An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels BAKANDAMIYAR GUMURZU Chapter 1: Kana tunkarar filin babu abin da zai fara maka maraba face karajin fusatar hatsabiban mutane da aljannu kai hada ma dodanni kururuwar mayakan asali ta yawaita, kasa ta rinka girgiza da raurawa kamar zata tsage duwatsu suka rinka farfashewa, itatuwa suka rinka kamawa da wuta, guguwar annoba ta tashi sama ta tokare hasken rana wananne ya ba filin yakin damar yin duhu, hatsabiban mutane da aljannu da dodanni suka rinka shawagi a sama suna fauce rayukan junansu tabbas wanan bakin gumurxun ya cika sunansa turnuku fadan ibilisai, daidai lokacin ne wata bakar gobara ta taso daga tekun bahar sufiyya inda makaman mazanjiya suke, saidai abin da zai baka mamaki idan aka ce maka duk wanan masifa da balain dake aukuwa bai sa bakaken rundunoniba suka dakata da yakar junansu ba saima kara himmatuwa da sukayi wajan yakar junansu da kaiwa juna sara da suka mutuwar yawa ta kara yawaita mayaka da dama sun afka tarkon mutuwa batare da sun ankara ba saidai lokaci daya wanan bakin gumurxu da ake ya tsaya shaidanun mutane da aljannu da dodanni da suke shawagi a sama suka silmiyo kasa domin tsira daga halaka duk wanan abu ya faru ne sanadiyyar bayyanar wani haske mai daukar ido yana saukowa daga sama a hankali hasken ya sauko kasa lokacin da ya gama saukowa sai hasken ya fara raguwa sai suka bayyana, bayyanarsu ce tasa kowani hatsabibi dake filin yakin ya shiga taitayinsa ga duk wanda ya karanta littafin mazan jiya farat daya zai shaida wadanan mutanen da suka bayyana"lallai kam to bari mubar wajanan tunda har manyan shaidanu sun fara bayyan me ya kawo su SARKI MAHRAZ DA SARKI DUJALU nan gurin bari kagani in bar gurin tun kafi ta ritsa dani'' cewar wani bakin katon mummunan aljani tsawar da yaji ce ta dakatar dashi daga tashi sama ba kowane ya kwantsama wanan tsawar ba face sarki dujalu sanan ya fara magana cikin murya mai amo yana cewa yaku mayakan birnin matsafa, jaruman birnin sadaukai duk dacewa kunsha tsimin dodo kiryanu, an saka ku a cikin ragayar tsafi tun kuna yara hakan ba zaisa ku taka matsayin murucin kan dutse ba mu mune muruccin kan dutse tsawar da sukaji itace ta tsaida sarki dujalu daga maganar da yake cikin zafin nama suka juya domin suga wani mai tsautsayine wanan juyawar su ita tayii dadai da karasowar wasu kibiyoyin tsafi wanda ake musu take da kibiya ratsa maza badan sarki mahraz yayi saurin dafa kafadar sarki dujalu sun bace ba da tuni kibiyoyin sun cake jikinsu sana suka bayyana a gefe cikin fushi suka daga kawunansu.... BAKANDAMIYAR GUMURZU Chapter 2: Yayinda su sarki mahraz da sarki dujalu suka daga kawunansu sama domin suga wani mai karar kwanane yayi musu wanan danyen aikin sai sukaga wani tsohon aljani mai kwarjini da cikar kamala zaune kan wata bakar kujerar tsafi tsaye kan iska hannun sa na rike da wani katon littafi a jikin littafin an rubuta da babban baki KUNDIN TSATSUBA da saukarsa kasa yayi daidai da sakin fitsarin wani katon bakin aljani saboda tsananin tsoro idan kayi duba zuwa ga tarin hatsabiban mutanen da aljannu da dodanni duk zakaga zabar tsorone da fargaba tab cike da fuskokinsu ” shin mi ya kawo SHAMHARU SHAHARARRE wajan gasar kwarzon kwaraza shida ya tsufa ko tafiya ma bashiyi" cewar sarki mahraz sarki dujalu yayi murmushi ya mayar masa da amsa ya kai aarki mahraz duk yanda kake tunanin wanan gasa ta wuce nan domin kaf sarakunan duniyar mutane da aljannu, dodanni zasu taru anan duk wani tsohon hatsabi zai nuna kansa don haka kada kayi mamaki dariyar shamharu ce ta katse musu firar tasu kafin bisani ya fara magana karyarku tasha karya duk da nasan ku ba kananun hatsabibaine ba kowani babba da babban sa don haka ni shamharu shahararre nine mamallakin kundin tsatsuba nine muruccin kandutse nine gagara badau kuma ni zan ci wanan gasar ta gwarzon kwaraza kamar walkiya ya bayyana cikin shiga ta tsaffin matsafa wanda suka amsa sunansu tsawarce da ya dakawa shamharu itace ta jawo hankalin manya-manyan hatsabiban saidai kafin a ankara dayawa daga cikin mayakan sun duke bisa gwiwoyinsu " lallai yau tamu ta kare tunda abin har ya kai ga bayyanar MARGANU" cewar wani tsohon mayaki wanda kana ganinsa kasan yaga jiya yaga yau anjima ana damawa dashi marganu ya fara magana da cewa ni MARGANU dan jaddadu jikan gundugurki magallabin maza nine zan cinye garsar gwarzo gwaraza... Zan cigaba BAKANDAMIYAR GUMURZU. Chapter 3: MARGANU ya cigaba da magana dalilina kuwa na cewa ni zan cinye wanan gasa ta gwarzon gwaraza ku saboda ni na ziyarci yakin makashin maza da gallabar maza kuma ni naziyarci kogon zakun kogon da ya gagari mutum da aljan shiga nine mutuman da ake zaton ya mutu bayan shekaru aru-aru na dawo dan haka ni yafi can-canta in zama gwarzon gwaraza guguwar da ta karade filin ita ta tsaida marganu daga maganar sa nan take kowa ya daga kansa sama ba komai ne ya haddasa wanan guguwa ba face kadawar fukafukan wani kato aljani ba ajima ba aljanin ya sauko kasa wani kyakyawan dogon dattijo ya duro daga kan aljanin durowarsa ce ta haifar da wata kura yayin da kurar ta yaye sai gashi ya bayyana cikin shiga mwadda ta nuna murdadden jikinsa irinna manyan sadaukan da suka amsa sunansu duk da cewa ya fara tsufa amma hakan baisa ba kuzarinsa ya ragu yana nan yadda yake ga wanda suka sanshi cikin murya mai amo ya fara magana cikin takama da tsantsar nuna isa yana mai nuna shamharu da marganu yatsa kai tsaffin banza kusani ku baku isa ku kira kanku da gwarazan-gwaraza ba kai shamharu idan baka san ko ni wanene ba ka tambayi yayarka tsohu mundiga da danta kulkulu zasu baka labari na nin e SADAUKI makashin dodo kusumu da sarki jata nine mamallakin zoben sihiri dan haka nine yafi cancanta da in zama gwarzon gwaraza, karan takun dawakan azabar da sukajine yasa kowa juyowa wohoho nan take kallo ya koma sama abida suka gani shi yasa kowa shiga taitayin ba komaine suka gani ba face jarumi shaddadu hannunsa na rike da mashin galilul haraz bayansa kuwa ziya'ul hak ce ke take masa baya gefen damarsa kuwa sadauki hantarune hannunsa na rike da takobinsa saiful lujara hagunsa kuwa sadauki hulkas ne mai hular lamsara a gefensa kiwa yar uwarsa ce jaruma siyama suna zuwa tsakiyar filin suka ja birki kura ta tashi sama lallai idan har kayi karfin halin duban fuskokin taron hatsabiban dake wanan filin zakaga du kowa ya kara shiga taitayinsa domin miyagun makaman dake hannnun mazanjiya bayan shiru na dan wani lokaci sai aka karajin takun sawayen wasu dawakan azabar kallo ya kara komawa sama gani wasu kyawawan mutane mace da namiji sun tunkaro filin sunyi shiga irin ta mazajen fama duk dacewa macen tayi shiga irin ta kamala domin ta rufe duk jikinta idan ka dauke kyakyawar fuskarta suma sukazo suka ja turjiya bayan shiru na dan wani lokaci sai namijin ya fara magana cikin murya mai amoyana cewa .... BAKANDAMIYAR GUMURZU Chapter 4; Kyakyawan saurayin ya fara magana cikin izza da takama nasan dayawa daga cikinku sun sanni musamman ma wadan da suka halarci wajan gasar GAGARA BADAU nine jarumi HASANUL BASARI makashin maza nine jarumin da ya zamewa sarki hamadu alakakai nine zakaran gwajin dafin da ya lashe gasar gagara badau wanan kuwa da kuka gani matatace jaruma safila uwar maza duk wanda ya halarci gasar gagara badau to yasan rawar da ta taka a tare da ita akwai rantsatsiyar takobin ta wanda ta gada daga wajan mahaifinta dirar wasu fararen dawakaine ya katse masa maganar sa hakika kowa na filin yayi mamakin ta yadda wadanan dawakai suka tsallake mutane da aljanun kai hadama dodanni suka dira a tsakiyar wanan filin nan da nan kowa ya zuba ido domin yaga wasu hatsabibanne wanan kuma da me suka zo yayinda matashiyar kurar da ta tashi sakamakon dirar dawakan ta yaye sai gasu sun bayyana cikin fararen tufafi dukkan jikinsu a rufe yake ba'a ganin komai sai idanuwansu dukkansu suna rataye da zabga-zabgan miyagun takubba duk ba wanan ya ja hankalin mutanen da ke filinba abinda aka rubuta a jikin takubban nasu shine yasa kowa dake filin ya kara shiga cikin taitayinsa idan ka cire jarumi basaru da matarsa safila wanda su maimakon firgici saima murmushi da sukayi na ganin "yan uwansu musulmai abinda aka rubuta a tkobin shine cikin manyan baki SAIFUL ISLAM nan take daya daga cikin jaruman ya yaye fuskarsa ga wanda ya karanta littafin saiful islam nan take zai shaidashi nan take ya fuskanci mazanjiya kafin ya fara magana cikin murya mai amo da yadda dakai yaku mazajen jiya ina mai baku shawara da ku bace mani da gani tun kafin a fara wanan gasar domin duk jarumin da ya sake mukayi arba dashi a wanan gasar har ya yadda makaminsa ya hadu da takobina ta saiful islam to hakika makaminsa zai narke domin kunfi kowa sanin takobina tana tarwatsa duk wani sihirin tsafi komin karfinsa saboda haka ina tausaya muku domin duk duniya babu wanda bai san irin bakar wahalar da kuka sha ba wajan mallakar wanan makamai ba na mazan jiya da irin rayukan da suka salwanta na masoyanku dama abokan gabarku dan haka ina mai shawartarku da kucire rai daga lashe gasar gwarzon gwaraza ....zan ci gaba. JARUMAN GASA SUN GAMA HADUWA SAURA SARAKUNA BAKANDAMIYAR GUMURZU. Chapter 5: Wanan maganar da jarumi HUZAIFA mai takobin saiful islam ba karamin batawa mazanjiya rai tayiba wanan ne dalilin da yasa ma sadauki HANTARU ya zare takobinsa dalilinda yasa haske mai daukar ido ya cika filin hade da wani yanayi na tsohon babban sihiri kafin ya afkawa sadauki huzaifa sai yaji an ruko rigarsa ta baya cikin fushi ya jiyo abinda ya gani shi yasa jikinsa yayi sanyi jarumi shaddadu ne ya rike masa riga yayi masa murmushi kafin ya fara magana me kake ci na baka na zuba ai inda ba kasa nan ake gardamar kokowa ka kyaleshi lokaci shine zai banbance, jarumi hantar yayi kwafa kafin yayi ajiyar zuciya sana ya meda takobinsa cikin kube dalilin da yasa yanayin wajan ya komo dai-dai hayaniyace ta mamaye wajan. Abin zai baka mamaki idan nace maka duk wanan cakwakiya da take aukuwa tana faruwane a wani shimfidedan katon fili wanda duba daya zaka masa kasan cewa an tanadeshi ne kawai saboda rana irinta yanzu wato saboda gasar gwarzon gwaraza filin zagaye yake da kananu kujeru mararsa adadi iya ganin mutum sana bangaren sama kuma wani dansamaline wansa akayi shi da zinare samarsa shake take da manya -manyan kujeru na sarauta wanda akayisu da zallan zinare cikin katuwar shema wanda akayita da zare na alharini aka mata cin zanzana da ruwan zinare hakika wajan ya kawatu kallo daya zaka yiwa wajan kasan an tanadesane saboda hamshakan fitattun sarakuna wanda sunansu ya shahara wanan fili na musamman an ginashi ne a bayan birnin ruma shine babban birni a