BA’A SHAN ZUMA… 01 NA LUBABATU MAITAFSIR & BENAXIR OMAR Kwance take tsakiyar wani dan karamin daki mai mugun bakin duhu, babu komai a cikin dakin sai yar tabarmar kabar da take kwance akai, ga wani irin sanyi ana yi, mai masifar buji, ta takure wuri guda, ta lullube kafafuwan ta da dankwalin ta, hannuwan ta ko ta hada su ta cusa tsakanin cinyoyin ta, domin kuwa ko arzikin zanin da zata rufa bata dashi. Bata da banbanci da prisonern da aka yankewa hukuncin daurin rai da rai! Wasu irin hawaye masu zafi ne suke sintiri akan kyakkaywar fuskar ta, tunani take ena rayuwarta ta dosa? Tun tana karama take shan azaba a hannun goggo wadda ta kasance kanwar mahaifi a gare ta. Cikin muryar kuka take cewa "anya kuwa goggo ta hada jini da mahaifina kamar yadda aka sanar dani?" Bata karasa rufe bakin ta ba, taji an banko kofar dakin tun karfi, ba tare da bata lokaci ba matar data shigo ta daga robar ruwan dake hannun ta, ta juye ta tass akan yarinyar, cikin tashin hankali tayi zumbur ta mike, tace "goggo dan Allah kiyi hakuri, wlh ban san asuba tayi ba" matar da aka kira da goggo ta karaso gaban ta, ta jawo gashin kanta tayi wurgi da ita zuwa tsakar gida, tace "uban mi kike nufi da baki san asuba tayi ba?" tsinanniyar yarinya kawai, mai hali irin na uwar ta, wuce ga bargunan fitsarin shehu can ki wanke su tass ki shanya, sannan ki wuce ki dibo mun ruwa tun kafin layi ya cika" tana kai wa nan ta hanbare ta da kafa, taja tsaki sannan ta wuce. Mikewa tayi jiki ba kwari, ga wata irin rawar sanyi da take yi, bargunan ta tattara, ta wuce ta zuba su a ruwa, ta wanke ta shanya, sannan tayi alwala, taje ta gabatar da sallar asuba. Tana sallamewa goggo ta dawo dakin tace "sannu yar milki, wato dan uban ki rainin da kikai mun har ya kai na in maki magana kiyi banza dani ko, yau zaki gayawa yan garin ku" ba tare da ta bar ta tace komai ba, ta fara jibgar ta, ga kayan jikin ta dama a jike, ga wani irin muku mukun sanyi da ake sararawa, amma babu tausayi, ba imani goggo taci gaba da kwalfarta har saida taji ta gaji, sannan ta kyale ta, ta fito daga dakin ta dauko wani Katon baho, ta wurga mata, tace "saura kuma in kin tafi ki kwana a can, kizo kiga yadda zan lallasa ki a gidan nan" cikin kuka ta mike ta dauki bahon ta wuce ta bar gidan… Borehole ta nufa a lokacin babu kowa saboda tsabar sanyin da ake yi, ta tara bahon, sannan ta fara buga famfon, cikin yanayi na damuwa da mugun tashin hankali, ga wata irin kyarma da take yi, hakoran ta sai gamewa suke suna wani irin kara. Ta cika bahon dam, dakyar ta dauka, ta dora a kanta, sannan ta dauko hanyar gida tana ta uban sauri. BA’A SHAN ZUMA…. 02 NA LUBABATU MAITAFSIR & BENAXIR OMAR A hanya ta fara ganin mutane kadan kadan kasancewar, gari ya fara haske. Gidan ta karasa, taje ta aje ruwan, sannan ta tattara wanke wanke, taje tayi, ta gama ta share tsakar gidan, duk su goggo ana daki ita da ya'yan ta, ta leka dakin goggon ta durkusa tace "na gama goggo" ba tare da ta kalle ta ba, ta dungura mata roba mai kosai a ciki, ta mika mata kofin kunu, ta ansa tayi godia, sannan ta wuce dakin ta, ta zauna ta cinye, ta jawo wasu kodaddun uniform, ta burma ta dauki jakan ta, ta wuce makaranta. One thing da zai birge ka a tare da Deedo shine kokarin ta wurin karatu, bata wasa dashi duk kuwa da wahalar da take sha a gidan goggo, domin kuwa babban burin ta a rayuwa bayan ta hardace Qur'ani, to shine ta zama medical Dr. haka rayuwar ta take tafia, bata da wani 'yanci balle kuma ayi maganar gata. WACECE DEEDO? Asalin sunan ta Nana Firdausi Kabeer Sani, yarinya ce mai shekara 12 a dunia, tana js2 a wata private skool, wadda scholarship ne ta samu daga Gov. Bauchi anan cikin garin Ningi. Mahaifinta haifaffen garin Ningi ne, ta jihar Bauchi. Su biyu iyayen su suka haifa daga shi sai qanwar shi Batula wadda ake kira da goggo. Goggo irin izgilallun matan nan ne, masifaffu masu ji da bala'i, irin mutanen nan da idan suka dauki karan tsana suka dora maka, sai kaji kamar ka bar dunia saboda masifar su. Tana da yara guda biyu, Hadiza da Shehu, mijin ta malam ilu, bata dauke shi bakin komai ba, domin komai ita take yiwa kanta, wannan yasa suma