BDƘB3P001 Manal ta buɗe idanu tana kallon Mama gaban ta na faɗuwa sosai tsoron ta ya bayyana a fili ƙarara, ƙirjin ta har ɗagawa yake saboda tashin hankalin abinda Mama tace wanda ko a mafarki bata shiryawa jin sa ba. Abinda bata yi zato ba shine ya fito daga bakin Mama, shiyasa hankalin ta ya taji har ta rasa abinda zata ce sai kallon amma da take yi idanu a waje. Daƙyar ta iya buɗe baki tace, “Mama ban gane abinda kika ce ba, kaina ya kulle ki yi min bayani yadda zan fahimta.” Mama ta kalle ta tace, “baza ki gane ba Manal, Daman bana so ki gane ɗin ki cigaba da zama da kai a kullen kai zai fi miki amfani, koda na so ki gane hakan ba ganewar zaki ba. Ki cigaba da zama cikin rashin sani. abu ɗaya na sani kin gama auren Adnan, babu ke babu shi har abada.” Manal ta tsorata sosai ta kalli Mubeena da take tsaye itama cikin tashin hankali ta sake kallon Mama tace, “Mama kin saka ni a ruɗani, ki cire ni daga cikin wanna ruɗanin don Allah. Zuciyata bugawa take kamar zata fito, ki taimaka ki sanar dani Mama.” Mama ta kulle ido ta buɗe tace, “baza ki taɓa fita ba Manal, baza ki fita daga cikin ruɗanin da kike ciki ba, gwara ki yi ƙoƙarin daidai ta hankalin ki tun kafin shima ya gushe. Mubeena tace, “Kenan Mama mahaifin Adnan mijin Manal shine mahaifin mu ko me kike nufi? Bamu gane ba ki ganar damu don Allah.” “İn zuciyar ku haka ta ɗauka ki ɗauka haka ne, in zuciyar ku ba haka ta ɗauka ba ku ɗauka ba haka bane. Abu ɗaya na sani kawai, auren Adnan da Manal tamkar rubutu ne a kan ruwa.” “Mama don Allah ki fahimtar damu” Mubeena ta faɗa cikin nata tashin hankalin. Mama ta daka mata tsaya tace, “baza ku fahimta ba, na faɗa muku baza ku gane ba meyasa ku ka cika naci ne? A bar maganar a wajan nan bana so a sake tayar da ita, bana so wata ta sake yi min maganar nan yanzu ko nan gaba. Ko waye shi a wajan ku a bar maganar nace” ta kalli Manal tace, “ki rubuta a zuciyar ki babu ke babu Adnan indai ina da rai” tana gama faɗar hakan ta bar tsakar gidan duk suna tsaye ko wacce da kalar nata ruɗanin. Mubeena tunanin ta kenan mahaifin Adnan mahaifin su ne, a yadda Mama tayi maganar Manal da Yayan ta take zaune matsayin matar sa ko me? Kenan mahaifin tane ya nemi yin lalata da ita?. To in ba mahaifin su bane waye shi? Ga Mama tace auren Manal da Bebi babu meyasa tace hakan?. Numfashi ta sauke babu mai bata amsa sai Mama, Amma zuciyar ta gabaɗaya babu daɗi, tsoro ya cika mata zuciya bata so tunanin ta ya zama gaskiya. Manal ma tunanin da take yi kenan, waye mahaifin Adnan a wajan ta? Uba ko kuwa uban miji?. Waje ta samu ta zauna a tsakar gidan ta rasa ma wanne tunani zata yi a lokacin, kawai ta dafe kai tayi shiru ta rasa abinda yake mata daɗi, Mama ce kawai zata fitar dasu daga wannan tashin hankalin gashi Mamn taƙi bada damar hakan. Tun fitar su Mama Bebi ya daskare a wajan tana kallon Abba da ya kasa motsi ya zubawa ƙofar da su Manal suka fita ido, Mummy ta kalli Bebi da yake tsaye suke haɗa ido ta sake kallon Abba da ya kasa motsin kirki tace, “Wacece ita? Ka san tane?.” A lokacin ya dawo daga tunanin sa ya kalli Bebi yace, “itace mahifiyar matar ka da gaske ko wasa?.” Bebi zuciyar sa bugawa take yi sosai saboda tsoro da tashin hankali yace, “itace Abba, Akwai abinda ya faru ne?.” “İnnalillahi wa’inna ilaihir raji’un!, kuma wannan yarinyar ma da suka zo tare ƴar ta ce?.” Bebi yace, “eh, yayar matar tawa ce sunan ta Mubeena. Abba me yake faruwa ne haka?.” Tissue ɗin da take gefe a ajjiye Abba ya zara ya goge gumin da yake yi tsatstsafo masa, ya kasa cewa komai tashin hankali ya gama dabaibaye shi. Kenan Mubeena da yake so da aure ƴar Zahra ce? Kenan Mubeena da ya nema a baya dan yayi lalata da ita ƴar Zahra ce?. A bayyane yace, “Ya rasulillahi! Ina zan kai wannan lamari?.” Kallon sa su Bebi suka yi Bebi ya matso kusa dashi yace, “Abba don Allah ka yi min bayani, Wacece ita a wajan ka?.” Bai iya cewa komai ba ya juya kawai ya fita da sauri, Bebi ya kalli Mama yace, “Mummy me yake faruwa ne haka? Meyasa tace Manal tazo su tafi? Meyasa tunda taga Abba ta canja?. Meye alaƙar su dashi har haka?.” Mummy tace, “nima tambayar da zan maka kenan, Wacece ita a wajan sa?.” Da sauri Bebi ya fita hankalin sa a tashe yake sosai so yake yaji abinda yake faruwa kawai ko hankalin sa zai kwanta. Office ya shiga ya kira wayar Manal ba jimawa ta ɗauka yace, “Me yake faruwa Manal? Daman Mamaa ta san Abba ne?. Ko kuma ta san fuskar sa a lokacin da abin nan ya faru a tsakanin ku?, ki yi min bayani Manal zuciyata ta gaza ɗauka.” Manal murya a raunane tace, “ta san labarin amma bata san shi ba, kuma ban faɗa mata ba, hankalina a tashe yake domin Mama ta ƙi yi mana bayanin abinda yake faruwa, daga ƙarshe tace kar wanda ya sake yi mata maganar.” Bebi yace, “kuma bata faɗa miki komai ba?.” Manal tace, “tace min indai ita ta haife ni aure na dakai ya ƙare, Mama tana cemin wanda nake kallo matsayin uba a wajan ka nima ubana ne.” “Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un! Kin san abinda kike faɗa kuwa? Kin ji yadda zuciya ta buga da jin wannan kalaman naki?.” Manal tace, “nima a yanayin da nake ciki kenan.” “Wanda kike kallo matsayin uba a wajana kema uba ne a wajan ki, me Mama take nufi da wannan kalaman nata? Manal don Allah ki faɗin min kafin zuciyata ta buga.” Manal a raaunane tace, “nima ban sani ba, iya abinda tace min kenan bayan shi tace kar na sake yi mata maganar. Mama tace min babu ni babu kai har abada, na tambayi dalili taƙi faɗa min.” Bebi salati kawai yake yi a zuciyar sa tsoro ya gama mamaye masa zuciyar sa jin abinda Manal take faɗa. Manal tace, “ka tambayi Abban ko zai maka bayani.” Bebi yace, “Manal shima Abba yaƙi cewa komai, ƙarshe yayi tafiyar sa ya bar ni a tsaye ina tunani. Manal me yake faruwa?.” Bata bashi amsa ba taji Mama tana magana daga bayan ta tana cewa, “Malama ki kashe wayar nan babu ke babu shi kamar yadda na faɗa miki.” Muryar Mubeena taji tana cewa, “Mama mijin ta ne fa.” A fusace taji Maman tace, “na fiki sanin mijin ta ne, daga yau ki fara saka ta a layin wanda basu da aure, domin auren ta dashi dole ya ƙare ko suna so ko basa so.” Daga nan yaji Manal ta yanke kiran. Tashin hankali ya taru ya yi masa yawa sai maimaita salati yake yi hannu yana rawa ya sake kiran ta amma bata ɗauka ba ya ajjiye wayar yana tunanin lamarin mai kama da shirin film. A haka suka koma gida dashi da Mummy da Maryam baya iya cewa komai, duk yadda yaso daurewa akan lamarin Manal da Maman ta kasawa ya yi, hakan ya sa yana ajjiye su Mama a gida ko ciki bai shiga ba ya ɗauki hanyar gidan su Manal. A ƙofar gidan ya ajjiye motar yana kallon gidan dan bai taɓa shiga kai tsaye ba, a ko yaushe itace take yi masa iso ko kuma Baba ko Yayan su Haruna. Fitowa tayi daga motar ya ƙaraso ƙofar gidan ya rasa abinda zai yi. Surayya ƙawar Manal ya ganj ta nufi gidan ganin sa ta tsaya tana murmushi na sanayya ta gaishe shi ya amsa tare da faɗin, “Yauwa don Allah ki faɗawa Mama zuwana.” Surayya ta amsa tana shiga cikin gidan. Ba jimawa sai gata ta dawo tace, “ka shigo.” Sai da yayi ajiyar zuciya ya shiga cikin gidan har cikin falon da aka saka masa sababbin kujeru ya tarar da Mama a zaune ita da Manal da Mubeena. Yayi sallama Mama ta amsa ya sake gaishe ta ta amsa ba yabo babu fallasa. Ya sauke nunfashi ya ce, “Mama don Allah zan iya sanin abinda yake faruwa?.” Mama ta kalle shi tace, “nace ka shigo ne daman saboda na yi maka iyaka da Manal, ka daina lissafa Manal matsayin matar ka daga rana irin ta yau, domin Manal baza ta sake zama dakai matsayin matar ka ba. ka ɗauka baka san wata mai suna Manal aba a duniya, ka ɗauka rayuwar da ku ka yi da ita tamkar a mafarki ne.” Adnan hankali a tashe, “Mama me yayi zafi haka?.” “Kaje ka tambayi mahaifin ka shine zai faɗa maka abinda yayi zafi bani ba, Abinda na faɗa shi za a yi koda bana raye, domin auren ka da ita babu shi!.” Mamaki yake yi jin yadda Mama take magana kamar ba ita ba ya kalli Manal da take gefe tana shafe hawaye yace, “Mama don Allah ki sanar dani abinda yake faruwa har kika ce haka, dukkan mu a ruɗani muke muna so mu san amsar tambayar da take zuciyoyin mu, don Allah ki sanar damu ko zamu fita daga cikin tashin hankalin da muke ciki.” Mama tace, “ai nace kaje ka tambayi mahaifin ka ko? Kaima kawai saboda girma mutuncin ka da nake gani ne ma ya saka nake sauraren ka wallahi, da yanzu ka tashi da ƙafar ka ka bar gidan nan saboda irin kalamam da zasu fito daga bakina. Kaje ka tambayi mahaifin ka kaji wacece Manal a wajan sa, in bai faɗa maka ba kar kayi tunanin zaka fita daga wannan ruɗanin da ka ke ciki har abada.” Tashi Manal tayi da sauri ta shiga ɗaki tana kuka. Bebi ya kalle ta kafin ya sauke numfashi gabaɗaya bashi da nutsuwa ko kaɗan a haka yace, “shikenan Mama na gode, zan je na tambaye shi in sha Allah.” “Yana da kyau.” “Sai anjima” ya faɗa yana tashi ya tafi jiki babu ƙwari ko kaɗan. Komawar sa gidan su ya tarar da wani tashin hankalin, domin kuwa Mamy ce a harabar gidan na su tana kuka tana dukan Maryam ta ko ina saboda abinda Maryam ta aikata. Da hanzari ya faka motar ya fito ya ƙaraso wajan yana cewa, “Haba Mamy! Don Allah ki bari a gaban mutane ki duba kowa yana kallo na gidan nan” ya faɗa yana nuna mai gadi da drivern su Mamyn ga mai aikin Mamy. Mamy tace, “Adnan zuciyata zafi take min, Lubna na san fyaɗe aka mata ita kuma fa? Da hankalin ta da tunanin ta meye zata yi min haka Adnan?” Mamy ta faɗa tana hawaye cikin ɓakin ciki da ɓacin rai. Adnan ya kalli Maryam da take kuka itama yace, “Na sani Mamy, amma ki yi haƙuri mu koma ciki wannan maganar ba ta nan bace.” Mamy bata ce komai ba ta cillar da madokin hannun ta ta juya ta koma gida. Ya kalli Maryam da take hawaye shima cikin ƙunar rai yace, “kin yi wasa da damar ki, kin ɓata wayon ki. Shekarun ki basu amfana miki da komai ba, girman da kike dashi na jiki ne kawai babu na hankali.” Ita dai kuka take ya sauke ajiyar zuciya yace, “ki shiga ciki.” Jiki a sanyaye ta shiga wajan Mama dan baza ta iya shig wajan Mamy ba. Bebi ya sauke numfashi yana salati a bayyane yace, “Wannan tashin hankali da me yayi kama? Daga wannan Sai wannan da wanne zan ji?, da damuwar Manal ita da Maman ta ko kuma da wannan damuwar?.” Wajan Mama ya shiga ya samu tana ta yiwa Maryam faɗa itama tana hawaye cikin ɓakin ciki da takaicin abinda ta aikata. Kasa zama yayi kawai ya fito a nan yayi karo da Daddy da kuma Uncle suka gaisa suka shiga wajan Abba shi kuma ya shiga mota kawai ya zauna ba tare da ya san abinda zai yi ba. Babu jimawa yaga ana kiran sa waya a ya ɗauka ganin sunan Daddy bai jima yana magana ba ya kashe ya fito daga motar ya shiga cikin gidan wajan Abba. BDƘB3P02 Bebi da ya shiga falon Abba a nan ya same su gabaɗaya har su Maryam da Yayyen sa maza da Mama da Mamy. Yana shiga kafin ya zauna Abba yace, “Kai ka tabbatar da Maryam tayi ciki?.” Bebi ya samu waje ya zauna bai ce komai ba, Abba ya sake cewa, “tambayar ka nake, ka tabbatar tayi ciki?.” Ya ɗaga yace, “eh Abba, da ciki yanzu haka a jikin ta.” Abba ya zabura yayi tsalle ya dira a gaban Maryam, ya tsinke da mari mai zafi, ya sa ƙafa ya mangare ta ta faɗi ƙasa ta kwanta a wajan. Cikin wani irin yanayi yace, “Maryam ni zaki wulaƙanta? Ni zaki tozarta a idanun duniya Maryam?. Cikin uban waye a jikin ki?.” Adnan yace, “Abba wannan fushin ba shi ya kamata ba a yanzu, abinda ya faru ya riga da ya faru sai dai a kiyaye gaba.” Abba bai kula shi ba yace, “zaki faɗa min uban da ya miki ciki ko san na tsine miki? Cikin uban waye a jikin ki?.” Maryam tana hawaye tace, “Na Kamal ne!.” “Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un!.” Shine abinda kowa ya faɗa suna tafa hannu Mamy ta ɗora da cewa, “Maryam mijin da yayi miki saki ɗaya, biyu, har uku shi kika komawa har ya miki ciki ba tare da aure ba Maryam? Maryam Kamal dai uban yaran ki guda biyu shi ne ya sake baki cikin na uku?.” Maryam bata amsa ba Sai kuka da take yi Mamy tace, “Maryam kin cuce ni, kin cuci kan ki, kin cuci rayuwar ki da ta ƴaƴan ki” Mamy ta faɗa tana kuka mai taɓa zuciya. “Kamal!” Abba ya maimaita yana kallon ta cikin tsananin ɓacin rai da tashin hankali, ya sake maimaita sunan yana kallon ta kafin yace, “har gwara ace wani na waje ne daban ya aikata hakan akan ace Kamal ne, Maryam….!” Sai ya kasa magana ya zauna ya dafe kai yana jin wani irin ɓaci a zuciyar sa wanda ko a kan Lubna bai ji hakan ba. Daddy da yake zaune bai yi magana ba sai lokacin yace, “Maryam meyasa kika biyewa zuciyar ki? Meyasa kika biyewa ruɗin shaiɗan har ya kai ki ya baro ki?. Tsohon mijin ki da yayi miki saki har uku shine kike ɗauke da cikin sa? Haba Maryam ina hankalin ki da ilimin ki yake?.” Maryam tana kuka sosai muryar ta na rawa tace, “Wallahi Daddy ba da son raina bane, wallahi Daddy ba a son raina hakan ya faru ba.” A fusace Yaya Isma’il ya kai mata mari a fuska ya ce, “kema fyaɗen yayi miki kenan? Sau nawa Adnan yana hana ki magana dashi?, Akan maganar nan har hisba Bebi yaje aka yi muku iyaka dashi, ya kai ƙarar sa har wajan iyayen sa duk dan saboda yana guje miki wannan ranar, amma kika saka ƙafa kika ɓarar ki sake bawa Kamal damar da tafi baya. Da kin ji abinda yake faɗa miki da yanzu hakan bata faru ba, sai da kika zubawa Adnan ƙasa a ido kika yi ciki Maryam.” Maryam ta sake fashewa da kuka cikin dana sani mara amfani ta kalli Bebi da shima ita yake kallo murya na rawa tace, “na san nayi kuskure babba, amma amfani yayi da wani abu nawa yana tilasta min aikatawa ba dan ina so ba.” Mamy tace, “ƙarya kike Maryam! Ƙarya kike daman kina niyar aikata hakan, kin kasa rabuwa dashi shiyasa ya samu wannan damar.” Maryam tana kuka sosai ta kasa cewa komai. Abba ya kalle ta cikin wata murya mai nuni da tsantsar ɓacin ran da yake ciki yace, “kin cuce ni Maryam kin gama cutar dani, amma zan ɗauki mataki a kan ki dashi kansa Kamal ɗin.” Mamy tayi caraf tace, “Me Kamal yayi? Me ya aikata…? Ga babbar mai laifi nan ai, shi dama ya samu kuma yayi amfani da damar sa.” Abba ji yake kamar yayi ta dukan Maryam har sai ta mutu saboda baƙin, ji yake kawai ya shaƙo wuyan ta ya riƙe har sai ya ga ta daina numfashi. Yace, “Cikin shege a gidana, a cikin gıdana aka samo min cikin shege?. Cikin shegen ma mai muni, cikin da aka samar dashi bayan anyi saki har guda uku. Maryam kin cuce ni, kin gama cutar dani.” Daddy yace, “abinda ya faru dai ya faru, tayi nadama ta gane kuskuren ta na tabbatar baza ta sake aikata abinda tayi ba sai ayi haƙuri kawai komai ya wuce a rungumi ƙaddara wacce ta riga fata.” Abba ya kalli Yayan nasa yace, “kenan ta haifi ɗan shege a gidan nan? Wallahi bazai yu ba sai dai ta bar min gidana taje ta cigaba da zama da Kamal ɗin ta ya haife shi a can, baza’a haifar min cikin shege a gidan nan ba wallahi.” Ƙanin Abba wanda suke kira da Uncle yace, “haka zaka yi haƙuri ka karɓi ƙaddara. Maryam bata da inda yafi nan, in kace ta tafi sake lalata lamarin ka yi.” Abba yace, “bazai yu ba, ji nake kamar na kashe ta wallahi.” Mama dai kallon Abba kawai take yi zuciyar ta wani tunani kawai take yi daban shiyasa bata ce komai ba. Shiru kowa yayi sai kukan Maryam da take yi Mamy ma kuka take yi, Mamy ta kalli Maryam tace, “Maryam Allah ya isa ban yafe ba.” Da sauri aka tari numfashin ta Daddy yace, “Haba Jamila! Meye na furta wannan maganar?, Meyasa baza ki karɓi ƙaddara ba?.” Mamy ta miƙe tace, “na fahimci baza ku gane irin abinda nake ji a zuciyata bane shiyasa, amma kar na sake ganin Maryam a inda nake, taje ta koma gidan Kamal su ɗora daga inda suka tsaya, bana son ganin ta daga nan har a tashi duniya” tana faɗar hakan ta fita Maryam ta sake rushewa da kuka. Abba ya kalli cikin baƙin ciki Maryam yace, “zaki min shiru ko sai na faɗi irin abinda uwar ki ta faɗa? Shegiyar yarinya mai zubin mutanen kirki ashe ta banza ce. A cikin gidana ace an samu wacce tayi cikin shege, kin cuce ni wallahi, kin gama dani, kin zubar min da mutunci a idon duniya.” Maryama ta rufe bakin ta tana jin tashin hankalin da bata taɓa jin irin sa ba a duniya. Kowa yayi shiru an rasa mai magana a cikin su sai Daddy yace, “ayi haƙuri a karɓi ƙaddara babu wanda ya wuce hakan ta faru a kansa, Allah ya bamu ikon cinyewa. Tabbas Maryam tayi rashin hankali ta kuma biyewa son zuciya, a zahiri mun san duk wanda ya biyewa son zuciya ƙarshen sa yana zama irin na Maryam ko yafi na Maryam muni. Amma tayi nadama a yanzu hakan bazai sake faruwa ba, ko wata ta gani na aikata irin abinda tayi Maryam mai yi mata faɗa ce. Shi kuma Kamal inda bai samu fuska daga wajan ta ba bazai sake koda yi mata magana ba koda a akan yaran su ne. Kamal fuska da dama ya samu shiyasa har aka zo ga wannan gaɓar, da ta riƙe mutuncin ta matsayin ta na ɗiya mace da kallon ta ma wahala zai dinga yi masa balle yayi mata magana. Mace itace take bada ƙofar aikata ɓarna, ko a akan Lubna in ku ka duba in da bata bawa Mujahid dama ba da hakan bazai faru ba. Biyewa Kamal da Maryan tayi shine babban kuskuren da ta tafka a rayuwar ta.” Yaya Isma’il yace, “abinda Bebi yake guje mata kenan amma ta kasa ganewa” ya kalle ta yace, “sai da lokaci ya ƙure mata ta sannan ta gane kuskuren da tayi wanda bazai gogu ba har abada.” Abba ya kalle ta cikin fusata yace, “tashi ki bane waje, shashasha mahaukaciya wacce bata sana binda take yi ba, in ina kallon ki a nan babu abinda zai hana ban yi miki baki ba. Ki kuma tattara kayan ki ki bar min gidana, don wallahi Allah baza’a haifi shege a gidana ba.” Maryam jiki a sanyaye ta tashi ta fito daga falon Abba ta rasa abinda yake mata daɗi a wannan lokacin. Haƙuri suka dinga bawa Abba kafin su Yays isma’il su tashi su fito daga falon, su Daddy ma fitowa suka yi bayan sun gama bawa Abba shawara akan karɓar ƙaddara. Falon ya rage daga Mama sai Abba wanda yayi shiru bai ce komai ba haka ma Maman. Ɗago kai tayi ta sauke numfashi tace, “kaji zafin abinda ya faru a kan Maryam ko?.” Da mamaki ya kalle ta yace, “wannan wacce irin tambaya ce?.” Mama tace, “kaji zafi a lokacin Lubna ma ko?.” Bai bata amsa ba tayi murmushi tace, “me ka fahimta akan abinda ya faru akan yaran ka mata guda biyu? Baka gane komai ba har yanzu?.” Kallon ta yake cikin rashin fahimta tayi dariya kaɗan tace, “Annabi Muhammad S.A.W yace duk wanda yayi zina da ƴar wani sai anyi da tasa ƴar, in kayi zina da matar wani sai an yi da taka matar, kai baka yi tunanin wannan ranar zata zo ba ko?.” Nan take gaban Abba ya faɗi matuƙa amma bai nuna ba yace, “Hauwa me kike nufi da abinda kike faɗa?.” Mama tayi dariya ta tashi tsaye cikin takaici da baƙin ciki tace, “abinda ka fahimta shi nake nufi. Matan banza da ka ke lalatawa a waje shine ya fara dawowa kan yaran ka, kayi da ƴaƴan wasu ne shiyasa kaima aka yi da yaran ka guda biyu, sai ka jira matar ka dan nasa kayi da matan wa…..” Mari ya ɗauke ta dashi a fuskar ta cikin zafin nama da ɓacin rai yana kallon ta a fusace yace, “ni kike faɗawa haka Hauwa?.” Mama bata bi ta kan marin da ya yi mata ba tace, “eh na faɗa maka, na fɗa in karya nake sai ka musa. An faɗa maka bamu san kana neman mata bane?, An faɗa maka bamu san kana ajjiye mata a gidan ka na nan Kano bane?, Ka ɗauka zaman da nayi da kai na shekaru sama da talatin a banza na yi su?. Wallahi duk wani motsin ka na sani, na san da kana neman mata shiyasa baka damu da mu matan da muke cikin gida ba, shiyasa ake neman naka saboda baka isa kayi lalata ƴaƴan su naka kuma kace ka killace su ba. Duk wayon ka, duk dabarar ka, duk iya tsarin ka wallahi baka isa ka yiwa Allah wayo ba.” Abba kallon ta yake yi zuciyar sa na bugawa sosai yace, “Hauwa fita ki bani waje.” Mama tace, “bazan fita ba, ina so na tuna maka ka san abinda ka yiwa ƴaƴan wasu suka ji irin raɗaɗin da kake ji yanzu shi ake yiwa yaran ka. Na gidan aure ma basu tsira ba, har gida za a iya zuwa ayi zina da Farida balle su Kausar da suke gida har yanzu. Dole hadisi yayi aiki a kan ka, koda Kamal bai yiwa Maryam ciki, koda Mujahid bai yiwa Lubna Fyaɗe sai hakan ta kasance ko da mai gadin gidan nan sai hakan ta faru, saboda baka isa ka yiwa na waje ba kai kuma kace zaka ajjiye naka a gida ba.” Abba ya kasa magana sai kallon Mama da yake yi tace, “ka cuci Maryam, ka cuci Lubna, abinda ka aikata ne yake bibiyar ka kuma yanzu ka fara gani wallahi, sai kayi dana sanin da baka taɓa yi ba a lokacin da abin ya tsallako kan matan ka da jikokin ka. Zina ai ba wasa bace, zina ai ba ƙaramin abu bace, zina ba ƙaramin laifi bace, zina ba ƙaramar illa bace ba. Allah da kan sa yace kar mu kusance ta, ta ya ya ka ke tunanin zaka aikata ta ka zauna lafiya?. Yaran ka suna zaman lafiya ka jawo abinda ka aikata ya shafe su.” “Kar ki sake ce min mazinaci!.” “Na faɗa mazinaci! Shi ɗin ne ai ko nayi ƙarya? Mata nawa ka yi zina dasu? Kai kan ka baka san adadin su ba sannan kace sunan bai kamace ka ba?..” juya yayi ya dafe kai yadda yake ji a zuciyar sa zai iya fasawa Mama baki a wannan lokacin. Mama tace, “ita sirikar taka babar Manal matar Adnan a harkar ta sanka ko? Yanayin kallon da take maka ba a mutum kirki ta sanka, Anya Manal ɗin ma ba taka ƴar bace….” Maganar Mama ta maƙale saboda Marin da Abba ya sake kaiwa fuskar ta cikin fushi da tsantsar ɓacin rai. BDƘB3P03 Mama kallon sa take shima ita yake kallo cikin tsantsar takaici da ɓacin ran da dukkan su suke ciki, hannun ta yana kan fuskar ta cikin mamakin sa, dan zata iya cewa tunda suka yi aure bai taɓa ɗaga hannu ya dake ta ba sai yau, bata ji zafin marin ba so take kawai ta isar da abinda yake bakin ta domin ya san sun san komai shiru kawai suke masa ba don suna tsoron sa ba. "Ni kike faɗawa wannan maganar Hauwa? Anya kina cikin hankalin ki?" Ya faɗa cikin ɓacin rai yana kallon ta. Mama tace, "A hankalina nake, gaskiya nake faɗa maka kai kuma itace baka so. Tsakanin ka da sirikar Adnan wallahi akwai wani abun a ɓoye, tunda ta ganka ta canja ƙarshe tace ƴarta ta biyo ta su tafi saboda kaii. Bana raba ɗayan biyu, in ma itama tana cikin ƴan matan ka na baya, ko kuma...." Sai Maman tayi shiru tana kallon sa kamar yadda yake kallon ta cikin tsantsar tashin hankali. Sai tayi murmushi ta kalle shi tace, "ka cuci yaran ka, ka lalata musu rayuwa da kan ka da kuma hannun ka. Bebi da ya kasance mai maka biyayya ko yaushe shima kana neman rusa masa tashi rayuwar, a yanzu zuciyar sa a karye take yana tunanin meye ya haɗa mahaifiyar ta da kai. Komai ya faru kai ne ka jawo, kana ganin kai yaran ka sun tsira saboda suna gida ko yaushe, kana ganin basa zuwa ko ina shiyasa hankalin ka a kwance ka ke lalata ƴaƴan wasu a waje kai kuma naka ka killace su. A gain ka zaka yiwa Allah wayo da dabara, ka manta da zina tabon ta baya taɓa gogewa." Abba yayi shiru yana kallon ta zuciyar sa bugawa take yi sosai, a take  a lokacin abinda take faɗa wanda ya manta da tunanin zai faru yake masa yawo a kansa. Ganin ya kasa motsi tace, "Ba a tsaya a na ba wallahi, zafin da kaji ba komai bane domin wannan somin taɓi ne. Za a cigaba da yiwa naka yaran ana saka maka ɗaci a zuciya ka kamar yadda ka saka ɗaci a zuciyar iyaye su. Ahh ai ka naka karuwai ne su suke kawo kan su ta ina iyayen su zasu ji ɗaci, wannan shine tunanin masu hali irin naka a ko yaushe, a ganin ka ai ba ta ƙarfi ka ke musu ba dan haka babu abinda zai samu ƴaƴan ka saboda biyan su ka ke. To ka sani ko kai ka ke sakawa a kawo maka su, ko su suke kawo kansu, ko biyan su ka ke, ko kyauta suke baka kan su zina dai sunan ta zina. Allah da kansa yace kar mu kusance ta balle mu aikata, amma yanzu kun mayar da abin ado in baka zina ma kamar baka waye ba. To ga naka sakamakon nan ka fara gani tun a duniya, kuma ina so ka sani yanzu aka fara wallahi, a hankali abun zai dawo kan matan ka in dai ka nemi matar wani!." Abba ya kasa magana a wannan lokacin yayi shiru kawai yana jin abinda mama take cewa wanda ya ɗaure shi da jijiyoyin jikin sa, ruwan kansa ya ɗauke ƙwaƙwalwar sa taje hutun rabin lokaci saboda baya gane abinda take faɗa ma gabaɗaya. Bebi yana tsaye ya dawo ɗaukar wayar sa da ya manta a falon, duk abinda Mama take faɗa yana ji idanun sa suka ciko da hawayen takaici da baƙin cikin abinda kunnen sa suka ji, hankalin sa ya tashi zuciyar sa sai bugawa take yi  saboda duk abinda Mama tace yaji. Da zafin nama ya juya ya bar wajan yana dana sanin abinda ya dawo da shi ya shiga ɓangaren Mama. Har cikin ɗakin ta ya wuce ya zauna a kan ƙaramar kujerar da take ɗakin ya dafe kai yana hawayen da bai san dalilin zuwan su ba. Motsin Mama da yaji ne ya saka shi saurin goge idanun sa ya tashi tsaye yana kallon ƙofar, a lokacin ta shigo ɗakin ta kalle shi ta ɗauke kai ta zauna a inda ya tashi babu walwala a tare da itatace, "me yake damun ka?." Bebi ya gyara nutsuwar sa yace, "Komai ma Mama, na manta wayata a falon abba." Mama tayi ƙaramin tsaki tace, "ya maganar Manal din? Kabi bayan ta amma dai ko?." Ya sauke numfashi yace, "daga gidan nasu nake na dawo nan." "To ya akayi a can ɗin?." Bebi ya ɗan kulle ido ya buɗe yace, "maganar ɗaya ce Mummy, tace babu aure tsakanina da Manal." Da mamaki Mama tace, "akan wanne dalili?." "Wallahi ban sani ba, babu wanda ya san dalilin. Abinda na lura dashi ba ni ne matsalar ta ba Abba ne." Mama tayi dariya kaɗan cikin takaici tace, "daman ai ba kai bane, kai fa tasan kaine ka ke auren ƴar ta, in da kai ne damuwar ta da yanzu ba wannan maganar ake ba. Shi mahaifin ku shine matsalar, yanayin kallon da take yi masa zaka tabbatar ba da arzuƙi ta sanshi ba." Bebi yace, "Allah ne ya sani" ya faɗa dan ya kawar da wancan maganar ta Abba. Mama tace, "Allah yasa ba ƙanwar ka ka ke aure ba." Mama ta faɗa a bayyane ba tare da ta sani ba, ya kalle ta sai yaga bata san ta faɗa ba alamun zancen zuci ne ya fito fili. Shi kansa babban tashin hankalin sa kenan, wannan tunanin yana daga cikin abinda yake ɗaga masa hankali yaji zuciyar sa na bugawa da sauri-sauri. In akace Manal ƙanwar sace ya zanyi? Ina zai saka ransa yaji daɗi?, Da wanne ido zai kalle ta!?. A wanne matsayi ɗan cikin ta yake?, ɗan sa ko kuma ɗan kanwar sa...?. Fita yayi daga ɗakin ya koma ɓangaren Abba ya shiga da sallama ya samu Abban a zaune yayi shiru alamun tunani yake yi, ya dauƙi wayar sa baice komai ba ya fita daga falon. Gidan sa ya wuce ya shiga falon ya tarar dashi kamar ko yaushe a share sai ƙhamshi air freshener yake. Zama yayi a falon ya dafe kai da hannun sa biyu ya rasa inda zai saka zuciyar sa yaji daɗi. Wayar ya jawo ya shiga sunan Manal ya kira amma bata ɗauka ba, ya sake kira bata ɗauka ba ya riƙe wayar a hannun sa ba tare da ya kuma kira ba yana ji zuciyar sa na harbawa sosai. Kiran ta ne  ya shigo wayar hannu yana rawa ya ɗauka bai jira tayi magana ba yace, "Ina cikin damuwa Manal, ina buƙatar ki a kusa dani, zuciyata gab take da daina aiki saboda abubuwa sun yi min yawa. A wajan ki zan samu sassauci gashi yanzu kin yi nisa dani, ban san me na yiwa Mama ta yanke wannan hukuncin ba, na lura ba laifina bane laifin Abba ne ya shafe ni, abin tambayar a nan me ya faru Manal?. Tsoro na da tashin hankalina kar ace ni da ke jini ɗaya ne, kar ace ni dake yaya da ƙanwa ne. Bana so hakan ta kasance ko a mafarki, ban san ya zanyi da raina ba in hakan ya faru." Kuka Manal take a banɗakin da ta shiga don bata so Mama taji tana waya murya a ƙasa tace, "Hakan bazai tabbata ba in sha Allah, in hakan ya faru mutuwa zanyi." "Baza ki mutu ba Manal, baza ki mutu ba, in mutuwar ne ni zan mutu ba ke ba, saboda zuciyata tafi taki yin nauyi Manal. Ina cikin tashin hankali, na dawo gida bakya nan duniyar tayi min zafi Manal. Kece maganin damuwa ta amma kin yi min nisa." Manal kuka take yi sosai ya rantse ido yace, "ki daina kuka, jin kukan ki sabon tashin hankali ne a wajena. Ki yi mana addu'a Allah kar ya kawo rabuwar mu nan kusa, Allah yasa mutuwa ce zata raba mu dake ba wani dalili ba." Numfashi yaji ta sauke a hankali yace, "ki kula da kan ki, kar ki dinga shan sugar kin ji?." Kukan ta ke yi sosai kafin ya sake magana ta yanke wayar ya kulle ido yana ji kamar yayi kukan shima. Manal sai da ta sha kukan ta a banɗaki sannan ta fito, ta dawo falon ta zauna tana jan numfashi na wacce tayi kuka ta ƙoshi. Mama tana kallon ta duk da dare yayi ba gani take sosai ba amma tana lura da duk wani motsin ta. Mama tace, "haka zaki kwanta baki ci komai ba?." Manal murya na rawa tace, "na ƙoshi." Mama tace, "kin huta, yunwa ba ƙanwar uwa bace balle taji tausayin ki." Kwanciya tayi a gefen Mama ta kalli Mubeena da take zaune ta kulle ido kamar mai bacci amma ba baccin yake ji ba. A haka ta kwana babu baccin kirki sai ruwan hawaye, ga yunwa da ta addabe ta gabaɗaya ta kasa samun baccin kirki da ta fara baccin zata farka tayi kuka ta koma. Sai da tayi sallar asuba sannan ta samu tayi bacci shima zuwa tara na safe ta tashi. Sai da tayi wanka a banɗakin Mama tayi sallar walha sannan ta fito tsakar gidan ta samu Mama ce kawai a zaune a inda ta saba zama da safe tana shan tea da biredin alkamar ta a gefe. Tsayawa tayi daga inda take tsaye Mama ta kalle ta tace, "ki ƙaraso kici abinci." Manal ta ƙarasa ta zauna kusa da ita Mama ta kalle ta tace, "wannan damuwar da wannan rashin cin abincin ba kowa zai cuta ba sai ke, aure ne babu shi a tsakanin ki dashi in zaki sake ki dawo kamar da yafi miki." Manal ta jawo flask tea ta zuba a kofin da Maman ta gama sha ta kai bakin ta sai dai salam babu komai a ciki sai lipton da kayan ƙhamshi. Riƙe take da kofin bata ce komai ba kuma bata sha ba sai kallon wani waje da daban da take yi. Sallamar Maman su Surayya ce ta saka ta kalli mai shigowa Mama ta amsa sallamar da fara'a ta ƙaraso ta zauna suka gaisa Manal ma ta gaishe ta ta amsa kafin ta kalli Mama tace, "Lafiya dai ko Maman Manal? Surayya tace min a gida Manal ta kwana, ina fatan lafiya dai." Mama ta kalli Manal da take juya cokali a cikin shayi tace, "Eh to lafiya amma lau ba, auren ta da Adnan ne ya ƙare." Manal ta kalli Mama da take kallon Maman su Surayya ta kulle ido da buɗe taji Maman Surayya na cewa, "Innalillahi wa'inna ilaihir raj'iun, Maman Manal me yayi zafi haka? Yaushe akayi auren Manal ɗin da za'a ce auren ya ƙare?." Mama ta sauke numfashi tace, "Zan fahimtar dake in lokacin hakan yayi, Amma a yanzu ki ɗauka Manal bata da aure Balaraba." Jin hakan sai Maman su Surraya tace, "to Allah ya shiga lamarin." Mama ta amsa da amin suka ɗan yi hira kafin tayi sallama ta fita. Tana fita Manal ta tashi zata shiga ɗaki Mama tace, "har kin gama cin abincin?." Manal tace, "na kasa ci, kwanciya nake so nayi" ta faɗa tana shiga da sauri dan kukan da yazo mata baza ta iya riƙe shi ba. ******* Mubeena suna zaune da Bilkisu a falo suna tattaunawa, Mubeena ta kalli Bily tace, "Bily ina cikin tashin hankali, na rasa abinda yake min daɗi na kuma rasa abinda yake shirin faruwa a cikin rayuwa ta." Bily tace, "nima tunda kika min waya hankalina yake a tashe wallahi, me ya faru?." Mubeena tace, "jiya na raka Mama asibiti duba Yayar mijin Manal, da muka shiga Mama suka gaisa da da Maman su Adnan ɗin da fara'a da komai, har Maman su Adnan ta bawa Mama wajan da take zaune fa, aka gaisa da mutunci da girmama juna. Amma tana ganin mahaifin sa nan da nan sai yanayin ta ya canja, ta koma wani iri tana yi masa kallon so take ta gane shi, yana faɗar sunan ta ta gane kawai tayo murmushi ta miƙe tsaye. Shima kuma kallon ta yake da irin nata mamakin har yana cewa Zahra da gaske kece, kin ga kenan ya san Mama." Bily tace, "ƙwarai ya san ta." "Daga nan sai Mama ta riƙo hannun Manal tace mu taho gida, muka dawo gida Manal ta takura akan Mama ta faɗa mata abinda yake faruwa, Mama sai tace wanda take kallo matsayin mahaifin mijin ta itama shine mahaifin ta." Bily ta wara ido tare da dafe ƙirji tace, "Mun shiga uku! Kenan mahaifin Adnan shine mahaifin ku? Kenan auren ya da ƙanwa akayi ko me?." Mubeena tace, "Mun kasa samun wannan amsar daga wajan Mama, Adnan ɗin da kansa yazo gidan cikin yanayin damuwa amma Mama tace ya tafi babu aure tsakanin sa da Manal, tana kuma bashi shawara daga wannan lokaci ya cire Manal daga ransa." "Innalillahi! Mubeena wannan abun fa ba ƙaramin abu bane." Mubeena ta sauke numfashi tace, "akwai wani abun da yafi wannan Bily." Ta kalle ta tace, "ina jin ki." Ta sauke numfashi tace, "Mahaifin Adnan wanda bamu da tabbacin a yanzu ba shine mahaifin mu, shine wannan Alhaji nawa da muka rabu." Bily ta ɗora hannu a kai tace, "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Mubeena da gaske kike wai ko wasa?." Mubeena tace, "wallahi da gaske nake shine, abinda yake ɗaga min hankali kenan Bily, in ya kasance shine mahaifin mu kenan shine ya nemi yayi lalata ƴar cikin sa?. A tarihin rayuwa ta dole na rubuta mahaifina yaso yin zina dani kenan Bily...." Ta faɗa cikin rauni mai nuni da damuwar da take ciki har zuciyar ta. Bily tayi hanzari ta tarar numfashin ta tace, "Ki daina wannan ƙazamin tunanin Mubeena, wannan ba abinda zaki tunani a kai bane. Taya zai kasance mahaifin ki Mubeena?." Mubeena tace, "meyasa Mama take cewa uban Manal ne? Indai har ya kasance mahaifin Manal nima mahaifina ne." Bily cikin tashin hankali da son ta kwantar mata da hankali ta kalle ta tace, "wataƙila Maman ta faɗa ne kawai amma ba hakan bane ba." "Meyasa tace auren Manal da Adnan ya ƙare to? Meyasa ta dage a kan Manal babu ita babu Adnan duk da son da take yiwa auren su?. Bily Mama tana son auren Manal da Adnan kema kin sani, amma yau itace take hana Manal ko waya dashi, in ba mahaifin mu bane waye shi?." Bily tayi shiru tana tunani ta kasa cewa komai saboda itama abin ya ɗaure mata kai sosai. Ganin hakan sai Mubeena tace, "indai har ya kasnace mahaifin Manal nima mahaifina ne, sai dai in nida Manal ɗin kowa mahaifin sa daban:" Bily ta kalli Mubeena kafin tayi magana Mubeena tace, "babu wanda muka sani da dangin mu na uwa da uba, dole zamu iya mu'amala da dangin mahaifin mu ko mahaifin na mu ba tare da mun sani ba, jikina yana bani tabbas wannan mahaifin Adnan ɗin kuma tsohon saurayina wani ne a cikin dangin mu, in ba mahaifin mu ya shafi ahlin mu." Bily ta sauke numfashi bata ce komai dan ta kasa magana ba dan bata san abinda zata ce ba. Mubeena tace, "Amma waye shi..? Meyasa Mama bata son wanda ya raɓe shi ne?, Meyasa take cewa babu aure a tsakanin Manal da Adnan?." BDƘB3P04 Mubeena ta sake kallon Bily da jajayen idanun ta tace, "babu mai bani amsar nan sai Mama, ita kuma Mama taƙi maganar gabaɗaya." Bily ta jinjina kai tace, "gaskiya wannan babban lamari ne ba ƙarami ba, ina Baba to?." "Baba baya nan, sai zuwa gobe ina jin zai dawo nasan da ya dawo wataƙila maganar tazo ƙarshe." Bily tace, "gaskiya wannan ba karamin abu bane ba, in ya kasance mahaifin ku keda Manal kenan fa babu aure tsakanin ta da Adnan fa, ga ciki ma take dashi. Subahanallahi wannan abin kunya har ina? Allah kar ka tabbatar mana da wannan lamari." "Amin. Bazan zo a raba Manal da mijin ta ba, yana sonta tana son shi. Nima bazan zo ace mahaifina ne yaso mayar dani karuwa ba." Bily tace, "ki daina wannan maganar, in sha Allah babu abinda zai faru wannan maganar baza ta zama gaskiya ba." "To waye mahaifin mu Bily? Ina dangin sa suke?." Bily tace, "Allah masani, Amma tunda aka zo wannan gaɓar komai ya kusa zuwa ƙarshe in sha Allah, mu cigaba da addua kawai." Mubeena tace, "to Allah ya bamu abinda zamu iya. Ni yanzu ko ba mahaifin mu bane, ko ba wani namu bane, Manal ta koma wajan Adnan da wanne ido ma zan dinga kallo Adnan?. Kin san Allah wannan shine dalilin da ya saka tun asalin farko Adnan bai min ba, ashe dashi yake min kama shiyasa haka nan baya burge ni. Shi kuma mahaifin nasa ashe ƙarya yayi min ya faɗa min suna na ƙarya saboda kar na gane shi." Ta sake kallon Bily tace, "Haba shiyasa lokacin da Mama bata da lafiya da ya ganni a asibitin su Adnan ɗin yace kar na sake zuwa, ashe ya san da ɗan sa a cikin asibitin, yana tsoron kar na san ɗan sa ko shi ya sanni. Yace min sunan sa Isah ashe Mu'azzam sunan sa. Ai in akace shine mahaifin mu sai nafi Manal shiga tashin hankali." Bily tayi ajiyar zuciya tace, "ki yi addu'a kawai Allah ya sassauta mana wannan lamari." Ta amsa da amin kafin ta raka Mubeena ta wuce gida. ****** "Dr tun ɗazu nake neman ka na sanar da kai, i'm sorry cikin jikin ta ya fita sakamakon faɗuwar da tayi. Alhamdulillah ya zo da sauƙi har ta farka ma" wata nurse ta faɗa tana kallon sa da shigowar sa kenan asibitin. Ya sauke numfashi jin daɗi yace, "ya jikin ta?." "Da sauƙi sosai." Bai ce komai ba ya shiga ɗakin da Maryam take ya same ta ita kaɗai ce kawai a ɗakin ya ja kujera ya zauna ya kalle ta yace, "ya jiki?." Bata amsa ba sai kuka da take yi ya sauke ajiyar zuciya yace, "wannan koke-koken duk ba naki bane a yanzu, ki yi facing abinda yake gaban ki don ganin kin warware matsalar. Ki kuma tuba ga wanda ya halicce ki domin mutuwa zata iya samun ki a ko wanne lokaci." Maryam ta goge ido tana furta astagafirullah a zuciyar ta. Kallon ta yayi yace, "nutsu sosai mu yi magana." Ta kalle shi kamar yadda yake kallon ta yace, "ga wayar Kamal a hannuna" ya faɗa yana nuna mata wayar, ya ɗauko hanun ta ɗaya da babu ruwa a jiki ya saka mata wayar yace, "ki shiga cikin wayar ki tabbatar kin goge komai, kar ki bar wani abu ko ɗaya a ciki, ki tabbatar kin goge domin kar ki sake aikata kuskure." Kallon sa take cikin mamaki ya akayi ya samo wayar Kamal, bata da bakin tambayar sa ya ɗauke hannun sa daga kan hannun ta ta kalle shi tace, "da gaske wayar shi ce?." "Zaki iya tabbatarwa." Da hannun ta ɗauka ta danna abinda ta san ya saka matsayin security na wayar sai kuwa gashi ta buɗe alamun bai canja ba. Numfashi ta sauke cikin farin ciki tace, "Bebi itace wallahi." Bebi yace, "ki yi abinda zaki yi da gaggawa, za'a mayar masa da wayar bana so ya ɗora whatsapp ɗin sa ko facebook a wata wayar daban, ki yi hanzari har chart ɗin da kuka yi na yanzu da na da ki yi clearing." Hannu na tawa ta shiga whatsapp ɗin ta goge, ta shiga facebook ɗin sa ta tara ya goge duk wani post ɗin sa. wajan hotuna ta shiga amma bata ga komai akan abinda ya shafe ta, ta kalle shi tace, "Babu komai." Yayi shiru ya san za'ayi haka babu lallai ya ajjiye su a inda za'a yi saurin samun su, karɓar wayar yayi yana dube-dube a nan ya gano wata secret folder amma sai da face id zata buɗe. Tashi yayi ya fita ba jimawa ya dawo shi da wani yaro da laptop a hannun yaron, ya zaunar dashi ya bashi wayar yace, "gashi ka duba min wata folder da aka ɓoye." Karɓa yayi ya jona wayar a laptop ɗin ya shiga danne-danne. Kusan mintina talatin yaron yana abu ɗaya kafin yace, "ga wata na gani mai suna Maryam." Adnan yace, "yauwa, bani" ya faɗa yana karɓa ya ɗora mata a kan cinya yace, "ki buɗe wannan mai sunan naki ki goge duk abinda yake ciki da gaggawa." A hankali ta shiga tayi clicking sai kuwa ga hotunan ta da videos kamar hauka. Ganin yadda ta runtse ido ya tabbatar abinda suke nema ne yace, "ki buɗe ido ki goge." Da sauri ta buɗe tayi marking gabaɗayan su ta goge duka hannun ta har rawa yake yi. Ta kalle shi tace, "na goge." Ya ɗauke laptop ɗin ya bawa yaron yace, "A goge wannan folder ta yadda ko anyi backup baza ta dawo ba, sannan ko charting ɗin kan wayar a goge yadda bazai dawo ba." Yaron ya amsa yana cigaba da dannawa har ya gama yace, "an gama, na sauke komai." Bebi ya girgiza kai yace, "Na gode, koma office ka jira ni." Yaron ya fita shi kuma ya sake duba wayar yana sake dannawa dan so yake ya tabbatar babu koda hoton fuskar Maryam a wayar. Kuka take yi sosai tana kallon sa yana aikin danna wayar tace, "na gode ɗan uwa, na gode Allah ya saka maka da alkhairi ya baka abinda ka ke." Ɗago ido yayi ya kalle ta bai yi murmushi ba yace, "amin. Nan gaba sai ki kiyaye turawa wani hotuna koda ya kasance mijin ki." "Har abada Wallahi." Lubna ce ta shigo da sallama ya amsa yana kallon ta ta gaishe shi amsa yana fita. Mubeena bayan ta koma gida a falo ta samu Mama tayi sallama ta amsa tana shiga ciki Mama tace, "shiga ɗaki ki gano min Manal tunda ta shiga bata fito ba." Mubeena ta shiga ta samu Manal a kwance ta ƙarasa ta zauna kusa da ita tace, "Manal lafiya?." Jin muryar Mubeena sai ta tashi zaune da sauri ta riƙr hannun Mubeena tace, "Yaya na rasa abinda zan yi naji daɗi." Mubeena tace, "Kaii jikin ki yayi zafi sosai, me yake damun ki?." Manal tace, "komai ma damuna yake Yaya, na rasa inda zan saka raina, ji nake kamar na samu suka na dinga cakawa kaina har sai na mutu." Mubeena tac, "to ki yi haƙuri, in sha Allah babu ƙaddarar da zata rabu ku da Adnan, kina son mijin ki shima yana son ki in sha Allah babu abinda zai faru. Na tabbatar duk inda yake shima yana nan cikin damuwa wataƙila tafi taki, ki yi haƙuri ki daina kuka kin ga zazzami ya rufe ki, babu abinda zai raba ku sai mutuwa." "Kafin zuwan mutuwar ni na raba su" Mama ta faɗa tana shigowa ta kalle su ta kalli Manal da take kuka tace, "Manal kukan ki babu abinda zai miki magani sai dai ya ƙara miki ciwo, nice na haife ki kuma bazan yi abinda zan cutar dake ba ke kin sani. Tunda kika ji nace babu auren ki da Adnan ya kamata ki fahimce ni, ba da wata manufa na aikata hakan ba sai dan dole hakan ya faru. Adnan bazai zama mijin ki ba a yanzu ko nan gaba, wancan zaman ma da ku ka yi na anyi shi a rashin sani ne, amma yanzu komai bayyane dole ki rabu dashi!" Ta ƙarasa maganar cikin tsawa. Manal bata ce komai ba tana jikin Mubeena tana jan numfashi cikin tsoro, Mama tace, "cikin da yake jikin ki da ina da iko sai na zubar dashi, kawai bana son aikata zunubi ne amma da baza ki haife shi ba wallahi." Mubeena da mamaki tace, "kin bar mu a duhu Mama, Mun kasa gane inda kika nufa. Ki faɗa mana dalilin aikata hakan hankalin mu sai yafi kwnaciya, wannan tashin hankalin zai iya sakawa cikin ta ya zube gabaɗaya." "Ai da zai zube ɗin haka nake so Mubeena, da ace cikin zai fita da nayi farin cikin da ban taɓa yin irin sa ba" ta kalli Manal tace, "malama ki taso kici abinci, tun safe babu abinda kika ci har azhar tayi, kizo kici abinci kafin ran ki ya ɓaci." Manal jin Mama tana yin maganar cikin faɗa sai ta bar jikin Mubeena ta sakko daga kan gadon amma ta kasa tsayawa saboda ciwon kai. Baya tayi kamar zata faɗi Mubeena ta riƙr ta tace, "Sannu Mama, Mama ya kamata mu kai ta aisibiti jikin ta yayi zafi sosai." "Damuwa ce da yunwa, zata warware da zarar taci abinci. Riƙo ta tazo taci abinci" Mama tana faɗa ta fita Mubeena ta fito da Manal ta zaunar da ita ta kawo mata tea da biredin su. Manal saboda Mama ta sha iya tea ɗin kawai, gashi yanzu bata iya sha saboda babu sugar daƙyar ta iya shanyewa ta kwanta a wajan tana sauke ajiyar zuciya. ***** Bebi bayan ya bar ɗakin da Maryam take office ya koma ya sallami yaron da yace ya jira shi ya zauna tare da kwantar da kansa akan table ya rasa abinda yake damun sa a zuciyar sa. Damuwar Manal ce ko ta Abba ko kuma ta Maryam?. Tun safe yake kiran Manal bata ɗauka hankalin sa ya gama tashi gashi ko text bata yi ba balle ya tabbatar tana lafiya. "Bebi team work is ready, kai suke jira za'a yi wannan surgery ɗin da aka yi maganar sa jiya." Jin magana a kansa sai ya ɗago yaga Huzaifa ne da Hamza akansa a tsaye tace, "ayi replacing ɗina da wani, I can't do anything wallahi" ya faɗa yana mayar da kansa inda yake a ɗazu. Hamza ya zagaya inda yake ya dafa shi yace, "Kwana biyu yawan shiga damuwar nan taka tayi yawa, me yake faruwa ne Bebi?." Bai ɗago ba bai kuma ce komai ba Huzaifa yace, "ka sanar damu in zamu iya taimaka maka mu taimaka, in baza mu iya ba sai mu yi maka addu'a. Amma bama jin daɗin ganin ka a wannan hali ko kaɗan." Ɗago kai yayi ya jingina da kujerar da yake kai yace, "abubuwan da suke damuna suna da yawa." "Faɗa mana mu ji, Muna da lokacin sauraren ka" Hamza ya faɗa yana kallon sa. Bebi ya sauke numfashi yace, "zan faɗa muku amma ba yanzu ba, in na faɗa yanzu sake dagula min lissafi zai yi." Huzaifa yace, "Shikenan, Allah ya kawo maka mafita." "Amin na gode, ku taya ni addua allah yasa kar abinda nake tunani ya tabbata. In hakan ya tabbata Allah zaku iya rasa ni gabaɗaya, bana tunanin zuciyata zata iya ɗaukar abinda nake hasashe, bazan iya ɗauka ba, bazan iya ba" ya faɗa yana sake jefa kansa cikin damuwa mai tsanani. Hamza ya kalli Huzaifa shima shi yake kallo kafin ya sake kallon Bebin yace, "to baka faɗa mana ba balle mu san abinda zamu ce maka a kai." Bebi ya kalle su yace, "kar ku damu." "Yanzu har abin ya kai ka fara ɓoye mana damuwar ka? Haka kayi mana wancan lokacin yanzu ma gashi ka ɓoye, a ganina babu abinda muke ɓoyewa junan mu saboda mu zama tamkar jini ɗaya" Huzaifa ya faɗa yana kallon sa. Bebi ya kulle ido bai ce komai ba ganin haka sai suka bashi waje dan ya huta. Ya jima a wannan yanayi sallah ce kawai take tayar dashi, ya kira Manal yafi a irga amma bata ɗauka hakan ya saka saka shi a damuwa matuƙa dan bai san a wanne hali take ba. Sai gab da magriba ya koma gida shi da Maryam da Lubna suka shiga cikin gidan shi kuma ya shiga wajan Mama. Tana kallon sa tace, "Subahanallahi! Bebi kaga yadda ka koma?, Anya kaci abinci yau?." Zama yayi baice komai ba ta kalli Kausar tace, "kawo masa abinci yaci." Ya kalli Mama yace, "bana jin yunwa bazan iya cin komai ba, Abba yana nan?." Mama tace, "Yana nan. Amma kaci wani abun Adnan ka faɗa lokaci ɗaya." "Zan ci sai anjima." Mimi ce ta fito daga ɗaki ta kalle shi ta kalli Mama tace, "Mama bashi da lafiya?." Kallon ta yayi ya kalli Kausar ya tashi tsaye yace, "in anyi sallah ina neman ku, ku kira Lubna ina san magana daku" yana faɗa yana fita. Mama ta girgiza kai tace, "Allah ya kawo mafita a lamarin nan, in Bebi ya rasa Manal zai iya samu matsala. Allah kar ka tabbatar da abinda zuciyar mu take hasashe, ya Allah kar ka saka Manal da Adnan su kasance mahaifin su ɗaya, Allah kar ka rubuta wannan ƙaddarar a shafin ƙaddarorin sa, Allah ka canja ta da mafi alkhairi." Duk sai a lokacin su Kausar suka gane abinda yake damun sa, suka yi shiru kawai su kansu maganar ta shige su balle kuma shi. Kamar yadda yace bayan magriba suka je ɗakin sa wanda a yanzu babu wanda yake zama a ciki duk yayi ƙura. Da sallama suka shiga yana tsaye yana kallon window ya amsa yana kallon su. Sai da suka shigo dukkan su sannan yace, "ba sai kun zauna ba wajan akwai ƙura sosai. nasiha nake so nayi muku wacce nake fatan zata shiga jikin ku har girman ku. Ko yanzu ko nan gaba kar ku amince soyayya ta ɗauki hankalin ku har tayi nasara a kan ku wajan ɗaukar hotunan tsaraicin ku turawa miji ko saurayi." Kallon su yayi yana karantar yanyin su yace, "ban ce turawa miji ya zama kamar haramci ba, Amma shawarar da nake baku matsayina na jinin ku har mijin kar ku turawa, kar kuma ayi video call ana nuna tsairaici domin shima za'a iya recording. Masoyi yana komawa maƙiyi, haka maƙiyi na komawa masoyi. Ku ji tsoran masoyin da ya koma makiyi, yafi illa saboda ya san komai naka yana da komai naka a hannun sa saboda da farko ya kasance masoyin ka. Mimi, Lubna da Kausar kar ku yi wannan gangancin a cikin rayuwar ku, ku duba goben ku da goben ƴaƴan ku, babu tozarcin da ya kai a yaɗa hotunan tsaraicin ka a duniya. Kar ku dinga gani a social media ku ɗauka baya faruwa a gaske, yana faruwa sosai ana blackmailing da abinda ka tura da kan ka koda mijin ne kuwa." "Wani mijin in ya rabu dake neman hanyar da zai tozarta ki yake, a ganina babu tozarci kamar wannan hotunan a duniya. Kar ku aikata koda wasa, a kiyaye domin wata rana zaka yi dana sani indai ka aikata wannan shirmen, ba soyayya bace hauka ne da rashin sanin darajar kan ka. Ba duka aka taru aka zama ɗaya ba, wani mijin koda ka tura masa bai ajjiye dan saboda ya tozarta ki koda ya rabu dake, amma akwai sace wayar, akwai ƙwancen waya. Ko iya wanda ya ƙwace wayar ne ya gani ya cuce ki. Ni kawai a shawarata kar ayi kar a fara." Jin yayi shiru sai Mimi tace, "in sha Allah Yaya zamu kiyaye." "In kuma akwai wacce ta taɓa aikatawa ku faɗa min, kar ku ji tsoro in da wacce ta turawa saurayin ta ta sanar dani." A tare suka haɗa baki suka ce, "wallahi bamu taɓa ba." Ya girgiza kai yace, "duk saurayin da zai tambayi ki turo masa wani sassa na jikin ki ba auren ki zai yi ba, ku kula. Lubna da Kausar da ku nake." Lubna tace, "in sha Allah." "Zaku iya tafiya" ya faɗa tana kallon window Lubna tace, "mun gode Yaya." Bai kalle su ba suka fita ko wacce na tunanin kenan abinda ya faru da Yaya Maryam kenan tunda gashi yana yi musu nasiha akan hakan. Yana nan tsaye ya sake kiran wayar Manal akayi sa'a aka ɗauka bai jira anyi magana ba yace, "laifi nayi ne nima? Manal ya kike so nayi kin ƙi ɗaukar wayata? Dame zan ji?." "Ba ita bace, Yayar tace Mubeena." Jin haka sai ya gyara tsayuwa Mubeena tace, "Manal yanzu haka bacci take, bata da lafiya sosai dan rabon ta da abinci ina jin tunda kafin tazo gidan nan, taƙi cin komai sai tea da ta sha kawai. Jikin ta yayi zafi sosai, bata da aiki sai kuka, ko bacci tayi ta tashi kuka zaka ga tana yi. Kai likita ne kasan damuwar nan zata iya sakawa cikin ta ya zube." "Hasbunaallahu wani'imal wakil!" Ya furta a sanyaye Mubeena tace, "A nan ɓangaren bamu san komai ba har yanzu, in da dama zaka iya tambayar mahaifin ka ko kai zaka samo wani dalili da ya saka aka aikata hakan kodan kwnaciya hankalin ka da nata, dan gaskiya Manal bata da lafiya sosai, yau wuni tayi kuka ga zazzaɓi. Shiyasa na zaɓi na amsa wayar ka na faɗa maka ko zaka samo mafita." Daƙyar ya iya cewa, "zaki iya yi min wani taimako?." Mubeena tace, "ina jin ka." "Zan kawo mata magani yanzu, kizo ki karɓar mata." Mubeena tace, "babu damuwa." Yana jin haka ya yanke kiran ya ɗauki key na mota ya fita da sauri. Sai da ya tsaya a pharmacy a hanya ya siyi maganin ya sannan tsaya a wani babban store ya shiga ya siyo duk abinda yasan zata iya ci a lokacin sannan ya ƙarasa gidan su Manal ɗin. Wayar Manal ɗin ya kira ba a ɗauka ba babu jimawa sai ga Mubeena ta fito ta ƙaraso wajan da yake, ya fito daga motar ya miƙa mata ledar yace, "ki tabbatar ta sha don Allah, sannan tana yawan son shan sugar a kwanakin nan kar ki bari hakan ta kasance, yanzu haka sugar ta is too high in ta kuma sha abin zai yi worst. In ta takura baza ta sha tea ba sai da sugar ga wannan" ya faɗa yana sake miƙa mata leda mai girma yace, "zata iya amfani da komai na ciki." Karɓa Mubeena tayi tace, "in sha Allah. Amma ka nemi mafita shine maganin wannan damuwar, Kwana na biyu kawai aka yi ga abinda ya faru, in kwanakin suka yi nisa abin bazai yi daɗi ba." "In sha Allah. Na gode, ki gaishe ta in ta farka, in da hali ki kira in ta tashi duk dare." Mubeena ta amsa tana wucewa gida shi kuma ya hau mota ya koma gidan su. Sai da yayi sallar Isha sannan ya shiga gida yana shiga kai tsaye wajan abba ya wuce, ya samu Abban da ƴan uwan sa maza guda biyu a zaune da alama magana mai mahimmaci suke yi. Yana shiga da sallama suka amsa ya zauna bai ce komai ba. Daddy ya kalle shi yace, "Adnan ya dai?." "Daddy ku saka baki Abba ya warware min abinda ya ɗaure min kai don Allah." Daddy yace, "me kenan adnan?." "Abba ina so na san wacece mahifiyar Manal matata a wajan Abba." Daddy ya kalle Abba yace, "ka sanar dashi wacece ita a wajan ka." Abba ya kulle ido ya buɗe ya sauke numfashi yace, "ita bata faɗa maka ba?." Bebi yace, "naje jiya, amma ta tabbatar min da babu aurena da Manal, ta kuma tabbatar min da kai ne matsalar ta ba ni ba." Abba ya sauke numfashi cikin damuwar da tayi masa yawa a zuciyar sa yace, "dole tace maka haka, domin kuwa yadda ka ke ɗana haka itama take ƴata Adnan!." BDƘB3P05 A firgice Bebi ya kalli Abba cikin tashin hankali da faɗuwar gaban da tazo masa lokaci ɗaya mai haɗe da tashin hankali, yadda ya wara idanun sa kawai zai tabbatar maka da yadda yake cikin tashin hankali a wannan lokacin. Tabbas in za'a auna bugun zuciyar sa a wannan lokacin za'a ga zuciyar sa bata bugawa daidai, sannan jinin sa za'a tarar ya hau saboda tashin hankali. Magana yake so yayi amma ya kasa saboda nauyin da zuciyar sa tayi masa sai ido da yake kallon Abba idanun sa a waje, bakin sane yake motsi amma ya kasa magana ganin yanayin da yake ciki ya saka Daddy yace, "kamar ya kenan me ka ke nufi? Nufin ka kaine mahaifin matar Adnan?. Daman mai riƙon ta yace ba shine ya haife ta ba kenan kai ne ka haife ta?." Abba ya kalli Yayan sa ya sauke numfashi cikin nauyin zuciya yace, "duk yadda zan muku bayani babu lallai ku gane, kaina ciwo yake sosai, damuwa tayi min yawa a abar maganar nan kawai zai fi." Uncle yace, "Ta ya ya za'a barta, in aka barta shi Adnan ɗin wanne hali ake so ya shiga? Ka duba yadda ya ƙame ƙam yana kallon ka kana ganin sa ka san yana cikin tashin hankali matuƙa, na tabbatar yanzu tashin hankalin da yake ciki ya ninka damuwar da kace kana ciki, da gaske kaine mahaifin matar sa?." Abba ya dafe kai yana kallon Adnan da shima shi yake kallo ya kulle ido ya buɗe ya koma ya jingina da kujera bai ce komai ba. Daddy yace, "kayi magana, wannan shirun naka ba shine mafita ba fa, ka tuna akan matar Adnan ake magana, ta ya zaka ce kaine mahaifin matar sa kuma kace a bar maganar?." Abba yayi shiru sai kansa da ya dafe yadda kansa yake ciwo baya jin zai iya cewa komai. Daddy ya kalli Adnan cikin rarrashi da tausar da murya yace, "Adnan nutsu don Allah, dawo hankalin ka." Kallon Daddy yayi cikin rauni yace, "hankali na bazai taɓa dawowa jikina ba Daddy, indai ba gaskiyar maganar nan naji ba bazan taɓa dawo daidai ba." Uncle da yake kusa dashi ya dafa kafaɗar shi yace, "zaka iya, ka nutsu babu wanda ya wuce ƙaddara a rayuwar sa, in ma ƙanwar taka ce...." Da sauri ya katse Uncle yace, "don Allah Uncle kar kace haka, bazan iya jure wannan kalaman naka ba. Ta ya ya za'a ce matata  wacce na rayu da ita tsahon kwanaki ƙanwata ce? Meyasa tun da baku gano hakan ba? meyasa tun lokacin da nake neman aure ta ba a ce ni da ita yaya da ƙanwa bane sai yanzu?. Ya ku ke so nayi?!"Ya ƙarasa faɗar maganar a sanyaye yana kallon Uncle. Kallon Abban Uncle yayi ya kalli Bebi yace, "in sha Allah ba haka bane, ka kwantar da hankalin ka, yanzu mahaifin naka ba lafiya ce dashi ba." Kallon Abban yayi ya kulle ido tsoro ya gama mamaye masa zuciyar sa, babban tashin hankalin sa kar maganar nan ta tabbata, in ta tabbata zai iya rasa ransa ? Ta ya ya zai cigaba da rayuwa da Manal a matsayin ƙanwar sa bayan ya fara rayuwa da ita matsayin matar sa?." Daddy yace, "ka nutsu Adnan, ka nutsu don Allah. Wannan damuwar illa zata yi maka, amma in ka nutsu ka dawo nutsuwar ka komai zai zo da sauƙi. Shiru yayi yana sauke ajiyar zuciya amma jikin sa har rawa take yi saboda tashin hankali. Tashi yayi a sanyaye ya fita ya daga falon dan zama a ciki zai iya saka shi hauka na wucin gadi, mota ya shiga ya fita daga gidan a guje. Sai da yayi nisa ya tsaya a kan hanya ya kifa kansa a kan sitiyarin motar cikin tashin hankali da tsoro mai yawa. Zuciyar sa bugawa take yi sosai ji yake kamar yayi hauka, tunanin sa yana ga abinda Abba ya faɗa masa, da gaske dai matar Manal ƙanwar sa ce ta jini ko wasa ake masa?, in hakan ya tabbata ya zai yi? In hakan ya tabbata me zai faru wanne hali zai shiga? In hakan ya faru ya zai yi da ransa?. Allah ya sani yana matuƙar qaunar Manal, yana kallon ta matsayin abokiyar rayuwar sa kuma bugun zuciyar sa, kallon matar sa ma'ajin sirrin sa yake mata, kallon Manal yake matsayin uwar yaron sa da yake cikin ta. Ta ya rana tsaka ake so a juya ta ta koma ƙanwar sa wacce suke uba ɗaya?, in hakan ya faru da wanne ido zai iya kallon ta matsayin ƙanwar sa da suke jini ɗaya? Ya matsayin ɗansa da yake cikin ta? Ɗan sa ne ko ɗan ƙanwar sa?. "In sha Allah hakan bazai faru ba, bazai tabbata ba in sha Allah!" Ya faɗa a bayyane yana sauke numfashin wahala, a wahale maganar take fita saboda nauyin da zuciyar sa tayi masa. Waya ya ɗauko a aljihun sa ya kira  number Manal a karo na babu adadi, ɗauka akayi kafin yayi magana Mubeena tace, "ba ita bace Mubeena ce, ta sha magani amma taƙi cin abincin gabaɗaya, ko tea taƙi sha komai aka bata sai tace wai bata so." "Ya salam! Tana ina?" Ya tambaya cikin raunin zuciya. Mubeena tace, "gata" ta faɗa tana bawa Manal wayar. Jin shiru sai numfashin ta kaɗan-kaɗan ya saka yace, "Partner meyasa baza ki ci abinci ba? Haka kike so ki zauna babu abinci?, ta ya zaki samu lafiya in bakya cin abinci?." Manal bata yi magana ba yana jin saukar numfashi ta yace, "please ki sha ko da tea ne, Amma kar ki ce sai kin saka sugar kin ga har yanzu sugar ki bai yi daidai ba. Bana so ace kin kwana baki ci abinci ba, ki daure ki ci." Sai a lokacin tace, "bazan iya ci ba." Jin yadda tayi maganar da rauni ya sake kwantar da murya yace, "zaki iya, ki gwada zaki iya ci in sha Allah." Yana ji ta sauke numfashi amma bata ce komai ba yace, "ko akwai abinda kike so na kawo miki?." Manal tace, "a'a." "To ki sha tea ɗin please." "To" ya amsa a taƙaice yace, "Yauwa ko ke fa, maganin zai saka ki bacci, ki sha bayan kin ci abinci zaki yi bacci." Nan ma ta sake amsawa da to kafin yace, "Partner!." Jin yadda ya kira ta sai tace, "uhum!." "ki kular min da kan ki, I love you so much" ya faɗa yana kashe wayar ya ajjiye a gefe ya ɗora hannun sa duka biyun a kansa. Bai san adadin lokacin da ya ɗauka a wajan ba, shi kansa ya san ya jima a zaune a wajan kafin yaja motar ya nufi gidan sa kai tsaye. Huzaifa da Hamza suna zaune a gaban Mama bayan sun gaisa kamar yadda suka saba cikin fara'a, Hamza yace, "Mama mun zo ne damn akan Adnan." Mama ta gyara zama tace, "to wani abun ne ya faru?." Hamza yace, "Mama gabaɗaya Adnan ya canja daga yadda muka san shi, yanzu ko yaushe cikin damuwa yake ko aiki baya iyawa sai dai ya zauna ya zubawa waje ɗaya ido yana kallo. Hakan baya yi mana daɗi, mun saba ayi wasa ayi dariya dashi. Mun tambaye shi me yake damun sa matsayin mu na manyan abokan sa kuma mun zama kamarƴan uwa, duk mun zama ɗaya bama ɓoyewa junan mu komai, amma sai yace shi babu abinda yake damun sa. Hankalin mu ya kasa kwanciya da abinda ya ce, dan mun san ba gaskiyar kenan ba.  Shiyasa muka zo wajan ki ko zamu ji gaskiyar abinda yake faruwa." Mama tayi murmushi tace, "ai bazai faɗa ba kun fi kowa sanin halin sa, wani lokacin kana jin damuwar sa wani lokacin bazai faɗa ba. Amma ku ai ba wanda za'a ɓoyewa damuwa bane, ku abokan kuka ne kuma abokan dariya ne. Maganar gaskiya yana cikin damuwa sosai, auren sa da matar sa ne yake ɗan rawa kaɗan, amma muna addu'a in sha Allah abinda ake tunani bazai faru ba." Huzaifa yace, "Subahanallahi! Mama Manal ɗin?." "Itafa Huzaifa, an kasa gane abinda yake faruwa daga nan ɓangaren da ɓangaren gidan su, mahaifiyar ta tunda taga Abban su Bebi a asibiti da Maryma tana kwance tace Manal tazo su wuce gida. Anyi-anyi ta faɗi alaƙar su taƙi, Babban abinda bama so Allah yasa kar ace da Adnan da ita Yaya da ƙanwa ne. Wannan shine abinda ya dagula masa lissafi, shiyasa ku ke ganin sa cikin damuwa." A firgice Hamza yace, "in sha Allah Hakan bazai kasance ba. Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, Lallai dole Adnan ya shiga damuwa sosai, wannan tashin hankali har ina?." Huzaifa ya kasa magana ma shi saboda tashin hankali da mamaki da kuma tausayin Adnan da ya mamaye masa zuciya, lallai dole ya shiga damuwa mai yawa, yadda yake matuƙar ƙaunar Manal in aka ce ƙanwar sa ce zai iya samun ƙaramin ciwo. Mama tace, "in sha Allah bazai kasance ba, in hakan ya faru a yadda Bebi yake sai wani abun ya same shi, in akace an raba su da Manal Adnan bazai dawo daidai cikin daɗin rai ba sai an haɗa da roƙon Allah,  gabaɗaya ya fita daga hankalin sa dan yana da juriya ne da yanzu ya kwanta ciwo." Huzaifa yace, "Allah ya amince Mama, ko ni na shiga tashin hankali da jin wannan maganar balle shi da kansa. Ya Allah ka kawo mana mafita da gaggawa." Mama ta amsa da amin kafin tace, "wannan shine silar canjin da kuka gani, yanzu ma naji ya ɗauki mota ya fita ban san inda ya nufa ba kuma." Hamza yace, "Allah ya kawo mafita a lamarin, Amma Mama dole ya shiga tashin hankali, ai wannan ba ƙaramin abu bane dole ya rasa nutsuwar sa. Allah ya daidaita lamatin." Mama ta girgiza kai kawai bata ce komai ba kafin su yi mata sallama su tafi.   ****Bebi bai jima da zuwa gidan saba aka kira shi Abba babu lafiya dole haka ya dawo gidan. Lokacin da yazo har sun kai shi wani ƙaramin private hospital da yake kusa dasu dan bashi taimakon gaggawa. Koda yaje Yaya isma'il ne kawai a ɗakin an sakawa Abban ruwa. Fita yayi ya nemi likitan da ya duba Abban a nan yake sanar dashi jinin sane yayi kasa shiyasa yake fama da ciwon kai mai tsanani amma da ruwan da aka saka masa ya ƙare zasu iya tafiya gida. Har ruwan ya ƙare suna nan, a lokacin sha ɗaya na dare suka dawo da Abba shi kuma shida Yayan da suka wuce unguwar su.                 Washe gari. Baba bai jima da dawowa daga Katsina ba yana zauna shida Mama Mubeena ta kawo masa abinci kafin ya fara ci ya kalli Mama yace, "ni ba wannan ba, ina shigowa unguwar nan da abinda aka fara tara ta dashi shine Manal kwanan ta biyu a gidan nan. Da gaske ne Manal ta kwana biyu a gidan nan?." Mama cikin mamakin halin mutane tace, "ikon Allah, Mutane da gulma suke, har a san ta kwana biyu a gida?." Baba yace, "kiwon mutum ake yi ba dabba ba ai, me ya faru tayi kwana biyu a gida? Adnan ɗin ne yayi tafiya ya turo ta nan?." A lokacin Manal ta fito a guje daga ɗaki, kafin ta kai ga inda fanfo yake ta fara shara amai a tsakar gidan hannun ta na dafe da kanta da kuma cikin ta saboda yadda take ji kamar basa jikin ta. Da hanzari Baba ya tashi Mubeena ma ta fito daga ɗaki ta ƙaraso wajan ta Baba yace, "Subahanallahi! Manal daman baki da lafiya ne?." Mubeena ta riƙe ta ta kwanta a jikin Mubeena Baba ya taɓa wuyam ta yace, "Zazzaɓi ne a jikin ta sosai, Mubeena daman bata da lafiyq ne? Ko daman rashin lafiyar ce ta saka ya kawo ta gida?." Kafin Mubeena tayi magana sai yace, "Ko da yake mai zai saka ya kawo ta gida dan bata da lafiya shi da yake likita?." Baba ya sake cewa, "An je asibiti kuwa?." Mubeena tace, "ba'a je ba, amma akwai maganin da take sha. Rashin cin abinci ne ya mayar da ita haka wallahi, bata son cin komai tunda tazo nan." Baba yace, "meyasa bata ci? Bata samu abinda take so ba?." Mama da take gefe tace, "Laulayin ciki fa take yi, sai a hankali." Baba ya kalli Manal ya sake kallon Mama yace, "duk da hakan dai, jikin ta akwai rashin lafiya ba iya na ciki bane wannan." Ya kalli Mubeena yace, "ga kunu can ki bata tasha sai yafi shayi riƙe mata ciki, in ta sha sai ta sha magani, in bata daina jin ciwon ba sai mu je asibiti. Kama ta ki shiga ciki" Baba ya faɗa yana ɗago Manal daga zaunen da take Mubeena ta riƙe ta ta shiga da ita ciki. Baba da kansa ya ɗebo ruwa ya zubawa wajan da tayi aman duk da babu komai a aman sai ruwa saboda babu abincin kirki. Wajan Mama Baba ya dawo ya zauna ya kalle ta a nutse yace, "baki faɗa min ba, me take yi a gidan nan a wannan halin?." Mama tace, "auren su ne ya ƙare." Da mamaki Baba yace, "kamar ya kenan? Sakin ta yayi ko me?." "Bai sake ta ba, Amma zai sake ta ɗin." "Ki min bayani na gane mana!" Ya faɗa yana ɗaga murya kaɗan. Mama tace, "daman ka san Ibrahim shine mahaifin wanda ka bawa auren Manal?." Baba yace, "eh Mu'azzam Alhasan shine mahaifin sa, meye aibu a nan?." Mama ta girgiza kai tana kallon sa tace, "to shine na ta mahaifin ta." Baba ya kalle ta da hanzari cikin faɗuwa gaba da tashin hankali yace, "ban gane ba." Mama tace, "ina nufin shine uban ta itama." "Ban yarda ba, taya ya zama mahaifin ta bayan nasan shi mahaifin ta ba haka sunan sa sa yake ba? Kar ki dagula min tunani ki faɗa min gaskiya abinda yake faruwa." Mama tace, "ai ban taɓa yi maka wannan wasan ba, tunda kaji na faɗa ka amince kawai in ba haka bane ai bazan faɗa ba. Auren ta da Adnan ya ƙare ko tana so ko bata so, saboda Adnan matsayin Yayan ta yake kuma kasan babu aure tsakanin Yaya da ƙanwa a musulunci." Baba ya bi Mama da kallo haka kawai yaji bai abince da abinda tace ba ko kaɗan. yace, "meyasa nake jin ban amince ba da abinda kike faɗw ba?." Mama ta tashi tsaye tace, "kuma gaskiyar kenan ba" ta faɗa tana wucewa ciki. Baba yayi shiru yana tunani kafin yace, "Hakan bazai yu ba, akwai abinda take ɓoyewa amma zan gano shi."       *******Bebi yana zaune gaban Abba kamar yadda ya saka a kira masa shi tunda suka gaisa bai ce masa komai ba. Ya jima a zaune yana jiran yaji mai zai ce shi kuma bai ce a saboda nauyin da yake a zuciyar sa bakin sa ya kasa furta komai. Sai daga baya sannan Abba yace, "Kana ta jiran tsammani ko Adnan? Nasan zuciyar ka tana cike da tashin hankali da wasuwasi akan auren ka da matar ka, ni kaina a wannan halin nake. Amma kafin nan ya maganar Kamal?." Bebi yace, "an gama da maganar Abba, duk dai ban bibiyi lamarin sosai ba saboda yanayim da nake ciki, Amma komai ya ƙare shi kansa Kamal ɗin yayi nadamar abinda ya aikata." Abba ya sauke ajiyar zuciyar yace, "nauyi nake ji a ƙirji na Adnan, lokacin ɗaya Allah ya saukar min da wannan nauyin a zuciyata. Ku yi haƙuri kaji." Bebi ya kalli Abba yace, "Abba me akayi?." Ya sauke numfashi yace, "komai ma anyi Bebi. Yanzu abinda zai faru ka tashi ka raka ni gidan su matar taka ina so naga babar ta." Bebi ya kalle shi  da mamaki da tsoro yace, "Abba baka da lafiya bai kamata ka fita ba." "Na sani Adnan, ina so muje ko dan kaima ka nutsu, in ban je mun yi magana da ita ba baza ka samu sauƙin abinda yake damun ka ba." Bebi ya sauke numfashi yace, "Abba ka bari kawai duk sanda ka samu lafiya sai mu je." Abba ya girgiza kai yace, "yau nake so muje kuma yanzun nan, ka Kira Yayyen ka maza mu je tare." Bebi ya amsa da to yayi musu waya da yake duk suna kusa sun taso duba Abban ba jimawa suka ƙaraso, a tare suka fito suka shiga mota zuwa gidan su Manal. Gaban Adnan sai faɗuwa yake yi da yake shi yake jan motar zuwa gidan, tashin hankalin sa ya bayyana sosai a zahiri dannewa kawai yake yi baya nunawa, Babban tashin hankalin sa ace Manal ƙanwar sa ce, ji yake zai iya yiwa kansa illa a lokacin da abinda yake gudu ya zama gaskiya, zuciyar sa zata iya bindiga nan take ta tarwatse. A ƙofar gidan su Manal ya faka cikin ikon Allah aai ga Baba yana niyar shiga gidan, ganin sa sai Bebi ya fito yana yi masa magana. Baba ya tsaya ya juyo yana cewa, "A'a Adnan kai ne tafe?." Suka gaisa da Baba ya amsa da fara'a kafin Bebi yace, "tare muke da Abbana, yace yana son magana da Mama ne shiyasa muka zo." Baba yace, "to jira ni,  bara na sanar da ita sai nazo mu shiga." Kafin ya shiga gidan har Abba sun fito daga motar, Baba ya tsaya suka gaisa sannan ya shiga ciki. A falon ya tarar dasu Manal na shan tea kamar tana shan maɗaci sai yatsina take yi, ya shiga da sallama ya kalli Manal yace, "Manal ya jiki naki?." Manal tace, "da sauƙi." "Allah ya ƙara sauƙi, ki daure ki dinga cim abinci kin ji?." Ta daga kai alamun to. Baba ya kalli Mama yace, "Adnan da mahaifin sa suka zo, suna  waje suna son shigowa saboda subyi magana dake." Mama ta kalle shi ganin ita yake kallo tace, "meyasa yake son magana dani kuma?." "In ya shigo sai ki tambaye shi" ya faɗa yana juyawa ya fita. Ta kalli Manal da take kallon ta tace, "Ku koma ciki." Manal ta tashi tana riƙe bango ta shiga ciki Mubeena ma ta shiga,  a lokacin suka ji sallamar Adnan da mahaifin sa da ma Yayyen Adnan ɗin. BDƘB3P06 Sallamar mahaifin Bebi da shiga falon ya saka Mama ta kulle ido ta buɗe, ko kusa bata yi maraba da zuwan su har zuciyar ta, in ba dan Baba ba babu dalilin da zai saka su zo mata har cikin gida. Zama suka yi dukkan su kafin yayi magana Mama tace, "me kuma kazo kayi a nan? Ko kazo ƙarasa abinda baka gama ba na shekarun baya da suka wuce?." Baba yace, "haba Zahra, ko gaisawa kya jira ayi sannan ki yi magana, wannan wacce irin magana kike yi?." Mama tace, "ko kaɗan bana maraba da zuwan sa nan balle na na tsaya a gaisa, ban shiryawa magan a yanzu ba ba kwata-kwata. Da ace na san hakan zai kasnace a yau wallahi da ban zauna a gidan nan ba." Abba yayi murmushin takaici yace, "Nima ban shiryawa hakan ba, lokaci ne yazo dole mu warware ƙullin da yake tsakani ko dan mu cire yaran mu daga duhu." "Har wani ƙulli ne a tskaanina da kai? Wanne ƙulli zan ƙulla dakai?." Abba yace, "na san babu." Mama ta girgiza kai ta rufe ido tace, "Adnan kawai nake kallo, Amma..." sai tayi shiru bata ƙarasa ba ta ɗauke kai gefe bata ce komai ba. Abba yace, "Nasan daman bani da darajar da zaki magana dani, rigar alfarmar Adnan da na shiga kuma na gode da hakan. Don Allah Zahra ki yi haƙuri da abinda ya faru a baya, na san ban kyauta ba daga na biyewa son zuciya amma dana sani, na kuma koma har inda kike da niyar baki haƙuri na tarar bakya nan." Abba ya sake cewa, "ba dan ni ba saboda Allah, ga kuma saboda Adnan da ya shiga damuwa akan wannan lamarin sosai, na tabbatar itama matar tasa a yanzu haka tana cikin damuwa." "Tsohuwar matar sa dai zaka ce, domin babu shi babu Manal" ta faɗa a fusace har lokacin bata kalle shi ba. Abba ya numfasa yace, "Ni ne nayi miki laifi ba Adnan ba, meyasa laifina zai shafe shi?." Cikin fusata Mama tace, "saboda bana da buƙatar haɗa jini da kai da irin ka gabaɗaya, sannan...." Haɗa ido suka yi da Adnan sai ya sunkuyar da kansa ƙasa itama sai ta kawar da kanta ta fasa faɗar abinda zata ce. Abba ya ga abinda ya faru yayi murmushin takaici yace, "gashi kin kasa faɗa saboda Adnan ɗin, na tabbatar yana da girma a idon ki da kuma ƙima sosai. Ban taɓa tsayawa Adnan ya samu abinda yake so ba, a ko wanne lokacin shi yake nemarwa kan sa abinda yake so. A wannan lokacin nazo ne domin na nemi afuwar ki sannan ki yi haƙuri kar laifina ya shafe shi." Mama tayi shiru bata ce komai ba Abba ya kuma cewa, "duk abinda kike tunani a wancan lokacin ba haka bane, babu yadda ban yi da Ali ba akan ki, na san ina da laifi amma a farko ban san da ƙudurin cutarwa a zuciyar sa ba, da na sani tun farko ba zan bashi goyan bayan aikatawa ba. Daga baya da na samu bayanin ƙudurin sa sai na biyewa son zuciya muka haɗa kai dashi. Babban kuskurena da nayi da na bar ki a wannan lokacin, ya kamata ace nayi wani abun ko dan saboda ƴaƴan ki da suke tare dake a lokacin amma san ban yi ba. Ki yi haƙuri komai ya wuce don Allah, haƙiƙa na ɗauki haƙƙin ki amma wallahi bani da laifi, ban ɗauki ko da ƙayar zarra a cikin abinda Ali ya ɗauka ba. Duk da nasan baza ki yarda ba, amma bazan rantse a kan ƙarya ba." Mama ta sauke numfashi ko kusa bata son a tuna mata da mahaifin su Manal, ta kawar da kai gefe bata ce komai ba. Abba ya sake cewa, "ki yi haƙuri ki yafe min a karo na babu adadi." Mama ta kulle ido ta buɗe tace, "ni daman ba laifi aka yi min ba, in ma an yi min ya wuce ko dan saboda Adnan ɗin." Abba yayi murmushi cikin jin daɗi yace, "na gode sosai, Allah ya saka miki da alkhairi ya jiƙan iyayen ki." Mama ta amsa da amin kafin tace, "kamar yadda kace baka taɓa tsayawa Adnan ya samu abinda yake so ba, wannan ne karo na farko da ka shige masa gaba dan ganin ya samu abinda yake so, Ni kuma a karo na farko zan hana Manal abinda take so. Babu abinda bana bata wanda take so koda shi kaɗai na mallaka a duniya ina sadaukar mata dashi. Amma a wannan lokacin zan juya sama ya koma ƙasa, zan hanata zama da Adnan ko tana so ko bata so. Saboda haka ra'ayina yake, yadda ban tashi da kowa a kusa dani ba, su ma haka nake so su tashi basu san kowa na su ba mu cigaba da rayuwa. Zata auri wani daban wanda bai sanni ba nima ban san shi ba, hakan shine mafita kuɓa shine kwanciyar hankali a wajena. In da ace na san zan haɗu da kai a da babu ƙaddarar da zata kaini zama a Kano, yadda na tashi nayi rayuwa babu wanda ya sanni haka nake so na koma ga Allah, hakan bazai faru ba sai Adnan ya fita daga rayuwar Fatima." Tsoron ya bayyane a fuskar Adnan ya kalli Mama yaga gefe take kallo ya kalli Abba da yake kallon ƙasa ya kasa cewa komai. Baba ne yace, "Haba Zahra, meye ribar ki in kika raba aure da yake tsakanjn Manal da mijin ta? Laifin wani baya shafar wani ko a wajan Allah." Da sauri Mama tace, "Bana son sake tuna wani abu da ya wuce ne, zaman shi da Manal tamkar dawo da hannun agogo baya ne, ka fita daga maganar nan kawai kar ma kace komai, haka za'ayi domin hakan nake so." Abba yace, "baki yafe min ɗin ba kenan?." Bata ce komai ba dan bata son yin magana a gaban Adnan, da ace babu Adnan da sai tayi masa wankin babban bargo, sai ya tabbatar da wacce ya sani a baya ba itace yanzu ba. Shiru Mama tayi bata kuma magana ba sai daga baya tace, "nace magana ta wuce a rufe wannan shafin bana son sake tunawa, maganar aure tsakanin Adnan da Manal ne babu. Sakin ta nake so yayi daga yanzu zuwa ko wanne lokaci, bana son zaman auren su ko da wasa." Abba ya kalli Adnan da yake zaune ya kasa ko motsi kansa yan ƙasa, ya kalli ƴan uwan Adnan ɗin kafin yayi magana Baba yace, "kar ka damu, babu abinda zai faru in sha Allah." Tashi Mama tayi ta koma ɗaki bata sake magana ba, dole suka fito dashi dasu Baba zuwa waje Bab yana cewa, "ranta ne kawai a ɓace, amma da zarar ta wuce babu wani abin damuwa. Babu abinda zai raba auren Manal da Adnan in sha Allah." Abba yace, "Allah ya amince, bana so laifin da nayi ya shafi Adnan bazai iya jure rashin matar sa ba." "Babu komai in sha Allah" Baba ya kalli Bebi za yake tafiya kamar mara laka a jikin sa yace, "kar ka damu Adnan, ɓacin rai ne kawai yake damun ta, kasan in ka tuna da wani abun da ya faru a baya ka kan kasa sarrafa ɓacin ran ka. Shine yake bibiyar ta amma da zarar ta wuce shikenan komai zai wuce in sha Allah." Adnan yayi godiyq sosai suka shiga mota suka bar ƙofar gidwn har lokacin shi bai gamsu da wannan zuwan basu ba. Suna fita Mama ta fito daga ɗakin ta ta shiga inda Manal take ta kalle su tace, "eh baku da alaƙa ta jini da Adnan, ba yayan ki bane haka ba kowa naki bane aure ne ya haɗa ku. Auren kuma ina so ya ƙare daga yanzu. Manal nasan kina son abinda nake so, ban kuma taɓa hana ki abinda kike so ba. Na san kina son mijin ki kina ƙaunar sa, ina so ki sadaukar min da wannan soyayyar indai na isa da ke matsayin uwa ki bar auren Adnan har abada. Bana son auren ki da shi kuma bana ra'ayin hakan" ta kalle ta tace, "zaki yi min ko baza ki min ba?." Manal jikin ta har rawa yake yi ga rashin lafiya ga tashin hankali, hawaye kawai take yi wanda ta rasa dalilin zuwan sa. Mama ta zauna gefen ta tace, "bazan iya jure ganin ki da Adnan matsayin mata da miji ba, zaki iya sadaukar min da soyayar da kike masa ko baza ki iya ba?." "Zan iya Mama, zan yi, Tunda bakya so na haƙura." Mama ta riƙe ta a jikin ta tace, "bawai bana son zaman ki da shi bane, kawai bana son tuna duk wani abu da ya faru a baya. Kamar yadda na san kin ji babu alaƙar jini a tsakanin ku, nace miki mahaifin sa shine mahaifin ki ne kawai saboda ki saka a ran ki babu ke babu auren sa, zaman ki dashi zai saka abubuwan da bana son bayyanar su su bayyana, ni kuma ban shiryawa hakan ba, faruwar hakan zai iya cutar dani shiyasa nake so ki rabu dashi ne Manal!." Manal ta girgiza kai tana kuka tace, "tunda kina so Mama zan yi." Mama ya rungume ta tana shafa bayan ta tace, "Allah zai baki wani wanda ya fi shi, zai baki wanda baki tunanin samun sa ba in sha Allah." Ta ɗora hannun ta a akan cikin Manal tace, "babu yadda zan yi da cikin jikin ki, Amma gaskiya..." sai kuma tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya. Manal dai kuka take tana jikin Mama dan babu yadda zata yi da ita ne, Amma tana son mijin ta bata son rabuwa dashi, kuma gashi bata ga laifin sa ba balle ace za'a raba su ta dalilin laifin. Daman tashin hankalin ta ace ita dashi jini ɗaya ne gashi yanzu ta tabbata babu abinda ya haɗa su meyasa Mama take so ta raba su?. Sakin ta Mama tayi ta tashi ta fita Mubeena tabi bayan ta tace, "Mama Manal tana son mijin ta, tana ƙaunar cigaba da zama dashi, meyasa kike son raba su don Allah?." "Mubeena bana son wannan maganar ta riga da ta wuce." "Mama in kika aikata hakan kamar...." Dakatar da ita tayi tace, "bana son sake jin bakin ki a akan wannan maganar Mubeena, ki ƙyale ni na san abinda nake yi ni ba mahaukaciya bace." Mubeena tace, "To Mama, amma me ya haɗa mu da shi mahaifin Adnan? Waye shi a wajan mu?, Gabaɗaya wannan tunanin shine ya cure mana ya tsaya a ƙirjin mu, waye shi?." Mama ta harare ta tare da yin tsaki bata ce komai ba ta wuce ta bar ta a wajan a tsaye. Bebi a haka suka koma gida babu wanda yayi magana har ɗaki suka raka Abba bayan ya zauna ya kalle shi yace, "Hankalin ka ya kwanta ko Adnan? Baku da alaƙa ta jini da matar ka, abinda ya saka nace maka itama ƴa tace saboda ƴar babban abokina ce na wancan lokacin." Bebi ya girgiza kai bai ce komai ba saboda zuciyar ta sa babu daɗi ko kaɗan, Abba ya kuma cewa, "in ka nutsu zan baka labarin dalla-dalla." Bebi yace, "Abba a nutse nake ina so na sani." Abba ya sauke numfashi yace, "dakai da ƴan uwan ka da kowa ma na gidan in an yi sallar magriba zuwa i'sha zan sanar daku a inda na san maahifiyar matar ka. Zan sanar daku abinda ya haɗa mu da abinda ya saka ta ke faɗar wannan maganar a kai na." Bebi yace, "Allah ya nuna mana lokacin." "Amin. In sha Allah matar ka baza ta kubce maka ba, zata dawo ku cigaba da zama matsayin ma'aurata, kar ka damu." Bebi ya girgiza kai cikin sanyi jiki Abba yace, "yadda ban tsaya maka a lokacin auren ka ba, zan tsaya maka a yanzu wajan ganin matar ka ta dawo gare ka in sha Allah. Kar ka damu, zan zamar maka mahaifin da ka jima kana buƙatar irin sa, ba ma kai kaɗai ba dukkan ku." Bebi ya girgiza kai dan ya fahimci canjin mahaifin nasu tunda daga kan wannan sa'in sa ɗin da suka yi da Mama. Bebi yace, "Allah ya tabbatar da hakan Abba." Ya amsa da amin suka yi masa sallama suka fito. Wajan Mama ya shiga bai jima a ciki ba ya fito ya hau mota ya tafi. Duk a gidan suka yi sallar i'sha saboda kiran Abban, suna idarwa ya dawo gidan burin sa kawai yaji me yayi zafi haka har Mama take son raba su?. Yana shigowa harabar gidan wayar sa ta fara ƙara, ya ɗauko ta daga aljihu ya duba ganin sunan Manal ya saka shi ɗauka da hanzari. Daga can ɓangaren Mubeena tace, "Dr Mubeena ce dai." Da hanzari yace, "ina jin ki." "Manal ce babu lafiya, yanzu haka muna asibiti. Kamar yana gaban ta ya wara idanu yace, "hasbunalalahu wa'inmal wakil! Me ya same ta? Wanne asibiti ne? Me suka ce yana damun ta?. Ki min bayani ya jikin nata?." Mubeena tace, "muna nan asibitin freedom" kafin ta ƙarasa yace, "gani nan zuwa" ya faɗa yana yanke wayar ya ƙarasa wajan mota da sauri ya shiga ya fita daga gidan a guje. Asibitin ya nufa gabaɗaya hankalin sa a tashe yake sai bayan ya shiga ya sake yi mata waya ta faɗa masa inda suke ya nufi inda take ya tarar da ita a tsaye a ƙofar ɗakin tana jiran sa. Ya kalle ta yace, "a wanne hali take ciki?." Mubeena tace, "da yake tun ɗazu muna nan har tayi bacci ta tashi, sun ce yunwa ke damun ta da kuma rashin samun bacci, in aka cigaba da tafiya haka jinin ta zai iya hawa saboda rashin bacci, sannan za'a iya rasa babyn." Adnan ya sauke numfashi yace, "tana ina?." Mubeena ta nuna masa ɗakin ya ya wuce ta ya shiga ya hango ta a kan ɗaya daga cikin empty ɗin gadajen ɗakin guda uku a zaune, ta zubawa waja ɗaya ido tana kallo, kana ganin ta ka ganta kasan tana cikin damuwa. "Partner!" Ya faɗa yana ƙarasawa inda take. Da hanzari ta dago tana kallon sa kawai sai ta fashe da kuka ya ƙarasa da sauri ya zauna a gefen ta ta rungume shi tana kuka sosai. Shima riƙe ta yayi a jikin sa yana shafa bayan ta a hankali cikin kewa da soyayya mai nuni da tsantsar kulawa. Yadda ta cukuwikwiye shi ne ya saka ya sake riƙe ta gam-gam a jikin sa, babu wani space da iska zata ratsa tsakanin ƙirjin su. "Ki daina kuka partner, ki bar kuka baki da lafiya" ya faɗa yana riƙe kanta a ƙirjin sa. Kuka take yi sosai cikin so da ƙauna da kuma kewar mijin ta, ta rasa ina zata saka ranta taji daɗi komai ya tsaya mata cak a lokacin da bata yi tunanin haka ba. Sassauta riƙon da tayi masa tayi ya ɗago ta daga jikin sa ya riƙe fusksr ta da duka hannayen sa guda biyun yace, "jikin ki akwai zafi har yanzu, Meyasa bakya son cin abinci?." Kallon sa take yi shima kallon ta yake ta lumshe ido ta sake komawa jikin sa ta kwanta tana kuka ƙasa-ƙasa. Bayan ta yake shafawa a hankali yace, "bana so naga kina kuka, ki nutsu mu yi magana." Zagayawa tayi da hannaun ta ta sake riƙe shi tana cusa kanta a ƙirjin sa, kewar mijin ta take ji sosai musamman ƙhamshin sa da tayi missing kwana biyu, ta kasa boye abinda take ji hakan ya saka take sake maƙale masa Ganin yadda take riƙe shi sai yayi shiru yana riƙe da ita bai ce komai ba itama bata ce komai ba. Ɗago kai tayi tana sake kallon sa shima ita yake kallo ido cikin ido kafin tayi magana yace, "ina son ki Manal, bazan iya jure rashin ki ba." Lumshe ido tayi taji yana goge mata hawaye yace, "Meyasa bakya cin abinci?." Buɗe ido tayi bata ce komai ba ya yi mata kiss a goshi, ya sake yi mata wani a wuyan ta, ya sake yi mata wani a kumatu ya riƙe fuskar ta yace, "meyasa?." Muryar ta na rawa tace, "bana iya ci." "Amma hakan zai iya cutar dake ai, in wani abun ya same ki ya zanyi? Don't forget your my life partner, ciwon kai in kika yi bazan so ba sai dan babu yadda zanyi, ki dinga cin abinci shine zai saka lafiyar ki ta inganta sosai." Manal tace, "kasan bana iya ci ko? Ko a gida bana iya ci ka san da hakan." "Shiiii! to daina kuka shi ne bana son gani" ya faɗa yana sake mayar da kanta jikin sa. "Babu abinda zai raba mu Manal, in sha Allah komai zai wuce kamar bai faru ba." Manal jin haka sai ta janye jikin ta tace, "i'm sorry partner!." Kallon ta yake yi alamun me ya faru tace, "kayi haƙuri, bazan iya ƙin yiwa Mama abinda take so ba, zan yi amma ba dan bana son ka ba. Wallahi Ina sonka, ina ɗaunar ka, Amma zan iya rabuwa da kai saboda Mama." A firgice ya kalle ta yace, "What! Manal me kike cewa?." "Abinda kaji nace, zan iya haƙuri da son sa nake maka nayi abinda Mama take so. Mama tace ba dan bata son ka dank ba, kawai tana so na rabu da kai partner..!" Ta faɗa tana kuka mara sauti. Ya girgiza kai yace, "ki daina faɗar haka, ki daina faɗa Manal, babu abinda zai raba mu sai mutuwa." Ta ja numfahsi tace, "kayi haƙuri, Kayi haƙuri!." Hannun sa ya saka a bayan ta ya riƙe ta sosai a ajikin sa kamar zai mayar sa ita ciki saboda yadda ya riƙe ta sosai. Itama haka take so dan duk da tana jikin sa amma kewar sa take ji kamar basa tare. "Zaki iya rabuwa dani partner? Zaki iya zama ba tare dani ba?." Bata ce komai ba sai sake gyara kwanciya da tayi a jikin sa yace, "Nasan baza ki iya ba, kina ƙauna ta kamar yadda nake ƙaunar ki. Wallahil azim lokacin da nake tunanin ke ƙanwata ce Allah kaɗai yasan irin damuwar da na shiga, Allah kaɗai yasan irin tashin hankalin da zuciyata yake ciki. Bana iya cin abinci, bana iya bacci, bana iya aiki, bana iya komai sai tunanin ki partner. Na tabbatar kece rayuwata, in na rasa ki rayuwata zata shiga wani hali Manal, don Allah kar ki rabu dani ki zauna dani har abada, rashin ki babbar illa ce a gare ni." "Nima ina son ka Partner, ina son ka!" Abinda tace kenan tana kwance a jikin sa. "Kar ki rabu dani Manal, duk runtsi duk wahala ki kasance dani, zaman ki tare dani shine kwanciyar hankalina." Numfashi take saukewa a hankali cikin azabar so da kewar mijin ta. Ɗan knocking ƙofar akayi a hankali hakan ya saka ya ɗago ta daga jikin sa ya kalli ƙofar, Mubeena ta shigo tace, "ga abinci ka bata kai zata ci." Ƙarasowa tayi ta ajjiye abinci ta juya tana aiyana dole ma tayi aure wannan soyayyar da Manal da Adnan suke yi ta saka mata son yin aure da gaggawa. Ɗaukar abincin yayi ya buɗe ya zuba mata ya ƙara da salad sosai ya kai, ya ɗebo ya kai bakin ta ta girgiza kai shima ya girgiza kai yace, "Sai kin ci." Turo baki tayi ya nata kiss a bakin ya fara bata abincin tana ci a hankali. Taci sosai kaɗan ta rage ya ƙyale ya ajjiye ragowar, sake kwatar da ita yayi a jikin sa yan shafa kanta zuwa bayan ta a hankali bacci ya ɗauke ta tana jikin sa. Ganin tayi bacci ya kwantar da ita a kan gadon yana kallon ta. Numfashi ya sauke ya taso ya fito a nan ya tarar da Mubeena a zaune ya ƙarasa yace, "Don Allah duk abinda ake buƙata ki kira ki sanar dani, in akwai wani abun duk dare ki faɗa min. Yanzu taci abinci sosai kuma tayi bacci, koda zata farka ki sanar min ɗon Allah." Mubeena tace, "in sha Allah zan faɗa maka." Yayi murmushi yace, "na gode da taimakon ki." Tayi murmushi kawai ya wuce ya fita ita kuma ta koma ta zauna. Kai tsaye gida ya wuce yana ajjiye mota ya shiga ɓangaren Abba a nan ya tarar da gabaɗaya ƴan gidan suna nan har lokacin da alama jiran sa ake yi. Ya shiga da sallama aka amsa Abba yace, "shikenan gashi nan ma, kowa ya zauna mu yi abinda ya tara mu." Bebi yace, "ayi min haƙuri naje asibiti ne." Abba yace, "an yi maka, zo ka zauna na warware maka wacece mahaifitar matar ka wajena." Jiki a sanyaye Bebi ya zauna yana jira yaji abinda Abba zai ce. BDƘB3P07 Abba ya kalle su gabaɗayan har dasu Mama da suke zaune ya sauke numfashi ya dafe kansa, nauyi yake ji a zuciyar sa musamman in ya tuna da abinda ya faru da Maryam da kuma Lubna. Hankalin sa tashi yake yi sosai ya rasa inda zai saka ransa shiyasa gabaɗaya ya shiga damuwa sosai. Daƙyar ya kawar da tunanin zuciyar sa yace, "A wani lokaci a baya shekara ashrin da wani abun da ya wuce, na kassane ina tafiye-tafiye daga wannan gari zuwa wannan gari don kasuwanci musamman siyan gonaki da dabbobi da sauran abubuwa masu daraja a wancan lokacin. Ina shiga garuruwa da yawa musamman garin fulani, na shiga na saro dabbobi na tawo dasu Kano na siyar. Ko na siyi gona a can bayan wani lokaci na siyar da ita ko na bada hayaa dinga yin noma ga mutanen ƙauyen." "Akwai wani abokina wanda muka haɗu a harkar siye da siyarwa ɗin nan da nake faɗa muku, muka saba dashi sosai dan mutum ne mai faran-faran da saurin sabo, kuma ya fini sanin harkar kasuwanci sosai wani abun shine yake buɗe min ido a kai, sabon mu yayi nisa har ya zama tare muke zuwa mu dawo tare. Shi yana zaune a Zaria ne ni kuma ina zaune a Kano, in gabas zamu yi zan je tashar Zaria mu haɗu dashi daga nan mu tafi, in yamma zamu yi zai zo tashar Kano mu haɗu mu tafi. Aliyu yana da ɗabi'ar son kuɗi sosai, dan a harkar kasuwancin mu ma ƙarara zai nuna zai yi maka wayo saboda ya fika cin riba, fara'ar sa da saurin sabon sa wani lokacin ya kan juye ya zama na cuta in ya samu dama." Abba ya kalli Mamy yace, "in zaki iya tuna shi ya taɓa zuwa wancan gidan, kuma a lokacin da ke kaɗai ku ka gaisa, a lokacin ina tunanin haihuwar Maryam ne ko Farida dai na manta. Amma kamar lokacin Hauwa bata nan basu haɗu dashi ba gaskiya." Mamy tace, "bazan iya tunawa ba tunda ba sanin kirki nayi masa ba gaskiya." Abba yaja numfashi ya kalle su yace, "na san da yawan ku musamman Bilal da Ismal'i da kuke ƴan kasuwa zaku san sunwn Alhaji Muhammad Jalingo, ko baku san shi ba nasan kun san wani baban mutum mai ƙarshen suna Muhammad Jalingo ko?." Yaya Bilal yace, "sosai ma kuwa Abba, family Muhammad Jalingo ba ɓoyyayyu bane a fannin kasuwanci. Kowa yasan Alhaji Ahmad Muhammad Jalingo, Wanda yake shine na uku a africa a fannin kuɗi na kasuwanci. Abba ya girgiza kai ciki gamsuwa yace, "Marigayi Muhammad Jalingo ɗin da kansa nake magana a kai yanzu, Allah ya gafarta masa yasa yana aljanna." Aka amsa da amin kafin Abba yace, "Garin Taraba state gari ne na mazauna yare kala-kala, baza ka keɓance yare guda ɗaya kace ai garin Taraba zamuna cikin sa wannan yaren ne kawai suke yi ba, yana da yaruka daban-daban wanda suke zaune a cikin sa." "Garin Taraba gari ne na kasuwanci musamman abinda ya shafi harkar noma da kasuwanci, tun a shekarun baya garin yana karɓar baƙi kala-kala wanda suke shiga don kasuwanci. akwai wani da yawon kasuwancin mu ya kai mu garin Taraba state cikin babbar birnin su Jalingo. Bamu san ko ina ba mu dai mun je da niyar kasuwanci kamar yadda muka saba, an sauke mu a tasha mu kuma mun shiga cikin gari. kasnacewar garin ya kasance yana da Fulani sosai, a wancan lokacin muka ɗari-ɗari saboda rashin yardar da Fulani basu dashi na lokacin baya." A cikin unguwar Gadi wacce take a cikin tsakiyar birin Jalingo muka samu wani babban masallaci don yin sallar azahar dan da wuri muka sauka a garin. Mun yi salla a babban masallacin mun fito dani da Ali muna tattauna inda zamu je mu kwana, bamu san ko ina ba haka bamu dan kowa ba karon farko da ya kai mu garin. Har gwara sauran garuruwan da muke zuwa muna da ido a can, dan akwai