daular rumawa inda babban sarki nawwar ke mulki bairnin da duk duniya anyi ittifakin babu birnin da ya kaishi kyawu da tsari hade ma da kwanviyar hankali abinka da birni da yake gefen teku duk wani tattalin kasuwancinsu ya ta'alaka da wanan teku wanan ne dalilin da yasa idan har kayi duba zuwa ga gabar teku a yau zaka ganta cike take da manya-manyan jirage kowani jirgi da dakwai tambarin kasarsa a manne jikinsa sanan akwai hatsabiban dakaru da matsafa dake tsaronsa karan bude kofar birnin da ita kanta abin kalloce shi yasa dukkan hatsabiban mutane da aljannu da dodannin juyowa suna jiran suga wanene zai fito karan tambura,algaita da kakin sune suka fara wa mutane sallama sana suka hango wata tawaga tana fitowa daga birnin nan take kowa kallo ya koma sama idan kayi duba ga fuskokin mutanen dake wanan fili zaka ga tsantsar mamaki a tattare dasu ba komaine yasa su mamaki face wasu aljannu masu siffar batoyi da suka gani sun masa rumfa tabbas wanan inuwa ita akeyiwa kirari.... ) BAKANDAMIYAR GUMURZU Chapter 6: Tabbas wanan inuwar ita akewa kirari da inuwar mutuwa domin duk wanda ya tunkari wanan rumfa da nufin kawo wargi ga wanan hashakiyar tawagar sunan sa gawa yayin da suka iso filin nan take mafiyawa daga cikin aljannu da dodannin da hatsabiban mutanen dake filin vikinsu ya duri ruwa saboda duk wanda ya kwana ya yini a duniyar hatsabibanci to yasan wanan sarkin "kai sarki hamad mai turnuku fadan ibilisai, gagarabadau hamshakin sarki" cewar jarumi basari hakika bakaramar wahala da azaba ba muka sha a hannunsa yayin gasar gagara badau badan mun nemi taimakon ubangijin musulunci ba da tuni ya shafemu daga doron kasa jaruma safila ce tayi wanan maganar taku yake dai-dai cikin takama da nuna isa ta hamshakan sarakuna yana tafe ana shimfida masa wani tattausan kilishi wanda akayisa da jan alharini ya tunkari wata jibgegiyar katuwar kijera wadda akayita da zallan zinare ya zauna ya harde kafin ya ida gyara zamansa ne aka karajin wasu tamburan da algaitu, kakaki kowa ya kara juyowa domin ganin wanene zai kara bayyana wata tawagarce ta kara tunkaro filin kowa ya zuba ido domin ganin ko wani sarkine wanan domin tawagar ta nunka ta sarki hamard yawa da tsaro yayinda tawagar ta matso kusa abinda suka gani shi ya kusan girgiza kowa dake wanan filin sarakuna ne guda biyu tafe suke suna fira cikin annashuwa sunyi shiga irinta sarki harmad sak ga wanda ya karanta littafin mutum da aljan da littaffin mazanjiya farat daya zai gane wanan sarakun SARKI LAFFARU ne da SARKI ALKASIM tafe suke cikin tafiya ta hamshakan sarakuna wanda suka amsa sunansu a wajan jarumta, tsafi, girman kai, kai da ka gansu kasan basa shakkar duk wani mutum da aljan kai hadama dodanni suma suka samu kujeru irinna sarki harmad sak suka zauna suka kame. Abinda ya ba kowa dake wanan filinamaki shine ganin har yanzu dakwao sauran kujeru har guda biyu wanda suka rage babu kowa a kansu nan take mutane suka zuba ido domin gani wasu issassun sarakuna ne zasu kara bayyan.... BAKANDAMIYAR GUMURZU. Chapter 8. Bayyanar labulayen da suka tokare da sama ce ta sa kowani hatsabibi dake cikin wanan fili kara shiga hankalinsa sanan kowanne daga cikinsu ya ware idanunsa yana mai kallon wanan abin mamaki labulen bakine sidik idan ka daga kanka sama zaka iya cewa ya tokare da sama domin iya ganinka shine zaka gani zukatan kowanne daga cikinsu na saƙa masa abubuwa da dama shin dama can wanan labule yana nan idan yana nan me yasa bamu ganshiba tun zuwanan mu lalle wanan aikine na tsafi kafin kowa ya dawo da nutsuwarsa ne sarki nawwar ya kara tafa hannunsa karo na biyu nan take wanan bakin labule ya fara nannade kansa yana yin sama abin da "yan kallo suka gani shine ya kara rudasu kuma tsabar mamaki ya kara gauraye fuskokinsu tabbas sarki nawwar ya cika hatsabibi ba komaine ya bayyana ba face yan kallo manya da yara kai hadama tsaffi suna ta hayaniya da iface-iface inda hayaniyarsu ta cika filin kowa ya kara ware idanunsa domin gani wanan abun mamaki ganin wadanan "yan kallo, jinsi ukku ne yammacin filin jinsin mutanene wanda suka hada manya da yara da tsaffi kabilu iri-iri, yare kala-kala, sanan ga banbancin launin fata wasu bakake, farare, jajaye, kai hadama ruwan tarwada, kowa na fadin albarkacin bakinsa kowa na ziga gwaninsa kallo daya zakayiwa wanan mutane kasan sun fitone daga nahiyoyi daban na duniya tabbas wanan gasa babu in da labarinta bai kaiba, ɓangaren kudu kuwa cincirodon jama'ar aljannu ne wanda suma kar mutane da ganisu kasan sun futone daga mabanbantan kabili, addinai, da yare, dakuma nahiyoyi, wasu bakake wasu farare wasu jajaye wasu munana, wasu ma fukafuki garesu wasu ƙahonnine a kawunansu haia zaka rinka ganinsu manya da yara da tsaffi, bangaren arewa kuwa dodannine suma kamar aljannu kabilu ne iri suma sun fito ne daga mabanbanta nahiyoyi kowa na koɗa gwaninsa saidai su dodanni ba kamar mutane da aljannu bane su kowanne daga cikinsu kan yana daure da wani jan kyalle wanda akyi masa wani hatimi na tsafi wanan jan kyallen yana nufin yarjejeniyar dake tsakaninsu da sarki nawwar na cewa bazasu taba cutar da wani ba imma bako ko dan gari duk kuwa wanda yayi yunkurin cutar da wani to nan take wanan hatimin na jikin wanan kyalle zaiyi haske yanyin haske kuwa nan take wanan dodo zai kubura ya fashe ga duk dodon da aka kamashi ya cire wanan kyalle to sunansa gawa domin akwai hatsabiban matsafa da mayaka da sarki nawwar ya tanada wanda zasu daka masa wawa su halaka shi. INA YIWA KOWA MURNAN ZAGAYOWAR WANAN RANA MAI ALBARKA. Umar Abdulhadi Mati ▶ DANDALIN LITTATTAFAN YAKI AND HAUSA NOVEL BY (IBNI ABDULLAHI ABDULLAHI) BAKANDAMIYAR GUMURZU. Chapter 9. A gabashin filin kuwa katuwar rumface wadda sarakuna suke zaune a cikin ta a gefen damar wanan rumfa kuwa wata karamar rumfa ce wadda take shake da manya-manyan kujeru zaune akansu wazirai ne da hamshakan attajirai, da manya-manyan hatsabiban bokaye wanda suka shahara, hagundin wanan rumfa kuwa wani dogon membari ne wanda shima cike yake da wasu kananu kujeru a gaban kujerun kuwa wani karamin teburi ne da yake dauke da manya-manyan takardu zaune a kan kujerun kuma alkalan gasa ne sanye suke da wasu fararen kaya masu shige da babbar riga sanye akansu wasu huluna ne na saki wanda akayi su da gashin ragon dawa kallo daya zakayi musu kasan lallai mutanen kirkine domin dukkansu dattijaine masu kamala da kwar jini sanye a idanuwan kowanne daga cikinsu wani sihirtaccen gilashin wanda yake zuko duk wani abu na nesa ya dawo kusa kaganshi yadda kasan ka taba hakan zai basu damar ganin duk wani abin dake faruwa a wanan fili ba iyakar nan amfanin wanan gilashi ya tsayaba yana taimaka musu wajan ganin duk wani algus da jarumin gasa yayi domin su samu samar yin hukunci bisa adalci alkalan gasar sun fito ne daga bangare biyu akwai manya-manyan likitoci wanda aka yadda dasu a wanan kasa ta ruma sanan akwai hatsabiban bokaye wanda suka san duk wani tuggu na sihiri da makircinsa. Zagaye da filin kuwa wasu hatsabiban kasurguman mazajen fama ne tunjim cikin sulke kallo daya zakayi musu kasan sun cika jarumai kuma hatsabiban matsafa domin bayan sulken dake jikinsu kuma damatsansu cike suke da guru da laya wanda hakan zai nuna maka a shirye suke tsaf dasu tunkari duk wani hatsabibi hakika tsarin wanan katon fili na gasa yayi ga duk wanda ya kalli wanan fili zai haka zai bada wanan sheda. Tashin sarki nawwar ne tasa hayaniyar dake wanzuwa a wanan fili ta lafa sana daga baya ya daga hannunsa sama lamarin da yasa filin ya ida yin shiru kenan kama mutuwa ta gitta sana ya fara magana cikin nuna isa da izza abin da zai baka mamaki shine .... BAKANDAMIYAR GUMURZU Littafin Umar Abdulhadi Mari Ebook created by Shuraih Usman Published at www.hausaebooks.com.ng (IBNI ABDULLAHI ABDULLAHI) BAKANDAMIYAR GUMURZU. Chapter11. Yayin da sarki nawwar yazo nan jawabinsa sai ya tsaya sana ya koma kan kujerarsa ya harde yana mai fuskantar filin gasar lokacinne shugaban alkalan gasa ya tashi hannunsa na rike da wani katon karfen da aka kwakware tsakiyarsa sana karshensa aka fadadashi kamar kaho ya kafa wanan katon kafen a bakinsa ya fara magana nan take muryarsa ta karade daukacin filin ya fara magana kamar haka yanxu batare bata lokaciba zamu fara wanan gasa ta gwarzon gwaraza don haka muna umartar jaruman gasa da su bar wanan fili su tafi wajan da aka tanadar musu nan take jaruman gasa suka rabu kashi ukku kowani kashi ya tunkari wani babban daki da aka tanada na musamman domin jaruman gasa mutane suka shiga nasu aljannuma haka dodannima haka kowani rukuni daga cikin rukunannan ukku sai da sukayi mamaki mutuka yayin da suka shiga wanan dakin gani bangon dakin cike yake da makaman yaki kala-kala da wanda suka sani da wandama basu taba ganiba kafin daga bisani suka zauna suna mai saurare nan take wanan alkalin gasar ya dauko wata takarda da akayi ta da jemammar fata wadda take dauke da sunayen jaruman gasa ya fara magana kamar haka wanda zasu fara fafatawa a yau sune SADAUKI DALƘUS da JARUMI SALJAM wanda dukansu sun fito ne daga jinsin mutane nan take "yan kallo suka zuba ido domin ganin wanan sadaukai ba'ajima ba sai gasu sun bayyana suna mai fitowa daga wanan katon daki na jaruman gasa tabbas kowa na filin saida ya girgiza dagani sadauki dalƙus domin shine ya fara fitowa daga wanan dakin sadauki dalƙus bakar fata ne kuma duk inda ake neman kato to sadauki dalƙus yakai gashi dukkan illahirin jikinsa a murde yake yadda kasan an jera masa duwatsu gashi da tsawo kallo daya zaka masa kasan cewa jarumin gaskene kuma fasa taro yana bayyana filin ya dau shewa da ihu yana zuwa tsakiyar wanan fili ya ja tunga yana mai dagawa masoyansa hannu nan take filin ya kara kaurewa da shewa, bayyanar saljam ce ta kara sawa filin ya kara kaurewa da ihu inda mabiyansa suka fara kiran sunansa saljam, saljam,.. Tabbas shima jarumi saljam ba bayaneba wajan girman jiki da murdewa hakama kwarjinisu da dalƙus zai iya zuwa daya banbancinsu da dalkus kawai tsawo ne domin shi saljam yanda kasan ragowar samudawa haka yake kafin ka samu mai tsawonsa a mutane sai ka jima, da bayyanar jarumi saljam aka buga kugen fara gasa nan take suka fukanci juna sai a lokacinne suka ƙarewa junansu kallo tabbas ko ba'a gwadaba sun san za'a sha fama kafin daya daga cikinsu ya illata dan uwansa.. January mar Abdulhadi Mati ▶ DANDALIN LITTATTAFAN YAKI AND HAUSA NOVEL BY (IBNI ABDULLAHI ABDULLAHI) BAKANDAMIYAR GUMURXU. Chapter 12: Yayin da sadauki dalƙus da jarumi saljam suka karewa kansu kallo tsaf kowanne na tunanin yadda zaiyi ya cutar da abokin gwaminsa ba'a jima ba suka fara zagaya juna yaddakasan an tsikare su a tare suka ɗaga makamansu suka