida ne baya neman 'karin bayani game da hakan. Parlorn shiru yayi, motsin kirki babu mai yi a cikin su illa hawaye, jikin kowa yayi sanyi musamman Marwa da Ammi da ko ka'dan basu ta6a kawo tunanin haka cikin zukatan su ba. Abinda ka'dai Zaitoon bata sani ba shine bata fa'da musu ba...'daya daga cikin su kuwa shine rashin son mage da Mufeeda bata yi bata san da shi ba, bata san a hannun mahaifiyar Dr Rasheed ta fara reacting ba domin basu samu lkcn da har zasu labarta mata ba suka rabu, so bata da labari har sai bayan zuwan ta gidan Ammi da suka je gidan Dada...ta kuma yi mamakin da har ta kasa 6oyewa, bayan ji da tayi daga bakin Ammi cewa Yaranta ma na da irin wannan abin a jinin su, baus 'kaunar mage, similarities din da take gani tsakanin 'diyar ta da yaran Ammi sai suka 'kara hauhawa amma still bata ta6a tunanin shi zai iya zamtowa mahaifi ga Mufeeda ba domin acewar ta baya 'kaunar yarinyar sam, 'kiyayyar da yake nunawa a gare ta me girma ce da ko nawi da kunyar bayyanawa baiyi koma a gaban wanene. Tace na jima da yin nadamar baro iyaye na da nayi tun lkcn da tashin hankali ya kusan yin awon gaba da numfashi na, ga zaman prison ga rashin Mufeeda ga kuma takaicin tuhumar da ake min da bansan ina makomata zata kasance ba uwa uba babu kowa nawa da ya san inda nake balle akawo min 'dauki, a lkcn Allah na fawwalawa dukkan lamari na, a kullum kuma na kan nemi gafarar sa cike da burin komawa ga mahaifana da zarar na samu damar barin prison 'din, Allah maji ro'ko ya amsa min, ya kuma dube ni a lkcn da bani da kowa sai shi, bani da gata sai wanda shi ya wadata ni da shi, cikin ikon sa kotu fa wanke ni, aka kuma dawo min da 'diya ta cikin kyakkyawan yanayi, sai kuma haduwa ta da Ammi...ko a lkcn idan baki manta ba Ammi na nemi da kawai idan taimako na kk son yi kawai ki bani kudi kk ce a a, ba komai zanyi da su ba face komawa mahaifata, sai dai Allah bai bani damar haian ba. Na yi 'ko'kari sosai wajen ganin na rufe mana sirrin rayuwar mu ba dan komai ba sai dan cewa da kaina nasan na aikata ba daidaiba, nabi son zucia ta akan rike Mufeeda ina kuma gudun ranar da asirina zai tonu irin hukuncin da zai iya hawa kaina shiyasa ban ware ko mutun guda da zan iya sanar da shi wannan sirrin ba na fitowa ta, na yi matukar mamaki da ku da kanku kuka fahimta, kuka fahimci cewa Mufee na 'diyar ku ce, kuka fahimci cewa ta ha'da jini da ku a zahiri duk da yake nasan akwai wasu abubuwa da kai tsaye suka bayyana hakan amma ni kaina ban saka su a mizanin da zai iya zamowa ta ha'din jini ba....amma ayau na tabbatar da cewa bani da wayo ba kuma ni da dogon nazari sam sam... Abu guda da zan iya nema agare ku ahalin yanzu shine afuwar ku bisa abinda na aikata, ina kuma rokon sassauci bisa duk irin hukuncin da kuka ga zaku iya yi min shi, hakika ban aikata hakan da in cutar da wani ko kuma ita Mufeeda ba, hasalima nayi ne domin ina kaunar ta shine na sadaukar da komai nawa sbd ita...ku yafe min kan hakan da na aikata koda bazaku yafe min kan dukkan laifuka na ba, bama ni da bakin cewa ku yafe min gaba 'daya domin nasan ban muku adalci ba, na wahal muku da yarinya na sa ta sha gwagwarmayar rayuwa tare da ni wanda nasan da ace tana wajen ku ko sanin cewa akwai irin wannan rayuwar bazata yi ba, a ashirye nake da na kar6i dukkan hukunci na domin nasan na cancanci koma wani rin hukunci ne...". Ta 'karashe da 'dauke siraran hawayen da ke bin kuncin ta. " Dalla rufewa mutane baki, munafuka kawai algunguma, wa zaki ajiye ki cika shi da 'karya da tatsuniyoyin bakin ki irin naku na mutanen karkara?...kin je kin kwaso cikin ki kin haife kin zo nan kina wani shirya 'karairayin da ko ma'ana babu balle 'kamshin gaskia ke har kin isa?...toh tun wuri kisan inda dare yai mk, kisan inda zaki nema wa 'diyar ki dangi amma ba nan gidan ba...domin duk zuriar nan babu sa'anki, mun wuce sanin ki balle wata banzar 'diyar ki can....". Cewar Amrah kenan tana mai nuna ta 'dan yatsa a hassale cike da kumfar baki. " Shut up..."! Rayyan ya doka mata tsawa da 'karfi ransa a matu'kar 6ace. Ita kanta Zaitoon kuka take sosai, sam kalaman Amrah basu dame ta ba, domin tasan babu mai goya mata ba, babu mai yafe mata, kalaman Amrah kuwa bata ji matsayin komai ba face tuni ga zafin da ha'da musu cikin ransu, ta kuma san cewa da tun farko itace ta kawo zancen da fiye da hakan ma zataji amma da kansu suka fahimta suka kuma nemi 'karin bayani daga gareta toh me zata 6oye kuma, ita dai tasan bata yi munafurci kamar yadda Amrah ke tunani ba, kuma babu abinda ta canza ko 'kara cikin labarin da ta bayar. Kukan da take ya ta'allaka ne da tuno wasu abubuwa da ta jima da binne su aranta, tuno wasu mutanen da suka kasance maha'din rayuwar ta ne, mutanen da bazata iya raba zuciyar ta sam sam da tunani da kewar su ba. Kallon wajen da Ammi take tayi ganin yadda ta rungume Mufeeda ajikin ta da tuni ma tayi bacci, wani kauna da tausayin yarinyar ya sake ratsa ta...amma yanzu da sauki tasan koda bata tare da ita atleast tana da nata dangin na kanta da kanta. Tsaye ta mi'ke duk da tana jin babu da'di cikin ranta kan tona sirrin rayuwar su da ta da'de tana 6oyewa, 'kafafun ta kansu sun yi sanyi sanadiyar da'dewar da suka yi tan'kwashe kuma bata motsa su ba..hanyar 'dakin ta tayi dan zuwa 'dauko musu shaidar da ita ka'dai ce agare ta da zai tabbatar musu da abinda take fa'da gaskia ne ba 'karya ba. Bata so dai dai da 'kwayar zarra suji cewa akwai 'karya cikin abinda take fada kamar yadda Ammi ta fara hasashe tun farko...ga kuma Amrah, bata kuma san meke cikin zu'katan sauran ba. Sai dai tun kafin ta bar parlorn baya kawai ta juya kafin ficewar ta taji an rungumo ta ta baya har abin ya 'kara bata tsoro. Yanayin 'kamshi da zubin halittar ya sa ta saurin fahimtar cewa Rayyan ne. 'Ko'karin fizge jikin ta ta fara hawayen ta na tsiyaya amma ya ki bata wannan damar sam. Shi kansa bai san me ke damun sa ba, amma ayau 'din kawai yaji aran sa cewa ta cancanci appreciation ba 'dan ka'dan ba..ta cancanci dukkan wani nau'in yabo daga gareshi, bai kuma san meya dace shi a matsayin sa na mahaifi ga Mufeeda yayi mata ba illa hakan. Tausayin ta gami da wani girma da daraja nata yaji ya shige shi nan take. Idanun sa lumshe ko kunyar sauran mutanen dake parlorn bai ji ba tunanin sa ma bai bashi hakan ba sam. Sosai ya shigar da ita cikin jikin sa, ba kuma yaso ya bu'de idanun sa balle ta fahimci halin da yake jin zuciyar sa a ciki, tsananin tausayin halin rayuwa da suka fuskanta da kuma tuna cewa wai da gudan jinin sa akayi wannan fa'di tashin sosai ya karya masa zucia, ga kuma 6acin ran kalaman Amrah abin duk sai suka taru sukai masa yawa, idanun sa sun ka'da sunyi jajir, jijiyoyin kansa suka fito sosai...mutsu mutsu ta fara jin irin ri'kon da yy mata amma still ta kasa raba jikin ta da nashi. Cikin kuka tace" Zan 'dauko jakan da mahaifiyar Mufeeda ta barmin ne, shine ka'dai shaidar da ke tare dani wanda zai tabbatar da gaskia ta....". " Ba bu'kata!" Ya fa'da da wata irin muryar dake tabbatar mata da cewar tun daga zuciyar sa ne. Duk da hkn bata fasa 'ko'karin cire jikin ta daga nasa ba domin ta kasa tantance manufar sa.... " Nagode!" Ya furta huci na biyo bayan maganar sa..." Thanks..so very much Zaitoon...Allah ya saka mk da alkhairi fin alkhairin da kk nufi 'diya ta da shi....". Ya ra'da mata cikin kunne yana mai rarrabe maganar da 'daddaya. Yana kuma gama fa'din hkn ya sake ta yayi gaba bai ko sake waigowa ba. Jikin ta sanyi yayi sosai, har ma ta kasa motsin kirki har 'karasa ficewa. " Meyasa zae gode mata? Meyasa zai zayyano mata kalaman godia irin wannan? aganin ta sam bata cancanci hakan ba! bata cancanci irin kalaman nan ba, Ita da take tunanin tayi laifi ta sace musu yarinya ta raba su na tsawon lkc? Ita da ta riga ta shirya kar6an hukuncin ta sanin da tayi ta wahal musu yarinya da irin tata salon rayuwar? Kullum sai tayi tunanin irin hukuncin da mahaifan yarinyar zasu yi mata idan suka ganota ashe ma cikin su take rayuwa bata sani ba, ashe suke ciyar da 'diyar su bata sani ba, sai kuma gashi suna gode mata...she is totally confused ita bata ga abin godia da tayi anan ba. Kalaman Amrah sun riga sun yi mata tasiri a zucia, hakan ya sa ta zubewa bisa gwiwoyin ta tana mai jin zuciyar ta na harbawa. Marawa ce ta taso da gudu ta rungume ta tana kuka take fa'din" Hakika Zaitoon ke 'diyar halak ce, wai dama duk wannan kaunar da kk yiwa Mufee ba kece kk haife ta ba Anty Nadian mu ce...? Ashe Mufeeda jinin mu ce ban sani ba...?" Kuka ta cigaba da yi tama kasa cigaba da magana. Haushi sosai ya kama Amrah ji take tamkar ta zo ta make su dukkan su. So take ta bar parlorn sbd tsananin takaicin da take gani amma tafi so taga 'karshen komai da idanun ta shiyasa ta kasa tafia ko ina. Ammi ce ta yi 'ko'karin daidaita muryar ta hkn kuwa ya jawo hankalin dukkan su gareta. Tasbihi ta fara yiwa Ubangiji sannan ta 'dora da dukkan kalaman da tasani na godia..sosai ta nuna farin cikin ta a fili, tace wai yau gani ga jinin Rayyan tare da ni, ban san da abinda zan saka mk ba Zaitoon a duniyar nan, abu guda da nasani kuma shine bazan ta6a gajia da yi mk fatan alkhairi ba har 'karshen rayuwa ta, sannan zan mk alkawari guda, Insha Allahu kwana kusa zan sada ki da mahaifan ki domin su kansu sun cancanci yabo da haifa 'diya irin ki da suka yi...zan miki jagora kamar yadda nayi alkawari ba tun yau ba, zaki koma ga iyayen ki ki nemi afuwar su bisa ga abinda ya faru, domin ina da yakinin duk halin tsananin rayuwa da kk fuskanta abaya bakomai bane face ka'dan daga cikin 'kuncin da kk barsu a ciki, kk za6i Mufeeda akan zama da su, iyaye ba wasa bane Zaitoon, duk lalacewar su da kaucewar su matsayin su baya canzawa kuma yin biyayya agare su dole matukar abin sa6awa ubangiji ba..." " Nagode sosai da 'kaunar da kk nunawa Mufeeda wanda nake da tabbacin ko da ace mahaifiyar ta ne iyake abinda zata yi mata kenan, sannan mu ma ki yafe mana bisa ga munana zaton da muka so yi mk a farko, duk da har ga Allah ni daga baya da kaina na fara kokonton kece kk haife ta amma dai still bani da hujjar da zata wanke min wannan zargin cikin raina..hkn yasa dole dai akan tunani na farkon duk muka tsaya, da ni Rayyan da duk sauran ahali na da suka aikata miki ba dai-dai ba...kiyi mana afuwa ki yafe mana kinji 'diya ta..? Bana jin wannan kyauta da kk yi min a yau akwai abinda zai kai min shi farin ciki har 'karshen rayuwa ta, bb mmk badan ke ba da har na bar dunia bazan samu rabon ganin jinin Rayyan da Nadia ba...nagode sosai Zaitoon Ubagiji Allah yy miki albarka ya raba ki da dunia da mahaifan ki lafia...Allah ya sa..." " Ammi shi wannan 'din hala mantawa da shi kika yi da har kike fa'din haka...ko...?" Cewar Amrah cike da raini da yatsina. Dagaske Ammi ta mance da shi ba 'karyar Amrah bace, hkn yasa tayi saurin dafe kanta wani murmushi na 'kwace mata da zai sanyatar da zuciyar Amrah. Anty Madeena ce ta banka mata uwar harara dama kufule take da ita tun farko da ta yiwa Zaitoon masifa, ga kuma sanin sirrin da ita kanta Amran bata san ta sani ba. " Ko kunya baki ji ba..?" Anty Madeena ta tambaye ta idanun ta cikin nata fuskar ta bb alamun fara'a sam. Sosai Anty Madeena tayi nasarar rissinar da ita, domin kawar da kai Amrah tayi nan take tana mai jin zuciyar ta na harbawa da 'karfi, har wani 'daci take ji na taso mata sbd tsananin takaici. Taso tarwatsa maganar Anty Madeenan dan fahimtar inda ta dosa amma ta kasa aikata hkn, illa tsoro da fargabar tonuwar sirrin ta da ya cika ta. Salmerh😘 [27/4/2023, 9:30 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Wattpad@* _Serlmerh-md_ 🅿️ *...95* ........" Abin kunya dan'kare cikin rayuwar ki amma har kina da guts fin tsomawa mutane baki cikin maganar su...?" Ko zancen Anty Madeena na farko bai kai wannan soya zuciyar Amrah ba. Sosai taji babu da'di ta kuma ji 6acin rai gami da fargaba matsananci ya kamata. Fargabar ta 'daya ce na rashin sanin ainihin abinda Anty Madeena ke nufi da maganar ta, tsoro take ji kar ace tasan ko da guda ne daga cikin sirrin ta. A zuciye ta tashi rungume da yaron ta mayafin ta na take mata baya tayi waje fuskar ta tamkar ba'kin hadari mai shirin zubda ruwa. Tsaki Anty Madeena taja bayan ficewar Amran...sai dai tun ma kafin ta gama dawo da kallon ta cikin Parlon Ammi tace" Baki kyauta ba Madeena..ai bazata ji da'di ba ke kanki kin sani...". "...so what rabu da ita dan Allah Hajia Aseeya, ina cikin yanayin farin ciki bana so takaicin ta ya canza ni...yarinyar bata da kunya ne sam...". " Amma dai ko ba komai ai 'dan dai da take magana akai 'din ai shi dolen mu ne, sbd jinin 'dan mu ke yawo a jikin sa...ni shaf mancewa nayi da shi ma shiyasa na fa'di waccan maganar....". " Ai dole ki mance tunda karere ne bb ha'din jini...". Cewar Anty Madeena a zafafe tana mai kawar da kanta. Duban hakika Ammi tayi mata tana mai son gano manufar maganan, a hnkl ta kirayi sunan ta sau 'daya tak..Anty Madeena yi tayi tamkar bata san Ammin tana yi ba. Marwa ce ta mi'ke kawai ta kar6i Mufeeda dake hannun Ammi sannan ta 'dago hannun Zaitoon suka yi waje, ganin hakan yasa Badi'a da Imrana ma suka biyo bayan su aka bar Ammi da Anty Madeena ka'dai. ***** Tunda ya fita ya bar parlorn yake jin zuciyar sa cikin wani irin yanayi da shi kansa bazai iya pointing takamamme halin da yake jin ta ciki ba, yana jin farin ciki tabbas da bayyanar wannan sirrin, amma ya rasa dalilin da yasa farin cikin nasa ya kasance ragagge. Ya kwanta a 'dakin sa yaji baya da natsuwa sam, hakan yasa ya fito duk da ciwon hannun sa yk hakan bai sa ya gaza tu'ka kansa da kansa a mota ba. Can gidan sa ya wuce yana sake tunowasu abubuwa da suka shu'de shekaru ka'dan baya. _Nadia_ ! Sunan ya gifta masa cikin kwanyar sa. Sai ya lumshe idanu ya kuma bude su nan take. Wannan karan lips 'din sa ne ya motsa wajen furta sunan Nadia akaro na biyu. Kai ya girgiza a hnkl yana jin wani irin cikin ransa. Ashe tsakanin su bai 'kare ba..! Ashe zai cigaba da ganin wani abu da ya dangance ta tare da shi...? Har ya isa gidan tunanin da ke ransa kenan kuma koda ya shiga gidan ma still dai Nadian ne. Sosai ya 6ata lokaci wajen tunani a wancan gidan, amma abinda yake 'daure masa kai shine rashin sukunin zucia...da 'kyar ya iya gano inda matsalar damuwar tasa take. Ba'kin ciki 'dacin rai yake ji da kuma tsananin kishin da ya jima bai tsinci kansa a cikin sa ba. Yanzu da ya tabbatar da cewa erh da gaske Aishatul Mufeeda 'diyar sa ce sai yafi jin haushin abinda Amrah tayi masa fiye da baya. Sultaan...! Wannan karan sunan da ya gifta masa cikin 'kwakwalwa kenan. Sai ya rintse idanu da 'karfin gaske yana jin zuciyar sa na harbawa. A yadda yake ji a halin yanzu baya ji akwai abinda yafi tsana da 'kin jini irin Sultan...Sultan yayi masa abubuwa masu dama da ya tabbatar daga yanzu har zuwa ranar da ransa zai bar dunia mawuyaci ne ya iya mancewa da su. Duk yadda yaso ya kawar da tunanin cikin ransa kuwa sam ya gagara yin hakan. Wata zazzafar wuta mai tiriri yake ji take ruruwa masa a zucia game da Sultan, tiririn da gaba 'daya yy nasarar lullu6e duk wani farin cikin da yake ciki. Da 'kyar ya taushi zuciyar sa har ya iya lali6o wayar sa ya 'kira Fawwaz. Bayan gaisuwa bai jira wani surutu ba, ko 'yar tsokana da Fawwaz din ke jansa da shi ma bai kula ba. Bayanin duk abinda ke faruwa yy masa atakaice domin yasan Fawwaz ba abokin 6oyewa matsala ko damuwar sa ba ne balle abu irin wannan da ya riga yasan Fawwaz din ya jima da hasaso komai tun ma kafin shi ya fara tunanin faruwar sa, duk bai ankare ba sai yanzun da komai ya bayyana masa sannan ya tunano maganganun Fawwaz na baya. Bai yi kuma mamakin yadda Fawwaz ya matukar nuna farin cikin sa a zahiri ba domin kuwa ya kasa 6oye tsananin farin cikin da ya shiga ga Rayyan. Bayan ya gama da Fawwaz wata number ya kuma 'kira yy 'yar takaitacciyar magana sannan ya kashe wayar bai ajiye ta ba sai da ya sake amsa waya har sau biyu sannan ya ajiye wayar yana sakin zazzafan numfashi. ***** Amrah kuwa can 6angaren ta ta koma ta fara zarya tama kasa zama waje guda balle tayi tunanin abinda ya dace, takaici da bakin cikin dake zuciyar ta gami da fargaba sune sukayi awun gaba da natsuwar ta gaba 'daya. Layin mummyn ta ta fara laluba amma cikin rashin sa'a bata same ta ba...hatta na mahaifin ta ta nema shima baya tafia, duk din su kuwa ta gwada fin sau a 'kirga amma duk bb wanda ta samu ya shiga. Haushi ya sake cika ta tayi saurin dafe goshin ta da hannun ta 'daya hawaye na ziraro mata. Ji take tamkar ta tarwatsa wayar nan take sai Sultan ya fa'do ranta..domin dole ma ta neme shi kan batun nan, maganganun Anty Madeena karan tsaye sukai mata a zuci tana bu'katar fassarar su da wurwuri. Tsoro take ji kar ace Anty Madeena tasan komai ne dan hk dole sai ta sako Sultan cikin lamarin dan 'kwa'kwalwar sa tafi tata ja acewar ta. Sai dai ko da ta 'kira layin san da ta tabbatar dashi yake amfani acan shima baya tafia..har ta gaji da gwadawa cike da haushi kuwa ta ha'da wayar da bango tana zubewa 'kasa cike da takaici da kuma rashin madafa. Karaya take ji na shirin yin galaba akanta dan haka kawai ta sanya kuka hadda 'daura hannu biyu aka hawaye na sakko mata shar shar. Tashin farko taji ta tsani Anty Madeena tsana mafi munin bayyanawa. Tuni wayar Amrah ta tarwatse a wajen, dama Samsung ba jure wahala take ba, ai kuwa lkc guda ta tashi a aiki dan ba 'karamin bugu tasha ba. Ranar haka tayi kwanan ba'kin ciki a 'dakin ta dan ko shi Arfan ma tare da Nannyn sa yake bata sake bi ta kansa ba. Notification na yawan neman da Amrah tayi masa da ya gani bayan bu'de wayar tasa washegari ya sa yayi tunanin neman layin ta amma baya tafiya. Yasan tana can gidan Rayyan a halin yanzu, dan sunyi magana da ita kafin tahowar ta gidan ta kuma bashi tabbacin zata koma shiyasa bai yi tunanin zuwa gidan mahaifin ta ba. Haka sauran yaran sa duk ya nemi layukan su akaro na barkatai domin kuwa tun kafin ma diran sa 'kasar yake neman su amma bai yi nasaran samun ko guda cikin su ba, so haka yanzun ma dai bai samu 'din ba...sai dai bai tsaurara bincike ko tsawaita tunani kan hakan ba, sau tari ma sai yaji tamkar 'kwakwalwar sa a cushe take ya kuma rasa dalilin hakan sam. Kwanan da Amrah tayi cikin ba'kin ciki yasa babu kalan tunanin dabai zo mata kanta ba kafin wayewar gari. Abubuwa da yawa ta sa'ka ta kuma kwancewa, kwata kwata bama ta iya tausan zuciyar ta sbd zafin rai, sosai take jin ranta nayi mata suya sbd bakin cikin Anty. Washegari kuwa sallah kawai tayi ta kama hanyar 'dakin Rayyan cike da masifa da tayi niyyan sau'ke masa akan maganganun Anty Madeena da suka fi tsaye mata fiye da komai. Ko da ta isa 'dakin na sa ko sallama bata iya tayi ba kawai ta banka 'kofa ta shiga. Yana tsaye jikin window hannun sa 'daya cikin aljihun wandon sa jikin sa farin singileti ne ka'dai da dogon wando na bacci. Shi kansa tun jiyan tunani yake da al'ajabin yadda abubuwan suka zo masa. Yana jin farin ciki sosai, yana kuma jin kishi mai zafi, walwalar sa duk tayi nesa da shi, a can wani 6ari cikin ransa yake jin tasirantuwar da wutar dake cin zuciyar sa ke da shi da fansar sa, atimes idan ya tuna da Mufeeda sai yaji komai ya kwance masa shi ka'dai sai kaga ya saki murmushi, yayin da wasu lokutan tunanin butulci da cin amanar da akayi masa sai yaji 'kaguwa da son ganin ya kama shi ya hana sa sukuni. Ko jiyan bai dawo da wuri ba sai da dare ya raba sosai kafin ya dawo gida. Tsaye yake idanun sa 'kir a haraban gidan motsin kirki baya yi illa idanun sa dake motsawa lkc zuwa lkc. Jin bugun 'kofa ya sa shi lumshe idanu ya bude nan take sannan ya waigo cikin hankali, sai dai tozali da idanuwan sa suka yi da Amrah yasa shi 'kan'kance shanyayyun idanun sa yana mai duban ta cike da mamakin ganin ta a wannan lkcn. Sau da dama idan ya dubi Amra sai yaga gaba 'daya kamar ba Amran sa ba, idan ya dube ta ya kuma tuna cin amana da tayi masa sai yaga ta juye masa izuwa wata halitta can ta daban ba Amra ba, ya fara ganin hakan game da ita ne kuma tun bayan fahimtar cewa Arfan ba jinin sa bane Sultan ta haifawa shi. Yana cikin 'dan nazarin ya tsinkayi sautin muryar ta cike da kaushi da izza mai tafe da 'kwarin gwiwar da shi kansa bai san inda ta samo shi ba. Ko da yake da kansa ya bata dama, ya bata dama a rayuwa fiye da yadda ya dace ya bata a ganin sa, shiyasa bazai yi mamaki ba dan abin ya biyo ta kansa. " Ka ja kunnen Antyn ka Baby ka sanar da ita, ta fita harkata, ta fita sha'anin rayuwa ta domin nafi 'karfin ta, ta daina interfering akan rayuwa ta tunda ba da uban kowa nake tsara yadda zan gudanar da rayuwa ta ba, na gaji da sa ido da bi diddigin da ake min agidan nan, for God sake me na tsare mata, me ya sa zata bi ta sakawa rayuwa ta idanu...? Ina ce kai nake aure ba ita ba da zata bi ta takurawa rayuwa ta, abin kuma har ya tashi akaina ya koma kan 'danka dana haifa....bandamu ba koma me zata ce 'amma ni dai adaina sakawa rayuwa ta idanu...na lura tun da aka yi ruwa akayi tsaki aka aura maka 'yar aikin nan kowa ma yake ganin dama na cikin gidan nan, dan hatta Ammi tsabar shishshigi da kuma son a nuna min ni ba kowa bace a wurin ta balle abinda na haifa..a gaba na take nuna ta ma mance da Arfan sai wancan 'yar mayu me kama da dodanniyar...." Bata kai ga rufe baki ba taji sau'kan mari lafiyayye saman bakin ta, wanda ya kai mata shi da bayan hannun sa na hagu...." Kasa magana tayi sbd ra'da'di daya shige ta batare kuma da 6ata lkc ba ta kai hannu ta dafe wajen. Idanun ta na tara ruwa tace" Baby...?" " Don't Baby me...!" Shima ya dakatar da ita a mugun tsawace da kuma sauri idanun sa na canza launi. ..." How dare u talk to my mother this way...?..is she ur mate..? Ohh 'dan iska kk 'dauke ni? Ko kuwa kece kk so ki nuna min cewa naki iskancin ne ya sake upgrading to another level...?" " Baby ni fa...?" Ta fara fa'di cikin kuka, da sauri ya dakatar da ita da fa'din" Shut up da Allah!" Idanun sa jajazir ya cigaba da fadin" Ke har kina da wani sauran kalma, daraja ko wani abin yi cikin gidan nan ne da har zaki zo gaba na..in front of me fa Amra? kina zagar min mahaifiya, da 'yan uwa na..?" Ya 'karashe da waro rinannun idanuwan sa akan ta yana mai nuna kansa da yatsan sa. " Baby please...." Ta fara magana cikin kuka amma Rayyan yaki bata cikakkiyar daman da zata tanka...tuni la66an ta sun kumbura sunyi suntum har kamannin ta ya canza... Hannu Rayyan ya 'daga mata hakan kuwa shi ya dakatar da ita ga abinda tayi niyyan fa'di. " Get out from my side...". Ya buga mata tsawan da ya sa ta tunowa da old Rayyan. Da gudu ta fice a 'dakin zuciyar ta cike da bakin ciki da tunanin wai duk menene wannan? Ta ko ina bb sauki? Ko da ta koma 'dakin ta ma bata zauna ba, mayafi kawai ta figa tayi waje ko ta kan Arfan ma bata bi ba haka tayi waje tana risgar kuka. Tsaki Rayyan yayi ya koma kan sofa ya zauna dabas yana me dafe kansa da yake jin na sara masa sosai, ga wani gudu da hannun daman sa ke yi masa yana jansa sakamakon 'dagawan da yy a fisge ya nuna Amrah da shi. Bai san me yasa hannun yaki warkewa gaba ' daya har yanzun ba, ya gaji da riritawan da yake masa, gaba 'daya ya maidashi tamkar wani mara kuzari duk da 'ko'karin yawan motsa shi da yake. Ta ko'ina abubuwa na neman cunkushe masa, ba Amra ba ba Sultan ba ba kuma lafiyar sa ba. ***** 'Bangaren Zaitoon kuwa tun tana kuka da farin cikin irin dangi da gatan da taga Mufeedan ta ke dashi har abin yazo ya fara bata tsoro, mamaki ya cika kwanyar ta, da ido kawai take bin kowa da komai, ashe ba 'karamin tauye yarinyar tayi ba, ashe ba 'karamin shiga hakkin ta tayi ba, ashe shiyasa a mafi yawan lokuta take ji can 'kasan zuciyar ta tamkar ta gaza, tamkar ta gaza bawa yarinyar kula da gata yadda ya kamata, sa6anin sauran mutane dake ganin cewa ta za'ke da yawa ne, ashe dagaske ta gaza 'din, ashe duk iya yadda zata so yarinyar da nuna mata gata bata kama 'kafan dangin ta ba balle mahaifiyar ta, har gara Rayyan ma dan shi tun wannan fitar da yayi basu sake saka shi cikin idanun su ba, amma idan ta dube su a yau ta ga yadda Mufeedan ta ke cikin 'yan uwa da dangin ta sai taji ta raina kanta gaba 'daya. Dangi da abokan arzi'ki na kusa duk sun zo dan tuni labari ya iske su..Anty Madeena da Marwa cike da farin ciki suke 'kiran waya suna bayyanawa 'yan uwa na kusa da nesa. Hatta can 'yan uwan Nadia an sanar da su sun kuwa yi mamaki suka kuma bayyana farin cikin su sannan su kara da bada tabbacin suna nan tafe suma dan su ganewa idanun su sam ba za'a bar su abaya ba... 'Yan uwan su 6angaren mahaifin su ma an sanar da su, haka ma su Anty Raihana da tace gobe gobe ma zata kamo hanya da Bassam har ma da maigidan ta gaba 'daya dan baza a bar kowa abaya ba. Hatta kishiyar Anty Madeena sai da tazo ganin Mufeeda abin tamkar a shirin film ko kuma labaran tatsuniyoyi. Albarka, addu'o'i da fatan alkhairi kuwa Zaitoon tasha shi har ta 'koshi. Sai da Ammi ta dakatar da su kafin suka daina sanar da mutane...Mufeeda kuwa tamkar yau suka fara sanin ta, Marwa koka'dan bata san yarinyar ta bar jikin ta gani take tamkar zata sake yin nesa da ita ne ko kuma idan ta matsa 'din ta rasa ta kenan har abada. Abubuwa da dama idan ta tuna na baya sai kawai taji daria ya kamata, ba komai tafi tunawa ba illa yayan ta Rayyan... Duk yadda Marwa taso yiwa mijinta albishir din wannan lamari abu ya faskara domin ta kasa samun sa a awaya sam..ta kuwa san shima zai yi farin ciki sosai tunda shima ahalin gidan ne, wannan tunanin Marwa kenan. Dole kuwa ta ha'kura amma can 'kasan zuciyar ta take jin babu da'di, ya kamata ace shi ta fara yiwa wannan albishir 'din kafin wasu daban amma bata san dalilin da yasa cikin kwanakin take yawan rasa wayar tasa ba..sannan shima baya 'kiran ta yadda ya kamata. Yadda kowa ke ta 'ko'karin jan Mufeeda ajiki ita kuma sai suka fara bata tsoro ma, dan har gara Marwa tana zama ajikin ta dayake dama mutuniyar ta ce amma sauran kam ha'de rai take sosai tayi tamkar zata saki kuka, dayake dama can Mufeeda ba baya ba wajen 'kiyuya kuma koda ta kara girman ma ba laifi takan 'dan ta6a, abin sai ya motsa mata yanzu. Idan ta gaji da kowa sai ta koma wajen Zaitoon ta shige jikin ta lafe tana fa'din Mammi. Hakan na matukar karya zuciyar Zaitoon sai taji tausayin junan su ya kamata...dan tasan sun sha'ku, irin sha'kuwar da rabuwar su sai ya doki kowanne daga cikin su, kuma da alamu rabuwar ta riga ta tunkaro su ne gadan gadan a yadda ta lura. Ta fahimci 'yan uwan Mufeeda ba sake bar mata yarinyar ta tafi da ita zasu yi ba, ta kuma san ita har Mufeedan zasu yi kewar junan su sosai, yau ka'dai ma da take ganin yadda kowa ke son janta ajiki ana nan nan da ita sai take jin ranta bb da'di ba wai dan tana ba'kin ciki da bayyanan 'yan uwan Mufee ba hasali ma bata jin akwai wanda ya kaita farin ciki a cikin su illa tsoron da bata san takamammai na menene ba daya cika ta. Har wata 'yar rama tayi, amma hakan bai sa tabi son zuciyar ta ba, da kanta take lalla6a Mufeedan idan wani ko wata na son 'daukar ta. Ayau 'diyar ta ta zam tauraruwa, Mufeedan ta ta zama yar dangi itama hakan ka'dai na sa taji alfahari sai dai tsoron dake ranta shi ya hana farin ciki da alfaharin nata bayyana kansu a fili. Duk wannan hayaniyar da ake agidan bb wanda ya kalli ko 'kwayar idanun Rayyan balle fuskar sa tun bayan fitar sa. Ko farin ciki da ake son taya shi ma babu wanda ya samu arzi'kin yi masa shi sbd rashin ganin sa. Har washegari kuwa bai yadda ya bayyana kansa ga kowa ba. Sultan ka'dai ne damuwar sa, burin sa kawai ya ga anyi ram da shi. Sultan kuwa bai samu isowa Naija a ranar da ya tsara ba har sai washegari sannan ya iso, a lkcn kuwa Anty Raihana ma ta iso ita har da mijin ta, Bassam ma 'kin zama yy duk kuwa da cewa yana makaranta dole sai da aka taho da shi. Kuma a washegarin ranar dangin Nadia suma suka iso hadda mahaifiyar ta, mahaifin ta ne ka'dai bai samu zuwa ba sbd yanayin 'karfin jikin sa sai a hankali a hakan ma Rayyan bai ta6a mancewa da su da taimakon su ba, sun sha kuka, sun nuna tsantsan farin cikin su a fili. Da farko ma duk basu lura da rashin Amra cikin gidan ba har sai da aka kwana aka kuma 'dauki hanyar yini da basu ganta ba sannan suka ankare da cewa bata nan, Rayyan ne yy musu bayanin cewa ai tana can gidan su ta tafi. Shima ya samu cikakken bayani ne daga bakin Nanny sakamakon kukan Arfan da yy yawa. Babu wanda ya damu duk cikin su illa Ammi sai ma kya6e baki da kusan dukkan su sukayi. Sbd suna ganin kamar gata ne yy wa Amran yawa da ke sata iskanci da raina mutane. Rayyan na komawa 6angaren sa bathroom ya shige ya sakarwa kansa ruwan sanyi, zafi yake ji kansa na 'dauka sosai hk ma zuciyar sa suya take masa sosai, sam ya rasa dalilin da ya sa aka daina samun wayar yaron nan kwata- kwata. Isowar mahaifan Nadia da wasu daga cikin 'yan uwan su yasa dole ya fito izuwa 6angaren Ammi. Sun gaisa cike da mutuntawa da karamci domin koda wasa bai bari an karanci 'kalilan 'din damuwa saman fuskar sa ba illa Ammi da ko batayi magana da shi ba duba 'daya take yi masa ta fahimci in ma akwai abinda ke damin sa ko a a. Sun masa barka da samun lafiyar sa sun kuma jimanta domin tun baya da suka zo duba shi daya ke kwance a lkcn ma bai san da zuwan su ba sai yanzun suka dawo, bayan wannan batun Mufeeda ne ya biyo baya. Mahaifiyar Nadia kuka ta ringa yi rungume da Mufeeda tana jin tamkar ta maida ta cikin ta sbd tsananin farin ciki da kauna. Ranar kam Nadia tasha Addu'o'i kowa dole sai da ya tuna da ita da mutuwar ta, yadda akayi kuka kuwa sai ka rantse aranar ne ma ta rasu. Kwanan su 'daya suka koma sbd sun bar mahaifin su a gida shi ka'dai, amma kafin tafiyar su sun ro'ki da a taimaka akai musu Mufeeda suma watarana ta 'dan yi musu kwana biyu. Rayyan dai bai ce komai ba illa murmushi da yy har suka tafi kuwa basu 'kara ha'duwa da shi ba, ya dai bar musu sa'ko a hannun Ammi. Irin tarin kyaututtukan da 'yan uwa da abokan arziki suka rinka kawo wa Mufeeda abin ba'a cewa komai, ciki hadda iyalan Alhaji Barau dan su ma ba'a bar su abaya ba..abokan Rayyan tamkar zasu maida ta cikin su...Mufeeda dai taga kaunar da koka'dan ita ba damun ta yy ba balle tasan muhimmancin sa, illah Zaitoon da abin ke matu'kar tsorata ta. Har fargaba take idan taga zuwan baki gidan sai taga tamkar zukatan wasun su zai iya tunzura suce sai an kulle ta sbd raba su da 'diyar su da tayi na tsawon lkc, wani bin ma tunanin ta bata yake akan ta gudu kawai kafin akai ga rufetan, sai dai sa6anin hakan sai taga wani girma da daraja ake bata da bata ta6a zato ko hasashen samu daga gare su ba, abu na biyu da ke 'kara tsaye mata arai shine batun auren nan da har yanzu bata ji wanda yy maganar sau'ke mata shi ba. ***** Lokacin da ya shigo 'kasar ji yayi ya sha'ki wata ni'imtacciyar iska mai sanyaya zu'kata, banda 'kamshi da alamun ruwan sama da iska ke tafiar da shi, sai dai ko ka'dan ji yayi bayi da lkcn 6atawa wajen bambance yanayin da yake ciki balle yanayin 'kasar, damuwar sa rufaffun asusun sa da bai san dalilin da yasa aka rufe masa ba sai kuma toshewar duk wata kafa da ku'da'de ke shigo masa suma duk ya daina jin motsin su. Taxi ne ya kawo shi gida, domin bai 'kira kowa ba balle asan da zuwan sa, hasalima shi a fa'dar sa ma ba ya so kowa yasan da dawowar tasa shiyasa bai 'kira gida ya nemi a tura mota ta 'dauko sa ba. Gidan sa ya fara sau'ka sai dai ban da mai gadi bai tarar da kowa ba, hakan yasa ya wuce 'dakin Marwa dan yasan mawuyaci ne ya tarar da nashin da cikakken tsabta tunda yasan Marwa bata san da da dawowar san ba. Tuni Rayyan ya samu labarin sau'kar Sultaan dan ba 'karamin securities yasa aka zuba a ta kowace kusurwar da yasan ta dace da dawowar san ba. Cike da hanzari yayi wanka ya fito wanda shima Sultan adaidai wannan lkcn wanka yake a 'dakin matar sa. Koda ya shirya 'dakin sa ya koma ya duba wasu takaddu sai dai bai da'de ba ya fito hannun sa ri'ke da key 'din motar sa. Mai gadi ya yafito da hannu yayin da ya taho da gudu dan cika umarni. Motar dake lullu6e da tampol yasa ya bu'de masa, tayi 'kura amma ba sosai ba sakamakon rufe tan da akayi. Sauran biyu dake fili gefe ka'dan da shi ya waiga ya kalla, 'daya daga cikin su yk son hawa amma bb key a hannun sa..dole sai dai wannan din. Family house ya wuce domin yadda ya 'kagu yaga Amra ko Marwa baya 'daukin ganin ta hakanan. Direct 6angaren ta ya wuce hankali kwance batare da fargaban komai ba, domin bai ta6a sanin Rayyan ya tashi ya cigaba da harkokin sa ba. Sauri yake yaji daga ba'kin Amra sannan ya wuce INFINITY yaji dalilin da yasa kudi suka daina shiga masa asusu daga nan kuma ya wuce Banks ma yaji nasu dalilin da yasa akayi barning asusun sa da gaba daya. A gobe kuma yk so in komai ya tafi masa yadda ya tsara Lagos zai wuce domin can ne ma yafi damun sa sbd share 'din dake shiga asusun sa daga Lagos yafi na ko'ina nauyi. Rayyan kuwa tun fitowar sa a wankan banda amsa 'kiraye- 'kiraye bb abinda yk yi..ya 'kira a kuma yi kiran sa shima. Ruwan sanyin da ya watsa yasa ya 'dan ji sanyi aransa ya kuma 'dan samu natsuwa. Hatta managern can Lagos din yy magana da shi, duk da yk companyn ba'a hannun sa take ba a hannun Sultan ne, amma hkn baya hana shi tambayar su duk wani abinda yk da bu'kata sbd duk sun san shine sama da Sultan kan dukiyar su. Tambayar su yy Sultan yaje ne suka ce a a. Bayan wasu 'yan maganganu da ya biyo sai ya cire wayar daga kunnen sa take kuma sai ya saki ya tsaki 'yar ta'kaitacciya tuno Zaitoon da yy. Kwanaki 'kalilan baya ita ke taya shi shiryawa, bai san matsalar ta ba a halin yanzu da duk ta 'kauracewa inda yk, duk da bawai hkn ya damesa sosai bane amma yau ka'dai da yake matu'kar bu'katan mutum kusa da shi sai yaji kewa da haushin rashin nata kusa dashi yafi shigan sa. Cikin hanzari ya samu ya shirya gashi har a lkcn hannun sa bai gama warwarewa ba ta maza kawai yk yi yana amfani da hannun tamkar baya jin ciwon komai. Shigowar ta kenan 6angaren duba wasu kayayyakin su, da yk dama ba 'diban kayan tayi ba in bama ya zam mata dole ba sbd Mufeeda da bb abinda zai sa ta zuwa 6angaren nan ahalin da ake ciki. Ko yanzun ma tafiyar da take tamkar tana yi akan ruwa ne, cike da hanzari ta shiga 'dakin ta tattaro abinda ya shigo da ita, mafia yawa ma kayan amfanin Mufeeda ne tsiraru ne nata aciki, rungume da su a 'kirjin ta ta fito...turus taja ta tsaya tana duban sa da tsantsan mamakin ganin sa, a lkcn fita zatayi sai ta gansa ya yaja jacket hannun sa na hagu ri'ke da hular sa P-cap ba'ka. Ihu tayi niyyan sawa sbd tsorata da tayi, tamkar cikin mafarki domin bata ta6a tunanin ganin sa anan ba. Kuma tashin farko wa'dancan mutanen da suka ta6a sace su abaya sune suka zo mata rai lkc guda. Baki ta bu'de tana duban sa da niyyan sakin ihu sai dai kafin sautin muryar ta ya bayyana a fili yy saurin rufe mata baki da hannun sa ya manna bayan ta da jikin bango. Sam bata san lokacin da ya iso kusa da ita ba balle faruwar hkn. Kallon kallo suka tsaya yi idanun ta cikin nasa yayin da jikin ta ko'ina ke rawa sosai sbd tsoro, duba 'daya zakai mata ka fahimci a tsorace take gaba 'daya, idanun sa ka'dai ne ya sa ta gane shi...amma hawaye ya kasa fita daga idanun ta duk da yake a matukar bu'kace take da yin kuka....'dan lumshe idanu yy ya kuma bu'dewa. Matso da fuskar sa yy sosai kusa da nata ya saita mazaunin hancin su har tana jin fita da shigan numfashin sa saman fuskar ta. Tuni kayan dake hannun ta suka yi 'kasa ta fara kiciniyar 'kwacewa amma ko motsin kirki bata iyawa. Ganin hkn yasa shi 'dage hannun sa daga bakin ta dan shima tuni yk ji tunanin sa ya fara canzawa. Yana cire hannun ta sau'ke wani nannauyan numfashin da ya sake zaburar da shi. 'Kokarin manna fuskar sa yy da nata tayi saurin kawar da nata gefe ranta a matu'kar ha'de. Sai ya dafe bango da 'dayan hannun sa shima 'din ya saki huci mai zafi. 'Kasa-'kasa muryar sa na rarrabewa ya furta" Miye toh?..me ne abin ihu dan kin ganni..? Yau kika sanni ne ko kuma yau kk fara gani na..?" Bata iya ta amsa ko guda cikin maganar sa ba kawai ta rintse idanu da 'karfi domin tiririn fitar numfashin maganar tasa na sau'ka mata ne a gefen kunnen ta...'Ko'karin kaucewa ta sake yi yy saurin ri'ke ta ya toshe mata hanyar guduwa gaba 'daya...yanzu kam ta tabbatar shine bb kokwanto, domin sautin muryar sa ya gama tona mata ko shi'din wanene, bata kuma bu'katar wata amsa ta daban. Afuwan ! Afuwan !! Afuwan !!! Inai wa kowa barka da sallah Allah yasa muna da rabon ganin wasu masu yawa cikin aminci. Salmerh😘 [24/8/2023, 4:23 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Wattpad@* _Serlmerh-md_ 🅿️ *...96* ........" Kin kasance jigon mafarki na Zaitoon cikin kowani baccina da zanyi..muradi na, duk wani buri na rayuwa ta kece Zaitoon, tsarukan rayuwata duk da ke nake tsara shi, ban ta6a ji ko a hasashe cewar baza ki zam tawa ba shiyasa a kullum fatana shine ki kasance tare da ni ki zam mallaki na har 'karshen rayuwa ta, ki fahimce ni pls kinji kuma ki sassauta min halin da nk ciki ta hanyar mallaka min jikin ki ko da na rana guda ne Zaitoon kinji...dan...Allah..hakan ka'dai ne zai iya rage min ra'da'din 'kaunar ki da ke cin zucia ta ko wani lkc". Ya 'karashe maganar a rarrabe sakamakon 'ko'karin dawo da fuskar sa saitin tata da yake yi. Wannan karon wani 'karfi ne taji yazo mata tuno wani abu da tayi daga cikin zuciyar ta...zancen su da Amra..ta kuma tuno Arfan...ta riga tasan komai dake tsakanin su ta kuma jima da fahimtar manufar sa akanta. Amma sam, ko cikin mafarki bata ta6a tunanin faruwar wannan 'kazamin al'amarin a tsakanin ta da shi ba. Angije shi tayi da iya 'karfin ta, Allah sai ya 'kara bata sa'a ya 'dan ja baya ka'dan tamkar mara laka a jiki, duk da yake bata isa ta ha'de 'karfin ta da nashi ba amma bata san ina 'karfin jikin sa ya tafi a wannan lkcn ba da har ta samu nasarar ture shi. Saurin juya mata baya yayi yana mai cusa hannu cikin gashin kansa yayin da 'daya hannun dake ri'ke da hular sa ya kama 'kugun sa da shi, tamkar wanda ya farko daga wani dogon nazarin da bai shirya shigan sa ba amma da alamu ya shiga damuwa ne 'yar ka'dan...Sosai idanun Zaituna ya rufe cike da 'dacin rai take shirin duban sa bayan ta kara ja da baya daga inda yake...kafin ta ankara da wanzuwar wani a wajen sai jin _Tasssss_ .....tayi, sau'kan wani lafiyayyen marin da ita kanta sai da ya sake hargitsa mata lissafi duk da cewa ba'a fuskar ta marin ya sau'ka ba. Kafin tayi wani yun'kuri ko fahimtar takamamme abinda ke faruwa sai gani tayi ya sake sau'ke wata dun'kulalliyar naushi saman fuskar Sultan dake yi masa duban firgici, take kuwa jini ya fara zuba ta baki da hancin sa. Sam ma bata lura da cewa da hannun sa mai ciwon ya kai naushin ba sai da ta isa kusa da shi a 'dari a kuma firgice tana me 'ko'karin ri'ke hannun sa da ya sake dun'kulewa da niyyar kai wani naushin sai kuwa ya hanka'de ta baya..'dan 'karamin ihu ta sanya me cike da zogin buguwa da tayi da bango...sai dai hakan bai hana ta shiga tunanin yaushe hannun san yy lafiyar da har ya iya kai duka da shi har haka ba. Madadin ta tsaya bibiyar zafin buguwan da tayi sai ta tsaya yi masa kallon mamaki. Shi kam Rayyan shaf ma mancewa yy da batun ciwon hannu, ashe wargi ma waje yake samu..6acin rai ko firgici babu irin abinda baya iya haifarwa na daga sabbin yanayi. Ganin yana neman yin kisa ne yasa Zaitoon dawowa hayyacin ta take ta saki wani ihu da 'karfi tana mai 'kiran sunan sa da kalmar ban hakuri amma ko gezau, tamkar kurma, tamkar namijin zakin da yunwa ta riga ta ciyo shi baya jin 'kira sam, baya jin ban hakuri balle ya sarara ga abinda yk niyyar aikatawa...bugun Sultan yake tamkar Allah ne ya aiko shi. Ihun nata bb inda be ratsa cikin gidan ba hatta da su Ammi sai da suka jiyo ta amma shi tamkar itace, tamkar bai san tana yi ba. Da gudu su Ammi suka yo 6angaren nasa batare da tsayawa kokonton daga inda ihun ke fitowa ko kuma ma'kasudin fitan sa ba. Kuka sosai Zaitoon take yi ganin yadda Rayyan ke ta jibgar 'dan uwan sa tamkar ya mance matsayin da yake da shi agare shi, jini ke fita ta hanci da bakin Sultan kuma duk ya 6ata masa fuska da jikin rigar sa amma hakan bai sa Rayyan ya sarara masa ba. Tuno Ammi yasa ta juya da gudu tayi hanyar waje dan neman agaji daga gareta nan suka yi karo da ita batare ma da dukkan su sun kula da tahowar juna ba. 'Kasa Zaitoon ta fa'di bisa gwiwoyin ra sakamakon ha'duwar bazata da suka yi. A firgice ta fara jan baya hannayen ta duk biyu dafe da 'kasa tana mai rushewa da kukan da jin sa kawai zai sa ka fahimci ba na lafia ba ne. Ciki ta fara nuna musu ta ma kasa fadin komai " Ya akayi ne meya faru Zaitoon...?" me ya sameki hakan nan...? " Kukan me kk yi ne?" Tambayoyin da suka shiga kunnuwan ta kenan daga bakunan su 'daya bayan 'daya. Da 'kyar bakin ta ya iya furta sunan" Yah Rayyaan..." Tana mai nuna musu ciki. Anty Raihana ce ta fara wucewa ciki jin sunan 'dan uwan ta da kuma tashin nishi ka'dan ka'dan da suke iya jiyowa. Take sauran ma suka bi bayan ta sai Marwa da ta tsaya ta 'dago Zaitoon suka sake komawa ciki da sauri...duk tunanin su wani abu ne ya samu Rayyan din su..dan bb wanda yasan da dawowar Sultan ma jballe ayi tunanin ko shine. Dukkan su babu wanda bai shiga ru'dani da ganin al'amarin ba. Turus dukkanin su suka ja suka tsaya baki bu'de. Ammi ce tayi 'karfin halin fara daka masa tsawa amma tamkar ba da shi take magana ba. Shigowar Marwa da sau'kan idanun ta akansu duk baifi cikin second uku ba tana dire idanun ta akan su tayi saurin sakin Zaitoon da mamaki ta dubi Rayyan ta dubi Subi Sultan, sau kusan uku tana bin su da kallo cikin mintinan da basu haura biyu da kyar idanun ta suka tabbatar mata da cewa shidin din ne dai...Sultaan ne, Yah Sultaan din tane yake hannun Rayyan jiki da fuska duk jini, da gudu ta nufi wajen a rikice take fa'din" Yah me ke faruwa...?..Yah Kashe shi zakayi ne? dan Allah Yayah kayi ha'kuri karka kashe min shi, jinin sa zai 'kare fa Yayah...Yayah baka ganin.halin.da yake ciki ne?" Ta 'karashe da sakin kuka mai kashe zucia. Abinda tun tasowar ta a gidan bata taba ganin faruwar sa tsakanin su ba kenan sai yanxun, ko cikin mafarki kuwa bata ta6a tunanin akwai ranar faruwar irin haka a tsakanin su ba. Rayuwar su gwanin ban sha'awa ce da birgewa, zu'katan su cike yake fal da so, 'kaunar juna da kuma mutuntawa...me ne ya kawo wannan sabon yanayin kuma? Me ya haddasa wannan canjin ne...menene musabbabin wannan husumar? Yah Rayyan ke yiwa Sultan wannan irin bugun mutuwar da hannun sa....?" Tuni numfashin Marwa ya fara sar'kewa ta dafe 'kirji tana 'dan ja baya domin ba 'karamin ka'data lamarin yy ba. Zaitoon ce tayi saurin ankarewa da ita ai kuwa tana zuwa kusa da ita hannun ta ta ri'ke tana mai girgiza ta, tana shirin tambayar ta abinda ke faruwa maganar ya tsaya mata cak sakamakon sumewa da taga Marwa tayi a hannun ta, nan suka zube kasa atare dukkan su dai dai da isar Ammi kusa da Rayyan. Yadda ya matse Sultan a bango ma ka'dai sai ya baka tausayi balle yadda yake jibgar sa. Naushi ya kuma niyyar sau'ke masa Ammi ta daka masa tsawa da fadin" Don't try it again Rayyan.."! Fuskar ta a matu'kar ha'de tayi maganar. 'Dan yatsa ta 'dago ta nuna shi da shi sam bb alamun fara'a ko walwala saman fuskar ta. " Wlh if u dare touch him again u ll definetely see my other side right now!" "......ar u out of ur mind?..nace baka da hnkl ne Rayyan?...'dan uwan naka..? 'Dan uwan ka kk bugu hakan nan? ko ma me yy maka why can't u warn and address him? or why can't u come and tell me..?" Hannu ya watsa yana mai sau'ke jajayen idanun sa da ke cike da ruwan hawaye kan fuskar Ammi da magana daddaya yace.." Ammi he touched my wife nd...nd...nd..." Sai kuma ya kasa 'karasawa sbd ba'kin takaicin da ke ci masa zucia. " Sakar min yaro nace"! Cewar Ammi da wani tsawan na daban dan ko bi takan maganar tasa ma bata yi ba. Rayyan kasa 'daga ko da 'dan yatsan sa daga jikin Sultan yayi sai ma wani mugun kallo da yake sake bin sa dada shi alamun still dai bai huce baba. " Sakar masa wuya nace ko ohh billahil azeem u ll regret my actions Rayyan...!" Ta fa'da wannan karan bada tsawa ba. Dai- dai Raihana ta 'dora da fa'din. " Dan Allah Yah Rayyan ka sake shi, kar ka kashe mana shi mana..."! Itama ta fa'da da muryar kuka..har a lkcn kuma duk 'din su bb wanda ya ankara da cewar Marwa ta 'dauke wuta 'dib. Sake shi yayi a fizge sai ga Sultan ya fa'di 'kasa jagwap tamkar wani kayan wanki duk jikin sa a sake. Rayyan kuwa yana sake shin azuciye yake bada amsar maganar Raihana inda yake fa'din " Ya mutu mana...I don't care! after all what he did still yana da guts din da zai zo har 'dakina yana ta6a min jikin mata ta...?" Da zafin rai sosai ko ganin 'kwayar idanun sa da kyau ba'ayi yake wannan maganar har ruwa ruwa zaka ga idanun sa sunyi sbd 6acin rai. " Me ma ya kawo shi 6angare na a wannan lkcn...ya bani ajiya ne ko me?" Ya fada da karfi yana watsa duk hannuwan sa da sake kai wa Sultan harbi da 'kafar sa. " Wajen abokiyar shashancin sa yazo mana..can't u understand..?" Anty Madeena da tun shigowar ta bata furta komai ba sai yanzun ta fa'di tana mai nuna halin ko in kula da yanayin da Sultan 'din ke ciki. Gaba 'daya sai duba da hnkln su Ammi ya dawo gareta sai dai 'karan sake gwara kan sa da Rayyan yy da 'kafar sa ya sake dawo da hankulan su gare shi domin wata 'yar 'karar azaba Sultan ya saki duk yy laushi. Wannan karon da laifiyayyan mari hannun Ammi ya kai ziyara saman kuncin Rayyan gami da tsawar " Ka kashe min yaro wlh sai na sa an 'daure min kai, mara hankali da tunani kawai..." Ligib Sultan ya fa'di ya mi'ke a 'kasan wurin babu alamun 'karfi koka'dan tattare da shi..sai numfashi da yk fitarwa da 'kyar dafe da wuyan sa da Rayyan yy masa ri'kon 'karfi. Shi kansa Rayyan 'din numfashi yk sau'kewa zazzafa yana sake bin Sultan 'din da mugun kallo. Ammi ce tayi saurin tallafo Sultan sai Raihana ta taya ta, sun yi 'ko'karin mi'kar da shi amma suka kasa dole hk suka jashi da 'kyar zuwa wajen motar Ammi a hakan ma da taimakon maigadi, sai dai bb makullin motar a hannu dole sai da Ammi ta koma 6angaren ta ta haura sama. Sai da ta canza mayafi kafin ta 'dauko key 'din motar ta fito, haka take yin komai cikin hanzari, gani take tamkar kafin ta fito za'a ce mata Sultan ya she'ka sbd yadda duk jikin sa ya saki. Dai- dai da fitowar su Anty Madeena, Zaitoon da shi kanshi Rayyan din dake 'dauke da Marwa duk a rikice suka shiga motar sa. Zaitoon na 'ko'karin shiga shi kuma yana zagayawa ta 'dayan 6angaren dan komawa mazaunin sa daidai zai gifta ta yace" ki koma gida "! Sosai tayi mamakin jin ta'kaitattun kalaman nasa sa gashi bb alamun wasa a ciki ta kowani fanni, ba kuma alamun da ya nuna ga da wanda yake maganar, waigawa tayi baya, gefe da gefen ta taga dai bb kowa sai ita ka'dai tsaye hkn yasa ta sake tabbatar da cewa da itan dai yk ba wata daban ba. Saroro ta tsaya bayan ji da kunnen ta da tayi yana fa'din a rufo masa 'kofar mota. Duk da dama ba cikin yanayi mai da'di take ba amma hkn bai sa ta kasa jin haushin maganar tasa ba. Tana nan tsaye har yaja motar da gudun gaske ya nufi wajen gate 'din gidan. Yana fita kuwa su Ammi suka rufa masa baya suma, sai dai ba asbiti 'daya suka je da shi ba..yadda Ammi tayi fushi ta kuma 'dau zafi yasa yau bata koyi tunanin zuwa Youheal ba gudun karma su 'karasa mata yaro...acewar ta. Waya ya ciro ya danna kira, 'yar ta'kaitacciyar magana yy da ba kowa zai iya fahimtar manufar sa ba. Daga nan ya sake 'kiran wata number nan ma babu wanda ya fahimci kan wayar tasa indai ba dama kasan kan zancen bane. 'Bangaren Zaitoon kuwa da gudu ta koma ciki tana mai sakin kukan ba'kin ciki da jin haushin sa, sam tunanin ta ya kasa bata manufar abinda yayi, 'karshe kawai sai ta bari akan ba komai bane face tsana da 'kiyayya wanda take da tabbacin bayyanar Mufee matsayin 'diya agare shi ne ya sake haifar da 'kiyayyar. A 'kofa taci karo da wata 'yar uwar su Anty Madeena mai suna Ramla, ita ta rike ta tana mai tambayar lafia, tun tana bathroom 'dazu tajiyo 'karan ihun ta yanzun kuma gata tana kuka. " me ya faru ina su Ammi Aseeyan suke duk bangan su ba...?" Ta tambayi Zaitoon tana mai bada hankali agare ta. Cikin kuka Zaitoon ta amsa ta da fa'din" Asbiti suka tafi ..Marwa da Yah Sultan basu da lafia...". " Subhanallahi...Marwa kam ba yanzu na barsu tare da Mufeeda na shiga watsa ruwa ba...?" Shiru Zaitoon tayi bata bata wata amsa ba illah hawayen ta data cigaba da sharewa. Ramlan ce ta kama hannun ta suka juya ciki bata ma yadda ta zauna a palorn ba ta kama Mufeedan ta suka shige 'daki ta ringa kuka sosai, ba komai yafi tada mata hankali ba irin dukan da taga Rayyan ya yiwa Sultan, yadda ya mai jinajina abin ya bata tsoro sosai tamkar wani babban ma'kiyin sa yake bugu ko alamun tausayi bata ga ya nuna agare shi ba...abin nan da ya faru yasa ta dasawa ranta cewar lallai Rayyan bai da imani tabbas muguntar sa ta shahara sosai. 'Bangaren Rayyan ma bayan ya sau'ke su Marwa ya gama duk abinda yasan ya dace ayi a hannun Dr Fawwaz ya bar ta ya fice domin hankalin sa har yanzun akan Sultan yake. Sam ji yake bai ma yi masa komai ba tukunna, har a yanzun bai masa bugun da zai sa yaji sanyi aran sa game da abinda yai masa ba. Yaso da an barshi, da Ammi ta barshi yayi masa bugun da ko shi da kansa bazai gane kamannin kansa cikin sauki ba balle wani daban. Yasan Matu'kar Ammi tayi fishi taki zuwa Youheal toh asbiti guda ya san zata wuce dan haka can ya nufa bai shiga ciki ba kawai tabbatarwa idanun sa yy cewa suna nan din bayan ganin motar su da yayi a waje daga nan ya juya ya koma gida yana mai amsa waya. Mintina Talatin 'kwarara basu cika ba sai ganin bayyanar jami'an tsaro akayi suka cika ko'ina a hospital 'din tamkar wani babban criminal ke jinya...Ammi har abin ya bata tsoro sosai. Tsoron ta bai gama tsananta ba sai da taga an lan'kayawa Sultan Handcuff an ha'de da jikin gadon asbitin da yake kwance akai...duk kuma yadda taso ayi mata bayani game da hakan bata samu gamsasshiyar amsa ba domin umarni suma aka basu daga sama. Sultan kam sai farkawa yayi ya gansa 'daure da 'karfen masu gagarumin laifi ga kuma duk jikin sa ciwo yake masa. Fuskar sa ta kumbura suntum ga raunika sun cika ko ina inba sanin asali kayi masa ba mawuyaci ne ka iya gane shi ma. Kai kawai ya fara juyawa gefe da gefe cike da ru'dani yana mai danasanin shigowar sa Nigeria gaba 'daya. Mene haka ya faru da har aka kai ga wannan matakin? Abubuwan sun faru masa ne cikin sau'ki a kuma bazata sosai. Bai ta6a yin zaton haka ba sbd bai kai tunanin sa da nisa kan rufe masa asusu da kuma tsayar da shiga da fitan asusun sa ba balle ya bibiyi batun yaran sa da yaji su dib. Hannun sa 'daya ya kai ya bugi kansa da haushin wautar da ya aikata nan yaji zafi sosai sakamakon ciwukan dake kan nasa. 