[2/1, 2:29 PM] Ummi Tandama.: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄 *27* WRINTING BY *SAJIDA* Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai, *SAJIDARKU CE* MARUBUCIYAR: *YAR MAHAUKACIYA* *DUK KARYAR KADA* *DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA* *NEMAN NA KAINA* ................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH.... Cike da fargaba Alaidine ya ce" Aba, ka fi ni sannin duniya mun zota ne na dan lokaci kalilan, dukan mai rai sai yayi kaura zuwa kiyama, ba ran da ba zai yi wafati ba, hakuri shi ne Allah yayi mana nuni da mu yi, domin dole ne bamu da yanda zamu yi Kallonsa kawai Aba yake, bai iya furta masa komai ba, kallo na tsoro, kallo na tsoron jin abinda zai fito a bakinsa Mom kam jikinta ya gama rikicewa da rawa, tsoron fal ranta ji take tamkar ta kwato magana a bakin Alaidine aman ya tsaya sai kwana kwana yake, cike da kosawa ta ce" kai Alaidine,.lafiya? Mai yake faruwa ne? Wani ne ya rasu? Ka fadawa mutane ka tsaya kana ta jan maganar bayan ka ga halin da Abanka ke ciki? Ta karasa maganar tanai masa tsawa tsawa Ajiyar zuciya ya sauke ya ce" Aba, rasuwa ne aka yi, kaninka ne ya rasu yanzun ma daga makabarta nake Zurbat suka mike daga Mom har Aba suna kalon Alaidine wanda ya sada kansa kasa yana dan damanma bai je anguwar ba Ajiyar zuciya kawai aba ya saki ya zauna yarab a kasa ya kurawa kasa ido Mom nan da nan ta fara sharar kwallah, ta kasa cewa komai banda innalilahi wa.ina ilaihi raj.une, tana gannin kannin mijin nata a idannuwanta, Aba ya jima bai yi wani motsin kirki ba , har sai da abin ya fara basu tsoro , a hankali ya ce" Alaidine yaushe ya rasu ne? Alaidine ya sauke kansa kasa ya ce" Aba yanzu na tarar za.a yi sutura aka yi da ni sai bayan an gama ne na fahimci shi ne Mom ta dago da idannuwanta da suka yi jajajir ta ce" kai kuwa wa ya nuna maka gidan? Ya aka yi har kake zuwa? A ina ka san gidan? Ajiyar zuciya ya saki yana kallon mahaifinsa ya ce" Mom ai ina lekawa wani lokacin, nakan je na tsaya gefe guda dan gannin halin da suke ciki, to yauma na je ne na ga ana fitar da gawar Kanta ta mayar wajen Aba, a hankali ta sanyaya muryarta ta ce" Aba ka yi hakuri, ka yi masa adu.a sannan mu tafi mu yi masu gaisuwa Aba, dukan mai rai mamaci ne karka rike a ranka domin karka manta muma jiran tamu muke Aba ya sauke ajiyar zuciya yana kallonta, can ya ce" tabas *MARWA* na yi imanin wanda ya amshe shi ya fi ni son sa, abinda ya tsaye min a rai shi ne rashin lafiya ya yi? Ya adinninsa ya canza wasu halayan? Ya wajen yiwa iyayenmu biyaya ya daina taurin ran nan nasa? Shin yana tuna ni nima kamar yanda nake tuna shi duda bamu wani mugun shakuwa ba a lokacin har na bar gidan? Ina cike da zulumin mutuwar kanina ne, ina adu.a ne a kasan zuciyata kan Allah ya datar da shi, Allah ya karbi bakuncinsa, sannan inna koka ranar tawa mutuwar harma ina adu.ar Allah ubangiji ya sa ranar mutuwarmu ita ce ranar farin cikin mu, ranar shiga kabarin mu itace ranar hutun mu, A tare suke amsawa da amen ya rabeel Alamen Nisawa ya kuma yi ya ce" ba zamu tafi gidan ba Momyn yara, domin karki manta Abana yayi furucin idan har ya kuma ganin kafata kalata koma mai kama da ni sai ya tsine min Albarka sannan sai ya kwana sallah kan Allah ya yi mana hisabi idan har ba sakin ki na yi ba na dawo gare su a lokacin da kike cikin halin rayuwa sanadiyana, daga baya da na koma ya rantse cewar ya kare da ni ya cire ni a yayansa, Kawai zamu yi zaman mutuwar dan uwana a nan, mu yi masa adu.ar uku da na sati mu bi shi da adu.a sannan mu yi kokarin gyara namu zuwan, Allah ya sanyaya Yana gama fada ya ciciba ya mike ya haye sama da niyar shiga dakinsa Ajiyar zuciya Mom ta saki ta kashe Tv ta kirayi kaf mutanen gidan ta sanar da su cewar an yi rasuwa a yi kokari a samawa gidan nutsuwa na zaman makoki Sosai ake zaman makoki a gidan Aba, mutane da dama na zuwa yi masa ta.aziya, adu.a kam mamacin na shanta ta sosai da sosai, tun daga kofar gida wajen Aba har cikin gida wajen su Wujdane wa.inda suka bude tsantsar sauka a kulun ta Allah sukan yi sauka wa mamacin nan su yi masa adu.a a wuni zikiri ana hailala da kurhuwalahu ana nemawa mamata rahamar ubangiji ( ya Allah 😭, ina rokonta dan sunayanka tsarkaka, Allah dan girman zatinka Allah, idan wani ya ji labarin mutuwata ko a ina yake, Allah ka bashi ikon bina da adu.a sannan ka bashi ikon furta alkhairi a kaina da ni da dukan bawan da zai amsa da amen da kuluyin musulmi ya ziljalalu wal ikram 😭) Dalilin zaman nan da ake, sai ya kasance Alaidine kulun yana gida, da shi da Anwar da matar Anwar da yayansa, dama Jamail ba yauba yake kokarin kaurowa gaba dayansa Alawiya har zuwa wannan ranar bata zo ba, ta tsiro karyar cewa bata da lafiya hakan ya saka ya kyaleta bai takurata ba, idan ya fice a gidan ta mike ta shiga sabgar gabanta hankalinta konce a fili takan furta wani zaman makoki na kin Allah bayan mutanen ba wani sannin zamanku suka yi ba? Boy na wajen Wujdane, yaron yana matukar sonta domin tana kyautata masa, tana yi masa wanka ta saka masa sutura tsaftatatu, ta bashi abinci a baki ta bashi chocolate t goya shi a batanta du irin girman shi kuwa, ita haka kawai take jinsa a ranta, domin Huzaifa irin yaran nan ne masu shiga rai, cikin jikinsa yake bulbul da shi, ga kyau masha Allah sannan ya maida Wujdane tamkar mahaifiyarsa ko baci ya dauke shi ta shinfide shi yana farkawa sai ihun mama mama yana nemanta, haka yake kiranta da sunna Mama kamar yanda ya ji suna kiran Mom. Khadija ba yanda bata yi ba dan ta hana shi rabar jikin Wujdane aman matsalar ita bata iya rarashi ba, bata iya jan yaro ba sai dai da yayi abu ta duke masa baki ko hannu shi yasa sam ba wata shakuwa a tsakaninsu Yau da wuri Alaidine ya dawo gidan dan ya farka da wuri ya tafi wajen sadakar bakwai, Tunda ya dawo yake lure da taketaken Alawiya, kazar kazar dinta take sam ba wani alamar rashin lafiya a tatare da ita Da wuri ya konta baci abinsa bayan ya gama nafilfilunsa, sai dai mai yarinyar nan tana yawan fado masa a cikin idannuwansa koda idannuwansa a bude suke, haka ya kwana juyi yana jawa kansa tsaki yana jin haushin kansa, harma ya yiwa kansa tambayar wannan wani irin tashin hankali ne haka? Sai dai ba amsa Da safe yana fitowa Alawiya ta sha kwaliyarta tana zaune tana shan shayi, Tsayawa ya yi a kanta ya mika mata hijabi, fuska a tanke ya ce" yau ko mutuwa kike a hanya sai kin je wajen rasuwar kannin mahaifina, dan haka ki mike mu tafi Ranta a hade ta saka hijabin ta mike ta bi bayansa, idan ranta yayi dubu ya baci da wannan lamarin, dan me yake son takura mata a rayuwa ne? Haka har suka karaso kowane bai cewa dan uwansa ufan ba Aba mutum mai mutane, sosai kofar gidan ta cika da mutane , a haka ta ratsa ta shige shi kuwa ya ja ya tsaya Malan Mahaifin su Wujdane sai jero adu.o.i yake suna amsawa har aka gama aka wawatse Matan cikin gidan ne ke ta fitowa har ya kasance du an fito sai na gida kawai Mikewa yayi ya shige gidan, Matar Anwar ce zaune saman tabarma, gefenta Wujdane ce rungume da Huzaifa tana bashi madara a bakinsa sai Aisha dake zaune itama da carbi a hannunta tana ja suna dan taba hira tsakannin matar Anwar da Wujdane Dan tsai ya yi daga nesa yana kallonta, yanda Boy idan ta kai bakinta ya dan zubun mata a habarta zai lashe abinsa yanai mata daria idan kuwa ta hana shi lashewar sai ya fashe da kuka, Ajiyar zuciya ya saki a can kasan zuciyarsa ya ce" Alaidine, ka san cewar a duniya ka yiwa kanka hani da soyaya da wata diya mace , ba dan komai ba sai dan gudun ta san sirrinka ta yi maka gori harma ta guje maka, Alaidine yarinyar nan lale mace ce, ta isa mace, aman konciyar hankalinka shine mafi girman bukatarka, so ka kawar da kanka a lamarinta , ko ba wannan fa karka manta ko ita wacece? Fitsarariya ce, yarinyar da kanninka ya so tamkar ransa har suka shaku, yarinyar da ta watsa kanta a banza , so plz ka fitar da tunanin nan, ka watsar da shi ka rufe idannuwanka a kyanta domin kyan dan maciji ne.... Toh fa readers kun ji dalilin Alaidine...........,,,,........ ku kanku kun san irin fitsarar Wujdane, toh aman ai Woujdane ba jahila bace🤔 [2/1, 2:29 PM] Ummi Tandama.: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄 *28* WRINTING BY *SAJIDA* Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai, *SAJIDARKU CE* MARUBUCIYAR: *YAR MAHAUKACIYA* *DUK KARYAR KADA* *DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA* *NEMAN NA KAINA* ................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH.... Kokarin rabawa ta gefensu ya shige yake, muryar matar Anwar cikin girmamawa take gaishe shi Dan dakatawa yayi yana amsawa ya tambayeta yaran? Muryarsa da Boy ya ji ya saka shi dago da kansa, shi din ne kuwa sai bangalar dariya ya shiga kiran Dad dad dad Alaidine ma ido ya zuba masa, sai yake gannin yaron har kamar ya kara wata kiba yayi fresh da shi, Dukaws yayi wajensa a hankali ya kasance kafar Wujdane dake mike na kusa da shi, jikinta dake jikin bango a jingine na facing dinsa, Hancin Boy ya dan lakato ya ce" boy ka buya ko,? Kana ta shan dadinka baka bani ko? Boy yayi dariya abinsa, cokalin karshe ne ta debo a hannunta sai Boy ya karbe ya kai bakinta da niyar ta sha Wujdane ta dan kawar da kai tana nunin ta koshi, Firr Boy ya kiya yana neman fara yi masu balebale a dole ta dan buda bakinta ya lasa mata madarar , sauran da ta rage a cikin cokalin ya nufo bakin mahaifinsa da ita Ido Alaidine ya dan zaro, sauran bakinta ne Boy yake son sai ya sha? Shi mai ma ya tsayar da shi a wajen su ne? Shi ko ruwa ka sha ka rage baya sha dan mugun kyankyani, a rayuwarsa ko sauran bakin boy baya sha bale na wani, baya hada cokali, ko kofofin shan ruwansa ba.a tabawa dan baya hadawa da na kowa, sai gashi abinda ya cusawa Wujdane a baki ya ciro da yawunta a jiki Boy zai saka shi sha??? Da yannayin yiwa yaro dabara ya ce" Boy, u see bana iya sha yanzu, ka ajiye min ko ka bawa auntynka ni sai ka bani tomorrow ohk???? Kwabe fuska yaron yayi, niyarsa ya kwala ihun kukan domin har idannuwansa sun cika da kwala Da sauri ya kai hannunsa wajen cokalin na hannun Boy dan kokarin sakinsa yakeya zube sai dai a rashin sa.a ya ji ya dora saman hannun Wujdane wace itama ta kawo da niyar tarewar kar ya zube mata a jikin hijab A tare suka kali junna wanda a yauma abinda suka tsinta cikin kallon junna kennan, faduwar gaba... da sauri ya cire idannuwansa a kallonta ya yi gagawar kai cokalin bakinsa ya shanye yar madarar ya mike ya dauki Boy ya fada falo da sauri har yana dan waiwayen kofar dakin A hankali take janye kafafuwanta daga mikewan da ta yi, Matar Anwar ta saki murmushi, a fili ta ce" yanzu na yarda da maganar yayana(Anwar) Juyowa Wujdane ta yi tana kalonta da neman karin bayani, Ta maida hankalinta wajen Aisha ta ce" kanwata, ya zamu yi mu raba amaryar oga da miskilanci mu koya mata yawan magana ko zata kara damke mana oga??? Gaba daya kalonta suke kawai, domin dai ba abinda suka fahimta, Ta ci gaba da fadin" idan ana irin haka na tabata akoy ranar da zai kasa rike nasa sarautar, aman fa sai ta fara zubar da nata, matsalar a nan ita ce shin ana iya raba mutun da yannayin halitarsa? Aisha ta yi murmushi, ita kanta yannayinsu ya birge ta duda su suna kusa sosai suna jin du abinda ke faruwa sun san ba soyaya bane, aman na nesa ko kashe shi zaka yi ya ga wannan yannayin ba zai taba lamuntar cewar wai ba wata aba wai ita soyaya a tsakaninsu, sai maganar canza yannayin Wujdane AISHA ta nisa ta ce" toh kin san ana cewa ba abinda baya yiwuwa, aman abin da kamar wuya wai gurguwa da auren nesa, sai dai a gwada a ganni mai yiwuwa a dace Matar Anwar ta gyara zamanta ta ce" shin kun san wanene Alaidine kuwa? Yaya Alaidine ni dai a kusa kusan nan ban taba cin karo da mai irin halayensa ba, ai shi mutun ne m........ . ..................nan ta yi ta basu labarin Alaidine, yannayin rayuwarsa da yanda mijinta ke bata labarin irin murdiyarsa, da fannin kyankyaminsa da irin hasashen arzikinsa da yawan sadakarsa da rashin son raininsa da irin yanda yayi ta aure aure aman bata san dalilin rabuwarsa da matan ba, haka ta yi ta basu labari wanda Aisha ta mayar da hankalinta kacokam tana sauraro ita kuwa Wujdane sai ma ta kawar da kai gefe tana kallon tsakar gidan a kasan zuciyarta tana fadin sai me karma ya kula tan Sosai su Aisha suka dage suna tataunawa kan lamarin wanda Wujdane take jan carbinta , ita ganni take aikin yi ne basu da shi (jama.a mu yiwa kanmu da kyau, Malan liman na baba yake cewa" idan ka mutun malan zaka ga nan da nan an manta da kai, wasu cikin yayanka da kake kokarin tarawa duniyar har adu.a suke Allah ya kar giwa ko sa ci nama, kalilan daga cikinsu zasu yi ta kokarin yi maka adu.a a cikin salarsu da sun mike sun zubar da komai, zaka ga ana tashin hankali kan dukiyar da ka tara, sai ka ga wasu kafin a dauke gawarka ma zasu shiga labarin ankon wurin biki, maza kuwa su fara neman kayan shayi dan abin zama ya same su, dadayku ne ke zulumin idan ka je mai zaka tarar? Basu fi a kirga ba da zasu zubar da hawaye dan tausayinka da tausayin kansu, mahaifanka idan ka girmama su a tsayin rayuwarka zasu yi ta binka da adu.a harma ka ga idan mamanka na wani abin ta dakata tsam ta share hawaye idan ka fado mata a rai, idan ka kasance mai kyauta mai sadaka mai hakuri zaka ga al.umma na yabonka suna binka da adu.a, idan ka gina masalaci ko rijiya ko asibiti na taimako sunnanka na yawo a bakinsu zakai ta samun adu.a, ya Allah ka sa mu dace) Alaidine na shiga suka yi arba da Alawiya wace tamkar ta fashe, du abinda ya faru tana kallo kyar domin tunda ta zo hankalinta daman na kan Wujdane wace ta mugun tsoratata, bata taba hasasho kamanin wujdane din haka ba, ita bata ma yi tunanin cewar Wujdane din wai wata babar baby ce ba a tunaninta kawai Aban ne da rarume rarumensa ya kwasowa mijinta wata dan kawai a takura mata, a yanzu abinda idannuwanta suka gane mata tsakanin mijinta da Wujdane ya mugun girgiza mata zuciya, ita ba zata manta ranar da ta yi gigin saka cokalinta cikin abincinsa sai barin abincin yayi yana fadan ta saka masa yawu, aman yanzu daga bakin Wujdane din aka fitar da abin aman ya saka a nasa bakin Yannayinta ya kalla ya kawar da kai ya samu waje ya zauna , Mom ce da Alawiyar da Lami da Khadija sai yaran wajen Anwar a falon Ba wani hira suke ba ana dai zaunen ne mai jan carbi na yi mai dannan waya na yi yaran kuwa na wasan su Yana zama aka fara silalewa a hankali sai yayi sauran Mom da Khadija da Alawiya Boy ya lafe a jikin mahaifinsa yayi lamo abinsa Mom na yi masa magana aman yayi shiru bai motsa ba Alaidine ya ce" Boy Mom ne fa? Ka je tana kira ko? Mom ta yi murmushi ta ce" ai yanzu da Wujdane ce da kafin ta nema zai tafi wajenta idan ba ita ba sai Jamail sai ko kai yaro sai kiwiya *WUJDANE* sunnan da yake ta maimaitawa a kasan zuciyarsa kenan, Mom ta mike ta nufi kicin tana fadin" bara na samo maka dan abin tabawa Taba tafiya khadija ta mike itama ta nufi waje daga can baya wajen mahaifiyarta dake hutawa Alawiya ta ce" aman ni ita wannan din ko daman kuna soyaya da ita ne? Banza yayi mata dan bata wani nuna da shi take ba, sai da ta kuma kiran sunnansa ta maimaita tambayarta A hankali ya juya kalonsa waje, wannan lokacin Aisha na kyarawa Wujdane akaifunta na kafa ita kuwa matar anwar tanai mata hira haka kasa kasa ita kuwa tana murmushi, Murmushinta ya shagala kallo, yana haska mata fuskarta sosai Tsaki Alawiya ta ja mai zafi tana kallonsa ta ce " wannan wani irin wulakanci ne? Idannuwansa ya sauke kanta, shi take yiwa tsaki? Rainin nata har ya kai nan? A kasan zuciyarsa ya kudurta abinda zai yi mata dan gobe ko ance ta yi masa tsaki ba zata kwatanta ba, sannan ya yi kokarin farawa tun a lokacin, cike da yannayin cusa haushi ya ce" sai na ga kamar ta cancanci samun soyayar nawa? Suba fa ki ga idan tana murmushi yanda yake kawata fuskarta, komai ta yi yana fido ainahin kyanta da personality dinta, kina gannin yanda take birge mace ma bale ni namiji mai rai da lafiya? Kin san menene? Da ace zan samu soyayar nata ko da kinga yanda ake yi domin da alama ita kudina baya gabanta , da ace yana gabanta da ta yarje ta ci kudin ta ci wulakanci! Please wife ki tayani yakin soyayarta mana? ( aa fa Alaidine, kaja nufin ka fadi haka ne dan ka baiwa Alawiya haushi ko abinda ke kasan zuciyarka kake bayanawa a lokacin da baka shirya ba? 🤣) Tabas ya kuna Alawiya, ya cusa mata bakin cikin da yafi wanda ta cusa masa, ta yi data sannin yi masa wannan tambaya, ta ji haushin wannan rana gaba daya, tabas ta auri Alaidine ne dan arzikinsa, hakan ya saka ta toshe kunuwanta a irin abubuwan da aka ringa fada mata, ta aure shi take kuwa dangwalar arzikin, aman a yanzu zata iya rantsewa cewar tana jinsa har kasan zuciyarta, tana sonsa Alaidine ba wai kyau da arziki kadai ne ta tara ba aa namijin mazaje ne, gwarzo ne, namiji mai watsa taro ne, a yau ta fito da shi kadai ya isa ta karyar da zuciyar wasu yan matan, shi yasa ko yan gidansu bata son yana anfana ko yana yawan raba, sai dai abin damuwar bata isa ta saka shin ko ta hana shi ba, a tsaye yake yana aikata abinda yaga dama ne, kuma a irin yanda ta san labarinsa na sakin mata sai take gannin wautarsu , yaushe ita zata fada masa kalmar nan da zata rabata da ni.imar nan? Ai sai dai idan ciwon hauka take, yanzu haka ta sani sarai Khadija da taki aure dan kawai ta koma masa ne Mikewa ta yi ta nufi can ciki, zuciyarta tamkar ta fashe , kuka kawai take bukatar yi ko zata ji sasaucin damuwarta....... Ba su su bar gidan ba sai bayan salar isha.i, a yau dinma wata maganar kirki bata hada shi da Wujdane ba, ko gaisuwa bata hada su domin ita tana gannin ita ce mace, komai talaucinta komai irin auren da aka yi masu shi ya dace ya fara yi mata magana kafin take saukowa, shi kuwa yana gannin fitsarar tata tayi yawan da tana kallo kowa na gaishe shi ko ana tsoron yin wani abin idan yana nan aman ita bata wani damu ba ya zuba mata ido yaga iya inda girman kan nata ya kai ne? Bayan anyi adu.ar bakwai a kulun Mom zata yi iya rarashi dan Aba ya amince su tafi gida koda ita ce zata shiga shi ya tsaya a kofa sai ya nuna sam bai san zancen ba wannan abin na damunta sosai cikin ranta sannan tana yawan yiwa kanta tambayar shin mai yake kai Alaidine ne? Ko ya daina fushin da su????? Alaidine kuwa wajen satinsa biyu rabonsa da gidan, yana dai yawan haduwa da abansa yana kuma kiran Mom dinsa, ba dan komai ya kuma dauke kafarsa a gidansu ba sai dan ya sakawa kansa tsari, yana tsoron abinda zuciyarsa ke bijiro masa sosai yana mugun tsoron irin abinda ke kokarin tarwatsa tunaninsa yana jin haushin kansa da na Jamail domin da bai dauko maganar yarinyar nan ba da bata shigo gidansu ba da baima santa a rayuwa ba Shirye shiryen tarewar Aisha Mom take sosai wanda du wani abu mai mahinmanci idan aka yiwa Aisha sai an yiwa Wujdane, ita abubuwan shan birgeta ma suke dan irin zakinsu sai kawai ta daina wani kula abinci koda yaushe tana didikar tsumi Mom da kanta ke shafe su da madara peak sai ta bushe a jikinsu a wanke da ruwa mai dumi dumi sannan da dare a kuma hada na kwai a shafa masu da lemun tsami, haka fatarsu ke haske da santsi saima ta wujdane dama da santsinta sai abin ya karu sosai Fannin turaren wuta da na kulakca ba.a kama hannun yaro, Mom mutun ce mai son kulawa da jikinta hakan ya sa ta iya hade haden turaruka masu mahinmanci ga jikin mata, sosai ta koya masu zama cikin kanshi wanda ya zame masu jiki Jamail idan ya zo gidan nan yakan cika da mamakin yannayin aisha, gashi ta koyi wata kisa ta karfi da yaji ko magana za.a yi masa kalarta daban da yanda za.a yiwa wani, hakan na ruda shi yana bannin mom an gama gyara ta bashi matarsa mana? Hajiya Wujdane dama ba gwanar yawan magana ba, sai hakan ya hadu ya hade mata biyu ya kasance kamar da gangan take yin wasu abubuwan, wato sai kace wada aka sakata a makarantar koyon yanga da jan aji sannan abin yana hawanta sosai Gashinta tun ranta na kiyawa idan Mom tayi kiransu kan gyaran gashi har ya zame mata jiki, ita da kanta take zuwa ta zauna mom ta gyara mata tas sai bulbulan kanshi yake ta zo abinta, sannan Mom ta kwadaita mata yi masa ado kala daban daban ta fannin nuna mata a tv tashar larabawa da indiyawa masu kalar gashinta ta hana ta saka yambo Ido ne Mom ta kawo ta sakawa alaidine, jiran ranar da zata ga ya shigo gidan take sannan sam bata taba kawo masa maganar matarsa ba, tana jiran shi ya yi mata magana ne Yau ta kama alhamis, sauran kwana biyu kawai Aisha ta tare a gidanta, tunda safe direba ya kawo su gida Inna ta sha mamakin yayan nata, gaba daya sun canza mata, sai yannayin nutsuwar Wujdane harma ta fara tunanin ko ta daina fada????? Sun kusan wuni da mahaifiyarsu da mahaifinsu da yan uwansu, sosai inna ta kara yi masu nasiha na zaman duniya, Da zasu tafi kamar su yi kuka haka suka juya suka tafi ransu a bace ba dan sun so ba (Uwa mai dadi) Zaune take a guarding tunda suka dawo tayi tsai tana kallon tsuntsaye na shawagi a filin Ba wata salama ba sanar da isowa khadija ta zauna face dinta , ta ce" kina nan kina faman amsar shirye shiryen amare bayan baki ma san wa kika aura ba? Baki ma san wanene asalin Alaidine ba???? Dago da kanta ta yi, a duniya tana maraba da ranar da zata nunawa wannan mata ta fita iya rashin mutunci aman tana adanna ranar nan, mikewa ta yi da nufin barin mata wajen sai dai mai, abinda kunnenta ya jiyo mata ya tayar mata da hankali, ya firgitata, bata san lokacin da ta juyo da mugun firgici ba da muradin jin maimaicin kalmar da Khadija ta fada wada ta kunshi harufa biyar kawai aman ta tara dukan tashin hankalin duniyar, kalmar da idan har haka ne tana da ja da wannan aure, kalmar da idan dai haka ne tabas zata daina gannin girman matar gidan dama dukan wanda ya rabu gidan................... [2/1, 2:29 PM] Ummi Tandama.: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄 *29* WRINTING BY *SAJIDA* Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai, *SAJIDARKU CE* MARUBUCIYAR: *YAR MAHAUKACIYA* *DUK KARYAR KADA* *DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA* *NEMAN NA KAINA* ................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH.... Yannayin yanda Wujdane ta shiga lokaci guda sai ya baka mamaki, cike da tsoro ta ce' aman Khadija kin san girman furucinki kuwa? Kin san irin tarin tashin hankalin furucinki kuwa? Khadija ta kada kai ta ce" komai girmansa idan gaskiya ya kunsa ai ba damuwa ana iya furta shi koda a gaban sarki ne A hankali Wujdane ta kai kasa zaune, tunani ne barkatai a kwakwaluwarta, Gannin irin yanda take tasiri a Wujdane ya sakata gyara zama ta shiga fayacewa Wujdane cewa" *MIJINKI DA KIKE MURNAR AN AURA MAKI HAR KIKE WANI RAWAR KAI SHEGE NE, SIRRI NE DA AKE BOYEWA YAYAN MUTANE HAR SAI SUN JI SUN BAYANA BACIN RANSU SAI YA SAKE SU YA MAYAR DA SU KANANUWAN ZAWARAWA* Kina nufin shine dalilin sakin mata da yake??? Sannan daman ba su Mom ne iyayensa ba? Cewar Wujdane Sune kam, su suka haife shi, Mom dai da Aba, bakya mamakin ana zaman makokin mutumin da mu bamu ma san shi ba? Toh a gidannan Mom da Aba kawai suka sanshi, dan uwan Aban ne, tun lokacin da suka tafka abin kunyarsu family dinsu suka cire su a sahun yan gidan, ya kasance sun kore su kwata kwata, yanzu zaman da suke yawancin jama.a kallonsu kawai suke domin ba wani yarda aka yi da a yanzun ma zaman aure ne ya hada su ba, mai yiwuwa sauran yayan ma hakan ne wato *SHEGU* ne Tamkar ta watsa mata barkono haka take ji, gaba daya duniyar tayi mata zafi, zuciya da ba kashi ba har zuciyarta ta karaya, a hankali ta mike tana langi ta nufi falo, direct wajen Aisha ta nufa wato dakinta Tana zuwa ta zube jikin Aishar dake konce tana waya da Jamail Firgigit ta mike tana kalonta, tsoron yannayin da take ciki ya firgita Aisha, cike da tashin hankali ta kashe wayar ta kamo hannunta tana aikin tambayarta lafiya? Wujdane dai bata yi wani kuka ba, sannan bata bude kwayar idannuwanta ba saima yamutsa hannunta da take a cikin gashinta, a hankali ta ce" ni abinda nake son sani a nan shine, Malan ya sani? Idan kuwa Malan ya sani toh tabas zaman halal suke, toh aman kadara ce? Ina mai rokon Allah hakan ya kasance kadara a kansa, ace daga kansa basu kara wani ba, ina cike da zulumin abinda na tsinta a yau Aisha kanta ya shiga duhu, zama ta yi sosai tana fuskantar Wujdane, tausayin yayar tata ya cika mata zuciya, ace a rayuwa mutun damuwa na damunsa aman baya iya kuka? Cike da muryar lalashi ta ce" ki fadan damuwarki Aunty plz Sai da Wujdane ta sauke ajiyar zuciya ta labartawa Aisha abinda ya faru, Ita kanta ta kadu da jin wannan baban furucin, tabas wata maganar zata kasance gaskiya koda watar bata kasance gaskiyar ba, Waje ta samu ta zauna gefen Wujdane, hannunta ta kamo ta rike tana kallonta, ta jima a haka kafin ta ce" aunty, ni kuwa sai nake gannin kamar kin yi saurin karaya a irin hare haren da za.a iya kawo maki Wujdane ta ce" mai kike nufi? Aisha ta nisa ta ce" Aunty shin kin manta wacece Khadija a wajen aban Boy? Khadija ita ce matarsa da suka zauna zaman aure, wace suka samu karuwa da shi, rabuwa ta gita ta dawo zama a cikin gidan iyayensa, wa.inda suka yi mata rana suka ki bari ta wulakanta kamar yanda mahaifinta ya koreta, suka karbeta suke ciyar da ita suna shayar da ita suna tufatar da ita, take zaune taki kula kowane namiji tana jiran wannan bawa da ta sheganta a yanzu harma ta sheganta iyayensa ya dawo ya aureta, shin aunty wannan bai saka kin dasa ayar tambaya ba? Kallonta take cike da mamakin Aishar, sarai sai yanzu ta shiga yiwa kanta tamabayoyin irin haka, duda hakanan ta kaleta ta ce" kina nufin karya tayi kenan da ta sheganta shi? Aunty idan shegen nema shi sai me? Aunty a yau yannayin rayuwar gidannan zaki duba ki yarda cewa akoy tarbiya, akoy girmama juna da gannin mutuncin juna, aunty yau koda mijinki, wanda mahaifinmu ya zaba maki ya kasance shege ya zaki yi bayan ki karbe shi ki rungume shi , aunty koda shine mai tara shegun kina gannin kinada yanda zaki yi bayan adu.a da neman Allah subahanahu wata allah ya shirya? Ni na tabata koda sunnan da ta kieayeshi da shi hakane aunty kadara ce zata fadawa su Aban wanda mu din nan kai har mahaifiyarmu bata fi karfin Allah ya jarabceta da hakan ba, na san abin da tsoratarwa irin yanda ta baki labarin, aman aunty kin san wani abu? Yau koda harda yaya Jamail a haka ko, wly a lokacin zan rungumi abinna, dan nayi imanin nima ban fi karfin Allah ya jarabceni da hakan ba, sosai na yi mamakin yanda kika fada a tarkon wannan da kika zauna da ita kika ganne nufinta ta fitar da ke ne ita ta shiga aunty Gaba daya jikin Wujdane yayi sanyi, wani sabon tunani nema ya darsu a zuciyarta, a can kasan ranta take ayana tabas ita yanzu nema ta ji ya fara birge ta, domin idan har haka ne rayuwarsu kusan iri daya ce, shi ana takura masa ana zaginsa dan kadara ta kasance a kansa, ita kuwa jama.a sun mayar da ita aljannah dan halitarta, A hankali take hasasoshi a idannuwanta, ita kadai murmuahi ya kubce mata da ta tuna musanyar hararan da suke shi da ita Nan ta zauna tana tsara abubuwan da ita kadai ta barwa ranta Mom ce ta turo ta shigo dakin nasu da salama A tare suka amsa mata suna kalonta Mom ta ce" dakin naki na je bakya nan sai nace kawai kina nan, tashi ki shirya mi tafi wajen mijinki ashe a konce yake ba lafiya, tana gama fada ta juya ta fice a dakin Tsai Wujdane ta yi bayan ta fito a wanka tana kalon kayan da Aisha ta fitar mata, Lesh ne kalar tsanwa ruwan shukoki da ratsin farifari a jikinsa, sai mayafi fari kar mai duwatsu sai takalmi mai dan tudu da sarka da dan kunaye masu kyan gaske Da ido take binta, ta shiga gyara mata gashinta ta daure shi a tsakiya ta hade shi waje guda Fuskar Wujdane ta gyara mata dan daidai ba wani makup bane, girarta ta bi da ja gira maroon sai gashin idannuwanta da ta caje mata da maskara sai dan jan baki ta dan goga mata kadan, Wujdane bata yi yunkurin hanata ba, domin itama ta yi kudurta fara gabatar da nata kuduri, Riga da sket ne, suka bi jikinta luf sket din ya kamata sosai ya fitar da kirar jikinta haka rigar irin mai babar wuyan nan ce sai kuma hannayen na salak ne Bayan ta gama shiryawa Aisha ta kashe mata daurin dan kwali wanda ta dan ja shi baya kadan daga gaba ya fitar da kontacen gashin kanta sannan dunkulelen ya fito a tsakiya Nan ne Wujdane tace aa, gaskiya a rufe mata ko.ina aman Aisha ta dage da magiyar dan Allah karta taba Tafe take takalmin kafarta na bada dan kara kwas kwas kwas suka sauko da Aisha Mom ce zaune da Khadija sai labari Khadijar ke bata Gaban Khadija sai da ya yanke ya fadi tayi gagawar kawar da kanta a kallon Wujdane tana jin kanta ta muzanta, Mom kanta sai da ta yi mata adu.a a kasan zuciyarta Mikewa Mom ta yi, suka yi daga da Aisha wace ta saka hijabinta dan ta raka su itama, Wujdane na karshe Har zata fita ta dakata ta dawo wajen Khadija ta ce" ji mana Khadija ta dago tana kallonta, Wujdane ta ci gaba" dole na gode maki, domin kin taimake ni sosai, na so tafka asara na kin karbar mijina a tafin hannuna , aman a yau maganar da kika fada min ta ainahin shi din wanene sai na ji du duniyar nan bani da wanda zuciyata ta aminta da shi da na so shi irin *Alaidine* wato ni wujdane koda Alaidine aljani ne ina sonsa 🤪 Nafa yi yaji gaskiya, na yi yaji kila wa kala zan kamala 😏🙄🙄🙄🙄🙄, ance ❤😍 kadai nake da muradi? Ga na yau byby [2/1, 2:29 PM] Ummi Tandama.: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄 *30* WRINTING BY *SAJIDA* Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai, *SAJIDARKU CE* MARUBUCIYAR: *YAR MAHAUKACIYA* *DUK KARYAR KADA* *DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA* *NEMAN NA KAINA* ................