afkawa juna suna masu kaiwa junansu sara da suka cikin baki zafinnama yadda kasan jikinsu ba na jini da tsoka bane wohoho!! Hakika wanda ya iya ya huta, babban goro sai magogin karfe gani yadda suke safkewa junansu azabar yaki ce tasa filin gaba daya ya dau shewa da tafi kowanne yana kiran sunan gwaninsa yana kodashi hakika su sadauki dalƙus da jarumi saljam sun cika jarumai wanda suka tumbatsa a fagen fama domin kowanne daga cikinsu ya himma tu da safkewa abokin karawarsa masifar yaki haka suka wanzu har tsawon sa'a hudu amma ga yan kallo kamar yanzu ma aka fara domin su wanan yakin yana nishadantar dasu sosai domin jarumtace ta hadu da sadaukantaka abinda ya ba jama'a mamaki shine ganin salon yakinsu da zafinnamansu yaxo daya yadda kasan malami daya ya koya musu yaki a haka suka wanzu har saida makamansu suka lalace ganin haka yasa suka rabu kowanne daga cikinsu yaja da baya yana mai maida numfashi saljam ne ya fara watsar da takobinsa da garkuwarsa domin sun jima da lalacewa sana ya fuskanci dalƙus yana mai dunƙule hannunsa hade da yin murmushin mugunta sana ya bude baki karo na farko yace da dalƙus tunda salon yakinmu yazo daya kuma makaman yakinmu sun lalace me zai hana mugwada "yar ƙashi nan take dalƙus shima yayi jifa da tagwayen addunan dake hannunsa hade da yin murmushi na yadda da kai "hm inda ba kasa ai nan ake gardamar kokowa cewar dalƙus nan take shima ya fuskanci saljam yana mai duƙule hannunsa lokaci daya sukayi kururuwa suka afakawa junansu suka wanxu suna mai kaiwa juna duka kafa da hannu lokacinne fa hankalin "yan kallo ya tashi domin ganin yadda suke jibgar junansu yadda kasan jikinsu ba na jini da tsoka bane babu alamun sassauci a tare dasu kowanne burinsa ya lahanta dan'uwansa kafin kace mai tuni sun hadawa junansu jini da majina da wuya tayi wuya gumu yayi gumu da kansu suka rabu suka ja da baya suna mai kallon juna kowanne daga cikinsu yana mai tunanin yadda zai illata dan uwansa kamar an tsikaresu suka fallo da gudu saida ya rage baifi taku ukku su haduba sai dalƙus ya daka tsalle ya tsallake saljam duk tsawonsa kafin ya juyone yaji... INA YIWA KOWA BARKA DA JUMA'A ALLAH HADAMU DA ALKAIRAN DAKE CIKIN WANAN RANA BAKANDAMIYAR GUMURXU. Chapter 13: Kafin jarumi saljam ya juyo ne yaji hucin tahowar wani abu a bayansa juyowar da zaiyi yayi dai-dai da saukar wani abu a mukamikinsa yadda kasan an janyeshi haka yayi "yar dungure har sau biyu sana ya baje a gasa ba kowane yayi masa wanan kyakyawan naushin ba face sadauki dalkus wanan bajinta da dalkus yayi ba karamin burge "yan kallo tayi ba nan take filin ya dau ihu, jarumi saljam ya shafa bakinsa ya ga yana yoyon jini hakan ce tasa ya fusata ya bugi kasa da hannunsa kafin sadauki dalƙus ya ankara sai gani saljam yayi a sama daidai kansa kafin yayi wani yunkuri tuni saljam ya sanya kafafunsa biyu ya bugi kirjin dalƙus yadda kasan an janyeshi haka yayi sama sai da yayi tafiya mai nisa sana ya fado kasa hakika dalkus yaji wanan dukan domin yana tari jini ya biyo baya nan take masoyan saljam suka dau ihu hade da tafi nan take saljam ya nufi dalƙus yana mai dariyar mugunta yana isa wajan da dalƙus yake kwance kamar gawa ya sukuya ya kamo kafar dalƙus ya jawo shi kasa ya kawoshi tsakiyar wanan filin sana ya kamo kafar dalƙus ta hagun ya sanya a tsakiyar ƙafafunsa yana yunkurin karyawa hakan tasa hankalin dalƙus ya tashi cikin karfin hali ya sanya kafarsa ta dama ya daki bayan saljam ya fadi can gefe yaje da fuska hakan taba dalƙus damar miƙewa cikin zafin nama kafin saljam yayi yunƙurin mike tuni dalƙus ya karaso yayi tsalle sama tun a sama ya rike kafarsa ta dama ya saita kafar saljam ya diro kanta jikake kats kashin ƙafar saljam ya karye saljam yayi wani irin ruri yana mai rike kafarsa data karye ya yunkura domin ya mike amma ya kasa nan take ya baje kasa hakan tasa filin ya dau shewa da ihun "yan kallo nan take wasu mutane su hudu sanye da fararen kaya suka shigo wanan filin suna rike da wani karamin gado suka sunkuci saljam suka dora a gadonan sana sukayi waje dashi hakan shike nuni da cewa dalƙus ne yayi nasara nan take dalƙus ya ɗaga hannun sa sama yana mai kwarara ihu nan take filin ya ƙara kaurewa da ihu da tafi masoyan dalƙus na kiran sunansa dalƙus, dalƙus.. nan take ƙofar wani daki ta bude dalƙus ya fada ciki yana dafe da ƙirjinsa. Shigar dalƙus ke da wuya wanan dakin sai wanan alƙalin gasa mai kiran suna ya ƙara tashi yana mai cewa dalƙus ya haye zagaye na farko na wanan gasa, jaruman da zasu kara yanzu sune dodo zalƙim babban jika ga dodo kiryanu da dodo kalkus jika ga dodanniya afjagata uwar dodannin duniya take wata katuwarkofa ta bude abinda "yan kallo suka gani ba karamin firgitasu yayib (IBNI ABDULLAHI ABDULLAHI) BAKANDAMIYAR GUMURXU. Chapter 14. Ba komai ne ya firgita "yan kalloba kuma ya dugunxuma hankalinsu ba face tozali da sukayi da mummunar jibgegiyar halittar da aka kira da dodo kalkus jika ga dodanniya abjagata uwar dodannin duniya tozali da dodo kalkus da "yan kallo sukayi ne yasa dayawa daga cikinsu musamman ma yara tsulewa da gudawa tsaffi kuwa fitsarine ya kuɓuce musu masu karfin haline daga cikinsu suka yunkura zasu gudu amma hakan bata samuba sakamakon tozali da dodo zalƙim da sukayi nan take suka ƙame waja daya razanar da sukayi ta farko ta daɗu hakan tasa wasu suka fara sumewa ganin haka yasa sarki nawwar saurin nuna wanan filin da yatsarsa hakan tasa wata ƙawanya ta haske ta bayyana wadda ta zagaye dilin gaba daya kamar gilashi hakan tasa "yan kallo fara dawowa cikin hayyacinsu tabba dodo kalkus da dodo zalƙim munana ne ajin farko girmansu ya wuce misali sanan ga tsawo da suke dashi dake barazanar kere doguwar katangar da ta zagaye wanan fili yadda kasan "yan biyu tsawonsu da girman jikinsu daya abin da kawai ya banbantasu shine shi dodo zalƙim yana da fiffike a bayansa sanan yatsunsa sogayene manne a jikinsu dogayan farata ne kamar takobi sai walkiya suke da alama wasasu yakeyi domin suna da kaifi da tsini matuka sabanin dodo kalkus wanda hannayensa hudu masu kama da na bil'adam a komani hannu yana rike da wasu miyagun tsafaffun takubba bakake bayyanarsu ce tasa jinsin dodanni ihu da kururuwa wanda hakan yasa filin yayi wata karamar girgiza lokacinne su dodo kalkus suka fuskanci juna hakika daga ganin yadda suke kallon juna karce tasan kar saida suka jima suna kallon juna kowanne daga cikinsu alamun shakku sun bayyana a fuskarsa karara domin wanan haduwace ta tantiran hatsabiban da suka buwayi duniya ma'ana dai babu wanda sunan sa bai shaharaba a duniyar mutane data aljannu kafin daga bisanni kamar an umarce su sukayi girgiza nan take mutane suka sha mamaki domin tsawonsune da fadinsu ya fara raguwa har saida tsawonsu da fadinsu ya komo kamar na bil'adam sana suka kwantsama wata uwar kururuwa sukayi tsalle suka afkawa juna... BAKANDAMIYAR GUMURXU. Chapter 15. Kururuwar da su dodo kalkus sukayi da takun sawayensu ne yasa kasar wajan ta fara girgiza da raurawa kamar zata tsage sai da ya rage baifi taku biyar ba su hadu sai suka daka wani wawan tsalle sukayi sama a samar suka ruguntsume da azababan yaki suka wanzu suna masu kaiwa juna sara da suka yawan kaikawo da suke a sama ne ya haifar da wata bakar guguwa badan wanan kawanyar haske da sarki nawwar ya samar ta tsafi mai kamar gilashiba da tuni wanan guguwa ta tada hankalin wanan fili yayin da gumurxu yayi gumurxu, naci da taurin kai da juriya ta hadu da kishiyarta sai abin ya kara muni domin kowanne daga cikinsu yaki yake iyakar karfin babu alamun saussauci a tare dasu kowa budewa abokin gwaminsa kofofin masifa yake idan faratan dodo Zalƙim suka hadu da tsafaffun takubban dodo kalkus sai kaga wani tartsatsin wata bakar wuta ya tashi tare da wani dunkulallen bakin hayaki wanda shikansa hayakin idan mutum ya shaƙeshi zai iya zama guba a gareshi yayin da masifa tayi yawa da kansu suka rabu dole kanwar naƙi domin kowa a cikinsu babu abinda yake sai maida nufashi hade da hucin fusata kafin su ja da baya suka ƙara kwarara wani sakaran ihu suka afkawa junansu saidai wanan karon fadan nasu ya sha banban da na baya domin wanan karon ruƙunƙume juna sukayi a sama sana sukayo kasa inda suka dira a tsakiyar filin gasar suka ruguntsume da wani azababban yaki mai taken ayita ta kare domin wanan karon kowa iyakar karfinsa yake yaƙar dan uwansa kowanne daga cikinsu ya wanxu yana juyewa dan uwansa dabaru da tsantsar muguta da masifar da suka jima ahlinsu na koyar dasu tabbas su dodo zalƙim yau sun nunawa duniya cewa su jinin dodanni ne domin kowanne daga cikinsu ya samu nasarar sarin ɗan uwansa amma abin mamaki maimakon jini ya biyo baya sai tartsatsin wutane ya tashi kamar sun sari mulmulallen bakin ƙarfe hakan tasa kowanne daga cikin su ya daka tsalle yayi baya yana mai kallon makaminsa da kuma abokin gwaminsa cikin tsabar mamaki da kaduwa domin dukkansu babu wanda bai yi imani da makaminsa ba sudai takubban da suke hannun dodo kalkus a wajan kakarsa dodanniya abjagata uwar dodannin duniya ya gajesu kuma tsafaffune wanda duk abinda ka sara dasu sai ya tarwatse ya ragargaje, su kuma faratan dodo zalƙim suma haka ahlinsu sunyi imani da cewa duk abinda suka sara da wanan farce nasu sai sun rabasa biyu, hakan ce tasa wanan dodanni ƙara fusata nan take kowanne daga cikinsu ya mayar da makaminsa hade da dunƙule hannu kamar an tsikaresu a tare....BAKANDAMIYAR GUMURXU. Chapter 16. Idan ka kalli fuskar kowa dake kallon wanan bakin gumurxu musamman ma bangaren dodanni zakaga tsabar tsoro ne da fargaba ya mamayesu kowanne yana ganin idan akayi wanan haduwa za'a iya yin galaba a kan gwaninsa yayin da su dodo zalƙim suka kusan haduwa sai suka yi tsalle sama kowanne daga cikinsu ya ware hannayensa iya ƙarfinsa suka gabzawa juna naushi shi dodo zalƙim ya samu nasarar gabzawa dodo kalkus naushi a baki wanda hakan yasa hakoransa na gaba futar burgu daga bakinsa hade da wani dunkulalle jin shi kuwa dodo kalkus a ƙirjine ya samu damar gabzawa dodo zalƙim naushi wanda hakan tasa numfashinsa ya sarƙe yayi wani sarƙaƙƙen tari yayo kakin wani bakin jini hakan tasa wanan dodanni silmiyowa ƙasa kowanne daga cikinsu ya baje a ƙasa a galabaice suna masu maida lumfashi sama-sama hakika wanan duka da suka yiwa junansu ya galabaitar dasu matuƙa kamar an tsikaresu kowanne daga cikinsu ya doki ƙasa da hannunsa nan take suka taso sama suka dire da ƙafafuwansu hakan ne ya haifar da wata ƙaramar guguwa kamar ba su baneba dazu suke a galabaice ba suka ƙara runguntsumewa da azababen yaki suka rinƙa jibgar junansu kamar babu jini da tsoka a jikinsu sukarinƙawa junansu luguden duka hannu da ƙafa hakan tasa suka hadawa junansu jini da majina tun suna