yaran suka raina uban nasu. Mahaifiyar Deedo mai suna Rukayya,yar asalin garin kafanchan ta jihar kaduna ce. Yanayin aiki yasa mahaifinta dawowa cikin garin kaduna da zama, inda ya tare a unguwar hayin banki. Su biyar ne iyayen su suka haifa, kuma duka mata. Akwai babbar yayar su Fatima, sai Labeeba sai umman deedo, sai Halima mai no mata, sai kuma Aminatu yar autar su wadda suke kira da baby. Riqon Deedo ya dawo hannun goggo ta sanadiyyar hadarin mota da iyayen ta suka yi, a hanyar su ta zuwa Kd, inda ita kuma Deedo a lokacin sun barta wurin inna mahaifiyar baban ta, saboda zuwa makaranta, wanda a lokacin duka duka bata fi shekara 5 ba a dunia!! Wannan tashin hankali shi ya haifar wa yar tsohuwar da ciwon zuciya, ga kuma tausayin yar marainiyar yarinyar da suka bari, hakan yasa ta kwanta ciwo sosai, inda daga bisani itama tace ga garin Ku nan dan dama malam mijin ta, ya dade da rasuwa. Tun asalin auren umma da Abban su Deedo, goggo take fama da baqin ciki da takaicin dalilin da yasa dan uwan nata ya rakito umma, kwata kwata bata son ta bata kaunar ta, kasancewar kafin yayi auren akwai kawar ta Badiyya data so ya aura, sai dai kuma shi bai yaba da halayen ta ba, hakan ya haifar da rikici a tsakanin su, inda daga karshe ta yanke shawarar fita harkar shi tare da matar shi, sanadiyyar tsanar da take yima mahaifiyar Deedo kuma ita ce ta shafe ta har ya kai ga ko ganin yarinyar bata son yi kamar ba jinin ta. Bayan inna ta rasu, yan tsiraran yan uwan da suka rage masu, suka yanke shawarar goggo ta dauki Deedo ta riqe, amma fur matar nan ta rufe ido tace babu dalilin da zai sa ta hada kanta da mugun iri, tace "wani a cikin ku ya rike ta mana, in kuma baku iyawa sai ku kaita gidan marayu" ta mike tayi tafiyar ta. Haka akai ta fama da goggo, inda daga bisani dai aka samu aka lallaba ta, ta dauke ta, a cikin zuciyar ta tace "ko bakomai na samu yar bauta" haka ta tusa keyar Deedo gaba, ta mayar da ita gidan ta. Tun daga wannan rana kuma Deedo tayi sallama da duk wani farin ciki na dunia, daga nan ta fara fuskantar tsananin rayuwa, dan tun tana karama take kwana a wannan dan daki mai kama da keji, Dan kuwa bata da ikon da zata matsa kusa da Hadiza, wadda suke kusan sa'anni, balle har ta samu damar hada shimfida da ita. BA’A SHAN ZUMA… 03 NA LUBABATU MAITAFSIR &BENAXIR OMAR Tsakanin ta da shehu kuwa banda kyara da hantara tare da wanke mai kayan fitsari babu abinda ke hada su, duk da lokacin ya kai shekara 9, amma haka yake miqewa ya sharta fitsarin shi a gado, ba ruwan goggo, balle tayi qoqarin hana shi. Bayan Deedo ta cigaba da zama a gidan goggo cikin kuncin rayuwa da ukuba, dangin mahaifiyar ta suka samu labari, Dan haka Fatima babbar yayar umman ta, tazo da niyyar tafia da ita, amma goggo ta rufe ido ta furza mata ruwan rashin mutunci, ta qara da cewa ita ce dolen Deedo, tunda mahaifin ta bashi da kowa wanda ya wuce ta, dan haka kuma babu wanda ya isa ya karbe wannan yarinya daga hannun ta. Haka Ummi kasancewar haka yaran ta suke kiran ta, ta tattara ta koma kd cike da tunanin halin da Deedo take ciki.. * *** Ana tashi daga makaranta ta sabo jakar ta, ta fara bunguza sauri, dan ta San halin goggo sarai, ta riga ta mata warning muddin Hadiza ta riga ta dawowa gida, sai ta yabawa aya zakin ta. Hally kawar ta, tana ta kwada mata kira, amma ina ta riga tayi nisa, da gudu ta karaso gaban ta, tana cewa "wai ke Deedo goggon nan taki sai kace mala'ika, baki so ki bata mata rai ko kadan" ta murmusa tace "Hally kenan, kin fa san komai, amma sai kina yi kaman baki sani ba, ina zan tsaya in sha na jaki, yau ma tunda asuba da shi na karya" suna haka suka kawo kwanar gidan su Deedo, hally kuma tai mata sallama ta mike hanyar gidan su. Tana shiga ta tarar da goggo a kofar dakin ta, ta karasa ta gaishe ta, bata ko kalli inda take ba, balle ta ansa, tace "sai yanzu kika ga damar dawowa dan uban ki? Wlh in kika yi wasa sai kin daina zuwa makarantar banzar nan, ke dama kwakwalwa irin ta uwa, babu komai ciki sai majina" ta saddar da kanta, tace "kiyi hakuri goggo, in sha Allah bazan qara ba" tace "munafuka wadda tayi gadon munafunci, tashi wuce ki bani wuri kin