[8/6, 5:59 PM] mrs bilkisu: ________________________________ BAN SAKETA BA!!! ________________________________ NA BILKEESA IBRAHEEM {Bilyn Abdul} ________________________________ https://mrsbilkisa.blogspot.com ALHAMDULILLAHI ALA KULLI HALIN. ya ALLAH kabani ikon faďin abinda zai amfani al'ummarka ka tsare harshrna daga faďar abinda zai cutar da al'ummarka.AMeen. 😂ina farincikin sake haďuwa daku a sabon littafina, mai suna BAN SAKETA BA😂👌🏻. Duk wanda ya canja mini wani abu aciki ban yafe masaba😎. Ina mi'ko ďunbin godiya da gaisuwa tareda fatan alkairi ga dukkan masoyana, ina godiya da ďubin gaisuwarku gareni, dason fara rubutun BAN SAKETABA,, da nabari sai bayan biki amma 'kaguwarku tasa bazan iya share bu'katunkuba,, dan haka zan fara, saidai zakumin uzuri dan zan gaza baku posting akowace rana, sakamakon nayi busy dayawa, ALLAH yasa mudace,, muje zuwa LABARI😁👌🏻. Sadaukarwa~ ya Abdul {city phone's} Page......1⃣ .......Yauma kamar kullum tana 'kasan dalbejiyar data zame mata tamkar ďakinta aduk lokacin da bata da lecture's. Kallo ďaya zaka mata kagane tana cikin duniyar tunani, da sauri taďago kai tana dube2, taja numfashi mai 'karfi, cikin sanyin murya ta ce, "hancina kadaina faďa min 'karya, ka daina sha'ko min abinda ba gsky ba, tunda nake awajen mutum ďaya nata6a jin wannan 'kamshin, kuma tunda yanisan ceni ban sake jiba, ban bashi damar dazan sake jiďinba, domin shi ya kasance mugu azzalumi, macuci!!!....ta faďa tana mai zubar da hawaye. Wlhy na tsaneka Isma'il!!! mayaudari kawai ta fashe da kuka mai ban tausayi. Haba iman kina ganin haka rayuwa zata kasance kullum cikin kuka da tunani??, maganar miss xoxo takatsema iman surutan datakeyi, iman mu masoyankine masu 'kaunarki 'kauna irinta 'yan uwan juna, tundaga randa muka fara ganinki a school ďin nan mukaji muna 'kaunarki, dan ALLAH badan muba ki sanar mana damuwarki kozaki samu sau'ki, idan kuma munada taimakon dazamu yimiki saimu taimaka miki koda da addu'ane. Gsky ne Miss xoxo yakamata iman tasanar mana damuwarta inhar ta yarda damu kamar yanda muka yarda da'ita, yau kusan shekararmu biyu da watanni tare bamu ta6a 6oye miki sirrinmuba, duk abinda yadamemu muna sanar da junanmu, ke kaďaice acikinmu kike 6oye mana sirrinki, bamusan dalilin hakanba kokuwa bamu cancanci sanin taki damuwar bane oho??, amma kinsan damuwarki itace tamu, farincikinki shine namu, wlhy inaji ajikina tamkar uwa ďaya uba ďaya suka haifemu. Gskyarki ne Reefat xoxo tafaďa tana gyara zama, takamo hannun iman ta rumtse anata, iman inhar kin ďaukemu a matsayin 'yan uwa ko 'kawaye na kwarai to ki sanar damu damuwarki, koda addu'ane mutayaki, mungaji da ganinki haka iman, shekara biyu ba kwana biyu bace, inkuma bazaki faďa manaba bazamu takurakiba, saidai zamu taimaka miki da addu'a insha ALLAHU. tami'ke Reefat tashi mutafi xoxo tafaďa tana kama hannun Reefat. Iman ta fashe da kuka dan ALLAH xoxo karku tafi, kuyi ha'kuri ku saurareni. Ya za'ayimu saurareki iman kullum haka kike faďa mana amma kin kasa faďa mana komai, kina ganin zamu cigaba da takuraki harsai kin sanar damune??, dammi zamu takura miki akan abinda bakida ra'ayin faďa mana???. Naji na amsa laifina amma dan ALLAH kudawo karkuyi fushi dani, wlhy nima ina 'kaunarku inajinku tamkar 'yan uwana najini. ALLAH sarki xoxo akwai tausayi dan haka saita jawo hannun Reefat suka dawo suka zauna, tsakiya suka saka iman, Reefat ta ce, "iman muna jiranki dan ALLAH ki sanar damu damuwarki kinji, 'kila mu iya taimaka miki da wani abu. Iman tasa hannu ta share hawayenta tareda ďanjan hancinta, tabi aminan nata da kallo, miss xoxo Reefat kuyi ha'kuri ban ta6a 6oye muku wani abu daya danganci rayuwata saboda rashin yarda daku ba, a'a ina ganin abinda yafaru dani tamkar sirrinane tunda yafaru dani a shekarun bayane kafin na haďu daku, sannan ina ganin abinda yafaru dani yariga ya faru ya wuce, amma ina neman afuwarku gareni, insha ALLAHU a wanan karon zan faďa muku wacece SAUDAT!?" saidai kuyi ha'kurin zuwa weekend sanan muna free saimuyi maganar atsanake. Zan faďa muku tushen rugujewar rayuwata da tushen tubalin ginin damuwata......ta fashe da kuka mai tsuma zuciya da ruhi, ganin haka Reefat da xoxo suka shiga tayata suma, saida sukayi kuka mai isarsu babu mai lallashin wani, saida suka gaji dan kansu sanan sukayi shiru. Mi'kewa sukayi suka nufi class kowa zuciyarsa babu daďi, iman sai waige2 takeyi danjin tamkar 'kamshin turaren yana bibiyarsu, Xoxo ta ce, "iman wai mikike nemane??, lokaci da dama nakan ganki kina waige2 miyasa??. Murmushi Iman tayi na takaici, wanan duk yana cinkin tarihin rayuwata xoxo karki damu asannu zaki gano abinda yakesani waige2 a wasu lokuta da dama. Daga nan suka shiga aji, babu daďewama malami yashigo suka fara ďaukar darasi...............✍🏻 Tofa masu karati komi wanan littafi ya kusa??, shin miye damuwar kawarsu Miss xoxo ne??, dani daku duk akan tambaya ďaya muke, domin nima bansan komai gameda hakaba, sai munbi wanan labari sannu ahankali sannan zamu samu amsar tambayoyin dake fal a zuciyarmu. Takuce dai Bilyn Abdul. Saikunjinei!!!!!!👌🏻 Luv u oll my fan's ©2017 Battery low🔋😜👌🏻 [8/6, 5:59 PM] mrs bilkisu: ________________________________ BAN SAKETA BA ________________________________ NA BILKEESA IBRAHEEM {Bilyn Abdul} ________________________________ https://mrsbilkisa.blogspot.com Sadaukarwa~ ya Abdul {city phone's} MIYAKAMATA NAYI???. amatsayina na uwa miya kamata nayi??, alokacin dana fara mallakar 'ya'yana 'kyautar ALLAH, 'kyakykyawan lafazi, yawan addu'a, nasiha alokacin dasukayi ba dai2ba, cusamusu tsoron ALLAH azuciyarsu tun suna 'kanana, domin icce tun yana ďanye ake lam'kwasashi, ALLAH yasa mu gyara. Page~2⃣ ...........miss xoxo & Reefat matasan 'yammata 'kyawawa, ga nutsuwa da ilimi, tundaga randa aka kawo iman school ďinsu suka haďu suka 'kulla abota mai 'karfi da zuminci, suna 'kaunar junansu, wanda bai saniba idan yagansu saiya ďauka 'yan uwan junane dama can, amma abin ba haka bane.. Miss Xoxo 'yar Kano ce karatune yakawota garin na ZARIA...Reefat kuma 'yar Yola ce ADAMAWA itama sanadin karatu tazo garin na ZARIA, itakam iman 'yar katsinace & kano . Bayan sun kammala luctures ďinsu suka nufi ďaki agajiye, Reefat tazube a tsakar ďaki tana faďin wash ALLAH na, nagaji wlhy, malamin nana yayi mugun wahalar damu gsky. Miss xoxo ta ce, kibar ďan iska Reefat saikace daga kansa aka fara ilimin boko, ALLAH na tsanesa tamkar mutuwata, shege gashi mummuna sai girman kan tsiya kamar ďan wani da wata. Kudai ALLAH ya shiryeku iman tafaďa tana fitowa daga bayi, kuzauna kuyita zagin malamanku saikace wasu 'kawayenku. Reefat ta harareta ai dama ke bazaki ganewaba, wannan ďan iskan malamin bashida kirki, kidubafa yanda yadaka miki tsawa ďazu ALLAH yabani haushi. To kuyi ha'kuri malamin mune, kunga yanada ikon nuna mini kuskurena kenan.. Xoxo ta ta6e baki kinga Reefat barta indai iman ce babu abinda zaki faďa akan malamai ta amince. Iman ta ce, "kudai kuka sani nikutaso muci abinci ALLAH yunwa nakeji. Yau juma'a 'yammatan suna free basuda lectures ko ďaya, suna gida, dawuri suka gama komai na al'adar rayuwarsu dan sonjin labari, suduka suna cikin ďakinsu sun saka tiren indomi a tsakkiya kowa da kofin shayi agabanta. Iman ta mi'ke domin ďakko wayarta dake ajikin caji, kamar jira ake ta kunna kira yashigo, tayi murmushi sanan ta ďaga, hello my bro's ya gida??. Daga can 6angaren aka amsa mata, ta ce, "yasu gwaggo??, Kowa 'kalao aunty, ya karatunki??. Muna nan muna bugawa. To ALLAH ya taimaka. Amin autan gwaggo. Dama Musayyeef ne ya ce, "nakira ki ku gaisa, okey yana ina??, gashi. Hello aunty Maa! kina lafiya??, lafiya lau musayyeef ykk ya makaranta??. Aunty maa! lafiya lau. To kana dai 'kokari ko??, eh mana, harma anty tace nafi kowa 'kokari a class ďinmu. Da 'kyau ďan albarka, to mikake bu'kata??, babu komai aunty maa! dama inaso na sanar miki jiya da dare uncle ďi na yazo. To naji sai anjima na kiraka muyi hira yanzu ina karatu. To aunty maa! sai anjima....yaron ya faďa cikin tsallen murna. Bayan ta kashe wayar tadawo ta zauna saidai fuskarta babu walwala. Xoxo ta ce, "lafiya naga kin canja fuska dawa kikayi waya??, tayi murmushin ya'ke lafiya lau mikika gani??, da Musayyeef nayi waya fa. Reefat ta ce, "miyasa baki bani shiba mun gaisa, autan gwaggo sarkin wayo, inason yaronnan wlhy kamar gwaggo tabani, iman tayi dariya mizai hana tabaki indai kinaso??. Xoxo ta ce, "aii koni ina 'kaunar yaronnan, duk yafi 'yan gidanku 'kyau, kamar ba ďan gidanba. Iman tayi dariya hakadai kukace, amma yama za'ayi yafimu 'kyau, aii banma yardaba, hakadai sukaita hirar Musayyeef har suka gama cin abincinsu. Bayan sun gaba duk suka nutsu suna sauraren iman, iman ta gyara zama sanan taja ajiyar zuciya mai 'karfi. SAUDAT SULAIMAN UMAR, shine cikakken sunana kamar yanda kuka sani, amma ana kirana da iman kasan cewar naci sunan kakata ta wajen uba, mu uku iyayenmu suka haifa, Aunty Salma itace babba saini saikuma auta Shamsuddeen muna kiransa da deeni. Asalinmu mu 'yan jihar katsina ne a 'karamar hukumar musawa, aikine ya kawo Abbah kano. Aunty salma ta girmeni sosai gsky dan tsakanin mu akwai mutum biyu amma sun rasu, ni 'yar gatace agidanmu saboda kasancewar naci sunan kakata dan haka Abbah yake jidani sosai, to itama gwaggo haka, inada muskilanci dan bakowa nake kulawaba shiyyasa natashi banida 'kawaye, lokacin dana gama primary ne muka dawo kano, ita kuma aunty Salam ta kammala secondary ďinta. A nana kano taci gaba da karatunta a FCE kano, nikuma secondary, deeni kuma yacigaba da primary kasancewar mahaifinmu ďan bokone, balaifi munada hali iya gwargwado dankuwa ba'a kiramu talakawa ti6isba, komai muka bu'kata mahaifanmu suna mana iya bakin gwargwado. Ina js 2 akayi bikin aunty salma da ya Abdu'majeed wani ďan uwanmune dake can katsina, shekarar su biyu a Kt aka dawo da ya majeed kano a wajen aiki, zuwa sannan sun haifi ďansu Bello suna kiransa Affan saboda sunan baban ya majeed ne. Agidanmu suka fara sauka, bayan kwana biyu suka shirya komawa gidansu sanan an kammala gyarawa. Ya Majeed ya bu'kaci su tafi dani nayi musu kwana biyu tunda muna cikin hutu, da Abbah ya'ki amma dasuka dage saiya yarda akan sharaďin danayi sati ďaya zan dawo gida, ba musu suka amince.. Ranar adaren muka tafi, gidan ya haďu dan ya Majeed ya gyarashi da 'kyau. Kwananmu uku da zuwa gidan ya majeed natashi da matsanancin ciwon ciki, haka na rin'ka kuka ina kiran gwaggo da Abbah, dan tunda nake ban ta6a ciwo mai kama da wannanba. Aunty Salma tashiga ruďu gashi ya majeed baya nan yafita aiki, tayi 'kokarin kiransa a waya ta shaida masa halin danake ciki, ya ce, "gashi nan zuwa dama baiyi nisaba. Cikin minti 15 ya Majeed ya iso, bai jira komaiba ya ďaukeni muka nufi mota, aunty Salma ta biyomu abaya, a bayan motar yasakani aunty Salma tashiga ta ri'keni ya amajeed yaja motar muka tafi asibiti. Waya yaďauka yakira wani abokinsa dake aiki a asibitin kansa, muna zuwa akayi mana tarbar gaggawa, aka kuma bamu taimako na musamman. Sai wajen 'karfe uku na yamma na farka, aunty Salma ce zaune akusadani sai kuma ya majeed zaune akujerar dake gefen gadon. Ahankali na buďe ido ina kallon silin, aunty Salma ta ce, "iman kin farka?, kai na ďaga mata alamar eh, ya majeed ya ce, "sannu iman ya jikin naki?, na ce, "da sau'ki yaya, ya kuma faďin yanzu ina yake miki ciwo?, ahankali na ce, "yaya babu ko ina saidai inajina akan laima. Aunty salma ta ce, "laima kuma?. Na ce, "eh. Aunty salma tasaka hannu a 'kasana saiga jini, ta ce, "jini kuma iman? miya sameki haka?, da sauri ya majeed ya ce, "jini kuma?, aunty salma ta ce, "wlhy kuwa yaya jini, ya mi'ke kinga bari nakira Isma'il yagani. Babu daďewa yaya yadawo tareda Dr Isma'il, yaďanyi dube2nsa sanan ya kalli ya majeed abokina karku damu, bawata damuwa bace yanzu ta tashi ta gyara jikinta bari na turo Nurse ta taimaka mata. Kai kuma mije na ganka a office. Suna fita saiga Nurse tashigo, itada aunty salam suka taimaka min na gyara jikina, Nurse ďin ta gyara gadon kamar komai bai faruba, nadawo na sake kwanciya dan jikina babu kwari ................✍🏻 Luv u oll my fun's ©2017 Battery low🔋😜👌🏻. [8/6, 5:59 PM] mrs bilkisu: ____________________________ BAN SAKETA BA _______________________________ NA BILKEESA IBRAHEEM {Bilyn Abdul} ________________________________ https://mrsbilkisa.blogspot.com Sadaukarwa ga~ ya Abdul (City phone's) MIYAKAMATA NAYI???. Kasancewata uwa yakamata nayi 'kyakykyawan lafazi ga ďan daba nawaba alokacin danaga yayi ba dai2ba, karna la'anci ďan wani kona kirashi lalatacce, shiriyar ALLAH yakamata na ro'ka masa, domin ďa na kowane, bansan mi gaba zata haifarba akan nawa 'ya'yan. ALLAH yasa mu gane. Page...3⃣ Ya majeed kam yana office ďin Dr Isma'il, bayan sun zauna Dr Isma'il ya kalli ya majeed abokina ba wata matsala bace take damun 'kanwarmu ba, ciwonsu ne na mata, dan tafara period ne, saidai yazo mata da matsalar ciwon mara, amma karku damu dama hakan yana faruwa, zamu bata magani insha ALLAHU komai zaiyi dai2, inagama zuwa anjima zan sallameku inasha ALLAH. to abokina mungodefa sosai ALLAH yabar zuminci. Daga nan sukaďanyi hira ya majeed ya fito dan Dr Isma'il yanada masu jiransa. Aranar aka sallamemu muka dawo gida, washe gari da yamma saiga Dr Isma'il yazo gidan ya majeed. An masa tarba ta mutunci, bayan an gama gaishe2 ya ce, "ni banga patient ďinaba kumani ita nazo dubawa. Aunty salma ta ce, "tana ďaki tanakuma jinmu inaga miskilancinne ya motsa mata, bari nakirata, bayan aunty Salma ta kirani na saka hijjab nazo, suna zaune a falo Affan yana cinyar Dr Isma'il, na zauna a'kasa cikin jin kunya na gaidashi, duk miskilancina da shagwa6a inada tsananin kunya. Cikin fara'a ya amsa, ya ce, "my patient ya jikinki??, "Na ce, "da sau'ki. ''Ya ce, "ALLAH yakara sauki. Na ce, "amin. Nami'ke da nufin komawa ďaki, Dr Isma'il ya ce, "a'a my patient sai ina kuma??, Na ce, "zanje cikine, ya ce, "da wuri haka?, kofa gaisawa bamuyiba kuma zuwannan nakine. Nayi murmushi wanda mutane dayawa suke faďamin yana 'kara min 'kyau, kasancewar ban cika yiba saboda miskilancina, idan nayi kumatuna sukan lotsa. A zuciyarsa ya ce, "ya salam yarinya 'karama zata haukatani. Ganin kallon dayake mini yasani tashi da gudu na shige ciki, yabini da kallo yana murmushi harna 6acema ganinsa sannan yaja ajiyar zuciya. Ya majeed ya ta6ashi abokina miye damuwarka??, Dr Isma'il yasaki sassanyar ajiyar zuciya sanan ya ce, "brother 'kanwarka ce damuwata, saidai tayi 'kan'kanta dan na lura bata wuce sha biyarba. Ya majeed ya tuntsure da dariya kai Isma'il wlhy kaidai baka rabo da wasa, kai yanzu idan ance ka tsaya jiran iman saika tsaya??. Dr Isma'il ya ce, "kajika da wata magana, aini koba ace najirabama zan jira kuma zaka sha mamakina.. To ALLAH ya taimaka amma saidai ta biyu ko??, harararsa Dr Isma'il yayi, ta biyu kota ďaya, aini kasan babu mata biyu a tsarina saidai kaddarar ALLAH, dan babu inda bata kai mutum. Ya majeed ya jinjina kai yana murmushi, amma abokina kana ganin ya Mansur da mama zasu yarda, yakamata fa ace kayi aure tuni, kosaika zama tunzurun zurun ne?. Dr Isma'il yay dariya, kana min wula'kanci wlhy majeed kaima naga duka shekararka nawa da auren?, su yaya kuwa banida matsala dasu, abinda nakeso suma shi suke so, kaidai katayani da addu'ar neman za6in ALLAH kawai. Shikenan ALLAH yaza6a mana abinda yafi alkairi. Amin Dr Isma'il yafaďa. Da dai ya majeed ya fahimci Dr Isma'il da gsk yakeyi, saiya shige masa gaba awajen Abbah. Abbah yayima Dr Isma'il tambayoyi kamar yanda shari'a ta tsara, yako amsa masa yanda yadace. Saiya bashi izinin neman SO a wajena, nikam bammasan abinda ake cikiba, dan lokacin da nadawo gida mun koma makaranta. Kai kutashi muyi sallah ďaya ta wuce, kuma ALLAH yunwa nakeji, Xoxo ta harareta ALLAH iman kin iya wula 'kanci saida labarin yafara ďaukar daďi zaki 'kir'kiroma mutane wani jin yunwa, inama laifin muyi sallar??. Iman tayi dariya sorry dear karki damu aii idan tunbi ya ďauka labarin saiyafi daďi ko??. Reefat ta ce, "ALLAH ni ko yunwarma banaji, burina kawai naji 'karshen labarinnan, karku damu aii muna gamawa zan cigaba. To gsky saidai asiyo abincin ko asake cin indomi dan in ba hakaba girki zai 6ata mana lokaci, gsky ne Xoxo kunga kuyi sallar tunda ni an hutar dani, kafin ku idar naje na samo mana abinda zamuci ko bai yiba??. Sukace yayi. Bayan sun gama cin abinci iman ta ce, "saitayi wanka sanan, saida tagama ja musu rai sanan taci gaba. Dr Isma'il yakasa sanar dani sirrin zuciyarsa saboda yana min kallon 'karamar yarinya, dan gsky asanan ban wuce sha biyar ba. Ahaka wata yazagayo al'adata tazo nasha wahala sosai, su gwaggo suka rasa yanda zasuyi dani, na daure na ce, "sukira aunty Salma. Babu 6ata lokaci aunty Salma tazo muka tafi asibiti wajen Dr Isma'il, shiyya dubani yamin allura yaďan kwantar dani na yini ďaya. Daga nanfa ciwon mara yazamemin jiki, har fargaba nake wata yazo, hakama gwaggo tana tausaya mini sosai. Ana haka Dr Isma'il yazo ma Abbah da zancen zai shiga soja, dan dama burinsa kenan tun yana yaro, amma saboda yayansa yanason yazama likita ya ha'kura yayi karatun likita, to yanzu damace tazo masa, shine yakeson yayi amfani da ita. Abbah ya ce, "ALLAH sarki, ai haka akeso Isma'il mutum duk inda yake yazama mai biyayya ga nagaba dashi, saiyaga yazama abinda baiyi zatoba arayuwa, dan masu iya magana nacewa dana gaba ake gane zurfin ruwa, to inamaka fatan Al'kairi arayuwar ka, domin kai yaron kirkine, ALLAH yabada abinda akaje nema, kuma ayo nasara. Amin Abbah nagode da addu'arka gareni ALLAH yasaka da al'kairi, babu damuwa abba yafaďa, kaga bari naturo maka iman ďin kuyi sallama ko??. Cikin jin kunya Dr Isma'il ya ce, "Abbah dama ka 'kyaleta. Abbah ya ce, "sabodami Isma'il?, ba sallama zakuyiba?, Dr Isma'l yaďan sosa gefen wuyansa saboda jin kunya ya ce, "Abbah karka damu, iman tayi 'karamane yanzu, inason saita gama koda secondary ne, saina fahimtar da ita nufina akanta, amma yanzu za'a raba mata hankali gida biyu. Abbah yay dariya to shikenan Isma'il ALLAH yay maka albarka, yakuma bada sa'a akan abinda akaje nema. Dr Isma'il ya ce, "Amin Abbah ngd da 'kaunarka gareni. Abbah ya ce, "karka damu aii kai yaron arzi'kine wanda ya cancanci a 'kaunacesa fiyema da haka.. Daga nandai sukayi sallama, Dr Isma'il yatafi training ďin soja na wata shidda.. Nikam ban saniba, nagadai bana ganin yana zuwa wajen Abbah yanzu kamar yanda yakeyi da, ban ta6a yun kurin tambayar waniba, dan babu wata ala'ka tsakanina dashi banda ta mara lafiya da likita, haka nacigaba da shan wahala duk 'karshen wata, dukda wani likita yana dubani a asibitin su Dr Isma'il, amma bai iya shawo matsalata kamar Dr Isma'il. Awata Asabar datayi dai2 da dawowar Dr Isma'il kano, dan ayanzu yazama soja, ALLAH yacika masa burinsa, yazama likitan sojoji, gashi likita gashi babban Soja. Aranar natashi da matsanancin ciwon mara wanda zan iya cemuku tamkar yafi na kullum ma dan har suma nake, gaba ďaya hankalin iyayena yatashi, ankira likitan dake taimaka min yaymin allurar amma abanza dan babu abinda ya canja agareni, har zuwa 'karfe huďu na yamma, saidai yalafa yadawo. Awanan lokacin tuni Dr Isma'il yana gida yana hutawa, amma sai barcin ya gagari idanunsa, dan tunda yashigo kano gabansa ke faďuwa zuciyarsa tanata kwaďaita masa son ganina, dan ba 'karamin kewata yayiba acikin shekara ďayar nan.. Zumbur yami'ke yacanja kayansa zuwa shadda mai 'kyau ďinkin zamani, dan Dr Isma'il yanada 'kyau babu laifi, yafito falo yana ďaura agogo, auntynsa matar yayansa ta ce, "a'a angona sai ina kuma??. Dr Isma'il yay dariya angon iman dai, kekam ga angonki nan akusada ke, ya nuna yayansa dake zaune yana masu dariya. Ta ce, "wacece iman kuma??. Dr Isma'il yay murmushi karki damu zaki santa kwanan nan, yanzuma sauri nakeyi amma kibini bashi idan na dawo zan sanar dake iman, yafice yana faďin yaya aunty saina dawo, yanaji tana kwala masa kira amma bai sauraretaba, motar yayansa ya ďauka yafice danshi bashida mota sai mashin, yayansa kuma baya masa shamaki da nasa motocin. Yayansa ya tuntsure da dariya nikam kina bani mamaki keda Isma'il ke yanzu har kin yarda da zancensa ne??. To ya bazan yardaba tunda bai ta6a kawo mana makamanciyar wanan maganarba. Ito hakane ALLAH yasa da gsk yakeyi. Dr Isma'il kuwa kaitsaye gidanmu yanufo, yay parking a kofar gida, yana tsaye gaban motar saiga deeni yadawo daga aika. Dr Isma'il ya ce, "zomana abokina, babu musu deeni ya'karasa garesa, ya gaishesa. Dr Isma'il ya ce, "dan ALLAH shiga gidanan kamin sallama damai gidan. Deeni ya ce, "wai Abbah??. Eh shinake nufi, ko kaima ďan gidanne ?, dan naga kana kama da Iman. Ya ce, "lah ina kasan aunty iman??, Dr Isma'il ya ce, "anan gidan, to aii yanzuma itace batada lafiya dan har suma takeyi, aruďe Dr Isma'il ya ce, "suma kuma??, deeni ya ce, "eh suma, to yanzun Abbah na nan?, eh yana ciki, jeka ce masa Isma'il ne yazo gunsa. Deeni yazo ya sanar da Abbah, Abbah yanajin Dr Isma'il ne da hanxari yafito, bayan sun gaisa Dr isma'il ya ce, "yanzu wani yaro yake sanar dani Iman babu kafiya?. Eh hakane Isma'il. Sun shigo gidan, sanda suka shigo inata mur'kususu ajikin gwaggo dan har wani shiďewa nake saboda azabar ciwo, gwaggo sai kuka take. Dr Isma'il yakalli Abbah aruďe Abbah idan bazaka damuba na ďauketa muje asibiti mana. Abbah ya ce, "babu wata matsala Isma'il......aibai bari Abbah ya 'karasa faďaba ya sunkuceni yay waje, amota yasakani Abbah yakaraso da hanzari yashige muka tafi asibiti, acanma ďaukata yayi, ďaki guda aka waremini nikaďai, ya shiga bani kulawa ta musamman, cikin 'yan mintina ya shawo kan matsalata harna samu barci................✍🏻 💕💚💕 Page~4⃣ ..........Washe gari nadawo dai2 ina kwance agado gwaggo tana zaune akusa dani, aunty Salma kuma tana tsaye tana waya, Dr Isma'il yaturo 'kofa yashigo da sallama, rissinawa yayi ya gaida gwaggo, gwaggo tami'ke tafita dan tanajin kunyar sirikin nata, itama aunty Salma saitayi waje, Dr Isma'il yajawo kujerar da gwaggo ta tashi ya zauna kusadani ya tsuramin idanu Iman ya jikin naki?. Cikin jin kunya na ce, "da sau'ki. yanzun babu inda yake miki ciwo?. na ce, "babu, ya ce, "Alhmdllh. Ince dai kinci abinci ko?, naďan kalleshi ta gefen ido na ce, "a'a na koshi, ya ce, "mikikaci da har kika 'koshi?, na ce, "nasha tee ďazu. Yay murmushi kice na shirya nemo maganin cin abinci matata batason cin abinci, da sauri na kalleshi, ya kannemin ido ďaya tareda ďaga gira, hannu nasa na rufe fuskata saboda kunya, ya ce, "inson mace mai kunya ashe ALLAH zai bani, na kuma cusa kaina cikin cinyoyina. Yay dariya sanan ya ďauki filet, kulan da aunty salma tazo dashi ya buďe, ya ce, "iman lallai ke 'yar gatace, wannan irin farfesu haka, nidai kaina na tsakiyar cinyoyina nakasa ďagowa saboda kunyar maganganunsa. Ya zuba farfesun yace nazo naci nasha magani. Na ďago kaina cikin jin kunya na ce, "kawo to, ya ce, "waneni da barin gimbiya cin abinci da kanta, aii da hannuna zan baki, na ce, "A'a ngd zanci da kaina, ya ce, "nikuma ban yardaba, haka dole na hakura yabani da kansa, saidai cikin matu'kar jin kunya nake kar6a, shikam sai dariya yake mini. Aranar aka sallameni muka koma gida.. Kunaga kutashi muyi sallar la'asar sanan saimu cigaba. Bayan sun idar da sallar la'asar iman ta ďora labari. Iman tabi Reefat da Xoxo da kallo tareda jan numfashi, wato 'yan uwa bayan kwana ďaya da sallamata Dr Isma'il yazo gidanmu, an masa tarba ta mutunci, dan su gwaggo suna son Dr Isma'il sosai. Bayan sun gama gaisawa Dr Isma'il ya ce, "Abbah dama nazone nayi muku bayani akan ciwon iman. Abbah ya ce, "ina saurarenka Isma'il. Dr Isma'il yay 'kasa da kai sanan ya ce, "wato Abbah naďanyi bincikene akan ciwon iman, saina gano ta hanya ďayane kawai zata iya rabuwa da ciwon, hanyar kuma itace......saikuma yayi shiru, Abba ya ce, "inajinka Isma'il karkaji komai ka sanar dani, Dr Isma'il ya 'kara kasa da kai dan maganar tayi masa nauyi abaki, amma ya daure ya ce, "hanyar itace aii mata aure, ta wanan hanyar kawai nake ganin za'a samu mafita. Abbah yay murmushi to aii Isma'il inadai hakane banida damuwa tunda lafiyarta muke bu'kata, inaga indai har iyayenka sun amince saisu turo, inyaso saita cigaba da karatun a ďakinta, dan haka nabaka dama kaje kayi shawara da nagabatanka, nima zanyi da gwaggonsu dakuma 'yan uwana. Dr Isma'il ya ce, "to ngd ALLAH ya 'kara girma. Abbah ya ce, "amin, yami'ke yana faďin bari na turo maka maman tawa. Bayan Abbah yashigo ya ce, "naje falon ba'ki ana jirana, na ce, "to, hijjabi nasaka na nufi falon, yana zaune akujera mai zaman mutum ďaya, yana cikin farar shadda ďinkin boda amma babu hula akansa, yayi min 'kyau sosai, dan Dr Isma'il farine 'kyakykyawa, yanada suma mai 'kyau wadda take shan gyara, bayida saje saidai wani ďan gemu na gayu daya ajiye, wanda ya'kawata 'kyawun fuskarsa, dogone sosai yanada 'yar kiba daidai misali, akwaishi da yawan fara'a, dan a yanda nakula kamar ba miskili bane. Da sallama na shigo 'kamshin turarensa ya bigi hancina, inason kamshin turaren tun sanda aka fara kaini asibitinsa, yaďanja gilas ďinsa kaďan zuwa 'kasan ido, yakuramin idanunsa matsakaita girma, na zauna saman carpet, yay saurin faďin a'a ban yardaba tashi ki hau kujera, cikin jin kunya na ce, "nanma ya isa. To shikenan nima bari na sauka kasan tunda nan kikeson mu zauna, ganin zai zauna kasa nayi saurin hawa saman kujerar, ya tuntsure da dariya to shikenan gimbiya, nidai kaina yana 'kasa na gaisheshi, ya amsa cikin fara'a, sanan ya ce, "ya jikinki??. Na ce, "aii ni na warke. Ya ce, "zakidai warke in sha ALLAHU nan gaba kaďan. Murmushi kawai nayi batareda nayi maganaba. Ya gyara zamansa sosai, tareda 'kara daidaita nutsuwarsa, yayďan gyaran murya alamar maganar dazaiyi tanada muhimmanci. Ya ce, "imaniii nasan kin sanni tunba yanzuba, tun sanda aka fara kaiki asibiti a matsayin patient ďina??, na ďaga kai alamar hakane, ya jin jina kai, to tun aranar naji kin kwanta min arai, nakamu da sonki na gsky, dalilin dayasa na sanar da majeed abinda ke raina kenan, shine ya shige mini gaba zuwa wajen abbah, banyi kasa aguywa ba wajen sanar da abbah sirrin zuciyata. Alhmdllh Abbah ya fahimceni yakuma kar6eni amatsayin siriki, tunkuma a wancan lokacin ya mallaka minke, yakuma bani damar neman so awajenki. Alokacin nayi wani nazari akanki, dan na lura ke yarinyace karama, wanan dalilin yasa na ce, "abarki sainan gaba, dama na sanar dasune kamar yanda addinina ya koyar dani, to saikuma wani uzuri yatasomin alokacin, natafi training ďin soja saboda tuni inason zama soja, saidai yayana yafison nazama likita, ina girmama bukatarsa dan haka nacika masa burinsa nazama likita, tonima sai ALLAH yacika min nawa burin nasamu damar zama soja ayanzu. Ranar dana iso kano saina tarar bakida lafiya, danayi bincike akan ciwonki saina gano nine maganinsa, dan haka nazo yaunayima abbah bayanin komai. Ya gyara zamansa to yanzudai zancen danake miki abbah yabani izinin turo iyayena su nemamin aurenki, shiyyasa nakeson jin tabakiki dan kar asoya mai amanta da albasa iman kina SONA kuwa???, nayi miki??, karki 6oyemin sirrin zuciyarki kinji.. Gsky naji kunyar zancensa dan haka na 6oye fuskata da tafin hannuna, Dr Isma'il yazare gilas ďinsa karkimin haka Saudat!!, ki daure kisanar dani kina SONA???. cikin jin kunya naďaga kaina alamar eh. Yasaki murmushinsa mai 'kayatarwa ya ce, "Alhmdllh, iman nagode da soyayyarki gareni, ALLAH yabarmu tare har abada, yakuma kaďe duk wata fitina dazata wanzu a tsakaninmu, ala66ana na ce, "amin ya rabbi. Ya kalli agogon hannunsa idan bazaki damuba zan sanar dake koni wanene dan naga munada sauran lokaci. Na ce, "babu damuwa. Lemo ya ďauka ya tsiyaya acikin kofi, yasha kaďan sanan ya ajiye, ya ďauki gilas ďinsa yasaka, gilas ďin yana matu'kar kara masa 'kyau sosai. ♡☆♡ Nidai sunan Isma'il Muh'd Basheer, mu biyu iyayenmu suka haifa, yayana Mansur saini auta, mu 'yan asalin garin sakoto ne, aikine yakawo mahaifinmu kano, mamata kuma 'yar tarabace Jalingo kenan, bafulatanace ta asali, dan harta bar duniya hausarta bata fita sosai, tuni mahaifinmu ALLAH yay masa rasuwa saka makon haďarin mota dayayi daga kano zuwa sokoto, sanan ina wata 6 a duniya, Rasuwarsa ta girgiza maman mu dan haka takamu da ciwon zucuya itama babu daďewa tabi bayansa, inada wata 10 sanan aduniya, 'kanuwar maman muce tacigaba da ri'konmu, itama tana aure anan kano dawani abokin Abbanmu. Sun nuna mana gata sosai wanda har muka manta da maraicin dake kanmu, dansu basu ta6a haihuwaba, sun taimaka mana munyi karatu mai zurfi, ina shekarar 'karshe a secondary ALLAH yayma uncle rasuwa, akabar mama da ďawauniyarmu, karatunmu tarbiyyarmu, cinmu shanmu, saidai abinda 'yan uwa suka taimaka mata. Natashi mutum mai yawan laulayi na ciyo, ina yawan yin rashin lafiya akai2, idan ina cikin wanan halin mama takan ruďe itada yayana, hakadai rayuwa tacigaba da garawa har yayana ya kammala digiri ďinsa, bai tsaya neman aikiba ya tsunduma kasuwanci, nikuma sanan na kammala sacondary, kullum burina bai wuce nazama sojaba, amma awajen yayana da mama ba haka bane, burinsu nazama cikakken likita, dan haka burinsu ya danne nawa, nadage nazama likita domin na faranta musu, yayana yayi aure tuni, yanzu haka yanada yara biyu, Marwan da Hadeeza, (deexerh) saidai sun rabu da maman yaran, yanzu yana auren wata mata mai suna Ramla, agida ďaya muke zaune muduka, yayi mana gini kowa da 6angarensa saikuma na mama agefe, wannan shine tarihina a ta'kaice, ALLAH yasa kin gamsu. Murmushi nayi ina satar kallonsa, na gamsu sosai, kuma tarihinka ya 'kayatar dani, ALLAH yajikansu mama ya yafe musu, yabamu hakurin rashinsu, ameen doctor yafaďa yanamai jin daďin addu'ata. Ya kalli agogon hannunsa sanan ya mi'ke iman bari na wuce ko, magriba tana gabatowa. Na ce, "to aii bakaci komaiba sai lemo, yayi murmushinsa mai 'kyawun gani, karki damu kasancewa dake kawai ya wadatar dani, na ce, "to na gode, naďan rakoshi bakin 'kofar falon ina faďin ka gaidamin dasu deexerh da marwan, saida yajuyo ya kalleni sanan ya ce, "zasuji insha ALLAHU. bayan fitarsa daga gidan na lumshe idona ina murmushi da maida nannauyan numfashi, babu 'karya nima inason doctor Isma'il, domin kuwa ya cancanci asoshi, mutumne mai kwarjini a ayuka da kuma dangan taka, ga yawan fara'a, uwa uba 'kyawawan halaye, amma baza'a kirasa mutum mai tsananin 'kyauba, saidai tsaka tsaki. Lalai na more da samun miji nagari, kamshinsa kawai ya wadatar dani burin kasancewa dashi har abada, saidai ina ba'kin cikin katsewar karatuna, dukda nanda wata shekarar zan kammala, amma ina bukatar rabuwa da wananan azababben ciwon dakansani tagumi tunkan kamawar wata, ALLAH dai yaza6a mana abinda yafi alkairi. Kwala kiran sallar limance tasakani fitowa daga falon nanufi cikin gida..............✍🏻 Kuyi ha'kuri dani, wlhy ina busy🙏🏻😁 Luv u oll my fan's (S)......2017 battery low🔋😜👌🏻 [8/6, 5:59 PM] mrs bilkisu: ________________________________ BAN SAKETA BA!!!. ________________________________ NA BILKEESA IBARAHEEM {bilyn Abdul} ________________________________ https://mrsbilkisa.blogspot.com Sadaukarwa ga~Abdul {city phone's} Page.....5⃣ 💞💞💞💞💞💞 *invitation*! *invitation*!! *invitation*!! U ar cordially invited to d wedding events of *Reefat Yahya*❤ *Walima* on 13th April 2017 Venue -Barr Yahya j Bobboi's residence @ marware ward Jada, Adamawa state. Time: 3:30pm *Arabian night* On 13th April 2017 Venue Atiku Abubakar science hall Jada. Time: 9:00pm *Kamu day* on 14th April 2017 Venue Atiku Abubakar science hall Time: 3:00pm *wedding fatiha* on 15th April 2017 Venue Barr.Yahya j Bobboi's resident marware ward Jada, Adamawa state. Allah ya bada ikon zuwa💞💞💞 Sako daga bilyn Abdul😁👌🏻 _________________________________ WANNAN page ďin nakune. KODA YAUSHE INA ALFAHAREE DAKU 👇🏻 Faty axlad maryam 'yar mama humy luv first lady hudallah salma Ali wada Sunher classic feedoh Zeenur Fareedat musa Kuďin nadabanne agareni, inafata alkairi da tarin basira da kwarin ido agareku, ALLAH yakara baku ikon nishaďantar damu da faďakar damu, yakuma karemu daga sharin ma'kiya baki ďiya. (Maryam 'yar mama👌🏻❤) MAHAUKACI ko BOYAYYAYEN MOSOYI!!!!!!???????. 🤔 Page.....5⃣ .......Babu 6ata lokaci aka shiga shirin bikinmu da doctor, domin iyayena basa son wata yacika al'adata tazo ba'a gidan mijinaba. Aranar wata juma'a aka ďaura aurena da doctor Isma'il, mutane dayawa sunsha mamakin aurar dani da'akayi, saidai basuda dama tsogumi tunda gidansu doctor Isma'il ba wasu masu 'kazamin kuďi bane saidai rufin asirin ALLAH, wannan ya hana mutane ďafewa aka kuďi abbanah yagani, saidai hakan bai hanasu yawan hasashe da hange2n daliliba, saidai sun rasa tsani ko tubalin hangowa, dan masu iya magana nacewa wani sirri sai hanji kasanshi. Da yamma akaje walima mai 'kayatarwa da birgewa, dayawa abokan Dr Isma'il sunyi mamakin ganina amatsayin matarsa, suna mamakin yanda akayi ya auri 'karamar yarinya haka, amma tunda basuda mai basu amsa sai sukayi gum, kamar ansakama kofar fada kwaďo. Waleemar ta 'kayatar sosai, karfe tara na dare aka tashi, gida aka maidani sanan akayi shirin iza 'keyata makarantar samun ladan aljanna, wato gidan miji, nasha kuka sosai na rabuwa da iyayena dakuma ďan kanina Deeni. An kaini gidansu doctor wanda zai zama familyna na biyu ayanzu, 6angaren mama aka kaini, dukda idanuna suna sinkife cikin hijjabi, ina a kwatan kwacin makauniyane, wanan bai hanani ďaukar sautin maganganun danginaba masu ambatar sunan wadda zata maye gurbin uwar mijinaba ayanzu, an dan'ka amanata ahannun mama, kuma ta kar6a tayi ammanar ri'keni amatsayin ďiya kamarsu doctor, to nimadai tawa zuciyar ta rungumeta amatsayin uwa tunda aure ya nisantani da gwaggota, bayan ďan faďa da nasiha aka kaini 6angarena wanda zai kasance fadata afanin sarautar gidan miji, masu kawoni basu wani ďauki dogon lokaciba suka fara kama gabansu dan komawa tasu fadojin domin kula danasu iyalin, kafin na farga gidan yayi tsit tamkar anyi ruwan sama anďauke, aunty salma kawai aka bari tana ďan gyaramin inda aka 6ata, itama zuwa wani lokaci tayimin halin ruwa, dankuwa bansan ta suďaďa ta ficeba saidai na riski shiru wai rai yayi halinsa. Abu biyu suka giftamin awanan lokacin, wato tausayin kai, da jimamin rabuwa da iyaye gatan 'ya'ya, agefe kuma ga wani tsoro dayake neman titsiyeni sakamakon jin shiru danayi narashinjin rai mai motsi akusadani. Ina nan cikin halin gajeren numfashi da dogon tunani, naji sallamar angon 'kamshi da gayyar abokansa masu masa rakiyar zuwa ďakin amaryar tasa, saidai afalo ya taka musu birki tareda mi'ka godiyar 'ko'karin dasuka nuna na fiddashi kunyar wanan rana, suduka sai suka shanya baki suna masa kallon sama da 'kasa, yayi murmushi yayinda shima yake maida musu murtanin kallon kwaji dashi, Raheem ya ce, "mutumina abin 'yar hakace ko?", doctor ya kaďa kai alamar babu shakku akan furicin abokin nasa da inda yadosa, to suma sun masa uzuri, dan dama daniyyar haka suka iso, tunda al'adarsuce haka, idan sun rako aboki basa fiya zazzarin shiga inda amarya take, daga bakin 'kofa suke tsayawa aja doguwar addu'a kowa yacika rigarsa da iska. To shima sun masa addu'ar da fatan alkairi harda na dawowa suna awata tara masu zuwa, 'yar dariya kawai yayi yana musu sallama dafaďin ALLAH ya huce gajiya. Ina zaune akan gado lullu6e cikin gyale jaa sai zabga 'kamshi nake wanda akasan amarya dashi, doctor yashigo da sallama cikin muryarsa mai shiga 6argon jiki da jini, tuni wata sabuwar nutsuwa tazo mini danjin ma'abocin 'kamshi yana kusantoni, acan kasan ma'koshi na amsa, cikin takunsa na burgewa ya 'karaso inda nake, ya ajiye ďan madaidaicin jakka mai kyawun gsk akusada gadon. Gadon ya hawo yana faďin amarsu ta ango mai daďin suna, ta angonta Isma'il, ya zauna akusadani tareda yaye gyalen dana lullu6a dashi, ahankali yafurta "AMINCIN ALLAH YA TABBATA AGAREKI HASKE MAI HASKAKA ZUCIYA, IMAN MAI FASSARAR IMANIIIII!!!". kasa nayi da kaina inaďan murmushi, yay 'yar dariya mai 'kayatarwa aikunya ta 'kare, tunda yau kin zama tawa ni kaďai, hannu nasa na rufe fuskata. Iman Ta hurema Reefat idanu, ajiyar zuciya Reefat taja mai 'karfi, suka tuntsure da dariya gaba ďaya, iman ta ce, "kai Reefat gaba ďaya kin zuba min idanu, xoxo ta ce, "kamar tana hangen daren farkonku!." To 'yammata aini ba haka nake nufiba, dama abinda kuke jira kuji kenan to bazan faďaba, aiko da kin cucemu dan nan muke jira muji, o, ke xoxo zan faďama momy aimiki aure kafin ki ida 'konewa wlhy, garama Reefat kaďan yarage ale'ka turaka😁👌🏻lol, ta faďa tana shiga bayi domin yin alwala. Tayo alwala tafito, xoxo ta ce, "oh ke iman ashe kinsan hanyar.........saikuma tayi shiru dan ganin hararar da iman take watsa mata, suka tuntsure da dariya itada Reefat, yayinda iman ta kabbara sallah tana murmushi. Bayan sun idar da sallah suka sake zama, Reefat ta ce, "dan ALLAH iman kibamu labarin komai karki rage mana, dan nasanki da shegiyar kunya. Iman ta ri'ke ha6a kai Reefat ALLAH ya shiryaki, zandai faďi abinda bakina zai iya, amma ba komaiba, xoxo ta ce, "da wanan surutun mudai aci gaba". Iman taci gaba da faďin, cikin sanyin murya na ce, "masa ina yini fuskata na rufe da tafin hannuna. Ya ce, "a'a bazan amsaba saikin buďe fuskarki, dole na buďe fuskata sannan na gaisheshi, ya amsa cikin shau'ki ya ce, "ya gajiyar biki?, nai murmushi bance komaiba, yaďanja hancina miyasa kike da yawan kunya iman?, nanma shiru nayi dan gaba đaya atakure nake, kunyarsa duk ta gallebeni. Mik'ewa yayi yana murmushi yafice, babu daďewa yadawo da filet ahannunsa da kofuna, saman kafet (carpet ) ďin dake gaban gadon yazauna, yajuye gasassaun 'yan shila daketa tashin kamshi, yazuba madarar akofuna. Saudatttt!!! Yakira sunana ahankali, tareda ďanjan sunan, na ďago ina kallonsa tareda faďin na'am, ya ce, "taso kici abinci nasan kinajin yunwa. Na ce, "na k'oshi". Ya ce, "k'oshi kuma?, zadai ki k'oshi yanzu, yafaďa yana k'arasowa gareni, cak ya ďaukeni ya dire ak'asa sanan shima ya zauna, jikinsa yajawoni bari kiga ďura zan miki yanzu. Na ce, "dan ALLAH kayi ha'kuri zanci da kaina, haka nayita tura naman nan ina kora madara badan nasoba. Bayan mun gama ya ce, "yana zuwa, na ce, "masa to", yana fita nasakama k'ofar key. wai kunsan wani abu??. Sukace a'a saikin faďa. Nifa duk wanan abun dayake faruwa babu tsoronnan da ake faďa na amarya ga angonta araina, danni wlhy bansan idan anyi aure mi'akeyiba, rufe ďaki danayi, nayi hakane dan inajin kunyarsa, amma badan ina tsoron faruwar wani abuba. Su xoxo sukasa mata dariya, lallai 'yammata kin haďu. Iman tayi 'yar dariya, ina gaya muku nacire kayana nasa na barci, na ďane gado na kwanta. Cikin barci naji ana shafani, abinda baka sababa dan haka natashi afirgice tareda wage baki zanyi ihu. Doctor yasa lallausan hannunsa ya rufe mini baki yana faďin iman nine fa, cikin rawar jiki na ce, "dan ALLAH ka dainamin wanan abun, wlhy gwaggo ta ce, "mini iskancine, kullum tanamin gargaďi, kokanaso na zubar da mutuncina??. Doctor ya kunna fitilar dake gefen gadon, yakamo hannuna ya zaunar ya ce, "tokiyi ha'kuri nadaina yimiki zoki kwanta, na ce, "saidai na koma 'kasa, ya ce, "a'a yi kwanciyarki, nibari na kwanta saman kujera. Haka yakoma saman kujerar dake a ďakin ya kwanta, nima na koma nakeanta atsorace, cikin ikon ALLAH babu daďeqa barci yay gaba dani dan akwai gajiyar biki a tattare dani. Shikam doctor yakasa barci, yana mamakin dama azamaninnan da aka lalace akwai yaran dabasu san minene aureba, lalai shikam yayi babbar sa'a, idan yatuna abokansa dayawa, waďanda bayan aurensu suke masa tambaya akan suffofin mace mai cikakken burci, saboda kokwanto dasuka shiga akan nasu matan, yagodema ALLAH dabai kasance mazinaciba, bare ALLAH ya jarabceshi da auren mazinaciya, haka yayta tunane tunane har barci ya saceshi. Kiran sallar farko ya farka, yatashi yaje bayi yay alwala, yayi raka'atainul fijir, saida aka kira sallar farko sanan yatasheni yafice masallaci. Saida gari yaya sha sanan doctor yadawo, zuwa lokacin harna sake 6ingirewa akan sallayar dan barcin bai isheniba, yabini da kallo yana murmushi, akan la66ansa yafurta 'yarrigima kenan, ďaukata yay caj yadire agadon sanan shima ya hawo, ahankali yanutsani da jikinsa gudun karna tashi nayi masa mazurai, nikam nariga nayi nisa abarci bansan bikin dayakeyiba ma...............✍🏻 💕💚💕 Page.....6⃣ Karfe 8:00am nafarka sainajini ajikin doctor, da sauri nazare jikina daga nasa amma bai farkaba, dan haka na nufi bayi danyin wanka, harna fito na shirya cikin riga da siket na atanfa bai farkaba, ganin haka yasa na nufi falon dan inga tsarin gidan, na tsaya cak atsakiyyar falon inabin ko ina da kallo babu 'karya komai yayi atalauce ba'a sarauceba, iyayena sun taka rawar gani saidai fatan ALLAH yabiyasu da mafificin alkairinsa, an k'awata falon da wasu manya2n hotinanmu nida doctor, wanda nibammasan lokacin danayisuba, wata zuciya tacemin tsarin computar ne kawai, jinai anbuďa k'ofa, da sauri na juyo azatona shine yatashi. Amma sainaga wata matace 'kyakykaywa, tanada ďan jiki babu laifi, na ce sannu, fuskarta babu walwala sosai ta amsa min da yauwa, na rissina ina gaisheta, batareda ta amsaba ta ce, "min ina isma'il ďin??, na ce, "yana barci. Barci kuma?, ta maimaita ayatsine, na ce, "eh". Ta kalli agogon dake manne afalon, ta ce, "karfe takwas da rabi mutum bai tashiba, yana inane??, da hannu na nuna mata ďakina, kai tsaye ďakin ta nufa, niko nayi sakake ina binta da kallon mamaki, saiwata zuciyata ce, "kibita kiga abinda zatayi. Aiiko nabita amma natsaya akofa, tana shiga ďakin tanufi bakin gadon, doctor yanata barcinsa hankali kwance, tasa hannu ta yaye bargon daya lullu6a dashi, ALLAH yasama dogon wandone ajikinsa da doguwar rigar dayaje masallaci. Tasa hannu taja yatsansa na kafa, yabuďe ido ahankali yana faďin iman yadai??, ta ce, "aii ba itabace, da sauri ya mik'e zaune danjin muryar auntynsa, cikin mamaki ya ce, "aunty kece?". Ta ce, "eh nice, saboda kayi sabon aure zakabar tsohuwar zuma. "Kamar yaya aunty?". Tokaga amarya ka manta da uwar gida mana. Azuciyata na ce, "uwar gida kuma?. Maganar doctor ta katseni a'a ni rabani dawata uwargida kije can kiji da tsohon mijinki, nima naji da amaryata. Naga alama maganar ta sosa mata rai amma saita dake, fuskarta ta 6oye fushinta, ta ce, "oh masu amarya, santin amarcin haryasa kafara mantawa damu?, to ka mi'ke". Breakfast yakammala kaida amaryarka kawai ake jira. Yaďan ja hancinsa to muna zuwa, yafaďa atakaice. Maimakon ta tafi saita zauna abakin gadon, tana faďin a'a bari najiraku anan salon ku kara shanyamu. Yarage fara'arsa, kinga aunty kije zanyi wankane, idan mungama zamuzo, duka yanzu karfe nawa?, kuma nasan yau yaya ba Zaije kasuwaba ya faďa tareda kallon agogon dake manne aďaki". Ganin fuskarsa ta nuna alamun 6acinrai yasata mik'ewa ta fito, ina kallo yarakata da harara sanan yay magana wadda nikaina banjitaba. Nashige cikin labulale dankar taganni, tafito tanabin falon da kallo tana ta6e baki, idanunta suka sauka akan hotunanmu ta kalla sainaga taja tsaki ta fice. Nabita da kallo ina tambayar zuciyata wanan kuma wacece??". Ina nan tsaye yafito, yabini da kallo a'a iman tunanin mikikeyi haka?, nayi 'kasa dakai ina murmushi na ce, "babu komai, narissina ina gaishesa. Ya ce, "bazan amsaba, tunda kika tashi kikaki tashina. Na ce, "to kayi ha'kuri bazan sakeba. Ahankali yak'araso tareda rungumeni, cikin kunnena ya ce, "to kin tashi lafiya??, na ce, "lafiya 'kalau, hannuna yakama zomuje ďakina nayi wanka, muje muyi breakfast kinga su yaya suna jiranmu, na ce, "kaje kayi wankan, nikuma bari nagyara ďakin kafin kafito. Yayi murmushi kedai bari kimin wayo kawai", a'a bahaka bane nafaďa ina murmushi dake kara bayyana kyawun fuskata, to shikenan jeki gyara bari nayi wankan. Dakina nanufa inata 'kokarin gyarawa, saboda sabo da gyara gadon gwaggo yasani gamawa da wuri, har falo nafito nakara gyarawa. Babu daďewa saiga doctor yafito cikin kananun kaya, yayi kyau sosai, sai tashin kamshin turarensa yake, ya ce, "taso muje nasan suna jiranmu, na ce, "to, naďakko gyale zansaka, ya ce, "anan gidannefa, kike niyyar saka mayafi, nađan kalleshi ina faďin kayi hakuri ALLAH inajin kunyar zuwa haka, yay murmishi to sarkin kunya mije. Munfito daga 6angarenmu muka nufi wani 6angare dayake iri đaya danamu, kuma zasu iya zuwa girma ďaya, saikuma wani acan gefe wanda bai kai girman namuba, tabaya yabi damu zuwa wata 'kofa wadda nake da tabbacin tanan zamu riski falon mai gidan, wato yayansa, k'ofar doctor ya kwankwasa, babu daďewa akazo aka buďe, matar dataje 6angarenmuce ďazu tabuďe, taja baya muka shiga sanan ta maida 'kofar tarufe. Falon ya haďu iya gwargwadon hali, sai tashin k'amshi yake, wajen wani k'ak'yk'yawan mutum muka k'arasa zan iya cemuku yafi doctor k'iba da haske sosai, suna tsananin kama, daka gansa kasan yayansane, saidai doctor ya nuna masa k'uruciya kawai, yana ganinmu yafara fara'a yana faďin oyoyo k'anwata sannunnku. Nikam cikin jin kunya na'kara nesa dashi kaďan, nazauna saman kafet ina gaisheshi cikin ladabi. Da sauri ya ce, "tashi kihau kujera kinji. Nak'ara k'asa da kai ina faďin nanma ya isa yaya". Shikam doctor kusada yayansa ya zauna, yawani narke ajikinsa kamar k'aramin yaro, yaya yarungumo doctor jikinsa yana faďin auta kuntashi lafiya kaida k'anwata??. Lafiya lauw muka tashi yayana". Alhmdllh yaya yafaďa". Yaďora da faďin k'anwata yagajiyar biki??. K'asa nayi dakaina saboda inajin nauyinsa sosai. Doctor ya ce, "ka gantanan yaya tacika kunya dayawa wlhy. Tokai idan banda abinka auta aii anason kunya, domin kunya tana ďaya daga cikin alamun tarbiyya. Hakane kuma yayana, doctor yafaďa yana masa jinjina👍🏻........ Aunty ta katse doctor da faďin to kutaso breakfast yana jiranku, muduka muka kalleta sanan muka mik'e. Doctor ya ce, "wai ina yaranane??, yayansa ya amsa masa da faďin suna 6angaren mama, kasan suna ganin ba'ki bazasu tuna damuba, sai bak'in sun tafi sanan. Doctor yaya dariya, yarana kenan sunaso sudai suga ba'ki. Munzauna cin abinci nidai duk akunyace nakecin abincin, dan ban saba dasuba. "Yaya ya ce, "k'anwata miyasa bak'ya son cin abinci?, ko baki son wannan acanja miki wanine?". "Da sauri na ce, "a'a". Yayi murmushi to kisaki jiki kici abincin nan gurin duk family ďinki ne, kuma gidankine. Na ce, "to. Doctor ya ce, "konazo nabaki da kaina??:" Da sauri na girgiza kaina. Ina kallon matar yayansa ta ta6e baki, dama tunda muka fara magana bata tankaba, abincinta kawai take dannawa. Hakadai muka gama. Yaya ya ce, "yakamata kuje 6angarenku, dan ba'ki zasu ringa shiga yimuku sallama, wasu yau zasu wuce. Okey doctor tafaďa yana mik'ewa. "6angarenmu muka koma. Muna shiga doctor yakwanta saman doguwar kujera wai yagaji, ya kalleni ko kema kinajin barcinne??. Kai na girgiza masa batare danayi maganaba. Yayi murmushi shikenan matana gwanar kunya. Muka ďanyi shiru zuwa wani lokaci, dan ni inajin nauyinsa, yajuyo idanunsa matsakaita yana 'karemin kallo, tafin hannu nasa na kare fuska, ya tuntsure da dariya, my iman rowar fuskarki kikemin??. Na kaďa kai alamar a'a". Yatashi zaune yana faďin babu waninan, bagashi dan ina kallonkiba kin rufe fuska, ban bashi amsaba saima na k'ara cusa kaina cikin cinyoyina, yataso tsam daga inda yake, ban ankaraba sainaji ya ďaukeni cak, yamaye gurbin inda nake zaune, nikuma ya ďorani saman cinyarsa. Da sauri na buďe idanu, kallo ďaya na masa nayi k'ok'arin kauda kaina, amma yarik'e fuskata yahanata juyawa. Ahankali yafurta wanan kunyar taki tayi yawa iman, yakamata naďan rageta, yana gama faďa yak'ara matseni ajikinsa. Kafin nayi wani yunk'urin kwacewa ya haďe bakina da nasa, hummm, ba tsoroba har ruďani nashiga, jikina sai karkarwa yakeyi, gashi yahanani wata damar dazanyi motsi bare nayi yunk'urin kwatar kaina. Yanda yaso yake sarrafa bakina da harshena, tamkar yasamu alawar lollipop. Sai ambatar sunayen ALLAH nake a zuciyata, dan banta6a tunanin faruwar hakaba tsakanina dashiba. Munkai tsawon minti shabiyar ahaka doctor yana abu ďaya yayinda tuni fuskata ta gama jik"ewa da hawaye, har shima tasa fuskar tasamu tsaraba. Ya zare bakinsa dak'yar yana maida numfashi asark'e, nikuma nayi saurin direwa daga jikinsa dan bashida karfin dazai iya rik'eni awanan lokacin, saboda laushi da nauyi da kasalar da suka kanainayesa. A ďari na afka ďakina na kulle, na haye gado can k'arshe kamar wadda tayi gamo da dodon mayu, sai maida numfashi nake da sauri da sauri.. Shikam ďan murmushi yayi saboda ganin gudun danakeyi, ya maida kansa ya jingina da kujera ya lumshe idanunsa yana cigaba da murmushi tareda 'kara lashe la66ansa (yayi k'yau 👍🏻😁likita bokan turai) lol😜.................✍🏻 Kucigaba damin uzureeeee!!!👌🏻! Plzzzzzz!!!!!!!🙏🏻 Luv u oll my fan's ((S))........2017 battery low🔋😜👌🏻 [8/6, 6:00 PM] mrs bilkisu: ________________________________ BAN SAKETA BA!!! ________________________________ NA BILKEESA IBRAHEEM {Bilyn Abdul} ________________________________ https://mrsbilkisa.blogspot.com Sadaukarwa ga~ya Abdul {city phone's} MIYAKAMATA NAYI???. gyara kayanka bazai zama sauke murababa, idan wani yayima ďanka gyara karka zargesa, kojin haushinsa, gode masa domin kuwa jihadi yatayaka, tarbiyyar 'ya'ya jihadine ga kowace uwa ko uba, bakasan miya aikata aka tsawatar masaba, dan haka kada kazama mai fifita son 'ya'yanka akan gsky. "Kaso naka duniya tak'isa." "Kak'i naka duniya tasosa." ALLAH yasa mu gane. Page.....7⃣. ..........iman tayi shiru tareda k'ok'arin mik'ewa, da sauri xoxo ta rik'eta, wai inakuma zakije?, dariya tayi haba my hafsy shikenan kuma bazamuyi barciba?, kofa sallar isha'i bamuyiba, karku manta kumafa gobefa idan ALLAH yakaimu monday, munakuma da luctures ďin safe....... Reefat tai saurin tareta, amma dai aii k'ya k'arasa mana koda nan gurinne, tunda nasan dai saiya biki har bedroom ďin. Iman taja numfashi mai nuna alamun gajiya, please my sisters kuyi hak'uri sai gobe idan ALLAH ya kaimu, ALLAH bakina zafi yakeyi kaina har wani ciwo yake. Xoxo ta kalli Reefat suka tuntsure da dariya, yayinda iman tayi galala tana kallonsu dan batasan inda dariyar tasu tadosaba. Ta ce, "incedai lafiya??." K'alau Reefat tafaďa cikin dariya. Xoxo ta ce, "iman kinsan miya bamu dariya?. ''A'a.. Iman tafaďa. Gudunkine yabamu matuk'ar dariya, wato dakika samu damar ku6ta saikika arce, suka sake kwashewa da dariya. Itama batasan lokacin data shiga tayasuba, saboda hangen gudun datayi take tamkar a yanzu yake faruwa, tashige bayi tana dariya domin ďauro alwala. ♡☆♡ Washe gari da wuri suka tashi kasancewa sunada lucture ďin safe, suduka gayu suka ďauka na birgewa, dan 'yan matan akwai kala, kowa ta iya ďaukar wanka na birgewa, a tsaitsaye sukasha shayi suka fito. 