mutanen Ali a can sosai saɓanin Jalingo. Muna ta tattauna abinda zamu aai ga marigayi ya fito daga masallacin." "Mutane suna ya bin sa a baya kamar sarki saboda yadda ake girmama a lokacin, yana da fara'a da yawan murmushi a ko yaushe, ga sadaka da ɗaukar baƙo tamkar ɗangida. Kai da ka gashi kaga asalin bafulata ni, yanayin jikin sa da kyau da Allah yayi masa kawai zaka kalla ka san wannan tsatson fulani ne. A lokacin ya manyanta amma in ka kalle shi sai ka kuma kallo saboda kamala da kyaun da yake dashi. Alhaji Muhmmad Jalingo attajirin mai kuɗi ne kuma babban malami, yana da dukiya mai tarin yawa a garin da ma wajen garin, ya tara dukiya da kuɗi na halak ga kuma ilimin addini da Allah ya bashi." "Ganin ana girmama shi kuma ganin sa dadtijo da yazo gifta mu sai muma muka gaishe shi da girmamawar da ake yiwa masu furfura, Sai ya kalle mu bayan ya amsa gaisuwar yace amms dai baƙi ne ku, muka amsa da eh shigowar mu garin kenan bamu zan ko ina ba. Yayi murmushi yace mu ɗauko kayan mu biyo shi." Abba ya bisu da kallo bayan ya dakata da abinda yake faɗa ganin alamun gajiya a tare dasu da alama basa jin dadin labarin burin su kawai aje ga inda suke so. Abba yace, "ina baku asalin labarin ne, daga nan zaku fahimci abinda yake faruwa." Ya sake cewa, "muka bi bayan sa kamar yadda yace zuwa gidan sa, ashe almajirai ne dashi sosai wnda yake koyarwa a cikin gidan sa, gidan tun a wancan lokacin babba sosai, yana da girma matuƙa soro-soro haka zaka dinga bi kafin ka shiga gidan. Aka sauke mu a wani ɗaki da ake saukar baƙi irin mu in mun je, ya kalle mu bayan ya saka an nuna mana ɗakin yana murmushi yace zaku iya zama a nan daga nan har zuwa lokacin da kuke so, zaku iya tambaya ta duk abinda ku ke so a duk sanda buƙatar hakan ya taso. Muka yi godiya sosai da addu'a ya amsa ya fita." "Bayan mun yi wanka muna huta gajiya sai muka ji ana sallama daga bakin ƙofa ba tare da an shigo ba, jin muryar mace kuma yarinya sai kuma taso gabaɗaya muka fito bakin ƙofar, yarinyar da aka aiko gani da ƙwaryar damammiyar fura nono a hannun ta, bayan ta kuma wani yaro ne da akushi a rufe da kuma ruwa a kwanon sha. Har ƙasa ta ɗurkusa ta gaishe mu cikin harshen hausar ta wacce bata fita sosai,muka amsa da fara'a ta bamu abinda aka bata ta juya ta koma." Abba ya kalli Bebi yace, "wannan wacce ta kawo mana abin shan itace Zahra mahaifiyar matar ka." Da sauri kowa yake kallon sa da mamaki Abba ya girgiza kai cikin son gamsar dasu tace, "ƙwarai kuwa itace. Bayan mun shiga ciki sai Ali yake cemin yarinyar nan da ta kawo mana fura akwai nutsuwa da kuma tarbiyya, gata da kyau. Nayi mamaki sosai saboda zama dashi na san shi mata ko kyaun su ko wani abun nasu baya gaban sa, shi kuɗi kawai ya sani, a kan kuɗi kuma zai iya aikata ko meye, yana da son kuɗi sosai yana kuma so yayi kuɗi ta ko wacce hanya ma in ya samu dama. Shiyasa nayi mamakin jin yana yabon mace wacce bata wuce ace mata yarinya a wannan lokacin ba." "Tun daga wannan rana bamu sake ganin ta ba, kwanan mu biyar a gidan bamu sake ganin ta ba kuma kullum sai Ali yayi maganar ta. A zaman mu na kwana biyar mun je mun gaisa da iyalan gidan, a bakin almajiran gidan muka san matan Alhaji Muhammad huɗu ɗaya ta rasu saura uku, da kuma ƙwarƙwara guda biyu ɗaya ta rasu saura ɗaya. Kun san masu kuɗin da ko manyan malamai ko sarakai suna ajjiye ƙwarƙwara a gidan su har ta haihu, hakan ya samo asali tun daga kan annabawa na san kun san da hakan. Abinda muka ji wanda ya girgiza mu tun a lokacin, Kaf gidan sun tsani wannan ƙwarƙwarar saboda ta kasance tana da kyau sosai, kuma ta fisu yarinta sai ya zama har matan auren ta fisu fada a wajan Alhaji Muhammad, ma'ana yafi son ta akan mataan sa na aure. Mu kan mun shaida kyaun da take dashi a gani ɗaya da muka yi mata, a yadda muka ji labari in tazo shan ruwa a kwanon sha hancın ta sai ya taɓa ruwan saboda tsahon sa." Ya kalle su yace, "Ita ƙwarƙwarar Alhajin wacce akace mana bayan rasuwar matar sa ya ƴanta ta ance kamar ruwa biyu ce, dan a hannun sarkin musulmi na sokkoto aka bashi ita amma asalin ta larabawan Sudan ne. Abinda zaka fahimta ita wacce ta kasance ƙwarƙwara duk da ancr ƴanta ta ta koma matar aure bata sakewa dasu, ware kanta take daban haka ma ƴar ta. Mutanen gidan basa son ta basa ƙaunar ta ita da yar ta, komai nasu iya su da taran su suke banda ita da ƴar ta. Haka muka bar gidan bayaan mun san labarin mutanen gidan musamman a bakin almajiran gidan. Abin mamakin Ali bai daina maganar wannan yarinyar da ko sunan ta bamu sani ba a wannan lokacin, haka muka rabu dashi yayi Kaduna nayi kano." "Cikin ikon Allah dabbobin da muka saro daga Jalingo suka ƙare, mun ji daɗi sosai dan mun samu riba dasu hakan ya saka bamu yi ƙasa a guiwa ba muka sake komawa bayan wata biyu zuwan mu. Gidan muka sake komawa dan marigayi yace duk sanda muka zo muna da masauki a gidan sa. Muka yi masa tsaraba a hanya muka kai masa dan yaji daɗi, ai kam yaji daɗi sosai ya kuma nuna mana hakan ta hanyar yi mana addu'a. Muka cigaba da zama muna fita muna siyan abinda zamu siya har lokacin bamu sake ganin wannan yarinyar ba sai da muka kwana biyu muka haɗu da ita a soron gidan ta dawo daga makarantar islamiyya. Ta gaishe mu ta wuce ciki Ali ya cigaba da kallon ta har sai da na riƙe shi, Sai yake cewa shi kam kawai yarinyar ta shiga ransa ne sosai." "A wannan zuwan muka san sunan ta Zahra mun ji mahaifiyar ta na kiran ta dashi. Mu ka sake dawowa gida muka cigaba da harkokin mu, in dai muka yi waya da Ali ta landline ko na tura masa saqo zai min maganar Zahra har na gaji nace kaje a baka ita mana, yayi dariya yace tafi ƙarfina nida nake da aure dan ma yaran nawa suna komawa ga Allah, Bamu sake komawa Jalingo ba sai da aka kusa shekara sannan muka je." Abba ya sauke numfashi yace, "a wannan zuwan mun yi baƙin zuwa domin mun je mun tarar da matar Muhammad Jalingo ko nace ƙwarƙwarar sa mahaifiyar Zahra kenan Allah yayi mata rasuwa. Mun ji rasuwar ta sosai duk da ba sabawa muka yi ba, nan muka yi musu gaisuwa har ita kanta Zahra dan ita za'a yiwa gaisuwa sai mahaifin ta. Da tausayin ta muka yi kwanakin da zamu yi muka bayan ɓun fahimci irin kular da take samu daga mahaifinta saboda rashin idon mahaifiyar ta, ya san yadda mutanen basa son ta. Sai da muka kammala komai na mu sannan muka sake dawowa Kano." Kowa na falon kallon sa yake yi a lokacin Abba yace, "Wallahi naji rasuwar mahaifiyar Zahra a wannan lokacin kamar mun saba da ita, kwata-kwata sau biyu kawai na ganta amma sai naji mutuwar ta a jikina sosai. Abinda ya saka na sake jin rasuwar ta saboda ita Zahra, yaram gidan kaf basa ƙaunar ta sai guda ɗaya wata Halima. Rashin mahaifiyar ta babban rashi ne a rayuwar ta, duk da mahaifin ta yana da rai amma ba kamar uwar ba." "Haka muka dawo kowa ya koma ga iyalan sa kowa zuciyar sa cike da tausayin Zahra." "A wannan lokacin muka sake komawa Jalingo kamar yadda muka saba gidan ne masaukin mu, a wannan zuwan mun tarar da tashin hankalin da ya fi na zuwan baya, domin mun tarar da Allah ya yiwa Alhaji rasuwa. Mutuwar sa ta jijjiga mu ta taɓa zuciyar mu sosai, muka zauma muka yiwa iyalan gidan gaisuwa suka amsa dan mun saba dasu sosai." Abba ya kalle su ya sake gyara zama yace, "mun kwashe kwanaki sosai kafin mu sake komawa garin dan albarkar da muke samowa a garin ya saka muke komawa akai akai. Lokacin da muka goma bayan rasuwar Alhaji nace baza mu je gidan sa ba saboda babu ransa wajan wa zamu je?. Ali sai yace ko dan kyautatawar sa gare mu yana da kyau mu je mu gaisa da mutanen gidan, jin abinda yace sai na gamsu muka je gidan." "A cikin kwanakin sun raba gado sun bata nata duk da lokacin bata mallaki hankalin kanta ba, dan baza wuce shekaru sha uku zuwa sha huɗu ba. Wannan labari da Ali yaji sai yazo ya same ni yace shi dai yana son auren ta." Abba ya sake cewa, "da farko naƙi bashi goyan baya amma da ya dinga tsara ni, yana faɗa min maganar da zan tausaya mata a zuciyata saboda rashin iyayen da bata dashi da yadda basa sonta sai na amince. Muka je aka karɓo auren Zahra a ranar da muka je a ranar aka bamu auren ta ba tare da bincike ba, ana ɗaura aure suka tattarawa Ali dukiyar ta suka ce ya tafi da ita." "A washe garin ranar ya dawo Zaria ya bar ni a can saboda na taho da kayan da muka siya shi kuma ya taho tare da matar sa. Sai da na gama komai sannan na wuce Kano kai tsaye ban shiga Zaria ba dan ina so nazo gida dan a kai abinda aka siyo kasuwa. Bayan na dawo yake sanar dani ya samu gidan haya ya saka ta a ciki nazo na ganta mu gaisa." "Nima kuwa washe gari na taso zuwa Zaria ya tare ni a tasha muka je gidan ya saka ta a ciki. Gidan haya ne mai mutum biyu ma'ana bashi kaɗai bane a gidan akwai wasu ƴan hayar, muka gaisa da ita a wannan lokaci ta amsa da fara'a dan ta shaida ni mijin ta ya faɗa mata waye ni a wajan sa da sauran bayanai. A gidan na kwana a wani shago da yake wajan gidan gari na dawo Kano a zuciya Ina jin kamar bamu kyauta mata ba." Abba ya kulle ido ya buɗe kafin ya ce, "daga wannan lokacin sai Ali ya daina sana'ar da muje yi, in na same shi da maganar sai ya fara yi min hanya-hanya, yau yace bashi da lafiya gobe yace min ya gaji da sauran su. Daga nan sai na watsar dashi indai akan business ne amma nuna waya dashi ta landline sosai har nace yaushe zai zo gidana don a lokacin an yi haihuwar Adnan. Bai zo ba nima ban je ba, na cigaba da harkokina har Allah ya kaini Zaria lokacin kusan shekara ɗaya da rabi da auren su. A nan naje na tarar da Zahra tana da cikin ƴar ta fari." "Bayan ta haihu aka saka mata sunan Maman ta ya cigaba da rainon ta cikin so da ƙauna har aka sake samun cikin matar ka Adnan!" Ya faɗa yana nuna Adnan da yatsan sa. Bebi ya kalle shi Abba ya kuma cewa, "lokacin ina yawan zuwa Abuja a kai a kai, to na kan tsaya a Zaria har na kwana a wajan sa, a haka na san matar sa ta farko duk da mun taɓa gaisawa da ita sau ɗaya, abinda na sani na san bashi da yara dan ya faɗa min ƴaƴa uku ya haifa duk sun rasu. Muna gaisawa da matar sa in naje sosai duk da bata san da matar sa biyu ba. Na yi masa magana me yasa bai faɗa mata ba yace haka yake so baya zo ko wacce ta san da ƴar uwar ta, na dinga faɗa akan me zai yi haka so yake yaran sa su taso basu san juna ba yace eh haka yake so. A lokacin yana da ɗa namiji guda ɗaya, sannan ya faɗa min ya taɓa yin aure a Kano amma basu jima da matar ba suka rabu, itama matar sa ta farko bata san da ita ba. Nayi fushi na tafi bai sake nemana ba nima ban kuma neman sa ba a wannan lokacin." "Sai da ya gaji da kansa ya neme ni muka shirya, yace min kuma ai ya faɗawa matar tasa har ta amince ashe ƙarya yake yi bai faɗa ba. A wannan lokacin aka haifi ƴar sa ta biyu matar Adnan kenwn, aka saka mata sunan babar ta wacce yake kiran ta da Fatima. Daga wannan lokacin Ali ya fars bayyanar da ƙudurin sa akan auren Zahra." "Tatttara dukiyar ta kawai yake yi yana siyar da na Jalingo yana siya a wani wajan a hankali ba tare da ya sani ba. Jasancewar ta mai ƙarancin shekara dan har ta haifi Manal bana tunanin tayi shekara ashirin ba, ta yarda dashi sosai ɗari bisa ɗari ta tamƙa masa duk abinda ta gada wajan iyayen ta a hannun sa, dukiya ce mai yawa sosai dan na faɗa muku waye mahaifin ta. Samun wannan dama a hannu sai Ali yayi amfani da ita wajan tattara duk wata dukiyar ta yana sakawa a aljihun sa. " "A haka ya gama siyar da komai bai barta da komai ba ya tattara komai ya gama siyarwa a hankali yana cigaba da haɗa plan ɗin yadda zai ɗauki uwar gidan sa su gudu. A lokacin muka haɗu dashi yake faɗa min shi zai kwashe kuɗin ta ya gudu ne in ina so zamu raba. Wallahil azim na ji tausayin ta sosai saboda bata da kowa sai shi, ina zata je in ya rabu da ita ga yara guda biyu..?. Amma ban nuna masa ba shaiɗan ya shiga raina nima naji ina da sha'awar cin wani abu a cikin kuɗin nata, tunawa da irin dukiyar da aka bar mata naji nima zan zo na samu kasona. Ya dinga dariya muka tafa muka gama tsara yadda komai zai faru, a nan yake faɗar daman shi dan kuɗin ta ya aure ta." Abba yayi shiru yana jin ɗacin abinda ya aikata a zuciyar sa, dana sani yake yi sosai dan da bai bashi goyan baya ba da wataƙila hakan bai faru ba. Abba yace, "ina ta jiran sa yace min ga kuɗi shiru, sai gashi a Kano yazo ya same ni da wani kuɗin da basu taka kara sun karya ba nace ai ni bazan karɓa ba. A taƙaice a nan muka yi rabuwar babu daɗi dashi ya kama gaban sa na kama gabana saboda bai bani adadin abinda muka yi dashi zai bani ba." "Haka kawai naji a zuciyata ina so naje gidan sa na faɗa masa gaskiya akan kar ya yi mata abinda yace in ba haka ba za'a cutar da ita. Ban tashi zuwa ba sai bayan sati uku da wannan tunanin nawa, ban kuma sake neman sa ba naje kai tsaye ne. Ina zuwa na tarar da ita ana korar ta daga gidan haya ga yara guda biyu tana kuka saboda bata da kuɗi, ashe ya ɗauke matar sa da kuɗin ya bar garin. Da hanzari naje nayi magana dasu na biya kuɗin take suka barta naje zan yi magana da ita a nan ta nuna min bakin mu ɗaya da abokina dan haka baza ta saurare ni ba naje duk abinda muka yi Allah ya isa. Ni kuma wannan haushin nunawa da tayi bakin mu ɗaya har tana faɗa min duk abinda yazo bakin ta sai raina ya ɓaci, na dinga faɗa mata magana sosai tana kuka na tafi na barta a wannan yanayi ba tare da na duba yaran da suke tare da ita ba, haushin mijin ta da ita kanta ya saka ban saurare ta ba." Abba ya kalle su yace, "tun daga wannan lokaci ban sake ganin ta bata sake ganina ba ba sai asibiti, nayi mamaki da ta gane ni dan shekarun da yawa sosai, girma ya cimmana furfura ta zagaye mana fuska, amma da yake ba'a mantawa da sharri ko alkhairi tana ganina ta gane ni nima na gane ta. Abinda nayi na san nayi kuskure na biyewa son zuciya, kuma har ga Allah ban ci ko naira biyar a dukiyar ta ba, ban kuma sake ganin Ali ba, dan bayan rabuwar mu na watsar da waccan sana'ar dan a lokacin shuganan ƙasa ya bani appointment na zama minister. Ban san ya akayi ta dawo Kano har tayi aure ta raini yaran ta ba." Mama da take jin sa har ya kai ƙarshe ta sauke ajiyar zuciya tace, "Yanzu dai mun tabbatar da ba kai ne mahaifin Manal ba abokin kane wanda ku ka so kwashe dukiyar ta tare dashi ashe cuta ce ta ɗau cuta, yanzu Ina abokin naka ya ke?." Abba yace, "baki ji me nace bane?." Mama ta ɗan taɓe baki tace, "ban ga laifin ta da tace baza ta bawa jinin ka auren ƴarta ba, bata sani ba ko wataƙila shima irin halin ku ne dashi da ya aure ta ya kwashe abinda ta tara." Bebi ne ya kalle ta yace, "Haba Mama!." Mama ta sauke kai dan wallahi ita labarin ma bai wani shige ta ba, gani take yi akwai abinda ya ɓoye a cikin labarin. Bebi yace, "yanzu Abba ina mahaifin nasu yake?." Abba yace, "wallahi ban sani ba. Yana da rai ko bashi da rai Allah ne kawai ya sani. Asalin sa dai ɗan garin katsina ne.” Yaya Isma'il ya girgiza kai cikin girmama labarin da aka bashi yace, "Kenan babar su Manal ƴar Muhammad Jalingo ce?." Abba ya ɗaga kai yace, "ƙwarai kuwa, ta gaji dukiya wacce ake kira duniya tun a wancan lokacin. In Ali yana da rai duk kuɗin da yayi a yanzu da dukiyar ta ya yi shi wallahi, Tabbas da naci wani abu a ciki nima da dukiyar da nake da ita a yanzu ta ta ce ba tawa ba." Abba ya kalli Bebi da yake kallon wani wajan daban kamar bai amince da abinda ya faɗa masa ba sai yace, "abinda na faɗa maka gaskiya ne Bebi, ka daina kokwanto a kan maganar ban tsallake maka komai a ciki ba na faɗa maka iya abinda zaka fahimta. Matar ka ba jinina bace, nace maka ƴata ce saboda ƴar tawa ce tunda a wancan lokacin bani da aboki kamar mahaifin ta. Kuma ni ne na karɓi auren mahaifiyar ta ni na zama waliyin mahaifin ta, kai hatta Fatima ni na ce a zaɓa mata a madadin Zahra kamar babar ta." Bebi ya girgiza kai cikin gamsuwa yana mamaki a zuciyar sa, Daman shekarun baya da suka cewa akwai macuta masu cutar da marayu?, Shi ya ɗauka a yanzu zamanin ya lalace ake cin dukiya ta halak da ta haram, ashe tun a da akwai su tunda gashi harda mahaifin sa ma a cikin su. Bebi ya kalli Abban sa da yake kallon sa yace, "Abba bawai ban amince da abinda kace bane ina so kawai ina so naji gaskiya akan maganar, don Allah baka ci komai a dukiyar ta ba?." Abba ya sauke ajiyar zuciya yace, "zare a dukiyar ta bai zo hannuna ba Adnan, yadda ya kawo min haka ya koma da abar sa dan ban karɓa ba." Bebi ya sauke ajiyar zuciya cikin rashin sanin abinda zai ce, gabaɗaya ya kasa furta komai mamaki yake a zuciyar sa yana jin kamar akwai wani abun a ƙasa bayan wannan. Abba ya kalle shi yace, "babu lallai ta amince ta baka Manal tunda ta san ni na haife ka, tana jin haushina sosai a zuciyar ta kuma nasan zata ji, duk da ban ci komai ba amma dani aka tsara guduwa a barta. Kuma da na koma bai kamata ace na barta ba ko me zata yi min saboda nasan a inda muka ɗauko ta, ban yi hakan ba na dawo gida na barta ba tare da nayi tunanin illar da hakan zai haifar ba." Bebi gaban sa sai faɗuwa yake sosai ya ja numfashi ya fesar yace, "in sha Allah Abba wannan ya wuce." BDƘB3P08 Abba ya kalle su gabaɗayan su cikin nauyin zuciyar da ya tokare masa ƙirji ya hana shi sauke numfashi, daƙyar ya iya jawo numfashin ya fesar ya kana bin su da kallo jikin sa ya sake yin sanyi sosai yace, "dare ya yi zaku iya tafiya gida." Bebi ya girgiza kaiyace, "Allah ya ƙara lafiya." Duk suka amsa da amin suka tashi kowa ya fito. Suna tafiya a harabar gidan shi dasu Yaya isma'il suna ta bashi baki da tabbacin Manal zata dawo gare shi cikin sigar kwantar da hankali. Rabuwa suka yi dasu a wajan ya shiga wajan Mama su kuma suka wuce gida. Yana shiga falon ya tarar babu kowa sai kawai ya tsaya a falon yana kallon waje ɗaya ba tare da ya zauna ba, yayi shiru baice komai ba yana kallon wani wajan daban kamar mai karanta wani abun. Mama ce ta fito daga ɗaki a tsaye tace, "Bebi baka wuce ba?." Ya kalle ta ya sauke numfashi yace, "Mummy ina nan, yanzu dai zan wuce." Ta kalle shi tace, "har yanzu hankalin ka bai kwanta ba? Naga yanzu ka san gaskiya Manal ba jinin ka bace akwai aure tsakanin ku, meyasa ka ke cikin damuwa kuma?." "Mummy Maman Manal baza ta amince da dawowar ta gare ni ba." Mummy cikin lallashi tace, "zata amince in sha Allah. Abun ne akwai ciwo sosai, ɓacin rai ne ya saka ta take faɗa maka haka. Amma in sha zata amince ai ba laifin ka bane ba." Cikin karaya da sanyin jiki Bebi yace, "Anya kuwa Mummy? Sai nake ji kamar akwai abinda Abba ya rage a labarin nan bai faɗa mana ba." Mama tace, "Nima haka nake ji, Amma wannan tsakanin su ne kaima tsakanin ku daman. in sha Allah zata baka matar ka farin cikin ka ya dawo kamar da. Ni ko su Hajiya ban faɗawa ba wallahi, cewa nayi saboda yanayin aikin ka yana zuwa na dare ga laulayin ciki shiyasa ta koma gida." Wani iri yaji a jikin sa jin Mama ta san da maganar cikin, ya kalle ta kaɗan dan shi ya san bai faɗa mata ba yayi mamaki da ta san dashi. Kunya ce ta kama shi ya ɗan kawar da kansa gefe yana jin nauyin Mummy a jikin sa sosai. Mama ta fahimta sai tayi murmushi tace, "Allah zai kawo mafita kar ka damu." Bebi yace, "Allah ya amince." "Amin ya Allah. Ina zaka je yanzu? A nan zaka kwana ko gida zaka wuce?." "Asibiti zan je, Manal ɗin ce a kwance babu lafiya, ɗazu yayar ta take sanar dani. Ɗazu da ban zo da wuri ba ma nan naje shiyasa na ɗan jima." Mama tace, "Subahanallahi! Me ya same ta?." "Rashin cin abinci ne da damuwa." Mama tace, "wayyo Allah, Allah ya bata lafiya." Ya amsa da amin tace, "a asibitin ku take?." "A'a, wani clinic ne nan kusa dasu." "Amma kafin kaje ka fara cin abinci mana, kaima ai ba ci ka ke ba." Yace, "Naci ɗazu Mummy, bana jin yunwa yanzu." Mama tace, "kawai dai damuwa baza ta barka ci ba." Ya murmusa baice komai ba ya fita bayan ya mata sallama. Yana shiga asibitin ya tarar da Manal ta farka tana zaune ita da Mubeena a ɗakin, da sallama ya shiga ɗakin jin maganar sa sai ta kalle shi suka hɗa ido, murmushi yayi mata mai kashe jiki ya kalli Mubeena da take zaune bayan ta amsa sallamar yace, "Sannu Yaya, ya jikin nata?." Mubeena tace, "jiki da sauƙi, yanzun nan ta farka tana tambayar ka." Ya ƙarasa ya zauna a kan kujera yana kallon Manal yace, "sannu." Kai ta ɗaga kawai bata ce komai ba yace, "me yake damun ki yanzu?." "Babu komai" ta faɗa a hankali. "Kin tabbatar babu?." Ta ɗaga kai alamun eh babu ɗin. Mubeena tace, "Sun ce dan ma dare yayi ne da zasu iya sallamar mu yanzu saboda ta samu lafiya, amma da safe zamu tafi in sha Allah." Bebi ya girgiza kai yace, "Allah ya nuna mana lokacin." Ta amsa da amin tana cigaba da danna wayar ta. Kiran ta akayi a wayar hakan ya saka ta tashi ta fita dan taga su ma suna buƙatar space. Tashi yayi ya koma kusa da ita ya zauna a gefen ta ya riƙe hannun ta yace, "akwai abinda kike so ki ci?." Ta kwantar da kanta a kafaɗar sa tace, "babu." Bebi ya ɗora hannun sa a kanta yace, "in akwai ki faɗa min, kinga ba abincin kirki kika ci ba." Kai ta girgiza kawai ya sauke numfashi yana shafa fuskar ta yace, "in sha Allah komai yazo ƙarshe, kar ki damu." Tashi tayi daga jikin sa tana kallon idon sa tace, "na kasa cika alƙawarin da na yiwa Mama, na cewa Mama zan barka tunda hakan take so amma na kasa yin hakan, so nake kawai na ganka a kusa dani fiye da komai. Ina son yiwa Mama abinda take so" ta faɗa hawaye na sakkowa daga idon ta. Murmushi yayi ya saka hannu ya share mata hawaye yace, "Ɓacin rai ne ya saka tace miki haka, Amma nan gaba da kanta zata ce nazo na sauke ki mu tafi gida Manal. Mama tana son zaman ki dani Manal, kawai ɓacin rai ne ya saka take cewa ki rabu dani, Amma wallahi tana son ki zauna dani sosai." Manal ta kalle shi tace, "ta ya akayi ka sani?." Bakin sa ya ɗora a kan nata yayi mata kiss na sacannin da basu wuce biyu zuwa uku ba ya janye bakin sa yace, "saboda haka abin yake Partner. Ni babban farin cikina da na tabbatar dani sake babu alaƙar jini balle ace aurena sake ya haramta, wannan shine farin cikin da naji fiye da tunanin ki kuma hankalina ya kwanta. Duk wata matsala in ba wannan ba zamu shawo kanta daga baya." Manal jin bakin sa take har lokacim a kan nata, Allah ya sani abinda take da buƙata kenan a wajan sa amma ta kasa bayyana masa hakan, dan gani take in ta bayyana ma bashi da amfani tunda basa gida kuma babu kwanciyar hankalin da hakan zai faru. Ya lura da idanun ta suna lumshe tunda ya mata kiss har ya gama magana bata buɗe ido ba, lumshe ido yayi ya buɗe dan kuwa tunda cikin ta ya bayyana y lura tana son zama inda yake sosai, tana son kwanciya a jikin sa duk da daman haka take tana da son jiki sosai, amma na yanzu yafi na baya. Fuskar ta ya riƙe da duka hannun sa yana shafa kumatun ta da yatsun sa yana kallon idon ta shigar kwantar da hankali da tausasa murya irin ta masoyan da suke cikin shauƙi yace, "me ki ke so?." Ta sauke ido ƙasa ta ɗora hannun ta a kan nasa saboda sanyin hannun sa yayi mata daɗi. Ganin tayi shiru bata ce komai ba yace, "ina jin ki, me kike so?." Ta girgiza kai alamun babu yace, "ban yarda ba, faɗa min me kike so, uhmm." Baki ta turo gaba bata kalle shi ba yayi murmushi mai sauti ya mata kiss a goshi yace, "faɗa min mana, baki taɓa faɗa ba tunda muka yi aure, faɗa min yanzu zan ji daɗin hakan." Hannun ta saka ta zagaya dashi bayan sa ta kwantar da kanta a ƙirjin sa tana jin yadda zuciyar sa take bugawa a kunnen ta tace, "ni ban san me zance ba." "Kin sani, faɗa min ko meye zan samo miki shi." Sake gyara kwanciya tayi a jikin sa tace, "ina kewar ka, bugun zuciyar ka na kwantar min da hankali sosai, bana so na daina jin sa a kunnena, tana bani nustuwa sosai." "Nima ina kewar ki Partner, ban ƙi na tafi dake yanzu ba, da bazan barki bacci ba sai na tabbatar kin samu abinda kike so fiye da yadda kika so a zuciyar ki." Ta ɗago kai ta kalle shi tace, "me nake so ɗin?." "Au baki sani ba?." Ta ɗaga gira yayi dariya kaɗan ya matso da bakin sa kusa da kunnen ta ya mata magana a tare da cizon kunnen nata. Da sauri ta mayar da kanta jikin sa tace, "Allah ni ban ce ina so ba, kar kayi min sharrii." "Ko baki faɗa ba idanun ki sun nuna haka, kar ki damu dole na samo miki mafita." Manal kamar zata yi kuka tace, "Allah ban ce ina so ba." Cikin nishaɗin da yake ji a zuciyar sa yace, "ni nasan kin ce." Ta yi masa dukan wasa a ƙirjin sa tace, "Allah ban ce ba." "To laifi ne in kin ce ɗin Manal? In ke kina ganin laifi ne to ni ina buƙatar hakan Manal. Wallahi ina buƙatar ki a kusa dani sosai." Hannun sa taji a kan cikin ta yana shafawa a hankali hakan ya saka ta lumshe idanu, ɗago fuskar ta yayi yana kallon ta fuskar yana ƙoƙarin kai bakin sa kusa da nata. Baya tayi da sauri tace, "Yaya zata iya shigowa." Ya girgiza kai yace, "baza ta zo ba" ya faɗa yana dawo da ita kusa dashi ya fara kissing ɗin ta a hankali itama tana taya shi. Kusan mintina biyu suna a haka kafin ya janye bakin sa saboda kar ya canja mata yanayi daman abinda take so kenan kar ya zama ya tsokano ta. Goshin su ya haɗe waje guda hancin su na gugar juna, idanun ta a lumshe tana sauke numfashi a hankali. A hankali ta buɗe idon suka haɗa ido sai ya ɗaga mata gira tayi dariya ta rufe fuskar ta da hannun ta, murmushi yayi mai sauti yace, "Manal zaki bi ni muje gida mu dawo?." Da sauri ta kalle shi ta janye fuskar ta yanayin ta ya canja tace, "Mama!." "Baza ta sani ba. Partner kina buƙatar mijin ki nima ina buƙatar ki, rashin ki yana cutar dani kema rashi na yana cutar dake yana cutar da abinda yake cikin ki. Please Manal ki yarda mu tafiya bazan bar hanyar da Mama zata gane ba, I really missed you, ki taimake ni ki taimaki kanki da babyn mu." Haɗa ido suka kuma yi da ita yace, "please Manal!." Ta sauke numfashi Allah ya sani tana son bin mijin ta amma baza ta iya yiwa Mama haka ba, ta kulle ido ta buɗe cikin sanyin jiki tace, "Yaya Mubeena tana nan me zance mata?." "Zata fahimta, kar ki damu da Yaya Mubeena zata fahimce mu." Manal tayi shiru tana ji yana cigaba da shafa jikin ta a hankali amma bata ce komai ba. "Muje?." Maganar sa ta katse mata tunani ta kalle shi tace, "ina so naje amma kuma bazan iya yiwa Mama haka ba" ta faɗa hawaye yana sakko mata. Numfashi ya sauke dan bashi da ta cewa tunda tace Mama bazai tilasta mata. Zare hannun sa yayi daga cikin rigar ta ya girgiza kai yana kallon ta yace, "shikenan, kin tabbatar hakan bazai cutar dake ba?." Ta kalli idon sa tana kuka tace, "uhum!." Ya sauke numfashi yace, "is okay, ki daina kuka." "Kai fa?." Kallon ta yayi yace, "kar ki damu dani." "Dole na damu da kai." Ya kawar da kai gefe yana shafa fuskar sa kafin yace, "yanzu in ku ka koma gida gobe shikenan bazan sake ganin ki ba?" Ya faɗa yana kawar da waccan maganar dan bayan son abinda zai tayar masa da hankali. Ta fahimci hakan sai taji babu daɗi a zuciyar ta, Allah ya sani tana son abinda yake so ya wakana a tsakanin su, wataƙila ma ta fishi so ɗin amma ya zata yi?. Ganin tana kallon sa ta kasa magana yace, "Zan tafi" ya faɗa yana kallon agogon hannun sa. Manal ta kalli agogon itama tace, "dare yayi sosai, ka kwana a nan." Ya kalle ta yace, "in na kwana zan samu abinda nake so ne a wajan ki?." Ta sunkuyar da kai yace, "hmm! gwara na tafi" ya faɗa yana tashi tsaye ta riƙon hannun sa tace, "fushi kayi?" Ta faɗa ido na sake cikowa da hawaye. "Ba fushi nayi ba, dare yayi na bar Yaya a waje gwara na tafi." "Allah fushi kayi, Gashi ka canja har fuskar ka ma ta canja" ta faɗa tama fashewa da kuka. Ya san daman tana da yawan kuka, amma samun cikin ta ya sake ƙara mata rigima da neman faɗa sosai, hakan ya saka shi ya koma ya zauna yace, "ba fushi nayi ba, akan me zanyi fushi ma?." "Gashi nan ka canja" ta faɗa murya ba rawa sosai. Ya goge mata hawaye yace, "ni ban yi fushi ba, ke kin san in fushi nayi bazan kula ki ba tafiyata zan yi, tunda kika ga ina nan ban tafi ba ki yarda ban yi fushi ba kin ji partner?." Ta girgiza kai ta kalle shi tace, "bana so ka tafi ka barni." "Nima bana so na tafi ɗin, amma dole na tafi saboda na bawa Mubeena dama ta kwanta tayi bacci. Inda asibitin mu ne sai na canja mana room mu bata nata mu kwana tare, amma kin ga nan ban taɓa zuwa ba sai ta dalilin ki." Manal tace, "haka ne." "To ba fushi nayi ba ki yarda, sannan ki saka a zuciyar ki komai ya zo ƙarshe." Ta ɗaga kai alamun to ya sake tashi tsaye yace, "zan tafi." Sakkowa tayi daga kan gadon ta tsaya a tsaye tana kallon sa, kamar zatayi magana sai ta fasa ta sake shiga jikin sa ta rungume shi. Dole ya riƙe ta ya sake matso da ita jikin sa sosai kirjin su ya haɗe waje ɗaya tace, "ina sonka partner." "ina son ki sosai partner, Allah ya baki lafiya ya fito mana da babyn mu lafiya" ya faɗa yana ɗago ta ya manna mata kiss a goshi. Itama a kumatu ta yi masa kiss tace, "Amin, Allah ya kiyaye hanya." "Amin milky." Tayi murmushi shima yayi ya ɗauki wayar sa da ya ajjiye a gefe ta riƙe hannun sa suna tafiya har bakin ƙofa sannan ta tsaya tace, "in ka je ka kira ni." "Okay ma'am" ya faɗa da girmamawa tayi dariya shima yayi kafin ya fita. A zaune ya tarar da Mubeena a ƙofar ɗakin tana waya tana cewa, "kee bari kawai, ai Manal da mijin nan nata kan su rawa yake, soyayya suke ji da ita shiyasa na fito nan na bar musu ɗakin. Ke kuwa yayar ta ce ni fa" ta faɗa tana dariya sosai. Bebi ya murmusa yana kallon ta daga gefen fuskar ta, tana yi masa kama sosai da wacce ya sani amma ya rasa wacece, amma tabbas ya san mai irin fuskar ta har maganar su kusan iri ɗaya. Ƙarasowa yayi yace, "Yaya Mubeena." Sai da ta firgita ta kalle shi tace, "Yaya kuma?." "Eh, ba yayar bace?." "Yayar Manal ba, amma ban da kai ban girme ka ba." "Tunda ta Manal ce nima tawa ce." Mubeena ta girgiza kai tace, "da sake." "Sai da safe, a kular min da ita don Allah. Anytime in akwai abinda ake so take so just call me please." Mubeena tace, "in sha Allah." Ya saka hannu aljihu ya ɗauko kuɗi ya miƙa mata yace, "ki riƙe ko za'a nemi wani abu." Ta kalli kuɗin tace, "ka barshi kawai, ai gobe zamu bar nan." "Ki karɓa." Ta karɓa kuwa yace, "goben in an yi discharging ɗin ku zan zo na kai ku gida." "Allah ya kaimu" ya amsa da amin ya juya ya fita da sauri. Da kallo ta bishi a bayyane tace, "Manal tayi sa'ar miji mai son ta, Allah yasa bai ɗauko halin bunsuraye irin na mahaifin sa ba, har tausayi yake bani in na tuna waye mahaifin sa" ta faɗa tana sauke numfashi a ranta tana ayyana da Mama zata ji labarin abinda mahaifin sa yayi mata da ko tana niyar mayar masa da Manal wallahi baza tayi ba shiyasa tayi shiru ta manta da batun. Da wannan tunanin ta koma ciki ta tarar da Manal a zaune tana goge idanu, bata ce mata komai ba ta warware ƙaramin bargon ta ta shinfiɗa ta kwanta a ƙasa. Washe gari kamar yadda yace ta kira shi bayan an sallame su ƙarfe takwas na safe ya shigo asibitin Mubeena ta gaishe shi ya amsa yana yi mata ya bangajiya, ya kalli Manal kafin tayi magana tace, "ina kwana." "Kin tashi lafiya madam? Ya jikin?." Mubeena tace, "ina ta kwana ma balle ta tashi lafiya? Kwana tayi tana share hawaye cikin shegiyar shagwaɓar da take ji da ita, ayi mata magana ta fara harare harare. Baccin da ta samu ƙalilan ne, kuma na faɗa mata harda rashin bacci a matsalar ta amma taƙi ji." Ya kalli Mubeena ganin tana hararar Manal ɗin ycae, "ayi haƙuri Yaya, yanayi ne ya kawo hakan." Kallon sa take yi, itafa haushi take ji in yana cewa yayar nan, bai san da ta amince da uban sa da yanzu Mama zai ce mata ba. Kallon Manal yayi yace, "bakya jin magana ko?." Kallon sa ita dai kawai take yi yayi kyau cikin yadi baƙi mai gajeran hannu kansa babu hula, ganin tana kallon sa sai ya dungure mata kai yace, "Nawa zaki biya na kwalliyar?." Dariya tayi shima yayi murmushi yace, "tashi mu je." Riƙe ta yayi ta tashi tsaye a lokacin Mubeene ta fita daga ɗakin, tana jin rufewar ƙofar ta shiga jikin sa da hanzari ta kwanta tace, "kayi kyau partner, Allah ya isa duk wacce ta kallar min kai a tahowar ka, in kai kuma ka Allah akwai Allah." Murmushi yayi mai sauti yaja numfashi yace, "babu wacce na kalla, ni da nake da ke wacce mace ce zata burge ni har na kalle ta?." Ta ɗago ta kalle shi tcae, "to na san an kalle ka ai ko?." "Sosai ma, da yake na shiga asibiti kafin nazo nan, harda wacce ta bani number ta tafe don Allah na kira ta." Ta wara ido tace, "kuma zaka kira?." Shima ya wara ido kamar yadda tayi yace, "Da gudu ma, daman ina cikin kewa in na kira sai mu yi hira." Kawai ta tashe da kuka tana cewa, "Allah ya isa in ka kira ta, Allah bazai yafe ba kuma itama bazan yafe mata ba. don Allah kar ka kira,Kayi min rai kar abin yayi min yawa." Kuka take amma cikin faɗa take maganar, yayi dariya ya sake matse ta a jikin sa ya riƙe ta gam-gam yace, "shiii wasa nake miki, babu wata mace da zata ga fuskar da zata bani number ta a wajena. Kin manta waye mijin ki ne?." Ta sake ƙamƙame shi tace, "ban manta ba, amma don Allah kar ka kula su nasan akwai masu son ka sosai." "To naji, ki daina kuka sarkin kuka." "Wai Manal baza ku fito bane an...." Tsayawa maganar Mubeena tayi ganin su ma rungume da juna sun barta a tsaye a waje ga shashasha marw abin yi. Haushi suka bata ta ja dogon tsaki ta bar wajan, jin hakan sai Manal ta bar jikin sa tace, "mun bar Yaya Mubeena ita kaɗai har tazo ta gan mu a haka." "Laifin ki ne" ya faɗa yana yafa mata mayafin da yake ajjiye a gefen, ta tsaka takalmi suka fito. A tsaye ya hango Mubeena girgiza kai tana gefe bata ce musu komai ba, ya saka Manal a motar ya kalle ta yace, "Yaya muje ko?." A fusace ta juyo ta kalle shi, har zata yi magana sai ta fasa ta shiga motar shima ya shiga suka tafi. BDƘB3P09 Suna shiga gidan kasancewar safiya ce Mama da Baba suna zaune a inda suka saba zama wato ƙasan bishiya suka shiga d asallama. Kafin Mama tayi magana Mubeena tace, "kai nayi mantuwa" ta faɗa tana fita da sauri. Baba ya kalli Manal da ta ƙarasa ta zauna yace, "Fatima jiki yayi sauƙi? Yanzu muke shirin zuwa sai ga ku." Manal tace, "Naji sauƙi sosai Baba, ina kwana." "Lafiya lau, ya jikin naki?." "Sa sauƙi" ta kalli Mama tace, "Mama ina kwana." Mama tace, "lafiya lau, ya jikin naki?." Ta amsa sai ga Mubeena ta shigo Mama ta kalle ta tace, "kin samu mai adaidaita sahun?." "Da yake a mota muke, mijin ta ne ya dawo damu" Mubeena ta faɗa da biyu dan tana so Mama ta san suna son junan su sosai. Bata ce komai ba Manal ta tashi jiki a sanyaye ta wuce ciki Mubeena ta wuce itama. Baba ya kalli Mama yace, "Fatima don Allah ki bar yarinyar nan ta koma gidan mijin ta, meye na wannan abubuwa da kike yi ne? Meye amfanin raba su?. So kike ta dawo ta cigaba da zama tare dake bayan kun rabu ta tafi gidan mijin ta?, zaman gidan mijin ta ba shine darajar ta a duniya ba?. Meyasa kika kasa yafewa ne? Naji an yi miki laifi, amma shi Adnan ɗin meye laifin sa? Lokacin da abin ya faru ko da an haife shi yaro ne, to meyasa laifin Baban sa zai shafe shi?." Mama bata ce komai ba tayi shiru yace, "tunda kin nuna min ba matsayin uban nake a wajan su Manal ba, ina roƙon ki ki barta ta koma. Tana son mijin ta mijin ta yana sonta, in kika raba su samun irin sa wahala zai baki, kinga kin cutar da ita kin kuma cutar da kan ki da abinda yake cikin ta." Mama tace, "matsayin uban ka ke a wajan Manal wallahi." "Wallahi ba haka nake ba, dan inda ni na haife su da bazan ce ki barta ta koma ki ƙi ji ba, inda ni na haife su bazan tsaya jiran umarnin ki ba, zan yanke hukunci ne kawai tunda kema a ƙarƙashina kike. Sunan Baba kawai nake amsawa a wajan su amma ba mahaifin ba shiyasa kika nuna min iyakata a kan su. Ko gudun bakin mutane bakya yi, auren da kwata-kwata bai wuce wata biyar ba ace yarinyar ki ta dawo gida?, ko ina zancen ake yi barin cikin gidana da kin san basa son Manal basa son ki. Amma ke hakan bai dame ki ba, tunda a wajan ki daidai ne shikenan." Mama ta kulle ido ta buɗe tace, "raba ni da dukiya ta da suka yi wannan bai dame bi ba, wulaƙanta ni suka yi da ni da yarana suka barni a titi an kore ni daga gidan haya. Ruwa a kaina yake ƙarewa da Manal da Mubeena saboda bani da inda zan je. In  ba dan rayuwar baya ba irin ta yanzu bace da a lokacin wani abun ya same ni, ko a sace ni ko a sace ƴaƴana. Bani da komai sai kayana da kuma kayan yara na. Waye ya taimake ni a garin Zaria in ba kai ba? Su kaɗai na sani a Zaria ina zanje? Zan komawa ƴan uwana ne a lokacin..? Bazai yu ba" ta faɗa hawaye na sakko mata daga idon ta. "Ƴan uwana na jini sune suka aurar dani a gare shi saboda kawai basa sona basa son mahaifiyata, ba bincike babu komai haka aka bashi ni ya tafi dani inda basu sani ba. Su kuma suka ci amanar halaccin da maahifina yayi musu, suka zalunce ni suka wulaƙanta ni basu yi tunanin maraicina ba. Ko da yake yake ƴan uwana ma suka rabu dani balle su?." Baba yace, "wannan ya wuce Zahra ya kamata ki manta." "Wallahi bai wuce ba, ina jin zafi da raɗaɗi a zuciyata. A lokacin da na haifi Manal ko shekara ashirin ban yi ba a duniya, basa tunanin akwai yarinta a tare dani suka barni a inda babu wanda na sani?. Taya zan so jinin Mu'azzam da Ali? Har abada." Mama ta sake cewa, "in ba dan kai ba da yanzu ina ina? Wataƙila na mutu har su Manal ɗin. Amma kai ka taimake ni ba tare da ka san ni ba, ka taimake ni har ka dawo dani nan wajan mahaifiyar ka nake zaune tamkar mahaifiyata, ta umarce ka da aurena baka ƙi ba ka aure ni ka riƙr min yara kamar wanda ka haifa. Kai akwai hisabi ranar lahira, tsakanina da ƴan uwana sai Allah yayi mana hisabi, akwai kallo a ƙiyama" ta faɗa tana goge idanun ta. Baba ya murmusa yace, "Hisabi tsakanin ki da Ali da Mu'azzam kika ce ba tsakanin ki da Adnan ba, laifin su bai kamata ace ya shafi Adnan da Manal ba. Raba su ba mafita bace lalacewa ce domin kuwa zaki musu illa dukkan su musamman ita Manal ɗin da ta kasance mace, in kika yi tunani zaki gane Manal bata cancanci haka daga wajan ki ba. Manal ta bar burin ta na son karatun dafa abinci saboda ke, saboda baza ta iya tafiya ta barki ke kaɗai ba a lokacin bakya gani ta haƙuraa ta zauna. Manal ta saudaukar da komai saboda ke Zahra, kar ki saka ta sadaukar miki da farin cikin ta a wannan lokacin don Allah. Nasan zata iya barin mijin nata saboda abinda kike so shi take so amma bai kai zuciyar ta ba, zata dinga ɓoyewa a zuciyar ta saboda kar ki gane bata ji daɗi ba har hakan yazo ya zamar mata babar illa. Ko ta samu ciwo ko wani abun ya faru, kinga ke kika jawo saboda baza  ta iya ce miki a'a ba. Wannan soyayyar ya kamata ki duba, shi kansa Adnan ɗin babu abinda ya haɗa ki dashi sai alkhairi. Ta silar sa kike gani a yanzu har kika gane mahaifin nasa da taimakon sa na samuwar ganin ki, ta silar sa lafiyar ki ta inganta har aka zo wannan mataki, bai cancanci wannan hukunci ko nace sakayyar daga wajan ki ba." Baba ya sauke tausasa murya yace, "Kin ce saboda shi kin yafewa mahaifin sa ko?." Ta girgiza kai alamun eh yace, "to ki bashi matar sa, yana buƙatar hakan daga gare ki dan babu yadda zai yi miki ne, in kika ganshi yanzu sai kin tausaya masa saboda damuwar rashin ta. Abin alfaharin ki ne ace ƴar ki ta samu mijin da yake son ta har haka, abin alfahari ne ƴar ki ta samu miji mai nagarta kamar Adnan." Mama ta katse shi tace, "amma ba abin alfahari bane zama sirikar Mu'azzam, wallahi ba abin alfahari bane a wajena." "Mantawa zaki yi da wannan ki kawar da kai kamar komai bai faru ba, sun so ki wulaƙanta amma Allah bai wulaƙanta ki ba. Duk dukiyar da suka kwashe basu kwashe duka ba sun bar ragowa basu sani ba, gashi da ita kika yiwa ƴar ki komai duk da haka basu ƙare ba. Kuma shi yace wallahi ko sisi bai ci a kuɗin nan ba, in ma ƙarya yake yi tunda yace wallahi yaci mu yarda, rantsuwar sa shi zata cutar bamu ba." Baba ya kuma cewa, "indai na isa da Manal kamar yadda kika ce ina so yau ta koma gidan ta." Mama ta girgiza kai tace, "shikenan." "Amma ina so ta koma saboda ra'ayin ki ba don bakya ra'ayi ba. Sannan bana so canjin fuska ya maye gurbin fara'a tsakanin ki da Adnan, komai ya wuce don Allah." Mama tace, "ka wuce ka nemi abu ban maka ba, babu komai wallahi ya wuce. Ko yanzu ka kira Adnan ya tafi da Manal har zuciyata ya wuce." Baba yayi murmushi yace, "Alhamdulillah! Na gode na kuma na ji daɗi hakan. Allah yayi albarka ya warware mana dukkan matsalar mu." Ta amsa da amin kafin ta miƙe tsaye tace, "bara naje yau na sanar da su Manal wacece mahaifiyar su." Baba cikin jin daɗi yace, "da kin kyauta kuwa, abinda suka jima suna so su ji kenan." Mama tayi murmushi ta wuce zuwa ciki. Suna zaune a falo da alama sun ji komai a yanayin jikin su da taga yayi sanyi ta gane hakan, ta kalle su bayan ta zauna  tace, "zan faɗa muku asalin waccee ni da mahaifin ku." Ta kalle su ta fara basu labari kamar yadda Abba ya bawa su Adnan labari kafin dalla-dalla kafin tace, "A zamana da mahaifin ku da farko zamana ne na farin ciki, zama ne wanda naji daɗin sa nake murna addu'a mahaifiyata ta karɓu da take yawan cewa Allah kar ya kai ni inda zan wulaƙanta. Duk da yarinya ce ni a lokacin amma na san jin daɗin aure, yana bani lokacin sa sosai yana kuma biye min ya mayar da kansa mai shekaru irin nawa. Sai bayan na haifi Manal na fahimci me mahaifin ku yake nufi dani, kuɗin da na gada na mahaifina da mahaifiyata shine silar karɓar aurena da yayi a wajan ƴan uwana da basa ƙaunata, da ya gama tattara dukiyar ya tafi ya barni ba tare da yayi tunanin ban san kowa ba sai shi." "Haka na fara rayuwa ni kaɗai sai ku sai matar da nake zaune a gida ɗaya da iya, bani komai ya kwashe ban iya komai ba saboda na tashi da gata ban iya wani abu na sana'a ba balle na fara. Ina zaune ni kaɗai a Zaria aka zo aka kore ni akace kuɗin haya ya ƙare, na koma zaman titi kamar almajira. Rana ta fito ta koma a kaina nida ku, ruwan sama yazo ya dake ni amma ƙoƙari nake na ɓoye ku musamman Manal da ta kasance ƙarama kar ta cutu. A wannan yanayin na kasance har kwana biyar a lokacin Allah ya kawo min baban ku, da yake a lokacin baya taimako bai yi ƙaranci kamar yanzu ba ya kai ni asibiti saboda ciwon da nake yi nida ke Manal, aka mana magani daga nan yace ya tambaye ni inda zanje nace masa bani da kowa, na bashi labarina ya tausaya min sosai sai yace zai kaini Kano wajan mahaifiyar sa, na amince saboda bani da zaɓi a wannan lokacin, in na ƙi ina zan je? Wa nake dashi da zai sake kawo min ɗauki? Wannan dalilin ya saka na amince muka taho Kano." Mama ta sauke numfashi tace, "mahaifiyar sa ta riƙe ni tamkar wacce ta haifa tana rainon ku kamar jikokin ta, tare da take haɗa ku da ƴaƴan Baban ku tayi muku ko mai tare har kuka fara tasawa. Daga nan ta bashi shawarar aurena bai musa ba ya amince ya aure ni matsayin matar sa ta uku ya cigaba da riƙe ku matsayin ƴaƴan sa." "Duk wani abu da ya shafi mahaifin ku da abokin sa da kuma ƴan uwana bana so, ko kusa bana so ayi min maganar shiyasa ban taɓa faɗa muku ba, Shima kuma na roƙe shi nace don Allah kar ya faɗa muku yace bazai faɗa ba. Wannan dalilin ya saka da naga Mu'azzam duk da ya girma amma na iya shaida shi saboda ba'a mantawa da alkhairi haka sharri ma ba'a manta shi. A gani na sune suka raba ni da farin cikina, da ace sun barni a gidan mu na tabbatar ƴan uwana dole zasu haƙura da ƙiyayyar da suke min su zauna dani saboda ni jinin su ce, duk da na kasnace ƴar ƙwarƙwara amma mahaifina ya mayar da mahaifiyata matar aure, kuma koda ace ni ƴar ƙwarƙwarar ce dole ace ni ƴar Muhammad Jalingo ce ko basa so. Suka raba ni da garin mu suka kai ni inda ban taɓa zuwa ba kuma suka barni, shiyasa nace kizo mu tafi saboda tuna hakan ya saka naji bazan iya haɗa alaƙa da Mu'azzam ba." Manal da Mubeena dai kuka suke yi sosai jin labarin mahaifiyar su da irin wahalar da ta sha kamar ba ƴar babban attajirin da har yanzu sunan sa bai ɓace daga doron duniya ba. Mama tace, "Tunda kina son Adnan bazan raba ku ba Manal, kamar yadda Baban ku yace na bar ki da abinda ki ke so zan yi, ki koma Manal har zuciyata na amince da ki koma gidan sa." Ta girgiza kai tana kuka tace, "Mama ashe haka kika sha wahala? Meyasa ƴan uwana ki basa son ki? Meyasa suka wulaƙanta ki?." Mama tayi murmushi tace, "A baya ban fahimci dalili na saboda ƙuruciya, amma da girma ya cimmin na gane dalilin hakan. Allah ya ɗorawa mahaifina son mahaifiyata fiye matan sa na aure, Allah ya yiwa mahaifiyata baiwar kyau wanda ake kira da kyau, duk kyauna da ake gani da kyaun Mubeena bamu ɗauko rabi da kwata a cikin kyaun da take dashi ba. Gabaɗaya hasken ta kika ɗauko Manal, haka tajr fara kamar tana shafa madara, inda da ace har kyaun gabaɗaya nata kika ɗauko da ban san wanne irin kyau zaki ba Manal." Mubeena tana kuka tace, "kuma basu sake neman inda kike ba? Basu sake waiwaiyar ki ba kema baki neme su ba?." Mama tace, "har abada wallahi bazan neme su ba, kuma kar wacce tace zata neme su yadda suka barni nima na barsu, yadda suka aurar dani ga wanda basu san shi ba suka bar ni a wajan sa aboda basu damu dani ba shikenan aje a haka kawai. Mu haɗu a lahira a lokacin da Allah zai tambaye su haƙƙina." Mubeena tace, "Mama to ina dangin Maman ki?."Mama ta sauke ajiyar zuciya tace, "Ban sani ba Mubeena, a lokacin baya da yawan wanda suke zama ƙwarƙwarori bayi ne, wataƙila Mamana tazo a baiwa ne har aka bawa mahaifina ita a matsayin baiwar sa. Mamana ta taɓa cemin dangin ta sun rasu kuma asalin ta ba ƴar nigeria bace, wannan dalilin ya saka na saka a zuciyata mahaifiyata bata da dangi." Mubeena tace, "mahaifin mu bai...." Kallon da tayi mata ya saka ta yin shiru tace, "kul kar na sake jin maganar mahaifin ku a bakin ki, dan na yafewa Mu'azzam har na barwa ɗan sa Manal ba hakan yana nufin na manta da abokin sa bane, Shima Mu'azzam ɗin in wani ne ba Adnan ba wallahi bazan bashi Manal ba. Kar ki sake maganar mahaifin ku, ko yana da rai ko bashi da rai wannan bai dame ki ba, ya neme ni bai neme ki ba babu ruwan ki, tunda ya kwashe dukiya ta wacce daman ita ta kawo shi ya tafi ya barni daku na shafe babin tarihin sa a duniya. Kwanciyar hankalin sa ya zama ya bar duniya, in ma yana duniyar kar ya zama yana tunanin inda nake ko kuma inda ku ke, domin shine kawai kwanciyar hankalin sa." Mubeena tace, "ki yi haƙuri." "Cikin dukiyata da suka kwashe abu biyu ne ya rage basu ɗauka ba, wata babbar gona da na gada a can Jalingo da kuma wani shago na kasuwa wanda aka siyar dashi baban ku yake juya kuɗin. Gonar kuma ita aka siyar da rabi aka yiwa Manal dake kayan ɗaki." Manal dai kuka take ta matso kusa da Mama ta riƙe ta tace, "Mama ki yi haƙuri" Mama ta riƙe ta itama tace, "baki min komai ba Manal, ni zan baki haƙuri da nake ƙoƙarin katse miki farin ciki." "Wallahi Mama zan iya yin komai a kan ki ciki harda rabuwa da Adnan." "Baza ki rabu dashi ba Manal, na amince da zaman ki dashi komai ya wuce kar ki masa zancen mahaifin sa domin mahaifi mahaifi ne, duk lalacewar sa shine ya a haife shi." Mubeena ma ta ƙarasa kusa da Maman tana kuka tace, "abubuwa dana aikata a baya Mama ki yafe min." Mama tayi dariya tace, "Mubeena kar ki damu komai ai ya wuce, na yafe miki na kuma tabbatar da kin yi hankali tun ba yanzu ba. Allah yayi muku albarka ya baki miji na gari, ke kuma da Allah ya baki na garin Allah yasa kar yayi halin mahaifin sa sannan kuma ya baku zaman lafiya har abada." Manal ta amsa da amin suka rungume Maman suna kuka, Mama tayi murmushi tace, "komai ya wuce, ku ne farin cikina a duniyar nan, burina na saka ku farin ciki ko yaushe a kuma ko ina. Ku jikokin Muhammad Jalingo ne, kuna da asali ba a bola aka haife ku ba." Ɗago su tayi daga jikin ta kalle su ta riƙe fuskar su tace, "yadda ku ke da kyawawan fuskoki ina so zuciyar ku ta kassance fiye da haka, don Allah kar ku ɗauko munin halin mahaifin ku, ku kasnace masu zumunci a ko yaushe, ku ƙaunaci junan ku, baku da kowa sai ni kawai, ni kuma na girma zaku iya rasa ni a ko wanne lokaci, da zarar ƙasa ta kulle idona baku da wani wanda zamu kalla matsayin dangin ku sai junan ku. Duk da nasan Baba kamar mahaifi ne a wajan ku yaran sa kamar ƴan uwan ku suke amma ba jini ɗaya ku ke ba, in kuka riƙe kan ku kuka mayar da Balaraba uwa, kuka mayar da Baban ku uban shikenan zaku zauna lafiya koda bani da rai." "Balaraba tayi min komai a rayuwa, lokacin da Baban ku ya aure ni bashi da wani hali sosai, itace take kawo min abinci a ko yaushe bata taɓa gajiya ba kuma bata taɓa yi min gori ba. Balaraba ƴar uwata nake kallon ta wallahi, a yanzu in akace na nuna dangina itace ta farko wacce zan nuna saboda ta zama kamar jinina duk abinda yake damuna ita nake faɗawa. Ban amince ku nemo ahlin jalingo ba, ban amince ku ce musu ku jinina bane. Haka zalika ko da zaku ga mahaifin ku kuma kun tabbatar shine ban amince ku nuna masa kan ku ba, yadda aka bar ku kuma ku bar su." Mubeena ta riƙe Mama sosai tana kuka tace, "in sha Allah Mama, baza ki tafi ma ki bar mu ba." Ta riƙe su  a jikin ta sosai tana kukan farin ciki suka kuma haka. Ƙaunar ƴaƴan ta take ji tana shiga ko ina na jikin ta, soyayyar su ta gama mamaye mata zuciya da gangar jikin ta, bata jin kowa a ranta sai ƴaƴan ta kawai. Ɗago Manal tayi ta kalle ta tace, "ɗauko wayar ki kira mijin ki ki ce masa yazo da daddare ina neman sa." Manal ta koma jikin Mama ta lafe tana kuka babu alamun tashi a tare da ita, Mama tayi murmushi tace, "sarkin kuka, ki bar wannan kukan ki yi abinda nace." Bata ɗago ba hakan ya saka Mama tace, "Yaya Mubeena bani wayar na kira shi da kaina." Mubeena ta bata wayar Mama tana kallon wayar tace, "ban iya iPhone ɗin ba, Kira min shi" ta faɗa tana bawa Mubeenawayar. Mubeena ta kira shi ta miƙawa Mama kafin ya ɗauka, Mama ta kalli screen ɗintace, "wannan sunan yan gayu haka, Mubeena me aka rubuta?." Mubeena tace, "life partner, abokin rayuwar ta." Mama tayi dariya ta daki Manal a baya tace, "Lallai Manal, kin gado mahaifiyata. Tun Ina ƙarama na san mahaifina yana son mahaifiyata haka itama tana son sa."         Bebi yana zaune a office shigowar Huzaifa kenan kiran Manal ya shigo ya ɗauka ya saka a kunne yace, "Yaya Mubeena ina fatan ba jikin na ta bane ba?."  Mama tace, "ba Mubeena ba ce Adnan, Maman su ce." Zabura yayi ya tashi zaune sosai yace, "Mama barka da safiya." "Barka dai Adnan, ya aikin?." "Alhamdulillah, ya ƙarfin jikin?." "Jiki da sauƙi." "Allah ya ƙara lafiya." "Amin. In kana da lokaci da daddare ka zo ina neman ka." Adnan yace, "to Mama in sha Allah zan zo." Mama tace "Allah ya nuna mana." Ya amsa da amin ta katse wayar. Kallon Huzaifa yayi da yake a tsaye yace, "Maman su Manal ce fa, tace tana son ganina da daddare. Wallahi gabana faɗuwa yake yi sosai, Allah yasa ba wani abun gane ba." Huzaifa yace, "kar ka damu, yanayin yadda tayi maka magana ya tabbatar daalkhairi ne in sha Allah." "Allah yasa hakan Huzaifa, Allah yasa tace ta bani Manal mu koma gida, ni kaɗai na san illar da rashin ta ya kawo min." "In sha Allah zata amince, shine dalilin kiran." Ya sauke numfashi ya cigaba da abinda yake yi shi kuma Huzaifa ya fasa faɗar abinda zai ce ya fita. Mama na kashe wayar ta kalli Manal da take jikin ta tace, "zaki koma gidan ki yau in sha Allah." Surayya ce da Maman ta suka shigo falon da sallama Mama ta amsa Maman su Surayya tace, "Manal sannu ya jikin?." Manal ta amsa tana cewa, "wallahi da sauƙi Mama." Surayya tace, "Milky ya jikin?." Ta amsa suka zauna Maman Surayya tace, "lafiya dai naga yanayin ku duk wani iri?." Mama tayi ƴar dariya tace, "yau dai na sanar dasu waye mahaifin su shine suke kuka." Mama tayi murmushi tace, "ai kuka dole ne, ni kaina nayi kuka a lokacin da na sani." Manal tace, "Au Mama daman kin sani?." Maman Surayya ta harare ta tace, "ɗauka ki ke aminitar ta mu ta wasa ce?." Mama tayi dariya tace, "faɗa mata dai. Yanzu ma nace Adnan ɗin anjima yazo su koma gida." Maman Surayya tace, "kai amma naji daɗi hakan wallahi, ai gwara ta koma yafi kwanciyar hankali da rufin asiri, Allah ya kaimu anjiman." Aka amsa da amin suka cigaba da hira ana dariya cikin walwala. BDƘB3P10 Bebi gabaɗaya bashi da nutsuwa tunanin sa yana ga dalilin kiran Mama, meyasa Mama ta kira shi?. Abinda zai faru kawai yake hangowa gabaɗaya ya ruɗe tunanin yaƙi barin zuciyar sa. A haka ya gama abinda zai yi wuce zuwa gida wajan Mummy, lokacin yamma tayi sosai yana shiga wajan Mummy da sallama ya same ta ita yaran ta mata suna zaune ana hira. Amsa sallamar sukayi ya shigo ya zauna yace, "Mummy barka da yamma." Ta amsa tana faɗin, "ya aikin?." "Alhamdulillah, ya gida?." "Lafiya lau Adnan." Mimi ta kalle shi tace, "Yaya sannu da zuwa." Ya kalle ta kaɗan yace, "Yauwa sannu" ya sake kallon ta yace, "ke wai bleaching kika koma ne? Indai zan gan ki sai naga kin sake haske, me kike shafawa?." Mimi tayi dariya har su Mummy Farida tace, "to ina ruwan ka? Kwanciyar hankalin auren kenan ai. Kai mun taɓa ce maka me ya saka Manal take haske?, daman ita ga haske har yaso ya yi mata yawa." "Ji mana, ki dinga haɗawa da tabarakallah. wannan haske nata maganar ki kawai sai ya saka shi disashewa, ko yaushe sai kin tanka kuma bakya haɗawa da ma sha Allah." Ta riƙe baki tace, "Allah ko Bebi? Lallai ka ga mai mata ko?. Taɓe baki yayi baice komai ba ya kalli Kausar da take karatu yace, "Kausar ina kika je jiya?." Gaban ta ya faɗi matuƙa ta ɗago kai alamun rashin gaskiya ya bayyana a tare da ita zatayi magana yace, "kar ki yi min ƙarya." Kausar tace, "Gidan su ƙawata naje a nan state road." "Me ake yi a gidan nasu?." "Kawai zuwa nayi, ziyara na kai mata." "Kuma duk direbobin gidan nan kaɗan suka yi miki da zaki fita da mota?." Kausar ta yi shiru yace, "bakya ji ne?." Kausar tace, "ina sha'awar tuƙa motar ne kawai shiyasa." Ya girgiza kai yace, "yayi kyau, ki cigaba kin ji, ki ɗauki halayen da ba naki ba." "Bazan sake ba, ka yi haƙuri. Kuma kafin na fita har Mama na faɗawa sai da ta bar ni na tafi." Ɗauke kai yayi baice komai ba ya kalli Farida sai ta riga shi magana tace, "Ni kuma me nayi Yaya?." Sai yayi murmushi itama tayi dariya ya sake mayar da fuskar sa yadda take yana kallon wani wajan daban. Mama ta lura dashi sai tace, "Mimi kawo masa abinci." Mimi ta tashi ta kawo masa couscous da miya a kai da cole slow a gefe, karɓa yayi ya kalli abincin ya kalle ta yace, "koma ki kwashe miyar nan ki kawo min ketchup." Farida tace, "Kaii matar aure ce fa, dan ta taimaka maka ta kawo maka abinci sai ka wahalar da ita?." "Allah ya sa aure ce da kansa" ya faɗa cikin baƙar magana yana kallon Farida. Farida tayi dariya tace, "wannan ikon Manal zaka yiwa ba ita ba." Mimi ta juya tana dariya tayi abinda yace ta kawo masa Mummyta kalle shi tace, "Wai cin couscous da zallan ketchup, ai bazan iya ba." Karɓa yayi kafin yace Mimi ta kawo masa ruwa ta ajjiye, fara ci yayi yaci sau ɗaya sau biyu sai ya ajjiye ya dafe kansa. Mama tace, "ya jikin Manal ɗin?." Jin muryar Mama sai ya kalle ta yace, "taji sauƙi, tana gida." "Yanzu nake faɗawa Farida su je su dubo ta ashe ta koma gida." "Uhum ta koma" ya faɗ yana jawo yana juya spoon ɗin hannun sa a cikin abincin. Yaya Farida tace, "ashe Mama bata san ma tana da ciki ba, nice nake ce mata laulayi take." Hararar ƙasan idanu ya yiwa Farida ba tare da yayi magana ba. Tayi dariya tace, "ƙarya nayi? Ba cikin ne da ita ba ka ke harara ta?. Ka raina ni wallahi, dan kaga har matar ka tana da ciki shiyasa ka ke ganin kan mu ɗaya." Kulle ido yayi cikin jin nauyin maganar a gaban Mama ya buɗe idon ya yiwa Faridan banza bai amsa ba. Mama tayi ƴar dariya dan ta fahimci kunyar ta yake ji ta share batun bata ce komai ba. Wayar sace tayi ƙara ya duba sai yayi tsaki yace, "Mummy yarinyar nan bata san bana son takura a waya bane? Ƙiris nake jira nayi blocking ɗin ta." Mama tace, "wacece?." "Ruman" ya faɗa cikin taƙaice. Mama bata ce komai ba kawai tayi murmushi dan bazai gane abinda yake faruwa ba. Shiru ya ratsa falon babu mai magana a cikin kafin ya ture abincin a bayyane yace, "Ya Allah!" Ya faɗa yana sauke numfashi. Mama ta kalli Farida da ƙannen sa suna kallon sa dukkan su tausayi yake basu. Kallon agogo yayi yace, "Mummy zan je gida, Maman Manal ta kira ni tace tana son ganina da daddare, bayan sallar i'sha in sha Allah zan je. Allah yasa kiran na alkhairi ne na gaji da wannan tashin hankalin, daga wannan sai wannan abubuwan yawa suke min." Mama tace, "kar ka damu kiran na alkhairi ne in Allah ya amince." Ya kulle ido ya buɗe yace, "Allah yasa Mummy, abubuwan sai sake lalcewa suke yi." "To ya za'a yi? jarawabar kenan." ya girgiza kai ya tashi ya fita. Kamar yadda ya faɗa bayan sallar i'sha yayi kwalliya cikin manyan kaya harda hula ya nufi gidan su Manal, kafin ya ƙarasa sai da ya tsaya yyi tsaraba sannan ya wuce. Da yaje ƙofar gidan babu kowa, babu wanda zai aika balle ya yi masa iso zuwa cikin gidan hakan ya saka shi kiran wayar Manal amma n Bata ɗauka ba. Numfashi ya sauke yana tsaye sai ga Mubeena ta fito daga gidan su Surayya da kwano a hannun ta ganin sa sai tace, "A'a Dr ya ka tsaya a nan kamar wani baƙo? Ka shiga ciki mana, muje ciki" ta faɗa tana yin gaba bai shiga ba sak da ya tabbatar ta sanar dasu sannan ya shiga cikin gidan da sallama. Tsakar gidan da haske sosai suna zaune a tsakar gidan gabaɗaya akan tabarma, shigar sa ya saka Baba ya kalle shi da fara'a yace, "banda abin Adnan sai ka tsaya a waje kamar wani baƙo?." Murmushi yayi ya ƙarasa suka gaisa da Baba ya zauna daga gefe suka gaisa da Mama ta amsa fuska sake kamar yadda ta saba. Mubeena ta kalli Mama tace, "Gashi Mama na samo mata." Mama tace, "kai mata mana, ki kira ta ma tazo nan." Mubeena ta shiga da kwanon ciki. Mama ta kalli Baba tace, "ai ni nace yazo da daddare ina neman sa." Baba yayi dariya yace, "Allah sarki, Gashi kuwa ya amsa kira." Mama tayi murmushi tace, "ai ba wani abun bane akan maganar Manal ce dai." Gaban sa ya faɗi matuƙa ya kulle ido yana jira yaji abinda zata ce masa sai addu'a yake a zuciyar sa. A lokacin Manal ta fito da hiijabi ta ƙaraso ta zauna Mubeena ma ta zauna Mama tace, "Adnan ka ɗauko matar ka Manal ku koma gida, komai ya wuce in sha Allah." Tana kallon yadda ya sauke ajiyar zuciya da yadda bakin sa ya furta alhamdulillah tare da yin murmushi mai sanyi. Mama tayi murmushi tace, "Komai ya wuce mahaifin ka mahaifin ta ne, kuskurena ne ma da na ɗauko ta tun farko bai kamata nayi haka ba. Ka yi haƙuri na ɗauko maka mata har tsahon kwanaki biyar bata gidan ka ba tare da izini ba." Adnan da yake murmushi farin ciki yace, "Babu komai Mama, ni zan bada hƙri a madadin mahaifina, ya sanar damu dukkan abubuwan da suka faru, ina ne..."Mama ta dakatar dashi daga abinda zai ce tace, "Adnan kamar yadda nace maka ya wuce ka ɗauka ya wuce ɗin, dawo da maganar baya bashi da wani alfanu Adnan." "Mun gode Mama, Allah ya ƙara lafiya." Ta amsa da amin ta kalli Manal tace, "Manali kije ki ɗauki abinda zaki ɗauka kizo ku wuce, ko da yake da me ma kika zo?." Manal na zaune ta kasa tashi saboda kunya, tana so tabi mijin ta amma sai taji nauyin Baba da Mama baza ta iya tashi ba. Baba yace, "ki tashi mana Fatima, dare yana yi kin barshi a zaune." Manal ta tashi ta shiga ciki Baba ya kalli Adnan yace, "Allah ya baku zaman lafiya, Allah ya kawar da idanun maƙiya a kan ku." Ya amsa da amin yana mai farin ciki sosai. Mubeena tace, "Ai gwara ta tafi na huta da takurar bala'i ga tsirfa kala kala, haka kawai ta tayarwa da mutane hankali wai dambu zata ci, ba dan Allah yasa Maman Surayya tayi dambu a ina zan samo mata?. sai kace in an kawo mata ci take" ta fɗa tana hararar Manal da lokacin da ta fito. Manal ma ta harare ta Mubrena tace, "kika sake hararar ta wallah sai na taso na daki idon na ki." Manal ƙasa-ƙasa tace, "in kin fasa." Sai kuwa Mubeena ta zabura zata tashi Manal ta gudu daga inda take, Mama ta riƙe Mubeena tace, "ke meye haka wai? Sai kin saka ta faɗi?." "Mama hararata take fa." Mama tayi tsaki tana nuna mata Adnan da ido Mubeena ta kalle shi tace, "oh, ni na manta yana nan ai. Ai gwara ya shaida wata rana zai ga idanun matar sa a kumbure wallahi. Mai ruwan zabiya kawai." Baba yana dariya yace, "yau naga aminta ku ke ji da ita, ya akayi ta ƙare da faɗa?." Mubeena tayi dariya bata ce komai ba Manal kuwa tana daga gefe a zaune akan kujera. Baba yayi dariya yace, "yi haƙuri Adnan yaran ne kamar abokan gaba wani lokacin. Tashi kaje Allah ya tashe mu lafiya ya tsayar da komai iya haka." Adnan yayi godiya sosai ya ajjiye ledar da yazo da ita ya tashi ya saka takalmin sa ya wuce Manal da take zaune ya fita. Baba tace, "Mubeena raka ta su tafi." Mubeena ta tashi ta ƙarasa wajan Manal ɗin take zaune sai ta taso ta dawo kusa da Mama ta rungume Mama kawai ta fara kuka. Mama tayi tsaki tace, "ke kinga matsalar ki wallahi, yanzu meye abin kuka kuma?." "Munafurcin fa?" Mubeena ta faɗa daga gefe. Baba yace, "Manal ta shi ku je kar ki barshi yana jira." Tashi tayi suka fita suka same shi a zaune a mota yana hango fitowar su ya zubs mata ido har suka ƙaraso yaga alamun kuka ma take. Mubeena tace, "Shikenan ki gaida gida." Manal ta kalli Mubeena cikin sanyi tace, "Yaya sai da safe." Yadda tayi maganar ssi Mubeena ta kalle ta taga hawaye take yi sai ta tausasa murya tace, "Allah ya tashe mu lafiya, ki dinga cin abinci in akwai abinda kike so ki faɗa min." Manal ta ɗaga kai tace, "to Yaya, ni dama zaki zo mu tafi can dake." Mubeena ta harare ta tace, "Baki da hankali ai." Manal tayi dariya ta rungume Yayar ta ta tace, "zan yi kewar wannan masifar taki." Mubeena tayi dariya tace, "ke a kan hanya muke, na wuce gida, a kular mana da unborn" ta faɗa tana janye jikin ta ta kalli Adnan da yake kallon su tace, "Sai da safe" ta faɗa tana wucewa Manal ta shiga motar suka tafi. Kukan da take yi ya saka shi bai yi mata magana ba har suka je gidan su, ya paka motar ya kalle ta yaga har lokacin hawaye take yi yace, "partner baki son dawowa ne?." Ta kalle shi da jajayen idon ta yace, "tunda muka taho kike kuka, nayi shiru na ƙyale ki saboda nasan kukan na Mama ne amma naga kamar dawowar ce bakya so." Idanun ta goge ta kawar da kai gefe ya buɗe motar ya fita ya zaga ya buɗe mata yace, "fito." Fitowa tayi ya kulle motar ya riƙe hannun ta zuwa ciki. Falon babu dauɗa sosai sai kayan da aka yi amfani dasu aka bar su a wajan. cup ɗin tea da aka sha aka bar shi a wajan, ga bowl da spoon har da glass cup da ragowar ruwa a jarka, ga lemo, ɓawon apple da na lemon zaƙi kana gani kasan namiji ne yake zama a falon. Wuce falon suka yi har zuwa ɗaki sa ya zauna da ita a kan gado ya zare mata hijjabin jikin ta yace, "Nasan yunwa kike ji, me zaki ci?." Manal tace, "Naci abinci a gida yanzu." "Kin tabbatar bakya jin yunwa?" Ta ɗaga kai alamun eh yace, "okay, bara mu yi rbs kwana biyu na san ba a gwada sugar ki ba" ya faɗa yana ɗauko abin gwajin ya dawo ya zauna kusa da ita, ya riƙo hannun ta ya fasa hannun ya saka jinin a abin gwajin ya kalle ta yace, "12.1 Manal, meyasa baya ƙasa ne? Kin ci abu mai zaƙi ko?." Girgiza kai tayi alamun a'a ya ajjiye abin gwajin a kan table yace, "in baki ci ba meyasa baya sauka?." "Ya sauka, wancan 13 kace fa." "Amma kwana nawa?." Tayi shiru bata ce komai ba yace, "ki dinga yi a hankali, kin san ciwo a wajan mai ciki illa ne dashi musamman wannan ciwon na diabetes, ki dinga daurewa kina kawar da kai kin ji my love?." Ta ɗaga kai alamun to yace, "yanzu sai muje ki yi wanka ko?." "Nayi a gida kafin kazo" ta faɗa tana kwantar da kanta a kafaɗar sa. Yace, "kaya zan ɗauko miki ki canja kenan?." Ta ɗaga kai alamun eh. ta tashi daga kafaɗar sa ya tashi ya fita bai dawo ba sai da ya kulle gidan gabaɗaya, ya kawo mata rigar bacci mara nauyi irin wacce ta saba sakawa ya zauna kusa da ita ya cire mata rigar jikin ta ya saka mata ta baccin. Kwanciya tayi ta kulle ido kamar mai jin bacci sai ya taji yace, "kar ki yi bacci baki yi alwala ba." Tashi tayi ta shiga banɗakin ta ɗauro alwala ta fito ta same shi yana cire kaya ta wuce shi ta kwanta a gefe tayi shiru labarin da Mama ta basu duk ya cika mata zuciya. A bayan ta taji ya kwanta yace, "tunanin me kike yi?." Manal tace, "labarin da Mama ta bamu akan wahalar da ta sha damu, in na tuna bana sanin ina kuka" ta faɗa tana murya na fara yin rawa. Adnan ya sauke numfashi yace, "ai ba abin kuka bane Manal, abinda ya faru ya wuce yanzu gashi ya zama labari." Tayi shiru bata ce komai ba shima bai ce ba dan bashi da abin faɗa tunda laifi har da mahaifin sa. Katse shiru yayi yace, "Da Mama ta kira ni ɗazu rasa nutsuwa ta nayi, so nake kawai dare yayi yazo saboda zuciyata ta kasa nutsuwa da kiran, wani ɓangaren yana faɗa min alkhairi wani ɓangaren na faɗa min akasin haka. Har Mummy na faɗawa ta yi min addu'a Allah yasa kiran alkhairi ne." Manal tayi murmushi ta juyo ta kwanta a jikin sa, daman abinda yake so kenan ya zagaya da hannun sa ya riƙe ƙugun ta tace, "komai ya wuce a wajan Mamana." "Na ga zahiri tunda gashi ta dawo min da farin cikina." Kallon idanun sa take yi cikin ƙarancin hasken ɗakin tace, "da gaske ni ce farin ciki ka?." "Ke cikin rayuwata ce Manal ba iya farin ciki ba, kwanakin da nayi a gidan nan babu ke Allah kaɗai yasam adadin azabar da nasha, tunanin ki kawai nake yi a ko yaushe. Rabon da naci abinci mai yawa wallahi Manal har na manta, tashin hankalina na farko kar ace nida ke yaya da ƙanwa ne, tashin hankalina na biyu kar Mama tace baza ta bani ke ba, ban san ya rayuwata zata kasance in babu ke ba." Manal tayi murmushi jin daɗi ta sake gyara kwanciya a jikin sa tace, "taɓ, nima da nace nida kai Yaya da ƙanwa ne ai da na daina fitowar ko ina" ta faɗa tana dariya shima yayi dariya yace, "hmm aikin gama dai ya gama, gaki da cikin mijin ki kuma yayan ki." "Innalillahi! Allah mun gode maka." Yayi dariya yana kallon idon ta ya ɗaga mata gira yace, "to ya dai? Na baki abinda kike so ko baki da lafiya?." Manal ta kulle ido tana sake saka kanta cikin rigar baccin sa yana dariya yace, "uhum faɗa min, ya za'a yi yanzu?." "Ni bana so" ta faɗa tana daga jikin sa bata ɗago ba. Yayi murmushi mai sauti yana shafa bayan ta yace, "to yanzu dai ki yi bacci tunda ba lafiya ce dake ba." Manal tace, "ni na warke." "Duk da haka ki huta." Manal kamar zata yi kuka tace, "A'a ni dai." "A'a ke dai me?. To nace ki faɗi abinda kike so kin ƙi, nace na baki abinda kike so kin ce bakya so, to ya zan miki?." Manal ta ɗago ta kalle shi suka haɗa ido taga kallon idon ta yake yi sosai yana murmushi kafin taga ya kashe mata ido ɗaya sai ta sake mayar da kan ta jikin sa. Hular kanta ya zame yana tura yatsun sa cikin gashin ta yace, "kedai kin cika gulma, ni kuma indai baki faɗi abinda kike so ba bazan gane ba." Shiru yaji tayi bata ce komai ba yace, "Milky." "Uhum." "Talk please, me ki ke so Adnan ya baki?." "Nidai uhum uhum." "You can say it, please ki faɗa" ya faɗa yana ɗauko ta jikin sa ya fara bin wuyan ta da hancin sa. Tayi shiru idanun ta a kulle ya kalli fuskar ta yace, "shikenan tunda babu abinda ki ke so mu yi baccin mu." Manal ta buɗe idanun ta suka haɗa ido zai yi magana ta hana shi maganar ta hanyar kulle masa baki, ya wara ido yana kallon ta tayi saurin kulle idon ta dan kar ma ya saka ta kasa abinda tayi niyar yi. BDƘB3P11 Washe gari ta riga shi tashi da safe saboda yunwar da ta fara damun ta, ta tashi ta fito daga ɗakin ta fita zuwa Babban falon gidan ta tarar dashi tass ba kamar lokacin da suka shigo ba. Ta wuce zuwa ɗakin ta tayi wanka sharp-sharp saboda yunwa, bayan ta fito ta buɗekayan ta ta saka doguwar riga ɗinkin fitted gown, ta aaka hijjabi tayi sallar walha kamar yadda ta saba bayan ta idar ta ɗaura ɗankwali ta fito zuwa kitchen. A tsaye ta tarar da mai aikin ta tana aikin goge kitchen ɗin duk yayi ƙura, gaisawa suka yi da Manal kafin tace, "Anty kwana biyu bakya na, kin dawo lafiya." "Lafiya lau Lubabatu, ya akayi kika san na dawo?." "Ant Khadija ce ta faɗa min kin dawo." Manal tayi murmushi mai aikin tace, "na gama zan koma, akwai abinda kike so?." Manal tace, "babu komai, in akwai zan kira ki." Ta amsa da to ta fita Manal tana kallon kitchen ɗn tana tunanin abinda zata ci don yunwa take ji sosai. Kittle ta kunna ta dafa ruwan zafi hannun ta har rawa yake yi ta haɗa tea da yaji uwar madara harda milo ta saka sugar, da sauri-sauri take yi saboda kar ya fito ya ganta. Duk zafin sa haka ta zuba a bakin ta ai kam bata iya haɗɗiyewa ba ta dawo dashi saboda zafin sa, ta sake sha a lokacin ta haɗɗiye harda lumshe ido saboda daɗi. Karɓar kofin taji anyi daga baya ta juyo suka haɗa ido gaban ta ya faɗi saboda kana gani yadda fuskar sa take ka san ta ɓata masa rai. wajan sink ya ƙarasa ya zubar da tea ɗin ya kuna fanfo ruwa ya tafi dashi ya ajjiye kofin baice mata komai ba ya wuce ya fita. Manal kamar zata yi kuka tace, "to ni ya zanyi? In ba sha ba bana jin daɗi wallahi" ta faɗa hawaye na sakko mata ta rasa ma abinda zata yi. Tana sharar hawaye tana ƙoƙarin haɗa breakfast amma yunwar da take ji baza ta bata damar hakan ba. Fridge ta buɗe taga babu komai sai yourgut guda ɗaya har ya zana ƙankƙara saboda sanyi, ta ɗauko ta duba jikin sa ganin unsweeted ne sai ta saka shi a ruwan sanyi dan ya narke ta sha. Rasa abinda zata yi tayi kawai ta fara kuka wiwi kamar wacce aka daka. Yana jiyo ta yana falo kawai bazai tashi bane dan ta ɓata masa rai ya kuma lura bata jin magana ko kaɗan. Tashi yayi ya fita ba jimawa ya dawo da leda a hannun sa ya ƙarasa wajan dining ya ɗauko plates a inda suke, abinda yake ciki ya juye a ciki ya nufi kitchen ɗin dan kukan nata ya ishe shi. "Dukan ki nayi kike min kuka?." Jin muryar sa a kausashe ya saka ta kalle shi ta ga fuskar a ɗaure matuƙa jikin ta har rawa yake saboda yunwar take ji. "Kawai dan shagwaɓa zaki fara yi min kuka dukan ki nayi ko wani abun aka yi miki?" Ya faɗa cikin faɗa yana kallon ta. Maimakon kukan ya tsaya sai hawaye ya sake sakowa yayi tsaki tace, "in baki daina kuka ba in nazo nan sai na miki abinda zaki kukan da hujja, Malama ki fito ki ci abinci in zaki iya." Ai da sauri ta ƙarasa inda yake ta raɓa ta gefen ta wuce, tana zuwa tsakiyar falon taga abincin ta zauna tana cin dankali da kwai kamar Allah ya aiko ta. Tana ci tana kuka saboda yunwa take ji ga faɗan da yake mata bata so. Kusan rabi ta ci ta sha ruwa tana sauke numfashi cikin jin daɗi har lumshe ido take yi, shi dai yana tsaye yana kallon ta ikon Allah, ta bashi tausayi sosai gabaɗaya cikin ya canja ta ta koma mai rigima ga yawan kuka sannan ga jin yunwa kamar wacce bata cin abinci. amma ta ɓata masa rai sosai tausayin ta bazai hana ya nuna mata kuskuren ta ba. Yana tsaye ta taso a guje zuwa sink ɗin wajan dining tana amai duk abinda taci a lokacin sai da ya dawo. Ruwa ya miƙa mata ta bayan ta, ta karɓa ta sha ruwan yace, "sannu." Ta ɗaga kai yace, "meyasa baki ce min bakya son ci ba?." "Dan ban sha tea bane shiyasa nayi amai." "Okay, zauna na kawo miki" ya faɗa yana zaunar da ita akan kujerar dining ta zauna ya shiga kitchen. Ba jimawa ya kawo mata tea ya ajjiye a gaban ta ya sake dauƙo wanda ta rage ya zauna a gefen ta yace, "Gashi nan ki sha sai kici." Kallon fuskar sa tayi suka haɗa ido taga fuskar a ɗaure babu damar da zata yi masa magana,ta sunkuyar da kai ta fara shan tea ɗin gabaɗaya baya yi mata daɗi in ba mai sugar ta sha bata jin daɗi. Sai da ta sha rabi sannan ta sake cin dankalin tana yi tana kallon sa. Yana ganin ta sai ya cigaba da danna wayar sa kamar bai san wata wajan ba. Tana daga inda take yaji tace, "baza ka ci ba?." Kai ya girgiza mata kawai baice komai ba ta cigaba da ci kafin ta ture alamun ta ƙoshi. "Kayi haƙuri, ba da son raina nake shan tea mai sugar ba wallahi." Tsaki yayi yace, "ke kuma kika sani" ya faɗa yana tashi ya bar mata wajan ta sauke ajiyar zuciya ta rasa abinda yake damun ta gabaɗaya. Tana zaune ya fito ya shirya da alamun fita zai yi ya kalle ta yace, "zan je aiki na dawo, zuwa yamma zamu je mu gaida Hajiya da Mummy." Ido ta ya ciko da hawaye tace, "amma kace min baza ka fita ba." "Fitar ce ta same ni dole sai naje. Kinga tunda bana nan ki sha abinda kike so kin ji, duk abinda kika ga kina so Manal ki sha son ranki" ya faɗa yana hararar ta ya ɗauki wayar sa ya fita ya barta a zaune. Kukan ta ta cigaba da yi sai da ta gaji ta tashi ko kayan bata ɗauke ba ta shiga ɗaki ta kwanta ta jawo waya kawai ta kira Mama. Mama na ɗauka ta sake ƙara ƙarfin kukan ta ba tare da tayi sallama ba, daga can ɓangaren Mama tace, "ke wai yaushe zaki hankali ne? Ba sallama ba komai sai kuka?." Murya na rawa tace, "ina kwana." "Lafiya lau." "Mama partner ya daina sona, yayi tayi min faɗa akan abinda ba laifina ba ne." Mama tayi tsaki tace, "Ke wai ban faɗa miki ki daina saka ni a cikin maganar dake tsakanin ku bane?." "To Mama ya zanyi? Ke nake iya faɗawa abinda yake raina. Mama laifina ne dan ina sha tea da sugar?, Mama ji nake yi in ban sha ba kamar zan yi hauka, kamar na dinga dukan kaina haka nake ji, a gida ma dan bani da lafiya ne kuma ina ɓuya Ina sha baku sani ba. Shine fa dan yaga ina sha da safe yake ta yi min faɗa ya kuma yi fitar sa bayan yace min bazai fita ba, kuma ko kira na bai yi ba har yanzu." Mama tace, "yayi daidai ai, tunda ke bakya jin magana baki san illar ciwon da kike dashi ba, gwara da ya fita ɗin Allah ya sa bazai dawo ba sai dare." "Mama ina so na daina, kuma ba laifina bane." "Kar ma ki daina kin ji, sannan kar ki sake kirana ki faɗa min wani abu da yake tsakanin ki da mijin ki, gargaɗi na ƙarshe kenan. In zaki gyara ki gyara da kan ki in baza ki gyara ba ke kika sani" Mama na faɗa ta kashe wayar Manal ta sake fashewa da kuka mai sauti. Bebi kuwa yana sane ya fita ya barta babu abinda zai yi a asibitin, kawai dan ta ɓata masa rai ne bata san hatsarin da yake tattare da ɗaukar ciki ga mai ciwo irin ta bane shiyasa take abinda take so. Asibitin yaje bai jima sosai ba ba ya fita ya shiga restaurant ɗinsu a can ya sosai suna hira da Usman kafin ya ɗauko hanyar dawowa gida. Da ya shiga falon bata nan an gyara shi dai yayi kyau ya wuce ɗaki ya ajjiye abinda ya taho dashi ya fito ya shiga ɗakin ta amma bata ciki. Motsin ta ya jiyo a kitchen ya shiga ya ganta a tsaye tana ta aiki kamar ba ita ba. Ƙarasowa yayi inda take tsaye yace, "aikin me kike yi?." Kallon sa tayi maimakon ta bashi amsar tambayar tace, "emergency ɗin kenan?." Banza ya yi mata kamar bai ji abinda tace ba ganin haka sai tace, "Mummy nake yiwa da Hajiya tunda kace zamu je, kaga ban taɓa kai musu komai ba." Bai ce komai ba ya juya ya fita ta kashe gas ɗin ta biyo bayan sa da meatpie a hannun ta tana ci, ta zauna a nesa dashi ta ajjiye meatpie ɗin a kan table tace, "Bana sane nake shan tea da sugar wallahi, ɗazu ma ji nayi in ban sha ba zan iya mutuwa shiyasa ka ga ina sha. Ka tambayi Yaya Huzaifa a da sugar na baya high saboda bana cin duk abinda aka hana ni ci.tunda na samu cikin nan shikenan nake shan wahala, in na sha tashin hankali in ban sha ba tashin hankali, shiyasa nace maka ni bana son cikin nan amma ka kasa ganewa" ta faɗa tana kuka shi dai kallon ta yake, kuka gabaɗaya baya yi mata wahala ko gajiya bata yi. "Burin ki zai cika ai, tunda bakya son cikin zai fita da kansa kin ga kema sai ki huta." Da sauri ta kalle shi tana goge ido tace, "Allah ina son cikin, wahalar dani da yake yi ne bana so." Ya ɗauke kai daga kallon ta bai ce komai ba tace, "ka yi haƙuri, in sha Allah bazan kuma sha ba. amma ka dinga min addu'a wallahi bana sane nake yi, tunda na samu cikin nan na canja, nima bana so nake sha saboda lafiyata" ta faɗa murya na rawa tana goge idanun ta. Sai ta bashi tausayi duk fushin da yake yi da ita ya kau daga zuciyar sa, tabbas ciki ne ya saka ta aikata hakan ya sani kuma babu abinda ta isa tayi a kai. Shi shaida ne a baya sugar ɗin ta ƙasa yake yi har sai an so ta sha wani abun mai zaƙi. Ya kalle ta a tausashe ya ce, "yawan hawan da sugar ki yake illa ne a wajan ki da abinda yake cikin ki, shi ciwon sugar ga mace mai ciki yana da matuƙar hatsari domin zai iya cutar da ita da abinda yake cikin ta. Wannan dalilin ya saka kika ga ina yi miki faɗa in kina shan abu mai zaƙi, bawai ina yin faɗan dan ki ji haushi bane ina yi saboda lafiyar ki. A shekarun ciwon sai yafi miki illa akan Mama, saboda ciwon yafi na tsatsanta ga wanda shekarun sa bai wuce naki ba Manal. Yawan high blood sugar da ake samu a kan ki ayanzu zai iya sakawa ki yi miscarriage, zai iya saka ki shan wahala a lokacin haihuwa fiye da tunanin ki, sannan zai iya sakawa sugar jikin abinda zaki haifa yayi yawa shima ƙarshe a haife shi da ciwon ko ya mutu." Ganin ta nutsu tan jin sa ya saka yace, "Diabetes can also stop babies from glowing nomally Manal, zasu iya zama either too small or too large. Hakan sai ya jawo ki faɗa wani abu da ake kira da Stillbirth a turance, ma'ana yaron ya mutu a cikin ki after 20 weeks ko kuma during labour. Azo ace sai an yi cs za a cire babyn shima kuma in dai sugar ki ya yi high ba zai yu a yanka jikin ki ba, in an samu yadda ake so ma za a jima kafin ki warke." Yadda ta bashi hankalin ta tana sauraren sa ya sake gyara zama yace, "let me give you example, kina da ciwon sugar sai sugar ki ya zama always is high, ga kuma baby a jikin ki wanda duk abinda kika ci shine zai dinga cycleting a jinin sa. Kin sha abu mai sugar sugar jinin ki yayi yawa sosai, ya kike gani in sugar ki yayi yawa a jinin ki bayan kuma shi jinin ki ne yake zagawa ko ina a jikin sa? Kina ganin zai rayu kasancewar sa fetus abinda bai zama mutum ba?." Ta girgiza kai alamun a'a yace, "abinda nake guje miki kenan, na san ba yin kan ki bane amma you have to be very careful, it's a very dangerous a blood sugar ki ya dinga zama high. Shi fa ciwon nan yana hana mata ɗaukar ciki, suna shan wahala kafin ma su samu su ɗauki cikin wasu sai an basu magani suna sha wanda zai taimaka musu wajan samuwar cikin, in sun samu sai dokoki su biyo baya saboda lafiyar su da ta yaron. Ke kin samu Allah ya baki cikin ba tare da kina shan wani magani ba kuma zaki salwantar?." "Na faɗa miki duk abinda kike so ki faɗa min ko tea din ne da madara ki faɗa min, akwai madara irin taki na siya na ajjiye miki amma bakya son sha. Akwai sugar irin naki na siya na ajjiye shima bakya sha, ba dole raina ya dinga ɓaci ba Manal? In wani abun ya same ki ya zanyi? Ke na fara samu kafin abinda yake cikin ki, rayuwar ki tafi min tasa mahimmanci, in na rasa shi zan iya samun wani, ke kuwa in na rasa ki na rasa kenan har abada." Jikin ta yayi sanyi da jin kalaman sa na ƙarshe ta taso ta dawo kusa dashi ta shiga jikin sa ya rungume ta yace, "shine abinda nake guje miki Manal, ko babu ciki shan sugar zai iya jawo miki illa babba. Yan saka ciwon ido, rama, bugawar zuciya, ciwon koda da sauran su duka ciwon nan yana sakawa musamman ke fa kike da ƙarancin shekaru." "Ka dinga yi mun addu'a Allah yasa na daina." "In sha Allah zaki daina. Yanzu ma na san kin ci cake ɗin da naga kin yi ko?." Ta ɗago tace, "Wallahi ban ci ba ko kaɗan, na dai yi unsweetened ban saka sugar ba yana nan na ajjiye, shi kuma wannan meatpie ɗin babu sugar a ciki ko kaɗan." "To meyasa baki faɗa min na saka an baki wheat flour a wajan Mummy ba? Ina ke ina normal flour itama ai ba abincin ku bace." "To bazan sake ba." Yayi murmushi yace, "ko yaushe haka ki ke cewa baza ki sake ba, to naji." "Ka yi haƙuri ka daina fushi dani." "Na daina, shikenan?." Tayi murmushi shima yayi sai ta haɗe fuska cikin shagwaɓa tace, "ka tafi ka barni." Yadda tayi maganar sai da yaji ta a ko ina na jikin sa, Manal ta iya shagwaɓa ta riga da ta zamar mata jiki kowa ma yi masa take yi duk da tasa ta musamman ce. Murya a ƙasa ya ce, "babu kuma abinda nayi ba, kawai saboda ki san kin yi laifi ya saka ni fita." Ta kalle shi tace, "kuma har harara ta kayi." Ya sake hararar ta yace, "yanzu ma na kuma." "Allah ka daina sona, na faɗawa Mama ka daina sona sai faɗa take min wai ba tace na daina saka ta a maganar mu ba." Yayi dariya mai sauti yace, "Manalin Mama, kice har kin bata labari?." Ta turo baki tace, "na faɗa mata, maimakon ta rarrashe ni ta dinga yi min faɗa." Ya dungure mata kai yace, "faɗan shine daidai dake ai." "To duk ba laifin ka bane." "To da nayi me?." "Da kayi min ciki mana" ta faɗa tana kwantar kanta a ƙirjin sa. Yayi dariya sosai mai sauti itama dariyar take yi yace, "Allah ko? To daɗin abin ba mutum ɗaya ne yake samar da cikin na dole akwai haɗin kan na biyu." Tana daga jikin sa tace, "ba wani haɗin kai, ta dole aka min." Dariya ta sake bashi sosai yana dariya yace, "haka kika ce? Shikenan zan kama kina hannuna yarinya." Ta ɗago daga jikin sa ya sake kallon tayace, "ya maganar school ɗin ki ne? Ana ta karatu babu ke hakan daidai ne?." "Allah ni na tsani makarantar gabaɗaya, dana shiga sai na fara jin amai yana tawo min." "Ba kina attending online ba?." "Kwana biyu na daina, amma zan dinga yi yanzu." "Ai yafi in ba haka ba burin ki bazai cika ba. A asibitin mu ina ji ana ta yabon ki, ana cewa indai girki ka ke so mai kyaunda sauƙi kaje page ɗin cookwithManal." "Da gaske ka ke?." "Da gaske nake mana." Manal cikin farin ciki tace, "ka san ana ta bani advert, dan kwana biyu bani da lafiya ne amma da kaga sabon update. Yanzu ma abinda nayi ai nayi vedio." yayi murmushi yace, "kice mai kuɗi ce a zaune a gabana." Tayi dariya shima yayi kafin yace, "Allah ya taimaka, Allah ya sa ki zama babba ki wuce inda ki ke tunani." Ta sake riƙe shi tana murna tace, "Na gode mijina, goyan bayan ka ne ya kawo ni wannan matakin." "In kin gama wacce makaranta zaki tafi ki yi karatu?." Manal ta sauke numfashi tace, "aikin ku baya burge ni da nace zan zama nurse ko midwife, aikin lawyer baya burge ni da na zama, kai ni komai ba burge ni yake yi ba. Na fi ganewa na buɗe babban cafe ko bakery na dinga siyar da abinda na ƙware a kai." Yayi murmushi yace, "ke dai kika sani." Kiran sallah akayi ya saka shi tashi ya fita itama tayi alwala tayi sallah ta cigaba da suyar ta. Da ya dawo ya same ta a kitchen ta kalle shi tace, "Yauwa na gama, don Allah ka zuba min a cikin wannan packs ɗin kayi min packaging." Kallon sama da ƙasa ya yi mata yace, "ni ɗan aikin ki ne?." "Allah nace ai." Ya shigo ciki kusa da ita ta nuna masa a inda zai zuba. Kallon sa yaga tana yi ya ce, "Faɗi abinda yake ranki." Tayi dariya tace, "ni fa na ɗauka komai in ina so a gidan nan zaka dinga min, kamar girki da shara da komai in ina so zaka yi. Abinda ya saka na fara sarewa da kai lokacin ka ƙin cin abinci saboda nayi warming, na ɗauka zaka haƙura kaci saboda ni ɗin ni ce, na ɗauka zaka ci saboda kar raina ya ɓaci. Amma sai ka ƙi ci ka tashi ka barni da kayana ka kuma ce na dafa maka sabo." Murmushi yayi ya kalle ta ya ce, "Da yake ga Mummy, dole naci saboda kar ran Mummy ya ɓaci." "To duk ba cikin so bane?" Ta faɗa tana kallon sa. Banza yayi mata baice komai ba sai murmushi da yake yi tace, "yanzu fa ko buɗe min mota baka yi in zan shiga ko zan fito irin na masoyan nan, rabon ka da buɗe min mota tun farkon auren mu lokacin kana lallaɓa ni. Shiyasa akace in kina amarya kiyi abinda kike so da zarar aure ya fara nisa komai canjawa zai yi, lokacin nan har haƙuri ka ke bani fa, yanzu kam taɓɗijam." Shi kam dariya yake bashi sosai ya kalle ta kamar zai yi magana sai ya fasa ya danne bai yi ba ta sake cewa, "ai naji haushi da ban yi amfani da dama ta na saka ka kuka ba." ya kalle ta yana dariya ya ce, "ke kuma so kike kiga nayi kuka?." Ta turo baki tace, "eh so nake, kuma so nake ka bani haƙuri." "Gashi baki da sirri duk abinda aka faɗa miki sai kin faɗa min." Manal tace, "abu ne a zahiri gashi ina gani, inda ina amarya ne har goya ni ka ke yi" ta kalle shi tace, "da ina amarya komai nayi lallaɓa ni ka ke yi, amma yanzu" ta faɗa tana girgiza kai. Ya ce, "yanzu ke ba amarya bace ba kenan?." "Gaskiya ni ba amarya bace ba." "I see" ya faɗa yana murmushi dan ta bashi nishaɗi kam sosai. Ta kalle shi tace, "to na gama, yanzu zanje na canja kaya sai mu tafi ko?." Ƙare mata kallo yayi cikin kayan jikin ta, tunda dawo yake so ya mata magana a kai maganar ciwon ta ya ɗauke masa hankali ya ce, "kin kuma yi kyau fa." Ta yi murmushi harda ɗaga gira tace, "Allah?." Shima girar ya ɗaga mata tace, "na gode" ta faɗa tana murmushi, ya lura tana so tayi abu a baya shi kuma hakan ya zamar masa jiki. Cake ɗin ya ɗauka yaci yana kallon ta tace, "Wai a ina kika iya abubuwa masu daɗi ne haka?." "Don Allah yayi daɗi? Kaga ni ban ci ba saboda kawai sugar a ciki." "Yayi sosai, hundred percent" ya faɗa yana mata jinjina. Tayi murmushin murna ya ce, "amma kin ajjiye min nawa ko?." "Ta ya zan yi ban ajjiye maka ba? Ai dole na ajjiye." "Kin Kyauta, na san kina sona daman." Ta kalle shi Sai suka haɗa ido tayi murmushi shima haka tace, "da fa kalllo mara mutunci nake maka, tunda muka haɗu a asibiti naje wajan ka da katin Mama ka koro ni dan naje babu Mama." Raina mata hankali yaso yi ya ce, "Au wai kece daman?." Ta harare shi tace?, "A'a aljana ta ce." Ya wara ido yace, "ni kike harara?." Tayi hanyar ƙofa tace, "ramawa nayi" ta faɗa tana fita a guje yayi dariya yana cewa, "malama ki daina gudu." Bata fito ba sai da ta shirya cikin atampa mai kyau ɗinki riga da siket ta saka mayafi nai girma kamar yadda yake so, ta same shi har ya canja kaya zuwa manyan kaya. Ta kalle shi tace, "manyan kaya suna yi maka kyau, amma ina so naga ka saka ƙananun kaya." Yayi murmushi ya ce, "bakya so ki ganni ba kayan?." Ta ɗan kulle ido ta buɗe ya ɗaga mata gira yace, "uhum bakya so? Ko bana yi miki kyau babu kayan?." Manal tace, "ni ina da kunya fa." Ya yi dariya sosai yana kallon ta ya ce, "ni kuma bani da kunya." "Ni shaida ce." "Kuma kin ga ni kina yi min kyau babu kaya, saboda...." Toshe kunne tayi tace, "Allah zan maka kuka." Ya murmusa ya ce, "muje na ɗauki kayan kar ki ce min daman ai da ne nake ɗaukar miki kaya." Dariya tayi suka fito daga ɗakin ya ɗauki abinda tayi ya fita dasu ya saka a mota ya buɗe mata gaban motar ya kalle ta ya ce, "na wanke laifina?." Ta shiga ciki tana cewa, "ai dan kaji na faɗa ne, don Allah ka bani na tuƙa" ya harare ta baice komai ba ya ja motar suka fita daga gidan suka nufi gidan Hajiya. BDƘB3P12 A kan hanyar su suka tsaya a wajan mai siyar da kayan marmari suka siyawa Mama da kuma Hajiya. Bayan sun siya suka ɗauki hanyar gidan Hajiya. Basu jima a can ba suka fito, a ƙofar gidan ne Manal tana tsaye Bebi ya fito ya kalle ta ya kalli wasu mutane guda biyu mace da namiji da suke kallon ta bai ce komai ba suka shiga mota. Sai da ya fara tafiya sannan ya kalle ta yace, "su waye suke kallon ki daga tsallake?." Manal tace, "ban ma kula ba balle na na gansu." Bebi yace, "amma kamar sun san ki, kallon sani suke miki." Manal tace, "ban ma kula ba ni." Ya kalle ta yace, "ai baza ki kula ba daman, ni ai na kula." "Tunda ka kula ai shikenan." "Yayi kyau." Murmushi kawai tayi bata ce komai ba ya kalle ta ganin tayi shiru tana kallon wani wajan sai ya riƙe hannun ta suka haɗa ido ya ce, "ya dai?." Ta sauke numfashi tace, "wani iri nake jina." "Ko muje wajan Mama?." Manal ta girgiza kai tace, "faɗa zata yi min tace ba jiya na tafi ba, mu wuce kawai." "Me yake damun ki?." Manal ta riƙe hannun sa da ya riƙe nata hannun tace, "babu komai, kawai bana jin daɗi ne." Sai kuma ta riƙe hannun sa sosai tana kallon cikin hannun na sa kamar mai son ganin wani abun a tafin hannun kafin tace, "yanzu kuwa kana ganin mahaifin mu yana da rai?." Ya kalle ta yace, "to ai baka sanin wanda yake da rai ko wanda ya bar duniya indai ba kaji labari baPartner." Manal ta ɗora hannun nasa a fuskar ta tace, "ni kam ina ji a jikina yana da rai, Ina so kuma na gan shi ko sau ɗaya ne." Shafa fuskar ta yayi a hankali ya ce, "Allah ya cika miki burin ki." Ta amsa da amin kafin tace, "amma Mama bata so." Shiru yayi bai ce komai ba ganin yayi shiru sai ta canja maganar tace, "Hannun ka sanyi." "Ke kuma naki babu sanyi, yadda hannun ki yake da ɗumi haka jikin ki yake." Tayi murmushi shima yayi murmushin bai sake cewa komai ba. A cikin gidan su ya faka motar suka fito aka ɗauki abinda tazo dashi da kayan marmarin da suka siya suka shiga ciki. Abin mamakin kamar jiya duka yaran Mummy ɗin suna suna aikin hira, ganin Manal ta shiga sai Mimi tayi ihuu ta taso tana cewa, "kin gani ko Mama na faɗa miki ta koma, barka da zuwa sister!" Ta faɗa tana rungume ta. Manal tayi murmushi tace, "yau kin zo kenan?." Mimi tace, "ai fushi nake, baku taɓa zuwa inda nake ba har yanzu." Mama da take gefe tace, "laifin ɗan uwan ki ne, kin san halin sa bazai je gidan ki ba, dana tambaye shi yaushe zai je sai cewa yayi kawai sai a ganshi a gidan ƙanwar sa?." Manal ta ƙarasa ta