'Kara ya saki mai ma'ana biyu na zafin ciwo da kuma zafin zucia na haushin abinda Rayyan yy masa. Idanu ya lumshe cikin ransa ya ayyana wautar sa akaro na biyu na barin Rayyan da yy araye har aka kai ga wannan matsayi gashi yanzu yana nema ya zame masa 'karfen 'kafa, ji yk da ya sani da ya kawar da shi tun farkon fari inyaso ya'kin sa ya rage da 'yan matan gidan ka'dai...gashi ya yi sake ya bari babban makiyin sa ya girma. Rayyan kuwa bai zame ko'ina ba sai can gidan sa da yk halaliyar sa inda yy rayuwa da matan sa acan ya kuma kashe dukkan wayoyin sa dan yasan dole Ammi sai ta neme shi. Marwa bata jima ba ta farfa'do sai dai ta kasa daina kuka muryar ta har na disashewa ta kuma 'ki bu'de idanuwan ta...illah kuka da surutai na 6acin rai da damuwa. " Yayah mijina ne fa ka manta..? Yah Sultan shine farin ciki na, shine farin cikin rayuwa ta, idan ka raba shi da duniyar ina kk so in saka raina...?..Yayah Dan Allah ka 'kyale shi...." Sai kuka ya biyo baya da 'kyar aka samu tayi shiru. Sai zuwa yamma suka dawo gida. Nan su Anty Madeena suka ringa lallashin ta da ban baki, gashi sun nemi wayar sa dan sanar da shi halin da ake ciki basu samu ba. Yadda jami'an tsaro ke tsaye tsayin daka kan Sultan abin gaba 'daya ya gigita Ammi, kuma har lkcn babu Rayyan bb dalilin sa...basu sani ba ma shi tuni ya wuce Lagos, hannun sa kuwa tun bayan da ya bigi Sultan da ya dawo gida daga kai Marwa asbiti ya kama hannun ya ja sosai ya mur'de shi sbd zogin da yake mishi daga cikin hannun tun daga ranar bai sake tunawa cewa hannun sa na ciwo bama balle ya hana shi wasu al'amuran sa. Kwanan Sultan biyu aka sallame shi, sai dai ga mamakin Ammi division aka wuce da shi tana ji tana gani aka tisa 'keyar sa. Tabi bayan su ita da Anty Raihana da wata Hajia Zahra dan sanin ma'kasudi da kuma neman belin sa amma abu ya faskara dole haka suka koma gida rai bb dadi, kafin komawar su kuwa Anty Madeena ta wuce gidan ta dan tace bama zata zauna ba balle Ammi ta fahimci tasan wani abu duk da yake ita kanta Anty Madeenan ba komai ne Rayyan ya sanar da ita ba. Allah Allah take akawo 'karshen komai a raba su da jarabbaben yaron nan da har Marwa ke son 'daurawa kanta cuta sbd shi. Da kyar suka samu ta dawo daidai sai da Anty Madeena tayi mata tatas tukunna take cewa ke baki ji da kunnen ki abinda Rayyan 'din yace bane, matar sa ya ta6a masa taya bazai bige shi ba, ko ya 'dauka kowa ma irin Amra ne dangin akuyoyi, kuma da kanki kinsan ai Rayyan ba zai aikata hakan sbd son zuciyar sa kawai ba, dole sai da wata kwakkwarar dalili, inba haukan ki bama abinda ya kamata ki damu da son sanin sa ba shi ne gaban ki ba sai wani can dan iska maci amana kk damin kanki ki damu mutane akan sa...? toh wlh ki kiyaye ni tun kafin ki 'kureni in sassa6a mk cikin gidan nan, wawuya kawai wacce bata san ciwon kanta ba....". Sosai ta 'kara shiga 'dimuwa domin Anty Madeena ta ankarar da ita wani abu da ada bata zurfafa tunani akan sa ba, kuma ma bata ta6a zargin hakan ba sam, nd babu shakka tana matukar kyautatawa Rayyan zato tasan bazai yi haka nan kawai batare da wani dalili ba..amma ai bugun yayi yawa, dole sai ta warware ta shiga tunanin abinda ya ha'da Rayyan da Sultan har aka kaiga wannan gandun gashi 'karshe a hannun hukuma Rayyan ya dam'ka shi an kuma nemeshi an rasa shi. Ta kan zauna jigum cikin su amma ba umm ba um-um sai dai idanu kawai, Zaitoon da Raihana kadai ke 'ko'karin kwantar mata da hankali, a hakan Zaitoon idan ta ke6e kuma ita kanta kukan take sosai domin gani take duk itace silar komai. In kaga Marwa na 'dan fara'a toh Mufeeda na tare da ita ne, da ita kadai take 'dan hira har ta biyewa shirmen ta wani lkc. Kwanaki biyar ana cikin wannan halin duk sun rasa meke yi musu da'di, duk yadda Ammi taso bu'de bakin aljihu dan ta samu belin Sultan abin ya faskara, har tsoro Rayyan ya fara bata yanzu. Wai wannan hauka ne ko kuwa kishi? tana yawan yima kanta wannan tambayar da ita kanta bata san amsar ba, duk tunanin Ammi kan ta6a matar sa da yace Sultan yy ne ka'dai, kuma in dai kan hakane ai bai kamata ya ja maganar har haka ba hadda hukuma, hukumar ma zazzafa indai ba wai dama da kwai wata a 'kasa wanda ita bata sani ba. Tunanin Ammi kenan kusan ko da wani lic, ta kuma so ganawa da shi Sultan 'din amma bata samu damar hakan ba. A yanzu kam ta gama fahimtar yanayin tafiyar da duniya take yi dama rayuwar gaba 'daya. Kai zaka haifi 'da ko 'ya da cikin ka amma watan watarana sai ya fi ka 'karfin iko da nuna isa, dan gashi zahiri taga misali ganin idanun ta akan ita da Rayyan. Ko da ya dawo daga Lagos 'din kuwa bai je gidan san bama talkmore of gidan Ammi. Hotel ya kama yayi zaman sa yana mai cigaba da harha'de hujjojin sa na shiga kotu, dan ba 'karamin nasara ya samo a wannan tafiya tasa ba. Yayi amfani da salon aikin sa na lauyoyi ya kuma samo duk hujjojin da yake bu'kata wa'danda suka shafi Companyn sa na can Lagos 'din dama wasu daban,..wannan karan da kansa yake so ya tsayawa ahalin sa, baya so ya wakilta kowa shi da kansa yake so ya bayyanawa dunia waye Sultan su gani, ba kuma dan baya son shi ko kuma dan ya tsane shi ba, badan komai ba kawai sbd 'yan baya da kuma Sultan shi kansa, so yake rayuwar Sultan da kuma hukuncin da za'ai masa ya zam darasi ga duk wani maci amana da kuma mai burin aikata irin hakan agaba..so yk Sultan yasan cewa yayi kuskuren da dole hukunci ya hau kansa..gagarumin darasi yk so ya bari wa 'yan baya. Kwatsam kawai lbr ya iso Ammi akan za'a shiga kotu ranar litinin mai zuwa wanda yyi daidai da kwanaki hu'du kenan masu zuwa daga lkcn da taji. Wannan lamari yafi komai tada mata hankali fiye ma da abinda ya faru abaya..abin ya mata bazata domin bata tta6a zaton hakan ba. Wai duk menene wannan, menene Rayyan yake nufi, Sultan 'dan ta ne kamar yadda yake 'danta, meyasa bazai iya yafe masa 'dan wannan abin da yai masan ba har sai ya dangana da hukuma 'karshe kuma kotu...meyasa bazau zo gida a zauna ayi magana ba, tunda wannan issues din na gida ne, bai kamata wani dan karamin family issue yasa ka rufe ido kai ta tafka rashin mutunci ba...watarana kai ne da kunya a tunanin Ammi kenan. Tabbas kuwa hakan ne, sai dai kuma bb mamaki rashin sanin takamammen abinda ke faruwa yasa Ammi tunanin cewa wannan abin family issue ne kadai. Ranta ya 6aci sosai musamman idan ta tuna daina ganin Rayyan da tayi cikin kwanakin sam, duk kuma wani wuri da tasan zata same shi taje bb shi, gidan sa, office, asbiti, Infinity duk bb shi, hatta abokan sa ta tuntu6e su bb labarin sa. Anty Madeena kam ko ajikin ta tamkar ma bata san meke faruwa ba kwata- kwata, gidan ya sake zama shiru kace gidan mutuwa ne, ba Raihana ko Zaitoon ba, ba Marwa ba kar ma Ammi taji lbr hatta tsirarun ba'ki dake gidan suma bb wanda yake cikin yanayi mai da'di...ko.Mufee da ke 'yar mitsil a gidan sai da ta fahimci gidan ba daidai yake ba sbd walwalar kowa da ta daina gani. 'Karshe Anty Madeena 'dauke Mufeeda tayi dan acewar ta basa bata kulawar da ta dace sbd wani 'dan iskan yaro can da bai san mtunci ba baza'a illata musu lafiyar yarinya ba. Ammi har rama tayi sosai, idan ka ganta sai ka tausaya mata cikin kwanaki 'kalilan. Ana gobe za'a shiga kotu Ammi ta rasa ta yadda zata sami Rayyan kawai taje ta siyi fili a gidan Talebijin aka mata cikiyar sa da kuma babban kashedi kan shiga kotun nan, wannan abu shi yaja ra'ayin mutane da dama kan zuwa kotun dan ganewa idanun su irin shari'ar da har ake kashedi akanta. Da yawan mutane kuwa da suka saurari jawabin Ammin fatan su kar ma ace Rayyan ya gani balle ya 'ki zuwa kotun burin su a gudanar su kuma gani da idanun su abinda ke faruwa. Salmerh😘 [24/8/2023, 4:26 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Wattpad@* _Serlmerh-md_ 🅿️ *...97* .......Yadda kuwa jama'a suka yi fata da buri hakan ne ya faru. Yayin da da yawan su suka kwana da burin zuwa kotu a wannan ranar...gaba 'daya hankalin jama'ah sai ya raja'a akan shari'ar Rayyan duk da shi ba hakan yaso ba, ita kanta Ammi bata san maganar da tayi tamkar sake janyo hankalin jama'a tayi kan shari'ar tasa ba kasantuwar tayi abin ne bisa zafin rai cike kuma da jin haushi, sa6anin yadda taso a janye ma gaba 'daya sai salon abin ya canza zuwa ga 'kaguwa ga sauraran wannan shari'ar. Ammi bata san hakan ba har sai washegari da idanun ta ya gane mata yadda jama'a ke ta tururuwar zuwa, kanta daurewa yy da farko sai da ta nisa kafin ta farga da kato6arar da tafka. Haushi kuwa ya kara cika ta. 'Bangaren Marwa da Zaitoon sun kwana ne cikin yanayi na tsantsan damuwa da rashin sukuni banda kuka babu abinda suke yi har wayewar gari. Anty Raihana da Ammi kuwa bazaka iya ma bayyana ainahin yanayin da zu'katan su ke ciki kai tsaye ba, Anty Madeena kadai ke cikin farin ciki marar misaltuwa, ganin cewa burikan ta na cika a hankali 'daya bayan 'daya batare da ta 'daga hankalin ta ko abin ya fito daga gareta ba. Amra bata san wainar da ake toyawa ba dan ita ba gwanar kallon talabijin bace, har sai da 'kawar ta Ameera ta 'kira take tambayar ta abinda ya faru, dan acewar ta taji ana sanarwa da sunan mijin ta da kuma maganar kotu a gidan talabijin..?" Cike da rashin damuwa Amra tace" wannan gayen! 'Kyaleshi ai fiye da haka ma zakiji indai Rayyan ne tunda ya saba dama..can aikin sane ya jingine ta..."! " Aikin sa!" Cewar Amira ta tambaya da mamaki. " Yes...ke da can kina nufin baki san shi Lauya bane..?" Da sauri Ameera ta tare ta da fa'din " ke wannan fa daban ne wlh 'kawata, ni kaina abin ya 'dauki hankalina da zan samu dama sai na halacci kotun nan wallahi tallahi, fata na ma ace bai ga sanarwar mahaifiyar tasa ba ayi zaman, 'kage nake da son sanin irin shari'ar da za'ayi, mahaifiyar sa ce fa da kanta ta bada kashedin..kinga kuwa babban al'amari ne ai". " Kai Ameerah kina nufin Ammi da kanta?" " Ita dai.. ko ke baki ga rahoton ba ne...?" " Ban ma bude Tv yau ba sam". " tab an kuwa yi bb ke madam..wlh kallo ya barki, ki tuntu6i mijin naki kiji labari toh, nayi mmk ma da har sai da Ammin ta kawo nan, shi da take da damar da zata han fita ko'ina daga gidan ma, taki ka'dan fa zatayi ta cimmasa a 6angaren sa amma har sai da ta kawo nan? ko de bakwa gari ne ke da shi..inji...?" " Muna nan.."! Ta bata amsa a takaice da 'dan sanyin sauti. " Ikon Allah, rabon dai muma muji labarin ne...". " Ai kuwa! Ku kuma 'yan jiran kota kwana ko? 'yan fa'di ku 'kara" Dariya Ameera tayi Amra kuwa tace" Wai me tace ne Ammin? Ameera dan Allah sanar da ni, kin sani a duhu fa wlh..ni kinsan ba lallai in sani ba ai..?" " Inajin shari'a ce tsakanin shi da wasu 'yaran nata daban a yadda dai bayanan suka fito, ko kuma cikin dangi haka da alamu kuma ita bata so hakan ba, ina jin bada son ranta aka shigar da 'karan ba..." " Yaranta kika ce Ameera..? " Erh"! " Anya kuwa?..Kinsan hadin.kan yaran.Ammi kuwa...bana tunanin hakan gaskia sai dai ko a dangi din..amma sunan wa kk ji ta ambata?" Amra ta tambaya wannan karan cike da ru'dani. Yayin da Ameera ta cigaba da fa'din" Sunan Rayyan ka'dai nima naji...ni kaina nayi mamaki, gasu sanannu a gari mafi yawa kowa ya sansu, shiyasa kowa ke 'daukin zuwa ganin tataburzar..." " Yah Subhanallahi...!" Amra tace tana dafe goshi, take ta nemi nutsuwar ta ta rasa, tsoron ta 'daya kar ace da Sultan za'ayi wannan zaman shari'ar, indai hakane kuwa itama ai zama bai ganta ba domin tasan kashin ta gab yake da bushewa. Bama tasan lokacin da ta raba wayar da kunnen ta ba sbd tashin hankali. Kalma guda kuwa ta innalillahi ta kasa zuwa mata kan harshen ta. Safa da Marwa ta fara cike da tashin hankali har wani zufa ke karyo mata banda jiri da take gani. Wani 'karan 'kira sake ji a firgice ta 'dago wayar abin mamaki wata tsohuwar kawarta da har ta mance ma da ita bama tasan har a lkcn tana ajiye d number din ta ba sbd rushewar da zumunchin tsakanin su yy da jimawa wai ita ke kiran ta. Ta riga tasan duk dai batun bazai wuce wanda ke gaban ta a yanzu ba..hakan yasa bata daga ba,.ko da wani kiran ya sake shigiwa a karo na biyu rejecting kawai tayi ta na mai jan tsaki cike da haushi biyu. Bayan nan ta sake samun kira daban daban har guda biyu da sabbin lambobin da bata ma san ko su waye ba amma duk bata koyi alamar zata daga ba har suka katse. Nombobin wayar Rayyan da na Sultan kaf sai da ta gwada amma bata samu ko guda 'daya tayi ringing bama balle ta samu arzikin 'dagawa. Hakan shi ya sake tayar mata da hankali ya kuma hargitsa mata lissafi baki 'daya. Ammi ka'dai ta samu, kuma itan ma bata 'daga wayar ba, haka ma Marwa da dama hankalin ta ba jikin ta yake ba a wancan lkcn. Hankalin Amra dai hankalin ta inyayi dubu to ya tashi..dama hausawa sukace..aikata alkhairi sai kaga alkhairi...in sharri ka aikata nutsuwar bata dawwama har abada. ***** _Washegari 8:22am_ .......Tsaye yake gaban madubi ya 'kure madubin da shanyayyun idanun sa da duk suka rine suka koma jajaye sbd stress, rashin bacci da kuma damuwar da ya sanyawa zuciyar sa..sai dai duk da wadannan 'kalilan din karaya ko sassauci babu tare da shi. Shirye yake cikin ba'kin dogon wandon wani ha'd'ddaden silky suit mai 'dan karen kyau da tsada, farar 'yar cikin kawai ya sanya sai Ma'daurin wuya da yake shima ba'ki, hular da kai tsaye take nuni da bayyana ko shi'din wanene rike a hannun sa ya mayar da idanun sa kanta tamkar bai ta6a gani ko amfani da ita ba akafta 'din rayuwar sa..tamkar yau ne farko ji yake tamkar a yau zai fara sakata. Kuma hakan yake ji har can kasan zuciyar sa, domin shari'ar da yake da burin gabatarwa ayau din tasha bambam, tabbas ta banbamta da kowanne...Bai ta6a tunani ko hasashen amfani da su nan kusa ba tunda ya ajiye su. Domin rabon sa da sanya su har ya mance, amma hakan bai sa ya mance da dai- dai da 'kwayar zarra daga cikin matsayi ko yanayin aikin sa ba. Sai ga shi ayau wata matsala ta tunzura shi ya sanya su, matsala ma ta cikin gida, matsalar da ta bambamta da duk wasu matsolin rayuwar sa. Duk da yake har a lkcn bai janye ba, bai kuma yi nadamar taki guda na abinda ya aikata ba, saima 'kwarin giwa da yake ji, amma can 'kasan ransa yake jin bb da'di, can 'kasan zuciyar sa yake jin kamar bai yiwa Ammin sa adalci ba da be nemi shawarar ta tun farko ba. Kuma sarai yasan halin ta, akan Sultan sosai zata nuna 6acin ranta idan taji abinda yake shirin aikatawa, amma ko hakan ma zaiyi ne sbd wani dalili, ba wai dan son zuciyar kadai ba. Dalili kuwa shine sbd _Ammin sa_ , domin matu'kar Ammi ta sani bazata ta6a barin a hukunta Sultan ba ya sani, 'karshe ma cewa zatayi a ' _kyale shi_ Wannan kalami na Ammi ya jima da haddace su, tun yana 'dan 'karami matukar akayi musu zalunci sai tace a kyale mai shi Allah na sane da komai..zata ce a kayle sa da halin sa ne ya riga ya sani..za kuma tace su yafe masa kawai abarshi yy rayuwar sa bayan basu da tabbacin iya gejin da abin zai tsaya, shin zai tsaya ne ko zai cigaba akansu da ma wasu daban, basu da tabbas din Sultan zai rabu da wannan ba'kar zuciyar da ya sanyawa ransa ya fuskanci dai- dai ko a a. A ganin sa hukunta Sultan shine dai- dai, dole sai ya hukunta yaron nan, dole sai yasa an ladabtar da shi, bawai dan baya so ko 'kaunar sa bane, ko dan ya tsane shi ba, a a zai yi komai ne bisa gaskia da adalcin da yasan Allah ma bazai ta6a kama shi da laifi akan sa ba...duk da yake yayi masa munanan abubuwa amma har a lkcn yana jin 'kaunar sa aran sa..'kauna matsayin dan uwan sa na jini, shi yasa yake jin nawin wa'dannan kayan dake jikin sa sbd Sultan, Marwa da Ammi. 'Dagowa yayi ya sake duban kansa a madubi still yana shafa hular aikin nasa, tamkar wanda aka bashi umarnin hakan lokaci guda ya tsaya cak, sai yaga tamkar mutum ne bayan sa a tsaye ba kuma ya ganin ko wanene sbd fuskar lullu6e take da fararan gashi ko'ina. Hular da ke hannun sa yaji an ansa. Kyam yaji ya tsaya tamkar mutum mutumi.hadda idanun sa guri guda suka tsaya suka daina juyawa. Bazai iya fasalta yanayin da ya shiga a lokacin ba domin ji yayi tamkar kwakwalwar sa ta dan je hutu da aiki na dan lokaci. Sanya masa hular yaji anyi akan sa, kana ba'kar babbar rigar aikin nasa itama aka warware ta aka rufa masa ita daga bayan sa. Sosai mamaki da al'ajabi suka kamashi ganin faruwar lamarin yayi tamkar cikin mafarki. Idanu ya lumshe ya kuma bu'de su cikin madubin bayan dawowar brain din sa daga aiki..sam ya kasa 'dauke idanun sa daga kan hoton sa da yake gani cikin mirror 'din kamar yadda ya kasa fahimtar abinda ya faru yanzun nan... shin shi 'din ne ya sanya kayan ko kuwa sanya masan akayi..? Yana kuma iya hango bayan sa babu kowa ba kamar dazu da yaga tamkar da mutum tsaye ba. Sam baiji tsoro ko firgici ba kasancewar Rayyan asali namiji ne, me dakakkiyar zuciay lamba daya. Hakan yasa bai ji tsoro ko shakkan waigawa ba gaba 'daya amma baiga kowa bai ga alamun kowa ba kuma illah kafa'dun sa da yake ji tamkar da hannun mutum a kai...Koda yayi niyyar 'dago hannun sa dan ta6a bangaren kafadar dayake jin tamkar an dafa shin kuma sai yaji hannayen sa kuma sun masa nauyi nan take. Hakan ya faru ne cikin 'yan 'kalilan din dakikai. Sosai kayan sukayi masa kyau, suka kuma canza masa kamanni daga Dr Rayyan Sa'ad izuwa Barrister Rayyan Auta. Kallon gefen kafa'dar tasa yy by his right inda yafi jin alamun mutum amma babu hannu akai shidai bai ga komai ba amma yana iya feeling dafa shi da aka yi hakan kuma shi ya haifar masa da tashin tsigar jiki. Sam bai ji ya tsorata ba, bai ji fargaba ko firgici da jin hakan ba, sai ma wata 'kwarin gwiwa da yake ji na shigan sa. Sau biyu aka buga kafa'dar tasa tamkar irin ana jinjina masa 'din nan. Cikin zuciyar sa kuma ji yake kamar ana yi masa magana ne da sauti mai shiga can cikin zucia, bai isa ya misalta yanayin sautin ba, ya dai yi kokari wajen ko kalma guda bata kubce masa na daga kalaman dake shigan sa" Kaje 'dana, kar kaji tsoro! kar kaji shakka, kai 'din jarumi ne, kuma namijin dunia ne, tafe kake da sa'a da 'kwarin gwiwar ka tun kana zanin goyo, ka tsaya akan gaskiyar ka, ka fiddo da ita fili, ba tonan asiri bane..ba kuma 'kiyayya ba, zallar shari'a ce da kuma hukunci, da iznin ubangiji kuma zakayi nasara yaro na! nasara taka ce, nasara ba tare da kai har abada Muhammad Rayyan...fatan alkhairi....". Daga haka bai sake jin komai ba illa wasi- wasi daga cikin zuciyar sa..amma still kwarin gwiwar sa na nan..sam babu karaya ko tsoro a tare da shi. Tamkar kuma an cirewa hannayen sa da jikin sa wani abu mai mauyi haka yaji shi ko ina nasa sakayau. Hannayen sa duk biyu ya sa atare ya kamo gaban rigar yana gyara mata zama idanun sa 'kur a cikin madubin..ya saki wata nannauyar ajiyar zuciya. 'Kafar sa ya 'daga ya 'danja baya ka'dan taki 'daya hakan bai masa ba, baya ya sake yi zuwa bakin gado batare da ya juya bayan sa ba, da baya yayi tafiyar zuwa inda wasu tarin takaddu ke ajiye kusa da pillown sa yasa hannu ya 'dauko su ha'de da makullin motar sa. Sai da ya rungume su tare da lumshe idanun sa saman la66an sa ya furta sunan da shi ka'dai yasan me ya fadi..sai dai in kana kusa da shi ne zaka iya tsinkayar sautin sunan... _Zaitoon_ acan 'kasa. Daga hk yy waje batare da ya sake waigowa ba. 'Karfe goma za'a fara shari'ar, dan haka bai yadda yy latti ba, duk da bai so hkn ba, bai so tafiyar da shari'ar a yadda yake ganin dole hakan zatazo ba, yaso tun a hannun hukuma Sultan ya amsa laifin sa amma taurin kai da kafia ya hana shi, dole sai ansha fama yasan dashi, sai dai sanin da yayi cewar ya tara 'kwararan shaidu da hujjoji yasa yake 'dan jin sanyi aran sa domin shi ba burin sa ayi doguwar shari'a ba, ba burin ayi ta kaiwa ana kawowa tsakanin.sa da Sultan ba, burin sa kawai ayi ta ta kuma 'kare batare da anaki ruwa rana ba, da so samun sa ne ma bai 'ki a yau kadai bama a kammala shari'ar sai dai yasan mawuyaci ne, ita shari'a sa6anin hankali ce dole sai an bi a sannu. Yadda yaga kotun cike da mutane tun daga haraba abin yaso bashi mamaki amma mamakin sa bai tashi tabbatuwa ba har sai da ya dangana kansa da cikin kotun a lkcn da mai girma alkali ya iso. Ji yayi tamkar ya wakilta wani a madadin sa amma wata zuciyar tasa ta garga'de shi da hakan nan take. Bayan gabatar da wasu sha'riah har guda biyu sannan mai gabatar da shari'ah ya gabatar da tasu shari'ar aka fara fafatawa tsakanin lauyan Sultan da kuma lauya Muhammad da Rayyan. Kotu tsit tayi tun daga lkcn da aka fara gabatar da shari'ar har zuwa lokacin da mai sha'ria ya 'dage 'kara zuwa zama na gaba. Da yawan mutane sun tafi ne da haushin Rayyan sbd dangantakar su da Sultan ya riga ya bayyana har su ke ganin rashin kyautawar Rayyan yayin da wasu ke tunanin dole akwai butulci ta 'daya 6angaren da har yanzun sun kasa gano daga ina ne, domin har aka tashi shari'ar Sultan ya ki furta ko kalma 'daya 'kwakkwara da yasan zata rufe shi, shiyasa wasu ke jin tausayin sa. Hankalin Ammi ba 'karamin tashi yayi ba da ganin Sultan a kotu da kuma yanayin da ta gansa, duk da yake basu samu isowa akan lkc ba sun zone a 'kurarren lkc, amma ganin yanayin Sultan ya sake rikita mata tunani, Rayyan kuwa ana kammala sharia aka neme shi aka rasashi yabi wata hanyar yy gaba abinsa. Duk yadda Ammi taso haduwa da shi abin ya faskara, hankalin ta ya tashi sosai, shiyasa ko fahimtar abinda ke faruwa cikin kotun batayi sosai ba. Anty Madeena ke 'dan kwantar mata da hankali da yake su uku suka zo da wata 'kawar Ammin. Duk yadda su Raihana suka zo zuwa Anty Madeena 'kin amincewa tayi, tace ta zauna da su Marwa a gida. Sam yadda Ammi take tunanin sha'riar ba haka bane, Anty Madeena da ta 'dan san wani abu akai, ta kuma fahimci ka'dan daga cikin shari'ar bayan zuwan su sai taji abin ya mata zam zam, taso fahimtar da Ammi amma ta kasa bada hankali ma balle ta fahimci manufar Antyn dan haka sai ta fita hanyar ta. Email ta yiwa Rayyan akan tana san ganin sa kota wanu hali a yau ba wai sai gobe ba, domin wayoyin sa duk" babu me tafiya. Ai kuwa har ta cire rai da zuwan sa, bayan isha'i sosai ma sai ga shi yazo, domin bai ga sakon da wuri ba, yaso ma tun yamma.ya wuce Lagos sai aka samu akasi jirgin Lagos 'din ya riga ya wuce sai kuma zuwa shida na safia, abinda ya hana shi wucewa kenan kawai ya tsaya duba sakonnin sa na email nan yaci karo dana Ammi, batare da 6ata lkc ba kuwa ya shirya ya tafi gidan ta domin yasan darajar mahaifiyar sa ba dan kadan ba. Fa'da sosai Anty tai masa na fara shari'ar da yayi batare da ya sanar da mahaifiyar sa ba ta kuma sanar da shi yadda duk hankalin Ammi yake a tashe sbd hakan. Ha'kuri Rayyan ya bata sannan ya 'dora da jero dalilan sa ya kuma ce ai ke ma kin sani Anty, kinsan halin Ammi..na kwammaci a kammala komai kafin haduwar mu sbd nafi kowa so da ganin an hukunta yaron nan, sanin cewa ba'a daukan doka a hannu ne yasa nk duk wannan ba dan haka ba da tuni na hukunta dan banza, ya cuce ni yaron nan Anty, ya min mafi tsanani da munin cin amana, yaci amanar mu gaba 'daya Anty, wlh na jima banga macuci mai tsananin son kansa irin wannan yaron ba...Anty...kuma nasan Ammi bazata ta6a fahimtar duk wani karatun da zan mata bisa wannan al'amari ba indai akan yaranta ne musamman ma shi..shiyasa na biyo ta wannan hanyar. Sai ya yi shiru ya kasa ci gaba da magana. Anty ma jikin ta sanyi yayi sosai...a hankali tace kayi hakuri Rayyan....." Da sauri ya tare ta yana mai girgiza kansa yace..." Not on these issue pls Anty...Ki barshi ya girbe abinda ya jima yana yiwa mutane, ki barshi ya girbe abinda ya jima yana shukawa kansa da kansa...". " Nima ban hana ka hukunta sa ba, but why can't u expel nd replace ur self with somebody else...I think is better than kai da kanka ace kk wannan shari'ar Rayyan, bayaga haka ma kar tafia tayi tafia kazo ka karaya bcuz Sultan is still ur brother nasani, that bond is still existing sbd u all raised with it...". Shiru kawai yayi bai ce da Anty komai ba, amma shi a karan kansa yana ji da kuma tabbatar da hakan ba tun yau ba, yana son Sultan ya na kuma kaunar sa matsayin dan uwan sa sai dai hakan bazai hana ya kasa mi'ka shi ga duk inda yasan zai samu hukunci dai dai da laifin da ya jima yana aikatawa ba.... Abu biyu zuwa uku da Sultan yai masa har baya 'kaunar tunawa da su, sbd abubuwa ne masu matukar ba'kanta rai da zucia, cin amana, ha'inci da kuma yaudara, tun asali ya tsani ma'abota ha'inci da cin amana, sannan ko da wasa bai ta6a zargin Sultan kan komai dake faruwa cikin ahalin su abaya ba, amma karo guda Sultan ya karyata mafarkin sa, ya wargaza yadda, amana da amincewar da akayi masa tun yana dan karami, ya tabbatar masa da cewa shi din ba 'dan halak bane na zahiri, ya kuma tabbatar masa da gaskiyar maganan nan da ke cewa tsintacciyar mage bata mage.... Da 'kyar da kalaman kwantar da hankali da kuma lallami Anty ta samu ya labarta mata komai da ya sani, nan ta 'kara 'daukan zafi akan Sultan, domin yanzu ta gama sanin komai ta kuma 'kara tabbatar da cewa tun da can baya ba a banza ne take jin tsanar yaron ba ashe da gasken gaske fuska biyu gare shi, ashe dagaske maci amana ne maha'inci....". Ammi sam bata tsoma baki cikin maganar tasu ba illa idanu data tsura musu cike da mamakin su duk biyu. A yadda ta fahimci Rayyan sam ko me zatayi bata ga alamun janyewa tare da shi ba...hakan yasa kawai ta mike da niyar basu waje tunani kawae ta fara na yadda zaymta 6ullo masa. Ganin tashin nata yasa Rayyan saurin kiran sunan ta...bata tsaya ba ta amsa shi da cewa"Nagode sosai Babana"! A yadda tayi maganar yasan me take nufi. Dan hk take ya mike yana fadin Ammi dan Allah kiyi..." Saurin tare shi tayi tana gab da barin parlourn tace" Kar ka damu jeka abinka...ngd ka kuma kyauta"! Daga hk tayi gaba abinta shi kuma ya tsaya cak ya dafe goshi gami sakin numfashi. Yaso yabi Ammi amma yasan ko da ya nemi dogon zantawa da ita batun dai 'daya ne indae Ammi ce shi kuma sam bazae iya ba a wannan ga6ar. Yadda yaga Anty Madeena ke share 'kwalla ya fahimci lalle abin gagarumi ne da alama wasu abubuwan take sake tunowa. Rayyan dai bai ce da ita komai ba kawai ya wuce ya tafi izuwa masau'kin sa. Ranar da aka koma zaman kotu Rayyan bai bayyana kamar ranar na farkon ba, shawarar Anty ya dauka kai tsaye sbd shi kansa ya sani akwai ga6ar da bazai iya jure tunawa da shi gaban 'dumbin jama'ar ba da ganin idanun sa sun ninka na baya, hakan ne yasa ya wakilta abokin sa mai suna Ahmad Fari shi kuma ya 6oye kansa, sai dai ko kalma guda cikin shari'ar bai bari ya wuce shi ba. Babu laifi kuma shari'ar ta tafi masa ne a yadda ya tsara domin shaidar sa da hujjoji daki- daki suka bayyana, kusan duk wanda ke zaune wurin jikin sa sai da yy sanyi, karma Ammi da ke ta farko farko taji labari, ta kuma yi hkn ne sbd son cafke Rayyan da kuma tsananin tausayin 'dan ta Sultan, sai gashi a lkc guda komai ya kwance mata, her one nd only Sultan kuma son in-law gareta revealed out as a biggest criminal, murderer, kidnapper, womanising, drug dealing, ta'addanci da kuma cin amanar su gaba 'daya. Abu 'daya da Rayyan bai yadda ya bayyana a kotun ba shine ala'kar dake tsakanin Sultan da Amra, ko bakomai matar sa ce, kuma tona maganar a cikin kotu tamkar ya tozarta ahalin sa ne da kuma asalin Arfan da a halin yanzu yake matsayi da bearing sunan uba agare sa. Bazai so yaron ya girma cikin tagayyarar rayuwa ba. Motsin kirki kasawa tayi zaune anan wajen, ji tayi tamkar an zuba mata ruwan zafi a jiki, da farko kasa amincewa tayi har take tunanin ko sharri akayi masa amma daga baya yadda hujjoji suka 'kara fitowa sai taji jikin ta ya fara yin sanyi. Idanu 'kur ta 'kura akan Sultan ta kasa ko da 'kyafta idanun ta a lkcn da bakin sa ya sake tabbatar da laifin sa gaban dubban mutane, inda ya 'kara bayyana hadda wanda ma bata san shine ya aikata ba..wato saka wuta a gidan Anty Madeena sbd duk su mutu shine burin sa. Cikin rai Ammi ke ambatan _Innalillahi wa inna ilaihi raji'un_ hakan kuwa shi ya haifar mata da 'yar natsuwar da har bakin ta ya iya samun 'kwarin gwiwar furta kalmar..." Ka cuceni Sultan, bakayi mana adalci ba..." Sai ga hawaye zirr ya sakko mata. Wannan kalma na Ammi karaf a kunnen Rayyan domin duk hankalin sa na akant a ne. Wata kamilalliyar natsuwa yaji tacshigesa da jin wannan furuci yasan yamzu shikenan ya gama da babin Ammi tunda ta fahimta da kanta. Sai dai duk irin natsuwar da samu din hakan bai hana shi shiga tashin hankali ba da ganin gudun ruwa a idanun mahaifiyar sa...shi dai Sultan sam Allah kadai zai fa ne zai raba su, bazai ta6a yafe masa koke koken da yy ta sanya masa mahaifiya ba, cak ya mike ya taho garesu 'karshen shari'ar bada su aka kammala ba yace su koma gida haka nan sbd Ammi ta kasa jure cigaba da sauraran abinda ake yi sai kuka. Da yawan mutane ranar da sunan Sultan da kuma irin yanayin tashi cin amanar suka koma gidajen su, wa'danda ma da farko ke kushe halin Rayyan cewa yana sharia da 'dan uwan sa duk jikin su yai sanyi, dama da kyar kotu ke nutsar da jama'a idan aka dauki hayaniya musamman in akazo daidai wani abin mmkn, wanda ta cikin irin hayaniyar ne su Ammi suka samu zamewa sukayi gida. Rayyan bai yadda zaman kotun ya 'kare ba har sai da ya tabbatar bb wata sauran ala'ka tsakanin su da Sultan, hatta da takaddar sakin Marwa sai da ya tabbatar Sultan ya rubuta. Sultan kuka yk sosai, ba 'karamin nadaman halayan sa yayi ba domin bai ta6a kawo faruwar irin ranar nan nan kusa ba. Tsarukan da ya yiwa rayuwar sa da burikan sa duk bai kai ga cika su ba, sabuwar rayuwar da ya jima yana tsarawa kansa bata tabbata ba, kenan duk wannan wahalar da yasha abaya da cin amanar da ya yiwa wanda yake matsayin uba gare shi, ya tashi abanza kenan..? Kenan wahalar banza yayi? Sam ya rasa ina fikira da basirar sa suka shige cikin kwanakin nan gaba 'daya... Daga kotu ba'a zame da shi ko'ina ba sai gidan kaso, gidan maza, cibiyar gyaran hali, inda kotu ta yanke masa hukuncin life imprisonment da kuma diyyan ku'da'de masu dumbin yawa amma Rayyan yace sun yafe, yaje ya girbi abinda ya shuka kawai da shi da masu hali irin nasa, shi da rayuwa da yawon 'kasashe dai kamar baya kam sai dai a kiyama idan yana da rabo. Sai a lkcn Rayyan yaji nutsuwa ta 'dan shige sa, duk da yk ba na sosai bane, amma dai atleast ya rage mugun iri, ya kawar da munafukin kusa, ya kawar da mugun dafin da ya tabbatar wanzuwar sa tare da su na iya illata kowa cikin ahalin sa. Ranar da ya tabbatar Sultan ya shiga gidan kaso a ranar ya koma gida. Direct 6angaren Ammi ya wuce sai akayi sa'a tana zaune palorn ta tana zaman jimami. Bisa gwiwoyin sa ya zube da alamun ban hakuri da neman afuwar ta, cike da karaya dan yasan ya 6ata mata sosai. Gaida ta yy ta amsa ba yabo ba kuma fallasa...amma bata wani kalle shi sosai ba. Hakan sai ya sake sakar masa da karaya har a zucia. Ga mamakin sa kalmar da ya fito bakin ta koka'dan ba yi da ala'ka da tunanin sa ba kuma shi ya tsammaci ji daga gare ta ba. " Allah yayi maka Abbah, Allah yasa 'ya'yan ka suyi alfahari da kai fiye da yadda kk sani alfahari...ngd". Da mamaki yake duban ta, dan sai yake gani kamar ba gaskia kunnuwan sa ke fa'din masa ba, tamkar ba.Ammin sa ke furta wadannan furuci ba, yanayin da yaga fuskar Ammi ya kuma sa mamakin nasa 'kara fa'da'da. Ammi dai..Ammi dai da ya san ta dau zafi kan batun Sultan fiye da kowa....? Juya abin yake ta faman yi aransa, yama kasa furta komai. Sam ya kasa yadda cewa zuciyar Ammi ta amince da furucin da bakin ta ya furta...dan haka dan hk sai ce" Ammi kiyi ha'kuri, nasan na 6ata miki rai akan Sultan amma dan Allah ki fahimci ba wai rashin so bane ya sa na aikata hakan agare shi ba...." " Nasani!" "..na riga nasan hk Rayyan.." Sai ta lumshe idanu da sassanyan sauti tace " rabu da shi, dama ance what u sow is definetely what u would reap.. barshi kawai ya girbe halin sa...ni kaina da nasan hk halin sa yake da tuni na jima da kai report 'din sa da kaina...da tuni na raba shi da ahalina" Duban ta ta mayar izuwa gare shi sannan da kulawa ta cigaba da fadin. " Matso kusa da ni ka bani labarin abinda ya faru..taho nan...kaji Baba na". Tana maganar ne tana jin kuka irin na zuci na taso mata tuno abubuwa masu yyawan gaske. Kasa motsi Rayyan yayi sai daga baya ya 'dan matsa ka'dan daga inda yk ya gyara zama yana sake bata hakuri. " Nace ban son ha'kurin nan ko..." 'Kasa yayi da kansa sosai ganin yadda duk Ammin sa tayi sanyi shima sai yake jin wani iri... A hankali yace " Ammi I have to...sbd ni ka'dai nasan halin da zucia ta ta shiga sakamakon fushin ki gare ni Ammi, na shiga rudani, damuwa tayi min sallama Ammi...karshe sai da na nemi duk wata natsuwa ta na rasa kaf, na rasa duk wata 'kwarin gwiwar da nake ikirarin ina da ita". Sai da Ammi ta yunkuro da kanta zuwa kusa da shi ta ri'ko hannun sa cikin kwantar da murya ta kwantar masa da hankali kafin ta samu ya 'dan bata labari a ta'kaice na duk abinda ya san ya kamata ace for now ta sani, wanda ya jima yana 6oye mata da wanda shi kansa ma binciken da ya zurfafa ne ya bayyana masa su duk ya sanar da ita, domin bb amfanin 6oye mata a halin yanzu, Sultan ya aikata abubuwa masu dama agare su da bai kamat ace har a zuwa yanzun 6oye laifukan sa ake agare ba, ita kanta Ammi kasa fa'din komai tayi, tsam tayi da rai tana fatan ba da gaske Rayyan yake wannan maganar ba... Idanun ta cikin nashi ta jefa masa tambaya dan tabbatar da gaskiyar sa da kanta. " Arfan kake nufi da yaron Amra da kace na Sultan ne ko kuwa wani Arfan daban...?" " Shi Ammi.." Zaman dirshan din da bata zaci yinsa ba shine ya kwace mata alokacin kirjin ta na dukan da gudun da ita kanta bazata iya kiyasta shi ba. Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Ta furta a fili kuma sau 'daya tak. Zafi take ji kirjin ta nayi mata amma bata so tata bayyana hakan gaban Rayyan sbd a halin yanzu bazata so.kara masa damuwa ba. Abin ya bata mamaki Matuka, 'karshe ma da kanta ta tabbatar tsoro take ba wai mamaki kadai ba. Wannan wani irin kazantacciyar rayuwa ce haka...? Kuma ma duk yausge haian ke faruwa da bata da masaniya. Ta tambayi kanta da kanta. Kai ta dan girgiza alamun nemawa kai er natsuwa. Kallon sa tayi sannan tace " Rayyan bb kyau zargi, ba kuma na son irin haka, dan kawai Arfan na kama da Sultan ba shine hujjar da zaka ri'ka dan tabbatar da cewa 'dan sa ne ba naka ba..." Zama ya gyara yana sake duban Ammi da kyau sannan yace. " Ammi ba hujja na baki da kamanceceniyar dake tsakanin su ba, ba kuma zargi nake da bani da tabbas akansa ba Ammi kawai dai na baki 'dan 'karamin misali ne ta yadda zaki fi fahimta ta da wuri, amma Ammi ai kin sanni, kinsan bana aikata abu batare da na tabbatar da inganci, dalili ko tushen hujja ba...kafin na amincewa zucia ta da zargin da wasu suka fara akan Mufeeda an 'dauki tsawon lkc Ammi, duk da yake na ci karo da 'kwararan hujjoji amma hakan bai sa nayi saurin amincewa ba har sai da na dangana da asbiti na kuma sake gwadawa ta hanyoyi daban- daban...amma Arfan Ammi.... Sai ya saki numfashi mai zafi.... Yana jin ciwon maimaita maganar amma ya zame masa dole ya furta ta ga Ammi. Kansa ya kwantar bisa kafadn Ammi ta hannun dama ya lumshe idanu. A hankali ya cigaba da magana. " Ammi meyasa baku ta6a tunanin dalilin da zai sa Arfan ya 'debo kamanni sak na Sultan batare da mun ha'da wata ala'ka ta jini da shi ba? in yayi kamanni da shi a fuska na san ba hujja bace da za'a ri'ka ka'dai Ammi, but ki tuna Ammi bb wani abinda ya ke ajikin yaron nan da yake da bambanci da shi Sultan, sannan the allergic reaction baya da shi...there ar so many reasons da suka sa na tabbatar da cewa Arfan jinin Sultan ne...babban dalilin ma da ya sa bazan iya yafe masa ko bari ya cigaba da rayuwa cikin mu ba shine kashe min ahali da yayi batare da sun aikata masa laifin komai ba, the Innocent Safaa Ammi, my darling Daughter Zamrud, my beloved brother Yah Kabir, my everlasting Mahaifi Abbah na...Abbah na wanda ni da shi da ma wasu daban can duk shine alfaharin mu, ya mana gata tare da shi, ya bamu ilimi da dukiyar sa,.ya ciyar da mu suttura da komai na rayuwa Ammii bai bambanta mu da shi ba...." Kai ya girgiza yana mai sunkuyar da kai sannan ya cigaba..." Ina jin tamkar hukuncin da akai masa yayi min ka'dan har yanzu Ammi..bazan ta6a iya barin sa cigaba da zama da mu ba kuma na riga na anso takaddar sakin Marwa daga yanzu bata bashi har abada....." Gaba 'daya a kunnen Marwa yy wa'dannan maganganun, kuka take sosai tunda maganganun Rayyan suka fara shiga kunnen ta amma da jin furucin sa na karshe sai ta kasa rike kukan ta. Hannu ta sa aka ta zube bisa gwiwoyin ta dasa wani uban ihu tamkar wacce akace mata Ammi ta rasu. Abinda ya jawo hankalin su gaba 'daya ya tattara kanta kenan hatta Ammi da ita ma take cikin tsananin zulumi. Duk kuwa yadda suka so jawo hankalin ta da kwantar mata hankali akan ta nutsu tayi shiru ta fahimci maganar da ake abin ya faskara gaba 'daya Marwa ta birkice. Fa'di take " Sharri akayi wa Yah Sultan..shi ba haka yake ba..wlh Yayah ba haka halin Yah Sultan yake ba dan Allah kasa a fito min da shi...Yayah meyasa zaka mayar da 'kanin ka tamkar abokin gaban ka..? yayah meyasa meyasa ka biyewa makiyan sa suka tsara maka duk wannan sharrin dan kawai a kawar da shi agaban ka? Yayah meyasa zaka raba mana auren mu batare da ka tambayi.ra'ayi na ba? Ammi ni dai wlh ina son shi dan Allah kice a dawo mana da shi gida...Yah Sultan yana da tausayi, kuma yana kaunar mu bazai iya cutar da mu dai dai da rana guda ba, taya za'ace shi ne sanadin mutuwar su Abbah ?...Safaa na accident sukayi ka manta ne Yayah....?dan Allah kar ka biye musu ku cutar da bawan Allah maraya dan kawai bayi da kowa..." Tsaye Rayyan ya mi'ke yama kasa furta komai ga Marwa, banda idanun sa da suka sake rage girma, ji yake tamkar ya make ta, ji yake wani tukukin bakin ciki na mamayar zuciyar sa. Wato ita Marwa soyayya ce kawai agaban ta shiyasa bata fahimtar komai a dai- dai. 'Dan 'karamin tsaki ya ja kawai ya juya yayi hanyar waje da niyyar barin musu gidan gaba 'daya. A hanyar fita ya ci karo da Zaitoon da 'diyar ta da kwanan ta 'daya kenan da dawowa gidan dama can take gidan Anty. Ruwan zafi take so ta duba a kitchen ta ha'da mata tea dan rigima Mufeeda wai ita zata sha. Duk yadda yake ji ransa babu da'di amma ganin yarinyar sai ya 'dan ji natsuwa ka'dan ta shige shi. Kuma rabon shi da ita har ya mance dan tunda ya fara wannan hidindimun kotun bai 'kara sata a idanun sa ba. Ganin ya tsaya yana kallon Mufee yasa Zaitoon wucewar ta ciki..Mufeeda na shirin bin bayan ta da wata kalar muryar da shi kansa bai san yaushe ta taho masa ba ya kira sunan" Mufeeda.."? A hankali, sautin murya ce mai nuna zallar 'kauna ta zahiri. Yadda Zaitoon ta tsaya cak haka Mufeeda ma ta tsaya tamkar an basu umarni. Ita kam Mufee hadda waigowa sakamakon sunan ta da ya ambata. Hannu ya bu'de yana mai tsugunawa a inda yake. Mufeeda ko motsi bata yi ba balle ta nuna alamun zata je wajen shi sai ma kallon mamaki da take bin sa da shi. Salmerh🥰 [24/8/2023, 4:36 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕         *( 'Yata ce)* *Wattpad@* _Serlmerh-md_ 🅿️ *...98*                ......Zaitoon dai bata waigo ba har yanzun kamar yadda bata 'daga 'kafa ta cigaba da tafiya ba. Lura da Rayyan yayi Mufee bazata zo wajen shi ba yasa ya ciro wayar sa sakamakon yawan hotunan su da yake gani da Marwa a status yasa wannan dabarar saurin fa'do masa. Camera ya shiga ya nuno mata fuskar wayar ai kuwa tana ganin hakan tatafi da gudu wajen sa tana washe baki. Murmushi ne shima ya wadaci ilahirin fuskar sa, batare da 6ata lkc ba kuwa ya 'dauke abar sa cak yayi gaba da ita. Duk wani yanayi na bakin ciki da yake ciki neman su yayi ya rasa sakamakon kasancewa tare da gudan jinin sa da yayi...wata ni'imtacciyar fara'a da yanayi na annashuwa ne suka maye gurbin yanayin sa na baya. Shirun da Zaitoon taji yasa ta waigowa da sauri nan taga wayam, babu Mufee babu Rayyan, alamar wanzuwar ta wajen ma bata gansa ba, take ta ha'de gira, sake fitowa tayi sosai ta le'ka gefe da gefe amma babu su gabas da yamma ta kalla bata gansu ba. Haushi taji ya kama ta amma matakin sa bai kai ba yadda take jin haushin sa abaya ba. Haushin ta fitowar da Mufee ta sa tayi ta kuma 'dauki 'kafa ta bisa. Itama cike da jin haushin ta koma 'daki sai kuma ta kasa zama...sarai tasan bazai cutar da yarinyar ba amma sam har a zuciar ta ta kasa jin nutsuwa. Window ta tafi tana hango waje...direct wajen parking windown ta ke hangowa, hakan ya sa ta 'kurawa wajen idanu ko kyaftawa ba bisa ka'ida take yin sa ba. Sai dai ko alamun gifatwan mutum kamar sa ma bata gani ba. Rayyan kam 6angaren sa ya tafi da Mufee haka kawai sai yake jin sanyi aran sa, wani farin ciki yake ji na taso masa marar misaltuwa, yana kuma 'kara godewa Allah da bai bawa Sultan nasarar kawar masa da ita a dunia ba har ya bashi sa'an gano matsayin sa gare ta. Youtube ya shiga ya sanya mata Nursery Rhymes a wayar sa nan ya fara ganin dariyar ta sosai tana nuna su kamar ta san su dama can. Rayyan zama kawai yy yana kallon ta kamar hoto, wai wannan halittar tashi ce...gudan jinin sa ce da gasken gaske..? Ji yake tamkar cikin mafarki. Wani murmushi ne mai kayatarwa ya kwace masa. Bai ma san lokacin da bakin sa ya bu'de ba. A hankali ya furta. " Nagode Nadia, ubangiji Allah ya gafarta mk, Allah yayi miki rahama ya saki cikin bayin sa muminai..." Kallon da yaga Mufee tayi masa ne yasa ya fahimci a fili yy maganar. Murmushin sa ne ya 'kara fa'da'da, da duk hannuwan sa biyu ya kama kuncin ta..." Bazan ta6a gajia da gode ma Allah ba Mamana, bazan kuma ta6a gajia da sanyawa mahaifiyar ki albarka ba na kyautar ki da ta barmin kafin barin ta dunia....daga yanzu har zuwa girman zanci gaba ne da jaddada miki cewar kiyi tasbihi ga mahalicci, ki gode masa ki kuma dawwama kinawa mahaifan ki biyu addu'a da ya azurta ki dasu, masu kaunar ki masu sadaukar da komai domin kiyi farin ciki kiyi walwala..."! Ba fahimtan komai tayi ba amma yadda taga yana murmushi itama sai ta murmusa har gefen kumatun ta na lotsawa...a hankali ta mayar da idanun ta kan abinda take kallo. Rayyan tashi yayi tsaye sannan ya sa hannun sa daya bisa kanta, cike da 'kauna ya shafa kan sannan ya shiga ciki da niyyan yin wanka, har kuwa ya gama ya fito Mufee na nan tana kallon wayar bata nuna alamun gajia ba. Murmushi ne ya kubce masa saman fuskar sa...kusa da ita ya matsa yana mi'ka mata hannu yace..." Precious how far..?" Kallon hannun tayi, sai kuma ta kalli fuskar shi. Kamar an tsikare ta sai ta ajiye wayar tana 'ko'karin sau'kowa bisa gadon da ya ajiye ta. " Tea.." tace tana duban sa. Ido ya waro domin bai fahimci abinda take fa'di ba. " Mammi..tea.."! Ta sake fa'da tana 'ko'karin neman hanyar waje tana dame fuska. Hakan da ya gani ya sashi fahimtar abinda take nufi Zaitoon take so. " Ok..ok bari in sa kaya sai in mi'ka ki ko  Precious 'dina...?" Yayi maganar da dukkan kulawa. Da sauri ya je ga kayan sa ya shirya batare da ko mai ya tsaya shafawa ba ya sake fitowa...kafin fitowar sa kuwa tuni 'kwalla sun gama wanke mata fuska sai dai bata fidda sautin kukan a fili ba sbd shakkan sa da take ji. *****          Kururuwa da hayaniyan kukan Marwa ne ya tado Raihana daga 'dan baccin da ta samu a sace ta bada jimawa ba. Idanun ta jajajir ta fito tana yatsina fuska, nan Babban parlor ta ci karo da ma'aikatan gidan su biyu sun yi cirko- cirko motsin kirki basa yi sbd tsoro da fargaban abinda ya samu Marwa take irin wannan kukan sbd ita din mutuniyar su ce. Ilahirin gidan sautin kukan ta ne ya cika shi. Ita kanta Raihana ji tayi hankalin ta ya shi da gudu ta nufi saman Ammin tana jin zuciyar ta na cika da fargaba. Tana zuwa tambaya ta fara jera musu..." Ammi lafia? Me ya faru, me ya samu Marwan ne...?" A takaice Ammi ta dan labarta mata cewa ita da Rayyan ne kuma akan Sultan ne amma ta kasa fahimtar su tun 'dazu take kuka tama kasa natsuwa ta ji abinda ke faruwa. Raihana bata san lkcn da ta sau'ke mata mari lafiyayye ba a zuciye, cike da ba'kin rai tace..." Akan wancan 'dan iskan yaron kk wannan haukan Marwa...? Hala bakiji cewa da akayi shine makashin 'yar uwar ki Safaa ba..? Batare da tausayi ba ya kashe mana Zamrud ya kuma kashe mana Yah Kabir da Abban mu..bayan cin amanar da yayi ta mana a 6oye duk kin manta?..akan sa kike wannan haukan kukan kuma Marwa...?" Baya taja tana mai dafe kuncin ta tace" Anty ai babu wanda ya tabbatar cewa shi Sultan din ne ko wani daban..kawai dan an tsane shi sai ace shine...". Hannu Raihana ta sake 'dagawa zata zabga mata wani marin Ammi ta ce" Kulll..Raihan.."! Tare da shiga tsakanin su. Tsaki Raihana taja cike da masifa da kumfar baki tace" Waye ya tsane shin..? Marwa anya kina cikin hankalin ki kuwa..? Wai Sultan dai Sultan dai...? akan Sultan kk so ki nuna mana wace ko? Toh ga hanya nan..sai kije can wajen Amra ki amso muku 'dan ku Arfan da ke wajen ta ki tattara ki bishi gidan prison din ku rayu acan da yaron ku tun da ke soyayya ta riga ta rufe miki idanu baki ji baki gani..." Daga haka taja tsaki ta juya ta fita ranta a matu'kar 6ace. A hanya suka ci karo da Rayyan da ya taho da Mufee bisa kafa'dar sa sun yi kyau gwanin birgewa. Kallo 'daya da yy mata ya fahimci ranta 6ace yake bai kuma san menene ba sai dai ya 'dan zargi ko itama ta goyo bayan Marwa ne tunda yaga ko kallon arziki bai samu daga wajen ta ba. Ita yy niyyan bawa Mufee amma ya fasa sai da ya wuce ma kafin yace" ki turo min mamin Mufee...." Inda yayi maganar yana hayewa saman Ammin shima. Tuni ma'aikatan sun koma bakin aikin su tun bayan fitowan Raihana. Dan haka tasan da ita yake ba da wasu ba, bada son ranta ba ta wuce 'dakin Zaitoon 'din dan sanar da ita sakon Rayyan. A 'kofa ma suka ci karo da ita, niyyar ta dama taje ta duba Marwa ne tun 'dazun bata ji motsin ta. " Yayah na 'kiran ki...."! Haka kawai Raihana ta fa'da sai ta juya ta wuce abinta. Tsam Zaitoon tayi tana tunanin dalilin da zai sa ya kira tan..sai kuma ta tuna ai 'diyar ta na tare da shi..babu mamaki bacci tayi yake so a 'dauko yarinyar shine ya kira Raihana a waya. Wannan duk zuciyar ta ne ya raya mata hakan ba dan tana da tabbas kai ba, amma dari bisa dari zuciyar ta tayu na'am da batun. Ji tayi badan tana son 'dauko abarta ba da bb abinda zai sata zuwa. Bada son ran ta ta fito ta nufi 6angaren na sa ba. Tunanin ta kawai ne ya bata har yanzu suna can tunda duk iya da'dewar da tayi bakin window bata ga fitan su ba. Sai dai tana sa 'kafa a parlon nasa ta fahimci manufar 'kiran da akai mata...dan babu laifi 6angaren yy 'kura...a tunanin ta dalilin kiran kenan..domin rabon ta da 6angaren har ta mance. Ba wai wani 'kura ne na har azo a gani ba, amma a yanayin da tasan yake tafi da rayuwar sa tasan dole  zaiga muhallin nasa tamkar dattin dunia aka tara masa. Bata wani jira ko neman inda suke ba kawai ta fara aikin ta tana yi tana tura baki cike da jin haushi...( Ni kuwa nace kede kk sa kanki 'yan mata...). Rayyan kuwa ko da ya hau saman Ammin Marwa ka'dai ya tarar dukun'kune tana ajiyar zucian kukan da tasha. Yayi tsayuwan kusan mintina uku batare da ya furta komai ko kuma motsin kirki ba. Duban Marwa kawai yake yana jin tausayin er kanwar tasa na ratsa shi. Bai san cewa har haka take so da 'kaunar Sultan ba sai yanzu, ya kuma gama fahimtar ko a zaman auren su zama ne sukai na triangular ita kadai ke son shi shi hankalin sa na wani waje can daban. Sai yanzu ma ya fara tunanin tabbas akwai wata manufa game da zaman auren Sultan da Marwa ba sbd Allah ya nemi auren ta yake kuma zama da ita ba. Tausayin ta ne ya kama shi sosai, yana son sistern sa yana kuma tausaya mata..hakika so masifa ne. Mufee ma Marwa ta 'kurawa idanu sbd 'kanta na 6oye cikin 'kafafun ta da farko bata gane wace bace. Sai daga baya ta fahimci Marwa ce. Nuna ta tayi da yatsa ta dubi fuskar Rayyan tace..." Anty..."! Tana mai nuna masa ita. 'Yar murmushi yayi kawai ya juya ya koma 'kasa bai tsaya ba kawai ya sake komawa 6angaren sa ganin bai ga Zaitoon din ba sai yy tunanin ko batanan ne ko kuma wani uzuri daban ko kuma halin ne ya motsa, cikin ukun dole yasan daya, hakan yasa ya yanke shawarar komawa da yarinyar 6angaren sa idan ya gama shiryawa sai su fita tare dan shi kansa yana bu'katan hutu, ko kuma kawai ya mi'ka ta gidan Anty Madeena...tunda bai ga alamun akwai mai cikakkiyar natsuwa cikin gidan ba a wannan rana. Yana shiga yaga yanayin iskan 6angaren ma ya canza banda tsab da ya ga ko'ina a parlon yayi. Dube- dube ya fara dan gano wanda ya aikata hakan bai ga kowa ba..a hankali ya fara takawa har ya kai rabin parlon sai yaji motsi daga bayan sa. Yana shirin juyawa sai yaji Mufee tace" Mammiii..."! Cike da farin ciki cikin sautin muryar ta. Waigowa yayi da sauri, nan yaci karo da ita, daga kitchen ta fito hannun ta rike da roba da mopping stick. Yadda Mufee ke zillo a hannun sa ya sa ya sau'ke ta da gudu kuwa ta 'karasa wajen Zaitoon dama gatanan ne tamkar a takure tun dazun bata saki jikin ta da shi ba, shi kuma a dole me 'diya 'karfi da yaji yake 'kokarin janta a jiki. Dan ma yanzu ba kamar baya ba, bata gudun sa sai dai akwai rashin sabo. Zaitoon rungume abarta tayi tana mai dur'kusawa gaban yarinyar ko sake kallon inda yake ma bata yi ba. Murmushi kawai yayi har ya juya zai shiga 'dakin sa sai yaji abin da Zaitoon ke tambayar yarinyar. Domin hannu ta kai cikin rigar ta ta shafo cikin ta...a hankali tace" _Kin sha Tea din...?"_ Yaso yaji amsar da Mufeeda zata bayar amma bai ji ba sbd da kai ta amsa ta. Kuncin ta Zaitoon ta kamo duka biyu har sautin muryar ta na canzawa dan bata ji da'di ba har ranta. " Ai ke 'din ce mama na, son yawo ne da ke, kinsan Tea kk ce min zaki sha har na fito dan ha'da mk tea din kuma sai ki kama ki bi wani mutum can daban alhali ba lalle ne ya fahimci abinda kk so ba.. yanzu gashi kin zauna da yunwa tun 'dazun abanza..." Cak ya tsaya..batare da ya waigo ba. " _So...wani mutum can daban!...nd she means me..._ " Wani murmushin mugunta ne ya 'kwace masa, har ya 'daga 'kafa zai cigaba da tafia sai kuma ya juya ya dawo baya. Tuno wani abu ya sa ya sake juyawa ya shiga 'dakin sa ya fito rike da makullai a hannun sa. Lokacin da ya fito rungume ya tarar da Zaitoon da Mufee...Mufeeda na fa'din"..Mammi...Anty..." Shi dai ba wani fahimtar maganar yarinyar sosai yake ba amma yaji Zaitoon na cewa" Tana can bari in gama aikin nan sai in kaiki wajen ta...". Gaba ya wuce yana sake fa'da'da murmushin sa. Fita yy ya rufe 'kofan ta waje ya shige motar sa yy gaba...da yake yasan kitchen 'din sa bayi da kofa ta waje dama 'kofan palor ne ka'dai mafitar 6angaren kuma ita ya rufe. Hankalin sa kwance ya ja motar sa ya fice ya bar gidan zuwa can gidan sa na asali. Zaitoon bata san me ya aikata ba sai da ta gama gyara ko'ina har 'dakin sa da da 'dayan 'dakin ta tsabtace su sbd ta riga ta saba yanzu 6angaren ba bakon ta bane takan iya shiga ko'ina illa 'dakin Amra ka'dai. Kalmar ta ke faman yi masa yawo aka, yana kuma soya masa zucia, _wani mutum can daban..._ har wani 'daci- 'daci yake ji sbd takaici. _Zanyi maganin yarinyar_ .... sai yy 'kwafa...yayi hakan yafi sau shurin masaki. Sam bai san yaushe Zaitoon zata daina raina shi ba, yarinyar Bata girmama shi sam sam...har sai yaushe zata daina yi masa wasu abubuwan tamkar shi 'din matsayin tsaranta yake ne. Kwata- kwata bai yi niyyan komawa ba, ada niyyar sa sai ta yini ta kwana a 6angaren ita kadai amma tuno Mufeeda dake tare da ita da kuma abinda take so ya sa shi jin bazai iya ba. Amma dole ne sai yy maganin Zaitoon hankalin sa zai fi kwanciya...haka ya ayyana sannan ya jinjina kansa cike da gamsuwa. Bai da'de ba ya sake dawowa gidan hannun sa rike da babban leda ya bu'de ya shigo. Zaitoon dake zaune a palor Mufee kwance ajikin ta ta rungume ta sosai. Ko dago idanu bata yi ba balle ta damu da sanin wanda ya shigo dan tasan shine bayan tsinkayar sautin sallamar sa ciki- ciki tamkar dole aka sanya shi. Zuciyar ta cike take da haushin rashin samun 'kofa a bu'de da batayi ba..ta kuma san shine kuma da gayya yy, hakan yasa ko kallon inda yake bata yi ba balle ta nuna alamun tasan da shigowar sa. Babban abinda ya 'kara zafafa takaicin ta shine duba 6angaren da tayi bata kuma ga ko alamar kayan tea ba kuma yasan Mufee nason sha ya kuma san bai da shi anan amma duk da hkn ya rufe su yy gaba abinsa batare da ko tausayi ba acewar ta. Mufeeda kuwa da yunwa ya isheta ta da 'kananun kuka tayi bacci. Shima Rayyan din bai iya ya mata duba sau biyu ba ya dauke kansa, amma yanajin dole fa sai ya tabbatar mata da cewa shi din fa ba wani mutumi can na daban bane kamar yadda take fa'da...dole ne sai ya koya mata hankali. Yana gab da shigewa batare da ya dakata da tafiyar ba yace ki ha'da mata tea 'din ta sha. Ko 'kala bata ce masa ba sai 'dan 'karamin tsaki da taja ta 'karashe da hararar ledan da ya ijiye can nesa da ita. Cikin ranta ta ayyana ashe ma ya san me yarinyar ke so shine dan mugunta zai wani kulle mu yy tafiyar sa. Wannan wani irin zalunci ne. Sai da ta tabbatar ya wuce ciki kafin tabi bayan sa da harara tana mai gyara zaman Mufee a jikin ta hadda yin 'kwafa tamkar wata 'ka'k'karfa. Ji take ayau da ace ita wata aba ce ko kuma sama take da shi da bb abinda zai hana ta zane shi tass da tsumagiya. A zuciye ta tashi ta nufi hanyar fita sai dai ga mamakin 'ta still kofan a rufe take zaton ta ya bu'de ne. Yadda ta zauna cike da jin haushi bayan barowar ta wajen 'kofan har sai da tasa Mufee motsawa, tana motsawa kuwa ta bude idanu ta 'dora akan rigimar da take kafin tayicbaccin. Dole badan taso ba ta tashi ta shiga kitchen ta 'dauko cup da spoon ta je wajen ledar da ya kawo 'din ta fiffito da shi. Sosai kayan cikin ledan suka bata mamaki suka kuma 'dauki hankalin ta, domin duk kayan cima ce ta yara, sai manyan kayan tea zuma da sauran su. Baki ta kya6e irin basu wani birge ta din nan ba amma har cikin ranta taji da'di bayan fahimtar duk sbd Mufeeda ya kawo. Tea 'din kawai ta ha'da mata sai ta ciro mata wani crackers da ita kanta sai da ya shiga ranta. Amma ta basar kawai ta sanya Mufeeda a gaba tana bata a baki. Da shigan sa bai da'de ba yaji wayar Ammin sa, ko da ya 'dauka tambayar sa tayi akan su Zaitoon dan taji shiru kuma Raihana ta sanar da ita akan cewa yayi cikiyar ta 'dazu kuma yana tare da Mufeeda..toh in ba fita suka yi ba ya turo mata su. " Ammi munje can gidan ne amma anjima ka'dan zamu dawo..." Ya bata amsa yana mai sakala wayar tsakanin kafa'dar sa da kunnen sa yana kuma kokarin cire safar 'kafar sa a lkc guda. " Can gidan kamar ya kenan? Su me zasu yi mk mk acan gidan Rayyan?" Ammi ta tambaya cikin rashin jin dadi. " Bakomai Ammi" Ya bata amsa a takaice yana lumshe idanu. Yanayin Ammi sake zafafa yayi. " Hk ake yi fisabilillahi...without informing me or ur sisters kawai sai ka 'dauke min yara zuwa can wani wuri daban...". Da sauri kuma da mmk yace " Haba Ammi!..nine fa! Kuma gida na nace ba wani waje ba daban ba...." " Bana so toh...ka dawo min da su right now". Daga hk ta kashe wayar tana sakin 'karamin tsaki. Shi kansa mamakin Ammin sai ya kama shi. Ca yake wa'dannan bayin Allahn dai a halin yanzu bb wanda ya isa ya kaisa iko da su kuma yana da daman fita da su zuwa duk inda yaso batare da an tuhume shi dalili ko ba'asi ba. Wayar ya ciro ya bita da idanu tamkar zai ga Ammin a ciki. Nan take Anty Madeena ta fa'do ransa bai bata lkc ba kuwa ya danna 'kiran ta. Ko gaisawa basuyi ba ya fara isar da abinda yasa yy kiran ransa a'dan 6ace. " Anty wai me ke damun Ammi ne ?" " Kamar Yaya meke damun ta, me kuwa zai dame ta banda damuwar halin da gidan ta ke ciki..ko wani abin ya faru ne?" " Kusan haka Anty.. shikenan ni ta ko ina ban isa nayi iko da 'diya ta ko matata ba sai an nuna min ni ba komai bane akan su...?Ita kanta yarinyar nan ta gama raina ni Anty kuma duk Ammi ce ke goye mata baya..." " Wace matar kk nufi ne na kasa ganewa..ca nake Amra dai na gidan su, me ze ha'da Ammin ka da lamarin ta a halin yanzu...? A kufule yace " Anty yarinyar nan fa...!..wai..wai..." sai kuma ya rasa me ze fa'di..." ni dai Anty dan Allah ki sa baki Ammi ta barni in sha iska, yadda take nuna musu shiyasa yarinyar nan duk tabi ta raina ni.." " Har yanzu bangane wace yarinyar kk magana ba malam..." " Wancan yarinyar...Mamin Mufeeda..."! " Toh dan me zata raina ka?..hala dai wani abin kayi mata". Shiru kawai yy yama rasa meze ce da Antyn. Shi dai yasan bb abinda yai mata ya kuma kasa gane manufar Ammi, dan tun ba yau ba ya fahimcicta bata so taga ta da'de inda yake. 'Kin fitowa yayi yama yi kwanciyar sa dan a har yanzun hutu bai ishe sa ba ga 'karin takaicin da ya kwasa daga dukkan 6angarorin uku. Marwa kuwa da 'kyar ta lallashi zuciyar ta tayi shiru amma ta kasa ji aranta cewa Sultan mai laifi ne dagaske kamar yadda ake fa'da. Sosai kuma ta ke so ta ganshi, tana matu'kar bu'katan ha'duwa da shi kuma aranta take ji dole sai tayi hakan kafin zata samu natsuwa.. 'karshe 'dakin ta ta koma ta kwanta tana tunanin abubuwa da dama da suka shu'de. Can 'kasan zuciyar ta take mamakin ina Zaitoon ta shige, dan tunda aka fara maganan bata go gilmawan ta ba..ba ita bb Mufee. Bayan kamar sa'a 'daya Ammi sai ta sake 'kiran sa a waya, har bacci ma ya fara 'daukan sa dan haka cike da jin haushi ya fito jikin sa ko kayan kirki babu kuma ko ta kan hakan bai bi ba sbd haushi. Zaitoon dake nan kan Dinning da Mufeeda har a lkcn da sauri ta rintse idanu tana ha'de gira...tacwani yamutse fuska. " Kai Subhanallahi...wannan wani irin rashin kunya ne haka...?" Ta fa'da a zuciyar ta not knowing that a fili tayi maganar... Cak ya tsaya sannan ya waigo ya 'kare mata kallon da tashi daya ya fahimci manufar rufe idanun da tayi, this girl is always trying me...amma wallahi zan koya mata hankali...bata san waye Rayyan bane... Jikin sa ya sake bi da kallo yaga dai bb laifi kayan wandon sa three quarter sai rigar sa armless bai ga wani aibu ga hakan ba. 