BDƘB2P001 Manal cikin wani irin tashin hankali da ciwon mara mai tsanani ta koma gida tana shiga gidan ta zube a falo kusa da Mama ta fashe da kika mai tsuma zuciya. Mama hankalin ta ya tashi ta lalubi fitila a gefe tace, "Manal lafiya? Me ya faru kike kuka?. Mubeena! Mubeena!! Zo da sauri." Mubeena ta fito wajan Manal ta riƙe ta Mama tace, "me yake damun ta haka? Manal Lafiya kike?." Yadda take yi ne a jikin Mubeena tana juyi hannun ta na kan cikin ta tana miƙewa tana kuka Mubeena tace, "Mama ciwon marar ta ne." Mama ta girgiza kai tace, "ya rasulillahi! Yau babu bacci kenan." Manal sai juyi yake tana kuka saboda azabar da take ji tana kawo mata barazana a marar ta da bayan ta. Mama tace, "ga Baban ku ba a nan yake ba ya, sai dai a kira Surayya akwai allurar da take yi mata ta samun sauƙi, Allah yasa Surayya bata yi bacci ba." Mubeena tace, "zanje na kira ta" ta faɗa tana fita ba jimawa suka dawo tare da Surayya ta yiwa Manal allura a jijiyar hannun ta. Mama tace, "Surayya taimaka da ruwan ɗumi, akwai wani ƙaramin towel a ɗakina ki haska ki ɗauko ki jiƙo shi da ruwan ɗumin." Surayya ta amsa ta yi abinda Maman tace ta kawo mata towel ɗin ita kuma ta cirewa Manal hijjabin ta ɗaga rigar ta kaɗan, a cikin ta ta ɗora towel ɗin tana matsa mata a hankali tana kwance a cinyar ta dan babu inda Manal take kwanciyar in bata da lafiya sai jikin Mama. Kuka Manal take har lokacin tana jikin Mama tana yi mata addu'a. A lokacin Baba ya shigo da sallama suka amsa ganin Manal a haka ne yace, "ciwon nata ya motsa kenen?." Mama tace, "ta ma ji sauƙi." "Allah ya ƙara lafiya" ya faɗa yana kallon ta suka amsa da amin kafin ya zauna yana kallon Manal a hankali bacci ya ɗauke ta. Huzaifa da yake jin abinda Bebi yake faɗa kamar ya tsinke shi da mari saboda takaici haka yake ji, ya rasa Bebi wanne irin mutum ne, ya rasa me yake damun sa baya iya sarrafa ɓacin ran sa, baya iya ɓoye damuwar sa zuwa wani lokaci, shi kawai a lokaci ɗaya zai aiwatar da abinda yake so. babu abinda bai ji ba, har lokacin da Manal ta juya shi kuma ya buɗe motar ya shiga yanayin sa gabaɗaya ya nuna tsantsar ɓacin rai da damuwa mai yawan gaske. Huzaifa baice masa komai ba haka suke tafiya har aka zo gidan su Bebi dan shi ya manta ma dashi a motar, yana faka motar Huzaifa ya fito sai a sannan ta kalle shi da jajayen idanun sa baice komai ba yayi gaba shima yabi bayan sa dan yana so ya nuna masa kuskuren sa akan abinda ya aikata tun da wuri. Suna shiga falon Bebin Huzaifa a fusace yace, "Kai a ganin ka abinda kayi wai daidai ne Bebi? Kai a rayuwar ka indai ran ka ya ɓaci sai ran kowa ya ɓaci? A ina ake wannan rayuwar ne?, a haka zaka yi auren kana wannan banzayen halayen?." Bebi bai bashi amsa ba ruwa yake sha ya rasa abinda zai yi yaji daɗi zuciyar sa. Zafi yake ji sosai yana ratsa shi, hakan ya saka yake shan ruwa kamar zai haɗa har robar ya shanye. Jin yayi shiru sai Huzaifa ya kuma fusata tace, "Kai waye da baza'a yi maka ƙarya ba? Yanzu da kaje ka samu yarinyar ka ke faɗa mata wannan maganar ka sani ko bata san maganar mahaifin ta ba? Ka sani ko an ɓoye mata saboda wani dalili?. Mutanen nan basu munafurci ka ba suka faɗa maka gaskiya saboda neman aure ake amma da yake kai ne na farko a duniya baza'a maka ba daidai ba, sai ranka ya ɓaci ka ɗauki ƙafa kaje ka samu yarinya ƙarama kamar ta mana cewa wai anyi disappointing ɗinka. Kai abu nawa ka ɓoye mata bata sani ba a kan ka? Kenan kai ne mutum ita ba mutum bace?." A fusace Bebi yace, "Wannan ba abinda ya shafe ka bane, rayuwata ce ko?." "Na san bai shafe ni ba, amma ka sani sai na faɗa maka gaskiya saboda bazan ɓoye maka ba." "meyasa ta ɓoye min? Meyasa bata faɗa min wanann yaron son ta yake ba? Meyasa bata faɗa min yayar ta yawon banza take ba?." "Saboda kai ma baka faɗa mata taka yayar tana bin tsohon mijin ta ba. Kamar yadda ka ke ganin wannan matsayin sirrin gidan ku ne haka itama a wajan ta sirrin gidan su in ya tabbata ma kenan, kenan kai sai dai kai ka ɓoye baza'a ɓoye maka ba?. Ka faɗa mata Rumana har gobe tana sonka?" Huzaifa ya faɗa cikin fusata sosai yana kallon Bebi. Bebi shima kallon sa yake yi jin abinda yace kafin yace, "Wannan ba damuwar ta bace domin ni ne zan aure ta ba itace zata aure ni ba, ni ne zan yi bincike akan lamarin ta ba ita ba. Tun farko na faɗa mata bana son ƙarrya, meyasa ta ɓoye min basa tare da mahaifinta da dangin su?" Ya faɗa shima a fusace yana kallon sa. Huzaifa yace, "yadda ka ke ji zaka yi bincike a kanta itama haka take ji, yadda zaka aure ta itama auren ka zata yi, indai zaka yi bincike a kanta itama zata yi. Kai meyasa baka uzuri ne a rayuwa? In bata san komai a kan iyayen nata bafa? Sannan koda yayar ta yawon banza take ya kamata ka faɗa mata haka?. Kai ka faɗa mata batun auren ka da Rumana? Nace....ta san da zaka sake aure bayan ka aure ta da wasu kwanaki? Ko ka faɗa mata soyayyar ka da Rumana?." Bebi baice komai ba Huzaifa yace, "Kai indai ranka ya ɓaci na kowa sai ya ɓaci haka ake rayuwa? A haka zaku yi zaman aure?. Baka bincike akan abu kawai sai ka yanke hukunci saboda a ganin ka hakan daidai ne, maganar da a waya ya isa ku tattauna amma kaje har gidan su yarinya kana faɗa mata maganar banza da wofi. Meye abin zuwa ka same a wannan maganar don Allah?." Bebi yace, "Na fasa auren, ai babu dole." "Itama tace ta fasa ai, kuma wallahi baza ka iya rabuwa da ita ba dole zaka koma mata na tabbatar maka da hakan. Zan baka amsa a lokacin da ka kasa jure rashin ta." Har ya juya zai fita sai ya juyo ya kalle shi yace, "Kai ka san Mujahid yaje har gida ya same ta yana ce mata ba auren ta zaka yi ba yaudara ce? Kai kasan da hakan?." Gani yayi Bebi yana kallon sa alamun mamaki sai ya girgiza kai yace, "Baka sani ba, ni nace zan faɗa maka tace a ƙyale ka kawai tunda ta tabbatar Mujahid ƙarya yake ta watsar da batun sa. Amma kai ka kasa sarrafa kan ka saboda wani banzan tunanin da banzar ɗabi'ar ka. Inda kaine akazo aka faɗa maka magana a kanta da yanzu ka hau kai ka zauna, amma ita sai ta bar maganar ta wuce." Bebi da mamaki yace, "kai ya akayi kasan da Muhajid yaje wajan ta?." "Saboda na fika daɗin mu'amala shiyasa ta zaɓi ta faɗa min ta ƙyale ka, ka gyara halin ka in ba haka ba babu macen da zata zauna da kai, in dai a haka zaka cigaba da rayuwa baza ka iya riƙe aure ba" yana gama faɗar hakan ya juya ya barshi a tsaye yana kallon sa. Wannan dalilin yana daga cikin abında yake ɓata masa rai game da Manal, ta yaya shi ne wanda zata aura amma tafi sakewa da wani Huzaifa a kan sa?, komai sai dai yaji daga bakin sa ita baza ta faɗa masa ba? Meye amfanin hakan?. Zama yayi a kan kujera gabaɗaya ransa a ɓace yake matuƙa ya rasa ma wanne irin tunani ya kamata yayi a wannan lokacin. So yake ya gano dalilin da ya saka tayi masa ƙarya amma ya kasa, ya tabbatar mata da baya son ƙarya baya son mai yin ta amma bai san meyasa ta zaɓi tayi masa karyar ba. At least ya kamata ta faɗa masa zancen mahaifin ta koda bata faɗa masa zancen Yayar ta ba, ya kamata ace yasan da cewa ba'a hannun iyayen ta take ba amma sai ta ɓoye masa. _Amma itama ai bata sani ba, kaga kamar bata da laifi kenan ko?_ zuciyar sa ta bashi amsa ya sauke ajiyar zuciya tare da furzar da iska daga bakin sa ya kulle ido yana hango ta lokacin da suke magana. _so ka ke kace ka fasa aurena? To ka fasa mana sai me._ kalaman ta suka zo ransa sai yaji kamar an soka masa wani abun a zuciyar sa nan take ransa ya sake ɓaci sosai ya kulle ido yana mamakin ta ashe zata iya cewa su rabu?. Yana ji an shigo an zauna a inda yake amma bai kalli waye ba, dafa kafaɗar sa akayi hakan ya saka ya kalli wanda yake gefen sa ganin wacece sai yayi ƙaramin tsaki ya ɗauke hannun ta daga kafaɗar sa ya jingina da kujera tare da cire glasses ɗin idon sa ya ajjiye a gefe. "Beb kar kayi min haka don Allah, don Allah don Annabin rahama kar ka auri wata kafin ni Beb, Ina sonka da kishin ka aikata hakan barazana ne ga rayuwa ta. Ji nake kamar zuciya ta zata buga wallahi, ban tabbatar da haka nake ƙaunar ka ba sai yanzu, don Allah ka amimce min kar soyayyar ka tayi silar mutuwa ta." Yana jin ta a yadda take maganar ya tabbatar kuka take yi don gashi nan yana ji muryar ta na rawa sosai amma hakan bai saka ya kalle ta ba sai ma ƙara cusa masa takaici da take yi a zuciyar sa, ga ɓacin ran da yake ciki ga kuma takaicin ta. "Na amince in ka aure ni ka auro wacce aka kaiwa kuɗin auren ko da a ranar da na tare a gidan ka ne, Amma don Allah kar ka hukunta ni ta hanyar fara auren wata bani ba. Nasan zaka ce nima ai na auri wani kafin kai, ƙaddara ce Beb amma ina sonka Allah ma yasan da haka, rasa ka zuciyata zata iya bugawa a ko wanne lokaci, ka taimake ni kar na rasa hankalina akan soyayyar ka." "In zuciyar ta buga ya shafe ni ne?, in kin rasa hankalin ki meye zai dame ni?. Ruman ki tashi ki bar min nan kafin nayi miki abinda yafi soyayyar da kike faɗa tsayawa a zuciya, shi take zai tarwatsa zuciyar ki bazai jira wani abu ba, ki tashi ki bani waje bana son magana bana son ganin ki ko kaɗan!" Ya faɗa da ƙarfi yana kallon ta itama shi take kallo ido cikin ido cikin tsoro. Duk da faɗa yake mata amma kallon idanun sa nishaɗi yake bata da tarin soyayyar sa da take huda ƙirjin ta ta shiga cikin zuciyar ta a wannan lokaci. "Ka taimaka min, na amshi laifina na baya, amma yanzu zan gyara komai, ka sake bani dama koda guda ɗaya ce." "Oh my god! Meyasa kike insisting akan wannan abun ne? Na faɗa miki bana sonki, bana son ki meyasa kike so ki takura min?. Ki tashi ki bani waje kafin ki ji saukar mari a kuncin ki." "Asslamu alaikum, Yaya ga abinci." Jin muryar Kausar sai ya kalli wajan da take yace, "Koma da abincin bana ci" ya miƙe tsaya yace, "zo kija ta ku bar min falon nan kafin na fasa mata baki, bana son ganin ta, kuma kar wanda ya sake zuwa falon nan indai bani na kıira shi ba" yana faɗa ya shiga ɗaki ya bar su a wajan. Rumana kuka take yi sosai sai ta bawa Kausar tausayi sosai, tunda ta guje shi da farko suke jin haushin ta amma yanzu tausayi ta bata ganin yadda yake mata tsawa ita kuma soyayya ta rufe mata ido tace, "ki daina kuka mu koma wajan Mama kar ya fito yace mun dame shi, yi haƙuri kizo muje." A haka suka fito zuwa wajan Mama suka same ta a zauna tana cin funkaso da miya ta bisu da kallo ba kamar Rumana da take kuka fuskar ta tayi ja sosai, kai tsaye inda Mama take ta nufa ta zauna a kasa tare da kwantar da kanta akan cinyar Maman tana sake fashewa da kuka. "Ina son shi Mama, ban tabbatar da hakan ba sai yanzu da zan rasa shi, ji nake zuciyata zata iya bugawa na mutu in ban aure shi ba, Ina ji zan iya haukacewa a lokacin da wata ta shiga gidan sa a matsayin matar sa Mama. Mama ki taimake ni kar na rasa hankalina akan Bebi, Ina son sa amma shi baya sona" ta faɗa cikin kuka sosai. Jin abinda take faɗa sai jikin Mama yayi sanyi sosai ta dafa kanta tace, "Haba Rumana! Sau nawa zan maimaita miki kalmar indai Ina da rai sai kin zama matar Adnan? Meyasa kike tantama Akan hakan?." "Ba tantama nake ba Mama, Amma yanzu shi baya sona yace baya son ganina, ni kuma wallahi Mama ji nake kamar ana zuba min son sa a zuciyata, da gaske in na rasa shi ban san ya zanyi ba." "Baza ki rasa shi ba in sha Allah, kar ki damu yana sonki kin san halin sa wataƙila yau ransa a ɓace yake shiyasa, ki kwantar da hankalin ki ke matar Adnan ce, kar ki yi tunanin dan zai auri wata ba ke ba kamar baya son ki ne. Ramuwa yake akan abinda ya wuce na tabbatar Bebi yana sonki. Haba kar ki manta kece first love ɗin sa fa, kin san first love ba'a mantawa dasu saboda mahimmacin su, na tabbatar shima bai manta dake ba duk abinda kika ga yana yi yana sane, ki yi haƙuri lokaci ne." Jin bata ce komai ba sai kuka Mama tace, "Tashi kije kiyi wanka ki kwanta wannan kukan ciwo zai saka miki." Daƙyar ta iya tashi ta shiga ɗakin da yake nata ko yaushe in tazo Mama ta bita da kallo. Kausar ta kalla tace, "me yayi mata haka?." "Ban sani ba Mama, ni kaina bai tsaya ma yaji funkaso bane yace na dawo dashi a lokacin tana zauna tana kuka shi kuma yana tsaye. Amma kamar ransa a ɓace yake sosai." Mama bata ce komai ba ta tashi ta shiga ɗaki itama Kausar ɗin haka. Cikin dare Mimi ta fito shan ruwa falo taga Rumana a zaune sai rawar sanyi take yi alamun zazzaɓi, da sauri tazo wajan taji jikin ta zafi sosai ta garzaya wajan Mama ta samu tana shirin kwanciya ta fito daga banɗaki ta sanar da ita suka fito tare. A kusa da ita Mama ta zauna ta taɓa jikin ta taji zafi sosai tace, "Mimi dauƙo min waya ta na kira Bebi." Da sauri Mimi ta koma ta ɗauko ta kira mata shi. A lokacin yana zaune bai yi bacci ba yana saƙa da kwancewa akan abinda ya yiwa Manal yaga kiran Mama na zuwa, ai da hanzari ya ɗauka yasan ba lafiya ba, Jin abinda tace sai ya tashi ya saka doguwar riga ya fito ya shiga falon da sallama suka amsa Mama tace, "zo ka duba ta da sauri, jikin ta yayi zafi sosai." Ƙarasawa wajan yayi ya miƙa hannu ya taɓa goshin ta da bayan hannu sa yaji zafi sosai ya kalli Mimi yace, "ki bata paracetamol ta sha zai sauka." "Paracetamol kawai?" Mama ta faɗa tana kallon sa cike da harara. Ganin irin kallon da Mama take masa sai yace, "me yake damun ki bayan zazzaɓin?." Rumana murya na rawa tace, "ciwon kai da ciwon ƙirji." Yayi shiru na wani lokaci Mama tace, "ko asibiti zamu je?." "A'a Mummy, akwai a ɗaki bara na kawo" ya faɗa yana fita, ba jimawa ya dawo da magani ya bawa Mama yace, "ta sha yanzu zata dawo dai dai in sha Allah." Mama ta karɓa aka bata tasha ya kalli Mama yace, "Allah ya ƙara lafiya. Sai da safe." "Allah ya tashe mu lafiya" ta amsa a ciki ya fita dan shima magani zai sha kan sa ciwo yake. Washe gari da ciwon kai da nauyin jiki ya tashi a haka yayi wanka ya fito ya shiga wajan Mamy suka gaisa ya tambayi Lubna tace taje makarnata daga nan ya wuce wajan Mama. Mama tana zaune ita kaɗai ya shiga da sallama ta amsa ya zauna yace, "Barka da safiya, ban iya fita sallah ba yau saboda ciwon kai shiyasa ban shigo ba." Mama tace, "Barka dai." Shiru yayi kafin ya kalli inda ake ajjiye abinci, yunwa yake ji sosai amma bazai iya cin komai ba gashi shi tea ba wani damun sa yayi ba balle yace zai yasha. Mama ta kalle shi tace, "in Rumana ta rasa ranta ta dalilin ka bazan yafe maka ba Bebi, ko wani ciwon ta samu ta silar ka bazan sassauta maka ba." Da sauri ya kalle ta jin abinda yake cewa yace, "Mummy lafiya?." "In da kana da mutunci kana zama a wajan nan ita zaka fara tambaya saboda a yadda ka barta jiya, ko baka ɗauke ta matsayin wacce zaka aure ba ka ɗauke ta matsayin ƴa ta, kai ko bata kai wannan matsayin ba zaka iya mata kallon mara lafiya a matsayin ka na likita. Duk bata samu wannan darajar ba Bebi, wata bare a waje ta fita mahimmaci a wajan ka." Bai iya magana ba yayi shiru dan bashi da abin cewa, koda akwai abin cewa ɗin ma Mama indai akan Rumana ne bata ɗaga masa ƙafa ko kaɗan. Mama tace, "zuwa wajan ka da tayi jiya shine silar ciwon da ta kwana dashi ta kuma tashi dashi, Amma da ka shigo ko ka tambaye ta saboda bata da wnanan mahimnacin a wajan ka. Jiya kai ne ka faɗa mata maganar da ta kai ta ga kwanciya zazzaɓi" Mama ta girgiza kai ta kuma cewa, "komai in nace kana yi min a duk lokacin da nake so, amma akan Rumana ka gaza yi min abinda nake so saboda wani banzan tunanin ka da ya riga ya wuce, ka kiyaye ni wallahi, ka yi a sannu, yadda ka ke gasa mata aya a hannu akan soyayyar ka wallahi kaima zan gasa maka taka ayar tunda abin naka haka ne. Kuma wallahi ka sani ƙiris nake jira na yanke alaƙar ka da wacce ka ke so ɗin, in na yanke sai naga na isa da kai ko ban isa ba." Shi dai Bebi yayi shiru yana jin abinda take cewa yaji tace, "ka kiyaye ni wallahi, akan Rumana babu abinda bazan maka ba. Ka zaɓi wata ta waje a kanta, duk tarin soyayyar da take mata ka rufe ido ka nuna kai baka santa ba, ka bani mamakk ban yi zaton hakan daga wajan ka ba." Kansa yana ƙasa bai ce komai ba ta harare shi tace, "Tashi ka bani waje." Jikin sa a sanyaye ya tashi yace, "ki yi haƙuri" yana faɗa ya fita tayi tsaki tace, "ya zama dole ko ta wanne hali Bebi ya amince da auren Rumana kafin waccan da yake so ta shigo, hakan shine mafita. Ta bakin ita Rumana ɗin in ya auri waccan zai manta da ita ne, dole ya zaɓa ko ya aure su ɗaya da Rumana ko kuma ya fara auren Rumana, in ba haka ba ya haƙura da auren ita yarinyar, dan bazan zuba ido Rumana ta rasa ranta saboda shi ba." BDƘB2P2       Manal jikin ta babu ƙwari ta farka dan bata yi baccin kirki ba ta fito tsakar gida inda take jiyo motsin Mama dan tasan ta tashi zuwa lokacin rana ta fito sosai. Ta ƙarasa inda Mama take ta zauna tace, "Sannu Mama." Mama tace, "kin fito? Ya jikin naki?." "Da sauƙi." "Tashi kije ki yi wanka zaki fi jin daɗi." Da to ta amsa ta miƙe ta shiga bandaƙin ta fito ta ɗebo ruwa dan ita ruwan zafi ba wani damun ta yayi ba ta wuce da ruwan cikin falon su ta shiga ɗakin Mama dake akwai banɗaki tayi wankan. Ba jimawa ta fito tsakar gidan ta saka riga da siket na kanti rigar mai ƙaramin hannu ta shan iska ta dawo inda Mama take ta zauna tace, "Mama ina Yaya?." Mama tace, "bata ciki?." "Ban ganta ba gaskiya." "To ta fice, Daman hanya take nema da yake taga Baban na ku ya fita tun safe shiyasa ta gudu. Taje tayi ai duniya ce." Manal tace, "Mama kin sha maganin ki? Ina glasses ɗin na ki?." "Ban sha ba, shi kuma ban san inda na ajjiye shi ba sai dai ki duba." Tashi tayi ta koma ba jimawa ta dawo dashi da maganin tace, "gashi na ɗauko." Ta bata ta saka, Maman ta kalle ta cikin ganin da ba bashi da auki sosai tace, "kin rame sosai, wannan ciwon mara yana wahalar dake, Allah yasa in kin yi aure ki daina." Manal ta amsa da amin zuciyar ta na tuno mata abinda ya faru jiya ta bawa Mama maganin ta sha Mama tace, "kije ki karya, na bayar an siyo kunu tun safe nasan yanzu ma yayi sanyi. Rashin glasses ɗin nan ne da da kaina zan dama." Manal ta tashi ta shiga kitchen ta ɗauko kunun tana sha Mama tace, "jikin ki babu ƙarfi, baza ki samu damar zuwa kasuwar bama yau. Sai ku je gobe in Allah ya nuna mana." Manal ta sauke numfashi tambayoyi ne sosai a zuciyar ta wanda take son yiwa Mama amma ta rasa ta wacce hanya zata fara, bata so silar tambayar Mama ta shiga damuwa amma tana so ta san waye mahaifin su? A Ina yake? Sannan da gaske Baba ba ɗan uwan sane bane kamar yadda take faɗa musu?. Ganin tayi shiru sai Mama tace, "tunanin me ki ke yi?. Jiya kince min zaki je wajan Adnan karɓo saƙo daga nan kika dawo babu lafiya, wanne saƙo ya baki?." Manal ta sauke ajiyar zuciya ta kalli Mam tace, "tambayata yayi daman wai mahaifin mu ba rasuwa yayi ba, sannan yace daman Baba ba ƙanin mahaifin mu bane nayi masa ƙarya." Kallon ta Maman take yi sai ta kawar da kai gefe tayi shiru bata ce komai ba. "Mama da gaske ne abinda ya faɗa? Da gaske Baba bashi da wata alaƙa damu ta jini?. Mama na shiga confusing don Allah ki sanar dani ko hankalina zai kwanta. Ina mahaifin mu? Meyasa kika ce mana ya rasu?." Mama ta kalle ta cikin rashin ganin ta sosai tace, "shi Adnan ɗin ne ya tsare ki da wannan tambayoyin?." "Mama ya samu labari ne saboda an sanar dashi komai game dani, kinga dai a ɓangaren neman aure ba'a ƙarya shiyasa Baba ya faɗa masa komai." "Cewa yayi ya fasa auren ki in baki faɗa  masa ba kenan ko me?." Jin abinda Maman tace sai ta kalle ta zata yi magana Mama tace, "in ma cewa yayi ya fasa auren ki har sai yaji labari akan mahaifin ki ya fasa ai baza ki rasa wanda zai aure ki ba, ba dole a maganar aure, in yaga ya fasa in Baban ku ya dawo sai aje a mayar musu da kuɗin da suka kawo wannan ba komai bane ba." Manal da mamaki take kallon Mama jin abinda take cewa tace, "Kenan Mama baza mu san asalin mahaifin mu ba...." Mama ta dakatar da ita cikin tsawa tace, "Kinga Manal ya ishe ni!, ke dai kin san ba cikin shege nayi na haife ku ba ko? To ki dakata min da wannan maganar bana son ji, in akan auren Adnan ne kike wannan maganar ai ba shine kawai namiji a duniya ba, na tabbata zaki samu wani wanda ya fishi wanda bai damu da yasan wannan maganar ba" ta nuna ta da yatsa tace, "Manal a bar maganar nan haka, bana so kar a sake yi min ita in dai kina son kwanciyar hankalina" ta faɗa tana tashi tsaye. Manal tace, "ki yi haƙuri" Mama bata tanka mata ba ta wuce ta Manal ta bita da kallo zuciyar ta na so ta hasaso mata dalilin Mama na wannan maganar.          Mubeena a lokacin da ta faki ido ta bar gidan kai tsaye gidan su Bily ta wuce, tana shiga Mummyn su ke tambayar ta kwana Biyu bata shigowa tace bata jin daɗi ta wuce zuwa wajan Bily. Tana shiga ɗaki ta same ta tana shan tea tan danna waya tace, "Bily meyasa zaki je gidan mu kice wai an kore ni daga makaranta?." Bily ta kalli Mubrena tace, "haba Mubeena, wannan wanne irin abu ne babu sallama babu komai sai dai naji maganar ki a kaina?." Mubeena ta zauna tana kallon ta tace, "abinda kika yi min ne sam ban ji daɗin sa ba, gashi nan dalilin hakan an kafa min tarko an hana ni zuwa ko Ina kamar wata yarinya ƙarama, komai nayi a kan idon mutanen gidan. Kin san ya akayi na fito yanzu kuwa?." "Eh, ai ni naje gidan na faɗa musu saka ido a kan ki domin lamarin naki yana neman wuce gona da iri, yanzu gashi da aka killace ki har kyau kin ƙara yi." "Kin san abinda hakan ya jawo min? An ƙwace min waya, an hana ni fita, na zama kamar wata marainiya saboda kaɗaici, Meyasa zaki aikata min hakan?. Ke kin san bana iya zaman awa guda babu waya amma kika zama silar da aka karɓi ta hanuna, gaskiya ban ji daɗi ba." Bily tace, "daidai kenan, indai kina tare da wannan Alhajin abinda zaki aikata ke kan ki baki sani ba, shiyasa na yiwa tufkar hanci." Mubeena tace, "auren Manal fa za'a yi har an saka rana amma ni babu kowa ta dalilin ki an raba ni da wanda zai aure ni, Meyasa zaki min haka?,  wallahi ban ji daɗi ba.." "Inda ace auren ki zai yi da kaina zan raka shi gidan ku lokacin da yazo gidan nan." Mubeena da sauri tace, "yazo kike so ki ce?." Bily tace, "yazo, na kuma faɗa masa aure za'a yi miki kuma kun koma garin ku kin bar kano." Mubeena da sauri ta kalle ta sai ta zabura ta koma kusa da ita tace, "Kina nufin yazo nan? Meyasa kika ce masa haka Bilkisu?." Bily tace, "saboda so nake ya rabu da ke, saboda tarayyar ku lalata ki zata yi  ni kuma matsayina na ƙawar ki dole na faɗa miki gaskiya na kuma yi abinda nake ganin shine daidai." Girgiza kai take yi tace, "wannan ba daidai kika yi ba Bily, meyasa zaki masa ƙarya bayan kin san Ina son sa shima yana sona? Waye yace miki da wani abun yake nema dani ba aure ba?." Bily tace, "ya taɓa miki maganar aure tunda ku ke?." Mubeena tace, "sai na faɗa miki?." "Surutun ki bazai saka ki yi shiru ba, bai taɓa yi miki maganar aure ba ko yaushe son taɓa jikin ki yake yi. İn sha Allah baza ki sake samun sa ba ya tafi kenan." Mubeena tace, "baki kyauta min ba wallahi, kin san halin da na shiga kwana biyu da bana ganin sa? Shi yanzu kin san halin da yake ciki?." Bily tace, "yana can tare da wata wanne hali zai shiga Mubeena? Ke kike haukan banza kina ganin yana tunanin ki baki san yana can tare da wata ya manta ma dake. Inda alaqar Allah da annabi ce da yanzu ya dawo ya sake neman ki amma bai sake zuwa ba saboda daman shi ba auren ki zai yi ba." Mubeena ranta ya ɓaci sosai tace, "ki ƙyale ni kawai bana son wannan maganar taki, ni zanje na nemo shi da kaina kuma sai na same shi" Tana faɗa ta fita Bily tana cewa, "kije ki tayi babu ruwana ko me zaki yi nan gaba wallahi, kin san daidai kin san ba daidai ba. Ƙarƙari na yanke alaƙa ta dake kowa ya kama gaban sa. Mubeena bata ma ji ba tuni ta fita da yakr bata ga Mummy a falo ba da sauri ta fice. Tafiya take yi a ƙasa ranta a ɓace akan abinda Billy tayi mata, kamar a mafarki kawai taga motar sa ta faka a nesa da ita. Cak ta tsaya sai kuma ta cigaba da tafiya tunawa da tayi wataƙila bashi bane tazo zata wuce ya sauke glass yace, "kin san mutane bana so su gane ni, ki shigo kawai." Jin muryar wanda yayi magana sai ta kalle shi ta gefen baya yaga an ɗaga glass ɗin ta tabbatar shine dan ga muryar sa nan ta buɗe motar ta shiga driver yaja suka tafi. Shiru babu wanda yayi magana tafiya kawai suke har suka je gidan sa aka buɗe gidan aka shiga driver sai ya fita daga motar. sai a sannan ya kalli Mubeena ido cikin ido yace, "Kenan kin kyauta?." Zata yo magana ya dakatar da ita yace, "mu je ciki bana son magana a nan" ya faɗa yana fita daga morar ya shiga ciki dole Itama tabi bayan sa. Tana shiga ya bita da kallo from head to toes kamar zai mata kuka yana kallon cikin idon ta yace, "yanzu kin kyauta kenan Baby? Me nayi miki da kika zaɓi ki ɓoyewa ganina? Wanne laifi na aikata miki da kike yi min wannan hukuncin mai tsauri da na kasa jure masa?." Mubeena tace, "Ba laifina bane ba, kana raina wallahi Baby, bani da waya kuma bana fitowa shiyasa." "Har gida na aika a kai miki waya akace bakya nan, naje da kaina sai akace min wai kin bar garin nan kin koma Adamawa kuma aure za'a yi miki" ya tako ya ƙaraso inda take ya riƙr hannayen ta duka buyun yace, "Ina kika shiga? Me nayi miki?." "Ba ɓuya nayi bafa, kana raina burina na samu dama na neme ka, tun daga lokacin bana fitowa sai yanzu na samu dama na fito." Bakin ta yake kallo yadda take magana tana turo shi gaba ya lumshe ido yace, "me ya faru haka?." "Ƙwace min waya ta akayi a gida, sannan aka hana ni fitowa." Murmushi yayi ya ja kumatun ta yace, "da girman ki a ƙwace wayar ki kuma a hana ki fitowa?." Sake turo baki tayi tace, "Allah da gaske nake, gashi ban haddace number ka ba balle na kira ka da wani layin." Yayi murmushi yaja hannun ta suka zauna yace, "ashe kin damu dani da yawa, yau ma hanyar gidan naku nabi ko zan ganki dan ban amince da kin tafi wani gari ba, kamar a mafarki sai ga ki." Murmushi tayi itama tace, "kaga alamun zuciyar mu ce a na waje ɗaya ko?." Yayi murmushi yace, "wannan gaskiya ne Baby. Yanzu dai bana so na sake kwana biyu ban yi magana dake b, ya za'a yi?." Ta sauke numfashi tace, "Nima ban sani ba." Yace, "babu batun maganar auren nan dai ko?" Ya faɗa yana haɗe fuska, tayi dariya tace, "Babu, Bilkisu ta faɗa ne kawai, Amma ni bani da saurayi ma." Ya sauke ajiyar zuciyar yace, "Naji daɗin hakan, ki samar mana da solution ya za'a  yi." Kafin tayi magana yace, "ko kuma na baki wata wayar ƙarama da sabon sim card in yaso sai ki dinga kira in kika samu lokaci mu dinga haɗuwa tunda doguwar waya baza ta yi ba ko?." Mubeena tace, "baza ta yu ba, hakan yayi sosai zan kuma nemi hanyar da zan dinga fitowa. Kawai Baba ne ya takura min, kuma ba shine baban mu ba." Yayi murmushi yaja hancin ta yace, "kar ki damu ai babu wanda zai sake raba mu a yanzu." Tayi dariya shima haka yana kallon ta kafin yace, "baza ki ci komai ba?." Ta ɗaga kai almaun eh yace, "kinga kin zo a lokaci da ya ƙure, zan yi tafiya anjima kaɗam zuwa Abuja, ko zaki raka ni?." Ta wara Ido tace, "A'a dai, Sai ka dawo." Yayi dariya yace, "bakya kewata ko?." Ta girgiza kai almaun a'a suna ta hıra har aka kawo waya ƙarama da sabon sim card, sai da ya tabbatar ya samu hanyar magana da ita sannan ya saka aka mayar da ita dan jirgin sa ya kusa tashi, badan haka ba da babu abinda zai hana bata kwana a inda yake ba amma a tara a gaba. BDƘB2P003 Bebi kuwa haka ya wuni a asibiti, jikin sa babu ƙarfi ko kaɗan ga maganar Mama ga kuma abinda ya yiwa Manal jiya, gabaɗaya abin ya dame shi dana sani ta gama mamaye masa zuciya. Bashi da wani kuzari komai haka yake yin sa sukuku damuwa ta masa yawa ya kasa sarrafa ta. Numfashi ya sauke ya ɗauki waya da niyar kiran ta amma sai ya kasa kunyar ma yi mata magana yake, ya ajjiye wayar tare da furzar da iska daga bakin sa. “Bebi yanee! Ka fito muje duba Muhammad.” Bebi ya kalli Hamza yace, “ku je kawai bazan iya zuwa ba.” Hamza ya bashi da kallo yace, “Meyasa kwana biyu ka ke bawa damuwa gurbi a zuciyar ka ne? Meyasa kwana biyu cikin damuwa kake aikin ma baka mayar da hankalina kai Bebi?.” Bebi ya wara hannayen sa yace, “damuwar nake ciki ne Hamza, na rasa gane wanne yanayi nake ciki a yanzu. Zuciyata a cushe take bana tare da farin ciki ko kaɗan.” “Me yake faruwa?.” “Komai ma ya faru.” “To kayi haƙuri, ko meye kayi ƙoƙarin magance shi zai wuce in sha Allah.” Ya sauke shi yar zuciya yace, “abinda nake ƙoƙarin nayi kenan amma na kasa, wallah azim Hamza Ina son Manal.” Hamza yayi ƴar dariya dan da alama bai san ya faɗa ba yace, “na san kana son ta mana Bebi, itace kuma wacce zaka aura. Meya kawo wannan maganar?.” Bebi yace, “na saka mata shakku a kaina, babu lallai ta amince da abinda zance mata.” Hamza yayi murmushi yace, “Zata amince mana Bebi, kai dai ka dinga sassauta ɓacin ran ka a ko wanne lokaci, taya zaka ce duk abinda ka ke so shi za’a yi? Kai ko yaushe in ranka ya ɓaci na kowa ma sai ya ɓaci? a Ina ake haka?.” Bebi ya sauke nimfashi yace, “Ku je kawai zan je wani lokacin.” Hamza Jin abinda yace sai ya fita ya bar shi dan yasan yana son katse maganar da ake yi ne shi kuma Huzaifa ya sanar dashi komai. Ya jima yana yana tunani shi kaɗai har akayi sallar la’asar ya kasa samun sukuni a zuciyar sa. Wani iri yake ji ya kasa sarrafa kansa gabaɗaya, kamar ya zubar da hawaye haka yake jin sa. Sai da akayi sallar magriba a lokacin ya bar asibitin kai tsaye gidan su Manal ya wuce domin ya saka a zuciyar sa zai je wajan ta kawai ya bata haƙuri. Muneeba lokacin da ta koma Mama bacci take, Manal na kallon ta ta wuce zuwa ɗaki ba tace mata komai ba itama bata ce ba amma a zuciyar ta tana yi mata fatan shiriya tunda gashi har an fara cewa tana yawon banza. Bayan sallar magriba suna zaune Mama da Manal gidan babu haske sosai sai na ƙwan solar guda ɗaya dan babu wuta. Manal tayi shiru tana tunani Maman ma haka, tun lokacin da Manal tayi mata maganar nan shikenan taga canji a wajan Maman komai tana yin sane kamar ba ita ba. Baba ne ya shigo da sallama Manal ta amsa Maman ma ta amsa ya ƙaraso ya zauna Manal tace, “Baba Sannu da zuwa.” Baba ya amsa yace, “ya jikin naki?.” “Naji sauƙi.” Baba ya kalli Mama yace, “Kema babu lafiya ne Fatima?.” Mama ta sauke nunfashi tace, “lafiya nake, maganar auren Manal da Adnan ne, tunda ya fasa babu amfanin cigaba da ajjiye kuɗin da ya kawo, a mayar musu tun kafin lokaci yayi Nisa.” Baba da mamaki ya kalle ta yace, “wacce irin magana ce wannan? Yaushe Adnan ɗin yace ya fasa auren ta?.” Mama tace, “bata faɗa maka ba ashe?, ai jiya yazo ya same ta yace shi bai san asalin mahaifin ta ba dan haka bazai aure ta ba, ni kuma indai a kan wannan ne gwara a fasa auren.” Baba ya kalli Manal yace, “haka akayi?.” Manal ta ɗaga kai alamun eh tace, “Yace na ɓoye masa ban sanar dashi hakan ba, na nemi Mama ta sanar dani amma sai naga hakan ya ɓata mata rai.” Baba ya sauke numfashi yayi shiru na wani lokaci kafin yace, “Wannan ai ba maganar fasa aure bace ba Fatima, magana ce a kan….” Waya aka yi masa hakan ya saka bai ƙarasa faɗa ba ya ɗauki wayar ya fita. Baba yana fita ya hangi Adnan a tsaye a jikin mota, hango Baban yayi ya ƙaraso ya gaishe shi da girmamawa Baba ya amsa fuska a sake kafin yace, “Gashi an yi kira, muje masallacin.” Tare suka je suka yi sallar i’sha suka fito suna tafiyya Baba yace, “Yanzu Fatima take faɗa min wata magana.” Adnan ya sauke ajiyar zuciya yace, “A kan maganar nazo Baba.” Baba yace, “mu ƙarasa daga ciki” Baba ya faɗa yana shiga ciki ya samu Mama ce kawai Manal ta tashi yace, “shigo mana Adnan.” Mama na zaune bata motsa ba dan hijjabin da tayi sallah yana jikin ta hakan ya saka da taji haka bata motsa ɗauko hijjabi ba. Bebi ya shigo da sallama Mama ta amsa ya ƙarasa kusa da Mama ya gaishe ta ta amsa Baba ya masa iso zuwa falon sa, suka shiga ya zauna shima ya zauna Baba yace, “ina jinka Adnan.” Bebi yace, “Baba ayi haƙuri da abin ya faru, ban yi hakan da wata manufa ba.” Baba yace, “da gaske kace ka fasa auren nata kenan?.” Bebi yace, “ban furta haka ba Baba. Allah ya sani bana so a ɓoye min komai musamman a wannan ɓangare na aure, da ake sanar dani magana akan mahaifin ta da kai sai nake ji meyasa bata sanar dani tun farko ba.” Baba yayi murmushi yace, “Adnan Manal bata san da wannan maganar ba ko da wasa, a ko yaushe kallon mahaifin su suke a matsayin matacce wanda ya bar duniya saboda hakan babar su tace musu. Har kawo gobe bana tunanin ta faɗa musu ba mutuwa yayi ba, haka zalika bata san ni ba jinin mahaifin su bane ka fahimta?. Bebi ya amsa Baba yace, “Abinda na sani Manal da Mubeena yara ne kamar kowa, da uban su da aka haife su ta hanyar aure ba ta lalatacciyar hanya ba. Wataƙila mahaifin su yanzu yana raye wataƙila ya mutu. Abinda nake so ka sani duk wata nagarta da ake nema a ɓangaren neman aure Manal ta kai wannan matakin, ba wai ina yabon ta dan ta kasnacewa tawa ba, a’a ina faɗar abinda yake gaskiya ne a kanta.” “Manal mace ce nagartacciya mai matuƙar ƙaunar mahaifiyar ta, bata so taga wani abu ya samu mahaifiyar ta ko kusa, duk wani tunani da ka ke a kanta duk ba haka bane. Manal baza tayi maka ƙarya ba, da ta san da wannan maganar da ta faɗa maka baza ta ɓoye ba. In akwai abinda aka ɓoye maka akan neman auren Manal bai wuce ciwon marar da take fama dashi a duk tsakiyar wata ba, jiya dashi ta kwana har yanzu bata dawo daidai ba. Wannan shine akwai abinda nasan na ɓoye shima na manta ne amma da har magabatan ka sai na sanar dasu dan a ɓangaran aure babu abinda ake ɓoyewa. Na san ka san tana da ciwon sikari, amma sai da na sake maimaita musu dan su ma su sani.” Baba ya sake cewa, “Mahaifiyar su bata son zancen mahaifin su ko kusa, duk wannan soyayyar da shaƙuwar da take tsakanin Manal da babar ta yau saboda tayi mata maganar da kayi mata ka gansu can shiru ko hirar da suka saba basa yi. Allah kaɗai ya san dalilin ta na ɓoyewa yaran ta waye mahaifin su, Amma in kana shakku akan abinda nace ba wani abu nane dan an warware maganar tunda ba nisa tayi ba daman.” Bebi da sauri yace, “A’a Baba ba haka nake nufi ba, iya wannan maganar da kayi min ma Alhamdulillah na gamsu sosai, kuma na amince da auren daman ban ce mata na fasa ba itace ta fassara maganata da haka.” Baba yace, “ni ban san daga inda maganar an fasa ta fito ba, dan da ita aka fara tarbata ta da na shigo gidan nan.” Bebi ya sunkuyar da kai yace, “duk kuskurena ne, kuma zan gyara in sha Allah. Ayi haƙuri Baba, a bawa Maman ma haƙuri.” Baba ya kalle shi yace, “ba dole fa Adnan, in kaga baza ka iya ba zaka iya ƙyale ta wataƙila babu alkhairi a cikin auren shiyasa abin yazo da haka.” “Kayi haƙuri Baba, wallahi babu wannan a zuciyata, don Allah ka yi haƙuri.” Baba yayi murmurshi yace, “Shikenan, Allah ya tabbatar mana da alkhairi.” Ya amsa da amin yana godiya har ya baya Baba mamaki. Baba yace, “kaji batu akan ciwon da yake damun ta ko?.” Ya ɗaga kai almaun eh Baba yace, “To ma sha Allah. Zan je yanzu zan turo maka ita ku gaisa.” Bebi yace, “A’a Baba, da ka barta tunda bata da lafiya.” “Gwara tazo ɗin, Manal akwai ta da mayar da ƙarami babba, yanzu in ta san kazo ka tafi sai ta ɗauka da gaske an fasa, kuma a haka zata ɗauka babu wanda zai canja mata tunani.” Adnan yayi murmushi Baba ya fita, Bebi ya sauke numfashi dan daman yana son ganin ta Allah ma ya sani. Yana nan zaune a kan carpet bai tashi ba yana danna waya ta shigo jiki babu ƙarfi da sallama, ya amsa yana kallon cikin ƙaramin hasken dake falon, fuskar ta tayi haske sosai amma ta ɗan kunbura kaɗan gashi fuskar babu annuri kamar yadda ta saba. Zama tayi muryar ta a ɗan dashe kaɗan tace, “Kazo karɓar kuɗin ne?.” Bebi bai ma ji mai tace ba kallon ta kawai yake yi cike da so da ƙaunar da yake mata wacce bai san iyakar ta ba. Ganin hakan sai tayi shiru ta kawar da kai gefe hakan bai sa ya daina kallon ta ba, shauƙi yake ji na soyayya yana shiga jikin sa har lumshe ido yake saboda daɗin kallon ta. Wayar sace tayi ƙara sai a sannan ya dawo hankalin sa ya kalli wayar ganin sunan Mummy sai ya ɗauka, yayi shiru almaun tana magana kafin yace, “yanzu zan dawo in sha Allah” daga haka ya yanke wayar ya kalle ta yace, “me ma kika ce ɗazu?.” Ɗago ido tayi ta kalle shi suka haɗa ido ya ɗaga mata gira ɗaya yace, “me kika ce?.” Bata yi magana ba ta sauke kai ƙasa ya murmusa yace, “na tuba, ki yi haƙuri ko a jiya ba abinda kika furta nake nufi ba. Allah bana son ƙarya kuma bana so a ɓoye min komaai Manal, shiyasa kika ga haka amma bawai dan bana son ki ko dan na fasa auren ki bane.” “In kai baka fasa ba ni na fasa, ba zan iya zama da wanda baya sarrafa ɓacin ransa ba. Ko da ace nasan da maganar da ka faɗa min iyaka abinda zaka min kenan balle ban sa ni ba sai a jiyan. ka cewa Yayata mai yawon banza, ko da gaske hakan ne ni jinin tace kallon idona ka faɗa wannan maganar akwai ciwo balle haka bane. Kace na ɓoye maka Yaya Haron yana sona ko? To kawai kaje ka samu wacce bata maka ƙarya kuma bata ɓoye maka komai ni ka barni dashi kawai. In kai baka fasa aurena ba ni na fasa Dr, aurena da kai zai zamar min damuwa ne ni kuma bana son ta. Indai a haka zan yi zaman aure da kai auren bazai taɓa yin ƙarko ba” ta faɗa tana kallon sa daga gefen idanun ta tana ganin yadda yanayin sa ya canja zuwa na tashin hankalin da nadamar abinda yayi, ita kuma bil haƙƙi da gaske ta fasa auren sa. BDƘB2P004 Kallon ta yake ya kasa koda ƙifta idon baya yi ganin da gaske fa take maganar har zuciyar ta take faɗa, ganin kallon da yake mata ido cikin ido sai ta ɗauke idanun ta daga kallon sa ta kawar da kai fece bata sake cewa komai ba. Shiru ne ya biyo baya bai daina kallon ta ita kuma bata yi magana ya sauke numfashi yace, "Manal!." Ƙirjin ta sai da ya buga sosai dan gaskiya yadda ya faɗi sunan ya shige ta daure bata kalle shi ba yace, "yadda ki ke tunani ba haka bane, ki manta da komai ya wuce don Allah.” Manal tace, "Kai kace na yaudare ka na ɓoye maka wani abun da ni kaina ban sani ba, ka cewa Yayata mai yawon banza, wannan kalmar kasan yadda na ji ta a zuciya ta kuwa?." Yayi shiru dan a yanzu ya gano kuskuren sa na faɗar abinda yace, ya kalle ta yaga fuskar ta babu walwala kwata-kwata kamar ba ita ce mai yawan murmushi ko yaushe ba. Dana sanin abinda yayi mata gabaɗaya ya dabaibaye shi. Murya a sarƙe cikin rauni yace, "i’m sorry Manal, nayi kuskure na kuma amince da kuskuren, hakan bazai sake kasancewa ba in sha Allah. Abinda nake so dake don Allah ki dinga faɗa min duk wani abu da ya shafe ki, Ina son zama da wanda yake faɗa min gaksiya a kaina ko a kan shi, bana son ƙarya Manal Allah ya sani." "To ni me na sani a kan ka? Ban San komai ba sai sunan ka akwai abinda na taɓa ce naka?. Ba mu yi wani dogon zama tare ba balle ace na fahimce ka sosai kaina baka fahimce ni sosai, Amma ka yanke min hukunci a gaban mutane cikin faɗa kamar ka haife ni, maimakon ka same ni mu yi maganar a nutse baka yi hakan ba, baka yi tunanin silar abinda kace zai iya saka ni a wani hali ba ko?." Wuta nepa aka kawo haske ya garwaye ɗakin sosai fuskar ta sake bayyana, kana kalla kasan bata da lafiya dan fuskar ta faɗa ga fuskar a ɗaure sosai. "don Allah Manal ki manta da wannan maganar." "Bazan manta ba, meyasa kai baka yi tunanin wannan lokacin ba kazo gare ni kai tsaye? A cikin maganganun ka na gane me ka ke nufi, aurena ne ka fasa daman babu dole. kawai a fasa auren bana son damuwa na sanar da kai zamana da kai zai iya zamar min damuwa, saboda baka sarrafa fushin ka sannan...." Dakatar da ita yayi ta hanyar, "Allah ce miki. Na amince na karɓi laifina kuma za’a gyara ba shikenan ba?.” Shiru tayi har ya gama magana kafin tace, “kawai gwara a haƙura, auren bazai yu ba tunda aka fara haka. A yanke alaƙar soyayyar yafi alkhairi a wajena, na san zaka cigaba da kallon Yayata a mai yawon banza, ni kuma bazan jure hakan ba kaga yafi alkhairi a haƙura.” Kallon ta yayi bayan tayi shiru yace, "Manal Ina son ki, so na gaskiya ba na wasa ba, bana son abinda zai raba mu. Ki taimaka min ki daina wannan maganar, furta a fasa ɗin nan da kike yi wallahil azim ni kawai na san abinda nake ji. So please keep your mouth shut." Manal tayi shiru bata ce komai ba, marar ta ɗaurewa take kaɗan-kaɗan ya kalle ta yace, "Kin haƙura?." Sai a sannan ta kalle shi yana kallon ta shima daidai lokacin marar ta ɗaure sosai ta runtse ido ta furta, "Wayyo Allah!." A gigice yace, "lafiya ki ke?." Ɗan sauƙin ɗaurewar da mara tayi taji hakan ya saka ta buɗe ido yana sauke numfashin azaba tace, "babu komai." "Akwai komai, Daman Baba yace min baki da lafiya gashi na tabbatar. Kin sha magani?." Kai ta ɗaga alamun eh yace, "wanne magani ne?." "Ban san sunan shi ba." "A Ina aka baki?" A hankali yake mata magana murya a tausashe cikin salo na kulawa hakan ya saka tace, "chemist." "Haba Manal meyasa? Maganin chemist kuma?, baki san wasu basu yi karatun komai ba suke bayar da magani ba?." Kamar zata yi kuka tace, "to ya zanyi?." Kallon so da tausayi yake mata domin duk macen da take fuskantar wannan ciwon abin a tausaya mata ne balle ita masoyiyar sa yace, "Sannu, in ne yake miki ciwo yanzu?." Kai ta girgiza alamun babu yayi murmushi yace, "in zaki iya ki sha ruwan lipton mai zafi kafin ki kwanta, in akwai paracetamol shima ki sha. Then send me the picture of medicine that you have taking." Kai ta ɗaga kawai yace, "ki koma gida zan tafi, ki je ki huta." Kallon ta yake yi ta tashi tsaye ta lumshe ido ta buɗe ta kalle shi tace, “Sai da safe" ta faɗa tana niyar fita yace, "baki ji ba." Ta juyo ta kalle shi tace, "smile please." Bata yi murmushi ba amma fuskar ta ta saki saboda yadda yayi maganar ta burge ta sosai, ta fahimce shi sosai ɗan soyayya ne amma soyayyar mai sanyi kuma halacciya baya zaƙewa da yawa, a haka sai kaga kamar bai damu da ita ba amma ba haka abin yake ba. Kawar da kai tayi ta fita bata ce komai ba yayi murmushi yana jin zuciyar sa rass tayi fari dan wallahi yana son Manal.        Manal lokacin da ta shiga wajan Mama tana zaune tana jin radio sallamar Manal ɗin sai ta kashe radio Manal ta zame hijjabin ta tana shagwaɓa tace, "Mama mara ta zata cire, ciwon ya dawo" ta faɗa tana ɗarasawa wajan Mama ta kwanta a jikin ta. Mama tace, "ki yi haƙuri zata daina." Manal tayi shiru hakan ya saka Maman tace, "Ya tafi ne?.” "Uhum." "Ai nace Baban ku ya turo min shi na faɗa masa indai akan hakan zai fasa auren ki ya fasa shine ya rasa ba wani ba, Baban ne ya hana yace na bar shi shi wai daman shi bai ce miki ya fasa ba haka ne?." Manal tace, "haka ne Mama, maganar ce tayi min yawa shiyasa nace kawai ya fasa, amma tsakani da Allah ba shine yace ba. A lokacin ciwon nan yana damuna sosai shiyasa kawai Mama ta sauke numfashi tace, "in ma shi ɗin ne sai ya fasa ɗin, abinda na sani ke ba shegiya bace da aure aka haife ki." Manal tayi shiru bata ce komai ba suka ji sallanar Yaya Haron yana shigowa Falon. Suka gaisa da Mama ya miƙawa Manal leda yace, "gashi in ji Dr yace don Allah hannu da hannu na baki." Karɓa Manal tayi ta buɗe taga magani ne kala biyu a ciki ta ajjiye maganin tace, "To Yaya na gode." Mama tace, "Kwana biyu ka ɓuya Haruna." "Wallahi Mama na koma kasuwa ne shiyasa ba'a ganina." "Wannan yana da kyau, Allah ya taimaka." Ya amsa da amin yayi musu Sai da safe ya fita. Mama tace, "ki sha maganin zaki ji daɗi, Baban ku ya faɗa min ai ya sanar dashi wannan lalurar ciwon marar naki, shiyasa ma ya aiko da maganin ki sha dan ki ji daɗi. In Allah ya taimake ki da kin yi aure sai ki daina, wasu kuma basa dainawa har sai sun haihu.” Manal ta wara idanu tace, "Mama aka faɗa masa? Yanzu daman ya san abinda yake damuna?." Mama ta kalle ta tace, "Ya sani." Manal kamar zata yi kuka tace, "na shiga uku, Mama meyasa aka faɗa masa don Allah? Yanzu daman da yake cemin nasha ruwan lipton da magani na kwanta daman ya san abinda yake damuna?, meyasa Baba zai faɗa masa?.” Mama tayi murmushi tace, "To ba auren ki zai yi ba? Meye dan an faɗa masa?.” “Amma Mama ba’a kyauta min ba, wallahi kunya nake ji.” “Mtsww! ke dai ki sha maganin." A lokacin Mubeena ta fito daga ɗaki ta fita waje jim kaɗan ta sake shigewa ɗakin bayan ta dawo, babu wanda ya tanka mata Manal ta tashi ta ɗauko ruwa ta sha maganin tana ta kumbure-kumbure.         "Kamal meyasa ka kira ni nan? Meyasa ka ke min wasa da hankalina?. Kenan amfani zaka yi da hotunan na hannun ka dan ka wulaƙanta ni?." Kallon ta yake yana daga zaune a kan kujera yayi murmushi yace, "ba wani wulaƙanci Maryam, abinda nake so zan faɗa miki yanzu, in kin yi na goge hotunan, in baki na wallahi bazan goge ba.” Maryam tace, "me ka ke so nayi maka ka goge wannan hotunan don Allah?." "Ai in kaf duniya zaki bani bazan goge wannan hotunan ba." Da matuƙar mamaki tace, "meyasa?." Yayi murmushi ya taso yazo kusa da ita yace, "saboda ina so na dinga gani ina tunawa dake." Maryam ta dafe kai tace, "Kar ka manta ka sake ni saki uku babu aure a tskaanina da kai, meyasa ka ke son kallon tsaraicina wanda a yanzu haram ne kallon sa a wajan ka?.” "Jin daɗi" ya bata amsa yana kallon fuskar ta. Za ta yi magana yace, "zan goge hotunan, Sai mun maimaita abinda muka yi yi ranar da bani da lafiya, ke kin san ko da muna da aure ni mayen ki ne saboda baiwar da kike da ita. To yanzu kwaɗayin ya tashi kuma ina buƙata sai a bani. Na san haushina ki ke ji ko nace ina so na ganki baza ki zo ba, shiyasa na biyo ta wannan sigar gashi kinzo." Maryam mamaki take tana kallon sa baki a sake tace, "Yanzu kana so kace min blackmailing ɗina ka ke da waɗannan hotunan?." Ya ɗage kafaɗa yace, "zaki iya kiran sa haka in da hakan yayi miki kama.” Ta girgiza kai cikin takaici da baƙin ciki tace, "baka isa ba wallahi, bazan sake mallaka maka kaina ba, wancan ma da ya faru kuskure ne bazan sake aikata hakan ba wallahi. Bazan sake aikata zina ba, kayi duk abinda zaka yi amma bazan kuma saɓawa Allah ba.” Yayi murmushi yace, "zan kuwa yi sharing hotunan nan inda baki yi tunani ba." Kallon mamaki da tsoro take masa tace, "yanzu da gaske zaka iya hakan? Ni fa tsohuwar matar kace uwar yaran ka guda biyu, da gaske zaka iya aikata min hakan?." Tayi dariya har yana tafa hannu yace, "Sai baki amince ba a lokacin zaki tabbatar." "Wallahi bazan amince ba, kayi duk abinda za kayi bazan sake aikata zina ba, abinda ban yi ina yarinya ba yanzu bazan yi ba” ta faɗa da ƙarfi tana kallon sa tare da juyawa zata tafi. Hannun ta ya riƙo ta juyo tana son ƙwacewa ya hana ta ya dauƙi wayar yana dannawa sai ga video ta ya bayyana tsirara tana tsaye tana haska ko Ina na jikin ta tana magana a sanyeye tana kiran sunan Kamal tare da shafa wani sassa a jikin ta. Runtsw ido tayi daidai lokacin da take cewa, _My love ka dawo, Ina son kasancewa da kai, kana ganin wannan ko? Shima yayi missing ɗin ka._ innalillahi wa’inna ilaihir raji’un take yi kawai, jikin ta har rawa yake yi saboda tashin hankali da kunyar da take ji kamar zata nutse ƙasa. Yayi murmushi ya kashe video ɗin ya jawo ta da ƙarfi ta faɗo jikin sa yace, "Na tabbatar yanzu ma yayi missing ɗina ko?" Ya faɗa yana kai hannu daidai inda ta nuna. Saukar hannun sa wajan shine ya dawo da ita daga tunanin da ta tafi, jiki babu ƙarfi ta ƙwace jikin ta tana hawaye tace, "yanzu daman saboda wannan rana ka saka na dinga tura maka hotunan tsaraicina a duk lokacin da ka bar gari?, a lokacin kana cewa kewa ta ka ke ashe daman saboda ka wulaƙanta ni ne?.” "No beb, a lokacin soyayya ce da shauƙi da sha'awar ki da yake damuna, amma a yanzu son sake mallakar ki ne." "Zan bi duk hanyar da zan bi wajan ka sake mallaka ta a matsayin matar ka, amma ka goge don Allah” ta faɗa tana kuka sosai. Ya danna wayar yana kallon ta tare da haska mata screen ɗin tace, "kin ga na danna delete ko? Yes kawai ake so na danna a tabbatar na goge shi duka, zan ajjiye wayar a haka da zarar na gama abinda nake so dake ki ɗauka ki goge da kan ki."  