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH.... I.m sorry plz wly biki muke Jansu direba ke yi sun yi shiru , Aisha ce a gaba Mom da Wujdane a baya, Tunani ne fal cikin zuciyar Wujdane na yanda zatana rama abubuwan da suke yi mata daga matar Alaidine har tsohuwar matarsa da shi din kansa, Wani murmushi ne ya subuce mata da ta tuna yanda fuskar khadija ta nuna firgici da kalamanta, ita kanta sai da ta ji maganar da ta fada wani banbarakwai da ita wai tana son Alaidine, Zata buga kwalon da suke bugawa ne, zata yi kokarin yin gem din, domin ta lura zama ne ake marar tsari, daga baya idan hankalin su innarta ya konta ta nemi sakinta a sawaka mata da irin rayuwar nan dan kuwa ita tun tana karama bata muradin cudanya da masu hannu da shuni dan ta rigaya ta hade su cewar basa kyautatawa talakawa basa mutunta talakawa A haka suka karaso gidan Alaidine, Ba aisha ba ita kanta sai da ta firgita, gaba daya ginnin irin ginnin nan ne na tsakiya shi ba a kasa ba shi ba a can sama ba, ana kiran gidan ne da gidan glasss, domin du rabin gidan glass ne, ta ko.ina kana iya kallon kanka dan kuwa ma.aikatan gidan suna yin aikinsu Mom ce a gaba sai su Wujdane na biye da ita, Jamail ne ya fito da gajeran wandonsa zai je gudu wajen motsa jiki na cikin gidan Da murmushinsa ya nufo su yana mai murnar ganninsu harda Aisharsa, Da Aisha da Wujdane gaba dayansu juya bayansu suka yi cike da tsoron ganninsa a haka domin kuwa su dai tunda suke basu taba gannin namiji baba haka da irin shigar nan, (zaku fada ne) Murmushi Mom ta yi, ta ce" ka ga malan tafi ka saka sutura mana ka sakan yayana jin kunyarka a haka Shima murmushin ya saki ya miko hannunsa wajen Aisha ya ce" madame zo mu tafi bangarena kafin su fito ko? Ai da sauri Aisha ta labe a bayan Mom harda rike hijabinta gam kamar wani dodo zai kamata Dariya yake sosai, ya koma bangarensa, a ransa shi dai yannayin tarbiyarsu na bashi sha.awa, Da kalo Alawiya ta bi shi, yana daria ta shiga tambayar kanta shi kuwa wannan dariyar menene yake haka? Kafin ta samu amsar tambayarta sai ga su mom din sun shigo gaba dayansu bayan sun yi salama Da ido kawai take binsu, irin kallon nan na an takura maka, wanda ya kashe su Wujdane da mamaki, wai mahaifiyar mijinka ne zata yi salama ka yi mata shiru, ta shigo ciki ka bita da kallon raini haka? Aa ya zaku shigo min gida har ku zarto min falo haka ba wani salama ba komai idan fa kuka tarar da abinda yafi kallon idannuwanku bayan kun san cikin gidana ne hakan na iya faruwa? Kamar an matseta ta shiga sakin zancen nan tana kallon Su Wujdane wato da su take banda Mom a tunaninta, Mom ta kada kai, bata ce da ita komai ba domin sam ta lura yarinyar bata da girmama mutane, sannan ai ta san sarai wscece Wujdane, idanma ta nuna an takura mata da zuwa gida ai yanzu gidan ba na ita kadai bane Wujdane wani malalacin murmushi ne ta sakar mata, bata da niyar tanka mata domin a gaban Mom suke, bata da niyar bata amsa a yanzu har sai ta karanci kalar nata rashin da.ar, Bayan Mom suka bi wace ta umarce su da hakan suka kama haurawa samA Da wata muguwar harara ta raka su, itama ta aniyar binsu saman wato bangaren Alaidine A nanma sun wanke isannuwansu da kallo , a falonsa yake, yana kwonce nan kasa saman capet din dakin mai ruwan ash color da bakibaki a jikin mai gashin mage Jikin dogon wando ne baki, irin na costume sai yar riga fara mai siririn hannu wace ta bayanar mai da damtsen hannunsa da rabi rabin fafadan kirjinsa , idan ka ganshi ba irin shigar nan sai ka sha mamakin irin yanda jikinsa yake Gefensa Boy ne da dan wandonsa ba riga yana ta bacinsa hankali konce Salamar Mom ce ta saka shi kokarin zaunawa yana amsa mata sannan ya mayar da hankalinsa kan kofar dan gannin Mom dinsa Maimakun Mom ta fara shigowa sai ta umarci Wujdane da ta fara shiga (tun farko Alawiya, rashin girmama girman mijinta da na sarakuwarta ya saka har Mom idan ta zo takan takawa da kanta ta haura wajen danta, a yau kuwa ta ja tunga ta tsaya ta tura Wujdane ne dan abubuwa biyu, na farko dai ta nunawa Alawiya dake tare da su irin kusanci mata da miji wanda a lokacin da yaronka yayi aure ya dace du wani abin da ya,shafe shi kafin kowa ya shiga ke matarsa kece farko, domin a yanzu a yannayin nan mai yiwuwa suturar jikinsa bai dace su shiga su tarar da shi a hakan ba, sai abu na gaba tana son shakuwa ta shiga tsakanin Wujdane da Alaidine ne) Fuska ta daure ta tsaya kan kofar danma kar Alawiyar ta shiga, domin a da can bata nuna damuwarta da hakan sai yanzu dan neman izgili A hankali ta tura kofar ta shiga da salama a bakinta, Dan dakatawa ta yi tana neman wanda ya amsa masu salamar sai dai bata ganshi ba domin sam bata kawo a ranta cewar zai konta a capet ba Juyawa ta yi ta duka ta bayar da kanta wajen kofa dan cire takalmin kafarta mai yar igiya siririya, Sai da ta gama cirewar ta mike a hankali ta juyo ta fara dan takawa tana mai kuma yin salama ta nufi capet dan ta zauna a tunaninta ko wani wajen ya shige ne? Kallonta kawai yake, a kasan zuciyarsa yana aiyana ta faru ta kare, wato ya guje mata dan kar ya ganta , yana jinyar fitsarariyar zuciyarsa yayi ya warke ya koma sabgogin gabansa sai gata ta zo wajensa, sannan ita fitinana harda juyawa ta nuno masa duwaiya dan ya ga tana da su(a tunaninka🤔😱?), shi a yau din nan, yarinyar nan ta gama firgita shi sannan ta bashi tsoro a lokacin da yake jin zuciyarsa na samun nutsuwa da alama daman itace damuwarsa wace take dauke masa baci yayi ta tunani a kan rayuwarta, wanda dalilin hakan ya je gidansu ya fi a kirga dan kawai ya san wacece ita? Me ta tagaza mai karfi haka da yake wargaza shi a hankali hankali? Idannuwanta ne suka sauka tsai cikin nasa, gabanta sai da ya yanke ya fadi ta yi gagawar juyar da kanta gefe domin idannuwanwa sun sauka tas a kan fafadan kirjinsa dake huci shi kadai Hannunta ta jimke dan kaduwar da ta yi, a ranta take ayana wai su basu da kunyar zama da kaya irin haka ne? Cike da rashin kunya ta ce" da Allah malan ka tashi ka saka sutura a jikinka da su Mom a kofa suna jira kar su gaji da zaman jiranka kai kuwa kana wani zaune da wasu kaya sai kace karuwin namiji🙆🏻‍♀😲😳 Alaidine jin magangannun nata yake tamkar a mafarki, tabas ya yarda yau da irin maganar da ake fada cewa mafadaciya ce bata da kunya dan akoy wani saurayi sale da ya tambaya kawai inane gidan su Wujdane,? Ai da ya takarkare ya fara yi masa zuba, domin ta taba wanka masa mari suka dambatu kuma shi yafi shan wahala, ya kara da fadin Wujdane Mama, banda yawo da masifa ma abinda take yi a rayuwa , harda rantsuwar yanzu haka yayi imanin wanda ya aureta ya kwashi masifa ne da kansa domin watarana idan ya yarda ya bata mata rai sai tayi masa lilis dan kowa a anguwar yana fadin tabas aljannu ne da ita masu saka mata karfin doki a jikinta (toh fa) Murmushi ya tsinci kansa da saki, ya mike a hankali yana takowa kusanta, du taku daya sai ya ayana irin kokarinta na ta kale shi ta tafka masa rashin kunya, Sai da ya zo daf da ita daga bayanta, yar ficik da ita idan suka jera, aman dan kokari ta iya buda fitsararen bakinta ta yi masa fitsara haka ko ji take Jamail ne? Wai karuwin namiji, bayan ita ce mai yawo? Tsahonsa ya rage, ya dora habarsa a daidai wuyanta inda sajensa yayi masauki a wuyanta da gefen fuskarta, a hankali yake dan goga sajen nasa yana shakar wani fitinanen kanshi dake dukan hancinsa , hannunsa a zagaye da jikinta ya riketa aman ba sosai ba Tsoro ne ya darsun mata lokaci guda jin wani abu na gugan fatar jikinta wanda bata taba jinsa haka tunda aka haifeta ba, da sauri ta kufce ta juyo da karfinta sai dai tana juyowar ta afka a cikin kirjinsa har sai da daurin dan kwalinta ya kufce ya fadi kasa, mayafinta daman ya jima da faduwa gashinta tufkar nan ta warware aman daurin mai kunce ba A hankali ta furta" innalilahi wa.ina ilaihi raj.une, A.uzubilahi minna shaidanin rajim Murmushi ya saki ya sasauta rikon da yayi mata, ai kuwa ta samu bakin magana ta dago kanta ido taf da kwala ta ce" meye wannan ? Me kake yi wannan? Idannuwansa ya kankance ya ce" karuwancin ne wai zan gwada maki Wujdane da ido ya raina fata ta janye jikinta a nasa ta ce" ka ga malan ni bana son salon iskancin nan............. Kafin Wujdane ta karasa maganarta sai jin wani dumi dumi ta yi a lebenta, wanda ta ji shi har cikin bakinta, Alaidine ne ya cafke bakinta da niyar ya hukunta yanda take kokarin yi masa rashin kunya gatsai gatsai haka , aman maimakun ya hukuntatan sai ya bige da bata wani zazafan kiss, wanda shi kansa bai taba sannin wai idan aka yi kissing din mace ana jin irin abinda yake ji a yanzu ba, bai taba kawowa ransa cewa just kissing zai hargitsa masa tunani ya rikita shi ba sai a yau, hannunsa na rawa ya saka ya talafe kanta , na damar kuwa ya rike bayanta ya matsota sosai jikinsa dan tana wutsil wutsil din kwatar kanta, a hankali ya........ 😳😳😳😳😳😳 ku ga du anyi zuru a ji yayi mai🤣🤣🤣🤣, naki din😎🤣🤣🤣 Shin Alaidine na kokarin fice gona da iri ne bayan ko nomata bai soma ba? Su Mom fa? Suna ina ne? Hajiya Wujdane sarakan fitsara ina bakin ya tafi ne???????????? [2/1, 2:30 PM] Ummi Tandama.: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄 *32* WRINTING BY *SAJIDA* Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai, *SAJIDARKU CE* MARUBUCIYAR: *YAR MAHAUKACIYA* *DUK KARYAR KADA* *DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA* *NEMAN NA KAINA* ................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH.... *ina barar adu.a bayin Allah , na gode* Kalar baya son rainin nan yayi da fuskarsa ya ce" mu tafi ka aje ni gidan Mom, na gaisheta na ga Boy Anwar ya mike ya shiga tatara kayan yayan nasa dangin su waya bai ce komai ba, can kasan zuciyarsa kuwa dariya na tukarsa yana ayana abubuwa da dama da ya ga sun canza a wajen yayan nasa a kasan ransa Shigowarsu gidan Mom gabansa ya yanke ya fadi, domin ya ga wani sabon babur a ajiye a nan daga an shigo toh aman bai saka komai a ransa ba sai sa ya hango Wujdane ta fito da gudu gudu ta nufo tsakar gidan da wata doguwar riga baka mai santsi a jikinta, garin gudun da take ya saka dan kwalinta ya fadi aman bata tsaya damar daukansa ba Lukman ne kamar yanda suka yi da Aba kan ya zo zai yi masa bayanin da zai saka shi kara gamsuwa ya yi amana da halin da yake ciki a yau ya shirya zuwan wanda ita bata san da zancen ba kwata kwata shi sin kansa bai san cewa wai a nan gidan take ba Tana zaune ta ga shigowarsa kamar a mafarki hakan ya tunzura zuciyarta ta mike ta nufo shi dan ta yi masa tas irin wulakancin da yayi mata domin ita rabonta da ta saka shi a ido tun aurensu sauran kwana uku gashi yanzu ya zo ya saka haka ta faru ta auri mutumin da bai san darajarta ba Shi dinma gidan yake karewa kalo, a kasan zuciyarsa yana aiyana lale Aisha ta shigo baban gida, yana kallon tsare tsaren gidan ya hangi budurwa na nufo wajensa da gudu gudu ko dan kwali babu a kanta hakan ya saka shi bada hankalinsa wajen daidai shigowar su Alaidine Tana isowa ta ja ta tsaya dan nesa kadan sa shi auka shiga aikawa juna da kallo, ita kallon haushi da tambayar abunda ya kawo shi gidan take shi kuwa kallon mamaki , soyaya kai harma da kokonton anya Wujdane dinsa ce? Hannunsa ya dago ya nunota cike da fara.a ya ce" WuWuWujdanena? Ke ce? Dan Allah ke ce? Daman Elhaj nan ya kawo min ke? Wujdane na daman kina raye? Daman ba.a yi maki aure ba yayanki yace na manta ki anyi maki aure? Daman na fada masa ko wa kike aure sai ya sake ki na auri abinna domin dan ni kadai aka halice ki Wujdane na, ni na san ba zaki taba mantawa da soyayarmu har ki auri wanina ba Anwar da ya lura da yannayin yayansa yayi kokarin bude motar dan ya karasa ya babala wannan mahaukacin da yake yiwa kallon bashi da hankali sannan ya kora Wujdane da har ta tsaya sauraron wani kato da aurenta ko shigar kirki babu a jikinta, aman mai sai Alaidine ya dakatar da shi Gaba daya jikinsa rawa yake, du irin sanyin ac din motar Anwar bai hana zufa karyo masa ba, a hankali ya bude motar ya fito ya dan matsa wajensu ya ja hannunsa ya harde a daidai kirjinsa ya tsurawa yannayin tsayuwarsu ido sannan yana iya jiyo abinda suke fada daga inda yake Wujdane ki amsa ni mana? Ina rokonki ki amsa ni Wujdane, 👏🏽 Lukman ya karasa da kalar tausayi yana kallon Wujdane da take jifansa da harara Cikin wata murya mai cike da takaici ta ce" Lukman, mai nayi maka a ranar nan? Abinda kawai nake son sani mai yayi zafi da ka so zubawa iyayena kasa a ido? Yanzun bai isheka ba ka biyo ni nan? Mai ka zo yi min a nan? Nan Lukman ya marairaicw murya ya ce" Wujdane ki gafarce ni, a wannan rana kadarata ce ta afka min, bani da sanin abinda zai faru sai ana sauran kwana biyu, an yi min aure da wata a gidanmu sannan an hana ni aurenki, ba yanda banyi ba dan su saurareni aman suka yi bilis da ni, Elhajin gidannan shi ya taushe ni harma na samu nutsuwa na tafi cike da kunyar malan, ashe ya kilace min ke a nan Wujdanena? Wani kallon sama da kasa ta bi shi da shi, ta ja uban tsaki ta ce" haka ne, an tarda su an fada masu Wujdane yar iska ce ko? An gargade su kar su yarda ka auri mai sifar aljannu ko? Lukman ni nayi imanin dama da wuya yan gidanku su soni aman banyi tunanin zaka shiga jikina haka sannan ka wulakantani ba, sai dai ka sani a yanzu ba wani abin da zai iya shiga tsakanina da kai domin an yi min aure, an aura min dan gidan Elhajin gidan nan dalilin da ya saka ka ganni a gidan, an aura min mijin da a duniyar nan ina gannin ina cikin mutanen da ya tsana, an aura min mijin da aka yi masa dole baya ra.ayin ganina baya maraba da ni, banyi tunanin mijin da zan zauna da shi zai kyamace ni ba, na dai yi tunanin dangin mijina aman a rayuwana na yau ina cikin gidan mahaifiyar mijin da aka aura min take sona tamkar yarta, aba na kulawa da rayuwana yan uwansa na mutunta ni, Lukman ba komai ka je Allah ya baka zaman lafiya da jakar matar da ka aura Tana gama fadan haka ta juya da nufin barin wajen, domin har ga Allah ita tana jin Lukman a ranta ko ba komai shine mutumin da ya jure haukanta harma ya saka tayi amana da shi Taku yayi da sauri ya riko hannunta ta baya, wanda ya saka numfashin Alaidine kusan daukewa, daman ya gama hawa caji tun daga yannayin bayannan Wujdane wa Lukman, somin shi ba abinda ya fahimta sai tsantsar soyaya a tsakaninsu wanda take jin haushin anki aura mata wanda take so a fahimtarsa sai maganar da tayi a dungule cewar ya gama jiga jikinta shi a nashi fasarar ya gama sanninta a ya mace zai guje ta, hankalin Alaidine ya kai kololuwar tashi da bacin irin yanda wannan garjejen kato ya tsaya gaban matar da take tasa ta suna yanai mata maganar soyaya harma tana nuna yannayin tayi missing din hakan Sai abinda ya tainke tunaninsa, ya tafi da lunfashinsa na seconni, ya rikita shi ya girgiza zuciyarsa , abinda idannuwansa suka gane masa Lukman ya riko hannun Wujdane a lokacin da take kokarin komawa ciki, Kafafuwansa ya daga bisa umarnin zuciyarsa, taku ne na gagawa irin kana jefa kafa ne a bisa umarnin zuciyarka, isannuwansa kyam a kan hannun nan na Lukman sa ya zama bakikirin a jikin lalausar farar fatar Wujdane Wujdane da mamaki da haushi haushi ta juyo ta daga hannunta na daman wanda ba shine Lukman ya rikw mata ba ta kawo hannun nata da zafin rai zata dauke Lukman da mari aman komai ya tsaya mata Sanadiyar mutumin da yake sakata faduwar gaba, wanda yake tsayar mata da tunani idan ya bukaci hakan har sai ta gama nasa tunanin, wanda tun ranar da ya dora lalausan lebensa saman nata da niyar hukuntata ya saka ta a tashin hankali, domin ko baci take sai tayi firgigit ta farka tana sauke ajiyar zuciya, hakanma ta dora a kan haushin Lukman ta ayana shi ya jaza mata wannan tashin hankali da ta tsinci kanta a ciki Aman a wannan lokaci ta kai iya kololuwar tsorata da yannayinsa, domin ido cikin ido yayi fixernta, da idannuwansa da suka yi jajajir tamkar gauta yake hukuntata, da tsatsauran kallon baki kyauta min ba, kin cuce ni, ni zaki kashe? Bakya tausaya min? Bakya sona? Wannan kazamin zai taba hannunki? Wani zaki saka a gonata? Mai ya fi ni? Yake jifanta da su wa.inda suka rufe da tsantsar soyayar da yake ji tun daga zuciyarsa tana watsa jini ko.ina tana gayatar balaki kala daban daban na tashin hankalin da zai zube masu, ta idannuwansa yake isar mata da sakon yau ta mutu ta lalace, ta idannuwansa ya gama kashe mata jiki da dukan wani inji mai aiki a cikin jikinta, tama kasa kwace hannun nata da ya rike sannan jikinta ya shiga saki kamar zata fadi a kan kafafuwanta, ta rasa kalon tsana take hange ko na tabacin zargin mazinaciyar da yake yi mata a kawayar idannuwansa Rigarsa ta saman costume dinsa wace yakan dauketa ne kawai sai idan zai shiga meeting harkar kasuwancinsa yake dora su saman chemise dinsa mai dogon hannu ya cire daga jikinsa ya karasa wajensu ya cire idannuwansa a cikin na Wujdane ya dawo da su saman hannun Lukman da yayi karkadaf ya rike yana musa cewar wai tana da aure Sai a lokacin Lukman ya lura da shi, gabansa ya yanke ya fadi , wannan ai Elhaji ne na sabon gari, wanda yake faman samun kayan wajensa tun bara har yanzu, sai dai yannayinsa ya tsoratar da shi, idannuwansa tamkar ba.a taba yin fari a cikinsu ba sannan gaba daya jijiyoyin jikinsa sun mimike ko ta jikin hannayen rigarsa ana gannin yanda suka yi birde birde da su yannayin bashi da nutsuwa a wannan lokacin, sai hannun Wujdane da ya ga ya bi da kallo wanda ya rike yana kokarin hana ta komawa ciki A hankali ya saki hannun nata, yana mai bin Alaidine da kalo Na zata Alaidine yayi masu a wannan lokaci, a lokacin da ake tunanin gannin mugumugun bacin ransa domin Anwar har ya gagauta fitowa cike da tsoron abinda yayan nasa zai iya aikatawa Lukman da Wujdane sai dai da mamakinsa rigar nan tasa da ya cire a hankali ya nufi kusan Wujdane sosai ya matse mata waje ya kamo hannunta ya saka mata rigar nan da tayi mata yawa sosai 👩🏻‍💼, ya saka hannunsa daidai gashin kanta ya shiga tatarawa yana kokarin labe mata su dan kar a ci gaba d kalonsu a haka, aman bai samu damar yi mata magana ba dan kuwa maganar ta makale masa a fatar baki Idan ya nuna ya san da mutun a wajen bayan wujdane toh tabas tiles din wajen zai yi magana, A hankali ya jawota jikinsa sosai ya kasance bugun zuciyarsu na dukan juna, bai daina hukuntata da kalon da ya narkar mata da zuciya ba har take jin kamar ta dora hannu bibiyu a kai tayi ta rusa ihu Jan hannun nata yayi ya nufi kofar baban falo da ita, bai ce mata kala ba, sai kara kare mata jiki da yake wanda ta gommace ya daketa da wannan shiru da yayi mata, sai a lokacin ta ga yannayin shigarta, rigar ta lafe mata sosai a jiki du wani waje mai motsi a jikinta da ta motsa yake motsawa har san pant dinta ta fitar, rigar nan irin ta ka sakawa mijinka ce da za.a yi mata gyaran jiki ya saka ta saka ta dan ko.ina na jikinta ake bi da kayan gyare gyare ana gyagyarata, sai ta jima a zaune kafin ta shiga wanka a nan ne ta hangi Lukman Suna shiga falon sai da ya karasa da ita har wajen kujerar nan baba ya zaunar da ita, tsugunawa yayi daidai guwarta ya dora hannunsa a habarta ya dan dago suka sauke kalon junansu a cikin idannuwansu, Ta faru ta kare take ayannawa ranta, wata irin guguwan abu take ji na taso mata wa dan uwa, bata taba tunanin zata tsinci kanta a irin wannan yannayi ba, a wannan lokaci muradinta shine su dawama a haka, bata son ko kuda ya rabu da shi, wani irin abu ne take ji gane da shi na muradin ya kasance nata ita daya, so take yayi mata masifa ya nuna bacin ransa a yannayin da ya same ta aman yayi shiru, so take ya nuna jin haushinsa aman ya dake, da ba dan idannuwansa da yannayin jikinsa da suka dan nuna wani abin yannayin bacin rai da sai ta fasa kukan cewa bai damu da ita ba, Kalon da ya kara yi mata a cikin kwayar idannuwansa yake aika mata da sakon zuciyarsa dan baya son ya buda bakinsa a lokacin yayi mata magana bai san abinda zai iya amayarwa ba, bai san yaya zaiyi furucinsa ba, yafi son ya koma wajen tsohon dan iskan saurayinta da ya saka Anwar ya tsare ya koya masa hankali kafin ta samu sauran bacin ran da zai rage, yana gudun fara sauke mata ya kara batawa kansa rai domin a yanda yake ji kamar idan ya bata mata ran shine zai shiga a wani tashin hankalin Sakin habar nata yayi ya mike a hankali ya juya da nufin barin falon Ido ta kwalalo, ta ji zuciyarta zata balo ta fito waje, bata tunanin zata iya kawar da kai ta barshi ya fice bata ji abinda ke ransa ba Da gudu gudu ta mike ta fada bayansa ta rukunkume shi ta baya ta makalkale shi kamar yanda zuciyarta ta umarceta da aikatawa Mutuwar tsaye yayi, kafafuwansa suka kasa daukansa, ya dan jima kafin ya banbare hannunta ya juyo da ita a hankali yana fuskantarta Yannayinta yake , a hankali ya banbare hannun nata da ta rike baya son yin magana ko kusa baya son tankawa Ba zaka yi min magana ba? Ba zaka yi min magana ba? Baka damu da koma mai zan aikata ba ko? Baka damu da abinda zan yi ba? Idan bai dameka ba danme zaka raba ni da Maso............ Bai barta ka kai aya da kiran wani masoyinta ba ya zabura ya jata kiiiii hannunsa a kan wuyanta ya kaita jikin garu ya bugata da zafin gaske sannan ya shake mata wuya dan ya tsayar da mumunan maganar da take son kara masa kan wanda ya gani, iya fita a hayacinsa kam ya fita ita kuwa kakari take taji shaka ta kasa kwatar kanta idannuwanta du sun firfito harda dan digon hawaye da ya tarun mata dayan hannunsa kuwa a daidai mazaunanta da ya fora ya kara hadeta da garun Cikin maganar da ya fizga da kyar yana kalon kwayar idannuwanta dake juyawa ya ce"":" 😕😟😟😟 sick😟😟😟😟 [2/1, 2:30 PM] Ummi Tandama.: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄 *31* WRINTING BY *SAJIDA* Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai, *SAJIDARKU CE* MARUBUCIYAR: *YAR MAHAUKACIYA* *DUK KARYAR KADA* *DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA* *NEMAN NA KAINA* ................