'Kofan ya bu'de sannan ya dawo kusa da ita ya tsaya, facing her gaba 'daya amma bai ce komai ba. Jin shiru ya sa ta ta 'dan bu'de idanun da ganin sa kusa da ita sai ta sake rintsewa da karfi...har tana fa'din wayyo Allah..a'uzu billahi minash shaidanirrajeem.....". " Ji!...kin raina ni ko...?" Yace a dake. Da sauri ta girgiza kanta. " Nine shi'dan ni ne maras kunya ko?" Da sauri ta girgiza kanta. " To ke kunyar gareki?...ko ko sai yau ne kk san da cewa idan kk ganni a haka rasar kunya ce? " Sake rintse idanu tayi da 'karfi dan ji take tamkar akwai kafa da ta rage bata rufe sa ba. " Waiyo Allah..".tace a ranta dan ta gama fahimtar manufar sa. " Sa'an ki ne ni ko..?..shiyasa kk raina ni.. " Sake girgiza kai tayi tana mai toshe fuskar da hannun ta duk biyu. Da rawar murya tace " Ni..wlh ba raina..ka nayi ba, gani nayi bb kyau mutum ya rinka yawo bb kayan kirki a jikin sa gaban mutane....." " Zan yi maganin ki...zaki ga rashin kyau kuwa ganin idanun ki yarinya..." Ya fa'da a zuciyar sa. A fili kuwa cewa yayi"  Ammi na neman ku.." Da sauri ta bu'de idanu da jin hk...da ganin bai matsa ba kuma sai ta sake rufewa nan take. Har daria take bashi yarinyar nan ta 'kware a pretending a cewar sa, lkcn da yake kwance bayi da lfy meyasa bata ji kunyar ganin sa ba sai yanzun dan rainin hankali. 'Yar 'karamin tsaki ya saki yana mai wucewa dakin sa, 'kasa yayi da idanun sa zuwa jikin sa, in ba iyayi da raina shi da tayi ba, menene abin jin kunya cikin shigar sa? wando three quarter ne zata ce ba kayan kirki ba ko kuwa rigar? a hakan yaso ko sallah zai iya yi batare da fargaban komai ba... toh in kuwa har zai iya yin sallah da wannan shigar why not ya iya fitowa cikin iyalan sa a hakan. Jin Ammi ke neman su ya sa da rawan jiki ta mi'ke bayan shigewar sa, 'diyar ta 'dauka sannan ta nufi 'kofa a sukwane gudun kar ya sake hana su fita. Bayan fitar su da kamar mintina sha biyar sannan ya sake fitowa. Madadin three quarter trouser din yanzu long trouser ne jikin sa sai dai bai canza rigar ba...nan kuwa yaci karo da ledan kayan da ya kawo wa Mufeeda Zaitoon bata 'dauka ba. A zuciye ya fizgi ledan ya fice da shi. Nan ya sami Ammi a parlon 'kasa, ita ka'dai tana shan fruits hankali kwance. Yasan dama ba lallai ne yaga Marwa ba, Raihana ma tun asali yasan halin ta da son ke6ancewa ba'a fiye zaman hira da ita ba balle wani abu ya gifta kuma ai sai a hnkl. " Barka da hutawa Ammi..." Yace yana 'dan rankwafawa. " Barka dai" tace tana mai mayar da hankalin ta gare shi. " Ya akayi...?" Tace tana duban sa. " Ko a kawo maka abinci. " A a Ammi". Ya bata amsa yana zama gefe ka'dan da ita. " Kamar ranka a 6ace?" Kai ya girgiza mata. Ta sake fa'din " Ko batun Marwan ne?" Sai ya yi shiru yana duban ta...Ammi kam cigaba da shan fruits 'din tayi tana fadin" Ai ta yi shiru, tana 'dakin ta, kasan dole ne abin sai ya dame ta tunda bata ta6a zaton faruwar hkn ba, abin yy mata bazata ne...kuma yarinya ce sai an bi ta a hankali....sai dai ko ni batun takaddar sakin da kayi saurin amsar matan banji da'din sa ba, sai naga kamar anyi gaggawa da yawa, da an bari zuwa wani lkcn daban..." " Me kuma za'a sake jira ne Ammi? bb fa'idar hkn sam, tunda na gano wanene Sultan bani da wani burin da ya wuce in ga na raba shi da duk ahali na sbd ba'kar zuciyar dake tare da shi, ban san wa yake hari bayan ni ba, ina tsoron ta'sar da zata bayyana bazata a lkcn da bani da ikon dakatar da komai...itama Marwa abata hkr dama shi aure rai gare shi, toh wannan dai kam ya mutu..kuma har abada bana fata, kamar yadda ko da bayan raina ban amince a sake tayar da wannan auren ba...". " Allah dai ya tabbatar mana da alkhairi ya raba mu da mugun ji da mugun gani...". " Ameen Ammi" Yace ata'kaice sai kuma ya mayar da duban sa kan ledar dake gaban sa. Zama ya gyara yana mai ciro wayar sa yake tambayar Ammi ina yarinyar nan tayi ne?" " Wace kenan". " Zaitoon"! Ya bata amsa batare da ya dubi Ammin ba. 'Dan jim tayi tana kallon da son karantar manufa da yanayin sa. Kaf kuma abinda take so 'din ta karanta tsaf. Kawar da idanu tayi daga kansa sannan tace" Me kuma ya sake faruwa ba yanzun suka shigo daga wajen ka ba...?" " Kayan su zan basu...". " Ohh..toh barshi anan zan sa a mi'ka musu...". Jin amsar Ammi ya sa shi 'dagowa ya dube ta...." Ammi wai shikenan ni bani da iko da ganin iyalai na a gidan nan, sai kace baki san waye ni ba...kuma fa hakan da kk yi yasa yarinyar nan duk tabi ta gama raina ni wlh Ammi...". Ya 'karashe maganar da rage sautin muryar sa...bai san ma ya akayi ya furta hkn ga Ammin nasa. Kalamai biyu zuwa uku cikin maganar tasa ne yasa shi jin wani iri. Ita kanta Ammi lafazin nasa ya bata mamaki. Da wannan yanayin kuma ta dube shi..dai dai yana kawar da kansa cike basarwa as in baiji dadin abinda Ammin tayi masa ba...sai dai can kasan ransa nauyin mahaifiyar tasa yaji sosai. Wani matashin numfashi ta fidda tana mai kawar da idanun ta daga kallon mamakin da tayi masa. " Yi hakuri toh sarkin san girma..kuma daga yau kar ka sake 'daukan min yara zuwa wani wuri batare da sani na ba...". Mai aikin ta 'daya ta 'kwalawa 'kira ko da tazo bowl 'din dake hannun ta ta mi'ka mata tana fa'din kira min " Zaitoon dan Allah...". Da fitan mai aikin Ammi ta cigaba. " In batun raini ne kuma ai koma me tayi maka kaine da kanka kaja...sai ka koma ta tuhumi kanka bani ba Rayyan...". Juyowa yy ya dubi Ammin cike da mamakin kalaman ta...taya kenan za'a ce shi yaja...ta wacce hanya, me yk yi me ya aikata? Ya kasa bawa kansa amsa. Gashi Ammi bata sake furta komai ba ba ma alamun zata furta 'din. Ba ada'de ba sai gata ta fito. Mufeeda tafe abayan ta hannun ta ri'ke da teddyn wasanta baby pink mai kyau da shi. Kusa da Ammi taje ta zauna daga 'kasa tana mai sake yi mata barka da hutawa.. ta sannan ta 'dora da fa'din bani ke 'kiran ki ba Zaitoon..dahauta nuna shi batare da ta dubi inda yake ba tace" Rayyan ne". Tamkar ba ma ya 'dakin haka yayi, kacokam 'din hankalin sa duk ya tattara wajen Mufee dake tahowa a hankali tana ha'de rai. Ita kanta Ammi hankalin ta naga yarinyar ne. Zaitoon kuwa kallon sa tayi sai ta kawar da kai kamar yadda taga yayi. Cikin ranta take mitar tamkar ba yanzun muka baro 6angaren sa ba inba fitina ba miye kuma yanzu...in 'diyar sa yake so ba sai yace akawo masa ita ba..ita kam menene nata kuma. " Ina yini yaya..." Tace da sanyin sauti duk da ba wai har cikin ranta taso gaishe shin ba amma rashin amsawar sa sai ya ba'kanta ranta sosai. Fuska ta yamutse tayi 'kasa da idanun ta tana wasa da en yatsun ta. Duk Ammi na lura da su amma bata tanka ba. Shi kam bai ma san tayi ba balle yasan 'karin laifin da ya aikata. Tana gama rufe baki kuma Ammi ta 'dora da fa'din." Hala wani abin kika yiwa Indolan nan naga tana ha'de rai.." Abinda ya hana jin haushin nata tasiri kenan itama ta dubi Mufeedan. Bata bawa Ammi amsa ba da yake ta riga tasan damuwar yarinyar...kawae sai tayi murmushi. Sai ya zama na baki 'dayan su dukkan hnkln su na gareta ne amma ita kuma duk bata su take ba hnkln ta na wajen Zaitoon kuma duk 'kira da maganar da Ammi ke mata bata ko nuna alamun taji ba balle tayi yun'kurin zuwa inda take. Jikin Zaitoon taje ta fa'da Zaitoon ta rungume abarta tana bubbuga bayan ta a hnkl alamar rarrashi. 'Yar daria Ammi tayi tana fa'din miskilar yarinya kawai..hala baki kaitaxwajen Antyn ta bane shiyasa.." Tsaye Rayyan ya mi'ke yana fa'din " Ammi zan shiga cikin gari sai na dawo". " A a zauna tukun ai bamu gama magana ba". Jin hkn yasa ya koma ya zauna 'din kamar yadda ta bu'kata. A zahiri ba hkn yaso ba, yaso ne ya kaucewa wani yanayi da yaji zuciyar sa na shirin bijiro masa da shi lokaci guda. Sam baya so ya biyewa zuciyar sa, hkn yasa yy tsam da ransa. Da kyar ya samu bugun numfashin sa ya daidaita duk dama yy sa'a bai 'dauki wani dogon lokaci ba... duban Zaitoon yayi yace" Ke kuma kayan da kk san na wanene bisa wani dalili zakictaho ki baro min su a can...?" Ledan ta kalla sannan ta 'dan cuna baki tana mai kawar da kan Mufeeda daga 6angaren ledan, domin tasan abinda takewa fushi akai 'din na cikin ledar...kuma dagangan ta baro shi. " Ai naga kayan za'ki ne duk, kuma ni ba so nk tana shan za'ki sosai ba shiyasa...". Wani ba'kin takaici ne ya taso masa bai san ma lkcn da ya banko mata wata uwar harara ba yana shirin magana Ammi tayi saurin 'daga masa hannu sannan ta dubi Zaitoon tace" Tashi 'dauki kayan kuje Zaitoon bana son gardama, ki duba ki za6i wanda yake 'dan dai dai sai ki bata...". Kamar yadda Ammin tace tayi suka fita itada da Mufee duk kuwa yadda Ammi taso yarinyar taje wajen ta ta 'kiya...hkn ma sai ya 'kara ba'kanta ran Rayyan..gani yake kamar koya mata kiyuya Zaitoon ke yi da gayya. Kwafa ya rin'ka saki yana me sar'kafe hannuwan sa. Bayan fitar su Ammi tana murmushi tace" Ayi hakuri dai mazaje...wannan fushin hk yy yawa.."! " Ammi kin dai ga abinda nk fa'da mk ko? wlh yarinyar nan ta gama raina ni a gidan nan...ko ba komai a sama nk da ita, sannan su'din iyalai na ne, ni ke da ikon siya ko 'kin abu idan nasan zai cutar da su ba wai itace zata rin'ka nuna min iyayi da gadara ba...". " Ni dai nasan Zaitoon bata da raini, kuma har abada bazata ta6a raina ka ba na sani, sai dai ko in wani abin kayi mata, sannan ba wai iyayi ko gadara take yi maka akan 'diyar ka ba dan na san me kake shirin fa'di, tana yi ne kawai dan kare lafiyar 'diyar ta.." " Ammi 'diyar ta fa kk ce..." " Yes..har abada Mufeeda wld surely remain her daughter ko da babu ranta a duniyar...batun iyalai kuma a side Pls...kasan akwai wani dogon tsauni da baka haura ba a gaban ka ko? Akwai wani matakin da dole sai mun haura shi, auren ka da yarinyar nan 'kaddararren abu ne da ya riga ya faru, kuma ya faru ne a dai dai ga6ar da baki 'dayan mu bamu zaci hakan ba, kuma bamu da daman hana sa sbd a lkcn yiwuwar sa muka fi bu'kata fiye da sa6anin hk, hatta ita dana tabbatar har ayanzun ba wai ta sanya shi akan ta bane balle ya dame ta bata da ikon hana kanta a lokacin.. nasani, sbd tausayi da kuma 'kaunar ta da son kyautata mana, ina kuma da ya'kini har ayanzu babu son auren a 6angaren ta, so dan Allah ka daina takura ta, ka daina 'kunatata mata sbd hkn na iya haifar da tsana mafi muni..kaucewa hakan kuwa sai an bi komai a tsanake kuma bisa tsari, ni kaina bazan so a takura ta ba gudun shiga hakkin ta, domin mun tauye ta abaya, tsawon rayuwar ta sadaukar da shi tayi agare mu, kayi tunani akai Rayyan, tun ha'duwar ta Mufeeda zuwa yau din nan menene guda daka tana yin sa sbd kawai jin da'din ta? Babu shi. dan haka abari har sai mun tabbatar ta amince mun kuma samo yaddar iyayen ta akan auren kafin muyi tutiya da shi, wanda Insha Allah ina kyautata zaton kwanan nan zamu je gare su da yaddar Allah, kuma idan basu amince mata zama damu ko kuma batun auren ba Rayyan dole ne mu bar mu su 'diyar su, haka itama idan bata amince da sake zama da mu ba dole ne mu barta tare da iyayen ta ma'ana zaka sawwa'ke mata ta zauna tare da mahaifan ta, yarinyar nan tayi mana 'ko'kari sosai, ta tauye kanta da iyayen ta sbd 'diyar ka, yarinyar da bata ta6a sanin wace ita ko tabbaci akan asalin ta ba, ta tauye farin cikin ta ta sadaukar da duk  lokuta mafi muhimmanci gare ta sbd Mufeeda, ta bautu iya bautuwa sbd kai kanka Rayyan...a lckn da kafi bu'katar taimakon wani makusanci naka, a lkcn da duk ma'kiyan ka zasu fi saurin samun kusanci da galaba akanka sbd baka san inda hankalin ka yake b amma ta kula da kai tsakanin ta Allah...sau da dama idan na zauna Rayyan rasa me zan yiwa yarinyar nan nake dan nuna mata godia da yabawa bisa abubuwan da tayi mana, kaga kuwa bazan so asake ce sbd son zuciyar mu mu takura ta akan abinda bata da ra'ayi ba har abada, tamkar 'diyata ta ciki na nake ji d ganin ta, bazan so bakin ciki ko damuwar ta ba kamar yadda bana 'kaunar ganin ta su Marwa haka har abada bana fatan ganin 'kuncin yarinyar nan....dan haka kayi hakuri da komai har zuwa lkcn da zamu ga abinda Allah zai yi..a halin yanzu wannan aure da shi da babu kusan duk 'daya ne...kaima ka kalle shi a haka nan kawai, inda hali ma hatta ita Mufeeda a bar mata abarta tare da ita tukunna....". Jikin sa yy sanyi sosai..kuma yasan gaskiya Ammi ta fa'di, but still cikin maganganun akwai wa'danda suka ba haushi da kuma mamaki. Wannnan maganar ta Ammi yasa yama kasa fa'din komai. Shiru kawai yayi ya koma ya jingina bayan sa da jikin kujera yana duban Ammin da lumsassun idanun sa..daga 'karshe ya lumshe su gaba 'daya yana murza goshin sa. Ta wani fanni yasan gaskia ta fa'da, domin da kansa ma yasan yarinyar tayi 'ko'karin da takai ayaba mata da lambar yabo mafi daraja, amma bai san meyasa yake ji can 'kasan zuciyar sa tamkar maganar Ammin bai samu  muhallin kirki a ransa ba. Ammin ce still bayan shu'dewar wasu 'yan da'ki'kai ta cigaba da fadin" Sannan 'yar uwar ka Marwa tazo min da wani batu ko ince neman alfarma na kuma yarje mata...". Ta 'karashe maganar da 'dagowa ta dube shi sosai dan ganin yanayin sa. Ko dan yatsan sa bai motsa ba balle wani sassa na jikin sa hatta idanun sa na nan a lumshe bai bu'de ba ya dai dafe kansa da hannun da yake murza goshin da shi. Cigaba da magana Ammi tayi inda tace" Marwa ta ro'ke ni akan tana so dan Allah abarta taje taga Sultan ko da sau 'daya ne tak...". Da sauri ya bu'de idanun sa ya sau'ke su akan Ammi inda yake binta da duban mamaki. Tace " Yes na kuma amince mata..sbd wasu dalilai..." " Ammi Sultan kuma?...bacin bb auren me zata je tayi a wurin sa...?" " Rayyan kar ka manta fa Sultan shima 'dana ne, kuma har abada ahakan yake ko bayan bb ni, sannan miji yake ga Marwa miji kuma mafi soyuwa a zuciyar ta, kayi tunani wata nawa da rabuwar su? Wata nawa bata sashi a idanu ba? A lkcn da ya iso ya kamata ta ganshi a lkcn ta cikaro da shi cikin mummunan yanayin da har sai da yasa ta fice hayyacin ta, baka tunanin rashin sa wani irin gagarumin illah zai iya jawo mata indai har aka cigaba ahakan..ka barta taje, ko ba komai ma ai Sultan tamkar wanta ne kuma hannun ka bai ta6a ru6ewa ka yanke ka yarda...". Idanun ya sake lumshewa yana sakin huci mai zafi daga bakin sa. Bai ce komai ba kawai ya mi'ke tsaye gaban rigar sa yake gyarawa fuskar sa tamkar bai ta6a daria ba sam, dan yau maganganun Ammin duk babu wanda ya yi masa da'di har a ransa. Ganin yana niyyar fita batare da ya bata cikakkiyar amsa ba yasa tace" Ina magana bakace komai ba...zuwa yaushe zaku je..? Gira ya 'dage ya 'dan waigo" Ammi dani ne..?" " Yes...haka na tsara! duk lkcn da ka shirya sai ka kaita Zaitoon sai ta rakata.." "Hmm " kawai yace ya sa kai ya fita. Salmerh😘 [30/8/2023, 9:44 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Wattpad@* _Serlmerh-md_ 🅿️ *...99* .......Tunda Amra taji batun kotun nan hankalin ta ya kasa kwanciya, gaba 'daya ta nemi natsuwar ta ta rasa...tsoro da fargabar ta a kullum 'kara yawaita yake, kusan kullum da shi take kwana ta kuma tashi da shi...tsoron tonuwar sirrin ta da ta riga tayi amanna da cewa rufe ruf yake..... Dama tunda taji Anty Madeena ta ta6a fara yin maganar ta fara jin fargaba dan ta fahimci sirrin nata ya fara bayyana amma bayan haka bata kuma jin komai game da hakan ba, kwatsam sai kuma ga batun kotu. Ita kanta tasan Sultan mai laifi ne, amma shakkan da take ji a halin yanzu ta tabbata ko shi Sultan din bai kaita shiga firgici ba. Tsoro take ji sosai, ba na komai ba kuwa sai na ratsowar sunan ta ko yaron ta Arfan cikin kotu gaban alkali, gaban 'dimbin jama'ar da ita kanta bata san iyakar su..kuma a har yanzun babu wani makami guda da ta rike da tke tunanin zai iya fidda ta cikin zargi domin bata kawo tonuwar sirrin ta nan kusa ba. Sai yanzu ma take ganin wautar ta, gaba daya ta rainawa kanta da wayon ta a halin yanzu...wannan sanarwa da Ammi ta fito tayi sai take ji tamkar dan ita kawai aka yishi, domin a tara jama'ah a kuma bayyana sirrin ta gare su. Innalillahi kawai take fada. Baki 'daya wa'danda ke tare da Amra sai da suka fahimci sauyin yanayi da tsantsan damuwa da ta shiga. Tsoron makomar ta take a wajaje da dama..ba ga iyaye ba, ba ga al'umma ba, ba ga kotun ba, ba ga shi kanshi uwa uba Rayyan ba. Bayan yanke Ameera, layin Marwa tayi ta nema bata samu ba sbd wayar da ta sake 'din na 'dan bata matsala hakan yasa ba ko da yaushe ake samun ta ba..uwa uba yanayin da itama take ciki. Gidan Ammi Ameera ta fara zuwa kuma tun asali dama ita tana da 'dabi'ar fara zuwa sashen Ammi gaida ta kafin isa 6angaren Amra..tun ma lokacin Amra na gidan haka take. Ko yanzun ma kamar yadda ta saba haka tayi. Ammi na jin da'din wannan halayya Ameeran sosai, ta kuma ji dadin zuwan ta na yau 'din bisa na ko yaushe. Dan ko bb komai tana so taji motsin su Amra amma Rayyan ya hana kowa zuwa ko tuntu6ar su acewar sa ai da kanta ta tafi so shi bb ruwan sa. Anan ne Ameera ke sanin cikakken bayanin ai Amra na gida sun je hutu tuntuni inda Ammi ta sakaya maganar sbd fahimtar cewa Ameeran bata san komai ba. Bata sha wani wahalar zuwa gidan mahaifin Amran ba da yake ta sanshi, sunsha hira da Amra sosai anan take bata labarin duk abinda ta sani game da zaman kotun. Sai a lkcn hankalin Amra ya 'dan kwanta bayan fahimtar ai bb sunan ta a zaman kotun har akayi aka gama. Dan tana da tabbaci da ace akwai sunan ta da Ameera bazata 6oye mata komai ba. Da kanta take bawa Ameeran labari a ta'kaice na abinda ke faruwa da har yasa ta dawo gida sai dai bata fito fili ta fadi mata waye Arfan ba, ta dai ce 'yan uwan Rayyan da 'kannen sa ke neman raina mata hankali ita kuma bazata iya zama tana kallon su ba, ba ma zata iya zuva idanu ana ci mata fuska akaran banza ba, hakan yasa ta dawo gida a kwatan mata 'yancin ta. 'Yar murmushin gefen baki Ameera tayi sannan tace" ban ta6a sanin baki da wayo ko na sisin kobo ba sai yau Amra.." Idanu ta waro akan Ameera da alamun tambaya. Kai Ameera ta jinjina mata alamun tabbatarwa ta sake fadin tabbas Amra baki da wayo sam sam". " akan wasu can 'yan uwan mijin ki, bama shi ba fa Amra..'yan uwan sa kk ce amma sai ki ri'ka wasa da auren ki? Shin bake ce kk ce min sun yi masa wani auren da 'yar aikin ki ba...?" Shiru Amra tayi tana me tunanin yaushe ma ta fa'di wannan abin kunyar. Ameera ta cigaba" Toh wlh tun wuri ki shafa kanki ruwa ki yiwa kanki fa'da, bb inda ya kai mk 'dakin mijin ki, ke in takaice mk ko yaron ki kular da zai samu gaban mahaifin sa ba 'daya yake da na wani wajen daban ba, haka kawai akan wani dangin da bama kullum kk ganin juna ba sai ki tattare ki taho gida da yaro..sai kace babu gurbin kwakwalwa cikin kanki...?" Da sauri Amra tace " Ke..har fa da mahaifiyar sa..?" Ameera ma cike da 6acin rai ta cigaba Sai kuma kiyi ai..ni dai ban ta6a ganin alamun hkan tattare da Ammi ba tun sani na da ita, matar nan tayi ne a rayuwa, kima gode Allah da ya azurta da samun irin ta matsayin uwar miji, wannan rawan kan tun wuri ki nema masa mashiga ki kama kanki...duk wanda zaice miki kin yi daidai toh wlh bb kaunar ki a ransa amma kin ga cewa batuna da kuskure ba tilasta nake yi ba, kina da ra'ayin kanki...kiyi yadda kk so..." " Matar da ko ba'ko me yaje gidan sai ya yaba da kirkin ta balle matar dake a matsayin matar 'danta...wlh Amra ki nutsu ki san inda ke mk ciwo, kinsan yadda 'yan mata ma ke bibiyan irin mijin ki kuwa? kina sane da kalar zamanin da muke a halin yanzu ko? kina nan zaune wata zatayi mk wuff da shi sai dai ki kuma jin labarin an mk wata kishiyar banda waccan da kk barsu tare a gida...." " Allah ya sawwa'ke Ameera dan Allah daina yi min wannan fatan, waccen ma ai tuni ina jin bb auren dan nasan ba lallai ne tayi masa ba..." " Da yake igiyoyin auren a hannun ki suke ai dole kice haka..mjin da kk kasa jinyar sa, kk kasa zama da shi a halin jinya kika juya masa baya duk ta maye wa'dannan gurbin kk tunanin zai iya rabuwa da ita cikin sauki...da alamu kanki sam baya jaa Amra..." Fa'da sosai Ameerah tayi mata kafin ta bar gidan. Sosai kuwa taji fa'dan Ameera, jikin ta yy sanyi, tunani kala kala ta zauna ta yisu ta kuma ku'durta komawa gidan mijin ta aranta tun kafin ai mata sakiyar da ba ruwa, tunda Allah bai sa an tona ta wajen kowa ba. Rayyan kuwa dama tasan halin sa mawuyaci ne yazo gidan sun musamman sbd ita tunda ba shine yace ta taho ba sarai tasan bazai ta6a zuwa sbd ita ba. Ko da ta komawa Mummyn ta da maganar komawa masifa ta fara yi mata, akan bazata koma 'din ba gidan da ake yi mata gorin sa, gidan da ake binta da sharri, gidan babu wani mai kaunar ta a cikin sa zaman me zata je tayi a cikin su banda zaman takura. Amra tana tura baki tace" Mummy ba fa shine yai min laifin ba, Antyn sa ce wlh..kuma kinsan sa da taurin kai da shegen son 'yan uwan sa bazai ta6a zuwa gidannan danni ba. " Sai yaje can da girman kan sa shi ya sani, ni dai babu mai kawo min wargi har cikin gidana in 'kyale sa wlh...dan rashin kirki ko 'dansu dake tare dake ma ai babu wanda ya damu ya zo ganin lafiyar sa balle ke da dama aka raina...a fili ake nuna mk kiyayya amma sam baki ganewa...". "...Mummy...dan Allah..." " Ke...! Ta daka mata tsawar da ya kusan firgita ta. " Nace ki bani wuri bb inda zaki...". 'Kafa ta fara bugawa a 'kasa tana kuka take fadin " Haba Mummy?..haba Mummy!!..fi sabilillahi mutun da mijin shi ace bazai koma gidan sa ba haka kawai, nifa wlh ina son mijina har yanzu..". " Sannu suda sarkin so...!ina ce kafar ki ta kawo ki da wuya ta koroki toh bazan san kinayi ba sam Amra har sai kin fito dunia kin nuna musu cewa ina son raba ki da mijin ki tunda nice naje har gidan naki na 'dauko ki...tsaban rashin zucia ma shi bai zo ko sau guda cikiyar ku ba sai kece zaki bibiye sa...". " Ni dai wallahi ba rashin zucia bane..mutun da gidan sa ace bazai koma ba...". Haka ta 'karaci mitar ta akan Mummyn nata bata ce da ita 'kala ba. Ko da ta koma 'dakin ta kuka sosai tasha, cikin ranta take jin kewa da tausayin Sultan amma bata da ikon zuwa gare shi sbd gudun zargi. Karo guda tamkar an tsikare ta ta tashi ta fara ha'de kayan ta, ba yau ta fara guduwa daga gida dan komawa 'dakin mijin ta ba amma yau 'din haka kawai sai taji bata so tayi hakan...tafi so tayi komai da yaddar mahaifiyar ta duk da bata ga alamun mahaifiyar tan na da niyyar mayar da ita ba. Magana take so ayi aja wa kowa kunne akan ita da yaron ta cikin gidan kuma hakan bazai samu ba har sai Rayyan ya kawo kansa gaban mahaifan ta ko kuma su mahaifan nata su nemi jin ba'asin.dawowar ta amma bata ga alamun faruwar ko daya daga cikin hakan ba sam, Abban ta ne dama kuma baya 'kasar tun zuwan ta, itama Mummyn nata dawowa tayi ta tarar da ita, shi dama Rayyan ba yau tasan halin sa ba matukar ba shine yace tazo gidan da kansa ba baya ta6a biyo bayan ta ba kuma ya bari wani yy hakan. Tun wani zuwa da ya ta6a yi mahaifiyar ta taso yi mar tijara ya yaye wa kansa bin bayan ta...ta san kuma idan shekara zatayi ba zuwan zai yi ba. Hakan kawai kuma sai ta tsinci kanta da son komawa, kayan ta ta ha'de kaf da na yaron ta ta ajiye a gefe. Washe gari da sassafe taje 'dakin Mummyn nata ta ri'ka yi mata kuka da magiya akan komawar , dan tasan Daddyn ta ba matsala gare sa ba shi. Yadda take kukan ya tilastawa Mummyn amince mata amma tace ita bb inda zata je, sai dai ta 'kira mijin nata yazo ya 'dauke su zuwa dare su koma. Hakan kuwa akayi, da komawar ta 'daki ta 'kira shi bayan gaisuwa sai ma ta rasa abin cewa. " Baby shine tunda muka taho ko sau 'daya baka zo ka duba mu ba..?" " Bani da lokaci ne". " Ayyah ..Arfan ma na gaida ka". " Ya yake?" "Lafiyar sa 'kalau..but he is missing you badly". Tayi maganar tana murmushi. Rayyan bai ce komai ba. " Baby yaushe zaka zo mu koma gida?" " Babu rana!" " Ayya pls mana Baby kayi hkr, i know ban kyauta ba amma Insha Allahu hkn bazai sake faruwa ba.." Tasan bazai zo 'din ba dan tun daga yadda taji yake amsa mata magana abin bai yi mata ba domin a wani da'kile yake amsa ta tamkar bai san yin maganar. Ai kuwa amsar da ya biyo baya bai mata da'di ba sam dan cewa yayi" Ai ni ban kore ki ba Amra, ban kuma ce ki tafi gida ba dan haka ni ban da lkcn wani zuwa 'dauko ki, kisha zaman ki ki huta a gida kawai tunda haka kk fi so...." Tace sam ita dai zata dawo sai yace Allah ya tsare hanya. Daga haka ya kashe kiran ya cigaba da harkokin sa. Anyi hakan da kwanaki biyu ta dawo gidan..kuma abinda ya bata mamaki har aka kwana biyu da dawowar ta Rayyan bai nuna alamun yasan da zuwan ta ba, sai ta ga ma duk wasu lokutan harkokin sa ya canza su ba kamar yadda ta sanshi abaya ba. Idan ya fita tun safe bai dawowa har sai ya tabbatar kowa yy bacci, kuma sannan rufe 'kofar sa yake ya wuce da keys 'din sa baya bari a shigan masa 'daki. Wannan sabon canjin ba 'karamin ba'kanta ran Amra yy ba ta kuma rasa ta yadda zata 6ullo masa. Shima 6angaren sa bata san tana cikin ransa ba, shi ba wai yayi farin ciki da da dawowan ta ko akasin hakan ba ba 'daya daga ciki, kawai so yake ya samu lkc yaji daga bakin ta akan Arfan 'karya guda kuma ta kuskuara tayi masa hukuncin sa bazai zama mai dadin ji ga duk wani mai kaunar ta ba. Abinda kullum ke ransa kenan game da Amra, bayan hakan bb komai, babu wata kauna tata a hahalin yanzu aransa, baba shauki balle kewa nata da ada ya saba jji da zaran ta nisance shi. Ai kuwa Amra ta kai kusan sati a gidan batare da sun ha'du da Rayyan ba dan 'karshe ma barin gidan yayi abinsa ya koma can gidan sa shi ka'dai yake rayuwar sa. Ranar da ta cika sati kuma aranar ya dawo da Mufee a hannun sa ya shigo 6angaren nata da misalin sha 'daya na safe dan aranar ne ya yanke zasu Prison da Marwa. Rashin ganin sa na tsawon kwanakin da batayi ba bai 6ata ranta kamar yadda taga ya shigo mata da Mufeeda suna daria tare ba. Take tayi kici kucin da fuska, ta tsani yarinyar tsana mafi girma da muni, ita kanta bata san iyakar kiyayyar da take mata ba..duk ta tasan a tatsuniyoyin da suka zayyano kwanaki sun ce wai itan 'diyar sace jinin sa, ita kanta ta ta6a hasaso hakan, amma tabbattuwar maganan bai gamshe ta ba sam har zuwa yau. Tana zaune a Palor tana shayar da Arfan suka shigo...wai duk uwar biyayyar karyar da nake yiwa mahaifiyar sa cikin kwanakin nan sakamakon da zan gani kenan .?" Ta ayyana aranta. Idanu ta lumshe ta bude su da sauri jin kamar hawaye na shirin zubo mata. Bata so ta nuna gazawar ta tun yanzu...hakan yasa ta nemo dauriya da dasawa zuciyar ta. Shi kansa sai da yayi turus da ganin ta a Parlon dan sam ya ma mance da ita a gidan kwata- kwata, gashi Amra bade iya tsara kwalliya ba...'yar gayu ce ta 'karshe. Basarwa yayi daga sallama bai 'kara ba ya sa kai kawai yana 'kokarin wucewa ciki. " Sannu da shigowa Baby". Tayi dauriyar fa'da tana mai mi'kewa tsaye tana gyara ri'kon Arfan a hannun ta. " Uhum..". yace a 'kasan ma'koshi.. " Hala tafia kayi babu sanarwa Baby". Yace " Ina nan..babu inda naje..". " Kuma sai ka....." " Pls ban san doguwar magana..akwai wani abin ne daban...?" Yayi maganar yana dakatawa. " Kaima kasan akwai shi...magana nake so muyi dan Allah....". Wani kallo daya waigo yy mata sai da yasa duk wasu maganganu da 'kwarin gwiwar da ta tattaro arcewa. Wani yawu ta ha'diye mai kamar 'kaya tana rarraba idanu a'kasan tiles. Shi kuma ya cigaba da tafiyar sa zuwa ciki batare da ya damu da jin maganar tata ba. Bai da'de ba ya sake fitowa Mufee biye da bayan sa, dalilin hakan ma yasa tafiyar tasa ta zam very slow sbd ita baya so yy nisa ya barta. Har a lkcn Amra na nan Palorn sai dai wannan karan zaune take ta rafka uban tagumi bata zaci fitowar sa yanzun ba, hakan yasa da fitowar tasa ta sake mi'kewa tsaye cikin hanzari amma ko kallon inda take ma bai yi ba balle ya tanka ta har suka 'karasa ficewa daga 'dakin. Da gudu ta nufi window tana le'ken sa tamkar yau ta fara ganin sa, ko kuma ya canza mata ne oho, wani zazzafan 'kaunar sa ke sake ratsa mata dukkan ga6o6in jikin ta. Raihana ta riga ta wuce tun jiya dan acewar ta ita kam bata ga me zata je yi a wurin Sultan ba, hakan yasa Marwa ce ka'dai da Zaitoon suka shirya tafiyar. A can bakin motar sa ta hango su yayin da shima Rayyan ya nufi can bayan ya 'dago Mufee a hannun sa ganin tafiyar ta ta shiga masa lkc take. Yana isa ya bu'de baya ya sanya Mufeeda suna 'ko'karin shiga ya wani ha'de rai yana duban su. " Me ke nan haka...? Ya tambaya yana mai rufe 6angaren da ya sanya Mufeedan batare da duban inda suke ba. Lkcn da yake zagawa dan shiga mazaunin driver yace da Zaitoon " ki koma gida". Turus suka yi dukkan su, sai suka rasa cikin.su da wa yake...ita Marwa tasan cewa a yau din da kansa ya kira wayar ta tun sassafe ya sanar da ita ayau zasu je ta kuma san ba 'dabi'ar sa bace sa6a alkawari dan haka mawuwaci ne idan da ita yake, tunda ko yanzun ma shine ya aika ta fito yana da abin yi a gaban sa. Uban ta mayar kan Zaitoon, adaidau lokacin da Zaitoon ma ta dube ta suka kalli idanun juna...sarai Zaitoon ta fahimci da ita yake a idanun Marwa...kenan 'yan uabnci za'a nuna min..?" Ta ayyana a zuciyar ta, har ranta bata zaci zai mata wannan rashin kirkin ba da ko da Marwa tace tare zasu je baza ma ta yadda ta shirya har ta fito ba. Bacin haka ma 'kage take sosai da son fitar nan itama ko dan sbd Marwa ma yadda taga ta damu...tana matukar 'kaunar Marwa, tana son farin cikin ta. Tunda taji lbrn abinda ya faru take tsananin tausaya mata. Irin kukan da tasha bazata iya tuna ranar da ta yishi sbd wani can ba. Yadda wani 'kullutun ba'kin ciki ya turnu'ke ta yasa hatta hannun ta ma kasa 'dagawa tayi. Dama baya take da niyyar shiga ba gaba ba, Marwa ce zata zauna a gaban so ita kanta Marwan ma kasa 'karasa shiga motar tayi duk suka tsaya saroro tamkar an dasa... " Kina 6ata min lokaci Marwa"! " Abinda ya sake shiga kunnuwanta kenan take ta dawo saiti. Da rawar murya ta ce " Yayah dan Allah ka barta muje man.....". " Idan baki shirya zuwa ba u can go back home Marwa...ni inada abubuwan yi agabana masu yawa kin sani..." Tana tura baki ta shiga ta zauna...sai ga hawaye shar sun gangaro tayi saurin goge su, dan tasan bb amfanin su, shi kafin ya fada ne wahala, amma idan ya furta ihun ka banza ne... cikin ranta take jinjina ba'kin hali irin nasa, ada idan Zaitoon ta fa'di haka 'karyatawa take amma zuwa yanzun ta fara fahimtar gaskiyar ta ne ba sharri take yi masa ba. Da shigar ta ya tada motar yaja suka yi gaba ya bar Zaitoon a wajen ko a kwalar rigar sa, duk kuma hakan ya faru ne akan idamun Amra dake le'kowa ta windown parlon ta. Mufee ganin sun fara tafiya Zaitoon bata shigo ba..ta kya6e fuska tace" Mammi tana waigawa bayan ta. Da kansa ya lalla6i yarinyar ya ha'da ta wayar sa sannan ya ci gaba da tu'ki...Marwa ko nuna alamun tana jin su ma batayi ba. Ba Zaitoon ka'dai ba hatta ita Marwan 'kwallan take shawarewa na takaici lkc zuwa lkc kuma ko a jikin sa...ko duban inda take bai yadda yy ba, sun gama tsara tafiyar su yazo ya wargaza musu komai, kuma ai dai Ammi ce ta tsara a tafi da Zaitoon din...amma sam Marwa bata jin yin wata doguwar magana...haushi kuma yasa ta'ki yi masa bayanin komai. Zaitoon kam da gudu ta koma ciki tana kuka sosai, bata yadda Ammi ta ganta ba ta shige 'dakin ta tana kukan da ita kanta bata san na menene ba. Cikin masu aikin Ammi 'daya taje da sauri ta same ta ta sanar da ita a yanayin da Zaitoon ta shigo domin ita taga fitan su tare da Marwa ta kuma ga shigowan ta ita ka'dai. Abin yaso ya firgita Ammi sai dai tuno wani abu yasa har ta mi'ke sai kuma ta koma ta zauna, umarni ta bawa mai aikin akan taje ta dubo mata su Marwa na nan ne ko sun wuce. Amsar da ya dawowa Ammin shi ya sa ta 'dan murmusa...biyo bayan fahimtar abinda ya faru. Waya ta 'dago ta 'kira shi...sai da ya kusan katsewa sannan ya 'daga da sallama...kasantuwan wayar na hannun Mufeeda ne. Cikin ransa ya ayyana" Nasan za'ai haka.." Ammi tace " Me ka yiwa 'diya ta Rayyan?" Ta fa'di hakan bayan ta amsa sallamar tasa yace" Babu abinda nai mata Ammi, ina hanya zan kaita". " Ba Marwa ba su nawa nace maka zasu je dama?". Wata makirar murmushi yy bai ce komai ba. " Wani laifin tayi ne da zai hana aje da ita?" Sai sannan yace" a a Ammi, kawai bazata je bane.."! " a wani dalili..?" " Haka nan kawai Ammi.." "Ka kyauta ai..kai baka da buri ko da yaushe sai san ganin ka hargitsa min yara ka sanya su cikin 'kunci ko..?" " Kiyi ha'kuri Ammi...ina tu'ki ne"!. Tace" Adawo lapia..". Daga haka ta yanke "kiran fuskar ta yalwace da murmushin da na kasa fahimtar kona mene. Da hannu ta bawa mai aikin umarnin tafia bayan ta 'kare wayar..bata kuma yi yun'kurin tashi wai dan zuwa duba Zaitoon ba dan tasan dole zata ha'kura tayi shiru da kanta ma tunda ba yau tasan halin sa ba..inda sabo a gidan ita yakamata tafi kowa sabo da bau'da'dden halin Rayyan. Amra tuni ta fito ta nufo 6angaren Ammi 'kage da son sanin kanun labarin, burin ta kawai taji inda zasu je da aka 'ki tafia da Zaitoon sai Mufee ka'dai. Domin ita dai hotunan faruwar lamarin kawai ta gani bata san komai akai ba..erh mana hotuna, tunda ko kalma guda bai fada kunnuwan ta ba. 'Bangaren Rayyan kuwa ya shirya zuwa da Mufeeda ne badan komai ba sai dan kawai ya nunawa Sultan cewa tafin hannu baya iya kare rana, sannan duk abinda Allah ya so sai ya faru, ya rayu tsawon lkc da 'kiyayyar su a ransa, da ba'kin ciki da 'kyashin kar yaga gudan jinin su a dunia musamman ma shi, sai ga shi Allah ya 6oye masa sani, bacin tare duk suke rayuwa da jinin nasa bai tashi bayyana musu ita ba sai adaidai lkcn da shi kansa ma fafutuka yake da tashi rayuwar balle ya iya cutar da wasu. Ga 'diyar shi nan da cikakkiyyar lafiyar wacce ta rayu cikin kariyar ubangiji bai kuma bawa kowa damar cutar masa da ita ba... Ko da Amra ta isa 6angaren ba ciki ta shiga ba tana isa parlon 'kasa ta ci karo da mai aikin nan na sakkowa daga saman Ammi. " Barka da shigowa ranki ya dade..". Tace da Amra cikin girmamawa. Bata amsa ba sai ma tsayawa da tayi Gaban ta...tace" Ina Ammi..?" " Tana sama" " Marwa fa..?" Sun fita da Yayan ta da Mufeeda.." " Ita kuma uwar Mufeedan fa..". " Tana can 'dakin ta da kuka ma naga ta shigo inaga 'kin zuwa aka yi da ita shiyasa....". Murmushi Amra tayi..tana 'dan waigawa take sake tambayar " Toh dama ina sazu...?" " Wajen mijin Hajia Marwa...". Idanu Amra ta 'kwalalo, take wannan murmushin ya 6ace 6at..tace" kin tabbatar..? " Erh Hajia, ai tun jiya ma suka so fitan Allah bai yi ba shi Alhaji Rayyan 'din bashi da lkc sai yau..." Juyawa kawai Amra tayi ta fita, ita kuma mai aikin ta kya6e baki, dama shegen surutu gareta tamkar aku...sai dai sam bata da munfunci ita. Da sauri Amra ta koma 6angaren ta 'karamar jakar ta kawai ta 'dauka da key 'din mota sai mayafi ta fito...gaba 'daya ta daburce, ta rasa me yk yi mata da'di. Rikice take gaba 'daya tsoron ta 'daya kar Sultan ya tona sirrin ta awajen su musamman da ta san hadda Rayyan aka je. Wannan wace iriyar masifa ce, inba nacin tsiya ba an riga an kulle mutum miye na sake ziyarta sa..? Gani kawai take tamkar zuwan ta ne shine mafita inyaso duk ma mene zai faru ta kwammaci ya faru akan idanun ta...'kila hkn ya hana Sultan furta wani abu daya dangance ta, hakan yasa batare da sauraran shawarar da 'daya 6arin zuciyar ta ke bata ba kawai ta 'dauki hanya tabi bayan su. Duk yadda tayi ta zuba uban gudu bata ha'du da su suba har ta isa bakin gate 'din Prison 'din. Da 'kyar ta samu aka barta ta shiga sai da aka kai ruwa rana, a hakan ma sai da ta dangana da cewar ita matar Rayyan Sa'ad ce kafin ta samu alfarmar shiga. Rayyan rungume da 'diyar sa a kafa'da Marwa na bin bayan sa suka shiga, su ma 'din sun 6ata lkc sosai kafin aka fito da shi...dan dole sai anyi wasu bincike bincike da cike - cike. Rayyan na ganin an fito da shi ya tashi ya bar wajen zuwa wani wuri can daban ya bar Marwa...cikin ransa yk kissima iya lkcn da ya yanke musu su zanta. Ita kam baki ta rufe ganin sa da uniform din Prisoners da babban numbern sa a gaba da bayan riga...ga wasu karfafa biyu masu gadin sa abayan sa. Kuka ta saka sosai shima hawayen ya fara da ganin ta, dan bai ta6a zato ba..da gudu taje ta rungume shi amma Sultan bai iya yy kamar yadda tayi masa ba. Marwa sai ma ta kasa fa'din komai sai kuka har sautin kukan na bayyana a sarari... Sultan ne yy 'ko'karin raba ta jikin sa yana me saukar da idanun sa kass. Baya ka'dan Marwa ta ja ta zauna a kujerar da ta tashi dafe da kanta domin jiri take ji na shirin 'diban ta... " Allah ya sani tana son Sultan da dukkan zuciyar ta shiyasa duk abinda taji akace ya aikata bb 'daya da yy tasiri a zuciyar ta, ta kasa yadda akan shine ya aikata sbd ta yadda dashi 'dari bisa 'dari. Abinda ya fara zuwa bakin ta bayan ta zauna 'din .." Yah Sultan shine ka biyewa yaya kace mishi wai ka sake ni ko..?" " Ba cewa nayi ba Marwa...rubutawa nayi da hannu na..."! Idanu ta waro akan sa..amma sam Sultan ya kasa ha'de idanu da ita. " Yah Sul..tan" Ta kira sunan shi cike da rauni jin abinda yake cewa. " Kiyi hakuri Marwa, babu yadda zanyi, sakin ki a wancan lkcn ya zame min dole ne ki fahimce ni...". Kuka ta sanya mai ban tausayi, cikin kukan take fa'din" Ba dole bane Yah Sultan, ni ai bance maka ka rabu da ni ba, bance maka na gaji da zama da kai ba, bance maka bazan iya rayuwa da kai cikin ko wani irin hali ba, meyasa zaka biye musu? Meyasa zaka yanke hukunci batare da kayi shawara da ni ba..? Yah Sultan ko tsawon wani lokaci zasu ri'ke anan ai zan zauna ina jira ka har ka fito mu cigaba da rayuwar mu tare meyasa kayi saurin rabuwa da ni Yayah...?" Ta karashe cikin kuka sosai mai ban tausayi. Murmyshi Sultan yy 'yar ta'kaitacciya yana mai kawar da kansa gefe ga inda Rayyan ke tsaye..amma bashi yake gani baba, bayan sa yake ka'dai yake iya gani sakamakon baya da ya juya musu. " Ba lallai ba Marwa, ba lallai ki iya jira na ba..ni fa nan yanzu shine gida na, bani da ranar fitowa Marwa, jama'ar gidan nan sune 'yan uwa da dangi na...bani da ikon sake rayuwa a waje kamar yadda nayi abaya, nan zan cigaba da zama har 'karshen rayuwa ta...kinga kuwa idan ban yanke igiyar auren mu bama ai nna shiga hakkin ki...." Kuka sosai Marwa ke yi, tace" Ka daina fa'din haka Yah Sultan kana sawa inji na karaya baki 'daya.. ni bazan iya barin ka ba, bazan iya barin ka cikin wannan halin ba, zan ro'ki Yayah ya san yadda zai yi a fito da kai...". Wani murmushin ya kuma yi da kana gani kasan na nadama ne. yace" Ke yarinya ce Marwa...bazaki ta6a fahimtar wasu abubuwan ba...Yaya Rayyan ai jarumi ne nasan zai iya fiye da yadda kk so ma, amma a halin yanzu ni kaina bana bu'katar rayuwa a waje kamar rayuwa ta baya, na fi so na girbe hali na, na cutar da ku Marwa sosai, na cutar da ahalin ki ta yadda baki ta6a zato ba, nasan bazaki rasa jin wasu daga cikin abubuwan da na aikata ba, ina kuma tabbatar mk hakan 'din ne na aikata Marwa ba sharri akayi min ba..." A hankali ya tako gaban ta ya durkushe bisa gwiwoyin sa sannan ya cigaba..." buri na dama in ha'da idanu dake ko da sau 'daya ne kuma Alhamdulillah kin zo da kanki waje na..hakan ka'dai da kk yi min bazan ta6a mantawa da shi a rayuwa ta ba... ngd sosai Marwa, abu na biyu da zaki yi min ki yafe min dan Allah, ki ro'kar min Ammi, Yayah Rayyan da Raihana duk su yafe min sbd Allah...ban yi muku adalci ba, na cutar da ku ina kuma jin takaici da ba'kin cikin hali na a halin yanzu, na ci amanar ki ta yadda baki ta6a zato ba Marwa, na zauna zaman auren ha'inci dake batare da ke kinsani ba, na nuna mk kauna ta 'karya, duk da ban samu yadda nk so ba..naso na haihu dake sbd in gaji dukkan dukiyar ku amma hkn bai samu ba...yanzu ne na fahimci cewa lallai idan Allah ya kare mutum bb wanda ya isa ya cutar da shi face da Allah ya da'da kare shi...dan Allah Marwa ki yafe min... laifuka na sun girmi tunanin ki Marwa, kwakwalwarki bazata iya 'daukan nawin laifuka na ba ko nace zan sanar dake baki 'daya...." _Me kuke tunanin zai faru....?_ Salmerh😘 [2/9/2023, 7:07 am] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Wattpad@* _Serlmerh-md_ 🅿️ *...100* ......." Nasan kowa yaji me na aikata a duniyan nan sai ya tsane ni, kowa yasan mene hali na na 6oye tsana ta zai yi, ngd sosai da baki tsane ni ba Marwa har na samu darajar da kk iya zuwa waje na duk da abubuwan da na aikata mk..ki yafe min dan Allah...ki yafewa wannan bawa mai tsananin son kansa da rashin tausayin wa'danda suka fi kowa 'kaunar sa a dunia, wa'danda suka nuna masa gatan da ko mahaifan sa basu nuna masa ba..wa'danda suka maishe shi mutum a lkcn da akayi watsi dashi...ki yafe min bisa ga cin amanar da nayi mk Marwa...dan Allah ki......" Amra da ke tahowa a gigice 'karshen maganar Sultan ce ta fa'da kunnuwan ta ai kuwa batare da ta fahimci komai kan maganar ba kawai suka tsinkayi muryar ta da 'karfi tana fa'din" Ka cucue ni Sultan...baka kyauta min ba, ta ya zaka saka Marwa agaba kana tona min sirri?..taya zaka zauna kana fa'da mata cewa kaci amanar ta? taya zaka fa'da mata cewa Arfan ribar cin amana ne Sultan...?" Sai kawai ta rushe da kuka ta sauka 'kasa bisa gwiwawoyin ta itama. A yadda tayi maganar da sauti mai 'karfi yasa ilahirin wa'danda ke keway e da wajen bb wanda bai ji me tace ba, ciki kuwa hadda Rayyan. Hakan kuma shi ya janyo hankula da idanuwan mutanen gaba 'daya kanta. Ba Sultan da Marwa ka'dai da har sai da ta ha'da da tsayuwa ba hatta Rayyan juyowa yy yana duban ta cike da tsantsan mamaki da takaici gami da jin haushin ta, me ma ya kawo ta kuma a wani dalilin ta tazo..?" Ya tambayi kansa. Marwa da yake ta riga tasan zancen bata iya tace komai ba illa kawai ta dubi Amra ta kuma dubi Sultan da cikin yanayin ya 'dage mata kansa alamar tabbatarwa. Idanun ta ne suka fara cikowa da sabbin ruwa batare da 6ata lkc ba kuma suka fara gangarowa. Sultan ta nuna da yatsa bakin ta na motsi amma ta kasa furta komai. Jikin ta rawa yake sosai, ta riga tasan da batun tun a gida a wancan ranar da Anty Raihana ta bayyana mata shi, sam bata ji ta yadda ba, hkn yasa hatta Zaitoon bata iya ta bawa lbrn ba...tazone dama taji gaskiyar lamarin daga gareshi sai gashi Allah ya turo Amra ta bayyana komai...a wancan lkcn sam sam ta kasa jin amincewa ne amma yanzu da kunnen ta ta tabbatar daga bakin da ta san cewa hakan kawae bazata yiwa kanta sharri ba. Sultan take nunawa tana son fa'din wani abu amma bakin ta ya kasa budewa. Da gudu ta juya ta fita bata tsaya ko ina ba sai jikin motar da suka zo ta rungume motar tana kuka sosai, irin kukan nan mai matukar ban tausayi a gani da sauraro. Ji take ko ina yai mata zafi a duniyan nan, taya hakan zai zam gaskia, taya ma ya faru? Wannan wace iriyar kwamacala ce? ace matar 'dan'uwan ta uwa daya uba 'daya sukayi tarayya da mijinta kuma har da haifa masa yaro...innalilallahi wa inna ilaihi raji un...wannan jagwalgwale har ina..?wace iriyar 'kazamar rayuwa ce wannan? Ji tayi baki daya duniyan tai mata zafi, ji tayi babu wani sauran farin ciki da ya rage mata a duniyan, ada bata yadda Sultan zai iya aikata kwatankwacin hakan ba amma zuwa yanzu tsoro ma take ji sosai kowa tsoro yake bata ba Sultan ka'dai ba. Rayyan kallon Amra yake yana 'karawa, mamakin ta duk yabi ya cika shi, kuka take amma bakin ta ya kasa yin shiru, da kanta take faman tonawa kanta asiri a bainar jama'a bacin bb wanda ya nemi ko ya tambaye ta jin wani abu. Shin tsoro ne ko kuwa firgici? ko kuwa tsantsan rashin gaskia ne ya sa tayi hakan. Takaicin ta bb inda bai ratsa cikin zuciya da jinin sa ba...har wani 'daci 'daci yk ji ke taso masa tsabar bakin ciki da takaici. 'Karamin tsaki kawai yaja ya nufi hanyar fita dai- dai lkcn da jami'an tsaro ke bawa Sultan umarnin komawa ciki shi kuma yana fa'din babu wani sauran sirri da ya rage min Amra...ban san amfanin ko wani sirri tattare da ni ba a halin yanzu, Arfan ka'dai gare ni sai Allah na, dama bani da kowa taimako na akayi aka bani dangi aka bani muhalli, aka bani sittira aka bani gida aka mutuntani aka mayar dani 'da amma na butulce...ban sani ba ashe tun farkon rayuwa ta ni ba mai sa'a bane, ni ba mai nasara bane tunda banyi nasarar fara rayuwa da mahaifa na bama, ban san jinsin ina ne ni ba, ban san matsayi na cikin al' umma ba, ban san matakin daraja ko kaskantar ahali na ba, tun afarko na rasa wannan damar, na rasa damar sanin asali na, yanzu nazo ga6ar da ko da ina dasu ma basu da wani amfani gare ni balle ma babu su, toh me zan rufe, me zan rufe a rayuwata, na riga na lalata jiya na, yau da gobe na kuwa duk anan gidan suke me zan rufe da zai min amfani? Da kaina na jawa kaina, da kaina na ja wa kaina sake rasa wata damar ta daban....." Bai gama magana ba aka tisa 'keyar sa ciki. Bayan sa kawai da Amra ta hanga shigewar sa ya sake sawa ta rushe da kuka, ba wai dan tana tausayin sa bane a a, kuka ne ba'kin ciki tsamtsa, kuka na takaicin wautar ta tun a farko, yanzu ace wannan shine mahaifin 'dan ta? 'Dan da ta bi ta Dunia ta kara'de ko'ina da hoton sa da 'karyar cewa jikan Marigayi Sa'ad Auta ne..? Meyasa ban ta6a tunanin rana irin wannan ba? Meyasa ban ta6a hasaso faruwar makamanciyar irin wannan lamari ba? Haushin kanta da kanta take ji sosai, sai ma ta rasa tun farko me ya ru'de ta har ta fa'da son shi, ta kuma biye masa har suka yi ta aikata alfasha sau aadadin da ita kanta bata san iyakar su ba, ta banzatar da auren ta sbd shi, meyasa bata yi tunani mai tsawo ba a lkcn...meyasa ta biyewa son zuciyar ta ne? Meyasa!...meyasa!!..meyasa!!!...tambayoyine ke barazanar tarwatsa mata kwanya. Wata zuciyar ta ce ta bata amsa da fa'din shai'dan ne hakika shaidan ne yy nasarar afkar da ita...a fili da kuma 'karfi ta furta" Shai'dan ka cuce ni...shai'dan baka yi min adalci ba...yanzu gashi ka kaini ka baro...hakan ta ringa nanatawa a fili ta na tafia tana dukan kanta tamkar mahaukaciya, ko tuna cewa da mota tazo ma batayi ba, key 'din motar ma da takalmanta anan ta anan ta barsu tayi gaba. Lkcn da ta fito tuni su Rayyan sun yi nisa dan ko 'kurar motar su bata gani ba. Kuma har a lkcn kuka Marwa take yy mata tsawan tayi shirun har ya gaji. Domin kamar ma bada ita yake ba..rana na farko da Marwa ta kasa bin umarnin Yayannata, rana na farko da sam tsawan sa yaya kasa daidaita ta...rana na farko da ta kasance da shi wuri gguda cikin irin wannan yanayin bata re da fargaba ko kuma tsoro ba...sam ta hankalin da zata nemo tsoron kansa bata ganshi ba... 'karshe shima Rayyan kansa tausayi ta koma bashi, hakan yasa bai sake kula ta ba har suka iso gida...ga Mufee ta koma jikin ta ta lafe sbd kukan da take yi ba hakan ta saba gani daga gare ta ba...Bai zame ko ina ba sai can gida yana isa kuwa ya cire key 'din ya bar su amotar bai san ma lkcn da suka shiga ciki ba shima damuwar dake ransa ta ishe sa ba a daidai yk jin natsuwar sa ba. Babban haushin sa ma yadda Amra taje cikin 'dimbin alumma ta fa'di wancan maganar take sirri ce gare su...tuni ya gama yanke shawarar zama da ita ya 'kare masa tun daga wamcan lokacin...sam bazai iya ba, bazai iya cigaba da zama da mace irin Amra ba ko da ace ita ce 'karshen matan dunia zai iya yafe ta. Haka nan Amra ta na'di hanya ta ringa yawo tana nanata wannan kalmar tamkar mahaukaciya, gaba 'daya ta zauce ta fita a hayyacin ta tamkar wata zararra. Ta kai kusan awa biyu tana yawo bata san ina hankali da tunanin ta ya tafi ba sai bu'de ido tayi ta ganta kwance a 'dakin asbiti kakkarfan haske a kanta...wani abokin Abban ta ya ganta ya dawo da ita gida duk bata san anyi hkn ba. Ko a lkcn kuma sumbatu take...ina son shi, amma naci amanar sa, ban kyauta masa ba, na haihu da 'kanin sa, Shaidan bai min adalci ba...shaidan ka gama cutata..." Jin irin kalaman bakin ta da yanayin da ya 'dauko ta yasa da kansa ya wuce da ita asbitin Dawanau dake nan cikin garin Kano sannan ya sanar da mahaifan ta. Mummyn ta rikice sosai itama ta ringa kuka da tsoron abinda ya sa canza mata yanayin yarinya da har za'a kaita Dawanau....dan da farko ma taso ta yi masa masifan meyasa zai kai mata yarinya cikin mahaukata amma bai tsaya ya saurare ta ba ya kaste wayan yayana jan tsaki. Aanayin da ta ga Amra bayan isowar ta yasa taja baki tayi gum kawai ta ri'ka kuka a bayyane dan ta kasa yin na 6oye..sai da hana ki, sai da nace kar ki koma Amra dubi abinda kika jawa kanki..."..kin biyewa soyayya kina neman haukata kanki...haba Amra..sai kace ba raino na ba..akan namiji...namiji dai..." Bayanan bakin likitoci ne ya sanya ta 'danji kwarin gwiwa. Duk da hakan ta sha wuya kafin ta samu Amra ta dawo dai-dai ba kuma kananun kudade ta kashe ba akan 'dan zarewan da Amran tayi...nan ta turke ta sai da tayi mata bayani dalla dalla. Ita kuka mummyn ta kuka tana fa'din ta cuce ta, dama duk wannan fama da 'daga muryar da take sata yi ashe zaman cin amanar mijin ma take yi...wannan abin kunya da me yy kama...innalililahi wa inna ialhi raji un... Tace shiyasa da ta sanar da shi batun rashin lafiyar fatan samun sauki kawai yy mata ya kashe wayar sa, kuma har suka dawo gida bai sake 'kira yaji yanayin jikin ba balle akai ga batun ba zuwa duba su ba. Mummyn Amra zaune take a 'dakin ta amma kunya da nauyin ahalin Sa'ad Auta take ji na shigan ta ta ko'ina. Sam sam bama tasan ta iina zata fara ba. Kunyar abubuwan da ta ringa yi musu akan 'diyar ta take ji... Sai gashi babban abin kunyar da 'diyar tata ta kwaso mata, ashe gwara shima auren yar aikin Amra kawai yayi aure kuma mai cike da shaidu ba haikewa yarinyar yayi ta haifa masa 'da ko yarinya ba. Gaba 'daya Amra tasa mahaifan ta cikin zullumi, kar ma mahaifinta bawan Allah yaji labari. Gaba 'daya ya kaurace musu, hatta gaisuwar su bai amsawa ita Amta har Mummyn nata, baya cin abincin ta fushi sosai ya 'dauka da ita, dama yasha fada mata batun yau ba akan zata 6ata Amra da matukar dai bata canza yanayin da take tafiyar da rayuwar ta ba, indai bata canza kalmomi da lafazi game da auren Amra ba tace sam dole ne ta kwatarwa 'diayrta 'yanci...sai gashi rana tsaka abinda ya tsinkaya...sam irin 'yancin da take ikirari akqi din bashi ya tsammata ba kuma bai ji da'di ba. Arfan kam tuni shan nono ya 'kare masa, tunda mahaifiyar sa ta shiga wani hali bata 'kara shayar da shi ba..toh ina ma zai ganta. Baki 'daya rainon sa sai ya koma hannun Nannyn sa dan guidan ahalin yanzu bb ma mai lkcn tunawa da shi. Zaitoon kuwa itama tun fitar su take kuka cike da haushin an hana ta tafiya tare da Marwa, haushi sosai take ji na hana ta da Rayyan yayi, gashi dalilin hanawan ba wani muhimmanci ta basa har a ranta ba, kusan kullum ma tunani da burin ta taji an yaye mata amma shiru sai ga wata sabuwar tsirfa wai bazata je waje ko kuma aikata abinda ranta ke so ba sai da iznin sa. Har suka dawo gidan bata huce ba, amma ganin yanayin Marwa ya sa ta tuni tayi watsi da nata takaicin ta rungumi na Marwa. Bata samu natsuwa ba har sai da ta ta tabbatar ta kwantar wa Marwa da hankl ta kuma samu bacci kafin ta nustu. Ta tausaya mata matuka, sosai ita kanta taji bb dadi, jikinta duk yai sanyi..taji ta karaya...ashe nata ba ma komai ba ne... dan sun tattauna batun da Marwa kafin baccin ya 'dauke ta. Ammi kanta bata san da dawowan su ba sai ganin Mufee kawai tayi nan ta fahimci ashe sun dawo. Rayyan ma bai je 6angaren ta ba yana can nasa 6angaren shima da nashi kalan damuwar dake nukurkusan shi. Kusan ilahirin ahalin kowa da nashi tashin hankalin kunshe a kirjinsa. Sai dai wannan karan ba Marwa ka'dai ba hatta Rayyan bai sake tattauna batun da Ammi ba sbd matakin 'karfin lafiyar ta sosai ya raunata cikin kwanakin...ita Marwa kam bama zata iya sake maimaita maganar gaban Ammi ba, kunya sosai take ji na borin da ta ringa yi musu akan Sultan...sai gashi da kansa ya tabbatar mata komai. Sai dai wani abu guda da ya 'daure mata kai har a lkcn ta kasa jin haushin sa, gani take kamar gazawan da tayi wajen haihuwa ya sanya shi neman Amra har suka haihu...soyayyar da take masa daga cikin zuciyar ta ne, ginin da soyayyar sa tayi cikin zuciyar ta yy girman da bazai iya misaltuwa ba...kuma bata jin zai iya barin ta a lkc guda. Da Zaitoon ka'dai ta iya tattauna batun kuma Alhamdulillah ta fahimce ta ta kuma samu natsuwa...dama can suna shawartar junan su idan abu yasha wa 'dayan su kai shiyasa yau din ma direct wajen ta tayi...akwai fahimta da shakuwa tsakanin su biyun fiye da zaton mai karatu. Ahalin Amra sun 'dauki fin sati biyu suna cikin yanayin zulumi, kunci da damuwa suma..Amra duk tayi sanyi ta rame kamar ba ita ba, dama ba wani auki gare ta ba sai ta 'kara zama very slim sai haske da ta 'kara, cikin lokacin Rayyan yazo har gida ya kawo mata takaddar sakin ta, ko neman ta bai yi ba balle Arfan da ya turo tun satin da ya wuce tare da mai kula da shi, bai nemi jin komai daga gare ta ba kawai ya bada takaddar ta a hannun mahaifin ta bayan gaisuwar mutunci da sukayi ya yi tafiyar sa. Tasan shikenan yanzu kam ta'kurunkus komai ya 'kare mata ne, ta faru ta 'kare tsakanin ta da Rayyan tunda har da hannun sa ya rubuta mata saki har guda biyu...ya kuma 'kara da fa'din idan ta samu miji tayi auren ta. Gaba 'daya jikin ta yy sanyi, wannan karan hatta Ameera bata iya labartawa ba, sai dai tayi ta kuka kullum bayan ta rufe kanta a daki...tayi kuka har kuka ya zame mata jiki..kwallan ta suka daina zuba sai dai tayi na zuci. Tayi nadama, tayi Allah wadai da hali irin nata, nadamar da bata jin zai yi mata amfani shine ya shige ta tun barowar ta asbitin mahaukata. Takaicin kanta sosai da sosai take ji, da ganin rashin wayon kanta da kanta. Ibada kuwa yanzu sai dai a koya daga wajen ta sbd yadda ta du'kufa rokon Allah gafara sai abin ya baka mmk, a kowani lkc burin ta shine Allah ya yafe mata kurakuran da ta aikata. Mahaifinta kuwa kullum indai yana gari sai taje ta gaida shi duk da ba amsawar kirki yake yi mata ba amma bata fasawa bata gajia da zuwa wajen sa..ta riga tasan koma menene ita tajawa kanta. Amra duk tayi sanyi rayuwa ta juye mata..juyi irin na waina a kasko...Kusan hakan ke faruwa kuma a 6angaren Mummyn ta. Ammi kanta bata san Rayyan yy sakin ba sai da ta fara mitan yawon da iyalan sa ke yi ya isa haka, sbd kullum basu nan yau suna can gidan gobe suna nan tace abin ya ishe ta haka nan yaje ya dawo da su gida yafi. Toh kawai yace amma bawai dan zai yi hakan ba. Tun Ammi nasa ran ganin su har ta fahimci bashi da niyya da kanta ta fara saka rana nan ma sai yake zamewa da kawo uzururruka adai dai lkcn da yasan zata yi masa zancen. Ko kuma sai ya tsiri tafia ba gaira bb dalili inyayi kwanaki sai ya dawo yace an 'kira shi a wani gari aiki ne, ko kuma yace branch na companyn su ke neman sa. Tun Ammi bata fahimta har ta fahimci dojewa kawae yk, Sai da tayi dagasken gaske kafin ta samu ta ritsa shi akan maganar dan ta gama harbo jirgin sa tun ba yau ba, gashi ko maganar taso suyi da Antyn sa itama bata samun kyakkyawan goyon baya sai dai ta kyabe baki tana kawar da kai...da alamu dai bakin su 'daya da shi. Abin ya ishi Ammi..dan haka a ranar ta ce ya shirya da ita suje nan ya so zamewa itama ta tirje ta toshe kowacce hanyar zamewa. Dole fa aranar sai da ya fito fili yy mata bayanin ai ya saki Amra tun ba yau ba. Ammi sosai kalmar sakin ya doke ta a uzubillahi minash shaidanir rajim...ta furta kamar wani abu ne ya tunkare ta. Ai kuwa ta inda take shiga bata nan take fita ba ta ringa masifa, ta yi ta fa'da tamkar ta ari baki, inda ta ha'da hadda Anty Madeena akan ai ita ke goye masa baya yake komai, ya kashe auren Marwa shima gashi ya kashe nashi sun zama 'daya...banda shashanci mene amfanin hkn toh. Ita a ganin ta bai kamata yy gaggawan sakin ba, ai har abada Sultan nasune, dan bayan wani yanayi ya same sa bai kamata ace sun juyawa zuri'ar sa baya ba, yadda kowa yake gani ya kuma a kuma ce Arfan nasu ne meyata bazasu cigaba a hakan ba, su tallafi yaron kamar yadda suka tallafi Sultan..Rayyan yace" Allah ya kiyaye Ammi...kina nufin har kin manta abinda Sultan yai mana agidan nan da har kk tunanin a sake maimaitawa? mu sake kwaso wani mu kawo cikin mu muyi rainon makashin 'ya'yan mu ko Ammi...?" Kai Ammi ta girgiza sannan tace" ance maka duk an taru ne an zama iri 'daya Rayyan...kenan dan ka aikata alkahiri an saka maka da sharri sai ka bigi 'kirji kace ka daina yin alkhairi ga kowa kenan har abada a duniya..? Rayyan ka lura mana...a kullum hanya ake hawa, accident ake, mutuwa ake amma hkn ya hana a daina tafiye-tafiye ne Rayyan? Bb abinda wani 'kalubale na rayuwa zai hana a cigaba da aikata shi.. Ai duk abin da za a yi duk rufin asirin junan mu ne, Sultan Namu ne, haka ma arfan har abada namu ne..."