gumurxun a tsaye har suka durƙushe ƙasa suna mai turmusuwa a ƙasa haka sukayi ta juyi a ƙasa wanan ya danne wancan wancan ya danne wanan..BAKANDAMIYAR GUMURXU. Chapter 17. Halin da su dodo zalƙim da kalkus suke cikine ya tada hankalin "yan kallo musamman ma bangaren dodanni domin dayawa daga cikin makusantan wanan dodanni sun fara zubar da hawaye domin sun sadaƙar cewa dolene a rasa ɗaya daga cikin wanan dodanni kokuwa ma a rasa su gaba daya a baɗini kuwa sarki nawwar yafi kowa razana da shiga tashin hankali domin idan har haka ta kasance tamkar an tarwatsa masa babban burinsane na duniya wanda ya shafe shekaru da dama yana tanadinsa amma duk wanan tashin hankali a zuciyarsa kaɗai yake idan kayi duba ga fuskarsa ma saidai kaga yana murmushi mai kama da na yaƙe. Ɓangaren dodo kalkus da zalƙim kuwa abin yayi muni matuka domin ruƙunƙume suke da juna sun shaƙe wuyan junansu numfashinsu na ƙoƙarin ɗaukewa amma saboda tsananin baƙin naci da tsabar taurin zuciya babu alamun sassauci a tattare dasu domin kuwa kowanne daga cikinsu ya gwammace ya rasa rayuwarsa akan ya faɗi wanan gasa saboda tsabar gaba da cakwakiya tsamar dake tsakaninsu kai hadama ahlinsu domin kowa yana ji kuma yana ganin ahlinsu ne mafi ƙarfi da buwaya da maita haɗe da tsabar hatsabibanci da mugunta a jinsin dodanni hakance tasa kowanne ya zage dantse iyakar ƙarfinsa domin ya rinjayi abokin gwaminsa domi faɗuwarsu dai-dai yake da jawa ƙabilarsu abin kunya da gorantawa a cikin jinsinsu na dodanni . Bangaren su dodo zalƙim da kalkus kuwa abin ƙara muni yake domin kowanne daga cikinsu ya fara jiyo ƙamshin mutuwa domin kuwa jajayen idanuwansu sun ƙara ja kuma sun fito fili yadda kasan zasu faɗo kasa hancinsu ya ƙara fadi sai wani baƙin hayaƙi ne ke fita fuskarsu ta ƙara baƙi da muni wanda da ace mace mai ciki zatayi arba dasu a wanan halin da suke ciki zata iya yin ɓarin ɗan dake cikinta saboda tsabar razana hakan tasa makusantan wanan dodanni fara yin magiya ga alkalan wanan gasa da su tsaida wanan gasa amma kash!! babu dama domin ƙaidar wanan gasa kenan duk tsanani idan aka farata babu zance a dakata sai wani ya samu nasara. Shure-shuren da su dodo kalkus suka fara ne yasa "yan kallo fara ihu nan take sarki nawwar ya nuna su dodo kalkus da yatsa wata guguwar tayi futar burtu daga hannunsa ta fincike su dodo zalƙim tayi jifa dasu kowanne daga cikinsu aka watsar dashi gefe a sume tabbas badan wanan guguwa ba ta sarki nawwar da tuni sun jima da sheƙawa barzahu. Ganin cillin da akayi da sune yasa ni fecewa domin kada a dawo kaina dan haka masu karatu saidai kuyi hakuri nima nayi takaina amma idan da masu rakiya sai suzo mu koma BAKANDAMIYAR GUMURZU. Chapter 18. Yayinda wanan guhuwa tayi watsi dasu dodo kalkus a sume nan take wasu likitoci daga jinsin dodanni suka shigo da wani katon gado na ƙarfe suka sunkuci su dodo zalƙim suka yi wajen fili dasu sai lokacin ne jama'a suka lura da cewa dare ya fara domin rana tuni ta jima da faɗuwa hakance tasa wanan alƙali mai kiran sunaye ya tashi tsaye ya kafa abin magana a bakinsa sana ya fara jawabi kamar haka"A ƙa'idar wanan gasa ba'ayinta da daddare don haka duba da yadda dare ya fara zamu tsaida wanan gasa sai gobe amma bayan haka a gaban idanuwanku kunga yadda wanan karawa ta wakana tsakanin dodo kalkus da zalƙim dan haka a daren yau alƙalan wanan gasa zasu zauna su yanke hukuncin da samun matsaya akan wanan fafatawa nan take aka buga wani kuge wanda ke nuni akan dakatar da wanan gasa inda sarakuna da manya-manyan hatsabiban bokaye da attajirai na duniya suka fara mikewa tare nan take dakaru sauka zagayesu domin tabbatar da tsaro, tawagar sarki nawwar ce akan gaba sana sarki hammad, sai sarki laffaru da sarki alkasim sana gimbiya aryala sai sarki dujalu da mahraz da sauran alƙalan gasa da manyan attajirai, matsafa sai mutanen gari wanda kowanne daga cikinsu sai ya nuna wata alama wadda take nuni da cewa shi haifaffen garinne sana za'a barshi ya shiga wanan dokace wadda sarki nawwar ya sanya duk baƙon da yazo saidai ya yada zango a wajan gari akwai rumfuna marassa adadi da aka tanada saboda baƙin da sukazo wanan gasa a jikin katangar wanan tamkeken fili kuwa wani ƙatan babban gidane mai cike da kayan ƙawa da kayayyakin alatu na more rayuwa wanan ƙaton gida an tanadeshi don jaruman gasa indai mutum bai kasance wani hamshaƙin attajiri ko sarki shine kaɗai aka yadda ya shiga cikin gari. Alamarin sarki nawwar kuwa yayi da ya shiga cikin garin ruma nan take sauran jama'ar da basu samu damar ziyartar wajan gasa ba suka rinƙa fitowa suna masu zubewa a ƙasa suna kwasar gaisuwa kowanne daga cikinsu fuskarsa cike da annuri domin suna matuƙar ƙaunar sarkinsu haɗe da matuƙar girmamashi saboda adalcin da yake nuna musu hade da matuƙar ƙaunarsu da yakeyi da nuna kishi a garesu wanan ce tasa suma suke ƙaunarsa da kishinsa. BAKANDAMIYAR GUMURZU. Chapter 19(BIRNIN RUMA) Tabbas samun birni mai kyawu, tsari kamar birnin ruma sai an tona idan ka shigo garin babban abinda zai fara ɗaukar maka hankali shine babban hanyar da idan ka bita ɗoɗar zata kaika har fadar sarki nawwar gefen wanan hanya cike yake da filawowi koraye firensu mai ƙamshi da ɗaukar ido, babu abin birgewa da ban sha'awa sama da gineginen wanan birni wanda dukkansu iri dayane banbanci kawai shine iyakar wadatarka da dukiyarka iyakar benayen da zaka ɗora a gidanka wanan shine dalilin da yasa dogayen gine-gine suka yawaita a wanan birni babban abin burgewa kiwa shine kowata unguwa da kalar fentin da gidajen unguwar suke dashi wanda hakan ce ma tasa kowace unguwa ake kiranta da sunan fentin da gidajen unguwar ke dashi misali unguwar ja, unguwar fara, unguwar ɗorawa, unguwar da gidan sarautar wanan birni yake kuwa sune suke da gine-gine ruwan zinare wanda kuwa duk gidan da kagani a wanan unguwa to gidane na sarauta wanda wanan unguwa kaf birnin ruma babu unguwar da ta kaita tsari, kyawu da tsaro a gefen unguwar kuwa wani tafkeken shimfiɗeɗen filine wanda yake cike da shaguna kowani shago kuwa cike yake da kayayyaki na amfanin yau da kullun, kallo ɗaya zaka yiwa wanan ƙaton filin kasan shine kasuwar wanan birni wanda take ci kullum wanan ne dalilin da yasa mafi yawancin mutanen wanan birni "yan kasuwa ne wananne salilin da yasa kusan mafi yawancin mutanen dake wanan birni attajiraine, ɓangaren sadaukantaka da jarumta a kaf wanna daula ta rumawa babu garin da ya tara jajurtattun sadaukai, hatsabibai kamar birnin ruma hakama a duniyar tsafi sun yiwa sauran birane fintinkau wanan nema dalilin da yasa sauran daulolin dake maƙwabtaka dasu ke masifar tsoronsu kuma suke binsu sau da ƙafa. Sarki nawwar ne a ƙuryar turakarsa tsaye yake yana ta kaikawo tun lokacin da sukayi ban kwana da su sarki alkasim kowa ya nufi masaukinsa dake cikin wanan gida shima ya nufi turakarsa yana zuwa alkyabbarsa kawai ya fidda yayi tilli da ita ya kama jiran bokansa amma har yanzu bai zoba wanan ne dalilin da yasa fuskarsa ta ƙara canzawa tsananin damuwane bayyane a fuskarsa ƙarara gyaran muryar da yaji ne yasa shi saurin juyowa bayan sa nan take yayi arba da boka nazara ne tsaye yana riƙe da wata sanda ta tsafi fuskarsa babu alamun annuri ko kaɗan wananne dalilin da yasa gaban sarki nawwar faduwa kenan tabbas abin da yake zato da tsammani na gab da faruwa.. KANDAMIYAR GUMURXU. Chapter 20.(burin sarki nawwar) Tabbas sarki nawwar ya girgiza da yanayin da yagani a fuskar boka nazara kafin ya fara magana ne ya ya tafa hannuwansa biyu nan take yanayin ɗakin ya canza iskar dake kaikawo ta canza ta koma wata tsaya cak komai na ɗakin ya koma kore cikin fargaba sarki nawwar ya tambayi boka nazara "ina fatan dai shirinmu bai tarwatse ba " sai lokacin boka nazara ya ya risina yana mai sakin fu skarsa ya mai duniya hakika shirin mu bai tarwatseba har yanzu yana kan hanya amma daga yanzu har zuwa gobe komai na iya faru ma'ana kowanne daga cikin wanan dodanni zaibiya rasa ransa yanzu na baro likitoci na jinsin dodanni sun duƙufa wajan ceto rayuwarsu don haka ba zamu ɗau wani mataki ba har sai munga mai gobe zatayi nan take boka nazara ya ɓace bat kamar bai taba wanzuwa ba shikuwa sarki nawwar futa yayi daga cikin turakarsa ya nufi turakar matarsa gimbiya shamila, shigarsa ɗakinnke da wuya ya isketa a zaune ta caɓa ado sanye take da kaya na alfarma wanda kallo daya zakayi wanan riga dake jikinta kasan ta isa jarin wani hamshaƙin attajiri kunnuwanta da wuyanta, hannayenta sanye suke da dankunnaye, awarwaro, sarƙa ta zinare tabbas shamila kyakyawa ce ajin farko domin samun mace mai kyawunta sai an tona wanan shiga da tayi shine ya ƙara fiddo tsantsar kyawunta jin shigowar sarki nawwar ce tasa gimbiya shamila ɗago kanta nan take ta tashi tana mai yiwa sarki nawwar murmushi nan take duk wata damu dake ran sarki nawwar ta yaye haka ake son duk wace mace wadda ta amsa sunanta ta kasance ga mijinta hakan na faru a duk lokacin da sarki nawwar ya shiga cikin bakin ciki da damu itace mai kwantar masa da hankali. A can ɓangare guda kuwa alƙalan gasane suka haɗu dukkansu idan kayi duba sosai zakaga shaharu, sarki mahraz, sarki alƙasim, sarauniya aryala ne a manya-manyan kujeru sana sauran alƙalan wanda suke zaune akan ƙananun kujeru ana tattaunawa akan wanan fafatawa ta dodo kalkus da dodo zalƙim inda sarki alkasim ya tashi ya fara magana cikin girman kai da taƙama ba komai ne ya haɗamu anan ba face dan mu tattauna akan wanan fafatawa da akayi tsakanin dodo kalkus da dodo zalƙim dan misamu cimma matsaya kuma mu yanke hukunci akan abinda ya dace...... Wannan ebook din yazo muku ne daga shafin www.hausaebooks.com.ng Domin jin karashen labarin sai ku cigaba day bibiyar shafinmu www.hausaebooks.com.ng BAKANDAMIYAR GUMURZU Kashi na Uku 3 Na Umar Abdulhadi Math Ebook created by Shuraih Usman Published at www.hausaebooks.com.ng AKANDAMIYAR GUMURXU. Chapter 21. Sarki alƙasim ya caba da bayani kamar haka dan haka yanzu idan da mai shawara a kan wanan zaman da zamuyi to muna jira sarauniya aryala ce ta tashi ta fara bayani dukkan mu mun jima da sanin cewa tun farkon duniya har zuwa yanzu idan har akayi ragas a tsakanin runduna ko jarumai biyu to wanan yana nuna ƙarfi yazo daya dan haka babu wani ɓangare da yayi nasara ko ya faɗi dan haka wanan hukuncin mai sauƙine dole cikin ɗaya ayi biyu imma dai a ƙara basu dama idan sun warke su ƙara fafatawa domin a samu wanda zaiyi rinjaye kokuma a idan sui kowanne daga cikinsu a sauya masa sabon abokin gwami yayin da sarauniya aryala tazo nan a zancenta nan take ta koma mazauninta ta zauna. Bayan "yar tattaunawa da alƙalan gasa sukayi ne suka yanke hukuncin za'a ƙara haɗa dodo kalkus da dodo zalƙim fada bayan sun gama jiyan