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH.... A hankali ya shiga shafa bayanta, wanda zuciyarsa ce ke umartarsa da aikata hakan sai gangar jikinsa da ya bayana karara bukatar hakan, Kamar ana dukansa yaji ana dukan kofar, muryar Mom na fadin" Wujdane ko baki gansa bane? Ko ba lafiya ne? Firgigit ya saketa, ta yi baya luuuu zata fadi ya riko hannunta ya tsayar da ita, Kalon yannayinta yake ya ga du ta firgice tamkar ba ita ba, har yar zufazufa na karyo mata, bugun zuciyarta ya karu sosai, Idannuwansa ya lumshe a kasan zuciyarsa yana mai jin haushin kansa, shi da ya je da nufin hukuntata meye na wanin binta a sannu, ? Kai ya kada kasa kasa ya ce" na motsa maki jarabarki ko? An jima ba.a sadu ba? Idannuwanta kawai ta lumshe dan har wani zazabi zazabi yake neman rufeta na tsoro da rashin sabo da firgici, tana mamakin irin yanda ko yaya ya riketa bata iya katabus bata iya komai dan kwatar kanta, a hankali ya cikata, ya dan daga murya ya ce" Mom shigo bana, Yana gama fada ya juya da sauri ya shige dayan dakinsa ya fada bayi Da gudu gudu ta rarumi dan kwalinta da mayafinta, sai dai ina kafin ta daura a kanta su Mom din har sun shigo ita da Aisha harda Alawiya wace ta yi kiran wayar mamanta tace maza maza ta dawo karta bar su daga su sai shi Gaba dayansu tsayawa suka yi kallonta, du ta wani firgice, ita wata kunya ce ta kara kamata a kasan zuciyarta take ayana yanzu mai yiwiwa sun gane abinda yayi mata? Mom ta kawar da kanta ta karasa shiga, a kasan zuciyarta take ayana kaji min yaro da gulma kace baka so kuma kana nuna son? Hade fuska Wujdane ta yi sannan ta daura dan kwalin tamkar an kule kaya a kan nata, gashin ya fito ta waje sosai Aisha gumtse dariyarta ta yi, a kasan zuciyarta tana mamaki wai Wujdane ce kuwa? Ita kuwa Alawiya ranta ne ya baci domin da suka shigo ta ga jan baki a leben Wujdane yanzu kuwa babu shi tas Basu kai ga zama ba ya fito da doguwar riga a saman wandon jins, du dan ya boye abinda ke tona shi Da ido suka bi shi Alawiya da Mom, Alawiya ta hangi inda jan bakin Wujdane ya labe, sam bai wanku ba irin mai kama fatar nan ne, Mom kuwa kallon yannayin jikinasa ne take shi da ba lafiya dan ta ga ko zazabi ne? Aisha ce ta shiga gaishe shi, yana amsawa da kula ba wani shiru shiru, Kansa ya dago wajensu ya ce" meye du kuka yi cirko cirko ku zauna man? A kasan zuciyar Wujdane dauki ba dadi take da zuciyarta, tana antayawa zuciyar tata ashar tana jin haushin kanta, sai Allah ya isan da take isar masa na taba mata jiki da yayi bayan tana jifanta da maganar cewa tana bin maza, Ita kuwa Alawiya ta gama sarewa lamarinsa, yannayin idannuwansa kadai ta kala ta gane halin da yake ciki kawai sai ta juya da sauri ta koma bata yi masa magana ba A hankali Wujdane ta nemi wuri kasa ta rabe ta hade kafafuwanta tama kasa gaishe shin Yan tambayoyi Mom ke yi masa na rashin lafiyarsa ya maida hankali yana bata gamsashiyar amsa Mom ta ce" toh mai ya hana ka zuwa gida kwana biyu?? Shiru yayi na yan dakiku, a hankali ya sauke idannuwansa a kan Wujdane da ta sada kanta tana kara sakawa kanta nutsuwa, kallon kurullah yake yi mata , kalo ne na tantance wai da gaske dalilinta ya kasa komawa gidansu? Aman ina jaruntarsa ta tafi ne? Wannan kwailar? (🤔), Maimaita tambayar Mom ta yi bayan ta lura sarai da abinda yake, da sauri ya bata amsa da fadin " Mom aiki ne da yannayin jikin nawa Mom ta ce" haka ne, aman ka ringa lekawa kafin abanka ya gama yanke hukuncin gidan da zaku zaunan da matanka dan ka ga itama iyalinka ce tana da bukatar kulawarka Da sauri Wujdane ta ce" Mom Aa, Kalonta suke yanda ta yi maganar ta zazaro ido, sai kuma kunyar Mom din ta kamata, ta sada kanta kasa ta ce" Mom tunawa ne nayi ashe na yi dori a gida na manta saman gaz Mom ta yi murmushi ta ce" ai Lami na nan zata kula maki yar gidan Mom Ajiyar zuciya ta sauke tana kikifta ido, Alaidine kuwa da kyar ya rike dariyar da yake jin tana kokarin fito masa, bai san ya aka yi ba du abinda ta yi yake bashi sha.awa Aisha kanta mamaki yaki barinta, tsoro ne take hangowa a idannuwan Wujdane? Wai Wujdane dinta ce kuwa ko sun baro tatan a gida? Wujdane dai Wujdane? Jamail ne yayi salama ya shigo, ya saka manyan kaya sai kanshi yake abinsa, ya gaisar da yayansa wanda ya bi shi da kallon mamaki, shi har yanzu mamaki Jamail ke bashi just 23 aman ya sakawa kansa fitina irin haka Ku tashi mu tafi xan mu yi jiran Mom ko? Jamail ya fada yana kallon su Wujdane Ai kamar jira take ta mike da sauri tana kara yafa mayafinta sosai a jikinta, suka kama hanyar fita ita da aisha Kamar daga sama Alaidine ya ce" ki rufe gashinki da kyau Yi tayi kamar bata ji shi ba ta karawa kanta mai ta fice a dakin tana sakin ajiyar zuciya Kwafa yayi yana jin haushin kin rufe kan da ta yi ya juyo Wajen Mom dake kallon diramar su Mom ta ce" Alaidine, da ka je ranar da abanka karami ya rasu wa da wa ka gani? Shiru yayi yana kallonta, baiwar allah du tsayin lokacin nan da iyayenta suka barta suka koreta dan kadara ta afka mata a kulun tana son jin labarinsu, tana farin cikin jin suna lafiya, tana mutuwar son saka su a idannuwanta, ajiyar zuciya ya sauke ba dan komai yake zuwa wajen nan ba sai dan mamansa, dan ya rage mata abinda ke damunta a rayuwa, a hankali ya ce" kamarku daya, duda ta tsufa ba sosai ba aman har yanzu da an ganta an san ita ta haife ki, shi kuwa haskensa kika yi da idannuwansa, daga nesa na hange su da farko ya kasa shiga gidan mutuwar da ta fito ta kama hannunsa sai suka tafi, Kana nufin da gaske Abanna ya tafi wajen rasuwar? Mom ta jefo masa tambaya Maimakun ya amsa mata sai ya yi dan baya da bayansa, zuciyarsa ta kama yi masa zafi, a yanzunma wani tashin hankalin ne ya darsun masa, ba komai bane sai tunanin idan har ya kara shiga jikin yarinyar nan ya rayuwarsa zata kasance? Idan har ta san ko shi wanene ta guje shi fa? A hankali ya lashi lebensa da har yanzu da jan bakinta a jiki radau ya juyo wajen Mamansa ya ce" ki ci gaba da adu.a zasu yafe maki nan kusa Mom, idanma suka ce sai na mutu zasu karbeki ki sani a shirye nake da komai dan su karbe kin, Wata irin zabura ta yi tana kalonsa, Tabas Alaidine ya fito a irin hanyar nan aman cikin ikon Allah sai Allah ya zuba mata wata irin kaunarsa ta da da mahaifi wace bata yiwa sauran yayanta, yakan bata tsoro sau tari idan yayi wani furucin, ajiyar zuciya ta sauke ta ce" du abin ba zai kai nan ba, tunda na jure tun baka kai mutun ba ban zubar ba, na haife ka na raini abina ba zan taba yarda na aikata laifi biyu ba, wanda na aikata ina cikin rokon Allah kan ya yafe min, ina kauracewa duk hanyar da zata mayar da ni sannan ina rokon allah da ya sansaya zuciyar iyayena, domin fushin zuciya suka yi tun da farko irin ka tarbiyantar da yaronka ne ya bilo maka da haka, aman ni nayi imanin Allah zai karbi tubana Murmushi ya sakarwa mamansa, ba dan komai ba sai dan kar ta rike yannayin fuskarsa a idannuwanta, Haka suka yi ta tataunawa tsakaninsu har ta mike tana fadin bara su koma gida ta bar yayanta na jiranta Har sun kusan fita a falon nasa ya ce" Mom Ta dakata tana kalonsa yayi tsai, can ya sauke ajoyar zuciya ya ce" ki taya ni da adu.a Mom Allah ya yaye min damuwata plz Cikin yannayin damuwa ta ce" Son mai ke damunka? Murmushi ya saki ya ce" Mom kawai rayuwar yau da kulun ce Ajiyar zuciya ta sauke ta ce" Allah ya sanyaya, ya iye mana abinda ba zamu iya ba, ya shige mana gaba Ya amsa suka fito ya rakota har wajen da su Jamail suke ta mikawa Wujdane Boy dake baci abinsa dan tace sai sun tafi da shi, Sam bai samu ko kalonsa wujdane ta yi ba sai wani kakauda kai take du iya son su hada idon da ya so ko dan ya kali kwayar idannuwan nan nata aman ta kawar da kanta gefe Aisha ta yi masa fatan kara samun karfin jikinsa, ya dan yi mata murmushi yana tsaye har suka fita a gidan Juyowa yayi ya koma dakinsa sai dai yana zuwa ya tarar Alawiya zaune a falonsa tana jiransa, Kalonta yake guguwar wutar sha.awarsa na ruruwa na ingiza shi wa ita Ranta a bace ta ce" yanzu fisabililahi ba zaku bari har ta taren ba ya zamo har gida zatana tardo ka ana kawota dan ka neme ta? Ko ciki kake so ne ni har yanzu ban samu ba? Ban kai mafe bane ni da zakana hangen wata? Danme ba zata tare ta zo mu jera ba sai dai a ringa yawo ana kawo min karuwanci har cikin gida? Zama yayi yana mai cire jalabiyarsa kamar ba zai yi mata magana ba , sai can ya ce" kin tabata kuwa kin karbi cikin da kyau? Dan kin ga Boy ya warware yana bukatar abokin wasa , nima ina matukar son yaya ke kuwa kin ki yarda ki dauka ko dai kina tsoron wani abin ne? Mai zan ji tsoro? Ni bana jin tsoron komai ko a cikin raina ciki dai ne bai shige ni ba kuma ba ni zan baiwa kaina ba, Kare mata kallo yake, Alawiya akoy kyau sosai da sosai, aman ya rasa mai yasa Wujdane ke fizgarsa A hankali ya mika hannu ya jawota jikinsa, ya shiga lalubarta Sosai Alawiya ke son romance aman tana tsoron ogan, a hankali ya karewa bakinta kallo yana ayana Allah ya sa ya ji abinda ya ji a na Wujdane, bakinsa ya kai da niyar kissing dinta, har ya hade ya fara kissing din yana neman dole dole sai ya ji abinda ya ji a na Wujdane ta kwace kanta ta ce" ko jan bakin da ka shanye nata baka goge ba zaka wani shafa min? Kansa ya dan kawar kadan domin idan kana daf da ita ta yi magana bakinta na bugawa, kuma ba wani rashin lafiya bane kawai brush daya take yi sannan ita ba wata dabara na cin yar cingam ba ba wani magana take da mutane a gidan ba, sannan ba dabarar idan zata gana da miji ta yi gagawar tsaftace shi ba, kwaliyar dai aka iya Kokarin ci gaba da yi masa jayayar take ya ki kula ta ya daneta hakan ba wani romance ya shiga kokarin samawa kansa nutsuwa na wannan fitinaniyar yarinyar da ta rikita masa yannayi daga zuwa Yau kwana uku kennan da barin gidan da su Mom suka zo ganninsa, zaune yake wajen aiki yana ta saka hannu a takardun kasuwancinsa yana kara bin harakokinsa da takardu da computer yana ka.ide du abinda baya zuwar masa a yanda yake muradi, Yana tsakar yin aikin yana duba wani ciniki da aka yi mai yawan gaske, wani kanfani ne a dubay da sunnan Wujdane, Tsai yayi yana kallon sunnan yana mamaki, a hankali ya shiga tarihin kanfannin nan yayi arba da masu kanfanin, larabawa ne sak, sannan sunan kanfanin sunan kakarsu ne wato wujdane A hankali ya dora kan hoton kakar tasu, yar tsohuwa jagwab da shigar abaya da gilashin ganni na ido, ta yane kanta da bakin mayafin masha Allah da ita, Haka kawai ya tsinci kansa da sakin murmushi yana ayanna irin tsufan wUjdane a zuciyarsa, jwata kwata ma shi ya saki layin aikin da yake ya koma wani layin yana aikin murmushi Knocking n ake a kofar wanda ya saka shi bai rufe wajen da yake karantawa ba ya dana kofar ta budu aka shigo Anwar ne ya biyo ganninsa dan ya kwana biyu bai ganshi ba ya biyo daga wajen aiki, Zama yayi suka gaisa yana tambayarsa yara shi kuwa yana bashi amsa Hannunsa ya mika gannin hoton tsohuwa a jikin computer yana fadin brother wannan fa wacece? Karantawa yayi ya ga sunnan Wujdane, a hankali ya dago yana kallon yayan nasa ya ce" cip, sunnan yar gidan Mom, aman ya ka ga tsufan wujdane rigima wayo bakin ko ci baba za.a yi da turo shi? Murmushi ya saki shima ya ce" no zuwa lokacin zata daina turo bakin domin zan ha.......... Shiru yayi jin abinda yake shirin fadi, sai a lokacin ya ankara dama maganar wa ake, kicin kicin yayo da fuskarsa ya sako kalar baya son raini ya ce""""..... 🤣 [2/1, 2:30 PM] Ummi Tandama.: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄 *34* WRINTING BY *SAJIDA* Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai, *SAJIDARKU CE* MARUBUCIYAR: *YAR MAHAUKACIYA* *DUK KARYAR KADA* *DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA* *NEMAN NA KAINA* ................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH.... Idannuwansa ya rufe ruf a fili ya furta" *Ya Rab* Muryarsa da ta ji ya sakata dago da kanta da sauri, wani tsoro da kunya ne suka rufo mata lokaci guda, ta yi gagawar rarumar blanket din saman bed din ta saki towel din ta shiga nadisiye jikinta a cikin blanket din, Jikinta kansa rawa take, ita sai ta rantse ko murzar nan da ake mata sai an sha darga a murza mata bayanta aman kirjinta da cinyoyinta ita ke murza abinta, ita ko mahaifiyarta ta jima rabonta da gannin tsiraicinta sai ga wannan bahugumen mutumin da ya gama gana mata wahala a kasa ya tarar da ita a wannan yannayin Ido ta bude cike da tsiwa ta sauke su saman kansa ta ce" Malan mai ya kawo ka dakina? Ko salon ka nemi fitina ne? Kai wai ni maima na yi maka ne? Auren nan da kake gannin anyi maka dole garama kai ka shaida ni, ni sai da Aba na gidan nan ya gwada min cewa kai aka aura min kaga kuwa kamar yanda kake ikirarin anyi maka dole nima hakannan ne, so please ka daina zuwa inda na......... Shiru ta yi ganninsa a gabanta yana kalonta, bakinta kawai yake kallo yanda ta bude shi take zazaga masa rashin kunya sai kace wani sa.anta wai harda cewa anyi mata dole aure da shi Tsaki ya ja ya ce" sai ki karasa rashin kunyar ko? Kanta ta sada kasa, ita ta rasa gane dalilin da ta saka wannan bawan Allah idan dai waje ya matse masu take shayinsa, tana mugun tsoron abinda zai iya yi mata tun ranar da ya tsotse mata baki, sannan a yanzu sai take jin hucin jikinsa tamkar zafi hakan ya kara kashe mata baki kawai a kasan zuciyarta take aiyana muguntar da zata aikata masa idan har ya yarda ya kuma yi mata irin abinda ya yi matan nan Ke yanzu idan ba rashin kunya da tayi maki kaura ba, dan kin ganni a dakin nan ai kin san da dalili, dalilin kuwa kin san ba dan na kali wannan kwailan jikin naki bane, dan haka ki kiyaye dan ya ruda wasu bai zama lale ya isheni kalo ba Yana gama fada ya karasa wajen miroir ya shiga bale botiran rigarsa, Sai da ya bale su gaba daya ya juyo dan daukan towel Da sauri ta sada kanta kasa tana ayana kunya cema ba a tsarinsa ba domin bashi da kunyar tsayuwa a gabanta a irin wannan yannayin Ta gefenta ya bi ya fice batan ya yar mata da rigar a nan saman bed dinta ya shige bayinta Da mamaki ta raka shi da kalo, a kasan zuciyarta take tambayar kanta mai hakan ke nufi? Mai zaiyi mata a bayi? Du bayin cikin gidan nan ya rasa na shiga sai wannan? Tsaki ta ja a fili ta ce" can da masifarka, wai a haka ne khadija ke kishinsa ke haukan son sa bata san irin muguntarsa bane (🤔) Da sauri ta zura doguwar riga ko pant bata saka ba ta dauki zumbulelen hijabinta ta kabarta sallah dan gabatar da shafa.i da wuturi Tana salamcewa ta zauna tana dan jan carbinta ya fito daga shi sai towel din nan, shi dinma daidai kugunda kawai ya daure shi hakan ya baiwa jikinsa tun daga wajen cibiyarsa har saman kirjinsa damar fitowa a fili A hankali ta dago da kanta dan jin motsinsa wajen turarukanta, ai bata san lokacin da ta mike tsaye jikinta gaba daya na wata irin rawa ba Hannunta ta nuno wajensa da niyar yin magana sai ta ga inna ba zata iya ba , da sauri ta juya dan barin dakin Du saurinta sai ta yi a tafke ta, jikinsa da danshi danshin ruwa da kanshin sabulun wanka da turaren da ya garwaye mai sanyin kanshi suka hade.suka gogi fatar hannayenta dake waje Bata ankara ba ta ji ya dauketa sama ya nufi bed dinta da ita Shinfideta yayi ta zabura da niyar barin wajen aman kafin ta mike ya mayar da ita da hannunsa na dama , idannuwansa ya sauke saman kanta yanda take kokarin shake kanta cikin hijabinta, a hankali ya ce" ki nustu mana Wujdane Dago da kanta ta yi, ta sauke kwayar nata idannuwan a kan fuskarsa, wani irin kwarjini ya kara yi mata sannan ya mugun yi mata kyau a idannuwanta, dan bakinta ta murmusa tana kallon idannuwansa wanda hakan ya tsoratar da shi, bai yi tunanin zata yi murmushi ba a tsiwarta Ajiyar zuciya ya saki irin yanda Ta yi wani irin kyau da tayi murmushin, yatsarsa mai bima baba ya dora a hankali saman lebenta ya dan zagaya da su, a ransa yana ayana *da ace ina da cikenken yanci, da ace nima mai yanci ne, da ace ina iya tunkaho da ni kaina, da ace na malaki yanci irin na yayan halak da na mayar da ke ni, ni ke, da na shayar da ke zuman soyayata da na nuna maki irin yanda nake tsananin sonki, nake matukar kishinki, nake muradinki domin Wujdanena ke ce macen da ta yi nasarar sakani fadawa a tarkon soyaya du irin lokacin da na dauka ina hana kaina hakan, sai da kika shiga zuciyata a lokacin da bani da tsumi bale dabara kika hadasa min rayuwa da soyayarki, Wujdane ina tsoron ranar da zaki ji ainahin ko ni wanene ki guje ni ko ki yi jifana da kalon kyama* Kamar an zungurinshi yayi gagawar barin kusanta ya shiga mayar da kayansa cikin wani irin sauri ya juya , har ya kusan fita a dakin ya dakata ya juyo yana kalonta, dan murmushi ya sakar mata ya ce" good night Wujdane Bai tsaya jin amsarta ba ya fice da sauri ya fada dakin Mom dinsa ya je direct wajen doguwar kujera ya fada ya rike kansa dake yi masa wani irin nauyi a hankali hawaye ya shiga ziraro masa mai zafin gaske, a fili ya shiga fadin" danme, danme zaki shiga zuciyata? Baki san cewa na hana kaina soyaya bane? Baki da labarin ina tsoron yin soyaya dan gudun wulakanci bane? WUJDANE *ina sonki* kamar na mutu sannan ina tsoronki kamar na mutu, just kalonki ina neman fita a hayacina taba jikinki na kawar da ni daga tunanina, Wujdane ki rage kaimin rikita min zuciya, idan kika bi ni a hankali ma nayi imanin watarana zan gaza balatana a yanda kike gudu wajen kanainaye dukan zuciyata, Wujdane nakan ji tsanarki da tsanar du wani namiji da kika taba burgewa ciki harda kanina, ina jin baushinki a du lokacin da na tuna ke baki ma san ina yi ba, sai dai tausayinki na rufe min zuciya idan na tuna idan dai ina raye ina shakar iskar duniya kin gama da wani namijin sannan ni ba zan iya biya maki bukatarki ba, My Wujdane nufina *u,r Mine*, zan kin zama yar kasona, domin irin yanda ke kike bi da zuciyata na san zan mutu ne nan ba da jimawa ba Haka yayi ta sambatu tun yana gane abinda yake har wani baci baci suma suma suka dauke shi irin bacin nan mai cike da zazafan zazabi da ciwon kai da cushewar zuciya wanda kana yinsa baka san a sama kake ko a kasa ba *MARWA, MARWA, MARWA* ki saurare ni mana, tun rasuwar abanna na rasa gane kanki Marwa, danme kike guduna idan inai maki magana sai ki yi kamar kin ga dodo ki kama waiwayan baya da gaba? Dakatawa Marwa ta yi, da ledarta da ta sayo manta a kanti, gabanta na faduwa ta zubawa *Abdul kadre* ido tana kalonsa, ta sani Allah ya jarabeta da son sa aman idan ta tuna hudubar mamanta sai ta ji du ya fice mata a rai, sannan kakarta tana yanwan yi mata fada da harkar samari, uwa uba wani lokaci kakansa *Elhaj Abdallah* ya taba yin wata magana a gabanta wanda ya tsoratata inda yake fadinai idan dai mai sunnanta zata biyo anyi halin banza, shima sai yayi kokari ya maimaita tarihi idan yayi halin mai sunnansa dan haka shi ba zai shiga ba a dawo ace laifinsa ne shi ya hana aman ya sani koda ya nace mata toh ya jawa kansa abin kunya ne Kanta ta sada murya kasa kasa ta ce" Abanmu ya aiko ni wajen kaka wato *Ehaj Muhammad*, yana kofan gida yana jirana ka yi hakuri Aman ai kin san Aban ya san muna tare da ke ko? ABDUL KADRE ya fada yana faman tsayar da ita Ju Uyowa ta yi ta hade rai ta ce" ka ga malan ka yi hakuri kawai, ai a gabanka aka kwatanta tafiyarmu ba mai yiwuwa bace, koda ban san takamaiman gaskiyar abinda ya faru da yayar Mamana ba hakan bai zama dole na yarda da fadar mutane ba, a kulun kamar yanda mamana ke adu.ar Allah ya bayana mata da yayarta nima haka nake yi ko na samu nima Mama ta biyu mai sunana, dan haka ka yi hakuri Saima ta daina yunkurin karasawa gidan kakanin nata ta juya kawai ta tsayar da dan adaidaita ta yi masa kwatancen gidansu unguwar Hotoro A bakin layi ya ajiyeta ta sauka ta bashi kudinsa ta shiga takawa cikin nutsuwa dan karasawa gida Ja tayi ta tsaya tana kallon kofar gidan amaryar unguwarsu wace ake ta fadin kirkinta, yama ce dai dare bai yi ba sosai aman ba mutane sosai dan wasun basu sauko daga kasuwa ba yawanci kuma yara du ana makarantar islamiya sai daidaiku A hankali ta shiga konkwasa kofar Mai gadi ya leko, gannin yar budurwa ya bude yana tambayarta ko wa take nema? Marwa ta ce" wajen Hajiya aka aiko ni Mai gadi na jin haka ya bata waje yayi mata nuni da inda zata nufa dan gannin hajiyar *Aisha* na kokarin jera kayan abinci a saman table , gefenta *JAMAIL* ne yana amsa waya sannan yana binta da kalo du inda ta yi, suka ji ana konkwasa dakin A tare suka kali juna dan ana iya hangen mai konkwasawar ita dai ce bata iya gannin mutanen cikin Kai Jamail ya dafe ya ce" ni kam na rasa cikin ji da ke wa yafi wani farin jinnin jajibar mutane, tunda safe aikin da ake kennan a gidan nan , sai shigowa yan anguwa suke, gaskiya zan dauke ki mu yi tafiyarmu mu huta ko na canza anguwa Murmushi ta saki tana gyara hijabinta ta nufi kofar dan budewa domin haka suke idan namiji ne shi ke tafiya ya bude idan kuwa macece komai kankartarta ita ke budewa , ta ce" kai Hubby ka sanfa yanda amarya keda farin jinni, ai da an kwana biyu zaka ga an rage daga baya ma a daina shigowar sai kuma idan ni ina da zumunci sai na kara tarawa kaina mutanen, Binta yayi da kalo har ta bude tana amsa gaisuwar Marwa Jamail dake zaune yayi gagawar dago da kansa dan haka kawai ya tsinci wata faduwar gaba daidai lokacin Aisha ta baiwa Marwa waje tana fadin" *aa ki shigo mana ai ba komai*............ Shin masu karatu suna biye da ni kuwa? Wa ya gane wacece maman Marwa? [2/1, 2:30 PM] Ummi Tandama.: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄 *33* WRINTING BY *SAJIDA* Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai, *SAJIDARKU CE* MARUBUCIYAR: *YAR MAHAUKACIYA* *DUK KARYAR KADA* *DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA* *NEMAN NA KAINA* ................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH.... Ya ce" mai kike son ji? Kina son sannin idan har na damu da wulakanta aurenki da kike yi ne ko kina son sannin idan saurayinki da kuka gama watsewa ya cika namiji? Kina so a yaba salon tsagerancin iskancinku ne na tsalake titi da yawon banza a dawo cikin gida, gidana na aure da igiyar aurena a kanki ya biyo ki a gaban idannuwan masu aiki da direbobi ya kuma kama jikinki a yannayin talar masa da kika yi? Ko kina so ki tabatar min da tsohon dan iskanki cikeken fitsararen namiji ne? Yakan mantar da ke duniyar sa kike idan ya..... Ya tsayar da maganar ya bi jikinta da kalo, ya sasauta rikon wuyan nata karshema ya cika mata wuyan wanda yayi jajajir har fuskarta suka hade suka dan haye , aman bai matsa daga kurace mata wajen da yayi ba, idannuwanta a lumshe tana yannayin tashin hankali aman wani irin kyau da haske da take yi masa a idannuwansa sannan numfashinta idan ta fitar shi yake shaka itama tana shakan nasa mai cike da kanshin cingam da ya dan tauna a office Yatsarsa mai bima baba ya dora a gefen kuncinta na dama, a hankali ya shafo har wajen habarta, lebenta ya tsurawa ido bugun zuciyarsa na tsannanta haushinta da soyayarta suna daukaka a zuciyarsa, a fili sannan kasa kasa ya furta" *Koda zamana da ke bai yi nisa ba, na yi maki alkawarin zuciyarki bata da masaukin kowa sai nawa, sannan daga wannan rana koda zaki mutu da bukatar wani namijin koda ni ne, domin baki kai girman ko darajar da zan yi taraya da kazamin jikinkin nan ba, kuma kinyi bankwana da wani sai dai idan bana numfashi a doron kasa jikinki wani dan iskan ya gama taba shi, ke duniyata ce wace nake da iko da ita sannan zan horata na kin yin shuka sma cikinta, ni masaukinki ne wanda du bukatarki ta duniya zaki iya zube min aman banda ta dalilin da ya saka ba zan rabe ki ba, da a ce zan iya kalon jikinki da zamu gwada ni da mazan da kuka gama watsewarku wa ya fi iya buga kwallon, ki tafi ki yi kukan rabuwa da duniyar...........wife!*! Yana gama fada ya saketa ya juya cike da mugun sauri tamkar ya tashi sama ya fice ya tarar da Anwar dake tsaye gefensa Lukman ne yayi tsuru du ya gama sarewa Yana karasowa ido ya zubawa Lukman, tunani ne birjik a cikin ransa fadi yake yanzu wannan ya gama sannin matata, yanzu wannan ya je wajen da ban je ba? Yanzu wannan ya kara gudun zuciyar matata? Anwar ya dan matso ya ce" yaya, ka yi hakuri ka sanyaya zuciyarka a yanda yake fada baima tabata tana da aure ba sai yanzu kuma wajen Aba ya zo wanda suka yi maganar zai zo su yi wata magana mai mahinmanci , yana neman afuwa ba zai kuma gigin aikata hakan ba Alaidine ya dago ya watsawa Anwar kalon bayan ya gama cutata? Kai ya kada ya ce" ban gamsu ba, ka je da shi zan shigo a kowani lokaci Yana gama fada ya juya dan ya koma gidan Cikin gidan Jamail da Aisha Zaune suke cike da soyayar juna da dumbin kulawa da juna duda a daren farko bai taba ta ba aman a darenta na biyu a gidansa a ranar Allah yayi abinsa, wanda hakan ya kara wani dankon kauna da shakuwa tsakaninsu duda irin wahalar da ta sha a hannunsa, domin ta jigata iya jigata sannan ta ji tsoronsa fiye da tunaninta, tana gannin girmansa fiye da dala da gauron dutse🤣, A unguwar hotoro gidansu yake, tankamemen gidan da Alaidine ya gina masu, gida mai amsa sunnan gida domin ya hadu ya gama hadewa A makotansu gidan wata datijuwa ce, wace zata kai shekaru arba.in da dan dori a duniya, yarenta biyu kawai a duniya da *MARWA* da Aliyu Sosai Marwar ta zama budurwa matashiya, ta dauko kyan gidan mahaifiyarta , yarinyar dai masha Allah ga kirki , sam bata da girman kai ga son amare a wajen Marwa Hakan ya saka tunda aka kawo Aisha anguwar take zumudi tana faman neman mamanta ta barta ta je ta gaida sabuwar amarya aman fir ta hana tana fadan ita ta rasa gane kan shirme irin na Marwar haka kawai daga an kawo amarya sai ta nace ita sai ta je? Duda al.adar hausawa yin hakan ba wani abin bane domin idan an kawo amarya akan shiga wasu dan zumuncin ne qasun kuwa dan tsegumi ne, aman maman Marwa ta nace kan ba inda zata je (Wacece maman marwa?) Alaidine, tunda ya shigo falo ya zaune Mom na zaune da Boy a gefenta yana ta fama da ice cream yana kallon tom and jerry a tv Mom cike take da shi, domin du rabin abinda ya faru tana sane a kan idannuwanta da ta ji wasu magangannun ne ta bar wajen, gashi yanzu ya kai minti ashirin zaune bai ce da ita komai ba bai shiga sabgar kowa ba Wasa wasa yama ta yi, magariba ta shigo, yannayin zamansa tun na farko shi ne, hannayensa bibiyu a dafe da kansa, Mom ta fito a kicin idannuwanta suka sauka a samansa nan take gabanta ya fadi, kar dai yaron nan bashi da lafiya ne? A hankali ta karaso wajensa ta dora hannunta ta ce" Alaidine, lafiyarka kuwa? Jikinsa zafi sosai haka dukan yannayin jikinsa ya saki a hankali ya dago idannuwansa da suka yi jajir ya sauke a fuskar mamansa, Abinka da Da da uwa, zuciyarta ta ji ta kara karyewa, tana hango fasarar da dan nata ya kasa amincewa, haka wani murna ya darsun mata a ranta na idanfa ya yarda da haka may be hanyar saukowarsa kasa kennan Sosai yake jin nauyin zuciyarsa, a hankali ya dora kansa a hannun mahaifiyarsa murya kasa kasa ya ce" Momna Mom ta ce" mai ke damunka son? Ajiyar zuciya ya sauke ya ce" ba komai Mom, Murmushi ta yi , shi kam zurfin cikinsa ba zai barshi ba, Mom ta ce" da kamar zazabi a jikinka, ka tashi ka tafi gidanka matarka ta kula da kai son, Ajiyar zuciya ya saki ya ce" Mom, zan tura direba idan bata da damuwa ya daukota, ina son na dan huta a nan ina son zama kusa da ke Mom Murmushi ta saki ta ce" son, yarinyar nan ina son taci gaba da karatunta kar a tauye ta, kafin Abanku ya yanke ranar tarewar tata itama ko? Shiru yayi wannan karon bai ce komai ba, bashi da niyar tankawa dan bazai yiwu Wujdane ta koma makaranta a haka ba, ba zai yiwu ya bari ta koma makaranta ba sai dai ya dauki malamai su rinka koya mata daga inda ta tsaya, Jin yayi shiru ta ce" ka mike ka haura sama ka yi alwallah ka yi sallah kafin lokacin cin abinci yayi, sai docter ya zo ya baka magani Kai kawai ya iya gyada mata dan gannin yanda ta damu, sannan da tace sama dakin wa? Su dai ba shiga bayinta suke ba, a saman kuwa daki biyar ne daya na Aba, daya na Mom, sauran nasu shi da kanninsa, bayan sun bar gidan kuwa sai Wujdane ta maye nasa, Aisha na Jamail, dayan kuwa Mom ta mayar da shi kicin dinta na biyu idan bata ra.ayin sauka kasa takan dora girki a saman, A yanzu dai ba zai shiga dakin da matar kanninsa ta shiga ba, a takaice dai Mom na nufin dakin da Wujdane take ciki? Toh idan zai kwana a gidan fa? A kasa dai dakin Khadija yake wanda koda wasa ba zai so ya tare a dakunnan falon kasan ba dan kar su hadu ko su hada makotaka da ita, aman ina zai je ya kwana? Ko dai gidansa yake tafiya abinsa? Yana nan zaune aka fara kiraye kirayen salar isha.i, ya mike da hankari ya fice ya nufi wajen bayin mai gadi ya shi ya fito yayi alwallah ya nufi masalaci Bayan ya gama dukan salolinsa da adu.o.insa ya fito yana tafe da carbinsa yana ja har ya karaso gida Yana shigowa ya tarar suna table suna cin abinci, aman bai hangi Wujdane ba, bai kawo komai a ransa ba ya zauna yana dana wayarsa Alawiya ce ta yi masa missed calls da yawa da test message tana fada masa ba zata iya zuwa ba dan bata jin dadi sannan ba zata bar gidan ba kowa ba Bakinsa ya yatsina ya ajiye wayar yana kalon Lami na jera masa abinci a gabansa tana faman fadin Uban gidanna ya jikin? Momy na fadin baka da lafiya Bai amsata ba sai bin kulolin abincin yake da ido, a ransa yana tambayar kansa wa ya dafa abincin? Bai taba ba, baiyi niyar ci ba don mugun kyankyamin dake damunsa Jifa jifa yakan daga idannuwansa ya kalo wajen dakinta sannan ya maido dubansa wajen Tv har su Mom suka gama suka dawo Falo Mom ta ce" Lami ki kuma duba min idan har ta farkan kin ji? Auntynsu a gaba a yi murzar ta dare ko? Aunty Agaishat ta ce " Momyn yara yau yar taki da alama rigima take so mu yi shi yasa ta konta da wurin nan tana fadin cikinta ciwo, aman yanzu zan hau na murjeta idan yaso ta yi ta fushin Mom ta yi murmushi ta ce" aa kinga a bi min yarinya a hankali yau yan mulkin ne ai kinga abincin ma ance ba a ci dan haka kar ku rikita min ita Du abinda suke tataunawa a kan kunayensa, har agaishat ta mike ta haye sama Tambayar kansa yake kenene murza kuwa? Yana nan zaune Mom na dan zantawa da mutanenta har aunty ta fito daga wajen Wujdane ita kanta sai kanshi take zubawa na kayan turaren da ta yi mata ta zauna itama aka shiga labarin da ita A hankali ya mike, ya jaye jikinsa ya haye sama Dakin Wujdane ya tura a hankali ya shiga daidai ta fito a wanka daga bayi daga ita sai tawul dan madaidaici wanda ya rufe mata mazaunanta kawai, wankan ruwan turare ne ta yi bisa umarnin Aunty Agaishat Kanta sai tsago yake na ruwa sannan ya dan kare mata ijiya bata ga Alaidine da yayi mutuwar tsaye yana kallonta ko dakin ya kasa rufewa bale yayi kokarin yin abinda ya kawo shi dakin Wayarsa ce ta...... [2/1, 2:31 PM] Ummi Tandama.: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄 *35* WRINTING BY *SAJIDA* Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai, *SAJIDARKU CE* MARUBUCIYAR: *YAR MAHAUKACIYA* *DUK KARYAR KADA* *DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA* *NEMAN NA KAINA* ................