! Ta kuma ce tunda har ka riga ka saki Amra batare da ko shawara da ni kayi ba, batare da sanina na ba..ya riga ya wuce ya wuce kam domin bani da ikon dawo da zancen baya amma ka sani ka.kuma maimaita irin wannan kuskuren Rayyan zan yi mummunan sa6a maka...kuma ka shirya zuwa jibi da yaddar Allah zamu wuce garin su Zaitoon baki 'dayan mu, Raihana ta riga ta wuce tun kafin itama a kashe mata auren tunda naga yanzu kisan aure kafi gwanancewa akai...dan haka tafiyannan bb ita.." 'Yar murmushi kawai yy...dan yasan Ammin zafi kawai ta 'dauka shiyasa ta fa'din hakan amma ai shi bai ga laifin abinda ya aikata ba, duk 'din su idan yace kowa ya cigaba da zaman auren sa ba shi ba, ba Marwan ba gaba 'daya zaman zargi, raini da rashin ganin darajar juna za'a yi, toh menene amfanin zaman auren da zai kai ka aljanna ba sai dai yaja ka izuwa wuta..Ai Allahn da ya halatta aure shi ya halatta saki. Wasu maganganun Ammi dariya suke bashi yayin da wasu ke sanya shi nisha'di matu'ka, Ammin sa akwai hikima yana kuma jinjina mata sosai. Babban abinda yafi tsayawa da burgesa sa cikin maganar Ammin shine batun zuwa wancan garin, bai kuma san dalilin sa na jin da'din ba...tsintar kansa kawai yy cikin tsantsan farin ciki marar misaltuwa. Kamar yadda Ammi ta tsara tafiyar hkn ne ya faru, domin hatta Rayyan bai nuna za'kewar sa kan batun tafiyar ba gaba 'daya ya barta a hannun su balle Zaitoon da fargaba da tararradin abinda zata je ta tarar acan shi yafi tsaya mata. Tsoro take ji sosai sai ma yanzu da kwana 'daya ya rage ayi tafiyar take jin ta cikin wani tsananin tashin hankali, most especially idan ta tuna da batun wannan auren na kanta tsoro da fargabar ta kara yawaita yake, ba kowa take kuma jin shakka ba kuma face Yayan ta, da wani idanu zata dube shi tace masa da aure akan ta bacin babban laifin da ta aikata gareshi na tafiyar da tayi batare da ya san da tafiyar ba balle inda ta shige. Bata yi 'kasa a gwiwa ba sbd fargaban da take ji ya riga ya rinjayi komai. Ammi ta samu kan batun auren inda ta ro'ke ta akan dan Allah ta sa ya sawwake mata auren kafin su tafi domin bata so tajewa mahaifan ta da igiyar auren wani akanta alhali ba sune sukai mata auren ba, aganin ta laifin ta 'kara ninkuwa zai yi awajen su. Murmushi kawai Ammi tayi mata, tace da ita" toh" kawai amma ba wai dan zata cikawa Zaitoon 'din burin ta ba domin sun riga sun gama magana da Rayyan akan haka, kuma shima hujjojin sa abin dubawa ne haka ma na ita Zaitoon, sai dai dole na wani ne zai rinjayi wani, shi aure sittura ne ga kowa ce 'diya mace, abu guda da zai iya sa ta bada goyon baya wajen raba wannan aure shine rashin amincewar mahaifan ta, ma'ana in suka nuna basaso...amma baya ga haka fatan zama me 'dorewa take yi musu, zama mai cike da farin ciki da walwala har zuciyar ta, duk da a har yanzu bata ga ko 'dis 'din alamu daga Zaitoon daya tabbatar mata da cewar tana na'am da shi ba amma tasan with time watarana zata so shi da iznin Allah. ***** ....." Innalillahi wa inna ilaihir raji'una...." Ta fa'da tana tafa hannuwa, salallamin bai dire ba sai da ta kai aya iya yanda yazo bakin ta, kafin ta 'karashe da nuna shi da 'dan yatsan ta. " Kana nufin kai jinin Jibirilla ne...?" Da kai ya amsa ta yana mai sakin 'kayataccen murmushin da ya sake 'kawata fuskar sa cike da annuri da farin ciki, duk da Goggon nasa ba cikin natsuwa take ba amma shi kallo 'daya yy mata ya fahimci ita 'din dagaske jinin mahaifin sa ne, duk bakar wahalan da ya sha kafin zuwan sa gare ta a yanzun duk babu su sun kauce, kallon Goggon nasa kawai ya gama wanke masa komai. Kuka kawai ta sanya ta kuma rufe fuska da dan hijabin da ke jikin ta. Shi kansa kukan yake jin yi amma ba hurumin sa bane a yanzu domin cikin tsananin farin ciki yake marar misaltuwa. Hannu ya mi'kawa Bello dake bayan sa ya kuma yi masa alamar shan ruwa da hanzari ya nufi mota dan 'dauko masa ruwan. Hafiz dake kishingi'de cikin motar a mazaunin driver da sauri shima 'din ya 'dago ya dube sa. " Ya akayi Bello an dace ne?" " Naga alamun hakan"! Cewar Bello yana 'ko'karin farka ledan ruwan ya zaro roba guda babba yana jinjina shan ruwa irin na wannan mutumi, daga ha'duwan su zuwa yanzu bazai iya irga robar ruwa nawa ya 'di'd'dikawa cikin sa ba tamkar mai hanjin roba. Hafiz zama ya gyara yana me bu'de gaban motar yace" Alhamdulillahi". 'Kafafun sa ya diro 'kasa sannan ya fito da duk jikin sa waje ya sha'ki ni'imtacciyar iska yana me gyara zaman rigar jikin sa yace. " Ina fatan ya kasance gaskia Bello, dan har ga Allah na gaji da wannan zaryar nan...kuma kasan mutumin nawa 'dan anace ne idan yy niyyan abu toh bb sassauci..." Murmushi Bello yy yana kan tafiyar ya amsa shi da fa'din" Kasan dangi gar'di gare su, kuma ba'a raina wanzuwar su, balle shi da ya rayu ya girma babu su dole nashi ya bambamta...dan ma mai zumuncin ne shi ba kamar wasu can baya da suka yi sanadin watsa zumunchin ba..." " Toh sarkin magana ni dai dakata a wajen ka jirani...nima shiga zanyi ai in ganewa idanuna na tunda an dace..." Cewar Hafiz yana mai 'kara hanzari domin taro shi. " Toh wai da sauri nk yace ruwa yk son sha..." "...kiyi hkr Goggo, dan Allah ki bar kukan nan, ban san ko zuwa ne ya janyo hkn ba, duk da nidai ba niyyata kenan ba..amma kiyi hakuri Goggo, ni na biyo bayan zumunchi ne na kuma biyo bayan 'yan uwan mahaifi na kamar yadda na sanar dake abaya, Alhaji Jibrin Adam 'dan Maliki shine asalin mahaifi na, kuma ni 'din nan nine 'da guda 'daya tilo a wajen sa..." Abinda ya sau'ka kunnuwan su Hafiz dake 'karasowa cikin gidan kenan bayan sunyi sallama. Yadda suka zuba mishi idanu suna kallon la66an sa da son jin abinda Goggon nashi zata fa'di yasa Adam 'dan murmusawa. Hk kuma itama goggon ke duban sa hawaye na bin kuncin ta. Bugu zuciyar ta keyi a duk lkcn da taji ya zayyano wannan sunan, bugu bibbiyu zuciyar ta ke yi a lkc guda, suna ne mai matukar daraja da 'kima awajen ta, sunan 'dan uwan ta abin alfaharin ta, 'dan uwan ta da ada yafi kowa son ta, 'dan uwan ta da tun kafin auren ta yy musu 6atan dabo...a yanzu shi da 'diyar da tayi irin 6atan sa take tunowa shiyasa ta kasa tsaida kukan ta...abin ya zame mata bibbiyu ne. Da 'kyar Hafiz ya bata baki ta rage kukan da take duk da besan dalilin kukan ba kusan ma dukkan su basu san dalilin ba amma shi'din dayake Allah ya bashi baiwar iya magana sosai kalaman sa sukai mata tasiri. Sun yi gaisuwa sosai sun yi hira sun tuna bayan rabuwa, ta kuma wadata su da duk wani abu da ta sani na tarbar ba'ko a 'kauye da zai matu'kar faranta zukatan su, dama ita gidan ta akwai yalwar 'dakuna, hkn yasa bata sha wani wahalar samar masu masau'ki ba. Ko da taji cewa Bello ma daga cikin 'yan uwan ta ya 'dauko shi farin cikin sai yy mata yawa...ta jima da cire rai akan ganin wani nata ashe indai da rai da rabo...'kaddarace kawai ta raba su ta kuma tabbatar da cewa bawa baya ta6a wuce 'kaddarar sa.... Duk wa'dannan sun biyo bayan kukan da ta yi tasha ne akan rasa mahaifiyar ta da ma wasu 'yan uwan ta da taji lbr daga bakin su ciki kuwa hadda Babban 'dan siyasan nan da yy 'kaurin suna a yankin dake makwabtaka da su wato Alhaji Jibrin 'Dan Maliki da bata san cewa 'dan uwan ta bane sai yau. A halin yanzu ita Goggon ka'dai ta rage masa dama ya sani cikin dangin sa, kuma Alhamdulillah burin sa ya cika yanzu, alwashin da ya 'daukan ma duk wani dake cikin ahalin mahaifin nasa ya samu cikawa...sai dai ita Goggon ce ya rage ya sada ta da 'yan uwan sun bayan tsawon shekarun da suka 'dauka basu ga junan su ba....su kansu suna matu'kar so su san inda take..amma sun kasa zurfafa bincike dan gano ta. Sun sha hira sosai, Goggo ta ri'ka bashi labarin yadda tayi kewar 'yan uwan ta anan ya 'daukan mata al'kawarin ai komai ya zo 'karshe Insha Allahu da kansa zai kaita wajen mahaifi da dangin ta duk da yake yanzun mahaifin nata tsufa ya kama shi sosai, shima yasha ba'kar wahala kafin ya samo ainahin inda suke...amma yanzu Alhamdllh complete yake jin sa a halin yanzu ta fannin dangi...saura abu guda tak ya rage masa...kuma bai ta6a cire rai da samun ta ba haka yake ji aran sa. Shiyasa ya'ki aure ya'ki 'yan mata ya'ki kowa, kowace mace ma bata birge shi haka suke yin hidimar bikin abokan su su gama batare da kowace mace ta burge shi ba, dama yan mata kam sai dai Hafiz shine gwani ta wannan fannin. Sam bai yadda sun kwana gidan Goggon ba amma yy mata al'kawarin dawowa da sassafe Insha Allahu kafin su wuce, breakfast ma yace a gidan ta zasu yi Insha Allahu kuma baza su da'de ba zai dawo dan sada ta da sauran ahalin ta. Haka suka 'dauki hanya zuciyoyin su cike da zulumi da jin da'di, sai dai suna ji tamkar baza su sake ganin juna bane. Tun ma kafin su bar 'kauyen yayi wa hajiyar sa albishir 'din wannan gagarumin nasarar da ya samo bata kuma 6oye farin cikin ta ba ita kanta, dan bata da son kai akan sa, duk 'kaunar da take yi masa da wahala da dawainiyar da tasha akansa zuwa daular da take ciki ayanzu ta sanadin sa, hakan bai sa dai- dai da rana guda tayi 'kyashin taya shi addu'ar ha'duwa da dangin mahaifin sa ba. Hafiz dake tu'ki ya juya ya kalle shi sau 'daya ya 'dauke kai. " Kasan mene...?" " Sai ka fa'da Hafiz..". Ya fa'da yana kashe wayar. " Da alamu kana cikin tsananin farin ciki..." " Ba 'dan ka'dan ba Hafiz!" " Nake gaya ma ji nake tamkar Alhaji ya dawo yaga wannan 'yar uwar tasa da idanun sa, da kansa ya ban labarin irin kewar ta da yake, aure ne sanadin rabuwar su kasan tunda sukai mata aure shikenan, toh shi kuma ko a lkcn ya jima ma bai zo inda suke ba shima sai daga baya ya neme su kuma ya samo inda suke amma bb ita". " Allah sarki...Allah ya ji'kan Alhaji ya gafarta masa...". " Ameen Yah Allah" suka ha'de baki wajen furtawa. Yayin da Hafiz ya cigaba da fa'din " Amma mutumi na kana fa da sauran aiki agaban ka....." " Name kenan.."? " Wannan Goggon mana...duba 'daya zakai mata fa ka tabbatar tafe take da damuwa gagaruma amma na jira na jira har yanzu ban ji ka furta komai akai ba...". Idanu ya zaro akan sa..." Hafiz ashe ba ni ka'dai na lura da hakan ba...wallahi tun 'dazun abin na raina na so in tambaye ta fa amma sai nayi tunanin ko duk rashin 'yan uwan ta ne, shiyasa ma na yanke shawarar dawowa ba da jimawa ba dan tafia da ita..naso tun yanzu nayi hakan amma kasan komai dole sai da iznin mijinta...". " Hakane...amma ka de 'kara bincikawa Man..kasan mata da iya 6oye damuwa har sai ta musu illa...". Shiru kawai yayi yana tunani, shi dai bazai ce ga halayya guda ko 'dabi'un mata ba sbd shi bai zauna da su sosai ba, Hajiyar sa ka'dai ce kuma she is free bata 6oye masa damuwar ta, wajen mace 'daya yasan wannan dabia'r amma ita kuma yanaga kamar 6oye damuwar ta yana da nasaba da irin rayuwar da ta riske ta ne.. ya riga ya zam mata jinin jiki kuma ne...shiyasa bai ta6a kawo shi akan kowa ba sai ita 'din ka'dai. Ko da suka isa masau'kin su, kusan raba dare yayi yana tunanin abinda zai iya sa Goggon nasa cikin damuwa, a halin yanzu ita ka'dai ce kyautatawar sa bata sau'ka kanta ba amma yafi so duk abinda zai mata duk taimakon da zai yi zai fiso ya kasance bisa tafarkin damuwar ta ya kuma wanke mata shi tass. Tsawon lkcn nan ya kasa hasaso komai sai ma yafi bawa ko matsalolin rayuwa ne kawai ko kuma ta 'da namiji... Da 'kyar ya samu yy bacci. Washe gari kuwa kamar yadda yy al'kawari sassafe ya tisa 'keyar su suka sake komawa Hafiz tamkar zai cinye sa 'danye dan cewa yayi ina ma laifin zuwa sha 'daya amma ace tun 'karfe takwas ya wani tashe su sai kace wacce yaji labarin zata gudu. Shi dai cewa yayi erh aje 'din dai yafi so ya gansa kusa da ita, kama ta jini dake tsakanin ta da mahaifin sa ya kansa yaji wani 'kauna da sanyi cikin zuciyar sa. Ita kanta Goggon tasa tayi mamakin ganin su a wannan lkcn amma farin cikin ta ya kasa 6oyuwa nan ta sake wadata su da kayan karyawa irin na karkara, koko da 'kosai ne da yaji yajin 'kuli. Duk 'din su babu wanda yayiwa zuciyar sa 'kyashi, ci suka yi babu wasa, dan kuwa Goggon nasu ba dai tsabta da iya tsara abu ba, da kansu suka fahimci haka. Sun 'dan sake ta6a hira inda Hafiz yaso jan Goggon da hira da kuma shan cikin damuwar da suke gani kwance kan fuskar ta duk da yake tana 'kokarin danne shi da farin cikin ganin su. Amma abin mamaki bb abinda sukayi nasarar ji daga bakin ta sai dai murmushi kawai. Daga 'karshe tayi dabarar ce da su..bata da wata damuwa da ta wuce ta rashin 'yan uwan ta kuma a halin yanzu tasan ta riga ta hau tsanin da zai sada ta izuwa gare su, a hnklai zata tsinci kanta cikin su tsundum. Dukkan su sun ji da'din maganar ta dan hk suka cigaba da hirar su amma Adam sam bai yadda hakan ne kadai damuwat Goggon ba...musamman ayau da yafi bada hankali sai ya fahimci cewa dagasken gaske damuwar ce 'karara kwance saman fuskar ta. 'Karge biyu saura suka ce zasu wuce sbd zasu tsaya suyi sallah sannan akwai tafia da kuma kur'da kur'da agaban su. Sun yi mata sha tara ta arziki amma Goggon sam ta'ki ansan komai nasu tace ita ai sune damuwar ta ba wani ku'di ko wani abin dunia ba. Burin ta kuma su cika alkawarin da suka 'dauka na dawowa domin ta. Dama yace Insha Allahu Goggo...bazan jima ba zan dawo. Wayar sa 'karama ya bar mata da wani Sim card 'din sa da ba sosai yake aiki da shi ba yace kullum safia zai ri'ka 'kiran ta su gaisa in yaso idan maigidan ta ya dawo ta nemi izninin nasa shi kuma zai dawo ya tafi da ita Iznin Allahu. Wayar kam bata ki ansa ba sbd tasan dole shine tsanin ta amma tana jin fargaba can 'kasan ranta. Shine ya nuna mata yadda zata na 'daukan 'kiran ya kuma fa'da mata yadda zata na cajin tace ma ai ba ita zata yi chajin ba masu chaji ne sbd bb wuta...yace toh shikenan hakan ma yayi. Daga nan sukai mata sallama suka kama hanyar fita Goggon na kallon su cikin tsananin farin ciki take 'daga musu hannu. Cak ya tsaya tamkar an bashi umarni, sai kuma ya juyo sakamakon tuno wani abu da yayi. Duk dai akan damuwar Goggon ne, dan shi kansa ya fahimci har yanzu da sauran damuwar ta sai dai dole wani abin ke danne wani. Sai ma yaga wautar sa da tun farko tunanin sa bai bashi hkn ba. Lokaci guda ya rayawa ransa damuwar Goggon baya rasa nasaba da rashin haihuwa.. ko kuma ta wani abin daban makamancin dai hkn.. sbd yasan inda ace Goggo nada 'da ko 'diya bazai yiwu ace har ya bar garin batare da ya gansu ko kuma tayi masa maganar su ba...kai yama san dole ne ta ha'da su musamman yadda ya lura da karamcin ta. Already su Bello har sun fice, ganin baya bayan su yasa Hafiz juyawa ya koma baya shima Bellon cikin ya koma. Tausayin ta sosai ne ya kamashi gudun kar abinda zai furta ya tono mata wani 6oyayyen mikin da ta dadewa da binnewa...but he hv to do it...hkn yasa yayi ta maza yace" Toh Goggo gashi har zan tafi kuma banga ko guda cikin 'yan uwana ba...ko ba nan kusa suka suke bane...?" Ri'kon da ta yiwa wayar ta sake ninka irin sa tamkar wacce akace 'kwace mata wayar za'ayi...dan da ace abu mai fashewa cikin sau'ki ne da tuni ya tarwatse a hannun ta. Muryar ta na rawa tace" ...'yan..uwan ka?... " Ina nufin yaran Goggo na..."! Ya fa'da yana 'ka'kalo murmushi. 'Kafar ta da take tsaye akai ma rawa ya fara allah allah take tambayar tasa wani abu daban take nufi ba hasashen ta ba. " Yaran Goggon...ka..?" Ta maimaita masa tambayar. Sai dai bai bari ta kai ga rufe bakin ta ba...taji ya tare ta da fa'din..." Ina nufin yaran ki Goggo, ban ha'du da kowa ba fa..gashi kuma har zamu wuce.." Yadda zuciyar ta ya harba da ace sun fahimta da har sai sun tausaya mata matuka, amma kawai sai ta tsura masa idanu tamkar mai shirin karanto masa amsar sa daga jikin rigar sa. Tsawon mintina biyu suna a hakan bb wanda yace da kowa komai, zurfin tunani Goggo ta fa'da yayin da Adam ke sake nazarta yanayin ta cikin tsanaki...nan dai tunanin sa ya bashi cewa hasashen nasa dai tun na farkon shi 'din ne...Goggon nasa bata da yaro ko guda..kuma hakan shine ma'kasudin shigar ta cikin yanayin damuwa. Tausayin ta sai kara 'karuwa masa a zucia yayi, 'kasa yy da kansa yana mai jin nadamar tambayar da yayi mata, sosai yake jin bb da'di, nan yk wa zuciyar sa fa'da meyasa sai da ta bari bakin sa ya furta mata ne. Da sanyin sauti mai cike da karaya yace " Kiyi hkr Goggo, ban san cewa magana ta bazata yi mk da'di har haka ba, ni dama buri na in san kowa da yake nawa ne shiyasa na tambaya, damuwar da nayi akan sanin dukkan 'yan uwana ne... kuma sai ya sanya ni na shagala da cewa ba kowa Allah ke bawa kyautar haihuwa ba...kiyi hkr Goggo ina mk fatan alkhairi, Ubangiji Allah yasa hkn shine silar shigan ki aljanna madaukakiya ...wani lkcn Allah ke 6oyewa kansa sani...amma a mafi yawan lokuta sai kiga rashin samun haihuwar wani bawa yafiye masa alkhairi fiye da samun nasa, hk kuma idan Allah bai so ba duk iya damuwar da zaka saka ranka bazai ta6a baka ba Goggo...Allah ya bamu ikon cinye jarrabawar da ya 'dora mu akai..." Su Hafiz ne suka amsa da Ameen. Daga hk ya juya ya fara tafia batare da ya yadda ya hada ido da ita ba...Tsinkayar muryar Goggon yayi tana fa'din" Tabbas...hakane, maganar ka gaskia ce, 'ya'ya Rahama ne, kyautar Allah, kuma amanar sa ce, 'ya'ya abin so ne kuma abin tambaya ne ga dukkan wanda Allah ya bawa, sukan 'debe kewa su sanya farin ciki amma, wani lkcn 'ya'ya masifa ne agare mu amma bb wanda zai san hkn sai wanda Allah ya jarrabce shi da samun 'dan da shawarar zuciyar sa kawai yake bi baya sauraran kowa..." 'Kasa tayi da kanta tana share 'kwalla ta cigaba fa'din" Kunya nk ji Adamu, ha'ki'ka ina matukar jin kunya in sanar dakai cewa kana da 'yar uwa amma bata tare dani...hasalima ban san duniyar da take ba a halin yanzu....tunani ma daban ne a halin yanzu, me zan ce da ubangiji na idan ya tsayar dani akanta ya tambaye ni..wani irin ri'ko na yiwa amanar daya bani..wace amsa gare ni..sam bani da ita...?" Daga hk sai ta rushe da kuka tana mai komawa ta zauna inda ta ta shi, bata san yaushe kukan ta zai 'kare ba, bata san sai yaushe zata rayu cikin farin ciki tamkar sauran mutane ba. Innalillahi wa inna ilaihi raji'un suka furta atare dukkan su. Take suka 'karaso cikin gidan kowa yana taya Goggo alhini a zuciya da fuskokin su. Shi Adam kam kasa ma fa'din komai yayi...tunanin sa ya tafi ne can can yana ta rarraba su a kokarin sa na lalu6o manufar kalaman Goggo...me ke nan take nufi da basa tare...shin aure ne kamar yadda itama ya raba ta da nata ahalin ko kuwa dai wani abin ne daban. Da 'kyar da nasiha da ban baki suka samu tayi shiru ta kuma basu labarin ainahin abinda ya faru ata'kaice na iya abinda ta sani. Sun 'dauki lokaci tare da ita kafin nan suka fito suka 'dauki hanya motar shiru baka jin motsin kowa..banda Adam dake ta kwankwa'dan ruwa babu wanda ke motsin kirki sai Hafiz dake tu'ki. Kafin zuwa wani lkc Adam yashanye roban ruwa uku yana na 'ko'karin shan na hu'du. Babu wanda ya tanka sai sakin huci yake...yana so ya samu natsuwa amma sam ya kasa samun sa. Baki 'daya labarin Goggon jin sa yake yana yi masa yawo cikin 'kwakwalwa. Amsa-kuwa yake yi masa aka...lkc- lkc kuma sai ya ri'ka ji tamkar yana wajen abin ya faru, sai yaji kusanci irin na kurkusa 'din nan game da labarin ya kuma kasa tantance dalilin hakan. Zaitoonan sa ta fara zuwa masa rai domin shigen labarin ta kenan sai dai da wuri ya kauda ita sbd baya hasaso yar uwar sa cikin 'kunci da tozarcin rayuwa sam- sam baya fatan hakan gare ta har abada. Ko da ya sake bibiyan labarin da Goggon nasa ta basa sai bai ji ya tsinci sunan ta cikin labarin ba hakan yasa yy saurin dakatar da Hafiz dake tu'ki...wani uban birki yaja tsakiyan titi. " Kai wai lafia?...menene hakan? idan kai ka gaji da duniyar ai mu da sauran mu...sai kace wani zarrare. " Hafiz ai ko baka fa'da ba ni da zararre babu da bambanci, shin kai baka ga yadda Goggo na take zubar da hawaye bane...?" " Na gani mana, ka samo mafita ne tun yanzu...?" " Dole zan samo ta...na riga na daukam kaina alkawarin hakan...fa'da min Hafiz...mene ne sunan yarinyar ma...?" " Goggo bata fa'da ba fa kasan ku fulanin nan sai a hankali..da uwar kunya..?" " Bar batun wasa Hafiz..."! " Maganar gaskia nk fada maka fa..." 'Karamin tsaki yaja ya waiga ya kalli bayan motar..." Bello sunan yarinyar Goggon dan Allah...nasan kai ba irin wannan banzan bane...". 'Yar murmushi Bello yayi yana girgiza masa kai a hankali alamun bashi da masaniya. Da 'karfi ya bugi saman Sit 'din motar cike da haushi. " easy man abi komai a sannu mana...". Cewar Hafiz yana 'ko'karin tada motar dan yin gaba. Zama Adam ya gyara da kyau ya dubi hanya sannan yace" Ya zam mana dole mu koma baya..."! " Ina wai...baya inda muka baro...?" Ya fa'da yana zaro idanu " Tabbas..kuwa ..sai fa naji sunan yarinyar nan...tunda kai har Bello bb wanda ya san sunan da Goggon ta fa'di...?" " A a Malam..bafa ta fada ba...inda ta fada kai mai ya hana ka rike da kanka?" Cewar Hafiz. Bello ma yace" Ba wani suna kam da ta fa'di Hamma." " Toh dole sai mun koma can...!" 'Dan karamin tsaki Hafiz yaja yana mita" Wallahi kai 'dan yawa ne Shaheed..menene amfanin sunan..me zaka yi dashi tunda ba sanin ta kayi ba". Bai ce da shi komai ba kawai ya lumshe idanu shi dai burin sa a koma kawai. Ko da suka koma nan inda suka bar Goggon anan suka tadda ta tana tunani duk kuwa sallamar da suke zubawa bata ji ko guda daga ciki ba. Sai da Shaheed 'din ya sake matsowa kusa da ita yy sallamar da 'dan sauti kafin tayi firgigi ta mi'ke tsaye. Sai kuma ta daburce tana rarraba idanuwa da goge hawayen dake fuskar ta. Bello na daga waje yaga motoci har guda biyu sun yi parking kusa da shi sai yy galala yana duban su, lafiyayyun motoci ne da suka ji naira ba na wasa ba, duk da bawai yasan farashin mota ba ne amma ai ido ba mudu ba...duban farko zaka fahimci abinda ya fahimta. Bai tsinke da lamarin ba sai da yaga an 6alle marfin motar da sauri wata kyakkyawar yarinya matashiya ta fito daga ciki ta nufi cikin gidan Goggon da hanzari. Shaheed ne yace " Kiyi hkr Goggo mun tsorata ki...mun dawo ne, baki san sanar da mu sunan yarinyar ba Goggo ..?" Kafin Goggo ta amsashi suka tsinkayi wani kamilalliya kuma sassanya sautin murya na furta. " _Assalamu alaikum..._ " Salmerh😍 [27/9/2023, 6:56 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Wattpad@* _Serlmerh-md_ 🅿️ *...101* .......Duk yadda yake jin damuwa gami da 'kaguwa da son jin abinda zai fito bakin Goggon nasa karo 'daya duk yaji wata fitinanniyar bugun zucia daya kore komai sakamakon tsinkayan sautin muryar da tayi sallama...amsa kuwwa sallamar ta rika yi masa a ka. Dukkanin su juyawa suka yi suka mayar da hankali wajen mashigar gidan..sa6anin Goggo da dama nan take fuskanta. Inka 'dauke goggo da tayi mutuwan tsaye cikin su bb wanda bai zaro idanu da bu'de baki da ganin ta ba. Atare Hafiz da Adam suka furta sunan" Zaitoona...!" Wanda hakan shi ya sanya Goggon Adam mayar da idanun ta garesu cike da tsantsan mamaki. Ita kanta a 6angaren ta ma haka abin yake. Cike da tsananin mamakin ganin sa tare da mahaifiyar ta tace" Yah Adam...!" Tana toshe baki da duk hannuwa biyu. Kasa amsawa yy kawai ya cigaba da duban ta..ji yk tamkar mafarki, ji yk tamkar idan ya motsa za ace masa ba gaskia bane abinda idanun sa ke gane masa illusion ne kawai da ya saba gani nata. Amma duk ganin da yake mata cikin mafarkai, hasashe da tunanukan sa bai ta6a kwatanta cikin wannan ni nimtaccen yanayin ba sai dai in zai gansa tare da ita. Shiga ta kamala, tsabta da kwanciyar hankali 'karara suka bayyana. Hafiz ne ya sake yin 'karfin halin furta " sunan ta akaro na biyu. Itama tace " Yah Hafiz"! Yaushe Zaitoonan sa ta waye? Yaushe ta samu rayuwar mai ingancin da shi ya kasa bata...? " Yayah Adam...Kai ne...?" Ta sake tambaya cike da tsananin mamakin ganin sa anan...hakan shi ya yanke masa 'dan guntun tunanin da ya fada. Wani 'kwarin gwiwa ne yaji ya zo masa nan take bayan tabbatar da cewa ita din ce dai. Kai ya sosa yana mai 'ka'kalo murmushi yace" Zaitoon Nine..bayan tsawon lkc sai gashi yau ga ni ga kuma ke..."! " Wa ya nuna maka gidan Inna ta...?" Ta tasake tambayar sa dan har a lkcn mamakin bai sake ta ba. Yace " Baiwa ta ta kawo ni.."! " Wace ita haka..?" " Da kaina nazo Zaitoon bayan kin guje ni...?" Tana shirin magana sai ta hango hadda Innani tayi mutuwar tsaye tana duban ta...fasa maganar tayi ta nufi Inna da gudu tana shirin rungume ta Inanni ta ja baya ka'dan ranta a matukar 6ace ta yadda ko fuskar ta bai 6oye hakan ba. " Innani ni ce fa...". Zaitoon ta fa'da da wata karyayyar zucia tana sake duban Innar tata. Wani lafiyayyen mari Innanu ta sauke mata saman kuncin ta, kafin Shaheed yy wani yun'kuri sai ga Innani ta sake sau'ke mata wani marin. Da duk hannuwa biyu Zaitoon ta dafe kuncin ta idanuwan ta na zubar da hawaye take duban Innani. Duk yadda Adam ya shiga tsakanin su hakan bai hana Innani son sake kai mata wani bugun ba..duk da baki 'dayan su hkr suke bata amma Innani tamkar bata sauraren su, ita kuka Zaitoon kuka, Innani fa'di take ta fita ta bar min gida kafin tayi mata mugun duka. Yadda Innani da Zaitoon ke kuka yasa hatta su Ammi dake waje suna jiran iso daga wajen Zaitoon din kawai suka nufo cikin gidan a tsorace. Nan suka tarar da hayaniyar. Tuni Zaitoon na dur'kushe bisa gwiwoyin ta tana kuka ta ha'de hannuwa da alamar ro'kon gafarar Innani. Ammi ce tayi saurin shiga tsakani tace " Haba haba Innan mu...mene hakan wai, sai kace wacce ta aikata wani gagarumin laifi..?" " Ta fita ta bar min gida nace!...bana son ganin ta, taje ta koma inda ta fito ta cigaba da rayuwar ta, mun riga mun cire ta a ran mu..mun ha'kura da ita..." Sai ma ta kasa 'karasa abinda tayi niyyar fa'di kuka ne sosai ya ci 'karfin ta. Nan ta koma ta zauna kukan takaici da bakin ciki na sake fizgar ta. Bazata ce bata yi farin ciki can 'kasan zuciyar ta da ganin Zaitoon ba, amma idan ta tuna wata sabuwar Zaitoonan ce tazo mata, ba tata ta asali ba, sai taji sam bata da wani 'kwarin gwiwa kuma. Tsoro take ji kar 'diyar ta yawon duniya taje da yasa tayi kyau haka ta dawo tamkar ba haihuwar jeji girman Ala raya irin Zaitunan ta ba. Shaheed ne yazo gaban ta ya dur'kusa bisa gwiwoyin sa a hankali ya 'kira sunan ta bata amsa. Sai da yaja gauran numfashi kafin ya sake cewa" Goggo!" Bai tsaya ba ya 'dora da fa'din" Kika ce ta tafi? Ta koma inda ta fito? Goggo kika ce kun cire ta a ranku, bacin mintina 'kalilan baya kafin isowarta idanuwan ki jike suke da ruwan kewa da rashin ta, meyasa bazaki bata dama ba Goggo? meyasa bazaki tsaya ki saurare ta ko da sau daya bane, na tabbata tunda kikaga ta dawo rana tsaka da kanta toh tuni tayi nadaman abinda ta aikata...Goggo Zaitoon din ki cefa! Har kin manta? Goggo Zaitoon 'dinki kamammiya ce a duk sanin da nayi mata, kuma har yau bana tunanin zata banzatar da kanta sbd wani abu Goggo, sai dai in kaddarar ta ce tazo da hakan...idan kin amince ni nan Goggo sai in baki labarin waye Zaitoon daga lokacin da ta bar gaban ki har zuwa iya abinda na sani....". Da sauri Innani ta dago kanta ta dube shi, kai ya jinjina mata alamun tabbatar wa, sannan ya cigaba, " 'Kwarai kuwa Goggo, kuma na fadi hakan ne da dukkan gaskiya ta ba wai dan in kare ta ko kuma dan wani abu ba..." Kallon sa kawai ta tsaya yi sai ma a lokacin ta tuna da batun yarinyar, nan ta fara dan kalle- kallen jikin Zaitoon bata ga alamun yarinyar ba. Hasalima yarinya guda ta hango can hannun wani kyakykyawan mutum, sai dai wannan kallo 'daya zakayi musu ka tabbatar cewa jinin sa ce..zuciyar ta ne ya tsinke da karfi...cikin ranta ta ayyana ina Zaitoona ta kai yarinyar mutane? " " Yarinyar tana nan tare da ita Goggo" Amsar da Shaheed ya bata ne ya sa ta fahimci a fili tayi maganar ba a zuci ba. Ya akayi ka sani...? Ya akayi kasan haka Adamu? " Sai yace " Na ganta a hannun wanda suka zo tare" shima yayi maganar yana mai waigawa inda suke tsaye. " Kana nufin wancan yarinyar?" Goggo ta fada tana nuna wanda ta hango tsaye da yarinya tana mai yatsine fuska. Da kai ya amsa ta, tana shirin sake yin magana ya mike tsaye dan baiwa ba'kin nasu wajen zama. 'Dakin nan da aka sauke su ya shiga da kansa da hanzari, ya 'dauko babbar tabarma ya shimfida musu yana kakka6e hannu yace musu bismillah ga wurin zama. Innar Zaitoon duk rikice take domin ko tambayoyin da take jerawa Shaheed a rude take yin su, dan ba halayyar ta bane. Tsoron abinda kunnuwan ta zasu jiye mata na daga rayuwar da Zaitoon tayi shi yafi rikita mata kwanya. Shaheed ne ya zauna yana fuskantar Goggo ya fara bata labarin duk abinda ya sani ata'kaice, 'karshe yace " Zaitoon ta rayu gaba na tsawon lkc ita da 'diyar ta Goggo, kuma har ta rabu da mu ban ta6a cin karo da wani abin zagi tattare da ita ba...Bata bar gida dan ta banzatar da kanta ba, ta bar gida ne kawai sbd 'diyar ta..kyakkyawar 'dabi'ar da take da shi ko a wancan lkcn shine ya kwa'daita min son auren ta sai dai ban yi nasarar cika buri na ba mukayi rabuwar bazata...haduwar mu ta 'karshe a kotu ne kamar yadda na fadi Goggo...kuma kafin inyi wani yun'kurin tunkaro inda take tuni ta sake min 6atan dabo, nayi matu'kar ba'kin ciki da rasa wannan damar a wancan ranar. Da yake ko nima a lkcn rikice nk sbd mahaifi na ga kuma ita Zaitoon...da 'kyar zuciya ta ta saba da rashin wa'dannan bayin Allah biyu..kuma har yau har gobe muna nan da kewar su cikin ran mu da fatan sake ganin su, ba ni kadai ba hatta da makwabtan ta suna kewar ta sosai Goggo musamman sbd zaman da tayi da su da zuciar 'daya...rayuwar Zaitoon abin koyi ce ga kowacce 'diya mace Goggo, rayuwa ce abin kwadaituwa ga iyaye bisa 'ya'yan su....." Maganar da Hafiz yazo yy masa cikin kunne shine ya sanya shi dakatawa da maganar da yake take ya mi'ke tsaye yana jero inna lillahi cikin ransa. Jikin mahaifin Hafiz ne ya tashi kuma har an dangana ma da asbiti tun tuni mahaifiyar sa da kanta ta sanar da shi. " I have to go Adam..bcuz i'm needed there..u pls stay with ur family Insha Allahu komai zai zo da sau'ki..." " Bazaka wuce kai kadai ba ai Hafiz...!" Shaheed ya furta yana mai sanya kafafun sa cikin takalman sa. " a a ai baza ai haka ba...kaga...." Da sauri Adam ya dakatar da shi da hannun sa, sannan yayi wa Goggo bayani amma da al'kawarin zai dawo gobe ko jibi ne da yardar Allahu...nan ya yiwa baki sallama idanun sa akan Rayyan da sam gayen ya tsaya masa a zuci tunda ya gansa...har suka tafi kalma guda bata ha'da shi da Rayyan ba. Duk ba haka yaso ba yaso yaji meke tafe da bakin nan amma Allah bai yi ba, shi kuma bazai iya banzatar da lamarin da ya shafi Hafiz ya fifita na kansa ba sbd Hafiz cikin ko wani irin yanayi ne yana nan tare da shi bai ta6a gudun sa dai- dai da rana ba. Hatta Bello a hanya suka so barin sa, ya kuma ciro ku'di mai tsoka ya mika masa dan ya koma gida kafin su dawo amma Bello yace sam shima 'kafar sa kafar su. Ammi da kanta ta bawa Innani kaf labarin da ta sani daga bakin Zaitoon dama wanda ya faru a gaban idanun ta, bata 6oye mata komai ba. Abu guda ne yafi tsayawa Innani arai shine batun auren nan da taji cikin labarin da Ammi ta bata...sai kuma batun cewa wai Aishatu 'diyar su ce ta halali...zallan iko da 'karfin mulkin Allah ne yayi aiki a wannan waje, bayaga haka taya ma hakan zai kasance? tace a can Bauchi ta tsinto ta ta kai ta gidan ta sai kuma daga baya suka fahimci ashe ma 'diyar dake tare da ita tasu ce...taya duk hakan ya faru cikin sauki haka..?anya ba wayo suka nunawa Zaitoon akan yarinyar ba, in kuma watarana dangin ta na asali suka bayyana fa...? wa za'a kama?" Sake kallon inda Rayyan yake zaune tayi Mufee na lafe a jikin sa...sam yarinyar bata tare da damuwar komai, kama ce kuma sosai ta jini a tsakanin su amma ta yaya toh suka gane ta...?" Irin duban da Innani ke binsu da shi yasa Ammi ta fahimci cewa bata fa yadda da su bane balle maganganun su domin a fili zaka fahimci shakkun dake tattare da ita. Ammin ce dai ta sake bayyana mata duk yadda abubuwan suka kasance bayan fahimtar yanayin Innanin duk da hakan kuma sai taji ina kanta ya ma kasa 'dauka sam sam. Nan ta ce ita bazata iya ba dan Allah su tafi wajen mahaifin ta tunda yana nan raye ko bashi nan ma akwai babban wanta wanda shine makwafin mahaifi agare ta, zai ma fi fahimtar su. Ammi duban Zaitoon tayi a hankali tace" Yah Bukar". Da kai Zaitoon ta bawa Ammi amsa tana mai share 'kwalla. Lokacin da zasu tafi Ammi tace" ai kamata yy dukkan mu mu je har ke Innar mu tunda kema ai 'diyar ki ce". Innani taso 'kin bin su kamar yadda Ammin ta bu'kata amma kwarjini da kamalar matar ya hanata musawa duk da tasan ba lallai ne zuwan ta gidan ya haifar mata kyakkyakyawan sakamako ba amma babu yadda zatayi, a hakan dai ta bisu suka je. Iyami na tsakar gida tayi biji biji da ita, ciwo take a tsaye da bata san kansa da tushen sa ba. Duk ta rame ta koma tamkar ba ita ba, ga cikin yarantan kaf bb mai tausaya mata illa Bukar, shi Goni kam ma tun lkcn da ya bar gida a wancan lkcn bata sake jin 'duriyar sa ba shekara biyu kenan yanzu idan watan Ramadan ya kama. Can take jin kishin- kishin din wai ai ya zama 'dan fashi da makami kuma an kashe shi ma. Damuwa tai mata yawa sosai, tana jin jiki amma ko tsinke sai tayi da gaske sannan Khausar ke taya ta dagewa cikin gidan, hatta wanke wanke yanzu ita ta ke yin abinta da kanta. Ga Abban su babu lafia shima babu mai kulawa da shi sai Yah Bukar, hatta Iyami wani sa'in sai ta yini bata leka inda yake ba, abinci wannan sai in Yah Bukar ne yazo sannan za'a bashi, shiyasa yanzu ya rage tafiye tafiye sosai, sai ya zam masa dole ne sannan yake tafiya kuma baya ta6a wuce kwanaki uku zuwa sati 'daya, ba kamar abaya da har wata guda yana iya yi ba, bubuwa duk sun dagule masa, 'ko'karin da yake kan jinyar mahaifin san yasa kullum Azeema ke faman yi masa fitina a gida and ba sosai take samun abubuwa kamar baya ba shiyasa rashin zaman lafiyar gidan ya rinjayi zaman lafiyar. Shi kanshi Yah Bukar din duk ya kare a tsaye sbd damuwa. A hkn ma wai batun auren Khausar 'din ake da Babaji tsohon saurayin Zaitoon, dan tunda ta 'kyalla idanu taga yanzu yana kashe 'yan canji Iyami tayi ruwa tayi tsaki sai da aka bashi auren khausar, sai daga baya take jin ashe wai ba a ma san sana'ar da yake ba, Iyami tayi banza da zancen ita dai in zai kashewa 'diyar ta ai shikenan..not knowing that 'kasurgumin 'dan ta'adda ya koma shima...duk wasu hare hare da aka kai a yankin su shi ke jagoranta...'dan ku'din da ake basu yake zuwa yy ta musu bagu da shi. Khausar banda 'dan banzan yawo bb abinda ta iya, ita kuma iyami bata iya tankata sai dai a bayan idanun ta tayi ta 'kananun maganganu, yayin da shi Yah Bukar tafi rainawa sama da kowa, shi ne me 'ko'karin yi mata amma kuma duk wani burbu'din masifar ta kansa take sau'kewa. Sai dai kawai yayi ta bata hakuri, shi dai fatam sa ya rabu da su lafia ne kawai. Ko yanzun ma masifa take faman zuba masa bisa laifin da yasan ita karan kanta tasani bashi ne ya aikata ba. Daga nan ta gangara wai baya kula da ita yanzu sai dai ubansa ka'dai, dan ya raina ta. Shi dai hakuri kawai yake bata...dan zuwa lkcn ya gama sabawa da 'daukan laifin da baisan mafarin sa ba balle 'karshen sa. Sallama suka ji daga bakin 'kofa atare dukkan su suka 'dago kafin su kai ga amsawa sai ganin wata matashiya suka yi ta bayyana. Gaba 'dayan su idanu suka zuba mata suna mata kallon sani banda Iyami da mi'kewa ma kasawa tayi. Duk da zuciyar ta cike yake da fargaba amma hakan bai hana ta 'karasowa gaban su ba, da sauri ta dur'kushe bisa gwiwoyin ta ta saki sabon kuka tana mai ambaton sunan Yayan ta. Sosai ya ha'de ransa yana duban ta, irin duban da ko ba a fa'da mata ba 'din nan tasan na menene. Sai da ya nuna ta da 'dan yatsan sa kafin da rawar murya yacm furta" Zai..toona.." Domin tabbatarwa. Tace" Yah Bukar..."! Inda tayi maganar cike da farin cikin ganin sa. " Me ya kawo ki gidan nan kuma...?" Ya karashe maganar yana hade ransa sosai. Tambayar da yy matan ba 'karamin hautsina mata 'ya'yan hanci yy ba...bata kai ga dawowa daga tunanin ba ta sake jin muryar sa yana fa'din. " Ki tashi ki koma inda kk fito Zaitoona, mu nan bamu bukatar sake ganin ki cikin rayuwar mu...kije ki cigaba da irin rayuwar da kk riga kk za6arwa kanki...ganin ki na sa inji tamkar wani babban ma'kiyi na ne a gaba na...ki bar gidan nan tun kafin inyi mk illah Zaitoona...." Bata motsa ba illa sautin kukan ta da ta 'karu. Tasan cewa dole zata fuskanci hakan koma fiye da shi, domin tasa duk cikin su bata yiwa kowa adalci ba tunda tayi tafiyar ta batare da sanin ko guda daga cikin su ba amma ai tana da dalili...musamman ma shi da ya bata muhimmanci fiye da kowa cikin 'yan uwan sa. " Ki tashi ki fita nace". Tsawan da ya sake daka mata yasa bata san lkcn ma data mi'ke 'da gudu tayi hanyar waje ko ganin gaban ta bata yi ba. Shi kuma da ke tsaye daga 'dan waje kaydan sautin tsawan yasa shi saurin takowa dan ganewa idanun sa, domin yasan tabbas da Zaitoon ake. Ya taho ta taho kowa da abinda ke ransa duk basu lura da juna ba karaf kawai suka yi karo, madadin yy baya shi kuma kawai sai ya rungume ta daga gefen sa yana mai bubbuga bayan ta jin irin kukan da take, ransa a matu'kar ha'de. Zaitoon da ba hayyacin ta take ba jin an tallafe ta yasa ta kwantar da kai ta cigaba da rera kukan ta tamkar mai shirin shi'dewa. Wanda bai san wace ita ba sai a 'dauka da gayya suka yi hakan. Ba Yah Bukar da abin ya 'kara turnu'ke shi ba hatta Innani sai da taji kunya ta kamata. Yayin da Ammi ta saki wani 6oyayyen murmushi tana kawar da kai gefe. Anty Madeena kuwa yi tayi tamkar bata ma san anayi ba. Yayin da Iyami ta fara tafa hannuwa da salallami...tace" Yau na shiga uku...wai menene nake gani haka ne? Bayin Allah nan ba gidan 'yan iska bane ba kuma dabar karuwa ba ce! mu 'din salihan bayi ne masu mutunci a idanun kowa, 'yar iskan gidan ta jima da barin sa ta tafi yawan barikin ta wata mai kama da waccan...dan Allah ku fita ku bamu wuri..kh fita ku bar mana gida bama bukatar irin ku yanzu...." Dogon tsaki Yah Bukar yaja sannan ya nufi hanyar barin gidan a zuciye yana cije la66an sa, sam sam kalaman Iyami basu yi masa dadi ba amma yadda yaganewa idanun sa sai yaji takaicin sa ninka na baya, hakika Zaitoon ta wuce tunanin sa a halin yanzu, duk ina tarbiya da nasihar da ya sha 6ata lkcn sa yana yi mata abaya ina hankali da natsuwar ta suka tafi ne..? Kafin ya kai ga barin gidan gaba 'daya Innani tayi saurin ri'ko hannun shi...sannan a hankali tace. " Dan Allah kayi ha'kuri Bukar, badan ita ba, ko dan darajar bakin nan ka tsaya ka saurare su.." Matar na da matu'kar kima da daraja a idanun sa kuma bazai iya musawa umarnin ta ba...balle kuma rokon sa tayi, hada sa da Allah tayi. Kallo 'daya Innani tai wa gidan tasan cewa ya canza ba kamar yadda ta sanshi ada can baya ba, ita dai kam rabon ta da gidan har ta mance...ko ayau din kuma in da badan dalilin yakai dalili ba da babu abinda zai shigo da ita. 'Daga kai Bukar yyi nan yy arba da Hajia Ammi Asiya, gefen ta Anty Madeena ce da tun zuwan su garin tamkar ansawa bakin ta Padlock bin komai kawai take da idanu..sai Rayyan da ke can rungume da Zaitoon ga kuma yarinya kwance saman kafa'dar sa daga 'daya gefen tana baccin ta cikin kwanciyar hankali. Marwa dai na can gida dan sam Rayyan hanawa yy ta biyo su sbd saurin ru'dewar ta ...dan haka babu ita wurin. Lokacin da Bukar ya sa babbar tabarma akayi musu iso sannan Anty Madeena dake 'dan kusa da shi tace" toh sai aje a zauna idan an gama rasar kunyar". Ta fa'da masa 'kasa 'kasa. Wata uwar harara suka sakarwa juna shi da Bukar kowa abinda ke cikin ransa daban. Dai dai da shigowan Khausar gidan tana 'dan rare wa'ka irin wanda ta saba. Dama tunda taga motoci a wajen dole tasan akwai baki gidan amma rashin sanin su wanene ya sanya bata wani damu ba dan ta san ba su da kowa a birni balle tace ko yau sun samu arzikin ziyara...sai tafi bayar wa aranta cewar ko sunyi 6atan kai ne ko kuma ba'kin mai garin ne suka ajiye motocin su a wajen. Cikin sa'a tana sako 'kafarta gidan idanun ta akan fuskar Ammi Aseeyah ya sauka ilai kuwa bata santa ba..arai tace" ohh ashe dai bakin na gidan mu ne.." Ta 'karashe da kya6e baki. Tana shirin kawar da kai sai idanun ta suka 'kyallo mata matashiyar yarinya mai kama da wacce ta sani, tasha jilbab 'din ta onion colour babba har 'kasa...fuskar ta tayi fayau tayi kyau abinta tamkar wata 'diyar sarauta. Bu'de idanu tayi sosai lkcn da ta fahimci wacece ita. Da hannu ta nuna ta ledan dake hannun nata na fa'duwa, 'kasa- 'kasa ta furta sunan.." Adda Zaitoona..." Gaba 'daya kanta idanu suka koma sannan wasu suka kalli ita Zaitunan. " Dama kina nan? abin mamaki!...ina kika shige haka?..kika 'karo kyau,toh har kin gaji da tara yaran ne kika tuno damu aka le'ko mu...?" Wani banzan kallo Rayyan da Anty Madeena suka jefe ta da shi a lokaci guda amma duk bata kula ba. Ita Zaitoon ma kanta na 'kasa tsananin kunyar shiga jikin Rayyan da tayi a rashin sani ne ya dame ta...amma yadda kalaman ta suka doke ta yasa bata ma an lokacin da ta furta sunan ta da 'karfi ba. Sautin sunan Khausar da Zaitoon ta ambata shi ya zaburar da Iyami ya kuma sa ta samu 'kwarin gwiwar mi'kewa tana duban ta tace" Bana son shashanci fa Khausar!..wacce Zaitoonar kk nufi wai..?" " Iyami wai kina nufin baki gane ta ba? wlh Zaitoona ce...Zaitoonan mu ce Iyami Zaitoonan Yah Bukar..Zaitoonan gidan mu ce!" Kasake Iyami tayi tana duban ta baki bu'de sai kuma can ta sake mayar da duban ta ga wacce akacr Zaitoona ce ta 'kura mata idanuwa...ita dai taga kamanni kawai. A har yanzu ta kasa yadda ita 'din ce da gasken gaske. Amma yanayin tsayuwa da kuma yanayi taga sak irin na Zaitoonan gidan ce. Lkcn da ta fahimci wace dagaske hannu ta 'dago ta nuna ta da 'dan yatsa tana mai 'kwalalo idanuwa da rawar murya tace" Ke ce...?" Adai- dai lkcn kuma Inanni tayi saurin furta.." Bukar dan Allah aji da ba'kin nan, ayau suke so su koma fa..Allah yasa mahaifin ku ma na kusa dai..." Khausar ce tayi saurin bada amsa da fa'din." Ai babu inda yake zuwa yanzu Innani, yana nan cikin 'dakin sa wata'kila bacci yake...". Ga Zaitoona ta mayar da duban ta inda ta cigaba da fa'din " Zaitoona wai dan Allah ina kk shige ne haka...? Da yaren su tayi wannan tambayar tana mai bada hankalin ta kacokam gare ta. Kallo 'daya Innani tai wa gidan tasan cewa ya canza ba kamar baya ba, ita dai kam rabon ta da gidan har ta mance...ko ayau 'din kuma in da badan dalilin yakai dalili ba da babu abinda zai sata shigowa. 'Daga kai Bukar yayi nan yy arba da Ammi Aseeya, gefen ta Anty Madeena ce sai Rayyan dake tsaye, dan Marwa sam Rayyan hanawa yy ta biyo su. Lokacin da Bukar ya sa babbar tabarma akayi musu iso a sannan Anty Madeena tayiwa Rayyan alamun ya 'karaso mana. Rungume yake da Mufeeda akafa'dar sa tuni ma baccin ta take...amma idanun sa na kan Zaitoon da har a lkcn idanuwan ta ke zubar da ruwan hawaye. Bukar ne yaje ya kamo hannaun Abban su ya fito da shi bayan yace masa baki akayi. Ji da ganin sa sosai suka samu rauni a yanzu sbd rashin lafiyar da yake fama da shi, ko da ya sake tambayar Yah Bukar " ba'ki daga ina? ko dai Gonin sa ne ya dawo gida? Yaa Bukar yace masa" a a Zaitoona ce da wa'dansu mutane". Da jin sunan Zaitoona ya waro idanun sa cike da tsantsan farin ciki yake sake tambayar Bukar domin tabbatarwa. Kafin Yah Bukar ya bashi amsa Zaitoon da tun fitowar su da idanun ta ya sau'ka kan mahaifin ta taga yadda aka ri'ko shi kawai ta tabbatar baya da lafiya isashshiya. Da gudu ta taho wajen da suke dai dai Bukar na ajiye sa a tabarma ta fa'da jikin su duk biyu ta saki kuka gwanin ban tausayi tana fa'din " Abban mu..."! Lalu6e da hannun sa ya fara da jin tashin muryar da ko cikin mafarki yaji ta baya 'kaunar abinda zai yankar masa da baccin adaidai wannan lkc balle kuma a zahiri uwa uba kusa da shi. Da hannun sa yake lalau6en inda take cikin hanzari bakin sa har na rawa wajen ambatan sunan ta. Sai ga hawaye ya sakko masa shaarrr. Lokacin da ya ji hannun sa ya ha'du da na 'diyar tasa wani irin gagarumin farin ciki ne ya lullu6e shi..farin ciki ne na asali mai fita tun daga can 'kasan zucia, farin ciki ne marar misaltuwa. Innani kawai sai ta kawar da kai tamkar bata ga abinda yake faruwa ba amma tabbas ya bata tausayi sai dai tausayin ragagge ne musamman idan ta tuna cewa kusan shine silar komai, da ace bai hana Zaitoona zama a gidan sa a wancan lkcn ba da wancan 'kadararren al'amrain ba da hakan duk bai faru ba...a hakikanin gaskia idan tace bata jin haushin bawan Allahn toh wallahi tayi karya, sai dai bata zafafa har na sosai ba...ta kan bawa kaddarar Ubangiji rinjaye fiye da komai. Da rawar murya Abban yace " Zaitoona ta...ke ce?..kece ko kuwa mafarkin da na saba yi akan ki ne kowace rana yau ma nake yi...?" Da kai ta bashi amsa cikin ru'dewa tana mai sake sanya hannun ta cikin nasa still tana kuka. " Ina kk shige Zaitoona kika tafi kk barmu tsayin lkcn nan?" Kasa bashi amsa tayi ganin yadda yake magana da 'kyar sai taji baki 'daya ta 'kara karaya tayi sanyi. " Nayi nadama Zaitoona, sosai nayi nadaman abinda nai mk abaya, abin ya dame ni sosai amma ban san ta inda zan fara neman ki ba..ban san nayi kuskure ba sai da akace min kin tafi bakya garin nan, na 'dauki abin wasa da farko, sai daga baya na fahimci dagaske ne fa kin min nisa...me yasa kk yi saurin yanke hukunci batare da kin kuma waiwayar mu ba..ina kk shiga tsawon lokacin nan..?" 'Karfin kukan da ta sanya shi ya sa shi dakatawa da maganar da yake yayi shiru yana jin ta, ji yake shima tamkar ya taya ta kukan, wai yau ga Zaitunan sa nan ta dawo duk da dama bawai ya cire rai da rabon sake ganin ta ba ne, amma tunanin ina ta shiga? fargabar sa kullum wani irin hannu ta fa'da? wace iriyar rayuwa take yi? wa ke bata abinci? Wake kula mata da yarinyar...kusan kowani wadannan tunanuka ke sako agaba su hana shi natsuwa...kullum kwanan duni da Zaitoon yake bacci a ransa...amma bai ta6a zaton cikin 'yan kwanakin nan zata dawo gare shi ba. Zai sake magana Bukar yy saurin janye jikin sa yana matsawa gefe yake fa'din" Abban mu tare take da ba'ki fa gasu nan ma kusa da kai zaune...." " Au toh" Yace yana mai 'dago kai, duk da dishi dishi yake gani ba sosai ba amma a hakan idanun sa na iya tantance masa yawan bakin nasa sai dai bazai iya ce ga kammannin su ba. Rayyan dake gefe duk wani motsi da tayi idanun sa na a kanta ne, da kanshi har ma sai ya fara bawa kansa haushi...a ganin sa za'kewar tasa na neman yin yawa, sai dai wata zuciyar tasa tayi saurin garga'din sa akan cewa ai matar ka ce kuma mallakin ka ce dole ka kula da komai daya dangance ta...balle irin kukan da yaga take yi yanzu sosai yk sosa masa zucia. Take yy na'am da batun sai dai bai sake yadda ya biyewa idanun sa ba ya sunkuyar da kai yana gyarawa Mufee 'dan Baby hijab dake jikin ta. Iyami ce ta harzu'ka ganin yadda cikin mintina 'kalilan aka cike musu gida alhali basu san kowa daga cikin su ba kamar yadda basu gayyaci kowa zuwa gidan su ba. " Wai do Allah bayin Allah meke faruwa ne? Na kasa ganewa..kun zo kun cika mana wuri kun mana zaune a gida batare da munsan su waye ku ko kuma dalilin zuwan ku ba...lafiya..?" Anty Madeena ce tayi caraf tace..." Muma baiwar Allah ai ba wai gidan zaman muka rasa ba, munzo ne sbd wata kwakkwarar dalili, wato sada zumunchi da kuma sake 'karfafa shi kawai...'diyar ku Zaitoon ita muka rako bayan tarin abin alkhairan dake 'kunshe cikin baku nan mu..." Ta kai 'karshen maganar ne tare da kawar da kai gefe tamkar dama can akwai wata 'kulalliya tsakanin su. Barka da zuwa Abban su Zaitoon yy musu sannan aka hau gaisuwa, Iyami dai na gefe tayi tsumu kamar yajin 'kosai....tun 'dazun sunan wancan yarinyarcake ta ambata while ita har a lokacin bata ga Zaitoonar b ta ga mai kama da ita. Ga kuma Khausar da itama ta kasa barin wajen so take da kunnuwan ta taji me ke tafe da su ba wai abata labari ba. Lokaci- lokaci take kai duban ta izuwa ga Rayyan dan gayen tun 'dazun da tayi tozali dashi taji ya shige ranta farat 'daya, 'dan banzan birge ta yayi shi da yarinyar da yake rungume da shi, gashi tunda yazo bataji ya furta komai ba. Yarinyar dake jikin sa ta koma kallo dan yadda taga yake nan nan da ita tashin farko zaka fahimci yadda yake ji da ita....sosai ta jinjinawa sbta da gayun da akayiwa yarinyar tamkar 'diyar turawa. Bacci take amma tana ta turo baki...hakan sai ya bawa Khausar daria..amma sai ta murmusa. Sosai taji yarinyar ta shige ranta. Bayan gaisuwa Anty Madeena ta fara gabatar musu da abinda ke tafe da su dan wannan karan jikin Ammi sanyi yi yayi sosai musamman sbd yadda taga Zaitoon ke kuka. Tun daga farko Anty Madeena ta basu labari tun barowar ta gida, mahaifiyar Zaitoon motsin kirki bata iya tayi ba da yake ta riga taji komai a halin yanzu tamkar maimaici ne ake yi mata dan ko Adam ya 'dan labarta mata wani yanki daga ciki. Yah Bukar kuwa rashin motsin sa ya samo asali ne daga tsuma da tafarfasar da zuciyar sa ke yi masa, jin dalili da kuma kalar irin rayuwan da 'kanwar sa ta faro. Ammi ce ta bawa Zaitoona daman cigaba da yi musu bayani da kanta domin aganin ta zasu fi tabbatar wa, bata so hakan ba amma bb yadda zatayi, haka take basu labarin tana yi tana kuka, lkc zuwa lkc take kai hannu ta share hawaye. Gurin yy tsit bb mai motsin kirki kowa na saurarenta ne, mamaki da ban al'ajab ya cika zuciyar ahalin ta kaf, na yadda tayi tunanin tafia ta barsu akan 'diyar da ita kanta bata san tushe da asalin ta ba. Ta jure irin wannan wahalwahalun rayuwar a 'dan shekarun tan nan alahali tana da mahaifa both side ga yan uwa masu son ta. Duk dauriyar Yah Bukar sai da ya share hawaye, haka ma mahaifin ta da dama dannewa kawai yake yi, Innani kam ai ba a cewa komai. Abu guda da take gode Allah akai shine da bai sa 'diyar ta ta fa'da harkar banza ba kamar yadda mafiya yawan 'yan garin nasu ke hasashe cewa abinda ya fitar da ita kenan. Ta kuma gode Allah har kamar zatayi sujudur shukur ma na yadda Allah ya tseratar da ita daga hannun 'yan iska titi..Bbn Abdul, Sultan da sauran su...ta gode Allah da ba'a samu nasarar kashe mata yarinya ba. Tun kafin Zaitoon ta kai 'karshen labarin nata Mufee ta farka a bacci sai dai luf tayi jikin Rayyan tana rarrabe idanu, jin yadda sautin muryar Mammin ta ke fita kuma cikin kuka ya sanya Mufee 'dagowa da sauri tana lalu6en inda zata ganta da idanu. Da ganin ta kuwa ta mi'ke tsaye ta nufi wajen ta cikin hanzari tana fa'din" Mammi..!" ta fa'da jikin ta.. Zaitoon sai ta rungume ta sosai wani sabon kuka na zuwa mata...tamkar zata maida ta cikin ta, wani sabon kaunar yarinyar ne ya shige ta a halin yanzu. Duk kan idanu sai ya dawo kansu ita da Mufee, ga wa'danda basu sani ba tunani suke mecece alakar Zaitoona da yarinyar nan...yayin da su Ammi.da suka riga suka sani murmushi kawai tayi..tasani indai Zaitoon da Mufeeda ne fiye da hakan ma za'a gani. Babu wanda yakai Yah Bukar, Khausar da Iyami waro idanu akansu...kar dai ace ace...kalma yake ta so ya ha'da amma ya gaza ha'dawa. Iyami kuwa tararradi take dama, anya kuwa wannan labarin gaskia ne?...sam ma bata gama yadda da cewa wannan ita ce Zaitoonan su ba..sbd kusan komai nasu ya bambanta da tasu Zaitoonan illa kamanni...amma ita wannan kyakkyawar yarinyar fa? Kar dai ace itace 'diyar Zaitoon wacce ta bar gida domin ta? Lokacin da takai 'karshe a labarin kusan za'a iya cewa daga Azeema dake can tsaye dan tsakiyar labarin ta samo bayan shigowan ta sai Iyami su ka'dai ne basu share hawaye ba..hatta khausar sai da ta zubda hawayen tausayin ta. Tace " Abban mu ". Ya 'dago kansa ya dube ta. Hannun ta tasa cikin nasa..ta kuma sanya na Mufeeda a tsakani tace..." Abban mu ga Aishatu na nan Allah ya raya ta, ta girma...Abba halin yanzu kana da ikon yanke hukunci tsakanin ni da ita, sbd a halin yanzu tafe take da garkuwan ta, tana da bangon da nasan zata dafa a rayuwa, tana da tsani ma'ana tana da ahalin ta kewaye da ita.. Abba ko abaya ban tafi sbd son zucia ta kawai ba Abba na tafi ne sbd tausayin ta, na amsa cewa nice na haifeta ne sbd tausayin ta kawai Abbah, nasan kona rabu da ita hannun wasu daban zata fa'da, bani da tabbacin zata samu isa ga mahaifin ta ta rayu tare ta da shi, bani da tabbacin zata samu ingantaccen rayuwa fiye da wanda zan iya bata, shiyasa na 'kwammaci ni in ri'ke ta awaje na...domin ni mahaifiyar ta ta bawa amanar ta Abba...na kwammaci insha kowacce iriyar wahala a rayuwa sbd ita domin ganin ban yi wasa da amanar da Allah ya dam'ka min ba...Abba ka yafe min...nasan abaya na 6ata maka sanadiyan Mufeeda...na kuma gode Allah daya bani damar zuwa da 'kafafuna gareku ya kuma bani ikon neman yafiyar ku da halshe na...Innani ku yafe min dan Allah..." Ga Yayan ta koma tace" Hamma ni nasan mai laifi ce awajen ka, bani da baki ko kalmar da zan baka hakuri, bani da wata gamsashshiyar kalmar da zan furta agare ka, amma Hamma kasani tsawon rayuwa ta inajin sam ban kyauta maka ba, tsawon rayuwar da nayi bana gaban ka kowscce rana ina jin ban kyautawa halaccin ka ba Hamma...ka yafe min....nasan ka riga ka sani Hamma bani na haifi Aishatu ba...amanar ta aka bani, ga mahaifin ta nan zaune, mahaifiyar ta anan garin namu aka akashe ta, ga dangin ta nan kewaye da ita kuma suna matu'kar 'kaunar ta...ko daga yau na rabu da Aishatu bani da wani sauran buri Hamma, sbd nasan zata rayu cikin farin ciki, zata rayu cikin mahaifa da 'yan uwan ta, wa'danda na tabbatar sun ninka ni 'kaunar ta..Hamma ko daga yanzu kace kar in sake ta6a jikin Aishatu har abada bazan sake ba......" Kai yayi saurin girgiza mata...yana mai janye hannun sa..amma ya kasa fa'din komai. Taya ma zai ce hakan, taya take tunanin zai furta hakan? Bayan da idanun sa ya gani, yarinyar daga jikin wanda akace shine mahaifin ta ta tashi...duk yawan su awajen bata ga kowa ba sai Zaitoon, ga Zaitoon ka'dai ta tafi ta fa'da jikin ta sbd 'kauna da soyayya, ta 'dauke ta ne tamkar mahaifiyar ta, 'kauna ce ta asali a tsakanin su, 'ka'kkarfar ala'ka ce tsakanin su a fili zaka fahimci haka, shi wane da ya isa ya raba wannan ala'kar? Sam bazai iya ba...bazai ma fara ba. Tunda Iyami taji cewa wa'dannan da suke tare sune mahaifan yarinyar Zaitoona ba 'karamin mamaki ne ya kama ta ba har ma da su sauran jama'ar. Allah cikin ikon sa ashe 'diyar manya ke tare da Zaitoonan basu sani ba...suka wulakanta baiwar Allah. Abu guda da Zaitoon bata fa'da musu ba shine batun auren dake kanta ahalin yanzu. Dan dama gudun ta kenan tun farko, bata so har lokacin zuwan su nan batare da an warware mata shi, ba bata so 'yan uwan ta su san da batun barin ma Yayan ta shiyasa ta kasa fa'da ko cikin labarin. Ammi kuwa bu'dan bakin ta bayan wani 'dan jawabi da tayi abinda ta fara furtawa kenan ta kuma nuna Rayyan matsayin mijin Zaituna ahalin yanzu... 