Girgiza kai take yi tana kuka sosai tace, "bazan iya ba, bazan iya sake aikata zina da tsohon mijina ba." Ya taɓe baki yace, "kin huta." "Allah ya isa, mugu, azzalumi, sai Allah ya saka min wallahi." Murmushi yayi ganin tana kuka tace, "baza ki yi kuka ba sai kinga hoton a Facebook." Ta share hawayen ta tace, "ka saka a tiktok ma in kaga dama." Yayi murmushi dan yasan tayi tunanin wasa yake yi yace, "Shikenan jeki, ki kasance always active yau zaki ga abin mamaki.” Ta fita guje tana kuka ya girgiza kai don sai ya tabbatar mata da zai iya aikata abinda yace, sannan sai ya tabbatarwa da Bebi shi ba kalar wanda za’a kai ƙara gida bane. A bayyane yace, "ba kare mutuncin ta yake ba? Zai ga abinda bai taɓa gani ba" ya faɗa yana yin ƙwafa ya koma ya zauna a kan kujera yana sake kallon hotunan da videos ɗin wutar sha'awar ta na sake huruwa a zuciyar sa. Bebi sai da ya tabbatar ya bashi maganin hankalin sa ya kwanta ya nufi gida, yana ajjiye mota yaga Maryam ta shiga cikin gida da alama itama ajjiye motar tayi. Karshe motar yayi ya ɗauki waya ya kira wata number ana ɗauka yace, "Baka bani review kaan abinda na saka ka ba." Shiru yayi ana masa magana yace, "kaga motar Kamal yau?." Shiru ya sake yi kafin yayi ƙaramin tsaki yace, "Shikenan na gode" yana faɗa ya kashe wayar ya jingina da kujera ya rasa ya zai yi da Maryam komai sake lalacewa yake yi. Ya jima a haka sannan ya fito ya shiga wajan Mama ya same ta a zaune babu walwala dan tunda maganar Manal ta ratso gidan Mama ta daina masa dariya, shi burin sa ma Allah ya sa kar Mama taƙi karɓar Manal. Y zauna a ƙasa kamar yadda take a akan carpet yace, "Mummy barka da dare." Kallon sa tayi tace, "tun yaushe na kira ka sai yanzu kaga damar zuwa? Da yarinyar nan ta mutu kenan ko a jikin ka?." Rumana ya kalla da take kwance a kan kujera kafin yayi magana tace, "Har Huzaifa na kira ya tabbatar min da kafin i’sha ka bar asibiti, wato kana can wajan wacce ka ke so ka bar min yarinya zata mutu ko?." Shi wallahi baya Jin daɗin wannan abinda da Mummy take masa amma bashi da bakin magana sai yace, "ki yi haƙuri Mummy, abinda ki ke tunani ba haka bane." Hararar sa tayi tace, "kai dai ka sani." Kallon Rumana yayi da ta buɗe ido, a lokacin ya fahimci serious ciwo take yi ba ƙarya take ba yace, "Sannu, me yake miki ciwo?." Ƙirjin ta ta nuna masa tana yarfe hannu da alama yana mata ciwo sosai yace, "baki da ulcer?." Sai ya kalli Mama yace, "Mummy bata da ulcer kuwa?." "Bata dashi gaskiya." Ya girgiza kai ya tashi ya koma kusa da Ruman ya riƙe hannun ta yana jin bugun zuciyar ta yadda take bugawa da gudu ya saka ya kalli Mama har lokacin bai saki hannun ta ba yace, "Mummy akwai abinda ya bata tsoro ne?." Mama tace, "meye zai tsorata ta? Lafiya?." Kai ya girgiza ya saki hannun ta suka haɗa ido da ita karo na farko da tun bayan rabuwar su ta bashi tausayi sosai sai yayi murmushi yace, "Sannu, Allah ya baki lafiya." Kai ta ɗaga tana murmushi ya daina kallon ta ya kalli Mimi yace, "zo mu je ki kawo mata magani, Ina da maganin da zai mata. Ki taho min da abinci" ya faɗa yana fita Mimi ta ɗauko abincin ta bi bayan sa. A tsaye ta same shi da maganin a hanun sa tana shiga ya bata yace, "ta sha yanzu gobe ma ta sake sha, damuwa ce tayi mata yawa itace ta jawo ciwon." Karɓa tayi tace, "to Yaya. don Allah Yaya ya sunan wacce zaka aura?." Kallon ta yayi suka haɗa ido sai tace, "Yaya ko sunan ta bamu sani ba shiyasa na tambaya." Wani kallon ƙasan ido yayi mata amma fuskar sa a sake take yace, "meyasa ki ke tambaya? Me zaki da sunan ta?." Ta langwaɓar da kai tace, "so nake na sani kawai, bai kamata ace ban san sunan matar ka ba, ai da kunya.” Yayi murmushi kaɗan yana zama tare da buɗe abincin yace, "sunan ta Manal." "Wowww! Kai sunan mai daɗi Yaya, don Allah hoton ta fa?." Ya kalle ta yace, "ke ni bani dashi." "To ka bani number ta mu dinga gaisawa." Ƙaramin tsaki yayi yace, "Malama kama gaban ki." Dariya tayi ta fita tana cewa, "ni na san mai kyau ce dan Yayan na mu yana son abu mai kyau." Yana jin abinda tace yayi murmushi sai ya fasa cin abincin ya ɗauki waya ya kira number Manal ɗin. Lokacin ƙarfe goma ta kusa na dare, daga can ɓangaren aka ɗauka da sallama ya amsa yace, "Ya jikin?." Daga can ɓangaren tace, "Da sauƙi, an kawo magani na gode." "Nima na gode." Shiru ne ya biyo baya bata ce komai ba ya katse shirun yace, "kin tabbatar kin ji sauƙi?." "Uhum na ji sauƙi." "Alhamdulillah, yanzu zan samu na nutsu har naci abinci." Bata ce komai ba yace, "yaushe rabon da ayi miki fbs?." Manal tace, "an jima, amma za'a yi gobe." Bebi yace, "ya kamata, ki kwanta ki huta Sai da safe?" Ya faɗa da sigar tambaya. Manal tace, "Allah ya kaimu, na gode da kulawa Allah ya bar zumunci." "Amin. Amma Allah ya bar ƙauna ya kamata ki ce ba zumunci ba ko?." Zata yi magana yace, "don Allah Manal kar ki ce, Wallahi ni kaɗai nasan abinda nake ji a zuciyata, bana so naji kina faɗar wannan kalmar, zafi nake ji a zuciyata, don Allah ki bari. I made a mistake but na tuba ai ko? Ya kamata ya wuce ko dan soyayyar da nake miki, ko so ki ke ace likitan zuciya yama zuwa ganin likite zuciya?. Please mana Manal." Ajiyar zuciya tayi bata ce komai ba ya sake cewa, “baki ce komai ba, baki haƙura ba har yanzu?.” Manal tace, "tsoro ka ke bani ne gaskiya, ina gujewa matsala ne nan gaba, iya wannan maganar ta tunzura ka har haka ina ga wani abun kuma?.” "Na daina baki tsoro, yadda kike tunani ba haka nake ba nasan kin fahimce ni." "Kaina na ciwo zan kwanta." "Ki yi bacci lafiya." Da Allah ya sa ta amsa ta yanke wayar, ya sauke numfashi yadda yake ji a zuciyar sa in Manal tace ta rabu dashi Allah sai yayi ciwo. BDƘB2P005 Lubna tana zaune a kan gadon ta da waya a hannun ta jingina da jikin gadon jikin ta yayi sanyi sosai kai da ka ganta kasan akwai abinda take saurare a wayar mai mahimmaci. Numfashi ta sauke tace, “ni bawai bana so ba ko ban yarda da kai ba, kawai tsoro nake ji ne wallahi. Na faɗa maka ko riƙe hannuna wani bai taɓa yi ba, dole na ji tsoro.” Mujahid da yake kan wayar yace, “Sweetheart mafita nake neman mana fa, bawai ina hakan saboda jin daɗi na ko wani abun ba, mafita nake so mu samu mu yi maganin damuwar mu. Kina sona Ina son ki, aure muke burin yi Yayan ki ya hana faruwar haka, shine nake nemar mana hanyar da za’a samu masalaha cikin sauƙi. Kar ki saka a zuciyar ki kamar abinda nazo nema kenan a wajan ki, ko kusa ba haka bane ba Lubna, neman mafita ce babu yadda zan yi hakan shine kawai zai faru a aura min ke ko da Adnan baya so.” Lubna tace, “Na sani Sweetheart, amma…..!” Katse ta yayi yace, “Lubna don Allah in zuciyar ki na rawa a kan maganar nan a barta kawai, kar ki yi tunanin zan karɓi virginity ɗin ki ne saboda haka nake so a zuciyata. Wallahi sam-sam ba haka bane ba my love, in a son raina ne sai bayan mun yi aure na mallake ki kin mallake ni, hakan shine burin na ba abinda yake zuciyar ki ba. Allah ya sani so nake na mallake ki a matsayin matata, duk wannan faɗi tashin da nake yi saboda ke ne, don girman Allah in kina ganin kamar wayo nake miki don na mallaki jikin ki daga baya na guje abar zancen nan kawai. Kin san ni ba mutumin banza bane, har yanzu ban taɓa riƙe ko da hannun ki ba, in da ace da wannan manufar a zuciyata da yanzu kin fahimce ni.” Lubna tace, “bawai ban amince da kai bane ba fa, na amince kawai tsoro nake ji ne wallahi. Ban taɓa aikata hakan ba kai ma ka sani, zuciyata rawa take sosai, shiyasa kaga kamar Ina kokwanto a kan ka amma bawai don ban amince da kai bane. Na amince da kai ɗari bisa ɗari, in ba dan kai ɗin ba bazan iya yin maganar da kowa ba.” “Tsoron me kike ji? Tsoron kar nayi amfani dake nan gaba na gudu na barki…?. Hmmm! In da wannan niyar nazo gare ki da zuwa yanzu kin fahimta Lubna, ban zo wajan ki da niyar lalata miki rayuwa ba, nazo da niyar auren ki amma Yayan ki ya hana faruwar hakan.Ban san me na yiwa Bebi ba, ban san meyasa baya sona, ban san meyasa yake son hana ni ke ba. A ganina duk laifin da nayi masa tunda har yanzu nazo nace neman aure nake bai kamata ace ya hana ni ba, saboda aure sunan sa aure, Kuma raya sunnar annabin mu nake so nayi. Ban san me nayi masa ba wallahi, a bayana saurayin Mimi yazo yanzu gashi an saka ranar auren ta.” “Duk laifin sa ne wallahi, ban san meyasa baya son farin cikina ba. Kuma su Yaya ne suke biye masa, Mimi da yake ita cikin su ɗaya ai gashi har an saka ranar ta, ni nice babba amma ya shiga ya fita ya hana na aure ka ban san meyasa ba.” “Shiyasa nake nemar mana mafita kina ganin abun kamar saboda jin daɗina ne, in hakan ta faru ko Abba ni zai aurawa ke balle shi.” Lubna tace, “ba haka bane ba, abinda zai faru yanzu mu yi wani tunanin ba wannan ba.”Mujahid yace, “to faɗi abinda kike so a ayi, wannan an barta tunda bakya so, bana so ki yi tunanin kamar ba son ki nake ba gwara a bar zancen kawai. Ya kike ganin za’a yi?.” “Zan je wajan Daddy na same shi nace masa ni kai nake so, kuma kai nake so na aura, na tabbatar zai yi wani abun a kan hakan.” “Waye Daddy?.” “Yayan Abban mu mana, shi kaɗai ne zai iya laƙwasa Yaya Bebi, ko Abba sai abinda Yaya Bebi yake so yake yi, amma shi yana jin maganar sa. Wajan sa zan je ko kazo mu je tare mu tabbatar masa da muna son junan mu zai yi wani abun.” Mujahid cikin muryar sa da take sokar mata zuciya yace, “kin tabbatar zai shiga lamarin? Na ƙagu na mallake ki matsayin matata Lubna.” Lubna tace, “Zai amince in sha Allah.Yaushe zamu je?.” “Yanzu ma dan dare yayi ne, amma gobe zamu je dan da zafi zafi ake dukan ƙarfe.” Lubna tace, “Allah ya nuna mana goben, in sha Allah ƙarshen damuwar mu tazo kaga ba sai mun aikata komai ba.” Yayi murmushin yaudara yace, “in hakan ta faru sai nafi kowa farin ciki.” Lubna tayi murmushi tana kallon sa kafin ta sunkuyar da kai, ya kalle ta yace, “in bai amince ba fa?.” Lubna tace ta kalle shi tare da karyar da murya taxe, “wanne irin fata ne wannan? Zai ma amince in sha Allah.” Yayi murmushi ya amsa da cewa, “fatana kenan.” suka cigaba da tattauawa kafin ya kashe wayar. Numfashi ta sauke tana kallon wayar dan duk yadda zata yi zata yi don ganin ta zama mallakin Mujahid. Washe gari. Manal da wuri ta tashi dan taji daɗin maganin wajan Bebi ko ciwon kai babu ta fito ta kunna gawayi ta ɗora ruwa, da yayi zafi ta zuba a boksiti ta shiga banɗaki tayi wanka ta fito ta shirya ta dawo ta dama kunu mara sugar. Baba ne ya shigo da sallama ta amsa ya kalle ta yayi murmushi yace, “Manal jiki yayi kyau sosai?.” Tayi murmushi tana jin kunya tace, “Ina Kwana Baba.” “Lafiya lau, ya jikin na ki?.” “Naji sauƙi” ta faɗa tana sunkuyar da kai dan kunya take ji sosai. Duk wata in hakan ya faru da ita kunya take ji har haushi take ji kowa yana abin sa lafiya amma ita kowa sai ya sani. Baba yace, “Ina Maman naki?.” “Tana kwance tana bacci, jiya ta jima bata yi bacci ba da daddare duk farkawar da zanyi sai naga idon ta biyu shiyasa yanzu take bacci.” Baba yayi murmushi ya girgiza kai dan yasan maganar mahaifin su ce ta hana ta bacci, shi ya rasa yaushe zata manta da abinda ya faru ta basu labarin waye mahaifin su oho. Yace, “ƙyale ta, zan je Kaduna wataƙila na dawo yau wataƙila na kwana, sai naga dai yadda hali yayi. In ban dawo ba zuwa ƙarfe tara na dare ku kulle gidan kin ji ko?.” Manal tace, “to Baba.” Ya saka hannu aljihu ya ɗauko kuɗi ya bata yace, “ayi cefane” ya sake bata wasu yace, “na san maganin ku ya ƙare ko? Gashi ku siya kar a kwana yau ba’a sha ba.” Manal ta karɓa tace, “to Baba Allah ya dawo da kai lafiya, Allah ya kiyaye hanya. An gode Allah saka da alkhairi.” Ya amsa da amin yace, “babu abinda ku ke so?.” Manal tace, “babu komai Baba.” “Baba Ina Kwana.” Mubeena ta faɗa daga gefe ya kalle ta yace, “lafiya lau Mubeena.” Mubeena tace, “Daman Baba Ina so zan je dubiya in anjima, shine nace bara na tmbaye ka kafin ka fita.” “Waye babu lafiya?.” “Maman su ƙawata ce.” “Wacece ƙawar taki? Bata da suna?.” Mubeena ta sauke numfashi tace, “sunan ta Khadija, tare muka fara makaranta.” Baba ya kalle ta yace, “ya akayi kika san bata da lafiya ke da baki da waya? Ko zuwa tayi ta faɗa miki?.” Gaban Mubeena ya faɗi sosai ganin za’a gano ta tace, “da na fita jiya Mama ta aike ni na ga ƙanwar ta ita ta faɗa min.” Baba ya bita da kalli sosai kafin yace,”Manal in zata tafi ki karata ku samo ladan dubiyar tare.” Manal tace, “to Baba.” Daga nan yayi musu sallama ya fita Mubeena ta miƙe a fusace ta koma ɗaki. Manal bata bi ta kanta ba ta tashi ta saka mayafi ta fita ta siyo ƙosai dan shi take son ci, ta dawo ta zauna ta sha kunun ta ta ragewa Mama dan tasan Mubeena ba sha zata yi ba. Tana nan zaune ta hango Mama ta fito tayi wanka a banɗakin ta da yake da glasses ɗin ta a ido tana iya gani duk da ba sosai ba, ta ƙaraso ta zauna Manal tace, “Mama barka da fitowa.” Mama tace, “Yauwa, ya jikin?.” “Na warke.” “Naga alama maganin da ya baki yana da kyau sosai, gashi kin ware. Allah ya sa kina aure ki huta da wannan ciwon.” Manal ta amsa da amin kafin ta kalli Maman taga fuskar ta babu walwala sosai tace, “Mama Baba yace na faɗa miki ya tafi Kaduna, ga kuɗin magani ya bani ga na cefane. Yace in bai dawo da wuri ba mu kulle ƙofar.” Mama tace, “Allah ya kiyaye hanya ya dawo dashi lafiya.” Ta amsa da amin kafin Manal ta sake cewa, “Maganin ki ya ƙare, Huzaifa yace in ya ƙare na faɗa masa saboda akwai wanda yake so ya baki, amma kafin nan bara na kira Surayya ta ɗauki jinin ki muje a gwada mana.” Mama tace, “ni kunyar Huzaifa nake ji, yaro kamar daman can ya san mu? Sai hidima yake mana baran ma yanzu da zaki auri abokin sa.” Manal tace, “ai yana da kirki sosai Mama, tun lokacin baya yake tausayina da farko ma na ɗauka sona yake yi ashe ba haka bane.” Mama ta girgiza kai tace, “nima da farko nayi tunanin son ki yake yi, ashe tsantsar kirki ne da mutunci.” Manal ta tashi ta fita ba jimawa suka dawo da Surayya ta gaisar da Mama ta ɗauki jinin ta suka fita tare. A bakin titi akwai ƙaramin lab a nqn aka gwada jinin suka dawo. Bayan ta dawo ta buɗe takardar tace, “Mama ya ɗan hau kaɗan amma.” Mama tace, “shi ya sani, ke ba’a gwada naki ba?.” “Na riga naci abinci gobe ayi min.” Shiru ya biyo baya kafin Manal tace, “don girman Allah Mama ki yi haƙuri, na saba da dariya ki wannan ɗaure fuskar yana cutar dani.” Mama ta kalle ta tace, “ya wuce ai Manal, kawai bana son naji kin sake yi min zancen mahaifin ki a gidan nan, bana so ba kuma na ƙaunar hakan. Ke da Mubeena yara ne na halak, in ma kina shakku a kaina ki daina.” Manal da sauri tace, “ni na isa Mama? Ki yi haƙuri.” Mama tace, “ya maganar Adnan ɗin na ki? Zancen ya wuce ko da saura?. Ina ji kuna waya ai nace munafuka daman kina son kayan ki.” Manal tayi dariya ganin Mama ta dawo da abin wasa tace, “Allah Mama shine yake nace min, amma ni da gaske da na fasa.” “Ƙarya kike wallahi, kina son sa kamar yadda yake son ki. Shine mijin ki haka nake ji a zuciyata dan haka komai ya wuce ki manta kawai. Ai dan yayi hakan ba laifi bane, kece wacce zai aura ki haifa masa yara ai ba laifi bane dan yana so ya san asalin babar yaran sa.” Manal jin Mama tana cewa haka sai taji komai ya wanke a zuciyar ta tace, “To Mama.” Mama tayi dariya ta ja kunnen ta tace, “ba wani to Mama, Daman kun shirya ai.” Manal tayi dariya ta tashi tace, “bara nayi sallah na kira Dr. “Wacce sallar kuma?.” Jin hakan sai Manal ta tuna ashe ba bata da tsarki sai ta wuce ciki. Waya ta ɗauka ta kira Huzaifa ai kuwa ya ɗauka suka gaisa ta faɗa masa zancen magani da kuma sakamakon gwajin Mama, suka gama maganar sannan ta kashe ta fito wajan Mama tace, “Mama yace min yana da aiki sosai yau, wai in zan iya anjima ko yanzu naje asibiti na karɓa, da nace in ya tashi ya aiko min dashi sai yace a’a tunda jiya baki sha ba kar ayi sake sosai, gashi daman na faɗa masa sakamakon nan yace ya ɗan hau kaɗan.” Mama tace, “To zuwan zaki yi?.” Manal tace, “shine nake tunani.” Mama tace, “ƙyale kawai, babu inda zaki je.” Manal ta amsa da to dan tasan daman baza ta barta ba ta shiga ɗaki. Sai bayan sallar azahar ta kasa haƙuri da rashin maganin ta kalli Mama da take kashingiɗe tana ja carbi tace, “Mama zan je kawai ba karɓo maganin nan kawai.” Mama ta dube ta tace, “bana son yawon nan ne Manal, ga hanyar asibitin nan nasu babu mutane, bana son kina zirga zirga ke kaɗai a wannan waje mai ƙarancin jama’a.” Manal tace, “To Mama ai dole sai na fita na siyo, gwara naje kawai ai ba wani nisa sosai.” Mama tayi shiru ganin hakan sai Manal ta tashi ta wanke fuskar ta da sabulu ta saka abaya maroon kala cikin wacce Yaya Haron ya kawo mata a wancan dawowar ta shi ta yafa mayafin tace, “Mama za je.” Mama tace, “kar ki jima Manal, ki kula don Allah kar ki tsaya a ko ina.” Manal ta amsa da to ta saka takalmi ta cross ta fita daga gidan. Wayar ta ta bayar a wajan masu chaji daga nan ta wuce asibiti su Bebi kai tsaye. Sai bayan ta sauka a napep kuma tayi tunani da wacce wayar kuma zata kira shi tace gata tazo? Dan gaskiya bata son shiga ciki. Tsaki tayi tana kallon asibitin daga waje tana jinjinga kyau da girman sa, a ranar ne ma ta ƙare masa kallo yana da kyau sosai a iya gani da ido ma zai tabbatar maka da asibitin kuɗi ne. Gama kallon tayi ta shiga ciki tana kallon ƙato filin asibitin ga motoci nan a ajjiye. Allah ya sani bata son shiga ciki ta ja ta tsaya tana tunani abinda ya kamata ace tayi a wannan lokacin. Kamar ance ta juya ta hango shi ya fito yana sauri da alama akwai inda zai je, sai tayi dariya cikin Jin daɗi yana zuwa gab da ita tace, “Sannu Yaya Huzaifa.” Da Sauri ya kalle ta yace, “Haba Manal, ke da nake expecting ɗin zuwan ki tun ɗazu sai yanzu?. Yanzu ma fitowar da nayi bayarwa zan yi a kai miki, kin san illar rashin shan maganin nan a wajan Mama?.” Karɓar ledar da ya miƙa mata tayi tace, “Sai yanzu na samu na fito.” Huzaifa yace, “ai kin kyauta, yanzu Ina zaki je?.” “Gida zan koma.” “Bara na saka a mayar dake rana tayi sosai.” Kallon inda motar Bebi take yayi yaga bata nan ya kalle ta yace, “ga mutumin naki baya nan, da yanzu ya fara harara ta.” Tayi murmushi kawai shi kuma yana buga waya amma ba’a samu wani a kusa ba balle ya kai ta. Manal ta kalle tace, “Dr ka barshi kawai yanzu zan ƙarasa gida.” Huzaifa yace, “za’a samu wanda zai kai ki.” Manal tayi shiru yana waya amma shiru babu wanda yakd kusa cikin direbobin nasu, Manal ta gashi tace, “ka barshi kawai zan wuce gida yanzu, na gode Allah ya saka da alkhairi.” “Amin Manal. Zaki samu abin hawa kuwa?.” “Bazan rasa ba in sha Allah.” “Gashi aiki nake, amma muje na tare miki napep.” Manal tace, “wallahi ka barshi, in ban samu ba akwai gidan wacce zan je, nagode Allah ya bar zumunci.” Ya amsa da amin ta fita shi kuma ya juya ciki. A kan titin ta tsaya amma babu napep ko kaɗan sai motoci da tsuke wucewa. Manal tayi ƙaramin tsaki hanyar gabaɗaya ba’a samun napep sai kayi sa’a. wata mota ce ta wuce ta sai kuma ta dawo aka faka daga gefe, na ciki ya fito ya ƙaraso wajan ta yana mata magana ita kuma Allah ya sani tsoron wajan take ji. Bebi da shigowar sa layin kenan ya hango wata a tsaye kamar Manal ɗin sa a tsaye ita da wani, gaban sa ya faɗi bai tabbatar ita bace sai da ya matso ya kalla yaga dai itace ga wani kusa da ita duk da yaga ta matsa amma ya sake matsowa inda take. Wani irin abu mai ɗaci yaji yazo zuciyar sa da zafin nama ya tako motar ya ƙarasa inda take tsaye kawai ya sauke glass ya kalle ta suka haɗa ido, Ajiyar zuciya tayi ta gode Allah ba wata magana kawai ta shiga motar ya ja ya bar wajan. BDƘB2P006 Tafiya suke bai ce komai ba bai kuma kalle ta ba amma kana kallon yanayin sa kasan ransa ya ɓaci sosai. Daman shi ba fuskar walwala ba gashi ya sake tamke ta sai taji ya bata tsoro sosai dan yanayin fuskar ma abin tsoro ne. Dogon tsaki taji yayi ya nemi waje ya faka motar ya juyo yana kallon ta yace, "meyasa kike son ganin raina ya ɓaci akan ki ne manal? Meyasa kike yin abu da gangan dan ki bani haushi?. Waye wannan yake tsaye a kusa dake har yana miki magana?." Manal tace, "ni fa ban san shi ba kawai naga ya tsaya ne." "Da ya tsaya me yake ce miki? Me ya fito dake daga gida ma har kika zo wajan nan?" A fusace yayi maganar sosai yana wara idanun sa a kanta ta kalle shi a shaagwaɓe tace, "ni ban san abinda yake cewa ba, dan a tsorace nake sosai tsoro bai bari naji maganar da yake yi ba." Ya daki sitiyarin motar har sai ta ɗan firgita yace, "to me ya fito dake yanzu? Me ya kawo ki wajan nan yanzu kuma baki neme ni ba?." Manal tace, "to sai faɗa ka ke min, ka yi a hankali mana sai nayi maka bayani." ta faɗa kamar zata yi kuka tana kallon sa. Kawar da kai gefe yayi bai ce komai ba tace, "Maganin Mama ne ya ƙare jiya bata sha ba, shine na kira Yaya Huzaifa na faɗa masa yace aiki ya yi masa yawa bazai samu damar zuwa ba nazo na karɓa. Ni kuma gudun kar lokaci ya ƙure bata sha ba shine nazo na karɓa, kaga maganin ma" ta faɗa tana ɗago masa ledar maganin. Juyowa yayi yana yi mata wata harara da ta saka ta daina nuna masa maganin ta turo baki gaba yace, "Okay ni bani da mahimmacin da za'a kira ni a faɗa min maganin Mama ya ƙare Sai Huzaifa ko?." Ta langwaɓar da kai tace, "Ba haka bane." "To yane? Faɗa min yane Manal Ina Jin ki" ya faɗa a ɗan fusace yana kallon ta. Manal tayi shiru bata ce komai ba ya girgiza kai yace, "ban san meyasa kike min haka ba, maganin Maman ya ƙare ni ba za'a iya faɗa min ba sai ki ɗauko ƙafa da ranar nan kizo har nan ki karɓi magani ki kuma fito zaki tafi baki nemi inda nake ba. Wato Huzaifa ya fini mahimmaci a wajan ki na lura da hakan, ko kina tunani ni ban damu da lafiyar Mama ba sai shi ko?." Ganin yaji haushi sosai sai ta tausasa murya tace, "wallahi ba haka nake nufi ba." Bebi ji yake kamar ya tsinke ta da mari in tana cewa ba haka take nufi ɗin nan ba yace, "Manal ya kike nufi? Meye tsakanin ki da Huzaifa da zai fi ni sanin abubuwa akan ki? Meyasa shi bakya ɓoye masa komai naki ni kike ɓoye min?. Anya Manal akwai soyayya ta a zuciyar ki?, na fara tantama akan son da ki ke min, rashin mahimmacin da bani dashi a wajan ki yayi yawa." Bata yi magana ba dan bata san me zata ce ba yace, "ni bani da mahimmacin da zaki faɗa min Mama magani ya ƙare? Sannan kin san wajan nan babu abin hawa sosai, kika taho ga yamma ta kusa kin yi kwalliya ko hijjabi babu kika tsaya a kan titi wani yazo yana miki magana, yanzu abinda kika yi kin kyauta min Manal?" Ya faɗa yana kallon ta. Haɗa ido suka yi sai ta kawar da kai yayi ƙaramin tsaki ya kwantar kansa a jikin sitiyarin motar Allah kaɗai yasan abinda yake ji a wannan lokacin. Manal ta raunana murya tace, "ka yi haƙuri, duk abinda ka ke faɗa ba haka bane." Bai amsa mata ba ya samu kusan mintina biyar a haka kafin ya ɗago ya kalle ta yace, "ki faɗa min Huzaifa ya fini a wajan ki ne?." Ta girgiza kai alamun a'a yace, "Meyasa ki ke fifita shi a kaina? Meyasa bakya faɗa min abinda yake damun ki shi kike faɗawa?." Manal tace, "ni babu abinda na faɗa masa, magani ne kawai, kuma kaga tun kafin na sanka a wajan sa nake karɓ...." Ya daki motar da ƙarfi yace, "yanzu kin sanni, kuma auren ki zan yi ba shine zai aure ki ba. Duk maganin da zai baki zan iya baki shi, duk lafiya da zai iya nemawa Mama zan iya nima, meyasa ki ke min gorin shi kika fara sani ba ni na?." Manal taga yayi zafi sosai tana murmushi a zuciyar ta dan tana so taga ana kishin ta haka tace, "Allah ya baka haƙuri." Ya girgiza kai yace, "komai Huzaifa, komai shi, abokina ne fa meyasa komai sai shi? Ni kin ajjiye ni gefe komai sai dai ya bani labari? A matsayin sa na wa a wajan ki Manal?." Manal ta dafe kai da farin hannun ta wanda bashi da girma sosai, gabaɗaya ya dagula mata lissafi bata son yawan faɗa amma ta lura bayan faɗa ma akwai shi da mitar abinda ya wuce ma. Ganin tayi shiru ya saka ya sauke ajiyar zuciya yace, "dole wannan alaƙar ta ku ta ja baya, duk abinda kike so ki faɗa min zan kawo miki da kaina, ba sai kin fito titi ba kan ki ba kin fahimce ni?." Manal tace, "na gane. Ka yi haƙuri" ta faɗa dan a wuce maganar ta gaji da maimaita ta. Ya kulle ido ya buɗe ransa a ɓace yake ji sosai, haushin Huzaifa yake ji da ita kanta Manal ɗin. Kallon ta yayi suka haɗa idanu yace, "Rashin mahimmacin nawa har ya kai ki kasa faɗa min Mujahid yazo wajan ki ko? shi da yake yana da mahimmaci sai kika bashi labari. Manal i am your life partner, meyasa zaki dinga ɓoye min abinda ya kamata ace na sani?." Kai ta girgiza domin mitar ta sa ta lura yawa ce da ita, ace an kasa wuce wajan daga wannan maganar ta wuce sai ya jawo wata kuma duk akan laifi ɗaya. Ta kalle shi tace, "Wallahi ban ɗauki maganar shi wani abu ba shiyasa ma ban sanar da kai ba, abinda ya saka na kira shi kawai Ina so na san da gaske Mujahid ɗin ya san ku. Shine ya faɗa min komai nace ya wuce kuma basai ya sanar da kai ba saboda babu amfanin ka sani." "Shi ai akwai amfanin ya sani tunda shine zai aure ki, ni kuma da nake a gefe babu." Ya faɗa yana kallon ta. Ta rausayar da kai tace, "don Allah ya wuce mana, kana ta maimaita maganar nan, nace bazan sake ba sai ka amince ko?." Girgiza kai yana kallon ta yace, "Alaƙar ku ce bana so." "Meyasa? Ba alaƙa bace mai muni meyasa ba ka so?." "Saboda ni ne wanda zan aure ki ba shi ba, Ina da ikon da zan hana ki sauraren wanda bana so, ciki kuwa Huzaifa ne farko dan na lura nan gaba in kika ganni zaki iya kirana da sunan sa." Tayi murmushi tana kallon titi tace, "yamma tana yi Mama bata sha magani ba mu je don Allah." Kafa mata ido yayi yana kallon ta har ta tsargu ta takure a motar ganin hakan sai ya janye idon sa yana kallon titi har lokacin zuciyar sa zafi take masa sosai. Kunna motar yayi suka tafi bai ce komai ba itama bata ce ba sai wayar sa da kira yake zuwa amma bai ɗauka ba ko kallon wayar ma baya yi ba tafiya yake yi kawai. Sai da suka zo bakin layin su zai shiga ciki tace, "Yauwa sauke ni a nan, zan karɓi wayata." Tsayawa yayi yace, "wa kika bawa wayar?." "Mai chaji mana." Kallon ta yake yi cikin sabon takaici yace, "mai chaji? Da kan ki kuma?." Ta kalle shi kafin tayi magana yace, "wai Partner meyasa baza ku samu mai yin aike a gidan nan ba? Ko yaushe kece zuwa siyo wannan siyo wannan. I can't tolerate it any more, ya kamata ki fahimci hakan. Duk inda mace take so nake naga an killace fa, ƙannena ko aike wajan mai gadi basa zuwa saboda bana son hakan, ki yi tunanin ya zanyi akan ki ko kuma ya zan ji a kan ki" ya faɗa yana tallafar haɓar sa yana kallon ta Manal ta kalle shi tace, "ba wani waje ai nake zuwa ba kaima ka sani "Nima ban ce kina zuwa wani waje ba, Amma tsakani da Allah meye na zuwa wajan mai chaji kina mace?." Manal ta sauke numfashi tana murmushi tace, "to zan daina." Kallon ta yayi haɗi da harara yace, "ko bakya so" ya faɗa yana miƙa hannun sa dashboard ɗin gaban motar da yake inda take dan yana tunanin akwai wani power bank da ya taɓa siya a ciki. Hannun sa ya gogi hannun ta a karo na farko tun bayan zaman asibiti. kamar bai san yayi ba haka ya nuna ya ɗauko sabon power bank a kwalin sa ya miƙa mata yace, "in an kawo wuta ki dinga saka shi chaji, in ya cika sai yayi kwana uku bai ɗauka ba. Bana so ki sake zuwa wajan mai chaji yau ne ranar ƙarshe Manal." Bata karɓa ba ya kalli fuskar ta ya kalli power bank ɗin hannun nasa yace, "ko na kai wa Huzaifa ya kawo miki ne?." Dariya tayi mai sauti jin abinda yace ta saka hannu biyu ta karɓa tace, "a'a, basai an yi haka ba, na gode." Hararar ta yayi ta sake tana murmushi ita kam tana son mutumin da zai nuna yana kishin ta sosai, hakan yana yi mata daɗi tana kuma ji a zuciyar ta ita matar so ce, shiyasa take son Adnan saboda yana kishin ta. Wani yaro ne yazo wucewa ya sauke glass ya kalli yaron yace, "kana ji, don Allah jeka shagom can ka karɓo min waya." Yaron yace, "to Ina katin shaidar karɓar wayar?." Ya kalli Manal sai tace, "ka ce mishi Manal ce ta aiko ka." Ya juyo ya kalle ta yace, "ohh har sunan ki ma ya sani ashe? Lallai." Abinda yace kenan tana ganin yaron yana nuno ta daga wajan maj shagon, sai da mai shagon ya hango ta a mota sannan ya bata wayar ya kawo Bebi ya bashi ɗari biyar ya tafi yana tsalle. Kallon wayar yayi yana juya ta a hannun sa yace, "Samsung ce?." Kai ta ɗaga alamın eh yace, "meyasa baki son iphone? Naga ƙannena mata dukkan su itace dasu, naga mata kun fi son ta." Manal tace, "Ina so, wannan wayar Yaya Haron ne ya bani ita." "Ohhh!" Yace kawai bai yi magana ba ya bata wayar a lokacin ta sa wayar tayi ƙara. Dubawa yayi yaga sunan Mama sai ya ɗauka daga can ɓangaren tace, "kar ka manta da maganin Rumana." Yace, "bazan manta ba in sha Allah Mummy, ya jikin nata?." "Taji sauƙi yau." "Ma sha Allah, a gaishe ta kafin na dawo." Mama tace, "Zata ji, in zaka dawowa ka taho mata da wani abun, zata ji daɗi ace kaina ka bata." Bebi yace, "to Mummy zan siyo." Manal da take zaune jin yana cewa Mummy sai tace, "Ina gaishe ta." Mama ta jiyo abinda akace sai tace, "Wacece take cewa tana gaishe ni?." Bebi ya kalli Manal sannan yace, "Manal ce." Mama tace, "Wacece Manal? Ko itace ƴar gwal ɗin taka?." Yayi murmushi bai yi magana ba Mama tace, "ƴar gwal mana, yarinya da ko sunan ta ban sani ba balle ace za'a haɗa mu a waya." Jin abinda tace sai yayi murmushi yace, "Mummy zata zo har gida ta gaishe ki." "Bana nema, tunda sai da na tambaya. Ashe kana wajan ta, Lallai Bebi ina ganin canji a halayen ka tunda ka haɗu da ita." Baice komai ba ta yanke wayar ya kalli Manal yace, "tace bata amsawa baki je Kun gaisa ba." Tayi murmushi kunya ma ita take ji kamar Maman na kusa tace, "Anya zan iya zuwa? Sai dai a waya." "Zaki iya mana, Mummyna ce fa." Manal tayi murmushi kawai sai ya fara ɗaukar ta hoto bata sani ba, a lokacin da ta ji shirun nasa yayi yawa ta ɗago sai taga hoto yake mata, ganin ta gan shi sai ya ajjiye wayar kawai bai ce komai ba. "Zan shiga gida" ta faɗa tana buɗe ƙofar motar yace, "a gaishe da Mama, ki tabbatar ta sha magani, idan eyes drops ɗin nan ya ƙare let me know." Kai ta girgiza tace, "in sha Allah, sai anjima" ta faɗa tana buɗe motar ta fita da ledar magani a hannun ta, ta buɗe ledar ta saka power bank ɗin a ciki ta nufi gida. Tsaki yayi bayan ya fita ya kalli ta yace, "Wai wannan mayafin na abaya gani suke kamar yana rufe musu jiki, yanzu meye amfanin wannan tana tafiya ana ganin jikin ta?." Ransa ne ya sake ɓace sosai daman babu walwalwa a fuskar sa ya ja motar ya bar wajan. Asibiti ya koma bai jima sosai ba ya wuce gida bayan yayi abinda Mama tace. Yana shiga wajan Mama ya wuce ya samu Rumana kaɗai a zaune. Tana zaune dan lokacin ana sallar magriba kan ta babu ɗankwali. Sallamar ta amsa da yayi ya kalle ta yace, "kina son zama babu ɗankwali." Ɗankwalin ta jawo ta saka tace, "kaina ne yake ciwo shiyasa na cire." "Ɗankwali ai bazai saka miki ciwo ba" ya faɗa yana miƙa mata ledar ta karɓa yace, "Shawarma ce." Murmushi tayi tana kallon sa domin ko da suna soyayya daman yana yawan siyo mata saboda yasan tana so sai tace, "Ashe kana sane da ina son Shawarma?." Ya zauna daga gefe yace, "ya za'a yi na manta kefe ƙanwata ce?." Murmushi tayi a lokacin Mama ta fito ta kalle shi ganin suna zaune gashi har tana murmushi tana cin shawarma hakan ya yiwa Mama daɗi sosai tace, "Adnan an dawo?." Ya kalli Mama yace, "na dawo Mummy, Ina su Mimi ban gan su ba." "Suna ciki" Mama ta faɗa tana zama ta kalli Rumana tana murmushi tace, "Shawarma tazo kenan." Rumana tayi dariya tana ci tace, "gashi ki ci." Mama ta girgiza kai tace, "Kyautar masoya uwa bata ci ba." Rumana tayi dariya tace, "Mama ashe yana sane har yanzu ina son shawarma." Mama tayi murmushi tana kallon sa tace, "Ya za'a yi ya manta? Yana sane." Ɗan sosa kai yayi kafin ya tashi yace, "Mama me ku ka dafa?." Mama tace, "Taliya suka yi." Mimi ce ta fito ya kalle ta yace, "ki kawo kin abinci" yana faɗa ya fita, Mimi ta bishi da kallo tace, "dama ban fito ba wallahi." Abincin ta ɗauka ta kai masa yana ɗaki ta ajjiye a falon a lokacin ya fito yace, Yayar ki Lubna, ya kike ganin yanayin ta yanzu?." Mimi tace, "Wallahi bana ce ba Yaya, amma ko magana bata yiwa mutane ko Mama ce sai taga dama, ɗazu kuma naga ta fita ban san ina taje ba." Bebi ya girgiza kai baice komai ba ta juya ta fita. Waya aka masa ganin Daddy ne sai ya ɗauka suka gaisa nan yake sanar dashi zuwan Lubna da Mujahid suka yi wajan sa akan maganar aure, ransa ya ɓaci sosai abincin ma ya fita daga ransa yace," Wallahi Daddy ba ina sane na hana auren su ba, in Mujahid miji na gari ne me zai hana nace bazai aure ba? Mujahid bashi da hali na gari gabaɗaya." Daddy yace, "na sani Adnan, tunda naga kayi mata katanga dashi na san kana da dalili.." Bebi yace, "Daddy na tabbatar ba son ta yake ba, yana amfani da ita ne saboda ni, amma ba wai don yana ƙaunar ta bane." Daddy yace, "ai na sanar dashi tunda baka amince ba su yi haƙuri kawai, kamar uba ka ke wajan ta, baza ka yi mata abinda zai cutar da ita ba, kaine matsayin uba a gare su tunda kaine a tare dasu, shi uban na ku yawon barikin sa yafi masa zama daku, su kuma yayyen naka ka zama kamar kai ne Yayan sune a ƙasa da kai." _Yawon bariki._ abinda ya maimaita a zuciyar sa kenan gaban sa yana faɗuwa,kenan Abba abinda yake yi kenan ko me?. Daddy ya katse shi yace, "kar ka damu Adnan ka ɗauka wannan damuwar ta wuce, duk da yarinyar ta turje wai tana son sa. Tsoro nake ji kar ya hure mata kunne." Bebi yace, "zanyi maganin damuwar daddy." Dadddy yace, "Allah ya baka iko. Ka gaida Babar ta ka." Ya amsa da to ya kashe wayar. kalmar bariki ce take masa yawo a kansa, yayi tsaki kaɗan kawai ya tashi kai tsaye ɓangaren Mamy ya wuce. Yana shiga ya samu Lubna a zaune ita kaɗai ganin sa sai da gaban ta ya faɗi, irin kallon da yake mata ya tsorata yace, "Ashe duk irin ja miki kunnen da nayi baki ji ba? Ashe duk abinda nake faɗa miki akan Mujahid baki rabu dashi ba?." Ta tashi tsaye tana turo baki gaba tace, "To Yaya ni Ina son sa kuma gaskiya auren sa...." Saukar marin da taji ne ya hana ta ƙarasawa, ta saki ƙara mai ƙarfi kafin ta dawo daidai ya sake sakar mata mari ta ta sake gigicewa ya nuna ta da yatsa yace, "stupid girl, ni ki ke kallo ki ke cewa kina son sa?." "A'a Bebi meye na duka kuma? Har falon babar ta kazo kana dukan ta me tayi maka?." Maryam ta faɗa tana riƙe Lubana da take kuka tace, "ni Ina son Mujahid Yaya, meyasa shi baya so? Meyasa bai hana Mimi kula Tahir ba ni zai hana ni kula Mujahid?." Mamy ce ta fito daga ɗaki tace, "Lafiya?." Maryam tace, "Bebi ne mana, har nan yazo yana dukan Lubna, Wai akan Mujahid. Na rasa me Mujahid ya tare masa baya ƙaunar sa." Mamy tace, "to Bebi meye matsalar Mujahid ne da baka son auren su da Lubna?." Bebi ya kalli Mamy yace, "Mamy haka kawai bazan hana ta shi saboda son raina ba, tunda ki ka ga na dage ina da babban dalili ne." Maryam tace, "to ka faɗi meye mana, in ma hali na gari ne bashi dashi ai kaima haka ka ke, tunda abokin ɓarawo ɓarawo ne. Kuma wallahi ko me zaka yi sai ta auri Mujahid, duk abinda yake yi ai tare ku ke yi, in shi ɗan iska ne kaima shine. Kai ba'a bada auren aka baka?." Takawa yayi zuwan gaban ta kamar zai mare ta sai ya tsaya tunawa fa yayar sa ce ba ƙanwa ba, Mamy da mamaki tace, "Bebi Maryam ɗin ma marin ta zaka yi? Lallai rashin kunyar taka ta kai maƙura." Bebi ransa ya sake ɓaci sosai kafin yayi magana Maryam tace, "kin gani ai da idon ki Mamy, Wai ni zai mara dan bashi da kunya bashi da mutunci. Kuma sai Lubna ta auri Mujahid naga abinda zaka yi, in kai ne ka haife ta ka hana faruwar hakan don Allah Bebi." Mamy ta fusata tace, "to wai meye damuwar ka ma akan sa? Naga da abokin ka ne ko? In shi lalatacce ne kaima haka ka ke kenan. Yarinya tana son sa ka bi ka kanainaye kace baza ta aure shi ba akan me?. Meye matsalar ka da Maryam da Lubna ne? Kullum cikin saka musu ido ka ke, su naka ƙannen sune na gari wannan kuma latattu ko?. Kaga Bebi bana son haka, ka ƙyale ta ta auri wanda take so kamat yadda aka bar Mimi zata auri wanda take so." Bebi kallon Mamy yake da mamakin abinda take faɗa, dan yana faɗar gaskiya shine zasu danganta shi da lalatacce?. Kai ya girgiza ya ce, "indai Ina raye bazan bar Kamal da Maryam, Lubna bata isa ta auri Mujahid ba. Lubna jinina ce, Ina da ikon zaɓa mata abinda nake so nake ganin daidai ne da rayuwar ta Mamy." Maryam tace, "Mamy ka ke yiwa rashin kunya dan baka da mutunci?." Mamy tace, "ƙyale shi, sai yau na tabbatar da Bebi ɗan kishiyata ne ba ɗana ba. Ina so ka sani ni kuma nice na haifi Lubna, sai kuma na aura mata Mujahid ko baka so, ai ba kaine ka haife ta bane ko? To zan nuna maka Ina da iko a kan yarana, sannan zan tabbatar maka da kai ba komai bane ba face ɗan kishiya." Juyawa yayi zai fita saboda baya son ya tunzura da yawa ya yiwa Mamy rashin kunya. Maryam tace, "sai ka hana in ka isa." Kallon ta yayi dan ita kam bazai bar mata ba yace, "sai dai in bana raye" ya faɗa yana ficewa zuciyar sa ma tafasa sosai. BDƘB2P007 Bebi yana fitowa da wannan ɓacin ran ya wuce masallaci don yaji ana kiran sallar i'sha. A haka yayi sallar zuciyar babu daɗi ya dawo gida yana zuwa zai wuce sai ga Kausar ta fito daga ɓangaren Mama ta kalle shi tace, "Yaya kazo in ji Mama." Bai ce komai ba ya wuce ta bi bayan sa yana shiga tana tsaye da alama jiran zuwan sa take tace, "sau nawa zan faɗa maka ka daina saka kan ka a cikin lamarinsu Lubna ne? Allah yana gani kayi iya bakin ƙoƙarin ka ba sai ka haƙura ba?. Wannan tayar da jijiyoyin wuyan da ka ke ba gani suke ba, wahalar banza ka ke yi gwara ka samawa kan ka lafiya ka watsar da maganar, ai duk wanda yayi na gari kan sa kuma kowa ya san daidai. Maryam ba yarinya bace, ta san abinda ya kamata duk abinda take aikatawa ta sani, ka zare hannun ka daga maganar nan kawai." Bebi yace, "Yanzu Mummy kenan na bar maganar nan Ina kallo suna yin ba daidai ba nayi shiru?." "Maganar taka yanzu amfanin me tayi? Me ya canja?. Lubna baza ta rabu da Mujahid ba, to meye naka na tayar da hankali akan wannan maganar?. Kayi iyakar iyawar ka ba sai a haƙura ba?." "Mummy Lubna jinina ce fa, duk abinda zan yi dan na kare ta ba faɗuwa nayi ba, meyasa zaki ce na bar maganar?." "Saboda su ba matsayin jinin nasu suke kallon ka ba, Mimi da Kausar sune ƙannen ka haka suka ɗauka kuma a zahiri ma hakan ne. Ka taɓa cewa Mimi ko Kausar kar ta kula wani ta kula? Ko ka taɓa cewa kar wata ta fita kuma ta fita?, shi Mujahid ɗin na da Mimi ya fara ba, da kayi magana yanzu wanne zance ake yi?. Kaga kenan ƙannen ka daban ƙannen Isma'il daban." Shi fa ransa a ɓace yake baya son yawan magana, in badan Mama ɗin bace da yanzu baya wajan hakan ya saka yayi shiru bai ce komai ba Mama tace, "ko ina suke son zuwa in kace kar su fita basa fita saboda sun ɗauke ka matsayin Yaya kuma uba, su kuwa suna maka kallon ɗan kishiya ne shiyasa baza su taɓa jin maganar ka ba. Suna ganin kamar kana cutar ta ne ka hana ta kula saurayi sannan ƙanwar ka da ku ke ciki ɗaya ka bari har an saka ranar auren ta. Kayi iya yin ka sai ka bar su da halin su sai me?." Ya sauke numfashi yace, "Mummy da Mimi da Lubna duka ɗaya ne a wajena." Mama ta fara fusata cikin faɗa tace, "na san ɗaya ne a wajan ka a amma a wajan su biyu ne ba ɗaya ba, su kallon yayan su Mimi suke maka Bilal shine yayan su, baza ka taɓa canja hakan ba ko me zaka yi, meyasa ka ke wahalar da kanka da lokacin ka a inda baka yin gwanin ta?." "Me yake faruwa ne?." Muryar Abba ta karaɗe falon duk da mamaki suka kalle shi yana tsaye a bakin falon dan rabon da su ganshi a falon ma sun manta, ganin suna kallon sa da alamun mamaki sai yace, "meya faru?." Mama tace, "A kan Lubna ne da Maryam, basa so Bebi yana shiga lamarin su meyasa bazai daina ba? Ya kasa fahimta hakan sai wahalar da kansa yake a banza a wofi." Abba yace, "Haba Hauwa, wacce irin magana ce wannan? Ya bar maganar Lubna da Maryam ki ka ce fa?." Ya kalli Bebi yace, "ka sanar dani abinda yake faruwa mana." Bebi ya kasa magana saboda harshen sa da yayi nauyi, kalmar bariki da Daddy ya faɗa itace kawai take masa yawo a kansa musamman da ya ga Abban sai yake gani kamar da gaske daga barikin ya dawo hakan ya saka ya kasa magana. Daƙyar ya iya cewa, "A akan Mujahid ne." "Wanne Mujahid?." "Mujahid dai abokin mu na baya." Abba yace, "me Mujahid ɗin yayi? Ban gane maganar ba." Kamar Mama zatayi magana sai ta fasa don akwai idon yaran sa baza ta faɗi abinda yake zuciyar ta ba. Bebi ya kalli Abba yace, "zuwa yake wajan Lubna tun kwanaki wai yana son ta, na hana ta kula shi amma taƙi ji, ƙarshe yau sai ta ɗauke shi suka je wajan daddy wai suna son junan su na hana su aure." A firgice Abba yace, "Mujahid ɗin take so?." Bebi ya girgiza kai alamun eh Abba yace, "ku kira su yanzu kuzo falo, ka kira yayyen ka maza ma kuzo yanzun nan" yana faɗa ya juya ya tafi Mama tace bishi da harara cikin ƙunar rai da baƙin cikin halayen sa tace, "Kana can kana yawon la taya zaka san abinda yake faruwa a cikin iyalan ka?, sai yanzu zaka wani firgita kana cewa wanne Mujahid ɗin?." Bata fahimci a fili tayi maganar ba sai da taga duk sun kalle ta sai ta basar kamar bata ce komai ba ta wuce ta bar wajan. Bebi fita yayi ya yi musu waya ya faɗa musu saƙon Abba ya zauna yayi shiru maganar Daddy kawai yake tunawa, baya so ya gasgata maganar yawon bariki a kan mahaifin sa amma ya kasa mantawa da maganar gabaɗaya. da ya rufe ido sai maganar ta sake dawo masa, hankalin sa ya tashi sosai baya so kalmar ta tabbata akan mahaifin sa ko kaɗan. Ba jimawa suka zo aka taru a falon Abba kowa ya zauna Abba  ya kalli kowa ɗaya bayan ɗaya yace, "na dawo sai naji magana mara daɗi tana yawo a gidan nan" ya kalli Lubna yace, "ke waye wannan a wajan ki?" Ya faɗa yana nuna mata Bilal da yake kusa da ita. Ta kalle shi tace, "Yayana ne." Abba ya sake nuna Bebi yace, "wannan fa?." Tace, "shima Yayana ne." "Amma shine dan uwar ki don uban ki zai tsawatar miki akan abu ƙi yi? har da zuwa ki samu Daddy ki ce kina son sa ya hana ki auren shi?." Mamy tayi ƴar dariya tace, "daga dawowar ka har an kawo ƙara kenan ko? To yayi." Ya kalli Mamy yace, "Jalima ban ce ki yi magana ba." Ya sake kallon Lubna cikin tsawa yace, "Tambayar ki nake." Lubna murya na rawa tace, "Allah Abba ni Ina son sa, kuma aurena ya ce zai yi." Abba yace, "Ina magana kina cewa son sa ki ke? Ni ki ke faɗawa wannan maganar?." Shiru tayi bata ce komai ba tana share hawaye yace, "to bazai aure ki ba, duk abinde Bebi yace a gidan nan shi za'a yi domin na tabbatar bazai yi abinda zai cuce ki ba. Tunda yace ki rabu da Mujahid dole ki rabu dashi in ba haka ba zaki fuskanci fushina wallahi. Baza ki aure shi ba ki rubuta ki ajjiye Lubna ta fashe da kuka hakan ya saka Mamy tace, "ni banga aibun yaron nan ba akan me za a hana ta kula shi? Kuma naga abokin Bebin ne in ma wani halin banzan ne dashi shima yana dashi tunda duk kanwar ja ce, a haka kuma shi Bebin aka bashi auren yarinya. Dan haka itama a barta da wanda take so. Itace babba a cikin su, amma da yake Mimi ce bai tsaya wata magana ba an tsayar da lokacin biki an barta ana cewa baza ta aure shi ba. Akan me? Bebi ai ba shine ya haife ta." Kowa kallon Mamy yake da mamakin abinda take cewa, babu wanda yayi zaton zata furta wannan maganar. Abba ya girgiza kai cikin takaici yace, "Tabbas ta tabbata kece ki ke goya mata baya, duk abinda take yi ke ki ke ɗaure mata g*** shiyasa take duk abinda take so saboda kin nuna mata bamu isa ba." Mamy tace, "to kai da baka gidan har wani abu zaka ce? Yaushe rabon da ka zauna da iyalan ka kaji abinda yake damun su?. Sai yanzu da yake ƴar gwal da ɗan gwal sun kawo ƙara zaka zo ka tara mu ana yin faɗa mara hujja balle makama, meye aibun yaron da za'a ce baza ta aure shi ba? Kenan kullum a laifi suke? Har yanzu zuwa yake yana cewa Maryam na zuwa wajan Kamal, kenan a haka yake kallon yaran nawa dan ba ciki ɗaya suke ba?." Yaya Isma'il yace, "Mamy don Allah ki yi shiru da maganar nan." Abba yace, "ƙyaleta, cigaba Ina jin ki." Jin hakan sai tayi shiru Abba ya kalle ta sosai ransa ya ɓaci da maganganun ta yace, "ba Lubna ko Maryam ba, kema a ƙasan Adnan ki ke, in yace kar ayi abu umarni zaki bi balle yaran ki" ya faɗa cikin fusata yana kallon ta. "Kuma na rantse da Allah na datse maganar Mujahid, in na sake ji ko gani ana maganar sa a gidan nan sai ran ki da nata ran ta ya ɓaci. In gaba da so take yi masa ta haɗɗiye zuciya ta mutu yafi daidai a akan ta aure shi. Dan shirme da rashin hankali yaron da yake lalata yaran mutane shi za'a bawa aure?." Shiru ya ratsa falon babu wanda yake komai kafin Abba yace, "Kun ji dai abinda nace, babu Lubna babu Mujahid in ba haka ba wallahi ni kaɗai na san matakin da zan ɗauka a kan ku gabaɗaya. Wannan ai shashanci ne da wulaƙanci, a gidana a dinga nuna banbanci tsakani yara? Duk ba jini ɗaya bane ba? A komai mata sai kun nuna kishi? Akan kishin banza da wofi zaki kai ƴar ki inda za'a cuci rayuwar ta saboda ƙarancin tunani." Nan ma shiru babu wanda ya amsa Abba yace, "yanzu aka tsiro da wannan shegentakar a kuma dakatar da ita kafin ran kowa ya ɓaci, na faɗa na sake maimaitawa babu Lubna babu Mujahid, in nima ɗan kishiyan ne sai ace dan ba ɗakin mu ɗaya ba." Mamy tayi dariya kaɗan tace, "To abu ne a bayyane ai, inda a ɓangaren nasu ne baza'a dakatar da maganar ba." Abba yayi banza kamar bai ji ba ya kalli Lubna da take kuka ya sake yace, "Allah ya sa na sake jin labarin kin saurare shi kiga yadda zan yi dake a gidan nan, Ana kishin ki amma ke bakya gani.  Yaron da bashi da tarbiyya bai san darajar mace ba shi za'a baki?. Shashasha mara hankali da tunani." Nan ma shiru falon babu mai magana  a cikin su, Abba ya ce, "Ku tashi ku bani waje, Allah yasa na sake jin magana makamanciyar wannan ku ga yadda zan yi daku." Jin haka kowa sai ya tashi Yaya Bilal da Yaya isma'il suka bashi haƙuri sannan suka fita. Tsayar da Bebi suka yi shima suka bashi haƙuri ya nuna kamar ba ayi komai ba ma shi ya wuce don yaji daɗin abinda Abba yayi sosai, haka nan yake jin wani abu ya ragu a cikin damuwar sa. Mama ta tashi zata bar falon Abba ya dakatar da ita yace, "dawo ki zauna, kin yi laifi wanda ban san ki dashi ba." Mama ta zauna tana kallon ƙasa yace, "meyasa ki ke taya ƴar uwar ki nunawa Adnan Akwai banbanci tsakanin Lubna dasu Mimi?." Mama tace, "haka ne ai, akwai banbancin domin inda ace Mimi ce in ya hana zata hanu." Abba yace, "bana son wannan maganar, dukkan su abu guda ne a wajan sa meyasa kike sage masa guiwa akan abinda ya saka gaba?." Mama tace, "ba sage masa guiwa nake ba, Abu ne a bayyane, in yayi ba gani ake ba, a gaban ka yanzu akace masa lalatacce ne dan kawai yana faɗar gaskiya, ba sai ya fita daga lamarin ba ai na ibada bane. Ko kunyar idona ba'a ji ba aka kira shi da wannan kalma, har ake cewa an bashi aure duk da ga halin da yake dashi." Abba yace, "bana son sake jin hakan don Allah, dukkan su jini ɗaya ne babu wani banbanci a tsakanin su." Mama tayi ajiyar zuciya ta miƙe zata tafi yace, "in kin koma ki kawo min tea da kan ki, ba Mimi na ce a bawa ba, ke zaki kawo min." Bata ce komai ba ta fita don taji nasihar Hajiyar su akan sa in ba haka ba wallahi baza ta saurare shi ba. Lubna tunda suka koma take kuka kamar ranta zai fita saboda baƙin cikin abinda ya faru, Allah ya sani tana matuƙar son Mujahid baza ta iya rabuwa dashi ba domin bata taɓa son wata halitta kamar yadda take son sa ba, hakan ya saka ta kuka saboda abinda Abba yace. Jin zuciyar ta take kamar zata fashe saboda zafi da ƙunar da take ji, ta kasa jure yanayin da ta tsinci kanta a ciki, ita ɗin ɗanya ce a soyayya shiyasa take ji kamar zata yi hauka. Maryam ta kalli Mamy tace, "Yanzu Mamy haka zamu zuba idanu a mayar damu kamar wasu wanda basu san abinda suke yi ba a gidan nan? Mamy kece babba a gidan nan fa, Meyasa ake yi miki irin wannan abubuwan ki ke ɗauka kamar ba kece uwar gida ba?. Bebi ne zai juya ki? A cikin gidan ki ace sai abinda yake so za'a yi? Nawa yake?." Mamy da ranta ya  kai ƙarshe wajan ɓaci akan lamarin tace, "bai isa ya juya ni ba Maryam." "Mamy gashi ya hana auren Lubna da Mujahid, indai auren nan ya hanu ya tabbata shine uba a gidan nan." "Bai isa ya hana ba, ai ni na haife ta ko? Zan nuna masa ina da iko akan abinda na haifa. Shima mahaifin na ku bazai dakatar da wannan auren ba balle kuma wani Adnan." Maryam tace, "komai yace Bebi komai shi? Su Yaya da suke manya a gidan an jingine su a gefe sai abinda Bebi yace sannan ake yi? Ina wannan abun da sake wallahi." Mamy tayi shiru bata ce komai ba amma sosai ranta ya ɓaci, ta kuma ji haushin abinda ya faru. Lubna tashi tayi ta shiga ɗaki ta kulle kanta ta zauna a kan gafo tana kuka sosai tana tunani, Lallai shawarar Mujahid itace kawai mafita a wannan lamarin, tabbas abinda ya faɗa shine daidai, da zarar wani abu ya faru a tsakanin su shikenan za'a aura mata shi ko ba'a so, hakan kuwa za'a yi domin faruwar hakan shine zai saka a aura mata shi ko kowa baya so. Hannu na rawa ta ɗauki waya ta kira shi dan ta amince da shawarar zuciyar ta ɗari bisa ɗari, bai ɗauka ba sai bata sake kira ba dan tasan zai kira ta. Ba jimawa ya kira ta tana ɗauka tace, "Sweetheart na amince da shawarar ka, na amince kawai babu wani jan lokaci." Mujahid yace, "me ya faru?." "Nidai na amince kawai, ka san abinda zaka yi kafin gobe" tana faɗa hakan ta yanke wayar ta dafe kanta da hannun ta tana sake amincewa da shawarar zuciyar ta. _Ki buɗe WhatsApp status ɗin ki zaki ga saƙo._ abinda Maryam taga Kamal ya rubuta mata kenan hannu na rawa ta kunna data ta shiga WhatsApp gaban ta sai faɗuwa yake yi. Hoton farko da ta fara gani shine hoton breast ɗin ta anyi posting sai dai ba'a nuna fuskar ta ba amma tana kallo ta san wannan jikin ta ne. "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Na shiga uku ni Maryam!." Hannun ta rawa yake yi sosai ta kalli kofar ɗakin da ta a buɗe  tayi sauri ta tashi ta kulle gaban ta sai faɗuwwa yake yi cikin jijiga da tashin hankali. Kiran Kamal ne ya shigo wayar ta ɗauka da hanzari murya a sarƙe tace, "Kamal meye haka? Hoton tsaraicina ka ke yaɗawa a duniya? Me nayi maka?, ni fa uwar ƴaƴan ka ce." Kamal yayi murmushi daga can ɓangaren yace, "na faɗa miki abinda za a yi amma sai ki ka ƙi yarda saboda taurin kan ki kina gani kamar ba zan iya ba ne, gashi kin gani na fara sharar fage kafin mu tsunduma cikin abun kai tsaye." Maryam tace, "meye ribar ka na aikata hakan? Kar ka manta nifa tsohuwar matar ka ce wacce ku ke da yara guda biyu, Meyasa zaka wulaƙanta ni a lokacin da ban yi tsammani ba?." "Ke kika so hakan ai, da kin bari mun yi abin mu ciki sirri babu wanda ya sani balle a zo wannan gaɓar, amma sai kika ƙi, kika nuna ke baza ki yi ba." "Ashe daman amfani ka ke dani tum ina gida ka? So ka ke wannan ranar tazo da zaka tozarta ni a idon duniya da yarana?." Yayi dariya yace, "ban tozarta ki ba Maryama saboda ban nuna fuskar ki ba, ban bar wata shaida a jikin hoton wacce zata nuna ke ce, in ba ni da ke ba babu wanda ya san jikin ki ne, kinga ai na kyauta miki ban kuma tozarta ki ba." "Amma kai ka san ni ɗin ce ai ko!?" Ta faɗa cikin murya mai amo dan yadda take jin zuciyar ta baza ta iya danne ɓacin ran ba. "Calm down my Baby, in ban da ni dake babu wanda zai gane kece, nayi miki haka ne dan ki san da gaske nake ba ƙarya ba zan iya yin posting video ki akan abinda nake so. Kece kike ganin kamar ba zan iya ba shiyasa na fara sharar fage dan ki gani ki tabbatar kuma zan aikata." Kuka take yi sosai hankali a tashi tace, "Meyasa Kamal! Meyasa!. Ni fa wacce ka taɓa aure ce, killace ni da mutunta ni ne ya kamace ka ba tozarci ba, ashe daman wannan lokacin ka ke jira shiyasa da ka ke saka ni tura mata hotunan tsaircina a gidan ka? Meyasa zaka min haka Kamal?. Ka tuna a baya ni matar ka ce, amma a yanzu ni ba matar ka bace amma uwar yaran ka ce." Kamal yayi dariya cikin nishaɗi  yace, "ban tozarta ki ba na faɗ miki tunda ban nuna fuskar ki ba, amma in kika cigaba da yi min gardama za ki tsinci abinda yafi haka a tiktok wallahi, wannan video ɗin zan saka na kuma saka sunan ki da na mahaifin ki, in kina da account ma nayi tagging ɗin ki sai kiga ƙarshen tozarci." Bata samu damar magana ba sai kuka da take yi  ya sake cewa, "in kin amince zan miki text na inda zamu haɗu gobe." "Babu inda zan zo, babu inda zan zo na fɗa maka kayi duk abinda zaka yi." Ya sake yin murmushi yace, "haka kika ce ko? Mu zuba" ya faɗa  yana yanke wayar ta zauna akan tiles tana kuka. Ƙarar shigowar saƙo taji ta kalli wayar taga shine ya turo mata ta buɗe whatsApp ta buɗe abinda ya turo, tashin hankalin abinda ta gani bata san ta kife wayar ba tana zare idanu ba, wasu videos ɗin nata da tayi ta manta dasu amma shi yana dasu. Hankalin ta ya tashi sosai domin abinda taga ya rubuta a jiki ya tsorata ta hakan ya saka ta ɗauki wayar hannu ta na rawa zata rubuta masa saƙo kira ya shigo ta ɗauka a raunane tace, "na amince a ina zan same ka?." "Guests house ɗin." "Zan zo, zan amince ko dan martabar yarana." "Dakyau! Ki taho da shirin kwana" yana faɗa ya yanke wayar ta sake fashewa da kukan da ya fi na ɗazu sauti, saboda ƙunar da take ji a zuciyar ta ninkuwa take fiye da baya. BDƘB2P008 Da safe da Bebi ya tashi bayan ya shirya wajan Mama ya shiga ya samu babu kowa a falon amma an yi breakfast da komai an ajiiye ya zuba abincin ya zauna yana ci yana aikin danna waya. Rumana ce ta fito jin motsi a falon ya kalle ta yaga ta rame ta sake yin haske idanun ta sun sake fitowa waje ta zauna tace, "ina Kwana." "Ya jikin ki? Ina fatan kin ji sauƙi sosai." Jin yadda ya tambaya da kulawa sai tayi tace, "naji sauƙi, tunda ka bani maganin nan ko ciwon ƙirjin bana ji yanzu." Ya girgiza kai yace, "Allah ya ƙara lafiya." Ta amsa da amin yayi shiru bai ce komai ba sai daga baya yace, "ina Mummy?." "Tana wajan Abba." Daga nan bai ce komai ba ya cigaba da cin abincin sa kafin ya ajjiye bowl ɗin ya ɗauki wayar sa jin ana kiran sa, ganin mai kiran sai ya ɗauka yace, "ina ji." Yayi shiru alamun ana bashi amsa kafin yace, "zan shigo" yana faɗa ya kwashe wayar ya saka aljihu ya tashi tsaye ya kalle ta suka haɗa ido alamun ta jima tana kallon sa, sai kuwa ya sake ɗaure fuska shi baya son yawan kallo mara dalili ta kuma sani yace, "In Mummy ta fito kice mata na tafi." "Gani ai" Mama ta faɗa tana shigowa ta kalli abinda yaci abincin tace, "kai dai ka shiga uku, ɗauke bowl ɗin ma baza ka iya ba don Allah?." Rumana ta tashi ta ɗauka tace, "ni zan ƙarasa cinyewa ma basai na zuba wani ba." Gaisawa suka yi da Mama ta masa tana kallon sa, ganin fuskar sa zai tabbatar maka da ransa a ɓace yake har lokacin tace, "kai ta saka ɓacin rai mara dalili a zuciyar ka kaji Bebi, Allah ya taimaka." Bai ce komai ba kawai ya fita dan Mama baza ta gane abinda yake ji a kan ƙannen sa bane shiyasa take faɗar hakan. Sai da yaje babban asibiti ya jima a ciki sai azahar sannan ya tafi gidan Hamza don a can suka yi zasu haɗu kamar yadda aka saba in zasu tattauna abinda ya shafi asibitin su. A falon Hamza ya same su dashi da Huzaifa suna hira da alama sun gaji da jiran sa. Yana shiga ya zauna bai ce musu komai ba Hamza ya fara magana akan abinda ya ajjiye su suka fara tattaunawa shida Huzaifa. Ko me zasu ce yana ji baya dai magana sai dai yace eh da a'a. Ya ƙular da Huzaifa har ya kasa shiru ya kalle shi yace, "wai kai meyasa ka ke haka ne? Sai a ɓata maka rai a wani wajan kazo kana ɗaurewa mutane fuska har muna magana baka tankawa daga eh sai a'a?. Ina ruwan mu da ɓacin ran ka?." "Lallai ne sai nayi magana?" Abinda yace kenan ya ɗauki lemon da yake ajjiye yana sha. Hamza yace, "Kai kullum ranka a ɓace yake a yanzu, mun zo muna tattaunawa kamata yayi ka ajjiye ɓacin ran ka faɗi shawarar ka, abu ne da zai amfane mu gabaɗaya. Da gaskiyar Huzaifa da yace ina ruwan mu da ɓacin ran ka? Abinda ya shafe mu muke yi a nan kaima abinda ya da ya shafe ka ne ya ɓata maka rai." Bebi ya kalli Hamza yace, "ka faɗawa abokin ka, alaƙar da take tsakanin sa da partner, ina nufin my life partner ya kawo ƙarshe ta ko kuma ya rage ta, I can't tolerate komai ace Huzaifa, komai ace ai na faɗawa Huzaifa, ya kamata ya sassauta ya san cewa she's my wife to be. In ma da yuwa a ajjiye ta a gefe ai ba dangin uwa babu na uba." Huzaifa ya ƙyalƙyale da dariya yana kallon sa cikin shaƙiyanci yace, "Kaga masu life partner, Daman akan Manal ne ka ke wannan ɗaure fuskar?. Ai daman nasan tunda ka ganta jiya tazo karɓar maganin Maman su na san sai an yi haka. Bebi kafin ka san ta na riga ka sanin  ta ya kamata ka tuna wannan. In da ace soyayya zan yi da ita da wataƙila ba wannan labarin ake ba yanzu." Wannan kalmar ta ya riga shi sanin ta haushi take bashi amma yaga alama shi baya ganewa bai kuma san kara ba, hakan ya saka ya ce, "Yanzu na santa, shiga rayuwar ta da lamarin ta ba baka bane. Kai ba ɗan uwan ta ko wani nata ba meye na ka na shiga rayuwar ta?." "Mutunci da girmamawa ne a tsakanin mu." "You have to cut it off, abin is too much na lura baka son a yi shiru ba baka san kara ba kuma." Huzaifa dariya ya bashi sosai ya dara, so yake ya tunzura shi ya sake zuwa wuya hakan ya saka  ya ce, "To ai ko ka aure ta bana tunanin zaka datse wannan alaƙar balle baka aure ta ba." Numfashi ya sauke baice komai ba ganin ya mayar da abin wasa shi kuma da gaske yake. Gani yayi Abba yana yi masa waya ya ɗauka ya fita. Hamza ya kalli Huzaifa da yake dariya yace, "ba abin dariya ba ne Huzaifa, ka san Bebi a kan ƙannen sa ma ya aka cika balle wacce zai aura?, ya kamata ka rage ɗin tunda baya so har gashi ya kasa jurewa ya faɗa maka. Kuma wacce zai aura ce, matsayin ka na likita shima  haka duk abinda zaka yi dan ka taimaka shima zai iya. Duk da ɓangaren ka ne amma ka ƙyale shi in abin ya kakare masa watarana zai nemo ka." Huzaifa yace, "wallahi rigima ce kawai irin ta sa, amma ni ban da wata alaƙar da ita da har zata ɓata masa rai haka, na san yana da kishi zai yi kishi dani amma ni wallahi taimakon ta nake ita da Maman ta  ba wani abun ba." "Nima ban ce wani abun ba Huzaifa, zaku iya zumunci saboda baza ta manta da kai ba a rayuwar ta dan ka taimaka mata kai da mahaifiyar ta, amma ka san yadda zaka yi zumunci da ita ɗin kar ana wasa da dariya yazo ya zama matsala, kai kasan ko ƙannen sa baya so a kula balle wacce zai aura, in ya bawa ƙannen sa tsaro na kashi sittin cikin ɗari ita zai bata ɗari bisa ɗari ne saboda auren ta zai yi.." Huzaifa yayi dariya a lokacin Bebi ya dawo yace, "in ya kwantar da hankalin sa ma na kusa tattarawa na koma Qatar, kuma ya san ina da wacce zan aura tun ba yanzu ba balle shaiɗan ya dinga kawo masa wani abu mara kyau a zuciyar sa. Manal kuma akwai kyakykyawar alaƙa tsakanin mu, akwai girmamawa da mutunta juna wani bai isa ya hana ba" ya faɗa yana kallon sa dan wallahi daɗin tsokanar sa yake ji. Bebi bai ce masa komai ba dan yaga so yake ya saka shi magana shiyasa ya share shi,  Hamza yayi dariya yace, "Huzaifa baka da kirki. Bebi kayi haƙuri Huzaifa zai daina shigewa wacce ka ke so." Huzaifa yace, "ni mamaki ma yake bani, ya manta lokacin da yake cemin son ta nake?, in auren nata nayi niya da yanzu ba wannan maganar ake ba." Bebi baice komai ba kawai ya ɗauki key ɗin motar sa da wayar sa ya fita, suka  sake yin dariya ba kamar Huzaifa da yake tunzura shi da gangan.        ********* Mujahid da yake jira Lubna tayi magana yace, "Ina jin ki Sweet, kin ce min zamu yi magana yau kuma gashi na zo amma kin kasa cewa komai." Lubna ta kalle shi ta kalli titin da yake gaban su tace, "Yaya Bebi ya kai ƙara ta wajan Abba a kan ka, Abba kuma yace babu ni babu kai."  Ta faɗa murya tana rawa sosai. "Innalillahi! Meyasa Adnan baya sona ne? Me na aikatawa wannan bawan Allah baya ƙaunar farin cikina?." Jin a yadda yayi maganar cikin tashin hankali da ruɗani Lubna tace, "shiyasa na amince da shawarar ka, hakan shine mafita kawai a cikin lamarin mu." Mujahid ya girgiza kai yace, "ki bar wannan maganar, bakya so baki amshe ta ba tun farko gwara a dakatar da ita kawai. Bana son mu aikata abinda zuciyar ki take rawa a kai, gwara a haƙura tunda kina ganin kamar zan cutar dake ne." Lubna tace, "yanzu na karɓi shawarar hannu biyu, na fahimci itace mafita bamu da wata hanya bayan ta ita." Ya kalle ta ya raunana murya yace, "da gaske ki ke?." Ta ɗaga kai alamın eh ya sauke numfashi yayi shiru kamar mai tunani kafin ya kalle ta yace, "Kin shirya?." Ta ɗaga kai alamun eh ya kulle ido ya buɗe ya sake cewa, "zan tambaye ki wani abu ki bani amsa duk yana cikin mafitar da nake nemar mana, kar ki manta ni likita ne." Ta ɗaga kai alamun to yace, "yaushe ki ka gama period ɗin ki?." Lubna tayi shiru alamun tunani kafin tace, "na manta, amma kamar za'a yi sati biyu." Ya girgiza kai yace, "okay. Yaushe ki ke tunanin zamu aiwatar da neman mafitar ta mu? Bana so a ɗauki lokaci gaskiya." Lubna dai zuciyar ta bugawa take amma ta daure tace, "ko yau ma." Murmushi yayi yana mata wani irin kallo na kin shigo hannu yarinya yace, "bai yi kusa ba?." "Bai yi ba." Ya sauke numfashi yana lumshe idanun sa ya kalle ta yace, "amma kamar kina jin tsoro, yanayin maganar ki ya nuna hakan." Ta sauke numfashi tace, "ban san meyasa nake jin hakan ba." Yayi murmushi yace, "kar ki damu ni na sani." Kallon sa tayi sai ya sake yin murmushi yace, "eh na sani." Kawar da kanta tayi zuciyar ta ta rabu biyu akan lamarin, ɓangaren dama tana hanata aikatawa, ɓangaren haggu kuma tana tabbatar mata da hakan ne ya kamata, hakan ne zai bata damar mallakar masoyin ta. Wannan tunanin ya rinjayi na farkon hakan ya saka ta kulle ido tayi shiru. Ganin tayi shiru  bata cewa komai ya saka yace, "yanzu ya mu ke ciki?." "Abinda kace." Mujahid yace, "mu wuce kawai?." Kai ta ɗaga alamun eh kafin tace, "ina zamu je?." Yace, "Gidana." Jin abinda yace sai tayi shiru ya kunna motar suka nufi gidan sa kai tsaye, shi kansa zuciyar sa rawa take yi akan lamarin amma bazai rasa wannan damar ba. ******** Bebi koda ya bar gidan Hamza hanyar gidan su Manal ya bi haka nan yake son ganin ta ko zai ji sauƙin ɓacin ran da yake zuciyar sa, daga can baya ya tsaya yana kallon layin su ko zai ganta amma babu ita babu alamun ta. Lumshe ido yayi ya ɗauki waya ya kira ta bata ɗauka ba ya sake kira sai a lokacin ta ɗauka da sallama. Bai amsa sallamar ba ya yi shiru zuciyar sa na bugawa sosai, shauƙin soyayyar ta yake ji yana fizgar sa zuwa  gare ta, daɗin sallamar da tayi sanyi yaji a zuciyar sa lokaci ɗaya hakan ya saka ya kasa cewa komai. Manal jin yayi shiru tace, "Baka jina?." Numfashi ya sauke murya a can ƙasa yace, "Manal I'm in love with you so much, kin san da hakan?." Jin abinda yace sai tayi murmushi tace, "ko sallamar baka amsa ba." Ya sake lumshe idanun sa yace, "ki gaishe da Mama." "Zata ji." Ta faɗa murya a sanyaye sai ya murmusa shima yace, "what wrong?." Manal tace, "babu komai." Yace, "akwai abinda zaki ce." "Babu komai, a gaishe da Mummy." "Bayan kin ƙi zuwa wajan ta." Manal tayi murmushi tace, "Zan je." Bebi matuƙar daɗin magana da ita yake ji hakan ya saka ya gyara zama yace, "Yaushe?." Manal tace, "ko yaushe." "Ba zuwa zaki ba." Kafin tayi magana ya rigata yace, "zan bada saƙo a kawo miki anjima, zan je asibiti yanzu." Ta amsa tana cewa, "Asibiti dai." Bai ce komai ba yayi murmushi ya karshe wayar yana Jin zuciyar sa abinda yake ji ya ragu sosai ya ja motar sa ya tafi. ****** Maryam kuwa bayan ƙarfe biyar na yamma ta fita napep ma ta hau saboda kar ma a gane ta kai tsaye guest house ɗin ta nufa kamar yadda yace. Tana shiga ta same shi a falo yana kallon ball cikin nishaɗi yana ganin ta sai ya tashi tsaye yace, "Barka da zuwa Masoyiya a bar ƙauna." Maryam tana kallon sa cikin rashin walwala tace, "gani, me kake so dani?." Ya bita da kallo yace, "abinda nake so a bayyane yake ai Maryam, kece ki ke gardama da hakan bata faru ba. Da yanzu mun wuce wajan amma sai dawo da hannun agogo baya kike." "Ka bani mamaki Kamal, ashe daman zaka iya amfani da tsaraicina wajan tozarta ni?." Yayi murmushi mai sauti yace, "Ba tozarci bane, soyayya ce." "Wannan ba soyayya be ce Kamal" ta fada cikin tsawa tare zama a kan kujera tare da dafe kanta. Ya zauna kusa da ita yace, "kar ki wani damu wannan ba abin damuwa bane." Ta kalle shi tana hawaye yace, "meye na kukan kuma?." Maryam tace, "gida zan tafi, ka faɗa min abinda zaka ce." "Ai na faɗa miki ki zo da shirin kwana." "Ni ba karuwa bace ka sani." "Nima ba ɗan iska ba ne kin sani." "Ka canja daga yadda na san ka. Don girman Allah, don darajar annabi, don darajar iyayen ka, don darajar yaran da muka haifa ka bar wannan maganar Kamal, ka ajjiye ta a gefe na tabbatar maka zan yi auren kisan wuta nazo na aure ka, wallahi zan bi ko wacce hanya wajan ganin na dawo gidan ka matsayin matar ka. Ka rufa min asiri ka adana wannan hotunan ko dan darajar haihuwar da muka yi, tsaraicina ne in ya fita na gama tozarta a duniya, ƙarshen tozarci a duniya a yaɗa hotunan tsairaicin ka. Don Allah kar ka yi min haka, ni tsohuwar matar kace da muka yi zaman lafiya ƙaddara ta raba mu, ka yi min rai ka fasa aiwatar da hakan don Allah." Kamal yace, "na faɗa miki bazan yi posting hotunan amma sai kin amince dani mun kwana yau kamar lokacin da kike gidana, hakan yana faruwa ni kuma zan goge." Ta rausayar da kai tace, "yanzu baza ka goge ba sai nayi zina da kai? A wancan lokacin na ɗauka tura maka hotunan tsaraicina soyayya ce ashe wannan ranar ka ke jira?." Yayi murmushi yace, "Ki daina wannan maganar Maryam, ki amince da abinda nake so in ba haka ba wallahi sai ƴar ki taga video nan." Maryam ta lumshe ido jin bazai saduba ba ita kuma bata san me zata ce, bata san abinda zata yi ba, bata san abinda zata aiwatar ba a wannan lokacin. Yanzu me zata yi?saɓon Allah ko martabar ta da ta yaran ta?. Ganin ta tafi tunani sai ya tashi ya shiga ciki yace, "in kin shirya ki same ni" ya faɗa yana barin wajan ta bi shi da kallo zuciyar ta na zafi sosai ta sake fashewa da kukan da bashi da amfani a yanayin da take ciki. ******* Rumana da ƙawar ta suna zaune a mota a ƙofar gidan su Manal ta kalle ta tace, "da gaske ki ke nan ne gidan su?." Ƙawar ta mai suna Zuby tace, "ai bazan miki ƙarya ba, nan ne." Rumana ta sake kallon gidan tace, "kalli gidan fa." Zuby tace, "ni na kawo ki gidan ai, ƙarshen kenan." Ta girgiza kai tana sake kallon gidan tace, "ni na ɗauka wata ƴar masu kuɗi ce ko ƴar masu sarauta ashe a nan ya ƙare?." Zuby tayi dariya tace, "a ganin ki su talakwa ne amma ba haka abin yake ba, suna da rufin asiri sosai fiye da tunanin ki. Iya sutturar da suke sakawa a nan zaki tabbatar da su ɗin ba talakawa bane, dan zan iya cewa abayoyin da yarinyar take sakawa ke baki dasu. Tafi saka hijjabi da abaya, ke in kika ga abayar jikin ta wani lokacin sai kin yi mamaki. Wannan dalilin ya saka kai tsaye in kika ganta baza ki ce a nan take kwana ba." Manal ɗin ce ta fito a lokacin sanye da hijjab jalbab kalar ja yayi mata kyau sosai ya haska milky face ɗin ta Zuby tace, "Gata nan, sunan ta Fatima amma Manal ake ce mata saboda sunan Maman ta ne da ita. Bata da wasu shekaru sosai, tana da kirki da yawan fara'a. Fannin karatu a secondry school ta tsaya, amma da yake private school tayi in tana turanci zaki ɗauka wata mai ilimin gaske ce. Itace wacce Bebin ki yake so." Sake wara ido take a kan Manal lokacin da take karɓar saƙon da Bebi ya turo mata ba tare da ta san dasu ba, sake kallon ta Rumana take daga sama har ƙasa ta kalli Zuby tace, "wannan farin na ta ni kaɗai nake gani?." Zuby tayi dariya tace, "ba ke kaɗai bace ba, haka kalar ta take, fara ce ita ba farin gama garin fari irin na ku ba. Shiyasa ƴan makaranta su suke mata take da milky beauty saboda wannan hasken nata yayi kama da madara. Kallo ɗaya zaka yiwa wannan hasken ya ɗauki hankalin ka, in ka tsaya ka nutsu kana ganin ta a lokacin zaka hango ƙaramin bakin ta wanda yake ja sosai kamar na larabawa." Rumana jikin ta yayi sanyi tana kallon Manal a lokacin da ta shiga tace, "Zuby shiyasa Yaya Bebi baya ta ni yanzu, kalli wacce ya ɗauko fa?. Ga kyau, ga hasken da ni mace ma ya burge ni balle shi, ga idanu, ga bakin ta mai kyaun gani, gata mai ƙarancin shekaru. Ta ya zai saurare ni yana ganin ni kusan sa'ar sa ce?." Zuby ta tausasa murya tace, "bata fi ki kyau bafa Rumana, wannan hasken ne ya saka ki ke ganin kamar ta fi ki, amma tsahon hancin ki yafi nata." Rumana tace, "ta ya zaki ce haka? Kalle ta fa?." Zuby tace, "Yayarta ta fita kyau ni a idona, ita kawai wannan hasken nata ne yake da ɗaukar hankali." Rumana ta kalli Zuby tace, "gadon kyau suka yi?." Zuby tace, "Maman su kyakykyawa ce sosai, dan naji ance ana tunanin halfcast ce, a wajan ta suka gado wannan kyaun. Duk da bata da wannan hasken wataƙila ita Manal ɗin a wajan baban su ta gado wannan hasken." "Zuby a haka ma babu hutu fa kenan, in ta samu hutu wanne irin haske zata sake yi?." "Ke dai tunda zai aure ki ai shikenan, kin takura an nemi miki ita gashi kin ganta kina kishi." Ruamana tace, "Dole nayi kishi Zuby" ta faɗa tana sake kallon ta inda Manal take taga bata wajan. Rumana tace, "wannan fa daga asibitin su Bebi yake, ga logo ɗin asibitin nan a bayan rigar sa, duk yadda aka yi shine ya bada wannan saƙon a kawo mata. Zuby Bebi ya iya soyayya, Bebi ƙarshe ne wajan soyayya, iya kallon da zai miki na soyayya shi kaɗai ya ishe ki balle ya buɗe bakin sa. Soyayya yake yi hankali, a nutse yake gabatar da ita babu shirme balle wani abu na banza, soyayya yake da zuciya ɗaya in yana so kawai yana so. Tun a lokacin baya na shaida baya wannan haukar soyayyar balle yanzu da ya sake hankali. Ina kishi da hakan sosai Zuby." Zuby tace, "ki yi haƙuri haka Allah ya yi." "In ya auro yarinyar nan zan iya samun ciwon zuciya, domin yana da kamar ta ne zai yi dani bazawara?." Sai ta bawa Zuby tausayi tace, "Yana son ki fa, ke ya fara so babu ruwan sa da kin taɓa aure wannan soyyayar na zuciyar sa, ke kin san meye first love?." Murmushi kawai tayi tace, "mu tafi kawai Zubaida." Zuby ta kunna mota taja suka tafi zuciyar Rumana sai bugawa take yi.                      Bayan kwana biyu. Tana tsaye tana amsa waya a banɗaki murya ƙasa-ƙasa tace, "to ba kaine kwana biyu baka min waya ba, ba dole na ɗauka ka manta dani ba." Daga can ɓangaren yace, "haba ni na isa nace na manta dake? Abubuwa ne suka yi min yawa shiyasa. Yanzu yaushe zamu haɗu?." Mubeena  tace, "ni na gaji da wannan abun, kawai kazo gidan mu ayi maganar aure a wuce wajan. Kana gani ƙanwata har an kusa bikin ta amma kai ko yaushe zancen ka a ina zamu haɗu, ka san bana kula kowa sai kai." Yayi murmushi yace, "har yanzu bamu gama fahimta juna dake ba ta ya zamu fara batun aure?." "Me baka sani ba a kaina? Ni dai kawai ka turo indai kana sona." "Shikenan Baby, amma kafin nan ina so mu haɗu mu yi magana." Mubeena tace, "na faɗa maka ba'a barina fitowa." Yace, "ki san yadda za ki yi ki fito sai ki min waya so nake mu yi maganar sosai." Mubeena tayi ajiyar zuciya tace, "ko yanzu ne na fito?." "Eh mana Baby, in kin samu kin fito ki faɗa min." Mubeena bata ce komai ba ta kashe wayar ta fita taga Manal bata nan sai Mama kawai itama bacci ya ɗauke ta kasancewar lokacin aka idar da sallar azahar. Ganin ta samu dama sai ta saka mayafi ta fita daga gidan da sauri. Sai bayan ta bar unguwa ma sannan ta yi masa waya ta faɗi a inda take, ba jimawa ya turo da driver ya ɗauke ta aka wuce da ita gida yake dan ba gidan da suka saba haɗuwa bane wani ne daban da ya canja. BDƘB2P009 Mubeena lokacin da ta shiga gidan a zaune ta same shi ganin ta sai ya murmusa yace, "barka da zuwa Baby." Ƙarasowa tayi ta zauna nesa dashi tace, "bana son zuwa gidan nan, in dai kana sona kayi abinda nace kawai shine mafita a gare mu, yawan ganina da ake a nan yanzu sai ayi min fassara ta daban." Murmushi yayi shi wallahi dariya ma take bashi, ko faɗa mata akayi ya shirya aure oho mata. Kallon ta yayi yace, "har yaushe muka saba da zaki dinga batun aure? Ko Abuja baki raka ni ba fa har yanzu." Mubeena ta kalle shi tace, "Sai na raka ka Abuja zaka aure ni?." Ya girgiza kai alamun a'a yace, "at least yana da kyau mu fahimci juna sosai kafin maganar aure tazo tsakani." "Ba wani fahimtar juna, ƙanwata daga haɗuwa da saurayin ta kwanaki kaɗan har an saka ranar auren su. Ni na gaji in kana sona kazo gidan mu wajan Baba." Girgiza kai yake ya lura yarinyar nan da gaske take sosai akan maganar auren sai yayi murmushi yace, "to yanzu haka za'a yi auren ba wani lokaci?." Kallon sa tayi tace, "me ka ke nufi?." Ya taso yazo inda take yace, "Haba baby ke fa babbar yarinya ce ya kamata tun wuri ki fahimci inda na dosa, amma sai wani kaucewa ki ke kamar ba ni da ke mu ka ɗan taɓa soyayya ba kwanaki. So nake soyayyar ta wuce ta ranar mu san junan mu sai auren ya biyo baya." Mubeena tace, "ban gane ba." "So nake kawai ki amince dani, ni kuma zan miki duk abinda kike so, har auren mu sai ayi a sati biyu mai zuwa." Mubeena tace, "wacce amincewa?" Ta faɗa dan ƙirjin ta ya fara bugawa sosai, tsoro ya fara shigar ta haka kawai ba kamar lokacin baya da take rasa tsoron ba. Kallon ta ya sake yi ya riƙe hannun ta yace, "ki bani aron yau kawai, ni kuma na tabbatar miki zan nuna miki so da qauna irin wacce ki ka jima kina neman ta, zan nuna miki soyayyar da film ma ba'a yin irin ta, zan gusar da hankalin ki da soyayya, sannan zan baki duk abinda ki ke so." Mubeena ta zare hannun ta daga riƙon da yayi mata tace, "Daman abinda ka ke so kenan ba aurena zaka yiba?." "Haba Baby waye yake ta aure yanzu? Wannan rayuwar itace jin daɗi meye baza ki samu ba?, zaki samu farin ciki fiye da wanda masu aure suke samu." Mubeena ta tashi tsaye tana kallon sa cikin tsoro da fargaba tace, "to shikenan baza ka samu abinda ka ke so ba, ni na tafi." Shima tashi yayi yace, "ki bar wasa mana, hakan ba ajin ki bane." Ta kalle shi tace, "sai an jima." Kafin ta motsa ya riƙo hannun ta yace, "babu inda zaki je, tunda kika zo nan yau sai na karɓi abinda na jima ina so. Ko ta lallami ko ta ƙarfi." Ganin da gaske yake fa sai ta fara ƙoƙarin ƙwace kanta amma ta kasa dan ya riƙe hannun ta duka biyun yana ƙoƙarin haɗa jikin sa da nata. Cizon hannun sa tayi ya sake ta da sauri tare da ja baya yana yarfe hannun, da hanzari ta buɗe falon ta fita a guje. Cikin takaici ya yunƙura zai bita wayar sa ta fara ƙara ganin mai kiran bazai iya sharewa ba dole ya tsaya ya ɗauka wayar ran sa a ɓace.      Mubeena a haka ta fita tana gudu sai da ta ɗan yi nisa ta tsaya ta yau napep kai tsaye gidan su Bily ta wuce har lokacin ƙirjin ta bugawa yake tsoron yaƙi barin ta gani take kamar zai biyo ta. Babu kowa a gidan sai Bily kawai a zaune a akan kujera tana kallo ganin yadda Mubeena ta shigo ya firgita ta ta bita da kallo tace, "ke wani abun ne ya biyo ki?." Mubeena bata ce komai ba ta ƙarasa wajan fridge ta sha ruwa ta dawo ta zauna ta dafe kanta bata ce komai ba. Ganin hakan sai Bily ta share ta cigaba da kallon ta sai da taji alamun kukan da Mubeena take yi sai ta kalle ta tace, "lafiya?." Mubeena cikin muryar kuka da fargaba haɗi da nadama tace, "da gaskiyar ki Bily, Alhajin nan so yake ya lalata min rayuwa ba aurena zai yi." Bily ta taɓe baki tace, "ba gani ki ke baƙin ciki nake miki ba Mubeena?. Meye abin baƙin ciki a wannan tsohon banzan? Kai da ka gan shi ka san cikakken ɗan bariki ne amma kika toshe kunne ki kuɗi ya rufe miki ido. Ai duk magidancin ko saurayin da ba zai nemi ganin iyaye ki ba da aure yake son ki ba, duk wanda zai dinga miki zancen yaushe zaku haɗu ko yaushe zaki zo inda yake wallahi ba na gari bane, maganar aure ba a gaban sa take ba iskanci ya bawa mahimmaci. Amma ki ka ce ke inaa ai auren ki zai yi." Mubeena tana kuka tace, "Ya nuna min alamun hakan a baya ban kawo komai ba, amma yau da ya so keta min haddi sai tsoro ya shiga raina, wallahi ban san lokacin da na gudo ba." "Baki daina zuwa gidan sa ba kenan ko Mubeena? Ke ko tsoro bakya ji a dinga ganin ki kina shiga gidan nan sa kina fitowa?." Mubeena ta share hawaye tace, "Ina son sa Bily, ina son sa shiyasa duk abinda yace nayi nake yi. Ke kin san daman bani da burin kula samari sai irin su shiyasa haka." "Kuɗin sa ki ke so ba shi ba, shiyasa shima da ya lura da hakan yake baki kuɗi ya siya miki abubuwa mai tsada saboda ya saka ki saki jiki dashi. Wani irin son kuɗi ki ka ɗorawa kan ki wanda yafi ƙarfin shekarun ki." "Allah ya sani ina son rayuwar kuɗi Bily." "Sai ki yi addu'a Allah ya baki miji mai kuɗin halak kuma na gari ba ki fara zuwa gidajen masu kuɗi ba." Mubeena tayi shiru kafin tace, "Yau Allah ya kare ni da yanzu na rasa mutuncina. Nayi dana sanin fara kula shi, nayi dana sanin abinda na aikata tare dashi. Allah ka yafe min." Bily tace, "me kika aikata?." Ta kalli Bily tace, "bazan iya ɓoye miki ba Bily,Mun yi romancing kwanaki. Bily hannun sa har cikin rigata." "Baki da hankali wallahi, gabaɗaya kan ki dusa ce a ciki bakya ganewa. Idanun ki sun rufe saboda kuɗi har bakya gane daidai da ba daidai ba. Hakan ta faru tsakanin ku amma baki daina kula shi ba?." Kuka take yi Bily tayi tsaki cikin fusata tace, "tun daga charting ɗin da ku ke yi tun farkon haɗuwar ku na faɗa miki ba na gari bane ba, samari da magidantan yanzu rabi da kwata sun lalace, da namiji yazo zai fara miki hirar banza ko ya fara ƙoƙarin riƙe hannun ki, in yaga kin bada fuska a riƙe hannu gobe rungume ki zai yi, in yaga ya rungume ki baki ɗauki mataki ba jibi zai shiga inda mijin ki kawai Allah ya halattawa shiga. In kuma ya fahimci irin ku ne lashe money da kuɗi za'a yi amfani a lalata ki, mazan yanzu kaɗan ne na gari. Na karanta miki haka amma baki gane ba sai kike ganin baƙin ciki nake miki, ke yanzu hannun ki ya riƙe yau baki ɗauki mataki ba, ya riƙe gobe baki hana ba, jibi ya rungume ki baki nuna bakya so ba, gata zai miki kiss ki nuna hakan daidai ne ba dole a kai ga shafe-shafe ba?. Ya shafa ki kin shafa shi hakan bai saka kin daina zuwa inda yake ba  gani kike soyayaya ce, sai ma ɗaukar ƙafa da kika sake yi yau kika je. Anya kina da hankali?." Mubeena tace, "nayi nadama Bily." "Ta banza ce, a lokacin da ake faɗa miki gaskiya toshe kunne ki ke yi kike ganin kamar Mama da Baba da Manal basa son ki ne ko kuma sune gidadawa basu waye ba?. Ita Manal haka tayi?. Ita da ta killace kan ta take kula samari na gari ba gashi yanzu maganar aure ta za'a yi ba? Ke ko da ita baza ki yi ko yi ba?. Ko da yake dole Manal ta fi ki samun nasara a rayuwa saboda tarbiyya da biyayya ga mahaifiya." Mubeena ta goge idon ta tace, "wallahi na daina." "Ƙarya ki ke, ko yanzu ya baki kuɗi zaki iya kwnaciya yayi abinda yake so dake. Tunda har aka je ga romancing wallahi zaki iya kwanciya dashi Mubeena, ke kika bada fuska da tun farko kin nuna masa ke mai tarbiyya ce da yanzu yaje ya samu Baba da maganar aure, amma sai kika nuna ke ta banza ce ta ya zai aure ki?. Bazan iya ƙawance dake ba Mubeena, ki kama gaban ki kawai tunda hakan kika zaɓa." Mubeena tace, "na daina wallahi na daina, haka kawai Allah ya saka min tsoran sa a zuciyata, gabaɗaya naji kuɗin basa raina a lokacin,  mutuncina yafi min komai. Ki amince dani wallahi nayi dana sani hakan bazai sake faruwa ba." Bily tace, "har fa hannun sa kika ce a rigar ki, an yi kiss anyi komai abinda ya rage a cika aiki. Amma baki kama kan ki ba kika sake zuwa inda yake, ni tantama nake anya ma komai bai faru ba?." Mubeena tace, "babu abinda ya faru. Inda ya faru ke kin san bazan ɓoye miki ba. Allah ne ya kuɓtar dani kuma nayi nadama zan nemi yafiyar Allah." Bily tace, "in har zuciyar ki ne da kin ji daɗi, kuma addu'ar Mama ce ta saka kika kuɓta wallahi, itace take kwana tana faɗawa Allah damuwar ta a kan ki tunda kullum cikin ɓata mata rai ki ke." Mubeena tace, "Shima na daina daga yau in sha Allah, har wayar da ya bani na cillar da ita a hanya zan yi duk abinda Mama take so. Zan zamarwa Manal Yaya irin wacce take so, in sha Allah zan samu kaɗan daga cikin ladan da Manal ta samu. Zuciyata har yanzu bugawa take saboda tsoro." Bily tace, "da kin kyautawa kan ki duniya da lahira. Baki da kamar Mama da Manal wallahi, na sha yin gulmar ki a raina in naga yadda ki ke girmama Mummy kuma bakya girmama Mama, sai nace wannan yarinyar bata sharar masallaci sai ta coci." Mubeena ta sauke ajiyar zuciya tace, "nayi hankali wallahi yanzu, har zuciyata zan gyara kuskurena, zan bi Mama nayi duk abinda take so. Allah na gode maka da ka bar min Mamana a raye, Allah na gode maka da bata rasu da baƙin cikina ba. ki raka ni na bawa Mama da Baba haƙuri." Bily ta sauke ajiyar zuciya tace, "Zan je ai tunda kin gyara." "Amma Bily ina son sa wallahi." Banzar hararar tayi mata tace, "wannan son dashi zai yi amfani ya same ki wallahi a banza ba tare da sadaki da shaidu ba, in dai baki watsar dashi kin manta dashi ba kina tare da wahala. Kuma shi wallahi bazai aure ki ba saboda ya san ke ba ta gari bace ta banza ce, ya riga ya gama latsa jikin ki tun a waje ya za'a yi ya aure ki?. Malama in zaki dage da addu'a ki dage, in baza ki yi ba ke kika sani." Mubeena tace, "zan yi, ki taya ni addu'a." Bily ta amsa ta cigaba da kallon ta Mubeena tayi shiru tana tunani don da gaske tana son sa wallahi. Bily ta raka Mubeena har gida ta bawa Mama haƙuri harda kukan ta mai nuni da tsantsar nadama a bayyane. Mama tayi farin ciki duk da bata tabbatar da shiryuwar ba amma taji daɗi sosai. Manal ma haka ta dinga murmushi itama tana yi mata addu'a. Bayan tafiyar Bily a lokacin yamma tayi Mama ta kalli Manal tace, "ke ba kin ce yau Dr zai zo ba?." Manal tace, "eh Mama." "Amma ban ga kina ɗan haɗa masa wani abun ba? Ke kullum haka yake zuwa ya koma bakya bashi komai?. Ki duba har iphone 14 ya aiko miki da ita fa" Mubeena da ta faɗa tana daga gefe a ɗarare kamar ba ƴar gidan ba. Mama ta kalle ta tayi murmushin jin daɗi tace, "gaskiya ya kamata Manal ki yi wani abun." Jin haka sai Manal ta turo baki tace, "To ni Yaya me zan yi masa?." Mubeena tace, "ke da ki ke hajiyar girki? Ki yi tunani." Tayi murmushi cikin jin daɗin sakewar Mubeena ɗin tace, "ni ban san me zan yi ba." Mubeena tace, "to ki yi cake mana ko?, naga ana son sa sosai." Manal ta kalli Mubeena tace, "in nayi cake ni bazan ci ba Mama ma haka."  Mama tace, "dan tani kin san bai dame ni ba balle ga lalura, ki yi kawai zai ji daɗi tunda yana kyautata miki. Wayar da ya baki fa Haron yace ta kusa miliyan. Kuma in yazo baya tafiya sai ya baki wani abun." Manal tace, "To Mama zan yi." Mubeena tayi murmushi ji take ina ma itace Manal ɗin,zuciyar ta sam babu daɗi in ta tuna abinda ya faru sai taji hawaye ya cika mata ido. Tashi tayi ta shiga ɗaki Mama ta kalli Manal tace, "Me ya kawo wannan canjin na ta?." Manal tace, "Addu'ar ki Mama, don Allah kar ki zaton komai wallahi addu'ar ki Allah ya amsa. Shiyasa ake so iyaye su dimga yiwa yaran su addu'a ba aibata su ba, yanzu gashi da ki ke yi mata lokaci ɗaya canji yazo." Mama ta girgiza kai bata ce komai ba Manal ta tashi don ta fara abinda aka ce. Nan da nan ta haɗa cake mai yawa Allah ya taimake  ta aka kawo wuta ta shiga gidan su Surayya suna gasawa a oven suna hira. Bayan sallar magriba ta dawo gida tana numawa Mama duk da duhu yayi ganin Mama ya ragu amma khamshin cake ɗin ya burge ta. Bata ɗauka ba ta hana ta ci saboda ciwon ta, Mubeena ce take ci ta bar mata a kusa da ita ta shiga wanka. Bayan ta fito sai da tayi sallar i'sha ta kai cake ɗin falon baba ta dawo sannan ta shirya cikin doguwar riga ta atampa ɗinkin mai aljihu ta ɗaura ɗankwali Mubeena ta kalle ta tace, "kin yi kyau. Kawai bakya ƙhamshi sosai." Manal tace, "ai baya son turare, yanzu in naje ina khamshi sai ciwon kai." Mubeena bata ce komai ba ta girgiza kai kawai Manal tace, "Don Allah Yaya in ya shigo gaida Mama ki zo ku gaisa, bai taɓa ganin ki ba yana tambaya ta ke." Mubeena tayi murmushi tace, "Wannan ai dole ne. Amma ki zuba cake ɗin ya kaiwa Maman su hakan zai ƙara miki girma a idon sa." Manal tace, "haka Maman Surayya tace, har na zuba nata a foil paper ma zan bashi." Mubeena bata ce komai Manal ta yi murmushi a lokacin Baba ya shigo yana cewa, "Manal ke kullum sai anzo an faɗa miki ana jiran ki?." Jin haka sai ta saka mayafi tayi kyau sosai duk da ko hoda bata saka ba amma tayi kyau, a haka ta fito zuwa falon. Yana zaune kamar ko yaushe yana aikin danna wayar sa ta shiga da sallama ya amsa tare da ɗagowa yana kallon ta. Sakin baki yayi yana sake ƙare mata kallo domin bai taɓa  ganin ta da atamfa ba sai hijjab da kuma abaya. Tayi masa kyau sosai don shi in kina so ki burge shi kawai ki yi kwalliyar atamfa hakan ya saka yake kallon ta har ta zauna suka haɗa ido tace, "ka daina kallona." Janye idon sa yayi kamar ba shi ba tace, "ina wuni." wani irin kallo yake mata na ƙasan idanu mai ciki da ma'anoni kala kala kafin yace, "kin wuni lafiya?." Wani iri take ji in yana mata wannan kallon hakan ya saka ta nutsu sosai tace, "lafiya lau. Ya aiki?." "Alhamdulillah." Juyawa bayan ta tayi ta ɗauko castrool mai kyau wanda aka siyo a cikin kayan auren ta, Surayya  ce ta ɓoye a hijjabi aka zuba cake ko Maman su bata gani ba. Ajjiyewa tayi da ruwa da lemo akan ƙaramin tray tace, "Bismillah ga cake." Kallon cake ɗin yayi dan casrool ɗin transferring ne ana kallo abinda yake ciki, cake ɗin ya burge shi ya kalle ta yace, "da kan ki ki ka yi?." Ta ɗaga kai alamun eh yace, "Allah ya sa baki ci ba." Ta girgiza kai tace, "ban ci ba." "Allah yasa hakan. Na gode." Muryar Surayya taji tana kiran Milky tun  daga tsakar gida jin shiru bata amsa hakan ya bata tabbacin an faɗa mata tana ina. Kallon ta yayi yace, "Meyasa ake ce miki milky?." Manal tayi farrr da ido tace, "cewa suke haskena ne kamar madara." "A ina kika samo sunan?." "Secondary school, duk wanda kaji yace milky beauty to tare muka yi makaranta. Yayi ƙasa da idanun sa yana kallon ta yace, "da gaske milky ɗin ce?." Sai ta kalle shi suka haɗa ido tayi murmushi tace, "nima ban sani ha." Yayi dariya kaɗan yace, "baki taɓa bani labarin saurayin ki na farko ba." "Kaima Baka bani labarin buduwar ka ta farko ba." "Ai ni na fara tambaya." "Sai ka ci girma ka fara faɗa min." Kawar da maganar yayi yace, "me kike shiryawa?." Manal tace, "akan me?." "Auren ki." Kawar da kai tayi tana murmushi tace, "babu komai." "Ki faɗi gaskiya" ya faɗa yana buɗe kwanon ya ɗauki paper cup cake ɗin guda ɗaya ya ciri kaɗan ya saka a bakin sa  dan kar tace bai ci ba, ya kalle ta yace, "Allah yasa ba a wani  bakery ɗin kika siyo ba." Bata ce komai ba sai yace, "Yayi daɗi sosai ƴan mata." Dariya ya bata tayi dariya amma shi bai yi ba yace, "Seriously ya kamata ki fara shirin abinda ki Ke ganin zai yu." Manal tace, "to in sha Allah." Wayar ta ce take ƙara sai ta kashe ya kalle ta yace, "waye yake miki waya?." Ta girgiza kai tace, "ba waya ake ba, film ne." "Kina kallon film?." Ta girgiza kai alamun eh yace, "Kdrama?" Ya tambaya dan a bakin ƙanen sa yake ji. Ta girgiza kai tace, "ina ganin kdrama amma ba sosai ba, nafi ganin American series." Ya ɗan wara ido yace, "Meyasa sai America? Naga mata kun fi son kdrama." "Baya burge ni sosai." "Meyasa America yake burge ki?." "Saboda ina gyara pronouncing sosai, su English suke yi ina sanin yadda zan faɗi kalma sosai." Ya girgiza kai yace, "hakan yayi kyau. Wanne film ki ke gani yanzu?." "The virgin and the billionaire." Bebi ya kalle ta jin sunan da ta faɗa yace, "The Virgin and the billionaire" ya maimaita sunan yana kallon ta sannan yace, "waye virgin ɗin waye billionaire ɗin?."  Shiru tayi bata amsa ba sai a sannan fassarar sunan film ɗin yazo ranta sai tayi shiru yace, "ina jin ki." Manal ta ɗauko wani abun a baya ta tayi cikin foil paper tace, "Ga cake ɗin Mummy a kai mata." Murmushi yayi yace, "Mummy ta gode, kamar kin san mummy na son cake especially wannan chocolate ɗin." Tayi murmushi bata ce komai ba ya lura ta kawar da maganar film ɗin sai bai sake dawo da maganar ba, zai yi magana aka kira wayar sa ya ɗauka yana magana kafin ya kashe ta kalle shi tace, "Emergency ne ko?." Kai ya ɗaga yace, "daga nan ma can zan yi." Ta taɓe baki tace, "kuma sai yaushe zaka koma gida?." Ya kalli agogon hannun sa kafin yace, "maybe sai gobe." "Tabɗijam! shiyasa bana son aikin asibiti tun farko." Ya kalle ta ta cikin glasses ɗin sa yace, "sai Allah ya baki likita." Tayi murmushi aka sake masa waya ganin daga asibitin ne yayi tsaki kaɗan ya kashe ƙarar wayar tace, "wai kuma har da daddare kana zuwa? Ko da yake hakan ya faru akan Mamana." Bai ce komai ba yace, "zan je na gaishe da Mama daga nan zan wuce. Amma nima wannan cake ɗin ki saka shi a foil paper nan kamar na Mummy zan tafi dashi, in naje aiki na huta." Ta amsa da to ya kalle ta yace, "Manal!." Ta kalle shi suka haɗa ido sai ya lumshe ido ya buɗe a kan fuskar ta yace, "ina son ki, ina son ki son da ban son adadin shi ba. Ina kishin ki, bana so naga kowa a kusa dake. Pls Manal alaƙar ku da Huzaifa bana so, na faɗa masa kema na faɗa miki bana so, ki san irin zumuncin da zaku yi." Manal jikin ta yayi sanyi saboda yadda yake furta kalmar yana son ta ya kashe mata jiki sosai. Ba kasafai yake faɗar kalmar ba sai yaga dama, shiyasa ko a rubuce in ya tura mata tana matuƙar jin daɗi. tace, "to ai ba......" katse ta yayi yace, "shiiii! Manal bana son musu, just say to." Manal ta girgiza kai tace, "to in sha Allah." Kai ya ɗaga ya tashi tsaye yace, "kai ni wajan Mama." Ta tashi  tsaye ya kalle ta yace, "kayan nan sun miki kyau." Kunya ya bata ta kulle fuska ya kalli hannun ta wanda burge shi sosai kuma yake burin riƙe shi, daga gani zai yi laushi amma baya son hakan ya faru sai ta zama mallakin sa. Murmushi yayi kaɗa yace, "jira na ake fa, kar ki saka na makara a rasa rai." Gaba ta wuce ya bi bayan ta suka shiga wajan Mama daman ta san da zuwan sa ta saka hijjabi suka shiga ciki. Da girmamawa suka gaisa fuskar ta a sake kamar ba sirikin ta ba,  yace, "ya ƙarfin jikin?." "Jiki Alhamdulillah, tunda na fara shan maganin nan shikenan." "Allah ya ƙara lafiya" ta amsa da amin. Manal a lokacin ta dawo falon sai ga Mubeena ta fito tace, "yau dai Allah ya yi zan ga Dr kuma mijin ƙanwata." Ɗago ido yayi suka haɗa idanu da Mubeena da take kallon sa tana murmushi. BDƘB2P10 Kallon sa take kamar yadda yake kallon ta, tana so ta tuna inda ta san shi amma ta manta shima a ɓangaren sa kallon sani yake mata, ɗauke ido ya yi ya saki fuska kaɗan suka gaisa ya musu sallama ya fita. A tsakar gidan ya tarar da Manal a tsaye ta bashi leda mai kyau da ta zuba masa cake ɗin ya karɓa ya tafi. Asibitin ya wuce sai dai bai jima sosai ba ya nufi gida ya faka motar ya shiga ciki wajan Mama ya same ta a zaune suna kallon tv har da Rumana ya zauna yace, “Mummy barka da dare.” Ta kalle shi tace, “barka dai.” Ya kalli Yayar sa Farida yace, “har yanzu kina nan?.” “Ina nan, muna ta tsara maganar bikin ka. Ni ban ji kace min komai ba ma fa har yanzu.” Yayi ƙaramin tsaki yace, “abubuwa ne sun min yawa sosai, Amma zan zo gidan sai mu tattauna.” Tace, “ya dai kamata, lokaci yana tafiya ko lefe ba’a fara haɗawa ba, gashi mu sarakan zumuɗi har mu yi order ɗin fabrics da zamu saka ranar dinner.” Ya kalle ta cikin rainin wayo yace, “au har dinner za a yi kenan?.” Farida ta harare shi tace, “ban sani ba. Ai wallahi baka isa ka saka ayi biki lami babu shagali ba, gwara ka sani tun yanzu dinner dai sai mun yi.” Yayi murmushi kawai bai ce komai ba ya miƙawa Mama cake ɗin yace, “Mummy ga cake.” Buɗewa tayi fuskar ta babu ya babu fallasa don bata so a dinga a maganar bikin sa a gaban Rumana, buɗewa tayi ta ɗauki ɗaya ta ci tana kallon sa tace, “amma ya yi daɗi, a ina ka siyo sarkin ciye-ciye?.” Yaya Farida ta ɗauka taci itama dukkan su suka ɗauka suna ci sannan yace, “ba siyowa nayi ba, bani aka yi na kawo miki.” Farida tayi dariya tace, “Manal ce ta bayar kenan?, lallai! Kaga soyayya. Ni tunda naga ka sha wankan shadda ɗazu na san ba asibiti aka tafi ba wajan ta zaka je. Kai amma ta kyauta wallahi, gashi da daɗi.” Murmushi yayi kaɗan ya kalli Mama ita kuma Mama ta kalli Rumana da take cin cake ɗin kamar magani ta kalle shi tace, “An gode.” Shiru wajan yayi Mama tace, “meye matakin kararun ta?.” Ya kalli Mama yana mamakin tambayar kafin yace, “ssce.” “Kana nufin ko diploma ɗin nan na zamani ba ta yi ba?.” Ya girgiza kai yace, “bata yi ba Mummy, amma zata yi.” Mama tayi shiru ta kalli Rumana Sai taga ta tashi tsam ta shiga ɗaki ta turo ƙofa. Mama ta kalle shi tace, “ban san me ka gano a jikin yarinyar nan wanda Rumana bata dashi ba, komai ta haɗa amma ka je ka nacewa wata a waje.” Bebi yace, “Haka Allah ya yi Mummy.” Bata ce komai ba Farida tace, “ni ko hoton ta ma ba’a nuna min ba” ta faɗa da kawar da wancan zancen. Bai ce komai ba ya tashi ya fita ya rasa meyasa Mama ta kasa fahimtar sa akan Rumana, idon ta ya rufe bata ganin kowa sai ita ta manta da cewa itace ta fara gudun sa kafin shi ya guje ta. Bebi yana fita Farida ta kalli Mama tace, “Don Allah Mama ki daina nuna masa bakya son wacce zai auro, in kina masa hakan zai dinga jin babu daɗi saboda ke mahaifiyar sa, zai ga kamar bakya son wacce zai aura ne.” Mama ta kalle ta tace, “ni ba son tane bana yi, yarinyar da ko sanin ta ban yi ba akan me zan ce bana son ta?. Kawai in na tuna yaƙi auren Rumana ne nake jin haushi.” Farida tace, “haka Allah ya tsara ba shine ya ƙaddara faruwar hakan ba. Don Allah ki daina nuna masa kamar bakya son auren sa da Manal, yana son ta zai dinga jin babu daɗi a kai.” Mama ta sauke numfashi bata ce komai ba. A ɓangaren Maryam tun bayan abinda ya faru tsakanin ta da Kamal a karo na biyu bai sake mata waya ba, hankalin ta ya kwanta ganin an kwana biyu bai neme ta ba ta nutsu duk da a tsorace ga zunubin da ta aikata. Lubna ma tun da Mujahid yayi tafiya a ranar da abinda suka tsara zai faru tafiyar gaggawa ta same shi, basu samu abinda suka tsara ya faru ba dole ya tafi tun lokacin bai zo ba, Sai dai suna waya yana faɗa mata yadda yayi kewar ta da kuma yadda abin zai kasance. ***** Waya yake hankali a tashe yana cewa, “yarinya guduwa tayi fa, taya hankalina zai kwanta bayan ta riga ta san fuska ta da komai nawa kuma ta gudu? A kano fa abin ta faru ba a wani garin ba. Sai yanzu nake dana sani wallahi, yanzu nake dana sanin kula ta, dan ni fuskar ta kama take min da wacce na taɓa sani a baya, Sai yanzu kamanin ta suke zuwa kaina.” Daga can ɓangaren akace, “ka kwantar da hankalin ka, wannan ba wani abun bane yarinya ce sosai ba wani abun zata iya yi maka ba. Bata waye sosai ba balle ace turo ta akayi dan ayi amfani da abinda ka yi mata. Ko kuma tayi maka video ko ta yi recording muryar ka, kar ka damu wannan ba komai bane.” “Baza ka gane ba, ina jin yarinya nan har cikin raina ba wai iya abinda nake so na rasa ba. Ita kanta bana so na rasa ta.” “To kaje gidan na su mana ka nemi auren kawai, ka aure ta ka ajjiye ta a abuja wani abun ne? Har ka aure ta matan ka ma basu sani ba.” Kai yake girgizawa yace, “ba wannan nake ji ba, Akwai wani abun da ni ban gane ma sa ba. Tabbas yarinyar nan akwai wani abun a tare da ita, tsoro ya cika min zuciya bana so abinda nake tunani ya tabbata.” Yayi dariya wa can yace, “wai ƴar hijira?hhhhhh kar ka wani damu da wannan domin ina tabbatar maka da ƴar hijira bata raye.” “Ta ya ka sani?.” “Kai ka san bana faɗa maka abinda ba haka ba, ka yarda bata nan ta jimawa da barin duniya. To kai meye haɗin ta da wancan abun da ya wuce? Kawai kana son Mubeena a san abinda za’a yi maka amma ka daina zancen nan.” Ya sauke numfashi yace, “ko ta wanne hali ina so a kawo min ita nan, in ba haka ba akwai matsala sosai, sunana zai iya ɓaci har kunnen iyalaina. Saboda yarinyar ta sanni sunana ne kawai bata sani, hankalina ya kasa kwanciya bana so na bar baya da ƙura, bana so wani abun ya faru ta dalilin ta” yana faɗa ya yanke wayar yayi shiru yana tunanin wacce ya sani a baya mai irin fuskar Mubeena amma baya so hakan ya tabbata. ********* “Na gaji Kamal, na gaji, yau kace nazo nan na same ka gobe kace na je can na same ka ya ka ke so nayi?. Na gaji da saɓon Allah da ka ke saka ni saboda hotuna na a wajan ka, na gaji wallahi, bazan sake aikata saɓon Allah ba” ta faɗa tana kallon sa tana kuka sosai shima yana kallon ta. Ya taɓe baki yace, “Maryam ban miki dole ba ai, ga hanya nan maza ki tafi.” Maryam tana shashsheƙa tace, “Meyasa ka ke min haka? Meyasa!.” “Saboda ina son ki ne na faɗa miki, amma kin kasa gane hakan.” “Wannan ba soyayya bace cutarwa ce, na gaji bazan iya jure wannan abubuwan ba, na gaji da saka ni zina da kake yi.” Yayi murmushi yace, “kin amince yaran ki da duniya su ga hoton tsiraicin ki?. In da ma za’a san daga wajena ne da sauƙi, to zan canja number ne na ƙirƙiri chatting na ƙarya ta yadda zan nuna samarin banza ki ke nunawa, zan miki abinda baki tunani ba.” Ta goge ido tace, “in ma ni zaka ɗauka ka kai musu tsirara sai dai kayi amma wallahi bazan saka ni aikata zina ba, na gaji wallahi ko kunya baka ji, da girman ka da komai ka ke tozarta ni.” “Maryam ga hanya nan ai zaki iya tafiya.” Maryam tayi hanyar fita tace, “zan fita yanzu, ka yi duk abinda zaka yi. Ba iya posting ba ka yi banner ka manna a ko wanne titi sai me?.” Murmushi yayi ta fita a fusace ta shiga mota tana kuka, a lokacin saƙo ya shigo wayar ta buɗe abinda ta gani ya saka ta kifa kaii akan sitiyarin motar numfashi ta na neman ɗaukewa a lokacin. “Maza jeki Maryam, ina da irin su sun fi guda hamsin, in kullum zan yi posting guda ɗaya a duniya zan iya ɗaukar wata biyu ina yi. In kina ganin wannan rashin kunya ne zai cece ki bismillah mu zuba nida ke, waye zai ji kunya? Waye baban sa yake ɗan siyasa?. Maza jeki sai kin dawo” yana faɗa ya wuce ya barta ta kada koda motsi saka sai kuka. Bata san adadin lokacin da ta kwashe a haka ba ta san dai tafi awa ɗaya a haka, daƙyar ta iya kunna motar ta nufi gida cikin rashin sanin abin yi. Bayan Kwana biyu. Biki yana ta matsowa ana ta shiri ba kamar gidan su Manal ana ta shirye- shirye, gidan su Bebi ma ana yi musmaman daga wajan Mama saboda bikin Mimi. Shima daga wajan sa ana ta shiri dan har an kammala haɗa lefe ginin gidan sa yana tafiya yadda ake so. Da yammacin ranar litinin yana tafiya a kan titi shi kaɗai yana so ya kaiwa Manal maganin ta, kamar an ce ya kalli gefen sa ya ga Manal a tsaye tana neman abin hawa, yayi ƙaramin tsaki shi ko dan wannan yawan fitar ta ta yake so ayi auren nan a wuce wajan ya dinga kai ta ko ina take so, baya so ya ganta a kan titi nan haushi yake ji amma ba shi da bakin magana tunda ya san ba mota ce da ita ba. Faka motar yayi ya sauke glass yana kallon ta ganin shine bata da mafitar da ya wuce ta shiga ya ja motar ya kalle yace, “kina son tsayawa a akan titi, baki san kallon ki ake ba ne wai?.” Manal ta karyar da murya tace, “to zan hana mutane kallona ne?.” “Hakan baya damun ki kenan? Yayi kyau” ya faɗa yana cigaba da tafiya alamun yaji haushi. Manal ganin haka sai tace, “baka hana mutane magana ai.” Yayi shiru bai ce komai ba yana cigaba da tafiya har bakin layin su bai magana ba, sai da ya tsaya sannan yace, “bana so na ganki a kan titi a tsaye Allah ya sani, Allah kaɗai yasan adadin mazan da suke kallon ki ko suke son yi miki magana amma kin kasa ganewa.” “Mama ce fa ta aike ni.” “Ki kira ni mana nazo na kai ki, Lallai sai kin hau napep?. Kar ki manta aure na dake ya kusa, meyasa kike so a gama kalle min ke tun a bakin titi?.” Shiru tayi bata ce komai ba, ya sake yin tsaki yace, “inda kin san abinda nake ji da baki aikata hakan ba Manal, amma na ga ke hakan daɗi yake miki ma. Ai kin kyauta.” Manal tace, “kayi haƙuri” ta faɗa dan ta katse mitar sa ta tsiya. Bebi yace, “ya zan miki dole nayi haƙurin tunda a riga an cuce ni an gama kalle ni .” Bata ce komai ba dan marar ta ɗaurewa take yi sosai dauriya take yi tana masa magana ya kalle ta yace, “me ki ke shiryawa?.” Manal tace, “babu komai.” “Kamar bakya murna da auren nan.” Sai tayi dariya kaɗan tace, “haka ka gani?.” “To ko yaushe in na ce me kike shiryawa sai ki ce babu komai, kamar bakya so. Ina ganin yadda Mimi take siyan wannan ta siyi wancan, tana ta shiri amma ke ko yashe babu komai ki ke cewa. Ko bakya sona ne?.” Ta ɗago ta kalle shi suka haɗa ido ta girgiza kai tace, “ba haka bane.” Ya gyara zama yana kallon ta yace, “to yanee?.” Sai tayi murmushi ita kunya yake bata in yan zancen auren nan, ta fi so su yi hirar duniya ko wata hirrar amma ba ta auren su ba. Shima kuma ya lura da hakan yana son kunyar ta ne sosai shiyasa yake mata maganar auren don rashin kunya yana daga cikin abinda ya saka Rumana ta fita a ransa. “Kina ji?.” Ta ɗaga kai alamun eh yace, “magana zamu yi ta fahimta, ki fahimci ni kar ki min wata fasara daban.” Manal ta kalle shi jin abinda yace ta nutsu dan taji me zai ce, yace, “kar Mama ta wahalar da kuɗin ta wajan yin wannan turaren wutar da ake yiwa amare, naga Mummy sai kashe kuɗi take ana yiwa Mimi, ayi miki kaɗan ba da yawa ba ni ba son shi nake ba, kuma dai daman dan ni za’a yi to bana so na hutar da kowa. In aka yi miki gyaran jiki ake ce masa ko? Wanda ake ƙhamshi na wuce masali, in aka yi miki irin sa sai na saka ki a ruwa har sai ya bar jikin ki.” Manal tayi dariya kaɗan tace, “zan saka ka so ne.” Murmushi yayi shima ya sake cewa, “magana ta gaba.” Ta kalle shi yace, “kar a wahalar dake ta hanyar baki magani barkatai Manal, ace ki sha wannan ki sha wancan saboda wani abu. please and please avoid it Manal, shima ai dan nu ake yi ko? To shima bana so na hutar dake.” Ɗago kai tayi suka haɗa ido ya wara idanu sa a cikin nata yace, “eh, kin ji abinda nace ai.” Kai ta sunkuyar bata ce komai ba yace, “ina ganin ai abinda ake yi a na mu gidan shiyasa nace zan faɗa miki dan ni wallahi bana so. Shiyasa daman nace zan faɗa miki, in ba baza ki iya cewa bakya so ba in an baki kar ki sha, in maganin infection ne irin wanda ake bawa amarya kar ki manta ni likita ne, da kaina zan baki wannan ba sai kowa ya wahala ba.” Manal kunya ya bata sosai dan magana mai nauyi irin wannan bata taɓa haɗa su ba sai yanzu hakan ya saka ta kasa magana ga marar ta da take ƙullewa sosai har yafi na ɗazu. Ganin shirun nata yayi yawa sai ya kalle ta sosai kafin ya ɗauki wayar sa duba date yaga yayi daidai da lokacin period ɗin ta ya ajjiye ya kalle ta yace, “ciwon ne?.” Kamar jira take ya tambaya sai hawaye sharrr suka zubo daga idon ta dan ciwon ya dame ta a lokacin daurewa kawai take yi. Cikin tausayawa yace, “Sannu.” Ya faɗa yana saka hannu aljanu ya ɗauko maganin da ya taho da niyar kawo mata yace, “karɓi ki sha” ya faɗa yana bata maganin ya ɗauko ruwa a yake a ajjiye a gaban motar guda ɗaya, duk da yayi zafi ruwan haka ta sha ta haɗa kai da guiwa cikin tsananin ciwo. Shiru yayi baice komai ba yana kallon ta, ya ƙaro mata a.c motar dan tayi sanyi sosai. Ita kuwa sai sauke numfashi take yi cikin ciwo mai tsanani, tausayi take bashi, ji yake kamar ya jawo ta jikin sa ta kwanta ko zata ji sauƙin ciwon da yake damun ta. Sanin babu wannan damar sai ya zuba mata ido kawai yana kallon ta bai mata magana ba. Sun fi minti talatin haka a sannan ya lura ma bacci tayi alamun maganin ya mata daɗi sosai. Murmushi yayi ya sauke ajiyar zuciyar ganin ta samu sauƙi ya kafa mata ido yana kallo. Suna nan zaune har kusan minti goma da fara baccin sai ta buɗe ido ta ɗago tana kallon sa, ganin idon ta yayi ja ga fuskar ta tayi wani iri sai ya tausasa murya yace, “ya jikin naki? Me ki ke ji yanzu? Marar ta daina ciwo?.” Kai ta sunkuyar cikin kunyar sa yayi murmushi yace, “ki bani amsa, Daman da maganin na taho na baki naga lokacin namu yayi.” Jin abinda yace sai bata ce komai ba ta buɗe motar ta fita, shima bai hana ta ba ya bita da kallo cikin tsananin soyayya da farin ciki. ******* Lubna na zaune a falon gidan Mujahid shima yana kusa da ita yana kallon ta yace, “Sweet kamar bakya farin ciki, in bakya farin ciki a haƙura kawai. Ni saboda ke nake komai ba dan farin cikina ba.” Lubna tayi ajiyar zuciya tace, “har yanzu ina jin tsoro ne shiyasa.” Mujahid yace, “na faɗa miki babu abinda zai faru ki amince dani amma kin ƙi.” Ta jan numfashi tace, “kar ka yi amfani dani daga baya ka watsar dani Mujahid, kar ka yi amfani da son da nake maka ka cutar zuciyata da kuma rayuwata. Na amince zan mallaka maka jikina saboda ina sonka, ina sonka kuma ina son auren ka, kar na wayi gari na buɗe ido naga baka nan, kar ka yi min abinda zan samu ciwon zuciya a lokaci ɗaya ba tare da na shirya ba. Kai fi kowa sanin ni ba ƴar iska bace, amma na amince da kai saboda ina son ka, ka ka cutar dani don Allah Mujahid.” Jikin sa ne yayi sanyi sosai murya a tausahe yace, “in da niyar hakan na zo gare ki da bazan je gaban iyayen ki ba Lubna, auren ki nake so nayi hakan mafita nake nema mana, ki amince dani ki daina kokwanto a kaina.” Numfashi ta sauke tace, “na amince da kai Mujahid, nasan baza ka cuce ni ba.” Yayi shiru yana kallon ta kafin yayi mata murmushi yana riƙo hannun ta tare da jawo ta jikin sa gabaɗaya ya rungume ta a jikin sa. A cikin lokaci kaɗan mujahid ya canjawa Lubna tunani duk da tana kwance kamar an dasa bishiya ko motsi bata yi amma shi hakan yayi masa yana aikata abinda yake so ran ransa cikin kwanciyar hankali babu doke-doke da fizge-fizge, yana aikatawa yana kuma hango fuskar Bebi a lokacin da ya samu Lubna a wannan yanayi, yana hango yadda fuskar Bebi zata kasance, wannan tunanin shine yake saka shi farin ciki mai ratsa zuciya. Tsoro da bugawar da zuciyar ta take yi shine ya saka ta ɗaukewar tunani na wani lokacin, ta suma bata san a wanne yanayi take ba tana dai hannun Mujahid sai yadda ya yi da ita. Shi kam sai da ya tabbatar komai ya tafi yadda yake so ya tashi daga kanta ya shirya tsaf tana kwnace har lokacin. Murmushi yayi ya ƙarewa surar ta kallo ya kalle ta ya shafa fuskar ta yace, “ki yi haƙuri Lubna, wannan ranar na jima ina jira na ganta kuma na samu dole zan barki, na nuna miki soyayya ne saboda na cusawa Yayan ki Adnan haushi, na nuna miki soyaya ne don na samu wannan damar na ɗanɗana masa zafin da ya saka na ɗanɗana. I’m sorry my sweetheart, duk soyayyar da nace ina miki ƙarya nake yi wannan abun kawai nake so a tare da ke kuma na samu. Zan barki a yanzu zan tafi inda baza ki kuma ganina ba, zan tafi inda baza ki sake tunanin kin taɓa ganina ba My love. Naji daɗin kasancewa dake, naji daɗin soyayya dake sweetheart. Ki yi haƙuri ƙarfin fansata akan Yayan ki yafi min alƙawarin da na ɗaukar miki.” Ya sauke numfashi yana yi mata kiss a goshi yace, “kina da daɗi my love, zan so sake kasancewa a cikin koramar ki. Sai mun sake haɗuwa in da rabo” ya faɗa yana kallon ta tana kwance, babu wani mayafi da ya suturta jikin ta a wannan lokacin. Wayar sa ya ɗauka da niyar yi mata hoto sai kuma ya kulle ido ya daki goshin sa tare da yin tsaki, maganganun ta yake tunawa hakan ya saka shi ya fasa abinda ya yi niya. Blanket ya ɗauka ya rufa mata yana kallon fuskar ta idanun ta a kulle amma hawaye take yi. Shafa fuskar ta yayi ya yiwa bakin ta kiss yan jin wani abu na shiga zuciyar sa game da ita. Da sauri ya miƙe ya fita ya barta a kwance a wajan ya turawa Bebi message cikin farin cikin cikar burin sa na lalata ɗaya daga cikin ƙanen sa, ko yanzu yaci riba dan ya tabbatar zai ji zafi sosai fiye da wanda yaji lokacin da aka ƙwace mata lasisin sa na zama likita, shima ya ƙwacewa ƙanwar sa budurcin ta, ko babu komai yayi masa tambari a zuciyar sa da dangin su gabaɗaya. Kuma shi ko babu lasisi zai iya aikin likita, ita kuwa har abada ta ras budurcin ta Kenan har abada. BDƘB2P11 Bebi yana zaune a office ya dafe kansa cikin yanayi na damuwa da tashin hankali haɗi da tsoro, yayi shiru ko motsin kirki baya yi kana kallon sa kasan akwai babban lamarin da yake nuƙurƙusar zuciyar sa. Hamza da Huzaifa ma sun yi shiru babu wanda yake magana dan sun san yana cikin damuwa sosai yi masa magana a wannan lokacin bazai samu damar magana ba. Dr Hadiza ce ta shigo office ɗin jin sallamar ta sai ya kalle ta alamun ƙarin bayani yake so, kallon sa itama tayi ta sauke numfashi tace, "I'm deeply sorry Dr. she was raped!." Bebi ya sauke ajiyar zuciya ya girgiza kai ta sake cewa, "abin mamakin kuma shine, a jinin ta babu wata ƙwaya ko wani sinadari da yake nuni da an gusar mata da hankali hakan ya faru, ko suman da tayi unconsciously take kuma subconsciously, tsoro ne ya saka ta suman ba dan an saka mata ƙarfi ko wani magani ba, kaga kenan kamar...." Kafin ta kai ƙarshe yace, "ita ta kai kanta." Dr Hadiza ta girgiza kai tace, "that's what i’m expecting. In ma ba hakan ba zai iya kasancewa akwai amincewar ta duba da budurwa ce, ko ya ya aka yi kokawa da ita za’a samu ciwo sosai a tare da ita.” Bebi ya kalli su Huzaifa suma shi suke kallo bai yi magana ba ta sake cewa, "yanzu idanun ta biyu, amma na saka nurse ta yi mata allurar bacci don ta samu hutu. An yi sa a babu tears, she’ll be fine soon in sha Allah." Tana gama faɗar hakan ta juya ta fita. Tana fita ya sauke ajiyar zuciya yana jin zafi da raɗaɗi a cikin ƙirjin sa. Ya kalli Huzaifa kafin yayi ya riga shi magana yace, "wannan duk ƙaddara ce Bebi, bawai Mujahid galaba yayi a kan ka ba, daman can haka Allah ya tsara zai faru kuma dole sai ya faru. Ka ɗauke shi matsayin ƙaddara." Hamza yace, "amma bai kamata a ƙyale shi ba, yana da kyau a kai maganar nan gaban hukuma. Fyaɗe fa ya mata, meye laifin ta ai Bebi ne mai laifi ba ita ba, yanzu aka san target ɗin sa na gaba kuma?." Bebi yana jin su idanun sa suna kalle ya buɗe ya gyara zaman sa yace, "ina da laifi nima, na ɗauka tunda Abba ya dakatar da maganar sa nayi tunanin ta daina bibiyar sa, Sai na watsar da lamarin a ganina zata ji maganar Abba ashe nayi kuskure." "Shine ƙaddarar ai, koda ace kana bibiyar ta sai hankalin ka ya ɗauke daga kanta na yau kawai saboda faruwar hakan" Huzaifa ya sake faɗa yana kallon sa. Shiru yayi bai ce komai ba Hamza yace, "yana da kyau gida su san halin da ake ciki, dare yayi yanzu na tabbatar ana can ana neman ta. Kuma maganar nan bai kamata a bar ta, ya kamata hukuma ta shiga cikin lamarin."  