mun tsuru da idanuwa kaman na mujiya" simi simi Deedo ta miqe tana matse yar kwalla, ta shige dan akurkin dakin ta, ta cire uniform dinta, ta canja kaya sannan ta fito tayi alwala, goggo sai hararar ta take, ta koma ta fara sallah, sai a sannan Hadiza ta dawo. Goggo ta washe baki tana "Dijangala ta mai gari, ita kuma tana wani yatsina, ta isa gaban goggo ta zauna, tace "ena abinci na" ba gaisuwa ba komai, abin ka ga ba tarbiyya, goggo tace "jeki kitchen indomie tana nan dana dafa muku keda shehu ki dauko" tana mikewa, shima ya shigo ya dawo daga makarantar, nan suka zauna suka kwashi indomien su, suka cire uniform din su, goggo ta kwada ma Deedo kira, ta fito da gudu gudu, ta duka gaban ta, tace "gani goggo" kafin goggo tace wani abu, Hadiza tace "ke kwashe kayan nan ki wanke su tas, kuma wlh kika mun wankin da bai fita ba sai naci uban yarinya" shehu yace "niko kinsan hali na, dan in zubarwa yarinya da hakora ba wani aiki bane a wuri na muddin kikai mun wankin da bai fita ba" bata ce komai ba, ta tattara kayan ta wuce wurin wankin, ta jawo roba zata diba ruwa, Goggo tace "dakata munafuka, in baza kije ki debo ruwan wankin ba, to ki kwashi kayan ki wuce can wurin famfon ki wanke su, ke ga yar iko ko? Har zaki diban mun ruwa kiyi wanki da shi" bata ce komai ba, ta koma daki ta dauko hijabin ta, tazo ta dauki katon bahon nan, ta wuce borehole. A hanya ta hade da hally zata tafi islamiya, kasancewar tahfiz take yi, hally na ganin ta, tace "ke Deedo ina zaki da wannan katon bahon kamar yar ga ruwa" kwallan da take boyewa suka gangaro mata, tace "Hally na gaji da wannan rayuwar da nake ciki, kullun cikin bauta kamar baiwar da aka ciyo a yaki" Hally ta kalle ta, tace "kiyi hakuri Deedo wata rana sai labari" ta goge hawayen tace "haka ne hally, bari naje kar na kuma yin wani laifin" hally tace "in tambaye ki mana" tace "ina ji" tace "wai ina dangin umman ki? Ki gudu wurin su mana" Deedo ta zaro ido, tace "suna kaduna fa, kuma saida suka zo tafiya dani goggo ta hana, kuma ni kinga ko bauchi ban taba zuwa ba balle kaduna" hally tace "shikenan, Allah ya saka maki cin zalin da ake maki" tace "amen" sukai sallama, ta wuce ta fara buga famfo, kasancewar babu kowa a wurin, ta cika bahon, ta kinkima ta dora akai, ta cigaba da sauri zuwa gida. BA’A SHAN ZUMA… 04 NA LUBABATU MAITAFSIR &BENAXIR OMAR Ta na isa ta tarar ba kowa a tsakar gidan, can ta jiyo waka tana tashi daga palon, hakan ya tabbatar mata kallo suke yi, ta wuce ta sauke ruwan, sannan ta fara wanke kayan, ta gama ta shanya, sauran ruwan da ta gama wanke masu ta dauko nata uniform din ta cuda a ciki, ta gama ta gyara wurin ta share, sannan tayi alwallar la'sar. Palon goggon ta shiga tayi sallama, ta rakube a bakin kofa, tace "na gama goggo" ta juyo a qufule tace "to uban mi kuma zan miki? Iyii?" Tace "bakomai" har ta miqe, goggo tace "ni wlh wannan bala'in ya fara isata, ace wannan shegiyar yarinyar kullun ni zan rinka cida ki, bazan iya wannan abu ba, ke ba uban komai kike mun ba, sai dai kizo ki tsugunna mun kice in baki abinci, na gano ki munafuka, mai mugun hali irin na uwar ta, wuce ga sauran kosai can na safe da shehu ya kasa ci ki dauka, dan ni dai ba abinda zan baki gare ni ba" ta mike tana tunanin wai wane irin hali ne uwar ta take dashi, wanda kullun goggo ta tashi sai tace mata mai mugun hali irin na uwar ta, kwalla suka kawo wa kuncin ta ziyara, tasa hannu ta share, tace "ya Allah kayi gafara ga iyaye na" ta shige kitchen din ta dauko sauran kosan dan wata muguwar yunwa take ji, ta tuttura shi, ta bi da ruwa, sannan ta mike ta bada sallar la'asar, ta dauko Qur'anin ta, ta fito. Palon ta kara komawa, tace "Hadiza zaki je islamiya ne?" Tayi banza da ita ta qyale, bata yi kasa a gwiwa ba ta kara nanata tambayar, ta mike daga shingidar da tayi, tace "yau naga bala'i, wai ke ko dai mayya ce? Shin in ma zanje islamiyar tare dake nake jerawa? Ko ni tsarar ki ce da zaki zo da wani guntun munafuncin ki kina tambaya ta" Tace "Allah ya baki hakuri, naga kamar baki san lokaci yayi bane" ta mike ta fita, goggo ko da yake itama ba ilimin addinin ya wadace ta ba ko kala bata ce ba, haka suka