'Kasa sosai ta 'karayi da kanta dan ko ba a fa'da mata ba tasan dole akwai wani canjin yanayi tattare da mahaifi har ma da Yayan ta Bukar, ilai kuwa hakan ne, sai dai sa6anin yadda Zaitoon tayi tunanin ita zai wa banzan kallo Ammi kawai ya kurawa idanu yana jin in bai yi hakan ba tamkar ba fahimtar ta zai yi yadda ya kamata ba. Afuwa ba 'dan ka'dan ba ammi ta nema bayan nuna tsantsan godiyar da tayi akan ri'kon da Zaitoona da yiwa 'diyar su, ta kuma yaba mata sosai kan wahalhalun rayuwa 'kunci, 'kalubale da kuma bautar da duk tayi domin ta.. harma da mahaifan nata baki 'daya ta yaba ta kuma gode musu. Ta kuma ce ba wai sun tilasta bane ko kuma zasu tilasta ba, amma suna masu ro'kon alfarma akan dan Allah su dubi girman Allah da manzo su dubi alkhairin da yarinyar nan ta yi musu su bar musu ita matsayin matar Rayyan, ta hakan ne ka'dai suke ganin zasu fi saka mata alkhairin da tai musu..amma sai in sun amince itama ta amince...tukunna. Anan Yah Bukar yy caraf yace wannan ne kuma bazai ta6a faruwa ba Hajia...Yace duk cikin su bb wanda zai sake amincewa Zaituna ta yi musu nisa kwatankwacin wanda ta yi musu abaya, bayan da kunnuwan su suka ji irin tarin wahalhalun da ta sha abaya acan 'din...yace sam dole sai dai a raba wannan aure. " Abubakar..."! Abban su ya 'kirayi sunan sa yana mai 'ko'karin sanya idanun sa cikin nasa. Yace " Sam ba haka na sanka da zafin rai ba...!" " Abbah babu inda Zaitoona zata sake komawa..ka barni in fada musu gaskia Abbah...agaba na nake so tayi aure ta kuma rayu kusa dani ba can wata uwa dunia inda kowa nata ba lalle yasan inda take ba...". Murmushi kawai Abban yayi..Baffa Liman ma cewa yyi zancen Habu gaskiya ne tunda ta dawo bb kuma inda zata sake koma wa a koya mata yahudanci...tunda 'diya dai kun gano cewa taku ce sai ku 'dauki abarku kuyi gaba, Allah ya ji'kan mahaifiyar ta ya kuma kiyaye na gaba, itama Zaitoona Allah ya bata ladan ri'kewa da wahalwahalun da tayi. Salmerh😍 [23/01, 6:51 am] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Wattpad@* _Serlmerh-md_ 🅿️ *...102* .......Wannan maganar ya matu'kar sosa zuciyar Anty Madeena da ma Rayyan kan sa, a wannan ga6ar Ammi ce ka'dai ta iya tankawa da" Ameen Ameen"..tana murmushin da iyakar sa kan fuskar ta ne kawai...domin a fili ta fahimci wani abu guda dangane da shi wanda aka 'kira da sunan wan mahaifin Zaitoonan. Bayan tattaunawar su tayi nisa ya iso da niyyan duba jikin 'kanin nasa sai kuma ya tarar da su suna kan maganar. Bata yi jayayya da su ba tace" bakomai..tana mai 'kara neman afuwar su kan shishshigin da suka yi na 'daurawa Zaitoon aure da ba tare da amincewar su ba..."! Wannan karan Abban Zaitoon ne ya amsa da " ai bakomai...sune ya kamata ma suyi godia..domin yadda ce ta kawo hakan, da basu yadda da ita da tarbiyar ta ba ai bazasu fara ha'da ta aure da 'dan su na cikin su ba..dan haka su ya kamata su gode acewar sa, ai shi aure garkuwa ne, aure 'karin martaba ne da kariya ga duk wata 'diya mace...shi dai a 6angaren sa bai 'kalubalanci hakan ba..sbd tun farko ai laifin su ne, da basu 'ki 'diyar su suka kasa zama da ita ba ai da hakan bai faru ba...toh ina laifin wanda ya tallafi naka, ina laifin wanda ya 'kaunaci naka a lokacin da yafi bu'katan taimako....?" Ammi tace " hakane...duk da hakan kuwa ya zam dole su gode su nemi afuwar su, dama kuma ba wai sun zo dan su tailasta bane, sun zo ne kawai dan nuna godiya gare su baki 'daya...tace tana fatan ha'duwar su ta kasance musu alkhairi a tsakanin su, alkhairi kuma mai 'dorewa har abada, idan kuma rabuwar kenan tana fatan zumunci ya 'karfafa tsakanin su kar a yada shi, tunda Allah ya riga ya ha'da. Ta 'kara nuna yabawa da sosai ga Zaitoon acewar ta har abada bazata gaji da gode mata ba domin kuwa tattausan zuciyar ta yasa komai ya faru..taimakon da tayi musu kuma ire- iren taimako ne da bakowa ke jure yin irin sa ba shiyasa ta bawa Zaitoon lamban yabo, dole ta jinjina mata, tayi matukar nuna jajircewa da jarumtaka a matsayin ta na yarinya mai 'karancin shekaru...tace har abada bazasu iya mancewa da ko guda cikin abubuwan da tayi musu ba, shiyasa suke fatan su 'karasa rayuwar su tare da ita amma tunda su mahaifan nata basu amince ba shikenan...su zasu koma..Allah yasa hakan shine mafi alkhairi gare su baki 'daya. Yadda Rayyan ya 'kurawa Ammi idanu bisa wannan karkatacciyar maganar ta ta har sai ya baka daria..duba da yadda yy kicin kicin da fuska..amma ba kowa zai iya fahimtar yanayin da yake ba sai wanda ya san shi sosai, lkc guda kuma yaji yy nadamar biyo sun da yayi ma duba da yadda ko kadan Ammi bata damu da shi damuwar da zai iya shiga ba take wani magana, meyasa tun farko da ya ajiye su bai koma ba ne? yace da yasan wannan shirmen za'a yi wlh da bai biyo su ba...kawai ya barsu da Fawwaz. 'Kirr ya tsaida idanun sa akanta so ma yake su ha'de idanu amma Ammi ta'ki bashi wannan damar sam. Cikin su babu wanda yace komai, Anty Madeena ma na son tace wani abu amma ta dake ta hana kanta tankawa. Gefe guda wata uwar harara take bankawa Rayyan da zaka rasa gane ko ta mecece. Zaitoon dai na nan zaune har a lkcn bata bar share hawaye ba...bata san takamammen yanayin da take ciki ba a halin yanzu illa bugun da take ji zuciyar ta nayi mata, bugu kuma da 'karfin gaske, bata kuma san dalilin hakan ba, ta dai san tana farin ciki, yau ga ta ga ahalin ta, ga ta ga mahaifi da mahaifiyar ta ga kuma 'yan uwan ta nan duk kewaye da ita amma ta rasa dalilin wannan damuwar da take ji ke sake taso mata sabuwa...da kyar ta samu ta lalu6o dalilin bai wuce na fargaban tafia da Mufeeda da take tunanin za'ayi ba ne ya sanya ta jin hakan. Sai dai lkcn da aka tsaida magana akan su zasu wuce amma zasu bar mata Mufee na kwana biyu in yaso zuwa lokacin da za'a zo 'daukan ta idan sun yanke shawara to sai a san wani mataki ya dace a 'dauka in ma takardar sakin ne ko kuma cigaba da zaman su, za6in naga iyayen Zaitoona ne. Baffa Liman yy karaf yace" Ba wani shawara Hajia..kawai a sakar mana 'diyar mu abinda mukafi bukata kenan a halin yanzu..." " Toh bakomai ranka ya dade Insha Allahu za'a kawo mata takardar ta...a hakan ma mun gode bisa karamcin da aka nuna mana..Allah ya 'kara girma..." Fawwaz abokin Rayyan shine yayi wannan maganar da alamun tabbatarwa. Wata uwar harara Rayyan ya banka masa Fawwaz duk na lure da shi amma yayi tankar bai gansa ba. Daria kawai yk kunshewa a cikin sa. Da rufe bakin sa Ammi ta cigaba...amma ita dai suyi mata duk hukuncin da zasu yi mata bisa duk abubuwan da yafaru indai sunga dacewan hakan burin ta guda ne a wajen su, tace su taimaka su bar mata 'diyar ta kar su ce a a, tace kar su yi tunanin cutarwa ko kuma wani abin daban tace koda ace Zaitoona ba matsayin matar Rayyan take ba a halin yanzu ya zam mata dole ne ta kula da ita da rayuwar ta, balle ace ta cigaba da kasancewa 'karkashin inuwar gudan jinin ta tace tamkar sauran 'diyoyi na nake ji da ganin ta...bazan ta6a bari wani abin ya same ta ba nayi muku alkawari... dan Allah kuyi hakuri ku sake bani wannan damar akan Zaitoon, kar ku raba auren nan, bamu san alkhairin da Allah ya 6oye acikin sasa ba... kuma fatan itama Zaitoonan kar tace a a..domin rashin amincewar ta kan batun daidai yake da rushe duk wani ginin da suke kokarin 'dagawa a halin yanzu. Ta fadi hakane dan tasan cewa ita kanta Zaitoon ma rigimammiyar kanta ce...ba abin mamami bane tace bata son zama da Rayyan musamman yadda ta ganta tsundum cikin ahalin ta. Komai Ammi bata basu ba dan ma kar suce sbd Zaitoona ne ko kuma dan wani abu, duk tarin alkhairan da suka zo da shi haka suka koma da abin su. Ita dai fatan ta su amince ne kawai sbd Allah ba dan wani abu ba....sun yi rabuwar alkhairi bb yabo bb fallasa...Rayyan ne farkon tashi ya fita ya shige mota na biyun sa Anty Madeena ce sai sauran suka fito daga baya. Yadda yake wani ha'de rai ya sanya Fawwaz 'kyalkyacewa da daria sosai. Yace..." Wai me yafaru ne kk wani ciccin magani..?" Wata hararar ya 'kara banka masa amma bai ce komai ba. " Tambayar ka fa nake...?" Yace " Ban sani ba.."! Fawwaz ya cigaba " Banga laifin ka ba dai...babu mamaki ciwon baki ne ya kamaka batare da mun sani ba...haba ni dai nace ko...tunda ba hana mutum magana akayi ba ai duk hukuncin da muka yanke dole a kar6e sa hannu bibbiyu..hadda wani ban sani ba...ina tabbatar maka da cewa zaka sani ne watarana..ba yanzu ba..sai lokacin da ka budi idanu kaga an daurawa baiwar Allahn aure da wani kafin zaka sani". " Only if kai ne zaka sakar min da ita kenan"! 'Yar Daria Fawwaz yy yana 'daga hannuwa sama yace" Ni a suwa kuma? Kaine da kanka zaka yi bani ba" Idanu Rayyan ya lumshe yana shafa go shin sa a hankali 'dan 'karamin nazari ya tafi, dagaske fa bai tankan ba ashe a can...toh amma har aka yi zaman aka gama ma ai bai ga hurumin magana awajen ba, mai ma zai ce toh. Sai bayan tafiyar su Ammi..Zaitoona ta fahimci ba wai farabagan rabuwa da Mufee bane ka'dai ke damun ta tunda gata ga Mufee a halin yanzu amma kuma bata daina jin fargaba da rashin sukunin ba, ta kuma rasa inda matsalar take...wata 'kila tunanin Marwa ne...ko kuma rabuwa da su Ammi...'karshe akan abinda ta bari kenan. Rayyan ma ko cikin motar bai ce da kowa uffan ba, duk irin tsokana da Fawwaz ke masa bai tanka shi ba...har suka isa cikin garin Maiduguri. Ammi duk na lura da shi. Can gidan su Ammi duk suka sau'ka, Washegari kuma suka yiwa gidan su Nadia diran mikiya. Sun sha hirar yaushe gamo...an jajantawa juna kan abubuwa da dama sannan aka hau hirar rayuwa. Nan suke basu labarin duk abinda ya faru. Sun yi matu'kar mamaki suma sun kuma nuna tsantsan farin cikin su a fili...sun kuma ce ko bakomai ya zam dole su ma su bada gudunmawa. Rayyan kam aranar ma 'kin kwana yy yabi hanya ya koma Kano abin sa ransa a matu'kar jagule. Duk yadda Abban Zaitoon yaso janyo hankalin Bukar da Baffa Liman sam sun 'ki fahimtar sa...kuma yasan ba shi da ikon tilasta su musamman ma shi Bukar 'din sbd yafi shi iko da Zaitoona. Dole sai dai yy amfani da kalaman kwantar da hankali dan janyo hankalin sa. Ya nuna masa mutuntaka da karamci da ya fahimci mutanen na da shi, sannan da ace masu cutarwa ne da bazasu yadda su biyo Zaitoonan har nan 'kauyen ta ba, tunda sun riga sun samu 'diyar su a hannun su amma basu yi hakan ba. Yace...kuma shi aure ai Allah ke ha'da shi ba wai iyawar mu ba, yace ka duba misali mana lkcn da take nan gida shekarar ta nawa da zancen auren Babaji? 'dan uwan ta ne amma kuma auren ya kasa yiyuwa sbd wasu 'kananun dalilan da mu da kanmu ba zamu iya ce ga irin su a zahiri ba balle har mu iya magance su..sam Allah bai bamu damar tantancewa ba...kasan dalili...? Ya girgiza kansa. Abba Yace" Saboda Zaitoona ba matar sa ba ce tun asali..." " Ka duba yadda wannan auren nata ya kasance? a yadda suka fa'da kai kanka kasan mu'kaddari ne kawai da kuma shirin mahalicci...basu ka'dai ba, bashi mijin ba hatta su iyayen nasa da suka shirya shi yazo musu ne a bazata da yake Allah ya riga ya rubuta sai anyi...baka ga anyin bane ?" Toh Bukar mu su waye da zamu ce sai mun raba abinda Allah da kansa ya shirya ya kuma ha'da shi? " Nasani da kanka kasan cewa ba mu ke rubuta 'kaddarar mu da hannun mu ba, ko kuwa ka mance cewa kowa da kalan tasa 'kaddarar yake tafe ne a rayuwa...? Mene amfanin sakin nata da za'ayi indai an yadda da nagartar mijin nata ai rabuwar babu amfani, baya ga haka ma bb wata matsala gagaruma a tsakanin su, ba rashin ci ba, ba rashin sha ba, ba rashin kwanciyar hankali ba..ba kuma wata cutarwa ake mata ba..dan Allah Bukar abarta tayi zaman auren ta kawai sbd Allah. Muyi mata fatan alkhairi, ka kyautatawa kowa zato..kayi mata fatan samun aljanna sanadin wannan aure bawai burin raba shi ba, dan Allah kayi hkr kaji ba wai na matsa bane kawai inaso ne..." Shiru Bukar yy bai iya ya sake fa'din komai ba. Ire- ire wannan maganar kusan ko wani lokaci idan zama ya ha'da shi da mahaifin nasa yake masa..kuma ya fara yi masa maganar ne tun washegarin tafiyar su Rayyan da safe daya je duba shi. Amma shi dai har yanzu ya kasa jin amincewa. Yana nan dai akan bakan sa na son zaman Zaitoona kusa da shi. Iyami kuwa dake yawan musu la6e kwafa kawai take yi tana cije baki. Kusan kullum hakan ke faruwa, haka zata tsaya ta jira wucewan Bukar ta sau'ke ruwan masifa kan Abban nasu...haka take yi masa kullum amma ya kasa canza ra'ayi, kamar yadda shima Bukar ya kasa jin aminta da batun da Abban ke zuwan masa da shi. Ita kuma Iyami da gangan take hura masa wuta dan ya janye maganar amma yya 'kiya...wannan karan so yake ya yiwa Zaitoon adalcin da tun tasowar ta gaban sa bai ta6a yi mata shi ba dai- dai da rana guda a rayuwar ta. Idan ta gama sau'ke masifan ta fita cikin gida sai ta 'daura da gorace gorace habaici da 'kananun maganganu...wai kwa'dayin abin dunia yasa shi nacewa kan batun...kuma indai hkne itama Khausar an fasa auren ta da Babaji sai dai ya samo mata wani 'dan birnin itama ta aura. " Kice dama damuwar kenan?" Sai anan ya tanka ta. inda ya cigaba da fa'din " wannan ne kuma baku isa ba.. daga ke har mai goya muku baya din, tun farko ku ka amince har aka gama magana dan hk wannan aure kamar an yisa an gama ne". Bai tsawaita ba yy shiru...Iyamin ke ta faman masifa da kumfar baki..ta inda take shiga bata nan take fita ba, tana ta hargagi ita ka'dai zuciyar ta ba'ki'kirin. Abban kai kawai ya girgiza a zucia yace.." Mai hali dai baya fasa halin sa.." 'Bangaren su Zaitoon kuwa a hankali yanayin ke shiga jikin ta, tamkar su Ammi sun tafi mata da walwala da farin cikin ta haka take ji, sau'kin ta ma 'daya an bar Mufee tare da ita, kuma babu laifi tana 'debe mata kewa, amma sam ta kasa walwala...bata ta6a sanin har haka suka shaku ba sai yanzun, bata san cewa zatayi kewan su Marwa ba sai yanzu. Ta riga ta nemi afuwan mahaifan ta kan abinda ta aikata 'daya bayan 'daya sun kuma yafe mata so sai ta rasa kwata kwata meke damun ta a zucia, amma kusan koda yaushe ji take bata da da natsuwa...fargaba take ji na yawan shigan ta...banda tsoro dake kusanto ta kusan kowace rana. Cikin lkc 'kan'kani labarin dawowar ta da 'diyar ta ya baza ko'ina a garin, wani abu da 'karamin gari da wuya magana ke 6oyuwa. Da yawan mutane zuwa suke domin ganin ta, yadda kuma akayi tsammani ba haka ake tarar da su ita da 'diyar tan ba, kowa sai ya ja bakin sa ya gimtse 'dai- 'dai ku ne ke fa'din" Hakika bariki tayi kyau, yawon bariki yy rana.. Zaitoona irin kyau haka..gaba 'daya ta canza ta zama wata 'yar gayu kamar ba ita ba, maganganu iri iri dai ke tasowa. Hatta Salele mai chemist sai da yazo ya ganta, Dije kuwa ranar da tazo sabon kuka suka dasa dukkan su biyun rungume da juna. Sai da suka sha kukan su suka gaji sannan Zaitoon ke bata labarin duk abinda ya faru, kuka sosai Dije keyi ta na faman jinjinawa 'kaddara..hakika dole aji tsoron Allah a kuma godewa ni'imomin sa. 'Dan yaron ta da bai wuce watanni bakwai ba kwance a jikin Zaitoon Mufeeda na tsaye tokare da jikin ta tana ta kumburin sai dai yabar mata jikin Zaitoon ita ta zauna...Dije tayi murmushi..." Aishatu ko kara babu? haka ke kuma kk da 'kin mutane?..gaskia baki gaji halin 'kawata ba..." Ta 'karashe tana 'yar daria. Murmushin itama Zaitoon tayi tana kallon Mufee tace" Halin Abban tane ai, shima bai son mutane sai ba'kin rai da mugun hali, amma yana da kirki sosai...". " Shiyasa naga ya siye zuciyar ki da kirkin nasa ai..." Idanu ta zaro sosai. Dije tace" erh mana". A a wlh...kar ki min sharri dan Allah..wancan mutumin fa!..lallai dan baki san ko waye shi bane shiyasa". " ai ke kin san shi ko...?" Dije ta sake tambayar ta still tana dariyar dai. " Erh mana.." " Toh ai bu'kata ta biya". Shiru Zaitoon tayi bata sake tankata ba. Amma sam maganar Dijen ya kasa barin ranta...dama tun zuwan su bata ta6a hirar sa da kowa ba, ko batun auren Innani bata ta6a yi mata ba, ko Abban ta in taje wajen sa nasiha kullum ke ha'da su ya kuma ce kar tayi wasa da addu'o'i ta nemi za6in Allah bisa komai nata na rayuwa..bai ta6a fitowa fili yace ga manufar maganan sa ba..balle Yah Bukar da har yanzu ma ba gama hucewa yy ba...gaisuwa ka'dai ke ha'da su shima 'din sama sama yake amsa ta. Khausar ce uwar surutu da rawan kai amma ko ita idan tazo burin ta kawai ta 'dauki Mufee su je yawo da ita ne...sai kuma ta ri'ka sumbatu akan rayuwar su wani sa'in..." Adda ke kam kinji da'din ki...Allah yana son ki sosai.." Da yake ba wani sake mata fuska take ba shiyasa hirar su bata wani fiye yin tsayi ba. Ummaru ne abokin hirar ta shima kuma kwana biyun nan duk bata ga idanun sa ba. Duk wani wanda ke zuwa gidan domin ta kuwa duk tasan yanayin da take tarbar su..ko bakomai ta 'karo ilimin zaman dunia..ba duk wanda ke yi maka daria ke 'kaunar ka har zuci ba...wannan karatun ta gama haddace shi ba tun yau ba, bata manta irin su Hajjaju mai 'yan mata ba... So bata hira da kowa, duk wa'danda tasan ada bata ishe su kallo ba sam bata sake masu dogon hira dan tasan gulma ce kawai ta kawo su da 'daukan magana..toh da wa zata yi hirar Rayyan 'din...sai fa yau da ta samu Dije suka sha hirar su har suka ta6o 6angaren sa...a ranar yini sukayi suna hirar su ta bayan rabo tamkar kada su rabu da juna haka suka ji. Shi kansa mijin Innani da farko 'kin amincewa yy da zaman su a gidan sa dan dama yana kan masifan yadda cikin kwanakin 'aka dinga yi masa zaryar ba'ki a gida..da kansa kuma sai ya sake fuska bayan fahimtar irin yadda Zaitoon ke girmama shi ga kuma Mufee da ke matukar son shi da ya 'kira ta take zuwa wajen sa tana daria, sai ma ya zamana baya iya shigowa gidan batare da ya ri'ko mata abin lasawa ba...Bayan kwanaki hu'du da tafiyar su Ammi sai ga Adam ya dawo. Yaso tuntuni ya zo ma amma jikin Abban Hafiz 'din ne sai a hankali. Direct gidan Innani ya wuce da yake yanzu yasan gidan ba sai yayi tambaya ba. Yana zuwa kuwa ya ci karo da Mufee na wasan ta a 'kofan gida ita da Ummari yaron Yah Bukar. Hamdala ya saki har a fili domin ganin tan ya alamta masa cewa zai sake ganin Zaitoon kenan..dan ba tun yau yasan halayyar Zaitoon har ma 'diyar ta ba...bata ta6a yin nisa da inda Zaitoon take. Sai kawai ya dur'kusa gaban ta ya 'kura mata idanu, sai kuma yaga ko kallon inda yake ma batayi ba balle ta nuna alamun tasan shi. A hankali yace" Feefy na kin manta da ni ko?.. Ko nuna alamun taji maganar batayi ba..ma'ana dai bai isheta kallo ba. " Wai Feefy kin manta da Daddyn ki...?" Ya fa'da cike da mamakin ta yana 'dan 'dage gira. Shifa ala dole gani yake bata manta shi ba. Kallon sa tayi 'kur cikin idanu sai dai madadin ta yi masa magana kawai sai ta tashi tayi ciki da sauri tana waigen sa. Sai da ya sake doka sallama kafin Zaitoon ta fito anan ta fahimci shigowar da Mufee tayi mata baya rasa nasaba da ganin ba'kon fuskar da tayi. " Ke de baki gaji hali ba wlh....". Ta fa'da cikin ranta. Ko ba a fa'da mata ba tasan wanene ke sallamar, domin ta yiwa sautin muryar farin sani tunda jimawa. Bata so fita ba amma tana da tabbacin Innani na sallah ne a wannan lkcn dole yasa ta zum6ula babban hijabi ta fito fuskar ta babu yabo babu fallasa. Fuskar fayau babu kwalliya...rabon ma da ko mai ta shafawa jikin ta har ta manta.. amma duk da hakan sai ta fito rass abinta da ko'daddiyar fuskar ta. Adam idanu kawai ya 'kura mata yana jin wani abu da ya jima da 6oyewa na son taso masa sabo fill, duk dama shi har ga Allah bai ta6a cire ta aransa ba dama can, amma dole ya danne 'kaunar da yake mata sbd ya fuskanci rayuwar sa...bai kuma ta6a gigin sake sanya wata 'diya mace cikin ransa ba balle yy tunanin 'kaunar wata macen zai iya danne na Zaitoon a ransa, har a yanzun dai ita 'din ce kuma ita ka'dai a zuciyar sa babu wata. Wani gagarumin farin ciki yake jin zuciyar sa ciki tun a wancan ranar, ba 'karamin dauriya yayi bama da ya iya kaiwa kwanaki har hu'du kafin ya dawo. Ji yake kaf a dunia babu wanda ya kai shi farin ciki..zuwan sa wajen Goggon nasa ya zame masa babban nasara a rayuwa..domin zai iya ce tsuntsu biyu ya jefa da dutsi guda..ya sada sa da farin cikin sa da har ya fara cire rai da samun sa. A hankali tace. " Yah Adam..kai ne ?" Kai ya jinjina mata yana murmushi. Tace " Barka da zuwa.." Ta fa'da batare da ta yadda sun sake ha'de idanu wa ba. 'Ko'karin lalu6o inda tabarma yake take yi da idanun ta yayin da shi kuma Adam ya 'kura mata idanuwan sa baya ko 'kyaftawa. Lokacin da ta hango tabarmar 'kafa ta 'daga da zummar zuwa wajen da hanzari sai taji sau'kan maganar sa cikin kunnuwan ta da wani irin sauti mai ratsa zucia.." Zaitoona!..." Cak ta tsaya jun sunan ta da ya ambata. " kin canza sosai.."! Murmushi kawai tayi batare da ta juyo ko ta tanka masa ba. Ita dai tana mamakin abinda yake kawo shi wajen Innar ta..kuma ko ita kanta Innar bata ta6a yi mata maganar sa ba. Ruwa ta kawo masa bayan ta shimfi'da masa tabarmar..tana shirin mi'kewa tace" Innar tana sallah ne...". Yace " Bakomai...ai gaki kafin ta idar...". Bata ce uffan ba sai kawai tayi 'kasa da idanun ta. 'Yar murmushi yayi yace" Abu guda ne bai canza wajen Zaitoon ba.."! 'Daga idanu tayi ta dube shi sai kuma ta kau da kanta da sauri. " Wannan alkunya da shiru- shirun sun kasa barin ki...". " Hmm" tace 'kasan ma'koshi. Ta dai fahimci wannan Adam 'din ba 'daya yake da Adam 'din ta na baya ba, ita kanta a halin yanzu jin ta take takure zaman da tayi kusa da shi, ga shi irin maganganun da yake yi mata ko ada bai mata irin su ba. Tana mai wasa da yatsun hannun ta ta 'dora da fa'din.." Kunzo lafia?" " Alhamdulillah..ya bayan rabuwa..". Tace" Mun gode Allah..Hajia fa?" " Tana nan..itama tana gaida ki..nayi mata albishir na ganki...tace itama tana nan zuwa da kanta watarana..." Tasan abu ne mawuyaci dan haka kawai sai ta mi'ke tana fa'din" Allah ya bata ikon zuwa..zan kuwa yi farin ciki idan mutum kamar Hajia ta tako har garinnan sbd ni". Ganin ta mike din ya sashi 'daga kai ya dube ta da hanzari yace " Shikenan?". Kai ta 'dage masa itama ta dube shi...sannan ta bashi amsa" Zan dubo Innani ne ko ta idar..naji ta shiru har yanzu..." "...Shikenan sai ita ka'dai?...ba ga ki ba, ga Feefy na, bazan yi hira da ku ba sai Inna Ka'dai...?". Bata ce da shi 'kala ba kawai ta wuce cikin 'dakin ta, hakan nan kawai take ji aranta zata kare martaba da darajar auren da ke kanta, kuma ai ko ba komai Adam ba muharramin ta bane, matsayin tsohon saurayin ta yake da wata 'kaddara ta raba su. Amma ita kanta bata san wani matsayi ko yanayi yake a zuciyar ta ba har suka rabu, domin har yau 'din nan bata ta6a jin wani abu game da shi a zuciyar ta ba..ita dai tasan tana bashi girma, tana kuma bashi daraja kwatankwacin yadda ya 'dauke su..ya mutunta su ita da Feefy, so ko ada 'din ma kyautatawar sa ne kawai yasa ta tilastawa kanta sha'kuwa da shi har ta amincewa auren sa bawai dan tana jin soyayyar sa ba. " Yah Adam..."! Ta fa'da tana murmushi. Akwai wasu abubuwa da ta tabbatar har abada bazata ta6a mancewa ba a tsakanin su ko da kuwa ace bb soyayyar sa a zuciyar ta, Adam ya nuna mata 'kauna ya kuma 6ata wani 6angare cikin lokutan sa masu muhimmanci domin ta. Shine ya fara 'daga darajar ta cikin sauran mutane tun bayan barowar ta gida. Kwanciya tayi bisa katifar su, Mufee tazo gaban ta itama ta kwanta. Cikin ranta take tariyo rayuwar su da Adam na baya" Ko ya Maman Abdul take oho..." Ta tambayi kanta. Canjin yanayin da ta fara fuskan ta daga gare shi ya sa ko tambayar ta su ma kasawa tayi... a hkn bacci 6arawo yy gaba da su ita har Mufeeda baki 'daya. Bai damu da baccin nasu ba sbd yasan yana da isashshen lokaci daga yau har zuwa gobe, hakan yasa sam bai damu ba, hira ka'dan suka yi da Innani yace zai shiga cikin gari amma zai dawo washegari, Innah tace babu komai, ai ma yana 'ko'kari sosai..Allah ya ji'kan mahaifa. Yace " Ameen Goggo..badan Mufeeda na bacci bama ai da ta rakani..." 'Yar daria Inna tayi masa tace" anya kuwa..? Wannan ma'kalematan zata yadda tabika kuwa..?" Suka daria atare dukkan su. Shi kansa ma fa'da kawai yake, amma sarai yasan halin Mufeeda da Zaitoon ba tun yau ba. Daga haka ya wuce fuskar sa cike da annuri har ya tafi. Koda Zaitoon ta tashi a baccin tayi mamakin irin bacci mai nauyin da tayi, domin sam bata san da tafiyar Shaheed ba, ba kuma tayi mamakin tafiyar tasa ba...dan dama tana da tabbacin wajen Inna yazo ba wajen su ba. Kamar yadda ya fa'da washegarin ranar ya dawo da misalin 'karfe goma da 'yan mintina. Shaheed sam baya da shamaki da gidan Innah, hakan yasa sallama kawai yake yi ya shigo gidan kansa tsaye bayan an amsa shi. Doguwar ba'kar riga ce jikin ta da wata jar hula taja shi baya sosai dan kusan rabin kanta ma waje yake baki 'daya. Wankin kayan Mufee take yi da wasu nata 'kalilan tana kuma yin abinta ne hankali kwance, yayin da Mufee ke faman takura ta da fitinar itama sai tayi wankin, tun tana hana ta tana qi da 'yar rigima har ta ha'kura ta 'kyaleta, ta kuwa ji'ka jikin ta sosai da ruwan wankin. Lokaci- lokaci takan ce Mufee bazaki bari ba..? Dubi yadda kk ji'ke jikin ki a banza?" Mufee ko gezau tamkar ma ba da ita take ba..sosai take jin nisha'di da wasa da ruwan..ita kanta Zaitoon nisha'din take ji a zuciyar ta da bata san na menene ba. Cikin rashin sa'a adai- dai lokacin da Zaitoon ta sakan kance tana wankin ta gami da surutu wa Mufee akaro na babu adadi shima ya doka sallamar sa har sau biyu..duk Zaitoon bata ji ba. Shigowar sa gidan yayi dai- dai da lokacin da take sake fa'din" wallahi in mura ta kamaki allura zan kai ki ayi maki babu ruwana..?" Sai ji tayi bazata anbata amsa" Ni kuma inada tabbacin bazaki ta6a iyawa ba..."! Ya fa'da yana murmushi. 'Daga kai tayi da sauri nan tayi arba da Adam tsaye yasha kyau har ya gaji. Fuskar sa sanye da farin gilashin da ya matu'kar 'kawata zubi da tsarin sa. Bata san lokacin da itama ta murmusa ba. Tana 'ko'karin cire hannu a ruwan ya 'karaso..." Kar ki damu, cigaba da wankin ki...ai ni ba ba'ko bane da kaina ma zan nemo abin zama.." Ya fa'da yana zama bisa wata kujerar da ya hango kusa da ita. " Toh ruwa fa..?" " Bani da bu'katar komai Malama ta..". Suka yi daria atare. Cigaba tayi da wankin ta. Cikin ranta tace " Yah Adam kenan..toh dama akai akai yake zuwa gidan nan ne..ko de yana da alaka da mai gidan Innani ne...? Babu mamaki hakane..."! Tayi tambaya kuma ta bawa kanta tabbacin amsar ta. Hannun Mufee ya kamo..." Ke kuma yarinyar Daddy bakijin magana ko?..nima da kk gani bazan hana malamar nan kaiki allura ba..gara ma ki kiyaye ki riqa jin magana kin ji ko...?" " Yah Adam tuna min kake da wani abu can baya idan kace min malama.." 'Dagowa yayi ya dube ta sosai suka ha'de idanu, dama hakan yafi bu'kata tuntuni amma sai tayi saurin mayar da kanta 'kasa ta cigaba da wankin sannan tace. " Da ace a rayuwa ta na samu matsayin zama malama kwatankwacin yadda kk fa'da yanzun, da na gama jin da'di..." " Idan hakan kk bu'kata har yanzu baki makara ba Hajia ta..zan iya miki al'kawarin zama malama daga yanzu har 'karshen rayuwa ta..indai ilimi ne baki da matsala da shi har sai kin gaji..." Sai tayi murmushi. " Wani abin kafin ya faru 'karshen sa ke fara bayyana Yah Adam...ha'ki'ka nayi rashi cikin rayuwa ta gagaruma...bazan ta6a mantawa da kai ba domin kaine malami na biyu da ya tallafi rayuwa ta...ko hakan ma nagode..."! " Ina kuma so in zamto na 'karshe a wajen ki idan kin bani dama Zaitoon...?" Ya fa'da yana mai mayar da hankalin sa sosai agare ta. Mufee dake wasa da agogon hannun sa take shirin 6allewa ya kalla, adaidai lokacin itama Zaitoon ta 'dago idanu sbd jin sigar da yai magana sai ya mata wani iri. Idanun ta ta sau'ke akan hannun nasa..abinda tayi niyyan fa'di ta fasa..inda akalar maganar tata ta sauya daga wacce tayi niyya zuwa" Indai Mufee ne tsab yanzu sai ta lalata maka agogon nan idan baka hanata ba.." " Sai kuma akace mk hakan matsalar ki ce ko..?" Kai ta girgiza...sai yace" Toh babu ruwan ki da yarinya ta.." Bata ce komai ba ta cigaba da wankin ta. Sai ji tayi yace" Sannu da hidima.."! " Ta me fa..?" Ta tambaye shi batare da ta 'dago ba. " Wankin kayan Mufee na mana.."! " Wannan kuma...ya riga ya zame min jiki ai.." " Allah ya baki lada Malama ta...ni ma bari in ta6a wannan ladan ko ta yau ka'dai ce kar ta wuce ni..."! Da sauri ta 'dago sai gani tayi yana tattare hannun riga yayin da agogon hannun sa ke hannun Mufee tana ta faman kokawa da shi. " Ba dai hannu zaka sa cikin wankin nan ba..?" Tayi tambayar cike da mamaki. Yace" yanzu kuwa..." " Dan Allah ka bari ai ma saura ka'dan in kammala.." " Ba'kin ciki kk min kar nima in samu tagomashin lada kenan...?" " Yah Adam..dan Allah.."! Ki bari idan mun kammala sai ki fa'da min cewa ban kyauta ba dan na yiwa 'diya ta wanki.." Shiru tayi ganin har ya tsoma hannu cikin wanda Mufee ke wasa da shi. Shiru ya 'dan biyo baya. Ahankali tace.." Yah Adam kasan idan Hajiyar ka taji labari bazata ji da'di ba.."! " Saboda wani dalili..?" Tace" Saboda kafi 'karfin yin hakan ga koma waye balle kuma ni Zaitoona...". Bai ce da ita 'kala ba kawai yayi 'yar daria. " Ki bini bashin wannan tambayar taki zan baki ita zuwa gaba...amma kafin nan zamu yi wata 'yar gasa...shara'din sa kuma shine in har kika fa'di gasar nan toh sai kin bani kyautar wani abu gagarumi kin amince..?" Shiru tayi tana 'dan rarraba idanu da tunanin abun kamar me zai iya kasancewa. Hannu ta 'daga da sauri tana daria tace" Gaskia a a..Yah Adam.." Gira ya 'dage yana duban ta..." ban amince ba..wlh". " Sbd mene..?". " Toh Yah Adam in kuma ya kasance bani da wannan abin fa..?" " Ina tabbatar mk da cewa kina da shi kuma sau'kin bayar wa gare shi...". " Fa'da min toh menene...?" " Ai baki amince ba tukunna." " Taya zan amince bacin bansan menene ba..." " Sannu mai rai sarkin tsoro..."! Ya fa'da yana daria gami da mi'kewa tsaye ya fara shanya kayan da ya gama wankewa..itama dariyar take yi...ta sunkuyar da kai ta cigaba da wankin dake gaban ta cike da annuri. Adam dake tsaye yana shanya shine ya fara hango mutun tsaye fuskar sa tamkar ba'kin hadari sbd yadda ya ha'de ta. Babu alamun yama ta6a daria a rayuwar sa. Gira Adam ya 'dage yana duban sa da mamaki yace" Malam lafia...?" Dan sam bai gane waye ba. Maganar Adam ita tasa Zaitoon 'dagowa da sauri ta dube shi ganin inda hankalin sa yake itama sai ta dubi wajen. Wani tsinkewa da zuciyar ta yayi har sai da taji tamkar bazata iya tsayuwa da 'kafafun ta ba amma ta dake. Tsaye ta mi'ke da sauri tana gyara zaman hular kanta. Sosai yake duban ta duba mai cike da takaici, bai sake kallon inda Adam yake tsaye ba...Mufee kam bata ma ankara da shi ba sam. Ganin sa ya matu'kar bawa Zaitoon mamaki, kuma sam ba zata iya ce ga tsayin lokacin da ya shafe tsaye a wajen ba. 'Kasa tayi da idanun ta yayin da shi kuma ya juya ya fita da hanzari sai jin tashin motar sa tayi da 'karfi ya fizge ta yayi gaba. Wani ajiyar numfashi ta sau'ke mai tsananin 'dumi tana duban Mufee.... Adam barin abin da yake yayi ya taho wajen ta shi kansa neman natsuwar sa yayi ya rasa ta da ganin sa.." Waye shi...?" Ya tambaye ta shima 'din fuskar sa babu alamun fara'ah tamkar ba shine ya gama daria yanzun ba. Tana zama bisa bencin da ta tashi ta amsa shi da fa'din" Abban Mufeeda ne "! " Ban fahimta ba?" Kai ta 'daga ta dube shi ido cikin ido sannan ta bashi amsa" Mahaifin Mufeeda ne.."! Wani turus yayi yana duban ta..bata san meyasa ba haka nan kawai sai taji gaba 'daya bata da sukuni, ji tayi ta takura baki 'daya. Yayin da Adam yama rasa abinda zai sake fa'di. Cikin ransa yake ta tunani. Mahaifin Mufeeda kamar Yaya? Taya kuma wannan zai kasance mahaifin ta? Shin dama yana raye ya bar su sukai irin wannan rayuwar ta alla wadai..? Yana raye ya bar su sukayi rayuwa tamkar almajirai?" Takaicin sa ma 'daya yadda lokaci guda ya fahimci canjin yanayi daga Zaitoon tun bayan ganin sa da sukayi. " Zaitoon...!" Ya 'kirayi sunan ta cikin yanayi marar misaltuwa. Kai ta 'dago ta dube shi. " Me yakawo shi a halin yanzu?" " 'Diyar sa yazo gani.."! Ta bashi amsa Kai tsaye. " Dama can yana zuwa ne..?" Shiru tayi bata bashi amsa ba dan bata ma san me kuma zata sake ce da shi ba. Salmerh😘 [23/01, 6:53 am] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Wattpad@* _Serlmerh-md_ 🅿️ *...103* ........Sallamar Inna shi ya dakatar da tattaunar da suke yi...Dukkan su sun amsa sallamar amma ciki- ciki. Inna kam bata ma lura da yanayin su ba fuskar ta yalwace da fara'ah take masa lale marhaban da zuwa. Ganin haka yasa shima ya danne damuwar sa ya 'ka'kalo fara'a kawai sbd Goggon sa. Sai dai ya kasa jin zuciyar sa cikin natsuwa, gashi bayi da isashshen lokaci ayau 'din hakan yasa bai da'de ba yayi wa Inna sallama ya tafi..da al'kawarin zai dawo bada jimawa ba...dan Inna tace da shi akwai maganar da take so suyi da shi muhimmiya. Ko ci kanka Zaitoon bata 'kara ce da shi ba sai da zai wuce sannan tai masa fatan sau'ka lpy shima 'din bai amsa ba yy gaba...Adam a fili ya fara fahimtar wani abu da zuciyar sa ke raya masa game da Zaitoon da Abban Mufeeda yana kuma tsoron kasancewar sa gaskia. Ko bayan fitar sa Zaitoon bata sake sakin fuskar ta ba, dama ba wata doguwar hira suke yi da Innar tata ba hakan yasa itama Inna bata wani damu da canjin yanayin ta da ta gani ba...a tunanin ta rashin sabo ne ko wani abin daban. Kwata- kwata Zaitoon bata samu natsuwar zucia ba tun bayan tafiyar sa, haka nan kawai take jin ranta cikin damuwa, ba kuma zata iya tantance mene asalin damuwar tata ba. 'Bangaren Rayyan kuwa har wani duhu- duhu yake gani sbd takaicin aabinda idanun sa suka gane masa, wai wannan yarinyar da ke da igiyar auren ssa akanta ce take irin wannan fara'ar ga wwani 'kato can da ko da wasa shi bata ta6a yi masa irin fara'ar ba. Ba 'karamin sosa masa zucia abin yayi ba. Yana isa direct gidan sa ya wuce ya zube kan kujera, jijiyoyin kansa duk na nunawa. Sam ya kasa tantance abinda ya gani, babban damuwar sa sanin ala'kar dake tsakanin su da har ya kawo wannan sha'kuwar. Babu wanda yasan ya dawo har dare, kuma duk 'kiran da ake yi masa ko damuwa ya duba masu 'kiran ma bai yi ba balle ya damu da 'dagawa. Fawwaz ne ma daya tashi a aiki bayan maghrib da ya 'kirayi layin nasa yy sa'a ya 'daga, cewa yy kana ina. Amma Rayyan ya'ki ce da shi komai kawai ya kashe wayar sa. Sai washegari da yamma yahe gida amma kana ganin fuskar sa ka san ba dai- dai yake ba. Ko da Ammi ta tambaye shi lafia nuna mata yy babu komai sai bata damu ba..tace kai ka sani ai tunda kai ba yaro bane. Haduwar su da Fawwaz kuwa har sai da ya 'kwammaci dama bai yadda anyi ta ba, dan ba 'karamin ssha'kar da shi yayi ba da dariyar mugunta. Be ma san meyasa ya labarta masa ba. Sai da ya gama dariyar kafin yace" In baka.shawara mutumi na?..ka tattaro kayan ka su dawo kusa da kai hankalin ka zai fi kwanciya..." Shiru yy bai tanka masa ba, tunani yake dama hakan zai faru da sai yafi kowa farin ciki, amma taya zai yi hakan toh bacin mahaifan ta basu amince ba har yanzu. Tashi kawai yayi ya bar Fawwaz anan yy gaba. Yaji da'din shawarar da ya bashin koba komai yy masa nuni ne izuwa mafitar 6ullewa. Kuma ya tabbatar in ba hakan yy ba bazai yi maganin Yarinyar nan ba. Bayan kwanaki biyu da faruwar lamarin sannan Shaheed ya dawo, shi kansa tun tafiyar tasa bai samu natsuwa ba, bai kuma yi kauran baki baba, dan ya labartawa Hajiyar sa komai, ya kuma zanta da Hafiz kan haka...Hajiyar sa dai tace ya cigaba da addu'ah yayin da Hafeez ya bashi shawarar fara tuntun6ar Goggon sa tukunna...ya kuma 'kara masa 'kwarin gwiwar da Iznin Allahu zaitun bazata kubce masa a wannan karon ba. Dalili ma kenan da ya sanya shi zuwa yau din, dan Hafeez yace masa da zafi- zafi ake dukan 'karfe, shi kansa badan jikin mahaifin sa ba da tare zasu kamo hanya..amma babu komai addu'ar su na nan tare da shi. Sosai Innah tayi farin cikin ganin sa dan dama abokin shawara take nema tsayin kwanakin nan. Abinda ta fara tambayar sa shine..." lafiya kam...kayi ciwo ne...naga duk kayi sanyi..?" Yace ba komai Goggo...rayuwa ce kawai sai a hankali.." Tace " Allah ya rufa asiri..". Sun tattauna sosai da shi da Innani akan batun Zaitoon. Adam yaji bb da'di jikin sa yy sanyi sosai, amma sam bai bari Innani ta fahimci komai daga 6angaren sa ba, bai kuma nuna son kansa ba, abu ne da ya riga ya faru, ya dace ya kuma cancanta, matu'kar aka auna sa a mizanin fahimta...toh akwai dacewa sai dai yana gudun a wula'kanta masa 'yar uwa watan wata rana. Akwai dacewa, akwai mutuntaka, sannan girmamawa da daraja, babban kuma shine 'kaddara daga indallahi. Haka Allah ya riga ya tsara su basu isa suja da yin Allah ba. Gefe guda yana jin zuciyar sa nayi masa zafi, lokuta da dama ya kan cire huci mai zafi da shi kadai ya san yyanayin da yake jin ransa. Domin sam sam bai zaci abin.hhar ya kai hk ba, bai yi tunanin kasantuwar hkn da wuri ba sam, amma meyasa bata sanar da shi ba da bakin ta.? Meyasa ta barshi ya sake famo tsohon mi'kin da ke binne cikin ransa bacin tasan babu ranar warkewar sa, meyasa ta barshi ya sake saka ransa ga samun daman mallakar ta..?" Adam bai ta6a tunanin Zaitoon tafi 'karfin sa ba ahalin yanzu, domin aure yasha gaban komai, bai san cewa akwai wannan irin 'ka'kkarafar katangan a tsakanin su ba...ya 'dauka ganin Zaitoon tamkar yayewar wani 6arin ba'kin ciki cikin rayuwar sa ashe yy kuskure, ashe wata sabuwar ba'kin 'kaddarar ke sake tunkaro shi akaro na biyu. Da ace ba a riga an 'daura mata aure ba bazai ta6a janyewa ba, da bazai ta6a cire rai da samun ta ba, dole zai gwada tashi sa'ar ne har sai yaga abinda hali zai yi, amma a halin yanzu bashi da wannan damar, da ce bbata riga ta zama mallakin wani ba da sai inda 'karfin sa ya 'kare, da bazai ha'kura hakanan kawai ba...zai yi addu'a..kuma ai yana da Goggo. Wannan labari da kunnuwan sa suka jiye masa ayau, kusan shine labari mummuna na biyu da ya shiga kunnuwan sa akaf din rayuwar sa. Na farko tarihin mahaifin sa ne..na biyu kuma labarin auren Zaitoon ne, dan ko lokacin da ya rasa a wancan karon bai cire rai da samun ta kamar yanxun ba, a wancan lokacin kwana yake ya tashi da tunani da tsamanin ganin ta duk da bashi da tabbaci. Amma wannan karo 'daya aka yanke masa kauna da samun ta, karo 'daya komai da ya fara ginawa cikin ransa ya rushe kaf. Bazai ta6a yadda a kashe mata auren ta sbd son zuciyar sa ba...Zaitoon na tare da shi ko akasin hk dole zai mata fatan alkhairi..ba yaga hk ma a halin yanzu jinin jikin sa take...hkn ma Alhamdulillah bai yi hasara ba, bai kuma bar wani ba'kin ta6o abaya da zai hanata yi masa kallon 'dan uwa babban wa agare ta ba. Sai dai duk da haka zai fi so ace shine da ita, zai fi so ace shi ya mallake ta ba wani can daban da babu ma wanda yasan asalin sa ba. Ya bawa Innani shawarar da yasan ta dace, ya bata shawarar da yasan ko bayan bashi baza a kuka da kalaman sa ba, ya kuma nemi a raka shi gidan mahaifin Zaitoonan domin shima ya duba shi da jiki. Sun yi gaisuwar mutunci tamkar ansan juna dan shi Adam badai raha da sakin fuska ba. Haka yy kokari sosai wajen danne duk wata ddamuwar da ke cinsa aransa. Sun tattuna sosai a tsakanin su wanda duk ya gama fahimtar manufar kowa, ya fahimci Bukar sam baya ra'ayin sake tafiyar Zaitoona Kano zaman aure..haka kawai sai ya 'danji sanyi a aran sa...shi dai bai matsa ba..amma koma mai zai faru falillahil Hamdu. Atare shi da Bukar suka 'dunguma wajen Baffa Liman anan ne suka so samun matsala da shi ma dan shi baya da fahimta sam, duk da dai dama maganar su yazo 'daya ne da Yah Bukar da Baffa Liman kusan ra'ayin su guda ne sai dai kawai manufa ce daban..a fahimtar sa. Kuma ko da wasa bai bari 'daya cikin su ya fahimci 6oyayyan matsayin Zaitoon awajen sa ba. Yazo musu ne kawai a matsayin 'dan uwan ta na jini. Adam yy kokari sosai wajen ganin ya janyo hankulan su duk su biyun, sosai ya ajiye son kansa, soyayyar da yake yiwa Zaitoon din ma ajiye ta yy itama wuri guda kawai ya sa aransa zai yi domin Allah domin ya fahimci cikin mahaifan Zaitoon akwai wadanda son zuciyar su kawai suka sa agaba. Shi kansa bazai so a salwantar masa da farin cikin 'yar uwar sa ba...tun anan ma ya yada makaman ya'kin sa ya saduda..yana fatan wa kansa canji da wata daban mafi alkhairi...amma da Baffa Liman yace sam, shi fa bai yadda da wannan aure na Zaitoona ba. Bukar yace shima dai bawai har zuciar sa ba amma indai ya fahimci Zaitoon na so bazai hanata komawa ba sbd bazai so tauye mata hakki ba, bazai so ya sake saka ta cikin 'kunci bayan wanda ta fuskanta a baya ba. Sai da aka kai ruwa rana kafin Yah Bukar yayi na'am da batun amma da shara'din amincewar ta tukunna. Shikan sa Adam ma yafi son hakan, domin wata zuciyar tasa na sanar da shi cewa shi Zaitoon take so ba wancan gayen ba...yana ji tamkar nasara na tunkaro shi ne cikin sauki. Bayan kwana biyu ya sake dawowa duk dai akan maganar. Yayin da duk tsawon lokacin nan babu Rayyan babu alamar sa. Hajan.sai ya fara kawo kokonto a zuciyar Yah Bukar amm sbd kar ya mayar da magana baya sai yaja bakin sa yy gum. 'Karshe dai Bukar kasa rike abinda kke ransa yy sai da ya furta shi, yace shi bai ga alamar wannan miji na Zaitoon ya damu da ita ba, yace idan aka cigaba a haka yana tsoron abinda zai je ya dawo, domin mutum abin tsoro ne, yace kar fa suyi kuskuren tura yarinya inda rayuwa zatai mata bakikirin sbd wai halacci, in kuwa hakan ya faru har abada zai ri'ka ji aransa tamkar bai yiwa Zaitoon bikin yar gata da ya jima yana tsarawa aransa ba...zai rika ji tamkar sadakar ta ya 'dauka ya bayar haka nan kawai ba auren daraja ba. Abbah ne ya taushe shi da fa'din yy ha'kuri ai komai mu'kaddari ne daga mahalicci, ba kuma komai da muke so muke samu kamar yadda muka tsaraba ba, dole akwai shirin ubangiji da ya riga ya rinjayi namu shirin kuma dole mu bisa. Suka ce haka ne, amma dai a bari aga nan da dan wani lokaci idan babu canji sai asan abinyi. Duk da haka Bukar ya kasa yin shiru mita kala kala yake yi...tun daga kan batun Rayyan har na rashin samun daman gatantawa er uwar sa da bai yi ba. Adam ne yace to ko za'a sake biki ne Bukar sai hankalin ka ya kwanta idan ka tabbatar kayi bikin ta kuma ka mi'ka ta 'dakin mijin ta da kanka hala zaka fi jin kwanciyar hankali". ya fa'da yana yar daria. " kaga ko mu ma akwai tamu rawar ganin da muke so mu taka a matsayin mu na 'yan uwan ta ai". Suka 'dan yi daria. Abban su kuwa yace sam suma yi hakuri dan bb wani biki da za asake, duk shirme ne kawai ba wani abu ba...yace indai biki ne su tari na khausar dake zuwa nan bada jimawa ba. Dole suka ha'kura suna murmushin 'karfin hali. A wancan ranar Adam bai yadda ya bar garin ba sai da ya tabbatar ya bada ku'da'de isassu wa Bukar sbd ganin yanayin jikin Abban su Zaitoon yace akai shi asbiti a duba lafiyar shi sosai. Zaitoon da taji labari sai da tayi kuka, shiyasa har kullum tasan darajar Adam na daban ne aran ta, yakan yawaita cika mata burikan da take faman sa'ka su cikin ranta tun kafin ta kai ga furtawa. Ha'ki'ka shi 'din 'dan uwane abin alfahari makwafin yayanta. Tun ranar da ta samu labari cewa shi 'din 'dan uwanta ne take jin ta cikin farin ciki...ta godewa Allah daya azurta ta da samun gwarzayen yayye masu so da 'kaunar ta har guda biyu. ***** Rayyan bai sake waiwayen su ba haka ma Ammi bata sake yi masa maganar su ba. Sai da aka cika kwanaki tara cif bata ma san yaje ba sai bayan ya dowa taji lbr. Ranar da ya sake komawa ma shi kadai ya kama hanya. Can gidan mahaifin ta ya fara dira suka yi gaisuwa sama sama da Iyami suka sanar da shi ai suna can wajen Innar su...yasan dama suna can din, dama kawai yazo nan 'din ne sbd bin umarnin zuciyar sa. Ko da ya tambayi Abbah kuwa Iyami kawai ce masa tayi baya gida. Shima bai bi taktakan batun ba yy musu sallama ya fito bayan yayi mata goma ta arziki. Bai nemi rakiyar kowa ba da yk ya riga yasan gidan Innan. Cikin rashin sa'a Inna ce ka'dai a gida, su Zaitoon na gidan Dije 'kawarta tun zuwan ta basu ta6a zuwa ko'ina ba illah gidan mahaifin ta kuma ko can din ma ba kullum take zuwa ba yau shi ne fitar su na farko zuwa wani wuri daban..shima 'din gorin Dije ne ya ishe ta akan ta'ki zuwa taga gidan ta..shine ta shirya suka je. Bayan sun gaisa da Innani ta bashi ruwa sai ta sanar da shi ai sun je gaisuwa amma bazasu da'de ba yanzu zasu dawo. Wani takaici ne yaji ya turnu'ke shi, take yayi kicin- kicin da fuska...wato ma ita hankalin ta kwance har ta samu 'kafar yawo agari, to inma tana tunanin zai sawwa'ke mata ne ta samu filin zama da yawo ko hira da nishadi da wasu mazan shi bazai ta6a sakin nata ba, sai dai koma me zai faru ya faru a shirye yake...in bama ta raina shi ba da auren nasa take biye- biyen gidaje batare da sanin sa ba bayan tasan bb abinda yafi tsana irin hakan..da yake ta riga ta raina sa kenan ko me...?" Ko dayake bazai yi mamaki ba, wacce ta iya zama babu ko 'kwakkwaran mayafi tana hira da daria da wani namijin toh menene sabo kuma dan ta tafi yawon ta batare dda sanin sa ba. Gashi Inna ba zaman hira tayi da shi ba balle sake saken zucin da yake su tsagaita..Rayyan har ya fara tunanin kawai yayi tafiyar sai dai sam ya kasa...haka nan kawai ya sawa ransa tsayawa yaga iya tsawon da'dewar su, kuma wata zuciyar tasa na kwa'daita masa so da muradin ganin duk su biyun ayau. Domin ba zai ce Mufee ka'dai idanuwan sa ke bu'katan gani ba, a ha'ki'kanin gaskia hatta ita uwar Mufeen yana da muradin ganin ta, yana kuma da tarin tambayoyin da yake son yi mata su wanda yake ji dole sai ta amsa masa su. Dalili kenan ma da ya sanya ya bi umarnin zuciyar sa akan ya tsaya ya jirayi dawowar su. Baya ga haka ma bazai iya irin wannan doguwar tafiyar kuma ya koma batare da ya cikawa idanun sa da zuciyar sa mura'dan su ba. Rayyan baki 'daya ya cika tamkar zai yi bindiga, fuskar sa ka'dai idan ka kalla kasan bb annuri dai- dai da mis'kala zarratin akan ta, dama tun asali fara'ar bata wadaci fuskar ba da ya ha'du da wannan yanayin kuwa abin kawai sai wanda ya gani. Gashi mijin Innani ma bayanan yy tafia balle ya samu abokin hira. Cikin rashin sa'a kuwa rikice Zaitoon ta dawo rungume da Mufee 'kirjin ta yarinya na neman sume mata da jiki jajazur... kuka take da hawaye sbd tausayin yarinyar...sam ma bata kula da wani mota da ta gani a 'kofar gida ba balle takalman da ke bakin 'kofa. Sallama tayi ciki ciki bata jira amsa ba kawai ta shiga cikin gidan. Sbd gajia ko kula da takalman dake gefen 'kofar bata yi ba ta shigo 'dakin da sauri idanun ta na tsiyayar hawaye. Kwantar da yarinyar take son yi kafin ta fara tunanin mafita, domin ko Inna tsoron taran ta da wannan yanayin jikin Mufeen take tasan wani zafin zata 'kara mata bb mamaki ma fa'da zata sha. Inda ta gode Allah ma basu yi arba lkcn da ta shigo gidan ba. Shigan ta ke da wuya tayi arba da mutum zaune ya wani kishingi'da mata a bakin katifa fuskar nan babu annuri ko ka'dan tamkar wanda akai wa kutse a muhalli batare da yaddar sa ba....baya taja a firgice tana shirin sakin ihu sbd ita har ga Allah ba ta gane shi ba bata yi tunanin zuwan sa ba. Mutsu mutsu da mi'kan da Mufee tayi a daidai lkcn ne ya hana ta ihun, madadin hakan kawai sai ta saki kuka tana jijjiga ta. Ganin hakan ya sa ya mike tsaye da sauri yana duban su shi kansa ya shiga firgici. " What happen to her...? meya sa me ta? Yayi tambayar a lokaci guda. Maimakon ta bashi amsa sai kawai ta mi'ka masa yarinyar ta sau'ka 'kasa bisa gwiwoyin ta kawai ta sanya kuka...tama rasa abin cewa. Kar6ar Mufee ke da wuya ya fahimci inda matsalar take. Bisa katifa ya kwantar da ita da tunanin yana da maganin da zai sassauta mata yanayin a mota...da hanzari yy waje yana mai lalu6a aljihun sa fuskar sa babu annuri ko ka'dan. sai dai me? ko da ya dubo motar bai samu maganin ba. Kai ya dafe cikin hanzari yana mai yawo da hannun nasa cikin gashin kansa. Tuno cewa maganin na a 'daya motar ne ya sashi sakin huci mai zafi...domin motar tana can Kano. Goshi ya dafe cike da damuwa.. tausayin yanayin da yaga yarinyar tasa yake. Ji yake tamkar ya zubarwa da Mufee hawaye sbd tausayin ta. Yasan yadda take mimmi'ke wannan ra'da'di take ji saman fatar jikin ta sosai..." ohh Allah" Yace a fili. Rashin samun maganin da kuma wannan tunani da tausayin 'diyar tasa sai suka sake hassala shi. Da 'dan hanzari ya sake komawa ciki, sam ma ya mance da gidan ba mallakin sa bane ba... fuskar sa tamkar bai ta6a daria ba, koda ya shiga 'dakin rungume da yarinyar ya sake tadda ta still tana kuka...wani banzan kallo ya bita da shi. Tsaban haushi ma bai san lokacin da ya daka mata tsawa ba" Shut up dallah malama! Me kk so ki proving me ne..?..is that the love that u are always claiming?..Ko kuwa dama can pretending kk wa mutane? ki 'dau min yarinya ki kaita inda kika san zai cutar da ita sannan kizo nan kina damun mutane da kuka.. for what?" Shiru tayi tana jin mmki gami da al'ajabin zazzafab kalaman na sa, sai taga wai za'kewar tasa ai tayi yawa..hakan ya sa ta tsaida kukan ta cak..'dago idanu tayi ta kalle shi suka ha'de idanu...sai kuma ta sake shiga firgici musamman sbd yadda taga idanun sa sun rine..tasan ya gama kaiwa 'kololuwa a yau 'din tunda farin sani tai masa..ba sanin yau ka'dai bane. Duk wata dakiyar da tayi 'ko'karin nunawa kasawa tayi..ba 'karamin tsoratar da ita yanayin nasa yayi ba, domin kusan zata ce wannan shine karo na farko da yy mata irin wannan masifar kai tsaye ita da shi. 'Kasa ta sake yi da kanta sai ga sabbin hawaye...cikin ranta ta ayyana wai duk akan Mufee ne? Rayyan tsaki yaja yana 'ko'karin zama ya furta. " Je kawo min gishiri da lemun tsami.." Ya fadi hakane bayan ya 'dan sassauta muryar sa sbd wani 'dan tunani da yayi, haka nan kuma sai yaji Zaitoon 'din ta basa tausayi, sai dai still adake yy maganar babu alamun wasa tattare da shi, batare kuma da ya ko dubi fuskar ta ba idanun sa na kan 'diyar sa yy maganar. Tamkar mara laka haka ta mi'ke, ya amshi yarinyar daga hannun ta yana 'daga mata riga. Ayadda take jin zuciyar ta da ace ba Mufee bace da bata ga abinda zai sata zuwa kawo gishirin ba, ba kuma zata sake ta6a masa jikin yarinyar sa ba..bar masa 'diyar sa zatayi yaje can da ita shi ya sani. Shin mene laifin ta anan wai? Gani yake bata 'kaunar 'diyar sa ko me? Yana tunanin da gangan takaita inda zata sanu attack din ko me? Bai san akwai rashin sani bane? Shin dama haka 'dan Adam yake da saurin mantuwa ko kuwa shi 'din ne dai kawai nasa hk?" Bata samu abinda yace ta samo masa ba, lemon tsamin ma sai a ma'kwabta aka samo shi...ko natsuwa taga abinda zai yi da shi ma ba ta yi ba. Kanta ta kifa bisa cinyoyin ta ta cigaba da rera kukan ta gwanin ban tausayi. Ajiyan zuciyan da yarinyar ta sauke bayan wani lokacj shine ya sata 'dago kai da sauri, cike da ki'dima ta 'dago kanta ta zuba musu idanu. Next abinda ya fa'da kunnen ta shine..." Mammi...."! Da Mufee ta ambata tun kafin ta 'karasa bu'de idanu. Wani sharp yun'kurin da Zaitoon tayi shi kansa Rayyan sai da ya kalle ta gami da mamakin ta. Gaban sa kawai ya ganta dur'kushe tana kamo hannun Mufee fuskar ta yalwace da farin cikin da ya san bana komai bane face na farin cikin dawowan yarinyar. Ita Mufee take kallo tana ambatan sunan ta out of farin ciki yayin da shi kuma ya zuba mata idanu yana noticing duk wani motsin ta. Farin cikin da ke kan fuskar ta a lokacin ya tabbatar ba iya fuskar ya tsaya ba direct ya wuce har can cikin zuciyar ta...ya kuma san cewa ko Nadia da ta haifi yarinyar nan iya abinda zata iya kenan akanta...hakika soyayyar bayin Allahn nan daga indallah ce. Wani 'ka'k'karfan abu yake ji na shiga cikin jini da zuciyar sa game da ita, yayi 'kokarin kawar da idanun sa ga barin kallon ta amma sai yaji bayi da 'kwarin gwiwar yin hakan.. sam ya kasa. 