❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️ *BEELAL* 💦💦💦💦💦💦💦 *FCW* 💛 Book 2 Page1️⃣➡️2️⃣ *LAGOS* Tun da suka sauka a garin Lagos a tasha, Idrisu ke tsangwamar Beelal saboda wai ba ya sauri kwata-kwata bai duba larurar da ke tare da yaron ba, ta nakasarar, da ke tare da shi ba, haka kawai yake jan hannunsa ƙiii suna keta mutanen da ke cikin tashar motar da aka saukesu. Babu wani wanda ya lura da su kowa sabgar gabansa yake, Beelal kwa banda hawaye babu abin da ke zarya a fuskarsa ga wata azababbiyar yunwa da yake ji. Sai da ya samu machine suka hau Beelal ɗin ne ya fara hawa sai shi ma ya hau bayansa haka suka zo unguwar da Idrisu ke zaune. A ƙofar wani shago da ke wurin aka ajiyesu ya fitar da kuɗin mai machine ɗin ya biya. " Kai gurgun mage ka ga inda nake kwana dan haka ba wai a kyauta nake zaune a ciki ba biya nake dan komai da kake gani a Lagos na kuɗi ne ba kamar can gida bane inda muka baro fa, a can ne wani ma zai iya bada kyautar shago dan kawai mutane su zauna a sadaka wasu har gida suna iya bawa mutane su zauna kyauta" Cewar Idrisu yana yiwa Beelal wani kallo. "To Baba zan ... "Ko da wasa kar in ƙara jin ka kirani da wannan sunan dan ni tuni na daɗe da barwa uwarka Fatima kai, dan haka zamu zauna ne a nan a matsayin masu taimakon juna idan ka taimakawa kan ka ka nemo kuɗi yadda ya kamata to zaka samu abinci idan kuma baka nemo ba to ka kwana da sanin da yunwa za kake zama" Hawaye sun riga buɗewar bakin Beelal zubowa, saboda ganin irin rayuwar da zai gudanar mai cike da uƙuba a birnin Lagos, an rabo shi da wajen mahaifiyarsa mai so da ƙaunarsa wacce duk runtsi duk wuya sai ta nemo masa abin da zai ci ko da a ce ita ɗin ba za ta samu ta ci ba to ta gwammace ta samo masa idan ya ci sai ta yi farinciki. An kawo shi inda bai san kowa ba sai wanda ya kawo shi wanda ke ƙyamatarsa ba ya ko ƙaunar ya kira shi da sunan mahaifi saboda nakasar da Allah ya halicce shi da ita. "Za kake nemowar kuwa? Duk da wasu na cewa wai zafin nema baya kawo samu, to ni dai na ƙaryata haka, sai dai in mutum bai dage ba, dan da ya dage dole ya nemo, sannan ka bar zubo min da wannan hawayen munafurcin dan taimakon ka na yi kar kasa wasu su zargi satoka na yi, to shin ma in ba barar ba menene ya dace da mutum irinka, mai irin suffarka, mai ɗauke da nakasa kamar kai" Ya faɗa yana hararar Beelal. Hannu ya sanya ya goge hawayen duk da ba wai kukan nasa ya tsaya bane, kai kawai ya sunkuyar yana jin ba daɗi har cikin rai da zuciyarsa, dan baya so ake kiransa da nakasashshe duk da yana ɗauke da nakasa in aka faɗa masa dan a muzanta masa sosai yake muzanta, sosai yake jin babu daɗi a cikin ransa dan yana gani kamar mutane na ganin shi ya yi kansa a haka suna manta cewar Allah ke halittar mutum a yadda ya so a kuma lokacin da ya so. "Wuce mu je ai dai ka ji abin da na ce in kuma ka ƙi to jiki magayi, dan ni idan ma baka kula ba ko a jikina wai an tsikari kakkausa" Cewar Idrisu yana yin gaba ya nufi shagon, cikin sanyin jiki Beelal ya bi bayansa tunanin mahaifiyarsa cike da zuciyarsa yana tuna irin tsantsar kulawarta garesa dan duk abin da uwa take yiwa yaro yana nan zaune daram da ƙwaƙwalwarsa in ma mai kyau ko akasin haka, Allah ba mu ikon tarbiyantar da ƴaƴanmu kamar yadda ya ɗora mana nauyin hakan amin .Suna zuwa Idrisu ya tura ƙofar da take a kare. "Wane ɗan iskan ne zai turo ƙofa babu neman izini" Aka faɗi hakan daga cikin shagon tare da ɗura wani zagi mai gunna. "Kai dalla can ni ne, kar ni ma ka harzuƙa ni yanzun nan mu hau sama mu faɗo" Shi ma Idrisun ya faɗa yana lailayo nasa ashar ɗin, tare da bankaɗe labulen shagon ya shige ko sallama babu. "A ah shegen ashe kai ne" Cewar Imran da ke ringishe a kan katifa yana zuƙar sigari. "Dallah can wai har ni kake yiwa wani eya ne" Cewar Idrisu yana miƙa wa Imran hannu ya bashi sigarin da yake zuƙa shi ma ya kai bakinsa sai da ya mata zuƙa biyu ya fesar sannan ya zauna a gefen katifar. "Ai na ɗauka wani ne, da ban zai kawo min raini" "Kai dai ka sani to ya ake ciki ne" "Kai dai bari Baaba wallahi al'amura duk sun caɓe babu wata hanyar samun kuɗi yanzu, ni machine ɗin ma da nake ja na mayarwa mai shi saboda sai in wuni ina yawo amma ba na samun fasinja wai sai a yi ta cewa a buge nake" Cewar Imran yana kallon Idrisu. "Da gaskiyar su ai" "Au haka ma za ka ce" "To ai kai ɗin ne ya za a yi ka shayu ka yi tatul kuma ka ce wai za ka samu fasinja, tsakani da Allah waye zai yarda ya hau bayan bugagge wataƙila ma duk kana warin sholi" "Dalla can rufe mana baki, ai duk kanwar dai ja ce daga ni har kai waye gwara, kai ma warin sholishon ai ko jikinka ba ya bari" Cewar Imran yana kai wa Idrisu wani uban duka a baya. "Kai maida wuƙar Malam na zo mana da hanyar samun kuɗi yanzu cikin sauƙi, duk da dai dama ba wai ba ma sakun kuɗin ba kawai dai suna ƙarewa ne a wajen siyan kayan maye da neman matan banza, amma dai yanzu ga wata haja da nake ganin za mu buɗe... "Kai rufa ni ka saya ni wallahi duk iskancina bai kai nan ba" Imran ya katse Idrisu yana wani harararsa. "Kamar ya? Kai fa matsala gareka, ai ka bari na mutu ma kafin ka binne ni" "Haba Idrisu daga tafiya gida wajen bushashshiyar matarka ko za ka samo mana kuɗaɗen da kake zato yayarta ta kai mata, kuma kawai sai ka saro mana hodar iblis ka ce mu buɗe haja, son kulawa su yi ram da mu, azo ana A'i ina indo" Wata irin dariya Idrisu ya ƙyalƙyale da ita, yana nuna Imran da yatsa. "Ka fi kowa sanin ba na son rainin hankali" "Ai Baaba dole na yi dariya daga ambaton haja sai ka ce hodar iblis ce bari ka ga hajar da nake nufi, mai lasisi ce, kuma hajar mai jini ce" Cewar Idrisu yana buɗe murya ya shiga ƙwalawa Beelal kira da ya daka ta a ƙofar shagon bai shiga ba amma yana jiyo duk surutan su. "Kai gurgun mage, gurgun mage!!" Ya shiga ƙwala masa kira kamar wani makaho. "Na'am" Cewar Beelal ya shiga share hawayen fuskarsa. Sannan ya ja ƙafarsa marar lafiyar ya tunkari shagon gabansa na dukan tara-tara. "Gurgun mage kuma waye ka samu haka ko shi ne ka baiwa ajiyar hajar tamu da kake ta faɗa" Cewar Imran yana son jin amsar sa daga wajen Idrisu. "Assakamu alaikum" Cewar Beelal daga ƙofar shagon amma ko labulen bai ɗaga ba yana jiran sai ana amsa sallamar tasa an bashi izinin shiga sannan ya shiga, kamar yadda Mamarsa ta koya masa. "Kai ba zaka shigo ba" Idrisu ya faɗa yana kwararo wani uban ashariya. Labulen ya buɗe a hankali ya miƙa ƙafarsa cikin shago ransa cike da tsoro fal dan gabaɗaya ma sai ya ji yana matuƙar tsoron su. "Kai amma kai dai Allah wadaranka Idrisu, ya za ka kirawo mana almajiri bayan ka san mu kan mu muna da buƙatar abinci" "Kai dalla sakarai ni ne kake cewa Allah wadaraina, to sai dai Allah wadaranmu baki ɗaya saboda suk kanwar ja ce, to wannan da kake gani tun daga arewa na taho da shi kuma shi ne hajar da nake baka labari yanzu" "Kana da hankali kwa Idrisu wannan abin ne haja? Ko dai ka samu taɓi ne bayan barinka garin nan" "Na manta kan ka na kwakwa ne, gabaɗaya ya zama dusa ba ya ja ko kaɗan to bari na maka gwari-gwari, wannan ɗan gidan wannan matar ne wacce take zaune da sunan wai tana aurena, to yadda ka ganshin nan a haka ta haifeshi shi yasa na sallama mata shi, duk da ma ba wai na san ɗawainiyarsa daga shi har ita bane, sai dai wannan zuwan na yi tunani zai mana mugun amfani a garin nan shi yasa ma na sato shi ba tare da ta sani ba na taho da shi" "Ikon Allah na zaune ya faɗi, kai yanzu wannan in banda dai wahala mai ka ɗakko mana yaro hannu a ƙame ƙafa a shantale to ma uban me wannan zai mana" Imran ya faɗa yana aikawa Beelal da mugun kallo dan shi gabaɗaya ma kallo ɗaya ya yiwa yaron ya ji ya tsane shi, ganinsa ma yake kamar aljani. "Maida wuƙar tukunna in faɗa maka manufata a taƙaice, daɗina da kai baka cin ribar zance, to wannan yaron na ɗakko shi ne dan yake bara yana samo mana abubuwan da muke buƙata, kama daga abinci kuɗi da dai sauransu" Idrisu ya faɗa yana wani murmushi tare da wani karkaɗa kai na jin daɗi. "Shegen ina yinka nawan wallahi ai kai fa kan ka na ja ba kamar nawan ba amma in jika, gaskiya ka mana babban kamun da za mu daɗe muna mora tabbas wannan duk inda ya shiga zai samo sadaka, baka ma ganin yadda tsofaffi wanda ma basu da nakasa suke samo sadaka irin waɗan da ke zuwa neman kuɗi daga arewa da sunan bara, ka ga tsohuwa ta takarkare tana zabga waƙar bara ƴar jagora tana mata amshi kuma fa ita ba gurguwa ba, ba makauniya ba babu wani ɓangare na jikinta da yake a nakashe amma kuma sai ta maida hakan hanyar samun kuɗi, kuma wallahi sosai suke samun kuɗi, ka gansu idan suka tashi tafiya gida arewa sun koma da maƙudan kuɗin da ba lallai ne wanda suka zo nan ɗin da sunan neman kuɗi ba su samu ko da rabin hakan ne" Imran ya kai ƙarshen maganar yana kallon Idrisu. " Kai ai sai yanzu nake jin mugun daɗi da na taho da yaron nan, dan na san tsuntsunmu zai kama tarko" "Sosai ma kuwa" "Kai gurgun mage ƙaraso ka zo nan" Idrisu ya faɗa yana kallon Beelal da ya takure daga wajen ƙofa ya ƙi shigowa cikin shagon. Haka ya janyo ƙafarsa ya ƙaraso wurinsu, ga ɗakin ban da warim sigari baka jin komai. "Kai idan za ka saki jikinka ka saki jiki, dan nan fa shi ne garin da za ka cigaba da rayuwa a cikinsa, idan kuma ba haka ba za mu ladabtar da kai ta ƙarfi da yaji" Imran ya faɗa yana yiwa Beelal wani kallo na tsana da tsangwama. Beelal dai kansa a sunkuye yana durƙushe a gabansu. "Ka ɗago ka bamu amsa mu ba ma son wannan munfurcin sadda kan irin na uwaka" Idrisu ya faɗa cikin ɓacin rai. "Zan yi Bab... "Ba?" Cewar Idrisu yana kallon Beelal da mamaki, dan ya san dai ɗazun nan ya gargaɗesa a kan kiransa da suna Baba . "Gaskiya da sake abokina ya ma za a yi wannan abin yake kiranka da Baba son ya ja ake kallon mu ai wannan abin kunya ne wallahi" Cewar Imran "Ni ban san ya zan ke kiranka ba, ba zan iya faɗar sunanka ba" Cewar Beelal yana hawaye ganin duk sun tsare shi da ido. "To haɗi garemu dan ka kirani da sunana ni fa na faɗa maka na janye dukkan alaƙa d dangantakar tsakani na da kai" Cewar Idrisu. "Kawai yake ce maka Alhaji, ko da wani ya ji ya kiraka da hakan zai ɗauka taimakonsa yake kuma wannan suna ne mai ɗaga daraja kawai yake kiranka da haka" Imran ya faɗa yana kallon Idrisu. "Amma na ji daɗi da ka samo min wannan suna to kuwa ba ni kaɗai zai ke faɗawa ba kai ma haka zai ke kiranka" Cewar Idrisu yana murmushi. "Kai tanƙwashen kifi faɗi mu ji, dan yadda ƙafa da hannun nan naka suka sha kwana sai suka min kama da kifi tanƙwashe" Imran ya ce yana kallon Beelal. "Alhaji" Cewar Beelal ƙwalla na taruwa a cikin idanunsa. Hahahahaha gabaɗaya suka ƙyalƙyale da wata irin dariya kamar mahaukata sabon kamu. MMN AFRAH 09030283375 ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️ *BEELAL* 💦💦💦💦💦💦 NA MAMAN AFRAH Book 2 *FCW*💛 Page3️⃣➡️4️⃣ "Yanzu ka san me za a yi abokina?" Imran ya faɗa yana kallon Idrisu. "Sai ka faɗa" "Ka san akwai keken guragu a cikin wancan rufeffen shagon na wannan gurgun da suke zaune a cikin shagon da ya mutu, sauran ma suka fasa hayar shagon to tun da ba wai so ake ba shi za mu ɗakko shi wannan sai yake hawa" "Kamar ya yake hawa, bayan yana tafiya gani nake duk inda zai je kafin ya je a keken ya je a ƙafa, kuma ma so kake ka sauƙaƙa masa tafiyar ya zama yana yin barar yana samowa a ɓagas ba zai san zafin nema ba kenan? Ai gwara dai yake yawo da ƙafafunsa duk da dai ba wata tafiyar kirki yake ba sai ka je wuri sau goma ka dawo ka tarar da shi yana hanya bai je ba" "Haba ka gane mana ba wai dan ya samu hutu za a bashi keken ba ka san yanzu idan aka ganshi zaune a keken kuma hannu da ƙafa a lanƙwashe za a ɗauka gurgu ne a haka sai ya fi samun sadaka, a kan a ce da ƙafarsa aka ganshi" "Shege Baaba wallahi kwanyarka na ja amma a wajen son samu fa" Idrisu ya faɗa yana baiwa Imran hannu suka kashe. "Wallahi nake faɗa maka ko kaɗan ni ma kawai jin maganar na yi ta sauka a kwanya ta ba tare da dogon nazari ko tunani ba na ce bari dai na faɗa maka tun da dai na san ai ni da kai bata ɓaci" "Ai tuni ma an gama yanzu je ka fito masa da keken ya hau ya fara fita tun yanzu ka san da zafi-zafi a kan daki ƙarfe" "Kai Idrisu wutar cikin naka ta yi yawa yanzu daga zuwanku kake cewa ya tafi bara ko hutawa baku yi ba kuma bai samu komai ya ci ba, kuma ma na ɗauka sai an ɗan nuna masa wajejen zuwa tun da ba inda ya sani kar ya je ya ɓata a shiga tara" Imran ya faɗa yana kallon Idrisu. "Kai ka jika da wani zance, to me ma za a bashi ya ci ai sai ya nemo mu ma za mu ci, kuma da kake cewa daga zuwanmu, zai fara fita to ma wai shin mai za a fasa mutuwa ko hisabi? Kuma zancen ɓata a shiga tara ai ko uku ba za mu shiga ba dan ya ɓata Allah raka taki gona gaba ta kaini