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH.... Shigowa Marwa ta yi tana dan rarabewa abinka da rashin sabo da mutane, sannan muryar namiji da ta ji ya tabatar mata da namiji a gidan Aisha ta bata damar zama ita kuwa ta nufi frij dan dauko mata jus Rabewa ta yi ta sada kanta, murya can ciki ta ce" ina yini Jamail kalo daya yayi mata ya amsa yana mai mikewa dan shigewa dakinsu, sai yake gannin kamar ya san yarinyar nan toh aman a ina ya santa? Tana miko mata jus din Marwa ta mike da sauri ta ce" aa aunty amarya zan koma gida sai Mamana ta barni zan dawo Kafin Aisha ta bata amsa har ta fice da sauri sauri dan yanda take jin faduwar gaba da tsoro Tana fitowa suka yi ido hudu da yayanta Aliyu, ya zabga mata harara ya juya da sauri ya rigayeta fadawa gidansu Mama mama, ai kuwa Marwa daga gidan amaryan can take, kin ganta nan Ta dago daga dana wayarta da take ta sauke kwayar idannuwanta a kan Marwa, yanda Marwar ke bari ta gane eh gaskiya ya fada , da hannu ta yafito ta dan Abanta yana gidan idan ya ji zai hana ta dukanta Marwa a hankali ta karaso tana son gane idan abanta na gidan ta wangale baki ko zai ceceta aman ina kafin ta fahimci hakan umanta ta damke hannunta ta ja kuncinta irin yanda ake yiwa yara ta kala mata yatsu a bakinta ta zazaro mata idannuwa ta ce" Marwa kennan bakya jin magana ko? Na hane ki da shiga gidan amryar nan shine kika shiga? Mama dan Allah ki yi hakuri, ba ita kadai na tarar ba mama Marwa ta fada jikinta na bari har kwalah ta fara ziraro mata Ta girgiza kai ta ce" da wa kika tarar da ita? Bata yi tunanin za.a tambayeta da wa ta tarar da ita ba, hakan ya kara tsoratar da ita ta ce" mamamamama da da mijinta yana gidan Hajiya ta kama kanta ta ce " Ya Allah, yanzu Marwa da mijinta a gidan har kika shiga? Ai yau sai na yi maki duka tunda bakya ji, dan kinga ina tsoron zuciyarki ko? Sai na lalasaki a gidan nan sannan mu tafi na basu hakuri tunda baki da hankali ke Mahaifinta ne ya fito daga falo da jarida a hannunsa ya ce" aa aa, banda lalasawa maman Marwa a yi mata hakuri, ina nema mata yafiya Ta dago ta kale shi, yayi alwallah da alama masalaci zai je ta saki hannun marwa ta mike ta nufe shi dan taya shi saka takalminsa bata ce komai ba aman Marwa ta bata haushi , danme zata shiga gidan amare a wannan lokacin, ita da ta tafi gidan kakaninta mai ma ya dawo da ita? Aman aban Marwa baya so a taba masa lafiyar jikinta hakan yake sakawa wani lokacin take tabararta sai idan daga ita sai ita a gidan ne sai ta nutsu ta san idan ta yi zata daku ne (Marwansi🤣) Baci barawo ne yayi nasaran dauke Alaidine a cikin irin halin da ya saka kansa, asubar fari kiraye kiraye ya farkar da shi inda yayi adu.ar tashi daga baci yayi salati ya sanar da ubangiji Kokarin mikewa yake idannuwansa suka sauka a kan mahaifiyarsa dake zaune tana jan carbi sai a lokacin ya tuna a dakinta ya kwana, Fitowa yayi ya dauki jakarsa da anwar ya kawo masa ya shige dakin wajen jamail, Tastas ya tarar da dakin babu wani abu da ta bari ko wata kazanta haka ma bayin kyalkyal da shi, dan haka ya saki jikinsa ya yi wanka ya dauro alwallah ya dawo wajen salaya Ya jima kafin ayi kiran sallah ya mike ya fice inda ya hangi hasken fitila dakin Wujdane hakan ya tabatar masa ta farka itama Karfe bakwai da doriya ya dawo gidansu, direct dakin ya koma dan ya sake hantsewa kafin ya fito falo Mom ce zaune a dakin, hakan ya nuna masa shi take jira dan haka ya zauna a hankali ya shiga gaisheta Mom ta amsa masa hankalinta a kansa har ya samu waje ya zauna ya dan tankwashe kafafuwansa Ajiyar zuciya ta sauke a hankali ta ce" Allah bai haliceka a yanda ya haliceka dan ka yi masa laifi ba, bai halice ka dan ka gama rayuwarka a kuntace ba, ka sakawa zuciyarka sasauci, ka sanyaya zuciyarka ka nema mata abinda take so, ka sani hakan ma da kake aikatawa laifi ne dan kamar kana fushi da yanda allah ya halice ka ne Cike da tsarguwa Alaidine ya ce" Mom wani abin aka yi ne? Ta yi murmushi ta ce" kar fa ka manta ni na haife ka Alaidine, shawara nake baka ka rungumi ni.imar dake tare da kai ka zama cikeken namiji tun kafin wuri ya kure maka Tana gama fada ta mike ta fice a dakin ta nufi wajen Aba Ajiya zuciya Alaidine ya sauke ya mike ya yaye labulen windows yana shakar sanyin safiya Wajen karfe tara na safe Wujdane ce ke saukowa daga sama, ta sha doguwar rigarta kalar ash irin na kanti din nan, kafarta saye da takalmi fari kar mara tudu, sai kanta da ta yane da mayafi, yau tunda ta farka da kewar gida kawai ta farka hakan ya saka a shiru shirun nata na da ta kara wani A hankali ta karaso inda ta sauke idannuwanta a kan su Mom da Alaidine dake zaune ya sake wanka ya canza kayansa sai kanshi yake da haske dake kara bayana a fuskarsa Har kasa ta kai tana gaishe da Mom wace take amsawa cike da kula, Bayan ta gama gaishe ta ta juyo da fuskarta wajen Alaidine ta sada kanta kasa ta ce" ina kwana *yaya*, Alaidine da ya ga abij wani banbarakwai domin ko matarsa bata yi masa irin gaisuwar nan da mutunci ko shi ko iyayensa sai ya ji kansa ya kara wani girma, hakan ya saka shi dan sakin murmushi ya ce" Morning Hajiya Wujdane Dago kanta ta yi jin yannayin amsa gaisuwar tasa kamar mai cike da farin ciki, ta dan murmusa ta mike ta koma can gefe aman bata hau kujera ba dan Mom na zaune a saman kujerar Mom ta ce" Lamy ki kawowa yarinyata abincinta ta karya yau tayi latin tashi, Wujdane ta ce" aa Mom, yau bana jin yunwa ne kwata kwata Mom ta shida dan mitan wujdane bata son cin abinci tunbama Aisha da bata gidan ba sai ya kasance ta rage cin abincin sosai Alaidine kuwa ido ya tsura mata yana karantar yannayinta, duda ba wani.mugun sabawa yayi da halayanta ba aman zai iya gane idan tana cikin walwala ko she's sad, Sai ya tsinci kansa da damuwa da yannayin da take ciki domin gaba daya sai ya ga kamar bata cikin nutsuwarta Mom ta mike ta nufi kicin da niyar bara ko dan jus ne ta hada mata ta sha karta zauna ciki ba komai Mai ke damunki? Alaidine ya jefo mata tambaya sannan bai kawar da idannuwansa s kallonta ba Dago da nata idannuwan ta yi, sai ta ji ba zata iya yin ido cikin ido da shi ba, a hankali ta mayar da kanta ta sada ta shida dan murza karamar yatsarta murya ciki ciki ta ce" ba komai A ransa yake ayana du miskilancina yarinyar nan ta fi ni da alama, bai gajiya ba ya ce" ko kina son fita ne? Da sauri wannan karin ta dago da kanta harda yar alamar fara.a a fuskarta sannan ta shagwabe fuskar ta ce" Innata😟 Bai ce da ita komai ba sai da jan hankicinsa da yayi daga gaban aljihunsa ya kara zuba mata manyan idannuwan nan nasa yana dan murmushin da shi kansa bai san ya shagalta a yinsa ba, shagwabarta ta dake shi sosai, a ransa yake ayana du yanda ka yi da ita idan tayi react@ sai yayi mata kyau Ita kuwa a ranta ta shiga jin haushin bakinta da ya furta masa damuwarta, domin tana gannin dan kawai ya tsankwaleta ne ya kara wulakantar da muradinta yayi hakan Mom ta dawo da jus na aya mai kauri ta mika mata tana fadin oya shanye min kafin a jima ki ci abinci Wujdane ta karba ta shiga kurba a hankali kamar mai zafi, shi kuwa ya mayar da ita tv dinsa ko kula da Boy dake faman yi masa labari bai yi bale mom da mamaki ya cikata na yanda soyaya ta mayar da Alaidine dinta A hankali ya ce" idan kika shanye zan kaiki ki ga Innar yanzu, idan kuwa baki shanye ba ba ke ba zuwa Ai da sauri Wujdane ta mike harda dan tsalenta ta kafa kai ta shanye gaba daya sannan ta nuna masa kofin tana kalon Mom ta ce" Momna kinga na shanye ko? Zai kaini ne? Mom cike da farin ciki ta ce maza jeki shirya ya kaiki ai shi yayi alkawarin hakan Da sauri ta juya abinka da riga mai lafewa a jiki takan nuna yannayin halita ne koda da wasu kayan a ciki, hakan ya saka jikinta rawa a cikin rigar wanda ya saka shi da sauri ya juyo wajen Boy ya shiga kokarin gyara masa rigarsa dan da shi zasu tafi Sosai wujdane ta yi wanka da turare a jikin lesh dinta da aka yi mata dinkin riga da zani da dan kwali, Bayan ta saka ta ciro mayafinta mai ruwan blue mai duwatsu farare kal a jiki sai takalmanta da yar jaka marar girma ta fito da dan kwalin dan Mom ta daura mata Da ido kawai yake binta, komai ta saka tana tafiya da imaninsa ne, du shigar da zata yi tana karbar fatarta ne sai gashinta dake bashi mamaki har yau, shi dai ya taba gannin mahaifinta bata kama da shi aman bai taba gannin mahaifiyarta ba Mom ta gyara mata gashinta ta daura mata dan kwalin, duda ba irin daurin zamanin nan bane aman sai yayi mata dan das da shi tamkar yar tsana Mom ta miko mata leda baba, wace ta saka mata turaruka da atampa biyu manya sai mayafi guda tace a gaishe da innar Cike da murna Wujdane ke godiya, bakinta ya ki rufuwa tana murnar gannin innarta Motarsa baka mai bakin glass ya dauko gaba dayanta baka iya gannin na ciki sai dai shi ya ganka, Ciki suka shiga suka dauki hanya wada Wujdane sai waige waige take tana kallon gari kamar wace ta shekara bata fito ba abinka da kafar yawo har suka iso anguwarsu Wujdane sai ta dawo sakin murmushi dan gannin yanda yara a birni ba kauye ba suke bin motar , har manyan kansu sai an raka motar da kallo anguwar kuwa datin nan na nan dankare ba.a canza ba Kofar gidan ya ja ya tsaya, ya shiga karewa anguwar kalo harma da ginnin gidan su Wujdane, juyowa yayi ya shiga kallonta ta yi ta yi ts bude motar ta ki buduwa sai ta zauna ta shiga kifta ido A ransa yake ayana Allah mai iko, yanzu cikin gidannan ne gidan da aka haifi wannan anjel din, ita kuwa bata wani damu ba dan sai ta ga an gyara wajen da ya dukan nan kamar zata fadi katangar aman yanzu an gyare ba.a hangen gidansu ta kofa So take ya bude mata ta fice aman ya ki budewar ta rasa dalili, dago da kanta ta yi da niyar yi masa maganar ya bude mata mana sai ji ta yi ya cafke mata lebe da ta saka jan bakinta yana walwali ya shiga sidewa ko ta kan Boy baya yi wanda ke baya yana buga gm bai ma san abinda ke faruwa ba Sai da ya side shi tas ya cika mata bakin yana dan hade fuska wanda da kyar ya saisaita numfashinsa, itama har dan kwalinta ya kunce sannan ta zazaro ido kamar an jijiga bera a kwano du ta rikice da sauri ta kai dubanta wajen Boy sai ta ga yana sha.aninsa ta juyo da niyar yin aikin nata wato fitsara Yatsarsa ya dora kan lebensa ya ce" idan kika furta kalmar da bata yi min ba zan juya da ke ne gida, ai kin san na hana ki shafa abinnan idan zaki fita aman kika shafa dan na sosa maki inda yake maki kaikayi, toh na sosan idan kuwa bai isa ba na kara? Da sauri take girgiza kai ta gyara daurin dan kwalin tana kara goge leben nata dan kar ya juya da ita haka kawai Murmushi yayi ya bude mata ta fita da sauri ta bar jakar nata a nan , Boy ya budewa ya bi bayanta shi kuwa ya shiga dan shafa geme a hankali ya furta" i love u so much Da murna ta shiga gidansu, inna na zaune tana yanke akaifa ta dago itama da murnar tana yiwa Wujdane dinta lale marhabin Waje ta samu ta zauna da boy ta gaishe da innarta wace cike da fara.a take amsa mata da tambayarta gida da iyayen mijinta da mijinta da kishiyarta Wujdane ta ce" ai da shi ma muke tafe Inna ta mike tana salalami ta dauko katon hijabinta ta saka wujdane ta yi masa iso, sannan ta shiga neman abinda zata bashi Gaba take yana biye da ita, abinda ya birge shi a gidan su wujdane shine yanda gidan ke share kyalkyal da shi, tamkar da masu gyaransa ne daban, sai yanda du kananta gidan ba zaka ga can kwano nan ludayi can kaza ba, komai a kilace yake wajen da ya dace Tabarmar da ya gani shimfide ya nufa a hankali ya cire takalminsa ya zauna da bismillah ya bi Wujdane da ido wada ta cire mayafin nata ta shanya a nan ta fada dakin Malan dan ta san inna nan ta shige Yelumun kuwa ta tarar da ita ta fitar da sabin kayan shan ruwan malan na azumi da jus kwaya daya bigi na coca bashi da sanyi kuwa ta mimiko mata tana fadin maza wanke ki zuba masa ruwan randar dakina Murmushi kawai Wujdane ta yi , innarta ba dai son karama baki ba , takan ajiye irin jus idan malan ya kawo bata shan nata sai ta boye dan gudun bakin kunya Haka ta fito ta yi yanda tace, sai da ta ajiye masa ta tsiyaya masa ruwan sannan innar ta fito ta yi masu salama ta samu waje dan nesa kadan ta dan zauna Tsugunawa yayi ya shiga gaisar da innar, wada sai a lokacin ya dago yana kallonta, sai da ya saki ajiyar zuciya hango kama a wajen innar da Wujdane har idannuwansu da farinnan Nan da nan ya ji kaunar tsohuwar ta shiga ransa sosai da gannin girmanta, sosai wata kunyarta ta rufe shi wada bai yi tunanin jinta ba hakama innar ba wani ido ta hada da shi ba dan kunyarsa take ji har suka gama gaisawa ta yi godiya ta mike ta koma dakinta Sun dan jima ya sha ruwan nan dan kanshin abin tulun ya mugun bashi sha.awa da tsaftar kayan , a ransa yake fadin kenan talauci baya hana tsafta ko wadatar fuska da fara.a Haka ya kali Wujdane yayi mata alamar da su tafi ko? Ta kuwa yi kicin kicin da fuska da niyar magiyar ya barta aman sai ya fita hade fuskar sannan kasa kasa ya ce" bakya so gobe na maido ki ne? Shiru ta yi ta mike tana cewa inna zasu juya Inna ta fito ta shiga yi masu adu.a da godiya sosai cike da fara.a, ta yi godiyar sakon Mom sannan ta ga dai ya ajiye envelope ta so tambatar meye aman har ya fice sai Wujdane ta dan tsaya suka dan zabta da innarta kan kara hakuri da biyaya a gidan aurenta sannan ta fice bata samu gannin malan ko yayunta ba Maimakun ya dauki hanyar gidan Mom da su sai ta ga ya canza hanya, aman bata ce da shi komai ba har suka iso anguwar su ELHAJ Muhammad ya ja ya tsaya can gefe wajen sa yakan tsaya idan ya zo shi kadai ya tsurawa kofofin ido yana kalo itama haka dan bata san infa suka zo ba Sun jima suna kalon nan, can ya sauke ajiyar zuciya bayan yanke hukuncin fada mata ko shi wanene da yayi ya juyo sosai da kalonsa wajenta dan ya gaji, ya gaji iya gajiya , bai san yanda xai iya dauka ba idan ya ci gaba da wannan wasan buyan, ya gane cewar shi ba komai bane a wajen abinda yake ji game da Wujdane, ya dauki aniyar idan har ta nuna bata ra.ayin hakan ba zai yi mata dole ba tun kafin abin yayi nisan da ba xai iya dauka ba, Hannunta na dama ya kamo cikin nasa, ya mayar da hankalinsa kanta sosai ya ce " *WUJDANE, KIN SAN INAJE NAN?* kalonsa take sannan ta kali kifofi biyun da ya nuna mata, ta dawo da kalonta da alamar bata san ko inane ba, Ya sauke ajiyar zuciya ya ce" *wa.innan gidaje da kije ganni, gidajen mutanen da suka kori iyayena ne dan an samu cikina ta hanyar da bai dace ba, wato gidajen nan gidaje kakanina ne wa.inda basa maraba da zuwana duniya dan ina matsayin.......* Sai yayi shiru ya kasa karasawa fan yanda wani tsoro ya diro masa da bugun zuciya da dana sannin fada mata maganar a wannan lokacin duda bai gane inda hawayenta suka nufa ba, hawayen an cuceta ne? Hawayen takaici ne ko na menene???????? 🤒😕☹ [2/1, 2:31 PM] Ummi Tandama.: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄 *36* WRINTING BY *SAJIDA* Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai, *SAJIDARKU CE* MARUBUCIYAR: *YAR MAHAUKACIYA* *DUK KARYAR KADA* *DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA* *NEMAN NA KAINA* ................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH.... A hankali ya sada kansa kasa, bai cika hannun nata ba hakan ya bata damar jin yanda jikinsa ke rawa karkarkar Hannunta na hagu ta saka ta share dan siririn hawayen da ya zubo mata sannan ta yi kokarin saisaita nutsuwarta ta kara waigawa ta kali gidajen nan biyu Hannunta ta kawo a hankali daidai fuskarsa ta saka ta dago da habarsa abinda bata taba yi ba inda jajayen idannuwansa suka shiga cikin nata wa.inda har suka tsoratar da ita aman ta dake da yar jarumtar da ta yi mata saura ta ce" *ABAN BOY ka mayar da mu gida kar Mom tayi ta duba hanya fa* Wani iri ya ji sunnan da ta kira shi da shi, sannan yanda ta basar da maganar da ya dauko abin sai ya bashi mamaki, a ransa ya tambayi kansa mai hakan ke nufi? Bama ta son sannin karashen maganar da ya saka aka kori iyayena dan ba zata iya zama da ni ba ko mai hakan ke nufi? Murmushi Wujdane ta saki wannan karon tayi watsi da tsorotsoronta ta ce cikin wata murya mai kontar da hankali" *Mijina ni fa yunwa nake ji, ka kaimu mu ci abinci tun kafin na rikice maka da kuka a nan* ta karashe tana mai yin kalar shagwaba sosai wanda ya saka tsikar jikinsa mikewa har ya kwalalo ido yana kallonta da mugun mamakin sunnan da ya ci a yau wato Mijinta, Boy ne ya miko masa wayarsa dake ringin yana hade rai an katse masa gm dinsa hakan ya ankarar da shi , bai iya daga wayar ba , bai iya tabuka wani abin ba bayan kuna motar da yayi cikin mutuwar jiki ya harbata kan titi ya shiga tuki Shiru ne ya biyo baya domin ko radio bai kuna ba, boy kuwa bai karbi wayar ba saima konci da yayi baci ya fara daukansa, Tsakanin Alaidine da Wujdane kowane na kokowa da tunaninsa, shi kam ya rasa a wani hali yake ciki hakan ya saka yana tuki ne yana dan kalo wajenta kadan, Ita kuwa tana tambayar kanta ne , ta kai darajar da zai fada mata wannan sirri nasa mafi girma wanda yake cin zuciyarsa kamar mai? To maima ya kawo shi har ya fada mata ne? Yana sonta ne ko mai? Ajiyar zuciya ta saki a cikin ranta ta ayana koma meye dalilinka na yin hakan , zuciyata ta jima da aminta da kai a yanda kake , ka rigaya ka gama da zuciyata Yana tsayar da motar ta bude ta fito , ta bude masa baya dan ya dauko Boy sannan ta kwaso wayoyinsa a hannunta Boy ya dauko tana gaba yana biye da ita tamkar iska zata dauke shi Haka yake ji, Suna shiga falon ta cire mayafin ta nufi wajen Mom Zama yayi bayan ya shinfide Boy a nan saman kujera, yayi tsuru yana tunani yana dan kada kafafuwansa Khadija ce ta karaso dauke da ruwa masu sanyi da kofi ta miko masa tana murmushi ta ce" yaya ga ruwa Dago da kansa yayi sai suka hada ido da Wujdane wada tayi tsai tana kalonsu, ranta na tafarfasa gannin ya mika hannun ya karba sannan bai daina kalonta ba harda yiwa Khadijar murmushi yace" thx dear Wata kwallah ce ta tarun mata a idannuwanta, a hankali ta mike ta haye sama ranta in yayi dubu ya baci haka kawai take jin haushinsa da na khadijar nan Zurbat ya mike da niyar binta sai idannuwansu suka sarke da na Mom wace ta lura sarai da abinda ke faruwa, ta watsa mada wani kalo na bashi da kirki ta juya ta fice daman makota zata shiga Zagaye Khadija yayi ya nufi saman wace ta bishi da kallo ta kada kai a ranta tana ayana " aban boy yana fadin babu macen da zata juya shi, yau ga wace take juya shin yake juyuwa ba tare da ya sani bama Ya kai sau uku yana dora hannunsa da niyar bubugawa aman sai ya daina, Har ya juya zai sauka ya dawo a hankali ya murda kofar ya shiga dakin A konce ya tarar da ita, tana kallon silling, gefen idannuwanta kuwa zar abin hawaye ne ya biyo ya zubun mata, Har kafarsa hardewa take wajen karasawa gefenta, yana kalon fuskarta a hankali ya zauna yana mai tambayar kansa hawayen kishinsa ne? Yatsarsa ya dora ya dangwali hawayen hakan ya saka ta mike da sauri tana kalonsa Yatsar nasa ya nuno mata ya ce" hawayen kishin Alaidine ne ko mai nake ganni a fuskar Wujdane? Kalon hawayen fiye da hakan ne ta yi masa ta kawar da kanta bata yi niyar tanka shi ba Zama yayi dangalgal saman kujerar ya ce" ki bani amsa bafa na son ina tambaya ana yi min banza fa Bakinta ta murguda cike da haushi ta ce" hawaye? Na yiwa wa hawaye? So fa kace? Kuma ka rasa mai zaka ce sai wannan? Aa ni ba hawayen da nake abu ya fada min a ido domin kaima ka fada soyaya karya ne, nima ban yarda da ita ba Yatsarsa ya dago ya daga murya ya ce" Wujdane, So soyaya ba karya bane, sai dai idan baka hadu da wada ya dace da zuciyarka ba Aman kina nufin bakya sona kennan har yanzun? Ya karashe yana kafeta da idannuwansa Ta mere bakinta ta mike tana kakabe zanin jikinta tamkar wada ta fadi kasa Janyota yayi da karfi ya rukunkumeta a jikinsa, bugun zuciyarsa na dukan nata bugun zuciyar , lumfashinsa na sauka a kan kafadarta murya a shake ya ce" *Ba Zaki so bawan Allah ba? Ba zaki sasautawa zuciyar da kika gama yiwa illah ba? Ko kema kina cikin masu kyamata ne? Kema kina kyankyamin Shege n......?* Da sauri ta raba jikinta da nasa ta tsura masa ido yanda du ya zama wani iri, gaba dayanta ta fada jikinsa ta rukunkume shi ta saki kuka mai sauti, wanda rabonta da irinsa ita har ta manta, wai dama haka soyaya ke mayar da zuciya mai rauni? Haka zata tsinci kanta a ciki ita Wujdane din inna da Malan? Cikin sarkewar Murya ta ce" danme du yanda na so na kauce ka furta kalmar nan sai da ka furtata? Idan rabuwa ne kake so da ni ai ba sai ka biyo ta wannan hanyar ba ko? Kai ka zubar da karatunka ne ko ka zubar da adininka ne? Dan Allah yayi ta haka ka fito an gaya maka ban sani bane? Ko an gaya maka idan ka mutu dan ta haka aka sameka shikenan layinka faban da sauran al.umar annabi? Ni ba rokonka zanyi da ka sasautawa zuciyarka ba tilastaka zanyi, ni ba kuka zan zauna muna yi a kulun fa kai ba kan hanyar da Allah yayi zaka zo duniya ba aa rayuwa zanyi da kai koda kaine na dari ba wai kadara na farko ba, kai baka san kadara bane? Ko an gaya maka akoy iyayen da zasu fito du lalacewarsu su nemi haka wa yayansu ne? Baka gannin kana saka su Mom a halin kunci bayan wanda suke ciki na rashin rungumar kadarar iyayensu ne? Baka san irin abinda suke ciki idan sun ga bacin rai a fuskarka ne? Du ni.imar nan da Allah yayi maka ba zaka gode masa ba ka watsar da wani tunani naka na daban ba? A kanka aka fara ne ? Kana so kace kai kana da zabin yanda ka so Allah yayi da kai da rayuwarka ne yaya? Ina mai rokonka a nan gidan duniya karka yarda ka kuma furtan wannan kalma da bana bukatar jinta daga bakinka Abin na wujdane tamkar mai sambatu domin idannuwanta ruf a rufe tana yakushinsa tana fada ne da gaskiyarta kan abinda ke bata mata rai Alaidine tsai yayi yana jin yanda wata kaunarta ke kara shiga zuciyarsa, har ransa yake jinta sannan magangannunta sun yi masa ba zata, daman akoy mata masu irin haka? Dama akoy mata masu hankali haka? Fada ne take yi masa kan abinda yake yiwa kansa kan bata so, ji yake tabas zai ririta Wujdane dinsa, zai malaka mata ko mai take bukata a duniya zai nuna mata soyaya a baki a aikace a gaban kowa, zai sota tamkar nama daya a miya, aman abu daya ne har yanzu baya gannin zai iya yi shine ya zama ita ta zama shi, su Zama abu guda , baya tunNin zai iya haka saboda tsananin kishinta da yake , idan ya tuna wani ya shiga gonarsa kafin shi yakan ji takaici har tsakar ransa hakan nema zai hana shi zama abu guda da ita aman fa soyaya sai inda karfinsa ya kare A hankali ya maida hannun nasa guda ya rungumeta a jikinsa sannan a kunnanta yake rada mata" shiiiiiiiiiit, is ohk kukan ya isa haka ki daina bana so please angel Ajiyar zuciya ra dawo saukewa a hankali bata kuma cewa komai ba tayi lamo a kirjinsa tana shakar ni.imtacen kanshin turarensA Maman Marwa ce ke shirin shiga gidan Aisha , hijabinta ta saka tana hararar Marwar dake tsaye tsaye tana dan sada kanta kasa tana tsoron kar mamanta ta make ta Fitowa suka yi mai gadi yanai masu A dawo lafiya ta mika masa ky din baban falon tana barin masa sakon idan Aliyu ya dawo ya fitar da mota karama a wanketa Wata makiciyarsu ce mai suna Mariama ta tsaya suna gaisawa ta ce" Toh Uman Marwa inna zuwa haka a kafa ? Hajiya *Shafa.atu* ta ce" uhum, ke dai bari umman khalifa zamu shiga gidan amrmaryan nan ne mu fito Haka suka karasa har kofar gidan Jamail Yauma mai gadi kafin ya bude sai da ya tambayi waye sannan ya leko ta yar kofar dake jikin kauran sannan ya bude masu *JAMAIL* ne ya fito da jakarsa ta wajen aiki a rataye a kafadarsa Aisha kuwa da hularsa tana murmushi zata mika masa su maman marwa suka yi masu salama hakan ya saka su jiyowo a tare suna amsa salamar inda amsawar ya tsaye masu a lebe tumba jamail ba da yayi mutuwar tsaye yana kalon Maman Marwa dake dan murmushi tana dan damanma basu shigo warhaka ba ashe mai gidan bai fita ba Bakinsa har yana rawa ya nunota da yatsarsa ya ce""":":""::::::::: Mmmmmmmmmmommmmmmmmmmmmmmmmm [2/1, 2:31 PM] Ummi Tandama.: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄 *37* WRINTING BY *SAJIDA* Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai, *SAJIDARKU CE* MARUBUCIYAR: *YAR MAHAUKACIYA* *DUK KARYAR KADA* *DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA* *NEMAN NA KAINA* ................