'Karshe lumshe idanu yayi sannan ya bu'de su akan Mufee dai- dai tana sake ambatan " Mammi...a karo na uku...". Mi'ka mata yarinyar yayi kawai ya mi'ke tsaye, sai ya saki wani dogon numfashi. Bai yi niyyan cewa komai ba a lokacin dan haka kawai sai ya nufi hanyar fita...sai kuma ya tsaya cak ya waigo, sam ita bama ta kula da tafiyar tasa ba hankalin ta kacokam na a kan yarinyar ne.." Mamana...Feefy na take fa'di tana mai shafo fuskar ta cike da 'kauna...'karshe rumgume ta tayi a jikin ta kawai ta saki sabon kuka ganin yarinyar bata sake yi mata magana ba. Rayyan dai yau ka'dai ya gama saduda, ya gama sallamawa al'amarin Zaitoon da Mufeeda domin shi kansa bazai iya cewa ya fita 'kaunar yarinyar tasa ba..." Ki yi mata wanka da ruwa mai 'dumi zata warware...". Abinda kawai yace kenan ya sa kai yy waje...ko Innani bai yi wa sallama ba ya fice ya 'dauki hanyar gida. Duk wasu buri da tarukan tambayoyin da yayo guzirin su haka ya hadiye abinsa ya bi bayan su da ruwa mai sanyi. Yadda yace 'din haka tayi, wanda sai bayan tafiyar tasa ne ma Innar Zaitoon ta ga jikin yarinyar abin ba 'karamin mamaki da tsoro ya bata ba..baki 'daya ta koma jajir da ita kamar an shafe ta jini. Baki Inna ta kama tace" Allah buwayi.." " Toh ina shi kuma uban yake yanzu..?" Kallon Inna Zaitoon tayi ta waro idanu domin sai a lokacin itama ta tuna da shi...". Ban sani ba Innah" tace tana mai sake mayar da kanta kan Mufee sannan ta 'karasar" Babu mamaki ya wuce domin ba 'karamin aikin sa bane tafia babu sallama...". Shiru Innani tayi amma sam bata ji da'din hakan da yayi ba, ai ko 'kwan zabbi ya tsaya ya tafi wa Mahaifiyar sa da shi...sai dai bata zafafa ba tai masa uzuri akan ko ciwon 'diyar tasa ne ya rikita shi shima. Cikin sa'a zuwa washe gari jikin yarinyar ya dawo normal tamkar ba ita ba, kuma bai hanata walwala tamkar yadda ta saba ba, dan ko washe gari ma da Khausar tazo duba ta tsokana tasa ta agaba da shi da tana fa'din" Yarinya garin mu ya kar6e ki sai wani 6ul6ul kike 'karayi kina zama wata jajir da ke...toh dai 'kauyen ku zaki koma mu bama maraba da ba'ki". Inda tayi maganar tana yar daria. Zaitoon ma murmushi tayi..cikin ranta ta furta Khausar kenan...da kinsan matsalar ta kika kuma san ya gidan su mahaifin ta yake da baki furta hakan ba...". Amma da yake tasan wasa take yi mata sai bata wani damu da maganar ba. A wajen Khausar take jin cewa ai jikin Abban su da sau'ki yanzu sosai jiya da yamma suka dawo sai zuwa wani sati wai za'a koma asbitin...da'din wannan albishir sai ya kwa'daita mata zuwa gidan itama ta duba shi. Bata je a ranar ba, washegari ta sanar da Innar ta akan zasu je can duba jikin Abban ta, Inna kuwa bata hana su ba, sbd ko ba komai ai mahaifi yake a wajen ta amma tayi musu fa'dan kar su da'de acan sbd tasan Iyami na nan da halin ta bata canza ba. Ko da ta fita bata wuce gidan direct ba..gidan Yah Bukar ta shiga, cikin sa'a kuma sai ta same shi a gida, tun daga 'kofa Ummaru yake ihu da murnar ganin su abinda ya jawo hankalin Azeema kenan ta mi'ke tsaye daga wankin da take yi ta tsumayi shigowar su, so take ta tabbatar wa idanun ta shin su 'dinne da gaske ko kuwa 'karyar Ummaru ce. Ilai kuwa su 'din ne dai, mamaki sai ya cikata, toh me ya kawo su gidan nan? Ta tambayi kanta. Abinda tuntuni take so ta fahimta kenan ta kuma gaza yin hakan domin sam Yah Bukar bai bata damar fahimta ba, shin dama ya sakko daga fushin da yake ne ya amshi Zaitoon bayan yawon iskancin da ta tafin ko kuwa dai. Tana so ta fahimta ta kuma 'kara sanin wani abu daga Zaitoon amma sam ko hirar ta 'dauko masa sai ya kawar da ita ya kawo wata. Ko sallamar tasu ma kasa amsawa tayi sai tsawa da ta buga wa Umaru da fa'din" Kai dallah can, ka bi ka ishi mutane da korototo sai kace wasu mutanen kirki ka gani..idan baka rufe min baki ba zakaci dukan tsiya wallahi a waje na...". Murmushi Zaitoon tayi da jin kalaman Azeeman, sai kuma ta sake doka wata sallamar...ta daban. " Lafia kam, ina fata ba makauniya bace ke?" Tayi maganar a zafafe tana duban ta. Kai ta girgiza mata sannan tace" Ko 'daya, gani nayi ita sallama cike take da manufofi na alkhairi wanda fa'idar amsa ta baya da iyaka". Bama ta bari ta gama ba tace" Toh ri'ke abar ki ni ba ita nake da bu'kata ba...ita alkhairi kewaye da ita nake kusan kowacce rana...Allah dai yasa lafia na ganku gidan mutane da wannan tsakar ranar..?" Kafin Zaitoon ta bata amsa Yah Bukar ya 'daga labile yana yi musu iso, domin duk abinda ake yi 'din a kan kunnuwan sa ne. Wajen zama ya basu fuskar sa babu yabo babu fallasa ya kuma 'kwala 'kiran Azeema akan ta kawo musu ruwa. Kwafa tayi sannan ta 'kira Ummaru tace ya kawo kofi...'debi ruwan can ka kai musu kai..." Yace" wannan?" Tace" Erh..shi nace" Tana mai tsare sa da idanuwan ta. Yace " Wannan fa ruwan..." Bata bari ya 'karasa ba ta watsa masa wata uwar harara. Hakan yasa shi yin gum da baki ya 'diba ya kai musu. Yana ajiye ruwan ya fara jan Mufee da wasa da yake ta sanshi da kansa ma ya sha zuwa can gidan Inna..yau 'din ma rashin 'karfin jiki ya hanata sakewa tayi wasan. Itama yau Zaitoon taka tsantsan take da yarinyar sbd masifar mahaifin ta..sosai take gudun duk wani abu da zai tta6a lafiyar ta..hkn yasa bata damu da rashin sakewar ta suyi wasan ba..tafiso dama ta ri'ka ganin motsin ta baya ga hk ma sam bata gane inda Azeema ta dosa game da su ba. Garin wasa 'kafar Ummaru ya ture cup 'din ruwan da ya kawo ya kuwa malale a 'kasa baki 'daya tun kafin su kai ga shan sasa. " Subhanallah" suka ce atare, fa'da Yah Bukar ya fara yi masa akan rashin natsuwa...sannan ya 'kara da fa'din maza je kawo abinda za'a goge ruwan da shi. Allah ma yasa leda carpet ne a 'dakin..Zaitoon da kanta ta ansa ta goge shi tass sannan ta shanya sa. " Daga zuwan mutane ka sasu aiki Ummaru, gashi ko ruwan basu sha ba ka malalar da shi, maza je ka 'debo musu wani ruwan su sha". " Yayah babu wani ishi ma fa, dayake dg gida muke ai" Ummaru ne yy caraf yace" Abba bama ruwan ai ya 'kare, waccen ma ragowar awaki ne da suka rage fa akace na 'debo musu". Idanu sosai Yah Bukar ya waro akan Ummaru cike da mamakin sa. Zaitoon dai kam batayi mamaki ba dan Azeema ba ba'kuwar ta bace..inda dai ta gode Allah da ya kasance ita har Mufeeda babu wanda ya kai ga shan ruwan. Cike da haushi Yah Bukar ya fita waje bai da'de ba sai gashi ya dawo da leda cike da robobin ruwa da na lemo. Azeema dake wanki cikin gida mamaki da takaici ya hanata cigaba da wankin. Shi kuma bai ce da ita 'kala ba ya sake wuce ta yy ciki. " Yayah duk wannan sai kace mun kai goma, ai dama baka siyo ba wlh sai kace wasu ba'ki.. " Shi dai bai ce komai ba, domin har ga Allah ba 'karamin kunyar bayanin da Ummaru yy musu yy ba..taya Azeema zatai masa hk...ya rasa amsar sam, meyasa ta aikata hkn ya kasa ganewa...shin matsayin Zaitoon a wajen sa ta mance ko yaya, ko kuwa dai tana tunanin ya canza ne? Dalili kenan ma da yasa shi jan su da hira duk da ba hk yy niyya ba, sun sha hira kuwa sosai irin wanda suka da'de basu yi irin ta ba. Can gida kuwa ashe tun bayan fitar su Rayyan yazo dan hankalin.sa yaya kasa kwanciya da yanayin da ya bar Mufeeda tun ranar nan...Inna ce ta sanar da shi ai sun tafi can gidan mahaifin ta. Baiyi 'kasa a gwiwa ba ya 'dauki hanya ko da yaje basa can. Haka ya 'dan zauna da mahaifin na ta nan ma yake samun labarin rashin lafiyar tasa, ya tausaya masa sosai, 'karshe ku'di masu yawa ya bawa Iyami kafin ya bar gidan wai ko zasu nemi wani abin tunda yana under medication ne. Can ya koma gidan Innani da tunanin ko sun koma ne ganin har fa ya bar gudan bai gansu ba...kuma bai ssamu labarin zuwan su ba. Abin mmk shiru har lokacin bb su babu alamar su. Waje ya koma cikin mota amma ya kasa zama, hk ya riqa shiga yana fita sam yama mance da cewa gidan sirkan sa ne. Har Innar Zaitoon ta gabatar masa da abin sha amma ya kasa yiwa abin ko kallan arziki sbd damuwa. Bakomai yake tunawa ba sai wancan ranar, ina kuma ta sake kai masa yarinya bai sani ba...ya rasa me yake damun Zaitoon kwanan nan..gani yake ta canza masa baki 'daya...haka nan kawai sai yake tuna wancan ranar da tarar da ita da Adam. Wannan tunanin ya hanasa sakat, ya kuma kasa tafia batare da yaga 6ullowar su cikin 'koshin lpy ba. Koda taje gidan kuma babu wanda ya sanar da ita batun zuwan sa, Abban su ne dai kawai ke bata labarin kirkin sa yana kuma sanya masa albarka, ita dai bata san dalili ba, bata kuma san meyasa yake sanya masa albarkan ba, shi kuma Abban bai ce da da ita a ranar ya shigo ba. Iyami kuwa tun shigar ta gidan ko gaisuwar kirki bata tsaya sunyi ba ta fice abinta har suka bar gidan kuwa bata dawo ba.. Khausar ma an shiga gari bata tarar da ita gida ba. Da ta gaji da batun Rayyan a bakin Abban kawai sai ta kawo wata hirar ta kawar da waccan. Basu suka koma gida ba kuwa har sai bayan sallar la'asar..Mufee rungume bisa kafa'dar ta tana baccin ta cikin kwanciyar hankali. Zaitoon baki 'daya tasha jinin jikin ta tunda taga mota a waje tasan shine domin sarai tasan kalar motocin da yake hawa. " Wannan dai anyi fitinanne.."! Ta furta cikin zuciyar ta tana me ha'de ranta sosai. Yau kam 'dakin Innani ta wuce direct sbd fargaban abinda zai biyo baya, dan tasan fitina kawai ta kawosa, kuma bata mance da masifar da tasha waccan ranar ba, gashi yau ma ta fita yazo bata nan. Ko Mufee Inna bata bawa masau'ki a 'dakin ta ba balle Zaitoon tace su koma nasu 'dakin tunda jiran su ake. " Inna yau dai rashin kirkin ake ji da shi" Ta fa'da cikin ranta. A fili kuwa cewa tayi" toh Innani bari in kwantar da Mufeeda sai inje mu gaisa.." Ta fa'di hakan ne da tunanin idan zata iya masa 'karyar ba da 'diyar sa ta fita ba. Ai kuwa Inna tace " sam..kai ta wajen ubanta ya ganta..kinsan da'dewar da yayi ne yana jiran zuwan ku...?" Baki ta tura ta fito tana gyara ri'kon Mufee ta sanya takalmin ta fita. Sallama tayi ciki- ciki ta kuma sa kai lkc guda tana mitar shigan mata 'daki da yake batare da iznin ta ba. Tana shiga kuwa ta tarar da shi tsaye hannayen sa duk biyu cikin aljihun sa. Kallo 'daya tai masa ta tabbatar ransa 6ace yake 'kololuwa. 'Kasa tayi da idanun ta wani mugun fitsari ya kamata. Banda 'kirjin ta dake rige rigen dukan uku uku. Juyawa tayi da niyyan barin 'dakin domin dagaske fitsarin ya matsa ta. Ganin ta juya 'din yasa shi yin gyaran murya dai- dai wayar sa ta 'dauki 'karan shigowar 'kira. Cak ta tsaya sai dai bata waigo ba. Yadda ta gyara ri'kon Mufee a kafa'dar ta da 'karfi har sai da yasa yarinyar farkawa. Rass ta bu'de jajayan idanun ta da bacci ya rina su ta sau'ke su akan Rayyan...sake waro idanu tayi sosai tana duban sa. Sosai Zaitoon ta ha'de ranta tamkar an yi mata wani gagarumin laifi...sam bata tsammaci ganin sa ayau din ba, sam batayi tunanin zai zo ba..toh me yakawo shi yau kuma...?..me yasa tun zaman da tayi a gida bata fita ba bai zo ba sai yau ka'dai da ta fita dan neman fitina. Tana tura baki da haushin da ke cika ta ta waigo, da sauri Mufeeda ma ta waigo tana duban sa" Ni fitsari zani..."! Ta furta still tana tura baki. Bai tanka ta ba idanun sa na akan wayar sa tamkar bai san da wanzuwar ta ba..har sai dda ya gama duba abinda yake gani cikin wayar kafin ya 'dago idanu. Mufee ma 'kura masa idanu tayi tana duban sa yana 'dago kai kuwa akan ta ya sau'ke idanun sa. " Mama na..sarkin yawo.."! Ya fa'da yana 'ka'kalo murmushi. " Zo mana mu gaisa...". Ya fa'di hk ne yana mayar da wayar sa cikin aljihun gaban rigar sa...gami da 'daga 'kafa ya tunkari inda suke tsaye. Zaitoon ji tayi 'kafar ta ya fara rawa tamkar bazai iya 'daukan su su biyun ba, tsoron masifar sa take, balle yadda taga ko kallon arziki Bata samu daga wajen sa ba. Duk iya sanin da tayi masa kuma a yanzun ta kasa fahimtar yanayin da yake ciki...sai dai sam fuskar sa babu walwala ma, ko wacce take gani 'din ma a zahiri kawai yk nunawa sbd 'diyar sa..sai ma taga yana ta 'kara ha'de girar sama da ta 'kasa..ko me akayi masa oho. Cikin takun sa na isa da 'kasaita ya iso gaban ta ya tsaya cak...hannu ya mi'kawa Mufee batare da wani musu ba kuwa ta tafi wajen sa. Hankici ya ciro yana tsane mata zufan dake saman goshin ta yake fa'din" sarkin yawo...bb ko gaisuwa ne...?" Ya 'karashe maganar da jan hancin ta, Mufee murmushi kawai tayi masa dan baccin bai sake ta. Yace" baki tambayi Ammi da Antyn ki Marwa ba...?" Jin sunayen da ya ambata yasa ta saurin darawa a hankali tace" Anty...". Yace " tana gaida ki itama"! Zaitoon kam hanyar waje tayi ganin ko ta kanta bai bi ba, 'diyar sa ce kawai agaban sa...wani ajiyan zucia ta sau'ke Jin Bai bi ta kanta ba da alamu zuwan nasa Mufeeda yazo gani. Har ta kusa fita ta tsinkayi muryar sa yana fa'din.." Ki ha'do min kayan ta...zan wuce da ita yanzu tunda yawo kawai kk iya koya mata..da zaman hira da wasu gardawa". Wani irin juyowa tayi ta jefa masa kallon firgici...bai kalli fuskar ta ba amma ya jinjina mata kai alamun dagaske yake. Bata san lkcn da ma tayi masa kallon baka isa ba tayi kicin kicin da fuska, bama shi ba hatta ita kanta sai da ta bawa kanta mamaki, bata san tayi hakan ba, Mufeeda ta kalla tana ji tamkar taje ta 'kwace ta a hannun sa..meyasa bai yi maganar ba har sai da ya tabbatar yarinyar ta shiga hannun sa? shin hakan adalci ne? Meyasa zai ce yawo take koya mata bacin tana da tabbaci Innani ta sanar da shi can gida suka je. Idanu ta lumshe ta kuma bu'de su akan sa suka ha'de idanu...zirrr kawai sai ga hawaye sun gangaro mata da gudun su. Bata furta komai ba kawai tayi waje da gudu ta nufi 'dakin Innani ta sha kukan ta son ranta. Ita kanta Innar bata san cewa tana 'dakin ba balle tasan abinda ke faruwa dan a lkcn tana cikin kitchen tana ha'da abinci.' Sai da ta kammala ta koma 'dakin da fatan Allah dai ya jeho mata wanda zata samu ya mi'ka masa abinci anan taga Zaitoon. " Ke kuma kukan me kk anan..yaushe ma kika shigo min 'daki..?" Cikin kuka tace " Innani wai tafia zai min da yarinya fa..kuma wlh bashi da kirki idan yy niyyan abu...". " Toh fa!..shin in tambaye ki mana? "..shin 'diyar nan taki ce ne ko kuwa tashi...?" " Innani ai dai tawa ce tunda tare ya gan mu da ita..ni dai dan Allah ki ce ya bar min kaya na..indai zaman hira da wasu ne bazan sake ba, kuma bazan sake zuwa ko'ina da ita ba" Tana kuka sosai take maganar. Cike da mamaki Innani ke duban ta..ganin yadda take kuka gami da ro'kon nata. " Wannan 'daurawa kai 'din har ina wai...mutum da 'diyar sa?" " Dan Allah Innani kice kar ya tafi min da ita.."! " Me yasa shi baki ro'ke shi da bakin ki ba sai ni da kika raina zaki zo nan kina wani yimin kukan banza...Ni tashi kije ki 'dauki abinci ki mi'ka masa kafin yace yanzu zai wuce..". Kamar bazata tashi ba sai kuma ta mi'ke simi simi...ta nufi hanyar waje. Innani ta cigaba da mita..." Yarinya sam bb wayo...kowa ma sai kin bari ya gano raunin ki...shiyasa zaki ta shan wahala a rayuwa ai..." Ko da taje 'dakin da sallamar ta ciki ciki ya amsa mata kamar yadda tayi tata sallamar. Fuskar sa wasai tamkar ba shi ba yana ta hira da Mufee duk da ba komai da take iya fa'da yake ganewa ba koda ta fa'da amma duk da hakan biye mata yake yana kuma jin nisha'di sosai..musamman da yaga yadda take 'dan sakin jiki da shi ba kamar baya ba. Ganin shigowar Zaitoon ne yasa shi canza akalar maganar tasa izuwa.." Mamana...dole zan tafi dake fa..bazan iya barin ki ana koya miki yawo a banza ba..."! Wani duka da zuciyar Zaitoon yayi ita kanta sai da ya bata tsoro, kuma ko da wasa ya'ki duban inda take..balle su ha'de idanu..take har ji tayi kanta ya fara sarawa. Kar dai da gaske yake tafiyan zai yi da ita. Abin hannun ta ta ajiye sannan ta zuba masa abincin dai- dai yadda tasan zai iya ci, kuma duk abinda take hawaye bai bar zuba mata ba bata kuma 'daga ido ta dubi fuskar sa ba sbd tsananin haushin sa da take ji..sai da ta ha'da masa komai kafin ta mi'ke tsaye..shima mi'kewar yayi ya tari gaban ta, bisa kafa'dar sa ya kwantar da Mufee ta kuwa yi luf. Sai ya zamana shi ka'dai ke fuskantar Zaitoon. 'Kasa sosai tayi da kanta wasu sabbin hawayen na sake sau'kowa. Ido kawai ya zuba mata ya'ki cewa komai. So yake kawai ta ro'ke shi da bakin ta amma taurin kai ya hana ta. Salmerh😍 [23/01, 6:53 am] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Wattpad@* _Serlmerh-md_ 🅿️ *...104* ........" Kukan fa...duk na menene haka?" Bata ce komai ba sai ya cigaba. " Baki so zuwa na ba ko?...nasani ai..fa'da min toh waye shi..mecece ala'kar ki da shi da har ya samu daman ta6a min kayan sawan matata da hannayen sa.." Ba shiri ta 'dago ta dube shi..suka hade idanu. Da sauri tayi 'kasa da nata idanun. Sai lokacin ma ta tuna..." Yah Adam wai?" Ta tambayi kanta. Sassauta muryar sa yayi. " Kina son shi ko?" Bata san lokacin.da ta sake 'dagowa ta dube shi ba hawayen dake idanuwan ta suka tsaya cak...tabi sa da kallon mamaki. Shi kuma ya cigaba.." Kar ki damu fada min waye shi, nayi mk al'kawarin..daga yau ma bazan sake zuwa ba..dama ita ke kawo ni..kinga idan na tafi da ita ai shikenan...sai kiyi ta yawon ki son ranki, ki yi walwalar ki da samarin ki son ranki babu mai hanaki..."! Gefen sa tabi da gudu ta fita tsakar gida ta zauna tana share wasu zafafan hawaye cike da tashin hankali. Rayyan bayan ta yabi da kallo tsawon mintina biyu yana tsaye a wajen sannan ya sake komawa ya zauna..zuciyar sa cunkushe yake jin ta. Sama- sama yaci abincin wannan ma sbd Mufeeda ne dan ya lura tana da bu'katar abincin, yana ci yana bata a baki, ka'dan ya ci bai sake kaiwa bakin sa ba sai dai ita, dan ji yake tamkar 'kaya yake taunawa sbd bakin cikin da ya riga ya cika shi, sai da ya tabbatar ya ishe ta sannan ya fara shirin tafia. Zaitoon ko tarin kirki bata iyawa sbd yadda ta matsu taga ya bar gidan ta 'dauke 'diyar ta zuwa jikin ta...addu'a take yi Allah yasa ba dagaske yake ba. Lokacin da ya fito tafia, wani shegen ajiyan zucia ta sau'ke da taji har yanawa Innani sallama bata ji batun Mufeeda ba, sai dai murnar ta ta koma ciki ne da ta tsinkayi muryar sa a 'karshen maganar yana ce da Innani Auwal zai zo 'kanin Nadia ya 'dauki Mufeeda tayi musu kwana biyu may be ko cikin Ramadan haka. Tunda Zaitoon tayi 'kasa da kai bata sake 'dagawa ba, ashe ma an gudu ne ba'a tsira ba, bata ma san lkcn da ya gama da Innani ya fita ba sai ji tayi Innani na fa'din ai sai ki je kiyi masa sallama da godia ko...?" Anan ta dubi Innani da idanu Innani ta nuna mata kayan da ke jibge a gefe da alamu siyayya yai musu kenan. Kamar bazata mi'ke ba sai kuma dai ta tashi ta fita. Ya shiga mota yana shirin tayarwa ya hango ta, hakan yasa ya dakata. Ko da ta iso 'kin duban fuskar sa tayi shima 'din bai damu da dole sai tayi hakan ba yace " Ya akayi..." Yana duban gaban sa. Tace" Angode..."! A ta'kaice " Da akayi me fa...? Ohh da na zo?...ai ba wajen ki nazo ba nazo ganin 'YATA CE..". Ji kawai tayi ta 'daga kai ta kalle sa anan suka ha'de idanu..sai ya sake waro mata idanun sa gami da jinjina kansa alamar tabbatarwa. Sai tace" Allah ya 'kara bu'di ya tsare hanya..."! Daga haka ta juya ta koma gida ko waigowa bata sake yi ba. Shi kansa yy mamakin 'karfin halin ta ayau 'din, yarinyar ta canza masa sosai. Ya da'de yana tsaye batare da ya ja motar ba kafin ya gathering courage yy gaba yana me amsa waya da sauti sassanya. Sam Zaitoon bata san zancen da ake ba, bata san komai dake faruwa ba dan Innani bata wani dogon hira da ita balle taji daga bakin ta. Haka kawai kuma tun wancan ranar bata sake fita gidan hakan nan kawai batare da 'kwakkwaran dalili ba, ko da fita ya zam mata dole ne sai ta ri'ka jin fargabar fita kar yazo yace dagasken yawo take koyawa 'diyar sa. Kusan ko wani lkc fargaba da gudun abinda zai janyo ya furta mata wata kalma akan Mufee take..balle wasu maza daban. Atai'kaice dai yakan yawaita zuwa mata rai duk da bawai ta tsara hakan cikin jadawalin rayuwar ta bane ko kuma a son zuciyar ta ba. Ko ranar da Yah Adam yazo tafia da su wajen dangin mahaifiyar ta ita har Innanin zuciyar ta fal fargaba, amma har suka je suka dawo bata ji natsuwa ba, tayi murna kam ta kuma yi farin ciki, musamman yadda taga Innani cikin 'yan uwa dangi da mahaifan ta abinda tun tasowan ta bata ta6a gani ba sai a lkcn, anyi kuka sannan aka sha hirar yaushe gamo, taga dangi sosai, taga soyayya ta zahiri, taga yadda ake nuna 'kauna ta 'yan uwantaka, hakika sunyi rashi sosai da basu san juna tuntuni ba, anan tasan ashe 'yan uwa da 'dadi ashe itama tana da nata dangin masu yawa, masu son ta, masu 'kaunar mahaifiyar ta da gaskia, domin duk wani wanda keda ala'ka da mahaifiyar ta a ranar sai da yazo suka ga juna..kowa na nan nan da su, hatta Mufeeda bb wanda ya nuna mata 'kiyayya ko kyara duk da Yah Adam ya riga yy musu bayanin wace ita matsayin 'diyar mijin ta ne... Haka ma Yah Bukar bb wanda ya ware sa. Amma ansha kuka, kuka ne irin ajiyayyen nan, kuka irin wanda ta jima bata ga anyi sa ba. Sosai da sosai ta tausayawa Innar ta. Kwanan su biyu cikin dangi suka dawo zuciyoyin su cike da kewar juna. Kamar ha'din baki kuma sai ga Auwal ma yazo washegari wai tafiya da Mufee zaiyi, abin sai yai mata yawa...kuka ta ri'ka yi babu ko kunyar idanu ta ri'ka share 'kwalla har sai da ta bawa Innani haushi. Yah Bukar ne ya lallashe ta da 'kyar ta bari aka 'dauki yarinyar...gani take tamkar raba su ake son yi shiyasa aka tsiri wannan tafiyar...ita kanta Mufeen kuka take tana 'kiran Mammi...Mammi har suka wuce ...ita kuka Zaitoon kuka. Bayan tafiyar su kuwa har zazza6i sai da ta kwanta, rama kuwa kallo guda zakai mata ka fahimci irin ramar da tayi. Amma Innani ta fita hanyar ta sbd ita aganin shishshigewan yayi yawa harma ta fara bata haushi. Babu wanda kai tsaye zai fahimci halin da Zaitoon take ciki sai wanda yayi wa sha'kuwar ta da yarinyar farin sani. Shiyasa Innani ke ganin ai za'kewar ta ce tayi yawa, wacce ma ta haifi yarinyar ai ta tafi ta barta balle ita karere...acewar Innani. Tunani kawai Inna tayi yau wannan idan akace za'a raba auren ta da uban yarinyar kuma su amshi 'diyar su wa ma yasan irin halin da zata fa'da...shiyasa bactun yau ba take mata addu'a da fatab dacewa. Fatan ta kawai Allah ya yi mata za6i mafi alkhairi..inma uban yarinyar inma wani daban. Tun bayan dawowar Zaitoon gida akalar adduar ta ya sauya. Rayyan kuwa bai sake zuwa ba haka kuma ko a waya basu yi magana da shi ba ya share ta... Sai da Khausar tazo ne ma take ji abakin ta cewar suma an kai musu kayan abinci sosai acan gidan kuma an sake tafia da Abban su asbiti sai dai bata san waye yasa ayi hakan ba. Wasa wasa sai da Mufeeda tayi sati, Zaitoon duk ta rame sbd damuwa ga azumi da aka fara. Mufee na ganin Zaitoon madadin tayi farin ciki a a kawai sai ta sanya kuka sai da tasa kowa daria. Duk wani abu dake faruwa abakin Khausar take jin sa. Abu guda da idan ta tuna ko da ita ka'dai ce a 'dakin sai tayi murmushi shine kasancewar Adam Shaheed matsayin 'dan uwan ta na jini, bata kuma san meyasa take jin hakan akan sa ba sosai dai abin nan ke yi mata da'di. ***** Anyi bikin sallah lafiya sai fatan Allah ya kar6i ibadun bayin sa ya kuma samu cikin bayin sa 'yantattu. Koka'dan Zaitoon bata ta6a neman abu ta rasa ba domin an wadata su da komai, a hakan sai abinda suke so suke ci, ita da Mufeeda, domin hatta Adam ba a barsa abaya wajen hidimta musu ba, har ma za'a ce yafi kowa tunda shi akai akai yake zuwa, ga Yah Bukar ga Rayyan ga 'yan uwan Nadia...abin ba'a cewa komai. Sallah da sati biyu aka 'dago maganar tafiyar su Kano wai zata koma matsayin matar Rayyan akaro na biyu. Abin sai yy mata bambara'kwai, itafa tunda taga an 'dauki lkc bai zo ba bai aiko ba bai kuma yi maganar Mufeeda ba shikenan ta saki ranta cikin yan uwa da dangin ta...kuma kusan kullum suna magana da Marwa da Ammi da wayar da Adam ya bawa Innani...kuma ko su ba sa mata maganar sa..sai dai Mufee. Har waya ake ha'da su da Mufee suyi, suyi video call suyi voice call kuma tana ganesu. Zaman aure da shi kuma dama ba 'kauna take ba tuntuni ma ta mance, duk zaton ta shikenan magana ta 'kare tunda bb wanda ya sake 'dago maganar, ita indai za'a bar mata Mufeeda tare da ita toh bata da damuwar komai. Shiyasa tuni ta saki rai taci gaba da rayuwar ta ashe ta'kaitaccen mafarki take. Baran ma da taga yanzu Alhamdulillah lafia ta samu ga Abban ta, yana gani sosai dan an masa aiki a idanu sosai..sai matsalar hawan jini da shima Alhamdulillah ya sauka sosai yanzu.. ashe wai Yah Adam ne ya fara 'daukan nawin kai sa asbiti, daga baya Rayyan ya 'karasa, sosai tayi masa godia tayi masa fatan alkhairi mai 'dorewa har 'karshen rayuwar sa...yace babu komai, ai shima Abban sa ne...hakika dan uwa dan uwa ne. Rayyan kuwa sai dai tayi masa addu'ah kawai tunda ba ganin sa tayi ba balle ta gode masa. Abban nasu ne yace sam sam shifa dagasje bai yadda a sake wata hidimar biki ba kawai a maida yarinya 'dakin mjin ta, shi dai Yah Bukar ba haka yaso auren Zaitoona ya kasance masa ba Amma tsarin Allah daban yake...sai dai duk da hakan zasu yi iya 'ko'karin su wajen ganin ba'a barsu abaya wajen nuna mata gata ba. Adam ma hakan yace...domin yanzu bakin su 'daya ne da Yah Bukar tamkar dama can sun san juna..'karshe dai aka yanke babu wani taron biki da za'ayi kawai gidan mijin ta za'a mi'ka ta kowa ya bita da fatan alkhairi kawai. Wannan magana ta komawar Zaitoon ba 'karamin tada hankalin Iyami yayi ba, ta ri'ka shiga tana fita amma ina...komai ya tsaya mata cak. Dama ba ko da yaushe nasara ke 'dorewa bawa ba...wani sa'in ka kanyi nasara, wani sa'in ka kan fa'di 'kasa warwass...idan ka matsa kuma sai kayi gangancin da zai iya kai ka ga nadama maras iyaka. Sun taka rawar gani fiye da zaton duk mai zato, yayin da Iyami duk jikin ta yayi sanyi ganin yadda kowa ke faman hidima da nuna farin cikin sa a fili. Ta kasa 6oye 'kyashi da ba'kin cikin ta. Babu kuma wanda bai nuna bajintar sa ba cikin yayyen ta, sai da suka yi mata kaya na gani a fa'da, kaya en gaske dake nuni da zallar gatan ta. Ammi kanta sai da tayi fa'da, ita aganin ta ai an riga an zama 'daya Zaitoon tasu ce ko da Mufeeda ko bb ita, dan kuwa zaman da suka yi yaci ace an bata wannan damar na yiwa Zaitoon kayan 'daki amma suka shammace ta kawai sai ganin kaya tayi. Sai a lokacin hidimar komawan nata Babaji yazo..duk ya lalace ya rame ya zama wani firgigi da shi. Kallon ta kawai yake amma shi kansa rasa abin da zai ce da ita yayi. Nadama kawai yake a zuciyar sa ashe rashi babba yayi da ya rabu da ita acan baya, duk da yake ba laifin sa bane amma kacokam ya 'dorawa kansa laifi a halin yanzu. Fatan Alkhairi shima yayi mata kawai yayi gaba. Shi kansa uban gayyar irin taron gayya da hayaniyar ba so yake ba hakan yasa yaji da'di da wannan tsari na Yah Bukar...kuma acan gidan su ma ba wata gayyar akayi ba en uwa ne na kusa ka'dai suka hallara domin nuna farin cikin su. Gyara sosai ya yiwa gidan sa kafin aka zuba kayan Zaitoon...abin kawai sai wanda ya gani. Khausar sai mita take tana 'kun'kuni biki sai kace na wata gagarumar bazawara salaf babu komai. Dije ce tace mata babu komai kar ki wani damu, a naku bikin ai sai inda 'karfin mu ya 'kare..sai mun gaji da ciwon jiki. A hakan dai ranar wata juma'a aka mi'ka Zaitoon gidan mijin ta Kano ta dabo timbin giwa.... Ranar tasha kuka, kuka irin wanda ta jima bata yi irin sa ba, ta kuma sha fa'da da nasiha, jin ta take tamkar ba ita ba har tsoron bu'de idanu take. Tunanin rayuwar ta kaf aranar daki daki sai da tayi, ta kuma jinjinawa 'kaddara, domin 'kaddara na gangara ta ganin daman sa wannan duniyar, a ganin ta 'kaddarar ta abar labartawa ce ga 'yan baya, 'kaddarar ta na iya zama abin koyi ko akasin haka, sai dai ita kanta bata san wani matsayi zata bawa ta kalar rayuwar ba. Gum ta rintse idanun ta ta kasa bu'dewa...bata so ta bu'de idanu ta ganta a gidan Rayyan matsayin matar sa...meyasa sai ita? Meyasa da ta koma gaban mahaifan ta ba'a barta ba..? Meyasa aka sake dawo mata da 'kaddarar ta baya. Shin ita ahaka zata 'kare rayuwar ta babu walwala babu farin ciki? Meyasa basu zaunar da ita sun tambaye ta waye Rayyan ba kafin su dawo da ita? Meyasa sukai dubi ga nagartar sa ta zahiri ka'dai...shin an mata adalci ko kuwa farin cikin ta ne babu wanda ya damu da shi? A ranar tayi kuka sosai, aranar ta zubda hawaye, tayi kuka kwatankwacin ranar da ta tsinci kanta ita ka'dai da goyon jaririya babu mai mata jagora ko yi mata nuni izuwa dai- dai. Marwa ce ke 'dan 'kara kwantar mata da hankali da kalamai masu sanyi, domin yanzu duk Marwa tai sanyi...ko lkcn da taje duba su acan garin su ma Zaitoon sai da tayi mamakin ta, baki 'daya kamar ba ita ba tayi sanyi sosai. Dama ita ba wasu 'kawaye gare ta ba Dije ce sai Kuma Marwan da Allah ya ha'de jinin su...Dije kuwa na 'dakin mijin ta an dai yi duk wasu hidima da ita amma bata zo Kano ba tace sai wani lokacin idan Allah yaso. Marwa tace" Kina sani inajin babu da'di Zaitoon, sai kace baki san waye Yayah ba, ba fa ba'kon ki bane shi, babu halin sa da agani na baki sani ba..toh menene abin damuwa saboda Allah...?" Cikin ranta tace " Marwa kenan..har abada bazaki ta6a ganewa ba, bazaki ta6a fahimtar waye Rayyan ba..". Lokacin da Marwa zata wuce Zaitoon kamar ta shi'de sbd kuka, gashi babu Mufeeda wai tana can wajen Anty zata zauna zuwa wani lokaci. Gidan sai yai mata girma sosai...ko ada da take ji su Marwa na labarin girman gidan bata ta6a shigan sa ba sai yanzun, bata ta6a tunanin ya kai hakan ba, shiru yai mata ranar ko bacci kasawa tayi...tsoro da fargaba sukai mata 'kawanya, kuma ko motsin Rayyan bata ji ba balle ganin sa, dan bai le'ko inda ma take ba balle tasan da wanzuwar sa cikin gidan, shima baccin sa yayi, dan shi kansa rasa yanayin da yake jin ransa yayi...shin farin ciki yake ko kuwa akasin haka?" Ha'ki'ka akwai wani yanayin da sam baki bazai iya bayyana su ba. Ko da wasa bazai iya zayyano yanayin da yake jin zuciyar sa ba, ya dai san yana jin natsuwa sosai fiye da mafiya yawan lokutan sa na baya..domin ko baccin da yayi aranar bacci ne mai cike da kwanciyar hankali da natsuwa irin wacce ya jima bai yi irin ta ba, wanda ya tabbatar hakan baya rasa nasaba da samun damar mallakan abinda yake mai matukar daraja ne a wajen sa da yayi, shi ka'dai yasan halin da yake ciki. A yanzu ji yake kamar babu wanda ya kai sa zama cikakkken mutum kuma mai kwanciyar hankali, domin wannan karan yanayin na daban ne. Shi Kansa daban yake Jin Kansa, kamar cikin mafarki, ji yake tamkar za'a tada shi a baccin da yake, yau wai gashi ga Zaitoon, Kuma cikin gidan sa, matsayin Mata agare sa, karkashin inuwar sa, zata rayu 'kar'kashin ikon sa ba na kowa ba, zata rayu ne bisa bin umarnin sa ba na kowa ba. 'Karfe uku ya tashi a baccin...bayaso ya tsawaita tunanin hakan yasa shi tashi ya 'dauro alwala, nafilfili yayi sannan ya zuba kirari wa mahalicci ya Kuma gode Masa bisa cika Masa wannan buri nasa..ya Kara rokon sa neman zaman lafia, kwanciyar hankali, zuri'ah masu albarka, ya roki Ubangiji ya wanzar musu da zaman lafia tsakanin su ya Kuma Sanya albarka cikin rayuwar gidan sa ya kawar da shai'dan ya basu ikon sau'ke hakkokkin junan su akan su. Rayyan ya dade yana addu'o'i kafin ya kammala, bashi ya sake komawa bacci ba kuma har sai bayan da ya dawo daga masallaci. Hatta iskar da ke ka'dawa yake sha'kan ta ma jin ta yake daban, ji yake tamkar wani gagarumin nawi aka sau'ke masa, shi da kansa yasan ko sakin fuska da walwalar sa ma ya bambanta da na baya, amma duk wannan yanayin baka isa tashin farko ka fahimci halin da yake ciki ba indai ba shi ne ya sanar da kai bisa radin Kansa ba. Tun jiya bayan shigowar sa bai sake amsa wayar kowa ba duk ma wayoyin sa akashe shi da kansa ya za6i ya bawa kansa hutu yadda ya kamata. Fawwaz yaso tsokanar sa ma a safiyar washegarin amma ga mamakin sa ya kasa samun sa Sam sam. 'Yar daria kawai yy a fili ya furta shegen kaya, zaka zo ka same ni ne. Bashi ya tashi a baccin ba sai goma na safia...wanka yy cikin tsanaki ya shirya, wanda hakan ya 'dauke sa cikakken mintina talatin domin bai wani zafafa ba...ji yy ga66an jikin sa kansu basu zafafa masa ba dan hka sai yy komai cikin natsuwa. Waya guda ya bu'de wacce yake tunanin ma'aikatan sa zasu iya neman sa ciki, duk da ko yanzu ma can ya nufa amma bai san ko da wani uzurin da zai iya ji kafin wanzuwar sa wajen ba. Key ya 'dauka cikin sassanyan yanayi da kwalliyar sa ta 'kwalisa gwanin birgewa, yayi kyau cikin shigar tasa ta milk colour 'din shadda 'dinkin zamani sai tashin 'kamshi yake ya nufi hanyar fita...da isar sa babban parlon da ya linking dukkan 6angarorin gidan sai yaja ya tsaya ya kasa yin gaba. Shin anya akwai adalci anan kuwa? Anya ya kyauta kuwa, amanar yarinya ya 'dauko gaban mahaifan ta cikin mutunci da mutuntaka aka bashi ya dace ya banzatar da al'amarin ta kamar hakan kuwa? Waige- waige ya fara cikin kamilalliyar yanayi kamar ance masa zai ganta cikin parlon ne. Tashin farko zuciyar sa ta bashi shawara kai tsaye...u have to go and check on that girl...kar wani abu ya samu yarinyar mutane. Bai yi jayayya ba ya biyewa zuciyar sa kai tsaye ya nufi 6angaren da ya san take hannun sa ri'ke da makullin mota da wayar sa. This is Mr Rayyan heading to Zaitoon's apartment as his wife...amazing!...sai yy 'dan murmushi. Ko da iya jikin 'kofan kasa bugawa yy kawai ya tsurawa 'kofan idanu. hannayen sa duk biyu ya zuba cikin aljihu fuskar sa bb yabo bb fallasa. Ya kai kimanin mintina uku tsaye wajen sannan ya iya sa hannu guda ya bu'de 'kofan..while 'dayan hannun still na cikin aljihu. Bakin sa kansa nawi yayi masa dan ko sallama kasa furtawa yayi, a hankali yake takawa cikin tsakiyar parlorn tare da 'kare masa kallo. Ba 'karamin kyau kala da tsarin palorn nata yayi masa ba..navy blue 'din kujerun sun tafi da imanin sa. Sai dai ba wannan ne yafi damun sa ba kamar yadda ya lura ko alamun motsin mutum babu a 6angaren, tamkar babu wani halitta mai arai cikin sa. Ciki ya 'karasa zuwa bedroom nan ma ya tura a hankali, babu wani wadataccen haske, hakan ya sa ya 'karasa saka kafafuwan sa ciki sannan ya mayar da 'kofan a hankali ya rufe shi. Makunnin wuta ya lalu6a ya kunna Nan haske ya gauraye 'dakin Nan take. Sai da ya 'karewa 'dakin kallo tsab yaga kamar babu dai alamun mutum cikin sa, ga dai dadduman sallah Nan shimfida da kuma mayafi akan sa wanda dukkan alamu sun nuna anyi amfani da shine bada jimawa ba..sai da ya gama yawo da idanun sa cikin dakin sannan ya kai duban sa izuwa saman gado. Nan ya lura da ita du'kun'kune cikin bargo har kanta. Tsayawa yy daga wajen yake da yake tsaye batare da ya motsa ba yake hangota da kuma tunanin meyasa take bacci har wannan lokacin tunda yasan ba halin ta bane hakan sam..dole cikin biyu akwai 'daya. A hankali ya taka izuwa bakin gadon ya sake ja ya tsaya a har lkcn bai cire hannun sa cikin aljihu ba. Ido kawai ya tsurawa mayafin da ta rufa da shi shi kansa bai san tunanin me ya tsaya yi ba kuma. Gani kawai yayi kamar mayafin na 'dan motsawa alamun rawan sanyi take sai ya 'dan 'kankance idanu. Me kenan? ya tambayi kansa. Bai san lkcn da ya zare hannun sa cikin aljihu ba, wanda da zaman sa da zarewan duk bai fi cikin en 'kalilan 'din sakanni ba. Hannu yakai jikin mayafin bisa umarnin zuciyar sa Dan haka Nan kawai wani Abu ke fizgan sa ga son ganin fuskar ta. Da niyyan janye duvet din ya Kai hannun sa, amma ga mamakin sa 'dumi sosai yaji mayafin yayi. Subhanallah yace gami da hanzarin zarewa. Wani yarr yaji tsikar jikin sa ta amsa sakamakon ganin yanayin ta da yayi. Alama kawai ya gani cewa a galabaice take. Bai ma san lkcn da bakin sa ya ambaci sunan ta ba. Amma Zaitoon bata amsa ba. akaro na biyu ya sake fa'din " Zaitoon!" Gami da kaiwa hannu saman goshin ta. A lkcn ne ya tabbatar da cewa tana jin jiki...domin yadda yaji zafin jikin da Kuma yadda jijiyoyin kanta ke harbawa abin har ya bashi tsoro " Mamin Mufee...!!" Ya sake fa'di da sanyin sauti sosai cikin tsananin tausayin ta. A hankali ta bu'de idanu ta dube shi take ta sake mayar ta rufe su " Me ke damun ki..ne Zaitoon..?" Sai ta girgiza masa kai. Yace " Na'am " Da kyar ta bu'di baki ta furta. " Nima ban sani ba ". Wanda sam sautin maganar ba wani fitowa yayi sosai ba. Bai sake ce komai ba kawai ya mi'ke ya nufi bathroom 'din da ke 'dakin. Sai ma ya rasa toh me zai yi. Babu komai ko towel babu a bathroom 'din kasantuwar jiya ne mamallakiyar dakin ta fara amfani da shi. Hakan yasa ya sake dawowa cikin 'dakin. Bazai ce yana wani cikin yanayi mai dadi ba, kamar yadda bai isa yace dai dai yake jin zuciyar sa ba...Amma duk da hakan ya na Jin kaguwar ya taimakawa Zaitoon. Inda take ya koma bai yi wata wata ba kawai ya sa hannu ya 'dago ta zuwa jikin sa, can 6angaren sa ya wuce da ita. Yanayin fitan numfashin ta kawai ya gama alamta masa wahalallan yanayin da take ciki. Kan gadon sa ya kwantar da ita. Rigar sa yayi saurin cirewa ya ajiye gefe inda ya rage Masa farar singileti kadai..ya nufi bathroom cikin hanzari... ( nace himma dai maza). Bai da'de ba ya fito da ji'ka'k'ken towel 'karami a hannun sa. Saman goshin ta ya 'daura shi take ta saki wani wahalallan ajiyan zucia takai hannu jikin hannun sa tana girgiza kai alamun yanayin Bai mata...ganin bashi da niyyan Bari a hankali ta bu'di Baki da dasashshiyar muryar ta tace" Yayah sanyi fa.." " Sorry...soon zaki daina ji..kinji..." Abinda kawai ya fadi kenan ya cigaba da saka towel 'din cike da kulawa har zuwa saman wuyan ta. Gani yai ta koma wata kamar ba ita ba duk tayi laushi. Ko da ya gama, Tea ya hado mata batare da ya sanya madara ba with less sugar gudun kar ta kasa sha nd yana da tabbaci Bata ci komai ba. Da kansa ya zaunar da ita sannan ya mi'ka mata cup din yace" Sha..."! Ba idanun ta ka'dai ba hatta fuskar ta kumbura sosai sannan ko bu'de idanun Bata iyawa da kyau....sosai ta bashi tausayi. Kai ta girgiza da sauri.." Banjin yunwa.."! " Meaning..?" Ya fada Yana 'dage gira Yana kallon lips din ta data motsa. " Sai tayi shiru, gefe ta Dan juya kanta Dan gujewa kallon sa da kallon da yake binta da shi. Rai ya ha'de sosai yana Mai cigaba da duban ta..batare da ya janye cup din daga mika matan da yayi ba...tamkar ma bai ji me tace ba ya sake fa'din..." Ansa kisha ". " Na 'koshi Yaya..". Ta fa'da kamar zatayi kuka. " Ansa kisha nace.." Ya sake fadi da 'dan daga murya kadan alamun ransa ya fara 6aci. Dawo da kallon ta tayi gare shi, ta lalle shi cikin idanun ganin da gaske fa Rai ya ha'de sai ta sa hannu ta ansa ta kai baki. Sau daya ta sha ta kasa mayarwa bakin ta, hannu bibbiyu ta rike cup din kawai tana duban cikin sa tamkar mai karantar wani abin a ciki. " Ki shanye sai kisha magani..". Ya sake fadi yana mai daidaita zaman sa. Hannun sa ta kalla dake rike da wasu maganin da bazata iya tantance su ba. A hankali ta sake kaiwa bakin ta..take taji ya yun'kuro mata sai ta kasa ha'diyewa. Jin kamar zatai amai yasa ta yi saurin mika masa kofin tana shirin sau'ka shi kuma yana matsowa da niyyar bata da kansa ganin alamun kamar bata da niyyan sha ne. Ha'duwan su waje guda da tahowan Aman duk cikin kankanin lkc ya faru, tayi kokarin kaucewa hakan Amma sai da ya faru, kawai ya kwace mata ta wanke su baki daya ita har shi. Tsoro taji ya kamata..ganin ta'asar da tayi Masa. Tasan yau kam Allah ne ka'dai zai 'kwace ta daga masifar sa. Jikin sa ta fara dubawa da lumsassun idanun ta taga yadda ta wanke masa fara tass din singlete din sa da amai tana mai dafe goshi take fadin " Dan Allah...kayi... hakuri..." Tana Mai Kara kokarin bu'de idanun ta sosai Amma Bata iyawa. Mayar da duban ta ga nata jikin tayi Jin Bai ce komai ba. " Innalillahi..." Ta furta ciki ciki. Take ta dago rigar jikin tan tana mai sake sunkuyar da kanta sosai tana yun'kurin mi'kewa. Hakan duk ya faru ne sakamakon ganin yadda rigar ta manne mata a kirji bayan aman ya taba ta. Shaf ta mance cewa rigar bacci ce jikin ta kuma yar yalololuwa maras kauri, Babu komai cikin rigar daga ita shikenan kuma iya gwiwar ta take. Itama din ta canza tane cikin dare da taji bacci na neman gagararta sai tayi tunanin ko kayan jikin tan ne ya hanata baccin ashe sign na fever ne. Kunya sosai ya kamata tunowa da tayi tun dazun a haka take agaban sa Batare da ta tuna ba. Sai ma yanzu da ta tuna cewa ba dakin ta take ba sannan ta sake jinta takure sosai. Gashi ta 6ata masa jiki da amai. Har kusan neman zazza6in tayi ta rasa..Saboda kunya da Kuma Fi abinda zai iya biyo baya, amma still bata jin tana da 'karfi ajikin ta sam sam. Idanu ta lumshe tana sauraron ta inda zai fara mata masifa..bazata sai taji ya sake 'dagota straight to his bathroom bai kuma furta komai ba. Babban abinda yafi takura ta ayanzu shine rashin isassar suttura, na biyu kuma 6ata masa jiki da muhalli da tayi alhali tasan halin sa da rashin son 'kazanta. Shi kam yadda take ta 'ko'karin rufe 'kirjin nata ne.ma yake dan so ya sashi daria. Wai dama can toh ina ta makara bata tuna ba sai yanzun, baya tunanin akwai wani Abu da ya rage da Bai kalla ba a wannan wajen. 'Kar'kashin shower ya dire ta rungume da jikin sa dan yasan ba 'karfin tsayawa da 'kafafunta take da shi ba...a hakan kuma ya sakar musu ruwa mai 'dumi dukkan su. Kallon ta yake yi sosai tun daga fuskar ta har zuwa 'kirjin ta da sam ya kasa 'dauke idanun sa daga kanta. Yayin da Zaitoon ta rufe idanu ruf ta kasa bu'dewa sai dai haka nan kawai she feels that strength of his looks aranta hakan sai ya sake takurata. Tayi 'kokarin raba jikin ta da nashi da nufin juya masa baya amma abin ya gagareta. Sa6anin hakan ma sai ji tayi kawai ya 'dago mata rigar zuwa sama da alama cireta yake da niyyan yi baki 'daya. Me kenan yake shirin aikatawa?" Tayi saurin tambayar kanta. Hannu takai da sauri ta rike kasan rigar tana girgiza masa kai alamun kar ya cire mata. A kunne ya ra'da mata" sbd meyasa?" Kamar zatayi kuka tace " bafa komai... a jiki..na..."! " Kar ki damu..ba gani Nan ba..nine komin ki ai daga yanzu". Ya fa'di hakan ne cikin wani irin salon da sam Zaitoon bata gane masa ba. Hannun dake rike da rigar yabi da hannun sa ya ri'ko...yatsun sa ya sar'ke cikin nata yana mai sake rungumo ta zuwa jikin sa sosai. " Kin min laifi kuma kina min taurin kai ko?. Shiru tayi dan ita kanta tasan tayi laifin dagaske, amma ai ba laifin ta bane. Shine ya kawo 'dakin sa batare da ya ko tambayi ra'ayin ta ba. Indai hakane ai itama laifin yayi mata da ya kawo ta alhali ko sutturar arziki bai bata damar sanyawa ba gashi ya jike mata wannan 'din. Tana can tana tunanin yadda zatayi da ji'ka'kkiyar kayan nan, sanin da tayi bata da komai anan bata ankara ba taji ya raba da rigar ma baki 'daya a rikice ta waigo ta shige jikin sa sosai ta rungume shi, a kokarin ta na son 6oye jikin ta. Rayyan sai da yayi murmushi..a hankali yace" Kar a kayar da bawan Allah dai Dan ba 'karfi gare shi ba a halin yanzu..". Hannu ya kai ya kashe shower 'din jin haka yasa Zaitoon ta sake ra 'kankame shi take hawaye ya gangaro mata. Wannan wani irin mugunta ce fisabilillahi. Ta fada cikin ranta. Dan har gwamma lkcn da ruwan ke zuba ma ta dan fi sakewa da Jin 'kwarin gwiwa fiye da yanzun. Shi kuwa Rayyan ko ajikin sa...yanayin rungumar da tayi masa na sosai da sosai yasa he can feel every part of her body into his...but bazaka ta6a ganewa yanayin da yake ciki ba bcuz bai nuna wani reaction ba. " Kinsan dai ina da abinyi ba zaman bathroom ka'dai ne routine 'dina ba..dan haka sakar ni..mutane na can na jira na a office...". " Toh kunna ruwan...?" " Anqi...so kike daga fever ki kama catarh ko?". " Dan Allah Yayah.."! " Anqi..nace.." Kawai ta saki kuka mai sauti..toh dan Allah ka 'dauko min kayana...ni wama yace ka zo ka kulani..". Rayyan ji yayi daria sosai na taso masa. " Yanzu laifi nayi dan na taimaka mk?" " Ai bance inason taimakon ba.." " Shikenan naji...sakar ni toh in 'dauko mk kayan..". " Toh rufe idon ka.."! " Anqi...". " Dan Allah fa..". " Anqi". " Dan Allah fa nace" " Toh mene abin rufe idanu..?..kina tunanin akwai abinda zan gani ne..?...ni bana ganin komai..Ni da ma zan taimaka in 'dauko mk kaya shine har sai an bani umarni..?" " Shikenan yi ha'kuri toh". Ta fa'da tana mai kokarin gwada sakin shi..amma ta kasa. Ji take tamkar ta rusa ihu . Wannan wace iriyar rayuwa ce for God sake. " Uhm". Yayi gyaran murya. Sautin kukan ta kara.." Fisabilillahi Ni ya zanyi?" Ta fa'da da muryar kuka. Kamar zai Yi daria sai Kuma ya fuske. " Bari in he". Ya fa'da Yana Mai gwada cire ta daga jikin sa. Sake kankame sa tayi sosai tana Mai 6oye fuskar ta a jikin sa. Yana 'yar Daria yace" ikon Allah". A fili. Zaitoon najin hk tayi saurin sakin sa idanun ta runtse ta juya Masa baya. Kai kawai ya girgiza cikin zuciyar sa yace " yaro dai yaro ne. Sai da cire kayan jikin sa kaf ya sake kunna ruwa ya sakar ma kansa sosai sannan ya wuce daki. Zaitoon ko motsin kirki batayi ba har ya kammala ya fita sai ma ta tsungunna a wajen ta du'kun'kune...pant ka'dai ne jikin ta babu komai. Hatta rigar da ya cire mata kuma duk ya tattare yy waje da su zuwa laundry room. Towel ya daura itama ya daukan mata towel 'din. Har wani ajiyan zucia ta sauke da taji ya sake bude bathroom din tayi tunanin ko kayan nata ya kawo mata. Towel din ya rufa mata daga bayan ta sannan yace " gashi nan toh.. tashi". Har jikin ta na 6ari ta kamo towel 'din...bayan fahimtar menene ji tayi tamkar ta saki ihu sbd haushi. Bata mi'ke ba tace..." Toh Yayah wannan kaya ne fisbilillahi...?" " In baki so bani kayana toh..?" Gam ta rike tana kokarin 'daura shi daga dur'kushen. " Hmm" kawai yace ya juya ya fito. Bedsheet 'din ya janye ya shimfida wani sannan ya 'dauke wancan ya fita da shi. Har kuma ya dawo bata fito ba tana ciki 'daure da towel 'din tana tunanin ta yadda zata fito. Murya ya dan ware yace" Zanzo na amshi towel 'dina idan har na irga uku baki fito daga bathroom 'din nan ba. Ido ta waro, sarai tasan halin sa zai aikata...hkn yasa ta fara takowa tana jajjan towel din 'kasa..amma tasan bazai ta6a rufe mata jiki yadda take so ba kasantuwar 'dan 'karami ne ba babba ba, hasalima ko rabin cinyar ta bai kai mata ba. Kuma bata ta6a tsayawa gaban kowa a hkn ba shiyasa abin ya dame ta...kunya take ji sosai. Kafin ta fito ma har ya shirya shi kam cikin 'kananun kaya. Direct bathroom din ya nufa ya tura kofan fuska a'dan hade...ya nuna mata hanya batare da ya furta komai ba. Kanta a'kasa ta wuce ta gaban sa...'kafafunta na sar'ke ta. Kayan da ya ciro ya nuna Mata yana mai nufan hanyar kitchen. Kuma yy hkn ne dan bata damar shiryawa dan yasan matukar yana nan bb abinda zatayi. Cikin hanzari kuwa ta sanya rigar bata da maraba da tata ta 'dazun sai dai kawai ta nuna mata kauri. Rigar fara ce 'kal sai dai tayi mata babba sosai..ba kuma trouser bai ajiye mata ba. Ai da sauri ta koma gadon nasa ta sake dukunkunewa cikin bargo har kanta. Tea din ya sake hado mata dan yafi so yaga tasha magani kafin ya fita. Koda yaga yadda ta sake komawan kuwa bai ce da ita uffan ba har sai da yazo ya ajiye cup din sannan ya furta" Madam ya haka kuma?..tashi min da Allah akan gado ko tausayin bawan Allah bakiji ba, ya gyara abin sa kizo ki 6ata masa." Ko motsi batayi ba. Sai yasa hannu ya fizge mayafin. Take ta mike zaune tana huhhura hanci gami da tura Baki. Tea din ya nuna mata shima babu walwala saman fuskar sa kafin ta kawo masa wargi Dan yasan hali. 'Ballan maganin yayi ya mi'ka mata..ta ansa tasha..tana shirin ajiye cup din ya 6alla mata harara, sai ta 'kara kaiwa baki..bayan fahimtar manufar sa. Rabi tasha tayi fiki fiki da idanu tamkar zatayi kuka. " Give me d cup..." Yace yana mi'ka mata hannu. " Bama dole Mufeeda ta zama mai kuka ba, ai tunda ta rayu da mutun irin ki kam sai abinda Allah yayi...". Ya fa'da yana mai tafia back to kitchen dan ajiye cup din. Da hanzari ta sauko ta nufi kofa da niyyan barin dakin amma ga mamakin ta rufe 'dakin yake da makulli. Gudun kar ya dawo ya samo ta tsaye a wajen da 'yar guntuwar riga ya sata komawa da sauri ta sake na'de jikin ta da mayafin ta koma ta kwanta. Wani bacci ma take ji na fizgan idanun ta a lkcn. Shi kuwa ko da ya fito bai sake bi takanta ba yayi waje abinsa. Bazai iya sa 'kafa ya bar gidan ba a halin yanzu duk da yasan bacci zatayi mai nauyi Amma yasan ko ya fita ma hankalin sa zai Zama a rave ne, hakan yasa shi yada zango anan palorn sa ya baje duk wasu kayan amfanin sa yana duba sakonni. Da wa'danda ya jima ma bai duba ba da kuma na kwanaki biyun nan. Ya amsa waya ya kuma 'kira wasu numbobin ma da kansa yayi magana da su duk kuma akan kasuwanci ne. Yana shirin ajiye waya 'kiran Fawwaz ya shigo. " Kace zaka shigo kuma naji shiru...?" " Na fasa ne.." Ya bashi amsa kai tsaye. " Saboda me ..?" Fawwaz ya tambaye sa. " Yarinyar nan bata da lafia Fawwaz...bana son barin gidan ne ba kowa...but may be zuwa yamma zan le'ko in naga yanayin jikin nata...". " Shegen kaya..mai ka aikata Rayyan...?" Da sannu ya waro idanu...Sai a lkcn ma ya fahimci maganar Fawwaz din. Da sauri yace " Fawwaz kai munfiki ne..? Me kake tunanin zan aikata...?" Ya fa'da yana yar daria. " Ka fini sani ai..." " Ni an fada maka irin kane wai..?" " Daga baya kenan". " Zaka yi bayani ne idan mun hadu". Daga hk ya kashe wayar dan baya so maganar tayi nisa. Ya riga yasan koma menene ahalin yanzu Zaitoon sirrin sa ce...bai kamata abinda yayi ko rashin yinsa ya zamto yy exposing ga koma waye ba. Kafin ya ajiye wayan ya kira Ammi..suka gaisa..tace masa ai ba'ki na nan zuwa gidan...yace ayau?" Ammi tace" erh.. Ba'ki ne kasan wucewa zasu yi. " Yace" Ammi da sun bari zuwa gobe zai fi.." " Tace sbd me...?" " Yace haka nan kawai Ammi..". Tace toh shikenan. Ina 'diyata?" Tana nan lafia. Agaida min ita. " Yace toh Ammi ". Ya za6i yace da Ammi hakanne sbd gudun sa6anin fahimta sam baya so tayi tunani irin wanda Fawwaz yayi. Bashi ya tashi a wajen ba har sai da yaji 'kiran sallahn azahar sannan ya mi'ke ya d'auro alwala ya nufi masallaci. Yadda ya barta tana bacci hakanan ya dawo ya tadda ta, bambancin kawai a yanzu fuskar ta na waje ne ba kamar yadda ta rude shi da farko ba. Tayi fayau da ita tana bacci abinta cikin natsuwa. Bai isa inda take ba kawai ya sa Kai ya wuce masallacin sa. Sai da yaje ya dawo kafin ya koma dan sake duba jikin nata. Goshin ta ya ta6a yaji bb zazza6in ya sau'ka dan har zufa ya goge mata saman kanta. Hannu ya kai cikin mayafin ya ta6o wuyan ta nan yaji baki 'daya bb zazza6in yanzu. Wani ajiyan zucia ya sau'ke cike da jinda'di...haka nan shima yaji sha'awar yin bacci ya kamashi, ko Dan ya samawa zuciyar sa hutu Koda Babu yawa ma. Hkan yasa ya kwanta agefen ta yana duban fuskar ta yana tunanin rayuwa har baccin yayi gaba da shi. Basu suka tashi ba har sai da akayi la'asar. Zaitoon ce ta fara tashi ganin sa kusa da ita yasa ta saurin matsawa. A hankali ta sau'ka daga 'daya 6angaren da san'da ta nufi 'kofa cikin sa'a bu'de ta same shi. 'Bangaren da aka saka ta jiya ta nufa har wani ajiyan numfashi ta sau'ke ganin ta samu fita daga 6angaren nasa. Bata ta6a jin ta cikin matsananciyar takura kamar yau din ba. Rayyan kuwa tunda ta tashi yake kallon ta har ta fice ...sam baya son takura ta, baya son matsa mata akan abinda yasan ba ra'ayinta bane..shiyasa Bai tanka ba. Duk abinda take ganin ya mata aranta shi bazai hanata ba..indai yana kan hanya. Juyawa yy ya kwanta bisa cikin sa ya saki wani nauyayyen ajiyan numfashi. Ya shafe akalla kimanin mintina biyar ahakan shi kansa bazai ce ga tunanin da yake ba bazai ce ga ainahin inda zuciyar sa ta nufa ba . Wannan lkcn agida ya sallaci la'asar 'din sa dan jam'i ya riga ya wuce sa. Ko da ya idar fita yy da key din mota dan yi musu take away din abinci tunda ya hana akawo daga gida ya kuma san dole zasu bukaci abincin. Koda ya dawo gidan sai da ya fara shiga 6angaren sa ya 'dauko maganin ta kafin ya nufi nata 6angaren wanda ada yake 6angaren Amrah ne kafin ya tattara su ya bar gidan, duk da yake a halin yanzu ba 'karamin gyara aka yiwa gidan ba amma duk da haka bazai gaza gane part part na gidan ba, da sallamar sa ya isa gami da tura kofa. Sallah ya same ta take yi bayan ta shirya cikin doguwar rigar atampa da alamu dai wanka tayi. Bai zauna ba kamar yadda bai ajiye abin hannun nasa ba. A wannan tsayuwar tasa ne kuma ya samu cikakken damar karewa 'dakin kallo tass fiye da yadda ya kalla da safe. Sosai ya yabawa kokarin yayyen nata, hakika sun nuna bajinta sosai, duk da ba hakan aka so ba shi kansa bai so ace Zaitoon tazo gidan sa matsayin matar sa da ko tsinke ba but yayyen ta sun nuna su sam sai sunyi nasu kokarin shiyasa aka Basu dama, hatta Ammi ba haka taso ba amma da yake sun matsa shiyasa aka bari sukayi. Sosai kuwa ya yabawa kokarin su, dan sai ma ya ga kamar nashi 6angaren bakomai bane akan nata. Kyau da tsaruwa kam 6angaren Zaitoon ya sha shi har ya gaji. Yana nan tsaye har ta sallame sallar...sai ta dube shi ta dauke kai tamkar bata San da wanzuwar sa ba. Shima din bai ce da ita komai ba. Sai da tayi addu'a ta shafa sannan ta sake duban sa tayi kasa da kai. " Ina yini Yaya?" Kallon fuskar ta yayi yadda tayi fayau da ita sai yaji babu dadi...ciwon ne ko yunwa bai san takamamme meke damin ta ba. Kamar kuma be kyautu ace tana karkashin inuwar sa wannan matsala ta same ta ba, Zaitoon ko ba ta tare da shi sai inda karfin sa ya kare wajen ganin ya kyautata Mata, ko da zai karar da dukiyar sa ba zai Yi kasa a gwiwa wajen ganin ya wadata ta da komai da take da bukata ba balle kuma hannun sa take. Duk da yake wannan shine karo na farko kuma farkon zaman su tare, bazai ce dagangan yayi haka ba, amma duk da haka yafi ala'kanta faruwar hakan da laifin sa, duk da yafi ala'kantawa da gajiya da kuma rashin samun natsuwa lkcn taron bikin shine ya haddasa mata wannan ciwon. " Ina ke mk ciwo yanzu ?" Da kai ta amsa shi alamun babu komai Yace" Ban jiba..."