raunukansu a haka wanan taro ya watse kowa ya koma masaukinsa. Tun da asubahi filin gasa ya cika da mutane aljannu, dodanni ayau mafi yawancin "yan birnin ruma kowa ya halarci wanan gasa domin kuwa waɗanda basu samu damar zuwa wanan gasaba jiya yau sune gaba-gaba domin kuwa sunji labarin irin baƙin gumurxun da akayi jiya kowanne daga cikinsu ya ƙagu gari ya ida waye a fara wanan gasa gari na ida wayewa ne aka fara jin ƙaran tambura da algaitu wanda ke nuni da cewa sarki nawwar ne da jama'arsa ke tafe hakan tasa "yan kallo fara nutsuwa. Shigowar su sarki nawwar ce tasa filin gabaki ɗaya yahau ihu haɗe da tafi domin kuwa shigar da su sarki nawwar sukayi tayi matuƙar burge ''yan kalla domin kuwa dukkan sarakunan wanan karon hadewa sukayi a tawaga guda dukkansu suna sanye da wasu irin riguna na alharini wanda akayi musu cin baki da ruwan zinare sanan suka ɗora alkyabbu farare hakan tasa ƙwar jinisu ya ƙaru ta yadda kallo daya mutum zaiyi masu ya gane cewa suncika hamshaƙan sarakuna wanda suka tumbatsa wajan tattalin arziƙi da girman masarauta har su sarki nawwar suka zauna a karagunsu "yan kallo basu daina taɓi ba zamansu ke da wuya sai wanan alƙalin mai kiran suna ya miƙe domin kiran waɗan da zasu fafata hakan tasa "yan kallo nutsuwa yadda kasan mutuwa ta gitta hakan kowa ya nutsu yana mai kashe kunne da sauraran sunan da za'a kira ba tare da ɓata lokaciba wanan alƙali mai kiran suna ya kafa abin magana a bakinsa sana ya fara magana yanzu ba tare da ɓata lokaci ba zamu fara wanan gasa ta gwarzon gwaraza yanzu jaruman gasar da zasu kara sune aljana zarma wadda akafi sani da RUWAN BALA'I tare da aljana zabariyya wadda akafi sani da TAURARUWA MAI WUTSIYA GANINKI BA ALKAIRI... Tsawar da alƙalin yaji ce tasashi dakatawa da ida maganarsa inda ya ɗaga kansa cikin firgici hakace ta faru ga duk mahalukin dake wanan filin nantake kallo ya koma sama domin abinda mutane sukayi tozali dashi ba ƙaramin firgitasu yayiba... BAKANDAMIYAR GUMURZU. Chapter 22. Guguwar annobar da tashi sama ce itace tayi sanadiyar rikita filin haɗe da ƙara tada hankalin filin gaba daya abin zai baka mamaki idan nace duk wanan tashin hankalin da ke faruwa a wanan filin bai shafi wanan hamshakan sarakunan ba domin su ko a jikinsu domin kuwa guguwarma ko kusantarsu batayiba kamar tana jin tsoron su tabbas "yan magana sunyi gaskiya da sukace "wani darene jemage bai gani ba" kana kallon fuskokinsu maimakon kaga tashin hankali da razana su murmushi ma suke na isa da taƙama ba komaine ya haifar da wanan baƙar guguwar ba face kaɗawar fukafukan wanan shu'uman, tantiran baƙaƙen aljannun da suka gallabi duniyar aljannu domin kuwa sunansu yayi shura matuƙa kuma labarin hatsabibancin su babu inda bai kutsaba a duniyar aljannu tozalin da ''yan kallo sukayi dasu ne shine ya zame musu baban tashin hankali da firgici wanda hakanne yayi sanadiyar sumewar wasu daga cikin ƙanan yara da tsaffi wanda basu saba arba da aljannuba musamman ma wanda yau suka fara halartar wanan fili ganin abin dake faruwane yasa sarki nawwar yayi saurin nuna filin da yatsarsa nan take wanan ƙawanya ta haske ta ƙara bayyana ta zagaye wanan fili dif kamar ɗaukewar ruwan sama wanan tashin hankalin da baƙar guguwar da ta addabi mutane ta ɗauke lokacinne hankalin kowa ya dawo jikinshi. A tare su aljana zabariyya suka sulmiyo ƙasa suka dira a tsakiyar wanan fili na gasa dirarsu ce tayi sanadiyyar tashin wata baƙar ƙura haɗe da wata ƙaramar girgizar ƙasa kamar haɗin baki suka juyo a tare suna masu fuskantar juna ganin bayyanar wanan hatsabiban aljannun ne yasa jama'ar aljannu ihu haɗe da tafi kowanne daga cikinsu yana kiran sunan gwanarsa yana koɗata wanda hakan ce tasa filin gasar ƙara rudewa kafin daga bisanni kowa yayi shiru yana mai maida hankalinsa kan wanan hataabibai biyu tabbas wanan haɗuwa itace ake kira da kar tasan kar domin kuwa wanan aljannu kowacce daga cikinsu ba ƙaramar hatsabibiya bace kuma ba ƙanan baƙaƙen azzalumai bane domin kuwa cikin ƙanƙanin lokaci sukan tarwatsa babbar ruduna ko ƙaramin gari na aljannu wananne dalilin da yasa hatsabibancinsu ya karaɗe duniyar aljannu kowa na fatan Allah ya kawo ranar da wani abu zai haɗasu a fafata domin a fidda wadda tafi hatsabibanci, jarumta, da ƙarfin dantse sai yau gashi sun haɗu a filin gasa tabbas aljannu sunfi kowa ɗauki da farincikin wanan haɗuwa wananne dalilin da yasa kowanne daga cikinsu ya murje idanuwansa da tattara hankalinsa da nutsuwarsa domin yaba idonsa abinci... AKANDAMIYAR GUMURZU. Chapter 23. Kallo daya zakayiwa fuskokin jama'ar aljannu kasan cewa sunfi kowa dauki da zaƙuwar a fara wanan fafatawa domin ko nufashin kirki babu maiyi kowanne daga cikinsu ya zazzaro idanuwa yayi ƙuri ko ƙiftawa bashi so yayi dan kada ayi wani abun bai ganiba kallo ɗaya na musu bansan lokacin da na bushe da dariya ba domin tunawa nayi da "yar ƙuriga hakika ko kai mai karatu kagansu a wanan hali idan baka da tsoro baka sanin lokacin da dariya zata ƙwace maka domin wasunsu saura ƙiris idansu ya faɗo. Yayin da aljana zarma ruwan bala'i da aljana zabariyya tauraruwa mai wutsiya suka fuskanci juna wananne karo na farko da suka fara haɗuwa gashi har zasu fafata kowacce daga cikinsu shakka ce ta hana ta afakawa "yar uwarta domin duk da basu taɓa haɗuwa ba sun san juna domin labari kowacce daga cikinsu babu inda bai zagayaba kafin su fara zagaya juna kowacce tana mai ji har cikin ranta cewa yau ta haɗu da gamonta ba'a jima ba suka fara zagaya juna suna masu ƙarewa juna kallo sai lokacinne suka lura cewa ai wanan filin gasar bazai ishesu su fafata ba hakance tasa kowacce daga cikinsu tayi girgiza nan take tsayinsu da girmansu ya ragu ya koma madaidaici hakan na faruwa kamar da haɗin baki a tare suka wangame baki suka kwarara wata uwar kururuwa wadda ta haifar da ƙaramar girgiza-gizar ƙasa wani dunƙulallen hayaƙi tare da wata baƙar wuta sukayi fitar burgu daga bakunansu suka tashi sama kafin su fallo da gudu wanda takun sawayensu kashi saida yasa ƙasa ta motsa kafin su haɗune aljana zarma ta zaro wasu tsafaffun baƙaƙen miyagun takubba inda itama aljana zabariyya ta zaro wani makami mai kama da lauje wanda saboda masifa da dafin dake jikinsa har wani tiririn baƙin hayaki ke tashi daga jikinsu a tare sukayi tsalle sama suna haɗuwa su kacame da azababban yake suna masu kaiwa juna miyagun harehare masu barazana fauce rayuka cikin baƙin zafinnama da azabar yaƙi cikin ƙwarewa kowacce take saraffa makaminsa tabbas "yan magana sunyi gaskiya da suka ce "wanda ya iya ya huta'' domin da kaga yadda suke sarrafa makamansu kasan sunjima ana damawa dasu a sama suke wanan faɗa amma saboda shawagin da suke haɗe da kaiwa da komowar da suke ne ya haifar da tashin wata ƙaramar guguwa tabbas waɗanan aljannu sun cika hatsabibai kuma shaiɗanu domin kowacce iyakar ƙarfinta take wanan yaƙi domin sunyi imanin cewa idan har sukayi sakaci to kwaf ɗaya za'a musu ba shiri suka dakata suna masu ja da baya taku takwas sana suka zubawa junansu na mujiya... Febru BAKANDAMIYAR GUMURXU. Chapter 24. Yayinda aljana zarma da aljana zabariyya suka zubawa juna ido kowacce babu abinda takeyi face hucin wani baƙin hayaƙi na fita daga ƙofofin hancinsu saboda tsabar fusata da kowaccensu tayi babu abinda kowacce take tunani wanda ya wuce ta yaya zata samu lagwan abokiyar fafatawar ta kamar an tsikaresu a tare suka ƙara fallowa da gudu suna masu ƙarajin fusata saboda tsabagen ƙarfin gudunsu har wata bakar guguwace ke masu rakiya suna haduwa suka ƙara ruguntsumewa da wani sabon azababen yaki wanda yayi sanadiyyar tashin hankalin filin gaba ɗaya a wanan karon kowacce da dukkan ƙarfinta take wanan yaƙin wanan ce tasa kowacce ta sauya salon yaƙinta suka haɗa da kaiwa juna duka da ƙafafuwansu haɗe da kai mazga da fuka-fukinsu haƙiƙa wanan karon abin ya ƙara muni matuka ana cikin wanan baƙin gumurzune aljana zarma tayi wani rimi sama tana mai kaɗa fuka-fukinta cikin azababban gudu tayi sama ganin hakanne yasa aljana zabariyya binta a baya amma kafin ta cimmata sai gani akayi tayi wani irin juyi a sama ta sulmiyo ƙasa kafin aljana zabariyya tayi wani yunƙuri tuni aljana zarma ta ɗaga wanan tsafaffun baƙaƙe takubbanta ta katawa aljana zabariyya wani wawan bahagon sara tabbas wanan jarumta da aljana zarma tayi ba ƙaramin burge "yan kallo tayiba nan take magoya bayanta suka ɗau ihu da tafi saidai kash abin da ya biyo bayane yasa murnarsu ta koma ciki domin kuwa ko ƙwarzane wanan takubba basuwa aljana zabariyya ba duk da taji saran har cikin ranta domin saida tayi wata ƙaramar ƙara haɗe da sulmiyowa ƙasa itakuwa aljana zarma tsabar mamakine tasa tayi kasaƙe tana mai kallon tsafaffun takubbanta domin a tsawon rayuwarta da yaƙe-yaƙenta da tayi bata taɓa samun saɓani ba irin wanan domin kuwa duk abin da ta sara wanan tsababbun takubba nata nantake take tsargeshi gidabiyu koda kuwa dutsine sai yanzune ta ƙara tabbatarwa da ta haɗu da gamonta idan har bata ƙara aage dantseba to tata tana gab da ƙarewa domin faɗuwarta a wanan gasa sa dai-dai yake da tarwatsewa kundin tarihin jarumatarta da shahararta a duniyar aljannu kuma wanan babban abin kunyane ga jama'arta kafin hankalinta ya dawo jikinta ne batayi aune ba sai ganin aljana zabariyya tayi a gabanta kamar an jefota ta zage iya ƙarfinta tayiwa aljana zarma wani kyakkyawan naushi wanda yayi sanadiyyar zubar mata da haƙoran gaba kamar an janyeta haka tayi ƙasa tim ta faɗo wanda hakan yasa ƙasar wanan filin motsawa. BAKANDAMIYAR GUMURZU. Chapter 25. Filin gasar yayi shiru yadda kasan mutuwa ta gitta babu abin da kake ji face fitar lumfashin mutane, aljannu haɗe da dodanni idan kayi duba zuwaga "yan kallo wasu daga cikinsu tsabar damuwace fal cike da fuskarsu yayinda wasu kuma mamakine ya mamaye fuskarsu saidai wasu dagacikin "yan kallon tsabar murnace da farinciki yayi musu katutu a zuƙatansu kowa ya zuba tsakiyar wanan fili idanu yana mai cike da kokwanto. Hannuwantane suka bara bayyana sana daga bisanni kanta ya fito fili hakan nna faruwa sai gangar cikita ya ida futowa daga cikin wawakeken ramin data samar a sanadiyyar naushi da aljana zabariyya ta mata ta silmiyo ta rikito daga sama ta faɗo kallo daya zakayiwa aljana zarma kasan ta bugu domin hannuta na riƙe da bakinta wanda yake yoyon jini hakan na faruwa filin ya ɗau ihu da tafi, mafiya yawan masu ihun da tafin suna yine domin ganin cewa wanan fafatawar bata ƙare ba domi dukkanasu sun rigama sun sare cewa aljana zarma zata iya miƙe har ta fuskanci aljana zabariyya wanda ƙalilanne daga cikin masu ihunne masoyan aljana zarma. farkon abinda ta farayi bayan ta miƙe shine shafa bakinta da taji yana mata zogi da raɗaɗi tana duba tafin hannunta