Zai yi magana kenan wayar sa ta fara ƙara ganin Mummy ke masa waya sai ya ɗauka tare da sakawa a kunne,  daga can ɓangaren tace, "Adnan Lubna har yanzu bata gida ba ga dare yayi sosai." Daƙyar ya iya buɓe baki yace, "mu na tare a nan asibiti, bata jin daɗi." "Me ya same ta? Amma ai da sai ka faɗa mana ko?, ka san dole hankali ya tashi." Yayi shiru bai amsa ba Mama tace, "me ya same ta?." Kallon su Huzaifa yayi da suke kallon sa sai yace, "zazzaɓi ne, ana kira na Mummy ina zuwa" ya faɗa ya yanke wayar dan bai san da wanne yare zai sanar mata raping ɗin ta aka yi ba. Huzaifa yace, "meye na ɓoyewar bayan ya faru?." Tashi yayi bai magana ba ya fita zuwa ɗakin da take. Bacci take yi ga ruwa nan an saka mata yana shiga jikin ta, ya zuba mata idanu yana kallon ta. Gata nan ras da ita babu alamun duka ko shan wahala a tare da ita, sai fuskar ta kawai da ta kunbura shima ya san kuka ne ya jawo hakan. Tunawa da babu komai a jikin ta yaje ya same ta, ya runtse idon sa ya buɗe zuciyar sa a karye ji yake kamar ya zubar da hawaye. Wayar ya duba yaga goma na dare tana ƙoƙarin wucewa ya sauke numfashi ya rasa wanne irin tunani ma ya kamata ya yi. Kiran Mujahid ne ya sake shigowa kamar bazai ɗauka ba sai ya ɗauka su Hamza a lokacin suka shigo ɗakin daga can ɓangaren yace, "ya kaga ƙanwar ta ka? Na tabbatar yanzu tana kwance a gadon asibitin tana karɓar magani" yayi dariya yace, "Ko da yake bata wani wahala sosai ba balle nace na san tana sume har yanzu, imani ne ya shiga zuciyata na sassauta mata, amma wallahi da sai na yi mata abinda sai an ɗinke ta in and out. Tausayi kawai ta bani saboda ta amince dani, amma da wallahi da yanzu ana nan ana aiki a kanta. Baƙin cikin da ka ɗanɗana min kai ma na saka ɗanɗana shi, na tabbatar yadda ka ke jin ciwo a zuciyar ka ya zarce yadda naji nawa ciwon a zuciyata. Ina so ka sani yanzu na fara ka jira haɗuwar mu ta gaba, kayi fatan kar idona ya faɗa akan wacce zaka aura don so nake kaji ƙuna fiye da yadda na ji a zuciyata." Bebi bai magana ba wayar ba kunnen sa Mujahid yace, "kai ba kana ganin zaka iya raba mu da ita ba? Gashi nayi amfani da soyayya na same ta a banza tare da amincewar ta, ba kokawa balle bugarwa,  tana so ina so shiyasa abun yayi daɗi sosai. Gaskiya ƙanwar taka akwai zaƙi mai gusar da hankali, har fata nake na sake komawa duniyar........." datse kiran yayi da hanzari zuciyar sa na bugawa sosai. Ya kalli su Huzaifa da suke tsaye yace, "Mujahid ya gama dani, duk ƙoƙarina na taimakawa yaran nan su riƙe kan su da mutunci su har gidan mijin su ya lalata min komai. Ku duba Lubna ce a kwance matsayin wacce aka yiwa fyaɗe, me lubna tayi masa ya ɗauki fansa akan ta? Meyasa bai saka an min abinda yake so ba?, Meyasa zai huce a kanta?." Huzaifa yaji tausayin sa dan duk wanda ya san Bebi ya san shi da son ƴan uwa sa da kuma son kare mutunci a ko yaushe, dole zuciyar sa tayi rauni da faruwar abinda bai yi tunani ba. Yace, "ƙaddarar kenan ai, kayi haƙura ka zo mu je ka barta ta huta sosai." Sake kallon ta yayi sai yayi ƙaramin tsaki ya kuma cewa, "Meye laifin ta?." Hamza yace, "don Allah ka yi haƙuri, mu mayar da hankali akan nemo shi bai kamata a bar maganar nan ba, ka kira Abba ka sanar dashi duk inda yake a binciko shi." "Yana da lokacin da zai saurare ni ne? Yanzu ina kiran shi zai ce meeting yake yi na kira anjima, bashi da wannan lokacin a rayuwar sa abinda ya saka a gaba shi kawai yake yi" Bebi ya faɗa cikin fitar hankali. Sun fahimci a fusace yake sosai dan bai cika maganar Abba ba, amma tunda yau ya ke yi sun tabbatar da baya cikin control. Wayar sace ta sake yin ƙara yaga sunan Mimi yayi banza bai ɗauka ba ta sake kira sai a lokacin ya ɗauka yace, "ku zo sama" abinda yace kenan ya kashe wayar ya fita daga ɗakin suma suka fito a lokacin su Mama da Mamy da Maryam da Mimi suka zo wajan. Mamy tace, "Adnan me ya samu Lubna ɗin?." Bebi ya daidai nutsuwar sa yace, "mu je office ku zauna tana buƙatar hutu." Basu yi musu ba suka bi shi har office ɗinsa suka zauna Mama ta kalle shi sosai dan ta gama karantar yanayin sa tace, "baka faɗa mana abinda yake damun ta ba." "Ba wani abun bane, ina zuwa" ya faɗa yana fita suka haɗu da Hamza taja hannun sa suka yi gefe yace, "ta wacce hanya zan faɗawa su Mama abinda yake faruwa don Allah?." Hamza yace, "haƙuri zaka yi, dole su sani ɓoyewar babu amfani." Kaii ya juya kawai ya koma ɗakin da take ya sake ganin bacci take har lokacin, ya fita ya shiga wani wajan duk dan kar ya koma su sake tambayar sa. Theater room kawai ya shiga ya zauna ya rasa abinda yake yi masa daɗi a zuciyar sa, wayar ya buɗe yana sake karanta abinda Mujahid ya turo masa sai ya fita da sauri cikin ƙunar zuciya. Hannun sa ne ya shiga wajan hotuna bai sani ba nan ya buɗe hoton Manal, ya zuba mata ido yana kallon ta sai ya fita daga wajan ya shiga kiran number ta. Ɗauka tayi da sallama ya amsa murna a raunane jin yadda ya amsa sai tace, "Lafiya naji maganar ka haka? Ko baka da lafiya?." Lumshe ido yayi yace, "ya jikin ki?." "Na warware, me yake damun ka?." "Don Allah ki ta magana kar ki daina, maganar da ki ke yi yana sani naji daɗi a raina. Zuciyata zafi take, maganar ki kamar ruwa mai sanyi ki ke zuba mata. Ki cigaba da magana ko da ban ce komai ba." "To, tunda baka jin daɗin zuciyar ka ka dinga maimaita salati a ranka zaka ji daɗi, na tabbatar ran ka ne a ɓaci ko wani abun ne da yafi haka, amma ka manta da komai ka dinga salati zaka ji daɗi." Ya girgiza kai kamar yana gaban ta yace, "bazan iya mantawa ba partner, an taɓa rayuwata, bazan iya mantawa ba har abada." Manal tace, "to ka yi haƙuri." Shiru yayi bai ce komai ba itama tayi shiru bata ce komai ba kusan minti biyu a haka kafin yace, "ki ce wani abu." Ita ta rasa abinda zata ce masa ne haka kawai ya saka ta dinga magana ba amsa kamar wata zararriya. Cikin taushin murya tace, "Komai ya faru zai wuce in sha Allah, ina tare da kai zan taimaka maka a duk lokacin da ka buƙaci hakan zan iya yi maka komai ka ke so. Ban san me ya faru da kai ba, kuma ko na sani ko ban sani ba zan iya taimaka maka wajan ganin ya kau daga zuciyar ka, bana so damuwa ta dinga mamaye zuciyar da farin ciki kawai ya kamata ace tayi, zuciyar ka zuciyata ne, zan iya aikata duk abinda ka ke so don ka samu sassauci." Idanun sa a lumshe yana jin abinda yake cewa yana shiga zuciyar sa sosai kuma yana jin sauƙin zafi da raɗaɗin da yake damun sa. Ajiyar zuciya yayi ya buɗe yace, "thanks you my life partner, thanks you so much and I love you" abinda yace kenan ya kashe wayar ya sauke numfashi mai ƙarfi. Kiran Mamy ya shigo wayar sa sai ya tashi ya fito ya sake shiga wajan lubna har lokacin bata farka ba, zai bar wajan kenan yaga Mama a bayan sa ta kalle shi tace, "Wai Lubna mutuwa tayi ne da ka ke wasan ɓuya damu?." Ya girgiza kai yace, "tana da rai." Kallon su Mamy tayi kafin ta sake cewa, "to meye na hana mu ganin ta?, kuma meye naƙin sanar damu abinda yake damun ta?." Ya nuna musu ɗakin alamun su shiga dukkan su suka shiga suka ganta ba yadda suke tunani ba. Dan sun ɗauka wani mummaan accident tayi taji ciwo sosai shiyasa yake ɓoye musu. Mamy ta kalle shi tace, "yadda naga kana ɓuyawa baka so mu san abinda ya faru nayi tunanin zan ganta an saka mata robar hanci, na ɗauka zan ganta jiki duk ciwo dan a tunanina wani hatsarin tayi mai muni. Amma sai naga ba haka ba, me yake faruwa ne?." Yace, "mu je office zan sanar daku." Tare duk suka fito suka shiga office ɗin yana tsaye a jikin ƙofa suna kallon sa hakan ya saka yace, "Mamy ina tace miki zata je a ɗazu?." Mamy tace, "ƙofar mata wajan Hajiyata." Ya kalle su yace, "Maganar gaskiya Mamy an....." "Dr! Sister ka ta tashi kuma kai take kira tana kuka" wata nurse ta faɗa tana kallon sa tunda yana bakin ƙofar a tsaye.  Bai ƙarasa faɗa ba ya fita da hanzari. Yana shiga ya tarar da ita sai kuka take ya ƙarasa ya zauna a kan kujerar da take kusa da ita ya riƙe hannun ta yace, "Lubna meye na kuka bayan baki da lafiya?." Kukan take yi sosai ta riƙe hannun sa tace, "Yaya kayi haƙuri, na yi kuskuren kasa fahimtar ka, ka yi haƙuri Yaya Adnan."hannun sa ta ɗauka ta ɗora akan fuskar ta tana kuka. Cikin taushin murya yace, "kukan zai ƙara miki ciwo, ki bar kukan haka." "Yaya Adnan ya cuce ni, Yaya Adnan duk naji abinda yake faɗa, nayi kuskuren ƙin bin maganar ka." "Lubna nace ki daina kuka." Kukan take yi sosai hannun sa na kan fuskar ta ta riƙe sosai,tausayi take bashi ji yake da yana da dama da ya canja mata wannan ƙaddarar amma inabai isa ba. Ta sake cewa, "Yaya Adnan da gaske ba sona yake ba kamar yadda ka ce, ya yi amfani da son da nake masa ya cuce ni." Adnan yace, "bai miki komai ba, ki bar kuka." "Yaya bazai taɓa bari wannan damar ta wuce sa ba, Daman ita yake jira kuma ya samu. Na shiga uku na cuci kaina." Ganin abin nata yayi yawa sai ya kalli gefen sa nan yaga allurar da aka yi mata ɗazu tayi bacci ya zare hannun sa daga cikin nata, ya ɗauki allurar yaja nan da nan ya mata a jijiya bacci a take ya sake ɗauke ta. Ajiyar zuciya yayi lokacin da tayi bacci ya saka hannu ya shafe mata hawaye fuskar ta ya janye hannun sa, yana juyowa suka haɗa ido da Mama. Mamy tace, "me ya faru?." "Mujahid ya yi mata fyaɗe" abinda yace kenan ba tare da ya kalli Mamy ba. "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Fyaɗe Adnan?" Mama ta maimaita a firgice cikin rashin hankali. Ya kalle ta yace, "Eh Mummy, ni da kaina naje har gidan shi na ɗauko ta kuma shine ya sanar dani da kan sa, na kawo ta nan aka tabbatar min da an yi." Mamy salati kawai take yi Maryam kuwa kamar munafuka gabaɗaya tsoro ya mamaye mata zuciya hankalin ta ya tashi, ita kuwa Mimi kuka take yi sosai ta ƙarasa wajan Lubna da sauri tana kallon ta tana kuka. Kallon Mimin yayi suka haɗa ido tana kuka ya ɗauke kai yace, "allurar bacci nayi mata, ki daina mata kuka a kusa ita" ya kalli su Mama yace, "mu je office a barta ta huta." Kamar wanda ƙwai ya fashewa a ciki haka suka fito Mimi sai kuka take yi suka koma office ɗinsa. Mama jiki a sanyaye tace, "amma dai an kama shi ko?." Bebi yace, "tukunna dai." Wayar sa ce tayi ƙara yaga sunan Abba sai ya ɗauka ya fita yana amsawa kafin ya dawo ya kalle su yace, "ku koma gida, ninina nan daman akwaintheater ɗin da zamu yi in an jima." Mamy murya a raunane tace, "ta ya zamu iya tafiya mu bar ta?." Maryam ma hawaye take yi tana tuna irin ta ta  badaƙalar da take aikatawa, sai satar kallon Bebi take har ya lura da yawan kallon sa da take yi. ita kam tunani take ya kamata ta faɗa masa matsalar ta da Kamal ko zata samu sauƙi dan abin ya ishe ta sosai. In ta kalle shi sai taji baza ta iya faɗa ba, da wanne baki zata iya ce masa tayi zina? Ƙanin ta ne na biyu, kuma shine wanda ya dinga faɗi tashi akan ta daina sauraron Kamal amma taƙi ji. Da wanne ido zata kalle shi? Da wanne ido zata ce masa ta aikata zina?. Dukkan su sun kasa magana sai kukan da Mimi take yi, bai hana ta ba dan shima ji yake kamar yayi kukan kawai babu damar hakan ne. Fita yayi ya bar su dan akwai abinda zai yi. Suna nan zaune shiru babu mai magana kowa zuciya tayi rauni, babu walwala dukan su ji suke kamar su yi kuka. Har sha biyun dare tayi babu wacce tayi ƙoƙarin tafiya, driver ya kira yazo ya saka suka tafi aka bar Maryam ta koma ɗakin da Lubna ɗin take itama ta ta damuwar.                      Washe gari. Har ƙarfe baƙwai na safe ma yana asibitin tun daren jiya kansa ciwo yake saboda bacci ga damuwa amma bai tafi ba, zuwan Dr Hadiza ne ya saka shi zuwa office ɗin ta da sallama yace, "Dr kina ganin zamu iya tafiya da ita gida?." Dr hadiza tace, "Dr har yanzu kana nan?." Bai mata amsa ba tace, "a dai barta ta sake hutawa a nan zuwa gobe sai ta tafi, in ka duba dole akwai ciwo saboda  kaga budurwa ce, a ƙyale ta a nan gobe sai ta tafi gidan." Kai ya girgiza cikin gamsuwa da abinda ta faɗa, tace, "yanzu in ta farka a samu tayi wanka da ruwa mai zafi, zata ji daɗi jikin ta in sha Allah." Amsawa yayi ya fita ya koma ɗakin ya ganta idanun ta biyu tana hawaye. Shi kukan ne baya so yaga tana yi, duk da laifin tane amma baya so yaga tana hawaye sake karya masa zuciya take yi. Ya kalle ta  yace, "na faɗa miki wannan kukan ba magani bane amma kin ƙi ji ko?." Lubna ta kalle shi tana tace, "Yaya Adnan ka tafi dani gida, bana son zama a nan, mu je gida na gaji da zaman nan." Ya kalli Maryam da take bacci yace, "A nan zaki fi samun kulawa sosai, kar ki manta baki da lafiya fa." "A can ma za a kula dani, kuma ni bana jin komai ka tafi dani na gaji" ta faɗa tana kuka sosai. Maryam ya kalla sai ta buɗe ido yace, "Yauwa, a samu tayi wanka da ruwan zafi sosai. A tabbatar ruwan zafin ya ratsa ta sosai." Maryam ta girgiza kai ta tashi ta ƙarasa kusa da Lubna ta taimaka mata ta tashi tsaye yana bin su da kallo suna tafiya a hankali, gani yayi ta tsaya tana kuka ta kasa cigaba da takawa, Maryam tace, "haƙuri zaki yi." Ta girgiza kai tace, "bazan iya ba, zafi nake ji sosai ga jiri." Maryam ta riƙe tace, "muje zaki iya." Kuka take tana ɗaga ƙafar daƙyar har suke je banɗaki. Gabaɗaya tafiyar ta ta canja salo kai da ka gani ko ba'a faɗa ba ka san akwai abinda yake mata ciwo a tsakanin cinyoyin ta. Numfashi ya sauke cikin rauni da tausayi ya fita sai suka haɗa da Mimi da Kausar a bakin ƙofa ya kalle su yace, "ku kuma daga ina? Ku dawa ku ka fito da sassafiya haka?." Mimi tace, "Saminu ne ya kawo mu, abinci muka kawo da kayan Lubna." Ya kalle su kana ganin su kasan damuwa ce a tare dasu son ganin ta ne ya saka suka fito a wannan lokacin, dan ya san halin su da shegen bacci basa ma tashi da wuri dan su taya Mama aiki wani lokacin, amma da yake abin yana ran su ko takwas bata yi ba sun zo. Hanya ya basu yace, "wanka take, ku shiga." Shiga suka yi shi kuma ya fita. Hamza ne ya ganshi ya ƙaraso inda yae yace, "Adnan har yanzu kana nan?" Ya kalli agogo yace, "yau ka san kana da ganin marasa lafiya sosai, Meyasa ka jima haka?." Ya kalli Hamza yace, "yanzu zan je gida nayi wanka na huta sai na dawo." Amsawa yayi ya wuce office ya sake zama kafin ya tashi ya ɗauki key da wayar sa ya dawo ɗakin a lokacin har sun fito Maryam tana bata shayi amma taƙi sha sai kuka take. Maryam tace, "Bebi ta ƙi shan tea ɗin kuma kai ne kace a bata." Ya kalle ta yace, "Lubna ki sha, zan je gida na dawo." Lubna tace, "To Yaya." ya kalli Mimi yace, "Hamza yana nan in akwai wani abun da ku ke so." Suka amsa da to ya fita ya hau mota ta tafi gida. Bai dawo ba sha ɗaya na safe, patients ya fara gani har azahar kafin ya shiga wajan ta ganin jikin nata da sauƙu kawai yace su wuce gida dan baya so mutanen asibitin su gano abinda yake faruwa. Shi ya riƙe ta tana jikin sa har motar Maryam ta shiga suka wuce gida. Ya jima a asibitin bai tafi ba sai yamma liss ko Manal bai kira ba, kuma ya ga kiran ta tun safe har sau biyu bai samu ya kira ba a haka ya tafi gida da niyar in yaje ya kira ta. Yana shiga gida ɗakin sa ya wuce bacci yake ji sosai a gajiye yake sosai dan bai yi wani baccin kirki ba. Yunwa yake ji dan indomie ya ci da safe bayan nan bai kuma cin komai. Baya ma sha'awar cin komai amma kuma yunwa yake ji sosai. Wayar sa ya ɗauka da niyar kiran Manal yaji ance, "Yaya Adnan!." Da sauri ya juyo jin muryar Lubna tana kuka. BDƘB2P12 Ganin yadda take kuka sosai sai ya ajjiye wayar ya nufo ta cikin rauni yana cewa, "me ya fito da ke bayan baki da lafiya?." Ganin yazo inda take sai ta faɗa jikin sa ta rungume shi tana kuka a ƙirjin sa. Jin yadda take kuka sosai sai ya ɗora hannun sa a bayan ta yace, "bana son wannan kukan na faɗa miki, komai ya riga ya faru ki yi haƙuri kawai." "Ni ce na jawowa kaina komai Yaya Adnan,da ace na bi abinda kake faɗa min a kansa da hakan bai faru ba. Ni da kaina naje har gidan Mujahid, ni da kaina na amince da shawarar sa, yace sai hakan ya faru sannan za’a bani shi ko baka so, wannan dalilin ya saka naje har gidan sa tare da amincewa ta komai ya faru. Yaya Adnan idona ya rufe ban yi shawara da kowa ba na amince dashi, a tunanina hakan shine mafita a gare mu nida shi, ashe nayi kuskure…..”ta faɗa cikin kuka sosai har lokacin bata sake shi ba tana jikin sa. Tausayin ta yake ji sosai, yasan laifin ta ne amma Lubna yarinya ce dole za’a yi amfani da raunin da take dashi a ci amanar ta, balle ya san waye Mujahid indai wajan iya sarrafa harshe ne akan mace yana da kambu a kai, shiyasa tun kafin alaƙar su tayi nisa yaso ya datse ta amma taƙi ji taƙi gani. Ɗago ta yayi daga jikin sa ya riƙe kafaɗun ta ya zauna ta kan kujera ya zauna kusa da ita ya riƙe hannun ta tace, "Duk abinda ya faru na sani, ke kika bada ƙofar da komai ya faru amma ba ke kika rubutowa kan ki ƙaddarar faruwar hakan ba. Allah ne ya rubuta kuma dole sai ya faru ko kina so ko bakya so, ita ƙaddara ba’a tsallake mata ko cikin mahaifiyar ka zaka koma sai tazo ta same ka. Dan haka ki kwantar da hankalin ki ki daina zubar da hawayen ki, zan tsaya miki a ko yaushe ganin an hukunta shi daidai da abinda ya yi miki." Hannun sa ta riƙe sosai hawaye wani na bin wani tace, "Yaya Adnan zina na aikata ko? Tunda ni na kai kaina…” ta faɗa murya na rawa sosai. Runtse idon sa yayi ya buɗe ya kalle ta yace, “ki kasance mai neman gafarar wanda ya halicce ki, yaudarar ki akayi Allah yana ganin komai.” “Yaya Adnan kunyar kowa nake ji.” Yayi shiru baice mata komai ba ta sake cewa, “kayi haƙuri." "Ya wuce Lubna, ki daina kuka." "Yaya duk abinda yake faɗa naji, Daman ashe ba sona yake ba, yana yin komai ne saboda kai, yana cewa wai ko babu komai zaka ɗanɗana zafin da ka saka ya ɗanɗana." Ya sauke numfashi yace, "Mujahid tare dashi muka buɗe asibitin mu, kamar yadda kike ganina da Hamza da Huzaifa a baya tare muke dashi. Abinda ya saka muka rabu dashi kama shi aka yi dumu-dumu yana yiwa mara lafiya wacce taje wajan sa neman lafiya irin abinda yayi miki. Da akayi bincike sai aka gano ba iya ita kaɗai bace, matan da ya yiwa haka suna da yawa. Ni Adnan ni na shiga na fita muka fitar dashi daga cikin mu, sannan na samu minister of health na nigeria da maganar shi kuma ya ƙwace lasisin sa na zama likita. Wannan dalilin ya saka yake neman hanyar da zai ɓata min kamar yadda nayi masa, yasan ƙannena ku ne rayuwata, bana so naga wani abu ya faru da guda ɗaya a cikin ku. Wannan dalilin ya saka yazo wajan ki da niyar neman aure bayan ya nemi Mimi bata saurare shi ba. Na yi miki magana a kai amma kika ƙi ji…” sunkuyar da kai tayi Hakan ya saka yace, “Koda yake yanzu wannan duk ya wuce, ki kwantar da hankalin ki babu abinda zai sake samun ki." Kuka take har lokacin, jin labarin da ya bata akan Mujahid ya saka ta sake yin dana sani da nadamar abinda ta aikata. Ji take meyasa tun farko bata amince da abinda yake faɗa mata ba?, da ta amince da wataƙila hakan bai faru da ita ba. tace, "na zama silar da ya baƙanta maka rai ko Yaya Adnan?." Ya ɗan yi ƙaramin tsaki yace, "Lubna ya wuce na faɗa miki." "Yaya zafi nake ji a zuciyata, ji nake kamar na kashe kaina na huta. Na rasa darajar da nake da ita matsayina ta ƴa mace.” Bebi yace, "ki ta addu'a komai zai wuce, na san wannan zafin ba zai bar zuciyar ki ba, amma in kina faɗawa Allah zai ragu in sha Allah." Kukan ta sassauta yana kallon ta ganin ta rame lokacii ɗaya, ta wani firgice kamar ba ita ba, tausayin ta yake sake ji a zuciyar sa amma bai ce komai ba. "Asslamu alaikum" Mimi ta faɗa tana shigowa falon. Kallon ta yayi ya amsa ta kalli Lubna da take zaune tace, "ana ta neman ki." Sai ta kalli Adnan tace, "Yaya Adnan Abba na kiran ka." Adnan ya girgiza kai yace, "zo ki riƙe ta ku tafi gani nan." Mimi ta riƙe Lubna suka fita shi kuma yana kallon su kafin ya tashi ya fito zuwa wajan Abba. Yana shiga ya tarar da kowa yana nan har Farida da yayyen sa maza suna zaune, ya shiga ya zauna suka gaisa da Abba kafin ya kalle shi yace, "Ina shi Mujahid ɗin yake ɗin uwar sa dan uban sa? Ni zai yiwa wannan lalatar har cikin gida?.” Bebi yace, “ban neme shi ba tukunna, hankalina yana kan ta samu lafiya.” “Laifin Lubna ne ai, nan aka zauna ana magana suka dinga magnaganu suna ganin kamar son su ne ba a yi ita da uwar ta, yanzu wa gari ya waya?." Jin yadda Abba yake faɗa sosai sai kowa yayi shiru ya sake cewa, "kai ku je ku zo min da ita nan.” Bebi yayi sauri yace, "Abba a ƙyale ta, tana buƙatar hutu sosai zuwan ta nan damuwa zai sake ƙara mata. Abba kaf ɗin mu a nan babu wanda yake jin kwatankwacin abinda take ji a zuciyar ta, mu taya ta muke kawai, don Allah a ƙyale ta." "Amma ai laifin tane Adnan, itace ta bada ƙofar da ya samu har ya lalata ta" Yaya ismal'il ya faɗa yana kallon sa. Bebi yace, "da hakan, kuma da ƙaddara wacce ta riga fata, komai ya riga ya faru sai dai ace Allah ya kiyaye gaba. Wannan faɗan damuwa zai saka mata." Farida tace, "amma yana da kyau a nuna mata kuskuren ta." Bebi yace, "ta fi kowa fahimta kuskuren ta a yanzu, don Allah a ƙyale ta taji da abinda yake damun ta." Abba yace, "Ina shi Mujahid ɗin yake?." "Mujahid baya ma ƙasar nan." "İn dai ba lahira ya tafi ba sai na saka an hukunta shi wallahi, in dai ina sa rai sai yayi zaman prison. Ni zai yiwa wannan rashin mutuncin har gida? Ƴar da na haifa ita zai yiwa fyaɗe?.” Yaya Bilal yace, "Abba babu hujjar da za’a kama Mujahid saboda laifin fyaɗe, ba kokawa suka yi da ita ba, ba sace ta yayi ba, ba wani magani ya bata ba, da kanta da amincewar ta taje har inda yake. Kaga wannan ba irin fyaɗen da za’a yiwa wanda ya aikata hukunci bane. Da amincewar ta bamu da hujjar da zamu ce ya yi mata fyaɗe.” Ran Abba ya sake ɓaci sosai, ƙunar hakan yake ji a zuciyar sa yace, "ni ta tozarta kenan? Ni ta ɓatawa suna a duniyar nan?. Na hanata kula yaro amma da yake bata da mutunci ta ɗauki ƙafa ta bi shi har gidan sa ta bashi kanta da sunan neman mafitar auren ta.” Shiru suka yi dan sun lura abin ya yiwa Abba ciwo sosai ya sake cewa, "a tunanin ta an hana ta auren sa ne saboda jin daɗin mu ko kuma saboda haka muka ga dama ko?" Ya kalli Mamy yace, "duk laifin ki ne, da baki bata goyan baya ba da yanzu hakan bata kasance ba, da kin nuna mata kuskuren ta kamar yadda muka nuna mata da wata maganar muke yi ba wannan ba. Sai kika sakawa idanun ki toka da wani kishin banza da wofi kika ce ke Adnan bai isa da yaran ki ba saboda ba uwa ɗaya su ke ba, gashi yanzu da matsalar da ake gudar muku ta faru shine dai yake ƙoƙarin gyarawa. Girman ki bai amfana miki da komai ba, tunda bakya tunani kafin ki aikata abu. A nan wajan kika dinga cewa akwai banbaci tsakanin Mimi da Lubna, su gashi da ya isa dasu in yace kar ayi basa yi gasu nan lafiya lau basu da wata damuwa. Yanzu wannan riba kika samu ko akasin ta?." Kowa yayi shiru dan tabbas da laifin Mamy a lamarin itama bata ce komai ba dan ta san da laifin ta, Abba ya sake yin tsaki zuciyar sa zafi take masa sosai, bai san haka iyaye suke ji a duk lokacin aka lalata yaran su ba sai yanzu, bai san haka abin yake da ciwo sosai ba sai da ya faru akan jinin sa. Bai san haka ake jin zafi da raɗaɗi ba sai yanzu da aka yiwa ƴar cikin sa fyaɗe. Bebi yace, "Haƙuri za'a yi, komai ya riga ya faru itama ta gane kuskuren ta nan gaba baza ta sake aikata hakan ba. Don Allah Abba kar kace zaka mata faɗa, nasiha da nuna mata kuskuren ta shine ya dace da ita ba faɗa ba, kuma don Allah maganar nan ta tsaya a nan kar ta fita waje." Abba a fusace yace, "ita zan tsaya na yiwa nasiha? To nace mata me? Nace mata kin ga abinda kika aikata abinda ya jawo miki ko?" Ya girgiza kai cikin fushi yace, "Wallahil azim da na ganta a yanzu babu abinda zai hana ban mata dukan tsiya, da girman ta ai da kuma hankalin ta taje ta aikata saboda cikar burin. Ƴar da na haifa ace na yi mata umarni taƙi ji ta tsallake taje wajan saurayi har cikin gidan sa? Saurayin ma wanda na hana ta kulawa?. Adnan waƙa ka ke so nayi mata?." Adnan ya fahimci ciwon Abban yace, "dukkan mu mun san tayi kuskure, kuma ko a nan ta fahimci illar ƙin bin umarnin ka da tayi. Don Allah Abba kayi haƙuri, Ina baka haƙuri a madadin ta, ita kaɗai tasan abinda take ji a zuciyar ta ,Abba don Allah ka sassauta mata." Abba yace, "ka ke zancen kar kowa ya sani to abin arzuƙi ne da za’a faɗawa mutane? Mtswwwww!. Kana ta maimata tafi kowa jin zafi a zuciyar ta uban waye ya kai ta? Ba ita ta kai kanta ba?.” Dukkan su sun yi shiru babu mai magana a cikin su, shi dai Bebi a gajiye yake dauriya kawai yake yana magana kan sa ciwo yake yi saboda ya gaji. Abba ya kalli Mimi da Kausar da suke gefe Kausar sai hawaye take yi yace, "gani ga wane ya ishi wane tsoron Allah." Sunkuyar da kai suka yi basu ce komai ba. Kiran sallar magriba ne ya saka taron ya watse matan suka yi cikin gida mazan suka tafi sallah. Bebi yana dawowa wajan Mama ya shiga ya same ta a zaune kamar ko yaushe an kunna hayaƙin turaren wuta wanda aka kawo na bikin Mimi ana gwada ƙhamshin sa, dafe kai yayi yace, "Wayyo Allah!." Mama tace, "Au, yi haƙuri bamu ɗauka zaka shigo yanzu ba. Farida maza ki kashe hayaƙin." Ruwan hannun ta ta zubawa wutar hannun sa yana kansa yace, "Mummy ba wani abinda zan ci?." Mama tace, "sai dai a dafa maka bamu yi girki ba yanzu." "Barshi kawai, ban san ma abinda zan ci ba." Mama tace, "Nima cake ɗin budurwar ka naci." Sai a sannan ya tuna ma da cake ɗin sai kawai ya juya ya fita. Maryam yaji tana yi masa magana ya juyo tace, "jikin Lubna zafi Bebi, Sai kuka yake wai kanta zai cire." "Subahanallahi!" Ya faɗa da sauri yana yin hanyar ɓangaren su ya shiga har ɗakin Lubna ya same ta a kwance sai rawar jiki yake yace, "Lubna Sannu." Jin maganar sa sai ta kalle shi tana hawaye yace, "sau nawa zance miki ki daina kuka ne wai? An faɗa miki shine maganin damuwar ki?. Na maimaita na sake faɗa miki ki daina kuka amma bakya jin magana ko?" Ya faɗa cikin faɗa yana kallon ta fuskar sa a haɗe. "To Yaya na daina!" Ta faɗa tana share hawayen ta, ya taɓa jikin ta yaji zafi sosai bai ce komai ba sai ya juya ya fita bai jima ba ya dawo da allura yayi mata a jijiyar hannun ta ya fito daga ɗakin ya kalli Mamy yace, "Mamy damuwa ce ba wani abun ba, amma zata dawo daidai in sha Allah" ya kalli Maryam yace, "Don Allah a samu tayi wanka in ta farka, zata ji daɗi sosai." Kai ta ɗaga dan ita jikin ta ya gama yin sanyi, yadda Abba ya dinga faɗa akan Lubna budurwa kuma fyaɗe aka yi mata Ina ga ita in yaji abinda take aikatawa? Lallai dole ta samo mafita. BDƘB2P013 Bebi yana fita ɗaki ya koma yayi wanka lokacin ake kiran sallah bai fito ba a ɗaki yayi sallah, bayan ya  idar ya ɗauko cake ɗin wajan Manal a fridge yana ci. Tunawa yayi bai kira Manal ba ya ɗauki wayar sa ya kira ta amma bata ɗauka ba, ya sake kira bata ɗauka ba sai ya ƙyale ta. Ba'a jima sosai ba ya kira kiran yana gab da zai tsinke ta ɗauka kafin yayi magana tace, "na damu da damuwar ka shiyasa na kira ka tun da farar safiya naji ya ka kwana ya ka tashi, amma baka tashi kira na ba sai yanzu bayan na san ka gani, ka san a yadda na wuni kuwa? Gabaɗaya tunani nake ke ko wani abun ne ya same amma kai ko a jikin ka ko?" Yadda take masa maganar kamar zatayi kuka ya saka shi murmushi mai sauti zai yi magana tace, "Okay, dariya ma na baka kenan ko? Shikenan to sai anjima" tana faɗa ta yanke wayar bata bashi damar magana ba. Dariya yake yi cikin nishaɗi yace, "Manal rigima, bata tsaya ma taji abinda zan ce ba." Yana ɗago kai suka haɗa ido da Rumana da take tsaye tana kallon sa, ya kalle ta ya rausayar da kai yace, "kina son shigowa wajena babu sallama babu neman izini, ban san dalilin hakan ba." Rumana tace, "nayi sallama baka ji ba kana waya." Ya ɗauke kai hawaye suka sauko daga idanun ta, soyayyar sa kullum yawa take a zuciyar ta amma ta lura shi da gaske yanzu ya manta da ita. Ido ta goge sannan tace, "Daman zuwa nayi na faɗa maka abinda nake ji ko zaka iya faɗa min abinda yake damuna." Nuna mata wajan zama yayi ta zauna yace, "Ina Jin ki." Rumana murya a raunane tace, "Ina fama da ciwon ƙirji sosai, Sai naji yayi min nauyi ko magana bana so nayi. Yana min zafi wajan musamman side ɗin heart ɗina, ko numfashi na ja zafi yake min, kuma zuciyata na bugawa da saurin da ya wuce ƙa'ida. Sannan in ina kwance ina wahalar yin numfashi sai na tashi zaune Kallon ta yake yi ido cikin ido tun ba yanzu ba ya fahimci damuwar da ta sakawa ranta zata iya bata matsala, janye idon sa yayi yace, "damuwa ki ka sakawa zuciyar ki shiyasa, inda zaki cire damuwar zuciyar ki abinda ki ke ji zai ragu." Rumana tayi murmushi tace, "damuwa ta bazata iya fita daga raina ba Beb." "Kin gab da kamuwa da ciwon zuciya" ya faɗa yana kallon ta a nutse. Hawayen idanun ta suka sakko kan kuncin ta tace, "na ɗauka ma na kamu ɗin." Bebi shi baya son kuka, ɗaga masa hankali yake yi in yaga ana na yi, baya so yaga ana kuka ko kusa hakan ya aka ya sake sassauta murya tace, "wacce damuwa ki ka sakawa zuciyar ki haka? Ki faɗa min as your childhood friend." "Soyayya ce, ban ɗauka tayi min wannan kamun ba sai yanzu da nake gab da rasa abinda nake so. Wallahi Beb zaafin da nake ji a raina Allah ne kawai ya sani, Ina son shi son da ban san iyakar sa ba, ji nake in wata ta aure shi ba ni ba mutuwa zanyi." Ya shafa fuskar sa ya kalle ta sosai yace, "waye yace miki yanzu ana saka soyayya har haka a zuciya Ruman?." Gaban ta sai faɗuwa yake yi saboda tsananin son sa take masa tace, "bani na sakawa kaina ba Allah ne." "To ki roƙe shi ya sassauta miki, in ciwo ya same ki kan ki kika cuta, in kuwa kika dage da addu'a kika bawa Allah zaɓi zai taimake ki, in alkhairi ne shi wanda ki ke so ɗin zaki aure shi ko yanzu ko nan gaba, in ba alkhairi bane a wajan ki Allah zai cire miki shi a zuciyar ki ki manta dashi kamar ba a yi shi ba." Tayi murmushi ta kalle shi tace, "na manta dashi fa kace? Bana tunanin hakan." "Allah nace nima, shine ya sakawa kuma shine zai cire ai ko?." Ta girgiza kai alamun haka ne yace, "ki sassautawa kan ki wannan damuwar, Allah yana sane dake ke, kawai ki dage da addu'a in sha Allah zaki ga canji a rayuwar ki." Ta sauke numfashi tana girgiza tace, "haka ne, na gode sosai Beb." Da ido ya mata alama da kar ta damu ya saka glasses ɗin sa da yake ajjiye yana jin yadda take kallon sa a jikin sa, shi kuma bai ɗago ba dan tausayin take bashi, har tausayin yana neman yin gurbi a zuciyar sa domin ya fahimci da gaske damuwar soyayyar sa zata iya saka mata ciwon zuciya, in hakan ta kasance bazai ji daɗi ba ko kaɗan. "Na shigo kana waya da Manal, ka gaishe ta ko ka bani ita mu gaisa." Ya kalle ta fuskar sa a sake yace, "to zan faɗa mata." Ganin ya amsa da sakin fuska sai tace, "Baza ka haɗa mu mu gaisa ba kenan?." Ya girgiza kai alamun ba haka bane tace, "to ka kira ta." Ya kalle ta yace, "baza ta ɗauka ba, zan haɗa ku gobe." Rumana tayi murmushi ta kalle shi tace, "kana son ta sosai ko?." Haɗa ido suka yi sai ya tuna lokacin da take ce masa yanzu bata son sa Jawad take so daman soyayyar yarinta tayi masa, janye idon sa yayi yace, "zaka auri mace ne kace baka son ta Rumannnn!?" Ya faɗi sunan nata da wani irin salon da ya saka ta kalle shi dan zuciyar ta sai da ta harba sau babu adadi. Ta girgiza kai alamun a'a yana cigaba da cin cake ɗin sa, ta tashi tsaye tace, "na gode da shawarar ka, amma don Allah ko sau ɗay ne a sati ka dinga zamar min kamar yanzu, zuciyata tayi sanyi fiye da yadda na shigo" tana faɗa ta fita ya bita da kallo ya sauke numfashi bai bari abin ya dame shi ba ya ɗauki waya yana kiran Manal. Kamar yadda yayi tunani bata ɗauka ba har sau uku ya kira bata ɗauka ba sai ya share ya cigaba da abinda yake yi. Kusan minitina ashirin ya sake kiran ta ta ɗauka yace, "baki tsaya kin ji me zance miki ba sai ki kashe min waya?." "To ai kai ne ka bani haushi, tun safe fa na kira ka amma baka kira ni ba sai yanzu, yanzu da rashin lafiya ce fa? Na kira Yaya Huzaifa kace ba haka ba." "Wai yaushe Huzaifa ya zama Yayan ki?." Tace, "girmamawa ce kawai, bazan iya kiran sunan sa kai tsaye bane shiyasa." "Iyayi dai" ya faɗa a taƙaice tace, "Naji." Yace, "kina ji, bana jin daɗi ne, abubuwa sun taru sun yi min yawa, ba dan na kira ki ba a jiyan nan ina cikin matsala, muryar ki ta zamar min magani sosai. Shiyasa kika ji ni shuru jinyar zuciyata ne. Amma kina raina, da na zauna zan kira ki ɗazu sai Abba ya aiko nazo." Manal tace, "jinyar zuciya? Yaudarar akayi a soyayya?." Sai ta bashi dariya yayi dariya mai sauti yace, "kusan hakan." Sai tayi murmushi itama tace, "amma at least ya kamata ka kira ni kasan bazan nutsu ba tunda na san a yanayin da na barka jiya, Amma sai ka share ni." "Baza ki gane ba Manal, yanzu ma Ina murmushi ne kawai, amma zuciyata Allah kaɗai yasan abinda yake cikin ta." "Meye ya same ka?." "Kar ki damu ya wuce." "Nima karanbani ne, nasan ban kai na san damuwar ka ba. Allah ya yaye maka." Yace, "ni ban ce haka ba." Bata ce komai ba jin hakan sai yace, "I'm sorry." Manal tace, "ya wuce." "Naji daɗin hakan, a asibiti na kwana jiya kuma har yanzu ban samu baccin four hours ba, yanzu gashi naji waya na shigowa daga asibiti da alama ana nema na, Ina so na huta Manal." Manal tace, "aikin lada ka ke partner, Allah zai baka lada amma ka dinga hutawa." Bebi yace, "zan huta duk ranar dana aure ki, a lokacin zanyi hutun da zan yi sati biyu ban je ko ina ba." Tayi murmushi tace, "kamar gaske." Yayi dariya yace, "Allah da gaske nake, kuma zaki gani, Allah ya nuna mana." Bata amsa da amin ba bata kuma ce komai ba sai yayi murmushi yace, "yanzu ya za'a yi? ana kirana." "Sai da safe?." Yayi ƴar dariya yace, "har kin tabbatar Sai da safem?." "Wannan aikin maka na san bazan sake samun ka ba sai gobe. Dalilin da ya saka ni likitoci ma basa burge ni." "Shine nace miki sai gashi zaki auri likita." "Nima ai nace maka waman ƙaddarallahu haƙƙu ƙadrihi." Yayi dariya mai sauti yana jin nishaɗi a ransa yace, "ƙaddara ce ni kenan ko?." Tayi dariya itama yana jin daɗin sabon da suka yi lokaci kaɗan da haɗuwar su yace, "na gode to." Bata ce komai ba ya kuma cewa, "Na gode parter, ko ya ya na rasa farin ciki waya ɗaya dake ya rage min damuwata, a gaishe da Mama." Amsawa tayi ya kashe wayar yana murmushi, Sai kuma ya tuna da Lubna ya tashi ya shiga ɗaki yana amsa wayar asibiti. Bayan kwana biyu. Kowa a gidan cikin kwanakin babu wata walwala har shi kan sa mai gidan, abinda ya faru da Lubna ya taɓa su sosai hakan ya saka kowa baya wani farin ciki kamar da. Sai kaɗan dai wanda baza'a rasa ba. Yau ta kam ranar lahadi da safe Abba yana nan Bebi ya shirya ya fito ya shiga wajan Mamy dan ya duba halin da Lubna take ciki. A cikin kwanakin tana shan gata a wajan sa, ko ina yaje sai ya kira ta a waya ya tambaye ta abinda take so dan kawai ya ɗauke mata damuwa. Da sallama ya shiga wajan Mamy ya same ta a zaune suka gaisa ya tambayi Lubna tace tana ɗaki. Har ɗakin ya shiga da sallama ya same ta a zaune a ƙazan tiles ta jingina sa bango tana aikin kuka, Sai ta bashi haushi ta cika kuka mara dalili, tunda komai ya faru meye na wannan koke-koken? yace, "ba bakya jin magana ko?." Jin maganar sa sai ta kalli inda yake tsaye tace, "Yaya Adnan ne zan yi? Mamy ko magana bata yi min, Abba ma baya yi min magana, ko gaishe shi nayi baya amsawa, kowa na gidan nan baya son kula ni" Sai ta taso tazo kusa dashi ta riƙe hannun sa ta kai wuyan ta tace, "kaji jikina yayi zafi ko? Kullum da zazzaɓi nake kwana nake tashi, kai ne kawai mai kula dani kowa baya sona" ta faɗa tana kuka tana kallon sa. Shiru yayi yana kallon ta har taje ƙarshen maganar ta yace, "waye zai ce baya son ki? Kawai ana numa miki kuskuren ki ne ko da nan gaba kar soyayyar wani ta rufe miki ido ki sake jefa kan ki a wani yanayin. Yanzu ai na san kin ga sakamakon abinda kika yi, kin rasa abinda har abada baza ki sake samun shi ba." "A barni da wannan ma ya shine ni hukunci, in na tuna haka Yaya Adnan kasa bacci nake yi, amma a gidan nan kowa ya kasa ganewa ni kaɗai na san abinda nake ji." Ya riƙe hannun ta suka fito zuwa falo, Mamy na zaune har lokacin ya kawo ta har kusa da ita yace, "Mamy don girman Allah ki yafe mata, ki sassauta mata hukunci da kike yi mata. Mamy bai kamata a dinga janye jiki daga inda take ba saboda ƙaddarar da zata ita faɗawa kan kowa, zata iya kamuwa da ciwo a wannan yanayin da ake ciki. In baki rarrashe ta ba waye zai rarrashe ta?." Mamy ta kalle shi tace, "me tayi min da take neman yafiya Adnan? Ai nice nayi laifin da zan nemi afuwar ta, tunda dana na amince da maganar ka da wataƙila hakan bai kasance ba. Nice na bada goyan bayan duk abinda ya faru." Adnan yace, "duk da haka, kice kin yafe mata taji daga bakin ki zata fi farin ciki da hakan." Mamy ta kalle ta tana zaune tana kuka tace, "Lubna ni baki min laifi ba, nice na miki laifi ke zan nemi yafiya domin nice silar da ya saka kika rasa abu mai mahimmaci a rayuwar ki." Lubna ta rungume Mamy tana kuka itama Mamyn sai da tayi hawaye amma bata bari  ta gani ba tace, "ki daina kuka ƙaddarar ki ce, Allah yana kallo zai saka miki." "Mun gode Mamy." Ya faɗa yana kallon Lubna kafin tace, "taso mu je wajan Abba." Ba musu ta tashi ya riƙe hannun ta suka fita Mamy ta kalli Maryam da take tsaye daga bakin ƙofar ɗaki tace, "na tabbatar da Adnan garkuwar gidan nan ne da mutanen da suke cikin sa, yana yin komai da jikin sa da zuciyar sa akan jinin sa. Haƙiƙa na amince da na bashi goyan baya a wancan lokaci da hakan bata kasance ba, ya yi iyakar iyawar sa wajan ganin ya kare Lubna daga sharrin Mujahid. Allah ya bashi masu yi masa." Maryam ta amsa da amin Mamy ta sake kallon ta tace, "lafiya ki ke kuma?." Maryam ta amsa lafiya lau tana barin wajan. Kai tsaye wajan Abba suka shiga da sallama ya amsa yana kashe wayar da yake yi yana zaune yana cin abinci, Bebi yana riƙe da hannun Lubna ya zauna a kan carpet itama haka yace, "Abba don Allah ka daina fushi da ita, kullum a cikin damuwa take kwana take tashi, ta fahimci tayi kuskure don Allah komai ya wuce." Abba ya kalle ta ta sunkuyar da kai ƙasa tana hawaye yace, "Fushin me zanyi da ita? Kanta fa ta cuta meye ya dame ni?." Bebi yace, "kar ka ce haka Abba, bawa baya tsallake ƙaddarar sa." Ya kalle ta yace, "shi kika yiwa rashin kunya akan ya faɗa miki gaskiya akan Mujahid, kika dinga zagi shi kina cewa babu wanda zai raba ku, kina cewa dan ke ba uwa ɗaya ku ke dashi ba. Yanzu gashi shine yake ƙoƙarin ganin farin cikin ki ya dawo, shine yake shige miki gaba a kan komai, kuma shine yake so yaga kin dawo da walwala kamar da. Sai ki faɗa min son ki yake ko ƙiyayaya ce?." Shiru tayi sai kukan da yake yi Abba ya kuma cewa, "ni baki min laifi ba, in ma kin yi ai ga sakamako nan kin gani. Ni babban burina Allah ya sa babu ciki a lamarin nan." Sai da gaban Bebi ya faɗi shima ya kalli Lubna sosai ya kalli Abba yace, "in sha Allah Abba." Abba yace, "ku tashi ku je, Allah ya kara lafiya." Suka amsa da amin suka fita daga falon. A compound ɗin gidan ya tsayar da ita yace, "Akwai abinda ki ke ji a jikin ki wanda zai nuna miki kamar kina da ciki?, ina nufin kina jin canji wanda baki saba dashi ba?." Hawaye take yi bata bashi amsa ba yayi tsaki kafin yayi magana tayi sauri tace, "bana jin komai." Kallon ta yake sosai amma bai ga wani sing da zai nuna masa akwai ƙaramin ciki a jikin ta ba hakan ya saka yace, "jeki." Hanyar wajan Mamy tayi bai mata magana ba ya wuce wajan Mama. BDƘB2P14 Lokaci yana tafiya biki yana sake gabatowa, an haɗa lefen Manal a gidan Farida an kawo gidan Mama ana kiran ƴan uwa suna gani kafin a kai. A lokacin an kawo lefen Mimi ana zuwa ana gani tare duk da ba zuwan ake ba sai na jiki kawai. Shirya-shirye ake sosai musamman Mimi da take ta shan gyaran jiki tayi kyau sosai sai ƙyalli take yi, kai da ka ganta kaga amarya dan ƙhamshin ta da fatar ta zai nuna maka hakan. A ranar da aka kai lefe gidan su Manal suma sun yi hidima sosai fiye da tunani, dan har ana ganin sun yi abinda yafi ƙarfin su dan karin maganar da bahaushe yake cewa yaba kyauta tukwici sun yi shi. Tunda aka kai lefen sai Rumana ta kwanta ciwo, ko yaushe babu lafiya gashi taƙi faɗawa Maman ta tunda ta bar gidan su Bebi tana gidan su hakan yasa babu wanda yasan tana rashin lafiya sai ita kawai. Ranar asabar tazo gidan suma nan ƴan  gidan suna nan gabaɗayan su ana ta zancen biki kowa ya ganta sai yayi maganar yadda ta rame. Suna cikin hirar da yamma ya shiga falon da sallama suka amsa nan take suka haɗa ido da Mimi, tunda aka fara mata wannan gyara jikin bai ganta ba sai a lokacin hakan ya saka yace, "Ke bleaching kika koma?." Farida tayi dariya tana kallon Mimi kafin tace, "Baka tambayi Manal ba sai ita?." Ya kalli Farida yace, "ana maganar gaskiya kina kawo wasa, baki ga yadda tayi haske bane?." Tayi dariya tace, "Amaryar kenan, kai wannan Manal ɗin taka da take da wannan hasken Allah kaɗai ya san yadda zata koma. Anya in ka ganta zaka iya bacci?." Ya harare ta yace, "saboda aljana ce?." Tayi dariya tace, "waye ya sani." A lokacin ya kalli Rumana da take zaune  yace, "Ruman baki da lafiya ne?." Hawayen da take ɓoyewa ya sauko daga idon ta  ta tashi ta shiga ɗaki ya bita da kallo har ta turo ƙofar, ya kalli Mama yaga irin kallon da take masa ya sauke numfashi kawai tabi bayan ta. Kuka ya shiga ya samu tana yi kamar ranta zai fita har ɗagawa ƙirjin ta yake yi, yana shiga ta kalle shi ta taho daga inda take tsaye ta faɗa jikin sa da sauri ta riƙe shi gam gam tana kuka. Runtse ido yayi yana jin ta a ƙirjin sa, tun farko itace mace ta farko da ba maharramar sa ba da ya taɓa haɗa jiki da ita, shima tun lokacin baya ne sau ɗaya ya dawo daga makaranta ta rungume shi tana farin cikin dawowar sa dan a lokacin suna tsaka da soyayya. Yana jin yadda zuciyar ta take bugawa ga kukan da yake yi a jikin sa, ya saka hannu a kafaɗun  ta ya cire ta daga jikin sa yana kallon ta yace, "Ruman ya mu ka yi dake akan addu'a? Kina yi kuwa?." Girgiza kai take tana nuna masa zuciyar ta har lokacin yana riƙe da ita, ƙarasawa suka yi bakin kujerar da take ɗakin ya zaunar da ita ya kalle ta cikin nutsuwa yace, "Ruman ki nutsu ki ja numfashi, ki bar wannan kukan mu yi magana." Ta kasa daina kukan dan yaƙi tsayawa ko kaɗan hakan ya saka shi yace, "ta ya zan faɗa miki abinda yake bakina bayan kina kuka? Kin san bana son kuka balle kuma kukan ki. Don Allah ki daina." Share hawayen tayi ya kalli gefen sa yaga ruwa wanda babu sanyi sosai ya ɗauko ya bata da kansa ta sha tana sauke ajiyar zuciya. Sai da yaga ta ɗan nutsu sannan yace, "Meyasa baki mayar da hankali akan addu'a ba kamar yadda nace miki Ruman? Haka kika zaɓarwa kan ki kenan?, Meyasa baza ki tawakkali ga Allah ba?." Numfashi take ja bata ce komai ta riƙe hannun sa, shima yayi shiru dan bai san me zai ce mata kalaman bakin sa sun kusa ƙarewa. Shiru ne ya biyo baya har lokacin tana riƙe da hannun sa tana so ta samowa kan ta nustuwa. Samu tayi abinda take ji ya ragu  tace, "maganar auren wanda nake so aka yi a gabana, Ina so na sake kamar kowa ayi komai dani amma na kasa, ba Ina sane nake hakan ba zuciyata ce." "Nima ban ce kina sane ba Ruman amma kin san wannan abubuwan da ki ke sakawa zuciyar ki zai iya saka miki ciwon zuciya? At your age ace kina da heart attack it's very risk Ruman, please ki nutsu ki cigaba da addu'a, amma wannan tashin hankalin babu abinda zai haifar miki sai ciwon da nake gudar miki." Kai take girgizawa tace, "to zan yi." "Ko ke fa, don Allah ki nutsu komai fa lokaci ne dashi." Ta kalle shi suka haɗa ido sai yayi mata murmushi itama tayi fuskar ta duk hawaye tace, "wallahil azim ina matuƙar son ka, ina yi maka son da ban san adadinsa ba, Ina kishi da wacce zaka aura tun kafin tazo, sarrafa soyayyar ka abu ne mai wahala a gare ni a halin da nake ciki. Rabon zan sha wannan wahalar ne abubuwan da suka wuce suka faru, da yanzu ba a zancen zaka yi aure, da yanzu kana son Rumana kamar da, da yanzu baka da wata mata sai ni. Amma yanzu baka son Rumana, tausayin Rumana ka ke ji Adnan." "Ruman......!" Sai ya kasa faɗar abinda zaice tayi murmushi tace, "na san baza ka min ƙarya ba shiyasa maganar ta maƙale, kar ka damu laifina ne nima na sani. Amma zan zauna da kai koda baza ka kalle ni matsayin matar ka ba, indai in aka ganni za'a ce wannan matar Adnan ce yafi min farin ciki koda kullum zaka zane ni ne, nasan kana min kallon bazawara baza ka iya zama sani ba, na amince ka aure ni ba sai ka ɗago ido ka yi min kallon matar ka ba, zan zama ƴar aikin ka kai da Manal. Ina so na mutu a matsayin matar ka Adnan..!" Zuciyar sa bugawa take yi bai san ya zai mata ba, ɗaure shi take da kalaman ta gashi tausayin ta ya gama mamaye masa jikin sa da zuciyar sa, tausayin ta ya samu gurbi a zuciyar sa har yana jin zai iya auren ta hakan ya saka yace, "kin wuce zama mai aikin Adnan Ruman, kina da matsayi mai girma a wajena wanda babu wacce ta same shi a duniya sai ke. Ki kwantar da hankalin ki in Allah ya rubuta zaki aure ni babu makawa sai hakan ya faru." Tayi murmushi jin daɗi tace, "Da gaske Ina da wannan matsayin har yanzu?." "Kina tantama ne?." "A'a, na san baza ka faɗa min ƙarya ba." Yayi shiru bai ce komai ba ta kalle shi tace, "Don Allah na roƙe ka wata alfarma?." "Komai ki ke so ki faɗa." Don Allah zan iya hugging ɗin ka?." Haɗa ido suka yi ta marairaice tace, "Allah nace kuma kace na faɗa." Hararar ta yayi sai tayi dariya shima yayi dariyar  tace, "Manal tayi dacen miji mai tsoron taɓa mata." "Har ke ma." Da sauri ta kalle shi sai taga kamar ba shi ne yayi maganar ba tace, "me kace don Allah?." Ya tashi tsaye yace, "cewa nayi taji daɗi." Ta sake yin dariya sosai hakan ya bashi farin ciki a zuciyar sa baya so yaga an shiga damuwa ta dalilin sa. Sai a lokacin ya lura su Mama duk sun shigo suna kallon su, bai san lokacin da suka ɗauka a wajan ba dan bai ji shigowar su ba kuma basu yi magana ba. Ya kalli Mama yace, "Mummy akwai maganin da zan aiko a kawo mata in naje asibiti yanzu." Mama ta ɗaga kai kafin tace, "Zo ɗakin Mimi ka same ni." Fita tayi dole yabi bayan ta ya bar su Mimi a wajan ta. Yana shiga ya same ta a tsaye ta kalle shi tace, "haka ka ke so a bar yarinya nan ta mutu saboda soyayyar ka Bebi? Ka duba yadda ƙirjin ta ya dinga yi ɗazu duk a kan son ka, ba dan kaine kaje wajan ta ba da ya zamu yi kenan?. Bebi ba ka tausayin ta, da kana yi da aure ta ko dan saboda tausayin ko saboda ni. Anya kana tausayin ta?." Ya kalli Mama yace, "Mummy Ina tausayin ta sosai, kin fi kowa sanin bana so a shiga damuwa ta dalilina." "Wannan ba damuwa bace mutuwa ce ai Adnan, in ka bar yarinyar nan tsaf zata iya rasa ranta a kan ka. Yanzu me ka yanke akan lamarin ta?." Yayi shiru bai ce komai ba Mama tace, "har yanzu baka karɓi auren ta saboda kana so ba ko?, Shikenan ka aure ta saboda ni ɗin, ko da baza ka haɗa ɗaki ɗaya da ita ba kamar yadda ta roƙe ka kayi mata." Bebi maganar tayi masa nauyi sosai yace, "in sha Allah Mummy komai zai zo da sauƙi." "Hmmm! Ya batun lefen da nace ka dinga yin biyu?." "Ai Mummy in lokacin yayi a rana ɗaya ma za'a haɗawa in sha Allah." "Gidan fa?." "Shima sai a siya." "Bana tunanin zan bari auren ku da ita ya kai shekara ɗaya bayan auren ka, zan je na samu Hajiya rana ɗaya nake so a ɗaura muku aure, in yaso sai ta tare daga baya." Yayi shiru bai ce komai ba Mama tace, "ita Fatiman ta san da batun auren Rumana?." Ya girgiza kai alamun a'a tace, "Meyasa baka faɗa mata ba? Saboda baka shirya auren ta ba ko?." Bebi yace, "wallahi ba haka bane ba, amma zan faɗa mata in sha Allah." Mama ta girgiza kai tace, "ka kai musu keys ɗin gidan?." "Eh na basu." "Allah ya sa albarka." "Amin Mummy." "Kayi min alƙawarin ko bani da rai ko yanzu na mutu ka tabbatar ka auri Rumana Adnan, shine zai saka ni farin ciki koda ina kwance a kabarina. Kaga ban ƙyamaci auren ka ba, ban ƙi wacce ka ke so ba, kaima kar ka ƙyamaci abinda nake so, kayi min shi ko da baka so." Bebi yace, "in sha Allah Mummy zan tabbatar da hakan." Tayi murmushi tace, "Allah ya yi maka albarka, naji daɗin yadda ka rarrashi Rumana, Allah ya cigaba da kulawa da rayuwar ka." Yayi murmushin  farin ciki ya amsa sannan ya fita zuciyar sa cike da tunani kala-kala ya wuce asibiti. Yana shiga asibiti kai tsaye wajan Hamza ya wuce ya samu Huzaifa ma yana ciki suna magana ya zauna suka kalle shi Hamza yace, "Ango ka sha ƙhamshi, daga Ina haka?." Ya sauke numfashi yana kallon Hamza kafin yace, "Daga gida nake." Huzaifa yace, "Ya batun dinner? Zaka yi ko ka fasa?." Bebi yace, "ba wannan ne a gabana ba yanzu, mafita nake nema." A tare suka kalle shi Hamza yace, "wacce mafita?." Ya zare glasses ɗin idon sa ya ajjiye akan table din gaban Hamza yace, "Ruman tana gab da da kamuwa da ciwon zuciya saboda dani, ko nace already ma ta kamu kawai abin bai yi zafi bane shiyasa ba'a fahimta ba." Hamza yace, "innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Abun har ya kai haka?." Yace, "ni kaina nayi mamaki, ban ɗauka haka take sona sosai ba, na ɗauka duk kalaman ta na ƙarya ne. Yanzu babu damar ayi maganar aurena a gaban ta, indai akayi koda da kuskure ne bata wuni lafiya. Abin ya zama yanzu dole rarrashin ta nake saboda lafiyar ta, a haka Mummy bata san da batun ciwon ba, amma ni na lura dashi tun ba yanzu ba." Huzaifa yace, "Tabbas ya kamata ka aure ta Bebi, ta cancanci soyayyar ka ko dan son da take maka." Ya kalle shi yace, "taya zan iya auren ta bayan aurena saura kwanaki kaɗan?. Ni ba wannan ne damuwa ta ba, Mama ta saka ni yi mata alqawarin ko babu ranta zan auri Rumana, ta kuma ce rana ɗaya take so a ɗaura aurena da mata biyu. Tsakani da Allah ta wacce hanya zan faɗawa Manal cewa zan auri Rumana? Nayi mata adalci kenan?." Hamza yace, "kaima tun farko da ka sani ka faɗa mata batun tunda ka san da maganar auren." "Haba Hamza, kawai sai na kalle ta nace mata in na aure ki da wasu kwananki zan sake yin aure?." Huzaifa ya girgiza kai yace, "to yanzu kai ya ka ke ganin zaka yi?." Yayi shiru na wani lokaci ya kulle fuskar sa da hannun sa yace, "ba auren nata nake ji ba yanzu, zan iya zama da ita saboda ciwon da yake barazana ga rayuwar ta, yadda nake ji a yanzu zan iya zama da ita koda babu Manal. In ba dan Allah ya kawo Manal ba da zan iya auren ta na zauna da ita kaɗai saboda ina tausayin ta wallahi. amma ya zanyi da Manal! Me zance mata? Da wacce fuska zata ɗauki abun?." Huzaidq yace, "Gaskiya kamar akwai rashin kyautawa ita Manal ɗin." Ya kalli Huzaifa yace, "ka fahimci abinda nake nufi, Manal fa bata taɓa aure ba sai a kaina, ta ya ya zan ce mata zan aure su rana ɗaya da wata wacce bata sani ba don Allah?. Ta amince dani, ta bani duk wata yardar ta, in na mata haka nayi adalci?." Hamza yace, "to yanzu ya za a yi kenan?." Ya wara hananyen sa alamun bai sani ba shima. Hamza yace, "ni dai a ganina Manal ta san da labarin nan gaskiya, in ka bari sai ka aure ta ka faɗa mata akwai tashin hankali, ka san mata akan kishiya balle ita da kishiyar zata zo mata wataƙila ko haihuwa bata yi ba."  Ya sauke numfashi ya mayar da glasses ɗin sa yace, "zan yi ƙoƙari wajan ganin ba'a haɗa bikin ba duk da ina tausayin Rumana. In yaso daga baya nayi mata bayani." Hamza yace, "yanzu zata fi gane bayanin ka akan bayan auren ku, yanzu bata aure ka ba bata san meye asalin kishin ba, in ka faɗa mata ta yarda kaga ko bayan auren wata fititar ta taso kana da hujjar da zaka ce ai kin sani tun kafin na aure ki. In ta aure ka ta san meye kishi, baza ta so wata mace ta raɓe ka ba Adnan. Faɗa mata yanzu shine mafita kaga tun farko ta sani." Ya zubawa Hamza ido yana kallon sa cikin rashin sanin abinda zai yi a raunane yace, "Ina son Manal, bana son wannan maganar ya zama silar rabuwar mu, kar na sanar da ita wannan maganar tace  ta fasa." Huzaifa yace, "baza ku rabu ba in sha Allah, zata fahimce ka kaje ka gwada." Ya sauke ajiyar zuciya yace, "in na bar nan zan wuce gidan su, Allah ya bani ikon iya faɗa mata. Amma zuciyata bugawa take yi sosai, ni kaina hasaso kallon ta da zanyi nace mata zan auri wata nan gaba nake yi, yarinyar nan ƙaramin abu ma babba take mayar dashi balle babba ne yazo da kansa, ya zanyi ni Adnan...?." Hamza yayi murmushi yace, "zaka iya mana, kamar ba kai ba. Baka jin tsoron magana da kowa fa." Ya kalle shi yace, "kai ba wancan Adnan ɗin bane, duk zafin kan wancan, duk iya maganar wancan, duk dakiya da ƙwarin zuciyar wancan babu a wajan wannan. Soyayyar ta tsoron kallon ta nake na faɗa mata wallahi." Huzaifa yayi dariya yace, "wanda zai auri mata biyu a rana ɗaya ai dole ya ajjiye zafin kai." "Hmmm!" Shine abinda yace yana tashi tsaye kafin yace, "bara na bada magani a kaiwa Rumana na dawo." Huzaifa yace, "an gama angon uwar gida Manal, angon amarya Rumana, Sai ka dawo." Bai ce masa komai ba ya fita zuciyar sa babu daɗi amma ya zai yi dole hakan zai aikata ko da baya so.      Lokacin da ya bar asibitin gidan su Manal ya wuce yana zaune a mota yayi mata waya ta ɗauka yace, "Partner zaki iya zuwa mota mu yi magana?." Manal tace, "baza ka shigo ba?." "Ƙanunu kaya ne a jikina kin san ban iya shigowa dasu, gashi urgently ina son magana dake." Manal tace, "to Ina zuwa bara na tambayo Mama." Ya amsa yana kashewa. Jim kaɗan ya hango tahowar ta da abaya kamar ko yaushe, gaban sa ya tsananan ta faɗuwa har ta ƙaraso wajan kallon ta yake yi zuciyar sa na hana shi yin abinda yazo dashi. Kuna goyan bayan Bebi ya fadawa manal kuwa?