'Yar tafiya kaďan takaisu aji (class), amma dayake akwai sauran lokaci saisuka samu k'ark'ashin wata bishiya suka zauna suna jiran lokaci yacika. Kamar wadda aka zirkuďawa allura tafara waige2, xoxo da Reefat suka bita da kallon mamaki, ta mik'e zumbur tana fidda numfashi da sauri da sauri tamkar wadda tayi gudun fanfalak'e a sahara. Inda tadasawa idanu ko k'yaftawa batayi suma su Reefat suke kallo, wani matashine fari atsaye jikin mota, dogone sosai da 'yar k'iba, saidai ba'a kirashi k'yak'yk'yawa sosai ba, amma babu laifi yanada nasadaidai k'yawun. Hannayensa aharďe kan k'irjinsa, hakama k'afafunsa suna harďe dajuna, idanunsa k'ur akan iman daketa rawar jiki kamar taga mala'ikan mutuwa. Murya k'asa2 xoxo ta ce, "da Reefat inagafa wanan iman takema wanan ruďin, ki lura da k'yau yana kama da musayeef. Reefat ta ce, "gskyar ki xoxo, toko shine Dr Isma'il ďin?...... Kafin Reefat ta rufe baki iman tabar wajen cikin sauri da da sassarfa gamida rawar jiki, binta yayi da wani mayen kallo tamkar zai cinyeta, dayawan ďalibai kallonsu sukeyi suma. Saida ta 6acema ganinsa sanan yaja ajiyar zuciya tareda ďan matse ido wasu k'ananan hawaye suka zubo kaďan a idonsa , hankacif ďin hannunsa yasa ya gige yanaďan murmushi k'arfin hali. Ahankali yafurta My SAUDAT yaushe zaki dawo gareni?, yaushe zaki yarda BAN SAKEKI BA!!. wlhy BAN SAKEKI BA, ki yarda dani, karki bari ciwon haukan sonki yacigaba damin illah, na tabbata babu wani likita dazai iya shawo kan matsalata saike kaďai. "Kece cikon farincikina." "Kice uwar ďana." Akanki kawai nake tanadin rayuwata, miyasa zakimin haka?, waye yay min wanan kullin?. waye!?. Waye!!?. Waye!!!......?. dasauri yafaďa motar danjin juwa zata juyeshi ak'asa, ya kwantar da kujerara motar da sauri ya kwanta, sai fidda numfashi yake sama2.... Cikin k'ank'anin lokaci yafara fita hayyacinsa, dauriya da jarumta tabashi damar jawo wayarsa, batareda yasan wayake kiraba ya kara akunne. Murya a sark'e ya ce, plz waye?. Cikin rikicewa nacan ya ce, "Isma'il kana cikin k'oshin lafiya kuwa??. Da k'yar ya iya faďin Nabil kazo katafi dani. Arikice Nabil ďin ya ce, "kana inane?.. Ina makarantar su Iman!. Hazbinallahu wani'imal wakil, Nabil yaketa ambata, yayinda tuni Dr Isma'il yasaki wayar k'asa dan numfashinsa yafara gagarar fita yanda yadace. Su xoxo dai suna tsaye suna shawarar zuwa inda motar doctor Isma'il yake, dan sunga kamar amawuyacin hali yashiga motar. Har ciki mai mashin yashigo da Nabil, yazaro ďari biyar yamik'ama mai mashin ďin, batareda yajira canjinba yay gaba. Tundaga nesa yashaida motar Dr Isma'il, yak'arasa da sauri yabuďe motar akuma daidai wanan lokacin su Reefat suka iso wajen. Tuni Dr Isma'il yafita hayyacinsa da alama ma numfashinsa shirin ďaukewa yake gaba ďaya. Nabil yay k'ok'arin matsar dashi kujerar gefen direba, ya maye gurbin inda Dr Isma'il yake da. Xoxo tayi k'arfin halin faďin lafiya kuwa?. Nabil ya kalleta arikice dadai sauk'i 'yammata, baijira amsartaba yatada motar yafice daga makarantar aguje. Kowadai kallon mamaki yabi motar dashi, wasuma har suna faďin mahaukaci. Jiki a sanyaye xoxo da Reefat suka k'arasa aji, saikuma suka tarar da iman zaune tanata rusar kuka, kamar zata k'arar da kwallar idonta. Tsakiya suka sakata suna lallashi, Reefat ta ce, "iman wai waye wannan mutumin??. Kasa magana iman tayi saima wani sabon kuka daya taho mata..... Shigowar malamin tahanasu cigaba da neman ba'asi. Itama iman tashiga hidimar share hawayen idonta dan fiskantar malamin. Acan kuwa Nabil ya isa da Dr Isma'il asibitine arikice, taimakon gaggawa suka shiga bashi shida abokan aikinsa, dan shima Nabil ďin likitane, da taimakon oksajin Dr Isma'il yafara fidda numfashi. A6angare ďaya kuma an manna masa k'arin ruwa da aka juye alurai har biyar aciki. Bayan lafawar komai Dr Nabil yakira yayansa yasanar masa. Cikin rikicewa yaya mansur ya ce, "Nabil badai ciwonsa bane ko??, ya akayima haka tafaru?. Wlhy yaya bansan Isma'il yatafi makarantar su iman ba, na barsa agida dan ya ce min zaiyi barci, nikuma nanufi wani uzuri daya ďan tasomin. Inama awajen yakirani ya ce, "nazo nafi dashi yana makarantar su iman. Yaya yaja wani gwauron numfashi, to yanzu yajikinsa.?. Da sauk'ima aii, yana barcine. To Alhmdllh. Dr Nabil yafaďi hakane kawai dan kar hankalin yaya yatashi, amma duk wanda yakalli Isma'il yasan yana cikin mawuyacin hali......... Yaya yakatsema Dr Nabil tunani dafaďi, to yaga iman ďin?. Wlhy yaya ban saniba, dan lokacin danajedai bata wajen, kodayake bawani saninta nayiba sosai. ALLAH yak'yauta yaya yafaďa cikin sauke numfashi. Amin dai". Amma yaya bama saikazoba insha ALLAHU zuwa anjima komai zai dai2ta. To shikenan Nabil, kaima ALLAH yasaka maka da alkairi kaji, samun aboki irinka sai antona. Babu komai yaya aii yiwa kaine, nida Isma'il munzama ďaya. To mungode saina kira anjima. To yaya agaishemin dasu deexerh. Zasuji insha ALLAHU. Dr Nabil ya yanke wayar tareda maida kallonsa akan Isma'il. Cikin lokaci k'ank'ane harya zabge, sai wani haske daya k'ara. Yana tausayama abokinsa, saboda yanda soyayya take masa juyin waina, ALLAH ka warware mana wanan kulli dake tsakanin abokina da matarsa. ya ALLAH ka bayyana gskyar lamari, kakuma maidasu amatsayin ma'aurata indai sunada rabon sake zama tare. (Na ce, "ameen Dr Nabeel). Itamadai iman zaune kawai take tana sauraren malamin, amma bata fahimtar abinda yake faďa; gaba ďaya tunaninta nakan Dr Isma'il SANYIN IDANIYAR TA. Yau tsawon shekara huďu bata gansaba, ashe akwai lokacin dazaizo suga juna, taga yak'ara k'yau da girma, gawata kamala da nutsuwa sun sake riskarsa, uwa uba kwarjinin data hango a fuskarsa da annuri na musamman. Ta share hawayen dasuka gangaro mata tareda ďan jan hancinta, lallai tayi dana sanin zuwan wanan rana. Yau Doctor yatada mata tsohon ciwon dake cin ZUCIYARTA tsawon shekara huďu. Tabbas da amafarki wanana ranar tazo mata da idan tatashi bazata sake komawa barcinba. Haka tayita sak'e2, har malamin yafice batareda tasaniba, bare tayi ik'irarin fahimtar abinda yakoyar dasu. Haryanzu hawayenta sun kasa tsayawa, dan haka k'awayenta sukaja hannunta domin fita susha iska, amma saita kakare dan bataso tafita waje tak'ara tozali da mugun mutuminnan mayaudari. Murya asark'e ta ce, "kubarni anan kawai." Saboda mi xoxo? tafaďa aďan raunane;. Iman tayi murmushi k'arfin hali, babu komai banason fitane kawai. Shikenan muma saimu zauna aii. Reefat ta ce, "iman wai waye wanan mutumin naďazu?. Iman ta cije le6enta na k'asa, muryarta da karsashi ta ce, "Isma'il!!. Xoxo da Reefat suka kalli juna, wai Doctor kike nufi?. "Kai kawai taďaga musu batareda ta iya maganaba. Suma shiru sukayi, kowa yana sak'e2n abin aransa, da mamakin abinda yaraba iman da doctor Isma'il, domin alamomi sun nuna suduka suna matuk'ar son junansu, da begen kasancewa a fada ďaya. Amma saigashi sun kasanance amabanbanta gurare, kuma cikin matuk'ar ruďani da nuna damuwa. "Komiye dalili!!!!!!!!???"..........✍🏻 💕💚💕 Page.........8⃣. ................Har suka gama kar6ar luctures nasu duka iman bata cikin walwala, zata iya kuma rantsewa yau bata tsinci komaiba a darissan da aka koyar dasu. Sukansu k'awayennata sun kasa gane kanta. Tak'i ci tak'i sha bare walwala". Ahaka suka dawo ďaki tanata basarwa, suna kuma zuwa ta kwanta batareda tasake shiga harkar kowaba. Suma k'awayennata saisuka ďaga mata k'afa domin bata hutu na wucin gadi, tasamu damar cuďaya jiyanta da yau. /^/ To shimadai a 6angaren doctor hakane, sai wajen gab da la'asar numfashinsa ya daidaita, zuwa wani kuma k'ank'anin lokaci yafarka. Dr Nabeel dake gefensa yafara yimasa sannu. Ya amsa cikin ďaga kai domin bakinsa yay masa nauyin dabazai iya maganaba. Da hannu yay masa nuni da ruwa alamar abashi. Dr Nabeel yamik'e da sauri yaďaukko gorar ruwa ya 6alle murfin ya tsiyaya akofi. Ya taimakama Dr Isma'il yatashi zaune ya jingina da gado, sanan ya kafa masa kofin ruwan abaki. Saida yasha kusan rabi sanan ya janye bakinsa alamar ya k'oshi. Dr Nabeel ya ajiye kofin yana k'ara yimasa sananu, ya haďa masa shayi mai kauri wanda yasan sai sunyi dagama kafin yashashi, dan bayason cin abinci yanzu sosai. Aii ko dak'yar yasha shayinnan, sanan yasha maganinsa yakoma ya kwanta. Har tsawon kwana uku Dr Isma'il yana jinyar jiki data zuciya, sosai yay jinya akwana ukunnan. Hakama gimbiyar tasa iman dukda bata kwanta ta ce, "batada lafiyaba jikinta da ayyukanta suna nuna alamar ciwo, danma tanada k'arfin hali da k'ok'arin 6oye damuwa, shiyyasa bakowane yake saurin gane matsalartaba kai tsaye. Amma k'awayenta suna kula da ita suna kuma tayata addu'ar samun sauk'i a al'amuranta na jiya dayau, da gobenta. Dr Nabeel yanason tanbayarsa miya faru amma yanajin tsoron dawo da hannun agogo baya dan haka saiya share kawai. Bayan kamar minti talatain Dr Isma'il ya ce, "zaiyi sallah. Abokina kabari zuwa anjima mana lokacin kak'ara samun k'arfin jikinka. Zan iya Nabeel kaidai kaini bayi kawai. Da taimakon Dr Nabeel yay alwala tareda rama dukkan sallolin da'ake binsa tundaga azuhur. Reefat ta kalli xoxo dake zaune iman kuma tana kwance agefenta, ta ce, "kutashi ga abincin. Xoxo ta ce, "sannunki da k'ok'ari, ALLAH bakiji irin yunwar danakejiba, iman tashi. Iman taďago jajayen idanunta dasuka kumbura saboda kuka, tunda takwanta kuka take awajen tanayine ahankali kawai saboda kar k'awayenta suji hankalinsu yatashi. Ahankali tafurta nak'oshi". Daga xoxo har Reefat galala sukai suna kallonta, dan ayak'ininsu babu wadda tafi cancanta da cin abinci kamar iman, tun tee ďin safe bata sake cin komaiba sai ruwa. Xoxo ta karyar da muraya cikin sigar lallashi ta ce, "haba iman, yakamata kiyi hak'uri hakanan, ki maida komai ba komai ba, kada kiyima ALLAH Butulci gameda ďunbin alkairai da ni'imomin daya azurtaki dasu. Kiyarda da k'addara akan abinda yasamu rayuwar aurenki, dukda bamusan abinda yarabaki da Dr Isma'il ba, munada yak'inin K'ADDARACE, duk wani mahaluki yakalli kallon da Dr Isma'il yaki miki aranar yasan akwai tsantsar SO da k'aunarki kwance azuciyar sa. Wlhy agaban idonmu aka tafi da doctor cikin mawuyacin hali, nasan kuma duk akankine yashiga wanan halin. Ki daure kitashi ga abinci muci, insha ALLAHU munyi alk'awarin taimaka miki da iliminmu da k'arfinmu. Ahankali iman ta tashi zaune domin maganganun xoxo sunyi tasiri azuciyarta, saidai kalmar shigar doctor cikin mawuyacin hali yak'ara sakata cikin ruďani da firgici. Jitake tamkar tayi tsuntsuwa taje inda yake dan ganin halin dayake ciki, to amma babu dama. Su sukaita tursasata hartaci abincin kaďan sanan ta lalla6a tayi wanka tayi salloli ta kwanta Su xoxo suna son acigaba damusu labari amma suna tausayin k'awar tasu da halin datake ciki a kwana kinnan. Dole sukai mata uzuri kasancewarta 'yar adam azija, suma suka kwanta badan sunajin barciba, saidan taya k'awar tasu jimami da tunanin jiyanta da yau, dan gobenta gaibuce. Dr Isma'il Doctor ya tsura ma abokin nasa idanu, cikin karsashi da dadishewar murya ya ce, "Nabeel wai saiyaushe ne iman zata amince BAN SAKETA BA?. shin haka zata cigaba da kasancewa da nauyin aurena akanta??, haka zata cigaba da barina kullum cikin AZUMI da bagenta?, tanisanta kanta dani, ta nisanta MUSAYEEF dani, alhalin yanzune nafi buk'atarsu akusadani....... Wasu 'yan kwalla suka mak'ale masa akan gashin idonsa na k'asa.....yacigaba da faďin, Nabeel inaga lokaci kaďan yaragemin a DUNIYA, domin SON iman yakusa hana numfashina aiki cikin kwarewa. Lokaci yayi dazanbarma IMAN duniya gaba ďaya k'ila bayan raina ta sanar daku BAN SAKETA BA.......... hanunsa Nabeel ya damk'e cikin sigar lalashi ya ce, "haba abokina kadaina faďar waďannan kalaman, kaifa MUSULMINE kuma mai ilimin addini dana zamani. Nasan kasan k'addara da wanzuwarta da shuďewarta, to inaso kaďauki wannan lamarin amatsayin JARABAWAR RAYUWARKU, na tabbata akwai wani k'ulli dabamu saniba. Nayi imanai IMAN bazatace kasaketaba alhalin BAKA SAKETA BA, bazata nuna takardar nanba abisa k'arya koson rabuwa dakai. Saidai abinda yake bani mamaki da ďaure kai waye yayi irin rubutunka? wajen rubuta sakin iman, indai har yanda kake bani labari hakane tafaru to tabbas akwai ruďi da wanzuwar SABON AL'AMAREE a lamarinku. Saidai babu abinda yagagari ubangijin al'arshi, dan haka mucigaba da tsananta addu'a insha ALLAHU komai yana daf dazu k'arshe, kuma ko waye asirinsa yana gab da tonuwa wlhy. Dan haka inaso ka kwantar da hankalinka kodan gudun tashin ciwonka da wanzuwarsa, Nida kai duk munga JIYAN MU, MUNGA YAU, amma bamusan GOBENMU BA domin kasancewarta GAIBUNMU. Musayeef kuwa kana zuwa ganinsa kana waya dashi aduk lokacin dakaso dan haka ka kwantar da hankalinka insha ALLAHU SAUDAT tana gab da dawowa FADARKA amatsayin SARAUNIYAR KA.. Dr Isma'il yasaki wani sassanyar murmushi tareda sauke ajiyar zuciya ahankali, to ALLAH ya tabbatar Nabeel, amma lamarin yana k'ara bani tsoro, atunanina nisanta kaina da iman zaisa randa tagani ta ďokantu. Amma kash ganina saiya sakata acikin ruďani da shiga uku, Nabeel inason Saudat wlhy sosai, zan iya cewa babu wani mahaluki daya ta6a son wata kamar ni. Asanadin iman nakamu da ciwon ZUCIYA da hawan jini, amma kash takasa fahimtata, takasa yimin uzuri, kodayake batada laifi itama tana cikin ruďanine kawai. Hakane abokina, iman tana cikin ruďani wlhy. Saidai kawai mucigaba da barma ''UBANGIJI "komai dominshi yanasane da shiga da fitar kowa, kuma shine masanin gaibu. Hakane, ALLAH yasa mu dace to. Haka Nabeel yayta kwantarma Isma'il da hankali harya samu 'yar nutsuwa, yakira yayansa suka gaisa harda Deexerh da marwan, dakuma mama da maman su deexerh, da aunty. WASHE GARI. duka 6angarorin biyu sun tashi sukuku, gakuma kowa yatashi da uziri, iman tatashi da uzirin text. Isma'il yatashi da uzirin aiki, an turasu kwantar dawata tarzoma a RIVERS STATE, dan kawai bashida ikon k'in zuwane amma daba inda zaije, sauk'insama harda Nabeel a tawagar tasu dan haka damuwar tasa tayi sauk'i. Babu laifi iman ma taďan saki jikinta dan yau harta iya rubuta wani abu a text ďin. Su Reefat sunji daďin sakin jikinta sosai, harma a fuskarsu sun nuna. Iman tana k'aunar k'awayen nata, dan duk wanda yadace da k'awaye irin xoxo da Reefat yagama dacewa, bakuma zai ta6a yima k'awa kallon baibaiba. Dahaka suka rarrafa zuwa ďaki agjiye. Amma wanan bai hanasu sonjin labariba kasancewar yau iman adaidai take sa6anin jiya da shekaran jiya data shiga cikin ruďin zuciya dana jiki. To itamadai yau harga ALLAH tayi niyyar cigaba dabasu kabarin dan haka suna gama komai suka zauna. LABAREE. .......Nakai tsawon minti talatin dashiga ďakin banji motsin kowaba, sai zuwa wani ďan lokaci naji ana buga k'ofar ahnkali, tuni jikina yahau 6ari da 6aran6arama, cikin rawar murya na ce, "waye......? Doctor ya ce, "kibuďe kinyi ba k'i. Da farko ban yardaba, dan azatona wayau zayimin, amma saina rink'ajin maganar mutane sama2, jiki babu k'wari na sakko daga gadon nabuďe k'ofa. Babu doctor awajen dan haka na k'arfafa jikina dankarsu zargi wani abu. Nazo na gaidasu, suka amsa cikin fara'a da bina da kallo. Matane dayawa yara da dattija da 'yammata, da alamadai danginsu doctorne. Babu daďewa doctor yafito daga ďakinsa, ya zauna kan hannun kujera kusada wata tsohuwa amma ba tukuf ba. Ya ce, "Saudat 'yan sakoto ne dangin mahaifinmu yanzu zasu tafi shine sukazo miki sallama. Kaina a k'asa na ce, "sanunuku, suka ce yauwa amaryarmu. Daganan ban sake furta komaiba kasancewar inajin kunyarsu dashi kansa doctor ďin. Sunďan ta6a hira da doctor sanan suka mik'e, tareda yimin sallama da fatan dawowarsu suna wata shekarar. Nidai bance komaiba sai doctor daya ce, "ALLAH ya tabbatar. Bayan tafiyar 'yan sokoto saiga deexerh da Marwan waďanda dama can nasansu ahoto, saidai yauce rana ta farko damuka haďu. Na tarbesu da murna dan deexerh sa'a tace, shikuma marwan nagirmesa, suma sai fariciki suke daganina, saidai bansan daliliba. Na kawo musu cincin muka zauna muna hira. Ahaka doctor yashigo yasamemu, cikin farinciki suka tarbosa suna faďin oyoyo uncle. Shima yataresu da murna, yarana ina kuka shigane haka??, muna nan uncle, kawaidai gajiyar bikice. Yay dariya kokuma ganin bak'iba. Suma dariyar sukayi suna faďin dama wanan ďin. Nakula doctor yana matuk'ar son deexerh da marwan, sunkuma shak'u sosai dan kusan a 6angarena suka wuni ranar sai nan nan yake dasu kamar wasu yaran goye. Washe gari 'yan jalingo suka tafi suma bayan sun shigo har 6angarena suma, tundaga randa aka kawoni bansake zuwa 6angaren mamaba bamma gantaba. Wanan yasa nayima doctor tsogumi, ya ce, "nayi hakuri saboda akwai bak'i a 6angarentane amma insha ALLAHU yau zanje. ''Na ce, "to shikenan..........✍🏻 💕💚💕 Page ......9⃣. .............Yau 6angaren mama mukaje cin abinci sa6anin da damukeci a 6angaren yayansa. Muka shiga da sallama. Tana zaune akujera mai zaman mutum biyu, k'yak'yk'yawace itama fara tas, tana matuk'ar kama dasu doctor, idan bama kasaniba saikace itace ta haifesu. cikin fara'a taďago tana amsa mana sallamar, ta ďora dafaďin lale da ďiyata, zonan kinji. Cikin jin kunya nak'arasa wajenta, kusada k'afafunta nazauna, na ce, "ina yini?. Ta amsa da lafiya lauw ďiyata ya bak'unta?". Nayi murmushi batareda na amsaba, suma sauran suka gaisheta. Bayan an gama gaishe gaishe muka ci abincin rana anan, sanan muka dawo falon aka sake zama. Doctor ya ce, "Saudat". Na ce, "Na'am". Ya gyara murya to kinga family ďina kamar yanda na sanar dake abaya, kuma kema yanzu kinzama 'yar cikin wannan family ďin. Da farkodai ga mahaifiyarmu wadda muke kiranta mama, ya nunan yayansa wanan kuma shine yayana Mansur, muna kiransa yaya, wanan itace matarsa ina kiranta aunty, yanuna matarnan dabatiminba. Yacigaba waďanan kuma sune yaranmu Hadeeza da Marwan. Dan haka ina rok'onki ki girmama family ďina kamar yanda kike girmama naki, gaba ďaya family ďina suna sonki suna farincikin kasancewarki acikinmu. Kaina yana k'asa na ce, "insha ALLAHU zaka sameni yanda kake buk'ata, kuma nima inason family ďina nabiyu, nayi alk'awarin zan zauna da kowa lafiya, kuma ina matuk'ar farincikin kasancewa daku nima. Ya ce, "to Alhmdllh". Nakula dukansu maganata ta burgesu, musamman dasukemin kallon k'aramar yarinya mara wayau, amma sai sukaji zance raďam kamar wata babar mace. Mama ta ce, "mungode ďiyata ALLAH yay miki albarka kinji, yakuma bamu zaman lafiya da zuri'a ďayyiba. " Duk suka amsa da amin". Amma bandani. Yaya ya ce, "to aini duk abinda zance kunriga kun faďa, saidai na ce, "ALLAH yabamu zaman lafiya. Nanma akace amin". Aunty kam batace komaiba, da doctor ya ce, "auntynafa mizakice??. Ta ce, "a'a ni banida abin faďa, wanda kuka faďa yawadatar. Nakula kamar maganar bataima kowa daďiba, musamman yaya, deexerh ma baki naga ta ta6e tareda gallama aunty harara. Daganan hira aka cigaba dayi, wadda sukaďai suke abinsu bandani, itama auntyn saita gadama take saka baki. Munďan daďe muna hira daga baya suka tafi sallar la'asar, nima muka tafi 6angarena nida deexerh. Inason deexerh kasancewarta k'yak'yk'ya nutsatstsiya, gata alamunta suna nuna mai hak'urice da kawauci. Muna idar da sallah muka dawo falo domin yin kallo, muna nan zaune doctor yadawo, yashigo da sallama muka amsa. Kusadani ya zauna yana faďin kundaiyi sallar ko?. Atare muka amsa da eh munyi. Ya ce, "masha ALLHU". Namik'e nakawo masa ruwansha, cikin murmushi yakar6a yana faďin ALLAH yay miki albarka. Na ce, "amin ngd". Deexerh ta shagwa6e fuska, uncle anbamu aikifa tun wancan satin, kuma gobe idan ALLAH yakaimu za'a amsa, nikam nakasa yin nawa. Dictor ya ce, "haba my daughter keďin aiba abinda zai gagareki saboda nasan kwakwalwarki akwai jaa. ALLAH uncle bawasa nakeba. Okey, tojeki ďakko nagani. Da gudu tafice daga falon, yayinda shikuma yadawo kujerar dana koma, yazauna kusadani tareda rungumoni zuwa jikinsa. Ina masifar son turaren doctor dan haka nak'ara kwantar da kaina ajikinsa ina shak'a. Shikuma yasake nutsani sosai a jikinsa, ahankali yafurta my iman ina k'yaunarki dayawa wlhy. Nima na ce, "ina k'yaunarka doctor. Da sauri yaďago fuskata yana kallo, yak'ara k'ank'ance idanunsa yana k'aremin kallo kasa2, da gsky Imaniiii!!!??. Yanda yaja sunan nawa saida tsigar jikina tatashi. Na ďaga kai ahankali". Yasaki k'ayataccen murmushi, ashe yau zaki amince mukwana gado ďaya kenan?, saboda na nuna miki tsantsar k'aunarki dake kwance acikin jinina da zuciyata. Kaďan naďago ina kallonsa, na maida kaina da sauri dan ganin ya kafamamin idanunsa......ahankali ya matso da fuskarsa kusada tawa danufin bani sumba sai deexerh tashigo ďakin. Yay saurin janye fuskarsa yana 'yan kame2 narashin gsky, yabani dariya amma saina gimtse nima nayi saurin tashi daga kujerar na canja wata. Deexerh tak'araso kusada shi ta zauna ta bashi littafin nata. Kar6a yayi yana satar kallona, nikam kaina yana k'asa. Bayan yagama dubawa ya ce, "my dee....bari nagaya miki kiringa rubutawa, babu musu deexerh tayarda dan kwakwalwar tata tanaja yanda yakamata. Ina zaune ina kallonsu yana faďa mata tana rubutawa har suka gama, yakar6a yagyara mata inda batayi daidaiba. Ya ce, "wai ina Marwan?." Deexerh ta ce, "yana ďakin mama uncle barci yakeyi. Barci da yammarnan haka?. Ta ďaga kai alamar eh. Baice komaiba yamik'e yashige ďakinsa, mukuma muka cigaba da kallo. Haka rayuwar take tafiya, ina gidansu doctor amatsayin amarya amma ta nesa, dan babu wata alak'a dake tsakanina dashi. Har yanzu bana shiga kicin aunty take mana girkin gidan itada 'yan aiki. Komai na rayuwar gidan yana tafiya yanda yakamata, saidai matsala ďaya nake fuskanta itace auntynsa, nakula ko kaďan bata sona agidan, tana nunamin abubuwa dayawa kawaidai ina sharewane. Kuma banta6a faďama kowaba, dan ba itabace agabana. Ana cikin haka kiran gaggawa yasamu doctor awajen aikinsa, dan haka yashirya yatafi badan yasoba. Ranar dazai tafi harda kuka nayi kashir6an mama na lallashina. Bayanda zanyi dole na hak'ura, deexerh tacigaba da tayani kwana, kodayaushe muna tare, dan haka shak'uwa ta musamman tashiga tsakanina da ita. Kullum kuma sai munyi hira da dictor ta waya indai yasamu lokaci kunsan soja sai ahankali. Wani abin mamaki shine tunda nazo gidan banyi al'adaba, dan haka babu zancen ciwon mara. Hakan yayimin daďi, duk wata kuma sai doctor yatanbayeni, cikin jin kunya nake cemasa banyiba. Ana haka doctor yadawo a safiyar wata juma'a. Babu wanda yafaďama zaizo saidai muka gansa kawai, munyi farinciki sosai da ganinsa dan watansa na uku kenan da tafiya. A6angaren mama ya ara sauka. Sai bina da kallo yake cikin mamaki dan ganin nayi k'iba kai harma da k'ara tsawo. Nikam duk kunya ta dabaibayeni dan ganin irin mayen kallon da yake bina dashi ko kunyar mama bayaji bare aunty.. Bayan angama gaishe2, yaci abinci yak'oshi, sannan yamik'e yana faďin mama bari naje nayi wanka na huta kafin lokacin masallaci. Mama ta ce, "to auta afito lafiya. Aunty ta ce, "nibazakamin sallamaba kenan, ko kallonta baiyiba yafice daga falon mama yana faďin ke asuwa kuma?. Dukda ta dake nasan maganarsa ta 6ata mata rai. Mama ta kalleni iman tashi kije wajen mijinki mana. Akunyace namik'e nafice, dan dama kunyartace ta hanani bin bayansa. Kutashi muyi sallah ko sisters. Xoxo da Reefat suka mik'e kowa baiso aka katse labarinba. Amma damun idar da sallah zakicigaba ko??, xoxo tafaďa tana bin iman da kallo. Insha ALLAHU my hafsy zan cigaba damun idar..................✍🏻 Am busy 😂👌🏻 Luv u oll my fan's ((S))......2017 Battery low 🔋😁👌🏻 .a [8/6, 6:00 PM] mrs bilkisu: *_________________________________* *BAN SAKETA BA* *__________________________________* *NA* *BILKEESA IBRAHEEM* *{bilyn Abdul}* *___________________________________* https://mrsbilkisa.blogspot.com _Sadaukarwa_~*ya Abdul {city phone's}* *MIYA KAMATA NAYI??.* _amatsayina na *MUSLIMI* baidace daniba nashagala da duniya da abinda kecikinta, a *DUNIYA* ake neman lahira, to tayaya zan nemi tawa_ *LAHIRAR?*. _mun shagala aduniya, kalon *FILM* karatun *NOVELS* awaya zuwa *biki*.......da sauransu sunsa mata dayawa mantawa da zan *MUTU* na riski *"UBANGIJINA"* ya salam, 'yar uwa ringa tunawa da mutuwa mai zuwa babu ďan aike, ringa tunawa da *sallah* ringa nafila, zikiri akowace rana, karkibari nishaďin duniya yasaki dana sani awata rana mai cike da *hargitsi,* tsarama kanki lokaci yanda ke da mijinki da 'ya'yanku zaku amfana, a duniyarku da lahirarku, duk wanda yay asarar *aljanna* amatsyinsa na *musulmi* to dolene atayashi kuka da jaje_. _muhaďu agaba domin jin yanda yakamata ki tsara_ *Duniyarki 'yar uwata*_domin keda *zuri'arki*ku amfana_ *a lahirarku* *ALLAH yasa mugane*. ~page.......~1⃣0⃣. *............*da sallam nashiga falon babu kowa alamun *doctor* yana cikin _bedroom_ kenan. Dukda inajin kunya wannan bai hanani nufar ďakinba, nashiga da _sallama_. Yana tsaye atsakiyar ďakin yana k'ok'arin cire kayansa, yajuyo ahankali yana kallona, nikam nayi k'asa da kai saboda kunyarsa danakeji. Yasaki _murmushi_ mai k'yatarwa, ahankali ya ce, " *my iman* k'araso mana. Nak'ara k'asa da kai saboda kunya, na ce, "bari naje falo idan kagama saina dawo, wlhy bammasan kana shirin wanka bane. Takowa yayi cikin takun k'asaita har inda nake tsaye. Nikam jinake tamkar na zura da gudu, amma babu dama.......kusantowarsa gareni tasa na ďago da sauri muka haďa ido. Nai saurin maida kaina k'asa. Baice min komaiba sai kama hannuna dayayi muka k'arasa cikin ďakin sosai. Ya zaunar dani abakin gado sanan yacigaba da cire kayansa. Araina na ce, "waishi doctor baisan inajin kunyarsa bane?. Ina nan zaune harya gama cire kayansa, ya k'araso yazauna kusa dani dagashi sai gajeren wando. Yaďan rungumoni jikinsa yana magana ahankali tamkar mai raďa ko baisan tada yaro mai barci. _farin cikina abar alfaharina, har yanzu kunyar tawa bata k'arebane?_. Maimakon nabashi amsar tambayarsa sainace kadawo lafiya?. Yakama hannuna danake wasa dashi yaďan matsa, naďago da sauri ina kallonsa dan naji zafi. *Ya ďaga min gira* Miyasa baki bani amsar tambayataba??, saikika sakko taki tambayar??. Nayi murmushi wanda yakeso yaga nakasance akoda yaushe inayi, amma ina niďin _muskilancina_ bazai barniba. To kayi hak'uri nafaďa atak'aice. To nahak'ura *saudat* nasameku lafiya?. Lafiya k'alau. Ya aiki?. Aiki *Alhmdllh* saidai kewarki da begenki sunta addabata musamman alokacin barci. Ban bashi amsabama yanzu. Ganin haka yasa yasake matseni sosai ajikinsa, saikuma nafara masa rawar jiki, nakan bashi mamaki idan yaga nashiga wani hali alokacin daya haďani da jikinsa, amma saiya basar. Yamik'e tareda mik'ar dani tsaye, zomuje ki haďamin ruwan wanka. Bayan gama haďa masa ruwan wanka na ce, "nagama. Kafin ya ce, "wani abu nafice. Rakani yayi da wani shu'umin kallo, ala66ansa yafurta iman kinkusa zuwa hannu aii, kunyar nan tana cutata dayawa. Bayin yashiga yayi wanka yafito, dashirin kwanciya yafito amma sai yaga lokaci yatafi kasancewar yau _juma'a_ shirin masallaci yayi cikin jar shadda sai maik'o takeyi. Ya murza bak'ar hula da bak'in agogo, turarensa na kullum ya fesa, tunkafin yafito k'amshinsa yayo gaba. Na tsurama k'ofar ďakinsa idanu, yayinda yafito aisai naga tamkar ba *Dr Isma'il* ďinaba, yayi kyau harya gaji. Sosai na dasa masa idanuna ko k'yaftawa banayi. Jinai anhuremin ido". Na sauke nannauyar ajiyar zuciya, tareda cusa kaina cikin cinyoyi saboda kunyar yakamani ina kallonsa. Kusadani yazauna yana dariya da faďin ďago abinki ki kalli _mijinki_ matana, niďin nakine ke kaďai. Ina nakasa ďagowa saboda ba k'aramar kunya najiba wlhy. Da kansa yaďagoni yakuma rik'e fuskar tawa tamau atafin hanunsa yanda bazan iya kwacewaba. Rintse idona nayi dan bazan juri haďa ido dashiba, shikam yadasamin mayun idanunsa tamkar yau yafara ganina. Yakai tsawon minti biyar yana kallona. Ban fargaba naji bakinsa cikin nawa, cikin kwarewa yake sumbatata, ban hanashiba domin nima inajin daďin hakan dayakemin, *kunsandai SO yanda yake, yakansa ka aikata abinda bakayi niyyaba* _dan so yahaďu da so, sai ahaďu asoye tare_ Munkai tsawon minti ashirin ahaka, doctor yana abuďaya, saida yayi mai isarsa sanan yazare bakinsa ahankali yana maida numfashi, fuskarsa cike da *annuri na musamman*. Yaji daďin yanda yau natayashi abinda yakeso. Saidai ni kaina nayik'asa ina fidda nawa numfashin ahankali. Wata sassanyar dariya yasaki akunnena, cikin sigar *Salon so* ya ce, "lallai my iman kin fara haddace karatun aure......... Bai k'arasaba marwan yashigo shima cikin shirin masallaci, doctor ya hararesa koma kayi sallama. Marwan ya narke murya *ALLAH* Uncle nayi bakujibane kawai. Banason k'arya". *ALLAH* kuwa marwan yaske faďa kamar zaiyi kuka. Na ce, "yayi sallamafa. Ya maido da kallonsa gareni, kinji kenan?. Kai naďaga batareda nayi maganaba. Yay k'asa da murya, kece kika rikitani har nakasaji nakasa gani, *INASONKI DAYAWA SAUDAT*. ajiyar zuciya nasauke ahankali, yayinda shikuma yamik'e yana kama hannun Marwan. My boy ya akayi?". Marwan ya ce, "daddy ne yadawo shine na ce, "bari na sanar dakai. Okey my son muje. Saida suka kai k'ofa sanan yajuyo ya ce, "idan kinjishiru munwuce masallaci. Kaina ak'asa na ce, " *ALLAH* yatsare, yadawo daku lafiya. Amin mungide yafaďa yana fita. Dr da Marwan suka nufi 6angaren yaya, da sallama suka shiga. Yayansa yana zaune shima cikin shirin masallaci da alama su yake jirama. Yamik'e da sauri tareda warema doctor hannu, alamar yazo. Aiko da sauri yak'arasa yashige, suka rungume juna da faďin kewar dasukayi na nisantar ruhinsu. Yaya ya ďago kan doctor suka haďa ido suna sakarma juna murmushi, autan mama *soja* kuma *likita*, katafi kabarmu da kewarka ko??. Kuyi hak'uri yaya wlhy nima nayi kewarku, duk son danake nazama *soja* yanzu sainaji yafita kaina. Yayansa ya nunasa yana dariya anya kuwa zan yarda dakai Isma'il??. Dr yayi dariya, wlhy gsky nake faďama yaya. Rungumesa yayansa yaskeyi saboda jin daďin maganarsa. Aunty ta balla musu harara batareda sun ganiba, azuciyarta ta ce, "naga *rai da mutum,* k'arewar 'yan uwantaka. Amma afili saita ce, "zakuyi missing ďin sallaffa Abban deexerh, dan ďaya harta kusa. Da sauri suka saki juna suna kallon agogo. Tak'araso tana salo ta fesama yaya turare tareda ďora masa hularsa akai. Ya ce, "ngd gimbiyata. Murmushi tayi masa, sanan tajuyo ga doctor zata fesa masa turaren, amma saiya kauce da sauri, yana faďin a'a wanda matata tasamin ya wadatar. Dariya yaya yamusu ya ce, " *ALLAH* yashiryaka Isma'il, kazama mara kunya dai. Fita doctor yayi yana dariya. Gaff sukai karo da mutum abakin k'ofa. Yaďago da niyyar masifa amma saiyayi shiru dan ganin wadda sukai karon. Suduka sun k'urama juna ido cikin wani yanayi wanda bakowane zai iya fassarawaba, Bawata bace illah *Raihan* k'anwar aunty Sadiya, matar yayansa. Shine yafara janye nasa idon akasalance, itako Kallonsa take tamkar zata cinyeshi ďanye. Yadaure ya ce, "Raihan kece a kanon mu yau??. Tasaki dariya cikin salo ta ce, "eh wlhy *yaa Isma'il*. Ya ce, "sannunki dazuwa to, yafaďa yana k'ok'arin kar6ar k'aton akwatin hannunta, wanda yanuna da shirin dogon zama tazo garin na kano. Taďan janye tana faďin haba yaa Isma'il aiiba girmanka bane..... Kafin yabata amsa yayansa yafito yana faďin kaidawa auta.......? Maganarsa ta kakare dan ganin Raihan tsaye da kaya nik'i2, wata 'yar fara'a yasaki maikama da yak'e, a'a Raihan kece tafe??. Ta ce, "eh yaya, ina yini. Bai amsaba ya ce, "shiga ciki mana. Suka kauce suna bata hanya. Taja akwatinta da jaka k'eeyyyy zuwa ciki. Wani ihun murna auntyn tasaki saboda ganin k'anwarta, doctor da yayansa suka fice kowa yana sak'a mai fisheshi azuciya. Nikam koda yafita saina mik'e nanufi ďaki domin fesa wanka, dan inason fara amfani da shawarwarin da deexerh take bani yau da kullum, akan narage kunya wajen kula da mijina, inba hakaba wata zata samu k'ofar dazata shigo rayuwarmu. Na yarda da batun deexerh musamman data bani na karanta wani *Novel na bilyn Abdul* mai suna *RASHIN SANI* naga yanda *Nazeefa ta ruďa ya Mus'aff* dayake mata kallon 'yar k'auye ada, har yana gudun aurenta, amma da aunty khadija ta gyarata yadawo yaganta saiya haukace akan *RASHIN SANI*. to barema ni nawa mijin yana sona. Nikam son danakema doctor aii bana fatan haka koda amafarkine, dan haka daga yau na zage damtsen yimasa abubuwa na ban mamaki. Karnayi saken da *sopy ta akan Abdul* a littafin *NI DA AMINIYATA* har fareeda ta samu damar kwace matashi, kodayake tasamu *uncle G* wanda yafi Abdul komai. Saidaifa ina hangen matsala kasancewar tun shekaranjiya marata take ciwo kaďan2, ina daurewane kawai saboda batamin ciwo kamar da. Haka na daure ina cije baki ina kwalliya tamkar dole. Na tsara kwalliya tagani da faďa, nasan kowa yaganni saiya sake kallo kodan k'yawun danayi na musamaman. Nidai doguwace sosai kamar yanda kuka sani, dan tsawona yasa har 'yar rankwafawa nayi kaďan, banida k'iba gsky dan kamar ahureni haka nake, bazance inada tsananin k'yauba amma *Alhmdllh* muna tsaka tsaki, inada ďan haskena iya gwargwado dan ba'a kirani faraba, idan ina kusada masu ra'ayin babu _chocolate colour_ aduniya, to dole akirani bak'a kuwa, _(dan wasu sunce kala biyu suka sani aduniya daga bak'i sai fari)_. Hancina kam ba dogo bane, saidai nace gajere, ga idanuna atsaka tsaki suba manyaba bakuma k'ananaba, ďan gashina daidai wadaida masha ALLAHU. wanan itace surata ni saudat amusalce, kunga kuwa niba mai mugun k'yau bace tafaďa da nunawa, irinmuma ba'a sakamu gaban mota ace za'a farty. Wata uwar harara *xoxo* tamata, ta ce, "iman aii dai godema ALLAH, duk wanda ya ce, "bakida k'yau saidai _hasidin iza hasada_ wanda yakali sama ya ce, "akarkace take". Reefat ta tuntsire da dariya, gskyar kine my xoxo. Bagashi ta haukata mana *Dr Isma'il* ba. Gaba ďaya suka shek'e da dariya suna tafawa. *(na ce, "kai 'yammatan nan suna burgeni ni bilyn Abdul)😁lol👌🏻* ...............✍🏻 *((S))........2017* *luv u oll my fan's* *Battery low* [8/6, 6:00 PM] mrs bilkisu: *________________________________* *BAN SAKETA BA!!!* *________________________________* *NA* *BILKEESA IBRAHEEM* *{bilyn Abdul}* *_________________________________* https://mrsbilkisa.blogspot.com _sadaukarwa_ *~ya Abdul (city phone's)* *MIYAKAMA NAYI???.* _ba matane kawai suka shagala a *duniyaba* harda abokan jinsinsu wato *maza*_ *maza* _ma sun shagala a *duniya* wlhy, zakaga babban mutum magidanci mai tarin *zuri'a* amma yana wasa da ibada, saboda uzurin office kona kasuwa._ _wani akan kunnensa liman zai kwala kiran sallah, amma saiyace bari yagama sallamar *customers* sannan, wani kuma idan a office ne saiya kawo uzurin k'are takardun dake gabansa_ _Haba ďan uwa duk abinda kakenema yana wajenfa wanda aka kiraka domin bauta masa, magidanta sunada matuk'ar sakaci awajen yawan nafilfili na dare da azumin nafila, saboda hujarsu tacewa sunje nema sun gaji_. _A'a ďan uwa gyara sai ALLAH ya gyara maka, gyara kodan iyalinka suyi koyi dakai, amatsayinka na uba, miji, shugaba._ _Abinda mukayi da shi 'ya'yanmu zasuyi koyi, su tsira mu tsira, aranarda aikinmune kawai garkuwarmu!!!!!!!._ *ALLAH yasa muga ne.* ~page........1⃣1⃣~ ................bayan sun idar da sallah suka sake zama. Iman ta ďora labari." Bayan nagama tsara kwalliya na baďe 6angarena dawani sabon k'amshin, dan nasan mijina ma'abocin son k'amshine, gida yaďauki haramin k'amshi tamkar gidan saida turare. Duk wanan aikin cikin dauriya da jarumta nakeyinshi, ina zama saiga deexerh tashigo da sallama, hannunta ďauke da filet. Naďago ina amsa mata tareda tsokana, ďiyar uncle mi'aka samomanane?. Kusadani tazauna tana dariya, abinda kike matuk'ar so nasamo, ammafa saidai ayi cinikinsa. Da sauri na ce, "indai har abinda nakeson ne, to mikikeso nabaki??, taďan langa6e kai alamar tunani, saikuma taďago tana faďaďa murmushinta, ba kuďi nakesoba, sonake ki lalla6a min uncle yasa dady yakaimu wajen mom ďinmu gobe idan ALLAH yakaimu mu wuni acan. Tabani tausayi matuk'a, amma gudun karna karya mata zuciya sainayi murmushin k'arfin hali, na ce, "insha ALLAHU dee.....ďin uncle zanyi wanan k'ok'arin. Ta faďaďa murmushinta tareda faďin ngd sosai auntyna k'awata, mamana, kuma ta biyu, shiyyasa akulum nake k'ara sonki, zuwanki gidannan yasa muka k'ara rage maraicin rashin uwa akusa, dukda k'ok'arin mama na son sharemana hawaye itada uncle, ta k'are magana da matso kwalla. Hannu nasa ina goge mata hawayen, badan karna k'ara tada mata hankaliba dana tambayeta dalilin barin mom nasu gidannan, amma saikawai nacigaba da lallashinta. Bayan wasu 'yan mintina ta lafa da kuka ta bani filet ďin dake rufe, cikin zaro ido na ce, "lah dee.... ina kika samo fara??. Tayi 'yar dariya, wlhy a school na siyo miki saboda nasan kina sonta sosai. Rungumeta nayi ina murna damata godiya harda addu'ar fatan alkairi arayuwa..........da sauri muka juyo danjin k'arar buďe k'ofa da matuk'ar k'arfi. Cikin sanyin jiki muke kallonta, sa6anin ita datake kallonmu cikin tsana da tsangwama, ta ta6e baki tana yatsina, bazanyi mamakiba domin yanzu mace da macema haďuwa suke su sa6i ALLAH. afirgice muke kallonta danjin ficinta mai matuk'ar muni da firgici. Deexerh ce ta iya daurewa tafurta wani abu, ta mik'e tana kallon matar baban nata cikin tsana, ''k *Sadiya!!!* kishiga hankalinki wlhy, muba shaiďanu bane bare ki jinginamu da wanan fasik'ancin, kuma tabbas daga yau munta haďaki da ALLAH kenan acikin sallolinmu harsai ya saka mana, kuma zakiga fasik'ai insha ALLAHU a zuri'arku, _tsumma mak'ullin cuta kawai_ *ALLAH zaimana maganinki komai daren daďewa* deexerh nagama faďa tafice daga falon tanufi 6angaren mama tana kuka. Nikam aii mutuwar tsaye nayi ga marata ta k'ulle tamau, itama auntyn tana tsaye tamkar gunkin da aka dasa awaje ďaya, ta maido da kallonta gareni zuwa sanan nafara shiga mawuyacin hali..... dan 6acin ran maganarta yasa marata tayi wata muguwar wakitawa, kafin tayi wani yunk'uri nafaďo k'asa ina murk'ususu, adai dai kuma wanan lokacin doctor yashigo falon. Da gudu yak'araso gareni yana kiran _iman! Iman!!_ ina nayi nisa cikin ciwo, arikice yaďagoni jikinsa yana girgizawa saiga su mama da deexerh sun shigo. Mama tak'araso arikece tana tambayar lafiya??, tanayi tana kallon aunty sadiya dan deexerh taje ta sanar mata abinda aunty taimana. Aunty ta ce, "wlhy mama bansan miya sametaba, nima naga kawai ta faďi tana rik'e ciki........doctor yakatse musu zancen da faďin karku damu mama nasan matsalarta, rik'eta ina zuwa. Mama ta kar6eni doctor kuma yafice domin nemo allura. Tunda yatafi nake murkususu ajikin mama dakiran sunan gwaggo, dakuma duk addu'ar datazo bakina. deexerh sai kuka take azatonta abinda auntyn tayi manane yakawo ciwon, lokacin da soctor yadawo har suma nake dan azaba, tareda yayansa suka shigo. Mama ta rik'eni yay min allurar, zuwa wani lokaci sainayi sakwat alamar ciwon ya gudu, harma barci yafara ďibata. Mama ta ce, "isma'il ďaukrta kakaita ďaki. Kamar jaririya haka ya ďaukeni yakai saman gado yadire, yana mai k'ara jin tausayina da tuhumar kansa akan sakaki, dan yasan shine maganin matsalata amma yakasa min maganin tunda wuri, saboda shagalal dayayi akan wata yawuce banyiba. Rashin lafiyata ta hana tada maganar da aunty tayi mana. Har dare ina barcina ba'a tadaniba. Dak'yar suka lalla6a doctor ya halarci wajen cin abincin, sai asanan mama da deexerh da marwan suka san da zuwan Raihan, basu canja da komaiba suka k'ar6eta kamar yanda suka saba, dan sunsan laifin yayartane, _(laifin wani kuwa aii baya shafar wani)_. Sai bayan isha'i na farka, lokacin doctor yatafi masallaci shida yayansa da marwan, deexerh ta taimaka min na gyara jikina tsaf kamar komai bai faruba, sanan muka nufi wajen mama. Tana falo zaune muka shigo, tabini da kallon mamaki 'yar nan wanan ciwo naki tamkar iska?. Nayi dariya tareda risinawa ina gaisheta, ta ce, "yajikin??. Da sauk'i mama aii yakuma tafi. To ALLAH yak'ara sauk'i ya kiyaye gaba, na ce, "amin mama, anan ne mama take bani hak'uri akan abinda yafaru ďazu, takuma rok'eni karna gayama mijina. Babu komai mama insha ALLAHU bazai jiba, kumani wlhy harma na manta. Yauwa ďiyar kwarai ALLAH yayi miku albarka kunji, nida dee....mukace amin. Muna nan zaune muna 'yar hira saiga marwan yashigo, mukai masa sannu da masallaci ya ce, "yauwa auntys, yajiki aunty??, da sauk'i marwan aina warke........kafin yabani amsa Raihan tashigo falon, muka amsa mata sallamar datayi, nidai sai binta nake da kallon mamaki dan bansantaba, saidai suna kama da aunty kam. Ta zauna tana min sannu da jiki, cikin sanyin jiki na amsa mata, deexerh ta ce, "k'anwar aunty ce, ďazu tazo. Na ce, "ayya sannu da zuwa". Ta amsa da yauwa kema sannunki. Doctor yashigo shima yana faďin dama kinan nan iman??, eh ina nan babu daďewa muka shigo nida dee...., okey yafaďa yana zama kusadani, ya ce, "yajikin naki??, Alhmdllh nafaďa kaina ak'asa saboda kunya. Mama ta ce, "auta kundawo?. Eh wlhy mama mundawo. Ta ce, "sannunku." Yauwa mama. Sau wajen huďu ina kama Raihan da doctor suna kallon juna, shi idan ya kalleta yakan janye idonsa amma ita ko gezau bare kunyar mama. Zuciyata tashiga nazarinsu, dan suna kallon junane cikin rashin gsky da alalomin tambaya??. abinda na kula bani kaďai nagane hakanba, harsu mama suna kallonsu, kallo ďaya nayima mama kuma nagano alamar 6acin rai afuskarta, da ga k'arshema sainaga kawai ta tashi tabar falon. Lokacin maga tamkar alamun tsoro sun bayyana afuskar doctor, akasalance yakama hannuna mukabar falon muma, tareda faďin saida safenku. Koda muka koma 6angarenmu ban tanbayesa wacece Raihanba?, zama kawai nayi saman kujera, shima yazauna yana shafa kaina my iman sannu kinji, wlhy lokaci k'an k'ani kinsha wahala. Ban cemasa komai ba, dan wasu abubuwa suna yawo akaina, ganin bazan tanka masaba yasashi mik'ewa yashiga ďakinsa. Babu daďewa yafito sanye da gajeren wando da bes, yazauna k'asan kafet ya ce, "nakawo masa kayan marmari yasha. Akasalance namik'e zuwa kicin yayinda shikuma yabini da kallo mai cike da tunani iri2. Nakawo masa yankakkun kayan itatuwa na ajiye. ya ce, "sannunki. na ce, "yauwa. Harna juya zan koma ya ce, "zo mana, babu musu nadawo, ya nunamin kusadashi, nanma ban musaba na zauna. Ya ďako abarba zuwa bakina, amma saina girgiza kai na ce, "nak'oshi. Yaďan rage fara'a, idan na amince kin k'oshin ko??, yafaďa yana 'yar hararata. ban ta6a ganin fuskarsa a haďeba sai yau, dan haka na buďe baki yasaka mini, haka yayta bani shima yana sha har muka k'oshi. Daganan falon muka zauna saidai yau babu hira, idan na kalli doctor ma sainaga bashida walwala, dahaka har goma tayi mukaije muka kwanta konace na kwanta. Dan harna fara barci sanan naji motsin shigowar doctor ďakina. Ban motsaba bare yagane na farka, ya hawo gadon ya kwanta saidai amamakina yau bai rungumeniba tamkar yanda yasaba, abin yabani mamaki amma saina danganta hakan da gajiyar tafiya dakuma fashin sallah danakeyi. Wasa2 har wajen k'arfe ďayan dare doctor bai runtsaba, nima ko barcin ya ďaukeni saina farka saboda yawan motsin da yakeyi, yanzu tunanina yatashi daga zargin farko, yakoma akan Raihan k'anwar aunty. Tabbas akwai abinda bansaniba, akwai wata alak'a tsakaninta da doctor da Raihan. _" wai wacece *Raihan* ne???._ Mutum ďayace zata bani amsar tambayata, wato _*deexerh!!!!.*_. Sai gabannin asuba barci ya ďaukemu, wanan yasa muka makara sallar asuba. Ban koma barciba nafice wajen aunty kamar yanda nafara kwanan nan dan yanzu dani ake girkin gidan. Shikam doctor barci yakoma. Haka mukayi aikinnan nida ita bamaima ďan uwansa magana dama haka mukeyi dan babu shak'uwa tsakanina da ita. K'arfe bakwai na safe muka gama haďa break 'yan aiki suka kwasa zuwa 6angaren mama, mukuma kowa yanufi ďakinsa. Koda naje ban kwantaba saikawai na hau gyaran 6angarena dukda bawani datti bane, tunda nakula doctor baya ra'ayin masu aiki nima saina daina sakasu gyaran wajena, nazage inayi da kaina. Bayan nagama nayi wanka nashirya tsaf cikin rigar material doguwa, ina fesa turare doctor yatashi. Yadaďe datashi ban saniba, idonsa na kaina duk motsin danayi saiďan murmushi yake yana lumshe idanu, tacikin madubi nagansa tsaye abayana sanye cikin pink ďin kayan barci. Najuyo ina faďin lah katashi?. Murmushi yayimin ya ce, "badoleba tunda gimbiyata tatashi bata tadaniba. Kaina ak'asa ina wasa da zoben hannuna na ce, "kayi hak'uri to dan ALLAH, naga bakayi barci ishashshe bane jiya. Maimakon yabani amsar tambayata ta k'arshe, saiya ďauki ta farko yay sharhi akai. hannuna yakama yana murzawa karki damu na hak'ura, aike bak'ya laifi awajena my iman, kinrigaya kin mallake zuciyar Isma'il daduk wani aikinsa. Huumm to shikenan ngd, yakamata kayi wanka ko?. Nafaďa ina zare hannuna daya rik'e. Bai iya amsaminba saidai bina da kallo dayayi harna fice, aďakinsa na haďa masa ruwan wanka, sanan nadawo shikuma yatafi. ☆ A falon mama duk mun hallara muna break, yauma tamkar jiya haka doctor da Raihan suke satar kallon juna, zuwa can kuma saina farga da taka k'afar doctor da Raihan takeyi ta k'ark'ashin tebir, shikuma yana janyewa. Abisa tsautsayi ta taka k'afata saboda nike kusada doctor, na kalleta muka haďa ido sosai, saitayi k'asa da kai cikin jin kunya. Dahakadai muka kammala break, yayansa ya ce, "yazo su tafi kasuwa.. Sallama sukai mana suka tafi, muka rakasu da ALLLAH ya kiyaye hanya.. _*miss xoxo da Reefat*_ sukace tofa kaji wata sabu kuma??, iman kin k'ara sakamu atunanifa. Shin wacece Raihan!!.? _*iman*_ tasaki murmushin basarwa, karku damu 'yan uwana, zuwa gobe zakusan wacece Raihan, ammafa kar tazame muku matsala, dan ita ba matsala baceba. To ALLAH yasa hakan, suka faďa kowa yana kwanciya................✍🏻 _*luv u oll my fan's*_ _*((S)).........2017*_ _*battery low*_ [8/6, 6:00 PM] mrs bilkisu: *________________________________* *BAN SAKETA BA!!!.* *________________________________* *NA* *BILKEESA IBRAHEEM* *{bilyn Abdul}* *________________________________* https://mrsbilkisa.blogspot.com _sadaukarwa_ *~ya Abdul {city phone's}* *MIYAKAMATA NAYI??,* _Komai ka rasa zaka iya samun wanda ya fishi, Amma banda kwanakin rayuwarka, idan sun tafi sun tafi kenan, Domin haka karka 6ata rayuwar ka wajen abinda bazai amfane ka ba, yi kokari wajan yin abinda zai amfaneka duniya da lahira...""_ _kyautata ibadarka domin danmu bautama ALLAH ya halicemu, idan baka iyaba ko kanada k'arancin ilimi nemi malami ya koya maka, ba'a ibada da jahilci, "ubangiji baya kar6ar ibadar jahili._ _muguji salwantar da yininmu da kwananmu akan duniya da abinda ke cikinta, domin lokacin ďan adam mai tsadane, asarar second ďaya ga mumini daidai take da asarar shekara dubu._ _Mizai hana mutsara lokacinmu domin ammafanarsa a ranar data dace_. ```Karka bari duniyarka taringa tafiya tamkar cin abinci, dakaci saikayi kashi, kaga kuwa sara kenan```. _gyara yau da gobenka domin amfanar jibinka_ *ALLAH yasa mugane.* _*wannan page ďin nakune 'yan group ďina, ina alfahari daku sosai, ina k'aunarku har bansan iya adadiba, ALLAH yabarmu tare, kuďin nadabbane agareni, luv u wujiga wujiga, 😂lol👌🏻.*_ ~*Page.......12*~ ..................Bayan tafiyarsu kowa yakama gabansa, deexerh da Raihan suka fita raka mama wani guri, aunty ma takama gabanta, nikam saina tashi nashiga gyara 6angaren mama wanda ayanzu nice nake gyarwa na hana masu aiki yi. Bayan na kammala na koma 6angarena, wanka na sakeyi dan 12 ta wuce, yau banajin kwalliya dan haka nashafa fauda kawai da abinda ya sauwak'a, bak'ar doguwar riga nasaka nayi k'yau sosai saboda k'ibar dana ďan k'ara, ga fatata ta murje gwanin sha'awa. Falo nadawo na kwanta saman doguwar kujera tareda lumshe idanunana ina tunanin karatuna, inason na koma makaranta na k'arasa karatuna. K'amshi yacikamin hancina, na buďe idanu ahankali, doctor nagani tsaye akaina yana min murmushi. Na mik'e da sauri ina faďin sannu dazuwa, ince dai lafiya??, ya ce, "saiba lafiya mai gida yake dawowa gidansa?." Na ce, "a'a, na kar6i ledar hannunsa dayake mik'omin, ya ce, "rakene nagani ahanya shine nasiyo miki ban saniba kozaki sha?. Murmushi nayi na ce, "ina sha mana". Na ajiye ledan saman tebir nanufi kicin, ruwa nakawo masa yasha, ya ajiye kofin yana faďin ngd sosai _gimbiya_, nikam duk kunya ta isheni dan haganin mayataccen kallon dayake bina dashi. Kamar daga sama mukaga an banko k'ofa, gaba ďaya muka maida kallonmu wajen, aunty sadiya ce, ta ce, "lallai Isma'il dawowa kayi da wuri haka, lafiya kuwa??. Ya daure ya ce, "lafiya lau aunty nazo ganin k'anwarkine. Ta ta6e baki yo har yanzu batada lafiyar??. Yaďan rage fara'a ta warke ina kwaďayin gani k'yak'yk'yawar fuskartane kawai.....nikam gaba nayi zuwa kicin domin haďo mada abin motsa baki. Batace komaiba tanemi guri ta zauna, ta jawo ledan raken gabanta mikuma aka kawo mana ne??, baice mata komaiba dan al'amuranta sun fara bashi haushi, nashigo falon da sallama, shikaďai ya amsa mini, naje gabansa na ajiye filet đin kayan marmari. Ya ce, "ngd babyna". Nayi ďan murmushi kawai sanan nakoma kujerar nesa dashi na zauna. Ya kalleni taso kisha mana?, na ce, "a'a duk nakane......kafin yayi magana aunty ta ce, "nida ba'amin tayiba bari nazo nasha, kan kujerar dayake zaune tadawo ta zauna kusadashi daf, taďauki cokali tahausha. Ya ce, "a'a aunty mu mun isa muk'i yimiki tayi yafaďa yana matsawa, dayake doguwar kujerace. Nikam nayi gum dan mamaki take bani idan tana wani 'yan kamancin, ya kalleni iman yadai?, ďan murmushin k'arfin hali nayi na ce, "babu komai. Itakam ko kallo ban ishetaba sai danna abinta take. Ya mik'e bari naje na watsa ruwa dan duk nagaji, na ce, "afito lafiya. Ya nufo inda nake ya kama hannuna yana faďin aikece zakimin wankan, baibi takan auntyba muka nufi ďakin yana faďin aunty muna zuwa. Wata uwar harara tarakomu da ita wadda nikaďai nagani, taja tsaki tatashi tafita, azuciyata na ce, " *kishin banza*. Miss xoxo ta ce, " *kishin banza kam* tunda ba miji kuka haďaba, wai dama ana samun irin haka??. Reefat ta ce, "sosaima, wannan shi ake kira kishin sauri, wlhy wasu irin wanan kishin yakesa suraba zumincin family ďin mazansu, akwai mata dayawa dake kishin banza kamar haka, kiga matar k'ani ta tsani matar wa, matarwa tana kishi da matar k'ani, tamkar mijinsu ďaya. Miss xoxo da iman sukace to ALLAH ya shiryamu *(ni bilyn Abdul na ce, "wanan asarar lokacine, yakamata mata kugane badan kishi aka haliccemuba bare ki 6ata lokacinki awajen kishin, garama ki nutsu kisan inda yake miki k'aik'ayi ki sosa, baki k'are akan kishin banza mara amfaniba, ALLAH yaganar damu)* Reefat tamik'e taje tayo fitsari tadawo, drinks ta ďakko musu tazubo cincin afilet ta ajiye musu dan labarin sai anayi ana jik'a makoshi. _(nima bilyn Abdul ina gefe danawa na katsire ina korawa dan inji daďin kwaso muku rahoto *lol*)_ Miss xoxo ta ce, "sis....jamije mana." Iman ta haďiye lemon dake bakinta, taci gaba. Bayan mun shiga ďaki ya zaunar dani bakin gado shima ya zauna kusadani, naďan takure jikina dan bako yaushe nakeso yata6aniba. Hannuna yakamo ya damk'e anasa yamatso kusadani sosai, yana faďin abinda bak'ya son, dan tuni nakula bakison na ra6u jikinki bansan miyasaba?. Na duk'ar dakai k'asa, ya ce, "faďamin kobaki sonane??, na girgiza kai alamar a'a, ya ce, "to minene dalili?. Ahankali nađago kai ina kallonsa, ganin ya tsura min idonsa yasa nayi saurin maida kaina k'asa, na ce, "dama umma ta ce, "mana karmu yarda namiji yarik'e hannunmu, inkuwa ba hakaba zamu samu ciki. Bai san sanda ya tuntsure da dariyaba harda kwanciya akan gado, nikam nasaki baki ina kallonsa, dan ba k'aramin k'yau dariyar taimasaba, inason sa sosai, harma bansan yanda zan musalta ba. Jinayi an huremin idanu, naja wata ajiyar zuciya mai k'arfi, yay murmushinsa mai k'ayatarwa, sannan yagyara zamansa ya ce, "saudat!....yakira sunan dawata irin murya mai cike da kasala. Na ce, "na'am". Ya ce, "aii gwaggo tafaďa miki hakane danki kare mutuncinki ga wanda ba mijinkiba, nikuma mijinkine yafaďa tareda nuna kansa, aii ni yanzu ko rik'e hannun naki nayi kika samu ciki babu matsala, su gwaggoma murna zasuyi da samun jika. K'asa nak'arayi dakai, shikuma yarungumoni sosai zuwa kikinsa yana faďin inasonki dayawa iman, ya ďago ya mannamin summba akumatu mai shiga jiki da 6argo. Nikam sai k'ara sinne kaina nake ajikinsa ina k'ara shak'ar daddaďan k'amshin turarensa. Jin anturo k'ofa ko sallama babu yasa yaďago kai da sauri yana kallonta, nima namik'e zaune sosai inaďan janye jikina daga nasa. Lafiya kuwa?, doctor yafaďa yana kallonta. Ta juya idanunta dasuke manya sosai nazo kiran iman ne mu ďora abinci. Ya ce, "to tana zuwa, ta kalleshi yanda yawaniyi kicin2n da rai, tasan halinsa sarai idan ransa ya6aci dan haka tayi waje tana kun kuni. Na kallesa ya haďe rai sosai kamar bashine yagama dariyaba yanzu, tsaki yayi sanan yamik'e yana faďin kwanannan zanyi maganin 'yar isakar matannan wlhy, nidai bance komaiba, yashige bayi. Nimadai abin mamaki yake bani dukda k'arancin shekaruna, kuma gidanmu bantaso naga kishiyaba, bare nasan yanda ake kishi, saidai nakanji ana faďar kishi kishi. To amma su waďancan ai mijinsu ďaya, nikuma ba mijinmu ďayaba, to kenan wanan kishin banzane takeyi??. Maganar mama naji tana faďin ina iman ďin takene?, namik'e da sauri na nufo falon ina faďin mama ganinan kundawo??. Ta ce, "eh nadawo su nabarasu acan. Na ce, "sannu dazuwa." Ta ce, "yauwa sannunki kema" Makullin 6angarenta naďauka muka tafi, nabuďe muka shiga, ruwa maisanyi naďako nabata tasha, ta ce, "ALLAH yayimiki albarka. Na ce, "amin mama". Doctor yafito daga bayi yaga bana nan, sai zuciyarsa tak'ara tunzura, wato yarinyarnan tafiya tayi wajen girkin tabarni saboda kiranta yafini ko??, yaja dogon tsaki yafice, ďakinsa yanufa yashiga wanka, yafito yay shirinsa cikin k'ananun kaya, yayi k'yau sosai. Yadawo falon yazauna, yana kallo yana shan raken daya siyo. Yaji shirun yayi yawa dan haka yamik'e yanufi 6angaren mama yagani idan tadawo. Da sallama yashigo ganin inama mama matsar k'afa sai yayi turus. Mama ta kallesa a'a auta kadawo?, ince dai lafiya?. Ya ce, "lafiya lau mama nadai dawone kawai, zaman kasuwarnan saisu yaya surutun yayi yawa, har kaina yafara juyawa shiyyasa nagudo. Yazauna yana hararata. Mama ta ce, "mitayi maka kake harararta ne?. Da sauri ya ce, "babu komai mama, yana magana yana sosa gefen wuyansa. Nayi k'asa dakai ina murmushi danya bani dariya sosai. Mama data fahimci inda muka dosa saitace yauwa ďiyata barshi haka ai k'afar tama saki sosai ngd. Nayi murmushi ta reda faďin to mama sannu. Namik'e nafita batareda na kalli doctor ba. 6angaren auntyn nanufa, kai tsaye nanufi kicin dan nasan sunacan da masu aiki. Koda nashigo saita haďe girar sama data k'asa, na ce, "sannunku da aiki, masu aiki kaďai suka amsa amma ita ko kallo ban ishetaba. Nima banbi takantaba dan indai miskilancine gidan ta taras. Haka mukayi aikin muka gama batareda mun kula junaba. 