gobarar titi na huta da yiwa gyatumarsa bayanin dalilin da ya sa na tafi da duk da dama ba wai tsoronta nake ba, shi idan ya ɓata sai na nuna ba ni ne na tafi da shi ba" "Ni fa ba wai rasa shi ne tarar da za mu shiga ba, to in dai zai ke samo mana kuma a rasa shi dole mu shiga tara tun da haryar samu ta toshe mana" " Kuma fa haka ne, amma yanzu idan ya hau keken mu za muke tafiya yana bin mu a baya sai mu kai shi inda za a fi samun sadaka muna daga gefe a tsaye kamar ba tare muje d shi ba idan muka ga ya tara mana abin da muke so sai mu dawo" Idris ya faɗa yana dariya. Shi dai Beelal yana nan durƙushe bai ce komai ba kansa sunkuye a ƙasa yana sauraren duk abin da suke cewa. "Bari na ɗakko masa keken" Imran ya faɗa yana miƙewa tsaye. "Zan yi a hakan ba sai da keken ba" Beelal ya faɗa cikin in'innarsa. "Kai dalla rufewa mutane baki, kai har wani zaɓi ne da kai, wato kai ma duk a yadda kaken nan a nakashe ta ko ina har kana ƙyamatar hawa keken guragu dan kar a kiraka gurgu ko?" Idrisu ya faɗa yana hararar Beelal da kansa ke sunkuye. "Ba haka bane Alhaji, ni da a ce ma bani da nakasa ba na jin zan ƙyamaci kowane irin halittar Allah kawai dai tun da Allah ya mini ni'imar samun ƙafa ina tafiya bai kamata in hau keken guragu ba, in ɓata ni'imar da Allah ya mini ta ƙafafu bayan ni ba gurgu bane saboda kawai in samu abin duniya sai na butulcewa baiwa da ni'imar da Allah ya mini" Ya faɗa cikin in'innarsa yana ɗago kansa a karo na farko ya sanya idanunsa cikin idanun Imran. Wani uban haushi ne ya turnuƙe Imran cikin zafin nama ya ɗaga hannu ya kaiwa fuskar Beelal wani gigitaccen mari, Beelal ma cikin sauri ya duƙar da kansa ƙasa, Imran ya mari iska, ganin iska ya mara bai samu fuskar Beelal ba daga Imran har Idrisu suka tsaya kallon -kallo da mamaki. "Kai har ni ka ɗaukewa kai na mari iska" Cewar Imran cikin ɓacin rai. "Ni ma mamakin da ya kasa barin raina kenan" Idrisu ya faɗa cikin mamaki. "Ai ban yi laifin da za a mare ni ba" Beelal ya faɗa cikin in'innarsa. "Lallai ma yaron nan, kai da kake a ƙarƙashinmu sai yadda muka yi da kai kana garin da baka da kowa baka da uwa ba uba babu dangin iya bare na Baba amma har kana da ƙarfin gwiwar butulcewa umarni ko tsallake abin da muka yi niyyar yi?" Imran ya faɗa yana wani zare idanu. "Bani da kowa amma ina da Allah, shi ke tare da bayinsa daɗi ko wuya, shi ne wanda baya gajiya da buƙatun bayinsa, shi ne yake bayarwa ya ƙara kuma yana tare da duk wanda bai manta da shi ba" Beelal ya faɗa hawaye na kwaranyo masa saboda gabaɗaya abin da yake faɗa daga ƙwalƙwalwarsa yake tahowa domin gabaɗaya kalaman Mamarsa ne wanda take faɗa mas suke zama daram a ƙwalƙwakwarsa. "Lallai gurgun mage ka ga makwancinmu wato har kai ma kana iya musayar yawu damu, a haka bakinka babu daɗi kana magana da in'inna har kana rufe idanu saboda in'innar amma a hakan kake faɗar ra'ayinka" Cewar Idrisu da mamaki fal a fuskarsa. Shi dai Beelal bai ƙara cewa komai ba. "Rabu da shi abokina da mu yake zancen, keke ne dai ko ba ya so sai ya hau dan shi da gurgun ni ban ga maraba ba" Imran ya faɗa yana fitowa daga shagon domin ɗakko keken a ɗaya rufaffen shagon. "Dan Allah Alhaji ka yi haƙuri ka ce kar ya ɗakko keken nan, ya kamata ɗan adam ya zama mai godiya ga ubangajinsa a duk yadda Allah ya haliccesa, Allah ya bani ƙafafu bai kamata nake yawo a keken da duk wanda ya ganni zai yi zaton bani da ƙafa ni gurgu ne, kuma in har a ƙafartawa ma nake iya rabona kawai zan samu a barar babu wanda zai haɗa min da rabon wani... "Kai dalla ka rufewa mutane baki waye sa'anka a cikinmu? Ko dan ka ga ana ɗaga maka ƙafa, to bari ka ji na faɗa maka kai baka isa ka sa mu yi abin da bamu yi niyya ba, sai shegen surutun tsiya, ga wa'azi kamar wani limami, kai ga wanda mahaifiyarka ke koya maka sanin Allah da sanin ya kamata" Idrisu ya katse shi cikin ɗaga murya. Shiru Beelal ya yi dan yadda Idrisu ya masa magana ya tsorata saboda da ƙarfi ya zafice shi dan haka sai ya ja bakinsa ya yi shiru. "Baaba na ɗakko keken nan fito ka gani, ko a san a bin yi ka san maganin abu a yi shi" Imran da ke can waje ya faɗa da ɗan ƙarfi. Haka Idrisu ya fito daga cikin shagon yana washe baki, ya baro Beelal a can ciki. "Kai gaskiya abokina ka iya bada shawara to ka ga wannan da babu shi ma sai mun nemo amma tun da gurgu ya bar wa ɗan uwansa gurgun mage gado ka ga mun huta da nema" Idrisu ya faɗa yana kallon tsohoh keken guragun da ya ya tsufa jikinsa duk tsatsa. "Eh mana, ai mu gaba ta kaimu gobarar titi, kai kana ina fito dalla ka zauna a ciki kamar wanda kake ganin dodanni" Imran ya faɗa yana kiran Beelal da bai fito daga shagon ba. "Ka fito da rarrafe saboda tsaro ba dan tsoro ba, dan yanzu idan ka fito da ƙafarka wani ɗan sa ido ya gani sai a gama gane lagonmu" Idrisu ya faɗa yana kallon shagon nasu yana jiran fitowar Beelal. A hankali Beelal ya sanya hannu ya share hawayensa, ya yi dibara ya miƙe ya tahowarsa a ƙafarsa ba tare da ya rarrafo ba kamar yadda aka buƙata. Ganinsa ya fito a tsaye sai Imran ya tafi da sauri ya je bayan Beelal ya sanya hannu ya hankaɗo Beelal, aikuwa Beelal ya tafi tagal -tagal sai kuwa ya faɗa a kan gwiwoyinsa aikuwa ya ji faɗuwar sosai wani zafi ya ziyarci gwiwoyinsa. "Ka min dai dai ai maganin marar kunya da rashin jin magama kenan" Idrisu ya faɗa yana kallon Imran. "Hasbunallahu wa ni'imal wakil, ya haka" Cewar Aminullah da ya ƙaraso wajen cikin sauri dan tun lokacin da ya shawo kwana ya hango Imran ya hankaɗa wani yaro da ya fito daga cikin shagonsu hakan ya sanya ya ƙaraso da sauri. "Kai ba fa da kai ake yi ba mu ba ma son shishigi da shiga shiri ba shanu" Idrisu ya faɗa yana hararar Aminullah. Aminulla kuwa ganin abin da suka yi da gangan ne sai kawai ya nufi wurin Beelal cikin tausayawa musamman ma da ya lura da larurar da ke tattare da yaron sai ya ji wani mugun tausayinsa ya mamaye masa zuciya. Cikin sauri da azama ya sanya hannu ya ɗaga yaron tsaye yana masa sannu tare da dudduba jikin Beelal ɗin dan ganin ko ya ji ciwo. Dan shi Aminullah duk tunaninsa ma yaron bara yake suka masa wannan wulaƙancin. "Kai fa wannan zaƙiyar da kake yiwa mutane, da shiga shirgin da ba naka ba, ba ka ji ba an ce mutum ya bar abin da babu ruwansa ba, amma kai kullum cikin kutsa kai cikin abin da bai shafe ka ba kake" Imran ya faɗa yana hararar Aminullah da ke riƙe da Beelal. "Ko ma dai me zaku faɗa ku faɗa amma dai abin da kuka yi baku kyauta ba in sadakar ce ba za ku bashi ba sai ku ce ya tafi amma ba wai ku masa wannan kora da halin ba" Aminullah ya faɗa shi ma yana kafe su da ido. "To kai an faɗa maka kowa ma irinka ne, ko kuma an ce maka bara yake, to wannan da kake gani tun daga arewa na taho da shi kudu saboda yake bara yana samo mini kuɗi, dan haka babu ruwanka ka sake shi ya zo ya hau kekensa" Idrisu ya faɗa yana kallon Aminullah. Baki sake Aminulla yake kallonsu yana rayawa a ransa wace uwa ce wanann marar dogon tunani za ta baiwa mutum kamar Idrisu yaro kamar wannan da sunan a zo da shi ya yi bara, Idrisu da ko ciwon kansa bai sani ba ta yaya har haka za ta faru. "Sake shi to tunda ka ji kanun labaran sai ka kiyaye shiga abin da baka ciki wanda babu ruwanka" Imran ya ce yana wani ɗaga kai sama. "Amma duk da kun ce ba ruwana ya za a yi ku ɗakko wannan tsohon keken ku ce ya hau bayan kuma keken ya riga da tsufa duk ya yi tsatsa, bayan ma yana da ƙafarsa ya za a yi ya hau keken guragu" Aminullah ya faɗa yana kallon fuskar Beelal cike da tausayawa dan ya san ba da son ran yaron ba. Da sauri Imran ya sanya hannu ya fisgi Beelal daga hannun Aminullah yana aikawa Aminullah ɗin wata harara tare da Beelal ɗin. "Ka rainawa mutane hankali har ka tsaya ja in ja damu, shin ma ina ruwanka da mu ne? Menene alaƙarmu da kai, ko muna da wani haɗi ne da kai bayan na addinin muslunci, da kuma haɗin kama hayar shago ɗaya? Dan haka ka fita idanunmu mu rufe in har kana son zama lafiya" MMN AFRAH 09030283375 ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️ *BEELAL* 💦💦💦💦💦💦 NA MAMAN AFRAH Book 2 *FCW*💛 Page 5️⃣➡️6️⃣ Aminullah yana ji yana gani Imran ya kama Beelal ɗin ƙiii ko tsayawa babu, har sai da ya dangana shi da kan ƙarfen keken, dan wurin zaman ko katifa babu ta cire sai ƙarfen kawai, yana zaunar shi tare da yiwa Beelal ɗin mugun kallo. "Tuƙa mu tafi" Idrisu ya faɗa cikin zafin rai, su duka daga Imran ɗin har Idrisun sai muzurai suke kamar waɗanda suka yiwa sarki ƙarya. "Ban iya ba wallahi ko taɓa hawa ban yi ba" Beelal ya faɗa kamar zai fashe da kuka. "Banda rainin wayo ya ma za a yi ka ce wai baka iya tuƙa kekenku na nakasassu ba, ai sabo da ku aka ƙeroshi dan haka yanzu ya zama dole ka tuƙa ko baka so" Cewar Imran yana kallon Beelal. "Bari dai ka ga ƙarshen rainin wayo dan ya ɓata mana lokaci ne yasa yake ja mana rai" Cewar Idrisu yana fisgar keken da uban ƙarfi suka fara tafiya, Imran na bin bayansu, Aminullah da ke shirin yin magana ganin sun ja keken sai ya saki baki yake bin su da kallo, yana ɗaga hannu kamar mai neman taimako. "Ku bishi a hankali dan Allah" Cewar Aminullah cikin ɗaga murya amma ko sauraronsa ba su yi ba. Beelal kuwa hannu biyu ya sanya ya riƙe wajen tuƙin ganin irin gudun gangancin da Idrisu yake yi da keken ƙura sai tashi take. Sai da suka ɗan yi tafiya mai ɗan tazara Idrisu ya saki keken ba tare da ya tsayar da keken ba, da sauri Beelal ya sauke ƙafarsa mai lafiyar ya taka ƙasa hakan sai ya zamana kamar ya taka birki ne, dan yadda Idrisu ya saki keken da ƙarfi kaɗan ya rage Beelal ya hantsila daga shi har keken. "Kai ka fara tuƙawa da kan ka ka ga mun baro waccan lungun da shagonmu yake mun fito cikin jama'a tun daga nan har zuwa ko ina ma na unguwar nan kasuwa ce dan haka yanzu za ka fara tuƙawa ka yi gaba mu kuma mu biyo ka a baya kuma kar ka nuna ma ka san mu, duk da ba lallai wani ya hango jirginmu ba, kuma ba lallai wani ya lura cewa mun sanka ba saboda babu yadda za a yi wani ya kalleka ya haɗamu da kai" Cewar Idrisu yana hararar Beelal. "Ka ga duk wannan faɗin wajen duk wurin ma kasuwa ce amma kar ka shiga can ciki ka je ka ɓata kake bararka a iya nan, ungo nan, duk wani abu na ci kake sakawa a nan kafin a samo maka robar da za kake sakawa, kuɗi kuma kake sakawa a acikin aljihunka idan sun taru muna gefe za mu karɓa sai ka cigaba da barato wani" Imran ya faɗa yana miƙa masa wata ledar yaluwa mai sarsar da ya fito da ita a aljihunsa. "To" Cewar Beelal yana haɗa hannayensa wuri ɗaya ya sanya hannun biyu ya karɓi ledar, dan Mamarsa ta koya masa cewa ba a karɓar abu da hannun hagu ko kuma a karɓa da hannu ɗaya sai dai duk abin da mutum zai karɓa ya sanya hannu biyu tare da ɗan rusunawa saboda hakan shi ne cikar tarbiya. "Ka taimaki kan ka" Idrisu ya faɗa yana faɗaɗa murmushinsa dan har ya hango sun fara samun kuɗi. "Me zan ke cewa barar, mai zan ke faɗa idan ina barar" Cewar Beelal cikin sanyin murya. "Ka ji wani rainin wayo kuma yanzu kai abin da kuke faɗa ne baka sani ba, ai a gani na nakasashshe babu wanda zai koya masa yadda zai yi bara tun da dan ita aka halicceshi a nakashe" Cewar Imran yana wani yatsina fuska. "Allah ya haliccemu ne dan mu bauta masa kuma Allah ya hore min rai da lafiya da sassan jiki dai dai gwargwadon yadda zan nemi ilimi in nemi halal ɗin ba wai in yi bara ba, Allah ba ya son roƙo ma" "Inyeee to wallahi wannan darasin sai dai ko ka bari sai ranar da ka koma gun wacce ta koya maka wato mahaifiyarka ka faɗa mata hakan idan da rabon zaku sake haɗuwa ma kenan, idan kuna da rabon sake sanya juna a idanu dan mu wannan karatun mun daɗe da saninsa" Idrisu ya faɗa yana hankaɗa keken da Beelal ɗin ke ka. Daddagewa Beelal ya yi ya riƙe kan keken, ya cije leɓensa na ƙasa da haƙorinsa, ya shiga ƙoƙarin tuƙa keken cikin iko da hikimar ubangiji sai gashi ya tuƙa keken. "Ɗan rainin wayo ashe ma ya iya ya sa kake wahalar turashi" Cewar Imran. "Rabu da shi mana in ma bai iya ba da ya ji uwar bari ai ya tuƙa dole ne ai ya nemo mana abin da aka kawo shi takanas domin ya yi wato bara" Idrisu ya faɗa yana dariya idanunsa na hango Beelal na jan keken dakyar. "Hahahaha ai dole ne a sha man amarya ko da taƙi" Imran ya faɗa. *ƘAUYEN MAZARI* ~FATIMA~ Cikin bacci ta fara jiyo ana kiran sallar asuba, dan haka a hankali ta buɗe idanunta tana yamutsa fuska alamar mai bacci. Hannu ta kai gefenta domin taɓo Beelal sai ta ji baya nan, hakan ya sanya ta ɗauka ko ya gangara gefe guda ne da yake har lokacin akwai sauran duhu haske bai riga da ya fara fitowa ba. Hannu ta kai inda take ajiye fitilar ta touchlight ta ɗauko, kunnawa ta yi ta haska amma abin mamaki haske na gauraye ɗakib sai ta ga wayam babu Beelal a inda yake kwance, bata kawo komai a