maida hankalin su ga kallon su, babu wanda yayi kokarin motsawa bare yayi sallah, daga gani ma babu wanda yayi ko da azzahar a cikin su. Sauri take tayi dan ta riga ta makara, tasan kuma dole ne ta anshi hukunci, tana isa Allah ya taimaka ta an gama taran yan makara, ta silale ta shige ajin su, nan ma malam bai shiga ba, nan fa yan ajin suka yo mata caa akan ta biya masu karatun da akayi jiya, domin yau za a anshi harda, kuma da yawan su basu iya ba. Ba tare da bata lokaci ba ta fara kwararo qira'a cikin muryar ta mai zakin sauraro, duka ajin aka yi tsit ana sauraren ta, haka ta gama biyawa, sannan kowa ya cigaba da nanatawa cikin ran shi, har malam ya shigo aka fara gabatar da darasi. Ana tashi daga Islamiyar bata tsaya bata lokaci ba ta kamo hanyar gida. Tana dab da shiga layin su, wasu yan samari suka tarye ta, suna tai mata magana amma ko kallon su bata yi ba, daga bayan ta taji ana cewa "ke Deedo dan kin samu ana kula ki shine har wulakanci kike wa samari ko, wlh bara naje gida sai na hada ki da goggo" juyowar da zata yi taga ashe shehu ne yake binta a baya ya dawo daga kwallo, kafar shi tayi budu budu kamar an tono shi daga rami. Ta tsaya tace "in ka fasa fada din, wadannan tsamayen mei zasu bani da zan tsaya in bata ma kaina lokaci a wurin su" ta juya ta cigaba da tafiyar ta. Aiko shehu ya daga kwallon dake hannun shi ya daddage ya seta keyar ta, ya halba kwallon, tayi tangal tangal ta zube a kasa, da samarin da sauran yaran da suke wurin suka dau ihu suna mata daria, wasu na cewa "katuwa ta sha kasa" wasu zafafan hawaye suka zubo mata, ta mike tace "wlh yau sai na rama, sai dai duk abinda zai faru ya faru, shiru shiru ai ba tsoro bane" ta samu wani dan dakali ta dora Qur'anin ta, sannan ta rugo ta cafki shehu, suka fara dambe, nan dai dakyar wasu dattijai suka raba su, ana rike shi yana cewa "shegiya mai mugun hali irin na uwar ta, yar tsintuwa kawai" ita kuma tace "na ji din, dadin abun dai ni bani fitsarin kwance, kuma in ka Kara ce mun mai mugun hali saina fasa maka baki wlh" wani dattijo yace "ke Deedo kyale shi da Allah, shehu ai ba sa'an ki bane" da yake Allah yasa ita yarinya ce mai girmama na gaba da ita, haka ta juya ta dau Qur'anin ta, ta wuce ta bar shi… BA’A SHAN ZUMA… 05 NA LUBABATU MAITAFSIR & BENAXIR OMAR Kafin ta isa gida ashe rahoto har ya isan wa goggo, tana shiga da sallamar ta, taje gaban ta ta duka tace "sannu da gida goggo" bata ansa ta ba, dan haka ta mike ta shiga daki ta cire hijab dinta, ta aje Qur'anin ta sannan ta fito zata fara aiki, Hadiza ta gani ta fito da dorinar malam Ilu kasancewar shi tsohon kurtun dan sanda, ta mika wa goggo, amma goggo tace bari shehun ya shigo da kan shi zai rama abinda tai mashi, bata ida rufe bakin ta ba, shehu ya shigo yana ta gurnanin kuka, goggo ta fara lallashin shi, tace "anshi bulalar nan ka dake ta yadda ranka yai maka" aiko shehu ya ansa ya fara tsula mata, tana ihu amma goggo ko motsi bata yi ba daga inda take, saida yai mata mai isar shi, sannan ta taso tace su debo mata ruwa a kofi, suka dibo suka miqa mata, ta juye shi a kan Deedo, sannan ta fara kwalfar ta, sai da tai wa yarinyar nan lilis kamar bata san hanyar da imani ya biyo ba, sannan tace "ke dan baki da mutunci, kin riga kinyi gadon butulci wurin uwar ki, har kin isa ki taba mun da, har kina ce mishi mai fitsarin kwance, to uwar mai fitsarin kwance ita take rufa miki asiri take cida ki, kuma daga yau baki da abincin dare a gidan nan, tsinanniyar yarinya kawai" tayi kwallo da ita da kafa, sannan ta wuce ta bar ta tana ta rera kukan da sautin shi ko fita baya yi… Haka ta qaraci kukan ta babu mai lallashin ta, daqyar ta lallaba ta mike tayi alwalla ta shige dan akurkin ta, a zaune ma take sallar saboda tsabar dukan da tasha, tana gamawa ta dan shingida akan tabarmar kabar ta, addu'a take a cikin zuciyar ta, ya Allah ya kawo mata karshen wahalar nan, shawarar da hally ta bata ita ta fado mata a rai, ta fara tunanin ko dai ta gudu din? Wata zuciyar tace "karatun naki fa Deedo, in kin gudu wa zai sa ki a wata makarantar har ki zama hematologist" a fili ta furta "duk runtsi duk wuya zan daure har inga na cimma