6angaren mama muka kai abinda yadace, har yanzu doctor yana can suna hira da mama, muka gama jere komai, sanan muka fita. Saida mukayi sallar azuhur sanan aka ci abincin, yauma saimu huďu kawai, tunda muka zauna cin abincin doctor yaketa haďe rai, nasan saboda aunty yakeyi dan haka abin bai dameniba. Muna gamawa na nufi 6angarenmu dan naji zufa ta tasomin, gashi arayuwata idan ina cikin al'ada sainatayin k'yan k'yamin kaina, sainayi wanka sau shida arana bai wadaceniba. Babu daďewa saiga doctor yabiyoni har yanzu fuskarsa babu walwala sosai. A bedroom yasameni ina shirin shiga wanka, nayi k'asa da kaina dan ganin ya nufo inda nake, gashi dagani sai guntun tawul, kama tawul ďin yayi kamar zai kwance, da sauri narik'e tawil ďin da hannunsa ina zaro ido ..........yaďan murmusa kaďan iman kincika tsoro wlhy, ahaka wai zaki haifamin yaran danake mafarki? , hannu nasa narufe fuska yayinda shikuma yasamu damar zame tawul ďin daga jikina....... Kai jama'a mutashi muyi sallah, miss xoxo ta harareta kai iman ALLAH kina jamana rai, wlhy kuwa xoxo Reefat tafaďa tana kwa6e fuska, yakamata kiďan k'ara mana nan. Dama muna binki bashi akan sanin wacece Raihan?. Mik'ewa iman tayi tana faďin 'yan duniya kudai wlhy sai gyaran ALLAH, yara baku tafasaba zaku k'one. Raihan kuwa kumanta da batunta ita bakomai bace. Xoxo da Reefat suka tuntsure da dariya suna faďin keda kika tafasa har kika k'one aii saiki nuna mana hanya. Dan wlhy duk kawaice2nki saikin bamu bayanin _firstnight_ , saikuma munsan wacece Raihan?. da sauri iman tashige bayi tana dariya, sumadai aminan nata dariyar suke tuntsurawa sosai................... *To nima bari na k'yak'yata*😂😂😂😂😂😜👌🏻 _lol._ _*((S)).........2017*_ _*luv u oll my fan's*_ _*battery low*_ [8/6, 6:01 PM] mrs bilkisu: *_______________________________* *BAN SAKETA BA!!!* *________________________________* *NA* *BILKEESA IBRAHEEM* _*{bilyn Abdul}*_ *________________________________* https://mrsbilkisa.blogspot.com _sadaukarwa_ *~ya Abdul {city phone's}* *MIYAKAMATA NAYI!??.* _ZAKA IYA MUTUWA YANZU_ _SHIN BA ZAKA JI KUNYAR ALLAH BA??, YA KAI 'DAN ADAM!!, Shin ba zaka ji kunyar ALLAH ba?? Kullum SHI yake baka ci da sha da numfashin da kake shk'a, Amma godiyarka ta tafi zuwa ga waninsa, Sa6onka kuma ya tafi zuwa ga ALLAH mahaliccinka._ _Kana nuna ma mutane kamar cewa kai mutumin kirki ne, alhali akwai Miyagun ayyukanka da kakeyi a 6oye, da kuma Miyagun tunanin dake Qunshe a zuciyarka._ _*Ubangiji* Ya san dasu amma bai ta6a tona maka asiri ba, Kullum rufa maka asirinka yakeyi, amma kai kuma kana Qara butulce masa._ _Kullum Qara turo maka_ _Ni'imominsa yakeyi, amma_ _Maimakon ka gode Mai sai kake_ _ganin kamar hikimarka ce ko kuma wayonka ne suke baka,_ _Yanzu idan kana dauke da Olsa_ _*(Ulcer)* ko Hawan jini ko_ _*Diabetes* (Ciwon Sugar) duk_ _abincin da likita ya hanaka ci,_ _Sai kayi shekaru baka cishi ba,_ _saboda mi??, Saboda kana_ _tsoron_ *MUTUWA!!!.* _Amma Ubangijinka wanda Ya hakicceka Yace maka_ _*- QARYA BABU KYAU.*_ _*- GULMA BABU KYAU.*_ _*- SATA BABU KYAU.*_ _*- SHIRKA BABU KYAU.*_ _*- GIRMAN KAI BABU KAYU.*_ _*- ZINA BABU KYAU.*_ _*- TUNANIN AIKATA FASADI*_ _*KOWANNE IRI MA BABU*_ _*KYAU..*_ ```Yace maka duk wad'annan HARAMUN NE, Kuma zasu kai ka Zuwa ga shiga Wuta, Amma duk da haka gashi nan kana yinsu babu dare babu rana...``` *SHIN GASKATASHI NE BAKAYI BA?? KO KUWA LIKITAN ASIBITI YAFI* *UBANGIJINKA* *FA'DAR GASKIYA NE???* _Ya Allah mun tuba Ka yafe mana... Idan mu halinmu ne muyi sa6o saboda raunin zukatanmu, To Kai kuma halinka ne yin Gafara da Rahama da Afuwa ga bayinka ba tare da hisabi ba, Ya Allah Ka_ _Tsaftace zukatanmu daga_ _dukkan abinda baka so._ _Ka sanyamu cikin bayinka Masu shiryuwa da kuma_ _shiryarwa zuwa gareka, Ba_ _Batattu ba, kuma ba masu_ _batarwa ba_ *ALLAH yasa mu gane* *~page.......13~* ..................iman tacigaba da faďin, koda yazame tawul ďin sainayi saurin buďe idanuna, ganina zir yasa na ranta cikin na kare zan shige bayi, taku ďaya ya damk'oni. Tuni jikina yafara 6ari dan haka nasa masa kuka, sakina yayi yana faďin sorry my iman jekiyi wankanki.......aii kafin yagama faďa nakai cikin bayin. Ya zauna bakin gado yana fidda huci, idanunsa sunyi jajur, yasan iman tabbas yarinyace, amma zata iya ďaukar nauyinsa, saidai yakula yarinyar tanada tsoro sosai, baisan yanda za'ayi ta fahimcesaba, gashi bayason binta da k'arfi, yafison komai ya wakana cikin ilimi da fahimtar juna. Wato da yardarta kenan. Tuni nagama wanka amma nakasa fitowa saboda kunya, ina bayi da tunanin yanda za'ayi na fito sainaji maganar deexerh tana kwala kiran uncle!. Ya ce, "baby shigo ganinan, daďan k'arfi yafaďa yanda zataji. Tashigo da sallama, yatashi zaune yana faďin harkun dawo?, ta zauna kusadashi tana dariya eh uncle, ashe kadawo daga kasuwar?. Nadawo tuni, kinsan banason hayaniya. Tayi dariya akaro nabiyu, wlhy rayuwarka tana burgeni uncle, shiyyasa kullum nake burin nayi koyi dakai, amma bakina baya iya shiru bansan miya saba. ďan murmushi yayi yana kallonta, to kizo nakoya miki. Ta ce, "da gsk uncle." Kai ya jinjina mata yana lumshe idanunsa.......kafin tabashi amsa Raihan tashigo ďakin. Suduka suka amsa, saidai gogan kamar baiyi maraba da zuwan nataba, gefensa itama ta zauna suka sakashi tsakkiya itada deexerh, sai kawai ya haye gadon sosai ya kwantan. Raihan tabishi da kallo dan tasan saboda ita yayi haka, suka haďa ido ya kauda kai, itakuma taja ajiyar zuciya, deexerh ta ta6e baki tana mik'ewa, uncle wai ina my aunty??. Muryarsa aďan ďarare ya ce, "tana bayi wanka take. Mik'ewa tayi tanufo k'ofar bayin tana kwankwasawa, da kiran aunty!!. Nayi gyaran murya dan babu damar magana abayi. Ta ce, "wai wanka kikeyi??. Kaďan na buďe k'ofar nalek'o tunda ta juyawa gadon baya, dan haka bazanga su doctor ba suma bazasu ganniba. Na ce, "dee.... kun dawo?. Kai taďaga mini alamar eh, tabini da kallo wai bazaki fitobane??, zan fito mana amma ďan ďakkomin zani da hijjabi a duriwa. Dariya tayi kai aunty kincika kunya, na ce, "babu komai nidai bani kawai. Babu daďewa takawo min zani da hijjab, lokacin doctor da Raihan sun fice, abin ya6atama deexerh rai sosai, dan haka tana bani zanin tarufa musu baya. Nikam dabansan wainar da ake toyawaba nafito nahau shirina. Adurkushe deexerh ta tarar da Raihan gaban doctor; da alama rok'onsa takeyi kokuma wani abun daban, shikuma yaďan kauda kai gefe fuskarsa babu yabo babu fallasa. Tana ganin deexeh tamik'e, tasamu kujera ta zauna, ďan siririn tsaki deexerh tayi itama tanemi guri ta zauna. Koda nagama shiri saina nemi gado na haye, babu daďewa barci yay gaba dani, ni azatonama sunbar gidan. Sai gab da magriba na farka, nabuďe ido ahankali saina ga doctor tsaye yana shirin masallaci. Yak'araso kusada gadon yana faďin my saudat kin tashi?, na ďaga masa kai ina yunk'urin tashi zaune, da sauri yatadani ya zaunar, ya ce, "kinsha barci ko?. Kai naďaga masa ina lumshe matsakaitan idanuna. Ya summbaci kumatuna yana faďin bari naje masallaci naji suna shirin tada sallah. Ban takashiba dan miskilancin yana kusa. _*bayan kwana uku*_ Bayan kwana uku nadawo normal, nayi wankan tsarki, dukda ban sanar da doctor ba yasani dan yana rik'e da adadin kwanakin danakeyi. Muna zaune nida deexrrh da Raihan muna kallo, dan takan shigo tareda deexerh, saidai bansan dalilintaba tunda har yanzu bansan abinda ke tsakaninta da doctor ba, kuma nakasa tambayar deexerh. Munacikin kallon saina farajin barci, dan haka nazame saman doguwar kujera na kwanta, nabarsu suna kallonsu. Doctor bayanan yafita tun ďazun. Cikin barcina nakejin k'amshin turaren doctor, nasake ware hancina dan ina matuk'ar son turaren, zan iya cemuku awajensa kawai nata6ajin turaren nan, nabuďe idanuna ahankali saboda kusantowar turaren sosai kusada hancina. Ware idanu nayi saboda ganin fuskar doctor kusada tawa, harma munajin saukar numfashin juna, naďan kauda kaina gefe saboda kunyarsu deexerh. Cikin jin kunya na ce, "doctor yaushe jadawo??. Hannunsa yasa yadawo da fuskata inda take da, idanuna naruntse dan bazan iya kallon kwayar idanunsaba. Bakina yasumbata ahankali yafurta my iman inason kunyarnan taki wlhy. Bance komaiba sai mik'ewa danayi dan nagashi bayajin kunyarsu deexerh dake folon. Karaf na haďa ido da Raihan tana kallonmu, ta haďe fuska tamkar zata haďiyi zuciya tamutu, tai k'asa da kai saiga hawaye sharrrr akan kumatunta, da sauri tashare dankar agane, saidai ta makaro dan duk mungani, deexerh ta ta6e baki. Amma fuskar doctor ta nuna alamun gizago. Deexerh ta ce, "sannu da zuwa uncle. Yauwa babyna ya gidan??. Ta ce, "Alhmdllh. Ganin haka itama Raihan ta ce, "sannu dazuwa yaa Isma'il. Itama ya amsata damar yanda ya amsawa deexerh. Dukda bansan matsalartaba tabani tausayi. Najuyo ina kallon doctor danufin tambayarsa mizan kawo masa, saiya saki murmushin basarwa kawai. Na ce, "mikakeso akawo maka?. Yaďan sosa sumar kansa yana satar kallon deexerh da Raihan, sai kawai yamik'e yakama hannuna muka nufi ďakinsa. Hummm wai kunsan miya faru?. Sukace a'a". Damuka shiga saiya hau tambayata wai miye matsalar Raihan??, yabani matuk'ar dariya, saboda kular danayi yana matuk'ar yimini kallon k'aramar yarinya. Sai kawai nayi amfani da damata na ce, "saboda kai take kuka mana. Aďan razane ya ce, "kamarya sabodani?. Nayi murmushi ina kallonsa, na ce, "nima amsar wanan tambayar nakenema, ina gama faďa nayo waje. Bina yayi da kallon mamaki, yakasa koda yunk'urin ďaga yatsa bare ya iya kiran sunana, nikam wallahy maganar tazominne kawai amma bada niyya nafaďaba. Abubuwan motsa baki nahaďo masa, har nadawo bai matsa daga inda nabarsaba, na ajiye tiren hannuna ina murmushi, naje nakamo hannunsa na zaunar abakin gado, nazuba ruwa akofi na đora masa abaki. Yako buďe baki yashanye dan yana buk'atar buk'atar abinda zai jik'a masa mak'oshi yasamu damar haďiyar yalwataccen yawu. Yanasha idonsa akaina, nima kaina mamakin kaina nake da irin wanan abubuwa, kwata2 babu kunya ataredani, ya shanye tas, sanan najanye kofin. Kusada shi na zauna ina faďin lfy kuwa doctor?. Wata wawuyar ajiyar zuciya yaja, yay saurin basarwa dan fuskarsa tana da k'ok'arin 6oye sirri, ya ce, "mamaki maganarki tabani kawai. Wata 'yar dariya nayi na ce, "lah nifa tsokanarka nake, bammasan maganartawa tayi kama da abin mamakiba aii. Nafaďane kawai dannaji tabakinka. Ya rausayar da kai gefe yana bina dawani shu'umin kallo, tabbas yasan nacanja salone, amma na burgeshi, dan hakan ya nuna masa bayyanar wayona, shima saiya basar kawai yay dariya. Amma iman kin iya kulli wlhy, harkinsa hankalina tashi, dan banason abinda zai 6ata mini ranki ko kaďan. Na ce, "ko?" Yajinjina mini kai alamar eh". Yayi k'yau nafaďa ina k'ok'arin mik'ewa, da sauri yajowoni saman cinyarsa, yamatseni akan faffaďan k'irjinsa daketa tashin k'amshi. Cikin kunnena ya ce, "kishi ko iman??, nasaki sassanyar dariya wadda yakejinta harcikin kwakwalwarsa, na ce, "a'a wlhy, tsam ya rungymeni a k'irjinsa yana fidda numfashi a sark'e. Yanda yake fidda numfashin sai tsoro yakamani, na ďago daniyyar tambayarsa lafiya saiya haďe bakinsa da nawa, naga takaina nafaďa azuciyata dan nasan saina sha murza bata wasaba. Aiko nashata dan yau har inda hannunsa baya kaiwa saida yakai, tuni tsoro da rawar jiki sun shigeni, nafara tsunguninsa da k'ok'arain zame jikina amma nakasa. Saida yayi mai isarsa sannan ya sakeni yana murmushi da fidda hakki, idanunsa sunyi matuk'ar ja. Da sauri na nufi k'ofa zan fice, ahankali ya ce, "plz karki fita su Raihan suna falon, zasu ganki awani iri. Cak natsaya amma ban juyoba saidai nabi jikina da kallo, gsky yafaďa dankuwa duk ya yamitsemin jikina da kayana, maimakon nadawo saina jingina kaina da k'ofa. Azatonsa kuka nake dan haka cikin nauyin jiki yataso gareni, tabaya yarungumeni yana magana ahnkali, sorry iman kibar kuka, badan na6ata miki raiba nakemiki hakan, saidai tsananin k'aunarki danakeyi, amma indai bak'yason hakan danakemiki nayi miki alk'awarin zan daina har saikin buk'ata da kanki. Da sauri najuyo dan muryarsa kamar yana kuka, ganin idona k'amas babu akamar kuka yasashi zaro idani waje. Sai kuma ya rungumeni, ya ce, "tsokana ko iman?, babu komai zan ramane. Nayi shiru dan nakasa bashi amsa... Bayan kamar minti talatin mun daidaita sai muka fito falon, amma wayam babu deexerh babu Raihan. Sainaga kamar doctor yaji daďin hakan. Amma ni sainace doctor bari nakira su Raihan su dawo ko?, kaga ka koresu. Da sauri ya ce, "A'a barsu kawai, aii hakan dasukayi shine daidai. Shuri nayi ina kallonsa dan ni aganina babu k'yau. Kallo ďaya yamin ya kauda kai, dan yakula zancen bai shigeniba. Babu yanda zanyi dole nazauna na barsu. Har zuwa dare yahanani zuwa ko ina, hakan ba k'aramin haushi yabaniba, nayima deexerh test akan sudawo. Amma saita turomin...👇🏻 _*hhhhhhh haba auntyna, babu wani dawowa dazamuyi, munbama uncle filine ya huta, dan haka saida safe, asamo mana baby mudai dan ALLAH😜.*_ Na ce, "ALLAH yashiryaki deexerh, zamu gauraya da safe aii. Har isha'i ban je ko inaba, saida yatafi masallaci sanan naje nayoma mama saida safe, natarar deexerh da raihan suna 6angaren aunty, dan haka najuyo danba zuwa wajen nakeba da daddare saidai idan takama dole. Ana idar da isha'i doctor yadawo, hannunsa ďauke da leda, bayan nayimasa sannu yabani umarnin juye abinda ke ledar. Nasamo filet najuye gasassun 'yan shila lafiyayu da madara mai sanyi. Gabansa natura duka yabini da kallo yana faďin kefa??, naďan marairaice murya na ce, "nak'oshi". Dariya yayi ya ce, "ko?". Na ďaga kai". K'asa yasauka yana cigaba da dariyarsa wadda bansan inda ta dosaba dan bansan *Sirrin zuciyarsa ba* sabon littafina mai zuwa insha ALLAHU, *(SIRRIN ZUCIYA)*. Baikuma cemin komaiba yajawoni jikinsa, yafara danna mini naman abaki, dole nakar6a inaci, yana koramin da madara mai sanyi. Bayan munci munsha yasa tishu yagoge min baki, daganan yamik'e zuwa ďakinsa, nima na gyara wajen nayi nawa ďakin. Na kalli agogo ko goma batayiba amma naga yau doctor kwanciyar wuri yake shirinyi. Nidama banida matsala da wuri nake barci. Nayi shirin barci tsaf na gyara kaina, nahau gado zan kwanta zuciyata fes babu wata damuwa. Doctor yaturo k'ofar da sallama yashigo, na amsa ina kallonsa dan ganinsa da jallabiya sa6anin kayan barci. Saida ya shimfiďa sallaya sanan ya ce, "taso kiyi alwala. Kaina tsaye na ce, "nafayi sallar isha'i. Eh nasani aii, zamuyi nafilane. Na ce, "yanzu nayi alwalar kwanciya ma. "Okey to taso". Tashi nayi na ďora zani akan kayan barcina, nasaka hijjabin sallata, shi yajamana sallah raka'a biyu, bayan munyi sallama ya dafa kaina tareda karanta addu'a kamar yanda addininmu ya koyar damu, daganan kuma yacigaba da kwararo mana addu'oi na musamman, tun yanayi har muryarsa tafara zuga alamar zuwan kuka, dan yanama iyayensa addu'ane, tonimadai tayasa nafarayi dan yabani tausayi. Yashafa nima nashafa sanan yajuyo yana kallona fuskarsa ďauke da murmushi. Nayi k'asa dakai dan kallonnasa yana bani kunya. Tambayoyi yaymin afannonin addinina. Alhmdllh nabashi amsa yanda yatambaya saboda ina zuwa islamiyya. Nakula ba k'aramin daďi yajiba. Reefat ta ce, "oh ke iman ashe kinsan turaka..........iman tabuge mata baki kafin ta k'arasa suka tuntsure da dariya. Miss xoxo ta ce, "ai gskyar Reefat wlhy, ashemu nan duk kallon kitse kike mana. Tashi tayi tana dariya da faďin kudai kuka sani.................. _*((S))........2017*_ _*luv u oll my fan's*_ _*Battery low*_ [8/6, 6:01 PM] mrs bilkisu: *________________________________* *BAN SAKETA BA!!!* *________________________________* *NA* *BILKEESA IBRAHEEM* _*{bilyn Abdul}*_ *________________________________* https://mrsbilkisa.blogspot.com _sadaukarwa_ *~ya Abdul {city phone's}* *MIYAKAMATA NAYI??.* _da mutuwa tana duban girma dabata ďauki tsofaffiba._ _da mutuwa tana duban milki dabata ďauki masu mulkiba._ _da mutuwa tana duban tsantseni dabata ďauki malamaiba._ _da mutuwa tana duban tausayi, dabata ďauki talaka da yaraba._ _da mutuwa tana duban jarumta, dabata ďauki matasa ba._ _da mutuwa tana duban addini, dabata ďauki musulmaiba._ _da mutuwa tana duban jin daďi, dabata ďauki turawaba._ _da mutuwa tana duban imani, dabata ďauki kafiraiba._ _da mutuwa tana duban kunya, da bata ďauki 'ya'ya, agaba iyayensuba, maza agaban matansuba, mata agaban mazansuba, iyaye agaban 'ya'yansuba._ _da!. da!!. da!!!!..........dayawa, sabodasu da mutuwa tabar kowa aduniyarsa._ _amma kash, itama tana cika umarnin *ubangijinta ne*, tunda mala'ikan mutuwa ya iya ďaukar ruhin mafificin halitta,_ _ma'abocin_ milki, imani, tausayi, talaka, _masoyi, mafifici, domin_ _addinima shine mai koyar da_ _muminai, dukiya,_ _(domin annbinmu baya cin sadaka,_ _kunga kuwa wadataccene,_ _danba tarin dukiya bace_ _wadata, a'a wadatar zuci,_ _dukmai wadatar zuci yawuce akirasa talaka), amma wanan bai hana yakusanci ubangijiba._ ```To yakamata, nida kai da ke da su da ku damu gaba ďaya, muringa tunawa akwai mutuwa maizuwa maka akowane irin hali, akowane kuma irin lokaci.``` ~Idan ko hakane yakamata kasancewarka musulmi mai imani, yaringa tunawa da zuwan mutuwa aduk halin daya tsinci kansa, walau alkairi ko sharri, inaganin idan muna tunawa da mutuwa zamu ringa rage aikata aikin sa6o.~ _Ka gwada na gwada ki gwada mu gwada mugani kozamu dace._ *ALLAH yasa mugane* ~*page........14*~ .................bayan mun kammala na haďa sallaya ďin na linke da hijjabina, doctor kuma yazauna bakin gado yana kallona da mamaki, dan ganin hankalina kwance babu wata fargaba. Na kammala linkewa na hawo gadon na kwanta acan nesa dashi kamar yanda na saba. Shima saiya gyara filo ya kwanta a k'arshen gadon. Shiru zuwa wani lokaci, ni ina addu'ar barci, shi yana tunanin ta ina zai fara, nagama shafa addu'ata tareda gyara kwanciya ina faďin saida safe doctor, mai makon ya amsa mini kamar yanda yasaba saiya jehomini tambaya. Iman! na tambayeki wani abu?. Naďan waigo da fuskata na ce, "eh tambayeni". Yaďanja numfashi yana matsowa tsakkiyar gadon, ya ce, "miyasa ni baki shafa min addu'arki??. Nayi shiru ian tunanin amsar dazan bashi. Ya ce, "kinyi barci?." A'a nafaďa". Okey ina saurarenki!. Na ce, "babu komai, amma aii ina tofawa ko ina na kusurwar ďakinnan, hakane yafaďa a sark'e. Tokuma miyasa bakison kwanciya kusada ni?. A wanan karon saida na kalleshi muka haďa ido kasancewar akwai wadatar hasken fitila, na ďan kauda idona daga kansa, na ce, "saboda kai namijine, nikuma mace. Murmushi yayi, saboda yaga amfara zuwa wajen, ya gyara kwanciya yana faďin amma aini mijinkine ko?. Na ce, "eh." Ya ce, "masha ALLAHU." To zoki shafa min addu'ar. Dukda ina jin kunyarsa hakan bai hanani amsawaba, saboda yauda kullum, sabo da soyayyarsa sun k'ara tasiri acikin zuciyata fiye da tunanin mai karatu. Koda nazo daf dashi sainace to kashe fitilar. 'Yar dariya yayi, saboda mi?, sai ankashe fitila?. Na ce, "inajin kunya. To sarkin kunya nakshe azo amin, yafaďa yana kashe fitilar gefen gadon. Na matso kusada shi sosai, dukda yakashe fitilar sai nake gani tamkar yana kallona, dan haka na rintse idanuna sannan nakai hannuna ajikinsa ina shafa masa addu'ar. Wadda shikuma yakejinta tamkar tafiyar tsutsa nake masa, ban ankaraba sainajini kwance a faffaďan k'irjinsa..........dan ALLAH basaina faďaba abarshi haka, iman tafaďa tana kallon fuskar Reefat da miss xoxo. Tab!!, suka faďa atare, wlhy babu ďaga k'afa sai an faďa mana komai. Iman tashiga lalla6arsu amma sukace basu yardaba saita faďa, basa son kwange. Babu yanda zatayi dole taci gaba, tunda alk'awari ta ďauka musu. ........'yar rungumenin daya sabayi yasa banji komai arainaba, bankuma kawo komaiba, saima k'ara nutsa kaina danake cikin k'irjinsa ina shak'ar daddaďan k'amshinsa, turarurrukan doctor sun kama jikinsa sosai wanan yasa duk motsin dayayi sai k'amshinsa ya baza waje. Nashagala da shak'ar k'amshin sai naji hannunsa wata tashar daban, naďago da zummar kwace kaina amma ina saiya k'ara matseni gam, cikin muryar mai fara shirin kuka na ce, "doctor pls kasakeni, muryarsa naji cikin kunnina yana faďin nutsu my saudat, zan ďansha k'amshinkine. Yanda yake maganar hannunsa kuma nacigaba da shafa inda tunanina baita6a kaiwa doctor zai ta6aminba, sai jikina yakama rawa, na fara kuka, bakina ya laluba ya haďe danasa. Tuni labari ya sauya salon tafiya, doctor yanata k'ok'arin kaiwa inda yake kwaďayin zuwa, nikam tuni kuka yaci k'arfina, amma doctor yakasa control ďin kansa domin lallashina. Hummm! aranardai doctor bai barniba saida ya maidani cikakkiyar mace, saidai nasha matuk'ar wahala, nayi kuka harna rasa hawaye, har sumar wucin gadi nayi. Shima kansa yasha bak'ar wahala, saidai yauďin yanajinta rana tadaban agareshi, har yarasa irin addu'ar dazaiyimin awanan lokacin, yana gefe yana maida numfashi, yayinda nikam naketa kuka mara sauti, saidai hawaye daketa zurara a kumatuna. Bayan kamar minti 15 yaja jiki kusadani, sosai ya ringumeni, nikan atunani zai k'arane dan haka na ruďe dabashi hak'u cikin magiya da dashashshiyar muryata. Yanda narikice masa saina bashi tausayi, ya janye jikinsa yana faďin sorry iman babu abinda zan sake miki, nima ina tausayinki. Mik'ewa yayi ya kunna fitilar ďakin, wata leda yabuďe yafiddo da magunguna kala2, wannan ya tabbatarmin da dama yashirya zuwan wanan rana kenan. Dakansa yayimin wanka ya sakani aruwan ďumi, har sanan ban daina kukakaba, shima yanata aikin lallashina, bayan an kammala wankan yasani nayi wankan tsarki sanan ya naďoni kamar wata jinjira yadire saman kujera, kasancewar gadon duk ya6aci da jini, saida ya cire zanin gadon ya juya katifar, yasake shimfiďa wani sananan ya maidani saman gado. Madara yabani nasha kađan, dan bana sha'awar komai asanan, bai takuraniba ya bani magani nasha, yamatseni yamin allura. Yasha raki kafin barci ya saceni. Ya tsuramin ido tareda sauke wata nannauyar ajiyar zuciya, fuskarsa cike da murmushi mai k'ayatarwa, acan k'asan zuciyarsa kuwa sai kwararamin addu'oi yake na musamman. Wanda ballagazar mace bata samun irinta.😜 Jiyake kamar shi kaďai ALLAH yayma wanan gatan na samun nutsatstsiyar mace, nagartacciya, kamila, ahankali yake shafa kaina yanata murmushi abinsa, aii dolene yayta godiyar ubangiji shikam daganan har wayewar gari, bargo yaja ya k'ara lullu6eni sosai saboda sanyin fanka, nikam bammasan yanayiba, inata barcina. yamik'e shima zuwa bayi domin gyara jikinsa. Yana fitowa yafara jera nafilfili da mik'a godiyarsa ga sarkin sarakuna, shugaban talikai, har k'arfe uku sanan yahawo gadon tareda rungumeni tamkar za'a kwace masani, cikin nishaďi barci yay awon gaba dashi. Da asuba yarigani tashi, dan haka bai tadaniba yay alwala suka tafi masallaci shida yayansa da marwan. Shidai yayansa sai kallonsa yake cikin mamaki, dan ganin yanda gabaďa ayyukansa ke nuna kasancewarsa cikin farinciki, saboda marwan kawai yakasa tambayarsa harsuka idar da sallah suka fito. Koda suka shigo gida sai marwan yawuce 6angaren mama, to anan yayansa yasamu damar tambayarsa ko lafiya?. Yayi murmushi yana sosa tsakkiyar kansa, babu komai yayana mikaganine?. Yaya yaďan tsura masa ido yana murnushi, ban yardaba auta akwai labari atareda kai gsky, gabaďaya ayyukanka suna nuna alamomin farinciki atareda kai. Nanma murmushi yayi yana ďan duk'ar da kai, yayansa yay dariya shikenan tunda ba'aso nasani, k'iladai k'anwatace tajagoranci farincikin, ALLAH yak'ara baku zaman lafiya. "Amin doctor yafaďa yana 'yar dariya cike da kunya. Kafaďarsa yayansa yaďan buga yana dariya shima, daganan kowa yanufi 6angarensa. Har zuwa sanan ban tashiba inata barcina, doctor yazauna gefen gadon saitin fuskata yana murmushi, ahankali ya janye bargon danake k'udundune aciki, ya rankwafo ya sumbaci kumatuna, saikuma yakoma shafa kaina ahankali. Na buďe idanuna dasuka ďan kumbura saboda kuka saikuma na maida na lumshe, cikin muryarsa mai daďi ya ce, my saudat adaure atashi ko?, yafaďa yanaďanjan hancina. Nakuma buďe jajayen idona na waresu akansa, kallo ďaya namasa na rufe fuskata da hannayena, yayi murmushi mai sauti tareda yaye bargon gaba ďaya, har yanzu idanuna arufe suke, dan haka yaďaukeni gaba ďaya zuwa bayi. Da sauri nabuďe idanuna danjin ansakani aruwan ďumi, narik'eshi da sauri da zummar tashi, amma saiya yimini k'yak'yk'yawan rik'o. Ashagwa6e nafara faďin ruwan da zafi doctor!. Cikin sigar lallashi yake ya ce, "sorry my iman, kinga idan baki shiga ruwan zafinnanba sosai gurin zai ringa miki ciwo, kidaure kinji jarumata, hakadai yaytamin kalamai masu daďi har ruwan ya huce. Yamin wanka, na ďauro alwala muka fito. Yaďakkomin zanin sallata da hijjab, yashinfiďamin sallaya nayi sallah, ina idarwa na kwanta akan sallayar na hau barci, shikuma yana bayi yana ďauraye zanin gadommu daya jik'a jiya da daddare. Cak ya ďaukeni yamaida saman gado, yarungumeni muka koma barci. _*9:30 am*_ Sai k'arfe tara muka farka, konace bugun k'ofa ya tadamu, doctor yatashi da k'yar yaje yabuďe k'ofar, aunty sadiya ce, bata jira wani abuba tadanno kai cikin falon, yabita da kallo tareda faďin lafiya kuwa?, wani kallo tasakar masa mai tattare da abubuwa masu tarin yawa, ya ďan kauda kai daga kallonta. Ta ce, "kalli agogo isma'il k'arfe tara da rabi baku tashiba kaida matarka, kunbarmu munata jiranku ayi break. ďan k'aramin tsaki yaja tareda nufo ďakina, saida yaje bakin k'ofa sanan ya ce, "kije muna zuwa, baijira amsartaba yashigo ďakina ya murza key. Jitayi kamar yadaka mata kulki akai, tacije le6e tana ballama ďakin harara sanan tafice tana k'unk'uni. Shikam yak'araso gaban gadon yatadani, dak'yar na iya tashi ina kare fuska nashige bayi, yakula kamar tafiyata taďan canja, dan haka yabiyoni yana faďin nak'ara shiga ruwan zafi, to na amsa masa akunyace. Shima ďakinsa yanufa domin yin wanka. Cikin 'yan mintuna muka shirya muduka, ina k'ok'arin fitowa yana k'ok'arin shigowa mukayi karo. Ya rungumoni da sauri yana faďin sorry dan naďan bige kaina ajikinsa, na lumshe idanuna saboda k'amshin turarensa dana shak'a. Ya ce, "harkin shirya?, kai kawai naďaga masa ina ďan murmushi, na ce, "ina kwana?, lfy lau tawan, yajikinki??, ahankali nafurta lafiyata k'alau nikam, ya ce, "ko?. Naďaga kai batarda nayi maganaba, shima 'yar dariya yayi yakama hannuna muka fice zuwa 6angaren mama. Da sallama muka shiga, kowa ya hallara mukaďai ake jira, muka gaida mama da yaya, na gaida aunty, su deexerh ma muka gaisa bayan sun gaida uncle ďinsu, na kalli kujerar danake zama yau Raihan ta zauna. Deexerh tasan wani k'ulline kawai, dan haka tamik'e akan tata takoma kusada aunty inda yakamata Raihan ta zauna, dama kujerarta kusada doctor take, nida ita muke sakashi tsakkiya, koda tatashi sai muka zauna, doctor yazauna inada deexerh ta tashi, nikuma nazauna kujerar dayake zama. Muka fara break, babu abinda kakeji saik'arar cokali da filet, mamadai sai kallona take, dan takula banida walwala ga idanuna sunďan kumbura da kuma ja. Nidai akunyace nakecin abincin dan gani nake kamar kowa yasan halin danake ciki, munhaďa ido da aunty yafi ak'irga tana hararata, nikam ko kallo bata isheniba wlhy, dan inada uzuri mai yawa agabana. Bayan mun kammala mama takasa hakuri ta ce, "iman kobakida lafiyane??. Cikin rawar baki nabuďe baki zanyi magana, idanuna kuma akan doctor, shima kallona yake, ganin kamar zan 6aro masa aiki, yay saurin cewa mama kantane yake ciwo tunjiya da daddare. Mama ta ce, "ayya sannu kinji ďiyata, auta tasha magani dai ko??, da sauri ya ce, "eh mama tasha, yanzuma idan munje zata k'ara sha. Yayansa dai dariya kawai yayi, dan tuni ya harbo jirgin k'anin nasa, amma dukda haka saida yaymin sanu, da kuma nuna tausayinsa akaina, hakama aunty ta gane komai dan haka adak'ile tamin sannu, Raihan ma dai dan dole ta ce, "sannu. Marwan kuwa da deexerh sun nuna tausayinsu sosai, marwan harda faďin aunty bari naje nasamo miki kayan jinya, gasassar kaza kikeso ko mi??, gaba ďaya akasa dariya afalon amma banda aunty, doctor ya ce, "lalai my son yau momy tazama abokiyar wasa kenan?. Nandai mukaita dariyarmu, daga baya doctor yajani muka koma 6angarenmu, yakuma bani magani nasha. Tsawon kwana uku doctor yana jinyata da riritani, aranar kuma yake shirin tafiya washe gari, jinake kamar karya tafi, gashi inatajin faďuwar gaba, harma na sanar dashi, ya ce, "nayita addu'a insha ALLAHU babu komai sai alkairi. Shawararsa nabi nayita addu'a azuciyata, da daddare koda muka kwanta yaso raya sunna, amma saiyaji jikina da zazza6i dan haka ya k'yaleni yabani magani nasha muka kwanta. _"sosai iman take kuka, wanda yabama su xoxo mamaki, hardai suka kasa hak'uri suka shiga tambayarta dalili, bata basu amsaba saida tayi kuka sosai, konace saida taga k'awayen nata suma sun fara, (kai jama'a wanan k'awance yana burgeni, dan cike yake daso da k'yaunar juna), ta tasagaita da kuka tareda share hawayenta"._ Ta ce, "abinda yasani kuka, shine tunowa da ranar cin amana, ranar data zamemini barazana arayuwata, har yanzu nakasa mantawa da ita. Bayan doctor yatadani yatafi masallaci hakanan na tashi jiki babu kwari, nayi sallah, kasancewar nasan tafiyar wuri yakeyi yasa ban koma barciba, sainaje na haďa masa shayi, nasoya kwai kawai dan banaso yatafi baici komaiba. Yana dawowa yatadda ina kicin sai kawai yaje ďakinsa yay wanka, yafito yashirya cikin kakin sojoji, kayan suna masa matuk'ar k'yau, yabaza turarensa na kullum, sanda yafito harna jera masa komai afalon. Cikin tsokana ya zauna yana faďin tawan kinaji dani wlhy, yanzunan har an haďamin breakfast, dariya kawai nayi na ce, "aika isane, ya ce, "ko?". Na jinjina kai ina murmushi, to nagode yafaďa shima yana shan shayi, saida yagama tsaf, sanan yashiga yimin nasiha mai ratsa jiki, daga nan yaje 6angaren mama da yayansa, bai daďe sosaiba tunda tun dare sukayi sallama, saiya dawo, duk abinda nake buk'ata tun adaren jiya yabani shi, dan haka koda yadawo saiya rungumeni yana faďin dama mama da yaya zasu yarda dasai muyi tafiyarmu musha amarci acan iman. Amma nasan bazasu yardaba, insha ALLHU nanda sati biyu zan dawo kinji. Nashare kwallar data cikamin ido na ce, "to ALLAH ya tsare minkai, yabada sa'a, yaka'ara ďaukakaka mijini. Amin yafaďa yana k'ara matseni ajikinsa, daga nana yahaďe bakina danasa, ayaudai nabada gudummawa, dan sosai nataimaka masa yasamu farinciki wajen sumbata, wadda inada tabbacin yasamu ďin kuma. Saida yayansa yakirashi awaya sanan yazare bakinsa daga nawa akasalace, baiyi maganaba ya ďauki jakarsa yasa akafaďa yana ďagamin hannu, nikam nai k'asa dakai saboda hawayen dasuka cikamin ido. Banyimasa rakiyaba gudun karnaje gaban mutane ina kuka, saikawai nakoma đakina nakwanta ina kukana. _*11:56 am*_ Har k'arfe shaďaya dawani abu ban tashiba, nayi kuka harna gaji, nikaina bansan dalilin kukan nawaba, saboda bayau doctor yata6a tafiya yabarniba, amma nafijin zafin tayau da kewarsa, zuwa shabiyu saura na hak'ura natashi domin gyara ďaki, ina cikin kakka6e gado naga takarda tafaďo. Harna ajeta saman durowar gado dazaton doctor ne ya manta da ita, saikuma zuciyata takasa nutsuwa na ďauka nabuďe. _"Inna lillahi wa'inna ilaihirra raji'un"_, kawai nake ammbata, jikina sai rawa yake. Adaidai wanan lokacin deexerh tashigo ďakin............... _*kuyi hak'uri dajina shiru, wlhy abubuwane suka min yawa, amma insha ALLAHU bayan biki zaku cigaba da samun book ďin yanda yakamata masoyana, ina alfahari daku sosai*._ *luv u oll* _*((S))..........2017*_ _*luv u oll my fan's*_ _*Battery low*_ [8/6, 6:01 PM] mrs bilkisu: *________________________________* *BAN SAKETA BA!* *________________________________* *NA* *BILKEESA IBRAHEEM* _*{bilyn Abdul}*_ *________________________________* https://mrsbilkisa.blogspot.com _sadaukarwa_ *ya Abdul {city phone's}* *MIYAKAMATA NAYI?.* _'yar uwa! ďan uwa!, yakamata dani dake da kai mutaru mu mutunta juna, k'yautata mu'amularku da jama'a 'yan uwanku, walau musulmai ko ba musulmaiba_ _karku zama masu girman kai, saboda wata ďaukaka ta duniya, babu wanda yafi wani gurin ALLAH sai wanda ya k'yautata ibadarsa, to ashe nidake da kai duk bamuda tabbas, domin duk k'ok'arin ibadarka wani yafika, ballema yanzu damuka lalace, muka shagala aduniya da kayan cikinta._ _saika samu mutum yahaďa shekara ďaya bai karanta *alkur'ani* ba, baya sallah akan lokaci, baya neman ilimi akan addininsa, baya tunawa da *ubangijinsa* sai masifa ta rikesa sanan ya ce, "ALLAH ne ya ďora masa, humm kaji ďan adam sarkin butulci da izgilanci, duk sanda alkairi yasamesa saiya ďauka wayonsa da iyawarsace tabasa, wanan kuskurene da jahilci._ _mudaure murunga neman _ilimi akan addini, bawai aboko_ kawaiba, _saikaga mutim yanata_ _fafa shi yanada digiri ko_ _difloma_ _ko yana karatu a jami'a kaza, amma_ _wlhy idan zaka tsaresa bazai iya_ _kawo maka alwala cikakkiyaba,_ _bare azo ga sallar kanta, amma_ _turanci da iya salo abakinsa ko_ _mista k'yarank'yan yashafa_ _masa lafiya, larabcikan sai ace_ _aiba yarena bane._ _to hajiyata alhajina shi turanci yarenkine?, hasalima turancin namak'iyankine, afannin addini al'ada jinsi, dan bature bazai ta6a k'aunar musulmiba kuma bak'in mutum, larabci kam abin al'faharinkine tunda koba komai *Annabinmu* yafito daga wanan tsatsonne._ _Inaga lokaci yayi dazaki gane ka gane na gane cewa da mutunci ake gano mutunci, da ilimi ake gano gyara, to *miya kamata nayi?* na nemi ilimi na addini bawai boko kawaiba._ *ALLAH yasa muga ne.* *~page.......15~* ..................da sauri deexerh ta rik'eni nafaďo hannunta dan tuni numfashina ya tsaya, k'arar da deexerh ta kwallace ta jawo hankalin jama'ar gidan harda yaya dadyn su deexerh. Da gudu suka iso 6angarenmu suna tambayar lafiya??, ganina akwance yabasu tabbacin nice babu lafiya ba deexerh ba, aunty ce tafara cewa akira doctor, amma yaya yahana, wani abokinsa aka kira, kafin ya iso yaya yazare takardar daya gani ahannuna, tuni zufa ta wanke masa dukkan sassan jikinsa, sai k'ara maimaita karanta takardar yake kamar wanda akabama hadda. Ya maimaitata yafi ak'irga, tuni kuwa ya haddace komai dake cikin takardar, mama tana lura da halin dayake ciki, zuwan doctor ne yahanata tambayarsa. Dr Auwal yadubani tareda mak'alamin k'arin ruwa, ya ce, "insha ALLAHU zuwa anjima zan tashi normal, yanzuma wani abune ya firgitani na suma, amma na farfaďo. Godiya sukai masa sanan yatafi. Dama tuni yaya yabar wajen, yana 6angaren mama, acan mama tasamesa zaune akujera kamar gunki, idonsa cike da kwallah, zuwan mama yasa yatashi sosai, yasa gefen rigarsa ya share kwallar data gangaro masa kaďan agefen ido. Jiki asanyaye mama ta zauna dan tabbas tasan ba lafiyaba, yaya yanada k'ok'arin 6oye damuwa komai tsananinta, amma yanzu hakan ya gagara, cikin sark'ewar murya mama ta ce, "Mansur miya faru ne?. Yaya yaja ajiyar zuciya, muryarsa naďan rawa ya ce, "mama Isma'il ya saki iman!!. Cikin wani irin yanayi mama take kallonsa, ta ce, "ban ganeba Mansur mikakeson faďamini?. Takardar hannunsa yamik'a mata, ta kar6a takaranta..... *ni Isma'il Muh'd basheer!. Nasaki matata saudat sulaiman saki uku!!. Idan tasamu miji tayi aure.* Tuni gumi ya wanke jikin mama, bata buk'atar k'arin bayani danhaka tayi tagumi kamar yanda yaya yayi. Yayane yay k'arfin halin faďin mama amma yaronnan ya cucemu, yanzu dan ALLAH dawane ido zamu kalli iyayen yarinyarnan?, ni abindama yake bani mamaki shine miya haďasu dahar zai mata saki har uku?, miya hau kan yaronnan haka?, kuma wlhy mama rubutunsane barema ya musa mana. Mama taja ajiyar zuciya toni Mansur ai komaima ya kwace mini, bansan yanda zan kira wanan abinba kuma. Haka mama da yaya sukaita tattaunawa, kuma wani abun mamaki sunkira wayar doctor arufe, mama ta ce, "tunda yasan miya aikata ai dole yakashe waya, kabarsa kawai. Nikam ina ďaki ina barci, aunty da deexerh da Raihan suna 6angarena, saidai basusan abinda yake faruwaba, dan deexerh ma bata karanta takardarba tunda tana zuwa ina suma. Haka akaita tafiya har zuwa yamma dana farka, mama dakanta ta taimaka mini nayi wanka, aka bani abinci naci kaďan har zuwa sanan kuka nake rurus. *bayan kwana uku* Yau tsawon kwana uku kenan angaza samun number doctor kwata2, nikuma namatsa zanje gida, dan yakama iyayena su san halin da'ake ciki, mama da yaya basaso natafi, hakama deexerh da marwan, amma yaza'ayi da k'addarar ALLAH, ganin namatsa yasa mama da yaya suka kaini har gida. Bak'aramin ruďani gwaggo tashigaba itada Abbah dajin abinda yafaru, dan su yaya basu 6oye musu komaiba, suka ďora dabasu hak'uri. Abbah ya ce, "babu komai haka ALLAH ya k'addara aii, bayan ďan tattaunawa dabawa juna baki su yaya suka tafi aka barni agida. Tunda nadawo gida banida wata walwala, kulum cikin kuka nake, ga rashin lafiya data tasoni gaba, dandanan nayi bak'i na rame kamar baniba, lokacin da labari yakai kunanen aunty salma da ya majeed ransu ya 6aci matuk'a, ya majeed ya ce, "bazai k'yaleba saiya ďauki mataki akan doctor, da k'yar abbah da gwaggo suka shawo kansa ya hak'ura. Ganin yanda na k'untata kaina agidan yasa ya majeed rok'on abbah yabari nakoma wajensu k'ila zanfi samun sakewa, abbah baiyi musuba dan dama farin cikina yakeso, aranar muka tattara muka koma. Acanma haka nayita rashin lafiya wadda tasa dole suka kaini asibiti, tofa wata sabuwa, bayan gwaje2 da likita yayi ya tabbatar mana inada ciki na sati uku, tun agurin nasa kuka sai anzubar dashi, amma ya majeed ya hana. Ranar nayi kuka harna godema ubangijina, duk wanda yaganni saiya tausaya mini. Muna dawowa gida ya majeed yasanarma su abba halin da'ake ciki, aranar kuma aka sanarma gidansu doctor, mama da yaya sunyi matuk'ar murna da wanan abin farinciki, dan cikin zai zama sanadin cigaban zumincin mu. Har tsawon wata ďaya babu labarin doctor kota waya bare kuma ayi maganar dawowa. Nikam inanan a6oye inata k'ok'arin zubar da ciki, duk abinda naji ance yana zubar da ciki saina sha a6oye, amma abanza wai man kaza, dan ciki ko gezau, saidai nasha azabar ciwon cikina. Ahaka aka akai wata biyu da sati ďaya. Awata ranar alhamis doctor yazo kano, saidai kuma yatarar da sabon tashin hankali, dan kowa ya ďauke masa wuta agidansu. Kowa ya tambaya iman sai suyi masa banza harsu marwan da deexerh. Hankanlinsa yatashi matuk'a, inda yaga sunk'i bashi wata amsa ta gamsarwa sai kawai ya tsare deexerh da marwan da bulala. Tsoro yakamasu sosai dan ganin yanda yaburkice musu ďinnan zasu iya shan duka abanza, aiko suka sanar dashi komai, atake jikinsa yay sanyi, yanufi wajen mama hankali tashe. Agabanta yashiga rantsuwar wlhy *BAN SAKETA BA!* mama, na rantse da ALLAH k'arya takemini. Mama tayi masa banza, wuni guda yana magiya da rok'o amma kowa yak'i saurarensa, dayaga nan babu ci saiya nufi gidanmu, to gara nan abbah yayi masa nasiha da nuna masa muhimmancin yarda da k'addara. Shidai doctor bashida wata magana sai *ban saketa ba*, tun suna kallon abun amatsayin wasa harya fara zarta tunaninsu, dan doctor neman zare musu yakeyi, awani daren litinin sai a asibiti ya kwana. Wasa2 dai al'amira sun fara tsauri, doctor baisan waye akansaba, kuma indai idonsa biyu bashida magana saita *ban saketa ba*, wannan yasa hankalinsu yayansa yafara tashi suka fara tausayinsa kuma, dan abin yafara wuce makiďi da rawa. Ahaka cikina yashiga wata biyar, nima kaina nazama mara lafiyar, kulum daga tunani sai kuka, duk sanda na kalli cikina sainayi kuka, har banason tuna inada ciki, duk halin da doctor yake ciki labari yana zuwa mini, dansu aunty salma suna zuwa ganinsa hakama su gwaggo. Jikin doctor yay tsanani dole aka maidashi k'asar indiya, dan ciwon zuciya yana neman aikashi lahira, kowa yana tausaya masa. Ban ta6a zuwa ganinsaba saidai kusan tare muke jinyar dan kullum zuciyata tana damuwa da halin dayake ciki. Karna jaku da nisa, haka cikina harya cika wata tara, zuwa sanan jikin doctor da sauk'i amma ba'a dawo dashi 9ja ba yana indiya abinsa. Awani dare juma'a na farka da nak'uda, cikin hanzari muka nufi asibiti, tun anasaran zan haihu acikin awa biyu har likitocin suka fidda rai, dan har washe garin ranar haihuwa shiru sai bak'ar azabar danake sha. Har k'arfe sha biyun rana haihuwa shiru, zuwa sannan k'arfina yagama k'arewa, ko ďaga hannuna bana iyawa bare kuma nayi wani nishi, ganin halin danake ciki aka yanke shawarar yimini aiki. Babu musu su abbah suka yarda, dadyn su deexerh yasa hannu a maimakon doctor, aka shiga dani ďakin tiyata. Ancuromin yaro namiji k'ato mai kama da babansa kamar an tsaga kara, lallai yau naga farinciki wajen dangin doctor danawa dangin, kowa kamar yacinye yaron haka yakeji, haka nima kowa yana tausaya mini da addu'ar samun lafiya. Duk wata hidima yayansa yayita, kuma shima ansanar dashi na haihu, yayi farinciki kuma yasha kuka, dan ranar saida ciwonsa yak'ara tashi, likitoci sunata faďa akan adaina gaya masa komai daya danganci 6acin rai. Ina gadon asibiti har tsawon sati uku, dan haka ba'ayi taron sunaba, andai raďama yaro suna *Musayyeef*, to iman ALLAH yaraya mana musayeef, amin. Bayan sati uku aka sallamemu, amma wannan karon gidanmu aka dawo dani, dan ina buk'atar kulawar gwaggona, haka nacigaba da rainon musayeef wanda kulum kallonsa yanasani tunawa da ubansa, dan kamarsu tayi yawa matuk'a, kullum mama tana k'ok'arin kwantar da hankalina, ahankali yauda gobe harna dake, komai yafara zama tarihi na maida hankalina akan rainon musayeef. Musayeef yanada wata ďaya da kwanaki aduniya aka dawo da doctor gida, danya samu sauk'i sosai, shima yawan addu'ar da aka dage ana masa yasa yadake yanzu, kwanansa uku da dawowa yayansa yarakosa yaga musayeef, jiyayi kamar yamaida musayeef acikinsa, yana matuk'ar k'aunar ďansa gudan jininsa, dak'yar yayansa ya lalla6ashi suka tafi. Yayi yayi yaganni amma nak'i amincewa, dole yahak'ura suka tafi wani abu na sukar zuciyarsa. Daya koma gida saida aka haďa da lalashi, dan yanzu ba'aso yana tada hankalinsa. Haka naci gaba da rainon musayeef nida gwaggo harya shiga shekara ďaya, asanane kuma ya majeed yabada shawarar nazana s,s,c,e ďina nakoma karatu, abbah ya yarda da shawararsa, dan haka nayi Exam, cikin amincin ubangiji nasamu result mai k'yau, dan haka ba'asamu matsalaba wajen nema mini makaranta. ALLAH yacidani samun nan (A B U zariya), samun makarantar yasa na yaye musayeef na maida hankalina akan karatuna. Shima doctor yakoma aikinsa yabarma ubangiji komai, amma lokaci2 yana zuwa duba musayeef, hakama yaya da mama da aunty. To yanzudai ansaka musayeef makaranta kuma yayansa ne da wanan aikin, idan anyi hutu yana zuwa gidansu hakama weekend ana kaisa yayi kwana biyu. Tunda nabaro gidan bansake haďuwa da doctor ba, bamma k'ara zuwa gidanba, idan yazo ganin musayeef kuwa bana yadda muhaďu, zadai akai masa ďansa, kuma susha hirarsu da gwaggo, ammani yagagara ganina, garama lokacin da maman su deexerh zata koma gidan naso zuwa amma ALLAH bai k'addaraba. Xoxo ta ce, "oh maman su deexerh takoma??. Eh yaya ya maidata yanzu hakama tana gab da haihuwa deexerh tace min. ALLAH sarki kai natayata murna wlhy, musamman ma su deexerh dan babu abinda yafi karayu da 'ya'yanka daďi. Wlhy hakane xoxo Reefat tafaďa. Iman ta ce, "to wanan shine sirrin dana daďe ina 6oye muku. "To miyasa kike yawan waige2? cewar Reefat. Iman tayi murmushi, wato tunda nazo makarantarnan lokuta da dama nakanji turaren doctor ya yawaita awaje, wanan shine ke sakani yawan kuka da waige2, kuma kunga ranar nagansa, wanan yatabbar mini dashi ďinne saidai yana 6oyema ganina. Tabbas labarin iman ya girgiza k'awayenta Reefat da miss xoxo, kuma sunyi alk'awarin taimaka mata har agano gsky, dan suma basu yarda cewa doctor ya saketaba, sunaji ajikinsu *bai saketaba*, amma basu sanar da ita zasuyi komaiba. Saidai sun tanmbayeta yanzu ina deexerh?. Deexerh tana nan, tana karatu a jami'ar abuja yanzun. "Kuna waya?". Eh muna waya sosai da ita, kuma aii kunsan haka, saidai sanan bakusan wacece itabane. Hakane suka faďa, xoxo ta ce, "yakamata mukaima deexerh ziyara. Iman tazaro ido ziyara kuma?, tanafa makaranta nece, eh aii makarantar zamuje, amma sai weekend, tunda bawani nisa bane tsakanin zariya da abuja. Shiru iman tayi dan batasan amsar daya kamata tabasuba, Reefat ta ce, "iman kinyi shiru. Ajiyar zuciya iman tayi, bashiru nayiba Reefat kawai ganin abun nake abaibai. Babu wani baibai, deexerh sa'ar muce, kuma tana k'aunarki aii yakamata zumincinku yacigaba karya yanke. Xoxo ai zumincinmu bai yankeba tunda muna gaisawa, kuma idan ina kano tana zuwa aii mugaisa, tana zuwa ta ďauki musayeef. Eh dukda haka, yakamata mukai mata ziyara. To shikenan saimu duba ranar daya dace saimuje kenan. Okey ALLAH yakaimu. Ammafa iman kinsamu akwali, wlhy da duk zatonmu gwaggo ta haifi musayeef. Dariya iman tayi ta ce, "tokuyi hak'uri. Suma suka dara tareda faďin yayuce, munyimi uzuri................. _*((S)).........2017*_ _*luv u oll my fan's*_ _*battery low*_ [8/6, 6:01 PM] mrs bilkisu: *_BAN SAKETA BA!_* *_NA Bilyn Abdul_* _sadaukarwa_ *ya Abdul (city phone's)* _*sak'on barka da sallah*_ _dolene nafara isar da sak'on barka da sallah ga masoyana aduk ida suke, kafin na tsunduma alabari_ _Nasan bazan iya jere sunanku dukaba, saboda yawa, wasuma bansansuba, amma dukda haka zan kawo sunayen kad'an daga cikinku insha ALLAHU._ *gaisuwa gareku* *_Aysha Manshat, Reefat yahya, hafsat (miss xoxo), Ayusher muh'd, Abba Gana, Sajna, Maman Shaheed, Maryam 'yar mama, cwtjiddah, feedo, saffiya galadanci, billy galadanci, Lemcy, Maman useey, my Ikilee, deexerh, hudallah, zarah ms, Feedausi, Maman 'yan biyu, Zainab Zanfara, Teema, Maryam Nijar, salma Nijar, sa'adatu sa'ad, hafsy, Aysha umar Abubakar, shamsiyya muh'd, umayma, fa'iza, Xee Salees, Fatee, Xee babe, ummy, Maman aneesat, Maman yasmeen ,muneerat,nanerh, khadeejarh, beauty angel, bby hanan, Aysha umar, d'an mom, ikram saje, kairat safyan, sadiya baby, mimin mom, Luby, Afra'ce, maigadon zinaree, sumayya waziri, Aysha mai'tama, Maman Affan, momyn sultan, momyn Aysha, ummulkairi, Mrs muh'd, Mrs Amman, Asma'u taura, ikileema Zaria, Maman Mubarak, Ruky, Ash-Nur, Mrs uwaisu, matar Safwan, ummy ta kano, Rashida madaki, Mrs isma'il._* _bari nadasa aya an an badan kun k'areba, kubini bashi a page nagaba, Dan bazan gaji da kwarara sunankuba awajen gaisuwar sak'on sallah, INA muku fatan Alkairi, da addu'ar ALLAH yakar6i ibadinmu baki d'aya, ya yafe mana zubanmu, ameeen_ *hak'uree* ```Kafin nacigaba zanba masoyana hak'uri, saboda jinkirin sosai Dana d'auka banyi typing ba, hakan yafaru me sakamakon bikin k'anwata, bayan kuma nadawo aka fara azumi, kuyi hak'uri dani, insha ALLAHU yanzu komai zai tafi yanda kukeso, ngd da k'aunarku gareni, Nina INA k'aunarku aduk inda kuke```. *luv u oll❤❤😁😁👌🏼*. *(Page 16)* Yau cikin damuwa sosai su iman suka tashi sakamakon yajin aiki dasuka wayi gari makarantarsu ta tafi, bak'aramin haushi abin yabasuba, Dan suna ganin aski yazo gaban goshi, nanda 'yan watanni zasubar makarantar Baki d'aya, amma saigashi matsala ta gitta musu. Agefe kuma sunajin kewar rabuwa da juna saboda tsananin tsak'uwar dasukayi, kowa ka kalla fuskarsa babu walwala har suka gama shiri tsaf,. Xoxo datun d'azu hawaye suka cikamata ido saboda harta fara kewar aminannata, ta share hawayen cikin dabara batareda su iman sun luraba. Wayar Reefat tafara wringing kobata dubaba tasan mai kiran, Dan wringing d'insa na musamman ne, ganin wayar naneman tsinkewa yasa iman tayi saurin d'auka tasa akunen Reefat. Jiki a sanyaye tayi masa sallama, ya amsa, bayan sun gaisa ya CE, "yafa iso, tafito sutafi Dan garinsu da nisa. Hawayene suka shiga gangaro mata akumatu, iman da Xoxo suka kalli juna, sanan sukace lfya Reefat?. Kusan atare sukayi furicin. Wani kukane yatawo mata, tafara shashsheka, cikin kukan ta ce, " ya Usman ne wai har yazo d'aukata. Kamar jira suke suma suka fashe da kuka, (nace tofa akwai matsala). Yanda suka had'e kai suna kuka dolene subaka tausayi, sukuma burgeka, sunkai minti sha biyar suna kukan, Dan saida ya Usman yak'ara kira sanan suka mik'e, 'yan kayanta suka ida had'a mata, sanan suka ja hannunta har wajen ya usman. Tundaga nesa ya hangosu, ya lumshe idanu ahankali yana sauke numfashi, jiyayi zuciyarsa tayi sanyi da ganin masoyiyarsa uwar 'ya'yansa nanda wani d'an lokaci, yana matuk'ar k'aunar Shareefat gsky, har suka iso kusadashi bai saniba, saida suka kuma had'a baki wajen yin sallamar sanan yay firgigit alamar dawowa daga tunani. Kusan atare suka gaisheshi harda Reefat, fuskarsa cike da murmushi ya amsa, idonsa akan Reefat, ya ce, "k'awayenmu ya karatu, Alhmdllh suka fad'a atare, sund'an ta6a hira da wasa da dariya, sanan ya ce, " Reefat tashiga sutafi lokaci yana k'ara ja. Rungume su Reefat tayi tasake fashewa da kuka, suma kukan suke, ya Usman ko yatsaya yana kallon ikon ALLAH, tosu wad'anan Randa suka gama makarantar sai Yaya kenan?. Ganin babu mai amsa masa tambayarsa yasa yafara lallashinsu da basu hak'uri, tareda dad'ad'an kalamai. Haka suka hak'ura Reefat tashiga mota suka tafi, su Xoxo suna d'aga musu hannu, har saida motar ta6acewa ganinsu suka hak'ura. Jiki a sanyaye suka koma hostel suka ida had'a kayansu Dan suma su kama hanyar kano, dukda dai babu wani nisa sosai. Bayan kamar minti talatin suma suka fito bakin titi, fira sukeyi kad'an2 kuma duk ta Reefat, iman tad'aga kai tana kallon yanda sararin samaniya ta had'e rai tamau. Ahankali ta sauke numfashi, my sisi garinanfa akwai hadari wlhy, itama Xoxo saman takalla, tamaido dakanta kan iman, tokodai mutafi tashane?. Tasha kuma?, aii mun maida hannun agogo baa kenan, wlhy saimunfi saurin samun mota anan gurin. Shikenan Xoxo tafad'a tana zama. Hadari kuwa sai k'ara d'aurewa yakeyi, garin Yakuma jajaur alamar akwai iska a hadarin. Lokaci lokaci sukan kalli agogon hannunsu, tun d'azur sai tare mota suke amma yawanci duk acike, gashi basu kad'ai bane awajen, akwai tsurarin d'alibai irinsu suna jiran mota, ahankali iska tafara kad'awa, mutane sai kaikawo suke kowa k'ok'arinsa yasamu mafaka. Hankali tashe Xoxo takalli imam, wayyo sweet sis kinga abinda kika jamana ko?. Itama iman hankalinta atashe yake, Dan ba k'aramar iskace tarufe titinba, wasu motocinma sai gangarawa suke k'asan titi suna tsayawa, kobasa ganin gabansune oho. Garifa yafara turnik'ewa fiye da tunaninsu, ahaka sukayi nasarar tare wata bos, amma kuma gurin mutum d'ayane, sukuma su biyune, afusace direban yaja mortar suna mita shida kwandastansa, tuni iman tafara hawaye, Dan batason ruwa yajik'ata hakan yana kawo mata Marsala sosai. Da k'arfi ruwan yafara sauka gakuma iskar na dad'a tasowa, wata jar motace tadawo dabaya Dan harta gotasu, daidai saitinsu tatsaya, deexerh tabud'e tafito, lah ashekuwa da gsk auntyn CE. Ajiyar zuciya iman tasaki itada Xoxo tareda fad'in deexerh kece?, nice aunty kushiga mutafi, cikin hanzari tabud'e but suka zuba kayan itada iman, xoxo kam harta shige baya. Suna gamawa wata iska ta taso wadda da'alama zata iya d'aukar mutum sukutum zuwa sararin samaniya, dasauri deexerh ta tura imam gaban motar, itakuma tashige baya. Iman bama tasan Inda tashigaba saboda k'ura yashigar mata ido, tunda ta zauna kanta yana cikin hijjabi tana k'ok'arin goge k'asar idonta. Dr Isma'il yajuyo yana kallon Xoxo, k'awarmu miya zaunar daku cikin wanan iskan haka?. Tunda Xoxo tashigo motar tagane Dr Isma'il dukda sau d'aya tata6a ganinsa, tayi murmushi wlhy, iman CE, tunda muka fito nace mata muje tasha tadage wai ana samun mota anan wajen. Tunda yafara magana gaban lman yafara fad'uwa danjin muryar Abun k'aunarta Wanda kuma take gani ayanzu babu Wanda ta tsana kamarsa. Deexerh ta ce, "lallai aunty akwai kasada, wlhy harmun wuce uncle ya CE, " wancan kamar aunty imam, na ce, "kai uncle anya kuwa?. Ya ce, " Baradai mutsaya muduba, shinefa muka dawo baya Ashe kuwa kune. "Wlhy mune!". kuwa,ammafa mugode sosai daddyn musayeef, d'an murmuahi Dr Isma'il yayi, ya ce, "yakaratu ?. Alhmdllh Xoxo tafad'a, hankalinta yana kan iman dataga tak'i d'agowa tun d'azu. Iman wai lfy kuwa?. Lfy lau tafad'a batareda ta d'agoba. Xoxo tasauke ajiyar zuciya, Kodai k'asa yashigar miki Idone?. Kai ta girgiza mata, alamar A'a. Dr Isma'il ya ce, " humm k'asane a idonki mana ai INA kallon sanda yashiga, kid'ago na cire miki. Banza tayi dashi kamar bama tasan dazaman saba. Deexerh ta CE, "aunty kibayar aduba miki karya Zame miki Matsala, ido baya son bak'o wlhy. Nifa babu komai a idanuna iman tafad'a ido arufe da hijjabi. Dr Isma'il yad'an girgiza kai, tareda tada motar ya haura saman titi, aransa yana fad'in idan kinga kin kasa gani ai k'ya bada aduba miki. Shiru yabiyo baya nad'an mintuna, daga nan Xoxo da deexerh suka cigaba da hirarsu ahankali, dansu Dr Isma'il basajinsu, hira suke akan abinda yafaru akansu iman d'in shiyayasa sukeyi ahankali. Agaba kuwa d'if kakeji babu mai magana, Dr isma'il yanata tuk'i ahankali, Dan baya gudu saboda ruwa akeyi sosai, iman kuwa har yanzu bata d'agoba dukda tacire k'asan daya shigar mata idanun. Saidai turaren Dr Isma'il dukya addabeta, nema yake yarikita mata lissafi gaba d'aya, shikansa yana tuk'i hankalinsa yana kanta, lokaci2 yakan kalli Inda take zaune atakure, yakand'an murmusa idan wani Abu yafad'o masa na rayuwarsu da iman abaya. Bayan sunyi 'yar tafiya iman tagaji da rude fuska tabud'e, amma ta kauda kai gefe tana kallon k'ananan k'auyuka, da saukar ruwan sama. Murmushi Dr isma'il yayi, Dan wata dabarace tafad'o masa, ganin yanda iman ta shagala da kallon waje, ga ruwa ana ketawa sosai, sai kawai yasauke Gila's d'in gefenta, wani iskane da feshin ruwa suka buso mata afuska, da Sauri tajuyo tana fuskantar Dr isma'il dake murmushi, takalleshi sosai shima daidailokacin daya juyo suka had'a ido, wani lallausan murmushi yasakar mata tareda kanne ido d'aya😉, harara tasakar masa, harda d'an murgud'a baki😏. "Nice one". Yafad'a ahankali cikin wata irin kasallaiyar murya. Muryar iman na rawa ta ce, " pls karufe INA jik'ewafa, kuma ruwanan zai iya cutar dani. Bai kalletaba bai kuma rufe Gila's d'inba, amma fuskarsa har yanzu d'auke take da murmushi, cigaba yayi da tuk'insa cikin kwarewa, Xoxo da deexerh kuwa suna baya suna k'unshe dariya, Dan duk abinda yake faruwa akan idonsune. Iman kuwa tamkar tafasa ihu takeji, wanan aii zalincine tafad'a azuciyarta, saida yaga tajik'e gurin data bada k'arfima yajik'e sanan yay sama da Gila's d'in, ahankali ta sauke ajiyar zuciya Dan wani irin sanyi tafaraji yana shigarta, tad'ago ido tasaci kallon Dr Isma'il, sanye yake da k'ananun kaya, blue d'in wando da jar Riga anmata digo2n fari, k'ugunsa d'aure da farar rigar sanyi ta sak'a, tad'an ta6e Baki azuciyarta tace saikace wani mace, kakama k'ugu ka d'aure da riga. Ganin irin kallon datake masane yasashi 'yar dariya, yaymata kallon fisha ya maida kallonsa saman titi, ahankali ya ce, "kallonfa?, ko namiki k'yaune?. Da sauri iman ta kauda kai tana fad'in mizan kalla anan. Ya ce, " handsome mana. Yanda yayi maganar saida tsigar jikin iman yatashi, Duk abinda yake faru su Xoxo basu saniba hankalinsu yana kan waya, deexerh tana nuna mata hotunan bikinsu iman d'in. Ya ce, "INA my son?. Baki iman ta ta6e tareda fad'in na siyar dashi. Wata 'yar dariya yayi, harda dukan tityari, ya ce, " dakin burgeni kuwa my sweedy!. d'an tsaki taja danjin ya ce, "mata sweedy, wayarta tajawo tafad'a kiran Reefat amma arufe. Tajuyo tana kallon su deexerh, sisi tafad'a tana kallon Xoxo!. "ma'am". Kinga No d'in Reefat yak'i tafiya, wlhy Nima tun d'azu nake gwadawa, amma inaga bata kunna wayarta bane. Kumafa hakane iman tafad'a tana gyara zama. Awani d'an k'auye Dr Isma'il yatsaya, Dan gsky ruwan yawuce tunanin jama'a, zugashi akeyi sosai, yanzuma harda k'an k'ara akeyi, gani yayai baya ganin gabansa sosai Dan haka yabi sahun direbobi masu tsayuwa, shima ya tsaya. Ju yowa yayi sosai yana fuskantar iman, itakuma ta had'e rai tamau.............. _kuyi hak'uri da wanan❤👌🏼_ *luv u oll my fan's* *(((S)))........2017* [8/6, 6:01 PM] mrs bilkisu: *_BAN SAKETA BA!_* *_NA Bilyn Abdul_* _sadaukarwa_ *ya Abdul (city phone's)* *Gaisuwar Sallah* *_Fateema sulaiman Nijar, zeenaseer, fatee Axlad, ummiee jafar, Ruk'ayya Kt, zaliha, hauwa kaka, humyluv, ummiee Khalil, hauwa lele, xeynab, sumie Carly, teemacool, Nafisa Raji, Maryam, ayusha umar, Maimunat (kakus), lawusa, ayeesh, muhmeelat, Mina, Raheenat Basheer, Asy Khalil, zee Elkaseem, Zainab muh'd bello, Maryam zuntu, zeenur, Asmy b, mammu magaje, Maman ihsan, shamsiyya abas, hamie danjani, Maman shureim, barakarh, haleema muh'd Ali, Maryam Ab, meenat, Aysha, khareema, ummu musakeen, Aliya jos, khairiyya, suhaila Tafida, umman marwan, Mrs Izz, zeenat A kabeer, Bily sokoto, Ameera Musawa, Ameera sokoto, 'yar India, mufeeda show, Ifteehal, Ameena kd, Asiya masak'a, Tani tani, badee, Bara'atu ce, Bahijja, Maman shamwul._* _Bari nadasa aya anan, muhad'u a page nagaba, INA fata duk kunyi sallah lfy??._ *(page 17)* 'Dan murmushi yayi Dan ganin yanda tawani d'aure fuska. Yajuya yakali su deexerh, yaga hankalinsu baya kansu, ta waya sukeyi. "Juyowa yayi kan iman, data maida kallonta ga Gila's, *_"Imman!"._* yafad'a dawata irin murya mai cike da kasala. Banza tayi masa kamar batajiba, ya ce, " wlhy koki juyo kona k'ara bud'e Gila's d'inan, nanama shiru tayi masa bata tankaba. Ganin bazata juyoba yasashi sauke Gila's d'in, wani sanyi yafeso harda k'ank'ara, babu shiri tajuyo tana sauke ajiyar zuciya, Gila's d'in yarufe yana 'yar dariya, haushine yaturnik'e zuciyar iman, sai Kawai tafashe da kuka. Jingina bayansa yayi da murfin k'ofa yadasa mata mayun idanunsa, ko k'yafatawa bayayi, sai yanzu yay mata kallon tsaf, ganin yayi tak'ara k'yau harda 'yar k'iba, dakaga Iman zakasan tana cikin kwanciyar hankali, atake zuciyarsa takawo masa wani tunani. "Koadai Iman k'arya take ita tarubuta takardar sakin nan Dan bata sonsa??, wani irin d'aci ya turnik'e zuciyarsa".. K'irjinsane yafara masa nauyi, indai hakane Iman taci Amanarsa, tajefashi cikin mawuyacin hali, ga ciwo ga matsananciyar sha'awarta dake addabarsa, saboda gudun fad'awa halaka yasashi kullum yake kasancewa cikin azumi, gashi yanzu dukda yana azumin dauriya kawai yakeyi, yarintse idanunsa, Azuciyarsa ya ce, " *BAN SAKETA BA!* miyasa zatace nasaketa?, shin dama bata k'aunatane?, wani dogon tsaki yaja, Wanda baisan yafitiba, gaba d'aya suka d'ago suna kallonsa. Tada motar yayi yafisgeta da k'arfin tsiya. Gaba d'ayansu hankalinsu atashe yake, ganin yanda yafisgi motar yasa deexerh datasan halin dayake ciki, kuma taga Iman na kuka sai hankalinta ya tashi. "Ta ce, ''Uncle lfy kuwa?". Baice mata k'alaba Dan yafara fita hayyacinsa, shikansa baisan ayanda yake tuk'inbama. Ganin sunfara yawo a titi yasa hankalin Iman komawa Kansa. " innalillhi wa'inna ilaihirraji'un", Doctor! Pls karka kashemu, kayi hak'uri Dan ALLAH. INA baimasan tanayiba, da sauri deexerh ta taso tayi nasarar tsaida motar, danta iya, gefen titi suka gangara, saura kad'an subigi wata bishiyar Tsamiya, Xoxo da deexerh suka k'ank'ame juna suna Addu'a, Iman ma Dr isma'il ta k'ank'ame tana kuka, dukda baya cikin Nutsuwarsa saboda nauyin da k'irjinsa yayi masa, wannan bai hanashi rungume Iman ba sosai. Ya kwantar dakansa jikin kujera yaruntse idanu, ga Iman rungume ak'irjinsa, sai wani irin Numfashi yake saukewa awahale. Jin motar ta tsaya dakuma saukar Numfashin Dr Isma'il yasa deexerh d'agowa da Sauri, gabantane yafad'i, afili ta ce, "nashiga uku, kardai ciwon Uncle ne yakeson tashi?. Sai asanan Xoxo da Iman suka d'ago, Iman tafara mutsu2n kwace kanta, amma takasa danba k'aramin ruk'o yaymataba. Da sauri deexerh ta kwantar da kujerar, Yakuma k'ank'ame Iman kamar za'a kwace masa ita. Motar tayi shiru bakajin motsin kowa sai saukar numfashin Dr Isma'il, da hannu yayma deexerh Nuni data bashi magani, cikin hanzari tabud'e motar tafita, gaban motar takoma, tabud'e wani waje, magungunansa tagani awajan, wani d'an farin roba tad'akko, Wanda tagani yana amfani dashi idan ciwon ya motsa kafin aje asibiti. Abaki tasaka masa yazuk'a sau uku, yajanye bakinsa, Yakuma rungume Iman yanda bazata samu hanyar barin jikinsaba, cikin 'yan sakwanni barci yay gaba dashi. Xoxo da deexerh bud'e mortar sukayi suka fita sabida an daina ruwan, said'an yayyafi. Ga Iman so kawai take takwace jikinta, amma dukda barci ya d'aukeshi ta kasa. Saida suka fita Xoxo talek'o. "Iman pls kiyi hak'uri kinutsu waje d'aya, dadyn Musayeef yana buk'atar taimakonki, kitausaya masa halin dayake ciki, mu zamu zauna a waje harya farka idanma kunyarmu kikeji. Shiru tayi dantasan maganar Xoxo gsky CE, to Amma aii babu dacewa, tunda ayanzu Shiva mijinta bane, gani take zunubi kawai zata kwasa abanza a wofi. Wasu zafafan hawaye suka zubo akumatunta, addu'a tashiga karantowa ahankali harta samu nutsuwa. K'ara gyara kwanciya tayi sosai, tak'ara kwantar da kanta visa faffad'an k'irjinsa, tunanin rayuwarsu tabaya tashiga yi da Doctor, taringa tuno so da k'auna gamida tattali daya ringa nuna mata, amma gashi yanzu k'addara ta rabasu, sunyi nisa da juna, ahaka taringa tunani da shak'ar kamshin daddad'an turarensa har barci yay ayon gaba da itama. (Nace da k'yau iman, anji k'irjin boss😜). Xoxo takalli deexerh, kinga gawata rumfa can kozamu koma Canne?. eh wlhy kuwa muje can, Dan naga ruwan yanad'an jik'amu ahankali. Kafin su wuce deexerh talek'a Dan taga halin da Uncle d'inta yake ciki, murmushi tayi tareda share hawayen tausayi, Dan ganin yanda itama iman barci ya d'auketa. Xoxo ta k'araso tana fad'in lfy kuwa?. Murmushi deexerh tayi tana nuna mata su iman, itama d'an murmushi tayi, sun bata tausayi matuk'a, suna kewar junansu sosai, amma zalunci yasa an rabasu, (tana k'ara tsinewa azalumin dayayi wanan zalincin, Dan tasan ALLAH bazai barshiba). Hannunta deexerh taja suka tafi runfar, wadda da'alama an tanajeta saboda irin hakan. Wuri suka samu suka zauba sunata hira, da tattauna yanda zasu taimakawa su iman. *Reefat* A6angaren Reefat kuwa, tunda suka tafi ta kifa kanta saman cinya tanata kuka, ya Usman bai hanataba Dan yasan zafin rabuwa da masoyi, tuk'insa kawai yakeyi, gashi yaga alamar hadari agarin. Saida sukayi tafiya mai nisa sanan yaga kukan na Reefat bamai k'arewa bane, Dan haka yay gyaran murya, tareda fad'in Shareefat!. Ahankali ta ansa, batareda ta d'agoba, ya ce, "d'ago mana kiji wani Abu. Bata musa masaba, tad'ago kanta, idanunta sunyi jajur, ya ce, " kalleni mana. Ahankali tad'ago tana kallonsa, yasakar mata lallausan murmushi, da Sauri tayi k'asa da kanta itama tana murmushin. Kokefa yafad'a yana dariya, kukan ya Isa haka, muyi hira. Nanma murmushi tayi, ahankali yarink'a janta da hira harta saki jikinta aka koma soyayy😜lol. Saida su Dr Isma'il suka d'auki tsawon minti Arba'in suna barci, Dr Isma'il yafara farkawa, yabud'e idanunsa ahankali ya sauke akan fuskar iman datake barci cikin kwanciyar hankali. Wani lallausan murmushi yasaki tareda jin wata zazzafar k'aunarta tana k'ara shigarsa, yashafa kumatunta ahankali. Da sauri tavud'e ido takalli inda fuskarsa take. "Ido suka had'a tai saurin kauda kai tana k'ok'arin tashi daga jikinsa, bai saketaba saidai k'ok'arin tashi dayakeyi da ita ajikinsa, zaunar da'ita yayi sosai acinyarsa. Muryarta na rawa ta ce, " dan ALLAH ka cikani kaga babu dacewa acikin hakan. Baicemata komaiba sai k'ok'arin gyara kujerar dayakeyi da hannu d'aya, hannu d'aya kuma yana rik'e da ita. Jingina yayi da kujerar sanan yakuma had'eta da jikinsa, yajuyo da fuskarta suna fuskantar juna, ido ta runtse dan bazata iya kallonsaba, bata ankaraba taji bakinsa cikin nata, tuni jikinta yafara rawa tacigaba da mutau2n kwacewa, sai faman tsungulinsa takeyi amma ko'a jikinsa, aika mata da sakwanni kawai yake cikin zafin nama. Da alama ya manta acikin mota suke, sunkai tsawon minti goma ahaka dakyar tasamu yasaketa, sai sauke ajiyar zuciya yake kamar d'an daya kwana uku baisha nonan uwarsaba. Itama da sauri takoma d'ayar kujerar tazauna tana maida numfashi, jikinta sai rawa yakeyi, ALLAH yasotama ba'a gabansu deexerh yaymata wanan abunba, aidaba k'aramar kunya tajiba wlhy. Ahankali ya rungume sitiyari yana ajiyar zuciya, bayan kamar minti uku, ya ce, "inasu deexerh d'in?. Kad'an ta kalleshi taga yana rungume da sitiyari, taja ajiyar zuciya, Nima ban saniba. Shiru yayi zuwa wasu 'yan sakwanni, sannan ya d'ago, bud'e motar yayi yafita, can yahango su deexerh zaune acikin runfar suna hira, yad'an d'aga murya yakirasu. Atare suka juyo sanan suka mik'e, sunaji dad'in yanda suka gansa, suka k'araso suna MASA ya jiki, ya CE, " da sauk'i. "Kushiga mutafi ko?, yafad'a yana Shiga motar. Sums Suka Shiga ya tada motar, iman bata kalli kowa acikinsuba, wata iron kunyarsu takeji dukda basuga abinda Dr Isma'il yayi mataba. Motar yayima key yaja suka tafi. Yanzukam gudu yake sosai, motar tayi shiru babu mai magana. Har suka shigo cikin kano bai sake kallo. Ko Inda iman takeba. Juyowa yayi yakalli xoxo, k'awarmu INA muka nufa?. Ta CE, " mije zan rink'a nuna maka. Okey yafad'a yana satar kallon iman, wadda tunda suka taho kanta yana k'asa. Da taimakon Xoxo suka Isa k'ofar gidansu, tayima Dr Isma'il godiya tareda addu'ar k'ara samun lfy. Ya CE, "ngd, kigaida mutanen gida, zasuji tafad'a tana k'ok'arin fita. Iman ma k'ofa takama Zata fice, yay saurin rik'o hannunta batareda yayi maganaba. Tad'an d'aure fuska, nimafa anan zan sauka, sai anjima zan k'arasa gida. Shiru yayi bai amsa mataba, Xoxo talek'o tana fad'in to Imam saimunyi waya, k'ila kuma gobe idan ALLAH yakaimu nashigo ma. Iman ta CE, " to ngd sosai my Hafsy kigaidamin da momy Dan ALLAH. zataji, Nima ki gaidamin da my Musayeef da gwaggo da deeni da Abbah, duk zasuji insha ALLAHU, saikinxo d'in. To sainazo, Ak'aramin godiya wajen daddyn Musayeef. Hararta iman tayi. Xoxo tabar jikin motar tana dariya. Saida yatada motar sanan yasaki hannunta. Daga nan gidansu iman yanufa. Tunda suka tafi gabanta ke fad'uwa tana addu'ar ALLAH yasa kada kiwa yagansu, Dan zataji kunya sosai wlhy. Ak'ofar gidansu yayi fakin, yana tsayawa deexerh tayi cikin gidan da gudu, shikuma yay saurin rik'e hannun iman dake k'ok'arin fita daga motar. Bata juyoba bakuma tacigaba da yink'urin fitarba, muryarsa kasa2 ya CE, "ngd da taimakonki gareni, dabaki a kusa dabansan irin halin dazan tsinci kainaba ayau, ngd sosai. Saidai zan k'ara tuna miki har yanzu akwai aurena akanki, *Ban sakeki ba!* Dan haka kicigaba da kula dakanki har lokacin da ALLAH zai bayyana gsky, Saudat kiguji abinda ALLAH zaikamaki da hak'in aurena, INA mana fatan Alkairi arayuwa, ALLAH ya albarkaci Musayeef da sauran k'annensa masu zuwa nangaba. Kicigaba da sakani cikin Addu'arki Dan INA cikin wani yanayi na ciwon sonki, asanadin sonki nakamu da ciwon zuciya da hawan jini, ga matsananciyar sha'awa na damuna, akullum INA ADDU"AR ALLAH ya gaggauta bayyana gaskiyar halin damuke ciki, dukda kekam naga hankalinki akwance yake. Amma nikam sai addu'a. Tuni hawaye ya wanke fuskar iman, tausayi da tsananin son mijinta suka k'ara mamayeta, ahankali tazare hannunta tafice daga motar, tana k'ok'arin rufewa deexerh tafito itada Musayeef, da Sauri Dr isma'il yabud'e motar, ya d'auki d'ansa ya rungume yana maijin wani matsanancin facinciki da nutsuwa, saiyajima ciwon NASA yak'ara raguwa. Jiki a sanyaye iman tashige gida tana share hawaye. Tashin mortar Dr Isma'il taji, da Sauri tashare hawen idonta ta lek'a,. Karaf idanunsu suka had'u yanuna Kansa da k'irjinsa ❤ sanan ya nunata ya had'e hannayensa🙏🏻, yatsu uku yad'aga mata, yaja motar da Sauri yabar wajen musayeef yana mata bey bey. 'Dan murmushi tayj Dan tasan abinda yayi mata yana nufin *"I luv u*. K'ara share hawayenta tayi sanan tashiga gidan da Salama. Gwaggo dake zaune tana gyaran alayayyahu ta amsa da far'arta, da Sauri iman taje ta shige jikin gwaggo tana mai far in cikin ganinta. Itamadai cikin farin cikin ta tarbeta............ *Dan ALLAH idan damai ban saketaba saga farko yad'an turomin nayi missing d'in NAWA*. 09093044460 *luv u oll my fan's* *(((S)))......2017.* [8/6, 6:01 PM] mrs bilkisu: *_BAN SAKETA BA!!._* *_NA Bilyn Abdul_* _sadaukarwa_ *ya Abdul (city phone's)* *BARKA DA SALLAH* *Bilyn Abdul H Novel's* *Zumunta group* *Online Hausa Writer's* *Home of Novel's* *House of Novel's* *Muhad'a kammu mata* *Hausa Novel-Farin ciki* *Asmy fan's club* *Billy Galadanci's Novel* *'Dan/zabuwa 2010 Graduation* *Fashion & Novel's* *Miss Xahras Novel's* *Hausa Novel's* *Mmn Shureim Novel's* *Talented Writers group* *Hausa Novel's* *Maryam G Novel's* *Ciwon 'ya mace* *House of Novel's 3* *Manshat Novel's* *Musan junah o,h,w.* *Ikkiram's Novel's* *Hausa Novel's* *Mmn Useey Novel's* *Feedo online Novel's* *Hawwa H Novel's*. *Faheemta Novel's Mrs jh* *Hama Gee's Novels Chamber* *Fareedat Novels*. *Mmn Shaheed Fan's* *MF&JH Hausa Novel's group* *Feedo online Novel's* *004 Hausa Novel's book's*. _baridai naja birki an an da mik'a sak'on SALLAH, INA muku fatan Al'kairi arayuwa, nagode da k'auna._ Duk Wanda baiga sunansaba yamin Afuwa, badan bana sonsa bane saidan yawa dakuke dashi, duk inda masoyina yake INA Al'faharee dashi, ngd. *luv u oll😘😘😁👌🏼* https://mrsbilkisa.blogspot.com *(page 18)* Iman kinga yanda kikayi k'iba kuwa?, lallai makarantar nan babu wahala. Kai gwaggo babu wahalafa kikace?, iman tafad'a tana turo Baki gaba. Dariya gwaggo tayi, oh ni wai sai yaushe iman zakisan kin girmane?, kiyi shagwa6a musayeef yayi. Dariya iman tayi tashige d'akin ta. Kayanta tacire, sai wani faman murmushi takeyi Wanda Nima bansan namiyeba masu karatu. Kayanta takai hancinta tana shinshinawa, talumshe idanu Dan jin dad'in kamshin turaren Dr Isma'il daya manne a kayanta. Gaban madubi tak'arasa tana kallon fuskarta, takai hannu kan la66anta tana shafawa ahankali, murmushi tayi Dan tuno irin kissing d'inta da Doctor tayi, afili ta CE, "ALLAH ngd maka daba agabasu Xoxo yayminba, nasan danasha tsokana. Wayarta tad'auka tak'ara gwada Number Reefat amma bata shigaba, ta ce, " lallai Reefat soyayya tayi dad'i an manta damu. Waje tayo tana fad'in gwaggo Dan ALLAH akwai ruwan d'umi agidanan?. Eh akwai acikin kicin wanka zakiyi ko?. Eh wlhy gwaggo gwara nayi naji dad'in jikina, ga garin akwai sanyi. Hartaje k'ofar kicin d'in saikuma ta juyo, gwaggo wai miyasa kika Ba deexerh Musayeef ne?. Kallonta gwaggo tayi, kijimin yarinya dawani zance, na hanata d'aukar d'an uwanta, kuma batacemin tare kuke da babansaba, to ko babu babansa itama aii ta Isa tazo ta d'aukeshi ko. Amma gwaggo aidai sabari mugaisa ko?. Uhmm kudai kuka sani, saiki kirashi kice yadawo miki da d'anki aii. Da Sauri iman tashige kicin d'in Dan tasan bak'ar magana gwaggo tafad'a mata. Koda tajuyo ruwan tadawo gwaggo ta tashi, d'aki tawuce abinta tayi wanka, doguwar Riga tasaka jaa, bawata kwalliya datayi tafito tsakar gida. Gwaggo ta ce, "ga abinci nan afalon Abbahn Ku, kid'ibo kici ko?. To gwaggo iman tafad'a a sanyaye, Dan wlhy duk kewar Musayeef ta isheta. Taci burin yau susha hira da *" Hasken idaniyarta"*. A6an garden su deexerh kuwa suna zuwa gida ta sa6i musayeef suka nufi 6angaren mama, Dan tasan dukkan ahalin gidan suna can tunda yau asabar babu makaranta. Dr Isma'il ma can yanufa, lokacin daya Isa falon ya kaure da murnar ganin musayeef, shima sai farinciki yake daganin 'yan uwansa. Mama tafara fad'in oyoyo autana, da murmushi afuskarsa yak'arasa Kusada mama yazauna, ya gaisheta, cike da fara'a ta amsa masa. Ina kasamo min mai gida na robar?. 'Yar dariya yayi danyasan Musayeef take nufi, ya ce, "gidan mukaje muka taho dashi. Mama tarik'e ha6a auta banda fin k'arfidai. Dariya yayi yana gaidasu Maman deexerh da aunty sadiya. Yamik'e mama bari nad'an watsa ruwa nadawo, aunty baba mikika tanadar minine?. Dariya Maman deexerh tayi, ta ce, " k'anina girki na musamman nayi maka, tunda kak'i kayi aure. Dariya yayi, Idan kunaso nayi aure kuje kudawo min da momyn Musayeef kawai yafad'a yana ficewa. Aunty tad'an ta6e Baki amma babu Wanda yaganta saini bilyn Abdul 'yar rahoto. Mama da Maman deexerh kuwa da kallon tausayi suka bishi. 6angarensa yanufa yasa key yabud'e wani k'amshi yadaki hancinsa yashak'a ya lumshe idanu, yasan wanan aikin Maman deexerh ne, Dan waccan mai kama da karuwar bazata ta6a gyara MASA wajeba, (aunty yake nufi😜). d'akin iman Nada yashige yakwanta Dan yanzu yamaidashi d'akinsa saboda yarink'a d'ebe masa kewarta. Yaja fillo ya rungume tsam ak'irjinsa idanunsa ya rintse Dan tuna abinda yafaru d'azu amota tsakaninsa da imam, wani irin farin ciki yakeji, yak'ara matse filon yanaji tamkar iman ya rungume, muntuna kad'an barci yay awon gaba dashi. Yana cikin barcinsa mai dad'i yaji Musayeef yana tadashi, yabud'e ido yasauke akan yaron. Musayeef yay 'yar dariya, daddy katashi?. Hannunsa yakamo yakwantar dashi agabansa, yarungumeshi, miyasa katadani INA barci Musayeef?. Daddy dare yayi, katashi ka kaini wajen aunty Maa!. Dr Isma'il yajuya yakalli agigon dake d'akin, 6:27pm, da Saudi yatashi zaune, innalillahi dama haka nadad'e INA barci?. Musayeef ma tashi yayi zaune yana fad'in daddy inzo muje ka kaini waje Aunty maa d'in?. Ma6allen rigarsa yafa cirewa yana fad'in Musayeef sai yanzu katuna da aunty maa d'in?, kabari sai gobe idan ALLAH yakaimu kaji. Kusadashi yazo ya zauna yad'aukeshi yad'orasa asaman cinyarsa, haba my boy bakason zama dani sai aunty maa?. Inaso mana musayeef yafad'a yana kallon babansa. Sumbatar kumatunsa yayi yauwa my lovely son, yanzu kaga kazauna kajirani nayi wanka kaji ko?. Daddy Nima zanyi wankan. A'a kabari sai zamuyi barci, kaga ga wayata kayi game. Cike da murna Musayeef ya CE, "daddy inaso zanyi game d'in, kamomin irin na aunty maa!. Dariya Dr Isma'il yayi, game ya nemomasa yabasa sanan yanufi bayi domin yin wanka. Wankan tsarki yayi Dan mafarki yaytayi yana tareda Iman, yad'auro Alwala yafito, sallaya yashinfid'a yafara rama sallolin da'ake binsa, Musayeef kam yana busy akan waya, game ya d'auke masa hankali gabad'aya. Dr Isma'il bai tashi ba saida akayi sallar isha'i, yayi addu'oi yatashi, gadon ya haye yakwanta Kusada Musayeef daketa aikin game, tsayawa yayi yana kallonsa sai murmushi yake Dan ganin yanda yaron ya kware da iya game d'in, waya koyamaka game d'innan Musayeef?. Ya CE, "daddy aunty maa mana, kullum idan bata tafi makarantaba sai munyi kafin muyi barci, daddy kaima kace mata ta koya maka. Aii bazata koya minba nasani Dr Isma'il yafad'a yana marairaice murya. ALLAH dady zata koya maka, nuna min Number ta nakirata tazo yanzu ta koya maka. Dariya sosai Dr Isma'il yakeyi, shikam Musayeef yatubure sai ankira aunty maa Tazo ta koya game, hardasu kuka. Ganin haka yasa Dr Isma'il kar6ar wayar danya kira iman, ALLAH ma yasoshi ya k'ar6i Number ta awajen deexerh, dayaga takansa da rigimar Musayeef. Iman kam tana zaune abakin gado sunata hira da Xoxo awaya tamkar ba yau suka rabuba, sun dad'e suna hira harsaida katin Xoxo yak'are sannan, iman tacire wayar daga kunnenta tana dariyar maganar xozo ta k'arshe, danna number ta tayi da zummar kiran xoxo, sai bak'uwar Number tashigo. Fuskarta cike da far'a tad'aga, azatonta Xoxo CE takirata da number wani d'an gidansu. 'Dagawa tayi tana fad'in shegiya sisi kud'inwa kuma zaki k'arema tanadi?, Dr Isma'il ya lumshe idanu danjin muryar Iman tadaki dodn kunnansa. Ta CE, "hello my hafsy bak'ya jinane?. Shiru Dr Isma'il yakasa amsawa, bayason ya amsa ta Yankee wayar, gashi shikuma bai gaji d'ajin muryartaba. Iman ta Yankee wayar tana fad'in inaga bata jina, kokuma bataso mai wayar ya ganota, kai ALLAH yashiryamin ke my Darling sis... Kiran Number yayi bugu d'aya aka d'auka, hasnfree yasaka sanan yabama Musayeef wayar.. Cike da d'oki Musayeef ya ce, ''aunty maa!.. Ajiyar zuciya ta sauke, ta CE, " habawa yaro babu wani aunty maa, aii mun 6ata. Tuni fuskar Musayeef ta Nuna alamun damuwa, ya CE, "yi hak'uri aunty maa mu shirya. A'a nikam babu wani shiri dazamuyi, bakana ganinaba d'azu amma kabi daddynka. Duk maganar dasukeyi Dr Isma'il yana jinsu. Musayeef yafara kuka yana fad'in Aunty maa bazan sakeba, mushirya. Shiru tayi na minti biyu.... Tabud'e Baki zatayi magana saitaji muryar Dr Ismail tadaki dodon kunnenta, Aunty maa plzz kiyi hak'uri mu shirya, gabantane yafad'i rasss. Yakuma cewa plzzzz!!, yanda yaja pls d'in saida tsigar jikinta ta tashi. Akasalace ta CE, " na hak'ura, wani ihun murna Musayeef yasaki, yatashi yana tsalle akan gadon, iman dake jiyo ihun Musayeef da tsallensa sai a bin yabata dariya, tashiga k'yalk'yata dariya, tama manta da Wanda yake kusadashi. Shikam Dr Isma'il tuni wutar dake taimakawa jikinsa aiki ta d'auke d'ifff, dariyar iman bak'aramin sakashi a shauk'i tayiba, yashala sosai a saurarenta. Ta ce, "ALLAH ya shirya minkai Musayeef tafad'a muryarta na rawa alamar har yanzu dariyar Tana cinta, Dr Isma'il ya CE, " amin ya rabbii. Gabantane yafad'i dama har yanzu yana rik'e da wayar?, da Sauri ta Yanke wayar tana dafe k'irji. Dr Isma'il yabud'e Baki zaiyi magana saiyaji d'if, alamar an Yanke. Musayeef yakara kunnensa zaiyi magana yaji shiru, yafara Kiran Aunty maa!, amma yaji tsit. Akasalace Dr Isma'il ya CE, "ta kashe Musayeef.... Aii kafinma yak'arasa Musayeef ya kware Baki yana kuka, lallashinsa yafara yi amma fir yak'i, shi sai ank'ara kiranta, dole Dr Isma'il yashiga kiranta amma tak'i ta d'auka. Ga musayeef sai kuka yake masa, test yay mata kamar haka. *plss My live!, kid'auka wlhy Musayeef kuka yakeyi saboda kin kashe, Dan ALLAH badan Niba* Iman tana kwance, tunda ta Yanke wayar, duk kiran dayakeyi tana kallo amma tayi burus da wayar. Shigowar sak'o yasa ta d'auki wayar, bud'ewa tayi ta karanta. Itama saita tura masa kamar haka. *kayi banza dashi idan yagaji zaiyi shiru aii* ta tura itama. Cikin hanzari yabud'e sak'on Dan kukan Musayeef yafara damunsa. Yad'an cije le6e sanan Yakuma tura mata *Dan Girman ALLAH fa nace my live!* Sanin girman ALLAH yasa ta yarda zata d'aga, kiranta Yakuma yi, saida takusan tsinkewa sanan tad'aga, hansfree Yakuma sakawa sanan yabama musayeef yana fad'in ishirunka my darling ga aunty maa d'in. Da Sauri yakara akkune yana sauke ajiyar zuciya, iman ta CE, " oh kai Musayeef saboda na kashe waya katasa daddynka gaba kana masa kuka?, To mikakeson kafad'amin?. Musayeef yasake share sauran hawayen fuskarsa, ya CE, "aunty maa kizo ki koyama daddy game. Azuciyarsa ta CE, " kaji kuma wata fitinar, yakatseta da fad'in kinji aunty maa. Musayeef inbada rigimadai yanzu yaza ayi nazo na koyama dadynka game, bakaga dare yayibane?. Yafara tirza k'afa alamar zaiyi kuka, da Sauri Dr Isma'il yamaida maganarsa zuwa turanci, ya CE, "pls my live kice MASA zakizo, in ba hakaba kukan zai k'arayi. Iman tace to kajirani ganinan zuwa yanzu. Cikin murna ya CE, " to aunty maa. Iman tayanke wayar tana fad'in musayeef rigima kenan........ *luv u oll my fan's* *((S))......2017* [8/6, 6:01 PM] mrs bilkisu: *_BAN SAKETA BA!!_* *_NA Bilyn Abdul_* _sadaukarwa_ *ya Abdul (city phone's)* https://mrsbilkisa.blogspot.com *Miyakamata nayi?* _kizama mai hak'uri arayuwa, mai tausayi Gana k'asa dakai, mai girmama manya, mai adalci, mai kunya, mai gudun zunubi komai k'ank'artarsa, mai gudun cutar dawani koda akan rashin Sanine, mai imani, mai gudun k'arya, mai Neman ilimi, mai yawan bautama ALLAH, mai yawan tsoron ALLAH._ _idan karik'e narik'e kika rik'e kuka rik'e, muka rik'e, inaga ZAMU zama cikin ceton fiyayyan halitta *ANNABI MUHAMMADU* tsira da aminci suk'ara tabbata agareshi._ *ALLAH yasa Mugabe* *(Page 19)* Koda suka gama wayar sai iman ta lumshe idanu, tareda rungume wayar ak'irjinta, jitake wani dad'i yana ratsata Wanda batasan dalilinshiba. Bata tashiba har saida deeni yazo yakirata sanan taje kiran. A6angaren Dr isma'il ma hakan take, tsintar Kansa yayi cikin tsananin farinciki Wanda yadad'e baiyiba, yayma musayeef wanka sukai shirin barci, haka ya rungume d'ansa sukasha barci mai dad'i abinsu. _washe gare_ Dr Isma'il dakansa yayma Musayeef wanka, dayake ana yawan kawoshi gidan sai yakasance akwai kayansa, tawul ya d'aura masa ya ce, "maza kaje wajen mom tasaka maka kaya. Dagudu Musayeef yanufi 6angaren su deexerh, Dr Isma'il yay murmushi yana binsa da kallo harya 6acema ganinsa. Ido yalumshe tareda zama bakin gadon, wayarsa yad'auka yafara sarrafata cike da k'warewa, haka kawai yaji yanason jin muyar Iman, yad'an dad'e yana tunanin idan ta d'auka mizaice mata, can yay wani tunani murmushi yayi tareda dialing d'in Number ta. Alokacin iman na zaune tana maida numfashin gajiya, bayan tagama gyaran gidan duka tahad'a musu abin Karin kumallo. Tabud'e idanu tareda fad'in wake kirana?, ko Reefat CE?, ko xox.......shiru tayi takasa k'arasawa Dan ganin number dake kiranta, tun adaren jiya ta haddace No d'in. Wayar ta Yanke, Dr Isma'il yad'an cije le6e yana fad'in pls my live karkimin haka, yana maganar yana k'ara kiranta, yanzuma saida takusa k'atsewa sanan ta d'aga Dan atunaninta ko Musayeef ne. Assalamu alaikum tafad'a tana zama abakin gadon, shiru na 'yana sakwanni, Dr Isma'il yakasa amsawa, bayaso yaymagana taji muryarsa ta Yanke. Ta ce, " Musayeef Baka jinane?. Muryarsa a sark'e ya ce, ''ba Musayeef bane daddyn sane, amma pls karki Yanke, zamuyi maganane Dan ALLAH. shiru iman tayi tana sauke numfashi ahankali, muryar Dr Isma'il tana ratsata, azuciyarta ta ce, "bama saika rok'eniba Nima bazan iya kashewaba Dan bangaji dajin sautin muryarkaba. Jin tayi shiru yasa yafara magana ad'an d'arare, my live kin bani dama?. Iman ta lumshe idanu, sanan ta ce, " kafid'i maganarka idan ba hakaba zan kashe. No my live pls karki kashe. Batace komaiba sai ma kwanciya datayi visa gadonta. Ya ce, "my live bakifa gaisheniba?. Ajiyar zuciya tayi ta CE, " INA kwana?. Lfy lau Rayuwata!, kin tashi lafiya. "Lau." Tafad'a atak'aice. Ya ce, "baki tanbayeni Musayeef ba, kobakiyi missing nashibane?. Karo nafarko datayi d'an murmushi, muryarta can k'asa ta ce, " idanma nayi yazanyi, tunda ka d'aukeshi. Ya lumshe idanunsa shima yana murmushi, a'a idan kinason ganinsama yanzu saina kawo mikishi. Humm na hutash sheka, kabarsa cikin 'yana uwansa suma suna buk'atarsa sosai. Dr Isma'il yagyara kwanciya danjin yanda Iman ta saki jiki dashi, aikema kina buk'atarsa, saboda kin dad'e baki gansaba. Hakane tafad'a tana k'ara rungume fillo ak'irjinta, nasan nayi missing NASA sosai, amma ai suma suna buk'atar kasancewa dashi, ni nikad'aice sukuma sunada yawa, so kaga sun rinjayeni sosai. Ya saki wani lallausan murmushi Toni Nazo kiganni. "A'a". Miyasa ni ba'a son ganina?, kodanni ba d'anki bane?. 'Yar dariya Iman tayi tana juya kwanciyarta, nidai ban fad'aba. Yanda take dariyar dukta kashe MASA jiki, ya ce, " kenan Nima ana missing d'ina?. Ido tawaro waje tamkar yana gabanta, ta ce, "mizaisa nayi missing NAKA nikam?. Maganarta yad'an ta6a zuciyarsa amma ya danne tunda Neman sulhu yakeyi da ita, ya ce, " amatsayina na daddyn d'anki!, masoyinki na har abada. Shiru Iman tayi hawaye suna bin kumatunta, bata sharesuba bakuma tasake maganaba. Jin tayi shiru Dr Isma'il ya ce, "hello kina jina?. Muryarta dad'an rawa ta ce, " eh!. Yanda ta amsa masa yasa yagane kuka take, Dan yasan Iman da halinta sosai. Shima jiyayi kwalla ta cika MASA idanu, muryarsa a sark'e ya ce, "kema kinajin yanda nakeji ko Saudat, da akusa dani kike dakinji yanda zuciyata take bugawa da k'arfi kamar zata Faso k'irjina tafito, nayi kewarki sosai Iman, kullum sainayi wankan tsarki saboda barci danakeyi mai cike da mafarkinki, pls Saudat kigayamin gsky waya ya rubuta miki takardar sakin nan?, idan kece kifad'amin? zanmiki uzuree kuma zanyi yanda zanyi nagyara komai batareda asirinki ya tonuba, Dan ALLAH kifad'amin gsky, yak'are maganar yana hawaye. Kuka sosai Iman takeyi har yanajin shashshekarta. Suduka sunyi shiru kowa yana kuka, _(Nima masu karatu kukan nake saboda tausayinsu😭)._ 'Diff iman ta Yanke wayar tanacigaba dakuka, da bak'incin maganar Dr Isma'il, wato duk tsawon lokacinanma ita yake zargi ta rubuta tankard ar sakin?, itakam tashiga uku, tunda take ko alabaran Novel's bata ta6ajin makamancin labarintaba, lallai tana cikin rud'u. Ita tana ganin mijinta yasaketa, to Ashe shikuma kallon ita tarubata takardar sakin yake mata, shin wazata tambaya gskyar lamarin?, kodai da gsk Dr Isma'il *Bai saketa ba!* to waye yarubuta takardai?, Kokuma raina MATA hankali yakesonyi ne?. Ta kuma kecewa dawani matsanancin kuka Wanda itama batasan tanayiba. Da Sauri gwaggo tak'araso d'akin danjin kukan Iman, Innalillahi Iman bakida lafiya?. Batabama gwaggo amsaba sai ma fad'awa datayi jikin gwaggo tafashe da wani Sabon kukan mai tsuma zuciya. Lallashinta gwaggo tashigayi, itakuma tanata raira kuka, saida tayi mai isarta sanan tayi shiru, gwaggo tad'ago fuskarta tanamai share mata hawaye, iman miyasakaki irin wanan kuka haka?, ko wanine yamutu?. "Girgiza kai iman tayi alamar A'a". Tomiye yafaru?, kosaboda Musayeef d'in baya nanne?., nanma kai ta girgiza gwaggo tayi shiru tana kallonta, can ta CE, " to kifad'amin gsky, nasan dai ke bak'ya k'arya, dan haka gayamin mike faruwa?, koda taimakon dazan miki amatsayina na mahaifiyarki. Iman tasake matso hawaye tabbas tasan batada kamar gwaggo, sai kuwa yayarta aunty Salma, saiko su Xoxo da Reefat da ayanzu take Musu kallon 'yan uwa suma. Tagyara kwanciyarta ajikin gwaggo, ta CE, "gwaggo daddyn Musayeef ne, anan takwashe yanda sukayi tafad'ama gwaggo. Shiru gwaggo tayi tana nazari, zuwa can ta CE, " iman wlhy bazan 6oye mikiba koni lamarin nan yana d'auremin kai idan nayi la'akari da halin da yaron nan yashiga bayan kin dawo gida, nidai gani nake kamar akwai wani kulli dabamu saniba, agefe kuma zamanki agida yana cin zuciyata, burin kowace uwa taga 'ya'yanta agidan miji k'ark'ashin inuwar aure, Iman shekararki hud'ufa kenan agida, tun cikin Musayeef yana k'arami gashi yanzu harya Shiga makaranta. Kullum Burina ALLAH ya warware wannan *Sabon Al'amaree* kema ki zauna lfy agidan mijinki, in kobazaki koma can gidanba kiyi wani Auren amma kullum abubuwa sai k'ara nisa sukeyi Abu kamar wasa. Iman ta CE, "gwaggo wlhy nidai dankunk'ine amma dakawai kun yarda nayi aurena, nasan shima idan yaga nayi Auren zai daina fad'in *Bai sakeni ba* d'in. Mama ta sauke ajiyar zuciya iman har yanzu ke yarinyace shiyyasa, bazaki gane had'arin hakanba, dolene mucigaba da Addu'a har komai ya bayyana, idan muka baki dama kikayi aure bazamu sami nutsuwaba, zamu rink'a kokwanto kokinyi *aure akan aurene*, tunda mijinki ya CE, " *bai sakeki ba*, kullum yana kan bakansa na fad'in hakan. Tokinga kuwa akwai Matsala kenan. Nasiha sosai gwaggo tashiga yimata, ta CE, "tadage da yawan addu'oi, suma suna nan suna mata akullum, komai zai zama labari insha ALLAHU. Saida gwaggo taga tad'an kwantar da hankalinta sanan takama hannunta suka tafi dansuyi breakfast. A6angaren Dr Isma'il kuwa kuka yashigayi rirus tamkar mace ko k'aramin yaro, tuni k'irjinsa yayimasa nauyi, tun yana iya kukan har komai yatsaya, numfashinsa yafara fita dak'yar, yasa hannunsa yadafe k'irjinsa. Musayeef kam yana FIta da gudunsa yanufi 6angarensu deexerh, ak'ofar fallo yaci karo da daddyn deexerh, da Sauri yad'aukeshi yad'agashi sama yana fad'in my son yaushe kazo?. Mom d'in deexerh dake bayansa tana musu dariya ta ce, " tun jiya aii yana nan, sunzo shida Isma'il da daddare Baka dawoba. Okey tafad'a yana sumbatar kumatun Musayeef, yarona INA momy?. Da hannu Musayeef yanuna mom d'in su deexerh. Dariya yayi a'a ba wannan nake nufiba mom d'inka..... Mom d'in su deexerh tak'atsemasa zancen dafad'in a'a aii Aunty maa zaka CE masa, in ba hakaba bazai ganeba. Dariya Yaya yayi, ya CE, "nikam sunann yana bani dariya wai aunty maa, nifa nama k'asa fassara ma'anarsa. Dariya itama tasakeyi ta CE, " yaro kenan shi INA ruwansa bayaji deeni yana cemata aunty ba, shikuma bazaice auntynba kad'ai bakuma zaice mamaba shine yahad'a gabad'aya yana fad'a aunty maa ko Musayeef?. Musayeef yay 'yar dariya Dukda ba gane maganganun su yakeba gaba d'aya. Shima dady dariya yayi ya CE, "to INA zaka make gudu?. Da Sauri ya CE, " daddyne ya CE, "nazo mom tasamin kaya, okey yaron mom to jeka, yafad'a yana mik'a matashi, amsarshi tayi tana dariya suka nufi d'akinta. Kowa ya hallara a 6angaren mama za'ayi break amma babu Dr Isma'il, Yaya ya CE, " Marwan tashi kakira mana Uncle d'inku, ko ya mantane ana jiransa. Marwan yamik'e yana fad'in to daddy. Da sallama yashiga ganin babu kowa a falon yasashi shigewa cikin bedroom d'in. Da Sauri yak'arasa bakin gadon danji Dr Isma'il yana sauke wani irin numfashi. Dagudu yakwaso yayi 6angaren mama yana kwala kiranta daddy! Daddy!! Kazo uncle zai mutu.... Aii tukafin ya isoma kowa yamik'e, ahanya suka had'u suka koma 6angaren Dr Isma'il, Yaya baijira komaiba ya cicci6eshi shida mom d'in su deexerh sukayo waje, amota suka sakashi sai asibiti........ *(Kai masu karatu INA tausayin Dr Isma'il wlhy,😭yana shan wahala)* *luv u oll my fan's* *((S))......2017* [8/6, 6:01 PM] mrs bilkisu: *_BAN SAKETA BA!!_* *NA Bilyn Abdul* _sadaukarwa_ *ya Abdul (city phone's)* https://mrsbilkisa.blogspot.com *miya kamata nayi?* _Duk wanda yace shine tofa bashi bane, idan ALLAH yay maka wata d'aukaka kada kazama mai wulak'anta mutane, kada kazama mai Girman kai, kada kazama mai izgilanci, kada kazama mai fankama da fad'i._ _dum abinda kasamu anan zaka barsa, duk girman d'aukakarka daga randa tauraranka yadishe kazama labari, 'yan kanzaginkama gudunka zasuyi, dama wasu ba k'aunarka sukeba, saboda d'aukakarka suka ra6eka_ _d'aukaka bakomai bace 'yan uwana, ita tamkar rana take, sanda ta haskaka kowa zai ganka, data dishe ka kasance cikin duhu sai kowa ya fara neman wata._ _Kigane nagane Mugane, mugyara kodan tsira awajen ubangijin talikai._ *ALLAH yasa mu gane* *(page 22)* k'arfe 5:00pm Xoxo tashigo asibitin, wayar deexerh takira tafito ta tareta. Cike da farinciki suka rungume juna, hannunta taja suka nufi d'akin da aka kwantar da Dr isma'il, danya farka, su yayama sunje gida, daga deexerh sai marwan aka bari a asibitin kafin Yaya yadawo sukuma su tafi. Lokacin dasuka shigo Dr Isma'il yana zaune akan sallaya ya idar da sallah yana addu'a. Guri suka samu suka zauna, marwan suka gaisa da Xoxo, suna 'yar hirarsu k'asa2 da deexerh, Dr Isma'il ya idar. Tasowa yayi Yakoma kan gadonsa yana murmushi, k'awarmu kece?. "Murmushi Xoxo tayi itama, wlhy kuwa nice daddyn Musayeef, Ashe kuma abinda yafaru kenan?. Wlhy kuwa k'awarmu. To yajikinka?. Jiki alhmdllh. Yagajiyar ranar?. Tayi 'yar dariya aikai za'a tambaya gajiya daddyn Musayeef kaida ka tuk'omu. Baice komaiba sai murmushi dayayi. Wayarsace tafara wringing, da Sauri marwan yad'auka yabashi, akunne yakara yana murmushi, Nabeel ykk?. Lfy lau abokina, gani a k'ofar asibiti. " kai haba da gsk?." "Wlhy kuwa Kasan bazan iya hak'uriba sainazo na ganka." Tom ga marwan nan zai shigo dakai. Marwan jeka shigo da Dr Nabeel. Okey uncle, marwan yafad'a yana mik'ewa. Bayan kamar minti hud'u suka shigo da sallama, su deexerh suka amsa, Dr Nabeel yak'araso gaban gadon, ayya abokina karame sosai wlhy, ya jikinka?. Dr Isma'il yay murmushi, Alhmdllh Nabeel. Su deexerh suka gaidashi, shi saima yanzu ya lura dasu, bakinshi nad'an rawa yanuna Xoxo, nikam a INA nasanki🤔. Xoxo tayi murmushi, amakarantar su jman, lokacin dakaje d'aukar daddyn Musayeef. Yes hakanefa. Murmushi Dr Isma'il yayi, danganin yanda abokisa ya waske, tunfa ranar yake damunsa akan yana son Xoxo, ya musalta masa kamanninta, shiyyasa randa ya d'akkosu kallo d'aya yaymata yaganeta, amma yanzu jiba yanda yanuna yama manta Inda yasanta. Daga nan fira suka farayi sosai, Xoxo data d'ago saisu had'a ido da Dr Nabeel, ita kunyarma kallon dayake mata takeyi, duk ya wani tsareta da mayun idanunsa. Xoxo takalli agogon hannunta, kai deexerh bari nawuce dare yafara yi, daddyn Musayeef ALLAH yak'ara lafya. Amin hafsat ngd sosai, Dan ALLAH kigaidamin 'yan gidan. Zasuji insha ALLAHU ngd Nima. Dr Nabeel ya mik'e, abokina bari nayi rakkiya ko, yafad'a yana kanne ido😉. Dariya Dr Isma'il yay yana jinjina kai. Suna fita wayar deexerh tahau wringing, kallon Number tatsayayi Dan bata ganeba. Har wayar ta yanke aka k'ara kira sanan ta d'aga da sallama. Assalamu alaiki gimbiya, muryarsa ta daki dodon kunnenta, ajiyar zuciya tasauke, tareda fad'in wa'alaikassalam. Humm kin manta dani ko?. Aiini bamma ganekaba deexerh tafad'a tana d'an murmushi. Oh God sorry, Sunana Umar farukh, Wanda muka had'u a asibiti. Okey nagane. Yauwa to ykk?. Ina lfy. Masha ALLAH. Dan ALLAH idan bazaki damuba inason kawomiki ziyara gidanku gobe idan ALLAH ya kaimu. Kai Haba malam daga had'uwa sau d'aya saikuma zuwa gida.......katseta tayi da fad'in pls gimbiyata, ke mai ajice bakidace da afad'amiki ana sonkiba awaya, dole sai anbaki girmanki zuwa gida. Murmushi deexerh tayi, shikenan gwanin dad'in Baki, zan turomaka address d'in. Babu dad'in baki komai nafad'a akanki gsky ne, ngd sosai saina jiki. A6an garden su Xoxo ma kusan hakan take, kiran deexerh da akayi awaya yayma Dr Nabeel dad'i, Dan gani yake yasamu damane. Yakalleta cike daso da k'auna, 'yammata nifa kinmun sata wlhy. Ido Xoxo tazaro😳sata kuma malam?. Yes yafad'a yana wani lumshe idanu, Xoxo ta had'e fuska kai malam banason sherifa, wanan idan wanima yaji aisai yazata gskyne? To aii gaskyar CE kedama kin zata wasa nakeyi. Mtsowwww malam bani hanya na wuce kaji, humm aii bakida damar tafiya saikin bani madadin abinda kika satar min, kokuma namiki ihu. Harararsa tayi, tokayi ihun mana, ya ce, "kin yarda kenan?. Banza tayi masa Dan yafara bata haushi, wayarta tad'akko tafara danna Kiran iman, fisge wayar yayi ya yanke kiran, 'yammata saifa kin saurareni. To tunda ana dole basai muganiba. Dariya yayi sosai, zan kar6i number ki wajen khadija zan gaya miki satar dakikamin, sanan kijira zuwan rundunar sojoji gidanku kar6ar madadin satar dakikamin.. Daidainan deexerh ta k'araso, yamik'a mata wayarta tareda fad'in sai kinjini, kud'i yad'akko yabama deexerh, khadija ga wanan kibama bak'uwarmu tahau mota. Deexerh ta rissina ta kar6a tana fad'in to uncle angode. Xoxo kan gaba tayi bata tanka musuba. Hannu yasaka a aljihu yana binsu da kallo har suka 6ace sanan Yakoma cikin asibitin yana murmushi masifar Xoxo. Dr Isma'il ya kallesa kai abokina duk kawani rud'e wlhy. Dariya Dr Nabeel yayi, badoleba abokina soyayya aii ba k'arya bace. Hakane Dr Isma'il yafad'a yana murmushi. Deexerh ta ce, " aunty hafsat Kodai Kodai keda uncle Nabeel ne?. Kodai2 me Xoxo tafad'a tana zaro ido😳. Dariya deexerh tayi, naga kamar sonki yakeyine?. Tab rufani ki sayani, ko d'aya tafad'a tana tare adaidaita sahu, saida tashiga sanan Deexerh tasaka mata kud'in da Dr Nabeel yabata a jaka, toga k'yautarki. Tab nifa bazan kar6aba ki maida masa kayansa. Habadai ai ba'a maida hannun k'yauta baya, ngd sosai kigaidamin mutan gidan. To zasuji mai adaidaita yaja suka wuce deexerh na d'aga mata hannu. Iman kuwa tunda suka bar asibitin tazama wata shiru2, koda suka koma gidama d'aki tashige tayi shiru, sallah kaiwai ketashinta, wajen k'arfe 6 taji wayarta tad'anyi wringing, d'auka tayi taduba, saitaga Xoxo, tayi murmushi 'yammata ni kikema flashing?. Komawa tayi takwanta, ganin xoxo bata sake kiraba yasa ta tashi, d'ari biyu ta d'auka tafice. Deeni na zaune afalo yana cin abinci tabasa, deeni idan ka gama Dan ALLAH d'an siyo min kati. To aunty, Dan ALLAH Nima d'an bani d'ari, inada d'ari nacika nasiyo katin, data nakeson saya. Hararasa iman tayi, kai Dama kud'inka aii a sayen data zasu k'are, ALLAH ya shiryeka. Amin aunty, nidai idan zaki bani aii babu matsala. Fita tayi bata tanka masaba, babu dad'ewa tadawo da d'ari biyu ahannu tabashi. Kai my aunty ngd, shiyyasa wlhy nake k'ara sonki. Iman tayi murmushi kawai takoma d'aki ta kwanta. Babu dad'ewa yakawo mata katin tasaka. Saida tafara gwada Number Reefat, har yanzudai bata Shiga, afili ta ce, "ALLAH yasadai lafiya. Xoxo takira bugu d'aya ta amsa, suka gaisa cike da kewar juna, Xoxo ta ce, " ai d'azu naso na kiraki nace miki INA wajen mijinki, saikuma aka samu matsala. Aii flashing d'inki Dana ganine ma yasa nakira da fushi nakeyi dake. Ohh my sis.... Kiyi hak'uri, wlhy zanzo gobe idan ALLAH ya kaimu insha ALLAHU, wani abunema yahana in zuwa jiya da yau. To shikenan na hak'ura, kinsan bana iya fushi dake, ALLAH ya kawoki lfy. Amindai, Wai Yaya kema har yau bakya samun Reefat?. "Wlhy bana samu, ni harma nafara tunanin ko lafiya?, wlhy Nina haka, to ALLAH yajishemu alkairi. " Ameen dai". Sukai sallama kowa ya kashe wayar. _Bayan kwana hud'u_ Jikin Dr Isma'il yayi sauk'i sosai harma an sallamesa yau. Iman dai bata sake zuwa dubashiba, bakuma takira wayarsaba, gwaggo da Abbah sunje har sau uku, hakama su aunty salma sun sake zuwa, Xoxo ma tak'ara zuwa. To Dr Isama'il ALLAH yak'ara sauk'i. *_WATA SABUWA_* Gidan su Dr isma'il yau cike yake da mutane, dangin mahaifinsu ne sukazo dubashi, ciki kuma harda baban su aunty sadiya, bayan anci ansha aka zauna ana hira. Acikin hirarne kawu Falalu yake fad'in sufa dawata magana sukazo, mama ta ce, "to falalu muna saurarenka. Kawu falalu yagyara zama yana kallon mama, ya ce, " maganace akan Sama'il, lokaci yayi daya kamata yayi aure, wanan zaman dayakeyi bazai haifar da d'a mai idoba, tunda kowa yasandai ba'a komawa saki uku, to Dan haka yama fidda rai akan matarsa, saidai idan darabon zama nan gaba zasu zauna. Hakane mama tafad'a fuskarta babu walwala, Dan tasan Dama ba alkairine yakawosuba. Kawu falalu yacigaba, to yanzu dai mun yanke shawara Nida Lurwanu da Maharazu, da Karima akan zamu k'ara k'ulla zuminci, mudai nida maharazu da Karima bamuda yara mata, sai Lurwanu, Dan haka muka Yanke shawarar aurama Sama'ila Zakiyya,(Raihan). Gaban Dr Isma'il ne yafad'i da Sauri yad'ago yana kallon kawu falalu. Kawu falalu yacigaba da fad'in, to yanzudai maganar damuke muku, ni na biya sadaki an d'aura auren tun a can, shinema dalilin dayasa kukaga mun taho da Raihan, gata nan munkawota suzauna lafiya, ga 'yar uwarta nan intayi ba daidaiba zata ringa tsawatar matane, kumadai saiku kula, intayi ba daidaiba a gyara mata Dan kunsan yarinyace karama sai hak'uri. Tunda yafara maganar falon yakarayin tsit, bakajin motsin kowa, sai aunty da Raihan Dasuke murmushi. Yaya ya bud'e baki zaiyi magana mama ta girgiza masa kai alamar yayi shiru. Shirun kuwa yayi amma idanunsa sun cika da kwallah, tu da mahaifinsu suka bar duniya, dangin mahaifinsu suka watsar dasu, basa kulawa dasu ko kad'an, basa zuwa Inda suke, har saida sukaga sun girma sun zama wani Abu, shine akazo aka k'ak'aba masa auren sadiya, zuwan sadiya baifi da wata ukuba uwar 'ya'yansa tabar gidan mamansu deexerh. To gashi kuma yanzu an mannama Isma'il Raihan, bayan abaya mahaifiyarta ta CE, "bata yarda Isma'il ya auri Raihanba baza'a tara mata 'ya 'ya agida d'ayaba........ Maganar mama ta takatse masa tunani. Shikenan falalu, mun amshi k'yautarku ALLAH yasanya alkairi, saidaifa kunyi kuskure Dan yakamata kafin kuyi Auren kukiramu asanar damu Dan aji tabakin Isma'il d'in, amma yanzu ya wuce saidai Atari gaba kawai. Baban su raihan ya katse mata zancen da fad'in, Maryama kinsandai munada iko da Sama'ila muma ko?, Dan duk duniya bashida iyayen dasuka wuce mu, ko Neman auren zashi wani waje dolene mune wakilansa, to tunda abin yazama na gida kuwa aikinga koya sani ko bai saniba, koya yarda kobai yardaba dolene yakar6i 'yar uwarsa yarik'e da hannu biyu, kuma naga dama suduka suna son juna daga sama'ilan har Raihan d'in, kawai abaya ALLAH ya rubuta bazata zama matarsa bane. Kaga Lurwanu nifa babu abinda nace maka, Dan haka maganarnan bata 6acin rai bace, aurene kun d'aura kuma nace mun kar6a, to saime?, duk wata maganarma kun Isa bata tasoba, Inda bama ku isanba aii wlhy babu mai aurama yarona aure batareda yardarsaba. Sunsan halin mama sarai Dan haka suka Shiga bata hak'uri da magana mai dad'i, anandai ka masu Dr Isma'il nasiha shida raihan. Deexerh taji zafin wanan had'in ammafa tawani 6angaren taji dad'i, Dan idan bata mantaba aranda suka Gana da bilyn Abdul tace musu inama Raihan ta Auri Uncle, da komai saiyafi saurin fitowa fili. Wanan yasa bataji haushiba sosai. Saidai ana gamawa da uncle d'inta aka dawo kanta. Kawu Maharazu ya ce, "kema hadiza mun Baki nan da wata Biyar Kodai ki fito da mijin aure kokuma muhad'aki aure da Kamilu na wajena. Ido deexerh ta zaro ta ce, " kawu Kamilufa kace?. Eh shifa nace, Dan haka saikiyi gaggawa..... Dr Isma'il ne ya katse masa zancen da fad'in a'a kawu nanfa ba huruminku baneba, domin khadija jikace agareku, mune iyayen khadija mu Muke da damar aurar da ita lokacin da mukaso, ayanzu kuma karatu takeyi, sainan da wata Tara zata kammala, saikuma ta kammala sanan zamuyi mata maganar aure, mudai damuke 'ya'yan d'an uwanku, Duk abinda kukaga dama kuyi damu, saboda darajar kun kasance jinin mahaifinmu na kusa..... Sama'ila mukake gayama haka Dan ubanka, to ai ko Mahammadu dayanada rai bazai fad'amin hakaba akan zuri'arsa...... Mama ta katseshi, Maharazu gskya fa Isma'il yafad'a bakuda hurumin za6ama hadiza miji, sudai dasuke 'ya'yanku zaku iya amma banda su hadiza jikoki. Ehh lallai maryama aii dama duk wata wuta kece kike kunnata tsakaninmu da yarannan, kece kikasaka basa ganin darajarmu, wanan mugun halin naki yasa Karima ta CE, "bazata biyomuba. 'Mama tayi wata 'yar dariya, Maharazu kenan, aiini duk abinda zakuce dangane da yarannan banida Matsala daku'. Kundai San inada iko dasu, todan haka maganarma ina 6ataku agunsu aii daga baya kenan, Dan tuni sukasan matsayin su agunku. Haka aikata cacar Baki, daga bayadai Yaya yashiga tsakani aka sulhunta. Washe gari su kawu lurwanu suka koma............. _to masu karatu koya Iman zataji wanan labari?,._ _Yaya zaman Raihan da Dr Isma'il zai kasance?._ _shin auren Raihan zai kawo mafita dangane da matsalarsu Dr Isma'il da Iman, kamar yanda Bilyn Abdul tafad'ama su deexerh?._ *humm kubiyoni danjin yanda zata kasance* *luv u oll my fan's* *(((S)).....2017* [8/6, 6:01 PM] mrs bilkisu: *_BAN SAKETA BA!!._* *NA Bilyn Abdul* _sadaukarwa_ *ya Abdul (city phone's)* https://mrsbilkisa.blogspot.com *miya kamata nayi?* _babu nakasashshe sai kasashshe, babu maraya sai rago._ _Karka zauna kadogara dawani, kadage kidake munemi nakammmu, addini yana ingantuwa idan masuyinsa suna cikin natsuwar wadata, ba tarin dukiya bane wadata, wadar zuci itace wada, komin k'ank'antar abinka ka rungumeshi kasaka masa albarka, kahangi na k'asa dakai, kada ka hangin nasama dakai, kagodema ALLAH dakad'an d'in daya Baka, duk Wanda yakasa Gode kad'an koya samu mai yawa bazai godeba._ _Duk Wanda yagaza godema ALLAH to kuwa zai godema azabarsa._ *ALLAH yasa Mugabe* *(Page 21)* Ya Majeed nagaba, hannunsa rik'e da affan, aunty salma tana bayansa, iman CE ak'arshe, tafiya take tamkar wadda kwai ya fashewa aciki. Saida suka shigo cikin asibitin sosai sanan ya Majeed yad'auki wayarsa yayikira, assalamu alaikum. Eh gamu mun iso, okey. Juyowa yayi yace kumuje nama gane d'akin. Ak'ofar wani d'akin suka tsaya ya Majeed ya kwankwasa, sanan yatura da sallama suka Shiga, d'akin cike yake da mutane, aunty salma da iman suka shigo, sannu dazuwa aketa musu, itadai iman kanta yana k'asa bata kalli kowaba. Jitai an rik'e hannunta da Sauri tad'ago danson ganin waye, deexerh tayi dariya my aunty nabaki tsoro ko sorry. Ido iman tazaro sai yanzu ta fahimci Wanda sukazo gani..... Deexerh ta k'atsemata tunani da fad'in kai auntyna naji dad'in zuwanki wlhy, murmushin yak'e tayi suka k'arasa, su aunty sunata gaisawa da mutane datanbayar mai jiki. Iman ma ta daure ta ce, "INA yininku, yamai jiki?. Gabad'aya aka amsa, Dr Isma'il dake a jingine da fillo, 'yan biyu sun sakashi tsakkiya, yasaki wata wawuyar ajiyar zuciya saboda ganin Iman. Gaba d'aya d'akin aka maida kallo gareshi, ganin wadda yake kallo yasa suka dawo da kallonsu kanta, babu Wanda yagane Iman da farko, saboda ta lull6e fuskarta da gyale. Mama ta ce, " hadiza wacece wanan?. Dariya deexerh tayi, lallai mama kindai k'ara tsufa wlhy, to aunty Iman CE, ta janye galen iman. Mama ta mik'e da sauri ta Isa Inda suke, hannun iman takama tana mai jin dad'in ganinta, iman 6oye mana kanki kikeyi?. Cike da kunya iman ta rusina tana gaida mama, mama ta rungumeta haba iman duk kin manta damu, Yaya da mom deexerh sai murmushin sukeyi, amma aunty tuni nasaka mata alamar tambaya, Dan afirgicema take kallon iman d'in. Mama takama hannun iman taje ta zaunar, harga ALLAH tana tsananin k'aunar iman domin yarinyar kirkice, k'addarace kawai tarabasu Dan basuda yanda zasuyi. Iman ta rissina tana gaidasu Yaya, cike da fara'a suka amsa, Yaya ya ce, "iman kin manta damu ko?. A'a Yaya wlhy karatune. Da k'yau, yanzu kina level nawa?. "Ina level 3, iman ta amsa kanta ak'asa. Lallai Iman kun zama manyan 'yan boko, murmushin tayi batareda tace komaiba. Ya Majeed ya ce, "zadai su zama nagaba kad'an, aii sun d'akko hanya Majeed Yaya yafad'a yana dariya. Iman tad'an kalli Dr Isma'il ta ce, " INA yini, ya jiki?. Dr Isma'il dake zaune ya dasa mata idanu ko k'yaftawa bayayi, ya sauke ajiyar zuciya ahankali ya ce, "da sauk'i ykk?. Shiru tayi bata amsaba, deexerh dake gefe sai zabga murmushin take, jitake inama har yanzu Iman tana tareda Uncle d'inta. " gsky lokaci yayi dazata taka rawar gani wajen binciko gskyar Al'amaree, amma zata nemi Xoxo akan shawarar dasukayi ranar na nema *bilyn Abdul*, ance tashahara wajen irin wanan aikin, akwaita da naci wajen nemo rahoto, insha ALLAHU zasu nemeta kuma ko nawa takeso zasu biyata taimusu aiki, itadai Uncle d'inta yasamu farinciki. Marwan da Musayeef suka shigo d'akin da sallama, Dama basanan an aikesune. Yana hango mamansa yasaki hannun marwan ya cilla da gudu ya rungume iman, aunty maa yaushe kikazo?. Kansa ta shafa tana murmushi, yanzu nazo Musayeef. Aunty maa kinzo ganin dadyna bashida lafiya?, kai tad'aga masa kawai, Yakuma fad'in danfa bakizo kin koya masa game bane ranar, yake rashin lafiya ko daddy?. Kai Dr Isma'il ya d'aga masa alamar eh. Yadawo da kallonsa kan iman, ni babu ruwana dake, yafad'a yana ja da baya tareda turo Baki. Mutuwar zaune iman tayi, a zuciyarta ta ce, "kajimin yaro zai d'aureni azaune. Yaya ya ce, " a'a my son aii ba'a 6atawa da uwa, zonaji miya faru?. Wajen daddynsu deexerh yanufa, Iman Addu'a take ALLAH yasa kada yafad'a tasan shegen surutun Musayeef. Wayonsa ya girmi shekarunsa. Yaya ya CE, "miya faru kaida aunty maa d'in kake fushi da ita. Dady ba ita bace, nasa daddyna yakiramin ita na ce, " tazo takoyama daddyna game, ta ce, "zatazo amma tak'i zuwa. To kayi hak'uri ai yanzu gata Tazo zata koya masa Kaje Ku shirya. Musayeef ya kalli iman, aunty maa wai zaki koyama dadyna game d'in?. Ganin yanda Dr Isma'il ya tsareta da idanu yasa ta gyad'a kai alamar eh, tsallen murna yafarayi. Yanufi dadynsa, hannun yasa ya d'auki d'aya daga cikin wayoyinsa dake gefensa yakaima Iman, to gashi zoki koya masa, idan mun koma gida sai muringa yi nida shi. Iman ta ce, ''kaga yanzu bashida Lafiya kabari saiya warke sainazo har gida na koya masa. Ehumm ehumm!, Musayeef yafad'a yana nok'e kafad'a da kya6e fuska😞. Iman tayi banza dashi Dan taga rigimarsa bamai k'arewa bace, yakware Baki zaiyi kuka. Da sauri mom d'in su deexerh ta ce, " kaga ishirunka yarona zata koya masa, jeka bata wayar. Jin anfad'i haka yasashi saurin kallon Iman, ta had'e fuska tana harararsa, yaja da baya yana hawaye. Dr Isma'il dake kallonsu saidai babu magana, sabida baya iyawa sosai, ahankali ya ce, "pls My live ki kar6a.. Dukda ahankali yayi maganar duk sunji abinda yace, aunty tana siririn tsaki Wanda basu jitaba. Hannun iman tamik'ama Musayeef ya d'ora mata wayar daddynsa ahannunta, yana dariya ga hawaye afuska. Aunty Salma ta ce, " hum su Musayeef rigima. Hannun Iman ya hau ja yana fad'in ki tashi to kinji aunty maa, kinji!. Mama ta CE, "ohni maigida kabi ka hanamin d'iya zaman lfya, kabarta ta huta Dan ALLAH. shidai kira yake kitashi kinji aunty maa. Marwan yay dariya, aunty Iman idanfa baki koya game d'innanba yau kinga takanki wlhy, garama kawai ki koya. Murmushi iman tayi ta ce, " Dan ALLAH marwan ka d'aukeshi kufita ALLAH dukya isheni. Harararta Dr Isma'il yayi, yakamo hannun Musayeef, ahakali yake magana, kaga Musayeef zokaji wata magana, deexerh ta d'auki Musayeef tad'ora kangado Kusada Dr Isma'il, akunne yafad'a masa maganar tuni Musayeef ya washe Baki yana Murna, yakalli iman yay mata gwalo ummmeeh 😛bazamu da aunty maa ba kuma. Gaba d'aya d'akin akasaka dariya, banda iman da Dr Isma'il dasuke murmushi. Aunty tamik'e zatafita itama batayi dariyarba, Yaya ya ce, "INA zaki? Zan siyo kati ne tafad'a tana tafiya. Yanzu nan ga Marwan ga Khadija bazaki bama wani yasiyo mikiba sai kinje da kanki?. Na hutar dasu tafad'a tana ida fita girgiza kai Yaya yayi Dan halin sadiya yafara isarsa, kwata2 bayajin dad'in zama da ita, sauk'inma ba ita kad'ai gareshiba aii datuni shima ciwon zuciyar ya kamashi. Deexerh tafaki idon kowa ta fice, Iman CE da Marwan kawai sukaga fitarta. Aunty nazuwa wani d'an lungu taciro wayarta a fos. Kira tayi Takara akunne babu dad'ewa aka d'aga daga can, ko gaisawa basuyiba ta ce, " k wai kinsan tsinanniyarnan yau harda zuwa asibiti ganin isma'il itada danginta. Wlhy kuwa. Tab aii bakiga barikiba, kwalliyafa tayi sosai in gaya miki, Tazo gabansa ta zauna sai wani fari take masa, ga d'anbanzan d'ansu d'innan sai ta6ara yakema mutane, wlhy na tsani yaronnan. Wlhy babban bala'ima kuwa tamabar gidan amma suma shegun 'yan gidan har yanzu Sonta sukeyi, munafukar tsohuwarnan harda rungumeta. Kibari kawai aii idan sunsan wata basu San wataba. Shikenan zamuyi waya anjima, yanzuma fitowa nayi nace zansai kati. Wayar tacire daga kunnenta tana fad'in itama shegiyar deexerh nan zanyi maganinta harda uwarta, gafff sukayi karo da mutum..... Da Sauri tad'ago saitaga deexerh. Aha aha khadija INA zaki haka?, mikike nema..... ?sukta rud'e, Yanda take maganar bakinta na rawa kad'ai ya Isa Kasan batada gsky. Deexerh tai mata kallon rainin hankali tareda fad'in adai juri zuwa rafi 'yammata. Bata jira amsartaba tabar wajen. Aunty tayi mutuwar tsaye amma saita sauke ajiyar zuciya tana fad'in nidai in bakiji wayar danayiba aii da sauk'i. Deexerh kan tana Barin gurin wayar xoxo takira, bayan sun gaisa tace nafara aikina aunty hafsat, kuma INA ganin nafara cikin nasara, lokaci yayi dazaki nemo mana Bilyn Abdul. Wani ihun murna Xoxo tasaki, aikinki na k'yau khadija, karki damu insha ALLAHU ayau zan nemo bilyn Abdul muyi magana. Itama iman zan kirata. Lah aii tana nan Tazo duba uncle, kinsan muna asibiti. Ya salam mikuma yafaru?, wlhy tundai ciwon ranar amma da sauk'i, tanan tareda ya majeed da auty salma nasandai sune suka tasota gaba. Kai amma naji dad'in wlhy, badamuwa Nina anjima zanzo inasha ALLAHU, kiyi masa sannu saina zo. Okey ngd sosai aunty hafsat saina ganki. Tom. Lokacin data Shiga aunty ta koma d'akin, marwan ya kannema deexerh ido tareda mata jinjina, itama jinjina MASA tayi, Dan tasanar dashi komai dangane da shawarar su da Xoxo. Dr Isma'il ya zame ya kwanta sosai, mama ta ce, Isma'il kagaji da zamne?. Eh mama yafad'a ahnkali. To sannu kai ya jinjina yana gyara kwanciya, kowama saida yayi masa sannu. Deexeeh tadawo Kusada iman ta zauna suna hirarasu k'as2, gaba d'aya aunty ta tsargi kanta, azatonta deexerh fad'ama iman take abinda yafaru, sai mutsu2 takeyi, hardai Yaya yalura ya CE, "sadiya wai lafiya kuwa?. " da Sauri ta CE, "lfy lau babu komai, tafad'a tana had'iye yawu da k'yar. Girgiza kai kawai Yaya yayi. Deexerh kan dariya aunty tabata, aranta ta CE, ''ki kwantar da hankalinki aii da sauran lokaci. Marwan dashima yana kula da halin da auty tashiga, yad'auki wayarsa yana latsawa, 'yar dariya yayi yana fad'in *" Mara gaskiya dai ko a ruwa ji6i yakeyi*. Yaya ya CE, "kaikuma waye Mara gskyar?. No daddy awaya nake karanta wani labari fa. Okey Yaya yafad'a. Marwan da deexer suka kalli juna sukayi murmushi. Wajen k'arfe 12:15 su ya Majeed suka mik'e zasu tafi, bayan sun masa addu'ar k'ara samun lfy suka fice, Dr Isma'il jiyake kamar kada Iman ta tafi, amma bashida damar hanata, musayeef yayi barci Dan haka iman taji dad'in Dan bataso ya ce, "zai bisu. Tunda suka tafi Dr isma'il ya lumshe idanu yay shiru kamar mai barci, k'arfe 2:09pm likita yashigo yay MASA tanbayoyi akan jikinsa sanan aka saka MASA k'arin ruwa Wanda yasakashi barci, daga nan kowa yafito Dan abarsa yahuta sosai, duk wanada yazo dubashi saidai sugaisa dasu Yaya awaje, yalek'o ta window yaga Dr Isma'il........... *luv u oll my fan's* *(((S))).......2017* [8/6, 6:02 PM] mrs bilkisu: *_BAN SAKETA BA!!_* *_NA Bilyn Abdul_* _sadaukarwa_ *ya Abdul (city phone's)* https://mrsbilkisa.blogspot.com *wanan page d'in nakine fa'iza amarya, ubangiji ALLAH yasanya alkairi yabaku zaman lafiya, 'yan uwa muna gayyatarku biki a gidana, _bilyn abdul h novels_ Dan za'a kwashi shoki💃🏻 zakuma aci rangam🍲 da kulora🍹.* _sakunzo_😂😜. *(page 23)* Yaya da Dr Isma'il zaune afalon mama tana musu nasiha. Mansur Isma'il INA mai k'ara Baku hak'uri da karfafa muku guywa akan godiyar ALLAH, da kar6ar k'addara, mai dad'i ko sa6anin haka, nasan dangin mahaifinku mutanene masu kwad'ayi da hange hange, 'yar uwata tasha wahalar zama dasu har ALLAH ya kar6i kayarsa. Nasan badan ALLAH suke aura muku Aure de 'ya'yansuba, to inason kukuma ku rik'esu Dan ALLAH, aure ibadane to Ku d'auka Ku ibadar kukeyi. Sanan lokaci yayi dazamu bincika Wanda yaraba Isma'il da matarsa, Dan Nima inji ajikina *Baka saketa ba*. Da Sauri Dr Isma'il ya kalleta yana murmushi, ngd mama dakuka fara yarda dani, wlhy *"ban saketa ba!"*. Na yarda Isma'il kuma zamu saka idanu insha ALLAHU har matarka tadawo d'akinta Ku rungume zuriar da ALLAH yafara Baku. Nanma murmushi yayi, Yaya yaji dad'in ganin yau k'aninsa d'aya tillo yana farin ciki abinda suka dad'e basu ganiba daga gareshi. To inaso kaima karik'e raihan da gsky kamar yanda d'an uwanka yarik'e sadiya. Karki damu mama insha ALLAHU bazakiji wani abuba sa6anin farincikinki. To Alhmdllh ngd. YAYA yayi musu addu'a suka mik'e kowa yanufi 6angarensa. Koda Dr Isma'il yashiga 6angarensa saiya zube afalo seman doguwar kujera, sai faman murmushi yakeyi, jiyakeyi tamkar iman tadawo gareshi. Yana nan kwance Raihan tafito daga d'akinta cikin kwalliya ta d'aukar hankali, saiwani juya jiki take adole ita sabuwar amarya. d'an k'aramin tsaki Dr yaja shi wlhy yama manta jiya ankawo masa amarya, Dan ko d'akin da'aka sakata jiya bai kallaba bare yaje Inda take. Amma dayake wawuyace yanzu taciwo kwalliya tazo gabansa tana karairaya. Ya d'auke kai daga kallonta Dan ganin wajensa take dosowa. Zama tayi Kusada shi, yana kwance itakuma tana gefen kujerar tad'an d'ofana d'uwawunta. Fuska Dr yakuma d'aurewa, abin yayma Raihan zafi amma saita basar, tayi far da idanunta, haba my one dama haka ango yakeyi idan ankawo masa sabuwar amarya, jiyafa aka kawoni amma ko Inda nake baka lek'aba. Koda yake nasan kanajin kunyar su babane..... Wani haushine ya turnik'e zuciyar Dr isma'il Dan ALLAH jiba yanda tasaki baki sai wani zuba surutu take _uwa an 6arka zani_, yatsani mutum mai yawan surutun tsiya, shiyyasa akullum yake k'ara tsananin son iman, komai NATA anutse, duk rashin son maganarsa iman tafishi, amma wanan redio d'in da aka kawo masa yaga takansa, dama can haka Raihan take da d'anbanzan surutun tsiya, saidai idan bata samu waje bane........ Raihan CE takatse masa tunanin dayakeyi, takamo hannunsa ta rimtse anata, ko motsi baiyiba, dukda tsananin sha'awa dake addabarsa basa yaji wani Abu dangane da rik'on data masaba. Aransa yace to yama za'ayi naji wani Abu, shegen hannunta kamar na k'aton gardi, yatuno iman d'insa mai laushin hannu da santsi, kai baiyi zaton aduniya akwai macen dazata kamo iman agurinsaba. Raihan ta shagwa6e fuska tana jijjigashi haba my one, ya inata maka magana kayimini banza tunanin mikakeyi?. Tunanin iman yafad'a muryarsa cike da karsashi, yafad'a mata hakane danta ji haushi ta k'yalesa. Aii ko taji matuk'ar haushi, Dan jitayi tamkar ta mangaresa, tunuwa da maganar aunty yasa tasaki murmushi Wanda a bad'ini yafi kuka ciwo, azahiri kuma na yak'ene, ta langa6e kai gefe, ayya iman Nima wlhy harka saka na tunota, mutuniyar kirki ga hak'uri da son mutane, Dan ALLAH yaushe zaka kaini na gaisheta. Wata ajiyar zuciya Dr yasaki, saikuma yaji yarage jin zafin Raihan d'in, saboda ta yabi Rayuwarsa, d'an murmushi yayi ya ce, "koyanzu kikeso zan kaiki ki gaisheta. Fakar idonsa tayi ta harareshi, suna had'a ido tasaki murmushi basarwa, aii nasan mama bazata bariba, kaga daga kawoni jiya yau mufita bai daceba, amma nan gaba insha ALLAHU zaka kaini, waima INA Musayeef?, naga kamar nagansa jiya agidannan. Muryarsa ad'an sake ya ce, " eh yananan, yana d'aki yana barci bai tashiba. ALLAH sarki yarona, amma dai yaa Isma'il anan zaka barminshi ko?. Sosai yake kallonta yanzu, Dan maganganunta sun fara tasiri akansa, yak'ara rumtse hannunta anasa, bazai yuwuba, kinga tun farko awajen mamansa yake, yanzuma Dan nazo d'an hutunnane na d'akkoshi, amma aii yana zuwa weekend, idan yazo saiya ringa zama a wajenki koda ba nanan. Woow!! My one ammafa ngd sosai da wanan karamci, ALLAH yaraya mana shi. Amin yafad'a yana d'an murmushi. Azuciyarta ta ce, "namijima dai sakaraine, jibi sanda nafito sai wani cika yake yana batsewa, amma INA d'orashi ajirgi harya haye. Kafin su k'ara wata magana aka turo k'ofar. Suduka suka maida kallonsu wajen, aunty CE d'auke da kayan break, tayi sallama tashigo, a Tebir d'in tsakkiyar falon ta ajiye, Raihan ta ce, " sannu da k'ok'ari auntyna. Yauwa auta kuntashi lafiya?, lafiya k'alau wlhy. Dr Isma'il kam yayi sagade yana kallon ikon ALLAH, aunty ta k'atse masa tunanin da fad'in k'anina ya angwaci?. Bai bata amsaba saima tambaya daya jeho mata, aunty mikika kawo mana?. Break mana tafad'a tana murmushi. Hannunsa yazare daga na Raihan yatashi zaune, sabodami zaki ware mana abinci bayan kuma gaba d'aya akeci?. 'Yar dariya tayi, a'a naga yau kana angwanci, bai kamataba aganku a family darning. To saidai idan ita zataci anan, nikam zanje can naci kamar yanda nasaba, yafad'a yana mik'ewa, d'akin Iman yashiga Inda yamaida d'akinsa ayanzu. Galala suka bishi da kallo, Raihan ta sauke ajiyar zuciya, wlhy aunty mutumin nan matsalane, amma zanyi maganinsa daga shi har shegiyar Iman d'in. Hummm aunty tafad'a, auta kenan aii kema kike fad'a anaji, bari nakoma da abinci kije ki lallashesa Ku taho ana jiranku. Yana Shiga d'akin ya tadda Musayeef ya tashi yana k'ok'arin sakkowa daga kan gado, da Sauri yak'arasa yad'agashi sama yana dariya, my boy katashi. Kai musayeef yad'aga masa yana dariya shima. Ya saukeshi saman gadon ya ajiyeshi atsaye yafara cire masa kayan barci, Musayeef ya ce, "daddy INA kwana. Lafiya lau my Darling, Dr isma'il ya lakaci hancin musayeef, fuskarsa cike da murmushi. Raihan dake bakin k'ofa tsaye tana kallonsu taja siririn tasaki Wanda bazai jiba, k'arasawa tayi Inda suke tana d'an murmushi Munafinci, a'a yarona katashi?. Idanu Musayeef ya tsuramata batareda ya amsaba,. Daddy wace wanan, yanuna Raihan?. Dr Isma'il bai juya ya kalletaba ya ce, " basunanta wannanba, sunanta aunty Raihan, musayeef baice komaiba, sai kallonta yake Dan harararsa takeyi. Dr Isma'il yad'agashi zuwa jikinsa, yauwa muje namaka wanna my sweedy na, muje kayi break ko. Da Sauri Raihan ta ce, "kawoshi nayi masa mana, wanan aii aikinane....... Uhm uhmyyyy musayeef yafad'a yana nok'e kafad'a alamar bayaso, ya ce, " bana son naki, na Daddyna nakeso, yaymata gwalo. Dr Isma'il baice komaiba yashige bayi yana dariyar gwalon da Musayeef yayma Raihan. Itakam aii tacika tayi FAM da haushi, Kutt wanan d'an yaronne zaimin rashin kunya, aii ko zan bud'e makarantar cin ubanka agidannan yaro, aii uban naka zai tafi zaka gane shayi ruwane. Dr Isma'il yayma d'ansa wanka fes, yanad'o kayansa a tawul, saman gado suka zube ya shafa masa mai, ya shiryashi cikin blue d'in wando jins da jar riga, ya d'ora masa falmaran d'in riga Mara hannu itama Jins, ta wandonce , yasaka masa Jan takalmi mai k'yau, brosh d'insa yasa ya taje masa kai, musayeef kanka yatara suma da yawa bari muyi break munje aski ko?. Musayeef ya jinjina masa kai. Yauwa to tashi muje ko kanunama mama da aunty deexerh gayunka da Yaya marwan, harzasu fita ya ce, "daddy ba'a turareba. Oh sorry big boy na mantane, komawa yayi cikin d'akin yad'auki turarurrukansa ya faffesa masa sanan ya d'aukesa suka fito. Raihan ta na zaune afalo, cike da haushin gwalon da musaueef yay mata, amma tana ganin sun fito tamik'e tana murmushi, har kun gama?. " eh mungama Dr Isma'il yafad'a. Ta mik'a hannu danta amshi Musayeef amma saiya k'ara mak'al k'ale daddynsa. Ta ce, "miyasa Baka son zuwa wajena Musayeef kodan ni ba mamanka bace?. " a'a bawani danba mamansa bace bai sanki bane kawai, barikiga kuyi kwana biyu tare, zai saki jiki dakene, Dan yanada saurin sabo yaronnan. To ALLAH yasa. 6angaren mama suka nufa, kowa ya hallara su ake jira, Yaya yamik'a hannu yakar6i musayeef, yana fad'in oyoyo yarona, suka gaggaisa, Dr Isma'il ya ce, "INA 'yan biyuna?.. Suna can suna barci basu tashiba, aii nagama k'ok'arin musayeef daya tashi da wuri, yaranan aii sunsha hidima jiya, maman su deexerh CE da wanan maganar. Wlhy kuwa sunsha momy, deexerh tafad'a, shiyyasa aii idan suka kwanta kamar matattu. Marwan ya ce, " musayeef fa harya fara bacci muna game, amma kamar an tsikareshi yatashi wai wajen daddy zashi, babu lalla6ar daban masaba amma yasamin kuka, aii dole saida nakaishi. To dama maigida aii rigima harda ta siyarwa akwai awajensa, mama tafad'a tana Jan k'afar musayeef yana dariya, Yaya kuma yana rik'ewa, a'a mama karki katsa mana k'afa kirage mana kasuwa. Mama ta ce, "yo dama aii bakuda wata kasuwa, Dan banason miji mai kama da mata, dariya akayi gaba d'aya wadda aunty da Raihan sunyine kawai Dan kar ace basuyiba. Deexerh da marwan suna kula dasu, deexerh ta CE, " munafukai a zuciyarta. Bayan anci ank'oshi Dr Isma'il ya mik'e yana fad'in bari nakai Musayeef aski. Mama ta ce, "o, danna CE mai kama da mata shine za'a kaishi aski?, to aii kun makaro. A'a mama dama can da niyar zuwa askinmu muka fito ko Musayeef?, kai musayeef yad'aga yana kama hannun daddynasa. Mom d'in su deexerh ta ce, " k'anina ka k'yale mama kawai tana kishine. Gskiyarki aunty babba, dariya nanma akayi gaba d'aya. Dr Isma'il ya d'auki musayeef suka fice yana d'aga musu hannu, suma sukace adawo lafiya. Wani bak'incikine ya turnuk'e zuciyar Raihan da aunty, wato ko saiya dawoma bazai cemataba, dolenefa ta d'auki gaggawar saita guy d'innan. Dr Isma'il kam aii yamanta dawata Raihan matarsa, yabud'e mota suka Shiga, yasaka d'ansa Agaba suna tuk'i tare suka fice. Suna tafiya suna hira, saida sukayi tafiya maid'an nisa, harya gotasu yadawo baya. Iman ce da Xoxo tsaye abakin titi da Alama adaidaita suke jira, suduka suna sanye cikin bak'ak'en dogayen riguna irin na larabawa, sun nad'e Kansu da gyale na zozo fari na iman jaa, kowacce rataye da jakar suwaga kalar gyalenta, hirarsu suke sunata murmushi......... *_"kuyi hak'uri dajina shiru jiya, anduba fayil d'inane, amma na warke"_* *luv u oll my fan's* *(((S)))........2017* [8/6, 6:02 PM] mrs bilkisu: *_BAN SAKETA BA!!._* *NA Bilyn Abdul* _sadaukarwa_ *ya Abdul (city phone's)* https://mrsbilkisa.blogspot.com *miya kamata nayi*. _karka yarda kazama abokin shaid'ain, domin duk wanda yamaida sa6on ALLAH k'aramin abu yazama abokin shaid'an._ _karka aikata zina domin zina shaid'ancice, duk Wanda yayi da uwar wani sai anyi da uwarsa, Wanda yayi da matar wani sai anyi da matarsa, Wanda yayi da yayar wani sai anyi da yayarsa, Wanda yayi da k'anwar wani sai anyi da k'anwarsa, Wanda yayi da 'yar wani sai anyi da tasa 'yar._ _nasan babu wani mahaluki dake fatan hakan ta kasance ga wad'annan 'yan uwa NASA mafi kusanci Dana lissfo._ _to *miya kamata nayi?* karna aikata Kawai, domin zina bala'ice, arzik'i da zina BASA zama a waje d'aya, ga d'unbin zunubi awajen ubangiji._ _to karkayi, karkiyi, nima insha ALLAHU bazanyiba, karmuyi gabad'aya domin tserar da kammu, da iyayenmu, matanmu, 'yayanmu, kannenmu, yayyenmu._ *ALLAH yasa Mugane* *{page 25}* Wai Dan ALLAH miye haka _doctor!?_. Idanunsa ya lumshe, danjin takirasa da sunan datake kiransa ada, ya sauke numfashi ahankali sanan yabud'e motar yafito. Baya yabud'e yashiga itakuma tana k'ok'arin fita, yay saurin rik'o hannunta tareda rik'e k'ofar, kinga kwantar da hankalinki magana zamuyi kitafi. Hararsa tayi. Kinga kidaina min wanan Harar Dan tayarmin da hankali take, zakija nadinga miki abinda bak'yaso wlhy. Shiru iman tayi. Saida yakalli musayeef sanan yadawo da kallonsa gunta. Ya janye hannun rigarta yana kallon k'unshin cike da sha'awa, sumbatar hannun yayi, iman tayi saurin janye hannunta tana k'ara d'aure fuska. Murmushi yayi, kai my life mai k'unshinanfa ta iya wlhy, kinganki kuwa, inga k'afar?, yafad'a yana duk'awa zai lek'a k'afarta. Da Sauri tajanye k'afarta ta tura k'ark'ashin kujera. Yad'ago yana kallonta, Indai bazaki bani naganiba tofa zamu kwana a motarnan. Baki ta murgud'a MASA. Bata ankaraba taji bakinsa akan NATA. Fisge2 tafarayi amma takasa kwatar kanta, tsotsar le6enta yake da harshenta tamkar zai ciresu, duk iya k'ok'arinta nata kwace takasa, Dan haka tahak'ura saida yayi mai isarsa sanan yasaketa yana sauke numfashi. Itakuma tafara hawaye. Ya ce, "nunamin konayi abinda yafi haka wlhy...... Kafin yak'arasa ta d'ago k'afarta. Murmushi yayi yajanye rigar yana kallo, yayinda ita kuma tarintse idanu tana hawaye. Shikam sai shafa k'afarta yakeyi, daga bayama saiya d'auki wayarsa yad'au k'afar ta da hannunta photo, tanajinsa tai masa banza. Xoxo kam tanacan sunshiga gidan makwafciyarsu Zara kar6o abu awajenta. Saida yagaji dankansa sanan ya ajiye kafar, fuskantarta yayi sosai. My life magana nakeso muyi. Bana buk'ata tafad'a idonta arufe. Saboda mi bak'ya buk'ata muyi?. Haka kawai. A'a akwai dalili dai. Banida wani dalili nikam. Aii duk abinda kikaga d'an Adam yayi akwai dalili. Toni banidashi, tafad'a cike da k'osawa. Tom shikenan tunda bak'yaso ambar maganar, yanzu yaushene tafiyar taku?. " jibi Idan ALLAH yakaimu". Hummm dabamu had'ubama saidai naji alabari ko?. Bud'e ido tayi tana kallonsa batareda tace uffanba, ita aganinita mizaisa tasanar dashi...... Yakatse mata tunani dafad'in koba hakaba. Tad'an yatsine fuska, ai baizama dole saika saniba danbamuda wata alak'a. 'Yar dariya yayi tareda fad'in "ko?." Kanta tsaye ta gyad'a MASA kai. Yad'an cije le6ensa, Ashe kuwa zan hana tafiyarnan wlhy. Da Sauri ta ware ido tana kallonsa. Ya ta6e baki, ya ce, kallonfa?. Kauda idonta tayi tace mizan kalla anan. K'yau mana yafad'a cike da murmushi. Ta ce, "Ashe";. Asheme?. Shiru tayi babu amsa. Zanbarkine kawai kije Dan ALLAH amma badan halinkiba, kuma kema idan kin dawo kifara shirin komawa naki gidan. Wata 'yar dariya tayi mai Nuna alamun ka ta6u, tamurd'a k'ofar zata fita. Yasake damk'e hannunta, INA zuwa kuma?. Batareda tajuyoba ta ce, " Dan ALLA kabarni inada abubuwa masu muhimmanci agabana. Nima aii hakantake. Batace komaiba. Nifa zan wuce tafad'a kanta yana kallon waje, Nima aii ba kwana zanyiba anan, kaika sani tafad'a azuciyarta. Ya ce, ''gobe idan ALLAH yakaimu zan shigo, kuma Nima inada zuwa d'aurin aure Adamawa nida Nabeel jibi. Dan haka kubari mutafi tare. Nikam bazan hau mortar kowaba. Humm karki hau mana, nidai nagama magana, ki had'oma musayeef wasu kayan Dan dashi zanje. Bata tankaba tabud'e tafice, daidainan xoxo tafito. Shima Dr Isma'il yafito, hannunsa rik'e da ledoji guda biyu babba da k'arama. Xoxo yabama k'aramar sanan yamik'ama iman babbar. Kallo d'aya tayi musu shida ledar ta kauda kai, nifa bana buk'ata, baki ya ta6e tareda ajiyewa kusada k'afarta, idan kingadama ki yarda yafad'a yana nufar mota. Xoxo tak'ara masa godiya, harya tada motar ya ce, "af na manta hafsat!. Xoxo ta ce, " na'am tareda zuwa jikin mortar talek'a kanta. Jibi dayaushe zaku tafi?. Tunda sassafe. Okey kujirani, dannima zanje Adamawa d'aurin Auren wani d'an uwan Nabeel, saimu tafi tare. To shikenen mungode sosai fa, ALLAH yak'ara lfy. Ameen saikunjini. Bayan tafiyarsa Xoxo takali iman datayi gaba tabar ledar a Inda Dr Isma'il ya ajiye. Dauka kawai tayi suka Shiga gidansu Xoxo.. Afalo suka iske umman su Xoxo, fuskarta cike da fara'a ta ce, "kun dawo?. Eh wlhy Umma munyi sauri ko?. A gsky kunyi Sauri. Kunshin suka Shiga Nuna mata, itakuma tana yabawa. Ta ce, " kunsamu adaidaita dawuri kenan d'azu?. Inafa Umma, wlhy sai daddyn Musayeef ne yakaimu, muna tsaye munata jira harmun fara gajiya saigashi shida musayeef zasuje aski, aiko shiya kaimu Yakoma ya d'akkomu. ALLAH sarki bawan ALLAH, ALLAH yasaka MASA da alkairi, amindai Umma, kingama abinda ya saya mana. Xoxo tamik'ama Umma ledanta, Umma tabud'e ledan saiga doguwar Riga mai d'anbanzan k'yau, da takalma, harda turare guda biyu, da kayan kwalliya. Kai amma kin code wlhy, wanan bawa akwai kirki, ALLAH dai yagyara wanan lamari iman ki koma d'akinki ki rungumi d'anki kema. Ameen Xoxo tafad'a tana dariya, iman kuma tayi k'asa da kai tanajin kunyar zancen Umma, amma dukda haka saida ta ce, "ameen azuciyarta, Dan itama tana fatan faruwan hakan, tana bala'in son Dr Isma'il sosai. Xoxo tamik'ama Umma ledan iman, kinga NATA itama wai bataso. Umma ta ce, " kai habadai, itama fad'a take kawai, Umma ta ce, "jeki ajiye mata zata bud'a anjima, murya kasa2 ta ce, " Umma kibud'a kigani mana. Dariya Xoxo takwashe dashi, kai iman akwai gulmar tsiya, anason daddyn musayeef ana kaiwa kasuwa, keda kikace bak'yaso. Hararata IMAN tayi, ita kuma Umma tabud'e ledar. Itama dogayen rigunane guda uku masu azabar k'yau, sai hijjabai Biyar manya, sai takalma biyu da kayan kwalliya. Umma ta ce, "ALLAH yasaka da alkairi, kukai d'aki Ku ajiye ga break d'inku can. To Umma Xoxo tafad'a tana mik'ewa. Anan gidan iman tawuni, Dan saida sukaje suka wanke kai sanan ta tafi gida da ledar kayanta, dakuma wasu turarurruka masu k'amshi da umman Xoxo tabata, *(so kunsandai kanuri sun had'u a wajen turare😉, Xoxo kuma kanuri ce😁)* Shikam Doctor daga nan gida ya wuce dasu, yana faka motarsa a harabar gidansu ya d'auki musayeef dake barci akan kafad'a. Da sallama yashiga 6angarensa, aunty da Raihan dake kuskus suka d'ago da Sauri suna kallonsa. Baice komaiba yak'arasa cikin falon, aunty tamik'e tana MASA sannu da zuwa, Raihan kuma tazo zata kar6i musayeef amma saiyace tabarsa. Baijira amsartaba yawuce d'akinsa, Wanda yanda yabarsa da datti haka yazo ya sameshi. Dan tsaki yayi, ya kwantar da musayeef saman kujera sanan yazo yafita. Yanzu raihan CE kawai afalon aunty ta tafi, baice mata komaiba yasake fita Babu dad'ewa saigashi tareda deexerh, suka wuce Raihan zaune tana kallo. Dakinsa yakira deexerh ta gyara Masa Dan haka yak'ara fita danufin d'akko kaya amota. Da Sauri Raihan tasha gabansa, yaa Isma'il wai Dan ALLAH miye haka? Wani kallo ya watsa mata ya ce, " a ina kenan?. Dukda atsorace take tadaure ta ce, "kashigo muna maka sannu Baka amsaba, sanan Nazo kar6ar musayeef ka hana, yanzu kuma naga kaje ka kira khadija mizata maka?. K'ara had'e fuska yayi, ya ce, " zata gyaramin d'akine ko akwai wata Matsala?. "A'a." Tafad'a a sanyaye. Ra6awa yayi ta gefenta yafice, babu dad'ewa yadawo d'auke da Leda, yanzu Raihan tabar falon tashiga d'akinta, tana Shiga waya ta d'auka takira aunty, aunty ki kwantar da hankalinki ba maganar damukayi yajiba Ashe, abin nasane ya motsa. Ajiyar zuciya aunty ta sauke ta ce, "kai harnaji dad'i wlhy, da nakasa zaune nakasa tsaye sai zagaye d'aki nake. To hankalinki ya kwanta yanzu Raihan tafad'a tana dariya. Babu dad'ewa deexerh tagama gyara d'akin, tamaida musayeef kan gado, tasaka MASA turare d'akin yad'au kamshi sanan tafito tasamesa afalo kwance, uncle nagama. Tashi yayi zaune yauwa deexerh sannu da k'ok'ari, bari naje na watsa ruwa, nazo mu gaisa da mama. To saikazo tafad'a tana fita. Tashi yayi yashiga yay wanka yafito tsaf abinsa sai 6angaren mama. Iman tana zaune ad'aki kayan da Dr yasiya mata take dubawa, kayan sun mata k'yau sosai Dan haka ta shiryasu cikin kayan zuwa adamawa, kad'an2 saitayi murmushi ta shafa le6enta, idan tatuna summbar da Dr yay mata saitaji wani farinciki na ratsata, dahakadai barci ya saceta. *9:39pm* Dr Isma'il zaune abakin gado, yajingina Kansa da fuskar gado, k'afarsa d'aya ak'asa d'aya lankwashe akan gado, musayeef yatada kai da ta lankwashen yana barci, hannunsa d'aya yana shafa kan musayeef d'ayan kuwa yana rik'e da waya yana dannawa, sai faman murmushi yakeyi Dan k'unshin iman yake kallo, harda fuskarta wadda batasan ya d'aukaba. Raihan dake tsaye abakin k'ofa tana kallonsa ta ta6e baki. Cikin d'akin ta k'arasa sosai, taje kusadashi tazauna, d'agowa yayi yana kallonta sanye take cikin rigar barci fara tas, wadda ta tsaya iya cinyarta, ta d'ora 'yar saman data kai mata had k'asa, tasaki igiyoyin rigar batareda ta d'aureba wanan yasa ake kallon k'irjinta daya cika rigar FAM danba bra. Kauda Kansa yayi daga kallonta yace lfy?. d'an farin tayi ta ce, "saibabu lafiya ake Shiga turakar miji?. Baice mata komaba yafara gyarama musayeef kwanciya sosai, ta kwanto da kanta ajikinsa muryarta anarke ta ce, " haba my one wai haka ake aure?. Cike da mamaki yake kallonta, ya ce, "to ya akeyi?. Tayi far da idanunta aii kaima kasani, ta turo Baki gaba, jiya na hak'ura na kwana nikad'ai yaukam bazan iyaba gsky. Shidai kallonta kawai yakeyi, yadaure ya ce, " to ya kikeso ayi?. Murmushi tayi tana shafa k'irjinsa Dan rigar baccinsa mai bud'ad'd'en k'irjice, yauwa my one sonake mukwana tare. Ajiyar zuciya ya sauke tareda janye hannunta daga k'irjinsa Dan abinda take MASA yafara tasiri akansa. Gyara kwanciyarta tayi sosai ajikinsa, tana k'ara Zame rigarta ta sama komai NATA na bayyana, kauda idonsa yayi daya fara canja launi zuwa jaa. Ganin haka yasa Raihan tadawo da fuskarsa Inda take, ta marairaice fuska Baka yarda mukwana tareba ko?. Yanda tayi maganar saita bashi tausayi kumashi ba dutse bane yana buk'atar abokiyar hallittarsa, yana daurewane kawai, amma ganin shigar dake jikin Raihan dukta sauya MASA tunani, ga wani fitinannen turare data shafa, Wanda dukya motsa MASA sha'awa. Kallon fuskarta yayi harta fara hawayen kissa, hannu yasa yana share mata hawayen, akasalance ya ce, "naji ZAMU kwana tare bar kuka. Ta turo Baki gaba tana yunk'urin tashi, a'a nikam banaso, aii hak'k'inane akanka, idanka tauyeni ALLAH bazai barkaba tamik'e zata fice. Da sauri yarik'e hannunta Yakuma dawo da ita jikinsa, shikenan naji yihak'uri to. Yanda yake shafa kan ta saitayi luf ajikinsa, ahankali takai hannu itama tana shafa k'irjinsa, ajiyar zuciya ya sauke yalumshe idanunsa tareda jingina kansa da gado. Daga haka ta fara yimasa abubuwa na d'aukar hankali, Wanda duk aunty CE ta koya matasu, Dan acewar aunty saita maida kanta Mara kunya sanan zata samu Dr ahannu, aiiko taga shawarar aunty tayi tasiri sosai, Dan gashi cikin sauk'i ta d'akko hangar samunsa. Baisan sanda yafara maida mata murtaniba, saida sukayi nisa sosai sanan yad'an janye jikinsa da k'yar yana kallon musayeef daketa barci abinsa, itama Inda yake kallo ta kalla, muryarta can k'asa ta ce, "lfy?. Muryarsa a sark'e ya ce, tashi muje d'ankinki kinga nan akwai musayeef. Ta ce, " shida yake barcinsa. Kai ya girgiza mata yana fad'in bazai yuwuba idan ya farkafa?. Tad'an ta6e Baki to idan muka tafi cand'in yafarka yay kukafa?. Mik'ewa yayi yana lilli6e musayeef karki damu aii nan zandawo na kwana. Banza tayi masa, aranta ta ce, "Idan na barkaba, tanayi yana Hararar musayeef dabaisan tanayiba. Bayan ya lullu6esa Yakama hannunta suka fita zuwa d'akinta............. 😡 *_"nidai masu karatu bazan bisuba kuyi hak'uri INA taya iman kishi"_*🙄 *luv u oll my fan's* *(((S))).........2017* [8/6, 6:02 PM] mrs bilkisu: *_BAN SAKETA BA!!._* *_NA Bilyn Abdul_* _sadaukarwa_ *ya Abdul (city phone's)* https://mrsbilkisa.blongspot.com *miya kamata nayi?.* _karka zama mashayi._ _Shaye shaye na 6ata rayuwar maiyinsa, ga d'unmin Zunibi awajen ALLAH Yana hana sallah akan lokaci, baya barinka kayi k'yak'yk'yawan tunani arayuwarka bare harka banbance fari da bak'i, bazai barka ka karanta alkur'ani mai girmaba balle harkasan yi da hani, bazai bari ka girmama nagaba da kaiba Dan kana ganin kowa daidai tsawonka, zaka iya ganin akuya atiti katsugunna ka gaisheta, zaka iya kashe mutum domin Baka tareda tunaninka, zaka zaka zaka zaka dayawa 'yan uwa._ _Dan ALLAH kubari shaye shaye ba wayewa baceba, abin damuwar yanzu harda mata, haba 'yar uwa keda kike amsa sunan uwa miya kaiki Aikata wanan aiki._ _Wanan duk yana d'aya daga cikin aikin shaid'an shugaban hassada ga aikin alkairi, kullum burinsa yaganka a wutar jahannama._ *ya ALLAH ka kiyashemu shigarta* *ALLAH yasa Mugane* *(Page 26)* Humm lallai yau su Dr Isma'il ansha amarci shida amaryarsa Raihan, saidaifa tabbas ya yarda mata suna suka Tara. Yana kwance akan gadon Raihan idanunsa alumshe tamkar Yana barci, Raihan dake tsaye Kansa ta dasa masa idanu, daga wanka tafito Dan d'aure take da guntun tawul iya cinya, wani irin farincikine yake ratsata wai yau itace ta kwana gadon d'aya da yaa Isma'il, lallai tayarda soyayyama iya wace, yaa Isma'il dabbane afagen iya soyayya. Ahankali yabud'e idanunsa akanta, kallo d'aya yaymata ya kauda kai, imance tafad'o masa arai, yatuna ranar Daren farkonsu ko ido bata iya d'agawa ta kalleshi bare tamasa kallon tsaf, haryay rayuwarsa suka rabu da iman baita6a ganin tazo ta tsaya gabansa da guntun tawul ba, ko wanka tashiga, yashigo d'akinta Indai har tasan Yana ciki to bazata fitoba kuwa, amma jibi ita wanan tawanizo ta tsaya masa getsetse agaba tamkar wata matar k'auye, koma irin 'yar kunyarnan babu........ Jiyay tana shafa bayansa, siririn tsaki Yaja sanan yajuyo. Haba my one katashi mana kallifa lokaci kagani, kar aita jurammu awajen break. Tashi yay zaune batareda tayi maganaba, ya ziro k'afafunsa k'asa ya sakko, hanyar fita yanufa, ta ce, ''my one!. Bai juyoba amma ya tsaya. Ince anan zakayi wankan?. Kai ya girgiza mata, sanan yace zanje nayima musayeef wanka, baijira amsartaba yafice. Itama da harara tarakashi, d'an rainin hankali, da daddare kagama yima mutane sambatu yanzu kuma kazo kana mazurai Mtsoowwww taja wani wawan tsaki. Shikam Yana shiga d'akinsa yaga babu musayeef da sauri yanufi bathroom nanma bata nan, ya ilahi INA yaronnan yanufa be?. Da sauri yasaka jallabiya yafito, 6angaran mama yanufa, saiya Tarar da musayeef suna game awaya shida Marwan, harna anyi masa wanka tsaf. Ajiyar zuciya ya sauke adaidainan deexerh tafito daga d'aki, ta ce, ''lah uncle lfy?. Musayeef yanuna mata, waya kawoshi nan?. Sai asanan Marwan da musayeef sukasan yashigo, musayeef yazo yarungume daddynsa. Deexerh ta ce, "ni na d'akkoshi jiya da daddare, naje na sanar dakai zan koma makaranta yau, Dan ana nemanmu da gaggawa saina Tarar musayeef yanata kuka ad'aki shi kad'ai. Nazata kana bathroom amma nakai awa d'aya ina jiranka shiru, babuma alamar motsin ruwa shine na d'akkoshi kawai muka taho nan. Ayya sorry my Darling, yafad'a Yana shafar fuskar musayeef. Deexerh kam da marwan kallon juna sukayi, deexerh ta harari Dr amma bai ganiba, fita yayi da musayeef ahannu. Marwan ya ce, "kinjifa aii bai bada amsaba saboda bashida gsky. Humm kabari kawai, aii dama dannaji zaice Yana inane?, tunda nagabaci 6angarensufa nakejin kukan musayeef amma babu Wanda yanemeshi acikinsu, sai yanzu zaiwani zoma mutane arikice, nasandai Yana d'akin Raihan. Mtsowwww!! Wlhy Uncle yafara bani haushi.......... Mama takatse musu zancen, kai kunci k'aniyarku, shida matarsa bazaije d'akintaba. Gaba deexerh tayi tana k'unk'unai, marwan kuma yace mama aiiba hanashi mukayiba. Sai bayan kamar Minti talatin suka fito cikin kwalliya, lokacin kowa ya hallara a dani, suma kad'ai ake jira, bayan gaishe gaishe suka zauna aka farayin breakfast, Raihan sai wani yatsine2 takeyi, Dr yana kallonta ya watsar da banza. Bayan sun gama break deexerh ta ce, " uncle nifa yau zan koma makaranta. Tofa wanan tafiya babu shiri, humm toyazamuyi karatun kenan aii. Shikenan babu damuwa, ALLAH yakaimu, Nima gobe zanje Adamawa d'aurin aure, da da musayeef zan tafi amma mama ta hana, wai za'a wahalar dashi, kuma zasu koma school ranar Monday. Eh ranar litinin zasu koma. To kinyoma auntynki sallama??. A'a wlhy amma munyi waya nagaya mata zan koma yau. Okey to shikenan, kud'i masu yasa yabata ya ce, "ALLAH yatsare, waye zai kaiki?. Marwan zai kaini uncle. " to shikenan hakanma tayi aii. ************** Wajen k'arfe 12 Dr Isma'il yaje gidansu iman maida musayeef, Yama Tarar bata nan, saidai sungaisa da gwaggo da Abbah dayay mantuwa yadawo gidan, annan yabar Musayeef Yakoma gidan. *_8:00pm_* Iman zaune agaban abbah, kanta ak'asa tana wasa da yatsun hannunta. Ya ce, "iman dadai inata damuwa da tafiyarnan taku Adamawa Ku kad'ai babu wani babba, amma yanzu hankalina ya kwanta, Dan Isma'il ya cemin tare zakuje, shima zaije wani d'aurin aure acan ko?. Abbah nima ban saniba. Okey to d'azu dayazo kawo Musayeef yake gayamin, Dan haka saiku shirya da wuri Dan gurine ba kusaba. Kanta Yana ak'asa tace to abbah. Tana mamakin yanda iyayenta suke son Dr Isma'il sosai, sun yarda dashi 100%, itakam da batayi niyar tafiya dashiba amma babu yanda zatayi tunda abbah yasaka baki. Bayan sun mata nasiha akan ta tsare mutuncinta takula da kanta ta tafi d'aki. Tana kwance akan gadon sai tunani takeyi, wayarta tashiga ruri, da sauri ta d'auka azaton Xoxo CE amma saitaga *_DM_* kamar bazata d'aukaba amma ta daure ta d'auka. "kodata kara wayar akunne saitayi shiru, shikam Dr yana falone zaune Duk kewar musayeef ta isheshi shiyyasa yakira iman." Assalamu alaiki, yafad'a ahankali. Saida taja lokaci sanan tace wa'alaikassalam. Shiru yabiyo baya babu maiyin magana, saican iman ta ce, "miyasa kazo gidanmu kace tare zamu tafi?. Murmushi yayi sanan ya ce, " saboda na Isa. Le6enta ta cije danjin furcinsa, yacigaba da fad'in ki shirya da wuri, Dan k'arfe 7 munafata mun kama hanyar Adamawa. Saidai kanemi da Wanda zaka tafi amma badaniba tafad'a tana murgud'a baki. Wata sassanyar dariya yayi yay k'asa da muraya ya ce, "ada idan akacemin Saudat ta'iya rashin kunya bazan yardaba, musassamman idan na tuno ranar data bani k'yautar budurcinta.........d'iffff ta Yanke wayar tareda cije le6e, afili tace wai yaushe mutuminnan yakoma Mara kunya hakane?, ALLAH ya shiryaka, haka zan bika kaje ka matseni ahanya. Shikam yanacan yanata dariya abinsa, my life sarkin kunya, har yanzudai ana nan da hali. Raihan dake tsaye kansa taja dogon tsaki Wanda yasa Dr juyowa yana kallonta. Ta k'ank'ance idanu tana fad'in wlhy andai fad'o kuma wanan iskancine tunda ayanzu ba matarka bace, kunzauna kuna aikata *Zinar baki*. To malama Raihan saka lasifika mana, yafad'a a harzuk'e. Shuru tayi Dan taga ya hau sama, shikuma yadoka tsaki yatashi yay shigewarsa d'aki yana had'a kayan tafiya. *Washe gari* Tundaga sallar asuba Xoxo da iman basu koma barciba shiri sukayi sosai sanan suka zauna zaman jiran Dr Isma'il. To shimadai bayan yadawo masallaci wanka yayi ya shirya cikin k'ananun kaya, yaje sukayi sallama da Yaya da mama, kamar bazai Shiga d'akin Raihan ba amma ya daure Dan tanada hak'k'i akansa, Dan haka yanufi d'akin. Tana kwance a gado rufda ciki kuka takeyi jin motsinsa yasa tak'ara k'arfin kukanta cike da kissa. Abakin k'ofa yatsaya ya ce, "kenifa zan tafi, banza tayi MASA kamar batajiba, danhaka yajuya yafice. Da gudu tabiyoshi ta rungumeshi ta baya, tsayawa yayi cak itakuma tak'ara fashewa da kuka. Tausayi tabashi Dan haka yajuyo Yakama hannunta suka zauna akan kukera, share mata hawayen yashigayi batareda yayi maganaba, aii saita k'ara mai tamkar yana zugata, ganin tana 6atamasa lokaci ya had'e bakinsa da NATA, humm shiru kakeji wai malam yaci shirwa, bakajin motsin komai saina saukar numfashinsu, bayan kamar Minti Biyar Dr isma'il yazare bakinsa yana maida numfashi, hannunta yaruk'o kinga kiyi hak'uri kimin addu'a kinji, baki ta turo gaba yaa isma'il yanzu ka daina sona ko?. Kallonta kawai yakeyi batareda yayi maganaba, ganin haka yasa tafara hawaye yad'an cije le6ensa, muryarsa da alamun k'osawa ya ce, " waye gayamiki na daina sonki?. Eh mana kadaina sona sai iman. Murmushi yayi tareda rungumeta yana shafa bayanta cikin sigar lallashi, kinga kibar wanan maganar INA sonki kema danhaka kimin addu'a kinji, yafad'a yana d'agota saga jikinsa. Dukda bata yadda da maganarsaba saitayi murmushi, ta ce, "ALLAH ya tsareminkai yasa kaje lfy kadawo lfy. Amin yafad'a yana murmushi tareda shafa kumatunta. Har tsakar gida tarakoshi Inda sauran 'yan gidan suke tsaitsaye, yabud'e mota yashiga Inda Dr Nabeel yake aciki, Dan shima anan gidan ya kwana, suka fice daga gidan ana d'agama juna hannu, Raihan harda yima hannunta kiss ta huro masa, ko kunyarsu Yaya bataji, shikuma yay saurin dafe k'irjinsa alamar sak'onta ya iso. Dr Nabeel yay dariya kai baban soyayya nanma harka afka?. d'an tsaki Dr Isma'il yayi kai wlhy babu wani afkawa, mazurai nayi mata saikuma tadawo tana bani tausayi, shiyyasa kaga INA biye mata Dan kawai hankalinta yakwanta, so ka gane?. Na fahimceka na iman Dr Nabeel yafad'a yana d'aga MASA gira. Fad'i kanka tsaye malam na imam nake baban musayeef. Angon Raihan amarya kuma Cewar Dr Nabeel. Hararsa Dr Isma'il yayi, ALLAH saima kaja afasa tafiyarnan da Hafsat. No Sorry sir karmuyi haka dakai, Kasan kuwa yanda namatsu naganta, jin tafiyar harda ita nak'ara samun kwarin guywar tafiyar wlhy. Dariya Dr Isma'il yayi, Nabeel kaimafa munafukine a 6angaren soyayya, shima ya tuntsure da dariya, to aii kasan zama da mad'aukin kanwa shike kawo farinkai inji masu iya magana, malam INA taredakai ban koyi soyayyaba aina fad'o wlhy, dolene ayimini jaje. Kaifa shugaban masoyane. Dariya kawai Dr Isma'il yayi batareda yace komaiba........... *luv u oll my fan's* *(((S))).........2017* [8/6, 6:02 PM] mrs bilkisu: *_BAN SAKETA BA!!._* *_NA Bilyn Abdul_* _sadaukarwa_ *ya Abdul (city phone's* *_"wannan page d'in nakine my Ikilee amarya, ubangiji ALLAH ya Sanya Alkairi yabaku zaman lfy keda angonki, ALLAH yasa bad'i mudawo sunan baby😉."_* *(page 27)* Kaitsaye gidansu iman suka nufa Dan a can itama Xoxo ta kwana, mintuna kad'an suka fito harda Abbah da deeni, su Dr Isma'il suka fito suka kwashi gaisuwa a wajen abbah sanan yaymusu 'yar nasiha da Addu'ar ALLAH ya tsare. Iman da Xoxo suka Shiga baya suma Dr Isma'il suka Shiga su deeni suna d'aga musu hannu. Su iman suka gaishesu, cike da fara'a Dr Nabeel ya amsa, amma Dr Isma'il gaisuwar Xoxo kawai ya amsa yashare iman. Ko ajikinta wai antsikari kakkausa, ita dama zai had'e ran harsuje Inda suka nufa hakan zaifiyimata dad'i, tunda suka shigo bai kalli Inda takeba ammafa yana satar kallonta ta madubi batareda ta saniba. Tun bayan gaisuwa babu Wanda yasake cewa komai, da Alama iman da Xoxo ma barci sukeyi, Dan barcin bai ishesuba aka tasosu. Jin shirun yayi yawa yasa Dr Isma'il lek'owa saiyaga Duk sunyi barci, ya ce, "kai sufa wad'annan barci sukeyi. Aii gara suyi anjima manna maka tuk'innan zanyi Musha hirar soyayya. Ashe zaka dad'a Baka shaba malam, dama ka ajiye wata soyayya saimun sauka kawai. Tab wanan ganganne aii idankai anyi maka fuskar shanu nikam Baka hanani. 'Yar dariya Dr Isma'il yayi batareda yayi maganaba. Sunyi tafiya sosai wadda had k'arfe 12:47pm su iman suna barci abinsu, Dr Nabeel da Dr Isma'il suna 'yar hira ahankali. Isarsu wani k'aramin gari suka tsaya, sai anan su iman suka farka, sunyi mamakin barcin da sukayi, bayan su Dr Isma'il sun fito sukace su iman suka fito, iman dai saifaman had'e fuska takeyi. Wani gurin cin abinci sukaje, bayan sun zauna masu kula da wajen suka tanbayi mi sukeso, su Dr Isma'il suka fad'a, ya maida kallonsa Kansu iman ya ce, " mikukeso?. Iman ta ce, "tak'oshi. Dr Nabeel ya ce, " kinga 'yammata kawo mana iri d'aya kawai. Bayan sunci sunsha suka mik'e wadda iman tacine kawai visa tursasawar xoxo, Dr Isma'il yabiya suka fito. "Hanya suka k'ara d'auka bayan sunyi sallar azuhur". Tunda suka fara tafiya abincin yake juyama iman, sai yatsine fuska takeyi, Dr Isma'il yana kallonta ta madubi. Tafiya yayi nisa ha suka k'ara tsayawa sukayi sallar la'asar, sanan suka ci gaba. Sosai iman takejin amai tana dannewane kawai, ruwa tad'auka tasha kozata samu a man datakeji Yakoma, amma INA lamarin k'ara ta azzara takeyi, candai ta ce, " atsaya zatayi amai, gaba d'aya kallonta sukeyi, Dan yanzu Dr Isma'il yake tuk'in, gefen hanya ya gangara. Tun kafin yagama tsayawa tafita da gudu, amai tafara shek'awa, da Sauri Dr Isma'il shima yafito, ko motar bai kasheba sai Dr Nabeel ne yakashe. Rik'e iman yayi tacigaba da aman, duk d'an abinda taci ta amayar dashi, saida tagama sanan yad'agota yana mata sannu, Dr Nabeel yamik'o MASA ruwa, da Kansa ya wanke mata bakinta da Inda tad'an 6ata ajikinta, duk tayi laushi so kawai take ta kwanta. Xoxo ta ce, "sannu iman, agalabaice ta d'aga kai, Dr Nabeel ya ce, " kozamu koma bayan asamu k'yamis. A'a mudaije gaba koza'a samu. d'aukarta Dr Isma'il yayi cak yakai cikin mota, bayan shima ya zauna ya CE, Xoxo takoma gaba Inda Dr Nabeel yacigaba da tuk'in. Kwantar da ita yayi yasaka kanta acinyarsa yana shafa fuskarta babu dad'ewa barci yay a won gaba da ita, ajiyar zuciya ya sauke yasunkuya ya sumbaci goshinta, tsurama fuskarta ido yayi nawani lokaci, saikuma ya kwantar da bayansa jikin kujera ya lumshe idanu. Duk abinda ke faruwa Xoxo da Nabeel suna kallon ta madubi, Dr Nabeel yay ajiyar zuciya tareda d'an kallonta gefen Xoxo yamaida Kansa ga titi yana fad'in toke 6arauniyar zuciya INA muka kwana?. Harararsa Xoxo yayi ta ce, "saika gayamin zuciyar Wanda na sata?. Yayi murmushi tawa mana, duk kinbi kin wani sukukutani yakamata aji danifa, kafin na koma Romeo irin Isma'il. Dariya abin yabama Xoxo Dan haka tadara. Dr Nabeel ya ce, " ngd da aka kar6eni. Ta kalleshi da Sauri waya gayamaka ka kar6u?. Dariyarki da fuskarki. Humm to Baka fahimta bane, abinda yabani dariya daban. Haba 'yan mata aii kuma kinzo hannu matar Dr Nabeel. Shiru Xoxo tayi masa shikam yacigaba da tsarata, _(aii ko kafin na farga har Xoxo ta afka, dama itama tanaso 😉lol.)_ K'arfe 6:57pm suka Isa Adamawa, lokacin har an idar da sallar magriba, damma ba k'aramin gudu Dr Nabeel yayiba, har sanan Iman barci takeyi. Dr Nabeel ya kalli Xoxo toku yanzu wace anguwa zamu kaikune?. E to saidai nakirata Dan na manta gashi kuma har yanzu iman barci takeyi tafad'a tana lek'a su iman. Dr Isma'il yad'an lek'a fuskarta iman da tuni ta juya kwanciyarta, yanzu tana fuskantar cikinsa, Dan har cikin cibiyarsa yanajin saukar numfashinta ahankali. Xoxo takira Reefat 'yar uwa gamufa a adamawarku, yama sunana anguwar?. Wani ihu Reefat ta kwala Wanda yasa dole Xoxo tacire wayar d'aga kunnenta tana dariya. Reefat ta ce, "kuna tasha bari muzo mu d'aukeku. A'a bana gaya miki za'a kawomu bane kifad'i sunan anguwar kawai. Bayan Reefat tafad'i sunan anguwarsu Xoxo ta sanarda Dr Nabeel. Ya ce, " to kenan anguwa d'aya zamuje, waima yaya ainahin sunan amaryar?. Xoxo tace aysha, amma anacemata shareefat. Angonfa?. Usman. Dariya Dr Nabeel yayi Ashe biki d'aya zamuje. Xoxo ta ce, "dawasa koda gsk?. Wlhy gsk. Tofa kaji ikon ALLAH Cewar Dr Isma'il. Dr Nabeel ya CE, Aida baban angon da mom d'ina mamansu d'aya babansu d'aya. Xoxo ta ce, " lallai bikin nakune ashe Ak'ofar gidan su Reefat sukaja tunga, Xoxo takirata ta ce, mun iso. Da gudu Reefat ta fito d'aga mak'ota taxo ta rungume Xoxo data fito tana mai farincikin ganinta, INA iman Cewar Reefat. Aii ko bata zoba Doctor ya hana. 6ata fuska Reefat tayi wasa ko gsk?.. Dariya kawai Xoxo tayi batace komaiba. Amota kam Dr Isma'il yashafa fuskarta iman, ahankali ta bud'e idonta, jin kanta acinyar mutum yasa ta ta tashi da Sauri. Ido ta waro Dan ganin Dr Isma'il dake binta da kallo, ya ce, "kinsha barci?. Batace komaiba sai duk'ar dakanta datayi saboda wata irin kunyarsa datakeji yau. Shima ya lura da hakan shiyyasa yayi murmushi, itakuma tabud'e mortar da Sauri tafito.. Da gudu Reefat Tazo ta rungumeta kai iman Ashe kina ciki?, wlhy da harna yarda da zancen hafsat. Murmushi iman tayi ta ce, " amarya kinsha k'amshi. Bayan Reefat sun gaisa dasu Dr Isma'il, ta ce, "lah ya Nabeel da harda kai?, wlhy kuwa Aysha aii bammasan ke k'awarsu my hafsat bace. Wlhy kuwa in k'awayenane, tunsanda kazo makarantarmu d'aukar Doctor naganeka bandai fad'a musu bane kawai. Ayya to bari muma muk'arasa cikin gida ko?. Okey to sannunku da hanya. Yauwa kema sannu. Dr Isma'il yamatso Kusada iman, ya ce, " kisamu ruwa mai zafi kiyi wanka zakiji k'arfin jikinki zuwa anjima zan kawo miki magani tunda kusane. Kanta ak'asa tace to. Koda suka Shiga gida Reefat sai tsiya takema iman, iman ta ce, "aii banibace abar yima surutu hafsat CE, saiwani 6oye manager take tsakaninta da Nabeel. Dariya Xoxo tayi kawai Dan sunxo k'ofar Shiga falon su Reefat. Tarba akaimusu ta mutunci Maman su Reefat taji dad'in ganinsu sosai. Liyafa aka shirya musu sosai suka koma gidan makwafta Inda su Reefat suke zamna kunshi, Dan gidansu Reefat cike yake dam da mutane. Saida suka fara yin wanka sanan suka zaunasukaci sukasha, aka baje kolin firar yaushe gamo, jisuke tamkar sun shekara BASA tare da juna. Acikin firarrne iman takecewa wai Reefat ya akayi hakane?. Idanun Reefat suka ciko da kwalla kubari kawai 'yan uwa, wlhy duk baffane da wannan aikin, wai tunda ba'asan randa za'a koma yajin aikinba to ayi auren kawai, dukda INA bala'in son yaa usman kuma kun sani amma wlhy banso hakaba, naso saina gama kawai. Xoxo ta ce, " to kiyi addu'a ALLAH yasa haka shiyafi alkairi, Dan wlhy nimafa aurennan zanyi. Gaba d'aya suke kallonta da mamaki. Nan ta labarta musu yanda sukayi da Dr Nabeel amota, ya ce, "shifa Sam baixo da wasaba, suna komawa daga bikinnan zaizo gidansu wajen iyayenta daganan aturo manya. Sunyi murna dajin haka danhaka suka rungume juna suna kukan dad'i. Xoxo ta ce, " saura iman kema muna addu'ar ki koma kwanannan gaky, Dan muna buk'atar k'anin musayeef. Hummm 'yana iska kunkuma dawo kaina. Bawani iskanci anan, Reefat yaufa acinyar Dr Isma'il taxo. Kai gaba?. "ALLAH kuwa". Iman wai haka?. Matsalarkuce iman tafad'a tana kwanciya. Kwashewa sukayi da dariya Reefat ta ce, " kice soyayya akasha amota?, lallai kallo ya wuceni. Aii kuwadai kallo ya wuceki, shiru iman yayi musu. Haka suka raba dare ranar suna hira. 6angaren su Dr Isma'il makuwa, komai daidai, tarba suka samu sosai dama mom d'in Nabeel tana nan tazo itada k'annensa. Bayan sun huta Dr Isma'il yamatsa sai sunje an siyoma iman magani, Dr Nabeel ya CE, "kaima kasan rashin Sabon tafiya mai nisane yasata aman bawani abuba, kuma datayi barci normal zata tashi. Badan yasoba ya hak'ura amma saida yakirata ya ce, tasamu farasitimol tasha. _" washe gari 2:30pm aka d'aura auren Shareefat da yaa usman"_ To saimuce ALLAH yasanya alkairi. Bayan angama d'aurin aure Dr Isma'il yaso ganin Iman amma hakan ya gagara, gashi yakira wayarta akashe, hakama ta Xoxo arufe, yasan sunacan sauna hidima, balle sune amararori k'irjin biki lol. K'arfe 7:30pm akakai amarya d'akinta, k'arfe 8:30pm za aje liyafar cin abincin dare, Dan haka su iman suna zuwa gidan suka hau shiri na k'asaita. Humm fad'a muku yanda suka had'uma aii 6ata lokacine ammafa sun kashe kalla, kuma dolene ido ya kallesu, babu Wanda zaiga iman ya CE, "ta ta6a aure barema harda haihu. Hakama amarya tayi k'yau sosai cikin kwalliyar amare abin sai Wanda yagani komai zam zam. Bayan sungama shiri abokan Ango suka fara kwasar k'awayen amarya Dan ance babu African time. Dr Isma'il da Dr Nabeel gafe suka tsaya Dan babu budurwar dazasu d'auka saisu Xoxo. Sukam sune k'arshe Dan tare suka fito da amarya, bayan amarya tashiga mortar da Ango ke zaune sukuma suka fara k'ok'arin Shiga wata motar guy. Da Saudi Dr Isma'il yaymusu magana suka juyo, su bamasu lura dasuba sai yanzu. Sunshiga motarsu Dr Nabeel suka tafi, Duk sunwani susuce da ganin kwalliyar su iman, dukda suma sunyi gayune cikin farar shadda d'inkin boda, yayi bala'in musu k'yau sosai, kowa yagani said k'yasa😉lol................... *_"Kuyi hak'uri dajina shiru wani d'an uzurine yarik'eni."_* *luv u oll my fan's* *(((S)))..........2017* *_BAN SAKETA BA!!._* *_NA Bilyn Abdul_* _sadaukarwa_ *ya Abdul (city phone's)* *miya kamata nayi?* _Humm *Mad'igo wa'iyazubillah* Kai jama'a wanan rayuwar ko dabbobi basayinta wlhy, haba 'yar uwa mizakiji ajikin 'yar uwarki mace?, miyasa zaki bari shaid'an yayi tasiri akanki?._ _tawani 6angaren ina ganin laifin iyaye, wata yarinyar datakai shekara goma zaka fara ganin tana buk'atar aure, zuwa shekara 15 tayi nisa da sha'awa, amma zakiga wata uwar bata kulawa._ _dayawa wasu yaranmu sunada tsoron yin iskanci da maza, saboda iyaye sunfi tsoratar damu akan karmu yarda da namiji, basu cika kulawa akan gargad'in tarayya da k'awayeba, shiyyasa saikiga k'awa ta dilmiya yarinyarki wajen biyan buk'atar juna, saboda wanan hanyar mai sauk'ice_. _zata samu biyan buk'atarta cikin sauk'i batareda an ganeta kai tsayeba, humm wata sa'in k'awanfa bala'ine wlhy_. Muhad'u a page nagaba. *ALLAH yasa mu gane* *(page 28)* Iman sai satar kallon Dr Isma'il takeyi yayi bala'in yimata k'yau, azuciyarta ta ce, "inama zai koma saka manyan kaya koda yaushe, wlhy da yaringa yin k'yau..... Tanacan tana zancen zuci saitaji wani lallausan hannu ya rik'o hannunta, da sauri tad'ago matsakaita idanunta ta sauke akan Dr Isma'il, Ashe sun dad'e da isowa bata saniba. Ta sauke idanunta ahankali, sanan tayi k'ok'arin zame hannunta amma hakan ya gagara. Muryarsa mai amo da alamun sark'ewa ta sauka acikin dodon kunnenta, ya ce, ''kifito mana, tun d'azun su Nabeel sun shige da amarya. Da sauri takalli gefenta babu Xoxo, Gavan motarma babu Dr Nabeel, tafito da sauri, tareda tambayar kanta wai har yaushe sukama iso da har bataji fitar Xoxo ba. Dr Isma'il yak'araso inda take gaff tamkar zai rungumeta, idanunsa akanta, ya ce, " wai tunaninmi kikeyi ne haka?. Shiru tayi tana k'yafta idanu. Yasaka d'anyatsansa d'aya akan le6enta dayasha uban janbaki sai walk'iya yakeyi, da sauri ta d'ago tana kallonsa, d'an yatsansa ya nuna mata Wanda ya dangwalo janbakin, wannanfa?, yafad'a yana d'aure fuska. Idanunta ta sauke k'asa batareda tace masa komaiba. "Tambayarkifa nakeyi?. Ak'ufule ta ce, " janbaki. Humm janbaki ya maimaita ahankali, ha6arta yad'ago yana kallon fuskarta, ita kuma ta lumshe idanunta dakeda gashi gazar gazar sunji maskara duksun mik'e. Yad'an cije le6ensa, dama wanan kwalliyar ta Matan aure ce?. Bud'e idanunta tayi ta sauke akansa, ban ganeba tafad'a tana ture hannunsa, baijanye hannunba, itama saita k'yalesa, amma ta maida kanta k'asa, tana kallon bak'i agogon dake d'aure a tsintsiyar hannunsa. Muryarsa cike da kishi ya ce, "wannan kwalliyar bata dace dakeba saudat saidai a d'akinki, amma kiduba taron jama'ar dake wajenan maza nawane dazasu kalleki, yabi jikinta da kallo doguwar rigace ta jan material bata kamata sosaiba amma dukda haka yaji kishi barinta tashiga wajen ahaka, Dan ALLAH kalli rigar dake jikinki. Iman ta ture hannunsa da k'arfi sanan tabi jikinta da kallo tad'ago tana kallonsa miye laifin rigarnan Dan ALLAH?, nifa gsky kafara takurama rayuwata, lokaci yayi dazaka barni nasha iska mai dad'i, kwalliya kuma nibanga aibuntaba koso kake nazo wajen kamar wata korarriyane, cike da tsiwa take maganar Dan haka ta k'ara tunzura masa zuciya. Takowa yayi zai matso Kusada ita ta matsa, ya matso, ta matsa, dahaka har suka dangane da wata mota, ta matse jikinta da motar tana k'ara d'aure fuska, shima fuskarsa tamau take kamar ba Dr Isma'il ba uncle d'in Deexerh. Wani irin tsorone yaratsa zuciyar Iman, Dan batasan miyake shirin yimataba, muryarta na rawa tace doctor please kayi hak'uri Dan ALLAH. dukda idanunta arufe suke wannan bai hanashi hararartaba, yamatsar da fuskarsa GAF da tata har sunajin saukar numfashin juna, cikin wata irin murya tamkar mai rad'a ya ce, " kina tunanin zan iya d'aga mini k'afa kishiga taron jama'arnan da wannan janbakin?. Da sauri ta bud'e idanunta kafin tace wani Abu ya had'e bakinsu waje d'aya, janbakin yashiga tsotsewa cike da nuna kwarewa, Iman sai dukan bayansa take amma a banza. Xoxo da Dr Nabeel suna zaune a tebir d'aya hira suke k'asa2, Xoxo tafara wayge2 waini inasu Iman ko har yanzu basu shigobane?... Kafin Dr Nabeel yabata amsa wasu guys suka k'araso wajen, Nabeel yamik'a musu hannu yana fad'in a'a Auwal kun k'araso. Eh wlhy d'an uwa, yaja hannunsa suka bar wajen, yayinda sauran abokan Auwal suka take musu bata, saida sukaje nesa da Xoxo sanan Auwal ya CE, Nabeel dama haka abokinka yake?. Da sauri Nabeel ya ce, "wane abokin nawa?, ko Isma'il?. " eh mana shi, bashine kukazo tareba. Shine Cewar Dr Nabeel. Hummm to wlhy gashi can a tsakanin motoci ya matse 'yar mutane yana sumbata. 'Yar mutane kuma?. Kai badai Isma'il ba, Dan bayida wannan halin, amma wane irin kayane ajikinta?. Kama hannunsa Auwal yayi, kaga muje kagani sai, k'ila kafi yarda da zancenmu. Dr Nabeel ya sauke numfashi yana kauda kai daga kallonsu Dr Isma'il, yaja hannun Auwal suka bar wajen. Auwal ya kwace hannunsa haba Nabeel yanzu nan barinsa zamuyi harsai yakai da yimata fad'e?, kallifa yanda take dukan bayansa alamar batason abinda yake mata. Tsaki Dr Nabeel yayi ya ce, "kai dallah malam matarsace fa. Matarsa kuma?. Eh Dr Nabeel yafad'a da k'arfi. Tofa amma yarasa a Inda zai mata wanan abun sai anan kuma aii koda kukazo banganku da mataba. Harararsa Dr Nabeel yayi, saika gammu tare zaka yarda ita matarsace?, to agidan su Aysha muka barsu, yaciro wayarsa a aljihu, ma'adanar hotuna yashiga saiga hoton Dr Isma'il da Iman da Musayeef suna dariya. Kalla kagani uban 'yan rashin yarda. Bayan yagani sauran abokan suka kar6a suka gani, wani ya CE, " kai ammafa sun dace wlhy. Dr Nabeel ya kar6e wayarsa, saiku muje ciki idan sun shigo Ku kalli yarinyar kugani basuyi kama data hotonnanba ne?. Ciki suka koma, Xoxo ta ce, "lfy dai, labari yabata, tayi dariya, ai tunda muka Shiga mota naga dama yana harararta. Murmushi Dr Nabeel yayi ya ce, " kinsan mutumina akwai kishi, Nima na daurene kawai nabarki da kwalliyarnan wlhy. Ta ce, "sorry sir, nidai amin hak'uri daga yau bazan sakeba. Dariya yayi yana jifanta da wani shu'umin kallo, Xoxo tasa hannunta tarufe fuskarta saboda kunya. Hummm su Dr Isma'il kam bama Susan wasu sun gansuba, saida ya tsotse janbakin tas sanan yacire bakinsa yana sauke numfashi a wahalce, itakam Iman sai hawaye takeyi tama k'asa wani motsi, yad'agota yarungume yana shafa bayanta alamar lallashi, kece kika jama kanji, ke kanji kinsan ni mutumne mai kishi miyasa zakiyi wanan kwalliyar?. Ina rik'onki daga yau karki sake kinji, inba hakaba wlhy zanyi abinda yafi haka. Yad'agota yana share mata hawayen, kinga karkuma ki 6ata kwalliyar k'awayenki suce namiki wani Abu daban. Harararsa tayi tana turo baki gaba. Yatsansa d'aya yasaka yabugi bakin Kad'an yana murmushi. Yakama hannunta kinaga muje karsu Nabeel suyita nemanmu. Wajen yayi tsit Dan ana addu'ane za'a fara abinda ya Tara mutane, takun takalmansune yasa gaba d'aya mutane suka juyo suna kallomso, Dr Isma'il yana rik'e da hannun Iman. Auwal ya ce, " kai guys wlhy da gsk matarsace, ammafa babu maicewa ita ta haifi yaronnan, sunfa burgrni. Sudai su Dr Isma'il wajen su Dr Nabeel suka k'arasa suka zauna, suma akayi addu'ar dasu. Xoxo sai kallon bakin Iman takeyi, dariya ta taho mata taduk'ar dakai tayi abinta sanan ta d'ago. Dr Nabeel ya kalli Dr Isma'il yana murmushi, yaje saitin kunnensa yace malam ka goge jambaki a le6enka. Murmushi Dr Isma'il yayi, tareda saka hanki ya goge bakinsa. Tunda aka fara abubuwa Iman kanta yana k'asa tak'i yarda ta had'a ido koda Xoxo, gani take kamar sunga abinda yafaru. Ko awajen lik'i Dr Isma'il hanata sakewa yayi, da'aka kirata tabama amarya shawarama tare sukaje wajen, aiko sunsha hotuna, wasu sai fad'i suke kun dace gsky. Haka aka gama taron Iman duk tana a takure saboda Dr Isma'il yabi ya katantaneta, karfe 12:00pm daidai aka tashi. Daganan gidan Amarya aka wuce dasu. Kowa yana zuwa yanemi makwanci amma bandasu Xoxo, hira suka dasa sabuwa. Xoxo ta ce, "Iman wai d'azu mikuka tsaya yi awaje keda daddyn Musayeef?. Babu komai tafad'a cikin rashin gsky. Hummm kinsan dakuka shigo miya birgeni?, Iman ta harareta kinsanfa banason iskanci. Babu wani iskanci, towaima miya kawo janbaki a le6en daddyn musayeef?. Kije ki tambayeshi mana ba abokin saurayinki bane. Xoxo da Reefat suka tuntsure da dariya harda tafawa. Iman takaima Reefat duka 'yar iska kema gobe iyanzu kina hannun yaa Usman, ALLAH yasa yay miki sambad'e bad'e, tana gama fad'a taja bargo. Duk iskancin dasuke mata bata sake kulasuba. Na ce, " humm 'yamma tanan akwai shafta gsky, ko Yaya za'a rabu yayin tafiyarsu Iman?............ *Luv u I'll my fan's* *((((S))))........2017* [8/6, 6:02 PM] mrs bilkisu: *_BAN SAKETA BA!!_* *_NA Billyn Abdul_* _sadaukarwa_ *ya Abdul (city phone's)* https://mrsbilkisa.blogspot.com *miya kamata nayi?* _iyaye muringa kula da 'ya'yanmu, muringa kula kuma dawa suke mu'amullah, akwai had'ari yanzu sosai akan yaranmu maza da mata, Dan kowane yana iya fuskantar k'alubale daga 6ata gari, yara mazama wai yanzu suma saikiji ance anyi musu fad'e. Humm ya salam._ _wai Dan ALLAH ina akeso mushiga mu 6uyane, wannan wane irin masiface, yanzufa takai wai kishiya da kishiya zasu iya mad'igo, humm mata wai ina kishin damuke ik'irarin munayi?, kai rayuwa Yaya da k'anwa saikiga suna mad'igo, hasbinallahu wani'imal wakil, wanan wanne irin k'azantace, muringa tuna yanda ALLAH yayi da jama'ar *"ANNABI LU'DU A,S"*, ni d'alibar ilimice shiyyasa bazan kawo ayaba, amma kuje kuyi bincike Wanda baisan makomarsuba tofa zaiji._ *ALLAH yasa mugane.* *_"cigiya 'yan uwa INA cigiyar 'yar uwata Riddallah 2days ta 6acema ganina😭."_* *(page 29)* Washe gari akayi walima da k'arfe 2:00pm Dan haka bak'in dake kusa suka fara kama gabansu, su Xoxo ma gobe idan ALLAH ya kaimu zasu tafi. Su kad'ai aka baro gidan amaryar, sunata hirarsu da tsokanar juna kamar bazasu rabuba. Har dare suna gidan, saida suka gyara mata ko ina sanan, abokan ango suka shigo hardasu Dr isma'il, bayan d'an hira da barkwanci irin na abokai suka mik'e zasu tafi. Tofa yanzufa akeyinta, Dan su iman rungume juna sukayi suna kwasar kuka, Dan daga yanzu bazasu dawoba tafiyar asuba zasuyi, abokan angon duk sun tsaya suna kallon ikon ALLAH, sun birgesu sosai daga gani k'awancen nasu yanada dank'o. Dak'yar suka rabu da juna, ya Usman yarungume Reefat yana lallashi, shima Dr Isma'il yacewa su iman kuyi hak'uri mutafi dare yanayi. Bayanda zasuyi suka fito kowa yana share hawaye, koda suka Shiga motama kukansu suka cigaba. Gidan su Reefat suka kaisu dansuyima mamansu Reefat sallama. Kayan biki nagani nafad'a Mmn Reefat ta had'a musu, harda tsaraba ta musamman, taso su kwana anan amma Dr Nabeel ya ce, "tayi hak'uri tafiyar asuba zasuyi. Bayanda zatayi haka tarakosu har Mota, daga nan ba gidan sukayi kai tsayeba zagayawa cikin gari Dr Nabeel yaytayi dasu harsuka d'an saki jikinsu, daganan yakaisu gidan dasu mom d'insa suke. Nanma tarbarsu akayi sosai k'annan Dr Nabeel sai murnar ganinsu sukeyi, Ayeesh da Maimuna, sumadai 'yammatane Dan zasuyi sa'anni dasu Xoxo, mom d'in Dr Nabeel sai murna take, ta ce, "to ina matar ta Isma'il ina kuma ta Nabeel?. Iman da Xoxo sukayi k'asa da kai sunajin kunya, Dr Nabeel ya ce, " mom ga Iman matar Isma'il yanuna iman. Wanan kuma itace..... Saikuma yay shiru yana Sosa k'eya, su Ayeesh suka tuntsure da dariya, ya hararesu. Masha ALLAHU 'ya'yana ALLAH yay muku albarka kunji, ALLAH yasa kuduka abokan arzik'in junane, Ameen su Maimuna suka amsa. d'aki d'aya suka kwana dasu Maimuna sunsha labari sosai, dansu Ayeesh akwai surutu, 😉lol. ana fitowa daga sallar asuba suka shirya, maimuna da Ayeesh sukace zasubi motarsu, hararsu Dr Nabeel yayi, ya ce, "tare mukazo dakune?, a'a maimuna tafad'a. Ayeesh ta ce, " Yaya Dan ALLAH kabarmu, kinsan ALLAH kokimin shiru kona bigeki anan, dama kuntafi wajen mom tunkafin dare yamuku, Ku saima gobe zaku taho. Babu yanda zasuyi haka suka hak'ura, dukda Magiyar da Dr Isma'il yay MASA akan yabarsu, ya ce, ''wlhy Isma'il bazasu bimubafa. Haka suka Shiga mota su Ayeesh suna d'aga musu hannu, anan ma kayan biki sosai mom d'in Dr Nabeel ta had'a musu. Dr Isma'il ne yake tuk'in yanzu, sharara gudu yake sosai yayinda iman da Xoxo sukayi barci kamar randa suka taho. Wanan karon basu tsaya ko inaba, Dan abinci mom tad'an shiryo musu, sai wajen k'arfe uku suka tsaya sukai sallar azuhur da la'asar, daga nan suka sake d'aukar hanya, cikin amincin ALLAH karfe 5:15pm acikin kano tayi musu, gidan su iman aka ajiyesu su, Dan Xoxo saida safe zata k'arasa gida. Gwaggo da deeni da musayeef sunyi farincikin dawowarsu, bayan sunyi wanka sukaci abinci aka zauna bama gwaggo labarin biki da yanda ya gudana, da hotuna. Gwaggo taji dad'in yanda aka karramasu sosai. A can kuwa saida Dr Isma'il ya sauke Dr Nabeel sanan yanufi gidansa, 6angaren mama yafara zuwa, bayan sun gaisa yashiga wajensu yayansa daganan yanufi 6angarensa, tun afalo yafara gamo da abin haushi domin falon kaca2 kamar ba'a sharewa, tsaki yaja yashiga d'akin iman Inda yamaida d'akinsa, kai kawai ya girgiza Dan nannmadai abin haushinne, yanda yabar d'akin haka yazo yasamu abinsa. Zagewa yayi yagyara tsaf, sanan yayi wanka, harya kwanta baiji motsin Raihan ba, haushinta yakeji Dan haka yay kwanciyarsa. Itakam bamata gidan, tun yamma suka Fita itada aunty sai k'arfe 9 na dare suka dawo, babu Wanda yace mata Dr Isma'il yadawo, Dan haka tana dawowa tashige d'akinta ta kwanta. *washe gari* Da Asuba yafita masallaci batareda ya kalli ko hanyar d'akintaba, saida gari yafara haske sanan yashigo, saida yaje suka gaisa da mama sanan yashigo. Raihan ta tsaya cak tana kallon ikon ALLAH, shima binta yake da kallo fuska a d'aure, dayake ta karantu da ilimin Rayuwa saita basar da mamakinta tazo ta rungumeshi. My one yaushe kadawo bansaniba?, baice mata komaiba, tad'ago tana kallonsa, ganin yanda yake hara rarta saita shiga aika masa da sak'wanni, Raihan irin fitunannun matan nanne, kwana ukunnan atakure tayisu ta daurene kawai. Ogafa yafara yin sanyi, Dan abinda take MASA komai dakewarsa saiya kalleta, baimasan sanda ya d'auketa sukayi d'akiba, Dama ga garin dad'an sanyi sayin hadari dake tasowa, humm afito lafiya🙄. Sai wajen shabiyu suka tashi tare sukayi wanka, Raihan sai salo takeyi ita matar so, (nace hummm), bayan sun shiryane yasata ta gyara falon da duk Inda yadace, 6angaren mama yaje sukaita hirarsu har aka kira sallar azuhur, daga nan yanufi masallaci. Koda yadawo bainufi wajen mamaba saiya wuce 6angarensa, harya gota d'akin Raihan saiyaji magana k'asa2 Dan haka yadawo bayan, ak'ofar d'akin ya tsaya cak danjin furicin aunty. Hummm ammafa auta kinyi k'ok'ari gsky, shiyyasa duk cikin k'annena nafi sonki, yanzu kina nufin yau da safe ya kusanceki?, kuma da maganin kikayi amfani?. Wlhy kuwa aunty, Aida ya had'e girar sama data k'asa zaimin buyagi, naje na rungumeshi, narigaya na gano lagonsa na Shiga aika masa sakwanni, ai tuni yakwasheni muka tafi d'akinsa. Da k'yau k'anwata, kidage amfani da maganinnan kamar yanda malam yace, ''saiya manta da waccan banzar dayake ik'irarin akanta ciwon zuciya ya sameshi, yanda mukayi nasarar fiddata agidannan haka zamuyi nasarar gogeta azuciyarsa. Idanu Dr Isma'il yazaro waje..... Raihan taci gaba da fad'in, aii ni wlhy aunty har yanzu lamarinki mamaki yake bani, yanda har kika iyayin rubutun Yaa Isma'il kamarshi ya rubuta, kuma kowa ya d'auka da gsk shiyya rubuta sakin. Dariya suka kwashe da ita suka ta6a kamar wasu k'awaye..........da k'arfi Dr Isma'il yadaki k'ofar d'akin, arikice suka d'ago suna kallonsa. Wani kukan kura yayi yadamk'i Wuyan rigar Aunty ya sharara mata mari saubiyu, yacigaba da jibgar banza. Ihun aunty da kururuwan Raihan yasa mama da mom da marwan isowa da gudu, sai janye Dr Isma'il suke amma bai daina dukan aunty ba. Su mama sunrasa yanda zasuyi gashi ya fasa mata kai Dan dukanta yake ta ko ina, waya mama tasa takira Yaya. Mansur komi kakeyi kazo gidan yanzunan babu lafiya, bata jira amsarsaba ta yanke wayar. Cikin minti 20 saiga Yaya sanan Dr Isma'il Yakoma dukan Raihan yabar aunty tana sauke numfashi da k'yar. Marinsa Yaya yayi, Isma'il wai bakada hankaline misuka yimakane?. Hawaye yafara yanna nuna su aunty dake kwance suna jiyyar Kansu, bakinsa sai rawa yake alamar yanason yayi magana amma ya kasa, ya dafe k'irjinsa da sauri, luuuuuu yayi baya zai fad'i da sauri Yaya ya rik'eshi yafad'o a hannunsa. Yaya ya girgizashi Isma'il! Isma'il!!, shiru, da sauri ya CE, marwan muje mota ya suma. Mama tafashe da kuka, tana fad'in wayyo Isma'il kana ganin rayuwa kaidai Dan ALLAH karka mutu kabarni. Marwan yana gyara mota za'a saka Dr Isma'il saiga Nabeel ya shigo, da sauri yak'araso yana tambayar lfy?. Suma yayi cewar Yaya, Dr Nabeel ya ce, "Yaya amaidashi ciki saina dubashi bama sai Anje asibitiba. Haka kuwa akayi aka maida Dr Isma'il d'aki, taimakon gaggawa Dr Nabeel yashiga bashi, bayan kamar Minti goma ya farfad'o. ALLAH yasama akwai allurai da ake MASA, Nabeel yay masa allura yasamu barci, saida yak'ara kwantar musu da hankali sanan yatafi. Mama takali su aunty da duk hankalinsu yake atashe tun d'azu, zuciyar Raihan tayi rauni sosai, bata ta6a ganin ciwon Dr Isma'il ba, batayi zaton haka yake shan wahalaba, tayi danasanin biyewa aunty, gashi tun ba'aje ko inaba komai ya rikice, tasamu Dr Isma'il kuma zai kufce mata alokacin datake buk'atar zama taredashi. Yaya ya katse mata tunani da fad'in saikumuje k'yamis kukuma Dan tabbas akwai wani babban Abu da kuka aikata ga Isma'il, kowa yasan hak'uri irinna Isma'il, amma har kuka kaisa mak'ura...... Aunty ta bud'e baki zata fara rantse2 yadaka mata tsawa, bana buk'atar jin komai daga bakinki harsai Isma'il ya farka. Shiru tayi Dan tasan halinsa zaiyiya k'ara mammaujeta ne. Marwan kam sai hararsu yakeyi, dama haushi suke bashi. A6angaren iman kuwa komai Normal, bayan taraka Xoxo tadawo tahad'a wankin gwaggo da musayeef tanayi musayeef yana tayata konace yana wasan ruwa. Tana gamawa tayima musayeef wanka suka shige d'aki, wasa suketayi tana biye MASA sunata dariya cike da farinciki, yau tunda tatashi takejin wani irin nishad'i na musamman Wanda ita kanta batasan na miyeba, jitake tamkar an sauke mata wasu kaya masu nauyi aka. Suna cikin wasansu duksun hargitsa gadon gwaggo talek'o, oh ni ALLAH ya shiryeku, kaidai ka maida uwar taka kamar wata kakarkama. Nidai kutaso kuyi mama girki da wanan shashancin. Iman tayi dariya to gwaggo. Fitowa tayi tana dariya Musayeef nabinta waisaita MASA goyo, tsugunnawa tayi ya d'ane bayanta suna dariya, ahaka suka Shiga kicin , gwaggo tabisu da kallo tana murmushi, ta d'aga hannu sama tana fad'in Ya ALLAH ka kawo farinciki da alkairi a rayuwar wanan yarinya da d'anta, ALLAH ka bayyana gsky itama takoma gidan mijinta kokuma tayi wani aunren... *_(Araina nace gwaggo addu'arki aii tadad'e da kar6uwa😁).............._* *luv u oll my fan's* *(((S))).........2017* [8/6, 6:02 PM] mrs bilkisu: *_BAN SAKETA BA!!_* *_NA Bilyn Abdul_* _sadaukarwa_ *ya Abdul (city phone's)* https://mrsbilkisa.blogspot.com *Gargad'i!!!.* _hummm namiki magana karki k'ara sakani group dabai daceba kink'iji ko?, wlhy idan kika k'ara kaini Group na iskanci kowanda aka danganta dawani Abu sainaci.......humm bana zagi, amma tabbas zakisha mamaki, banason ciki da iskanci kinjiko, banmiki kama da 'yar iskaba, Dan haka kishiga hankalinki_ _sauwajen uku ina tsintar kaina agidan banza, kuma idan naduba sainaga kece kika kaini, nafarko namiki nasiha k'ink'iji, nafita anabiyu bantankakiba, yanzu kinkaini na uku, to wlhy ana hud'u ubanki zanci, bazan fad'i sunankiba amma kinsan kanki, kuma kika k'ara zan yayatakine wlhy._ _Kikama kanki kafin watan cin ubanki yatsaya, shaid'aniya kawai maikafa gidan banza mtsooooww._ *idan kunne yaji👉🏻😡* *(page 30)* Gaba d'aya ahalin gidan suna falon mama, kowa yayi jigum jugum Dr Isma'il kawai ake saurare, ya share kwallan dasuka cika MASA ido tareda cije le6e. Yaya ya ce, "isma'il kayi hak'uri kasanar mana abinda ke faruwa, gaba d'aya kunsakamu aduhu wlhy. Dr Isma'il yawatsamasu Raihan harara tareda girgiza kai, idonsa yak'ara cikowa da kwalla yanuna aunty Yaya dama matarka itace silar shigata Matsala arayuwa, itace ta rabani da farincikina matata. Haba sadiya minayi miki?, mina tare miki agidanan?, mi saudat tayimiki ne haka da zafi?. Tunda yafara maganar suke binsa da kallon ikon ALLAH, su kalleshi su kalli su Raihan, mama ta ce, " Isma'il bamufa ganeba har yanzu. Raihan ta fashe da kuka wlhy mama nidai ba laifina bane aunty CE tace muyi haka, amma ALLAH bani baceba, Dan ALLAH ya Isma'il karka sakeni INA Sonka wlhy, rashin mafitane yasa na yarda da shawarar aunty alokacin...... Wata razananniyar tsawa Dr Isma'il yadakama Raihan, walhy kokimin shiru kona shak'eki kimutu!!!!!. Yaya Yakama hannunsa yamaidashi zaune, ya ce, "Raihan fad'a mama mike faruwane?. *_Tuna baya_* Kamar yanda kuka sani munso juna da yaa Isma'il sosai bayan bikin aunty da Yaya, harma anyi maganar aurenmu amma Mamana ta ce, " bata yardaba baza'a had'a mata yara agida d'ayaba, dagani harashi. Mumshiga damuwa har aka hanani zuwa gidanan gaba d'aya. Bayan kamar shekara uku da faruwar haka sainaji auren yaa Isma'il dawata baniba, hankalina yatashi matuk'a amma babu yanda zanyi na hak'ura, kowa yazo bikin daga sokoto amma bandani saboda kishi, bayan komawarsu sukaita bani labari akan Yaa Isma'il yarinya ya aura amma sun dace, wannan yasa hankalina yatashi nakira aunty ta ce, "nashirya nazo kano. Bansamu matsalaba su mama suka barni nazo domin itama tafara son Ya Isma'il sanan, amma bansan dalilintaba. Hankalina yatashi sosai daganin matar ya Isma'il, gakuma soyayya dayake nuna mata wadda ni ko rabinta bai nuna minba sanda muna tare, wannan yasa muka fara k'ulle k'ullen rabashi da IMAN nida aunty, mun aikata abubuwa dayawa ga iman amma bata ta6a fad'awa kowaba, inaga sai deexerh, ganin munyi2 babu nasara yasa aunty takirani awani daren juma'a. *(" Raihan kinason Isma'il da gsk?. Eh wlhy aunty inasonsa. Kinason samunsa?. Dasauri na ce, "eh mana. Dariya aunty tayi irinta muguntarnan, tamik'omin takarda, kar6i ki karanta wannan".)* Takardar nakar6a na karanta wadda aka rubuta takardar sakin iman, nasan rubutun ya Isma'il sosai Dan haka nad'ago da sauri INA kallon aunty, aunty kina nufin Yaya dakanasa yarubuta sakinnan?. Kallona tayi tana murmushi, miyasa kikamin wannan tambayar?. " aunty naga irin rubutunsa. Dariya, tobashine yarubutaba nice nan. Kece kuma? To tayaya?. Hummm auta haryau ke yarinyace, bazaki ganeba, nad'au tsawon lokaci ina kwaikwayon rubutunsa hardai ALLAH yabani nasara na iya, dama saboda irin ranarnan nakoya. Jinjina kai nayi INA mamakin kalamanta, to aunty tayaya kike gani Yaya zaiba iman takardar sakinnan?. Aunty tayi murmushi wannan ai mai sauk'ine kedai kisaka idanu kisha kallo. Bayan kwana uku dayin maganarnan da yamma sai aunty takirani tabani takardar wai naje k'ark'ashin filon iman nasaka, cike da tsoro nake kallonta tadakamin tsawa, ke sakara idan bazakiyiba abarsa kefa nake taimako zaki zauna kina kallona. Jiki tana rawa na kar6a na nufi 6angaren iman, babu kowa afalon sai TV daketa 6a6atu, asand'a nashiga d'akin iman nanma babu kowa saidai naji motsin ruwa abayi alamar tana wanka, da Sauri nad'aga filon farko nasaka takardar nafita da Sauri, gafff mukai karo da Ya Isma'il ak'ofar Fita daga falo, yanda jikina ke 6ari saiya tsaya yana kallona. Kekuma lfy?, yafad'a idonsa akaina. Da Sauri na daidaita nutsuwata na ce, "wlhy 6era Nagano Kasan kuma INA tsoronsa. d'an murmushi yayi yana girgiza kai, kekam keda 6era kun k'ulla, amma ta inama 6era yashigo gidanan?. Na ce, " halan ta k'ofar baya ko. Hakane kuma, bari zan fad'ama saudat taringa rufe wajen idan yamma tayi. Okey bari nawuce dama nazo Neman Deexerh ne Ashe bata nan. Tom saida safe tafad'a tana shigewa. Dagudu na Isa 6angaren aunty na rungumeta INA dariya na ajiye wlhy ammafa ankusa kamani, anan nabata labari tayi dariya kedai akwai shegen tsorone kawai. Shikenan matsalarmu ta k'are muka tafa. Washe gari bayan tafiyar yaya iman tasamu takardar....... Raihan tak'are maganar da shashshekar kuka, wannan shine abinda ya faru. Gaba d'aya falon aka d'auki salati da tafa hannaye. Aunty da Raihan sai kuka sukeyi. Yaya yanisa yamaida hankalina akan Dr Isma'il, ya ce, "to kaikuma alokacin miya hanaka kiran wayarmu?, miya hanaka dawowa bayan sati biyu kamar yanda kace. Dr Isma'il yacije le6e, bayan barina gida anturamu Maiduguri, bayan zuwanmu da kwana hud'u aka harbeni a kafad'a yajanye rigarsa, hudin shigar bullet suka gani akafad'arsa, mama ta fashe da kuka, yacigaba da fad'in bayan harbi nasamu raunika sosai wannan yasa nahana akiraku Dan banason hankalinku yatashi, saida nayi jiyya ta wata biyu dawasu kwanaki, inasamun lfy nataho kano dannaga halin dakuke ciki shine natara wai matata bata gida. Mom da mama da marwan duk kuka suke suma na tausayin Dr Isma'il, falon yayi shiru babu abinda kakeji sai shashshakar kukansu. Mama ta ce, " kunga kutashi mutafi gidansu iman yanzunan. Haka kuwa akayi gabad'a suka d'unguma said gidansu iman. *Gidansu Iman* Iman da musayeef suna tsakar gida zaune tana ninke kayansa data wanke, shikuma yana d'ebowa daga kan igiya, gwaggo tana kicin tana girkin dare. Da Sauri iman tajuyo danjin sallama, da Sauri tamik'e Dan ganin kaf 'yan gidansu Dr Isma'il, dagudu Musayeef yaje ya rungumesu yana murnar ganinsu. Gwaggo tafito daga kicin danjin ihun murnar musayeef, Ita kanta tatsorata daganinsu amma dukda haka saita ce, "sannunku dazuwa. Yauwa suka amsa mata, ta ce, "kushigo. Iman dai tana tsaye tamkar gunki, Dr Isma'il yak'araso gareta tareda kama hannunta, da Sauri ta fisge hannun takoma ta zauna, sukuma suka wuce cikin falon Inda gwaggo take musu maraba. Bayan sun zauna suka gaisa da gwaggo, Yaya ya ce, gwaggo Abbah fa?. Yana wajen aiki mansur ALLAH yasadai lfy?. Alhmdllh gwaggo saidai munason ganinsa munzone dawata magana. Babu damuwa bari akirashi gwaggo tafad'a tana d'aukar waya. Bugu d'aya abbah ya d'auka tamasa bayani komai, ya ce, "gashinan zuwa gidan. Gwaggo takoma kicin ta had'o musu kayan sha tadawo, har yanzu iman tana tsakar gida zaune ta rabga uban tagumi da hannu biyu. Ita atunaninta kosunzo su k'ar6i musayeef ne, tab lallaikam Ashe yau da bala'i wlhy, Dan mairabani da yaronnan saiya shirya, wlhy koza'a kasheni bazan yarda su d'aukeshiba. Tana cikin zancen zuci abbah yashigo, a'a iman lfy?. Ta share hawayenta abbah Dan ALLAH karku yarda sunzo kwace musayeef ne nikuma wlhy bazan basuba. Abbah baice komaiba Yakama hannunta suka Shiga falon ,Dan shima komai za'ayi bazai basu musayeef ba. Bayan anyi gaisuwar mutumci da tambayar rayuwa Abbah ya CE, ALLAH dai yasa lafiya. Lfy lay Alhaji alkairine yakawomu. Yaya yacema Raihan ta maimaita abinda tafad'a agida. Tiryan2 ta zayyane komai, Dr Isma'il ma ya d'ora da nashi, salati su abbah sukaitayi, itako iman kuka Rurus takeyi tamkar ranta zai Fita, wlhy ko amafarkinta bata ta6a kawo hakan arantaba yanzu dama mijinta *bai saketa ba* aka rabasu kai ALLAH yarabamu Da saharrin mak'iyidai. Bayan maida zance abbah ya ce, " INA Neman wata alfarma agunku mansur da Isma'il harda ke mama. Suka amsa dato suna saurarensa. Abbah ya ce, "Dan ALLAH karku saki matanku kubarsu kawai, Haka ALLAH ya hukunta. Arazane Dr Isma'il yake kallon Abbah, abbah ya ce, " alfarma nanema inafata zakuyi mini. Mama ta ce, "shikenan Alhaji insha ALLAHU bazasu sakesuba. Dr Isma'il yay wani murmushi mugunta, azuciyarsa ya ce, " wlhy sai sungwammace inama mun sakesu, Dan zasusha mamaki humyimm k'yarrrk. Anan kuma Dr Isma'il ya ce, "yanason sutafi da iman yau. Itako tafashe da kuka ta ce, bafa yauba. Mama ta ce, " a k'yaleta to har sanda tasa shiya, aii bama zaiyuwuba Isma'il, kata6a ganin an raba mutum da gidansu tashi d'aya, kabarta har sai sanda ta shirya,....... A'a abbah ya katseta, insha ALLAHU nanda sati d'aya ko kwana goma zata dawo d'akinta shima nace hakane saboda shirye2. Dr Isma'il ya ce, "abbah kardai asayama iman wasu kayan d'aki tunda ba'a kwaso wad'ancanba, insha ALLAHU awanan karon nizanyi komai, iman kawai da musayeef nake buk'ata. Shike nan Isma'il ALLAH yayi muku albarka. Iman tashi tayi tashige d'akinta tana hawaye, Dr Isma'il yabita da kallo. Gado tafad'a tana kuka, wai Ashe Doctor yak'ara aure bata saniba, dama Ashe Raihan budurwarsa CE ya6oye mata, kuka take sosai, wlhy badan kar iyayenta sauce ta rainasuba da babu Inda zata, dabazata koma gidansaba saidai ya saketa kuwa, haka taita kuka zuciyarta na k'una saboda kishi, sai yanzu tagano canjin dayay mata. Dr Isma'il kam badan yasoba yabi su Yaya suka tafi, yaso ace ayau aka bashi iman suka tafi tare, amma yazaiyi dolene yabi Maganar many a............... *luv u oll my fan's* *(((S)))..............2017* [8/6, 6:02 PM] mrs bilkisu: *_BAN SAKETA BA!!_* *_NA Bilyn Abdul_* _sadaukarwa_ *ya Abdul (city phone's)* https://mrsbilkisa.blogspot.com *miya kamata nayi?* _humm hattara 'yammata rayuwar kece raini had'ari CE, duk Wanda yace shi wani ne, kosai yazama wani, tofa yana tareda wahala arayuwarsa._ _wanan rayuwar tana bala'in wahalar da 'yammata da matan aure, abinda wance tayi nima sainayi kota halin k'ak'a, hakan ba daidaibane, wanan rayuwar tana jefa mata dayawa fad'awa zina mad'igo kowani mummunan yanayi, burin sainafi wance kosaina tarar da wance yajefa matan aure dayawa bin maza._ _haba 'yar uwata miya rud'eki saboda San duniya kiringa zina da aurenki?, shin kinmanta da d'unbin zunubin dake bibiyarki ga cin amanar Addininki, cin amanar aurenki, ga cin amanar 'ya'yanki, ga cin amanar iyayenki, ga cin amanar 'yan uwanki._ _tsaya matsayinki domin haka ALLAH yayimu wani yafi wani, indai zaka ringa kallon na sama dakai to kanatare da wahala da asarar rayuwa kuwa._ *ALLAH yasa mugane* *(page 31)* Haka iman tawuni ad'aki tana kuka, da musayeef yaje wajantama koroshi tayi, yafito yana kuka, gwaggo ta ce, "lfy na gwaggo?. Aunty maa ce takoroni wai na 6ace mata dagani anan. Jawoshi gwaggo tayi jikinta tana share masa hawaye, kaga ishirunka yau aunty maa batada lfy ne, kabarta ta huta, kaji na gwaggo. Kai yad'aga alamar to, yauwa na gwaggo, Abbah yafito daga d'aki yana shirin fita, a'a Na gwaggo lfy dai ko?. Shida mamansane, kasan iman da zuciyar tsiya. Murmushi Abbah yayi, yakama hannun musayeef kaga muje karakani anguwa. Tsalle musayeef yafarayi na murna, suka fice shida abbah, gwaggo kuma tanufi d'akin iman. Kwance take akan gado idonta arufe amma hawaye sunata zirara, filon duk yajik'e alamar tadad'e tana kukan. Gwaggo ta girgiza kai tareda k'arasawa Inda iman take, bakin gadon ta zauna tad'ago da kan iman tamaida kan cinyarta. Batayi maganaba amma tana shafa kan iman tareda d'an bubbuga bayanta alamar lallashi, sunkai tsawon minti15 ahaka, har iman tayi shiru saidai ajiyar zuciya datake saukewa ahankali. Gwaggo ta ce, " haba iman miye kuma abin kuka muda yau abin farinciki ya riska, kinsan kuwa yanda muke farinciki nida abbahn Ku?, kobakison komawa ne?. Da sauri iman ta gyad'a kai. Humm to saboda mi?. Gwaggo yafariga ya k'ara aure, gwaggo tayi murmushi, yo iman Dan isma'il yak'ara aure shine bazaki komaba?, kowa bada halinsa zai zaunaba agidan, karki mantafa yanada hurumin auren mata hud'u fa. Nifa gwaggo bawai ina nufin haka bane, wlhy ina tsoron abinda zaije yadawo, tunkafin tazo gidan suka iya fiddani balle yanzu tana cikin gidan amatsayin matarsa. Gwaggo ta ce, "hakane iman, nidai abinda nakeso dake kizama mai yawan addu'a da Neman kariyar ubangiji, kid'auka abinda yafaru a baya yana cikin k'addararki, jiyanki tawuce yanzu gobenki zaki tsunkanya, fatana kiyi nasara a gobenki da jibinki, amma ta yaya?. Ta sanadin hak'uri da yawan juriya akan lamarin rayuwa, indan kika rik'e k'yautatawa da biyayya tsafta tattalin mijinki da 'yan uwansa ina mai tabbatar miki kece mai nasara insha ALLAHU. Isma'il yana sonki karki manta asanadin rashinki yakamu da ciwo mai ban tsoro, Dan ALLAH ina rok'onki karki maida hannun agogo baya, nasanar da 'yar uwarki tanata murna itada mijinta, muma gamu muna cikin farinciki, haka family d'in Isma'il suna cikin farinciki, mizaisa kebazaki kasance a farincikiba?. " kebak'ya buk'atar farin cikinmune?, kobaki so musayeef yarayu agidansu cikin 'yan uwansa, wanan yawon da'ake dashi bashida wani fa'ida". Ina buk'ata gwaggo, iman tafad'a tana share hawayen idonta. Yawwa 'yar albarka toki kwantarmin da hankalinki kinji, kizama mai tawakkali arayuwa, kefa yanzu uwace, idan kina saurin karaya arayuwa yaza'ayi ki k'arfafama musayeef gwuywa shikuma?. Kinutsu kicigaba da walwalarki, kinga nanda kwana goma abbahn Ku yace zaki koma, to yakamata mufara shirye2 Dan yanzu bake kad'ai baceba. Itadai iman batace komaiba sai kai data d'agama gwaggo alamar to. Haka gwaggo tayi ta mata kalamai masu dad'i harta saki jikinta. Su Dr Isma'il kuwa suna zuwa gida yanufi 6angarensa, Raihan madai ganin kowa yanufi NASA 6angaren yasa itama jiki a asanyaye tabi bayan Dr Isma'il. Afalo ta iskeshi zaune saman doguwar kujera, yajingina bayansa da kujera Kansa Asama idanunsa alumshe sai faman murmushi yakeyi. Tayi tsaye tana kallonsa, jitake wani bali'in sosa yana k'ara ratsa sassan jikinta, tamkar taje ta rungumeshi haka takeji, amma babu dama. Gwuywa a sa6ule taje gabansa ta durk'usa, muryarta narawa ta ce, "yaa Isma'il!. Yanajinta yay shiru, amma ya daina murmushin dayakeyi. Takuma fa d'in my One!. Ak'ufule yad'ago ya ce, " a'a uban my one, yanunata da d'anyatsa "k kishiga hankalinki wlhy, idan kika k'ara kirana da wanan sunan sai jikinki yayi tsami, kuma tun wuri ki 6acemin dagani kafin na 6a66allaki na 6allah banza. Da Sauri ta mik'e tabar falon tashige d'aki tana hawaye. Yarakata da wata uwar harara, yana tsaki ai bama kiyi kukaba yariya sainan gaba, saikince inama sakinki nayi yafimiki alkairi, yamaida kansa ya kwanta, kiran Dr Nabeel ne yashigo wayarsa, yad'aga suka gaisa. Isma'il ya jikin?. Da sauk'i d'an uwa, wai kasan miya faru kuwa?. A'a saika fad'a cewar Dr Nabeel. Labarin duk abinda yafaru yabashi, Al'ajabi da mamaki suka cika zuciyar Nabeel, ya ce, " lallai nayarda kaidin mata yafi na shaid'an, irin wananan k'ulli haka, amma miyasa Abban Iman yahanaka sakin banza?, aii daga ita har yayarta sun cancanci saki wlhy. Humm karka damu Nabeel wlhy saisun gwammace mun sakesu da zamansu atare damu, nikad'ai nasan abinda nake shirya musu zasuci ubansune aii, kaidai zakasha labari. Nanda kwana goma iman zata dawo, ka saurari zuwana gobe idan ALLAH ya kaimu. To shikenan ALLAH yakaimu goben saikaxo, Nima zan lek'a gidansu Hafsat ne, wlhy harnayi kewarta. Humm mutumina kaimafa kashiga dayawa. Dariya Dr Nabeel yayi, bama kasan nashigaba sai hafsat tazo gidana. To ALLAH yakaimu lokacin, aii gara mu aurar dakai muhuta da tuzurancinka. Hhhhhh zan rama sai iman tadawo. Zadai karame na hafsat. Wayar suka yanke kowa yana dariya. *bayan kwana uku* Dr Nabeel yabama Xoxo labari, Dan haka tazo har gida tak'arajin bayani, tayi farinciki, takumayi bak'incikin Auren Raihan da Dr Isma'il yayi, amma zata bar gidanne da k'afarta wlhy. Xoxo tabama Umma labari, lamarin ya girgiza Umma sosai, kuma tad'au aniyar gyara iman Dan jinta take kamar Xoxo, har gida taje tarok'i gwaggo da abbah suka bata iman ta taho da ita. d'aki guda aka ware mata, gyara na rikita guys ake mata, bata fita ko k'ofar d'aki, duk abinda take buk'ata Xoxo take mata. Humm masu karatu kunga kuwa yanda iman takoma, abin sai Wanda yagani, dolenefa mace ta rikice balle namiji, (nace humm su Dr Isma'il za'a🙊 baridai nayi shiru). To a6angaren Dr Isma'il mafa gyara sosai akema 6angarensa, Dan yayansa ya ce, "shine ya cancanta yayi komai, ALLAH sarki Yaya da ana samun yayye irinku da k'anne bazasuyi kukaba, gaba d'aya gidan ansake MASA fenti tamkar za akawo sabuwar amarya, Raihan da Aunty sunata kallon ikon ALLAH, _(lallai zakaran da ALLAH yanufa da cara, ko ana mazuru ana shaho saiyayi)._ Suna cikin tashin hankali kam, Dan yanzu babu mai kulasu agidan, sunzama tamkar mujiyoyi, yaya ma dayake mutumne mai zuciya, haryau baicema Aunty komaiba, ammafa yadaina Shiga d'akinta, baya amsa gaisuwarta, ko kallo bata isheshiba dama yagaji da mugun halinta, idan yashiga 6angarensa yaganta afalo zaune d'auke kai yake kamar bai gantaba, idan tashiga d'akinsa ya korota. (Tashiga tashin hankali, gara ace yazaunar da ita yay mata masifa akan shareta d'in dayakeyi yanzu). Suna zaune itada Raihan sun zabga tagumi. Raihan tashare hawayen dasuka cika mata idanu, aunty yanzu yakike ganin zamuyi, nifa wlhy har yanzu inason ya Isma'il, gashi yanzu yace ko shigowa yayi yaganni afalo wlhy saina gane kurena, kina ganin yanzu andaina cin abinci damu, babu mai mana magana agidanan, aunty kinsakamu amatsala munshiga uku mukam, munzama mujiyoyi. Aunty ta ce, "humm Raihan kenan, nifa d'azu marwan marina yayi wlhy,. Marifa kikace?, marwan d'in?. Wlhy kuwa Raihan, kuma babu damar ramawa bare nad'au wani mataki, nifa sonake kawai Mansur yasakeni. Kai aunty kidaina manager fatan saki wlhy, k'ila nangaba su hak'uri, kinsandai zaman sokoto d'innan bawani dad'i bane, ko abincin arzik'i babu. Nima abinda nake hangowa kenan Raihan shiyyasa d'azu na k'yale marwan. Mucigaba da hak'uri akan duk abinda ZAMU gani watarana sai labari aii. Shikenan ALLAH yabamu ikin jurewa. *(ni bilyn Abdul na ce, " humm, jurewar nan dakamar wuya, musamman idan Deexerh tadawo, ah ah ah,)* Marwan ya Sanar da deexerh komai Dan haka tak'agara su gama Exam ta taho gida, ita kad'ai tasan muguntar data shirayama k'ananan 'yan iskannan, gashi takira wayarsa Iman akashe, Dan haka ta hak'uri tabar komai saitazo gidan. Iman kam tanajin gyara wajen ummansu Xoxo, aunty Salma tana aikawa da nata agefe, itamadai gwaggo tana bada gudummawa sirrinsu na manya, Xoxo da iman ma suna 'yar tasu fasahar dasuka sani, _(nace humm zafa Ku haukata Dr Isma'il)._ Shi hankalinsama atashe yake, Dan saikiran wayarta yake akashe, arikice yazo gidansu gwaggo ta ce, "aii batanan, d'aukar Musayeef yayi suka yafi gidan aunty Salma, nanma akace MASA batanan,. Aunty pls.... Karku haukatar dani Dan ALLAH tana ina?. A'a k'anina bazaka haukaceba, iman sunyi tafiya da hafsat, amma insha ALLAHU zasu dawo nanda kwana hud'u. Aunty nanda kwana hud'ufa kikace, randa iman zata koma gidana. Hakane insha ALLAHU. Kai Dr Isma'il yadafe, yana fad'in wayyoni ALLAH na. Aunty tayi dariya, to kwana hud'u aii kamar yaune insha ALLAHU, daga nan ba kayarka za'a maida makaba. Dariya ya Majeed yayi, kai abokina kadafa kayimana kuka wlhy, irin wanan damuwa haka, idan sak'one kawo nabata. Dr Isma'il ya hararesa, aii nama lura hardakai aka kulla 6oyeta. Hhhhhh yanzu kuma kaina zaka dawo, to bazadai mu bayarba sainan da kwana hud'u. Tashi Dr Isma'il yayi yasa6i musayeef dayayi barci akafad'a, aii shikenan zan rama Nima, nabarku lfy. Dariya sosai aunty Salma da ya majeed suke masa, shima Fita yayi yana dariyar. *RANA BATA K'ARYA* yaune wa'adi yacika, tunda sassafe akadawo da iman gidansu, gwaggo sai latsa jikin iman takeyi cike da mamaki, iman kin canja mi umman hafsat d'in tarink'a bakine haka?, kai ALLAH yasakama wanan baiwa da Alkairi, ALLAH yasa munada Rabon ganin bikin hafsat haka. ( Na ce, "amin gwaggo). Dukda Dr ya ce, " kar a kaita da komai, saida aka k'ara siya mata kayan kicin Nagani na fad'a, ga d'inkuna sababbi cike da akwati da aunty Salma da ya majeed sukai mata, ummansu Xoxo ta had'a mata turarirrika masu sirrin k'amshi, najiki na d'aki nagashi na kaya, kai lamarinfa sai godiya. *_8:00pm_*................ *luv u oll my fan's* *(((S)))...........2017* [8/6, 6:03 PM] mrs bilkisu: *_BAN SAKETA BA!!_* *_NA Bilyn Abdul_* _sadaukarwa_ *ya Abdul (city phone's)* https://mrsbilkisa.blogspot.com *miya kamata nayi?.* _kizama mai kamunkai, wlhy 'yammata iskanci baida wata riba, babu abinda yakai budurci daraja ajikin 'ya mace, shin miye ribarki idan kin rabama guys naki a titi?._ _randa kikayi aurefa akwai Matsala wlhy, duk d'an isaka baya son auren 'yar uwarsa 'yar iska, burinsa yasamu nitsatstsiyar mace kamila ya aura, kinga wanan kawai ya Isa ya nuna miki kin fad'i babu nauyi, idan aure kikeso karkiji kunya kisanar da iyayenki, idan bazaki iyaba samu wani a 'yan uwanki kisanar masa yasanar da iyayenki, wanan rashin kunyar tafi sauk'i akan kizubar da darajarki awajen wani sakarai Wanda baisan muhimmancin budurcinkiba, 'yar uwa tattali abinki kikaima mijinki domin yasaka ranar farkonku acikin muhimman kundin tarihinsa, duk mijin da matarsa takai masa budurcinta bazai ta6a mantawa da wannan k'yautarba har k'arshen rayuwarsa._ _wallhy 'yar uwa gsky nake gayamiki budurci mutunci, kuma, nagarta, donk'on so, tattalin so, k'auna ta musamman yake jawowa gadukkan macan data kaima mijinta._ *ALLAH yasa mugane* *(page 32)* *_8:00pm_* kowa yagama shiri za'akai iman, gayyace guda y'an rakiyya, Dan Matan anguwar dayawa sunshigo Dan rakiya abin kamar wasa. Xoxo dake kusada iman zaune sun gama waya da Reefat sun bata labarin komai tanata murna, kira yashigo wayar Xoxo, takalli wayar tana murmushi Dan wringing na musamman tasaka masa, itadai iman sai binta take da kallo kawai, ga zuciyarta taf da fargaba. Assalamu alaiki gimbiyata. Wa'alaikassalam sarkina. Dr Nabeel yay murmushi tamkar yana gabanta, ngd sosai dasamun sarauta, amma haryau baku maida mana amaryarmu bane? Tab aii wanan amaryar ta gskce, saikunzo da motama, 'yan rakiya fal gida. Kai haba?. ALLAH kuwa. Ku sauraremu gamu nan zuwa, kafin tace wani abu ya yanke wayar. Iman ta ce, "karfa ya d'auka gskne sisi. Oh keda wasa kika d'auka, kina ganin idan basuzoba saidai wasu mutanan suhau keke napep fa. Iman ta ta6e Baki, kenifa daza'a fasa zanyi murna. Dariya sosai Xoxo takeyi, haba 'yammata babu fashi yau saimun kaiki, ak'irjin Daddyn Musayeef zakiyi barci. Duka iman takai mata ta kauce tana dariya, wlhy hafsy ke 'yar sikace, amma Dr Nabeel zaimana maganinki, kamar yanda yaa usman yay maganen Reefat. Xoxo tamik'e tana fad'in Ashe za'a dad'e ba'ayi maganin nawaba....... Sallamar aunty salmace ta k'atse Xoxo, tamik'ama iman kaya, kinga tashi ki shirya abbah sai fad'a yakeyi. Iman takar6a tana turo Baki haba nikam naga takaina yau. Bakiga takankibama sai anjima aunty Salma tafad'a tana Fita. Dariya Xoxo tasaka, harda yima iman gwalo gsky ne auntyn mu, sai anjima zataga takanta. Iman tamik'e tanufi Xoxo, itakuma tafita da gudu, zan kamaki aii humyim. Xoxo tak'arasa inda aunty Salma take, saitin kunnanta ta gwargwad'a mata magana. Aunty Salma tayi dariya dgsk hafsat?. Wlhy kuwa aunty suna k'ofar gida, hannu aunty tabata suka ta6a, shiyyasa nakesanku 'yan k'annena kanku akwai kawo haske😉. Xoxo tayi dariya, aunty aigara muje musu ashirye su tabbatar wa mak'iya da gsk mukeyi. Tafawa suka sakeyi, ALLAH yamiki albarka k'anwata, yakaimu naki da Dr Nabeel. Da Sauri Xoxo tafita tana dariya, dansu ummanta suna gurin, itama taxo za'a raka iman da ita. Aunty Salma ta ce, "to jama'a ga motoci ankawo yakamata muyi harama. Kowa yamik'e akayi waje, aunty Salma tashiga ta Tatar Xoxo ta gama d'aurama iman d'ankwali, kwalliya sosai Xoxo tamata dukda bataso amma Xoxo ta dage saida tayi mata, tayi k'yau kamar wata aljana, _(nikaina mace saida na k'yasa😉)_.. Kamar wasa saiga iman tana rabzar kuka, gwaggoma kukan takeyi, ahakadai aka lalla6a akyo waje da iman. Dr Nabeel ya kalli Dr isma'il dake cikin mota zaune, bayaso agansa, ya ce, " Alhaji aii yau kad'auka sabuwar amarya za'a kaimaka. Murmushi Dr isma'il yayi yashafa sumar kansa datasha aski da gyaran fuska, "o, kaida mika d'auka za'a kaimin?. To kamabar wani tunani amarya gal aleda za'a kaimin. Nabeel yay dariya, cikin musayeef kuma aruwa tasha ko?. Rankwashi yabashi akai, to d'ansa ido koma ya akayi ina ruwanka...... Kafin Dr Nabeel yay magana su Xoxo suka iso rik'e da hannun iman daketa shashshekar kuka. Nabeel yabud'e musu suka Shiga, shima yashiga yatada motar, shiru Dr isma'il yayi Dan bayaso agane dashi akazo, amma tuni k'amshin turarensa yacikama Iman hanci. Bata kawo yana motarba, azatonta motarsace shiyya turaren Yakama motar, har lokacin shashshekar kukanta takeyi. Dr Nabeel ne gaba, mota biyar ta 'yan rakiya suna binsa abaya. Tunda suka shiga cikin gidan suke rangad'a gud'a kamar ankawo sabuwar amarya, ananma gidan cike yake Da makwafta, Dan tarba tamusamman mama da mom suka shirya musu. Yauma tarihi ya maimaita Kansa, saida aka fara kaita 6angaren mama, mama ta rungume iman tana hawayen dad'i, itama iman kukan takeyi,, an dank'a amanar iman a hannun mama akaro na biyu, wanan karonma mama ta kar6i Amanna tareda addu'ar fatan alkairi ga iman, sannan tabada k'yauta abama iman wadda babu Wanda yasan komiye aciki. d'aukarta akayi daganan har 6angarensu mom, itama dai amanar iman aka bata itada Yaya, suma sun kar6a. Su aunty dai anzama 'yan kallo, bak'inciki fall ransu saidai babu damar koda tarine mai k'arfi😜. Daga nan 6angarenta aka kaita, tofa anafa kallo yakoma sama. Jar ubancan kai, kai masu karatu, kunga wani sabon salon gyara da akayima 6angaren kuwa?, hu'ummm nabaku dama kutambayi Xoxo labarin tsaruwan da 6angaren yayi😉. 'Yan rakiyadai sunata tofa albarkacin bakinsu, har tsakkiyar gadonta aka kaita, gadone na alfarma, mai musalta muku tsaruwarsa sai Xoxo dasuka kasance amara kirjin biki, lol. Bayan 'yar nasiha da aka k'arayima iman, 'yan rakiya sukayo waje, umman su Xoxo kawai aka bari ad'akin da aunty Salma, Umma ta koro Xoxo waje, fitowa tayi tana zum6ura Baki, mumadai ankusa daina korarmu idan za'ayi wanga zance, shiyasa Zarah Bukar ta ce, "bata zuwa rakkiyar amarya da manya, Ashe da gskyarta. Tana tsaye tana kunkunai Dr Nabeel ya iso gareta, humm wanan bayajin kunyar gamo da Umma ne. Abubuwa su Umma sukabama iman, wasuma suna d'akin tashiga bayi tayi amfani dasu, aka bata wasu tasha, sanan suka fito, itakuma taja filo tarungume tana kuka. ALLAH yasa Musayeef yazo yanzu, Dan ita rabonta dashi tunkafin taje gidansu Xoxo, yau data dawo akace yana nan gidan. Bayan kamar minti15 gidan yay tsit, kowa Yakama gabansa, taso Xoxo tashigo su k'ara yin magana, amma Umma ta korata. ************************* Har k'arfe goma Dr isma'il bai shigoba, itakam bata daina kukanba, Dan ita azatonta yana wajen Raihan, datayi shiru ta kalli agogo saita k'ara fashewa da kuka. Dr Isma'il kam yana d'akinsa kwance, yama rasa irin murnar dazaiyi, tashi yayi yay wanka yashiga gyaracan goge can tamkar wani mace. Yarasa kayan barcin dazaisa, candai idonsa yatsaya akan wasu fararen kayan barci masu taushi, wandone iya gwuywa da riga mai bud'ad'd'en k'irji, yabaza turare na d'aukar hankali. Ledar da Dr Nabeel yabasa yad'auka yanufi d'akin iman. Wasu hawaye suka wanke kumatun Raihan dake bakin k'ofa tana kallonsa, takoma cikin d'akinta dagudu tana kuka. Shikam dama baisan tanayiba yatura k'ofar iman ahankali yashiga, bakinsa d'auke da sallama. Wani k'amshin dad'ine yabugi hancinsa, yashak'a ya lumshe idanunsa, ahankali yabud'e ya saukesu akan iman dake kwance tana kuka, Dan shigowarsa saita k'arajin sabon kuka. Cikin takun nutsuwa yak'arasa gaban gadon, ya ajiye ledar ak'asa sanan yahaye saman gadon shima. Gabanta yaje ya kwanta yana fusakantar ta, da Sauri tamik'e zaune tana hararsa. Wani murmushin gefen baki yasaki, Wanda ya kashe zuciyar iman, taisaurin duk'ar da kanta k'asa Dan murmushinsa ya tsayar da hawayenta cak. Hannunta yakamo yarumtse anasa, Amincin ALLAH ya tabbata agareki my life. Bata tankashiba saima k'ok'arin zare hannunta takeyi. Bai bata damar hakanba, yakuma damk'e hannunta sosai Wanda yakejinsa kamar auduga dan laushi. Muryar iman can k'asa ta ce, "INA musayeef?. Murmushi yak'ara yimata yana murza hannunta, lallenta yaymasa k'yau sosai, muryarsa cike da salo ya ce, " gadai daddyn musayeef atare dake, musayeef kuma yana wajen mom d'in Deexerh. Shiru tayi babu amsa. Yatsunsa biyu yasa yad'ago ha6arta, sai kawai tamatso hawaye. Yad'an rintse ido yabud'e, ahankali ya ce, "har yau bakibar kukan rabuwa dasu gwaggonba ne?, yakamata kiyi shiru haka nan, tun amota kike kukafa. Aii kamar ya zugata saima ta fashe masa da kuka. Jawota yayi yarungume yana lallashi, my life please ya Isa haka, inko bakiyi shiruba nima zan fara miki kukan, yafad'a yana d'ago fuskarta. Yanda ya yamutse fusaka kamar yaro saiya bata dariya. Ta murmusa. Shima yasaki lallausan murmushi yana kallonta. Matsawa tayi baya tana turo baki gaba. Yagyara zamansa wauni gudunama akeyi kenan?, duk'ar dakai iman tayi tana wasa da zoben hannunta. Yakuma matsowa daf da ita ta matsa baya, ya matso tamatsa, suka dangane da jikin gado, murmushi yayi ya ce, " to munzo k'arshe sai Yaya kuma?. Kallonsa tayi da runannun idanunta datasha kuka, ta ce, "saina barmaka d'akin. Hhhhh duk Inda kikaje yau zan bikine aii. Mik'ewa tayi danufin barin gadon, yajawota tafad'o jikinsa, zobe yaymata da hannunsa yarungumeta tsam ajikinsa. Tafara mutsu mutsun kwace kanta, yakuma matseta, cikin kunnenta ya ce, " yaufa babu wata hanyar ku6ta Dan mak'ogwarona abushe yake da k'ishirwa. Tad'an kalli fuskarsa akaro na farko, wani shek'in angwanci taga fuskarsa tanayi, takawar da kanta daga kallonsa, jitayi zuciyarta tana wani zafi saboda kishi, aranta ta ce, "namiji munafiki. Yalura da canjin fuskarta, ya sumbaci yuyanta dake wani tashin k'amshi mai rikitashi, my life baki yarda da maganata bane?. Baki ta ta6e tana k'ok'arin tashi, yazanyi na yarda bayan kaima Kasan ba haka bane, harma mai amarya yayi k'ishirwa. Hannunta yaruk'o Dan harta mik'e daga jikinsa, ta kauda fusakarta data jik'e da hawaye. Dawo da ita yayi saman cinyarsa, yajuyo da fuskarta suna fuskantar juna, saita rintse ido tana k'ara zubo da hawaye. " aransa ya ce, "kishi". Afili kuma saiya huro iska daga bakinsa, yana hura mata akan idonta, nan take hawayen suka tsaya, kafin ta bud'e ido ya had'e bakinsa maicike da k'amshi danata, sannan yaymata k'yak'yk'yawar runguma wadda babu maganar kwacewa................... *_hummmm masu karatu........... Baridai na shiru kawai🙊._* *luv u oll my fan's* *(((S)))..........2017* [8/6, 6:03 PM] mrs bilkisu: *_BAN SAKETA BA!!_* *_NA Bilyn Abdul_* _sadaukarwa_ *ya Abdul (city phone's)* https://mrsbilkisa.blogspot.com *_"wanga page nakine k'anwa Marak'isiyya alkairin ALLAH yakaimiki, nayi missing naki sosai, yakamata kidawo haka nan"._* *(page 33 & 34)* Cike da wani irin salo yake sumbatarta, lakwas tayi takasa yunk'urin kwacewa, shikam saiya k'ara k'aimi cike da nagarta. Sunkai tsawon minti18 ahaka sanan yazare bakinsa, idonsa yayi jajur, yarungumeta tsam yana hawayen farinciki, itama kukan take danji take zuciyarsa nafaman bugawa da k'arfi, hannu tasaka saitin zuciyar tasa ta danne wai ko zata dainajin bugun. Ahankali yad'agota yana murmushi, tacire hannunta daga k'irjinsa, yakama hannun nata yamaida ak'irjinsa, karki cire my life, kusantowarki gareni yasa zuciyata ta canja salon bugu ayau, jinake tamkar zata Faso k'irjina tafito, inasonki dayawa my life, bazan iya yafema wad'anda suka rabamuba har tsawon shera hud'u da Rabi, dolene su fuskanci hukunci da horo mai tsanani........ Lallausan hannunta tasaka tarufe masa baki, tayunk'ura ahankali ta tashi zaune sosai akan cinyarsa. Share masa hawayen tashiga yi yayinda itama idonta kezubar hawayen, tanason Dr Isma'il sosai, shiyyasa bazata iya jure ganin saukar hawayensaba, shikam aii saiya k'ame k'am, Ashe har yanzu iman d'insa tana sonsa?. Muryarta cike da taushi ta ce, "karka damu _Zuciyata_ muyarda da k'addara bana son zubar hawayenka, kad'auka mukeda nasara tunda gani nadawo gareka, iman takace kai kad'ai, kuma zan cigaba da kasancewa taka har a aljanna insha ALLHU RABBI. wata sassanyar ajiyar zuciya ya sauke ahankali, yakuma rungume iman tareda nuna mata wani sabon salon soyayya na musamman mai tsadar gsk, _(nidai bilyn Abdul kauda idona nayi gefe Dan lamarin yagirmi wayona),_ humm. So makahone. Ganin zai wuce gaba yasata rik'e hannunsa, duk jikinta yayi sanyi lakwas, ya tsura mata rinannun idanunsa wad'anda suka k'ank'ance, muryarsa a sark'e ya ce, " tashi muyi sallar godiya ga ubangijin talikai. Tsorone yashigi iman data tuno da Daren farkonsu, tasha wahala, nantake kanta yakawo mata haske, tayi k'asa da ido tana k'arema k'irjinsa kallo, muryarta dad'an rawa ta ce, "nifa ina danja. Ban gane kina danja ba?. Cusa kanta tayi a k'irjinsa cike da kunyar abinda zata fad'a, muryarta can k'asa ta ce, " ina fashin sallah. Shiru yayi na 'yan sakwanni, lallai danja kam, gsky kika fad'a Dan an6ata masa show daya dad'e yana shiryawa.😜 Jin yayi shiru yasa tad'an d'ago dantaga lfy, murmushi yasakar mata, Wanda takeda tabbacin iyakarsa fuska, ta maida kanta tana gumtse dariya, Dan yabata dariya wlhy, ta ce, "yanaji kayi shiru?. Manneta yayi sosai da jikinsa, acikin kunnenta yarad'a mata wani abu, Wanda Nima banjiba. K'ara cusa kanta tayi tana wata irin dariya maicike da amo. Shikam saita k'ara narkar dashi, gudun kar ayi abin kunya yasashi d'agota, my life dariya kikemin ko??, hummm zan ramane aii, tashi kici abinci. Tashi tayi zaune tana kauda kai, nifa ba dariya nake makaba, humm to mikikeyi?, babu komai. Shikenan zamu had'une aii. Dakansa yabata naman gasashshiyar kaza mai dad'i, sukaci suka k'oshi suka d'ora da sassanyar fresh milk. Koda zata saka kayan barci saita shige bayi, murmushi kawai yayi, yaja filo yarungume. Can k'arshen gado ta lalla6a ta kwanta, azatonta yayi barci, batasan yana kallontaba yayi shirune kawai. Saida takwanta tayi addu'a, sanan yajuyo had'e da rungumota yana fad'in 'yammata aii tuni an wuce wanan k'arnin kokin mantane. Shiru tayi batace komaiba Dan kunya. Dukda baisamu abinda yake k'ulafucinba tasha jagwalgwala sosai, dan saida ta gwammace dama batayi masa k'aryarba, sai wajen k'arfe 2 yabarsu suka runtsa. Da asuba yatashi dak'yar yashiga bayinta, saida yayi wankan sanan yay alwala, bai tada iman ba dan yasan bata sallah, d'akinsa yanufa yasaka jallabiya yanufi masallaci. Iman kuwa yana fita tabud'e ido, gwalo tamasa sanan tasakko daga gadon tashiga bayi, alwala tayi tazo tayi sallar asubahi, tamaida kayan barcinta ta haye gadon kamar komai bai faruba. Saida gari yafara haske suka dawo daga masallaci shida marwan da Yaya, kowa 6angarensa yanufa. Sanda yashigo d'akin iman takoma barci Dan bai barsu sunyi barci ishashsheba da daddare. Kwantawa yayi shima tareda rungumeta sai barci. *_7:48am_* iman ta farka, ahankali ta zare jikinta daga NASa gudun karya tashi ta saka masa filo, falo tafito, dukda babu wani datti mai yawa saida ta k'ara gywarashi, tabaza k'amshi, d'akinsa tashiga, tabi ko ina da kallo, ancanja komai bawanda tasani bane, tagywara d'akin tabaza k'amshi nanma, anan tayi wanka tad'anyi kwalliya sanan tanufi d'akinta. Ahankali take komai dankar ta tadashi, tasaka kaya dasuka kara fidda tsarin halittarta, siket ne da Riga na atanfa, kai telan nan ya iya fidda d'inki gsky, ta nad'a d'aurin d'ankwali mai tsari sanan tafeshe lungu da sak'o najikinta da turare. Ahankali Dr Isma'il yabud'e ido yana kallonta, tunsanda take d'aurin d'ankwali yake kallonta, tajuyo danufin fita saitaga idon doctor akanta, lallausan murmushi tasaki tana fad'in dama katashi?. Baiyi maganaba saidai ya mik'o mata hannunsa alamar yanason tashi, matsawa tayi gaban gadon ta kama hannunnasa, ahankali yatashi zaune har yanzu idonsa akanta. Ita kallon nasama kunya yake bata, ta daure ta ce, "kallonnanfa ya Isa haka. Kamo hannunta yayi yazaunar saman cinyarsa, akunnenta yay magana wadda tasakata saurin saka tafin hannunta ta rufe fuska, da sauri tamik'e daga jikinsa ta gudu........ Yakatseta dafad'in ni wazaimin wankan?, ashagwa6e yay maganar. Da d'an gudunta ta ida fita daga d'akin, yay 'yar dariya, my life sarkin kunya, mik'ewa yayi yashiga bayinta, tawanke bayin tsaf sai k'amshin dad'i yake, ga ruwan wanka anhad'a Wanda yakeda tabbacin nasane. Wankan yafarayi zuciyarsa cike da tunanin iman, gabad'aya yarinyar ta canja masa, komai nata yak'ara girma musamman ma k'irjinta, duk motsin datayi saita kuma rikitashi, yakuma nutsa kansa cikin ruwan yana murmushi. Iman tana fita sukaci karo da Raihan tafito sanye da kayan barci, da alama yanzu ta tashi, har iman tayi niyyar wuceta saikuma tadawo baya tana murmushi. Taje gaban Raihan ta tsaya fuskarta fes, ta ce, " Raihan kin tashi lfy?. Wani k'ududun bak'in ciki yatokare zuciyar Raihan amma saita dake, itama ta CE, "lfy lau. Ashe kin dawo?. Iman tayi murmushi danjin tambayar rainin wayo daga Raihan, tad'an dafa kafar Raihan tana cigaba da murmushi, nadawo Raihan cikin huncin ALLAH, mammallakin zuciya da abinda ta sak'a, tad'aga mata gira, ina fata kema bazaki tafiba zaki zauna murayu tare, harmu haifo k'annan misayeef k'yautar ALLAH...... Tana gama fad'a tayi gaba tana wata irin dariyar rainin hankali, saida taje dai dai k'ofar shiga d'akin doctor sanan tajuyo, cikin wani salo ta ce, *_" BAN SAKETA BA!."_* tadafe saitin zuciyarta sannan tayima Raihan jinjina da hannunta d'aya👍🏻😉tad'an gira sannan tashige. Sagade Raihan tayi tanabin iman da kallon harta shige d'akin Dr, zuciyarta cike da d'aci, wai waccan 'yar yarinyarce take gaya mata bak'ar magana a fakaice?. Hummmm iman kikira kanki sorry kawai, fuuuuuu tashige d'aki, tafasa kuka tareda fad'awa kan gadonta daya had'a kwana uku babu gyara. Iman kam tana d'akkoma Dr kaya tana faman murmushi kamar wadda akayima albishir da aljanna, k'anan kaya ta d'akko masa masu k'yau, tafeshesu da turare sanan fito. Tayi murmushi Dan ganin babu Raihan, tayi zaton zata fito ta isketa aii. Dakinta tawuce, agurguje tagyara ko'ina tabud'e d'akin da k'amshi, sanan tadawo falo ta zauna. Fitarta babu dad'ewa Dr tafito, yabi d'akin da kallo yana mai jin dad'i, iman akwai tsafta, amma awannan karon tazo masa da sabon salon k'amshi na musamman. Tsaf yashirya tamkar wani matashin saurayi, babu Wanda zaiga Dr ya ce, "iayi aure harda d'a, falon yanufo shima. Musaueef yashigo falon da d'an gudunsa, cak yatsaya yana kallon iman, fuskarsa d'auke da mamaki, tayi masa murmushi tareda bud'e hannayanta alamar yazo. Zuwa yayi yashige jikinta yana 'yar dariya, aunty maa yaushe kikazo?. Bata bashi amsaba sai faman murmushi take zabgawa na jin dad'in ganinsa, ta ce, " I miss u my derling. Dr Isma'il yana tsaye yana kallonsu fuskarsa d'auke da murmushi. Iman tashare 'yan kwallan dasuka taru mata agefen ido najin dad'i, tad'ago Musayeef daga jikinta ta sumbaci kumatunsa sanan tamik'a masa nata, shima sumbatarta yayi. Sai asanan yaga dadinsa, dagudu yasaki iman yanufi Dr dake tsaye. Dr yatsugunna tareda ware hannunsa musayeef yazo yashige. " daddyna!." "Musayeef d'ina!." Shima yafad'a cike da jin dad'i. Yad'agosa yana dariya, katashi lafiya?, lfy lau daddyna, da k'yau na gwaggo. Musayeef ya ce, daddy!. Ma'am, Dr Isma'il ya amsa. Daddy itama aunty maa tadawo gidanmu. Saida ya kalli iman suka had'a ido tayi k'asa da kanta tana murmushi, sanan yadawo da dubansa kan musayeef, kai ya d'aga masa tareda lumshe ido yana murmushi. Yeeeeeeee musayeef yashiga fad'i yana tsallen Murna, Dr da iman kallonsa suke sunata dariyar jin dad'in ganin farincikin tilon d'ansu. Raihan dataji ihun Musayeef tafito tawani doka uban tsaki tashige cikin, babu Wanda ya kulata danshi Dr ko kalloma tata isheshiba, da ita da babu duk d'ayane agurinsa. Mik'ewa yayi yad'auki musayeef suka k'arasa Inda iman take zaune, zama yayi Kusada ita yad'ora musayeef kan cinyarsa. Kinga yanda musayeef yake farinciki momynsa tadawo ga daddynsa. Murmushi iman tayi batareda ta ce, komaiba. Musayeef ya ce, "aunty maa ina uncle deeni da gwaggo da abbah. 'Yar harara tamasa ta ce, "sai yanzu katuna dasu?. Musayeef ya kalli daddynsa, daddy aii dai Kaine kace zaka kaini ko?. Kai yad'aga masa ya ce, " insha ALLAHU big boy. Dariya sosai musayeef yakeyi wadda tasaka iyayen NASA dariya suma. Iman tamik'e kunga bazan iya wannan shiritarba bari naje na gaida mama dasu Yaya. Shima Dr mik'ewa yayi d'auke da musayeef muma Baza a barmu abaya ba aii, muje muyi breakfast ma. Haka suka rankaya abin sha'awa kamar kasacesu ka gudu, sunsan su yayama suna 6angaren mama, Dan haka suka nufi can kai tsaye, ilai kuwa suna can. Sunbama su mama sha'awa, marwan ya ce, "family ya had'u dee.... CE kawai babu, dariya akayi harda su Dr dake shigiwa. *_(Ni bilyn Abdul na ce, " tofa, mi marwan yake nufi, bayan babu aunty da Raihan agurin, naga suma duk suna cikin family🙊😜)_*. Gaisuwa aka shigayi, kowa saiji da imam yake, itakam kunyarsuma takeji, ta ce, "marwan yaushe dee...... Zata zo?. Aina San weekend d'innan saitazo, dan taji haushi kin dawo bata nan, murmushi iman tayi ta ce, ALLAH yakaimu lfy. Ya CE Ameen. Sun dad'e anan anashan hira, sannan suka koma 6angarensu. Suna zama wayar iman tahau wringing, takalli wayar. My sweet hafsy tagani, tasaki murmushi tareda d'agawa................... *_" kuyi hak'uri idan nadad'e INA typing wayar k'amewa takeyi"_* *luv u oll my fan's* *(((S)))...............2017* [8/6, 6:03 PM] mrs bilkisu: *_BAN SAKETA BA!!_* *_NA Bilyn Abdul_* _sadaukarwa_ *ya Abdul (city phone's)* https://mrsbilkisa.blogspot.com *miya kamata nayi?* _6arna NATA yawa a bayan k'asa, amma anrasa miye tushenta?._ _hummm akwai tushe tushema ba tusheba, misali idan na d'auki yanda al'ummarmu suka maida zina a yanzu._ _zakiga uba mai cike da kamala ariga da fuska, amma idan yaje office shida sakatariyarsa saidai addu'a, zai makad'awa matarsa k'arya yatafi k'asar waje kasuwanci amma yana hotel da 'yammata, k'ilama harda k'awar 'yarsa, ko k'awar matarsa, ko k'awar k'anwarsa._ _to jama'a Dan ALLAH, indai maganarnan da ake fad'in Wanda yayi zina da uwar wani sai anyi da tasa mizai hana matar magidancinnan fad'awa tarkon zina, tunda k'ila harda matar wani yakeyi, mizai hana 'ya'yan magidancinnan fad'awa zina, tunda yayi da 'yar wani, mizai hana k'anwar magidancinnan fad'awa zina, tunda yayi da k'anwar wani, mizai hana yayar magidancinnan fad'awa zina tunda yayi da yayar wani._ _kunga tadalilin mutum d'aya mutane dayawa sun fad'a tarkon 6arna, shikad'ai ya wargaza family d'insu, Dan abin zaita bibiyarsune har 'ya'ya da jikoki._ _wa'iya zubillah, Dan ALLAH magidanta kuji tsoron ALLAH kodan katange family naku fad'awa cikin bala'in fasik'anci, saimun gyara ALLAH zai gyara mana, sakawa 'ya'ya da k'anne sasari na hana Fita bazai hana ubangiji ya aiko wani k'ato har gidanka ya6ata maka rayuwar mata, 'ya'ya, k'anne, yayye, ba a yima ALLAH wayau d'an uwa._ *ALLAH yasa mugane* *(page 35 & 36)* Ayyeee mata kuk'ame k'am sabuwar rawa. Iman Doctor Ku k'ame k'am kusami nutsuwa......... Dariya iman tayi kai sisi ALLAH yashiryaki wlhy, ina kuma kika samo wanan wak'ar?. Hhhhh sabuwar wak'ar gwanja ce amaryar, k'amshi, ya amarci. Hummmm amarci kuma?. Eh mana. Yana wajenku. Tofa mu asuwa, haryau banbar kwana agadon Umma ba, aiiko bana amsa sunan amaryaba. Karki damu lokaci kad'an yarage kikoma kwana kusada....... Saikuma tayi shiru tana kallon Dr isma'il dayake kallonta. A'a yakikayi shiru fad'i mana, Xoxo tafad'a tana dariya. Iman takauda kanta daga kallo sa ta tashi tashige bedroom, 'yar duniya aiba kasa fad'a nayiba, doctor ne akusadani, kuma yakafeni da ido yanajiran mizan fad'a. Hehehe 'yammatan gaya ga k'yau ga gayu, kice soyewa ake nakira, bari nabarki sai anjima....... Kafin iman tace wani Abu Xoxo ta yanke wayar tana dariya. "ALLAH yashiryaki iman tafad'a itama cikin dariyar. Falo tayi yink'urin dawowa Dr yashigo d'aukeda musayeef dayayi barci, kad'an yarage suyi karo tad'anja baya. Saman gado yad'orashi sanan ya zauna, iman dake tsaye tana kallonsu cike da sha'awa tayi murmushi. Dr isma'il yad'ago yana kallonta, ya ce, " har angama gulmar?. 👁👁gulma kuma?, gulmarwa mukayi?. Ya za'ayi nasani tunda kin gudo d'aki. Hu'um to ba gulmar kowa mukeyiba mudai. Murmushi yayi yana mai k'are mata kallo cikeda shauk'i.......garammm aka bugo k'ofa, da sauri iman tamatsa Dan k'ofar tad'an daketa kad'an. Auntyce da Raihan, iman taimusu kallo d'aya ta d'auke kai, Dr Isma'il yatashi zaune yana kallonsu. Shigowa sukayi cikin d'akin, (amamakin iman saitaga sun durk'usa ak'asa), tofa sabon salo iman tafad'a azuciyarta. Raihan ta ce, yaa isma'il Dan girman ALLAH kuyi hak'uri Ku gafarcemu, Dan ALLAH kabama Yaya hak'uri shima ya yafema auntyna wlhy tana bala'in sonsa. Wani kallo yakemusu, amma kuma bai fahimci zancen nasuba, baikuma tambayesuba. Itadai iman tana tsaye tana kallonsu. Aunty tajuyo tana kallon iman, iman Dan ALLAH kiyafe mana kema, munyi kuskure ki gafarcemu..... Tak'are maganar hawaye sunan sauna a kumatunta. Sumba iman tausayi Dan haka tabud'e baki zatayimusu magana, Dr Isma'il ya ce, "my life karkice musu komai. Shiru tayi tana kallonsa, yataso ahankali yakama hannunta, saman cinyarsa ya d'orata, dukda tanajin kunya haka ta dake ta zauna, yajuyo da fuskarta suna kallon juna. My life ke harkin yarda da tuban wad'annan shaid'anun?, sunefa masu kulla raba aure, abinda ALLAH bayaso, dukda bansan abinda Yaya yayiba nasan yayi dadai wlhy, banaso ko a mafarki kiyafema Wanda ya rabani dake NA tsawon shekara hud'u, wand'anda suka jawo na kwanta a asibiti natsawon wata uku, wad'anda suka hana zukatan dangina nutsuwa, nasan basuyi nadamaba Dan har yanzu basu riski makarantar nadamaba. Iman ta kad'an kai batareda tayi maganaba. Shikuma yadaka musu tsawa, wlhy koku fitarmin ad'aki kokuma kufuskanci mummunan 6acin rai daga gareni, wlhy na tsaneku banason ganinku, shaid'anu kawai. Sum sum aunty da Raihan suka fice, kowa zuciyarsa tana zafi. Suna Fita suka kalli juna sukai murmushi, aunty ta ce, " sakarkaru sunfa zata da gsk Neman yafiyar mukazo. Raihan tayi 'yar dariya bar kidahumai aunty. Aunty ta ce, "ina fata kin saka?, kinsan malam ya ce, " bayaso asamu Marsala ana farko. Nasaka aunty saura kuma nagobe, ai zasuci ubansune agidanan, sai sunyi Dana Sanin barinmu, aunty da Raihan suka ta6a tamkar wasu k'awaye. (Ni Bilyn Abdul na ce, "hummmm 👁👁.) Dr Isma'il da iman kam rakasu sukai da ido, iman har zuciyarta ta yarda sunyi nadama, Amma Dr yanaji ajikinsa akwai abinda suke shiryawa, badaicema iman komaiba akan hakan saiyayi bincike. *bayan kwana uku* Bayan kwana uku da dawowar iman, kullum tana zubama Dr k'arya tana fashin Sallah, saiya Fita saitayi sallarta, shikam ko kad'an baikawo k'arya takeba a ransa. Yauma suna gama break yay shiri cikin watad'anyar shadda jaa yamurza bak'ar hula, iman natsaye tana kallonsa, saida yagama saka hular sannan yajuyo yana kallonta, murmushi sukaima juna, yamatsa daf da ita, my life nafa fara gazawa gsky. Kallonsa tayi tana murmushi ta CE, ''akan mi ka Gaza?. Akanki yafad'a yana rungumeta. Ajiyar zuciya ta saki batareda tace komaiba. Yad'agota daga jikinsa yana kallon fuskarta, ya ce, " bakice komaiba. Mikakeso nace to?.. Kicemin bak'onki ya tafi....... Kafin tabashi amsa musayeef da 'yan biyu suka shigo da gudu hannunsu d'auke da kayan sweet. Dr Isma'il yasaki iman yana kallon su musayeef. iye 'yan yara yara waya Baku?. Cikin tsalle sukace aunty deexerh ce. Kai ina aunty dee.... d'in?, tana wajen mama suka fad'a suna tsalle. Iman ta ce, "lallai dee.... Tana fushi damu, harta dawo babuko waya. Dariya Dr Isma'il yayi, ina bayanta tayi fushi sosai, kin dawo gidan uncle d'inta bata saniba, dama tagayamin kin shareta. aii laifi tamin shiyyasa na shareta. A to bari nayi shiru da bakina saikun had'u kenan. Dariya iman tayi. Ya ce, " bari nawuce ana jirana. Iman tad'an ta6e fuska towaima wanan kwalliyar ina ta dosane?. Gira yad'aga mata ya ce, "tad'i mana, kisan nasamo ta uku, iman ta had'e fuska sosai ta ce, to na mamajo saura ta hud'u. Dariya yayi danganin yanda ta had'e fuska, ya shafa fuskar tata yana d'aga mata gira, karki damu itama tana hanya uwargidana, baijira cewartaba yafice da Sauri Dan Dr Nabeel yana jiransa. Wasu hawaye suka zubo a kumatun imam itafa azaton da gsk yakeyi, bakin gado ta zauna zuciyarta na zafi. Deexerh dake tsaye tun d'azu tayi murmushi Dan taji zancensu na k'arshe, ahankali tak'arasa Inda iman take ta zauna. Imam tajuyo catake shine yadawo saitaga deexerh, Harar deexerh tayi tayunk'ura zata mik'e. Dasauri deexerh tarik'o hannunta sorry my aunty Dan ALLAH ki saurareni mana. Komawa imam yayi ta zauna, deexerh ta ce, " haba aunty na laifin mi nayi ake fushi dani. Hawaye imam tashare Dan haryanzu maganar Dr yana cizon zuciyarta, ta ce, "a'a deexerh Niba auntyki bace tunda har kika iya 6oyemin uncle d'inki yayi aure. Nasan dama komai dad'ewa kikaji labarinnan zakiyi fushi dani amma wlhy ban 6oye miki Dan wani abuba, danni ban d'auki Auren waccan sakaran a komaiba, amma kiyi hak'uri Dan ALLAH. Murmushi iman tayi, shike nan na hak'ura. Yauwa aunty na dee..... Tafad'a tana dariya, amma aunty nayi bak'inciki da ban nan randa kika dawo, amma marwan Duk yabani labari, nadad'e banyi farincikin dawowa gidan nanba kamar wanan karon. Dariya imam tayi kai dee..... Banda k'aryafa?, ALLAH kuwa aunty, saidai nadawo da d'ammarar cin uban shegunayennan, sai sunbar gidannan kwanannan. Imam ta zaro ido, kai dee.... A'a Dan ALLAH karkiyi musu komai, wlhy sunyi nadama ranarma saida sukazo Harnan suka bamu hak'uri. Humm aunty kenan ke har kin yarda da tubansu?, ni nace miki k'arya suke, nasan halinsu sosai Dan aunty dakike gani ba k'aramar shaid'aniya baceba, kemafa kin zauna da ita kinga wasu daga cikin halayenta basai nabaki labariba, ke ganauce ba jiyauba.. Hakane kuma imam tafad'a, haka dai iman da deexerh sukaita hira har aka kira sallah suka tashi sukayi. Bayan sun idar suka nufo fallo daniyar tafiya 6angaren mama, a fallo suka iske Raihan zaune tana kallo Dan yau takeso ta ida cika aikin malam so take kawai imam tafita ad'akinta taje ta aiwatar. Deexerh tasaki wani wawan tsaki tanabin Raihan da kallon banza, aunty yanzunan har kinyarda kowanne datti yazauna miki afalo?. Da Sauri Raihan ta kalleta dantasan da ita take, imandai batace komaiba, Raihan har zatayi magana saikuma tayi shiru, dee.... Tayi dariya mai bakin ja6a yakuma kika kasafad'a, fad'i maganarki karta kasheki. Iman taja hannun dee... Suka fice, kai dee.... Kibari Dan ALLAH matar uncle d'inkicefa kuma 'yar uwarki. Hummm wannan duk ada ne, ayanzu kam babu wata alak'a atsakaninmu, yanzuma tafara gaini Indai nice. Suna fita Raihan ta share hawaye, zanyi maganinki kema, baridai nagama da wad'annan sakar Karun, hankalinta kwance tanufi d'akin iman, katifarta tad'a tasaka wasu layu ko k'yan gani babu, tatsaya gaban gadon tana wani sirkulle. tana gamawa tajuyo zata Fita saifaman murmushi take Dan tasan daga yau imam tagama yawo. Turus tatsaya baki bud'e tanabin Dr dake tsaye da kallo atsorace. Takowa yayi cikin d'akin batareda yace komaiba, saida yaje gaban gadon sanan ya ce, "zoki cire abinda kikasamata agado. Jikin raihansai rawa yake tazo tad'aga tacire layun data ajiye, ya ce, " nasan bayau kika fara saka mataba d'ebo sauran ma, da Sauri taduk'a k'ark'ashin gado saiga wani kasko da da tsokar nama an cacccaka k'ayoyi ajiki. Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un Dr yaketa ambata, gaba d'aya zufa ta jik'e MASA jiki, waya ya d'auka yakira yayansa. Yaya kana kasuwane?. A'a isma'il INA gida yanzu babu dad'ewa nashigo. Yaya Dan ALLAH ka tattaro 'yan gidanan kuzo kuga abinda Nagani INA d'akin imam. Kagani kuma, minenen kagani??. Yaya saidai kunzo kawai. Raihan dai tana duk'e ak'asa da 'yan kayan surkullenta sai hawaye takeyi, shikenan aunty tak'ara sakata amatsala itakam tashiga uku, wlhy batason rasa Dr Isma'il Dan tana bala'in sonsa. Babu dad'ewa saiga gayyar 'yan gidan duka, kowa yashigo saiya rik'e baki, iman ta ce, "na Shiga uku ni saudatu wanan kuma daga INA Doctor?. Baiyi maganaba saidai nuna mata Raihan yayi. Jikake tauuuuu deexerh ta d'auke Raihan da wani wawan mari, shima Marwan yabata d'aya a d'aya kuncin, dukanta zasu farayi Yaya hace karsu daketa, Dr isma'il ya ce, " Yaya wlhy kabarsu su zaneta aii ita tajama kanta, kuma nidai gsky Yaya ayau zan saki jahilar nan, wlhy bazan iya jurewaba, kije na sakeki saki uku!!!!. Wani ihu ta buga tareda rik'e kafafun doctor tana kuka, Dan Girman ALLAH ya isma'il kamin rai narantse da ALLAH bazan sakeba, wlhy aunty CE tasakani. Yaya yay murmushi itama aii bazata tsallakeba, kema kibita na sakeki saki uku kema, saikuma kuje wani gidan. Wlhy kummin daidai 'ya'yana ALLAH yay muku albarka, zama da wad'annan yaran aii masifa CE, mamace mai wanan maganar. Dr isma'il ya ce, "aii wlhy mama banda Abba dakansa yafad'a mana iyayen yarannan 'yan uwansane nikam danace suba jininmu bane, tsinannu gadon tsiya gadon jaraba, wlhy minti talatin nabaku kubar gidanan. Raihan da aunty kuka suke suna rok'on ayi hak'uri wlhy bazasu sakeba sunyi nadama. Deexer da marwan suka kalli juna suka shek'e da dariya suka fice. d'akunan su Raihan sukaje suka ringa Watso musu kayansu waje, duk abinda sukasan na kud'ine sun d'aukeshi Dan iyayensu suka siya, daga aunty har Raihan babu wacce aka kawo dako kofi daga gidansu, duksu yayane sukai musu kayan d'aki. Kafin su fito duk su dee.... Sungama Watson Musu kaya waje, haka suka Shiga tattarawa suna kuka, Yaya yabasu kud'i ga kud'in mota nan sai abi wani sarkin. Har k'ofar gida su dee.... Suka rakosu 'yan unguwar sai fitowa suke kallonsu, wasu sai tsine musu suke wasukam suna shima su Yaya albarka, Dan Ansan mugun halin su auntyn a unguwar. Kowa baya jin tausayinsu bare goyen baya. *_(ni bilyn Abdul na ce, "tsuntsun dayaja ruwa shi ruwa kan doka Raihan da aunty)_*............... *luv u oll my fan's* *(((S)))......2017* [8/6, 6:03 PM] mrs bilkisu: *_BAN SAKETA BA!!_* *_NA Bilyn Abdul_* _sadaukarwa_ *ya Abdul (city phone's)* https://mrsbilkisa.blogspot.com *miya kamata nayi?.* _duk matakan tsaro dazaka sakama family naka saboda kasancewarka fasik'i bazai hana ALLAH kuntata makaba kaima, Dan ALLAH ba ayi MASA wayau_. _yanzu mud'auki waya k'aramar alhaki, anyi ittifak'i aduniya babu abinda bature yayi aduniya yakar6u kamar waya._ _zakaga duk talaucin mutum ya mallaki waya, waya tashiga hannun babba da yaro, mace da namiji, talaka da amai kud'i, waya tazama babbar fitina ga rayuwarmu, Dan 6arnarta tafi amfanin yawa, wlhy yanzu 'yarka tana cikin gida saita fad'a tarkon fasik'anci ta dalilin waya_. _Yarinya tanada waya, zata iya Shiga duk Inda takeso hankali kwance, dama tanada sha'awar yin wani Abu Mara k'yau to amma bata samu hanyaba, saikuma ga waya ta mallaka, zakaga tana chart da k'awarta ta makaranta ko wata 'yar uwarta, 'yar uwarnan tata zata kaita group Wanda babu wata 6arna acikinsa._ _to matsalar da ake fuskanta a group bakowane nagariba, akwai gur6atattu Wanda suna 6oye kansune, to idan tsautsayi yafad'a akan 'yarka sai gur6atattunnan su d'auki No. d'inta sukai wani group nasu, (tunda dama haka sukeyi Idan suka kaika group d'insu inkai irinsune saika zauna idan ba irinsu bane kafita)......._ _kuyi hak'uri mu had'u a page na gaba._ *ALLAH yasa mugane* *(page 37 & 38)* Dr yatsaya kaida fata iman bazata Shiga d'akintaba wai ko akwai wani Abu dasu Raihan suka 6oye. Iman ta langwa6e kai tana kallonsa, daddyn Musayeef ka kwantar da hankalimka, insha ALLAHU babu abinda zai faru, nad'azuma ba wayonmu yasa ka ganiba. Hakane my life amma aii hanyar lafiya Abita da shekara ko. Babu yanda zatayi dole tahakura suka Shiga d'akinsa akan da safe za'a bincike d'akin NATA. Kayansa yacire yashiga wanka, itakuma tana zaune abakin gadon. Musayeef yashigo d'akin yana d'ingishi, da Sauri ta ce, "kai kuma lfy kake d'ingishi?. Gabanta yak'araso fuska ayamutse yana yarfe hannu, ya Nuna mata babban yatsan k'afarsa dayake jini. Ya salam a ina kaje kaji ciwo?. Aunty maa afalo nabige da kujela. Ta sauke ajiyar zuciya tana d'aukarshi, saman cinyarta ta d'orashi takama k'afar zata duba doctor yafito daga bayi. K'arasowa yayi Inda suke yazauna Kusada iman yana tambayar lfy?. Kafar musaueef tanuna masa batareda tayi maganaba. Woow! Shugaban hidima a INA kaji ciwo?. Daddy a falo, yafad'a zaiyi kuka. Kaga yi shirunka karkayi kuka, kaida zaka zama soja wanan d'an ciwon zakama kuka, ina zuwa.. Iman ta ce, " lallai su soja manya. Dr Isma'il yazauna yana fad'in baki yardaba kenan??. A'a nikam miye nawa ALLAH yakaimu lokacin. Haka nikeson ji kawai. Yagyarama musayeef wajen, ciwonma baida yawa amma sai jini. Musayeef ya ce, "aunty maa yunwa nakeji. Yunwa kuma musayeef?, ita saima yanzu tatuna babu Wanda yaci abincin rana agidan, Dr Isma'il dake bayansu yana saka kaya, ya ce, " badole yaji yunwaba inagama tun break d'in safe, wad'an nan shaid'anun sun mantar damu yunwar cikinmu. Iman dai batace komaiba ta sauke musayeef daga cinyarta. Kaga bari nafara maka wanka sanan saimuje kaci abincin. Ya nok'e kafad'a alamar bayaso. Ta harareshi kainifa banason ta6ara kamije namaka wanka. Guduwa yayi Inda Dr yake, yarungume k'afafunsa yana fad'in daddy 6oyeni nifa bana son wankan. Dr yarik'eshi yana murmushi, haba big boy rashin wankafa k'azantane, ko kanaso aringa cemaka k'azami. A'a daddy. Yauwa to jeka amaka wankan. Nidai daddy saina fara cin abinci za'amin wankan. Dr yad'ago yana kallon imam, aunty maa Dan ALLAH amana hak'uri muci abincin munajin yuwafa sosai. Itama fuska ta marairaice Dan ALLAH karka biye masa, kallifa kayan jikinsa, ni bammasan inda yaje yay wannan dattinba. d'aukar musayeef yayi yana fad'in mudai mun tafi saikin taho. Rakasu da ido iman kawai tayi, yazatayi da uba da d'an. Wanka itama tashiga, bayan tafito ganin lokacin sallar la'asar yayi tayo alwala, kayanta da Dr yad'ebo daga d'akinta yasaka a durowarsa taduba tad'akko zani da hijjab. Tana cikin yin sallah, tayi raka'a ta farko tana ta biyu Dr yashigo d'akin tamkar anjehoshi, tsayawa yayi cak yana kallonta tamkar yau ya fara ganinta. Ya ce, "hummm dama manya suna k'arya?. Iman dai sallarta takeyi, saima yanzu ta tuna da shirinta, saurin kauda tunanin tayi tacigaba da sallah anutse. Dr yafito daga bayi da Alama alwala ya d'auro, ya fice yana wata 'Yar dariya wadda iman batasan fassarartaba. Koda ta idar da sallar duk jikinta yayi sanyi, tamanta wlhy har tayi saken da Dr yakamata, tagama shafa mai tayi 'Yar kwalliya, sanan tanufi 6angaren mama Dan taci abinci. Musayeef yana ganinta yagudu cinyar mama, iman ta ce, " haba yaro zan kamakane aii. Mama da deexerh sukayi dariya, mama ta ce, "mi mai gidana yayine?. Mama wankafa zanma yaron nan shine yabiyo daddynsa suka fito wai yunwa yakeji, maimakon yaci abincin yadawo namasa wankan shine Yakama wata tashar. Mama ta shafa kan musayeef asheni mijin nawa k'azamine ban saniba. Deexerh ta ce, " a'a mama yanzu zamu cakire abinmu, musayeef zomuje ni nayimaka kaji. Babu musu yabi deexerh. •+•+•+•+•+•+•+• Iman zaune abakin gado tanama musayeef shirin barci, Dr yafito daga bayi da'alama wanka yayi. Musayeef ya ce, "daddy zaka koyamin game d'in d'azu?. Dr ya d'aga masa kai, zan koya maka amma ba yauba yaro. Um'um musayeef yafad'a a shagwa6e, nidai daddy yanzun. Lallai yaro ka d'obo da zafi, yau baranar koyon game bace ba, Dan inada babban game adaren yau. Iman ta kalleshi cike da rashin fahimta, shima ita yake Kalo, yad'aga mata gira, ta kauda kai tana girgizawa. Musayeef dake danna wayar daddynsa shi adole game yake nema, yatako inda Dr yake yabashi wayar, daddy gashi kamomin. Kaga jeka bama mamanka ta kamomaka nikam mai nake shafawa. Musayeef yajuya wajen Iman shikuma Dr yacigaba da shirinsa. Tana kamomasa game ya haye gadon yanayin abinsa. Dr ya kalli Iman my life bazakiyi shirin barci bane?. A'a ba yanzuba. Sai yaushe?. Sai anjima yanzu banajin barci. Yawani kafeta da idanu, saikuma yayi murmushi aidama yau ba ranar barcinki bane, kedai tashi kiyi wanka kawai, danma saboda oga na k'yaleki datuni kin tsinci kanki cikin ruwan wanka. Murmushi Iman tayi, tajuya tana kallon musayeef dayayi busy akan waya, ta ce, ni barinmuku d'akinma zanyi. Baice komaiba yamik'e yay shiri cikin kayan barci. Tana zaune yafice saigashi da fresh milk akofi, itadai kallonsa kawai takeyi. Yazauna Kusada musayeef, my dear son tashi kasha madara. Musayeef yathi zaune ya haye cinyar daddynsa. Da Kansa yabashi madarar, yana gama sha yazame yay barci. Cikin mamaki Iman take kallon Dr, yad'aga mata gira yana gyarama musayeef kwanciya. Doctor wai mikabama yaron nan?. Bai bata amsaba saida ya lilli6e musayeef da bargo, sanan yanufota, cak yad'auketa yanufi bayi, tafara zille2. Bata ankaraba tajita acikin ruwa. Wani d'an kukan ta6ara tasakar masa, yay dariya Saita burgeshi, dakansa yay mata wanka tanata rufe ido har aka gama, yanad'o kayarsa atawul. Ta ce, "pls kasaukeni Dr yaron nanfa zai iya farkawa. Hhhhh kwantar da hankalinki, Indai musayeef ne saikuma gobe idan ALLAH ya kaimu. Cike da alamar tambaya ta kalleshi. Yayi murmushi, dainamin tuhuma da ido, maganin barci nabasa kawai. Ido Iman tazaro saboda mi?. Saboda yau babu sauk'i, daddynsa da momynsa zasu angwance. Kafin ta ce, " wani Abu ya had'e bakinsu waje d'aya. Cikeda salo yake mata abubuwa, lallai tayarda mijinta yayi missing nata, komai a yunwace yake matashi, dukda tana cike da tsoro haka tadake ta hak'ura. Yayinda akafara nisa sainajawo 'yammatan k'afafuna nayo waje🚶🏻‍. ************************ Bari mu waywayi su Raihan. Tunda suka bar gidan basu nufi tashaba, gidan wata k'awar aunty sukaje. Cike da mamaki take kallonsu, tofa Sadiya yana ganku rik'im2 dakaya?, incedai lfy?. Inafa lfy Zubaida, kedai muje daga ciki. Afalon zubaida suka zube, takawo musu abinci sukaci, dama yunwa sukeji. Bayan sunci sunsha suka mik'e k'afa suna bama zubaida labarin komai. Zubaida tarik'e Baki lallaima sadiya ya akayi kukayi sakaki haka, yo ALLAH na tuba bakuyima 'yan iska mai kankat. Aunty ta CE, "kamar ya mai kankat?. Wata dariyar mugaye zubaida tasaki, tagyara zama tashiga fanfasu sosai. Zancen natadai bai yuce zuwa wajen malam da boka ba. Sunkuma hau sun zauna daram, gobe asubar fari awani k'auye zata musu. (Ni bilyn Abdul na ce " ajuridai zuwa rafi). Wacece zubaida ne?. Zubaida dai 'Yar sokoto CE, kuma k'awar aunty CE tun a sokoto, adaliln aunty ma tayi aure kano, Dan awajen bikin anuty tayi gamo da mijin dasuke tare yanzu. Ko kad'an bayajin dad'in zama da ita, Dan zubaida halinsu d'aya da aunty jirgi d'ayane yad'ebosu. Saboda bala'inta yaraba musu gida itada matarsa uwargidansa kenan. Itadai ta haihu Dan yaranta biyu duk mata. To yanzudai gashi tayima su Aunty hanyar malamai to kozasu dace, saimun bisu asannu sanan zamu tabbatar....... *luv u oll my fan's* *(((S)))............2017* [8/6, 6:03 PM] mrs bilkisu: *_BAN SAKETA BA!!_* *_NA Bilyn Abdul_* _sadaukarwa_ *ya Abdul (city phone's)* https://mrsbilkisa.blogspot.com *_wanan page nakune Basma er Lele & Zarah bukar, ALLAH yak'ara basira da hikima, bilyn Abdul namuku fatan alkairi arayuwa_* *```(Zuma saidai wuta)*``` Acigaba da gashi zarah🤠. *(page 39 & 40)* Asubar fari zakara yabama su aunty sa'a. Ba k'aramar tafiya sukayiba har dawaki, adawakinma wani k'auye suka shiga cikin ruk'uk'in daji. Aunty tatsaya tana maida numfashi saboda gajiya, Dan yanzu dak'afa suke da6awa saboda hanyar batada k'yau, babu kuma d'an mashind'in dazai yarda yashiga dajin, itama zuby bazata yardaba. Kai Zuby wai har yau bamuzoba ne?. 'Yar dariya zuby tayi, tareda dafa kafad'ar aunty, haba sadiya biyan buk'ata aii yafi dogon buri, ki daure aii munkusa, duk Wanda ya iya jure zama da mak'iyi, aii zaijure zuwan ranar d'aukar fansa kuwa. Hakane aunty tafad'a tana murmushin mugunta. Tafiya suka cigaba dayi, itadai Raihan binsu kawai takeyi cikeda fargaba da fad'uwar gaban. Zuby ta ce, "banga laifinkuba dominku 'yan hutune, mazanku sun tsaya muku daga mota sai gida, muko ALLAH natuba yaku bayi wake ta tamu, idan tafiya zata tashi daga nan har birnin lantsandan zamu iya kai kammu da k'afa. Kafin aunty ta ce, " wani abu sun iso wajen wani k'aton dutsi, zuby ta kallesu nanfa zamu hau. Raihan ta gwalalo ido cike da mamaki tana kallon zuby, aunty zuby yanzu nan mutum ke zaune akan dutennan?. Kwaraikuwa zuby tafad'a. Aunty dai batace komaiba, saidai tana mamakin zuby sosai, tasan ta sanadinta zuby tasan kano, hartai aure aciki, amma yanzu tafita sanin birnin kano da kewaye, Inda tasani ita ko azance bata saniba. Maganar Raihan ta katse tunanin aunty, aunty zuby to yanzu ta INA zamu hau?. Wata matattakala zuby ta nuna musu, wadda babu shakka kayi kuskuren takawa tuni zakayo k'asa ka rugurguje visa k'ananun duwatsin wajen. Ajiyar zuciya suka sauke suduka, cike da fargaba suka fara tattaki ga matakalar, saida suka kai k'arshe cike da jindad'i, abisa tsautsayi k'afar Raihan ta goce, takwala wata k'ara Dan tsorata, jitayi anyi sama da ita akan dutsen, sassanyar ajiyar zuciya ta sauke yayinda taga ta tsira, saidai tana bud'e ido tashiga wata sabuwar fargaban. Zaratan samari tagani majiya k'arfi, wad'anda da mutuwa na tsoron mutum idan tagansu guduwa zatayi. Aunty ma binsu take d'aya bayan d'aya, sunkai adadin goma k'artan, saikuma wani wargajejen mutum fari tas azaune, Wanda bana tsammamin yasan kalma d'aya tak daga yaren Hausa. Aunty da Raihan suka kalli zuby wadda ita hankalinta akwance take babu alamar fargaba ko tsoron atareda ita..... Mamakinsu bai k'aruba saida sukaga zuby tak'arasa wajen wargajejen mutum nan mai kamada tankin ruwa ta gurfana tamkar zata MASA sujada. Ya sarkina dodo yataya maka. Daya daga cikin zaratan k'artan nan ya ce, "sarki ya amsa miki jinin dodo. Aunty da Raihan suka zaro ido, tuni jikin su yafara rawa. Zuby ta kuma gurfanawa agaban k'aton muminnan ta ce, " ya sarki ga alk'awari na cika kamar yanda nayi, nakawo k'awata ga dodo harma da k'arin k'anwarta idan dodo yana buk'ata. d'aya daga cikin k'artin Yakuma amsawa, dodo da sarki sun jinjina miki tareda babban yabo, kin kuma tashi daga jinin dodo kin koma baiwar dodo, daga yau kema kinzama d'aya daga cikin 'Yar kungiya. Hhhhhhhhhhhhhhhhhhh!!!!!!!. Wargajejen k'aton nan ya tuntsure da dariya, wadda duk kanin dajin ke amsawa, dutsen dasuke kai kuwa har girgiza yakeyi. (Na ce, hummm, dabadan dariyar da k'aton nan yayiba saika d'auka gunkine aka dasa awajen wlhy.) Aunty da Raihan tuni sun fara sakin fitsari awando, jikake tsulululu..., wani garjejen k'aton yazo yadamk'i gashinsu, tuni jikin su yak'ara tsananta rawa, summa rasa hawayen kuka. Sunaji suna gani aka aske musu gashi, akayi musu zindir, wanka akayi musu da ruwan jini Dana magani, sanan akabama zuby su takai cikin wani k'aton tanki...... Aunty da Raihan suka fashe da kuka, bakin aunty na rawa ta ce, "Haba zuby yanzu nan muzakiyima haka........ Hannu zuby tad'aga mata kinga dakata kunama mai haihuwar d'an sharri yimin shiru. Rama cuta ga macucu ibadane. Zuby nikam azatona banta6a cutar dakeba. Wani kallon banza zuby tabi aunty dashi, saikuma ta kwashe da dariya tana zagayasu, sukuma suna binta da kallo, sady baby! Idan maye yaci yamanta uwar d'a bazata mantaba. Tare muka tashi dake tun muna k'anana, amma ayayin dakika samu damar auren mai kud'i saika manta dani atsarin rayuwarki. Ban 6oye mikiba tunkan aurenki nace inason k'anin mijinki isma'il, kikayimin alk'awarin kota yaya zakisa ya aureni amma daga baya sainaji shiru wai malam yaci shirwa. Wani abun mamakima saiga labarin yazo gareni zai auri k'anwarki, haka nashiga nafita NASA mamarku ta ce, bata yarda da auren isma'il da k'anwarki ba. Bayanan ban gajiyaba nakuma tada miki zancen inason isma'il, amma saikikayi burus da batuna. Babu yanda zanyi dole na hak'ura na auri murtala badan INA sonsaba, na aureshi visa tursasawar babana. Kinsani sadiya kinsan halina kokad'an banida tsoron arayuwata, kuma bana Barin bashin gaba. Wanan yasa nafara tunanin INA zan samu kud'i Dan nawuce da ajinki. Ina cikin wanan tunanin ranar na hau WhatsApp saiga wani group anturo ana gargad'ar kada mutane sushiga na 'yan mafiyane. Take kaina yakawo wuta Dan Dama kud'i nake burin yi toga hanyar mai sauk'i, tuni nake gaya miki na afka group d'in nan zuciya ta adake, Ashe mutane da gsk sukeyi group d'in na 'yan mafiyane, babu wani 6ata lokaci na afka cikinsu, saidai bazaka zama cikakken d'an cikinsuba saika sadaukar da d'aya daga cikin masoyanka. Bazan iya bada Mamana ballantana baba, ko 'ya'yana, hakama murtala dukda banason da bazan iya bada jinin saba saboda mutumin kirmine, ko kad'an bankawo araina zan kawokiba kema, Dan burina saina zama mai k'azamin kud'i sanan na nuna miki wutsiyar rak'umi tayi nesa da k'asa. Saidai kuma labarin ya canja alokacin da'akace idan bankawo wani nawaba za'abama dodo jinina, tuni kaina yakawomin haske akanki, saidai bansan a INA zan damk'ekiba. Kwatsam saigaku jiya kumzo gareni cikin sauk'i, Dan haka nayi matuk'ar farinciki, ayanzudai taku tak'are Dan na cika umarnin dodo da sarki, kuma nazama cikakkiyar 'Yar kungiya, zanyi kud'i na Shana. Ta kuma kewayasu tana dariya, sady baby yau wai INA babban gidan da ake mana raini akansa, INA motar hawan da ake hura mana hanci, INA mijin da ake mana salo, duk babu, saki uku gakuma mutuwa dake jiranku. Hhhhhhhhhhh, kin fad'a tarkona sady baby, kin fad'a tarkon zuby, Zuma ga zak'i ga harbi. Kuka sosai aunty da Raihan sukeyi, suna rok'on zuby tayi hak'uri k'artan badasu, wlhy komai take buk'ata zasuyi mata. Bata sauraresuba ta iza k'eyarsu cikin kwantaina da mutane dayawa ke cikin, tsirara duk jikin su wani iri babu k'yawun gani, su tsoroma suke basu, Dan haka suka raku6e waje d'aya suna rabzar kuka. (Nace duniya makaranta, Wanda baizobama jiransa takeyi). Kowa yagina Ramin mugunta........ **************************** Iman da Dr kam ansha soyayya, daren nan zir a angwaci suka cinyeshi, iman ta murzu, Dan Daren jiya Sabon Daren farko Yakoma musu. Wanan karan dai babu kuka amma yasha shagwa6a da ta6arar iman, da k'yar suka tashi sukayi sallar asubar, suka sake bud'e sabon babin barci. Sai shabiyu dawani Abu suka tashi, alokacin tuni musayeef ya tashi yay tafiyarsa 6angaren su yaya. Imam ta tashi da k'yar, fuskar Dr ta tsurama idanu, barcinsa yake amma tamkar yana murmushi, fuskarnan fayau sai hasken angwaci yakeyi, talumshe idanu tasake bud'ewa akansa, tana k'aunar Dr harma batasan iya adadin k'aunar datake masaba, tana fata ALLAH ya sa babu wata k'addara dazata sake raba rayuwarsu anan gaba. Ahankali tamik'e tanufi bayi danyin wanka, Dan jikinta sai ciwo yakeyi wlhy. Ruwa mai zafi ta had'a ta gasa ko INA najikinta hartaji d'an k'arfi. Tafito d'aure da tawul tana goge jikinta da k'arami, Dr dake kwance yatsura mata idanu jiyake tamkar ya had'iyeta saboda so, tunda yake baita6a tunanin yaso wani Abu bayan iyayensa da mama da ya'yaba bayan IMAN, yanajinta sosai azuciyarsa, fatansa ALLAH ya tsawaita rayuwarsu suci amfanin juna. Iman dabatasan yanayiba ta k'arasa jikin madubi tayi kwalliya mai sauk'i, durowa tanufa, tad'akko wata dakakkiyar shadda zani dariga, ta d'aura zanin, tana k'ok'arin saika riga suka had'a ido da Dr da idonsa yake tsaye kam a k'irjinta ko k'yaftawa bayayi, da sauri tasaka rigar tana fad'in daddy katashi?. Bai amsataba baikuma daina kallontaba, d'ankwalin kayan tad'auka tak'araso Inda yake tareda rankwafowa ta hura MASA iska a idonsa. Ya lumshe ido yana sauke ajiyar zuciya. Ta ce, ''kallonfa?, aii saika karemin muni Dr. Murmushi yayi tareda ziro k'afafunsa k'asa, yakafeta da idanunsa yana fad'in, aii kozan shekara dubu INA kallonki bazanga muninkiba. A'a daddyn musayeef banda zigadai. Tasowa yayi yarungumeta tabaya, yad'ora Kansa saman kafad'arta suna kallon juna tamadubi, ahankali ya CE da gsk nakeyi Ni'imatullah. Cike da mamaki take kallonsa ta ce, "wanan sunanfa daga ina?. Saitin kunnenta yamatsar da bakinsa ahankali yarad'a mata maganar danima banjiba masu karatu. Ta zaro ido waje saikuma tasa hannu tarufe fuska tana fad'in nidai babu ruwana kaje kayi wankanka. Dariya yayi yana k'ara matseta ajikinsa, nikam da ruwana harda d'an tsaki tsaki. Dariya tayi, nidai kaje wanka Kasan musayeef zai iya shigowa d'akinnan akowane lokaci. Da sauri yakalli gadon, o, wai yana INA?. Hummm sai yanzu kalura baya nan?. ALLAH nazata yana barcine. Tab wanan yaronne zaikai sha biyu dawani Abu yana barci?, Nima tunda natashi ban ganshiba. Musayeef sarkin wayo kenan, shiyyasa dole NASA agyara MASA d'akinsa azuba komaiba Yakoma da kwana can. Aiigara dakayi wanan tunanin da anka, Dama INA niyar yin magana. Dariya yayi yanufi bayi yana fad'in to an hutash sheki. Bayan Dr yafito daga masallaci yanufi 6angaren mama Dan iman tanacan suna shan hirarsu itadai deexerh. Deexerh nabata labarin Umar farukh, iman ta ce, " amma dee.... Miyasa bazaki bashi Dama yazo gidaba Dan asan dashi. Wlhy aunty inajin tsoro, shima kullum nacinsa kenan, sau biyu yana kaimin ziyara amakaranta, yanzu haka yana fushi dani akan nak'i had'ashi da uncle. Kai amma dee.... Bakida kai, ke Matan na Neman mijin aure ido rufe ke kina zillewa bayan kin samu, kobak'ya sonsane?. Wlhy aunty INA sonsa kawai inajin tsoron kamar yanda nafad'a miki. Tsoron kuma?, tomiye abin tsoron anan?. Kinsandai uncle yanada sauk'in kai amma bazan iya tunkararsa da wanga batuba, shiyyasa na CE, "farukh yatsahirta harna kammala makaranta. Cabd'i Jan, tsaya kallon ruwa kwad'o yaymiki k'afa 'yammata, yanzu idan ansamu tattali ake. Ni kibar komaiba ahannuna zan Sanar da daddyn musayeef, shima Umar d'in kisanar dashi yashirya zuwa bayan na Sanar da Dr saiya saka MASA ranar zuwa. Waye kuma? Dr dake shigowa yafad'a. Atare suka kalleshi, yazauna kusada iman, dee.... Tai saurin tsungunin iman wai kada tafad'a yanzu. Dariya iman tayi ta ce, " zan Sanar maka amma ba yanzuba. Okey ko yaushene INA saurarenki. Daga nan suka d'ora hira, har marwan yadawo daga makaranta mom ma tashigo akacigaba da hira mai dad'i irin ta 'yan family d'in dasuka shak'u da juna sosai............... *_kuyi hak'uri, wlhy nayi typing sosai, Nazo zanyi posting na danna delete, bakuji iron haushin danakejiba yanzu wlhy😭._* *luv u oll my fan's* *(((S)))........2017* [8/6, 6:03 PM] mrs bilkisu: *_BAN SAKETA BA!!_* *_NA Bilyn Abdul_* _sadaukarwa_ *ya Abdul (city phone's)* https://mrsbilkisa.blogspot.com *(page 41 & 42)* Dr kishingid'e gefen gado, kan musayeef na kan k'irjinsa yayi filo dashi, barcincisa yakeyi ajikin babansa, ahakali Dr ke shafa sumar yaron data kwanta luf luf, yakai dubansa ga iman dake tsaye tana shirin barci. My life wai wace maganace zaki fad'amin d'azu ne?. d'ago idonta tayi tad'an kalleshi tana murmushi, saida ta d'aure igiyar rigar barcinta sanan taja kujerar madubi tazauna suna kallon juna. Uhmm damafa akan d'iyarkane deexerh, deexerh kuma?, mike faruwa da ita?. Babu komai sai alkairi. Yaushene kuke ganin zakubar dee.... Tafara kula samari harta sami mijin aure?. Kallonta yake cike da mamaki, yad'an k'an k'ance idanunsa, miya kawo wanan maganar?. Iman ta juya kwayar idonta tana gyara zama, bafa wani Abu bane, ni kawai ina ganin lokaci yayi dazaka bata dama tafito da miji. Ajiyar zuciya Dr ya sauke, yad'an tashi zaune tareda gyarama musayeef Kwanciya, hakene my life, saidai ina ganin abarta ta kammala karatun shiyyafi a'ala, kinsanfa yarannan dasun fara soyayya saisu zubar da komai mai muhimmanci arayuwarsu. Murmushi iman tayi, hummm Dr kenan, zan iya yarda dabatunka tawani 6angaren, amma tawani gefen zand'an musaka, musamman Idan na kalli rayuwata. Karka manta ina ss 2 secondary aka cireni aka baka, miyasa iyayena basuyi wanan tunaninba. Kai ya girgiza yana murmushi, kema asanan akwai abinda yakawo dalili, amma dukda haka na fahimceki, yanzu ita khadijan tanada Wanda takesone?. Ajiyar zuciya iman ta sauke, tareda fad'in abinda nakeso ka tambaya kenan. Yasake murmusawa amma baice komaiba. Dee..... Tanada Wanda takeso, sun had'une alokacin dakayi wata jiyya a asibiti, 'yarka tanason guy d'in sosai domin na fahimci haka a zancenta, shima kuma yana Sonta bil'hak'i da gsky, Dan har yana buk'atar ganinka daga nan yaturo iyayensa, kaga bayan kammala makaranta saimusha biki. Dariya Dr yayi, Dan ganin yanda ta k'arasa maganar cike da d'oki, yashafa kansa yana kallonta, my life nima nakusa zama kaka ko?, yak'are maganar da d'aga gira. Jinjina masa kai tayi tana d'an zaro ido, fuskarta d'auke da murmushi, ta sara masa alamar girmamawa. Dariya yayi sosai, my life kodai kema zaki zama soja ne?. Kagako damun kafa tarihi miji soja mata soja, d'ansuma zaizama soja, lamarin so nice. Dr yalek'a fuskar musayeef yana fad'in gsky zamu bada ma'ana, da maganatu idonsa biyu datuni labarinnan yakai kunnen mama da yaya da aunty. Iman tamik'e tana dariya, ta hawo gadon tazauna kusada Dr tareda d'ora kanta akafad'arsa, aii wanan d'an naka har nakan rasa inda ya koyo magana, gashi kai ba gwanin surutuba, nimadai hakan nake, amma shi magana kamar akku, tad'anja hancin musayeef daketa barcinsa. Dr yashafo fuskarta yana fad'in kin manta da deexerh, aii dukkanain surutunta musayeef yad'obo. Uhhmmm kumafa hakane habibi na. Kallonta yayi sosai, ya maimaita sunan ahankali habibi!.. Kai takad'a masa tana murmushi, rungumeta yayai yana sumbatar wuyanta daketashin k'amshin wani fitinannan turare. Yad'ago suna kallon juna, ngd sosai. Ka cancanta tafad'a cike da salo. Nima nayi dace yafad'a ahankali. Nice nadace habibi na, nima nadace my life yafad'a yana rungumeta. *++++*• *++++++*• *++++* Washe gari iman tabama dee..... Labarin yanda sukayi da Dr, cike da farinciki Dee.... Tarungume iman, kai aunty nayi farinciki sosai wlhy, yaushe ya ce, "yazo su had'u?. Nanda kwana biyu, Dan zaikoma wajen aiki ranar lahadi, woow! Bari na gumtsama bobo na. Tofa Dee.... Kinfa afka da yawa. Um'um aunty kefa kikace karna tsaya kallon ruwa kwad'o yamin k'afa. Haka batun yake d'iyar uncle isma'il, maza kira surikina ki gumtsa masa bayani kawai. Dariya sukayi harda tafawa...... Shigowar Xoxo yasa suka mik'e suna ihun murna, cike da farinciki suka rungume juna. Bayan sun zauna iman ta ce, " haba my sisi abin ko waya babu. Uhummm kedai bari, gidanne zasuyi bak'i shiyyasa nahad'o inawa inawa nayo nan. Bak'i kuma kamarya?. Xoxo ta harari iman, kina nufin daddyn musayeef bai fad'amiki komaiba. A'a wlhy basanar dani komaiba, k'ila ya manta. Lallai daddyn musayeef zan ramane, wai ina kishiyarki naji gidan tsit, gashi kuma kuncika gida da ihu keda dee..... Deexerh dake ajiye tire ta ce, "lah wai aunty bata baki labarin mun iza k'eyarta gidan tsohoba. Xoxo tad'an zaro ido, kamarya dee....?, Kaini 'yan ganau mana. Gilas kof dee.... Tamik'ama Xoxo cikeda lemo, hhhhh aii randa nadawo ranar suka kama hanyar sokoto da sakamako mai k'yau har uku uku. Xoxo takwashe da dariya, dee..... Wai kina nufin anshare tarihinsu saidai alabarin kundin k'addara. Wlhy kuwa, sunyanki tikitin barin kano tuni. Shegiya dee..... Shiyasa nake k'ara sonki, ammafa yau zanyi barci mai dad'i. Iman dake zaune tanajinsu ta girgiza kai kawai batareda tayi maganaba. Xoxo ta kalli iman, lallai sisi shine koki Sanar minma. Kai saikace wani abin farinciki?. Okey keda abin bak'inciki kika d'aukeshi, tab ni fishinma danake da daddyn musayeef ya wuce na huce. Iman ta ce, " kudai kula sani", ni Dan ALLAH miya faru agidan har bak'i suka koroki?. Ki tambayi mijinki shiyyafi cancanta yasanardake. Kai sisi.... Bafa ya nan suna kasuwa tareda yaya, saifa anjima zai dawo, nikam wlhy nak'agara naji. Hhhhh saiki maida kwad'ayinki Dan bazakiji mutuwar sarki abakinaba, shine abokin ango mafi kusanci. Iman tazaro ido waIkina nufin komai Normal?. xoxo t` ce, "bafa zakijiba. Da�sauri imaf tq tashi`saigata da waya, Dr takira, bayan sundganyi musa}ar kalaman!soya{yaRsu ta"ce, " ha�sat fa tazo maoa yini. Woow! Kice kawai amaryarmu insha ALLAHU. $ban!gangba?� Oh my life sorry Dan ALLAH, w,hy ~Aman4c nabaki!L`bary, randa nadawo dazumud'in fad'a miki abinna� yafaru, ka�ji damu ganinan ztwa gidan yanzu. Tom s`ikazo iman tafad'a tana Yanke wayar. Bab�!dad'e�a Dp ya iso gidan, lallai amarya saikika gudo kenan?. Dariya Xoxo tayi, bayan sun gaisa ta ce, "badole na gudoba kun cike gidan da mutane. To aii haka akeso, babban taroma yana nanzuwa a hanya. Iman ta ce, " wai nikam sai k'ara 6addani kuke. Ruwan data bashi yad'auka yasha yana dariya, karki damu yanzu zakiji komai, amma ina dee.....?. Taje kaisu musayeef islamiyya. Okey. Kiyi hak'uri wlhy narikicene, idan kintuna randa abinnan yafaru nasu Raihan dasafe kafin faruwar haka ai na Fita nace zamuje tad'i. Iman ta ce, "eh. Yauwa to Dama gidansu hafsat mukaje muka gaida Abba, muka kuma nemi izinin turo manya. A take yabamu dama, shinefa yau manya sukaje tambayar auren, ranar nataho dazumud'in fad'a miki, aka dakushe farincikina. Dasauri iman taje ta rungume Xoxo ta na murna. Shidai Dr sai dariya yake musu. Dr yamik'e kunga bari nad'an watsa ruwa, mitumin ma yacemin yana zuwa yanzu. Dr Nabeel kake nufi?, iman ta tambaya. Eh, nagaya masa gimbiyarsa tana nan, shine yace gashi nan zuwa. Xoxo tace nayi gudun gara....... Kinfad'a gidan zagoba Dr yak'arasa mata yana dariya. Cikin 'yan mintina Nabeel ya iso. Xoxo sai 6oye fuska take wai ita kunya. Zama yay d'an nesa da ita yana dariya, gimbiyata yaukuma nine nazama abin jin kunya?. Iman tayi dariya itama, to aii dole aji kunyar Ango, barima nabaku guri. Hhhhh tomun gode, amma ina my boy?. Suna islamiyya shida 'yan biyu. Okey, ALLAH yasa sudawo kafin nawuce nayi missing nashi. Zasu dawo insha ALLAH Iman tafad'a tana shigewa d'aki. Anan suka wuni akasha soyayya Xoxo da Nabeel, harma tsare tsaren yanda auren zai gudana sukayi. Dan Nabeel ya ce, "kusa ya ce, " asaka bikin shima yasha angwanci kafin akoma yajin aiki. Itadai Xoxo tashitai tashige d'akin iman saboda kunya, sukuma suna mata dariya. Sunsha yini bayan magriba su iman sukaje suka maidata hargida, Umma tanata godiya dak'ara sakama wanan k'awance na iman da hafsat albarka. Bayan sun ajiyema Umma alkairi suka dawo gida. Bayan gama cin abincin dare, akadasa hirar family, anan yaya yake Sanar dasu, kawu yakirashi wai su Raihan basuje sokoto ba. Dr ya ta6e baki, to yaya mu miye namu, mudai aii mun Fita hak'insu, tunda tun randa muka sakesu muka kirasu muka shaida musu, Dan haka sunemi yaransu can ba ananba. Mama ta ce, "a'a dukda hakadai kuyi hak'uri Ku nemesu ko dan zumincin dake tsakani. Mama wane nemansu zamuyi su aii ba k'anana yara bane, kinsandai halin wad'an nan 'yan iskan yaran yanzu haka suna gidan zubaida Mara mutuncin k'awarnan tata. Wlhy kuwa yaya suna canma, garama tun wuri su kirasu nidai wlhy babu abinda zanyi, yamik'e afusace yabar falon. Kowa da kallo yabisa, Dan sunsan halin fushin isma'il, idan yasoka yasoka, idan yak'ika kashiga uku........... *_" hummm masoya ina alfahari daku akowace dak'ik'a ta rayuwata, ngd sosai da k'aunarku gareni, kuna k'aramin kwarin guywa gsky, ngd sosai, Nima ina k'yaunarku aduk Inda kuke, duk Inda masoyina yake ina alfahari dashi, kona sanshi ko bansanshiba ALLAH yabarmu tare, inamuku fatan alkairi arayuwa."_* *luv u oll my fan's* *(((S))).....2017 [8/6, 6:03 PM] mrs bilkisu: *_BAN SAKETA BA!!_* *_NA Bilyn Abdul_* _sadaukarwa_ *ya Abdul (city phone's)* https://mrsbilkisa.blogspot.com *_(page 43 & 44)_* Deexerh ta kalli iman atsorace, aunty miyasa uncle yake kirana Dan ALLAH?. ke babu komaifa wlhy, naga duk kin wani rikita kanki. Ba haka bane aunty wlhy tsoron uncle nake tun randa yazane su Raihan, iman takama hannunta suka fice tana fad'in saikuma akace kema dukanki zaiyi. Afalo suka iskeshi kwance kan doguwar kujera, suna shigowa yatashi zaune, deexerh tak'arasa kusada k'afafunsa ta zauna a k'asa, iman kuma tafice dasu had'a break itada mom. Kalon minti d'aya yayma dee.... Ita kuma kanta yana k'asa tana wasa da zoben hannunta Wanda Umar yabata, gabanta sai dukan tara tara yakeyi. Dr yay gyaran murya tareda jingina bayansa da kujera, khadija yakira ainahin sunan deexerh. Muryarta nad'an rawa ta ce, "na'am uncle. Yad'anja numfashi sanan ya ce, " waye Umar farukh??. Gabantane yafad'i, tad'an d'ago atsorace tana kallonsa saitaga shima ita yake kallo, da sauri ta maida kanta ak'asa, muryarta na rawa ta ce, "wanine. Wanine kamar ya?, inason nasan matsayinsa agurinkine. Ido tad'an zaro kanta na kallon k'asa, tayi shiru Dan bazata iya cewa saurayinta bane. Ya ce, "ke nake saurarefa. Iman tashigo falon da sallama zata d'auki Abu akicin d'intane, harta gotasu zata shiga kicin saitaji Dr yana fad'in bakida bakine???. Iman tadawo baya tana kallon Dr, daddy musayeef miya farune?. Babu komai my life, kawai ina tambayarta matsayin Umar agareta tamin shiru. Murmushi iman tayi, tazauna kan hannun kujerar dayake zaune, ta ce, " Dr tanajin kunyane fa, kasan babu yanda za'ayi tabud'e baki tace maka saurayintane. Hummmm to Ashe bata sonsa kenan?, ni inasonjine daga bakinta, Dan muyi magana nida yaya anjima shiyyasa. Iman dai batace komaiba, yajuya kan deexerh ya ce, "khadija kina sonsa?. Da gudu dee.... Ta tashi tafice. Iman ta tuntsure da dariya, Dr kam yasaki baki yanabin hanyarda dee..... Tafita da kallo, juyowa yayi yana kallon iman baki bud'e, my life kigammin yarinyafa, daga tambaya ta gudu. Cikin dariya iman ta ce, " amsar kenan aii, hakan yana nufin tana sonsa. Jin jina kai yayi tareda fad'in to ALLAH ya k'yauta. Iman tamik'e itama tana cewa ameen. +++++++++++++++++++++ Bayan Dr sunyi maganar dee.... Da yaya, yaya ya ce, "shi miye nasa, aii shine babnta duk abinda yadace yayi, su 'yan ALLAH ya Sanya al'kairine. Dr yaji dad'in furucin yayansa sosai, Dan haka yasanarma mama itama, tayi murna sosai da fatan alkairi, mom ma yasanar da ita, itama bakinsu d'aya da yaya Dan cewa tayi ita ina ruwanta shine babanta duk yanda yayi daidaine. *_(ni bilyn Abdul na ce, " su dee.... Ankusa shiga daga ciki🤣.)_* 💎+💎 Washe gari aka tashi da hidimar tarbar Umar, hummm masu karatu yau naga hidima, saikace shugaban k'asa zaizo, girke girke akayimasa na musamman, wanan duk aikin iman ne, dee.... Sai dad'i takeji. K'arfe hud'u bayan idar da sallar la'asar Umar ya iso tareda abokansa guda biyu, an tarbesu abin gwanin ban sha'awa, afalon su iman akai musu masauki. Dee.... Da iman suna d'aki, dee.... Anci kwalliya ta musamman sai baza k'amshi take, marwan yashigo da sallama, suduka suka juyo suna kallonsa. Yay dariya aunty sirikinkifa ya iso, yana falo tareda abokinsa. Alhmdllh iman ta fad'a. Dee.... Kuma ta sauke ajiyar zuciya, marwan ya ce, ALLAH ya shirya aunty dee..... Irin wanan ajiyar zuciya haka, idan uncle ya ce, "baimasabafa yazakiyi?. Dee..... Ta watsama marwan harara, to d'an fatan tsiya bakinka yasari d'anyen kashi, shiyyasama wlhy nak'agara nabar maka gidan d'an buk'ulu kawai. Dariya iman da marwan sukeyi sosai danjin bal'in da dee..... Takeyi, ko had'iyar yawu batayi. Dr yaturo k'ofar yashigo da sallama, yana sanye cikin manyan kaya, jar shadda sai maik'o take amma kansa babu hula. Kukuma lfy kuketa dariya haka?. Iman ta ce, "yarka mukema dariya, Dr yakalli dee..... Daketa Harar marwan. Tofa amarya miya faru?. Hannu tasa tarufe fuska tana fad'in kai uncle. Marwan yashiga zayyane masa komai. 'Yar dariya Dr yayi, ya ce, " kwantar da hankalinki Indai umarne kin samu da izinin ALLAH, yanzu kitashi kije wajensu, bayan sund'anci wani Abu saiki kirani. Akunyace ta tashi tafita, marwan yana rakata da sheri irinna sako da sako. Suna fita Dr yarungume matarsa suna murmushi, acikin kunnenta ya ce, yaran zamani babu kunya my life. Dariya yayi ta ce, "tomukuma 'yan wane k'arnine?. Ya juyo da ita suna kallon juna, kinason sani ne?. Tad'aga masa gira d'aya tana murmushi, bakinta yasumbata hannunsa yana shafa bayanta. Tajanye bakinta Dan ganin zai zarce, habibi bak'ifa garemu. Hannu yasa yadawo da fuskarta Inda take da, ya kafeta da idanunsa Dan munyi bak'i sai akace baza abani sweet na shaba, lumshe idonta tayi tana murmushi, ahankali ta ce, " nid'in takace aii. Ya k'afta idanunsa idan hakane miyasa aka hanni bayan gobe iyanzu nayi missing naki, wlhy jinake tamkar karna koma, shiyyasa dolene na nemi taransfa da wuri. Iman tad'an canja fuska, wlhy Nima banason katafi habibi, kasa nasaba da abubuwa dayawa, Wanda rashinka zaisa bazan jureba, ALLAH yasa mu koma yajin aikinnan akusa kodan nakusata dakai. Idanu yalumshi ya had'e bakinsa da nata. Kowa aikama d'an uwansa sak'o yake cikin alamun nuna kwarewa.... Hummmm kunga bari na lek'a dee..... Wad'an nan sunfi k'arfina. Tad'an dad'e tsaye ak'ofar falon Dan kunyar shiga takeyi, amma saita dake tashiga da sallama kanta ak'asa. Umar dake zaune akujerar farko yad'ago manyan idanunsa yana kallonta, ahankali yamik'e cike da d'okin ganinta, jiyake tamkar ya rungume kayansa amma babu dama. Nawas yakamasa yazaunar, kai malam bi ahankali mana agidan surukai mukefa. Dee..... Dake tsaye tana satar kallonsu tayi murmushi, cike da ladabi ta gaishesu, Nawas da Abbas ne kawai suka iya amsawa, amma Umar tuni yafad'a koginso. Takuma gaisheshi, nanma bai amsaba saida Abbas ya zungureshi. Ya sauke ajiyar zuciya, matana duk kin wani rud'ani wlhy, miye sirrin?. K'asa dee..... Tayi dakanta tana murmushi, tak'arasa gaban tulin kayan abincin ta ce, "bismillafa kuci abinci k'arfe biyar uncle zai shigo Ku gaisa. Hummm Abbas yafad'a danganin irin romon lagwada da'aka shirya dansu kawai, lallai shima ALLAH ya bashi surukai irina Umar wad'anda sukasan darajar mutane. Basu kwari kansuba suka nad'e hannun Riga suka kwashi gara. Bayan sunci sunyi nak sunata santin girki dee.... Tagyara wajen tsaf, sanan tankoma ciki kiran uncle. Abin yabata mamaki Dan ganin uncle da iman sun canja kayansu, tararwama tayi iman nasake sabuwar kwalliya, bayan kuma agabanta tayi kwalliya d'azu. (Na ce, " hummm dee.... Bazaki ganeba, bayan fitarki akasha soyayya). Shikanshi Dr yalura da kallon da Dee.... Take musu Dan haka ya maze ya fita. Tunda Dr yashiga falon su umar suka sakko k'asa domin girmamawa, dak'yar yasa suka koma saman kujera bayan sun gaisheshi. Yayaba da abinda sukayi kwarai da gsk, kuma sun burgeshi. Su Umar kam duk Kansu na k'asa saboda kunya, Dr ya ce, ''tom waye sirikin nawa?. Nawas ya nuna Umar dayay k'asa dakai yana murmushi, Dr ya ce, "masha ALLAHU. Dr yashiga yima Umar tambayoyi gameda kansa. Kan Umar ak'asa ya ce, " sunan Umar faruk Abubakar, anhaifeni anan garin kano, inada yayye biyu mace da namiji, sanan inada k'anne biyu duk maza, nayi karatu afannin likitanci yanzun haka ni likitan fatane, ina aiki a asibitin M. Aminu kano. Masha ALLAH Dr yafad'a yana murmushi, lallai kayi k'ok'ari kuma na yaba, Dan haka nabaka dama katuro mayanka muyi maganar aunrenku da khadija, so bayana ta kammala karatu nanda wata takwas sai ayi biki, yaka gani?. Yayi uncle kuma ngd sosai da karramawa, insha ALLAHU zanmusu bayani. To shikenan Alhmdllh, yanzu kutashi muje ku gaida mamanmu kakar khadija kenan dakuma mahaifinta da mahaifiyarta dakuma matana. Har cikin gida yakaisu, suka gaisa da mama dasu yaya, kowa ya yaba da Umar 100%, gashi k'yak'yk'yawa ga tarbiyya, Dan saida Dr yay bincike akansa sanan yabashi damar ganinsa. Hakadai komai yagudana cikin girmama juna. Bayan tafiyarsu dee.... Tasha tsokana wajen mama da marwan da aunty iman , barmusu falon tayi, tashige d'akinta tanata tsallen murna harda rawa, ta mallaki Umar abin sonta😁👍🏻. Washe gari Dr Yakoma wajen aiki cike da kewar iyalinsa, tare suka tafi da dee... Zai sauketa a makaranta. Tunda suka tafi iman saitaji gidan babu dad'i, kewar mijinta dukta addabeta, dauriya kawai takeyi, ga surutun musayeef ya isheta. Samu tayi ta lalla6ashi yatafi wajen mom, itakuma tasamu tad'an kwanta tareda fad'awa duniyar tunani. Haka rayuwa tacigaba da gudu da Sauri, dagari ya wayd sai dare yayi, saikaga rana ta bace dare yashigo, ahaka Dr yasamu wata biyu dakomawa wajen aiki, duk k'arshen sati yana zuwa gida weekend saidai idan baisamu damaba, sosai suke shan soyaya shida iman tamkar sababbun aure, kowa yagansu saisun birgeshi abin kamar majina bisa tuwon masara. Ahaka aka shiga hidimar bikin Dr Nabeel da miss Xoxo, kwata kwata iman batada lokacin kanta shiri suke babu kama hannun yaro, masu karatu yakamata Ku shirya Dan sanan bikin yadace kowa yajeshi🤠. A6angaren su aunty da Raihan kam lamarin sai addu'a, iyaye sun duk'ufa da nema, ada su yaya sunyi burus da zance amma ganin lokaci ya shud'a saisuka saka hannun wajen nemansu. Yanzu hakadai Anbada cigiyarsu agidajen redio. Duk abinda akeyi zubaida na ji saidai tayi dariyar mugumta Dan tad'an sun tafi kenan har abada baza a gansuba.... Nace hummm zubaida abin aii na ALLAH ne, wai yaro ya tsinci hak'ori.................. *_luv u oll my fan's_* *((S))........2017* [8/6, 6:04 PM] mrs bilkisu: *_BAN SAKETA BA!!_* *_NA Bilyn Abdul_* _sadaukarwa_ *ya Abdul (city phone's)* https://mrsbilkisa.blogspot.com *_(page 45 & 46)_* A yau Reefat ta iso kano itama, kai tsaye gidan iman ta sauka, Xoxo ma tana gidan suka rungume juna cike da kewa, iman ta ce, "madam Reefat mizan gani haka?, kina bakiso bakiso harkin k'unso mana baby. Hararta Reefat tayi cikin wasa, ALLAH bana son iskanci iman, ni banida komai. Ki rantse Xoxo tafad'a tana dariya. Kukam ALLAH yayi 'yan iska, nidai babu ruwana, 'Yar rainin hankali kema aii cikinne dake. Iman ta gwalalo ido ke 'yammata rufamin asiri, musayeef ya isheni. Wata dariya Reefat ta tuntsure da ita suka tafa da Xoxo, my hafsy kinjifa wani sa6o, idan k ya isheki Dr yana buk'ar wasu, gashima harya bayar. Iman takalli cikinta kamar zatayi kuka Dan ALLAH Reefat kidainamin wanan fatan, ni ALLAH banida komai. Ahakan Reefat tafad'a tana kallonta?. Eh wlhy tafad'a tana 6ata fuska. Hummm wlhy sisi kiyi gwaji ammafa kinada ciki, kokuma kisa daddyn musayeef yayi miki. Xoxo ta toshe baki tana dariya, cikin dariya ta ce, " Ku yanzu idan aka koma makaranta haka zaku koma mana da baby's?. Harararta iman Take, haba 'Yar iska indai cikine kema dashi zaki koma da izinin ALLAH. HHHHH ta yaya 'Yar fatan tsiya?. Dariya Reefat da iman sukeyi harda tafawa, Reefat ta ce, amsarki tana wajen Dr Nabeel, wanan rawar kan dakikeyi kina tunanin zai d'aga mini k'afane hhhhhh suka kwashe da dariya. Jikin Xoxo kuma saiyayi sanyi, ta ce, "Dan ALLAH kubar tsoratani, ALLAH zaku sakani kuka. Kuka kuma Reefat tafad'a tana gwalalo ido?. Eh wlhy Xoxo tafad'a cikeda gsky. Iman tayi murmushi tana dafa kafad'ar Xoxo, kinga kwantar da hankalinki kinji, komai zaizo da sauk'i aii. Xoxo ta jinjina kai tana had'iye yawu da k'yar. Haka sukasha hirarsu suna k'ara bama Xoxo haske akan zaman aure. Haka biki yacigaba da gudana cikin nasara sosai, can naga 'yan *_HOME OF NOVELS_* suna baza kala, Dan bikin nasunefa😁. Can nahango su Zarah Bukar dasu Rano su 'yar ficika autar hajiya su Nafi anka, mjey, hajja ce, waliyya, khadija Kandy, Basma er Lele, anata hidima, manyan k'awayen amarya kenan tun na yarinta🤣😜. Tom nimadai bilyn Abdul angayyaceni kuma na gayyaci 'yan group d'ina, muma zamuci Rangam da lemon roba💃🏻😜. Biki yayi bikifa anata shagali, naira nakuka tamkar ba'asan ciwontaba, amarya da ango sunata bada ma'ana cikin kwalliya ta alfarma kai lamarin sai fa Wanda yagani. Ni bilyn Abdul nama rasa ta Inda zan sambad'o muku rahotanni. Umma bakinta har kunne zata aurar da 'Yar d'iyarya abar alfaharinta, Abba kam ba'a magana, yau ranar tasace zaikai hafsat gidan miji. Su Dr isma'il sune na hannun damar ango, duk sunyi busy anata hidima. Hakama gidansu Nabeel momynsa sai farinciki take, da 'yan k'annensa Ayeesh da maimuna (kakus), suma sun gayyato k'awayensu anata hidima. Biki yayi biki, ayau aka d'aura auren Dr Nabeel Sageer Alhasan, Da amaryarsa Hafsat (miss Xoxo) to saimuce ALLAH ya sanya alkairi, yabama amarya da Ango zaman lafiya, ALLAH yasa bad'i mudawo suna. Bayan d'aurin aure hidimomi suka cigaba da gudana, Dan 'Yar bidi'ar nan saida aka d'ana, muntaka rawar ak'ame k'am, munci rangam da ruwan roba, harda lemon gwangwani, kai munfa Shana abikinga wallah. Bayan hidimomi da 'yan bidi'oi aka mik'a amarya Xoxo d'akinta cikin tangamemen gidanta na alfarma, tasha kukan rabuwa da ummanta da Abba harda 'yan k'annenta. Zuwa k'arfe tara kowa Yakama gabansa sai k'awayen amarya mafi kusanci aka bari, zuwa k'arfe tara da rabi gayyan anguna suka shigo akasha shafta da nasiha ga ango da amarya kowa Yakama gabansa aka barsu cikin aminci. Dr Isma'il yad'auki iman d'insa sukai gida harda Reefat, Dan sai jibi zata wuce. Gida tsit kamar bai tara mutaneba daga Ango sai amaryarsa. Dr Nabeel yana gaban Xoxo yak'ura mata idanu kamar za'a kwace masa ita, itakam tayi k'asa da kai cike dajin kunya dakuma kewar gida da fargabar sabuwar rayuwa. Yasa hannunsa yad'ago fuskarta datasha kwalliya sai k'yalli take. Ta lumshe idanu Dan bazata iya had'a ido dashiba, yay murmushi mai sauti yana cigaba daraba ido afuskarta, 'yammata yau babu tsiwa ko, anrufe bakin magana ruf. Itadai Xoxo ko motsi batayiba, ahankali yamatsar da bakinsa Kusada NATA, sunajin saukar numfashin juna, magana k'asa2 yace tunda bakin arufe yake bayan su isma'il sun siya, nima bari nayi nawa siyen bakin, kafin tayi wani yunk'uri ya......... Hum baridai nayi shiru, (Tawan saida safe nabarku lafiya asha amarci k'alau😉). *_Washe gari_* Na ce, "bari nad'an lek'a muku amarya, wajen misalin k'arfe 12 nashiga gidan, a get nagamu da gayyar mutane sun fito daga gidan, da'alama bak'ine masu tafiya sukaga d'akin amarya. Nidai bayan mun gaisa na ra6a nashige, afalo na iske mutanen gidan, Xoxo kwance tayi fillo da cinyar Dr Nabeel, hannunsa na shafa gashinta ahankali, itakam ta shagwa6e fuska wai barci takeji. Ya sumbaci goshinta yana murmushi, aidole kiji barci my hafsat Dan jiya kin....... Da Sauri tarufe masa baki da lallusan hannunta plzz nidai karka fad'a ga bilyn Abdul nan tsaye, yanzu saita iya sambad'awa ashafin littafi nikam gsky banaso. Yacire hannun yana 'Yar dariya to shikenan nafasa fad'a aii, yamik'e tareda d'aukarta kamar wata baby yay bedroom yana fad'in ALLAH yasa kada wani bak'o yasake zuwa subarmu musha barcinmu. Tsuru nayi tamkar munafuka, to masu karatu tunda sungudu Nina aii saina kama gabana (nimafa soyayyarna inada gwarzona agida, to aii gwara na lalla6a gurin kayanaba😂). Yauda gobe kayan ALLAH, su Xoxo anashan amarci kamar babu gobe, tayi k'yau bul bul da ita, alamomin jin dad'i sun k'ara bayyana sosai atareda ita, wanan kad'ai ya Isa yanuna Dr Nabeel yana kula mana da ita sosai. Suna shan amarci kam, yayinda iman taketa fama da laulayin ciki, Wanda tunda oga Isma'il yagane yaketa faman murna, jiyake tamkar ya had'iyeta Dan dad'i, sai kaf kaf yake da ita. Hummm xoxo mafa kamar ansamu, Dan naje gidan daga fara gaisuwa naga tayi bayi da gudu sainajiyo yunk'urin amai, lallai Dr Nabeel mai sa'a ne, lol. A6angaren Reefat ma dai cikinta harya fito abin gwanin sha'awa, ya usman yanaji da ita, ana shan soyayya kamar babu gobe. Ana cikin haka makarantarsu takoma daga yajin aiki, haka suka tarkata suka koma makaranta kowa da k'aramin cikin, aiiko anashan shafta, idan weekend yazo mazansu suzo su kwashesu kowa yasha soyayya da matarsa. Agida iman tabar musayeef hannun mom, bai damuba tunda yasaba dasu dama. Bikin deexerh yanata matsowa Dan haka aka fara shirye shirye yanda yakamata. ####################. Su aunty madai yau cikin hikimar ALLAH suka samu ku6ta daga hannun su zuby, anzubasune amota za'a kaisu legos Inda tushen k'ungiyar take, sukai had'ari ahanya, dayawan 'yan k'ungiyar sun mutu yayinda masu taimakon gaggawa suka ku6tar dasu Raihan, babu 6ata lokaci aka kaisu asibiti, yayinda hukumar 'yansanda tayi bincike aka gane 'yan ta addane abakin d'aya daga cinsu zuby Wanda bai mutuba, ram akayi dasu zuby dasauran 'yan k'ungiyarsu dake Legos, dama k'aramar k'ungiyace basuda wani fawa yanzu suke kafata shiyya suka baza group ta WhatsApp, to ALLAH ya kiyaye gaba. Bayan su aunty sunsha jiyya a asibiti harna tsawon watanni biyu aka sallamesu tareda damk'asu hannun iyayensu. Sunsha kuka da nadamar rayuwarsu, sun k'ara gane zancennan na hausawa dakance idan zaka Gina Ramin mugunta ka ginashi gajere Dan bakasan wazai afkaba. Sud'inan da da suka Shana ga k'yau ga dama amma yanzu sune suka koma jemai jemai duk kamaninsu sun canja sunyi bak'i sun kod'e kai babu gashi, ALLAH ya yafe musu suma suzama mutanen kirki kamar kowa haka suke fata. Lokaci ya shura sosai, gasu iman sun sami nasarar mammala karatunsu, zuwa yanzu cikinsu duk sunfito suduka ukun, Reefat ma tana gangarar haihuwa, Dan cikinta ya tsufa sosai haihuwa koyau ko gobe, dak'yarma ta iya kammala exam d'in. Sunsha kuka lokacin rabuwa, su iman sukayo kano Reefat tayi Adamawa da alk'awarin data haihu zasu zo. Sumadai akanon kowa gidanta mijinta yawuce da it a cike da farinciki. Musayeef yayi murnar ganin aunty maa d'insa, yak'ara girma shima yayi tsawo sosai babu laifi, walima sosai Dr isma'il da Dr Nabeel suka shiryawa Matan Nasu na murnar kammala karatu lfy, to ranarmadai mun karya k'ashi aradu. Bikin dee.... Ya kankama su iman duk sunzama busy, ga cikin ga hidima, hakadai tadaure tanata kai da kawo saboda mom Tanama iman kara, komai aka nema irin na uwa saitace aje wajen iman, hakama yaya ya mik'a ragamar komai ga Dr isma'il, shiyyasa bikin yazama Nasu iman. Ina k'ok'arin shiga 6angaren iman Inda amarya da k'awayen ta suke, bayan mun gaisa da iman da Xoxo dake tsaye suna shawara akan walimar gobe idan ALLAH ya kaimu, saiga wasu mata su biyu. Daga iman har Xoxo dani bilyn Abdul tsayawa mukayi muna binsu da kallonta mamaki........... Tofa masu karatu kosu waye wad'an nan mata oho, muhad'u a page nagaba danjin su wanene??????.............. *luv u oll my fan's* *(((S)))........2017* [8/6, 6:04 PM] mrs bilkisu: *_BAN SAKETA BA!!_* *_NA Bilyn Abdul_* _sadaukarwa_ *ya Abdul (city phone's)* https://mrsbilkisa.blogspot.com *_gaisuwa da fatan Al'kairi gareki Ayusha muh'd, ya mura?, kisaurari zuwan gasassun kaji Dan sune maganin murarki, masu yaji za'a kawo miki😂😜._* *```{zuciya, kowa da irin tasa}*``` Acigaba da gashi👌🏼 *_(page 47 & 48)_* Ba wasu bane face Raihan da aunty, kallo d'aya zaka musu kagane sun fita hayyacinsu, wai sund'anyi k'yauma akan sanda aka kwatosu. Xoxo tayi k'arfin halin cewa wad'annan kuma daga INA?. Iman ta sauke ajiyar zuciya tana kallonsu, idonta tuni yacika da kwallah, muryarta ad'an sark'e ta ce, "su Raihan ne. Raihan kuma?, wai kina nufin kishiyarki?. Kai iman tad'aga mata tana share hawaye. 6angaren mama suka nufa Dan basu kula dasu imanba. Xoxo tad'an tallafe cikinta daya fito sosai. Kai iman yunwafa nakeji. Iman tayi 'Yar dariya, sisi gsky Nabeel fa, babynmu nasaki cin abinci dayawa. Hummm kifita batun hayatee shi bai iya komaiba sai sheri wlhy, amma zan ramane saina haihu. Iman tayi dariya, Ashe zaki dad'e baki ramaba, idan kika cika mana Baki, bayan sati uku da haihuwa saimu Baki wani babyn. Ido Xoxo tazaro kai wanan fatan tsiyarfa daga INA?, aii tunda kikace haka gida zani wanka. Dariya sosai iman take mata, suka koma ciki Inda k'awayen dee.... Suke anata shafta, amarya dai tana gefe ana mata k'unshi, duk bakinnan na dee.... Yau yayi tsit, na ce, lallai aure manya. Xoxo ta d'an ta6a dee.... Datayi shiru tana kallon mai k'unshi kawai, haba amarya lfy dai ko?, naji yau duk kinyi wani sanyi mike faruwa?. Numfashi ta sauke tareda yamutse fuska, ALLAH ni jinake kamarma afasa, nifa dukma auren yafita raina. Dariya iman da Xoxo sukayi, iman ta ce, " haba my dee.... Ina son umari ya mak'alene?. Wlhy aunty yana nan, ammafa ni duk tsoronma auren nakeyi. Teema ta shek'e da dariya, 'Yar iska deexerh Ashe zakiji tsoron aure, sanda akayi bikina babu irin sherin dabakiminba, kema gashi yau yazo kanki, su Ikilee ma baki yamutu. Harara dee.... Ta sakar mata, amma batace komaiba saidai idonta yacika taf da kwallah. Iman ta rungume kanta tana lallashi damata magana mai dad'i. (Ni bilyn Abdul na ce, "dee.... Yau ina zumud'in??)😁 Haka biki yacigaba da gudana cikin far in ciki, su aunty sai 6oyewa sukeyi dankar mutane su gansu, amma sun makaro Dan dayawa angansu sai kallonsu ake da zind'ensu. Kai iman wlhy nagaji sosai, anya zan iya zuwa dawuri gobe idan ALLAH ya kaimu?. Haba sisi na zaki iya wlhy, kinsandai kece abokiyar shawarar tawa, karki damu dakunje gida Dr zai k'ara gasa miki jikin da ruwan zafi, harma da tausa, tak'are maganar da d'aga gira. Xoxo ta ce, "hummm kokuma yak'ara taramin gajiya ba. Dariya iman takeyi, cikin dariya ta ce, " toya muka iya tunda ALLAH yabamu masu hali d'aya. Kibari kawai iman, keni wlhy idan nagaji kuka nake saka masa, ga wanan kayan anlik'a mana, amma baza'a barka ka hutaba, danma momy ta turomin su maimuna da Ayeesh sunad'an ragemin wasu aiyukan, aidanaga banu, wlhy dayaga shagwa6a salo salo. Hhhhhh nasan zaki iya sisina aii da wanan shagwa6ar kike k'ara rikita mana Dr Nabeel....... Sallamar Dr isma'il ce tasa iman yin shiru, ya ce, "nashigo?. A'a karka shigo iman tafad'a cikin tsokana. Yad'aga labulen yashigo yana murmushi, aii saina koma cikin k'awayen amaryarnan naza6i d'aya, kinga gobe idan ALLAH yakaimu sai a d'aura auren baba da 'yarsa. Cikin dariya Xoxo ta ce, " dakun kafa tarihi kuwa. A'a hafsat kadafa ayi kuzo keda k'awarki kuna zanemin mata, yafad'a yana kallon iman data had'e fuska. Kasan kuwa tsaf zamu iya. Tokin gani, aii gwara na hak'ura na lalla6a da 'Yar saudat d'ina. Iman ta harareshi. A'a yi hak'uri gimbiya. Xoxo dai dariya take musu, yamik'e yana fad'in hafsat Nabeel fa yazo d'aukarki. Yauwa wlhy dama shi nake jirafa. Har k'ofar gida suka rakata Inda Dr Nabeel yake tsaye yana jiranta, suna fitowa yanufosu, hannun Xoxo Yakama tareda rungumota jikinsa, wayyo ALLAH my Angel nasan kin gaji sosai ga babyna. Xoxo ta wani narke masa jiki, ALLAH bakaji yanda nakejiba hayatee. Tokodai na d'aukekine kawai.. A'a. Dr Isma'il yay dariya, abokina kaimafa bakada dama. Awajenka na koya aii, ko iman?. Dariya iman tayi batareda ta ce, "komaiba. Sukuma suka Shiga mota iman nak'ara rok'on Xoxo akan tazo da wuri Dan ALLAH gobe, tunda daga gobe shikenan. Dr isma'il yaja iman falon bak'i, da mamaki take kallonsa, Doctor mikuma zamuyi anan?. Baibata amsaba saida suka Shiga falon, yazauna saman doguwar kujera itakuma ya d'orata kan cinyarsa. Itadai kallonsa takeyi, yahure idanunta, wai Dan ALLAH kwana biyunnan bakiyi kewatabama?. Kewarmi zanyi taka bayan kullum muna tare?. Ya harareta kwana kawai ke had'amu shima nesa da juna, jiya da shekaranji ba kina ganin musayeef yazo tsakkiyarmu ya kwantaba. Dariya tayi Dan ganin yawani shagwa6e fuska, kai habibina shagwa6afa, kaikayi musayeef yayi tawa zan duba?. Musayeef kuma dolece tasa yake kwana damu, d'akinsa k'awayen deexerh ne aciki kaima kasani, d'akina kuma su Raihan suke kwana. yarungumeta sosai to yanzu yaza'ayi nikam nakai k'arshe gsky. Tad'an marairaice fuska, tareda shafa ciki, doctor ya ce, " fa na huta. Shima hannunsa yad'ora saman cikin nata, to aii nine doctor d'in yanzu kuma nace na Shana. Iman ta tuntsure da dariya, kai habibi wayonkafa yayi yawa wlhy, juyo da ita yayi sosai suna fuskantar juna, kallon juna suke ido cikin ido cikeda shauk'in so, ya sakarmata tattusan murmushi. Sanan ya kauda kai yana fad'i. Kinga kwanta ki huta muyi wata magana. Babu musu ta kwanta tayi filo da cinyarsa, rankwafowa yayi yana kallon fuskarta. Ta ce, "INA jinka to. Baiyi maganaba saidai tallafo fuskarta yayi da hannu d'aya, d'ayan kuma yana rik'e da hannunta sun d'ora saman cikinta, bata ankaraba taji bakinsa cikin nata. Wata Sumba yake mata maicike da kashe jiki, itama maida masa take da murtani cikeda k'auna, sun shagala sosai da faranta ran juna aka turo k'ofar. Raihan ce da aunty da mamansu, takirasu nanne danta kwantar musu da hankali akan suk'ara hak'uri da mutane, dolene aita kallonsu da abinda suka aikata abaya, amma idan sun danne sun hak'ura komaiba zai wuce sucigaba daneman gafarar ubangiji. Turus sukayi suna kallon su, Maman su Raihan takoma da baya, amma aunty da Raihan sun kasa ko motsi bare d'aga k'afa. Dr kam basu San da shigowarsu ba, sun tsunduma sosai wajan faranta ran juna, babu abinda kakeji sai saukar numgashinsu da k'arar AC. Wasu zafafan hawaye suka wanke fuskar Raihan, dayanzu tana tareda mijinta suna soyayya, amma aunty taja mata fad'awa tarkon wahala, gashinan wadda sukayi Dan ita tadawo gareshi sunata shan soyayyarsu hankali kwance, harda ciki na biyu. Shashshekar kukan Raihan ne yadawo da Dr hayyacinsa, yad'ago da k'yar yana kallon k'ofa, ganinsu Raihan tsaye saiya had'e rai, iman kam ta yunk'ura zata tashi zaune amma ya hanata, babu yanda zatayi dole ta hak'ura tabi yanda yakeso. Lafiya dai ko?, yafad'a afusace. Raihan da aunty auka tako har Inda suke suna kuka, suka durk'usa har k'asa suna rok'onsu akan su yafe masu, wlhy aunyi nadama, kuma har abada bazasu sakeba, Dan ALLAH su gafarcesu kozasu samu haske arayuwarsu tanan gaba. Dr yabud'e baki zaiyi magana ransa a6ace iman tasa hannu tarufe bakinsa, a'a habibina Dan ALLAH kayi hak'uri mu kar6i tubansu, wlhy na yarda sunyi nadama, muma munama ALLAH laifi kuma ya yafe mana badan halinmuba, Dan ALLAH awanan karon INA rok'on arzik'i agareka ka yafe musu, nidai harga ALLAH na yafe musu kuma komai yawuce agareni, dawowatama gareka kad'ai ya Isa wankemin duk wani taumashe Dana samu na farinciki abaya, tacire hannunta asanyaye tana fad'in, karfa ka manta ALLAH yasaka maka harda k'arin ribar wanan, tanuna masa cikin dake jikinta. Ajiyar zuciya ya sauke ahankali, ya jinjina kai shikenan na yafe musu ALLAH ya yafemu gaba d'aya. Murmushi iman tayi ta ce, "ngd habibina. Raihan da aunty suka Shiga godiya ga iman, ta ce, " babu komaiba wlhy, kutashi kuzauna muyi hirar zuminci ta yaushe gamo. Abin yabama Dr haushi amma saiya danne, su Raihan suka zauna aka dasa hira, shidai bama sosai yake saka bakiba, daga k'arshema saiya jingina bayansa da kujera ya lumshe ido, hannunsa na shafa cikin iman. Sunata hirarasu Raihan sai satar kallon Dr takeyi, akowane dak'ik'a jitake k'aunarsa tana sake nunkuwa a zuciyarta, amma tasan yayi mata nisa da zira'i dubu. ************************ Ranadai bata k'arya saidai uwar d'iya taji kunya, auyau juma'atu babbar rana aka d'aura auren Umar farukh da khadija deexerh ababban masallacin juma'a na anguwarsu, d'aurin auren yasamu halartar manyan mutane abokan Yaya Dana Dr isma'il, ga gayyar 'Yan sokoto, to saimuce ALLAH ya Sanya alkairi Dee... Yabada zaman lafiya da dank'on soyayya. Tab amaryafa yau ranartace abin sai Wanda yagani, Shiga take ta kece raini kamar tauraruwa, hakama ango Umar abin sai Wanda yagane, sai washe baki yake yau ya mallaki abin sonsa, abokansa su Nawas sai tsokanarsa sukeyi, shikam yau dai dai yakejinsa gani yake yafi kowa sa'a. Tab masu karatu yaufa ranarmuce nida 'yan gidana, Dan haka muka ware munata kwasar rawar Shoki, idan nai k'asa k'asa na kwaso saina manneta a idon dama😂, Alkur'an yau ranar tadabance. 'Yan *_"BILYN ABDUL H NOVELS_* fa babu sauk'i, Ashe duk sun iya rawar shoki, aiko sunata kwasota su iman Xoxo sunata manna mana lik'i, jar uban can, mawak'i gwanja ya haukace yaga ruwan kud'i sai kod'a amarya da Ango yake da iyayen amarya Dana Ango, Dr da iman susha washi kam babu k'arya. Bayan munsha bidi'oin m aka saka amarya tsaka dangi namata fad'a, sai kuka takeyi, harda su aunty amasu nasiha (araina na CE, lallai su aunty anga duniya). Bayan ankaita Yaya da mom sunmata suma aka kaita 6angaren su Iman, Dan babban uba yayi fad'a Dr kenan. Tofa sabon salo nafad'a Dan ganin Dr isma'il yana sharar hawaye, bayason rabuwa da babynsa amma yazaiyi, daurewa yayi yayimata nasiha mai ratsa jiki, tanata kuka. Dakansa Yakama hannunta har mortar daza'a kaita Inda abokan ango suke jira, yana sakata tafito da Sauri tana kuka, tafad'a jikin Dr tana fad'in itafa bazataba ta FASA auren. Rungumeta yayi shima yana sharar kwallah, (na CE tofa kaga uba yana kuka 'yarsa zata gidan aure). Dak'yar ya lallashi Kansa yad'agota tareda sumbatar kanta, kiyi hak'uri kinji babyna wanan shine yak'in Matan, kowace mace haka akayimata, bakiga auntynki ba iman harta saba da gidanku, itama haka aka kawo mana ita tana kuka, momynki ma haka, gashi datayi hak'uri harta Haifa mana Ku, to kema ahankali zaki saba da Sabon family naki kinji. Kai tad'aga masa tana shashshekar kuka, yashare mata hawayen yana murmushi, sanan Yakama hannunta yasake sakawa amotar, iman tashiga gefenta tareda k'anwar mom d'insu deexerh, aka saka dee... Atsakkiya. Dr yarankwafo yana gayama iman magana akunne, ta jinnina kai tana kallonsa tace to. Ya ce, "babyna ALLAH yabada sa'a kinji. Su iman sukace amin. Iman ta ce, " yauwa na manta musayeef na nan ad'akinka yana barci, karya tashi yayta kuka yaji gidan tsit. Okey babu damuwa aii zuwa zanyi namayi wanka. Daganan motocin amarya suka shilla, saida yaga 6acewarsu sanan Yakoma ciki, A get yay gamo da marwan yajingina da Bango yanata kuka kamar wani mace, Dr ya girgiza kai tareda kama hannunsa suka Shiga ciki yana lallashinsa. Na CE, "ALLAH sarki marwan abokiyar fad'a ta tafi sai hak'uri kuma aii........ *luv u oll my fans* *(((S))).......murar [8/6, 6:04 PM] mrs bilkisu: *_BAN SAKETA BA!!_* *_NA Bilyn Abdul_* _sadaukarwa_ *ya Abdul (city phone's)* https://mrsbilkisa.blogspot.com 🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚 *_(page 49 & 50)_* Tawagar amarya ta isa had'ad'd'en gidan Umar farukh, har yanzu dee.... Kuka takeyi, motar da aka d'akkotace kawai tashiga cikin gidan, sauran duk awaje suka tsaya. Iman takama hannunta har k'ofar falon, sanan ta ce, "kiyi addu'a kafin ki shiga. Cikin sauke ajiyar zuciya dee.... Tayi addu'a sanan suka k'arasa cikin bedroom d'inta dayagama had'uwa masha ALLAH. Sauran mutanema sun shigo sunata zagaye ko ina, kowa sai yabawa yake, dan su Dr sunyi k'ok'ari wajen had'a 'Yar d'iyar tasu. Dee.... Kam tanacan kangado mak'ale da hannun iman, ita adole tayi wayau kar iman ta gudu. Bayan kamar awa biyu akafara cewa su fito, mutane suka fara ficewa gudun karsu rasa mota. Kafin kace kwabo gidan tsit, sai iman kawai datake k'ara mata nasiha, danuna mata wasu turarurruka da yanda zatayi amfani dasu. Kai kawai take d'aga mata tana hawaye, bayan tagama nuna mata tayimata sallama. Tab aiisai dee.... Ta k'ank'ame iman tana sake bud'e sabon shafin kuka. Itama iman d'in sai kuka takeyi. Aunty Zainab ce taji shirun yayi yawa Dan haka tabiyo baya, sun burgeta sun kuma bata tausayi, dak'yar ta 6an6are dee.... Daga jikin iman, ta zaunar da ita kan gado tana lallashi, cikin dabara da wayo suka gudu suka barta. ****************** Jiki a sanyaye iman tashiga gidan, 6angaransu tawuce itadasu Raihan, suka shiga d'akinta itakuma tawuce d'akin doctor. Yana kwance rungume da musayeef, idonsa biyu amma ya lumshesu yana d'an girgiza k'afa. Iman tayi sallama tashigo, ahankali ya amsa baikuma bud'e idanunba. Jiki a sanyaye tazauna gefensa saitin cikinsa, ta shafa kan musayeef dake saman cikin doctor, tasauke ajiyar zuciya wadda tasa dole doctor bud'e idanu akanta. Takauda kanta Dan bataso yagane kuka takeyi, yunk'urawa yayi yatashi zaune, yakwantar da musayeef saman gadon sosai, rungumo iman yayi jikinsa kema kukan kikeyi ko?. Yashafa cikinta yana murmushin kuka, yanzunan nima idan mace kika haifamin haka za'a d'aukemin ita kamar yanda aka d'aukemana khadija a yau?, haka za'a kuma k'ara d'auke mana husaina wata rana?. Kai iman dama haka iyaye sukeji aranar auren 'ya'yansu??, murmushi iman tayi tana zubar da hawaye, tasauke huci mai zafi daga bakinta, hakane doctor, haka iyayenmu sukaji alokacin dasuka Baku mu, suna sonmu suka hak'ura sukabi umarnin ALLAH. Amma wanan baihana maza k'untata zukatan matansuba, baihana namiji raina iyayenmuba saboda yana gadarar shi mijine....... Manneta yayi sosai ajikinsa yana fad'in kuyi hak'uri my life insha ALLAH U mu bazamu zama daga cikin wad'ancan mazanba kinji. Haka yaytayi mata kalamai masu d'ankaren dad'i hartayi shiru, daga nan aka bud'e shafin soyayya. 🏳 Amarya kam tunda su iman suka tafi tak'ara tsananta kukanta, dama angon yana gidan, kuma bai gayyaci wani abokiba domin sayen baki. Suna tafiya yashiga d'akin amaryar tasa, tuni tausayinta yakamashi, jiki amace yahau gadon, d'agota yayi yarungume, yana lallashi. Sorry my Khadee kibar kuka plzz, kukanki yana cin zuciyata, yau ranar farincikinmu ce mun mallaki juna amatsayin zaman dindindin. Namiki alk'awarin zan kula dake tamkar agidanku. Itadai tana jinsane kawai, amma ita kad'ai tasan k'unar da zuciyarta take mata, ga tsoro fal ranta. Da lallashi yasamu taci wani Abu, sanan sukayi sallah. Hummm dagananfa oga Umar yanuna kwad'ayinsa afili, yayinda tuni idon dee..... Ya raina fata. Tana ganin yafita zaicanjo kaya, tasakama d'akin key, shirin barci tayi tahaye gadon ta kwanta. Bayan kamar minti20 saiga Umar yadawo, yanata6a k'ofa yaji GAM, komawa yayi d'akinsa yad'akko wani key d'in. Barci yafara d'ibar dee..... Taji motsin mutum akusada ita, afirgice tabud'e ido, tako daddage zata kurma ihu, dasauri yasa hannunsa yarufe mata Baki, ninefa khadija yafad'a cikin kunnenta. Jikinta na rawa ta ce, to Dan ALLAH nidai kafita. Murmushi yayi yana rungumeta, habadai kinta6a ganin ango da amarya sun raba wajen barci?. Tabud'e baki zatayi magana ya........ Hummmm saida safe my dee.... Asha amarci lfy. Haka rayuwa tacigaba da shurawa, akwana atashi babu wuya wajen ubangiji. Zuwa yanzu cikin iman yashiga watan haihuwa, haihuwa koyau ko gobe. Reefat ta haihu tuni, tasamu mace maisuna Fateema Zarah, su iman sunje sunan suma, to ALLAH yaraya mana fateema. Itama Xoxo cikinta yafito sosai, anan ana zubama Dr Nabeel shagwa6ar da'aka saba😂. Su dee..... Amarya, yanzukam andaina kuka, sai amarci da'akesha babu k'arya, tayi wani bul bul da'ita, Umar kam jiyake tamkar yacinyeta saboda so da k'auna, abin Nasu acan acan. Yau tunda iman ta tashi takejin garin sama sama, gashi Dr bayama garin, yana wajen aiki. Tana kwance akan kujera doguwa sai cije le6e takeyi, marwan yashigo da sallama rik'e da hannun musayeef daya d'akkosu daga makaranta, bata cikin hayyacinta ta amsa sallamar. Atsorace marwan ya ce, aunty lfy kuwa?. Murya asark'e tace marwan kiramin mom..... Aii kafin tak'arasa yayi waje, musayeef yazo gabanta yana kiran aunty maa miya sameki?, bakida lfy ne?, bata amsashiba Dan bazata iyaba.... Ahaka mom tashigo da gudu itada mama, hasbinallahu wani'imal wakil, iman haihuwa?, marwan muje fiddo mota. Haka suka taimaka mata zuwa mota, dole da yaran aka tafi suma Dan gidan babu kowa. Saida aka shiga da iman d'akin haihuwa sanan mom takira yaya ta shaida masa. Cikin hanzari yabaro kasuwa. Yana zuwa likita yana fitowa, yauwa yaya dama kaina fito nema wlhy, inagafa zamu bud'e tsohon aikintane na haihuwar musayeef kawai. Babu damuwa Dr yaya fad'a ahanzarce, hannu yasaka musu amadadin Dr Isma'il. Babu 6ata lokaci suka Shiga aikinsu. Bayan wani lokaci aka fito da k'atuwa baby mace, masha ALLAHU suka Shiga fad'a suna amsar yarinyar kowa bakinsa har kunne. Yaya ya ce, "maman fa?. Itama tana cikin k'oshin lfy, mun kaita d'akin hutune. Kafin kace mi, asibiti yacika da 'yan uwa da abokan arzik'i, su dee..... Amarya duk an iso, hakama Xoxo tazo danata kayan itama. Dr imsa'il ma an sanar masa, farinciki kam aii ba'a magana, haukacema yaya yai da ihu awaya. Satin iman biyu a asibiti aka sallameta, sukadawo gida cike da farinciki, zuwa sanan Dr yazo. Shirin suma akafarayi, dafarko iman ta ce, " bazatayi taroba, Dr ya ce, "wlhy bai yardaba, ba'ayi haihuwar musayeef ba yanzuma ta ce, " baza'ayiba, aii wlhy suma kamar anyi angama. Su dee... Ne 'yan zuga Dan kullum tana gidan, danma Dr ya ce, "karya k'ara ganin k'afarta sai ranar suna. Badan tasoba ta hak'ura, amma tak'udiri anan zata kwana ana gobe suna. Na ce, " humm. Masha ALLAHU munsha suna yarinya taci sunanta Nafeesa, tom ALLAH yaraya mana nafeesat. Bayan anci ansha anrak'ashe an k'walle kowa Yakama gabansa, xoxo da dee... Da aunty Salma kawai aka bari sune amarori k'irjin biki, saida suka gyara ko'ina sanan kowa mijinta yazo d'aukarta suka tafi. Umar kam dayazo dee.... Ta tubure saita k'ara kwana d'aya, bayason 6acin ranta Dan haka yabarta sai goben, babu Wanda yasan yanda sukayi, tatsula k'arya wai shiyace tak'ara kwana. (Haba dee.... Nagane wayonki sokike sai kun soya rago kawai, zan turo miki Rano ta tayaki Dan nasan tana son hanji😂). ++++++++++++++ Iman zaune tagama shirya baby feena dakaya masu azabar k'yau, musayeef na saman gadon yana game d'insa na fama da wayarta, yanayi yanacin biskit, yauwa yarinyar daddy kinga ki kwanta ga yaa musayeef nan naje nayi wanka. Musayeef ya ce, "aunty maa goyamin ita to kafin kiyi wankan. A'a kabarta takwanta tagaji da goyo bari nayi wanka nafito kaga daddynka yakusa dawowa. Tana Shiga wanka Feena tafara kuka, musayeef yajuyo yana mata magana cikin wasa baby feena ta daddy, yafad'a yana lakayar kumatunta, biskit d'in ya 6alla yasaka mata abaki. Iman batasan hidimar dayakeba tazata feena tayi shirune saboda was an da musayeef yake mata. Hankali kwance tayi wankanta ta fito, zuwa sanan biskit d'in ya narke abakin feena, shikam yak'ara saka mata wani azatomsa ta shanye, da sauri iman taja k'ofar bayi tarufe tak'araso gaban gadon tana fad'in na Shiga Tara ni saudatu musayeef mika batt?. Adaidai nan Dr yashigo shima, iman tad'ago feena tana girgizata musayeef bakada hankali kabata biskit. Da sauri Dr yak'aro gurin biskit kuma, wlhy habibi biskit yabata nikam naga takaina, kar6ar feena Dr yayi da sauri, bakinsa yad'ora akan na yarinyar yafara zuk'e biskit d'in daga bakinta, saida yatabbatar babu komai abakin sanan yamik'ama iman ita, kinga bata nono tasha. Musayeef dake zaune yana kallonsu yayi shiru Dan yagane abinda yayi ba daidai bane, Dr yakalleshi oh kai musayeef haka zakayi naka rainon kai kuma?. Wanefa raino, aii sainama zaneshi, haka kawai zai kashemin yarinya. Musayeef najin zancen duka yasa kuka, daddy Dan ALLAH kabama aunty maa hak'uri karta dakeni, nibansan feena batacin biskit ba. Jawoshi Dr yayi kaga karkayi kuka, amma daga yau karka sake bata kaji, ita bata fara cin irin wad'@nnan ba sainan gaba, nono ne kawai abincinta kaji. Kai yad'aga masa, daddy bazan sakeba aii. Yauwa d'an albarka. Itadai iman tanajinsu bata tankaba, saida feena tak'oshi sanan tamik'ama Dr ita, shikuma yad'auketa yanna fad'in Ummm my sweet feena. Iman ta harari musayeef kaikuma zamu gamu. Dariya Dr yayi ya ce, "babu wani gamuwa aii mun baki hak'iri dai. To ban hak'uraba. Hummm to mikeso muyi miki yanzu. Zaneku zanyi kawai. A'a kiyi hak'uri, amma albishirinki?. Goro tafad'a tana kallonsa. Hafsat ta haihu yanzunnan namiji................ *luv u oll my fan's* *(((S)))........2017* [8/6, 6:04 PM] mrs bilkisu: *_BAN SAKETA BA!!_* *_NA Bilyn Abdul_* _sadaukarwa_ *ya Abdul (city phone's)* https://mrsbilkisa.blogspot.com 🔚😁👌🏼 *_(page 50 to 60)_* Wani ihun murana iman tasaki, shima musayeef ganin haka saiya fara tsalle, Dr kam dariya kawai yake musu. Dandanan tashirya suka nufi gidan Xoxo. Tana shiga suka rungume juna cikeda farinciki. Iman tad'auki sargad'ed'en yaron fari tas masha ALLAH. Kai tawan yarona yafiki k'yau. Hhhh ALLAH ya kiyaye, kuma kunsan nagaba yayi gaba aii. Dariya iman tayi ta ce, ''ki k'ara kallon madubi to, babu wani kalla dazanyi nasan nafi k'yau, Haka sukaita gardama suna tsokanar juna. Ansha sunan baby Wanda yasami sunan muhammad, ya ALLAH karayamana Muhammad mai babban suna. Sunakam yayisuna Dan munrak'ashe mun k'walle, su Rano ne 'yan suyar hanji, kunsan nantafi afana🤣, Dr yayi hidima sosai, to balle uban gayya Dr Nabeel Wanda bakinsa yak'i rufuwa, kad'an kad'an saiya lek'a maijego, safaman soyayya suke agaban mutane ko kunya babu👍🏻😁. ------------------------------------------ *Banyan wani dogon lokaci.* Abubuwa dayawa sunfaru, masu dad'i da akasin haka, rayuwa tayi nisa sosai. Zuwa yanzu Reefat tanada yaranta uku, hakama Xoxo tanada biyu, dee.... Ma ta silli6o mana 'yan biyu mace da namiji, Dr yasamu jika kamar yanda yake fata. Anyi bikin marwan dawata yarinya Zuh'ra, harma da tsarabar ciki. Su aunty da Raihan sunyi aure suma, sunan zaune acikin garin sokoto, suma yanzu komai daidai sun shiryu tareda tsaida zuciyarsu waje d'aya, sunan zuwa kano zuminci hakama su iman suna zuwa, aunty dai har yanzu bata haihuba, amma raihan ta haifi d'iyar mace. Hummmm masu gayya da aiki kam yaransu hud'u yanzu, bayan musayeef, feena, an haifi ummukhursum, da Al'mustapha, Wanda take goyo yanzu haka. Dr anzama babban soja kuma aikinsa yadawo kano, yana kula da iyalinsa yanda yakamata. Musayeef yazama d'an saurayi masha ALLAH, yanzu rayuwarsa tafi yawa wajen mom da yaya, dansun kwaceshi. Lokaci lokaci yana zuwa gaidasu gwaggo shida k'annensa, deeni ma anzama samari masha ALLAH, Dan shirin aurensama akeyi. Hakama aunty Salma tana zaune gidanta lfy tareda 'yan yaranta biyar masha ALLAH. *_BAYAN SHEKARA 25_* feena tashigo dagudu tana kwala kiran aunty! aunty!!. Dr da iman suka fito da sauri suna fad'in feena lfy dai ko?. Bayan Dr taje ta mak'ale, daddy ya Musayeef ne zai dakeni Dan kawai nad'an d'ebo shamfo d'insa na wanke kai....... Kafin tarufe baki musayeef yashigo rik'eda belt d'in wandonsa, ganin iyayen nasa tsaye yasa shima yatsaya yana Harar feena. Dr yagirgiza kai, saboda tayi anfani da shamfo d'inka kabiyota zaka Daka?. ALLAH daddy bafa yau tafaraba, hakama ranar itada husaina da Nawal d'in aunty dee.... Sukaje sukamin 6arna ad'aki, nahukura bance komai, shine danta rainani yau takoma d'ibarmin shamfo. Iman ta hararesa to ba k'annenka bane, dansuyi amfani da kayanka shine kaketaman yima mutane wani babbotai, ALLAH ya shiryeka musayeef, taja tsaki takoma d'aki rik'e da hannun al'mustapha dayazama d'an saurayi shima. Dr ya ce, "tom kayi hak'uri bazasu sakeba kaji ko. Kai ya jinjina yafita, aransa kuma yana fad'in wlhy nakamata saina rankwashi kanta sau bakwai Dan Nasan bazata dainaba, itama husaina k'atuwa da ita tana biyema feena. Wai kuma ahaka ake shirin auramin ita kanta na rawa, hummmm yarinya zan saitakine. (Nikam Bilyn Abdul nayi dariya, wai yakaga musayeef da mata gwangwazo😂). *_TAMMAT BI HAMDULLAH_* ```INA FARINCIKIN KAMMALA WANAN 'DAN LITTAFI NAWA.``` kuskuren danayi ALLAH ka yafeni, abinda nafad'a daidai ALLAH yasa ya amfanemu gabad'aya. _Godiya mai tarin yawa ga masoyana abin alfaharina, bansan dawana baki zan godema masoyaba, amma zuciyata tana tsananin k'aunarku, kunacikin abubuwa muhimmai na rayuwata, ya ALLAH kabarmu tare, yak'ara dank'on zuminci atsakaninmu, ngd ngd sosai da k'ok'arin bibiyata._ *Bazan iya mantawa dakuba Dan tun farkon fara rubutuna kuna tare dani.* deexerh. sa'adatu sa'ad. zulaiha. my Ikilee. Riddallah. marak'isiyya (k'anwata). Aysha Manshat. Reefat yahaya. Ayeesh. 'Dan mom. Teema. Adama gages. Uwargida. Sakina gages. Hafsy. Binta (kakus) *_HOUSE OF NOVELS_* (gidan Abba Gana) Kuntaka rawar gani sosai atafiyata, Dan shine gida nafarko dasuka fara karanta buk d'ina, shiyayasa bazan ta6a mantawa dakuba har k'arshen rayuwata, ALLAH yabar zuminci. *_(Kaima Abba Gana ngd kana taka rawar gani arayuwata ta rubutu, ngd sosai)._* _godiya gadikakanin groups na Novels ALLAH yabar zuminci ngd da k'auna kuda Admins naku, ALLAH yabar zuminci_ *_"yan Group d'ina abin alfaharina, ALLAH yabarmu tare❤😁👌🏼."_* *_taku har kullum BILKEESA IBRAHEEM (Bilyn Abdul)_* _marubuciyar_ *_RASHIN SANI_* *_AUREN K'ADDARA ko BIYAYYA?_* *_K'ANWAR UWACE ko KISHIYAR UWA?._* *_NIDA AMINIYATA_* *_NAWAFF_* *_SABON AL'AMAREE_* *_KUKAN KURCIYA...._* *_BAN SAKETA BA!_* sai mun had'u asobon littafina mai suna_ *ABDUL-MALIK (Bobo)* Shima zaizo muku danasa sabon salon na musamman. Inafata zaku watsar daduk wani kuskure danayi kasancewata ajiza. Inakuma Baku hak'uri wajen jinkirin akan rubutun littafinnan ngd ngd ngd. Luv u oll❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣ 😁 *Bilyn Abdul*👌🏼 [8/6, 6:04 PM] mrs bilkisu: *_BAN SAKETA BA!!_* *_NA Bilyn Abdul_* _sadaukarwa_ *ya Abdul (city phone's)* 🤝🤝🤝🤝🤝🤝🤝🤝 _Assalamu alaikum masoya na, godiya tamusamman agareku, k'auna mai yawa agareku, jinjina da fatan alkairi su tabbata agareku, banida bakin gode muku, lallai Ku wani 6angarene narayuwa da tarihina, duk inda masoyina yake ina alfahari dashi, kuma ina k'aunarku_ _ngd da d'umbin k'aunar dakuka nuna mini, ALLAH yasaka da alkairi yabar zuminci._ _naga sak'onninku, wasu na amsa wasu ban samu damaba saboda matsalar network dana fuskanta ajiya, kuyi hak'uri ngd sosai, kuma ina alfahari daku arayuwata._ _abaya nace muku Next Novel d'ina *ABDUL-MALIK* to yanzu ansamu canji saboda wasu dalilai, yanzu Next Novel d'ina shine *CIKI DA GASKIYA......*, insha ALLAHU zai zomuku anan kusa danasa sabon salon, Dan gsky ban ta6a rubuta Novel makamancin wannanba, Dan haka ina Neman addu'arku agareni gudun shiga had'ari._ _```masoyi abin sone, masoyi abin alfahari ne, masoyi abin tunk'ahone, masoyi abin k'aunane, inasonku fiye da tunaninku, ALLAH yabarmu tare_``` _nasan wasu zasuyita tunani saboda nace atayani addu'a a buk d'ina nagaba, kunsan rayuwa kowa da irin fahimtarsa, wasu zasu iya tunanin labarin nawa ya shafesu, kuma ko kad'an ba haka bane..... Bari nabarku karna cikaku da magana, saimun had'u a *CIKI DA GASKIYA, WUK'A BATA HUDASHI* zaizo muku cikin cikakkiyar Hausa kamar yanda yadace_. SAIYA ZO...👌🏼👌🏼 *_masoyi abin alfahareee_*❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣ *_CIKI DA GASKIYA.....!_* *_CIKI DA GASKIYA.....!!_* *_CIKI DA GASKIYA.....!!!_*🗡🔪 🤙🏻🤙🏻🤙🏻🤙🏻🤙🏻🤙🏻🤙🏻🤙🏻 Bilyn Abdul.