taga jini hakance yasa cikinta fara tsuma gashin kanta ya miƙe jajayen idanuwanta suka ƙara rinewa yadda kasan an zuba musu jini sana suka ƙara girma ƙofofin hancinta suka ƙara faɗi fuskarta ta ƙara baƙi yadda kasan an shafa mata shuni jijiyoyin jikita suka fito burɗiga-burɗiga kamar saiwar bishiya wani baƙin hayaƙi ya rinƙa futa daga cikin ƙofofin hancinta ta hangame baki tayi wata uwar kururuwa wadda saida tasa gabaki ɗaya filin gasar yin girgiza kowa dake wanan filin saida ya done kunansa haɗe da durƙushewa ƙasa saboda tsabar tashin hankali da kaɗuwa idan kafidda wasu ƙalilan daga cikin "yan kallo da malaman gasa, hamshaƙan matsafa da sarakuna wanda su ko a jikinsu domin su idan da sabo ma har sun sama domin sun jima suna baƙin artabu da azzaluman aljannu sa hatsabiban dodanni dan haka su wanan ihun ba baƙone ba a wajansu haƙiƙa aljana zarma ta fusata, fusatar da bata taɓayi ba domin a yau an rusa mata ginin tarihin jarumtarta wanda babu wani mahaluki da ya taɓa fitar mata da jini nan take ta fuskanci aljana zabariyya wadda itama tuni taja daga haɗe da dunƙule hannu tabbas a yanzune za'a fara waccan fafatawar kamar sharar fage ce. Kai masu karatu gaskiya na firgita bazan iya tsaywa kallon wanan turnuƙu faɗan ibilisai sai na samu jaruman mazan da zasu iya kareni sabod KANDAMIYAR GUMURXU. Chapter 26. Ganin halin da aljana zarma ruwan bala'i tashiga ne yasa dayawa daga cikin "yan kallo tsurewa musamman jama'ar aljannu domin kuwa sun fi kowa sanin ko wacece ita. Ita kuwa gogar taka wato aljana zabariyya jinin jikita tasha nan take itama ta fuskanci aljana zarma tana mai dunƙule hannayenta biyu. Aljanna zarma ta ware fuka-fikinta haɗe da kurma wata uwar kururuwa karo na biyu sana ta fallo da gudu tana mai tunkarar aljanna zabariyya ganin haka yasa itama aljanna kurma wani sakaran ihu haɗe da fallowa da gudu tabbas karo da dubu sai dubu ta taru domin kowacce a cikinsu idon ta ya rufe basu ganin komai aface azabar yaƙi saura taku biyar su haɗu kowacce ta daka wawan tsalle haɗe da buɗe hannayenta tun daga sama suka ruƙunƙume juna sukayo ƙasa sun faɗowa suka kacame da azababban yaƙi suka rinƙa jibgar junansu kqmar jikinsu ba na jini da tsoka bane haka suka wanzu tsawon lokaci kowacce aka nausa daga cikinsu sai tayi sama ta faɗo amma saboda baƙin naci da taurin zuciya sai kaga zumbur ta tashi ta rama haka sukayi ta tamola da kawunansu tare da yiwa junansu luguden naushi hannu da ƙafa ba'a jima ba suka haɗawa jinansu jini da maji suka wanzu sunaasu tanƙaɗi yadda kasan susha kwaya ana cikin hakane aljana zarma ta shammaci aljana zabariyya ta gabza mata wani uban naushi kamar an janyeta haka tayi sama sana ta faɗo tana mai bajewa a ƙasa cikin tsanani galabaita ta yunƙura zata miƙene ta ƙara ganin aljana zarma a gabanta kamar a zuƙota ta ƙara sunkutarta tayi hajijiya da ita a sama har sau ukku sana ta fyaɗata da ƙasa hakanne yasa aljana zabariyya tayi wata uwar tsiwa haɗe da dafe ƙugunta tayi yunƙurin miƙewa amma ta kasa nan take wani baƙin hawaye ya gangaro mata daga idannuwanta na takaici da baƙin ciki domin kuwa tasan tunda har ta kasa miƙewa to ta faɗi wanan gasa nan take alƙalan gasa suka kaɗa wata ƙaraurawa wadda take nuni da wanan karawa tazo ƙarshe nan take aljana zarma ta ɗaga hannayenta sama filin ya ɗau ihu haɗe da tafi dai-dai lokacinne kuwa wasu likitoci daga jinsin aljannu suka shigo wana filin suna ɗauke da wani gado na ƙarfe wanda ake ɗaukar marar lafiya suka ɗora aljana zabariyya akai sukayi waje da ita sunzo gittawa ta kusa da aljana zarma ne sai aljana zarma ta kalli aljana zabariyya tana mai mata murmushin raini haɗe da mugunta hakan ce tasa aljana zabariyya ta ɗago kai haɗe da tiwa aljana zarma wani irin kallo mai ɗauke da ma'anoni da yawa wanda aljana zarma ta kasa tantance ko mai wanan kallo yake nuf BAKANDAMIYAR GUMURXU. Chapter 28. Yayin da aljana zarma ruwan bala'i ta fita daga filin gasa nan take filin yayi shiru kowa ya zuba ido haɗe da kashe kunne domin sauraren wasu jaruman gasa ne za'a kira, ba tare da ɓata lokaci ba alƙalin gasa ya tashi hannunsa na dama yana riƙe da wata doguwar takarda mai ɗauke da sunan jaruman gasa yayin da hannunsa na hagu yake riƙe da bututun magana nan take ya kafa wanan bututun magana a bakin sa ya fara magana masu gasa na gaba sune sadauki salka baƙin dutsi zai fafata da jaruma nuriyya basadaukiya nan take filin yayi shiru kowa ya ware idanunsa domin ganin wanan jaruman gasa, fitar burtun da wani baƙin mulmulallen ƙatone yayi zuwa tsakiyar wanan fili yasa hankalin kowa dake wanan fili ya koma tsakiyar wanan fili tabbas sadauki salka yaci sunansa baƙin dutse domin kuwa surar jikinsa ce zata tabbatar maka da hakan domin kuwa illahirin jikinsa a murɗe yake yadda kasan an jera masa baƙaƙen duwatsu fatar jikinsa kuwa baƙa ce siɗik gashi da tsawo da kauri mummuna ne mai jajayen idanu da ƙaton hanci sanan da zai buɗe bakinsa zaka iya rantsewa da cewa ƙara masa girma akayi tabbas duk jarumtarka idan kayi arba da sadauki salka dolene gabanka ya faɗi kallo ɗaya zakayi masa kasan ya cika sadauki kuma hatsabibin azzalumi wanda hakan ya jima yana zaluntar bayin Allah. Tozali da wanan garjejen ƙato da ''yan kallo sukayine yasa dayawa daga cikin "yan kallo dafe ƙirji haɗe da ajiyar zuciya domin duk wani bafatake dake kasuwanci a wanan nahiya ta rumawa to ya jima da sanin ko wanene wanan baƙi ƙato domin idan bai taɓa tareshi a dajiba to yaransa sun taɓa tareshi domin kuwa sadauki salka shine shugaban "yan fashin dake wanan nahiya gaba ɗaya ya gallabi sarakuna matsafa da fataken da kaikawao a wanan nahiya domin shi garƙami ne wandon ƙarfe kuma kiciɓus ake dashi mugun gamo a kowani lokaci zaka iya haɗiwa dashi kuma kowa yayi karo dashi sai yayi asara idan baiyi ta rai ba yayi ta dukiya tabbas mafi yawan mutanen dake wanan fili sunyi mamakin ganin wanan. Y (IBNI ABDULLAHI ABDULLAHI) BAKANDAMIYAR GUMURXU. Chapter 29. Tabbas mafi yawancin mutanan dake wanan dake wanan fili sun girgiza da da ganin wanan taƙadirin, hatsabibin ƙasurgumin ɓarwon da ya buwayi wanan nahiya ta rumawa gashi yanzu ya bayyana a matsayin jarumin gasa kuma zai kara da mace kowa ya zuba masa idanu yana mai ƙaremasa kallo domin wanan ne karo na farko da ya ayyana kanshi gashi har za'a haɗashi faɗa da mace idan ka dubi fuskokin dayawa daga cikin ''yan zakaga wasu tsabar tausayin wanan jarumar ce a fuskokinsu duk da bata bayyanaba kuma basusan kowacece ba amma kawar da baƙin azzalumi kuma taƙadiri wanda ya jima yana hallaka dukiyoyi da rayukan al'umma kamar sadauki salka sai dubu ta taru in dubu ta tarun ma sai an kai ruwa rana tabbas wanan jaruma yau zata haɗu bala'i haɗe da masifar yaƙin da bata taɓa ganiba yayin da buskokin wasu suke ɗauke da tantsar, tsantsagoran tsana haɗe da baƙin ciki wanda mafi yawancinsu manyan attajiran "yan kasuwane wanda sadauki salka yayi musu sanadin rasa dukiyarsu, wani sashe na jikinsu, masoyansu, kai hadama lafiyarsu tozali da sadauki salka ne ya fama musu ciwon da ya jima a cikin zuciyoyinsu tabbas sun jima suna addu'ar akan Allah ya kawo sanadi ko haɗarin da zai kawo ƙarshen sadauki salka yayin da kuma wasu tsabar tsoro ne ya mamaye zuƙatansu na tozali da mummunar fuska da surar jikin sadauki salka wanda mafi yawa ƙananan yara ne da tsaffi babban abin tashin hankali ma shine tunda ya shigo wanan fili babu abin da yake sai zare jajayen idanunsa haɗe da huci kamar baƙin kumurci shi ko ɗan ɗagawa "yan kallo hannuma baiyi ba tabbas sadauki salka ya zama guguwar annoba a duk wanan nahiya. Bayyanar kyakyawar matshiyar jarumar ce tasa hankalin "yan kallo tashi kamar tsuntsu daga kan sadauki salka zuwaga wanan kyakyawar jaruma wadda aka kira da basadaukiya tabe take fuskarta cike take da annuri da murmushi yanayi tafiyar da take kaɗai ya isa ya tabbatar maka da cewa cikakkiyar jarumace kuma basadaukiya domin tafiya take irin ta mazan jiya.. BAKANDAMIYAR GUMURXU. Chapter 30.(Basadaukiya & sadauki salka). Bayyanar kyakyawar matashiyar jarumar da aka kira da basadaukiya ce tasa filin gaba ɗaya ya kaure da ihu da tafi mafi yawancin masu tafi da ihun mutanen birnin ruma ne tozali da basadaukiya da sukayine yasa zuƙatansu suka samu nutsuwa nan take fuskokinsu suka canza daga tsananin fusata da baƙinciki zuwa tsabar farin ciki da annashuwa tabbas sunsa rai kuma suna kyautata zston yaune burinsu zai cika ga mai share musu hawayensu tazo bakomaine ya kawo wanan baban canji a wanan fili ba face bayyanar basadaukiya dirkar birnin ruma. Jaruma nuriyya itace ɗiya ƙwara ɗaya a wajan sarkin yaƙin birnin ruma mai suna fargam tabbas matsayin da yyake kai ya cancanta dashi domin tsabar jarumta, bajinta, hatsabibanci, da yake dasu yasha baƙar wahala kafin ya taka wanan matsayi yayi abubuwan al'ajabi da dama lolacinsa sana daɗin daɗawa adaline mai kyawawan halaye wananne babban dalilin da yasa ya shahara gabaki ɗayan mutanen birnin ruma suke matuƙar ƙaunarsa. ''Yan magana sunyi gaskiya da sukace barewa bata gudu ɗanta yayi rarrafe domin kaf halayen sarkin yaƙi da tsantsar jarumtarsa da bajintarsa babu wanda jaruma nuriyya bata gadoba tun tana "yar shekara biyar mahaifinta yake bata horon yaƙiai tsanani lokacin da takai shekara bakwai ya fara fita da ita wajan yaƙi tun lokacin takan iya shiga cikin turmutsutsu na yaƙi ta fita lafiya tabbas dayawa daga alummar birnin ruma sun sallama da cewa tafi mahaifinta komai wanan nema dalilin da yasa ake kiranta da BASADAUKIYA babban abinda jaruma nuriyya ta tsana aduniya shine zalunci da azzalumai wananne dalilin da yasa tun tana ƙarama take bincike akan sadauki salka kuma taci alwashin ganin bayan sadauki salka amma hakan ta gagara sunsha yin baƙin artabu haɗe da gumurxu a dazuzzuka daban-daban amma babu wanda ya samu nasara a tsakaninsu saidai su jigata juna haɗe da yiwa juna mugayen raunuka sai sun ga mutuwa ƙarara sana suke rabuwa kowa yaje yayi jiyar rauninsa wanan ne dalilin da yasa ayau aka haɗasu a wajan wanan gasa kuma dukkan wanan abu shirin basadaukiya ne domin ita taje wajan alƙalan gasa ta nemi alfarmar a haɗata da sadauki salka a wanan gasa dole tasa alƙalan gasa sukayi mata wanan alfarma saboda girmanta da darajarta a wanan birni wananne ma dalilin da yasa aka haɗasu faɗa yau domin ayita ta ƙare a gaban mutane. Rataye take da wata zabgegiyar takobi jinkinta yana sanye da baƙin sulke ta tubƙe dogon gashi ya zubo har gadon bayanta .. Wannan littafin yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.com.ng Domin samun cigaban littafin sai ku cigaba da bibiyar shafinmu BAKANDAMIYAR GUMURZU Kashi na hudu 4 Na Umar Abdulhadi Mati Ebook created by Shuraih Usman Published at www.hausaebooks.com.ng (IBNI ABDULLAHI ABDULLAHI) BAKANDAMIYAR GUMURZU. Chapter 31. Tungar da Basadaukiya taja a gaban sadauki salka shine yayi sanadiyyar tashin wata matashiyar ƙura tsayuwa tayi irin ta sadaukai mata hannunta na dama na riƙe da zabgegiyar takobi ta ɗorata akan kafaɗarta yayin da hannunta na hagu ke riƙe da faffadan madaidaicin ƙugunta ta zubawa sadauki salka daradaran fararen idanuwanta tana mai masa wani irin murmushi mai nuna tsantsar yadda dakai, haɗe da raina abokin gaba. Karon farko da ta buɗe baki ta fara magana cikin wata zazzaƙar murya sadauki salka baƙin dutse ko? To yau ko baƙin ƙarfe kake ni basadaukiya naci alwashin sai na ladabtar dakai ayaune watan jin kunyarka ya kama, ayau sai ka amshi hukunci na zaluntar ba'yin Allah da ƙwace musu dukiyoyi da kakeyi tabbas kai gagarabadau ne a wanan nahiya tunda ka gagari sarkuna, attajirai, matsafa, da sadaukai, ka maida dayawa daga cikinsu marayu wasu kayi sanadiyyar karyewar tattalin arziƙinsu dan haƙa ayau ni Basadaukiya sai na ɗaukar musu fansa saina sa zuƙatansu farin ciki saina sa ka zama abin dariya ga alummatai dake wanan nahiya saina... Tsawar da sadauki salka ya dakawa basadaukiya ce tasa ta dakata da maganar da takeyi, haƙiƙa sadauki salka ya gama fusata domin saboda tsananin fusata har wani baƙin hayaƙine ke fita daga hancinsa kamar ba ɗan adamba cikin wata kakkausar murya marar daɗin ji ya fara magana ke yarinya idan kina cin ƙasa ki kiyayi ta shuri wanda ya rigaka kwana dole ya rigaka tashi sadauki salkan da kika sani a da bashiine ba a yanxu a gabanki azatonki bani bibiyar duk wani motsi naki, kina ''yar shekara goma yarana sun haɗu dake a dajin dake iyakar wanan ƙasa taku yayin da kika fita farauta kece mutum ta farko da kika mani ɓarnar da ba zan taɓa mantawa ba domin kin kashe mani ɗan'uwa yayin da kukayi arba har sukayi ƙoƙarin yi maki fashi tare da ƙoƙarin cire maki kyallen da kika rufe fuskarki tun daga nan na fara bibiyar alamuranki, bayan nan mun ƙara haɗuwa dake karo na biyu lokacin kina "yar shekara shabiyar a daji inda muka fafata ƙazamin yaƙi a tsakaninmu amma babu wanda yayi nasara daganan bamu ƙara haduwa ba sai yanzu da muka haɗu a filin wanan gasar kisani kamar yadda kikayi mummunan tanadi a kaina nima haka nai miki mummunan tanadi dan haka idan baki shirya ba ma ki shirya dan ga maza nan bisa kanki nan take sadauki salka ya zare wasu adduna guda biyu haɗe da kawarara wata uwar kururuwa wadda saida tasa "yan kallo suka rufe kunnuwansu batare da ɓata lokaciba ya fallo da zababbben gudu......BAKANDAMIYAR GUMURZU. Chapter 32. Saboda tsananin gudun da yakeyi har wata guguwa ke take masa baya, itakuwa basadauki zuba masa ido tayi tana mai masa murmushin mugunta ko zare takobinta batayiba saida ya rage baifi taku ukku ba sadauki salka ya isa inda Basadaukiya ke tsayeba sai ya daka wani wawan tsalle haɗe da ɗaga addunansa guda biyu sama cikin mugunnufin a niyarsa yayiwa Basadaukiya farat ɗaya ya yagalgala namanta, idan kayi duba ga duk wanda ke wanan fili zaga ya zazzaro idanuwansa cikin tashin hankali da kaɗuwadomin tuni sun saɗaƙas cewa ƙarshen Basadaukiya yazo saidai kafin wanan sara ya isa gareta cikin tsabar zafinnama kamar walkiya ta zare takobinta ta kare wanan sara cikin ƙwarewa da tsantsar jarumta ganin abinda ya farune yasa "yan kallo suka ɗau ihu haɗe da jinjina a gareta shi kuwa gogannaka wato sadauki salka ƙara fusatashi wanan ihun na "yan kallo yayi nan take suka ruguntsume da azabbban yaƙi cikin baƙin zafinnama tamkar walƙiya suke kaiwa junansu sara da suka kai hadama magara da kai duka haɗe halbi da kafafuwa nan da nan suka tashi hankalon filin su kuwa "yan kallo wanan faɗa annashuwa yasa su domin kuwa faɗane na mazan jiya wanda aka jima suna baƙin artabu haɗe turmutsutsu da mazaje, ganin an ɗauki lokaci ana wanan gumurxu babu wanda ya samu nasarar koda lakutar jikin ɗan uwansa... I ABDULLAHI ABDULLAHI) BAKANDAMIYAR GUMURZU. Chapter 33. Ganin babu wanda yayi nasarar koda lakutar jikin abokin karawarsa ne yasa wanan jarumai biyu ƙara fusata haɗe da tunxura, fusatarsu da tunzurarsu ce tasa wanan yaƙi ya ƙara caɓewa haɗe da cukurkuɗewa kowanne daga cikinsu ya ƙara zage dantse haɗe da buɗewa abokin karwar sa salo-salo na ƙofofin masifar yaƙi cikin baƙin zafin nama da juriya ta ban mamaki suke kaiwa junansu sara da suka haɗe da dukan junansu hannu da ƙafa duk wanda aka kaiwa sarako suka yana kaucewa ko ya kare kafin ya maido martani sai kaga an kaimasa duka da hannu ko da ƙafa amma saikaga kamar walƙiya ya kare ko ya kauce cikin ƙwarewa da bajinta saikaga shima ya maida raddi da masifa tayi masifa wanan jarumai sukaga iya yaƙi yana neman zuwa ɗaya sai kowa ya fara tunanin canza salon yaƙi domin ya samu damar lahanta ɗan uwansa ba tare da an kai ruwa rana ba hakance tasa kowanne daga cikinsu himmatuwa haɗe da ƙara zage dantse wajan safkewa dan uwansa salo-salo na masifar yaƙi ana cikin wanan turmutsutsu ne sai Basadaukiya ta shammaci sadauki salka ta daka wani uban tsalle haɗe da juyawa a sama sau ukku sana ta dire nesa kaɗan da inda sadauki salka yaja tunga sana ta gyara tsayuwarta jaɗe da yin murmushin mugunta hade da raini wanda yake nuni da cewa wuyar aiki ai bama 'a faraba domin wanan yaƙi da sukayi kamar sharar fagene, shi kuwa sadauki salka wani irin kallo yayiwa Basadaukiya wanda ke nuni da cewa "wai wanan yarinyar dame take taƙamane" ba'ayi auneba sai ganin Basadaukiya akayi tayi shiga tsalle sama haɗe da ware hannayeta kamar mai fukafiki haka ta sulmiyo ƙasa tayi di dirar mikiya akan sadauki salka, baiyi aune ba sai ganinta yayi a samar kansa kafin yayi wani kyakyawan yunƙuri tuni ta kawo masa wani bahagumen sara cikin baƙin zafinnama ya kare amma kafin ya ankara tuni ta sanya gwiwar ƙafarta ta masa wani wawan duka a fuska duk da yayi ƙoƙarin kaucewa amma sai da tayi nasarar samu gefen fuskarsa wananne yasa sadauki salka yaji wani azababben raɗaɗi ya ratsa masa ƙwaƙwalwarsa duk da haka abin bai tsaya nanba domin kuwa Basadaukiya wulƙila jikinta tayi haɗe da juyowa ta ƙara kawo masa walfta kamar shaho... (IBNI ABDULLAHI ABDULLAHI) BAKANDAMIYAR GUMURZU. Chapter 34. Kamar shaho haka Basadaukiya takaiwa sadauki salka safta duk da yayi saurin duƙewa haɗe da juyo hakan bai hana Basadaukiya samun damar yankanshi a kafaɗa ba kafin ta dire da ƙafafuwanta nesa kaɗan da inda sadauki salka yake, wanan tsananin jarumta da bajintar Basadaukiya ce tayi yasa "yan kallo wanda suka haɗa da alummar aljannu dodanni da mutane ihu haɗe da tafi su kansu hamshaƙan sarakunan da suke zaune a wanan fili saida sukayo mata jinjina domin ya burgesu matuƙa, shi kuwa gogannaka wato sadauki salka fusata yayi zuciyarshi ta ƙufulo gashin jikinsa ya mimmiƙe idanuwansa suka ƙara ja jijiyoyin jikinsa suka futo sukayi burɗa-burɗa idan ka ganshi a wanan hali da yake ciki zaka iya cewa yana ɗaya daga jikin manyan dodannin da suka halarci wanan gasa saboda gaba ɗaya ya rikiɗa cikin tsananin fusata da ƙunar rai ya shafa kafaɗarsa yaga jini cikin ransa yace tabbas ko yanzu aka raba wanan faɗa wanan tarin ar ta mani abinda babu wani sadauki da ya taɓa mani dan haka idan har ban mata kisan wulaƙanciba to bazan taɓa hucewa ba nan take ya gyara tsayuwarsa haɗe da wurgi da takobinsa yana mai yafito Basadaukiya alamun su gwada "yar ƙashi hakan tasa Basadaukiya ta fallo da gudu tana mai soke takobinta a jikin kubenta tana zuwa gab da sadauki salka ta daka tsalle da niyyar tayi masa ɓarin makauniya shikuwa sadauki salka tsawa yayi kyam yana kallonta sai ƙafarta tazo gab da sukarsa cikin baƙin zafinnama ya cafketa ya wulwulata sau ukku a sama sana ya fyɗata da ƙasa ya ɗaga ƙafarsa ya baketa saida tayi sama sana ta faɗo ƙasa cikin galabaita hannuta na dafe da ƙugunta ta yunƙura zata tashi amma ta kasa saboda tsanani buguwa da tayi nan take hankalin kowa dake wanan fili ya tashi murna ta koma ciki, sadauki salka ya nufi Basadaukiya yana tafiya cikin taƙama da fusata yana mai ɗaukar takobinsa haɗe da yi mata murmushin mugunta ganin irin murmushin da sadauki salka ke mata ne yasa ba shiri ta miƙe haɗe da ƙara zare takobinta domin ta tabbata in har ta bari sadauki salka ya isketa a wanan hali da take ciki kashinta ya bushe domin ranta kawai zai nema nan take ta ɗaga takobin ta ta buga wata uwar kururwa haɗe da fallowa da gudu hakan ce tasa shi (IBNI ABDULLAHI ABDULLAHI) BAKANDAMIYAR GUMURZU. Chapter 34. Kamar shaho haka Basadaukiya takaiwa sadauki salka safta duk da yayi saurin duƙewa haɗe da juyo hakan bai hana Basadaukiya samun damar yankanshi a kafaɗa ba kafin ta dire da ƙafafuwanta nesa kaɗan da inda sadauki salka yake, wanan tsananin jarumta da bajintar Basadaukiya ce tayi yasa "yan kallo wanda suka haɗa da alummar aljannu dodanni da mutane ihu haɗe da tafi su kansu hamshaƙan sarakunan da suke zaune a wanan fili saida sukayo mata jinjina domin ya burgesu matuƙa, shi kuwa gogannaka wato sadauki salka fusata yayi zuciyarshi ta ƙufulo gashin jikinsa ya mimmiƙe idanuwansa suka ƙara ja jijiyoyin jikinsa suka futo sukayi burɗa-burɗa idan ka ganshi a wanan hali da yake ciki zaka iya cewa yana ɗaya daga jikin manyan dodannin da suka halarci wanan gasa saboda gaba ɗaya ya rikiɗa cikin tsananin fusata da ƙunar rai ya shafa kafaɗarsa yaga jini cikin ransa yace tabbas ko yanzu aka raba wanan faɗa wanan tarin ar ta mani abinda babu wani sadauki da ya taɓa mani dan haka idan har ban mata kisan wulaƙanciba to bazan taɓa hucewa ba nan take ya gyara tsayuwarsa haɗe da wurgi da takobinsa yana mai yafito Basadaukiya alamun su gwada "yar ƙashi hakan tasa Basadaukiya ta fallo da gudu tana mai soke takobinta a jikin kubenta tana zuwa gab da sadauki salka ta daka tsalle da niyyar tayi masa ɓarin makauniya shikuwa sadauki salka tsawa yayi kyam yana kallonta sai ƙafarta tazo gab da sukarsa cikin baƙin zafinnama ya cafketa ya wulwulata sau ukku a sama sana ya fyɗata da ƙasa ya ɗaga ƙafarsa ya baketa saida tayi sama sana ta faɗo ƙasa cikin galabaita hannuta na dafe da ƙugunta ta yunƙura zata tashi amma ta kasa saboda tsanani buguwa da tayi nan take hankalin kowa dake wanan fili ya tashi murna ta koma ciki, sadauki salka ya nufi Basadaukiya yana tafiya cikin taƙama da fusata yana mai ɗaukar takobinsa haɗe da yi mata murmushin mugunta ganin irin murmushin da sadauki salka ke mata ne yasa ba shiri ta miƙe haɗe da ƙara zare takobinta domin ta tabbata in har ta bari sadauki salka ya isketa a wanan hali da take ciki kashinta ya bushe domin ranta kawai zai nema nan take ta ɗaga takobin ta ta buga wata uwar kururwa haɗe da fallowa da gudu hakan ce tasa shi sadauki salka ɗaga addunansa biyu ya fallo da gudu yana mai ruri mai tsorata