ranta ba hakan ya sanya ta yi zaton ko fitsari ya fita duk da ta yi mamakin fitarsa fitsarin ba tare da ya tasheta ta raka shi ba ko kuma ya karɓi fitila ba. Sai kawai ta danganta hakan da kawaici da sanin ya kamata irin na Beelal ta tabbata wataƙila dan ya ga tana bacci ya ƙi tashin ta ya gwammace ya fita fitsarin a duhu. Sai lokacin ta shiga karanto addu'ar tashi daga bacci (Alhamdulillahil lazi ahyana ba'adama amatana wa ilaihin nushur) Sannan ta miƙe ta fito daga ɗakin ganin shimfiɗar Idrisu ba ya kwance sai ta yi mamaki kar dai tashi ya yi dan zuwa ya yi jam'i a masallaci mutumin da ko kaɗan ibada bata dame shi ba shi dama jam'i ma ba zuwa yake ba a gida yake sallarsa shi ma ba a kan lokacin ba. Hamdala ta shiga yi tana ganin dama kwana biyun nan da ya yi da dawo wa ya canja mata gabaɗaya ba kamar yadda ta saba ganinshi ba, ashe dai canjin har na ibada. Addu'a ta shiga yi a kan Allah ya ƙara shiryar da shi ya gane gaskiya ya daina zaluntarsu ita da Beelal. Tun tana tsaye tana jiran fitowar Beelal daga bayi har dai ta fara haska fitilar daga inda take tana haska bayin tana karkaɗa fitilar tare da kiran sunan Beelal ɗin dan yanzu ta fara danganta shiga bayin nasa da kashi, dan tana ganin jimawar tashi ta zarce fitsari. "Beelal ka kula ka fito mana mu yi sallar kar lokaci ya ƙure, kuma ma ka je ka shiga bayi babu fitila ai da ka tashe ni na baka fitilar" Ta faɗa da ɗan ƙarfi yadda zai ji. Jin shiru sai kawai ta ɗan ji gabanta ya faɗi amma bata kawo komai a ranta ba. Takalmi ta sanya ta nufi bayin cikin ɗaurewar kai dan ta san dai Beelal ko gyaran murya da ya mata, amma kuma shirun da ta ji sai ta fara tunani ko dai zamewa ya yi a bayin ya faɗi, wannan tunanin sai ya sanya gabanta mummunan bugawa a nan take sai ta ƙara sauri dan zuwa ta ga mai ke wakana. Addu'ar shiga bayi ta ( Allahumma inni a'uzu bika minal kubisi wal kaba'isi) Da mugun sauri ta afka bayin abin da ya ƙara sanya gabanta faɗuwa ganin bayin wayam babu alamar wani bil adama a ciki. Idanu ta zaro tana ƙwala kiran sunan Beelal ɗin tare da ƙara haske bayin wai ko idanunta ne basu gani dai dai ba amma sai ta ƙara gani babu ma wata alamar an shiga bayin, dan ko ɗigon ruwa ma babu. "To ko dai Beelal da Babansa suka tafi masallacin?" Wani ɓangare na zuciyarta ya jefa mata tambayar. "To kuma indai tare suka tafi masallaci to a ina suka yi alwala, tun da dai babu alamar ruwa ma ya taɓa bayin sannan ga butoci nan a cike kamar yadda na ajiye" Ta sake baiwa kanta amsa. "Amma kuma Baban Beelal ba ya son ko kaɗan Beelal ya raɓe shi to ta yaya zai tafi da shi masallaci?" "Kika sani ko ya canja ra'ayi, tun da dao kin ga tun da ya dawo ya sakar da fuska ba kamar da ba, kuma kika sani ko a masallacin za su yi alwalar" Wata zuciyar ta raya mata hakan. Wata ajiyar zuciya ta sauke jin wannan tunanin sai ta ɗan ji hankalinta ya kwanta. A haka ta daure ta yi tsarki ta gabatar da alwala duk da ba wai hankalinta ya kwanta bane dan ta san Idrisu ko kaɗan ba ya ƙaunar Beelal in dai ba ra'a yi ya canja ba duk da cewa wanda ya ce ba ya yi da kai to kuwa ba ya yi da kai ɗin ne har abada, duk wanda ya ce ba ya ƙaunarka to ba ya ƙaunarka ɗin ko da ya dawo daga baya ya ce yana sonka to tabbas ba lallai ya kasance so na gaskiya ba so na haƙiƙa ba. Shi yasa ma manzo S.A.W ya ce idan za ka so mutum to kada ka zurfafa son sa domin wata rana zai iya zama maƙiyinka idan za ka ƙi mutum kar ka zurfafa ƙinsa domin shi ma zai iya zama masoyinka. Allah haɗamu da ma su son mu da gaskiya amin. A haka ta gabatar da salla tare da yin addu'o in ta kamar yadda ta saba, bayan ta gama sai ta shiga gabatar da azkar ɗin safiya, tana yi amma kuma tana jiran jin shigowar su Beelal, a haka har gari ya yi haske tangararai amma babu wanda ya shigo, so take ta tashi ta fita amma kuma bata so ta yi laifi a wajen Idrisu haka ya sanya ta ƙara daurewa. Zuwa can ta ji haƙurinta ya ƙare ba za ta iya cigaba da zama ba tare da ta ga Beelal ba dan haka cikin sauri ta fito daga ɗakin gabanta na dukan uku-uku dan ta san dai matsawar masallaci suka je da Idrisu kuma suka tsaya a masallacin ko kuma a wani wajen to tabbas ba za ta fita b a wajen Idrisu duk da yana mata ɗan faram-faram sai ya mata masifa amma haka ta daure dan ta san dai duk abin da zai mata nafila ne a kan halin da take jin zuciyarta tana ciki yanzu. Tana fitowa ta ga ƙofar gidan a buɗe, haka ta shiga duba sawun amma abin mamaki sai take ta ganin sawun Idrisu babu na Beelal, sannan tun da ta fito daga gidan sai ta ga sawun Idrisu bai bi hanyar da masallaci yake ba, a hankali take bin sawun cikin faɗuwar gaba dan tabbas sai yanzu take jin hankalinta bai kwanta da kasancewar Beelal a wajen Idrisu tana bin sawun duk da tana haɗuwa da mutane jifi-jifi har da masu tambayarta ko lafiya. Amma bata da ƙwarin gwiwar amsa musu tambayarsu sai dai kawai ta gyaɗa musu kai, ganin sawun Idrisu ya nufi hanyar fita gari a take wata mummunar faɗuwar gaba ta ziyarci zuciyarta duk da ta kasa gane menene hakan ke nufi. Mmn Afrah 09030283375 ❤️❤️❤️❤️❤️❤️ *BEELAL* 💦💦💦💦💦💦 NA MAMAN AFARAH *FCW*💛 Book 2 page7️⃣➡️8️⃣ Idanu Fatima ta zaro cikin tashin hankali, tun da dai ta san ita ma da ta tashi da asuba bata ga Beelal ko Idrisu ba, to kenan tun kan asuba suka fito, ko kuma ma ya aka yi bata ganin sawun Beelal sai na Idrisu kawai, wannan tambayoyin take jefawa kan ta hankali tashe, dan ita dai ta san waye ɗanta babu yadda za a yi Beelal ya fita ko da nan da ƙofar gida ne bai faɗa mata ba, ko da, da rana ne bare kuma dare bare ma Beelal ba ya yawo dama gidan su Hameeda ne yake zuwa amma tun da iyayenta suka mutu su kuma wanda take hannunsu wato Yayan mahaifinta da matarsa sun tsani Beelal ɗin ya raɓi Hameedar ma ban da ma uwar wahalar da suke bata kamar baiwa, bare ma yanzu ta kwana biyu bata ga Hameedar ba gashi ko gidan ta je matar gidan ta ringa ci mata fuska, kuma ba za ta bari ta ga Hameedar ba hakan ya sanya ta daina zuwa. Wani uban birki ta ja ta tsaya ganin sawun Idrisu dai ya nufi hanyar barin gari ko lanƙwasa babu gashi kuma ta ma rasa wane irin tunani za ta yi ta ina za ta fara. Hawaye ne suka shiga zarya a fuskarta wani irin jiri ta ji ya fara juyawa da ita hannu ta miƙa ta dafe wani maina da ke kusa da inda take tsaye. "Wai ni ke Fatima me kike dubawa a ƙasa ne ko kuɗi kika jefar ne, tun daɗewa kowa zai wuce ana tambayarki lafiya amma sai ki ɗagawa mutane kai kamar wata ƙadangaruwa, kuma lafiyar ce ta sanya yanzu kike zubar da hawaye har kina neman faɗuwa sai da kika riƙe maina" Cewar wani matashi da yake mata magana cikin muryar ƴan shaye-shaye sai wani tangaɗi yake idanun nan jajawur. " Wayyo Allah na Beelal nake nema wallahi ban ganshi ba da na tashi" Wani uban tsaki ya ja sannan ya ce "To kuma menene dan baki ga wannan mai ƙafa a lanƙwashen ba, ke ba ma kya ganin irin baƙin jinin da yaron nan ya jawo miki a garin nan tun da kika haifeshi amma har wani ruwan hawaye kike dan baki ganshi ba ai na zata mur... "Ba wai na faɗa maka bane dan ka ci mini mutunci, kamar yadda kowacce uwa take so da ƙaunar ɗanta to haka ni ma nake matuƙar ƙaunar nawa ɗan in ma ban fi wata uwar ƙaunar ɗana ba, kuma wani baƙin jini a wajen mutane bai dameni ba dan jahilci ne yake damunsu suna mantawa da cewa Allah shi ke halittar mutane shi ke yin kowa yadda ya so shi ke barin kowa a yadda ya so babu wani mahaluƙi da zai ja da ikon ubangiji ko ya canja halittar ubangiji ko da kuwa ta kiyashi ce bare kuma ta ɗan adam, dan haka ina ƙaunar Beelal ko da kuwa gabaɗaya mutanen duniya za su tsane ni su ƙyamace ni, ni na san ubangijina yana so na, kuma yana sane da ni, sannan soyayar ubangiji a gareni ne yasa ya bani Beelal bayan ya hana miliyoyin mutane haihuwa ni kuma ya bani dan haka ina daɗa gode masa a bisa ni'imarsa gareni" Ta ɗora da cewa "Wallahi da a ce mutane za su san waye Beelal wace irin baiwa Allah ya yiwa yaron ta fili da ta ɓoye, baiwar ƙwalƙwalwar da ba kowa yake da ita ba, Beelal Allah ya halicceshi da nakasa amma kuma ya bashi ɗinbin baiwar da mararsa nakasa basu da ita ga kyan zuciya. Ni na kasa gane kan mutane na kasa gane kansu bare ƙafarsu ɗan adam da bashi da ikon canja mutum amma yana adawa da yadda aka halicceshi, shin sai yaushe ne mutane za su farga, sai yaushe ne za su farka daga baccin da suka yi mai nauyi su gane cewa Allah dai ɗaya ne kuma bashi da abokin tarayya a komai shi ke halitta kowa kuma babu wani wanda ya isa ya canja dan haka kowa ya godewa Allah a yadda ya halicce shi ba wai a tsaya kai da fata sai an samu wanda za a tsangwama dan kawai Allah ya masa halittar da ya so, shin jiki da fata da ƙasusuwan da za a maida su cikin ƙasa menene na damuwa da su? Komai daren daɗewa mutuwa ce za ta ɗauki kowa kuma cikin ƙasa za a sanya kowa duk kyau da tsarin halittar mutum, fari ne ko baƙi ne, ƙasa ce makomarsa, duk mulki da sarautar mutum bashi da makomar da ta wuce cikin ƙasa dan haka babu abin da ya dace da kowa face yin biyayya da bin dokokin ubangiji da yin ibadah da ƙasƙan da kai domin samun rabauta da kuma samun sakamako mai kyau domin bautar Allah ita ce gaba da komai ƙauracewa shirka da manyan zunubai su ne abin gudu. Saɓawa Allah ba shi ne abin yi ba ga wanda bashi da tabbacin ƙara second ɗaya a koyaushe a duniyarsa,mutane su bar kiwon mutane ƴan uwansu su maida hankali da abin da ke gabansu, shi ne ya fi dacewa da kowa ba wai lura da rayuwar wasu ko ƙyamatarsu dan wata halittarsu ba" Fatima ta kai ƙarshen maganar tana kuka sosai, lokacin har mutane maza da mata sun taru yara da manya duk suna sauraron abin da take faɗa kowa sai jijjiga kai yake alamar tausayawa da kuma da na sani a kan abubuwan da ake musu a gari ita da ɗanta, basu da damar su raɓi mutane, basu da damar su sake, su yi rayuwa irin yadda kowa ke yi, ɗanta bashi da halin ya shiga cikin yara ya yi wasa, bashi da damar ya je makarantar boko ko ta arabiya sai an rakoshi har gida ana tsokanarsa, kuma ba dan ya yi komai ba sai dai suna yi ne a kan abu ɗaya kawai wato NAKASAR da ke tare da shi nakasar da bashi ya yi kansa ba, Allah ne ya yi shi, nakasar da ita kanta wacce ta haifeshi a haka ta ga ta haifeshi amma aka ɗauki gabaɗaya laifin aka ɗora a kansu, ita da ta haifa da shi wanda aka haifa, hatta wanda suka haɗu suka haifi ɗan bai barta ba wato uban ɗan shi ma ƙyamatarsa yake, to shin ina suke so Fatima da Beelal su sanya ransu?. "Dan Allah Aunty Fati ki yi haƙuri ki bar kukan nan wallahi waɗannan kalaman naki sun sanya na ji gabaɗaya duniyar ta ishe ni, sun sanya na ji nadama a kan duk wata ƙyamatar wata halittar ubangiji koda kuwa masu nakasar da ta fi ta kowa abin ƙyama kama daga kuturu makaho da dai wasu masu nakasa kowacce iri ce, tabbas yau kin zama madubi da kika haska mini abubuwa da dama da suka shige mini duhu" Cewar wannan matashin mashayin yana share hawayen fuskarsa. "Ba komai kar ka damu ni zan bi sawun nan domin zuwa in ga inda Idrisu yake ko Allah zai sa in ga Beelal a tare da shi in samu sassauci duk da na ga ban ga sawun takalmi ko ƙafar Beelal ba amma na tabbata Beelal ba zai fita daga gida ba tare da sani na ba. Dole zan bi sawun Idrisu dan na san tabbas akwai lauje cikin naɗi" "Zan faɗa miki inda Idrisu yake kuma ina tabbatar miki suna tare da Beelal sabodanna gansu da idanuna a daren jiya su... "Dan Allah yana ina ka faɗa mini dan girman Allah" Cewar Fatima cikin tashin hankali dan jin ya ce suna tare kuma tun daren jiya sai ta ji hankalinta ya yi mummunan tashi. " A daren jiya bayan dare ya tsala, duk da bansan ko ƙarfe nawa ba amma na san tsakiyar dare ne, na dawo daga yawo wurin wani abokina da ke ƙauyen sama da mu, to tare muke da abokin nawa ya ɗakko ni a machine amma dama tun daga can yace ba zai kai ni har cikin garin nan ba, tun da dare ya yi zai ajiye ni a bakin bari in ƙaraso shi ma ya koma dan yana tsoron Babansa ya san baya gida, dan ba a san ya fito ba ta katanga ya ƙetara ya fito muka je mu da sauran abokananmu muka haɗu muka yi shaye-shaye, amma in sha Allahu ni da shaye-shaye har abada dan kalamanki na yanzu sun shigeni har na ji cewar ina so in zama mutumin kirkin da za a yi alfahri da ni. Ina cikin tafiya sai na hango wani machine ya taho daga bayana ya samu wuri ya faka ua sauka ya tsaya kamar dai yana jiran wani abu, to bai ganni ba da yake akwai duhu, sai na ɓuya inaso in ga mai zai aikata, duk tunanina cikin ƙauyen zai je yin sata, zuwa can sai na hango wani mutum ya taho da yaro a saɓe a kafaɗarsa, cikin mamaki sai nake tunanin masu satar yara ne, gabana na faɗuwa ina so na fito amma ina tsoro dan ni a buge nake duk da dai ba sosai ba amma dai babu wani ƙarfi a tare da ni, mutumin na