zauna suka gaisa da Mama ta amsa da fara'a tace, "yanzu maganar ku muke yi, nace kai lafiya Adnan babu shi babu labarin sa tun jiya da yace min zai je gidan ku, Sai Farida tace ai wallahi Mummy tunda kika ji shi shiru an bashi matar sa, sashi kuwa an bashi ke ɗin. Ya jikin naki?." Manal tayi murmushi cikin jin kunya tace, "na ji sauƙi Mummy." "Allah ya bada lafiya, ya raba lafiya." Ta amsa da amin cikin jin nauyin Maman. Kallon Farida tayi tace, "Yaya ina wuni." Yaya Farida tayi murmushi tace, "yi haƙuri Manal na zuba miki ido ina kallo ban yi magana ba, jiya jiyan nan ya gama cewa Mimi bleaching take yi, to ke kuma me ki ke yi kenan?. Wannan haske naki ma sha Allah, da ana ƙwacewa da yanzu na raba ki dashi." Manal tayi dariya kawai bata ce komai ba Kausar tace, "Ai Anti baza ki ga hasken ta ba sai kin je gidan nan kin tarar da ita babu kaya, wallahi fatar ta kamar...." Kallon da yayi mata ya saka ta rufe baki tana dariya. Farida tace, "ai a fuska ma an san tana da haske balle jikin ta." Mama tayi dariya tace, "ta bakin sa ki dinga haɗawa da tabarakallah kar ki disashe masa hasken mata." Suka yi dariya Manal ita kunya take ji sai ta sunkuyar da kai tana murmushi. Mama ta kalle shi tace, "ka fito da ita bayan bata da lafiya?." "Mun je mun gaishe da Hajiya ne muka biyo nan." Kausar ta kalle shi tace, "Yaya me aka kawo mana?." Hararar ta yayi ta tashi ta buɗe abinda aka shigo dashi ta miƙawa Mama ta karɓa tace, "harda hidima Manal keda babu lafiya?." Manal tayi murmushi tace, "babu komai Mummy." Bebi ya kalli Farida da Mimi yace, "wai me kuka dawo yi ne yau?, ba jiya ku ka zo ba?." Farida tace, "Abba ne babu lafiya muka zo duba shi." Bebi yace, "Abba babu lafiya babu wanda ya faɗa min? Me ya same shi?" Ya faɗa yana tashi tsaye ya fita ba tare da an bashi amsa ba. Mama ta kalli Kausar tace, "raka ta wajan Abban su gaisa sai tazo taci abinci." Kausar ta tashi suka fita da Manal. Farida ta kalli Mummy bayan fitar Manal tace, "wallahi Manal tana burge ni Mama, akwai kunya da hankali." Mama tace, "gaskiya babu laifi, har yanzu bata iya haɗa ido dani. Ba ke kaɗai ba Farida ni kaina farin ta ma burge ni yake, ba kamar yanzu da yake ya haɗu da ciki hasken nata ya daɗa bayyana." Farida tace, "Dole ta dinga gigita miki ƙwanyar ɗa ai Mama, kallon ta kawai abun burgewa ne saboda hasken ta na musamman ne." Mama tayi dariya kawai bata ce komai ba dan Rumana ce tazo zuciyar ta. Manal kuwa da suka shiga wajan Abba samu suka yi Bebi yana zaune a gefen sa yana duba maganin Abban, suka shiga da sallama kan Manal yana ƙasa dan bata so Abba ya shaida fuskar ta. Abba ya amsa suka ƙarasa suka zauna a kan carpet Kausar tace, "Abba Manal ɗin Yaya Bebi ce." Abba sai ya tashi zaune sosai Manal tace, "Barka da dare Abba, ya ƙarfin jikin?." "Lafiya lau Manal, jiki Alhamdulillah." "Allah yasa kaffara ce." Ya amsa da amin. Abba ya kalle ta cikin son jan ta da hira yace, "ya sunan ki na gaskiya?." Manal tace, "Fatima." Abba ya girgiza kai yace, "sunan Maman ki kika ci kenan?." Manal ta ɗaga kai alamun eh kanta na sunkuye. Abba yace, "Yayar ki fa? Meye sunan ta?." "Sunan ta Nusaiba, amma Mubeena ake ce mata." Abba ya girgiza kai yace, "sunan kakar ku kenan." Manal ta ɗaga kai tayi shiru bata ce komai ba. Abba yace, "madallah na gode, duk sanda kika je gida ki gaishe min da mahaifiyar ki." Manal ta amsa suka tashi suka fita. Wajan Mama suka koma suka zauna Farida tace, "Manal ya school din?." Manal ta ɗan turo baki gaba tace, "wallahi Yaya gabaɗaaya na tsani makarantar." Farida tace, "Meyasa?." "Oho min" ta faɗa tana ƴar dariya kaɗan. A lokacin ya dawo falon Mama ta kalle shi tace, "ga abinci fa, yau abinda ka ke so muka yi funkaso." Ya zauna yace, "Mummy meyasa jini Abba yake hawa ne, daman yana da hawan jini?." Mama tace, "ban sani ba wallahi, amma gabaɗaya ya canja ya koma kamar ba shi ba." Bebi ya sauke numfashi bai ce komai ba yana tunanin damuwar da take damun mahaifin sa har haka, dan shi ya ɗauka damuwar Maman su Manal ta wuce. A lokacin aka kawowa Manal nata abincin ta girgiza kai tace, "na ƙoshi Kausar." Mama tace, "kin ƙoshi a ina? Karɓi kici rai da sha'awa, banda lalura ma a hana ka shan zaƙi ko a kafa doka akan abinda ka ke son ci?. Bana son baƙuntar nan taki Manal, har yanzu kin kasa sakin jikin ki a cikin mu." Manal tace, "ba haka bane ba Mummy." "To karɓi ki ci." Mimi tace, "wallahi yayi daɗi kuwa, ya sha sugar." Manal ta karɓi plate ɗin da aka miƙo mata ta kalli Bebi suka haɗa ido sai ta kalli Mama tace, "Allah Mummy ba sai na ci ba." Mama tace, "ina gani kina kallon sa ai, shiyasa ya ɗaure fuska saboda kar ki ci. Ni nace ki ci indai kina so." Manal ta girgiza kai tace, "A'a Mummy ba haka bane, sugar na yayi high in naci zai sake yin sama, shiyasa ba zan ci ba tunda Mimi tace da sugar." Farida tace, "Allah ka raba mu da lalura, kina son ci lalura ta hana." Manal tayi murmushi ta ajjiye amma ya bata sha'awa son ci kawai take yi. Yana kallon ta ya san tana son ci sosai amma bazai yu ba dole tayi haƙuri. Manal ta kalli Kausar tace, "Sis don Allah kai shi kitchen in ina gano zan iya ci." Kausar ta ɗauka tace, "sannu, Allah ya yaye miki wannan ciwo." Ta girgiza kawai bata ce komai ba. Message taji a wayar ta sai ta duba taga shine ya rubuto mata, _Ki yi haƙuri, yanayin ciwon ki ne ya saka hakan amma naga kina so ki ci ko?._ Manal bata kalle shi ba ta mayar masa da, _Ina so, amma na haƙura._ ajjiye wayar yayi bayan yaga abinda tace bai bata amsa ba. Lubna ce ta shigo da kaskon turaren wuta hayaƙi yana tashi ttace, "Mama wai in ji Mamy kiji ƙhamshin sa." Ganin Bebi a zaune sak tace, "Lah Mama Yaya Bebi yana nan na tafi" ta faɗa tana ficewa da sauri. Murmushi yayi kawai baice komai ba. Farida ta kalli Manal tace, "wai har yanzu bakya yin turaren wuta a gidan ki?." Manal ta ɗaga kai tana murmushi tace, "Sai dai nayi da safe in ya fita kafin ya dawo ƙhamshin ya ragu sai kaɗan." "Ji ƙaddara" Farida ata faɗa tana kallon sa. Ta sake kallon Manal tace, "To ki koya masa so ta dole mana, ki dinga kunnawa ko yana nan." Manal ta wara idanu tace, "taɓɗijam! Rufa min asiri Yaya." Mimi tayi dariya tace, "kice halin nasa yana nan." Kallon Mimi yayi sai tayi shiru tana dariya, Bai kula suba ya tashi ya fita ya bar musu falon. Sai bayan magriba suka tafi suka biya gidan Huzaifa daga nan suka wuce gida. Bai shiga gida ba sai da yayi i'sha ya shiga ya samu har tayi wanka ta idar da sallah. Kallon ta yayi ya ajjiye mata leda ce, "karɓi wannan ki yi blending ki dinga sha" ya faɗa yana nuna mata ledar cucumber da green apple. Manal ta duba ledar ya sake cewa, "zaki iya haɗewa duka waje ɗaya ki markaɗa, ya zama kamar shine lemon ki ko yaushe ki dinga sha, zai taimaka miki wajan redusing sugar ki." Manal ta cire hijjabin jikin ta tace, "to bara naje nayi yanzu." "In kuma kina ganin zaki jurewa ci ko yaushe ba sai kin mayar dashi ruwa ba." Manal tace, "gwara nayi blending ɗin zai min daɗi." Ta miƙe tsaye ya ce, "muje na raka ki." Tare suka shiga kitchen ya samu waje ya zauna yana kallon ta. Wanke su ta fara yi ya ce, "ki saka gishiri ki wanke." Ta amsa ta saka musu gishiri ta yanka sannan ta saka a juicer ta mayar dashi ruwa. Sai da ta gama samu babban jug ta juye ta buɗe fridge ta saka, sannan ta ɗauki glass cup ta zuba wani a kofin ta sha ta kalle shi tace, "wallahi daɗi sosai." Yayi murmushi yace, "kuma zai taimake ki sosai, dan cucumber tana saurin saukar da sugar da hawan jini, masu hawan jini da ciwon sugar ana so su dinga yawaita amfani da ita. Ita kaɗai ta isa tayi miki maganin ciwon ki, kuma kinga tana rage ƙiba kuma zata taimaka miki a other room." Manal ta sake sha tana kallon tace, "meye kuma other room." Ya wara ido yace, "baki san other room ba?." "In na sani zan tambaya ne?." "Zan faɗa miki, gama tukunna." Manal tace, "ko ɗan gyara wajan nan wai baza ka taya ni ba? Gaskiya baka iya soyayya ba." Bebi yayi dariya yace, "naji muje a haka, bazan yi ba. Wai ke ni ɗan aikin ki ne?." "Ba shi bane, dan ka taya ni aiki ai ba komai bane." "Ke dai kika sani, bazan yi ba." "Shiyasa nace baka iya ba ai, inda a india ne tare zamu yi." "Shima a film ko?." Manal tayi dariya tace, "har a zahiri ma." A bayan ta taji ya tsaya ta tsakanin hannayen ta ya sako hannun sa ya riƙe abinda take ɗaurayewa ya kalle ta yana yi mata magana a daidai kunnen ta tare da fesa mata numfashin bakin sa ya ce, "kince na taimaka miki ko." Shiru tayi dan ko yaya ta jita a jikin s a yanzu sak ta canja daga yanayin da take ciki, shi kuma yana sane yake haɗa jikin sa da nata yana riƙe hannun ta da sunan wanke-wanken da take yi zai taimaka mata. Shirun da yaji tayi ne ya saka shi ya tabbatar akwai wani abu, bai ce komai ba ya ajjiye abinda take yi ya juyo da ita yana kallon ta ya ce, "ya dai?." Sai kawai ta kwanta a jikin sa idanun ta a kulle tana dhafa bayan sa a hankali. Riƙe ta shima yayi ya ce, "faɗa min me ya canja ki?." "Ba kaine ba." "Da nayi me kenan?" Ya faɗa yana karyar da murya. Sake riɗe shi tayi soaai yayi murmushi ya ce, "kin ce ban iya soyayya ba ko? Bara na nuna miki adadin soyayyar da Adnan ya iya a yau, fatana kar ki nuna min kin gaji" ya faɗa yana sunkuya ya ɗauke ta, ko hasken kitchen ɗom bai kashe ba ya shiga ɗaki da ita. Bayan wasu kwanaki. Cikin Manal ya bayyana sosai kai da ka ganta ka san ya girma dan a lokacin yana wata na takwas kenan kana ganin ta zaka tabbatar ta kusa haihuwa. Ta raini cikin lafiya da taimakon Bebi dan ba dan shi ba abinda yake cikin ta yana cikin hatsari babba saboda yanayin ciwon da take fama dashi. A hakan ma duk kwana uku sai ya auna blood sugar ɗin ta dan ba a so ya kasance yayi high kafin haihuwar ta ko kaɗan. Cikin ikon Allah baya sama saboda tana ƙoƙarin kawar da kai daga abinda take so saboda lafiyar ta. A cikin kwanakin babu wata matsala da ta sake taspwa daga gidan su Bebi, matsalar Maryam an maganace ta tuni Kamal bai sake waiwayar ta ba itama ta manta dashi ta cigaba da rayuwar ta. Manal na zaune a falo ita da Mubeena suna hira Mubeena tace, "ke umrah ai da daɗi zan so mu sake komawa, tunda dai Mama tace kuɗin ta za'a kashe tunda daman dalilin ɓoyewar saboda mu ne, amma yanzu tunda mun san komai za'a sake komawa." Manal tace, "in dai za'a koma kan dani za'a je, Wancan ai ba a tafiyar Mama naje ba." Mubeena tace, "hutar da Maman akayi mijin ki ya kai ki." Tayi dariya ta kalli Mubeena tace, "Yaya Mubeena har yanzu babu wanda kika tsayar ne?." Mubeena ta kalle ta sak tayi murmushi tace, "Na tsayar mana, Mama bata faɗa miki ba?." Cikin zumuɗi tace, "bata faɗa min ba, waye shi?." Mubeena tace, "Sunan sa Munir yana aiki a Abuja iyayen sa duka shna can, a sa'anni da tsaho da jiki bazai wuce mijin ki ba amma shi ya taɓa aure matar sa ce ta rasu bayan sati biyu da auren su. Har sun yi magana da Baba ma fa, Baba yace yaje zai neme shi." Manal da farin ciki ta riƙe Mubeena tace, "Allah ya tabbatar mana da alkhairi Yaya, Allah yasa shine mijin ki." Mubeena tace, "amin ya rabbi." "An munafurce ni, da ban tambaya ba za'a faɗa min ba kenan?." "Na ɗauka kin sani ne ai, ashe Mama bata faɗa miki ba." "Kai amma naji daɗi wallahi." Mubeena tayi ƴar dariya tana kallon tv Manal ta tashi tsaye tana cewa, "da alama Abuja zamu je kenan" ta faɗa tana shiga kitchen. Ba jimawa ta fito a lokacin Bebi ya shigo da sallama ba tare da ya kalli cikin falon ba ya hango ta a tsaye tana ajjiye abinci a kan dining yace, "shugabar masu girki ba nace kar ki abinci ba?" Ya faɗa yana ƙarasawa inda take. Manal tace, "na san ai wajan wannan matar zaka yi order shiyasa nayi." Yayi dariya yana kallon ta yace, "kishi ki ke da ita dan tana siyar mana da abinci mai daɗi?." "Kishi sosai ma kuwa, ta ya zaka dinga yabon abincin ta a gabana?." Yayi murmushi yace, "yau Babyn mu ya motsa kuwa? Ban ji kin kira ni kina bani labari ba." Manal tace, "yau ai dambe yake da hanjin cikina, Allah yasa ba dan china zamu haifo ba dan wallahi dambe yake yi yau." "Amma shine ko a bani labari?." Manal tayi dariya ta kalli Mubeena tace, "Yaya Mubeena ce ta ɗauke min hankali daga kiran na ka." Kallon inda take kallo yayi dan shi wallahi shi bai ganta ba sai yanzu, ya ce, "A'a Yaya Mubeena, Sannu da zuwa." Mubeena haushi take ji in yace Yayan nan, amma tunda yaga bata so yake faɗa shiyasa take amsawa kawai. Murmushi tayi tace, "Yauwa, ina wuni?." "Lafiya lau, ya Mama?." "Tana nan lafiya, tana gaishe ku." "Muna amsawa." Manal tace, "kana ji, kuɗin auren Yaya Mubeena za'a kawo, Mun ksa shan shagalin biki." Mubeena ta kalle ta tace, "ke wai..." sai kuma tayi shiru bata faɗi abinda zata ce ba. Bebi yayi murmushi yace, "Allah ya sanya alkhairi ya nuna mana lokacin." Manal ta amsa da amin kafin Mubeena ta tashi tace, "ke ni zan wuce." Manal tace, "don Allah tsaya na baki saƙon Mama" ta faɗa tana shiga kitchen ba jimawa ta fito da flaks biyu na abinci tace, "Yaya don Allah ki kai mata." Mubeena ta harare ta tace, "wai ke yar aiken kice ni?." Manal tace, "Allah nace, kuma Mama za'a bawa." "Kawai sai na fita da flaks ɗin abinci, salon ace nazo gidan ɗanwata na tafi da abinci." Manal tace, "to meye? Ai ba gidan ƙanwar wani bace ƙanwar ki ce." Mubeena ta karɓa tana cewa, "samun abin bawa ma a layin nan naku ko wahala." Bebi dai ya basu waje baya wajan, abinda Mubeena take faɗa yaji lokacim ya fito yace, "muje na kai ki" ya kalli Manal yace, "daman zan koma asibiti sai zuwa seven zan dawo, na zo naga ya kike ne kawai saboda baki yi min waya bw." Idon ta ya cikl da hawaye ganin hakan sai ya ƙarasa inda take yace, "don Allah kar ki min kuka, yanzu fa biyar da rabi zuwa nan da bakwai zan dawo ai bazan jima ba." Ta kawar da kai tace, "a dawo lafiya." Ya girgiza kai ya wuce Mubeena ta harare ta tace, "banza shagwaɓaɓɓiya" ta faɗa tana fita. A mota ta samu Bebi ta shiga gaba ya ja motar suka fita. Babu mai magana a cikin su sai sautin radio da yake tashi a motar kaɗan-kaɗan, bai ce komai ba itama bata ce komai ba. Wayar Mubeena ce tayi ƙara ganin sunan Manal sai ta ɗauka tace, "ya akayi?." Manal tace, "kinga na manta da man shanun miyar tuwon, don Allah ki dawo ki karɓa." "Kan bala'i! Ni zan dawo ma na karɓar miki man shanu? Lallai Manal wallahi kin jima da gama raina ni." "Kin san Mama tana san man shanu a tuwo, don Allah ku zo ki karɓar mata na san partner zai dawo." "Baki ma da aikin yi ne, shagwaɓaɓɓiyar banza kawai. Gwara dama Allah ya raba mu da kullum bakin ki a fashe yake" ta faɗa tana kashe wayar tana cewa, "gabaɗaya Mama ce ta sangarta ki, komai kuka kamar wata yarinya ƙarama." Bebi yana jin ta yayi murmushi kawai ya kalli Mubeena sai tayi shiru tunawa fa da mijin Manal ɗin take tare sai tace, "ina ta yiwa matar ka faɗa ko? Naga kana kallona." Baice mata komai itama tayi shiru har suka zo ƙofar gida ya faka motar tace, "to na gode sosai." Bebi yace, "in babu damuwa zan iya tambayar ki?." "Ina jin ka." Bebi yace, "kin taɓa sanin mahaifina? Ina nufin kun taɓa haɗuwa dashi kafin ki san shine ya haife ni?." Gaban ta ya faɗi sosai ta danne bata nuna ba ta kalli Bebi tace, "meyasa ka ke tambayata?." Bebi ya sauke ajiyar zuciya yace, "yanayin fuskar ki na yanzu kawai ya nuna min kamar abinda na tambaya amsa ta itace eh." Mubeena ta girgiza kai tace, "mamaki abinda kace ya bani ne, ban taɓa ganin sa sai a asibiti lokacin da muka je da Mama amma kafin nan ban san shi ba, Sai dai in shi Abban ne ya sanni wani wajan amma ni ban san shi ba." Kallon fuskar ta Bebi yake yi yana karantar yanayin ta sai dai bata bashi damar da zai gano wani abun ba a tare da ita. Bebi yace, "to shikenan na gode sosai." Mubeena tace, "babu komai, a gaishe da mutanen gidan" ta faɗa tana fita daga motar ta wuce gida shi kuma yana motar yana tunani. Wacece Mubeenan da abokin Abban sa yaji yana cewa itace silar damuwar sa?, Abinda ya saka ya zata wannan Mubeena ce saboda kallon da tayi masa a asibiti yayi tunanin akwai wani abun, amma gashi tace ba ita bace, to in ba ita bace wacece? In kuma ita ɗin ce fa?. BDƘB3P13 Mubeena kuwa tana tsaye ya wuce a mota dan a soron ta tsaya tana kallon sa, ta sauke numfashi bayan ya wuce tace, "meyasa ya tambaye ni? Ya taɓa ganina da mahaifin sa kenan ko kuma hasashe yake?. To me zai saka ya hasaso ni haka kawai ina matsayin Yayar matar sa?." Mubeena ta sauke ajiyar zuciya tace, "Tabbas yaji wani abu game dani shiyasa yake so ya tabbatar, amma me yaji a kaina? Me aka faɗa masa?." Ya dafe kanta tace, "ya Allah kasa kar ya san gaskiyar lamarin nan, sanin gaskiyar tonuwar asiri na ce da ma mahaifin sa gabaɗaya. Allah yasa maganar ta tsaya iya haka." Sai da ta daidai ta nutsuwar ta sannan ta shiga ciki wajan Mama. Shi kuwa asibitin ya wuce kamar yadda ya cewa Manal sai da akayi sallar i'sha sannan ya fito ya tafi gidan su. Wajan Abba ya shiga ya same shi a zaune yana kallon labarai ya zauna a ƙasa yace, "Abba barka da dare." Abba ya kalle shi yace, "har an dawo ko za'a tafi?." "Na dawo yau bazan fita da daddare ba." "To Allah ya sa albarka." Bebi ya amsa da amin kafin ya kalli mahaifin nasa da ya rame ya koma wani iri kamar ba shi ba ya ce, "Abba jiya naji Alhaji Magaji yana yi maka wata magana, duk da bata shafe ni ba amma indai itace silar damuwar ka sai mu yi maganin ta." Gaban Abba ya faɗi sosai ya tashi zaune sosai yana kallon sa ya ce, "ne kaji yace?." Bebi ya ce, "Naji yana cewa yanzu akan ka rasa Mubeena ka koma haka? Me zai hana baza ka nemi auren ta ba ai zata amince. Abinda naji ya ce kenan, shine nake so na tabbatar da hakan in da dama, in har da gaske Abba itace silar damuwar ka babu laifi in ka aure ta ɗim." Abba kawai kallon sa yake yi amma zuciyar sa rawa take saboda tashin hankali da fargaba, shirun da Bebi ya ji ne ya saka shi ya kalli Abba suka haɗa ido sai Abba ya ce, "to wacece Mubeenan? A ina take?." Bebi ya ce, "shine ban sani ba nazo na tambaye ka, in dai itace silar komawar ka haka Abba gwara ka aure ta yafi." Ɓoyayyiyar ajiyar zuciya Abba yayi cikin jin daɗi ya ce, "wannan tsohon labari ne Bebi, tsokana ce kawai dake tsakanina dashi amma ba maganar yanzu bace ba. Wannan maganar zata kai shekara goma da suka wuce, a wancan lokacin na ɗan yi ciwo ne akan yarinyar, wannan dalilin ya saka ko ya ya nace bani da lafiya sai ya dinga tsokana ta da sunan ta." Bebi yace, "to Abba meye yake damun ka? Ka rasa nutuswar ka gabaɗaya ka koma kamar ba kai ba, ko fita baka yi ko yaushe kana gida. Kuma naga maganar Maman su Manal ta wuce, komai ya warware kowa ya cigaba da harokin sa. Abba me yake faruwa wanda mu bamu san da shi ba?." Abba yayi murmushi ya ce, "A baya in ina fita ai bakwa so Bebi." "Abba ka tafi kayi kwanaki ba tare da iyayen mu ba shine abinda ya saka muke magana bawai fitar taka ce bama so ba. Zaman gida ai ba na ka bane sai dai lalura, wancan lokacin ma kwanakin da kake yi baka gida ne yake saka mu mgana." Abba ya sauke numfashi ya ce, "Bebi fitar tawa bata da amfani, kunyar kaina nake ji da kuma kunyar mutanen gari har daku kan ku." Bebi ya kalli mahaifin nasa yaga ya kulle ido ya buɗe ya ce, "ni kaɗai na san abinda yake zuciyata, baza ka fahimci abinda yake damuna ba kawai ka cigaba da yi min addu'a, Allah ya yafe min laifukan da na aikata ya bani lafiya ya kuma sanya min nutsuwa a zuciyata, in kuma babu rabon samu ya sa mu cika da imani." Bebi ya ce, "Amin Abba, amma wannan damuwar zata iya saka maka babban ciwo, ya kamata ka rage ta ko ka sanar damu damuwar ka." Abba ya girgiza kai ya ce, "zan rage saka damuwar Bebi, zan rage in sha Allah" ya faɗa yana kulle idon sa Allah kaɗai ya san abinda yake damun sa. Bebi dole ya taso jiki a sanyaye ya fito ya shiga wajan Mama. Yadda Mama ta gan shi jiki a snayaye sai ta bishi da kallo tace, "ya akayi?." Yace, "Mummy Abba ne, me yake damun Abba ne har haka? Ya rame sosai ko yaushe cikin tunani yake. Tunda maganar nan da mahaifiyar su Manal ta bayyana shikenan ya koma haka, meye kuma yake faruwa bayan abinda ya faɗa mana?." Mama ta sauke ajiyar zuciya tace, "Nima ban sani ba, nayi-nayi ya faɗa min amma ya ƙi." "Don Allah Mummy ki je yanzu ko zai faɗa miki, na shiga damuwa a akan yanayin nan na Abba." Mama ta sauke ajiyar zuciya tace, "to bara naje naji" ta faɗa tana tashi ta shiga kitchen ta haɗa kunu flasks sannan ta fito ta fita. Da sallama ta shiga falon Abban ya amsa yana kallon ta ta ajjiye abinda tazo dashi ta zauna kusa dashi tace, "Alhaji ga kunun gyaɗa kai ne mai son sa" ta faɗa tana zuba masa a kofi ta bashi ya karɓa yace, "ai kam na gode." Sai da ta bari ya sha rabin kofin sannan tace, "don Allah me yake damun ka? Damu da yaran ka mun shiga damuwar wannan chanjin naka, ka sanar damu damuwar ka ko zamu iya maka magani, in kuma baza mu iya ba sai mu taya ka addu'a." Abba ya ajjiye kofin a kan center table ya kalle ta yayi shiru baice komai ba tace, "ko dai maganar babar su Manal ɗin ce har yanzu? Akwai wani abun ne bayan abinda ka faɗa mana?." Ya girgiza kai ya ce, "wallahi abinda na faɗa muku shine iyakacin abinda ya faru kenan, bayan wannan babu abinda ya faru." Mama ta tausasa murya tace, "meye silar damuwar ka?." "Hauwa abinda yake damuna jin sa bazai miki daɗi ba, zai ƙara miki damuwa ne a zuciyar ki, gwara kar ki ji dan jin sa bazai miki daɗi ba." Mama tace, "ina so na sani indai har zaka faɗa ɗin." Ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "kawai Allah ne yake hukunta ni tun a duniya kafin naje gare shi, na aikata laifuka masu yawa sosai, na saɓawa Allah ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba, ni kaina bazan ce ga sau adadi ba. Gashi Allah yana hukunta ni tun a duniya, duk da nayi nadama da zuciyata da gangar jikina, na kuma tuba amma duk da haka sai na girbi abinda na shuka. Ki duba sau biyu ana zuwa auren Lubna amma da nace an taɓa mata fyaɗe ba a sake dawowa, shiyasa ko Bebi ban bari ya sani ba saboda zai fi ni shiga damuwa saboda ni na haife su amma yadda yake ni damuwa dasu zai fi ni shiga tashin hankali. Ga Maryam ma, yanzu duk wanda yaji ta taɓa yin ciki da tsohon mijin ta don Allah zai aure ta?." Mama ta girgiza kai tace, "auren zai wahala, amma za'a yi indai akwai rabon ta sake yi ɗin." "To duka fa laifina ne Hauwa, duka ni na jawo  musu da hannuna matsayina na uba a gare su, da na zauna a gida kamar sauran iyaye da yanzu hakan bata faru ba. Da ace bana bin yaran wasu a waje nima da ba'a bi nawa yaran ba. Maganar ki gaskiya ce na fifita na waje akan ku, Hakan ne kuma maganar ki gaskiyar ce, a duk sanda nace muku zan yi tafiya wallahi Hauwa wani lokacin ina cikin garin Kano cikin ɗaya daga cikim gidajena, ina ciki tare da ƴan mata in wannan tazo wannan ta tafi" ya faɗa hawayen yana sakkowa daga idanun sa. Gaban Mama ta faɗi ganin hawaye a idanun mijin ta, duk wani haushin ko takaicin sa da take ji a zuciyar ta sai taji babu shi, duk da yana faɗa mata abinda yake aikatawa ne amma sai taji rauni ya mamaye mata zuciya ta kalle shi tace, "Hawaye fa ka ke yi." Ya shafi hawayen fuskar ta sa yana kalla ya ce, "na yi shi yafi sau babu adadi, daga maganar da kika faɗa min bayan abinda ya faru da Maryam hankalina ya dawo jikina. Bayan nan na fita ranar juma'a huɗubar da akayi a ranar akan zina ne, gabaɗaya abinda kika faɗa gaskiya ne wani abun ma kin rage baki faɗa ba. Ina killace nawa a gida ina ganin babu abinda zai same su, ban san da cewa alƙhawari ne duk wanda yayi zina da ƴar wani sai anyi da ta ko da da mai gadin gidan sa ne. A ranar naji illolin ta da kuma tsantsar haramcin da yake tartare da ita. Hauwa a ranar naji koda ka shekara ɗari a duniya kana aikin alkhairi zinar kwana bakwai sai ta rinjayi wannan aikin alkhairin. Bayan na dawo gida na dinga turawa manyan malaman da na sani message akan illar zina amma abun da naji shi aje sake maimaita min, yadda wani zai faɗi azabar da Allah ya tanadarwa masu aikatawa tafi ta wani malamin zafi. Daga lokacin na fara gani ni na cuci Maryam da Lubna, basu da laifin komai laifina ne, dole sai hakan ya faru dasu saboda nima na yiwa yaran wasu." Kuka Abba yake yi mara sauti mai nuni da nadama ƙarara a tare dashi ya ce, "ina zan kai wannan zunubin Hauwa? In wani abun ya sake tsallakowa ya same ku ya zanyi?. Ban san adadin matan da aka kawo min ba, wasu suka kawo kansu wasu kuma ni na nemo su. da yawan lokaci indai a Abuja ne ban cika mu'amala da karuwa ba, Hauwa sabuwa ake ɗauko min wacce ni zan fara sanin ta, wata daga wannan lokacin bazan sake ganin ta ba wata kuma zata yi kwana biyu daga nan na sallame ta saboda haka tasarına yake. Wasu kuma neman taimako ne zai kawo su gare ni, da zarar sun yi min bazan taimaka musu ba sai sun bani kan su, wasu su amince wasu su faɗa min baƙaƙen maganganu su tafi. Amma daga baya na daina neman masu son taimako a wajena saboda gudun tonan asiri na. Wallahi Hauwa wasu matan ma ni ne silar shigar su bariki, na san Allah bai gama hukunta ni ba akwai wani abun da zai same ni yanzu ko nan gaba" ya faɗa yana kuka mai ƙuna. Ita kanta Maman kuka take yi sosai jin abinda bata taɓa ji ba, ta san mijin ta yana neman mata amma bata san abin nasa yayi yace tsanani haka ba. Cikin muryar kuka ya ce, "Ina zan kai wannan zunubin nawa Hauwa? Ina zan kai wannan tashin hankalin da na saka kaina a ciki?. Ina dake ina da Jamila amma na ke tsallake ku na tafi wajan na banza, wallahi duk nishaɗin da zaka samu a wajan karuwa bai kai rabin na wajan matar ka ba, amma mun ajjiye wannan sanin saboda shaiɗan da kuma son zuciya." Mama kuka take yi mai sauti dan abin ya shige ta sosai hankalin ta ya tashi bata da mafita sai kukan. Abba ya ce, "to ba dole na shiga damuwa ba? Ba dole na shiga tashin hankali ba?, ba dole ku rasa abinda yake damuna ba?. Hauwa ba dole na zama haka ba?. Anya bazan kai kaina kotu a yanke min hukuncin da addini ya tanadarwa irin mu ba?." Bata ce komai ba sai kukan da take yi sosai kafin ta tsayar da kukan tana jan numfashi tace, "ka gode Allah ka fahimci hakan tun kana da rai ka kuma nemi tuba daga wajan Allah, Allah ya so ka da rahama da ya saka ka gane laifin ka yanzu kafin ka koma gare shi." Ya kalle ta ya ce, "Lokaci ya ƙure min Hauwa, na fi shekara goma a bariki, raina ba a hannuna yake ba, amma na san bazan kai shekara biyar masu zuwa da rai ba. Laifin da aka aikata a cikin shekaru sama da goma kina ganin a cikin sauran numfashin da ya rage min har ya ishe ni na tuba?." "Allah mai yafiya ne a ko yaushe, indai ka tsarkake zuciyar ka kar ka fitar da ran a yanzu ma ya yafe maka." Yayi murmushi ya ce, "su kuma yaran fa? Zasu yafe min?." Mama tayi shiru bata ce komai ba Abba ya ce, "na cutar da ku, ku yi haƙuri na cuce ku na tabbatar da ko haƙƙim ku bazai bar ni ba." Mama kuka take yi shima kuka yake yi, itace take iya rarrashin sa dan kukan da yake yi ne ne yake karya mata zuciya, duk da duk abinda ya faɗa gaskiya ne amma ganin hawayen sa babban tashin hankali ne a wajan ta dan bata taɓa gani ba, ko iyayen sa da suka rasu bata ga hawayen sa ba. "Allah ya so ka da rahama da ya haka ikon tuna a yanzu, indai ka tabbatar ka daina kayi nadama Allah zai yafe maka." "Wallahi na daina Hauwa, na daina aikata komai Hauwa, komai ya gama fita daga raina, a yanzu babu abinda nake hange sai lahira ta Hauwa." Mama tace, "Allah zai amsa, in sha Allah zai yafe maka ka cigaba da addu'a. Indai ka daina shikenan Allah yana kallo." Ya girgiza kai ya saka tissue ya goge idanun sa yayi shiru bai ce komai ba amma shi kaɗai yasa  abinda yake ji a zuciyar sa. Mama ta goge idon tace, "ina zuwa." Ta faɗa tana tashi ta fita. Kamar yadda tayi zato Bebi jiran ta yake yi yana ganin shigar ta ya taso yana kallon ta ganin alamun kuka tayi sosai ya ce, "Mummy lafiya?." "Babu komai, kaje gida dare yayi ka bar mai tsohon ciki a gida." "Mummy ga alamun kuka ina gani a tare dake kice min babu komai, me ya faru don Allah?." Mama tace, "babu komai nace maka, ka tafi gida kuma yanzun nan kar na dawo na tarar da kai" ta faɗa tana sake fita ta koma ɓangaren Abban. Tana shigata zauna tace, "Bebi ne ya damu, shi naje nace ya tafi gida saboda ya bar matar sa a gida ga tsohon ciki." Abba ya kulle ido ya buɗe tare da sauke ajiyar zuciya, yana son faɗa mata abinda ya haɗa su da Mubeena amma ya kasa saboda nauyin abin yake ji shi kansa. Waya aka yi masa ya saka hannu ya ɗauka ya saka a kunne, salati kawai Mama tajj yana yi kafin ya yanke wayar jikin sa har rawa yake yi. Mama hankalin ta ya tashi tace, "me ya faru kuma?." Abba ya ce, "company na na Lagos shine yake gobara." "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Garin ya hakan ta kasance?." Gani tayi kamar baya cikin hankalin sa ta ƙarasa inda yake tana kiran sunan sa amma idon a kulle da sauri ta fita taci karo da Bebi a harabar gidan yana shirin shiga mota ta kira shi, ganin ta hankali tashe shima hankalin sa ya tashi ya bita. Yanayin da yaga Abban ya saka shi hankalin sa ya tashi, gashi shi kaɗai ne babu sauran mazan dole sai driver ya kira suka riƙe Abban suka fita zuwa asibiti. Cikin ƙaramin lokaci aka isa asibitin da gaggawa aka fara taimakon Abba aka masa allurar bacci bayan an masa allurai an saka masa ruwa. Duk Bebi ne yake yi da kansa sai taimakon wani likita da suke a team work ɗim ranar, basu jima a ciki ba suka fito daga ɗakin ya kalli inda aka tanada dan zama yaga Mama  da Mamy sai Maryam a kusa da ita, sai gefe kuma Lubna da Kausar ne da yayyen sa maza duka a zaune. Ƙarasawa wajan su yayi kowa jira yake yaji abinda zai ce ya kalle su ya ce, "ku kwantar da hankalin ku ba wani abun damuwa bane, jinin sane ya hau soaai shiyasa hakan ta faru, amma mun yi solving problem ɗin yanzu da ya farka in sha Allah zafi warware." Yaya isma'il yace, "ka tabbatar da abinda ka ke faɗa Bebi?." "In sha Allah." Mama dai kuka take yi hakan ya saka Bebi ya ce, "Mummy me ya firgita Abba lokacin ɗaya haka?." "Waya aka yi masa akace company na lagos yana ci da wuta, tunda yayi salati ya ajjiye wayar shikenan." Yaya Bilal yace, "an kira ni an sanar dani, amma wutar ta tsaya a yanzu kuma ba'a yi asarar rai ba. Dukiya ce dai an yi asara amma sai naje gobe da safe na gani da idona." Bebi ya sauke numfashi yace, "ku kwantar da hankalin ku in sha Allah zai samu lafiya" yana faɗar hakan ya juya ya bar wajan ya sake komawa inda Abba yake. Suna zaune a wajan har tara na dare ta wuce duk sun shiga sun ga Abba sun fito dan hankalin su yaƙi kwanciya gani suke kamar an ɓoye musu wani abun akan Abban. Farida ma sai da tazo da mijin ta saboda hankalin ta bazai kwanta ba in bata zo ta ganshi ba. Bebi ne ya dawo wajan da suke ya ce, "Mamy ya kamata ku tafi gida dare yayi, ni zan zauna dashi a nan duk abinda yake faruwa zan sanar da ku." Mamy tace, "A'a ai babu wanda zai iya tafiya yanzu, dan in mun tafi hankalin mu bazai kwanta ba." Yaya Bilal yace, "haka zamu tafi Mamy, haƙuri za'a yi tunda gamu a nan ai babu wata damuwa." Maryam tace, "Nima dai zan zauna bazan iya tafiya na bar Abba a nan ba." Bebi yace, "ku yi haƙuri duka amma babu wanda zai zauna a cikin ku, Allah ya nuna mana gobe da safe sai ku dawo." Shiru sukayi duka kafin Mummy tace, "ko kuma Mamy ta zauna mu sai mu tafi." Bebi ya sauke numfashi kawai ya juya ya shiga office ɗin sa. A nan yaga wayar sa na haske dan ya kashe ƙarar ta, ya ƙarasa ya duba yaga kiran Manal babu adadi hankalin sa ya tashi da tunanin wani abu ya same ta ya kira ta da sauri amma bata ɗauka ba, ya sake mira bata ɗauma ba har sau uku. "Ya Rabbi! Me ya same ta?" Ya faɗa yana fitowa wajan yana kuma kira amma bata ɗauka ba dai. A kira na biyar ta ɗauka ya ce, "ina kika shiga? Lafiya kike dai ko?." "Lafiya lau, na shiga banɗaki ne. Kana ina har goma na dare ta wuce baka dawo ba? Cewa kayi fa ƙarfe bakwai zaka dawo." Bebi ya ce, "ki yi haƙuri ina asibitin har yanzu, amma yanzu zan turo miki Kausar ko Lubna ku zauna tare ko nace ku kwana ma....." katse kiran yayi saboda kiran sa da yaji ana yi masa sai ya fito. Bai jima a can ba ya dawo ya samu suna nan inda ya bar su ya kalli Kausar ya ce, "Kausar ko ke ko Lubna wata tabi Yaya taje su kwana da Manal, bazan koma ba yau gaskiya, in ma zan koma sai dare sosai." Mamy ta kalle shi tace, "A'a Bebi, ba a barin mai tsohon ciki ita kaɗai a gida ba daidai bane, cikin ya shiga watan haihuwa fa, bai kamata kana yin nisa da ita ba." "Mamy shiyasa nace Lubna ko Kausar wata taje, duk abinda yake faruwa sai su sanar dani." Mummy tace, "tunda kace komai lafiya kaje gida in yaso sai ka dawo kaima da asuba." Huzaifa ne yazo wajan suka gaisa da su Mama yake cewa kwana zai yi   A asibitin Mamy tace, "Shikenan ma, Kaga ga Huzaifa ma abinda yake faruwa ya faɗa maka. Amma me Kausar ko Lubna zasu iya yiwa Manal in haihuwar ta samu?, in suka yi maka wayar ma kafin kaje daga nan ta galabaita." Ya sauke numfashi ya ce, "Shikenan Mamy" ya faɗa yana barim wajan. Sun riga shi tafiya sai da ya gama duba wani file sannan ya hau mota shima ya wuce gida lokacin sha ɗaya na dare tayi. A zaune ya samu Manal fuskar nan tayi ja da alama yaci kuka dan ya san daman za'a yi haka, ita daman baka mata laifi bama tana kuka balle an yi mata, balle kuma bai faɗa mata dalilin zaman sa ba. Ɗarasowa yayi ya zauna ya kalle ta kafin tace komai  ya ce, "Abba ne babu lafiya yana asibiti a kwance shiyasa na jima.." Jin abinda yace sai tayi sak kuma ta gyara zama tace, "Me ya same shi?." "Jinin sa ne ya hau." "Allah ya bashi lafiya, ko nazo muje a duba shi?." "A'a ki bari sai gobe." "Allah ya kaimu" ta faɗa tare da yin shiru. Kallon ta yayi ya ce, "kin ci abinci?." Ta ɗaga masa kai alamun eh tace, "Akwai naka ma in zaka ci, daman ni tuwon alkama na yiwa Mama shi naci, ga naka abincin nan a ajjiye." "Girki biyu kika yi? Meyasa ni ma baki ajjiye min tuwon ba?." "Ai na san baka ci." Ta kalle shi jin bai bada amsa tace, "na kawo abincin?." Ya tashi yana cewa, "huta, zan ɗauko da kaina duk da bana jin yunwa ma" ya faɗa yana buɗe abincin yana zubawa a plate. Zai ci ne kawai dan kar ta sha wahala tayi bai ci ba, a yanayin da take ciki bata fashin yin girki shiyasa zai ta daure yaci ba dan yana jin yunwa ba sai dan in bai ci ba baza ta ji daɗi ba. Dawowa yayi ya zauna ya fara ci amma bai ce komai ba itama bata ce ba, daman bai zuba da yawa ba ya cinye ya ajjiye plate ɗin. Ta kalli abincin da yake kan dining tace, "bara na saka shi a fridge gobe sai a bayar tunda dare yayi yanzu." Hana ta tashin yayi ya tashi ya ɗauki abincin ya fita dashi, bai jima ba ya dawo da flaks ɗin ya kai kitchen ya wuce ɗakin sa. Tana nan zaune bai fito ba sai ta tashi ta kashe hasken falon ta wuce ɗaki ta zauna dan tasan yau yana cikin damuwa baya son yawan magana in yana cikin damuwa.  Tana zaunen ya leƙo ɗakin ya ce, "baza ki zo mu kwanta ba?." Tashi tayi tsaye ta ƙarasa bakin ƙofar ya riƙe hannun ta suka fita daga ɗakin zuwa na sa ɗakin. BDƘB3P14 Washe gari tana bacci ma ya fita ya je asibitin yana zuwa ya samu Mamy tana nan kuma Abban ma ya farka idanun sa biyu sai dai har lokacin bai magana ba. Wajan Abban ya fara ƙarasawa bayan sun gaisa da Mamy ya ce, "Abba Sannu, ya jikin naka?." Kai ya ɗaga alamun da sauƙi Bebi ya ce, "Abba magana zaka yi halan shine zai saka mu san kaji sauƙi." Mamy da take gefe tace, "faɗa masa, yaƙi magana tunda ya farka." Abba maganar sa bata fita sosai ya ce, "da sauƙi." Bebi yaji daɗi a zuciyar sa ya ce, "Allah ya ƙara lafiya, Mamy ki je gida ki huta tunda nazo." Da to ta amsa Bebi ya kira wanda zai kai ta ya bashi motar sa yace ya kai ta ya dawo. Tana fita Abba ya kalli Bebi ya ce, "Adnan zo nan." Bebi ya ƙarasa kusa dashi Abba ya ce, "ka cigaba da kula da ƴan uwan ka ko bani da rai kaji?, duk da daman kai ne mai kula dasu bani ba, ka cigaba da jajircewa akan lamarin ƴan uwan ka." Nan take tsoron ya mamaye zuciyar Bebi amma bai nuna ba ya ce, "in sha Allah Abba, zaka samu lafiya amma sai ka rage damuwa a zuciyar ka, itace ta jawo maka wannan ciwon da ka ke fama dashi a yanzu." Abba ya ce, "damuwa baza ta tafi ba a wajena Adnan, Sai dai ma damuwa ta ƙaru ba dai ta tafi ba, ni kaɗai na san abinda nake ji." "Haƙuri ake yi Abba, Asara takin arzuƙi ce abinda aka rasa Allah zai mayar. Kuma tunda aka yi sa'a gobarar bata ci rai ba sai mu gode Allah." Abba ya kalle shi dan shi ba akan gobara yake magana ba, daman yasan tunda ya kulla alaƙa da zina ai dole ya dinga asara a rayuwar sa. Abba ya sake kallon sa ya ce, "ka cigaba da haƙuri akan abubuwan da zaka ji suna ɓullowa a kaina, ka kula da iyayen ka da kowa na gidan kamar yadda ka saba, kar ka gajiya ka yiwa kowa abinda ya kamata daidai da rayuwar sa Adnan." Bebi jikin sa yayi sanyi dan gani yake Abba kamar wasiyya yake bashi hakn ya saka ya zauna kusa da Abba ya ce, "Zaka tashi in sha Allah Abba, ai ciwon ba mai wahalar warkewa bane. Jinin ka ne ya hau sosai kuma yanzu ya sauka so nake ka samu hutu sosai a nan sannan ka koma gida, Mun tabbatar da ko bacci baka samu shiyasa abubuwan suka yi maka yawa amma zama a nan zai saka ka warware in sha Allah." Abba ya murmusa kaɗan ya ce, "to Bebi." Daga nan bai kuma cewa komai ba, Bebi ya tashi ya ɗauko abin gwada jiki ya auna jinin Abban yaga ya sauka amma dai ba yadda ake so ba, a lokacin su Mama suka shigo ganin ta da abinci Bebi ya saka aka zubawa Abban abinci yaci sannan ya sake saka masa ruwa bacci ya sake ɗauke shi. Yana fitowar daga ɗakin da Yaya Isma'il ya haɗu yaja Bebi gefe suka ɗan yi tafiya kaɗan kafin ya ce, "faɗa min gaskiya abinda yake damun Abba Adnan." Bebi ya ce, "wallahi Yaya damuwa ce da rashin bacci dama rashin abinci shine yake damun sa, amma yanzu jikin nasa ya ɗan sauka kaɗan na sake saka masa ruwa in sha Allah in ya farka daga baccin jinin zai sake yin ƙasa, saboda akwai rashin bacci a lamarin sa in yayi bacci sosai wani abun zai ragu sosai." Yaya ya ce, "bayan nan babu komai?." "Babu komai, in akwai bazan ɓoye maka ba." "To Allah ya bashi lafiya." "Amin ya Allah. Ya maganar company? Yaya Bilal  yaje?." "Yaje, yana can ma zai yi waya zai sanar damu halin da ake ciki in sha Allah." Bebi ya amsa kafin ya bar wajan ya cigaba da aikin sa. Sai sha ɗaya na safe ya kira Manal ta ɗauka kafin yayi magana tace, "Partner ina kwana." "Kin tashi lafiya? Ya kike?, ya kuma Baby?." "Sai kace ya me sunan ka." Yayi murmushi ya ce, "to ya me sunana?." "Yana nan sai naushi na yake a ciki." "Lafiya lau yake kenan, kin ci abinci?." Manal tace, "uhum na sha tea sannan kuma na ci salad ɗin da na haɗa jiya." "Kin tabbatar kin ƙoshi?." "Sosai ma, ya jikin Abba?." "Jikin sa da sauƙi sosai." "Allah ya ƙara lafiya." "Amin. yanzu babu wani abun ko?." Manal tace, "babu komai, sai dai ina so zan zo asibitin na duba Abba." Bebi yace, "to babu damuwa, sai dai bana son ki ce zaki yi driving. Abinda zai faru zan turo azo a ɗauke ki kawai, kin gama abinda zaki yi?." Manal tace, "na kusa, nan da kamar minti talatin." "Okay, in kin gama sai ki faɗa min" ta amsa da to ya kashe wayar ya cigaba da abinda yake yi. Manal bata zo ba sai da tayi abinci shinkafa da miyar kaji da lafiyayyen salad, ta saka a basket mai kyau tayi masa waya tace a zo a ɗauke ta sannan ta shiga wanka ta shirya cikin doguwar riga waacce zata sake a ciki suka tafi. Lokacin da taje asibitin duk ƴan gidan suna nan  har sirikai matar Yaya Bilal da Yaya Isma'il suna nan. Itama da ta je ta shiga cikin su aka zauna bayan taje ta ga yanayin jikin Abban. Hira suke yi da Mimi sama-sama dan zaman ma ya fara isar ta ita kar ta bar wajen aga kamar tayi rashin kunya. Mamy ce ta lura da gaji da zaman  tace, "Manal kin gaji da zaman nan, ina Bebi kije office ɗin sa ki huta." Maryam tace, "gaskiya ki je ki samu ki zauna ki miƙe ƙafar ki ko ki kwanta, kin gaji da zaman naga alama. Mimi ki raka ta ai kun san office ɗin." Tashi suka yi suka tafi ita da Mimi, lokacin da suka shiga office ɗin babu kowa a ciki.Manal ta zauna akan doguwar kujera ta kwanta tana yatsine fuska tace, "wallahi Mimi Mamy ta taimake ni, badan tace ba bazan iya tashi ba." Mimi tace, "sai ki cuci kan ki kuma?." "Kunyar su nake ji fa ni, ko Mummy ban so ta ganni ba wallahi." "Lallai kina da aiki, haka Mama tace min ai tunda cikin ki ya fito kika daina zuwa gaishe ta sai dai a waya." "Baza ki gane bane."  Mimi tayi dariya kawai dan ita kam sha'awar Manal ɗin take ita ko cikin ma bata dashi. Zama tayi tace, "bara na taya ki na matsa ƙafar nasan ta yi miki tsami" ta faɗa tana zama a gefen ta tana matsa mata ƙafar ta suna hira. Bebi ne ya shigo yana amsa waya ya kalle su sai ya tsaya ba tare da ya zauna ba, bayan ya gama wayar ya ƙaraso yana kallon Manal da Mimin ya ce, "lafiya take?." Mimi tace, "lafiya lau take, ta gaji da zama ne shine Mamy tace tazo nan ta huta." Kallon sa tayi ta tashi zaune ya ce, "ko zaki koma gida?." Ta girgiza kai alamun a'a ya ce, "to in kin zauna a nan ɗin me zaki yi? Ko zaki je gidan Mama to?." Ta noƙe kafaɗa alamun a'a tana shagwaɓe fuska harda turo masa baki tace, "ni a nan zan zauna, kawai sai naje wajan Mama bayan ga Abba baya da lafiya?." "To zaman ki shine zai bashi lafiya?." "Indai a'a zan zauna a nan." Ya zuba nata ido na wani lokaci bai ce komai ba, itama kallon sa take kafin ya janye idon sa ya kalli Mimi da take kallon su tana murmushi ya sake kallon Manal ɗin da take kallon sa kafin yayi magana tace, "Yunwa nake ji." Yayi ƙaramin tsaki ya ce, "Manal kina da damuwa, damuwar ki yawa ce da ita. Shiyasa nace kije gidan ai  kika ce ke a'a, yanzu ina zan samu abincin da zaki ci?." Jin ya fara magana cikin faɗa sai tayi shiru bata ce komai ba. Yayi ƙaramin tsaki ya fita. Mimi tayi dariya tace, "Yaya Bebi masifa, ashe har ke bai bari ba." "Yana nan yana yi, wani lokacin in yana faɗa kamar ni da shi abokan gaba ne. Ni har tunani nake ya akayi ma na aure shi" Manal ta faɗa tana taɓe baki. Suka yi dariya a tare tace, "ai wallahi duk masifar babu inda zanje, kawai naje gida na zauna ni kaɗai ba gwara nan ɗin ba." Bai jima ba ya dawo ya kalle ta ya ce, "kina ji? Dole ma kije gida ni ban san wanne irin abinci zan kawo miki da ya dace dake a nan ba, ke kin san a wannan yanayin ba a so blood sugar ɗin ki ya hau." Manal ta sauke numfashi tace, "to shikenan ba sai na ci ba" ta faɗa cikin kalar tausayi. "Ke wai gidan ne baza ki tafi ba? Biki ake yi a nan ɗin da ki ke son zama?" Ya faɗa yana kallon ta. Manal ta turo baki tace, "to in naje ni kaɗai fa zan zauna." Mimi tayi dariya tace, "bara naje a cikin wanda ta kawo naga ai basmati ce shinkafar kuma akwai salad sai taci" ta faɗa tana tashi ta fita. Ya harari Manal ta murgaɗa masa baki tare da juya idanun ta, ya girgiza kai ya wuce inda yake zama yana duba abinda ya kawo shi office ɗim tun farko. Sai da yaga Mimi ta kawo abincin ya tabbatar yayi daidai da Manal sannan ya fita. Har yamma Manal tana nan tunda ya fita ma shi bata sake ganin sa ba, har ta gaji da zaman ta fito cikin mutane duk da ba hira ake yi ba. Abba ko da ya tashi daga baccin Bebi ya ce a kira masa a lokacin ne taga ya wuce ta ya shiga inda Abban yake. Bayan ya shiga Abba ya kalle shi ya ce, "Adnan na samu lafiya a gida nake so na kwana yau." Bebi ya ce, "Abba a nan zaka fi samun hutu sama da gida, nan ya kamata ka zauna na kwana uku zaka fi warwarewa in sha Allah." "A'a Adnan, gida nake so na koma kuma zan koma ɗin." Bebi ya kalli Yayan su da yake tsaye yac e, "Yaya ka saka baki ko gobe Abba ya bari sai ya tafi, a nan zai fi nustuwa saboda zai fi samun kulawa." Yaya ya ce, "don Allah Abba kayi haƙuri zuwa goben." Jin abinda yace sai  kawai yayi shiru bai ce komai ba.  A ranar an karɓi baƙuncin baƙi maza dan zuwa duba Bbba, har dare zuwa ake wannan yazo ya tafi wannan yazo ya tafi wasu sun san su wasu kuma basu san su ba. Ƙarfe tara na dare Mama ta kira Adanan gefe tace, "kai wai wanne iri ne, kana da mai tsohon ciki ka zaunar da ita har dare baza ka kai ta gida ba?." Ya kalli Manal da take zaune alamun gajiya ya gama bayyana a tare da ita ya ce, "wallahi Mummy tun azahar nace zan saka a mayar da ita amma taƙi ji." "Yanzu sai kazo ka wuce ku tafi dare yayi, Isma'il yace yau a nan zai kwana." Da to kawai ya amsa ya kira Manal yace mata zasu tafi, sai da ya shiga wajan Abba kafin ya fito su tafi gida. Kwanan Abba biyu a asibitin ya matsa sai ya tafi, a cikin kwanaki biyu labarin gobarar company sa ta baza ko ina kowa yaji labari, anyi asarar dukiya ba kaɗan ba, dan kayan amfani na ciki duk sun ƙone wasu an samu ragowa wasu kuma babu ma ragowar sun zama toka. Ana ta taya shi da addu'a Allah ya mayar da alkhairi shi kuma a ɓangaren sa a wani abun daban yake kallon lamarin. Manal na gida a zaune da yamma tana waya da Mama tana cewa, "Amma Mama ya kamata ace kun zo kun duba Abban, har a asibiti fa ya kwanta kuma kince komai ya wuce." Daga can ɓangaren Mama tace, "Manal ai baki fini sanin ya kamata ba ko?." "Eh Mama" ta faɗa a hankali dan kar Maman tayi mata faɗa. Mama tace, "zamu zo in sha Allah, in kin je kice ina yi masa Allah yaƙara lafiya, shima Adnan ɗin kice ina yi masa ya mai jiki." A lokacin ya shigo falonsai ta kalle shi tace, "Shikenan ma gashi ya shigo" ta faɗa tana bashi wayar tace, "Ga mama." Karɓa yayi suka gaisa bayan sun gama ya bawa Manal wayar ya ce, "Ashe Maman babu lafiya baki faɗa min ba?." Manal tace, "cewa tayi basai mun zo ba tunda Abba ma babu lafiya." "Rashin lafiya ai rashin lafiya ce, da kin sani kin faɗa min sai muje mu duba ta." Manal bata ce komai ba ta jingina da kujera ya kalle ta ya ce, "yau zamu fita da daddare mu je farkon estate ɗin nan mu dawo." Manal tayi kamar zata yi kuka tace, "wallahi gajiya nake yi, ni bana son fitar nan." "Dole kuwa sai mun yi, tafiyar shine zai saka ki samu sauƙin doguwar labour, zai rage miki wahala." "Daman ai wahala ake sha in za'a haihu." Cikin son ya kwantar mata da hankali ya ce, "A'a ai kowa da yanayin yadda Allah yake bashi, yadda kike da ƙoƙarin ibada da addu'a na tabbatar Allah zai baki haihuwa mai sauƙi, sai dai ma ki haihu baki san kin yi ba." Manal ta sauke numfashi jin yadda yayi maganar a nutse ba tsokana sai ta yarda tace, "to Allah yasa hakan, amma ni tsoron nake ji. Anty Samira baban yayar su Surayya ta sha wahala wajan haihuwa, daga ƙarshe ta rasu" ta faɗa cikin rauni da nuni da gaskiyar abinda yake zuciyar ta kenan. Hannun ta ya riƙe ya ce, "shiyasa nace miki ko wacce mace da yadda Allah yake bata sauƙin haihuwar, ita ajalin ta ne a wajan shiyasa ta sha wahala sosai, ke meye na jin tsoron bayan kina dani? Kar ki manta fa ni likita ne." Ta kalle shi ido na kawo ruwa tace, "Amma ba likitan haihuwa bane ba ai." Ganin zatayi kuka ya ce, "amma zan iya karɓar haihuwar ki, dan haka kar ki damu ina gefen ki daga lokacin da zaki haihu har Allah ya sauke ki lafiya." Ta kwantar da kanta a kafaɗarsa tace, "in kana kusa dani bazan sha wahala ba?." "Baza ki sha wahala ba in sha Allah, zan dinga yi miki addu'a ina shafa miki, gashi kuma blood sugar ɗin ki ya sauka yanzu kin ga babu wannan damuwar." Motsi taji alamun ana shigowa ta kalle shi tace, "baka kulle babban falon ba? Naji ana shigowa." "Surprise!" Aka faɗa ana shigowa falon da suke, duk suka kalli wacce ta shigo ba kamar Bebi da yake kallon ta. Rumana tayi murmushi tace, "gani nazo." Ya ɗauke kai daga kallon ta tace, "Sallamar kenan?." "Kai baza ka gane bane, wallahi nayi kewar ganin ka sosai, in na kira ka a waya ko ɗauka baka yi" ta faɗa tana zama a kusa dashi ya zama sun saka shi a tsakiya ita da Manal. Yafi zaka very close da Manal amma ita Rumana kafaɗar ta tana dukan tasa saɓanin Manal da kanta yake kafaɗar sa. Kallon Manal yayi yaga shi take kallo ya kalli Rumana ya ce, "Ke wai yaushe zaki hankali ne?." Rumana tace, "dan na zauna kusa da kai shine ka ke cewa haka? To na matsa" ya faɗa tana matsawa gefe tana kallon Manal da take kallon ta. "Sannu Amarya" ta faɗa ba tare fuska a haɗe tana kallon Manal ɗin da itama ita take kallo. Kafin Manal tayi magana tace, "Beb wallahi nayi kewar ka sosai, amma kai tunda ka kira ni farkon zuwa na kace ya jikina baka sake min waya ba, amma na san kana yi min addua." Shi Bebi wani iri yake ji a jikin sa in tana yi masa magana a gaban Manal sai ta ɗaure shi da jijiyoyin jikin sa, saboda bai taɓa bawa Manal labarin abinda yake tsakanin sa da Rumana ba. Canja maganar yayi ya ce, "Ya mutanen Abuja? Kowa yana lafiya?." "Lafiya lau Beb, Mun zo duba jikin Abba ne." Ya girgiza kai baice komai ba Manal ta tashi zaune sosai Rumana ta kalle ta tace, "Amarya ina sannu baki amsa ba." Manal tace, "ban ji ki ba, kin zo lafiya?." Rumana tayi wani irin murmushi tace, "lafiya lau, i'm sorry hankalina yayi wajan Beb mun jima bamu haɗu bane, kin san kuma akwai shaƙuwa sosai a tsakanin mu." Manal ta girgiza kai tace, "na ga alama." Jaka ta buɗe ta ɗauko wata a cover tace, "Beb na kawo maka kyauta" ta faɗa tana buɗewa sai ga azurfa mai kyau a ciki, ta ciro ta riƙe a hannun ta kafin ta riƙo hannun sa da niyar saka masa. Da hanxari ya ƙwace hannun sa yana yi mata wani irin kallo zai yi magana ta riga shi tace, "kyauta na kawo maka fa, ko baza ka karɓa ba ka bari na saka maka in yaso sai ka cire ka dawo min da ita. Don Allah kar ka mayar da hannun kyauta baya, na jima ina dakon ta kawai dan na baka ita matsayin tsaraba" ta faɗa a raunane tana kallon sa. Manal ya kalla yaga kallon su kawai take yi duk sai yaji babu daɗi a zuciyar sa kamar mara gaskiya ya kalli Rumana ya ce, "Shikenan bani, na gode" ya faɗa yana miƙa mata hannu ta bashi azurfar ya ajjiye a gefe. Manal ta kalla sai a lokacin ta lura da cikin jikin ta kulle ido ta buɗe ƙirjin ta yana bugawa sosai, tana tunanin anya zata iya haƙuri da Mama take faɗa mata?. Sake kallon Manal tayi suka haɗa ido Manal taƙi ɗauke ido daga kanta kuma bata ce komai ba sai  Rumana tace, "ashe mun kusa samun Baby." Babu wanda ya bata amsa Manal ta kalli Bebi shima hankalin sa yana kanta  dan yaga ta tamke fuska kamar ba ita ba duk sai ta sake ruɗa shi, ya diririce ya rasa ina zai kama ba tare da ya san dalilin hakan ba. "Lafiya ki ke partner? Akwai abinda yake damun ki ne?" Ya faɗa yana kallon ta da murmushi. Manal ta girgiza kai tace, "me zai same ni? Kawai ina kallon dramar ku ce ta burge ni" ta faɗa tana kallon Rumana. Rumana ta maimaita drama a zuciyar ta, lallai ma wannan yarinyar nan Manal bata da mutunci, wato ma drama ce ita ba ma kishi take ba. Manal yunƙurin tashi take yi ya tashi da sauri ya ya riƙe ta ya miƙar da ita tsaye ya riƙee hannun ta, Manal ta kalle ta tace, "Ina zuwa yanzu zan dawo" ta faɗa tana fara tafiya shi kuma yana riƙe da ita har cikin ɗaki. Suna shiga ɗakin taga yana kallon ta kamar wanda yayi wani laifi, tsoro ya bayyana  sosai a kan fuska sa, Hakan da ta gani ne ya saka zuciyar ta take rawa akan sa da kuma Rumana, amma bata ce masa komai ba ta share batun kawai ta shiga banɗaki. Wajan Rumana ya dawo a fusace ya kalle ta ya ce, "har cikin gidana, a gaban matata zaki zo kina yi min wannan shirmen tsabar wulaƙanci? Ke baki da hankali ne baki san ya kamata ba?." Rumana ta tashi tsaye tace, "me nayi? Zuwan nawa ne matsala ko kyautar da na kawo maka?." "Zuwan ki gidan nan bani da matsala dashi, amma meyasa lallai sai kin nunawa matata kamar ke wata ce a wajena? Akan me?." Rumana tace, "ni ba wata ɗin bace a wajan ka?." Ya Harare ta ya ce, "wacece ke ɗin to?." Idon ta ya ciko da hawaye tace, "ni ka ke cewa wacece ni?." "Matsayin Kausar kike a wajena, bayan wannan babu wani abu na faɗa miki ba yau ba jiya ba. Ki shiga hankalin ki, ko nan gaba kar ki sake maimaita wannan kuskuren a ko ina. Kar hannun ki ya sake zuwa inda nake, kar ki sake zuwa ki ganni a waje ki zauna a kusa dani, ki tsaya a matsayin ki." Rumana ta kalle shi tace, "har yanzu baka canja ra'ayin ka a kaina ba? Baza ka tausayi min ba duk da ciwon da na samu ta dalilin son da......" ya dakatar da ita  saboda kar Manal ta jiyo ya ce, "ya isa malama! Na faɗa miki kar ki sake wannan kuskuren" yana faɗa yana komawa ɗakin Manal ya tarar ta fito daga banɗakin a lokacin. Ya kalle ta ya ce, "magriba tayi, in mun yi sallar i'sha sai mu fita ko?." "Ta tafi ne?." "A'a tana nan." Manal ta kalli fuskar sa tace, "Sai naga ka canja, lafiya?." Bebi yace, "babu komai." Bata ce komai ba ta fito falon sai ta tarar da Rumana bata nan. Kallon bayan ta tayi ta ganshi ya fito daga ɗakin tace, "kace min tana nan." "Ta tafi kenan." Kallon idanun sa take yi ta matso kusa dashi sosai tana kallon sa tace, "na taɓa tambayar ka meye tsakanin ka da ita kace min ƙanwar kace, tun a lokacin na faɗa maka ba kamar su Mimi take jin kanta ba. Matsayin ta yafi na su Mimi a wajan ka, ba iya ƙanwar ka bace ba. Dan na tabbatar  ko Yaya Farida baza ta yi abinda tayi maka abinda tayi yanzu a gabana ba. Ya maganar take?." Ta fahimci ya ruɗe duk da yana ƙoƙarin dannewa sai ta kawar da kai ta kalli gefe shi kuma ya ce, "babu komai, kawai tana rayuwar turawa ne ita a ganin ta hakan wayewa ce shine kawai." Manal ta sake kallon sa tace, "kenan kowa ma haka take masa kamar yadda tayi maka?." Bebi ya ce, "eh kusan hakan." "Ka tabbatar hakan ne?." "Haka ne mana." "Bana so naji wani abun da ba wannan ba nan gaba." Yayi murmushi ya ce, "babu abinda zaki ji." Bata ce komai ba ta wuce shi ta shiga ɗaki ba dan ta amince da abinda yace mata ba. Bebi ya bita da kallo yana jin wani iri a zuciyar sa,  Allah ya sani yaso ya faɗa gaskiyar lamarin mata amma yanayin da take ciki ne baya son tayar mata da hankali shiyasa ya kawar da maganar, amma nan gaba zai faɗa mata wacece Rumana a wajan sa da kuma alƙawarin da ya ɗauka akan ta. BDƘB3P15 Tafiya suke yi a hankali ta saka slippers kamar yadda aka saba suna tafiya a hankali yadda baza gaji ba. Sun saba suna tafiya tana magana amma yanzu tayi shiru tun daga lokacin da Rumana tazo shikenan walwalar ta ta ragu. Kallon ta yayi cikin hasken layin nasu ya ce, "yau kin yi shiru, bakya bani labarin komai." Ta kalle shi sai ta ɗauke kai tace, "babu labarin ne." Bebi ya ce, "ni na san akwai, kawai yau baki yi niyar bani labarin bane ba, ko akwai abinda yake damun ki ne?." "Babu komai." "Yanzu kin ga kuna lokacin ƙarshe a makaranta, in kika gama me zaki yi?." Manal tace, "Sai abinda Allah ya zaɓa min." "Amma ai kina d abinda yake sanki wanda kike burin Allah ya tabbatar miki." Manal tace, "ni dai na san ina da ra'ayin buɗe bakery da cafe kuma ka sani, daga nan shikenan kawai." "Allah yasa ya kuma cika miki burin ki." Ta amsa da amin y ace, "kuma naga zaki iya sosai." Bata ce komai ba tayi masa shiru tafiya kawai take yi kafin ta tsaya ya kalle ta tace, "bayana naji ya riƙe, ruwa zan sha." "Oh god! Gashi ban ɗauko ruwa ba yau." Manal tace, "muje kawai." "A'a tsaya na koma na ɗauko miki." "A'a bar shi zan iya." Tafiya suka cigaba da yi a hankali har suka je farkon estate ɗin kafin su dawo, daƙyar take tafiya sosai bayan ta ya riƙe ganin baza ta iya ba sai ta samu wani ɗan tudu a ƙofar wani gida ta zauna a kai tace, "na gaji." Da yake yana da ɗan faɗi kaɗan sai ya zauna shima ya ce, "Sannu." Kai ta ɗaga yana kallon fuskar ta, gabaɗaya babu walwala a tare da ita shi kuma ba haka ya saba ganin fuskar ta ba duk ya damu da hakan. Wayar sa ake kira ya ɗauka yana magana kafin ya kashe wayar ta kalle shi tace, "aikin ne?." Ya girgiza kai yace, "akwai wacce aka yiwa aiki shine ta farka, ba sai naje ba zan saka ayi handling case ɗin." Bata ce komai ba ya kira waya yana magana kafin ya sake kashe wayar. "Assalamu alaikum." A tare suka kalli wajan da akayi sallamar Bebi ya amsa yana kallon matar da take tsaye a kan su, Babba ce mai shekaru duk da bai nuna ta ba amma ido ba mudu ba ya san kima, kana ganin ta ka san ta manyanta dan shekarun zata kai sa'ar Mama ko ta girmi Mama. Tayi murmushi tace, "Sannun ku fa, nazo na tsaya a kan ku baku sanni ba. Ku yi haƙuri tambaya nake yi." Bebi yace, "babu komai, Allah yasa mun sani." Ta kalli Manal da take kallon ta tace, "wallahi matar ka ce take min kama da wata wacce na sani, shine nake so na tambaye ta naji ko ta santa?." Bebi yace, "babu komai ki tambaye ta." Ta kalli Manal tace, "sannu daughter, ya jikin?." Manal ta amsa matar tace, "Allah ya raba ku lafiy, ya baki haihuwa mai sauƙi." Ta amsa da amin ta kalle ta tace, "Akwai wata da na sani fuskar ta irin ta ki ce, duk da nasan baza ki san wacce na sani din ba amma duk yadda akayi kamar kina da alaƙa da ita. Don Allah kin taɓa sanin ahlin marigayi Muhammad Jalingo?." Gaban Manal ya faɗi sosai ta kalli Bebi shima ita yake kallo yana jiran yaji abinda zata ce, Manal ta kalli matar bayan ta aro nutsuwa tace, "Muhaammad Jalingo! Gaskiya ban san su ba, ban taɓa jin sunan ba ma sai yanzu da ki ka faɗa min." Ta girgiza kai tace, "kaico! Wataƙila kama ce kawai, amma kin yi kama da ita sosai hakan ya saka nake ji a jikina kina da alaƙa da ita, ki yi haƙuri na ɓata miki lokaci." Bebi zai yi magana Manal ta riƙe masa hannu hakan ya saka ya kalle ta ta kalle shi ta ɗauke kai daga kallon sa tace, "babu komai." Ta yiwa Bebi godiya ta shiga wani babban gida da yake kusa da wanda suke zaune tana sake waiwayen Manal. Manal tashi tayi daƙyar shima ya miƙe ya riƙe ta suka cigaba da tafiya bai mata maganar ba dan so yake sai sun je gida. Ba jimawa suka je gida bata zauna hutawa ba tayi wanka ta saka riga ta fito taci zogalen da ya haɗa kafin su tafi, ta sha ruwan cucumber da Apple da ya zaka kamar ruwan shan ta. Sai da yaga ta dawo hankalin ta sannan ya zauna kusa da ita ya ce, "amma Partner meyasa kika cewa matar can baki san ahlin kakan ki Muhammed Jalingo ba?." Shiru tayi bata yi magana ba hakan ya saka ya ce, "magana nake miki fa kin yi min shiru." Ta kalle shi tace, "Mama bata bani damar hakan ba, umarnin ta nake jira in ta bani dama zan yi magana. Kuma meye ma amfanin maganar? Mutanen da suka aurar da mahaifiyata ga wanda basu sani ba, kuma suka bashi ita ya tafi da ita duk inda yake so alamun yaje da ita su basa da buƙatar zaman ta. Me zai saka ma in na gansu nace ni ahlin su ce? Yadda suka zare Mamana daga cikin su babu amfanin faɗa musu, koda dukkan su zan gani wallahi bazan nuna na san su ba" ta faɗa tana kallon wani wajan daban. "Ƙaddarar zuwan ki duniya, ƙaddarar abinda yake cikin ki shine ya saka duk abubuwan nan da kika faɗa suka faru. In hakan bai faru ba da yanzu wataƙila bakya duniya, Allah yayi nufin halittar ki shiyasa hakan ta kasance." Taɓe baki tayi alamun maganar bata wani ratsa ta ba ta cigaba da kallon tv zuciyar ta na zafi in ta tuna riƙe hannun sa da Rumana tayi. Azurfar da Rumana ta bashi ta kalla taga tana inda ya ajjiye bai ɗauke ba tace, "baka son kyautar buduwar taka ne ka bar ta a wajan?." Kallon abinda take kalla yayi ya kalle ta ya ce, "Partner wacece budurwa ta kuma?." Ta kalle shi tace, "Ka fini sani ai." Ƙoƙarin tashi take ya riƙe hannun ta ya ce, "wai daman akan ta ki ke wannan fushin Partner?." Ta kalle ta tace, "akan me zan yi fushi bayan tare na gan ku? Ƴar uwar kace kuma wacce ta kasance ta musamman a wajan ka, meye na Manal da aka auro daga gefe ita da ba ƴar uwa ta musamman ba?. Akan me zan yi fushi da wacce na gan ku tare? Ƙanwar ka ce fa." "Partner!" Ya faɗa yana amtsowa kusa da ita sosai yana kallon ta tare da riƙe hannun ta yace, "meye na wannan maganar? Ko ya mahimmacin ta yake ai bata kai ki ba ko?." "Anya kuwa, ko bata kai ni ɗin ba tana gab da zuwa ta wuce ni." "Haba Manal, kokwanto ki ke a kaina?." "Zahiri na gani." "A duniya Mummy kawai za'a cire sai ke, duk wata mace a duniya bayan ki zata biyo ko ya muke da ita." Manal ta ɗauke kai daga kallon sa ya ce, "ban saba da wannan fuskar taki ba, kin saba da fuskar walwala da murmushi don Allah ki cire wannan ki saka waccan ta fi yi miki kyau." "Ka kasa faɗa min meye alaƙar ka da ita ne." "Ai na faɗa miki wacece ita a wajena." "Ban yarda ba, gwara ma ka san wallahi ban yarda ba na jika ne kawai." Yayi shiru yana kallon ta tace, "har gidana, har cikin falona tazo tana riƙe hannun mijina kuma ace min babu komai a tsakani?, daga yadda ka yi mata magana nuni yake da ta saba yi maka. Tun a gidan Mummy na tabbatar da akwai wani abun a ƙasa, saboda kallon da take maka da yanayin da take maka magana daban da na ƴan uwan ka, yadda take kallon idon ka tana magana ko ni bana yi. Kuma kawai sai kace min babu komai a tsakanin ku ƙanwar kace kawai na yarda? Meyasa Mimi, Lubna, Kausar duk basa yi sai ita?." Ganin ta fara fusata tana magana cikin faɗa sai shi ya sauka dan ya san laifin sa ne da ya faɗa mata tun farko da ba haka ba. ya ce, "ki kwantar da hankalin ki, faɗan nan ne bana so saboda yanayin da kike ciki." Ta kawar da kai gefe fuskar nan a daure soaai bata ce komai ba. Ya ce, "yanzu ya ki ke so nayi miki? Na faɗa miki abinda yake gaskiya amma kin ƙi yarda, to ƙarya zan faɗa miki?." Ta kalle shi tace, "ƙaryar ka faɗa ka ɓoye gaskiyar, a kan fuskar ka ga hakan nan ya bayyana. Wallahi ban yarda babu komai tsakanin ka da Rumana ba, Akwai abinda ka ke ɓoye min wanda baka so na sani." "Partner ni nake miki ƙarya?." "Ban ce kayi ƙarya ba, nace kawai ƙaryar ka faɗa ka ɓoye gaskiyar. In baza ka faɗa min ba shikenan a bar shi kawai ba sai naji ba" ta faɗa tana sake yunƙurawa da niyar tashi. Komawa tayi ta zauna saboda ciwon da taji ya riƙe mata baya ga marar ta na riƙewa. "Me kike ji? Lafiya dai?" Ya faɗa yana kallon ta. Ta kalle shi tace, "babu komai." Shiru yayi ya sauke numfashi yana son faɗa mata gaskiya amma tashin hankali ne baya so ta shiga Allah ya sani, hakan ya saka ya ce, "zan faɗa miki ko meye ma yake faruwa akan ta amma sai kin haihu." Ta tashi da ƙarfin hali tace, "ka riƙe abinda ka kawai ba sai na ji ba, ai ni ganau ce ba jiyau ba" ta faɗa tana shiga ɗaki ta bar shi a wajan a zaune. Numfashi ya sauke bai tashi ya bita ba dan yasan baza ta saurare shi ba, yayi shiru yana kallon tv domin kuwa yana tunanin lokacin da Mama zata dawo da maganar da ta wuce. Ranar haka ta kwana sai shi ya bita ɗakin ya kwanta dan bata sake fitowa ba kuma bata ce masa komai ba, duk da yana yi mata magana akai akai amma taƙi bashi amsa dole ya ƙyale ta duk da taso fusata shi haƙuri yayi ya danne. Bayan kwana biyu da zuwan Rumana gidan cikin dare Manal ta fara naƙuda, babu ɓata lokacin ya ɗauke ta suka tafi asibiti aka karɓe ta da gaggawa dan haihuwar tazo sosai. Allah ya taimake ta bata yi doguwar naƙuda ba tana shiga labour room ɗin Allah ya sauke ta lafiya ta haifi ɗan tanamiji, babu wanda ya faɗawa haihuwar saboda dare ne lokacin, sai bayan ta haihu lafiya lau ya jira akayi sallah gari ya waye sosai sannan ya kira Mummy ya faɗa mata ya faɗawa Mamy ma, ya dauƙi wayar Manal ɗin ya ɗauki number Mubeena ya faɗa mata. Ɗakin da take hutawa ya koma ya tarar ta tashi daga baccin tana kwance ta riƙe kai da hannun ta ya ƙaraso yana kallon ta ya ce, "Sannu Partner, kan ki ne yake ciwo?." Kai ta ɗaga alamun eh ya ce, "ko jinin ki yayi ƙasa? Bara mu duba" ya faɗa yana fita ba jimawa ya dawo da abin auna jini ya gwada jinin ta anan yaga abinda yake tunani sai ya sake saka mata sabon ruwa. Kallon ta yake bayan ya saka ruwan idon ta a lumshe kafin yayi magana tace, "bazan sake haihuwa ba yanzu, ni sai nan da shekara biyar." Dariya ce ta kama shi dan kuwa an sha raki kala-kala ko yace an sha ihu, duk da tayi ƙoƙari sosai ta daure abinda zata iya daurewa.  Cikin son ya tsokanar ta ya ce, "ni da ina tunanin nan da shekara ɗaya kin dawo." Da sauri ta buɗe ido tace, "wallahi ba dai ni ba" ta faɗa zata masa kuka yace, "yi haƙuri kin ga ba lafiya ce dake ba." Kallon gadon Bebin tayi ta gashi a kwance a ciki yana ta motsa hannu da alama ma idanun sa biyu, kallon Bebi tayi yace, "naso kin shayar dashi kafin mintina talatin da haihuwar ki, hakan zai ƙara masa lafiya ya kuma kare shi daga cututtuka manya da ƙanana. Amma hakan bai yu ba saboda ciwon kan nan, sannu partner, kin yi ƙoƙarin haifo mana shi, Allah ya miki albarka" ya faɗa yana shafa kanta ta tare da yin kiss a goshin. Tayi murmushi ta amsa da amin tace, "ka ɗauko min shi." Ya ɗauko mata ya kawo mata shi ta ɗan tashi zaune tana riƙe dashi tana kallon sa. Fari ne shima sosai kamar ta, ta kalli Bebi tace, "da wa yake kama?." "Dake mana, ai yadda kika sha wahalar nan dole ma yayi kama dake." Tayi murmushi tana kallon sa soyayar sa na ratsa zuciyar ta tana shiga ko ina na jinin ta, bata taɓa jin abinda yake shiga zuciyar ta lokaci ɗaya ba kamar sa. Sunkuyowa yayi yana kallon ɗan shima kafin ya kalle ta yace, "Dake yake kama fa babu zancen wasa."  Manal tace, "ni da Mamana naga suna kama." Yayi murmushi yace, "zaki hango ki ɗin ma tunda kin gano Mama." Buɗe ƙofar akayi tare da shigowa da sallama hakan ya saka shi miƙewa tsaye sosao yana kallon wanda suka shigo. Huzaifa ne da Hamza baki har kunne suna murmushi Huzaifa ya ce, "ashe haka akayi shine ko labari? Gaskiya Bebi kaci amanar mu." Hamza yace, "Sannu Manal, Allah ya ƙara lafiya ya raya abinda aka samu." "Amin Dr, na gode sosai." Huzaifa ya kalle ta yace, "Sannu Manal, Allah ya raya mana shi ya masa albarka." Tayi murmushi tace, "Amin Yaya Huzaifa na gode" ta faɗa ta bawa Bebi yaron ta koma ta kwanta saboda baccin da taji yana sake dawowa. Bebi ya bawa Hamza shi suna ta yabawa ganin ta fara lumshe ido alamun bacci sai ya ce, "muje waje bacci zata yi, jinin ta yayi ƙasa." Ta buɗe ido tace, "Partner waje akwai sanyi kar yayi mura." Huzaifa yayi dariya ya ce, "da gaskiyar ki Manal in muka fita dashi mura zai yi." Bebi yayi dariya shima yace, "kar ki damu zan kular miki dashi." Jin hakan sai ta kulle ido suka fita daga ɗakin. Zuwa wani lokaci kaɗan Mubeena da Maman Surayya da Surayyan sun zo, sune zaune a ɗakin da yaron a hannun su ana ta yaba shi, ma'aikatan asibitin suna ta zuwa ganin yaron ana taya su murna har lokacin Manal bacci take yi sosai. Basu jima ba Mama da Mummy da Maryam ma suka zo asibitin suka zauna tafredasu Mama ɗin ana taɓa hira kaɗan-kaɗan. Manal sai sha ɗaya na safe ta buɗe ido, idanun ta na buɗewa kukan jaririn ne ya fara ratsa kunnen ta, ta tashi zaune tana kallon su Surayya tace, "Sannu Milky." Ta amsa tare da faɗin, "Mummy ina kwana." Mummy ta amsa tana yi mata barka suka gaisa da Mamy ma da Maman Surayya kafin Maman Surayya tace, "ai ki karɓe shi tun ɗazu yake kuka yunwa yaje ji. Surayya bata shi." Gaban Manal ya faɗo lokacim da aka bata taron a hannu, wai yanzu a gaban şu zata kwaye riga ta bawa yaro nono duk suna gani? Ga Mummy ma a zaune a gaban ta zata ɗaga rigar ta sama ta bashi nono? Taɓ ashe bazai sha ba kuwa. Mummy tace, "ai Hajiya Balaraba sai kin koya mata, ina Manal zata iya shayar dashi yanzu?." Maman Surayya ta tashi ta ƙarasa inda Manal take Manal tace, "Mama ni kunyar su Mummy nake bazan iya shayar dashi ba." Mama tace, "to meye na kunya? Bana son shirme Manal ki bashi ya sha yunwa yake ji ko na aika kira mijin ki." Zip ɗin ta buɗe daga baya amma ta kasa yin abinda ya kamata. Maman Surayya tace, , "baza ki ciro ki bashi bane ba wai yaro yana kuka?." Manal ta sauke numfashi ita bata san taya zata fara bane wallahi. Manal harda ƙwalla ta tana so tayi amma ta kasa dan da gaske kunyar take ji ba wai da wasa ba. Ta kalli Mama tace, "don Allah Mama ki bani mayafin ki na yafa sai na bashi." Mama tace, "akan me zan bari ki rufe shi sai kin tosshe masa hanci?." "Allah bazan toshe ba." Mama tayi tsaki ta kalli Surayya tace, "bani mayafinki, wai kunya take ji ita baza'a ga nonon ta ba." Mummy tayi dariya Mamy ma haka Mummy tace, "da gaskiyar ta, mu sai mu bata waje ma tafi sakewa." Mama Surayya tace, "don Allah ku yi zaman ku, shirme ne irin na Manal." Mummy tace, "A'a bara mu koma waje tafi samun nutsuwa." Mama tace, "to mu ma sai mu biyo ku in yaso sai a turo mijin ta sai ya taya ta tunda shi wataƙila baza ta ji kunyar sa ba." Mamy tayi dariya tace, "A'a dai ki yi haƙuri ki zauna" ta faɗa suna fita. Manal ta kalli Mama tace, "Mama yanzu fa har yaro ina dashi kice ina shirme?, haihuwa nayi fa kuma haihuwar da wahala." Jin yadda tayi maganar cikin shagwaɓa Maman Surayya tace, "Sai na bufe miki baki, dallah malama ki shayar dashi ko na ciro da kaina na bashi wallahi." "Yi haƙuri" Manal ta faɗa tana yafa mayafin ta ciro guɗa ɗaya Mama ta nuna mata yadda zata yi tana cewa, "ki daure zaki ji zafi amma zaki daina." Da to manal ta amsa da ya fara sha harda kuka wai zafi, Sai da taga Maman Surayya na yi mata faɗa sosai sannan ta daina kukan sai hawaye.  Ya jima yana sha kafin ta karɓe shi Mubeena ta karɓa a hannun Maman tana yi masa hotuna dan yaron ya burge ta sosai. Wajan su Mummy Mama ta fito ta bar Surayya da Mubeena a can ana ta zuwa sai dai a shiga wajan Manal ɗin. Lokacin da Bebi ya shiga ita kaɗai ya samu a ɗakin duk suna waje a zaune har yaron yana wajan su, ya zauna a gefen ta ya ce, "ya ciwon kan? Ya naga kamar kin yi kuka meya faru?." "Ba Mama bace ta dage sai na shayar dashi, kuma wallahi zafi nake ji." Yayi murmushi ya ce, "yanzu ɗan zafin da kika ji shine na kuka? Partner yanzu fa ke uwa ce ki tuna mana." "Allah da zafi, ni kaɗai na san abinda naji." "To shikenan yi haƙuri zaki daina ji in sha Allah." Ta ɗaga kai ya ce, "an masa test komai nasa lafiya lau yake." Tayi murmushi tana kallon sa ya ce, "amma yadda kika dage wajan ƙauracewa zaƙi da cikin sa haka za'a sake maimaitawa Partner." Manal tace, "zan yi ko dan shi" ta fada tana kwanciya a jikin sa tace, "yana hannun waye da ka shigo yanzu?." "Yana hannun Surayya." "Kar fa Surayya taje ta ƴar min dashi, wallahi ba wani iya riƙe shi tayi sosai ba." Ya kalle ta yaga harda turo baki ya ce, "ta ya zata ƴar dashi?." "To ta san zafin haihuwar ne? Ni fa na shiga labour room ba ita ba." Yayi dariya sosai yace, "ƙwarai kuwa kece, amma duk da haka baza ta yar miki dashi ba." Tayi shiru yayi dariya ya rungume ta ya ce, "kina ji dashi ko? Nima ina jin sa har zuciyata kusa inda ki ke a zuciyata, ji nake kamar na karɓo shi na dinga kallon sa kawai. Ina son ki Manal kin mayar dani uba a yau." Tayi murmushi ya sake ta  yana kallon ta ya ce, "in kin warware zamu wuce gida." Manal tace, "gidan Mama?." Ƙwanƙwansa ƙofar akayi sai ya tashi daga kusa da Manal ya ce, "a shigo." Maman Surayya ce ta shigo tace, "zan ɗauki wayata ne." Yayi murmushi ya ce, "Mama ma gwara da kika shigo, zamu tafi gida da ita yanzu ya zaa yi?." Mama tace, "au ba gida zata tafi ba kenan?." Ya girgiza kai ya ce, "Nafi so ta zauna a gidan ta gaskiya." Mama tace, "wannan ai ba damuwa, daman mun yi magana da Maman ta ka kan hakan, babu damuwa ni da kaina zan zo na zauna da ita." Ya ce, "kai amma naji daɗi soaai, Allah ya saka da alkhairi" ta amsa da amin ta fita ya kalli Manal yace, "ga Maman Surayya zata zauna dake." "Ni nafi son tafiya gida Allah." "Sai ki yi haƙuri, ai na faɗa miki daman bana son zaman gidan nan bayan ina da ina baƙi zasu zauna" ya faɗa yana fita ya barta. Ba jimawa suka tafi gida Maman Surayya ta wuce gida da niyar haɗa kayan ta na kwana, su kuma suka wuce gida saboda Abba yaga yaron. BDƘB3P16 Gidan Maman suka fara zuwa a kai mata yaron dan ta ganshi, Surayya ne da Mubeena a bayan motar yaron yana hannun Mubeena tace, "Manal ba sai kin fito ba bara ba kaina Maman saina dawo dashi." Surayya tace, "gaskiya dai ki zaman ki Milky, mu je Yaya Mubeena" suka buɗe motar suka fita. Bebi ya kalle ta bayan sun fita ya ce, "sannu." Ta kalle shi ta daga kai ta mayar da ido ta kulle. Hannun ta har lokacin da flasta ya riƙe hannun nata ta sake kallon sa tace, "hannun ka sanyi." "Me yake damun ki yanzu?." "Ni komai ma damuna yake." Ya girgiza kai yace, "Sai a hankali." Da Mubeena ta shiga da yaron Baba yana nan shi ta fara bawa ya karɓa yana yi masa addu'a yana cewa, "in da rai akwai rabo, hausawa suna cewa in da rai da rabo watarana jariri ango ne, yau ga ɗan da Manal ta haifa ne a hannuna, Allah mun gode maka." Mama murmushi take ya bata ɗan tana kallo tace, "ai wannan yaron babu ta inda ya bar Manal." Baba yace, "nima abinda na gani kenan, kama suke da ita kam sosai ma." Ganin Surayya bata wajan sai Mubeena tace, "Mama wai Maman Surayya ce zata zauna da Manal?." Mama tace, "itace Mubeena." Mubeena tace, "kuma babu takura? Ni Sai naga kamar zata takura." Mama tace, "babu yadda ban yi ba amma tace Manal ƴarta ce zata je har gida ta zauna da ita, ni cewa nayi ta dawo gida ma tace a'a mazan yanzu basa so zuwa wankan gidan na saai dai dole, tunda tana da yalwataccen wajen da za'a zauna gwara aje can ɗin. To kar na dage akan maganar taga kamar wani abun shiyasa na amince. Kuma daman Manal ta faɗa min baya so tazo gida, kuma Baban su Surayyan kinga yayi tafiya kuma ya kan yi sati uku zuwa huɗu baya nan." Baba yac e, "gwara da kika amince, Balaraba ai ba ƙashin yar wa bace ba. Kuma tunda tace zata je ai ba wani abun bane tunda Adnan ɗin baya so yazo zaman gida." Mubeena tace, "Mama bani shi na kai musu suna mota." Mama ta miƙa mata shi tace, "kice ina mata sannu, shi kuma Adnan ɗin kice ina yi masa barka." Mubeena ta amsa ta fita ta ƙarasa inda suke ta buɗe gaban motar ta bawa Manal yaron ta kalli Adnan tace, "Mama tace nace maka tana yi maka barka da samun ƙaruwa, Ke kuma tace tana yi miki sannu Allah ya ƙara lafiya, tace nace miki ta san ke raguwa ce babu abinda kika iya sai rakin tsiya." Manal tace, "Mama baza tace min haka ba, wannan faɗar ki ce kawai." Mubeena tayi dariya tace, "Sai nazo Maman baby boy" ta faɗa tana kulle mata motar ta juya ta shiga gida.  Manal kuwa ta rufe ɗan da mayafi tana cewa, "Rana tana damun shi." Murmushi yake ya ja motar suka tafi zuwa gidan su. A harabar gidan su ya faka motar Kausar na ganin şu ta taho a guje ta buɗe gaban motar ta karɓi yaron a hannun Manal tayi cikin gidan da sauri. Ya kalle ta ya ce, "ki yi zaman ki zan kaiwa Abba shi." Manal tace, "kuma nazo sai na zauna a mota?." "Eh haka nace." Kai ta ɗaga kawai ya wuce zuwa cikin gidan. Basu jima sosai ba suka dawo ya shiga motar Kausar ta bata yaron tana cewa, "Sis meye sunan da zamu dinga faɗa masa?." Manal tace, "sai kin zo zan faɗa miki." Tace, "ai kam zan zo an jima kaɗan." Manal tace, "ƙarya." Kausar tayi dariya tana cewa, "wallahi zan zo in sha Allah." Manal ta amsa da Allah ya kawo ki ta rufe motar suka tafi. Da suka je gida shi ya karɓi yaron ya shiga dashi gida ya kwantae dashi a kan kujera ya dawo ya riƙe ta suka shiga ciki. tana shiga falon ta kalli inda ya ajjiye yaron tace, "kai partner a kan kujera ka ajjiye min shi?, in ya faɗo fa?. Dan baka san zafin haihuwa ba sai ka bar min yaro a nan?" Ta faɗa tana ƙarasawa ta zauna tare da ɗaukar sa. Shi dariya take bashi in yaga tana ji yaron, ya lura so zata yiwa yaron ba na wasa ba dan gashi ya fara ganin alamu hakan.  ya ce, "Allah ya baki haƙuri wacce ta san zafin haihuwa, amma ina so na tuna miki ɗan Adnan ne." "Eh na sani, amma rabin sa ne naka ba duka ba, dan ba kai ka shiga labour room ba. Kai other room ka iya shiga" ta ƙarasa faɗa ƙasa-ƙasa. Yayi dariya ya ce, "ai na ji ki, wato ni other room na iya shiga ko?, to ai kinga an raba, ke kin shiga labour ni na shiga other room." "Amma ai a labour room wahala ake sha ga azaba wacce ta wuce misali, can kuwa fa?." Idon ta yake kallo ya ce, "can kuwa me ake ji? Shi nufin ki ba'a shan wahalar?." Ta ɗauke kai tana murmushi ya ce, "ki faɗa mana, an faɗa miki samar da cikin sauƙi ne dashi?." Kallon sa tayi tana taɓe baki tana ɗage gira alamun bata yarda ba sai tayi murmushi tace, "wanka nake so nayi." Shima yai dariya ya ce, "okay jira na dawo" ya faɗa yana shiga ciki ba jimawa ya dawo yace, "kawo shi na kai ɗaki tunda kinga yayi bacci, ga baby bed ɗin shi can ma na haɗa miki" ta miƙa masa shi ya karɓe shi tace, "ko iya riƙe shi baka yi ba, nidai ka bi a hankali kar ka ƴar min da ɗana." "To mai ɗa" ya faɗa yana dariya ya shiga dashi ya kwantar dashi tare da yi masa kiss a goshi, shi kansa ƙaunar yaron yake ba kaɗan ba amma ya lura in bai yi da gaske ba Manal zata danne tasa ƙaunar. A hanya suka haɗu tana takowa a hankali yace, "Yauwa ki dinga daurewa hakan shine zai saka ɗinkin ya warke da wuri." "Kawai a ɗinke mutum kamar wata ƙwarya, ni ba sai a barni haka ba." "A barki haka? Kin ƙaru fa." "Eh zan ragu ne." Yayi murmushi yana biye da ita har banɗakin. Tana shiga banɗakin saka hannun ta acikin ruwan tace, "ai babu zafi sosai." "Eh babu ke babu ruwa mai zafi sosai ɗin na ai har sai kin warke." Manal bata ce komai ba ya ce, "kafin zuwan Maman Surayya da kaina nake so nayi miki wankan saboda na kula da stitches ɗin sosai." Manal ta kalle shi tace, "Sai tazo taga ka fito daga banɗakin?." "To akwai aibu ne?" Ya faɗa yana fara cire mata rigar jikin ta tace, "don Allah ka bari nayi da kaina" ta faɗa tana zama a gefen bathtub ɗin daƙyar. Ya girgiza kai yace, "da kaina zan miki kawai ki tsaya." Babu yadda zata yo haka ya mata wanka tas yana yi yana gasa nata jikin ta dan shi tazsan ta wahala wajan labour shiyasa yake tauyasa mata. Sai da ta gama ta ɗaura towel ya riƙe ta suka fito ta zauna a gefen gado ya ɗauko mai ya shafa mata ya ɗauko kaya ya ajjiye a gefen ta, fita yayi ba jimawa sai gashi da trolly ɗin da aka je asibiti da ita  ya buɗe ya ɗauko pad ɗin ta ya kawo mataya ajjiye, ya koma ya ɗauko undies ya ajjiye. Kallon ta yake yi ya ce, "na shirya ki?." Tayi murmushi tana kallon sa tace, "zan shirya kaina." "Okay Madam" ya faɗa tana mata kiss a goshi tare da jan hancin ta yana murmushi itama tana yi. Kallon sa take yi tana murmushi tace, "Bacci ka ke ji ko?." "Sosai ma kuwa, wanka zanyi yanzu nayi sallah sai nayi bacci." "Ya kamata, ka gaji da yawa." "Duk gajiyata ban kai ki ba, kin yi ƙoƙari sosai na tabbatar da ke ɗin jarumar mata ce." Tayi murmushi tana kallon sa yana daga tsaye yana kallon ta tace, "kaje kayi sallar." Ya ɗaga mata kai ya fita ita kuma ta fara shiryawa zuciyar ta cike da farin ciki. Tsab ta shirya cikin riga da siket kamar ba ita ce ta haihu ba, ta ƙarasa wajan Baby bed ɗin ta jawo shi da yake yana da taya ya a ƙasa biyo ta tazo dashi har wajan gadon ta zauna tana kallon yaron da yake bacci. A gefen ta taga wayar ta dan tasan shine ya ajjiye ita ina taga tunanin waya lokacin da suka bar gidan, ɗaukar wayar tayi tana yi masa hotuna masu kyau tana kallo tana murmushi. Ya ɗan jima kafin ya shigo yana cewa, "Maman bata ƙaraso ba?." Ta kalle shi tace, "bata zo ba, kasan sai ta gama da komai na gida sannan zata taho. Sun barni ni kaɗai kamar mara gata, bayan in an haihu cika gida ake ana yiwa mai jego sannu. Ai ko Yaya da Surayya ne yaci ace sun biyo ni." Yayi murmushi yace, "to ai baki yi kama da wacce ta haihu ba Manal, ni kaina mamaki nake yi. Amma nasan addu'ar da na dinga yi miki ce tayi tasiri, kullum fatana Allah ya raba ki da cikin nan lafiya gashi Allah ya amsa." Tayi murmushi itama ya zauna kusa da ita yana kallon ta ya ɗauko yaron ya riƙe shi ya kalle ta ya ce, "kin san ya sunan shi?." "Ba kace min sunan Abba ba?." Ya girgiza kai ya ce, "sunan sa Ibrahim Mu'azzam. Wanne suna zaki dinga faɗa masa?." Manal ta kalli yaron tace, "Ayan." Ya haɗa goshin su waje ɗaya da nata ya ce, "Allah ya raya mana shi, Allah ya yi masa albarka." "Amin Partner." "Kamar wasa wai ɗan mu ne nida ke ko?." Manal tayi murmushi tace, "abun kamar a mafarki." Ya yiwa bakin ta kiss ya ce, "ba mafarki bane, da gaske ni da ke iyaye ne yanzu" ya faɗa yana riƙe hannun ta yana kallon ta. Ta kwanta a kafaɗarsa ya sake cwwa, "na gode da kika mayar dani uba Manal." Tayi murmushi tace, "nima na gode da ka mayar dani uwa, yanzu na tashi daga Manal na dawo Ammin Ayan." Yayi murmushi ya ce, "gaskiya ne wannan Partner, bakya jin yunwa?." "Bana ji ai naci abinci, amma nasan kai kana ji ko?." "Ina ji, amma bazan ci ba sai na tashi daga bacci." Ya sake cewa, "zan kulle babbar ƙofar farko da ta tsakiya, zan bɗe ta falon tsakiya a dinga shigowa ta nan. In ina can babu wanda ya san ina nan." Manal tace, "yadda ka yi Daddyn Ayan." Ya girgiza kai yace, "A'a kar mu zo nan, kira ni da partner bana son wannan Daddy ko Abban wane ɗin nan." Tayi dariya sai kuma ta tsaya da dariyar tana yatsine fuksa tace, "Wayyo, daman in aka yi dariya sosai zafi ake ji?." "Ayya sorry, ai ba'a dariya mai yawa, tari ko attishawa duk sai kin ji a jikin ki. Amma da ya fara warkewa shikenan, kedai ki lallaɓa ya warke in ba haka ba sabon stitches yafi haihuwar wahala." Manal tace, "Allah ya tsare ni." Yayi murmushi ya amsa. Wayar ta aka jira ganin Maman Surayya ce sai ya fita ya same su a babban falo ya raka ta har ɗakin Manal ɗin shi kuma ya shiga ɗakin sa ya kwanta dan ya huta. Ana ta zuwa barkar haihuwa Manal suna tare da Mama duk abinda bata sani ba tana faɗa mata cikin kwana uku ta fara jin sauƙin ciwon ɗinkin dan Mama na kula da ita sosai. Duk yan gidan su babu wanda bai zo ba da matan yayyen sa kowa yazo har da kaya aka dinga kawo mata na barkar samun Ayan. Har daga gidan su Bebi sai da aka kawo kayan haihuwa ita dai nata ido sai bayan an tafi Mama sai tace ai haka ake yi. Matar Huzaifa da matar Hamza ranar da suka zo wuni suka yi har dare kafin su tafi gida, ai kam taji daɗi sosai sun yi hira kuma sun sake sabawaa da juna kamar mazajen su. Ranar suna da yake ba'a yi taro Manal tace bata so kai baza nace ma ranar suna ba, sai na gida kawai ƙannen sa da kuma sunMubeena kawai. Manal tayi kwalliya har lalle anyi mata, suka ɗauko mai hoto yazo gidan ya yi musu hotuna ita dashi masu kyau sosai. Ranar saurayi Mubeena ma yazo barka har da kayan barkar sa bayan ya tafi Manal ta dinga tsokanar Mubeena kamar ba yayar ta ba. Manal na samun kula a wajan Mama sosai ta ko wanne ɓangare, gashi jegon ya karɓe ta tayi kiɓa duk da ba sosai ba amma da ka ganta ka san ta canja, Ayan ɗin ma yayi kiɓa abin sa kowa ya ganshi sai ya yaba saboda kyau. Kamar sa ta fito soaai kama ɗaya sak da Manal har hasken irin nata ne dogon hancin ne kawai na baban sa da tsaho. Ranar da suka cika sati biyu Manal tana zaune ita kaɗai a ɗakin ta da yamma Bebi ya shigo da sallama ta amsa tana kallon sa ya ƙaraso ya zauna kusa da ita ya ce, "Partner nayi kewar ki, rabon da mu zauna haka ni dake ma na manta." Ya ɗauki Ayan a gadom sa ya dawo ya zauna ya ce, "Sai kallona ki ke yi, ke ba tani ma kike ba, kyau kawai kike yi abin ki." Manal tayi dariya tace, "ni na isa nace bana ta kai? Allah nayi kewar ka nima sosai." Ya Harare ta yace, "ba wani nan, inda kin yi kewata bazan gan ki haka ba." Ta shagwaɓe fuska tace, "Allah nayi kewar ka sosai." Ya ajjiye Ayan ɗin a kan gadon ya kalle ta sosai yace, "to nuna min na gani." Ta saka hannu biyu ta riƙe fuskar sa sai ya ɗaga mata gira tayi dariya ta rufe fuskar ta da hannun ta, Bebi ya ce, "My Partner, kunyar nan tana miki kyau." Ta matso sosai kusa dashi ta shiga jikin sa ya rungume ta harda sauke ajiyar zuciya ya ce, "yaushe rabon da na jiki a jikina? Gaskiya nayi kewar ki my love" ya faɗa yana sake riƙe ta sosai itama ta riƙe shi dan tayi kewar sa tunda ta riga da ta saba ko yaushe tana jikin sa. Ya mata kiss a goshi ya ce, "Yaushe zamu kwana nida ke a haka? Ina kunyar Maman Surayya ne da Allah yau tare zamu kwana."  