ƙanan sadaukai tabbas du wanda ke wanan fili ya tsorata da wanan haɗiwa da za'ayi saboda sunsan cewa idan har akayi wanan haɗuwa dolene a samu matsala..... February 24 at 1:03 PM · Facebsadauki salka ɗaga addunansa biyu ya fallo da gudu yana mai ruri mai tsorata ƙanan sadaukai tabbas du wanda ke wanan fili ya tsorata da wanan haɗiwa da za'ayi saboda sunsan cewa idan har akayi wanan haɗuwa dolene a samu matsala..... February 24 at 1:03 PM · BAKANDAMIYAR GUMURZU. Chapter 36: Haƙiƙa ba ƙaramin tashi hankalin waɗanan jarumai ba yayi ba komai yasa hakan ba face ganin wankin hula na ƙoƙarin kaisu dare hakance tasa kowanne daga cikinsu ya ƙara fusata kamar hadin baki nan take kowanne daga cikinsu yayi watsi da makamin dake hannunsa hakanna faruwa basadaukiya ta dunƙuƙe hannunta haɗe da kwantsama wata uwar kururuwa ta falfalo da azababban gudu tana mai tunkarar sadauki salka cikin mugunnufin ayita ta ƙare saboda tsananin ƙarfin gudu da take ne yasa har wani tashi sama take, ganin hakance tasa sadauki salka shima ya dunƙuƙe hannunsa haɗe da kwarara wata uwar kururuwa yana mai dukan ƙirjinsa da hannuwa biyu kafin ya fallo da gudu shima zuciyarsa cike take da mugunnufi suna kusan haɗuwa sai kowanne daga cikinsu ya dako uban tsalle yana mai kaiwa ɗan uwansa mugun naushi kowanne cikin zafinnama ya kare kafin su silmiyo ƙasa suna dira suka kacame da wani azababben yaƙi "mai taken ƙarshe tika tik" haka suka dunga jibgar junansu kamar jikinsu ba na jini da tsoka bane ana cikin wanan baƙin gumurzu ne sadauki salka ya shammaci badaukiya ya gabza masa wani mummunan nashi a ciki kamar a janyeta haka tayi tsalle ta tumu da ƙsa a can gefe tana mai dafe cikinta cikin galabaita domin ko numgashinta ma da kyar yake fita kafi ta dawo cikin hayyacinta ne sadauki salka ya ƙara dako tsalle daga inda yake ya ƙara shaƙar wuyanta yana mai ɗagata sama nan take ta fara wutsul-wutsul tana mai kakarin mutuwa tabbas wanan shaƙa da sadauki salka yayiwa basadaukiya bata wasa bace ya kalleta yana mai mata wani murmushi mai ɗauke da tsabar xunxurutun mugunta ya fara maga cikin izza ''hm haba yarinya waya faɗa maki ana zama wani a banza, azatonki a banza na buwayi sarskuna,matsafa,sadaukai da jarumai na wanan nahiyar tabbas a yaune zan zare maki numfashinki sai na miki kisa mafi muni wanda a tarihin duniya ba'a taɓa yiwa wani irinshiba yana zuwa nan a maganarsa ya ƙara shaƙeta nan take idanuwanta suks fito numfashinta ya sarƙe ta fara jiyo ƙamshin mutuwa ganin haka yasa alƙalan gasasuka fara shirin kaɗa ƙaraurawar da ke nuni da tsayawar wanan gasa sadai kash! Adaidai lokacinne sadauki salka ya jimƙe hannuwansa na hagu nan take wata koriyar wuta bayyana, bayyanar wanan koriyar wuta ce yasa kowa dake wanan fili ya tsorata yana mai dafe ƙirji domin duk wanda yasan labarin sadauki salka to yasan bala'in wanan wuta tasa domin da wanan sirri na koriyar wutane ya fitini sadaukan jinsin mutum, aljan, kai hadama dodanni ...BAKANDAMIYAR GUMURZU. Chapter 37. Ganin wanan koriyar wuta yasa sarki nawwar saurin miƙewa kafin hannun sadauki salka ya isa kan basadaukiya tini sarki nawwar ya nuna sadauki salka da yatsarsa nan take wata iska mai ƙarfi ta suri sadauki salka ta yi hajijiya dashi sana ta damfara da ƙasa ganin hakane yasa yaran sadauki salka wanda suka shiga cikin "yan kallo suka saje dasu tashi tsaye haɗe da zare makamansu saidai kash basu samu damar ida nufinsu ba suka ja suka tsaya cak sakamakon tsawar da sukaji haɗe da rugugi inda ƙasa ta rinƙa girgiza kamar zata rufta ganakace taba filolin da suka tokare rufin da ya zagaye fadar fara zabtarewa suna danne "yan kallo duk wanan bai isaba bayyanar baƙar inuwar data lulluɓe dukkan filin ita ta ƙara sa "yan kallo durƙushewa inda wasu suka faɗi haɗe da dunƙulewa waje ɗaya cikin firgici da kaɗuwa haɗe da tashin hankali hakance tasa suka ɗaga kawunansu domin ganin masifar da ta haifar da wanan bala'i abinda suka ganine yasa su ƙara gigicewa haɗe da firgicewa wanda dayawa daga cikinsu saida sukayi danasanin ɗaga kawunansu sama da sukayi shikuwa uban gayyar wato sarki nawwar tashi tsaye yayi karon farko da tsabar tsoro da tashin hankali ya bayyana a fuskarsa ganin mawuyacin halin da mutanensa suka shigaba shiri ya tafa hannayensa nan take baƙin labulen da ya nannaɗe kansa tun farkon wanan gasa ya ƙara bayyana yayiwa "yankallo hijabi , sukuwa manyan gayyar ko a jikinsu wai an nyakushi kakkausa ƙara gyara zamama sukayi sadai dakarunsu da suka zo gabansu suka ja daga suna masu raba idanuwa saboda tabbatar da tsaro .... (IBNI ABDULLAHI ABDULLAHI) BAKANDAMIYAR GUMURXU. Chapter 38. Bakomai ne yayi sanadiyyar afkuwar wanan bala'in ba face bayyanar haɗaɗiyar baƙar rundunar da ƙunshi jinsin mutum dana aljan babban abin tashin hankali haɗe da firgici ga wanan baƙar runduna shine baƙin Ƙaton mummunan aljani dake jagorantar wanan baƙar runa domin duk wanda ya kwana ya tashi a duniyar hatsabibanci da jarumta to yasan aljani FARGAM aljani da baya domin baya da shekara sittin da biyu shike riƙe da kambun jarumtar na duniyar baƙaƙen aljannu tabbas dole sunan aljani fargam ya watsu a duniya idan akayi duba da irin gwagwarmayar da ya jima yanayi da hatsabibai, duk da sarki nawwar ya sanya shaki na labulayen tsafi tsakanin "yankallo da aljani fargam amma kallon farko da "yan kallo suka masa saida yasa dayawa dsga cikin sumewa masu ƙaramin ciki kuwa sukayi ɓarinsa, masu ƙarfin haline daga cikinsu ne suks durƙuce haɗe da ƙara dunƙulewa waje ɗaya tabbas kallon aljani fargam ma kanshi babban tashin hankaline ga ƙananun sadaukai cikin murya mai amo wadda take ɗauke da tsantsar amon izza da buwaya irin ta mazajen jiya ya fara magana cikin isa da taƙama "sarki nawwar mai daular ruma sarkin dake burin zama sarkin- sarakan duniya, tabbas ka ɗebo ruwan dafa kanka kaɗebo wa kanka aikin da yafi ƙarfin ka duk da cewa duniya ta shaida kaima sadaukine kuma hamshaƙin matsafi wanda ake damawa dashi a duniyar tsatsuba, amma kasani ba'a zama sarkin sarakai a banza kuma kana zaune a gida ko sarki sahibul kairi bai kai wanan matsayiba saida ya bar karagarsa, ƙasarsa, ya shiga duniya yayi gwa-gwarmaya da hamshaƙan baƙaƙen aljannu da mutane wanda suka amsa sunansu hatsabibai kuma gawurtattu kamar irinsu sarki BARUSA da matar sana ya kai wanan mataki sai kai kake tunani da sa rai cewa zaka taka wanan matsayi kana zaune a gida haƙiƙa kayi kuskure duk da cewa ka taɓuka wani abu saidai kuskurenka ɗaya shine da ka sanya yaudara da ha'inci a cikin lamuranka da bokanka wanan shine babban kuskuren da kuka tafka kai da bokanka... Happy juma'at kareem.BAKANDAMIYAR GUMURZU. Chapter 39. Nasan zakayi mamakin ta yadda nasan wanan babban sirri naka duk da cewa kayi amfani da da layarka ta ɓata wajan ɓoye wanan sirri wadda a tunaninka idan har kayi amfani da ita kaf duniya babu wani mahaluki da zai iya wanan sirri naka wananne dalilin da yasa ka tara wanan hamshaƙan sarakunan da matsafa, jarumai daga sassa daban daban na duniya duk da cewa kowannensu saida yayi bincike akan wanan gasar kafin ya taho amma babu wanda ya samu damar ganin wanan sirri naka tabbas wanan sarƙa taka tana ɗaya daga cikin abubuwa biyar mafi daraja a duniya, hm!! amma idan kayi duba da matsayin da na taka a dunuyar tsatsuba wanan ba komai bane kasani shi ilimin tsafi kogine da kowa ke kamfato iyakar iyawarsa ba dole bane abinda na ɗakko yayi daidai da wanda ka ɗauko ba wanan ne dalilin da yasa tun lokacin da aka fara wanan gasa nake bincike akanta daga ƙarshe na gano akwai wani babban sirri dake ƙunshe da ita yayin da na matsa bincike sai na gano babu yadda za'ayi in gano wanan sirri sai na haɗa jinin jinsi huɗu na zubashi a kwatarniyar tsafina sana in haska wanan jinin da madubin tsafina sana inga wanan sirri gani hakane yasa na nazo wanan birni a sirrance na haɗu da aljana zabariyya, daga jinsin dodanni kuwa na nemo su dodo zalƙim, jinsin mutane na nemo sadauki saljam na musu bayani komai inda suka amince kowanne ya zuba jininsa a wanan kwatarniya tawa ta tsafi sana muka kamo wani bijimin zaki muka yankashi mua zuba jinin sa a wanan kwatarniya hakan na faru sai na fiddo maɗubin tsafina na haska wanan jini hakan na faruwa sai ga hotonka da na bokanka yayi da kuke tattunawa akan tsafin ds kake so ka haɗa wanda zaka zama sarkin sarakuna ka gallabi .mutum ɗa aljan daga wanda hakan bazai yiwuba har sai kun mallaki jini, ɓallen ƙashi, da haƙoran manya-manyan sadauksi da hatsabiban jaruman da suka gagari duniya a wanan zamanne kuka samu matsayar cewa zaku aika takardar gayyata zuwa ga sadaukai jarumai da manya-manya hamshaƙan sarakuna... (IBNI ABDULLAHI ABDULLAHI) BAKANDAMIYAR GUMURXU. Chapter 40. Kai ya isa haka sarki nawwar ya dakawa aljani fargam tsawa cikin wata kakkasar murya mai cike da tsabar ɓacin rai da fusata haɗe da hasala idanuwansa sunyi jawur jikinsa sai tsuma yake karon farko da sarki nawwar ya fara magana cikin murya mai amo" Haƙiƙa ka cika hatsabibi Kuma tantiri da lokaci ɗaya ka tono babban sirrin da na jima ina ɓoyewa, ka cutar dani ka katse mani babban burina na duniya, hakika kayi nasarar tsaida wanan gasa ,saidai baka isa ka hanani cika wanan burin ba duk rintsi duk tsanani koda zatakaimu ga yaƙar juna sai na ida cika burina a yanzu na mallaki ballen ƙashin sadauki salka lokacin da aka karyashi a ƙafa, inada haƙorin aljana zabariyya yayin aljana zulma ta nausheta haƙorinta guda na gaba ya fita , ina da ɗigon jinin dodo zalƙim da dodo kalkus yanzu abin da ya rage shine in mallaki aɗigon jini shahararrun jarumai na guda ukku wanda suka fito daga dauloli ukku sune daular hindi,daular asiya,daular kisra, A yanzu haka ina da ɗigon jinin sadauki salka wanda kowa yasan hafaffen ɗan daular habasha ne sai kuma jini basaudakiya wanda ita kuma kowa yasan haifaffiyar daular rumawace, waɗanan dauloli sune dauloli mafi girma da ƙarfi, yawa da shahara a duniya idan har na kammala haɗa wanan abubuwane zan haɗa da jini na dana matata sana ina haɗa da farin ƙarfe mai daraja ta farko a duniya wanda ake haƙowa a ƙasar kogin nil wanda tuni na mallakeshi in sana'anta KARAGAR MULKI wanda duk wanda ya hauta sai ya shahara, ya tumbatsa, ya gallabi al'ummar mutane data aljannu kai hadama dodanni sai ya kafa tarihin da har duniya tanaɗe baza'a daina tunashi ba, sai ya kasance sunansa kaɗai aka faɗi sai mutum ya girgiza sai ƙowani sarki da ya shahara a duniya yazo ya durƙusa gabansa, sanan babu wanda ya isa ya hau karagar sai jinina... " kai!!! dakata ya isa haka sarki alkasim ya katse sarki nawwar cikin murya mai cike da ƙarfin izzar mulki da tsabar jarumta ya fara magana.... An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels