*BAƘAR ZUCIYA!.* *_True life story_* *_🥰MAMAN ƊAN ALBARKA CE 🥰✍️✍️_* *_LITTAFIN KOWA YAƘI JI YA KAMMALA COMPLETE, GA DUK ME BUKATA TA TAMIN MAGANA TA WANNAN NUMBER 09014644247_* *Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai.* *Allah yadda ka bani ikon fara rubutu nan lafiya, ya Allah na roƙe ka ka bani bani ikon kammala shi cikin aminci. Ya Allah ka bani ikon rubuta abinda zai amfani al'ummar musulmai.* *Wannan labarin ya faru a gaske, labarine ya wanda ya faru akan wata baiwar Allah. Ban fara rubuta shi ba har sai da ta bani izinin rubuta shi. Saboda haka duk wani abu da kuka ga ya zo ciki tabbas abu ne ɗaya faru a gaske. Sai ɗan abin da baza'a rasa ba, wanda na ƙara saboda yanayin labari dan ya tafi yadda ake so, sai canjin suna da gari da sunaye. Ban amince a juya shi ta kowacce siga ba sai da izinina.* *PAGE1️⃣* Hayaniya ce take tashi ta ko'ina, a cikin ɗan matsakaicin tsakar gidan, yanayin mutanen dake kai kawo kawai zaka kalla kasan akwai wata hidima da ake gudanar wa, dan mata ne cike da gidan, kowacce sanye cikin kayan anko taci kwalliya ta dai-dai iyawar ta. Wata mace ce tsaye bakin ɗan madaidaicin banɗakin dake gefen zauren gidan in ka shigo, wadda a ƙalla ba zata haura shekara talatin da biyar ba zuwa da shida. Ita ma sanye take cikin kayan ankon, tasa hannayen ta biyu a cikin aljihun doguwar rigar dake jikin ta. Sai da ta kalli tsakar gidan ta kuma kallon banɗakin tare da jan dogon tsaki. Ta matsa jikin banɗakin tare da kara bakin ta a ƙofar tace "Wai Rahamah me kike tun ɗazu baki fito ba, kowa ya kammala shiri ke kin wani shige ban ɗaki sai kin ja mana faɗa wajen Baba. Gashi waje ba kusa ba, salon rana ta yi." Wata mata ce ta fito daga ɗaya daga cikin ɗakuna ukun dake jere, tana ƙoƙarin sa takalmin ta take kallon matar dake tsaye bakin banɗakin tace "Wai Jamila kina nufin har yanzu yarinyar nan bata fito ba, sai kace me shirin canja fata, wanne irin wanka take haka wajen awa guda." Ta ƙarasa maganar dai-dai lokacin data ƙaraso wajen Aunty jamilar. "Ke ma dai kya faɗa Aunty Zulai, ki zo dai ki mata magana da kanki ko zata ji taki, Wallahi na fi minti goma ina magana yarinyar nan ta yi biris ta ƙyale ni, Kuma banji alamun wanka take ba, tunda banji motsin ruwa ba." Cewar Aunty Jamila kenan, tare da matsawa Aunty Zulai ta ƙarasa bakin banɗakin. Ni kam ina jin su duk maganganun da suke, kuka na nake sha kawai. Asalima tunda na shiga toilet ɗin, ban cire ko zanin jikina ba bare na kai ga wankan, ina tsaye ina sharɓar kukana, zuciyata cike da fargabar da tsoron rabuwa da iyayena. Yanzu Shikenan ina wankan nan, in na fito na shirya zasu ɗauke ni su kaini can wata uwa duniya, Shikenan sun raba ni da ƴan uwana, sun raba ni da Abbanmu da Amminmu masu sona da ƙauna ta. Sun rabani da Aunty Zulai ɗina me gudun ɓacin raina, sun raba ni da Aunty Kairat wadda duk wuya duk daɗi muna tare muyi faɗa mu shirya. Haka duk zan barsu na tafi da sunan aure, Ya Allah. In har na tuna uwa duniyar da za'a kaini, sai na ji tamkar n fito nace musu na fasa auren baki ɗaya a barni na zauna cikin ƴan uwana, amma babu hali nasan yanzu haka an riga da an ɗaura auren, auren da nake jin sa wani irin banbarakwai, Ni ba farin ciki ba Ni ba baƙin ciki ba. Gani nan dai kawai za'a ce. Jin yadda Aunty Zulai ke bugun ƙofar yasa na had'iye kukan nawa, cikin dashshsiyar murya nace "Gani nan Aunty." Daga can waje taja tsaki ta ƙara buga ƙofar cikin faɗa tace "Na rantse da Allah Rahamah in baki fito ba, da kaina zan shigo banɗakin in yaso na fito dake. Ya ya zaki shanya mutane suna jiran ki kin wani yi zaman ki, bayan kin san abin dake gaban mu." Na sani sarai zata aikata, tsaf zata shigo banɗakin muddin ban fito ba kamar yadda tace. Dan haka sai na tsugunna na fara kaɗa ruwan botikin a zuwan na fara wankan, ko zasu tafi dan bana jin zan fito banɗakin nan yanzu. Hakan kaɗai ne nake gani a matsayin mafaka, kafin su tilasta Ni na fito. Kallon Aunty Jamila aunty Zulai tayi tace "Mu je mu jira ta, kin ga yanzu ta fara wankan tsabar ta raina mu." Suna shirin juyawa, sai ga wani dajjito Kyakykyawa baƙi wanda a ƙalla ba zai haura shekara sittin ba, ya shigo sai baza babbar rigar shi ya ke tare da amsa gaisuwar matan dake zazzaune a hanya. Hango su Aunty Zulai da ya yi, ya ratsa tsakiyar matan yana faɗin "Ina Rahamah ina fatan dai kun shirya? Dan kun san babu lokaci yanzu angwayen zasu iso." "Baba za dai mu shirya ɗin mu mun gama, amma ita Rahamah tana banɗaki tana wankan." Sai da ya gyara zaman babbar rigar shi, sannan yaja tsaki cikin faɗa-faɗa yace "Ya kika bari haka ta faru Zulai? Kin fa riga da kin san yanayin tafiya yanzu, hanya babu kyau bana son ku yi shigar dare, nafi son duk abinda za ku yi ku yi kafin mota ta zo, shi yasa na baro wajen ɗaurin auren na dawo." Sauke kai Aunty Zulai tayi, cikin ladabi Muryar ta a ƙasa tace "Ka yi haƙuri Baba in Sha Allahu yanzu zamu gama." Juyawa ya yi, yana faɗin "Kun dai ji abinda nace muku." Ya fice daga gidan baki ɗaya. Ai tun lokacin dana ji muryar Baba Usman, tuni na fara wankan cikin sauri, dan na riga dana san halin shi sarai, bashi da sauƙi baya son ɓata lokaci akan komai, komai nashi cikin gaggawa ya ke gudanarwa baya son jira da shirme. Baba Usman wa ne a wajen Abbanmu, uwar su ɗaya uban su ɗaya, shi ne waliyyin dake ɗaura auren yaran gidanmu. Mutum ne me mutumci da son zumunci, yana da son Ƴan uwan shi Sosai. Sai dai yana da zafi, baya ɗaukar shirme da shashanci ko kaɗan. Allah bai bashi haihuwa da yawa ba, Ƴaƴan shi uku kawai, Aunty Zulai sai Labaran, sai kuma Abdullahi. Saɓanin gidan mu, Abbannmu me Suna Malam Kabir, yana da mata biyu, Mahaifiyar su Aunty Jamila ita ce babba. Sunan ta Hajara, muna kiran ta da Mama. Ƴaƴan ta biyar, Zainab ita ce babba, sai mai bi mata Yaya Yusuf, sai Yaya Musa, sai Khalid shine Sa'ana, sai autar su ita ce Bilki muna kiran ta da Ummi. Sai ɗakin mu, Majaifiyar mu sunan ta Sa'adiyya, muna kiran ta da Ammi. Mu bakwai ne a ɗakin mu, Babban Yayanmu sunan sa Abubakar, sai Ya Mudassir, sai Aunty Khairat, sai Aunty Fati, Sai Yakubu daga shi sai ni Rahamah, sai kuma ƙaramar ƙanwata Aminatu. Wani uban bugu da akawa ƙofar banɗakin, shi ya dawo dani daga tunanin dana tafi. Firgigit na ɗago na kalli ƙofar. Muryar Umma Safiya ce ta ratsa kunnuwana, ƙanwa ce a wajen mahaifiyar mu, cikin faɗa take faɗin "Wai Rahamah kin raina mutane ne, tun ɗazu ke ake jira fa, ke komai naki sai kin sa shashanci a ciki." Ai da sauri na ɗaga botikin ruwan, na juye a kaina dama na gama wankan tuni. Ɗaura zani nayi na zura ƙaramin hijabana, na Turo ƙofar na fito. Yadda na tarda su tsatstsaye a bakin ƙofar, kamar irin masu jiran wani sarki ko me muƙamin nan, sai da abin ya so bani dariya dan dai kawai bana cikin yanayin da zan yi dariyar ne. Yadda naga kowacce na jefo min harara, yasa ban tsaya ba cikin sauri na sunkuyar da kaina, na ratsa tsakiyar su na wuce na nufi ɗakin mu. Mutanen dake tsakar gidan na ganina, suka fara min kirari irin na amare, musamman abokan wasa. Da sauri na faɗa ɗakin Mama Hajara, dan dama anan nake gudanar da komai na, sakamon irin haɗin kan da iyayenmu suke da shi, sam basa irin kishinnan na jahilci, suna mutumta juna sosai, haka muma yaran baki ɗayanmu kanmu a haɗe ya ke. In ba'a faɗa maka ba, ba zaka iya banbance ƴan ɗaki ɗaya ba, saboda kusan duk kamannin Abbanmu muka ɗauka. Shi yasa tun da aurena ya taho, ban wani bawa kaina wahalar zuwa wani waje daban ba, a cikin gidanmu na gudanar da komai na, dama walima ce kaɗai na yi tun jiya, bayannan banyi komai ba. Bakin gado na tarda Mama Hajara, ganin shigowata yasa ta kalle ni, cikin sanyin Muryar ta wadda a haka halittar ta take tace "Yanzu ke dama baki yi wankan ba sai yanzu Rahamah? Me yasa ke komai bakya ɗaukar shi da muhimmanci ne?." Bance komai ba, na wuce wajen akwatin kayana, zuciyata cikin wani irin yanayi me nauyi, gani nake kawai kowa ya gaji da ni ne, gaba ɗaya sai faɗa suke min akan na shirya na shirya sai kace basa sona dama. Ita ma Mama Hajara tun maganar ta ta farko, da taga nayi shiru bance komai ba, tasan ba magana zan yi ba kenan. Shi yasa bata ƙara cewa komai ba, ta tashi ta fita daga ɗakin. Aunty Jamila da Aunty Zulai ne suka shigo, nan suka tsaya a kaina har sai da na shirya, cikin lafiyayyiyar atamfar Vlisco me laushi, wadda aka wa lafiyayyen ɗinkin riga da zani, kayan sun zauna kamar a jikina aka ɗinka su. Aunty Jamila da kanta ta amshi ɗan kwalin, ta ɗaura min shi irin ɗaurin simple ɗin nan bai cika hayaniya ba. Daga nan suka ɗauko lafiyayyun turaruka, bayan sun gama feshe ni sun bani na shafawa dana gogawa duk ko ina ya ɗauki ƙamshi. Suka ɗauko babban mayafina, wanda ya dace da kalar kayan, suka lullu'ba min shi. Aunty Zulai ta kama hannuna, ta jani zuwa tsakar gidan Aunty Jamila na bin mu a baya tana sakin guɗa. Gaba ɗaya hankalin mutanen dake tsakar gidan ya dawo kanmu, aka min caaa ana hayaniya irin ta gidan biki. Kaina sunkuye ya ke, ta cikin mayafin nake kallon kyawawan ƙafafuna waɗanda suka sha zanen jan lalle, a hankali nake taka tsakar gidan mu dasu. Zuciyata cike da wata irin fargaba, ji nake duk taku ɗaya in na ƙara, tamkar ina sake nesantar ƴan uwana ne. Kai tsaye ɗakin Ammimu suka nufa dani, cikin hayaniyar mutanen dake binmu a baya, muka sa ƙafa a ɗan madaidaicin farlon Amminmu wanda ke cike da baƙin ƴan biki. Zuciyata na wata Iriyar rawa lokacin da Aunty Zulai ta zaunar dani a tsakiyar mutanen, Amminmu na gefe a zaune cikin shigar atamfa riga da zani, irin shiga dai da iyayen amarya ke yi tamu ta gargajiya. Da ɗai-ɗai suka shiga min nasiha akan haƙuri da zaman aure, da biyayya da ga mijina da yadda zan rungumi kowa nashi tamkar dangina. Kar na sake na nuna banbanci ko wani abu da zai sosa masa rai, ga ƴan uwan shi ko wani wanda ya raɓe shi. Sosai aka min nasiha, har ban san lokacin da wani k'akk'arfan kuka ya ƙwace min ba. So nake Naji Ummanmu ta tofa albarkacin bakin ta, amma sai na ji tace wadda suka min ma ta isa, in sha Allahu tana fatan na ɗauka na kuma yi amfani da ita. Ita bata da abin cewa, fatan ta Allah ya bamu zaman lafiya, ya kaɗe fitina, ya bamu zuri'a ɗayyaba, ya bani ikon yiwa mijina biyayya. Dai-dai lokacin da suke shirin tashi tsaye dani mu fita naji hayaniyar angwaye, ga kuma an turo wai Abbanmu ya dawo yana farlon sa yana jiran mu. Ai ina ganin mun miƙe, na fusge a guje nayi kan Ammimu, na faɗa jikinta tare da fashewa da wani irin kuka mai taɓa zuciya. Ita ma rungume ni tayi kawai, ta kasa magana sai ɗan bubbuga bayana da take a hankali. Gaba ɗaya sai muka bawa Kowa dake ɗakin tausayi. Kowa sai jikin sa ya yi sanyi, haƙiƙa rabuwa da iyaye ba abune me sauƙi ba, musamman mahaifiya, babu wanda zai san hakan sai wadda suka shaƙu matuƙa da mahaifiyar ta. Irin shaƙuwar da muka yi da Amminmu, kai ko da baki shaƙu da mahaifiyar ki ba, rabuwa ba wasa bace. Wata irin shaƙuwa ce me matuƙar shiga rai tsakanina da Amminah, duk wanda ya ganni ni da Amminah, sai mun bashi sha'awa saboda yadda bata iya ɓoye soyayyar ta gare ni, haka nima bana iya ɓoye tata soyayyar. Ba alfahari ba duk gidanmu suna ji dani, daga kan mazan har matan kowa ya samu abu sai dai ka ji yace Rahamah. Allah ya min baiwa ta saurin shiga rai. Ban sani ba kodan ni ɗin banda damuwa da komai, ban raina kowa cikin yayuna ba kamar yadda ya ke tarbiyyar gidan mu, haka duk abinda na samu to ba zai rufe min ido har na hana ɗan uwana ba, ƴaƴan yayuna kullum cikin hidimta musu nake. Ina zaman lafiya sosai da kowa, shi yasa aurena ya zama daban a cikin gidanmu, duk da ba'a kaina aka fara auren nesa ba, dan Aunty Fatin mu ita ma Lagos ɗin take aure, a dalilin zuwa ziyara wajen tane ma Allah ya haɗa ni da mijin da ya aure ni me suna Al'amen. Kuma unguwar mu da tasu babu wani nisa, dan haka kowa kewa Aunty Fati murnar ta samu ƴar uwa kusa tunda da ita kaɗai ce. Ganin kukan nawa ba mai ƙarewa bane, gashi har angwayen sun nemi izinin shigowa. Hakan yasa Aunty Zulai dake share hawayen tausayi, tsugunnawa kusa dani a hankali cikin lallashi ta ɗago ni, ta shiga bani haƙuri tare da cewa Amminmu "Ku yi haƙuri Ammih, zamu tafi addu'ar ku kawai mu ke buƙata." Da ya ke ita ma Ammih take kiran Amminmu. Ita kanta Amminmu dauriya kawai take, a hankali tasa hannu ta share hawayen da ya ciko idanun ta. Ta jinjina kai tare da zare hannunta cikin nawa, ina ƙoƙarin ƙara kamata Aunty Jamila ta ƙaraso ta kama ni, Ina kuka ina komai suka fito dani daga ɗakin Ammin, suka nufi ɗakin Mama Hajara dani. Kamar yadda aka kaini wajen Amminmu, haka aka kaini farlon Mama Hajara. Cikin sanyin ta ta shiga min nasiha me ratsa zuciya, daga ƙarshe muka rungume juna ita harda kukan ta, dan ita macace da kuka baya mata wahala, gata da kirki da mutumci bata taɓa nuna mana banbanci tsakanin mu da ƴaƴan ta ba. Cikin kukan suka kama ni, muka nufi farlon Abbanmu dake hanyar zaure, kamar yadda kuka sani ana yi in an fito da amarya, bayan mu zugar yara ce ƴan biki, har ma da wasu daga cikin manyan, sai da zamu shiga aka dakatar da su. A hankali na zauna kusa da ƙafar Abbanmu dake kan kujera, idanuna kan lallausan carpet ɗin dake malale a tsakiyar farlon, Allah shi kaɗai yasan me ke zuciyata. Sai yau nake tambayar kaina, ashe dama haka ake ji in za'a rabu da iyaye? Ba zan manta ba lokacin da za'a kai Aunty Fati Lagos, har da Ni a masu mata tsiya ganin irin kukan da take, duk da nima nasha kukan dana ga za'a tafi da ita ɗin da gaske. Amma da farko kallon wasa nawa abin, ashe ita tasan me taji. A hankali naji sallamar Yayuna suna shigowa, da ɗai-ɗai da ɗai-ɗai. Dukanmu yaran gidan, manya da yara mun hallara. Sunana da Abbanmu ya kira, shi yasa na ɗan daidaita muryata, cikin sanyin da dashewar da ta yi na amsa da "Na'am Abba." A hankali ya yi gyaran murya yace " To Rahamah yau cikin hukuncin Ubangiji an ɗaura auren ki. Alhamdulillahi ina godiya ga Allah daya nuna min ranar dana aurar dake lafiya, duk da ba a kanki na fara aurar da ƴaƴana ba. Amma ina jin farin ciki bisa ga rabuwar da zamu yi lafiya cikin aminci!. Haƙiƙa bana jin ki Rahamah, ina miki Kyakykyawan zato bisa ga tarbiyyar da muka baki, da kuma kyawawan halayen ki da kowa ya san ki dasu. Ina fatan zaki ƙara akan yadda na sanki, ki linka haƙurin ki ya fi nada, nutsuwar dana sanki da ita ki linka ta, ladabin ki da biyayyar ki da rashin ɗaukar komai ba komai ba, duk ina fatan zaki linka su sufi nada. Saboda wannan zaman da zaki je, ba kamar zaman da ki ke a gidannan bane, zama ne na ibada, wanda baya yiwuwa sai da haƙuri da ladabi da biyayya." Ya ɗan sauke ajiyar zuciya, ya cigaba da magana "Rahamah a matsayina na mahaifin ki, ina umartar ki da kiwa mijin ki biyayya, matuƙar hakan bai saɓawa Addini ba, ki mutumta shi ki girmama shi, ki sani aljannar ki na ƙarƙashin ƙafar sa, sai kin kyautata masa kin masa biyayya sannan zaki samu aljanna. Kada ki kasance me jayayya da shi, ko yawan ƙorafi da mita, ki zama me ɗauke kai akan komai ki maida komai ba komai ba. Kar ki zama me ɗaga murya gare shi, Allah baya son hakan, duk matar da ke ɗaga murya sama data mijin ta, hakan babban zunubi ne Rahamah. Ki zauna lafiya da shi, dan ace shima mutumin kirki ne, bashi da matsala da kowa kowa ya shaida shi, dan Allah karki bari na ji matsala ta fito daga ɓangaren ki. Ina roƙon Allah ya baku zaman lafiya, ya kauda shaiɗan a tsakanin ku, ya baku zuri'a ɗayyaba me albarka." Yasa hannu ya dafa kaina, ya jima yana min addu'o'i Sannan ya ɗauke hannun sa. Sosai nake kuka harda shashsheka, babu wanda ya hana ni yi, sai ma wasu daga cikin su dake share hawaye. Haka Yayan Abbanmu shima ya shiga ta shi nasihar, a ƙarshe ya kira sunan Aunty Fatin mu yace ta matso kusa. Tasowa ta yi ta ƙaraso kusa dani kamar yadda ya umarce ta, da kanshi ya taso ya kama hannuna ina kuka ina komai, ya kama hannun Aunty Fati ya haɗa. Nan ya shiga mana nasiha tare, akan mu riƙe junanmu, mu zauna lafiya da junanmu in girmama ta, in ɗauke ta tamkar uwa gare ni. Duk wata damuwa ko shawara da zan nema, kar na sake na tunkari wata ko wani, na nemi Ƴar uwata na faɗa mata, zata bani shawara. Har ya min misali da ita akan shekarar ta goma sha a gidan miji, amma mijin ta bai taɓa kawo ƙarar ta ba, haka ita ma bata taɓa kawo ƙarar sa ba, yana alfahari da Aunty Fati duk cikin ƴaƴan gidanmu ta fita zakkah tanan. Nima yana so nayi koyi da ita, na zama mace ta gari ga mijina. A ƙarshe ita ma yace amana ta na hannun ta, ta riƙe ni tamkar ƴar data haifa, ta nuna min kuskurena in nayi, in wani abu ya taso ta tsaya min tamkar yadda su zasu tsaya min in suna kusa dani. Ƙarshe aka rufe da nasiha akan zumunci, aka yi addu'a a gurguje sakamakon cewar da aka yi angwaye sun fara shigowa. Haka kowa ya tashi jiki a sanyaye, saboda yadda hayaniyar tayi yawa, sai ta ƙofar baya suka bi dani muka koma ɗakin mu na ƴammata. Nan na tarda ƙawaye na zazzaune, mutum biyu ne kaɗai zasu bini a cikin su. Amira sai Binta. Binta ita ce babbar ƙawata kuma Aminiyata tun yarinta, mun yi wata Iriyar shaƙuwa da ita wadda har ta kai watarana tana kwana gidanmu, kasancewar ita Allah yawa Mahaifiyar ta rasuwa, a hannun matar yayanta take da zama. Ba wani wahala take sha ba, aiki ne kawai take mata. Ganina duk sai suka miƙe tsaye cikin hayaniya irin ta ƙawaye, Aunty Zulai da basu san tana bayana ba, tana shigowa ɗakin ya yi tsit kowacce ta fara magana ƙasa-ƙasa. Sun riga da sun san halin ta, bata son raini da shirme kwata kwata bata shiri da Binta ƙawata. Dan in da son ranta ne, ba zan yi abota da Binta ba, a cewar ta yarinyar bata da tarbiyya ta cika rawar kai da feleƙe da iyayin tsiya. Basu gama tunani ba kuwa, aikwa ta daka musu tsawa tace "Duk ku fice ku bamu guri Muna son magana." Sum-sum suka fara fita, a raina banji daɗin yadda ta musu ɗin ba, amma banda yadda zan da Aunty Zulai na rasa wacce irin mutum ce ita, akwai zafi kamar mahaifin ta Baba Usman haka take. Aunty Khairat ce ta shigo, hannun ta riƙe da tukunyar kazar amaryar da aka dafa min. Wadda ta ji kayan magunguna, tun jiya ake bin kaina akan na zauna naci naƙi zama. Saboda bana son ko ganin ta nayi, dan wani irin duhu da naman ya yi daga ido ma nasan ba daɗi zai yi ba. Sai gashi an binciko shi an kawo min, Ni kam na ga ta kaina. Haka suka sani gaba, ina kuka ina komai sai da na ci kazar nan, kamar zan yi amai saboda baurin ta, amma zare idon da Aunty Zulai take bisa dole nake haɗiyewa. Wajen shan romon ne da nace ina, banzan iya ba suna ƙoƙarin tilasta ni, Aunty Jamila da Aunty Fati da Umma Safiya suka shigo, kowacce a shirye take tsaf cikin lullu'bin ta. Haka suka kama hannuna suka ce mu kaɗai ake jira, dan tuni angwaye sun daɗe a mota. Ai ba sai kukana ya dawo sabo ba, babu wanda ya saurare ni, duk irin yadda nake rusga kukan. Ganin zasu fita dani baki ɗaya yasa nace "Zan yi fitsari." Wai ko zasu ɗan sake ni, nawa gidan namu kallon bankwana. Amma babu wanda ya kula Ni, muka yi waje baki ɗaya. Kowa na bin mu da fatan alkhairi, tare da addu'o'i kala-kala. Aunty Zulai da Umma Safiya sune suka sani a tsakiya, sai ƙawata Binta data zauna a gaban mota kusa da direba. Sauran kuma suka shiga sauran motocin. Nan muka ɗauki hanyar barin lungun gidanmu, ina kuka irin na bankwana, da rabuwa da dangi da abokan arziƙi. *_🥰MAMAN DA ƊAN ALBARKA CE 🥰✍️✍️_* [1/18, 07:15] Ummu Sultan Ceh3: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/EJJOOxsRu8dKh9gocmSFuG *BAƘAR ZYCIYA!.* *_🥰MAMAN ƊAN ALBARKA CE 🥰✍️✍️_* *_LITTAFIN KOWA YAƘI JI, YA KAMMALA COMPLET. GA DUK ME BUƘATA TA MIN MAGANA TA WANNAN NUMBER 09014644247_* *PAGE2️⃣* Tunda motar mu ta ɗauki hanya, bamu tsaya ba sai a garin Mina sakamakon lokacin sallah da ya yi. Bayan munyi sallah muka ci abinci a wani haɗaɗɗen Hotel, duk yadda naso noƙewa bisa dole na sake naci abincin, dan bana mantawa rabona da abinci tun daren jiya bayan dawowar mu daga walima. Yanzu na ji nayi kamar zan faɗi, da ya ke su ma sun zo da mata ƴan daukar amarya su biyu. Ɗayar wadda tafi kama da Al'amen ce ta lura dani, ta matso kujerar da muke kai tawa Aunty Zulai maganar a sa naci wani abu, Shi yasa har na iya ci ɗin. Ban san Al'amen a ido na ba tun bayan ɗaurin auren, sai da muka zo komawa mota zamu cigaba da tafiya. Daidai lokacin da Aunty Zulai ta kama hannuna ta buɗe motar, ɗagowar da nayi idanuna ya faɗa nashi. Sanye ya ke ciki shadda sky blue, sai hular da ya sa wadda tayi daidai da kalar kayan. Muna haɗa ido ya washe min baki, tare da ɗage min gira harda wani kashe min ido. Da sauri na kauda kaina, zuciyata cikin wani irin Yanayi, madadin ya burgeni sai naji kamar raina na son ɓaci. Bayan mun zauna Aunty Zulai ta rufe motar, sai na runtse idanuna a hankali, ina tariyo yadda Al'amen ya ke min a duk lokacin da muka haɗa ido. Shi yana yi ne dan ya burge ni, Ni kuma bai fahimci hakan ɓata min rai ya ke ba. Shi tashi salon soyayyar kenan?na tambayi kaina. A zuciyata na bawa kaina da kaina amsa, Eh haka ya iya, tunda tun haɗuwar mu ban taɓa ganin sabon abu daga gare shi ba, bayan ina son ki Rahamah, zan aure ki zaki zauna dani Rahamah? Sai kuma in mun haɗa ido ya kashe min ido, ko ya washe min baki, ko kuma ya ɗage min gira irin ta ƴan duniyar nan. Badan ya samu kyakkyawar shaida daga bakunan mutane ba, sannan bai taɓa furta min wata kalma mara kyau ba tun haɗuwar mu, tabbas da na sashi a wani bigire na daban. Daga wani ɓangare na zuciyata yace _Ki masa uzuri, in kika duba shi ba yaro bane, wataƙil yawan shekarun sa zai sa ya yi tunanin haka shike burge ku ƴammatan zamani._ Ji nayi nayi na'am da wannan batu na zuciyata, a hankali na maida kaina na jingina da jikin kujerar motar, na faɗa duniyar tunani. Sai na fara wassafa kamannin Al'amen. Al'amen Muhammad kenan, kuma mijina. A ƙalla zai iya kaiwa shekaru arba'in da takwas zuwa da tara, Kakkaura ne yana da tsayi da jiki, dan harda wani uban tumbi a gaban sa, wanda har yau nake yawan tambayar kaina dama zan iya auren miji mai tumbi? Banda amsar tambayar, tunda gashi har na aure shi za'a kaini gidan sa. Sai dai a sanina tun tasowa ta, bana shiri da mutum mai tumbi kwata kwata namiji mai tumbi ko mai ƙiba baya taɓa burgeni, sai gashi cikin hukuncin Ubangiji yau Ni Rahamah na auri namiji mai ƙiba har ma da tumbi. Lamarin Allah kenan, babu yadda baya juya lamarin sa. Al'amen Muhammad ba wani Kyakykyawa bane, babu laifi yana da ɗan kyansa dai-dai yadda ba za'a sashi a layin munana ba, fuskar shi nada faɗi da tsayi, yana da hancin shi tubarkallah Masha Allah ɗan madaidaici, kasan hancin ɗauke ya ke da bakin mai faɗi da kaurin la'bɓa, yana da saje da gemun sa wanda bai cika yawa ba, sai furfura kaɗan kaɗan data fara fitowa. Yana da ɗan hasken fata, ba za'a sashi a layin farare ba, haka ba za'a sa shi a layin baƙaƙen ba. Duka da haɗuwa ta dashi da auren mu, bai fi sati Uku ba. A sati na huɗun ne aka ɗaura auren mu dashi. Bana manta farkon haɗuwar mu dashi, na kai ziyara wajen Aunty Fati Yayata daga Kaduna, zuwa wajen ta Lagos. Ranar ta aike ni kasuwa na amso mata saƙo wajen Abban Mubarak, mijin ta kenan. Bayan na dawo ne, dai-dai lokacin da mashin ya sauke ni a bakin get, ina ƙoƙarin ƙwank'wasa ƙofar dan a buɗe min. Shi kuma Al'amen ya sawo kan motar shi, da niyar shiga nasu gidan. Ganina yasa ya dakata, ya buɗe motar ya fito ya nufo inda nake. Dai-dai lokacin har an buɗe min ƙofar ina shirin shiga, jin anmin magana ana faɗin "Ƴammata. Hakan yasa na juyo, nayi tozali dashi cikin shigar farar shadda irin ɗin kin babbar rigar nan, daga kallon farko naji sam bai min ba, in ba ƙarya idanuna suka min ba, zai iya haifar kamata, saboda duka na banfi shekara ashirin ba. Cikin raina nake faɗin _Shi kuma wannan bai duba shekarun sa ba, ya ke wani kirana da ƴammatan._ ina mai Allah wadai da hali irin na wasu mazan, nayi shigewata na ƙyale shi. Ina jin yana magana da Sani me gadin su Aunty Fati, bansan ya suka ƙare ba na shiga farlon Aunty Fati ina mita. Aunty Fati dake gyaran farce, ta ɗago ta kalle ni tace "Ke kuma dawa kike faɗa haka?." Tsaki naja na shiga ƙoƙarin aje ledar hannuna, ina faɗin "Wani tsoho ne ya biyo ni, kai duk farin gashi amma tsabar son zuciya, shine harda wani ce min ƴammata, bayan nasan a haife ya haifi kamata." Dariya Aunty Fati tayi tace "Kar kiga laifin sa, yaga ƴar duma-duma ne shi yasa, ki ka sani ko shine mijin, tunda anyi anyi dake ki fito da miji kin ƙi." Haushi naji, cikin ɗan ɓata rai nace "Allah ya kiyaye ke kin ganshi, har da wani uban tumbin fa." Cigaba tayi da jana da wasa, har sai da nayi fushi taga raina ya ɓaci, ina shirin sakar mata kuka sannan ta ƙyale ni. Kamar da wasa da dare, sai ga Sani me gadi ya zo ƙofar farlon Aunty Fati, wai ana sallama da Rahamah. Cikin mamakin wake sallama na kalli Aunty Fati, sai naga tayi murmushi ta kalli malam Sani tace "Wake kiran ta?." Washe baki ya yi yana wani irin sosa kai yace "Hajiya ai ba wani ke kiran ta ba, sai Jagaba." Da sauri naga Aunty Fati ta zabura, ta kalle shi da sauri tace "Ka je kace gata nan zuwa." Ganin ya juya ya tafi, na kalle ta ina ɓata rai nace "Me yasa kika ce ina zuwa?." "Dallah tashi ki je, ke kinsan waye Jagaba kuwa?." Ba tare da damuwar komai ba nace "Ban sani ba, waye shi kuma a ina ya ke?." "Dallah ta shi ki je, in kin dawo zan miki bayani, fatana Allah ya tabbatar mana da alkhairin sa." Duk yadda naso na kaucewa zuwan, bisa dole Aunty Fati ta tilasta min fitar, haka nasa Hijabina cikin k'uncin na fita. Koda na fita bakin get na tarda mota, ganin banga kowa ba yasa na juya dan komawa ciki. Gani nayi an buɗe ƙofar motar an fito, cikin mamaki nake kallon mutumin. Wannan dai na ɗazun nan ne daya tsaida ni. Ji nayi raina ya ɓaci, na daure na amsa sallamar shi, ganin har ya ƙaraso wajena. Cewa ya yi na shiga motar muyi magana, nace masa bana shiga motar mutane, ya faɗi komai zai faɗa anan. Haka ya shiga min bayanin kansa, shi ɗane ga maƙocin su Aunty, ya ganni ya ga na masa a matsayin matar aure da sauran duk bayanai dai. Jin shi kawai nake, sai dai abinda ya girgiza ni jin cewa da ya yi bai taɓa aure ba, cikin mamaki nake kallon shi, sam na kasa yarda ace mutum kamar wannan wai bai taɓa aure ba. Shima dariya ya yi ganin ina kallon shi, ya gyara tsayuwar shi yace "Zan faɗa miki dalili amma sai nan gaba, nasan kin shiga kokonto yanzu ko?." Danne mamaki na nayi nace "A'a" dan Allah-Allah nake na tafi, yoh Ni ina ma zan bari mu ƙara haɗuwa, da har zai wani ce zai min bayani. Haka ya ƙaraci surutun shi, da nagaji nace zan shiga gida. Yace Sai na faɗa masa ya min ko kuwa? Dan Allah in faɗa. Ganin yana shirin ɓata min lokaci, gashi tsaiwar duk ta gundure ni, sai kawai nace masa "Eh" dan ya ƙyale ni. Koda na juya zan tafi, haka ya zaro kuɗi, damin ƴan dubu guda, wato dubu ɗari kenan, ya miƙo min wai na amsa. Zagaye shi nayi na tafi abina, ko juyowa banyi ba duk irin kiran da ya ke min, a zuciyata ina cewa _Haka kawai ya wani bani kuɗi, ko ance masa kuɗi nake so._ Koda na koma cikin farin ciki, Aunty Fati ta shiga bani labari akan shi. Wai ɗan maƙocin su ne, mahaifin sa mai kuɗi ne, yana da mata huɗu ɗaya ce kawai bahaushiya sauran duk yarabawa ne. Mahaifiyar Al'amen ita ce babba, shine ɗan ta na biyu. Suna da arziƙi sosai dan shi Al'amen ma ana zaton ya gado mahaifin sa ne a dukiya, dan duk yafi sauran kuɗi waye-waye, duk dai ta dinga koɗa shi. Harda cewa yana da kirki, ga kyauta kowacce rana cikin rabawa mabuƙata kuɗi da abinci ya ke, yana da mu'amala me kyau tsakanin sa da mutane. Kowa na yaba kyawawan halayen sa, aure ne dai bai yi ba har yanzu, sakamakon duk yarinyar da ya nema sai an ci kuɗin sa, daga baya a hana shi auren ta. Ya daɗe yana neman matar aure, har addu'a ake masa a masallatan unguwar akan Allah ya bashi mace ta gari, saboda yadda ya ke kai taimako makarantu da masallatai. Duk maganganun ta, iya inda tace yana taimakon Mabuƙata ne kawai ya burgeni, har ma na ɗan ji tausayin sa akan rashin auren da aka ce ba'a bashi. Tashi nayi na nufi ɗakin dake farlon, wanda anan na sauka nace "Allah ya bashi mace ta gari Aunty." Sallamar Sani me gadi dana ji yana faɗin "Ga saƙo ance a bawa Rahamah, ita ta dakatar dani daga shiga ɗakin. Na juya na kalli Aunty Fati wadda idanun ta ke kallon ƙofar farlon. Kuɗin dai dana ƙi amsa, shine ya bawa sani ya biyo ni da shi. Ita kanta Aunty Fati na fahimci bata so ya aiko kuɗin ba, dan haka na cewa Malam Sani ya maida yace an gode. Kafin ma ya dawo na rufe ƙofar farlon, dan bana son damuwa, dama mijin Aunty Fati baya gari, yaranta kuma sun je gidan ƙanin mijinta hutu. Washe gari sai ga shi ya zo, ƙiri-ƙiri naƙi fita. Aunty Fati ganin bana son lamari, dole ta haƙura da tilasta min ɗin da take akan fitar. Kwana biyu tsakani na shirya na koma Kaduna gida, dan dama sati biyu nayi niyar yi mata kuma nayi. Komawata gida da sati ɗaya, wata ranar juma'a ina zaune ina wa Mama Hajara tsifa, naga ana kirana da baƙuwar number. Ina ɗagawa na gane Muryar me maganar, dan yana da irin saurin maganar nan. Mutumin dai da na baro a Lagos ne, sai da nayi dana sanin ɗaga kiran. Wallahi dana san shine ba zan ɗauka ba. Ce min ya yi zai shigo Kaduna satin nan, yana son zuwa Kano sarin wasu kaya, in na bashi dama zai zo ya ganni ya gaida su Abbannmu. Kai tsaye nace bana so, ya riƙe gaisuwar shi Nagode sosai. Mama Hajara da taji abinda nace ne, bayan na yanke wayar. Ta shiga tambayata waye ya kira yace zai zo nace Ban yarda ba? Dan sun san halina na ƙin kula samari duk da na wuce ace ina hakan. Ƙarya ba halina bace, dan haka na bata labarin komai. Cikin sanyin ta tace "Ki bari ya zo ku gaisa mana, gaisuwa ai ba komai bace Rahamah. Me son ka shi ne kaɗai zai damu da kai, har ya so ganin ka haka." Bamu gama magana ba, sai ga wani kiran nashi ya shigo. Bisa dole na ɗauki kiran, maganar ce dai ta zai zo wai akwai wani kaya da ya ke so ya siya a Kano, in yana zuwa zai sauka a Kaduna mu gaisa sai ya wuce, da dai sauran surutun sa. Gudun Mama Hajara ta yi fushi nace Allah ya kawo shi lafiya. Wallahi na manta da munyi magana da shi, bayan kwana biyu sai ga kira a wayata wai in faɗa masa sunan unguwar mu, gashi yana cikin garin Kaduna. Kuma in sanarwa da su Abba zai zo ya gaida su, sosai na kaɗu da jin batun sa. Taya zan cewa su Abba zan yi baƙi zasu gaida shi, bayan ƙa'idar gidan mu yarinya bata tsayawa sa saurayi sai da izinin mahaifanmu. Kuma Ni ba son shi nake ba, bare nace wai ko zai zo ne saboda ni ɗin. Dan haka sai nace masa, ba sai ya gaida su Abba ba ni zan fito mu gaisa, duk da nasan hakan laifi ne a gidan mu . Amma a ganina gwara hakan, in yaso faɗa kawai za'a min Shikenan an wuce wajen. Cewa ya yi shikenan, na kwatanta masa unguwar tamu kawai. Haka na faɗa masa sunan, na shirya na nufi gidan Aunty Baraka matar Yayan ƙawata Binta, dan akwai wata walima da zamu je da yamma, ina son na kai mata Hijabina ta goge min tunda mu wutar gidanmu ta samu matsala. Kwata-kwata na manta da wani batun Al'amen tun da naje na samu fira,wayata ma na cikin jakata kuma na sata a silent, munfi awa biyu muna shan firar mu da ita, ita ta rako ni har wajen ƙofar gidan mu sannan ta koma, ina ce mata in na shirya zan kirata a waya. Sai da na na zo shiga gida, ganin baƙin motoci ya tuna min da maganar Al'amen. Hannu nasa na ɗan dafe kaina ina faɗin "Kash nama manta da mutumin nan." Nasa hannu a jakata tare da ciro wayata, ganin miss call nayi rututu sun fi ashirin, kuma duk shi ya kira ni. Tsaki naja na tura k'yauren gidan mu na shiga, tun daga bakin zauren na fahimci gidan namu akwai baƙi. Dan ƙofar farlon Abbanmu takalma ne na maza da yawa. Zagayawa nayi ta bayan ɗakin Abban dan shiga ainahin cikin gidan, dan bana son wucewa ta gaban farlon dan sai an ganni. Ganin mutanen gidanmu nayi kusan baki ɗaya a farlon Mama Hajara, cikin mamaki naga gaba ɗaya ni suke kallo. Na cire hijabina na zauna kusa da Aminatu ƙanwata, ina faɗin "Lafiya naga duk kun taru anan?." Ummi ce tayi caraf tace "Ba dole ki ganmu anan zaune ba, tunda kin bamu mamaki Aunty Rahamah, Ashe dai tuni ke kin yi miji abinki na nunawa Sa'a." Da sauri Mama Hajara ta kai hannu ta doke bakin ta, cikin zare mata ido tace "An tambaye ki rasai? Dan ƙaniyar ki tashi ki bawa mutane waje." Sum-sum ta tashi hannun ta dafe da bakinta, ta fita daga farlon. Kaina ne ya ɗaure baki ɗaya, dan haka na kasa daurewa na kalli Mama Hajara da ke magana da Ummanmu ƙasa-ƙasa nace "Wai Mama ban gane ba, baƙi muka yi a gidan ne yau?." Yakubu ne da ya sawo kai ɗakin, ya bani amsa "Ki ji yarinyar nan da rainin hankali, tambaya ki ke baƙi aka yi bayan ke kika turo su?." Amminmu ce tace "Barta ina ga yanzun ma raina mana hankali za ta yi." Gaba ɗaya sun ɗaure min kai da maganganun su. Sai daga baya nake ji wai ashe Al'amen ne ya zo harda wasu manyan mutane, wai Ni na turo su sun zo da shirin komai harda sadaki ya shirya aure na. Mun riga da mun yi magana da shi tuni. Sosai na kaɗu da jin batun, na rasa me zance musu sai kuka dana fashe da shi, ina rantsuwar wallahi bani na turo shi ba, cewa ya yi kawai zamu gaisa nace ya zo. Duk irin yadda na so su fahimce ni, sun ƙi fahimta ta. Bayan tafiyar su Al'amen ɗin ne Abba da Baba Usman suka kira ni suma. Nasha faɗa sosai kafin ma su faɗa min Maƙasudin kiran nawa, nan suka maimaita min abinda su Ammi suka ce min, na Al'amen ya ce mun gama magana tuni. Ni na bashi izinin ya zo ya nemi aurena, in da Baba Usman ya hau faɗa a ina aka taɓa haka, kai tsaye a zo neman aure. Amma tunda Ni na turo shi da kaina, su sun ce ya basu kwana biyu za su yi bincike akan shi, tunda abin ya zo da sauƙi ance maƙocin su Aunty Fati ne. In yaso sai su bashi auren nawa, tunda dama sunyi-sunyi dani akan na fito da miji naƙi ina musu yawo da hankali. Na fuskanci abin ya ɓata ran Abbanmu sosai, na zuwan Al'amen kai tsaye. Hankalina ya matuƙar tashi da wannan batun, Allah ya sani ban sa a raina zan yi aure kusa ba, ga kuma wannan mutumin me tulelen ciki da ya zo ya haɗa Ni da iyayena. Kwana nayi kuka zuciyata cike da k'uncin, wayar Aunty Fati ce ta tashe ni daga barci. Cikin magagin barci na ɗaga. Nan ta hauni da faɗa akan na munafunce ta ashe ina son Al'amen har mun gama shirya komai, gashi har ya zo Kaduna neman aurena, shine ko na faɗa mata tsabar gulma na nuna bana son shi. Su Abba ne suka kira ta da mijin ta jiya da dare, suka ce a musu bincike akan halayen Al'amen da yadda ya ke gudanar da mu'amalar sa da jama'a, da duk wani bincike da ya kamata ayi kafin a bada aure. Sosai maganar ta bugeni, ya tabbata dai mutumin nan ya ɗaure ni da jijiyoyin jikina, ta ko'ina ya gama sawa sun yarda Ni na tura shi neman aurena. Duk yadda naso nawa Aunty Fati bayani, ƙin yarda ta yi da batuna. Ga shi shegen duk kiran da nake masa yaƙi ɗauka kwata-kwata, ina son tambayar shi yaushe muka yi haka da shi ne kawai, sannan na roƙe shi ya janye maganar aurena ni bana son shi. Sai da aka shafe kwana uku a gidan mu, ina ƙoƙarin wajen ganin na fahimtar da su bani na turo shi ba. Amma kowa cewa ya ke na sani, tunda Aunty Fati ta bada shaidar na san shi, kuma ita bata san yadda aka muka shirya junan mu ba. Ganin na tashi hankalina, yasa Baba Usman cewa in har da gaske bana son shi, kuma bani na turo shi ba, to na fito da wanda na ke so kafin su gama bincike akan shi. Su kuma zasu fasa bashi ni, dan sun gaji Da yadda nake musu wasa da hankali akan fito da miji, gashi har Ummi da Aminatu sun kusa taddo ni ban fito da miji ba. Hankalina ya tashi, saboda ban da wani tsayayyen saurayi, ba kuma dan banda samarin bane. Ina da masu sona sosai, amma ban bawa Kowa damar zuwa gidan mu ba, saboda nasan in har aka bawa mutum izinin zuwa zance wajen mace, to fa in aka yi bincike aka tabbatar dana kirki ne, ƙa'idar gidanmu ba bu ke babu tsayawa da wani muddin shi wannan ya shirya auren ki. Ina ji ina gani aka ce an gama bincike akan Al'amen, an kuma tabbatar mutumin kirki ne zai riƙe ni amana. Cikin binciken harda wasu kyawawan halayen daban waɗanda Aunty Fati bata faɗa min su ba. Ni dai ina jin yadda ƴan gidanmu ke koɗa mutumcin Al'amen ɗin, harda masu cewa zai riƙe ni amana, tunda bai taɓa aure ba dama da dai sauran su. Ina ji ina gani, aka tsaida ranar auren mu sati biyu, kamar yadda ya buƙata. Har mamaki na dinga yi sai kace wanda ya asirce iyayena da dangina, dan kowa ya bon shi ya ke babu wanda na ji yace ya min tsufa ko duba lamarina, akan cewar da nayi bana son shi. Bisa dole na rungumi hakan a matsayin biyayya ga iyayena, tunda banda hanyar bijirewa auren tunda har sun amshi sadaki, dan dangin sa dake Lagos su suka zo neman aurena. Ina jin yadda ake yaba karamcin su da mutumcin su. Haka aka shiga shirye-shiryen aurena, sai da auren ya rage sati ɗaya Sannan Al'amen ya bari muka haɗu. Na shirya in na ganshi sai na ci masa mutumci. Sai dai abin mamaki muna haɗa ido na nemi kowacce kalma a bakina na rasa, Wallahi ban iya masa ko tari ba da sunan rashin kunya. Sai dai ina jin wani zafi a ƙasan raina, ina jin kamar tsaiwar da nayi wajen shi ma tilasta ni aka yi. Haka ya ƙaraci maganganun sa yana wani kashe min ido, wanda ya cika shi da wani uban kwalli kamar irin tsohon ɗan duniyar nan. Cikin jin haushi na koma cikin gida, bayan shiga ta sai ga shi an aiko manyan ledoji cike da kayan maƙulashe, da su turaruka da kayan kwalliya wai yace a bani. Ni dai ina zaune, ƙannene suka dinga ɗaga kayan suna santin kyansu, kayan ƙwalamar suna ta watandar su ina zaune ko kallo basu ishe ni ba. A haka har ranar auren ta zo aka ɗaura auren mu. Wannan shine ainahin abinda ya faru. *** *_DAWOWA LABARI._* Bamu shiga garin Lagos ba, sai wajen ƙarfe biyu da rabi na dare. Kai tsaye muka wuce ainahin family hause ɗin su Al'amen kamar yadda aka tsara, an ce anan zamu zauna na kwana biyu. Daga baya zamu koma ainahin gidan shi Al'amen ɗin dake can wata unguwa daban. Tunda motar mu ta tsaya a farfajiyar gidan, wajen gaba ɗaya ya cika da hayaniyar mutane ta ko'ina, babu mai cewa dare ya yi sakamakon hasken da ya cika harabar gidan. Maganganun jama'a ke tashi na Barka da zuwa, wasu da Hausa wasu da Yaren yarabanci kowa na faɗin Barka da zuwa amaryar mu. Da ƙyar suka bari aka fito dani daga mota, saboda yadda wajen ya cika kowa na faɗin yana so yaga amaryar Jagaba. Muna fitowa naji wajen ya cika da hayaniya da tashin guɗa, naji an fara min feshin turare ta ko'ina. Ba tare da nasan waye mai fesa min ɗin ba, hannun Aunty Zulai na ƙara damƙewa, na kwantar da kaina a jikin Umma Safiya tare da rufe fuskata gudun kar su fesa min turaren a ido. A haka har muka shiga wani ƙaton farlo, wanda daga shigar mu sanyin AC ya mamaye jikina har wani sanyi sanyi nake ji. Ba zan iya tantance mutanen dake farlon ba, sakamakon fuskata dake rufe, amma tabbas farlon a cike ya ke da jama'a masu yawa har bakin ƙofa. Zaunar dani suka yi gaban wasu mutane, waɗanda ban tantance su waye ba, sai da naji an dafa kaina ana min addu'a cikin Yaren Yarabanci. Mace ce me addu'ar, sauran na amsawa da Amen. Ɗaya bayan ɗaya suka dinga min addu'a, wasu su rungume Ni, wasu su dafa kaina duk da sunan sa albarka. Gaba ɗaya ji na nayi cikin wata sabuwar duniya ta daban, dan duk wannan abin ba al'adar mu bace ban taɓa ganin. Irin hakan ba. Daga nan bayan sun gama min duk wasu addu'o'in su, haka aka dinga bi dani sashi zuwa sashi, wai ashe wajen kishiyoyin maman sane. Ta farkon ita ce mamar sa da ƴan uwan ta. Ta ƙarshen da aka kaini wajen ta ce, naji hankalina yafi kwanciya da ita, dan Hausa naji ta mana kuma cikin nutsuwa ta tarbe mu. Da wasu dake farlon nata da suma na ji suna Hausar. Daga nan sai farlon mahaifin sa, in da shima albarka yasa da addu'a. Da muka fito aka wuce dani sashin da aka ce nan zan zauna kafin mu koma namu gidan. Babban sashi ne, me ɗauke da ɗakuna biyu, da toilet ɗaya a farlo kowanne ɗaki da nashi, kuma duk wasu kaya na amfani akwai a ciki kama daga gado da sauran kayan amfani. Haka aka cika mu da kayan ciye-ciye kala-kala. Ni dai ina kallon yadda su Binta da Ummi ƙawata, da su Aunty Fati suka dinga cin abincin su. Ban iya ko kallon abincin ba, haka bayan sun gama suka dinga rige-rigen shiga wanka. Kowa na son huta gajiya kafin asuba. Ina naɗe akan gadon, zuciyata cike da tunani kala-kala, ina ganin komai kamar a mafarki. Sai na ji wayata na ƙara. A hankali na duba sunan mai kiran (Al'amen) na gani kamar yadda nayi sv ɗin number. Kamar ba zan ɗauka ba ganin ƙarfe uku harda minti ashirin na dare,sai kuma na ɗauka tare da yin shiru ina sauraren sa. Daga can naji Muryar shi "Rahamah ki fito ina bakin ƙofar farlo mu wuce sashina mu kwanta." Shine kawai abinda kunnuwana suka jiye min. *_🥰MAMAN ƊAN ALBARKA CE 🥰✍️✍️_* [1/18, 07:15] Ummu Sultan Ceh3: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/EJJOOxsRu8dKh9gocmSFuG *BAƘAR ZUCIYA!.* *_🥰MAMAN ƊAN ALBARKA CE 🥰✍️✍️_* *_LITTAFIN KOWA YAƘI JI YA KAMMALA COMPLET, GA DUK ME BUƘATA TA MIN MAGANA TA WANNAN NUMBER 09014644247_* *_PAGE3️⃣_* Shiru nayi na rasa abin cewa tsabar mamakin rashin hankali irin na wannan mutumin, wai na fito me je mu kwanta sai kace a garin mahaukata, daga kawo ni yau ga ƴan uwana ga kowa, dan ni ce Sarkin daɗi miji, sai na tashi na bishi kawai mu kwana a sashin sa. Magana ya ke ta yi, nayi shiru kamar bana ji, ƙarshe na katse kiran ina jan dogon tsaki. Aunty Jamila da ta fito wanka ta zauna gefen gadon, ta juyo ta kalle tace "Ke kuma wa ki ke wa tsaki?." Maida kaina nayi na kwantar jikin fillon nace "Ba kowa wani abu na tuna." Taɓe baki tayi tace "Kyaji da shi dai, ayi mutum ya yi ta ɗacin rai sai kace bake ki ka fito da mijin kika ce kina so ba." Ni dai bance mata komai ba. Daidai nan Aunty Zulai ta fito daga toilet, wajen jakunkunan kayan su taje, sai taga bata ga jakar kayan ta ba. Tambayar Aunty Jamila ta yi, sai tace akwai wasu kaya a ɗaya ɗakin da su Binta suke, ta je ta duba ko suna can. Tsaki taja ta nufi hanyar fita a ɗakin, tana mitar me yasa aka kai mata jakar ta wajen ƴammatan can. Dan dama ita ta kora su can, wai ba zamu kwana ɗaki ɗaya dasu ba. Umma Safiya ce tace ita zata je ta kwana dasu, dan kar a barsu suga an ware su. Aunty Fati kam dama muna sauka, da taga an dangana ni da ɗakina ta ware nata gidan, tunda maƙota ne ta dai ce da safe zata dawo. Koda Aunty Zulai taje ɗakin, duk sun yi barci babu wanda ya yi wanka bare ayi batun canja kaya. Tsaki taja tace "Ƙazaman banza da wofi." Ta kalli yadda Binta tayi ɗai-ɗai a gadon tana sakin munshari, haushi ya kamata ta juya ta fita hannun ta riƙe da jakar. Tana ƙoƙarin tura ƙofar ɗakin da muke taji ana ƙwank'wasa ƙofar farlon, dawowa ta yi ta tsaya a bakin ƙofar tace "Waye?." duk da zuciyar ta na rawar tsoro, ganin dare ya yi amma tuna biki ake yasa ta dake. Daga can taji kamar Muryar Al'amen, ta ƙara kasa kunne sai ta ji yace "Ni ne Aunty Zulai." Cikin mamakin me ya kawo shi a daren nan?, ta buɗe ƙofar tana bin shi da kallo, ganin shi cikin shigar jallabiya fara kanshi babu hula, sai jallabiyar ta ƙara bayyana girman tumbin sa. Hannun shi riƙe da manyan ledoji. Sunkuyar da kai ya yi irin na girmamawa. Aunty Zulai dake bin shi da kallo tace "Lafiya ko? Ko wani abun ka ke so a baka?." Yana ɗan shafa kai a zuwa kunya ɗin nan yace "A'a dama wai Rahamah na zo in tafi da ita, naga tun ɗazu bata zo ba ga dare ya yi, kar gari ya waye ba tare da mun farga ba." Ikon Allah Aunty Zulai tace a ranta, shi kuma haka aka ce masa ana yi. Daga kawo amarya ko tafiya ƴan kawo ta ba su yi ba sai ta kwana da ango. Ganin yana tsaye ya tsare ta da ido, yasa wata dubara faɗo mata ta kalle shi tace "Ayya ai Rahamah tuni ta yi barci, kanta ke ciwo tunda muka sauka." Ba sai ga mutumin ku ya ruɗe ba, ya yo bakin ƙofar kamar zai ture Aunty Zulai Yana faɗin "Subhanallahi Aunty, shine baku kira ni ba tun ɗazu." Ƙin matsawa ta yi tace "Ai da sauƙi ma, ka je ka kwanta sai da safe in Allah ya tashe mu lafiya." Ta juya tana ƙoƙarin rufe ƙofar. Ganin hakan da ya yi yace "Am Aunty ga wannan a bata dan Allah ." Ya miƙo ledojin dake riƙe a hannun sa, amsa Aunty Zulai tayi zuciyarta cike da mamakin Halin Al'amen. A haka kamar me hankali, amma abinda ya yi ya bata mamaki, sai kace an ce masa ba zasu tafi ba zama za su yi. A haka tana mita ta koma ɗakin, har barci ya fara ɗauka ta. Jin yadda take ɓaɓatu akan shirmen Al'amen, yasa na buɗe idona na yunƙura na tashi zaune. Ta kalle ni tace "Ke fa angon ki ya zo wai na kira ki, ku je ku kwanta dan tsabar wauta." Dariya ce ta so kamani, ganin yadda ta ke maganar, sai kace irin wanda ya aikata wani gagarumin zunubi ɗin nan. Na fuskanci abin ya mata wani daban, shi yasa take ta maimaita maganar. Ina shirin komawa na kwanta nace "To ai ni ya fara kira a waya, wai na fito yana waje mu tafi. Shine fa na kashe wayar, shine ya kira ki kenan." Na ƙarasa faɗar ina kwantawa cikin dariya. Ƙoƙarin saka hular dake riƙe a hannun ta take, bayan ta gama sa kaya ta kalle ni taja tsaki tace "Waya sani ko su haka suke abin su, Ni kunga ma ya bani leda wai na kawo miki, bari na buɗe na ga me ye a ciki. Ta tsugunna ta shiga fito da abubuwan dake cikin ledar. Wasu irin dank'wala-dank'walan kaji ne masu rai da motsi, sun ji gashi sai tururi suke. Maida kaina nayi na kwantar, ko sha'awa basu bani ba. "Kunga mutumin nan ko Jamila, wato mu suka haɗa da naman kasuwa shi muka iya ci shi yasa aka haɗa mu dasu, duk kuɗin sa ba zai iya yanka mana ka ji a soya a tarbe mu da su ba. Amma da ya ke yana son cin amarci ai kinga ya siyowa Rahamah." Dariya Aunty Jamila ta yi tace "Kai aunty Zulai baki da dama Wallahi, to mene dan ya siyowa matar shi, muma ai an sa mana nama a miya munci." Sai da ta gutsuri naman kazar tasa a baki tace "Ai ba cewa nayi laifi bane Jamila, duk da muma Alhamdulillahi ba wai yunwar naman muke a gidajen mu ba. Amma ga mutum mai arziƙi irin Al'amen ya kamata mu samu tarbar data ɗara wadda aka mana." "To ina ga su haka suke abin su fa, shi yasa bakya ganin ba Yaren mu ɗaya ba." Cewar Aunty Jamila kenan. "Dallah rufe min baki, ke baki san me ke tafiya a duniya bane tunda kullum kina gida bakya zagawa, ai ko lokacin da muka zauna a ilori da Dadyn Fadila Wallahi yarabawa suna da mutumci da kara, basa abin ƙaranta komai nasu cikin wadata suke yin sa. Ko biki ne suke kai bare ma sai ka ci kasha komai a Wadace." Ni dai ido ne nawa, haka suka dinga tattaunawa akan maganar. Ƙarshe Aunty Zulai tace na taso muci naman, Allah ne ya tsaga da rabon su shi yasa. Cewa na yi na ƙoshi na maida kaina na kwantar, nan da nan barci ya ɗauke ni. Da asuba Umma Safiya ta ƙwank'waso mana ƙofa, muka tashi muka yi sallah. Bayan idar da sallar mu, sai na koma na zan kwanta. Cikin tsawa Aunty Zulai tace "Yau naga ikon Allah Rahamah barci za ki yi? Kina amarya ace kin kwanta ba tare da kin yi wanka ba." Ina ji ina gani ta hanani barcin, sai da nayi wanka ta zaɓo min kayan cikin kayan da Abbannmu ya ɗin ka min daban, dan tace Duk cikin kayan da ke akwatina bata ga wani babba da zan sa na fitar kunya ba, dan ba wani laifen ku zo mu gani ya min na duk kuɗin sa. Les ɗin da na sa ma kyauta ce wadda Abbanmu ke bawa Kowacce daga cikin ƴaƴan sa in za ta yi aure. Ba ƙaramin kyau nayi ba, kasancewar Les ɗin fari ne irin fari tas ɗin nan, sai ratsin golden da duwatsu farare. Ɗinkin doguwar riga ne sai akai mata aikin wuta tun daga sama har ƙasa. Da kaina na ɗaura ɗankwalin, kasancewar nima gwana ce ta wannan fannin, na iya kafa ɗauri kala-kala. A hankali nake bin kaina da kallo yadda nayi wani irin sihirtaccen kyau na musamman, kyakkyawar fuskata nake bi da kallo, wadda take a cike daidai gwargwado, inada hanci ɗan madaidaici Masha Allah wanda ya yi daidai ya zauna a fuskata. Sai ɗan madaidaicin bakina wanda ke ɗauke da fararen haƙorana wanda suke jere gwanin sha'awa da wushiryata yar daidai a tsakiyar su. Yayin da in nayi dariya duka kumatuna ke lotsawa Dimple ɗina na bayyana, wanda ke ƙara min kyau na musamman. Ina da cikar gashin gira dana ido, wanda bai sani ba zai ce ina sa Eyelashes ne. Babu laifi, ina da ƴar ƙiba amma ba irin sosai ɗin nan ba, ko'ina na jikina a cike ya ke bani da rama ko kaɗan. Dan haka kayan suka wani irin zama a jikina. Turaruka na musamman na faffesa a jikina, su kansu su Aunty Zulai sai da suka dinga tsokana ta akan nayi kyau. Babu jimawa sai ga ƴan aike wasu mata biyu, ɗauke da manyan fulasai, da kuloli sun kawo abincin karyawa. Bayan mun gaggaisa suka ce mana in mun gama, a kaini na gaida uwar ango da uban ango suna farlon Dady. Aunty Jamila ce tace basu san ina ne ba, shine suka ce in mun gama za su zo su raka mu. Ni dai kasa shan shayin nayi, dan ko alamar citta babu bare ayi batun sauran kayan ƙamshi, da alama iya ruwan zafin ne aka tafasa da Lipton. Sai gwangwanin madara da milo da sugar da aka haɗo da su. Sai kuma soyayyen ƙwai da dankalin turawa shima soyayye. Shikenan abin karyawar. Su Binta ne kawai suka iya ci, Nan da nan Aunty Zulai ta kira Aunty Fati a waya tace ta aiko mana abinci, babu jimawa sai ga Aunty Fati ta zo. Shi muka ci abinmu, babu jimawa wannan matar da tace zata taka mu gaida Maman Al'amen ta zo. Sai yau na samu damar ƙarewa gidan kallo, Babban gida ne mai ɗauke da sashi daban-daban, kuma duka iri ɗaya ne. Ban dai san guda nawa bane dan ta can baya ma ina hango wasu gine ginen. Sashin da aka ce na mahaifiyar Al'amen ne muka shiga da sallama. Wasu mata dake zazzaune suka amsa mana a tare, kaina a ƙasa ban iya banbance abubuwan dake farlon ba. Sai dai idanuna dake kallon lafiyayyen carpet ɗin dake malale a tsakiyar farlon. Gaban matan aka tsugunnar dani, hannuna cikin na Aunty Zulai Dan ita kaɗai ce ta biyo mu. Haka na dinga gaida su, ta ƙarshen ce naji ta riƙe ni ta miƙar dani tare da fashewa da kuka. Cikin mamakin meye abin kuka, na ɗan buɗe mayafin fuskata dan ganin wace. Babbar mace ce irin masu jikin nan sosai, kamar su ɗaya da Al'amen kamar an tsaga ƙara babu abinda ya raba su. Cikin kukan da take, ta shiga samin albarka. Wai na kyauta mata na share musu hawayen da suka daɗe suna zubarwa, na auri ɗan ta ba tare dana guje shi ba. Maganganu dai kala-kala tana ta sharɓa kuku, haushi duk ya ishe Ni da ta taimaka ta sake Ni ma da yafi Wallahi. A zuciyata kam cewa nake _Ni ma baki san fin ƙarfi na aka yi ba, har na auri ɗan naki. Ƙaddara ita ta kaini in ba ita ba da baki ganni ba._ Bata sake ni ba, sai da ta gama kukanta san ranta, sannan ta sake ni ta wani jani kusa da ita ta zaunar. Allah ya sani nayi danasanin zuwa gaisuwar nan, dan ina ji ina gani ban fita a wajen ta ba, ƙarshe Aunty Zulai tafiya tayi ta barni tace zata dawo. Haka nayi tsuru-tsuru cikin su, bana jin abinda suke cewa sai surutu suke zubawa cikin yare. Nafi awa ɗaya sannan tace a kaini wajen Dady wato mahaifin Al'amen. Shi da ya ke bahaushe ne, cikin ladabi na gaida shi ya dinga jero mana addu'o'i, daga ƙarshe ya sa mana albarka muka taso muka nufi sashin da aka sauke mu. Aunty Zulai kamar zata ari baki saboda faɗa, cewa take an ƙi bari mu huta mu da muka sha uwar tafiya, babu in da zata ƙara bari na fita ya isa haka. Haka da rana gidan ya cika da jama'a, muna jin su suna kid'en-kid'en su da raye-raye, duk cikin mu babu wanda ya fita sai Binta da Ummi, dan Binta cewa tayi sai ta je ta gano. Naji daɗin yadda Aunty Zulai ta tsaya tsayin daka ta hana a shigo ko ɗakin da nake, dan kowa ya zo cewa take bana jin daɗi a barni na huta. A zuciyata nace _Mutum me faɗa ma yana da ranar sa._ Kwana ɗaya su Aunty Zulai suka ce zasu ƙara, gobe zasu tafi. Duk yadda na dinga roƙon su akan su ƙara kwana biyu, cewa suka yi garin ya ishe su, kuma ba hauka bane abin daga kawo amarya su zauna suƙi tafiya, sun fahimci ango kanshi a matse ya ke su tafi gwara su tafi abinsu. Gaba ɗaya jikina a sanyaye ya ke, har na fara fargabar tafiyar su in suka tafi ya zamu ƙare da wannan mutumin?. Da daddare Muna cikin fira dan nace yau ba zan yi barci ba, gwara mu yi firar bankwana. Ina ganin wayata na kawo haske, saboda na sata a silent gudun kar mutumin nan ya dame ni, Dan tun da rana ya ke kirana wai na fito yana wajen parking ɗin motoci, so ya ke ya ganni kawai. Naƙi fita na daina ɗaga kiran shi baki ɗaya. Shine yanzu ya ke ƙara kirana, ina sane naƙi ɗauka muka cigaba da firar mu da su Aunty. Can muka ji ana gyaran murya a bakin ƙofa, cikin mamaki aunty Zulai tace "Waye?." Gani muka yi ya sawo kai ɗakin kai tsaye da uban tumbin sa a gaba, yana faɗin "Ni ne Aunty." Rige-rigen gyara zama aka shiga, masu neman ɗankwali su ɗaura nayi, masu lalubar hijabi nayi dan duk mun haɗu harda su Umma Safiya da su Binta muna fira. Hakan da ya gani bai sa ya juya ya fita ba, sai cewa da ya yi "Ina wunin ku." Idanun sa baki ɗaya a kaina, sai wani murmushi ya ke sakar min abin haushi. Takaici da haushi ne ya kama Aunty Zulai, ganin yadda ya kafe ni da kallo kamar tsohon maye. A ranta tace _Ikon Allah wannan mutumin anya kuwa?_ Ai bata gama tunani ba ta tsinci Muryar shi "Aunty Dan Allah a ɗan bamu waje, ina son magana da Matata ina kiran ta tun ɗazu bata ɗauka ba." Dukan su kusan daskarewa suka yi a zaune, basu gama mamaki ba suka ga ya nufi gadon ya zauna a gefen Rahamah. Babu shiri suka tashi a kunyace suka fita, kowa da abinda ya ke saƙawa a ransa, suna mamakin hali irin na mijin Rahamah kamar me motsi a kai. Banyi zaton rashin tunanin sa zai sa ya iya aikata haka ba, dana san su Aunty Zulai fita za su yi da na riga su fita. Ban gama tunani ba naji ya kawo hannun sa ya kama nawa. Ji nayi kamar an watsa min wuta, da sauri na fusge hannuna na miƙe tsaye akan gadon na fara ja baya. Da hannu nake nuna shi ina faɗin "Kar ka matso kusa dani, karka taɓa ni bana so. Shima biyo ni ya yi yana wani mirgina tumbi kamar randa, yana wani lumshe ido cikin ƙasa da murya yana cewa "Dan Allah Rahamah ki tsaya, babu abinda zan miki ganin ki kawai zan yi. In kuma bakya so anan ki taho mu je ɗakina kawai, kinga nan dama ga su Aunty kar su ga na hana su sakewa." Kallon shi kawai nake, ina jin zuciyata kamar ta faso k'irjina saboda takaici, ikon Allah ni kam wanne irin miji ne wannan? Wa nake aure ?. Babu zato naji ya rungumo ni ya wani matse ni a jikin shi. Iya ƙarfina na shiga ƙoƙarin ture shi, sai dai yadda kasan dutse, ko motsi bai yi ba bare yasan ina yi. Ai ina ganin ya fara ƙoƙarin kai hannun sa wajen zip ɗin rigata, na taƙarƙare iya ƙarfina na gasa masa lafiyayyen cizo a hannu. Babu shiri ya sake ni, tare da hankaɗa ni kan gadon nayi baya na faɗi. Da sauri na miƙe ina gyara zaman rigata, cikin fitar hayyaci nace "Na rantse da Allah in baka fita a nan ba, zan baka mamaki." Kallon hannun sa kawai ya ke, ya ɗago ya watsa min idanun sa da suka yi wani irin ja, tare da nuna ni da hannun sa yace "Wallahi sai kin biya bashin da kika ci, zamu haɗu dake ne ai baƙin zasu tafi." Bai ƙara magana ba ya sauka daga gadon, da ƙyar yana nishi saboda tumbin sa. Da harara nabi bayan shi da kallo, tare da jan tsaki me ƙarfi nace "Mu zuba Ni da kai aga wanda zai yi nasara." Har ya kai bakin ƙofa, jin abinda nace yasa ya juyo ya sakar min wani irin murmushi, wanda ban san ma'anar shi ba ya fice a ɗakin. Da sauri na tashi na gyagygyara kan gadon, gudun kar su Aunty Zulai su yi zaton wani abu, nasan ni zai bari da kunya tunda shi ya yi gaba. Ina cikin gyaran suka shigo, cikin ikon Allah kuma babu wadda tace komai, suka nemi waje kowa ya kwanta da saƙe-saƙe kala-kala a ransa. Firar da bamu yi ba kenan kuma, da asuba suka shirya suka ce zasu tafi, da ya ke akwai direban da aka ware aka ce zai maida su gida dan haka a farfajiyar gidan muka yi sallama. Nasha kuka harda birgima, haka suka dinga bani Haƙuri, suka kuma ƙara min da nasiha da ban haƙuri. Harda cewa sai nayi haƙuri da mijin nan nawa, dan sun ga alamun bai da seti da sauran su. A raina nace _Ni zan faɗa muku bai da seti._ Sauƙin abin ma ina da Aunty Fati, suna tafiya na maza na faɗa sashina na kulle ko'ina na bar makullan a jiki dan bana son ganin wannan mugun mutumin ko kaɗan. *_🥰MAMAN ƊAN ALBARKA CE 🥰✍️✍️_* [1/18, 07:15] Ummu Sultan Ceh3: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/EJJOOxsRu8dKh9gocmSFuG *BAƘAR ZUCIYA!.* *_🥰MAMAN ƊAN ALBARKA CE 🥰✍🏻✍🏻_* *_LITTAFIN KOWA YAƘI JI YA KAMMALA COMPLET, GA DUK ME BUƘATA TA MIN MAGANA TA WANNAN NUMBER 09014644247_* *PAGE 4️⃣* *AL'AMEN* Tun lokacin da Rahamah ta cije shi, ya sawa ransa zai nuna mata kuskuren ta. Amma kuma daya tuna amarya ce, sai ya ga bari ya bita a sannu gudun kar ta botse masa baki ɗaya. Allah-Allah ya ke ƴan Kaduna su tafi, dan shi har ga Allah Aunty Zulai ɗin nan ta bashi haushi, ko ledar daya bata, ya bata ne wai ko zata gane nufin shi ta yi kara ta taso Rahamah. Sai ta amsa ta rufe ƙofar, in da hakan ya bashi haushi sosai, gashi ita ma Rahamah ta ƙi bari ya ganta kwata-kwata. Shi yasa ya je har ɗakin ya cire kunya dan ya ganta, shine suka ƙare a faɗa a ƙarshe. Yanzu ma zaune ya ke a tafkeken farlon shi, wanda ke ainahin gidan shi wanda zasu zauna da Rahamah dake unguwar Mile 12. Ba ƙaramin girma gidan ya ke da shi ba, dan a ƙalla yana ɗauke da part kusan biyar banda na shi, wanda shi harda bene irin me hawa biyun nan. Shine a matsayin ɓangaren Al'amen ɗin. Wani mutum ne kusa da kujerar da Al'amen ke zaune. Fari ne sosai mara jiki, daga kallo ɗaya zaka gane asalin bafulatani ne babu sirki. Sanye mutumin ya ke da riga da wando na wani yadi fari, fuskar shi ɗauke da dogon gemu da saje daya cika ta. Sai irin hirami nan baƙi daya yafa a kafaɗar sa. Idanun sa sanye da kwalli ya yi rau. Shi kuma Al'amen sanye ya ke da jallabiya ruwan ƙasa (Brown color). Kuɗi ne gaban Al'amen dami-dami a wata jaka, a hankali ya raba jikin sa da jikin kujerar ya turawa mutumin kuɗin baki ɗaya. Mutumin ya ja jakar ya fara zaro kuɗin yana dubawa. Can ya ɗago ya kalli Al'amen yana jinjina kai, cikin murya irin ta malaman nan ƴan ƙaƙale yace "Masha Allah ai na faɗa maka, ribar wannan satin sai ta linka ribar shekara guda daka samu, gashi yanzu kaima ka shaida tun ba'a je ko'ina ba." Ya rufe jakar ya miƙawa Al'amen. Al'amen yana murmushin jin daɗi, ya amshi jakar yace "Wallahi nima na gani tabbas, dan in ba ƙarya nayi ba zan iya cewa, ribar nan tama linka ta shekarar data gabata." Murmushi mutumin ya yi tare da gyara zaman hiramin shi, ya yi gyara murya yace "To ka gani, Fatana zaka dage sosai akan aikin nan. In har ka dage zaka ga cigaban daya zarce wannan, amma fa ina mai baka shawara da ka bi a sannu, tunda dai yanzu ne aka fara." "Ai ba sai ka faɗa ba, in sha Allahu duk wani mataki, da sharaɗin da ka ce zan bi su kaga ga lada da addu'o'i da zan samu, ga kuma cigaban da nima zan samu." Cewar Al'amen kenan. Miƙewa mutumin ya yi yana ƙara gyara zaman hiramin shi, ya kalli Al'amen ɗin yace "Ni zan tafi, duk yadda za ka yi karka ƙara bari a samu matsala, a daren nan komai ya wakana. Zuwa sati na gaba da kanka zaka zo ka tarda ni gida, ka bani labari akan cigaban da aka ƙara samu." Yunƙurawa Al'amen ya yi, da taimakon hannun kujerar daya dafa ya miƙe. Ya kalli mutumin tare da nuna masa jakar kuɗin yace "Ka ɗibi abinda zai ishe ka, kafin ka tafi dan anan nake son cire wanda za'a kai masallacin juma'ar nan." Tsugunnawa mutumin ya yi, ya ɗauki dami biyu yana murmushi yace "Wannan ma ya isa, sauran in ka kai masallaci sai ka shigar dasu cikin kasuwanci." Sai da ya rakashi har bakin motar shi, suka yi sallama yaja motar ne gadi ya buɗe masa ya fita. Cikin hanzari da ɗan gudu-gudu Al'amen ya juya ya nufi sashin nasa. Yasan yanzu baƙin sun tafi, dan sun yi waya da Habu direba, yace sun shirya ɗazu dan dama shi tuni ya riga daya sallame su. Ya bawa Hajiyar sa dubu goma-goma yace a bawa baƙi da zasu tafi su sha ruwa a hanya. Kuma ya bawa Habu kuɗi har dubu talatin ya sai musu abinci a hanyar su ta komawa. Yana da tabbacin zasu ji daɗin kyautar nan, har ma su ƙara ganin mutumcin sa. Yana shiga farlon, kai tsaye saman bene ya nufa, yana haurawa ya tura ƙofar ɗakin dake farko dan dama ƙofa biyu ce a saman. Wani haɗaɗɗen farlo ne ya bayyana, ya fara takawa cikin hanzari ya nufi bedroom. Wasu irin haɗaɗɗun kayan gado ne a ciki, masu shegiyar tsada daga gani ba ƴan nan bane na waje ne. Kan tamfatsetsen gadon ya nufa, ya ɗauki wayar shi da wasu makullaye. Har ya juya zai fita a ɗakin, ya tuna wani abu da sauri ya koma ya nufi wata loka, yana buɗewa ya ɗauko wata leda baƙa dake ƙulle. Ya zura ta a aljihun sa, sannan ya jawo ƙofar ya fita ya nufi ƙasa. Kai tsaye daya fito wata haɗaɗɗiyar mota ya shiga ya jata da nufin barin gidan. A bakin get me gadi na hango shi, ya miƙe a guje ya buɗe ƙofar yana ɗaga masa hannu cikin kirari yana faɗin "Sai Jagaba Jagaban mu maganin kukan mu, na gaida uban gidana maganin kukana, Barka da fitowa Jagaban talakawa." Yana zuwa daidai inda me gadin ya ke, a hankali ya zuge glas ɗin motar, yana sakin murmushin jin daɗi ya leƙo da kanshi yace "A'a Malam Iliya Barka da safiya, fatan ka tashi lafiya." Da sauri mai gadin ya ƙara matsawa kusa da motar, yana wani irin washe baki yace "Lafiya lau Jagaban mu, ya kwanan amaryar da baƙi." Amsa masa ta yi da "Lafiya lau." Yasa hannu a aljihun jallabiyar shi, ya ciro kuɗi ya irga dubu uku ya miƙawa malam Iliya yace "Gashi ayi cefane ko." Da sauri malam Iliya ya amsa yana mai jin daɗi a ransa, ya shiga rattaba godiya da fatan alkhairi. Cikin jin daɗi Al'amen yaja motar ya fita a gidan, iya wannan ya ishe shi farin ciki, yaga ana nuna masa shi mutumin kirki ne, babu abinda ke bashi nishad'i bayan haka. Kai tsaye Family hause ya nufa, idanunun shi cike da mararin ganin Rahamah, yana hasasowa kan shi yadda zai ganta yana son wannan tsiwar tata, ba ƙaramin kyau take masa ba in tana yi, ga wani irin ƙamshi na musamman da ya ji yana tashi a jikin ta a Jiya da ya rungume ta. So ya ke ya ƙara shaƙar k'amshin, tunda ya ke bai taɓa jin turare me daɗi da kwantar da zuciya ba irin wanda ta yi amfani da shi. Yana cikin tuƙin wayar shi ta shiga ƙara, ganin sunan dake yawo a jikin fuskar wayar, ya ja tsaki tare da katse kiran ya cigaba da tuƙin. A ransa yana jin, a yanzu ko kira nawa number za tayi ba zai ɗauka ba, dan baya buƙatar abinda zai ruguza masa wannan farin cikin nashi. ***** *RAHAMAH* Tunda na kulle ƙofar farlon, na nufi bedroom ɗina na shiga shima na kulle shi ina sauke ajiyar zuciya. Sai da naji hankalina ya ɗan kwanta, sannan na nufi toilet da nufin nayi wanka. Ina fitowa wanka na duba cikin kayana na ɗauki doguwar rigar abaya baƙa, bayan na gama shafe-shafe na na saka rigar, ɗankwalin abayar na ɗaura a kaina nabi lafiyar gado dan Ni kaina nasan jikina na buƙatar hutu. Cikin barcin da nake, kamar a mafarki naji ana bugun ƙofar sama-sama. Tsaki naja na maida kaina na kwantar, ina faɗin "Duk nacin ka duk maitar ka zaka gaji da bugu ka tafi, dan ni ba mahaukaciya bace da zan buɗe maka ƙofa." Ba'a daina bugun ƙofar ba, babu jimawa kuma wayata ta fara ringing. A hankali na jawo ta dan duba wake kiran. Ganin sunan Aunty Fati na ɗauki kiran cikin Muryar barci nace "Aunty Fati." Daga can taja tsaki tace "Wai ba za ki zo ki buɗe ƙofar ba, ina ta faman bugun ƙofa kin barni a tsaye." Zabura nayi na tashi ina mutstsuka idona, na lalubi ɗankwalin da tuni ya kunce ya yi nashi wajen na ɗaura. Na sauka a gadon na nufi Ƙofa na fita. Ina buɗe kofar farlon, naga Aunty Fati tsaye sanye Cikin hijabi har ƙasa, hannun ta riƙe da basket ɗin abinci sai gefen ta Kamal yaranta na biyu hannun sa riƙe da wata leda. Yana ganina ya yo kaina cikin murna tare da ɗane jikina, yana faɗin "Aunty Rahamahtah." Nima ɗaukar shi nayi duk da babu laifi yana da nauyi, dan a ƙalla zai kai shekara bakwai ga shi kuma yana da ɗan jiki kaɗan. Cikin murrmushi nace "Kamal ɗina ya kake ina Islam?." Kokawar sauka ya shiga yi yana faɗin "Aunty Islam na gida, wai ita ba zata biyo mu ba tayi fushi tunda Mami bata kaita Kaduna ba." Jan hannun shi nayi muka nufi ciki ina faɗin "Ka ƙyale Islam, zamu gauraya ne ba bata da kirki, yarinya sai zuciya kamar tsohuwar kuturwa." Aunty Fati dake biye damu a baya, ta aje kwandon hannun ta tace "Ai ni na fahimci ma baki ganni ba Rahamah, wato ta ɗan ki kike kenan." Juyowa nayi na kalle ta, dai-dai lokacin dana ɗora Kamal a kujerar farlon nace "Ki yi haƙuri Aunty Fati, ina kwana." Sai da ta cire hijabin jikinta ta zauna sannan tace "Lafiya lau, ya kwanan me gidan da kewar ƴan tafiya." "Lafiya lau Aunty, kamar kin san har na fara kewar su Aunty Zulai." "Ai dole ki yi, yanzu na kira suka ce min sun yi nisa da tafiya." Cewar Aunty Fati kenan. "Allah ya sauke su lafiya." Nace hakan tare da komawa kujerar kusa da ita, muka shiga firar zumunci. Ta janyo basket ɗin da ta zo da shi, ta firfito min da abincin data kawo min, Indome ce ta mata dahuwar ruwa-ruwa dan tasan cima ta kenan, taji kayan haɗi sosai sai tashin ƙamshi take. Sai ɗayar da ta soya dankalin turawa ba tare da tasa ƙwai ba,sai stew da tayi daban wadda taji hanta, sai damamen kunun tsamiya wanda yaji kayan ƙamshi. Duk cima ta ce ta sani, amma yanzu iya indomen nake da buƙata, sai kunun dana sha kaɗan. Muna cikin hira na tuna ban rufe ƙofa ba, na tashi da sauri na nufi Ƙofar zan rufe. Sai naga wata mata na ƙoƙarin shigowa, hannun ta riƙe da kuloli guda biyu. Ta kalle ni tare da sakar min murrmushi tace "Amarya kin tashi lafiya, ya kwanan baƙunta." Da "Lafiya" na amsa tare da miƙa mata hannu dan amsar kayan hannun ta, dan a ƙalla zata iya kaiwa sa'ar Aunty Zulai a shekaru. Cewa tayi na barshi, na matsa ta shiga farlon. Bayan sun gaisa da Aunty fati ta juya ta tafi. Bayan tafiyar ta ina ƙoƙarin rufe ƙofa Aunty Fati tace karna rufe, bansan wanda zai zo ba, in barta a buɗe tunda gidan ba mu kaɗai bane. Badan naso ba na bar ƙofar a buɗe, dan bana so ta fahimci akwai matsala ne kawai, da rufe ƙofar zan yi kawai. Muna cikin fira sai ga Al'amen ya turo ƙofar, da sallama ɗauke a bakin sa ya shigo, hannun sa riƙe da wata baƙar jaka. Bayan sun gaisa da Aunty Fati, ya nufi bedroom ɗina kai tsaye. Ganin ina zaune ban motsa ba, yasa Aunty Fati ta galla min harara tace "Ke dai kam Rahamah baki da wayo, kina kallon mijin ki ya dawo, babu sannu da zuwa babu amsar kayan hannun shi ki kai masa ɗaki, ya shiga ɗakin ma madadin ki bishi kin ƙara gyara zaman ki." Ɗan turo baki gaba nayi, cikin narke murya nace "Aunty ba sai na bishi bafa, kuma zan masa sannu da zuwa gani nayi fa kina nan, kawai sai na tashi na wani amshi kayan hannun sa na shiga ɗaki dan rashin kunya." Tsaki taja tace "Ki ji min munafuncin banza.Ni dake wa zai ji kunyar wani, ina ce in Kika zo gidana kina zaune nake tashi, na tarbi Abban Islam na kuma shige ɗakin wani lokacin ma bana fitowa sai ya yi wanka. Shine ke zaki faɗa min wani kunya ki ke j..." Maganar tace ta katse, sakamakon jin Muryar Al'amen da muka yi yana kiran sunana "Rahamah Rahamah, kina ina ne?." Dukan mu muka ɗaga kai tare muka kalli ƙofar bedroom ɗina, Al'amen ne tsaye ya zuro kanshi bakin ƙofar yana kirana. Ƙasa-ƙasa Aunty Fati tayi da Muryar ta tace "Ai sai ki tashi ki je, daga nan in za ki tafi ki kai masa abincin nan, tunda nasan ba cinyewa za ki yi ba." Cikin jin haushi na tashi na nufi basket ɗin na ɗauka, ina gunguni ina komai na nufi bedroom ɗin. Yana ganin na taho ya koma ciki, ya zauna bakin gadon yana wani washe baki. Ban yarda na shiga ɗakin baki ɗaya ba, na coge a bakin ƙofa tare da ajiye basket ɗin hannuna, cikin turo baki murya a cunkushe nace "Ga abinci nan in zaka ci." Na juya da zummar barin ɗakin. Muryar shi ce ta dakatar dani, cikin mamaki na juyo ina kallon shi. "Rahamahtah dan Allah kar ki tafi yanzu,ki dawo ki ɗan zauna karki sa Aunty Fati ta zargi wani abu. Wallahi ban yi niyar yi miki komai ba, babu abinda zan miki Allah kin ji ma na rantse." Ba dan ya ce baya son Aunty Fati ta zargi wani abu ba, wallahi ba zan dawo ba. Dan dai kawai nima bana son tasan akwai matsalar ne, dan in akwai abinda na tsana shine ace wata matsala ta ɓullo daga ɓangarena. Nafi son komai mu yi shi tsakanin mu, in yaso in yaji gashi da kanshi zai fita harkata kowa ya yi harkar shi. Ban yarda na zauna can ciki ba, daga kan kujerar madubi dake bakin ƙofa na zauna, ya kalle ni cikin tausasa murya yace "Dan Allah ki saki ranki Rahamahtah, ki zuba min abincin naci yau hanci komai ba." Ina kumbura baki ina komai, na zuba masa soyayyen dankalin da miya, ba tare dana tambaye shi ba na zuba masa kunun cike da wani ƙaton kofi. Saukowa ya yi daga gadon, fuskar shi ɗauke da murrmushi yana faɗin "Kai amma Nagode, amma kin san bana shan kunun tsamiya dan dai kawai daga hannun ki ya fito shi yasa zan sha." Ya ƙarasa maganar tare da zama Ƙasan carpet ɗin dake malale a ɗakin, ya wani irin bajewa yana nishi da ƙyar. Dana kalle shi sai da dariya ta kusa kama ni, dan zaman da ya yi sai ya zamana tumbin nasa shima ya zauna abin shi daban, kowa na har kar shi kenan. Harara na galla masa na ɗauke kaina, ba tare da ya ganni ba ya shiga danna ƙatuwar loma. Dankalin ma, in ba gizo idanuna suka min ba, kusan uku-uku ya dinga haɗawa yana turawa a ƙaton bakin sa. Abin mamaki wanda yace baya shan kunun tsamiya, sai gashi ya zuƙe kunun tas, harda su lashe baki yana faɗin "Wallahi kuma kinga wannan da daɗi, ai nayi zaton irin kunun nan ne mara daɗi da zaki ji tsami kawai, gashi wannan harda ƙamshin su citta ya ke yi." Ya ɗago ya kalle ni yace "Ke kika dama mana hala?" Haushi da takaici da suka kama ni, yasa ban bashi amsa ba na share shi, nayi kamar ban ji abinda yace ba. Shi kanshi yasan na ji nayi banza da shi, dan haka ya jinjina kai a ranshi yana cewa _Zan lallaɓa ki har na cimma burina, yarinya sai iskanci kala-kala dan kinga kina da kyau, kuma ina lallaɓa ki._ Yana gama ci na tattara kwanukan na fita. Aunty Fati na ganina ta shiga murmushi, tana ta yabona wai ko Ni fa, yanzu da naje ba yafi ba, ai da ita zai wa kallon babbar banza. Ni dai bance komai ba na koma na zauna, muka cigaba da firar mu. Babu jimawa sai ga Al'amen ya fito, yana wata tafiya kamar bijimin sa. Haushi yasa na ɗauke kaina, ina addu'ar Allah yasa kar Aunty Fati ta kalle shi, dan sai naga kamar abincin da yaci yasa tumbin nasa ƙara bayyana. Sai naga ashe ma tuni kallon shi take, a ranta tana faɗin _Ikon Allah. Ashe dai da suke wa Al'amen kallon me tumbi, dan basu ganshi kusa bane shi yasa. Sai yanzu ta lura da uban tumbin nasa kamar rumbu, ita kanta sai da tace Allah ya bawa Rahamah lafiya._ Sallama ya mana, akan zai je ya duba wani aiki da ya bada a masa, na ginin masallaci, daga nan zai je shagon shi sai ya dawo. Aunty Fati ce ta bishi da addu'a. Bayan tafiyar shi wuni guda muna tare da Aunty Fati, sai bayan la'asar ta tafi. Gidan ya rage sauran Ni kaɗai, tunda nasan ba girki zan yi ba, sai kawai na shige ɗaki na ƙara kwanciya. Da Magriba sai ga aiken abinci, wai in ji Hajiyar Al'amen. Dana buɗe da sauri na rufe, dan bana shiri da amala kwata-kwata a rayuwata. Ita ce cike da kula a mulmule a leda, sai miyar ayayo da d'anyar kuɓewa da stew wadda aka zuba mata ganda da namomi manya-manya. Miyar ce kaɗai ta burgeni, sanin ba ci zanyi ba, sai kawai na ajiye a farlo na koma ɗaki. Tunda nasan na rufe ƙofar farlon, kai tsaye bayan nayi sallar isha'i na yi shirin barci cikin shigar doguwar riga har gwiwa, na sa hular net na bi jikina da turaren humra me ƙamshi na shafe, koda ina gida na riga dana saba in zan yi barci sai na shafa humra dan akwai ni da san ƙamshi. Can cikin barci naji kamar motsin mutum ya shigo ɗakin, cikin tsananin tsoro na tashi ina raba ido cikin duhu, na shiga laluben makunnar fitilar ɗakin dake jikin gado. Da ƙyar na kunna ɗakin ya gauraye da haske baki ɗaya, Al'amen na gani tsaye cikin shigar manyan kaya, hannun sa riƙe da ledoji. Muna haɗa ido ya wani washe min baki, yana bin jikina da kallo kamar tsohon maye. Lura da abinda ya ke kallo, da sauri na jawo bargo na lullu'be ƙirjina, zuciyata na wani irin bugawa, ina tambayar kaina _Ta ina ya shigo bayan nasan na kulle ƙofar?._ Ban gama tunani ba naji Muryar shi "Har kin fara barci kenan My Babynah, to ki tashi ki sakko tafa samu, dan kaji ne waɗanda suka linka na rannan a girma, sannan na haɗo miki da lemuka masu sanyi dan ki ji daɗin cin su." Duk da irin tsoro da fargabar da nake ciki, hakan bai hana ni galla masa harara ba, ina jin takaicin maganar shi _Wai na tashi naci kaji sai kace ance masa mayya ce ni, dan tsabar rainin wayo irin nashi harda wai sun fi na rannan, ko an faɗa masa naci wancan ne bare wannan._ Maida kaina nayi gefe nace "Bana ci. Dan Allah na roƙe ka ka fita a ɗakin nan, in ka fita ka ja min ƙofar." Dariya ya yi ya nufo bakin gadon, yana faɗin "Wanne irin na fita daga ɗakin ki, bayan ni ɗin mijin ki ne kuma sabon ango a daren nan." Yana nufo gadon ina ja baya, ganin haka yasa ya fashe da dariya yace "Au Wai gudu ki ke? Ki kwantar da hankalin ki, komai a sannu nake so mu yi shi, bana son wannan tsoron da ki ke nunawa dan Allah." Ganin bai hau gadon ba, ya tsaya ya aje ledar hannun sane, hakan yasa na sauke ajiyar zuciya ina ƙara ƙanƙame bargon dake jikina. *09014644247* *_🥰MAMAN ƊAN ALBARKA CE 🥰✍🏻✍🏻_* [1/18, 07:15] Ummu Sultan Ceh3: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/EJJOOxsRu8dKh9gocmSFuG *BAKAR ZUCIYA!.* *_🥰MAMAN ƊAN ALBARKA CE 🥰✍🏻✍🏻_* *_LITTAFIN KOWA YAƘI JI YA KAMMALA COMPLET, GA MAI BUƘATA TA MIN MAGANA TA WANNAN NUMBER 09014644247_* *PAGE 5️⃣* Yana aje ledar, naga ya fara cire babbar rigar jikin sa. Da sauri na ɗauke kaina ganin yana ƙoƙarin cire rigar jikin sa. Aiko ina juyowa nayi mugun gani, dan ya cire rigar daga shi sai dogon wando, da singlet, tumbin ya ƙara zazzagowa ƙasa. Zama ya yi dirshan a ƙasan carpet ɗin, ya jawo ledojin daya shigo dasu ya fara fito da kayan ciki. Ɗauke kaina nayi, gaba ɗaya zuciyata ta kasa nutsuwa, Ni kaɗai nasan fargabar da nake ciki akan zaman shi a ɗakina. Har hararo halin da zan shiga nake, in na shiga hannun wannan azzalumin, daga ganin shi ba tausayi zai yi ba bare ayi maganar sassauci. "Ki sakko ki ci fa, dan babu abinda ya dame ni, rashin cin da za ki yi ba zai hanani abinda zan yi ba." Maganar shi ta sa na juyo, addu'o'i na fara ja a zuciyata kawai. Ina neman tsari da wannan mutumin. Sai dai addu'a ta bata amso ba, zama ya yi ya dinga haƙar naman kamar wanda bai taɓa cin nama ba, yana gama ci ya kora da madara me sanyin, tare da sakin gyatsa me ƙarfi babu Alhamdulillahi babu komai ya tashi tiɓi-tiɓi ya nufo gadon. Wani uban tsalle na buga da nufin sauka, sai dai na makaro tuni ya kakkane bakin gadon babu hanyar gudu. Ina ji ina gani ya tarda ni, duk irin kiciniya da tirje-tirje nake da su cizo da yaƙushi a banza. Yadda kuka san dutse, haka mutumin nan ya koma kamar wani mahaukacin kare ko kurma. Kwata-kwata duk abinda nake bai san ina yi ba, dan gaba ɗaya kamar ba'a a hayyacin sa ya ke ba. Ina ji ina gani ya rabani da kayan jikina ba tare da tausayi ko imani ba ya fara ƙoƙarin cimma burin shi. Tun ina kuka da ihu har sai da ƙarfina ya ƙare. Ban ƙara sanin inda kaina ya ke ba, sai da sanyin asuba ya buge ni na buɗe idona a hankali na sauke su akan fankar saman dake wulwulawa. Kaina naji ya wani irin sarawa kamar zai rabe biyu, a hankali na yunƙura da niyar tashi. Wata irin azaba da raɗaɗi da naji yasa na koma na kwanta ba shiri, tare da fashewa da wani marayan kuka da duk wanda ya ji sai na bashi tausayi. Uban munsharin da naji an fara saki, yasa na juya gefena a hankali. Da sauri na runtse idanuna ina jin wata irin tsanar shi ƙyama takaici baƙin ciki, duk suka kama ni a lokaci guda. Kwance ya ke babu komai a jikin shi, ya wani irin bajewa yana barci da sakin munshari, abin babu kyan gani. Duk kuma kukan da nake bai ma san ina yi ba, dan da alama yana da nauyin barci. Na daɗe ina kuka wai ko zai farka ya taimaka min, saboda a kunne na aka sallame sallar asuba, burina na samu na shiga toilet na yi wanka na gasa jikina na yi sallah. Sai dai ina bai san ina yi ba, ganin haske ya fara shigowa ta window alamar gari ya fara wayewa, dole na fara jan jiki duk da irin raɗaɗin da nake ji na sauka gadon. A zuciyata Allah ya isa kawai nake jerawa wannan azzalumin. A haka da jan jiki na kai kaina toilet ɗin, cikin dubara na tara ruwan zafi a kwamin wankan, na surka shi kaɗan. Da ƙyar na zauna saboda zafin ruwan, amma bani da wata mafita bayan hakan, hakane zai sa naji dama-dama. Sau uku ina canja ruwa, sai sannan naji dama-dama har na iya miƙewa tsaye. Alwala na ɗauro ina tafiya a hankali na fito, cikin dubara nake komai har na zura doguwar riga, na sa hijabi na tada Sallah. Na daɗe zaune ina kai kukana wajen Allah, akan Allah ya zaɓa min abinda ya fi zama alkhairi a rayuwata. Can naji motsi na juya na kalli gadon, shi na gani ya farka ya tashi zaune, kuma har lokacin bai suturta jikin shi ba, ko kunya ba ya ji shi gashi ba kaɗan ba. Kauda kaina nayi na cigaba da azkhar ɗina, dan bai ganni ba da alama barcin bai gama sakin shi ba. Ji nayi ya buga wani irin ihu, yana nuna ni. Cikin tsoro na kalle shi, da sauri na ƙara kauda kaina ina kallon gefena ko yaga wani abin tsoro ne, dan har lokacin ba komai a jikin shi yana tsaye bakin gado. "Baki da hankali baki jira ni ba ki ke sallah?." Ya faɗi hakan yana nufo inda nake. Cikin mamaki nake kallon shi, wanne irin in jira shi in zan yi sallah? Sai kace shi zan wa sallar. Jin da nayi ya fincike dardumar da nake kai, har sai da nayi baya na faɗi, cikin jin zafi nace "Wash me na maka?." Rufe ido ya yi ya fara faɗa "Ya za ki yi sallah ba tare da izinina ba, gashi yanzu kin ɓata min komai kin ɓata min aiki, wayyo Allah na wannan yarinyar baki da hankali wallahi." Yana gama faɗin hakan ya wuce ni tiɓi-tiɓi ya ɗauki wayar shi dake gefen gado. Sakin baki da hanci nayi ina kallon ikon Allah, wanne irin sai na jira shi zan yi sallah? Ban gama tunani ba naji ya danna kiran waya. Cikin tashin hankalin dake shinfiɗe a fuskar shi ƙarara yace "Hello Malam Barka da safiya." Jim kaɗan naji yace "Ina fa lafiya yarinyar nan ta ɓata mana aiki baki ɗaya." Bansan me wancan yace ba naji yace "Kasan nauyin barcina fa Malam, to Wallahi sai farkawa nayi na ganta zaune har ta gama sallah, ta cuce ni wallahi." Gaba ɗaya ban fahimci abinda yake nufi ba, kaina duka ya ɗaure, ina mamakin duk akan sallar da nayi ya shiga tashin hankali haka? Ko kuwa wani abin na masa daban da ya tashi hankalin sa?. Da sauri naga ya aje wayar, ya juyo ya kalle ni a wani irin fusace ya yi ƙwafa ya nufi toilet a yadda ya ke bai ɗaura komai ba, ya banko ƙofar. Na daɗe zaune yadda kuka san wadda aka dasa a wajen, gaba ɗaya ban san dame zan kira abinda ya faru yanzu ba. Har ya fito toilet ɗin ɗaure da towel a ƙugun shi, jikin sa sai maiƙo ya ke kamar ba wanka ya yi ba watsa ruwa ya yi. Haka ya nufi kan gado, cikin mamaki naga ya ɗauki kayan da ya cire jiya ya saka ba tare da ya goge jikin sa ba. Yana sawa ya ɗauki dardumar da ya yi cilli da ita, ya shimfiɗa cikin mamaki nake kallon shi ganin ba gabas ya kalla ba kuma ya tada Sallah. Sai da ya yi raka'a biyu, ya daɗe bai ɗago ba. Ba tare da sallama ba naga ya jawo wani dogon carbi ya fara ja. In ba ƙarya nayi ba, ya fi awa yana zaune, dan ƙarshe tashi nayi na koma kan gado saboda yadda jikina ke amsawa, ga wani irin zazzaɓi da ke son rufe ni. Duk da kuwa tarin yunwar da nake ji, amma nafi buƙatar hutu akan abincin. Gani nayi ya ƙara tashi ya juya dardumar gabas, ya tada Sallah normal kamar yadda ake yi, ya yi sallama ya zauna cikin mamaki naga harda Alqur'ani ya ɗauka, tiryan-tiryan naji ya fara karatun Alqur'ani, babu ɓata ko gyara yana fitar da kowanne harafi dai-dai, sai dai salon karatun nashi Irin na yarabawa ne, yana yi ne kamar waƙa-waƙa. Rasa wanne matsayi ya kamata na aje shi nayi, to ita waccan sallar da ya yi ya sunan ta? da uban carbin da ya dinga ja duk da ban san abinda ya ke cewa ba. Dan bakin sa ne kaɗai ya ke motsi. Yana gama karatu ya ɗaga hannu ya yi addu'a ya shafa, ya tashi ya naɗe dardumar ya maida ta wajen ta. Ganin ya nufo gadon nayi saurin runtse idanuna kamar mai barci. Zama ya yi a gefen gadon, ya yi murrmushi me sauti tamkar bashi ba yace "Dama kin daina wahalar da kanki kin tashi, ba wani abu zan miki ba buƙatar hakan bata taso ba." Ya ɗan ja bargon dana rufe rabin ƙafata dashi. Da sauri na zabura na tashi ina zare ido. Ya kalle ni tare da fashewa da dariya abin takaici, ya shiga nuna ni yana faɗin "Matsoraciya wato yanzu kin banbance aya da tsakuwa kenan? Ni kinga fita zan yi, kuma ba daɗewa zan yi ba dan haka in akwai abinda ki ke son ci ki faɗa min, sai na taho miki dashi dan nasan ba iya shiga kitchen za ki yi ba. Kuma ki kasance cikin shiri dan muna da babban baƙo yau a gidannan, bana son ki yi wani abu da zai ɓata min rai ko ki ja min wata asarar kin ji na faɗa miki." Gaba ɗaya ban fahimci zan cen saba, sakamakon yadda ya yi maganar ta yadda ba zan fahimta ɗin ba. Dan ni ban fahimci asarar da ya ke nufi na ja masa ba, bare har na ƙara yanzu. Dan haka na ja tsaki cike da tsiwa nace " Kai ka jiyo mugu azzalumi kawai, kuma abinci bana ci ka barni yunwar ta min abinda zata min." Cikin fusata ya kawo hannu kamar zai dake ni, ko me ya tuna sai ya dunƙule hannun tare da cije baki cikin kakkausar murya yace "Daraja ɗaya ki ka ci, ke ɗin baƙuwa ce bayan haka jiya da daddare kin bani nishad'i duk da ba yadda na saba samu bane, amma sa'ar ki ɗaya na same ki da mutumcin ki. Da sannu za ki san ko ni waye, watarana ko an baki kuɗi akan ki min rashin kunya ba za ki min ba." Yana gama faɗin haka ya miƙe, fuska a ɗaure ya fita daga ɗakin tare da bugo ƙofar. Tsaki naja nabi bayan shi da harara, na maida kaina na kwantar ina jin tsanar shi na ƙara samun wajen zama a zuciyata. **** Barci ne ya ɗauke ni mai nauyin gaske. Wata azababbiyar yunwa ce ta tashe ni yadda kuka san babu ƴaƴan hanji a ciki na. Da ƙyar na yunƙura na tashi ina jin ciwo a jikina har lokacin, na sauka gadon da dubara na nufi toilet, fitsari na yi na wanke fuskata na fito ina tafiya a hankali jikina duk ciwo ya ke min. Farlo na fita, a buɗe na tarda ƙofar farlon naja tsaki na je na rufe. Sai lokacin hankalina ya kai wajen Dining table sai naga kulolin abinci har biyu, sakamakon yunwar da nake ji sai naji wani daɗi a raina. Ina buɗewa naga shinkafa ce fara, sai wake dafaffe ɗaya ƙaramar kular miya ce da ganda da kifi. A zuciya nake faɗin _Da sanyin safiyar nan aka dafa shinkafa_ Sai da na kalli agogo naga har ɗaya ta gota, ashe barci nasha haka ban sani ba. Kitchen na shiga na ɗauki filet, na zuba shinkafar na sa iya kifin dan ganda bata wani dame Ni ba. Ba dan daɗi ba naci abincin, dan miyar bata min yadda nake so ba. Bayan na gama na wuce ɗaki, sai da na ƙara wanka na gasa jikina sosai na ɗaura alwala na fito. Sallah nayi na ɗan tattara ɗakin zuwa farlon. Ban damu da wata kwalliya ba, dan banga abinda zan wa kwalliya ba duk da irin son gayuna kuwa. Iya riga da sket na atamfa nasa abuna, ko ɗaurin ɗan kwallin ban wani tsaya ba kaina wahala ba haka na coke shi. Wayata na ɗauko na dawo farlo na zauna, sai na tarda miss call da yawa, harda na su Aunty Zulai da Abbanmu sai Mama Hajara ita ma kira biyu na gani nata. Wata irin kunya na ji ta kamani, ban kyauta ba tunda su Aunty Zulai suka tafi da na kira sau ɗaya suka ce suna ilori ban ƙara kira ba. Haka su Abbanmu tunda aka kawo ni, ban kira kowa ba, to ina naga kwanciyar hankali ma. Kiran Abbanmu na fara yi, na gaida shi cike da ladabi. Ya amsa min yana faɗin "Babu kiran gida Rahamah, ko baki ji kewar mu ba?." Idanuna ne naji sun ciki da ƙwalla, murya na rawa nace "Ka yi haƙuri Abba, fatan duk kuna lafiya yasu Amminmu da Mama Hajara, da su Yakubu da Ummi da Aminatu." Amsa min ya yi kowa lafiya, nan ya shiga yi min nasiha akan zaman aure. Cikin mamaki sai naji yace "Al'amen ya kira ni yau, yana ta jera godiya, har ya turawa Baba Usman kuɗi har dubu ɗari uku wai a rabawa duka dangin mu, ya yaba da tarbiyyar ki da hankalin ki. Rahamah dan Allah na roƙe ki ki riƙe mijin ki hannu bibbiyu, daga gani mutumin kirki ne, kuɗin shi bai taɓa burge ni ba Rahamah, karki zauna da shi dan dukiyar shi ki zauna da shi dan Allah. In sha Allahu ba za ki yi nadamar auren shi ba." Ni dai sauraren Abba kawai, a zuciyata ina faɗin _Abba baku san wa kuka aura min bane._ Nan ya gama min nasiha, ya ƙara da ban haƙuri da lallashi akan zaman kaɗaici ya kuma ce baya son ya ji ance ga matsala daga ɓangarena. Ina sallama da Abba nabi sauran kiran, nasha ƙorafi wajen Aunty Zulai akan ban kira ba. Na dai bata haƙuri wannan ta wuce, na kira su Amminmu da ƙannena muka gaisa. Ana kiran la'asar Islam ɗin Aunty Fati ta shigo, bayan ta gaida ni ta bani abincin da Aunty Fati ta aiko ta kawo min. Da ya ke bata wani sakewa dani, bata jima ba ta tafi abinta. Kaiwa kitchen nayi ina jin daɗi, na huta da cin abincin waɗan can mutanen. Wajajen magriba sai ga sallamar Al'amen, cikin mamaki nake kallon bayan shi ganin shi tare da wani mutumi sun shigo farlon kai tsaye ba tare da neman izini ba. A rikice na fara neman ɗankwalina na ɗaura, na haɗe rai sosai ganin mutumin ya zauna a kujerar dake fuskantar tawa, ya wani zuba min ido dake cike da kwalli kamar tsohon boka, ga wani uban carbi fari sai faman ja ya ke yana mui-mui da baki. Kujerar da nake kai Al'amen ya zauna. Ya wani ɗora min jabgegen hannun sa a kafaɗa, ya matso da fuskar shi saitin tawa yana wani lumshe ido shi a lallai sai ya nuna min love. A takure nake sosai, dan kusan rabin cinyar shi akan tawa take. Dan kujerar me biyu ce shi kaɗai ma ya isa ya cinye ta. Kauda kaina nake ta faman yi, dan in ba ƙarya hanci na ya min ba kamar ina jiyo wari-wari na tashi a hammatar shi. Ga ya kawo bakin sa dai-dai fuskata yana magana, sai feshin yawu ya ke min, iskar dake fita a bakin sa kanta na min wani irin wari wari. Gaba ɗaya zaman wajen a takure nake. Gyaran murya mutumin ya yi yana wani ƙasa-ƙasa da ido yace "Jagaba a ɗan rage haka mana, bari mu gama magana in ya so in na tafi ayi soyayyar ko." Ya ƙarasa maganar cikin ƴar ƙaramar dariya. Washe baki Al'amen ya yi, babu zato naji ya yi kin kiss gefen kumatuna ya sake ni yana gyara zaman shi yace "Ai yarinyar ce Malam ke sa na rasa nutsuwata." Dariya ya yi kaɗan ya gyara zaman hiramin shi, ya shiga ƙare min kallo yace "Ai babu laifi naga Kyakykyawace dai-dai da yadda nace maka." Gaba ɗaya rasa tunanin da ya kamata nayi nayi, anya Al'amen yasan meye Musulunci kuwa? In ya sani me yasa ya ke abubuwa kamar jahili, Ni kaina duka ya ɗaure na rasa a wanne matsayi zan sa shi, wasu abubuwa nake gani a tare da shi, tun safiyar yau har zuwa yanzu waɗan da basu yi kama da koyarwar addinin Musulunci ba. Tun daga kan ihun da ya min akan nayi Sallah, zuwa sallar da shi ya yi ba tare da ya kalli gabas ba. Zuwa wayar da ya yi da maganganun da ya faɗa min na karna ƙara ja masa asara. Sannan ga shigo min gida da ya yi kai tsaye da wannan mutumin da sam bai min kama da mutanen kirki ba, kama ya ke min da irin malaman tsubbu ɗin nan. "Yanzu dai ba wannan ke Amaryar mu wajen ki na zo takanas, nasan baki Sanni ba tunda yau kika fara gani na. Ni sunana Malam Mustafa, Ni ne ke kula da duk wasu harkoki na cigaban kasuwancin mijin ki, Alhamdulillahi kuma ina alfahari da hakan, tunda kullum yana ƙara ganin buɗi da yalwa a cikin kasuwancin nasa dan yana taimako sosai a ciki." Gaba ɗaya maganganun sa ƙara tsunduma ni cikin kogin tunani suka yi, magana ya cigaba da yi "To yanzu kin take wani Sharaɗin mu ne yau, amma bisa dole mun miki uzuri sakamakon rashin sani ne ya jawo hakan. Ya kamata ace kafin ki yi sallah ki nemi izinin mijin ki, ya faɗa miki yadda za ki yi, sai kika kalli gabas kai tsaye ba tare da cika umarnin mu. Ya kamata ace kin fara kallon arewa tukun, sannan ki ja carbi akwai addu'o'in dana koyar da shi, in ya koya miki sai ki yi su. To daga nan zaki iya sallar ki ki kalli gabas harma da sauran ibadun ki, muna dai so ace ita wadda ake kallon arewa ɗin kika fara." Gaba ɗaya ji nayi jikina na wani irin rawa, nan da nan zuciyata ta fara min zafi. Buɗe baki na nayi da nufin sauke masa kwandon fitsara daga shi har wanda ya kawo shi. Sai dai muna haɗa ido jikina ya yi wani irin lak'was kamar an watsa min ruwa, yadda kuka san an sa makulli an kulle min baki gaba ɗaya na kasa magana. Sai faman raba ido da nake, zuciyata na wani irin zafi kamar ana hura min wuta a cikin ta. *_🥰MAMAN ƊAN ALBARKA CE 🥰 ✍🏻✍🏻_* [1/18, 07:15] Ummu Sultan Ceh3: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/EJJOOxsRu8dKh9gocmSFuG *BAƘAR ZUCIYA!.* *_🥰MAMAN ƊAN ALBARKA CE 🥰✍🏻✍🏻_* *_LITTAFIN KOWA YAƘI JI YA KAMMALA COMPLET GA DUK ME BUƘATA TA MIN MAGANA TA WANNAN NUMBER 09014644247_* *PAGE6️⃣* A Hankali nake bin su da kallo dukan su, ina sauraren bayanin da mutumin da ya kira kan shi da Malam ya ke. "Kina jina Amarya. Yanzu tunda kin riga da kin ɓata mana cikin rashin sani, ki tashi ki yi alwala ki zo ki yi sallar a gaban mu, dan karki yi kuskure komai zai yi daidai." Jinjina kai Al'amen ya yi, ya kalle ni ganin ban motsa ba har lokacin. Ya kama hannaye na duka biyun, yana bin fuskata da kallo cikin son na kalle shi yace "Rahamah ki tashi ki je ki yi alwala ki zo ki yi sallar kin ji." Kauda kaina nayi ba tare dana kalle shi ba, so nake na buɗe baki na na ci musu mutumci, na faɗa musu su ji tsoron Allah amma na kasa hakan. Bana jin duk abinda zai faru, zasu iya rinjayata na biye musu na aikata shirka, dan ni iya fahimta ta kenan shirka Al'amen ya ke aikatawa saboda neman duniya. Cigaba ya yi da magana cikin lallashina "Rahamatah ki tashi ki je Please, ko ba kya son ki cigaba da more rayuwa ne?." Yi nayi kamar ba da ni ya ke magana ba, a zuciyata nace _More rayuwa a ina? Mugu kawai cutar da rayuwa dai._ Daga ƙarshe da naga sun min rubdugu akan na tashi na yo alwala, sai na zare hannuna cikin nashi, na miƙe tsaye ba tare dana kalle su ba nace "Babu alwalar da zan yi na zo, ku cire rai zaku iya dilmiyar dani ni Rahamah bana haɗa Allah da kowa." Ina gama faɗin haka na wuce bedroom na kulle ƙofar na bar mukullin a jiki, bakin gado na zauna ina sauke ajiyar zuciya. Iya wannan maganar da na faɗa musu, ba ƙaramin ƙoƙari nayi ba wajen dakewa, ina faɗar maganar zuciyata na wani irin bugawar tsoron su duka biyun. Ni kaina nasan Allah ne ya bani iko kawai na iya faɗa. Al'amen cike da tashin hankali ya fara kiran "Rahamah Rahamah! Ki dawo fa." Ya tashi da ƙyar ya bi bayan ta kafin ya ƙarasa ta rufe ƙofar. Bugun ƙofar ya shiga kamar zai ɓalla ta, yana faɗin na zo na buɗe ko raina ya ɓaci. Ina ji nayi shiru na ƙyale shi, ko me zai yi sai dai ya yi amma ba zan buɗe ƙofar nan ba Wallahi. Ina jin lokacin da Mustapha ya zo bakin ƙofar, yana faɗin "Jagaba ƙyale ta, mu mata uzuri a bita a sannu watarana da kanta za ta yi ba sai ka sata ba, kaga taho mu tafi ka ji." Da ƙyar ya janye Al'amen wanda ranshi ya kai ƙololuwar wajen ɓaci. Ina jin shi yana faɗin "Za ki san ni kika wa gardama ai ba'a ɗakin za ki dauwama." Tsaki naja a zuciyata ina neman tsari daga sharrin su. Dai-dai nan na ji kiran sallar magriba, tashi nayi na ɗauro alwala na tada Sallah. Na daɗe ina addu'o'i akan Allah ya tsare ni daga kaidin Al'amen. Dan na fuskanci dole sai na tashi tsaye da addu'a, wannan abin nashi ba lafiya ba, dole akwai wata ƙullalliya a ƙasa. Amma nasan Allah shine kaɗai zai yi maganin duk wani shirin su. A fahimta ta kenan Aurena ma da Al'amen ya yi, bisa umarnin wannan mushrikin ne kenan? Danƙari ashe akwai matsala kenan da jan aiki a gabana. Na daɗe zaune ina kaiwa Allah mai kowa mai komai kukana, har sai da aka kira sallar Isha'i na yi tare da shafa'i da wuturi. Ina jin yunwa amma naƙi fita saboda bana son ko ganin shi nayi bare wani abu ya haɗa mu. Haka nayi wanka na ɗaura alwala tare da shirin barci, nayi duk addu'o'in da annabinmu (S,a,w) ya koyar na shafe jikina na kwanta ina jin zuciyata cikin wani irin yanayi. ***** *AL'AMEN* Ranshi a matuƙar ɓace ya ke da abinda Rahamah ta masa, da ƙyar Malam Mustapha ya rarrashe shi suka fita. Dama da motar Al'amen ɗin suka zo, dan haka suka shiga dan ya maida Malam gida. A hanya Al'amen dake tuƙi cikin fushi ya kalli Malam Mustapha yace "Na rantse da Allah kai ka dakatar dani, da sai yarinyar nan ta gane kuren ta." Dafa kafaɗar shi Mustapha ya yi yace "Kai matsalata da kai baka bin komai a sannu, karka manta ni ne wanda na shawo kan komai har ka samu ka auri yarinyar nan. Ko dai ka manta aikina ne, kar ka bari fushi ya jagoranci lamarin ka da yarinyar nan. Dan na fuskanci tana da ɗan motsi a kanta, dan yadda ta mana yanzu alamu sun nuna ba ita kaɗai bace. Zai iya yiwuwa tana da aljanu dan wannan kwallin dana sa a idona, babu halittar da zan kalla da shi bayan aljanu in basu umarni su take. Dan haka yanzu mu je ga aiki na gaba, ita zamu dawo kanta." Sai lokacin Al'amen ya ɗan ji dama-dama. Ajiyar zuciya ya sauke ya kalli Malam Mustapha yace "Amma kana ganin in aljanu ne da ita ba zasu dinga ɓata mana aiki ba?." Jinjina kai malam Mustapha ya yi yace "Eh to gaskiya ban tabbatar su ɗin bane, dan zargi nake ka bari na gama tabbatarwa tukun in ya so sai na duba naga waɗanne irin aljanu ne kafin na tantance komai." Maida kan shi ya yi ya cigaba da tuƙin yana faɗin "Shikenan in ka yi binciken maji. Maganar ɗaya aikin na riga da na samu yarinyar tuni, yanzu haka anjima zan je sabon gida dan mun yi da Bukar zai kawo ta anjima, matsala ɗaya ce kawai bana son nayi dare a waje tunda kaga yarinyar nan na nan. Gasu Hajiyar mu, bana so su zargi wani abu suga ban dawo da wuri ba." Gyara zaman shi Mustapha ya yi yace "To me zai hana zuwa gobe ka tattara ta ku koma sabon gidan, kaga sai ka fi samun sakewa, tunda can a kwai ɗakuna da sashin da ba kowa ma. Dan gaskiya aikin mu na buƙatar lokaci." Nan da nan ya yi na'am da wannan shawarar, ya amsa da "Hakan ya yi." Daidai lokacin da suka iso ƙofar gidan Malam Mustapha, gidane ƙarami irin na masu ƙaramin karfi, yana sauke shi ya buɗe ƴar ƙaramar ƙofar gidan ya shige. Al'amen ya juya kan motar ya ɗauki hanyar sabon gidan shi. Koda ya shigar da motar, bayan sun gaisa da me gadin shi. Kai tsaye ya nufi ƙofar babban farlon shi. Zaune ya tarda wani mutumi baƙi dogo,bashi da jiki kwata kwata irin siraran mutanen nan ne. Gefen kujerar da ya ke kai, wata mace ce zaune tana da ɗan jiki kaɗan a ƙalla zata kai shekara talatin, fara ce amma daga gani farin mai ne. Idanun ta a tsatstsaye suke daga gani irin marasa kunyar matan nan ne, sai faman taunar cingum take tana wani kwarkwasa. Sanye take da wasu irin riga da sket na atamfa, waɗan da aka musu wani shegen ɗinki duk kusan jikin ta a waje ya ke. Hannu Al'amen ya miƙawa mutumin, wanda na ji ya kira da Bukar. Idanun shi akan yarinyar da ita ma ta ƙure shi da ido. Bayan sun gaisa, Bukar ya miƙe yana nuna yarinyar yace "Gata nan dai Jagaba, nasan duk wani abu da kake buƙata zaka samu a gare ta, dan Sa'a bata da matsala ƙwararriya ce ta gaske." Dariya Al'amen ya yi yana wani bin matar da kallon ƙasan ido, ya kalli Bukar tare da miƙa masa hannu suka ƙara gaisawa yace "To ka kyauta sosai, ta yi min nima kuma yadda nake so." Yasa hannu a aljihun sa ya ƙirga kuɗi dubu ashirin ya bawa Bukar. Amsa ya yi yana washe baki, ya yi godiya ya juya tare da cewa yarinyar sai sun haɗu, ya fice daga farlon. Al'amen kam nufar ta ya yi ya miƙa mata hannu, babu musu ta bashi nata tana wani irin kwarkwasa. Kai tsaye saman bene suka nufa, ɗakin farko ya kaita ya rufe ƙofar. *** *RAHAMAH.* Can cikin barci na ji kamar ana shafa ni, zabura na yi na tashi zaune ina zazzare ido cikin duhun ɗakin. Ji nayi an ƙara kamo ni, ba sai an faɗa min ba, nasan Al'amen ne. Sai dai ina mamakin yadda ya ke shigo min ɗaki, koda kuwa na rufe ƙofar na bar makullin. Ture shi na shiga yi ina faɗin "Dan Allah sake ni, wai me ma ya kawo ka ɗakina, ta ina ka shigo min ma?." Kunna fitilar gefen gadon ya yi, ina iya ganin shi shima yana gani na. Ya wani kafe ni da ido cikin wata irin murya yace "Ke ki ke da gidan Da za ki na tambayar yadda na shigo?." Ya ƙara yowa wajena da nufin kama ni, kaucewa na yi da sauri dan gaba ɗaya wani irin wari ya ke min, kuma ba warin komai bane sai warin zufa. Irin mutum ya wuni a ranar nan ya sha aikin wahala ya yi zufa ɗin nan. Ga bakin shi da in ya yi magana kusa dani, da nake jin yana tashi. Har ga Allah har wani amai-amai nake ji. Saboda a rayuwata na tsani wari, haka hancina yana da saurin jin wari ko ƙamshi ko ya ya ne kuwa. Ina ja baya ina komai, haka ya haɗe ni da fuskar gadon. Yau ma abinda ya min jiya ya maimaita, sai dai yau cikin hayyacina nake. Nasha azaba ba kaɗan ba. Yana komawa gefe na tashi da ƙyar na nufi toilet na fara sheƙa amai kamar zan amayar da ƴaƴan hanjina. Saboda uban warin da na shaƙa a jikin shi, gaba ɗaya cikina ya hautsine. Ban fito daga toilet ɗin ba, sai da nayi wanka na haɗa da wankan tsarki na ɗauro alwala, ina bin bango na fito na sa kaya na tada Sallah. Raka'a biyu nayi na daɗe a sujjadar ƙarshe ina kaiwa Allah kukana. Na zauna tare da yin addu'o'i na, akan neman mafita wajen Allah akan wannan auren nawa. Anan barci ya kwashe ni. Jin motsin mutum kusa da ni yasa na buɗe idanuna dake cike da barci, cikin mamaki na ƙara ware idona akan shi. Al'amen ne tsaye yana Sallah a gefe na, cikin shigar jallabiya. Cikin nutsuwa ya ke sallar tashi, kuma gabas ya kalla saɓanin jiya. Kallona na kai ga agogon ɗakin, sai naga ƙarfe ukun dare 3:0am. A zuciyata nace _Ikon Allah shima nafila ya ke yi kenan?_ gaba ɗaya na rasa in da ya kamata na aje Al'amen. Dan abubuwan da ya ke ƙara sani cikin ruɗani suke baki ɗaya. Yana idar wa naga ya ɗauki Alqur'ani, ya shiga karatu kamar yadda ya yi a safiyar yau. Tun ina kallon shi har barci ya ƙara ɗauka ta. Da safe koda na farka ban ganshi a ɗakin ba. Dan haka na tashi na tattara ɗakin na gyara, na fita farlon shima na gyare shi tsaf rana ta farko dana ji sha'awar in sa turaren wuta a gidan. Dan haka na koma ɗakin, cikin kayana da suka rage anan, saboda duk sauran dama ba'a kawo su nan ba, kai tsaye wancan gidan da yace zamu zauna aka kai har kayan gadona da komai an gama min jere na. Zuwa kaɗai ya rage. Nan iya abubuwan da zan yi amfani dasu ne kawai. Ina cikin zuba turaren sai ga sallamar shi ya shigo, sanye dai ya ke da jallabiyar da zan iya cewa ta gado ce. Dan tunda nazo ita naga yana sawa. Hannun shi riƙe da carbi alamar daga masallaci ya ke. Tunda na kalle shi sau ɗaya na ɗauke kaina, sai ya ƙaraso kusa dani yana ƙoƙarin riƙo hannu na na kauce. Ya ɗan ɓata rai yace "Gaida ki zan yi tunda naga ke baki iya gaisuwar ba, duk da nasan ba tarbiyyar da aka baki kenan ba kin tsirowa kan ki ne." Bance masa komai ba, na ƙara ja baya. Ya kalle ni tare da taɓe baki yace "Ki riƙe jikin ki, Ni yanzu abinda nake son faɗa miki, ki kasance cikin shiri yau zamu koma sabon gidan mu. Saboda haka ki wuce ki fara shiryawa. Sannan ki je wajen Hajiyar mu ku gaisa, dan tace dama bakya zuwa kina gaida kowa a gidan nan tun ranar da aka kawo ki. Ki kula bana son rashin mutumcin ki ya shafi iyayena, duk abinda za ki yi ki yi ƙoƙarin kaucewa ɓata musu, karki bari a dinga kawo min ƙarar ki." Yana gama faɗin haka, ya juya ya nufi bedroom. Ganin ya kusa shiga yasa na ɗaga murya nace "Babu in da zani na gaida waɗan da ba jin Yaren su nake ba, Iya gidan Aunty Fati kawai zan je na mata sallama." Har ya kama mariƙin ƙofar zai shiga, jin maganata yasa ya fasa ya dawo da baya. Ya ƙaraso wajena ya nuna ni da hannu cikin kashedi yace "In kin cika mara kunya karki je, in har baki je ba ko gidan Aunty Fati ɗin ba zaki je ba." Ya juya ya tafi ya barni tsaye. Tsaki naja na bi bayan shi da kallo, kamar nayi dariya ganin yadda ya ke tafiya a wani barbaje kamar buhun fulawa. Na kauda kaina na zauna kan kujera ina shawara da zuciyata. Allah ya sani bawai son shiga cikin gidan ne bana yi ba, kwata-kwata wannan hayaniyar tasu ce bana so. Basu iya komai a hankali ba, sai ihu da hayaniya ka rasa ma me suke cewa duka. Nasan in ya hana ni zuwa gidan Aunty Fati, ban isa na je ba. Dan sai me gadi ya buɗe min ƙofar zan fita, na kuma san cewa zai yi kar ya buɗe min. Dan haka sai kawai na nufi ɗakin, zaune ba tarda shi ya baje a ƙasa babu ko riga a jikin shi. Daga shi dai gajeren wando wanda ko cinyar shi bai gama rufewa ba. Kuɗi ne dami-dami a gaban shi yana ta faman lissafi. Yana ganina ya wani haɗe rai, na kauda kaina tare da taɓe baki na wuce wadrobe na ɗauki Hijabina har ƙasa nasa, na kalle shi nace "Na tafi wajen Hajiyar." Bai min magana ba, sai jinjina kai da ya yi ya cigaba da lissafin sa. A zuciyata nace _Ko ance masa kuɗin sa ya dame ni ne? Da ya wani haɗe rai dan ya ganni_ Da sallama na shiga farlon, wata mata na gani zaune da alamar ƴar aiki ce. Tana ganina ta miƙe ta shiga gaida ni cikin gurbatacciyar hausar ta. Amsawa nayi nace "Ina Hajiya?." Nu ni ta min da saman bene tace "Ya shiga ciki." Waje na nema na zaune a kan ɗaya daga cikin kujerun farlon, na ɗaga idanuna ina bin farlon da kallo a hankali. Gani nayi matar ta doshi saman, alamar zata sanarwa Hajiyar da zuwana kenan. Babu jimawa ta sakko tace min "Yace ka shiga." Ba dan na so ba, na tashi na nufi saman ina bin ko'ina da kallo. Ƙofa ɗaya ce kawai a saman, dan haka na tura na shiga da sallama a bakina. Ɗan ƙaramin farlo ne, me ɗauke da setin kujeru ɗaya, da tv dake manne a bangon dake kallon ƙofa, sai wani ɗan tebur ƙarami dake tsakiyar farlon remote ne akan shi da wani ɗan kofi alamar Abu aka sha a ciki. Daga ciki na ji ance "Ki shigo ina ciki." Nufar ƙofar da na ji maganar na yi, na yi sallama aka amsa na shiga. Tana zaune a bakin gado, gaban ta wasu takardu ne tana duddubawa idanun ta sanye da gilashi irin na ƙara ƙarfin gani ɗin nan. A ƙasan carpet ɗin nake ƙoƙarin zama, ta ɗago ta nuna min gefen ta tace "Dawo nan ki zauna, ya za ki zauna a ƙasa." Zama na yi nace "Ki barshi Hajiya nan ma ya isa, dan ina ganin yau dai ba zan iya zama kusa da ita ba, dan haka baya cikin kunyar da aka sanmu da ita ga surukai mu Hausawa kenan. Ganin na riga dana zauna, sai bata ce komai ba ta aje takardun ta fuskance ni tana murrmushi. Na gaida ta ta amsa, tare da tambayar lafiya ta, harda cewa fatan ina kula mata da yaron ta yadda ya kamata. A bakinta ma nake ji, ashe Al'amen yana da yayu maza biyu da mata uku, sai ƙaramar ƙanwar shi tace tana aure a ibadan. Kuma tace gidan Yayan Al'amen ɗayan ma yana jikin gidan mu, matan sa biyu da yaran sa. Ni dai jinta kawai nake, a raina nace _Sai kace na tambaye ta._ Ta daɗe tana bani labarin su, tare da min nasiha akan dai na kula mata da ɗan ta. Ni kam nace _Ɗan ki kaɗai ki ka sani, ba ruwan ki da ƴar mutane da halin da take ciki._ Ban wani ɗauki lokaci ba nace mata zan tafi, nan ta tashi ta biyo bayana. Kitchen ta shiga ta haɗo min wasu abubuwa a leda, tace "Gashi na ɗan yi aiki da su kwana biyu, Al'amen na son su shi yasa. Ba tare dana san meye ba, na amsa na tafi. Koda na koma na tarda ya fito a ɗakin, anyi Sa'a ya yi wanka ya canja kayan jikin sa. Ko zama ban yi ba na aje ledar. Nace masa zan je wajen Aunty Fati. Miƙewa naga ya yi yace "Mu je na raka ki, dama ai ban je na mata ya gajiyar biki ba." Kallon mamaki na shiga bin shi da shi nace "Ba sai ka bi ni ba, ina zaton ai in zaka gaisheta zaka iya zuwa daban ko?." "To ni tare nake so mu je, in ba haka ba sai dai ki fasa tafiyar." Bisa dole ina ji ina gani haka muka jera, duk da muna fita muka shiga gidan Aunty Fati ɗin, amma sai na tsinci kaina da jin kunyar yadda na jera da shi abu Ruguzaza haka. Wajen me gadin Aunty Fati ya zauna, na wuce ciki na tarda yara ne kaɗai a farlon. Suna ganina suka taso a guje suna min Oyoyo. Iya Kamal kaɗai na ɗauka, na dungurewa Islam kai nace "Ke ba ruwana da ke, dan baki da kirki matsa ki bani waje dan Allah, wannan shi ne ɗana." Matsawa ta yi tana ɓata rai, ban bi ta kanta ba na wuce bedroom ɗin Aunty Fati kai tsaye dan Kamal yace tana ciki. Linkin kaya na tarar tana yi. Tana gani na ta fara fara'a tana kallona cikin murna tace "A'a Amarsusu ta angon ta mai abin mamaki, ku ne tafe kenan?." Ta ƙarasa faɗar tare da miƙewa tsaye ta nufo ni. Aje Kamal na yi muka rungume juna, cikin dariyar farin ciki nace "Gamu kam Aunty Fati." Taja hannuna muka zauna bakin gado, ta fita ta dawo hannun ta ɗauke da filet da ruwa da lemo me sanyi. Bayan nasha ruwan na cire ɗankwalina ina gyara zama na kan gadon ta, ina bin ɗakin nata da kallo nace "Wai Aunty kayan ɗaki ki ka canja?." Tana dariya tace "Wallahi kam ai tun kafin bikin ki, Abban Kamal ya canja min baki kula da kujerun farlon ba kenan?." Girgiza kai na yi ina jin daɗi a raina, haƙiƙa Aunty Fati ta yi sa'ar mijin aure. Yana matuƙar son ta yana kyautata mata sosai, baya barin ta ta yi kuka akan komai, duk wani abu na jin daɗin rayuwa yana ƙoƙari wajen ganin ya wadata su da shi. Koda ina budurwa ina sha'awar rayuwar su, gwanin burgewa ba zaka taɓa jin kan su ba. Sai na ji dama nima haka na yi sa'ar miji kamar ta, ai da na more bani ba kuka. Cikin farin ciki nace "Allah ya sanya alkhairi, wallahi kuma naga farlon ya canja min fa, Allah dai bai bani ikon in lura da kujerun ba." Tashi muka yi muka nufi farlon, na dudduba tsadaddun kujerun har Tvn bango Ya canja babba ce yanzu, na musu addu'ar Allah ƙara masa buɗi na alkhairi. Ta amsa da Amen. Sallamar me gadin ta ita tasa muka juya, sai lokacin na tuna da Al'amen nake tare. Cewa ya yi wai Al'amen yace ya na neman iso. Salati Aunty Fati ta fara tana tafa hannu idanun ta a kaina tace "Ke yanzu dama tare ku ke? Ki ka shanya bawan Allah a waje baki ce na shirya ya shigo ba." Turo baki na yi gaba murya a shagwaɓe nace "Ni fa murnar ganin ki ce tasa na manta da shi." Dungure min kai ta yi ta nufi ɗaki tana faɗin "Ina kin ga dama ki je ki shigo da shi." Ina ɓata rai ina komai na fita, a bakin ƙofar farlo na tsaya na ɗaga muryata da ya ke ina hango su nace "Wai ka shigo." Na juya na koma ciki abina, Aunty Fati ce ta fito sanye da hijabi. Sai gashi shima ya shigo da sallama, hannun sa cikin na Kamal Yana wani sunne kai kamar na Allah. Zama ya yi kan kujerar, ya gaida Aunty Fati harda yin ƙasa da kai a zuwan girmamawa, yana wasa da Kamal daya haye cinyar sa. Shiru muka yi duka, Aunty Fati ta kalle ni ta banka min harara tace "Tashi ki kawo masa ruwa da lemo." Ba dan bana so ta gane wani abu tsakanina da shi ba, da cewa zan yi ba zan kawo ba. Haka na tashi na shiga kitchen na buɗe frij na ɗauko ruwa da lemon na kawo. Haka ta maida ni na ɗauko kofi, sai da na zuba masa tukun ta ƙyale ni. Ruwan yasha kawai, ana jimawa ya miƙe yace "Zamu tafi." Kallon shi na yi nace "Ka je ni ma zan dawo." Girgiza kai ya yi ba kunya yace "Kin san akwai shirin kayan da za ki yi, ki taso mu wuce tunda kun ga juna." Mamaki ma nake ganin bai ji kunyar Aunty Fati ba, ina ƙoƙarin yin magana Aunty Fati tace "Ka je ka ɗan jira ta tana zuwa." Kafin ya fita, ya zaro kuɗi dubu ɗai-ɗai ya bawa su Islam. Ɗaki ta jani ta hauni da faɗan bata Sanni da halin musu ba, ya nake son ɓata wayona abinda bana yi shi zan nawa mijina. Ganin ranta ya ɓaci na bata Haƙuri, nace mata yau zamu koma gidanmu tunda dama ban faɗa mata ba. Addu'a ta bini da ita, tare da ƙara bani shawarwari. Ta haɗo min kayan mata da su turaruka da abubuwan da baza'a rasa ba, tace ita ma zata shigo anjima kafin mu tafi. Har waje ta rako mu, muka tura get muka shiga ina jin zuciyata duk ba daɗi. *_🥰MAMAN ƊAN ALBARKA CE 🥰✍🏻✍🏻_* [1/18, 07:15] Ummu Sultan Ceh3: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/EJJOOxsRu8dKh9gocmSFuG *BAƘAR ZUCIYA!.* *_🥰MAMAN ƊAN ALBARKA CE 🥰✍🏻✍🏻_* *_LITTAFIN KOWA YAƘI JI YA KAMMALA COMPLETE, GA MAI BUƘATA TA MIN MAGANA TA WANNAN NUMBER 09014644247_* *PAGE7️⃣* Bamu tafi ba sai da daddare, na samu rakiyar wasu daga cikin mutanen gidan, sai Aunty Fati daga nawa ɓangaren. Bata bar gidan ba sai da ta tabbatar ta ɗan gyara min wasu abubuwan, duk da ba wani aiki bane tunda an gama jere tuni. Sauran tace da safe Ni ma na gyara. Ni kaɗai na tsaya ina ƙarewa ɗakina kallo, haƙiƙa ba ƙaramin ƙoƙari iyayena suka yi ba, wajen narka dukiyar su suka sai min kayan ɗaki na gani na faɗa. Addu'a nayi musu akan Allah ƙara buɗi, ya basu ikon yiwa sauran ƴan baya fiye da haka. Na cire kayana na nufi toilet na yo wanka, da ya ke Al'amen ya je maida waɗan da suka rako ni. Nasan kuma zai dawo ko ma yaya ne, dan haka ban wahalar da kaina wajen rufe ƙofar ba na barta a buɗe nayi kwanciyata bayan na gama addu'ar barci na shafa. Ina cikin barci na ji maganar shi, tashi na yi zaune ina murtsuke ido na. Dan na yanke shawarar na daina nuna tsoron shi, tunda dai banda maganin shi sai Allah, gwara na kwantar da hankalina kawai zai fi. Kallon shi kawai nake, ganin shi da wata yarinya me kimanin shekara sha uku, wai ya kawo min ita ne ta dinga ɗebe min kewa. Ƴar wajen Ƴayan shi ce, Allah yawa mahaifiyarta rasuwa, yana fatan zan riƙe ta amana, kuma bai kawo ta dan na dinga sata aiki ba, iya karatu kawai za ta yi a hannun mu, yana son ace shi ya aurar da ita da hannun sa sakamakon zumuncin shi da ɗan uwan sa. Kallon shi kawai nake lokacin da ya ke maganar. Har zan ce ba zan riƙe ta ba, sai kuma nayi tunanin ai ba yarinya bace zata iya yiwa kanta komai, sannan ni ba aiki zan sa ta ba ba komai ba, to me zai dame ni da har zan ce ba zan riƙe ta ba. Ce masa na yi shikenan kawai, madadin naga ya kaita ɗaya daga cikin ɗakunan dake farlo. Sai naga ya fita ya kinkimo wata katifa ƴar madaidaiciya, wadda ban san ina ya samo ta ba, ya aje katifar a tsakiyar ɗakin. Ni dai ina ta kallon ikon Allah, ya kalle ni yace "Rahamah bani zanin gado ɗaya na shimfiɗawa yarinyar nan." Tashi na yi na zauna na kalle shi nace "Wai me kake nufi, ba dai a ɗakin nan yarinyar nan zata kwana tare damu ba?." "A ina ki ke so ta kwanta to? ko so ki ke na barta a can ɗakin ta kwana mu muna nan kwance bayan amana ce ita gare mu." Al'amen yace hakan yana wani zazzaro ido. Ita kam yarinyar tana tsaye wajen madubi na, tana kallon mu. Cikin rashin damuwa nace "Amanar ka dai ba tawa ba, dan ni babu ruwana da ita Wallahi, kuma banga ta inda aka taɓa haka ba, yarinya kamar wannan kace ta kwana ɗaki ɗaya damu. To ai wannan ko ƴata ce Wallahi ba zan kwana da ita ɗaki ɗaya ba" Cikin fusata ya shiga magana "To Wallahi sai dai ki yi duk abinda za ki yi, amma tabbas tare zamu kwana da yarinyar nan." "To kwa bazan bada zanin gado na a shimfiɗa ba, kwana kuwa in ka ga dama ka kwanta kusa da ita ku yi barcin tare, tunda dai ba a gadona zata kwanta ba ai da sau.." Jin saukar wani gigitaccen mari a fuskata ya hana ni ƙarasa maganar, idanuna cike da hawaye na ɗago ina kallon shi hannu na dafe da kumatuna. Ban san lokacin da ya ƙaraso wajena ba, bare in san sanda ya ɗaga hannun shi, iya marin kawai na ji. "Ni ki ke faɗawa magana haka Rahamah?." Ya shiga nu na ni da hannu cikin kakkausar murya "Wallahi daga yau duk ranar dana ƙara magana, ki ka tsaya kina musu da ni sai na miki abinda baki taɓa zato ba, mara kunyar banza da wofi. Yarinya kuma anan zata kwanta, ba bu in da za ta je." Yana gama faɗin haka ya juya ya fice a fusace. Ni dai ina zaune na kasa cire hannuna a fuskata, hawaye ne kawai ke sintiri a kumatuna. Rabon da a taɓa lafiyar jikina har na manta, sai ga shi yau akan abin da bai kai ya kawo ba, wannan azzalumin ya ɗaga lafcecen hannun shi ya mare ni. Ina zaune ya dawo hannun shi ɗauke da ƙaton bargo, da alama na shi ne ya ɗauko mata. Haka ya shinfiɗa ya kamo hannun ta kamar ƙaramar yarinya, yace ta kwanta tayi kwanciyar ta abinta. Babu jimawa shima ya hawo gadon, lokacin tuni na gaji da zaman na kwanta, har lokacin hawaye basu daina zuba a idanuna ba. Ni kaɗai nasan halin da zuciyata take ciki. Ina jin shi ya jawo ni jikin shi ya shiga yin abinda ya saba, ko tari ban yi bare na hana shi yadda kuka san gawa haka na koma. Ina jin shi yana ta faman jan tsaki bayan ya gama abinda zai yi. Ya koma gefe ya kwanta, sai tashin munsharin sa da naji. Aman dai dana saba sai da nayi, ban yi barci ba tsahon daren baki ɗaya, kuka ne na yi shi har sai da naji idanuna na min zafi. Wajen ƙarfe huɗu na tashi nayi wanka na ɗauro alwala. Saboda katifar da ya aje babu inda zan shinfiɗa abin sallah, sai kawai na fice na koma farlo na tada Sallah. Raka'a biyu nayi barci ya ci ƙarfina, sama-sama nayi addu'a na rarrafa kan kujera sai barci. Ina shiga ɗakin naji wani uban zarni ya daki hancina, hannu nasa na toshe hancin na shiga bin ɗakin da kallo. Idanuna na sauke akan yarinyar da har yanzu bata ta shi ba, barcin ta take hankali kwance. Na kalli gadon sai naga babu Al'amen, duk yadda aka yi masallaci ya tafi. Na ƙarasa kusa da ita ina bin katifar da kallo, da ya ke gari ya waye sosai, a toilet ɗin farlo na yi alwala sai da na idar da Sallah na shigo ɗakin. Ganin bargon data kwanta a kai nayi a jiƙe Jagab. _Kenan fitsarin kwance take?_ Na tambaya kaina, nasa hannu naja fillon da ta kwanta akai. Ban san sunan ta ba sai na shiga faɗin "Ke ke ke tashi gari ya waye." Zabure ta tashi yarinya ba sai ta fashe da kuka ba. Tsayawa nayi kawai ina kallon ikon Allah, na shiga tambayar ta "Lafiya me ya same ki?." Muna cikin haka sai ga Al'amen ya shigo, ganin ta na kuka ya fara tambayar ta a ruɗe idanun shi a kaina. Ni dai naji Anisa da yace kawai, da alama tambayar ta ya ke, dan da yare ya ke maganar. Cikin kuka na ji ta masa magana da yarabanci, bansan abinda tace masa ba tunda ba jin Yaren nake ba. Nayi zaton in yaga fitsarin zai mata faɗa, dan in dai ba baya jin wari ba yaci ace tun shigowar shi ya ji warin fitsarin a ɗakin. Sai naga ya kamo ta ya miƙar da ita, jikin ta na ɗigar fitsarin ya kama hanyar toilet da ita yana faɗin "Dan kin yi fitsari shine ki ke kuka, wuce mu je ki yi wanka." Sai kuma ya canja baki zuwa Yaren su, kamar dai lallashin ta ya ke. Wata sabuwa kenan, abinda ba zan ɗauka ba kenan kwana da me fitsarin kwance ni da ban ko haihu ba, ace ina shaƙar uban warin fitsarin gardiya. Ina tsaye sai gashi ya fito, ya kalle ni yace "Ki tattara wajen ki kwashe bargon ki kai baya, anjima in me wanki ya zo sai ya wanke." Yi na yi kamar ba dani ya ke magana ba, nayi banza da shi na fice a ɗakin. Har farlo ya bini yana magana, "Ba dake na ke magana bane wai Rahamah." Dakatawa na yi na juyo nace "Wallahi ba zan yi aikin fitsarin kowa ba, ita data yi ta tattara ta fitar wajen. Kuma ta gyara min ɗakina tsaf dan ni bana ciki da ƙazanta." Ƙwafa ya yi ya juya yana faɗin "Duk abinda za ki yi, ki cigaba da yi Rahamah yarinya ce babu in da za ta fitsari kuma larura ce." Da kanshi ya ɗauke bargon, ya fito da katifar ina kallon shi ya kai waje ya shanya a rana. Babu jimawa ita ma yarinyar ta fito, ta yi wanka ta canja kaya. Kallo na take tana wani raɓe-raɓe, na ɗauke kaina na yi kamar ban ganta ba. Tashi na yi na shiga kitchen dan naga lokaci ya fara tafiya. Breakfast me sauƙi na nema mana, ina gamawa na jere komai na wuce ɗaki. Gyara ɗakin na yi da har lokacin nake jin zarnin fitsarin, haka na goge ko ina nasa turaren wuta dana tsinke da room freshener sai lokacin na ji ɗakin ya ɗan min dama-dama. Koda na fito na tarda tuni har sun fara karyawa, sun baje a tsakiyar farlon sunwa gun kaca-kaca babu kyan gani. Cikin mamaki na ke kallon flarsk ɗin shayin babu basu rage min komai ba, sai iya doyar dana soya Dan ita nayi sha'awar ci shi yasa na soyata da ƙwai. Ita ɗin ma duk sun sa hannu a ciki, haka kawai naji zuciyata bata kwanta da naci ba. Sai na wuce kitchen Dan na nemi wani abin, dan har ga Allah shi kanshi Al'amen ɗin, k'yank'yamin shi nake ji bana jin zan iya cin abin hannun shi. *** *BAYAN WASU KWANAKI* A haka rayuwar mu ta cigaba da gudana. kullum Al'amen ƙara fito min da sabbin halayen sa ya ke, waɗan da suke girgiza tunani na. A hankali na gama karantar shi, duk wasu abubuwan shirka da tsubbace-tsubbace ya iya su, sadaka kala-kala yasha shigowa da jar dawa ya Juye a ƙwarya ya sa kuɗi a kai da goro ya fita da su, wai sadaka zai bada saboda ƙarin haɓakar arziƙin sa. Yama daina ɓoye min komai yanzu, kai tsaye yake nuna min komai zai iya yi dan neman arziƙin sa. Duk da lamarin na damuna sosai, amma yadda kuka san wadda ka rufe wa baki nasha yunƙurin faɗawa Aunty Fati, sai na ji na kasa faɗa mata. Ga matsalar da muke yawan fuskanta a duk sa'ar daya kusance ni, aman nan sai na yi shi ga warin fitsarin Anisa da kullum sai ta tabka shi. Bisa dole na fara guduwa farlo duk da uban sanyin farlon, daga naga ya yi barci nake guduwa, kuma har yau babu ruwan shi in ya zo yana warin shi yana komai zai kusance ni, bana tantance komai sai wahalar da nake sha. A hankali na fara rama a tsaitsaye, kullum dare ya yi ina fargabar Al'amen ya matso kusa dani, ga fargabar warin fitsari banda takaicin yadda ya ke gudanar da wasu abubuwan nashi waɗanda ke birkita tunani kullum. Yau gaba ɗaya na tashi jikina babu daɗi, wata irin kasala nake ji haka kawai zuciyata ta dinga tashi. Ko abinci ban iya ɗorawa yau ba, har wajen ƙarfe takwas na safe ina kwance a farlo. Haka ya dawo masallaci ya tarda ni kwance, ganin ban ɗora komai ba, ba tare da ya tambaye ni lafiya ba? Ya hauni da faɗan iskanci ne ya hana na yi musu abincin karyawa. Na bar marainiya da yunwa waye-waye, maganganun dai kala-kala, Ni dai ina kwance ko ɗaga kaina na kasa yi saboda yadda nake jin wata irin hajijiya. Ina kwance ya fita ya dawo hannun shi ɗauke da ledoji, alamar abinci ya siyo musu dan harda tambarin gidan abincin a ledar. Ba tare da ya damu da ni me zanci na suka zauna suka ci suka ƙoshi, ya ja hannun Anisa suka fita. Kusan wuni guda na yi a farlon kwance, iya Sallah ce kaɗai ke tada ni na kasa sa komai a bakina. Ko ruwa nasha haka nake dawo dashi, gaba ɗaya na gama galabaita. Dana ji wuya sai na yanke shawarar kiran Aunty Fati, sai dai na kira yafi sau biyar bata ɗauka ba. Haƙura na yi da kiran na koma na kwanta idanuna na zubar da hawaye. Wajen ƙarfe huɗu na yamma sai gashi ya dawo, ban ga Anisa ba ko ba tare ya dawo da ita ba. Duk da ya ganni a yadda ya barni ya same ni, hakan bai sa ya nuna tausayawa ba ko kuma ya tambaya ni me ke damuna ba. Abincin sa kawai ya tambaya, da ƙyar na iya ɗagowa na kalle shi ganin yadda ya tsaya a kaina kamar me shirin yaƙi, ya wani turo tumbin gaba fuskar shi a haɗe kamar wanda aka aikowa da saƙon mutuwa. Cikin dauriya na buɗe baki nace "Banda lafiya ban iya girka komai ba." Ai kamar wanda na watsawa wuta, haka ya hauni da faɗa ta inda ya shiga ba tanan ya ke fita ba. Wai tsabar rainin hankali ne da wulaƙanci yasa naƙi yin abinci, waye-waye maganganu marasa daɗi ba tare da nuna tausayin halin da nake ciki ba ko kaɗan. Ƙarshe yace na tashi na shiga kitchen na girka masa abinci, dan shi ba zai yi aure ba ya ƙare a siyan abinci a waje ba da mutumcin sa. Ko da bai yi aure ba bai yi wannan ba, Hajiyar su na masa lafiyayyen abinci ba ma irin kwaɓar mu ta hausawa dana saba masa ba. Gaba ɗaya surutun sa ya ishe ni, nan da nan naji kaina ya fara amsawa, ga shi dama tsayawar da ya yi kusa dani duka warin jikin sa ya addabeni . Kafin kace meye wannan na fara kelaya amai, tamkar zan amayar da hanjin cikina. A zato na zai nuna min tausaya, ganin halin da nake ciki. Sai naga yaja tsaki ya juya ya fita ya cigaba da mitar shi. Gaba ɗaya na fara fita hayyacina, sakamakon dama babu komai a cikin nawa iya ruwa kawai nake amayarwa. Da kaina na lallaɓa na gyara wajen ina kuka. Na koma kan kujerar na kwanta, nan da nan wani sanyi ya kamani. Ina jin wayata na ringing, amma na kasa ɗauka. Ƙarshe jin kiran ya yi yawa, na miƙa hannu da ƙyar na ɗauka. Ganin wadda ke kiran jikina na rawa na amsa. Ko magana banbari tayi ba, na fashe mata da kuka. Daga can Aunty Fati tace "Haba Rahamah me ke faruwa ki ke kuka haka? Yanzu na dawo daga unguwa na manta waya a gida, na tarda kiran ki har biyar. Gabana ya faɗi nace ko lafiya? Ina ƙoƙarin biyo kiran, sai ga kiran mijin ki wai ya ce ki masa abinci kin ƙi masa. Har da su rashin kunya, yace ya kawo yarinyar Yayan shi ki riƙe bakya kula da ita, ko abincin bakya bata sai ya bata ga rashin mutumci kala-kala kwata-kwata bai isa ya saki ki yi abu ba, sai kice ba za ki yi ba." Cikin kukan da nake, haɗe da mamakin rashin kunya irin ta Al'amen. Na ce "Wallahi Aunty bani da lafiya ne." Nan na kwashe komai na faɗa mata, tun daga kan kawo yarinyar dake min fitsari da kasa zaman ɗakin da nake. Zuwa yau da banda lafiya yace na yi abinci. Sai dai na rasa me ya hana na faɗa mata maganar shirkar da ya ke, da kuma dukan da ya ke yawan kai min. Dan abu kaɗan nayi, baya shakka ko a gaban waye kai min duka ya ke. Haƙuri ta bani, ita ma tace bai kamata ba ya kawo min yarinya kamar Anisa mu dinga kwana ɗaki ɗaya, koda kuwa bata fitsari bare kuma tana yi tafi kowa sanin halin k'yank'yami na. Ƙarshe ta lallashe ni, tace gata nan zuwa gidan. Babu jimawa sai gata. Lokacin Al'amen baya gida, ganin halin da nake ciki yasa ta kira shi a waya tace ya zo tana son ganin shi. Faɗa sosai ta rufeni da shi, akan me ya hana tun farko ban kira ta ba. Haƙuri na bata nace na yi zaton zai daina. Ba'a wani ɗauki lokaci ba, sai gashi ya dawo, tiɓi-tiɓi hannayen shi riƙe da ledoji. Abin mamaki ganin Aunty Fati, sai ya fara washe baki ya shiga gaida ta. Amsa masa ta yi babu yabo babu fallasa. Sakin baki nayi kawai ina kallon salon makirci irin na wannan mutumin, ganin yadda ya ƙaraso kaina yana wani narke fuska, yana faɗin "Sannu Rahamatah. Ya jikin naki?." Gaba ɗaya kaina ya kulle, a zuciyata nace _Dama ba mata kaɗai suka iya munafurci ba, harda maza kenan._ Ganin haka yasa Aunty Fati kallon shi tace "Ya kamata mu kaita asibiti, dan jikin nata ya yi zafi da yawa." Cikin nuna damuwar data bayyana a fuskar shi sosai, ya miƙe yana faɗin "Ina zuwa bari na je na shirya." Bayan tafiyar shi Aunty Fati ta kalle ni tace "Rahamah ki ka ce ya nuna bai san baki da lafiya ba, bayan gashi ya nuna damuwa akan ki sosai, ki ga harda abinci ya siyo mi ki." Shiru na mata kawai, na ma rasa me zance mata. Ban ga amfanin yi mata bayani ba, dan nasan bama zata fahimce Ni ba. Tunda fuskar daya nuna mata ta kirki, tasa ta manta halin da ta zo ta same ni. Ganin na yi shiru yasa tace "Ni dai ina faɗa mi ki Rahamah, ki ji tsoron Allah. Babu ruwan Allah da rashin son da kika ce bakya yiwa mutumin nan. Mijin ki ne, in kika ɓata masa Allah ba zai bar haƙƙin sa da kika ci ba. Saboda haka ki bi a hankali kin ji na faɗa miki." Ganin Al'amen ya fito, dole tayi shiru. Harda su Hijabina ya ɗauko, yana ta rawar jiki yana jeramin sannu. Aunty Fati ce ta taimaka min na tashi. Yana ganin haka ya matso wai zai riƙe ni, tuna bala'in da nake shaƙa a jikin sa yasa na ƙwace na maida kaina jikin Aunty Fati. Bai ce komai ba ya matsa, muka fita muka shiga mota yaja muka nufi asibiti. Ina jikin Aunty Fati a kwance, ji nake kamar nace ta wuce dani gidan ta. Ko zan huta da rayuwa da wannan makirin mutumin me fuska biyu. *_🥰MAMAN ƊAN ALBARKA CE 🥰✍🏻✍🏻_* [1/18, 07:15] Ummu Sultan Ceh3: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/EJJOOxsRu8dKh9gocmSFuG *BAƘAR ZUCIYA!.* *_🥰MAMAN ƊAN ALBARKA CE 🥰✍️✍️_* *_LITTAFIN KOWA YAƘI JI YA KAMMALA COMPLET GA DUK ME BUƘATA TA MIN MAGANA TA WANNAN NUMBER 09014644247_* *PAGE 8️⃣* Tun da muka baro asibitin, kuka kawai nake kamar wadda aka sanarwa da saƙon mutuwa. Na fara kukan ne tun sa'ar da likita ya faɗi kalmar data tafi da ɗan sauran farin cikin da ya rage min a rayuwa. Ni Rahamah ni Rahamah, ace ina ɗauke da ciki cikin ma na wannan mugun azzalumin. "Ya Allah." Na furta hakan a fili. Na fuskanci daga shi uban gayya, da tunda aka sanar da samuwar cikin ya ke washe baki. Da ita Aunty Fati da ke ta faman aikin lallashi, babu wanda ya fahimci kukan baƙin ciki nake. Duk tunanin su farin ciki yasa nake kuka, saboda Aunty Fati ta sanni da shegen son yara. Eh tabbas ina son yara a rayuwata, sai dai duk da irin son da nake musu, ban yi fatan samun haihuwa da wannan mutumin ba. Wanda nake wa kallon mugu kuma azzalu, me halin dabbobi. Sai gashi ashe ni ina tawa ne, Allah kuma na nashi Allah ya riga daya ƙaddara sai na samu rabo da shi. Tunda gashi ina ɗauke da cikin shi, har na tsawon sati biyu. Ganin kukan yaƙi ƙarewa kamar ana daɗa tunzurani, Aunty Fati da ta fara zargin kukan ƙiyayyar cikin nake. Ta ɗan ture kaina daga jikin ta tace "Wai ke Rahamah haka ake yi fisabilillahi, dama in mace ta samu ciki kuka take ba farin ciki da addu'ar su rabu lafiya ba take?." Maida kaina na ƙara yi kafaɗar ta, na cigaba da kukana kamar ba dani take magana ba. Al'amen dake tuƙi kam zuciyar sa fes take, tun sa'ar da likita ya sanar da samuwar ciki ga Rahamah, ya ji wani daɗi ya ratsa shi. Allah ya sani yana son ace yau shima ga ɗan shi an nuna ance ɗan Jagaba ne, koba komai hakan ƙarin daraja ne da kima a gare shi a matsayin sa na mutum na mutane. Jin da ya yi Aunty Fati nawa Rahamah magana, hakan yasa ya juyo ya kalle su yana murmushi yace "Ki bar ta ta yi kukan farin ciki ne, kin san dama tace min tana addu'ar Allah yasa ta samu ciki kusa. Ashe ma abin ya na tare da ita bamu Sani ba." Ya ƙarasa faɗar hakan yana kallona, dai-dai lokacin da na ɗago ina kallon shi, cikin mamakin jin ƙaryar da min ido-da ido ba kunya bare tsoron Allah. Idanun shi fes a cikin nawa, babu ko alamar kunya a ciki ko nuna ba haka bane. Ji nayi kamar na buɗe baki na danna masa zagi, sai dai hakan ba tarbiyyar da aka ɗora ni a kai bace. Wani munafikin murmushi ya sakar min, ya ɗauke kan shi ya cigaba da tuƙi kamar wani na Allah. Harara nabi bayan shi da shi, babu shiri na nemi kukan da nake na rasa. A zuciyata nake faɗin _Lallai wannan mutumin lamarin sa ya wuce_ _tunina, wani abin in ya shirya ko ni da nake mace bana tunanin zan iya shiryawa._ Mun sha kwantar gidan Aunty Fati kenan, maganar shi ta ratso kunne na yace "Am yawwa Aunty Fati, ina son dan Allah kiwa Rahamah magana. Kar ta dinga shan maltina madara, da yawan cin ƙwai, dan tana da jarabar son ƙwai kullum sai ta soya taci. Ni kuma bana son abinda zai jawo yaron cikin ta ya yi girman da har sai an mata aiki, kin san abubuwan nan na kumbura yara su yi girman da ya wuce misali." Tunda ya fara magana Aunty Fati take kallon shi, a ranta take faɗin _Ikon Allah yau naga abinda ya fi karfina, Ni Fatima. Cikin da bai kai ko wata ɗaya bane ake sawa doka har haka? To Allah ya jiƙan mu mu da muke shan ta kullum_ Nan ta tuna cikin Islama kullum bata da wata cima sai ƙwai, maltina kuma ita ta zama kamar ruwan shanta. Kuma babu abinda ya same ta ko babyn, asalima Islam ba tayi wani girman ku zo mu gani ba, lafiya ta haifi ƴar ta ba tare da komai ba. Jin dukan mu mun yi shiru, hakan yasa ya juyo yace " Aunty ki yi haƙuri fa, na faɗi hakan ne dan ki mata magana ta rage, gani nayi bai dace ace tana ci kullum ba. Tunda har likitoci sun ce suna hura yaro." Murmushin yaƙe Aunty Fati ta yi, ta kalle shi tace "Karka damu zan mata magana, amma ni a ganina abubuwan da ka lissafa babu abinda suke sa yaro, sai ƙarin lafiya da kuzari ko a asibiti likitoci na cewa a yawaita cin dafaffen ƙwai." Nan da nan ya haɗe rai, cikin cunkushashshiyar murya alamar ranshi bai so tace hakan ba yace "Ni dai abinda nace kenan, ki faɗa mata bana so ta jamin aiki dan ba son aiki nake ba. Gwara ta haifa da kanta kawai." Bansan lokacin da na ja tsaki ba, da sauri ya juyo ya kalle ni daidai lokacin da muka ƙaraso ƙofar gidan Aunty Fati. A bakin get ya yi parking gaba ɗaya fuskar shi a haɗe, ba sai ji na yi Aunty Fati tace "Am Jagaba Ina so ka barta a nan ta ɗan huta, in yaso zuwa dare sai ka biyo ka ɗauke ta ku tafi." Bata jira cewar shi ba, ta kama hannuna ta buɗe motar muka fita. Raina fes, ji nake kamar an cire min ƙaya, dama ace in na shiga gidan ta ba zan ƙara komawa gidan shi. Ganin har taja hannun ta, ba tare da ta jira izini daga gare shi ba, hakan ya ɓata masa rai. Kamar yace bai yarda ba, ko me ya tuna sai ya washe baki yace "To shikenan Aunty, an jima dai daga anyi sallar Isha'i ta shiry, zan zo mu tafi. Ban jira ya ƙarasa maganar shi ba, na zare hannuna ana Aunty Fati nayi gaba. Ina jin su suna sallama, yana jaddada mata ta kula dani sosai, kar ta bari nayi abinda zai taɓa cikin jikina. A zuciyata nace _Sarkin rashin kunya, ayi mutum babu ta ido ba kunya bare kara._ Shigowar Aunty Fati tuni na cire Hijabina, na baje a kan carpet ɗin dake malale a farlon, ina shan sanyin fankar dana ƙure. Jina nake yau kamar na samu wani ƴancin kaina ne, kafin ya zo ya yanke min jin daɗi na ya maida ni cikin fursun ɗin gidan shi. Zama Aunty Fati tayi a kan kujerar dake gefen inda na kwanta, ta kalle ni tare da aje jakar ta wajen ƙafata tace "A gaskiya Rahamah kina fama, wannan mijin naki na fuskanci sam bashi da kunya, ki ga daga samun ciki har ya fara rawar jiki abinka da ba saban ba. To an daɗe ba'a yi aure ba, yanzu har ga shi za'a samu ɗan kai, ko wane likita ne yace masa ba'a cin ƙwai da shan maltina da madara in an samu ciki?." Ɗan kama ƙafar kujerar da take kai nayi, na miƙe zaune tare da faɗin "Wash, na gaji wallahi." Na juyo gaba ɗaya na fuskance ta nace "Ke iya rashin kunya kika fahimta a tare da shi kenan?." Jinjina min kai tayi tace "Ƙwarai Rahamah bashi da kunya, ko dan shi ɗin ba bahaushe bane oho?." "Uhmm tunda abinda ki ka fahimta kenan, ina roƙon Allah ya bayyana sauran halayen shi, yadda kowa zai fahimce shi bama ke kaɗai ba." Da sauri ta dafani, cikin nuna ƴar zaƙuwar ta da son in bata amsa tace "Waɗan ne irin halaye ya ke dasu Rahamah?." Haka kawai naji na kasa ce mata komai, sai kawai na tsinci kaina da girgiza kai nace "Babu komai addu'a ce na yi, ina fatan kuma Allah ya amsa." Ajiyar zuciya ta sauke, tare da jan tsaki tace "Har kin faɗar min da gaba wallahi, nayi zaton wani abunne daban. Allah ya shirya ki Rahmah, na fuskanci har yanzu akwai wauta a tare dake." Ban ce mata komai ba, na maida kaina na kwantar kawai. Ni kaɗai nasan me meke damuna a zuciyata. Har dare muna tare da Aunty Fati, haka ta dinga nan-nan dani tana kawo min abubuwan ƙwadayi irin na masu ciki. Kusan har dare tana kitchen, ko da ya zo ɗauka ta haka ta cika min kula da dambun zogalen da nace mata ina so. Tunda na shiga motar ko magana ban masa ba, shima bai ce min komai ba, sai motar da naga ya shigar gidan su. Har ya buɗe ya fita ban motsa ba, ganin haka yasa ya leƙo fuska a haɗe yace "In kinga dama ki fito mu shiga ki gaida Hajiya." Kamar kar na fita, tuna inda muke abu kaɗan zan yi ya sani a idon mutane. Hakan yasa na fito ina ɓata rai nabi bayan shi. Farlon Hajiyar su muka nufa, kuma har yau ina mamakin me yasa baya kaini wajen sauran matan Baban shi, ko bai ɗauke su a matsayin iyaye bane ban sani ba. Dan ko suma ƴan uwan nashi, basa wani damuwa da lamarin shi sai in buƙatar su ta kawo su, wasu daga cikin su kenan waɗan da ƙarfin su bai kai nashi ba. Sai da muka shiga wajen Hajiyar na ƙara tabbatar da Al'amen baida kunya, dan ba wata damuwa yace mata, ina da cikin sati biyu. Nayi zaton zata ji nauyi, sai naga ta hau murna tana addu'ar, Allah ya rabamu lafiya. Ni dai gaba ɗaya a takure nake jina, daga ƙarshe sai ga Anisa ta fito wai zamu tafi tare da ita. Ashe tunda ya fita da ita wajen Hajiyar ya kawo ta. Ni sai naga kamar Hajiyar ma na wani harhaɗe min rai, dan bata wani sake min yadda ta saba ba. A raina nace _Ke kika sani, daga ke har ɗan ki bakwa gabana._ Haka muka baro wajen ta, yace Anisa ta jira mu a mota muka shiga wajen Dadyn su ance baya jin daɗi. Na tausayawa bawan Allah, ganin halin da ya ke ciki na ciwo. Yana kwance a farlo akan katifa, an ɗaura masa ruwa, ciwon lokaci guda har ya rame. Har ƙasa na tsugunna na gaida shi, da ƙyar ya amsa na masa addu'a akan Allah ya bashi lafiya. Al'amen ya gyara masa kwanciya, muka masa sai da safe, ya bimu da addu'ar zaman lafiya muka tafi. Muna isa gida na riga su fita a motar, kai tsaye wuce ɗakina, farkon abinda na fara shine fito da katifar Anisa daga ɗakina. Daidai lokacin dana ɗire katifar ina ƙoƙarin juyawa ya sawo kai farlon. Ban dakata ba na cigaba da tafiya, ina jin shi yana kiran sunana yana faɗin "Lafiya Rahamah ki ka fito mata da katifa?." Ban kula shi ba, ya biyo Ni har cikin ɗakin cikin fushi yace "Wai ba dake nake magana ba?, ya ina tambayar ki zaki share Ni ki yi banza dani." Ba tare dana kalle shi ba na ƙarasa bakin gado na zauna nace "Na rantse da Allah ka ji na rantse ko? Muddin kace Anisa zata cigaba da kwana a ɗakina, to sai dai ka zaɓi ɗaya. Ko Ni ko ita, dan in har kace ta cigaba da kwana daga yau na haramtawa kaina kwanan ɗakin, in yaso sai ku dinga kwana tare." Na yi tunanin zai hayayyaƙo min, kamar yadda ya saba in maganar ta haɗa mu. Cikin mamaki naga ya sassauta murya yace "Ki yi Haƙuri ba za'a yi haka ba, na yarda ta daina kwana a ɗakin, amma yanzu ki taso mu je ki taya ni mu gyara mata ɗakin farlo, tunda ba komai a cikin sa." Tsaki naja na kauda kaina nace "Babu in da zan je, kai dai da ka ɗauko ta kaga zaka iya da hidimar ta ai sai ka je ka gyara mata." Al'amen gaba ɗaya daurewa yake, yana Binta a hankalina ne kawai saboda sharaɗin da Malam Mustapha ya bashi, tun sa'ar da ya sanar da shi tana da ciki. A waya ya kira shi. Nan ne fa yace ya yi ƙoƙari wajen bin duk abinda take so, ko zasu samu ta saki jiki da shi ta dinga abinda suke so. Tunda dai yanzu Allah yasa tana da ciki, me ciki na son kulawa ya dinga daurewa. Wannan shine dalilin da yasa har ya sassauta muryar shi yanzu. Ina jin shi ya fita yana kiciniyar sharar ɗakin, har ya gama ya dawo lokacin tuni nayi wanka na kwanta. Ganin yana shirin hawa gadon ba tare daya yi wanka ba, nayi sauran tashi na zauna ina kallon shi nace "Kamar yaya zaka kwanta ba wanka?gaskiya in har ba kayi wanka ba, bana tunanin zan kwana a ɗakin nan sai na koma farlo abuna." Ban yi zaton zai sauka ba, sai naga ya sauka tare da jan dogon tsaki ya nufi toilet. Babu jimawa sai gashi ya fito ɗaure da zanina a ƙugun shi. Cikin takaici na kalle shi, ban ma san yaushe ya buɗe Wardrobe ya ɗauki zanina ba, haka kuma ya nufo gadon jikin shi duk ruwa da niyar kwantawa. Ƙara tashi nayi na dakatar da shi ta hanyar ɗaga masa hannu nace "Kaga dan Allah ka fara goge jikin ka, kuma ni karka ƙara ɗaura min zani na haka kawai akwai towel a toilet ba babu ba." Bai ce min komai ba ya nufi wadrobe, cire zanin nayi ganin zai maida wadrobe nace "Karka sa dan Allah, baka ga ruwa a jikin ka ba. Rataye zanin ya yi a kan katakon jakunkuna na, ya ɗauki gajeren wandon ya saka ya hawo gadon yana ta jan tsaki. To ranar dai dama-dama zance, sunan ya yi wanka ne amma har lokacin jikin shi bai daina tashi ba. Yau cikin Sa'a sai banyi amai ba. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, cikin ikon Allah na cigaba da rainon cikina, inda a halin yanzu har ya kai wata uku, kuma duk abinda nace Al'amen ya min yana ƙoƙarin yi sosai, ba tare da musu ko cewa ba zai yi ba. A hankali ƙaunar cikin jikina ta fara shiga raina, koba komai nima jinina ne kuma bashi da laifin komai a gare ni, tunda bai min komai ba. Bai san me ke tafiya a duniya ba, addu'ar da nake kawai shine, Allah ya bani nagari ya tsare shi kar ya gado mahaifin sa ko karta gano mahaifinta. Yau ina kitchen da rana, sai ga shi ya shigo hannun sa riƙe da wata leda. Ajiye wa ya yi yace "Ga wannan ki yi min Farfesu, kan rago ne bana so a haɗa da harshen amma, ki cire shi daban tun daga tushiyar sa har ƙarshe. Bayan nan ki dafa min faten wake, ina son raba sadakar su ne." *_🥰MAMAN ƊAN ALBARKA CE 🥰✍️✍️_* [1/18, 07:15] Ummu Sultan Ceh3: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/EJJOOxsRu8dKh9gocmSFuG *BAƘAR ZUCIYA!.* *_🥰MAMAN ƊAN ALBARKA CE 🥰✍️✍️_* *_LITTAFIN KOWA YAƘI JI YA KAMMALA COMPLET DOCUMENT, GA DUK ME BUƘATA TA MIN MAGANA TA WANNAN NUMBER 09014644247_* *PAGE 9️⃣* Kallon ledar nayi na ɗago na kalle shi, sai ya shiga washe baki yana faɗin "Dan Allah Rahamah ki yi yadda nace, iya harshen kaɗai za ki cire bari na je na amso wani saƙo, tare nake so na haɗa na raba." Ganin yana ƙoƙarin tafiya, na cire hannuna a ruwan da nake wanke shinkafa nace "Kaga dakata. Dawo ka ɗauki wannan abin daka kawo min, ba zan dafa ba dan babu ni a cikin shirka, Wacce irin jarabace wannan fisabilillahi ace kan rago za'a dafa ayi sadaka kuma bayan an cire harshe, wannan ba sadaka bace Wallahi sai dai in wani salon tsubbu ne." Na ƙarasa faɗar tare da shure ledar da ƙafata, aikuwa sai ga kan rago ya fito gudan shi, da alama ma yanzu aka yanka dan ga jini nan kaca-kaca. Da sauri na ɗauke kaina naja baya tare da sa hannu na toshe hancina. Aikuwa ya dawo da sauri ya tsugunna ya ɗauke kan ragon, ina kallon shi yasa a leda nayi zaton zai ce wani abu. Sai naga ya juya ya fita a kitchen ɗin kawai, tsaki naja ina Allah wadai da halin shi duk zatona da naji kwana biyu baya cewa ayi sadaka, nayi zaton ya daina ne ashe yana nan yana sha'anin sa. Addu'ata kullum ita ce Allah ya tsare ni daga sharrin sa, dan gaba ɗaya yanzu ya dawo min da tsohon tsoron shi a raina. Babu jimawa kuma sai gashi ya dawo kitchen ɗin, hannun shi riƙe da wata roba duk jini ya ɓata ta, da sauri nasa hannu na toshe hancina ina faɗin "Dan Allah ka fitar da wannan abin daga nan bana so." Wani kallo ya watsa min yace "Ni da gidana zaki hanani abinda nake so, Wallahi Rahamah duk iskancin da kike kina cin wata alfarma ne kawai. Karki bari nayi fatali da hakan, duk ranar da ki ka kaini ƙarshe zan shayar dake ruwan mamaki." Tsaki naja cikin ɗaga murya raina a matuƙar ɓace nace "Kar na ƙara cin wannan alfarma da kake faɗa, Haba Al'amen ka ji tsoron Allah mana, me ka ke nema a duniya a yanzu da Allah bai maka ba? Me za ka yi da dukiya bayan wadda ka tara ? Wanne irin son zuciya da son duniya ka saka wa ranka da har ka ɗauki shirka a matsayin. Aikin ka. Me ka ke so? Me ye baka samu ba, Wallahi ka guji ranar da Allah zai kama ka akan ayyukan ka, shirka kwata-kwata ba abin yi bace, duk cikin Laifuka shirka ita ce babban zunubin da Allah baya yafewa me yin ta muddin bai tuba ba ya mutu a cikin ta, duka duniyar guda nawa ce, me zaka tara wanda ba'a tara irin shi a duniyar nan ba, anyi biliyoyin ka a kuɗi mulki kai komai ma, dan ba kai ka fara ba anyi fiye da kai, duka suna ina yanzu? Duk sun tafi in da zasu amshi sakamon ayyukan su." Cikin fitar hayyaci na cigaba da magana ina hawaye, dan na daɗe abin na cimin tuwo a ƙwarya, a duk sa'ar da nayi niyar faɗa masa gaskiya sai na ji kamar an rufe min baki. Yau ne Allah ya bani iko na ji har bakina ya buɗe "Ka ji tsoron Allah. Ka ji tsoron Allah ba dan komai ba sai dan mutuwa bata sallama, bayan nan ka tausaya min ka duba ɗan dake kwance a marata, bana san ya fito duniya ya tarda irin muggan halayen k.." Kuka ne ya ci ƙarfi na, na zube a kan gwiwowina na fashe da wani rikitaccen kuka wanda ke fitowa daga ƙasan zuciyata. Yana tsaye riƙe da robar kamar wanda ya ji nasihar da aka masa, ƙasan ransa kuwa wani irin ɓacin raine kwance. Shi yarinyar nan zata kalla tace yana aikata shirka, ina shirkar da ya ke aikatawa? Shi bai ɗauki duk abinda ya ke a matsayin shirka ba tunda sadaka ce ake bashi , sai ɗan abinda baza'a rasa ba a cewar shi neman arziƙin bata yadda ba'a yi. Dan haka ya ja tsaki ya kalle ni da har lokacin ina zube a ƙasa ina kuka yace "Karki ƙara kira na da mushriki, saboda ban aikata shirka sadaka ce nake yi karki ƙara haramta min sadaka ki kira ta da shirka." Yana gama faɗar haka, ya wuce ni ya ƙarasa cikin kitchen ɗin, da kanshi ya shiga wanke naman kan, babu shiri na bar masa kitchen ɗin ina kuka na nufi ɗakina. Shawara na dinga yi da zuciyata, akan na kira Aunty Fati na sanar mata halin da ake ciki. Wata zuciyar kuma tace _In kin faɗa kamar kin tonawa kanki asiri ne._ Sai nayi kamar na kira ta sai na fasa, a haka har aka kira azahar na tashi na nufi toilet, wanka nayi na ɗauro alwala na tada Sallah. Hayaniyar da na fara ji a farfajiyar gidan, yasa na shafa addu'ata cikin hanzari na leƙa window. Cike da mamaki nake kallon Al'amen, wanda ke zaune a kan kujerar roba kusa da bakin get, yara ne da yawa a gaban shi, da alama yaran almajirai ne duba da irin shigar dake jikin su. Ganin kamar yana miƙa musu abu, yasa na fito farlo wajen window na leƙa ta baya tunda dama part ɗina shine na farko. Faten wake ne a gaban shi, da naman kan ragon daya yi Farfesun shi, cikin mamaki nake kallon yadda ya ke zuba musu a roba, in ya zuba musu sai ya zari nera hamsin hamsin, waɗanda ke kujerar gefen shi, sai ya haɗa da goro ya basu su amsa suna godiya su tafi. Ji nayi kaina na wani irin sarawa, wanne irin abu kenan tunda nake ban taɓa ganin kwamachala irin wannan ba. Kamar wadda aka mintsina na juya cikin hanzari na koma ɗaki, wayata na ɗauka na danna number aunty Fati, cikin kuka nace "Wallahi Wallahi Aunty na gama zama da mutumin nan, ni Kaduna zan tafi ba zan ƙara awa ɗaya a gidan shi ba." Ina gama faɗin haka na yanke wayar, nayi wurgi da ita akan gadon na fashe da wani irin kuka me cin rai. Ina kallon yadda take kirana naƙi ɗauka, ta jera min kira yafi goma data gaji ta daina kira. A can kuwa hankalin Aunty Fati ba ƙaramin tashi ya yi ba, jin abinda ƙanwar tata tace. Gashi taƙi ɗaukar kiran ta bare ta ji lafiya, ita kaɗai take faɗin "Na rasa gane me ke damun yarinyar nan, ayi mutum kamar me aljanu ko ƙiyayya hauka ce." Dan ita yanayin maganganun da Rahamah take akan mijinta, bata fahimtar su tana bata abin a dunƙule bata fahimtar komai, Iya abinda idanun ta suka gani da shi take amfani. Dan haka ganin taƙi ɗaukar kiran, bisa dole ta kira mijinta tace zata gidan Rahamah ta duba ta bata jin daɗi. Cewa ta jira shi ya zo ya kaita, ji take ba zata iya jira ba, haka ta tattara yaran ta kaisu gidan dake jikin nata, Matar gidan nada mutumci sosai, suna zumunci da ita ita ma bahaushiya ce. Ganin yadda Aunty Fatin ke ta sauri yasa tace "Ni kuwa Maman Islam ina za ki haka? Naga kamar bakya tare da nutsuwar ki." Da ya ke wani lokacin suna ɗan tattauna matsalolin dake damun su, sai ta ɗan ja tsaki tana tafiya tace "Ki bari na dawo Aunty Zainab zan faɗa miki." Da yake ta girme mata, shi yasa take kiran ta da Aunty. Mashin ta tara, dan bata jin zata iya tsayawa ta jira mijin ta da yace zai dawo ya kaita. Asalima bata so yasan me ke tafiya a gidan ƙanwar tata. Ina zaune a inda nake ko motsawa banyi ba, naji sallamar Aunty Fati. Kwanciyata nayi na juyawa ƙofar shigowa baya. Yanzu Al'amen ya shigo muka gama cashewa da shi, na tata masa rashin mutuncina, ya fita ranshi a matuƙar ɓace, wai ashe yana ƙoƙarin shigowa ya ji ina waya da Aunty Fati, shine wai me yasa zan kirata? Na kira ta nace Babu komai karta zo, shine nace ba zan kira ba harda mari na ya yi ƙarshe, ya fice yana faɗar maganganu. *** *AL'AMEN.* Ba ƙaramin tashi hankalin sa ya yi ba, lokacin da ya zo ya tarda Rahamah na waya da Aunty Fati tana faɗin zata bar gidan shi. Tambayar kan shi ya shiga yi _Taya haka ta kasance? bayan Malam ya tabbatar masa ta shigo gidan sa kenan babu fita, ita ce makullin arziƙin sa ya riga daya mallake masa ita ba zata iya zuwa ko'ina ba._ Shine yanzu ya ji tana batun tafiya, da sauri ya shiga ya ce ta kira tace karta zo, da taƙi shine ya mare ta ya fita ranshi a ɓace. Bai zarce ko ina ba sai gidan Malam Mustapha, kiran shi ya yi a waya, sai gashi ya fito yana wani ƙoƙƙobarewa. Ko gaisawa ba su yi ba ya kora masa bayani, cikin mamaki da ya kama Mustapha yace "Kana nufin ta fara maganar rabuwa? Lallai akwai aiki a gaban mu, na faɗa maka yarinyar nan nada aljanu baka yarda ba, gashi yanzu suna neman juya mata tunani su cuce mu. Bayan kasan ita ce ƙarfin arziƙin ka, bari na shiga gida na fito dole a rufe mata baki karta ja mana aiki." Yana gama faɗin haka ya juya ya shiga gida, dawowa ya yi hannun sa riƙe da wani magani. Miƙawa Al'amen ya yi yace "Ungo wuce muje ka samu kuɗi ƴan nera goma-goma sai a barbaɗa maganin, in dai anyi haka sai a raba su ga yara na kan hanya. Ana yi ba zata iya tona maka asiri ba, ko ta yi niya bakinta zai yi nauyi. Haka kuwa suka yi, suka fita ya samo canjin a wajen wani me shago dake aje masa canji musamman, sun yi Sa'a an taso yara ƴan makaranta, haka suka dinga raba musu kuɗin nan suna gamawa suka juya. Ya cewa Al'amen "Kafin ka koma gida yanzu ba anjima ba, ka kira Iyayen ta ka gaishe su ka ɗan tura musu wani abu ta account ɗin yayanta, tunda kace shi kaɗai ka ke da shi kuma in kace zaka tura suna hanawa, karka faɗa musu sai ka tura, sai kace a rabawa yara ba su ka bawa ba." Tsaki Al'amen yaja yace "Kasan abinda ke ƙona min rai da mutanen nan, da zarar nace na tura kuɗi sai su ce basa so, su fatan su na riƙe musu ƴar su amana da gaskiya." Cikin nuna ƴar damuwa yace "Gaskiya Malam ina tsoron ranar da zasu san halina, har ga Allah na fara ƙaunar Rahamah dan yarinyar ta kai a sota, kawai dai son da nake mata ba zai hana in gudanar da manufofina ba." Ɗan dafa shi Malam Mustapha ya yi yace "Karka damu dan so dama nasan zaka iya son ta, amma ka bi a hankali kar ya sa ka fara taka sharruɗan da na kafa maka. Batun iyayen ta ka aje shi a gefe, su waɗan nan kasan basu damu da duniya ba na riga dana gama rufe bakin su, kar ka yi fargaba akan asirin ka zai tonu, muddin ina tare da kai hakan ba zata faru ba." Sai lokacin Al'amen ya ji hankalin sa ya ɗan kwanta, nan Mustapha yace masa, ya wuce ya koma wajen hidimar sa, babu abinda zai faru. Haka ya sauke shi a ƙofar gidan shi, ya juya yana sauke ajiyar zuciya ya kama hanyar kasuwa. *** *RAHAMAH.* Tambayar duniya Aunty Fati ta min, akan na faɗa mata matsala ta na kira ta na tada mata hankali. Babu abinda nake sai kuka, naƙi furta mata komai sai cewa da nake "Wallahi na gama zama da shi tafiya zan yi, gashi dai ina son in faɗa amma na kasa. Ƙarshe haushi na bawa Aunty Fati, ta miƙe tace "Rahamah ni zan tafi, Allah ya yaye miki abinda ke damun ki, zan kira su Abba na faɗa musu ga irin iskancin da ki ke wa mijin ki, in yaso in wani abun ne nasan su ba zaki ɓoye musu ba. Ganin tafiyar za ta yi da gaske, hakan yasa hankalina tashi bana so su Abba su ji wani abu, tunda ba iya faɗa zan yi ba ko an tambaye ni. Da sauri na kama ƙafafun ta na durk'usa, tare da fashewa da kuka nace "Dan girman Allah Aunty karki sanarwa su Abba, bana son hankalin su ya tashi dan Allah." Juyowa tayi ta kama ni ta miƙar, fuskarta ɗauke da yanayin tausayawa, ta sassauta Muryar ta cikin lallashi tace "Haba Rahamah, ya kike so nayi dake to nace ki faɗa min matsalar ki kin ƙi, gwara ki bari na kira su Abba ya fi ko su za su iya sawa ki faɗa." Kuka na ƙara fashewa dashi, gaba ɗaya ji nake kamar an rufe min baki na kasa faɗar komai, ga maganar ina son yi amma babu hali. Duk yadda ta dinga lallashina akan na faɗa, ƙi nayi sai kuka da nake ta yi naƙi bari ta tafi. Ƙarshe ta fusata ta fincike daga riƙon da na mata, tayi tafiyar ta ta barni tace "Ba zan faɗawa kowa ba, tunda haka ki ka zaɓawa kanki, koma me ne in ya dame ki za ki ne me ni, in kuma iskanci ne yasa kike haka sai dai na miki fatan Allah ya shirye ki." Ina ji ina gani ta tafi, na zube a wajen ina kuka kamar wadda aka ce uwa da ubanta sun mutu. *** *AUNTY FATI.* Rai ɓace ta bar gidan Rahamah, bata taɓa jin ɓacin rai irin na yau ba, ace yarinya sai taurin kai da kafiyar tsiya. A haka ta na mita ta ƙarasa gidan Aunty Zainab. Ganin ranta a ɓace yasa Aunty Zainab cewa "Ya ya naga kin fita kina sauri, kin dawo ranki a ɓace haka?." Tsaki Aunty Fati taja ta zauna kan kujerar dake kusa data Aunty Zainab tace "Daga gidan yarinyar nan nake." Nan ta kwashe komai ta faɗawa Aunty Zainab ɗin. Ta gumi kawai Aunty Zainab ta yi, sai da ta gama jin ta tsaf, ta gyara zaman tare da sauke numfashi tace "Gaskiya Fati kema kin yi kuskure tun farko, ya ya yarinya zata ne me ki akan matsalar ta, amma ki kasa yarda da ita. Ai tun lokacin da ki ka tarda ta a kwance ba lafiya, miji baya kusa da ita babu kulawa cikin ciwo, kawai dan kin ga ya dawo yana nan-nan da ita sai ki ƙi yarda da ƴar uwar ki, shi ki yarda da shi?." A hankali Aunty Fati ta fara tunani, tabbas gaskiya Aunty Zainab ta faɗa. Bata taɓa tunanin Al'amen zai iya yin fuska biyu ba, sai yanzu da ta tuna mata duba da yadda bai ji kunyar ta ba wajen cewa ta hana Rahamah shan maltina da ƙwai, ga kuma kalmar shi ta ƙarshe wai ta kula da ita kar ta bari wani abu ya samu cikin. _Tabbas biri ya yi kama da mutum, in kuwa hakane akwai matsala._ Ta faɗi hakan a ranta. Nan Aunty Zainab ta cigaba da magana "Kin ga Fati, duk mutumin da ki ka ga an fiye yabon halayen sa a waje, ki bincika gidan shi ki duba irin zaman da ya ke da iyalin sa, ba duka bane hakan. Amma yawanci duk masu hali irin na Al'amen, fuska biyu gare su a waje salahai a gida kuma saɓanin haka." Sauke ajiyar zuciya Aunty Fati tayi, fuskarta cike da jimami tace "Yanzu ya za'a yi? Kin san na baro ta na kuka ne, harda kama ni tayi na ƙwace na taho." Tsaki Aunty Zainab taja tace "Wallahi kin bani haushi Fati, har wani ɗan iska ya isa na zaɓe shi akan jinina, kin fa san halin ƴar uwar ki ba baki sani ba." "Uhm Aunty Zainab, ai ni sai yanzu ne ma duk abubuwan ke dawo min, kin san Allah Rahamah bata da matsala, da wuya a mata abu sau ɗaya ta magantu, tana da wani irin haƙuri me wuyar samu a wajen mace. Sai yanzu nake mamakin yadda take yawan faɗar laifin mijin ta." Cewar Aunty Fati kenan. Miƙewa tsaye Aunty Zainab tayi tace "Bari na sako hijabi mu je gidan Rahamar, tunda dama lokacin islamiyya ya yi, sai mu sauke yaran a makaranta mu wuce. Kafin na fito dai ki kira shi mijin nata a waya, ki ce zamu je gidan shi ya dawo ya same mu, dan in mun haɗa su waje ɗaya dole su faɗi matsalar su, in ita bata faɗa ba dole shi zai yi abinda zai tona asirin sa ko yaya ne. Kin san ni mutum in har bashi da gaskiya, to sai dai bai tsaya gabana ba, amma yana magana nake fahimta. Dariya Aunty Fati tayi tace "Dama ku lauyoyi, har sai an nuna muku mara gaskiya, sai dai in kunga dama kun ƙyale shi. Haka kuwa suka yi, Aunty Fati ta koma gida ta shirya yara, suka sauke su a islamiyya da ya ke a motar Aunty Zainab ɗin suka fita. Tuni ta riga da ta kira Al'amen ɗin, yace mata yana zuwa. Bai yi zaton ba ita kaɗai zata zo ba, suna hanya ya bugo mata waya wai ta tsaya a gida ya zo ya ɗauke ta. Nan tace masa su sun kusa ƙarasawa gidan na shi ma. Aunty Zainab dake tuƙi ta duk tana jin abinda suke cewa, ta juyo ta kalli Aunty Fati tace "Kin ga abinda nake faɗa miki ko? Ki ji tsabar munafurci wai zai zo ɗauke ki, ke da za ki wajen Ƴar uwar ki ya cutar da ita." Haka suka cigaba da tattauna maganar, har suka kai gidan Rahamah. A inda Aunty Fati ta bar ni anan suka tarda ni, ganin ta tare da maƙociyar ta Aunty Zainab. Sai na ɗan ji dama-dama, dan matar akwai mutumci da karamci tun ina budurwa, lokaci ina zuwa wajen Aunty Fati muna shiri sosai. Kama ni ta yi ta miƙar dani tana faɗin "Subhanallahi Rahamah, ya za ki kwanta a ƙasa kina kuka haka? Bayan ba ke kaɗai bace." Faɗawa nayi jikin ta na fashe da kuka, lallashina ta shiga yi taja hannuna muka zauna bakin gado. A hankali ta shiga jera min tambayoyi cikin lallashi tana shafa kaina, tace min Al'amen ɗin shima yace zai zo yanzu. Jin haka da nayi yasa na ɗago kaina da sauri, cikin kuka nace "In ya zo ku tambaye shi abinda ya min, Ni ba zan iya faɗa ba." Tsawa Aunty Fati ta daka min, ta kalli Aunty Zainab tace "Kin ga abinda ya ke bani haushi da ita ko? Yarinyar nan na da kayan takaici Wallahi." Ɗaga mata hannu Aunty Zainab tayi tace "Kin ga Fati, ke matsalar ki sauri fusata, ki kalli yarinyar nan ki duba yadda take cikin damuwa, tabbas akwai abinda ke damun ta faɗar ne ba ta yi ba kawai." Ta ƙarasa tana bina da kallo cikin nazari. Babu jimawa sai muka ji ƙarar motar Al'amen, alamar ya dawo kenan. Kiran wayar Aunty Fati ya yi, yace mata ya dawo zai zo yanzu tana ina. Ce masa ta yi ya zo part ɗina tana nan. Duka muka fita muka nufi farlona, muna zama babu jimawa sai gashi ya shigo. Da sauri na sunkuyar da kaina cike da kunya, ganin yanayin shigar dake jikin Al'amen. Da sauri Aunty Zainab da Aunty Fati suma suka kauda kai, Aunty Zainab da ta kasa shiru tace "Auzubillahi." Sanye ya ke da gajeren wando, wanda ko cinyar shi bai gama rufewa ba, sai rigar dake hannun shi wadda ya kare iya gaban shi da ita. Bayan su babu komai a jikin sa, haka ya shigo tiɓi-tiɓi ya nemi kujera ya zauna. Aunty Zainab da ta kaɗu da rashin hankalin daya nuna, kasa daurewa ta yi ta kauda kanta tace "Dan Allah in ba damuwa, ka fara suturta jikin ka kafin mu fara magana. Dan ko yadda ka shigo nan a haka, ba al'adar mu ta hausawa bace da aka sani da kunya, hakan ba daidai bane ko ba komai mu ma muna da mazaje matan wasu ne." Ba ƙaramin burgeni na ji Aunty Zainab ta yi ba, haka kawai naji wani daɗi ya kama ni, ko ba komai yau na samu wanda ya iya tsayawa gaban Al'amen ya faɗa masa magana kai tsaye. "Ku yi haƙuri." Ita ce kalmar daya iya faɗa kenan, ya juya ya fita yana jin haushin Aunty Zainab, dan ya santa, tunda gidan Aunty Fati shi ya raba tsakanin gidan su da nata. Babbar lauya ce kuma sannaniya, duk faɗin unguwar gidan ta ne kawai basa wani ganin darajar shi daga ita har mijin ta, yaranta kam dama duk basa ƙasar suna Ƙasar waje karatu, dama su biyu ne duka maza. Haka ya sako riga akan gajeren wandon, ba tare da ya saka dogon wando ba ya zo ya zauna. Kallon shi Aunty Zainab tayi tace "Al'amen mun zo ne sakamakon kiran da Rahamah ta mana, tace akwai matsala a tsakanin ku, mun tambaye ta bata faɗa mana ba, ko kai zaka iya mana bayanin abinda ya haɗa ku yau?." A zabure ya ɗago ya kalle ni, da sauri na ɗauke kaina dan ko kallon shi bana son yi yau. Kame kame ya fara, yana faɗin shi babu abinda ya faru a tsakanin mu, kawai in yace nayi abu ne kai tsaye nake ƙin yi. Ga rashin kunya da nake masa, bai isa ya min magana ba sai na taso masa. Ba sai ga mutumin ku ya fara kuka ba, harda su jan majina wai Wallahi shi yana sona, nice dai bana son shi shi yasa har nake masa sharri yana takura min. Kallon shi kawai nake ina mamakin ganin yadda yake kuka,sai kace ba shine mugun nan ba me duka na. Ita kanta Aunty Zainab kallon shi take cikin nazari, a nutse ta karance shi tsaf ta gane bai da gaskiya, dole kuma akwai wani abu da ke ɓoye wanda basu sani ba. Dan haka ta kalle ni a gaban shi tace "Rahamah ina so karki cutar da kanki, in har kin san yana miki wani abu ki fito ki faɗa, karki cuci kanki bayan mun tafi ki yi dana sani." A hankali naji kamar an buɗe min baki, sai dai ba abinda naso furtawa ne ya fito a baki na ba, "Ni matsalata dashi shine faɗa, abu kaɗan in nayi sai ya min faɗa, bayan nan kuma baya son canja gajeran wandon shi sai ya yi dauɗa, kuma baya gyara jikin sa ko ya yi wanka kamar bai yi ba, Wallahi har amai nake yi." Na ƙarasa cikin kuka. Wata ajiyar zuciya Al'amen ya sauke a fili, jin abinda Rahamah tace, har ya shiga tsoron kar ta tona masa asiri, amma tunda har ta fara iya faɗar haka tabbas nan gaba zata tona asirin. Ya zama dole ya ɗauki mataki, musamman Zainab ɗin nan dake son shigar masa rayuwa. Gaba ɗaya suka yi shiru, suna nazarin maganganu na, Aunty Fati dai ta ɓangaren ta abin kunya ya bata. Ita kuwa Aunty Zainab a hankali take nazartar fuskata, abin da take gani kamar bashi ne a zuciyata ba. Dan haka ta ƙara tambaya ta, ƙara tabbatar mata da cewa shine kawai, ina jin wani irin zafi a zuciyata kamar zata faso ƙirjina. Haka ta samu gaba ta mana nasiha, babu kunya ta faɗawa Al'amen gaskiya, kai tsaye tace masa in ita ce bama zata ɗauki ƙazantar sa ba. Ya ji haushin yadda ta dizga shi babu kunya, bare kuma ayi batun mutumtawar da jama'a ke masa, haka dai suka lallashe ni tare da ban haƙuri suka tafi. Bai min magana ba, ya tashi ya fice daga farlon. Ko da dare ban ganshi ba, hakan ba ƙaramin daɗi ya min ba, ranar nayi barcina cikin kwanciyar hankali da lumana. Tun daga ranar sai ya canja, harda su fesa turare ya ke yanzu. Haka in zamu kwanta yana ƙoƙarin yin wanka. Ya daina zama da jallabiya guda, wanke baki ne dai sai a hankali. Sai yafi sati bai wanke ba, wannan bai dame ni ba dan ko kusa da bakina bana bari ya kawo nashi. Haka rayuwar mu ta cigaba da tafiya, yau daɗi gobe akasin ta. A haka cikina ya shiga wata na shida, gaba ɗaya na wani irin kumbura jikina ya buɗe. Kwatsam yau na tashi naga ya shigo da masu kayan gado, ana auna ɗakin da Anisa ke kwana. Har na share ban tambaye shi ba, zatona ita zai sawa tunda a katifa take kwana. Sai dai ganin ba kayan ɗaki kaɗai ba, harda akwatuna ake shigowa dasu yasa na sawa raina zan tambaye shi in ya dawo, dan akwatunan ba sabbi bane kamar dai irin za muyi baƙi ɗin nan. Ni a gani na ko baƙi ne, ai akwai part har uku da ba kowa a ciki, banda na shi, dan haka sai na zuba ido ina jiran shigowar shi. *_🥰 MAMAN ƊAN ALBARKA CE 🥰✍️✍️_* [1/18, 07:15] Ummu Sultan Ceh3: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/EJJOOxsRu8dKh9gocmSFuG. *BAƘAR ZUCIYA!.* *_🥰MAMAN ƊAN ALBARKA CE 🥰✍️✍️_* *PAGE 1️⃣0️⃣* *_LITTAFIN KOWA YAƘI JI YA KAMMALA COMPLET DOCUMENT, GA DUK ME BUƘATA TAMIN MAGANA TA WANNAN NUMBER 09014644247_* *AL'AMEN* Zaune suke shi da Malam Mustapha a bakin babban shagon da ya ke saida shaddoji da atamfofi da sauran su, Inda bashi ke kula da wajen ba, ya ɗora yaran aiki ne dake kula da wajen, shi sai dai ya zo ya duba in an kwana biyu. Bayan nan yana da shaguna a kasuwanni daban-daban, banda kowanne da abubuwan da yake zuwa ya ɗora yaran aiki, wani kayan masarufi wani kayan gini wasu katifu kai gasunan dai, shi ɗin komai da ruwan kane. Tare suka zo da Malam Mustapha, akan zai yi wata ajiya a shagon, saboda kasuwancin sa yanzu gaba ɗaya ya fara ƙasa, shi yasa ya zo suka duba wannan, da ya ke sun zo da maganin sai ya cewa yaran shagon su bashi waje. Bayan sun aje maganin can ta bayan kantar shagon inda baza'a gani bane, sai suka zauna a bakin shagon daga gefe yadda ba za'a ji su ba suna tattaunawa, akan yadda zasu sauran shagunan su gudanar da ayyukan su ba tare da wani cikas ba. _Allah ya kyauta, wasu mutanen suna yin_ _kuskure a rayuwar su. In da wasu basu ɗauke shi a bakin komai ba, wai sai an bada maganin kasuwa sannan za'a yi ciniki, shin akwai maganin kasuwar da ya wuce ka riƙe Allah ko ki riƙe Allah, ba wai ina kushe hakan bane kai tsaye, Ni a tawa fahimtar da kuma sani na babu wani maganin kasuwa da ya isa yasa ka samu kasuwa, muddin ba Allah ne ya dafa maka ba, in kuma kaga ance yi kaza dan farin jinin kasuwanci ko yi kaza dan ka samu kasuwa, tofa tabbas sai an kauce hanya ko yayane, yaku ƴan uwa ku sani ba'a wa Allah wayo, duk wata hanya da zaka a ɗora ka wadda zata kawo cigaba, muddin ba dabarun kasuwancin ko kasuwancin za'a koyar da kai ba, ko baka jari ko ace ka tashi ka roƙi ubangijinmu ba, to tabbas mu guji hanyar nan wata damfara ce wata kuma shirka ce aka mata kwaskwarima, Wallahi mu guji hakan mu tsaya tsayin daka akan gaskiya da riƙon amana a kasuwancin mu, mu tsaida sallah mu tashi mu roƙa wajen me kowa me komai, shi ɗin mawadaci ne shi kaɗai ne zai bamu ya ƙara ba tare da ya gajiya ba, in kuma ya bamu mu gode masa in mun rasa mu gode masa, Wallahi ba zamu taɓe ba, cigaba kuma zamu ganshi a rayuwar mu da albarka._ *_ALLAH YA MANA TSARI DA SHIRKA DA DUK WATA HANYA DA ZATA KAIMU GARE TA KO MAI KANKANTAR TA ALLAH KAR YA BAMU IKON BIN TA._* Bayan sun gama suka tashi suka shiga mota dan zuwa gaba, a hanya ne Al'amen ya kalli Malam Mustapha yace "Kana ganin ba yarinyar nan bace ta jawo min asara? Duba da bata bada haɗin kai yadda ya kamata, sannnan kaga bar wasu abubuwa da kake sani saboda masifar ta." Cikin nazari Mustapha ya kalle shi yace "Kuma fa kayi magana anan, amma ai nace kayi ƙoƙari ka dawo da yarinyar nan gidan ka, kaga sai ta kula da Anisa sannan kuma duk wasu ayyuka da Rahamah taƙi maka, sai ka bata ta maka ina ga kamar hakan shine mafita." Girgiza kai Al'amen ya yi yace "Yanzu haka ana can ana gyara ɗakin, amma kasan ni ba wani son shiga harkar yara nake ba, ita kuma yarinyar nan na dawo da ita ne dan itama ta samu ta ƙarasa karatun ta, tunda ga Anisa a gidan koba komai Anisa zata rage zaman kaɗai ci, kuma ko wani abu Rahamah tayi bana nan ina so ta dinga sanar min. Amma in batun ayyuka ne, gwara mu nemi wata hanya kawai bana son yarinyar ta san sirri na tunda tana min kallon wanda taƙi a baya." "To shikenan ka bari na je gida yanzu, zan yi bincike sakamakon da bincikena ya bani da mafitar zan faɗa maka." Cewar Malam Mustapha kenan. Da wannan suka rufe firar, haka suka wuni ranar suna yawo kasuwanni, duk wani shagon dake amsa sunan na Al'amen sai da suka je suka sa maganin kasuwa. Ban da sadakar da Malam yace ya raba, ya yi ɓarnar kuɗi ranar kamar bai san ciwon su ba. A gajiye ya shigo gidan, gaba ɗaya babu abinda ya ke buƙata bayan ya kwanta ya huta, dan haka ko sashin Rahamah bai je ba ya wuce nashi. A farlon ƙasa ya baje kan carpet yana numfarfashi, madadin ya fara wanka ko gajiyar zata ragu. _Al'amen kenan, namu na gargajiya akwai kyakkyawar alaƙa tsakanin shi da zama da warin rana😂_ *** *RAHAMAH.* Tun ina zuba idon ganin shi, lokaci da naji shigowar motar shi, sai naji shiru babu shi ba labarin shi gashi har sun gama gyaran su tafi. Fitowa farlo nayi, cikin Sa'a na tarda Anisa zaune tana kallo. Har wata ƴar ƙiba yarinyar ta ƙara da haske, alamar ta samu jin daɗi, to Ni dai ba ruwana da ita iya kaci na dafa taci, gaisuwa ma sai taga dama take min jifa-jifa yawanci sai Al'amen na nan. Takawa nayi na ƙarasa kujerar dake gefen ta, a hankali na zauna saboda nauyin da cikina ya fara. Na kalle ta cikin harshen turanci nace "Anisa in tambaye ki mana?." Cikin mamaki naga tace "Ina jin ki." Zaro ido nayi waje nace "Dama kina jin Hausa.?" Jinjina min kai tayi, cikin haɗiye mamakina nace "Wai waye zai dawo ɗakin ki, naga sai gyara ake an sa sabbin kaya?" Ɗan rage volume ɗin tvn tayi tace "Aunty Shukhra ce zata dawo, Aunty na ce Baba yace tare zamu zauna da ita, wai itama ta ƙarasa karatun ta tunda banda me kulawa da ni." A zuciyata nake faɗin _Wace Aunty Shukhra kuma?."