Manal tana ɗago daga jikin sa tace, "na fahimci kana kunyar ta sosai, ko zama baka iyawa in tana nan. Itama kuma kunyar taka take ji." Yayi murmushi ya ɗago ta daga jikin sa ya ce, "nima na kula hakan, tsoran tsoro muke yi ni da ita." Ta girgiza masa kai alamun eh yace, "Allah sarki! Ai tayi ƙoƙari soaai, ta baro gidan ta da yaran ta ta taho nan kawai saboda ta kular min dake, gashi kin yi kyau har ƙiba ma kin yi kamar baki da ciwon sugar, Me ya kamata mu yi mata in lokacin tafiyar ta ya kusa?." Manal tace, "Ai Mama tana sona tun ina yarinya in ji Mama, da yake ni age mate ɗim Surayya ce komai a gidan su nake yi har makaranta tare muke zuwa." "Faɗi abinda kike so mu yi mata." "Abinda kace shine daidai." Ya sauke ajiyar zuciya yayi shiru kafin yace, "kafin lokacin zamu san abinda zamu yi in sha Allah. In anjima da daddare zamu je asibiti akwai likitan da zata duba min ɗinkin jikin ki." Manal tace, "to Allah ya kai mu, ai na warke ma fa gabaɗaya na daina jin sa." Ya amsa da amin yana Kallon bakin ta. Sai ta rufe bakin ta da hannun ta ganin hakan sai ya mayar da fuska kalar tausayi yace, "ni ko? Ni ko? Shikenan na gode." Manal tayi dariya ta ɗauki Ayan a cinyar sa ta kwantar dashi a gefe, ta juyo da fuskar sa ta ɗora bakin ta akan nasa, abinda yake jira kenan nan da nan yayi accepting. Sun fara mantawa da inda suke kissing ɗin ta romantically itama kum haka, dukkan su sun yi kewar junan su yanayin su zai gwada haka saboda yadda suka riƙe juna kamar za'a ƙwance ɗaya a cikin su. Buɗe ƙofar kawai suka ji anyi a tare suka kalli wajan suka haɗa ido da Rumana da take tsaye kamar zata haɗɗiye zuciya ta mutu, ganin Rumana ce sai kawai yayi tsaki ya sake juyo da fuskar Manal ya sake mayar da bakin sa cikin nata. Da sauri Manal tayi baya ta ta raba kanta daga gare shi ta  sake kallon Rumana da har lokacin tana kallon su cikin kallon da yake nuna zallan kishin da yake addabar zuciyar ta. Muryar Mummy suka ji tana cewa, "tsayuwar me kike yi? Manal ɗin bata nan ne?." Jin kamar tawowar Mama sai Bebi ya miƙe tsaye Manal ɗin ma haka ta ɗauki ɗankwalin ta ta ɗaura. A  lokacin Mama ta shigo ganin suna tsaye cirko-cirko ta kalli Rumana ta sake kallon su sai tace, "Manal ki fito mu gaisa" ta faɗa tana barin wajan dan bata san Bebi yana ciki ba da baza ta kai kanta wajan ba, ganin motar sa bata nan bata ɗauka yana gidan ba. Manal ta dauƙo Ayan tazo ta wuce Rumana da take tsaye har lokacin kamar an dasa ta, Sai da Bebi ya fito ya wuce ta sannan ta iya takowa ta zauna akan kujera ta dafe kanta. Ganin Ammi sai ya ɗan yi murmushi Ammi tace, "ashe kana nan, mu da muka ga motar ka bata nan mun ɗauka kana asibiti ai." Bebi shi kansa kunyar su yake ji duk da basu suka gan shi ba amma ba daɗi. yace, "motar na bayar a kai Maman Surayya gida shiyasa. Mummy barka da rana." Mummy ta amsa tana sake kallon yaron tace, "Sumayya na faɗa miki yaron kamar Ɓaman sa, ma sha Allah akwai haske." "Ammi barka da rana." "Barka dai Bebi, ga Ayan ma sha Allah yayi kyau." Manal ma ta gaishe su suka gaisa da fara'a kafin ta kalli Mummy tace, "Mummy ban san zaki zo ba ai da na shiryawa zuwan ku, zuwan ki gidan nan na biyu kenan." Mama tayi dariya tace, "To Manal ai zuwan sai ya kama ake yin sa." Tayi murmushi ta tashi ta kawo musu ruwa da lemo da apple wacce bata rabuwa da ita. Ammi tace, "ki zaman ki Manal hakan ma mun gode." Tayi murmushi tana zaune cikin jin nauyin su. Bebi fita yayi daga falon Rumana tunda ta dafe kai bata ɗago ba, daman hanya ce ta biyo dasu Ammi tace su shigo suga yaro dan haka basu jima ba suka tafi Manal har bakin motar ta raka su driver yaja suka tafi har lokacin Rumana babu abinda tace yanayin ta gabaɗaya ya canja. Rumana suna komawa gidan Mummy ta shiga ɗakin Mummy a guje Ammi ta bita da kallo ta kalli Mama tace, "Wai ke yarinyar nan take nufi ne?." Mama tace, "na fahimci akwai wani abun tun zuwan mu gidan." "To Mama kishi take da matar sa kenan?." Mama ta  ɗaga mata hannu ta bi bayan sa ta samu tana wani irin kukan da ya bawa Mama tsoro, da sauri ta ƙarasa kusa da ita tace, "Rumana lafiya kike? Me ya faru?" ta faɗa tana riƙe kafaɗun ta amma kuka take yi bata daina ba. Hankalin Mama ya tashi tace, "kin faɗa min meye ya faru? Ki daina kuka ki faɗa min lafiya kike? me ya same ki?." "Mama Bebi baya sona, Mama zan mutu ji nake kamar ƙirjina kamar zai fita Mama. Matar sa yake ao ba ni ba, baya ƙaunar ganina ko kaɗaan!" Ta ƙarasa faɗa tana kuka. A lokacin Ammi ta shigo dan kukan ta har falon ana ji, ta tsaya tana kallon su Mama tace, "ki bursu ki faɗa min, akwai abinda yace miki ne?." Abu ɗaya take maimaitawa tana cewa, "Baya sona, wallahi baya sona ya daina sona, Shikenan na shiga uku na, in ban aure shi ba mutuwa zan yi. Mama ƙirjina zafi yake min, ƙirjina yana min zafi Mama, ƙirjina!." Hankalin Mama da Ammin ya tashi şuna salati Mama tace, "ina kika ajjiye maganin ki? Ina maganin ki?." Bata jin abinda suke cewa ƙirjin ta kawai take nunawa tana kuka sosai daga zaune dan in ta kwanta ciwon yafi azaba. Mama ta kalli Ammi tace, "maza kira min Bebi yanzu Sumayya, Kira shi da gaggawa." Hannun Ammi na rawa take kiran wayar Bebi amma bai ɗauka ba. "Rumana! Rumana!! Rumana!!!" Mama ta faɗ tana jijiiga ta amma ina Rumana ta jima da barin  hankalin ta. BDƘB3P17 Bebi kuwa bai san abinda yake faruwa ba, bai shiga gidan ba sai da yayi sallar i'sha ya shiga har falon da su Manal suke ya samu Maman Surayya ita da ƙaramar ƴarta ƙanwar Surayya suna ta hira da Manal. Zama yayi yana murmushi yace, "Mama kin dawo ashe?." Da murmushi tace, "na dawo Adnan, ga auta ta yau ta maƙale min." Ya kalli wacce ta nuna masa ta gaishe shi ya amsa da fara'a ya kalli Manal ya sake kallonMama yace, "Mama zamu je asibiti da Manal za'a duba ɗinkin ta, yanzu zamu dawo in sha Allah." Mama tace, "Allah ya dawo daku lafiya." Ya amsa da amin ya tashi ya fita. Manal ta saka hijjabi akan kayan jikin ta ɗauki Ayan ta fita ta shiga motar suka tafi. Asibitin su suka wuce tun kafin su hau sama suka wuce office ɗin likitan da zata duba ta suka shiga da sallama ta amsa tana cewa, "ga Maman Ayan." Manal tayi murmushi ta ƙarasa ciki ta karɓe shi tace, "Kaii ma sha Allah! Haka yayi girma yayi yawo?." Ta kalli Bebi tace, "an maka two zero fa, yaron nan da babar sa yake Kama wallahi." "Shikenan na huta" ya faɗa da ɗan sakin fuska dan babbar likita ce kuma a shekaru ma babba ce shiyasa yake girmamata. ya kalli Manal yace, "bara naje office na dawo." Likitan tace, "ai kam ƴan gidan ku ma suna gidan nan, tun ɗazu naji ana neman wayar ka bata shiga, nima na kira ka ko zan same ta ban samu ba." Wayar ya ɗauko a aljihu ya duba yaga kiran Mama dana Ammi yace, "Subahanallahi! Amma dai lafiya ko?" ya faɗa yana fita da sauri. Likitan tana ta tsokanar Manal ta duba ta bayan ta gama tace, "ai ɗinkin naki ma ya warke, kin yi ƙoƙarin kula dashi sosai. Ki cigaba da shiga ruwan zafi kina zama a ciki." Manal tayi murmushi tace, "na gode." "Babu komai,Allah ya ƙara lafiya" ta amsa suka fito tare Ayan yana hannun likitan. Inda su Maman suke suka nufa a nan taga Mama a zaune akan kujera da Ammi da kuma Kausar kowa da alama hankalin sa tashe yake. Manal ta ƙarasa ta zauna Kausar ta karɓi Ayan a hannun likitan ita kuma Manal ta kalli Mama tace, "Mummy waye babu lafiya?." Mama ta kalle ta tace, "Rumana ce, ina ta kiran ku dake dashi babu wanda ya ɗauka." Manal tace, "waya ta tunda na saka chargi na manta ma da ita wallahi, Allah ya bata lafiya." Ta amsa da amin suka yi shiru ba wanda ya kuma magana. Bebi ne ya fito daga ɗakin da take ya kalli Mama da take kallon sa ya ce, "Mummy ai babu damuwa bacci take yi, daman rashin shan magani ne kwana biyu ya saka hakan ya faru amma yanzu zata warware in sha Allah." Mama ta girgiza kai bata ce komai ba yace, "lokacin da kike min waya wayar na silent ban ji ba gabaɗaya kuma ban yi amfani da wayar ba shiyasa, yanzu ma Dr ce take faɗa min kuna nan." Mama tace, "babu komai, na nasan baka ji ba" ta faɗa tana kallon sa dan ta san bai ji ɗin bane. Ya kalli Ammi yace, "in sha Allah Ammi zata warware." Ammi ta amsa da Allah ya sa ya wuce zuwa office ya zauna dan a yanayin da Mama take yana barin asibitin faɗa zata yi masa. Har tara na dare suna asibitin Manal tana office ɗin sa a lokacin saboda Ayan ya tashi yana kuka dole ta koma can saboda ta kula dashi. Bebi ya koma ɗakin da Rumana take ya kuma fitowa Mama tace, "bata farka ba?." "Ai allurar bacci aka yi mata Mummy, kawai rashin bacci a damuwar ta gaskiya, amma da ta warware Shikenan in sha Allah." "Allah ya sa." "Amin." "ka koma gida, Manal ta jima a nan na san ta gaji gata da ɗanyen jego. Duka abinda yake faruwa zan yi maka waya." Ya amsa da to yaje suka fito da Manal ta dawo ta yiwa su Mama sallama suka wuce gida. A mota manal ta kalle shi kafin tayi magana ta riga ta ya ce, "Dr tace min kin warke sosai, ɗinkin yayi kyau." Manal tace, "eh haka tace min." "Gaskiya Mama tayi ƙoƙarin kular min dake, Allah ya bata lada ya saka mata da aljanna." "Amin ya Allah." "Daman na ƙagu ki warke wannan jinin ya ɗauke ki dawo office, kinga yanzu kin warke saura jinin ya rage." Ta kalle shi suka haɗa ido kafin ya janye idon sa ya cigaba da tuƙa motar tace, "wanne office?." Bebi yace, "ai kin san wanda nake nufi." Manal ta turo baki tace, "to ai sai an kwana arba'in." Ya girgiza kai ya ce, "ba dai a gidan Adnan ba kuwa, ai indai kin gama jini bana jin zan ƙara miki kwaya ɗaya Manal, ni kaɗai nasan halin da nake ciki, tunda kin samu lafiya jini kawai zan jira ya tafi kwana arba'in wannan maganar hausawa ce." Manal tace, "to nida bazan koma ba sai an ɗauki mataki akan yin ciki, dan na faɗa maka sai nan da shekara biyar zan haihu." Yayi dariya ya girgiza kai yace, "an gama ranki ya daɗe." Tayi murmushi tace, "ya jikin Rumana ɗin?." "Da sauƙi, ciwon ta ne ya tashi, daman ai na faɗa miki tana da ciwon zuciya ko?." Manal tace, "uhum ka faɗa min." "Ciwon ne ya motsa amma zata dawo daidai in sha Allah." "Allah sarki! Wataƙila wani abun ne ya tayar mata da hankali." Bebi yace, "eh zata iya yuwa hakan, kin san ciwon ƙaramin ɓacin rai sai ya kai mutum ga kwanciyar asibiti." Manal ta kalle shi tace, "amma ni nafi tunanin ganin da tayi mana ɗazu ne ya saka ciwon ya tashi." Ya kalle ta kaɗan kafin ya ɗauke kai yace, "kawai dan ta gan mu sai ciwon ta ya tashi?." Manal tace, "eh mana, kishi ne kawai." Cikin dakiya da basarwa yace, "mijin tane ni da zata yi kishi?." "Wanda take so ya zama dai." Bebi yace, "Manal ki daina wannan maganar ba yadda kike tunani bane." Manal ta taɓe baki tace, "hmmm! Faɗa ka ke kaima amma wallahi akwai wani abu a ɓoye dake tsakanin ka da Rumana, baka so na sani ne kawai, Baka san gwara ka faɗa min ba da na gano da kaina." canja maganar yayi yace, "Mu shiga mu gaida Mama ko?." Manal tace, "dare yayi sosai mun bar Maman Surayya ita kaɗai, gwara mu koma." Shiru yayi bai ce komai ba sai tayi murmushi tare da yin ƙwafa ya kalle ta ya ce, "na faɗa miki babu wannan maganar gwara ki barta, Meyasa kike min haka ne?, kina kawo tunanin da ba shine yake faruwa ba na faɗa miki kuma kin ƙi yarda. Ya kamata ki daina wannan tunanin kar kishi ya rufe miki ido." Ganin ya fara yi mata faɗa alamun ransa ya fara ɓaci sai tace, "kwantar da hankalin ka, meye na faɗan kamar mara gaskiya?." Jin abinda tace sai ya sauke numfashi kaɗam ya ɗauke kai daga kanta yana cigaba da jan motar. Manal tace, "Shikenan ai babu komai, kaji na sake cewa wani abun ne?." Bai ce komai ba itama tayi shiru a haka suka koma gida babu wanda ya sake yiwa wani magana a cikin su. Suna shiga gidan Manal ta wuce wajan Maman Surayya tana cewa, "Mama na jima ko? Wallahi wata ƙanwar sa Rumana aka kwantar a asibitin ciwon zuciya yana damun ta, shiyasa muka zauna a wajan Mummyn sa." Mama tace, "Allah sarki! Allah ya bata lafiya." Manal ta amsa da amin fuskar ta babu walwala ta shiga ɗaki. Shima a lokacin ya dawo yana sake maimaita mata abinda Manal ta faɗa mata Mama tace, "Manal ta faɗa min, Allah ya bata lafiya." "Amin Mama, Mun barki ke kaɗai." "Babu komai kar ka damu, ga Aysha ai muna tare." Fita yayi daga falon Mama ta kira Manal da ta canja kaya ta zuwa na bacci tace, "nayi abinci fa, ki kai masa ko zai ci." Manal ta sauke numfashi ta shiga kitchen ɗin. Dambu Mama ta ajjiye musu da alama ma daga gida tazo dashi ya sha gyaɗa da zogale, Sai salad ɗin Manal da ta haɗa mata da basmati rice da aka dafa. Zuba masa dambun tayi daidai yadda ta san zai cinye ta nufi falon da ta san yana can, ta same shi a zaune yana kallon ball ta ajjiye masa ta ɗauko ruwa da lemo ta ajjiye. Ta kalle shi taga ya ɗaure fuska ko kallon ta bai yi ba tace, "Wai duk akan Rumana ka fusata haka? Kuma a haka ka ke so wai na yarda babu komai?. Hmm! Kana ɗauka ta mara wayo ne kawai Partner, ko na ce kallon yarinya ka ke yi min har yanzu" ta faɗa tana niyar barin wajan bai ce mata komai ba. Kallon sa tayi itama kamar zata sake magana sai ta fasa kawai ta wuce ta koma falon ta ta zuba nata abincin tana ci harda kunu ma Mama ta yi mata mara sugar. Tana shan kunun tana cin abinci Mama tace, "baki bani labari ba, ya ɗinkin naki?." Manal tace, "maganar rashin lafiyar ce ta ɗauke mim hankali, ɗinki yayi kyau sosai Mama." "Ma sha Allah" ta faɗa bata sake mata magana ba domin ta fahimci daga fitar si zuwa dawowa su akwai canji a fuskokin su. Tana gama cin abincin tashi tayi ta koma ciki ta kwanta tana aikin tunanin meye alaƙar shi da Rumana haka? Tana so ta tambayi Mimi ko Kausar amma kuma wata zuciyar na hana ta aikata hakan kar aga kamar ta cika bin diddigi, daƙyar ta iya daurewa tayi bacci. Washe gari. Da wuri ya fita ya shiga babban asibiti kafin ya wuce nasu saboda Rumana da take a can a kwance amma da baza shi ba. Da yaje ɗakin da yasan tana ciki ya shiga ya samu Mama ce a wajan ta tana zaune tana hhan tea, Rumana ma tana zaune amma da ka ganta ka san bata da lafiya ta ɗan rame lokaci ɗaya fuskar ta ta faɗa kamar wacce tayi zawo. "Mummy barka da safiya." Mummy tace, "barka dai Adnan, ya Manal da Ayan ɗin?." "Lafiya lau, ya mai jikin?" Ya faɗa yana kallon Rumana da take kallon sa tun shigowar sa. Mama tace, "gata nan a zaune, da sauƙi tunanin komawa gida ma muke yi." "Allah ya ƙara lafiya" Mama ta amsa da amin kafin ya tashi daga gaban Mama ya zauna a kan kujera ya kalli Rumana yace, "ya jikin ki?." Kallon sa take yi babu abinda yake zuwa idon ta sai lokacin da ta buɗe ɗakin da suke ciki shi da Manal, yanayin da ta gansu a ciki da kallon da ya mata tare da yin tsaki ya sake juyo da fuskar Manal ya ɗora daga inda ya tsaya. Runtse ido tayi nan take idon ta ya ciki da hawaye cikin tsananin zafin kishin da yake azalzalar zuciyar ta tace, "da sauƙi." "Allah ya ƙara lafiya" ya faɗa yana ɗaukar wasu magani da suke ajjiye a gefe yana kalla yace, "Mummy wannan ne maganin da aka bata? Wanne likita ne ya bata?." Mama tace, "eh sune, wata likita ce kamar ma bata jin hausa." Ya girgiza kai ya ajjiye maganin ya kalli Mama tace, "wallahi Mummy damuwa ce kawai take tayar da ciwon nan nata, in bata daina saka abinda yafi ƙarfin zuciyar ta ba nan gaba ciwon zai ninka wannan. Sai tana daurewa tana haƙuri ko dan lafiyar ta." Mama ta girgiza kai tace, "na sani Bebi, amma damuwar ta zo ƙarahe in sha Allah." Gaban sa ya faɗi sosai ya kalli Maman suka haɗa ido ta ɗauke idon ta, ya sauke numfashi ya tashi tsaye yace, "zan je na duba marasa lafiya." Mama ta ɗaga masa kai ya fita. Bayan fitar sa da ɗan jimawa Mama ta masa waya tace sun wuce gida ta gaji da zaman tunda dai ta warware. BDKB3P018 Mama sai da ta saka Rumana tayi wanka taci abinci ta sha magani ta tabbatar ta huta sannan ta zauna a gefen ta tace, "Rumana na san damuwa ce ta kawo miki wannan ciwon naki, tunda muka je gidan Bebi na lura da kin taho da damuwa, haka za'a cigaba da tafiya kenan sai dai ki daina zaman Kano saboda Bebi?." Ta kallli Mama tace, "wallahi Mama ina daurewa kasawa nayi." "Haka zaki cigaba da dauriyar, lokacin da muke jira ya kusa zuwa, matar sa ta haihu duk abinda za'a yi an kusa ayi a wuce wajan." "Mama in na ganshi tare da ita ne sai naji zuciyata na bugawa fiye da ƙa'ida." Mama ta riƙe hannun ta tace, "Shikenan baza ki ganshi da matar sa ba kenan? Yanzu in kin aure shi din ma haka za'a dinga yi?. Haka zaki dinga saka damuwa a zuciyar ki saboda kishi? Kan ki fa kike cuta bashi ko ita ba." Ta fara hawaye tace, "Wallahi Mama baya sona ne yanzu, har kyauta na kai masa amma da ya karɓa a inda yake a nan ya ajjiye. Sai kallon matar sa da yake saboda naje gidan kamar yana jin tsoron wani abun. ni naga alamun ma bai faɗa mata maganata ba, bata san maganar ba gaskiya." Mama ta sauke numfashi tace, "dole ai yaji tsoron matar sa saboda matsayin kishiyar ta ki ke, yana son ki yana son ta dole hakan zai kasance." "Mama ni ce nake son sa shi baya sona wallahi." "Ki daina faɗar haka wallahi, Bebi yana son ki na tabbatar da hakan." Rumana tayi murmushi kawai amma bata yadda ba dan tasan ba haka bane, Mama tace, "ki kwantar da hankalin ki ina da rai da lafiya har yanzu, koda bani da rai auren ku babu fashi balle ina numfashi a doran duniya. Ki kwantar da hankalin sai kin aure shi in sha Allah." Rumana ta kwanta a jikin Maman tace, "Allah yasa Mama, ina son sa wallahi, in na rasa shi bazan iya rayuwa ba." Mama ta dafa kanta tace, "kar ki damu, zaki rayu dashi har ki haifa masa yara in sha Allah." Tana kwance a jikin Mama ta share hawayen ta Mama tace, "ki kwanta ki yi bacci." Ta kwanta kamar yadda Maman tace tayi shiru tana tunanin ƙaunar da Adnan yake yiwa Manal. Mama da ta fito falo Kausar ce da Lubna suke karatu ta kalle su tace, "in Bebi yazo ku ce masa ina neman sa." Suka amsa da to ta shiga ɗaki. Ba jimawa ya zo ya shiga wajan Abba yaga baya nan ya dawo falon Maman duk suka gaishe shi ya amsa sannan ya ce, "Ina Abba yaje yau?." Kausar tace, "yace gaisuwa yaje amma zai dawo yanzu." Ya girgiza kai kawai bai ce komai ba ya shiga wajan Mama. Ganin ta a kwance kamar mai bacci sai ya juya zai fita yaji ta kira sunan sa ya tsaya tare da juyowa tace, "dawo daman neman ka nake yi" ta faɗa tana tashi zaune shima ya koma ya zauna a carpet ita kuma tana kan gadon a zaune. Mama ta kalle shi bayan ta tattaro nutsuwar ta tace, "Manal ta san da maganar auren ka Rumana kuwa?." Wani irin abu yaji ya tsirga masa tun daga kansa har ƙafafun sa, ya kulle ido ya buɗe ya sauke numfashi cikin yanayi mara daɗi. Mama duk tana kallon sa tana karantar yanayin sa tace, "baka ji me nace ba?." ya ɗago ido ya kalli Maman ganin tana kallon sa sai ya sauke kai ƙasa ya ce, "bata sani ba." "Amma tun farko nace ka faɗa mata ko? Kenan baka yi abinda nace ba?." Bebi ya ce, "ba haka bane Mummy, na ɗauka an bar maganar ne." Da mamaki take kallon sa jin abinda ya ce baki buɗe tace, "an bar maganar kace? Lallai da gaskiyar Rumana da tace yanzu baka son ta. Kenan kai ka manta na ce maka ko bayan raina in kana so na kwanta a kabarina cikin farin ciki ka auri Rumana ba? Ka manta na faɗa maka haka?." Ya sunkuyar da kai Mama tace, "saboda maganar tawa da alqawarin da kayi min bashi da mahimmaci ko?, saboda ka raina ni ni ka ke kallo kana cewa ka ɗauka an bar maganar, wato da na mutu shikenan baza ka iya cika min alƙwarin da ka yi min ba?." Ya girgiza kai cikin tashin hankali yace, "A'a Mummy, ba haka nake nufi ba don Allah......" ta dakatar dashi cikin fusata tace, "ya ka ke nufi Adnan? Inda na isa da kai baza ka furta abinda ka furta min yanzu ba." "Ki yi haƙuri don Allah, amma ba haka nake nufi ba." "Haka ne mana, gashi ka manta da alƙawarin da ka ɗaukar min na zaka auri Rumana ko bana numfashi a duniya, har ka manta saboda ka auri wata kun haihu ko?. Saboda kana da wata a gida ka manta da alƙawarin mahaifiyar ka ko?." Bebi cikin rauni ya ce, "ki yi haƙuri Mummy, ba haka nake nufi ba, ina sane da maganar alƙawarin da na yi miki a kan ta. Wallahi Mummy zan iya yin komai a kan ki, ki daina cewa na raina ki don Allah." "To indai baka raina ni ba kuma kana son farin cikina ka cika alƙawarin da ka yi min yanzu, indai kana son ganin walwala a kan fuskata ka auri Rumana a cikin kwanakin nan Adnan. Na bar ka ka zauna da matar ka har ta haihu nayi maka adalcin da ya kamata ace nayi maka matsayina na uwa, kaima lokacin ka ne da zaka yi min adalci matsayin ka na ɗa a wajena. Yanzu ba sai anjima ba kaje wajan Hajiya da kan ka kace mata kai ne ka ke son auren Rumana ba ni nace maka ba, daga nan ka dawo a cigaba da magana." Gaban sa faɗuwa kawai yake yi ya rasa ya zai yi balle yayi magana Mama tace, "ka sanar da Manal yanzu dan ta san ka kusa kawo mata abokiyar zama. Tun farko na ce ka faɗa mata ka ƙi, yanzu sai ka san da fuskar da zaka sanar mata tunda haka ka zaɓa." Ya sauke ajiyar zuciya ya kasa magana gabaɗaya, bakin sa ya kulle ya rasa abindai zai cewa Mama. Zuciyar sa bugawa take in ya tuna akan auren Rumana take magana, babban tashin hankalin sa bai wuce Manal ba. Da wacce fuska zai tunkare ta har ta fahimci abinda yake nufi?. Mama ta lura da yanayin sa sai tace, "Bebi da ace ina da wani ɗan ba kai ba wallahi banza dinga ɓata lokacina ina faɗa maka kana ƙin yi ba, da yanzu na aura mata shi na ƙyale ka tunda kai baza ka iya yi min abinda nake so ba sai kaje ka ƙarata. Matsalar da aka samu kai kaɗai Allah ya bani shiyasa ka ke min abinda ka ke so." Da sauri ya kalle ta ya ce, "Mummy don Allah ki daina wannan maganar, kina da ikon sakani nayi duk abinda kike so koda ni bana so, ki yi haƙuri ba haka nake nufi ba." Tayi tsaki tace, "bani da wannan ikon, da ina dashi baza ka kalle ni kace min kai ka ɗauka an bar maganar auren ka da Rumana ba." "Don girman Allah ki daina wannan maganar, wallahi babu abinda zaki ce nayi ban yi miki ba, ki yi haƙuri." "in dai hakan ne kayi abinda nake so, ka auri Rumana yanzu ba nan gaba ba. Saboda kai ta samu ciwon zuciya amma komai ko a jikin ka, to bazan bari na rasa ta ba saboda kai, auren nan za'ayi a yanzu dan bazan bari a ɗauki lokaci ba Adnan." Bebi jikin sa ya gama yin sanyi Manal kawai yake tunani ba kowa ba, in ba dan ita ba zai amince a lokacin ma a ɗaura masa aure da Rumana, sai dai kash in ya tuna Manal sai yaji komai ya fita daga ransa lokaci ɗaya. Amma ya zai yi? hakan zai daure ko da baya so, zai san hanyar da zai bi wajan faɗawa Manal halin da ake ciki duk da ya san baza ta taɓa fahimtar sa ba. A hankai ya ce, "To Mummy, Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi" ya faɗa kamar zai yi kuka. Mama ta kalle shi jin yadda yayi maganar tace, "Allah ya yi maka albarka." Ya amsa da amin a lokacin wayar sa take ƙara. Ganin Huzaifa ne sai ya ɗauka yayi shiru alamun ana yi masa magana kafin ya ce, "to yanzu zan koma gida sai kun zo" ya faɗa yana kashewa ya kalli Mama yace, "ƴan gidan su Huzaifa ne zasu zo, zasu zo har nan gaishe da Abba." Mama tace, "Allah ya kawo su lafiya." "Amin, zan koma dan na tarbe su." "sai ka dawo." Miƙewa yayi ya fita zuciyar sa sai bugawa take yi. A haka ya tafi gida cikin sanyin jiki da rashin walwala da kuma bugawar zuciya, jikin sa har zafi yayi saboda tashin hankali dan bai san da wacce fuska zai yiwa Manal bayani na. Da ya shiga gidan ya faka motar ya fito yashiga cikin gidan. Mama ya samu a zaune a falon da Ayan a hannun ta tana saka masa kaya suka gaisa da girmamawa yana yi mata sannu da aiki tace, "Manal ɗin ai tana ciki." Bai shiga ba sai ya koma ɗakin sa saboda haka kawai yake jin kunyar ta, haka kawai yake jin bazai iya haɗa ido da ita ba domin babu adalci a abinda yake shirin yi mata. Mama ganin bai shiga ba kuma Manal bata fito ba sai ta ƙwalawa Manal kira tana fitowar tace, "mijin ki ya dawo." Manal ta sauke numfashi dan har lokacin haushin jiya bai bar zuciyar ta ba, ta wuce ta shiga ɗakin nasa ta same shi a zaune ya zubawa waje ɗaya ido alamun tunani. Sallama tayi hakan ya saka ya kalle ta sai ya tashi tsaye yana kallon ta, ta ƙaraso inda yake tana kallon sa itama kamar yadda yake kallon ta, ganin kallon da yake binta dashi kamar wanda ya jima bai ganta ba sai tace, "lafiya? Jikin Rumana ɗin ne ya tashi?." Jin abinda tace sai kawai ya jawo hannun ta ya rungume ta a jikin sa, tayi sak gaban ta yana faɗuwa sosai ba tare da ta san dalilin faruwar hakan ba. Bugawar da zuciyar sa take yi take jin sautin ta har cikin kunnen ta gashi ya riƙe ta sosai a jikin sa kanta yana kwance a ƙirjin sa a daidai saitin zuciyar sa. Ɗagowa tayi daga jikin sa ta ɗora hannun ta a saitin zuciyar sa tace, "lafiya zuciyar ka take bugawa haka? Me ya faru?." Kallon idanun ta kawai yake yi kafin ya ɗauke ido, ya kulle idon sa ya buɗe ya sake kallon ta yaga dai shi take kallo har lokacin tace, "ka faɗa min me ya faru, zuciyar ka na bugawa sosai alamun kana cikin tashin hankali, me ya faru Partner?." "Ina sonki Manal" abinda yace kenan yana sake mayar da ita jikin sa tare da zagayawa da hannun sa ƙugun ta, faɗar hakan da yayi sai ya sake tsorata ta ta riƙe shi amma zuciyar ta na ta kawo mata abubuwa kala-kala akan hakan. Ɗago ta yayi daga jikin sa yana kallon ta yace, "Huzaifa da ƴan gidan su zasu go ganin Ayan, a samu ayi musu abinda zasu ci ko ya ya ne." Ta riƙe hannun sa duka biyun tace, "kafin wannan, meye damuwar ka?." "Kar ki damu ba wani abun bane, zan sanar dake bara su zo baƙin su tafi." Manal tace, "amma ka tsorata ni, da zaka faɗa min yanzu zan fi jin daɗi." Ya murmusa kaɗan yace, "kar ki damu." Manal ta sauke numfashi tace, "Sury tana nan, bara naje sai a san abinda zaa yi. Na kawo naka abincin?." Ya girgiza kai yace, "bana jin yunwa." "Amma baka ci komai ba tun safe." "Na sha tea da naje office." "Amma tea ba abincin ka bane, gwara ka ci abinci." Ya kalli hannun ta da yake cikin nasa ya ce, "in su Huzafa sun zo sai mu ci gabaɗaya." Ta zame hannun ta daga nasa tace, "to bara naje." Ya girgiza kai bai ce komai ba ta fita. Ya zauna a gefen gadon ya ce, "taya zan faɗawa Manal Mummy?, Mummy ta ya zan cewa Manal zan auri Rumana a cikin kwanakin nan?" Ya faɗa yana dafe kansa cikin damuwa mai yawa. BDƘB3P19 Abba ko da ya fita babban store ɗin sufi mart yaje da yake zoo road saboda abinda yake so zai siya, yana son fita da kansa dalilin da ya saka bai saka an kai shi ba ya dauƙi driver ba ya tafi da kansa. Yana cikin duba abinda yake so ya hangi Mubeena daga ɓarin turaruka ita da ƙawar ta Bily suna kallon wani turare suna dariya. Jikin sa ne yayi sanyi sosai ya kulle ido ya buɗe a kan su yana jin nadama da dana sanin abinda ya aikata. Godiya yake ga Allah da bai bashi ikon aikata wani abun da Mubeena ba, duk da jajircewar tace ta kawo hakan da an biye tashi da yanzu wataƙila ya ɗauki wuƙa ya cakawa kansa saboda baƙin ciki. Ajiyar zuciya yayi yana kallon ta har lokacin tana wajan sai dai ta matsa gaba daga inda take tsaye, kulle ido yayi ya buɗe ya tattaro nutsuwar da ya samu ƙarfin guiwar nufar inda take da niyar neman afuwar ta. Kasancewar ta juya baya tama ɗaukar turare bata ganshi ba sai maganar sa taji a bayan ta yace,"Mubeena." Juyowa suka yi ita da Bily dariyar da take yi ta tsaya ganin wanda yake gaban su a tsaye. Mubeena ta ɗaure fuska matuƙa ta juya ta cigaba da abinda take yi bata kalle shi ba. Ganin hakan sai Abba yace, "Ba wani abun zance ba Mubeena, zuwa nayi nace miki...." Da sauri ta juyo tace, "kace min me? Meye nayi min magana bayan na riga na manta da abinda ya faru a baya?, Na manta da kai a cikin rayuwata, na share ka na cigaba da mu'amala da dangin ka saboda ɗan ka Adnan!. Shi ɗin mijin ƙanwata ne,  bana son wata hatsaniya ta haɗa ni da kai saboda matsayin da ka ke dashi a wajan ƙanwata, amma ba dan haka ba baka isa ka tsaya a gabana kana yi min wata magana ba." Abba ya girgiza kai ya ce, "na sani, amma ki yi haƙuri da abinda ya a baya faru." "Wannan ai bani ta shafa ba kai ta shafa ba wani ba, kai zaka ga sakayya da idanun ka tun a duniya ba wani ne zai gani ba. Ko iya kunyar yaran ka ma ta ishe ka a duk ranar da halin ka ya bayyana a gare su. Sannan ina so ka sani Adnan ya san komai, duk abinda ka ke ɓoyewa Adnan ya sani.  Har ni Mubeena ya samu da maganar ka, kasancewar ka mahaifin a wajan sa ya saka ban furta komai a kan ka ba saboda duk lalacewar ka kai ka haife shi, amma wallahi da wani ne daban bashi ba da na haɗa kai dashi na wanke tas. Ka gode Allah da ban faɗawa Mama abinda ya faru tsakanina da kai ba, da ta sani yafe maka ɗin da tayi wallahi baza ta yafe ba, sannan kuma dole ta raba auren ƙanwata da ɗan ka" ta faɗa tana kallon Bily. Bily tace, "Mubeena zo mu tafi, kar mu tarawa kan mu jama'a" ta faɗa tana jan hannun ta suka bar wajan. Abbba ya tsaya a wajan kamar an dasa shi a wajan, babban abinda ya saka ƙafafun sa yin sanyi da yaji Adnan ya san maganar Mubeena. Zuciyar sa bugawa take yi sosai bai iya siyan abinda yazo siya ba ya fito ya tafi.        *** Manal koda ta bar wajan Adnan wajan Surayya taje ta faɗa mata abinda yaje faruwa suka shiga kitchen tare suka dan yi fan cake da yake shi bashi da wahala. Aikin gabaɗaya Surayya ce tayi Manal tana daga zaune ne kawai tana kallon ta, ba jimawa aka gama aka zuba an abu mai kyau suka ajjiye. Mama ce ta shigo tace, "ku ace muku za'a yi baƙi tun daga wata ƙasa amma ku rasa ne za'a basu sai cake? Ina laifin ayi abinci?." Surayya tace, "haka nace nima, Sai tace yace ayi abinda ya samu kawai." Mama ta kalli Manal tace, "ya faɗa ne ai kawai amma ba wai dan kar ayi ɗin ba, iyayen aminin sa ne fa zasu zo, kuma daga wata ƙasar zasu zo sai mu rasa me zamu basu sai fancake?." "Mama ba sai a haɗa musu da naman sunan can ba?tunda akwai sai sake soya shi saboda kar yayi tauri da yawa." Mama tace, "A'a bazai yu ba, Surayya maza ɗora koda couscous ne tunda yana da sauƙi kafin a gama gaisawa ma ya yi koda sun zo, akwai miya a fridge sai ki ƙara naman ciki a soya ta, akwai salad ɗin Manal shima a gyara shi a haɗa musu dashi." Surayya ya amsa ta fara ƙoƙarin ɗorawa ita dai Manal tana tzaune kawai a gefe. Fitar Mama ya saka  Surayya ta kalle ta tace, "wai lafiya ki ke? Gabaɗaya kin canja me ya same ki?." Manal ta sauke ajiyar zuciya tace, "ban sani ba, amma akwai abinda yake damun partner yaƙi sanar dani." Surayya jin hakan sai ta cigaba da abinda yake gaban ta kawai bata ce komai ba dan bata shafe ta ba maganar. Lokacin da motar su ta tsaya lokacin Surayya tw zuba couscous a ruwan da ta ɗora, shigowar mutane falon suka ji hakan ya saka Manal tashi ta fito falon da ta saba zama ta tarar mata guda huɗu, ƴan mata biyu da yarinya wacce bata wuce shekara goma ba, Sai babbar mace wacce ta kasance mahaifiyar su, dan kana kallon ta zaka ga kama da Huzaifa sosai. Manal tayi murmushi ta ƙaraso tana cewa, "Sannun ku da zuwa." Ƙaramar yarinyar cikin su tace, "woww! I thoroug you can't speak hausa." Wacce take zaune kusa da ita ta doke ta tace, "kin cika magana ko gaishe ta baki ba." Manal da murmushi ta ƙarasa ta gaisa da Maman su Huzaifa ta amsa da murmushi tace, "an samu ƙaruwa ko." Manal ta amsa Maman ta sake cewa, "Allah ya raya mana shi, Gashi kuwa sak ke" ta faɗa tana kallon yarpn da yake hannun ta. Manal tayi murmushi ta kalli ƴan matan tace, "Sannun ku." Babbar cikin su tace, "Sannu Sis Manal, yau dai gashi min gan ki ido da ido, bikin ku duk waya muka gani." Manal tace, "gaskiya dai kam, ya sunan ki?." "Sunana Fatima amma ana kirana da Baby." Manal ta buɗe ido tace, "sunan Mamana ne dake." Baby tace, "kice na gyara zama gidan ƴata nazo." Manal tace, "ki yi abinda ki ke so Mamana." Ɗayar da take zaune tace, "duk da baki tambaya ba sunana Aisha." Ƙaramar tace, "ni kuma Ayra." Aka yi dariya harda Maman su Manal tace, "your welcome Ayra, sunan ki mai daɗi." "Bai kai naki ba Anty Manal." Surayya ce ta fito da flaks ɗin abinci dana fan cake ɗim ta ajjiye musu suka gaisa, aka kawo ruwa da lemo da kofuna da kuma kayan marmari. Mama tace, "mu da zamu tafi ina mu ina cin abinci?." Maman su Surayya tace, "ai kam ko yaya ya kamata ku taɓa."  Manal kallon Aisha take yi ganin tana yatsina kana ganin ta kaga mai iyayi tayi murmushi tace, "Aisha iyayin ki irin na Yayata." Aisha tayi dariya tace, "wai iyayi, don Allah da gaske? Tana ina?." Manal tace, "Tana gida." Buɗe ƙofar akayi ya saka Manal ta kalli wajan Bebi ya kalle ta yace, "ki zo ku gaisa da Daddy." Manal ta amsa ta tashi ta shiga ɗaki ta ɗauko mayafi Ayra ta tashi tace, "ni zan ɗauki mai irin sunana na kaiwa Daddy." Maman su tace, "sai kin yar dashi?." Manal tayi dariya tace, "ƙyale ta Mama, daman sunan su iri ɗaya ita Ayra shi Ayan" Manal ta faɗa tana bata shi suka nufi falon Abban. A zaune ta same su da Daddy da Huzaifa da wani ɗan saurayi da alama  shima ƙanin Huzaifa ne a zaune sai Bebi da yake tsaye ya ajjiye musu abin sha. Ayra ta ƙarasa wajan Daddy tana cewa, "Daddy kaga Ayan mai kyau, kuma sunan mu iri ɗaya ne dashi, Anty Manal ɗin ma tana da kyau sosai" ta faɗa tana bawa Daddyn shi ya karɓa yana cewa, "Sarkin magana, aka baki jariri sai kun faɗi ke da shi?." "Daddy gashi na kawo maka shi bai faɗi ba." Manal ta zauna a ƙasa suka gaisa da Daddy ya yi mata barkar samun ƙaruwa tare da addu'a kafin yace, "ku yi haƙuri fa, ana ta saka rana zamu zo zamu zo Allah bai yi ba sai yau." Manal tayi murmushi tace, "daman komai sai Allah yayi." Daddy yace, "gaskiya ne." Manal tace, "hakan ma mun gode Allah ya ƙara girma." Daddy ya amsa da fara'a kafin ta miƙe tana cewa, "bara a kawo abinci." Daddy yace, "A'a, ki barshi ba sai mun ci komai ba." A lokacin Manal ɗago kai ta kalli fuskar sa a lokacin shima ya kalle ta sai tayi murmushi  tace, "A'a Daddy, gwara dai ku ci ko ya yake, bara na kawo." Sak Daddy yayi ya kasa magana yana kallon ta fuskar har ta ɓace daga falon, gaban sa ne yake faɗuwa tunawa da wani abu da ya faru a shekarun baya, zuciyar sa lokaci ɗaya ta harba cikin tunanin da yazo kansa lokaci ɗaya. Suna zaune aka kawo abinci suka ɗan ci kaɗan kafin su gama yace a kita yaran suka fito gabaɗaya har Manal ɗin,  Daddy ya bawa Manal kayan da aka kawowa Ayan da nata kayan har da kuɗi. Har bakin mota suka raka su suna godiya kafin su shiga mota su tafi gidan su Bebi. Komawa ciki su Manal suka yi Mama tace, "to gashi sun ci, da kuna baza'a ayi girki ba. Ai in aka sanar da kai zuwan mutane da wuri ana nufin ayi musu tarba mai kyau." Manal ta zauna tana cin abincin tana cewa, "Wallahi kuwa Mama, ba dan ke ba da mun ji kunya." Surayya tace, "tun farko ai nace miki ayi kika ƙi." Manal tana cin abincin tace, "to ba gashi an yi ɗin ba, kin cika mitar tsiya." Surayya tayi dariya itama ta zuba abincin ta fara ci.   Su Daddy kai tsaye gidan su Bebi aka wuce dan a gaishe da Abba, suka faka motocin a harabar gidan Bebi yayi musu iso zuwa wajan Abba kai tsaye tunda ya san da zuwan nasu. A falon Abban suka samu Mamy da Mummy  a zaune suna magana da Abban, suka shiga da sallama. Abba yana kashingiɗe akan kujera, Mummy tana daga gefe ganin su sai tayi murmushi tace, "Sannun ku da zuwa, Yauwa Bebi yi sauri kazo jikin sa yayi zafi" ta faɗa tana kallon ew. Bebi ya ƙarasa kusa da Abba da sauri Abba ya tashi zaune yace, "Zazzaɓi ne kawai ba wani abun ba, ƙyale ni Adnan ga baƙi sun zo in mun gaisa sai ka duba ni ɗin." Ganin Abban ya tashi si ya bashi waje suka ƙaraso aka zauna. Abba ya kalli Daddy tare da miƙa masa hannu yace, "Barka da zuwa mutanen Qatar, sai yau Allah yayi zamu gana, ana ta saka lokaci ana saɓun saɓani, sai yau da Allah ya nufa gani ga ka." Daddy ya kalli Abba  da murmushi yana miƙa masa hannu alamun su yi musabaha. "Kaiii!" Daddy ya faɗa yana zare glasses ɗin idon sa yana kallon kamar yadda Abban ma shi yake kallo da matuƙar mamaki a kwance a kan fuskar sa. Sun ƙamar da hannun basu gaisa ba kuma basu janye hannun ba sai kallon juna da suke yi cikin mamaki da kuma al'jabi. Abba ne ya miƙa hannun sa sosai suka gaisa ya ce, "wai idona ne suke gane min abinda nake gani ko kuwa gaskiya ne?, fuska nake gani kamar ta wanda taɓa sani a baya. Sai dai wannam fuskar cike take da girma da kuma farin gashi." Daddy yayi dariya mai sauti wacce take nuni da tunanin sa ya zama gaskiya ya riƙe  hannun Abba yana jijjigawa yace, "nima irin hakan nake gani, kar kace min Mu'azaam ne." Abba yayi murmushi ya ce, "Aliyu dollar." Jin sunan da ya faɗa Sai Daddy ya ƙyalƙyale da dariya ya ce, "Wallahi kai ne, wallahi wannna abokina ne Mu'azzam." "Ali ashe rai zai sake ganin rai?." "Gashi kuwa  mai haɗawa ta haɗa mu. Mu'azzam daman kai ne mahaifin Adnan? Ikon Allah kuma ya aka yi ban yi saurin fahimta a kan fuskar Adnan ba?, Ko da yake shekaran da yawa, maganar shekara sama da ashirin ake yi." Abba ya girgiza kai ya kalli iyalan Ali yace, "kowa ya tara iyalai ma sha Allah, amma babu wanda ya san wani, an rabu kamar ba a taɓa haɗuwa ba." A lokacin iyalan Daddy suka  gaishe da Abba ya amsa da fara'a kafin ya kalli Huzaifa yace, "Huzaifa ashe daman wannan shine ya haife ka?, Ai na jima da sanin mahaifin ka shekaru da yawa da suka wuce, wani dalilin ne ya raba mu amma da na tabbatar har yanzu muna tare. Da yake Allah yayi dai yau zamu sai aka dinga samun saɓanin haɗuwar tamu." Daddy yace, "bari kawai, kuma na neme ka daga baya, Allah dai bai yi za'a sake haɗuwa ba sai yanzu ta silar Adnan da Huzaifa." Abba yace, "Huzaifa shine yaron da na sani yana yaro?, shine wanda dai nake gani?." "Shine wallahi, Allah ya raya min shi gashi har ya girma ya ajjiye iyali. Da yake kamannin sa gabaɗaya sun canja baza ka iya gane shi ba" ya kalli Manan su Huzaifa yace, "Mu'azzam ne fa abokina a Zaria, kin gane shi?." Mama tayi murmushi tace, "na gane shi mana, ai ganewa ba ma ɗaya ba, ba shine wanda yake zuwa daga nan Kano ba ku ke barin garin tare?." Daddy ya girgiza kai alamun shine yana murmushi. Abba ya kalli Mamy kafin yayi magana tace, "na gane shi yanzu." Abba ya kalli Mama yace, "daman dake ne baku taɓa haɗuwa ba, amma ya taɓa ganin Adnan ne ko Farida na dai manta waye a cikin su. A'a Muhammad ne Yayan Adnan da ya rasu." Mama tayi murmushi kawai bata ce komai ba. Daddy ya kalli Abba yace, "Alhaji Mu'azzam na iyayen kowa." Abba shi kaɗai yasan me sunan yake nuri hakan ya saka yace, "wannan suna ai ya zama tarihi." Suka yi dariya gabaɗayan su da alama dai sun ji daɗin sake ganin juna. Abba ya kalli matan sa yace, "Hauwa ku je da baƙin su ci abinci dan tafiya ba yanzu ba sai dare." Daddy yace, "ko ma gobe ba, aje dai ayi hira dan munci abinci a gidan Adnan." Abba yayi murmushi ya girgiza kai duk suka fita aka bar Abba da Daddy kawai. Abba ya kalli Daddy yace, "Alhaji Ali, sai ka ɓace ɓat bayan ka tattara koma ka gudu." Daddy yayi murmushi yace, "kuma wallahi kana raina, daga baya ne na manta da komai." Abba yace, "Wai kuwa ina Zahra matar ka?." Daddy ya sauke numfashi ya ce, "daga baya na dawo ina neman ta amma ban same ta ba, na shiga damuwa sosai a kanta, dan wallahi nayi dana sanin abinda nayi mata matuƙa. na dawo da niyar na bata haƙuri na kuma mayar da ita ɗakin ta amma ban ganta ba. Har yau ina yawan tunanin ta ina kuma so na sake ganin ta." Abba yace, "Yanzu wannan arzuƙin da ka tara har ya kai baka zaman nigeria duk da duniyar ta ka shi ko?." Ya sauke numfashi yace, "To ya za'a yi? Haka Allah ya yi." Abba yayi murmushi yana girgiza kai yace, "ai abinda muka yi bamu kyauta mata ba daga ni har kai, haƙƙin ta sai ya bibiye mu ni da kai, dan mune silar barin ta cikin ahlin ta." "Wallahi na sani, na sani kuma nayi nadamar tafiya na barta bayan nasan bata da kowa sai ni. Gaskiya ban kyauta ba nima na sani, saboda haka har Baby na sakawa sunan ta Zahra, duk sanda na kira sunan Zahra ina tunawa da ita nayi mata addu'a a zuciyata, in tana da rai ina so na ganta ko dan na nemi afuwar ta, in bata raye Allah ya jiƙan ta, ammaa na san Allah zai tsayar damu ni da ita yayi mana hisabi." Abba ya kalle shi yace, "in akace tana da rai abin zai fi zuwa da sauƙi, ka nemi yafiyar ta tun kafin zuwan mu lahira." "Inda hakan zai kasance wallahi zan ji daɗi sosai." Abba yace, "Zahra tana nan da rai, yaran ka biyu da ka bari a wajan ta suna nan suna numfashi, ɗaya har tayi aure ma ta haihu, ɗayar tana nan ance itama an kusa bikin ta." Gaban Daddy ya faɗi sosai, ya kalli Abba yace, "da gaske ka ke? Ka ganta ne kai?." Abba ya girgiza kai yace, "tabbas na ganta, na kuma san inda take, amma ita bata san na san inda take ba, kuma bata san ina da rai ba har yanzu" ya faɗi haka dan yaji me Daddy zai ce. Daddy da hanzari yace, "to muje mu ganta mana, ina so na bata haƙuri akan abinda nayi mata wallahi. Nayi kuskure na kuma yi nadamar abinda na aikata, gwara mu je mu nemi afuwar ta kafin rai yayi halin sa." Abba yace, "Da gaske ka ke kayi nadama? Ni dai har zuciyata nayi wallahi, Allah ne shaida ta." Daddy yace, "Wallahi nima nayi, ai girma yazo yanzu, ko a da na faɗa maka na karɓi kuskurena balle yanzu. Duk abinda muka yi mata in aka yiwa yaran my haka ai bazan mu daɗi ba koda muna kabarin mu ne." Abba ya sauke numfashi yana girgiza kai yace, "hakan babu daɗi ko kaɗan, Akwai ciwo a yiwa ɗan ka abinda ka yiwa ɗan wani, akwai radaɗi da azabar da baza ka gane abinda nake cewa ba sai ya faru dakai." Daddy ya ce, "muje mu ganta yanzu ba sai anjima ba, saboda halin rai nake gudu kar na faɗi na mutu bata yafe min ba, muje duk hukuncin da zata yanke min a shirye nake da na ɗaukr shi. Na cutar da ita ni kaina na sani." Abba yayi shiru bai ce komai ba Daddyn ma yayi shiru suna tunain abinda ya faru a baya, jin abin suke a zuciyar su suna ji kamar a lokacin yake faruwa. Abba ya tashi tsaye yace, " indai ka shirya muje na raka ka inda Zahra take." Daddy ya goge hawaye idanun sa yace, "gabana faɗuwa yake sosai, amma dole na tunkari Zahra domin neman ya yafiyar ta da yafiyar yaran da na bar mata, na cutar da iya cuta mai muni har bana son tuna abinda ya faru." Abba ya murmusa kawai bai ce komai ba Daddy ya miƙe tsaye suka fito. Tare suka fito harabar gidan Huzaifa da Bebi suna tsaye suna tattauna batun Rumana, ganin sun fito ya saka suka ƙarasa wajan su, da mamaki suke bin su da kallo ganin duk yanayin su ya canja kamar ma kuka suka yi. Bebi ya ce, "Daddy lafiya? Me ya faru?." Daddy yace, "zamu je wani waje mu dawo, kar ku damu yanzu zamu dawo." Huzaifa yace, "To Daddy ba sai mu kai ku ba." Daddy yace, "ku bari muje da kan mu." Abba yace, "babu komai Alhaji Ali, su kai mu ɗin."  Ya kalli Abba yace, "taya zamu je dasu? Kar ka manta inda zamu je." "Ina sane, sanin hakan ne ya saka nace muje dasu. Huzaifa ku shiga motar mu je." Huzaifa ya shiga gaaba Bebi ya shiga mazaunin driver su kuma suna baya ya fita da motar. Sai bayan ya fita da motar sannan yace, "Abba ina zamu je?." Abba yace, "kai mu unguwar su Manal." Da sauri Bebi ya kalli Abba ta miror ya kalli Daddy ma nan take zuciyar sa ta fara bugawa zuciyar sa na zargin wani abun wanda bai kawo shi a zuciyar sa ba ko kusa. Har ƙofar gidan su Manal Abba ya suka je sannan yace su tsaya, Bebi ya kalli Huzaifa shima ya kalle shi kafin su ji Abba yace, "a wannan gidan take rayuwa." Tare suka kalli inda Abba ya nuna, Huzaifa bai san labarin ba amma Bebi shi nan take ya gano ƙarshen zancen dan har ga Allah da ake maganar abokin Abba ne bai kawo hakan a zuciyar sa ba. Bakin sa na rawa yace, "Abba, kenan Daddy shine....." kasa ƙarasa maganar yayi Abba ya buɗe motar ya fita shima Daddy ya fita. Suna fitowar daga motar suka tsaya a kofar gida, Bebi ya kasa fitowar daga motar ya ƙame ƙam a ciki ya kasa motsin kirki, shi kam Huzaifa bai gane inda maganar ta dosa ba tunanin sa me suka zo yi a gidan su Manal?. Da wannan tunanin ya fito daga motar shima Bebi ya fito da sanyin jiki ya ƙarasa inda suke Abba ya kalle shi yace, "Adnan kayi mana sallama da mutanen gidan." Waya Bebi ya ɗauka jiki a snayaye ya kira number Mubeena akayi sa'a ta ɗauka, sai da suka gaisa sannan yace, "in kina gida ki sanar da Mama zamu shigo yanzu, tare muke da baƙi." Ta amsa ya kashe wayar ba jimawa ta kira shi ya ɗauka jin abinda tace sai ya kashe ya kalli Abba ya ce, "Abba mu je." Da sallama suka shiga cikin gidan aka amsa daga cikin falon suka ƙarasa ciki tsoro da fargaba ya gama mamaye su, yayi da mamaki da bugawar zuciya ke tattare da Adnan. Da Abba suka haɗa ido kafin ta ɗauke ido ga  kalli wanda yake gefen sa shima kuma ita yake kallo cikin matuƙar mamaki. BDƘB3P20 Kallon sa Mama take yi kafin ta ɗauke kai ta sake kallon sa a lokacin ya cire glasses ɗin idanun sa shima yana kallon ta da matuƙat mamaki. Kallon Abba yayi a lokacin da suka shiga falon Abba ya ɗaga masa kai alamun itace dai ya sake kallon Mama da lokaci ɗaya fuskar ta ta sauya. Baba ne kawai suka gaisa dasu amma banda Mama da ta miƙe tsaye daga inda take. Baba ne ya kalle yace, “Fatima ina zaki je? Kina ganin ga baƙi sun zo wajan ki?.” Mama ta kalli Baba tace, “wannan ba baƙin da zan zauna nayi magana dasu bane, basu da wannan daraja da mutunci a idona da zan saurare su.” “Me kike cewa haka? Wannan wacce irin magana ce?” Baba ya faɗa yana kallon ta. Mama tace, “Bani da wannan lokacin” ta faɗa tana shiga ɗaki duk suka bita da kallo. Baba ya tashi ya bita ɗakin da ta shiga yace, “Haba Zahra meye haka? Wannan wanne irin hali kika ɗauko wanda a baya baki dashi?. Baƙi su zo ganin ki ki dinga faɗa musu wannan maganar? Kar ki manta akwai mahaifin Adnan a cikin su da shi kansa Adnan ɗin, kuma shi sirikin ki ne mijin ƴar da kika haifa.” “Ba shiyasa nace zan raba auren ba ka hana ni? Ba shiyasa nace Manal ta bar auren sa ba ka dage akan sai ta koma masa ba. Bazan taɓa ganin mutuncin sa ba har abada, da ya tashi sake zuwa sai yazo min da wanda na tsana bana son ganin sa har duniya ta tashi, bana ƙaunar sake kallon sa bana son tunawa da komai. Da ka barni na raba auren Manal da Adnan na tatatta ta mun bar garin nan ta yadda babu wanda zai san inda nake balle ya sake zuwa wajena, saboda Manal kawai nake zaune a garin nan sai kuma kai, amma wallahil azim da yanzu bama garin nan na jima da barin sa na koma inda babu wanda zai san inda nake. Wanda ya sanni a baya bana so ya sake ganina.” Baba yace, “waya shi wanda yazo miki dashi ɗin yanzu?.” Mama ta share hawaye ta tace, “kaje ka tambaye su, don Allah ka bani waje bana son magana.” Baba ya juyo ya fito yana kallon su da alama duk abinda ta faɗa sun ji. Abba ya kalli Baba yace, “wannan shine Aliyu.” Baba ya kalle shi ya girgiza kai yace, “na gano inda maganar ta nufa, kenan ta fahimci kaine na kuma gane ka shiyasa ta bar wajan nan.” Mubeena da take zaune a wajan da mamaki tace, “Baba meye ya sake faruwa? Waye wannan ɗin?.” Baba ya kalle ta ya kalli Ali da yake kallon Mubeena, nan take idanun sa suka yi ja dan ko ba a faɗa masa ba ya san ƴar sa ce, ga kama da Aysha nan ƙarara a kan fuskar ta. Baba yace, “Mahaifin ki.” Da sauri ta kalli wanda aka kira mahaifin ta ta sake kallon Baba tace, “mahaifina Baba? Taya zai zama mahaifina bayan Mama tace mahaifin mu ya jima da barin duniya?.” Baba yace, “Ta faɗa miki ne kawai, amma wannan shine asalin wanda ya haife ki.” Mubeena ta sake kallon Daddy tana sake maimaitawa abinda Baba yace mata kafin ta girgiza kai tace, “to Baba in ma da gaske shine mahaifin na mu me yazo yayi mana?.” Baba ya kalle ta yace, “wacce irin magana ki ke haka kema?, mahaifin ki fa nace miki?.” “Da gaskiyar ta ai, me yazo yayi mana?.” Baba zai yi magana suka ji murya Mama tace, “yanzu ba anjima ba bana son sake ganin wani a cikin gidan nan, don Allah a fita daga cikin sa bana son ganin wanda suka shigo” Mama ta faɗa tana sake komawa ciki dan ganin da take musu ji take kamar ta yi hauka saboda ɓacin rai. Daddy ya sauke numfashi ya kalli Abba da yayi shiru shima, Daddy ya kalli Mubeena da take kallon sa amma ya kasa cewa komai. Baba yace, “Alhaji Mu’azzam ku yi haƙuri, ku tazo mu koma waccan ɗakun mu tattauna a can, Ku yi haƙuri” ya faɗa yana kallon su. Daddy yace, “wannan ba abinda za’a bamu haƙuri bane, me akayi mana da za’a bamu haƙuri?.” “Duk da hakan muje mu yi magana.” A tare suka tashi zuwa ƙaramin falon baba jikin su a sanyaye. A falon Baba suka zauna Baba ya kalle su ya ce, “Alhaji Mu’azzam Ku yi haƙuri da abinda Mubeena da mahaifiyar ta suka yi, amma zan so ka sake yi min bayani yadda zan fahimta, tana magana a juye cikin fushin da ta jima da binnewa a zuciyar ta.” Daddy ya kalle shi cikin sanyin jiki yace, “in akwai abinda yafi fushi ya kamata ace Zahra tayi shi, bamu cancanci ta zauna damu ayi magana ba wallahi. Ni kunya duk ta rufe ni.” Baba ya sauke numfashi yace, “Kenan da gaske kaine mahaifin su Mubeena, kaine wanda na san labarin ka a bakin ta.” Ya girgiza kai yace, “ƙwarai ni ne, na san baka san labarina mai daɗi a bakin ta ba.” Baba ya girgiza kai yayi shiru bai ce komai ba dan bai san abinda zai ce ba, kan sa ya kulle gabaɗaya ganin abun yake kamar a mafarki. Baba ya sake kallon su yace, “Dani da ita da yaran ta duka tana ce mana ka rasu ne, a haka muka ɗauka gabaɗayan mu, a yanzun ma ba dan da Alhaji Mu’azaam kazo ba kafin na amince kaine mahaifin su gaskiya za’a ɗauki lokaci sosai. Amma yanzu na gasgata kai ne mahaifin su, kuma kazo kayi magana da ita ne ko?.” Daddy ya goge idanun yace, “nazo nayi magana da ita, domin akwai abubuwa da yawa da nake so na faɗa, ina so na bata haƙuri daga ita har yaran nata.” Baba yayi shiru bai ce komai ba Daddy yace, “Bani da idanun da zan iya kallon ta ni na sani, bani da bakin da zan yi mata magana ta amince dashi. Ta dauƙi yarda ta bani ni kuma naci amanar ta a lokacin da take matuƙat buƙatar kula daga gare ni, ban ji komai a lokacin da zan aikata ba, ban ji ɗar na tsoran yaudarar ta ba a ba sai bayan na aikata. Wallahi Allah ne shaida na neme ta daga baya amma ban same ta ba, amma yanzu ko me zance baza ta amince ba.” Baba ya sauke numfashi yace, “gaskiya a yanzu ko me zaka ce mata baza ta amince ba, a yanzu baza ta tsaya ayi magana da ita ba, a yanzu baza ta sake sauraron wanda zai yi magana da kai ba balle kai da kan ka. A kaf duniya babu abinda take tunawa take zubar da hawaye kamar wannan maganar, babu abinda take tunawa ta kwanta a gadon asibiti sai wannan. Tana yawan cewa da ana goge abinda ya wuce tabbas da ta goge abinda ya faru a rayuwar ta da kai, ba kai kaɗai ba ba hatta ƴan uwan ta na jini tace bata son sake haɗa ido dasu, magana da ita ba yanzu ba gaskiya, sai zuciyar ta tayi sanyi. Iya Alhaji Mu’azzam kawai ta gani ta tayar da hankalin ta har taso raba auren ƴarta da ɗansa ina kuma ga kai?.” Daddy cikin rauni yace, “na sani, hukuncin da ya kamace ni kenan daman. Ni ba mutum na gari bane a idon ta, ni ba mutum mai adalci bane a idanun ta, ni mutum ne mai son kansa wanda bashi da tausayi ko kaɗan. Ni naje har gidan su na karɓi auren ta na baro ta da asalin jahar ta da dangin na taho da ita inda nake, amma da na tashi barin ta banyi wani tunani ba na tafi na bara. Ban yi tunani abinda ta haifa a lokacin ba, dan a lokacin ƴar mu ta farko ma ƙaramar yarinya ce sannan ga ta biyu wacce ta kasance jaririya. Ban yi tunanin inda zata kwana ba, ban yi tunanin ina zata nufa ba, ban yi tunanin halin da zata faɗa ba,  ban yi tunanin babu wanda ta sani sai ni kawai….gaskiya ban cancanci ta haɗa idanu dani ba, na cutar da ita” ya faɗa yana sake cire glasses ɗin idanun sa yana share hawaye. Baba ya sauke numfashi  cikin sanyin jiki yace, “kar ka damu Alhaji Aliyu, zata saurare ka in sha Allah, amma ba yanzu ba sai dai abi komai a hankali.” Abba da yayi shiru tunda aka fara maganar yace, “in dai muna da tsahon rai zamu dinga bin ta har ta yafe mana dukkan mu, duk da mu ba mutanen kirki bane a wajan ta.” Baba yace, “Allah ya kaimu lokacin, Allah ya sassauta mata zuciyar ta, ku da ku ka yi nadama Allah ya yafe gabaɗaya.” Suka amsa da amin Daddy ya mayar da glasses ɗin idanun sa yace, “Mubeena itace Nusaiba?.” Baba yayi murmushi itace, “itace.” “Ina Fatima?.” Baba yace, “Manal kenan, itace matar Adnan a yanzu” ya faɗa tana nuna masa Bebi da yake zaune kansa a ƙasa kamar baya wajan. Daddy ya kalli Baba da mamaki ya kuma kalli Adnan ya sake kallon Baba ya ce, “kenan yarinyar da muka je barkar abinda ta haifa a matsayina na mahaifin abokin mijin ta itace Fatima?.” Baba yace, “Tabbas!, Itace fatima wacce muke kira Manal.” Daddy idanun sa suka sake cikowa da ƙwalla yace, “kenan abinda ta haifa jikana ne?.” Baba ya sake ɗaga masa kai yana murmushi tare da cewa, “ƙwarai kuwa, rashin sanin kenan.” Daddy ya dafe kai kawai ya fashe da kuka mai ciwo yana cewa, “ban cancani Zahra ta kale ni ba, wallahi ban cancanci ta haɗa ma idanu da ni ba. Bayan na auro ta na raba ta da dangin ta a lokacin da take ciki maraici, na kawo ta inda babu wanda ta sani, na zauna da ita na wani lokaci daga baya na kwashe kaf dukiyar da ta gada wajan iyayen ta na gudu bayan na sake ta. Na tafi na barta ba tare da nayi tunanin yaran da na bari tare da ita ba, banyi tunanin babu wanda ta sani sai ni ba, ban yi tunanin ina zata nufa ba, banyi tunani rayuwar ta da ta yaran ta ba. Abinda ya kai ni ga auren ta na samu na kuma tafi na barta a inda babu wanda ta sani ni. Yanzu kuma yara sun girma har ɗaya ta haihu kuma sai nazo bace nawa ne?, Ban isa ba” ya faɗa yana girgiza kai yana kuma zubar da hawaye. Abba ma kukan yake yi  sosai, Adnan da Huzaifa gabaɗaya jikin su ya gama yin sanyi ganin iyayen su maza suna kuka kamar yara ƙanana, sun kasa furta komai kan su yana ƙasa amma Allah kaɗai ya san abinda suke ji a zuciyar su. Adnan ne ya tafi ya fita dan bazai iya jure ganin hawayen mahaifin sa ba, ganin haka Huzaifa ma ya biyo bayan sa ya same shi a zaune a mota ya kifa kansa a kan sitiyarin motar. A mazaunin gaba ya zauna jiki a sanyaye ya ce, “Bebi na kasa fahimta abinda yake faruwa? Su waye su Manal a wajen Daddy? Wacece Maman Manal a wajan Daddy?. Ya akayi suka ana ta?. Sannan me yasa suke kuka akan abinda suka aikata?.” Bebi ya ɗago ya kalle shi bayan yayi ajiyar zuciya yace, “Mama matar Daddy ce a wasu shekaru da suka wuce, Manal da Mubeena duka ƴaƴan sane kuma ƙannen ka.” “Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un! Meyasa baka taɓa sanar dani ba sai yanzu?.” “Nima yanzu na san da hakan.” Huzaifa ya kasa cewa komai sai ƙirjin sa da yake bugawa sosai ya kalli Bebi da ya kulle ido ya buɗe yace, “Amma akace mahaifin Manal ya rasu.” Bebi ya kalle shi yace, “Yana nan da ran sa, gashi nan a ciki tare da Abba.” Huzaifa yace, “to me ya shigo da Abba maganar? Ya akayi suka haɗu har suka rabu? Meyasa bai sake waiwayon Maman ba har su Manal suka kawo wannan matakin?. Wacce dukiya Daddy yake magana a kai Bebi? Kaina ya kulle ka warware min abinda ban sani ba don Allah.” Bebi yayi murmushi mai ciwo yace, “zaka fahimta in lokacin ka fahimta ɗin yayi, yanzu ka cigaba da zama da kullewar kan har sai ka tambayi Daddy.” Hango su Baba suka yi sun fito suna ƙarasowa wajan motar hakan ya saka suka dakata da maganar, Daddy da Abba suka shiga motar bayan sun yiwa Baba godiya. Bayan sun shiga murya a dashe Abba yace, “Adnan mu tafi.” Kunna motar yayi ya tafi amma hankalin sa baya jikin sa shi kansa. Babu wanda yayi magana kowa yayi shiru tafiya kawai suke yi. Bebi yace, “ina zamu je?.” Abba yace, “mu koma gida.” BDƘB3P21 A harabar gidan su Bebi aka faka motar Abba ya ce, "mu wuce mu yi sallah sai mu shiga ciki." Haka kuwa aka yi sallah suka yi suka dawo cikin gidan suka zauna shi da Abba. Bebi Abba ya kira a waya yana ɗauka yace, "ka kira min kowa a cikin ƴan uwan ka, har Mimi da Farida in suna da damar zuwa a yanzu su zo ina son ganin ku." Bayan ya kashe wayar ne ya kalli Daddy yace, "gwara na nuna musu kai matsayin mahaifin Manal, na basu labarin komai da ya faru ya kamata komai ya zo ƙarshe ko zan huta da abinda yake damuna." Daddy ya kalle shi ya ce, "yanzu kai sirikina ne, ɗan ka yana auren ƴata, ko da yake ban cancanci kiran ta da ƴa taba." Abba yayi murmushin takaici tunawa da abinda ya faru tsakanin sa da Mubeena, zuciyar sa nayi masa ciwo sosai yanayin jikin sa duk ya canja. Daddy ya ce, "zuciyata bugawa take yi, dana sani da kunya lulluɓe ni suke yi, amma babu yadda zan yi abinda ya faru ya riga ya faru." Abba yace, "tun daga lokacin da na ganta ta ganni ban sake samun lafiya ba, ko yaushe zuciyata cikin zullumi take da tashin hankali." "Nima na san bazan sake samun lafiya ba, abinda ya faru a baya nuƙurƙusar ƙasusuwan jikina yake yi." Daddy ya sake cewa, "da wanne ido zan kalle ta balle yaran da basu sanni ba?, yanzu da wanne ido zan kalli yaran nan nace musu ni ne mahaifin su?, Mubeena har na barta ba fi shekara ɗaya ba, da wanne ido zan kalle ta nace ni na haife ta?. Meyasa na aikata hakan Mu'azaam? Meyasa na butulcewa amanar da aka bani?." Abba ya dafe kai idanun sa sun yi ja yace, "wannan duk ihu muje bayan hari, abinda ya faru ya riga da ya faru , yafiyar ya zamu dage mu nema koda zata dinga yankar naman jikin mu, inda hali mu koma Jalingo mu nemo dangin ta mu mayar musu amanar ta da suka bamu." Daddy ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "mun yi kuskure, mun tafka babbar asara, mun bar baya da ƙura, yanzu gashi yanzu mun dawo zamu share ƙurar da muka bari wacce zata bamu wahala matuƙa." Abba yace, "in aka yi sallar i'sha zan nuna musu kai matsayin mahaifin Manal." "Nima duka su taru na faɗa musu duka binda ya faru, kusuren da muka aikata, butulci da satar da nayi da komai ma." Ajiyar zuciya Abba yayi jikin sa ya sake gumewa da zazzaɓi.. Sai da akayi sallar i'sha sannan Abba ya kira kowa yace yazo har ƴaƴan Daddy da mahaifiyar su da suke wajan su Mama. Kowa tsoron ya kama masa zuciya na dalilin kiran, Huzaifa da Bebi ne kawai suka sani har su suka shiga aka zauna dan jin abinda za'a gabatar a wajan. Bayan kowa ya zauna duk suka bisu da kallo ɗaya bayan ɗaya sannan Abba yace, "na san kowa zuciyar sa tana cikin zullumi da ruɗanin wannan kiran, musamman iyalan gidan Alhaji Ali, zasu dinga mamaki daga zuwa baƙunta an haɗa meeting har dasu. Dalilin kiran na ku dukka ba komai bane illa na sake maimaitawa muku abinda na fa muku kwanaki, na san kun san wacece Manal matarAdnan a wajena, kun san labarin iyayen ta da komai na faɗa muku. Cikin ikon Allah labarin ya gama bayyana kansa, babu zato babu tsammani ƙarshen labarin yazo a lokacin da bamu yi tunanin faruwar hakan ba. A yau ga mahaifin Manal da Mubeena, abokina Ali wanda na baku labari sa, wanda na tsaya masa ya karmi auren Zahra mahaifiyar Manal matar Adnan kenan. Yau gashi a zaune a kusa dani" ya faɗw yana nuna Daddy da yake zaune. Kowa kallon Daddy yake yi ana kallon Abba da mamaki haɗi da al'ajabi, Yaya Isma'il ya ce, "Abba shine mahaifin Manal kenan?." Abba yace, "ƙwarai shine, shine mahaifin Manal matar Adnan da kuma Yayar ta Mubeena. Kaka a wajan ɗan da aka haifawa Adnan cikin kwanalin da suka gabata." A lokacin Daddy ya kalli Maman su Huzaifa da kansu ya kalle suna buƙatar ƙarin bayani, yace, "Eh, gidan Adnan da muka je barka matar sa ƴata ce, bayan ita akwai Yayar sunan ta Mubeena." Mama kallon sa take yi cike da mamaki tace, "ban gane ba, ban fahimci maganar sosai ba zaka iya min bayani yadda zan gane?. Yauhe ka aure ta har ta haihi kamar su ban sani ba?." Daddy yace, "Gaskiyar maganar kenan, abinda kika ji shi ne gaskiya kuma ya faru. Na auri mahaifiyar su Manal a lokacin da nake yawon zuwa gari-gari domin kasuwanci, na tare da ita a garin Zaria kina wani wajan daban tana wani wajan daban, baki san ta bata san ki ba gwara ita ta san akwai ki amma ke baki san akwai ta ba. A haka muka haifi yara biyu da ita kafin na barta mu koma Abuja dake." Mama kallon sa take yi mamaki ya hanata magana, gani take kamar labari yake bata ko kuma raina mata hankali yake yi. Ganin hakan Daddy ya ce, "zan warware muku duk abinda ya faru yanzu" ya faɗa yana fara basu labarin da Abba ya bawa su Adnan har ƙarshe. Ya shafe hawayen idanun sa ya ce, "Zahra bata da kowa sani, ni kaɗai ta sani domin ko dangin babar ta bata sani ba, saboda kyaun da take dashi dangin ta suka tsane ta daga ita har mahaifiyar ta. Na karɓi auren ta duk da nasan bata da uwa bata da uba, da taimakon abokina gashi muka karɓi auren ta babu bincike babu komai aka bani ita na dawo da ita Zaria. Allah ya sani a zuciya ba niyar zama da ita na aure ta a farko, amma da naga tarin duniyar da aka haɗo ta da ita sai tuannina ya canja gabaɗaya. Da farko Mu'azzam bai goyi bayana a kan hakan ba, amma daga baya ya bani goyan bayan ɗauke kadarorin da ta gada wajan uwa da uba ɗari bisa ɗari." "Ta yarda dani, ta bani dukkan kadarar ta wacce ta mallaka masu yawan gaske, dan ko zunzurutun kuɗim da aka bata suna da yawa sosai balle kadarar. Mun fara zama na wasu lokaci, babu yadda Mu'azzaɓ bai yi ba akan na faɗa miki maganar Zahra amma naƙi, ƙarshe da ya dage sai na faɗa miki sai nace ai na sanar sake bayan baki san labarin ta ba, ita dai ta sanki a baki ta kuma san Huzaifa a baki. Saboda barin ta ita kaɗai a gida tana kwana in ya kasance bana gidan ya saka na samu gidan haya mai mutane biyu, tana jin motsin mutane kuma babu abinda zai same ta ba a sani ba." "Nayi amfani da wayo da dabara wajan kawar miki da hankali dan kar ki gane ina da wata matar musamman ta hanyar yadda nake kwana a gidan, cikin ikon Allah baki gane ba. A lokacin kuma kika haifi Aysha ita kuma ba jimawa ta haifi Nusaiba. Matar da suke gida ɗaya itace ta kula da ita soaai, tayi mata komai cikin ƙauna saboda mace ce wacce take da haƙuri da kirki sosai. Tazarar haihuwar Nusaiba da Fatima shekara ɗaya da rabi ne ta haifi Fatima, ni kuma a lokacin ina kan tattara dukiyar ta ina siyarwa saboda gabaɗaya a Jalingo suke." Daddy ya sauke ajiyar zuciya yayi shiru kafin yace, "Sai bayan na gama komai a lokacin Fatima bata fi wata bakwai zuwa goma ba, na rubuta takardar saki na ajjiye mata bayan na faɗa mata ƙudurina a kanta. Saɓanin da muka samu da Mu'azaam akan kuɗin ne, yaƙi karɓar wanda na bashi saboda ya yi masa kaɗan ni kuma sai nace bazan ƙara ba shi kuma yace baya so, daga wannan lokacin muka raba hanya bamu sake haɗuwa ba ko a mafarki sak yanzu, dan daga wannan lokacin Abuja muka koma da zama kafin arzuƙi yayi nisa mu koma ƙasar Qatar da zama." Daddy ya kalle su gabaɗaya kowa ya nutsu yana sauraren sa  ya ce, "na barta ban san a yanayin da take ciki ba, na kwashe komai nata ban bar ko ɗaya da ya rage ba, na tafi na barta da yara bayan na san ni  ne kawai wanda take dashi a duniya. Na manta da amanar ta na karɓa daga gidan su, na manta da marainiya ce, na manta da rana irin wannan, na manta da cewa haƙƙin ta bazai taba barina naji daɗi ba. Amma daga baya na koma, bayan shekaru biyu na koma don na ganta amma...." Mama mahaifiyar Huzaifa ya dakatar dashi tace, "daga baya ka koma kayi mata ne? Ka koma ka ƙarasa kwashe abinda baka kwashe ba?" Ta faɗa murya na rawa da alama kuka zata yi. Daddy yayi shiru ya sunkuyar da kai ƙasa Mama ta kalli su Mummy da Mamy ta sake kallon Daddy tace, "amma kaji kunya wallahi, marainiyar yarinya tun a lokacin baya ka wulaƙanya haka, daman akwai irin ku tun duniya na kwance, daman akwai irin ku a zamanin da yafi na yanzu tsafta?." Huzaifa ya kalle ta yace, "Mama don Allah" ya faɗa yana mata alamun tayi shiru. Shiru falon yayi babu wanda yake magana saboda abinda suka ji wanda ya taɓa musu zuciya, Mamy ce tace, "ku yi haƙuri dukkan ku, amma gaskiya baku cancanci yafiya daga wajan Zahra ko ahlin ta ba, tayi matuƙar ƙoƙarin da ta bar Manal tana auren jinin ku, tayi ƙoƙari da ta iya haɗa zuri'a da ku." Bebi ya kalli Mamy da alamun don Allah tayi shiru tace, "bazan shiru ba Adnan, su basu ji kunyar abinda suka aikata ba bazan ji kunyar faɗar gaskiya ba. Wallahi in nice ita ƙafar ku na gani a inda nake kotu ce zata raba ni daku." Mummy da take zaune ta kalle su tayi murmushi takaici tace, "yanzu kana sane da cewa dukiyar da ka tara, da komai da ka mallaka nata ne?" Ta faɗa tana kallon Daddy. Daddy yayi ajiyar zuciyaAjiyar zuciya ya kalli Abba yace, "ko a shekarun da suka wuce a lokacin iya kuɗin da bar mata sun fi naira miliyan biyar, kasancewar lokacin babu banki a buhu aka shirya mata, naira miliyan biyar ɗin da wacce a yanzu ta tafi miliyoyi masu yawa, banda gidaje da filaye da gonakin da aka siyar." Abba ya girgiza kai kawai bai ce komai ba Daddy ya kalle su ya kalli Mamy yace, "Me ma kika ce?, Bamu cancanci yafiya ba ko? Nima na sani, nasan bamu cancanci a yafe mana ba. Kuskuren da muka aikata baza mu taɓa goge shi ba, mun ci amanar yarda da amincewa, Mun kuma cutar da marainiya." Yaya isma'il yace, "kuskure an yi shi Daddy, an aikata kuskure sosai fiye da tunanin mai tunani. Amma in sha Allah zata yafe komai ya wuce kamar bai faru ba, Sai an bi komai a sannu an nemi yafiyar Allah ba iya ta ta yafiyar ba." Abba yace, "ta ina komai zai wuce? Komai bazai wuce ba isma'il." Shiru ya biyo baya babu wanda ya sake magana a cikin su, kowa da irin abinda yake zuciyar sa wanda yake tunani. wayar Bebi ce take ƙara ya ɗauko ya duba ganin Manal ce sai ya mayar da wayar ya ajjiye bai ɗauka ba, Daddy ya kalle shi sai  ya kulle ido ya buɗe bai ce komai ba. Fitowar suka yo daga falon masu kuka suna kuka masu ƙunar zuciya suna jin raɗaɗin a ransui Abba da Daddy dai sun jima a cikin suna magana kafin Daddy ya fito sauran matan su fito su hau mota su tafi kowa jiki a sanyaye kamar an yi musu dukan tsiya. Bebi wajan Mama ya shiga ya same ta a zaune da yaran ta mata ko wacce yanayin fuskar ta zaka kalla ka san abinda suka ji ya shiga ran su, ya kalli Mimi da Farida yace, "baza ku tafi bane?." Yadda yayi maganar ma tausayi ya basu Farida tace, "yanzu zamu tafi." Ya kalli Mama yace, "zan wuce gida Mummy, ki tabbatar Rumana ta sha maganin ta." Mama ta girgiza kai tace, "to Allah ya kiyaye hanya. Amma Adnan magana ta gaskiya ko; ko nice mahaifiyar su Manal sai na raba auren ku, domin ba zan bar ƴata tana auren ɗaga irin mahaifin ku ba." Kallon Mama yayi fuskar sa babu walwala kana gani kasan yana da damuwa sosai, kamar zai magana sai kuma ya fasa yayi murmushin yaƙe, Mama tace, "ban san a shekarun baya akwai macuta irin iyayen ku ba." Bebi ya sauke kai ƙasa ya sake kallon Mama yace, "Sai da safe, Mimi ki kira mijin ki wuce gida ita waccan ta saba" ya faɗa yana fita bai sake cewa komai ba amma zuciyar sa mugun bugawa take yi sosai, tashin hankalin sa yafi ko yaushe dauriya kawai yake yi. BDƘB3P22 Lokacin da ya shiga cikin gidan babu kowa a falon har nata falon bai ji motsi ba alamun sun kwanta kenan, bai shiga ciki ya shiga ɗakin sa yana cire lins ɗin jikin rigar sa tare da cire agogo ya ajjiye. Buɗe ƙofar aka yi aka shigo ya kalle ta itama shi take kallo tace, "Sannu da zuwa." Maimakon ya amsa sai ya zuba mata ido yana kallon ta yana so ya ga ko tana kama da ƴan gidan su Huzaifa ko Daddy, kallon ta yake yi har ta tsargu bai ga kama da kowa a cikin su ba dan ita da Maman ta take kama gabaɗayan ta. Kallon sa take yi cikin mamakin kallon da yake mata tace, "Lafiya?." Ɗauke kai yayi daga kallon ta ya ce, "na jima ko? Muna tare dasu Abba ne da Daddy shiyasa." Manal tace, "sannu da zuwa, abinci fa?." Ya girgiza kai yace, "ƙyale abincin nan bazan ci ba." "Amma yau gabaɗaya baka ci komai ba." "Naci ɗazu tare dasu Huzaifa." Ta matso kusa dashi tace, "Shikenan baza ka kuma ci ba?." Ya kalle ta yace, "bana jin zan iya gaskiya, ki saka a fridge gobe sai a bayar dashi tunda dare yayi" ya faɗa yana wuce ta ya shiga banɗaki. Zama tayi a kan stool ɗin da yake gaskiyar ɗakin, tayi shiru tana tunanin abinda yake damun sa haka duk yabi ya canja ko abinci baya ci sosai. Tana nan zaune ya fito ya shirya ya samu waje ya zauna, ya ɗauki wani littafi yana dubawa wanda yake dauke da hoton zuciya a bangon sa. Shiru yaji  tayi bata ce komai ba sai ya ɗago ido ya kalle ta yaga shi take kallo ya ajjiye littafin shima ya zuba mata yana kallon ta bai ce komai ba ita bata ce ba. Katse shirun tayi ta hanyar cewa, "akwai abinda ka ke so ka faɗa min ka ƙi ka faɗa min, tun ɗazu na lura da hakan amma kace babu komai." Jin abinda tace ai ya tuno da maganar Rumana dan maganar Daddy ta danne ta ta, ya kulle ido ya buɗe yaji ta zauna kusa dashi tace, "baka son faɗa min damuwar tunda nazo gidan nan a matsayin matar ka, in zan tambaya sau ɗari baza ka faɗa min damuwar ka sau ɗaya ba. In baka faɗa min damuwar ka ba wa zaka faɗawa? Ni ce a kusa dakai yanzu sama da kowa, ko kana ganin bani da hankalin da zan iya baka shawara akan abinda yake damun ka?." Ya girgiza kai ya ce, "A'a ni ban ce haka ba, babu abinda yake damuna ɗin ne shiyasa ban faɗa miki ba." Manal ta yi murmushi tace, "Hmmm haka kake cewa daman ai, ko yaushe kace babu abinda yake damun ka bayan kuma a zahiri ana ganin ka an san kana da damuwa. Shikenan Partner, bazan sake tambayar damuwar ka ba, kayi haƙuri tunda baka so naji na daina tambayar ka, na daina tambaya balle kace min babu naji haushi" ta faɗa tana niyar tashi, ya riƙo hannun ta ya dawo da ita ta zauna. Ya kalle ta yace, "Kar ki canja min magana don Allah, babu abinda yake damuna in akwai kece ta farko da zan faɗawa. Kar wannan tunanin ya shiga zuciyar ki in kika ce haka baki min adalci ba." "Ka taɓa faɗa min damuwar ka ne? Ka taɓa buɗe baki kace min ga abinda yake damuna?. Ko yaushe ce min ka ke yi babu kuma wallahi akwai, Kaga tambayar bata da amfani tunda nice baka so na sani." Ya kalle ta ya riƙe fuskar ta da hannun sa yace, "in akwai babu abinda zai saka na ɓoye miki my life partner. Ni yau wani na gani mai matuƙar kama dake." Jin ya canja maganar sai ta share shi itama bata ce komai ba. Yayi murmushi yace, "Haba partner meye na fushin kuma?." Ta kalle shi idanun ta a buɗe tace, "ni fushi nayi? Akan me zanyi fushi to?." Yadda tayi magana tana juya idanun ta sai yayi murmushi ya yiwa idanun nata kiss yace, "Wannan ido suna da kyaun gani." Nan ma tayi masa shiru bata ce komai ba ya sake cewa, "Seriously yau naga mai kama dake Manal, kuma babban mutum ne har nake tunanin anya ba mahaifin ki bane ba, har zan je na yi masa magana dan na san zaki murna in kika gan shi, Sai kuma na fasa saboda Abba yana kira na lokacin." Manal ta taɓe baki tace, "gwara ma da baka je ba." Ya kalle ta yace, "Meyasa?, kefa ki ka cemin kina son ganin mahaifin ki." "Yanzu bana so. Kuma lallai ne dan ya kasance muna kama sai ya zama maahifina?." "Kama fa sosai na gani, ko ba mahaifin ba kuna da alaƙa ta jini dashi." Kafin tayi magana yace, "bana shakka ma mahaifin ki ne, kuma zan je na nemo shi ko dan ke." Manal ta kalle shi tace, "wallahi kar ka fara, haka aka ce maka ina da buƙatar ganin maahifina ne?." Da mamaki yace, "haka kika ce min mana, kin manta muna tafiya a mota kika ce kina so ki ganshi?." "Yanzu bana so wallahi, bana so ko kaɗan." "bakya son ganin sa?." "Ko a mafarki kuwa, shi yanzu in ma aka nuna masa ni akace ni ƴarsa ce sai ya kalle ni matsayin wacce ya haifa?." Bebi yace, "to me zai hana? Ba mahaifin naki bane." Manal tace, "amma akwai rashin ta ido ma a cikin abun, ya tafi ya bar mu a wajan mahaifiyar mu bayan ya kwashe dukiyar ta bai yi tunanin daga inda ya karɓo ta ba, bai yi tunanin bata da kowa sai shi ba, bai yi tunanin halin da ya barta ba, bai yi tunanin a inda zamu rayu ba. ya tafi sama da shekaru masu yawa yanzu kwatsam sai ya dawo yace mu ƴaƴan sa ne?." Kallon ta yake yi kafin yayi magana tace, "bai san komai namu ba ya tafi ya bar mahaifiyar mu da wahalar mu, bai san ci da shan mu ba, karatun mu da suttura, tarbiyya da kula damu duk bai sani ba, rana ɗaya sai yazo yace ai shine ya haife mu?." Bebi yace, "to ai ba ƙarya bane shi ɗin ne ya haife ku." "Shi ya haife mu kuma ya bar mu ba, ya haife mu ya tafi ya barmu tunda ya samu abinda yake so. To yaje ya sha zaman sa da shi da iyalan sa wanda ya zaɓa ya kuma gina rayuwar su da dukiyar Maman mu, mu kuma ya bar mu mu cigaba da rayuwa yadda muka saba, babu shi a rayuwar ba babu abinda muka fasa sai cigaba ma da mu ke yi." Bebi ya tausasa murya ya ce, "Manal Mahaifi ne fa." A ɗan fusace tace, "shi din fa, ina ruwana dashi? Muna da Baba ai, yayi mana abinda har ya mutu bazai yi mana kwatankwacin sa ba. Maman mu ta rayu babu uwa, babu uba, babu dangin uwa, babu dangin uba, babu yaya, babu ƙanwa, babu uban yaran ta. Ta rayu duka babu waɗannan a gefen ta sai mijin da Allah ya bata mai jin ƙai, sai kuma maƙociya da take da ita kamar ƴar uwa. Ita ta rayu babu waɗannan jigogin a gare ta ta rayu kuma lafiya lau har ta kai ga aurar da ƴarta lafiya ba tare da wata damuwa ba. Mu kuma dan kawai babu mahaifin mu sai mu kasa rayuwa?. Ina da uwa, ina da uba, ina da Yaya, ina da kai kuma, to me zai dame ni?. Wallahil azim har addu'a nake yi yanzu akan kar Allah ya haɗa fuska ta da ta mahaifin mu in yana raye, in kuma ya mutu Allah ya jiƙan sa, amma fatan haɗuwa dashi ko dangin Mama bana yi saboda na tabbatar daga ranar Mama ta haɗa ido dashi ko dangin ta babu lallai ta kwana lafiya, ni kuma wannan shine babban abin baƙin cikina, ba kuma zan yafe musu ba, lokaci ɗaya tsanar su zata yi min dirar mikiya a zuciyata." Ganin yadda take maganar a fusace kuma har zuciyar ta maganar take fitowa sai ya tausasa murya yace, "duk abin bai kai haka ba ai, ita rayuwar nan da muke ciki ba dan Allah yana yafe mana laifin da muke yi masa ba da dukkan mu bama doran duniya, Allah da ya halicce mun yi masa laifi ya yafe mana balle kuma ɗan adam ɗan uwan ka? kuma mahaifin ki ne duk da wannan abubuwa da kika lissafi biyayya a gare shi a wajan ki, ba dan komai ba sai dan albarkacin sunan mahaifi a wajan ki." Manal tayi ƙaramin tsaki tace, "balle ma baza mu haɗu ba har abada balle hakan ta kasance, ni Wallahi gabaɗaya ka ɓata min rai da maganar nan" ta faɗa fuska a ɗaure tana kawar da kai gefe. "To Manal meye na ɓacin ran? Abu ne wanda zai faru a yanzu ko nan gaba." "Bana wannan fatan, bana so ganin sa ya sha zaman sa a inda yake mu ma muyi zaman mu a inda muke." Ya sauke numfashi yace, "hmm Manal kenan." Ta kalle shi tace, "Wai me ya kawo wannan maganar?." "A jikina nake ji kamar mahaifin ki ya kusa nuna kansa." "To ka daina jin hakan, bana so wallahi. A yadda nake jin zuciyata ba dan kai ne ka ke min zancen sa ba wani bai isa yayi ba. Don Allah kaima ka bari haka." "Shikenan na bari" ya faɗa yana riƙe hannun ta. Miƙewa tsaye tayi tace, "zan je na kwanta dare yayi sosai." Ya kalle ta yana daga zaunen yace, "ki kwana a nan." Ta girgiza kai tace, "Mama fa tana nan, kawai sai ta farka bata ganni ba?." "Ai ta san inda ki ke, kuma ita Mama bata ce kar ki kwana a wajena ba ko?." Manal ta turo baki tace, "eh bata ce ba, amma dai..." katse ta yayi yace, "please Partner ki kwana a nan." Ta kalle shi tace, "To Ayan ɗin fa? Anytime zai iya farkawa." "Sai mu dawo dashi nan." Tayi shiru tana kallon sa alamun tunani yace, "ki ɗauko baby bed ɗin nasa ya kwana a nan." Ta sauke ajiyar zuciya ta fita ya bita da kallo yana jinjina lallai za'a sha artabu da ita akan Daddy, amma yasamn zata yi sanyi da zarar ta tabbatar da mahaifin ta shine mahaifin Huzaifa, Tabbas Daddy zai ci albarkacin Huzaifa a wajan ta da wajan Maman ta. Da Ayan ɗin ta dawo a hannu ya tashi tsaye ya karɓe shi ya kwnatar dashi a kan gadon yace, "ina nashi gadon?." "Bana so Mama ta farka shiyasa ban ɗauko ba" ta faɗa tana zama a gefen gadon. Kwanciya tayi a gefe ya kashe hasken ɗakin ya kwanta a gefe shima ya zama Ayan ɗin yana tsakiya ya matsa kusa shi yana kallo yana wasa da kumatun sa. Tashi taga yayi ya ɗauke Ayan ɗin ya mayar dashi bayan sa ya yi masa makari da filo, ya matso kusa da ita ta kalli Ayan ta ce, "ya zaka mayar dashi baya in ya faɗa fa?." "Bazai faɗa ba, baki ga na kare shi ba?." "To sai kayi bacci ka danne shi? Nidai ka dawo dashi kusa dani yayi min nisa." Jawo ta jikin sa yayi yace, "shi bakya so yayi miki nisa ni kuma kina so nayi miki nisa ko?."  Kafin tayi magana ya kuma cewa, "saboda shi ke kika haife shi ko?, kin fi ji dashi a kaina?." Ta kalli idanun sa ta turo baki gaba tace, "to shi fa jariri ne, kai fa?.". "Nima jariri ne a wajan ki, in kika so zaki mayar dani kamar shi." "Kamar shi? Shifa baya cin abinci ka manta ne?." "Nima sai na daina ci, na koma shan abinda yake sha." Ta wara idanu waje tace, "eyee!." Ya ɗaga mata gira yace, "uhum" ya faɗa yana haɗa fuskar sa da ta ta. Tayi dariya tace, "kace zaka zuƙe ni ne kawai." "Shi Ayan ɗin ya zuƙe ki?." "To kai dashi ɗaya ne?." "Ɗaya ne mana, ni na fishi ma dan ni ɗan kaɗan zan dinga sha." Tayi dariya tace, "ban yarda ba." "Ni kuma na yarda daga yau za'a fara, bara ki ga." Da sauri ta riƙe hannun sa tace, "A'a don Allah, yi haƙuri dai." "Yau bakya so?." Ta kalle shi ya ɗaga mata gira yace, "ki bani amsa, yau bakya son na...." Ta rufe masa baki da hannun ta tana girgiza kai. Yayi dariya ya cizi hancin ta yace, "matsoraciya." "Uhum naji ɗin." "I missed you" ya faɗa yana sake riƙe ta sosai a jikin sa. Ta riƙe shi itama tace, "duk da ba wani sosai nayi kewar ka amma dai nayi." Yayi dariya yace, "mai ƙarya..?." Bata ce komai ba ta kwanta a jikin sa tana dariya  ya riƙe ta yana sauke ajiyar zuciya. Rumana ke zuwa zuciyar sa da maganar Daddy, bai san ya zai yi da batun Rumana ba, Allah ya sani baya buƙatar a tarwatsa masa farin cikin gidan sa, dan furtawa Manal zai auri Rumana daidai yake da lalata farin cikin gidan sa. Sai asuba Manal ta koma ɗaki duk kunya ta ishe ta suka gaisa da Mama bata ce mata komai ba sai karɓat Ayan da tayi tace, "Sarkin haƙuri wani lokacin sarkin rigima, ki canja masa pampers ɗin jikin sa." Manal ta amsa da to ta ɗauko pampers ɗin amma ta kasa saka masa, Mama tayi dariya tace, "ai kuwa ke zaki saka masa, bazan karɓe shi ba anjima ma ke zaki yi masa wanka." Manal tayi dariya tace, "Allah yasa kar na shaƙa masa sabulu a hanci." Mama tayi dariya tana nuna mata har ta saka masa sannan ta kwanta itama Maman ta kwanta. Sai kuma Ayan ɗin ya farka yana kuka, Manal ta tashi ta fita dashi falo yana kafaɗarta yana jijjiga shi amma yaƙi shiru, ta zauna ta bashi nono amma yaƙi yayi shiru duk ta ruɗe. Adnan ne ya fito har ya shirya da kofi a hannun sa yana shan yourgut. Ganin ta a ruɗe gashi yana kuka ya ƙaraso ya karɓe shi yace, "lafiya yake kuka?." "Nima ban sani ba, yaƙi yayi shiru kuma." "Ko bashi da lafiya?" ya faɗa yana duba jikin sa har lokacin kuka yake sosai. Manal ta ruɗe kamar zata yi  kukan ita tace, "ban sani ba." "Ba yunwa yake ji ba kuma?." "Yaƙi karɓa, Sai kuka yake yi." Mama ce ta fito da hijjabi a jikin ta jin muryar Adnan ya saka ta sako hijjabi, tace, "rigima ce irin tasa, kawo shi" ta faɗa tana karɓat sa a hannun Bebi ya gaishe da Maman ta amsa kafin yace, "Mama anya ba wani abun ne yake damun sa ba?." Mama tayi dariya tace, "Lafiya lau yake wallahi, gashi yayi shiru." Mama ta kalli Manal tace, "shiyasa nace miki zan dinga bar miki shi, rainon nashi ne baki iya ba shiyasa yake wannan kukan" ta faɗa tana shiga ciki. Manal ta sauke numfashi ta dafe kai tace, "duk ya ruɗa ni." Bebi yace, "Lallai duk ranar da Mama ta tafi za'asha aiki, mata kuma iyaye zasu yi aiki." Ta kalle shi yayi murmushi ya ɗauki  glass cup ɗin sa yace, "zan fita." "Baka yi break b?a." Ya nuna mata cup ɗin hannun sa ya ce, "wannan ya isa." "Kwana biyu baka son cin abinci, ka tsaya na kawo maka, akwai doya da kwai ta jiya sai na yi warming." Hararar ta yayi yace, "ke ni fa ke kaɗai za'a yi warming a kawo min na ci, amma in ba ke ba bana cin abu jiya na maimaita shi yau." Manal tace, "to ni abinci ce?." Numfashi ya sauke yana kallon idamun ta ya zuba hannayen sa a aljihu yana yi mata kallon ƙasa-ƙasa tare da lashe lips ɗin sa. Dariya tayi ta rufe ido da hannun ta dan ta fahimci mai hakan yake nufi, idanun ta a rufe tace, "Ashe nima sai an ɗumama ni kenan?." Yayi ƴar dariya ya kalli ɗakin da Mama ta shiga ya sake kallon Manal yace, "ke ai ko kwana dubu ki ka yi ko babu warming i will enjoy it" ya faɗa yana kashe mata ido. Dariya tayi tana girgiza kai tace, "ashe iyayin naka bai yi nisa ba, na ɗauka har ni ai." Yayi dariya tare da girgiza kai yace, "wato kin haihu yanzu kin yi free ko?, saboda kina ganin har yanzu baki da tsarki ko?, Shikenan zan kama ki" ya faɗa yana ƙarasowa ya yi mata kiss a goshi ya juya ya fita. Yana fita gida yaje wajan Abba amma sai ya tarar duk gidan bacci suke dan lokacin ko tara na safe bata yi ba. Yana niyar fita daga falon Mama Rumana tace, "Ina kwana Yaya Adnan." Kallon ta yayi ta zuba masa ido saboda yayi kyau cikin black ɗim suit mai kyau da laushi yace, "Lafiya Ruman, ya jikin ki?." Rumana tace, "lafiya lau. Ya Babyna Ayan?." "Yana Lafiya lau." "Nace ka turo min pictures ɗin sa bqkq turo min ba. yace, "bani dasu, amma zan tura miki." Tayi murmushi tace, "zan faɗawa Mummy ka shigo in ta tashi." Ya amsa ya fita ta bishi da kallo tana dafe zuciyar ta saboda bugawar da take yi. Asibiti ya wuce ya shiga office ya fara abinda yake gaban sa. Suna da treater ta dashen zuciya ƙarfe sha ɗaya na rana hakan ya saka shi gama yin komai da wuri, wayar sa ma a office ya barta suka shirya dashi da team ɗin ranar aka shiga don aiwatarwa. Suna fitowa lokacin sallar azahar yayi ya hau sama zai shiga office kenan ya haɗa da Huzaifa, Adnan yace, "Ashe ka zo?." Huzaifa yace, "na zo kun shiga treather." Bebi yace, "yanzu muka fito sallah nayi na dawo nan, yunwa nake ji sosai." Huzaifa ya kalle shi yace, "Muje office to akwai abinci da nazo dashi sai kaci, dan ni na kasa ma ci wallahi." Tare suka shiga office ɗin nasa Huzaifa ya ajjiye masa abincin doya ce da kwai  da plantain sai sauce a gefe. Huzaifa ya kalle shi yace, "yanzu Bebi da gaske abinda yake faruwa gaskiya ne? Daddy shine mahaifin su Manal?." Bebi da yake ƙoƙarin fara cin abincin ya kalle shi ya ce, "gaskiya ne mana Huzaifa, wannan ai ba ɓoyayyen abu bane ba ne, abu ne a bayyane." Sallama Hamza yayi ya shigo ganin su su biyu sai ya tsaya daga bakin ƙofa yace, "okay na dawo." Huzaifa yace, "ka shigo mana." Ya shigo yana cewa, "ai naga kamar kuna tattaunawar sirri ne." Ya zauna Huzaifa ya kalli Hamza yace, "wani abu ne yake damuna ko nace yake damun mu Hamza." Hamza yace, "to ina jin ka." "Manal ɗin Bebi Daddy mu shine mahaifin ta, shine jinin ta wanda yayi silar ta zuwa duniya." Hamza da mamaki yace, "ban gane abinda ka ke faɗa ba." Huzaifa yace, "ya kamata ka gane, abinda nake nufi kenan, jiya an tabbatar da mahaifina shine mahaifin ta." Bebi ya kalli Huzaifa dan Hamza ya kasa magana yace, "ya ka baro Daddy? Ko Baka je ba?." "Naje, yana nan kwance ina jin ma bashi da lafiya. Gabaɗaya  yanayin sa ya canja ba shi kaɗai ba kowa na gidan." Hamza yace, "Nifa kun barni a duhu." Bebi ya kalle shi yace, "zaka fito haske in an baka labari, amma yanzu ka cigaba da zama a duhun ka, abinda Huzaifa ya faɗa maka kuma gaskiya ne." Huzaifa ya kalle shi ya fara bashi labarin duk abinda ya faru kamar yadda aka faɗa masa, duk da a taƙaice ya bashi labari bai kuma faɗa masa zancen dukiyar Mama ba. yana gama faɗa yace, "wannan shine abinda ya hana mu zuwa jiya, ta yadda ma za'a fahimtar da Maman su Manal ɗin shine aiki." Hamza ya girgiza kai cikin wani irin yanayi yace, "Allah gwanin hikima. Wato shiyasa Allah bai saka maka son Manal a zuciyar ka ba tun farko, Sai ya saka maka tausayin ta kamar ƴar uwar ka ashe ƙanwar kace ta jini. Da ace yanzu kaine ka ke auren ta har da yaro da labarin ya sake canja salo." Huzaifa yace, "har ka saka gaba ya faɗi, bari kawai." Bebi baice komai ba yana goge hanun sa da tissue tare da shan ruwa, Huzaifa ya kalle sjk yace, "Ka sanar da Manal ɗin ne?." Ya girgiza kai alamun a'a yace, "ɓata baki ne in na faɗa mata, Manal duk abinda Maman ta take so shi take so, in Mama ta karɓi Daddy ta kuma ce komai ya wuce Manal zata kalle shi matsayin mahaifi. In kuma akasin haka ya faru Manal baza ta tanƙwaru ba a yanzu." Wayar Huzaifa ce take ƙara ya kalla sai yace, "kaga Manal ɗin ce take min waya." Bebi yana kallon sa ya ɗauka ya saka a speaker Manal tace, "Yaya Huzaifa ina wuni? Don Allah in kuna tare da Partner ka faɗa masa Mama babu lafiya na fita na tafi asibitin, ina ta kiran wayar shi bai yi picking ba" ta faɗa a haɗe ba tare da ta bari ya amsa gaisuwar ba. Huzaifa ya kalli Bebi da yake kallon sa sai yace, "Shikenan zan faɗa masa in sha Allah, a wanne.....!" Kafin ya ƙarasa tambayar ta sunan asibitin ta yanke wayar.  