burina, ya Allah ka taimake ni" tana nan har aka kira isha'i, ta mike tayi ta a zaune, sannan ta koma ta kwanta, a haka bacci ya sace ta duk da matsananciyar yunwar da take ji. Ba ita ta farka ba, saida taji saukar robar ruwan goggo tunda bakar asuba… BA’A SHAN ZUMA… 06 NA LUBABATU MAITAFSIR & BENAXIR OMAR Tamike a firgice, tana kokarin shafe baccin dayaci fuskanta sannan tamike,goggo tace cikin bacin rai "tsinanniyar ya, baki iya komi ba sai yada baki kiyi bacci saikace gidan uwarki!,, ni da Allah fice ki debo min ruwa," Tafito tana dirin sanyi tadauko bahon ta ijiye agefe ganin goggo tashige yasa ta yi sauri tadauro alwala sannan tashige dakin don tayi sallah, tana ruku'un karshe taji saukan zuban ruwan sanyi akanta, a shide tatashi tazauna don tayi tahiyya, goggo kuwa tasa kafa ta tokareta sannan tace "munafukar yarinya , ni zaki rainawa hankali? Awan ki nawa kina sujjada?, wawiyar ya!," bata yanke sallahn ba saidata yi sallama alokacin takafayin wani tari wanda yasata gigicewa, goggon ta kamota sannan tajefo waje inda tazfadi agefen bahon, abunka da tsohon bahon daya tsufa, jira yake yaji nauyi yafashe tuni ya tsage, habawa kamar goggo jira takeyi ta fasa, tadubo gefen gadon shehu tadauko belt takafa zugeta, inda take shiganta deedo ihu take tana ambaton Allahnta, makwabta dasuke shirin zuwa masallaci hankalinsu duk ya tashi anma bawanda yashigo balle yakawo agaji don sunsan halin goggo sarai, Bayan tagama shiganta da duka kwakwaran motsi deedo batayi, tafice tabarta agun, kanta nawani matsanancin ciwo, tadauki dayan katon bahon wanda shi goggon tace tadauka kuma tacikoshi akanta, tafito tana tafiya dakyar haka ta dingisa har borehole , sanyi na shiga jikinta gashi tagagara motsawa, haka ta ajiye bahon tacigaba da zama jiratake taji dadin jikin tamike donta tuko ruwan, akanta taji taku, bata dago ba balle tagane waye, sallama yayi bata amsa ba, ganin haka yasa yaja bahon yaci sannan yacika jarkarsa daya dauka, sannan yace "baiwar Allah ko zaki taimaka kitashi,yayi safiya dayawa ace mace ta zo tazauna anan, bata kulashi ba, donhaka shima yaja yazauna, saidata fara jinta daidai sannan tadago kanta, alokacin yaganeta, deedon gydan goggo, uhm yagane komi kobata mishi bayani ba, donhaka kawai sai ya ce "tashi muje na taimaka miki " yadauki bahon akansa dakyar nauyin har kirjinsa yaji , toh shi namiji kenan ballatana kuma mace, tana biye dashi har suka isa kofar zaure googo tagani a kofar gun takama kunkumi gabanta yakara fadi rassssss BA’A SHAN ZUMA… 07 NA LUBABATU MAITAFSIR & BENAXIR OMAR Wani mugun salati goggo ta kwasa, tace "lallai yarinyar nan, abinda kika koma yi kenan? Meye hadin ki da wannan katon? Wato kullun na aike ki dama shi yake dauko miki ruwan ko? Yau zaki sani" Tana kokarin warto ta, Ado ya shige tsakiyar su, yace "goggo wlh ba laifin ta bane, naga ne bata da lafia, shine na taimako mata da ruwan, kiyi hakuri hakan ba zai kuma faruwa ba dama yau aka fara" tace "habawa munafukai, yau duk sai kun ci uwaku" tayi cikin gida da sauri, Ado ya lallaba ya sauke ruwan, dagowar da zaiyi yaga goggo da wani dan icce ta nufo kan shi, da gudu suka runtuma waje daga shi har Deedo, ta leko tana cewa "shegu, yau da kun tsaya da kunga karyar munafunci, ke kuma kya zo ki same ni ina nan ina jiran ki" ta juya ta koma ciki. Deedo dai banda kuka babu abinda take yi, Ado yace "kiyi hakuri Deedo, muje ciki in yi mata bayani, na san zata fahimta" suka juya suka shiga cikin gidan a tare, goggo ta kare masu kallo, tace "wai Ado dama kaine?" Yace "eh wlh goggo, kiyi hakuri baza a kuma ba" tace "ka ci albarkacin kai ne, amma wlh kar in kuma gani ka taimakawa waccen tambadaddar" Ado yace "baza a kuma ba goggo" ya juya zai fita sai ga Hadiza ta fito daga daki sanye da uniform, tana wani karairaya, tace "Ado ne yau a gidan namu" ya watsa mata wani kallo, sannan ya juya, ya fice. Goggo tace "Dijangala wai ba dai wannan Adon bane dama kike fada mun?" Tayi narai narai da ido tace "shine goggo, kinga ma ko magana baya mun" goggo tace "aihoo, shi yasa waccen tsinanniyar ta fara shige mai kenan, to wlh ki shiga taitayin ki, Ado ba irin mazan ku bane