! Sai da ta 'dan cuno baki sannan tace" Bako ina". " Kan naki fa?" " Yana ciwo ka'dan". " Kince bako ina kuma..?" " Ai da sauki sosai.." " Ok". Yace yana matsowa kusa da ita. Ledan ya ajiye mata sannan maganin, yace" kici abinci kisha magani zanje in dawo ki kuma tabbatar kinsha magani if not kuma...hmm". Ya fada yana dage gira. Bata ce da shi komai ba haka shima bai 'kara ba yayi gaba abinsa yama fice daga gidan zuwa gidan Anty. Salmerh😍 [03/02, 11:59 am] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Wattpad@* _Serlmerh-md_ 🅿️ *...105* ........Kamar yadda yace haka tayi, abincin ta caccakula sannan ta ta kora maganin tana yatsine fuskar ta. Yamma ta riga tayi sosai dan haka bata so ta sake kwanciya musamman ma sbd ganin maghrib ta gabato, hakan yasa kawai ta yanke shawarar zagawa cikin gidan, amma sam sai taji zuciyar ta bai yi na'am da hakan ba, tsoro ma taji ya tsirga mata lokaci guda. Nan ta zauna tana tunani bata ankara ba sai jin 'kiran sallar maghrib tayi...bata 6ata lokaci ba ta mike ta gabatar da sallan ta har tayi isha'i kuwa bata jin motsin kowa ba...nan tsoro ya sake shigan ta sosai. Tashi tayi taje ta rufe 'kofan ta da makulli, windows ma duk ta rufe su ta gyara curtains 'din ma tsaf sannan tayi shirin bacci. Duk kuwa abinda take yi cikin sanyin jiki take yin sa dan ko motsin kirki bata iyawa balle ta6a abinda tasan zai bada sauti a zahiri sbd tsananin tsoro...wani turare ma da ta 'dakko zata fesa jin yana bada sautin 'yar 'kara da sauri ta ajiye sa ta 'dauki wanda tasan bai fidda sautin komai illah kamshi tayi amfani da shi...domin ta jima da koyon son 'kamshi wajen Marwa. Tana gamawa tayi kwanciyar ta ta rufe har kanta cikin duvet sannan ta fara karanto azhkar cikin ranta. Tana 'kewar Innar ta, Mufee, da su Marwa amma ba halin magana da su. Sam bata san amfanin kawo wannan gidan ba, haka nan kawai an tsamo ta cikin 'yan uwanta aka jefo cikin wannan gida da baida maraba da kurkuku...gidan da hatta Mufeedan ta ma shamaki yy mata da ita. Lokaci guda sai tunannin ta ya koma baya, can baya lokacin da aka ta6a sace su ita da Mufee...yanayin halin da suka shiga da yanayin mutanen, a hankali tunanin ta ya gangaro kan Sultan. Wani sabon firgici da tsoro ne ya diran mata lokaci guda da ko dan yatsanta bata 'kaunar motsawa balle jikin ta, illah addu'a da take iya yi shima a zuci. Haka nan kawai sai taji wasu zafafan hawaye na sakko mata. " Banda ba'kin hali ina ma laifin akaita gidan Ammi, da yanzu suna can tare da Mufee da Marwan ta". Ta sake ayyana hakan cikin ranta. Haka ta dauki tsawon lokaci cikin wannan yanayin, bayan ta gaji da kukan bacci 6arawo ya sace ta. Bata san lokacin da ya shigo gidan ba dan haka ko motsin sa bata ji ba. Dan yakai kusan karfe tara kafin ya dawo, Mufee ya samu itama 'din nata 'kananun kuka wai Mammi, 'dan zaman da sukayi a gida garin su Zaitoon su ka'dai ya 'kara 'karfafa sha'kuwar su, ita nan Mufeeda wai har ta fara mance mutane. Tana ganin sa kuwa ta taho wajen sa da gudu ta rungume shi..koda ya 'dago ta luf tayi ajikin sa tana sauke ajiyan numfashi, sosai ta bashi tausayi. Ya riga yasan damuwar ta dan haka cikin ransa yake tunanin mafita. Bahijja ya 'kira yake tambayar ta inda wani chocolates ta kawo masa dan shi babu abinda ya riko. Anty najin haka tace" Rayyan za'kin nan fa...ban fiye son ana bata ba gaskia?" " Ba abinda zai mata Anty". Tace" Toh..Allah yasa". Kafin akawo din ne suka samu daman gaisawa da Anty. Yana bu'de mata Mufee ta dago tana duban hannun sa jin karan ledan..sai da ya sa mata abaki kafin ya bata sauran a hannun ta. " Abbah..?! Yaji dadi sosai da sunan da ta 'kira sa da shi. Hakan yasa shi amsa ta cikin tsananin farin ciki yace" Na'am.. Mamana ". Tace" Mammi.."! " Ita kike so?" Sai ta 'dage kanta sama. Murmushi yayi haka ma Anty itama murmushin tayi inda ta 'kara da fa'din" ai Mufeeda badai kulafucin uwa ba..na jima ban ga yaro irinta ba gaskia". Kusa da kunnen ta ya ra'da mata" zanzo in kaiki wajen ta kinji mamana amma ba yau ba..". Yasan ba fahimtar sa zatayi ba dan haka bai damu da amsawa ko rashin amsawar ta duk da yake Mufee sai da ta dage masa kai sama alamun ta amsa din. Kafin ya bar gidan ma har tayi bacci ajikin sa, Bahijja ce tazo ta 'dauke ta zuwa makwancin ta. A hankali tayi mata shirin baccin gudun kar ta farka dan ranar Mufee rigima take ji da shi...abinda ta yini musu da shi kenan. Sun 'dan tattauna da Anty kafin ya bar gidan, daga nan kuma gidan Ammi yayi shiyasa sai da ya kusa kaiwa tara kafin ya dawo. 'Bangaren ta ya fara nufa dan duba lafiyan ta da yake dama duk abinda yake tana nan zaune cikin tunanin sa...cikin rashin sa'a sai yaji 'kofan a rufe. Baiyi mamaki ba dan yasan halin ta, babu mamaki har tayi bacci ne. 'Bangaren sa ya wuce ya watsa ruwa yayi shirin baccin sa kafin ya tattaro wayoyin sa da duk wasu 'kananun abubuwan da yasan zai bukata ha'de da spare key ya dawo 6angaren. Koda ya shiga 'dakin wani ni'imtaccen kamshi yake da ya matukar shiga masa zuciya. Mayar da 'kofan yy ya kulle sannan ya 'karasa ciki. Sai da ya kunna AC bisa sassau'kan yanayi kafin ya isa bakin gadon wayoyi biyu dake hannun sa ya fara direwa sannan ya danja mayafin kannata zuwa 'kasa kadan. Bacci take amma yanayin baccin kana gani kasan ba cikin natsuwa tayi sa ba. Hannu ya kai ya dafa goshin ta nan yaji babu sauran zazza6in..wani sanyi yaji cikin ransa. Zama yy ya dan duba sakkoni kafin ya ajiye wayoyin ya bi lafiyar gado. Haka nan kawai yau 'din yaji bazai iya barin ta ita ka'dai kamar jiya ba. Ta6a mata abin rufa da yayi ya sata farkawa. Tayi tunanin ko haka nan kawai ne ko kuma itake ta6a abinta, amma sai taji kamar alamun mutum kusa da ita..gashi 'dakin babu haske sai na compound da ke 'dan dimming ka'dan a 'dakin. Hakan sai ya sake ta azzara tsoron dake ranta, sosai ya tsanan ta, musamman dayake dama a tsoracen ta kwanta. Hannu takai domin tabbartawa tunanin ta nan kuwa taji dai tabbas mutum 'dinne. Shikuwa yayi luf yana ji da ganin duk abinda take yi. Matsawa tayi baya da sauri ta bude baki ta saki ihu. Abin yai masa bazata duk da yake ba lallai ne ya iya dakatar da ita ba amma da sam bazai bari tayi ihun ba, domin sam babu da'di ihu da wannan daren sai azaci ko wani abin yai mata ko kuma ya cutar da ita. Kafin ta samu damar sakin ihu na biyu Rayyan yayi wani zazzafan yun'kuri ya dawo kusa da ita ya ri'ko ta. Hakan sai ya sake firgitata...bu'de baki tayi da iya 'karfin ta zata saki wani ihun jikin ta na 6ari sosai..without any doubt kawai Rayyan ya rufe mata baki da nasa. He can feel yadda jikin ta ke 6ari da son 'kwace kanta...amma ta kasa...sosai firgicin ta ya tsananta. Ka'dan ya rage ta sume masa kafin ya samu da 'kyar ya sanya hannun sa cikin nata ya ha'de musu yatsu waje guda. Tuni yaso shagala cikin yanayin amma mutsu mutsun da take ya hanasa, shi kansa natsuwar ta yake da bu'kata a wannan halin ba abu daban ba. Ganin kamar abin na neman fizgar sa ne ya shi sakin ta ya rungume ta sosai cikin jikin sa. " Miye hakan wai, ki nutsu mana, bana son wannan firgicin sam..."! Ya ra'da mata cikin kunnen ta yana shafa bayan ta. Da jin muryar sa tayi lakwas sai ma lokacin ta tabbatar shi 'dinne da gasken gaske. Amma kawai sai ta saki kuka mai sauti. Rayyan bai hana ta kuka ba, dan atleast tayi kukan fin na mintina biyar yana sauraren ta rungume da ita illah shafa bayan ta da yake yi a hankali. " Toh ya isa haka nan..."! Ya furta bayan ya tabbatar ta 'koshi da kukan cikin wata disashshiyar sautin da fitar ta ya matu'kar yi masa wahala dan sai da yayi da gaske kafin ya iya bu'de bakin sa. Abu ne da bai wani faru cikin niyya ba, coincidence ne, dan shi sam be zo 'dakin ta da niyya ko fatan samun wani abu daga gare ta ba, amma faruwar abinda ya farun sai ya kusan birkita masa asalin yanayin sa. " Kiyi shiru please..."! Ya sake furtawa ciki- ciki. Dole ta rage sautin kukan dan ita kanta ayau tayi matu'kar mamakin sa. Rayyan sam baya hana mutum kuka, if u intend to do it dama yake baka kasha kukan ka son ranka..amma sai gashi yau yana dan tausan ta akan kuka dole ta tsagaita. Sosai take jin haushin sa bisa faruwar abubuwa biyu zuwa uku amma hakan sam bazai hana ta fahimtar canzuwar furuci da kalamai da yanayin sa ba. Motsi tayi 'kakkarfa da niyyan raba jikin ta da nashi amma yaki bata wannan damar sai ma sake rungumata da yy zuwa cikin jikin sa. Saukan zazzafan numfashin sa da take ji saman wuyan ta ne ya sa ta 'kara yunkurin janye jikin ta. Wannan karan bai hana ta ba amma bai bari space 'din da ke tsakanin su yy fa'da'da ba. Da sauri ya kamo hannun ta cikin nasa..." Matsoraciya kawai". Yace atakaice. Bata ce komai ba kawai tayi 'kasa da idanun ta. " Kinci abincin?" Da kai ta amsashi. Saura magani kenan.." " Nasha...". Ta ce da shi ciki ciki. " Kin tabbatar..?" Bata amsa ba sai ma 'dago kai da tayi ta dube shi ta kuma mayar da kan 'kasa. " Jikin ma naji ai da sau'ki ko.." Tace" Umm...bana jin komai". " Bakya jin komai sai rigima ko?". Tayi shiru. Yace Allah ya 'kara afuwa..." Saman la66a ta amsa da" Ameen...". Yace" koma baccin ki toh sai ki samu natsuwa..dan nima kaina ba 'karamin firgita ni kk yi ba a yau". Yana fa'din hakan ya sakin mata hannu. Yana kallon ta gyara ta kwanta ya rufa mata mayafin kafin ya juya 'daya bangaren ya 'dauki wayar sa, rasa me ma zai yi da wayar tasa yayi ayau dan kawai scrolling ya ri'ka yi yana dawowa daga 'karshe kawai ya ajiye wayar yana mai sakin ajiyar numfashi. Kamar wasa daren ranar sai bacci ya gagare sa, abu ne da ya jima bai faru gare shi ba, dan ko da ace ya tsinci kansa cikin wani yanayi ya kan yi masa wahalar daidaita kansa koda kuwa ace yabi hanyoyin da yasan sukan kawo masa sassauci..ayau din kuma baya jin bin wadancan hanyoyin, haka kawai yake ji aran sa ayau yana tare da sassaucin sa kusa da shi ba bukatar wani kuma. Kamar wasa bacci ya gagare sa, rungumar da yawa Zaitoon ne ya matu'kar tsaye masa arai ya kasa mantawa. Wannan yanayin yake so ya sake jin sa ciki koma fiye da hakan, juye juye ya riqa yi har tsakiyan dare. Da 'kyar bacci ya 6arawo ya sace sa. Lokacin da yazo ya farka ba 'karamin mamaki yayi ba da yayi tozali da fuskar ta kusa da tashi fuskar, bu'de idanun sa ke da wuya da fuskar ta yy tozali, idanu kawai ya zuba mata batare da mamakin ta ya hakan ya faru ba dan yasan bacci ne, da ace tasan tana kusa da shi da tuni ta matsa gefe. Bai yiwa kansa ba'kin ciki ba ya kalle ta son ransa 'karshe hannayen sa 'ya 'dago ya fara zagaye lips 'din ta a hankali. Sosai yake birgesa ba tun yau ba..haka nan kawai ya tsinta kansa da son kusan ta kansa gare su. Cikin bacci kawai taji abinda ke faruwa, duk zaton ta mafarki ne so bata wani damu sosai ba, balle da tasan kafin tayi bacci hakan ya faru sai tayi tunanin ko shi 'dinne yake dawo mata. Sai da taji yanayin na neman canza salo sannan ta dawo hankalin ta amma ina ta riga ta makara, domin ya yi nisan kiwon da muwuyaci ne waigowar sa. Duk 'ko'karin da tayi wajen ckwace kanta abu ya faskara kawai sai ta saka masa kuka. Abanza..domin kuwa Rayyana bai ma san ta nayi ba. Burin sa kawai yake da mura'din cimmawa, kuma awannan lokacin ji yake idan bai samu abinda yake so ba zai iya shiga wani hali. Tasha kuka, shi kansa ya sani, domin ba 'karamin galabaitar da ita yayi ba, duk da yake kuma is not her first time amma sai da ya jin mata ciwo. Shi da kansa ya tallafa mata ta gyara jikin ta sannan ta sake kwanciya hadda juya masa baya kawai sai yayi murmushi. Daga baya kenan yarinya. Ya fa'da cikin ransa yana murmushin jin dadi. Alwala yayi kawai ya hau gabatar da sallar nafila domin alfijir ya riga ya keto yaso fita masallaci sallah amma sai bai fitan ba kawai yaja su suka yi a gida, da 'kyar ma Zaitoon ta bishi sallahn kuka take yi tamkar wacce aka ce mata Mufeeda ko Innar ta 'dayan su ta mutu. Sai da taji yace in batai shiru ba zai kuma yi kafin ta tsagaita ta bishi sallahn. Bacci suka koma atare amma Zaitoon ta'ki bari ko kusa da ita ne yazo saima cewa da take yi ya koma can 6angaren sa ya bar mata 'daki. Rayyan Yace yaqi. Haka wani baccin ya sake 'dauke ta tana cuna baki da busashshen hawayen ta. Da yake ya riga ta tashi so 6angaren sa ya koma ya sake yin wanka ya shirya sannan ya nufi kitchen ya shirya musu breakfast sassauka yadda zai iya dan shi ba gwani bane ta wannan fannin...ko yau din ma farin cikin da yake ji can 'kasan ransa shine ya 'karfafa masa gwiwar shiga kitchen din sbd ita. Hakika ya jima bai tsinta kansa cikin farin ciki irin wannan ba..ko wancan karon da makamancin hakan ya faru bazai iya tantance yanayin da ya shiga kamar wannan ba. Sosai ya yaba da juriya da faranta masa da tayi. Hakika Zaitoon kyautar Allah ce, Allah ne ya jefo masa ita cikin rayuwar sa domin ta kasance masa abin farantawa ta kowani fanni...ya kuma gode masa matuka da wannan gagarumin kyauta da Allah yy masa. Zaitoon kam koda ta farka hawaye ta riga yi daga kwancen ta'ki motsawa...ji take tamkar ba wannan ne farkon yanayin nan da ta shiga ba. Haushi take ji sosai, tunanin ta kuma na son zurfafa izuwa can watannin baya da makamancin ciwon nan ya riske ta...sai dai bazata iya cewa ga sila ko sanadin sa ba. Amma meyasa yace min inyi wanka...? Dagaske wannan yanayin ne ya faru ko kuwa mene? had'nt be banyi wankan ba a lokacin ya yanayin ibada ta kenan daga wancan lokacin har zuwa yanzu? Haushin sa sosai ya kamata, taya ma zai yi mata irin wannan abin batare da sanin ta ba, taya ma hakan ya faru ta kasa fahimta. Lokacin da ya shigo 'dakin abin hannun sa ya ajiye bisa drawer sannan ya ta6a goshin ta yaji dai babu zazza6in komai hakan kuwa yasa shi jin sanyi a ransa. Ya gane ba bacci take bane sakamakon ganin yadda eye lashes din ta ke rawa ga kuma 'dan ji'kan ruwan hawaye ka'dan daga saman idanun. " Ya jiki". Yace da ita dai- dai kunnen ta yana me sake cusa hannu izuwa saman wuyan ta. Da sauri ta kai hannu ta cire nasa hannun har taso bashi dariya. Idanu ya 'dan zare yana murmushi yace" Alamu kina lapia kenan zama a iya maimaici kenan ko...? Da jin haka ta girgiza kai da sauri. " Ni wlh banda lafia.." Ta bashi amsa cikin kuka. " Banga alama ba..". Kukan ta cigaba dayi..yace" naji jikin ki lafia kalau babu zazza6i...". " Jikina ke min ciwo sosai..". Haba dai ya 'dan sake zare idanu...hannun ta ya kama yace" ciwon daga ciki ne kenan...?" Yana ta6a skin nata yake fadin haka kamar bai fahimci manufar ta ba. Tace" a a"...yace" toh yayane?...nuna min ciwon toh in gani". Da Jin haka kawai sai ta sanya kuka sosai. Sai ma ta kusan bashi Daria Amma ya fuske. Da 'kyar ta yadda ya rungumo daga gefen kafa'dar sa yana 'dan bubbuga bayan ta..." Shikenan toh ya isa haka nan". Abinda ya fada kenan Kuma taqi yin shirun, da ya gaji da Jin Kuna nata ma lkc guda kawai ya doka mata tsawan" ya isa mana..haba!". Tuni kuwa ta ha'diye kukan tsab. " Rigimar yawa gare ta wlh". Ya 'kara Fa'di da sassau'kan sauti. Breakfast ya bata ta 'dan ta6a ka'dan sannan ya sake ha'da mata wani warm water din yasa ta taje tayi amfani da shi wai da haka ciwon zai tafi...in kuma bai tafi ba zai duba yaga irin maganin da ya dace ya bata. Ai tana jin wannan batun dubawan da ta shiga bathroom din ba ita ta fito ba sai da ta ha'da ruwan 'dumi kusan sau uku tana Yi tana canzawa ta yadda ita kanta sai da ta tabbatar wa kanta ta ji dama dama sannan ta fito. Rayyan daria kamar ta cinye shi ta ciki da ya fahimci abinda tayi amma bai bari ya fito fili ba. Bata san shi kam gaba ta kaisa ba, gara ta warware da wuri kar inya sake dawowa ayi masa rakin ciwo. Sai dai ya tabbatar bata da bu'katan komai kafin ya fita ya bar gidan zuwa wajen aikin sa, nan ma bai wani zauna ba. Kawai yaje Wani uzurin sa daga nan yayi mata siyayya ya dawo gida. A kitchen ya same ta, ya kuwa ji da'din hakan sosai, ba wai burin sa ta wahala wajen hidimta masa ba, amma koba komai motsa jikin yana da alfanu. Koda ya tambayi ya jikin ta ma bata amsa shi ba. Shima bai sake takura mata akai ba, tunda dai ta warware ai shikenan. Kusan kwanaki hu'du kenan bai sake neman komai daga gareta ba. Kuma ba laifi ta 'dan fara sakin jiki da shi har suna hira, ko ya tsokane ta suyi wasa da daria, ko ayau sunje gidan Ammi, inda tayi musu nasiha sosai, Zaitoon da Marwa sun sha hira tamkar kar su rabu, har tana ce da Marwa tazo su koma can tare tunda anqi dawo da ita nan kusa da su, Marwa tace a a bazata iya barin Ammin ta ita ka'dai ba, ga Anty Madeena tayi kane- kane ta hana kowa Mufee sai dai akawo ta yini...wai har sai nextweek kafin za'a dawo da ita nan. " Hmm" kawai Zaitoon tace, domin ita ka'dai tasan irin yadda tayi kewar yarinyar ta. A hanyar su ta komawa gidane tace da shi" toh yaya Mufeeda fa..Ni kam shikenan bazan ga yarinya ta ba.." Yace" sannu mai yarinya, ba gaki ga ubanta ba menene daban kuma ?" Hararan sa tayi ya dan yi daria yana tu'ki...sannan ya cigaba da magana" Wajen Ammi za'a mi'kata ta cigaba da zama..Koda ta dawo yanzu Ammi tace ta hutar da ke" Da hanzari tace" Hutu Kuma ...Kuma sai ta koma can kenan da zama?" Yace" yess mana...ba ga Marwa a gida ba.." " Ni Fisabilillahi nace na gaji be?" " Ke...ki barta can, kema ki huta Mana, Baga Ni ba!" Bata sake tanka shi ba har suka dawo gida direct ta wuce da'kinta fuskar ta ko alamar walwala babu. Sai da ya gama abinda yake yi kafin ya taho 6angaren nata. Da yake ya riga yasan damuwar ta, sannan yaga ko kula sa batayi ba tana ta harkokin ta ita ka'dai har tayi shirin bacci ta kwanta.. ya riga yasan kwanan zancen. Kusa da ita ya matsa ya janyo ta zuwa jikin sa sosai, tana shirin matsawa ya ra'da mata cikin kunne" fushi wai ake da Abban Mufee?" Shiru tayi kamar bata ji shi ba. Mamin Mufeeda ba magana?" Kawai sai kuka ya 'kwace Mata. Ha6a ya Kama ya duban ta cike da mamakin ta. " Ni Dan Allah ka dawo min da Mufee gida..." Bai ma Bari ta karasa ba yac" toh Can a daji take ne?" " A a..amma ai ina so in ganta, ina so in zauna tare da ita..." Fuskar sa yakai saman wuyan ta ahankali tare da cusa hannu cikin rigar ta sannan yace" ki bar musu ita kawai...ki haifa mana wata daban sai mu rike abin mu anan...". " Yayah ai da'dewa ake kafin a haifa wani fa". " Waya fa'da mk, ai ayau ma in kina so zaki haifi abinki..?" " Tayaya?" Ta tambaya with her innocent voice tana duban sa da mamaki. Yace " Ta yadda ake yi Mana, innuna miki?" Sai kuma tayi shiru Bata amsa shi ba sai ma kawar da Kai da tayi. Inda taji sau'kan hannun sa ne ya sata motsawa da sauri, maganganun nasa ne suka 'dauke hankalin ta Baki daya har Bata Ankara da yawon da hannun sa ke Mata ajiki ba sai yanzun. Kuma Rayyan yaqi bata damar raba jikin ta da nashi har ya kai ga cimma burin sa. Washegari bacci Zaitoon take har ya kammala shirin sa bata tashi ba. Lokaci- lokaci yakan waiga ya dube ta sai yy murmushi ya ci gaba da shirin sa. Sa'ilin da zai daura agogon hannun sa ma sai da ya dube ta thinking that da idanun ta biyu da ta taimaka masa domin yasan ta 'kware ta wannan fannin. Ai kuwa gefe ya ajiye sa, ya gama feffesa turarukan sa sannan ya 'dauki agogon ya nufo inda take kwance fuskar sa yalwace da murmushi dan yasan baccin nan bana komai bane face na gajia, domin da kansa yasan bai mata da wasa ba. A hankali cikin kunne ya ra'da mata" Mamin Mufee atashi gari ya waye Daddyn Mufee na bu'katan tallafi". Idanu ta bu'de a hankali. Sai kuma ta cuno baki gami da sake rude idanun, da yake ba gefen da yake fuskar ta take ba. Iska ya sake hura mata a hankali cikin kunne dan yasan bata so ai kuwa sai gata zaune tamkar wacce aka tsikara. Tana cuno bakin ta dube shi. " 'Yan mata mene kuma? Har yanzu fushin ne?". Shiru tayi bata amsashi ba. 'Dan matsawa kusa da ita ka'dan yy yace" Common ba komai ya wuce.. kinji da'din ki ba..? Take ta 'kara ha'de fuskar ta. Rage murya yy sosai yace" Kece fa kk riqa ro'ka na akan in 'kara.. don't come here and blame me, babu ruwan bawan Allah..". Ya karashe maganar hadda dage hannuwa sama to proof his innocent kamar gaske. Ai kawai sai ta fa'da jikin sa da sauri ta saki kuka dan tama rasa me zata ce da shi. Wata makirar murmushi ce ta 'kwace masa. Da hannun sa 'daya ya dafa bayan ta yana 'dan bubbugawa alaman rarrashi. Sai da yy aikin rarrashi da gaske kafin tayi shiru, ya bata agogon ta 'daura masa..tana 'daurawan yana duban hannun ta yace" Shine yau Ko gaisar da Abban Mufee baza'a yi ba ko? muryar ma kwata- kwata anqi motsata balle inji.." Sai lokacin ta tuna ashe ko gaishe shi ma bata yi ba, sai kuma taji kunya ya kamata. Da sauri ta mi'ke ta nufi bayi, sam ta kuma mance cewa ba wani kayan arziki ke jikin ta ba sai data mi'ke 'din kafin ta ankara, ai kawai sai ta 'karasa bathroom din aguje..abin ya ha'de mata biyu. Shi kam me zai yi inba daria ba bayan fahimtar manufar gudun nata. Cikin ransa ya ayyana" Yarinya kenan, mene yy saura kuma yanzu...?" Bai bar gidan ba sai da ya tabbatar tayi breakfast kafin ya fita. Itama daga nan ta mi'ke ta kama aikace aikacen gida dan dama ita ba gwanar son jiki bace. Bayan sati biyu..... Har zuwa wannan lokacin Marwa bata ziyarce ta ba. Haka kuma ba'a kawo Mufee ba, babu ma wanda yazo gidan domin ta ko sau guda sai dai kawai masu kawo sa'ko, hatta daga gidan Ammi an aiko masu aikin gidan sun kawo mata sa'ko madadin Marwa ta kawo sakon da kanta suga juna amma sai aka bawa ma'aikatan gidan. Haushin rashin zuwan Marwa kadai idan ta tuna wanisau tari sai dai taji kwalla na sauko mata. Gashi itama Rayyan Bai sake kaita can ba, tamkar wacce aka kawo gidan kaso shiru bb kowa, sai dai tayi zaman ta ita ka'dai indai Rayyan bai nan, tun tana dan jin tsoro har tazo ta fara sabawa da Zaman ka'daici. Da yake shima ya sani so ko ya fita baya wani 6ata lokaci sosai yake dawowa wai dan kar ka'daici ya dame ta..so in dai ba wani uzuri ya ri'ke shi ba bai fiye da'dewa ba. In kuwa yana gidan bai barin ta ta huta, ya riqa tsokanan ta kenan, ayi fushi a shirya, wani sa'in in ya kunna ta sai taqi ko kallon fuskan sa ne sbd tasan daria zai sata. Allah da ikon sa cikin lokaci 'kan'kani sukayi wani mugun sabo da juna, ita kanta atimes inta zauna ta kan Yi mamaki, shin dama haka Rayyan yake ne ko kuwa yanzu ne ya canza. Sau da dama in Yana wani abin kallon sa baya idan ta Sam. Tun tana mamaki har tazo ta daina. Ina fa'da, hantara da kyarar da ada ta sansa da su, duk taga Babu su yanzu. Ko kuwa dama can tsanar da ya mu su ne yasa yake musu komai da fada, hadn't been bai aure ta ba har zuwa yanzun, that means hakn zai cigaba kenan ko kuwa? Da kanta tazo ta fahimci ba hakan bane Sam. Rayyan bayi da bakin Hali Amma akwai zafin Kai Yana Kuma da fushi in aka riski wajen fushin...Amma sanyin halin sa ya rinjayi komai. Hayaniya ce ta fahimci Bai so har gobe. Wani lkc takance wata'kila dan yaga ta zama matar sa ne kuma cikin gidan sa shiyasa ya canza amma wata zuciyar takan ce da ita sam ba haka bane ya canza ne sbd akowani lkc yaga dama zai iya neman abu tattare da ke kuma bai 'kaunar a ahana sa..shiyasa ya canza dan gujewa hakan. Sai dai sam can kasan zuciar ta ta kasa yin na'am da wannan batun, can cikin ranta take ji kamata yai tayi masa adalci..tasan idan hakan ya shiga ranta ya kuma samu waje ya zauna, toh mawuyaci ne ta ri'ka masa kallon daraja Koda Nan gaba. Bata tsawaita tunanin take dakatar da shi, yawanci dama kuma zaman kadaici ke sata zurfafawa. Gashi ko waya babu hannun ta balle ko Innar tane ta 'kira taji 'duriyar su. sosai tayi kewar gida, yan uwa da danginta. Sau da dama kuka kawai take sanyawa in ta tuna yadda 'kaddara ke walagigi da ita da rayuwar ta. Musamman wannan da take ciki a halin yanzun, 'kaddarar aure tasa ta yi nesa da gida gashi ko wanda zai zo ya le'ka yaji ya take ma babu shi. Ko ayau ma tunanin da take kenan. Tana cikin wannan kukan Rayyan ya samo ta. Da kyar ya samu tayi shiru sannan ya nemi jin dalilin kukan. Bata yi 'kauran baki ba ta sanar masa kewar gida take da su Innar ta. Ido ya 'dan zaro" Shine abin kuka har haka?" Ta dube shi. Shi kam ya cigaba da magana" naga ko jiya nace dake suna gaidaki, hatta Yah Abubakar ma munyi waya, kusan kullum ma muna gaisawa da shi toh menene abin damuwan hadda kuka irin hk.. ?" Harara ta doka masa 'kasa'kasa, cikin ranta ta ayyana lalle ma wannan mutumin. Afili kuwa cewa tayi" Kai ai kana tare da Ammi koda yaushe bazaka gane ba ?" Tana fa'din haka ta kawar da kai. Ya fahimci magana ta fa'da masa. Sai kuma yaji jikin sa yy sanyi. Shi kansa yasan bai kyauta ba sam. Domin bai ta6a ha'da ta da 'yan uwanta awaya ko na rana guda bane. Yana Kuma da yakini hatta 'yan uwan nada muradin jin muryar ta amma ya fuske kuma yasan ita batada waya a hannun ta balle suji juna. Jikin ta ya janyoshi ya rungumo ta ta baya, da hannun sa 'daya ya 'dago kuncin ta, sai dai ya dubi fuskar ta sosai ya karanci yanayin da take jin zuciyar ta kafin ya sau'ke mata kiss saman goshin ta then saman la66an ta a hankali...suna ha'de idanu ya furta" I'm so sorry wifey". Idanu ta lumshe bata ce komai ba. " Me kk so ayi yanzu, tell me..karki 6oye min..kinji?" Yy maganar a rarrabe. Da jin hakan tayi saurin bu'de idanu sai dai bata motsa ba..lips din ta ka'dai ta motsa wajen furta" Mu koma can gidan kawai kusa da Ammi yafi...". " are u sure?" Ta 'dage masa kai slowly. " Wasa kike yarinya.." Ya fa'da yana murmushin da tasan bana nasarar ta bane. Raba jikin ta tayi da nashi..ta gyara zaman ta sosai ta fuskance shi. " Dan Allah fa Yayah! " Ya dube ta sosai suka hade ido. Sai ta toshe baki" Aww abban Mufee.." " Hmm" kawai yace. " Pls mana, ba Kaine kace in Fadi yadda nk so ayi ba...?" " Yess...but ki canza wani ba wannan ba. ". " ni dai mu koma can dan Allah, nafi so in riqa kallon mutane amma nan shiru kullum sai ni kadai.." " Bagani ba". " Ni a Ina nake ganin ka?" Duban ta kawai yy cikin idanu. Sai tayi shiru. " Bakya gani na kk ce?" Zata sake magana ya tare ta" Yarinya better keep quite wooo, bb wani inda zaki koma apart from this house, banda abinki ma nan fa gidan mijin ki ne, mallakin ki, kiyi iko da gidan ki, kiyi da mijin ki, kiyi da yaranki, kiyi da ma'aikatan ki toh me zai dameki.." " Ni wlh duk ban so, Allah gidan yy girma sosai". " Haba dai?" Yace yana 'yar daria. Tayi saurin 'dage kai alaman erh. " Ai shikenan, dama wani abokin aikina ya bani kyautar 'diyar sa na aura, sai nace Masa ai Ni matata amarya ce ba yanzu Zan Mata abokiyar Zama ba, Amma yanzu tunda kince hk kawai zan aurota sai ku zauna ku biyu abinku. No more ka'daici or Girman gida... shikenan ko?" " Oyah say thank u to me"! Shiru bata amsa shi ba, Bai San wani tunani take ba but sarai ya fahimci maganan bai wani firgitata ba ita dai zaman nan 'dinne bata so kuma shine gaban ta a halin yanzu. Mamaki ta bashi matuka, wai kardai ace yarinyar nan har yanzu bata san kishi ba?" Bai tsinke da lamarin ba sai da yaji tana fa'din... " Nidai nafi son gidan Ammi gaskia, idan ka auro waccan din kawai sai ka kawo ta gidan nan ita, amma dai kar ka ajiye ta a'daki na can 'dakin ka zaka kaita ko kuma aduba mata wani daban itama...". " Wai dagaske kk ne?" " Erh mana". Ta fa'da da 'kwarin gwiwar ta. Sai yy murmushin mugunta. A fili kuwa yace" Shikenan zaki koma can 'din amma ba yanzu ba sai na kusan kawota sannan zaki koma, amma dai ni nafi so mu rayu anan mu biyu da yaran mu ka'dai" " Sai zuwa yaushe zaka kawota?. Zaitoon ko ta kan waccen maganar Bata bi ta ta jefa Masa wata sabuwar tambaya. Yace " Nan da lokaci ka'dan bi'iznillah" Bayan kwana biyu Rayyan ya kawo mata waya wai Marwa nason magana da ita. " Amarya bata laifi..". Cewar Marwa tana murmushi . Itama Zaitoon murmushin tayi bayan fahimtar waye kan wayan. Tace " bacin kun 'kini...kowa ma mancewa yy dani". " Ba haka bane wlh Mamin Mufee, Ammi ce ta hana mu zuwa, wai ba yanzu ba tukunna, amma ai ko su Badiyya na son zuwa amma anhana kowa wai sai kin huta...". " Sai kace wacce tayi gagarumin aiki?" " Wama ya sani ne?" Cewar Marwa...tana daria...sannan ta cigaba. " Kinsan hutun kala kala ne, toh ban dai San wanda Ammi take nufi acikin su ba, amma zuwa yanzun wata guda kam ai nasan dai kin huta ko waya ataimaka abaki ko dan 'yan uwa ma da abokan arziki...Abinda na kira in fa'da mk kenan, wani shekaran jiya ya kir a wai yana neman ki, Inna tasa aka tura masa layina a tunanin ta wai muna tare ne, toh ko jiya ma ya kira nace ban hadu dake ba amma zan fada mk...yace sunan sa Shaheed. " Laaa...Yah Adam ne!..dan Allah ki gaida min shi..." " Anqi, ki 'kirasa mana, ai ni kam na gama nawa tunda na cika alkawari.." " Kai Marwa, kar ki koyi halin mana kema, kin fa san ba waya gare ni ba, wannan mutumin kuma ko aron tasa baya bani toh taya zan 'kira sa...?" Ta 'karashe da sanyin sauti tamkar zata Yi kuka. Jikin Marwa sai yayi sanyi..tace" Toh shikenan idan ya sake Kira zan fada masa Insha Allahu..." " Nagode sosai". " Kar ki damu bakomai." Daga nan sukayi sallama. Taso ta kira Innar ta amma wayar ta riga ta rufu dole ta hakura. Kawai kuma sai ta saka wayar agaba hawaye na bin kuncin ta. Gaba daya tunanin gida ya mamaye ta lokaci guda. Ji tayi da tasani da ma tun farkon fari dama bata amince da wannan auren ba...gashi ya sake nesanta ta da mahaifa da yan uwanta akaro na biyu. Bangaren Marwa kuwa suna kammala wayar ta tashi da nufin zuwa bangaren Ammi sai kuma ta tuno ashe ma bata nan. Ba ita ta hadu da Ammi ba har sai bayan maghrib. Ai kuwa bayan gaisuwa abinda ke mata yawo a rai ta fara furtawa. " Ammi wai dan Allah baza'a saiwa Mamin Mufee waya bane, kinsan fa tana da yan uwa dole zasu so ji daga gareta wuri ba kusa ba Ammi...dan Allah ki yiwa Yaya magana ya sai mata ko kuma in kai mata 'dayan tawa". " Ni ai bansan babu waya a hannun ta ba Marwa...ai kam babu dadi, bari yazo zan masa maganar, ai bama sai dangin ta ka'dai ba, rayuwar yanzu da komai ya koma lamari na waya ai dole ta bukace ta..". Koda Ammi tayi masa maganan bai wani damuba, domin shi kansa ma yy tunanin siyan mata amma dai bai sa lokaci ba. Ganin kamar baya da niyya yasa Ammi fara fada da zafi zafi ta kuma ce a yau ba sai gobe ba take so a siyan mata waya. Yace toh Ammi Rayyan ya kawo mata waya Samsung mai dan karan kyau da tsada hadda layin wayar ta a ciki. Yana mika mata ledar fuskar sa ba yabo ba fallasa yace" Shine kika hada ni da Ammi dan kinasan waya ko?" Da sauri tace" Ni kuma Yayah..yaushe? Wlh ban yi magana da Ammi ba kwanan nan". Shiru kawai yayi ya basar da zancen domin guarantee yasan aikin Marwa ne tunda Zaitoon tace ba ita ba ce kuma ya fahimci iya gaskiar ta kenan. Koda ta bude taga waya ce duban sa tayi rike da kwalin wayar. A hankali yace" Taki ce". Wani tsalle ta buga ta gyara zama..bama tasan lkcn da ta rungume sa ba. Ranar murna hadda kyautar Sumba ya samu.....godia kuwa ya sha shi har ya gaji da amsawa ya kulle mata baki da nashi kafin ya samu tayi shiru. Numbers din Innar ta, Abban ta da Yah Bukar kadai ya sanya mata sai na yan uwan sa Ammi. Aranar kuwa duk din su sai da ta kirasu suka gaggaisa cike da tsananin murnar ta da farin ciki. Abinda ya kwantarwa Inna da su Ya Bukar hankali kenan jin yadda take farin ciki..hatta da Ammi ma haka. Marwa kuwa tana samun numbern tayi saving. Koda Shaheed ya sake kiran ta take ta tura masa tace ya kira wannan layin zai same ta. Sun sha hira sosai ranar da ya same ta awaya, duk da sanin da ya riga yy mata da natsuwa da hankali but ayanzun ya fahimci natsuwar ta ta ta dabance...hakika aure na kara kima martaba da girma. Lokacin da ta tambayesa inda ya samu layin ta bai boye mata ba yace Marwa ce ta tura masa...Zaitoon sai tayi yar daria...yace mene kuma.? "Kai Yah Adam kamar wanda ya tsargu." Ba wani tsarguwa ai tambaya ce nayi kawai. " Toh yaya ko dai.. " " kodai me? " Um um dai...toh ya akayi ka samu numbern Marwa ba kasamu ta Yah Rayyan ba?" " Ban ma yi tunanin neman na san ba kuma..dayake ma kinsan mutumin naki akwai zafin kai shiyasa. " Kuma sai ka su ta Marwa?" 'Dan jim yayi..." wai yarinyar nan me kk nufi ne?... dan na kira Marwa awaya..laifi ne?" Salmerh🥰 [03/02, 11:59 am] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Wattpad@* _Serlmerh-md_ 🅿️ *...106* ........Haka nan kawai ta kwashe da daria batare da ta amsa tambayar sa ba....'kit ya kashe wayar yana fa'din in kin gama dariyar mayi magana. Sosai ya bawa Zaitoon dariya, shi yana can yana mitar da jin haushin yadda ta tuhume sa kan Marwa ita kuwa duk lkcn da ta tuno sa da yadda ya dan shiga rudu sai kawai tayi murmushi. Can 'kasan ranta take jin wani farin ciki, tsananin farin ciki ne marar misaltuwa. Adam kuwa sam bai ma saka maganar cikin kansa ba balle ta dame sa...sai zuwa dare da ta ga bai sake 'kiranta ba sannan ta 'kira shi. Yana 'dagawa tace " Yah Adam ba dai fushi akayi da 'kanwa ba...?" " Fiye da fushin ma in anayi dole zanyi ai don 'kanwar ta 6ata raina..". " Kai Yayah!". " Yes mana..kawai ki wani mai da ni abin wasan ki..". Idanu ta zaro tana dan toshe baki. " Yayah ba haka bane fa...kawai ina jin farin ciki ne sosai, kasan in akaji cewa an samu cigaba dadi akeji...". Cike da mamaki yace " Farin ciki?..Jin 'dadi?..duk na mene?" Adam tunanin sa zata ce sbd kiran da yai mata ne. Sai kuma yaji sa6anin haka. Tace " Ina mk murna...indai marwa ce inayi mk albishir 'din babu kai bb samun matsala in ba wata kaddarar ba..babu kai babu korafu da iznin Allahu...kuma baka da matsala tsab zan bk ita insha Allah.." Ta karashe tana yar daria. Gishi ya dafe. Sai yanzu ya gama fahimtar kaf inda ta dosa. " Yah Subhanallahi.." Ya furta a fili. " Zaitoon ba dai ni yarinyar nan kika raina har haka ba...wai me kike nufi ne? Wani darian ta kuma tana mai yanke wayar. " Indai tayi tsami maji komai Yayah". Ta Fa'di hakan ne a fili still with a bright smile on her face. Shi Kansa Shaheed murmushin yayi bayan tunanin Yan dakikan lkc da yayi kasake da wayar a hannun sa. " Zaitoon kenan" ya fa'da Yana ajiye wayar. Lokaci lokaci Kuma sai maganan Zaitoon ke zuwan masa rai hakan nan kawai bai san dalili ba. Har aka kwana biyu kwata- kwata bai ji zuciyar sa cikin salama ba. Throghout those days abu guda ke masa yawo a zuci. Kawai sai yanke shawarar sake Kiran Zaitoon. Koda ya dago wayar Kuma na take batare da ya san dalili ba haka nan kawai akalar yin 'Kiran ya canza daga Zaitoon zuwa Marwa. Bai tashi sanin yayi 'kundumbala ba sai da yaji wayar ta fara ringing. Sai Kuma ya fara tunanin me zai ce da ita toh. Firgigi yayi lkcn da ya tsinkayi sassanyan muryar ta da akoda yaushe yake Jin ta cikin sanyi tayi Masa sallama. Bai amsa ba sayMi a karo na biyu kafin ya amsa ta. shima wata kamilalliyar muryar da shi kansa bai san yana da ita ba bai ma san yaushe yayi hakan ba sam. Sun gaisa kamar yadda suka saba, sama sama, sai yace Mufeeda fa..? 'Dan jim tayi sannan ta amsa shi" ai bata nan, ba a kawo ta ba". " Ohh tana ina ne har haka? " Wajen Anty." " Zaitoon...?". " No.. Antyn mu fa.." " Ok.. Ina so inji muryar ta ne ya za a'yi kenan yanzu..?" Yatsine fuska tayi sosai cikin ranta take ayyana" ji wani kalan dangi anan". Ina dai 'diyar tamu ce bata kowaba. Tana cikin tunanin taji ya sake fa'din " yaushe za'a ha'dani da ita?" " Babu rana gaskia dan basan actual ranar da zasu zo ba". " Common please...ki yi tunanin wata hanyar mana, dagaske i really missed my daughter". "...toh fa, ai kuwa sai dai in sun zo...". " adai duba...baza a min alfarma ayau a ha'da mu ba...?" Baki ta tura sosai. " Mufeedan fa ba ma magana ta iya sosai ba..." " Nasani...ni dai please ki ha'da ni da ita ayau...ina jiran 'kiran ki..kinji". Bata amsa masa ba daga inda take sai ma 'karawa bakin ta tsayi da tayi...shima jin shiru ya sashi cire wayar daga kunnen sa sannan ya kashe ta...fuskar sa yalwace da murmushi. Yasan cewa ya shiga rayuwar ta ayau dinnan..amma he have to do ths sbd yana son ya kasance ne cikin tunanin ta daga yanzu har zuwa dare... **** ........" Baccin ki ya fara yawa 'yan mata...ban fiye son hakan ba sam ya kan sani jin badadi araina...". Ya fa'da yana ha'de musu goshi waje guda. A hankali tace" Nima ban fiye son baccin ba Abban Mufee, amma baccin da kansa yake zuwa ya takura ni ko ban so sai nayi.." Shiru yayi bai furta komai ba...hannun sa 'daya ya 'dago zuwa bayan ta a hankali ya sau'ke zip 'din rigar zuwa 'kasa yana dropping mata sumba a kuncin ta yace" kinga har kwanan nan body warmness 'din ki yafi na baya sbd yawan baccin nan precious, bana so yy affecting naki koka'dan...". A hankali tace" Ni kuma dadin sa nake ji sosai, baya takurani, amma bakomai za'a rage". " Zan fi son haka". Bata 'kara fa'din komai ba kasantuwar canjin yanayin jiki da ta fuskanta sakamakon abinda ya fara yi mata ajikin ta. Washegari...... Tana kitchen 'karan doorbell ya kara'de palourn lkc guda. Da sauri ta wanke hannun ta tana tunanin waye haka dan tasan ba Rayyan bane. Baki ta kama cike da mamaki take bin su da kallo 'daya bayan 'daya sannan ta dire kallon ta bisa fuskar wacce ke gaban ta. "......7weeks da kwana biyu kenan da kawo ni gidan nan amma har sai yau kika ga daman zuwa Marwa? Ta fa'da bayan ta bu'de mata 'kofan main Parlour 'din. " Ko in koma?" Tace tana 'yar daria. " Bismillah..dama wa ya gayyato ki" Ta bata amsa cikin nuna halin ko in kula. Juyawa tayi Marwa tamkar dagasken gasken komawa zatayi. Hannun ta Zaitoon ta riko cikin sauri. " Miye hakan wai?". " Kince in koma...". " Kuma sai ki koma din?" " Why not..?" " Da kuwa nima na biki mun koma tare". Daria sukayi atare dukkan su sannan Marwa ta 'daga 'kafa ta shiga, bayan ta Imran ne, sai ga Affan ma yaron Antyn Raihana...." baki Zaitoon ta kama.." wannan kuma yaushe kuka zo..?" Ta tambaya da mamaki...tana kamo hannun sa. Yace " Jiya aka kawo mana shi hutu. Bata kai ga furta abinda tayi niyya ba sai ganin Badi'a tayi rungume da Yarinya bisa kafa'dar ta. Tuni ta sake washe baki, wannan irin tafiyar bazata haka?" Yarinya na jin muryar Zaitoon ta 'dago kai daga jikin Badi'a ta kalle ta. " Mufee na"! Ta furta with an excitement..ta yadda sautin muryar ta ka'dai idan kaji kasan cewa tana jin farin ciki. Take Mufee ta washe baki tana 'ko'karin sakkowa tace" Mammi...."! Da gudu tazo ta rungume ta, sai ga hawaye a idanun Zaitoon. Kuncin ta ta yiwa curve da hannayen ta duk biyu tana murmushi tace. " Shine kika 'ki zuwa in ganki ko Mufeeda? " A ka qi kawo ta dai malama". " Kuma kika cigaba da kukan nan tsab zan sanar da Ammi sai a ma daina kawo ta balle in kin ganta ki riqa kuka wa mutane....". Marwa ta fa'da tana 'yar daria. Duk da yake zuwan na bazata sukai mata amma irin tarbar da Zaitoon tai musu har sai ya baka mamaki a ahakan ma Ammi ta hana a sanar da su dan wai kar ta bawa kanta wahala wajen hidimta musu amma duk da hakan an yi ne amma ba a tsira ba. sosai ta gwada bajintar ta, as there first visit to her house dole ta tarbe su da kyau ta faranta rayukan su...she was so exited. Ko ba komai tsananin farin ciki da suka sanya ta ayau 'din yafi mata komai. Duk inda tayi Marwa da idanu take binta, yayin da Mufee ke bibiye da ita tana cire 'kafa Mufee zata jefa nata, tun Marwa nayi mata tsiya har ta gaji ta 'kyalesu. Lokacin da tazo ajiye musu zo6o ne kasa kasa Marwa ta furta, " wani abu na kasa ganewa fa Mamin Mufee?" Hankali ta bata baki 'daya jin yadda tayi maganar tamkar tana 'kage da son jin amsar ta. Marwa na gyara zama tace" Me Yaya yake baki kika canza baki daya cikin lkc kankani hakane.. kin ganki kuwa?" Hararan ta Zaitoon tayi" Allah ya shirya Marwa, kin wani sa na nutsu zatona wani abin kirkin zaki fadi" " Wannan ba abin kirki bane kk nufi? ba fa da wasa ba, Allah Mamin Mufee kin canza". " Canzawa wata iri wai dan Allah?" Inda tayi maganar cike da mmk tana mai sake duban jikin ta..kin yi haske kin murje abinki kamar bake ce waccan slim beauty din nan ba...kin dawo wata ta musamman again..gaskia asanar damu sirrin mu jarraba mu ma". Ta 'karashe tana yar daria. Itama Zaitoon dariyar tayi. " Ki bari zan fada wa Yah Adam ya neman mk sirrin idan lkc yayi...". Take Marwa ta ha'de rai da jin hk ta wani dame fuskar ta. " Ke kuma kika jiyo, ni ban ta6a ganin inda laifin wani ya shafi wani ba sai a wajen antyn kin nan Mufee...shikenan a rayuwa babu jarrabawa sai kace duk an ha'du an zama daya...?...wani abin fa dole sai an bada 'kafa Marwa sannan ake gane inda al'amura suka fuskanta...muna dai rokon alfarma ayi hakuri a bamu dama muma mu jarraba sa'ar mu...". " Hmm" Kawai Marwa tace bata 'kara fadin komai ba. Dama in kana son ta'kaita maganar Marwa toh sako mata hiran Adam ko wani makamancin sa cikin hirar ku...yanzu zaka ga taja ta fiske. Tun ranar da ya sata ta ha'da sa da Mufee ta dan yi gardama ya fara shiga cikin rayuwar ta. Lokuta da dama ta kan saka wayar ta flight mode sbd shi, sbd yawan 'kiran sa, dan ta riga ta fahimci manufar sa tuntuni, tun ma kafin ya kaiga furtawa, koda ya furta din kuma abin bai yi mata bazata ba amma ya sake worsening lamarin ta ne. Ta kance ita a halin yanzu ba batun soyayya ko aure ne gaban ta ba, me ma zatayi da auren? Wanda ta so ta kaunata, ta bada yadda da amincewar ta ha'intar ta yayi, ya rayu da ita zaman cin amana...ya cutar da ita, yayi mata illolin da har abada tabon su bazasu ta6a barin ta ba...me ta tsinta daga gare shi. Banda bakin ciki da takaicin da suka kusan aika ta lahira. Ta so shi ta 'kaunace sa amma yayi mata hakan balle wani can daban...tuni Sultan ya 'kona duk wani shaukin 'kauna dake zuciyar ta ya kuma yi watsi da tokar da yadda ha'de su waje guda zai yi mata matukar wahalan gaske. Amma duk da haka Adam sai da ya cusa kansa cikin rayuwar ta, duk da yake akwai wani da sukayi schl tare shima ya nuna mata kauna amma tuni ta dakatar da shi, akwai dan gidan Alhaji Barau shima ya kasa samun fuskar ta duk da kuwa tasan Alhaji Barau makusancin mahaifinta ne amma hakan bai sa ta yi masa wannan karar ba, akwai wani ma Lameen shima tuni ta dakatar da shi amma shi Adam da ke isashshe ne bai tsaya bi takan maganganun ta ba, bai tsaya ya gama fahimtar manufan ta game da batun aure ko soyayya ba, bai tsaya yaji ra'ayin ta game da so ko 'kin sa ba kawai ya dangana kansa da manyan ta...aka kuma amince masa sbd nagartar sa da kuma kyakkyawan shaida da ya samu... Shiyasa a halin yanzu tafi jin haushin sa fiye da kowa har cikin ranta. " Ki dai bi a hankali dan Allah Goggo Marwa, kuma A cigaba da addu'ah shine mafita..kar a zafafa kuma kar a barmu cikin tararaddadi...dan Allah.." Lokacin da zasu tafi kyaututtuka Zaitoon ta bawa yaran masu daraja, yayin da ta bawa Marwa wani ubansun turare mai kyau da tsada..ga sanyin kamshi. Ita kanta marwa ya matukar birge ta ba dan kadan ba. Wajen tafiyan ne aka samu matsala, dan Mufee ihu ta fara kamar wasa ta rungume 'kafafun Zaitoon...itama kawai sai ga hawaye. Marwa rasa ma abin fadi tayi ta tsaya duban su. Cikin sa'a kuwa sai ga motar Rayyan ta danno kai. Shi kam cewa yy abarta kawai zai kaita da kansa an jima. Da haka su Marwa suka wuce. Koda labarin ya iski Ammi murmushi kawai tayi a fili tace" Ja'irar kaya kawai, wato ita nan taga uwar ta, aini wayon Mufeeda na bani mmk... Badi'a dai bb fara'a tinda aka baro Mufee da kyar Ammi ta lallashe ta sannnan ta dan saki fuska. Da tunanin dagasken za akai musu yarinyar har gida. Mayarwan da Rayyan bai yi ba kenan sanadiyyan da rikon mufee ya dawo wajen su, ita dama Anty najin yadda suka yi tace a hada kayan Mufee kaf dan kuwa tatafi kenan, ba yau tasan halin kayanta ba indai Rayyan ne. Ilai kuwa hkn ne ya kasance, biris suka yi suka zuba masa idanu kamar yadda yy dan kuwa cikin su kaf bb wanda ya tado zancen, nan ma suka fahimci ashe ko ada din ma da ya kyale kara kawai yk. Bb abinda ya canza daga yawan baccin Zaitoon sai ma abinda ya karu, ga zazza6in tsakiyar dare, a kullum sai ya takura ta kusan sati guda kenan yanzu. Rayyan tun yana kawar da kai har dai ya fara ha'de puzzle din waje guda ya kuma dasa ayar tambaya akanta. Abinda ya fara dasuwa cikin ransa shi ya kusan haukata masa lissafi. Had'nt been ya kasance gaskia da bai san irin farin cikin da zai tsinci kansa ba. Amma a zahiri shi kansa yasan matar sa ta canza sosai, kama daga yanayin jikin ta, cimar ta da kuma yanayin tsarin halittar ta ba sai an fada masa ba. ***** .......Angama maganar bikin Marwa har an saka rana wata biyu masu zuwa, Marwa tamkar ta yi bindiga sbd takaici, ba wai Adam ne bata so ko kauna ba, ita maganar auren ne baki daya bata muradi. Domin hasalima duk da ba maganar kirki take yi masa ba amma duk ranar da ya shafe rabin yini batare da ya kira ta ba sai ta dan shiga damuwa, atimes har haushin kanta da kanta take ji sbd haka, kuma yanayin shigan sauri yai mata batare da ta shiryawa faruwar sa ba. Haka nan kawai ta tsiri zuwa wajen Anty Raihana wai hutu, Adam yaso dakatar da ita amma ta 'kiya, kamar hadin baki kuma shima Rayyan yace a a bb inda zataje. Tasha kuka har ta koshi, dan duk wanda ke tare da ita ma ya fahimci hkn. Ammi ta 'kira Rayyan take bashi hakuri akan ya bar ta taje dan baki 'daya ya hargitsa mata autar ta. Yace sam zai ma zo ya dauki Mufee anjima weekend din ya isa hk nan...daga nan ya kashe wayar sa. Ammi tabi wayar da kallo kawai. Sakkowa tayi a hknl ta tafi izuwa bangaren Marwa domin ban baki amma bata same ta dakin ba illa Mufee dake fama da Nursery Rhymes cikin waya...ta kuwa bada hankalin ta sosai akan wayar. Ammi bata jima da shiga dakin ba sai ga ta ta fito daga bathroom da alamu wanka daga wanka take. " ...Ammi da kanki har nan?...ai da kin aika sai naje in same ki acan.." " No..Karki damu bakomai..dama batun tafiyar taki ne marwa...kinga yayanki yace sam bazaki ba, amma zan sake magana da shi Insha Allahu, kin sanshi wani lkc sai a hankali ga danzan kafiya da yake da...dan hk ki kwantar da hankalin ki kinji, ayi agama bikin nan lafia inyaso duk inda kk son zuwa sai kuje da mijin ki ba wajen Antin ki kadai bama hatta dangin mahaifin ki da nawa duk sai kuje...kinji daughter". Marwa kawai kuka ta sanya tana mai zama gefen Ammin ta kwantar da kanta bisa jikin Ammi, kukan da yasa hatta Mufee da ke kallon waya dagowa ta dube ta. Ammi kanta sai ta sake jin bb dadi, don dama tasan za'ayi hk..shiru kawai tayi ta zuba mata idanu, a hankali ta kai hannu take bubbuga bayanta alamar rarrashi...sau da dama Marwa na bata tausayi a gidan nan, bata fiye son ana takura ta ko tauye ta ba sam, bcuz yarinyar goes through alots a rayuwa, sannan tana da matu'kar ha'kurin da bata jin kaf 'ya'yanta ta haifi madadin ta wajen hakuri da kawar da kai bisa abubuwa. Shiyasa tace dole zata sake magana da Rayyan. Cikin kukan Marwa take fa'din " Ammi ni dai abarni dan Allah inje, indai akan auren nan ne toh ni bana son shi, na fasa bana so ma na sake yin wani aure Ammi, maza duk macuta ne mahain'ta...Ammi ni har abada bana so in sake zama da wani...dan Allah kice Yayah ya barni inje.." Ta karashe maganar hade da rushewa da kuka mai sauti. " Haba Marwata, haba dan Allah, Haba Auta ta shin so kike ki nunawa Allah cewa baki yadda da 'kaddara ba ko me...?" Kai ta fara juyawa" Ammi na yadda da kaddara mana, na yadda cewa Komai nufin Allah ne, amma Ammi ni me zanyi da aure yanzu, me na tsinta a cikin sa banda ba'kin ciki, Ammi mijina fa yayi sanadin mutuwan mahaifina, shifa ya raba shi da duniyar baki 'daya, mijina fa Ammi yayi sanadin raba ni da yar uwa ta, babban yayana da duka ahalin sa, haba Ammi, kina nufin duk kin mance? aure ne ya shafe min kaf ilahirin farin cikin rayuwa ta Ammi, wanda a kullum nake kwana in tashi cikin bakin ciki da takaicin sa. Halittar da a kullum nake ikirarin mijina ne kuma dan uwana shine fa ya haihu da matar Yayana Ammi, dan uwana jinin jiki na...Ammi that same person ya shirya kashe min ragowar ahali na...taya zan mance da duk wannan Ammi...wallahi har zucia ta bana son auren nan yanzu Ammi..dan Allah ku barni inyi tafia ta inda babu wanda ya sanni sai Aunty na ka'dai". 'Kit wayar da ke hannun mufeeda ta tayi karan yankewar 'kira. Domin tuntuni aka 'kira Mufee ta 'daga Batare da ta san tama yi hakan ba. Yayin da Marwa ta cigaba da magana" Ammi idan zan 'karashe rayuwa ta a haka nan bazan ta6a sha'awar sake yin wani aure ba duniyar nan. Ji nake ban yadda da kowa ba Ammi, Dan Allah abarni in rayu da 'yan cina, abarni in rayu cikin natsuwa ta da farin cikin da na samu a halin yanzu...". Ta 'karashe maganar cikin kuka Mai tsananin ban tausayi tana mai zamewa daga jikin Ammi tana kokarin durkushewa bisa gwiwoyin ta. Da sauri Ammi ta tarota ta rungume ta. Ita kanta jikin ta yayi sanyi sosai, domin da kanta tasan Marwa tayi hakuri, marwa tayi tawakkali fiye da yadda ta tsammata, Marwa ta kunshe abubuwa masu dama cikin zuciyar da ba kowa ne zai iya hakan ba, duk da depression da ya kusan kama mata yarinya amma she fight this battle, nd she fight it alone batare da kowa ba, tayi yaki da zuciyar ta sosai domin da badan haka ba da yanzu wata maganar ake ba wannan ba. Mufee ma ganin yadda Auntyn ta ke kuka da gudu ta zo ta rungume 'kafafun ta...tace " Anty"! Ammi bata 'kara fa'din komai ba illah hakuri kawai da take 'kara bata. Bata san.ya zata yi ba amma itakanta bata san ana sake tauye Marwa...yarinyar nan ta shiga rudani iri da kala cikin rayuwar ta tun tana yar karama da ita, kama da ga kan rasa 'yar uwar ta Safaa da tayi har zuwa yau din nan bata samu cikakken farin ciki ba. Cikin rai Ammi ta ayyana dole zata yi magana da Rayyan kan Marwa. Sai da ta bari Marwa ta natsu sannan tayi mata nasiha sosai. Kan duk abinda ya samu bawa jarrabawa ce daga ubangijin sa...kuma duk yanayin da kaddara tazo mk dole ne ka amshe shi hk nan kuma da hannu bibbiyu domin shine cikar imanin bawa ga Mahaliccin sa. Sa6anin hakan idan ka aikata tamkar ka gaza yadda da kaddara ne, dan hk ta kwantar da hankalin ta, kar tace zata biyewa past din ta ta kasa daidaita rayuwar ta ta gaba while tana da daman hk. Lokuta da dama nadama na zuwa bawa ne bayan lokaci ya kure masa, so kai da ka samu dama kafin kurewar lkc yi kokari ka amfanu da shi...ba duk halittun Allah aka zam 'daya ba, sannan kowani bawa tafe yake da tashi kalan kaddarar inma mai kyau ko akasin hk..tace Marwa ba wai muna tilasta ki kan batun aure bane, kawai munayi ne sbd munsan shine sittirar ki kuma alkhairin rayuwar ki, muna fata ne wannan ya kasance mk na har abada kuma abin alfahari agareki...taushi zuciyar ki akan komai kinji uwata.."! Sosai Ammi taja hankalin ta har sai da taga ta dan sake kafin ta kyaleta...tace tashi ki shirya ko. Ko da ta koma dakin ta kuwa Rayyan ta fara 'kira sai dai bai 'daga ba. Shi kuwa ya na can Office abubuwa sun rinca6e masa, baki 'daya sun sha kansa ko bi takan wayoyin nasa ma bai yi ba. Haka nan kawai sai yaji yana bukatan makusanci wanda zai riga taya shi wasu abubuwan ko da bai nan, sannan yana bukatan driver again amma har yanzu zuciyar sa ta kasa yin na'am da koma waye. Shiyasa ya kwammaci ya tuka kansa zuwa duk inda yake so duk da hkn na dan takurashi wasu lokutan. Amma mutane sun riga sun dasa masa shakkan su cikin ransa..bai ma san ta ina zai fara ba a halin yanzu. Lokaci guda kawai Bello ya fado ransa, Bello wani matashi da ya gani can cikin 'yan uwan Zaitoon. Sai da ya tashi a aiki ya bi gidan direct, nan Ammi ke masa maganan tafiyan Marwa yace ai Adam ma ya 'kira sa da yamman ranar, kuma shima duk kan batun ne, abin ya 'kona masa rai matuka, dan zaton sa Marwa ta tilasta shi ya kira ya rokesa kawai dai ya basar ne. Duk da Ammi bata da tabbaci amma a zahiri tace" anya kuwa..bana jin Marwa zata aikata hkn gaskia?" Ita dai tana kokonton Marwa ce ta sanya shi. Amma rashin tabbas yasata jan bakin ta tayi shiru. Toh wayar tata ma tun lokacin data taho da Mufee nan bayan sun lallashi Marwa wayan ke 'dakin Ammi kuma har yanzu gatanan dake tana silent ita dai ko 'karan wayar bata ji ba. Rayyan yace" Yanzu ina take?" Tana can 'dakin ta. " Hmm" Yace ya cigaba da kallon wayar sa. Ashe Marwan yake kira, sai kuma yaji bata picking. Dan 'karamin tsaki yaja mai sauti. Ammi me yasa bata 'daga waya toh?" " Wai Marwa kk kira?" Yace " Yes kuma bata picking call din". Ya yi maganar fuskar sa 'daure tamau. " Gafa wayar can saman drawer Mufeeda ta kawo shi nan tun azahar..Sai dai ka 'kira landline". Umarnin zuwa saman Ammi ya bata kawai ya ajiye kan wayar. Bata 6ata lokaci ba kuwa sai gata. Fuskar ta duk ya kumbura haka ma idanun ta...kallo daya zakai mata kasan cewa tayi kuka. Duk yadda yake jin zafin rai amma duba daya yai mata yaji tausayin ta ya tsirga masa ilahirin jiki da zuci. Gaban sa ta dur'kushe tace" Ina yini Yaya? Ya aiki" Cikin sassanyan sautin da ya sakwme karya nasa zucia. " Alhamdulillah". Yace ata'kaice. Ta waiga ga Ammi tace " Ammi barka da hutawa.." " Yauwa Marwa". Bayan shu'dewar wasu 'yan da'kiku sannan ya 'kira yi sunan ta cikin sanyin sauti yace. " Marwa"! Tace " Na'am" Tana mai sagowa ta dube shi. " Shine kika ha'da ni da saurayin ki dan kina son kiyi tafia ko?" Bata san me maganar tasa ke nufi ba dan haka kawai zuba masa idany tayi tana kallon shi. Ji tayi aranta sam kamar ba da ita yake wannan maganar ba hala yayi batan hanya ce yayi. Toh ita ina ma taga saurayin balle har ta ha'da su da yayanta. Ganin yanayin ta ya sa shi fahimtar cewa bata gane kan maganar tasa ba dan haka sai yace..." Adam ya 'kira ni akan dan Allah na baki daman yin tafiyar nan, nasan kuma ke ce kika sanya shi kirana..." Sai lokacin ma ta tuno da Adam a yau din. A kuma lokacin ta sake tuno cewa ashe fa har an riga an bashi auren ta lokaci kawai ake jira ya cika. " Ni kuma Yaya? wlh yau ma duk ban yi waya da shi ba, ni babu abinda nace masa koma ba yau din ba...." Gauron numfashi ya sauke, yace " Ki shirya, next week zaki wuce kuma 1 Week kadai zaki yi ki dawo in kika wuce haka.. Marwa..." Ya 'dago ya sanya idanun sa cikin nata yana me bu'de idanun sosai alamun gargadi. Basai yace komai ba. Ita kanta tasan me yake nufi dan haka sai tayi 'kasa da nata idanun cikin sauri. Farin cikin daya tsirga mata a wannan lokacin ya rinjayi komai a wannan da zai zo mata sa6anin sa. Dan haka take murmushi ya mamayi fuskar ta, ya kuma kore duk wani takaicin dake kunshe cikin zuciyar ta yinin ranar. With an exitement tace " Nagode Yayah..Ammi thank u..Allah ya kara girma". Tana gama fa'din haka ta mi'ke. Ammi tayi caraf tace" Wayar ki na ciki, Mufee ta taho da shi tun dazun ke kuma baki biyo sahu ba. Bata yi musu ba ta 'dauko wayan, sai ma yanzu ta tuna da ita baki daya. Tana shiga dakin ta ta fa'da kan gado ta lumshe idanu. Ji tayi aranta tana so da bukatar fa'da ma wani ataya ta farin ciki..Safaa da ta fado ranta tayi saurin kawar da tunanin ta domin tasan 6ata mood in ta zatayi nan take..ta riga tasan that soul has gone forever nd she ll never ever come back to her.." A hankali ta bu'de idanu ta 'dago wayar. Tarin missedcall 'din da ta gani su suka kusan firgita ta. Me ya faru Adam yayi min irin wannan missedcall haka ta tambayi kanta. Ba shi tayi niyyan kira ba amma hka nan kawai ta danna kiran layin nasa dan tsintan zuciyar ta tayi da son jin meke faruwa. Shiru tayi bayan ya amsa kiran. Yayin da shi kuma ya saki ajiyan zucia. A hankali ya kira sunan ta " Marwa"! Tace" Na'am". " Kin tada min hankali yau Marwa"! " Kayi hakuri". " kin hana ni sukuni, kinsa na kasa jin farin ciki..wai me ke faruwa ne?" " Babu komai Yah Adam". " Marwa"! Tace " Umm". " Baki sona ko?" Tayi shiru. " Please tell me" " Ba haka bane". " me yasa baki 'daga wayata Marwa?...throughout d day kinki picking call dina...why please.."