_ Ashe wata zai sa a ɗakin, shine ni banda darajar da zai faɗa min ni da ɓangaren, in zai kawo mutanen shi ai ba hana shi zan yi ba, amma wannan sashin nawa ne ba nashi ba. Dan dai in ji kan maganar, sai na shiga tambayar yarinyar cikin dubara. Nan ta faɗa min komai, wai yarinyar yayar Hajiyar Al'amen ce, kuma da yaƙi aure an so a haɗa su tace bata son shi, to yanzu ta samu gurbi karatu ne anan garin tunda dama ƴar ilori ce, shine ta zaɓi gidannan tace anan zata zauna. Sosai maganar ta bige ni, wa Al'amen ya ke shirin kawo min? Tsohuwar budurwar shi fa kenan? Cab aikuwa da sake ba ruwana da kishin sa tunda ba son shi nake ba, amma ya zama dole ya canja mata waje ba a cikin farlo na ba, ya kaita wani ɓangaren su je can su ƙarata ko auren ta ma ya yi, amma ba dai waje na ba. Ganin yaƙi shigowa har wajen la'asar, hakan yasa na kasa daurewa na nufi sashin sa, rana ta farko kenan da zan taka ɓangaren nasa. Dan ina jin gwara koma meye, muyi maganin shi kafin saukar baƙuwar. Yadda na same shi ya wani baje kamar kayan wankin, sai da raina ya ɓaci ganin yadda ya tuɓe daga shi sai gajeren wandon sa na gado, ga uban kayan tumbin da ya wani baje shi a kan carpet ɗin, tumbin daban shi ma daban. Tsaki naja na dafa kujerar bakin ƙofa, na tafa hannayena da ƙarfi dan naga kamar bai san da shigowata ba. Wata irin zabura ya yi, ya fara yunƙurin tashi zaune, ganina tsaye yasa ya washe baki yana faɗin "A'a baƙuwa nake da yau kenan? A me yasa baki shigo ba ƙaraso mana Rahamahtah." Hararar kawai nake auna masa cike da jin haushi, sai wani washe dargajejen bakin sa ya ke kamar ganda. Miƙo min hannu ya yi yana faɗin "Kin ga zo nan, waya taɓa ki naga kin shigo kina harara haka ko dai na zo ne, zo ki kama ni mu je bedroom naji matsalar taki a nutse." Ya ƙarasa maganar yana ƙoƙarin miƙewa tsaye. Ɗaga masa hannu nayi, zuciyata na min wani irin zafin ƙiyayyar shi nace "Dan Allah kaga dakata, ba abin da ya kawo ni wajen ka kenan ba, Allah ya min tsari da hakan ina neman tsari da ranar da zan kawo kaina gare ka. Na zo ne na ji wa kake shirin kawo min farlona, naga ansa kaya Anisa tace budurwa zaka kawo min mu zauna tare, duk faɗin gidannan ka rasa ina zaka aje ta sai farlona." Na ƙarasa cikin karaji, ji nake zuciyata kamar zata faso ƙirjina ta fito. Miƙewa tsaye ya yi, ya shiga bina da wani ƙasƙantaccen kallo, sai da gabana ya faɗi dan ya koma min ainahin Al'amen ɗin dana sani tun na baya, amma gudun yaga kasawata yasa na dake ina bin shi da harara. Takowa ya fara sai da ya kusa ƙarasowa inda nake, ya min nuni da ƙofa ranshi a matuƙar ɓace yace "Fice min a nan, Ni zaki kalla ki nemi tsari da zuwa gare ni? Me ma kika ɗauke ni ne Rahamah? To bari kiji da na ƙyale ki saboda ban ɗauki son ki gare ni wani abu ba, amma tunda har tsaurin idon ki ya kai ki zo wajena ki faɗa min haka, to Wallahi sai kin yi nadamar faɗar kalmomin da kika jefe ni dasu, kuma in kina ganin ba zaki iya zama da wata a farlon ki ba, sai ki ƙara gaba ban tilasta ki ki zauna dole ba." Yana gama faɗar haka, ya juya zai shige bedroom ɗin sa na farlo. Da sauri nasha gaban shi nace "Wallahi baka isa ka min wani abu ba, bayan nan zama nace ba zan zauna da wata a farlo na ba, kasan yadda zaka yi da ita amma ba wajena zata zauna ba." "Bani hanya na wuce." Shine abinda yace min cikin tsawa. Ƙin matsawa nayi na ƙara tare hanya, nace sai ya wuce munje yasa an kwashe kayan an fitar. Babu zato naji ya sa hannu ya hankaɗa ni baya, wata irin faɗuwa nayi Allah yasa na sa hannu na tare cikina, da kan cikin zan faɗa. Ba tare da damuwa da abinda ya aikata ba, ya wuce ɗakin sa rai a ɓace. Da ƙyar na yunƙura na tashi, sai na nemi kukan ma na rasa, ashe Al'amen bashi da hankali bai duba cikin jikina ba ya ture ni? Ina ɗingishi ina komai na nufi sashina, ni kaɗai nasan meke damun zuciyata. *** *AL'AMEN.* Haƙiƙa kalmar Rahamah da tace Allah ya kiyaye ta so shi, ta buge shi ba kaɗan ba. Me ta ɗauke shi kenan? Bai kai a soshi ba ko me?. Tsayawa yayi a gaban madubi yana kallon kanshi, a hankali ya ke kallon kanshi tun daga fuskar shi, zuwa gangar jikin sa. Shi kanshi yasan in ba kuɗi ba, ko abinda ake cewa so hana ganin laifi, to babu kyakykyawar mace kamar Rahamah da zata so mutum kamar shi. Ya daɗe yana tsaye ƙarshe ya wuce ya ɗauki wayar shi, Number Mustapha ya kira ya faɗa masa duk abinda ke faruwa, Ranshi na masa ciwo. Daga can Mustapha yace "Gaskiya bata kyauta ba, shi yasa tun farko nace ka bari a mallake maka zuciyar ta, yadda bata isa ta tsallake maganar ka ba koda kuwa iyayen ta zasu tsaya suyi magana, in kayi taka to ita zata bi. Amma ka ce a'a, gashi yanzu abin ya fara damun ka, tunda kaima kasan badan mun rufe bakin kowa ba da ko auren ba za'a baka ba bare ita ta zauna da kai." Jinjina kai ya yi kamar Mustapha na gaban shi yace "Ai yanzu ya zama dole ta gane kuren ta, dole na azabtar da zuciyarta da rayuwar ta, so nake ta yi nadamar abinda ta aikata min, so nake ta dawo tamkar baiwa a gare ni, so nake duk wani abu in na ce shi za tayi, ina son na lalata rayuwar ta na ruguza farin cikin ta na ɗai-ɗai ta duk wani kyau da take taƙama dashi, ƙarshe ta dawo komai sai nace za tayi, ina son taji in babu ni ba zata iya rayuwa ba, ina son ka sa mata wani irin zazzafan sona a ranta wanda duk bugun numfashin ta, ya dinga hauhawa yana ƙaruwa. Sai ta yi nadamar abinda ta min, a lokacin da nadamar ba zata amfanar da ita ba." Jinjina kai Mustapha ya yi yana wata dariya yace "Da kyau, yanzu na yarda Jagaba ne a gabana, karka damu zan birkita tunanin ta da duk wata nutsuwar ta, sai ta dawo tamkar yadda kake son ta zama." Ya ɗan numfasa ya cigaba da magana "Yanzu abinda nake so da kai, dama kasan nace zan yi bincike akan mafitar kasuwancin ka." "Eh mun yi haka, yanzu wacce mafita ka samo mana?." Cewar Al'amen kenan, da yake jin ran shi fes jin batun, za'a sawa Rahamah son shi. "To gaskiyar magana, iya binciken da nayi mafita ɗaya na hango, dole ne ka ƙara aure muddin kana son sirri, kuma ba wata zaka aura ba sai bazawara me ƴaƴa uku, kuma ta kasance me jiki a ƙalla ta fika jiki, sannan bayan ita dole ka dinga aure-aure a kai-akai, ta ukun ba'a so ta daɗe a gidan ka, sauran kuma zaka barsu amma duk wadda ta nemi tada ma hankali ka kore ta, sai kuma wani aure da zaka yi wanda shi zai kasance na biyar, ba wata zaka aura ba sai wadda take da kusanci da Rahamah sosai, dole dai wadda ta san Rahamah." Da sauri Al'amen ya tari numfashin sa yace "Kana nufin sai na auri mataye da yawa har haka? Ta yaya za'a bani auren mata bayan an san ina saki, bayan nan me mutanen gari zasu ɗauke ni? Kana ganin hakan ba matsala bane?." "Ai mafitar kenan, dole kuma in kana son dukiyar ka ta ɗore sai kayi haka, dan ina hango fitintunu da yawa a gaban ka, in baka tashi tsaye ba sai ka dawo baka da ko sisi, maganar mutanen gari ka bar min komai a hannuna, babu me zargin ka kowa yabon ka zai na yi, in kaga an fara surutu kai ka so saboda haka ka rage yawan fushi kaima." "Shikenan zan rage fushin, amma baka ganin taso da Maganar aure na yanzu ba zai zama cece kuce ba?." Cewar Al'amen kenan. "Eh to in kana ganin zai zama tuhuma gare ka, zai fi kyau ka tura ita Rahamah ɗin gidan yayarta, tunda dama kace tace ba zata zauna da Shukhra ba, in yaso sai na dakata da aikin da zan yi a kanta har sai bayan ka ƙara auren ka, a yadda take jin ƙiyayyar ka yanzu in ta tafi zata ce ba zata dawo ba. Kaga sai ka fake da wannan ka ƙara auren ka, in yaso sai mu aiwatar da aikin mu cikin sauƙi, yadda zata dawo gare ka da ƙafarta tana neman yafiyar ka akan ka maida ta, kaga sai ka murza kambun sarautar ka yadda kake so." Nan da nan Al'amen ya ji ya yi na'am da shawarar Mustapha, nan dai suka cigaba da tsara yadda zasu yi komai ba tare da an zarge su ba. Daga ƙarshe ya ce, ya bawa Malam Mustapha wuƙa da nama, ya nemo masa bazawar irin wadda yace ana so, wato me jiki kuma me ƴaƴa uku. Zuciyar Al'amen fes ya shige toilet, wanka ya fesa ya fito ya sa kaya harda su turare, kai tsaye sashin Rahamah ya shiga. Bai ganta a farlo ba, dan haka ya wuce bedroom ɗin ta kai tsaye. Zaune nake bakin gado, na yi tagumi ina ta faman aikin nawa wato tunani, _Yanzu in nace zan bar gidan nan ma ina zani? Komawata Kaduna a wannan halin wani surutu zai zamewa iyayena, za'a ce na ƙi zaman aure duka wata nawa, sannan da cikin jikina zan kama hanya na tafi kenan? In naje aka tambaye ni me zance musu? Ni da ba iya magana nake ba ko an tambaye ni._ Ina nan ina zaune, in sak'a wancan in kwance komai nayi tunani naga ba mafita bace. Shigowar sa da na ji yasa na ɗago na kalle shi, yana tsaye bakin ƙofa fuskar shi a haɗe ya dafe k'yauren yana kallona. Haɗa ido muka yi, da sauri na ɗauke kaina ina jin wata tsanar shi na taso min. Cike da gadara ya fara magana "Ki tashi ki ɗora girki, dan yanzu zan je na dawo da Shukhra, bana so ta zo ta tarda gidan babu abinci tayi zaton banyi dacen mata ba, tunda ita bata aure ni ba abin ya zama abin dariya." Ko motsawa ban yi ba, ina zaune kamar ba dani ya ke magana ba, ji nake kamar na tashi na zazzage shi ko zan ji sanyi a raina. Magana ya ƙara yi cikin faɗa yace "Wai ina magana kin share ni, wato rainin dake tsakanin mu dake ya dawo kenan, sai anyi magana kice bakya sona bayan ga kishi nan kina yi ƙiri-ƙiri." Wata irin zuciya ce ta ɗebe ni, jin da nayi yace wai kishin shi nake. Dan haka cike da tsiwa na tashi na kalle shi a wulaƙance na shiga nuna shi da hannu nace "Ka kalle ka fa dan Allah." Nayi wani irin murrmushi me ciwo nace "In ba ƙaddara ba da rabon wannan cikin, me zai haɗa ni da kai ko a hanya? Wallahi kai da kanka kasan nafi ƙarfin ka na wuce ajin auren ka, ƙaddara ce kawai ta kawo ni cikin gidan ka, kuma a kullum ina addu'a Allah ya warware min auren nan naka, wanda ya zame min dana sani, ya zame min masifa da baƙin cikin rayuwa." Nan da nan kuka ya ƙwace min, na koma na zauna ina yin shi cikin ƙunar rai. Tsaki yaja me ƙarfi, ranshi a ɓace ya nuna ni da ɗan yatsan shi yace "Wato ni ne na zama masifa a rayuwar ki ko? To ki tattara ki wuce ki je gidan Aunty Fati ki yi sati biyu, na baki hutu bana ciki da raini. In yaso in ina da amfani a rayuwar ki zaki sani, karki bari na dawo na same ki a gidannan, wallahi in na dawo na same ki kome na miki ke kika siya." Yana gama faɗin hakan ya juya ya fice, ya barni zaune na cigaba da kukana. Can kamar wadda aka mintsina na tashi da sauri, tuna kalmar shi da yace ya bani hutu. To ai ni gaba ta kaini, in sha Allahu in na bar gidannan na barshi kenan har abada. Da sauri na ɗauki wayata na kira Aunty Fati. Tana ɗagawa Bayan mun gaisa nace "Aunty kina gida ne?." "Eh ina gida lafiya ko?." Daga can Aunty Fati ta amsa min. "Babu komai, gani nan zuwa yanzu." Nace mata tare da katse wayar. Iya hijabi kawai na ɗora akan kayan jikina, na ɗauki jakata ƴar ƙarama da iya wayata da ƴan canji ne a ciki. Ina fita kai tsaye titi na fita, in da nasha tafiya kafin na isa dan ban taɓa fita ni kaɗai ba tun da na zo gidan. Da ƙyar na samu abin hawa, kasancewar titin babu cikowar ababan hawa. Ana sauke ni ƙofar gidan Aunty Fati na biya me mashin ɗin na shiga. Bakin famfo na tarda ta tana wankin kayan yara, kujera Ƴar tsugunno dake gefen ta na zauna ina faɗin "Kai nasha wuya wallahi." Ɗagowa tayi tana bina da kallo, idanun ta akan fuskata tace "Lafiya naga fuskar ki a kumbure kamar wadda ta kwana tana kuka? Sannan ina mijin naki kika zo ke kaɗai?." Cire hijabin jikina nayi na miƙe tsaye nace "Cewa ya yi na taho nan na huta, iya abinda yace min kenan ni nagaji bari na je na ɗan kwanta.'" Ban jira cewar ta ba, na nufi farlo dan da gaske a gajiye nake." Babu shiri Aunty Fati ta tsame hannun ta a ruwan wankin, ta biyo bayana tana faɗin "Wanne irin ki zo ki huta a gidana? Ko dai wani abin ne ya faru tsakanin ku yace ki taho ɗin?." Sai da na zauna akan kujera ina nishi nace "Wallahi babu komai, bayan dai abinda ya haɗa mu akan kawo ƴar yar Hajiyar su da yace zai yi farlona, nace karya kawo ta ya kaita wani sashin. Har dai saɓani ya haɗa mu dashi, muka ɗan yi faɗa yace sai ya kawo ta ban isa ba, yanzu ina ɗaki zaune ya same ni da maganar abinci, daga magana kaɗan yace na wuce gidan ki na huta tsahon sati biyu. Zama Aunty Fati tayi a gefena tana bina da kallo tace "Um um Rahamah, kodai wani abin ne ya faru daban?, dan da wuya yace ki tafi gida haka kawai ba tare da wani laifi ba, iya wannan maganar bata ci ace yace ki taho nan ba." Ta ɗan numfasa da maganar kaɗan tace "Kuma da yace ki taho nan a garin mahauka muke ne, ai ba anan ya ɗauke ki ba a Kaduna ya aure ki, Nima zaune nake gidan wani da zai ce ki zo wajena ki zauna." Gyara zamana nayi nace "Wai kina mamaki ko? To ki daina mamaki kaɗan daga haukan Al'amen kenan, in ina faɗa miki baida seti ai ke ke goya masa baya, gashi yanzu kema kin gani ai." Girgiza min kai tayi tace "Ko yanzu bawai zan yanke hukunci bane Rahamah, dole a neme shi a ji ta bakin sa shima tunda ba'a yanke hukunci da ɓangare ɗaya, dole sai shima anji ta bakin shi tukun na." "To shikenan Aunty, ku kira shi ɗin ku ji da kunnen ku, banga amfanin ƙarya da zan muku ba." Na faɗi hakan a sanyaye. "Ba ƙarya nace kin min ba Rahamah, dan ni tuni na fara dawowa daga rakiyar Jagaba, kawai dai ina son tabbatarwa ne daga shi ɗin." Daga haka tace zata kira mijin ta, shi zai nemi Al'amen tunda shine namiji. Haka kuwa aka yi ta kira shi ta faɗa masa, sai aka ci Sa'a yace yana kusa da gida ma. Koda ya dawo shi da kanshi ya yi mamakin abinda nace, haka ya dinga tambayata ko dai wani abin ne daban, in akwai wani abu na faɗa musu kafin su nemi Al'amen, dan su san irin matakin da zasu ɗauka. Cewa nayi iya wannan ne, ina ji a ƙasan raina kamar zan iya faɗan komai amma na kasa. Kiran wayar Al'amen Mijin Aunty Fati ya yi yace yana son ganin shi, babu kunya yace shi ba zai zo ba, sai dai in ana son magana da shi a je a same shi. Da ya ke a hansfree ya saka wayar muna jin komai. Cikin fushi Aunty Fati tace "Dan Allah ka ƙyale ɗan wulaƙanci, Rahamah tafi ƙarfin wulaƙantawa wallahi, gari na wayewa zata tafi Kaduna, ai ba daga sama ya samo ta ba, tana da gatan ta da komai." Ɗaga mata hannu mijin Aunty Fati yayi yace "Kar ki ce haka Ammin Islam, shi lamarin aure ba'a masa gaggawa, haka in matsala ta faru tsakanin ma'aurata ba'a shiga barin su ake, kar ki zaƙe da yawa, ku bari na je wajen nashi ni da kaina, in yaso duk yadda muka yi in na dawo zaku ji." Badan ranmu ya so ba muka amince, haka ya tafi wajen Al'amen ɗin. Fitar shi babu daɗe wa, muka ji tsaiwar mota a farfajiyar gidan. Cike da mamaki nake bin yaran dake shigowa da kallo, hannayen su ɗauke da akwatuna na har biyu, sai wata babbar jaka ta ita ma cike da kaya. Binsu muke da kallo kawai, dan ita Aunty Fati ta kasa komawa ta ƙarasa wankin ma. Tambayar su muka yi waya aiko su, suka ce Jagaba ne yace su kawo, suka juya suka tafi abin su. Cike da takaici Aunty Fati ke faɗin "Wallahi na yarda da maganar ki Rahamah, kai amma wannan mutumin ba ƙaramin ɗan iska bane." Ni dai ina zaune zuciyata cike da baƙin ciki, me hakan ke nufi? Duk da bana son shi amma banyi zaton cin mutumcin zai kai haka ba. Miƙewa nayi tsaye nace "Wallahi ba zan ƙara kwana ɗaya a garin nan ba, tafiya gida zanyi Aunty ai ina da iyaye ba wai banda su ba." Ita ma cike da takaici tace "Ai maganar tafiyar ki gida ma ta zama dole, sai dai tausayin ki nake da wannan cikin na jikin ki Rahamah." Tsaki naja nace "Wallahi ko da cikin nan zai zube sai na bar garin nan, ba zan iya ƙara kwana ɗaya ba ji nake kamar ana hura min wuta a garin nan." Muna cikin tattaunawa sai ga mijin ta ya dawo, ranshi a matuƙar ɓace ya ke, ko sannu da zuwan da muke masa bai amsa ba, ya kalle mu ya kalli kayan dake gaban mu yace "Kenan kayan sun iso ashe?." Aunty Fati ce tace "Gasu kana gani ma, wai ya ku ka yi da shi ma tukunna?." Zama ya yi yana yi Faman jan tsaki yace "Ammin Islam wannan mutumin yau na tabbatar baida hankali, ke kin ga haukan da ya dinga min a cikin mutane yana aibata yarinyar nan, Wallahi da ace nasan abinda zai yi kenan ba zan je ba." Ina ganin haka na fice ina jin zafi a zuciyata, Ni kaɗai nasan halin da nake ciki dan tsabar baƙin ciki. Kallon shi Aunty Fati tayi cike da lallashi tace "Ka yi haƙuri me ya faɗa maka?." Kwashe yadda suka yi da shi ya yi ya faɗa mata, yace Al'amen yace Rahamah bata jin maganar shi, sannan ko abinci bata dafawa sai taga dama, kuma bata yi masa abinci me daɗi kullum sai ya fita ya siyo, kuma in yace tayi irin nasu na yarabawa tace ba zata yi ba. Ga shi bata bashi haɗin kai a wajen kwanciya." Yana kawowa nan ya dakata cike da takaici yace "Kawai dai abar sauran maganar, Wallahi wasu batutuwan bai kamata ace sun fito daga bakin sa ba, dan ni kallon me hankali nake masa ada." Tsaki Aunty Fati taja cike da takaici tace "Me yace kuma dan Allah?." "Babban baƙin cikina shine, yadda ya dinga ɗaga murya a cikin kasuwa, wai harda cewa shi ba daɗin mu'amalar aure ya ke ji da ita ba, kuma da alama ba yau ya fara faɗa ba, dan har wasu daga cikin abokan kasuwancin sa da suka ji muna magana suka taso, harda me ce masa haƙuri ake ai rannan ya bashi shawarar ya sai mata maganin sanyin." Ya kalli Aunty Fati cike da takaici yace "Ki ji wannan abin kunyar dan Allah." Gaba ɗaya kan Aunty Fati ya gama kullewa, sabuwar magana take ji wadda bata taɓa zaton ba, lallai Al'amen kura ne da fatar akuya yau ta yarda da Rahamah, dan ita kaɗai tasan me take ji. Maganar da mijinta ya cigaba yasa ta bashi hankalin ta "Kin san har haƙuri na bashi akan ya maida yarinyar nan, sai ce min yayi Wallahi sai ta yi sati biyun da yace, in da kuma zaki san bai da hankali wai harda bani kuɗi wai na sai mata abinda take so. Ban amsa ba takaici yasa na baro wajen cike da kunya da ya sani." Nan fa Aunty Fati ta hau faɗa, ta inda take shiga bata nan take fita ba. Har Ni dake farlo ina jin ta. Nan tacewa Abban Islam dole na tafi gobe, yace tabbas tafiya ta ita ce mafita, ta bari ya sai min tiket ɗin jirgi dan kar na wahala na tafi gobe. Akan wannan maganar suka tsaya, Ni kam jina nake a yau akace nabi ko mota ce tafiya zan yi. Dole suka ce na bari da safe na tafi, ba dan naso ba na haƙura. Kuma nace kar Aunty Fati ta faɗawa su Abba dan Allah, har sai na bar garin tukun. Koda gari ya waye Mijin Aunty Fati yace ba'a samu tiket ɗin yau ba, wai na bari sai gobe na tafi. Haukace musu nayi ina kuka, nace ni a yau nake son tafiya wallahi ba zan ƙara kwana a garin nan ba." Bisa dole ganin yadda nake kuka, sai ga shi an memo min tiket ɗin tafiya. Haka suka kaini filin jirgi ƙarfe biyu na rana jirgin mu ya ɗaga daga Lagos zuwa garin Kaduna. _Rahamah sai dai muce Allah ya kiyaye hanya._ Haka su Aunty Fati suka shiga mota suka koma gida, gaba ɗaya jikin su a sanyaye ya ke. Me gadin su ne ya tare su a guje, hakan yasa suka dakata daga niyar shiga cikin farlon suna kallon shi. Wasu uban kayan abinci ya musu nuni dashi a bakin ƙofar ɗakin sa na gadi, ya zaro envelope a aljihun sa yace "Al'amen ne ya kawo yanzu, yace a bawa Rahamah abincin da zata dinga ci kenan. Sauran kaɗan Aunty Fati ta danna ashar, ta kalle shi cike da masifa tace "Uban wa yace ka amsa to? To yadda ka amsa maza ka ɗauka yanzu ga kuɗin mashin nan, ai kasan shagon da ya ke zama na kasuwa, in ka je kace masa Bama buƙata Rahamah ma bata garin nan a halin yanzu." Haƙuri ya shiga basu ganin ransu ya ɓaci, ya amshi kuɗin mashin ɗin ya nufi kasuwar da Al'amen ya ke. A ranshi yana faɗin _Dama shi aka bawa wannan abincin, wallahi da ba zai maida ba, yo hauka ake da zai maida ai in shine Aunty Fati riƙe wa zai yi._ A haka ya ƙarasa kasuwar, Al'amen dake zaune a cikin shagon da shi da wani abokin cinikin shi, ya hango me gadin Aunty Fati na sakko da kaya daga adaidaita. Da sauri ya tashi ya tare shi yana faɗin "Lafiya ka dawo da shi?." Kora masa bayani ya yi, ya miƙa masa komai ya juya yana tafiya a hankali, wai ko zai ce ya dawo ya ɗauki kayan ya bashi, sai ya ji yana faman faɗa yana ƙunduma ashar, jin cewa Rahamah bata garin ta tafi Kaduna. A rikice ya ɗauki waya ya kira Mustapha, yana gama faɗa masa abinda ya faru. Sai Mustapha yace, ya kwantar da hankalin sa yanzu zai wa tufkar hanci, ba dai ta tafi ba da ƙafarta zata dawo in Sha Allahu. Kawai ya koma ya cigaba da harkokin sa, ko taje Kaduna ba zata iya faɗar komai ba, har ita Aunty Fati ɗin dake zugata zai yi maganin su yanzu nan. Da wannan hankalin Al'amen ya kwanta, ya koma yana hidimar sa amma ranshi duk babu daɗi. *** *RAHAMAH.* Ƙarfe shida na yamma a ƙofar gidan mu ta yi min, ina sauka tun daga ƙofar gida yayuna ke bina da kallon tuhuma. Da ya ke cikin abokan su suke, sai kawai na gaishe su na wuce ciki. Haka cikin gidan kowa Ni ya ke kallo, da alama mamakin zuwana suke a wannan lokacin, bayan ban sanar zan zo ba, sannan ga ciki. Gaisuwata suke amsawa, amma bakin kowa motsi ya ke alamar tambaya ta ake son yi, haka kuma naga an fara hallara kowa ya shigo, jiki a sanyaye na ƙarasa ɗakin Mama Hajara, sai naga Amminmu da Mama Hajara sun biyo ni ciki. Kamar haɗin baki kuma suka ce "Allah dai yasa lafiya?." *_ALHAMDULILLAHI ANAN NA KAWO ƘARSHEN FREE PAGE, NA LITTAFIN BAK'AR ZUCIYA!._* *DOMIN SAMUN DAMAR CIGABA DA KARANTA WANNAN LABARIN, 700₦ NE KACAL, SAI DAI AKWAI GARABASA GA MUTUM GOMAN FARKO DA ZASU FARA BIYA, ZASU TURO 400₦ IYA MUTUM GOMA NACE.* *ZAKU TURO KUƊIN KU TA WANNAN ACCOUNT NUMBER ƊIN 9014644247 FATIMA MUHAMMAD OPAY SAI SHAIDAR BIYA TA WANNAN NUMBER 09014644247* _KU HANZARTA KARKU BARI AYI BABU KU, RANAR MONDAY IN SHA ALLAHU ZAN FARA SAKIN CIGABAN💃💃💃MU JE ZUWA MASOYA._ *TIRKASHI🤔 YANZU NE FA ZA'A FARA BUGA WASAN, DAN HAR YANZU BAMU TSUNDUMA CIKIN AINAHIN LABARIN ƘADDARAR RAHAMAH BA. YANZU NE ZAMU FARA TAFIYAR, DAN BAMU TAƁO AINAHIN GUNDARIN LABARIN BA, DAN AKWAI TARIN KALUBALEN DA RAHAMAH KE FUSKANTA A RAYUWAR TA, DUK KUMA ZA KU JI SU NE ANAN GABA IN MUN SHIGA AINAHIN LABARIN.* *KAR FA KU MANTA NACE MUKU, AINAHIN LABARIN YA FARU A GASKE BA ƘIRƘIRARREN LABARI BANE.* *ME KU KE TUNANI ZAI FARU A GABA?.* *1) SHIN AL'AMEN DA MUSTAPHA ZA SU YI NASARA AKAN AIKIN SU AKAN SAWA RAHAMAH SON AL'AMEN?.* *2) SHIN AL'AMEN ZAI SAMU BAZAWARAR DA MALAM YACE YA AURA, KUMA ZAI AURE TA? IN YA AURE TA YA ZAMAN SU ZAI KAYA?.* *3) SHIN ZAI YI AURE-AUREN DA AKA SASHI? KO KUWA ZAI ƘI YI NE YA BARI DUKIYAR SHI TA ƘARE A BANZA?.* *4) A CIKIN MAKUSANTAN RAHAMAH WA KUKE TUNANIN ZAI AURA?.* *5) YA ZAMAN SHUKHRA TSOHUWAR BUDURWAR SHI ZAI KASANCE A GIDAN?.* *6) ANYA KUNA GANIN AL'AMEN ZAI SAMU NASARAR BAUTAR DA RAHAMAH KUWA?.* *7) DUK IN YA YI ABUBUWAN DA AKA SA SHI, SHIN DUKIYAR SHI ZATA DAUWAMA KAMAR YADDA AKA CE?.* *BANGAREN RAHAMAH.* *1) KUNA GANIN ZATA IYA MAGANA TA TONA ASIRIN AL'AMEN? KO KUWA SUN SAMU NASARAR RUFE MATA BAKI?.* *2) WANNE IRIN MATAKI IYAYEN TA ZASU ƊAUKA?.* *3) ZATA KAMU DA SON NASHI KO KUWA TA TAFI KENAN?.* *4) ZATA DAWO DA ƘAFARTA KO YAYA?.* *NASAN AKWAI TARIN TAMBAYO ARANKU, DUK AMSO SHIN SU ZA SU ZO MUKU ANAN GABA.* *_KU DAI KU YI HANZARIN TURA KUƊIN KU, DAN KAR KU BARI AYI TAFIYAR NAN BABU KU, TAFIYA CE ME CIKE DA SARƘAƘIYA,TAUSAYI SOYAYYA,KISHI,FADAKARWAR NISHADANTARWA DA SAURAN SU_* _*RANAR MONDAY IN SHA ALLAHU ZAN CIGABA DA POSTING.*_ *_🥰MAMAN ƊAN ALBARKA CE 🥰✍️✍️_*