kucakai" ta juya wurin Hadiza tace "ki bar komai a hannu na dije na, zo ki karya kumallo ki wuce kar kiyi latti" ta zauna ta fara cin abincin tana galla wa Deedo harara, ita dai bata ce uffan ba, ta koma zaure ta dauko bahon ruwan ta, ta kawo ta aje. Da sauri ta wuce daki ta cire hijabin ta, sannan tazo ta fara wanke wanke, ta gama ta share ko ina duk tayi aiyukan data saba, sannan ta shige ta burmo uniform dinta ta fito ta leka dakin goggo bata nan, ta koma Palo a can ta ganta ta cake dauri, ta dora daya kan daya tana sakacen hakori, a gefe guda kuma tana sauraren radio… BA’A SHAN ZUMA… 08 NA LUBABATU MAITAFSIR & BENAXIR OMAR Da sallama ta rakube a kofar palon tace "goggo na gama zan tafi" a harzuke ta dago tace "ki gaida su, ko kuma wata tsiyar kike so in miki, iyiii?" Tace "a'a bakomai" ta mike ta fito, har ta kusa zuwa kofar zaure goggo ta kwala mata kira ta dawo, ta duka tace "gani goggo" ta watsa mata harara tace "munafuka, sai kace mutuniyar arziki, mtseww wuce ga dumame can ki dauka, nasan abinda kika tsugunnawa kenan" tace "nagode" ita kuma ta cigaba da banbami tana ta faman soka mata zagi kamar wata mahaukaciya sabon kamu. Ita dai Deedo dumamen ta kawai take kwasa dan ta riga ta Saba da wadannan munanan halaye na goggo. Tana gamawa ta wanke hannun ta, tasha ruwa, tayi sadaf sadaf zata fita goggo ta kwada mata kira, ta juyo a firgice, goggo ta kara hankado dankwalin ta gaban goshi tace "an shi nan tsinanniya" tayi mata dakuwa, Deedo ta dukar da kanta kasa, ta matso ta bata rankwashi tace "Allah yasa in kinje gwamnati tace ta daina biya miki wannan kudin makarantar dan banga uwar da kike koyowa ba, ke ni da ina da iko ma da da kaina zanje wurin gwamnan in sa a kore ki wlh," taja tsaki, ta ce "nasan maganin ki shegia, mai hali irin na uwa, wuce ki ban wuri" ta juya sum sum ta wuce, tana zuwa zaure ta arta da gudu, dan kar goggo ta biyo ta, gashi dama ta riga ta makara. * *** Tana tasowa daga makaranta kamar yadda ta saba ta fara bunguza sauri kamar zata tashi sama. Hally ta fallo da gudu tazo ta sha gaban ta, tace "ni anshi nan uwar yan tsoron goggo" ta mika mata bakar leda. Deedo ta dan murmusa tace "menene wannan kuma" hally tace "man shafawa ne da sabulun wanki da na wanka, dan na lura ko wanka bakiyi Deedo, ga sanyi duba kiga yadda kika yi furtutu, shi yasa na roki mama nace ta siyo in kawo miki, saura kuma kije ki kai wa wannan mala'ikar mutuwar" ta fada tana murguda baki. Deedo ta rungume ta, tace "nagode hally, in sha Allah idan na zama likita ke zan ba albashi na na farko" suka sa daria duka, sannan hally ta anshi ledar ta sa mata cikin jaka, suka juya suka cigaba da tafia suna firar exams da zasu fara next week… BA’A SHAN ZUMA… 09 NA LUBABATU MAITAFSIR & BENAXIR OMAR Deedo ce ita kadai tsaye gaban borehole tana ta faman buga famfo tun karfin ta, ga kiraye kirayen sallar maghriba ana ta kwadawa, amma bata da yadda zata yi, dole ta debi ruwan nan, in ba so take taci na jaki a wurin goggo ba. Daga gefe taji ana cewa "shine kika zo kina ba kanki wahala bayan nace ki daina buga famfon nan zai iya yi miki illa a matsayin ki na diya mace mai karancin shekaru" ta juyo da dan murmushin ta, tace "bana son kullun ina sanya ka cikin matsalolin rayuwa ta, nagode da kulawar ka" Ado ya karaso gaban ta yace "wuce ki zauna, bara na ida cika miki" ganin fuskan shi ba alaman wasa yasa Deedo ta koma baya, ya ida cika bahon ya dauko, yana gaba tana bin shi a baya, dan yanzu kullun shi yake dauko mata ruwa, da sun zo zauren gidan goggo, sai ya dora mata ta shige. Haka nan kuma yaji Allah ya dora mashi masifar tausayin yarinyar, wani lokacin har kudi yake bata amma bata ansa, haka zai gaji ya maida yan kudin shi cikin aljihu. Suna karasowa zauren yace "to matso ki ansa" ta matso ta miko kanta, shi ma ya matso zai dora mata, basu tantance ba suka ji muryar goggo ta fasa wani mugun ihu, Ado da ya daga bahon ruwa zai dorawa Deedo bai san lokacin da bahon ya subuce ya fadi kasa ba, goggo wani irin ihun munafunci take kurmawa tana salati tana cewa "Deedo daman abinda kike yi kenan? Jama'a ku taimaka mun na shiga ukku na lalace, wayyo Allah na yan iska