? " Bakomai fa". " Murya ta ne baki son ji ko?" Da sauri ta girgiza kanta tamkar yana gaban ta, sai kuma tace" Ba haka bane fa, Mufee ce ta kai wayan can wajen Ammi..shiyasa". " Meaning?" " wayan bata yini tare da ni ba.". Shiru ya dan yi na 'dan sakanni. Ita kanta sai take jin bugun zuciyar ta na 'kara hauhawa, sake manne wayan tayi da kunnen ta lokacin da ya sake 'kiran sunan ta. " Ki min alkawari Marwa bazaki sake kuka sbd wani namiji ba?" Shiru tayi. " Please Marwa, ki yi min alkawarin bazaki sake tunawa da past din ki har ki zubda precious hawayen ki sbd hkn ba..." " Hakan abu ne mai wahala Yah Adam..." " So promise me zaki rage..." " Insha Allahu.." " Good girl". " Ya batun tafiyar ki?...kin fasa din?" " No!" " Zan tafi..Yayah ya barni inje..."! Ta fa'da with full of excitment. Shima kansa murmushin jin dadi yayi..for once ya fahimci tana farin ciki.. a hankali yace " haba dai?..yaushe ya barki". " Yanzun nan...". " Kai dear". " Dagaske Yayah Adam...yanzun haka ma yana gidan nan.." " Masha Allah...congratulation my dear, i mean for both of us, nima zan sami sukuni yanzu, amma shine ko a kira a fada min wannan kyakykyawan albishir din..?" " Ba gashi na 'kira yanzu ba..." Yar daria yayi " hakane but wannan kiran ai nasan manufar sa dabanne..." Tace " Manufa kuma?...ba komai fa" " Fadi gaskia madam, nasan kin kira ne sbd kinga tarin missedcall dina, tunanin ki ko wani abin ne ya samu masoyin ki...". " Wayyo Allah, ni Allah ba haka bane..". " Toh menene?" " Kin 'kira ne kiji ya nake, ko na yini lpy ko kuma a a?..ni dama nasan wannan 'kiran 'kauna ce...?" " Kit ta kashe wayar tana murmushi rungume da wayar a kirjin ta. Shima murmushin yayi, yana mai sake jin tausayi da kaunar ta na ratsa masa zucia. Bai ajiye wayar ba sai da ya rubuta sako ya tura mata kafin nan. Tana cikin murmushin taji karan shigowar sako, ko da ta dago wayar sai taga daga Adam ne. Da sauri ta bude sakon. Haka nan kawai sai take jin ta kage da son karantashi. _If ur love nd emotions get ignored.... do urself a favor nd walk away._ _You're worth so much more than what people have unfortunately made u to believe my Marwa, u ar very special, rare and precious_ . _Wait to be with someone who cherishes u nd is proud to have u with every day that passes._ _Someone who actually knows ur worth...Someone who is there for u nd genuinely wants to know ur heart's needs nd desires. This is what your life needs Marwa ta._ Marwa ta karantacsakon nan fin sau bakomai amma har a lkcn bata gaji da karantawa ba..haka nan kawai sai ta ji sakon yai mata dadi ya kuma tsaya mata a zucia. Tun lokacin da Adam ya ga Marwa ya fahimci cewa she is depressed, but bai san meyasa ya kasa tsananta bincika kan hakan ba, ya dai riga yasan Zaitoon bazata ta6a cutar da shi ba kamar yadda yasan bazata bari wani yayi hakan ba, inda wani abu 6oyayye da ya kamata ya sani zata sanar masa. Hakan yasa bai wani damu sosai ba sai dazun da ya kira waya yana zaton ba a san an 'daga wayar ba ma Allah dai ya nufe shi da jin ka'dan daga cikin abinda ya ke damun ta sannan ya gaskata zargin sa. Ya dai san Marwa ta ta6a Aure, kuma wanda ta aura din tamkar dan uwanta yake, a yadda labari ya riske shi, kuma sun rabu ne sakamakon shigan sa gidan yari bisa wani gagarumin laifi da yayi. Toh shi bai damu da sanin laifin ba tunda ba Marwa ce tayi sa ba, kuma bai isa yace ya 'kita sbd hakan ba bai ma da hujjan nuna mata 'kiyayya musamman da ya ke shima mahaifin sa a gidan yari Allah ya 'dauki ransa, in muguwar tarihi ce yasan nashi yafi na kowa. After all zuciyar sa ta riga tayi na'am da yarinyar dari bisa dari, baya jin zai iya barinta sbd wani dan kalilan din dalili. Kuma bai 6oye musu batun mahaifin sa ba, duk da Ammi ta riga tasan da batun tun can baya, amma duk da hakan basu 'kyamace sa ba, suka dubi kyawawan halayen sa, suka dubi nagarta da kamalar sa, suka dauki auren 'diyar su da suke ji da ita suka bashi. Ita kanta hajiyar sa bata yi zaton zasu bashi cikin sauki haka nan ba duba da cewa manyan mutane ne ba na wasa ba, 'korafin da taso yi ma shine wai sbd Marwa bazawara ce amma itama bata ja maganar har na tashin hankali ba. Ya kuwa ce shi sam ba wannan ne gaban sa ba, ai sunnar ma aiki ce ma dan ya fara da auren bazawara, abin dubi kawai shine hankali da natsuwar yarinya, kuma ya tabbatar Marwa capital A ce ta wannan fannin. Maganar da yayi da Hajiyar sa cikin natsuwa yasa bata kara jayayya bisa hakan ba, domin ta riga tayi alkawarin bazata 'kara tauye sa ba har karshen rayuwar ta...indai yaso abu toh taya shi son abun zatayi har zuciyar ta...fatan ta kawai shine su kasance alkhairi ga junan su..alkhairi kuma dawwamammiya. ***** Shirye- shiryen tafia Marwa ta fara yayin da gefe guda kuma ake faman shiryen shiryen biki babu 'kakkautawa. Kwatsam lokaci guda tafiyar gaggawa ta taso wa Rayyan zuwa Madina batun kasuwancin sa. Duk yadda yaso akalar tafiyar ta canza abin ya faskara, dole sai shi 'din ne zashi...ko anan ma yayi kewar makusanci ba dan kadan ba. Shiyasa kwanaki da yayi sha'awan shigo da Bello cikin al'amuran sa bai yi kasa a gwiwa ba ya nemi Bukar awaya kan batun, bai sani ba ashe Adam ya riga yayi masa shigan sauri, bama Bello kadai ba hatta shi Yah Bukar din da kanshi yanzu 'karkashin Adam suke aiki. Haka ya tarka iyalan sa ya kaisu gidan Ammi, dan bazai iya barin su su ka'dai a gidan nan ba alhalin yana can wata dunia. Hakan ya matukar yiwa Zaitoon dadi dan tunda aka kawo ta Kano bata ta6a zuwa gidan Ammi ta kwana ba sai dai yini amma wannan karan bama kwana zatayi ba har kwanaki masu yawa..bakin cikin ta daya batare da mutuniyar ta Marwa zatayi wannan zaman ba. Domin kwanan su biyu da zuwa Marwa ta wuce, tama so tafiya da Mufee amma Ammi tace sam, taje kawai, tunda tare zasu dawo da su Raihanan ai shikenan, kuma ma in ta tafi da Mufee wa zai riqa 'debewa Zaitoon kewa. Ana gobe zata wuce Adam ya tura mata ku'di 200k tayi tsaraba wa Affan. Bata so hakan ba dan aganin ta me zata siya masa har na wannan uban kudin. Shima Adam kawai ya saka wannan kudin ne sbd baya son tayi 'korafin sunyi yawa amma ba abinda yayi niyyan turawa ba kenan, sai dai duk da hakan bai tsira ba. Kawai sai yayi murmushi...lokacin da tace masa, ai Ammi, da kowa sun siya musu tsaraba ita bata san me zata siya ba kuma. " Ohh toh kowa yayi nasa sbd ni kuma ban isa ba shiyasa baza'a ansa nawa ba?" " Ba haka bane". " toh menene?". Tayi shiru. " Hmm" kawai yace ya yanke wayar. Yasan akwai ciwo a zuciyar Marwa baya so ya rika takura ta kan abu, sbd gudun fama mata miki ko kuma cutar da ita, Marwa na matukar bashi tausayi ba wai dan ta kasance wani abu bu, No, kawai sbd irin abinda kunnuwan sa suka jiye masa, sai daga baya ma da ya matsa sannan Zaitoon ta bashi kaf labarin. Tausayin kaf ahalin ya zauna masa a zuci, sai da yaji ma ai shi nashi rayuwan bakomai bane compared to nasu. Wannan tausayin shi ya 'kara habbaka 'kaunar da yake yiwa Marwa, har yake jin tamkar bai ta6a son wani abu a dunia sama da ita ba, shiru shiru ko rashin damuwa da shi din da bata yi sam bai damesa ba, bcuz yasan with time zata yi healing. Komai dake faruwa ga bawa jarrabawa ce, kuma mukaddari ne, fatan sa kawai shine ya kasance mata haske kuma madogara abin alfahari har karshen rayuwar ta. Marwa kam cikin tunani ya barta, tasan babu komai da take bu'kata sai dai ta siyan masa tsaraban shi, kamar yadda yace tun farko, haushin kanta ma taji, meyasa lokacin da yace ta tura masa acc din nata bata yi wannan tunanin ba..ko da yake cewa yayi sa'ko zai bata in zata dawo ta siyan masa wani abu da yake so daga can, tayi tayi da shi kuma ya fadi abin kawai basai ya tura kudi ba yace sam, ai fannin kasuwancin sa ne, bai kamata ta siya masa haka nan kawai ba, sbd zai riqa ji tamkar ita yaje wa kasuwanci. Maganar tasa ta sata daria sosai. Sun kuwa yi dariyar a tare dukkan su. Adam ba karamin nishadantuwa yake da irin yanayin ba idan suka tsinci kansu. Zaman gidan Ammi da ya kama Zaitoon a wannan karan daban take jin sa sosai, a zahiri bazata ce bata jin dadin sa ba, domin babu wani abin arziki da take yi, duk da wani lokacin takan ji sha'awar ta shiga Kitchen wajen masu aikin ta taya su amma Ammi sam ta hana, nan nan take da ita tamkar 'kwai, abin wani lokaci har na bata kunya, ko sau'kowa zatayi a stairs sai tace mata tayi a hankali. Sam bata bari ta 'dauki Mufee balle ace ta goya ta sai dai tace 'daya cikin masu aikin su goya ta ko wani abin...duk kuma abinda take so taci babu 6ata lokaci ake samar mata shi bisa umarnin Ammi, wani lokacin ma Ammin dakanta zata ce baki bu'katan wani abin ne tace a a Ammi...ita har kunya take ji wasu lokutan. Kafin cikar wasu kwanaki ta 'kara kyau da haske gwanin birgewa. Ita kanta tasan ta canza sosai..Ko in.suna waya da Rayyan ta kan.tsokane shi wani lkc tace" Wlh Ammi ta fika kulani, kaga yadda ake nan nan da ni ba kamar kai ba da kullum masifa". Ranar da ta fada masa haka ba karamin daria yayi ba, yace ni ne mai masifan?" Tace " Erh mana, amma Ammi ba ruwan ta..ni dama kar in koma can". " Ai baki isa ba yarinya..kima kasance cikin shiri duk ranar da na shigo Kano gidan ki zaki kwana". Duk yadda Rayyan yake son suyi video call kuwa ta'ki amincewa, sai dai ta ha'da sa da Mufee ko kuma ta rufe wajen camerar ayi a haka sai ta gansa shi kuma yaji muryar ta. " Yarinya kina wasa da ni ne, duk ranar da kk kuskura na sanya 'kafata a Kano wlh zaki gane kuren ki ne...". Sai tayi daria kawai. Salmerh 😘 [23/01, 4:25 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Wattpad@* _Serlmerh-md_ 🅿️ *...107* .......Yanda kuwa ake shirin bikin Marwa abin har zai baka mamaki..gagarumin shiri ake na gani a fada babu kama hannun yaro. Babu wanda ya yadda aka barsa abaya wajen shiri. Haushin Zaitoon 'daya Marwa Bauchi za a akaita ba Nan Kano ba, tayi tayi da Adam kuma ya barta nan Kano amma yaki. Yace an'ki wayon, yace meyasa ke ba a barki can wajen Innar ki ba aka kawo ki nan..in haka ake yi ai kema can za a barki..". Tace" ai ni qin amincewa akayi amma nafi son can, kuma itama Innar ba yadda zata yi ba kasani...". " Toh nima naqi amincewa, kuma ina da tabbacin itama Ammi ba yadda zatayi abar Marwan anan ba...gara dai akawo min amarya ta nan kusa da ni da Hajiya ta yafi min". Har ta 'dan yi fushi da shima ta daina daukan wayar sa na kwana biyu kuma sai ta zo basar sanin ya fita gaskia...ba hujja gare ta ba. Dama ita mace bata da zabi, duk inda kaddarar aure ya kaita dole taje kuma ta zauna...tadai san dole Marwa zatayi kewar gida sosai, suma kuma zasu yi kewar ta, shiyasa tun yanzun take jin tausayin ta. Domin a kaf din tarihin Marwa da ta sani tun tashin ta har kawo girman ta bata ta6a barin gaban Ammi ba, har auren ta na farko tare suke, kusan ma tare da Ammin take rayuwar ta kuma har yau basu rabu. Ana biki saura 1week suka dawo, ranar kam Zaitoon ansha farin ciki domin saukan bazata sukai musu. Adama Ammi nata mita da fadan me suke jira acan ne har lokacin basu dawo ba, ga Adam ma ya ishi Zaitoon har ya yi niyyan tafia amma Zaitoon ta hanashi sbd Marwa ta sanar da ita abinda ya sa basu taso tuntuni din ba sakamakon gyran jiki da ake yi mata. Da kyar ta samu Shaheed ya bar batun tafiyar nan. Ai kuwa ganin yadda kowa ya damu da batun amarya bata Kano ga masifan Ammi dan ita kan ma cewa tayi abar gyaran jikin nan kawai su taho, hakan yasa suka yi musu diran bazata. Gidan ya cika makil baki na nesa da na kusa. Yadda kuwa Marwa ta sha gyaran jiki tayi matu'kar kyau tamkar ba ita ba inka dube ta har ji zakayi tamkar ba ita ba. Tun daga ranar Zaitoon ta fara tsokanar ta da suna amarya bata sake kiranta da wani suna sabanin hakan ba. Tana dariyar mugunta ta kira Adam tace albishirin ka.." Yace" goro fari tass...kar kice min gimbiya ta ta iso". " Wani gimbiya, ana maganar kyakykyawa, kazo gida yau kaga wata yar kykkyawan babe agidan mu..". 'Yar daria yayi " Kice kyakykyawa ta ta iso mana Zaitoon, nakira ai bata 'daga ba...". Baki ta kama tace " Kai ya Adam ya akayi ka sani alhalin muma zuwan bazata akai mana..". Daria sosai kawai yayi ya yanke wayar. Ana fitowa a sallahn maghrib daga nan masallacin yayo gidan. Marwa tana tura baki ta iso inda yake. " Shi kuma fushin na menene?.. Ya tambaya yana duban fuskar ta. Bata ce komai ba sai ma sake jade rai da take. " Gimbiya ko in koma ne naga alamun sam ba ayi farin cikin gani na ba..". " Fisabilillahi ko hutawa baza'a bar mutun yayi ba sai ka wani zo...". " Taya kk tunanin za'a bar mutum ya huta bacin an 'kyan:kyasawa bawan Allah kykkyawa ta dawo..". " Mamin Mufee ko?" " Ni dai ban ce ba..". Ya bata amsa yana daria. " Amma dai koma waye ne ai ni ya taimake ni ne da kallon wannan kyakkyawan bai wuce ni ba ayau". Murmushi kawai tayi...a hankali tace" Ina yini..?" " Lafia kalau..hope kun dawo lafia..?" " Alhamdulillah. " Ya cikin gidan?" " Suna kalau..". " Kinyi kyau Marwa ta, kin yi kyau sosai...". Yayi maganar yana kjingina bayan sa jikin kujeran motar da yake zaune. Kai ta kara sunkuyar wa sosai. Shi kuma ya cigaba. " Wai da ma ke kina tunanin zan iya sanin kin dawo ayau kuma in kasa zuwa ganin ki ne..ai sai in kwana ina firgita cikin bacci..in ma na iya baccin kenan". Daria sukai dukkan su. Marwa ta kuma sunkuyar da kai tana murmushi take fadin. " Toh me ne a ciki...sai ince maka mun kwana ne a hanya bamu samu isowa da wuri ba ai....". " Dan kawai a cuci bawan Allah ko...". " Hmm.."kawai tace sannan ta cigaba. " Amma dai tsakani da Allah Yah Adam 'kamshin nan naka fa yayi yawa, yanzu haka ka taho tun daga gida kana wannan 'kamshin har zuwa nan...?" " Toh me zai yi..kin mance Ango ango nake yanzu...". " Ya dai yi yawa, ai sai ayi ta waigowa ana duban ka idan ka gifta..". Acikin motar...?" Ya tambaya da Mamakin kalamanta. " Ko dai an kishi ne 'yar yarinya" Baki ta tura gaba..tana kya6e baki tace. " Kishin me zanyi ni kuma..kawai dai ina fa'da maka ne sbd babu kyau..?" " Ni fa namiji ne ba mace ba Marwa..ko kin manta?". Shiru tayi, tayi tsam da ido tana duban sa, sai kuma ta sunkuyar da kanta 'kasa tana mai jin kunyar za'kewan da tayi. Sam sai ma ta rasa me yasha kanta ne ma haka. Yana daria yace " Hafiz dina yana gaida ki, kinsan tare muka zo, kuma bazamu koma Bauchi ba sai da Amaryar mu. Hmm kawai tace..bata sake wata doguwan magana ba har suka rabu. Bayan kwana biyu da dawowan su aka kawo lefe, abin sai wanda ya gani kawai, kaya ne nagani afada, sam barka ake ta kowani kusurwa ka leka, sai fadi ake Marwa tayi goshi tubarkallah. Babu wanda yakai Zaitoona farin ciki, domin ita 6angare biyun duk nata ne, kowani 6angare aka yaba jin dadi take, duk da yake dolene wani kusancin yafi wani...amma tana cikin tsananin farin ciki. 'Kokarin da Adam keyi ana kuma yaba masa ita farin cikin ke mamaya. Sannan dattaku da aka nuna daga gidan su Marwa idan aka yaba musu farin cikivyake sanyata. Innar Zaitoon taso zuwa Bauchi bikin nan amma Allah bai yi ba domin maigidan ta baya jin dadi cikin kwanakin. Amma wasu daga cikin yan uwan su da yawa sun zo ta kuma yi farin ciki da hka...hatta Yah Bukar ba a barsa abaya ba, musamman ma dayake shima yanzu harkokin sa sun koma Bauchin. Ana gobe 'daurin aure Rayyan ya dawo. Can gidan sa ya sau'ka sannan ya 'kira Zaitoon akan ya dawo ta taho yanzu. Tace" toh". Ta cigaba da hidimar ta. Anyi kamu anyi walima sai kuma gagarumin dinner da aka shirya acan Bauchi wannan kam tun ma kafin ya dawo yace bazata Bauchin bama ballan tana Dinner. Duk Zaitoon ta 'dauka wasa yake. Yana can yana jiran ta shiru shiru..har ya gaji da jira gashi yana ta 'kiran wayar ta bata 'dagawa. Ya 'kira na drivern gidan ma yace shi fa bai ma ganta ba balle ya taho da ita. Bai san meke damun Zaitoon ba sam, yarinyar nan ta raina shi dayawa, bata san yadda yayi kewar ta ba ne. Ko da ya isa gidan makil ya iske shi cike da mutane, dama yasan Ammin sa da jama'a dole taron in taro ya taso a 6angaren ta gidan ta ya tumbatsa da mutane. Ta baya ya samu ya shiga gidan ya haye saman Ammi can bedroom dinta ya shiga, amma bata nan sai da ya 'kira wayan ta kafin ta san da zuwan sa cikin sa'a kuwa ta 'daga wayar da yake wayar na hannun ta ne. Da fara'ar ta ta iske shi tana masa lale marhabin da zuwa. Nan tasa aka gabatar masa da abinci da na sha...sannan ta tura a nemo mata Zaitoon ta koma can 'kasa wajen ba'kin ta. Zaitoon tasha kyau har ta gaji, komai dinkin su da Marwa tare akayi musu kala ce kawai ke bambanta su, idan ka dubi Zaitoon bazaka ta6a zaton itama ba 'yar jami'a bace sbd kyau da kalan wayewar ta da zaka gani a zahiri. Idan ka kalle ta sai ka zaci itama amaryar ce ko kuma Ammi na aurar da su su biyu ne. Pictures kuwa har gajia da 'dauka tayi ta tafi takwanta wai ta gaji, haka itama Marwa zamowa tayi ta tarar da ita a 'dakin. " Sannu amarya". Cewar Zaitoon. " Ai kece ma amaryar..wai kuwa kinsan yadda kika koma, Allah ban ta6a lura da ke da kyau ba tunda na dawo sai yau dinnan, anya ba akusa sama mana kannen Mufeeda ba...?" " kamar yaya kenan..?" Kamar yadda kk fahimta. " Wa kenan zai samo su?" " Wa kuwa in ba keba". " Ke goggo Marwa raba kanki da wagga zance..ta ina zan samo su ni kuma?" " Kin fini sani ai". " Wlh ba wasa nk ba kin canza kamar ba keba Mamin Mufee..". " Toh dan na canza sai akace mk kuma wani abu ne, baki ganin yadda Ammi ke hanani yin aikin komai ne, kullum fa ina kwance babu aikin komai taya ma bazan canza ba..ke de madam kice kina kishi nayi kyau ranar auren ki...". " a a fa ke dadina da ke kanki sam baya yaja..Mtheww"! " Sai ki tayani jansa ai Hajjaju..". Inda tayi maganar tana tashi daga kwanciyar da tayi. " Ke banda abinki wannan ma bai ishe ki wata ayar tambayar ba...Ammi haka nan kawai a tunanin ki zata hanaki yin aiki ne batare da wani dalili ba...". " Dan Allah ni ki daina..dalili ya wuce dan bata so in wahala". " Shikenan naji, na daina, amma tsakanin ki da Allah yaushe rabon ki da yin period..?" Idanu ta zaro tana duban Marwa. " Tanan kika 6ullo kuma?" " Ke dai fada min dan Allah..ko ban fada mk ba nasan kin riga kin san wannan...yin sa da rashin yin sa duk akwai dalili kwakkwara ko?" Wani bugawa da 'kirjin ta yayi sai da 'kwalla ya cika mata idanu tuno rabonta da yin shi. " Tsoro kike bani Marwa, dan Allah ki daina maganar nan....". Suna cikin wannan maganar aka zo nemanta wai inji Ammi tana can samanta. Batare da wata damuwa ba ta tashi ta tafi, dama tafi son kaucewa magananar da Marwa ta dauko a wannan lkcn, tuni kuwa ta watsar da batun dan cika umarnin Ammi. Bama ta san ina Mufeeda take ba..sai da ta doso dakin taji muryar ta tana 'kyalkyala daria sosai. Kawai sai tayi murmushi. Dayake 'kofan bai rufe baki 'daya ba kawai turawa tayi tana mai furta sallamar ta a hankali. Ita kanta Mufeeda yinin ranar kaf bata ga Zaitoon ba, sai dai wajen 'daukan pictures amma ko a lkcn bata zo wajen ta ba. Da ganin ta yanzun kuwa da gudu ta taho wajen ta tana 'kiran sunan ta. Sama tayi saurin dago ta ta rungume, yarinyar tayi kyau sosai, tasha gyaran kai mai ban sha'awah..da dinkin ta kalar gown kalar na amarya. " Mufee na yau anyi Scarce..duk murnar bikin Antyn naki ne....? Ta fa'da tana rage sautin maganar ta jin 'kamshin turaren sa cikin 'dakin dai- dai lokacin da Mufee ta 'kirayi sunan ta tana mai nuna mata shi. Tsam tayi da idanu kawai tana duban inda yake zaune, shi kuma yi yy tamkar bai ganta ba. Batayi mamakin ganin sa ba dan tana sane da cewar ya iso Kano. " Yayah...barka da zuwa". Ta fada tana dan kara stepping kafanta zuwa kusa da shi. Cigaba da cin abincin sa yayi...sai da ta 'karasa kusa da shi ta zauna gefen sa kafin ya dube ta suka ha'de idanu. A hankali ta maimaita abinda ta fada tun farko. Rayyan kam idanu ya tsura mata yana mai 'dage gira. Kallon mamaki yaso yi mata amma ya basar...Spoon ya 'dauka zai cigaba da cin abincin sa Zaitoon tayi caraf ta ri'ke hannun sa. 'Dagowa yayi ya dube ta alamun tambaya. Da sauri ta sanya idanun ta cikin nasa tace" I'm sorry yalla6ai...". Gira ya 'dage yana duban ta. " Sorry for what kuma?..ba dai ni ba, ni kk raina ko?". " Kayi hakuri". " Hmm" yace Ya fara shirin mi'kewa. " Har ka kammala cin abincin ne?" Ta tambaya tana duban abincin. " Ya ishe ni". Mufee na ganin ya mi'ke ta tafi wajen sa. Sama ya 'dago ta sannan batare da ya dubi Zaitoon ba yace"...tashi mu tafi gida..ki same ni a mota.." " Yayah dani kuma?" Ta tambaya kamar me shirin yin kuka. Kallon ta yayi, sannan ya dubi Mufee. " Feefy na wai ina Antyn ki..?" Nuni kawai tayi da kofan fita, sai yayi saurin sau'ke ta, je 'kira min ita kice Abbah na 'kiran ta yanzu.. ". Ya 'karashe maganar yana gyara mata rigan ta cike da kulawa. Sai da yaga fitan ta kafin ya waigo ga Zaitoon. " Me kika ce..?" " Bako..mai". Ta bashi amsa a takaice. " Kince wani abu ai". " A a kam..banyi magana ba.." " Hmm" yace yana mai takowa zuwa inda take. " Da kina nufin nan zaki sake kwana bayan ina cikin Kano... yaudaran kanki kike..wuce muje ko kuma abinda kk gudun faruwar sa acan din ya faru nan 'dakin Ammi....". Ido ta zaro da sauri ta matso tun kafin ya kaiga 'karashe maganar ta rufe masa baki da hannun ta. " Kai Yayah...miye haka...?" Jinta kusa da shi yasa shi matsota sosai yana mai ri'ko 'kugunta da hannun sa 'daya, yayin da hannun 'daya ya sa ya cire hannun ta saman bakin sa...dayake bai wani bada 'karfi ba kawai sai ta 'ki bashi daman cire hannun. Tsoron ta wai kar ya fa'di wani abinda za a ji su zo suji kunya. Yayin da tenderness na hunnun da taushin da yake da shi yake 'kara fisgan sa. Cizon cikin hannun yayi dagangan, kuma cizo mai zafi..da sauri ta dage hannun tana watsa shi dagasje da zafi dan har ya nuna alamu yy ja gurbin hakoran...wash...wash tace kafin ta 'kara fadin na uku sai jin sau'kan la66an sa tayi saman nata. Wani deep kiss ya bata wanda hakan ka'dai ya tabbatar mata da cewar ba 'karamin kewar ta yayi ba. Ayau din jin sa yake cikin tsananin farin ciki, bai tabbatar da maganar Anty Madina ba sai da yaga Zaitoon ayau din shi kansa yayi mamaki, yana fatan zato da hasashen su ya kasance gaskia. Anty Madina ce ta fara kyankyasa masa cewar tana ga kamar ciki ne ajikin Zaitoon, duk kuma yadda yaso yagan ta a video call yaga irin canzawar da akace masa tayi Zaitoon taki bashi wannan damar. Shi kuma bai yadda ya tura ta asbiti baya gari ba zai ga kamar bazai samu sahihin labari ba duk da kuwa cewa ya matukar yadda da abokin sa Fawwaz. Bata tashi kokarin neman raba jikin ta da nashi ba sai da taji kamar ta kusan makara...domin tuni Zip 'din rigar ta yayi 'kasa...sannan ta dakatar da shi. Tana mai girgiza masa kanta. Shima kansa ya dafe yana mai zama bakin gadon Ammi...Zaitoon baya ta juya masa tana kokarin daidaita yanayin ta. Ruwan da aka kawo masa abinci da bai sha ba ya daga bai sauke ba sai da ya shanye sa tass sannan ya saki ajiyan numfashi. Ido ya waro sosai sannan ya sake mi'kewa. Hannun ta ya kama batare da ya dube ta ko furta wata kalma ba kawai yayi gaba, bata da za6i illa binsa, Allah ma yasa tana tare da 'dan mayafi saman kafa'dar ta...kuma zuwa lokacin duhun maghrib ya shigo hakan ya kara taimaka wa wajen rufe sirrin ta acewar ta. Nauyi take ji sosai amma da alamu shi sam babu abinda ya dame sa, bb ruwan sa da kowa...direct wajen motar sa ya kaita ya bu'de mata ta shiga sannan ya zaga shima ya shiga. Mufeeda kam ko wajen Marwa ma bata 'karasa ba aka rike ta tun anan Parlour...dan hatta yan uwan Nadia sun zo bikin nan kowa farin ciki yake da ganin yarinyar. Marwa bata tashi cigiyan Zaitoon ba sai wajejen karfe tara, nan ta fara neman ta har wajen Ammi, tace ai Ammi ce ta aika tazo ko dai sata tayi ta kwanta ta huta tunda tun lokacin bata kuma ganin ta...Ammi tace" ni na isa? bacin isasshshen ya iso ina ni ina sa ta huta..". " Hala yaya ya dawo ne..?" " Tun da yamma ya iso..". " No wonder..shiyasa naji matan nan shiru" ta fa'da cikin ranta. Ai kuwa tun ma kafin ta koma 6angaren ta fara neman layin ta, unfortunately kuma wayar na nan 'daki anan Zaitoon ta barshi. Ba 'karamin murza tasha wajen Rayyan ba, dan kuwa duk wani takaicin da ya kwasa sai da ya sau'ke sa tass. Da kanshi kuma ya yabawa 'ko'karin ta, sai ma ya fara jin tasauyin ta, dan ba 'karamin juriya tayi masa ba. Sai da ya tabbatar ya ladabtar da ita kafin ya 'kyale ta...tana mai sauke ajiyan zucian kukan da tasha. Kuncin ta yaja..yace " Gobe ma a 'kara min taurin kai da bijirewa umarni na". " Ai nace bazan 'kara ba..". Ta fada cikin kuka tana mai juya masa baya. " Kima kara...as u can see maganin ki zanyi...". Baccin wahala tayi ranar, yayin da Rayyan yayi kwanan farin ciki, ta kowani fanni farin ciki ke ratsa shi. ya samu biyan bukatar sa, sannan yana hasashen matar sa na da juna wanda yake da burin tabbatar da gaskiyan lamarin a gobe in sha Allahu, sannan Marwan sa zata auri nagartaccen miji da ke matukar kaunar ta. Ko kokarin da Adam yayi wajen hidiman bikin nan kadai shi kansa Rayyan ya jinjina masa. Lefe kuwa abin sai son barka. Yadda kuwa a ko'ina yake nuna yadda yake 'kaunar Marwa abin na matukar yi ma Rayyan dadi. Burin sa ya kusan cika ta fannoni da dama. Fatan sa nagartar Adam ta 'dore, fatan sa Adam ya kasancewa Marwa mijin marainiya sa6anin mijin ta na baya, fatan sa ya toshe mata duk wani miki dake 6oye cikin zuciyar ta.. yana matukar son ganin Farin cikin yarinyar nan tun ba yau ba. Washe gari da safe yaja su Jam'i Zaitoon na wani shashshare sa. Ta gaida shi. " Toh wannan fushin fa wai duk na menene. Baki ta tura..." Fisabillilahi mutum na wajen taro a wani tsamo shi ya kwana anan, yanzu da wani idanu zanje in dube su dan Allah...?" " Da wannan idanun mana..da can da wani idanu kk duban su...?". " Toh haka ake yi ne..?! " An ma riga anyi ai madam sai dai in za a sake..". Ta dan harare sa. Yayi daria.." toh ai gaskia ne...in kuma kinga bazaki iya komawa ba kina jin kunya shikenan sai kiyi zaman ki anan, nima da naje aka 'daura auren zan dawo in same ki musha hutun mu har su gama bikin su...". " Ai tafiya zasu yi toh su barni anan.." " Ina zasu tafi kenan?" " Can Bauchi mana..". " Kyale su suje abinsu, dama ai ke babu inda zaki". Ido ta waro" gidan amaryan..?" " Sau nawa zamuyi maganar nan ne nikam, nace banda ke a zuwa Bauchin nan..kin ki daina maganar...". Ya 'karashe da jan dan 'karamin tsaki. Kawai sai ji tayi wani zufa ya karyo mata, take ta fincike hijabin, tana duban sa, gani take kamar wasa yake, amma yanayin fuskar sa ka'dai ya tabbatar mata da cewa dagasken gaske yake. Take sai ta fara kuka, kuka fa irin sosai din nan. Rayyan kuwa tashi yayi ya ma bar mata 'dakin ya koma can nata 'dakin. Sai dai bai ji ya nutsu ba ya sake dawowa. Hijab din da ta cire wajen yin kukan ya 'daukan mata ya sanya mata sannan ya kama hannun ta zata yi gardama ya 'daga baiwar Allah sai gaban motar sa. Direct Youheal ya wuce da ita aka kira Dr. Hauwa yayi mata takaitaccen bayani, both jini da fitsari aka diba, in minutes sai ga sakamako ya riske shi. Cikin office din Dr Fawwaz ya yi sujudush shukur yana mai yiwa Allah kirari. Fawwaz kan sa farin ciki yake yana 'karawa..ita kam tana can office din sa baccin ta ma take dan tunda aka diba jinin da yaga ta fara jin bacci ya sa a kaita can. Yasha tsiya wajen Fawwaz kafin su baro asbitin Zaitoon duk bata san wainar da ake toyawa ba...ita dai taga bakin sa kamar gonar auduga, fara'ar dake saman fuskar sa bama zata iya misalta shi ba. Lokaci lokaci ta kanji ya saki hamdala sannan yakan yawaita duban ta. Har suka je gida. " Kina jin baccin ne har yanzu?" Ya sake tambayar ta bayan sun isa gidan. Kai ta girgiza masa alamun a a..dan sosai take son komawa can gidan. kai ya girgiza shima" a a madam....dole ki kwanta fa ki huta, kafin inje daurin auren nan in dawo ko...?" " Zata yi magana yace" Please..bana son musu"! Dole tayi shiru...tayi rau rau da idanu. Kawar da kai yy tamkar bai gani ba. Da kansa ya kaita 'dakin sa ta kwanta idanun ta zubda hawayen takaici.. shima kwanciya yayi gefen ta...hannun sa ya 'daura saman marar ta har ya bata tsoro tunanin ta ko wani abun zai sake yi mata amma sai taga daga hakan bai matsa ba. Goshin ta ya sumbata.." I love u wifey". Ya fa'da da sauti mai taushi. Lumshe idanu tayi cikin ranta ta ayyana" nidai wa'dannan abubuwa duk ba birge ni suke ba burina ka barni in je wajen Marwa ta yanzu. Komawa yayi ya kwanta gefen ta, still hannun sa na saman cikin ta, cikin ya 'dan dago ka'dan amma ba sosai ba, sannan marar tayi 'karfi ba kaman da ba. " Baki taba jin canjin yanayi tattare da ke ba da zai sa ki zargi wani abu?" Da sauri ta girgiza masa kanta. Sai ya danna cikin ta saki 'yar 'kara. Yace" yanzu fa." Tace" da ciwo". Sai ya saki ajiyan numfashi yana kallon saman 'dakin yace" Kiyi min addu'a wifey...na taimake ki zaki 'kara samun wata ko wani babyn in Allah ya yadda''. Shiru tayi bata ce komai ba kawai tana 'ko'karin fasa maganar tasa dalla-dalla. Take maganar Marwa ya dawo mata. " Wai dagaske ne?" Ita kanta bata san tambayar ta fito fili ba sai dai jin amsar da Rayyan ya bata shi ya tabbatar mata da cewa a fili tayi maganar. Yace " Yes mana..kina kokonto ne?" " Yah Rayyan ni ce zan haifi Babyn?" Ta kara jefa masa tambayar. Yace" ni nafi son hakan ma kodan in huta da raki ma in anga ana da yara har biyu". " Yayah wai dagaske nice zan haihu?". Ta 'kara tambaya a mamakance..domin.sosai maganar tasa ke bata mamaki. Yace " A a Ni ne"!. " Ohh..da sauki". Tace da iya gaskiyar ta. Kai ya 'dago tamkar zai rufe ta yana duban fuskar ta yace" wai me kk so in baki as in tukuici..?" " Ni...?" " Yes..". " Tukuicin mene?" " Ke de fadi duk abinda kike so"! " Ka tabbatar zaka bani?" " Me zai hana, ai ni abinda kika bani ya sha gaban koma me zan baki.." " Toh ni ban son komai, kawai ka barni inje Bauchi tare da Marwa..". " Wannan kawai?" Da kai ta amsa shi idanun ta cikin nashi. Cikin idanun ta ya kalla na 'yan da'kiku sannan ya kawar da kansa yana mai sakin 'karamin numfashi. Tashi ki shirya in sau'ke ki. Zaitoon na jin haka ta yun'kura da sauri yace" kiyi a hankali mana, kina so in fasa ne ko?". 'Dakin ta ta wuce ta yi wanka cikin 'kankanin lokaci ta shirya cikin wata ubansun atampa da yake duk kayan hidimar bikin na can gidan. Har ta shirya ta fito Rayyan bai shirya ba 'karshe ita ta taimaka masa ya 'karasa shirin sa. sannan suka fito. Allah yasani sosai take jin kunya ta kuwa san hatta Marwa ba barinta zatayi ba sai ta mata tsiya ayau 'din nan..dan haka sai ta hade rai sosai tabi ta 'kofar baya ta shiga zuwa 6angaren Marwa. Cunkus ta same shi da mutane. Allah ya taimake ta bayan gaisuwa babu wanda ya tanka ta cikin su illa Marwa dake mata dariyar mugunta 'kasa- 'kasa. Dayake tasan hali, dama tasan dole Marwa sai ta tanka, hakan yasa bata nuna tama fahimci dariyar me take ba. Da abin ya ishe ta cewa tayi yarinya yi ki gama dariyar naki lokacin na nan zuwa zan rama ne...". Ko su Ammi bata iya taje gaida su ba, haka ta hau shirin ta ta gama ana ta hada hada, sai dai in hanya ta hada ta da mutun bkawai su gaisa ta cigaba da harkar gaban ta. Rayyan kuwa duk sai dayaje ya gaida su a lokacin ma ana shirin tafia 'daurin aure...so bai dade ba ya fito Ammi na tambayar sa Zaitoon fa yace tana cikin gida. Daf da zai fita yaga Mufee hannun wata mata yace" 'yan mata..". Muryar sa kawai taji ta fara waigen sa ai kuwa tana hango sa ta nemi a sau'ke ta ta nufe shi tana fa'din" Abbah..". Yace" Na'am maman Abbah...I missed u..". Ta wani sar'ke shi a wuya..." Mufeeda cikin taro fa zanje zaki hautsina min kayana kuma...". Wata yarinya ya yafito a gefen sa, ya mi'ka mata Mufee ta kuwa ki zuwa, yace bari inje allura in dawo kinji mamana, mai kike so in kawo mk...ta cuna baki ta girgiza kai alamun bakomai. " Zanzo muje Yawo anjima..ko?" Da sauri ta washe baki..." sarkin son yawo kawai" Yarinyar ya mikawa ita yana fadin" Kaita wajen Ammi na direct kar ki bada ta ga kowa". Yace da yarinyar sannan ya shiga mota ya fita. Dubbanin jama'ah ne suka shaida 'daurin auren...Adam Shaheed Jibrin 'Dan maliki tare da amaryar sa Marwah Sa'ad Auta bisa sadaki mai matukar daraja. Marwa kam da jin an 'daura aure ta fara kuka, duk wani uban make-up da akai mata sai da ta goge sa tass. Sai yanzu tunanin barin gida yazo mata. Zaitoon ma kukan take haka nan kawai bata san dalili ba. A haka aka 'karasa yinin nan har zuwa la'asar basu da walwala. Lokacin da za'a tafi da amarya Mufeeda na can dakin Ammi tana Bacci...Rayyan yaso tabi Zaitoon sbd kar tayi rigima idan taga babu su duka amma Ammi tace sam..damun Zaitoon kawai zatayi acan ta takura mata, abar mata ita agida kawai. Da kansa ya 'dauki amarya da Anty Madeena sai Matar sa Zaitoon da wata yar uwar Ammi sai ragowan motocin kuma suka dauki ragowan yan rakiyan amarya zuwa garin Bauchi. Memories da yawa Zaitoon ta bari cikin garin nan, akwai abubuwan da har abada bazata ta6a iya mancewa da su ba. Kawai sai kukan ta ya dawo sabo.. a hankali hawayen ta ya fara sauka.... Sau daya Rayyan ya dube ta ya dauke kansa. Ba sai ya kaiga tambayar ta ba yasan me take tunawa, sbd dama yasan dole ne ta tuna 'din...daya daga cikin dalilan da ya sa tun farko yace bazata zo ba. Wani abin tamkar ciwo yake kasancewa a zuciya wanda abu 'kalilan ke iya fame sa. Serlmerh😍 [23/01, 4:25 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕 *( 'Yata ce)* *Wattpad@* _Serlmerh-md_ 🅿️ *...108* ........Da kukan nata ya ishe sa ne...a zuciye yaja wani uban birki tsakiyan titi..." Rayyan lafia?...Ya akayi?" Anty Madina ta jefa masa tambaya cike da mamaki tana mai waigen baya. Bai bi takan maganar ta ba..sai ma duban Zaitoon da yayi. " I swear idan na sake ganin digon hawayen ki bazaki 'karasa shiga cikin garin nan ba zamu koma...haba da Allah"! ya 'karashe maganar a zafafe. Sai a lokacin ne ma duk suka ankara da cewan tana kuka. Anty Madina da 'yar uwan Ammi ne suka fara yi mata nasiha cikin natsuwa, ita Anty Madeena dayake duk tasan meke faruwa, ita kuma 'yar uwan Ammi tunanin ta ko kukan rabuwa da Marwa ne. Nasiha duk suka hadu sukai mata bayan yaja motar a fizge, shiru kawai tayi ta sunkuyar da kanta. Wani tangamenen gida aka kai Marwa da fa'dar irin tsari da girman sa ma 6ata lokaci ne. Amma su Anty da kansu sun yaba sosai tun ma ranar da suka kawo kaya. Sun kuma samu tarba mai kyau daga Hajiyar Adam, domin gidan ta aka fara kai Marwa kafin gidan mijinta. Kuka kawai Hajia Talatu ta sanya, lokuta da dama idan ta tuna abinda ta yiwa Zaitoon ko ita ka'dai ce cikin 'daki sai taji kunya ta kamata. Sai gashi ashe ma Shaheed din Zaitoon tsoka da jini suke ta yadda babu wanda ya isa shiga tsakanin su sai wanda ya ha'da. 'Karin abin kunya ma yau gashi dalilin ita Zaitoon din Adam ya samu kamilalliyar matar aure 'yar gidan mutunci da nagarta. Hakika kowani dan Adam nada tashi kalar tasirin cikin rayuwar kowa. Matukar mutum ya shigo cikin ka rayuwar ka toh ka mutunta shi, domin Allah shi kadai ne yasan manufar shigo da shi cikin taka rayuwar. Anyi addu'a sosai da fatan samun zaman lpy ga juna sannan aka mika amarya gidan mijin ta. Gida kam tabarakalla komai yayi...hadda abinda bai yi bama yayi sbd kyau da tsaruwar sa. Sauran abubuwan da ba'a kammala gyara mata bane washe gari aka tashi da aikin su nan ma Anty Madeena tayi kane kane ta hana Zaitoon yin komai. Taso taje taga maman Abdul amma Rayyan yaki bata dama acewar sa babu inda zataje dan yasan aikin kuka kawai zata je tasha abanza. Kafin la'asar suka fara niyyan komawa. Domin Rayyan ne zai koma da su, ya kuma fara azazzalan su akan su fito su wuce. Marwa kuka, Zaitoon kuka, Anty Madeena har haushi suka bata tamkar ta doke su hk taji.. tun tana ban baki da rarrashi har ta fara masifa. Dama tun agida wajen yiwa Marwa nasiha tafara masifa ganin yadda Marwa ke kuka 'karshe ba ama kammala da ita ba ta fito. Sanin halin Rayyan da tayi yasa tun ma kafin ta isa wajen Mota ta rage kukan sai dai Marwa kam babu ma alamun zata tsagaita. Rayyan sau 'daya ya kalli Marwa bai 'karaba sbd wani mugun tausayin ta daya fizge shi. Abinda yayi niyyan fada mata ma kasawa yayi. Sai dai kukan nata ya mugun tsaya masa arai sosai. Shi dai ga Ubangiji ya dam'ka ta, amanar ta ya bawa Allah sannan Adam, yasan duk abinda zai same ta sai in Allah yaso, so babu wani mahalukin da zai iya cutar masa da yar uwa face da yardar ubangiji...dan haka yana mata fatan dacewa, yana mata fatan alkhairi, fatan zaman lpy da kwanciyar hankali, fatan wannan auren ya kasance mata yanki na jin dadin rayuwar ta ya kuma sada ta da aljannar sa ma'daukakiya. Tunda suka 'dauki hanya babu wanda yace komai acikin su. Hatta da Anty Madeena ma shiru ba ta furta komai ba, Zaitoon ajiyan zuciya kawai take saukewa, yayin da Anty Madeena ke sauke gauron numfashi. Zaitoon kam tasan ba 'karamin kewar Marwa zatayi ba, domin tun ranar da Allah ya ha'da fuskokin su basu sake rayuwa a mabanbantan waje ba har sai da ta tafi garin su sannan...a koda yaushe suna tare da juna...suyi shawara tare, suyi sirrin su tare, suyi fada su kuma yi dadi. Marwa bata ta6a nuna mata banbamci ko girman kai ba shiyasa take kaunar ta sosai...amma karo guda an 'dauke mata Marwa an kaita wani gari can daban. Suna shiga Kano Rayyan ya dire su a 'kofan gidan Ammi yayi gaba da matar sa. Dayake lokacin dare ya riga yayi wanka suka yi suka ci abinci dan sun taho da take away sai kawai sukayi shirin bacci. Ita Zaitoon ko abincin ma ba wani na kirki ta ci ba yana lura da ita. Ga haushin 'kin barin taje taga Maman Abdul da yayi banda masifar da yayi mata ma hakan yasa ta juya masa baya. " Kinsan ban so ko?" Ya fa'da batare da ya waigo ya dube ta ba. Da sauri ta juyo tana tura baki gami da 'ku'k'kuni taki ma duban fuskar sa. " Wai fushi ake da bawan Allah..?" Kawai sai ta sanya kuka. " Ohh Allah Zaitoon me ke damun ki ne kwanan nan..abu kadan sai kuka..". matsota yayi sosai jikin sa ya rungume ta, cikin kunne ya ra'da mata" kin wani damu akan Marwa.. ba aure tayi bane, kiyi mata fatan alkhairi yafi kukan nan, ke da kika yi auren ki kika ce kinji kin gani zaki bar kowa kizo ki zauna da Rayyan waye yace miki zai biyo ki ko ya mk kuka...? " Ture sa ta fara yi tana mai 'kara sautin kukan ta sosai..." Ni yaushe nace zan zauna da kai?" " In tuna mk ne?" Shiru tayi ta cigaba da kukan ta. " Still dai..bana son kukan sam..in wani abu kike so pls ki sanar da ni..". " Banga Inna ta ba, kuma naga kowa amma banganta ba...". " Abban gidan ta ne bai da lafia shiyasa bata zo ba ki kwantar da hankalin ki..." Ya bata amsa nan take. " Ka min masifa kuma ka hana ni zuwa in ga maman Abdul...?" " Wannan kam ban amince ba, nasan in kun hadu banda kuka babu abinda zakiyi shiyasa bazan yadda kije ba...ki bari ba yanzu ba..kinji..Insha Allah watarana zaki je idan na tabbatar kin girma kin daina kuka". " Ni nace zanyi kuka ne?". " Da ban sanki bane yarinya..sai kice komai..". " Hope ba abinda ke damun ki, naji jikin ki da zafi sosai..". Shiru tayi. " Ko in mk allura.." Da sauri ta girgiza kanta. Shiru ya dan biyo baya. " Kinsan mene?". Ta girgiza kanta. " Kina bani mamaki wani lokaci" Da sauri ta 'dago ta dube shi yace" Yes mamaki sosai fa..". Cigaba da duban sa tayi, duban da shi da kansa yasan 'kage take taji abinda zai fito bakin sa. " Abinda har kullum nake tsammanin inji ya fito bakin ki ban ta6a ji kin furta ba...ban kuma san dalili ba, ko baki da ra'ayin sane ban sani ba..". Duban fuskar sa kawai take yi tamkar ance mata amsar maganar tasa na kwance saman fuskar sa ne. Saman idanun ta ya sumbata ta lumshe idanun sai dogayen eye lash dinta dake dan motsawa " Meyasa baki ta6a yi min magana akan karatun ki ba? Ko baki ra'ayi..?" " Kai nake jira inji kayi maganar ai..". " In kuma ban yi bafa?". Tace" Shikenan"? Hancin ta yaja, nifa ina so kiyi karatu ki zama likita kamar ni, Feefy na ta zama Barrister kamar ni itama m...sannan zaki haifa min sojoji da yawa inta ganin su ina jin dadi...". " Hmm" Kawai tace bata ce komai ba. " Amsar ki kenan..hmm?". " Toh ni me zance?" " Kice toh Insha Allah sai nace sun isa...kice kinji kin gani sai kin cika min burina kamar yadda kk jajirce kk ce kinji kin gani sai kin cika min burina na kasanewa tare da ke.." Da sauri taja hancin sa. " Sannu sarkin sharri..." Ta fa'da tana mai dan jin nawi gami da murmushi. Yace " Ba wani sharri...barni in fada gaskia..ni kadai nasan irin jajircewan da kk fa". Ita dai in ba sharri irinta Rayyan ba yaushe tace taji ta gani sai shi. Ranar sun sha hira sosai kafin sukayi bacci. Washegari kuwa sassafe ta danna 'kiran Marwa...bata same ta kan layin ba. Kira kusan uku babu respond...hankalin.ta sai ya kasa kwanciya. Shaheed ta 'kira yana 'dauka tace ina kwana Yayah..wai ina Marwa ne sam na kasa samun ta kan layin ta. " Bacci take Zaitoon sai dai ko zuwa anjima kadan". " Bacci kuma har yanzu, Marwa fa ba haka take ba Yayah...". " Kinsan in ki'da ya canza dole rawa ma zai canza, barta tayi bacci sister..anjima zan ha'da ku...". Alhamdulillah duk yadda 'yan uwan Marwa ke mata fata da buri samun sauyi sama da gidan ta na baya Alhamdulillah Adam bai bar burbushin da zai basu damar tunawa da baya har ace gara na baya ba. kowa sai san barka yake, ana fadin Allah yasa a 'dore haka nan, domin Marwa ta samu farin ciki da kwanciyar hankali. Soyayyar su suke zubawa gwanin birgewa. Ita kanta Zaitoon abin na birge ta sosai, duk da itama yanzu ba baya ba wajen kula da mijin ta...amma tafi kaunar ta kira waya taji Marwa ta kyalkyata daria fiye da komai..ji take duk damuwar ta ta yaye tass..a kullum burinta shine taji Marwa cikin farin ciki. A hankali cikin ta ke 'kara girma dan a halin yanzu wata bakwai kenan cikin amma inka gansa bakace ya kai hakan ba, sai dai ya hura ta tako ina, kuma babu abinda ya canza mata abu guda ne kawai bata so shine kifi..amma normal take cikin bai takurata ta kowacce fanni ba. Tuntuni aka dawo da Mufeeda wajen ta, domin Ammi tace gidan zai na mata shiru tunda shi Rayyan ba mai zama bane, amma tana tunanin hidima da Mufee ga kuma ciki ma. Hakan yasa ta ha'do su da 'daya daga cikin masu aikin mai 'dan madaidaitan shekaru kuma wacce tasan sun riga sun sha'ku. Batun makarantar ta kuma Ammi tace da zaran ta haihu zata fara shi. Hakan bai kawo ma Zaitoon matsalar komai ba domin ita ba mai shiga sabgar mutum bace kuma abu da yawa bata bari ta jira sai anyi mata tuni zata mi'ke ta aiwatar sai 'dan abinda ba a rasa ba. Mufee yanzu an girma baki ya fito sosai surutu kuwa sai abinda ya yi gaba. Kusan kullum sai sunyi waya da Antyn ta, ayi video call da sauran su idan ta dawo School. Marwa kam ta murmure abinta da ka ganta kasan ta samu kwanciyar hankali. wata uku da auren su Adam ya kawo ta da kansa suka gaida su Ammi da sauran yan uwa kwanan su 'daya suka koma ai kuwa tun lokacin Zaitoon ke faman tsokanar ta wai bata yadda da ita ba. " Za ma kiyi ki gaji ne yan mata...ni babu wani abinda nake da shi, sai kace ke..". Duk da maganar nayi mata wani iri amma haka take chigaba da tsokanar ta..amma inta kebe banda tunani babu abinda take yi. Wai dagaske ashe itace zata haihu, shine da farko Rayyan yace mata shine ba ita ba...." banda shirmen ki Zaitoon ina kk taba jin namiji ya haihu". Wata zuciar tata ta ankarar da ita.. a lokacin duk tunanin hakan bai zo mata ba ta amince da maganar sa sai daga bata ta sake tabbatar da cewa lallai shirmen ta ya kai intaha. Ita bakomai yake bata tsoro ga haihuwa ba sai yadda taga Mahaifiyar Mufeeda, abin idan ta tuna yakan bata tsoro. Domin Rayyan tun bai fahimta ba har yanzu ya fahimci manufar tsoron nata ya kuwa yi mata nasiha sosai, ya nuna mata bambancin zanen 'kaddara, kowa da kalar tashi yake tafe, ba duk Allah ya halicce mu da 'kaddara iri guda ba kamar yadda bai yo mu da kalar fata, hali da zucia iri daya ba. Ba lallai bane dan abu ya sami wanin ka kai ma kayi tunanin zai iya samun ka. Da irin nasihun nan ya ci galaba akanta ta fawwalawa Allah komai. A halin yanzu fata da burinta kawai shine Allah ya sauke ta lafia sai kuma tsananin son ganin Innar ta da take. ***** " Ki cigaba da 'daga min hnkl kiga ko hkn zai baki nasara...zancen zuwa ko'ina ai ba tun yau na sanar mk babu shi ba, na soke ba yanzu ba kin manta hk nace...?" Ya 'kare maganar da zuba mata idanun sa masu matukar tasiri a zuciyar ta. Kasake tayi tana kallon sa itama, dagasken kuma yanzu hawaye ke sau'ko mata bb 'kakkautawa. Bata san cewa la66an ta sun motsa har ta jefeshi da tambayar da ke cikin zuciyar ta ba sai lkcn da taji cikkakkiyar amsa daga bakin sa. " Kin san bana magana biyu Precious.. pls ki bar zancen nan ba yanzu ba...". A iya sanin ta Rayyan ba ya son ganin ko kwayar zarra na hawayen ta musanman na bakin ciki, amma meyasa yau 'din yy mata banza ya manna mata hauka har hk. Tashi tayi kawai batare da ta sake tanka shi ba ta fice fuu ranta na sake yi mata 'kunci. Rayyan sai yy 'yar murmushi cikin ransa yk jinjina rigima irin tata, wani lkc in tayi abu ko Mufee ma albarka. Bayaga hk taya take tunanin zai 'kara barin iyalin sa 'daukan wancan hanyar with that same yanayi? Sam abu ne mai wahala ya iya barinta tafia cikin wanna halin...zasu je amma ba yanzu ba..yau kam kici kukan ki ki more yan mata". Maganan sukayi da Marwa ashe ita kuma ta labartawa Ammi. Tana zaune sai ganin 'kiran Ammi tayi nan take bata baki da ban hakuri akan ta bari ta haihu tukunna, ta daina 'daga hankalin ta, ai kamar yanzu ne zata je, amma ta tabbatar duk yadda zata kai ga 'daga hankalin Rayyan bazai bari taje a wannan yanayin ba, ba kuma wai dan bai san 'kaddara bane a a kawai bazai samu nutsuwa bane koda ya barsu tafiyar sannan zai ri'ka tuna baya. Gashi ma doguwan tafiya ce babu dadi...". Tace" bakomai Ammi...nima ban matsa ba..kawai dai..". " Nasani Zaitoon..ai nasan halin ki, ki 'kara hakuri kinji, kuma kar ki riqa biyewa fushin Rayyan har kike sawa aranki irin na baya, kinsan shi zafin rai gare sa amma yana da sanyin hali a mafi rinjayen lokuta". " Hakane Ammi.. Nagode sosai" . " Bakomai 'diyata...Allah ya albarka ce ku baki daya..." " Ameen Yah Allah". " Agaida min waccen yar jaridan idan ta dawo" Suka yi daria atare. Zaitoon bata sake tada maganar ga kowa ba hatta shi Rayyan din. Da kansa sai da yayi mamaki. Haka kuma yadda take kulawa da shi da bukatun sa abin ba karamin birge sa yake yi ba..ya kuma kara dawwamar da kaunar ta cikin ransa. Shi fa har kullum ya kan zauna ya ta tunanin me zai yiwa yarinyar nan ne ya biya ta abinda ta yi masa, ta bashi 'diya akaro na farko domin bisa taimkon ta ne Mufee ta rayu, ta kula da shi a lokacin da shi kansa bai san waye shi ba, ta bashi farin ciki, ta zauna da shi ta jure dukkan damuwa da bukatun sa sannan gashi tana shirin bashi kyautan wani diya ko 'dan abinda yafi muradi a ahalin yanzu. Hakika ita din wata ni'ima ce ga rayuwar sa da bazai taba iya raba zuciyar sa da begen ta ba. Rayuwa na tafia al'amura na tafia musu normal ko ta ina farin ciki ke wanzuwa, hakika bayan wuya akwai ni'imar Allah idan akayi hakuri, ayau ga Zaitoon da yaron ta santalele da shi wanda yaci sunan mahaifin Rayyan Wato Muhammad Sa'ad ita kanta ayadda haihuwar tazo mata abin ya bata mamaki. Hakika Allah gwanin baiwa ne da hikimomi. Sosai take godewa Allah idan ta dubi yaron nan, wai ita ta haife shi. Haka ta hada su da Mufee ta rike abinta tsab. Sunje gida bayan ta haihu suka yi kusan wata biyu sannan suka dawo gida. Da yake Marwa bata zo sunan Muhammad ba wai bata da lafia ashe ashe wata 'karuwar suka samu. Dan kuwa Muhammad nada wata takwas Marwa ta dire musu santaleleliyar 'diya kyakkyawa da ita...Yarinya taci sunan Zaitoon dan Adam cikin ransa yayi al'kawarin sai yawa 'yar 'kanwar nan tasa takwara..ya kuwa cika burin sa cikin yarda da amincewar ubangiji. Abin ya yiwa Zaitoon da kowa ma dadi, da'din da'dawa ma Shaheed ya hana a 6oye mata suna..little Zaitoon ake kiran ta wasu kuma suce little Zee. A hankali Little Zee yabi yarinyar dole ya kyale su. Tuni Zaitoon ta fara makarantar ta, domin SS2 ta fara tana kaiwa karshen shekarar kuwa ta zana waec ta cigaba da karatu. Tuntuni kuma take wa Rayyan magana akan Arfan amma yaki bata hadin kai kan maganar, bawai dan yana jin haushi ko ya tsani yaron ba, kawai baya son wata harka ta sske hada sa da Amra ne sam..shiyasa yake sharewa. Kuma yasan Arfan bazai ta6a neman abu ya rasa ba tunda yasan waye mahaifin Amra kuma yasan karkashin sa suke. Dai- dai da rana guda bai ta6a zuwa duba yaron ko kuma neman jin ya yake ba, kwatsam bayan haihuwar Marwa labari ya iske su cewar Allah ya kar6i ran Arfan sakamakon wata yar gajeruwar rashin lafiya da yayi. Mutuwar ta dokesu baki dayan su, domin duk sun san basu kyauta ba yadda sukayi watsi da lamuran sa, basu yi kasa a gwiwa ba suke je gaisuwa Ammi da mukarraban ta amma Rayyan bai yadda Zaitoon ta bisu ba..haka shima bai je ba. Sai daga baya ya kira mummyn Amra yayi mata ta'aziya. Ranar da Amra taga su Ammi ba 'karamin kukan nadama ta sha ba, duk da kuwa ta jima da yin nadaman amma ganin su sai ya dawo mata da komai sabo, a duk lkcn da idanun ta zasu kalli wani ko wata cikin ahalin Rayyan bakinta baya iya rike neman afuwar ta kamar yadda zuciyar bazai taba iya danne damuwar ta batare da ta bayyana shi ba. Ammi tayi mata nasiha sosai itama haka suka baro gidan jikin kowa yayi sanyi. Rayuwa kenan. Amra duk ta lalace tayi duhu kamar ba ita ba. Ita kuma Iyami rashin lpy take sosai, sai an daga sai an kwantar, yayin da lafia ingantacciya ta samu ga Abban su Zaitoon tamkar ba shi ba. Komai na tafia masa normal ayanzu, sai ci mai kyau yasha mai kyau ya kishingida bisa lafiyayyan shimfida baya da matsalar komai. Domin Allah ya sanyawa yaran sa albarka sun kuma tallafa wa rayuwar sa. Shiyasa a kullum yake faman sanya musu albarka, haka cikin kowacce sallar sa addu'ar sa gare su baya taba gajiyawa. Iyami anje asbiti kusan sati hudu abu babu cigaba hakan yasa likitoci suka sallamo su da shawaran su koma gida a nema mata maganin hausa. Jiki dai yaki dadi, a kullum abinda zai bullo daban dana gobe. Ga idanun ta rass zataji zata gani amma babu motsi babu tankawa. Tana son yin magana akan abu da yawa amma babu dama, haushin hakan in ya cika ta sai kaga tana zubda hawaye. Kwanakin talatin da uku kwance a gida ranar wata laraba aka wayi gari bata numfashi. Kwanan ta ya kare, duk wani abu da aka shuka an tafi an barshi nan dunia babu amfani, an tafi can gidan gaskia gidan girbe munana da kyawawan ayyuka. Sau fatan Allah ya jikan musulmi ya kyautata namu karshen idan yazo. Bayan rasuwar Iyami da wasu watanni rana guda kawai kwatsam Zaitoon na zaune sai ji tayi an saka wa Bello da Khausar rana wata uku kacal masu zuwa abin yai mata bazata. Ko da ta nemi jin ta bakin Khausar dariya kawai tayi mata. " Khausar wai ina Babaji?" " Yana nan Adda..Allah bai sa da shi za'a yi ba ya musanya min da wannan". Fatan alkhairi Zaitoon tayi mata da fatan Allah ya nuna musu lkc. Hakika tafi kowa farin ciki da faruwar wannan lamari. Bello dan uwan ta ne kamar yadda Khausar take yar uwar ta ta jini. Ita kam me zata ce da ubangiji idan ba godia ba. Rayuwar Marwan ta a gidan Shaheed kadai ya ishe ta dawwama cikin farin ciki sai ga wani karin abin farin cikin ma. Daddy 'karami yana gudun sa ko'ina yanzu dan ko School Zaitoon ba zuwa da shi take ba, Mufee da na da shekara biyar da haihuwa yanzu tana kuma kokarin shiga Nursery 3...amma shagwaban Mufee babu abinda ya canza har yanzu. Rayyan ne ma mai taka musu birki, domin sau da dama ajiye masa Daddyn sa ake agefe a dauki Mufee a rungume har sai tayi bacci...wani sa'in kuma tace sam Zaitoon take so ta goya ta...haka nan zaka dauke ta ta goya abinta. Rayyan abin na bashi haushi, saukin daya ma shi Daddy karami hakurarre ne, baki data ya amshe girman ya bar Mufee da shagwaba. ko bacci suke Mufee zaka gani rungume da Zaitoon shi Dady na gefe yana bacci ko wajen mai aiki. Da abin ya ishi Rayyan ne ya tarkata kayan ta kaf yasa akaita gidan Ammi wai ankaita hutun shekara. Kamar wasa tun Zaitoon na ganin kamar wasa har tazo ta saduda ganin fa dagaske yake, yace abin naku hadda shiga hakki ai, bacin ni na hakura an tauye ni abaya sannan babana ba za'a barshi ba sai an tauye shi....yace daga can gidan Ammi inta gama shekarar can gidan Anty za'a mika ta..daga nan sai Bauchi sai wajen Innani, sai kuma Maiduguri..Mufeeda tabar zama gaban ta kenan har sai ta girma ta bar wannan iskancin shagwaban. Yace Dama Raihana ma tace tana so ta dauke ta dan aikin mijin ta ya koma Italy, so basu ita zai yi su tafi can kowa ma ya huta. " Toh kuma makarantar ta fa.". Yace" A hakan zatayi, ba Affan ma na School ba, ko ina take zata karatu ai". " Ni dai dan Allah kayi hakuri adawo min da yarinya ta, wlh zan daina goya ta zan daina daukan ta ma kwatakwata..". Ta fada tana share 'kwalla. " Yace sai kuma kiyi..". Fita yayi ya barta a dakin taci kukan ta koshi...dan tasan mawuyaci ne ya janye abinda ya fada. Tammat bi Hamdallah. Salmerh😍