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH.... Bakinsa na rawa ya nunota da yatsa yana mai yi mata kallon mugun mamaki ya ce" Mommmmmm??? Aa aman fuskar nan da ta mom suna mugun kama, amann ya aka yi haka?.... ............. Du sai yake kame kame wanda Maman Marwa ta kasa fahimtar inda ya dosa da maganarsa, shi dai bai taba ganninta ba itama haka hakan ya saka ba wanda ya san dan uwansa Dan ja tayi ta tsaya kawai tana kallon yaren yanda mijin ke ta binta da kallo ita kuwa Aisha tama rasa mai zata yi Cikin sanyin jiki ta matso kusan maman Marwa ta ce" Mama ki yi hakuri dan Allah, kin yi mana kama da mahaifiyarmu ne, mamansa Da sauri Maman marwa ta dago da kanta tana kallon Aisha , har rawa Muryarta take ta ce" wacece ota maman naku? A ina take ne yarinya? Ya sunnanta? Yanzun kuwa gaba dayansu suka fara bata tsoro hakan ya saka ta dan matsa gefe kusan Marwa dake rabe tana tsoron duka ta shiga raraba idannuwa tana kallonsu Da sauri ta matsa kusan Jamail, bata yi wani dar ba ko wani jin nauyi ba ta saka hannunta ta kamo hannunsa ta dago tana kallon fuskarsa ta ce" yaro kai din dan gidan *MARWANA NE*? Hadiyar wani yawu yayi sannan ya shiga gyada mata kai tamkar an yanke masa halshe an hana shi magana kenan Wani irin zaman yan bori ne ta kai kasa, ta shiga furta Alhamdulilah alhamdulilah ni Shafa.atou na gode Allah yau na ga jinnin yar uwata, ya Allah ka sa da gaske ne ba mafarki nake ba Jin magangannunta ya saka su Marwa gannewa ko mai take nufi , Jamail kansa binta yayi ya duka ya ce" Mama, ko ke ce Shafar Mom? Hannunsa ta damko sosai ta ce" ina auntyna take yaro? Dama tana raye? Har tayi yaya haka? Aman ba a nigeria take ba ko, domin nayi nema nayi nema ina cikin nemanta ban taba samun labarin ga inda take ba Ajiyar zuciya ya saki, ya waigo wajen su Aisha yana murmushi ya ce" Aisha wannan kanwar Mom ce, ku mu shige daga ciki zai fi Hajiya Shafa.atou ta riko hannunsa ta ce" yarona idan ba zaka damu ba ka kaini na ga yar uwata dan Allah ko farin cikina zai zama cikake Ajiyar zuciya ya saki, ya mike ya shige daki, jim kadan ya fito rike da hijabin Aisha sai wayarta shi kuwa ya mayar da jakar aikin nasa wato dai yau ba damar fita Tuki yake kadan kadan yana kalon yannayin Shafa.atou, Aisha da Marwa sun saka ta a tsakiya ta ririko hannayen kowace da alamar a tsorace take Bin gidan suke da kalo Hajiya shafa.atou da Marwa, kai ginin gidan ya ginu, tsarinsa yayi iya yi, wani farin ciki ya mamaye zuciyarta a kasan zuciyarta take godewa Allah idan har nan ne gidan yar uwarta Wayarta ce ta dau tsuwa daidai lokacin da ta fito a motar sai ta daga tana amsawa aban Marwa dake kaduna Tambayarta yake sun karasa gidan ne? Ta ga ita din ce? Ajiyar zuciya ta saki lokacin da ta hango Wujdane dauke da ball din boy sai Alaidine yana goye da shi suna tafe suna ta sakin dariya da yannayinsu yannayin suna cikin farin ciki ne wanda su Aisha mamaki kamar ya kashe su dan basu da sabon labarin sabuwar soyayar da ake zubewa a gidan Mom wace Aba har ya bada amanar a shirya tarewarsu Bin bayan su Jamail tayi suna salama da mijinta ta bada hankalinta kan ta inda zata ga yar uwarta Mom ni bana ci ni mom ki hana shi yi min durar nan mon Wujdane ne ke kawo karar kar Alaidine yayi mata dura shi kuwa yana tsaye da plat din shinkafa da miya da cokali yana yi mata a taro a taro ya hade rai kan sai ta ci abinci shi ya gaji da rashin cin abincinta Mom ta dafe kai ta ce" ni wai yaushe ne tarewar naku ne? Da sauri Alaidine ya ce" Mom mu tafi yanzu mana? Da mamaki da dariya ta dago tana kalonsa, kwana biyun nan ita kanta farin cikinta baya musaltuwa na irin yanda yaran ke nunawa junansu kauna da kulawa, duda ta lura abin iya shakuwar ya tsaya domin da waje ya matse masu zai zile ne ya tsere da wayo bata san dalili ba Mom ta ce" anki din, ban gama shirya yarinyar ba zan hada ka da ita? Wujdane dai tayi tsuru tsuru tana kalon yanda shifa ya dage sai ta ci wannan uban abincin bayan da safe ma sai da ta ci, Mom ki bani ita toh na bata abincin nan, ya fada da gaskiyarsa wai a bashi ita tamkar baby Mom kam sun gajiyar da ita, ta mike da niyar bara masu wajen da gudu Wujdane ta rungumeta karta barta shima ya zo ya shiga kokarin sai ya kwaceta a hannun Mom din Salamar su jamail ta dakatar da diramar da ake faman sha, suka Mom ta bada hankalinta dan amsa salamar inda ya samu damar janye Wujdane a jikin mom ai kuwa ta fada jikinsa ta rukunkume shi ta kai bakinta daidai kunensa ta sakar masa kukan shagwaba tana jan numfashinta tamkar zata sike masa da gangan Bai shirya ba ya cikata ya juya da sauri ya haura baima tsaya gannin su waye suka shigo din ba kokarinsa ya fada dakinsu ko zai samu nutsuwa, yana yiwa kansa tambayar" Alaidine zaka iya kuwa? Zaka iya ci gaba da jure jin jikin matarka a jikinka sannan ka hanawa kanka kasancewa da ita? Zaka iya jure zama da ita na dindindin ba tare da ka jita a jikinka bba? Aman idan hakan ne ta ya zaka iya jure irin feeling din da take hadasa maka da kuma fitinar ta kasance a jikinka da take yawan yi? Alaidine kana yi mata muguwar soyaya, kishinta ya hana ka yin wani yunkurin kasancewa a gonar da take malakinka dan wani ya taba saka kafa a ciki A hankali ya lumshe idannuwansa ya konta saman bed dinta yana shakar dadadan sansanyan turarenta yana sauke ajiyar zuciya Kalon kalo suke ya kai na tsayin minti biyu kafin Mom ta nunota da yatsa ta ce" Shafana???? Hajiya shafa ta fashe da kukan da take rikewa tayi kokarin kaiwa kasa Da sauri Mom ta tarota ta riketa gamgam a jikinta suka fashe da kukan a tare suka yiwa juna riko na kirki tamkar za.a kwace masu daya dan uwansa Alaidine kansa saukowa yayi ya ja xan gefe yana kalonsu Cike da muryar kuka Shafa.at ta ce" danme kika tafi kika barni da rigimar duniyar nan Aunty? Danme kika yi irin nisan nan da ni tsayin shekarun nan kika barni da tashin hankalin cikin duniyar nan ni kadai ? Mom ta fara sasauta kukanta, tana sauke ajiyar zuciya ta shiga gogewa Shafa hawayenta ta dan nuno yatsarta ta ce" aa fa shafana an girma ba.a daina rigima ba? Ya isa hakannan kukan yanzu ba gani ba? Shafa ta kalota ta ce" du girman da zan yo a gabanki ina jina tamkar jaririya, ina jin du duniya ba wanda ya isa ya talura min idan ina kusa da ke, dan me kika tafi kika barni haka? Fushin zuciya na sakawa a manta da dan uwa? Mom ta sauke ajiyar zuciya ta dan kawar da kanta ta ce" yar uwata ba fushin zuciya na yi nayi nesa da ke ba, *BANI DA ZABI NE* ba.a tambayen nawa ramayin ko muradina ba, an dora min ne sharadi wanda ya kasance dole nayi nesa da kowa dan ba zan iya aikata hakan ba, aman yanzu ki bar maganar nan tunda Allah yayi zamu hadu kafin mu koma gare shi ai sai mu ci gaba da zumuncinmu ko? Kina nufin ba zaki je wajen su Dad da Mamy ba?????? Shafa ta jefo mata wannan tambaya Tsam Mom tayi, 8dannuwanta suka hasko mata rantsuwar mahaifinta kan idan ta saki ta dawo mada da cikin shegen nan na jikinta , ta je ta zubar a hanyar iskancin da ta saba sai ta dawo muhalinsa idan kuwa ba haka ba sai ya tsine mata idan ta dawo masa gida da cikin, Ajiyar zuciya ta saki ta bi su Wujdane da kalo, tana tsoron yin maganar a gaban Wujdane taji sirin Alaidine, tana tsoron wata fitinar a irin yanda Alaidine ya shaku da wujdane tana hudun idan ta ji wannan lamari ta guje masa domin abin yan matan nan na zamani basa tunani sai dai su haye kan tsani Jamail kam ya fahimci Mom dinsa hakama Alaidine wanda ya sada kansa yana sauraron abinda ke faruwa Mikewa Jamail yayi ya kali wajen Aisha Da Wujdane ya ce" madame mu tafi dakin Mom mana mu barsu su zanta da matar yaya Alaidine ya dago da kansa ya sauke kan Jamail, sai ya saki dan murmushi ya maida kalonsa kan Wujdane sai kuma ya kali khadija da ta fito itama take kalon abinda ke faruwa, haka ya juya wajen Marwa, a kasan ransa ya baiwa kansa amsar ta san dalilin da ya saka mamarta da yayarta suka yi nisa da juna dan haka ya ce cikin murya mai nuna kasala da an tabo maka miki ya ce" ka barta Jamail, *Matar Alaidine* ta aminta da yanda yake, a haka take zaune da ni saima idan na nuna damuwa ne a kan lamarin take hukuntani da fushinta, aman ka ganta nan bani da abinda zan boye mata daga Mom dina da Aba sai ita du fadin duniya domin sai da ta ji wanene ni kafin ta koyi sona Kalonsa kawai Mom take cike da mamaki da kuma tausayin Wujdane, a hankali ta maido da dubanta wajen Wujdane ta sakar mata da tsadaden murmushi mai tsayawa a zuciya sannan ta dawo da dubanta wajen kanwarta dake kalon Alaidine tana tambayar kanta shine? Shine yaron wajen yayarta ya zama cikeken mutun haka mai cike da kamala da kwarjini? Shine wannan kakarfan namijin haka? Da abansu ya matsa har aka zubar da cikin nan da ya tafi shikenan? Mom ta ce " shafana, inajin ba zaki manta yanda muka yi da Dad ba, a gabanki yayi rantsuwar kar na dawo masa sai na barar da kyautar nan da ya zamto garkuwa gareni da ni da dukan jama.ar da ta zagaye shi, na san ko a cikin anguwa zaki ji sunansa *Elhaj Alaidine*, shine wannan yarona da shi da Anwar shi soja ne sai Autansu Jamail shima kinga matarsa, sis ina cikin kewarku fiye da tunaninki aman ya zaki yi da rantsuwar dad ? Jikinta ne yayi sanyi, ta mikawa alaidine hannu kan ya zo gareta, A hankali ya taka ya karaso wajenta ya zauna, ta shafa gefen fiskarsa da sajensa ta saki murmushi ta ce" SON, Shima kalon nata kawai yake ya dan juyo wajen su Wujdane sai ya ga wayam basa nan ya dawo gareta ta ce" insha Allahu ni zanyi yanda zan yi dan na ga kun dawo gida gaba dayanku, da gatanku a kulun Mamy maganarta ke tayi ta tambaya ko yanzu mai kike yi? Ko kuna tare da Yaya? Ko kin haihu? Rayuwarki ta ci gaba? Abinda dai taki amincewa shine kin mutu takan cewa ita tana ji a jikinta kina raye, su yaya du ba a gari suke ba domin du sai tsoron Dad ya saka kowane yayi nesa da shi sai nice nake gari nima sai na jima ban saka shi a idona ba, Mamy tana zaune da shi a haka, ta kawar da kanta tayi hakuri aman a kulun burinta ta ji labarinki bata san cewa yarta ta zama big hajiya ba ga jikokinta har sun yi aure komai da komai Bakin Mom yaki rufuwa hakama na yar uwarta sai labarin yaushe gamo suke sannan tana rike da hannun Alaidine wanda ya gaji da zama yana ta hangen sama Zaune suke, Aisha na biyewa Marwa labari Wujdane kuwa na gefe tayi gum da bakinta , iya du surutunsu ya cika mata ciki tana son ta dan zanta da yar uwarta aman abin ya hagara domim marwa ba dai labari ba Tsuru take bin Wujdane da kalo, ta lura Wujdane bata da magana aman ita ta birgeta sosai da ita fa amaryar anguwarsu suna da kyau sosai wato Aisha, saima da taji cewar itama amarya ce ta zuba tagumi can ta ce" Oh nima watarana amarya ce ko aunty? A tare suka juyo wajenta Aisha ta bushe da dariya, kai Marwa bs dai dirama ba ta ce" sosai mai sunnan Mom, ki ci gaba da kare mutuncin kanki kin ji? Kema watarana amarya ce Wujdane ta danyi murmushi domin sai yarinyar ta bata dariya, wai iya nan so take ayi mata aure kenan, toh maima ta sani a auren? Haka dau sukayo ta yin labari har Marwa ta bingire nan baci yayi gaba da ita Da sauri aisha ta dawo ta tsare Wujdane da kalo irin na kurullahn nan Wujdane ta ce" meye? Kallon fa? Aisha ta saki murmushi ta ce" ai sai a bani dadadan labari an shirya da big yaya, kai aman kun birge ni aunty yaushe aka tsunduma a soyatar haka? Wujdane tayi tsam tana kallon kasa fuskar Alaidine kawai ke yawo a idannuwanta da kuma zuciyarta, tabas ta sani yanzu ta fada soyaya mai tsauri wace ta saka zuciyarta a garari domin tana mugun kishin Alaidine fiye da tunanin mai karatu dan kuwa kwana biyun nan da suka yi a karkashin innuwa guda suna cin abinci tare, suna kulawa da yaronsu suna kulawa da du motsin dan uwa sai take tunanin idan zai koma gidansa ya zata yi da ranta? Sai take jin haushin Alawiya , yanzu du kulawar nan da kallon da yake jifanta da shi mai tsuma zuciyarta haka zai je yanaiwa wata can? Sai kawai taji hamkalinta ya tashi iya tashi harma ta tsiri share shi sai yayi lalaba, Aman abinda ke bata mamaki shine idan yana zaune ko suna hira da ta fada jikinsa zai yi gagawar zameta ne ya bar wajen, ta rasa mai ke damunsa haka? Aman fa kulawar duniya yana bata yana kare hakinta yana nuna kishinta karara domin ko masu aikin gidan maza yayi masu shamaki da shawagi a tsakar gidan falo kuwa yama haramta masu shigarsa Murmushi ta saki da ta tuna idan zata yi baci yakan zauna ne ta zuba mata ido bayan yayi mata adu.a hannunsa cikin nata idan sun hada ido sai ya furta mata " *i love u*, har tayi baci sai ya gyara mata rufarta ya dawo wajen boy su konta Aisha ta kama baki ta ce" lale, wannan ita ake kira soyaya mai tsada, ka ga salon soyayar miskilai kenan Bata kai ga rufe bakinta ba ya turo kofar ya shigo, dan dakatawa yayi yana kalon wujdane dake zaune ta jinginar da bayanta jikin abin bed din kafafuwanta a mike, doguwar rigarta ta ja sama sai ta fitar da fararwn kafafuwanta waje tana zabga murmushi tana sauraron Aisha dake ta yi mata tambayoyi tamkar wata yar jarida Angel, ya furta murya ciki ciki Wujdane ta dago da sauri tana kalonsa da ido yayi mata nunin ta gyara rigarta Tana ja kuwa sai ga Jamail ya shigo shima yana fadin" hajiya ki tashi mu juya yama na yi sosai Aisha ta mike tana gyara rufar mayafinta, ita kam gulma na cinta sosai aman ya zata yi? Haka ta bi bayansa bayan sun tayar da Marwa suka sauka tare da niyar su tafi su juya da Marwar aman banda mamanta dan ta je ta baiwa yayanta abinci sannan su juyo da shi su dauki mamansu A hankali take takawa kyam idannuwansa a kanta har ya kure mata waje A hankali ya duka, ya mika hannunsa ya kami hannunta na dama ya dora lips dinsa ya sumbuta wanda hakan ya saka mata faduwar gaba da wani irin abu da taji har tsakiyar kanta Dago da kansa yayo yana kalon fuskarta, shi kam a kulun kara masa haske take a idannuwansa, ya shiga dan murza hannunta murya ciki ciki ya ce" Auntynki bata da lafiya har an kamata a asibiti, tana da bukatar kulawata a gefenta shi ya saka zan juya gida dan na kula da ita Wani irin faduwa gabanta yayi, yanzun tana murnar yana kusa fa ita shine kuma zai yi maganar tafiya, duda rashin lafiya ne aman ai itama tana da bukatarsa a kusa da ita ko? Fuskarta ya shafo a hankali ya ce" Angel baki ce komai ba? Ko zaki zo mu yi tafiyar mu? Ajiyar zuciya ta saki, koda wasa ba zata nuna zalamar muradin kasancewa kusa da shi ba du irin shakuwarsu kuwa, hakan ya saka ta shiga dan janye hannunta a hankali ta ce" ka je ka kula da lafiyarta hakimta ne, Allah ya bata lafiya Adu.ar kirki tayi masa aman sai yake gannin ba a farin ciki tayi hakan ba, mikewa yayi ya zauna sosai ya rungumota jikinsa duda yanda yake jin bugun zuciyarsa na karuwa aman ya riketa sosai a jikinsa, a hankali ya shiga kokarin lalubo lebenta wanda ya saka suka shiga shakar numfashin juna, Jikinsa na bari ya shiga kokarin zaro harshensa dan kaiwa nata cafka yana ta yawo da kwayar idannuwansa a cikin nata idannuwan ta farkar da shi ta hanyar furta" Corazon, karfa dare yayi maka ka ga da nisa anguwowin, gashi har magariba ta shigo fan haka sai mun yi waya ko? Tana gama fada ta kubcewa rikonsa domin sam jikinsa ba wani karfi , shi bai samu abinfa yaje neman ba sannan du jikinsa ya zama tamkar an zare masa laka sai uban kanshin jikinta da ya kwasa wanda ya kara saka shi zama wani shiru shiru A hankali ya mike yana kalon bayin da take tsaye, ransa ne yaji yanai masa zafi kenan in dan ita ne yayi ta tafiya ko? Bata wani damu da hakan ba take nufi in dan na ita ne yafi ruwa gudu? Juyawa yayi ya nufi fita wanda yana bude kofar ya maido mata ita gam ya rufe mata A hankali Wujdane ta silale a nan jikin bayin hannunta kan kirjinta tana jin irin yanda yake bugawa da yanda wani dumi dumi da taki gaskatawa take jin yana kokarin silalo mata na wahalar kishi, a fili ta furta" na shiga uku ni wujdane, meye hakan ne? Tamkar zai tashi sama cike da fushi ya zo da niyar gifta su ya fice dan tafiya gidansa , Muryar Shafa ce ta katse masa hanzari inda ta ce" aa Son sai tafiyar ba? Juyowa yayi, Alaidine bai iya boye fushinsa ba hakan ya saka ana iya gannin damuwarsa a fili, ya dan dawo ya ce" eh mama zan tafi Kalonsa Mom take, sai tace" jikin alawiyar ne ba? Bai san lokacin da bakinsa ya tona shi wajen fadin" *ANGEL CE* Dago da kansa yayi da sauri jin abinda ya fada wanda shi kansa yayi surprisen dinsa, Mikewa yayi ya juya kafin su furya wata kalmar ya fice a dakin kwatakwata Da mamaki Shafa ta juyo wajen Mom ta ce" wacece Angel? Mom tayi murmushi ta gyara zama ta shiga baiwa yar uwarta labarin rayuwar Alaidine, harda na khadija da sauran matan da yayi ta aura, da wada ke gidansa a yanzu da kuma Wujdane da a kanta Allah yayi zai kamu da matsanancin soyaya har ita dinma ta kamu da hakan aman basu tare ba, ta kara da fadin" Wujdane itace Angel mai yiwuwa wani abin ya hada su Hajiya shafa ji take dama tana nan, ai kuwa ta shiga fadan,Khadija ta koma gidan ubanta danme zasu barta ta zauna a nan bayan ta furra mumunar kalma haka? Mom tayi murmushi ta ce" ai fa zuciyar nan da yaronku yayi ni na san taki ce aman har yanzu ba.a daina rigima ba ? Shafa.atou ta sauke ajiyar zuciya ta ce" ni zan gyara yarinyata, itama wannan yar rainin hankalin ta gidan nasa zanga abinda take takama da shi....... Mom kam murmushi kawai take, ta so kiran agaishat aman jin shafa zata gyaratan sai ta bari domin ta san kanwarta a irin fanonin nan tun basu kai ko.ina ba take irin gyaregyaren nan danma dad dinsu ya hana da ta tsundumu a harkar Barcin wahala a wannan ranar shi wujdane tayi, da kyar ta samu tayi.bacin bayan tayi adu.a ta rufe jikinta da bargo har baci ya dauketa Bayan ta farka tayi sallah ta fita ta gaishe da kowa har aba na fadin jiya bai tardota ba tace eh baci ne tayi da wuri, Sai labari suke sha da Mom na Shafa domin bata bar gidan ba sai da ya dawo suka hadu a jiya Dakinta ta dawo ta gyara ta yi wanka ta canza tufafinta ta koma bed zuciyarta tamkar ta fito ta balo ta bar gangar jikinta dan bacin tai, Shafa ce da Marwa suka turo dakinta suka shigo, hakan ya farkar da ita ta tashi tanai masu sannu ta duba agogo nan ta ga har goma ta gifta Shafa ta yi murmushi, tabas inda zata fi baiwa karfi wajen karin gyaran toh kasan ne aman duda haka sai tayi tayi mata su dilka ne da sairansu dan kogi ma na son kari Zama ta yi ta shiga hada dilkarta bayan ta yi mata umarnin ta daura tawul kawai a jikinta Wujdane tsuru tayi da tawul tana mamakin mai za.a yi mata kuma bayan gyare gyaren da aka yi mata???????? Shafa ta juyo ta ce" cire Tawul din yar kirki Ido ta zaro ta ce" mai za.a yi min ba tawul???????????????? Toh fa anya kuwa gyaran nan zai yiwu da hajiya Wujdane????? *Godiya mai tarin yawa na ta.aziya da jama.a suka yi min, ni Sajida bani da bakin magana sai adu.ar Allah ya kara saka haske a rayukanku ya kara arziki na halal mai anfani ya kare duniya da kiyama, bakwa irguwa bakea lisafuwa hakan ya saka nayi jimila, Allah ya saka da alkhairi da adu.o.i, papy kam ya sha adu.a allah ya karba* [2/1, 2:31 PM] Ummi Tandama.: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄 *38* WRINTING BY *SAJIDA* Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai, *SAJIDARKU CE* MARUBUCIYAR: *YAR MAHAUKACIYA* *DUK KARYAR KADA* *DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA* *NEMAN NA KAINA* ................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH.... Shafa ta kare mata kalo, a kasan zuciyarta ta gama fahimtar Wujdane ba abinda ta sani, aman idan haka ne ai da Alaidine sai ya ji kunya sosai Kalonta ta maido wajen Marwa karama ta yi mata umarnin ta fice ta basu waje Marwa ta turo dan bakinta ta fita tana fushin danme za.ana korarta idan za.a yi wani abin A hankali Shafa ta zauna kusa da Wujdane ta kamo hannunta ta ce" y.ata, kinsan du mace ta duniya ana so ya kasance tana gyara jikinta komai kyanta, ki saki jikinki da ni domin ni ba zan boye maki abubuwa masu mahinmanci na rayuwar gidan miji ba, Wujdane ladabi da biyaya, tsafta, gyaran jiki , idan nace maki gyaran jiki ina nufin bayan wani kwaliya kasan ya kasance a gyarw yake Da sauri Wujdane ta dago ta Kali Shafa, tayi gagawar sada kanta kasa cike da wata muguwar kunya, ita dai ba wani kawaye tayi ba bale ta ringa jin irin zancecekun nan a bakin wasun, innarta bata taba yi mata irin maganar nan ba, a makaranta nema idan ana wa.azi akan yi irin jan hankalin nan dan kai ya kara wayewa a kara zaman lafiya a gidajen aure shima tana saurare ne a dolenta bata ma fahimtar inda maganar ta nufa Shafa tayi murmushi ta ce" kul, kar ki yarda, karma ki fara da kishiyarki ki sako kunya a lamarinki ki cuci kanki, gaba dayanku yayanmu ne, bazan taba koyar da ke ki yiwa kishiyarki fitsara ko wani rashin da.a ba, aman kishi halita ne ina so ki yi kishi na wayewa, kishi na mai ilimi ba kishin hauka ba Wujdane ki kasance....Da farko anason mace ta kasance me aji da iya yanga,kar ki zamto dosoruwa da kika rako mata duniya domin yanga tana daya daga cikin abinda ke burge namiji,anason ko da yaushe ki kasance kina tafiya a gaban miji kamar kwai ya fashe miki a ciki kar ki maida kanki gardiya kina tafiya kasa na amsawa,ko ki dinga tafiya bazar bazar ba kintsi,ko ki dinga kinkimar kaya a gaban miji,gara ki dai daita tafiyarki kina kada mazaunai da kirji Ya kamata ki zama shagwa6a66iya domin shagwa6a wata dabi a ce da ake son mace ta iya ta salo salo domin tana daga cikin abinda ke janyo hankalin miji kanki Ki kasance me hakuri,domin shine babban jigo a rayuwa da rayuwar aure gaba dayanta,domin bayan kwanciyar aure hakuri shine abu na biyu wajen gudanar da zaman auren,idan miji yayi miki kan kara kar kice za kiyi masa na itace,yin hakan zai zubar miki da kima da daraja kuma daga karshe kece da jin zafin abin Don haka ki kasance me hakuri adukkan lamuran rayuwar gidan aurenki,in yayi miki wani abun ki gayawa Allah,kiyi ta addu a Ki kasance me son jiki da fara a ga mijinki,idan nace son jikiba ina nufin kiwa ba,ko kiki yin aikin gida ba,a a ki dinga yawan manne masa tare da kwanciya a jikinsa idan yana zaune ki kwanta kiyi matashi da kafafuwansa idan a kwance yake kiyi pillow da cikin sa,ko 'ya'ya nawa zaki haifa kar ki raga masa sai dai ki canza taku sabida yara,wannan shine son jikin da ake wa miji Sannan ki zama me fara a domin aba ce dake sanya soyayyarki da kara miki farin jini a wajen miji,anaso da kun hada ido ki sakar masa fara a tare da murmushi musamman lokacin da zai fita da kuma idan ya dawo gida Haka Hajiya Shafa ta shafe lokaci tare da Wujdane tana fada mata sirinkan zaman gidan miji, inda tayi iya yinta tun Wujdane na nokewa kamar ta nitse kasa har ta dawo ta koma sakin murmushi tana rufe fuskarta da tafukan hannunta, A haka cikin hikima wujdane ta dan yaye tawul dinta inda Hajiya Shafa ta zagine ta dilke mata jiki da dilkar nan sannan ta shiga cikin ruwan turaren da ta hada mai dumi dumi ta zauna bayan ta wanke dilkar da ruwa kawai, Ta jima kafin ta fito, inda a yau yi na farko kawai ta ringa jin wani irin canje canje tun daga kasanta da take jin kamar ko fitsari tazo yi yanai mata wuyar fita da kuma irin yanda jikinta ke wani santsi da kanshi Bayan sakar isha.i har ta konta baci, domin magungunan sanyi da na zafi ne ta hada mata ya kasance sune ruwanta, Hajiya Shafa ta dawo ta tasheta ta bata wani damun zuma da wani magani mai dabri dabri ta sha tana yamutsa rai dan ba dadi sam, ta kara yin brushing din bakinta ta koma bacinta da haushi haushin irin yanda Alaidine ya shareta tana ta ayana daman soyayar cuta ce Kwana wajen hudu yana faman jinyar zuciyarsa, Alawiya dai bata rage shi da komai ba domin girki, konciyar aure a kulun tana karo lesson din yanda zata tarbeshi duda kafin ya samu nutsuwa da kuka da komai aman hakan take jurewa dan ba idanma da laifin mahaifinsa a yi masa aure toh itama mai yiwuwa dan tana mugun tsoronsa a bed ne ya saka yake yi mata irin jiji da kai din nan hakan ya saka idan dai ya bukata toh zata bada kai bori ya hau du irin wahalar da zata sha kuwa, tana dan gyara falo da dakinta aman dakinsa bata wani shigama dan a tunaninta ba sai ta gyara ba, Babar matsalarta, babar damuwar dake damunsa da ita, baban bacin ransa da ita shine irin yanda ko a fuskarta ta kasa boye yanda take adawa da iyayensa da yan uwansa, domin shi ba makaho bane du irin yanda suke dasawa idan maganar zai yi taimako ne, ko sadakar da yake yawan yi, da irin yanda yake yawon taimakon bayin Allah sai ya kasance sai idan Allah ya kwata maka ka tardo shi a farke, ko ka same shi a masalaci sai dai karfin rabo domin idan har ita ka tarar zata shuka maka rashin mutuncin da zaka ji makoshinka ya bushe ne, ita dai idan ba yan gidansu ba toh ba zaya kara kowa ba ciki harda iyayensa tana mugun adawar ya yiwa wani anfani koda na kasar gidansa ne Yana ankare da irin rayuwarta, shi mutun ne mai son sadaka da taimako sai ya bi koyarwar musulunci yake yin abinsa wato ya bayar da hannun dama ba tare da hannun hagun ya sani ba, abinda idannuwanta suka gani kawai take adawa da shi Abinda yafi damunsa, yaudai sauran kwana goma Wujdane ta tare rabonsa da ya saka ta a idannuwansa tun ranar da ya fito cikin fushin taki amincewa ya ji dan dumin jikinta duda ya tabata daga hakan ba wani waje zai zarce ba, Sai yake gannin wani kyamarsa nema take ko har yanzu ita bata jin irin abinda yake ji game da ita, sai yake gannin a irin shakuwar da suka yi, a irin yanda suke nunawa juna kulawa ya dace a ce ta jima da yarda da wannan dan abin wanda yayi imanin shine kawai za yana hada shi da ita, aman cikin ikon Allah sai ta kauce masa ta ki karbarsa wai shi zata yiwa wayo ta tunkuda shi wajen wata ita kennan ba abinda ya dame ta Ba zai iya taba manta irin yanda tsohon saurayinta ya damko tsintsiyar hannunta, idan bai saba yin hakan ba ba zai taba gigin gwadawa ba duda irin rantse rantsen da yayi ta masa, a yanzu haka ya rage zama da Jamail dan sai zuciyarsa ke fada masa irin haukan soyayar da Jamail ya nunawa wujdane har ta furta masa yayi mata kankanta mai yiwuwa girman nasa ta gani ta yi furucin nan (😳🙄) Tunanin mai kake dear tun dazu ina baka jus din aman baka ma san ina nan ba? Muryar Alawiya ta katse masa tunaninsa yayi firgigit ya karbi jus a hannunta ya bi shigarta da kallo ta saka yar bintilar rigarta wace ta dan dara pant dinta ta zauna tana kalonsa tana yaba du kwanan duniya irin yanda fuskarsa ke kara haske (salar asubah a kan lokaci) Dan murmushi ya dakar mata, ya bude jus din ya kai bakinsa bai ce da ita komai ba ya dan fara sha yana ayana dama Wujdane dinsa ce a haka ya zauna yayi ta kalonta har garin Allah ya waye, Anya kuwa zai iya kara jan fushin nan????????? Ranar monday, ya kama sauran kwana uku kawai Wujdane ta tare Alaidine na zaune a park dinsa yana kallon motocin da suka fito sababi na sabon watan nan yana zaben wa.inda ya dace yayi oda a fara gwadawa da su su gani ko zasu shiga, yana ta karanta yanda makerinsu ya rurubuto masa yanda kowace take A hankali ya cire hular kansa, ya dan kara gudun ac domin aikin ba karami bane ya cire agogonsa dan ji yake yayi masa nauyi ya kara dan tatare rigarsa ya ci gaba da aikinsa da dan jus da faro a gefe sanyi karai yana dan kurba yana ci gaba da aykinsa Yar karamar wayarsa kirar samsung fara kar ta kuma daukan tsuwa, wannan wayar masu numberta yan gidansu ne kawai sannan yafi dangata mai kiran da anwar ne dan sunyi maganar zasu kirayi juna aman yayi kira daya biyu bai daga ba ba sai ya hakura ba, cike da jin haushi ya janyo wayar bai duba sunnan ba ya dana ya kara a kunansa da hannunsa na hagu na damar kuwa a kan computer bai yi magana ba Kana jina kuwa hello???????? Muryar Aba ta farkar da shi da sauri ya dago yana mai yin salama a wayar Yana bada hankalinsa sosai Aba ya ce" kana ta aikin naka ko tamkar agogo Elhaj Alaidine sarkin aiki Alaidine yayi murmushi yana sauraron Dadynsa yana dan shafa kansa kadan kadan alamun yaji kunyar nan Aba ya ci gaba" gidan nan fa an gama, komai har mun je da Momynku da auntynku sun ga yannayin tsarin gidan dan kayan da zasu kawo, sun nace su sai sun je dubai sayen kayan amaryar aman ni nace aa, domin a yanzu a kano an jima da ci gaba, abinda zasu tarar a dubai din akoyshi a nanma, lokoci ba zai isa su tarki tafiya dubai kafin yarewar ba shine Momynku tace ko a matsa ranar tarewar Alaidine bai san lokacin da ya ce na.am?? Tun karfinsa ba domin kunnuwansa suka cuce shi bai shirya jin cewa za.a ce a matsa tarewar Wujdane ba bayan baban tashin hankalinsa kenan tayi ta tare ta zo kusa da shi ko zai huta da rashin bacin dare da yawan tunani ba Aba yayi dan tsam , jin Alaidine yayi shiru ya ce" magana ce? Alaidine da sauri ya ce" aa Dad ba magana bace Aba ya ce" toh shine ni kuwa na ga aa, ba zai yiwu ana saka rana ana matsawa ba, a yanzun su tafi su sayo abinda yayi masu idan ya so daga baya sai su kuma zuwa su canzo harda ita dinma ina fatan ba takura Alaidine ya sauke wata nanauyar ajiyar zuciya ya ce" ba takura ko taya Dad, du yanda aka yanke Aba yayi murmushi daman ya san ba zai wani tanka ba ya ce" yawa sai ita dayar matar taka, idan ka koma itama ka bata wani abin mai tsoka wanda zai isheta ta canza kayanta harma tayi wani abin ka ji ko? Hakan zai kara wanzar da zaman lafiya a gidanka Alaidine ya amsa da insha Allah dad Haka Aba yayi masa salama ya shaidawa Mom yanda ya yanken haka za.a yi kawai Alaidine ya jima kafin ya dawo a nutsuwarsa, mamaki ne ya kashe shi irin yanda magana ta fito masa bai shirya ba kawai dan an ambaci Wujdane, Yayi murmushi yana shafa kansa da sajensa da ya tuna nan da kwana uku za.a kawo masa ita su yi zamansu a innuwa daya hankalinsa ya konta ya dawo waje guda Computersa ya kala ya yiwa baturen nan message cewa su hadu gobe su karasa maganar dan a yanzun komai ya kunce masa wata fitinar son ganninta ne kawai ya mamaye masa zuciya, ga waya aman girman kansa ya hana yayi kiranta idan har ba ita ce ta neme shi ta bashi hakuri kan irin yanda ta nuna halin ko In kula da shi Murna Alawiya take tana juyi na chek din da ya miko mata bata ma tsaya ta ji na menene ba Kudi ne har million biyar da sunnanta da nufin yayi mata kyauta, sai da ta gama juyinta yana kallonta shima da murmushin a fuskarsa dan kuwa du yanda kuke da ita idan kayi mata kyautar kudi zata nuna farin cikinta ne a fili, Dakatawa tayi ta dare cinyarsa, cike da murna ta ce" husband ni dai ba birthday dina bane, sannan ba lokacin tafiya maka bane bale nayi tunanin guzurin jama.ar da zasu tafi ne aka bani na raba da nawa, aman kyautar nan duka na menene? Alaidine yayai murmushi ya kara gyara zamansa ta saki jiki sosai a jikinsa tana ta lalubarsa sosai har ya dauko caji, ya ce" an gama ginnin gidan nan ne, wanda zaku tare tare da Wujdane, wannan ina so ki yi abinda kike da bukata idan zaki canza gadajenki ne duda akoy sababi aman sha.aninku na mata, idanma wani abin ne aman banda sutura da mota domin nayi maku odarsu, Tunda ya fara magana ta dakatar da dokin da take, ranta ya gama bacewa ta mike daga jikin nasa cike da fada ta ce" yanzu daman dan wannan ne har kake wani sakin murmushi? Kenan da gaske ne sai ta zo mun jera kishin da ita? Ita nan har macece banda farin mai zata nuna min? Du irin yanda nake kulawa da kai