har cikin zauren gida na" kafin wani cikin su ya ce wani abu, tuni wurin ya cika dam da mutane masu zuwa masallaci, yara da manya.. BA’A SHAN ZUMA… 10-11 NA LUBABATU MAITAFSIR & BENAXIR OMAR Shidai Ado tsayawa yayi yana mamaki, ikon Allah bata karewa, gwaggo ta tara musu jama'a sannan takiyin shiru balle su fahimci me ake ciki, cikin sanyin murya yace "ba abunda kike tunani bane, taimaka mata kawai nayi" Ta katse shi da karfi tareda cewa "kaidin banza kaidin wofi, meya hadaka da ita? Lalata ka zatayi don yanzu idonta a bude yake gwara kadena bata lokacinka" Wata makwabciyarsu tace "Kaga kai ado duk da taimako kakeyi, amma kaga wa ita kake jawa balai, donhaka ka kiyaye kawai" Kansa akasa ya amsa, nan akadan fara watsewa gwaggo kuwa tariko kunnen deedo sannan tayi cikin gida da ita, rufeta tayi adaki tasa shehu ya tsinko bulali, ta sa ta kwanta, ta zuba mata ruwan sanyi tashiga zuba mata bulalinnan, tas suka karye ajikinta, deedo bata iya tashiba don mazaunanta kumbura sukayi tum, nan da nan jikinta yayi jajur, sai hadiye numfashi takeyi, domin kuwa kukanma guduwa yayi yabarta ahaka, Da ja jiki ta isa daki, tayi kuka tagode Allah, takuma roki Allah daya gaggauta fitar da ita cikin wannan kangin datake ciki, sallama taji tundaga tsakar gida, muryar haly donhaka taji gabanta yafadi, don zuwa gidansu ba aladan haly bane, gashi dare yarufa sosai, gwaggo ce ta tareta tareda cewa "mekuma kikazo yimata?" "Assighnment fa aka bamu, toh tabat nata shine nakawo mata tana sauri zataxo gyda" "Kokuma tana sauri taje gydan saurayinta ba, dake a ke hada baki ai" "A a wlh gida fa kawai take zuwa, bata tsayawa" "Toh koma dai meye, ki tattara kiyi kibar gydannan, minti biyu nabaki" Itadai haly jikinta narawa tashigo , da tocinta ahannu ganin halin da deedo take ciki tasaka kara… NA LUBABATU MAITAFSIR & BENAXIR OMAR Gwaggo tashigo tareda cewa "meye kuma?" " naganta kamar ta mutu ne, gwaggo kitaimaka akaita asibiti wlh zata mutu" Ganin haly zata bata mata rai yasa tajanyeta ta wullata waje tarufo kofan, dakinta tawuce batare tadamu da halin da deedo take ciki ba Haly akofar gidan hankalinta a tashe tarasa wazatayiwa magana, kuka nabin idonta donhaka gida takoma tana addua wa kawar tata, Haka deedo takwana da asuba kuwa gwaggo tashigo da ruwan sanyinta, ta kwara mata anma bata motsa ba, hakan yasa taji jikinta yayi sanyi tafara jijjiga deedo,harsai da ta juyo fuskanta, jini tagani naxuba, bashiri tamike tace "shehu jeka kiramin malam audu(likitam gargajiya), shegiya tsinanniyar yarinya zata tonsmin asiri, ta Allah bataki ba " Da gudu yafita, mituna kadan saigashi yashigo "Malam tayar min da yarinyyan" "Anma dai kinsan cewa yaune na hudu dana ke xuwa don ceto rayuwarta, idan har bazaki iya riketaba kikaita gidan marayu mana" "Kai tsaya banson raini!, kana abu ba lissafi, ni meruwana da mutuwarta ko ranta,ai inta mutu zanfi kowa jin dadi, damuwana kawai karta mutu ahannuna" Girgiza kai yayi donganin jahilci a filin Allah Ya dubata yaga dogon suma ne, nan da nan yayi dabarunsa sannan tafara tari, saidai jikin baya motsawa, yajuyo yakalleta sannan yace "tafarka saidai dole kibari tayi jinyan jikin" "Badamuwa naji" ficewa yayi don bazai iya kallon wannan bakim cikiba, Yana ficewa tariko kunnen deedo "Bari ingayamiki ba mutuwa ko hadiye ranki kikayi bazaki mutuba, don wlh bazanje prison akan yar mage ba. Shegiya tsintacciya, laananniyar ya, ido kamam na mayu," hawaye ne kawai yakebin idon deedo, "Sannan kitashi kisan yadda zakiyi kidebo ruwa yarana zasuyi wanka!" Tafice tanata guna guni, deedo tayi godiya wa Allah kamar yadda musulunci ta bukaci kowani dan adam yake godewa Allah bayana tir da halin dayake ciki ba, musamman in kashiga wani Hali, kamata yayi kasa hakuri dangana kasaka cewa Allah kadai zai taimakeka yarufa maka asiri, shikadai keda iko akanka , shike baka jarabawa, kowani hali kake ciki akwai wanda yafika wahala, sai ka godemishi daya barka da ranka. Wani yanemi rai baisamuba , hakan nakara karfin imani, donkuwa koda tayi godiyan tariko bango, tabi bango har jikin ginin sannan tariko bahon tana bi da bango harta isa bakin zauren jitayi anhakadata