🤔 BDƘB2P15 Sallamar ta da kulle ƙofar motar ya saka shi jan dogon numfashi tare da lumshe ido, ƙhamshin turaren gyara jiki da ake mata ne ya daki hancin sa, turaren babu ƙarfi sosai yayi sanyi a hancin mai shaƙar sa hakan ya saka ya burge shi har ya lumshe idanun sa bai sani ba. A hankali ya buɗe ido ya kalle ta sai yaga kamar an saka ta a machine an wanke ta hasken ta ya sake fitowa sosai kamar ƴar tsanar roba. Waya ya kunna ya sake haska fuskar ta duk da hasken fitilar motar suka haɗa ido ganin irin kallon da yake mata wanda bai saba yi mata irin sa ba sai tace, "Ina ta gaishe ka baka amsa ba." A sannan ya kashe wayar ya jinjina da kujera yace, "Ina zaki kai wannan kyaun?." Manal ta kalle shi tayi murmushi tace, "gidan ka." Ɗan wara ido yayi ya girgiza kai  yace, "Anya bai min yawa ba?." "Zaka san yadda zaka yi dashi" ta faɗa ba tare da ta kalle shi ba tana kallon hannun ta da ya fara komawa yellow saboda haske. "Ba nace miki in aka miki wannan ƙhamshin sai na saka ki a ruwa har sai ya fita ba?." Manal ta kalle shi kamar zatayi kuka tace, "to yanzu wannan yawa yayi? Saboda kai fa kaɗan ma ake yi min" ta faɗa tana turo masa small lips ɗin ta wanda suke jajaye tamkar na larabawa. Saurin kawar da kai yayi, baya son bada kansa a wajan ta har sai ya aure ta shiyasa yake ƙoƙarin kiyaye duk abinda yazo ransa in suna tare,  kulle ido yayi ya buɗe ya kalle ta yace, "yanzu haka kika wuce kowa yana jin wannan ƙhamshin?." "To ba kai kace nazo ba?." Ya zuba mata ido yana kallo itama haka sai ta janye nata idon tace, "ka daina kallona." Bai ɗauke ido daga kanta ba kallon nata yake yi don in yace bai ji wani abu a kanta a wannan lokacin ba ƙarya yake, ji yake kamar ya jawo ta jikin sa dan ta gama rikita masa lissafi. Kallon sa tayi taga ya canja kamar bashi ba sai kallon ƙurilla yake mata kamar ba shi ba, jikin ta ne yayi sanyi kamar yadda taga na sa jikin yayi. Ta fahimci canji a yanayin sa sosai sai ta sunkuyar da kai bata ce komai ba. Daƙyar ya daure ya sauke numfashi yace, "me kika shirya?." Manal tace, "duk abinda ka shirya." Ya ɗan ɗage gira yace, "kin san abinda na shirya kuwa?." "Ban sani ba, amma nima shi na shirya." Yayi murmushi yana kallon ta yace, "zamu gani." Shiru ne ya biyo baya gabaɗaya ya rasa ta ina zai fara sanar da ita abinda ya kawo shi hakan ya saka shi yin shiru kawai baice komai ba. Manal ta gaji da shirun tace, "kace kana son magana dani." Ya ɗago ido ya kalle ta yace, "ganin ki kawai nake so nayi, babu abinda zan ce miki." Ta kalle shi sosai tace, "amma sai naga kamar da gaske kawai abinda zaka ce ɗin, yanayin ka ya nuna min akwai magana a bakin ka" Ya shafa kansa ya kalle ta yace, "Tabbas akwai, amma na fasa faɗa miki yanzu." Bata ce komai ba tana kallon gaban motar tace, "Shikenan zan iya tafiya? Mama na jira na."  Ya sauke kai ƙasa ya ɗago ya kalle ta kamar zai yi magana sai ya fasa ya canja maganar yace, "to amarya." Manal ta murmusa tace, "ba haka zaka ce ba ango, akwai abinda yazo zuciyar ka ka kawar dashi. Ka faɗa min ko meye ina jin ka." Ya girgiza kai yace, "a bar shi kawai, in kika zama mallakina zan sanar dake, amma yanzu abun babu daɗin ji." Manal ta girgiza kai cikin rashin damuwa tace, "to shikenan." Murmushi yayi kaɗan tace, "zan koma, a gaida Mummy." Kai ya ɗaga yace, "zata ji in sha Allah." Bata ce komai ba ta buɗe motar ta fita ya bita da kallo ganin tana sauri ya lumshe idon sa gabaɗaya ya rasa ƙarfin guiwar faɗa mata abinda ya kawo shi, a haka ya ja motar sa ya ƙara gaba. Manal da sallama ta shiga gida ta wuce falo wajan Mama da Mubeena da suke zaune, ganin ta Mubeena tace, "har kin dawo?." Zama tayi sannan tace, "na dawo, kuma Mama kin san babu abinda yace min. Kawai wai so yake ya gani." Mama tayi ƴar dariya dan ta lura da gaske Manal bata jin kunyar faɗa mata abinda yake tsakanin ta da Adnan tace, "an kusa kai masa ke ai, sai yayi ta kallo har ya gaji." Manal ta kalli Maman a shagwaɓe tace, "Mama naga kamar so kike na tafi ma na bar miki gidan." Mama tace, "so nake mana Manali, ki tafi ki barni da Ummata a kusa dani." Manal ta kalli Mubeena da yake gefe tana dariya Manal tace, "Mama kin daina sona wallahi." Mama tayi dariya bata ce komai. Mubeena tace, "ya shirin events ɗin ne? Wanne da wanne zaki yi?." "Nace kamu nake so Mama tace baza ta je ba, kuma don Allah taya za'a yi  kamu babu Mama?." Mubeena tace, "gaskiya Mama ki je." Mama ta girgiza kai tace, "duk wani abinda ake buƙatar uwa a wajan ga Balaraba nan, amma ni babu inda zanje. Ku yi kamun ku da komai ma amma babu ni a ciki." Manal kamar zata yi kuka tace, "ni in dai babu ke babu abinda zanyi, henna party ɗin ma na fasa." Mubeena tace, "A'a baza'a fasa ba, ko iya shi ɗin zamu yi. Amma Mama don Allah ki je." Mama ta girgiza kai tace, "bazan je a gida min hoto ana yaɗawa a duniya ba, babu inda zanje." "To Mama dan anyi wani abu ne? Naga lokaci ne ko ya kawo ki. Kuma in bakya so sai mu hana yin hoton." Mama ta kalli Mubeena tace, "Mubeena bazan je bafa, bana ra'ayi zuwa kawai." Manal kawai ta fara hawaye tace, "To Mama don Allah haka za'a  yi komai babu me?Maman su Surayya Mama ce amma ba kamar ke ba, haka kawai azo ana kiran ki ace baki zo ba?. Ni dai sai dai kawai a barshi." Mama tayi dariya kawai bata ce komai ba dan kuwa babu inda zata je bazai yu tana gefe a ɓallo mata ruwa ba, yadda ta killace kanta bata son wani ko wata su gano ta har su nemo ta. Haka Manal ta wuni har dare tana ƙunci har Baba ya dawo ya tambaya Mama ta faɗa masa ya zauna yana cin abinci yana dariya yana cewa, "Haba Fatima, Ke kuwa akan wannan kike ɓata rai?." Manal tace, "Baba Mama ce fa tace baza taje b." Baba ya kalli Mama yace, "to a kan me?." Mama tace, "share Manal kawai. Manal tashi kije ciki." Manal ta tashi ta shiga ciki ranta duk babu daɗi. Mama ta kalli Baba tace, "Alhaji an je an gano gidan Manal fa." Baba yana cin abinci yace, "to ya ake ciki kenan?." "Balaraba tace min gidan babba ne kamar yadda muka yi tunani daman, tace babu sama dai a gidan flat house ne, amma a hakan ma falo uku ne a gidan. Gasu tace manya-manya ne sosai ba kamar guda biyu na farko, ɗaya ne bai kai girman su ba. Sai bedrooms guda huɗu suma kasan ba ƙananu bane, ga kitchen da ɗakin mai aiki daga wajan kitchen ɗin. Shine nace bara ka dawo mu ji ya za'a yi." Baba yace, "ma sha Allah. Allah ya sa albarka." Mama ta amsa tace, "Mubeena! Kawo wayar Manal baban ku yaga gida." Ta kalli Baba tace, "Mubeena ce tayi video." Ba jimawa ta kawo wayar Baba yana ganin gidan yana girgiza kai don yayi kyau kai kana gani kasan sabo ne aikin sa ake yi. Ya ajjiye wayar yace, "na gani, yanzu me kike so ayi?." Mama ta juya baya ta ɗauko takarda ta miƙa masa tace, "Gonar jalingo." Baba ya kalli takardar ya kalle ta yace, "Gonar Jalingo?." Mama tace, "eh ita. A siyar da ita a siyawa Manal duk abinda take so. Alhaji ko tsinke Manal ta gani tace tana so a siya mata, su kuma kayan gadon a dinga siyan biyu ita da Mubeena saboda ita lokaci ake jira." Baba ya girgiza kai yace, "Kin san kuɗin gonar nan kuwa?." "Na sani." "A tunanin ki zata yi nawa a yanzu?." Mama tace, "ban sani ba." Baba ya murmusa ya ajjiye takardar yace, "A ƙalla zata kai naira miliyan tamanin zuwa ɗari koma sama da haka, Zahra'u ita kike so ki siyar? Ayi me da kuɗin?." Mama ta sauke numfashi tace, "Ko miliyan dubu ce na amince a siyar a siyi kayan gadon." Baba yayi murmushi yace, "ai nima ban san kuɗin na ta ba, na faɗi dai abinda nake hasashe ne a kai. Amma ko bata wuce ɗari ba zata tsaya a haka saboda tsohuwar gona ce, bishiyun cikin ta ma jarin gaske ne balle ita kanta gonar. Mutanen garin amfana suke da ita sosai, addu'ar da suke miki a duk sanda naje bakya so a siyar da ita ba." Mama tace, "duk da haka dai, meye amfanin kadarar ne Allhaji? Kadara ana ajjiye ta ne saboda in amfanin ta ya taso a kau da ita ayi amfani da kuɗin shine rufin asiri." "Amma na faɗa miki indai kayan ɗakin Manal ne kudin ki na wajena zasu yi basai kin kawar da wannan babbar kadarar ba, kuma nima uba ne a wajan Manal dole zan sauke haƙƙin ta da yake kaina matsayina na uba." Mama tace, "a'a Alhaji, wallahi nairar ka biyar bana so tayi ciwon kai, Ba wai dan na raina ko baka da abinda zaka min ba, kai kasan bazan taɓa raina abinda zaka bani ba kafi kowa sanin hakan. Iya riƙe min yara da kayi tamkar naka yafi min komai wallahi. Ka tsaya akan tarbiyayyar su, makaranta ma ta kuɗi ka kai su ba ta gwamnati ba, ka saka Mubeena a jami'a kayi mata komai daga baya ta watsa maka ƙasa a ido. Baka gajiya ba ka cigaba da bibiyar tarbiyar ta, ka karɓi auren Manal kayi bincike akan wanda zata aura ka bashi auren ta. To da me zan biya wannan? Dan bani da tausayi sai nace kuma Ina jira kayi musu kayan ɗaki? Lalala in ji larabawa." Baba yace, "Ai na faɗa miki bana kallon yaran nan a matsayin bani na haife su ba, kullum kallon yarana wanda na haifa nake musu wallahi. Ta ko Ina aka zaga ni mahaifin su ne dan na ɗauki nauyin kula dasu ai mahaifin su ne ni haƙƙina ne, kuma dole na yi duk abinda uba yake yiwa yaran sa a lokacin da za'a aurar dasu." Mama tayi murmushi tace, "na san da hakan. Amma ni na yafe hidimar biki ai da yawa  wani abun sai kayi, amma batun kayan ɗaki Allah ya hore min da ace bani dashi ne sai ka taimaka min, Amma Ina dashi kafi kowa sanin hakan." Baba yace, "ni dai bazan bari ba. Ina jin ki cigaba da waccan maganar." Mama tace, "a siyar da rabin gonar to, ni abinda ya saka nake so a siyar gabaɗaya kaga abubuwa tsada suke yi yanzu, babu abinda yake sakkowa shiyasa nake so har Mubeena a haɗa a siyi komai in yaso a kai gidan Balaraba a ajjiye. Ko in an kwana biyu da aurar da Manal ɗin a kai gidan ta ajjiye kayan, in Allah ya kawo mata miji da yace kule muce chass." Baba yace, "wannan gaskiya, amma za'a kashe kuɗi da yawa." Mama ta tarin numfashi sa tace, "A kashe, wallahi ko kaf ne zasu ƙare ayi. Meye burin nawa a duniya in ba wannan ba? Me zan yi da kadarar ma to? Dan su take ajiiye daman lokacin ta yazo sai a kawar da ita. So nake yadda suka kawo lefe na alfarma kaya sama da kala ɗari a kai musu kayan ɗaki na alfarma, yadda Manal take son kitchen a ƙawata mata shi daidai da ra'ayin ta, ko tsinke Manal ta gani tana so a siya a kai mata. Sannan ayi mata gara ta sarakai a kai ta da ita." Baba yace, "Shikenan Zahra, za'a yi abinda kike so in sha Allah." "Yauwa Allah ya amince. So nake ayi komai cikin bajinta, ɗan babban gida ta auro dole mu nuna musu mu ma ƴan manya gida ne." Baba yayi murmushi yace, "Wannan biki dai shi ake kira da bikin ƴar gata." Mama tayi dariya kawai bata ce komai ba Baba ya tashi yace, "bara na shiga gida na fito, ki ajjiye takardun sai an samu masu so sai na karɓa." "Aa, in ka dawo ka adana su a wajan ka ni sun bar hannuna." Baba bai ce komai ba ya fita. Mubeena da Manal da suke zaune a falo suna jin duk abinda ake cewa tsakanin Mama da Baba Mubeena ta kalli Manal tace, "Manal kin ji abinda naji? Wai wacece Mama ne? A Ina ta samu kadarar naira miliyan ɗari?." Manal tace, "nima abin ya ɗaure min kai, Wacece Mama? Meyasa ta ɓoye mana asalim ta?." Mubeena tace, "abinda yake ɗaure min kai kenan, duk yadda akayi Mama daga wani babban family ta fito." Manal tace, "wata rana zamu sani in muna da rabon sani din, amma abin yana bani mamaki, gonar naira miliyan ɗari kuma mallakin Mama?." Mubeena ta girgiza kai tana ji a ranta dole ta nemo wacece Mama. BDƘB2P16 Bebi a haka ya koma gida gabaɗaya ya rasa abinda zai yi, zuciyar sa yana son faɗawa Manal maganar Rumana amma ya kasa. Yana ajjiye motar yaga Mama a harabar gidan da alama ta rako ɓaki ne, ganin ta ganshi sai ya wuce ɓangaren ta da sallama aka amsa suna zaune sun baje kaya ana dubawa. "Yaya Bebi sannu da zuwa." Ƙanwar Rumana ta faɗa jin abinda tace sai dukka cousin ɗin nasa da suke zaune kowa ya faɗi abinda tace. ya ɗan ɓata rai yace, "Waye Bebi?." Sai suka yi dariya a tare suka ce, "Sannu da zuwa Yaya Adnan." Sai ya ɗan saki fuska kaɗan yace, "Ya ku ke?." "Lafiya lau." Ɗaya a ciki tace, "Ya shirin biki." Har yayi gaba wajan Mama yace, "gashi nan kuna yi." Suka yi dariya suka cigaba da duba ankon da zasu saka ranar dinner. A zaune ya tarar da Rumana tana shan tea Mama na amsa waya, tunda ya shiga ta kafe shi da idanu tana kallon sa cikin so da ƙauna, ganin haka sai ya tako inda take yace, "Ya jikin naki Ruman? Ina fatan kin samu lafiya? An kawo miki maganin?." A lokacin Mama ta gama waya tace, "ya kawo maganin, tunda ta sha ta ɗan samu sauƙi har tea tace a kawo mata." Ya girgiza kai yace, "ai yana da kyau Mummy, in zata dinga sha kullum sau ɗaya zata ji daɗi sosai" ya kalle ta yace, "yana da rules tablet ɗin nan Ruman, kar ki sha sama da ɗaya. Then da safe ake sha kar ya wuce sha biyu na rana." Rumana tace, "in sha Allah zan kiyaye. Na gode sosai da kulawa." Ya dan saki fuska kaɗan yace, "you deserve it." Ya kalli Mama yace, "Mummy yunwa nake ji wallahi, me zan samu?." "Akwai wake da shinkafa shi suka yi ɗazu." Ya ɗan wara ido yace, "Mummy a daren nan? Gaskiya Mummy a san ya za'a yi dani." Mama tace, "kaje ka girka, ka san suna wannan hirar babu wacce zata so yi maka girki. Kuma daman sune suka yi na ɗazun." Ya sauke numfashi yace, "Shikenan ƙyale su, bara naje sai nayi order a kawo min." "a wajan mutuniyar taka Leemers delicious ɗin? Nasan baka da wacce ka ke siyan abinci ta sai ita. Ga dai restaurant ɗin ku kai da Usman amma baka ma zuwa ka bar komai a hannun ɗan uwan da Farida." "Allah Mummy wannan leemars delicious ɗin nan ta iya abinci sosai, especially wannan funkason da mandi rice, Mummy ai kin taɓa cin mandi rice ɗin ta kema kin sani. Kuma batun restaurant wallahi mantawa nake dashi, shiyasa Usman yace ai sun kore ni siye hannun jari na zasu yi." Mummy tayi murmushi tace, "To ke Rumana sai ki dage kina ji ta iya mandi rice da funkaso, ki koya a wajan ta in zata yi classes kema ki dinga masa. Dan Mimi ta taɓa shiga online classes ɗin ta, in tayi mandi gidan nan kwana yake yana ƙhamshi." Rumana ta murmusa tace, "Yanzu ma zan masa mandi rice Mama" ta faɗa tana tashi tsaye. Ya kalle ta yace, "Ruman ban saka ki ba, ki bar shi na gode." Sai tayi sak alamun bata ji daɗi ba Mama tace, "ya zaka gwale ta kuma?." "A'aMama ba haka bane, bata da lafiya taya zata yi girki?. Bata san shiga waje mai hayaƙi zai iya sakawa ciwon ƙirjin ta ya tashi ba?." Mama ta kalle ta tace, "to kin ji abinda yace" ta faɗa tana kallon ta da murmushi dan taji daɗin abinda yace. Rumana tace, "Mummy zan iya, nidai ya barni nayi masa kawai." Mummy ta kalle shi tace, "tunda kaji tace zata iya ka barta kawai." "Mummy I'm so worry about her sefety, taya zan bari tayi girki bayan bata jin daɗi?. In wani abun ya same ta bazan ji daɗi ba." Rumana farin ciki ya mamaye zuciyar ta fuska a sake tace, "Zan iya Yaya Adnan." Ya kalle ta suka haɗa ido murya a ƙasa yace, "you're sure?." "Yes, let make you see" ta faɗa tana wuce su sai kuma ta tsaya tace, "Mama ina mandi spices ɗin suke?." Mama ta ɗaga kai ta kalle ta tace, "ki tambayi Mimi." Amsawa tayi da to ta fita tana murmushi Ganin farin ciki akan fuskar ta Mama ta kalle shi tana murmushi tace, "Allah yayi maka albarka, yadda ka ke sakata dariya a yau ya burge ni sosai. Allah ya baka abinda ka ke so." Addu'ar da tayi masa yaji daɗi sosai, ya lura in dai akan ta ne yan shan addu'a.  yayi murmushi yace, "Amin Mummy." Daga haka ya fita zuwa falon, Lubna da take zaune cikin su  ganin ya fito tace, "Yaya Adnan." Jin maganar ta sai ya tsaya cak ya kalle ta ya saki fuska sosai yace, "Lubna." Tana murmushi tace, "Yaya muna zancen dinner har yanzu baka ce komai ba." Ya ɗage gira tare da kama ƙugu yace, "wacce dinner kuma?." Kausar tace, "ta bikin ku mana Yaya." "Oh har dinner za'a yi kenan?." Suka kalli juna jin abinda yace Mimi tace, "Yaya har Abba an faɗawa yace ayi masa list na komai a kai masa, har mun zaɓi event center da za ayi dinner a ciki. Jira muke ka faɗa mana ranar da Anty Manal zatayi kamu dan mu yi arrenging komai." Ya kalli Mimi yace, "yen yen yen yen! Kin iya tsara biki kamar wata event planer. Daman a nan kika fi auki indai a maganar kiɗa ne. Sai ku yi ai" yana gama faɗar hakan ya fita ya barsu basu san matsaya ba ya wuce zuwa ɓangaren sa. Wanka yayi canja kaya zuwa dogaye na bacci masu ta santsi kalar baƙi da ash ya fito ya zauna suna waya da Huzaifa kafin ya kashe ya kira Manal bata ɗauka ba ganin haka sai ya ƙyale ta ya ajjiye wayar ya kunna tv yana kallo. Wani American film yake gani ba dan yana fahimta ba, ganin ana romancing a film ɗin sai Manal tazo ransa yayi ƴar dariya yace, "yarinyar nan wataƙila abinda take gani kenan ya saka ta nacewa American series."  Kiran ta yaga yana shigowa sai ya katse kamar ko yaushe ya kira ta ta ɗauka da sallama yana amsawa yace, "meye ma kika ce min sunan American series ɗin nan da kike gani yanzu?." Manal tace, "Me zaka yi dashi?." "Gani nake so nayi, kin ce yayi kyau amma na manta sunan da kika faɗa min." Manal tace, "tunda ka manta shikenan sai ka kalli wani." "A'a wancan nake so, something virgin ko?." Manal tace, "nima na manta." Yayi ƴar dariya yace, "to naji, bani sunan wani na kalla." "To wai me zaka yi dashi kai da baka kallo?." "Who told you bana kallo? Ina kallo sosai kuma yanzu irin naki nake son gani." "Wannan aikin naka ma taya zai barka kallo?." "Ina yi in na samu lokaci." Tayi murmushi tace, "kawai ka haƙura."  Yayi dariya yace, "kawai baza ki faɗa ba, amma ki sani da zarar kin shigo gidana tare zamu dinga kallo." "Wai Ina kaga lokacin kai da kana asibiti?." "Waye yace miki bani da lokaci wai?." "Kai dai ayi shiru kawai, na san yanzu ma za'a maka waya ace emergency." Yayi murmushi yace, "to laifi ne?." Bata yi magana ba yace, "Ki yi fatan kar ranar da aka kawo ki ma na fita aiki." Manal tace, "Hmmm!." Abinda tace kenan sai yace, "baki ce komai ba." Manal tace, "ai ba emergency ba ko meye babu wanda ya isa. Ka san me? Ni fa bazan yi toleting wannan fitar ba, gwara ma ka sani." Yayi dariya yace, "Allah ko Manal?, kice akwai abubuwan da kika shirya wanda zaki saka na kasa fita." Sai tayi dariya itama bata ce komai ba. Sallamar Rumana da amsawar da yayi ne ya saka shi bai ce mata komai ba amma Manal tana jin abinda ake yi Rumana tace, "Yaya Adnan ga Mandi rice ɗin naka na kawo maka" ta faɗa tana ajjiyewa tare da zama. Bebi yace, "sannu da aiki, kin kyauta." "Kina ji, zanci abinci in ban fita ba zan kira ki." Manal tace, "kawai sai da safe." Yayi murmushi yace, "Au haka ne? Zan baki mamaki yau babu inda zani." Rumana da yake zaune tace, "bani ita mu gaisa." Bai hana ba ya miƙa mata wayar kafin ta karɓa ta kalli screen ɗin wayar taga life partner ya saka mata ga hoton ta da yake kai da alama in dai ta kira hoton ta ne zai fito, gaban ta ya tsananta bugawa ta saka suka gaisa. Yaji dai tana faɗa mata sunan ta Rumana daga haka ta miƙo masa wayar ya karɓa yace, "I will call you back, a gaida Mama" yana faɗa ya yanke wayar ya ajjiye. Rumana tace, "Tana da kirki kamar ta sanni ina jin sautin murmushin ta, ga voice ɗin ta mai daɗi." Bai ce komai ba ya jawo abinda ta ajjiye ya buɗe ya kalli abincin ya kalle ta yace, "a daren nan kika yi wannan girkin?." Tayi murmushi tace, "ga zahiri ka gani." Ya zuba a plate ya barta a kan table ya tashi  ya bar wajan ya wanko hannun sa ya dawo yace, "kin san cin mandi yafi daɗi da hannu." Tayi murmushi kawai ya fara ci ba laifi da daɗi, amma shi tunda Leemars delicious ta shagwaɓa shi da mandi rice ɗinta wallahi baya jin daɗin ko wacce sai wacce yake siya a wajan ta ita, ta ta ƙhamshin ma is different kamar kana saudia ko Dubai kana buɗe pack ɗin ƙhamshin zai dake ka. Yaci kuwa sosai ko dan taji ɗaɗi ya kalle ta yace, "yayi daɗi sosai Ruman, na gode." Tayi murmushi cikin jin daɗi tace, "nice da godiya da na bayar aka ci." Ya sake yin murmushi yace, "dole aci ai ko ba a so." Ƙarar shigowa saƙo wayar sa ya saka shi ɗauka yana dubawa yaga Manal ta rubuta, _bazan tsaya jiran ka ba nasan asibiti zaka tafi, bacci zanyi ka kwana lafiya partner._ Murmushi yayi a bayyane yace, "Manal kenan." Tunawa da Rumana a wajan sai ya kalle ta ya ajjiye wayar, ganin haka sai ta tashk tace, "to Yaya Adnan sai da safe." "Ki kwana lafiya." Ta amsa da amin ta fita shi kuma ya tashi ya koma ɗaki.   ********* "Wallahi Kamal na gaji, na gaji da abinda ka ke sakawa nayi. Bazan zo ba wallahi kayi duk abinda zaka yi." Kamal da yake jin ta a waya yayi dariya yace, "kar ki damu Maryam, kar ki zo ni kuma zan tabbatar da yau video ki ya cika social media wallahi." Maryam na hawaye tace, "kaje ka yi, ka yi ɗin sai me kayi nace. Sai me dan ka yasa ni a duniya sai me nace? Ai ba nice farkon wacce aka fara sakawa ba, haka zalika ba nice ƙarshe ba. Naa gaji da wannan wahalar da ka ke saka ni, na gaji da saɓon Allah da kake saka ni aikatawa ta dole, babu inda zan zo wallahi. Ba gobe ba ko jibi ne wallahi bazan zo ba, in kaga dama ka yi abinda yafi haka" ta faɗa tana kuka sosai. "Ke da wa kike magana kina kuka!." Abinda taji ance daga bayan kenan,  jin muryar Adnan gaban ta ya faɗi sosai, zuciyar ta ta shiga rawa da fargabar Allah ya sa ba ji abinda take faɗa ba. BDƘB2P17 Ganin yadda take kallon sa a firgice ya saka shi kallon ta sosai yana nazarin ta dan ya tabbatar akwai abinda take ɓoyewa yace, "da wa kike waya kike kuka? Waye yake tilasta ki? Me yake faruwa kika gigice haka?." Hawayen ta share ta kalle shi tace, "babu komai" ta faɗa zata wuce ya riƙe hannun ta yace, "ya zaki ce babu komai bayan gashi nan kina zubar da hawaye? Ga ki nan a gigice da alamun tashin hankali a tare da ke ki ce min babu komai?. Tun daga ɗaki nake jiyo amon maganar ki a nan, kar ki ɓoye min abinda yake faruwa ki sanar sani. Meye yake faruwa?." Kallon idon sa take yi tana so ta faɗa masa gaskiya amma zuciyar ta na faɗa mata shi fa ƙanin ki ne ba yaya ba ki share kawai, dan a ganin ta akwai raini mai girma da kuma zubar da mutunci indai ta faɗa masa damuwar ta. Hannun ta ta zame a hankali tace, "babu komai, Mahaifiyar ƙawata ce ta rasu shine ake sanar dani, babu komai sai da safe" tana faɗa ta wuce da sauri bata ma bashi damar magana ba. Da mamaki ya bita da kallo dan bai amince da abinda take cewa ba, ya koma ɗaki zuciyar sa duk babu daɗi akan damuwar ta duk da bai san me yake faruwa ba. Waya ya ɗauka ya kira ya saka a speaker yace, "kana bibiyar min Kamal?." "Sosai ma kuwa, kwana biyu ko ganin sa bana yi, dana tambaya sai akace ya kwana biyu bashi da lafiya." "Ko me ka gani sabo ka sanar dani." "İn sha Allah" yana faɗa ya yanke wayar ya ajjiye a gefe. "Dawa take waya haka? Waye yake takura mata?." Iska ya furzar domin bashi da amsa, ya tashi ya shiga ya kwnata amma zuciyar sa cike da abinda yake damun Maryam wanda bai sani ba.                        Bayan kwana biyu. Da yamma ya shiga wajan Mama ya tarar da ita da ƙanwar ta Maman su Rumana kenan wacce suke kira da Ammi da kuma Yayar ta wacce ake kira da Umma. Ganin su sai yayi murmushi ya shiga ciki ya zauna, gaishe su yayi suka amsa Umma, "Ango ya shirye-shirye?." Ya murmusa kaɗan yace, "Alhamdulillah" ya kalli falon yaga babu Mimi ya kalli Mama yace, "Ina yaran suke?." Mama tace, "suna can gidan Farida, sun ce min na faɗa maka sun tafi." Umma tayi dariya tace, "ai sai an musu uzuri yanzu, bikin Mimi guda ba zama." Ammi ta kalle shi tace, "kai wai haka za ayi bikin nan  muna iyaye babu wanda yasan amaryar a cikin mu?." Mama ta taɓe baki tace, "ɓoye ta yake yi ai, sau ɗaya aka haɗa mu a waya muka gaisa shikenan. Har cake ta kawo min, aka kuma kawo min meat pie ne ko fish pie shima ba'a bani lambar ta bama balle na gode mata." Bebi yace, "Mummy ni ba ɓoye ta nake ba." Mama tace, "kai dai ka sani, ga biki yazo ai dole a ganta." Ammi tace, "ni kam baza ka tafi ba sai ka nuna min hoton ta na ganta, ko me zaka yi yau sai naga hoton ta kar ma kace baka dashi." Yayi murmushi daman yasan halin Ammi kamar yayar sa take tunda tace sai ya nuna sai ya nuna zata ƙyale shi, hakan ya saka ya ɗauko waya a aljihu ya dubo wanda yayi mata a mota ya miƙa mata wayar ta karɓa. Ammi tace, "la la la! Dole a dinga ɓoye mana ita, ma sha Allah wannan kyau kamar yar aljanu?." Umma tace, "kema kamar baki san Adnan ba? Tun yana yaro yake da son abu mai kyau. Bani ita na gani, muna iyaye mun ƙare da ganin sirika a waya." Ammi ta miƙa mata wayar ta kalla tace, "A'a wannan ai Manal ce ko?." Kallon sa tayi shima ya kalle ta yace, "itace." "Ai na santa, Ina yawan ganin ta gidan su Hajiya Balaraba wacce take min turaren wuta." Mama tace, "Mai turaren wutar nan dai taki?." "Ita fa Hauwa, da wahala naje gidan ban ganta ba ko bata nan naje ina zaune zata shigo. In ban ganta ba har tambaya nake saboda yarinyar akwai fara'a ga saurin sabo" ta kalli Bebi tace, "kayi haƙuri amma akwai ta da magana, surutu kamar an saka mata battery. In tana magana kallon ta nake kamar ƴar tsanar roba, dan gaskiya tana da kyau da haske. Amma naji daɗi sosai, dan yarinyar akwai girmama mutane." Mama tace, "ba kyawun fuskar ba kyan hali." Umma tace, "wallahi tana dashi, in kin ji yadda Balaraba ke yabon ta zai baki mamaki." Wayar ta miƙawa Mama ita kuma taƙi karɓa tace, "ai nace bazan ganta ba sai an kawo ta, tunda an yi min rowar ta bazan gani ba." Umma ta miƙa masa wayar tana dariya tace, "to ɗan lelen Mummy kaji me tace." Ya karɓa yana ɗan murmushi Umma ta kuma cewa, "in kin kwantar da hankalin ki Hauwa ke da za'a kawo miki ita har gida kuma matsayin yar ki?." Shi dai bai ce komai ba ya fita, amma yaji daɗi da Umma ta san Manal ko babu komai ya san zata faɗa Mama halin ta koda guda ɗaya ne.       Yana fita aka yi masa waya sai ya zauna a mota yana amsa wayar a lokacin su Mimi suka dawo gidan a mota. Nabila ƴar Umma itace take tuƙa motar ganin sa sai suka ja suka tsaya dan su yake kallo amma waya yake yi Kausar tace, "ke kallon mu fa yake." Mimi tace, "bazai ce mana komai ba, ai ya san mun yi busy." Su ka yi dariya Mimi ta kalli Lubna tace, "dake yake ji yanzu a cikin mu, don girman Allah in mun je ki taimaka ki masa maganar ranar bikin nan, abu saura kwanaki kaɗan amma an kasa samun matsaya kullum ana ta abu ɗaya." Lubna tace, "kar yayi min faɗa." Nabila tace, "bazai miki ba, mu je." Suka fito suka tunkare shi kai tsaye, suna zuwa wajan suka je wajan sa yana kashe wayar a lokacin suka gaishe shi ya amsa kafin Lubna tace, "Yaya Adnan don Allah ka haɗa mu da Anty Manal a waya zamu tambaye ta wacce ranar ne na event ɗin ta" kallon ta yayi sai ta ɗan tsaya da maganar kafin tace, "kaga lokaci yana tafiya. Kar mu je mu saka rana daidai da ranar da zata yi event." Shiru yayi musu kafin su ga ya miƙa mata wayar ashe kiran Manal yayi, ta karɓa tana kallo su suka kalli juna ana munafurcin sunan da ya saka mata da ido, Manal ta ɗauka Lubna tace, "Assalamu alaiki Anty manal." Daga can ɓangaren Manal tace, "Wa'alaiki Salam Anty mai magana." Da yake a speaker ta saka sai suka yi dariya Lubna tace, "Sunana Lubna ƙanwar Yaya Adnan, a tare dani Akwai...." Sai tayi shiru in wannan ta faɗi sunan ta sai wannan ma ta faɗa, sai wannan ma ta faɗa Manal tayi dariya tace, "Nabila, Mimi, Lubna, Kausar, Fadila, Humaira, Ummi, Yusra duk ya ku ke?." Suka amsa suna dariya jin a yadda ta faɗa kafin Lubna tace, "Muna ta so Yaya Adnan ya tambayar mana ke ranar ever ɗin ki, kinga lokaci yana tafiya har yanzu bamu tsayar da date ba." Manal tace, "Allah sarki, ai ni event ɗina guda ɗaya ne kawai, combine kamu da henna day ranar Wednesday." Mimi tace, "Yauwa Anty Manal Allah yayi miki albarka. Sai kuma dinner ranar Friday ko?." Manal ta amsa suka dinga tambaya ta suna ta hira kamar sun saba sai da ya musu magana sannan suka bashi wayar, yana karɓa ya yanke kiran bai ce komai ba ya kulle motar kawai ya fita. Kamar haɗin baki suka ƙyaƙylƙyale da dariya a tare suka yi ciki ana cigaba da shirya yadda biki zai tafi.          An shiga satin biki ya a lokacin ya ɗauki hutu a wajan aiki yana shirye shirye, gidan amarya Manal an gama haɗa komai, an zuba kaya na alfarma, babu ɗakin da ba'a zuba mata kaya na ƴan gayu ba. Ko ita Mimi baza ta faɗawa Manal kaya masu kyau da tsada ba, dan an kashe kuɗi an ƙawata mata gidan komai yayi yadda ake so.           Ranar tuesday aka fara da event ɗin Mimi aka yi ƙauyawa day, ranar wednesday aka shirya na Manal a gidan Anty Khadija Yayar Surayya, da yake babban gida ne akayi decoration mai kyau wajan yayi kyau sosai kamar bikin wata babbar mai kuɗin. Shigar atamfa Manal tayi ɗinkin doguwar riga aka yi mata mayafi mai adon atamfar a jiki, ba wata gayya sosai sai tarin ƙawaye ƴan makaranta dan ƙawaye. Mubeena ma sun fi yawa a wajan. Abin yayi kyau sosai an yi hotuna da video yanayin fuskar Manal da yake da kyau nan da nan event ɗin ya fara trending a social media. Washe gari Manal babu abinda suke yi kamun Mimi akayi ita tana gida kamar ba biki ake a gidan ba babu wasu mutane balle ace da ƴan mata wanda zasu kwana kamar yadda aka saba. Mama ta kalli Manal ɗin da tayi shiru tana kallon wani wajan daban tace, "ke tunanin me kike yi ne?, tun ɗazu nake miki magana amma bama kya jin abinda nake cewa, me yake damun ki?." Ta kalli Maman kamar zata yi magana sai ta fasa kawai sai ta fara kuka ta kwanta a jikin Mama tana kuka sosai, sai ta raunana zuciyar Maman amma bata yi kuka ba ta dinga rarrashin cikin kalamai masu daɗi har ta samu ta daina kukan ta ɗago ta dafa jikin ta tace, "ko kefa Manali na, Ina Yayar ki? Baza su je bikin ƙanwar ta sa ba?." Manal tace, "Wai baza su je ba." Mama tace, "sun huta, tashi kije ki huta yau ce fa kawai ranar hutun naki." Manal ta koma jikin Mmaan ta kwanta sai ta ƙyale ta tayi shiru tana tuno lokacin nata auren da irin abubuwa da suka faru. Itama Manal mamaki take wai da gaske auren ta ake yi, abin ganin sa take kamar a mafarki musamman in aka ganta akace amarya sai taji wani iri. Ranar friday bayan sallar juma'a a babban masallacin cikin gari aka ɗaura auren Mimi da Tahir, a masallacin Murtala da yake zoo roaf aka ɗaura auren Adnan da Manal. Ɗaurin auren ya tara mutane sosai manya, gwanoni na garuruwa sun zo an yi damu, an cika sosai daga nan wani babban event center aka wuce akayi reception wanda Daddy ya haɗa a madadin Abba da baya ƙasar. Bayan an tashi daga taron reception ne ango da abokan sa Hamza da Huzaifa da wasu guda aka tafi gidan su Manal domin yin hotuna kamar yadda aka saba yi. Manal tana gidan su Surayya kasnacewar babba ne shi sosai tana zaune cikin jan lace da mayafi, yayi mata kyau sosai an mata ɗauri an ja shi baya kaɗan baƙin tashin ta ya bayyana ta gaba. Bata yi make up ba amma in ka kalle ta sai ka sake kallo saboda yadda tayi kyau sosai kamar a sace ta a gudu. Bata ma san sun shigo gidan ba sai da taji hayaniya a gidan da zuwan Mubeena tana ce mata ga ango nan haka kawai sai gaban ta ya faɗi sosai hawaye suna ciko mata idanun ta. Tana nan zaune bata motsa ba gaban ta yana faɗuwa taji an tsaya a a kusa da ita, hawayen da suke idanun ta suka sakko kan kuncin ta, kukan na ƙaruwa a hankali har ya kai ga shi da yake kusa da ita yana jin sautin sa. Bebi yana tsaye yana kallon ta yana murmushi kafin ya zauna a kusa da ita, ya riko hannun ta duka biyun a a karo na farko tun fara soyayyar su ya miƙar da ita tsaye yana kallon fuskar ta ita kuma tana sunkuyar da kai ƙasa tana kuka. Hankici ya ɗauko a aljihun sa ya saka yana goge mata idon ta a hankali yana cewa, "kuka ba naki bane Manal, we're married now, ni mijin ki ne ke matata ce, so ki ajjiye kukan zuwa anjima in aka kawo min ke  zan san yadda zanyi dashi." Hotuna kawai ake musu ana ta yaba dacewar su da kuma nutsuwar angon dan bashi da rawar kai kamar wasu angwayen. Kasancewar akwai dinner a gaggauce aka bar gidan don ta shirya shima ya shirya. A can gidan su Adnan ma ɓangaren Mimi haka ne ya faru, anyi hotuna duk da gidan babu mutane sosai kasancewar sai asabar Mama zata yi yinin ta. Bayan tafiyar ango da abokan sa aka fara shirye-shirye dinner gagaruma wacce aka shirya a daren ranar juma'a. make up artist duk sun zo aka fara yi ko wacce da wacce zata yi mata. Rumana na zaune tunda ta tabbatar an ɗaura auren Manal da Adnan take cikin wani yanayin mara daɗin gani, zafi zuciyar ta take yi ga jikin ta yayi mugun zafi har in ka kalli idon ta zaka iya gane bata jin daɗi. Mama ce ta shigo ita da Umma ganin ta zaune Mama tace, "Rumana baza ki make up ɗin ba?." Kallon Mama tayi Mama ganin yanayin ta tace, "innalillahi! Rumana lafiya?." Rumana ta nuna ƙirjin ta tace, "Zafi yake min Mama." Mama ta zauna kusa da ita tace, "Subahanallahi! Tun yaushe?." Kai take girgizawa sai kuka da ta fara a lokacin, ta rungume Mama jin yadda jikin ta ya sake yin zafi hankalin Mama ya tashi sosai tace, "Ina waya ta na kira Bebi?." Kausar ce ta shigo a lokacin Mmaa tace, "Kausar kira min yayan ku yanzu a waya da gaggaawa, kice nace yazo." Kausar ta ɗan yi turus jin abinda Maman tace  amma ba yadda zata yi ta kira shi bai ɗauka ba ta faɗawa Maman.  Mama tace, "kira shi da wayata." Umma da take tsaye tace, "Ina maganin ta? Tunda kin ce min tana shan magani shi ya kamata ace ta sha ai, shi da yake cikin jama'a  yanzu Ina shi Ina zuwa nan?." Rumana ta nuna maganin a gefe aka bata ta sha tana jikin Mama har lokacin, Mama ta kalli Umma itama ita take kallo a lokacin Ammi ta shigo tana neman Mama, ganin halin da Rumana ta ciki sai kawai ta fita. Rumana na jikin Mama a kwance har tayi bacci sannan suka fita.        Manal ma da lafiya ciwon kai ta wuni dan ta tace ta fasa zuwa dinner ɗin su Mubeena ne suke bata ƙarfin guiwa, a haka aka tafi wajan mai make up akayi makeup mai kyau ta shirya cikin gown brown colour, an mata ɗauri wanda ya kwanta aka ɗora mayafi dogo a kan ɗaurin, tayi kyau sosai kamar ka ɗauke Manal saboda kyau. Duk Mubeena ce take tsara komai dan itace ta san harkar ƴan gayu, ai kam Manal tayi kyau baza ka ce ita bace duk da bata da walwala, fuskar nan mai yawan murmushi babu murmushin. Sai bayan i'sha ango yazo ɗaukar amarya a tafi dinner, Bebi ya yaba da kyaun da Manal tayi, bai taɓa ganin ta a shigar da ya ganta ba hakan ya saka tayi masa kyau sosai fiye da tunanin sa. A haka aka fara dinner aka fara gabatarwa cikin tsari wanda ya burge kowa, kai da kaga wajan ma da abinda aka tanadar kasan naira tayi kuka. Kowa yabon kyaun Manal yake musamman in aka ga Mubeena akace Yayar ta ce sai mutane suce anya ba halfcast bane saboda kyau?. Duk wani abu da ake yi na Maman amarya Maman su Surayya ce take yi, tayi kara sosai tayi liƙi kamar itace Maman nata da gaske. A haka aka yi dinner aka gama kowa yaga dai a ranar Manal wanda basu san ta bama sun santa.       Washe gari Asabar ranar za'a kai amarya Manal, tun safe take kuka tayi gaji ta huta ta cigaba. Fuskar ta tayi ja musamman hancin ta, kana kallon ta ka san kuka tayi ko take yi. Sosai kanta yayi mugun zafi zazzaɓi ma ya rufe ta saboda tsabar kuka, babu abinda take hangowa sai rabuwa da Maman ta a daren ranar. Ana ta hidimar yini ana ci ana sha abinci sai wanda ka ke so, kowa mamaki yake yi ganin bajintar da ake yi dan sa guda aka yanka a bikin, shiyasa kowa da nama yamke cin abinci. Gidan Baba kam babu su a hidimar, suna daga gefe suna gulma da yaran su, ba dan Baban bama da baza su zauna ba dan a duniya basu ga abinda Mama zata yi so sota ba. Tun bayan la'asar aka fara yiwa Manal nasiha tafiya gidan miji tana kuka, ji take kamar a fasa auren kawai ta huta, ita ta fasa tafiya ta barta a barta da Maman ta kawai. Da aka kai ta wajan Mama kasa ce mata komai tayi, Manal tana kwance a jikin ta tana kuka kamar wacce aka yiwa rasuwa, itama kanta hawaye take dan rabuwa da Manal abu ne mai wahala a wajan ta, amma ya zata yi aure tayi wata ran ma barin duniyar zata yi. Manal ta riƙe Mama sosai tana kuka na fitar hankali, har ta jawo attention ɗin mutanen biki da su Mamy da suka zo ɗaukar amaryar. Daƙyar Maman Surayya ta iya cire ta daga jikin Maman, daman kowa yasan za'a yi haka a tsakanin su, aka fitar da Manal daga gidan nan ita kanta Maman kuka tayi sosai da ta tabbatar Manal dai ta tafi gidan mijin ta, ji take kamar sun rabu kenan baza su sake haɗuwa ba. Manal kuka take sosai Maman Surayya na aikin rarrashi tana yi mata magana amma ta kasa dainawa, har Mamy da matar Dadday sai da suka dinga bata baki amma Manal ta kasa daina kuma a haka aje gidan su Bebi. Gidan a cike saboda suma ana hidimar tafiya kai Mimi ga ƴan biki aka shiga da ita wajan Mama, a nan suke zaune gabaɗaya da Mama da kuma Mamy da suka shigo tare don karɓar sabuwar ƴa da Allah ya basu.       Tana cikin lafaya fara aka zaunar da ita a kan carpet aka fara yi nasiha daga aka yi raha da wasa da dariya kafin su tashi a kai ta gidan Daddy a madadin Abba shima ya mata nasa nasihar aka wuce da ita zuwa nata gidan.                Rumana tana kallo aka fita da Manal daga falon Mama ta lumshe ido tana hawaye, shikenan ta tabbata dai Manal matar sa ce a yanzu, ita kam tasan babu abinda zai yi da ita tunda ya auri wacce yake so. Kuka take wanda yaƙi tsayawa tunda aka fara bikin, ta wuce ta ɗauki maganin ta tasha tana kuka sosai mai tsuma zuciya.     Gidan Manal babba ne sosai amma flat house ne babu sama, duk wanda yasan Bebi yasan baya ra'ayin gida mai sama yafi son sa haka, hakan ya saka ya tsara nasa babu sama amma yayi kyau yaji haske da fulayoyi ya kuma burge mutane sosai.  Su Mubeena ne da Bily da Surayya kawai a gidan Maman su Surayya dasu Inna da aka rako Manal ba dan anso ba aka shigo da ita gidan suka zaunar da ita a falo har lokacin kuka Manal take. Surayya ta koma kusa da ita a tausashe tace, "haba Manal, kukan ya isa haka tun safe har yanzu kina abu ɗaya? Anyi i'sha fa." Maman Surayya tayi murmushi tace, "ƙyale ta Surayya, yanzu ku saka ta tayi sallar magriba da i'sha." Daƙyar ta iya tashi saboda jiri suka raka ta banɗaki, ana ta yabon gidan saboda kyau amma ita bata ma fahimtar maganar su balle taga gidan,alwala tayi ta dawo falon tayi sallah ta kwantar da kanta kujera ta ɗora daga inda ta tsaya. Zuciyar ta zafi take in ta tuna ta bar kwana tare da Mama, Sai ta tuna waye zai dinga bawa Mama magani?, in ciwon ta ya tashi bata sani ba fa?, waye zai kular mata da Maman ta?. Tuna hakan sai ya sake karya mata zuciya. Duk yadda suka da ita tayi walwala taƙi, kukan ma bata daina ba balle kuma ta yi fara'a ko tayi magana, suka share ta suka cigaba da hirar su har zuwan ango da abokan sa guda biyu kacal. Bayan an gaisa aka zauna suka fara nasiha kamar yadda suka saba, sun yi maganganun su da wanda suke yi dan ita bata ji ma balle ta ɗauki abinda ake faɗa mata. A haka suka gama jawaban su suka tafi bayan Adnan ya jaddawa Huzaida kai su Mubeena gida. Bayan sun tafi ya dawo ciki ya sanar da sabon mai gadin sa akan ya kulle gidan shi kuma ya kulle ƙofar falon ya shiga yana kallon ta har lokacin kuka take. BDƘB2P18 Matsowa yayi kusa da ita sosai ya janye mayafin da ta kulle fuskar yana kallon ta, fuskar ta tayi kaca-kaca da hawaye tayi wani irin ja ga jiyoyin kanta sun tashi kana gani ka san ciwon kai yana damun ta sosai. Ko buɗe ido bata san yi idanun suna kulle sun kumbura. Hannu sa ya saka ya taɓa wuyan ta ji yayi zafi yace, “Subahanallahi! Manal jikin ki yayi zafi sosai, don Allah ki bar wannan kukan. Duk kukan na meye haka? Tun safe ki ke kuka har yanzu kin kasa dainawa.” Bata iya magana ba kuma hawayen basu daina sakkowa ba lokacin, ya sauke lafayar daga kanta ya dafa goshin ta yaji yadda jijiyoyin kanta suke harbawa, ya sake kallon fuskar ta yace, “Manal don Allah ki yi shiru ki saurare ni, wannan kukan babu abinda zai ƙara miki sai ciwo, ki daure ki dakatar da wannan kukan haka.” Idanun ta sun yi nauyi ko buɗe su bata iyawa suna kulle sai hawaye da yake fitowa daga jikin su. Kallon ta kawai ya tsaya yana yi, ya rasa abinda zai ce mata wanda zai saka ta tsayar da hawayen idanun ta. Tashi tsaye yayi ya shiga ciki ɗakin da yake mallakin sa ya cire kayan jikin sa yadda zai samu ya kula da ita da kyau, ya dawo ya tarar tana yadda ya barta ya riƙe hannun ta duka biyun ya miƙar da ita tsaye. Jiri ne ya ɗauke ta yayi saurin tare ta a jikin sa ya riƙe ta sosai yana takawa a hankali itama tana bin sa dan idon ta a kulle yake inda yabi nan take bi har ɗaki. bai zaunar da ita ba sai da ya fara laluben ta yadda zai kwance lafayar jikin ta, bayan ta yaji inda aka ɗaure ya kwance ya ware lafayar ta gabaɗaya. Doguwar riga ce a jikin ta ta atamfa wacce bata kamata ba ya zaunar da ita a kan doguwar kujerar da take ɗakin. “Ka mayar dani wajan Mama, Bazan iya zama a nan ba, wajan Mama nake son tafiya” ta faɗa sabon hawaye yana sakko mata, har lokacin idon ta yana kulle ji take kamar ba a duniya take ba saboda kewar Maman ta da take yi. Kallon ta yayi tare da yin murmushi dan daman ya san hakan zata faru, shaƙuwar ta da mahaifiyar ta yasan dole abin ya taɓa ta duk ranar da zasu rabu, amma bai ɗauka zata yi wannan kukan har haka ba. Tashi tsaye yayi ya fita ya ɗauko hollandia milk cikin wanda suka zo dashi, duk da ya san sweeted ne haka ya zubo ta a glass cup ya dawo ɗakin ya zauna a gefen ta yace, “Kina so zuwa wajan Mama ko?.” Ta ɗaga kai a hankali sai kuma ta rutse ido ta dafe kan yace, “ciwoo ko?.” Bata amsa ba yace, “ki daina kuka sannan ki sha madarar nan.” Bakin ta ya kai kofin amma taƙi buɗe bakin ta sha yace, “Manal don Allah ki sha, sai kin sha sannan zaki ji daɗi magani yayi miki aiki.” A hankali ta buɗe bakin ta sha kaɗan ta kawar da kai. Ganin da gaske dai ba sha zata yi ba sai ya ajjiye ya ɗauko magani da ya taho dashi a aljihun sa ya riƙe fuskar ta daidai bakin ta ya matse bakin, bakin nata ya buɗe ya saka maganin a ciki sannan ya saki fuskar ya bata ruwa ta sha maganin ya tafi. Tashi ya sake yi ya shiga banɗaki ba jimawa ya dawo ya jiƙo towels guda biyu ƙananu da ruwan sanyi ya dawo ya zauna kusa da ita, ya ɗora ɗaya a kanta bayan ya ninka, ɗaya kuma ya zagaya shi a wuyan ta. Taji daɗin hakan sosai sanyin da ya ratsa ta yayi mata daɗi, sai dai har lokacin idon ta a rufe yake bata iya buɗewa ba. Ya riƙe hannun ta guda ɗaya yana kallo yace, “Partner Mama ta amince dani shiyasa ta bani ke a matsayin wanda zai maye gurbin ta wajan kula dake, ki daina kuka ki buɗe idanun ki ki kalle ni.” A hankali ta fara ƙoƙarin buɗewa ta buɗe su kaɗan dan sun yi mata nauyi baza ta iya buɗewa duka ba yace, “in baki daina wannan kukan ba maganin babu abinda zai miki, ki daina bana so kin ji.” “Ni wajan Mama zan je.” Ta kuma faɗa bayan ta buɗe idon. “Mama tana gida, itace ta turo ki nan saboda zaman ki a nan shine farin cikin ta ba zaman ki a inda take ba Manal. Meyasa kike son cutar da kan ki? Kalli yadda kika koma, idon ki ya kumbura ga fuskar ki tayi ja, haba Manal ya isa haka.” Shiru tayi bata ce komai ba ya sake ɗauko milk ɗin da ya ajjiye yace, “ki shanye ta yanzu.” Kai take girgizawa a hankali shima ya taya ta yace, “Sai kin sha, sai kin sha zaki ji daɗi, ki daina girgiza kai Allah sai kin sha, Take it” ya faɗa yana sake kai shi bakin ta. “Akwai sugar.” “Na sani, ni na baki ai” ya faɗa yana sake kaiwa bakin ta dole ya sake ta buɗe baki ta sha a haka har ta shanye kofin ya ajjiye. Ya kalle ta yace, “in da zaki cire wannan rigar ta jikin ki zaki fi jin daɗi sosai” ya faɗa a hankali yana cire towel ɗin da ya saka mata a wuya ya cire na goshin ta. “Kwanciya zanyi” ta faɗa a sanyaye dan so take ta kwanta jikin ta ciwo yake yi. Bebi yace, “kin yi sallah?.” Ta ɗagaa kai alamun eh yace, “to ki cire rigar nan sai ki kwanta” ya faɗa yana jan zip ɗin bayan rigar zuwa ƙasa. Ta zabura zata yi kamar wacce aka sokawa allura, zata yi magana yace, “shiiiii! Kar kice min komai Partner.” Manal ta tsorata sosai duk da babu lafiya a tare da ita tace, “zan cire.” Kallon fuskar ta yayi kamar wanda yayi tunanin wani abu sai ya ɗauke hannun sa daga bayan ta yace, “Ina zuwa.” Ya faɗa yana tashi ya buɗe wardrobe ya ɗauko irin kayan jikin sa riga da wando wanda ya siya ya kuma yi alƙwarin su zasu saka a ranar da suka tare ya ajjiye mata yace, “na baki two minutes ki saka zan dawo” ya faɗa yana fita don kar ya sake firgita ta. Manal ƙarfin hali kawai tayi ta tashi ta cire rigar ta saka wanda ya ajjiye, sun kuwa yi mata daidai basu kamata ba kuma basu yi mata yawa ba, tana cire ɗankwalin kanta ya shigo ɗakin yana kallon ta cikim kayan daga sama zuwa ƙasa, basu kama ta ba amma sun bin jiki ta sun yi mata kyau sosai hakan ya saka shi ƙare mata kallo, dan in zaka saka masa wuƙa a wuya bai san surar Manal ba tunda a hijjab yake ganin ta ko abaya. Kuma bai damu da ya sani ba dan ba surar ta yake so ba ita yake so. Ganin kallon da yake mata sai ta zauna tace, “kai na a buɗe babu hula.” Rigar da ta cire ya ɗauke daga ƙasa ya ajjiye a kan mirror yana kallon ta yace, “ki kwanta zan ɗauko miki. Naga akwai kayan ki a ɗakin can zan duba na samo ko ɗankwali ne.” Kwanciyar tayi kamar yadda yace, ya ƙaraso ya sake taɓa jikin ta yaji har lokacin da zafin kawai ya ragu ne ya san kuma baccin yana daga cikin abinda zai saka ta samu lafiya dan akwai gajiya. A kusa da ita ya zauna ya rufe ta da blanket ya ɗora hannun sa fuskar ta, sai kuma ya miƙa kansa inda fuskar ta take ya yi mata kiss a goshi yace, “ki yi bacci lafiya, ban da kuka” ya faɗa yana shafa kanta. Hasken da wayar sa da take yi a gefe yake gani ya ɗauka ganin sunan Huzaifa sai abin ya bashi mamaki, ya kalli agogon wayar yaga goma na dare har ta wuce. Tashi tsaye yayi ya kashe hasken ɗakin ya fita don ya kira Huzaifa. A falo ya kira shi yana ɗauka Bebi yace, “Huzaifa lafiya?.” Huzaifa yace, “Bebi daga nan asibiti ne….” Kafin ya kai ƙarshe ya katse yace, “shine me? Daman akan wannan ka ke kirana kenan?.” “Ka tsaya kaji mana, Rumana ce a nan a kwance an kawo ta unconsciously, su Mama gabaɗaya suna nan itace tace na kira ka nace kazo kaine ka san ya ciwon nata yake shiyasa na kira ka. I’m sorry ba yadda ban yi ba, nace mata akwai wacce zan kira ta kula da ita amma Mama tace kai take so, kuma naga yanayin Rumana ɗin kamar sai kai ɗin daman kace mana kamar kana expecting heart attack a tare da ita, zan iya cewa ya zamo gaskiya kuma conditions ɗin nata is very bad.” Shiru Bebi yayi ya kasa koda motsawa balle yayi magana, abin ya ɗaure masa kai sosai ya kuma bashi mamaki ya ma rasa abinda zai cewa Huzaifa da yake jiran amsar sa. Huzaifa yace, “kayi shiru baka ce komai, Allah ya sani ban so kiran ka ba Adnan saboda darajar yau a gare ka, amma babu yadda zan yi da Mama.” Bebi ya numfasa a sanyaye yace, “Huzaifa yanzu goma ta wuce fa, da wa zan barta a gidan nan na fito don Allah?.” Huzaifa yace, “ka bincika ko su Kausar ne, in sha Allah baza ka jima ba zaka dawo.” Bai ce komai ba ya yanke wayar baya son yin wani dogon tunani kar zuciyar sa ta fara faɗa masa Mama bata son Manal hakan ya saka shi neman number Kausar da sauri. Tana ɗauka yace, “kina Ina?.” Kausar tace, “Muna gidan Yaya, da aka dawo daga gidan Mimi muka taho nan.” “Saka hijjab ɗin ki kizo compound ɗin gidan gani nan zuwa” ya faɗa yana yanke wayar ya fita daga falon zuwa gidan Yayan nasa tunda kusa suke. Mai gadin na ƙofar gidan ganin sa sai ya buɗe masa, Kausar ganin sa sai ta ƙaraso inda yake kawai taga yayi gaba bai ce komai ba, dole ta bi bayan gaban ta sai faɗuwa yake dan bata san me ya faru ba. Sai da suka shiga falon gidan nasa ya kalle ta yace, “ki zauna a nan, zan je asibiti yanzu na dawo. In kina jin bacci zaki iya shiga ciki.” Mamaki abin ya bawa Kausar da tunanin me zai yi a asibiti kuma, amma yanayin fuskar sa bazai bata damar tambayar sa ba tana gani ya fita ita dai ta zauna falon ita kaɗai Allah yaso ta ɗauko waya. Da kayan baccin jikin sa ya wuce asibitin ya manta ma da wanne kaya ne a jikin sa, ko mai gadin asibitin ganin sa a wannan lokacin sa da yayi mamaki, amma bai tambaya ba shi kuma bai ce komai ba ya shiga ciki. Kowa na asibitin kallon sa yake yi da mamakin ganin ango a asibiti a daren angwancin sa, babu wanda ya iya yiwa magana yana gani dai ana kallon sa bai ce komai ba ya wuce ciki. Da Huzaifa suka haɗu zai sakko Bebi kuma yana hawa saman yace, “Tana Ina?.” Huzaifa yace, “tana sama.” Saman ya wuce shima ya bi bayan sa. Yana shiga ɗakin ya tarar da Mama da Umma da Ammi harda Farida. Bai yiwa kowa magana ba ya wuce inda take kafin ya kalle su yace, “Mummy za ku koma waje.” Fita suka yi ya tsaya akan Rumana yana yi mata abinda zai taimaka mata don ya tabbatar da ciwon zuciya ya kama ta sosai amma sai an mata gwaji zuwa gobe zai tabbatar. Suna fitowa daga ɗakin Umma ta kalli Mama tace, “yanzu Hauwa sai da kika taso yaron nan a daren nan? Ko a ba faɗa ba yanayin fuskar sa ya nuna bai ji daɗin wannan fitowar ba, kema kin san bazai ki daɗin ta ba. Naga Rumana ta samu sauƙi ba kamar yadda muka zo ba, akwai likitoci da yawa ba lallai sai shi ba, meyasa lallai sai da kika fito dashi?. In kina yi masa haka zai ga kamar bakya son matar sa fa.” Mama tace, “wallahi ban ce yazo saboda wani dalili nawa ba Yaya, kawai naga shine yasan abinda yake damun ta kwana biyun nan da ya bata magani sai kiga ta ware shiyasa nace yazo amma ba da wani nufi ba.” Ammi tace, “amma na faɗa miki Mama bai kamata a fito dashi ba, kowa a nan zai iya bata taimakon gaggawa ba lallai sai shi ba. Dare fa yayi matar sa ita kaɗai ce a gida, barin ta babu kowa hatsari ne a yadda duniyar ta lalace.” A lokacin ya fito daga ɗakin ya kalle su yace, “kuna tsaye a nan ku shiga wannan ɗakin mana” ya faɗa yana nuna musu wata ƙofa da take kusa dasu. Wucewa yayi ba jima ya sake dawowa ya kuma shiga ɗakin da Rumana take ciki, bai jima a ciki ba ya fito ya samu sun shiga ɗakin shima ya shiga da sallama suka amsa yace, “Ku kwantar da hankalin ku in sha Allah zata samu lafiya, jikin nata yayi sauƙi yanzu numfashi nata yana dawowa daidai a hankali, zuwa gobe zata samu lafiya.” Umma tace, “Allah ya sa Adnan, sannu an fito da kai a daren nan.” Dan murmushi kawai yayi bai ce komai ba ya fita daman bai shigo ba yana daga bakin ƙofa. Wajan Huzaifa ya shiga ya same shi a tsaye da yana tattara kaya da alama tafiya zai yi Huzaifa ya kalle shi yace, “ni zan wuce, daman saboda Mama nake zaune a nan.” “To sai da safe. Ka bar min nan ɗin a buɗe.” Huzaifa ya kalle shi da mamaki yace, “a nan zaka kwana ne?.” Ya kalle shi shima yace, “zan cewa Mummy zan tafi ne?.” Huzaifa yace, “amma bai kamata ka kwana a nan ba, ka bar yarinya ita kaɗai a gida, hatsari ne babba barin ta ita kaɗai a sabon gidan da aka tare yau.” “Hmmm! Na fika sanin hakan” ya faɗa yana zama kawai ya dafe kansa dan shima kan nasa ciwo yake yi. Huzaifa yace, “Akwai mutum uku da suke on duty daga nan har safe, me zaka zauna ka yi har safiya Bebi?.” Bebi yace, “Mummy ta san dasu tace na zo ai ko? Kaga kenan bani da tafiya a yanzu, kaje kawai.” Huzaifa ya fita,shi dai yana zaune ya dafe kansa yana son kiran Kausar yaji ko Manal ta farka amma baya son kiran ta kar yaje tayi bacci ya tashe ta daga bacci ga gajiyar biki da sauran su. “Adnan!.” Yaji muryar Mama hakan ya saka ya ɗago kai yana kallon inda yaji sautin muryar ta ta ya tashi tsaye yace, “Mummy ta farka ne?.” Ta ƙaraso kusa dashi tace, “bata farka ba.” Yayi murmushi yace, “zata samu lafiya in sha Allah Mummy, damuwa ce tayi mata yawa kawai shine ya haifar da hakan, amma in sha Allah zuwa gobe zaki ga kamar ba ita ba.” Mama tace, “Allah yasa.” Ya amsa da amin yace, “ki zauna Mummy” ya faɗa yana ja mata kujera bata zauna ba tace, “kayi haƙuri na fito dakai a daren nan.” “Mummy haƙuri kuma?” Ya faɗa yana kallon ta a sanyaye. Mama tace, “eh kayi haƙuri, na san yadda yau take mahimmaci a wajan ka Adnan amma saboda Rumana nace kazo kuma ka tsallake matar da aka kai maka yau ka fito kazo nan ka barta ita kaɗai. Ban yi hakan dan lalata maka yau ɗin ba Adnan, ban yi kuma don bana son Manal ba, Ina son Manal wallahi, kar kaji a ranka ko son ta ne bana yi. don nasan zaka yi tunanin inda Rumana ce a yau a tare da kai bazan ce ka fito ba.” Bebi ya rausayar da kai cikin nauyin abinda tace zai magana tace, “kar kace komai nasan baka so fitowar ba kawai babu yadda zaka yi ne saboda ance ni na kira ka, kai kan ka kana son hutawa auren ka aka gama yau kana buƙatar hutu. Na ruɗe ne ɗazu shiyasa nace Huzaifa kawai ya kira ka, gani nake kamar kai ne kawai maganin matsalar ta na manta akwai wanda zasu bata taimako koda baka nan.” “Don Allah Mummy ki daina cewa haka.” “Dole nace ai, ga dare yayi ka fito ka bar ƴar mutane ita kaɗai a wannan gidan duk saboda baza ka iya tsallake kira na ba. Maza ka koma Allah ya tashe mu lafiya, Allah yayi maka albarka ya baka masu bin ka kamar yadda ka ke bina Adnan.” Yayi murmushin jin daɗi yace, “Amin Mummy.” Mama tace, “to maza kaje kaga sha ɗaya har ta yi, sai da safe” ta faɗa tana fita yayi sauke ajiyar zuciya, Allah ya sani yaji daɗin hakan don ba a son ran sa ya fito ba kawai saboda ita ne. Fita yayi ya hau mota ya koma ya gida tarar da Kausar inda ya barta tana video call da sauran ƴan matan ya kalle ta yace, “ke bama kya jin bacci?.” “Yauwa Yaya ka dawo? Ka mayar dani gidan Yaya don Allah duk suna can.” Ya koma da baya yana cewa, “muje.” Har gidan ya mayar da ita sai da yaga ta shiga sannan ya dawo na sa gidan ya kulle falon ya shiga wajan Manal. Tana kwance kasancewar da duhu baya hango ta sai da ya ƙarasa ya zauna kusa da ita ya taɓa goshin ta yaji babu zafin alamun zazzaɓin ya sauka, ya sauke ajiyar zuciya cikin jin daɗi babu zazzaɓin. Juyi tayi sai cikin baccin yaji tace, “Mama kina Ina?.” Gefen nata ya koma ya kwanta, ya ɗauke ta gabaɗaya daga kan katifar ya dawo da ita jikin sa, ta kuwa riƙe shi dan ita ta ɗauka Mama ce, ta Murmushi yayi yana jinjina qauna tsakanin Mama da Manal a haka bacci mai dadi ya dauke shi. Sai da gari yayi haske sannan ya farka da sauri ya kalli agogo yaga shida na safe ya kalli Manal da take jikin sa har lokacin bacci take yi ya janye ta ya tashi ya shiga banɗaki bai jima sosai ba ya fito ya dawo gefen ta ya zauna ruwan hannun sa ya shafa mata a fuska yace, “partner tashi lokacin sallah ya wuce.” Buɗe ido tayi suka haɗa ido sai a lokacin ta tuna a inda ta kwana, kunyar sa taji lokaci ɗaya ganin gefen ta a yamutse da alama a nan ya kwana shima ta saka hannu ta kulle fuska yace, “ki fara tashi ki yi alwala komai ma ya biyo baya.” Tashi zaune tayi kanta na sarawa har lokacin akwai sauran ciwon kai, ganin ta dafe kan yace, “ciwo ko?.” Ta ɗaga kai yace, “Sannu, taso ki yi alwala in kika yi sallah kika sake yin bacci zaki ji daɗi, zo mu je” ya faɗa yana riƙe hannun ta ta tashi tsaye, har bakin banɗakin ya kai ta yace, “ki yi sauri ina jiran ki mu yi sallah.” Bata yi magana ba ta shiga ya dawo yana tunanin inda zai samo hijjabi, ya fita zuwa ɗakin da aka jera kayan ta wanda yake kusa da wanda suke. A nan ya samu hijjabi guda ɗaya na roba mai ɗan girma ya dawo ɗakin a lokacin ta fito ta tako a hankali, yana kallon ta tun daga farcen ƙafar ta har kanta da yake buɗe ya bata hijjabin ta karɓa ta saka ya tayar da sallar ta bi bayan sa. Bayan sun idar ne ya juyo ya kalle ta yaga tana kallon waje ɗaya sai kuma ta kalle shi tace, “Ina kwana.” Bai amsa ba kallon ta yake yi kafin yace, “ba lafiya lau ba, ta yaya zan kwana lafiya lau bayan baki kwana lafiya ba?.” Murmushi tayi kaɗan tana wasa da hijjabin yace, “tashi mu je ki kwanta ciwon kan zai daina.” Ta zauna a gefen gadon ya kalle ta yace, “ki cire hijjabin.” Ta girgiza kai alamun a’a ya zare shi da kansa tana zaune tana kallon ikon Allah yace, “kwanta ki huta, naji jikin ki da zafi har yanzu.” Kashe hasken ɗakin yayi ya koma kamar dare babu ta inda haske yake shigowa ɗakin ya dawo kusa da yace, “ki kwanta mana.” “In bani da lafiya bana iya bacci, in na kwanta ma bazan iya ba.” Ya kalle ta yace, “zaki iya.” Ta kwanta saboda kar ta yi masa musu amma ita tasan in bata da lafiya a jikin Mama kawai take bacci, jiyan ma bata yi wani bacci ba sai da tayi mafarkin tana jikin Mama sannan bacci ya ɗauke ta. Bata san ya kwanta ba sai da taji ya jawo ta jikin sa a kunnen ta yace, “bakya iya bacci sai a jikin Mama ko? Daga yanzu zaki dinga yi a jikin mijin ki” ya faɗa yana saka hannu ya zare ribbon ɗin kanta da ya fara tujewa. Tayi shiru tana jikin sa bata ce komai ba, bata san ya akayi ya san wannan sirrin nata ba da dai ita bata faɗa masa ba. Hannun sa taji a bayan ta ta ɗan yi baya zata sauka daga jikin sa ya riƙe ta bai ce komai ba dole ta koma ta kwanta a haka baccin ya ɗauke ta. BDƘB2P19 *12:00pm*          Sai a lokacin Bebi ya tashi ya kalli Manal da take jikin sa tana bacci hankali kwance yayi murmushi yana kallon ta cikin farin ciki, kamar a mafarki wai shine da Manal a kwance a waje ɗaya matsayin mata da miji. Hannu sa ya ɗora a kan fuskar ta ya gyara mata gashin kanta a zuciyar sa yana tabbatar da hasken da ake cewa tana dashi. Janye ta yayi ya tashi ya shiga banɗaki yayi wanka ya fito har lokacin bacci take ya shirya ya fita zuwa falo. Sai a sannan ya duba wayar sa yaga kiran wayar Yayan sa tun goma na safe, hakan ya saka ya kira shi ya ɗauka suka gaisa yake cewa, "Daman Hadiza ce take waya an aiko da abinci amma baka ɗauka ba, amma tace an ajjiye a nan bakin ƙofar falon." Bebi yace, "Allah sarki! An gode sosai." Daga nan ya yanke wayar ya buɗe kofar yaga food flakas da aka ajjiye ya shiga dasu ya ajjiye akan dining. Kiran sallah yaji sai ya fita zuwa masallacin da yake layin don yin sallar azahar. Lokacin da ya dawo a kan gadon ya same ta a zaune ta riƙe kai da alama tashin ta kenan, a hankali ya tako yana kallon ta ya shigo ya zauna kusa da ita yace, "Amarya ciwon kan ne?." Ɗan yatsine fuska tayi tace, "ba sosai ba." Ta kalli agogo ganin lokacin sallah yayi ta sauke numfashi tace, "wayata nake nema." "Tana falo" ya faɗa a daidai kunnen ta hakan ya saka ta kalle shi suka haɗa ido sai ya ɗaga mata gira ɗaya ta sunkuyar da kai cikin jin kunya. Kallon ta yake yi cike da so da ƙauna da tsantsar shauƙi kafin ya riƙo fuskar ta ta ya juyo da ita yana kallo amma bai ce komai ba, motsawa tayi daga inda take tayi tace, "wanka nake so nayi sannan nayi sallah." "Bismillah." "Ba a nan ba, a ɗaya ɗakin." Tashi tsaye yayi yace, "muje na raka ki?." Hannun sa ta kalla da ya miƙo mata, bata miƙa masa nata ba sai taga ya riƙo nata hannun ya ja ta ta tashi tsaye tace, "washhh." "Sannu, in kika yi wanka kika ci abinci zaki daina ji." Har ɗakin ya kai ta dan baya son ya saka tayi wankan a wancan ɗakin saboda kar ta firigce, ta kalli ɗakin da suka shiga yayi mata kyau sosai ganin hoton da aka kafa a ɗakin sai ta kalle shi suka haɗa ido yace, "na raka ki bathroom ɗin ne?." Ta girgiza kai bata ce komai ba ta wuce ta shiga banɗakin shi kuma ya fita yana kiran waya. Ya jima bai koma ba har tayi wanka ta fito ta saka kaya a inda Mubeena tace ta ajjiye mata ta shirya cikin atamfa doguwar riga, ta saka babban mayafi tayi sallah. Bayan ta idar ta ɗauki ɗankwali bata ɗaura ɗankwali ba yana hannun ta ya shigo. Ta kalle shi shima ita yake kallo tayi masa kyau sosai dan kwaliyyar atamfa na burge shi sosai. Daf da ita yazo yana kallon idanun ta sai ta sauke nata ƙasa ta ɗan kulle ido ta buɗe ta lura yana son kallon idon ta. Hannun ta ya jawo ya rugunme ta a jikin sa ya zagaya da hannun sa bayan ta ya riƙe ta sosai, a kunnen ta yace, "First hug, halal hug" ya faɗa murya a tausashe cikin salon soyayya. Tana kwance a jikin sa ta lumshe ido, ƙhamshin sa da bashi da hayaniya take ji a hancin ta, abin mamaki yake bata wai itace tayi aure sai taga kamar a mafarki. Ɗago da ita yayi daga jikin sa ya ɗago fuskar ta a hankali ya matso da fuskar sa daf da ta ta yace, "the most smallest and shining lips" ya faɗa yana kai bakin sa kusa da nata, sai ta runtse ido yayi murmushi ya ɗora nashi a kan nata yayi mata kiss mai zafi, in less than two seconds ya ɗauke bakin sa yana kallon ta yace, "na jima Ina craving ɗin shi, but now it's mine" ya faɗa yana shafa lips ɗin da hannun sa a hankali yana kallon fuskar ta. A goshi ya sake yi mata kiss hakan ya saka ta komawa jikin sa ta kwanta ta riƙe shi sosai saboda kunyar sa take ji kamar ƙasa ta buɗe ta shiga. Riƙe ta shima yayi yana jijjiga su dukkan su yace, "I love you so much my life partner, I so much love you, zan kuma nuna miki you're the one and only." Murmushi tayi tana jikin sa tana jin daɗin abinda yake cewa har zuciyar ta, janye jikin ta tayi ta ɗan ja  baya tana mamakin sa tace, "ina wayata?." Miƙa mata wayar yayi sai ta koma gefen gadon ta ajjiye ɗankwalin a kan gadon ba tare da ta ɗaura ba tana danna wayar burin ta kawai ta kira Mama. Zama yayi a kan gadon kusa da ita yana kallon ta a lokacin da aka ɗauki wayar tace, "Mama!" Sai ga hawaye sharrr sun sakko mata. Daga can ɓangaren Mama tace, "Ke kuma sallamar taki kenan Manal?." Manal tace, "Mama Ina kwana" muryar ta rawa take sosai tana kuka ganin hakan sai ya riƙo hannun ta ya jawo ta ya mata mazauni a jikin sa, ya saka hannu yana share mata hawayen yana ji Mama tana cewa, "Ke kinga matsalata dake, haka kika kwana kina masa wannan banzan kukan naki ko? Mutuwa nayi?. Tun jiya ki ke kuka da safe har yanzu ko?." Jin bata yi magana ba sai kukan da take yi sai Mama ta tausasa murya tace, "Ban da abin ki Manali meye na kukan? Ni Ina nan Ina farin ciki Manalina yau ta wayi gari a gidan miji ke kina can kuka? Haba takwara ta meyasa kike haka?." Manal muryar na rawa sosai tace, "Mama Ina kewar ki, ni gida zan dawo, dake kawai nake so na zauna kawai. Mama bazan iya haƙura na zauna ba, ki yi haƙuri." Mama tace, "haƙuri ya zama dole Manal, ni nasan kaf duniya babu mai son farin cikina kamar ki haka ne ko?." Kamar tana gaban ta ta ɗaga kai tace, "Haka ne Mama." "To farin cikina shine zaman ki a gidan mijin ki lafiya, zaman gida yanzu ba naki bane ba ai Manal. Sai dai kizo da ziyara ki koma amma bawai ki zauna ba. Dan haka farin cikina shine zaman ki a gidan mijin ki, ki kwantar da hankalin ki babu abinda zai same ni, zan kasnace lafiya fiye da lokacin da kina nan, kuma ga Yayar ki a tare dani ba shikenan ba?." Kuka take yi ta kwantar da kanta a kafaɗaar sa hawayen nata yana sauka a wuyan sa tace, "Ina kewar ki Mama, Ina so na ganki." "Gashi kin ji magana ta ai kewar sai ta ƙare kuma. kuma ƙarya ki ke ba wata kewa ta da kika yi, kin yi kewar ta shine baki min waya ba sai azahar?." Manal tace, "Allah Mama nayi kewar ki." Mama tace, "ni ba wata kewar ki da nake yi ina nan yanzu na gama cin abincina ma ni." Sai kuma ta ɗago daga jikin sa da hawayen a fuskar sa ta turo baki tace, "da gaske Mama baki kewa ta ba?." "Ga zahiri, inda nayi da da sassafe zan miki waya." Sai ta fara buga ƙafa tace, "Allah Mama kin yi kawai faɗa ki ke amma ni na san kin yi kewata." Mama tayi dariya tace, "Ba wata kewar ki da nayi ni nan, shagalina kawai nake yi. Kinga kema sai ki rama ki daina kewa ta kawai." Manal tayi murmushi tace, "Ni bazan iya dainawa ba." Mama jin tayi murmushi muryar ta ta saki sai tace, "ban yi kewar ki ba saboda na san na aurar dake Manal, yanzu ke ba yarinya bace wannan yarintar duk ajjiye shi zaki ki fuskanci auren ki. Wannan autancin da kike ji dashi ya koma gefe dan nan gaba kaɗan zaki zama Mama kema." Manal tace, "To Mama kafin ki fara min wa'azin, kin sha maganin ki? Kuma baki sha sugar ba dai ko? Kinga ana bikin nan na kama ki kina cin cincin." Mama tayi dariya tace, "wannan ido naki da shegen gano miki naci abu yake, to yau dai ban sha sugar ba kuma magani na sha." Manal tace, "To Mama don Allah kar ki sha." "To bazan sha ba, Ke Ina zuwa, baƙi nake sallama ki gaishe da Adnan ɗin, kice Ina yi masa nace ya haƙuri dake." Manal tace, "Mama haƙuri dani?." "Eh ke fa, milky beauty in ji Surayya, ke fa nake nufi." Manal tayi dariya tace, "Mama dama ki koma cemin haka, kin ji yadda kika ce beauty ɗin kamar baturiya?. Anya Mama ba a ƙasar waje aka haifo ki ba?." "Shashancin ki ya ƙaru, bani da lokacin ki" ta faɗa tana dariya tare da yanke wayar itama Manal ɗin dariyar take yi cikin ƙaunar Maman nata da kewa. Shi kam burge shi take yi ita da Maman ta yadda suke ƙaunar junan su suke wasa da dariya kamar Yaya da ƙanwa, hakan ya saka shi zuba mata ido kawai yana kallo yana kuma murmushin jin daɗi ganin tana dariya. Kallon sa tayi sai ta sunkuyar da kai tana murmushi tana kuma kan cinyar sa har lokacin yace, "mai kuka tana dariya." Sai ta yi murmushi sosai har haƙorin ta ya bayyana yace, "Milky beauty, murmushi yana yi miki kyau sosai" ya faɗa yana sauke ta daga jikin sa yace, "Muje ki ci abinci." Tare suka fito ƙaramin falon ya zauna ya zaunar da ita yace, "me zaki ci?." Murya a ƙasa tace, "tea zan sha kawai." Zuba mata tea ɗin yayi har zai kai m mata sai ya fasa, ya saka tea spoon ya ɗebi tea ɗin ya zuba a bakin sa yaji babu sugar sannan ya bata. Sai taga ya tashi ya shiga kitchen sai gashi da sugar irin nasu na masu ciwon sugar ya saka mata tace, "ni haka ma nake sha fa." "Ki dinga amfani da wannan." Tea ɗin ta shanye ya kalle ta yace, "sai me zaki ci?." Ta rausayar da kai tace, "babu komai." Tare ya zuba musu abinci a plate ɗaya ya jawo center table ya ɗora a kai yace, "sai kin ci, mu ci tare" ya faɗa yana ɗibar abincin ya kai  bakin ta. A haka suka ci sosai shi da ita ya bata magani ta sha. Wayar sa ya kalla yaga ƙarfe biyu na rana har ta wuce yayi mamakin gudun lokacin, call log ya shiga yaga babu kiran Mama abin ya sake bashi mamaki sosai. kiran Abba ne ya shigo hakan ya saka shi lumshe ido ya buɗe yana jin wani ɗaci a zuciyar sa, ace mahaifin ka ayi bikin ka baya nan yana wani wajan sai yanzu ya samu lokacin kiran ka. Ɗauka yayi da sallama suka gaisa kafin yace, "Adnan sai haƙuri fa, abubuwa sun riƙe ni a nan, amma nasan Daddyn ku ya kammala  komai fiye da ina nan. İn sha Allah zan dawo zan kuma zo har gidan naka da kaina." Adnan yayo murmushi yace, "To Abba, Allah ya dawo da kai lafiya." Ya amsa daga nan ya kashe wayar. Manal ya kalla yaga ta saka waya a kunne tana magana da Mubeena kafin yaga ta kashe ta kira Surayya suna gaisawa tana dariya duk da bata bayar da amsa sosai sai dai tace hmm kawai. Bayan ta kashe ne yace, "kowa kin sake dashi kina hira ban da ni." Hanun ta ya riƙe yana kallon tafin hannun nata ya sha ƙunshi mai kyau, kasancewar ta fara ya haska hannun nata yace, "wannan hannun naki na jima Ina so na riƙe shi ban samu dama ba sai yanzu." Murmushi tayi ɗankwalin da ta yafa ya sauke ya zare ribbon ɗin kanta yace, "Wai haka Manal ɗin nawa take daman ban sani ba? Ko yaushe an kulle kai a hijjabi da abaya bana ganin komai. Gaskiya an cuce ni da ba'a nuna min komai ba sai yanzu nake gani." "Allah kunya maganar ka take bani, da baka min irin wannan maganar haka" ta faɗa tana kwantar kanta a kafaɗar sa yayi dariya yace, "sai na kama ki ma ai yarinyar, yanzu baki ga komai ba ki jira Allah ya kaimu anjima. Kafin nan sai kin min bayanin wannan film ɗin... meye ma sunan sa? The virgin ko?." Riƙe rigar jikin sa tayi sosai yayi alamun kunya take ji dariya yana riƙe da bayan ta. Wayar sace tayi ƙara ya duba tare da ɗauka yana magana kafin ya sauke wayar ta kalle shi tace, "Asibiti ne ko?." Ya ja kumatun ta yace, "can ne." "Zaka fita ɗin kenan, jiya ma Ina jin ka da daddare ka tafi na san kuma emergency ne." "Baki bacci ba ashe." "Uhumm ban yi ba, in bani da lafiya wahala bacci yake min, Ina ji an fita da mota na san kaine." Bai amsa ba ya ɗauki glasses a aljihu ya saka tace, "amma basu san kayi aure bane? Kuma kai da kace min zaka bani mamaki babu ina zaka je.." abinda yaji ta tambaya hakan ya saka shi ya kalle ta ya wara idanun yana kallon idon yace, "ohh! Ashe fa nayi aure ko? Ni kaina na manta ai nayi aure saboda" sai yayi shiru ya kai bakin sa kusa da kunnen ta yace, "ban kasance kamar ko wanne ango ba, zan tuna nayi aure ne in na tabbatar da wannan milky da ake faɗa akwai ta. Sannan indai mamaki ne ki kwantar da hankalin ki zaki gani, sai na tabbatar na baki mamakin da zaki kasa ɗago ido ki kalle ni." Tashi tayi zata gudu ya jawo ta da ƙarfi ta dawo jikin sa gabaɗaya yana ƙasa tana saman sa, idon ta a rufe yana jin wucin numfashin ta itama tana jin nasa, hancin ta ya ja yana kallon bakin ta. A hankali ya matso da na sa kusa da nata ba tare da tunanin komai ba ya fara kissing ɗin ta a hankali yadda abin zai tsaya mata a rai itama. Yuƙurawa tayi zata tashi ya saka hannu sa a bayan ta ya sake matse ta dole ta dakata da niyar tashin idon ta har lokacin yana rufe dan ita wallahi kunya da mamaki yake bata, ko sau ɗaya bai taɓa ƙoƙarin riƙe mata hannu ba amma yanzu gabaɗaya ya canja kamar ba shi ba. A hankali ya dakatar da abinda yake yi har lokacin idon ta na kulle ya kai hancin sa wuyan ta ya shaƙi ƙhamshin body mint ɗin da yake jikin ta ƙhamshin sa mai sanyi. Jin ya sassauta riƙon da yayi mata sai ta fincike jikin ta tashi a guje ta yi cikin ɗaki,  yayi murmushi ya ɗauki waya dan ya turawa asibitin abinda suka nema. Tana ɗakin a tsaye tana raba idanu tana sauke numfashi kamar wacce tayi gudu ya shigo ta bayan ta ya sake rungume ta yace, "in anyi sallar la'asar zanje asibiti na dawo." Sai ta buɗe ido tace, "har a jiya da yau ɗin baza a barka ka huta ba?." "Ni dai zan zo naga hutun nan da Manal take so nayi." Bata amsa ba yace, "am sorry jiya na fita ko? kin san Rumana?." Manal tace, "mun taɓa gaisawa da ita a wayar ka." "Exactly, itace bata da lafiya a jiyan kuma ana expecting ta kamu da ciwon zuciya ne, shine hankalin Mummy ya tashi sosai har aka yi min waya. Kin san ƴar kanwar Mummy ce zaki ji suna ce mata Ammi, kuma a hannun Mummy ta tashi." Manal tace, "Allah sarki, Allah ya bata lafiya." "Amin. Ita nake so naje na duba in anyi sallah." "Hakan ya kamata, nima zan je." "Babu inda zaki je ƴan mata, ki jira dai na dawo sai na samu na huta kamar yadda kike so" ya faɗa yana mata kiss a wuyan ta. "Bazan iya zama ni kaɗai ba, kawai ka tafi dani." "A nan zan barki ki, zan barki ke kaɗai ki shirya yadda zaki bawa Adnan abu mai sunan ki." "Meye?." "Milky" ya faɗa a kunnen ta tare da cizon kunnen nata kaɗan ya sake yana murmushi. Ita kunya yake bata wallahi ta rufe fuska da hannun ta yace, "koma meye a jira na dawo." Bata buɗe fuska ba ya kalli agogon hannun sa yaga lokacin sallar la'asar ɗin ma yayi yace, "kina ji, mu yi sallah a nan sai na fita." A ɗakin suka yi sallah bayan sun idar ta kalle shi  tace, "kaje ka gano jikin nata, in naji mai irin ciwon na nan na Mama tausayi yake bani. Don Allah kaje ka gano ta wataƙila ana buƙatar zuwan ka." "Kin yarda na je?." Ta ɗaga kai alamun eh ya matso da fuskar sa kusa da ita yace, "kiss me before i leave." "Na shiga uku" ta faɗa tana cusa kanta a jikin ta yayi dariya ya tashi ya fita yana jin nishaɗi a zuciyar sa, iya kwana ɗaya da suka yi ya yarda aure ni'ima ne kuma farin ciki ne musamman in ka auri wacce ka ke so take son ka. BDƘB2P20 Bebi yana shiga asibitin suka fara gaisawa da mutane kafin ya shiga ciki, da likitan da yasan yayi handling case ɗin Rumana ya haɗu a hanya ya tsaya suka gaisa yana tsokanar sa Bebi yace, "ba wannan ba, ya jikin ƙanwata?." Dr ya ɗauko wani magani a aljihun sa ya nunawa Bebi yace, "wannan maganin ta sha overdose shine ya kawo wannan bugawa zuciyar kamar yadda ka sani." Bebi ya karɓi maganin yana kalla kafin yace, "yanzu ya jikin nata?." "Jikin da sauƙi, dan yanzu da na fito daga wajan ta tana zaune amma ba wai ta ware ba, ta dai ji daɗin jikin ta." Bebi ya girgiza kai Dr yace, "Sannan an yi mata gwaji an tabbatar da tana da heart attack." Bebi ya sauke numfashi yace, "na sani." "Amma meyasa baka faɗa mata matakan kare kai ba? A shekarun ta hatsari ne wannan ciwon a gare ta kafi kowa sani, yanzu ciwon nata yana stage one ne Dr, in aka cigaba da samun matsala ba sai nace komai na kafi kowa sanin yadda yanayin yake." Adnan ya kulle ido ya buɗe ya kalle shi yace, "zan san abinda zan yi in sha Allah." Sallama suka yi shi ya fita shi kuma ya wuce zuwa ciki, bakin ɗakin a nan yaga Mama da Ammi da Mamy harda Farida da mahaifin Rumana a tsaye. Ya ƙaraso a sanyaye suka gaisa da  kowa ya Mama ta kalle shi cikin raunin da ya bayyana a tare da ita tace, "Adnan daman kasan Rumana tana da ciwon zuciya ne?." Ya sauke ajiyar zuciya yace, "ban sani ba Mummy, na dai yi hasashen hakan saboda yanayin ciwon nata, na bata magani da shawarwari wanda zasu taimaka mata tayi yaƙi da ciwon kafin ya same ta amma bata yi amfani dashi ba. Sannan maganin da na bata take sha jiya shi ta sha yayi mata yawa shine ya kwantar da ita, a gaban ki nace mata maganin sau ɗaya tak ake so a sha amma bata ji ba." Mahaifin ta da yake tsaye yace, "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Abin har ya kai wannan matakin yanzu?." Adnan yace, "babu damuwa Abba, in sha Allah ciwon bazai kai yadda ku ke tunani ba. Indai zata dinga kula da shan magani, da gujewa ɓacin rai da damuwa zata warke." Abban ya sauke numfashi cikin damuwa yace, "Adnan ciwo ai sunan sa ciwo, ciwon zuciya akace ba ciwon kai ba, dole hankali ya tashi duba da yanayin shekarun ta gabaɗaya nawa take?." Bebi yace, "Haka ne, in sha Allah babu abinda zai same ta, zan yi Ina bakin ƙoƙarina wajan samar mata da lafiya." "Allah ya sa." Bebi ya amsa da amin suka haɗa ido da Mama sai ya kawar da idanun sa ganin irin kallon da take masa irin na ai dik kaine ka jawo. Ɗakin da Rumana take ya shiga ya same ta a zaune ta jingina da bango gadon ta kulle idanun ta, Bebi ya zauna a kan kujerar da take kallon gadon yana kallon ta, ganin bata buɗe ido ba sai ya riƙe hannun ta yana auna bugun zuciyar ta. Buɗe ido tayi ta kalle shi suka haɗa ido gaban ta ya faɗi sosai. gani tayi yayi mata kyau a idon ta, kai kana ganin sa kaga ango fuskar sa har ƙyalli take yi haka idanun ta suka gano mata. "Meyasa bugun zuciyar ki ya canja daga yadda yake bugawa yanzu?." Kallon sa take yi kafin tayi magana ya sake cewa, "ya jikin ki?" Ya faɗa yana sakin hannun ta ya ɗora hannun a kan goshin ta ya janye hannun nasa yana kallon ta. Rumana kallon sa take babu ko kifta ido, Allah ya ɗora mata wata irin soyayyar sa a lokacin da bata yi tunanin hakan ba, a lokacin da take ganin zata jajirce akan sai ya aure ta ko ta wanne hali sai gashi soyayyar ta saka tayi laushi ko ɗaga murya ma bata so balle abinda zai saka shi a damuwa.Tana ji tana gani ya zama mallakin wata ba ita ba har ya kwana da ita ya tashi sai yamma lis yazo ganin ta matsayin ta na wacce take ciwo saboda shi. "Ruman!" Ya faɗa yana ɗan dukan gefen gadon ganin ta kafe shi da ido kuma bata ce komai ba, kulle ido tayi a hankali ta sake buɗewa tace, "da sauƙi." "Kin tabbatar?." Ta ɗaga kai alamun eh yace, "Meyasa kika sha maganin ki overdose bayan na yi miki gargaɗi akan hakan? Kina so ki kashe kan ki ne Ruman?." Ta sauke numfashi tace, "inda zan mutun ma zan fi jin daɗi akan wannan azabar da nake sha ba dare babu rana, ni kaɗai na san abinda yake damuna, duk yadda zan yi kwatance baza'a gane ba." "Waye ya ɗora miki ciwon?." Jin tambayar da yayi mata ta gane a fili tayi maganar ta kulle ido ta buɗe saboda ciwon da take ji tace, "Allah ne, kuma shine zai yaye min." Bebi yace, "Meyasa kike yiwa kan ki fatan mutuwa bayan kin san da haka?." Idon ta ya cika da hawaye hakan ya saka da sauri yace, "don Allah kar ki yi min kuka." Sakkowa hawayen suka yi kan kuncin ta tace, "rayuwata bata da amfani ne." "Saboda kin rasa ni?." Da sauri ta kalle shi suka haɗa ido ta tabbatar shine yayi maganar ba wani ba, bata daina kallon sa ba tace, "eh, na rasa ka har abada na tabbatar da hakan." Bebi cikin tausasawa murya yake mata magana hakan ya saka yace, "baki da wannan tabbacin, kuma lafiyar ki na da mahimmaci a rayuwar ki da ta wanda suke tare dake, zama cikin damuwa da sakawa kan ki damuwa yana saka wasu da suke kewaye dake a damuwa ciki har dani Ruman!." Kallon mamaki yaga tana yi masa yace, "eh har ni! Ina damuwa da shiga damuwar ki saboda kema damuwa ta ce, abinda ya dame ki ya dame ni. Meyasa baza ki sassautawa kan ki ba ko dan irin mu da muke kewaye dake ne Ruman?. Meyasa ko dan saboda mu da muke shiga damuwa saboda damuwar ki baza ki daina sakawa zuciyar ki abinda yafi ƙarfin ta ba?." Kallon sa take yi da mamakin abinda yake cewa tace, "Da gaske ka damu da damuwa ta?, da gaske kana cikin masu jin zafi a zuciyar su in bani da lafiya?." Ya sake nutsuwa sosai yace, "in ban damu dake ba bazan fito jiya nazo wajan ki ba, in ban damu dake ba babu abinda zai fito dani yanzu. Na fito daga gida kawai saboda nazo naga ya jikin ki, dake na kwana a zuciyata, ya kika kwana ya jikin naki haka na dinga tunani har garin Allah ya waye. Meyasa baza ki daina bawa kan ki damuwar da tafi ƙarfin ki bane?." "Ya zanyi? Bani na ɗorawa kaina ba, Allah ne kuma shine zai yaye min." Bebi ya sauke ajiyar zuciya cikin tsananin tausayin ta yace, "kema sai kin yi ƙoƙari sannan zaki ga addu'ar tana tasiri a kan ki, Ruman don Allah kar ki bawa ciwon ki damar zuwa stage na gaba, hakan bazai yi mana daɗin ji ba a kunnen mu, ki taimaka mana kar ki bari damuwa tayi tasirin da zata haddasa miki wani sabon ciwon wanda ya zarce wannan." Ta girgiza kai tace, "bazan iya ba, in nace na cire damuwa ƙarya nake, yanzu na fara shiga damuwa Beb, yanzu na fara" ta faɗa murya na rawa sosai. Ya gyara zaman sa ya fuskance ta ya riƙo hannun ta yace, "ai daurewa ake yi, ba a lokaci ɗaya ake iya aikata abinda ake ba, sai kin jajirce kina addu'a ba dare babu rana sannan zaki samu sassauci. ai babu abinda yafi ƙarfin Allah, nima zan taya ki wajan yaye miki damuwar ki." Ta kalle shi sanyin hannun sa na ratsa hannun ta ta sake riƙe hannun sa sosai tace, "da gaske zaka taya ni bayan kasan kaima damuwa ta? Taya zaka yaye min damuwar soyayyar ka da take tare dani?." Yayi shiru bai ce komai ba tayi murmushi tace, "Ni nasan baza ka iya ba, baka sona a yanzu gabaɗaya, yaye min damuwa na nufin zama tare dani a matsayin matar ka kuma baza ka iya ba." "Ina son ki mana Ruman, waye yace bana son ki?." Ta lumshe ido tana girgiza kai tace, "ba irin wannan son ba, daga jin yadda kayi saurin furta shi ba wancan bane." Yayi murmushi yace, "daman shi so kala-kala ne?." Ta ɗaga kai alamun eh ya sake yin murmushi yace, "ni dai ɗaya na sani kuma gashi na faɗa miki, ki kwantar da hankalin ki ki cigaba da addu'a, in auren Adnan Alkhairi ne a gare ki Allah zai zaɓa miki shi, in ba alkhairi bane Allah zai canja miki da mafi alkhairi. Ki daina saka damuwa akan abinda baki da tabbas na mallakar sa, saboda ko yau za'a ɗaura min aure dake sai Allah ya rubuta zaki aure ni sannan za'a kira ki da sunan Matata. dan haka ki barwa Allah kawai shine maganin damuwar ki a ko yaushe, in kika bashi zaɓi zai zaɓa miki alkhairi a rayuwar ki, in ni ɗin ne alkhairi wallahi sai na aure ki, in ba ni bane bazan aure ki ba." Rumana tayi murmushi sai a lokacim ta tuna waye shi, yana yi mata wannan kalaman ne kawai saboda ciwon da aka ce tana dashi, shi kuma matsayin sa na likitan zuciya kwantar mata da hankali da saka ta murmushi aikin sa ne,  in ba dan haka ba bazai zo ma inda take ba. Shiru tayi ta koma ta kwanta har lokacin da murmushi a fuskar ta shi kuma ya saki hannun ta ya tashi ya fita. Office ɗin sa ya shiga ya tsaya yana tunanin damuwar Rumana, shi dai baya tunanin zai iya auren Rumana amma yana tausayin ta fiye da tunanin mai tunani, yana jin tausayin ta har a jinin sa amma auren ta kam baya jin zai iya. Ya sauke ajiyar zuciya ya kulle ido ya buɗe zuciyar sa na sake tuna masa da ciwon da ta kamu dashi, a bayyane yace, "zan iya auren ta ko dan wannan ciwon nata, Allah ka kawo man mafita ni da ita." Bai bar asibitin ba sai da yayi magriba yana ta kiran Manal bata ɗauka ba hakan ya saka shi wucewa gida. Falon farko babu kowa an gyara shi dai sai ƙhamshin turaren wuta yake yi wanda baya ƙauna, nan take kansa ya sara jijiyoyin kan suka fara harbawa yayi tsaki ya shiga na biyun a nan ya jiyo hayaniya da alama ba ita kaɗai bace. Abinda yaji ana cewa ne ya tabbatar masa da ƙannen sa ne dan maganar sa kawai suke yi ana bawa Manal labarin saka aikin sa ana dariya, jin hakan sai ya ɗaure fuska kamar ko yaushe ya shiga falon da sallama duk suka amsa suna kallon sa kowa yayi tsit babu wanda ya kuma cewa komai. Kallon Manal yayi ganin ta a zaune cikin su ana hira da dariya kamar sun jima da sanin juna, in ka shigo ka gansu ma baza ka gane wacece matar gidan ba a cikin su. Ya kulle ido yayi ya buɗe dan ƙhamshin ya cika falon yayi tsaki kawai bai ce komai ba ya wuce zuwa ɗaki. Yana wucewa Kausar tace, "me na faɗa miki Fadila? Wallahi wannan ƙhamshin ne ya jawo yake ɗaure fuskar, Sai da nace kar ki yi kika yi Anti Manal gashi nan ta jawo miki mijin ki kai zai fara ciwon kai yanzu" ta faɗa tana kallon Manal. Suka miƙe a tare Kausar suka ce, "Anti Manal ai mu kin ga tafiyar mu, tunda kika ga bai kula mu ba gwara mu tattara kayan mu mu koma." Tayi dariya tace, "da wuri haka? Allah na ɗauka sai anjima." "Da bai dawo ba sai mu kai bayan I'sha, da yana fara'a sai mu kai har goman dare ana hira har dashi, yanzu in fara mana faɗa sai mun ji Ina ma bamu zo ba" Kausar ta faɗa tana yin gaba duk suka suma suka bita Manal ta raka su har bakin ƙofa tana musu godiya kafin ta dawo ta shiga inda ya shiga. Tana shiga ta same shi a zaune ya dafe kansa tayi sallama ya amsa ya ɗago ya kalle ta yace, "Amma nace miki bana son wannan ƙhamshin ko? Meyasa kika yi bayan nace miki yana cutar dani?." Manal jin yadda yake magana a ɗan kausashe sai tace, "am sorry, bani nace Fadila ce itama mistake ne, in sha Allah bazan sake ba." Ya kulle ido lokaci ɗaya yake ji kansa na yi masa ciwo dan yasan shikenan ta masa haramcin zaman falon har gwara ma ƙaramin zai iya zama kafin ƙhamshin ya fita. Buɗe idon yayi ya ganta a tsaye ta sunkuyar da kai bata ƙaraso ba  yaji tace, "Ya mai jikin?." Ƙoƙarin komawa daidai yayi duk da kan sa ciwo yake amma ya dake yace, "daga nan zan faɗa miki? Zo ki zauna." Ba musu ta tako kusa dashi zata zauna ya jawo ta jikin sa hancin sa a wuyan ta yace, "I missed you." Tunawa lokacin sallah yayi sai ya sake ta yace, "mai jiki da sauƙi." Ta tashi daga jikin sa shima ya miƙe tsaye yana nannaɗe hannun riga alamun alwala zaiyi ya kalle ta yace, "ki yi alwala mu yi sallah ko?." Ta amsa da to ya shiga alwala ita kuma ta fita daga ɗakin. Har ya fito ya jima a tsaye yana jiran ta bata dawo ba sai da yayi kamar zai fita sai gata ta shigo tace, "na jima ba? Mama ce ta kira ni." Baice komai ba ya tayar da sallah itama ta tayar. Sun idar da i'sha suka sake yin sallah raka biyu, sannan suka yi shafa'i da wutir. Tana zaune a bayan sa suka yi addu'a kafin ya juyo yana kallon ta yace, "jiya ya kamata ace mun yi sallar da muka yi yanzu, Amma rashin lafiyar ki saka aka ɗaga sai yau." Bata ce komai ba sai sunkuyar da kai da tayi ƙasa tana wasa da hannun ta yace, "zo mu je ki raka ni kitchen" ya faɗa yana tashi tsaye itama ta tashi tsaye, ya kalle ta yaga atamfa ce a jikin ta amma yanzu riga da siket ne yace, "ki cire hijjabin mana" ya faɗa yana matsowa ya zame shi da kansa ya bita da kallon up and down yace, "wait! Wai daman Manal ɗin da gaske tana da body shape ne ko dai dai?." Jikin sa ta faɗa ta kulle fuska tana jin kunyar sa sosai shi kuma yayi dariya yace, "a faɗa min gaskiya, in na gaske ne na sani in a kasuwa aka siyo shima na sani." Bata ce komai ba sai sake riƙe shi da tayi tana sake cusa kanta a ƙirjin alamun kunyar take ji yayi dariya mai sauti yace, "okay, bara na duba da kaina naji na gaske ko na ƙarya" ya faɗa yana ƙoƙarin kai hannun ƙirjin ta. Da sauri ta sake mannewa a ƙirjin sa tana girgiza masa kai, ya sake yin dariyar nishaɗi da farin ciki yace, "Shikenan a cigaba da ɓoyewa, zamu gani." Ya faɗa yana ɗago ta daga jikin sa amma ta rufe ido da hannu ta, ya saka hannun sa ya cire hannun nata amma ta kulle idon ta. "Kinga buɗe idon ki kitchen zaki raka ni, mu je" ya fada yana jan hannun ta suka fita sai a lokacin ta buɗe idon suka shiga kitchen kamar yadda yace. Tana nan tsaye taga ya ɗauko leda a fridge ya ƙaraso ya buɗe ledar taga kaza ce a ciki yace, "warming ɗin ta zamu yi tayi zafi sosai kamar wacce zata ci." Ya faɗa yana kallon ta ta gefen ido ganin bata fahimta ba yayi murmushi yana kunna sabuwar microwives, plates ya ɗauka ya saka gasassun gajin guda biyu ya saka a microwave ɗin ya kunna ya basu mintina goma. Manal ta kalle shi tace, "akwai abinci fa an kawo daga gidan Yaya." "Na sani, wannan zan ciyar da kazata ne, shiyasa nake so tayi zafi kamar yadda kazar tawa take da zafi." Manal tace, "kazar ka?, kaza tana cin kaza ne daman?." Ya wara ido yana kallon ta yace, "baki sani ba?." Ta girgiza kai alamun eh kafin tace, "sai kace wata kare ko kura?." "Ai ni kaɗai nake ciyar da kaza da naman ta, saboda so nake taci tayi ƙwari sosai dan in na tashi yanka ta na samu abinda nake so nima. Haka zan gasa ta yadda nake so bazan tausaya mata ba duka zan cinye  naman ta tass, kinga ai na mayar da kazar da na dinga bata ko?" Ya tambaya yana kallon ta. Manal ta taɓe baki ba gane wannan lissafin nasa tayi ba tace, "ni wallahi ban gane ba." Yayi murmushi mai sauti bai ce komai ba ya kashe na'urar ya ciro kazar sai tiriri take kuwa ya canja plate ya kalle ta yace, "yanzu mu je mu ci abinci sai na kaiwa kazata naman ta." Tare suka fito ya zauna a ƙaramin falon tace, "kazo muje abincin yana ɗaya falon." "Bazan iya sake komawa ba, kaina ciwo zai yi." Manal tace, "bara na ɗauko." Zata wuce shi ta tafi yace, "tsaya ni mu je." Daurewa yayi kawai suka fita aka ɗauko abincin suka dawo ya zauna yana zuba musu abincin tare kamar ɗazu, yana bata tana ci, bai bata sosai ba yace dole sai taci kazar nan in ta rage zai kaiwa kazar sa ragowar. Ta cinye cinya guda ɗaya tace ta ishe ta tasha ruwa tace, "ni na ƙoshi zan je nayi wanka." Da kai ya bata amsa ta tashi ta shiga ɗaki shi kuma ya murmusa ya ɗauke kazar ya mayar fridge ya fita da abincin ya bawa mai gadi ya juye ya bashi kwanon ya dawo dashi ya ajjiye a kitchen shima ya shiga nasa ɗakin da niyar yin wanka na musamman. Lokacin da ya gama shiryawa ya fito zuwa ɗakin ta ya shiga itama ta shirya cikin riga wacce ta wuce guiwa kaɗan amma tana da faɗi sosai kuma roba ce. Kallon ta yake yi a zuciyar sa yana tabbatar da Manal ɗin sa fa akwai sura ba ciko bane na gaske ne amma a zahiri sai yace, "zo mu je wancan ɗakin ki ga wani abu." Bayan sa ya biyo zuwa nasa ɗakin suna shiga ya kulle ƙofa yace, "nan ne makwancin ki ba can ba partner, ki kwanta in bacci ki ke ji."  Manal ta kalle shi bata yi magana ba ya kashe hasken ɗakin duhu ya mamaye ɗakin bata ganin gaban ta tace, "ni fa ba bacci zanyi ba, ka kunna don Allah." A gab da ita taji maganar sa yan fesa mata iskar bakin sa yace, "nima ba baccin zan yi ba." Hasken idanun juna suke gani tsoro ya cika mata zuciya tunawa da abinda zuciyar ta take faɗa mata zai faru tace, "to ka kunna hasken." Fuskar sa daf da ta ta yace, "mu zauna a haka Manal!" Ya faɗa yana kai bakin sa kunnen ta yana fesa mata iskar bakin sa a cikin kunnen nata. Kan gadon ta zame ta zauna tsoro ya mamaye mata zuciya ƙirjin ta har ɗagawa yake saboda tsoro, shima ya zauna kusa da ita ya riƙo kanta yana kallon idon ta ita kuma ta kulle nata idon a hankali yake kai bakin sa kusa da nata kafin ya sauke nasa a hankali ya fara kissing ɗin ta slowly in romantic ways. In less than ten minutes ya canja tunanin Manal, ta fara tunanin anya itace kuwa, domin kuwa a sabuwar duniyar da bata taɓa tunanin zuwa cikin ta take a wannan lokacin. Yadda yake kissing ɗin ta kaɗai ya gama tafiya da ita balle da tafiya ta fara miƙawa, ta shiga hannun sa sosai ya riƙe ta kamar yadda kuku yake riƙe kaza a hannun sa, ya fara sararafa ta kamar yadda ake sarrafa jariri, ta kasa koda motsi saƙon sa kawai take karɓa har zuciyar ta ba iya gangar jikin ta, domin kuwa abin ya girmi gangar jiki kawai dole zuciya ta shigo ciki. Bebi ganin da gaske fa ya gama rikita Manal taje inda yake so taje, damar da yake so ya samu ya tabbatar ya same ta a hannu a wannan lokacin, bai yi wasa da wannan damar ba ya riƙe ta hannu biyu ya tabbatar ya keta hazon Manal cikin salon soyayya da tsantsar qaunar da yake nuna mata ruwa ruwa. A wannan lokacin Manal ta farga jin kiɗa ya canja rawa ma ta canja, ta yuƙuura zata kwanci kanta amma Bebi yaƙi bata wannan damar sai da ya tabbatar ya mayar da ita cikakkiyar matar sa, ya ɗora mata iddar sa ko a lokacin ya faɗi ya mutu bayan takaba sai tayi masa idda. BDƘB2P21 Manal tana kwance a jikin sa tana kuka tare da jan numfashi kaɗan-kaɗan cikin matuƙar gajiya da ciwon da take ji a jikin ta da kuma can cikin jikin ta. A wahale take ƙirjin ta da ko ina na jikin ta zafi yake mata, daƙyar take iya numfashi saboda wahala da gajiyar da take tare da ita. Adnan kam yana riƙe da ita sai aikin rarrashin ta yake yi duk ya ruɗe, ko kaɗan baya so yaji tana kuka saboda Manal ɗin baya ba itace yanzu a zuciyar sa ba, matsayin ta ya sake tashi daga mataki na da yawa ya koma matakin babu adadi. "Bayana!,Bayana ciwo yake min, Wayyo Allah mara ta zata cire!" Ta faɗa tana kwance a jikin sa cikin wahalar da take ɗawainiya da gangar jikin ta. "Sannu, zai daina kin ji, ki yi shiru ki daina kuka, ni kukan ne bana so" ya faɗa yana jijjiga ta a jikin sa kamar yadda ake yiwa jariri in yana kuka. Girgiza kai take a ƙirjin sa tace, "ni ka kaini wajan Mama, bazan kwana a nan ba, ka kaini wajan Mama. Kaina zai cire ka taimaka min ka kaini wajan ta." Hannu ya saka ya taɓa screen ɗin wayar sa yaga ƙarfe ɗaya na dare ya dawo da kallon sa ga fuskar ta duk da babu haske sosai yace, "I'm sorry partner, ki daina kuka don Allah bana son jin kukan." Bata daina kuka ba tace, "ni kawai ka kaini wajan Mama, ni kaɗai na san abinda nake ji. Mara ta cirewa zata yi." "In marar ta cire ni kuma nayi ya kenan? Baza ta cire ba kin ji my love, ki yi haƙuri ki daina kuka shine bana so. Kinga jikin ki har yayi zafi." Shiru yaji tayi ta daina magana tana kwance a jikin sa tana juya kanta a ƙirjin ta dan ya fi matsanta mata da ciwo,ya dafa kanta yaji yayi zafi shima a hankali yace, "sai kin daina kukan zaki samu sauƙi Manal, kinga kan ki ma ciwo yake ki daure." Shiru tayi ta kulle idon ta abubuwan da suka faru suna mata yawo a idon ta da ƙwaƙwalwar ta, ta kasa amincewa ita Manal ce ta kasance haka da wani namiji, wai itace a kwance a jikin wani namiji bayan ya kammala abinda yake so da ita, ganin abun take tamkar a mafarki wanda take yi tana jira lokacin farkawar ta yayi. Irin kalamai da maganganun da ya dinga mata in ta tuna iya su kaɗai kunya take ji balle in ta tuna ita dashi yanzu an zama abu ɗaya, babu saura abinda zata ɓoye masa a jikin ta shima babu sauran abinda zai ɓoye mata a jikin sa. Da wannan tunanin bacci ya ɗauke ta sai saukar numfashin ta yaji ya sauke ajiyar zuciya, kusan mintina arba'in kenan yana so tayi bacci ta ƙi sai koke-koke take yi shi kuma baya so saboda ya san laifin sa ne. Sake gyara mata kwanciya yayi a jikin ta yadda zata ji daɗin baccin sosai kafin ya kulle ido shima bacci ya ɗauke shi. Alarm ɗin da ya saka a wayar sa nee ya tashe shi, ya farka da sauri ya kashe saboda kar ta tashi ya kalli agogon yaga asuba tayi ya tashi ya shiga banɗaki, shi kansa bayan sa ciwo yake sosai da yana da dama kamar ita da yayi kuka shima kamar ita. Sai da ya fito daga banɗakin ya kunna hasken ɗakin kaɗan ba duka ba ya tako zuwa inda take ya sauke numfashi a hankali yana tunanin tashin ta kafin yace, "Partner lokacin sallah yayi" ya faɗa yana riƙe hannun ta tare da taɓa wuyan ta ko zai ji zafi.  Buɗe ido tayi suka haɗa ido sai ta kulle idon da sauri yace, "tashi ki yi alwala, lokacin sallah kar ya wuce mu kamar jiya." Ƙoƙarin tashi take yi ya riƙe ta ta tashi zaune tana dafe kai, riƙe hannun ta duka biyun yayi ya tayar da ita tsaye tace, "Wayyo Allah, ƙafata tayi tsami" ta faɗa tana komawa ta zauna cikin rauni. Sunkuyawa yayi ya ɗauke ta cak zuwa banɗakin ya ajjiye ta a gefen bathtub ya kalle ta yace, "na yi miki alwalar?." Kai ta girgiza alamun a'a bata kalle shi ba sai ya fita ya barta har da ja mata ƙofa dan baya so su rasa lokacin sallar. Bata jima sosai ba tazo bakin ƙofar tana takawa daƙyar harda hawaye saboda ragwanci da shagwaɓa irin ta ta, tana buɗe ƙofar ta ganshi a tsaye yana jiran ta, bai tsaya yi mata magana ba ya ya sake ɗauko ta ya dire a tsakiyar ɗakin ya bata babban hijjab da zanin da ya je ɗakin ta ya binciko, ganin ta kasa ƙarba sai ya saka mata da kansa hijjabin ya sauka har ƙasa yace, "daure mu yi sallah." Ta ɗaga kai kawai bata iya magan ba. Sallah suka yi raka'a biyu sannan ya sake tashi ya ja su sallar asuba.  (Sallar raka'a biyu kafin sallar asuba annabi Muhammad s.a.w yace tafi girman duniya da abin da yake cikin ta. Ƴan uwana mu dage da sallar raka'atar fijir, alkhairi ne a baibaiye da ita ta ko ina, a duniyar zaka ga sakamakon hakan balle aje lahira). Bayan sun idar ya juyo yana kallon ta yaga kanta yana ƙasa tana niyar yin magana ya riga ta yace, "Ina kwana milky beauty." Bata amsa ba kuma bata ɗago ba, ya murmusa kaɗan yana sauke numfashi ya dawo kusa da ita yana leƙa fuskar ta yaga hawaye take yi cikin raunin murya yace, "oh Manal! kukan na meye kuma?, akwai abinda yake damun ki? Me kike ji?. Ki faɗa min in akwai damuwa muje asibiti." Manal murya na rawa cikin kuka tace, "komai ma damuna yake" ta faɗa tana kwanciya a jikin sa tana kuka, ya riƙe ta cikin tausayawayace, "Shikenan ki daina kuka, na tuba, na karɓi laifina a yafe min." Zame hijjabin jikin ta ya fara yi ya cire ya kalle ta yaga zanin ma ya kwance yana gefe, rigar sa ce fara mai maɓallai a jikin ta iyakacin ta cinyar ta, ko ina na farin jikin ta a bayyane yake musamman daga ƙirjin ta maɓallan a buɗe suke ana iya ganin rabin farin ƙirjin ta sosai, a haka yake kallon ta yana sake bin ƙirjin ta da kallo yana hango ƙirjin nata a zahirin su babu wani mayafi da ya rufe su. Tsigar jikin sa ta tashi, nan take abinda ya faru jiya da yanayin da ya shiga a jiyan ya dawo kansa da gangar jikin sa, cikin sake son kasancewa a yanayin da ya bari ya kalle ta muryar sa a ƙasa yace, "taso ki kwanta" ya faɗa yana miƙewa ya riƙe ta, itama ta tashi suka ƙarasa ya kwantar da ita a kan gadon idanun ta a kulle har lokacin. Hasken ɗakin ya kashe ya dawo ya kwanta inda ya tashi yana kallon fuskar ta da idanun ta suke a rufe, kulle ido yayi ya buɗe zallar sha'awar ta tana sake fizgar sa, so yake ya daure amma kamar bazai iya ba. Da kanta ta dawo kusa dashi ta shiga jikin sa tana cusa kanta a ƙirjin sa, hakan da tayi ya sake saka shi a cikin sabon yanayi ya kulle ido ya buɗe cikin tsantsar shauƙi ya riƙe bayan ta yana shafawa a hankali. Hannun sa dake gaba ya fara buɗe maɓallan da yake gaban rigar ta har ya buɗe su duka ya fara yawo da hannun sa a jikin ta a hankali. "Partner ka daina!" Ta faɗa a hankali idon ta a kulle har lokacin. daidai kunnen ta ya kai bakin sa yana cigaba da yin abinda yake yi yace, "it's just a massage" ya faɗa yana ɗora bakin sa kunnen ta yayi kissing na lokaci kaɗan kafin ya gangaro wuyan ta cikin salon da zai ɗauke mata hankali. Kashe mata jiki yake da kisses masu zafi wanda ya saka ta yin shiru, idanun ta suna kulle har lokacin amma gangar jikin ta suna karɓar abinda yake mata sosai tana enjoying, ba kamar yadda yake kiran sunan ta a hankali sai yayi shiru ba ya cewa komai bayan wani lokaci sai ya sake kiran sunan ta. Sai da ya tabbatar zai samu abinda yake so ba tare da turjiya ba sannan ya canja hanya ba tare da yayi tunanin sabuwar ƙofar da aka buɗe ta samu akasi wajan buɗewa, kafin a sake shiga wannan ƙofar yana da kyau a bada lokaci wajan gyaran ta. Manal tayi ƙara mai sauti wacce bata yi ta a lokacin farko ba yayi saurin rufe mata baki bai daina abinda yake yi ba domin bazai iya dakatawa ba, a wannan lokacin jin sa yake a sama yana yawo cikin gajimare. Lokacin da ya farga da abinda yayi mata da hanzari ya miƙe yace, "Subahanallahi! Na shiga uku ni Adnan." Kallon ta yake tana kwance tana kuka bai tsaya tunanin komai ba ya shiga banɗaki kawai, bai jima ba ya dawo ɗaure da towel ya ɗauke ta ya shiga da ita banɗakin zuciyar ta gabɗaya babu daɗi. A cikin ruwan da ya haɗa mata ya saka ta dan taji sauƙin abinda take ji. "Wayyo Allah, Wayyo Mamana!" Ta faɗa a firgice lokacin da ta jita a ruwan zafi. "Relax please, zaki ji daɗi ki daure." Manal ta fara masa doke-doke cikin ragowar ƙarfin da ya rage mata tace, "ka barni ka fita, ka ƙyale ni ka tafi, ka tafi ka ƙyale ni" ta fada tana dukan sa da duka hannun ta Hannuwan na ta ya riƙe yace, "i'm sorry partner, I'm sorry please" ya faɗa yana riƙe fuskar ta da har lokacin take kuka yana ɗurkushe yana kallon ta. "Ni dai ka fita, ka fita kawai" ta faɗa muryar ta har sarƙewa take yi. Ganin kukan yayi yawa sai ya fita ya barta gabaɗaya zuciyar sa babu daɗi dan ya san bai kyauta ba. Da sauri ya koma ɗakin ta yayi wanka ya fito ya dawo ɗakin ya saka doguwar riga ya yi knocking banɗakin da take ciki dan yaji ba motsin ta. Murɗa handle ɗin yayi ya shiga ya same ta a zaune ta saka bathruf sai rawa jikin ta yake yi. Da hanzari ya shigo ya ƙarasa inda yace, "Manal lafiya? Me yake damun ki?." Fuskar ta ta riƙe yaji zafi alamun zazzaɓi ne yake son kamata ya ɗauko ta ya dawo da ita kan gadon ya ajjiye ta yace, "Ina zuwa" ya faɗa yana fita. Bai jima ba ya dawo da tea a hannun sa da magani, turus yayi yana kallon ta ganin ta a kwance har tayi bacci, yayi murmushi ya ajjiye cup ɗin da maganin ya ƙaraso ya zauna ya taɓa fuskar ta yaji da zafin har lokacin. Kallon gashin kanta yayi ya ganshi a jiƙe sosai ya tashi ya shiga bathroom ɗin ya ɗauko ƙaramin towel ya dawo yana goge mata gashin kanta yana murmushi  yana ji kamar ya mayar da ita ciki saboda so. Ribbon ɗin ta ya ɗauka ya ɗaure gashin ya gyara mata kwanciya sosai yana riƙe da kanta yace, "Manal rigima, ko da yake na tsokano ki ne" ya faɗa yana mata kiss a goshi ya rufe ta ya tashi ya fita zuwa falo, ba jimawa ya dawo shima ya kwanta dan a gajiye shima yake sosai.     ****** "Me ka ke so kace min ne Alhaji Mu'azzam?." Kallon sa Abba yayi bayan ya sauke ajiyar zuciya yace, "har yanzu babu yarinyar da take tsaye a raina kamar Mubeena, Ina ji a zuciyata in ban samu yarinyar nan ba bazan ji daɗi ba ko nace zan iya shiga wani hali, in fact a zuciyata Ina jin zan iya auren ta na zauna da ita matsayin matata." Da mamaki Alhaji magaji yake kallon sa bayan ya zaro ido waje yace, "Aure! Aure fa kace? Wannan mitsitsiyar yarinyar ka ke zancen aure a kanta?." Ya dawo ya zauna shima a raunane yace, "To ya zanyi? Har cikin zuciyata nake jin ta, na rasa ta inda zan ganta, ta kulle ko wacce ƙofar da zata sada ni da ganin ta. Da na koma Kano gidan su zan nema naje na kai kaina matsayin wanda zai auren ta, na gaji da dakon abinda nake ji a raina, kewar jin muryar ta kawai nake yi gashi ban san ya zanyi ba." Alhaji Magaji ya girgiza kai yace, "maganar da ka ke yi ya tabbatar min ba wasa ka ke ba, yanzu duk matan garin Abuja, duk matan ƙasar waje, fararen mata da ƙakaken mata ka rasa wacce zaka zaɓa sai wannan yarinyar da ko wayewa bata yi?." "Saboda rashin wayewar ta ta nake so na aure ta, da farko ba da niyar aure nake tare da ita ba, amma yanzu auren ta nake so nayi har zuciyata. Ban san abinda nake ji a kanta ba." Alhaji Magaji ya jinjina kai yace, "wahala ce bata ishe ka ba, na gidan ma ya ka cika dasu da zaka ɗaukowa kan ka wata?." Tsaki yayi jin hakan sai ya share bai ce komai ba Alhaji Magaji yace, "ya batun yaron nan Muhajid wai? Haka za'a ƙyaale shi ya yiwa banza kenan?." Abba ya fusata yace, “shi ɗin banza? Waye shi? Yaushe aka haife shi?. Wallahil azim sai na hukunta shi, sai na tabbatar na saka masa zafin da ya saka min a zuciyata. Yar cikina a yi mata fyaɗe kuma na bar maganar? Bari na koma Kano kai dai kaga abin mamaki, zan je cikin kwanakin na saboda zan gaisa da matar Adnan da kuma mijin Mimi, duk abinda ma zan yi zan aiwatar dashi." Alhaji magaji yace, "ya kamata dai, ni kaina abun har zuciyata balle kai, wannan ai wulaƙanci ne da cin zarafin mu da iyalan mu." Abba ya girgiza kai cikin jin zafin abinda aka yiwa Lubna gefe ɗaya kuma soyayyar Mubeena ta gama mamaye zuciyar sa. BDKB2P22 Manal ko da ta farka bata gane yanayin garin ba saboda  ɗakin da duhu sosai ta tashi zaune tana yatsine fuska. kunna haske ɗskin akayi aka shigo yace, "good afternoon my dear wife, have a wonderful evening with your beautiful loved ones" ya faɗa yana shigowa yana kallon ta da fara'a a fuskar sa. Haɗa ido suka yi kafin ta janye nata idon yana kallon gefe fuskar ta babu walwala, sai yaga ta rame fuskar ta tayi ja gata tayi wani iri kamar ba ita ba, ganin hakan sai ya ƙaraso ya zauna agefen ta ya kai hannu wuyan ta ta kare da hannun ta tayi gefe alamun bata so ya taɓa ta. Ya bita da kallo yace, "body temperature ɗin ki kawai zan ji fa" ya faɗa a sanyaye yana kallon ta. Numfashi take saukewa a hankali bata ce komai ba  kuma bata kalle shi ba yace, "kina fushi da ni ne kyakykyawar matata?." Banza ta masa dan bata da niyar magana yace, "okay naji, amma ki fara tashi ki yi wanka lokacin sallar azahar ya kusa, in kika yi sallah then ki ci abinci komai meye zan iya ɗaukar sa." Kallon ƙasan ta ta taga yana yi itam sai ta kalla taga gabaɗaya fararen cinyoyin ta a waje suke, ta jawo bargo ta rufe ta kawar da fuska. Allah ya sani haushin sa da kunyar sa take ji shiyasa ta kasa yi masa magana. "I'm sorry my dear, amma kina buƙatar ki yi wanka zaki ji ɗaɗi a jikin ki, sannan nasan kina jin yunwa sosai." Bata ce masa komai ba sai daga baya ta sauke numfashi muryar ta a shaƙe tace, "ɗakin can zan koma, don Allah ka barni naje" ta fada murya na shaking alamun zata yi kuka. "Don't cry, don't cry my love. Zan dauƙe ki da kaina na kai ki amma kar ki yi kuka" ya faɗa yana ɗaukar ta ya fita da ita zuwa ɗakin ta ya ajjiye ta a gefen gado ya tsuguna a gaban ta yace, "Shikenan?." "Kaje" ta faɗa bata buɗe ido ba ya tashi ya fita dan ya ƙyale ta. Ya jima bai koma ba sai da ya tabbatar ta gama duk abinda zatayi sannan ya shiga ya same ta a zaune ta idar da sallah ta miƙe tsaye, durƙusawa yaga tayi ido ya sake cikowa da hawaye ta dafa gadon da yake kusa da ta zauna tana jan numfashi. Ƙarasowa yayi yana ƙare mata kallo cikin tausayin halin da ya saka ta yace, "taso mu je ki ci abinci."  Manal tace, "bana ci." "Manal taso mu je nasan zaki ci." Kawai ta tashi ne saboda kar ta yi masa musu ya ɗauko ta zuwa falon ya zaunar da ita ya haɗa mata tea ya bata tana sha amma ba sosai ba. A hankali take shan tea ɗin yana zaune a gefen ta yana aikin kallon ta. Sai da ta sha rabi sannan ya karɓa ya ajjiye ya bata dankalin turawa da aka soya ta ɗauki ɗaya tana ci daga nan tace ta ƙoshi. Maganin ciwon jiki ya bata ta sha yana zaune a kusa da ita yana murza hannun ta a hankali yana kallon fuskar ta cikin shauƙin soyayyar ta yace, "bana so na ganki haka, nafi so naga muna hira da dariya dake." Bata ce masa komai ba yace, "Manal i so much love you, Ina alfahari dake abinda ya faru kamata yayi ki yi alfahari da hakan ba fushi ba." Shiru tayi bata amsa ba ya sakko ya zauna a kanta carpet yana kallon ta kamar sarauniya da hadimin ta yace, "to gani ki min hukuncin da kike so." "Kamar nai ta dukan ka haka nake ji" ta faɗa bata san ta faɗa ba dan zancen zuci ne ya fito fili. Dariya yayi yace, "to gani ki ta duka Manal har sai kin gaji, indai dukan zai saka ki daina wannan fushin ki dake ni, ni naki ne gabaɗaya." Rufe ido tayi cikin jin kunyar sa dan bata so yaji ba,  yayi murmushi ya tashi ya dawo kusa da ita ya zauna ya kwantar da ita a kan cinyar sa ya zame ɗankwalin kanta yana shafa gashin ta yace, "Partner na gode, na gode da kika mallaka min kan ki a matsayin cikakkiyar mace, bani da abinda zan baki sai dai nace Allah ya bar mu dake har aljanna. And I you have to know that you're my love of my life, Wallahi Manal i so much love you, ni bazan iya cewa ga adadin son da nake miki ba. Ki gode Allah, Allah ya miki baiwa daban daban wacce ni kaɗai na san da ita, that's the why I gone crazy about you, you're so truly special person, and you exceed all my expectations. Shiyasa kika ga na kasa daurewa sai da na sake tara miki gajiya, shauƙin son ki ne kawai Partner, ban yi hakan dan na baki wahala ba. I love you so much" ya faɗa yana mata kiss a bakin ta ƙarami wanda yake burge shi da ɗaukar hankalin sa Tana jin sa bata ce masa komai ba dan maganar ma wahala take mata, amma tayi murmushi ganin hakan sai ya dungure mata kai yace, "nima fa Ke kika yi disvirgin ɗina, tare muka wahalar da juna amma ni ban yi abinda kika yi ba, raguwa kawai." Bata ma bata buɗe ido ba sai ma saka hannu da tayi ta kulle idon cikin jin kunya, yayi murmushi yaje daidai kunnen ta yace, "in kin ji daɗin abinda nace a ƙara min mana. Sannan nima ki faɗa min ya kika same ni? Saurayi ne ni ko kuma akasin haka?." Buɗe ido tayi suka haɗa ido sai ya kashe mata ido tare da ɗaga mata gira da alamun roƙo, ganin abinda yake yi sai ta kulle fuskar ta da sauri yayi dariya a bayyane yace, "Manal rigima." Tashi zaune tayi zaune a hankali yana ta juyo da fuskar ta amma taƙi juyowa tace, "don Allah ka barni, kunyar ka nake ji." Yayi dariya yace, "ni Meyasa bana jin kunyar ki? Naga dai tare muka aikata abin nan ko? In ɓera da sata daddawa da warin ta." Ta kulle ido da kunnen ta yayi murmushi. Kallon agogo yayi yaga rana tayi sosai kuma an sanar dashi an sallami Rumana tun ɗazu yana so yaje wajan Mama ko dan su gaisa. Baya son fita yayi nisa da ita, ji yake kamar ya cigaba da gadin ta kar ƙuda ya taɓa masa ita. Ya kalle ta yana murmushi yace, "Partner zan je wajan Mummy na dawo, akwai abinda kike so?." Da sauri ta girgiza kai dan so take ya fita tayi waya da Maman ta. Murmushi yayi ya matsa kusa da fuskar ta yayi kissing lips ɗin ta sannan ya tashi ya fita. A mota ya zauna yana waya da Huzaifa yana faɗa masa bikin sa saura sati biyu shi, shi ya ma gabaɗaya dole anjima su haɗu ko dan a tattauna. Sai da yayi la'asar sannan ya shiga gida, wajan Mamy ya fara shiga suka gaisa ya tambayi Lubna akace tana wajan Kusar Maryam kuma bacci take. Yana shiga wajan Mama ɗakin ta ya wuce ya same ta a zaune Rumana tana bacci a gefen ta, da girmamawa kamar ko yauahe ya gaishe ta Mama ta amsa da fara'a tace, "Ina Manal?." "Tana gaishe ki Mummy, ya jikin Ruman?." Mama ta sauke numfashi tace, "da sauƙi, mu koma can ɗakin mu yi magana." Ya amsa tayi gaba ya bi bayan ta tana shiga ya shigo shima ta kalle shi tace, "kayi haƙuri daga kai maka mata shekaran jiya zan fara wani zance ko? Dole ce ta saka hakan duba da halin da akace mun soyayyar ka ta saka zuciyar Rumana." Gaban sa ya faɗi sosai amma ya danne bai nuna ba tace, "Adnan na yake hukunci wanda nake ganin zai maka kuma nima zai min, zan maka adalci zan yiwa Manal adalci zan kuma yiwa Rumana ma adalci. Zan tura ta Abuja gidan Yaya Mubakar taje ta cigaba da rayuwa a can, amma....." Sai tayi shiru tana kallon sa. Bebi ya kalle ta yace, "Mummy amma me?." "Ka tuna kayi min alƙawarin auren ta a wannan ɗakin ko?." "Ina sane Mummy, ban kuma canja ba, bazan karya alqawarin ki ba." Mama ta girgiza kai tace, "Shikenan Adnan. Rumana da ta warware zata koma Abuja baza ta dawo ba sai lokacin da nace ya cika. Zaman ta a nan tana ganin ka barazana ne ga lafiyar ta, in tana can zata fi samun sauƙin wani abun. Sai ka shirya ka kuma kasance mai cika alƙawarin mahaifiya, da zarar shekara ɗaya tazo ko bani da rai ka san abinda zaka yi" tana faɗar hakan ta fita ta bar shi a tsaye zuciyar sa bata amince da abinda Mama tace ba gabaɗaya. Da kallo yabi Mama ya rasa me take nufi da abinda tace masa kafin ta fita shi dai bai fahimta yadda ya kamata ba, ɗaga ƙafa yayi da niyar bin ta ya tambaya sai ya fasa amma yana tunanin me take nufi kenan?. Fitowa yayi falon a nan ya tarar da Lubna da Kausar a zaune suka gaishe shi ya amsa har ya gifta su sai ya tsaya ya kalle su yace, "kar ku ga babu idona a gidan nan, wallahi duk motsin ku Ina sani, gwara ku nutsu domin ina nan babu inda naje, ana ta murna sarkin takura baya nan ko?." Lubna tayi dariya tace, "ai Yaya duk abinda kace yana nan babu saɓawa." Yace, "ku kuka sani dai" ya faɗa yana niyar fita Kausar tac, "a gaishe da Anty Manal." Baice komai ba ya fita, yana fita wayar sa tayi ƙara ya duba ganin sunan Mimi sai abun ya bashi mamaki lafiya take yi masa waya da yammar nan?. Ɗauka yayi daga can ɓangaren tace, "Yaya Ina wuni." "Lafiya lau, ya gidan?." "Lafiya lau Yaya, ya Anty Manal? Na kira ta bata ɗauka ba, tana kusa?." "Bana gida, Ina gidan Mummy. Ina mijin naki?." Mimi tace, "wallahi Lafiya lau." Shiru tayi bata yi magana ba kuma bata kashe ba, jin hakan ya saka yace, "shikenan abinda zaki ce?." Mimi tace, "Daman kira nayi na gaishe ka." "To na gode" ya faɗa yana niyar kashe wayar Mimi tace, "Yaya!." "Faɗi kan ki tsaye ban son a rarraba min magana." Mimi tayi murmushi a ranta tana maimaita Yaya Bebi faɗa tace, "mun gode Allah ya saka da alkhairi, Allah ya yi maka abinda kayi mana, Allah ya kula da kai kamar yadda ka kula damu, Allah ya yi maka tukwici da aljanna. A lokacin baya ɗauka muke takura mana ka ke yi, mu dinga jin haushin ka muna yi maka rashin kunya a zuciyar mu, amma yanzu na fahimci kare mutuncin mu ka ke yi Yaya, Allah ya saka da alkhairi, ya barka da Anty Manal" tana faɗa ta yanke wayar ya kalli wayar sai ya murmusa baice komai ba ya ƙarasa wajan motar sa ya shiga ya fita. Gidan Hamza ya wuce yana tuƙi yana tsaki, takaici yake ji haka kawai an fito dashi daga gidan amaryar sa ko hutawa bai gama yi ba.  Yana tsayawa a ƙofar gidan ya ɗauki waya ya kira Manal amma bata ɗauka ba, ya sake kiran ta bata ɗauka ba haka kawai sai jikin sa yake bashi ba lafiya take ba tunda gashi Mimi tace masa ta kira bata ɗauka ba. Yana wannan tunanin ta kira shi ya katse kiran ya kira ta yace, "Partner hankalina ya tashi Ina kiran ki bakya picking, lafiya kike?." Manal tace, "uhum bana kusa ne." "Kina ina? Me kike yi da har kika yi nisa da wayar?." "Nauyi wayar tayi min" ta faɗa a shagwaɓe kamar zata yi kuka. Yayi murmushi yana kallon titi cikin nishaɗi yace, "Ayya dole ta miki nauyi jikin ki ma ya miki nauyi na sani, in na dawo zan dinga ɗaukar ki kin huta da nauyin gabaɗaya." Bata bashi amsa ba yace, "kinci abinci?." "Bana jin yunwa" ta bashi amsa yace, "in zan dawo me zan kawo miki?." "Babu." "Na siyo miki kaina?." "Uhum!" Ta bashi amsa a taƙaice. "Kina so?." Manal tac, "ina so mana, ka siyo." Bebi yace, "to zan siyo tunda kina so, zan shiga wajan su Huzaifa yanzu bazan jima ba zan dawo.  Sun takura min da waya." "Allah ya dawo da kai lafiya" ta faɗa murya can ƙasa ya amsa ta kashe wayar. Yana ta jin shigowar kiran Hamza da suna waya da Manal sai a lokacin ya kira shi yace, "gani a ƙofar gida, an ishe ni da waya kamar wanda ake bi bashi." Kashe wayar yayi ya fito daga motar ya shiga ciki kamar yadda suka saba. BDƘB2P23 A nan gidan Hamza yayi sallar magriba yana ta yi musu mitar da ya saba kafin ya ɗauki hanyar komawa gida. Yana shiga Babban falon  ya tarar dashi a gyare daman a haka ya barshi da ƙhamshi air freshener na tashi, ya wuce na biyun a nan ya same ta a zaune tana karatun alkur'ani. Zama yayi a gefen ta a lokacin ta rufe alkur'anin ta ajjiye ya kalle ta kafin yayi magana tace, "Sannu da zuwa." "Ya jikin ki?" Ya faɗa yana kafe tada idanu tare da kai hannun sa wuyan ta. Manal tace, "da sauƙi,ya Mummy da mai jikin?." "Da sauƙi, Mummy na gaishe ki." "Ina amsawa" ta faɗa bata kalle shi ba. ya kalle ta yaga tayi wani iri da alamun damuwa a tare da ita, ɗago da fuskar ta suka haɗa ido yace, "me yake damun ki?." Manal ido ya ciko da hawaye tace, "jikina ne babu daɗi, komai bana jin daɗin sa, kaina yaƙi ya daina ciwo in na tashi kamar zan faɗi, kuma ina kewar Mama" ta fada kamar zatayi kuka idanun ta na kallon ƙasa. A ƙirjin sa ya kwantar da ita yace, "Sannu, zai daina a hankali zaki dawo daidai. Mama kuma in sha Allah zan kai ki ki ganta ki daina damuwa bana so." Hawaye yaji tana yi tace, "bana jin daɗin jikina sosai, har yanzu ina jin zafi." "Zai daina, kar ki yi kuka kin ji?." "To ka kaini wajan Mama kaji, kwana biyu fa banga Mama ba, ji nake in na ƙara kwana na uku kamar zan mutu." "Shiii! Baza ki mutu ba zaki ganta in sha Allah amma ba yau ba, ki kwantar da hankalin ki ba kun yi waya ba?." Ta ɗaga kai alamun eh yace, "to kin gani, zaki ganta kar ki damu." Ya riƙe ta sosai a jikin sa tayi shiru tana hawaye yace, "Bayan wannan bakya jin komai?." Manal tana hawaye tace, "ni fa bana jin daɗi gabaɗaya, na gaji, bayana a riƙe yake." "Sorry, sai kin ci abinci sannan zaki dawo daidai." "To bakina babu appetite taya zan ci?." "Zaki iya, ina zuwa" ya faɗa yana cire ta daga jikin sa ya tashi ya shiga kitchen ɗin da kansa. A nan yaga sabon abinci daga gidan Yaya ya buɗe yaga macaroni ce yaga harda cole-slow, cole slow ɗin ya ci yaji da zaƙin sugar a ciki sai ya zuba mata iya pasta ɗin ya kawo mata, ya zauna kusa da ita yana bata tana ci a hankali. Taci da ɗan yawa tace, "ya ishe ni, kaima ka ci." Ya girgiza kai yace, "bana cin pasta ni." "To me zaka ci?." "Kaza ta" ya faɗa yana kallon ta. Manal tace, "to ka ɗauko mana ai naga akwai ko?." Ya girgiza kai yace, "ba wannan ba, ni wannan ta ishe ni." Bata kalle shi ba tace, "to wacce?." Daidai kunnen ta yaje ya sakar mata kiss sannan yace, "Ke mana." Ta kalle shi suka haɗa ido ya kashe mata ido tayi saurin kawar da idon ta kafin yayi magana tace, "daman jiya da ka ke cewa kazar ni ce?." Yayi dariya yace, "kin makara ƴan mata." Ta taɓe baki ta ɗauke kai daga kallon sa yace, "ana kiran sallah, zan fita da abincin na bayar ya ishe ki?." Ta ɗaga kai alamun eh ya tashi ya fita da abincin ya bawa mai gadin sa ya wuce masallaci. Bayan ya fita itama sallah tayi bayan ta idar tayi shafa'i da wutir ta idar ta tashi ta shiga ɗakin ta. (Sallar shafa'i da wutir an rawaito Annabi Muhammad s.a.w yace duk wanda baya yin ta a ranar lahira sai yayi dana sani. Allah ka raba mu da yin dana sani a ranar tashin alƙiyama amin.) Wayar ta ta ɗauko ta dawo ta zauna, a lokacin ya shigo ya kalle ta ya ƙaraso ya zauna yace, "yunwa nake ji." Manal tace, "to me zaka ci?." "Nima ban sani ba." "Ka sha tea mana." Ɗan tsaki yayi kaɗan yace, "ni bai dame ni ba." "Kai dai komai baka so" ta faɗa ba tare da ta kalle shi ba. Yayi murmushi bai ce komai ba. "Milky!." Manal tace, "Uhum." "Bikin Huzaifa za'a yi." Ta kalle shi ta saki fuska tace, "yaushe?." "Nan da sati biyu, kuma da yake mahaifin yarinyar ya rasu ba jimawa babu wani shagali da za'a yi, ɗaurin aure ne kawai." "Allah sarki, Allah ya jiƙan rai. Shine Yaya Huzaifa ko ya faɗa min? Lallai ya kyauta" ta faɗa  da fara'a a fuskar ta. Haɗe fuska yayi yana kallon ta yace, "Partner dan nayi zancen Huzaifa shine kike sakin fuska haka? Nace miki fa..." kafin ya gama tace, "Allah ya baka hakuri, bazan sake ba." Girgiza kai yayi ya kawar da kai gefe ta kalle shi tace, "to ai nace kayi haƙuri ko?." Ya kalle ta yace, "to nayi, Shikenan?." Tayi murmushi ta ɗauke kai daga kallon sa dan wallahi kunya yake bata. Ganin hakan sai yayi dariya yace, "ai na faɗa miki zan baki mamakin da zaki kasa haɗa ido dani, gashi tun a kwana ɗaya da fara baki mamakin kin kasa kallona." Bata kalle shi ba sai wayar ta da take juyawa a hannun ta, kunyar sa take ji sosai dauriya tayi har take zaune a kusa dashi bata gudu ɗaki ba. In ta tuna ita dashi a yanzu babu wani hijabi sai kunya ta kamata, sai ta dinga mamakin abun taga har yaushe ma suka haɗu gashi har anyi aure an zama abu guda. Mubeena ce take mata waya sai tayi murmushi ta ɗauka tace, "Yaya Mubeena Ina ta kira ɗazu baki ɗauka ba." Daga can ɓangaren tace, "bacci nake, ya gidan?." "Lafiya lau, kin ƙi zuwa." "Ke wannan mijin naki haka nan bai min ba, Kama yake min da wani wanda na sani shiyasa bana son sakar masa fuska kar ya raina ni." Manal tayi dariya kaɗan tace, "Kai Yaya, da wa yake kama to?." "Wani banzan saurayina ne, amarya ya amarci?." Manal tayi murmushi tace, "Yaya ina Mama?." "Ƙaryar banza, wai ke kunya kike ji ko?. Ke mazan yanzu ba son kunya suke ba in zaki daina ma ki daina, ƴar wahala ƙarya kike kema munafurci ne." Manal tayi dariya ta kalli inda yake sai taga ya tashi ta tashi ta shiga ɗaki itama suna cigaba da waya da Mubeena kafin su yi sallama ta yanke wayar. Mama ta kira suka fara hira tana yi tana canja kaya har ta saka doguwar riga ta bacci iya guiwa dan ba ta son kwana da kaya masu nauyi ko a gida. Suna gama waya da Mama ya shigo ɗakin, tana tsaye a gaban madubi ta hango shi ta madubin ya canja kaya shima zuwa na bacci yana kallon ta. Ƙarasowa yayi inda take ya rungume ta ta baya yana kallon fuskar ta ta madubin ta sunkuyar da kai ƙasa, ya ɗago da kan nata yace, "sunkuyar da kan nan baya miki kyau, zo muje ayi miki Rbs." Hannun ta ya riƙe suka dawo falo suka zauna ya riƙe babban ɗan yatsan ta kafin tayi aune ya ɓula shi ya saka jinin a na'urar yana gani, kallon ta yayi yace, "ya ɗan hau kaɗan, yana da kyau ki fara motsa jiki shima zai taimaka miki." Manal tace, "kuma ni babu abinda naci." "Nima ban ce kin ci ba ai" ya faɗa yana riƙe hannun da ya fasa yace, "shekarar ki nawa da ciwon?." "Bai fi uku ba." "Kina ƙoƙarin kiyayewa" ya faɗa yana mayar da na'urar cikin jakar ta. "Ka koya min yadda ake yi in naje sai na yiwa Mama." Ya kalle ta yace, "a sake fasa hannun naki?." Ta girgiza kai tace, "a'a a gwada a kan ka." Yayi dariya kaɗan yayi ɗin yana nuna mata tare da fada mata yadda normal yake da yadda zata gane in ya hau. "Na gane, in zan je wajan Mama zan tafi dashi sai nayi mata." "An gama ƴar Mama" ya faɗa yana murmushi suka haɗa ido tace, "baka da yawan murmushi amma yau naga kana ta yi, abu kaɗan sai naga kayi dariya." Ya sake faɗaɗa murmushin sa yace, "ke ɗauka kike yau ɗin rana ce ta wasa a wajena? Hmmm baza ki gane yadda kazar nan tawa take da daɗi bane, kamar kar na daina cin kazar nan haka naji. A yanzu ma bani da wani maradi da ya wuce na sake samun ta naci matsayin abincina na dare, kin ga daman ban ci abinci ba" ya ƙara faɗa yana karyar da murya yana kallon ta. Ɗauke kai tayi daga kallon sa gaban ta ya faɗi sosai yaga lokaci ɗaya ta canja zuwa na tsoro, matsawa daga kusa dashi tayi ganin tayi haka shima sai ya matsa kusa da ita, ta sake matsawa tace, "don Allah kayi haƙuri kar ka ka yi min komai, wallahi har yanzu da ciwo daurewa nake kawai amma bai daina ba." "Meye na ja baya kamar kin ga dodo Partner?" Ya faɗa yana riƙo hannun ta yace, "baza ki tausayin min ba?." Ta girgiza kai ta fara hawaye tace, "nice abin tausayi, don Allah kayi haƙuri." "Bafa da yawa na, kaɗan kin ji Manal" ya faɗa da rauni kamar zai yi kuka. Kuka ta fara mai sauti tace, "don Allah ka ƙyale ni." "Shikenan ki daina kuka, wasa nake miki nayi haƙuri ba yau ba" ya faɗa yana kallon fuskar ta da take hawaye.  Murya a sarƙe tace, "Don Allah kar ka sake yi." Ya wara ido yace, "kar na sake kuma?." Ta ɗaga kai alamun eh yayi murmushi nishaɗi, nishaɗi yake ji a zuciyar sa, ganin taƙi daina kukan sai ya matsa kusa da ita sosai yace, "in baki daina kuka ba bazan haƙura ba." Da sauri ta goge idon ta bai ce komai ba ya tashi don ya kulle ƙofar falon. Yana dawowa ya kashe hasken falon, sai ji tayi ya ɗauke ta kawai yana cewa, "nauyi ne fa dake daƙyar nake iya ɗaukar ki" ya faɗa tura ƙofar ɗakin da ƙafar sa yana shiga da ita ɗakin sa ya kwantar da ita a kan gado ta tashi zaune tace, "ba bacci zan yi ba." "To me zaki yi?." "Kallo zanyi a wayata." Ya kashe hasken ɗakin yace, "kunna mana mu gani tare, daman nace zamu dinga kallo film tare dake." Hannun ta har rawa yake dan a tsorace take dashi, ya kula da hakan ya riƙe hannun na ta sai ta firgita tana kallon sa, murmushi yayi yace, "ki nutsu." Jin abinda yace sai ta haɗɗiye yawu na tsoro ta ɗauki wayar ta kunna series ɗin da take gani, yana kwance a gefen ta kanta na ƙirjin sa. Kamar gaske aka fara kallon film sun yi shiru suna sauraron abinda ake faɗa a film ɗin. Romancing aka fara da kisses a film ɗin tayi sauri zata wuce ya riƙe hannun ta yace, "tsaya ki cigaba da gani, ai da bakya tariyewa yau don gulma sai ki ce zaki tariye?." Daina kallo tayi ta ɗauke kanta daga kan wayar, ganin hakan sai ya zare wayar daga hannun ta ya ajjiye a gefe ya tallafo fuskar ta ya fara kissing ɗinta a hankali, kwacewa take so tayi amma ya hana ta hakan ya riƙe fuskar ta sosai dole ta tsaya kawai gaban ta sai faɗuwa yake saboda tsoro. Jin abubuwa da yake yi sun yi yawa ta buɗe baki murya na rawa sosai tace, "Don Allah Dr, don Allah akwai ciwo har yanzu." "Babu abinda zan miki" abinda ya iya ce mata kenan ya cigaba da sarrafata son ransa. A tsorace take sosai tana kuka tace, "nidai don Allah ka ƙyale ni, bana so." Jin tana kuka sosai sai ya kalle ya da raunanun idanun sa yace, "na ce miki babu abinda zan miki, meye na kukan?." Ganin ta kasa daina kukan sai ya jawo ta ya kwantar a ƙirjin sa yace, "shikenan na bari." Har jan numfashi take alamun taci kuka sosai, tana jikin sa a kwance har tayi bacci. Bayan kwana biyu. Ranar laraba ya kama kwantan Manal huɗu a gidan Bebi, soyayya suke sha hankali kwance duk da har lokacin bai sake mata komai ba, ya ɗaga mata ƙafa ne saboda ya san ya wahalar da ita ranar farko, kuma a firgice take dashi shiyasa ya bata lokaci ta sake kafin ya mayar da ita ruwa. Ai kuwa ta sake dashi sosai, ko yaushe hira suke da nishaɗi haɗi da ƙaunar junan su.Duk da kewar Mama ta da take yi ya hana ta kwantar da hankalin yadda ya kamata. A ranar yaje gida ya gaida su Mummy ya dawo ya tarar da ita a zaune tayi tagumi  ya zauna kusa da ita tare da zare hannun ta daga fuskar ta yace, "Partner meye haka?." Sai kawai ta fashe da kuka ta kwanta a jikin sa tace, "Ina son ganin Mama partner, ka kaini wajan ta don Allah." Kai ya girgiza yace, "shikenan, in an idar da sallar i'sha sai muje tare." Ta riƙe shi sosai tana murna ya ɗago ta yaja kumatun ta yace, "ƴar autar Mama." Tayi dariya ta goge idon ta ya kwanta a kan cinyar ta yana kallon ta yace, "Ya school ɗin ki?." Manal tace, "ina nan ina jira kace na fara." Yayi dariya yace, "nayi magana da wata a nan haɗeja road, tace min nan da two months zasu fara ɗaukar student kin ga sai ki shiga ko? Kuma shekara ɗaya ne cousin ɗin, kina gamwa zaki zama professional chef." Manal cikin farin ciki tace, "da gaske?." Ya ɗaga mata gira alamun eh baice komai ba tace, "Alhamdulillah, na gode sosai Partner." Yayi murmushi yace, "schools ɗin a Abuja da Lagos sun fi kyau sosai gaskiya." Manal tace, "to naje Abuja ɗin mana." Ya Harare ta yace, "sai ki barni ni da wa?." Ta turo baki tace, "ka koma gidan Mummy." "Lallai bakya sona." "Ni na isa" ta faɗa tana dariya cikin farin cikin burin ta zai cika. "Nayi alƙawarin zan cika miki dukkan burikan ki, faɗa min bayan wannan sai me kike so?." Manal tace juya ido tace, "ina so zan fara koyar da girki a ig, kasan akwai arewa food bloggers ko?." Ya ɗaga mata kai alamun ya sani tace, "to ina so na shiga cikin su." Yayi dariya yace, "baki da damuwa Manali, ki fara amma banda nuna fuskar ki." Farin ciki ya saka ta yi masa kiss a goshi tace, "na gode my love, na gode sosai." Ya ja hancin ta yace, "Allah yasa kar ki dinga yi musu jagwalgwalo." Ta juya ido tace, "hmm baka san yadda na iya abinci bane." Yayi dariya yace, "zamu gani. Zan saka a kawo miki ringlight ɗin da zaki dinga video dashi, sai a canja wayar ma a samo iphone 15 ko 16. Amma sai kin yi biyayya." Farin ciki ya cika mata zuciya ta sunkuyar da kanta ta ɗora a kan fuskar sa tace, "na gode sosai, na gode komai kace min kuma zan yi." Ganin tana farin ciki sai ya kalle ta yace, "to sai me kuma?." Ta ja numfashi tace, "sai ka koya min mota." Ya tashi zaune yana kallon ta yace, "a koya miki mota kawai kike so?." "Eh mana, ina so naga ina driving." "Bakya so a siya miki?." Suka haɗa ido kafin tayi magana yace, "bakya so kenan. Shikenan ki shirya zan fara koya miki mota sai na dinga ara miki tawa." "A'ani tawa nake so." Bebi yace, "Ke kika ce bakya so koya kike so ki yi." "Allah ina so" ta faɗa da shagwaɓa harda buga masa ƙafa. Ya sauke numfashi yace, "kinga wannan shagwaɓar taki? Hmmm!" Ya girgiza kai bai ce komai ba. Manal tayi dariya dan ta fahimci hakan na taɓa shi sosai ita kuma tana sane take yi duk da ta riga ta saba. Bayan sallar i'sha taci kwalliya cikin abaya mai kyau har da jaka ta ɗauka kana kallon ta kaga amarya mai komai sabo suka fita gidan Mama kamar yayi mata alƙawari. Tun a motar ya lura da irin muryar da take yi, wacce ta kasa ɓoyewa sai murmushi take yi, shi kam sai dai ya ɗauke kai ya cigaba da abinda yake yi. Suna tsayawa ta ƙofar motar ta fita da sauri gidan ta shiga cikin gidan harda gudu. Mama tana tsakar gida ita kaɗai, kasancewar da bikin Manal an saka solar a gidan ko ina da haske. zogale Mama take ci Manal ta faɗo gidan a guje ta faɗa jikin ta kawai ta saka kuka. Mama da ta ji tsoro ta kalle ta tace, "Subahanallahi! Manal kin bani tsoro wallahi." Bata iya magana ba sai kuka da take yi a jikin Mama, Mama ta ɗago ta tace, "meye na kuka kuma? Ke haka ake yi aure ko sati bai yi ba har kin fito yawo?." Sak Manal tayi tana kallon Mama da hawaye a fuskar ta tace, "Mama baki murnar ganina ba?." Mama ta girgiza kai tace, "Ban yi ba, to wai ke rashin ki damuna ɗin me zai yi bayan ina da wata?." Kawai Manal ta saka ƙara ƙarfin kukan ta kamar yarinya ƙarama, Baba da yake ɗaki ya fito yace, "Fatima daina kuka tayi kewar ki faɗa kawai yake yi." Jin muryar Baba sai ta dago tace, "Baba ko bacci bana iyawa saboda tunaninMama, Amma shine zata ce wai me nazo yi." Baba yayi dariya yace, "Wasa take miki, tayi kewar ki yanzu ta gama maganar ki." Sai kuma ta goge idon ta tace, "Baba ina wuni." Mama tayi dariya tace, "sai yanzu aka tuna da gaisuwar?." Baba ya amsa yana murmushi jin daɗi ganin ta cikin walwala yace, "Ina Adnan ɗin?." "Yana mota." Mama tace, "kika bar shi a mota, shi bazai shigo ba?." Manal tace, "ni na manta ma dashi." Mama tace, "kin kyauta ai." Baba ya girgiza kai yana dariya ya fita dan ya shigo da Bebi gidan. Mama ta kalle ta tace, "sai ki shafe hawayen kar ya shigo ya ɗauka dukan ki nayi." Ta goge ido tana turo baki sai ga Mubeena ta fito Manal ta tashi a guje ta rungume ta tace, "Yaya Mubeena kin ƙi zuwa keda Surayya, Wallahi Allah bakwa sona tunda baku je inda nake ba." Mubeena tayi dariya tace, "inyee kaga amarya, kinga yadda kika yi kyau? A haka kike kewar Maman kin yi wannan kyaun a kwana huɗu?." Sallamar Baba ya saka ta bata yi magana ba Bebi ya shigo da sallama shima yan ƙarasowa, Mama ta amsa tana murmushi ya ƙaraso ya zube a ƙasa suka gaisa Mama ta amsa da fara'a sosai ta tambaya shi mutanen gidan ya amsa da kowa lafiya. Mubeena da take gefe ta gaishe shi ta ɗago ya amsa Mubeena tace, "Allah Baba ba wani kewar Mama da take yi, kalle ta fa ƙiba tayi a kwana huɗu kawai,ashe da gaskiya Mama da tace ita bata kewar ta, tunda gashi ita mai ihun tana kewar Maman tayi kyau abin ta." Manal kamar zata yi kuka tace, "Baba kace ta daina cewa bana kewar Mama, Don Allah partner bana kewar Mama?" Ta faɗatana kallo Bebi. ya sakar mata harara dan kunya ta bashi a gaban su Mama take yi masa shagwaɓa tana cewa masa Partner. Murmushi yayi kawai amma bai ce komai ba. Mama tace, "to ni dai ban gani ba, ga Yayar ki ma bata gani ba." Ta kawar da kai kawai ta cigaba da hawaye Mama tana dariya Baba yace, "yarinya tazo ganin ki a dinga saka ta kuka, yi haƙuri Manal wallahi duk faɗa suke yanzu ta gama maganar da kina nan da kin takura mata da shan magani." Ta goge idon ta tace, "Mama daman nazo na duba sugar ki na gani" ta faɗa tana buɗe jakar ta ta ɗauko na'urar. Mubeena tace, "iyayi, har wani iya gwaji kika yi?." Ta kalle ta kafin ta kalli Babtace, "Baba kaga babu ruwan ta dani" ta faɗa tana girgiza kai Baba yace, "Ɗazu anje wajan Huzaifa ya Duba Maman taki ya tabbatar da tana lafiya, kar ki damu na maye gurbin ki wajan nema mata lafiya." "Allah sarki Yaya Huzaifa yana sona yana son Mama, Amma duk da haka fa sai na gwada ki Mama" ta faɗa tana matsowa harda kwance rolling ɗin kanta. Ganim shirmen Manal ɗin yayi yawa sai ya tashi ya yi musu sallama ya fita bayan ya ajjiyewa Mama kuɗi. Mamata kalle ta tace, "mijin ki ya fita tashi ku tafi." Manal tace, "ai yasan ina kewar ki kuma nace masa zan gwada ki." Mama tace, "Wai yaushe kika koya?." "Shekaran jiya" ta faɗa tana matsowa ta riƙe hannun Mama tayi mata kamar yadda ya nuna mata tana kallon range ɗin tace, "to na gani." Mubeena tace, "maƙaryaciya, babu abinda kika iya." Baba dai dariya yake ganin duk suna nishaɗi abin daɗi yake masa, Maman ma haka taji daɗin ganin Manal ɗin tana walwala, daƙyar Mama ta saka Manal fitowa daga gidan da kuka ta fito shima sai da Mubeena ta rako ta. Ta shiga gidan su Surayya bata jima ba ta fito har bakin motar Mubeena ta raka ta tana ta tsokanar ta ta shiga motar ya ja motar ya nufi gidan Mummy kai tsaye. BDƘB2P24 Tafiya suke tana share hawaye ya juyo ya kalle ta kamar zai mata magana sai ya fasa ya cigaba da tafiya, sai yaga ta goge idon tayi shiru tana kallon titi ta naɗe hannun ta a ƙirji. Hannun sa guda ɗaya ya miƙa ya ciro hannun ta daga ƙirjin ta yana murzawa a hankali yana cigaba da tuƙin sa bai ce komai ba. Sake kallon ta yayi yaga duk ta canja yace, "da na san kuka zaki yi da ban kawo ki ba." Manal ta kalle shi da shagwaɓa tace, "to ai na daina." Yayi murmushi yace, "Zamu je wajan Mummy yanzu." Manal ta kalle shi da sauri tace, "Wajan Mummy kuma? Amma baka faɗa min ba?." "Yanzu na faɗa miki." "Haka zan je ban kai mata komai ba? Ni gaskiya a fasa sai na shirya." Juyowa yayi ya kalle ta yace, "sai kin kai wani abun? Gaishe ta kawai zamu yi ai." Manal tayi shiru haka kawai taji gaban ta yana faɗuwa ta sake kallon sa tace, "wallahi kunyar zuwa haka nake, kuma kunyar Mummyn ma nake ji sosai." Ya ɗan kalle ta ya ɗauke kai ya cigaba da tuƙin sa yace, "Zaki daina." Shiru tayi har suka je ƙofar gidan yayi horn aka buɗe masa ya shiga cikin gidan ya ajjiye motar ya kalle ta yace, "muje" ya faɗa yana buɗe ƙofar ɓangaren sa ta riƙo hannun sa hakan ya saka ya dakata yana kallon ta tace, "kana ganin ya dace naje wajan ta da Abaya? Baka ganin kamata yayi na saka atamfa?." Shi mamaki ma take bashi, gabaɗaya ta ruɗe hakan ya saka yace, "ko ki ɗinka bargo ki zo dashi ba, ki fito mu shiga dare yana yi inda abin yi." Dole ta fito suka shiga cikin gidan su kai tsaye wajan Mummy suka nufa. Da sallama ya shiga suna zaune dukkan su suna cin shawarma suka amsa sallamar Kausar ta taso a guje tana cewa, "ga Anty Manal oyoyo." Manal ta riƙe ta tana murmushi tace, "Sis ya gida?." Mummy da take zaune tana kallon tace, "Manal ce da kanta yau kenan? Shigo mana kamar baƙuwa." Manal ta ƙarasa ciki ta zauna a kan carpet ta gaishe da Mama da girmamawa Mama ta amsa tana murmushi tace, "kema ya koya miki cewa Mummy ɗin kenan?, shikenan ku biyu ne masu cewa Mummy, kin zama kishiyar sa." Manal tayi murmushi kawai bata ce komai ba Mummy tace, "ina fatan kuna zaune lafiya?." "Lafiya lau Mummy." "Haka ake so, Allah ya bada zaman lafiya ya baki haƙurin zama dashi. Don zama da Bebi sai an shirya, zaki sha tsirfa kala-kala, baya cin wannan baya son ƙhamshin wannan. Saka aiki kuwa sai kin gaji" ta faɗa tana kallon sa yana gefe yana murmushi. Kausar da take gefe tace, "Wallahi kuwa." Banzan kallon da ya mata ya saka ta yin shiru tana dariya. Mama ta kalle shi tace, "yaushe zaka kai ta gidan Hajiya ne? Wai Hajiya guda ace har yanzu baka kai mata Manal ba?, ko da yake auren naku ma kwana nawa? In badan zamani ba ai bakwa fito ko kwana bakwai baku yi ba." Bebi yace, "maganar Hajiyar nake gudu amma da yanzu zamu je, to Hajiya ta dinga cemin har an fito, har anyi kaza da kaza shiyasa nace naje daga baya. Amma zamu je gidan Umma da Ammi a satin nan in sha Allah." Mama tayi dariya ta kalli Manal da kanta yake a ƙasa tayi shiru alamun baƙunta Mama tace, "ki ɗago mana kamar wata baƙuwa Manal?, nan ai gidan ku ne kema. Kamar Kausar kike a wajena kar ki ji komai ko kallon banza ya miki kizo ki faɗa min." Maanal tayi murmushi kawai bata ce komai ba. Kausar tace, "Sis kin yi shiru da yake a gaban Mama ne kamar bakya magana." Mama tace, "raka ta wajan Mamy su gaisa sai tazo ku ci abinci." Tare suka da Kausar Mama ta bita da kallo ta kalle shi tace, "Ma sha Allah, akwai nutsuwa da kunya. Ga kyau, ashe tafi kyau a hakan ta babu makeup, da bikin ku sai ta koma kamar wata yar tsana saboda haske." Mmurmushi kawai yayi baice komai ba, kar ya tanka Mama tace wani abu shiyasa yayi shiru. Ba jimawa suka dawo Mama ta saka ta koma kan kujera kusa da Kausar da Lubna da ta biyo su, Rumana ce ta fito daga ɗaki tana cewa, "kai amarya ce guda a gidan nan ko a min magana?." Ƙarasowa tayi ta zauna kusa da Kausar dake kusa da Manal ta kalli Manal tace, "Amarya nice Rumana" ta faɗa tana bata hannu alamun su gaisa. Ɗago ido tayi ta kalle ta sai gaban ta ya faɗi haka kawai bata san dalilin haka ba, ta bata hannu suka gaisa tana murmushi Rumana ta kalli Bebi tace, "Beb ya kamata ace an sanar dani zuwan nan na tarbi amarya." Kafin yayi magana Manal tace, "ya jikin ki?." Rumana ta kalle ta tace, "Alhamdulillah da sauƙi, ashe ya sanar dake bani da lafiya." Manal tace, "Uhum na sani, Allah ya ƙara lafiya." "Amin na gode amaryar mu." Sai a sannan Bebi ya kalli Rumana yace, "naga kin samu lafiya." Rumana ta murmusa tace, "Alhamdulillah zamu ce, naji sauƙi sosai." "To haka ake so" ya faɗa yana cigaba da danna wayar sa. Mama tace, "Kausar kawo mata abinci taci." Bebi yace, "a bar shi kawai Mummy, in mun koma zamu tarar matar Yaya ta kai abinci." Mama tace, "koma meye sai taci abincin gidan nan, sarkin tsari." Baice komai ba aka kawowa Manal wainar shinkafa da miya. Manal ta kalle shi suka haɗa ido kafin ya janye nasa ya kalli wayar sa, ita kuma ta fara ci dan tayi daɗi amma da sugar a ciki. Fara ci tayi da niyar taci kaɗan sai gashi taci guda biyu ta bar biyu a plate ɗin. Ta ajjiye plate ɗin a lokacin Mummy ta fito daga ɗaki tace, "ba dai kin ƙoshi ba." Tace, "Eh Mummy na ƙoshi." Mummy ta zauna Rumana ta kalle shi tace, "Beb baka ce min yaushe zan tafi Abuja ba?." Ya kalle ta yace, "na san baki shirya ba." Tayi murmushi tace, "in zan tafi ma zan zo har gida na yiwa amarya sallama" ta faɗa tana kallon Manal da itama ita take kallo, suka haɗa ido Manal tayi murmushi kawai. Kausar tace, "Sis muje ki wanke hannun ki." Bin bayan ta tayi ta wanke hannu ta dawo ta zauna Bebi yace, "to Mummy zamu wuce dare yayi har tara ta wuce Mummy ta miƙawa Manal leda mai ɗan girma tace, "Humra ce aka kawo min jiya da turaren wuta, har na haɗo da turaren wutar na tuna mijin ki aljanun ƙin turare ne dashi sai na kawo miki humrar kya yi amfani da ita." Manal ta sauka har ƙasa ta karɓa tace, "an gode Mummy, Allah ya saka da alkhairi." Mama ta amsa da amin tana murmushi. Mamy ce ta shigo tana cewa, "ina sauri kar nazo kun tafi, Manal ga spices ayi girki. Kin san angon naki baya wasa da abinci" ta faɗa tana bawa Manal ledar. Manal tayi murmushi ta karɓa tana godiya Mamy ta amsa tana fita. Har waje Kausar da Lubna suka rako Manal ta shiga mota suka tafi zuwa gida. Ta hanyar gidan Farida suka zo wucewa yaso su shiga amma dare yayi ya dawo wani lokacin. Manal sai murmushi take yi yadda aka karɓe ta hannu biyu a gidan ya burge ta ta kuma ji daɗin yadda aka dinga haba-haba da ita sosai. Ta ɗauki humrar wajan Mama ta buɗe tace, "Partner kaji ƙhamshin humrar nan kuwa?." Ya kalle ta yace, "wannan ne me khamshi? Don Allah ki rufe kar ya saka min ciwon kai." Manal ta rufe tace, "nidai sai na shafa kayanata gaskiya, ai Mummy ce ta bani." Baice komai mata komai ba tace, "Partner." Ya amsa da "partner ya akayi?." "Rumana ɗin nan amma ba ƴar Mummy bace ba?." Ya kalle ta yace, "ƴar Mummy ce mana, ai na faɗa miki a hannun Mummy ta tashi shayar da ita ne kawai Mummy bata yi ba. Ƴar Ammi ce autar su Mummy." Manal ta girgiza kai bata ce komai ba yace, "Meyasa kika tambaya?." Manal tace, "gani nayi yanayin yadda take kallon ka daban da nasu Kausar." Yayi ƴar dariya bai ce komai ba amma shi kansa mamakin warewar ta yake cikin ƙaramin lokaci haka, Tabbas akwai abinda Mummy ta shirya wanda shi bai san dashi ba. Lokacin da suka ƙarasa unguwar sai da suka shiga gidan Yaya isma'il suka mata godiyar hidimar kawo musu abinci da ake yi, sannan suka shiga gidan Yaya Bilal aka gaisa daga baya suka shiga gida. Suna shiga kitchen ta wuce ta ajjiye spices ɗin ta sannan wuce daƙi ta ta buɗe humrar wajan Mama tana shaƙar ta domin akwai ƙhamshi, abayar jikin ta ta cire, ƙaramar riga ce a ciki sai dogon wando ta shafa a hannun ta tana sake shaƙar ƙhamshin, a wuyan ta da ƙirjin ta ta shafa kafin ta rufe ta ajjiye. Wayar tace tayi ƙara ganin sunan Surayya sai ta ɗauka ta zauna a kan stool tana amsawa suna hira dan da shiga gidan bata nan, kusan mintina goma kafin ta tashi ta ajjiye wayar tana niyar shiga banɗaki ya shigo dakin nata. Kallon ta yayi tun daga sama har ƙasa cikin tsananin shauƙi soyayya, vests ɗin jikin ta daga sama a buɗe take sosai gata da siririn hannu hakan ya saka shi bin ta da kallo yana shigowa ɗakin. Kusa da ita yazo ya kai fuskar sa kusa da wuyan ta ya kulle ido ya buɗe ya zagaya da hannun sa ya riƙe ƙugun ta ya jawo ta jikin sa da ƙarfi ya manna ta da jikin sa yana cigaba da shaƙar ƙhamshin wuyan ta. A kunnen ta yace, "kika ci masa mai sugar ko?." Tana jikin sa ido a rufe tace, "bazan iya wa Mummy musu ba." "Amma kin san ci ba naki bane tunda kika ji akwai zaƙi...." Ya faɗa yana jan kalmar ƙarshe yana sake bin wuyan ta yana shaƙar ƙhamshin jikin ta da yake tashi a hankali. "Bazan sake ba" ta faɗa itama a hankali tana jikin sa. Tattare rigar ta yake yi daga ƙasa ta riƙe hannun sa da sauri a kunnen ta yace, "Partner kwana biyu fa, ki yi haƙuri da yau bazan iya haƙura" abinda yace kenan yana tattare rigar gabaɗaya ta baya, ya ɗauke ta zuwa kan gadon ɗakin ta wanda basu taɓa kwnaciya a kai ba ya kashe hasken ɗakin. Manal ganin sa a kusa da ita cikin tsoro tace, "Partner don Allah..." ya katse ta yace, "A'a Manal, bazan ƙyale ki ba yau" ya faɗa yana dauƙo ta ta dawo jikin sa gabaɗaya. Rumana kuwa su Manal suna fita daga falon ta fara hawaye Mama ta kalle ta tace, "yanzu meye na kukan?." Rumana tace, "Mama yana son ta, nice baya so." Mama tace, "duk wannan maganar ta wuce yanzu ai, mun gama wannan maganar dake kin tabbatar min da baza ki sake tayar da ita ba meye na dawo da ita baya kuma?." Ta goge ido tace, "na kasa jurewa ne." "Haka zaki danne domin itace matar sa ta farko, kuma yana sonta ba baya sonta ba, kin sani na sani iya kallon Adnan kika yi kin san yana son matar sa sosai. Akan me zaki yi kishi da ita a yanzu? Saka damuwar ta a zuciyar ki ba mafita bace a wajan ki, ki manta da komai kawai komai ya wuce." Ta girgiza kai tace, "to Mama." "Yaushe zaki tafi Abujan?." Jibi." "Allah ya nuna mana, kije can ki huta da zarar lokaci yayi zan ce ki dawo." Rumana ta tashi ta rungume Mama tace, "To Mamana, Allah ya biya ki da aljanna, kece kawai kike son abinda nake so." Mama ta riƙe ta tana shafa bayan ta cikin tausayin ta tace, "Rumana ke fa ƴata ce, haihuwar ki ce kawai ban yi ba." Rumana tayi murmushi domin ko babu komai zata mallaki Bebi matsayin mijin ta koda baya son ta. ******Maryam gabaɗaya ta rasa walwala ta zama mai zaman ɗaki a koda yaushe, ko yaushe cikin damuwa take domin lamarin Kamal ya ishe ta ta kuma ce duk abinda zai yi yayi ta gaji da saɓon Allah. Tana zaune tayi shiru ita kaɗai Lubna ta shigo ciki ta zauna kusa da ita cikin kulawa tace, "Yaya akwai abinda yake damun ki amma sai kice babu, kin canja gabaɗaya kin rame saboda damuwa. Ki ta addu'a, ko ki faɗawa Yaya Bebi in zai iya yin abinda zai iya wajan ganin ya shiga miki gaba damuwar ki ta yaye. In kuma maganar ba tasa bace ki ta addu'a." Ta kalli Lubna itama ita take kallo Lubna ta share idon ta da suka ciko da hawaye tace, "Yaya a yanzu yadda nake son Yaya Bebi ko Abba bana so wallahi, shine kawai zai tsaya a kan lamarin koda ka ɓata masa a baya, bazai duba ɓata masan da kayi ba zai tsaya maka har sai ka samu abinda ka ke so. Baya gajiya, da jikin sa da zuciyar sa da aljihun sa zai yi abinda zai taimake ki. Meye ban yi masa akan Mujahid ba? Amma da na shiga matsala shi ya dinga bin su Mamy yana cewa su yafe min. Dan haka Yaya ki sanar dashi in kina da damuwa na tabbatar zai nemo miki mafita." Maryam ta girgiza kai kawai Lubna ta tashi ta fita, Maryam ta sauke ajiyar zuciya cike da tunani da kuma damuwa, da wanne ido zata fara tunkarar Bebi da wannan maganar? Me zata ce masa?. Ta dafe kai wannan tunanin shine yake hanata sanar dashi tun farko, Amma a wannan lokacin zata sanar dashi koma meye zai faru ya faru ta gaji, zata faɗa masa kodan martabar ta da ta yaran ta. Bayan sati biyu. BDƘB2P25 Manal tana zaune a kan kujera tana kuka shima yana zaune kusa da ita yana kallon ta da mamaki yace, "yanzu dan nace zan koma aiki shine kike kuka? So kike na dinga zama a gida?." Manal tace, "bana so aikin nan naka, in ka tafi sai ka kai dare kuma kana dawowa kace zaka koma. Ni dai bana so wallahi. Don Allah kayi zaman ka ba sai kaje ba." Yace, "to ya za a yi? Ceton rai nake, ina kuma fatan wannan aikin ya kaini har aljanna. Ke ba abin alfaharin ki bane ace mijin ki yana aikin neman lada?." "To to to ba sai a baka hutu wata biyu ba, yanzu tsakani da Allah kwanan mu nawa da zaka koma aiki?, ko gama sabawa bamu yi ba gashi zaka dinga tafiya kana barina." Yayi dariya yace, "Manal wata biyu? Ai yayi yawa sosai, ke dai ki bari zan ɗauki hutu nan ba da jimawa ba har umra nake so mu je in sha Allah. Amma yanzu ki daina wannan fushin baya yi miki kyau." Manal tace, "nidai gaskiya bana so ka koma aiki" ta faɗa tana juyowa tana kallon sa. ya riƙe fuskar ta yana kallon ta yace, "ai ba kullum zan dinga zuwa ba, zan ware ranar da zan dinga zama available ko yaushe muna tare dake, amma in ana nemana emergency dole naje. Manal a haka fa dan bana aiki da asibitin gwamnati, da sati biyun ma bazan samu ba." Manal ta sake fashewa da kuka tace, "tsakiyar dare haka zaka dinga tafiya kana barina?." "Haba dai! Akwai Ummi ƴar Yaya isma'il ai kin san ta suna zuwa nan, da ita zaki dinga kwana in ya kasance zan je night duty. Amma ba ko yaushe zan dinga zuwa ba saboda ke kawai." Manal tayi shiru bata ce komai ba fuska a shagwaɓe tana turo baki, ya kalle ta yace, "ki daina wannan kukan shine bana so." Ta share hawaye tana kallon gefe ɗaya yace, "ki yi dariya mana." Taƙi yi ya fara yi mata chakulkuli dole tayi dariya ba dan taso ba yace, "ko kefa. Yanzu ki duba store abinda babu sai ki faɗa min. Daman nace ranar da na koma aiki ranar zaki fara girki kin ga jibi kenan." Manal tace, "zan duba." "Fushin ne dai har yanzu? Ashe haka ake so na zauna ban sani ba?, Faɗa min meyasa kike so na zauna?." Ta kalle shi tace, "bana so naga baka kusa dani." Ya ɗaga mata gira yace, "sannan kuma bakya so kiji bana yin me?." Manal ta kalle shi tace, "ni babu abinda nake nufi." "Ƙarya ne, kina so kina kaiwa market." Tayi dariya tana rufe fuska shima yayi dariya. Ta kalle shi tace, "to yanzu ya za'a yi da koyar mota ta?." Shima ya kalle ta yace, "ai kin iya, kafin na siya miki taki sai na tabbatar kin ƙware. Dan haka zaki fara amfani da waccan farrar" ya faɗa yana nuna mata motar ta window. Kalla tayi ta kalle shi cikin murna tace, "da gaske ni kaɗai zan dinga driving?." Ya kalle ta yace, "eh to, sai dai naga yanayim tuƙin na ki." Tayi tsalle ta faɗa jikin sa ta sarƙafo wuyan sa da hannun ta tace, "na gode Partner, ina son ka" ta faɗa tana yi masa kiss a goshi cikin farin ciki.         Ranar Monday ya koma bakin aiki haka ta tashi da sassafe daman wannan ta saba yi a gida tayi masa abinda zai ci ya ci, bayan ya gama breakfast suka yi sallama harda kuka suka rabu ya tafi asibiti. A cikin kwanakin ta saba da zaman gidan babu shi duk da bai cika night duty ba amma ana kiran sa in an samu emergency, akwai ranar da har ta fara bacci ya tashe ta suka tafi asibitin tare. Zaman su ma sha Allah za'a ce babu wata damuwa sai abinda baza'a rasa ba na saɓani tskaanin ma'arauta, duk da har lokacin amarya ce bata laifi ba wani faɗa ake yi ba sai zaman soyayya. Har lokacin Abba bai zo ba ya dai dawo gida sai ya yiwa Bebi waya yace yazo a gaggauce amma yayi haƙuri zai dawo.         Wata ɗaya da ƴan kwanaki da auren su har lokacin ana zuba soyayya Sai dai halin kowa ya fara bayyana a cikin su. Halin da ake dannewa saboda amarci sun fara bayyana kan su a hankali. Da daddare ranar talata ta kawo masa abinci bayan ya dawo daga wajan aiki ta ajjiye masa a gaban sa, ya kalli abincin ya kalle ta yace, "wannan ba abincin jiya ba ne?." Manal tace, "shine, da naga akwai da yawa sai nayi warming ɗin sa kawai kar ayi asara." Ya zuba mata ido bayan ya haɗe hannun sa ya tallafi haɓar sa yace, "kin taɓa ganin na ci abinci da rana na sake cin sa da daddare?." Ta girgiza kai alamun a'a yace, "shi ne kuma zaki kawo min na jiya?." "Gani nayi yana da yawa ne shiyasa kawai na saka a fridge.” "To ki ɗauke kayan ki bana cin abincin da aka yi warming, bana cin abu na sake maimaita indai ba tuwon Mummy ba. Ki ɗauka a bayar ki dafa min Indomie" ya faɗa yana tashi daga kan dining ɗin ya koma cikin falo. Kan ta ciwo yake mata sosai ga marar ta na riƙewa, tayi mamakin rashin zuwan period ɗin ta sai a wannan lokacin take jin alamun sa, bata kwashe kayan ba ta shiga kitchen ɗin ta dafa masa indomie ta kawo ta bashi ya karɓa yana kallon ta yace, "me yake damun ki?." "Kaina ne yake ciwo" ta faɗa tana zama a kusa dashi ta kunna tv. Labaran siyasa ake ita kuwa ba ganewa take ba ta canja channel ta ajjiye remote ɗin. Ba tare da ya kalle ta ba yace, "Za'a fara reg na school ɗin ki ranar Monday in sha Allah, zamu je dake ki zaɓi course ɗin da kike so." Farin ciki ya mamaye zuciyar ta tace, "to Allah ya kaimu, na gode sosai Partner Allah ya saka da alkhairi." Ya amsa da amin tace, "Ina so gobe ma naje gidan Mama Yaya Mubeena ce bata da lafiya, tun lokacin da tazo gidan nan da zazzaɓi tazo ashe tana kwance yanzu." "Allah ya ƙara lafiya, Allah ya kaimu goben." Ta amsa da amin yana cigaba da cin indomie sa yana duba waya yace, "gobe ba sai kin yi girki ba, bara na mana order abincin leemars delicious." Manal ta ɗaure fuska tace, "kai ta yabon abincin matar nan ni kuma haushi nake ji wallahi." Yayi dariya kaɗan yace, "Haba Partner ai bata kai ki iya abinci ba, kawai na saba da cin nata ne ina gwauro, sai naga dama nake ci yanzu." Manal ta murguɗa baki tace, "nidai wallahi bana so ka dinga order  abincin nan, zan dinga daga maka ko me ka ke so." "Ni nasan haka, nasan kin iya abinci Manal sosai fiye da yadda nake tunanin ki. Bawai zan siya saboda ta fiki bane kawai ina sha'awar cin abincin nata ne, musamman wannan mandi ɗin ta da wannan funkason." Manal tace, "to ai na iya mandi rice ɗin, sai nayi goben ba sai ka siyo." "Ai na riga ma nayi payment, ki huta daman baki da lafiya." Manal ta ɗauke kai dan taji haushi ya kalle ta yasan taji haushi sai ya share ta, yayi murmushi ya rasa meyasa yake kishi da leemars delicious shi kam yana son abincin ta yana masa daɗi sosai, ya sha bada handle ɗin ta in ana neman abincin fita kunya na ƙaramin abu. Wayar sa take kallo yana ta yawo a instagram har ya wuce wani hoto da shi bai ma kula dashi ba, da sauri tace, "partner ɗan dawo baya naga wancan hoton." Bayan ya dawo ta kalla tace, "wannan mutumin algungumi ne, ɗan iska tsohon banza. Ɗan sake yi min zooming hoton na gani." Kallon ta yake dan ya tafi tunani kafin yace, "meye haka?." Manal ta karɓi wayar tayi zooming hoton ta nuna masa tace, "wallahi shine, partner ina gidan da na nuna maka nace an kaini lokacin da Mama babu lafiya?." Bai amsa ba dan so yake yaji ƙarshen maganar tace, "to wannan tsohon banza shine ya saka a kai masa ni, ko kunya baya ji ƴar cikin sa ce ni, wataƙila ma yayi jika dani amma ya nemi yi min fyaɗe. Ka Ganshi ko? wannan shine wanda nake faɗa maka" ta faɗa tana nuna masa hoton Abban sa wanda ya cika screen ɗin wayar sa. Kallon ta yake yi bai san ya yarda bowl ɗin hannun sa ba ya zuba mata idanu zuciyar sa na bugawa da mugun gudu cikin tashin hankalin da bai taɓa tsintar kansa a ciki ba sai a wannan lokacin, wata irin zufa yake ji a fatar jikin sa ya rasa abinda zai ce hakan ya saka shi zuba mata ido gashi ta kasa gane hakan sai zuba take. Daƙyar ya iya buɗe bakin sa yace, "kin san me kike cewa?." Manal tace, "na sani mana Partner, wallahi wannan mutumin ne. Tsohon banza ne babu abinda ya iya sai lalata yaran mutane, badan Allah ya taimake ni ba da yanzu ba wannan magana ta ake ba. Sai Allah ya saka min kuma...." Wallahi bai sai ya kai hannu ya mari kuncin Manal ba sai da yaga ta dafe kuncin sannan ya fahimci abinda ya yi. Wara ido take yi tana kallon sa wayar ta kife a ƙasa daga hannun ta tana kallon sa yana kallon ta tace, "Partner ka mare ni? Me nayi da zaka mare ni? Dan ina faɗar gaskiya akan abinda ya faru dani? In bai aikata ba ai bazan faɗa ba." Hawaye ya zubo daga idon ta. Bai iya cewa komai ba ya tashi bai ce komai ba ya bar mata falon ya koma ɗaki cikin ruɗani da tashin hankali. Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un kawai yake maimaitawa, babu abinda yake dawo masa cikin kansa sai lokacin da Daddy yace masa yana can yana harkar barikin sa, kenan da gaske dai mahaifin sa neman mata yake shiyasa bai damu da iyayen su ba? Kenan da gaske ya nemi Manal matar da yake aure a yanzu ita kuma tana matsayin sirikar sa?." "Hasbuhannah Wani'imal wakil!" Ya furta a raunane kansa ya sara lokaci ɗaya saboda tashin hankali, wani irin ɗaci yake ji a zuciyar sa bai san lokacin da yanzu fara hawaye ban baƙin ciki ba. Wacce irin rayuwa ce wannan Abba ya ɗaukarwa kansa? Meyasa bazai ƙara aure ba in matan su mun yi masa kaɗan? Meyasa ya zabi hanyar saɓon Allah?. Tunanin da yake kenan amma  zuciyar sa tayi nauyi sosai ya rasa abinda zai yi yaji daɗi. Bai san adadin lokacin da ya kwashe a haka ba kawai ya san ya tashi ya shiga banɗaki yayi alwala yazo yana sallah ko zai ji daɗin abinda yake ji a zuciyar sa. Zuciyar sa tafasa take ya rasa inda zai saka kansa, sai bugawa take fat fat fat har ya kai ga ya danne gefen zuciyar sa. A nan wajan yayi bacci sai asuba ya tashi ya shiga banɗaki ya sake yin alwala ya fito ya fita zuwa masallaci. Sai bayan ya dawo ya tarar da bowl ɗin da ya cillar da wayar sa da wayar Manal ɗin duk suna wajan. "To ita me tayi min? Gaskiya ta faɗa min kuma bata san Abba na bane" ya faɗa a bayyane tunawa da Manal ya furzar da iska zuciyar sa na faɗa masa, _Amma ai ko kama da Mimi zata iya gani ta tabbatar da shi ɗin wani nasa ne, Meyasa zata faɗi wannan kalamai a kansa?. Ai da taga hoton sa sai tayi shiru ba lallai sai ta faɗa maka ba._ wannan tunanin ne ya rinjayi zuciyar sa ya koma ɗaki ya kwanta ya bar wayar a falon dan baya tunanin ma akwai inda zai iya zuwa. Manal kam haka ta kwana kuka tana tunanin laifin da tayi masa har ya kai ga ya mare ta, tunda suka yi aure basu taɓa raba makwanci ba amma yau daga faɗat gaskiya gashi ya barta. A  haka ta yi sallar asuba itama, tana jin fitar sa zuwa masallaci dan taji an buɗe gate ta san shine ya fita. Bayan ta idar ne ta zauna tana jan jarbi marar ta na sake ɗaurewa. Bacci ne ya kwashe ta a wajan sai takwas ta tashi ta fita falo ta samu mai aikin da take zuwa daga gidan Yaya isma'il har ta fara gyara falon, Manal tace mata ta fita da abincin jiya na kan diniing ita kuma ta shiga kitchen dan haɗa masa breakfast. Bayan ta gama ta ajjiye a kan dining ta koma ɗakin ta ba jimawa ta fito ta shiga nasa cikin fargaba da tsoro. A tsaye ta same shi yana kallon harabar gidan ta window da alama ko wanka ma bai yi ba. "Ina kwana" ta faɗa a sanyaye murya na rawa alamun kuka zata yi. Juyowa yayi ya kalle ta kawai sai ta tashe da kuka ya kulle ido ya buɗe cikin nauyin zuciya, ya tako zuwa inda take ya ja ta zuwa jikin sa ta kwanta a ƙirjin sa tana kuka tace, "ban san me nayi maka ba, in abinda nace akan mutumin nan ne ya ɓata maka rai har ka mare ni ka kuma share ni kayi haƙuri." Ya lumshe ido ya buɗe ya sauke ajiyar zuciya yace, "ki yi haƙuri ban san hannuna ya kai jikin ki ba, ki yi haƙuri don Allah ban yi da niya ba kuma ba halina bane." Bata yi magana ba har ya gama faɗar abinda ya faɗa sannan tace, "to me ya faru?." "Ɗauko min wayata a falo." Sakin ta yayi ta fita ba jimawa ta dawo da wayar ya karɓa ya zauna a kan gadon itama ta zauna ya bata wayar yace, "ki shiga photos na tabbatar akwai abinda zai baki mamaki a ciki." Karɓa tayi ta shiga tana danawa gaban ta na faduwa, hotunan bikin Huzaifa ne sai na bikin su a hankali take scrolling  taga har tazo kan hoton sa shida Abba. Gaban ta ya faɗi sosai ta buɗe hoton ta kalle shi ba tare da ya kalle ta ba yace, "Shi ɗin mahaifina ne Manal." Bata san wayar ta faɗi a hannun ta ba ta diririce jikin ta ya fara rawa sosai cikin tashin hankali da kunya da dabaibaye ta, ta kasa magana sai zare ido take yi ta dan bata san abinda zata ce ba. Yunƙurawa tayi zata tashi ya dawo da ita ta zauna yace, "da gaske shine yayi amfani da rashin lafiyar Mama wajan raping ɗin ki?." Gaban ta ya faɗi tsoro ya mamaye mata zuciya ta rasa me zata ce masa kawai sai ta fara kuka na borin kunya,ya kulle idanun sa yana girgiza kai dan Allah ne kawai yasan zafin da yake ji a zuciyar sa. "Ki faɗa min." Ta kasa magana sai zare ido kawai take yi tana tuna irin abubuwan da ta faɗa a kansa duk da tayi ne a rashin sani amma ta tabbatar ta cancanci abinda yafi mari ma. "Ki yi magana" ya sake katse ta idon sa a kulle. "Kayi haƙuri, wallahil azim ban san shine....." ya dakatar da ita yace, "na sani, nasan da kin san shine mahaifina baza ki aure ni ba, nasan da kin san shine mahaifina ko kin aure ni baza ki bari na san wannan labarin ba. Baki da laifi abinda aka yi miki kika faɗa min matsayina na mijin ki, babu wanda zai hana ki faɗa a duk lokacin da kika so. Ki tabbatar min da abinda ki ka faɗa min da gaske ya faru Manal...!" Ya faɗa cikin rauni yana kallon ta cikin bugun zuciya. BDƘB2P26 Manal tayi shiru jikin ta yayi sanyi kunya ta gama rufe ta ya sauke numfashi ya kalle ta yace, "ki faɗa min Manal da gaske shine?." Manal ta kasa magana ko kallon sa ta kasa yi saboda kunyar kalaman da tayi amfani dasu. Ganin hakan sai yace, "bayan ni akwai wanda ya san maganar nan?." Ta girgiza kai alamun a'a ba tare da ɗago ba tace, "Ko Mama bata sani ba." Ya sauke ajiyar zuciya yace, "don Allah a barta a nan, bana so kowa ya sani, ki riƙe min wannan amanar Manal ko dan saboda ni, sannan ki daina kiran sa da...." Sai ya kasa faɗa ya dafe kai cikin takaici da baƙi ciki da ƙunar zuciya, Wai uban ka mahaifi ace shine ya nemi matar da ka ke aure, wannan wanne irin abun kunya ne? Ai shi ya kamata yaji kunya ba Manal ba. Manal tace, "in sha Allah babu wanda zan faɗawa har Mama, kuma ni na yafe ma." Yayi murmushin takaici jin abinda tace zuciyar sa na hasko masa mata irin ta nawa aka kai masa, zuciyar sa na hasko masa wataƙila kokawa suka yi da Manal ɗin ta gudu bata bashi haɗin kai ba. Wani irin takaici yaji bai san ya runtse ido ya furta, "hasbunallah!." Ya sauke numfashi mai ƙarfi yana ji kamar ya zubar da hawaye. Wai mahaifin ka ne yaso lalata matar da ka ke aure, wanne irin abin kunya ne wannan? dole yaji ɗaci a zuciyar sa ɗacin da bai yi tunanin zai taɓa jin irin sa a duniya ba. Sum-sum Manal ta tashi ta fita cikin nauyi da jin kunya, sai da ya nuna hoton mata Abban a waya take ganin kamar sa da Mimi da kuma Yaya Farida wanda a baya bata gani ba. sai a lokacin lura har shi Adnan ɗin suna yanayi da Abban, kawai yafi kama da Mama ne. Salati kawai take a zuciyar ta domin kuwa ko sakin ta Bebi yayi a jiya baza ta ga laifin sa ba dan irin kalaman da tayi amfani dasu wajan zagin mahaifin sa masu muni ne. Haka Bebi ya kwana biyu babu walwala ko aiki baya zuwa mgagana ma ba sosai yake yiwa Manal ɗin ba balle a zauna su yi hira kamar yadda suka saba. A cikin kwanakin sai da ya tabbatar ya gano inda mahaifin sa yake zama ya kuma tabbatar da batun Manal gaskiya ne babu ƙarya a ciki mahaifin sa neman mata yake yi yara da anya, ƴan bariki da wanda shine yake zama silar fara barikin nasu. Su Huzaifa da Mummy babu wanda bai tambaye shi abinda yake damun sa ba amma sai yace babu komai. Manal kam sai dai ta bi shi da ido ko abinci baya iya ci ko ta dafa, ƙoƙarin da take yi ta san yana son kunu sai ta dama ta zuba masa a flasks shi kawai yake sha sai abinda baza'a rasa ba. Ranar asabar da yamma ranar yaji sauƙin zuciyar sa saboda addu'ar da yake yi a kan lamarin, ya shiga ɗakin ta ya same ta a zaune tayi shiru alamun tunani take yi ya kalle ta yace, "Manal ki shirya zamu je mu gaida Abba." Gaban ta ya faɗi sosai ta kulle ido ta buɗe ta girgiza kai alamun to daga nan ya fita. Kaya ta canja ta saka lace ɗinkin doguwar riga butterfly ta yafa mayafi a kanta ta fito falon a lokacin ya shirya shima yana tsaye yana jiran ta, ya kalle ta sai ya ɗan saki fuska kaɗan yace, "kin yi kyau." Murmushi tayi bata ce komai ba suka fito suka shiga mota zuwa gida. Shi kansa ƙirjin sa bugawa yake yi baya son haɗuwar Abba da Manal, baya so Abba ya gane ta balle ya tuna abinda ya faru a tsakanin su, in hakan ta kasance bai san wacce irin kunya zai ji ba. Yana faka motar wajan Mummy suka shiga da sallama ta amsa tana bin su da kallo tace, "Bebi ku ne tafe?." Ya amsa suna gaisawa kafin yace, "Mun zo mu gaishe da Abba." "Ya kamata kam, tunda akayi auren ku baku gaisa ba. Ai yana falo ku je kar ya fita sai ku dawo nan ɗin in Kun gaisa." Jiki a sanyaye ya tashi Manal ma ta tashi suka fita, Mama ta bishi da kallo da tunanin abinda yake damun sa, dan yau ta yi kuɗurin sai taji abinda yake damun sa duk kauce-kaucen sa. Abba yana zaune yana waya suka shiga da sallama ya amsa yana ajjiye wayar yana cewa, "Adnan ni da na ce zan zo da kaina sai ku ka riga ni?." Bebi yayi murmushin yaƙe ya zauna a kan carpet kana yace, "Mun hutar da kai zuwan." Manal kanta na ƙasa bata ɗago kai ba suka gaisa da Abba, ta tabbatar bai ga fuskar ta ba dan kanta na duƙe sosai. Abba ya amsa da fara'a yana tambayar ta mutanen gidan su da yanayin zaman nasu tace Alhamdulillah. Taƙaitacciyar nasiha yayi musu duk ba jin sa suke ba saboda hankalin su baya jikin su, kowa da tunanin da yake hakan ya saka har ya gama maganar bata ji ba sai gani tayi yana miƙo mata kuɗi, a nan ta fahimci ya gama faɗar abinda yake cewa. ta saka hannu biyu ta karɓa tayi godiya shima Adnan ɗin ya gode Abba yace, "ɗazu Mimi ma da mijin ta suka zo." Bebi yace, "ai dole, baka nan akayi biki gabaɗaya." "Bari kawai, abubuwa sun min yawa ne sosai." Bebi yace, "Allah ya taimaka." Ya amsa da amin kafin yace, "lafiya dai ka ke?." Ya amsa da Lafiya lau daga nan suka koma wajan Mummy. Manal ta takura saboda yanayin da take ciki, gashi su Kausar basa nan, ga Mummy ta shiga ɗaki shi ma yabi bayan ta, gabaɗaya zaman ya ishe ta kawai daurewa take. A haka ta zauna tayi shiru ta rasa abinda zata yi taji daɗi. Yana shiga ɗaki wajan Mama tace, "Bebi me yake damun ka? A karo uku nake tambaya." Bebi yace, "Mummy babu komai fa." "Ƙarya ka ke. Ka faɗa min abinda ya faru har ka koma wannan yanayin." "Mummy babu komai fa, kawai yanayi ne." "Hmm Adnan kenan, na haife ka kace zaka min ƙarya dan ka ɓoye min damuwar ka, kawai baza ka faɗa min abinda yake faruwa bane. Kuma na Lura damuwar ka ta shafi matar ka, itama yadda jikin ka yake a sanyaye itama haka, bata da walwala kamar yadda ku ka saba zuwa, gabɗaya a ɗarare take. Na san halin ka ɓacin ranka na shafar kowa na kusa da kai haka damuwar ka, to kar ka shiga haƙƙin ta, kar hakan ya saka ka canja mata saboda wani dalili na ka, damuwar ka taka ce kai ka ɗorawa kan ka, in damuwar ka ta shafe ta ka shiga haƙƙin ta." Bebi ya girgiza kai yace, "babu abinda yake damuna Mummy." "Kai dai ka sani" ta faɗa tana fita daga ɗakin. Ya fito shima ya kalli Manal da take zaune yace, "zan je asibiti na dawo." Ta amsa da to ya yiwa Mama sallama ya fita. Mummy ta kalle ta cikin nutsuwatace, "me yake damun ku gabaɗayan ku ne Manal?.Ke a cikin damuwa shima haka, na damu da yanayin ku ba haka ku ka saba zuwar mana ba." Manal ta sauke numfashi tace, "Mummy ni babu abinda yake damuna, shine dai ban sani ba in na tambaya sai ya ce babu komai." "Kema hakan yake ce miki kenan? Bebi akwai rainin hankali." Manal tayi shiru bata ce komai ba Mummy tace, "Allah ya kyauta. Yau kin zo abokan hirar taki basa nan naga duk naga kin takura." Manal tayi murmushi kafin tayi magana Mama tace, "Akwai zoɓo mara sugar da na yiwa Abban su a fridge in zaki sha yana ciki sai ki ɗauka, akwai abinci ma a kitchen in kina jin yunwa." Manal tace, "to Mummy." Hira suke yi kaɗan-kaɗan, Mummy tana so ta ɗebe mata kewar su Kausar ita kuma nauyin Mummyn take ji, ba laifi ta sake da Mummy kafin Mummy ta shigaaki. Maryam ce ta shigo da sallama Manal ta amsa suka gaisa kafin tace, "Ina Bebi?." "Ya tafi asibiti." Maryam tace, "Shikenan bara na kira shi a waya" ta faɗa tana fita Manal ta ɗauki waya tana dannawa cikin rashin sanin abinda zata yi. Mummy ta fito daga ɗakin tace, "Manal in kin gaji da zaman shiga ɗaki ki kwanta, wannan tafiya asibitin na sa ya kai dare bai dawo ba." Manal ta amsa da fara'a tana jin daɗin yadda Mummy take ke yi mata kamar ba sirikar ta ba. A can asibitin ma ko wajan su Huzaifa bai je ba a office yayi zaman sa sai dai ya shiga nan ya fita nan bai bar asibitin ba sai bayan i'sha ya dawo gidan Mummy ya ɗauki Manal suka tafi gida. A ƙofar gidan sa ya ga Huzaifa da Hamza suna ƙoƙarin shiga da alama sun ɗauka yana nan. Ya shiga da motar sa gidan ya faka motar Manal ta shiga ciki bayan suma sun shigo harabar gidan. shiga babban falon nasa suka yi suka zauna. Manal ta kawo musu ruwa harda lemo da cake ɗin da tayi masa bai ma kalle shi ba saboda damuwa. Bayan barin ta wajan Hamza ya kalle shi yace, "Bebi baka ɓoye mana damuwar ka, dukkan mu bama ɓoyewa juna damuwar junan mu, me yake damun ka ka koma haka har ya shafi aikin ka?." Huzaifa yace, "damuwar ka ta saka mu a damuwa, bamu taɓa ganin ka cikin wannan yanayin ba. Dan duk damuwar da ka ke ciki bata hana ka aiki, wannan ta hana ka aiki Hakan ya tabbatar mana da ba ƙaramin abu bane ba. Me yake damun ka?." Bebi ya sauke numfashi yana kallon su yace, "babu abinda yake damuna, kawai yanayi ne yake kawo hakan amma ba wani abun bane." Hamza yace, "Yanayi fa kace? Babu wani yanayin da ya taɓa saka a wannan damuwar, ko lokacin damuwar Lubna baka shiga wannan damuwar ba balle yanzu. Kawai baza ka faɗa mana abinda yake faruwa ba ko hankalin mu zai kwanta." Ya sake kallon su yace, "Ba haka bane Hamza, kawai dai abubuwa ne sun fita daga raina, sai dai a hankali kawai." Huzaifa yace, "Shikenan, Allah ya yaye maka. Daman damuwa da damuwar ka ce ta saka mu zuwa dan mu ji lafiyar ka shirun naka yayi yawa." "Na sani, na gode kuma Allah ya bar zumunci." "Amin. Hamza tashi mu je" ya faɗa yana tashi tsaye sai kuma ya kalli abinda Manal ta ajjiye yace, "sai naci dan ya burge ni." Bai ce komai ba ya ɗauka zai fita Manal ta fito da hijjabi tace, "Yaya Huzaifa Mama ta faɗa min ka sake canja mata da magani har gida, na gode sosai Allah ya bar zumunci." Huzaifa yayi murmushi yace, "haba dai, kar ki damu babu komai ai an zama ɗaya." Ta kalli Bebi da yake kallon ta tace, "ka taya ni yi masa godiya." Huzaifa yace, "indai wannan ne ashe zan bushe in dai godiya zai min, kar ki damu kawai" ya faɗa yana dariya suka fita ita kuma ta koma ciki. Ajiyar zuciya yayi ya kulle ido ya buɗe yana jin zuciyar sa babu daɗi ko kaɗan. A nan yake zaune yafi awa ɗaya a wajan ba tare da yana yin komai ba sai aikin tunani, sai da ya gaji sannan ya tashi ya shiga ɗakin sa yayi wanka ya canja kaya a lokacin ƙarfe goma na dare ya fito ya shiga ɗakin ta. A kwance ya same ta amma ba bacci take ba tayi shiru da alamun tunanin take itama, ya shiga da sallama ya zauna a inda take kwance yace, "Partner babu abinci ne?." Tashi zaune tayi tana yatsine fuska tace, "ban yi ba, in nayi baka ci sai ai ta asara shiyasa ban dafa ba. Amma bara naje na dafa maka yanzu" ta faɗa zata tashi ya zaunar da ita yace, "bar shi kawai, ya naji jikin ki da zafi?" Ya faɗa yana taɓa wuyan ta. "Mara ta ce take ciwo tun jiya." Ya kalle ta sosai yace, "shine baki faɗa min ba?." "Ban ga fuskar da zan faɗa maka ba." Wani iri yaji a jikin sa na rashin kyautawa jin abinda tace kuma ya san haka ne amma sai yace, "wannan ba hujja bace Manal, ko a wanne yanayi nake in akwai abinda yake damun ki ki sanar dani zan nema miki lafiya. kar ki sake wannan kuskuren." Ta ɗaga kai alamun to. Ya kalle ta yana nazarin ta kafin ya saka hannun sa a rigar jikin ta yana shafa ƙasan cikin ta a hankali yace, "sosai ki ke jin ciwon?." Ta girgiza kai tace, "a'a ba sosai ba." Kallon ta yayi na wani lokaci kafin ya ɗan saki fuska da niyar kawar da komai a ransa yace, "kodai-kodai?." Manal tace, "kodai me?." Yayi murmushi wanda tunda abin ya faru bai yi ba yace, "ko dai na baki baby mana, yanayin ki ya gwada kamar kina da shigar ciki fa Manal." Manal ta wara ido tace, "ciki? A'a ni bani da komai kasan daman ina ciwon nan, last month ma nayi." Hannun sa ya saka a rigar ta yana shafa cikin a hankali yace, "wannan ba irin wancan bane, wannan na musamman ne. Allah kina da ciki in zan iya tunawa bazai wuce two weeks ba, dan ranar ni kaina nasan daƙyar ba a samu rabo ba saboda....." sai yayi shiru ya jawo kunnen ta ya faɗa mata abinda zai ce tayi dariya tana ɓoye fuskar ta a jikin sa, yayi dariya shima yace, "Allah kuwa, kinga kenan kina da cikin kwana sha huɗu da ƴan awanni, dan in lissafi za'a yi zan iya faɗa miki lokacin da aka same shi." Manal tace, "ni bani da komai, daga aure ƴan kwanaki sai kace ina da ciki? Haba kamar daman cikin nazo nayi?." Dariya ta bashi sosai yayi dariya yana kallon ta yace, "to daman ai shi kika zo yi, kowa yasan zaki yi ciki ki haihu. Kuma kin san masu irin ciwon ki suna jimawa basu ɗauki ciki ba, ke gashi Allah ya baki cikin sauƙi." "Aa nidai ka daina faɗar haka bani da komai, kawai sai aji ina da ciki daga yin aure? Ni dai a'a." Yayi dariya yace, "Shikenan na bar miki musun ki, Amma zan tabbatar miki da kina da cikina Manal" ya faɗa yana janye ta daga jikin sa ya ɗaga rigar ta yayi mata kiss a cikin. "Waye yake miki allura in kina ciwon nan da kina gida?." "Surayya ce, ta karanta community nursing yanzu haka aiki take yi." "Ma sha Allah, duk sun yi miki yawo." Bata ce komai ba tayi shiru tana jin yadda yake murza fatar cikin ta a hankali. "Manal in da gaske kina da ciki zan yi alfahari da hakan, ina so naga jinina Manal, ina so a nuna yaro ko yarinya ace wannan ɗan Adnan ne. Manal bani da abinda zan saka miki dashi sai addu'a da kuma tsantsar soyayya." Manal tace, "ka bari cikin ya samu in yaso sai kayi wannan maganar, ni bani da wani ciki ka daina cewa zaka yi alfahari" ta faɗa tana turo baki gaba, ya kalle ta yana ƴar dariya ganin da gaske dai bata son yin ciki a wannan lokacin, ya kama bakin ta da hannun sa yan shafawa a hankali yace, "to bara mu samar dashi yanzun nan, tunda kin ce babu bara na baki a huta, ni da wuri nake so ki haihu dan na tabbatarwa da mutane ni ba rago ba ne, ni jarumi ni" ya faɗa yana matso da fuskar sa kusa da ta ta. "A'a ni bana so" ta faɗa tana yin baya ta kwanta ya biyo bayan ta yana cewa, "ni ina so" ya faɗa yana hana ta magana dan so yake ya tabbatar mata da komai ya wuce duk da ya san bazai wuce ba a zuciyar ta da ta sa zuciyar ba. BDƘB2P27         Mubeena suna zaune da Bily suna tattaunawa akan abinda ya shafe su, Bily ta taɓo Mubeena tace, "Kamar wasa Manal tayi aure abin ta ta bar mu, yaushe zamu je gidan ta?." Mubeena ta taɓe baki tace, "tunda aka yi bikin ta sau biyu naje, Shima shegiya takurar ta ce ta kaini, ko yaushe in muka yi waya maganar ta ɗaya Yaya yaushe zaki zo. Shiyasa naje ba don nayi niya ba." "Ke kuwa meyasa? Kece kawai ƴar uwar ta wacce take da ita a duniya, in baki je gidan ta ba waye zai je?." "Wallahi mijin ta ne sam Allah bai haɗa jinina dashi ba, haka kawai bai min ba." "Meyasa bai yi miki ba?." "Haka kawai wallahi, sai naga kamar na san shi a wani waje." Bily tayi dariya tace, "kin taɓa ganin sa ai,Ina ranar da ku ka  haɗu da wannan shegen Alhajin?." Mubeena ta ɗaga kai tace, "eh." "Ina wani wanda ya wuce mu har nake ce miki ga wani handsome? Har kika ce ke bai miki ba saboda ba fari bane?." Mubeena ta dafe kai tace, "haba, nidai na san na taɓa ganin fuskar sa wallahi, ashe a nan na san shi." Bily tace, "a nan kika gan shi dai ba kika san shi ba, me ya haɗa ki dashi da zaki san shi?." "Bayan nan na sake ganin sa, in ma bashi bane to naga mai kama dashi." Bily tace, "Ke kuwa ai daga yanayin sa zai yi kirki, Meyasa bai miki ba?." "Haka kawai, ke ni ba wannan ba, so nake na gano asalin wacece Maman mu wallahi." Bily tace, "Meyasa ki ke so ki sani wai?." "Saboda ina so na san asalin mu, Wacece Mama da take da kadarar sama da naira miliyan ɗari iya waje ɗaya kawai?, ki duba gidan Manal fa ke baza ki ce ba ƴar babban mai kuɗi bace, ki kalli kayan da aka zuba mata bayan nan aka kai ta da gara. Ke wallahi Mama ba ƙaramin mai kuɗi ne ya haife ta, duk abinda aka yi fa da kuɗin ta ne, nima aka siya min nawa. Gaskiya ina so na nemo ko dan na san wacece ita." Zata yi magana aka kira ta a waya ta kalli wayar  tayi tsaki tace, "sabuwar lamba, ko waye ya san ni da wannan sim card ɗin ma oho" ta faɗa tana ɗauka ta saka wayar a speaker. "Mubeena na sha wahala kafin na samu number ki, na samo gidan ku number ki ce yayi min wahala samu, gashi bana so nazo gidan ku ba tare da mun yi magana dake ba." Mubeena ta kalli Bily gaban ta ya faɗi sosai tace, "waye yake magana?." "Na san kin gane mai magana "me zaka yi da number ta har da ka kira ni?." "Alkhairi mana Mubeena, ina so mu yi magana don Allah ki bani dama." "Har abada babu wata dama da zan sake baka, na tsane ka tsana mai muni ma kuwa, in kana tunanin zan saurare ka ma ka daina domin wallahi ko sunan ka bana so naji na faɗa. Nayi gaggawar goge lambar ta daga wayar ka dan babu amfanin da zata yi maka." "Kar ki kashe don Allah Mubeena, a wannan karon da alkhairi nazo, auren ki nake so nayi wallahi, in kin bani dama ina zo zan so gidan ku ayi maganar auren." Mubeena tace, "kar kayi wannan gangancin, kar ka fara dan wallahi bazan saurare ka ba, kaje ka samu ƴan iska irin ka dan ni ba ƴar iska bace, tsakanina dakai kuma Allah ya isa abinda kayi min sai an yiwa ƴar da ka haifa" tana faɗa ta yanke wayar tana kallon Bily. Bily tace, "gwara da kika masa haka, wannan mutumin ɗan iska ne wallahi, Wato ya bi ta wancan hanyar kin ƙi bashi haɗin kai shine yanzu yazo da maganar aure, aure ko auren sha'awa?." Mubeena tace, "wallahi lokaci ɗaya na tsane shi a raina, da ina son sa a zuciyata tunda nake addu'a yanzu tsatson sa ma bana son su balle shi." "Ke dai Allah ya kiyaye mu daga sharrin su." Suka amsa da amin suka cigaba da hirar su. ****** Manal da Bebi zaman su ya dawo kamar da ya manta da abinda tace a zahiri amma a baɗini ya kasa cire abin a zuciyar sa, yayi ƙoƙari ya ware ya cigaba da harkokin sa kamar ba shi ba. Sai dai a kullum cikiin yiwa mahaifin sa addu'a yake, Allah ya kawo sanadin da mahaifin sa zai shiryu ya daina neman matan waje. A satin Manal zata fara zuwa Culinary school ya samu driver da zai dinga kai ta duk da ta nace akan ta ita yace bata iya sosai ba sai hannun ta ya faɗa zata fara ja. A satin ta fara zuwa daga ƙarfe sha biyu na rana zuwa karfe huɗu na yamma an tashi. Ranar talata da yamma bayan an tashi daga school ɗin ta dawo, a ranar bai je aiki sai da daddare zai fita, hakan ya saka ta same shi a falon farko a zaune yana kallon ball a tv da cup ɗin lemo a hannun sa yana sha. Kamar an cillo ta ta faɗo falon ko sallama babu ta wuce shi a guje ta nufi sink ɗin da yake dining room tana amai. Da sauri tashi ya bi bayan ta ya tsaya a bayan ta yana kallon ta yace, “sannu" ya faɗa lokacin da ta gama kuskure bakin ta da ruwa. Ya riƙo hannun ta zuwa falo ta zauna a kan kujera ya jawo ragowar ruwan da ya sha a roba ya bata ta sha yana zaune a kusa da ita yace, "Sannu, daman baki da lafiya yau ban sani ba?. Meyasa baki faɗa min ba ki ka tafi school da ciwo?.” Ta girgiza kai tace, "lafiya ta lau, kawai makarantar ce yau ta saka ni amai, a can ma sai da nayi." "Subahanallahi! Kuma bayan shi bakya jin komai?" Ya faɗa yana dafa kanta kafin ya ce, "jikin ki da zafi kuma. Me yake damun ki bayan wannan? Babu abinda ki ke ji?.” Manal tace, "bana ji, kawai ina ji kamar na rufe kaina na duka, kaima ji nake yanzu kamar na zane ka wallahi, na rasa me yake min daɗi komai haushin sa nake ji." Duk da dariya da ta zo masa sai bai yi ba ya danne yace, "Ayya sorry, kin san haka yanayin yake zuwa wani lokacin in zaka yi period." Manal ta kalle shi kamar zata yi kuka tace, "to yaƙi zuwa sai wahalar dani yake, zuciyata har tafasa take dauriya kawai nake. Wallahi makaratar ma ta fita daga raina" ta faɗa tana hawaye cikin rashin sanin abin yi. Ya fakaici idon ta yayi murmushi kafin ya kalle ta yace, "haƙuri zaki daina ji, da zarar yazo zaki daina jin abinda kike ji daman rashin zuwan ne ya kawo haka." Manal tayi shiru bata ce komai ba sai kuma ta kalle shi tace, "kuma daman ana haka? Period yaƙi zuwa gashi ina jin alamun ciwo mara?, hakan normal ne ko naje naga likita dai?." "Ni ba likita bane?." "Amma kai zuciya ka sani." "Koma meye ai likita sunana. hakan kuma normal ne, in dai bai zo ba baza ki daina jin haka ba, kawai ki cigaba da daurewa da yazo shikenan fa." Manal ta girgiza kai cikin ƙin amincewa da maganar sa tace, "bai taɓa yi min irin haka ba fa, ni dai tsoro nake ji kar naje wata cutar ce da ni." Ya girgiza mata kai yace, "kar ki damu babu wani ciwo." Kallon ban yarda da kai ba take yi masa hakan ya saka shi kallon ta shima yace, "baki yarda ba?." "Gaskiya ina kokwanto, bara na tambayi Mama naji me zata ce akan abinda nake ji" ta faɗa tana ɗaukar wayar ta kafin ya gama mamaki har ta kira Mama. Bai hana ta ba ya gyara zama dan yaji dramar ta da Mama dan yasan tunda tace zata kira sai ta kira ta. Mama ta ɗauka da sallama Manal ta amsa suka gaisa kafin tace, "Mama daga makaranta nake ina ta amai." Mama tace, "Ayya sannu, Daman baki da lafiya?." "Lafiya ta lau, bana faɗa miki ina jin ciwon mara ba?." Mama tace, "kin faɗa min." Cikin shagwaɓa tace, "Wallahi Mama yaƙi zuwa har yanzu, gashi wahala nake sha ko yaushe a cikin ciwo nake, kamar ana ƙulle min mara haka nake ji, kuma kusan sati huɗu fa ina jin ciwon amma har yanzu bai zo ba. Ni na gaji Mama haushin kowa nake ji wallahi, ji nake kamar na dinga marin kai na." Mama tayi dariya tace, "ke da kike da likita a kusa dake Manal, shi zaki faɗawa wannan damuwar taki bani ba." Ta kalle shi shima kallon ta yake yi ta turo bakin ta gaba tace, "na faɗa masa yace wai ai hakan ba abin damuwa bane, amma ni na damu gabaɗaya wannan ciwon ya canja min yanayina, makarantar ma wallahi na tsane ta Mama. Kowa haushi yake bani, wani iri nake jina kamar ba ni ce Manal ɗin ki ba." Mama tace, "gaskiya dai yana baki wahala, gashi kin ce min ke baki da ciki ko?." Manal tace, "eh mana." "To ki cigaba da haƙuri zai zo." "Ni na gaji da haƙurin, asibiti zan je." Mama tayi dariya tace, "sai kin dawo Manal, nayi baƙuwa sai anjima." Manal tace, "To Mama, a gaida Yaya Mubeena" ta faɗa tana yanke wayar ta ajjiye a gefe gabaɗaya ta rasa abinda yake mata daɗi. Shi dai kallon ta yake yi ganin tayi waya da Maman da alama bata samu mafita ba, tsabar taurin kai irin nata ga gaskiya amma taƙi yarda ita, ita a lallai bata da ciki gashi nan tun ba'a je ko ina ba ya fara nuna kan sa amma taƙi yarda har yanzu. Ganin yayi shiru bai ce mata komai ba kallon tv yake yi sai ta kalle shi tace, "kai ko a jikin ka ko?, duk abinda yake damuna ni kaɗai ya shafa, kallon ball ɗin ka ma ka ke yi wato na mutu kawai" ta faɗa tana kallon sa a ƙufule. Ya rausayar da kai yace, "haba dai Partner, ni kuwa nake ji a jikina in baki da lafiya ai ni ne bani da lafiya." "To kayi min abinda zan ji na daina jin komai don Allah, wallahi ni kaɗai na san abinda nake ji" ta faɗa a sanyaye tana kallon sa tana hawaye. Kusa da ita ya dawo sosai ya riƙo ta ta kwanta a jikin sa ya goge mata idanun ta yace, "ki daina kuka, kar ki damu ki kwantar da hankalin ki zaki daina jin abinda kike ji sai a hankali."  Manal tana kwance a jikin sa tace, "amma ban taɓa jin irin haka ba, sai dai nayi ciwon da yafi haka zafi amma bana jin wannan yanayin." "Banbancin wancan lokacin baki da aure, yanzu kuma kina da aure shiyasa kike jin haka." Manal ta riƙe shi sosai tace, "amma nafi son wancan duk da nafi shan wahala bana jin irin haka, yanzu fa komai haushi yake bani ji nake kamar an canja ni." Bayan ta yake shafawa a hankali cikin shigar rarrashi yana murmushi cikin farin ciki yace, "Wannan ɗin ma zaki daina ji in sha Allah, ki yi haƙuri na ɗan lokaci. Yanzu me kike so kici?." Manal tace, "babu komai, kawai bana so naji kayi nisa dani, ka zauna a haka don Allah." Ya sake riƙe ta sosai a jikin sa yace, "ai gani a kusa dake, Amma ki faɗa min abinda zaki ci." "Tea nake so na sha, amma a saka min sugar don Allah." "Kema kin san hakan bazai yu ba, Ta ya ya zaki sha sugar?." "Shi nake so nasha, a saka madara da coffee a saka min sugar a ciki." "Zaki sha madara dai amma banda sugar." Manal a sanyaye tace, "Shikenan na haƙura." Numfashi ya sauke ya janye ta zai miƙe tsaye ta riƙe shi yace, "zan kawo miki tea ɗin ne, ga lokacin sallah ma yayi." "Ka bar tea ɗin kawai, in ka dawo daga masallaci na sha." "To sai na dawo" ya faɗa yana kallon ta ta ɗaga masa kai yayi murmushi ya fita. Yana fita ta tashi ta shiga kitchen da sauri ta haɗa tea ɗin yadda take so, ta zuba sugar son ranta da madara ta bar shi ya wuce ta tayar da sallah. Tana idarwa jikin ta har rawa yake ta fara shan tea ɗin saboda yadda take ji in bata sha ba zata iya mutuwa, tashi tayi ta ɗauko cake ta dawo tana sha da tea ɗin tana cin cale har lumshe ido take saboda daɗi. Kwace cake ɗin taji anyi an karɓi cup ɗin hannun ta ta kalle shi a tsorace gaban ta yana faɗuwa. Tea ɗin ya kai bakin sa ya haɗɗiye daƙyar ya kalle ta cikin rashin fara'a yace, "haba Manal, meye haka? Wannan sugar ko mai lafiya ya sha ya za'a cika dashi balle ke? Meyasa kike wasa da lafiyar ki ne? Kina so ciwon nan yayi miki illa ne?." A shagwaɓe tace, "to shi nake so na sha ya zanyi?." "Ba sai ki ɗauki ɗaya ba ko tea ɗin ko cake? Sai ki haɗa biyu ko wanne da sugar a ciki?." Manal ta ɗauke kai gefe dan ita kam bata ga tayi laifi ba dan abinda take so ta aikata. Tsaki yayi ganin abinda tayi ya wuce ta ya kai kitchen ya zubar da ragowar shayin da cake ɗin ya dawo inda take ya ɗauko laptop ya zauna yana aiki tana gefe tana kallon sa. Tana nan zaune shiru yana aikin sa tana gefe har akayi sallar i'sha bai ce mata kanzil ba ya tashi yaje  sallah ya dawo ya shiga ɗaki, tana zaune ya fito daga ɗakin cikin ƙananun kaya yace, "zan tafi aiki, bazan dawo ba maybe sai cikin dare ko gobe, zan turo miki Ummi yanzu in akwai abinda kike so ki min waya." Kallon sa tayi tace, "don Allah kar ka tafi ka barni." Ganin har ta fara hawaye sai yace, "aiki zanyi Manal dole naje." Ta taso ta dawo kusa dashi ta riƙe hannun sa tana narkewa tace, "nidai don Allah kaje dani bana so kayi nisa dani, ka tafi dani bazan iya zama baka nan ba." Rungume shi tayi tana kuka a jikin sa dan da gaske bata so ya tafi ya barta. Yace, "Manal asibiti zan je fa ba wani resturant ɗin ba, Taya zan je dake ni da zan yi aiki?." Bata ɗago ba sai kuka da take yi yace, "shikenan ɗauko hijjabin ki mu je, amma kar kizo kina cemin na barki ke kaɗai a office na je wani waje." Da sauri ta shiga ciki ta ɗauko hijjabin ta ɗauki wayar ta tabi bayan sa ya kashe hasken gidan suka hau mota suka tafi. BDKB2P28 Kwanaki na ta tafita manal ciki na ta ƙara kwanaki a jikin ta har lokacin bata yarda ba shi kuma ya share ta yana bita a babu ɗin amma duk abinda take so babu abinda baya mata, cikin nata ma mayen sane duk inda yake bata son yin nisa dashi sai dole, makaranta kuwa ta daina zuwa sai online take lectures dan tace ta tsani school ɗin. Shigowar sa gidan kenan ya tarar da Maryam a zaune a falo ita kaɗai, ya shigo da sallama cikin falon yana bin ta da kallo ganin gabaɗaya ta canja ta koma wani iri kamar ba ita ba. Sallamar ta amsa ya kalli falon yace, "ina matar gidan ta bar ki ke kaɗai a zaune?." Ya faɗa yana zama a kan kujera yana kallon ta. Maryam tace, "Yanzun nan ta shiga ciki." Manal ce ta fito a lokacin ya kalle ta sai tace, "sannu da zuwa" ya amsa kafin ta juya ta koma ciki. Ya kalli Maryam a nutse yace, "hankalina ya tashi tunda kika ce kina gida kina jirana, me yake faruwa haka? Me ya same ki kika canja kamar wacce tayi rashin lafiya?." Maryam ta sauke numfashi ta kalle shi tayi shiru na wani lokaci tace, "Bebi Kamal ne." Gaban sa ya faɗi mutuƙa ya kalle ta yace, "wani abun ne ya faru?." Ajiyar zuciya tayi ta goge idanun ta da suke zubar da hawaye bata ce komai ba ta sunkuyar da kai. "Kin yi shiru, hankalina a tashe yake ki sanar dani me yake faruwa ma." Maryam ta kalle shi tace, "Ban san ta ina zan fara sanar da kai abinda ya faru bane, nauyi nake ji a zuciyata ban san da wacce fuska zaka kalli abinda zance maka ba shiyasa nayi shiru. Amma bani da wanda zan sanarwa sai kai na gaji da abinda yake faruwa gwara ka sani ko zaka yiwa tufkar hanci." Girgiza kai yake yi yace, "ina jin ki." Maryam ta kulle ido ta buɗe ta kalle shi tace, "Kamal ne yake amfani da...." Sai tayi shiru bata ƙarasa ba yace, "ki sanar dani mana, me Kamal ɗin yake amfani dashi?." "Kamal ne yake blackmailing ɗina da wasu hotuna na wajan sa." "Blackmailing! Kamar ya blackmailing ɗin ki ban fahimta ba, wanne irin hotuna ne wannan da yake amfani dasu?." Maryam ta kulle ido ta buɗe nauyin sa take ji har cikin zuciyar ta hakan ya saka ta kasa magana, sai da ta daure ta haɗɗiye yawu ta kalle shi tace, "hotunan tsaraicina ne!." "Hasbunallahu wani'imal wakil! A ina ya same su? Kar kice min ke kika tura masa?." "Ni na tura masa." Da sauri ya kalle ta kafin yayi magana tace, "Bebi wallahi ba hotunan yanzu bane, tun ina gidan sa hotunan suke wajan sa, na ɗauka da muka rabu ya goge ashe bai goge ba, yanzu dasu yake amfani wajan tilasta min nayi zina dashi!." A firgice ya kalle ta idanun sa a waje saboda firgicin abinda yace, "kar ki ce min kin aikata Yaya Maryam, kar kice min kin biye masa kin aikata zina." Shiru tayi ta share hawaye tace, "ban aikata ba Bebi, so nake yanzu a san ya za'a yi a goge hotunan daga wajan sa." Kallon ta yake yi haka nan zuciyar sa bata amince da abinda tace ba yana kallon ta yace, "kin tabbatar da abinda kika ce?." Kallon da yake mata ne ya saka ta kasa magana yace, "tun farkon rabuwar ku yake yi miki barazana da hotunan kuma har aka zo yanzu babu abinda ya faru?, kina so kice barazana yake miki daga lokacin har yanzu bai miki komai ba?. Yaya Maryam ko aurena an ɗauki lokaci a yanzu balle rabuwar auren ku." Kulle ido tayi ta buɗe ta dafe kanta tana kuka tace, "yace in ban amince ba sai yaɗa hotunan a duniya, tsoron kar hotunan su fita waje ya saka na....!" "Ya saka kika aikata zina Yaya! Ya saka kika biye masa kika aikata zina saboda tsoron abinda zata ce duniya a kan ki kika saɓawa Allah?." Sai da ta tsorata saboda yadda yayi maganar cikin tsawa zallar ɓacin rai kamar ba Yayar sa ba tace, "Saboda Nabila da Nabil Bebi, posting yace zai yi a social media in hotuna suka shiga duniya da wanne ido zan kalle su?." Kamar zai dake ta yace, "saboda gudun maganar mutane sai kika saɓawa Allah?, Allah da ya halicce ki bakya jin kunyar sa sai kunyar ƴaƴan ki?." "Saboda hotunan ne wallahi ba da son raina ba, ka fahimci ni!." "Bazan taɓa fahimtar ki ba, har abada bazan taɓa fahimtar abinda zaki ce min ba yanzu ko nan gaba. Meye amfanin tura hotunan?." Ta kalle shi tana kuka tace,"lokacin ina auren sa." "Ko lokacin da kike matar tasa ne meye amfanin tura masa hotunan tsaraicin ki? A ganin ki soyayya ce ko?, a ganin ki ƙauna ce ta kawo hakan ko?. Kin ɗauki hotunan tsaraicin ki kin tura masa saboda taƙamar ki mijin ki ne, kin manta da zai iya ajjiye wayar a wani wajan wani ya ɗauke ko iya shi kaɗai yaga hoton a wayar ya cuce ki. Wannan lokacin da muke ciki na ƙwacen waya in aka ƙwace wayar tashi fa? Mahaifin ki dan siyasa ne da wannan kawai za'a yi amfani wajan lalata masa siyasar sa, ke duk baki tunanin wannan ba a lokacin ba?, soyayya ta rufe miki ido, shi kuma da yake yana da wayo baya tura miki nasa sake uwar soyayya! Yanzu gashi dasu yake amfani yake ruguza miki rayuwa!." Kai yake girgizawa yana magana cikin murya mai amo yana nuna ta da tsaya kamar ba Yayar sa ba yace, "ba ko wanne miji ne in ya rabu dake yake kare mutuncin ki ba, ba ko wanne namiji ne in ya rabu dake yake so yaga kin samu nutsuwa ba, ba ko wanne namiji bane in ya rabu dake yake so ki yi walwala a duniya ba. Wani burin sa yaga kin wulaƙanta, burin sa yaga kin tozarta, wani burin sa so yake yaga kin dawo bara a kan titi, wani so yake yaga ya kulle miki hanyar da wani zai aure ki. Ba ko wanne masoyi ne yake zama masoyi ba, Annabi Muhammad S.A.W da kan sa yace ka so masoyin ka sama-sama saboda wata rana zai iya zama maƙiyin ka, sannan ka ƙi maƙiyin ka sama-sama wata rana zai iya zama masoyin ka. Har gwara ace maƙiyin ka ne ya dawo masoyin ka akan ace masoyi ya koma maƙiyi, saboda maƙiyin ka bai san komai naka ba, masoyin ka da ya koma maƙiyi babu abinda bai sani naka ba, da zarar ya koma maƙiyin ka ya san hanyar da zai bi ya cuce ka saboda duk wani lagon ka ya sani. Meyasa baki yi tunanin hakan ba? Ke a ganin ki tura masa hotunan tsaraicin ki da kike yi ƙauna ce ko? Yanzu wa gari ya waya? Gashi yana amfani da hotunan yana saka ki aikata zina dashi bayan yayi miki saki uku!, kin cutar da kan ki da hannun ki." Kuka take sosai mai nuni da nadama mara amfani, yanzu ta gano kuskuren ta da ta tafka a rayuwar ta, yanzu ta gane gangancin da ta yi da rayuwar ta, yanzu ta gane tura hotunan tsaraici ga wani mijin ba soyayya bace. Cikin shashsheƙa tace, "nayi nadama Bebi, nayi nadama bazan sake aikatawa ba, na jima ina so na sanar da kai sai na kasa faɗa maka, amma yanzu ka taimaka min kar hotunan su shiga duniya. Yace in ban je na same shi gobe ba zai watsa su a duniya, ni kuma na gaji da aikata saɓon Allah." Kuka take yi sosai zuciyar ta bugawa take yi sosai hankalin ta ya tashi matuƙa, nada sani ta gama mamaye zuciyar ta. Ya kalle ta idanun sa sun koma jajajur saboda ɓacin rai da takaici da ƙunar zuci yace, "har sau nawa hakan ya faru?." Ta sunkuyar da kai bata kalle shi ba kuma bata yi magana ba. yayi ƙaramin tsaki tare da murmushin takaici yace, "sai da komai ya lalace zaki neme ni?." Maryam tace, "ka gyara komai Bebi, ka gyara ka ceto mutuncin Yayar ka, ka taimake ni bana so Mamy ta san maganar nan don Allah. Baza ta iya jura ba, kwanaki Lubna yanzu kuma ni." Ya yi shiru yana sauke ajiyar zuciya, zuciyar sa nayi masa zafi sosai ya kalle ta cikin baƙin ciki da yaje kina zuciyar sa yace, "ki amsa min tambayata, sau nawa kika je wajan sa?." Kasa magana tayi ta kulle ido ta buɗe yace, "ke kan ki baki sani ba ko? A haka kike so na taimaka ki?." "Ka manta da wannan ka taimake ni." "Ke kika kai kan ki Maryam!." "Ka dawo dani Bebi!" Ta faɗa tana tasowa tazo inda yake tsaye ya juyar da fuska gefe ɗaya. Numfashi ya sauke ya kalle ta yace, "baki da buƙatar taimako na." A ƙasa ta zube guiwowin ta ta haɗe hannayen ta waje ɗaya tace, "ina roƙan ka Adnan, ba don ni ba dan zumuncin da yake tsakanina da kai ka ceto rayuwata. Naci alfarmar ƴaƴan ka Nabil da Nabila ka ceto ni daga hannun Kamal." Yawu ya haɗɗiye daƙyar ya sunkuya ya ɗago ta daga ƙasa ya riƙe kafaɗar ta ganin tana kuka sosai yace, "zan san abinda zan yi a kai." Maryam tace, "yau kawai nake da ita, in ba yau ba gobe zai iya aikata abinda yace." Ya kalle ta ya cire glasses ɗin sa yace, "bakya jin kunyar wanda ya halicce ki sai kunyar yaran ki?." Tayi shiru ta sunkuyar da kai yayi tsaki yace, "i'm highly disappointed." Kuka take yi sosai tace, "ban san ya zanyi bane ba Bebi, ban sani ba." Lumshe ido yayi ya kalle ta yace, "kin ɓata komai Maryam, gyara shi yanzu bashi da amfani tunda kin aikata ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba. Sau nawa ina ja miki kunne akan Kamal kike ganin kamar takura miki ki nake yi? Sau nawa ina miki iyaka dashi kin ji?." "Naji Bebi wallahi, na fara ja baya da zuwa inda yake daga baya ya fara amfani da hotunan." "Ke kika jawo! Da baki tura masa ba da bashi dasu ai, ɗauka kike soyayya ce shiyasa kike tura masa hotunan tsaraicin ki. Ki yi addu'a Allah yasa a yanzun ma ba video yake miki ba a duk lokacin da kuke aikata zina!" Ya faɗa cikin murya mai amo saboda ɓacin ran da yake ji a zuciyar sa babu abinda zai hana bai kifa mata maruka masu zafi ba. Shiru tayi tana kuka mai taɓa zuciya, ya sauke numfashi ya ƙarasa fridge ya ɗauki ruwa ya sha yace, "kar ki damu zan san abinda zan yi, ki je gida kawai." Ta girgiza kai tace, "na gode Bebi" ta faɗa tana niyar fita daga falon tana goge fuska, ya bita da kallo kafin yace, "zaki iya tafiya da kan ki?." Ta ɗaga kai alamun eh ya kulle ido yace, "ki tafi a nutse." Ta ɗaga kai ta fita ya bita da kallo zuciyar sa na bugawa sosai. Tunda ta fita ya koma da baya ya zauna bai iya motsawa daga inda yake zaune ba ya dafe kansa yayi shiru ya rasa abinda yake damun zuciyar sa, tunani yake ta wacce hanyar zai bi wajan samun hotunan a wajan Kamal? Ta ina zai bi ya samu hotunan har ya goge su?. Manal tana daga ciki tana jiyo amon muryar sa yana faɗa har mamaki abin ya bata kamar ba da yayar sa yake magana ba, jin shirun yayi yawa sai ta fito falon tana kallon sa. A yanayin da ta ganshi ya saka ta ƙarasowa a hankali har yazo inda take, ɗago kai yayi a lokacin ya kalle ta, ganin yadda fuskar sa tayi sai ta ja ta tsaya bata ƙarasa kusa dashi ba tace, "Akwai abinda yake damun ka?." Banza yayi mata kamar bai ji ba kafin ya tashi ya bar falon ba tare da ya bata amsa ba. Mugun haushi taji a zuciyar ta, Daman ya aka cika da ita cikin kwanakin nan baka yi mata komai ba ma ran ta ya ɓaci balle kuma kayi mata?. Bata sake bi ta kansa ba ta share shi itama ta wuce ciki ta cigaba da harkar ta bata sake sauraron sa ba. BDƘB2P29 Manal har dare bata sake ganin sa ba itama bata neme shi ba dan neman nasa bashi da amfani. tana zaune tana cin indomie ɗin da mai aikin ta ta dafa mata ya shigo falon da take ya ɗauki laptop ɗin sa bai mata magana ba ya fita itama bata ce masa komai ba. Mummy ce ta kira wayar ta ganin sunan Mummy sai ta ɗauka suka gaisa Mummy tace, "Ina Adnan?." "Yana ɗaki Mummy." "Jeki kice masa nace ya kira ni yanzu, ina ta kira baya ɗauka." "To Mummy" ta faɗa tana tashi tsaye Mummy ta kashe wayar. Ɗakin nasa ta shiga ta same shi a tsaye ya riƙe ƙugu yana kallon sama alamun tunani yake yi tayi sallama ya amsa a ciki ba tare da ya juyo ba tace, "Daman...!" Katse ta yayi yace, "Daman me? Manal bana son magana don Allah ki je." Ranta ya sake ɓaci tace, "to ka jira kaji abinda zan ce maka mana kafin ka kore mi." Da faɗa tayi magana cikin nuna fusatar da take ciki hakan ya saka shi kallon ta yace, "bazan ji abinda zaki ce ɗin ba, ki fita ki bani waje nace ko?." Ranta ya sake ɓaci sosai tace, "Daman ba zama nazo yi ba, aiko ni akayi tunda baka buƙatar ji ka huta." Tana faɗar hakan ta fita rai a ɓace ba tare da ta faɗi aiken Mummyn ba, ya bita da kallo cikin ƙunar rai da zallan mamakin ta. Lallai ma shi take yiwa tsawa har haka kamar wani sa'an ta? Lallai ta samu sake da yawa, ya sakar mata fuska amma zai yi maganin matsalar. Waya ya ɗauka da key ɗin mota ya fita daga ɗakin zuwa waje, mota ya yau ya bar gidan kai tsaye unguwar su ya shiga bai ma tsaya a ƙofar gidan su ba ƙofar gidan maƙocin su ya tsaya ya danna horn, mai gadin ya buɗe ƙofar gate ɗin ganin motae Adnan sai ya ƙaraso yace, "Allah dai ya biya Adnan, yau kai ne a gidan namu, wallahi ka ƙi gayyataa gidan amarya." Bebi yace, "kana ji? Magana nazo mu yi." "Ahh ai ko yaushe ni mai baka haɗin kai ne Oga. Kai ne fa ka yi belina da lakwaye suka dafe ni." Bebi yace, "wayar wani nake so a ƙwato min." Yayi dariya yace, "a farɗe cikin sa a wajan karɓar wayar ko hannun sa ka ke so a cire?." "Bana so ayi masa komai, wayar hannun sa kawai nake da buƙata da gaggawa." Wanda yake amsa sunan ɗan ƙaura yace, "an gama Oga, a ina yake?." Bebi ya bashi address ɗin Kamal da number wayar sa da hoton sa da komai sannan yace, "an gama Oga, in kaga bamu karɓi wayar nan ba to ka tabbatar da bai fito ba, Amma indai ya fito idona idon sa wallahi ba rabon sa bace." Bebi yace, "kar kayi masa komai, ka karɓa kawai ka wuce." "An gama Oga, amma in yazo da gardama ko yatsa biyu ne zamu datse." "A'a ban ce ba, kayi abinda nace kawai." "An gama." Bebi yace, "zaka ji alert." Yayi dariya yace, "sai da kai oga" Bebi ya kulle glass ɗin motar ya ja motar ya tafi. Sai da ya shiga wajan Mummy dan yaga kiran da tayi masa kafin ya wuce gida. Lokacin da ya shiga gida ya tarar Manal har tayi bacci a kan kujera, ya tsaya yana kallon ta kamar ya shiga da ita ciki sai kuma kawai ya share ya fita. Shi kam kasa baccin yayi tunani sun masa yawa sai kai kawo yake ya rasa abinda yake masa daɗi a zuciyar sa, bashi ya aikata zina ba amma shi yake jin zafin ta a zuciyar sa saboda zallar tsanar da yayi mata. Mahaifi na aikata zina, ga Yayar sa Maryam ga Lubna da aka yiwa fyaɗe. Yana wannan tunanin bacci ya ɗauke shi ko ɗakin bai samu ya shiga ba. Washe gari bai tashi da wuri ba ta kuma tashe shi ba tayi abinda zata yi a gidan ta fita daga gidan da niyar zuwa makaranta. Ko da ya tashi bai ganta ba yaga dai har abinci ta ajjiye an gyara ko ina na gidan. Wayar ta yake kira ta ɗauka yace, "kina ina?." Manal tace, "naje school z'a yi practical yau." "Waye ya tafi kai ki?." "Mai kuɗi ne." Yayi shiru hakan ya saka tace, "daga nan zan je wajan Mama." "A gaishe ta" ya faɗa yana yanke wayar itama ta kashe. Bayan ƙarfe huɗu suka tashi ta ya ajjiye ta gidan Mama tace bayan i'sha yazo ya ɗauke ta. Mama na zaune taga ta shigo a guje ta shiga banɗaki tayi fitsari ta fito Mama ta bita da kallo tace, "ke sallamar taki kenan?." Manal ta zauna tace, "wallahi fitsari ne kamar ya zubo daƙyar na shigo gidan nan." Mama tayi shiru Manal ta gaishe ta ta amsa tana kallon ta kafin tace, "Daga ina kike haka?." "Naje school ne mun yi practical yau." Mama tace, "yau kin iya zuwa kenan?." Manal tace, "daƙyar ba, daurewa kawai nake yi saboda kin ce na dinga daurewa kar ayi asarar kuɗi Allah da bazan je ba. Yau ɗin ma facemask biyu na saka bayan na shafa musu humra. Kuma kinga online nake lectures kawai practical ɗin ne sai naje." Mama tace, "ai gwara ki je abinda kike so ne, wannan yanayin da kike ji na ɗan lokaci ne." Manal tace, "na ɗan lokaci, shima haka yake cewa. To me ya kawo min hakan? Anya ba wata cutar ce ta hana ni period ba kuma ta saka min wannan ciwon?." Mama tayi tsaki ta kalle ta tace, "ke wai ina ilimin ki da wayon ki ya tafi ne Manal? Ke yanzu sai an zaunar dake an miki bayanin ciki ne dake?." Manal gaban ta ya faɗi harda dafe ƙirji tace, "Wai Mama da gaske cikin ne?." Ta harare ta tace, "To da kan ki ne?." Manal ta wara idanu tace, "amma ban sani ba." "Ya faɗa miki kin ƙi yarda shiyasa ya ƙyale ki a hakan, nima da farko ai cemin kika yi ke baki da wani ciki. Ki nutsu ki raini abinda yake cikin ki bana son wannan shirmen naki. Ki san yanzu kin girma kin kusa zama uwa, wanne jini ne zai kai yanzu bai zo ba kuma kina zaune babu wanda ya kai ki asibiti?." Hawaye ta fara yi Mama tace, "ke bana son shirme? Meye na kukan?." Manal ta kasa magana kunyar Maman ta haɗe mata da takaicin samun ciki da wuri har haka. Ta kalli Mama tace, "Mama samun cikin yayi kusa, har yaushe aka yi auren da za a ce ina da ciki?." Mama ta harare ta tare da yin tsaki tace, "sai yanzu kika san da hakan kenan?. kuma Allah ne ya baki, wasu shekarar su nawa a gidan mijin suna son haihuwar Allah bai basu ba?, Ke gashi daga auren ki ya miki kyauta shine kike kuka?." Manal bata sake magana ba ta tashi ta shiga ɗakin Mama ba jimawa ta fito Mama tace, "fitsarin kika sake yi?." Ta ɗaga kai alamun eh Mama tace, "Anya sugar ki bai hau ba?." Manal ta turo baki ta zauna tace, "ban sani ba kwana biyu ba'a duba ba, ni haushi ma yake bani." Mama tace, "mijin naki?." "Shi fa Mama, wallahi sai naji kamar na masa dukan tsiya, duk shine ya jawo min." Mama tayi dariya ta girgiza kai jin wai shine ya jawo mata, kamar ba da haɗin kanta aka yi cikin ba. Kallon ta Mama tayi ta sake girgiza kai tana maimaita Manal da ciki a zuciyar ta. Waya aka yi mata ta ɗauka jin tana salati yaja hankalin Mama tana gamawa tace, "lafiya?." Manal tace, "Yaya Maryam, Yayar sa ce tayi hatsari yanzu haka tana asibiti." Mama tayi salati tace, "Amma jikin da sauƙi ko?." Manal tace, "Kausar ce take faɗa min naji maganar ta babu ruɗani sosai da alama bai yi muni ba." Mama tace, "Allah ya bata lafiya." Manal ta amsa da amin kafin tace, "in Mai kuɗi yazo sai naje na duba ta ko Mama?." "Eh ya kamata, nima gobe zamu zo da Mubeena in sha Allah." Manal tace, "tana ina ne ma? Ban ganta ba?." Mama tace, "na aike ta yanzu zata dawo." Manal tace, "kafin ta dawo bata naje gidan Mama" ta faɗa tana fita da niyar zuwa gidan su Surayya. Bayan sallar i'sha da mai kuɗi yazo ya ɗaukar ta ta tace su wuce asibitin da Maryam take daman tasan bazai rasa sani ba sai gasu a asibitin su Bebi ya sauke ta ya raka ta har ƙofar ɗakin da Marym ɗin take. Da sallama ta shiga aka amsa ana kallon ta, tana ƙarasawa ciki taga Mummy ce da Mamy ga Bebi da Mimi duk suna ciki. Gaishe su tayi suka amsa ta tambayi mai jiki akace da sauƙi, kallon Yaya Maryam ɗin tayi ta ganta tana bacci an saka mata ruwa an ɗaure mata kanta da farin bandage. Wani irin jiri ta fara ji gabaɗaya yanayin ɗakin bai yi mata ba, dafe kai tayi tana daga zaune amma ji take kamar zata fika. Bebi yana lura da ita Mummy ma tana lura da yanyin ta. Wata likita ce ta leƙo da rigar likitoco tace, "Dr minti ɗaya." Jin haka sai ya bar dakin ya fita wajan ta. Mimi da take kallon Manal tace, "Anti Manal lafiya kike?." Mummy ta kalli Mimj tace, "ba lafiya ba dai, na lura kamar jiri take." Mimi ta dawo kusa da Manal tana kallon ta tace, "Sannu." Manal ta ɗaga kai ta rufe ido dan sosai take jin amai yana taso mata. "Mimi amai nake ji" ta faɗa mata ƙasa-ƙasa, Mimi zata yi magana ta riƙe ta tace, "kar ki faɗa a ji don Allah." Mimi tace, "to taso mu fita." Tashi suka yi zasu fita Mummy tace, "ina zaki kai ga ita da ba lafiya gare ta ba?." Mimi tace, "Wajan Yaya Bebi zan raka ta yanzu zamu dawo."  Fita suka yi kai tsaye office ɗin Bebi Mimi ta wuce da ita, ta buɗe suka yi sa'a buɗe yake suka shjga suka ganshi yana tsaye shi da likitan da tazo ta kira shi, bin su yayi da kallo suka wuce shi suka nufi inda suke tunanin banɗaki ne Manal ta shiga tana amai. Bayan su ya biyo ganin tana amai ya tsaya yana kallon ta Mimi sai sannu take mata, ganin yazo wajan sai Mimi tace, "tun a ɗakin da Yaya take tace amai take ji, shine na rako ta nan bata so su Mummy su san bata da lafiya." Kai ya ɗaga mata kawai Mimi ta fita daga office ɗin.  Manal ta fito ta zauna kanta har sarawa yake yi saboda yadda ya fara mata ciwo. Miƙar da ita tsaye yayi ya ja hannun ta suka fita daga office ɗin zuwa scaning room. Likitan da take aiki a ciki ya saka ta yi mata scaning shi kuma yana tsaye har aka gama. Sai da ya riƙo hannun ta suka dawo office ɗin sannan ya fita. Ba jimawa ya dawo ya zauna a kusa da ita bai ce komai ba itama bata ce ba dan haushin sa take ji sosaai a zuciyar ta. Jin ciwon kan nata ya ɗan ragu  sai ta tashi tsaye tace, "zan koma wajan su Mummy." Kallon ta yayi suka haɗa ido yace, "ki wuce gida." Kamar zata yi kuka tace, "in naje babu kowa ni kaɗai zan zauna ga dare yayi." "To ki zauna a nan." Zama tayi yana kallon ta har na wasu sakanni kafin ya janye idanun sa daga kallon ta a lokacin aka shigo office ɗin da sallama. Tashi yayi ya ƙarasa wajan nurse ɗin da ta kawo masa takardu guda biyu ya karɓa ta fita, yana daga tsaye ya fara buɗe ta Manal yaga cikin ta har ya shiga wata sati sha uku, ya kulle ya buɗe ɗayar takardar. Tabbatar da abinda aka faɗa masa akan Maryam yayi, da gaske dai itama cikin ne da ita har na Manal ma ya fi nata ƙwari. Kenan hakan yana nufin ba'a jima da samun sa ba. BDƘB2P30 Wani irin shock ya ji a zuciyar sa sakamakon ganin result ɗin Maryam, yammmm haka yake ji a fatar jikin sa saboda tashin hankali. Ajiyar zuciya yayi cikin ƙunar zuciya ya dawo ya zauna ya dafe kansa ya rasa abinda yake masa daɗi komai ƙona masa zuciya yake yi. Manal ta kalle shi kamar zatayi magana sai ta share shi dan ba sauraren ta zai yi ba ƙarshe ranta yazo yana ɓaci taji haushi. A haka ya jima a zaune baya cewa komai itama bata cewa komai kafin ya tashi ya fita.Da kallo ta bishi tace, "haka dai, kullum cikin damuwar da kai baka san dalilin ta ba amma ta shafe ka." Ƙaramin tsaki tayi ta kawar da kanta daga kallon ƙofar. bai jima ba ya dawo ya kalle ta yace, "mu tafi gida." Tashi tayi suka fito tace zata koma tayi musu sallama yace basai ta je ba su wuce. Koda suka je gidan ɗakin sa ya shiga dan ita fitsari ya matse ta da gudu ta shiga banɗaki, Sai ta yi wanka ta fito ta saka rigar bacci mata nauyi ta shiga kitchen ta haɗa corn flakes ta sha ta goge bakin ta dan kar ma ya gani ta shiga ɗaki tayi kwanciyar ta. Tana jin sa ya shigo ɗakin nata ya kwanta a kusa da ita amma bai ce mata komai ba, Sai juyi yake yi alamun ba bacci yake ba wani abun yana damun sa sosai. Tana jin sa tayi masa banza bata kula shi ba, daga baya ma sai taji ya buɗe ƙofa ya fita ta taɓe baki ta cigaba da baccin ta. Tana idar da sallar asuba ya shigo ta kalle shi tace, "ina kwana." Baice komai ba ya ƙaraso ya sunkuya ya ɗago ta daga ƙasa ya zaunar da ita gefen gadon ya ɗauko glucometer ya saka sabon syringe ya fasa babban ɗan yatsan ta ya saka a na'urar. Kallon ta yayi tana kallon fuskar sa itama muryar sa a ƙasa yace, "yanzu ke a ganin ki hakan daidai ne? Fbs ba ma rbs ba ace sugar ki yace tafi 13.0 Manal? Ke a ganin abinda kike yi taimakon ki yake yi?, ki ɓuya ki sha corn flakes, ki sha custard, ki sha tea a ganin ki daidai ne?." Kafin tayi magana yace, "ke kin san illar da ciwon yake yiwa masu shekarun ki? Mama ma da ta fiki shekarun baki ga illar da yayi mata ba Manal? Meyasa bakya kiyayewa kike cin duka abinda kike so ne yanzu?. Kina so wani ciwon ya kama ki ne? Ko kina so ya dinga kwantar dake a asibiti?." Manal ta goge hawayen da ya sakko mata kanta yana ƙasa murya a sanyaye tace, "wallahi bana sane, haka kawai yanzu in ban sha abu mai sugar ba sai naji kamar zan mutu shiyasa nake sha, Amma ba don ina so ba." Jin yadda take magana sai yace, "duk lokacin da kika ji kina so meyasa baza ki faɗa min ba? Ke kin san farin sugar yadda yake da illa ga mai lafiya ma ina ga ke?. Sannan kin san illar da ciwon da yake yiwa irin ku masu ciki? Ko cikin baya bari a samu da wuri ke Allah ya baki, amma kina so ki salwantar dashi ta hanyar shaye-shayen sugar nan naki." Tayi shiru tana kuka yace, "duk abinda kike so akwai irin naki sai a siyo miki shi, amfani da wanda ba naki bane illa ne a gare ki. tunda naga kina yawan fitsarin nan na san blood sugar ki yayi high, bana so naga kina ciwo Manal, bana ai naga wani abu ya same ki meyasa bakya tausayina?. Yanzu in ciwo ya kama ki kin yi min adalci kenan?." Manal a sanyaye tace, "bana sane, ni kaina ban san ina sha ba wallahi." Numfashi ya sauke ya ɗaga rigar ta ya saka hannun sa a cikin ta yana shafa fatar cikin ta a hankali yace, "ciki ne dake har na wata uku Manal, duk abubuwan nan da kike ji shi ne yake saka ki. Yawan faɗa da kike yi min, tsanar makaranta, son shan sugar, jin bakya son magana da komai shi ne yake saka hakan sai nan gaba zaki daina ji." Ta ɗora hannun ta akan hannun sa da yake cikin ta ta kalle shi ya ɗaga mata kai yace, "akwai abinda yake shirin zama mutum a cikin marar ki Manal, kin kusa zama uwa kema shiyasa kike jin duk irin wannan abubuwan. Duk abinda ki ke yi alamu ne na kin girma Allah ya yi nufin halittar sabuwar halitta daga tsatson ki." Tayi shiru tana kallon sa shima ita yake kallo yace, "duk lokacin da kike son wani abu ki faɗa min, yanzu ba ke kaɗai bace lafiyar ki tana da mahimmaci ga abinda yake cikin ki." "To bana ganin fuskar faɗa maka ai, yanzu kusan ko yaushe ranka a ɓace yake, kuma bani na ɓata maka ran ba amma ɓacin ran har ni yake shafa." Yayi murmushi yace, "ko a wanne yanayi nake ki sanar dani kin fi min mahimmaci akan duk abinda zai ɓata min rai ɗin, kece gaba da ko meye lafiyar ki tafi min komai." Manal tace, "nidai ɓacin ranka ya daina shafa ta partner. Bani nayi maka ba amma ko magana sai ka daina yi min bayan ko damuwar ta ka ban san dalilin zuwan ta ba." Ya sauke numfashi yana kallon ta yayi murmushi yace, "yanzu me kike so?." Ta kwanta a kafaɗar sa tace, "bacci nake so nayi a jikin ka." Ya mata kiss a wuyan ta yace, "an gama partner." Maimakon baccin kamar yadda tace sai taji yana mata abinda ta kasa jurewa ta kasa riƙe kanta har ta fara amsa masa itama cikin kewar juna da mararin junan su.       Sai ƙarfe sha ɗaya na safe sannan ya fita ya koma asibiti wajan Maryam, zuwan sa ya tarar da Mummy da Mamy a zaune Maryam ɗin ta farka sai kuka take yi. Mummy ganin ya shigo kafin ma ya gaishe ta tace, "Bebi da gaske ne Maryam ciki ne da ita?." Gaban sa ya faɗi sosai ya kalli Maryam ɗin da take kuka  yayi shiru Mummy tace, "da gaske ne kenan" ta kalli Maryam tace, "Maryam meyasa haka?." Bebi yace, "don Allah Mummy mu jira a koma gida ayi maganar nan, yanzu bamu kaɗai ne a asibitin nan ba." Mummy tayi shiru kawai tana girgiza kai bata ce komai ba. Mamy ita kam hawaye take yi Maryam ɗin ma kuka take yi sosai kamar ranta zai fita. Bebi yace, "Don Allah Mamy a bar kukan nan haka, komai zai zama daidai in sha Allah." Mamy ta kalle shi tace, "ka san tana da cikin kenan kai? Kenan ka ana cikin waye a jikin ta?." Ya sauke ajiyar zuciya yace, "Don Allah Mamy a bar maganar mu koma gida." Mamy tana kuka tace, "ya isa haka Bebi, bazan iya zama a nan ba in na cigaba da zama ina kallon ta zan iya tsine mata" tana faɗa ta bar ɗakin, Bebi ya bita da kallo ya rasa abinda zai ce. Fita yayi jikin sa a sanyaye sosai ya bar "akin ya koma office. Sai bayan sallar azahar Manal tazo ta samu Mummy ce kawai a wajan sai Maryam ɗin da kana kallon kasan tayi kuka. Yanayin da Mummy ta amsa gaisuwar ta san akwai wani abun a ƙasa amma bai shafe ta ba sai tayi shiru. A kan kujera ta zauna nesa sa Mummy babu wanda yake magana a cikin su. Tana nan zaune sai ga Abba ma ya shigo ɗakin da sallama, Manal ta amsa bayan ta kai kanta ƙasa tace, "Abba barka da rana" ta faɗa tana zamowa daga kan kujerar. Kallon ta yayi ya amsa Mummy tace, "Manal ce matar Adnan." Abba yyi murmushi yace, "Allah sarki." ya kalli mummy yace, "Hauwa wai jikin Maryam ɗin ne har haka? Ni na ɗauka ma kun koma gida?." Manal ta kulle ido saboda tunawa da abinda ya faru tsakanin ta da sirikin nata, ta yi saurin kawar da abinda yazo ranta. ya sake kallon Mummy yace, "ina magana kin yi shiru, me yake faruwa ne haka?." Mummy ta kasa magana a lokacin Manal ta tashi ta fita saboda wayar ta take ƙara. Tare da Mama da Mubeena suka shigo suka tarar da Abba yana ciki har lokacjn ga Bebi da Mummy. Sallamar Mama ya saka duk suka kalli ƙofar da ake shigowa Mummy na kallon ta dan bata san ta. Mama tace, "barkan ku da yamma, ya masu jikin?." Mummy tace amsa da fara'a kafin ta kalli Manal tace, "ai ko ba'a ce na san Maman ki ce, ga kama nan kuna yi." Manal tayi murmushi Mummy ta tashi ta bata wajan da take tace, "bismillah ki zauna." Mama tace, "haba don Allah, ki zaman ki." "Haba dai, zauna don Allah" Mummy ta faɗa tana bata wajan Mama ta zauna tana sake yi mata Sannu. Da Bebi suka gaisa ta amsa tana tambayar sa mai jikj ya amsa da girmamawa. Tunda Mubeena ta shigo idon ta ya haɗu da na Abba da yake waya gaban ta ya faɗi shi kansa ido ya wara waje saboda ganin Mubeena a tsaye a bayan wacce ake kira babar matar Bebi. Mummy ce ta katse tunanin sa tace, "wannan ce yayar Manal ɗin?." Mama tayi dariya tace, "Itace." Mubeena tayi murmushin yaƙe tana sake kallon Abba da shima ita yake kallo ya kasa sauke wayar daga kunnen sa. Ɗago ido Mama tayi suka haɗa ido da Abba, ta tsayar da idon ta ƙyam a kansa kamar yadda yake kallon ta. glasses ɗin idon ta ta cire wai ko ba daidai yake nuna mata ba ta sake mayar dashi idon ta tana kallon sa. Mama tantama take akan shine ko kuwa ba shi bane, duk da ga kamanni na suna na saj canji na girma da aka samu amma bata fatan ace shi ɗin ne "Zahra'u ce!" Abba ya faɗa yana kallon Mama. Wani mayaudarin murmushi Mama tayi jin abinda yace ta tashi tsaye ta kalle shi ta kalli Bebi ta sake kallon Manal tace, "Manal waye wannan?." Manal taji wani iri saboda tambayar da Mama tayi hakan ya saka jiki a sanyaye tace, "Mama Abba ne mahaifin Dr." Mama ta girgiza kai tace, "kenan shine sirikin ki?." Manal ta girgiza kai tana kallon Mama da mamaki sosai. Mubeena da take gefe tace, "what! Mahaifin mijin ki Manal?." Manal ta kalli Mama ta kalli Mubeena tace, "eh mana." Abba ya kasa magana sai kallon Mama da yake yi Mama ta sauke ajiyar zuciya ta kalli Manal tace, "Manal zo mu tafi" ta faɗa tana riƙo hannun ta Manal tace, "Mama me yake faruwa ne?, ina zamu je?." Mama ta kalle ta tace, "nace ki wuce mu tafi ko?." Cikin tsawa tayi maganar Manal ta firgita sosai tana mamakin abinda ya canja Mama. Mama ta kalli Mubeena tace, "kema mu je." Sai a lokacin ta kalli Mummy tace, "Allah ya ƙara lafiya." Mama ta faɗa suka fita zuciyar kowa cike da tashin hankali a cikin su. Tunda suka tafi Mama bata ce komai ba, haka Mubeena bata yi magana ba, Manal kuwa tashin hankali ya hanata magana har aka je gida. A tsakar gida Manal ta tsaya tana kallon Mama cikin tashin hankali tace, "Mama me yake faruwa ne? Kin san mahaifin Dr ne? Meyasa kika ce na taho gida tunda ki ka ganshi?." Mama ta kalle ta tayi mata banza kamar bata ji ta ba. Manal zata sake magana Mama tace, "Zaman auren ki da Adnan ya ƙare Manal." A tare Manal da Mubeena suka kalli juna, Mubeena ita kanta a tsorace take so take taji waye mahaifin Adnan a wajan Mama har ya santa ta san shi haka. Mubeeena a sanyaye tace, "Mama me kike cewa ne? Auren ta da Adnan ya ƙare kuma?." Manal a ruɗe take sosai hakan ya saka tace, "Mama me yake faruwa ki sanar dani don Allah, kin saka zuciyar mu a ruɗani mun kasa gane inda kika nufa. Mama meyasa ki ka ce mu taho gida?, Mama meyasa kika ce zaman aurena dashi ya ƙare?." Mama ta kalle ta cikin ƙunar rai ta tace, "Manal na taɓa miki abinda zai cutar dake ne?." Manal ta girgiza kai tace, "a'a Mama, amma Ina so na sani, Meyasa kika canja tunda ki ka ga mahaifin sa har muka dawo gida?." Mama ta ja dogon tsaki ta dafe kai tace, "Dole ki bar aure Adnan koda bakya so, dole ya sake ki ko yana so ko baya so, zaman aure tsakanin ku bazai taɓa yuwa ba." Manal kanta ya sake kullewa kamar zata yi kuka tace, "saboda me Mama?." "Saboda wanda aka nuna min shi matsayin uban Adnan kema uban ki ne Manal!." End of book 2. Mu haɗe a book3 domin jin yadda zata kaya. Da gaske Manal da Adnan uban su ɗaya? To ya za a yi da cikin jikin maryam? Ina labrin Rumana? Wacece Maman su Manal?. 09030398006. 0 701 809 8175