ƙarasowa sai na ga ashe Idrisu ne ya ɗakko Beelal a kafaɗarsa dan yana zuwa wajen mai machine ɗin suka fara magana ya ɗora Beelal ɗin da ke bacci da alama ma bai san ya ɗakkoshi ba, sai da ya ɗora shi a machine ɗin ya falka. amma haka Idrisu ya tsawatarwa yaron dan dole ya yiwa bakinsa linzami ba dan ya so ba, cikin mugun gudu abokin nasa ya ja machine ɗin suka bar wajen, ni kuma dama da na ga ƴan garin nan ba ƙaunar yaron kowa yake ba sai kawai na ga an samawa kowa lafiya duk da ban san ina zai kai yaron ba bare kuma da na ga Babansa ne ma duk da kowa ya san ba ya ƙaunar yaron, sai kawai na taɓe baki na fito daga moɓoyata na tafi, amma ki gafarceni " Kallonsa kawai Fatima take da idanunta da ke zubar da hawaye tamkar an kunna famfo ita kan ta ba za ta ce ga irin tsananin damuwar da ta kaiwa zuciyarta farmaki ba lokaci guda, ban da wacce take ciki. Ji take tamkar a jijjigata a ce ta tashi bacci ne take komai da ya faru ba a gaske bane mafarki ne. "Dan Allah jama'a ku jijjijgani in falka daga wannan mummunan mafarkin da nake, mafarkin nan da yake kokarin rabani da wanda na fi ƙauna duk cikin duniyar nan, shin ya mutum zai ji a lokacin da aka rabashi da wanda ya fi ƙauna? Ya uwa take ji a lokacin da mutuwa ta rabata da ɗanta, duk da ta san mutuwa dole ce kuma wanda ya karɓi kayansa dama shi ne ya bata kuma ya fi ƙaunar ɗan nata fiye da yadda take ƙaunarsa, amma a haka take jin damuwa ta mutuwar ɗan nata shin ni kuma da wane kwatance za a kwatanta halin da nake ciki, har gwara mutuwa mutum ya ce mutuwa ce amma fa a raba uwa da ɗanta bayan yana raye shi kuma wane irin ƙunci zuciyar uwa za ta shiga? Shin matan aure da mazanjensu suke sakinsu su rabasu da yaransu ya suke ji a duk lokacin da suka koma gidan iyayensu , ji suke tamkar an rabasu da wani sashe na farincikin rayuwarsu, a koyaushe uwa tafi so ta kasance a tare da ƴaƴanta, idan har wacce ta baro yaranta a gidan mijinta za ta shiga damuwa duk da ta san inda yaran suke, to ina kuma ga wacce bata ma san inda yaronta yake ba, sannan ta san yaron yana hannun wanda baya ƙaunarsa, dan Allah jama'a ku kwantanta yadda nake ji yanzu a cikin raina, kowa ya san Idrisu ba ya son Beelal saboda nakasar dake tare da shi, kamar yadda mutanen gari ma basa son sa basa ƙaunar ya raɓi inda suke ma, yau kuma ya ɗauke min shi cikin talatainin dare ya gudu dashi dan Allah ku taimaka min" Fatima dake bin mutanen wurin ɗaya bayan ɗaya tana kuka tare da neman agaji a garesu dan ta kasa dakatar da zuciya da kuma hawayenta, babban tashin hankalinta ma shi ne ina Idrisun ya kai yaron. Kowa na wurin babu wanda za ka kalli fuskarsa ba tare da ka yi arba da hawaye sun gama wanke masa fuska ba, gabaɗaya wurin sun matuƙar tausaya mata irin tausayin da kaf garin babu wanda ya taɓa musu, haka suke rayuwa a cikin garin tamkar wasu haure da basu da kowa da komai a cikin garin, amma sai gashi yau sanadin kalaman Fatima kowa ya ji tausayinsu ya kamashi, kalaman Fatima kalamai ne wanda akwai hikima, ilimi da kuma iya furta kalma kowacce a mazauninta an bata haƙƙinta. Haƙuri aka shiga bata wata dattijuwa ce ta kama Fatimar ta rungume ta dan ta samu sassauci, dan tabbas a duk lokacin da ɗan adam ya tsinci kansa cikin damuwa to idan har aka rungumeshi aka lallashe shi to ko da a ce damuwar nan bata bar shi duka ba zai samu sassauci ko da kaɗan ne a cikin ransa. Musamman a ce wanda zai rungumi mutum ya kasance uwa ce wato mahaifiya dan ita uwa ɗumin jikinta da ban yake haka nan soyayyarta ta zarta ta kowa ta kuma wuce a misalta ta. Fatimar kwa kamar jira take sai kawai ta kwantar da kanta a jikin matar da ta mata ƙawanya da hannayenta a bayanta, Fatima idanu ta rufe hawaye na kai koma a fuskarta, ji take tamkar a jikin mahaifiyarta, ko Kakarta, ko Yayarta take domin su ne duk duniya suke bata mafaka a baya kafin barinsu duniya, yanzu kuma sai Yayarta Hajiya Laɗifa kawai wacce kuma yanzu ta yi nisa da ba za ta samu taimakon gaggawa na runguma da lallashi a gareta ba. Da a baya ko Yayarta bata nan idan tana cikin damuwa mijinta wanda ya kasance abin so da ƙauna a gareta wato Idrisu shi yake sanyata farinciki a duk lokacin da ta shiga damuwa in Yayarta bata kusa, kafin ya juya mata baya, kafin ya sauya mata daga Idris zuwa Idrisu, kafin ya manta da so da duk wata ƙauna da yake mata ya maye gurbin ƙauna da ƙiyayya, haka kuma ya yi watsi a duk wata kulawa da nauyinta da ke kansa, kafin ya canja daga fari zuwa baƙiƙƙirin wanda har yau bata san dalilin yin hakan ba, duk da an ce mata da dama su kan auri namiji aure irin na so da ƙauna amma idan an je gidan daga baya komai ya kan canja, sukan rasa duk wanann abubuwan zaman ya dawo sai na haƙuri da zaman ƴaƴansu, amma ita nata salon da ban yake da na saura dan ita abin ya wuce misali sai dai fatan Allah kawo ƙarshen abin. Dattijuwar nan bata cire Fatima daga jikinta ba har sai da ta ji ta ɗan tsagaita kukanta tana sauke ajiyar zuciya, sannan kuma Fatimar ce da kanta ta ɗago kanta daga jikin tsohuwar tana share hawayenta, dan kuka ya zame mata jiki dan ita kullum idan har za ta tuna da damuwarta to kuwa za ta kasance ne ciki kuka, kuka kamar matar marigayi, dama kuma Beelal shi ne yake ɗauke mata kewa da duk wata damuwa, zama da ita ne da kuma halin da suka tsinci kansu shi da ita ya sanya yaron ya zama tamkar wani babba, ya iya lafazi da kalamin da yake kwantar mata da hankali waɗanda a wajenta yake koya saboda da su take amfani wajen lallashin sa da kuma koya masa zama da mutane da haƙuri da rayuwa a duk halin da mutum zai tsinci kansa daɗi ko akasin haka. "Bari na je na bi sawu na karɓo Beelal ɗin na gane garin kusa da Kazaure ne wajen abokinsa ne zan je in gani" Ta faɗa tana runtse idanunta ta buɗe su ko ta ke gani sosai saboda kukan da ta yi sun kumbura suntum, har bata iya gani sosai. "Babangida ɗakko machin ka kaita" Cewar wani mutum da ke tsaye ya faɗa wa ɗansa, da to matashin ya amsa ya je ya ɗakko machine ɗin Fatima ta hau ya ja suka tafi kowa yana tsaye ana jimantawa har sai da suka daina gango machine ɗin su Fatima sannan kowa da ya taru ya watse dan lokacin sosai rana ma ta fito wajen ƙarfe tara saura ne. MMN AFRAH 09030283375 ❤️❤️❤️❤️❤️❤️ *BEELAL* 💦💦💦💦💦💦 NA MAMAN AFARAH *FCW*💛 Book 2 Page 9️⃣➡️1️⃣0️⃣ *KATSINA STATE* *UNGUWAR* *KAFIN SOLI* ~HAMEEDA~ Tun lokacin da Ramma wacce za ta kaita wurin aiki ta je ta taho da ita, Ramma tana kai yara ƴan mata da yara mata gidan masu kuɗi su yi aikace -aikace kama daga shara wanke-wanke goge-goge raino da dai sauransu. Ta tafi da Hameeda da sauran wasu yaran a inda ta yiwa iyayen kowacce yarinya alƙawarin idan an biya kuɗin aiki za ta kawo musu sannan duk ƙarshen wata idan aka bada kuɗin aikin yaran za ta kawo musu ita ma su bata kason ta. Garin Katsina ta nufa da su Hameeda su bakwai ne amma Hameeda ce ƙarama a cikinsu. Sai da ta kai duka yaran saura Hameeda kaɗai ta rage dama kuma akwai wata Hajiya da ta ce tana son yarinya ƙarama dan haka can gidan Hajiyar suka nufa. A ƙofar tangamemen get ɗin ɗan sahun ya ajiyesu Ramma ta biya shi kuɗinsa. Tun da aka sauke su a ƙofar gidan Hameeda ta maida hankalinta kwacakom a kan tsararren gidan kallo kawai take tana tunanin gida ne za a kaita aiki. "Wuce mu je kin tsaya saboda ƙauyanci kina kalle-kalle" Muryar Ramma ta katse mata tunaninta, cikin sauri ta yi gaba riƙe da ledar kayanta. Sai da suka je jikin get ɗin Ramma ta sanya hannu ta shiga ƙwanƙwasa get ɗin gidan, mai gadi ne ya buɗe ƙofar ganin Ramma sai ya washe baki ganin Ramma dan ya gae ta Hajiya Zulaiha matar gidan ta sanar da shi zuwanta kuma sai da ta tabbatar ta masa kwatancenta dan dama tana ɗan zuwa gaishe da Hajiyar lokaci zuwa lokaci. Gaishe da shi Hameeda ta yi cikin ladabi ya amsa yana gaishe da Ramma suka gaisa tare da tambayar bayan saduwa. Cikin gidan suka nufa domin Hajiyar ta san da zuwansu, kuma gidna ba baƙon Ramma bane, Hameeda gabaɗaya ta shagala da kallon cikin gidan dan sai da ta ga cikin gidan ne ma ta ga ashe dai bata ga komai a waje ba gidan ya haɗu ya kuma tsaru. Ramma ce ta wani fisgi hannunta suka fara sauri sai wani hararar Hameeda take, a ƙofar part ɗin Hajiya Zulaiha suka tsaya Ramma ta fito da waya ta kira Hajiyar ta sanar mata gasu a ɓangarenta, umarni ta musu a kan su shiga, haka suka kutsa kai cikin ɓangaren nata, tangamemen falon da ya gaji da haɗuwa da kayan alatu suka shiga bakinsu ɗauke da sallama sai dai ba kowa a falo dan haka shiga suka yi kawai tun da ta ce su shiga. A ƙasa Hameeda ta zauna rungume da jakar ledarta, sai ƙarewa falon kallo take tana rayawa a ranta wannan ce aljannar duniya. Ramma kuwa kan kujera ta haye ɗare -ɗare. Jim kaɗan sai ga Hajiya Zulaiha tana sakkowa daga upstairs sanye take da rigar leshi an mata ɗinkin buba, sai sarƙa da ɗankunne na gwal sanye a jikinta, ƙafarta cikin takalmi wanda ya yiwa ƙafarta kyau. A hankali take sakkowa kai da ganinta ka san kuɗi sun samu wurin zama, Ramma ganin Hajiyar na sakkowa sai ta sauka daga kujera ra zauna a ƙasa tana washe haƙora. Ɗaya daga cikin kujerun da suka ƙawata falon ta samu ta zauna, da ɗan murmushi a fuskarta take kallon kyakkyawar fuskar Hameeda a gefe ɗaya tana ganin kamar ta yi ƙanƙanta a kan aikin da za ta mata, sannan kuma tana ganin wautar wasu iyayen dake aika yaransu aikatau ba tare da tabbas ɗin a hannun waye za su yi aikin ba ko kuma wane irin zama za su yi a gidan su dai kawai burinsu a samo kuɗi a basu. "Hajiya barka da yamma" Cewar Ramma tana ɗan rusunawa daga zaune da take. "Barka Ramma ya hanya" "Lafiya lau wallahi " "Saukar yaushe?" "Wallahi da azahar muka sauka to na tafi raba sauran yaran gidajen aikinsu, to wannan ita ta rage kuma ita na ga ta yi dai dai da wacce kika ce kina so" Cewar Ramma tana nuna mata Hameeda. "Ina yini" Cewar Hameeda cikin sanyin murya. "Lafiya lau, yarinya ya sunanki?" "Hameedatuwa" Ramma ta karɓe. "Hameedatuwa kuma suna ne?" Cewar Hajiya Zulaiha tana kallon Ramma. "Eh mana" Cewar Ramma. "Ke yarinya ya sunanki" Cewar Hajiya tana kallon Hameeda. "Hameeda" Cewar Hameeda tana wasa da yatsunta na hannu. "Ma sha Allah suna mai daɗi" Cewar Hajiyar tana kallonsu. "To Hajiya ya kika ganta ta yi kuwa?" Cewar Ramma tana washe baki. "Haba Ramma wannan ai ta yi ƙanƙanta, ba za ta iya yin aikin da nake buƙata ba sai dai kawai a barta take yin goge -goge da ɗan abubuwan da ba a rasa ba" "Hajiya ƙanƙantar ta kike gani, amma wannan babu abin da ba za ta iya ba saboda mariƙiyarta sai da ta tabbatar ta hore ta sannan ta bayar da ita aiki" "Ikon Allah, wato ma ba mahaifiyarta bace ta bayar da ita?" "Eh ba ita bace mahaifiyarta ta rasu ita da mahaifin suka ci maganin ɓera a abu shi ne silar barinsu duniya, ita wannan matar Yayan Babanta ce" "Ayya marainiya ce ashe?" "Eh wallahi" Hameeda tun da suka fara maganar iyayenta, hawaye ya gama wanke mata fuska, sosai rayuwarta da mahaifanta ta dawo mata da Yayanta Beelal amma mutuwa ta mata yankan ƙauna, gashi Beelal ɗin ma an rabata da shi, Allah sarki maraici. Jaraba Ramma ta fara mata wai daga zuwan su ta fara kuka saboda ita kuka ba ya mata wahala, sai da Hajiya Zulaiha ta ce ta ƙyaleta ai kuka dole ne kuma wajibi ga duk wanda ya rasa iyaye tabbas ya yi kuka. Abinci Hajiyar ta sanya aka gabatar musu Hameeda dai bata ci ba amma Ramma ta zage ta ci ta ƙoshi duk da sun ci abinci a wasu gidajen da ta je kai sauran yaran amma a nan ɗin ma dai bata tsallake tayi ba. Sai da ta ci ta yi nata sannan Hajiya ta kawo kuɗi dubu goma ta bata kuɗin aikin Hameeda na watan da za ta fara sannan ta bata dubu biyar nata da atamfofi guda biyu, haka ta yiwa Hajiyargodiya tare da sallama ta tafi tana murna, da yake tana da ƴar uwa a cikin Katsinar to a can take zaune sai dai ƴar Mai mazari ce tana zuwa lokaci- lokaci. Tun da ta tafi Hajiya ta sanya wata dattijuwa mai mata aiki mai suna Baba Ramatu ta tafi da ita sashensu na ƴan aiki. Baba Ramatu a ɗakinta ma ta ce Hameeda ta zauna saboda ganin ƙanƙantar ta bata ce ta je ɗakin sauran ma'aikatan ba kuma tana ganim ta yi ƙanƙanta a ce ta zauna a ɗakinta da ban Sosai Hameeda ta ji daɗin zama a wajen dattijuwar saboda yadda take bata kulawa da nuna tausayi a gareta. Bayan sallar magariba Hameeda Hajiya ta bata plates daga kicin ta kai kan dinning, da sallama ta shigo falon da ƙaran TV a cika shi, tana shigowa ba tare da ta tsaya komai ba ta nufi kan dinning ɗin za ta ajiye plates ɗin. "Ke! Bakya ganin mutane ne ko baki iya gaishe da mutane ba" Cewar wani matashi da ke zaune a kan kujera ya jingina bayansa a jikin kujerar ƙafarsa ɗaya kan ɗaya yana danna waya ba tare da ya ɗago ya koda kalleta ba. Da sauri ta baro dinning area ɗin ta taho har gabansa