Huzaifa yace, "Allah yasa ba maganar jiya bace zata tayar mata da ciwon ta." Bebi ya miƙe yace, "Allah dai ya kiyaye kawai, bara na kira ta naje asibitin tunda an faɗa min." Huzaifa yace, "nima zani bara na sakko." Tare suka fita su ukun dan shi Hamza yana da marasa lafiyar da zai gani da shima zai je. BDƘB3P23 Manal lokacin da suka shiga asibitin Mubeena ce ta faɗa mata inda suke ta shiga ɗakin da Maman take, ɗakin mai mutane biyu ne a ciki, wata mata tana kan gadon ta kwance sai kuma gadon Mama. Ganin Maman tayi a zaune tana cin salad tayi turus Maman su Surayya da take bayan Manal tace, “ashe jikin da sauƙi.” Mama ta kalle su tace, “Balaraba daman ba wani ciwo bane ba, Mubeena ce ta nace sai mun zo asibitin dan a nan muka kwana.” Mubeena tace, “Wallahi Mama da daddare jikin ta zafi yayi, har rawa jikin ta ya dinga yi shine kuwa na kira Baba muka zo nan.” Manal da take jin su tace, “daman wai tun dare bata da lafiya ban sani ba?.” Mama ta kalle ta tana hararar ta tace, “ke tafi can, banda ma zamani ina ke Ina fitowa Manal? Haihuwar da ko wata ɗaya ba’ayi ba har yanzu amma yawon ki kike daga nan sai nan.” Manal ta turo baki gaba tace, “To Mama ai wajan ki nazo.” Ta ƙaraso kusa da Maman ta riƙe hannun ta tana kallon ta tace, “in akace min baki da Lafiya Mama hankalina tashi yake sosai, wallahi kawai ganina nayi nazo ban san ta ya akayi ba.” Mama tayi murmushi bata kula ta ba tace, “Mubeena bani Ayan ɗin na gan shi, yaro mai sunan ƴan gayu, ko nace Khalil dan ni bazan ce wani Ayam ba.” Mubeena ta bata shi tana kallon sa tace, “tabarakallah, yaron yayi nauyi sosai yayi kiɓa kamar yayi wata biyu, kema gaki nan sharr dake lalɗai Mama tana baki kulawa.” Manal tayi dariya tace, “ai duk lokacin Mama ta dawo gida ban san ya zanyi ba, Mama ko pampers fa ban iya saka masa ba.” Mama tayi dariya tace, “zaki koya ai.” Da sallama Bebi da Huzaifa suka shigo ɗakin Mama ta kalli ƙofar ɗakin da suke tsaye tace, “Adnan ku ne tafe?.” Sai Bebi yaji daɗi ganin Mama bata canja masa ba duk da bata san waye Huzaifa a wajan ta ba, ya ƙaraso suka gaisa da Maman suka sake gaisawa da Maman Surayya kafin yace, “Mama ya ƙarfin jikin?.” “Da sauƙi.” Huzaifa yace, “Amma Mama da babban asibiti aka je ba’a zauna a nan ba. Ni ban ma san asibitin nan ba sai yau.” Mama tace, “Mubeena ce ta takura ni da bazan zo asibiti bama, sun ce yanzu ma zamu wuce gida babu wata matsala daman zazzaɓi ne kawai.” Bebi ya ce, “Amma duk da haka Mama ba nan ya kamata azo ba, kuma da gaskiyar ta ai ko ya ciwo yake ba a wasa dashi, musamman irin ciwon da kike dashi mai hatsari.” Mama tayi murmushi kawai bata ce komai ba. Basu jima sosai ba suka yi sallama suka fita. Manal ta biyo bayan sa ta samu zai shiga mota tace, “Partner.” Jin muryar ta sai ya dakata da shiga motar ta ƙaraso gaban motar tace, “zan bi su Mama gida in an sallame su.” “To” ya furta a taƙaice. Kallon Huzaifa tayi taga yana kallon ta sai tayi murmushi tace, “Yaya Huzaifa ina Ayra?.” “Ayra tana nan Manal, Sai maganar ki take yi.” Ta sake yin murmushi tace, “Ai ƙawata ce, a gaishe su har su Aisha da Mama har Daddy ɗin ma. Na kira Aysha na yi musu bangajiya ban same su ba, amma don Allah kace ina yi musu bangajiya” ta faɗa tana komawa ciki da sauri. Huzaifa ya shiga motar yana sauke ajiyar zuciya cikin wani irin yanayi. Bebi ya ce, “ka kula da fuskar Mubeena kuwa? Suna kama da Aisha.” Huzaifa yace, “na gani wallahi, abinda zan ce maka kenan maganar Manal ta ɗauke min hankali, kuma kaga a baya ban gani ba amma yanzu yanayin su gabaɗaya iri ɗaya ne.” Bebi yace, “shiyasa nake tunanin a inda na san mai irin fuskar Mubeena, Ashe Aisha ce. jini ba wasa bane” ya faɗa yana jan motar suka fita. Basu jima a asibitin ba suka koma gida gabaɗayan su har Maman su Surayya, sai bayan ta raka Mama gida ne sannan ta shiga nata gidan. Suna zaune tare da Mama Ayan yana hannun Mama tana ta yi masa wasa kafin ta kalli Manal tace, “Manal.” Manal ta kalli Maman kafin Maman ta kalli Mubeena tace, “abubuwa suna ta faruwa a cikin rayuwar ku wanda baku yi zaton su ba ko?.” Suka yi shiru babu wacce ya amsa Mama ta sake cewa, “Ko bayan raina kar ku karɓi wanda yazo yace muku shine mahaifin ku, ku cigaba da rayuwa kuna ɗaukar Baba matsayin mahaifin ku ba wani daban ba. Kar wani yazo yace shine ya haife ku ku amince dashi, kar wani yazo yace shi dangina ne shima ku amince dashi. Yadda aka nuna ba’a sona kuma ba’a son ku a ƙyale ku ku cigaba da rayuwar ku Allah yana son ku.” Mubeena tace, “Daman Mama ni babu wanda zan iya kallo matsayin mahaifina bayan abubuwa da aka yi miki, zuciyata baza ta iya yafe musu ba wallahi.” Mama tace, “Ku cigaba da riƙe kan ku kuna zumunci da juna, ga uwa nan kuna da ita a kusa Balaraba, duk abinda zan muku wallahi zata kwatanta saboda tana son ku gabaɗaya ku.” Manal tace, “me ya faru ne?.” Mubeena tace, “au baki sani ba? Mijin ki bai faɗa miki da wanda suka zo gidan nan jiya ba?.” Manal ta girgiza kai alamun a’a tace, “bai faɗa min komai ba.” Mubeena tace, “da wani suka zo tare da mahaifin Adnan ɗin wai shine mahaifin mu.” Gaban Manal ya faɗi sosai ta kalli Mama ta kalli Mubeena tace, “kuma da gaske shine mahaifin na mu?.” Mubeena tayi shiru suna kallon Mama suna kuma so su ji me zata ce. Mama tayi ajiyar zuciya tace, “ƙwarai shine, bazan ɓoye muku shi ba, Tabbas shine wanda yayi silar zuwan ku duniya. Ko da za’a shekara ɗari fuskar sa baza ta taɓa ɓacewa daga idanuna ba.” Manal tace, “kuma bai ji kunyar zuwa yace mu yaran sa bane?” Manal ta faɗa ido yana cikowa da hawaye. Mama tace, “wannan duk bai tashi ba Manal, zama zaku cigaba da yi a matsayin wanda mahaifin su ya rasu, sannan dukiyar da take wajan sa ko yanzu zan faɗi na muku ku tabbatar kun karɓa, ko da baza ku yi komai da ita ba ku sadaukarwa da marayu.” Manal tace, “to Mama ni me zai haɗa ni magana dashi har da zamu tambayi wata dukiya? Yaje ya cigaba da cin haram, lahirar sa yake lalatawa ba tamu ba, shi zai girbi abinda ya shuka a lokacin da hakan bazai masa amfani ba.” Mama ta riƙe hannun su tace, “baku da wani uba in ba Baba ba, a yanzu da nan gaba da ko ma yaushe ne babu wani wanda zamu kalla matsayin uba in ba shi ba.” A lokacin Baba ya shigo ya ji abinda take cewa ya ƙaraso yana cewa, “Haba Zahra, haba wannan wacce irin magana ki ke faɗawa yaran nan?.” Sai kuma ya kalle su yaga gabaɗaya hawaye suke yi ya kalle ta yace, “Wannan mutumin da ake magana a kai fa mahaifin su ne, kin amince da shine ya haife su meyasa zaki saka su a gaba kina faɗar wannan maganar?.” Mama tace, “bashi da wannan darajar a idona balle na cewa yarana su kalle shi da wannan mutuncin.” Jin abinda tace sai Baba yace, “Mubeena, Manal Ku koma falona ina zuwa.” Tare suka tashi suka fita jikin su a sanyaye. Baba ya zauna ya kalli Mama yace, “wannan kalaman da kike faɗa marasa daɗi akan mahaifin su ba daidai bane, ke in bakya son sa saboda abinda ya yi miki ai ke ba haihuwar ki yayi ba, su kuma ki tuna haihuwar su yayi kuma akwai jinin sa a jikin su. Ya zaki dinga kiran da mara mutunci a gaban yaran da ya haifa? Wannan ai ba magana wacce ya kamata ta fito daga bakın ki bace, har kice wai basu da wani mahaifi sai ni? A wajan ki hakan daidai ne?.” Mama tayi shiru bata ce komai ba Baba yace, “na san bai kyauta miki ba, bai kyau tawa rayuwar ki da ta yaran ki ba amma duk da ya tafi ya bar ki ɗin me kika fasa? Kin daina numfashi?, kin daina rayuwa?, kin daina ci da sha?, kin rasa suttura da farin ciki?, kin rasa cigaban rayuwa ne ko akasin haka?. Babu abinda kika rasa, rabuwar ki dashi wani sabon shafin ya buɗe a cikin rayuwar ki, farin cikin da ki ke yi a yanzu a lokacin da kuna tare baki yi shi ba, kwanciyar hankalin da Allah ya baki a lokacin da kuna tare baki samu ba. Meyasa baza ki tura masa aniyar sa ba? Meyasa baza ki share maganar komai ya wuce bane ba?, In ke bai wuce a wajan ki ba meye na zuga yaran sa akan kar su ga mutuncin sa?, ke a ganin ki tarbiyya ki ke koya musu?.” Mama tace, “Saboda bai cancanci naga mutuncin na sa bane, bai kai wannan matsayin da za’a girmama shi ba, bai kai wannan darajar da yarana zasu kira shi Baba ba. Wallahi ba dan Manal na son Adnan ba har shi sai ta bari, baban sa ya shafa masa baƙin fenti.” Ganin ta fara zubar da hawaye Baba yace, “babu wanda ya san abinda kike ji a zuciyar ki sai ke ɗin kawai, ɓacin ran da kike ji a ƙarƙashin zuciyar ki sai dai ke ɗin kawai. A san an cutar dake anyi miki ba daidai ba, an tozarta ki sosai amma yanzu waye yazo yake son magana dake?, waye yazo yana so ki bashi dama kawai ku yi magana? Fatima faɗa min waye yazo gare ki saboda ya nemi yafiyar ki?.” Mama hawaye take sharewa bata ce komai ba Baba yace, “dan kin nisnta kan ki dashi daman yanzu babu komai tsakanin ki dashi amma yaran sa fa? Dole ko bakya so Manal da Mubeena shine ya haife su, meyasa kike faɗar ko wacce magana a kansa a gaban idanun su?, ɗa da mahaifi fa sai Allah, su zasu iya karɓar sa a matsayin uba a gare su, daga baya kuma su dinga miki kallon wacce take aibata baban su a gaban idanun su, har abada baza su manta da wannan kalaman da kika faɗa akan wanda ya haife su ba, dan kin cire sunan sa a gaban sunan su a makaranta baza ki taɓa goge shi a cikin jinin su ba Fatima. Mahaifin su ne komai lalacewar sa, ko a yanzu da kike zuga su akan sa in suka yi masa wani abun ba daidai ba zunubi Allah zai rubuta musu, in a baya basu san shine ya haife su ba yanzu sun sani. Haba Zahra, kamar ba ke ba kike irin wannan maganganun?, ko dan gaba ba’a aibata iyaye a gaban ƴaƴan su, saboda ke auro ki yayi su kuma haifar su yayi, ke a yanzu baki da gadon sa in ya bar duniya, amma su ko yau ya mutu sai an raba gado an basu kamar yadda Allah yace. Don Allah ki dawo nutsuwar ki.” Mama tayi shiru kawai bata ce komai ba, maganganun sa kuma ba shigar ta suke yi ba shiyasa tayi shiru. Ban baki ya cigaba da yi mata yana nuna mata kuskuren ta kafin ya koma wajan su Manal ɗin. Su ma faɗa yayi musu akan faɗar ko wacce magana akan mahaifin su, ya kuma nuna musu ko meye shine ya haife su kuma yana da haƙƙi a kan su, ko yanzu suka zage shi suna da zunubi dan sun san baban su ne. Babu wacce tace komai har ya gama musu faɗan ya fita, Manal tsabar haushi ko tashi ma bata yi daga wajan ba tayi zaman ta zuciyar ta gabaɗaya babu daɗi. BDƘB3P24 Manal bayan sallar magriba Baba ya saka ta tafi gida, tare suka koma da Mama duk da tana cewa ta kusa godowa gida tunda ta warware kamar ba mai jego ba. Da suka koma gidan Bebi baya nan, Manal ta zama wani iri har Mama ta tambaye ta abinda yake damun ta ganin yanayin ta. Bata ɓoye mata ba ta bata labarin komai, Mama ta dinga jinjina lamarin ta bata haƙuri tacigaba da rarrashin ta. Bebi sai da ya tsaya ya taho musu da abinci dan ya san baza a samu damar girki ba, a kan hanyar sa ta wucewa zuwa gida yaga ana tsayar dashi. Tsayawa yayi da motar ya suke glass ganin matar da suka taɓa magana da ita a lokacin da suka fito tattaki shida Manal da cikin Ayan. “Kayi haƙuri, na tsayar da kai akan hanya, Wallahi na jima a nan a tsaye ina jiran ka.” Bebi yace, “babu komai, Allah yasa dai lafiya.” “Ba lafiya ba.” “Ina jin ki.” “Don Allah ka faɗa min gaskiya, Tsakani da Allah matar ka tana da alaƙa da dangin Muhammad Jalingo?. Wallahi ban gamsu da abinda tace ba kwanaki, gabaɗaya zuciya faɗa min take ita jinin gidan ce, suna matuƙar kama da matar gidan margayiya Hajiya Nusaiba, wannan kamar ta tafi fitowa da ƴar gidan da ta ɓace aka nema aka rasa, in ka san wani abu ka sanar dani son Allah.” Bebi ya sauke numfashi yace, “amma meye alaƙar ki dasu wanda ki ke magana a kai?.” Matar tace, “Sunana Halima, wannan gidan shine gidan da nake zaune a duk san da nazo kano. Ni ƴar Muhammad Jalingo ce, hakan ya saka nake da tabbacin wannan jini na ce, saboda akwai wacce ta ɓace mana itace ƙarama a gidan mu, mun nema ta sama da ƙasa amma mun rasa, Sai nake ganin kamar wannan ɗin ce duk da shekarun ba ɗaya bane amma ni wallahi na kasa gasgatawa.” Kallon ta Bebi yake yi ganin kamar bai yarda da ita ba sai tace, “bazan maka ƙarya ba, a haife na haifi wanda suka fi ka shekaru. Da gaske nake ni jinin marigayi ce kuma abinda na faɗa maka shi iyalan gidan mu suke so su ji gabaɗayan mu.” Bebi yace, “ina da buƙatar ganin iyalan gidan naku gabaɗaya in akwai damar hakan.” Matar tace, “me zai hana, Sai dai yawanci su ba a kano suke zaune ba a Abuja suke, mazauna Jalingo ɗin kaɗan ne kuma mata ne wanda aure ya zaunar dasu a can. Amma gobe zan iya haɗa maka zama da babban Yayan mu gabaɗaya na gidan, wataƙila ko zata gasgata abinda nake faɗa.” Bebi yace, “zan so hakan.” “Ga number ta, gobe in sha Alalh zai zo Kano gaisuwar rasuwa zan maka waya kazo ku je inda yake a nan garin.” Bebi ya saka hannu ya karɓa tayi godiya sosai shi kuma ya ja motar ya tafi. Bazai faɗa mata wacecw Manal ba har sai ya tabbatar da abinda take faɗa gaskiya ne sannan zai sanar dasu Manal jinin su ce. Ko da ya shiga gidan a falon sa a tsaye ya same tana kwashe kaya, yayi sallama ta amsa ya bita da kallo ganin ta babu walwala ya san gaji labari. “Sannu da zuwa” ta faɗa daƙyar ya amsa yana kallon ta kafin yace, “ga abincin nan, ki kawo min nawa” ya faɗa yana ajjiye mata ya shiga ɗaki. Ɗauka tayi tare da yin abinda yace ta kaiwa Mama ragowar da yawa ta fito ta ɗauki wanda ta zuba ta kai masa. A zaune ta ganshi yana danna waya ta bashi abincin ya karɓa ta ajjiye masa ruwa da lemo zata wuce ta fita ya ce, “An baki labarin mahaifin ki kenan.” Ta kalle shi shima ya ɗago ido ya kalle ta tace, “uhum an faɗa min, shiyasa ka ke min maganar sa jiya ashe?.” “Kin san waye?.” Ta kalle shi ta girgiza kai tace, “bani da buƙatar sanin waye, domin ni har yanzu bani da mahaifi ba kuma zan yi ba.” Bebi yace, “ai tunda kika zo duniya kina da mahaifi Manal” ya faɗa yana cin abinci. “To in ma akwai ni na goge shi a rayuwata.” “Bazai taba goguwa ba faɗa kawai ki ke, darajar mahaifi ya wuce ace an goge shi.” “Nawa maahifin bashi da wannan darajar, hanyar inda daraja take ma bai sani ba.” Ya kalle ta jin abinda tace ya kalli abincin yana juya cokali a ciki yace, “Daddyn su Huzaifa shine mahaifin ki.” Duk da maganar ta shige ta sosai da jin abinda yace amma sai ta taɓe baki tace, “Sai me dan ya kwance maahifina?.” “Sai ki masa biyayya domin ki dace a wajan Allah.” “Har abada” ta furta zata bar ɗakin ya ce, “ki zauna ki yi tunani, wannan abin da kike ba shine mafita a gare ki ba, mahaifi mahaifi ne duk lalacewar sa, duk abinda ya aikata laifi ne an sani amma matsayin ki na ƴar sa magana mara daɗi a kansa ba naki bane.” Bata ce komai ba ta buɗe ƙofar kawai ta fita shima bai saurare ta ba yaci abincin ya bar kayan a wajan ya tashi ya shiga banɗaki. Washe gari. Karfe takwas na safe matar ta kira Adnan a waya a lokacin ma ahirim fita yake yi, ganin kiran sai ya duba ya ɗauka da sallama ta amsa tace, “baka gane mai magana ba? Nice wacce na baka number tq jiya nace zan haɗa ka da yayan mu.” Bebi yace, “na gane, ina kwana.” “Lafiya lau, In kana nan shi Yayan na mu yazo a ina zamu haɗu sai muje?.” “Ki faɗa min inda yake zan zo.” “Muna nan Sultan road nasarawa gra.” Bebi ya ama da cewa, “in nazo zan kira sai a faɗa min gidan.” Ta amsa ya kashe wayar ya fito suka gaisa da Mama amma bai ga Manal ba. Yayi tunanin bacci take saboda safiya ce, Mama tana masa yi tayin abinci ganin harda kunu sai ya zuba kunun yasha zallan sa ya dauki key ya fita. Sai da ya biya gida suka gaisa da Abba da yake kwance shi ba mara lafiya ba kuma shi ba mai lafiya ba, ya shiga wajan Mama ya ta farka suka gaisa ya fita dan baya son ma ganin Rumana. Har ya shiga mota da niyar zuwa sai kuma ya canja shawara ya kira ta, tana ɗauka yace, “Hajiya ki yi haƙuri bazan samu damar zuwa ba a halin yanzu, sai dai in zaku zo gida.” Shiru yayi alamun ana bashi amsa kafin yace, “shikenan sai kun zo.” Kashe wayar yayi ya kunna motar ya nufi gidan sa. Yana ajjiye motar ya shiga ciki ba jimawa tace gasu da yake ya bada damar a shigo aka buɗe musu gate suka shigo suka ajjiye mota sannan suka shiga falon gidan. Manyan mutane dattawa guda biyu kana kallon su kasan sun manyanta da shekaru sannan kuma suna ji da kuɗi saboda yanayin shigar su, ga mata guda uku suma manya kana ganin su ka san sun girma suma. Adnan ya kalle su yace, “Bismillah.” Duk suka zauna kafin a gaisa gaisuwar mutuncin da girmamawa. Bebi yace, “Ku yi haƙuri na saka kun zo gida.” Babban ciki yace, “kar ka damu, daman mu ya kamata ace mun zo ai. ni sunana Ahmad Muhammad Jalingo, wannan ƙanina ne Bello Muhammad Jalingo, ga ƙannena mata da Hajara, da Safiyya da kuma wacce ta kawo mu nan Halima. Ta tabbatar min da cewa tana ganin ka da wata wacce tayi kama da ahlin mu, don Allah ko tana da alaƙa damu? Saboda kawai ƙaramar mu da ta ɓace shekaru masu yawa, Sai muke tunani ko ita ko kuma jinin ta ce.” Bebi ya sauke numfashi yana kallon su yace, “Wacece wacce ta ɓace ɗin a cikin ku?.” Alhaji Bello yace, “Sunann ta Zahra, kuma ba ɓacewa tayi ba aurar da ita akayi ga wani mai suna Aliyu da abokin sa ibrahim. Daga wannan lokacin bamu sake ganin ta shekara kusan ashirin da wani abun yanzu. Kullum cikin addu’ar son ganin ta muke yi amma shiru, mun fitar da rai da ita a tunanin mu bata duniya, Halima ce tazo tana cewa lallai taga mai kmaa da ita, to kuma kasan abinda ka ke nema ko ya akace an ga mai irin sa baza ka yi sanya zuwa ka gani ko za’a dace, shine muka zo muji ko wataƙila jinin mu ce.” Bebi ya sauke ajiyar zuciya yace, “Eh to kusan zan iya cewa itace, ba wai ita ƙanwar ta ku da kuke nema ba, ƴar ƙanwar ta ku.” Mamaki ya bayyana a fuskar su Alhaji Ahmad yace, “tana ina?.” Bebi ya kalle su yace, “zan kira ta ku gaisa, amma bana so wani ya nuna mata kun san wacece ita, zata fito ku gaisa matsayin baƙi ne kawai daga nan sai ta koma ko meye zamu tattauna shi bayan barin ta nan.” “Hakan ma yayi mana, don Allah ka kira ta.” Bebi ya ɗauki waya ya kira Manal yace tazo falo su gaisa da baƙi. Ba jimawa ta fito da hijjabi har ƙasa ta tsuguna ta kalle su tace, “ina kwanan ku.” Duk kallon ta suke yi kowa yana kallon kowa, Manal ma kallon su yake yi dan ta gane matar nan da ta tare su a hanya amma bata nuna ba ta gane ba. Gaisawa suka yi kafiin ta juya ta koma ciki. Alhaji Ahmad yace, “itace wallahi, wannan jinin Zahra ce, kama take Zahra sannan yanayin hasken ta sak na Gwaggon mu mahaifiyar Zahra ɗin kenan. Kuma mun san mahaifiyar Zahra ita kaɗai ta haifa.” Bebi yace, ƙwarai itace, sunan ta Fatima ƴar Zahra ƴar uwar ku da ku ke nema. Ita ɗin matata ce.” “Alhaamdullahi! Alhamdullah! Allah na gode maka, Allah na gode maka, Allah na tuba ka yafe min, Allah ka yafe min. Allah na gode maka da ka nufa zan sake ganin Zahra a duniya, Allah na gode maka da ka nufa zan nemi yafiyar ta baki da baki ya Allah” ya kalli Bebi yace, “don girman Allah a ina zan ga mahaifiyar ta?.” Bebi yace, “Tana nan lafiya lau cikin aminci, bayan Fatima wato Manal akwai yayar ta Nusaiba wacce ake kira da Mubeena. Suna zaune a nan unguwar tudun maliki a yanzu haka.” Alhaji Ahmad ya goge ƙwallar da tazo idanun sa yace, “zaka iya raka mu yanzu mu ganta?.” “Eh to, gaskiya da zamu bari zuwa wani lokaci saboda akwai wani abun da yake faruwa a yanzu, zuwan ku….” Ya dakatar dashi yace, “ko meye zamu iya fuskatar sa, ka bamu address ɗim gidan zamu je mu ganta.” Bebi ya sauke ajiyar zuciya yace, “shikenan, zan sanar daku.” Bebi ya faɗa masu inda gidan su Manal yake, suka sake masa godiya shi har nauyi yake ji ganin suna yi masa godiya haka, manyan mutane dasu suna yin godiya kamar shine a sama dasu. Har bakin gate ya raka su suka tafi shima ya hau mota ya fita. Bebi daga gidan asibiti ya wuce ya fara abinda yake gaban sa. Wajan ƙarfe sha biyu na ran sai ga kiran Abba duk inda yake ya dawo ya ɗauki Manal su je gidan su. Hankalin sa ya tashi sosai haka ya bar asibitin ya koma gida yace Manal tazo su je gida suka tafi har Maman dan hankalin Maman ya tashi bata san me ya faru ba. Daddy a hanyar su ta zuwa gidan su Manal yake kallon Abba yace, “na takura da yawa ko? Na gaji ne bana so na sake kwana da haƙƙin ta a kaina, ko me zata yi min gwara tayi, zan haƙura zan kuma jure duk abinda zata faɗa indai zata yafe min. Jikina yana bani kamar bazan ƙara wasu kwanaki ba shiyasa nake son neman afuwar ta da ta yaran ta.” Abba yace, “nima haka nake ji, ina buƙatar yafiyar ta baki da baki ko zan samu sassaucin abinda nake ji a cikin zuciyata, abubuwan sun yi min yawa, abinda nake ji a raina zan iya cewa yafi abinda ka ke ji wallahi.” A ƙofar gidan su Manal suka faka, aka yiwa Baba waya yan kasuwa ya dawo ya tarar basu shiga gidan ba sai da yazo yayi musu iso har cikin gidan. Dukkan su suka shiga a lokacin Mama tana zaune ita da Maman Surayya da Mubeena da Surayya da kuma Manal. BDƘB3P26 Tunda suka yi sallama kowa ya tsaya cak yana kallon su saboda mamaki, kowa ya kalli Mama da ta kawar da kai gefe kamar bata gansu ba.  Baba ya kalli kowa da yake wajan, ganin hakan sai Maman Surayya da Surayya suka miƙe zasu tafi Baba ya dakatar dasu yace, "Ku yi zaman Balaraba, ku ai ahlin mu ne." Baba ya kalli Mama zai yi magana ta riga shi tace, "amma mun gama maganar nan da kai ko? Meye zaka sake ɗauko min su ka kawo min bayan ba shiryawa hakan ba?. Meyasa zaka min haka don Allah?" Ta faɗa cikin rauni sosai, idanun ta suka ciwo da ƙwallah. "Afuwa muka zo nema a wajan ki ko nace nazo nema a wajan ki, na yi laifin da bazan taɓa goge irin sa ba a rayuwata, na aikata kuskuren da girman sa ya wuce tunani wanda ake bawa labari. Ni mai laifi ne a wajan ki gaba da baya na sani, duk wani hukunci daga wajan ki na cancance shi saboda ban riƙe amana ba, ban kuma yi tunanin abinda zai biyo baya ba na aikata son raina ne na kuma tsallake nayi tafiya ta. Bani da abinda zance miki wanda zai wanke laifina, na san babu, kowa ma yasan babu shi a duniya. Na kasa nustuwa, a kullum tunani nake kamar mutuwa zata riske ni a ko yaushe tunda na haɗa idona dake, fargaba da tunanin mutuwa da haƙƙin ki ya gama mamaye min zuciya. Zahra don girman Allah ki yafe min, ki yi haƙuri don Allah ba dan halina ba kice kin yafe min, in baki yafe min ba ban san inda zan saka raina ba a wannan yanayin da nake ciki, bani da buri a yanzu illa naga kin ce kin yafe min duk da na san abu ne mai matuƙar wahala a wajan ki, amma ki duba Allah ba ni ba kice kin yafe min." Muryar Daddy rawa take yi kowa a wajan ya tausaya masa har Manal da Mubeena, wani iri suke ji a zuciyar su jin yadda yake roƙon Mama muryar sa tana rawa, suka kalli Mama da tunda ta kulle ido bata buɗe ba. Hakan ya saka Baba yace, "Fatima don Allah ki yafe masa ko dan darajar ɗan sa Huzaifa." Ido ta buɗe ta kalli Baba yace, "eh, Huzaifa shine babban ɗan sa, shine yaron da yake faɗa miki a wancan lokacin yace miki yana da yaro guda ɗaya saboda. Na san Huzaifa ba abin yarwa bane a wajan ki, to ko dan shi ki yafe masa." Kallon Huzaifa tayi taga yana zaune kusa da Adnan sun sunkuyar da kai, sai ta ɗauke kai ta kulle idanun ta tana girgiza kai. Zuciyar ta tunani take wanne tsautsayi ne ya kai ta ga amincewa da Manal ta auri Adnan oho, yanzu da duk wannan tashin hankalin bai faru ba, da tana nan lafiya lau babu abinda ya taso nata wanda bata son tunawa. Shiru falon yayi, babu wanda yake magana a cikin su sai kukan Ayan ɗin Manal wanda yake hannu Surayya, sai Surayya ta tashi ta fita tsakar gida tana jijjiga shi dan yayi shiru. Daddy ya sake cewa, "Allah ya san zuciyata nayi dana sanin abinda na aikata, babu lallai ki amince a yanzu amma Allah shine shaida nayi nadamar abinda nayi miki dake da yarana. Kuma na koma har Zaria neman ki amma akace min ai bakya nan. Hankalina ya tashi na rasa inda zan neme ki, kullum cikin fatan Allah ya haɗa ni dake nake yi ko dan ki yafe min abinda anyi miki. Gashi yanzu na gan ki, don Allah don annabin rahama ki yafe min, ki yi haƙuri." Baba ya kalle ta jin ta sake yin shiru kamar ba da ita ake maganar ba yace, "baki ce komai ba." Ta sauke numfashi ta cire glasses ɗin idon ta ta goge idanunta sake mayar dashi tare da kulle idon bata ce komai ba. Ɗakyar ta iya cewa, "to me zance? Wani lokacin bawa baya sanin ya aikata kuskure sai lokaci da nadama ta riske shi, daga wannan lokacin sai a fara dana sani ana kiran aikin shaiɗan ne. Bayan tun farko kai ne ka bawa shaiɗan damar da ya shiga zuciyar ka har ya samu gurbin zuga ka kai kuma ka ɗauki zugar sa, lokacin bama fahimtar hakan, amma da lokacin nadama tazo mana duk sai mu fita daga hankalin mu. Na rasa mahifiyata na zauna lafiya, na rasa mahaifina na zauna lafiya, na rasa ƴan uwana na zauna lafiya, ban san kowa a dangin mahaifiyata ba shima na zauna lafiya. Dawowar wani abu a rayuwa a yanzu bana tunanin zai bani farin ciki ko meye shi." A hankali take maganar hakan ya saka Manal fara kuka, Mama ta kalli Manal da Mubeena da suke zaune Manal tana kuka. Manal ta kifa kanta a cinyar Mubeena tana kuka ita kuma ta riƙe bayan ta tana hawaye, Mama murmushi itama hawaye sun cika idon ta tace, "ƴaƴana ne, na rayu babu uwa da uba da kowa nawa, su kaɗai nake kallo naji farin ciki a zuciyata saboda ni ce na haife su, a kaf duniya basu da wani kamar ni bayan ni sai kai Baban su. Bana tunanin dawowar mahaifin su zai basu farin cikin da yafi wanda suke ciki a yanzu." Baba ya kalle ta a tausashe ya ce, "Haka ne, amma mahaifi sunan sa mahaifi, Sai dai a kira wani madadin mahaifi  ba mahaifi ba, dan duk inda mahaifi yake martabar sa daban take." Mama ta kalli Baba tace, "kuma har shi yana cikin masu martaba daban ɗinn?." Baba yace, "shi ba mahaifi bane?." Sai tayi murmushi ta kawar da kanta gefe ta kalli saman ɗakin kamar mai karantar wani abu, ta sake sauke kai ƙasa ta rufe ido ta buɗe alamun ta rasa ma abinda zata ce. "Shekarar Manal ashirin da huɗu zuwa da biyar, ta rayu a hannun wanda ba shine ya haife ta ba, ya saka ta a makaranta ya bata ci da sha da suttura, ya yi mata tarbiyya da har aka gani aka zo neman auren ta ya kuma aurar da ita. To wanne mahaifi zata buƙata a cikin rayuwar ta a yanzu?. Tana da uban da yayi mata abinda mahaifin bai yi mata ba, babu amfanim bayyanar wani da sunan mahaifi a wajan ta." Baba yace, "maganar Manal da Mubeena duk babu ruwan ki a ciki, mahaifin su ne zasu iya ji sun yafe masa har zuciyar su. Yanzu a kan ki muke maganar ba a kan su ba." Mama tayi ƙaramar dariya ta kalli Huzaifa da ita yake kallo a lokacin ta sauke ajiyar zuciya tace, "ni ban san abinda zan ce ba." Sallama aka ji a tsakar gida ta mutane aka amsa kowa yayi shiru ana jira sun shigo cikin falon. Sake maimaita sallamar akayi a lokacin da aka shigo falon kowa ya bi su da kallo cikin rashin sani, Bebi ne kawai ya san maganar a amma babu wanda ya san su ko ya san da zuwan su. Wanda ya shigo cikin falon yace, "Barkan ku, muna neman izinin zama." Baba ya kalle su ya kalli Mama da take kallon maza guda biyu farko da matan da suke bayan sa. Baba yace, "bismillah ku zauna." Da yake falon na da girma sosai duk ya dauƙe su aka zauna. Alhaji Ahmaf yace, "Ku yi haƙuri mun katse ku, Gashi na san baku san mu ba." Mama kallon su take yi kamar yadda suke kallon ta suna murmushi. Baba yace, "gaskiya bamu shaida fuskar ba" ya faɗa dan yana so ya faɗa da kansa ne amma shi ya san shi. Ya girgiza kai yace, "Sunana Ahmad Muhammad Jalingo, Yaya a wajan Zahra Muhammad Jalingo." Sauke kai Mama tayi ta kulle ido sai ta miƙe zunbur kamar an yi mata allura sai ganin ta suka yi a tsaye. Halima da take cikin matan ta taso ta zo wajan Mama tace, "Tabbas ke ɗom jinina ce Zahra, kin gane ni? Nice Halima Yayar ki, nice Halima da muke kwana waje ɗaya mu tashi waje ɗaya, nice waccs muke cin abinci tare, nice wacce komai namu yake zana iri ɗaya hatta kayan sakawa. Don Allah kar kice baki gane ni ba Zahra, kar kice baki gane ni ba, bani da laifin komai, nayi kukan barin ki gida tun a wancan lokacin, nayi kuku Zahra" ta faɗa tana kuka tana kallon Mama da jikin ta yake rawa sosai hawaye na zuba mata masu yawa. Hannun Mama ta riƙe tace, "ki kalle ni, zaki gasgata da gaske ni ce, na jima ina neman ki, duk inda naga wani mai irin fuskar ki ko ta gwaggo sai na masa magana ko ya san ki?. Zahra don Allah ki kalle ni kar laifin da ban aikata miki ba ya yafe ni." Mama bata iya buɗe ido ba hawaye ne yake zuba wani yana bin wani, jikin ta ya fara rawa kanta yana mugun sarawa, da hannu ɗaya ta dafe kanta kafin a farga Mama ta suma a wajan. A haukace Manal ta taso tayi wajan ta tana kiran sunan ta tana jijjiga ta amma ina Mama bata numfashi, kuka Manal take tana jijjiga tana cewa, "Don Allah Mama ki tashi, ki tashi Mama kar ki tafi ki bar mu, bamu da kowa sai ke, ke kaɗai ce gatan mu a duniya. Ku taimaka min Mamana bata numfashi." Mubeena ta taso tana kuka itama tace, "bamu buƙatar taimakon kowa, mu muka saba kula da ita kuma zamu cigaba da kula da lafiyar ta, Baba zamu kai Mama asibiti" ta faɗa tana zuwa kusa Maman tana girgiza ta. Addah Halima da take tsaye a gaban Maman tace, "ni likita ce zan iya duba yanayin jikin ta, don Allah ku bani wannan damar" ta faɗa tana riƙe hannun Mama tana jin bugun zuciyar ta. "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Zuciyar ta na bugawa na wuce ƙa'ida, nunfarhin ta yana tsayawa ayi hanzarin tafiya asibiti" ta faɗa tana kuka sosai tana kallon Yayan su. Da kansa ya tashi ya ɗago Mama daga kwance da take yana cewa, "Zahra kar ki yi mana haka don Allah, kar ki mana haka." Nan take hankalin kowa ya tashi ana ƙoƙarin fita da Mama daga falon Mubeena tace, "wallahi in wani abun ya samu Maman mu babu wanda zamu yafewa, mun haƙura da kowa a bar mu da ita daman da ita muka rayu." Fita akayi da Mama hankalina tashe da kansu suka saka Mama a asibiti ba tare da sun san asibitin su waye ba aka wuce da Mamaa asibitin su Bebi. Suna zuwa aka karɓe ta, Bebi da Huzaifa sun ƙarasa asibitin da gaggawa Bebi ya fara auna zuciyar Mama aka saka mata abinda zai taimaka mata numfashi ta ya dawo daidai, aka saka mata ruwa da allurai a jijiya. Sun cika asibitin gabaɗaya hankalin su a tashe yake, gani suke kamar Mama zata mutu hankalin su yaƙi kwanciya. Manal da Mubeena sun ware a waje ɗaya har lokacin Ayaan yana wajan Surayya dan itama ita da Maman ta sun biyo su. Bebi da ya fito wanda basu ana likitan Mama bane kallon sa suke yi kafin yayi murmushi yace, "Kar ku damu, zata dawo daidai nan da anjima in sha Allah. Firgice ne ya haifar da hakan kasancewar daman tana da ciwon zuciya." Alhaji Ahmad da yake cikin ruɗani da tashin hankali yace, "tana da ciwon zuciya?, Kaine Dr Adnan?." "Eh ni ne, tana da ciwon zuciya kamar yadda nace. Na san condition ɗin ta kusan file ɗin ta a hannuna yake yanzu." Alhaji Bello yace, "kuma kai ne mijin Manal ƴar ta?." Ya ɗaga masa kai alamun eh haka ne ya kalli inda Manal ɗin take dan kukan ta gabaɗaya ake ji a wajan. Ji yake kamar ya je ya ɗauke ta ya samu waje mai kyau ya rarrashe ta amma babu damar aikata hakan dan bata cikin hankalin ta. Daddy ya kalle shi yace, "Adnan ka tabbatar zata samu lafiya?." "İn sha Allah Daddy, zata warke da izinin Allah, ta firgita ne sosai." Daddy ya kalli Alhaji Ahmad da yake kallon sa shi ma, kafim Daddy yayi magana yace, "Ali ko?" Ya kalli Abba ma da yake zaune yace, "Ibrahim, ku ne wanda nake tunani ko?." Daddy ya ɗaga masa kai alamun eh yayi murmushi yace, "har abada fuskar ku baza ta ɓace min ba." Bebi ya kalli agogo ganin lokacin sallah yayi sai ya wuce masallaci, suma duk suka wuce aka yi sallah aka sake dawowa aka zauna kowa ya kasa motsawa saboda gani ake kamar in aka tafi za'a ce Mama ta rasu ne, shiyasa suka kasa suka tsare a wajan ana jiran farkawar Mama. BDƘB3P27 Suna nan a tsaye ana jiran tsammani Baba ya kalli Mubeena da Manal da suke tsaye yace, "ku samu waje ku zauna, tunda muka zo kuna tsaye, tsayuwar bata gaji daku bane?." Mubeena tana riƙe da hannun Manal Maman Surayya tace, "Manal ki karɓi yaron nan, tun ɗazu yake kuka har yanzu." Surayya ta kawo mata shi dan itama kuka take yi, Baba ya kalli Adnan yace, "Adnan don Allah kaje dasu inda zasu zauna, kamar tsoron kowa suke yi a nan sai ɗari-ɗari suke." Bebi ya wuce zuwa inda suke Baba yace su bishi ya kai su wani falo ƙarami mai kyau, Surayya na riƙe da Ayaan suka zauna Surayya ta bata shi ta karɓa ta riƙe shi amma ta kasa yi masa komai. Suna zaune a tare ta bashi nono yana sha ita dai idon ta a rufe yake saboda tashin hankali yayi nata yawa. Ruwa Surayya ta miƙa mata kamar yadda Bebi ya bata yace ta bata ta sha, ta karɓa ta sha ta ajjiye ragowar tayi shiru hankalin ta na wajan Mama. A nan Mubeena da Surayya suka yi sallah basu jima da idarwa ba sai suka fita a lokacin Ayaan yayi bacci tana riƙe dashi a hannun ta. Bebi ne ya shigo inda take bata ɗago ba ya ƙaraso kusa da ita ya ɗauƙe Ayaan daga jikin ta, a lokacin ta buɗe ido ta kalle shi ya kwantar dashi kan kujera mai zaman mutum ɗaya ya dawo ya zauna kusa da ita yana kallon ta idanun ta wanda ta sake rufe su, kafin yayi magana ta kwanta a jikin sa ta riƙe shi sosai tana kuka. Shima riƙe ta yayi yana shafa bayan ta a hankali cikin sigar rarrashi da son kwantar mata da hankali. cikin kuka Manal tace, "Don Allah kar ka bari wani abun ya samu Mama, kar ka bari wani abun ya same ta, in Mama ta bar duniya nima mutuwa zanyi, bazan iya rayuwa babu Mama ba. Bana buƙatar kowa Mama kawai nake buƙata, bazan yafewa musu ba tunda sune silar shigar Mama na wannan hali." "shiii! Ki daina fadɗar haka Manal, Allah shi yake ɗorawa bawan sa ciwo duk lokacin ya so, wani ko wata basa sakawa wani ciwo sai Allah kawai. Ki mata addu'a Allah ya bata lafiya kuma na faɗa miki jikin nata akwai sauƙi sosai." Bata ce komai ba tana jikin sa ya ɗago kanta ya riƙe kan nata yace, "ki yi haƙuri ki daina wannan kukan, kan ki ciwo yake yi sosai." Ko ido bata buɗe ba balle tayi magana, ya share mata hawayen da suke fuskar ta yace, "don Allah ki nutsu kinga ba wani lafiya ne dake ba har yanzu, ki dawo hankalin ki don Allah." Zama tayi sosai akan kujerar tayi shiru ya kalle ta yace, "ina zuwa" ya faɗa yana fita daga ɗqkim ta bi bayan sa da kallo gabaɗaya hankalin ta baya jikin ta. Haka suka wuni a asibitin kowa ya kasa tafiya kar ace Mama ta rasu, har bayan i'sha Mama bata farfaɗo ba har goma na dare ana zaune ana jiran tsammani. Manal ta fito suna tare da Mubeena waje ɗaya, kallon kowa suke kamar bare ita da ita ne kawai suke zaune basa yiwa kowa magana indai ba Baba ba. Baba ya kalli Manal da take zaune ya kalli Bebi yace, "Adnan ba yanzu zaku tafi gida bane?." Adnan ya kalli shi yace, "yanzu zan tafi." "Yanzu za ku tafi dai, me Manal ɗin zata yi a nan?." Manal ta girgiza kai tace, "Baba don Allah kar kace na tafi." "Na ce Manal, haƙuri zaki yi ku tafi zaman ki bazai bata lafiya ba. Allah ya kaimu gobe sai ki dawo." Jin abinda yace sai tayi shiru kawai bata ce komai ba. Manal ba dan ta so ba haka suka tafi gida ita dashi ko Maman Surayya ma bata biyo su ba dan bata cikin wannan nustuwar itama ta manta ma shaf da batun a gidan Manal take. Kwanan Mama biyu a asibitin Bebi ya hana a ganta dan ta farfaɗo a kwana na farko yana sane ya hana kowa ganin ta sai da aka kwana biyu saboda a samu ta huta sosai, Manal da Mubeena kawai ya iya bari suka ganta su ma basu san ta fardaɗo ba lokacin da suka shiga bacci take yi. Ranar kwana na biyun da rana yake sanar dasu farkawar ta kowa yayi farin ciki da hakan, aka shiga ana yi mata sannu tana amasawa amma bata cewa komai sai dai ta ɗaga kai kawai. A ranar suka koma gida dan tace ta gaji da zaman asibiti babu wanda ya bita daga Manal dai Sai Mubeena saboda kowa tsoro yake yi kar ta sake faɗawa wani yanayin. Sai washe gari ta kama ranar juma'a bayan sallar juma'a Mama tana zaune da Manal da Mubeena duk da ba magana suke yi ba amma duk kallon ta suke yi dan tunda tayi rashin lafiya bata sani warware sosai ba. Baba ne ya shigo da sallama suka amsa ya kalli Mama yace, "Fatima ki shirya akwai babban baƙo da zai shigo yanzu." Mama ta saka hijjabi Manal ma daman da mayafi a jikin ta suka gyara sai ga Baba ya shigo da babban Malami wanda aka san fuskar sa a ko ina wato Malam Habib Usman. Ganin Malam sai mamaki ya kama Mama ta gyara zama tace, "Malam barka da zuwa" ta faɗa da girmamawa tana mamakin abinda ya kawo shi gare ta. Aka ɗaukowa Malam farar kujera ya zauna kowa ya gaishe shi ya amsa da fara'a ya kalli Mama yace, "Ya ƙarfin jikin naki?." Mama tace, "da sauƙi, jiki yayi sauƙi." Malam yace, "Allah ya ƙara lafiya." Aka amsa da amin kafin Malam yace, "na san kin yi mamakin ganina a gidan nan ko?." "Gaskiya dai nayi mamaki, ni da a radio ko a waya nake ganin ka yau ace ga Malam har gidana?, abin ya ɗaure min kai." Malam yace, "ni na san hakan, amma ba wani abun bane gyara zumunci nazo nayi." Malam ya sake cewa, "ƴan uwan ki maza da mata sun je har gida sun same ni akan abinda ya faru, sun faɗa min komai sun kuma nuna min nadamar su a bayyane, sannan suna kuma buƙatar ki dawo ciki ahlin su, sannan suna so ki yafe musu ki shiga cikin su a cigaba da rayuwa cikin farin ciki da zumunci. Faɗa min hakan da suka yi sai nace bara na taso da kaina nazo na taya su baki haƙuri da kuma neman afuwa, dukkan su suna shakkar zuwa saboda kar ciwon ki ya sake tashi. Shiyasa nazo ni kaɗai ba tare da rakiyar kowa a cikin su ba." Mama ta sauke ajiyar zuciya bata ce komai ba Malam yace, "Zahra'u a labarin da aka bani a kanki tabbas ba a kyauta miki ba, sun watsar da zumunci babu kuma sun yi watsi da wasiyyar mahaifin su a kan ki. Sun ɗauki tsana sun ɗora miki akan abinda ba laifin ki ba, itama mahaifiyar ki ba laifin ta ba amma saboda wata baiwa da Allah ya baki keda ita suka kasance basa zumunci dake. Duk da dai yanzu ba a tuna baya, ina faɗe ne dan ki san na san komai an faɗa min har aurar dake da suka yi ga wanda basu sani ba duk na sani, duk abinda na faɗa miki anyi ko?." Mama ta ɗaga kai tace, "anyi Malam." Malam ya sake cewa, " yanzu da suka dawo suna neman afuwar ki meyasa baza ki yi haƙuri ki karɓi ƴan uwan ki ba?." Mama ta girgiza kai tace, "bana ji a zuciyata zan iya hakan Malam, saboda in na tuna abubuwa da suka faru sai naga gwara ma nayi rayuwata ba tare da su ba, gwara ace na cigaba da rayuwa har mutuwa matsayin wacce ƴan uwan ta suka wulaƙanta ta suka barta. Bani buƙatar su gabaɗaya, bana buƙatar su shiyasa kawai nace ni ba zan iya magana da kowa ba." Malam yace, "kar ki ce haka, ai babu wanda ya wuce kuskure a rayuwa. Na san sun yi kuskure babba mai girman da manta shi a rayuwar ki za'a jima. Kin san da cewa sun jima suna cewa na taya su da addu'a akan Allah ya bayyana musu ke ko ahlin ki? Basu da tabbacin kina raye amma kullum cikin neman ki suke, Meyasa yanzu sun gan ki baza ki yi haƙuri a ƙarasa rayuwar da ta rage ba, ko Malam?"Malam ya faɗa yana kallon Baba. Baba yace, "Gaskiya ne, shekaru sun ja mutuwa kowa yake jira." Malam yace, "Allah maɗaukakin sarki yana magana akan masu haƙuri da yafiya yace, "Kuma idan kuna so rama abinda aka muku, to ku rama daidai da abinda aka muku. Kuma idan kun yi haƙuri, lalle shi ne mafi alheri ga masu haƙuri. Wannan ayar tana cikin suratul nahli aya ta 126. Akwai hadisin Annabi Muhammad S.A.W da yake cewa, "Allah yana umartar ku da ku gafartawa wanda ya zalunce ku, kuma ku gafartawa wanda ya hana ku, kuma ku ƙulla soyayya da wanda ya rabu da ku." Ganin maganar tasa tana shigar Mama sosai sai Malam ya sake cewa, "Afuwa tana daga cikin dabi'un Annabin mu Muhammad (SAW), shi ne shugaban dukkan masu yin afuwa, shi ne mafi tausayin masu tausayi (SAW). Kuma Annabi Muhammad (SAW) ya faɗawa Ukubatu bin Amir (RA) lokacin da ya tambaye shi kan ayyuka mafiya falala sai ya ce: "Ya Ukbatu! Ka sadar da zumunta ga wanda ya yanke maka, ka ba wanda ya hana ka, kuma ka yi afuwa ga wanda ya zalunce ka." "Afuwa tana jawo babbar lada a wurin Allah, Allah maɗaukaki yace; Wanda ya yi afuwa kuma ya gyara, to ladar sa yana wurin Allah. A wannan aya Allah bai faɗi yawan ladar ba, kuma kowa ya san Allah Mai kyauta ne ba da lissafi ba idan ya ga dama. Don haka tunda ya ce ladar mai afuwa tana wurin sa ai a tunanin mai tunani ma ya kamata ya san ba ƙaramin tagomashi Allah zai masu sakayya dashi ba." Malam ya kuma cewa, "a hadisin da na faɗa miki a farko kin ji inda annabi Muhammad S.A.W yake cewa; ka ƙulla zumunci da wanda ya yanke shi, hadisin sai ya tafi kamar dake ake, wani abun in ya faru aai kaji kamar da kan hadisin ya sauka ko ayar. Zahra ki kasance mai yafiya a ko yaushe, ba ina tilasta ki akan ki yafe bane ina faɗa miki falalar da take cikin yafiya, ina faɗa miki falalar da Allah ya tanadawar mai haƙuri da kuma yafiya. Allah da kansa yace; kazam mai haƙuri da yafiya ladan mai yi yana gare shi, ni dake da kowa ya san wannan lada ba ƙaramin lada bane ba." Mama take yi sosai imani na shiga zuciyar ta Malam yace, "bayyanar ƴan uwan ki ki ɗauka kamar alkhairi ne ya bayyana a gare ki da kuma yaran ki, ki karɓi ƴan uwar ki hannu biyu kar ki zama mai raba zumunci a tsakanin ki da ƴan uwan ki ko yaran ki. Kar laifin da aka yi miki a baya ya saka ki dinga aibata ƴan uwan ki, ko ki dinga ji a zuciyar ki yadda suka nuna basa son ki kema bakya son su. In kin yi hakan ba laifi bane saboda ɓata miki akayi, amma haƙuri da yafiya da cigaba da zumuncin yafi riba yanzu ko nan gaba." Mama da take kuka tace, "haka ne Malam, na amince da duk abinda kace, kuma dukkan su na yafe musu." Malam yace, "har zuciyar ki kika yafe ko kuma maganar da nayi miki ce ta saka kika yafe musu?, Kar ki yafe a baki a zuciya kuma baki yafe ba." "Wallahi har zuciyata Malam, nayi haƙuri na yafe wallahi har cikin zuciyata. Ina so na shiga cikin wanda Allah zai yiwa tagomashi na musamman a ranar lahira." Malam yayi murmushi yace, "haka ake so, naji daɗin hakan da kika karɓi gyaran ki lokaci daya, haka ake son zuciyar musulmi ta kasance, ana so musulmi ya kasance mai saurin ɗaukar shawara ko gyara a duk sanda hakan ya riske shi. Naji da kika amince na tabbatar ladan ki yana wajan Allah." Ya kalli Manal da Mubeena da suke kuka yace, "kuma duk kun ji abinda nace, ku yafewa wanda ya cutar daku, duk da rama cuta ga macuci ba laifi bane amma haƙuri shine riba. Kar ku riƙe su a zuciyar ku domin su iyaye ne a wajan ku gaba da baya." Mubeena tace, "in sha Allah malam, Allah ya sakq da alkhairi ya ƙara girma." Malam ya amsa da amin ya sake musu nasiha mai shiga jiki sosai kafin a koma raha yana tsokanar su akayi dariya Malam yayi sallama ya tafi. BDƘB3P28 Mama ajiyar zuciya tayi bayan Malam ya fita ta kulle idanun ta ta buɗe ta kalli Manal da take zaune tana kuka haka Mubeena ma. Kafin tayi magana Baba ya dawo daga raka Malam ya zauna ya kalle ta fuskar ta duk tayi ja saboda kuka, haka fuskokin yaran ta suma sun yi ja saboda tsabar kuka. Baba yace, “Kar ku ɗauki nasihar Malam kamar tursasawa, Ku yi abinda zuciyar ku take so ba abinda aka yi muku dole ba.” Mama tace, “Baban Manal ai ya riga ya wuce kuma, dukkan su na yafe musu daga kan mahaifin su Manal ɗin har ƴan uwana. Zan kuma cigaba da zumunci dasu tunda bani da wanda ya fisu a duniya. Sai dai zan dinga addu’a Allah ya kawar min da shaiɗan daga zuciyata dan in ina tuna irin abubuwa da suka faru na kan kasa mantawa.” Baba jin haka sai yaji daɗi sosai har ya nuna akan fuskar sa yace “Alhamdulillah! Haka ake son ko wanne musulmi Zahra, ya kasance mai afuwa da yafiya ga wanda ya cutar dashi. Naji daɗi da kika ce komai ya wuce, nayi farin sosai Allah ya yafe mana baki ɗaya.” Ta amsa da amin ta kalli Manal da Mubeena tace, “na janye kalamai na a kan mahaifin ku, ku karɓe shi hannu biyu, kamar yadda Malam yace baku da kamar sa tunda shine ya haife ku.” Manal ta goge idon ta tace, “Haka ne Mama, komai ya wuce ko Yaya Mubeena?.” Mubeena ta ɗaga kai tace, “komai ya wuce mu ma Mama, tunda kin yafe musu mu ma haka, daman laifi ke aka yiwa ba mu ba, mun tsinci abun a sama ne kawai.” Mama ta sauke ajiyar zuciya ta kalli Baba tace, “Amma fa duk wani abu da ya kasnace mallakina ne Ali sai ya dawo min dasu, ina nufin dukiyata da take wajan sa, ya tattaro ya dawo da ita na barwa yarana.” Baba yace, “baki yafe ɗin ba kenan?.” “Na yafe masa duk abinda yayi min, kawai dai kuɗim ne sai ya dawo dasu ko yanzu ko nan gaba.” Baba yayi murmushi yace, “to ki yi me da kuɗin?.” Mama ta kalle shi tace, “ko zuba musu fetir zan yi na ƙona kuɗina ne ko?.” Baba yace, “naki ne, amma kar ki manta kina da wani kuɗin, kina da kadarar da yanzu in aka siyar da ita Manal da Mubeena in suka juya kuɗin in Allah ya saka musu albarka babu abinda baza su yi ba. Wannan gidan da muke ciki naki ne na kan ki, to me kike nema kuma?.” Mama ta girgiza kai tace, “kuɗin wajan sa nake nema.” Baba ya girgiza kai kawai yace, “Shikenan.” Ta kalle shi zata yi magana yace, “zan kira su anjima dan dukkan su hankalin su yana ga abinda zaki ce, Ashe Yayan ki ma yana da abinda zai yi a Abuja amma ya bari saboda ke, kaf ƴan uwan ki na Jalingo da wanda suke aure a wani wajan duk suna Kano saboda ke.” Mama ta kawar da kai bata ce komai ba tana kallon Manal da take zaune sai tace, “Manal har yanzu jego ki ke fa, ki tashi daga tsakar gidan nan ki koma cikin falo nan da sanyi.” Manal ta sake jingina da bango tace, “nan yafi daɗi Mama.” Surayya ce ta shigo da Ayan yana kuka Mama ta kalli Surayya tana murmushi tace, “uwar goyo ya tashi kenan?.” Surayya ta bawa Manal shi tace, “Ya tashi Mama, tun ɗazu yake kuka.” Manal da ta karɓe shi sai ta tashi ta shiga ciki bata iya bashi nono a gaban Mama kunyar su take ji. Tana jiyo hirar su sama-sama daga falon da ta gama shayar dashi yayi shiru ta kwantar dashi itama ta kwanta a kan gadon tana yi masa wasa yana kallon ta tana kallon sa har bacci ya ɗauke ta. Kiran wayar ta ne ya tashe ta ta tashi zaune ta kalli wayar ganin mai kiran sai ta ɗauka ta saka a kunne tace, “Hello partner.” Daga can ɓangaren yace, “Partner ya naji muryar ki haka? Ba dai kuka ki ke yi ba?.” “Nayi kuka dai ɗazu, amma yanzu bacci nake ka tashe ni.” “Ayya sorry ban san kina bacci ba.” “Ya aiki?.” “Bana asibiti ma, ina nan wajan Abba bashi da lafiya, ga Daddyn su Huzaifa ma shima jinin sa ya hau sosai.” Manal ta sauke ajiyar zuciya tace, “Allah ya bada lafiya.” Ya amsa da amin kafin yace, “Ina Ayaan?.” Ta kalli gefen ta taga baya baya wajan tace, “Nayi bacci yana kusa dani, yanzu dai ban ganshi ba na san Yaya Mubeena ce ta ɗauke shi ko Surayya.” Yayi murmushi yace, “Ina Maman Surayya? Bamu gaisa ba gabaɗaya, ɗazu na kira number ta da kika bani ban same ta ba.” Manal tace, “nima tun safe da muka gaisa ban koma ba, tace mun ai na gama jego ɗakyar in bata gudo gida ba.” Yayi ƴar dariya yace, “nima naga kin gama jego ɗin ai, kin kyau abin ki.” Tayi dariya kaɗan kafin yace, “zan kira ki” ya faɗa yana yanke wayar ta ajjiye wayar ta fito a nan ta lura ma har magriba ta kusa. Hannun ta ta wanke tare da bakin ta, ta shiga kitchen ta ɗebo abinci tazo kusa da Mama ta zauna tana ci. Mama ta bita da kallo tace, “ya kamata ki fara shirin komawa gida kuma ko? Magriba tayi.” Manal ta amsa da to ta gama cin abincin ta koma ɗaki. Bayan sallar i’sha Manal na tsaye tana cewa, “Mama kiran sa nake bai ɗauka ba.” Mama tace, “ya kamata dai ki wuce ki tafi, kar kuma ki sake fitowa sai kin kwana arba’in. Wannan jego na zamani sao shagwayi kike a unguwa ko kwana arba’in baki yi ba, yau kina nan kina can ko ɗan wankan jegon ma bakya yi. Sai wani na towel shima kuma dan iyayi wai babu ruwa mai zafi.” Manal tayi murmushi kawai bata ce komai. Sallama aka yi aka shigo gidan duk suka amsa Manal ta fito tsakar gidan dan taga su waye. Idon ta akan Daddy ya fara sauka da Abban su Bebi ga yayyen Mama da suka zo suma gabaɗyan su dan suna da matuƙar yawa sosai. Manal tace, “Sannun ku da zuwa.” Mama ta fito tsakar gidan ta kalle su dukkan su sai tayi murmushi tace, “Sannun ku da zuwa, Mubeena zo ki shimfiɗa mana tabarma mu zauna a nan.” Mubeena ta fito da babbar tabarma aka shimfiɗa a tsakar gidan kasancewar da haske sosai kuma yanayin garin na zafi ne. Mama ta kalle su tace, “bismillah.” Mamakin canjin ta kowa yake yi mazan suka zauna aka sake saka wata tabarmar matan kuma suka zauna suma. “Barkan ku da dare” Mama ta faɗa tana kallon kowa da yake wajan. Yaya ta Alhaji Ahmad yace, “Barka dai Zahra, ya ƙarfin jikin ki?.” Tayi murmushi tace, “Jiki yayi sauƙi sosai ai Yaya, na samu lafiya.” Kallon ta yayi jin da sunan da ta kira shi, yaji sanyi har cikin zuciyar sa farin ciki ya mamaye ko ina a tare dashi yace, “Allah ya ƙara lafiya ƙanwata.” Mama tayi murmushi tace, “Amin Yayana.” Ta kalli matan da suke zaune dukkan su Yayyen ta ne tace, “cikin ikon Allah babu wacce na manta sunan ta ko fuskar ta duk tashon wannan shekaru da aka kwashe bamu haɗu ba, kuma nima nayi mamaki da har kuka iya gano fuska ta akan fuskar Manal.” Babar yayar su mace wacce suke cewa Yaya Bara’atu tace, “Kin taɓa ganin ɗam uwa ya manta da fuskar ɗan uwan sa? Ko kin taɓa ganin in da hanta da jini suka rabu?” Ta riƙe hannun Mama tace, “duk da lokacin da komai ya faru ni bana cikin gidan, ko nace kusan dukkan mu bama nan keda Halima ne da Hadiza kawai tunda ku ne ƙananu, amma ni ma na nuna miki rashin so da ƙauna ƙanwata. Wannan hali da muke nuna miki ba komai bane face haka muka tashi muka ga ana yi, dukkan mu bamu da laifi a kan turbar da aka ɗora mu kenan, amma don girman Allah….” Mama tayi saurin tarar numfashin tace, “Haba Adda wannan maganar ta wuce har cikin zuciyata, na dawo cikin ƴan uwana da na rasa shekaru masu yawa da suka wuce. Ki ɗauka kamar ɓata nayi aka neme ni aka rasa yanzu kuma na bayyana, kar ki wani tunani a zuciyar ki ki ɗauka hakan ce ta faru.” Kowa kallon ta yake yi cikin farin ciki da walwala tayi murmushi tace, “daman bani da kowa sai ku, ban taɓa sanin inda dangin Gwaggona suke ba, har ta bar duniya ban yi wani wayon da zan tambaye ta ina suke ba balle na san su. Ku kawai na sani, ku kawai nake kallo matsayin ƴan uwa kuma komai nawa. Lokacin da na rasa iyayena bani da kowa dai sai ku ɗin kawai, har yanzu har gobe ku ne ɗin ne kawai dani bayan ku bani da wasu.” Adda Halima tazo ta riƙe hannun ta tace, “ana jima ina neman ki, nayi kukan rashin ki, naji ciwon rabuwar mu duk da bamu da shekaru a lokacin.” Mama ta kalle ta tana dariya kaɗan tace, “Adda Halima yanzu na dawo duk da shekaru sun tafi, babu lallai ma mu kai gobe a duniya, amma in Allah ya ara mana numfashi muna tare daga nan har Allah yayi ikon da akan kowa.” Halima ta rungume Mama cikin farin ciki tana kuka. Mama ma hawaye take yi ta ɗago ta daga jikin ta tace, “Komai ya wuce, na yafewa duk wani wanda yayi min ba daidai ba” ta kalli Daddy da yake zaune yayi shiru kamar mara lafiya shi da Huzaifa ne kawai ko Bebi babu kuma Abban su Bebi yana nan. tace, “Har kai mahaifin su Manal, komai ya wuce na yafe maka, sannan ga yaran ka nan Nusaiba da Fatima kamar yadda ka sani, Fatima tayi aure harda yaro Nusaiba ma an saka ranar auren ta.” Daddy farin ciki hana shi magana yayi, ya rasa abinda zai ce kana kallon sa ka san ya ruɗe saboda abinda yake nema ya samu. Ya kalli Alhaji Ahmad yana cewa, “Ku taya ni godiya ta yafe min, Ku taya ni yi mata Godiya, nayi mata abubuwan da yawa, bancancanci a yafe min ba, amma tace ta yafe min Ku taya ni gode mata.” Yayan ta ya kalle shi yana jin ciwon labarin da Daddy ya bashi akan abinda yayi mata, amma in ya tuna su ƴan uwan ta sune suka fara barin ta sai ya rasa bakin magana. Mama tayi murmushi tace, “babu komai kar ka damu komai ya wuce, na yafe maka saboda Allah da kuma alfarmar Huzaifa..” Daddy yace, “Na gode sosai, Allah ya jiƙan Gwaggo da Baba, Allah ya gafartawa duk wanda kika rasa a rayuwar ki.” Mama ta amsa da amin kowa ma ya amsa addu’ar. Alhaji Ahmad ya kalli Manal da take ta goge hawaye yace, “Ke ce Fatima?.” Manal ta kalle shi ta girgiza kai yace, “Fuskar ta sak kanwata Zahra, amma hasken na a Gwaggo ne.” Mama tayi murmushi ya sake kallon Manal yace, “ku zo kusa dani.” Tasowa sukayi Ayan yana hannun Adda Halima daman suka ƙaraso suka zauna a kusa dashi ya riƙe hannun su yace, “Allah ya yi muku albarka, Allah ya raya ku ya bamu zuciya irin ta mahaifiyar ku.” Suka amsa da amin kafin ya kalle su yace, “mu nan duka iyayen ku ne, baku da ya fi mu a duk duniyar nan, duk abinda kuke so daga yau ku sanar dani, komai tsadar sa komai wahalar samun sa nayi alqawarin mallaka muku shi.” Mubeena tayi murmushi tace, “İn sha Allah.” Yaya Bello da Alhaji Abubakar ma kamar zasu cinye su, haka sauran mazan guda biyu da suke zaune. Manal ta kalli Huzaifa da yake gefe ta kalli mahaifin sa sai ta tashi ta koma kusa dashi tace, “Daddy ka daina kuka, komai ya wuce bana so naga kana zubar da hawaye.” Da sauri ya kalli Manal sai yaga tana murmushi ya kalli Huzaifa da yake gefe shima yana murmushi ya sake kallon Manal yace, “da wanne suna kika kira ni?.” Manal ta sake yin murmushi tace, “Daddy nace.” Kawai sai ya sake fashewa da kuka, Manal ta riƙe hannun sa duka biyun tace, “Don Allah Daddy ka bar kuka yana karya min zuciya” ta faɗa muryar ta na rawa sosai alamun zata yi kuka. “Eh Daddy, ka daina zubar da hawayen ka hakan yana sakawa muji babu daɗi” Mubeena ta faɗa tana dawowa kusa dashi. Farin ciki ya yiwa Daddy yawa ya rasa inda zai saka ransa saboda murna, ya rƙe su a jikin sa cikin zallan farin ciki yace, “na gode ƴaƴana, Allah ya yi muku albarka, na gode sosai, na gode, Allah ya faranta muku.” Manal tace, “Amin Daddy, ka daina yi mana godiya mu fa ƴaƴan da ka haifa ne.” Daddy ya sake kulle idon sa yana hawaye saboda farin cikin da yake zuwa zuciyar sa da gangar jikin sa. Manal ta kalli Huzaifa da yake kallon ta yana murmushi tace, “Yaya Huzaifa ashe yayan da nake cewa ta jini ce ba ta kara ba.” Yayi murmushi yana kallon ta ya kasa cewa komai ganin abun yake kamar a mafarki. Mama ta sauke ajiyar zuciya so take tayi maganar dukiyar yaran ta amma kuma sai bakin ta ya sarƙe ganin yadda yaran suke wajan sa kamar zasu ji babu daɗi in ta yiwa mahaifin su haka. Ɗuke kai tayi bata ce komai ba. Alhaji Ahmad yace, “Yaushe zaku zo Abuja?.” Manal ta kalli Mama itama ta kalle ta tace, “meye zaki kalle ni? Zan hana ki ne?.” Manal sai tayi murmushi tace, “Duk sanda aka shirya zamu zo.” “Ya kamata dai, sannan ina so ku je har Jalingo akwai dangi sosai a can duk su gan ku. Gidajen ƴan uwan mu duk za’a zaga a san ku.” Manal ta girgiza kai tace, “in sha Allah zamu zo.” Adda Halima tace, “daman ni maƙociyata ce ke Manal, waje ɗaya muke zama in nazo Kano, dan haka yau sai kin shiga gidana.” Manal tayi murmushi tace, “To Mama.” Mama ta kalli Yayan ta tace, “a kaf duniya bani da wanda ya taimaka min kamar wannan bawan Allah, a lokcim da nake Zaria shine ya ɗauko ni ya taho dani Kano bai sanni ba ban san shi ba, ya kai ni wajan maahifiyar sa ta riƙe ni hannu biyu, Manal da Mubeena kuwa ta riƙe su kamar jikokin ta. Ita ce ta bashi shawarar aurena duk da lokacim yana da mata guda biyu, ya kuma amince ya karɓi shawarar hannu biyu.” “A cikin dukiyar da na gada a wajan Baba akwai abinda ya rage guda biyu wanda ban rasa ba, na farko takardar gona ce a Jalingo, sai takardar gida shima a Jalingo. Na bashi wannan takardun yaje har Jalingo ya gano wajan ya tabbatar suna nan gonar aka bada ita haya, gidan kuma da yake babu kowa aka siyar dashi a lokacin, amma ita gonar tana nan duk da an siyar da rabi saboda hidimar auren Manal. Ya riƙe min Manal da Mubeena hannu biyu, ya saka su a makarantar kuɗi sun samu ilimi mai kyau tun a wancan lokacin, ya saka su a islamiyya babu wacce bata sauke alkur’ani a cikin su ba, ya basu tarbiyya matsayin mahaifin su babu abinda nake siya musu komai shi yake musu kamar yadda ko wanne Mahaifi yake yiwa yaran sa. Hatta auren Manal da kayan ɗaki ta wani abun duk shine yayi. wallahi bani da kamar aa a duniya, bai taɓa nuna banbanci tsakanin su da yaran sa ba, ko yaushe a cikin basu tarbiyayya yake yana kuma kula da rayuwar su kamar suna gaban mahaifin su ne. Basu taɓa kukan rashin mahaifi ba, shiyasa ko a makaranta nace ya saka musu sunan sa a gaban sunan su dan basu da mahaifin da ya wuce shi a duniya, ba dan shi ba da yanzu ban san inda nake ba, ban san inda yaran suke ba.” Muryar Mama rawa take yi kuka yaci ƙarfin ta akayi shiru tana kuka, sautin kukan kawai ake ji kafin ta tsayar da kukan tace, “Daga shi sai Balaraba babar ƙawar Manal Surayya, tunda nazo unguwar nan a nan na san gidan ta, Manal da Surayya ƴar ta sa’anni ne tana son Manal ta ɗauke ta kamar wacce ta haifa. Ganin ta nake kamar Yayara, duk abinda ya dame ni zuwa nake yi na sanar da ita ta bani shawarar ta kuma rarrashe ni dan ta girme ni, ta san komai a labarina amma bata guje ni ba ta riƙe ni hannu biyu tana nuna min so da qauna. Ko rashin lafiya nayi itace ke zama wajena, itace ke kawo min abinci, maganar da nake muku ma yanzu itace a gidan Manal tana kula da ita tunda ta haihu. Da auren ta amma ta bar gidan mijin ta taje dan ta zauna da Manal kawai, dame zan sakawa waɗannan mutane don Allah?” Ta faɗa tana kuka sosai tana kallon ƴan uwan ta. Maman Surayya da shigowar ta kenan taji ana maganaar tace, “Haba don Allah, kamar wani abu wannan ai ba komai bane an zama ɗaya.” Alhaji Ahmad yace, “ai gwara ta sanar damu duk mu sani, alkhairi ai ba a ɓoye shi duk ƙanƙantar sa.” Mama ta sake cewa, “A fannin rashin lafiyata da ta Manal, na san baku san ina da diabetics ba Manal ma tana dashi, ni abun sai ya haɗu da ciwon zuciya da na ido har idona ma ya kulle bana gani. Amma ta silar Huzaifa da Adnan mijin Manal na samu lafiya har idona suke ganina yanzu, da yake Allah ya ƙulla auren Manal da Adnan ta silar rashin lafiyata suka san jyna har Allah ya kai su ga samun rabon haihuwa. Sun bamu gudumawa sosai ta fannin lafiyar mu, magani da komai kyauta Huzaifa yake bawa Manal saboda kawai yana kallon ta kamar ƙanwar sa ce, ashe Allah ne ya saka masa ƙaunar ta kasancewar ta ƙanwar sa, da gaske ita ɗin jinin sa ce.” Alhaji Ahmad yace, “gaskiya ne wannan, duk inda jinin ka yake sai ka ji shi a jikin ka, ai jini ba wasa bane. A kan fuskar mutum kana iya gane wannan jinin ka ne.” Mama tace, “sai Haruna ɗan wajan Baban su Manal, shima bai taɓa banbanta Manal da ƙannen sa ba, komai yana yi mata kamar yadda yake yiwa ƴan uwan sa.” Alhaji Ahmad ya kalli Baba zai yi magana Baba yace, “don Allah kar kace komai, Mubeena da Manal tamkar ni na haife su haka nake kallon su nake kuma jin su a jikina. A wajena suka tashi kaga kenan uba ne ni a gare su, maganar godiya ko wani abun duk bai tashi ba, dan ba’a godewa uba dan ya yiwa yaran sa hidima.” Alhaji Ahmad ya girgiza kai yana murmushi yace, “Wannan gaskiya ne. Allah ya saka da alkhairi.” Aka amsa da amin kafin Alhaji Ahmad yace, “duk bamu da abinda zamu iya biyan ku dashi sai addu’a, amma ina muku albishir da aikin hajj bana daku za’a yi in sha Allah. Balaraba dake da iyalan ki kaf nayi miki wannan alkƙwarin, kulle gidan ki zaki yi ki tafi saudia a can zaki yi babbar sallah. Haka Malam Usman, kaima da kai da matan ka da yaran ka mata dasu za’a yi wannan tafiyar nan in sha Allah.” “Allahu akbar! Gaskiya wannan Babban tukwuci ne a gare mu da kuma ahlin mu gabaɗayaa. Na gode Allah ya nuna mana wannan lokaciin, ya kuma tabbatar da zuwan namu.” Baba ya faɗa da farin ciki aka amsa da amin. Mama dai ta kasa magana saboda farin ciki sak kallon Maman su Manal take yi dan ta kasa furta komai. Mama tayi dariya kaɗan tace, “Balaraba ta kasa magana.” Aka yi dariya gabaɗaya Alhaji Aliyu yace, “kar ki damu, an zama ɗaya ba sai kince komai ba. Ni ma kuma na yiwa Haruna alƙawarin sabuwar mota, sannan Alhaji Usman Baban Manal kenan na yi masa alƙawarin mota da kuma gida, in kuma nasa yake so a gyara duk zan ɗauki nauyi. Balaraba kuma na yi mata alƙawarin mota itama, sannan duk nauyim karatun ƴaƴan ta zan ɗauka.” Nan da nan waje ya sake zama wajan farin ciki ana ta murna, Alhaji Bello shima yayi nasa alƙawarin duk dan su nuna sun ji daɗin yadda aka riƙe musu ƙanwa da ƴaƴan ta. Waje ya dawo wajan farin ciki sosai kamar komai bai faru ba, ana ta tuna baya labarim ƙuruciya ana dariya. Mama ta kalli Manal ta kalli Huzaifa tace, “Huzaifa ka ɗauki ƙanwar nan taka ka mayar da ita gida darw yayi, sannan daga yau kar na sake ganin ki a gidan nan.” Manal ta kalli Mama tace, “Allah Mama bakya sona yanzu.” “Eh bana son ki.” Yaya Bara’atu tace, “tunda bata son ki ai mu Muna son ki, taho wajena ma ki ƙyale ta.” Manal ta koma kusa da ita ta zauna ta riƙe kafaɗun Manal. Mama tace, “Adda har yanzu ko kwana arba’in bata yi bafa da haihuwa, Sai yawo take yi, ko gidan nan tazo yafi sau biyar.” Tace, “to kwana arba’in ai ta bahaushe ce, tunda ta samu lafiya ai zance ya ƙare ko Manal?.” Ta faɗa tana kallon Manal ita kuma tana kwance a jikin ta ɗaga mata kai. Baba ya kalli Mubeena yace, “Mubeena ki bi Daddyn ki ki kwana cikin ƴan uwan ki ko?.” Mubeena ta kalli Daddy taga alamun yana son hakan sai tace, “To Baba.” Ta tashi ta shiga ciki tana ji ana ta tsokanar Manal ta fito ta tarar Daddy da Huzaifa sun fita sai ƴan uwan Mama kawai kamar ba manya ba sai hira ake ana dariya. Manal ta kalli Maman Surayya tace, “Mama muje?.” Ta kalli Manal tace, “Sai gobe zan zo miki zuwan sassafiya, saura aje a sha sanyi da abu mai zaƙi.” Manal tayi dariya tace, “ai na daina.” Maman Surayya ta fita Manal ma suka fita suka tarar Huzaifa da Daddyn suna jiran su, suka shigar motar huzaifa ya ja suka bar wajan. BDƘB3P29 A motar shiru babu wanda yake magana Ayan yana hannun Mubeena tana yi masa wasa ita kuma Manal tana kallon gefen ta. Daddy jin shiru yayi yawa sai yace, “Mubeena an ina kika tsaya a karatu?.” Mubeena ta kalli Daddy din da yake kallon ta tace, “Na fara Digree a Yusuf mai tama sule na samu matsala na daina zuwa.” Daddy yace, “Manal fa?.” Manal ta kalle shi tace, “ni saboda Mama daman ban fara zuwa ba, kuma ni ko wanne karatu baya burge ni nafu son culinary school, yanzu haka ina yin diploma a kai.” Daddy yayi murmushi yace, “ma sha Allah, ashe muna da professional chef bamu sani.” Manal tayi murmushi Daddy yace, “Mubeena ya kamata ki samu wata school ɗin ki fara, abinda zai faru zan saka a duba ko private school ce sai ki shiga.” Mubeena ta amsa da to suka sake yin Shiru suna tafiya har gidan Daddy. Manal da Mubeena suka fito daga motar suka shiga cikin gidan gabaɗayan su. Duk suna falon ana ganin su aka fara musu sannu da zuwa. Har Daddy ya zauna a falon yana murmushi ya kalli sauran matan yace, “Ummimi, Aysha, Ayra, Baby, Sultan da kuma Amir ga Yayar ku Mubeena da kuma Manal.” Ayra ta dawo kusa da Manal tace, “ƙawata” ta faɗa tana bawa Manal hannu suka tafa. Manal ta kalli Ayra ta kalli Aysha Mubeena tace, “Yaya kamar ke.”Mama da take zaune tayi dariya tace, “Wallahi kamar su ɗaya.” Aka yi dariya Daddy yace, “a nan zata kwana damu yau.” Mama tace, “ma sha Allah kace yau nuna da babbar baƙuwa duk da ba baƙuwa bace ba.” Dariya aka yi kafin Huzaifa ya shigo yace, “Manal muje na kai ki gida, dare yayi.” Manal ta kalle shi tace, “dama ka masa waya kace zan kwana a nan.” Daddy yace, “A’a ban amince ba, tashi ku tafi.” Ta kalli Mubeena tayi mata gwalo, Manal cikin shagwaɓa tace, “Daddy kaga tana yi min gwalo ko?.” Daddy cikin farin ciki ya kalli Mubeena yace, “A’a Yaya Mubeen, kar ki saka aurar Mama kuka.” Mubeena tayi dariya tace, “Daddy ta cika shagwaɓa ne.” Aka yi dariya Manal da Huzaifa suka fita. Har gida Huzaifa ya kai ta ya samu Bebi ya dawo shima a lokacin ya ajjiye motar sa, ganin su sai ya tsaya har suka fito daga motar ya ƙaraso ya karɓi Ayan a hannun ta yace, “ina kiran ki bakya ɗauka, nayi zaton kin dawo gida.” “Yayan ta ya dawo da ita, akwai damuwa ne?” Huzaifa ya faɗa yana kallon sa da sigar tsokana. Bebi yayi tsaki yace, “ba da kai nake ba ai.” Huzaifa yace, “Manal nuna masa waye ni a wajan ki yanzu.” Manal tayi murmushi kawai bata ce komai ba. Kallon Huzaifa tayi tace, “Yaya Huzaifa ka gaida gida.” Ya amsa ta shiga ciki Bebi ya kalle shi har lokacin Ayan yana hannun sa yace, “da alama komai ya zama normal ko?.” “Alhamdulillah, wallahi komai ya daidaita, sai aby ya koma raha ana farin ciki. Yanzu haka Mubeena tana gidan mu a can zata kwana, itama Manal ɗin wai na kira ka nace maka zata kwana.” Yayi murmushi yace, “haka ake so, Allah ya sake daidaita tsakani.” Ya amsa da amin kafin ya shiga mota ya fita shi kuma ya shiga ciki. A tsaye ya ganta a falo ya kalle ta yaga shi take kallo ya ƙaraaa ya ajjiye Ayan a kan kujera ya kalle ta yaga dai kallon sa take yi, ya ce, “kallon na meye ƴan mata?.” Murmushi tayi ta matso ta rungume shi ta kwantar da kanta a ƙirjin sa. Hannu biyu ya saka ya zagaya da hannun sa bayan ta ya riƙe ta yace, “akwai labari ne?.” “Ka taya ni murna partner, maahifina da ƴan uwan Mama duka komai ya zama daidai. Farin ciki nake ji sosai a raina, nayi murna da bayyanar dangin Mamana, ko babu komai na san ƴan uwan Mamana a kusa dani.” “Ina taya ki murna Manal ɗina, Allah ya baki ikon yi musu biyayya, Allah ya cigaba da saka ki farin ciki har abada.” Ta sake riƙe shi sosai tace, “amin Partner. Yanzu Mama kuka ya ƙare in sha Allah, damuwar Mama tazo ƙarshe, wannan dalilin yafi min komai daɗi wallahi.” Ya ɗago ta daga jikin sa yana kallon fuskar ta ganin sai murmushi take yi yace, “ai in sha Allah rayuwa za’a yi mai daɗi wacce ba’a yi ta a baya ba, addu’a ai ba ƙarya bace ba Manal. Kuma na faɗa miki mahaifi mahaifi ne, dole ki ji farin ciki a zuciyar ki Manal.” Ta girgiza kai tace, “gaskiya ne wannan, na amince. Ka san me Yayan su Mama ya yiwa Baba da Maman Surayya alƙawari?.” Ya girgiza kai alamun A’a ta sauke numfashi tace, “Duk ya biya musu aikin hajji, kowa sai murna yake yi, wajan ya koma wajan farin ciki.” Bebi yace, “ma sha Allah, amma ya kyauta sosai nima naji daɗi.” Mayar da ita jikin sa yayi ta sake kwanciya a ƙirjin sa ya lumshe idon sa, Manal tace, “Naji daɗi nima sosai.” “Daman ba tare ku ke da Maman ba?.” “Uhum tace sai gobe zata zo.” “Allah ya nuna mana, ai kin ma ware kamar baki haihu ba kin yi kyau sosai, ta kular min dake yadda ya kamata jira kawai nake ta dawo min dake ɗakina. Allah Manal na gaji, nayi haƙurin rashin ki, na sake yi na kuma yi amma na kusa kasa jurewa abin yayi yawa. Kin warke tuni baki da wata matsala amma ko kwana inda nake bakya so, kin barni kamar maraya bayan ina dake. Gaskiya na gaji Manal, na gaji wallahi, ke kin san nayi ƙoƙari sosai” ya faɗa yana ɗago ta daga jikin sa yana kallon ta. Manal tace, “to har yanzu fa bani da tsarki, nima na gaji na tsani wannan jinin wallahi, yaƙi tafiya ya barni.” Yayi murmushi yace, “kora shi zan yi dan da gaske ya fara cutar dani, na gaji ina missing ɗin ki sosai, baza ki gane abinda nake ji bane shiyasa.” Tace, “in ka faɗa min zan gane.” “A’a baza ki gane ba, gwara nayi shiru.” Tayi dariya tace, “kayi min girki yunwa nake ji, baka taɓa yi min girki ba don Allah yau kayi min” ta faɗa tana kallon sa a shagwaɓe. Ya kalle ta ya ce, “haka nace miki na iya girki?.” “Indai kayi min, Allah yunwa nake ji, yaron nan sai ya dinga cinye mim abincin jikina.” Ya kalli Ayan da yake ta kalle-kalle dan idon sa biyu ya kalle ta yace, “muje dai na haɗa miki tea ba girki ba, akwai wheat bread ai nazo dashi.” Ta fara yi masa dara tana buga ƙafa tace, “ni Allah bana son tea abinci nake so kuma kai nake so ka dafa min.” Yace, “Manal me zan dafa miki? Na gaji daga aiki na dawo fa baza ki tausaya min ba?. Muje dai na haɗa miki tea da kaina amma batun girkin nan ki barshi. Mu je har kwai sai na soya miki.” Manal ta bishi da kallo tace, “yanzu baza ka yi min ba?.” Bebi ya kalle ta yace, “ƙarya da ciwo, in nace zan miki ƙarya nake yi. Zo muje dai” yayi gaba yana jan hannun ta zuwa kitchen ɗin tace, “Allah inda a novel ne mijin novel sai yayi mata girki duk abinda take so, amma kai bak iya soyayya ba.” Cak ya tsaya yana kallon ta yayi dariya kafin yayi tsaki ya ɗauki akwai guda biyu ya ɗora fan a kan wuta ya saka mai, ya fasa akwan a kai ba tare da ya saka maggi ko albasa ba yace, “yanzu zai yi sai ki ci.” Manal ta kalli kwan tace, “kalli fa ko maggi babu, kuma baka saka albasa ba taya zan ci abu yana ƙarni?.” Ya wara ido yace, “au soya miki ɗin ma da nayi bai miki ba kenan?.” “Bai min ba” ta faɗa tana kallon gefe ɗaya ya girgiza kai ya ce, “kin yi da ɗan halak.” ta murguɗa baki kafin tace, “na bar ɗana a falo” ta faɗa tana fita da sauri sai gata ta dawo dashi a hannun ta ya kalle ta ya ce, “Ke bakya jin kunyar cewa ɗanki ki ko a gaban Mama?.” Manal tace, “to ba ɗan nawa bane?, ai ni na sha wahalar haihuwar sa ko?.” Yayi ƴardariya yace, “naki ne.” A lokacin ya cire ƙwan daga cikin fan ɗin ya saka mata a mini plate yace, “to gashi nan.” Taja kujera a kitchen ɗin ta zauna tace, “saura tea ɗin, kuma ka wanke fan ɗin kar ka bar min shi ya kwana.” Ya harare ta ya ce, “to sannu Mummy, ita ce zata bani wannan umarnin ba ke ba.” Tayi dariya yace, “ƙyayi dariya ai.” Manal tace, “kai ko karar nan baka yi min, haifar maka ɗa nayi ya kamata ka dinga yin abinda nace.” Ya ajjiye mata tea ɗin yace, “yanzu kika ce min ɗan ki ne” ya faɗa yana buɗe fridge ya ajjiye mata bread ɗin. Manal tace, “eh ɗana ne, amma kaima ɗan ka ne.” Ya girgiza kai yace, “A’a naki ne ke kaɗai, na bar miki.” “Ni kaɗai na haife shi?.” “Eh mana, ba kin ce ke kaɗai kika shiga labour room ba?.” “To waye yayi min cikin?.” Da sauri ya juyo yana kallon ta, sai ta rufe bakin ta da hannun ta tare da kulle ido. Yayi dariya yana girgiza kai yace, “Lallai Manal kin waye, ko ƴar kunyar nan da ki ke ji yanzu guduwa take yi. Wato waye yayi miki cikin ko? Eh tabbas ni nayi wannan. daman tun kafin a haifi Ayan ki ka ce min nayi miki ciki.” Shiru tayi bata amsa masa ba ta fara shan tew ɗin yana ta tsokanar ta taƙi kula shi har ta gama ta koma ɗakin ta tana dariya, ta ajjiye Ayan tayi wanka ta saka kayan bacci, ta canjawa Ayan kaya tana gyara shi ya shigo yace, “Muje ko?” Ya faɗa yana ɗaukar baby bed ɗin da Ayan a ciki ya fita dole tabi bayan sa. Bayan Kwana biyu. Manal na shan baƙi masu zuwa gidan ta, kullum sai ƴan uwan Mama sun zo da yaran su ana gaisawa. Kullum cikin baƙi take in ba’a zo ba ita zata je, kwanakin ya zamar mata na farin ciki ta san wanda bata sani ba a ƴan uwan ta sosai. Har gidan su taje ta yini har dare tana can ana hira ta saba da kowa da kowa ta kuma sake kamar daman can a gidan ta tashi. Mubeena da Mama sun je Abuja kwanan su biyu a can ana ganin gidan ƴan uwa Mama tace Manal Sai Ayan ya gama yin ƙwari taje daga baya. Zuwa Jalingo ne Manal ta dage sai taje, da Bebi ya hana harda kuka dole ya haƙura ya sallama ta da yaron sa suka tafi Taraba state. Kwanan biyu suka yi suka dawo cikin kewa ʼƴan uwa dan kowa yaji daɗin ganin Mama da yaran ta harda jika. Lokacin da suka dawo kuma Daddy yake son suje dangin sa da suke garin Zaria da cikin Kaduna, haka aka sake ɗaukar hanya bayan kwana biyu suka dawo kasancewar babu ƴan uwa a can sa na uba. Manal dai tana ta shan yawo Ayan har ya fara mura da zazzaɓi mai zafi, ranar da suka dawo daga Zaria Bebi yace tayi haƙuri amma babu inda zata sake zuwa sai ɗan sa yayi ƙwari ya gaji da wannan yawon da take yi. Maman Surayya tunda Manal suka fara yawon nan ta tattara ta koma gida, amma ta gama gyara Manal ta ko ina ta ta kuma tsuma ta yadda ya kamata. Washe farin da suka dawo daga Zarria Bebi ya saka ta a mota suka je har gidan Maman Surayya siyayyan kayan abinci, da kayan sakawa da kuɗi suka je aka yi mata godiya mai yawa aka kuma bata wannan kyauta. Taji daɗi sosai tayi murna mijin ta ma da ya dawo yaji daɗin yadda suka karrama Mama ya kuma yaba domin sun san alkhairi. Ita kanta Mama taji daɗim abinda suka yi mata dan yaba kyauta bahaushe yace tukwici. A ranar bayan sun dawo daga gidan su Surayya Manal tayi wanka ta shirya Ayan ta tayar da shafa’I da wutir kenan Bebi ya shigo ɗakin. Kallon ta yake yi da mamakin yaushe ta fara sallah bai sani ba? har ta idar yana zaune ya kalle ta ya ce, “shine ko labari?.”Tayi dariya ƴar tace, “jiya ne fa.” Ya Harare ta tace, “ko yau ne ai ya kamata na sani. zazzaɓin jikin sa ya sauka?” Ya faɗa yana taɓa jikin Ayan sai yayi ƙaramin tsaki yace, “har yanzu akwai, Murar nan ta dame shi wallahi.” Manal tayi shiru bata ce komai ba dan da tayi magana zai ce ai itace ta jawo ya sake kallon ta yace, “to Madam muje ko?.” Ta ɗan kalle shi tace, “kai ko jan ajin nan babu?.” Zai yi magana aka kira shi a waya ganin sunan Mama ne sai ya ɗauka. Hankalin sa ya tashi jin Mama tana kuka yace, “Mummy lafiya? Me ya faru naji maganar ki haka?.” Mama tace, “Adnan Abban ku ne, kazo gida jikin sa yayi zafi yace bazai je asibiti ba, kazo don Allah yanzu.” Kashe wayar yayi yace, “Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un.” Manal da ta miƙe tsaye tana kallon sa tace, “Meya faru?.” Ya kalle ya ce, “ina zuwa” ya faɗa yana fita da sauri. Hankalin ta ita kanta yaƙi kwanciya saboda bata san abinda ya faru ba, shi kuma Bebi kai tsaye gidan ya wuce. Yana zuwa ya tarar da kowa yana zaune an saka shi a gaba shigar sa sai Yaya yace, “Yauwa gwara da kazo Bebi, yaƙi yarda a tafi asibiti kuma jikin sa yayi zafi sosai.” Bebi ya ƙaraso ya riƙe hannun Abban jin da zafi sosai yace, “Abba don Allah muje asibiti, zaka fi samun kwanciyar hankalina can.” Abba ya tashi zaune yace, “ba sai naje ko ina ba Adnan, kawai ku tafi gidan ku zan samu lafiya.” Bebi yace, “don Allah.” “Ka bar min magiya bazan je ba.” Bebi ya kalli Yaya da yake tsaye yace, “zan je na ɗauko abinda ya kamata ayi masa yanzu na dawo” ya faɗa yanafita ya hau mota da hanzari ya nufi asibiti. Bai jima sosai ba ya dawo yana higowa ya auna bp ɗin Abban kamar yadda yayi tunani ya hau sosai ya saka masa ruwan da zai saukar dashi har da lalurar bacci yayi masa. Suna zaune kusa dashi ana yi masa sannu har bacci ya ɗauke shi, duk suka fito aka bar shi dan ya samu yayi baccin sosai Mamy ce kawai ta rage a wajan sa. Lokacin sha biyu na dare har ta gota ya hau mota ya tafi gida gabaɗaya jikin sa yayi sanyi akan lamarin damuwar da Abba yake sakawa a zuciyar sa. Haka ya shiga jiki a sanyaye ya kulle gidan gabaɗaya ya shiga ciki. A ɗakin sa ya same ta a kwance tana ji ya buɗe ƙofar ta tashi zaune tace, “baka faɗa min abinda ya faru ba, na kira ka yafi sau a irga baka ɗauka ba, me ya faru don Allah?.” Ya ƙaraso yace, “Jikin Abba ne ya tashi, amma yanzu yayi bacci.” Manal tace, “amma shine ka ƙi faɗa min? da sauƙi dai ko?.” Ya ɗaga kai yace, “da sauƙi yayi bacci” ya faɗa yana shiga banɗaki. Tana zaune ya fito ya saka riga da wando na bacci ya kwanta a gefen ta yana kallon sama alamun akwai abinda yake damun sa. Kallon ta yayi ganin tana kallon sa sai yace, “babu komai fa kar ki damu.” Bata ce komai ba, dan da alama ya manta tace ta daina tambayar sa damuwar sa. Haka suka kwana baya cikin walwala, abinda yayi kuɗurin yi baya cikin farin cikin aikatawa. Da safe ya sake komawa wajan Abban ya samu jikin yayi kyau sosai dan abinci ma yake ci Bebi ya zauna yace, “Abba ya sauƙin jikin?.” Abba yace, “jiki yayi kyau Adnan, ko ciwon kan bana ji.” “Haka ake so, amma Abba damuwa tayi maka yawa ita take saka ka a wannan yanayin.” Abba ya girgiza kai bai ce komai ba sai daga baya yace, “Yauwa, akwai wanda yake neman auren Maryam, yanzu haka maganar na wajan Daddyn ku.” Bebi yaji daɗi a ransa sosai yace, “Allah ya tabbatar da alkhairi.” Ya amsa da amin. Shigowar Daddym su Huzaifa ne ya saka Adnan ya tashi tsaye, bayan sun gaisa yayi musu sallama ya fita. Daddy ya kalle shi yace, “Ya jikin naka? Huzaifa yace min ba lafiya.” “Naji sauƙ, daman jinin ne ya hau.” Daddy ya kalle shi yace, “akwai damuwa kenan?.” “Babu komai, abinda ya wuce ne kawai bana son tunawa, kai kan ka kunyar ka nake ji.” Daddy yace, “ni ya kamata ai naji kunya ba kai ba.” Abba yayi murmushi kawai bai ce komai ba dan bazai gane abinda yake nufi ba, shi kuma nauyim faɗa masa yake yi. Daddy ya kalle shi yace, “na gama tattara abinda zan iya na dukiyar babar su Manal zan mayar mata.” Abba yace, “in kace zaka yi haka kaf abinda ka tara nata ne fa, da dukiyar kayi ƙarfi haka.” “Na sani, wani abun aai na koma qatar zan sake tattarowa.” Abba ya sauke ajiyar zuciya yace, “hakan yayi, gwara ka fita haƙƙin ta, ko da baza ta karɓa ba dai kai ka bayar ka huta. Allah na gode maka da ban ci ko sisi a kuɗin ba, da yanzu tashin hankalin da nake ciki yafi haka.” Daddy yace, “so nake na gama da magana da damuwar nan gabaɗaya, na juya neman matata ta uku, wacce na faɗa maka ita na fara aura kafin babar su Manal.” Da sauri Abba ya kalle shi yace, “kana nufin akwai wata ma wacce ka tafi ka bari kenan?.” Daddy ya girgiza kai yace, “ƙwarai kuwa, ai na faɗa maka tun a shekarun baya ka manta ne. Amma ita na san dangin ta har gidan su na sani kuma ita ban barta da yaro ba, dole zan je na nemo ta a duk inda take ina da buƙatar neman yafiyar ta itama.” Abba ya kalle shi da mamaki yace, “bayan ita sai wa kuma?.” Daddy yace, “ita kaɗai ce wallahi, su kenan su uku na aura. Kuma ita ban ɗaukar mata komai ba kawai nayi auren sha’awa da ita ne, ban taɓa zina ba kuma ban son yin zina kai ka sani, shiyasa tun a lokacin na amince na aure ta da na lalata ta.” Jin abinda Daddy yace sai Abba yayi shiru jikin sa yayi sanyi ya sauke numfashi yace, “ka huta, kasan komai bazan ɓoye maka komai ba, nasan kasan sirikin da Allah ya baka, saboda Adnan yana auren Manal ƴarka hakan bazai hana ni faɗar abinda ka sani ba. Aliyu sharrin aikata zina ne yake bibiyata, yarana biyu a cikin gidan nan duk an yi zina dasu saboda nayi da na wasu. Ka huta da Allah bai saka ka a layin irin mu ba, da yanzu duniyar nan gabaɗaya baza ta tyi maka daɗi ba.” Daddy yace sauke ajiyar zuciya yayi shiru yana jinjinwa hukuncin Alalh a kansu kafin yace, “kaima ai kayi nadama, kuma ka nemi tuba komai ya wuce.” Abba yace, “baza ka gane ba, baza ka gane irin ɓarnan da naso nayi ba shiyasa ka ke faɗat haka, Allah na gode maka da haka bani ikon aikata komai ba.” Daddy yace, “yanzu taimaka min zaka yi na nemo ta na bata haƙuri itama komai ya wuce.” Abba yace, “a ina take?.” “A nan kano take, a cikin unguwar…” ya faɗa yana tuna sunan unguwar kafin yace, “Unguwar Tarauni.” Abba ya sauke ajiyar zuciya yace, “meye sunan mahaifin nata?.” Daddy zai yi magana Mama ta shigo da sallama suka amsa ta kalle su bayan su gaisa da Daddy tace, “Su Sumayya ne suka zo gaishe ka dasu Yaya Mubarak.” Abba yace, “bismillah su shigo.” Suka shigo da sallama aka amsa suka zauna Yaya Mubarak ya kalli Abba yace, “Alhaji ya jikin?.” Abba ya amsa yace, “Ya Abuja?.” “Alhamdulillah.” Suka gaisa da Yayar Mama da kuma Sumayya ƙanwar Mama. Rumana ma na gefe suka gaisa da Abban. Daddy waya yake yi gabaɗaya hankalin sa baya kan au Ssi da ya gama ya kalle su suka gaisa da Yaya Mubakar yana kallon sa shima yana kallon sa. Sumayya ce ta kalle shi sosai shima ita yake kallo, ɗauke ido yayi ya sake kallon ta ya kalli Yaya Mubakar ya sake kallon Sumayya ya kalli Abba yace, “Iyalan gidan Alhaji Abdullahi gwarzo ne?.” Abba ya ɗaga kai yace, “eh sune mana, Maman su Adnan ai ƴan uwan tane, lafiya dai?.” Daddy ya kulle ido ƙirjin sa ya buga sosai ya kalli Sumayya da take kallon sa ya nunawa Abba ita yace, “itace wacce nake faɗa maka yanzu, itace matar da nake faɗa maka na aura. Meyasa abubuwan nan suke zuwar min haka? Meyasa suke zuwa a haka ne?, Meyasa duk abin ya zama wani iri?.” Kowa kallon shi yake yi, Sumayya ta kalle su ta sake kallon sa amma bata ce komai ba. Yaya Mubakar yace, “in na fahimta daidai Aliyu ne a zaune girma ya kama shi haka ko?.” Mama da take gefe tace, “ban gane ba wai, waye shi ɗin?, kar dai kice min shine.” Sumayya ta girgiza kai tace, “shine Mama, shine wallahi.” Rumana kallon su take yi a ranta tana maimaita shine wa….? Mama da take gefe tace, “kenan kina nufin shine mahaifin Rumana?.” Sumayya ta ɗaga kai alamun eh shine. BDƘB3P30 Mama kallon Daddy tayi Abba ma kansa mamaki yake yi jin abinda yake faɗa, abin ya ɗaure masa kai sosai ya sake kallon Daddy ya ce, “Kenan Sumayya itace wacce ka ke min maganar ta yanzu?.” Daddy ya ɗaga kai ya ce, “itace” ya faɗa a raunane. Mama ta kalli Rumana ta kalle shi ta kalli Sumayya tace, “kina nufin dai da gaske shine mahaifin Rumana?.” Sumayya tace, “shine.” Gaban Mama yayi mugun faɗuwa, ba komai ne yazo ranta sai tunawa da tayi kenan da Manal da Rumana mahaifin su ɗaya?. Ƙirjin ta bugawa take yi saboda tashin hankali. Sumayya tace, “lokacin auren bakya nan kina saudia lokacin Farida na fama da wannan ciwon cikin, hakan ya saka baki san shi ba har auren ya mutu kina can, kuma lokacin ba zamanim waya bane balle a tura miki hoto.” Yaya Mustapha Yayan su Mama yace, “to wannan ai ba wani abun bane, daman ƴar sa ce bai sani ba kuma gata yanzu a zaune.” Daddy ya kalli Rumana da take kallon sa ta kalli Ammi ta ɗaga mata kai tace, “Shine mahaifin ki, na faɗa miki daman ban sani ba ko yana da rai ko baya da rai, yau gashi kin ganshi.” Daddy kallon Rumana yake yi cikin faruwar gaba ya kalli Sumayya kafin tayi magana Yayar ta Umma tace, “babu wanda ya san da ciki a lokacin da ka sake ta, sai bayan kwana biyu sannan aka tabbatar dashi, gashi kuma ka ɓace balle a sanar da kai akwai rabo tsakanin ku. Wannan dalili ne ya saka aka ajjiye batun ka har ta haihu ta raine ta da ta tashi yaye ta ta bawa Yayar ta Hauwa, a nan gidan Rumana ta girma a nan ta rayu a hannun yayar babar ta.” Rantse ido Daddy yayi tare da yin shiru, shi muka tasa ƙaddarar kenan, karkasuwar yaran sa wanda ya sani da wanda bai sani ba saboda auren mata a waje daban-daban. Mama ta kasa magana tayi shiru kawai gabaɗaya tsoro ya mamaye mata zuciya. Abba ya kalle shi yace, “aka sake samun karuwar ƴa, daga biyu sun zaka uku.” Daddy ya rasa me ma zai ce yayi shiru kawai ya sunkuyar da kai cikim sanyi jiki. Yaya Mustapha yace, “rabon zasu ga junq ne ya kawo mu yanzu, da rabon Rumana zata san mahaifin ta.” Wajan yayi shiru babu wanda yake magana saboda tashin hankali, Daddy ya kasa ko motsin kirki kunya gabaɗaya ta dabaibaye shi, bai yiwa Sumayya komai a lokacin auren su ba, bai wulaƙanta ta kamar yadda ya yiwa Maman su Manal ba, ita cikin ruwan sanyi suka rabu bayan yace mata tayi haƙuri wani dalili ya saka zai rabu da ita. Rumana dai kallon sa kawai take yi cikin tashin hankali gabaɗayq wani iri take ji a zuciyar ta. Ta kalli Mama. Tace, “Mama da gaske shine mahaifina?.” Mama bata amsa ba sai Umma da tace, “shine Rumana.” Rumana ta kalli Daddy da ya sunkuyar da kai bai ce komai ba ta sake kallon Babar ta. Abba yace, “kar ki damu zai warware miki komai, Aliyu ya kamata ace a sanar da iyalan ka kowa ya san Rumana ya kuma san labarin Rumana da mahaifiyar ta. Rai ba a hannun mu yake ba ko yaushe rai zai iya yin halin sa, gwara kowa ya san ta kafin mutuwa ta ratso tsakiya.” Sumayya ta taɓe baki ganin sai wani sauke kai ƙasa yake yi, duk da ita baza tace ga abinda yayi mata ba, kawai dai auren ta auren bai kai shekara biyu ba suka rabu shine kawai matsalar. Mama ta kalli Dady tace, “Bayan Sumayya kuma sai wacece? Tunda na lura auren mata ka ke yi kana sakin su kana barin ƴaƴan ka, tun a shekarun baya daman akwai irin ku?.” Daddy bai iya magana ba Yayan Mama ya kalle ta yace yace, “meye haka Hauwa? Wacce irin magana ki ke yi haka? Bakya ganin ga ƴar sa nan a zaune?.” Mama ta kau da kai gefe Daddy yace, “barta ta faɗa, gaskiyar ta ne haka lamarin yake, suke nan matan da na san na aura a rayuwata, kuma dukkan su babu wacce ban yi nadamar bari ba, ban san kuma cewa Sumayya akwai ciki a lokacin ba da ba’a kawo wannan lokacin ban san ƴata ba” ya faɗa yana kallon Rumana da idon ta ya cika da hawaye. Yaya Mustapha yace, “aure ai rai ne dashi, rabon zata je wani gidan tayi aure har ta haifi yara huɗu bayan Rumana ne ya saka auren ku ya mutu. A shekarar da auren ya mutu bayan ta haihu tana yaye Rumana Allah ya bata miji tayi aure dalilin da ya saka Rumana ta tashi a hannun Yayar ta kenan, to ni ban ga abin damuwa a nan ba, rashin sanin ƴar ka ne daman kawai matsalar kuma ka ganta, kaga shikenan sai ka nuna ta ga iyalan ka a cigaba da zumunci.” Abba yace, “haka ne, amma don Allah ku tsaya a kira iyalan nasa gabaɗayq su zo nan a sake maimaita maganar nan. Ya kamata ayi komai da hanzari kar rai yayi halin sa, gwara ka sanar dasu su san tun a yanzu” ya faɗa yana kallon Daddy da ya kasa magana. Daddy ya girgiza kai ya goge idanun sa yace, “haka ne, kira Huzaifa.” Yaya Mustapha yace, “wannan gaskiya ne, ni dai yanzu akwai meetingin da zan yi amma zuwa dare zan iya dawowa in an mayar da taron zuwa dare.” Abbba yace, “Babu komai Alhaji Mustapha, Allah ya nuna lokacin za’ar sanar da kowa ya zo zuwa dare a tattauna abinda ya kwnata.” Ya amsa ya tashi ya fita duk suka bi bayan sa har Rumana da take kuka. Daddy ya kalli Abba bayan fita yace, “Duk wannan kunyar duniyar da nake ji haƙƙin mahaifiyar Manal ne fa, haƙƙjn ta ne saboda itace marainiya gaba da baya kuma na wulaƙanta ta. Wannan shine kwatankwacin kunyar duniya kenan, ina ga kunyar lahira?. Ni dai zan je yanzu na kai nata documents ɗin nan ko zan samu hankalina ya kwanta. Kaga fa ashe ina da wata ɗiyar bayan su Mubeena, gwara su na san dasu tun farko, amma ita ban san da ita ba. Wacce irin rayuwa nayi a baya ne? Wanne irin kuskure na dinga aikatawa?.” Abba yayi murmushi takaici yace, “kuskuren da kayi ba komai bane akan wanda nayi, na faɗa maka kai kan ka da zaka ji abinda na aikata tabbas da zaka yi baya dani, zaka tsana ni ka kuma tsani halayya ta. Nayi abubuwa da yawa wanda yanzu nake dana sani bayan na fara ganin sakamakona tun a duniya. Wallahi na gwammaci mutuwa a akan wannan rayuwar da nake ciki.” Daddy ya sauke ajiyar zuciya yace, “duk kuma da ilimin mu a lokacin, Mun san gaskiya muka dinga bi muna saka ƙafa muna takewa. Allah ka yafe mana, Allah ka raba mu da jin kunyar lahira, ta duniya dai mun ji ta.” Abba ya amsa da amin Daddy ya miƙe tsaye yana jiri ya dafe kai yace, “zan kira Huzaifa yazo muje gidan su Manal ɗin, ayi komai a gama.” Kai kawai Abba ya ɗaga masa ya fita ya shiga mota driver ya fita dashi. A ƙofar gidan su Manal suka haɗu da Huzaifa da yace ya same shi a a ƙofar gidan su Manal, Huzaifa ya kira Baba a waya ya sanar dashi baya nan amma yanzu zai dawo. Suna zaune a motar kuwa sai gashi ya dawo Daddy da Huzaifa suka shiga ciki da ispm Baba. Mama ce kawai a gidan Mubeena tana can gidan ƴan uwa, Mubeena bata zama itace nan itace can ana gaisawa da ƴan uwa. Su Abba suka shiga cikin gidan da sallama. Mama ta amsa tana kallon su tace, “A’a sannun ku da zuwa.” Suka amsa har cikin falon suka shiga Huzaifa ya gaishe ta amsa kamar ko yaushe suka gaisa da Daddy kafin yace, “Fatima haƙƙin ki da yake rataye a wuyana shine yake ɗawainiya dani, abubuwa daga wannan sai wannan suna ta faruwa. Shiyasa nazo na sauke haƙƙin ki da yake kaina.” Mama bata ce komai ya fito da taron takardu a babbar jaka ya ajjiye a gaban Baba yace, “wannan shine takardar duk wani abu da na mallaka wanda yake Kano da wajan kano, takardar company da komai suna ciki. Gidan da na mallaka a Qatar ne kawai babu shi a nan saboda shi yana can, amma in na koma duk zan tattaro na kawo mata zan kuma tashi daga gidan, kuɗi kuma suna da yawa zan turo maka duka a cikin account ɗin ta, tunda haƙƙiin ta ne ba nata ba.” Baba bai ce komai ba ya kalli Mama da take jin abinda yake cewa tace, “ni nace maka dukiyar tana gabana ne?.” Daddy yace, “baki ce ba, amma haƙƙin ki da na raba ki dashi yanzu na dawo dasu. Nazo naje na samu Alhaji Ahmad ma sai akace min ya koma Abuja, shiyasa nazo da wakilan kema ga wakilin ki ayi komai gaban su, na dawo miki da dukiyar ki da na ɗauka na tafi da ita a wancan lokacin.” Mama ta sauke ajiyar zuciya tace, “ka ɗauke documents ɗim ka ni bani buƙatar wasu dukiyar ka, da ka ɗauka Allah yayi zasu zaɓa rabon ka, kawai ka tabbatara ka koma dasu tunda ban neme su a baya ba a yanzu da Allah ya sake rufa min asiri ƴan uwana suka bayyana bani da buƙatar amfani da wata dukiya, dukiyar ƴan uwana ta ishe ni yin duk abinda nake so nayi, dan haka ka ɗauka kaje ka cigaba da kasuwancin ka.” Daddy ya girgiza kai yace, “bazan iya komawa dasu ba saboda haƙƙim ki ne, in na tafi dasu haram nake ci saboda naki ne ba nawa ba, don haka ko bakya so zan tafi na bar su a nan zan kuma tashi daga duk gidan da na kawo miki takardar da, abubuwan da na mallaka kafin auren ki sune nawa, amma daga lokacin da na aure ki dukiyar ki da siya na cigaba da amfani ba tawa ba. Gabaɗaya dukiyar tawa bata taka kara ta karya ba, shiyasa na tabbatar da komai na mallaka naki ne ba nawa ba.” Mama tace, “na sani, amma ina faɗa maka bani da buƙatar su ne ka tafi dasu kamar yadda suke a wajan ka, ni na yafe.” Daddy yace, “bazan iya ba, a hannun ki zan barsu saboda haƙƙin ki ne ba haƙƙina ba.” Mama ta kalli Baba da yake jin abinda ake yi tace, “ka sanar dashi ya ɗauke dukiyar sa bani da buƙayar ta a cikin rayuwata, yaje ya cigaba da harkokin za komai ya wuce har dukiyar na bar masa. Bana so ba kuma na so a dinga tuna min da abinda ya riga ya wuce, yadda na manta da komai a bar ni a na manta ɗin, tunawa zai iya jawowa na furta wata kalma mara daɗin ji.” Baba ya kalli Daddy yace, “kaji abinda tace, kaje dasu ta yafe.” Daddy ya girgiza kai yace, “A’a, bazan iya ɗauka na tafi dasu ba, yadda na ɗauko na dawo dasu sun bar wajena, duk kadarorin na siyar da asalin su amma duk na mayar dasu ga takardun su zan kuma zo muje da kai na nuna maka duk inda dukiyar take. Akwai company a lagos na shinkafa duk zamu je in Allah ya ara mana rai da lafiya ka.” Mama ta kawar da kanta gefe bata ce komai ba Daddy ya miƙe tsaye ya kalle ta ya ce, “na gode da karamcin da aka yi min, na gode da aka yafe min ɗin da akayi. Huzaifa mu je” ya faɗa yana yin gaba Huzaifa ya biyo bayan sa suka fita daga gidan. BDƘB3P31 Bayan fitar Daddy daga gidan su Manal Mama ta kalli Baba tace, “ka mayar masa da takardun sa bani da buƙatar su, kallon su yana tuna min da abubuwa da yawa dana manta a rayuwata. Don Allah ka mayar masa bana so yarana ma basa son dukiyar.” Baba yayi murmushi ya ɗauke takardun ya fita dasu ya adana a wajan sa da niyar zai mayar masa sai ya samu lokaci zai kai masa har gida. Tunda tace ta yafe ai shikenan shi gaba ta kai shi tunda dai dukiya maganar mai ita take ji. Manal ta dawo daga school tana zaune a falo tana shan ruwa Ayan kuma yana cinyar ta yana shan nono. Lokacin yamma tayi magriba na gab da yi Bebi ya shigo falon da sallama yana kallon ta har lokacin damuwar jiya bata wani bar shi sosai ba, ta amsa sallamar tace, “sannu da dawowa.” Ƙarasowa yayi ya zauna kusa da ita ya yi mata kiss a goshi yana kallon Ayan da take shayar dashi idanun sa a kulle ya shafa gishin sa yace, “ya school ɗin?.” “Alhamdulillah, sai yanzu na dawo.” “Gaki nan a gajiye ai.” Manal ta zare Ayan ganin yayi bacci ta gyara rigar ta tace, “ko abinci ban maka ba, bara na tashi na dafa maka.” Ya buɗe ledar hannun sa yace, “kar ki damu, na tahp mana da abinci na san daman zaki jima a school.” Kallon abincin tayi tace, “yau ba abincin mutuniyar ka bane ba kenan?.” Yayi murmushi kaɗan yace, “Mun yi magana da ita bata yi ba yau, amma kema kin san da nata zan kawo.” Ta kalle shi ta girgiza kai tace, “baka yi min kara wallahi.” Yayi dariya yaja kumatun ta yace, “ƴar lukuta mai kumatu” ya faɗa yana tashi ya shiga ciki ya barta a zaune. Jin ana kiran sallah sai itama ta shiga ciki tayi sallah ta dawo falon ta ɗauki abincin ta kai microwaves tayi warming ɗin sa yayi zafi sosai ta fito dashi a lokacin ya dawo daga masallaci tace, “ga abincin.” Zama yayi ta kawo abincin, kasancewar basmati rice ce ga kuma salad tare suka ci a plate ɗaya kamar yadda suka saba in suna shiri. Ya kalle ta yace, “sallar i’sha kawai nake jira ayi in shigo zan kulle gidan nan, babu inda zan sake zuwa sai gobe in sha Allah.” Manal ta kalle shi tace, “Meyasa?.” Ya kalle ta yace, “saboda yau zan kasnace da sabuwar amaryata ta wacce na kwana kusan hamsin ban kasnace da ita ba, ko nace na wuce kwana hamsin ma, saboda tunda cikin ya shiga wata tara shikenan kika fara guduna. Gaskiya na yi ƙoƙari sosaj wallahi, kusan wata biyu fa kenan?. Hmmm ki shirya wallahi, dan wata biyu bazai tafi a banza ba.” Tayi murmushi kawai tace, “kai Baka jin kunyata wai?.” “Ke kunyar tawa kije ji? Haka kika kalle ni kika ce nayi miki ciki.” “Ai suɓutar baki nayi.” “Ni kuma ba shi nayi ba ina sane na faɗa.” Tayi murmushi tace, “to nidai ba wata amarya a yau ɗin nan, kowa yayi ta kansa.” “Wallahi baki isa ba, yau zan fanshe dararen da suka wuce ni. Dan haka yau ki ɗauka sabuwar amarya ce aka kawo min ke, ba tausayi ko ɗaga ƙafa wallahi.” tayi dariya kawai bata ce komai ba ta sukunyar da kai ƙasa, yayi dariya shima ya ɗauki wayar sa ganin ana yi masa waya. Tsaki yayi yace, “Huzaifa zai takura min.” Manal ta kalle shi zata yi magana ya dauƙi kiran ya saka a speaker yace, “sarkin takura ya aka yi?.” “Kai da Yayar matar ka kake magana ya kamata ka dinga nustuwa.” Bebi ya kalle ta ganin tana murmushi sai yayi tsaki yace, “malam lafiya?.” Huzaifa yace, “Da kai da Manal ake son gani yanzu a gidan ku.” Bebi yace, “kamar ya ake son ganin mu? wani abun ya faru ne?.” “To nima dai ban sani ba, an saka na kira ka na kuma kira kowa na gidan mu kowa yazo gidan ku za’a tattauna, ka taho da Manal za’a fara meeting daga nan zuwa bayan sallar i’sha.” Bebi yace, “to Allah yasa lafiya.” Ya amsa da amin ya kashe wayar ya kalle ta yace, “to kin ji, sai ki shirya mu je.” Manal tace, “me kuma ya sake ya faruwa?.” “Allah a’alam” ya faɗa yana shan ruwa ya tashi ya fita. Sai da akayi sallar i’sha sannan suka fita zuwa gidan, lokacin da suka je an taru a falon Abba, abinda ya bashi mamaki ganin Rumana kuma da Maman ta da kuma yayyen Mama. Basu ce komai ba suka zauna Mubeena ma tana nan aka buɗe taro da addu’a kafin Daddy yace, “Na san kun yi mamakin wannan jira na gaggawa a kuma wannan gidan a karo na biyu. To ikon Allah dai baya ƙarewa a ko yaushe, kuma abinda kayi kai ka manta shekaru da yawa watarana zai bayyana.” Jin yayi shiru sai Abba yace, “magana ake akan Sumayya ƙanwar mahaifiyar Adnan, wacce mahaifin ku ya aura kafin mahaifiyar Manal. Auren bai wuce shekara ɗaya da wani abun ba ya mutu ba tare da wata damuwa ko matsala ba, ya bar garin kano ya koma asalin garin su Zaria bai san ita Sumayya tana da ciki ba. Har ta haihu yarinya ta girma da komai bai sani ba dan shi har suka rabu bai san akwai ciki ba. Sai ɗazu da yazo ya same ni akan yana so yaje gidan su domin ya nemi afuwar ta haka kawai ya rabu da ita babu dalili, nan yake sanar dani sunan mahaifin ta nace ai sunan mahaifin babar su Adnan ne, ana haka sai ga su sun shigo duba ni a nan ya ganta ta gane shi shima ya gane ta.” Maman su Huzaifa ce kawai tace, “kuma dai?.” Abba yace, “ƙaddarar kenan ai. Yanzu duk mun kira ku ne dan mu nuna muku ƴar uwar ku gata” Abba ya faɗa yana nuna Rumana da fuskar ta tayi ja alamun ta sha kuka sosai. A tare kowa ya kalle ta da mamaki sosai da kuma al’jabi, Bebi ya sake kallon Rumana ya kalli Ammi ya sake kallon Manal ya sake kallon Rumana cikin ruɗani. Abba yace, “itama jinin ku ce mahaifin ku ɗaya, duk Allah bai yi nufin za’a san wanna ba tun a baya saboda Alhaji Ali bai taɓa zuwa mun haɗu dashi ba, duk alaƙar Adnan da Huzaifa sai dai mu yi waya amma bai taɓa ganina ba nima ban gan shi ba. Silar rashin lafiya da kuma silar haihuwar Manal ya saka shi yazo ashe duk rabon wannan abubuwan da aka binne ne zasu bayyana.” Huzaifa ya kalli Abba yace, “Abba kenan itama Rumana ƙanwata ce kamar Manal da Mubeena?.” Abba ya girgiza kai yace, “ƙwarai kuwa, ƙanwar kace itama jinin mahaifin kace.” Huzaifa ya kalli Rumana ya kalli Manal ya kuma kalli Bebi da shima shi yake kallo kafin tace, “ikon Allah.” Abba yace, “daman shine dalilin kiran kowa ya san ƴar uwar sa saboda halin rai, kar lokaci yayi halin sa ba tare da an nuna ta a gare ku ba.” Maman su Huzaifa ta kalli Daddy tace, “bayan ita babu wata?.” Daddy ya kalle ta yace, “babu, babu wata matar da na aura a duniya iya wannan ukun ne kawai. Na san baki san da Sumayya ba amma ita ta san dake, kamar yadda ya faru a ɓangaren Zahra.” Mama ta kawar da kai gefe tana sake kallon Daddy ɗin tana girgiza kai. Alhaji Mustapha yace, “shine daman maganar kowa ya san da juna kafin rai yayi halin sa. Manal, Mubeena, Rumana duk Alhaji Aliyu ne ya haife su kuma duka ƙannen ka ne Huzaifa. Shine abinda aka tara ku asanar daku daman.” Bebi da ya kasa magana sai a lokacin ya kalli Abban su daƙyar yace, “kenan da Manal da Ruman mahaifin su ɗaya ne?.” Abba ya girgiza masa kai alamun haka ne, da sauri ya kalli Mumny da take kallon sa ya sake kallon Rumana da ita shi take kallo zuciyar sa na bugawa sosai. Mummy ta kalli Abba da Daddy tace, “Rumana ta kasance a hannuna tun daga yaye har ta girma ta kai minzalin aure a wajena take. Sun shaƙu da Adnan sosai, kasancewar tare suka tashi in ya girme ma bai shekara uku zai bata, kuma girman mace da namiji sai ya zama duk tare suka tashi gabaɗaya har ita Farida ɗin kusan a cikin su take. Shaƙuwar Adnan da Rumana har ta niye ta koma soyayya tunda suka yi hankali suka tabbatar da babu alaƙar ta jini a tsakanin su, kuma ban shayar da ita ba balle ya zama babu aure a tsakanin su ya fara son ta ta fara son sa. Babu wanda bai yi tunanin Rumana ba Adnan zata aure ba, duk da baya nan ya tafi karatu ba amma shaƙuwat su bata taɓa yin baya ba a kullum ƙaruwa take. Yana karatu a wata ƙasar tana karatu a nan har ya kammala digester ɗin sa na farko, ya dawo a lokacin har an fara tunanin zai aure ta ne sai ƙaddarar zata yi aure ta gifta a tsakanin su, a lokacin Rumana ta nuna akwai wanda zata aura ba Adnan ba.” “Kowa yayi mamaki abinda tace saboda kowa yasan irin son da suke yiwa junan su. Adnan yaji babu daɗi soaai dan yana son ta kowa ya shaida amma lokaci ɗaya ta bar shi, tana yin aure ya sake komawa karatu inda ya juya ɓangaren karanta zuciya. Auren Rumana bai wuce shekara ɗaya ba auren ya mutu ta dawo ta cigaba da karatu a lokacin Adnan ya dawo. Rumana taso alaƙar su ta cigaba daga inda ta tsaya a wannan lokacin, Amma Adnan ya nuna shi baya da buƙatae ta a rayuwar sa a fannin soyayya, yana kula ta matsayin ƙanwar sa ne amma ba da sunan soyayya ba, a haka aka cigaba da zama har kawo yau.” Mama ta kalle su tace, “Da farko ban bashi goyan bayan auren Manal ba, saboda ni Rumana kawai nake da burin ya aura ya sani kuma yayi min alaƙawarin auren ta. Sai da yaje ya haɗa ni da mahaifiyata akan Rumana sannan tace babu ruwan na ƙyale shi ya auri wacce yake so kamar yadda aka bar Rumana ta auri wanda take so a farko. Na amince da auren sa na farko amma na saka masa sharaɗin da yayi min alƙawarin cikawa ko bani da rai.” “Na faɗa masa dole zai auri Rumana bayan shekara ɗaya da auren sa da Manal, yaso ya turje ya nuna ƙin amincewar sa amma na tabbatar masa da haka za’a yi ko bani da rai, ya amince da hakan ya kuma yi min alƙawarin auren ta ko ina da rai ko bani da rai. Shirye-shirye bikin sa da aka fara sai ya jefa Rumana a damuwa mai yawa, har abin ya kai ya kawo da Rumana ta kamu da ciwon zuciya saboda soyayyar da take yiwa Adnan. Son da ta yiwa Adnan a baya ba komai bane akan wanda ta ke yi masa yanzu, hakan ya saka hankalin ta ya tashi har ya kai ta ga ciwo. Daga nan Adnan ya fara rarrashin ta yana bata baki amma duk da haka ciwon baya yin baya sai gaba. Ranar da aka ɗaura auren Adnan matar sa ta tare ranar a asibiti Rumana ta kwana babu numfashi.” Mama ta sauke numfashi tace, “bayan ta samu lafiya hankalina ya tashi, ganin yadda na damu akan lamarin ciwon Rumana Adnan ya sake jadadda min alƙawarin da yayi min akan auren Rumana, ni kuma wannan damuwar da rashin lafiyar nan nata sai ya dame ni, saboda babar ta haihuwar ta tayi kawai amma ni ce uwar ta. Naje na samu mahaifin Adanan ina kuka da kuma Yayana na sanar dasu halin da Rumana take ciki, suka tambaye ni me nake so ayi nace kawai ina so a ɗaura auren Rumana da Adnan a washe garin ranar.” Gaban Adnan ya faɗi ya kalli Mummy a lokacin itama shi take kallo tace, “da farko Yayana yaƙi amincewa da auren, amma na dinga yi masa magiya har ya amince. Washe gari bayan sallar azahar mutanen da suke cikin masallacin da Abban sa da kuma Yayana suka ɗaura auren Adnan da Rumana. Aka kawo min rogo da alewa da sadakin ta farin cikina ya kasa ɓoyuwa na sanar da Rumana abinda ya faru, na tabbatar mata da ita matar Adnan ce a wannan lokacin wallahi a ranar ta wartsake.” “Bayan ni da Ita da Abban su da kika Yaya babu wanda ya sam maganar ko mahaifiyar ta. Ni nace mata ta koma Abuja gidan Yaya ta cigaba da zama da zarar Manal ta shekara ɗaya zata dawo, a lokacin kowa zai san da maganar auren su sai ta tare a gidan ta. Haihuwar Manal ce ta dawo da ita suka zo garin nan da matar Yaya, lokacin da muka je gidan Adnan a ranar a asibiti Rumana, sai ta kwana biyu a can sannan ta tashi. Na sake maimaitawa Adnan magana akan auren ta yace yana sane ya kuma san yayi min alƙawari tunda shi bai san an ɗaura musu auren ba.” Mama ta kalle su dukkan su tace, “na baku wannan labari ne saboda kowa ya sani, ga shaidun ɗaurin auren Rumana da Adnan nan a zaune. Dalilina na bada wannan labari shine; yanzu Manal da Rumana mahaifin su ɗaya, kuma addini ya haramta namiji ya auri ƴan gida ɗaya. Dole sai dai Adnan ya ɗauki ɗaya ya bar ɗaya a cikin su. A yanzu Manal da Rumana mun shaida mahafin su ɗaya, kuma mijin su guda ɗaya ne, dole sai dai ɗaya ta haƙura ta barwa ɗaya, ina so ku tuna da wannan” ta faɗa tana kallon sa kamar yadda yake kallon ta tashin hankali ya bayyana a ƙarara a tare dashi. “Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un! Tabbas haka ne Hauwa, Tabbas anyi haka ni shaida ne mahaifin sa ma shaida ne. Mun yi abu ba tare da mun san hakan zata kasance ba” Yayan Mama ya faɗa yana kallon ta. Abba yace, “ƙwarai anyi haka, yanzu kenan Rumana ma matar Adnan ce kamar yadda muka san Manal matar sa ce” ya kalli Adnan yace, “yanzu dole ɗaya zaka ɗauka ka bar ɗaya haka addini yace, in Manal ka ɗauka zaka saki Rumana, ina in Rumana ka ɗauka zaka saki Manal.” BDƘB3P32 Bebi gaban sa faɗuwa yake yi sosai, ya runtse ido ya buɗe ya kalli Mummy da take kallon sa ya ɗauke kai daga kallon ta, ya kalli Rumana yaga ta kulle idanun ta ƙirjin ta yana up and down, ya kalli Manal yaga ta kifa kanta a kafaɗar Mubeena ko ba a faɗa masa ba yasam kuka take yi. Ya kalli Huzaifa da yake kallon sa shima kawai ya sunkuyar da kai saboda bai abinda zai yi ba. Abba tace, "Adnan ƴan uwa ne su biyun, dole ka gaggauta ɗaukar hukunci ran mu duka ba hannun mu yake ba. Babu kara ko tunanin wani abun ka ɗauki abinda ka ke ganin zaka iya, ka ajjiye wanda baza ka iya ba." Bebi ya kalli Alhaji Mustapha kamar zai yi kuka, ya buɗe baki zao yi magana ya kasa ya sake mayar da kansa ƙasa gabaɗaua ya shiga ruɗani, wa zai ɗauka wa zai bari a cikin su?. Shiru wajan ya saka yi babu mai magana a cikin su kowa da abinda yake damun sa a zuciyar sa, Alhaji Mustapha ya sake cewa, "Adnan wannan ba magana bace ta wasa, yana da kyau ka gaggauta furta wacce zaka zauna da ita a ka kuma sauke nauyin auren ka da yake kan ɗayar, wannan ba abinda za'a baka lokaci bane, kayi ka furta kawai a wuce wajaan." Bebi ya sauke numfashi ya kalli Mummy yaga shi take kallo ya sake runtse idon sa, sai a lokacin yake ji ina ma babu alaƙar jinji a tsakanin Manal da Rumana, ina ma babu alaƙa ta jini a tsakanin su da ya cigaba da zama dasu matsayin mata sa, yanzu ya shiga wani hali wanda bai san ya zai yi ba. Ɗago kai yayi yana salati a zuciyar sa ya sake kallon Rumana ya ganta yadda numfashin ta yake yi, ya san tana da ciwo komai zai iya faruwa da ita, ya kalli Manal itama tana jikin Mubeena tana kuka, suka haɗq ido da Mubeena yaga itama kallon sa take yi tana so taji me zai ce. "Hasbunallah!" Ya furta a snayeye yana sauke kansa ƙasa. Kowa yayi shiru shi ake saurare ya ɗago ya kalli Alhaji Mustapha yace, "Daddy ni..." sai ya kasa magana yayi shiru ya dafe kansa. Alhaji Mustapha yace, "ina jin ka, faɗi abinda yake zuciyar ka kar kaji tsoro, kowa ya san ƙaddara babu wanda zai tsallake ta, in ba dan haka ba da dukkan su zaka zauna dasu ne matsayin matan ka. Amma yanzu bazai yu ba saboda kasancewar su ya da ƙanwa dole ka bar ɗaya ka ɗauki ɗaya." Bebi ya sake ɗagowa ya kalli Huzaifa yayi masa alamun ya nutsu ya ɗauke kai ya kalle su, ya kulle ido ya buɗe kafin yace, "Daddy ni ban san da an ɗaura aurena da Ruman ba, ban san akwai aurena a kanta ba. Sannan kuma Manal..." sai ya kasa ƙarasawa ganin irin kallon da Mama take masa dole yayi shiru. Alhaji Mustapha yace, "eh mun san baka sani ba, daman ba ayi niyar faɗa ba sai matar ka ta shekara a gidan ka, an yi hakan ne saboda yanayin ciwon da ita Rumana Allah ya ɗora mata ba dan wani abun ba. Amma yanzu kana da ikon zaɓar wacce zaka zauna da ita, Bawai dan bamu san wa kake so a cikin su ba, sai dan haka addini yace ayi. Dan haka ka zaɓi abinda yake ranka ko ne ya faru haka Allah ya rubuta, duk wacce ka zaɓa dole ɗayar ta ɗauki ƙaddara." Kukan da Ayan ya fara ne ya saka shi ya juya ya kalle shi a hannun Mubeena tana ɗago Manal dan ta ta karɓw shi amma taƙi ko motsawa shi kuma kukan nasa ƙara gaba yake yi. Maman Adnan ce tace, "Bani shi Mubeena." Mubeena ta janye Manal a jikin ta ta bawa Mama shi ta saka shi a kafaɗa tana jijjiga shi sai kuwa kukan ya ragu. Dawo da kallon sa yayi ga Mama ya sauke ajiyar zuciya ya kulle ido ya buɗe ya daure ya fizgo maganar yace, "na yanke hukuncin zan zauna da...." Kallon Mama yayi yaga ta ɗauje kai daga kallon sa ya kalli Alhaji Mustapha ya sake yin shiru. Alhaji Mustapha yace, "Adnan da Manal uwar ɗan ka zaka cigaba da zama?." Kamar nai ciwon wuya ya ɗaga kai alamun eh, Alhaji Mustapha yace, "to ka warware auren Rumana da yake kan ka." Ya kulle ido ya sake yin ƙasa da kansa yace, "Na sake ta" ya faɗa murya na rawa soaai. Alhaji Mustapha yace, "ka saki wa?." "Ruman!" Ya furta yana rufe idanun sa ya buɗe akan Rumana da ta rintse idon ta tana sauke numfashi a hankali. Alhaji Mustapha yace, "Alhamdulillah!. Yanzu Rumana ba matar Adnan bace kamar yadda kowa yaji abinda yace, babu kuma aure a tsakanin su indai yana tare da Manal matsayin matar sa. Ke Rumana yanzu kina matsayin ƙanwar sa ne kuma Yayar matar sa, Allah ya baki matsayin har guda biyu a lokacin da baki tunanin samun sa ba, sai ki yi haƙuri ki ɗauki ƙaddara, Allah bai rubuta zaki zauna da shi matsayin mijin ki ba shiyasa tun farko baki aure shi ba ki ka auri wani daban. Sannan Allah ya taimake mu komai ya bayyana kafin a kai ga aikata haramci, ina nufin kafin ki kai ga tarewa da Adnan Allah ya bayyanar da ke ƴar uwar matar sa ce. Sai ki yi haƙuri Allah ya fito miki da miji na gari." Falon yayi shiru sai kukan Ayan kaɗan-kaɗan Mama ta kalli Manal tace, "yaron nan yunwa yake ji, Mimi miƙa mata shi" ta faɗa tana bawa Mimi shi ita kuma ya bawa Manal. Idanun Manal a kulle suke Mubeena tace, "tashi mu fita waje sai ki bashi nan ana kallon ki." Tashi suka yi su biyu Mubeena tana riƙe da Ayan ta kuma riƙe hannun Manal suka fita daga falon. Alhaji Mustapha ya ce "Shikenan ai komai ya ƙare ya kuma zo ƙarshe. Aure tsakanin Rumana da Adnan babu shi a yanzu babu shi, wancan da ya faru ya zama labari kamar ma bai faru ba, Manal itace matar sa har yanzu ba Rumana ba. Kowa ya san Rumana ƴar uwar sace a yanzu dan haka komai ya wuce ai ko?." Daddy ya girgiza kai yace, "komai ya wuce." "To ma sha Allah. Sai wata nasiha da nake so nayi muku ku yara" ya faɗa yana kallon Huzaifa da da Adnan da Sultan da kuma yayyen Adnan yace, "Kar wani abu ya kai ku wani gari ko wata ƙasa ku yi aure ku bar matar a can ko da ciki ko babuciki, ku dawo garin ku ku manta ma kun yi wani aure, irin wannan abubuwan da suke faruwa ba sai kaga ba tare da sanin ka ba sai kaje wata ran kana soyayya da ƴar cikin ka baka sani ba. Hakan bashi da amfani kuma bashi da fa'ida ana kuma cutar da zuciya, yanzu kalli Rumana kowa yasan an raunata mata zuciya daman gata tana da ciwon zuciyar, ita kanta Manal ɗin an raunata ta Allah kaɗai yasan abinda take ji a zuciyar ta. Irin hakan bashi da wani amfani, in zamu yi aure a tsananta bincike ba iya halin yarinyar ba har halin iyayen ta sai kun sani, kai in da yuwa kakannin ta ma ya kamata ace kun san halayen su kafin auren yazo, ta haka za'a samar da zuri'ar da babu kwaɗo a cikin ta." Yace, "yanzu da ace Huzaifa shine ya auri Manal ko shine ya auri Rumana don Allah wacce irin kunyar duniya za'a ji? Yaya da ya kasance uba ɗaya ya auri ƙanwar sa ta jini ba tare da ya sani ba?. Kuma iyayen su ne suka jawo suka raba kan yaran su wani yana nan wani yana can ba tare da an sani ba, babu riba ka auri mace ka barta da yara baka sake waiwaiyar ta ba babu ribar haka, wata ran zaka haɗu da ƴar ka ba tare da ka san ita bace, wataƙila kayi nata wata ɗabi'a mara kyau ko ita tayi maka, in ta bayyana ƴar ka ce itama ta san kai baban ta ne kazo kana jin kunya kuma duk kaine ka kawo hakan. In mata sama da ɗaya zaku yi ku yi amma ku tara su waje ɗaya, wannan ya san wannan, wannan ma yasan wannan. Yanzu a iyalan Alhaji Aliyu haka zasu tashi babu shaƙuwa a tsakani, Manal da Yayar ta kawai ta shaƙu saboda ita kaɗai ta sani matsayin ƴar uwar ta, sauran yaran suma da ƴan uwan su suka shaƙu dasu saboda su suka sani, haka Rumana yanzu itama gani zata yi kamar zata yi rayuwa a cikin wanda bata sani ba. Don Allah a dinga gyarawa, a dinga sanin abinda ya kamata ayi kar ana ana dana sani mara amfani." Daddy y san maganar kaf dashi ake kuma haka ɗin ne sai girgiza kai yake yi kawai zuciyar sa tayi rauni sosai. Dagq nan dai taro ya tashi maza duk suka fita sai matan ya rage a falon. Adnan ya kalli Huzaifa a harabar gidan su suna tattaunawa yace, "baka ganin irin kallon da Mummy take min? Wallahi gabaɗaya na tsoro ta." Huzaifa yace, "dole zata yi maka wannan kallon, amma zata warware in sha Allah, ina Manal ɗin?." Bebi ya kalli wajan yace, "nima ban ganta ba, da alama tabi Mubeena." Huzaifa yace, "sai kayi haƙuri" ya faɗa yana kallon sa ya girgiza masa kai kawai. "Wayyo Allah! Yaya Adnan Rumana ta Suma! Ta suma kazo" Kausar ta faɗa da ɗaga murya tana yi masa magana, ya kalli Huzaifa da hanzari suka shiga inda suke. Yadda suka barta a jingine akan kunar ashe ta riga ta suma a haka, Bebi ya ƙarasa inda take Mama tace, "Kar ka sake hannun ka ya taɓa fatar jikin ta, tunda baka ƙaunar ta kar na sake ganin ka a kusa da ita, kai kar na sake ganin ka daga yau ka fita ka bani waje!, kar na sake ganin ka a gidan nan!" Ta faɗa cikin ɗaga murya wacce ta firgita Adnan. Kallon Mama yake yi hankalin sa a tashe sosai tace, "baza ka fita ba kenan?." Da sauri ya juya ya fito ya jinjina da mota cikin damuwa. Yana tsaye Huzaifa ya fito da Rumana a hannun sa kamar ƴar tsana aka aaka ta a mota aka wuce asibiti. Shima motar ya hau ya tafi asibitin jikin sa a sanyaye sosai zuciyar sa na yi masa ƙuna sosai. Tunda ya tunkari inda suke yake jin kukan Mama ana ta bata haƙuri amma bata daina kuka ba, ya tsaya yana jin ɗaci a zuciyar sa jin kukan mahaifiyar sa kuma shine silar faruwar hakan. A lokacin Huzaifa yazo wajan ya riƙe Huzaifa yace, "me yake faruwa?." Huzaifa yace, "Dr Fulani yana kanta, amma condition ɗin ta is very bad Adnan, numfashi ta yana gab da barin jikin ta." "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Kukan Mummy nake jiyowa haka?." Huzaifa ya juya ya kalle su yace, "ba iya Mummy ba, dukkan su kuka suke yi." Adnan yace, "Huzaifa ya zanyi, abinda zan iya shi nayi amma Mummy baza ta fahimce ni ba, ina zan saka raina ne?." Huzaifa yace, "a yanzu baza ta fahimce ka ba, amma zuwa nan gaba zata sakko fushi tayi kawai sai kayi haƙuri." Huzaifa ya wuce shi yana nan tsaye yana kallon yadda Maman sa take kuka ta dalilin sa. Yana hango fitowar Dr Fulani ya fito duk suka yi kansa suna tambayar sa yanayin jikin ta, bayanin halin da take ciki yayi musu da nutsuwa yadda baza su firgita ba yazo zai wuce Bebi ya riƙe hannun sa yace, "ya jikin ta?." Dr Fulani ya kalle shi yace, "Gaskiya yanayin babu daɗi, komai zai iya faruwa. Numfashin ta yayi ƙasa da sixty percent. So lamarin sai addu'a kawai." Bebi ya sauke ajiyar zuciya ya dafe kansa, Dr Fulani ya wuce shi kuma ya ƙarasa ya shiga office ya zauna ya dafe kansa da duka hannayen sa kamar zai yi kuka. Bai san adadin lokacin da ya ɗauka a haka ba kafin ya tashi ya fito zuwa inda suke yana kallon Mama har lokacin kuka take yi. Ɗago kai tayi ta kalle shi kawai tana miƙewa ta wanke fuskar sa da mari mai zafi dan a fusace take dashi. Bata san ma hannun ta ya sauka a kan fuskar sa ba, kawai ji tayi ta mare shi cikim rashin sani saboda ɓacin ran da yake taso mata daga zuciyar ta. "Ka bani kunya, a yau na tabbatar da baza ka iya bani farin ciki ba tunda ka kasa yi min abinda nake so. Me kazo yi nan?, Kazo ta gan ka ta kuma shiga wani yanayin?, Kazo ta ganka ka sake jajjada nata baka son ta Adnan!" Ta faɗa cikin murya mai amo. Tunda mare shi fuskar sa na gefe yana ɗaya yana kallon tiles ɗin ƙasa yana sauke numfashi zuciyar sa na yi masa zafi. Umma ce ta da tsaye ta riƙe ta tace, "Haba Hauwa meye haka? A asibiti muke kuma shi laifin me yayi miki har zaki mare shi?." "Shine ya jawo komai, shine ya kawo komai Yaya. Da yayi abinda nace da yanzu haka bata faru ba, da ya aure ta tun farko da hakan bata kasance, yanzu tana kwance ba'a san a yanayin da take ciki ba, zata rayu ko baza ta rayu ba babu wanda ya sani, yadda likitocin suke fitowa zai tabbatar maka da halin da take ciki yayi muni. Wallahi in Rumana ta mutu bazan yafe masa ba." Suman tsaye Adnan yayi jin abinda Mama tace, bashi da bakin yin magana a wajan yayi saurin barin wajan kar ya jawo tayi wata maganar da zata saka shi a kwantar dashi shima a asibitin. Office ya koma ya rasa abinda yake masa daɗi, hankalin sa ya kai ƙarshe wajan tashi damuwa tayi masa yawa har ya fara sana sanin zaɓar Manal da yayi a matsayin matar sa ya bar Rumana, ji yake ina ma bai sake ta ya cigaba da zama da Rumana ɗin kodan hankalin Mama ya kwanta. Bai san yana hawaye ba sai jin ɗumin su yayi a kuncin sa, yayi sauri ya goge yana kallon waje ɗaya cikin tsananin damuwa. Ya jima sosai a haka sai da ya kira Dr Fulani ya dubo masa ita ya tabbatar da numfashi nata yayi sama sannan hankalin sa ya ɗan kwanta. Huzaifa ne ya shigo yace, "Bebi ka nustu kaje gida zan kula da komai a nan, ga Dr Fulani ma zai kula da komai. Zaman ka a nan damuwa zai saka maka ba komai ba." Ya girgiza kai yace, "bazan iya tafiya su Mummy suna nan ba." "Haƙuri zaka yi, zaman ka a nan babu abinda zai ƙara maka sai damuwa, kuma Mama baza ta baka damar zuwa inda take ba, haƙuri zaka yi ka tafi." Yayi shiru bai ce komai ba Huzaifa ya dinga bashi baki a haka ya fito ya tafi gida hankalin sa gabaɗaya baya jikin sa. Yana ajjiye motar ya shiga cikin gidan ya samu falon babu kowa bai bi ta kan Manal ba ya shiga ɗaki dan bashi da nutsuwar sauraren ta a wannan lokacin. Manal kuka yake yi kamar ranta zai fita, hankalin ta ya tashi sosai jikin ta har rawa yake yi saboda kuka. Kukan Ayan yake ji yayi yawa soaai ya saka shi ya fito ya shiga falon nata yaga bata nan ya shiga ɗaki ya hango ta a zaune tana kuka gashi a jikin ta shima yana kuka. Daƙyar ya iya cewa, "ki bar wannan kukan ki kula da Ayan kina ji yana kuka." Tayi masa banza kamar bata ji abinda yace ba, Bebi yace, "ba magana nake miki bane?." Nan ma tayi masa banza ransa ya ƙara ɓaci cikin faɗa yace, "ba magana nake miki bane? Kina jina kin min banza tsabar kin raina min hankali?." "Eh ina ji ɗin. Bazan amsa bane sai me?" Ta faɗa cikin matuƙar faɗa da fusata itama. "What!" Ya furta yana kallon ta jin abinda take cewa kafin yayi magana Manal tace, "Meyasa ka munafurce ni ka ɓoye min maganar ka da Rumana? Meyasa baka faɗa min aurena da kai shekara ɗaya kawai ka ke jira ka kawo wata ta tare ba?" Tayi wani murmushi takaici tana kallon sa tace, "shiyasa ko yaushe cikin damuwa ka ke akan ta, in na tambaya ka ɓoye min ashe kai ka san munafurcin da ka ƙulla ka kasa faɗa min, Meyasa ka zaɓe ni? ai da ka sani ka ɗauke ta tunda ita ƴar uwar ka ce kuma wacce ka fara so a duniya. Ni daman na san akwai munafurci a lamarin ka kai da ita, yanayin kallon da take maka da yadda ka ke faɗar sunan ta daman na san za'a zo wannan gaɓar, da nayi magana kace kai ba haka ba ashe ka san abinda ka ƙulla ka munafurce ni baka faɗa min ba" Manal ta faɗa cikin tsananin ɓacin rai da nuna zallar fusatar da take ciki. "Munafurci!" Ya maimaita a zahiri yana kallon ta cikin ɓacin ran da ya ninka nata. Manal cikin ɗaga murya tace "munafuci, ka munafurce ni, na sake faɗa ka munafurce ni. Daman tun da ni nasan za'a zo nan saboda yadda alaƙar ku take, meyasa ka zaɓe ni wai? Meyasa baka zaɓe ta ba tunda itace wacce ka so kafin ni?." Tashi tsaye tayi ta kwantar da Ayan a lokacin ya ƙaraso inda take ya ɗaga hannu zai mare ta sai kuma ya fasa ya nuna ta da yatsa yace, "in kika sake furta wannan kalmar zaki dana sani, ke wacece da zan munafurce ki?, Har kin kai matsayin da zan munafurce ki?, Wacece ke?." "Ka mare ni mana, ko kashe ni zaka yi bazan fasa faɗar abinda yake zuciya ta, kayi min duk abinda zaka yi min. Adnan sai ka mare ni sannan zaka nuna min Rumana ta fini mahimmaci a rayuwar ka, in baka mare ni baka ƙaunar Allah. Na faɗa ka munafurce ni, meyasa baka zaɓe ta ba?, meyasa ka zaɓe ni bayan ka san ita ka ke so? Meyasa ka aure ni bayan kasan ka ƙulla munafurci a zamana da kai ba?. Na faɗa ka munafurce ni kai munafuki ne, sai mee?!." Bai san ya tsinke ta da mari ba sai da yaga tayi baya ta haɗu da bango ya san ya mare ta, ya nuna ta da yatsa yace, "in kika sake furta wannan kalmar ta munafurci wallahi sai kin yi dana sani. kuma Ina so ki sani saboda wannan ya saka na ɗauke ki, ba dan Ayan ba da ke kin san ko kallon inda kike bazan yi ba. Kuma wallahi kika sake yi min wata magana sai na yi miki abinda naki taɓa tunani ba." Manal hannun ta na kuncin ta tana kallon sa tana kuma tace, "ka mare ni?." A fusace yace, "na mare ki ko zaki rama?" Ya faɗa cikin faɗa sosai. Kuka take yi sosai muryar ta har bata fita saboda kuka tace, "da ka sani baka zaɓe ni ba, yanzu ma kana da ikon saki na ka aure ta sai ka bar mata Ayan ɗin ta kula dashi. Kuma kalmar an munafurce ni bazan fasa faɗa ba. Ka munafurce ni na maimaita ka yi duk abinda zaka yi, munafuki ne kai na faɗa, in kaga dama ka kashe ni kar ka barni da rai." Dafe kai yayi zuciyar sa nayi masa mugun zafi akan kalaman ta, hannun sa rawa yake haka zuciyar sa tunzura shi take ayi akan ya buɗe bakin da hannun sa na jan gangar jikin sa zuwa jikin ta. Ganin bai ce komai ba sai jikin sa da yake ɓari ta bishi da harara da jajayen idanun ta tace, "kuma wallahi bazan kwana a gidan nan ba, in na fita ka kawo Rumana ta cigaba da zama da kai, amma ni wallahi bazan zauna ba." "In kinga dama kar ki sake kwana daga yau, in kin ga dama in kin tafi kar ki dawo, in kin ga dama daga nan in kin fita ki bar duniyar. Stupid girl wacce bata san abinda take yi ba" ya faɗa yana fita ya barta dan in ya cigaba da zama zai iya yin abinda zasu yi dana sani shi da ita. Manal ta ɗauki jakar goyon Ayan ta ɗaura a jikin ta aaka hijjabi ta, ta saka shi a jakar goyon tana kuka sosai jikin ta har rawa yake yi, ta ɗauki key na mota ta fita a guje. Fitowar sa daga banɗaki kenan yaji fitar ta da mota da mugun gudu. BDƘB3P33 Manal tana fita daga estate ɗin taja ta tsaya tana kuka sosai, kanta ta kifa akan sitiyarin motar tana kuka cikin baƙin ciki da kishin da yake damun zuciyar ta. Kallon Ayan tayi da yake kwance a kajerar gaba ta gyara masa kwanciya ta jingina da kujera tana kuka. Tunani take yi ina zata je?, Gidan Mama ne yazo ranta ta girgiza kai a zahiri domin baza ta iya zuwa wajan Mama tace ta baro gidan mijin ta ba, kuma tana da tabbacin Baba bazai barta ta kwana ba. Gidan Adda Halima wacce suke cewa Mummy nan ma taga baza ta iya zuwa tace mata ai faɗa suka yi da mijin ta ba, ta sauke numfashi gidan Daddyn ma yazo ranta taga shima baza ta iya zuwa ba. Ƙwanƙwasa glass ɗin motar akayi hakan ya saka ta kalli masu ƙwanƙwasawa taga vegilanty ɗin da suke gadin estate ɗin ya sauka ta sauke galss ɗin ya kalli Manal yace, "Hajiya lafiya kika tsaya a nan?." Manal ta goge idon ta tace, "lafiya lau, zan je duba Mamana ne nata jin daɗi." "Amma Hajiya da kin fito da driver naga kina cikin wani yanayi." "Babu komai yanzu zan ƙarasa." "Allah ya kiyaye" ya faɗa yana matsawa ta ɗaga glass ɗin motar kawai ta wuce gidan Huzaifa. Tana shiga gidan ta faka motar ta ɗauki Ayan ta shiga ciki a nan ta tarar Ayra ƙanwar su tana gidan.  Zama Manal tayi a falon matar gidan da take fitowa daga ɗaki tace, "Ahh Manal kece tafe da daren nan?." Yanayin fuskar Manal ɗin kawqi ta kalla tasan akwai damuwa, dan ɗaga mata kai kawai  Manal ɗin tayi sannan tace, "ina wuni." "Lafiya lau, kawo Ayan ɗin" ta faɗa tana karɓar sa idanun sa biyu yana ya kalle-kalle. Manal shiru tayi tana kallon wani wajan daban, ganin hakan sai bata ce mata komai ba dan yanayin ta ya nuna ba lafiya ba. Ganin shiru yayi yawa sai tace, "Manal ki shiga ciki ji huta mana" ya faɗa tana kallon ta kafin ta kalli Ayra tace, "Ayra raka ta ɗaki." Manal ta tashi ta shiga ciki ta barta da Ayan a hannu, ya jima a wajan ta kafin ta kai mata shi. Huzaifa bai san tana gidan ba dan ya jima bai dawo ba har dare, ko da ya shigo bacci yayi bata sanar dashi zuwan Manal ɗin ba sai da safe suna breakfast ta kalle shi tace, "Beb Manal fa a gidan nan ta kwana." Kallon ta yayi da mamaki yace, "wacce Manal ɗin?." Tayi dariya tace, "wacce Manal ka sani? Ina tunani a kaf duniya ita kaɗai ka sani mai suna Manal." Ya ajjiye cokalin hannun sa yace, "Wai Manal matar Bebi?." Matar sa tayi dariya tace, "ita fa, tazo tun dare da ganin ta kasan akwai damuwa sosai. Ban tambaye ta abinda ya faru ba, kuma har yanzu bata fito ba na ji kukan Ayan dai." Huzaifa yace, "Subahanallah! Allah ya sa lafiya." Ta amsa da amin sai ga Manal ɗim ta fito ita da Ayra Ayan a hannun ta. Zama tayi akan kujear falon ba tare da ta ƙarasa dining ɗin ba tace, "Yaya Huzaifa ina kwana." Ya kalle ta yace, "lafiya lau Manal, ya Ayan ɗin?." "Lafiya lau, ina kwana Antyn mu" ta faɗa tana kallon matar sa. Ta amsa da murmushi tace, "ai na shiga naga bacci ki ke har Ayra ɗin, ga breakfast ɗin ku." Manal tace, "na jima ban yi bacci ba jiya shiyasa."  Waya ake yiwa Manal ta ɗauka bayan ta kashe ta kalle su tana cewa, "delivery man ne, bara na karɓo saƙon" ta faɗa tana tashi ta fita. Jim kaɗan sai taga ta dawo da leda a hannun ta tana zama. Huzaifa kawai ta gani a akan kujera da ta dawo ya kalle ta sosai bayan ta zauna yace, "Manal lafiya dai?, na san ba lafiya bace zata saka ki fito daga gida har ki kwana a nan ba, me ya faru?." Manal ta sauke numfashi ta kalli gefe yana kallon fuskar ta a nan yaga shatun hannun Adnan a gefen fuskar ta, abin ka da fara gefen fuskar har kumbura yayi ja kana gani ka san marin ta aka yi. Sosa kunne tayi tace, "kunne na ne yake ɗan yi min ciwo." Shiru yayi bai ce komai ba dan shatin marin da ya gani a kuncin ta zai iya saka ta ciwon kunne. Hawaye ta fara yi tana gogewa, ya kalle ta a nutse  yace, "Manal ba kuka nace ki yi ba, ce miki nayi lafiya kika fito a daren jiya ba tare da Adnan ba?." Manal murya na rawa tace, "ni na bar auren sa Yaya." Da mamaki Huzaifa yace, "kamar ya kin bar auren sa?." Manal tace, "bazan koma ba, na gama auren sa." Yayi murmushi jin abinda tace dan ya fahimci faɗa suka yi yace, "A'a ki daina faɗar hakan." "Yaya meyasa ya ɓoye min batun Rumana tun kafin ya aure ni?, Meyasa bai faɗa min lokaci yake jira zai kawo ta gidan ba?. Ai ya kamata tun kafin ya aure ni na san da maganar amma bai taɓa yi min maganar ba ko da wasa." Huzaifa ya girgiza kai yace, "kar kice min a kan wannan maganar kika bar gidan ki Manal?." Ta kawar da kai gefe tana turo baki tana goge idon ta bata ce komai ba. Huzaifa yace, "wannan ai ƙaramar matsala ce tunda yanzu babu wannan maganar bai kamata ace ta ɓata miki rai har kizo gida ba, yanzu ai babu aure a tsakanin su ko?." Manal tace, "amma da hakan bai faru ba fa?, da sai dai naga an kawo ta ance itama matar da ce ba tare da ya faɗa min ba?. Meyasa zai ɓoye min tun farko?." Huzaifa yace, "eh bai kyauta ba. Tun farko yana da kyau ki san da maganar. amma bai kamata ace wannan maganar ta kai ga kin baro gida ba, a tsakanin ku ya kamata ku tattauna komai zai wuce. Kin san halin mijin ki kema ya san naki, in ku ka nutsu ku ka yi magana shikenan." Manal tace, "ni bazan koma ba, da nace zan tafi cewa yayi in naga sama kar na dawo, kuma ai cewa yayi in ba dan Ayan da na haifa ba babu abinda zai saka shi ya zaɓi zama dani akan ta. Dan haka ni a na zan zauna." Yayi dariya yana girgiza kai ya san halin Bebi matuƙa tsaf zai aikata abinda tace. Manal tace, "don Allah ka barni na zauna a nan, kuma don Allah kar ka faɗa masa koda zai tambaye ka kace baka san inda nake ba. Inda ya damu dani zai neme ni amma ko waya bai yi min ba har yanzu" ta faɗa hawaye yana sake sakko mata. Huzaifa yace, "kina da ikon zama a nan Manal kar ki damu, kuma bazan faɗa masa ba. Amma kin san jiya yana cikin ruɗani ne shiyasa hakan ya faru, da kin sani baki yi masa maganar a jiya ba, sai ki bari sai an kwana biyu sai ki masa maganar sai ya baki haƙuri a wuce wajan, kin fini sanin halin mijin ki." Manal ta kalle shi tace, "Shine zai bani haƙuri?."Huzaifa ya murmusa yace, "zai baki mana ai laifi kike ganin yayi miki." Manal tace, "hmmm! Shi ya sani dai, ni dai kayi min alƙawari baza ka faɗa masa ba." Yayi murmushi yayi yace, "bazan faɗa masa ba sai ya neme ki." Manal ta taɓe baki tace, "ko ya neme ni bazan koma ba" ta faɗa tana buɗe ledar da aka kawo mata, yaga kayan Ayan ne ta ciki da tayi order aka kawo mata wato baza ta koma ba ɗin ba. Ya girgiza kai yace, "ki je kici abinci." "Zan ci, zan ma je makaranta "Allah ya kiyaye" ya faɗa yana tashi ya shiga ciki.      Bebi gabaɗaya ya shiga damuwa tafiyar Manal ta dame shi sosai a haka ya kwana bai kira ta ba sai da safw ya kira number amma user busy. A haka ya shirya ya fita daga gidan ya wuce asibiti wajan Rumana. Da yaje Mama bata nan sai Ammi kawai hakan ya bashi damar shiga cikin ɗakin yaga halin da take ciki, har lokaci bugun zuciyar ta da numfashin ta bai yi daidai ba amma an samu cigaba. Bebi ya sauke ajiyar zuciya yana kallon Rumana da take kwance ya kulle ido ya buɗe zuciyar sa na bugawa sosai cikin rashin jin daɗi. Jiki a sanyaye ya fito suka haɗu da Ammi da take zaune a waje ya kalle ta yace, "Ammi ina kwana?." Da fara'a tace, "Bebi ashe ka shigo, Lafiya lau ya gida?." "Lafiya lau Ammi, ya mai jiki?." "Jiki da sauƙi." "Allah ya ƙara lariya." Ta amsa da amin tace, "Ina Ayan, yana lafiya?." Girgiza kai kawai yayi alamun lafiya lau. Mama ce tazo wajan ta ƙaraso ta zauna ya kalle ta bayan ya tsuguna yace, "Mummy ina kwana." Banzan kallon da tayi masa ne ya saka shi sunkuyar da kai gaban sa ya faɗi sosai tayi tsaki tace, "Dallah malam wuce ka bawa mutane waja, kar na sake ganin ka wajan Rumana ka barta ta mutu tunda baka ƙaunar ta." Ya buɗe baki zai yi magana cikin tsawa tace, "nace ka wuce ka bani waje, kar ka ce min komai ka tashi ka bani waje kawai." Jiki a sanyaye ya miƙe tsaye ya fita zuwa office ya zauna ya dafe kansa gabaɗaya zuciyar sa a raunane take. Hamza ne ya shigo office ɗin nasa kafin ya gama shigowa Huzaifa yazo wajan suka ƙaraso ciki suka mipa masa hannu duk suka gaisa Huzaifa yace, "naga yanayin jikin nata ba kamar jiya ba." Ya ɗaga kai kawai baice komai ba. Hamza yace, "Allah ya ƙara lafiya, ni bara na koma bakın aiki" ya faɗa tana fita. Huzaifa ya kalle shi yace, "ka daure wannan raunin ya daina bayyana a fuskar ka, rauni baya dacewa sa kai Bebi." Ajiyar zuciya yayi kawai baice komai ba. Ganin baya son magana sai ya tashi ya fita ya bashi waje kawai. Kwanan Rumana uku asibiti ta samu lafiya ba laifi dan ta farfaɗo har magana tana yi. Bebi gabaɗaya ya rasa yadda zai yi, Manal wayar ta bata shiga duk a tunanin sa tana gidan Mama shiyasa hankalin sa yake a kwance bai wani tashi hankalin sa yqna neman ta ba, yana so yaje gidan nasu amma so yake ya daidai ta da Mama sannan ya neme ta hankalin sai zai fi nutsuwa. A kwana na ƙarfe sha biyu na rana su Mama suka fito daga asibitin da Rumana da aka sallame ta. Bebi ganin su sai yazo wajan ya buɗe motar sa yace, "Don Allah Mummy ku shiga." Ammi ce ta ja hannun Rumana suka shiga tana riƙe da hannun ta ganin hakan Mummy ma ta shiga suka tafi. BDƘB3P34 Gidan Hajiya tace su je suna shiga gidan Hajiya suka tarar da Yaya Mustapha da kuma mai bin da Yaya Sulaiman a wajan Hajiyan. Suna shiga Rumana ta zauna a kan kujera tana jan numfashi gabaɗaya ta canja lokaci guda. Hajiya tace, "sannu Rumana, ya jikin naki?." Ɗakyar tace, "da sauƙi Hajiya, na sannu lafiya." "Allah ya ƙata lafiya, sannu kin ji komai na duniya haƙuri ake yi." Ta ɗaga kai kawai bata ce komai ba. Hajiya ta kalli Bebi da yake zaune kai a ƙasa ta kalli Mummy tace, "Hauwa duk bawa baya tsallake ƙaddarar da, Allah bai rubuta Rumana zata zama matar Adnan ba tun farko, shiyasa ki ka ga an samu saɓabi tun suna soyayya bai aure ta ba saboda ba matar da bace, ina so ki tuna wani baya auren matar wani, matar mutum ta kasance kabarin sa kamar yadda hauaawa suke faɗa, kamar yadda wani baya shiga kabarin wani haka babu wanda zai auri matar da ba tasa ba. A zanen ƙadarar Adnan babu Rumana a ciki, Fatima itace matar da  Allah ya rubuta zai aure ba ita ba, fushi da kike dashi kamar kina fushi da hukuncin Allah ne, domin kuwa ba shi ne ya ƙaddara hakan ba Allah ne, Allah ne ya rubuta hakan shi kan sa bai isa yayi abinda Allah bai nufa ba." Mama tace, "ba fushi nake dashi ba Hajiya, kawai ina jin haushin yadda ya iya barin Rumana duk da yanayin ciwon da ta samu saboda shi, Hajiya ciwon zuciya ne da ita fa, amma bai tausaya mata ya zaɓe ta  matsayin mata ba." Hajiya tace, "yanzu in ya zaɓi Rumana ya bar Fatima an yi mata adalci kenan ita? Matar da ce fa wacce suka zauna tsahon watanni ina tunanin watan gobe zasu shekara da aure, ga ɗan da suka haifa shi da ita. Kuma yarinyar nan bata san maganar Rumana ba tun farko, kenan ita dan ba ƴar ki bace in ya sake ta ya zaɓi ƴar ki yayi mata adalci kenan? Daga shekara ɗaya da yin auren sa da ita ace ya rabu da ita saboda cikar burin ki?, hakan daidai ne Hauwa?." Mama ta sauke ajiyar zuciya tayi shiru bata ce komai ba,Hajiya ta kuma cewa, "Allah bai rubuta zai auri Rumana ba, kuma gwara da Allah ya bayyana matar sa da Rumana uban su ɗaya, da yanzu sai bayan ta tare a zo ana da an sani ana jin kunya. Yaron nan yayi miki biyayya duk da baya son auren ta ya amince zai yi saboda ke, bayan ita lokacin da nuna bata so ba'a tilasta mata ba an barta tayi abinda take so. Shi kuma ya amince zai aure ta sai kuma Allah ya bayyanar da wannan maganar amma kin kasa karɓar ƙaddara kina ganin kamar shine ya cutar da Rumana." Hajiya ta riƙe hannun Rumana da take kusa da ita tace, "na san kina son Adnan Rumana, na san da cewa ke kaɗai kika san abinda kike ji a zuciyar ki, na san ke kaɗai kika san raɗaɗin da kike ji a zuciyar ki. Amma ina so ki tuna haka jarabawar ubangiji ce, Akwai zafi sannan akwai sakamako nai kyau. Wannan duk abubuwan da suke faruwa dake wataƙila wani alkhairin ne zai faru dake, sannan Adnan ba alkhairi bane a rayuwar ki tunda har aka zo wannan ɓangaren, inda ya kasance alkhairi a wajan ki tun kafin a kai ga auren sa da Fatima ke zai fara aure amma da yake Allah bai ƙaddara hakan ba kalli abinda faru har hakan ya zama silar bayyanar mahaifin ki. Kar ki ɗauka Adnan ya ƙi ne, Wallahi Adnan yana sonki matsayin ki na ƴar uwar sa, da kin tsaya a wannan matsayin da na tabbatar miki zaki fi kowa da sa'ar samun ɗan uwa mai kula da lamarin ki. Bai zaɓi matar ya bar ki saboda baya son ki ba sai dan hakan shine mafita, in ya zaɓe ki ya bar matar sa a ganin ki yayi adalci?." Rumana ta girgiza kai alamun a'a tana hawaye Hajiya tace, "kin gane abinda nake nufi kenan, ki yi haƙuri ki ta addu'a wataƙila ke matar gwamna ce ma baki sani ba, kinga ni za'a yiwa first lady." Rumana tayi murmushi Hajiyan ma dariya take yi kafin ta kalli Mama tace, "komai ya wuce Hauwa, bana so ki canja wa matar sa, bana so ki cigaba da ganin Adnan da laifi don Allah, bashi da laifi  matar sa ma haka, don Allah ki sassauta masa sai hararar sa da ki ke yi." Mama ta girgiza kai tace, "in sha Allah Hajiya ya wuce." Hajiya tace, "Yauwa haka nake so naji, Allah yasa haka shine mafi alkhairi." Aka amsa da amin har Rumana da take zaune ta goge idon ta tace, "Ni gidan Abban Abuja zan koma da zama gabaɗaya" ta faɗa muryar ta na kakarewa saboda yanayin yadda numfashi ta yake sauka. Alhaji Mustapha yace, "babu komai Rumana, kina da ikon zama a duk inda kike so. Amma ki tuna yanzu mahaifin ki Allah bayyana shi, in kika samu lafiya sosai zaki je ki gaisa da ƴan uwan ki dashi kan sa mahaifin naki. Ki je kowa ya san ki in yaso sai ki dawo Abujan mu cigaba da zama." Alhaji Sulaiman ya ce, "gaskiya ne wannan, yana da kyau yanzu tunda kin labari ki je gidan dangin mahaifin ki a gaisa kowa ya san ki ki kuma san su, in yaso daga baya sai ki tafi Abuja kafin Allah ya kawo miki miji na gari ki yi auren ki." Hajiya ta amsa da amin suka ɗan cigaba da tattaunawa akan batun kafin su tafi gidan Mama da Rumana da Maman da kuma Adnan. Bai shiga falon Maman ba sai da yayi sallah sannan ya shiga wajan Maman yaga bata nan ya shiga ya  shiga ɗakin Mmaan da sallama ya hango Rumana a zaune a kan gado, ya ƙarasa ya zauna akan kujerar ɗakin yace, "Ya jikin naki?." Rumana ta gyara zama tace, "yayi sauƙi." "Me kike ji yanzu?." "Numfashi ne dai har yanzu bai min daidai ba" ta faɗa tana alamun sama da hannun ta ba tare da ta ƙarasa ba sannan tace, "in na zauna bana jin daɗin ƙirjina." Yace, "sannu, Allah ya ƙara lafiya. Ki dinga shan magani shi zai taimaka miki ki samu lafiya." Ta ɗagq kai alamun eh yayi shiru bai ce komai ba itama bata ce komai ba. Ya ɗago ido ya kalle ta suka haɗa ido alamun yace, "ki yi haƙuri da abinda ya faru Ruman." Tayi murmushi tace, "babu komai, kamar yadda Hajiya ta faɗa ƙaddara ce na amince da haka, Allah ya rubuta ƙanwata ce matar ka shiyasa tun farko Allah bai baka ikon amincewa da...." Ta kasa ƙarasa faɗa saboda kukan da ya taso mata. Tasowa yayi daga inda yake ya ƙarasa kan bedside ya zauna yace, "ki daina kuka don Allah, shima zai cutar dake."  Ta goge ido amma kukan yaƙi tsayawa ta kasa daina zubar da hawaye yace, "Allah bana so naga kina kuka, bana son ko kaɗan kin sani, don Allah ki daina bana jin daɗi." "Mafarkina na zama matar ka bazai tabbata ba, mafarkina na so a kira ni matar Dr Adnan bazai tabbata ba har abada,da gaske ba da wasa ba ina son ka, amma son bazai min amfani ba” ta faɗa muryar ta na rawa sosai tana kuma sarƙewa. "Allah bai rubuta hakan alkhairi bane a wajan ki shiyasa bai faru ba tun farko, tun kafin na san zan san wata me suna Manal a rayuwata nake tare dake, in da Allah ya rubuta zan aure ki da yanzu nuna da yara biyu dake ko uku ma Ruman. Kinga ko bayyanar mahaifin ki a yanzu bazai canja komai ba saboda Manal ba kowa bace a wajena. Amma rabon haihuwar Ayan shine ya kawo wannan tangarɗar tun asali, ba laifin ki bane ƙaddara ce wacce Allah ya rubuta faruwar ta bamu isa mu tsallake mata ba dole tazo ta tarar damu a inda muke." Ta girgiza kai ta kalle shi idon ta yayi ka sosai tace, "haka ne, ni ma na amince hakan amma zuciyata ta gaza fahimta, na kasa gane hakan shine gaskiya." "Zaki gane, zaki fahimta amma sai kin dawo hankalin ki kin nutsu sosai zaki banbance abinda yaje gaskiya da wanda yake ba gaskiya ba. Shaiɗan ne yake miki ihu a kunnen ki shiyasa kike ganin hakan ba daidai ba, amma da zarar kin nutsu kina karatun Al kur’ani zaki dawo daidai Ruman!" Ya faɗa murya a can ƙasa yana kallon idon ta. Hannun ta ta ɗora akan hannun sa ya kalle ta suka haɗa ido ta riƙe hannun sa sosai tace, "zuciyata zafi take min sosai, na rasa yadda zan yi na cire son ka a zuciyata, ka bani shawara don Allah" ta faɗa tana kuka tare da ɗora goshi ta a hannun sa yana jin ɗumin hawayen ta a hannun sa. Shiru yayi ya rasa abinda zai ce mata jin yadda take kuka sosai tana kuma riƙe da hannun sa. Baya son kuka yana daga cikin abinda yake ɗaga masa hankali. Kukan babba ko yaro ko kaɗan baya son ji yanzu sai ya damu. Daƙyar ya ce, "Na faɗa miki wannan kukan damuwa ce a wajan ki, kuma komai sai a hankali ba lokaci ɗaya zaka sauƙin abinda kike ji ba a zuciyar ki. Addu'a zaki dinga yi." "Ka taya ni addu'a Allah ya cire min kai daga zuciyata, Allah ya bani ikon kallon ka matsayin Yayana kuma mijin ƙanwata. Ka dinga yi min addu'a kaji, in ba haka ba zan iya rasa rayuwata saboda yadda nake jin zuciyata nayi min ƙuna" ta faɗa tana kallon idanun sa da jajayen idon ta sake riƙe hannun sa duka biyun. Ta bashi tausayi matuƙa, har zuciyar sa yake jin tausayin ta musamman maganar ta ƙarshe ji yake kamar in ta rasa rayuwar ta shine silar faruwar hakan.  Tausayin ta ya dabaibaiye shi sosai, jikin sa yayi sanyi sosai. Daƙyar ya iya furta, "baza ki mutu ba, zaki cigaba da rayuwa da farin ciki kamar kowa." Ta kalle shi tace, "Farin ciki...?" Sai tayi murmushi mai ciwo tace, "tunda na rasa ka bana tunanin zan iya sake samun farin ciki a rayuwata, Wallahi kaine farin cikina." "Babu ta inda ɗan adam yake zama farin cikin wani, Sai dai ya za silar farin cikin wani Ruman. Allah ne yake bada farin ciki ga bawan sa a duk sanda yaso, don Allah ki miƙa lamarin ki ga Allah zai taimake ki zai kuma share miki hawaye." Kai ta girgiza ya sake cewa, "in kina wannan maganar sai naga kamar baki amince da ƙaddara ba, kamar baki amince da Allah ne yake yi ba." "Na amince, abin ne akwai ciwo." "Haƙuri zaki yi, Allah ya baki ikon cinye jarabawar nan" ta girgiza kai ta kalle shi har lokacin bata saki hannun ba. Ta kalle shi tace, "Da gaske ka daina sona?." "Rumana wannan ba maganar da zamu tattauna bace." "Na sani, ina so na sani ne kawai. Da gaske ka daina sona ko kana faɗa min ne dan naji daɗi?." Ya sauke ajiyar zuciya yace, "bazan miki ƙarya ba, amma Allah ya cire min soyayyar ki raina daga lokacin da kika auri Jawad. Na shiga irin wannan damuwar amma da na bawa Allah lamarina sai komai ya zama tarihi. Soyayyar da nake miki ta Yaya da ƙanwa ce da kuma shaƙuwar da muka yi wacce baza ta taɓa gushewa daga zuciyata ba." Ta kalle shi ido jajaye tace, "da ka rasa ni kaima kaji abinda nake ji?." Yayi murmushi yana kallon ta ya ce, "Ruman don Allah ki adana wannan maganar, mu yi facing abinda ya faru a yanzu mu karɓi ƙaddara kawai ni da ke." Ta girgiza kai tace, "haka ne, Allah ya baka zaman lafiya da ƙanwata Manal" ta faɗa murya na rawa sosai. Ya zame hannun sa daga riƙon da tayi masa yace, "Amin ya Allah. Allah ya baki wanda ya fi ni." Zatayi magana ya ɗaga mata hannu yace, "Allah na roƙa kar ki ce min komai." Ta ɗan murmusa kawai tana kallon wani wajan daban kafin tace, “ko babu komai na amsa sunan matar ka na ƴan kwanaki.” Bebi ya kalle ta ya share abinda tace ya ce, "a ko yaushe ƙofa a buɗe take in kina son magana dani. Shawarar ko abinda yayi kama da haka zaki iya sanar dani nayi miki alqawarin baza ki zubar da hawaye ba. Matsayin biyu kike dashi a wajena ko nace uku, matsayin ƙanwata, ƙawata, kuma Yayar Matata." "Kuma tsohuwar budurwar ka." Suka yi dariya a tare ta share hawayen ta ya kalle ta yana murmushi yace, "matsayin huɗu ne dake zan ce." Tayi murmushi itama tana girgiza kai bata ce komai ba. Mummy ce ta buɗe ƙofar ta shigo ɗakin hakan ya saka ya kalle ta, ganin kallon da take yi masa ya saka gaban sa ya faɗi sosai , Mama ta kalli Rumana ganin da hawaye a fuskar ta kalle shi tace, "Ka tashi ka fita daga ɗakin nan yanzu." Rumana ta kalli Mama gani yadda ranta yake a ɓace sai tayi murmushi tace, "Mummy babu komai fa, hira kawai muje yi nida shi ba wani abun da kike tunani bane." Hararar sa tayi sai ya tashi tsaye a lokacin wayar sa take ƙara bai duba ba ya wuce ya fita. BDƘB3P35 Bebi ko da ya fita bai ɗauko wayar daga aljihu ba da yayi sallah ya fito daga masallaci ya ɗauko wayar yana dubawa, ganin sunan Mubeena sai gaban sa ya faɗi matuƙa, hankalin sa ya dawo jikin sa akan Manal, da hanzari ya sake kiran number ta amma bata shiga ya dafe kai yace, “na shiga uku, ina yarinyar nan ta shiga ne?” Ya faɗa gaban sa yana faɗuwa sosai. Mubeena ce ta sake kira ganin kiran ta yana shigowa ya daure ya amsa da sallama ta amsa tace, “ina yini.” “Lafiya lau, ya Mama? Ina fatan tana lafiya.” “Tana nan lafiya. Don Allah ina Manal? Tun jiya nake neman number ta bata shiga na yi mata magana ta WhatsApp duk a banza.” A hanzari ya wara idanun sa waje gaban sa ya faɗi sosai har sai da ya dafe ƙirji yace, “bata zo gidan ba?.” Mubeena tace, “rabon Manal da zuwa nan ai ta kwana biyu, bata zo ba kuma Mama ce take son magana da ita shiyasa ma ba kira ka. Don Allah in ka koma gida tana nan ka haɗa ni da ita.” Hankalin sa ya tashi tsoro ya mamaye masa zuciyar sa daƙyar tace, “to in sha Allah, ki gaida Mama.” Ta amsa tana kashe wayar. “Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un! Ina Manal taje?, Kenan bata gidan Mama?. Meysa ma na bari ta fita a daren nan?” Ya faɗa yana dafe kansa, da sauri ya nufi inda motar sa take zai shiga aai ga Kausar ta leƙo tace, “Yaya kazo in ji Mama.” Motar ya kulle ya shiga gidan amma hankalin sa gabaɗaya baya jikin sa. Yana shiga falon ta bishi da kallo ita kanta taga kamar ba a nutse yake ba amma bata nuna masa ba ya zauna a kan carpet yace, “Mummy gani.” Ta kalle shi tace, “lafiya ka canja haka? Me ya faru?.” “Babu komai Mummy, an kira ni daga asibitin ne kiran gaggawa shine zan je.” “To kaje, daman ba wani abun bane akan maganin Rumana ne in akwai wanda zaka canja mata sai ka bata, dan kamar maganin da ka bata da farko yafi na wannan arnen likitan. Amma kaje sai ka tawo dashi.” Kamar jira yake ya miƙe ya fita da sauri ya shiga mota ya bar unguwar. Tafiya yake yana tunani ina Manal taje tunda bata gidan Mama, hankalin sa gabaɗaya ya tashi, laifin kansa yake gani da ya bari ta fita bai bi bayan ta ya dawo da ita ko da a wuyan sa ba ne. Tunawa da gidan Daddy Sai ya ɗauko waya hannu na rawa ya kira mahaifin Manal yana yi yana tuƙa motar, daga can ɓangaren Daddy ya ɗauka yace, “Adnan ya aikin?.” “Lafiya lau Daddy, ya ƙarfin jikin?.” “Alhamdulillah, ashe an sallami Rumana sa ɗazu da yaran suka je akace ai tana gidan ku.” “Eh daddy, an sallame ta suna gida da Mama yanzu.” “Allah ya ƙara lafiya, abin ne sai a hankali yazo a yadda ba a yi tunani ba, a yadda aka bamu labarin ta zata ji babu daɗi musamman in ta tunda da ta rasa ka har abada.” Bebi yace, “haka ne, amma in sha Allah komai zai wuce” ya faɗa yana faka motar saboda baya cikin nustuwa gashi yana waya. Daddy yace, “haka ne kam, Allah ya daidaita komai ya haɗa kansu baki ɗaya.” Ya amsa da amin kafin yace, “Daman kira nayi mu gaisa.” Daddy yace, “Allah yayi albarka, a gaishe da Fatima duk da jiya mun gaisa a waya.” Bebi jin haka ya tabbatar da bata gidan ya amsa a sanyaye ya kashe wayar yana dukan sitiyarin motar. “Ina taje? Tana ina har kwana huɗu?.” Bashi da mai bashi amsa ya sauke numfashi ya saka jan motar ya tafi Hanyar gidan sa ya wuce ya faka motar a ƙofar gidan Adda Halima yana kallon gidan yana tunanin shiga, kamar wasa sai gata ta fito a mota da alama fita zata yi, Sai ya sauke glass ya fito daga motar ganin sai ta tsaya tana murmushi tace, “A’a Adnan kai ne.” “Ni ne Mummy. Barka da dare.” “Barka dai, ya gida dasu Manal?.” Jin haka nan ma sai yayi sak jikin sa yayi sanyi yace, “Lafiya lau Mummy, daman zan wuce ne nace bara na tsaya mu gaisa.” Tayi dariya tace, “ai kam ka kyauta, gobe ko jibi ma zan zo gidan naku in sha Allah, zan mata sallama zan wuce Lagos.” Bebi yace, “Allah ya kaimu.” “Amin. Gashi ka tarar zan fita ina ya sauri “”Babu komai, Allah ya kiyaye” ta amsa tana dariya ta ɗaga glass ɗin sama ta ja motar ta tafi ya koma mota jiki a sanyaye sosai ya zauna. Kiran Huzaifa ne ya shigo wayar sa kamar bazai ɗauka ba sai ya ɗauka ya saka a speaker Huzaifa yace, “Bebi gamu kusa da gidan ka nida Hamza, mu ƙaraso kana nan?.” “Gani nan” ya faɗa yana kashe wayar ya ja motar ya tafi. ya ƙarasa bakin gate ɗin ya danna horn aka buɗe mota yana ajjiye motar suma suka shigo. Yana tsaye suka fito daga motar suka shiga gidan suna bin falon da kallo kana gani kasan babu nace a gidan, kofu nan tea da suke ajjiye akan table, ga plate ga bowl ga jakar ruwan da ta lemo. Bebi yace, “sorry falon babu gyara.” Hamza yace, “indai wajan ajiyar irin wannan ne ka saba tun kana gida, daman a gajiye muje fa muka tsaya a nan mu kalli ball sannan kuma mu ci girmin ƙanwar mu.” Bebi ya kalle su ya zauna ya furzar da iska yana sake kiran wayar ta amma bata ɗauka. Huzaifa ya kalla a sanyaye yace, “a cikin gidajen ƴan uwan ku don Allah Manal bata je ba?.” Huzaifa ya kalle shi ganin da gaske yake maganar yace, “kamar ya Manal bata je ba? Yau ko jiya?.” Bebi ya sauke numfashi yace, “tun ranar da abin nan ya faru da daddare, bata je gidan ku ba?.” Huzaifa yace, “Manal bata je ba gaskiya, kuma bani da labarin taje gidan wasu ƴan uwan mu. Wai kana nufin tun ranar bata gidan nan?.” Ya ɗaga masa kai alamun eh kafin yace, “tun a daren ta fita da mota, nayi tunanin gidan Maman su taje dan nasan babu inda zata iya zuwa in ba’a nan ba, ɗazu Mubeena ta kira tana sanar dani Maman su ma tana son magana da ita ne.” “Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un! Kuma baka neme ta ba kai tun ranar Bebi?, Ka kira wayar ta? Meyasa ma ka bari ta fita a da daddare?” Huzaifa ya faɗa yana kallon sa. Bebi yace, “wannan shine kuskuren da na yi, don Allah baka san inda take ba?. Na Kira ta sau babu adadi amma ta saka wayar a dnd na rasa inda zan saka raina, na kira Daddy yadda yayi min magana ya tabbatar da Manal ba a gidan ku take kwana ba.” Huzaifa ya kalli Hamza da ya saku baki yana kallon Adnan yace, “Hamza kaji fa, yanzu ace Manal ta fita da daddare baza ka tashi neman ta ba sai yau? Wannan wacce irin rayuwa ce? In wani abun ya same su ita da ɗan ta fa?.” Bebi yace, “babu abinda zai same su don Allah kar ka sake hargitsa ni. A Daren ka san ina cikin ruɗani saboda abinda ya faru da yadda Mummy tayi min, kai kace na taso gida ma daga asibiti saboda na huta da damuwar da take damuna. Ina dawowa ta dinga min banzayen tanbayoyi kuma kun san yanayin da nake ciki in ina cikin bacın rai.” Hamza yace, “Allah ya sa ba sakin ta kayi ba.” Ya kalli Hamza ya girgiza masa kai yace, “wacce irin magana ce wannan?.” “Ɓacin rai da zai saka ta fita daga gidan nan ƙarshe sha ɗaya na dare ai ba ƙaramin abu bane, kaima a lokacin zaka iya furta ko wacce kalma ba tare da ka sani ba.” Huzaifa yace, “kuma in ransa ya ɓaci zai iya furta hakan bai sani ba, ashe duk kulawar taka akan ƙannen ka kawai ta tsaya babu matar ka, dan na tabbatar da ace Kausar ce baza ka barta ta ita kaɗai da wannan daren ta fita ba, duk yadda zaka yi zaka dakatar da ita koda ta fita zaka dawo da ita. Amma ita ta fita yau kwana har huɗu baka neme ta ba sai yanzu da daddaren nan? Gaskiya ka bani mamaki wallahi, ban ɗauka kulawa da kishin naka akan ƴan uwan ka kawai ya tsaya ba.” A fusace Bebi yace, “Huzaifa ya ishe ka, ina faɗa maka abinda yake damuna ne kawai saboda ka faɗa min inda take ba ka dinga yi min maganar banza ba, in ka sani ka faɗa min, in baka sani ba zan nemo inda take. Na faɗa maka na san nayi kuskure a kan hakan, kuma nayi dana sanin barin ta fita duk da raina ne a ɓace sosai.” “Dole na faɗa maka domin haƙƙin nemo ta ba a kan ka ya tsaya kawai ba har dani, ina so na tuna maka Manal ƙanwata ce in wani abun ya faru da ita kai matar ka ya samu ni kuma ƙanwata ya samu, kowa yana da matsayin da yake kallon ta yana da kuma kalar damuwar da zai yi a kanta. Wallahi ka bani mamaki, nayi mamaki sosai, ban ɗauka hakan daga wajan ka zai zo, ban ɗauka zaka yi sakaci da rayuwar ta har haka ba.” Bebi ransa ya sake ɓaci yace, “Kaga in ka sani ka faɗa min in baka sani ba ka daina min maganar banza da wofi, ƙanwar kace amma ai baka kaini son ta ba ko?, Baka kai ni sanin darajar ta ba, baka kai ni rayuwa da ita ba, kuma baza ka kai ni damuwa in ta shiga wani hali ba. Ka barni naji da abinda yake damuna ba da wannan maganar ta ba.” Hamza yace, “wannan maganar taku ba itace mafita ba, ku tsaya a nemo mafita mu tambayi inda ake tunanin zata iya zuwa. Ku yi haƙuri don Allah kowa ya nutsu a samo mafita.” Bebi a fusace yace, “ba mafitar nake nema ba yana nema ya sake ɓata min rai, ya barni naji da abinda yake damuna mana, ai bazai kaini shiga damuwa ba in wani abin ya same ta ba. Yasan irin tashin hankalin da nake ciki a yanzu?, Har wajan Yayar maman su naje amma bata je can ba, hankalina ba a jikina yake ba meyasa ka kasa fahimta?.” Huzaifa yayi ƙaramin tsaki ya tashi tsaye yace, “tunda har na tabbatar da Manal jinina ce bazan bari wani abu ya same ta ba, ina da haƙƙin da zan nunawa mijin ta kuskuren sa in yayi sakaci da lafiyar ta. Yaje ya nemo ta matsayin sa ba mijin ta, matsayin a na yayan ta zan je na nemo ta nima. Zaman tattaunawar bashi da wani amfani dan ba mafita zai kawo ba” ya faɗa yana fita daga falon. Hamza ya kalli Bebi yace, “ka kwantar da hankalin ka ka nutsu ka tuna ƴan uwan maman ta na wani garin ka kira su kaji ko taje can.” Bebi yace, “ba kowa nake da number sa ba a cikin su.” “Ka san yadda zaka samu ka kira koda da niyar gaisuwa ne in tana can zaka fahimta, in bata can ma zaka gane. Amma maganar gaskiya kayi kurkuren Adnan.” Bebi yace, “na sani Hamza, na karɓi kuskurena bazan kuma bari hakan ta kasance ba. Raina ne ya ɓaci sosai kuma ta dinga yi min maganar da bazan jure ba.” Hamza yace, “shiyasa nake faɗa maka tun a baya kenan ka dinga sarrafa ɓacin ranka, kar kace in ranka ya ɓaci na wani ma sai ya ɓaci, kaga yanzu hakan bashi da amfani.” Bebi yace, “na gane hakan, zan san inda take a daren nan in sha Allah.” Hamza yace, “Allah ya bayyana ta yasa tana cikin ƙoshin lafiya” ya faɗa yana fita ya bar Bebi cikin tunanin inda take. BDƘB3P36 Hamza da ya fita a mota ya samu Huzaifa yana danna waya yana shiga yaja motar suka fita daga gidan ya kalle shi yace, “Huzaifa Bebi na cikin damuwa bai kamata ka yi masa haka ba.” Huzaifa yace, “ina sane nayi masa haka dan na nuna masa kuskuren sa na barin ta ta fita da daddare, tun farko mun faɗa masa ya sanar sa ita maganar Rumana yaƙi, duk akan ta ake wannan abun.” “Daman bai faɗa mata ba?.” “Bai faɗa mata ba wallahi, ita kuma yanzu damuwar ta wai da Rumana bata kasance jinin ta ba da yanzu sai dai a kawo ta matsayin matar sa. Kasan mata da kishi, a daren ya hau sama saboda fushi, itama ta hau sama saboda kishi dole a samu matsala.” Hamza ya kalle shi yace, “kai ya akayi ka san da hakan?.” “Saboda tana gidana, tun a daren taje gidana ban ma san ta kwana ba sai da safe” ya faɗa tana kallon Hamza. Hamza tayi dariya yace, “amma kai ɗan iska ne wallahi, kana ganin yadda ya haukace baza ka faɗa masa tana gidan ka ba?.” Huzaifa yace, “wallahi bazan faɗa masa ba, Sai ya gane kuskuren sa na barin ta ta fito ita kaɗai ga jariri, sannan sai ya gane illar kasa saarrafa ɓacin ran sa akan komai. Duk da ba duka labarin ta bani ba amma akan Rumana aka yi faɗan, shine tayi fitowar ta ta tafi gidana.” Hamza yace, “gaskiya dai bai kyau ba, amma itama banga abin barin gida a nan ba.” Huzaifa yace, “mata ne fa, yanzu ƙaramin abu zai koma babba. Kuma abinda ya saka ban dawo masa da ita ba rashin neman ta da bai ba, kuma tunda fushi tayi sai ta huce ta sauka sai ta koma.” Hamza yace, “gaskiya ne. Amma don Allah gobe ka sanar dashi in ba so ka ke a samu matsala ba, kai ka san irin son da yake mata zai iya shiga wani yanayi.” Huzaifa yayi tsaki yace, “na raina son da yake mata ai wallahi, babu wani so duk a baki ne. Kuma sai na nuna masa nima ƙanwata ce yadda yake kishin su Mimi ina kishin ta.” Hamza yayi dariya tace, “kana so ka wahalar dashi kawai, amma batun so kai ka san yana son ta, ka kalli yadda ya koma dai” yayi dariya ya cigaba da jan motar suka tafi. A daren Bebi ya rasa yadda zai yi duk yadda yake tunani abin ya wuce haka, hankalin sa ya kai ƙarshe wajan tashi akan rashin Manal, a haka ya kwana da duk inda ya san zai nema ta yayi amma babu Manal babu labarin ta. Kai da ka kalle shi ka san yana cikin damuwa, a haka ya yanke shawarar zuwa Abuja kawai gidan Alhaji Ahmad ko tana can. Da safe asibitin yaje da niyar ɗauko maganin Rumana da Mama ta tuna masa a waya, ya ɗauko maganin ya fito suka haɗu da Huzaifa ya kalle shi shima ya kalle shi Huzaifa yace, “ya ake ciki Bebi? Jiya nayi waya ko ina amma Manal bata ɓangaren Daddy, ka tambayi ɓangaren Maman su?.” Bebi ya kulle ido ya buɗe yace, “zan je Abuja yanzu dan ma ban samu jirgin safe bane da yanzu ina can, za je gidan Yayan su Maman ko Allah zai saka tana can.” “Anya zata iya tafiya Abuja? Kar ka manta da daddare fa ta fita, ni nafi tunanin anya bata gidan su?.” “Na faɗa maka Maman su ma magana take son tayi da ita, ai kaga baza ta yi min wasa da hankali ba ko?.” Ya girgiza kai alamun haka ne yace, “kuma wallahi bata gidan mu, Gashi su Daddy suna nan balle nace ko sun tafi Qatar da ita.” Bebi ya sauke ajiyar zuciya yace, “zan je Abuja in sha Allah.” Huzaifa ya kalle shi ganin ya canja gabaɗaya sai ya bashi tausayi, yayi rauni sosai da ka ganshi ka san yayi laushi hakan ya saka ya ce, “duk kayi wani iri, kar kaje su ga kamar su fahimci akwai matsala. Gashi in kowa yasan bata nan za a ga kamar baka kula da ita. Ace ta bar gida tun kwana biyar baya baka neme ta ba sai yanzu.” Bebi yace, “ni kaɗai nasan abinda nake ji Huzaifa, tashin hankalina bazai kwatantu ba wallahi. Nima bana so kowa ya sani musamman Maman ta, in ta sani hankalin ta zai tashi sosai ga yanayin ciwon ta.” Huzaifa yace, “in sha Allah komai zai zo ƙarshe kar ka damu, yanzu kafin ka siyi ticket ɗin Abuja ka zo muje inda nake tunanin zata iya zuwa saboda suna da ƴan mata a gida, gidan ƙanin Daddy ne ko zuwan farko ta sake sosai anyi hira da ita kamar ta saba, wataƙila ko zata je can. Kaje ka dawo sai mu je.” Bebi yace, “ina za je na dawo? Muje yanzu kawai.” Huzaifa yace, “bara mu yi sallar azahar sai muje.” “Kaji matsalar ka, muje can nayi sallar kawai.” Huzaifa yace, “akwai abinda zan ƙarasa yanzu, kaje ka dawo.” Bebi yace, “me zaka yi? Don Allah kayi hanzari mu je kawai.” “Ni fa nace maka zamu je, kaje ka dawo kawai.” Bai ce komai ba ya fita ya bishi da kallo yana dariya. Hamza da yake kallon su yace, “ka tausaya masa don Allah ka kai shi ga matar sa.” Huzaifa yayi dariya yace, “can zamu je, ai yayi laushi sosai ya kamata ace ya ganta.” Hamza yayi dariya ya wuce ciki shima ya wuce. Ba jimawa Bebi yazo lokacin Huzaifa ya fito harabar asibitin ya kalle shi yace, “muje.” Motar sa ya shiga shima ya shiga tasa Huzaifa yayi gaba Bebi na bin sa baya yana fatan Allah yasa Manal tana gidan. Ganin sun nufar hanyar gidan Huzaifa abin ya bashi mamaki bai magana ba sai da yaga Huzaifa ya shiga gida yayi tsaki ya ɗauki waya ya kira shi yace, “wai meye haka? Ni da zamu je wani waje meye na zuwa gidan ka?.” Huzaifa yace, “Daddy ne a gidan yace mu zo da kai, ka fito ku shiga ciki” yana faɗa ya yanke wayar. Bebi mamaki yake yi jin yace daddy kawai ya saka ya fito ya shiga cikin gidan. A ƙofar falon ya tarar da Huzaifa suka shiga ciki babu kowa a falon Bebi ya kalle shi yace, “Ina Daddyn? Ni ban yarda ma da batun Daddy yana nan ba kana yi min yawo da hakali ne kawai dan kaga ni nake nema a wajan ka.” Huzaifa yayi dariya kaɗan zai yi magana kenan Manal ta fito daga ɗakin da take tana cewa, “Ayan yunwa nake ji duk kukan ka sai naci abinci.” Kallon wajan tayi inda suke taga Bebi yana kallon ta daga tsaye ta kalli Huzaifa da yake tsaye shima yana kallon ta. Ganin kallon da take musu sai Huziafa yace, “zo ki zauna Manal.” Ta kalle shi tace, “Yaya Huzaifa ba haka muka yi da kai ba.” “Na sani, dole ce ta saka ni na karya alqawarin ki. Ki zo ki zauna.” Bebi kallon ta yake yi kafin ya kalli Huzaifa ya ce, “Amma kaci amanata, daman duk wannan yawon da nake yi ina neman ta tana gidan nan?.” Huzaifa yayi dariya yace, “tana gidan Yayan ta. Manal ki shiga ki ɗauko duk wani abin da kika sani na naki ne ki bi mijin ku koma gida.” Kamar zatayi kuka ta girgiza kai tana kallon Huzaifa tace, “Ni ba zan koma yanzu ba.” Huzaifa yace, “A’a Manal, abin yayi yawa. Tun jiya naso na mayar dake Allah bai yi ba sai yau.” Manal tace, “Bazan koma ba, ba shi yace in tafi kar na dawo ba? To bazan koma ba” ta faɗa tana juyawa ta koma ɗaki. Huzaifa ya kalle shi yace, “kaga abinda ka jawo mana saboda banzan ɓacin ran ka da baya iya sarrafa magana. bara na bita Allah ya taimake ka na iya lallaɓa ta” ya faɗa yana nufar ɗakin da ta shiga sai ya kalle shi yace, “zan je mu tattauna matsayin Yaya da ƙanwa” ya faɗa yana dariya. Huzaifa ya same ta a zaune tana kuka ya ce, “Manal haƙuri zaki yi ki zo ki koma.” Ta share hawayen ta tace, “Yaya bazan iya komawa.” Huzaifa yace, “meyasa?.” “Tunda na fita bai neme ni ba sai yanzu? Ni bazan koma ba.” “Wallahi tallahi ya neme ki ni shaida ne, ya rasa inda kike gabaɗaya a cikin damuwa ki yake.” Manal ta goge ido tace, “bazan koma yau ba Yaya, don Allah ka ƙyale ni.” “Manal kwanakin sun yi yawa, ki daure ki tashi ki bi mijin ki fushi ya isa haka. Koma meye in kin je gidan sai ku ƙarƙare shi. ki fito muna jiran ki” ya faɗa yana fita ya ƙyale ta. Ya kalli Bebi bayan ya fito ya ce, “muje kafin ta fito.” Bebi yabi bayan sa a sanyaye. A harabar gidan Bebi ya kalli Huzaifa ya ce, “Daman tana nan baka faɗa min ba? Kasan irin wahalar da na sha akan neman ta kuwa?.” “Tun daren nan tayo kai tsaye, da safe take sanar dani ita bazata koma ba kuma don Allah kar na faɗa maka. Da naga tana cikin damuwa sosai sai nayi shiru ban sanar da kai ba amma a jiya nayi niyar dawo maka da ita hutun ya isa. Da naga yadda ka tayar da hankalin ka sai nace bara na ƙyale ka naga zaka nemo ta. Kuma abinda ma ya bani mamaki ban ji kayi zancen bata nan ba, sai nayi tunanin kenan ba neman ta ka ke yi ba, baka so ka san inda take shiyasa kawai na ƙyale ta ta zauna.” Bebi ya sauke numfashi yace, “ka ɗauki haƙƙina wallahi. Ta ya zaka je bana neman inda take? Matata ce fa.” Huzaifa yayi dariya ya ce, “ka san meye problem ɗin ka? Kai baka so a ɓoye maka wani abu amma kai kana iya ɓoyewa wani. Tun farko mun faɗa maka sanar da ita lamarin Rumana shine mafita amma sai ka ƙi, sai ka ke ganin in ka aure ta faɗa mata zai fi zuwar maka da sauƙi, kaga a yanzu babu aure tsakanin ka da Rumana amma kishi ya hanata fahimta hakan. Yanzu ma taƙi fitowa tace baza ta koma ba, kawai na bata umarnin fitowa ne ba don son ranta ba dan in na biye mata nan da sati ma baza ta koma maka ba, tace ai kace in ta tafi kar ta dawo.” Bebi ya sauke numfashi ya ce, “na fahimci kuskure na, kuma ni ba wai naƙi faɗa mata bane tashin hankali ne bana so.” “Yanzu gashi ai ta saka ka a damuwa na kwana biyar, itama ta jefa zuciyar ta a damuwa da kishi. Sannan kuma Bebi ɗaukar hannu ka mari mace ba halin miji na gari bane ba.” Bebi ya kalle shi Huzaifa ya ce, “bata ce min ka mare ta ba, ni naga shaidar hannun ka a fuskar ta, fuskar ta kumbura har kunnen ta sai da ya yi ciwo saboda marin. Don Allah ka dinga sarrafa ɓacin ranka ka in ba haka wallahi za’a samu matsala nan gaba, baka san lokacin da zaka furta kalmar saki ba.” Bai ce masa komai kallon hanya kawai yake ganin Manal ta fito ita da matar Huzaifa fuskar ta babu walwala ko kaɗan, tana ƙarasowa Huzaifa ya riƙo hannun ta Bebi ya kalli hannun nasa yana jin wani iri zuciyar sa da gangar jikin sa. Jikin sa yayi sanyi sosai gabaɗaya baya bai ji daɗin wannan riƙe ta ɗin da Hamza yayi ba. Huzaifa yace, “Manal mu je na kai ki mota da kai na.” Da matar Huzaifa suka gaisa tana tsokanar Manal Huzaifa yana riƙe da hannun ta har bakin motar, Bebi ya fito da Ayan a hannun sa da kuma kaya a leda ya saka kayan a bayan motar ya ƙaraso inda suke Manal da Huzaifa suke tsaye. Hannun sa ya saka ya riƙe hannun Huzaifa ya raba hannun sa da yake cikin na Manal yace, “hakan bai kwantan min ba wallahi, zuciyata ciwo take min.” Huzaifa yayi dariya yana girgiza kai tace, “Au Allah? Dan na lallaɓata ta fito ko?. Na rantse da Allah sai nace ta koma sai ka bani haƙuri, Sai ka tunzura ni na nuna maka ni babban Yayan ta ne dole ayi min biyayya.” Huzaifa ya faɗa yana buɗe mata gaban mota ta shiga tana jin su bata ce komai ba. Bebi ya bata Ayan a cinyar ta ya kulle gaban motar ya kalli Huzaifa yace, “in ka fasa.” Huzaifa ya girgiza kai yace, “Wallahi naso kafin ka aure ta aka tabbatar da ni jinin Manal ne, Wallahi da sai na baka wahala fiye da tunanin ka, sai nayi maka test da exmas ɗin da ka ke yiwa samarin ƙanen ka.” Bebi ya Harare shi bai ce komai ba ya buɗe gaban mota ya shiga ya sauke glass gefen da Huzaifa yake tsaye ya yi masa wani banzan kallo, Huzaifa yayi dariya shima dariyar yayi yaja motar suka tafi. BDƘB3P37 Tafiya suke bata ce masa komai ba shima ya kasa magana sai kallon ta da yake yi ta gefen ido, ta haɗe fuska sosai tana yiwa Ayan wasa da yake kwance a hannun ta. Kallon sa tayi suka haɗa ido ta ɗauke kai daga kan sa ta cigaba da yi masa wasa ganin yana dariya sai tayi dariya itama tare da ɗaukar wayar ta tana yi masa hoto. Wayar ta ce tayi ƙara taga sunan Mubeena ta ɗauka a bayyane tace, “Yaya Mubeena ina yini.” Shiru tayi alamun ana bata amsa kafin tace, “to sai kun dawo, ina Maman?.” Shiru ta sake yi kafin tace, “To Mama Allah ya kiyaye sai kun dawo” ta faɗa kamar zata yi kuka kafin ta girgiza kai tace, “to Mama, Allah ya kiyaye hanya.” Daga nan ta kashe wayar ta sauke numfashi. Hannun sa taji akan nata ta kalle shi taga ba ita yake kallon ba ta kalli hannun nasa wanda yake da kyau a ko yaushe, musamman azufar hannun sa da kuma agogon da yake ɗaure a tsintsiyar hannun nasa. Bata motsa ba kuma bata janye hannun ta ba ya cigaba da tafiya har suka zo ƙofar gidan, mai gadi ya buɗe masa gate ya shiga da motar ya faka motar har lokacin hannun sa yana kan nata. Zame hannun ta tayi ta buɗe motar ta fita ta shiga cikin gidan ba tare da ta kalle shi ba. Numfashi ya sauke yayi murmushi yace, “My life partner” ya faɗa yana shafa kansa yana murmushi. Fitowa yayi daga motar ya ɗauko kayan da ya saka a motar ya shiga ciki zuwa ɗakin ta. A tsaye ya same ta tana kaɗe gadon Ayan kafin ta kwantar dashi tana kallon ɗakin. Juyowa tayi suka haɗa ido taga yana yi mata kallon ƙasan ido kawai sai ta shiga banɗaki ta barshi a wajan. “Zan je na dawo yanzu, duk fushin da kike zan iya ɗauka sa Madam” ya faɗa yana murmushi ya fita. Bai jima da fita ba ya dawo da white bread, da maradar da take sha da sugar da komai wanda ya san tana amfani dashi ya siyo. Yana shiga falon ya sauke ajiyar zuciya saboda ƙhamshin air freashner da ya daki hancin sa,Gashi ta kwashe komai na falon ta gyara shi yayi tas kamar ba shine wanda ya tara masa kaya ba. Kitchen ya shiga ya tarar ta wanke komai sai ƙyalli kitchen ɗin yake yi, murmushi yayi a bayyane yace, “gida ba gida bane in babu mace, Allah ya ƙara miki lafiya Fatima na” ya faɗa yana ajjiye abinda yazo dashi ya fita zuwa ɗakin ta. Bata ciki ɗakin amma shima ta gyara shi hakan ya saka shi fitowa zuwa na sa ɗakin. Kamar yadda yayi zato tana ciki ta yaye zanin gafon gabaɗaya ta ajjiye a ƙasa, ya kalle ta yace, “sannu da aiki Partner. Meyasa baki bari nazo na taya ki ba?” Ya faɗa yana matsowa kusa da ita. Kallon sa tayi ta taɓe baki ta wuce zata bar wajan ya riƙo hannun ta ta baya ya dawo da ita kusa da ita, ya riƙe kafaɗun ta yana kallon idon ta yace, “fushi kike ko? Na san kin cancanci ki yi fushi amma na gane kuskurena kuma bazan sake maimaitawa ba.” Bata ce komai ba ta zame jikin ta ta fita daga ɗakin ko kallo bai ishe ta ba, bai bita ba shima ya koma wajan Ayan da yake ta wasa akan lilon sa da ta shigo dashi ɗakin yana yi masa wasa. Manal dawowa tayi da zanin gado sabo a leda ta warware ta shimfiɗa a kan gadon, ta ɗauki jakar filon ta saka ta ɗauki turaren ƙhamshi tana fesawa a jiki, ta ɗauke wanda ta cire ta saka shi cikin wardrobe ɗin ɗakin. Tana juyowa daga taga yazo gab da ita har ƙirjin ta yana taɓa nasa gashi tana jikin wardrobe, gefe tayi zata wuce ya hana ta, ta sake komawa ɗaya ɓarin ya sake hanata, sai ta tsaya cak bata sake motsawa ba. Kallon ta yake yi ya riƙe fuskar ta da hannun sa biyu yace, “Partner ki daina fushi dani don Allah.” Kallon idon sa tayi na wani lokaci shima yana kallon ta kafin ta ɗauke idon ta daga kan sa, hannu ya saka ya riƙo ƙugun ta ya jawo ta ya haɗa ta da jikin sa sosai yace, “ki yi magana don Allah.” Bata ce komai ba tana ƙirjin sa ya saka hannu ya riƙe bayan ta sosai, ya kai bakin sa daidai kunnen ta yace, “i’m sorry! i’m sorry!! I’m sorry!!!. I’m sorry Partner na san nayi ba daidai ba, ki ya yafe min.” Tana jikin sa sosai dan ya matse ta a jikin sa tana jin duk abinda yake faɗa a kunnen ta tayi shiru bata ce komai ba, ya ɗago fuskar ta daga jikin sa yana kallon ta yace, “kice wani abun mana, na sha wahala kafin na gano inda kike, na tabbatar da ke ɗin rayuwata ce, in babu ke rayuwata tana cikin wani yanayi mara dadɗ. Na shiga damuwar rashin ki sosai, kice wani abun mana Partner, nayi kewar maganar ki” ya faɗa yana matso da bakin sa kusa da nata yayi mata kiss ya sake kallon ta yace, “talk to me please.” Bata ce komai ba ya sake mayar da ita jikin sa yana sake riƙe ta sosai yace, “nayi kewar ki.” Nan ma bata ce masa komai ba ya ɗago ta daga jikin sa yana kallon ta ganin idon ta ya ciko da hawaye yace, “kar ki kuka don Allah, ki mayar da hawayen nan bana son ganin su partner .” Sakkowa hawayen suka yi daga idanun ta yace, “oh my god! Nace ki yi haƙuri fa meyasa baza ki haƙura ba? Hakuri nake baki fa partner.” Goge idon ta tayi ta kalli Ayan da yake kallon su kamar ya san abinda ake yi ta kalle shi kamar zata yi magana sai ta fasa, yace, “don Allah ki yi magana kar ki fasa.” “Cewa zan yi ka ƙyale ni.” “bazan iya ƙyale ki ba, me kike so nayi miki kuma Na baki haƙuri ya kamata ace komai ya wuce.” Kallon sa tayi tare da murmushin tace, “ba kace saboda Ayan ka zaɓe ni ba? To ka bar ni na tafi sai ka ɗauki Ayan ɗin ka bata ta riƙe maka” tana faɗar hakan ta fita ta bar shi a tsaye yana kallon ta. Shafa kansa yayi dan shi ya manta da wannan kalaman da yayi mata gabaɗaya, lallai dole tayi fushi sosai. Ajiyar zuciya yayi ya ƙarasa ya ɗauki Ayan suka fito falon dan so yake ayi ta ta ƙare ya gaji da zaman kaɗaici. Ɗakin ta ya koma ya same ta tana tsaye tana saka kayan Ayan a cikin baby wardrobe ɗin sa tana kuka sosai, a hankali yake takawa ya ajjiye Ayan a kan gadon ya dawo kusa da ita ya rungume ta ta baya, ƙoƙarin ƙwace jikin ta take yi tana kuka ya matse ta sosai, tun tana son ƙwace jikin nata har ta gaji saboda yadda ya riƙe ta sosai sai jikin ta yayi sanyi tana kuka sosai. A kunnen ta yake furta, “I’m sorry! I’m sorry!.” Kukan take yi sosai ya matse ta a jikin sa ya hanata motsi har sai da kukan nata ya ragu sannan yace, “Fatima na ki daina kuka.” Kamar bazata yi magana ba sai nasihar Mama da tazo kunnen ta lokacin da za’a kawo ta gidan sa matsayin amarya, inda take cewa, _Kar ki kasance mai taurin kai, kar ki ga mijin ki yayi miki laifi yana bin ki yana rarrashi ki dinga jan aji ki ƙi bari komai ya wuce, in kika fara aikata hakan rarrashin ki zai sire masa, saboda zai ga yana bin ki yana rarrashi amma kina botsarewa. In kin ciza ki hura, ma’ana In kika ja ajin kaɗan sai ki bar komai ya wuce, in ba haka ba nan gaba in yayi miki laifin zai daina bin ki saboda zai ce ya san ba rarrashin zaki ji ba, gwara ya bar ki duk sanda kika so zaki dawo daidai._ wannan tunanin ya saka Manal tace, “Ka daina sona, kace saboda Ayan ka zaɓe ni ba dan kana sona ba. Meyasa ka zaɓe ni bayan ka san baka sona?” Ta faɗa murya na rawa sosai. “Ina son ki Manal, kece rayuwata.” “Baka damu dani ba tunda har ka iya barina na fita daga gidan bayan ka san goma na dare ta wuce, a daren ko kiran wayata baka yi balle kaji inda nake, a haka zaka ce min nice rayuwar ka?.” Ya sasauta riƙon da yayi mata ya juyo da ita yana kallon ta yace, “na damu Partner na damu, kema kin san na damu dake kuma ina son ki. Ban san kin fita ba sai kulle gate naji, a tunani zaki je gidan Mama ne shiyasa na bari kika tafi, ina cikin ruɗani ne a wannan lokacin amma ba wai don ban damu dake ba.” Raba jikin ta tayi da nasa ta zauna a gefen gadon ta kalle shi tace, “amma ai cewa kaka yi in na tafi kar na dawo nai ta zama har abada, sannan ka kalle ni kace darajar Ayan naci da babu abinda zaka yi dani.” Ya zauna kusa da ita yayi yace, “Raina ne a ɓace, ina cikin damuwa a gaban ki komai ya faru, Mummy ko magana bata yi min, gani take kamar komai da ya faru ni ne silar faruwar sa. Na dawo gida saboda na samu nutsuwa a wajan ki kema kika so da taki maganar. Duk abinda ya faru laifina ne da kuma naki laifin, na san kina da tambayoyin da ki ke so na amsa miki da sai ki jira sai washe gari lokacin na nutsu, ban ce kar ki dawo da wata manufa ba, bance na zaɓe ki saboda Ayan dan da gaske hakan ne a raina ba, ke kin san ina sonki ko babu Ayan.” Ta kalle shi tace, “Meyasa tun kafin ka aure ni baka taɓa yi min maganar Rumana ba?, Meyasa baka ce min bayan aurena da kai da shekara ɗaya zaka aure ta ba?, Meyasa ka ɓoye min kayi min shiru bayan kai ne mai cewa baka so a ɓoye maka komai kuma kai ka ɓoye min?. Ka manta abinda ya faru kafin ka aure ni? Ka manta saboda kana ganin kamar na ɓoye maka wani abun kaso ka fasa aurena?. Meyasa ni ka ɓoye min? Kenan kai ne mai zuciya ni bani da ita?.” Ta kalli cikin idon sa tace, “baka taɓa faɗa min abinda ya shafe ka, ko yaushe cikin ajjiye sirrin ka kake a zuciyar ka, bani da martabar da zan san damuwar ka.” Ya girgiza kai yace, “fargabar kar na faɗa miki ki fasa aurena shine ya saka ban faɗa miki ba, in zaki tuna kafin auren mu ranar da nace kizo mota ki same ni har nace akwai abinda zan faɗa miki a lokacin maganar zan faɗa miki Manal. Amma da kika zo zai na kasa saboda zuciyata tana faɗa min kamar in na faɗa miki zaki ce kin fasa aurena ne. Bayan na aure ki sai na fahimci gwara na faɗa miki kafin na aure ki da ace na faɗa miki bayan kin zama mallakina, hakan ya saka na dinga ɓoye miki damuwata indai akan Rumana ne, bana ɓoye miki komai a kaina in kinga kin tambaya bance miki komai ba tabbas Mummy tayi min zancen ta.” Ta kalli idanun sa tace, “da gaske ka so Rumana a baya?.” Ya sauke idon sa ƙasa ya kalle ta ya girgiza kai yace, “na so ta, itace mace ta farko da naso a rayuwata na kuma so na aure ta Allah bai yi ba. Tun daga lokacin da tayi aure Allah ya zare min ita daga zuciyata.” “Kenan ba ni ce first love ɗin ka ba?.” Yayi Shiru ya kalle ta yace, “kamar yadda na ce miki na so Rumana a baya.” Hawaye ya sakko mata tace, “‘meyasa baka aure ta ba?.” “Allah ne ya zare mun ƙaunar ta daga zuciyata, kuma Allah bai yi ni mijin ta bane.” “Yanzu sai ka koma mata ai” ta faɗa zata tashi ya hanata yace, “wannan maganar ta riga ta wuce ya kamata ki manta da komai.” “Meyasa ka ɓoye min? Meyasa baka sanar dani ba?. Kaine ka ke cewa baka son a ɓoye maka komai meyasa kai ka ɓoye min?.” Ya riƙe hannun ta yace, “na faɗa miki dalilin, Nayi hakan ne saboda nayi rayuwa dake, Kuma babu ita a raina na manta da ita ke kawai nake gani.” Ta girgiza kai tace, “ban amince ba, kaima kana son ta har yanzu saboda sunan da ka ke faɗa mata ma daban da yadda kowa yake faɗa, ban amince baka son ta ba domin abinda aka fara so yana da wahalar bari zuciyar wanda yaso.” “Manal bazan miki ƙarya dan na wanke laifina ba, da gaske na san na so ta a baya amma daga baya komai ya zama labari, in ba ganin ta nayi ba ina mantawa da nayi soyayya a wannan lokacin. Na san mun shaƙu da ita sosai kasancewar a gida ɗaya muke zaune kuma tare muka tashi shekarun da na bata basu da yawa, har yanzu akwai wannan shaƙuwar a zuciyata amma babu batun soyayyya.” “next month zamu yi shekara da aure kenan da sai dai naga an kawo ta matsayin matar?” Ta faɗa tana wara idanun ta kafin ta girgiza kai tace, “da bazan iya rayuwa ba, mutuwa kawai zan yi” ta faɗa tana kuka ya kwantar da ita a jikin sa tana kuka ya ce, “wannan duk maganar fa ta wuce Manal, Ruman yanzu Yayar ki…” ɗago kai tayi ta kalle shi tace, “bana so na sake ji kace Ruman ɗin nan, ka faɗi sunan ta kamar yadda kowa yake faɗa.” Yayi murmushi ya shafa bayan ta tace, “Shikenan! Rumana, in kika tuna yanzu…” ta sake dakatar dashi tace, “Meyasa yadda ka ke faɗar sunan ta bambamta da yadda mutane suke faɗa?.” “To Manal ya zanyi?, haka maganata take zan canja ne?.” Ta kawar da kai gefe yace, “Yanzu Ruman…oh sorry Rumana ƴar uwar ki ce, tana matsayin Yayar ki a wajena kuma matsayin ƙanwata.” Ta kalle shi kallo irin na ban yarda da kai ba tace, “Shikenan matsayin da take dashi?.” “Shikenan bayan wannan, zan girmamata matsayin yayar matata, sannan zan kalle ta matsayin ƙanwata wacce muka tashi kusan tare da ita.” Ta goge idanun ta tace, “har yanzu zuciyata rawa take yi.” “Ta daina rawa a kaina, har zuciyata nake faɗa miki wannan maganar kin san bazan miki ƙarya ba.” Ta girgiza kai tace, “Meyasa baka faɗa min an ɗaura maka aure da ita ba? Meyasa ka ɓoye min?.” Bebi yace, “yadda kika ji labarin haka naji wallahil azim ban sani ba, na san dai ta tafi Abuja kuma Mummy ta maimaita min maganar aurena da ita bayan wannan ban san da aurena a kanta.” Manal tace, “yanzu ko a tarihi sai ance mata biyu ka aura ko?.” Yayi murmushi yace, “mace ɗaya na aura kuma itace ke.” Ta kulle ido ta buɗe tace, “bayan ita babu wata kuma?.” Yayi ƴar dariya yace, “akwai.” Kallon sa tayi ya ɗaga mata gira yace, “akwai Fatima na kuma Mummyn Ayan, ita kaɗai ce a zuciyata bayan ita babu ko wacce mace da nake kallo da fuskar soyayya.” Ta sauke ajiyar zuciya tace, “ba wani nan, bayan kwana biyar nayi baka neme ni ba.” Bebi yace, “Allah ne kawai ya san irin tashin hankalin da na shiga, duk yadda zan faɗa miki baza ki gane ba, Allah ne kawai yasan yadda zuciyata take bugawa saboda rashin ki. Babban abin haushin ma muna tare da Huzaifa bai taɓa faɗa min kina can ba, har gidan nan yazo yana cewa shima zai nemo ki matsayin sa na yayan ki bai nuna min kina gidan sa ba. Ai ya ɗauki haƙƙina wallahi kuma zan rama abinda yayi min.” Manal tayi dariya kaɗan tace, “Yayana ne.” “Yayan naki fa, ya munafurce ni.” Ta girgiza kai tace, “Allah zan ce sai ka bashi haƙuri zan haƙura.” Yayi dariya ya ce, “girman ki ne, in hakan ki ke so sai ayi indai zaki huce.”dariya tayi ta kwanta a jikin sa yace, “Allah ya azabtar dani, na shiga tashin hankali sosai. Na rasa inda zan saka raina, nayi waya kin ƙi ɗauka na zaga inda nake tunanin zan same ki amma bakya nan. Kar ki sake nisa dani partner rashin ki illa ce a gare ni.” “Ni kuma bani da kamar sa, Yayana ne da babu kamar sa.” Yayi murmushi yace, “ni kuma abokin adawata ne.” Tayi murmushi ta riƙe shi tace, “Partner amma akwai wata maganar fa.” Ta ɗago daga jikin sa tana kallon sa tace, “a cikin zaman auren da muka yi da kai bamu shekara ɗaya ba amma ka mare ni sau biyu, na so ace ina cikin matan da zasu kafa tarihi a rayuwar auren su suce ce shekarar su hamsin da mijin su bai taɓa dukan su ba, ban samu shiga wannan layin ba duk da burina ne hakan. Don Allah Partner kar ka sake cewa zaka dake ni, ka kalli kunnena ka gani sai da na sha magani saboda marin da kayi min sai dai kunnen yayi ciwo. in dai ranka zai ɓaci ka ce zaka ɗaga hannu ka dake ni rayuwar mu zata dinga lalacewa, girman ka da matsayin ka zai dinga raguwa a idona har a kai ranar da ba’a a bana fatan zuwan ta…” kafin ta ƙarasa yace, “Ranar da zan mare ki ki rama ko?.” Ta ɗaga masa kai alamun eh ya riƙe kunnen ta yake ciwo yana kallon cottin ɗin da take ciki yace, “ki yi haƙuri bazan sake ba in sha Allah, hakan ba halina bane raina ne ya ɓaci sosai, amma nayi miki alƙawarin duk ɓacin ran da zan shiga bazan sake marin ki ba. Roƙona a wajan ki duk lokacin raina yake a ɓace ki dinga ƙoƙarin ganin kin gujewa abinda zai sake ɓata min rai, ki dinga ƙoƙarin taimaka min wajan kawar da ɓacin ran in ba haka ba za’a iya samun matsala fiye da wacce tafi waccan.” Ta ɗaga kai tace, “in sha Allah zan yi iya ƙoƙarina. Kayi haƙuri da kalaman da na faɗa maka a ranar, na shiga tashin hankali ne kawai maganar na fitowa daga bakina ne ban san ina yi ba.” “Komai ya wuce, kar ki damu daman laifina ne.” Tayi murmushi tana kallon hannayen sa da suke cikin nata ta kalli Ayan da yayi bacci ta kalle shi tace, “Mummy bata ji daɗin hukuncin da kayi ba ko? Meyasa ka zaɓe ni?, da gaske alfarmar Ayan ne ya saka ka zaɓe ni?.” Kiran sallah ya jiyo ya kalle ta yace, “ana kiran sallah, zan je nayi sallah na dawo zan faɗa miki dalilin da ya saka na zaɓe ki, abu ɗaya nake so ki riƙe a zuciyar ki ni Adnan naki ne ke kaɗai in sha Allah. Bani da wacce nake so sai ke Manal, Allah ne ya saka min ke a zuciyata. Ko da Ayan ko babu Ayan zan zaɓe ki a cikin mata dubu, kece ɗaya tilo bayan ke babu wata” ya faɗa yana yi mata kiss a goshi ya tashi tsaye ya ƙarasa wajan ya yi masa kiss ya fita. Yana fita aka kira ta a waya ganin sunan Addah Halima ce sai ta ɗauka tana murmushi nan take sanar da ita gata ta zo gidan, da farin ciki Manal ta fito ta tarar ya buɗe musu falon sun shigo shi kuma ya fita. Adah Halima ta jima a gidan suna hira Manal tayi musu girki aka ci ana dariya da raha cikin zumuncu, bata bar gidan ba sai bayan sallar i’sha Manal tayi farin cikin zuwan ta sosai duk da sallama tayi nata tace washe gari zata wuce Lagos. Bayan fitar su ya jima bai dawo ba har ta gama kwashe kayan da akayi amfani dasu ta gyara wajan tayi wanka ta shirya dan ta san ranar ta musamman ce a wajan sa shi da ita. Tana fitowa falon yana shigowa yace, “na jima ko?, Naje wajan Mama na kai mata maganin Ruman.” Kallon da tayi masa ne ya saka yace, “Oh Sorry, Rumana zan ce” ya faɗa yana zama tayi dariya tace, “na kawo maka abinci ko ba yanzu ba?.” “Bani yanzu.” Ta wuce ta kawo masa abincin ta zauna a gefen sa tana ci itama. Wayar sa ce tayi ƙara taga yayi saurin danna wayar ta ɗauke ta kalle shi tace, “wannan hanzari na danna power na meye? Waye yake maka waya haka?.” Bebi yace, “daga asibiti ne bana so a takura min.” Ta jingina da kuskure tana kallon sa tace, “oh daga asibiti, Lallai kam.” Bai ce komai ba yana cin abinci ta kalli wayar tace, “ko yaushe wayar ka na kusa da kai kamar mara gaskiya, me ka ke ɓoyewa a ciki?.” “Me zan ɓoye a ciki? Babu komai, wayar mutum sirri ce ai ko?.” Manal tace, “ni meyasa tawa bata zama sirrina ba?.” Yayi dariya kawai baice komai ba kafin ya kalle ta ganin shi take kallo yace, “babu komai a wayar fa, zaki iya ɗauka ki duba abinda kike so.” Manal tace, “a nasihar da aka yi min kafin nazo gidan nan ance min banda duba wayar ka, na kuma gamsu da nasihar, a yanayin yadda aka kira ka kashe da sauri ya nuna min akwai wani abun a ƙasa.” “Tunanin ki budurwa ta ce?.” “Ni dai ban ce ba, kawai nace akwai wani abun a ƙasa.” Yayi murmushi bai ce komai ba ya cinye abincin ya tashi ya shiga ciki itama ta ɗauke abinda ya gama ci ya shiga ciki. Tana tsaye tana shaye abinda Maman Surayya ta bata tun ranar da zata gidan ya shigo yana kallon ta itama tana kallon sa, ta ajjiye abinda ta shanye ya shigo yana kallon ta yana lumshe ido ya buɗe ya sake kallon tq yace, “kin shirya amma ko?.” Ya zo gab da ita yana kallon idon ta tace, “na shiryawa me?.” “Kin shirya zama sabuwar amarya a yau? Dan no excuse, four to six rounds in sha Allah. Dan wannan kwanakin da aka ɗauka Allah sai na fanshe su a yau.” Ta wara ido tace, “Six kamar wata machine?, A’a kar mu yi haka da kai ka san bazan jure ba.” Yayi dariya ya kai hancin sa wuyan ta yace, “ki shirya dole ma ki jure ko bakya so.” Cikin shagwaɓe a tace, “Allah ka san bazan iya ba, kaima faɗa ka ke amma kaima baza ka iya ba.” Yadda tayi shagwaɓa ya burge shi ya kuma shige shi sosai, ya jawo ta ta faɗa jikin sa da nata yana zame rigar ta daga sama yace, “kina kokwanto bazan iya ba?.” Tana daga jikin sa tace, “uhum!.” “Mu gwada?.” “Ni dai a’a ban yarda ba” ta faɗq tana sake motsawa a jikin sa hakan ya sake saka shi a sabon yanayin. Ɗagowa tayi ta kalle shi tace, “why did you choose me?.” Ta faɗa a lokacin da yake sauke rigar ta ƙasa. Fuskar ta ya riƙe yace, “Because” ya faɗa yana yi mata kiss a wuya yace, “Because you’re you” ya yi mata kiss a wuyan ta yace, “loving” ya sake yi mata kiss yace, “beautiful” ya dawo goshi ta yace, “smart” ya yi mata kiss a idanun ta yace, “brave” ya sake matsawa wani wajan yace, “unselfish” ya sake matsawa wani wajan yace, “your smell” ya faɗa tana kai hannun sa ko ina na jikin ta da kuma hancin sa. Ya kai bakin sa cikin nata ya yi kissing sannan yace, “your taste.” Manal ta lula wata duniya a wannan lokacin salon da yake amfani dashi yana yi mata maganar ya saka ta a sabon yanayi wanda bata ɓata shiga irin sa ba, murya a sarƙe tace, “it’s feels so good when you touch me Partner.” Jin abinda tace sai ya ɗauke ta cak ya ajjiye a kan gadon ya bi bayan ta ba tare da wani dogon tunani ba. BDƘB3P38 Manal ta jima tana bacci kukan Ayan ne ya tashe ta ta miƙe zaune daƙyat ta kalli inda yake jin kukan sa ta ganshi a hannun sa yana jijjiga shi yace, "na rasa yadda zan masa yayi shiru, ba dan naso ba kika tashi" ya faɗa yana ƙarasowa ya hau kan gadon ya zauna kusa da ita. Lumshe ido take yi ta dafe kai tace, "kaina ciwo yake min, Wallahi bayana ya riƙe sosai." Yayi ƴar dariya tace, "ba ke kika ce min bazan iya ba?" Ya faɗa yana ɗora mata Ayan a jikin ta tare da ciro nonon da kansa ya saka masa a baki ita kuma ta tallafe kansa ya kalle ta yace, "har yanzu bakya riƙe shi sosai, in kina masa wannan riƙon zai dinga gaggarawa yana zuwa kunnen sa" ya faɗa yana ɗago hannun ta ya daidai ta mata yadda zata riƙe shi. Manal ta jingina da fuskar gadon ta rufe ido, a gajiye take sosai ta sha wahala a hannun sa fiye da tunanin ta, kiss ya yi mata a baki ta kalle shi ya ɗaga gira yace, "ya muje round seven ne?." Ta bata fuska kamar zatayi kuka tace, "Allah ka bani wahala soaai, na gaji bayana ciwo yake min Gashi yunwa nake ji." Yayi murmushi yace, "nima na gaji, amma dole ce ta saka na kasa haƙura dake. Ji nayi kamar an canja min kw kin dawo sabuwa tal kamar ranar da aka kawo min ke." Ta kalle shi suka haɗa ido sai yayi dariya tunawa da wannan daren ita kuma ta kulle idanun ta cikin jin nauyin sa. "Mai kunyar matata, har yanzu kin kasa daina kunya ta hakan kuma yana burge ni sosai. Kin san dai jiya daren nan ya zama na musamman, dan yaso yafi na farko ma, kawai dai dan na farko na farko ne amma da sai nace wannan yafi na farko. Saboda wannan da taimakon ki ya zama na musamman, Wancan kuwa kamar matacciya haka kike a kwance." "Allah ka daina faɗa min bana so." "Allah sai na faɗa, kin ji daɗi naji daɗi, na farko kuma kin sha wahala naji daɗi shine fa kawai." Manal ta rantse ido yayi dariya yaja hancin ta yace, "gulamammiya kawai." Tayi murmushi ta zare Ayan daga jikin ta ta bashi shi tace, "ni ka ɗauke shi ku fita bacci zanyi"sai kuma ta kalli Agogo tace, "Wallahi ina da class yau, Gashi har lokacin ya wuce." Ya kalle ta ganin da shagwaɓa tayi maganar yace, "matata ko babu culinary school ita ɗin professional chef ce, jiya ma na shiga page ɗin ki na Instagram naga ana ta missing posting girkin ki." Ta kwanta a kafaɗar sa tace, "ina jin daɗin goyan bayan nan da ka ke bani." Ya saka hannun sa a rigar ta yace "in ban baki goyan baya ba wa zan bawa?, duk abinda kike da buri zan cika miki shi in sha Allah." Hannun sa ta doke tace, "ka bari bana so." "Ni ina so kuma." "Allah bana so na gaji" ta faɗa tana kallon sa kamar zata yi kuka. Shima ya kwaikwaye ta yace, "Allah ina so ban gaji ba." Suka yi dariya a tare ya tashi ya kwantar da Ayan yace, "taso mu je nayi miki wanka ki ci abinci" ya faɗa yana riƙo ta ta tashi tsaye ya kaita har banɗakin. Wanka kuwa yayi mata ya fito da ita ya shirya ta ya riƙo hannun ta suka fito bayan ya kai Ayan falon. Abincin ya kawo mata ya ajjiye ta ɗauki tea tana sha yace, "yau ki ci girkin Adnan." Ta ɗauki dankalin tana ci tace, "wannan har wani girki ne? Ai abu ne mai sauƙi." Bai ce komai ba tace, "yau dai na ciri tuta an yi min girki, gaskiya na yarda yau ɗin ta musamman ce." Yayi dariya yace, "giyar amarci ne ya saka nayi miki ban ma san nayi ba." Ta kalle shi tace, "ni na sani, in ba dan haka ba ni na isa?." "Har kin yi yawa, ai duk abinda ki ke so zan yi miki ranki ya daɗe." Kamar waccs ta tuna wani abu da sauri ta kalle shi tace, "Partner na shiga uku." Shima da sauri yace, "meye?." "Partner bamu ɗauki ko wanne mataki ba kar nayi ciki a jiya fa." Ya wara ido yace, "ai kam zaki iya, dan jiyan nan ni kaina na san daƙyar ba a samu rabo ba." Ta ajjiye plate ɗin abincin tace, "Innalillahi, na shiga uku partner, wallahi bana son sake haihuwa yanzu, ka taimaka min a san abinda zam yi." Ganin da gaske hankalin ta ya tashi yayi dariya yace, "wasa nake miki, kar ki damu baza ki samu ciki yanzu ba in sha Allah." "Dame ka dogara?." "Ke dai ki yarda mana, kar ki manta ni likita ne fa. Zaki iya samun ciki a duk sanda Allah ya nufa amma in sha Allah da sauran lokaci." Ta sauke ajiyar zuciya tace, "har naji daɗi, sai na huta zan haihu in sha Allah."  