ina baka hakinka ashe bai isheka ba? Toh da ka bani million biyar ita din matar so fa? Nawa ka bata? Na tabata Abanka zai kara mata ne ko? Ko mai kake Idannuwansa kawai ya rintse yana mamakin mata, wai bata aike shi ba, bata biyarsa bashi, ba adini ba, dan kawai yayi niyar faranta mata sai ta buda baki ta yayaba masa magangannu haka, Mikewa yayi da zafin nama ya damko hannunta da ta juya zata bar masa wajen aman bata yar da takardar ba, ya juyota da karfinsa da niyarsa na bata mata rai wayarsa ta ma.aikata ta dauki ruri, Idannuwansa ya wurga ya ga sunnan john ne wanda suke maganar mota da shi Bai daga ba , ya juyo wajenta yana kalonta zuciyarsa na bugawa Hannun nata ya saki ya dauki wayar da sauri ya haura sama dan tuna maganar abansa na idan ransa ya baci yayi shiru ya daina daukan mataki a cikin bacin rai Alawiya nan ta zube tana kuka itama cike da kishin Wujdane, haka kawai bata son su kasance a waje daya da ita da Wujdane da Alaidine, tana tsoron su kasance a inuwa daya su raba kwana da Wujdane Gini ne na gani na fada, ginin da manya da yayan manya suka yi mangarinsa da mamakin lale dan zaki ya girma, ginnin da sosai Aba ya saka aka yi ta saukar alkur.ani dan idan aka ji ko aga ga mai shi baki kadai zai iya dirar masa, nanfa rayukan yan mata masu ji da kansu da yayan manya ya girgiza ya tashi suka fara haukan son kasancewa daya daga cikin matan mai gidan, ginnin da ko a kasar waje sai wanda ya ci ya tada kai zai gina shi, ya ginu, ya tsaru, ya kawatu, ya haska anguwar gre Mom ce da Aunty shafa da Marwa karama da Aliyu da Anwar ke zaune a katon falon bayan masu gyaran gidan sun gama jera komai da komai har setunnan kujeru sun kawata komai wanda falo daya ne tal tankameme wanda gyaransa sai an hadu sai dakuna a laye sannan babu etage duka plat ne aman irin gidan nan ne da ake cewa a tsakiya dan sam ba a kasa yake ba an wani dogale shi Anwar ya ce" tap ai fa masu kallon gidannan gonda su yi su gama dan kuwa na tabata gobe i warhaka mai shi ya garkame da kwado dan ba mai son hayaniya bane Aunty shafa ta ce" kai gaskiya nima ina goyan bayan ya rufe, ka ga gobe idan aka kawo Wujdane insha Allah muma sai mu dauke kafa kuma a bar yara su yi zamansu sai Fatan Allah ya kade du wani fitina Mom ta sauke ajiyar zuciya, tana tuna ranar da yayi rantsuwar ba zai yi aikin gwomnati ba sai dai ya nemi na kansa, duka duka abansa dubu hamsin ce ya bashi yace ya je ya juya dan kawai ya nuna masa ba zai iya haka da yarintarsa ba ya bari idan ya fara na gomnatin daga baya sai yayi kasuwancin aman cikin ikon Allah yau wannan ginin da take zaune a ciki da kudin Alaidine aka gina, Allah ya sakawa rayuwarsa gaba daya albarka, Kida ne ke tashi sosai daga dakin dake kusa da na Alaidine wanda Alawiya ta buga kai da kas cewar shi take so, ita da yan uwanta ne ke tayawa gyaran gadonta da dakunan dake cikin dakinta gaba daya suna ta murna ana casu Marwa karama ta kwabe fuska ta ce" Mom, dan allah ki fadawa mama tare da aunty Wujdane zamu tare aman fir ta ki zancen Aunty Shafa ta dafe kai ta kali anwar ta ce" Anwar ka lalasa min jikin yarinyar nan tun kafin ta saka min hawan jini Mom ta jawota tana fadin" ana me? Danma kunga ana dokin amaryar? Takwarana kyale su, da tayi yan kwanaki zaki dawo kema abinki ga dakinki ku yi zamanku da auntynki kin ji? Marwa ta lafe a jikin Mom tana sakin ajiyar zuciyar tsoro, dan idan da wanda take tsoro to bayan Anwar ne yanayinsa tsoro yake bata dan kuwa abinka da soja sai yana daure mata fuska sosai Haka suka gama bade gidan da turaren wuta mai kanshi, inda Alawiya ky din dakinta kawai da na falon aka bata suka tafi da na Alaidine da Wujdane bayan an kara yin sauka a ko.ina suka tafi sunaiwa ma.aikatan da aka zuba birjik a gidan salama Alawiya bata dauro alkhairi a zuciyarta ba, domin du irin tsaruwar gidan nan sai take kushewa tana fadin dan ya kara aure ne ya rantsatsa wannan gidan ya saka su ita sam bai birge ta ba inda a nan wata cousine dinta take mamaki harma tana adu.ar Allah ya sa ita yace zai kara ta ukun fa ita ai koda a ta gudun zata shigo ita a guje zata shigo wannan gida haka? Haka suka gama suka tafi da duban alkhairi na bajinta da tayi masu na su je su gwada tana gidan hutu Alaidine kansa ya ga kokarin ma.aikatan abansa, ya shigo sabon gidansa da bismillah ya kwana yana sallah yana godewa allah da rokon Allah ya sa su mora *RANAR KAI AMARYA* [2/1, 2:31 PM] Ummi Tandama.: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄 *40* WRINTING BY *SAJIDA* Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai, *SAJIDARKU CE* MARUBUCIYAR: *YAR MAHAUKACIYA* *DUK KARYAR KADA* *DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA* *NEMAN NA KAINA* ................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH.... Wani dan malulun abu ne ya hadiye har ta zauna bai samu arzikin kalo daya da ta yi masa ba Janet ce ta shigo ta shiga zuba masu abinci a nan cikin falon ba kan dining ba bisa umarninsa Abincinsu suka fara ci bayan ya yiwa kowace bismillah Aman Wujdane ko kallon gefen plat din bata yi ba bale ta yi niyar ci, Alawiya kuwa sai iya yi take yi masa tana ta jansa da hira tana faman fadin honey Sarai ya lura da yanayinta, a kasan zuciyarsa yake jin ba dadi ko kadan aman shima yana cike da irin yanda ta yi watsi da lamarinsa bata wani damu da shi ba Bayan sun gama karyawar, yana lure ko jus ko ruwa ba abinda ta taba hakan kuwa bai yi masa dadi a ransa ba Gyaran murya yayi, ya gyara zamansa bayan ya dan kara matsawa daga gefen Alawiya dan ta mugun matse masa waje yana mamakin wannan sabon salo da ta fido a yan kwanakin nan, Cike da nutsuwa, da dora doka ba alamar wasa ya fara magana kamar haka" Na tara ku ne a nan dan mu kara jadada cewa zaman aure ya hada mu, zaman aure koda daga ke sai mijinki ne yana bukatar hakuri da fahimtar juna da kawar da kai da yiwa juna uzuri ta hakan sai zaman lafiya ya yiwa kansa matsuguni a tsakaninmu Alawiya, ga Wujdane, Wujdane ga Alawiya...gaba dayanku matana ne, ko wace tana da ikon gyara gidanta idan ta so zaman lafiya, Wujdane , Alawiya yayarki ce, ina so ki girmamata ki bata girmanta ku zauna lafiya Alawiya Wujdane tamkar kanwa take a wajenki, ki sakata a hanya madaidaiciya ki kasance mai hakuri da ita ko gidanna zai zame min wajen hutuna Sai maganar kwana , ance idan aka kawo amarya takan yi sati kafin a dawo raba kwana ko? Da sauri Alawiya ta dago ta sauke idannuwanta kansa ta ce" au kennan budurwa ce?? A tare suka zuba mata ido, Alaidine sai da gabansa ya fadi, shin Alawiya ta san wujdane ne daman? Ita kuwa Wujdane mamaki ya kasheta a zaune, wannan wata irin banzar tambaya ce? Toh idan ita ba budurwa bace karuwar uban wane ce? Alawiya ta daga kafadu irin bata sani din nan ba, ta ce" aman wancen zuwan da ka yi gidan ba wajent kake kwana ba? A hakan baka yi mata satin ba ko so ake tun ba.aje ko.ina ba a fara nunan iyakata??????? Alaidine ya daga mata hannu, dan kansa ba karamin daukan ciwo yayi ba da ta danganta abin sonsa da nufin ba budurwa ba duda shi ya fara a zuciyarsa shi ya san da hakan aman bai taba yin irin maganar nan da ita ba, ta ina ma ta samu wannan maganar da a duniya itace ta uku dake bata masa rai dake tayar masa da hankali? Cikin bacin rai domin idannuwansa har sun canza kala ya ce" bafa zan dauki tsunguri tsoma da some somen son tayar min da fitina a muhali ba, da kike fadin hakan kina da shaida ne? Sannan da kike maganar na kwana a wajenta tarewa ta yi ne? Bana so! Dan haka sai na yi mata sati gudan kafin a dawo maganar kwana dadaya da zakuna yi Tunda suka fara magangannunsu du irin ci kashin da aka yi mata bata tanka ba sai a wannan lokacin da ta dago da dara daran idannuwanta da suka dan canza launi na bacin rai da jin haushin bata shako wuyan ALAWIYA ba ta nuna mata eh uar iskar ya aura ba, ta saukesu a fuskarsa wanda ta hango karara kamar maganar da ta fada shima yana kokonto a kanta, a nan ne abubuwa suka ringa fado mata a ranta, a nan ne ta samu amsar tambayarta na dalilin da ya sa du irin kisancin da zasu samu yake gudun kokarin yin wani abun da ita A hankali ta ce" eyah, ba sai anyi ja in ja da maganar nan ba fa, na yafe kwanakin, na yanzun ma ki ci gaba da dauka du ranar da kuka ga ya dace sai ku bani Tana gama fada ta mike ta kama hanyar dakinta wanda a tare suka bita da kalon mamaki, Alawiya ta so ta biye mata su fara shuka rashin mutunci ta yayaba mata magana tun yau aman sai Wujdane ta yi mata ba zata Cike da kunan Rai Alaidine ya mike ya bi bayanta har kafafuwansa na sarkewa da juna Yana shiga ya tarar da ita ta cire hijabin da doguwar rigar ta daura tawul tana kokarin cire pant dinta dan ta sake yin wanka ta konta ta huta Turo kofar da yannayin shigowar nasa ne ya sakata dagowa da sauri hana kalonsa A tare suka kwalalo ido yayi saurin juya bayansa gabansa na faduwa tamkar zai tsinke ya fito Bangaren Wujdane ma da sauri ta warci hijabinta ta saka ta yi kicin kicin da fuska ta ce" Malan kuma lafiya? Ko abinda kuka yi ne bai isheku ba ka biyo ka kara wannin? Alaidine ya juyo da sauri ya nunota da yatsarsa ya ce" Wujdane kinga ki daina wulakantar da ni , ki daina ci min fuska, dan baki damu da ni ba dan ban dadaki da kasa ba shine har zaki wani ce kin wani yafe kwana da ni? An gaya maki nima idan na kwana a dakin naki zan nemi wani abin ne a wajenki? Ina so in fita a hakinki ne aman ke kina kokarin botsare min? Danme baki bani wani mahinmin mahinmanci ne? Wujdane ta yatsina bakinta wai itace ma mai laifi, dan kawai ta ce ta yafe, ta sasauta muryarta ta ce" eyah ba haka nake nufi ba, na ga ai ta fadi gaskiya ne sanin gaskiyar ta fada ya saka na goya mata baya harma na furta na yafe, ai dan karna takuraka ne na jima da sannin ba abinda zaka neman ko ba wannan wace ta shigo a baya da wace aka tarar ai ba daya bane, rikon mace biyu ma ai sai a hankali, Ni nace na yafe ba da nufin cin fuska ko wani abin ba, na bar mata kwanakin da nawa da natan ta hade Tunda ta furta kalmar Alawiya gaskiya ta fada na maganat ita ba budurwa bace ya daina fahimtar yarenta, hankalinsa ya gama tashi, shi kam ya jima da sakawa ransa hakan aman a yanzu da ta furta masan sai yaji du duniya bashi da wani farin ciki, Du hasken fuskar Wujdane sai ta dawo masa bakikirin a idannuwansa ya ji lumfashinsa na garwaya da tsananin bacin rai da muradin sannin wanda ta baiwa kanta har take ikirarin hakan ma kunyar Allah ba tsoronsa Taku biyu yayi ya damki wuyanta da hijabin, hakan ya saka tawul din faduwa daga ita sai hijabinta a jikinta ya jata har jikin bangon dakin , muryarsa ta canja dan masifa ya ce" WuWujdane, uban wa kika yarda ya keta maki hadi har kike maimaita min? Ki fada min wani dan akuyan ne ya zo maki har kike maimaita cewar kin yafe? Wujdane danme kika yi min haka? Danme kika zabi na ringa kwana ido biyu ina zubar da hawaye da girmana? Wujdane fahimtar da kika yi inai maki matsanancin so bai isheki aya ba da zaki kiyaye furtan wani ya taba zuwa wajen da aka halito min? Bakya tausayina ne ke? Wujdane na zo da niyar just nayi kissing dinki kika zile min dan me? Wanda kika yi hakan da shi shine kika fi so ko ya fini zama namiji ne ? Ko Wujdane sai an biya ki ake taba jikinki ne ban sani ba? Da hannu daya ya riketa aman ta kasa kwatar kanta, banda kakari da take yi tana jujuya idannuwanta sai wani hawaye da ya ziraro mata na wahala A kasan makoshinta take furta "aa aa aa (Wujdane an ji shaka) Jikinsa ne ya ji ya yi masa wani nauyi, hakan ya sa ya cikata ya tafi luuu ya kife nan kusan bed dinta ya dora hannunsa biyu a kansa ya rike sosai idannuwansa a rintse Wujdane da ta dawo hayacinta ta nufo shi da sauri ta dago kansa ta dora a jikinta tana rizgar kukan da ta rasa dalilin yinsa,. ........a hankali take furta" ka tuna da hadisi wanda yake yi mana nunin zato zunubi ne koda ya kasance gaskiya ne, Karka manta koyarwar adininka wato zurfafa tunani da kuma daukaka fushi ko kiyaya, Alaidine, bani da bakin da zan iya furta maka wata kalmar da zaka yarda da ni, aman ina so ko gobe zaka yi furucinka cikin bacin rai ka tuna cewar nima mutun ce, musulma ce, ina da gatana, sannan du talaucinmu kudi ko wani abin ba zai saka na je na baiwa wani kaina ba na cire maka kadara, Alaidine karka yanken hukunci ba tare da ka san wacece ni ba, har yanzu sunana da gudanmu da yanda wasu mutanen ke fasara ni ka sani, ka yi hakuri karka sakawa kanka ciwon kai sannan ka tayar da ciwon da ya jima bai tashi ba, ka yi hakuri koda baka son na zauna a gefenka ne a gidanka ne sai na kara gaba da ya kasance ni mace ta biyu na nayi imanin *nafi ko wace mace sonka* a duniya zanyi sanadin shigarka a kunci ko da yaushe, ka yi hakuri ka sanyaya zuciyarka Alaidine, a yau yau a yanzu zan bar maka gidanka sannan zan je na sanarwa Aba nice nan na nemi hakan ba laifinka bane Alaidine domin ka sani shi mutun idan ana sonsa farin cikinsa ake nema masa, du sauran su biyo baya ne Du abinda take fada Alaidine na sauraronta, har lokacin da ta shiga yinkurin tashi tana mai tabatar masa zata yi nisa da shi Da sauri ya mayar da ita zaunen, ya kankame cinyoyinta ya cusa kansa a hijabinta, ya kamo hannunta na hagu ya dora saitin zuciyarsa, Murya a shake ya ce" kina jin yanda take buga min, na jima ban ji emotion din da yake mitsa min ita ba, kina jin kuwa yanda take duka, kin gama zagayeta Ki zauna da ni, ki yi hakuri ki kula da ni My Wujdane Sai.kawai hawaye ya shiga bin kuncinsa wani na bin wani A haka ta janye kafafuwanta ta silale kusansa ya kankameta a jikinsa suna sakin ajiyar zuciya ( Alaidine bai dai daina yarda cewar Wujdane a rufe take ) Wannan kennan Yau kwannan Wujdane hudu a gidan Alaidine, Shakuwarsu ta yanzu ta zarce ta baya nesa ba kusa ba Du irin sa idon Alawiya ta dan daga dan ita ke gannin abinda ranta zai bace domin ko a falo baba Alaidine kan jawo Wujdane a doguwar kujera idan yana konce ta hau kusansa sosai ta dora kanta a kirjinsa yana shakar kanshin turarenta yana dan shafa hanayenta da suke tamkar fatar mage wani irin santsi da taushi, Hakan na saka su su duka a wani mugun yannayi wanda nan da nan idannuwansa zasu canza launi du yannayin jikinsa ya tona shi ta hanyar nuna bukatunsa, itama takan fara mika wace ta kasa gane ko ta mecece, jikinta ya mutun mata, ta fara hama bayan ba baci taje ji ba ba kuma yinwa ba, aman ko kiss a baki bai taba zuwa nema ba dan yana cike da fargaba, yana gannin su duka sun fara alamar bukatuwa yakan yi dabarar ko daga waya ko ya fice da nufin yana zuwa har sai ya dan fara nutsuwa kafin ya waiwayeta, Yau ta kama lahadi, Wujdane ta gama kimtsa kayanta da ta wanke abinta da hanunta bata saka a mashine ba, ta daura tawul ta yi wankanta ta fito ta yi salar azahar , Ta mike ta cire hijabin ta konta da yar doguwar rigarta ta baci ruwan pink tana tunanin ko Alaidine ya dawo daga fitar da yayi wajen gaisuwar rasuwa da aka yi a anguwar Baci ne ya dan fara daukanta wanda tayi juyi sai jinta ta yi a jikin mutun, ta bude idannuwanta da sauri sai ta ga Alaidine ne ya konta a gefenta Shigar jikinta ta dan bi da kalo, ta yi kananta sosai domin gaba daya cinyoyinta a waje suke aman sai ta ja bargo cikin dabara a tunaninta bai ankara da ita ba ta dan rufe har daidai kugunta A hankali ta furta har ka dawo??? Alaidine ya gyada mata kai kafin ya ce" har na yi wanka, i miss u Ta yi murmushi, wai gata ga shi yana fadin yayi missing dinta, Jin ya jawota kirjinsa ne ya saka ta fahimci rungumar ce ake bukata dan haka sai ta saki jikinta a kirjinsa dan ta san ba abinda zai yi mata Alaidine dake da dan gajeran wando yayi saurin rintse idannuwansa jin yanda ake dan harba masa anai masa :::::dil.....dil....dil😳, Ya dan shafa bayan Wujdane sai ya ji har daidai inda pant dinta ya tsaya domin rigar nan ce mai shefen santsi wace ido na iya gannin abinda ta boye hakama hannu na iya ji idan ya laluba Da sauri ya maido hannun nasa wajen gashin kanta yana dan shafawa yana sinsinawa, yana matukar mamakin yanda a koda yaushe ya rabo jikin Wujdane sai ya ji tamkar ya suma da bukatuwa ko dan tana sabuwa a wajensa ne ko mai Igiyar yake ji ta taurara, bakinta na ambaliyar amai mai haske wanda yake kara tabatar da lafiyarta da bukatar aikata aiki Lumfashinsa ya fara fitar sauri, Wujdane dake konce daidai zuciyarsa ta dago da sauri tana kalonsa ta ce" Yaya baka da lafiya ne? Sometimes sai na ji bugun zuciyarka ya tsananta bayan da farko ba haka kake ba Idannuwansa ya rintse da wata kunya da ta kama shi, somin dai du yarinyar da ta san namiji karshen sani zata fahimci halin da yake ciki aman sai Wujdane ta ringa raina masa wayo ta hanyar yi masa tambayoyi kamar wace ba abinda ta sani Mayar da ita yayi kirjinsa ya rungume , dan ya kasa furta mata ba komai din ma A hankali jikinsa ya fara daukan zafi, wanda ita dake konce a samansa ta fara jin hakan, Hannunta ta saka a cikinsa a hankali ta daga rigar wajen cibiyarsa ta dora hannunta da niyar yin sama da hannun nata dan ta ji ko zazabi ne ke shirin rufe shi wanda hakan ya saka shi dan zabura bai san lokacin da a fili ya furta " *Wayo Alahna* ba Da sauri ta mike zaune ta dan ja bargon tana kalonsa da tsoron kar aje bashi da lafiyar ne? Ta furta" baka da lafiya ne yaya Alaidine? Bata kai da karasa tambayarta ba, ta ji gadan gadan tamkar kura ya wawuri bakinta yayi masa riko tamkar marayan zaki ya shiga tsotsa tamkar za.a kwace masa Yanda jikinsa ke rawa, hanayensa na kokarin cire mata rigarta lumfashinsa na sauka a hancinta Da sauri ta saka hannayenta biyu cikin mugun tsoro ta ririke rigarta da yake kokarin cirewa, gashi bakinta a cikin nasa ta kasa fitar ds kalamanta, hankalinta ya kai kololuwar tashi tsoro ya bayana a act dinta, bugun zuciyarta ya tsananta da tsananin tsoronsa haka idannuwanta ke yawo suna kokarin sai sun shiga nasa ko zai farka ya gane da yake kokarin aikata hakan . ...........ni kuwa nace wa ya gaya maka Alaidine , kai har ka isa ka kunacewa mace guri haka du muninta koda ba komanka bace ai mace da namiji tamkar auduga da ashana ne, aman kayi gagawar sakawa, tambayar a nan itace WUJDANE zata iya kwatar kanta ne ko kuwa a kada mata ta mutu ta lalace?🤣 sannan mu yi gangamin zuwa gashi🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀ [2/1, 2:31 PM] Ummi Tandama.: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄 *39* WRINTING BY *SAJIDA* Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai, *SAJIDARKU CE* MARUBUCIYAR: *YAR MAHAUKACIYA* *DUK KARYAR KADA* *DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA* *NEMAN NA KAINA* ................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH.... Baci take na mamaki, tun bayan salar asubah aunty shafa wace ta kwana a gidan ta bata kari da kwayar maganin baci daya ta sha hakan ya bata damar rama bacin da ta jima bata yi ba dalilin tunani Bacinta take hankali konce saman lalausan gadonta da rufar bargonta mai laushi cike da dadadan mafarkai Wasa wasa sai da ta kai salar la.asar tana baci Mom da Aunty Shafa da Inna wace Mom da kanta ta je dan ta yarda ta zo ta kara yiwa yarta adu.a suna dan zantawa, duda bata fiya yin magana a zancen ba aman ta bayar da hankalinta kansu can kasan zuciyarta kuwa tana mamakin bacinnan ma Wujdane sannan ta cika da mamakin yanda ake shirye shiryen tarewar wujdane din a gidan mijinta hakan ya kara kontar mata da hankalinta ta saki jiki tayi amanar yarta ta samu karbuwa Mom ta kali aunty Shafa ta ce" shafana ki dubo min yarinyana plz, bacinnan bai isa haka ba kuwa? Aunty shafa ta mike tana murmushi ta ce" aunty ai tayi bacin yana da kyau, bara na koma na gano Tana tura dakin ta tarar Wujdane saman salaya ta gama salolinta tana karanta alkur.ani cikin zazakar muryarta sannan idannuwanta cike da hawaye Murmushi tayi a ranta tana ayana baiwar Allah du a tsorace take zata yi nisa da gida Bayin ta shiga bayan ta dauko yan jarkoki na hade haden da tayi na wannan rana, ta koma bayin ta tara ruwan wanka masu dumi sosai har suna hayaki dan itacen da za.a zuba a cikinsu su dahu, ta rufe wajen gudar ruwan ta dawo Wani inji inji ne, wanda ake saka mutun sai kansa kadai a waje aka sakata a ciki, hayakin siracinsa na dukan jikinta har kasanta domin zindir take dake cikin wanda ke watso hayakin mai kanshin lemun da aka yanyanka a cikin ruwan hakan ya saka jikin ya dauki kanshin lemun da kuma santsi na mamaki Idannuwanta take rufewa dan zafin wannan siraci har aka gama ta fito da tawul dinta ta shiga bayin ta shige ruwan zafin bisa umarnin aunty shafa Har dan ihu take na azabar zafinsaduda ya mugun huce aman fatar jikinta ta dawo tamkar ta jariri hakan ya saka kadan ta ji wuya tana ficewa a hayacinta Bata gama tantance abinda take ciki ba aunty shafa ta shigo bayin ta hade rai danma karta ce zata fice a ruwan ta shiga kunce rufkar da ta yiwa gashin kanta ta dauko sabulun wanke kan mai hade hade sai kanshi yake ta shiga wanke mata kan nata da shi sosai har tana lumshe ido dan tunda ta fara yi mata gyaran jikin rabonta da kanta ya samu ruwa Ba su su fito a bayin nan ba sai da suka kusan dauke minti talatin Wujdane ce a gaba da labcecen tawul dinta, Aunty a bayanta dauke da kaskon turaran wuta da tayi mata turaran tsuguno Suna fitowa aunty ta jawo wani lakadeden bargo ta sakata tsayawa ta kara wara kafafuwanta ta saka mata turaren jiki mai sanyin kanshi wanda ta rufe mata har kanta da damshin ruwan wankan nan a jikinta turaren nan ya bigeta sosai har sai da ta dawo ta gaji da tsayuwar kafin Aunty ta bude mata rufar Ya salam kawai nake iya furtawa domin fatar Wujdane yanda ka san fatar jariri sabon haihuwa haka take daukan ido da haskawa, idan ka latsa kuwa sai kayi zaton jini zai biyo yatsar naka Kanta a sade tana dan yamutsa fuska na an dameta gashinta ya bazo ya kare fuskar nata aman ya dan saka duhu a hasken nan nasa dalilin turarukan da yake sha na gyaran gashi da mayuka kala daban daban Zama ta yi a bakin bed ta karbi abincin da aka miko mata ta shiga ci cikin nutsuwa nan aunty ta fice dan ta shigo da mai mak up din da aka kirawo da su Mom Abincinta take ci hankalinta konce duda yanda take ji gabanta na dan faduwa, sai ruwan garaigarai da dafafen sasaken baure da mazarkwaila da sauransu da aka dafa mata tana dan kurba a haka aka turo kofar suka shigo Dago da kanta ta yi jin muryar Mom sai idannuwanta suka sauka a kan Mom da innarta Wangale baki ta yi tana murna ta ce" Lah innata, Sannan ta bi shigar innar nata da kalo, dinkin bugagiyar atamfa ne ta sha wuyanta da sarka da yan kunaye da awarwaro masu shegen kyau, kai harta innar tata sai ta ga ta dawo wata fresh🤣 Zama suka yi ai kuwa ta shige tsakiyarsu ake ta labari, innar kanta ta tsorata da yanda kyan Wujdane ke daukaka da wani kwarjini da take fitarwa, sai tayi hamdallah a can kasan zuciyarta ta godewa Allah da kuma iyalan Aba Sai bayan sun gama salar magariba mai mak up dinnan ta dan gyarawa Wujdane fuska , ba wani makup ne ta yi mata ta cika mata fuska ba, an dai gyara mata girarta an saka mata dan jan baki kalar kasa mai man lebe sai kwali da aka daidaita aka bi mata a idannuwanta Gashin kanta aka shiga gyarawa, coiffure ne aka yi da shi inda ta dunkule shi a tsakiyar kan ya bayar da kala ya mugun fito da fuskar yayi mata kyau sosai Ana tsaka da kimtsata Aisha ta karaso sai matar Anwar itama da yaranta sai wata datijuwa makociyarsu itama tana falo Lafaya ne irin na larabawa kalar ja mai ratsin fari sai duwatsu masu kyalkyali birjik da suke haskakata aka fitar, irin sababin bugowar nan ne na dubai Wani yan kunaye ne siraru masu dan tsayi na gwal aka daka mata, su kadai ba.a saka mata sarka ba ba.a saka mata wasu awarwaraye ba Bra fara kar aunty Shafa ta bata da pant shima fari kar wa.inda suke zubar da kanshi inda Wujdane ta labe ta saka tana ta sine kai dan su duba kin fita suka yi sun saka ta a gaba Doguwar riga mai siririn hanu mai santsi mai bin jiki fara kar mai shigen rigar baci ne aka bata ta saka wace za.a yana lafayar a sama, Rigar sai ta bi jikinta ta lafe sosai ta fitar da ainahin kirar jikinta wace ko mace sai tayi mata kalo biyu dan karya ne ki yi mata daya ki kawar da kanki sai kin kuma ko dan ki tantance sannan ki sarawa ubangijin da ya halici halitar nan AUNTY shafa ta gyara mata ta yi mata daurin dama, aka rufe mata har kanta, Aisha dake dauka da katuwar wayarta android iPhone7, wani irin shauki da murna sun cika mata zuciyarta su Auntu da Matar anwar suka shiga yi mata wanka da ruwan turare bayan wanda ke jikin tufafinta da fatar jikinta (kun san du yawan turare baya saka amarya mura koda mai huka ce baya tashi wannan nice kat), Kanta a sade, ta kasa tsayar da hawayen dake ziraro mata daga idannuwanta a lokacin da aka tsugunar da ita a gaban iyayenta, wato mahaifiyarta da mahaifiyar mijinta wa.inda su kansu zuciyarsu ta karaya sun kasa wani kwakwaran motsi Wujdane ji take yaune za.a rabata da gidan iyaye, wannan rabawar da za.a yi mata ita tafi daga mata hankali domin ta farko bata wani damu ba, aman a wannan ji take tamkar ba zata kuma ganninsu ba sosai take jin tashin hankali na rabuwa da iyayenta Mom ta yi gyaran murya a hankali ta ce" y.ata, a zaman da nayi da ke baki taba bata min ba, kin kawo min haske a cikin gidana, kin sha shayar da ni mamaki, Wujdane ina jinki a raina tamkar yar da nayi ta nema ban samu ba sai gaki Allah ya bani, ki rike jawaban da auntynku tayi ta yi maki ki rike hakuri sosai Wujdane, Allah yayi maki albarka sannan ki yafe min nima kin ji? Ai kuwa wujdane har kankame hannayenta take dan kuka, kukanta take sha harda haki, inda suka bi inna da tayi mata jawabi Inna ta saki murmushin karfin hali ita kam daman basu kawota ba dai take ji tamkar zata kara rabuwa ne da Wujdane, Ajiyar zuciya ta kuma saki ta ce" Mai zan ce? Ai hajiya kun gama yiwa Wujdane fada kun fada mata komai, ni Wujdane abinda zan kara fada maki shine *ki rike mijinki, ki bi mijinki, ki yi masa biyaya Wujdane , ko mai zaki zama a gidan duniya ke Wujdane koda shugabar kasa zaki zama karki yarda karki amince ki daga muryarki sama da ta mijinki, ke ba kowa bace sai darajar da ya luluba maki, ke ba komai bace idan ba shi, kyau kuwa da kuruciya masu gushewa ne, ki rike masa mutuncinsa ki kare masa hakinsa, daman ban sanki da kawaye ba karki yarda ki fara ki rike kafafuwanki a duk inda yayi maki umarni da zama, ki kasance mai yi masa godiya da girmama shi* Allah ya yi maku albarka Sosai suke dan share hawaye har Aunty ta samu ta mikar da ita suka kamota suka nufi bangaren Aba wanda yayi mata nasiha daga shi sai ita yayi tayi mata godiyar da ta rasa inda zata tsoma ranta dan kunya ya salameta suka fito Dankareriyar mota ce fara kar, sabuwar limousine, mai tafi da gidanka mai bakin gilas, nan aka shiga da amarya inda Anwar ne direban sai gayar da yayi na abokansa sojoji da yan anguwar suka layu da motocinsu aka saka ta amaryar a tsakiya ake tafe a hankali A haka suka shigo gidan su ba tare da sun san har an karaso ba dan tafe take kamar bata tafiya Abin mamaki shiru kake ji sai ma.aikatan dake dan kai kawo sai tsuntsaye dake karansu A hankali aka fitar da Wujdane daga motar, gaba dayanta a jikin Aunty take tana sakin ajiyar zuciya tana biya karatun dake dan tashi a wayar aisha wace ta sako bakara dan samun nutsuwar wajen Du Yanda Aunty ta rada mata take bi, a hankali take ta hailala a kasan zuciyarta bata buda idannuwanta ba bata san mai ake ciki ba inda muryoyin mutane ke furta waouh masha Allah har aka shige falon nata da it wanda matan kawai suka shiga sai Anwar da ya daga kansa yana kalon window din Alaidine wanda ya tabata yana ciki duda duhun dakin Karasawa suka yi, sauran suka zauna a falon Aunty ta shige da ita da AISHA ainahin dakinta wanda yake facin din nasu Sosai Aunty ta kara yi mata nasiha, ta kara jadada mata hakuri Haka tana ji tana ganni suka kama hanya suka fice suka barta inda ta fashe da kuka mai cin rai Fitar motocin ya saka shi sakin labulen ya juyo yana kallon Alawiya da ta sha shigar kananun kayanta ta sha mak.up dinta ta tardo shi ta fara kokarin kuna shi, gannin hakan ya saka shi mikewa ya yakice ta ya dawo wajen windows din, hakan ya kona ranta har ta fara sharar hawaye tana mitar tunda yayi auren nan yake haska mata wulakanci Ajiyar zuciya ya saki yana kalonta, wani farin ciki na cin kasan zuciyarsa yau kam sai dai tayi hakuri dan ba zata iya bata ransa ba Murmushi ya sakar mata ya ce" kin yi kyau Alawiya Da sauri ta dago tana kalonsa, bai taba yaba adonta ba sai yau maimakun ta ji dadi sai ta kushe a ranta take ayana dadin baki ne dan ya zile wajen wacen mai sifar aljannun Hannayensa ya watsa ya ce" kindai san yau ba kwanankii bane, dan haka ki bi abin a tsare bana son fitina Yana gama fada ya dauki laptop dinsa ya fito baban falo ya zauna Akawiya gadi ya same ta, domin du wasu yan mintuna sai ta fito ta nufi kicin ko ta dawo wajen frij ko tayi ta dan zagayenta inda yake zaune yana kamar mai aiki a laptop dinsa yana ta aikin tunanin ya je gareta ko kuwa ya tsaya ya ga idan har ta damu da shi kamar yanda take gwadawa itama? Wujdane sai da ta kari kukanta har kanta yana sara mata kafin ta mike ta dauro alwallah Sallah ta tayar ta shafa.i da wutiri, bayan ta gama ta dukunkune a kan salayar cikin hijabinta , tun tana jin sanyi sosai har ta dan sake baci yayi gaba da ita a takuren nan Bacin falo yayi, yana ta jan tsaki har karfe uku Alawiyarma bata konta ba dadi ya cikata gannin bai shiga dakin Wujdane ba a fili ta furta"indai wulakancin Alaidine ne kema zaki sha shi tunda kin shigo Kiraye kirayen sallar asubah ya tayar da shi daga konciyar takurar da yayi, ya mike a hankali ya nufi dakinsa dan dauro alwallah, itama Alawiya a lokacin tayi konciyarta dan ta tabata yanzu kuma safiya ta waye sai dai wani daren Bayan Wujdane ta gama azkar dinta sai ta kasa komawa baci jiki da sabo, sai ta yi zaune cikin doguwar rigar shadar da ta saka wace ta sha aiki har ta gaji, Ji take tamkar ta hadiye zuciya a kadan ranta tana furta" na ga iyakata, na san matsayina kuma zan nunawa mutun nima inada tawa darajar dan talauci ba hauka bane kuma ban kamu da mugun son da zai saka na ci kashi ba Sai wajen karfe takwas ta gota ta ji ana dukan kofar nata, irin bugun nan na sauri hakan ya saka ta diro bata daure kanta da dan kwalin bama ta bude kofar tana kalon mai bugawar Tun daga kanta har kafarta alawiya ta bi da kalo, sai ta saki wani dan murmushin wulakanci ta ce" du tanadin nan sai aka kwana da pillow, mijina yace na kirawo ki domin a gajiye yake ya kwana ibada jiya , ta kashe mata ido daya ta juya Wujdane kam ta ji ciwo a zuciyarta fiye da tunanin mai karatu, ta juya ta dauko hijan dinta kalar adon shadar ta saka mai hanaye ne ta fitar da hannun waje A hankali take takowa kanta a kasa har ta karaso inda take da yakinnin nan suke dan jin muryarsu kadan kadan Salama tayi ciki ciki wanda hakan ya hautsina nutsuwarsa A hankali ya dago da kansa ya sauke a fuskarta, du irin yanda ta kai da hada rai ta gama tafiya da imaninsa [2/1, 2:32 PM] Ummi Tandama.: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄 *42* WRINTING BY *SAJIDA* Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai, *SAJIDARKU CE* MARUBUCIYAR: *YAR MAHAUKACIYA* *DUK KARYAR KADA* *DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA* *NEMAN NA KAINA* ................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH.... Kalonsa ya mayar wajen Mom wace ke dan share hawayenta kanta a kasa tana jin irin yanda zuciyarta ke kewar iyayenta, ajiyar zuciya ya sauke ya ce" Marwa Dago da kanta ta yi ta sauke idannuwanta a fuskar mijinta, mutumen da ya daukaka darajarta, ya kare mutuncinta, shi kansa yayi nesa da iyayensa a dalilinta ya watsar da gatansa dan kar rayuwarta ta tagayara ya rungumeta ya rungumu abinda Allah ya basu A hankali ta sakar masa dan murmushi tana kokarin boye damuwarta ta amsa da " na.am Aban Alaidine Ajiyar zuciya ya sauke ya ce" ku tashi mu waywayi gida Wata irin zabura ta yi ta mike tana dan firfito idannuwanta ta ce" Aban Alaidine da gaske kake? Zamu tafi gida yau? Ya lumshe idannuwansa yana lalubar number Alaidine ya ce" kwarai da izinin Allah zamu tafi gida yau Fita yayi yana amsa kiran Alaidine wanda yayi masa umarnin su hadu a gidan kakaninsa Alaidine dake zaune yana feeding din Wujdane bayan ya takura mata sai ta ci abincin ya dan yi tsam da cokalin abincin hanunsa ya fada duniyar tunani A hankali take kalonsa, a kasan zuciyarta ta karanci ya shiga damuwa bayan yanzun yana cikin farin ciki marar musaltuwa Duda ranta a jagule sannan yannayin jikinta har yanzun da dan rashin kwari duba da yanda ya zo mata sai ta ji ba dadi gannin yanda mood dinsa ya canza A hankali ta dora hannunta saman nasa mai rike da cokalin , hakan ya saka ya dago idannuwansa ya zubasu cikin nata Gabanta ya yanke ya fadi ganin yanda lokaci daya idannuwansa suka yi jajajir saman goshinsa jijiyoyin suka mike suka yi rado rado da su Da sauri ta saki hannun tana dan ja da baya kadan domin ta tsorata da yannayinsa Ajiyar zuciya ya sauke yana kalonta bai daina binta da kalo ba A hankali ya mika mata hannayensa yana nufin ta matso gareshi A hankali ta matso daf da shi kanta a kasa hakan ya baiwa gashin kanta damar zubowa gefen fuskarta sosai Hannunsa ya saka ya dage gashin nata ya jawota a hankali ya rungumeta a jikinsa ya saki ajiyar zuciya Bata hana shi ba sai ma kara shigewa jikinsa da ta yi tana jim yanda zuciyarsa ke bugawa Sai da ya tataro nutsuwarsa ya ce" Aba ne yake kirana, zamu tafi gidan iyayensu shi da Mom Da sauri ta dago da kanta tana kalonsa, a kasan zuciyarta take furta dole ya shiga wani yannayi aman sai ta dane abinda take tunanin ta dan saki fuskarta ta ce" masha Allah, ai abin murna ne wannan Allah ya amshi adu.ana Kalonta yake da mamakinta ya dan kamo habarta ya dago da fuskarta Idannuwanta ta saka cikin nasa da yannayin na eh hakan take nufi Idannuwansa ya dan kankance yana kokarin cire nasa a cikin nata domin idannuwanta na hadasa masa jin wani yanayi a jikinsa ya ce" har adu.a kike su je ? Gidan da aka kore su? Toh idanma sun yi niyar tafiyar ai ba dole ba sai da ni ko? Kin manta dalilin karuwata da aka samu aka kore su? Idan suka koma su kadai ai za.a fi maraba da su ba wai da ni........ Kafin ya gama fadar maganar ta dora yatsarta a lebensa tana jifansa da wani kalon Bata ce komai ba ta mike a hankali ta dauko masa ky din motarsa ta karaso kusa da shi A hankali ya mike tsaye inda ta dawo daidai da kirjinsa tsayinta ya tsaya iya nan Idannuwanta ta sauke a fafadan kirjinsa , kanshin turarensa ya mamaye hancinta ta lumshe idannuwanta a hankali ta mika masa ky din tana dan kalon yanda botiran rigarsa biyu na sama suke a bale hakan har ya baiwa gashin dake kirjinsa damar lekowa baki yana sheki A kasan zuciyarta ta ji wani kishin ya fita a haka aman ba zata taba nuna masa ba dan kar ya saka cewar ta sauko da sauki haka Ky din ta kara damka masa a hannunsa ta ce" ka je kiran Aba, ka yi hakuri ka kai zuciyarka nesa, Allah da ya haliceka yafi kowa sannin dalilinsa na yin haka da rayuwarka sannan a yanzu da ya fito maka da wannan hanyar ya fi kowa sannin me ya lulube a cikin hakan Magana take shi kuwa kalon lips dinta yake, yana kara godewa Allah da ya bashi ita a matsayin matar aurensa ta sunna sannan ya saka masa kaunarta ita kuwa ya bata damar girmama shi a yanda yake ba dan arzikinsa ba ko baiwar halitarsa ba Bata gama maganar da take ba ya dago da kanta ya hade bakinsa da nata ya shiga kissing passionately Tsit ta tsayar da maganarta tana dan zaro idannuwanta domin bata yi tsamanin hakan ba Maimakun ya cikata ya tafi sai kawai ya juyo da ida a hankali yana daga mata tafiyarta yana kara matsawa da ita har wajen kujerar falon ita bata sani ba sai ji ta yi ta fada sannan ya rufa mata baya ba tare da ya cikata ba A hankali ya saka hannunsa cikin doguwar rigarta mai santsi yayi sama da hanun nasa daidai cinyarta ya shiga shafawa a hankali stil bakinsa cikin nata yana tsotsa bai saketa ba bai bata damar yin magana ba Wannan karin sarai tana maraba da abinda yake yi mata domin ba irin na jiya da yama bane, wannan karin cike da soyaya yake binta hakan ya saka take sakin ajiyar zuciya a kai a kai Dan mutsumutsu take tana tsoron biye masa tana tsoron kar aje ta kasa jan ajin da ta yi niya, tana mugun tsoron kar ta dawo dadi miji A hankali ya saki bakinta yana sakin ajiyar zuciya, kur ya kura mata ido bai ciro hannunsa daga inda ya kai ba, yana kalon kwayar idannuwanta a hankali ya mana mata kis a hancinta ya ce" *i'm sorry wifffe, im so srry, kin ga ba zan kara yi maki abinda na yi ba, na ji haushin kaina, da nan* ya jawo hannunta ya dora inda yake nufi wanda ta ji zambal ana tsaye tamkar soja da sauri ta janye hannunta tana kawar da kanta a kasan ranta tana aiyana da bashi da kunya ko kadan? Ya ci gaba da fadin" ba zan gajiya da jadada maki kalmar so ba, ba zan gajiya da baki hakuri ba, ba zan gajiya da neman ki manta komai mu rungumi rayuwarmu ba domin ke din ke kika san wanene Alaidine kuma kika yi masa fada a kan damuwarsa, *Wujdane* ko jama.ar anguwarku ina daukaka darajarsu a idannuwana balatana ke, su Malan ban san da me zan saka masu ba a gidan duniya zan ci gaba da yi masu adu.a , rokona Allah ya sa ki saki jiki da ni mu rayu cikin jin dadi Dukan kalamansa suna sauka cikin kunanta har zuciyarta, ko wace kalma tata tana shiga kunuwanta da matukar mahinmanci da tsada sannan tana jin dadinsu aman a fuskarta sai ta maze tana kokarin tashi daga jikinsa A hankali ta ce" yau zaka komawa matarka, dan haka ka hanzarta kar su Aba su yi jiranka Dan tsi ya yi yana kalonta, shifa gaskiya bai san yanda zai kare da maganar komawa Alawiya ba domin a yanzu muradinsa ya dawama da Wujdane dinsa Murmushi ya sakar mata ya ce" sai na dawo Ya mike yana gyara kayan jikinsa yana kalonta A hankali ta gyada masa kai bata ce komai ba, ya dan yi jim yana kalonta ya ce" i love u Ya juya ya fice inda ta bi bayansa da kalo ta sauke ajiyar zuciya ta furta " i lv u too mijina Ta saki wani murmushi tana boye fuskarta kamar wanda wani ya ganta Tunda ya karaso ya hango motocin gidansu, yan uwansa ne da matansu a motocinsu sai Abansa da mahaifiyarsa sai aunty Shafa da Marwa karama a dayar motar suna dan nesa da gidan kakaninsa da alama shi kawai suke jira Du sun firfito suna jiran fitowarsa inda ya fito a hankali ya nufo su kai tsaye ya gaisa da yan uwansa ya gaisar da iyayensa Tunda ya fito Mom ke kallon yannayin fuskarsa, a kasan zuciyarta tana adu.ar Allah ya takaita fushinsa ko bacin ransa, kwarai ta yi mamakin zuwan nasa ma domin sosai yake fushi da kakaninsa Gabanta ne ya fadi daidai lokacin da suka kusa karasawa kofar gidansu, ta hango wasu tsofafi biyu a kofar gidan saman kujeru na karfe suna magana a tsakaninsu suna zantawa da gani aminan juna ne Gabanta ne ya fadi daidai lokacin da ta fahimci mahaifinta ne da mahaifin Aba a zaune a inuwa daya suna magana ba ta fada ba A hankali Alaidine ya kama hannun nata na hagu domin Aba ya jimke na daman nata dan karfafa mata gwuiwa suka nufi gidan su Marwa Ja ta yi ta tsaya jikinta ya kwashi bari dan nesa kadan da su, wanda su kiwa hankalinsu gaba daya ya yo wajen su Marwa suna kallon mutanen dake nufo su cike da haiba Tsai mahaifin Marwa yayi yana kare masu kalo, shafa ce yake gani da wasu mutane hakan ya saka shi bada hankalinsa sosai har yana dan mikewa dan da gani bakin gidansa ne A hankali Shafa ta kamo hannun Marwa ta dan jawota ta ce" ki nutsu aunty, Tana gama fada ta jawota ta nufo iyayensu da ita Tsai yayo yana kallon Marwa, fuskarta sak ta matarsa lokacin yar kuruciya, sai dai ita da dan tsayinta sannan yanayin jikinta luwai luwai hakan na nuna hutu da ya zauna mata Kara kalonta yake , ya fada duniyar tunani kaf cikin yan uwa da yaya yarinya daya ce ta yo wannan kamar, yarinya mafi soyuwa a zuciyarsa wace a da kiyayarta ya maye soyayarta daga baya soyayarta ta dawo sabuwa fil a cikin ransa sai dai kunyar mahaifiyarta da ita kanta ya hana shi wani yunkurin A hankali ya matso kusansu ya dago hannunsa wanda abin tsufa ya saka fatar ta dan jaja da ita, A hankali ya kai hannunsa wajen fuskarta wanda tsoro ya saka ta rufe idannuwanta ruf ta fashe da wani irin kuka dan a tunaninta marinta ne zai yi ta kai kasa tana kankame jikinta Sak irin abinda ya faru a lokacin da ya farga cewar ciki ne a jikinta Muryarsa ce ta shiga dardarwa da dukan hanayensa yake nunata ya ce" Mamama...marwa?????????? Da sauri ta dago da kanta tana kalonsa, a daidai wannan lokacin har su Alaidine sun karaso gannin tana kuka Da sauri ya maimaita" Marwana ce? Marwana???? Yana fadi yana kokarin tashinta daga tsugunin yana ture hannayen samarin dake kokarin tayar da ita , du ya rikice ya ce" ku daina taba min Marwana.... , Marwana ke ce? Marwana ina kika shige kika bar mu? Dan mun yi fushin zuciya sai ki manta da mu? Marwana ina kika shige kika barmu??????? Dukansu sun cika da mamakinsa, wani farin ciki ya lulube su daidai lokacim Mahaifin su Alaidine ya karaso da sauri yana fadin" Marwa? Da gaske ke ce? Ina dan uwanki Marwa ko ya rasu ne? Ina ya shige Marwa kuka tafi kuka barmu? [2/1, 2:32 PM] Ummi Tandama.: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄 *41* WRINTING BY *SAJIDA* Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai, *SAJIDARKU CE* MARUBUCIYAR: *YAR MAHAUKACIYA* *DUK KARYAR KADA* *DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA* *NEMAN NA KAINA* ................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH.... Tamkar a mafarki Wujdane ke kalon abinda ke shirin faruwa da ita, sai da ta lura cewar Alaidine ya daina gane yarenta hankalinta ya kai kololuwar tashi, A wannan lokacin ta gama raina karfinta da ya fincike uar bintilar rigar jikinta ya barta daga ita sai pant domin Wujdane akoy sarar zama ba bras Wani kuka ne ya kwace mata, tun karfinta jin hannayen Alaidine saman mamarta, ido ta kwalalo a daidai wannan lokacin ya cika mata baki ya dawo da bakinsa wannan waje da tunda aka haliceta wani dan adam cikin jinsin mata da maza ba wanda ya taba dora hannunsa haka kai harma ya kai ga saka bakinsa sai a wannan rana, Zafi take ji sosai domin Alaidine yanai masu murzar wace ta saba ne ba wai sabon shiga ba Zufa take kamar yanda yake zufa du karfin ac din dakin, jikinsa bari yake a yanda jikin Wujdane keda laushi da santsi sai ya kasance ko.inama damka yake yana kai lebensa yana bi da sakawa wajen albarka daidai gwargwadon iyawarsa Alaidine yayi nisa baya jin kira, Wujdane kuka take tana yakushinsa dan ya farka ya cikata hakan tun bai kai ga aikata baban ba A hankali ya kai bakinsa daidai kunanta ya karanta adu.ar saduwa da iyali, ya dane jikinta yanda ba zata iya kwatar kanta ba Idannuwansa lumshe cike da masifar dake taso masa na bukatar a yau ya kasance da Wujdane koda kuwa sauran wanin ce, soyayar da yake yi mata ga zama kusa da ita ya ci karfin tunaninsa Wani razananen ihu ne Wujdane ta saki a daidai lokacin da taji bakon al.amari na kokarin ratsa jikinta Muryarta ne ya dishe hannayenta du suka mutun mata ta kasa tafuka komai sai kuka inda Alaidine ya fice a hayacinsa ya shiga wujijigata tamkar bai taba samun hakan ba ko tamkar yana dambe da sa.ansa, babu abinda bakinsa ke furtawa shi dinma sai wayo Mom wayo Wujdane wayo Jamail wayo anwar🤣☹🚶🏻‍♀🚶🏻‍♀🚶🏻‍♀🚶🏻‍♀ Ya dauki lokaci kafin ya samu nutsuwa hakan ya saka ya kankame jikin Wujdane wace ta jima da sadakarwar cewa yau mutuwa zata yi domin ta yiwa Alaidine gardama hakan ya saka ya karbi hakinsa da karfi wanda karfin ba daya ba domin shi ya dauka rainin wayon ne zata hana masa sannan a matsayin wace ta saba ya zo mata, ita kuwa abin ya zo mata a ba zata sannan tsananin tsoron abin ya sakata kokarin kokowar hanawa a kai mata (eyah sowie Wujdanina ) Ya kai minti biyar gefenta a yashe yana maida numfashi, a hankali wani hawaye mai mugun dumi ya shiga yiwa fuskarsa zarya, a daidai wannan lokaci hadisi ya shiga dawo masa a kunansa tamkar wani ke karanto masa cewar Zato zunubi ne koda ya kasance gaskiya ne Kasa dago da kansa yayi, kasa kalon Wujdane yayi, wata irin kunyarta da wata irin tsananin soyayarta da gannin girmanta ne suka dabaibaye zuciyarsa, kunyar mahalimcinsa ne ta rufe idannuwansa, kunyar iyayensa da na Wujdane ne suka nemi kasalantar da shi, a yau yana kunyar kansa da kansa, kunyar kaninsa da yayi zargin ko ya taba zuwarma matarsa kafin ta zama malakinsa ta kama shi, A hankali yake furta " Astagrullah, innalilahi wa.ina ilaihi raj.une, ya Allah ka yafe min ya Allah ka yafe min ya Allah Dan tari ne Wujdane ke yi na wahala, muryarta a shake domin ga sanyin ac ga kukan da ta ci hakan ya hadasa mata mura, Nan da nan jikinta ya dauki zafi domin bata taba shan wahalar da ta sha a yau ba Da sauri ya mike ya suturta jikinsa ya dawo ya mika hannunsa cike da tausayin Wujdane gannin yanda du jikinta yayi jajajir ba.a ma maganar fuskarya wace ta cakule ta kumbure mata Kanta ya dago ya dora kan kafafuwansa, a hankali yake tatara gashin kanta yana hadewa waje guda, bai iya furya komai ba sai jikinsa ne ke iya nuna mata irin yanda yayi nadama, Cicibata yayi, ya samu ya dauketa ya nufi bayi da ita du irin yanda ta kara rusa kukan aman bata iya tabuka komai sai kukan Sai bayan ya sakata a ruwan sanyin ya shiga sirka shi da na zafi, shi tsoroma yake kar aje ruwan zafin ya kone mata fata (🤣), A kala ya dauki minti goma kafin Wujdane ta ji muryarta na dan iya fitowa, zo ka ga kurmanci🤣🤣🤣 da nunawa da hanu sai kace daren oo😌, murya shake ta nunoshi da yatsarta ta ce" ashe baka taba sona ba? Ahse daman abinda kake so kenan kayi ta lalaba ni? Sai da ka gama wulakantar da ni haka Alaidine? Toh tun wuri ka sake ni dan ba zan iya ci gaba da zama da mijin da ya zo min a haka ba, Kalonta kawai yake tamkar ya samu sabuwar halita a kasan ransa kuwa ajiyar zuciya yake saukewa yana ayana Allah ya yiwa fushinta tsawa dominfa shi ko hauka yake a yanzu ba wanda ya isa ya raba shi da matarsa, koda su Mom suka saka baki saidai ya bar masu kasar idan sun huce ya dawo ga wujdane, dan kuwa Wujdane ta zama wani jigo na rayuwarsa, ta taka rawar gani a cikin tarihin rayuwarsa, a kanta ya ga Aya! Wujdane fadanta take tana yi masa nunin ya fice mata a bayin ya barta aman Alaidine ya mayar da ita tamkar tv, shi mamakima yake ba zata yi hakuri har muryarta ya saku sai ta yi masa aman a hakan take nuni da hannunta tana fitar da yan kalmominta tana fada tun karfinta kan baya sonta toh ya saketa Idannuwansa ya lumshe yana bin kunfar da ta cika bahon wankan, a hankali ya bude wajen fitar ruwan ya juye shi sannan ya kuma tara mata wani mai zafin aman ba mai kunfa ba ya dawo ya zuba wani a buta ya kawo kusanta, a hankali ya saka idannuwansa cikin nata ya dan lumshe ya ce" ki yi hakuri na yi maki wankan jana....... Tun kafin ya gama maganar ta zaro ido murya shake ta ce" zan iya ni zan iya kayana ni ka fice min ka yi tafiyarka ka rubuto min takardana Ajiyar zuciya ya sauke a hankaki yana dan watsa mata ruwan a jikinta ya ce" kin san fa girman zunubin matar da ta budi baki ta cewa mijinta ya saketa ko Bae??? Wata uwar harara ta zabga masa ta ce" ohk ka manta girman zunubin zato? Idannuwansa ya lumshe domin bashi da bakin magana, bai san ta inda zai fito ya kare kansa ko ya rarasheta ba, du abinda ta fada a yau iyakar gaskiyarta ne take furtawa A hankali ya mike ya shiga cire kayansa hakan ya sakata sada kanta jikinta na rawa ta nutsu bata kuma furta komai ba bata kuma kokarin dago da kan nata ba Murmushi ya saki ya dauko shower ya yi wankansa sosai na sabulu da kuma wanka ya dauko tawul sabo fil ya nade jikinsa ya juyo bayan ya fada mata sai ta fito ya fita Ta jima tana share hawayen dake biyowa gefen kincinta, ta gama gasa jikinta ta samu ta yi wanka ta fito a hankali tamkar mai tsoron taka kasa Har salar magariba ta shige hakan ya sakata shinfida dardumarta ta shiga gabatar da sallah Alaidine bai dawo gidan ba sai can dare ya shigo da leda a hannunsa, shigar da ya canza shada ne gizner kalar ash sai hula, annuri ke fita a fuskarsa haka ya je dakin Alawiya ya kai mata ledarta wace ta bishi da kalon mamaki har ya fice a dakin ya nufi dakin Wujdane A hankali ya tura ya shiga ya tarar da ita nade kan bed din, daman ya canza shinfidar aman ta dauke zanin da ya cire A hankali ya karasa gefen gadon ya mika hannunsa yana dan shafa gashin kanta yana kama sunnanta Idannuwanta ta bude sannan ta dan zabura ta ja baya tana yi masa kalon tsoro domin a yanzu tana mugun tsoron su kasance daga ita sai shi Murmushi yayi ya ce" ki taso mu ci abinci please, ki daina irin haka ba abinda zan yi miki My Wujdane Wujdane ta hade wani yawu ta ce " bana jin yinwa ni ka je kawai bana jin yinwa ta karashe tana matsar kwallah Kai ya girgiza ya ce" kinga bani da niyar yi maki wani abin a yanzu, aman idan ya kasance abincima ba zaki ci ba toh fa zan mayar da ke abina bcaus ba zai yiwu na saka maki ido a haka ba Sosai take shakarsa, ita fata take ta warke tayi gaba domin ba zata amince tana ji tana gani ya kasara mata rayuwa ba hakan ya saka a hankali ta jingina da abin bed din ya shiga mika mata steck da dankalin turawan tana dan karba a haka ya balo mata magani ya mika mata du ba alamun wasa a tare da shi ta karba tana hade rai ta sha sannan ta A hankali ta fara lumshe ido domin maganin da na zafin ciwon ne da na baci , nan ta silale ta shiga bacinta harda ajiyar zuciya Hawa saman bed din yayi sosai yana kalon face dinta, a fili ya furta" taya ma zan iya rabuwa da ke bayan ke na fara so? Ya kike hasashen yin nesa da ni bayan kin dandana min abinda har na gama ina lilo a wata duniyar daban, ke Wujdanena ya kike furtan kalmar saki a kanki bayan na malakeki na farko, kina zabin mahaifina, wannan gonata ce wace na shigota da ganganci, ba zan kuma yi mata irin shigar nan ba, Wujdane a yanzu zaki fahimci mainene so, yanda kika rungumeni tunda kika san ko ni waye kika daukeni, duda aurenmu an hada mu ne a matsayin *BAKI DA ZABU*, ba zan taba cire igiyar nan da aka daura ba, ke sai dai rabon wani ya kaini kiyama ki zama tasa aman nu dake mudin raina A hankali ya cire rigarsa ya gyara konciyarsa, a yau lokacin kowa da komai ne bashi da, bashida lokacin kowa sai na kalon abin kaunarsa, fatansa Allah ya sanyaya zuciyarta ya bashi ikon faranta mata Asuba ta gari angon Wujdane🤷🏻‍♀ Aba ya ja dogon numfashi bayan ya gama jin korafin Shafa kan su tafi gidansu, ya dago da kansa ya sauke kan Mom, tausayin matarsa yana jagorancin tunaninsa, shi yama di tausaya mata kan kowa a rayuwa, a yanzu da ta ga yar uwarta sai ya kasance itama ta samu wani farin ciki a duniya domin ta samu abokiyar shawara A hankali ya ce" sister, ke yanzu a ganinki kawai sai mu dirar masu haka? Ya kike gannin zamu kwashe? Idan fa kilu ta jawo bam? Shafa ta dago ta ce" yaya, shekara fiye da talatin? Tunda cikin Alaidine fa, baka ga yanda mama tayi ta kuka a ranar da na nuna mata hoton Aunty da na yara, Dad dinmu ne kawai nake da tantamar hucewarsa aman sufa musulmai ne? Dan Allah ku fitar da wani dar a zuciyarku mu tafi Kalonsa ya maida wajen Mom wace ke dan share idannuwanta ya ce"""" 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻 [2/1, 2:33 PM] Ummi Tandama.: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄 *43* WRINTING BY *SAJIDA* Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai, *SAJIDARKU CE* MARUBUCIYAR: *YAR MAHAUKACIYA* *DUK KARYAR KADA* *DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA* *NEMAN NA KAINA* ................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH.... Rige rigen ta tare shi suke jikin Aba inda bakunansu ke fusta subahanalah subahanallah Talabe shi Anwar yayi yana kokarin fitar da shi inda Aba ya dakatar da shi yayi umarnin su fice asibiti kawai Hakan kuwa aka yi du suka dugunzuma suka nufi asibiti da Alaidine wanda kwata kwata baya numfashi Likitoci sun karbe shi inda suka yi kokarin gannin nunfashinsa ya daidaita ya dawo daga sumar da ya yi kafin su bincika su ga dalilin sumar da kuma abinda zai magance maimaituwar hakan Sun dauki lokaci kafin suke mayar da shi dakin hutu suka bukaci gannin iyalinsa ko iyayensa Aba ne ya mike ya bi bayan docter domin har zuwa wannan lokacin ba.a kawo matan nasa ba Jamail ya je ya dauko su da kansa Aba ya jima kansa a kasa yana sauke ajiyar zuciya, daman ya san hakan ne za.a fada din Alaidine ya cika zurfafa damuwa kwatakwata bashi da saurin shafe abu a zuciyarsa, irin hakan kuwa bashi da kyau ga mutun dan adam domin dole ne zaka rayu cikin farin ciki da kuma bakin ciki ko wanene kai Sauke ajiyar zuciya ya kuma yi ya ce" insha Allah docter zamu ci gaba da yin iya kokarinmu dan gannin ya rage zurfafa abu, Docter ya ce" idan kuka yi hakan da yardar Allah zai daina irin sumar nan domin ciwon bai mugun shigarsa ba za.a iya mangance hakan tun kafin ya shige zuciyarsa Aba ya amsawa docter ya mike ya fito, a kasan zuciyar Aba kwarai ransa a mugun bace yake da irin zuciyar yaron nasa, toh mai Alaidine yake nufi da irin haka ne? Idan har ya kasa karbar kadarar rayuwarsa ya kasa yin hakuri ya yake so a yi masa? Dubansa ya kai wajen Mom wace du ta fi kowa damuwa sai matansa da Wujdane kanta ke kasa ba zaka fahimci ainahin abunda ke ranta ba Alawiya a gefen Mom itama fuskarta karara ta bayanar da tashin hankalin halin da mijinsu ke ciki Yan tsofafin ya mayar da dubansa wajen su, sai ya ga kowane ya mugun tsure, da alama kowane yana tuhumar kansa ne, wannan rana da ya dace ta kasance masu babar rana, ranar da suka samu farin cikin su ya dawo, iyayensu suka karbe su, sai ga shi tana kokarin karewa da wani tashin hankalin Murmushi yayi kokarin saki, ya karaso wajensu yana sauraron dumbun tambayoyin su wanda kowane bukatarsa ya ji abinda docter ya fada ke damun Alaidine Aba yayi murmushi ya ce" ba wani abu ne mai tashin hankali ba, kun dai san Alaidine da saka abu a rai, hakan ne ya tayar masa da hankali Alawiya ba zato ba tsamani ta ce" mai ya saka a ransa shi kuwa? Mai ke damunsa bayan matsalar kakaninsa wace ya jima bai nuna ba sai yanzu da wannan ta tare??? Ta karasa maganar tana nuna Wujdane a wulakance Aisha ta kamo hannun Wujdane ta saka tafin hannunta cikin nata irin kar ta daga hankalintan nan Da mamaki Aba ke dan kalonta sai ya juyar da kansa ya basar ya ci gaba da fadin" docter ya ce idan har aka konyar masa da hankali ciwon bai wani shige shi ba, dan haka mu yi kokarin kontar masa da hankali Allah ya bashi lafiya Elhaj Muhamad dake sauraron du abinda ya faru ya dago ya kali aba ya ce" Abdul Kadri, daman bashi da lafiya ne? Aba kam kansa ya sada kasa, domin yana jin nauyin fada masu dalilin sumar alaidine, aman ya zai yi? A hankali ya ce" Eh aba daman yakan dan yi irin hakan, toh yanzun ma tashin hankalin da ya sakawa kansa ne na zuwa wajenku da muka yi, yana tunanin wani abin daban shi ya sa hat hakan ta faru aman docter ya ce abin bai yi nisa ba dan haka kar a daga hankali Kansa kawai yake dan girgizawa, a kasan zuciyarsa kuwa hawaye ne ke zuba, a hankali ya ce" mun yiwa kanmu, mun horar da yaron da ba laifinsa ba tun kafin ya shigo duniya, mun kasa daukan kadarar da Allah ya hukunto a kanmu, mun guji kunyar duniya mun batawa mahalicinmu, mun kori yarenmu a lokacin da suke bukatar mu dan kawai son zuciya irin tamu Da sauri Mom ta karasa ta kamo hannayen mahaifinta tana girgiza kai dan gannin du yanda ya so hanna awaye zubowa daga idannuwansa sai da suka zubo, ta ce" Abana, ai dan adam din kenan, mukan aikata laifi kala daban daban, banban laifinmu idan bamu tuba ba Shin dama dan da aka haifa ya isa ya rike iyayensa a rai komai girman laifi? Abanna tun kafin ku gama yi mana laifi muke yafe maku, domin mun san kuma hakan ne , dukan abinda ya faru rubutace ne ba wanda ya isa ya kauce faruwarsa, rashin lafiyarsa Allah ne ya dora masa ba wai dan ku ba Aba, dan haka Na roke ku da ku cire komai a ranku Ta karasa tana shatatar hawaye Anwar ne ya matso gannin du iyayen nasa ba wanda zai baiwa dan uwansa hakuri abu da an jima ana jiran ranar kuma ta zo a haka sannan du mutane na shige da fice wasun suna kalo wasun kuwa sai su fice ya saka shi yin gyaran murya ya ce" Aba ina gannin a takaita koke koken nan haka a samu wa.inda za.a bari wasun kuwa mu je gida a shirya a dawo ko? Aba ya dago kansa ya jinjina irin ya amince da hakan sannan ya shiga bayar da hakuri Sun dan sami nutsuwa aman ba wanda yake da alamar zai tafi ya bar dan uwansa Alawiya zaune take kusa da matar Anwar, a kasan zuciyarta tana cike da wannan lamari, kwarai ta sani kyan Alaidine da arzikinsa ya kaita aurensa aman tunda aka daura masa aure da Wujdane take jin tsantsar kaunarsa da kuma kishinsa, hakan ya saka take mugun kara gannin bakin surukanta domin du laifinsu ne su ne suka aurawa mijinta wata bayan suna zamansu lafiya Ita yanzu banban burinta ta ganshi, somin fushi take yi masa kwana biyu na yana kwana dakin Wujdane aman a yanzu kam ba zata iya komawa gida ta barshi haka ba ba zata iya samun nutsuwar zuciyarta ba, yan uwansa du su tafi su bar mata shi ta yi jinyar mijinta [2/1, 2:33 PM] Ummi Tandama.: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄 *44* WRINTING BY *SAJIDA* Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai, *SAJIDARKU CE* MARUBUCIYAR: *YAR MAHAUKACIYA* *DUK KARYAR KADA* *DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA* *NEMAN NA KAINA* ................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH.... Aba ya kai dubansa wajensu gaba daya, can ya nisa ya ce " Wujdane ku tashi a kai ku gida ku je ku kimtsa sai ku yi shawara cikinku wace zata dawo ta kwana asibitin Tun kafin Wujdane ta yi magana Alawiya ta ce" aa ta je kawai sai ta kwana a gidan ni zan tsaya na kula da shi Tana maganar ne tana mikewa ta dan kara gaba kusa da kofar ta tsaya ta basu baya , halaya dai na haushinsu take ji matuka Aba ya girgiza kai ya ce" ku mu je kawai Haka suka bi umarnin Aba ba dan sun so ba Jamail da Aisha ne suka kai Wujdane har gida, suna tsayawa Wujdane ta tsare Aisha da ido, irin yanda take yi idan tana cikin tashin hankali kuma tana son magana da yar uwarta Aisha ta kalli jamail, daidai lokacin Wujdane ta fice a motar kawai ta shige fallon su Aisha cike da nutsuwa ta ce" yayana Jamail yayi murmushi yana kallonta ya ce" shikennan yau jamail sunansa maraya, Aisha ta sakar masa da murmushi mai sanyaya zuciya, a hankali ta matsa ta yi hogging dinsa, ta mana masa kiss a kunci kafin ta kara masa wani a lebensa, ta ce" in dai Aishan Jamail na raye in sha Allah ba zai yi maraici ba, mu je kawai idan hankalinka ba zai konta ba Murmushi yayi ya shafa fuskarta, ya ce " ke ce mar.atun saliha Aishanna Ki je kawai zan dawo na dauki abinna idan hankalin auntynmu ya konta Aisha ta sakar masa da murmushi ta ce " na gode mijina Shima murmushin yake har ta bacewa ganninsa, Yana jin dadin yanda take girmama shi, sosai yake jinta a ransa Aisha na shiga ta tarar da Wujdane sai kai kawo take a falon ta cire hijabin dogon gashinta mai ruwa na jar fata sai yalwa yake yana bin bayanta domin a tufke yake har karshensa Idannuwanta kuwa sai wulik wulik suke wannan kalar mai shigen na maciji sai yawo yake farin kuwa ya dan canza launi , gaba dayanta a figice take hankalinta a wajensa zuciyarta haka take dokawa , ta fita sonsa, ita batai masa soyayar kudinsa ita ya dace ta zauna a gefensa duda ta ji haushin yanda ya kara saka damuwa a ransa a daidai lokacin da ya dace ya dawo mata da farin ciki, aman ya ta iya? Sonsa take bata son bacin ransa ko kadan, sai fa da ya yi mata alkawaron zai kiyaye aman shine zai wani sume har docter yayi ikirarin ciwon zuciya? Ina mijinta lafiarsa kalau kuma da yardar Allah zai kawar da komai a ransa, ita haushinta daya yanda ya kasa hakura da lamarin ubangiji, dalilin wannan abin ya kaurace kansa daga cikin mutane, ko su matansa baya iya zama su fahimci juna yana tsoron su guje shi ko su yi masa gori, yana rabuwa da mata dan haka..... yanzu da Allah ya tilasta zuciyarsa kamuwa da soyayar Wujdane duda ta nuna masa tana sonsa koda wani iri ne shi aman yana wani nemanta da izgilanci? Toh zata yi hakurin ya warke su yi du abinda zasu yi idan har bai mayar da kansa mutun ba A hankali Aisha ta karasa kusa da ita ta damko hannunta dan ta tsaya ta daina kai kawon nan Wujdane ta juyo tana kallon Aisha, kun dai san irin zurfin cikinta aman Aisha bata iya boye mata komai takan fadawa aisha abinda ke damunta ne koda tsakiyar dare ne, ita kuwa ta iya rarashinta Aisha ta ce" danina Wujdane ta tsareta da kallo, Du duniya Aisha Aba da uma ne kawai basu taba nuna mata kyara ba ko a fuska, du irin yanda kuwa yayanta zai daketa Aba baya yi mata sai dai ya girgiza kai ya bita da adu.a, mama na kwatanta dan dukan kamar idan ta samu yayan mutane ta daka aman ba wai a nuna mata kyama ba dan fatar jikinta, a hankali ta bi Aisha suka zauna Aisha ta yi murmushi ta ce" hasashena gaskiya ne? Wujdane na kallonta bata ce komai ba Aisha ta ce" danina na soyaya? Wujdane ta kawar da kanta, aisha ta yi yar dariya domin ita ko tana barci wujdane ta yi abu ta san me take nufi da abun Aisha ta ce" ki yi hakuri, na tabata shima ya damu da ke Wujdane ta juyo tana kallonta , can kamar ba zatai magana ba ta ce" laifinsa ne dan an same ahi ta wannan hanyar Aisha? Aisha ta yi gagawar girgiza kai Wujdane ta gyada kanta, can ta ja tsaki ta ce" to tunda na bi shi ta laluma ya ki ya fahimta zan fito masa a mahaukaciyata! Komai son da nake masa ba zab lamunci na zauna da shi yana irin halayan nan ba Aisha ta zaro ido, wujdane ce ta yi doguwar magana haka?, aman dan kar ta daina sai ta ki juna mata ta ce " to aunty ya zaki yi yanzu, ci gaba zaki yi da nuna masan har Allah ya sa ya gane Wujdane ta yatsina fuska ta ce" kin dai fi kowa sannin waye wujdane,! Yau a fidanmu zan kwana sai dai aba ya kashe ni idan dukanna zai fara ko ita umman ta kashe ni Aisha ta zaro ido, a fili ta furta" na bani ni aisha , Aunty ki rufa mana asiri.... kina so ki ce zaki yi yaji daga dan abin nan? Toh haka ake yin yajin ne? Ai wannan tsakaninki ne da mijinki Aunty na roke ki kar ki irin haka kin ji? Wujdane dake maida hijab ta juyo ta ce" idan kin gama ki rufo dakin ki baiwa masu gadi kys din Da sauri aisha ta mike tana biye da ita tana bata hakuri, Wujdane ta dakata tana kallon Aisha , can ta ce" me yasa shi bakin mutun ya fiya baiwa kansa wahala ne,? Kinfa san ba hakuran zan yi ba aman kuma kike ta babatun nan? Aisha na sani na yarda na kamu da soyayarsa bayan bai dace da ita ba domin shi bai furtan kirikiri wani kalmar so ba sai ta yaudara, sannan du irin halayanna na sauke inai masa biyaya dan na samu ya daina tsangwamar kansa dan Allah ya halice shi ta wannan hanyar aman yau shine a gadon asibiti a konce wai kuma dan wulakanci matarsa da ba kwananta bane ita zata kwana da shi? Du ana kallo dan ni talaka ce matar cushe shine aka koro ni? To ba zan yiwa aba rashin kunya ba aman na tafi gidanmu sai ya dawo ya kaiwa aba takardana shi kuwa ya nema malan baba ya bashi ehe Tana gama fadar hana ta yi tafiyarta abinta ta bar Aisha da kikifta ido kafin take samun waje ta zauna ta yi kiran number Jamail da wayarta dan ya dawo ya dauketa domin Kuwa Wujdane har ta fada adaidaita kuma ba ko sisi a wajenta ( mai hali baya daina halinsa🤦‍♀) Farkawa yayi, a hankali yake gannin dishi diahi kafin idannuwansa su washe kan Alawiya dake baci rabin jikinta saman bed din nasa rabi kasa ta yi mugun konci har jikinta yayi tsami A hankali yake tuna abubuwan da suka faru, kansa ya girgiza ya ce" Alaidine me kayi haka? Ya salam ba gangan na suma ba tabas suma na yi , ya Allah ka sasauta min irin wannan zuciyar Sai a lokacin Wujdane ta fado masa a rai Ya kai dubansa wajen Alawiya, aman ai yau ba kwannan alawiya bane, idan bashi da lafia mai kwanansa zata kwana da shi mana , Kansa ya dafe ya ce" ya Allah ko yaya Wujdanena zata ji? Matar amana , mai fada min gaskiya, Wujdane sonki kawai nake A hankali ya mike ya tsalake Alawiya ya gyara mata konciyarta ya shige bayi ya dauro alwallah Nafila kawai yake jerawa yana godiya ga Allah sannan ya roki Allah da ya bashi ikon yafe masu sannan ya kara nemarwa iyayensa gafara wajen Allah Wujdane Walahi walahi walahi idan baki fada min uban me kika zo nema a gidan nan kafin malan ya dawo sai na yi maki nunusar hankali A hankali ta kalli yayan nata, ta ga dai yanzu fa ta zama yar gayu, idan kuwa ta yarda sai ya jinyatata a banza, Mikewa ta yi ta shiga kakabe hijab dinta ta kalli mamanta dake tsaye ta kama haba tana tarababi da Wujdane batai hankali ba? Ta zo masu kawai tace a nan zata kwana bayan an raba rigimarta da dan adaidaita tace masa ya kawota sadaka har yana kokarin kwave riga wai su daku ita kuwa ta tsaya tana jiran ya kwaben yayanta ya karaso ya biya ya toso keyarta yana tambayar lafiya me ta zo yi? Shine tace ta zo kwana gidan ubanta ne haka gatsal ba kwana ba komai Wujdane ta yiwa mama murmushi ta ce" kifa daina damuwa mamanmu mana, kin ga bashi da lafiya ne yana asibiti kuma ba kowa a gidan, kin dai ji labarin gidan ni tsoro nake kuma gidansuma ba kowa shine na yo nan Mama ta kama baki ta ce" kuma? Karya kika fara? Da dai ko kashe ki za.a yi bakya karya Wujdane Kanta ta dafe bayan ta tabatar da ta saka jikinta dakinsu ta rike kofar da kyau ta turo ta rufe ta leko ta window ta ce" yi hakuri umanmu *Yaji na yi* To fa zan karasa ko sisina ta daina fushi da ni🤣🤣😍😍😍😍 [2/1, 2:33 PM] Ummi Tandama.: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄 *45* WRINTING BY *SAJIDA* Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai, *SAJIDARKU CE* MARUBUCIYAR: *YAR MAHAUKACIYA* *DUK KARYAR KADA* *DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA* *NEMAN NA KAINA* ................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH.... A tare suka ce" yaji? Wani irin yaji? Wujdane ta dan dafe kanta , ta girgiza kai kawai ta cire hijab dinta ta zauna bakin tabarmarsu tana kallon dakin Ke Wujdane ko ki bude dakin nan mu yi maganar arziki da ke, ko na bale kofar nan na hada maki jini da majina kin ji na rantse Bakinta ta tabe ta shiga jujuya kafarta Mama ta zauna yarab, ta dafe kanta, kafin a yiwa Wujdane aure tana da fada da rigima a waje aman idan ta shigo gida bata son bacin ran iyayenta, ita kuwa wannan wujdane din kai tsaye take maimakun ta yi laushi sai take ga kamar ta kara tsaitsaye mata, ajiyar zuciya ta sauke kafin take karasawa bakin kofar ta ja ta dan tsaya Muryarta a konce ta ce" yar abanta, menene haka kike fada? Kina son hankalina ya tashi ne ko me? Wujdane ta dan cuno bakinta tamkar maman na ganninta ta ce" umma, kina gani na hane shi abu, bayan ya gamai min maganar ba zai yi ba ya je yayi, haka ake rayuwa? Mama ta girgiza kai ta ce" aman Wujdane ke ya dace ki bi shi fa Wujdane ta dafe kai , can ta ji muryar mahaifinta ya shigo, nan umma ta labarta masa komai, Zama ya yi ya tsurawa Dakin ido, can ya nisa kasa kasa ya ce" umma, kin ga yanzu dare ya yi sosai, ko menene zamu ji da safe in sha Allah Umma kam ta dai yi shiru ne dan bata saba yi masa musu ba ta mike ta shige dakinsa dan yau dole ta kwan a nan dan Wujdane ta garkame daki Kamar yanda Aba ya saba yayi nafilfilunsa ya tsaya tsayuwar dare, rokonsa Allah ya nutsar masa da yayansa bale wujdane, ya yiwa Wujdane adu.a sosai ya roki Allah da ya shiryar masa da ita Da asuba tun daga soro Aba yake jin ana dimar abu muryar yayan su Wujdane na tashi kadan kadan yana fadin" in dai ba zaki yi magana ba sai na bala ki yau ni da ke a ga mai taurin kai Kai kai kai wannan yaron menene haka? Matar aure ce fa? Kulll in ganni ka kuma dukanta Aba ya fada yana azamar tare dukan Wujdane ta dago ranta a bace fuskarta a jagule , har ta juya zata koma daki ta dawo ta ce" yaya ko dai kaima kana cikin masu tsangwamana ne dan kalar fatana da kuma idona? Na rasa gane kanka kai kawai a rayuwa baka da abin huce haushi sai jikina? Har kana dira a kaina kana tatakani kuma ka fita waje a ce maka wa? Tun ina karama kake horani yanzun ma ban fi duka wajenka ba? Kai dai Allah ya shiryeka Rana gama fada ta yatsina fuskarta ta shige dan yin Sallah Aba ya girgiza kai ya dubi yanda su umma suka saki baki suna kallon dakin su Wujdane Murmushi yayi ya juya kofarsa ya zauna yana jan carbinsa hankali konce Sai da ta gama azhkar ta shafa fatiha ta fito cikin nustuwa ta duka har kasa ta ce" abana barka da safiya Aba cikin jin dadin gannin yanzu Wujdane har tana magana haka nauyin bakinta ya dan rage ya ce" barma mamana, kin tashi lafiya? Wujdane ta yi murmushi tana kallonsa kadan Aba ya sauke ajiyar zuciya ya shiga yiwa Wujdane nasiha cikin nutsuwa , can ya ce" aman abin mamaki Har kin yi fushi Wujdane na? Wujdane ta turo bakinta ta ce" Abanna, ba wai ban dauki nasiharka bane, Ta dan sauke ajiyar zuciya ta ce" dan ya ga na damu da shi ne? Bayan ya ce ba zai kuma yin abinda raina zai bace ba shikenan sai kuma ya yi? Me ya yi? Aba ya tambaya yana son kara gaskata abinda zuciyarsa ke fada masa idan ta fara nutsuwa ko da saura wato tana son mijinta ko har yanzu rigimar an hadata da wanda baya sontan ne? Wujdane ra dago tana kallon Abanta, haka kawai sai take jin ba zata iya fada masa gatsau dalilin da ya sa take jin haushin mijinta ba, to kawai sai ta ce dan yana jin haushin shi ........ne? Aaa koda mahaifinta ya san wanene mijin da ya aura mata ba zata iya maimaita masa ba, kanta ta sada , na farko a rayuwarta da ta ji kunyarsa, kunyar Aba take sosai harma ta ji haushin kanta ya aka yi ta kwaso ta zo? Aba yayi murmushi yayi godiya ga Allah a ransa, ya ce" tashi ki je ki karya zamu yi maganar..... Yayi haka ne dan baya so ya kwasheta ya koma da ita haka? Tabas ya sani yaji bashi da alkhairi ba dabi.a bane aman kuma baya so yayi abinda za.a ga ko dan yana talaka yake rawar kai haka, da farko ya yi masu auren nan ne ba tare da yardar dayansu ko na mahaifiyarsu ba, ya tisa keyar su an kai su wajen da basu shirya ba ba shiri irin na amare, ya sani halayen yarsa na taurin kai aman sai Allah ya dora mata kunyarsa, tana jin nauyinsa a rayuwa fiye da komai , batai masa musu.........shi ya sa shima yake mata uzuri da fatan alkhairi, ba zai dauketa a yanzu karo na biyu ba tare da ya binkici abinda ke faruwa ya mayar da ita gidan mijinta ba, idan har yayi bincike ya ga shirme ne irin nata baya ce masa komai ya dauketa da kansa a adaidaita sahu ya bi bayanta ya mayar da ita gidanta Lokacin da su Aisha suka zo da jamail, a wannan lokacin kowa ya samu zuwa asibiti, Alaidine yana bin mutane da kallo da an bude kofar an shigo sai ya kali wajen da sauri ko zai ganta aman ina sai ya ga ba ita bace, a ransa yake ayanna ke kuwa mai zuciyar Alaidine ina kika makale haka ne? Wujdane ki fa shigo kar ki saka na yi abin kunya na tambayeki a gaban jama.ar nan Shiru shiru har lokacin salar la.asar yayi, wanda Alaidine ya daure ciki ya shiga wani hali na rashin gannin matarsa, tana ina? Me take ? Ya aka yi bata zo ba? Bayan ya fada mata mata irin son da yake mata, du alkawarurukan da yayi mata na sakata jin dadi a tare da shi,? Ko bata da lafiya ne? Shi bai san kuma zaman me suke a asibitin ba bayan ya warke ya farfado daga suma kuma rikon me ake masa haka har da familynsa ta tare a asibitin sai wani nan nan suke da shi su mom kuwa an samu yan uwa kadan ta motsa sai an tareta sai dadinta kawai take ji ta kasa lura Wujdane bata wajen Boy a kama ka ka yi alwallah ka samu ka yi sallah ko? Aba ya tambaya yana tsare Alaidine da kallo Alaidine ya gyda kansa, Suna mikewa ya ce" Aba ni zaman me muke kuma bayan da sauki jikina? Ina likitan ne ya zo ya salameni haka mana Aba ya ce" aa, ka ga ka yi hakuri har likita ya salameka da kansa Alaidine ya mugun tsare fuskar Aba da kallo, irin kallon nan na ka ji kaina Kakansa ne ya ce" kai aboki , an ki a sake kan, yo naga da yawa kai patient kai ne zaka ce a sake ka? Ya yatsina fuskarsa tamkar zai yi kuka, ya ce" ABA wujdane A tare suka kallo shi, Alawiya ta mugun juyowa daga wajen yanke farcenta da take, ta sauke kwayar idannuwanta a fuskarsa Abama kallonsa yake, WujdNe yace, masha Allah da canji, masha Allah da canjin nan da aka samu, iyeh Alaidine da ya mayar da mace hula, bashi da wata damuwa a lamarin mace ta zauna ko ta yi gaba, kai muguwar makiyiyarsa yake dubanta yace mace guba ce, macijin kmba, sari ka noke, kyau ne da ita cikinta baki ne, mata daga mai masa sata sai mai yi masa gori, sai mai tunanin wayo take yi masa, aman yau ya birkice gida zai je matarsa? Aba gannin du an tsare shi da ido ya ja abinsa suka yi bayi, bayan ya raka shi ya dawo ya shiga baiwa iyayen nasu labarin wacece Wujdane, yana tsaka da haka Alawiya ta mike ta fice bayan ta yi masu kallon tsaf gaba dayan su Alaidine na yin sallah da ya gama ya ga an dan rarage du yawancin mazan basa nan ya yafito Aisha Matsawa ta yi kusa da shi kanta a kas tana jin kunyarsa na yayan mijinta kuma mijin ysyarta Kansa ya girgiza murya kasa kasa ya ce" tana ina? Aisha ta dago tana jin kunyar abinda zata fada masa , sai dai bata iya karya ba, ta ce" wai ta je gida, tace tana fushi ta yi yaji Ai bai san lokacin da ya mike ba ya ce" ta yi me? Yana zaro dara daran idannuwansa Aisha ta san ja baya, Momy ta taso tana kallon su ta ce" lafiya kai? Alaidine ya kaleta, ya kalli mutanen du sun wani zuba masa ido, sun yawaita kallonsa shi fa baya son haka! Juyawa ya yi kawai ya fice a dakin , momy ta juya wajen Aisha wace ta fada mata komai , Momy ta ce" ita ce maganinsa, aman ina zai je? Hajia ta yi dariya ta ce " ja.iri sarkin soyaya, madallah da wannan yarinya da gani zatana dawo da shi hanya Aisha a ranta ta ce " kaiya, Allah ya sa toh Nan suka ci gaba da zama basu san tsiyar da Alaidine ya tafka masu ba Tana zaune tsakar gida ta baje tana cin wake da shinkafa wanda take jin dadinsa ta yi missing dinsa sosai, fuskarta kuwa da jan san hannun da yaya ya wanka mata mari, tana ci tana karawa tana dan murmushi ta ga hannu ya rike hannunta Da sauri ta dago ta sauke idannuwanta kan hannunsa, wani irin sanyin dadi ne ta ji ya mamayeta a zaunen nan, aman yaushe ya shigo? Ta ina ya shigo? Ya aka yi ya san tana nan? Rai bace ya shiga shafa gefen fuskarta inda ya yi ja, murya a cinkushe ya ce" wa ya dake ki? Wujdane ta turo baki ta ce" ba yaya bane wai dan na yo yaji Alaidine ya dafe daidai zuciyarsa ya ce" to shi yaya ina ruwansa ko shi akaima yajin ne? Ya zai taba lafiyar jikin matata ya raunata min zuciyata? Ta kara turo baki jin an bi batanta ta shiga ture kwannon abincin tana kallonsa ta ce " haka ya ce sai na koma bayan na yi maka fushi mai tsannani , bayan na karyata son da kake min a zuciyata, kai kana gannin idan na yi murnar ganninka na yiwa zuciyata adalci kennan? Ke, ya fada yana dora yatsarsa saman lebenta, ya ce" ina jama.ar gidan ne? Gwara su zo su shaida idan ba.a bani matana ba zan iya haukacewa Wani yamyam ta ji har tafin kafarta, haukatata zai yi da soyayarsa, sonsa kawai take, 😍 [2/1, 2:33 PM] Ummi Tandama.: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄 WRINTING BY *SAJIDA* Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai, *SAJIDARKU CE* MARUBUCIYAR: *YAR MAHAUKACIYA* *DUK KARYAR KADA* *DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA* *NEMAN NA KAINA* ................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH.... 4⃣6⃣ *ND* *ND* ..... ......... *ND* *ALHAMDULILAH* Wani yam yam ta ji a jikinta har tafin kafarta, haukatata zai yi da soyayarsa, sonsa kawai take Sai a lokacin ta lura da suturar jikinsa ta asibiti ce irin wace ake sakawa patient, to aman bata gane ba daga ina yake haka? Ta san dai ba za.a taba barinsa ya fito daga asibiti da kayan mararsa lafiya ba, suna da tsaro sosai Yayansu ne ya shigo da leda a hannunsa dan kawowa iyayen nasa sako, nan ya tarar da Alaidine a gidan Dan dakatawa ya yi har suka ankara da shi kafin yake kwala salama Mikewa Alaidine ya yi yana amsawa yana binsa da kallo Shima da dan murmushi ya mika masa hannu sukai musabaha Alaidine da Wujdane du shi dai suke kallo inda ya zabgawa Wujdane wata uwar harara ta haushin bai ci mata uwa ba har gari ya waye gashi yanzu mijin nata nema ya biyota da sasafen nan ko me ya biyo mace yi bayan ta yi masa yaji? A zuciyar Alaidine kuwa murmushi yake, shima kamarsu daya sai dai idannuwansa ba irin na matarsa bane Salamarsa ce ta fitar da su Aba, nan Alaidine ya duka har kasa suna gaisawa Aba ya ce" wannan ja.irar ka biyo ko Alaifine ya dan sosa kansa bai ce komai ba Ina ta ce" ni ai jira nake malan din ya fita shi da ya tare a daketa, aikin banza aikin wofi yarinya sai shegen taurin kai wai gatsau ta kale mu tace da mu yaji ta yi sai kace auren abin wasa ne,? Kamar an saka ina kawai ta shiga fada tsakaninta da Allah, Ai kuwa halayar da Wujdane bata da ita wanda ko me za.a ce mata a fada bata nunama ta san da ita ake aman yanzun gaban Alaidine sai kuwa ta shagwagwabe fuska ta saki kukan sangarta harda ture kwanon wakenta nan da nan kuwa ido ya kade mata , baki ta barke masu kuma tana kallon Alaidine Zumbur ya mike daga tsugunnin da yayi, rasa me zai yi ko zai ce ya yi, da sauri ya dauko hijabinta dake rataye kan igiya ba ruwansa ya nufota yana kokarin saka mata Dan kaucewar da take tana dane mahaukaciyar dariyar da ta taso mata ne ya saka ya dan tsaya yana kallonta, murya a raunane ya ce" ina, ABA, dama yaya ku yi min rai dan Allah ku yi hakuri kar ku bata mata rai, ba laifinta bane laifina ne kuma ba zamu kara bari kowa ya ji kanmu ba da yardar Allah, inna ki yi shiru fadan na tayar mata da hankali Hannu inna ta kai ta rufe bakinta, kunya ta kamata irin yanda yake so sai ya hanata kuka du kuwa da tana kaucewa aman riketa yake sosai a jikinsa, Da sauri inna ta shige daki ta boye bayan kayan Malan dake rataye Malan ya dane dariyarsa ya ce" toh maza tashi ki bi mijinki kin ji Mikewa ta yi tana gyara hijabinta Yaya ya girgiza kai a fili ya ce" ya lafiyar kura bare ta yi hauka? Yaya Alaidine kai ke daure ma Wujdane ko? In dai Wujdane ce .....ya girgiza kai, ya kuma kallo shi ya ce" mu dai ta kuma shigo mana gida wai yaji sai na balata takamarta an yi mata aure bata tashi a Wujdane yarinya ba! Alaidine ya yi murmushi domin kuwa ya gane wasa Yayan ke masa, ya kama hannunta ba abinda ya dame shi suka fito suka nufi motar da bata sanshi da ita ba suka shiga Bayan sun fara tafiya ne ta ga wata carte ta dauka tana karanta an rubuta Docter Aliyu, Nan take bin motar da kallo ta ga ashe motar docter ya dauko shi ya sa aka bar shi ya fita, aman ina doctern ya yarda ya barshi? Asibiti ya koma direct, suna zuwa aka barshi ya shige ya yi parking, ya fito stil ya zagaya ya riko hannunta suka nufi ciki A hankali ya tura kofar nan ya ga du an yi cirko cirko ana ta kiraye kirayen waya hankali du ya tashi ana neman inda ya shiga Mom ce ta bi su da kallo, baki sake ta sake kallonsa, Nan ta maida dubanta wajen docter Aliyu da a nan sukai sabo shima zuwa asibitin ya sa suka saba sosai da shi ta ce" Docter ka ga tafiyarmu, mu kam mun tafi idan ma zai kara kwana ne ni kam ba zan zauna ba , yaran zamani Allah ya shirye su, yanzu Alaidine ka fita ka bar mu muna jinyar iska? Ka je da kayan asibiti ka dauko matarka ko kunyar iyayenta baka ji? Yama aka yi suka mika maka ita a dasha haka? Yaron nan baka da kunya, kai Aunty ce tana dariya ta ce" kai hajiata ke kuwa ya isa haka, docter a bamu salama idan ya warke mu tafi abinku ai ni yata saima na bata kyauta Wujdane kuwa labewa take bayansa kar a ganta , sai yanzu ta ji wata wai ita kunya, to ya aka yi bata jita ba a wajen su Aba? Docternma yana dariya ya basu salamarsu inda nan suka fito du aka dugunzuma mota aka nufi gidan su Momy Suna zuwa Wujdane ta silale ta bar su nan sai labari suke ta nufi dakinta na da Tana zuwa ta tube ta shiga wanka Tana fitowa ta tarar da shi konce yayi dadaya yana kallon sama Da sauri ta karasa ta zauna jikinsa ta ce" me ke damunka? A hankali ya dago, ya dago fuskarta yana kallonta, muryarsa ya raunana ya ce" da na ji bakya tare da muhalina zuciyata ta kusan bugawa, Wujdane ki ce kina so na ko hankalina zai kara kwontawa Idannuwanta ta kikifta tana kallonsa A hankali ya matso jikinta sosai ya bata runguma ta kirki ya shiga kissing dinta Dan ture shi take murya a raunane ta ce" wai ya aka yi kai ba ruwanka du inda ya kama ka kana yin abinka ne ? Gidan momy ne fa? Murmushi ya yi yana lumshe idannuwansa, ba zai iya bata amsa ba, sam ba zai iya ba, yana da muradin ji daga bakinta cewar tana son sa sai dai ta kasa faranta masa A hankali ta shafa dan turaren da ta lakato, ta karaso inda yake ido lunshe, murmushi ta saki ta raba kafafuwanta ta yi mazauno saman cinyarsa, A hankkali ta shiga lalubo lebensa ta cafke na kasan ta shiga aika masa da kiss, Haukace mata ya yi yana ta lalubenta, da kyar ta samu ta kai bakinta wajen kunensa ta ce" ina son ka, ina son ka, ina son ka Alaidine ya birkice, ya damketa ya kaita wajen da baya tunanin zata manta, ya bata soyayar da bai taba ba wata mace ba, bai nuna kyankyaminta ko wani abu ba ya baiwa komai hakinsa, Sun yi kukan samun nutsuwa sum zuba sambatun da lale du wanda ya yarda ya bi ta wajen dakin sai ya jiyo su, bayan komai ya lafa suka mane da juna suna masu godiya ga Allah da ya halatawa junansu juna Bayan shekara biyu Tsayayar Alawiya , nuna isarta, rashin yiwa iyayensa biyaya ta saka dole Alaidine yayk watsi da ita domin ya fada bai ga ba macen da zata raina masa iyaye ya zauna da ita koda kuwa Wujdane ce Rayuwar su Aba ta samu baban ci gaba domin Alaidine ya dankarawa aba ginin Makarantar islamiya ta kasa da kasa, wace aka zuba malamai da katon masalaci ....sosai makarantar ke tafiya tana kara bunkasa domin mai jan ragamarta baya yi da son abin duniya sai dan kara habaka adinin musulunci Sun samun canjin muhali, yaya kuwa ya samu fita waje dan ci gaba da karatunsa da ya tsaya a da saboda halin babu Aisha na dauke da tsohon ciki tana karantar nurce inda mijinta jamail ya ci gaba da kasuwancisa shima wani ne sosai a harkar Park suke, Alaidine ne ke dauke da wata kyakyawar yarinya kanta luflufluf da gashi tana ta dariya da halewar tsinke a hannunta tana ta laluma sai goga masa take a jikin tigarsa ta shafa fara kar Idannuwanta ta juyo tana nuno wani waje tana cewa" mama mama mama Nan na ga idannuwanta itama tamkar na Wujdane sannan wajen da take nunawa Wujdane din ce tsaye da bakar abayarta ta yane kanta fuskarta da dan karamin gilas na gayu tana rike da hannun yaronta tana nufo su Kanta ta dafe ta ce" HABIBY rigarka *Iman* ta bata maka da dati Murmushi ya yi ya ce" toh ya na iya hearty? Ku mu je kar su aba su gaji fa Nan suka antaya Boy sai labari yake basu na makaranta da yan ajinsu Ma.asalam Nan na kawo karshen litafin WUJDANE, Allah ya bamu ladan dake ciki ya yafe mana kura kuran da muka aikata a ciki Maman Lalla ce wato SAJIDA