ta zubar da gwiwoyinta a ƙasa ta ce. "Barka da dare" A fusace ya ɗaga hannu zai wanke ta da mari Hajiya da fitowarta daga kicin kenan idanunta suka sauka a kan su cikin hanzari ta ce. "Kar ka kuskura ka dake ta musty shin me ma wannan ƙaramar yarinyar ta maka da zaka ɗaga hannu ka dage ƙarfinka za ka duketa?" Ta faɗa tana ƙarasowa wajensu. Jimƙe hannun nasa ya yi wanda zai yi marin da shi ya naushi iska yana wani kumbura baki, tare da aikawa Hameeda wata uwar harara. "Hameeda me kika masa?" Cewar Hajiya tana kallon Hameeda da ke dafe da kuncinta dan tun da ya ɗago hannu zai mareta ta sanya hanu ta dafe kumatunta, duk da cewa mari duka da duk wasu uƙubobi babu wanda bata fuskancesu ba a hannun matar wan mahaifinta. *BEELAL* Tun da ya fara tuƙa keken nan sai ya ji gabaɗaya tausayin kansa ya kama shi, tabbas ana shiga damuwa idan aka rasa iyaye kamar yadda ya ga Hameeda ta shiga ƙuncin rayuwa tun daga lokacin da iyayenta suka rasu. Sai dai shi gashi iyayensa a raye amma ya zama tamkar maraya marar uwa da uba. Duk da cewa babu sanin mahaifiyarsa, kuma babu hannunta a tahowarsa amma dai ga mahaifinsa nan da saninsa kuma da sanya hannunsa kai shi ne ma ummul aba isin shigarsa wannan halin. Haka ya cigaba da tuƙa tsohon keken nan gashi babu katifa ko wani tsumma a wajen zaman, ga duk tsatsar jiki sai zuba take jajawur da ita, hawaye gabaɗaya ya gama wanke masa fuska a lokacin da ya tuno irin halin da Mamarsa za ta shiga ta kuma kasance a duk lokaci da ta gane ba ya nan, sannan ya san da ace ta san yana nan yana bara to da kuwa ya san ko ta halin ƙaƙa ba za ta bari haka ta kasance ba. Hannu ya sanya ya goge hawayensa saboda ganin ya zo cikin mutane. Haka ya ƙarasa wani waje inda mutane ke ta siye da siyarwa ya tsaya daga gefe kusa da wani maina, yana tunanin ta ina zai fara bara. Bayansa ya waiwaya inda su Idrisu suke, aikuwa dama kamar jira suke suka fara wani ɗaɗɗaga masa hannu suna masa alama da ya fara bara, kansa ya ɗauke daga kallonsu, zuciyarsa na masa ƙuna wai yau shi ne zai yi bara ba wai kuma dan ya fi ƙarfin hakan ba sai dan wadatar zuci da suke da ita shi da mahaifiyarsa duk rintsi basa yin bara duk halin da za su shiga kuwa. Yana cikin tunanin abin da zai ke cewa in zai fara barar ya jiyo waji sautin wani almajiri yana cewa. "A bani ta annabi, a taimaka min da sadaka da abin da Allah ya hore" Cikin sauri Beelal ya waiga ya kalli mai barar aikuwa idanunsa suka sauka a kan wani matashin gurgu da ke rarrafe a ƙasa, gwiwar ƙafarsa ya sanya tsumma ya ɗaure saboda rarrafen, sannan takalmansa sai ya saƙala kowane ɗaya a hannu ɗaya yana rarrafawa gabaɗaya ƙafafunsa a lanƙwashe suke, da sauri Beelal ya kalli keken da yake zaune a kai sai ya ga da wannan gurgun ya dace ba shi ba, sai ya ga gurgun ya fi buƙatar keken ba shi ba da yake da ƙafafunsa amma dole uwan naƙi ta sanya shi ya hau ba tare da ya shirya hakan ba. Ƙwallar da ta cika idanunsa ya yi ƙoƙarin maidata, cikin sanyin jiki ya fara tuƙa keken a hankali wajen mutane ya nufa amma laɓɓansa sun ƙi bashi haɗin kai ya furta abin da yake son furtawa. Yana nan ya ga wannan gurgun ya zo ta kusa da shi ya wuce. ganij a wurin babu wanda ya baiwa gurgun sadaka sai ya cigaba da ɗan tafiya kaɗan ya ƙara tsayawa ba tare da ya ce komai ba. "Ungo nan almajiri" Cewar wani mutum da ke suɗe hannu yana miƙawa Beelal sauran abinci a cikin kwano. Hannu biyu Beelal ya sanya ya karɓi kwanan yana mai cewa. "Allah saka da gidan aljanna" "Amin yaro" Cewar mutumin yana wanke hannunsa da pure water. "Idan ka cinye ka baiwa waccen mai siyar da abincin kwanon" Mutumin ya faɗa yana nunawa Beelal wata budurwa dake siyar da abinci. "To" Beelal ya ce, ganin mutumin ya juya ya yi tafiyarsa, sai ya ɗakko ledar da Imran ya bashi ya shiga juye abincin a ciki dan ya tabbata su Imran suna hangoshi yunwa yake ji amma babu damar ya ci saboda kar ya yi laifi haka yana ji yana gani ya kuye abincin ya ƙulle ledar tare da rataye ta a jikin hannun keken, kwanon ya suɗe tare da hannunsa ya ƙarasa ya baiwa mai abincin kwanonta, ya ɗauki wata buta mai ruwa da ya gani a wajen ya wanke hannunsa, ya cigaba da zagaya wurin amma har lokacin bai yi bara ba. MMN AFRA 09030283375 ❤️❤️❤️❤️❤️❤️ *BEELAL* 💦💦💦💦💦💦 NA MAMAN AFARAH *FCW*💛 Book 2 Page1️⃣1️⃣➡️1️⃣2️⃣ *FATIMA* Tun da Babangida ya ɗauke ta a machine ɗin gabanta yake mugun bugawa tana jin kamar dai akwai wani abu da ke shirin faruwa dan haka sai ta kasance a cikin muguwar damuwa. Tafiya suke amma gani take kamar ma basa sauri gani take garin ya mata nisa sosai. Sunayen Allah ta fara karantowa tare da yiwa annabin rahma S.A.W salati cikin hikimar ubangiji sai ta ji hankalinta ya ɗan kwanta ta samu nutsuwa. Suna shiga garin suka yi tambaya gidan su abokin Idrisun sai wani daga cikin mutanen da suka tambaya na majalissar ya kwatanta musu inda za su samu mutumin. Haka suka tafi wajensa, tun daga nesa suka hangoshi a wajen mai gyaran machine yana tsaye ana duba masa iska a machin ɗinsa. Sun kusa ƙarasawa sai machine ɗin nasu ya tsaya, da sauri Fatima ta sauka daga kan machine ɗin dan ita dama ji take kamar ta tashi sama ta isa gareshi. Cinkin hanzari ta isa wurinsa har tana tuntuɓe zuciyarta tamkar ta tsaga ƙirjinta ta fito haka take ji musamman da ta hango shi babu Idrisu bare Beelal, amma dai tana rayawa a ranta cewa ba zai rasa sanin inda suke ba tun da an sanar mata shi ne ya ɗaukesu da daddare. Gabaɗaya bata cikin nutsuwarta dan haka komai ya kwance mata, sallama ma baya zo mata a ranta ba, shi ma abokin Idrisun da bai kula da zuwanta ba kawai sai ganinta ya yi a gabansa tamkar an jefo ta. Kafin ya gama tantance daga ina take, mai kuma ya kawo ta sai ji ya yi ta jefo masa tambaya. "Ina Idrisu yake???" Ita ce tambayar da ta fara jefo masa, da farko bai gane ta ba sai da ta yi masa tambayar ya gane matar Idrisun ce. A maimakon ya bata amsa sai ya fara zare ido kamar ya yiwa sarki ƙarya, abinka da marar gaskiya ko cikin ruwa sai ya yi gumi a take a wurin sai ya fara inda-inda a maimakon ya bata amsa kai tsaye. " Na ce maka ina Idrisu yake, saboda an faɗa mini kai ne ka ɗakko shi a machine jiya da dare tare da Beelal ka faɗa min ina ka kai su?" Ta jefa masa tambayar a karo na biyu. "Eh, eh, am eh haka ne" Ya faɗa yana wani inda -inda. "Yana ina???" Shi ne tambayar da Fatima ta masa cikin gushewar hankali dan gabaɗaya a firgice take ji take kamar kawai ta shaƙe shi ta yi da jibgarsa ko hakan zai sa ya yi gaggawar bata amsar da take nema, sai dai a gefe ɗaya kuma tana cike da fargabar amsar da zai bata. "Idrisu fa ya tafi Lagos da yaron nan" Wannan ita ce wata mummunar kalma da ta ziyarci kunnuwan Fatima wacce har sai da maganar ta yi amsa kuwwa a cikin kunnuwanta. Sai da jinta ya ɗauke na wasu sakanni kafin ya dawo mata. "Ya, ya, ya" Ta rinƙa maimaita ya, ta ma kasa haɗa kalmomin da za ta yi masa maganar da su, hakan ya yi dai dai da ƙarasowar Babangida wurin yana tura machine ɗin da suka zo a ka. "Ki yi haƙuri dan yanzu na san sun bar Kano sun hau hanyar Lagos dan tun sassafe suka bar garin nan, a can bakin titi suka hau mota" Ya faɗa yana mata nuni da bakin titin. Da ido Fatima ta bi hannun nasa da ke mata nuni da bakin titin, tun da ta ƙura ido a titin ta kasa ɗauke idanunta daga wurin sai hawaye kawai da ke malala daga idanun nata.Kallon wurin take ko ƙiftawa babu, kamar dai wanda aka ce ta yi ta kallon wurin za ta ga Beelal ɗin ya fito. "Lagos kuma amma me yasa zai tafi da yaron Lagos? Ba tare da sanin mahaifiyarsa ba?" Babangida ya jefa masa tambayar. "Ni ma dai ban sani ba, kawai dai ya mini waya jiya ya ce in zo in ɗakkoshi a machine, sai da na je ma na ga ashe harda yaro to ni dai bansan dalilinsa ba kuma ma da na ga ɗansa ne waye zai masa shamaki da ɗansa shi yasa ban kawo komai a kai ba" Ya faɗa yana wani sussunƙui da kai ƙasa. Fatima a hankali ta shiga juyo da fuskarta daga kallon bakin titi zuwa fuskar abokin Idrisu, ta ma rasa mai za ta ce wani haushi take ji wanda da a ce yanzu za ta ga Idrisu tabbas idan ta ci kwalarsa sai dai a ƙwaceshi a hannunta in yaso hakan ya zama sanadin mutuwar wannan ƙaddararren auren nata da shi. "Kai yanzu ko da ɗansa ne zai ɗakko yaro mai larura ya tafi da shi Lagos ba tare da sanin mahaifiyarsa ba? Kuma ma dai in har tafiyar tsakani da Allah ce, zai ce ka je ka ɗaukeshi tsakiyar dare?" Babangida ya faɗa yana kallonsa. "Dakata malam ba fa za ku zo kuna min wasu tambayoyi ba kamar wasu ƴan sanda, kamar wani ɓarawon da ya yi ƙatuwar sata, kuma wannan tambayoyin ai ba ni ya dace ku yiwa su ba, Idrisu ya kamata ku yiwa" Ya faɗa yana wani haɗe rai kamar zai hau su da zagi, dan yana ganin kamar abin nasu ya zo da rainin hankali tun da dai shi ai ba shi ne ya kar zomon ba rataya aka bashi. "Au haka ma za ka ce ko, to shikenan amma ka saka kan ka a matsayin da nake, shin ya za ka ji? Ko ka saka matarka ko ƙanwarka idan su ne wani irin abu za ka ji a cikin zuciyarka? Shin ka san ciwo da raɗaɗin da suke yiwa uwa suka a duk lokacin da ta rasa ɗanta kuwa, ka san yadda nake ji kuwa a cikin zuciyata, amma tambayoyin da muke maka domin samun mafita su ne har ka ƙosa da su, bayan kuma kai kan ka, ka san babu inda za mu samu amsar tambayarmu sai a wajenka, babu wanda ya san amsar tambayarmu sai kai, to babu damuwa Allah mana maganin matsalarmu" Cewar Fatima cikin kuka duk wanda ya ganta a halin da take ciki yanzu sai ya tausaya mata. Mutane har sun fara taruwa, juyawa Fatima ta yi ta kalli Babangida idanunta cike da hawaye ta ce. "Tada machine ɗin mu tafi Babangida" Ta faɗa tana sanya bayan hannunta ta goge hawayenta, shi ma Babangidan bashi da ta cewa dan gabaɗaya tausayin Fatima da ma Beelal ɗin baki ɗaya ya cika masa zuciya, haka ya tada mashine ɗin ta hau ya ja suka tafi, shi kuma abokin Idrisu ya bisu da ido jikinsa sanyi ƙalaw dan kalamin Fatima sun gama kashe masa jiki. Tun da suka ɗau hanya babu wanda ya yi magana daga Fatimar har Babangidan, sai dai Fatima tun da suka fara tafiya hawaye ya kasa ƙauracewa idanunta, saboda kawai ganin abin take tamkar almara, wai yau Beelal ɗinta ne bai kwana a gida ba abin takaici ma wai Idrisu ne ya ɗauke mata shi ya tafi da shi Lagos, wannan abin idan ta tuna shi yake sa ranta yake ƙuna. Ji take da a ce tana da dama da tuni ta zama tsuntsuwa ta bi bayansu, tana ta saƙar jakin nan ta saƙa ta warware a hakan har suka shigo garinsu, har ƙofar gida Babangida ya kai ta, yana ta faman bata haƙuri ita dai kai kawai take iya ɗaga masa dan hawaye sun ƙi yankewa idanunta, ji take har ƙwara a ce da mutuwa Beelal ɗin ya yi ake bata haƙuri da sauƙi tun da dama kowa ya san mutuwa dole ce, amma yanzu kuma yana raye bata san halin da yake ciki ba wannan abu yana matuƙar sanya zuciyarta damuwa. Fakyar ta iya yiwa Babangida godiya ta juya ta shige gida, dan mutane har sun fara taruwa masu son jin ƙwaƙwaf suna tambayar Babangida ba a samo Beelal ɗin ba, bayan da lokacin yana nan babu wanda ya damu da su.Fatima kuwa ta san tana buɗe baki kuka zai ƙwace mata dan yanzu ma burinta kawai ta gan ta a cikin gida. Tun da ta shigo cikin gidan idanunta suka sauka a kan kayan Beelal na wanki wanda ta wanke masa jiya da yamma, tana kallonsu wata shuɗiyar riga da shi da kansa ya shanya rigar yana ta cewa take bashi shi ma yana wankin, ta ce sai dai suke shanya tare saboda hannunsa marar lafiyar har yana cewa idan ya ƙara girma zai ke yin wankin take ce masa. "Haba Beelal ai duk girmanka ni zan ke maka wanki saboda larurar da ke tare da kai, idan kuma Allah ya hore mini sai in ke biya ana wanke maka idan ka yi aure dan kar a ɗorawa matarka wahala dan ba kowace mace ce za ta ɗau ɗawainiyar wanki ba bare matan yanzu da basa son wahala su ma so suke a hidimta musu" "Ni ba wani aure da zan yi Mama a gida zan zauna muke zaman mu tare da ke, ni fa a duniya kwata-kwata ba na son rabuwa da ke sai sai in mutuwa ce kaɗai za ta raba mu ita ma dan dole ce" Wannan kalaman nasa na jiya suna faɗo mata sai kuwa wani kuka mai ƙarfi ya ƙwace mata ganin gashi ma ashe kwana ɗaya ya rage musu jiyan raba tsakaninsu duk da kasancewarsu masoya na haƙiƙa amma rashin imani da tsoron Allah ya sanya Idrisu ya raba su, idanunta ta sauke a kan katifar da Idrisu ya kwanta a kanta jiya wacce ke a waje ɗaure da net ɗin da ta sanya masa wani haushi da takaici ta ji a lokaci da ta kalli katifar kuka ne ya ƙwace mata. Hannu ta sanya ta toshe bakinta da kukan ke fitowa ɗaki ta nufa da ɗan gudu-gudu, tana shiga ɗakin ta faɗa kan katifar ta a ribda cike ta kwanta tare da kifa fuskarta a kan tafukan hannayenta ta saki wani kuka mai ƙarfi wanda yake fitowa da ɓacin rai haɗe da zunzurutun kewar ɗanta