Ta fada tana cigaba da cin abincin. Yayi dariya yace, "matsoraciya ce ke ai." Ta taɓe baki tace, "na faɗa maka ba ka san me ake ji a labour room ba" ta ɗago tana kallon sa tace, "a other room kafi kauri." Dariya yayi soaai yace, "baza ki daina faɗar maganar nan ba ko?." Manal tace, "ai gaskiya ne, inda ka san wahalar da ake sha baza kace min matsoraciya ba." Yayi dariya yace, "gaskiya ni other room ne ɓangarena, haƙƙin da Allah ya ɗora min nake sauke miki." Ta taɓe baki bata ce komai ba. "Ina so gobe zan kai Ayan circumcision." "Ai gwara ka kai shi ayi masa ya huta, bana so naga sai yaro ya girma ace za'a yi masa." Ya bita da kallo yace, "ahhh kenan daman kin san meye circumcision ɗin?." Manal tayi masa hararar wasa tace, "ai tunda na san wannan kalmar mai take nufi na daina faɗa da hausa, kunya nake ji a gaban mutane a dinga faɗa babu sayawa." Bebi yace, "to sai meye dan ance kaciya? Hausawa suna sayawa suce shayi ko?." Manal tace, "wallahi bana so, gwara da turancin yafi." "Meye na kunyar?." "Oho min" ta faɗa tana dariya. Yayi murmushi yace, "ke komai kunya yake baki ai." Manal tace, "naji, da kace bani da kunya gwara kace ina da kunya." Murmushi yayi suka cigaba da hira yana tsokanar ta. Tana gama cin abincin ta kwashe kayan ta kai kitchen ta shiga ɗaki ta tarar Ayan ya tashi ta ɗauke shi tayi masa wanka ta shirya shi suka fito falo suka zauna yana hannun ta. Shigowa falon yayi ta kalle shi ganin bai shirya fita ba tace, "baza ka fita ba?." Zama yayi kusa da ita yace, "babu inda zan je, yau a gidan na zan yini." Manal tace, "babu aikin kenan?." "Akwai mana, kawai bazan fita bane a gida zan zauna." Ta ɗan yi murmushi bata ce komai ba. Agogo ya kalla yace, "lokacin sallar la'asar har ya kusa, zan je na gaishe da Mummy na dawo." "Bana jin daɗin jikina da nazo mun je tare." Wani irin kallo yayi mata yana murmushi yace, "ki yi zaman ki naje na dawo, nima bana so ki fita nafi so ki huta saboda kar ki gaji kafin anjima." Ta kalle shi tace, "me ka ke nufi?." "Kin fini sani." "Koma me ka ke nufi a gajiye nake wallahi, jikina ciwo yake min." "Ki sha magani" ya faɗa yana matsawa kusa da ita yayi mata kiss a goshi ya tashi tsaye yace, "zan cewa Mummy kina gaishe ta" ta ɗaga masa kai ya fita da sauri. Bayan Kwana biyu. Manal tana zaune akan kujera Bebi yana kwance yayi matashi da cinyar ta yana duba wayar sa ita kuma tana wasa da gashin fuskar sa. Sallama akayi tare da shigowa inda suke. A tare suka amsa ya kalli inda aka shigo ya tashi zaune yana bin wacce ta shigo da kallo itama tana kallon su. Rumana ce ta shigo ta rame fuskar ta kamar an saka sirinji an zuƙe ta, ta koma ƴar ƙarama kallo ɗaya zaka yi mata ka tabbatar da tayi doguwar jinya. Murmushi Rumana tayi wanda sam bai mata kyau ba saboda ramar da tayi. Rumana ta ƙaraso ta zauna bayan ta ɗauki Ayan tace, “Sis barka da yamma.” Manal tayi murmushi tace, “barka da zuwa, ina yini.” “Lafiya lau, nazo babu sanarwa.” “sai kace wata baƙuwa?, ya jikin naki?.” “Jiki alhamdulillah, sallama nazo nayi mu ku zan koma Abuja.” Bebi kallon ta yake tunda ta shigo cikin tausayawa, yasan duk a kan soyayyar sa ta koma haka, bai san adadin raɗaɗin da take ji a zuciyar ta ba amma ya tabbatar da raɗaɗin bawai kaɗan bane yana d zafi sosai. Ganin yana kallon ta sai tayi murmushi tace, “Barka da yamma Bebi.” Maimakon ya amsa sai yace, “haka kika zaɓarwa kan ki? Kalli yadda kika koma don Allah, kina shan magani ma kuwa?.” Rumana tayi murmushi tace, “nifa naji sauƙi wallahi.” “Ita wannan ramar daga ina ta zo?.” “Bana ce ba, kawai nima naga ina ramewa ne amma bawai dan akwai dalilin ta ba.” Bebi yace, “Ruman kar ki min ƙarya, ke kin san na san halin ki, babu ta yadda za’a yi ki ce min wai kema baki san daga inda ramar nan tazo ba. Damuwar da nake cewa ki cire daga ranki ce kika kasa har ta haifar miki da wannan ramar.” “Ba yadda ka ke tunani bane wallahi.” Kallon ta yake yi kafin yace, “hmmm! Ki sausautawa kan ki dai, in ba haka ba damuwar illa zata yi miki. Na maimaita miki maganar nan na sake maimaita miki amma bakya ji, ai shikenan Ruman ki yi abinda ki ke so.” Ganin yadda yake mata magana cikin tsantsar nuna damuwar sa a kanta sai tayi murmushin jin daɗi tace, “balle ma ba abinda ka ke tunani bane. Ƙanwata mijin ki baya so wani abun ya same ni.” Manal tayi murmushi kawai bata ce komai ba. Tashi yayi ya fita ya bar su su biyun a zaune, ba wata hira suke ba sai maganar tazo bata jima ba ta miƙe tsaye da niyar tafiya. A lokacin ya shigo falon yana daga tsaye Rumana tace, “ni zan wuce, gobe Abuja zan tafi in Allah ya kaimu. Zamu dinga gaisawa a waya.” Manal tace, “Allah ya kiyaye hanya, a gaishe da mutanen Abuja.” Rumana ta amsa da amin ta bata Ayan tana cewa, “Zan yi kewar Baby Ayan.” Manal bata ce komai ba Rumana ta kalli Bebi tace, “na tafi.” “Allah ya kiyaye hanya, ki cigaba da kula da shan maganin ki komai zai zama tarirhi in sha Allah.” Tayi murmushi zata wuce shi tayi tuntuɓe da carpet zata faɗi ya yi saurin riƙo hannun ta yace, “ki bi a hankali, daman kin zama kamar kara ba dole komai yayi ƙoƙarin kayar dake ba.” Tayi dariya ta kalli Manal tace, “ƙanwata mijin ki baya girmama ni.” Manal murmushin yaƙe tayi tace, “kun fi kusa ai.” Ta sake yin dariya tayi hanyar fita Manal ta raka ta har harabar gidan ta shiga mota driver ya ja suka tafi. Shima a nan suka rabu ya hau mota ya fita, haka Manal ta koma ciki ranta duk babu daɗi a haka ta kai dare har lokacin da ya dawo. Bai lura da yanayin ta ba dan bai jira tazo ta zuba masa abinci ba da kansa ya zuba yaci dan yunwa yake ji. Sai bayan ya shirin kwanciya ya fito suks haɗu a falo tana niyar shiga ɗakin sa. Kallon sa tayi tace, “Mummy tace tana kiran ka baka ɗauka, in kazo ka kira ta.” Kai ya ɗaga yana kallon ta wuce shi bata sake magana ba. 39 Bebi bayan ya gama wayar ɗaki ya same ta a zaune a gefen gado ya kalle ta yace, “lafiya ki ke?.” Ta ɗaga kai tace, “lafiya.” “Ban yarda ba, tun daga zuwan Ruman kika canja.” Ta runtse ido ta buɗe ta kalle shi tace, “ka kasa daina cire harafin ƙarshe na sunan ta, na faɗa maka bana so amma ka kasa.” Ya dafe kai yace, “i’m sorry, na riga na saba ne ba ina sane nake faɗa ba. Kar ki ce min da Yayar ki kike kishi Manal?.” “In nayi kishin ma ai ba laifi nayi ba, tunda ka ganta ka rikice kamar ba kai ba, kace wannan kace wancan kamar wanda aka sakawa battery. Harda riƙe mata hannu a gabana” ta faɗa tana kallon sa tare da nuna kanta da yatsa. Ya sauke numfashi ya ce, “Manal Rumana fa yayar ki ce uba ɗaya, meye na kishi da ita don Allah?. Kuma laifi ne dan na tambayi lafiyar ta?, baki ga yadda ta koma bane?.” Ta kawar da kai gefe tana goge idanun ta tace, “yanayin yadda ka ke tambayar ta ta daban dana sauran mutane, tunda ta shigo ka ke kallon ta har ta fita.” Yayi murmushi ya ce, “Manal kar ki manta nima ƴar uwata ce, nuna damuwa akan damuwar ta ba laifi nayi ba. Sannan kar ki manta tsananin son da take yi min ne ya saka mata ciwo, in ban rarrashe ta ba waye zai rarrashe ta taji daɗi?.” Manal ta kalle shi jin abinda yace tana yi masa wani kallo kafin tace, “eh gaskiya kai ɗin ne kawai. Faɗa min tana yi maka son da ya saka mata ciwo, cigaba da faɗa min son da take yi maka ni ban yi maka irin sa. Tunda ni son ka bai saka min ciwo ba ita ya saka mata, kaga kenan yadda take son ka ni bana son ka haka. Ina jin ka cigaba.” Dafe kansa yayi jin ta canja maganar dan shi dariya take bashi ya ƙaraso ya zauna ya ce, “ni na isa nace haka? Waye Adnan da zai cewa Manal haka?. Ni ba da wani abun na faɗa ba ina faɗa miki ne dan ki fahimci tausayi take bani.” “Hmmm! Tausayi yana komawa soyayya” ta faɗa ba tare da ta kalle shi ba. Ya ce, “to ke banda rigima irin taki ina ni ina soyayya da ita? Yayar ki ce fa.” “Hmmm kuma ita ka fara so kafin ni ba.” “Manal kina da tayar da zaune tsaye wallahi, meya kawo batun ita na fara so kuma yanzu?. ni da nake kishi da Huzaifa ki ke ganin laifina kema gashi yanzu kina kishi da Yayar ki.” “Har abada babu aure a tsakanina da Yaya Huzaifa, ko mazan duniya zasu ƙare bazan aure shi ba saboda Yayana ne. Kai kuwa ko yau akace babu Manal zaka iya auren ta domin ba maharramar ka bace, kaga kenan na fika hujja akan kishi da ita.” Ya riƙo ta jikin sa ya ce, “to naji, yanzu dai wannan maganar ta wuce. Kin sani, na sani maganar ta ya riga da ya wuce gabaɗaya.” Ta kalle shi tace, “Ni da Yayana ya riƙe min hannu a gaban ka nunawa kayi kana kishi da hakan, amma kai a gabana ka ke riƙe hannun wacce ba maharramar ka ba.” Da mamaki “Baki ga faɗuwa tazo yi ba? Kenan sai na bari ta faɗi?.” “Ba sai ka jira na taso na riƙe ta ba? Lallai sai ka nuna min ita ka fara so bani ba?.” “Na shiga uku na!. Allah ya baki haƙuri, shikenan?.” Ta kawar da kai bata yi magana ba sai goge ido da take yi ya ce, “na ce ki yi haƙuri ba shikenan ba?.” Ta sauke numfashi ta kawar da kai gefe tace, “taya zan yi haƙuri bayan har yanzu sunan da ka ke faɗa mata daban dana mutane?. Nunawa ka ke har yanzu ita ta musamman ce a wajan ka.” Yayi murmushi ya ce, “in sha Allah na daina cewa Ruman sai Rumana daga yau, shikenan dai ko?.” Kai ta ɗaga yayi dariya yace, “Manali na mai sona.” Tayi dariya itama ya ja hancin ta yace, “rigimar ki bata ƙarewa.” Murmushi take yi tana jikin sa a kwance kafin su tashi suje su kwanta cikin soyayya da shauƙin junan su.             Bayan wasu kwanaki. Komai ya lafa a cikin family, Rumana ta samu lafiya sai abinda ba a rasa ba, ta karɓi ƙaddara dan har gidan Manal din taje sannan kuma taje gidan su Huzaifa da na ƴan uwan su kowa ya ganta aka gaisa kafin ta koma Abuja da zama. Bebi da Manal soyayya akwai suke sha a cikin kwanakin, in ba aiki ne dashi ba baya zuwa ko ina itama kuma a satin aka bata certificate na zaka professional chef. A cikin kwanakin ya takura mata sai ta shiga wata school ɗin ta cigaba da karatu ita kuma tace bata so dan baza tayi jamb ba yace zata fara private university. Ba yadda ta iya haka ya nemar mata makaranta ta ɗora daga inda ta tsaya. Ranar juma'a suka tashi da farin ciki kasancewar ranar da za'a ɗaura auren Maryam da sabon mijin ta Mahmud, inda kuma a ranar aka karɓi kuɗin auren Lubna da ita da saurayin ta Sani. Dukkan su suna gidan saboda farin ciki har Manal tana gidan suna tare dasu Mimi suna hira, har Mama suna falo a zaune gabaɗaya ana hira. A gidan suka wuni har dare kafin kowa ya tafi gida dan ba ranar Maryam zata tare ba. Ɓangaren Maryam farin ciki take yi da sabon auren da tayi, duk da sabon mijin nata bai san da badaƙalar da ta aikata ba amma tana addu'ar Allah yasa bazai sani ba. A ranar da aka ɗaura auren da yamma angon ta yazo ya ɗauke ta suka fita yawo basu dawo ba sai dare sannan ya kawo ta gida ya tafi. Kwana biyu da ɗaurin auren ango shi da amaryar sa soyayya suke yi, a cikin kwana biyu zasu fita baza su dawo ba sai dare. Ranar litinin ya kama ranar Maryam zata tare ƴan gidan gabaɗaya suna nan harda Manal, suna zaune a falon Mama ana hira Bebin  ya shigo da sallama yana amsa waya Mama ta kalle shi tace, "Sarkin amsa waya, kuma a wayar bashi da magana kuma sai ta aiki." Bai zauna ba sai da ya kammala wayar sannan ya zauna yace, "Mummy Hajiya tace nace miki akwai bikin ko ƴar gidan gwaggo wa dai na manta." Mama tace, "jiya tace ka faɗa min ai ka manta sai yanzu?." "Na manta wallahi, sai yanzu na tuna shiyasa ma nazo na faɗa miki kafin na kuma mantawa." Farida ce ta fito tana cewa, "Mama Mun yi magana da likitan ranar laraba zamu je." Ya kalli Farida yace, "wanne likita?." Ta zauna tana cewa, "ina ruwan ka?." Mama tace, "zamu je a kai Mimi ne wajan likitan da zai duba ta."ya kalli Mimi da take gefe yace, "bata da lafiya?." Mama tace, "eh kusan hakan, tana matsalar infertility." "Infertility!" Ya maimaita yana kallon Mimi Mama tace, "eh." "Mummy har yaushe akayi auren da za'a fara jawo mata problem na infertility?." Mama ta harare shi tace, "Kun wuce shekara ɗaya da aure fa, ga Ayan nan har ya fara gane babar sa da baban sa saboda yayi wayo. Ita kuwa ko missing period bata taɓa yi ba, kuma sai mu zauna ba za'a ga likita ba?." Bebi yace, "amma Mummy shekara ɗaya ne fa kawai, ai lokacin bai yi tsahon da za'a fara zancen infertility ba." "Kai baza ka gane ba ai." Yace, "ba sai taje taga likita ba akwai maganin da za'a bata ta sha shima Tahir ɗin ya sha and akwai...." Sai kuma ya fasa faɗar maganar yace, "zan dai duba dai, in likitan zata gani akwai Hamza in kuma bakuwa son na gida akwai wacce zan haɗa ku da ita daga india take zuwa." Mamma tace, "A'a Bebi, na san halin ka kar ka shiririntar da maganar fa." "Bazan manta ba, anjima da daddare zan je asibitin zan kawo mata in sha Allah." "Allah sa a dace." "Amin Mummy. kar ki damu fa, wannan ba abin damuwa bane,  just one year a fara zancen infertility" ya faɗa yana tashi tsaye yana kallon Farida yace, "duk ke kika shirya wannan abun." Farida tayi dariya tace, "tunda taka ta haihu ai haka zaka ce, dole na shirya saboda bana son ƙanwata ta shiga matsalar dangin miji." "Ba wani nan, kema dangin mijin ce ai." Farida tace, "maganar gaskiya ko Manal ɗin ce aka zo yanzu bata haihu ba da muna nan muna cewa anya lafiya." Yayi dariya yace, "to dan an yiwa Mimi ashe babu laifi."Ita dai Manal tana zaune murmushi kawai take yadda suka mayar da ita tamkar ƴar gida yana yi mata daɗi sosai. Kallon Manal yayi suka haɗa ido sai ta ɗauke kanta Farida na kallon sa tace, "wallahi baza ta bika ba, yau tana gidan nan har sai mun kai Maryam." Dariya yayi mai sauti yace, "in nace zamu tafi zaki hana ne?." Mama tayi dariya tace, "ka raina Farida wallahi, kuma har goya ka tayi." Da sauri ya kalli Mama yace, "Haba Mummy, kwata-kwata nawa take da zata goya ni?. To ko Maryam ai bata goya ni ba balle wannan." Farida tace, "duk bala'in ka dai ni Yayar ka ce." Baice komai ba ya fita daga falon yana dariya. Abba dashi da Alhaji Magaji suna zaune yanayin fuskar Abba zaka kalla ka tabbatar yana cikin farin ciki saboda yadda yake murmushi yace, "ai da naji Sani ɗan kane nayi farin ciki sosai, ko babu komai na san inda Lubna zata shiga." Alhaji Magaji yayi murmushi yace, "da yake bana ƙasat aka yi komai, sai bayan komai ya faru nake jin labari ashe Lubnan wajan ka ce." Abba yayi murmushi yace, "itace wallahi." Alhaji Magaji yace, "Wai Lubna ba itace wacce aka yiwa fyaɗe ba?." Abba ya kalle shi yace, "eh itace." "Shi Sanin ya sannan an yi mata fyaɗe ko kuma akuya kuka bashi da farar kura?." Abba yace, "ya sani mana, ai ba a bayar da aure a ɓoye ko?." Alhaji Magaji yace, "kuma sai ya amince?." Abba bai bashi amsa ba ya bishi da kallo yace, "to maganar gaskiya ko shi ya amince ni bazan amince ya aure ta ba, saboda ni da kai kar ta san kar ne, babu abinda baka sani nawa ba babu abinda ban sani naka ba. Ba dan Allah ya kiyaye mu daga aikata luwaɗi ba da baka da abokin aikin ka sai ni. Dan haka auren Lubna da Sani ka mata dashi kawai, domin bazan iya bari ya aure ta ba." Abba a firgice ya kalle shi yace, "me hakan yake nufi?." "Alhaji Mu'azzam Sani bazai auri Lubna ba saboda bazan iya haɗa haɗa zuri'a da kai ba. Bazan iya kallon ka matsayin siriki ba, haka ƴar ka bazan taɓa kallon ta matsayin sirika ba, sannan baza ta iya samun kwanciyar hankali a gidan ɗana ba. Gwara a ƙyale ta in wanda yayi mata fyaɗen ya dawo da niyar auren ta sai ya aure ta kawai a rufawa juna asiri, amma gaskiya ni bazan bawa Sani ita ba." Abba ya kasa magana sai kallo Alhaji Magaji da yake yi ya kasa cewa komai. Alhaji Magaji yace, "Yayar matar Adnan kuma ƴar abokin ka Mubeena ka neme ta, ita kanta matat Adnan ɗin itace yarinyar da na kawo maka nace itace daidai kai ka tuna?, ka tuna yarinyar da muka yi amfani da rashin lafiyar babar ta da dan mu same ta?." Abba ya wara ido waje ƙirjin sa yana up and down Alhaji magani yace, "eh itace, nasan babu lallai ka gane ta saboda matan sun yi maka yawa. To itace, itace yarinyar da ta gudu a lokacin baka yi mata komai ba, kai baka ganr ta ba amma na san ita ta gane ka. Da irin wannan mummunar ɗabi'ar zan haɗa zuri'a da kai?. Inaa...!kawai a cigaba da zama a abokai aamma babu zancen zama sirikai ni da kai." Kallon Abba yayi yaga ya kasa magana yace, "dole ka kasa magana ai, daman abinda nazo na faɗa maka kenan wannan aure bazai yu ba, Allah ya bata wani dan wannan baikon an soke shi" ya faɗa yana miƙewa tsaye ya fito harabar gidan. BDƘB3P40          A can falon Mamy kuwa Maryam ce da angon ta a zaune fuskar sa a ɗaure sosai ita kuma gaban ta sqi faɗuwa yake yi saboda yanayin da ta ganshi a ciki ya bata tsoro. Maryam tace, "kace min zaka zo gida mu yi magana kazo kuma baka ce komai ba." Mahmud ya kalle ta yace, "Meyasa kika ɓoye min kin yi ciki shege na tsohon mijin ki?." Gaban Maryam ya faɗi ta kalle shi tace, "a ina kaji wannan maganar?." "Saboda kina tunanin ba zan sani ba kika ɓoye min? Ashe ke ƴar iska ce mai bin tsohon miji?." Maryam ta yi Shiru ta sauke kai ƙasa tace, "ba yadda ka ke tunani bane wallahi, blackmailing ɗina yayi."  yayi tsaki yace, "koma meye da haɗin kan ki aka yi, iskanci sunan sa iskanci ko mai ƙarancin sa. Kin cuce ni wallahi, kin  cuce ni da har aurena ya hau kan ki. Ban san da cewa ke ɗin karuwa bace ba sai yanzu, ban san da cewa baki da daraja ta mace ba sai yanzu. Nayi dana sanin auren ki, nayi dana sanin haɗa jikina dake." Bebi ne ya shigo falon da sallama da niyar su gaisa da Mamy ganin Mayam da mijin ta sai yayi murmushi ya ƙaraso ya miƙa masa hannu alamun su gaisa  yace, "A'a Mahmud, barka da wannan lokaci Ango, ba dai kazo ɗauke matar ka ba." Musabaha suka yi ya kalli Maryam da take kuka ya kalle shi kamar zai magana sai yaga ba hurumin sa bane. Ya juya da niyar fita Mahmud yace, "na saki maryam saki biyu, na sake ta saki ɗaya, saki uku kenan. Aurena da aka ɗaura da ita ranar juma'a na warware shi a yanzu." Gaban Bebi ya faɗi sosai ya juyo da sauri yana kallon sa Mahmud yace, "eh na sake ta, bazan iya zama da karuwa wacce tayi ciki tare da tsoron mijin ta ba, zan nemana yarana uwa ta gari ba irin ta ba. Shiyasa na sake ta a gaban ka domin ka zaka shaida, ni ba irin mijin da zai aure ta bane, domin ko na aure ta baza ta fasa bin tsohon mijin ta ba, dan haka taje ta cigaba da mu'alama da mijin ta ni na sake ta saki uku!." Bebi kallon sa yake yi rai a ɓace matuƙa zai yi magana Mahmud ya miƙe tsaye yace, "ba sai nace komai ba, har labarin yadda ka hanata sauraren sa naji, amma da yake bata da hankali bata mutunci bata san mutunci ba, da yake ta saka neman maza a gaba..." Bebi ban san ya ɗauke shi da mari ba sai hannun sa da ya gani ya chakume wuyan sa yace, "ka sake ta kece ko? To ka fita ka bani waje kar na sake jin wata magana mara daɗi a kanta, in kuma ba haka ba wallahi sai na fasa maka baki." Mahmud yace, "kut ni ka mara Adnan?." Bebi yace, "na mare ka, in kana ganin zaka rama gani gaka, kuma in ka sake faɗar wata magana a kanta wallahi sai na cire maka haƙori." Sakin sa Bebi yayi Mahmud yayi hanyar fita yace, "ko me zaka yi dai kayi, ni ba zan zauna da karuwa ba mai neman tsohon mijin ta." Da zafin nama ya biyo bayan sa lokacin yaje harabar gidan ya riƙe kwalar sa ya sake tsinke shi da mari. Mahmud shima bai ƙyale shi ba ya kai masa duka ya same shi a gefen fuskar sa. A lokacin Alhaji Magaji yana niyar shiga mota yaga abinda yake faruwa, kafin kace wani abu duk mutanen gidan sun fito har Abba ya fito wajan ana riƙe Bebi.  Mahmud ya kalle shi yace, "in ka sake ɗaga hannu ka taɓa jikina  zaka yi dana sani Adnan." Bebi ya tankaɗa shi ya nuna amsa gaye yace, "fita ka bani waje, kar na sake ganin fuskar ka har abada." "Bazan fita ba, gwara da kowa ya fito ku shaida na saki Maryam saki uku, domin bazan zauna da karuwa wacce ta gama lalacewa da tsoron mijin ta ba, nj ba lusarin namiji bane domin uwa ta gari nake son nemana yarana, matata da ta rasu ta kirki ce bazan ɗauko ta banza na kai gidana ba. Na sake ta na sake maimaitawa kowa yana ji, bazan iya haɗa zuri'a da mutanen gidan nan ba domin dukkan ku a lalace ku ke. Hakan kuma ya samo asali ne daga shi shugaban gidan, duk a wajan sa kuka yi gado." Bebi ya zabura zai yi wajan sa Alhaji Magaji ya riƙe shi yace, "ƙyale shi Adnan, ai gaskiya yake faɗa ba ƙarya yayi ba, kuma an rufe shi da tun farko sai a faɗa masa wacece wacce za'a wanke a kai masa da duk hakan bata faru ba. Nima yanzu na waraware baikon da aka yiwa Sani da Lubna, domin ba zai auri wacce aka lalata ba, kuma bazai iya haɗa zuri'a da mahaifin ku ba." Bebi kallon sa yake yi da matuƙar mamaki kafin yace wani abu Alhaji Magaji yace, "kai Mahmud ka hau motar ka kayi tafiyar ka, dan ka sake ta ai ba komai bane nima na warware baikon ƴar sa da ɗa na" ya faɗa yana ƙarasawa ya shiga mota Shima Mahmud ya shiga motar sa suka fita daga gidan. "Abbaaaaa!" Mimi ta faɗa da ƙarfin hakan ya saka suka juya suka ga Abba a kwance a wajan a sume. Hankalin mutanen gidan ya tashi da taimakon mai gadi a saka Abba a mota Bebi ya ja motar da ƙarfi ya fita zuwa asibiti hankalin sa a tashe sosai. Taimakon na musamman aka bawa Abba sai dai an tabbatar da jinin sa ya hau sosai har lokacin kuma baya hankalin sa. An samu ya farfaɗo daga suman da yayi a lokaci. Amma bai buɗe ido ba ba kuma ba’a tunanin zai buɗe ido a kurkusa. Hankalin iyalan gidan ya kai ƙarshe wajan tashi, ga fasa auren Lubna da akayi ga sakin da aka yiwa Maryam gabaɗaya hankalin su baya jikin su duk sun ruɗe gabaɗayan su. Haka suka kwana a wannan a cikin ruɗani washe gari da safe asibitin ya cika da iyalan gidan amma Abba bai farka ba a haka aka kwash kwana uku. A ranar da Abba ya kwana biyar a a asibiti a ranar ya buɗe ido, a lokacin Bebi yana tsaye a kusa dashi ganin ya buɗe ido sai yayi hamdala ga Allah ya kalle shi yace, "Abba sannu, ya jikin naka?." Kallon sa Abba yake yi ya mayar da ido ya kulle ya sake buɗewa ya kalle shi amma bai ce komai ba. Jinin sa Bebi yake dubawa ganin har lokacin bai sauka ya sake ɗauko ruwa ya sakawa Abban ba jimawa ya sake yin bacci. Awa ɗaya ya samu yana bacci ya farka a lokacin ma Bebin ne kawai a zaune a ɗaƙin, ciwon kai an damun Abba amma a haka ya riƙo hannun Bebi yaji zafi sosai ya kalli Bebi idanun sa da suka yi yarrrrr sun juye sun kuma yi ja yace, "kar ka taɓa kuskuren aikata zina a rayuwar ka, in ba haka ba ta zata dinga bibiyar ka har yaran ka da jikokin ka. Ita nake ganina yanzu shiyasa nake baka shawarar ka faɗawa ƴan uwan ka” Abba ya faɗa murya na shaƙewa numfashin sa na ƙoƙarin barin jikin sa. Gaban sa ya faɗi sosai, ya riƙe hannun Abban yace, "Abba ka daina magana don Allah, ka kwantar da hankalin ka a samu jinin ka ya sauka. Wannan tunanin da ka ke yi shine ya saka jinin ka yaƙi yayi ƙasa, ka yi haƙuri." Abba ya girgiza kai yana runtse idanun sa yace, "illar zina nake gani, kar ka yi wannan kurkuren Adnan. Ka bawa Lubna haƙuri, ka basa Maryam haƙuri duk ni na jawo musu" tarin da yake yi ne yayi yawa harda jini, cikin ihuuu Adnan yayi magana wanda yasa ƴan gidan su da suke waje sun ji, suna zaunen dai ga likitoci biyu sun shiga a guje sai hankalin su ya sake tashi. Duk yadda aka so ayi wajan ceto ran Abba abin yaci tura, Abba dai rai yayi halin sa a daidai wannan lokacin Alalh ya karɓi kayan sa. Dr da yake duba shi bayan ya tabbatar da rasuwar sa ya kalli Adnan ya sauke ajiyar zuciya yace, "i’m sorry Dr, Allah ya karɓi kayan sa." "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!!" Ya furta cikin gigicewa tare da zama a kan kuskure ya kulle idanun sa kawai ya fara hawaye. Dr ganin haka sai ya zauna a gefen sa yace, "kayi haƙuri ka daure, in kana hawaye su kuma uwan ka ƴan kenan?, ka yi haƙuri ka yi masa addu’a Allah ya bashi ikon amsa tambayar kabri.” Ya kasa koda motsin kallon Abba yake daga kwance an kulle masa fuska ya tashi ya ƙarasa inda yake ya riƙe hannun sa ya ɗora a fuskar sa yana kuka sosai. Duk yadda likitan yaso rarrashin Adnan abin yaci tura, yafi mintina ashirin yana kuka kafin ya iya daurewa ya goge idanun sa ya kalli tagar ɗakin ya hamgo ƴan uwan sa dukkan su suna tsaye alamun jiran fitowar su suke. Ya kulle idon sa cikin zafi da raɗaɗin mutuwa ya jingina da bango yana kallon Abba, gani yake kamar wasa ake masa Abba bai rasu ba yana nan da ran sa. Daurewa yayi ya ɗauki waya ya kira Yayan sa yana ɗauka yace, "Yaya Abba ya rasu." Abinda yace kenan ya kashe wayar dan bazai iya fita ba. Yaya yayi ta maza ya daure ya kalle su da kowa shi yake kallo yace, "hayaniya tayi yawa, Bebi yace ku koma gida dukkan ku yanzu ba'a son hayaniya." Mamy da take kallon yanayin sa tace, "kar ka yi mana ƙarya, ka faɗa mana abinda ya faru fuskar ka ba haka ta nuna ba. Abba ya rasu ne?." Ya sauke ajiyar zuciya ya buɗe ido a kansu yace, "Allah ya karɓi rayuwar Abba." Gabaɗaya su suka haɗa baki akayi salati ana fara koke-koke a wajan daƙyar aka lallaɓa su suka tafi gida sunkuma suka taso da gawar Abba. Bayan anyi sallar la'asar aka yiwa Abban suttura aka tafi kai shi gidan sa na gajiya gaskiya. Gidan da yake jira kowa, gidan da babu mai shigar maka sai dai ka shiga, gidan da abinda ka aikata yake jiran zuwan ka, gidan da mala'ikun Allah ke jiran zuwan ka, gidan da tun kafin kaje masu tarbar ka suna jiran ka, gidan da za'a saka maka ƙasa a saman kanka ta rufe ka, gidan da babu hasken fitili sai hasken aikin ka, gidan da za’a yi maka tambaya akan ubangijin ka, gidan da sai ka amsa wannan tambayar zaka samu haske a cikin sa, gidan da babu fanka balle ac a cikin sa, gidan da babu taga balle kaji iska, gidan da bashi da faɗi balle kayi kwanciyar yadda ka ke so, gidan da alkur'ani ne zai kawo maka ziyara ku yi hirar ka in kana karanta shi, gidan da sallolin ka zasu kawo maka ziyara in aka aikata au da kyau. Ya Allah ka sa mu dace, ka sa mu yi kyakykyawan ƙarshe amin. Duk wani masoyin su ya tauaysawa iyalan gidan saboda rasa bangon gidan da akayi, mutuwar ta zamar musu tamkar ba a taɓa yi ba duk da Yayan Farida ya taɓa rasuwa amma gidan ya zama kamar ba'a taɓa yi musu mutuwa ba. Har akayi kwana uku da rasuwar Abba kuka suke yi, Daddy ya dawo dashi ake karɓar gaisuwa, mayan mutane suna ta kawo ziyara ba zaka ce gidan rasuwa bane saboda yadda ake cika shi. Sai da akayi kwana bakwai sannan kowa ya watse babu kowa sai iyalan gidan kawai. Maryam tafi kowa shiga tashin hankalina bayyane saboda tana ganin ta silar ta abba ya bar duniya, kullum a kuka take da tashin hankali ko fitowa bata yi. A ranar da ya kwana takwas da rasuwa ta suka tara ƴan uwan şu mata da maza aka fara zancen raba gado dan a sauke masa nauyi da wuri, a nan Adnaan yake sanar dasu wasiyyar da yace ya faɗa musu nan da nan waje ya sake dawo ɗanye, mutuwa ta dawo zabuwa fil kamar a lokacin aka yi ta. A hankali mutuwar ta fara bin jikin su kowa ya fara warewa ana cigaba da harkoki tunda wanda ya rasu dai bazai dawo ba ya tafi kenan. A ranar lahadi da yamma wanda a lokacin satin Abba uku da barin duniya Bebi ya fito daga wajan Mama yaji Lubna tana kiran sunan sa ya tsaya yana kallon ta ta ƙaraso kusa dashi tace, "Yaya daman akwai abinda nake so na faɗa maka." Ya gyara tsayuwar sa yace, "ina jin ki." Ta sauke ajiyar zuciya tace, "tun kafin rasuwar Abba ake yi min message da wata number amm bana bayar da amsa, shine yay aka kira ni da na ɗauka sai naji wanda yake min wayar na san shi." Bebi ya kalle ta yace, "waye?." "Yaya Mujahid ne!." BDƘB3P41 Da mamaki yake kallon Lubna yace, "Mujahid fa kika ce? Shine yake yi miki waya?." Lubna ta ɗaga kai tace, "shine Yaya, da ake yi min messages ban san shi bane zai da ya kira ni sannan na gane muryar sa." Bebi ya girgiza kai ya kalli wani wajan daban ya sake kallon ta yace, "kin tabbatar shine yake yi miki waya?." "Shine wallahi" ta kalli wayar ta sannan tace, "kaga ma number ce take kirana." "Ɗauki ki saka naji" ya faɗa yana kallon ta. Ta ɗauki wayar ta saka a speaker daga can ɓangaren yace, "Lubna don Allah ki saurare ni, magana nake so mu yi dake ta fahimta, Wallahi nayi nadamar abinda na yi..." Kit ya datse wayar ya miƙa mata wayar ya ce, "Kar ki sake ɗauka in ya kira ki, sannan duk inda zaki je ki tabbatar na dani dan zai fara bibiyar ki ne, in kika ganshi a wani waje ki sanar dani." Lubna ta amsa da to ta juya ta koma ciki shi kuma ya shiga mota ya tafi gida. Yana shiga ya tarar da Manal ta yi girki mai kyau tana yiwa abincin hoto kamar yadda ta saba yi. Ganin sa sai tace, "Partner barka da zuwa." Ya kalle ta ya ce, "barkan ki my chef." Tayi dariya ta rufe abincin tana kallon ta ƙaraso inda yake tace, "wai meye sirrin ne?, naga kana yin kyau kwana biyu.” Yayi ƴar dariya ya ce, "wanda ya rasa mahaifin sa ina shi ina yin kyau Manal?, kar ki manta Abba bai yi wata ɗaya da rasuwa ba.” “Na sani, kuma in sha Allah Abba yana aljanna.” Ya sauke numfashi yace, “Allah ya tabbatar da hakan.” Amin. Amma ni dai naga kayi kyau sosai." Ya zauna yana ɗaukar Ayan da yake cikin gadon sa yace, "kema kin yi kyau din ai." Ta zauna a kusa dashi tace, "na kawo maka abinci yanzu?." Ya girgiza kai yace, "bara mu yi magriba naci, yanzu bana jin yunwa." Kallon Ayan yake yi yana wasa da kumatun sa ta kalle shi cikin tausayawa. Rasuwar Abba ta taɓa shi sosai, tun a farkon rasuwar zaka tabbatar da rashin Abba ya shige shi, haka zai shiga ɗaki ya kulle kansa yayi kuka ya gode Allah sannan ya fito. Addu’a da sadaka kullum cikin yiwa Abba yake yi, daga rasuwar Abba zuwa yanzu bohol biyar ya saka aka haƙa a ƙauyukan da basu da ruwa da niyar Allah ya kai ladan kabarin Abba. Dukkan su ƴan gidan sun yi haɗin guiwa ana gina babbar islamiyya da za’a dinga yin karatu da komai kyauta da niyar Allah ya kaiwa Abba ladan kabarin sa. Adnan yana jin ɗacin rasa mahaifin sa a ko yaushe, daga baya ne abin ya lafa har ma yake iya dannewa. A tausashe tace, "Partner na so da kai Ayan yake kama ba dani ba." Ya kalle ta ya ce, "da yayi kama dake baki ga yadda yake da farin jini ba? da dani yake kama baza’a dinga ɗaukar sa ba.” Ta turo baki tace, "ni kai nake so yayi kama dashi." Yayi dariya kawai baice komai ba dan bai san abinda zai ce ba. In ya biyewa surutun ta baza ta bar shi yayi shiru ba. Ta sake kallon sa tace, "Gobe ina so zanje gida muna ta shirin bikin Yaya." Ya girgiza kai ya ce, "Allah ya nuna mana goben. Nima ɗazu Huzaifa yake min maganar nace ni zan faɗa masa ko shi ne zai faɗa min?." Tayi dariya tace, "gaskiya dai kai zaka faɗa masa." Ya kalle ta ta gefen ido ya ce, "bana son munafurci." Tayi dariya tana kallon sa yana murmushi ya kalle ta kafin ya saukar da ƙwayar idon sa ƙasa yana kallon ta ya ce, "wai yau kallon nan da ake yi min na meye ne?, Matso kusa dani ki faɗa min kallon na meye." Manal ta sake yin dariya ta matsa kusa dashi kamar yadda yace ya kalle ta ya ce, "ina jin ki, kallon daga ina yake haka? me za’a bani ake kallona?." Ta sake yin murmushi tace, "kawai ji nake yau na naita kallon ka har sai na gaji." Yayi murmushi ya ce, "to ki fara mana, ki ta kallona har sai kin gaji ɗin." Murmushi tayi tace, “ai bazan gaji da kallon ka ba, kana da kyaun da idanuna baza su gaji da ganin ka ba” ta faɗa tana shafa fuskar sa wacce take ɗauke da murmushin da yake masa kyau in yayi. Ya yi hannun nata kiss ya ce, “duk kyauna ban ka ki ba, ke ce baza’a gaji da kallo bani ba. Kefa ko babu kaya a jikin ki kyau ki ke yi, ni kuwa bama kya iya kallon nawa balle ki ga kyaun.” Fuska ta ɓoye a jikin sa yayi ƴar dariya itama dariyar take yi yace, “ko ba haka bane? Tsakanin ki da Allah kin taɓa ƙare min kallo ko sau ɗaya?.” Manal tace, “sau nawa kuma.” “A’a ƴan mata, baki taɓa ba.” Dariya ta sake yi tace, “Allah kunya ka ke bani.” “Aikin kenan.” Dariya kawai tayi bata ce komai ba ya riƙe hannun ta ta kalle shi taga Ayan yake kallo sai tayi shiru bata ce masa komai ba. A kafaɗar sa ta kwanta haka kawai take jin farin ciki a zuciyar ta, in ta kalle shi sai taji daɗi sosai tana godewa Allah da ya bata shi a matsayin mijin ta. "Partner zaka iya yi min kishiya?." Dariya ta bashi sosai ya dara yana girgiza kai ya ce, "kawai kice min duk wannan kallon tambayar da kike so ki yi min kenan, daman ni na san akwai wani abu a can ƙasa." Manal tace, "A'a wallahi, kawai tambayar ce tazo raina. Zaka iya haɗa ni da wata mace a duniya?." "To yanzu me ya kawo wannan batu na ƙarin aure? Shekarar mu ɗaya da kwanaki da aure, wani abun kika gani da yake nuna miki zan iya ƙara aure ko ya ya?." Tayi murmushi ta ɗago tana kallon sa tace, "Allah ba haka bane, kawai ina so na ji." Ya taɓe baki yace, "to ni ban san me zance miki ba, ki adana tambayar ki zan amsa miki wani lokacin." Wayar sa ce tayi ƙara sai ya tashi ya ajjiye Ayan a gadon sa ya ɗauki wayar yana daga tsaye kafin ya kashe ya kalle ta yace, "Zan je nayi sallah daga nan zan je wajan Daddy, sai zuwa bayan i'sha dai zan dawo." Ta ɗaga masa kai tana kallon idanun sa ya dawo kusa da ita ya manna nata kiss a goshi yace, "naga alama yau babu baccin dare ko?" Ya faɗa yana ɗaga mata gira yana dariya itama dariya ta tayi ya fita. Kafin ya dawo tayi wanka dan da gaske soyayya take ji da ita ranar ta shirya cikin shigar da yake atampa ɗinkin riga da siket, siket din street mai tsaga ta baya, tsagar mai tsaho dan duk digagin ta a waje yake, rigar ƴar ƙarama bata da wani tsaho hakan ya bawa halittar ta damar bayyana a cikin kayan sosai.Abincin ta jera masa a dining da lemon da ta haɗa masa ta bar falon ta shiga ciki. Ba jimawa ta jiyo tsayuwar motar sa alamun ya dawo. Shi kuwa shida Huzaifa ne suka haɗa a ƙofar gida shima yazo gidan sai suka shigo tare. Sai bayan sun shiga falon Huzaifa yake kallon falon yace, "gaskiya ka samu ƙanwata a ɓagas, ka duba falonnan kamar yanzu aka gama yi masa fenti. Ina jin haushi wallahi, naso ace na wahalar da kai kafin na bana ita wallahi." Ya kalle shi gace, "yanzu ma sai ka kwace ta ai" ya faɗa yana ƙarasa wajan dining ya zuba abinci a plate ya dawo ya zauna. Huzaifa yace, "baza ka yi min bismillah ba?." "Ba gidan ƙanwar ka bane?." Jin hakan sai yayi dariya kawai ya tashi yaje ya zuba kamar yadda Adnan ɗin yayi ya taho da ruwa ya zauna yana ci. Adnan ya kalle shi yace, “tsabar rashin kunya wai Yaya ne yake zuwa gidan ƙanwa har yaci abinci, anyi asara.” Huzaifa yayi dariya yace, “kaga malam kar ka saka na ƙware, in kai kana ganin hakan ba daidai bane a wajena daidai ne.” “Sai kai tayi ai.” Huzaifa yayi masa banza ya cigaba da cin abincin sa. A lokacin Manal ta shigo falon tana cewa, "to wai me zan maka ne? Sai kuka ka ke yi?" Ta faɗa tana kallon Ayan da yake hannun ta. Dukkan su kallon ta suka yi jin ta fito tana magana. Bebi ya tsaya cak da cin abincin ganin yadda tayi kyau sosai cikin atampar da ta saka, tayi ɗaurin ɗankwali wanda ake turo shi gaban goshi, tayi ado da gashi ta baya fuskar ta dai ƙyalli take gashi ta zagaye laɓɓan ta da lips gloss. Ganin Huzaifa a zaune sai tace, "lah Yaya yaushe kazo?." Murmushi yake yana kallon ta yace, "ina nan ina cin girkin ki." Tayi murmushi ta ƙaraso ta zauna tace, "naji dawowar ka amma ban ɗauka tare ku ke ba" ta kalli Bebi suka haɗa ido sai ya ɗauke kansa ya cigaba da cin abincin sa. Huzaifa yace, "bani Ayan ɗin" ta tashi ta yi ta miƙa masa shi ya karɓe shi ta dawo ta zauna Huzaifa yace, "yanzu nake cewa mijin ki ya samu garaɓasa da ya same ki, gaskiya kina ƙoƙarin gyaran gidan nan sosai. Gida kamar yau aka yi shi?." Tayi dariya tace, "aikin ai babu yawa yaya, duk da akwai mai taimaka min." "Gaskiya kina ƙoƙari sosai, ga abinci mai daɗi." Tayi dariya tace, "Ina Anty? Kwana biyu bamu yi waya ba, jira nake kawai ace ta sauka." Huzaifa yace, "ana nan ja dai, ɗazu ma Mama ta kira ni take cewa bata haihu ba nace zata haihu basu sani ba ne?." Manal tace, "Allah ya raba su lafiya." Ya amsa da amin. Huzaifa ya ajjiye abincin da yake ci yace, "hanya ce ta biyo dani na shigo mu gaisa, da alama mijin ki yaji haushin zuwan sai harara ta yake ko magana ma yaƙi yi." Ta kalli Adnan da kamar ma bai san suna nan ba abincin sa yake ci hankali kwance. Manal tace, "Haba shima zai ji daɗin ganin Yayan matar sa.” Huzaifa yayi dariyar shaƙiyanci yace, “dan rashin kunya kuma ko gaishe ni bai yi ba, abincin ma da kaina na zuba.” Manal tayi dariya tace, “ahh gaskiya bai kyauta ba.” “Ƙyale shi, baya neman albarka ta ne. Amma zan nuna masa ikon da nake dashi akan ki.” Manal murmushi take yi dan ta fahimci tsokanar sa yake yi tace, “Na gode sosai Yaya, Yaya Mubeena ma ɗazu tace min ai kaje ka gaida Mama." "Naje jiya mun gaisa an kuma duba blood sugar ta, har ta bani wani dambun kaza mai shegen daɗi." Manal tayi dariya Huzaifa ya tashi ya zo har inda take zaune ya bata Ayan sannan ya kalli Adnan yace, "Bebi zan wuce." Ya kalle shi baice komai ba Huzaifa yayi dariya ya kalli Manal yace, "ƙanwata assalamu alaiki" ya faɗa yana miƙa mata hannu alamun su gaisa. Manal ba tare da tunanin komai ba ta saka hannun ta a cikin nasa suka gaisa tana dariya tace, "a gaishe Anty." Ya zare hannun sa yana cewa, "zata ji. kin san Daddy yace min zuwa jibi zai zo, Ayra mutuniyar ki sai murna take tace a gidan nan zata zauna." Manal tace, "kuma ɗazu mun gaisa dashi amma bai faɗa min ba. ina nan ina jiran Ayra aminiya ta." “Wallahi kuwa sun kuwa zuwa saboda bikin Mubeena." Magana yake yana tafiya tana bin bayan sa suna hira har yaje bakin ƙofar falon sannan yayi mata sallama ya fita. Tana juyowa taga baya falon ga abincin da ya gama ci ban ya bar kayan a wajan ya kuma tafi da Ayan. Kayan ta kwashe ta shiga ciki ta ajjiye ta fito taga abincin ya ƙare tayi hamdala dan bata son yayi ragowa shiyasa take yin kaɗan. Ruwan cucumber da apple ɗin da ta saba tasha ta zuba a kofi mai ɗan girma ta fito tana sha ta shiga inda yake cikin son burge shi da shigar da tayi saboda shi. BDƘB3P42 A zaune ta hango shi ta ƙarasa ta zauna a kusa dashi tana shan ruwan lemon. Kafin ta yi magana ya kalle ta ya ce, "Meyasa kike yi min abinda bana so ne? Sai raina ya ɓaci nayi fushi kuma kizo kina complain akan na cika yawan fushi da sauran su. Meyasa bakya gujewa abinda zai saka zuciyata a ciki. fushin?." Manal ta kalle shi da mamaki ta haɗɗiye abinda yake bakin ta tace, "me nayi?." Ya kalle ta yace, "baki san ma abinda kika yi min ba kenan?." Ta kalle shi tace, "to naga a yadda muka rabu da zaka fita, ta ya ya zan san abinda nayi maka." Ya girgiza kai ya ce, "da kika fito kika ganni da Huzaifa meyasa baza ki dawo ki saka mayafi ba? Kika zauna a gaban sa da wannan shigar a jikin ki har da zuwa kusa dashi ki bashi Ayan. Sannan dan tsabar wulaƙanci harda wani gaisawa dashi ko?." Mamaki ya bawa Manal ta ajjiye glass cup ɗin hannun ta tana kallon sa tace, "Partner ka manta waye shi a wajena ne? Yayana ne fa na jini." "Na sani ai. Amma na faɗa miki har yanzu ba kallon Yayan ki nake yi masa ba, kallon abokina Huzaifa nake masa ba wanda ku ke uba ɗaya dashi ba, zafin abin nake ji a raina amma kin kasa ganewa” Ya faɗa yana kallon ta fuskar sa a ɗaure. Manal tayi murmushi tace, "to ni naga hakan ba komai bane, ko rungume ni yayi babu zunubin da Allah zai rubuta mana.” “Oh haka ne ko? Yayi kyau.” Manal tayi dariya tace, “Ni kallon Yayana nake masa, kuma kaga muharramina ne harda shi a cikin wanda Allah ya lissafa su ga kwalliyata. Dan ya ganni da wannan shigar ba komai bane, ko mutuwa nayi zai iya yi min wankan gawa, kai ko ban mutun ba ko da raina in akwai lalura zai iya ganin tsaraici na.” Yayi ƙaramin tsaki baice mata komai ba yana runtse ido, ya san abinda tace gaskiya ne amma kishi bazai bar shi ya amince ba. Fata yake a xuciyar sa kar Allah ya kawo ranar da Huzaifa zai ga ko da gashin kanta ne balle tsaraici. Tayi dariya ta matsa kusa dashi sosai tace, "haba my life partner, kishi ka ke da Yayana kenan?." Ya kalle ta yace, "eh wallahi! har yanzu bana kallon Huzaifa matsayin Yayan ki kallon abokina nake masa, ina mantawa dashi yayan ki ne indai ba maganar aka yi ba, shiyasa nake jin babu daɗi a zuciyata. Shi kuma da gangan yake yin wasu abubuwa duk dan naji haushi." Tayi dariya ta ɗora kanta a kafadar ta tace, "mijina mai ƙauna ta a ko yaushe. Kayi haƙuri ka dinga kallon sa matsayin Yayana don Allah, ka daina jin haushi kaga daman abinda yake so kenan kuma gashi kaji haushin.” Ya kalle ta baice komai ba tayi masa kiss a kumatu tace, "ko kace nayi kyau duk kwalliyar nan saboda kai nayi " ta faɗa tana tashi tsaye ta tsaya a gaban sa. Ƙin kallon ta yayi ta saka hannu ta ɗago da kansa sai ya kulle idon tace, "don Allah ka kalle ni." Bai buɗe idon ba ta dauke Ayan daga cinyar sa ta ajjiye shi a gefen ta maye gurbin Ayan ɗin a jikin sa ta riƙe wuyan sa tace, "baza kace nayi kyau ba?." Banza yayi mata bai ce komai ba amma a zuciyar sa ya yaba da kwalliyar ta sosai dan tayi kyau ɗin kawai haushi yake ji da Huzaifa yaga kwalliyar ta. Kallon fuskar sa take idon sa a kulle tana murmushi a hankali ta kai bakin ta kan nasa ta fara kissing Buɗe ido yayi suka haɗa ido ya sake mayar da idon sa ya lumshe sai ta daina abinda take yi ta haɗa goshin sa da nata tace, "mijina mai kishi da yayana." Kallon ta yake yi shima yayi murmushi kaɗan baice komai ba. Tashi tayi daga jikin sa lafin ta gama miƙewa ya dawo da ita jikin sa ya zagaya hannun sa bayan ta ya ɗora hancin sa wuyan ta yana shaƙar ƙhamshin ta mai daɗi da sanyi wanda baya cutar da halittar sa. Shiru yayi a haka baice komai ba tana jikin sa a zaune. Ayan ne ya fara kuka hakan ya saka shi ya buɗe ido itama shi take kallo ta kalli Ayan sai ta tashi daga jikin sa ta zauna a kusa dashi ta ɗauki Ayan ta ɗora shi a kan cinyar ta. Tashi yayi ya bar falon ita kuma ta fara shayar dashi. Ya ɗan jima kafin ya dawo ya samu har ta cire shi daga nonon ya kalle ta ya ce, "dole ya dinga yawan kuka bakya tsayawa ki bashi yadda ya kamata, da kin fara sai ki cire kamar naki." Ta kalle shi tace, "to da na waye?." "Saboda ki shayar dashi Allah ya yi shi a jikin ki ba don kwalliyar ko dan ado ba, ko dan.." ya faɗa yana kallon ta itama shi take kallo tace, "cigaba mana, ko don me?." Samun kasan yayi da murmushi mai sauti harda shafa fuskar sa ya kalle ta kawai suka yi dariya a tare. Ya tsagaita dariyar ya ce, "wait! dariyar me kike yi?." Tace, "kaima dariyar me ka ke yi?." "Ina da dalilin dariya ta." "Nima ina dashi." Ya matso ya kalli Ayan ɗin ya ce, "har yayi bacci kenan, sai na anjima kuma in ya farka." "Wannan a rubuce yake" ta faɗa tana tashi tsaye ya karɓe shi a hannun ta ya wuce ya kai shi ɗakin sa bai ce komai ba. Ɗakin ta ta shiga ta cire ɗankwali ta ajjiye kenan ya shigo ya kalle ta yace, "au kwalliyar da ban gani ba zaki cire?." Ta kalle shi cikin shagwaɓa tace, "to ba ka ƙi cewa nayi kyau ba." "Ba Yayan ki kika nunawa kwalliyar ba?.” Tayi murmushi ya ce, “Allah Manal har yanzu zuciyata bata kallo Huzaifa matsayin yayan ki, abokina Huzaifa a haka nake kallon sa. Kishi nake yi dashi sosai, a duk sanda ku ka haɗu naga kina yi masa murmushi zuciyata bugawa take yi.” Tayi murmushi ta zagaya da hannun ta ta riƙe kugun sa tace, "to yanzu so ka ke kace min har yanzu sharaɗin ka akan sa yana nan?." "Da hakan zai faru da naji daɗi." "Inaaa! kaima kasan wasa ka ke Partner. Sharaɗin ka akan Huzaifa ne, wannan kuma Yaya Huzaifa ne Yayana na jini." Ya taɓe baki yace, "to naji ya zan yi?." Ya faɗa yana kallon ta. Ta taɓe baki tana ɗage gira sama. Sakin sa tayi ta taka zuwa wajan madubin ɗakin ya bita da kallo yace, "kin yi kyau sosai, kayan nan sun miki kyau." Tayi murmushi ta juyo ta kalle shi tace, "na gode mijina." "Daman kin zama ƴar lukuta shiyasa komai ya fito a kayan, kin yi caras dake ƴan mata." Manal tace, "ni bana ganin ƙibar nan da kake faɗa." "Ai kam kin yi ƙiba, har mamaki nake saboda nasan ciwon ku baya bari kina ƙiba amma ke gashi kin yi." Tayi dariya kawai bata ce komai ba yace, "abincin ɗazu yayi daɗi sosai, in akwai saura a ajjiye min gobe naci." Da sauri ta kalle shi ya wara idanu yace, "eh a ajjiye min zan ci." Tayi dariya tace, "kai da kanka zaka ci abincin da ya kwana kuma?, Ka manta baka maimaici ne?.” "Gori za’a yi min kenan?." "A'a ni na isa." "To ayi abinda nace." "Wallahi babu ko kaɗan." Ya ɗan yi tsaki ya kalle ta tana dariya yace, "to tsayuwar me kike yi wai? Muje a faɗa min kallon da ake yi min yau na meye." Manal tace, "to jirani na cire kayan nan sun ishe ni." "Ko kin saka wani suma cire su zaki ki, zo muje bana son iyayi" ya faɗa yana jan hannun ta suka fita daga ɗakin.      Washe gari. Bai fita ba sai sha ɗaya na safe shima dan yana da abin yi ne da babu abinda zai fitar dashi a wajan mtae sa zai zauna su kwashi roman soyayya. Asibiti yaje lokacin da yaje Huzaifa da Hamza babu kowa dan haka bai bi ta kansu ba aikin sa yake yi. Yana zaune a cikin office bayan sallar azahar Huzaifa ya shigo yana cewa, "Mijin ƙanwata ashe kazo." Ɗago ido yayi ya kalle shi Huzaifa yayi dariya yace, "kana ji, Hamza baya jin daɗi yana kwance a gida in mun tashi sai mu biya mu duba shi ko?." Bebi yace, "Allah ya nuna mana lokacin." Ya amsa da amin ya kalle shi yace, "baka zo da wuri ba shiyasa na ɗauka ma baza ka zo ba, har zan kira ka sai aka ce min kazo.” "Ban yi niyar fitowar bane bama wallahi, kawai dole ce ta fito dani. Dr Fulani yana nan?a kwai file ɗin da nake so a kai masa."  Huzaifa yace, "tunda ya fita bai dawo ba gaskiya." "Okay" ya masa a taƙaice yana ɗaukar wayar sa. Knocking ɗin ƙofar aka yi Huzaifa ya amsa aka buɗe aka shigo. A tare suka kalli wanda ya shigo Huzaifa ya kalli Bebi shima ya kalle shi ya sake kallon wanda ya shigo har ya mayar da ƙofar ya rufe ya tako a hankali cikin office ɗin. "Mujahid!" Huzaifa ya faɗa da mamaki yana kallon sa. Mujahid ya miƙa masa hannu alamun su gaisa, bai bashi hannun ba ganin hakan Mujahid sai ya janye hannun sa daga gaban Huzaifa ya miƙawa Bebi hannu, Bebi ya harari hannun nasa yace, "wato kaga ka aikatawa ƙanwata laifi na barka ka cigaba da yawo a duniya ban kai ka prison ba shine ka samu damar zuwa inda nake?." Mujahid ya sauke ajiyar zuciya yace, "Adnan ya haƙurin rashin Abba da muka yi?. Allah ya jiƙan sa ya gafarta masa.” A laɓɓan Bebi zaka san ya ce amin Mujahid yace, Adnan don Allah kayi haƙuri, na ssn na ɓata maka rai akan ƙudurina na banza da wofi, don girman Allah kayi haƙuri ka yafe min abinda nayi maka. Nayi nadamar abinda na aikatawa Lubna wallahi, tunda na bat wajan ta bani da kwnaciyar hankali har yau, don Allah kayi haƙuri ka saurare ni." "Haƙuri ka ɗin banza da wofi, kai har kana da zarrar da zaka zo gabana kana cewa nayi haƙuri? Ka manta abinda ka yiwa ƙanwata ne?." "Ban manta ba, rashin mantawar shine ya kawo ni yanzu gare ka. Don Allah don Annabi ka yi haƙuri ka yafe min, nayi nadamar abinda na aikata mata, nadamar da na yi a zuciyata itace ta saka na kasa mantawa da ita har sak da nazo yanzu duk da ba na san ɗauki lokaci. Kayi haƙuri don Allah." Adnan ya kalli Huzaifa da ya kasa magana ya sake kallon Mujahid kafin yayi magana yace, "Wallahi Lubna ce mace ta farko da nayi nadamar abinda nayi nata, itace mace ta farko da naji babu daɗi akan abinda na aikata mata. Itace nace ta farko da nake ji a zuciyata in bata yafe min ba kamar wani abun zai iya faruwa dani. Shiyasa nazo gare ka kafin naje gare ta, don Allah ka yafe min komai ya wuce." "Komai ya wuce ka ke cewa fa Mujahid, fyaɗen da kayi mata shine komai zai wuce?." Mujahid yace, "nasan a wajan ka da ita da kowa ma nata bazai wuce ba, amma ku daure ku yafe min tunda na bar nan kullum cikin tunanin ta nake, na so na daure na kawar da komai daga rajna amma abin yaci tura na kasa. Wallahi Adnan Allah ya ɗora min son Lubna a lokacin da ban yi zaton haka ba, a yanzu ji nake in ba da Lubna ba bazan iya rayuwa ba." A fusace Adnan yace, "za kuwa ka mutu, domin baza ta taɓa yin rayuwa da kai ba har abada wallahi. Ka ma rajna min hankali, dan kaga an yi shiru da maganar ko?, To yanzu ka kawo kan ka, in naso sai na zama silar zuwan ka gidan yari." Mujahid yayi murmushi yace, "wallahi Ina son Lubna so na tsakani da Allah, tun bayan abinda ya faru ban sake aikata abu makamancin wannan ba, zan iya cewa shiryu, tun daga kanta nake na daina aikata komai wallahi. Kayi haƙurj ka bani dama na same ta na bata haƙuri. A fusace ya sake cewa, "babu ita babu kai, babu kai babu ita. Na rantse kaka da Allah na ganka da Lubna sai na saka anyi maka dukan da ranka zai iya barin jikin ka. Burin ka na ƙona min rai ya cika ka yiwa ƙanwata fyaɗen meye na dawowa rayuwar mu yanzu?, Ko kana tunanin wannan fuskar da ka sako zata iya yaudarata ne?, Ka tuna waye a gaban ka kafin ka fara tsara min labari." Yayi murmushi yace, "ba labari bane. Wallahi da gaske nake. Ina son Lubna kuma inda za’a bani sama auren ta....." "Kar ka sake ka ƙarasa, kar wannan kalmar ta fito daga bakin ka domin zaka iya tsintar haƙoran ka a tafin hannun ka wallahi. Ni zaka kalla ka faɗawa wannan maganar? Ni zaka zo har inda nake kana faɗa min wannan maganar banza da wofin?. Na sanka ciki da waje, baka isa ka raina min hankali na ɗauka ba, kuma wallahi in ka sake ka bibiyi Lubna wallahi sai na yi maka abinda zaka yi dana sanin sanin Adnan a rayuwar ka, sai kayi dana sanin sanin Lubna a rayuwar ka. A yanzu ma ka jira sammaci zan maka ka a kotu dan dawo da hannun agogo baya." Mujahid zai yi magana Adnan cikin tsaya yace, "ka fita ka bani waje!." Mujahid yace, "zan fita, amma inda ace ba har zuciyata maganar nan take ba da baza ka ganni a nan ba wallahi, da gaske nake maka duk abinda na faɗa ba ƙarya nake ba." Huzaifa yace, "baka da kunya wallahi, baka san kara da mutunci ba. A zaman amanar da akayi da kai ƙanwar Adnan ƙanwar ka ce, ko wani ka gani zai yi mata kwatankwancin abinda ka yi mata kai mai iya kare ta ne, amma kai ne da kanka ka yaudare ta har ka aikata mata fyaɗe. Tirr da halin ka wallahi, za kuma kayi dana sani a lokacin da baza tayi maka amfani ba." Ya kalli Huzaifa yace, "Nayi dana sani. A yanzu ina kan yin ta ma Huzaifa." Landline Bebi ya ɗauka yana kiran security na reception, ganin haka sai Mujahid yace, "zan fita Adnan, amma zan sake dawowa" ya faɗa yana fita daga office ɗin duk suka bishi da kallo cikin tsananin ɓacin rai. BDƘB3P43 Yana fita Adnan ya kama ƙagu yana zagaye office ɗin Huzaifa yace, “tun farko naso ace an kama Mujahid Adnan, da yana prison yanzu da ba haka ba.” Adnan ya kalle shi yace, “bani da hujjar da zan kama Mujahid, Mujahid ba tilastawa Lubna yayi ba itace ta kai kanta har inda yake, bani da hujjar da zan kai shi kotu akan laifin fyaɗe ba.” “Kana da hujja, ko iya hujjojin asibitin nan sun isa a kama Mujahid, kuma ita yarinyar da message ɗin da yayi maka duk hujja ce da zata saka a kama Mujahid.” “Magana ake ta shekara ɗaya da wani abun da faruwar wannan abun fa Huzaifa.” “Ko shekara goma ne akwai hujja da za’a kama Mujahid, barin Mujahid yanzu barazana ne ga Lubna, zai sake ƙoƙarin cusa mata kansa a zuciyar ta ƙarshe azo ana dana sani.” Adnan ya girgiza kai yana tunani kafin ya fita daga office ɗin. Sun jima a cikin asibitin kafin su fita su je su gaishe da Hamza daga nan Adnan ya wuce wajan Mama. Sai da yayi sallar magriba a masallaci sannan ya shiga wajan Mama da sallama ya same ta ita da Farida suna hira. Zama yayi kafin ya sauka daga kan kujerar ya tsuguna yace, “Mummy ina kwana.” Mama tayi dariya tace, “kwana kuma?, Da alama yau baka fita ba.” Yace, “Au ina yini Mummy” ta amsa tana kallon sa ya koma ya zauna Farida tace, “Wallahi ƙiba ka ke yi yaron nan, ko da yake kana auren chef ai dole ka yi ƙiba.” Ya ɗan saki fuska kaɗan yace, “nima na gani wallahi, kwana biyu bana traning ne.” Mama tace, “ɗazu Manal tazo ta gaishe ni har dambun kaza da wainar shinkafa ta kawo min mai daɗi, yanzun nan Kausar ta cinye wainar.” “Ban sani bama.” “Haka tace, daman tace min baka san ma zata zo ba gida taje sai ta biyo ta nan. Sai iv bikin Yayar ta da ta kawo min.” Farida tace, “ai gaskiya tana da kirki, ni da farko na ɗauka kirkin nata na farkon zuwa ne, gashi tafiya tayi nisa bata canja ba. Ba wai dan kaji daɗi nake faɗa ba,wallahi in bata dashi a gaban ka zan faɗa dan baza ka dake ni ba” ta faɗa tana kallon sa. Taɓe baki yayi kafin yace, “Ya maganar Mimi kuwa? Taga likitan?.” “Wanne ganin likita ana zancen Allah ya kawo rabo” Farida ta faɗa tana kallon sa. Ya kalle ta ya ce, “daman ai ke ki zugawa akan taje asibiti, haka kawai shekara ɗaya kacal ku fara zancen infertility kamar wacce ta shekara goma.” Farida tace, “dole fa mu damu, dangin miji basu da daɗi yanzu sai a fara tunanin wani zance ana cewa bata haihuwa ko wani abun.” Ya kalle ta yace, “kawai dai mata bakwa rasa abin magana ne kawai. Amma Allah na tuba shekara ɗaya tal a fara zancen wani infertility ana zaune lafiya?” ya faɗa yana kallon Mama. Mama tayi murmushi kawai bata ce komai ba. Ya sauke ajiyar zuciya ya miƙe tsaye ya kalli Mama ya p ce, “Mummy na wuce gida, tun safe ina asibiti sai yanzu na dawo na gaji sosai.” “Allah ya kiyaye, ka yi min godiya wajan Manal na gode.” Ya sauke ajiyar zuciya baice komai ba. Farida tace, “lafiya dai ka ke ko?.” Ya ɗan motsa hannun sa yace, “to lafiyar dai zan ce. Sai da safe” ya faɗa yana fita daga falon. Yana shiga cikin gidan sa ya samu Manal a tsaye a falon Ayan sai kuka yake tana ta zagaye da alama ya jima yana kukan. Ya kalle ta yace, “ya dai? Lafiya yake kuwa?” Ya faɗa yana karɓar sa daga hannun ta. Manal tace, “tunda na dawo yake kuka wallahi, na rasa abinda zan yi masa yayi shiru.” “Kuma ba yunwa yake ji ba?.” “To ya ƙi karɓa ma, na rasa ya zanyi duk ya ruɗa ni.” Har lokacin kuka yake yi yana hannun sa yana jijjiga shi amma yaƙi shiru, sake karɓar sa tayi ta zauna ta sake bashi nonon yaƙi karɓa sai kuka kawai yake yi. A hankali kukan nasa kuma sai ya fara raguwa tana jijjiga shi a jikin ta sai yayi bacci. Ajiyar zuciya tayi ta kalle shi yana kallon ta tace, “ni na san lafiya lau yake wallahi, kawai rigima ce wacce ya saba” ta faɗa tana kwantar dashi a hankali tana tsoron kar ya tashi. Ɗaki ya shiga yayi wanka ya fito ya samu bata falon ya ƙwala mata kira ta shigo falon ya ce, “bani abinci yunwa nake ji.” Manal tace, “yanzu zan ɗora.” ya juyo yana kallon ta ya ce, “yanzu zaki ɗora fa kika ce?.” “Tunda na dawo yake kuka ban samu na ɗara daga falon nan bama balle na shiga kitchen, girkin nake taso nayi maka amma na rasa ya zanyi.” Tsaki yayi yace, “yanzu har sai na jira an dafa abinci sannan zan ci?.” Manal tace, “to ya zanyi?.” Tsaki ya sake yi alamun bai ji daɗi ba ya ce, “ki barshi kawai, bazan iya jira har a dafa ba gaskiya.” Manal tace, “ina da waffles in zaka fara ci kafin na dafa maka abincin, akwai dambun kaza ma kafin na fita na yi.” Ya ɗan kalle ta kafin ya amsa ta wuce kitchen ta kawo masa ta ajjiye a gaban sa. Ganin sai ɓata rai yake yi sai taji babu daɗi tasan baya so ya dawo bata gama abinci ba tace, “kayi haƙuri, yanzu zan dafa maka couscous tunda yafi sauƙi.” Ya fara cin waffles ɗin da ta shafe shi da chocolate sai ƙhamshi yake yi ya ce, “ko barshi ma, in naci wannan ya ishe ni.” Ta kalle shi tace, “ni ma baka ci abincin ba dole na dafa yunwa nake ji sosai.” “Na taho da fura ki buɗe mota ki ɗauko sai ki dama ki sha ko?.” Manal tayi ajiyar zuciya tace, “na huta” ta faɗa tana ɗaukar key ɗin motar sa ta fita harabar gidan. Ba jimawa ta dawo ta ajjiye makullin ta shiga ciki ta dama fitar ta dawo tana sha duk da babu zaƙi amma taji daɗin ta ta kuma ƙoshi sosai. “Mummy tace min kin je.” Ta ɗaga kai tace, “eh na biya da na dawo, na kai nata iv bikin Yaya. kaima ga naka can a jakata.” Ya kalle ta yace, “tace min kin kai mata dambun kaza harda wainar masa, an gode.” Murmushi kawai tayi bata ce komai ba. Tashi tsaye yayi ya ce, “Partner kwanciya zanyi, na gaji yau sosa bacci nake ji.” Manal tayi murmushi tace, “A huta lafiya.” “Sai kin shigo” ya faɗa yana wucewa ya shige ɗaki ba tare da ya kalle ta ba. Itama sai da ta gama abinda yake yi sannan ta shiga ɗakin nasa a lokacin ma har yayi bacci. Washe gari ya tashi da mura da ta saka masa ciwon kai, bai fita ba yana gida a kwance dan sosai kansa yake ciwo. Manal tana zaune kusa dashi ta taɓa jikin sa tace, “Partner jikin ka yayi zafi, kaci abinci ka sha magani.” Bai iya yi mata magana ba yana kwance sai ta fita ba jimawa ta kawo masa kunu a kofi. Zama tayi kusa dashi tace, “ga kunu ka tashi ka sha sai ka sha magani.” Daƙyar ya tashi zaune ta matsa kusa dashi sosai ta saka masa kofin a baki ya sha kaɗan yace, “ya ishe ni, bani pcm na sha.” Tashi tayi ta kawo masa ya sha ta sake taɓa wuyan sa taji da zafi sosai. Ƙin sakin hannun ta yayi ya riƙe shi a wuyan ta yana jin sanyin hannun ta. Tashi tayi ta rage kayan ta ta ƙarasa kan gadon ta zare ƙaramar rigar jikin sa ta maye gurbin rigar a jikin sa. A hankali yake jin daɗi sanyin jikin ta yan shiga jikin sa a haka bacci ya ɗauke su. Da ya farka yaji daɗi babu laifi Manal sai lalaɓa shi take shi kuma hakan daɗi yake masa. Kwana biyu yayi a kwance har da masu zuwa dubiya dan shima mai yi ne. Ranar da ya ji sauƙi ya fita asibitin yaje ya gama abinda zai yi ya dawo gidan su. Abinda ya bashi mamaki mazan gidan nasu suna nan duk da kasancewar yamma ce. Yana ajjiye motar ya shiga wajan Mama ya samu bata nan babu kowa a ciki, fita yayi ya shiga wajan Mamy a nan ya same su gabaɗayan har da Farida da Mimi da alama meeting suke yi. Ganin sa sai Yaya Isma’il yace, “A’a Adnan ashe ka warware?.” Adnan ya ƙarasa shiga ciki yace, “eh na samu sauƙi, tun safe ma bana nan. Wai taro ku ke yi yau ban sani ba? Ke Lubna meye ya saka ki kuka kuma?” Ya faɗa yana kallon ta. Yaya Bilal yace, “zauna zaka ji duk abinda ya tara mu a nan.” Zama yayi a akan kujera kamar yadda suke yace, “Allah ya dai lafiya dan naga Lubna tana kuka.” Mamy tace, “magana ake akan auren Lubna.” Bebi yace, “har ta samu miji bani da labari? A ina yake?.” Yaya Bilal yace, “Mujahid ne ya takura mana da sintiri da magiya da koke-koke, jiya har yayan sa ya turo min akan ayi haƙuri a bashi auren Lubna. Shine muka taru a nan dan mu yi shawara.” Adnan ya kalle su da mamaki yace, “To Yaya Bilal meye amfanin zama akan Mujahid don Allah? Me ake tattaunawa a kan sa?.” Yaya Bilal yace, “to Adnan Mujahid dai shine ya yiwa Lubna fyaɗe, kuma saboda wannan tabo ko nace tambarin ya saka aka fasa auren ta a wancan lokacin. Shine muke ganin tunda yayi nadama ya kuma gane kuskuren sa me zai hana baza mu bashi auren ta ba?.” Wara idanu Adnan yayi cikin mamakin abinda ya ce, “a bashi auren ta kace fa Yaya? Auren Lubna ɗin za’a bawa Mujahid?.” Yaya Isma’il yace, “tattaunawa muke a kai bamu kai ga yanke hukuncin ba.” “Ai wallahi ko a yanke hukuncin sai an dawo baya tunda na shigo, babu wanda zai aurawa Lubna Mujahid indai ina da rai.” Yaya Isma’il ya ce, “Ai ba cewa muka yi za’a aura mata shi ba, shawara muka zauna muna yi a kai, in ana ganin hakan zai yu ba sai ayi a wuce wajan ba.” Mamy ta kalle shi tace, “Kuma Bebi shine wanda ya yi mata fyaɗe, a ganina shine ya kamata ace ya aure ta tunda shine wanda ya fara sanin ta a matsayin ɗiya mace. Duk macen da hakan ta faru da ita ta kan rasa darajar ta a wajan mijin da zata aure, kaga in ya kasance shine mijin ta an huta da duk wani tashin hankali da zai ɓillo bayan auren ta.” Maryam tace, “kuma kaga yace yayi nadama har yana bada haƙuri, a ganina nima a bashi auren ta kawai zai fi.” Tashi tsaye yayi yace, “shine dogoran ku?, saboda yazo gaban ku yana kuka yace yayi nadama shikenan kawai sai a bashi auren ta?. To Wallahi Allah bazai aure ta ba, ko da ace da gaske Mujahid yayi nadama bazan amince ya auri Lubna ba indai har na kasance yaya a wajan ta. Kar ku manta neman mata halin Mujahid ne, kuma ina so ku tuna wannan hali nasa shine dalilin da ya sa muka fara faɗa ni dashi, ai baku kaini sanin sa ba dan dukkan ku ta dalilina ku ka san shi. Kenan dan yace ya tuba akan Lubna shikenan sai mu ɗauke ta mu kaita gidan sa kamar wacce bata da gata?. Wallahi bazan amince a aura mata shi ba koda zan ga nadamar Mujahid na zuba a ƙasa bazan yarda ba. Zan tsaya tsayin dana wajan nema mata wanda zai riƙe ta hannu biyu, wanda zai aure ta da zuciya ɗaya ba tare da yayi tunanin wani abinda ta rasa ba, wanda zai so ta tsakani da Allah ba don wani abu nata ba.” Ya kalli Lubna da take ta kuka yace, “Lubna kina tare ni ko kina dare dasu Yaya akan auren Mujahid?.” Tashi tayi ta dawo kusa dashi tace, “bana so, kar ka bari hakan ta faru, wallahi Yaya Adnan bana so.” Ya riƙe hannu ta ya ce, “Ku yi haƙuri! amma Lubna baza ta auri Mujahid ba, in ganin ta a gaban ku ne ya saka ku ke son aure mata shi zan ɗauke ta ta koma gidana ta cigaba da zama har ta samu mijin aure” ya faɗa yana jan hannun ta zasu fita. Tsayawa yayi ya kalli Yaya Isma’il yace, “kayi haƙuri, ban yi dan ɓata muku rai ba, nayi haka ne kana kare martabar ta, na yi hakan ne dan na aurar da ita ga mijin da ya dace da ita. indai ina da rai bazan bari a kai jinina halaka ba” yana gama faɗa ya fita shida Lubna BDƘB3P444 Kowa ya bishi da kallo bayan ya fita daga falon Farida tace, “Maganar Adnan fa gaskiya ce Yaya, nima bana goyan bayan haka domin tun asali ya kasance mazinaci ne. Meye ribar auren mazinaci?.” Mamy tayi ajiyar zuciya tace, “ƙwarai Adnan ya fi mu gaskiya, ta dalilin neman marasa lafiya da yake yi aka ƙwace lasisin sa na zama likita.” Mama tace, “nima ban ga amfanin aura masa ita ba wallahi, zina tabo ne da ita zata dinga bibiyar sa ne har ƴaƴan sa” ta faɗa a sanyaye da alama ta tuna Abba. Yaya yayi murmushi yace, “ai magana ta wuce, tunda kowa ya fahimci abinda yake nufi daidai ne. Allah ya kawo mata miji na gari.” Kowa ya amsa da amin Mamy tace, “Ku kira shi ya dawo da Lubna babu abinda zai faru in sha Allah, babbar budurwa kamar ta ya kaiwa matar sa yace zata zauna?.” Maryam tayi dariya tace, “ki ƙyale shi Mamy, yanzu ko ance bazai dawo da ita ba, a bari tayi kwana biyu.” Farida tace, “gaskiya dai, gani zai yi kamar auren za a yi mata.” Bebi kuwa yana fita shi da Lubna sai da ta ɗauko wayar ta da kayanta kala biyu ya saka ta a mota suka wuce gida. Da suka je gidan Manal bata falo ya kalle ta yace, “ki shiga ciki tana nan” ya faɗa yana shiga ɗakin sa ita kuma ta wuce wajan Manal. A zaune ta samu Manal tana canjawa Ayan kaya ganin ta sai tayi dariya tace, “A’a sis barka da zuwa.” Lubna tayi dariya ta zauna tace, “Sis barka da dare, ya Baby Ayan” ta faɗa tana ɗaukar sa kafin tace, “gaskiya Ayan yana da kyau ma sha Allah” ta faɗa tana fara yi masa hoto. Manal tace, “Ya Mamy da Mama? Suna nan Lafiya?.” “Lafiya lau wallahi, ya zaman gidan nan?.” “Bari kawai Sis, zaman shiru ai babu daɗi.” Lubna tace, “tare muke da Yaya fa, ya shiga ɗaki.” Manal ta miƙe tace, “Au ai ban sani ba, ina zuwa” ta faɗa tana tashi ta shiga ɗakin sa. Kaya yake sakawa da ta shiga ɗakin ta kalle shi tace, “Sannu da zuwa Partner, ya jikin?” Ta faɗa tana matsowa ta taɓa jikin sa ta riƙe fuskar sa tace, “jikin ka da zafi kaɗan, sannan fuskar ka ta nuna min alamun ran ka babu daɗi” ta rungume shi tace, “me ya faru?.” Ajiyar zuciya yayi rigar da zai saka tana hannun ya rike ƙugun ta ya ce, “Lubna zata zauna a nan na tashon wasu kwanaki, in naga kwanakin ma bai yi aiki ba zata dawo nan da zama gabaɗaya.” Manal ta kalle shi tace, “da gaske ka ke?.” Ya kalle ta shima yace, “eh, bakya son zaman nata ne?.” Manal tayi dariya tace, “farin ciki nake da zuwan ta, ko babu komai zan daina zama shiru na samu ƙawar hira.” Ya ɗauke idon sa daga kanta yace, “aure dole zasu yi mata shiyasa na gudo da ita nan.” Manal tayi dariya ta koma ta kwanta a kan fatar ƙirjin sa tana shafa gashin da yake kwance a ƙirjin a hankali tace, “wai ka gudo da ita. Gaskiya su Lubna sun yi sa’ar samun Yaya kamar ka. Allah ya ja da ranka ya baka lafiyar cigaba da yin abinda ka ke yi.” Kiss ya manna mata a kumatu yace, “Amin my dear Wife. Ina fatan zuwan ta ba zai takura miki ba?.” Mintsinin sa tayi a ƙirjin sa tace, “takura ko sakewa? Ai ni zuwan ta yayi min daɗi wallahi, Allah yasa ma ta dawo nan ɗin gabaɗaya da na huta.” Yayi murmushi yace, “Na gode.” “Kai dai abin godiya baya yi maka wahala” ta faɗa tana raba jikin ta da nasa tana kallon sa. Ƙare nata kallo yake yi cikin shigar da tayi ta vowel mai kyau yace, “kin yi kyau amaryata.” Kallon sa yake sai ta tuna farkon haduwar su tayi dariya tace, “ka san me na tuna?.” Ya saka rigar sa yace, “me kika tuna?.” “Ranar da na fara ganin ka.” Ya kalle ta yace, “ranar na sace zuciyar ki ko?.” Tayi dariya mai sauti tace, “Ka ɓata zuciyar ta dai.” Yayi dariya shima mai sauti tace, “wai yaushe ka fara sona?, ni dai naga ba wata maganar kirki muka yi da kai ba a wancan lokacin, tsoron ka ma nake ji saboda tsawa da haɗe rai. Kallon mara kirki nake yi maka ashe fuskar kace a haka amma kai ba haka ka ke ba. Yaushe ka fara sona?.” Ya kalle ta yana murmushi ya ce, “nima bazan ce ba ga ranar da na fara jin ki a zuciyata ba wallahi, kawai na wayi gari naji in ba ke ba sai rijiya.” Tare suka yi dariya yana kallon ta yace, “Manal ɗina, I so much love you” ya faɗa yana ɗaukar wayar sa. Tayi murmushi tace, “nima ina sonka.” “Yanzu muje ki bani abinci, yunwa nake ji.” Ta amsa da to suka fito falo suka ƙarasa inda Lubna take. A falon suka zauna suna ci abinci har Lubna suka gama Lubna ta ɗauke plates ɗin da aka ci ta kai kitchen ta ajjiye ta dawo ta zauna ya kalle ta yace, “kar ki ji komai Lubna, ki saki jikin ki nan ma gidan ku ne, sannan babu wanda zai miki abinda bakya so indai ina nan.” Tayi murmushi tace, “ni na san na samu kariya tunda Allah ya bani Yaya kamar ka. Allah ya cigaba da kare ka Yaya Adnan, Allah ya baka abinda ka ke so ya saka maka da gidan Aljanna. Yadda ka ke kula damu gabaɗaya Allah ya baka mai kula da naka yaran, Allah ya jiƙan Abban mu ya gafarta masa, Allah ya bar ka da matar ka da ka ke so, Allah yasa baza ka yi mata kishiya ba.” Manal tayi caraf tace, “Amin Lubna, wannan addu’a ce mai kyau.” Fuska a sake yake kallon Lubna bayan ya amsa da amin yace, “cin hanci ta baki?.” Lubna tayi dariya tace, “A’a, kawai bana so ka yi mata kishiyar ne Yaya.” Yayi murmushi ya kalli Manal yace, “Abbana ma matan sa biyu, nima biyu zan yi.” Manal tace, “kayi huɗu ma.” “Ƙarya kike wallahi, na tabbatar yanzu gaban ki ya faɗi.” “Harda wallahi, to meye abin kishin?.” “Oho miki” ya faɗa yana kallon ta, Lubna tayi dariya tana kallon su cikin burgewa, ya tabbatar Manal ta gama dacen miji ba dan ya kasance Yayan ta ba. Ta tabbatar Yaya Adnan mijin na gari ne lamba ɗaya. Sun jima a zaune suna hira kafin Lubna ta tashi ta shiga ɗakin Manal, itama Manal ɗin tashi tayi ta shiga ɗakin da Ayan a hannun ta. Kwantar dashi tayi ta canja kaya zuwa na bacci Lubna ta fito daga banɗaki Manal tace, “na baki kayan bacci?.” Lubna tace, “Yauwa bani.” Manal ta ɗauko mata ta bata Lubna ta karɓa ta ajjiye a kusa da ita. Manal nauyin Lubna take ji baza ta iya fita ta tafi wajan Adnan ba hakan ya saka ta zauna tana gyarawa Ayan kwanciya. Lubna tace, “Sis ki bar min shi ya kwana a wajena.” Manal ta kalle ta tace, “zaki sha kuka kuwa, Wallahi hana ki bacci zai yi.” Lubna tace, “bar min shi na ɗana kafin nawa nima su zo.” Manal tayi dariya ta miƙe tace, “to bara naje na dawo” ta faɗa tana fita ita kuma ta tashi ta canja kaya ta ɗauki Ayan da yake bacci ta kwantar dashi a kan gadon ta kwanta a gafe tana kallon sa. Manal tana shiga ɗakin Adnan ya kalle ta yace, “ina Ayan ɗin?.” Ta ƙarasa inda yake zaune ta zauna ta kwanto a jikin sa tana kallon sa tace, “Lubna tace na bar mata shi.” “In yayi kuka me zata iya yi masa? Ke kuma sai kika bar nata shi ɗin?.” “Haba Partner, ka bar mata shi in ya tashi yana kuka zata neme ni.” Ya Harare ta yace, “kawai saboda ɗaukar haƙƙin sa yana kuka har sai an fito daga can nazo nan ana buga min ƙofa?, Ai kawai ki tashi ki karɓo shi.” Ta kalle shi tace, “Don Allah ka bar mata shi tunda itace ta nema, in naje karɓe shi baza ta ji daɗi ba.” Shiru yayi baice hakan ya saka ta kalle shi tace, “Wai wannan glasses ɗin naka na gayu ne ko kuwa na ƙara ƙarfin gani ne?.” Ya zare shi daga idon sa yace, “idona ras yake har na fiki gani, ina sakawa ne saboda hasken computer da hasken takarda.” Manal tace, “ai ku likitoci dole ma idon ku ya mutu saboda kallon tsaraicin mutane.” Yayi ƴar dariya yace, “waye yace miki kallon tsaraici mu ke?.” “Shi ku ke yi mana, abinda har haihuwa kuna karɓa.” Ya kalle ta yace, “ni da nake cardiologist me ya haɗa ni da haihuwa?, Sai nayi wata ɗaya ban bi hanyar maternity ba indai ba Hamza nake nema ba ko wata likitan. Ni ai ɓangarena bai wani shafi kallon tsaraici ba gaskiya.” “Amma in zaku yi theater ko zaku yi gwajin zuciya ai sai mace ta cire riga ko?.” Ya kalle ta yana murmushi bai ce komai ba tace, “eh nan ma ai tsaraicin ne, balle kai da ka ke aikin zuciyar har taɓa ƙirjin matan kana yi.” Ganin yanayin ta ya canja sai ya sake yin murmushi yace, “eh haka ne, amma wallahi in dai ba na san mutum ba da zarar ya bar asibitin na manta dashi balle har surar wata mace ta tsaya min a rai, mutanen suna da yawa sosai, in ba sanin mutum nayi tun farko ba bana gane shi in ya bar asibiti sai dai shi ya gane ni.” Manal tace, “amma dai kana ganin ƙirjin matan ko?.” “Duk cikin aiki ne Manal.” Turo baki tayi tana kallon gefe tace, “wallahi zafin hakan nake ji.” Ɗan murmushi yayi yace, “ai ba wani abun bane, ni da ba gynecologist ba, sune suka san mata ciki da waje, yadda gyne ya san jikin mace ku matan baku sani ba.” “Naji daɗi da ba kai ba ɗin bane, Allah da ka kasnace gynecologist bana tunanin zan iya bacci in ka fita, dan kawai gani zanyi mata kawai ka ke kallo.” Yayi murmushi ya ja hancin ta amma bai ce mata komai ba. Ido ta lumshe tace, “Bacci nake ji.” “Bacci fa kika ce? Kuma a ɗakin nan?.” Ta kalle shi tace, “eh mana.” “Lallai ma, kema kin san ba a shigowa ɗakin nan ayi bacci ko?.” Ta kalle shi tace, “kamar wani labour room?.” Yayi dariya mai sauti yace, “da alama ɗakin nan da kika shiga ya gigita ki, da anyi magana kice labour room” ya faɗa yana dariya sosai yana kallon ta. Shan kunu tayi yana dariya ya riƙe kumatun ta duka biyun yana ja yace, “Bani labarin labour room ɗin, ya yake shi da gaske ba a bacci a ciki?.” Murguɗa masa baki tayi ya sake yin dariya ya jawo ta ta ya kwantar da kanta a ƙirjin sa, ya yi mata kiss a goshi yana shafa bayan yace, “my dear wife, mother of my child. Ke ta musamman ce a rayuwar Adnan.” Ta kwanta a jikin sa tana dariya tace, “nima kai na musamman ne a rayuwar Manal.” Bai bata amsa ba sai murmushi da yake yi tace, “Don Allah ka dinga murmushi kamar haka kafi kyau wallahi. Kai kullum fuska a ɗaure?.” Ya kalle ta yace, “to ya zan yi da halittar da Allah yayi min?.” Tayi murmushi tace, “wallahi in ka ɓata rai tsoro ka ke bani.” Murmushi ya sake yi bai ce komai ba tace, “bacci nake ji fa.” “Baki isa ba ai, babu ke babu bacci.” “To kaima ai baccin ka ke yi.” “Da bani da lafiya ba, yanzu na samu lafiya kuma kinga nayi missing ɗin ki.” Manal tace, “tsoron ka nake ji, in aka kwana biyun nan ba a yi komai ba in ka waiwayo wahala ka ke bani” ta faɗa tana kallon sa a shagwaɓe. Ya sake yin dariya yace, “kema cewa kika yi in ba a yi komai ba, to ai kwanakin da ba a ayi ɗin ba nake fanshewa.” “Nidai a’a, kamar ma period zan yi.” “Kafin ki yi ɗin yanzu lokaci na ne ƴan mata.” “Don Allah kar ka yi min mugunta” ta faɗa tana kallon sa a lokacin da ya kashe hasken ɗakin ya tunkaro ta. “Shiiii! Ki yi shiru” ya faɗa yana zama kusa da ita tare da ɗauko ta gabaɗaya ta dawo jikin sa. Manal murya a sarƙe tace, “ni dai partner….” Shiru tayi ta ja numfashi jin abinda ya sa tsaya cak da maganar. Kwanan Lubna biyu a gidan babu wanda ya ce mata ta dawo gida, daɗin zaman gidan itama take ji in ya fita hira suke sha da Manal, shima yaji daɗin zaman ta saboda in zai yi aikin dare bashi da matsala tafiya yake dan ya san duk abinda zai faru da ɗayar su ɗaya zata iya kiran sa ta faɗa masa. Maganar Mujahid ta lafa babu wanda ya sake yi mata maganar shima Mujahid ɗin bai sake yin magana ba sai dai Allah ya jarabce shi da ƙaunar Lubna mai tsanani wacce ya tabbatar da bazai same ta ba a wannan lokacin. A cikin kwanakin aka yi bikin Mubeena su Manal an sha hidima kullum bata nan dan ya hanata kwana duk dare zai je ya ɗauko ta da safe ya kai ta. Su Daddy sun zo Kano shi ne ya bada auren Mubeena da kansa aka yi komai lafiya lau aka kai amarya Abuja a ranar ne Manal ta kwana can washe gari suka dawo Kano. Satin da ya dawo aka fara da Surayya Manal bata huta daga na Mubeena ba aka shiga hidimar bikin babbar ƙawa. Manal tayi hidima sosai ta kuma bayar da gudunmawa da jikin ta da kuma aljihun ta, kowa ya yaba da abinda tayi dan tayi bahinta mijin ta ma yayi. Maman su Manal kan ba’a magana, dan babban abu ta ɗauka a hidimar bikin tace itace ta ɗauki nauyi gabaɗaya, ta faɗawa Daddy shima ya ɗauki nauyin kayan ɗakin amarya gabaɗaya. An yi kara da karamci sun rama alkhairin Maman su Surayya da alkhairi. Bayan wasu kwanaki. BDƘB3P45 Yaya Isma’l ne da Yaya Bilal da Adnan a zaune wajan Daddy kamar yadda ya kira su, suna zaune a gaban sa yana amsa waya suna jira ya ƙarasa wayar dan su ji kiran da yake musu. Sai da ya kashe wayar sannan yace, “na kira ku kuma ina amsa waya. Na san kuna ta tunanin dalilin kiran ko?.” Yaya Isma’il yace, “ba abin Mamaki bane ba ai Daddy.” Daddy yayi murmushi yace, “Magana ce akan ƴar uwar ku Maryam, tsohon mijin ta Kamal shekaran jiya ya dawo ya same ni akan yana son mayar da Maryam ɗakin ta. Yazo cikin yanayi na damuwa da nuni da nadamar sa a bayyane yana kuma burin mayar da ita ɗakin ta. Bayan ya tafi jiya sai ya aiko min Yayan sa da ƙanin mahaifin sa akan shi dai yana son a sake bashi auren Maryam. Shiyasa ba kira ku naji ya ku ke gani?.” Yaya Bilal yace, “Kamal!, Kamal ne yake son auren Maryam duk abubuwa da suka faru Daddy?.” “Eh Bilal, yazo a kan yana neman auren ta a karo na biyu. Yazo ya same ni cikin sanyin jiki da tsantsar nadama a bayyane.” Yaya Isma’il ya ce, “Amma abin da mamaki Daddy.” Daddy yace, “nima nayi mamaki, amma abun ne a bayyane, nadama yayi ya gane kuskuren da ya aikata ya dawo ya gyara. Kuma ni a wajena indai har da gaske mayar da ita zai yi daman babu wanda ya cancanci ta komawa kamar sa, taje can su gyara abinda suka ɓata sannan ta cigaba da rainon yaran da Allah ya basu. Tare suka aikata kuskuren da suka aikata shi da ita, yanzu kuma ko wanne a cikin su yayi nadama yana kuma son a sake bashi dama ya gyara kuskuren sa. Ni a wajena indai har dai har Maryam tana ji a zuciyar ta zata komawa Kamal daman babu wanda ya kamata ta komawa kamar sa. Amma ya ku ke gani?, Shine dalilin kiran da nayi muku.” Yaya Isma’il yace, “gaskiya ne Daddy, in da wanda ya kamata ace Maryam ta aura bai wuce Kamal ɗim ba. Amma abinda ya kamata muyi ita Maryam ɗin zamu tambaya, in tana da ra’ayin komawa sai ta koma, in bata dashi sai ta zauna Allah ya kawo mata wani.” Yaya Bilal yace, “haka ne, amma duk wanda yazo neman auren ta ya bincika ya samu labari irin wanda Mahmud ya samu babu lallai ya aure ta. Komawar ta wajan Kamal shine yafi saboda ta riga ta ɓata rayuwar ta, ko ya ya aka zo bincike a kanta abinda ake gudu shine zai sake faruwa.” Daddy yace, “duk maganar ku a kan gaskiya take, amma kune yayyen ta ky ya kamata ku zaunar da ita ku nuna mata hakan, in Allah ya yi wajan sa zata koma sai kaga silar rabuwar ta da Mahmud ɗim kenan.” “A yadda muka sani duk wacce mijin ta yayi mata saki uku a addinance koda zata koma masa sai bayan tayi wani auren auren ya mutu, sannan kuma sai mijin da ta aura ya ɗora mata idda. Shi kuma Mahmud bayan kwana biyu da ɗaura musu aure yazo yace ya sake ta ba tare da ta tare ba. Kun ga kenan in har bata yiwa Mahmud idda ba dole sai ta sake wani auren kafim ta komawa Kamal. Amma zamu iya tambayar malamai wataƙila akwai wata fatawar da wannan ba.” Daddy yace, “eh da gaskiya ka Bilal, gaskiya a yadda na sani nima sai sabon mijin ta ya kwanta da ita sun rabu ko ya mutu tayi idda sannan zata komawa mijin ta na baya da yai mata saki uku, amma kun san shi ilimi kogi ne, abinda na sani wani bashi ya dani ba, kullum ilimin sake yawaita yake. Kun ga kenan in bata yi idar Mahmud ba babu zancen komawar ta wajan Kamal.” Yaya Isma’il ya kalli Adnan da tunda suka fara magana bai ce komai ba yace, “Adnan baza ka yi magana ba?.” A sannan ya kalli Daddy yace, “Daddy Maryam tayi idar Mahmud, ta sanar da ni da kanta tun bayan rasuwar Abba.” Daddy yace, “to ya ka ke ganin maganar koma masa?.” Adnan yace, “da farko bincike ya kwnata a tsannanta a kansa a tabbatar da abinda yayi mata ba halin sa bane, wataƙila ita kaɗai ya yiwa wataƙila suna da yawa. In dai akan ta ya fara ya kuma gama dan ta koma masa ba wani abun bane tunda daman daga wajan sa ta taho.” Daddy yace, “wannan in sha Allah duk za’a yi. Abinda ya kamata ku zauna da ita Maryam ɗin in zata koma masa shikenan sai ku san abinda za’a yi, in kuma bata da ra’ayi ai babu dole.” Suka amsa masa da to kafin ya saki murmushi yace, “Sai kuma maganar abokin ka Adnan” ya faɗa yana kallon Adnan da shima shi yake kallo. Daddy yace, “Usman nake maka magana. Wato ashe duk wannan zaman da yayi babu aure ƴar gida za’a yi. Sati biyu kenan yana yi min magana akan shi fa Kausar yake so, nace to kaje ka samu Adnan ko Isma’il ko Bilal kayi musu magana mana. Sai yace ai gwara su Bilal ɗin da dai yazo wajan ka neman auren gwara ya fasa, nayi dariya nace daman son da kake mata bashi da ƙwari.” Suka yi dariya gabaɗayan su har Adnan ɗin kafin yace, “ai kawai Daddy ka bar ni dashi, ba dai yace sai dai ya fasa ba?, zai fasa ɗin kuwa.” Daddy yana dariya yace, “Wallahi haka yace, amma ya kasa daina min maganar, ɗazu ma da zai fita sai da yace don Allah Daddy ka barni na je wajan ta kai tsaye kamar wani baƙo.” Yaya Bilal yace, “da gaskiyar sa, kamar wani baƙo ace sai an sanar damu mun bada izinin ganin Kausar?.” Daddy yayi dariya yace, “ai neman aure sunan sa neman aure, babu ƴan uwantaka a fannin neman aure, yadda za’a yiwa na waje haka za’a yiwa na gida. Nace masa yaje ya samu Adnan in ya gama yi masa first interview sai ya tafi wajan ka kaima kayi masa taka sannan yazo wajena.” Suka yi dariya jin abinda Daddy ɗim yace. Adnan yana murmushi tace, “da dai ban yi niyar faɗa ba, akwai abokin aikina Dr Yasir a asibitin mu yake, yana zuwa a kai a kai musamman in aka samu aikin da yayi shafi zuciya yana zuwa mu yi aiki tare dashi. Tunda yazo yi min gaisuwar rasuwar Abba ya ga Lubna yake yi min maganar ta, da farko na share batun sa saboda kamar ba serious bane dan an ɗauki lokaci bai sake min zancen ya ba saboda ba ya ƙasar gabaɗaya. Yanzu ya dawo ya takura min akan shi da gaske yake yana son Lubna kuma auren ta zai yi, ya san komai akan abinda ya faru da ita yace min shi ita yake so ba wani abun ba. Kuma Alhamdulillah na san komai na sa Daddy, bashi da wani bad background a iya sanin da nayi masa gaskiya, yana da kirki sosai wallahi. Dan yau ko gobe ma zai zo ya same ka akan neman auren Lubna duk da ko ita bata sani ba.” Daddy ya faɗaɗa murmurshi yace, “Alhamdulillah! Kace ƴan matan namu duka lokaci ɗaya zasu tashi. Nan ma Fadila da Yusra Allah ya kawo mazajen ana tunanin ma bazai ɗauki lokaci ba.” Yaya Isma’il yace, “lokacin yazo, gaskiya abin farin ciki ne wannan sosai. Allah ya tabbatar mana da alkhairi.” Aka amsa da amin kafin ya Adnan ya kuma cewa, “Na tabbatar zai zo wajan ka Daddy.” Daddy yace, “Allah ya kawo shi, ai abin yayi min daɗi sosai. Kaga Allah ya yi lokaci ɗaya ya kawo mata miji na gari mai nagarta, dan tunda har ka buɗe baki ka yabe shi na san nagartar sa ta kai. Da an biye ta yayyen ka da yanzu sun bata Mujahid.” Yayi murmushi kawai bai ce komai ba. Yaya Isma’il yace, “gaskiya dai Adnan yana da kaifin tunani Daddy, gashi dai shine ƙaramin mu amma yafi mu hangen abinda zai je ya dawo. Muna matuƙar farin cikin samun sa a cikin ahlin mu gabaɗaya.” Yaya Bilal yace, “gaskiya ne wannan, Adnan ya zama kamar garkuwa a gidan mu. Sai dai muce Allah ya tabbatar da farin cikina rayuwar sa.” Daddy yace, “wannan gaskiya ne. Adnan na daban ne yana da hangen nesa da kaifin tunanin da yafi na wasu manyan mutanen. Allah ya jiƙan mahaifin ku ya sa yana aljanna.” Suka amsa da amin kafin su yiwa Daddy sallama su ka tafi. Kai tsaye gida suka wuce a tare suka shiga da mota suka ajjiye, kai tsaye suka wuce wajan Mama da niyar gaishe ta. A nan suka samu Mamy ma a zaune da Maryam suna ya hira. Ganin shigar su tare sai Mamy tace, “daga ina haka na ganka gabaɗayan ku?.” A tare suka gaishe su suka amsa Yaya Isma’il yace, “Mun je wajan Daddy ne shine muka biyo mu gaisa.” Yaya Bilal yace, “Daman akwai maganar ma da muke so zamu tattauna daku” ya kalli Lubna da Kausar da suke zaune yace, “Lubna ku shiga ciki.” Suka amsa da to suka tashi suka shiga ciki. Yaya Isma’il yace, “Daddy ne ya kira mu akan maganar auren Maryam.” Gaban Maryam ya faɗi matuƙa ta sunkuyar da kai ƙasa. Mama tace, “to wani abun ne ya faru?.” “Kamal ne yaje wajan Daddy akan yana son mayar da Maryam ɗakin ta, kafin yaje wajan Daddy ma ashe ya fara zuwa wajan Adnan bai saurare shi ba shine yaje wajan Daddy. Yana son mayar da ita ɗakin sa su gyara abinda suka ɓata, shine Daddy ya kira mu ya sanar damu ya muke ganin lamarin.” Mama ta girgiza kai tace, “Kamal dai? Lallai bashi ma da kunya.” Mamy tace, “to yanzu me ku ka yanke ku?.” Yaya Bilal yace, “sai abinda ku ka ce ai Mamy, shiyasa muka zo mu sanar daku.” Mama ta kalli Maryam tace, “Sai abinda Maryam ɗin tace dai, in taga zata koma sai ta koma ɗin.” Maryam dai kanta yana ƙasa hawaye na zubawa daga idanun ta wanda bata san dalilin su ba. Yaya Isma’il yace, “to mu dai gabaɗayan mu nuna goyan bayan ta koma indai an yi binkice an tabbatar da wani hali mara kyau bai shigo cikin halayen sa ba. Har Daddy ya amince da hakan saboda komawar ta shine mutuncin ta da na yaran ta. Bama so a sake samun matsalar da aka samu da Mahmud, tunda aure dole sai an yi bincike, in dai za’a yi bincike kuwa za’a iya samun matsalar da aka samu da Mahmud.” Mamy tace, “wannan gaskiya ne, nima ina goyan bayan hakan gaskiya amma in taga zata koma. Babu lallai babu dole.” Yaya Bilal ya kalle ta yace, “Maryam me kika yanke?, Kina ganin a bawa Kamal damar mayar dake ɗakin ki ko kuma bakya ra’ayina hakan?.” Maryam tana kuka tace, “Kamal bashi da kirki, bazai iya kare martabata a matsayina na matar sa ba. Kamal ya fita daga raina gabaɗaya, saboda ko na koma auren sa gani nake bazai riƙe ni da mutunci da daraja ba.” Yaya Isma’il yace, “wannan tsakanin ku ne kuma ai, kuma ko meye ya faru ai ke kika bayar da ƙofa, yanzu kuma yana buƙatar ku gyara tsakanin ku. In kinga zaki koma daidai ne, in kin ga baza ki koma ba shima daidai ne. Babu wanda zai miki dole a gidan nan, kina da ra’ayin da zaki ce baza ki koma ba.” Yaya Bilal yace, “to in bata koma ba waye zata aura?, Ko irin waccan damuwar da tayi silar barin Abba duniya ita take so ta sake dawowa cikin gidan nan?.” Sai a lokacin ya kalle su Adnan yace, “Yaya ku bata dama tayi tunani.” Yaya Bilal yace, “Tunanin me zata yi? Bafa yarinya bace ba kuma sabon aure zata yi ba. Mijin nata dai da ta bari shi zata komawa, Kun sani rashin haƙuri ne kawai ya raba su tun farko, ba dan yana ƙuntata mata ko yana yi mata wani abun mara daɗi ba.” Adnan yace, “Duk da haka Yaya, a bata lokaci tayi tunani ta kuma nemi zaɓin Allah.” Yaya Isma’il yace, “Shikenan tayi tunani, Allah ya zaɓa abinda yafi alkhairi.” Suka amsa da amin kafin Yaya Isma’il ya sake cewa, “Sai kuma batun akan ƴan matan ku Mamy.” Mamy tayi murmushi tace, “to labari ne mai daɗi dai ko?.” Yayi murmushi yace, “Labari ne mai daɗi kuwa. Kausar dai Usman ɗin Daddy ya matsa akan shi ita yake so. Ina jin ma shida ita sun daidaaita kansu tunda har ya yiwa Daddy magana. Sai kuma abokin Adnan Dr Yasir da yake masa magana akan a Lubna, Shima yau zai je ya samu Daddy akan izinin yin magana da ita.” A tare Mamy da Mama suka ce, “Alhamdulillah, Allah ya nuna mana ya tabbatar mana da alkhairi a ciki.” Suka amsa da amin kafin Mamy tace, “kuma shi Dr Yasir ɗin ya son komai akan Lubna Bebi?.” Adnan ya ɗaga kai yace, “Ya sani Mamy, bamu da matsala dashi in sha Allah, na yarda dashi ɗari bisa ɗari, zai riƙe Lubna da mutunci in sha Allah.” Mamy tayi murmushi tace, “tunda ka yarda dashi dukkan mu bamu da matsala dashi, kowa ya san baza ka kawowa ɗayan su abinda zai cutar dasu ba Aka yi dariyar farin ciki kafin Yaya Bilal yace, “Kun ga abinda yake hango mana ko Mamy? muka so aurawa Lubna Mujahid a kwanakin baya, da yanzu nuna nan nuna dana sani.” Mamy tace, “bari kawai, Allah ya cigaba da haɗa kan ku gabaɗaya.” Suka amsa da amin. Adnan ya kalli agogon hannun sa kafin ya kalli iyayen nasa yace, “Mamy da Mummy tunda ku ka fita daga takaba ban ji kuna zanjen zaku yi wani aurem ba.” Mamy tayi dariya kafin tayi magana Mama tace, “Aure kuma Adnan? Wanne irin aure ana zaune lafiya?.” Bebi yace, “aure dai nake nufi Mummy, kuna da damar da zaku sake zama a inuwar wani namijin kafin rai yayi halin sa.” Mamy tace, “To Bebi ban da abin ka auren me zamu yi? Ko nace auren me zan yi?, har gwara Mummyn ka babu wanda zai kalle ta yace ta haifi kamar ku, amma ni ai kowa ya san na girma. Me kuma zan nema wanda ban samu ba?, ai sai dai fatan Allah ya sa mu cika da imani.” Yaya Bilal yayi murmushi yace, “Amin Mamy. Amma duk da haka in kuna da ra’ayin hakan ba laifi bane.” Bebi yace, “yauwa abinda nake so nace kenan, wasu yaran su ne suke hana iyayen su mata aure, dalilin hakan wasu iyayen ko suna so saboda yaran su sai haƙura dan kar yaran su ga kamar an ci amanar mahaifin su. Mummy, Mamy wallahi mu muna da ilimi, mun kuma san daidai da ba daidai ba, in har kuna da ra’ayi babu ɗaya a cikin mu da zai baku matsala. Zamu baku goyan baya sosai in sha Allah.” Mummy tace, “mun san da hakan, amma ni a ɓangarena gaskiya bana wannan tunanin a yanzu, ban sani ba ko nan gaba. Amma a yanzu dai zamana a cikin gidan nan yafi min komai kwanciyar hankali.” Mamy tace, “kema kenan balle ni, tunda har aka bar gidan nan ba’a raba gado dashi ba, aka barshi matsayin gidan mahaifin ku in sha Allah kamar yadda aka fitar da gawar mahaifin ku daga gidan nan haka mu ma za’a fitar da mu. Ko yanzu Nabilan Maryam da Ummin Isma’il da Nana Farida sun isa ayi musu aure, muna kai jikokin mu ɗaki mu ma sai su kai mu ɗaki?.” Bebi yayi murmushi yace, “ba a nan take ba ai Mamy, tunda dai kunce bakwa ra’ayi shikenan, amma ko yaushe ƙofa a buɗe take in ra’ayin yin ya tashi zamu karɓe ku hannu biyu.” Yaya isma’il yace, “in sha Allah.” Mama tayi dariya tace, “Allah yasa mu cika da imani. Suka amsa amin Bebi yace, “To ni zan wuce gida” ya faɗa yana tashi tsaye. Mamy tace, “a gaishe da Manal da Ayan.” Ya amsa da zata ji ya fita. BDƘB3P46 Bebi bayan ya fita kai tsaye wajan motar sa ya nufa dan gida yake so ya koma. “Adnan!.” Yaji Maryam tana kira sunan sa ya tsaya a jikin motar yana kallon ta tana tahowa inda yake. Ta ƙaraso inda yake tsaye tace, “Kaji abinda su Yaya suke cewa akan Kamal, ya ka ke gani?.” Ya harɗe hannayen sa a ƙirji ya jingina da mota ya ce, “To ai yanke hukunci naki ne ba nawa ba, in kina ganin zaki koma masa ki koma mana.” “Na sani, neman shawara nazo yi wajan ka da kuma a ka ke gani, a tunanin ka ya kamata na koma ko kar na koma?.” Yayi murmushi yace, “ai tunanin nan naki ne.” Tace, “ai na faɗa maka shawarar ka nake so.” Ya sauke ajiyar zuciya ya ce, “mutuncin ki na ɗiya mace da na yaran ki duka ya karkarata ne a kan komawar ki wajan Kamal, darajar ki da ta yaran ki duka tana gidan Kamal saboda abinda ya faru. Amma matsalar itace; ina jin tsoro in ya canja daga halin da kika sani a baya, ina jin tsoron kar muje daga kan ki ya cigaba da neman mata ko wani abun da yayi kama da haka. Kin fi kowa sanin halin sa, in kina ganin akwai halin sa wanda yake yi dashi a baya wanda daman bai yi miki ba zaki iya ƙin komawa, amma yadda ki ka gani” Maryam tace, “A baya Kamal bashi da wani hali mara kyau da zance bazan koma ba saboda dashi, rabuwar auren mu ma ƙaddara ce da saurin fushi irin nasa. Amma ba wai dan saboda wani hali nasa mara kyau ba.” Adnan yace, “to in dai har aka tabbatar yanzu bai canja hali ba zaki iya koma masa.” Maryam ta yi ajiyar zuciya tana kallon sa yace, “kar ki damu, abinda ya faru a baya bazai faru ba. Nasan zaki kiyaye matsalar da ta jawo aka samu babbar matsalar a rayuwar ki, nasan baza ki sake aikata kuskuren da kika yi ba. Shi kuma amfani yayi da wannan dama kawai, in da babu ita bazai neme ki ba.” Maryam tace girgiza kai tace, “har abada, hakan bazai sake faruwa ba.” Yayi murmushi yace, “ina goyan baya ki koma auren sa indai har bai canja hali ba.” Tayi murmushi tana kallon sa tace, “shikenan na gode Bebi.” Yayi murmushi bai ce komai ba ya shiga mota ya bar gidan. Da wannan fara’ar ya shiga gida yana kiran Manal tun daga falon yana cewa, “kyakykyawar Matata, kina ina?.” Faɗa yake yana shiga ciki amma bai ganta ba har ya shiga ɗakin ta, a nan ya same ta a zaune sai jan numfashi take yi alamun babu lafiya. Da sauri ya ƙarasa ciki ya zauna kusa da ita yace, “Manal Lafiya? Me ya same ki?.” Manal cikin yanayin rashin lafiya tace, “cikina ne yake ciwo, mara ta ɗaurewa take yi.” “Sannu, amma kin jima baki ciwon marar nan ba in zaki yi period, to yau me ya kawo shi?.” Manal tace, “haka kawai yau yake damuna, kaina ma ciwo yake min sosai.” Kallon fuskar ta yake yi yana nazari ta, tunanin sa kar fa yaje ciki ne da Manal hakan ya saka yace, “period ɗin yazo ne ko bai zo ba?.” Ta girgiza kai tace, “bai zo ba.” Ya sauke numfashi yana son yi mata allaura yana tsoron kar yaje da ciki a jikin ta. Tashi yayi ya ɗauko mata pracetamol ya bata ta sha ya kwantar da ita a kan gadon, ya zauna a kusa da ita bayan ya ɗauko towel ya jiƙa shi ruwan ɗumi ya ɗora mata a kan marar ta. Shafa kanta yake yi tana jikin sa a haka har yaga ta fara rufe ido alamun bacci zata yi ya cigaba da shafa kanta har tayi bacci. Sai da baccin nata yayi nisa ya tashi ya ɗauki Ayan da ya fara kuka ya fita daga ɗakin a bayyane yana cewa, “kar fa naje Manal na da ciki, to kwata-kwata kwanan Ayan ɗin nawa da zata yi ciki?. Dole ayi test in ta farka” ya faɗa yana yana ta rarrashin Ayan da yake ƙananun koke-koke. Manal ta jima tana bacci har magriba sannan ta farka, tana tashi ya shigo ɗakin ya kalle ta yace, “ya jikin?.” Ta tashi zaune tace, “naji sauƙi, naji alamun zuwan period ɗin ma yanzu.” Ajiyar zuciya yayi cikin jin daɗin hakan amma bai nuna mata ba, ta kalle shi tace, “da ina ta fargaba kar naje ciki ne dani.” Yayi yar dariya tace, “matsoraciya.” Bata ce komai ba ta tashi ta shiga banɗaki shi kuma ya fita yana cewa, “ki yi sauri ɗan ki yunwa yake ji.” Bayan kwana biyu da maganar Maryam da Kamal yazo gidan wajan Maryam, shi kansa kunya yake ji dole ce ta kawo shi gidan da bazai iya zuwa ba. Bai iya gaisawa da Mamy ba a harabar gidan ya tsaya Nabil ya sanar da Maryam tare suke. Nauyin fitowa ta dinga ji dan bata san saka tozali dashi, zuciyar ta rawa take yi cikin tsananin tashin hankali. Yaya Bilal ne ya same shi a tsaye nan yayi masa iso har babban falon Abba ya ce zai turo masa Maryam ɗin. Babu yadda Maryam ta iya ta amsa kira ta ahiga falon zuciyar ta ma bugawa hawaye yana sakkowa daga idanun ta. Tunda ta shiga taja ta tsaya sai kuka da take yi, jikin Kamal yayi sanyi sosai ya sunkuyar da kai ya rasa abinda zai ce mata. Sun kwashe mintina sama da ashirin a haka kafin yayi ƙarfin halin cewa, “ina sake baki haƙuri a karo na babu adadi Maryam, ki yafe min ki bani dama na gyara kuskure na. Na san na cutar da ke cuta mai yawa, ki yafe ni ki bani dama a karo na biyu.” Bata iya magana ba kuka take yi sosai shi kansa hawaye yake yi ya sauke ajiyar zuciya ya ce, “ki yafe min Maryam, na yi nadamar abinda na aikata miki tun ba yau ba.” Cikin kuka tace, “saɓon Allah da ka saka na aikata shi ka ke na yafe maka Kamal?. Me na yi maka ka zaɓi yi min wannan hukuncin? Me na aikata maka ka zaɓi wulaƙanta ni?.” “Baki yi min komai ba sai alkhairi, sharrin shaiɗan da son zuciya ne ya kaini ga abinda na yi.” “Daman kana da niyar hakan, kana sane ka saka na dinga tura maka makaman da ka yi amfani dasu wajan lalata min rayuwa.” Kamal ya goge idanun sa ya ce, “babu lallai ki amince da abinda zan ce miki, amma wallahi na yi nadamar duk abubuwan da suka faru. Ko wani na gani zai aikatawa wata makamancin abimda na yi miki ni mai hana shi ne.” Maryam tayi murmushin takaici tace, “wai ni ka dinga tozartawa da hotuna, ni ka ɗauki hotona ka saka a duniya duk dan saboda na saɓawa Allah.” Kamal ya ce, “Wallahi Maryam bazarana ce, bazan taɓa iya aikata abinda nake faɗa miki ba. A status ɗin da na saka wallahi sai da na cire number kowa na bar ki ke kaɗai ce zaki gani. Maryam in da ace da gaske zan yi posting da na yi tun farko, wallahi ba zan iya aikawa ba.” Bata ce komai ba sai goge ido da take yi ya ce, “ki yafe min.” “Wataƙila ka mayar da neman mata sabuwa halayyar ka yanzu.” “A’a wallahi, bayan ku mata na guda biyu wallahi ban taɓa bin wata mace ba har yanzu.” Maryam ta kalle shi kallo irin na takaici tace, “wata zaka bawa wannan labarin ta yarda ba ni ba Kamal. Tun farko ni ce na bada fuskar faruwar komai, da na ji maganar ɗan uwana da hakan bata faru ba. Na dinga biyewa zuciyata nake zama tare da kai. Laifina ne ba naka ba.” Kamal ya zube guiwa biyu a ƙasa ya ce, “ki yi haƙuri, ki yafe min na san nayi miki ba daidai ba amma ki sake bani dama na gyara abinda na ɓata. Ina son kare martabar ki ta ɗiya mace da ta yaran ki, bana so a sake samun matsalar da aka samu a auren ki da Mahmud. Ni na jawo miki, ni na shafa miki baƙin fenti. Na dawo yanzu da ƙarfin guiwar goge wannan tambarin da nayi miki Maryam.” Kallon sa take yana durƙushe yana hawaye ta ja numfashi bata iya sake magana ba ta fita daga falon. Tashi yayi cikin jiki dan ya san daman hakan zai faru ya fito ya tafi. Bayan wani lokaci. Lokaci yana ta gudu Maryam da Kamal cikin ikon Allah sun daidaita kan su da taimakon zaɓin da ta barwa Allah, har antsayar da lokacin auren Kausar da Lubna, Maryam kuwa ba a ɗauki wani lokaci ba ta koma gidan mijin ta. Mujahid ya shiga tashin hankali jin wannan labarin amma daga baya ya tabbatar da sharrin sa ne yake bibiyar sa ya koma kansa. Rumana ma da take garin Abuja ta samu mijin da take ganin zata iya rayuwar aure dashi. Mama ta kira ta fara faɗawa labarin, Mama tayi farin ciki sosai kafin ta kira Manal ta faɗa mata. Tana zaune suna waya da Rumana ya shigo ya zauna a lokacin Manal na cewa, “Na taya ki murna Yaya Rumana, Allah ya sanaya alkhairi.” Rumana tace, “amin ƙanwata. Kin yi nisa sosai shiyasa ba’a haɗuwa, ko yaushe muna tare da Mubeena, ɗazu na dawo daga gidan ta.” Manal tace, “nima ina nan zan zo Abuja saboda bikin ƴar Daddy, zan biyo mu sha hira.” Rumana tace, “Allah ya kawo ki, ki gaishe da Bebi in ya dawo.” Ta kalle shi tace, “zai ji in sha Allah.” Kallon ta yayi bayan ta kashe wayar kamar zai yi magana sai ya fasa tace, “An saka auren Yaya Rumana.” Ya girgiza kai tace, “Mummy ta faɗa min, Allah ya sanya alkhairi” ya faɗa yana yanayin fuskar sa yana canjawa. Manal ta kalle shi tace, “Amin. Lafiya naga ka canja?.” Ya ɗan kulle ido yace, “lafiya lau. kice muna da biki sosai. Ga lubna, ga Kausar, ga Ruman, ga Ummi, ga Yusra da Fadila. Duka ƴan matan ƙannen namu zasu yi aure, kuma tsiran auren nasu bai wuce sati ɗaya zuwa biyu ba.” Manal ta girgiza tana murmushi tace, “gaskiya ne. Ina so naje Abuja gidan Yaya Mubeena sannan naje na duba Daddyn Jalingo, Mama tace min yayi rashin lafiya sosai. Sannan ga gida Daddyn mu ma, tunda suka dawo Abuja sau biyu kawai naje. Kuma kaga har da biki Ummi, ya kamata muje shirye-shirye.” Ya girgiza kai yace, “sai ki shirya ki je ki yi kwana biyu ki dawo. Ɗazu ma mun haɗu da adda Halima tace nace miki ta dawo Kano zata shigo.” Manal da murmushi tace, “da gaske? Ai kam da daddare zan je mu gaisa.” Ya ɗaga mata kai tace, “Allah ya nuna mana lokacin.” Ta amsa da amin tana kwantar da kanta a jikin sa. Da daddare suka je gidan adda Halima suka gaishe ta kafin su wuce gidan Mummy. Mimi da Farida suna nan saboda shirin biki da ake ta yi, suka shiga da sallama aka amsa suka samu waje suka zauna. Munmy ta kalle su tace, “barka da zuwa, gwara da kika zo a tattauna daku. Ga shi nan ya faɗa muku nauyin me mai ɗaukar muku da bikin ku.” Yayi murmushi kaɗan yace, “Mummy duk abinda suke so ai sai su faɗa min.” Mimi tace, “Yaya daman ina ta so na kira ka, Akwai wata allura da aka rubuta min akace wai na tabbatar na siye ta.” Ya kalli Mimi yace, “a ina aka rubuta miki?.” “Anc ɗin da nake zuwa,ka ganta” ta faɗa tana miƙa masa takardar da take hannun ta. Karɓa yayi ya kalla ya kalle ta yace, “jinin ki wanne group ne?.” Mimi tace, “AA ce ni.” “ba genotype nake nufi ba, blood group.” “Oh B positive ne.” Ya girgiza kai yace, “Shi kuma Tahir fa?.” Mimi tace, “AB negative.” Ya bata takardar ya ce, “shine matsalar, jinin ki positive ne nasa negative shine matsalar da aka samu.” Farida tace, “matsala kamar ya? Bamu gane ba.” Ya kalle su yace, “ba wata damuwa bace ba ai, kawai kin taɓa ganin inda wuya da ruwa suka haɗu waje ɗaya?.” Farida tace, “A’a, ai dole sai ɗaya ya kashe ɗaya.” “To shine matsalar da yaron cikin ta yake ciki, jinin ta positive ne na mijin ta negative, kuma jinin su ne yake cycleting a jikin yaron. Ya jan nata positive, ya jan nasa negative a ganin ki me zai faru?.” Farida tace, “taya zan sani?, amma yaron zai iya mutuwa yaron.” Adnan yace, “Wannan shine amfanin yin wannan allurar da aka baki. Amma kar ki damu fa bawai babyn zai mutu bane, kina haihuwa za’a yi miki wannan allurar kuma zaki raini yaron lafiya. Tunda har aka baki allurar ai babu damuwa, ana yi miki ita shikenan. Hatsarin ma yafi ga babyn na biyu ko na uku, na farko bai cika mutuwa ba.” Mimi tace, “yanzu yaushe kenan za’a siyi allurar?.” “A’a sai kin haihu, in kika siya yanzu zata lalace ne. kar ki damu fa ba wani abin damuwa bane wannan.” Mama tace, “ikon Allah, tsirfa dai kala-kala.” Yayi murmushi bai ce komai ba ya tashi ya fita. Hira suke ta yi yadda biki zai kasance har dare yayi yazo suka tafi. Bayan wasu shekaru. BDƘB3P47 A cikin shekarun walwala da kwanciyar hankali ta wanzu a ahlin gabaɗaya. An yi shagalin biki  dukkan su babu wacce bata haihu ba a cikin wanda aka aurar. Daddyn Jalingo ya cika alƙawari,duk wanda ya yiwa alƙawarin aikin hajji yaje ya sauke farali ya dawo. Babu sauran matsala ko damuwa a tare dasu rayuwa suke hankali a kwance. Bangaren Maman Manal itama rayuwa take da ƴan uwanta cikin ƙauna da zumunci. Mama sun canja gida, duk da dai a cikin unguwar ne amma sun koma babba mai kyau har matan Baba, an canja musu gida. Abban Jalingo ya siyawa  Haruna mota kamar yadda yai alƙawari. Mama ita kaɗai take rayuwa a gidan sai masu aikin ta, sai kuma Ayan ɗin Manal da tunda aka yaye shi yake zama a wajan ta, duk da indai yaga Manal sai ya bita itama Manal ɗin tana son ɗan ta ya zauna kusa da ita. Manal da Adnan kuwa sai da suka yi shekara ɗaya basa nigeria saboda aiki ya kai shi India, duk da in wani abun ya samu a nasu asibitin yana dawowa yayi abinda zai yi ya koma amma Manal na can bata dawowa. Manal tayi kyau sosai ta sake yin fari, duk da bata yi ƙiba soaai ba amma kai da ka ganta ka san tana cikin farin ciki da kwanciyar hankali. Lokacin da suka dawo nigeria ta fara karatun ta a wata private university tunda dai taga mai gidan yana so amma in a ra'ayi tane ba wani karatu da zata yi. Burin ta ya cika, ta buɗe baban cafe da ake siyar da kayan snacks da coffee mai daɗi, ta zuba ma'aikata da kanta take zama a ciki in bata da makaranta. Goyan bayan da mijin ta yake bata shine silar ɗaukakar ta, dan a lokacin tana cikin best arewa foods bloggers. Kowa ya san ta, musaaman da bbc suka gayyace ta aka yi hira da ita a nan aka san fuskar ta. Ranar wata juma'a ta tashi daga cafe sai ta wuce gida dan ta gaida Mama. Har cikin gidan ta shiga da motar ta ajjiye sannan ta shiga ciki. Tun daga ƙofar falon take jiyo hayaniya, tana shiga taga Adda Halima da Adda Hadiza da kuma Mubeena sai Ayan da yake kan cinyar Mama yana wasa da wayar Mubeena. Ayan ganin Manal sai ya taso a guje yana kiran Ammi yana faɗawa jikin ta. Riƙe hannun sa tayi suka shiga cikin falon ta zauna ya hau kan cinyar ta ta kalli Adda Hadiza tace, "Mummy barka da rana" ta amsa tana cewa, "Hajiya Manal, ke dai bakya ƙiba abin ki kullum gaki nan kamar budurwa." Tayi dariya ta gaida Addna Halima ta amsa kafin ta gaishe da Mama ma ta amsa. Kallon yaya Mubeena tayi tace, "Taɓ Yaya Mubeena Wallahi kin zama lutiya." Mubeena tayi dariya da ɗan ta a jaririn da ta haifa mai sunan Daddy suna kiran sa da Hydar, sao ai babbar ƴar ta mai sunan Maman mijin ta da suke kira da Baby a kusa da Mama a zaune. Mubeena tace, "kema ai kin yi ƙibar ai." "Ai in na kai ki ƙiba na daina fita" ta faɗa tana dariya sosai. Mama ta kalle ta tace, "Ke wai Manal baza ki yiwa kan ki faɗa ba?." Gaban Manal ya faɗi ta kalli Mama tace, "Mama me nayi?." "Baki san ne kika yi ba ko?." Manal tayi shiru bata ce komai ba Mama tace, "shekarar Ayan huɗu a duniya, kin fara karatu har kin kusa gamawa amma baki da ciki har yanzu. Kalli Yayar ki, a bayan bayan auren ki tayi aue, yanzu gashi ta haifi ɗan ta na biyu. Ke a ganin ki daidai kenan?." Adda hadiza tace, "Wallahi abinda yake zuciyata kenan, ke waye ya faɗa miki ana yin family planning daga yin haihuwa ɗaya?. Da yarintar ki da komai har shekara huɗu baki kuma haihuwa ba me kike jira?." Manal idon ta ya ciko da hawaye zata yi magana Mama tace, "da anyi magana ido ya ciko da hawaye har yanzu kin kasa canjawa daga yadda kike a da. Haka kawai daga haihuwar farko sai ki ɗauki zugar mijin ki sha wani abun?, Ki bari ki yi guda biyu mana in yaso sai ki yi tazarar, yanzu in haihuwar ta tafi kenan fa?." Adah Hadiza tace, "aure zai yi mana, zai zauna da wacce take da da ɗaya ne." Addah Halima tace, "Manal planing ɗin yayi yawa, ki dakatar da duk abinda kike yi yanzu ki samu ciki ki haihu, in ba haka ba a dangin mijin ki za’a fara yi dake ana cewa ai kin ƙi haihuwa dan haka ya ƙaro wata. Ba laifi bane dan kin huta bayan haihuwar ki amma hutun naki yayi yawa, shekara huɗu fa da yawa, ko yanzu kika samu ciki kafin ki haihu an tafi shekara biyar." Manal ta fara kuka ta sunkuyar da kai ƙasa Mama tayi tsaki cikin fusata tace, "aikin kenan, da an yi mata magana sai kuka, kije ki yi Manal kar ki haihu kin ji." Adda Halima ta kwantar da murya tace, "kar ki damu Manal, faɗa min me kike sha ko me mijin naki ya saka miki?." Manal kuka take yi dan in tace musu babu abinda take yi ba yarda zasu yi ba gwara tayi shiru kawai. Mama tace, "ƙyale ta kar ta faɗa, ita ta sani." Manal ta kalli Halima tace, "Wallahi small Mom babu abinda nake sha, tun bayan haihuwar Ayan ban taɓa shan komai wai dan kar na haihu ba, kuma bai taɓa bani magani ba, sannan bai saka min komai ba." Mama tayi tsaki tace, "kyaji da ƙaryar ki. kinga Manal rayuwar ki ce fa ba tamu ba, ni ba planing ɗin nayi ba amma Allah ku biyu kawai ya bani daga ku ban sake ba, ke da kika ga ɗayan ya ishe ki ai shikenan." Adda Hadiza tace, “to mijin ta da wadatar sa da komai family planing ɗin me zata yi?, in ma son yin take ina laifin na shekara biyu?.” Mama bata ce komai ba. Addah Halima tace, “Ai ba laifi bane dan tayi, kawai ba a cika son masu haihuwar fari su yi bane saboda gudun matsala, amma ba wani abun bane.” “Halima Manal fa tana sane tayi, saboda ta gama makaranta ba ciki babu jego shine ya saka tayi.” Adda Halima tace, “tace bata shan komai, mu yi mata uzuri. Kuma kun san ciwon nan nata yana ham ɗaukar ciki da wuri, wataƙila matsalar sa ce ta kawo hakan.” Mama tace, “ke kike goya mata baya Adda, komai tayi sai kin yi ƙoƙarin kare ta. Mijin ta fa likita ne, shi yasan irin surkulan ku na likitocin da yayi mata aka kawo yanzu bata haihu ba.” Adda Halima tace, “wallahi babu lallai akwai abinda ya bata, ciwon ta kawai zai iya hanta ɗaukar ciki da wuri” ta kalli Manal tace, “amma in kina da ra’ayin samun cikin yanzu ki dinga shan folic acid kullum guda ɗaya, zai taimaka miki wajan samun cikin.” Adda Hadiza tace, “lallai ke kike zuga ta, wato in tana da ra’ayi ko?.” Mama ta kawar da kai kawai bata ce komai ba. Hadiza tace, “Manal ai gwara ki yiwa kan ki faɗa, kinga Ayan yana wajan Maman ki kema kin samu wanda zai zauna a wajan ki.” Mama tace, “Manal ce zata bar min Ayan?.” “Gashi kuwa yana wajan ki.” “Jira kiga dashi zata tafi, daman hutun makarantar ya ƙare ai. Baban sa har ya fita yi min kara.” Suka yi dariya suna kallon Manal. Manal zaman gidan gabaɗaya ya ishe ta, ta tashi ta shiga ɗakin Mama ta kwanta Ayan ya biyo ta ahima ya kwanta a kusa da ita. Mubeena ta shiga ɗakin itama ta zauna tace, "ke wallahi kar ki wani damu ni da nayi haihuwar da wuri haushi nake ji, gwara ɗan ki da ya girma har makaranta gashi yana zuwa. Su Mama ɗauka suke haihuwar yanzu irin ta dah ce, yanzu kana hutawar ma ya ka cika balle kana haihuwa a kai a kai. Wallahi kin ganni na je na saka infant, bazan sake haihuwa ba sai nan shekara biyar in sha Allah, wannan cikin ma bisa tsautsayi aka same shi." Manal ta kalle ta tace, "Balle ma Yaya Mubeena wallahi babu abinda nake sha, babu abinda nake yi balle nace shi ya hana ni sake yin ciki." "Ke kar ki damu da fadan su, ki cigaba da karatun ki a nutse." Tare suka zauna a ɗakin suna hira har su small Mom suka tafi. Itama sai gab da sallar magriba ta bar gidan dan baya so tana yin tuƙin dare da baza ta tafi ba sai dare, da wannan damuwar ta tafi gida dan tunda suka sako maganar zai ƙara aure shikenan hankalin ta ya tashi. Tare da Ayan suka koma tunda ya ganta ya maƙale mata. Sai da tayi wanka shima tayi masa wanka sannan ta fito ta shirya shi suka fito falo ta kunna masa cartoon yana gani ita kuma ta wuce kitchen ta ɗorawa Bebi abinda zai ci. Bayan ta gama girkin tayi sallah ta fito falon ta zauna suna kallon tare aka aka kira ta a waya. Kallon lambar tayi taga sabuwa ce bata santa ba sai ta share bata ɗauka ba aka sake kira, Ayan yace, "Ammi ana yi miki waya." Ɗaukar wayar tayi ta saka a kunnen ta daga can ɓangaren akace, "Fatima meyasa in ina miki waya bakya son ɗauka?." Gaban ta ya faɗa jin muryar wanda bata yi tunani ba tace, "Malam na faɗa maka ni matar aure ce, Meyasa ka ke takura min da waya ne?." "Baki kama da matar aure ba Fatima, inda kina da aure zan sani ko a bakin ƙawayen ki, amma gabaɗaya baki kama da wacce take da aure ba." Manal ta dafe kai tace, "to in baka daina kirana ba zan faɗawa mijina, akan wanne dalili na faɗa maka ina da aure ka ƙi daina bibiya ta?" tana faɗa ta datse kiran tana cewa, "wannan mutumin ya takura min, haba don Allah, na faɗa masa ni matar aure ce meyasa yake takura min da waya?." "Waye ya takura miki da waya?." Gaban ta ya faɗi matuƙa jin maganar Adnan, ta wara ido waje ta waiwayo a hankali tana kallon sa. Yana tsaye daga nesa yana aiko mata da kallon da ya saka ta ruɗewa. Sam bata ji motsin sa ba balle ta san ya shigo sai maganar sa kawai ta ji a kanta. A dabarbace tace, "sannu da zuwa." Ayan ya tashi a guje ya faɗa jikin sa shi kuma ya dauƙe shi yana murmushi yace, "ɗan gidan Mama, yaushe kazo?." "Tare da Ammi muka zo, Abbie ka siyo min popcorn?." "Ai ban san kana nan ba Ayan ɗina, da na san kana nan da zan siyo maka." Zama yayi a nesa da ita Ayan na jikin sa yana yi masa surutu shi kuma yana biye masa suna hira. Tashi Manal tayi jiki a sanyaye gabaɗaya tsoro ya kama ta, tsoron sa take ji a duk lokacin da ta san tayi ba daidai ba ya haɗe mata rai. Duk da nature ɗin sa ce ɗaure fuska amma in tayi laifi yanayin daban yake. Abinci ta kawo masa bai kalli abincin ba ya riƙe hannun Ayan suka tashi suka shiga ɗakin sa. Shi kaɗai ya fito bayan ya canja kaya ya zauna ya fara cin abincin, har ya gama bai kalle ta ba kuma bai yi magana ba. Sai da ya gama ta kwashe kayan ta kai kitchen ta dawo ta zauna tayi shiru ta kasa magana. Kallon ta yayi ya ce, "sai nace ki faɗa min sannan zaki faɗa?." Manal ta sauke ajiyar zuciya tace, "takura min yake yi da magana a school bana kula shi, ban san a inda ya samu number ta ba ya fara kira na jiya. na faɗa masa ina da aure amma yace wai banyi kama da mai aure ba. Nayi blocking wancan number shine ɗazu ya canja number ya sake kirana har yanzu bai yarda ina da aure ba." Yayi ƙaramin tsaki yace, "kenan bani da amfanin da zaki faɗa min tun lokacin da ya fara yi miki magana?." Manal tace, "kayi haƙuri, naso na faɗa maka tsoro nake ji." "Tsoro! saboda dukan ki zan yi?. Wani banza yana yi miki magana a makaranta yana cewa yana son ki baza ki faɗa min ba?, Har ya samu lambar ki ya kira ki shima baki iya faɗa min ba?." Ganin faɗa yake mata sosai sai sai tace "kayi haƙur...." Ka katse ta yace, "bazan yi haƙuri ba, in kika sake cewa nayi haƙuri sai na fasa miki baki. Ni zaki yiwa wannan wulaƙanci Manal?, Namijin da ba maharramin ki ba ya dinga yi miki waya har kina amsawa? Meya amfani na da ba'a ki faɗa min ba?." Ta sunkuyar da kai tayi shiru bata ce komai ba. Cikin fusata yace, "dan tsabar shirme da tsabar shashanci wani yace yana son ki a makaranta baza ki faɗa min ba?, saboda kin raina ni ko?.” Nan ma tayi shiru bata ce komai ba yake yin dogon tsaki alamun ran sa ya ɓaci sosai yace, "meye sunan sa?." A ray bane tace, "Malam Umar Haɗeja, yana koyar damu Food hygn." Kai ya girgiza ya tashi ya bar nata falon. Ajiyar zuciya tayi bata so yaji maganar ba gashi yanzu abinda tazo masa dashi ya watse bazai saurare ta ba. Koda ta shiga ɗakin nasa ma yayi kwnaciyar sa shida Ayan, ta kalli gadon Ayan da yake gefe ta sake kallon sa tayi ajiyar zuciya. Ta kalle shi dan ta san idon sa biyu a sanyaye tace, "kayi haƙuri." Tsaki yayi bai ce nata komai ba ta zauna kawai tana kallon sa. Da wuri yayi bacci ba tare da ya sake yi mata magana ba, ita kuma tana zaune tana kallon sa kafin ta tashi ta ɗauke Ayan ta saka shi a bed ɗin sa ta kwanta a gefen sa bacci ya ɗauke ta. Da safe ta riga shi tashi lokacin da ya tashi har ta shirya Ayan ta gama haɗa breakfast. Yana tashi wanka yayi ya ɗauki key ɗin mota ya fita daga gidan, bai jima ba ya dawo yayi breakfast ya canja kaya ya sake fita bai ce mata komai ba. Itama fita tayi ta shiga cafe ɗin ta ita da Ayan a nan suka zauna har la’asar sannan ta fito suka je gidan Mummy dan ta gaishe ta. A falon Mummy ta samu Bebi yana cin kilishi da take gaban Mummy a ajjiye. Ayan yana shiga ya tafi wajan Mummy a guje ta riƙe shi dariya tace, "A'a Ayan saukar yaushe?." Ya zauna a kusa da ita ta bashi kilishin yana ci sannan ta kalli Manal suka gaisa Mama tace, "shine kika je kika ɗaukowa Mama shi?." "A'a wallahi, jiya ne da naje ya ganni sai ya maƙale min." "Amma Ayan ba alƙawari" Mama ta faɗa tana jan kumatun sa. Mama tace, "Manal kici mana." Ɗauka tayi tana ci Adnan ya tashi ya fita Mama ta kalle ta tace, "Ya makaranta?." Manal tace, "Lafiya lau Mummy, jiya Mama tace na gaishe ki." Mummy tace, "ina amsawa" ta faɗa tana murmushi. Mummy ta sake cewa, "Kausar tazo tana ta ciwon baki tace baki je ba." Tayi dariya tace, "Wallahi Mummy yau nayi niyar zuwa, to ban samu dama ba har yanzu." "Ai na sani na faɗa mata, nace laifin Yayan ta ne." Manal tayi dariya tana cin kilishin. Ganin magriba tayi sai ta miƙe tace, "Mummy bara na wuce." Mummy tace, "baya son tuƙin dare ko?." Ta ɗaga kai tace, "Baya so." "Allah ya kiyaye. Ayan ka tafi ko?." Ya maƙale kafaɗa alamun bazai tafi ba, Mummy tace, “a nan zaka zauna?.” Ya ɗaga kai alamun eh Manal tace, "Mummy na bar miki shi" ta faɗa tana murmushi ta fita ta hau mota ta tafi gidan ta. Ko da ta koma aallah tayi sannan tayi masa abinci tana ta sauri kar ya dawo, tana gamawa ta shiga wanka a lokacin ya shigo ya sake fita sai da yayi sallar i'sha sannan ya dawo. Da ya shigo ya same ta a zaune akan dining bai ƙarasa ba ya zauna akan kujera yace, "Kawo min abincin nan." Ta amsa ta ɗauko ta kawo masa ta zuba masa ya fara ci itama tana ci a plate ɗin da yake ci. Yana gamawa ya tashi ya shiga ciki ya tare da yace mata komai ba. Ta san fushi yake da ita shiyasa yaƙi yi mata magana, ta kwashe ragowar abincin na cikin kwanon ta kaiwa mai gadin gidan sannan ta kai kayan kitchen ta ajjiye ta shiga ɗakin ta. Kayan ta cire ta saka na bacci ta saka body mint ɗin da yake so a jikin ta sannan ta wuce zuwa ɗakin sa. A zaune ta same shi yana danna waya ta ƙarasa ta zauna a kusa dashi ya kalle ta ya ce, "Ayan ɗin fa?." Manal tace, "yace a wajan Mummy zai kwana." Shiru yayi bai ce komai ba ya cigaba da abinda yake yi. A raunane tace, "kayi haƙuri, na san nayi maka laifi amma ka yafe min don Allah." Kallon ta yayi ya ɗauke kai bai yi magana ba, ta sake cewa, "Don Allah, Don Annabi ka yi haƙuri. Bazan sake ba in sha Allah." "Saboda kawai kin raina ni, kin raina aurena da yake kan ki wani yana cewa yana son ki a waje baza ki iya faɗa min ba. Harda samu number ki yana kiran ki shima baki sanar dani ba. Dan tsabar kin gama raina ni sai kika ce wai tsoro kike ji, dukan ki zan yi in kin faɗa min ko me?." Ta riƙe hannun sa duka biyun tace, "kayi haƙuri don Allah, nayi laifi na sani amma kayi haƙuri bazan sake ba." "Bayan shi sai waye?." Manal tace, "babu kowa." "Ban yarda ba, domin ina zuwa school ɗin ɗazu ina faɗar sunan ki shugabar makarantar taku tambaya yake daman da gaske kina da aure. Manal ki faɗa min waye bayan shi?." Ta fara kuka tace, "Wallahi!, Wallahi!! bayan shi babu kowa, in akwai za’a faɗa maka." "Naji. Meyasa suke miki kallon baki da aure? Ɓoyewa kike yi bakya so a san ke matar aure ce?." Ta rausayar da kai tace, "ta ya zan rufe darajar da Allah yayi min?, Wallahi bana ɓoyewa kowa faɗa nake ni matae aure ce a ko ina. Kuma har da Ayan ina zuwa, an san ni na haife shi.” Ya girgiza kai yace, "ban lamunci cigaba da saka abaya in zaki je makaranta ba, dole ki dinga saka dogon hijjab kamar yadda kike yi a baya." Manal tace, "to, daman kuma bana shigar banza kafi kowa sani." "Na dai faɗa miki, gwara ma ki yi kiyi ki gama makarantar a huta." Tayi shiru jin abinda ya ce kamar ba shi ne ya takura mata akan karatun ba. Jin yayi shiru sai ta kalli fuskar sa tace, "ka yi haƙuri." Ya kalle ta ya ce, "ya wuce, amma kar ki sake ɓoye min irin wannan ko a makaranta ko a hanya, yanzu da naji labari naje school ɗin naku nayi musu gargaɗi, in ya sake yi miki magana ki faɗa min." Manal tace, "to zan faɗa maka in sha Allah." Baice komai ba ya cigaba da danna wayar sa. Tayi shiru bata ce komai ba sai wasa da hannun ta da take yi. Ya ɗago ya kalle ta ganin alamun da magana a bakin ta ya ce, "me kike son cewa?." Manal ta kalle shi tace, "to ka ƙi ka saki fuskar ka, akwai abinda nake so na faɗa maka wannan fuskar ce bana so.” Ya kalle ta yace, "me kike so kice?." "Don Allah kayi dariya, na fa baka haƙuri kuma kace ka haƙura." "Abin ne yake min ciwo, matata ace wani yana bibiyar ta a waje kuma bata faɗa min ba. Bazan ɓoye miki ba kin bani haushi kuma kin ɓata min rai." Manal ta kulle ido jin ya dawo da maganar da ya ce ta wuce tace, "ka yi haƙuri, bazan sake ba in sha Allah." "Daman laifina ne ai da na saka kika koma makaranta, a yadda kike ɗin nan ba dole ma ace ana son ki ba?. Mtswww!" Ya faɗa cikin takaici. Manal tayi shiru dan ta san daman zata sha mita kafin wannan maganar ta wuce. Jin tayi shiru sai ya kalle ta yace, "wato ke maganar bata damun ki ma ko?, Ko da yake ni aka taɓa daman ai ba ke ba." "Don girman Allah ka yi haƙuri, ka yi haƙuri maganar nan ta wuce don Allah" ta fada cikin gajiya da maganar sa tana hawaye. “Maganar ta wuce ko Manal? Wani yana waje yana son matata ki kalle ni kina ce min maganar ta wuce ko?. Kin kyauta.” Manal ta dafe kanta tayi shiru bata ce komai ba. Bata son mitar nan tasa, tafi so in tayi laifin ta bashi haƙuri ya haƙura a wuce wajan kawai. Amma shi in ya dinga maimaita abin da ya wuce sai kaji kamar a lokacin ya faru. Ya kawar da kai gefe ta riƙo hannun sa duka biyun ta saka a wuya ta tace, "kaji damuwar nan har zazzaɓi ya saka ni, ka yafe min ka daina fushi dani don Allah." Ba tare da ya kalle ya ba ya ce, "Nace miki ya wuce ai ko?." "Amma ko dariya ka ƙi kayi min." "To Manal dariya zan saka ki a gaba ina yi kamar wanda bashi da hankali?." "Amma ko kaɗan ne ka saki fuskar mana." Zuba mata ido yayi na wani lokacin kafin ya ɗauke kansa bai yi dariyar ba kuma fuskar sa a ɗaure. Tashi tayi tace, "tunda ka ƙi min dariya na baka haƙuri ka ƙi haƙura shikenan" ta faɗa zata wuce shi. Kamar ya share ta sai dai ƙhamshin da take yi ya ɗauki hankalin sa sai ya riƙo hannun ta, bata juyo ba yace, "to ai nace na wuce ko? Ina kuma zaki je?” Ya faɗa yana kallon ta. Bata juyo ba sai hawaye da yake yi ya tashi tsaye ya matso kusa da ita ya juyo da ita ya ce, "haba Manali meye na hawayen kuma? Ai na ce wuce na daina fushin." Ta kalle shi tana turo baki tace, "ina ta baka haƙuri ka ƙi ka kula ni, tun jiya ko magana baka yi min ba. Kai ta wulaƙantani im nayi laifi, na dinga bin ka kamar jela ina baka haƙuri kana share ni.” Yayi ƴar dariya ya kwantar da ita a ƙirjin sa ya mayar da hannun sa duka biyun ya riƙe bayan ta yace, "ke kin san in dai abu a kan ki ne bana ɗaga ƙafa, haushin da naji da baki faɗa min ba shiyasa na nuna miki kuskuren ki. Sai da naje makarantar na yiwa tufkar hanci hankalina ya kwanta. Wallahi da abin na kwana a raina shiyasa ina tashi can naje.” Tana kwance a ƙirjin tace, "to ai nace na karɓi kuskurena, nan gaba ko an samu irin haka zan faɗa maka." "Uhum haka kika ce" ya faɗa yana kai hancin sa wuyan ta yana jan numfashi. Kallon fuskar sa take yi shima ita yake kallo sai tayi murmushi tana shagwaɓe fuska alamun an yi mata ba daidai ba, murmushin shima yayi ya ce, "to yanzu na daina fushin me zaki bani?, Kin ga dai ɗan ki baya nan kamata yayi till down a bani milky" ya faɗa yana sake mayar da ita jikin sa idanun sa a lumshe. "Na tara maka da yawa amma yanzu na fasa baka" ta faɗa tana murguɗa baki. "Haba my love ni ɗin? Ni ne fa" ya faɗa yana ɓalle bottles ɗin gaban rigar ta. Manal tace, “ba wulaƙanci ka ke yi min ba.” “Ai na daina daga yau biyayya zan dinga yi miki, duk abinda ki ke so shi zan dinga yi.” Kafin tayi magana yace, "my life partener....me zaki bani? A tausayawa Adnan ɗin Mummy” ya faɗa yana zame rigar ta daga sama. Lokaci ɗaya masoyan suka hargitsa kan su da salon soyayyar da suke yiwa junan su. BDƘB3P48 Washe gari da yake weekend ne har ƙarfe goma na safe suna kwance makaƙe da juna,bai tashi ba itama ya hanata tashi. Tana kwance a jikin sa yana bin zanen kitson kanta da yatsan sa a hankali. Kallon sa tayi tace, “Partner ka bari naje nayi mana breakfast, yau ko buɗe ƙofar falo baka yi ba. Gashi naji zuwan Lubabatu har ta juya ta koma saboda ban buɗe ƙofa ba.” “Babu inda zaki je yau, nuna tare a nan, matso kusa dani” ya faɗa yana sake jawo ta jikin sa. Ta mirgina tayi ruf da ciki jikin sa tana kallon idon sa tace, “to in ban fita ba yau me zamu ci?.” “Gani gaki.” Ta turo baki gaba tace, “gani gaka me?.” Ya ja kunnen ta ya faɗa mata abinda zai ce, kifa kanta a ƙirjin sa tana dariya. Ya ja gashin kanta yace, “Matata mai jin kunyar mijin ta.” Ta ɗago ta kalle shi tace, “ni dai ka bari naje nayi girki, in kace abinda zamu tayi kenan ai ba ƙoshi zamu yi ba yunwa zamu dinga ji.” “A’a ni dai ƙoshi zan yi” ya faɗa mata yana komawa saman ta ta dawo ƙasa. Runtse ido tayi tace, “Wayyo Allah ka danne ni bana iya numfashi.” Hancin sa yake gogawa akan nata tace, “don Allah ka ɗaga ni.” komawa yayi inda yake ya kwanta tana ta jan numfashi ta kalle shi shima ita yake kallo tace, “na tambaye ka?.” Gira ya ɗaga mata alamun yana ji, Manal tace, “Meyasa lokacin auren mu kace in aka bani magani kar na sha?.” Yayi dariya mai sauti yana kallon ta yace, “Ke kuma duk wannan shekarun da aka ɗauka baki taɓaa tambayata ba sai yau?. Ai da ranar da aka kawo ki zaki tambaye ni.” Ta kalle shi tace, “yau abin yazo raina, a lokacin na dinga tunani nace shi bawan Allah nan meyasa yace haka?. Kuma kamar wacce ka nawa umarni komai aka bani bana sha, na san dai na sha wani magani da kunu shikenan abinda na sha.” Dariya yake yi yana kallon ta yace, “ahhh yaro man kaza, wato meyasa ko?.” Tayi dariya tace, “ka faɗa min.” “Ke da an bani wannan maganin da daren mu na farko Allah sai na farka ki, daƙyar baki kwana a asibiti ba. Wahala zan sha kema wahala zaki sha.” Manal tace, “shine dalilin?.” “Eh mana, kuma bana so a baki maganin da zai canja min asalin taste ɗin ki, Nafi so na san kina taste ɗin da Allah yayi miki, na san ya zaƙin zumar matata yake shiyasa nace don Allah kar ki sha. Yanzu kinga na san asalin ki, in ma wani abun aka baki kika canja na sani.” Manal tace, “amma ko abinci ne aka saka masa maggi yafi daɗi.” “Ita kuma sabuwar zuma mai kyau kin taɓa ganin an saka mata sugar kafin a sha?.” Ta girgiza kai alamun a’a yace, “in aka ƙara mata sugar ma zaƙin na cutarwa zai zama, misalin ke kenan.” “Ai ni ba zuma bace.” “Kafi zuma ce, na tabbatar miki da kin fita zaƙi.” Ta kulle idanun ta yayi dariya yace, “ni haka nake so na ji ki bana son wannan shaye-shayen na banza. In zaki yi ma ki yi natural wanda zaki haɗa da kan ki. balle ke da kike shan cucumber ma kike cin Apple ai ba ba’a magana” ya faɗa yana ɗaga mata gira yana cizar lips ɗin ta. Manal tace, “gwara ma da ban sha ba, a haka ma na sha wahala ina ga na sha wani abu.” Yayi dariya yace, “kina gani kasa ƙyale ki nayi da asubar ranar sai da na sake ɗanɗana zumar ki, ke ɗin ta daban ce my love. Asalin zaƙin ki saka ni yayi na fita daga hayyacina, na rasa inda zan saka raina a wannan ranar. Duk da yanayin da ki ke ciki na ciwo da raɗaɗi na kasa ƙyale ki sai da na sake komawa. Ke ta daban ce my love” ya faɗa yana shafa fatar cikin ta a hankali. Manal ta ɗan sunkuyar da kai tana murmushi ta kalle shi tace, “ina so na daina jin kunyar ka amma na kasa.” Yayi dariya yace, “baza ki iya ba, halittar ki ce a haka. Me za’a yi da mace da bata da kunya?.” Numfashi ta sauke yanayin fuskar ta ya canja zuwa na damuwa ya kalle ta yace, “ya dai?.” Ta kalle shi ta ɗora hannun ta a akan fuskar sa tace, “Partner yanzu in akace daga Ayan bazan sake haihuwa ba zaka zauna dani kaɗai baza ka ƙaro wata ba?.” “Meya kawo wannan maganar nuna cikin nishaɗi kuma?.” “Kawai tambaya nayi.” “Hmm Manal nasan ki fa, akwai dalilin tambayar.” Manal tace, “Wai baka ga tunda na haifi Ayan ko missing period ban ƙara yi ba?, ana ta yi min faɗa wai planing nake yi nace babu abinda nake sha an ƙi yarda dani. Partner anya babu abinda ya hana ni sake haihuwa?.” Kallon ta yake da mamaki ya tashi zaune itama ta tashi yana kallon ta yace, “partner Ayan ɗin har nawa yake da zaki damu?.” Ta sake karyar da murya tace, “ni dai ina so na sake haihuwa a kwanakin nan, Mama ma sai faɗa take min Yaya Mubeena daga auren ta tana da yara biyu ni har yanzu ban sake ba. Partner kuma bana sha komai ba ko?.” “Babu abinda kika sha lokacin zuwan ta ne bai yi ba kawai.” “Nidai yanzu ina so, Ina so na kuma haihuwa partner.” “Ikon Allah, kece mai kuka a cikin Ayan saboda kin samu ciki da wuri, da kika haihu kika dinga jaddada min ke kafin ki dawo ɗakina ba sai na kai ki an baki maganin family planing baza ki haihuwa ba sai shekara biyar. Yanzu shekara biyar ɗin ma bata yi ba kin fara complain, ɗan Adam mai iya mana sai Allah. Wancan ya baki haihuwa da wuri kika dinga kuka, wannan ya jinkirta miki kin nuna kin damu.” Manal tace, “bawai na damu bane, mutane ne suka ganin kamar family planing nake yi.” Adnan yace, “ina ruwan ki da mutane? Indai dan mutane zaki yi abu kina haihuwa ma wani cewa zai yi kin haihu da wuri.” “Ni dai ka san yadda zaka yi dani.” Yayi dariya yana mamakin ta yace, “ya zanyi dake kuwa?, ɗauko ciki zan yi na buɗe bakin ki na zuba a ciki?.” Manal ta turo baki tace, “ba kai ka san ta ya akayi aka samu wancan da wuri ba?.” Yayi dariya yana girgiza kai yana mamakin autancin Manal yace, “ai kam na sani, zan kuma sake bin wannan hanyar amma ina da sharaɗi.” Manal tace, “ina jin ka.” Adnan yace, “na farko ba complain; ke kin gaji bayan ki ya riƙe waye waye babu, na biyu babu guduwa ki kulle kan ki, na kuka babu yi min kuka.” Manal ta kalle shi idon ta yayi rau rau kamar zatayi kuka. Ya wara hannayen sa yace, “ba dole a lamarin nan fa, ke kika kawo kan ki.” Manal a sanyaye tace, “to naji na yarda, amma kar ka dinga min mugunta kaji.” Yayi dariya yace, “wannan kuma duk daga baya ne, ba dai ciki kike so ba?.” Ta ɗaga kai tana kallon sa, yadda ta ɗaga kai ya bashi dariya sosai ya girgiza kai yace, “ki ɗauka an yi an gama. In dai ciki ne cikin kwanakin nan zan samar miki dashi.” Kallon sa tayi tace, “ban yarda da wannan murmushi na ka ba.” Yace, “oho miki dai, taimaka miki zan yi fa.” Manal tace, “to dan zaka taimaka min baza ayi min mugunta ba.” Ta sake kallon sa yana dariya ya kalle ta ya sake yin dariya yace, “Hajiya Manal, kar ki damu kin kusa yin ciki.” Manal bata ce komai ba sai kallon sa da take yi ganin ya mayar da abin wasa. Bebi yace, “ko zamu fara ɗaukar hanyar daga yanzu ne?.” Ta rausayar da kai tace, “yunwa nake ji.” “Kin ji matsalar ai, taya zaki samu ciki a haka?, da an yi magana ki kawo uzuri.” Manal ta turo baki tace, “ni fa sai a fasa wallahi.” “A fasa mana, wa za’a yiwa kishiya saboda bata sake haihuwa ba?.” Ta kalle shi tace, “Da gaske zaka iya yi min kishiya saboda ban haihu ba?.” “Eh, yara da yawa nake so kuma ke ɗaya kika haifa.” “Amma baka kyauta min ba,kuma duk son da kakw cewa kana yi min ba so bane” ta faɗa tana fara yi masa kuka. Baya so a ɓata masa daddaɗan maraicen da yake ciki mai daɗi da zallar soyayya sai yace, “Wasa fa nake miki, ki daina kuka ke baki san wasa bane?.” Manal tace, “tsoro nake ji kar kace zaka ƙaro wata saboda na haihu sau daya.” Ya kwantar da ita a jikin sa yace, “ni ko baki haihu ba babu wacce zan ƙaro balle ga mai sunan Abbana ina dashi me zai deme ni?.” “Da gaske ka ke?.” “Da gaske nake mana Manal.” “Amma meyasa yanzu ban haihu da wuri ba?.” “Haka Allah ya rubuta, kuma na faɗa miki ciwon ki yana hana mata irin ku saurin samun ciki, a lokacin farko ma Allah ya taimake ki kika samu da wuri, a wannan lokacin ma Allah ya jinkirta miki. Kuma ni naji daɗin hakan, kinga ga Ayan har ya far zuwa makaranta in kika haihu baki da fargabar raino zai haɗar miki biyu.” Manal tace, “nima naji daɗi da ya kai wannan shekarun ban kuma haihuwa ba, kaga har makaranta na kusa gamawa hankali kwance. kawai ina jin tsoro kar naje haihuwar ta tafi.” “Babu inda ta tafi, indai haihuwa sai kin gudu da ƙafar ki. Amma in kina son samun cikin zan kawo miki folic acid ki dinga shan da kullum zai taimaka miki wajan ɗaukar ciki.” Manal tace, “Haka ma Small mom tace min ɗazu.” “Shi folic acid ko wacce mace in tana son ɗaukar ciki zata iya shan sa, bashi da side effect.” Manal ta kalle shi ta sauke tace, “ina son haihuwa amma tsoron haihuwar nake ji, kuma tsoron wannan shan sugar da nayi a lokacin Ayan nake yi.” Adnan yace, “ke dai kika sani, kince kina so kince bakya so kuma yanzu.” Ta kwanta a jikin sa tace, “ina so bana so.” Yayi dariya yana tungure mata kai yafe, “daga baya kenan.” Wayar sace da take gefe take ƙara ya kalla yaga Huzaifa ne ya kalle ta yace, “Wannan Yayan naki ya takura min, amma bara nayi maganin sa” ya faɗa yana ɗaukar wayar ya saka a speaker. Huzaifa yace, “wai kana ina ne? Baza ka fito ba yau?.” Adnan yace, “bazan fito ba, ka ishe ni da waya ka takura min, babu damar na zauna a gida da matata sai ka fara yi min waya?. Itama gata a zaune tace ka takura mata ka hanata sakewa da mijin ta, malam kar ka sake kirana kana ɓata min yanayin da nake ciki.” Manal ido a buɗe take kallon sa ya kalle ta ya ɗaga mata gira. Huzaifa yace, “ƙarya ka ke, ƙanwata baza ta taɓa faɗar haka ba wannan sharrin ka ne. Kai ta zama in kaga dama kar ka fito sai ta haihu sau goma.” Bebi yace, “ka san da hakan ka kira ni?.” “Kai ta zama kaji, kar ka fito. Kuma wallahi wani abun ya samu ƙanwata maganin ka zan yi.” Adnan yayi dariya kawai ya kashe wayar yana kallon Manal. Tace, “wai baka jin kunyar da ka ke faɗa masa haka? Yayana ne fa.” “Yayan naki fa, ai na faɗa miki ni a Huzaifa nake kallon sa ba Yayan Manal ba.” Ta tashi daga kan gadon ta sakko ƙasa ta tsaya a tsaye tace, “Kaji tsoron ranar da zai murza kambun sa na babban Yaya, sai ka zube masa a ƙasa.” Ya Harare ta yace, “wuce nan my love, sau ɗaya ya raina min hankali kuma ya wuce.” Tayi dariya tace, “partner yunwa nake ji ni dai fita zan yi.” Shima sakkowa yayi yace, “muje tare.” Tare suka fito suka shiga kitchen tayi musu girki yana zaune har ta gama, suka ci abincjn bayan sun gama ta wanke kwanukan a lokacin ya koma daki ta san wanka zai yi yayi alwala saboda lokacin sallah. Itama ɗaki ta shiga tayi tana ta jin haushi ko walha bata yi ba gashi azahar tayi. BDƘB3P49 Adnan sai da yaje yayi sallah ya dawo ya sake samun ta a kitchen, ya shiga yana kallon ta yace, “my chef me za’a dafa mana ne?.” “Yanzu zan ɗora lunch.” Ya kalle ta yace, “yanzu fa muka yi breakfast, ki bar girkin ba sai kin yi ba kizo mu koma inda muka fito” ya faɗa yana rƙo hannun ta. Ta turo baki tayi tana turjewa tace, “ko gyara ɗakin ma ban yi ba fa, kuma ni zaman ɗakin isa ta yake yi.” Ya bin fuskar ta da rikitaccen kallo yace, “ke fa kika ce kina son haihuwa, to in baki zo mun koma ba taya zaki samu cikin?, Ki kashe gas ɗin nan ki zo mu je, in a falo ki ke so sai mu zauna a falon” ya faɗa yana kashe gas ɗin yana kallon ta. Manal ta kalle shi ta fara buga ƙafa tace, “yanzu fa rana ce zamu iya yin baƙi.” Da ƙarfi ya jawo ta jikin sa yana binta da shegen kallo yace, “na cewa Sayyadi ya cewa duk wanda yazo bama nan, na faɗa miki till down zamu yi.” Zata yi magana ya ɗora hannun sa kan bakin ta yace, “Bana son complain” ya faɗa yana jan hannun ta suka koma ɗakin. Duk yadda Manal taso a ranar ya hana ta motsi, till down ɗin da yace kusan hakan ne ya faru har dare suna maƙale da juna, sallah ma su biyu suke yi da an idar zai sake jawo ta jikin sa duk tayi laushi amma babu bakin magana tunda yace ai ita tace tana so. Washe gari Manal ta siyo kwalin pt stick ta ajjiye tana gwada fitsarin ta ko za’a samu ciki. Ranar da ya gani ya dinga dariya yana cewa, “kice tafi da gidan ki kike yi, wannan shine sauke tukunya juye ɗin, da an fito daga wanka sai ki shiga ɗaki sai ki hau duba mudubin ki ko?.” Taƙi kula shi ya dinga tsokanar ta mai son yin ciki dole tayi masa biyayya. A cikin satin Ayan ya gudo wajan ta tashi sasafen da ta tsana ya dawo saboda shirya shi makaranta, haka take tashi tayi masa abinci ta yi masa wanka ta shirya shi school bus tazo ta miƙa shi ya shiga sannan ta dawo. Ranar alhamis bayan Ayan ya tafi makaranta Adnan yana gida ranar yace bazai fita ba aiki zai yi, Manal ta fito daga ɗaki a guje ta faɗa kansa tana murna. Ya kalle ta yace, “ke lafiya dai ko?.” Manal ta nuna masa PT stick ɗin ya kalla yaga jajayen zane guda biyu alamun tana da ciki. Tashi tayi daga jikin sa ta fara tsalla ya riƙo hannun ta yace, “ki daina tsalle mana ko kina so a rasa shi?.” Komawa tayi ta rungume shi tana murna. Yayi dariya yace, “sai a bani kyauta, na samar miki da abinda kike so cikin kwanaki kaɗan, kinga adadin capacity ɗin da nake dashi nasan kin tabbatar ɗin jarumin gaske ne. A bani kyauta ko nan gaba na rama.” Manal tayi dariya tace, “to me ka ke so?.” Ya kalle ta yace, “a sake bani damar till down. Kin san wancan lokacin na ji daɗin harkar sosai. Ta yi masa Hararar wasa tace, “da cikin?.” “Ai na san yadda zan yi.” “Ni dai a’a ka zaɓi wani abun.” “Lallai ɗan Adam butulu ne, ni za’a yiwa haka Manal? Shikenan zan rama.” Tayi dariya tana sake kwanciya a jikin sa ya riƙe ta ta sosai yace, “Shikenan burin ki ya cika kin samu ciki ko?.” Ta ɗaga masa kai tana riƙe da wuyan sa taana murmushi. murmushin shima yake yi yana kallon ta yace, “to sai mu fara kula dashi kafin Allah ya kawo mana shi duniya, shekara biyar ɗin dai da kika furta sai ta kusa zaki haihu. Allah yasa wannan ba irin cikin Ayan bane a fannin sha sugar, Allah yasa wannan irin wancan ne akan son maƙale min.” Tayi dariya tana kwanaciya a jikin sa cikin farin ciki. Sai kuma ta tashi tsaye ta ɗauki waya ta dawo jikin sa ta zauna tace, “bara na faɗawa Mama.” Ya girgiza kai bai hanata ba dan yasan sai ta faɗa mata. Manal ta kira Mama tana ɗauka kafin Maman tayi magana Manal tace, “Mama ina da cikiiiiii!.” Mama tayi tsaki tace, “Manal yaushe zaki hankali ne wai ke? Wannan itace sallamar taki?.” Manal a shagwaɓe tace, “to Mama ba ke kike min faɗa akan ban haihu ba, na dage kuma na samo cikin shine na kira na faɗa miki.” Mama ta sake yin tsaki tace, “kin kyauta da kika dage kika samo ciki kin ji, Allah ya inganta mara kunya” ta faɗa tana kashe wayar. Dariyar da yake riƙewa ya fara yi yana kallon ta. Baki ta turo tace, “dariyar me ka ke min?.” Yace, “wato ni ki ke jin kunya amma Mama duk abinda yazo bakin ki faɗa mata kike yi. Wato kin dage kin samo ciki ko? To faɗa min irin dagewar da kika yi har kika samo.” Manal ta kalle shi tace, “Nifa ba da wani abun na faɗa ba, shiyasa tace min mara kunya ashe itama abinda kayi tunani take nufi” sai tayi dariya tace, “ko da yake ai dagewar nayi, har sharaɗi aka saka min fa kuma na haƙura nabi sharaɗin. Anya ma kuwa ba ranar bane?.” “Ba a ranar bane me?.” Ta juya ido sai kuma ta rufe idon tana dariya. Ya ja hancin ta yace, “ai jin kunyar tawa duk ta ƙarya ce, tunda gashi kina cewa Mama kin dage kin yi ciki.” Manal tayi dariya tace, “zan je school fa, bara na tashi.” Ya zauna da ita yace, “yau dai a ƙyale school ɗin nan mu zauna mu yiwa Babyn mu barka da zuwa. Kafin nan ki saka hujjabin ki muje asibiti mu tabbatar da kwanakin sa ko?.” Ta amsa da to ta tashi ta shiga ciki ta ɗauko hijjabi suka fita. Da suka shiga asibitin basu tarar da Huzaifa ba sai da ya nufi office, tana bayan sa bayan an gama yi mata scaning suka haɗu da Huzaifa zai wuce. Manal ta kalle shi tace, “Yaya ina yini.” Huzaifa yace, “A’a Manal kin yiniLafiya?.” “Lafiya lau Yaya, ina Anti da Amna?.” “Lafiya lau, yau kece a asibitin namu?.” Bebi ya kalle shi yace, “ji mana, ya zaka dinga magana da mayar mutum bayan baka nemi izinin mijin ta ba?.” Huzaifa yayi tsaki yace, “Manal gab nake da nunawa wannan mijin naki ikon da nake dashi a kan ki, na lura yana wasa dani yana kuma mantawa ni babban Yyan ki ne, amma zan tuna masa.” Manal tayi dariya tace, “ya dai kamata Yaya.” “Ɗazu naje wajan Mama ai, naje an gwada sugar ta.” Manal tace, “ta faɗa min kaje ba.” “Indai naje sai an faɗa miki?.” Tayi dariya kafin tayi magana sai result ɗin ta an kawowa. Bebi ya karɓa kalle ta yace, “ba sai mun shiga bama ga abinda muke jira” ya faɗa yana buɗe takardar ya kalli fuskar ta ya sake kallon takardar sai yayi dariya bai ce komai ba ya ninke ya saka a aljihu. Ya kalli Huzaifa yace, “meye ka ke kallona ne?.” Huzaifa yace, “kai da wanne ido ka san ina kallon ka?.” “Ka dai taya mu murna mun kusa samun new baby ko partner?” Ya faɗa yana riƙo ta yana kallon ta. Mintsinin sa tayi a hannu, Huzaifa ya harare shi yace, “ina taya ƙanwata murna, Allah ya inganta mana.” “Ƙanwar ka kawai ka sani kenan? Da yake ita ta…” da sauri tace, “partner wai meye haka? yaya Huzaifa ne fa, bana so irin haka ka daina don Allah.” Huzaifa yayi dariya yace, “kaga inda ake girmama Huzaifa, kar ki damu Manal indai wannan ne ai ya saba” ya faɗa yana wucewa shima ya ja hannun ta suka fito. Sai da suka je gida take cewa, “Meyasa ka ke wannan maganar a gaban Yayana?.” Bebi yace, “ke takura min yake shiyasa nayi maganin sa, shi ai bai ɗauke ki ƙanwa ba.” Ya ɗauko takardar yana duba yace, “kin san date ɗin cikin nan yayi daidai da ranar Sunday ɗin nan.” Manal tace, “to daman an samu banza kuma ina so ba dole ba.” Murmushi yayi ya girgiza kai yace, “Au abun haka ne?, Shikenan zamu gani.” Dariya itama tayi ta tashi ta shiga ɗakin ta. Bebi da Manal rainon ciki aka fara cikin kulawa da nuna tsantsar soyayya, makaranta ma ya saka ta daina jan mota kai ta ake ya ɗauko ta, gurki ma yace ta rage yi zai dinga taho musu da abinda zasu ci wani lokacin. A wannan cikin taba bin dokar shan sugar sai dai bata son warin gas ko kaɗan, hakan ya saka aka kulle shi aka ajjiye ta koma amfani da electric gas. Kwance tashi ba wahala a wajan Allah Manal ciki har ya girma kuma cikin ikon Allah lafiy lau tana bin dokar ƙin shan abu mai sugar sosai. An yi scanning an tabbatar mace ce a cikin Manal ta fara kiran ta da sunan Maman ta dan tace sunan Mama zata saka shi kuma ya amince mata. Cikin ikon Allah Manal ta haihu lafiya amma ta sha baƙat wahala fiye da haihuwar Ayan,sai dai Babyn da tazo da jendus sai da kwana uku a nursery sannan aka sallame ta suka dawo gida. A gida Manal ta cigaba da jegon ta da taimakon Addah Halima da tazo wajan ta take kula da ita. Ranar suna yarinya taci sunan Maman Manal tayi mata laƙabi da Ayda. Satim Mama Halima uku a wajan Manal ta koma gida bayan ta bata kulawa sosai yadda ya kamata, ganin ta warke ta dawo daidai ne ya saka ta tafiya kasancewar ba haihuwar fari bace ba. Mutanen Abuja kowa yazo har Daddy da kansa yazo har gidan yayi mata barka ya kawo kaya da abubuwa masu yawa matsayin sa na mahaifin ta. Rumana, Mubeena dukkan su sun zo duk da ba a yi taron suna ba amma sun zo sun yi mata barka sun tafi. Bayan sati biyar da haihuwar tana zaune a falo tana ta yiwa Ayan faɗa akan wai sai ya ɗauki Ayda. A lokacin Adnan ya shigo yana amsa waya a lokacin da take cewa, “Wallahi Ayan zan dake ka, ina yi maka magana ka sake yi?. Baza ka ɗauke ta ba kuma kayi min kuka sai na dake ka wallahi.” Kashe wayar yayi saboda kukan Ayan ya kuma nufk wajan sa ya zauna a kan cinyar sa yana kuka. Tayi tsaki tace, “ya cika shagwaɓa da kuka mara dalili.” Kallon ta yake yi cikin mamaki wai itace take cewa wani yana kuka mara dalili. Bai mata magana ba ya fara rarrashin Ayan har ya daina kuka yayi bacci a jikin sa. Kwantar dashi yaje yayi a ɗaki ya dawo ya ɗauki Ayda a kan cinyar ta yana kallon ta, dan wannan karon dashi take kama ba da Manal ba. Bata kula shi ba dan shima haushin sa take ji ya kuma sani neman shiri yake shiyasa take share shi. Ya ajjiye Ayda akan gadon ta ya kalli Manal yace, “Haba Fatima na kuma Mummyn Fatima, har yanzu baki gama fushin ba?.” Ta kalle shi ta ɗauke kai yayi murmushi yace, “to yanzu me kike so na yi miki? Ai na faɗa miki komai ya wuce amma kin ƙi.” Manal tace, “haka kawai ka dinga yi min faɗa akan abinda ba laifina bane, na faɗa maka in ranka ya ɓaci ya daina shafa ta amma ka ƙi. Ban san waye ya ɓata maka rai ba, ban san a inda aka ɓata maka rai ba amma kazo ka dinga yi min faɗa akan abinda ban san anyi ba.” “To ai nace miki ya wuce ko?.” “Ni a wajena bai wuce ba” ya faɗa tana kawar da kanta. Murmushi yayi ya riƙo ta ya matse ta a jikin sa yace, “to me kike so nayi miki ki daina fushin?.” Ta kalli idon sa ya hura mata iska cikin idon ta, lumshe idon ta kuma buɗewa yace, “kina girma kina sake kyau.” Ta turo baki tace, “daɗin baki kawai ka ke min, ina kyau a wajan mai yara biyu? Kaine dai ka ke kyau shiyasa ƴan mata suke bin ka.” Yayi dariya ganin ta sakko yace, “yara biyu ne fa dani, ina ni ina soyayya Fatima ta?!” Ya faɗa yana kai hancin sa wuyan ta. Ta ɗan ja baya tana kallon sa shima yana kallon ta yace, “ya dai? Yau dai dole a tausayawa Adnan, na gaji da zaman jira. Tunda ki ka haihu shikenan ki ka raba kan ki dani.” Ta kalle shi tace, “nidai tsoro nake ji kar na yi ciki da wuri, na sha wahala a haihuwar Ayda wallahi, gaskiya bazan haihu ba sai nan da shekara….” Yayi saurin dakatar da ita yace, “kar ki faɗa da baki mala’iku, kinga haka wancan kika faɗa sai da biyar ɗin ta tabbata.” Ta kawar da kai yyai dariya yace, “Kina da abin mamaki, kince baza ki haifi Ayda ba sai nan da shekara biyar amma kafin lokacin kika tayar da hankalin ki ke kin zama juya, Allah ya baki yanzu zaki sake cewa ke baza ki sake haihuwar ba sai nan da wasu shekaru?.” Manal tace, “na sha wahala sosai, ni su biyun nan ma sun ishe ni, Mamana ma ai damu kawai ta rayu gashi yanzu mun tara mata guda huɗu. Ni na gaji bazan iya wahala ba.” “Ai ba kai zaka tsayarwar da kan ka haihuwa ba Allah ne, ka’ide abinda zaka haifa a rayuwar ka babu kyau saboda Allah ne yake bayarwa ba kai zaka zaɓawa kan ka ba. Dan haka ki jira lokaci kawai, amma baza ki haihu da wuri ba sai Ayda tayi kamar yadda Ayan yayi in sha Allah.” Ta kwanta a jikin sa tace, “to Allah yasa. Ga rigimar Ayan isata take yi, yayi ta kuka kara dalili.” “Wannan kuma ke ya gada har yanzu haka kike.” “Kace kaima na sha baka haushi ko?.” “Eh babu laifi kina bani, musamman in ban yi miki komai ba ki fara yi min kuka.” Manal tayi dariya tana sake gyara kwanciya a jikin sa yace, “kinga ba kwanciya zaki ba, tashi zaki mu tafi kafin wannan yaran albarka nuna mu su farka mun yi abinda zamu yi. Tashi don Allah.” Ta kalle shi tace, “ƙarfe tara na dare fa.” “Zamu mori lokaci sosai, ke kan ki kin san yau ɗin ai ba ta wasa ba ce” ya faɗa yana tashi tsaye ya ɗauki Ayda ya tafi da ita ɗakin ya kwantar da ita ya dawo ya ga Manal ɗin a inda ya barta. Ya tartare hannun rigar sa yace, “Wulaƙanci ko? To bara ki ga” ya faɗa yana ɗaukar ta tana dariya ya shiga da ita ɗakin sa. BDƘB3P50 Washe gari bai tashi da wuri ba sai gab da sallar azahar, a firgice ya tashi ya shirya da sauri ya fito falo ya tarar da Manal a tsaye tana waya ya kalle ta yace, “zan fita.” Ganin a yadda ya fito sai ta kashe wayar tace, “lafiya?.” “Ina zuwa sauri nake” ya faɗa yana fita da sauri. Bata yi tunanin komai ba ta cigaba da abinda yake yi. Kusan awa ɗaya da fitar sa sai gashi ya shigo bayan sa wata mata kyakykyawar mace mara mai jiki da fatar ta kamar ta larabawa. Manal na zaune taji yana cewa, “shigo mana.” Ta shigo tana kallon Manal da take zaune da Ayda a hannun ta. Manal kallon sa take yi tana kallon baƙuwar ta miƙe da murmushi tace, “sannu da zuwa.” Matar cikin iyayi ta miƙawa Manal hannu alamun su gaisa, Manal ta bata hannu suka gaisa cikin murmushi ta karɓi Ayda cikin hausar ta da bata fita sosai tace, “sunana Zainab.” Manal da murmushi tace, “Ni kuma Manal.” Dr Zainab tace, “wow! Nice name.” Ta kalli Ayda tace, “beautiful baby.” Manal ta miƙe ta je wajan fridge ta kawo mata ruwa da lemo da glass cup ta ajjiye mata. Dr Zainab ta kalli Adnan tace, “Matar ka kyakykyawa.” Yayi murmushi yana zaune bai motsa ba. Kallon Manal yayi yace, “ki kaita ɗaki ta huta in anjima tazo taci abinci.” Dr Zainab tayi murmushi tace, “Thanks you handsome.” Jin abinda tace sai Manal ta kalle ta sannan ta kalle shi suka haɗa ido sai ya ɗauke idon sa. Karɓar Ayda Manal tayi ta bawa Adnan ita sannan ta raka ta ɗakin da yake kusa da nata tace, “bismillah.” Ta kalli Manal tana murmushi tace, “na gode sosai.” Manal bata ce komai ba ta fito zuwa falon. Tana fitowa ta same shi a tsaye ya bata Ayda yace, “sauri nake yi yanzu zan dawo.” “Ko abinci baka ci ba.” “Yanzu zan dawo” yana faɗa ya fita ta bishi da kallo. Dr Zainab ko da tayi wanka kwanciya tayi bata fito ba sai bayan la’asar, ta fito cikin doguwar riga ta shan iska dan sisirin hannu ce da ita kamar vest, kanta babu hula ta ɗaure gashin kanta kamar wacce take a gidan ta. Tana zama a falon Adnan yana shigowa ya zauna suna hira da ita a falon, da kansa ya kawo mata abinci dan bai ga Manal ba. Ayan yana kusa da ita tana ta yi masa wasa suna hira da Adnan cikin harshen turanci suna dariya. Manal tunda ya jiyo dariyar su gaban ta faɗi,ta fito tana kallon su cikin wani irin abu da yazo zuciyar ta ganin ta zaune daf dashi sai Ayan da yake tsakiyar su kai kace mata da miju ne. Wani irin kallo take yiwa Adnan tana murmushi tana kuma kai hannun ta jikin sa. Manal ta daure ta ƙaraso da sallama Dr Zainab ta kalle ta cikin harshen turanci tace, “Madam kin fito?. Na tashi tun ɗazu har naci abinci, mijin ki ya dawo yana taya ni hira.” Manal tayi murmushin yaƙe ta kalle shi suka haɗa ido ta kawar da kai ta zauna a falon zuciyar ta a cushe ganin yadda take masa dariya shima yana sakar mata fuska kamar ba shi ba. Zaman wajan ya ishe Manal sosai ta tashi tsaye da Ayda a hannun ta ta wuce ciki ɗaki, tayi tunanin zai biyo ta amma bata gan shi ba tana dai jiyo tashin muryar ta. Sai gab da magriba taji shigowar sa ɗakin ta ya kalle ta yace, “Manal zamu je asibiti da Dr Zainab, zamu dawo zuwa anjima.” Manal ta kalle shi tace, “Sai kun dawo.” “Na manta ban faɗa miki ba, a nan zata kwana duk dare zamu dawo tare.” Tayi murmushin takaici ta ɗaga kai shi kuma ya fita. Haka ta gama zaman ta a gidan babu walwala zuciyar ta a cushe, basu dawo ba sai goma da arba’in na dare, zuwa lokacin ta gama zuwa wuya saboda ɓacin rai da kishi mai tsanani. Dr Zainab tana ganin Manal tace, “barka dai Madam, mun dawo.” “Sannun ku da zuwa” ta amsa ba yabo babu fallasa. Ɗaki ta shiga itama Dr Zainab ɗin ɗakin da aka bata ta shiga. Waya ya yiwa Manal yace tazo ɗakin sa ta fito tana shiga ya kalle ta yace, “Yauwa ki bata abinci, a nan zata kwana, maybe sai jibi ma zata tafi.” Kallon sa take yi bata yi magana ba, ganin irin kallon da take masa sai yace, “baki ji abinda nace ba ne?.” “Naji.” “Amma ki ka tsaya kina kallo na baki yi abinda na ce ba?.” Manal ta gyara tsayuwa tace, “amma wacece ita?Meyasa baka faɗa min zuwan ta ba?, sannan meyasa baka ce min a nan zata kwana ba?.” Da mamaki yake kallon ta yace, “Yanzu ai na faɗa miki ko?. A nan zata kwana ki bata abincin da zata ci yanzu.” Manal ranta ya sake ɓaci, kishi yana sake azalzalar zuciyar ta tace, “ina matsayin matar gidan nan ace an kawo ɓakuwa cikin gidana zata kwana ban sani ba?, sai dai kawai na ganta ace min kwana zata yi, hakan daidai ne?.” Ya kalle ta da mamaki abinda tace ya ce, “amma ai na faɗa miki yanzu ko?. Meyasa ki ke son maimaita magana ɗaya?, meyasa ki ke son mayar da ƙarami babba?.” “Wannan dai kamar wulaƙanci ne ai. Wacece ita da zata zo har cikin gidana tana zama da mijina a falo tana hira kamar matar ka?.” tsaki yayi kawai bai ce komai ba ya fita ya bar mata wajan gudun kar ta saka shi magana ga baƙuwa suna da ita. Da kansa ya kai mata abincin ya same ta a zaune a falo da kayan bacci riga da wando, wandon iyakacin sa guiwar ta gabaɗaya fararen ƙafar ta a waje suke. Ta fara cin abincin ya zauna suna tattauna batun aikin su. Manal ta fito sake ganin su a haka ga kayan da yake jikin Zainab ɗin, hakan ya sake ɓata mata rai sosai ta danne ɓacin ranta a lokacin dr Zainab take dariya harda dukan kafaɗar Adnan. Rantse ido Manal tayi ta zo ta wuce su bata ce musu komai ba ta shiga ɗaki. Dr Zainab ta kalle shi tace, “matar ka tana da kirki sosai.” Yayi murmushi kawai bai yi magana ba. Ya jima a wajan ta suna hira kafin ya tashi ya shiga ɗaki itama ta shiga ɗakin ta bayan ta leƙa Manal ta yi mata sai da safa. Manal saboda takaici bata ma sake zuwa ma inda yake ba a haka suka kwana tana ɗakin ta yana ɗakin sa. Ƙarfe baƙwai na safe ta tashi ta shirya Ayan ya tafi makaranta, tana kwashe kayan da Ayan yaci abinci taji motsin fitowar sa. Juyowa tayi ta kalle shi taga fuskar a ɗaure tace, “ina kwana.” Ya amsa shima babu fara’a sannan yace, “ki haɗa breakfast yanzu zata tafi” yana faɗa ya wuce ta. Bata ƙi yi ba ta dafa ta ajjiye ta koma ɗaki. Tana jiyo motsin baƙuwar sai da ta gama cin abincin sannan ta shiga wajan Manal ta yi mata sallama suka fita. Ran Manal ya kai ƙarshe wajan ɓaci haka take a ɗaki har ya dawo lokacin ƙarfe goma na safe. Tana jin motsin sa bata fito ba shima bai je inda take ba. Shirin aiki yayi ya zauna yaci abinci bai nemi inda take ba ya fita zuwa wajan aiki dan kar ma ta ɓata masa rai. Zuciyar Manal kamar ana tafasa ta a haka ta wuni a gidan, ranta a ɓace kishi yana azalzalar zuciyar ta tana ganin kamar Adnan ya gama wualaƙanta ta. Da yamma ta fita wajan school bus ɗin su Ayan a nan taga motar Huzaifa zata wuce ta ƙofar gidan, ganin Manal ɗin a bakin gate sai ya tsaya ya sauke glass kafin yayi magana ta riga shi tace, “Yanzu Yaya ba dan ba ganka ba wucewa zaka yi?.” Zai yi magana tace, “ai kawai ka shigo mu gaisa” ta faɗa tana komawa ciki tana riƙe da hannun Ayan. Huzaifa ba yadda zai yi ya shiga gidan ya zauna a falo tana murmushi tace, “yanzu da ban ganka ba sai ka wuce ko mu gaisa ko Yaya?.” Yayi dariya yace, “gaskiya ban yi niyar shigowa ba, Allah yayi dai sai na shigo mun gaisa.” Ta zauna tace, “ina yini.” “Lafiya lau, ya gidan?.” “Lafiya lau Yaya, ya Anty da ɗana?.” “Lafiya lau suke.” Ya riƙe hannun Ayan da yake tsaye a kusa dashi yana tambayar sa ya makaranta. Fuskar ta ya kalla yaga duk ta canja kamar mara lafiya yace, “Manal lafiya ki ke?.” Ta kalle shi ta sauke ajiyar zuciya tace, “Don Allah Yaya wacece Dr Zainab?.” Huzaifa ya ɗan yi shiru kafin ya ce, “wacce Dr Zainab?.” “Wacce taje asibitin ku jiya.” “Jiya da daddare bana asibiti, amma daga ƙasar waje tazo?.” Manal tace, “ina tunanin hakan.” Huzaifa yace, “Dr Zainab babbar illikita ce a ƙasar Canada, tana zuwa asibitin mu in muka buƙaci hakan musamman a ɓangaren zuciya dan ƙwararriya ce sosai. itace tazo kenan?.” “Eh tazo tun jiya, a nan gidan ma ta kwana.” Huzaifa ya girgiza kai dan ya san dole Manal tayi kishi da ita. Zainab a gaban kowa nunawa take yi Adnan kamar wani saurayi ta ne saboda ita a wajan ta ba komai ba ne. Kuma a baya ta so shi ɗin kawai bai bata fuskar soyayya ba ne saboda lokacin yana tsaka da ƙaunar Rumana, sai dai zumunci da kuma abota akan aiki. Manal tace, “Kuma Yaya don Allah babu wani abu a tsakanin ta da Partner?.” Yayi dariya yana kallon ta yace, “ban da abin ki Manal wanne abu ne a tsakanin su?, Kawai jinin su ya haɗu sosai tun ɓuna makaranta, kuma ta girme mana dan ba mate ɗin mu bace ko a makaranta. Muna level two ita a lokacin level four take. Kawai tana da kirki ne kuma jinin su ya haɗu da mijin ki.” Manal ta taɓe baki ta sauke ajiyar zuciya idon ta ya ciko da hawaye, ganin hakan sai Huzaifa yace, “kar ki wani damu fa babu komai kin ji?.” Ta ɗaga masa kai ya tashi yace, “zan je asibiti yanzu.” Manal ta tashi tsaye itama tace, “to Yaya a gaida Anti, zan zo in sha Allah.” Ya amsa yayi mata sallama ya tafi. Asibitin ya wuce ya samu Adnan a tsaye yana magana da wasu masu jinya ya kalle shi yace, “Bebi in ka gama..” ya faɗa yana yi masa nuni da hannu kafin ya wuce ciki. Sai da ya gama abinda yake yi sannan ya hau saman wajan Huzaifa ya same shi a tsaye shi da Hamza da Dr Yasir mijin Lubna da Dr Hadiza suna magana. Ya tsaya yana kallon su bai ce komai ba, Yasir ya kalle shi yace, “Babban Yaya barka da zuwa.” Adnan yayi ƴar dariya yace, “shiyasa ka ke yin albarka saboda girmamawa yayan makat ka da ka ke yi.” Huzaifa yace, “shiyasa wani baya albarka saboda raina yayan matar sa da yayi.” Bebi ya harare shi yace, “me zaka ce min ka saka ni nazo na?.” Hamza yace, “gaskiya baka kyautawa, ya Yasir zai dinga girmama ka kai kuma baka girmama Huzaifa?, gaskiya hakan bai daidai bane.”Kallon banza ya yiwa Huzaifa aka yi dariya Yasir da Hadiza suka fita suka bar su su kaɗai. Huzaifa ya kalle shi yace, “Zainab ɗin ta wuce ne?.” Bebi yace, “ta tafi. tace min Abuja zata je, taso mu na raka ta kawai baza je ba.” Hamza yace, “ai shige maka ɗin da take yi yayi yawa, ta san kayi aure ma baza ta ƙyale ka ba. Har yanzu tana son ka, bata ƙi kace zak aure ta ba.” Bebi bai bashi amsa Huzaifa yace, “ashe a gidan ka ta kwana.” Ya kalli Huzaifa ta ƙasan idanun sa yace, “a nan ta kwana, sai ya ya?.” “Amma ka san bai kamata ka kaita gidan ka ba. na farko dai Zainab tana acting kamar kai da ita soyayya ku ke yi, duk da kowa ya san tana sonka amma nunawa take kaima son ta ka ke, na biyu kai ka san ba wani tarbiyya kirki ne da ita ba, ta girma amma kallon kanta take a yarinya mai ɗanyen jini. Kuma ka san ana zargin ta da lesbian tun a makaranta.” Adnan ya kalle shi yace, “to ina ruwana ni?. Magana ce akan aiki ya saka na gayyato ta tun daga Canada tazo ƙasar nan tayi theater saboda ni kawai, in ban sauke ta a gidana ba a gidan wa zata sauka?. Ina ruwana da zargin ta da ake yi?, Ni ban taɓa gani tana yi ba kaga bazan tabbatar da abinda ban sani ba.” Ya sauke ajiyar zuciya Hamza yace, “amma matar ka baza yaji da daɗi ba saboda wannan shegen iyayin Dr.” Adnan yayi tsaki ya kalle Huzaifa bayan ya riƙe ƙugu yace, “Wai Manal ce tace maka na kai ta gidana?.” “Tambayata tayi wacece ita nake faɗa mata. Da yake na biya ta gidan naka kafin nazo nan.” Yayi tsaki yace, “mata suna da matsala, yanzu meye aibu dan na kai ta gidana ta kwana don Allah?. Bafa da ɗaki ɗaya muka kwana da ita ba, amma ita tunanin ta kawai budurwa ta ce, ba’a mutunci sai soyayya. Ni na gayyato matar nan tun daga wata ƙasa kuma tazo, ai ta cancanci karramawa fiye da haka a wajena.” “Ba matsala bace ba fa Adnan, dole ko wacece tayi kishi da Zainab. Kar ka manta Rumana da ba matar ka ba tayi kishi da Zainab a shekarun da suka wuce, to ina ga Manal kuma matar ka?.” Huzaifa ya kalli Hamza da yayi magana yace, “kuma ni ba ƙarar sa ta kawo min ba, tambaya ta take yi akan Zainab ni kuma na bata amsa.” Bebi ya taɓe baki yace, “daga baya kenan, in ma ƙarar tawa ta kawo maka ai ba duka zaka yi ba ko?. Kuma ka faɗa mata bazan fasa ajjiye baƙuwa a gidana ba, ba Zainab ba; ko wacece in nayi ra’ayi zan kai ta gidan ta kwana. Na gayyato mata tun daga Canada tazo dan ta kwana a gidana a dinga yi min ƙananun magana?.” Hamza yace, “Kai dai ka sani, amma tsakani da Allah dole tayi kishi da ita, dan a wajan Zainab dan ta rungumee ka a gaban Manal ba komai bane.” Yayi tsaki ya cigaba da aikin sa yana jin haushin Manal a zuciyar sa dan shi bai ga wani aibu ba da har zata faɗawa Huzaifa. Koda ya koma gida fuskar sa a ɗaure ya koma babu fuskar da zata yi masa magana sai ta share shi itama ta ajjiye masa abinci amma bai ce mata komai ba itama bata ce ba. Tana kwashe kayan abincin bayan ya gama ci yake cewa, “shine harda faɗawa Huzaifa wai nazo da ɓakuwar gidan nan, to me Huzaifa zai yi min? Duka na zai yi ko me?. Ko kina ganin faɗawa Huzaifa zai hanani saukar baƙuwa a gidana ne?.” Kallon sa tayi bata ce komai ba ta kwashe ta bar masa wajan. A haka suka kwana bata ce masa komai ba shima haka sai dai duk abinda ta san yana so zata ajjiye masa amma magana bata haɗa su. A haka aka kwana biyu tana yi masa wannan hukuncin da bai fahimta ba sai daga baya, ya jure shiru nata har ya gaji, in yayi mata magana daga eh sai a’a kawai, ta canja kamar ba ita ba ko dariya bata yi. Ko a falo suka haɗu zata bashi hanya ya wuce itama ta shiga inda zata je, in maganar ta zama dole sai dai tayi masa text a waya amma ba ta fatar baki ba. BDƘB3P51 A ranar alhamis yayi nufin zama da ita yaji meye matsalar, hakan ya saka shi ya dawo daga aiki da wuri duk da dare yayi ya same ta tana waya da Maman ta da take Jalingo taje ziyara. Bayan ta gama ne ta kalle shi fuska ba yabo babu fallasa tace, “sannu da zuwa.” Ya amsa yana kallon ta kafin ya ce, “ki kawo min fruit ɗaki” ya faɗa yana shiga ɗakin. Manal ta miƙe ta kwantar da Ayda da tayi bacci a hannun ta ta shiga kitchen haɗa masa fruit salad ta kai masa ɗakin kamar yadda yace. A zaune ta ganshi yana danna laptop ta ƙarasa ta ajjiye masa a kan table ɗin da yake aikin. Wucewa tazo yi ya riƙo hannun ta a tausashe yace, “zo ki zauna.” Bata yi musu ba ta zauna fuskar ta babu walwala ko kaɗan. Yabi fuskar ta da kallo kafin ya ce, “Duk akan na kawo Dr Zainab gidan nan ta kwana ki ke wannan fushin Manal?.” Shiru tayi bata yi magana ba ya ce, “Partner dake nake magana, duk akan Zainab abin ya zama haka?. Magana ma sai kin ga dama ki ke yi min?.” Manal tayi ƙaramar ajiyar zuciya tace, “akan ne zan yi fushi kai da gidan ka?, Gidan ka ne kana da ikon kawo duk wacce ka ke so.” Kallon ta yayi yaga fuskar ta a haɗe babu alamun walwala da alama bata huce ba, ya ture laptop ɗin gaban yace, “to meyasa kike fushi har na kwana uku?. bakya yi min magana, bakya dariya, wani lokacin in na dawo da daddare ma sai na tarar kin yi bacci. Fushin na meye haka?.” “Ba fushi nake ba fa.” “To me ki ke yi?.” “Kawai na janye jiki na ne saboda baga baƙuwar taka ta fini a wajan ka.” Yayi murmushi yace, “ya za’a yi baƙuwata ta fiki Manali?.” Ta taɓe baki bata ce komai ba ya gyara zama ya ƙce, “tun daga ƙasa Canada tazo saboda na gayyato ta tazo mu yi wani aiki tare a asibitin mu, ta amsa gayyata tazo kinga dole na girmamata nayi mata abinda nan gaba in na sake nema zata zo. In ba dan ni ɗin ba ganin ta ma wahala yake yi, amma ta taso daga wata ƙasa tazo nan kawai dan ta fito da martabar asibitin mu, kinga ta cancanci na sauke ta a gidan nan ko?.” Manal tayi shiru bata amsa ba ya kalle ta ya ce, “kin yi shiru.” Ta ja numfashi tace, “Zuwan ta bai dame ni ba, ko kwana ɗari zata yi a gidan nan bazai ɗaga min hankali ba saboda ba a kaina zata zauna ba. Duk da gidan ka ne ba nawa ba, kana da ikon yin duk abinda zaka yi a cikin sa, amma kasan ni ma a gidan nake zaune yana da kyau in zaka yi baƙuwa ka sanar dani zuwan ta ka kuma faɗa min a nan zata zauna kafin tazo. Ban san da zuwan ta ba sai ganin ta kawai nayi, sannan baka ce min zata kwana ba sai bayan tazo. Ta fito falo da kayan bacci kamar matar gidan ta zauna, kaima ka zauna kuna hira da ita har ta dinga taɓa ka saboda daɗin labari. Daga ƙarshe sai abin ya zama har faɗa ka dinga yi min a kanta, ka share ni ko abinci da ita ka ci ka manta ma dani. wacece ita da zaka yi min faɗa har haka a kanta?, wacece ita da ka tattara nutsuwar ka gabaɗaya a kanta har ka manta dani?.” Ya kulle ido ya buɗe yana kallon ta, kafin yayi magana ta tashi tsaye tace, “tunda tazo ko abincin na daina ci kayi, baka damuwa da naci abinci tunda tare ku ke ci kai da ita. Da kace min ka tafi kai ta baka dawo min ba sai dare ka dawo kana cewa na faɗawa Yaya Huzaifa dukan ka zai yi. Ba dukan ka zai yi ba, na faɗa masa ne dan na ji sauƙin abinda nake ji a zuciya ta saboda shi ɗin jinina ne, ban damu ba dan baka kallon sa a haka, ni a matsayin jinina nake kallon sa. Bayan duk abin nan da kayi min sai ka daina shiga harkata, fuska a ɗaure ka ke dawowa kullum a haka ka ke komawa. Sai dai naji kana waya da ita kana yi mata bagajiya bayan ni baka san ya na kwana ba. Shekara biyar da auren mu amma har yanzu na kasa fahimtar ka, ko laifi kayi min a ko yaushe ni ce mai laifi ba kai ba, amma in nice nayi laifin ba kai ne kayi ba ni ɗin ce. Tunda haka ka zaɓa shikenan” ta faɗa tana wuce shi ta fita daga ɗakin. Dafe kai yayi bayan ta fita, tabbas bai kyauta ba duk abinda ta faɗa haka ne, ya kamata ace ya faɗa mata kafin zuwa Zainab. wannan shine kawai laifin sa da ya gani amma shi bai ga laifin zuwan Zainab ba. Kukan Ayda ya jiyo sosai hakan ya saka shi ya taso ya fito falon ya same ta sai kuka take yi ya karɓe ta yace, “me ya same ta?.” Manal tace, “faɗuwa muka yi ni da ita, shine kanta ya ɗan bugu.” Jijjiga ta yake a kafaɗar sa ita kuma ta zauna a kujera tana kallon hannun ta da ta faɗi a kai tana goge hawaye. Bacci tayi a kafaɗarsa ya wuce da ita ɗakin sa ya kwantar da ita a gadon wanda yake kusa da wanda Ayan yake bacci. Ya dawo falon ya zauna kusa da ita ya kalle ta yace, “ki zo muje ki kwnata tayi bacci.” Ta girgiza kai bata ce komai ba ya miƙe yace, “muje ko?.” Ta kalle shi tace, “zan shigo.” “Ki tashi mu tafi tare.” Kawar da kai gefe tayi bata ce komai ba kafin ta tashi ta wuce ɗakin bata kalle shi ba. Tunda yaga ta kwanta a can ƙarshen gadon ya san abinda yake nufi, shima bai tunkare ya ba ya share yayi baccin sa kamar yadda tayi bacci. Sai da aka sake kwana biyu Manal bata dawo daidai ba tun yana ganin abin kamar wasa har abun ya dame shi ya fara neman hanyar shiri amma taƙi bada dama, sai dai yayi magana ta amsa ta ajjiye masa abinci wani lokacin ma kafin ya tashi ta fita ta tafi cafe ɗin ta. Duk ya damu saboda ba haka suka saba zaman ba, ya jure shirun na ta amma ya kasa shiyasa yake shige mata amma ko sauraren sa bata yi. Da yammacin ranar asabar ta dawo daga cafe ta shigo falon tana kallon agogo dan lokacin magriba ya kusa, ta sauke ajiyar zuciya saboda gajiya a bayyane tace, “na gaji yau..” “Hello my love, welcome back” ya faɗa yana kallon ta da murmushi a fuskar sa yana ƙarasowa inda take. Kallon sa take har ya ƙaraso ya karɓi Ayda da take hannun ta yana yi mata wasa. tace, “Yauwa, ashe ka dawo?.” “Na dawo ina ta jiran ki.” “Yau akwai customers sosai a can, na kuma gana da wasu guests ne suna so zamu yi serving ɗin su a events ɗin da zasu yi, shiyasa na daɗe.” “Good. yanzu ki shiga ki yi wanka ki huta ga abinci na gama haɗa miki.” Kallon sa tayi yayi mata murmushi ta ɗauke kai tace, “Okay” abinda tace kenan a taƙaicr ta wuce ciki. Bata fito ba sai da tayi wanka dan taji alamun tafiyar period ɗin ta sannan tayar da sallar da ta wuce ta. Tana idarwa ya shigo yana kallon ta yace, “oh ashe period ɗin naki ya tafi. Anyway, mu je kici abinci.” Kallon sa take yi kafin ta tashi tsaye ta biyo bayan sa ta zauna a akan kujera ya zuba mata basmati rice da gasheshshiyar maza da kuma salad, ta kalle shi dan ta san a wajan leemars_delicious yayi order, yanayin ƙhamshin abincin ya tabbatar mata da abincin ta ne dan ƙhamshin abincin ta na daban ne. Ta hana shi cin abincin matar nan amma kamar tayi masa asiri a abincin, in yace ya dai bazai iya ba sai dai taga kawai ya siyo. Ta iya girki sosai, ta iya abinci mai daɗi musamman mandi rice ɗin ta in kana ci sai ka ɗauka a saudia ka ke, har ta ta taso tafi ta saudia daɗi saboda ita da ɗanɗano ta saudia kuwa haka take salam. Iya abincin ta ne ya saka Manal take kishi da ita, akan me duk iya girkin ta ya kasa haƙura da cin abincim matar nan?. “Abincin leemars_delicious ne don Allah ki ci, kinga basmati rice ce ga salad.” “Amma nace bana son abincin matar ban ko?, Kenan abincin ta yafi nawa daɗi?.” “Haba Manal me ya kawo wannan maganar?, saboda na hutar dake ne ya saka ni na siya ba wani abu ba.” Manal tace, “ni dai bazan ci ba.” “Saboda a waja ta na siya baza ki ci ba?.” “Kafi kowa sanin bana so ai ko?.” “Ba da wani abun na siya ba fa, saboda ke ne.” “Shiyasa nace bana ci.” Zai yi magana kenan aka yi sallama aka shigo suka kalli masu shigowar tare da amsa sallamar, Yaya Farida ce da Mimi da kuma Kausar. Ɗan ɓata rai yayi dan bai ji daɗin zuwan su ba, ita kuma Manal ta taso daga kan dining ɗin tana murmushi tace, “Barkan ku da zuwa, daga ina haka?.” Mimi tace, “biki muka je muka biyo nan mu yi sallah.” Manal ta zauna kusa da Kausar kafin tace, “Yaya ina yini.” Yaya Farida ta amsa tana kallon Bebi da yake a tsaye ya harɗe hannayen sa a kƙrji yana kallon su tace, “Ko mu koma ne?.” Manal ta kalle shi suka haɗa ta ɗauke kai ya kallo Farida yace, “kawai sai nace ku koma?. Daga ina haka da daddare?.” Farida tace, “daga biki muke, ina Ayda da Ayan ɗin?.” “Ayda tayi bacci, Ayan kuma…” ta faɗa tana kallon Bebi dan bata ana inda ya kai shi ba ita kuma bata tambaya ba. Bebi yace, “yana wajan Mummy.” Mimi tace, “Mama dai na ji da Ayan.” Kausar tace, “to ke sunan miji wasa ne?.” Suka yi dariya har Manal kafin tace, “ga abinci.” Mimi ta tashi tace, “bara nayi sallah naci abincin.” Kausar ta tashi ta shiga ciki tana cewa, “ni ma dai sallah zan yi.” Falon ya rage daga Farida sai Manal dashi da yake tsaye sai kallon Manal yake yi. Yaya Farida ta kalle shi ganin Manal yake kallo, ta kalli Manal da ta ke ɗauke da yarom Kausar tana yi masa wasa. Tayi dariya hakan ya saka Manal ta kalle ta tace, “ina su Baby?.” Farida tace, “suna gida,yunwa nake ji.” Manal tace, “bara na kawo miki.” “A’a yi zaman ki” ta faɗa tana tashi ta ƙarasa wajan dining ɗi. Bebi ya kalli Manal yace, “zan je na dawo.” Ta ɗaga kai kawai ya kalli Farida yace, “Nasan kafin na dawo maybe kun tafi.” Farida tace, “gaskiya dai ba jimawa zamu yi ba.” Ya buɗe ƙofar ya fita. Hira suka dawo suka tayi suna cin abinci ana dariya cikin nishaɗi. Farida ta ɗauko wani abu a leda ta bawa Manal tace, “an kawo mana shi daga sokkoto bashi da matsala ki karɓa kema ki sha.” Manal kunya ta kama ta amma ta saba indai Farida ce ta saba bata irin wannan kayan. Manal tace, “To Yaya na gode, Allah yasa babu zaƙi” ta faɗa tana buɗe murfin robar tana kallon maganin. Kausar tace, “babu zaƙi ko kaɗan, kuma yana da kyau sosai.” Farida tace, “Shiyasa na bata ai, dan a taimakawa ƙanin nawa da alama fushi ake yi dashi, yadda ya barwa Mama Ayan a yau a taimaka a taimaka masa.” Manal ta fasa sha tana dariya. Mimi tayi dariya tace, “ai gwara tayi masa haka, shima baya raga mata.” Manal ta kalle ta tace, “Allah yayi miki albarka, in yana yi min faɗa kamar bai taɓa sanina ba ko kuma abokan gaba ne ni dashi.” Kausar tayi dariya tace, “Yaya Bebi manya, har yanzu halin sa yana nan babu inda yaje.” Manal tace, “hali ai baya canjawa, ni gani nayi ma har gwara da akan yanzu.” Mimi tayi dariya tace, “kice dai kawai an samu cigaba a lamarin na sa. Kai Yaya Bebi bala’i ne, in ya fara zazzaga masifa baya ji baya gani. Sai dai kuma yana ji dake fa.” Manal tayi dariya Kausar tace, “eh ai gaskiya ne, yana ji dake ko yayi faɗan ma zai bada haƙuri. Wani kallo yake yi miki yanzu kamar ya ɗauke ki, ni na san Yaya Bebi ɗan soyayya ne.” Farida tana dariya tace, “Allah ya sa ya dawo ya ji ku.” Mimi tace, “to ko ya ji mu yanzu ai ba da bane, sai dai hararar kawai.” Suka yi dariya gabaɗayan su kafin Yaya tace, “to ga wani turare ma ki shafe jikin ki tass dashi, ni so nake a daren nan a siya miki private get.” Mimi tace, “kin manta waye mijin nata ne?.” Manal tana dariya tace, “Yaya ta manta gaskiya, so take aljanun sa su tashi.” Suka yi dariya gabaɗaya Farida tace, “na ɗauka kin canja shi ai ashe hali yana nan.” “Yana nan, baya son turare mai ƙarfi har gobe musamman ma wannan oil ɗin, kuma ko ya na saka sai ya gane shiyasa na daina.” “Ahh bara na mayar jaka to, ni da nake so a baki jirgin sama in kika shafa ai ko keke baza ki samu ba.” Suka sake yin dariya suka cigaba hira da nishaɗi har suka tafi. Manal bayan ta sun tafi ta shanye abinda Yaya ta bata sannan ta shiga ciki ta shirya a lokacin taji ya shigo. Har ɗakin ya bita yana yace, “kizo kici abinci tunda sun cinye wancan.” Manal ta biyo shi ta zauna a nesa dashi ya buɗe meatpie ne da fish pie, sai kuma basmati rice da salad. Ta ɗauki fish pie ta fara ci yana ci shi kuma yana kallon ta. Guda uku tashi ta tashi ta shiga ɗaki ta shiga banɗaki tana wanke bakin ta ta fito ta ganshi ya leƙo suka haɗa yace, “Ayda ta tashi.” Yana faɗa ya juya ya fita daga ɗakin zuwa ɗakin sa. Fitowa tayi daga ɗakin ta ta shiga ɗakin nasa, tana shiga ya kulle ƙofar ta kalle shi ta kalli Ayda da yake bacci a nan ta fahimci wayo yayi mata. Hannu ta harɗe a ƙirji ta kawar da kanta gefe bata ce komai ba. Ya riƙe hannun ta da yake ƙirjin duka biyu yace, “har yanzu baki huce ba?.” Bata ce komai ba yace, “babu wata baƙuwa da zata sake kwana a gidan nan in sha Allah, tunda bakya son hakan na daina.” Manal tace, “ni wacece da zan hana baƙuwar ka zuwa gidan nan?.” “Ke matar gidan.” “Bani da wannan mahimmacin ai.” Ya karyar da kai ya ce, “maganar nan ta huce don Allah, indai Dr Zainab ce ko tazo zata sauka a hotel ba sai tazo nan ba.” Manal tayi dariya tace, “in tana hotel ɗin ma sai ka biya ku yi hira?.” “Ni na isa?, Babu inda zan je ko da tazo, duk abinda ya kamata a kai mata zan aika a kai mata.” Ta taɓe baki tace, “Waya da ita kuma fa?.” “Abokiyar aikina ce kuma tana sama dani, ina samun ƙaruwa sosai in nuna tattaunawa da ita. Amma zan rage tunda bakya so.” Kallon ido sa tayi tace, “zaka rage ba zaka daina ba?.” Ya girgiza mai yace, “in nace miki na daina ƙarya nake miki, gwara na faɗa miki gaskiya zan rage ba zan daina ba.” Ta girgiza kai bata ce komai ba yace, “yanzu batun ta ya huce, baza ta sake zuwa ba in sha Allah.” “Meyasa take ce maka handsome? Sannan Meyasa ka ke bari tana taɓa ka?.” “Wannan sunan tana faɗa min tun nuna makaranta har yanzu bata daina ba, kamar yadda a gida suke ce min Bebi basu daina ba har yanzu itama haka. Sannan a turawa take rayuwa, ita bata ɗauki riƙe min hannu wani abun ba, amma in zaki min adalci zaki ga ina kaucewa saboda na san haram ne.” Manal tayi shiru ta sunkuyar da kai ƙasa ganin hakan sai ya samu damar riƙo ƙugun ta yace, “wannan fushin naki ne bana so, kin hora ni da yawa na kasa jure wannan shiru shirun naki. Na amince nayi laifi kuma bazan sake ba in sha Allah, amma ki saki ranki, ki bani dama na wanke laifina a daren nan.” Ta kalli idanun sa da idanun ta da suka ciko da hawaye tace, “Kana sona har yanzu?.” Ya riƙe fuskar ta da duka hannayen yace, “soyayyar ki ƙaruwa tayi a zuciyata fiye da baya, ina son ki ina ƙaunar zama dake har a aljanna.” Ta kwanta a ƙirjin sa ya sauke ajiyar zuciya ya riƙe bayan ta yana lumshe idanun sa tace, “ina kishin ka sosai, kar ka yi min kishiya kaji.” “In sha Allah dake kaɗai zan yi rayuwa har mutuwa.” “Don’t sugarcosting me.” “Ni na isa na yi miki daɗin baki?.” “Ka dinga girmamawa Yayana.” Jin abinda tace sai ya ɗago ta daga jikin sa ya kalle ta sai tayi dariya shima yayi dariya yace, “dole ki yi dariya ai.” Ta koma jikin sa ta kwanta tace, “ina sonka my life partner.” Ya matse ta sosai a jikin sa yace, “nima ina son ki my life partner, Allah ya bar mu tare har aljanna.” Ta amsa da amin tana murmushin farin ciki shima kan sa farin cikin yake ji yana ratsa zuciyar sa. Bayan wani lokaci. Hajiya Manal ta zama shararriyar ƴar kasuwa fitacciya a ɓangaren iya sarrafa abinci. Abin ya kawo duk wani biki da za a yi a nigeria da ya amsa suna biki a ƙarƙashin gidan abincin Manal ake yin abincin biki. Lokaci kaɗan ta ɗaukaka matuƙa iyawar ta ya zaga ko ina dan ko yaushe cikin koyo ta ke, koyan girki ya kai ta har ƙasar dubai da america ta koyo abubuwan da itace ta fara sarrafawa ta siyar dasu a nigeria. Tun yana ɓoye fuskar ta har fuskar ta ta zama sananniya a ko ina kowa ya santa. Ta sake yin haske jikin ta yayi kyau duk da baya yi ƙiba sosai ba amma ka da ka ganta ka ga hajiyan kuɗi kuma matar mai kuɗi. Ɓangaren Adnan asibitin su ya bunƙasa sosai ya zaga inda basu yi tunani ba, sun samu kyauta daga ƙasashe sosai sun sake zamanatar da asibitin ta inda ya zama lamba ɗaya a arewacin najeriya. Ganin Adnan ma a asibitin wahala yake yi saboda baya zama yau yana wanna gari gobe yana wata ƙasa ganin sa sai da dogon booking ko da sanayya. Rayuwa tayi musu daɗi ƙalubalen da aka fuskanta ya zama labari komai ya wuce farin ciki ya mamaye ko ina a dangin su. Ranar juma’a Manal bata fita ba tana gida ganin lokacin masallaci ne sai ta haɗa wuta tana turaren wuta kafin ya dawo. Hayaƙin ya baibaye ko ina kawai sai gashi kamar an cillo shi. Runtse idanu yayi ta kalle shi ta wara idanu tace, “yi haƙuri ban san zaka dawo yanzu ba.” Bai tanka mata ba ya wuce ciki ta kashe wutar ta kunna a.c sannan ta shiga wajan sa. A tsaye ta same shi sai yatsina ya ke yi tace, “ka yi haƙuri ban san zaka dawo yanzu ba, ina fatan bau ciwon kan ko?.” Kallon ta yayi bayan ta ƙaraso ya ce, “haka ki ke yi kwana biyu, kin san bana son abu amma sai ki dinga yi.” Ta rausayar da kai tace, “ai na bayar da haƙuri ko?.” Wayar ta da take hannun ta ce take ƙara ta duba taga baƙuwar number ta ɗago ta kalle shi ya ce, “ɗauki.” Ba musu ta ɗauka ta zauna ana zancen abincin biki da ake so ayi tana faɗa musu yadda tsarin yake. Ganin yana kallon ta sai ta ce zata yi musu magana a whatsapp ta kashe wayar. Murmushi ya yi ya ce, “Chef Manal.” Tayi murmushi tace, “Dr Bebi.” Ƴar dariya ya yi ya ce, “Wannan Bebi dai yaƙi barin bakin ƴan gidan mu da su Yayan ki, yarana biyu amma a dinga ce min Bebi.” Tayi dariya tace, “wannan suna ai bazai ɓata ba.” Ya sauke numfashi ya ce, “Su Ayan basu dawo bane?.” “Tunda ka ganni a nutse har na samu damar yin turaren ƙhamshi ai basa nan, in suna nan ni na isa?.” Yayi murmushi ya ce, “in basa nan gidan baya daɗi.” Ta zuba masa ido tace, “kenan ni hoto ce ko?.” Ya girgiza kai yana taɓe baki ya ce, “ni dai ban ce ba, kawai nace in ƴaƴana basa nan gidan baya daɗi.” Jin ya maimaita sai taji haushi har a fuskar ta ta nuna hakan. Bata yi magana ba ya ga tayi shiru yayi dariya kafin ya yi magana tace, “akwai wacce na yiwa alfarmar ganin ka ranar monday a asibiti.” Ya ɗage gira yana kallon ta ganin ta canja ya ce, “to har alfarma ki ka fara yi ban sani ba?.” Ta kalle shi tace, “ko ban isa nayi ɗin bane? In nima sai an bani long booking ɗin sai a faɗa min kar na wahalar da baiwar Allah.” Dariya yayi ganin ta fusata ya ɗaga hannun sa ya ce, “wane mutum inji mutuwa?. Tuba nake ranki ya daɗe Allah ya kaimu monday ɗin.” “Amin” ta amsa a taƙaice bata kalle shi ba. Wayar ta ake kira ganin school ɗin su Ayan ne sai ta tashi ta fita ya bita da kallo yana dariya dan ya san ya tsokano ta. Babu jimawa sai ga Ayan ya shigo a guje ita kuma tana riƙe da hannun Ayda. Falon ya fito suka zauna tare gabaɗaya a nan suka ci abinci har lokacin bata saki ranta ba. Bacci suka yi ta kai su ɗakin su ta zauna a ɗakin ta tana yiwa matar da suka yi waya bayani a whatsapp. Shigowa yayi ya jingina da bango yana kallon ta yana murmushi ya ce, “Kafin na samu Ayan da Ayda Ammi na fara samu, Ammi itace fitilar gidan Adnan, Ammi itace hasken da yake haska ko wanne lungu na dinga Adnan. Manal ɗina itace jin daɗina da walwala ta a cikin gidan nan.” Kallon sa tayi ya tako ya zo inda take ya ce, “ki daina fushi akan nace in su Ayan basa nan gidan babu daɗi, wasa nake miki kema kin sani.” “In ma da gaske ka ke ai gaka gasu nan.” “Wasa nake yi, ni da nake da kamar ki ai so zan yi suje wajan Mummy ko wajan Mama su yi hutu su bar mu mu sake.” Murmushi tayi ya zo inda take ya dungure mata kai ya ce, “ni na san fushin naki bashi da dalili.” Tayi dariya ya kalle ta ya ce, “Ayda shekarar ta uku Manali, yaushe za a haifar min Jidda?.” Ta rausayar da kai kafin tayi magana ya ce, “har yanzu tsoron haihuwar ne? To kawai kema ki ce min a other room ki ka fo zaƙewa, a labour room kema raguwa ce.” Tunawa da abinda ya wuce sai suks yi dariya gabaɗayan su ta taso daga inda take ta shiga jikin sa ya rungume ta tace, “Allah ina tsoron haihuwa har yanzu.” Yayi dariya ya ce, “haka zaki daure a samo min mai sunan Mummy na Jidda kenan. In ba haka ba kema na fara yi miki gorin babu abinda ki ka iya sai harkar other room.” Tayi dariya tace, “Kamar wata kai?.” “Au haka ne? To mu gani a ƙasa.” Tayi dariya ya sake riƙe ta yana jin farin ciki a zuciyar sa. “Ni fa ko na haifi mace Ayra zai saka mata, sunayen ƴaƴana daga A zasu dinga farawa.” “Don iyayi?.” “Haka nake so.” Ya taɓe baki ya ce, “to ni dai in dai na saka sunan Mummy Jidda zan ce.” Manal tace, “babu ruwan ka kuma da wannan, ai ni zan haife ta ko?” Ta faɗa tana kallon idon sa. Shima kallon ta yake ya ce, “ke zaki haife ta, amma waye zai baki cikin?.” Manal tace, “Allah. Ko lokacin cikin Ayda da ka dinga yi min wayo Allah ne fa ya bani ba kai ba.” Yayi dariya mai sauti ya ce, “na san Allah ne ya baki, amma waye sila?.” Manal ta kawar da kai gefe tana dariya ya juyo da fuskar ta ya ce, “faɗi mana, a ruwa ki ka sha ko a ƙafa ki ka tako?.” Manal ta tayi dariya tace, “oho dai.” “Ammi zan sha corn flakes.” Muryar Ayan da suka ji sai ya sake ta ya shigo ɗakin ta kalle shi tace, “Ayan baka jima da cin abinci ba fa, daga yin bacci a farka sai a sha corn flakes?.” “Ni dai Ammi ina so” ya kalli Adnan yace, “Abie ka cewa Ammi ta bani corn flakes.” Yayi murmushi ya riƙe hannun sa ya ce, “zo mu je mu sha tare.” Suka fita ita kuma ta shiga wajan Ayda ta tarar itama ta farka ta riƙo ta suka fito falon. Tare suke sha dashi ita dai kallon su take yi tana yi musu video cikin ƙaunar su gabaɗaya. Aka yi kiran sallah suka tafi masallaci da Ayan itama tayi sallah. A ɗakin sa ya same ta tana gyarawa ya rungume ta ta baya yana bin wuyan ta da kiss mai kashe jiki tana lumshe idanun ta kafin ya ce, “In na kalle ki keda Ayan da Ayda ina jin matuƙar farin ciki Manal.” Ta juyo tana kallon sa bayan ta riƙe hannun sa tace, “da kuna shan corn flakes video nake yi muku saboda ina ƙaunar ku gabaɗaya Partner.” Tayi masa kiss a kumatu ta kwanta a ƙirjin sa tace, “ina ji a raina kamar babu wacce ta kai ni yin sa a a gidan auren ta.” Bayan ta yake shafawa a hankali ya ce, “Tarbiyar da ki ke bawa Ayan itace ta saka nake ji a raina da na rasa ki da nayi babbar asara a rayuwata. Ina son ki Manalin Mama.” Tayi murmushi tace, “Nima ina son ka Bebin Mummy. I so much love you.” Yayi dariya zai yi magana suka ji Ayan ya ce, “i love you Ammi, i love you Abie.” A tare suka kalle Bebi yayi murmushi yayi masa alamun ya taho ya ƙaraso a guje Ayda tana bayan sa ya haɗa su ya rungume a jikin sa yana hamdala ga Allah maɗaukakin sarki. Alhamdu lillah! Staring writing on August 2024 Completed on December 2024 Released on 1th January 2025 Finished on February 2025. _Abinda na rubuta daidai Allah ya bamu ladan, wanda na yi kuskure Allah ya yafe mana Amin. Allah ya sa mu cigaba watan ramadan lafiya mu ga ƙarshen sa lafia, Allah ya karɓi ibadar mu ya bamu lafiya bauta masa a wata mai girma Amin._ _Ni ce taku Nana Haleema, na gode masoyana Allah ya sake haɗa mu a sabon littafina wanda zai zo a ƙarshen shekarar 2025 in muna da rai da lafiya. In kuma an samu labarin mun amsa kira mahaliccin mu a taya mu addu’a Allah yasa zaman kabari ya fi mana zaman duniya daɗi Amin._ Nana Haleema❤️ 0701 809 8175 09030398006.