tilo Beelal, tana jin zafin da zuciyarta take mata, tausayin yaronta yana daɗa ninkuwa a ranta tana tunanin irin rayuwar da zai yi a wani waje da babu ita babu wani wanda ya sani sai Idrisu mutumin da ba ya ƙaunarsa kuma yanzun ma ta tabbata ba ƙaunar ce ta sanya ya ɗauke yaron ba, illa wani ƙudiri nasa marar kyau da Allah ne kaɗai ya sani, tausayin Beelal na ƙara shigewa zuciyarta tana tunani ya zai ke aiwatar da abubuwan da ba ya iya wa sai dai ita ta masa saboda NAKASAR da ke tare da shi. Sai da ta yi kuka mai isarta, aikuwa idanun suka sake suntumewa, amma bata damu da hakan ba, cikin sauri ta tashi daga kwanciyar da ta yi ta ɗauki abu ta goge fuskarta tas, da hanzari ta tashi domin duba wayarta wacce Hajiya Laɗifa ta turowa wani mai pos da ya tura mata acc no sa ta turo kuɗi aka sake mata wayar ko sati biyu bata yi ba, fatan ta dai Allah sa Idrisu bai ɗauke wayar ba, wurin da ta ajiye wayar ta je ta duba cikin ikon ALLAH sai ta ga wayar tana nan, dan dama ta siyar da tsohuwar, hannunta har karkarwa yake da ta ɗakko wayar dan ta tabbata idan har da ya ɗauke wayar shikenan ya datse mata abin da ta saƙa a ranta yanzun nan. Wayar ta kunna ta kamo sunan Yayarta har ya kira kafin kiran ya shiga sai ta katse saboda tana ganin Hajiya Laɗifa idan ta ji abin da take shirin yi za ta iya dakatar da ita dan haka sai ta fsa kiranta, buɗe wayar ta yi ta fitar da sim ɗin ta karya shi, cikin hanzari ta tashi kamar an tsikareta ta fito da sauri, takalmanta ta saka ta nufi hanyar ƙofar gida. Shagon siyar da wayoyi ta nufa, kawai jefa ƙafarta take kamar wanda ake hankaɗata, tana zuwa kuwa ta yi sa'a a buɗe, ta sanar da mai shagon wayar take son siyarwa ganin wayar kamar ma yanzu aka buɗeta a kwalinta ya shiga son jin dalilin siyar da wayar dan dai ya fara tunanin ko dai wayar ce take da matsala dan a zahiri dai babu wasu alamu da suka nuna haka. Faɗa masa ta yi amfani take son yi da kuɗin, nan ya sayi wayar dubu 25 wayar da dubu 35 aka siya haja ta siyar masa dan ita bata da lokaci ko nutsuwar da za fa yi ciniki ko jayayya da shi. Kuɗinta ya bata ta kamo hanyar gida, tana shigowa ta ɗauki ƙaramar pos ɗinta ta sanya kuɗin wani hoton kati na Beelal ta ɗakko ta tsaya kallon hoton cike da alhinin nisa da ya yi da ita, hoton lokacin Beelal yana tsayuwa aka ɗaukeshi, ƙafar nan marar lafiya ta karkace ya ɗaga hannunsa mai lafiyar sama yana dariya, tunowa da shekaran jiya tana gyaran ɗaki ta ɗakko hoton Beelal da ke game a wayarta ya dakata ya karɓi hoton yana dariya ya ce cikin in'innarsa. "Mama kamar ba ni ba a nan kin ga na girma" Ya faɗa yana dariya. "Eh mana ai kowa ma da haka ya girma, wata rana ma magidanci za ka zama" Ta faɗa tana dariya. "Mama ki bani hoton in ajiye shi a wurina" "Ai wannan hoton babu wanda zan baiwa nawa ne sai dia idan ka girma zan sa a wanka maka shi, sai kaima ka ajiye, amma dai wannan nawa ne, duk inda ka gan shi to ni ce na kaishi wurin dan babu wanda zan iya bawa sai dai in mutuwa na yi" Maganar da suka yi da Beelal shekaran jiya a kan hoton ta faɗo mata, kafin ta ankare sai ganin ɗigon hawayenta ta yi a jikin hoton cikin sauri ta goge hawayen daga jikin hoton ta sanya a cikin jakar. Tsayawa ta yi tana ƙarewa ɗakin kallo yana rayawa a ranta cewar sai kuma in rai ya kai, dan ita dai ta san a ƙudurin da ta yi babu gudu ba ja da baya.Ƙwaɗo ta ɗakko da mukullan ta kulle ɗakin, tana fitowa waje ma ta rufe ƙofar gidan. Shagon mai caji ta nufa wanda suke waya wani lokacin da Hajiya Laɗifa a wayarsa idan Hajiyar ta kira wayar Fatima ta ji a kashe, saƙo ta bashi a kan cewa idan Hajiyar ta kira ya ce mata ta tafi Lagos. Mai machine ta samu ta ce ya kaita Kazaure, a tasha ya sauketa ta biyashi haƙƙinsa motar Kano ta hau suka ɗau hanya. Wajen sha ɗaya da rabi suka ido cikin Kano. "Allah sarki Yayata ki yi haƙuri da abin da zan aikata na san ba za ki ji daɗi ba, sai dai hakan shi ne mafita kuma shi ne kwanciyad hankalina dan matsawar na zauna a nan ban tafi neman Beelal ba to tabbas rayuwata za ta ƙare ne a ƙunci! Ki yafe mini yau gani a cikin garin Kano amma ba wai dan in je gidanki in kai miki ziyara ba sai dan kawai hanya ce ta kawo ni, ki min afuwa Yaya!" Cewar Fatima a zuciyarta tana share hawaye, dan shigowar motarsu garin Kano ya ƙara tada mata mikin abin da ke damunta a cikin ranta. A ƴan kaba aka saukesu, ɗan sahu ta samu ta ce dan Allah ya kai ta inda za ta samu motar da za ta kaita Lagos, har wurin ya kaita ta bashi haƙƙinsa ta samu wuri ta zauna dan ba ma lokacin motar za ta tashi ba. Sai wajen ƙarfe uku motarsu ta tashi, amma duk zaman Fatima a wurin ko ruwa bata sanya a bakinta ba sallah kawai ta gabatar, ko yanzu ma da suke tafiya kanta kawai ta jingina idanunta a rufe tana jin yadda mutane ke ta hira a motar amma ita ko abin da suke cewa bata sani ba damuwar da ke tattare ita ta wargaza mata komai, dan rashin Beelal a kusa da ita ba ƙaramin abu bane. MMN AFARAH 09030283375 ❤️❤️❤️❤️❤️❤️ *BEELAL* 💦💦💦💦💦💦 NA MAMAN AFARAH *FCW*💛 Book 2 Page 1️⃣3️⃣➡️1️⃣4️⃣ *HAMEEDA* Tana ƙoƙarin buɗe baki ta yi magana Musty ya aika mata da wata uwar hararar da ta sanya ta kama bakinta ta yi shiru. Hajiya Zulaiha kallon Mustyn ta yi ganin sai wani kumbura baki yake yana ƙunƙune sai ta ce "Hameeda maza jeki uzurinki" "To" Haeeda ta faɗa cike da ladabi ta tashi ta bar falon. "Haba Mom wai ya kike min haka ne, a gaban wannan ƙaramar yarinyar kina son ta rainani ne?" "Oh wato ka san ma ƙarama ce yarinyar da bata fi 7yrs ba kai kana kusan 19yrs amma kamsr wata sa'arka kawai daga shigowarta sai kake neman dukanta kuma na san halinka babu wani laifi da ta maka" "Ko ma ta mini laifi ko bata mini ba ai dai bakya fifita ƴar aiki a kan ɗan gida ba ko" "Sannu masu gida" Cewar Hajiya tana kallonsa. Alhaji Tahir ne ya shigo da sallama. Amsa masa Hajiyar ta yi shi kuma Musty ya ce "Oyoyo Dad" "Wato baka san ma na dawo gidan ba, daga masallaci fa nake yanzu kana can yawonka na dawo ba yanzu na dawo ba" "Haba Dad yawo kuma ai ina can wajen friends ɗina" "Ohk hakan ma ya yi kyau" Kallonsu kawai Hajiya ta yi ta ɗauke kai abinta ta yi wajen dinning ɗin, su ma bin bayanta suka yi Dad ne ya jawa Musty kujera ya zauna sai shi ma ya zauna Mom ta shiga zuzzuba musu abinci. Sai da suka kammala cin abincin nasu sannan suka dawo falon suka cigaba da hira abinsu. *BAYAN SATI BIYU* Da la'asar sakaliya ne Musty ya shigo gidan da moyarsa bayan mai gadi ya wangale masa get, yana yin parking ya buɗe mptar ya fito hannunsa riƙe da leda, hango Hameeda ya yi tana shanya wasu dosters da ta yi goge -goge shi ne ta wanke su take shanyawa. Tun daga nesa yake kallonta da yake ta bashi baya ne, bata ma san yana yi ba. Wajen ya ƙarewa kallo sai da ya tabbatar ba kowa ya a kusa ya ƙarasa wajenta. "Ke!" Ya faɗa ƙasa-ƙasa. Da sauri Hameeda ta waiwayo dan kwata-kwata bata san da zuwansa wajen ba dan haka maganar da ya mata sai ta ɗan razana. "Ungo nan wuce ki kai min part ɗina ki ajiye mini a falo a kan kujera" Ya faɗa yana miƙa mata baƙar ledar da ke hannunsa. Hannu biyu ta sanya ta karɓa tana ɗan ja da baya ganin ya zo dab da ita ita dama kuma tsoronsa take. "Wuce ki tafi kuma ki yi sauri kin wani miƙo hannu kina ja baya kamar wanda kika ga dodo" Ya faɗa yana miƙa mata ledar. Karɓa ta yi tare da cewa "To" Ta faɗa muryarta har rawa take, haka ta wuce ta nufi ɓangaren nasa duk da bata taɓa ko da bin hanyar ba ma, dan ita bata son duk wani abu da zai haɗa ta da Musty dan ta lura da take-takensa ba ya ƙaunar ko da ganinta ne. Tun da ta karɓi ledar ta kama hanyar part ɗin nasa sai sauri take zubawa da yake da ɗan tazara tsakanin part ɗin da sauran ɓangarorin. Tun da ta juya ta tafi ya shiga waige-waige irin na marar gaskiya wanda ko cikin ruwa gumi yake. Sai da ya tabbatar babu kowa a wajen kuma babu wanda ya ganshi ya kama hanya bi bayanta. Sauri take yi dan so take kawai ta je ta ajiye ta fito masa daga ɓangarensa dan ma kar ya je ya ga wani abu ba dai dai ba ya ce ita ce ta ɓata masa. Da yake wani corridor ne a farko idan ka shiga dan haka kafin ta kai falon sai da ta wuce shi, tana shiga falon ta ajiye ledar a kan kujera kamar yadda ya buƙata, cikin sauri ta juyo za ta fita sai kawai ta ji ta yi karo da mutum, da sauri ta ɗago kanta aikuwa ta sauke su a kan fuskar Musty yana wani washe haƙora tare da shafa haɓarsa da hannun damarsa na hagun ɗin kuma ya kama ƙugu da shi. "Ka yi haƙuri dan ALLAH ban lura da kai ba" Cewar Hameeda cikin sanyin murya. Jin bai ce mata komai ba sai wani kallonta yake hakan ya sanya ta ɗan raɓa shi za ta wuce, aikuwa ya miƙa hannu ya kamo hijabin da ke jikinta, Hameeda da ke tafiya sai ji ta yi an janyo da ita baya ƙiii an dawo da ita ta hanyar janyo hijabinta. Sai da ya dawo da ita gabansa sannan ya kafe ta da ido kamar yau ya fara ganinta, Hameeda kuwa duk da bata san manufarsa ba sai ta ji tsoro ya mamaye ta, a take sai jikinta ya ɗauki karkarwa dan ita duk tunaninta ma dukanta zai yi ko wani laifi ta yi a shigowarta falon yanzu. "Dan, dan Allah ka yi haƙuri Ya Musty" Ta faɗa cike da tsoro. "Haba baby mai kyau laifin me kika yi da kike bani haƙuri in ma laifin ne ni ne nan zan miki shi yanzu, dan na san laifin da zan miki yanzu wataƙila ba za ki taɓa yafe mini ba domin laifi ne da zai ruguza rayuwarki gabaɗaya, laifi ne da zai shafi kowane fanni da kowane ɓangare na rayuwarki wataƙila ma ki kasa yin farinciki har abada!" Ya faɗa yana wani lashe baki kamar tsohon maye. Hameeda kuwa bata san ina kalamansa suka dosa ba sai dai kawai ta tsorata sosai burinta kawai ya sakar mata hijabinta ta fice daga ɓangarensa. "Duk abin da zan miki idan kika sake kika mini kuka ko ihu sai na yanka ki, kuma ij saka ki a buhu in fita da ke in jifa a kwata ba tare da kowa ya sani ba amma idan kika yi shiru baki yi kuka ko ihu ba ana ɗan jimawa zan ce ki tafiyarki har da alawa zan baki" Ya faɗa yana kallon Hameeda da gabaɗaya kan kallonta ka san a mugun tsorace take kamar ka ce kulle ta ce cass. "Kin ji abin da na ce ai ko?" Ya faɗa yana zare mata ido. Kanta ta shiga ɗagawa alamar ta ji. Sakin hijabin nata ya yi, wani sanyi ne ya ratsa zuciyar Hameeda har sauke wata ɓoyayyar ajiyar zuciya, dan duk tunaninta ya barta ta tafi ne, tun da bata yi iju ko kuka ba, tana shirin ɗaga ƙafafunta sai kawai ta ji an yi sama da ita, an ɗaga ta kafin ta tantance sai ganinta ta yi a kafaɗar Musty ya nufi hanyar bedroom ɗinsa da ita, baki ta buɗe za ta yi ihu tunowa da ta yi ya ce idan ta yi ihu ko kuka sai ya yanka ta hajan ya sanya ta sanya hannayenta biyu da toshe bakinta. Yana shiga bedroom ɗin ya nufi kan lafiyayyen gadonsa ya ajiyeta ya koma ya maida ƙofar ya rufe har da sanya mukulli. Hameeda kuwa gabaɗaya jikinta rawa yake dan duk tunaninta ma yankatan zai yi, yana gama rufe ƙofar ya juyo ya fara tahowa wajenta yana washe haƙora hannunsa a kan wandonsa yana cire belt ɗinsa, sai da ya cire belt ɗin ya yi wurgi da ita a tsakar ɗakin, ya cire wandonsa daga shi zai gajeran wando, rigarma ya cire ya wurgar hatta singlet ɗinsa bai bari ba. Gadon ya nufo gadan-gadan Hameeda kuwa ganinshi tuɓe daga shi sai gajeran wando ta sanya hannu ta rufe idanunta bakinta kuwa haɗeshi ta yi ta damƙe dan kar kuka ya fito a yankata.Yana zuwa ya sanya hannu ya fisge hijabin jikinta ya yi wurgi da shi da yake doguwar riga ce a jikinta sai ya shiga kiciniyar rabata da ita, hannu biyu ta sanya ta daddage ƙarfinta ta riƙe rigar dan duk da ƙaracin shekarunta dan a lokacin shekararta shida da wani abu bata ƙarasa shekaru bakwai ba. Amma ƙaracin shekarunta basu kasa sanyawa ta gane manufarsa a kanta ba saboda yadda mahaifiyarta ta koya mata komai kafin barinta duniya, sannan duk da Hameeda yarinya ce amma akwai shegen wayo da gane abu. Dan Ummarta ta sha gargaɗinta a kan kar ta kuskura wani ya cire mata riga ko wando kar ta bari wani ya ce zai taɓa mata wajen fitsarinta ya bata alewa dan duk ranar da ta bari wani ya taɓa mata mutuwa za ta yi, Ummar Hameeda ta yi amfani da hikima shi yasa ta tsoratat da ita da mutuwa dan yaro bai san cutarwar da za a masa ba idan aka masa fyaɗe sai dai ka tsoratar da shi a kan abin da yake tsoro cewar idan fa aka yi kaza to kaza ne zai same shi. Yadda mahaifiyarta ta yi ta ƙoƙari da naci wajen ganin ta koya wa ƴarta abubuwa sai gashi har bayan barinta ma duniya yarinyar bata manta ba shi yasa ake cewa koyawa yaro abu yana da muhimmanci sannan yaro ƙwalƙwalwarsa bata manta abu saboda abu yana zaunawa a ƙwalƙwalwar yaro tamkar rubutu a kan dutse, amma a ta babba tamkar rubutu ne a kan ruwa. Yana da kyau iyaye mata mu koyawa yaranmu abin da zai tsare tarbiya da mutuncinsu tun suna yara hakan zai sanya su taso sa abin a zuciyarsu, ba wai sai sun girma ba a ce za a koya musu ita tarbiya daga gida ake somawa sannan itace tun yana ɗanye ake tanƙwasa shi idan ya bushe aka tarki tanƙwasa shi to zai karye ne Allah sa mu dace amin. Kiciniya suka shiga shi da ita shi yana jan rigar ita kuma ta kama ta daddafe, dan har ta fara saƙawa a ranta idan ya dage sai ya cire mata kaya cizo za ta gantsara masa, ganin ta ƙi saka rigar kuma lokaci yana ƙure masa gashi kuma baya so Mom ɗinsa ta zo, ta same shi dan ya san ko da wane lokaci za ta iya sakkowa daga sama ta fito daga part ɗinta.Hannu ta sanya ya ɗauketa da mari da sauri ta saki rigar ta dafe kumatunta saboda zafi da raɗaɗin mari duk sai ta ji ta gigice, hannunta da ta ɗauke daga kan rigar shi ya bashi damar ɗage mata rigar, aikuwa cikin sauri ta saki kuncin ta mayar za ta riƙe rigar dan har ya kai rigar wajen cikinta , ganin haka sai ya sanya hannunsa ya haɗe hannayenta wuri ɗaya ya riƙe da ɗaya hannun nasa ya shiga ƙoƙarin cire mata pant ɗinta. *FATIMA* Motar su na tsayawa a inda aka tanada dan motoci idan sun kawo fasinja, ta shiga rarraba ido dan ita tun da suka shigo garin Lagos ta shiga mamakin ganin garin dan bata taɓa zato Lagos har ta kai haka ba. Ko ina ta duba mutane take gani hausawa da wanda ba hausawa ba da farko ma ta so ta karaya ganin yadda garin yake dan ta fara tunanin ta ina ma za ta fara neman Beelal? Sai dai kuma da ta tuna cewar duk faɗin gona akwai kunyar ƙarshe kuma duk nisan jifa tabbas akwai ranar da zai dawo ƙasa sannan matambayi bai taɓa ɓata ba, kuma duk wanda ya miƙawa Allah al'amuransa to tabbas zai taimakeshi. Haka ta biyo sahun masu fitowa daga motar tana fitowa ta fara tafiya abinta dan dama ko kaya kala ɗaya bata ɗakko ba daga ita sai ƴar pos ɗinta mai ɗauke da sauran kuɗinta da kuma hoton Beelal yana ƙarami sai ɗan abubuwan da suke a ajiye dama a cikin jakar wanda bata fitar da su ba. Tun da ta fara tafiya take ta kalle-kalle dan ita tun da dai an ce Beelal yana cikin garin Lagos to fa tun shigowar motarsu garin take sanyawa a ranta za ta iya ganinsa haka yasa yanzu ma da take tafiyar nan kawai gani take a kowane lokaci za ta iya haɗuwa da shi dan bawa ba ya fidda rai daga rahmar Ubangiji. Sai da ta yi tafiya mai nisa ta ji ta gaji kuma idanunta ko ƙiftasu bata son yi saboda kar Beelal ya ɓace mata, ganin bata ganshi ba kuma ga yunwa da ƙishirwa sun dame ta dan rabonta da abinci tun daren da Idrisu zai ɗauke Beelal da suka ci tuwo da daddare tare da Beelal ɗin. Gashi kwanansu biyu a hanya kafin suka ƙaraso amma bata sanya komai a cikinta ba ta san dai ta sha ruwa a hanya sai kuma waji cincin da ta siya ta ɗan ci shi ma dan ta ga tana ganin jiri saboda yunwa. Wani wurin siyar da abinci ta zo wucewa wata mata tana daga gefen wurin inda aka tanada dan wanke-wanke tana wanke-wanke, rumfar wurin kuma ga mutane nan maza da mata kowa yana sabgar gabansa wasu na cin abinci wasu suna hira. Ƙarasawa wurin Fatima ta yi bakinta ɗauke da sallama duk da idan ka ganta ka san tana cikin damuwa sannan ga uwa uba yunwa daje tare da ita.kowa yana uzurinsa sai wani matashin saurayi ne amsa, wanda yake zaune yana cin abinci kuma wata budurwa ta kawo masa wani abu a baƙar leda da alama wani abincin ne zai tafi da shi. Ƙarasowa wurin ta yi babu wanda ya kula da ita, saurayin nan ne da ke cin abinci ya tsaya yana kallonta, ganinta gabaɗaya kamar a birkice take amma kuma ya ga da hankalinta ba mahaukaciya bace sai ya danganta hakan da yunwa ce ko kuma babu ma'ana talauci. Ganin haka sai ya ɗauki abincin da yake ci ya bata dan duk tunaninsa neman taimako take, Fatima kuwa kai ta jijjiga msa alamar a'a hakan ya sanya ya ajiye plate ɗin abincin a wajen dan dama ya gama tafiya kawai zai yi, ledarsa kawai ya ɗauka ya fito daga rumfar, wani machine da ke fake wurin daga gefe Fatima ta ga matashin saurayin nan ya je ya tada machine ɗin ya hau ya tafi abinsa. "Me kike so?" Wata murya da hausa bata gama ratsata ba ta jefowa Fatima tambayar. ❤️❤️❤️❤️❤️❤️ *BEELAL* 💦💦💦💦💦💦 NA MAMAN AFARAH *FCW*💛 Book 2 Page1️⃣5️⃣➡️1️⃣6️⃣ *BEELAL* Duk yadda yake zaga wurin ko sau ɗaya bai buɗe baki da sunan yin bara ba. Kawai zagaya wuraren yake amma ko kaɗan ya kasa buɗe baki ya yi bara, ga yunwa bashi da karazana ko kaɗan, dan gani yake ma tuƙin keken ma kamar ba zai iya ba. Wanda Allah ya sa yana miƙa masa kuɗi ko a bashi abinci. Tun da suka ƙaraso wajen da yake suka tsaya daga can gefe, Idrisu sai harara yake aika masa amma Beelal bai ma san suna yi ba, hankalinsa ba a kan su ba yake, ya tafi tunanin Mamarsa. Idrisun ne ya cigaba da tsayuwa a wajen shi kuma Imran ya gewaya a hankali yadda mutane ba za su lura ba ya je wajen Beelal ɗin cikin ɗaure fuska ya kalli Beelal ɗin ya ce "Dalla ka wani zo ka tsaya a wuri ɗaya kai baka yi barar ba ka tsaya sai kallon mutane kake kamar ka ga hoto" "Ina yi mana" Cewar Beelal da sai lokacin ya lura da Imran. "A gidan uban wa kake yi, ka ɗauka duk ba ma ganinka to duk abin da kake muna hangoka, bani abin da aka samu" Ya faɗa yana miƙa wa Beelal ɗin hannu. Ledar ya miƙa masa tare da sanya hannu a aljihunsa ya ɗakko kuɗin ya miƙa masa,lissafawa ya yi, ya ga ɗari uku da arba'in ne sai da ya duba ya ga babu wanda ya lura da su ya ce "Wallahi ka kutsa cikin mutane ka ware murya ka yi bara ta kirki ka samo mana abubuwa, dan wannan in'innar ma sai kana danneta saboda ake fahimtar bara kake, dan na ga alama in'innar za ta sa ake kasa gane bara kake ko roƙo, ko kuma waƙa, murya ce gabaɗaya a dagule" Imran ya faɗa yana yiwa Beelal wani kallo tare da miƙa masa wata ledar da zai cigaba da zuba abincin in ya samu, juyawa ya yi, ya bar wajen, da kallo kawai Beelal ya bishi yana jinjina rashin tausayi da imani irin na Babansa da abokinsa su basa ma ta shi kawai ta kansu suke ya samo abincin amma sai hannu ya suɗe sun karɓe za su je su cinye dan zalunci. Imran na ƙarasawa inda Idrisu yake suka bar wajen suka koma ƙasan wata bishiya kusa sa wata mota suka zauna suka cinye abincin suka sayi pure water suka sha abinsu. "Gaskiya abokina ba ƙaramar dibara ka mana ba da ka taho mana wannan annakasun" Cewar Imran yana cilla ledar pure watern da ya gama sha, sama ya bugata da ƙafarsa ta yi gefe guda. "Ai nake faɗa maka sai da na yi dogon tunani kafin na yanke hukuncin" Idrisu ya faɗa yana wani washe baki jin abokinsa ya yabe shi da abin da ya yi. "Aikuwa dai ka ceto mu daga yunwa da rashin kuɗi, ji fa yanzu ba ko asinmu amma mun ci mun sha har da kuɗin kashewa gashi za mu raba, dan ma dai na ga kamar har yanzu bai saki jikinsa ba yana ɗari-ɗari da abin da za mu samu ma ya fi haka" "Rabu da shi zai ware ne, yanzu dan farko ne amma idan ya ga dole uwar naƙi dole ya rage dantse ya samo mana ko dan ya ci shi ma, dan idan bai samo da yawa ba yana ji yana gani za mu cinye ɗan wanda ya samo ɗin" Idrisu ya faɗa yana dariyar ƙeta. "Kana lokacinka nawan" Cewar Imran yana miƙawa Idrisu hannu suka tafa. Beelal kuwa ganin sun karɓe abincin da kuɗin sai ya rasa ma ya zai yi dan yunwa yake ji kamar me gashi kuma la'asar ta yi sosai, haka ya shiga can ciki yana bin wurin sana'ar mutane yana tsayawa wani wajen a koreshi, wani wajen a tambayeshi mai zai siya, idan ya ce sadaka yake nema sai a hantareshi a ce barar ce kuma ba za kake yi da bakinka ba sai ka tsayawa mutane zoƙoƙo. Hakan ne ya sanya Beelal ɗin ya cigaba da tafiya sai dai yana bara saboda ya ga ba a bashi sadaka saboda ba ya bara dan haka babu yadda ya iya ba dan ransa ya so ba haka ya shiga faɗin. "A taimakawa almajiri da sadaka, almajiri yana bara" Amma duk lokacin da zai ambaci sadaka sai ya ji wata ƙwalla ta kawo idanunsa saboda ya san dai ragas yake Allah bai masa nakasar da zai ke yin bara ba. Cikin iko da hikima ta ubangiji sai kawai yake ta samun sadaka, dan sai ya ga jama'a ma kamar shi kaɗai suke baiwa sadakar saboda idan ya ce "A taimakawa almajiri da sadaka, almajiri yana bara" Sai kuma ya ƙara da cewa. "Duk wanda ya bayar domin Allah, Allah zai mayar masa fiye da abin da ya bada" Wannan hikimar d ya sanya a cikin barar tasa ita ce ta sanya mutane ko basu da niyyar bashi sadakar sai su bashi, shi kuma wannan hikimar maganar ya koya ne a wajen Mamarsa, saboda idan suna da ishashshen abin da za su ci, kuma sai almajiri ya yi bara to tana kiran almajirin ne ta bashi ko da a cikin wanda za ta ci ne, idan Beelal ɗin ya ce "Mama ya kika bayar da abincin da za ki ci kika bar ɗan kaɗan?" Sai ta ce masa "Beela ai duk wanda ya bayar domin Allah to Allah zai mayar masa fiye da abin da ya bada, ka ga kenan idan na bai wa almajiri sai Allah mu ma ya ƙara kawo mana ta wata hanyar da bamu yi zato ba" Wannan abin da take faɗa masa ne yasa yake saka hikimar maganar tata cikin barar tashi sai gashi kuma hakan ya sanya yana samun sadaka, lallai abin da uwa za ta koya wa ƴaƴanta ba iya lokacin zai musu amfani ba har da bayan wasu lokutan ma dan yanzu gashi Beelal ya yi amfani da abin da ya koya daga mahaifiyarsa ya samu hanyar samun bara cikin sauƙi.Tabbas tarbiya ba ƙaramin makami bane mai kyau da uwa take bai wa ƴaƴanta wanda wannan makamin zai amfane su duniya da lahira, mahaifya ta gari idan ta bai wa ƴaƴanta tarbiya mai kyau haƙiƙa tana jifan tsuntsu ne da dutse biyu, tarbiyar za ta amfane su duniya ne da kuma lahira. Sai da ya ji an fara kiran sallar magriba ya fara tuƙo keken yana fitowa daga cikin jama'a, yana ta kallon yadda mata inyamurai ke ɗakko ƙaton baho ko daro a kansu cike da kaya, tabbas ya jinjina musu dan ya san hausawan mu ba za su yi haka ba. Yana fitowa ya hangi wurin da ya ga su Imran suna tsaye amma basa wurin hakan ya sanya ya rinƙa kutsa mutane ya samu ya fito ya samu gefe guda, cikin abincin da ya samu, ya sanya hannu ya fara ci, sai da ya ɗan ci amma ba sosai ba dan yana tsoron kar ya ci ya ƙoshi su gane ya ci su masa wani abun. Ledar ya ƙulle ya rataye ta a jikin hannun keken nasa, masallacin da ke kusa wanda ya ji ana kiran sallah ya nufa yana zuwa ya ajiye keken a gefe guda, aikuwa sai da ya faki idanun mutane ya tashi tsaye daga kan keken gudun kar a ganshi da ƙafarsa a ce ya hau keken guragu mutane ba a iya musu duk da ma dai akwai nakasa a jikinsa amma ba wacce zai hau keken guragu ba. Wajen famfuna ya nufa ya yi alwala ya shiga masallacin sai da ya yi sallar la'asar dan bai yi sallah ba amma Idrisu bai damu da ya ce ya yi sallah ba ko abincin da zai sanya a cikinsa, ko dan shi ma Idrisun sallar ba damunsu ta yi ba. Ya idar da sallar kenan sai aka tada sallar magriba dan dama wa'azi aka gama a masallacin shi ne kuma za a yi sallah. Bayan an idar da sallar ya yi addu'arsa sai ya fito ya ƙarasa wajen keken, idanun mutanen dai ya faka ya hau keken ya baro cikin masallacin, yana fitowa kwa ya hango Idrisu da Imran sai sintiri suke a wajen suna nemansa, hangoshi da suka yi, ya fito daga masallacin cikin hanzari suka nufo shi suna wani zare "Kai gurgun mage ina ka tafi ka sa sai duba ka muke a wajen nan?" Idrisu ya jefa masa tambayar yana kallon ledar da Beelal ɗin ya rataye a jikin keken wacce abinci ne da yawa a ciki. "Masallaci na shiga na yi sallah, ko la'asar ban yi ba" "To sallau, wato kai ga mai sallah to mu nan ko azahar bamu yi ba" Imran ya faɗa yana kallonsa. Shiru ya yi shi dai Beelal bai ce komai ba dan shi in banda larura ma babu yadda za a yi ya haɗa salloli amma su gasu manya da su wai ko azahar basu yi ba kuma gashi yanzu har an yi magariba, kuma ko alamar yin niyya babu a tare da su. "Kawo kuɗin" Cewar Idrisu. Hannu ya sanya a aljihun nasa ya fito da duka kuɗin dan a farar leda ma ya sanya sannan ya sa a a ljihun. Su duka baki suka washe ganin har da ƴan ɗari biyu guda biyu a ciki sauran kuma canjuna ne, lissafawa ɗari takwas ne da naira ashirin. Hannu Imran ya sanya a cire ledar abincin ya ce. "Miƙo hannunka mu san maka abincin" Hannu Beelal ya haɗe duka biyun Imran ya zuba masa abincin, Idrisu naira ashirin ɗin ta saman kuɗin ya miƙa wa Beelal ya ce. "Karɓi wannan in ka tafi hanya ko za ka siyi wani abu ka ƙara" Abincin hannun nasa ya cinye ya karɓi ashirin ɗin. "Ai dai ka ga inda muka biyo a tahowa, waccen hanyar inda da wancan motar yashin take tsaye, ka bi nan ka koma shagon namu, mu akwai inda za mu je" Cewar Imran yana kallon Beelal. "To" Kawai Beelal ya ce ya juya kan keken nasa ya tafi, su ma suka kama gabansu. Wata mai soya dankalin hausa ya bai wa ashirin ɗin ita ma da ta tausaya masa ganinshi a kan keken gurragu kuma ga in'inna kawai sai ta cika masa farar leda. "Duk na ashirin ɗin ne wannan" Ya faɗa da mamaki. "A'a sadaka na baka sauran" Mai dankalin ta faɗa tana murmushi dan sai ta ji ya birgeta ganinshi mai nakasa kuma mabuƙaci amma kuma har yana buƙatar halal ɗinsa kawai. "Allah karɓa, ai na ɗauka ko baki lissafa dai dai bane" "Ina sane" Ta faɗa tana zubawa wani fa ya sayi dankalin a baƙar leda. Haka ya kama hanyar da suka biyo da su Imran yake tafiya da yake ma unguwar duk jama'a ne sai ya zama ko ina ma akwai mutane ga haske tarr kamar safiya, cikin ikon Allah sai gashi ya gane shagon, a buɗe ya ga ƙofar lokacin da ya zo, keken ya ajiye yana jin bayasa duk ya ƙage ga mazaunansa duk ciwo suke saboda zaman kan ƙarfen keken. Daga bakin ƙofa ya tsaya yana yin sallama hannunsa riƙe da ledar dankalinsa. Amimulla da ke ciki jin muryar Beelal sai ya tashi da sauri ya fito aikuwa yana fitowa ya ga Beelal ɗin ne wani tausayin yaron ne ya ji ya kama shi hakan ya sanya ya amsa masa sallamar tare da miƙa hannu ya kamo Beelal ɗin ganin shi kaɗai ne babu iyeyen gidan nasa wato su Imran 09030283375 ❤️❤️❤️❤️❤️❤️ *BEELAL* 💦💦💦💦💦💦💦 *BOOK 2* FCW Book 1 free Book 2 paid 300 Mai buƙata zai biya ta asusun Fa'iza abubakar unity bank 0020281885 Shaidar biya ta 09030283375 Last free page 1️⃣7️⃣➡️1️⃣8️⃣ *HAMEEDA* Gabaɗaya ta yi narai-narai da ido za ta yi kuka, sai dai tuna furucin Musty a kan yankan da yace zai mata sai ta fasa sakin kukan, hannu biyu ta sanya ta dafe pant ɗinta, shi kuma ya shiga kiciniyar rabata dashi, amma duk yadda ya so ya cire pant ɗin abin ya faskara dan dama da ya haɗe hannayen nata ya riƙe ƙafafunta da take haurawa tana bangajarsa da su hakan ya sanya shi sakin hannayen nata ya maida hankali wajen cire mata wandon. Hakan ne ya bata damar riƙe pant ɗin nata gamgam taƙi sakawa, dan duk da ƙarancin shekarunta amma bata manta yadda Ummarta ke nuna mata kar ta yadda wani ya cire mata wando bare har ya taɓa mata wajen fitsarinta, da yake komai yana zama ne a ƙwalƙwalwar yaro shi yasa bata manta da hakan ba duk da cewar mahaifiyar tata bata duniya amma tarbiyar da ta bata tana nan zaune daram a ƙwalƙwalwarta, shi yasa ake son kar ka raina ƙanƙantar yaro ka ce wai sai ya ƙara girma zan koya masa abu kaza da kaza shi yaro abu yana zama a kwanyarsa fiye da yadda zai zauna a kwanyar babba. Dan abu a kwanyar yaro tamkar rubutu ne a kan dutse baya goguwa saɓanin abu a kwanyar babba da yake kamar rubutu ne a kan ruwa gogewa yake. Ganin ƙaramar yarinya na son wasa fa damarsa da kuma lokacinsa sai ya sanya mugun ƙarfi ya fisgi wandon nata daga gefe guda cikin nasara kuwa sai pant ɗin ya yage daga kan ɗinki, amma dan ƙarfin hali irin na Hameeda sai ta ƙara riƙe saitin da ya yaga mata, cikin fusata ya sanya hannu ya hankaɗata ta faɗi reran a kan gadon, haka ya haye kan gadon jikinsa babu kaya sai ƙaramin wando dan ya sanya a ransa a yau sai ya biya buƙatarsa da yarinyar dan shi babu abin da ya fi masa sama da ya kusanci ƙananan yara ya lalata musu rayuwa babu ruwansa su yi rai ko su mutu. "Mustapha, Mustapha,Mustapha" Musty ya jiyo muryar Mom tana ƙwala masa kira daga falo kamar ta ari baki, wani irin miƙewa ya yi tare da sakkowa daga kan gadon cikin ɗaga murya ya shiga amsawa a lokaci guda kuma yana ƙoƙarin maida kayansa. Hameeda zaune ta tashi a kan gadon tare da kama wurin da ya yaga mata wandon ta shiga ƙullewa ta ja rigar tana rarraba ido, yana gama maida kayansa hakan ya yi dai dai da kama handle ɗin ƙofar da Mom ta yi domin buɗewa jin ƙofar a rufe sai ta shiga nocking tana kiran sunan Musty. Musty kuwa gabaɗaya hankalinsa a tashe yake bashi da wata nutsuwa ko ƙwayar zarra a yanzu gabaɗaya hankalinsa ya ɗugunzuma zuwa maɓoyar da zai sanya Hameeda a ciki, waige-waige ya shiga yi har dai ya samu wurin da ya ɓoyewa ta tare da zare mata ido ya mata gargaɗi a kan kar ta kuskura ko tari ta yi bare magana ko kuma ta yi yunƙurin fitowa. Sai da ya murje idanunsa suka yi ɗan ja sannan ya buɗe ƙofar yana wani yamutsa fuska irin ta mai bacci, Mom kuwa gadan -gadan ta nufi shigowa ɗakin sai matsawa ya yi ya bata hanya ta wuce ciki shi ma ya mara mata baya. A jikin mudubi ta ɗan jingina da katakon ta zubawa Musty ido da ya ƙaraso yana sakin wata uwar hamma ta mai bacci amma baccin ƙarya, ya samu bakin gadon ya zauna yana fuskantar Mom ɗin. "Wai yaushe ma ka dawo? Ina aiken da na maka? Kawai sai motarka na hango kuma ashe har kana nan kana bacci" "Kaina ke mini ciwo Mom ina dawo wa ban samu ƙarasawa ɓangarenki ba na zo na kwanta dan in ɗan ji sauƙi shi ne bacci ya samu nasarar ɗibana" Cewar Musty cikin muryarsa ta baccin ƙaryar da ya ƙirƙira. "Ayya sannu ni fa in ce ashe dai akwai abin da ke damunka shi yasa baka je ka faɗa min aiken ba" "Eh, eh, eh" Cewar Musty da ke ƙoƙarin bai wa Mom amsar sai dai haɗa ido da hijabin Hameeda da ya yi wanda ke yashe a ƙasan ɗakin ya sanya gabansa mugun faɗuwa har hakan ya sa maganar da yake son yi ta zama inda-inda shi bai san dalilin da yasa yarinyar bata ɗauke wannan ƙazamin hijabin nata ba, kuma shi ma da yake ba a nutse yake ba burinsa kawai ya ɓoyeta sai bai lura da hijabin ba, gashi tana neman ta jaza masa jaraba a kansa, dan idan Mom ta ga hijabin ai asirinsa ya gama tonuwa . Cikin sauri ya faki idon Mom ya sanya ƙafarsa ya tura hijabin ƙasan gadon ba tare da Mom ta lura da abin da ya yi ba. "Eh me?" Ta tambaya tana kallonsa dan ta ga ya ɗan ruɗe sai dai bata san dalilin hakan ba. "A'a cewa na yi eh akwai abin da ke damuna, amma ai na karɓo miki saƙon naki" "Ohk yana ina?" "Yana falo a kan kujera, dama nufina idan na ji ɗan dama-dama sai na miƙa miki" "Ayya sannu bari in ajiye maka wannan sai in ɗan barka ka huta in na fita na ɗauki saƙon nawa" Ta faɗa tana barin jikin mudubin tare da yin hanyar bayi da wasu robobi guda biyu a hannunta da sai yanzu Musty ya lura da su amma ya ta,allaƙa hakan da rashin nutsuwar da yake ciki da kuma ruɗu shi ya sa bai ga robobin ba. A sukwane ya tashi daga bakin gadon da yake zaune, wanda shi ma bai san hakan ba sai dai ganinsa da ya yi tsaye cankarkar a kan ƙafafunsa yana zare ido kamar wanda ya yiwa sarƙi ƙarya dama ƴan magana sun ce marar gaskiya ko a ruwa gumi yake. Aikuwa cikin sauri ya sha gaban Mom yana ƙirƙirar dariyar yaƙe ya ce "Mom mai za ki yi a bayina kuma?" "Haba Mustapha kai da baka da lafiya ya za ka taso, kuma ma mai zan yi a bayi wurin da ba kicin ba shi ba ɗaki ba, wannan robobin da kake gani shampoo ne da conditioner wanda na maka odar ɗinsu kwanaki sai jiya suka ƙaraso to shi ne zan ajiye maka" Ta faɗa tana ɗaga masa robobin hannun nata.Kafin ya haɗa kalmomin da zai rinjayeta ta fasa shiga bayin ta kewaye shi ta nufi bayin gadan -gadan. _FATIMA_ "Tambaya nake dama?" "Tambaya kuma" Matar ta tambayi Fatima cikin mamaki. "Eh tambaya nake, wani nake nema sunansa Idrisu" Ta faɗa tana kallon matar. "Ikon Allah wato dai matar nan ke ba ma ki san wanda kike tambaya ba ko wani ne ya ce miki a nan wurin yake zama?" "A'a ni ban sani ba, hasali ma daga arewa na taho nemansa mijina ne" Cewar Fatima cikin sanyin murya. Tabbas ta ƴan magana ne da suka ce in da ranka kasha kallo, in ba ƙarfin hali ɓarawo da sallama ba ma za yi ki taho tun daga arewa ki zo neman mijinki, bayan in ban da rashin godiya irin na wasu matan mijinki ya barki ya taho nemo muku abinci, amma ki biyo shi, saboda son zuciya da kishi gani kike nan ɗin wani saɓon Allah yake aikatawa ko wani abun da ban wanda bashi ya zo yi ba, to yanzu ko zaki yi shekara kina zaga garin Lagos ai ba za ki ganshi ba" Cewar ɗaya daga cikin masu cin abinci a wurin. "Ikon Allah wai mai yasa mutane suke da saurin yanke hukunci ba tare da sanin ainihin gundarin magana ba? Daga tambaya kai baka san mai ya baro da ni gida ba har na biyo shi amma ka saki baki kana ta faɗar maganganu mararsa kai da ƙafa, Allah na tuba idan ba dalilin Beelal ba ni mai ma zai sa na ɗakko hanya na biyo bayan Idrisu tun daga arewa zuwa kudu, to ma kishin mai zan yi? Mutumin da bai sauke nauyin haƙƙinmu a kansa bane har zan ɓata lokacina wajen yin wannan doguwar tafiya da bibiyar rayuwarsa, ai komai ya yi kansa kuma kowa ya aikata da kyau zai ga da kyau" "Malama ki bar nan ki ƙara gaba ko kya samu wanda za su ɓata nasu lokacin a kanki, amma ba dai a nan ba" Matar nan ta faɗa wanda hakan ne ya katsewa Fatima zancen zucin da take. Cikin sanyin jiki ta juya ta bar wajen, tana jiyo muryarsu suna ta faɗar son ransu a kanta. Haka ta dinga tafiya tana ta kalle-kalle tana fatan Allah sa ta yi gam da katar na haɗuwa da tilon ɗanta a hanya, amma haka ta karaɗe wajen gabaɗaya amma ko mai kama da Beelal bata gani ba sai dai ta sha ganin masu nakasa a hanya wanda hakan ke sanya ta ji raunin zuciyarta ya ƙaru sannan damuwar son ganin Beelal ɗin ta ninku a ranta. Har ƙarfinta ya ƙare amma bata samu cimma burinta ba na ganin Beelal ko kuma Idrisu wanda zai sada ta da Beelal ɗin. Duk lokacin sallah ta kan siya pure water ta yi alwala ta gabatar da sallah, a haka har ta ƙaraso wata unguwa mai shiru kamar ba mutane kowa yana cikin gida sai mutane jifa-jifa da ke ɗan wucewa, lokacin ana kiran sallar magriba ƙarewa unguwar kallo ta tsaya yi kamar mai son gano wani abu, daga ƙarshe dai ta samu ƙofar wani gida wanda ke da benci a wurin ta yada zango a kan bencin.Shiru ta ɗan yi a ranta tana ƙiyasta ina ma za ta hango Beelal yanzu da bata san irin farincikin da za ta tsinci kanta a ciki ba, amma ina... Hakan bai samu ba a haka ta yi alwala da sauran pute water guda ɗaya da yake wurinta ta shimfiɗa ɗankwalinta ta gabatar da sallar ta yi addu'o inta a kan samun nasarar abin da ta zo nema wato ɗanta. Tana nan zaune a wajen har aka kira sallar ishsha'i, ta yi sallar ishsha'in bayan ta kammala ta koma kan bencin ta zauna ta lula duniyar tunani. "Allah sarki rayuwa kenan wato shi bawa babu abin da ya sani wanda zai faru a yau ko gabe Allah shi ne masanin haka, da a ce na san Idrisu zai ɗauke Beelal da a ranar ko runtsawa ba zan yi ba bare har ya samu damar hakan. Amma kaddara ta riga fata, bawa bai san mai zai faru ba hakan ya sanya ma ubangiji ya ɓoye wa bawa ranar da ajalinsa zai sauka, dan da a ce mutum ya san ranar mutuwarsa da zai rayu ne cikin tashin hankali amma cikin hikima ta ubangiji sai ya ɓoye hakan, ko da a ce saura minti ɗaya ne tak a ɗauki ran mutum amma sai ka ga bai sani ba. Wannan kaɗai ya isa ya sanya bawa yin abubuwan masu kyau domin samun yardar ubangiji" Ƙaran buɗe get ɗin gidan da Fatimar ke zaune a ƙofar shi ya dawo da ita daga tunanin da zancen zucin da take, mota ce ta fito daga ciki, sannan wani mutumi ya ja get ɗin ya rufe da alama dai mai gadin gidan ne. Da ido Fatima ta bi motar da ta zo ta wuce ta gabanta wacce ke ɗauke da gilashi baƙi wanda hakan ba ya barin na waje ya hangi wanda ke cikin motar. Har motar ta ɓacewa ganin Fatima sannan ta koma ta ɗan kishingiɗa a kan bencin. Jin ta take garau babu alamar bacci a tare da ita bare kuma yunwa, tabbas ashe dai lafiya da kuma kwanciyar hankali ke sanya mutum jin yunwa har ya ci abinci sau uku a rana ko ma fiye da hakan, amma ita yau da take cikin wani hali sai ta ji yunwar ma bata ji Kimanin awa guda kenan sai ga motar ta dawo, har motar ta gifta Fatima sai kuma cikin sauri motar ta dawo da baya, sai da ta zo dai dai inda Fatimar ke zaune ta tsaya cak, hakan ya sanya Fatima saurin tashi zaune daga kishingiɗen da take ta shiga wurwurga ido gabanta na faɗuwa, dan bata san su waye a cikin motar ba sannan mai ya tsayar da su a wajenta, alkairi ko akasin haka? Shin korarta za su yi daga ƙofar gidansu ko kuwa taimakonta za su yi, ko kuma wani abu ne yake tafe sa su saɓanin abubuwan da zuciyarta ta ƙiyasta mata... Shin ya rayuwar Beelal za ta cigaba da kasancewa a garin Lagos? Rayuwarsa a hannun mahaifinsa da abokin mahaifinsa da basu da tausayi bare imani sai tarin son zuciya. Menene dalilin tsayuwar motar wannan a gaban Fatima shin su waye a ciki? Ya Fatima za ta kasance a cikin Lagos yaushe ne za ta haɗu da Beelal a kwana kusa ne ko sai an ɗauki dogon lokaci. Ina labarin Hajiya Laɗifa wane hali za ta tsinci kanta idan ta samu labarin barin Fatima da Beelal arewa? Shin wace waina za a cigaba da toyawa a wannan gidan da basu da alƙibla masu bahagon aƙida wanda basu san komai ba sai ƙyamar nakasassu, shin waye ɗan da Hajiya Nuratu ta haifa mai zai zame musu a cikin gidan? Akwai tarin tambayoyi wanda ake buƙatar amsar su, da kuma wasu abubuwan da sai dai wanda ya karanta labarin Beelal har ƙarshe zai sani, dk amsoshin suna tattare da 300 da zaki biya kuɗin karatu ki karanta har ƙarshe ba tare da kn jira wani ya samo miki ba wataran ma ki rasa wani page ɗin. Ko daga yau zaki iya biyan kuɗin karatunki, alƙalamin maman afrah ba ya rubuta shirme😍 Mai buƙatar buk 1 ya min magana kyauta ne, mai son buk 2 ya biya 300 idan complt ne 500 09030283375