dakarfi ta tsinci kanta akasa BA’A SHAN ZUMA… 12 NA LUBABATU MAITAFSIR & BENAXIR OMAR Tayi baya luu zata zube, Allah ya taimaka tana dab da bango ta dafa shi tun karfi har saida hannun ta yayi kara, cikin bacin rai goggo tace "tsinanniya, ni zaki ja wa sharri? Iyii? Zaki fita kina wani bin bango kamar kadangaruwa, wlh ko ki mike ki dauka bahon nan ko na kwada miki wannan iccen a gadon baya" ta nuna mata wani katon icce da yake rike a hannun ta. Bata jira taji mai zata Kara cewa ba, ta warci bahon, tayi waje cikin sauri. Saida ta danyi nesa da gidan sannan ta samu wuri ta zauna ta dan huta, sannan ta dau bahon ta karasa gaban famfon ta fara tukawa, ta cika shi, ta kinkimo ta dora a kanta, ta fara zabga sauri zuwa gaban goggo. Tana isa ta tarar da tulin bargunan fitsarin shehu, tana aje ruwan goggo tace ta kama su ta wanke ta shanya. Duk mai imani idan yaga halin da Deedo take ciki a wannan lokacin dole ya tausaya mata, amma goggo da yake ta kwashe kayan ta daga gaban manzo, ko kallon ta bata yi balle taji tausayin ta. Haka yarinyar nan ta wanke kayan nan, ta shanya, ga wata rawar sanyi tana yi, Jikin ta yayi zafi rau, haka ta cigaba da bauta a cikin gidan nan, tana gamawa ta lallaba ta shige dan akurkin dakin ta, yau bata ma jin zata iya zuwa makaranta, dan haka ta dan shingida a saman tabarmar kabar ta, tasa hannuwan ta ta tallabe kanta, saboda azabar ciwo da yake mata. Muryar hally taji tana kwada sallama, goggo tayi caraf ta fito tace "ke ko almunayar yarinyar nan, ba jiya na kore ki ba, shine kika lallabo kika dawo" ta dan galla mata harara, sannan tace "nazo ganin jikin Deedo ne, kuma ma in kika yi hakuri ni ba nan zan kwana ba" muryar Hadiza suka jiyo tana cewa "ke wlh kar ki wa mutane rashin kunya anan kisha shegen duka" bata tanka ta ba, ta bi ta gefen goggo zata shiga dakin Deedon, ta ko jawo kunnen ta, tace "wannan ya zama shine zuwan ki na karshe gidan nan, dan na kula ke kike koya wa waccen shegiyar iskanci, in ba haka ba wlh kika kara zuwa sai na karya wannan shegun kafafuwan naki masu kama da na sauro" tasa kara, tace "ni dai sake mun kunne gaskia" goggo ta hankada ta, tayi gaba, tana yi mata Allah ya isa cikin zuciyar ta. BA’A SHAN ZUMA… 13 NA LUBABATU MAITAFSIR &BENAXIR OMAR Yadda taga Deedo ta takure wuri daya tana wata irin kyarmar sanyi, abin ya bala'in bata tausayi, nan take taji wata muguwar tsanar goggo ta kara shiga ranta, wasu kwalla masu zafi suka zubo mata, ta karasa gaban ta, tana yi mata sannu, Deedo kasa magana tayi, hawaye ne kawai yake anbaliya a fuskan ta. Hally ta ciro rigar sanyin jikin ta, ta sanya mata sannan ta tayar da ita zaune, ta bude skool bag dinta ta fito da biredi da shayi a cikin roban coke, ta mika mata, kamar tasan abinda yake damun ta, ba tare da bata lokaci ba Deedo ta ansa ta fara yagar bread din nan, bata saurara ba saida ta gama cinye shi tas, sannan ta kora da ruwan shayin tayi gyatsa, hally da hawaye suka cika idon ta, ta share ta fito da paracetamol ta mika mata tasha. Sannan tace "ki kwanta ki huta, zan fada ma form master baki da lafia, anshi sauran maganin nan ki boye in anjima ki kara shan guda biyu, kiyi hakuri Deedo ki dauka wannan bakomai bane, wata rana sai dai ki bada labari in sha Allah,kinsan ita rayuwa daman ta gaji haka, kuma BA'A SHAN ZUMA SAI AN SHA HARBI, ina ji a jikina akwai ranar da goggo zata bukace ki, ranar da bata da wani mataimaki bayan ke, Allah ya sauwake kinji" ta dago idanuwan ta cike da kwalla, bakin ta na kyarma tace "nagode hally, Allah ya saka maki da alkairi, ke kadai kike sona duk fadin duniyar nan, Allah ya biya ki da gidan aljanna" ta rufe mata baki da hannun ta, sannan ta share mata hawayen, ta dau jakan ta tayi mata sallama, ta fito ko kallon inda goggo da ya'yan ta suke bata yi ba, ta wuce ta bar gidan. Deedo na nan kwance kamar gawa, dan ko motsin kirki bata iyawa, goggo ta leka dakin, tana kiran sunan ta amma shiru, ta karasa gaban ta tasa kafa ta hankada ta, cikin gigin bacci tayi firgigit ta mike tana zara idanu… BA’A SHAN ZUMA… 14 NA LUBABATU MAITAFSIR & BENAXIR OMAR Kafin ta karasa washewa taji goggo ta damko gashin kanta tayi waje da ita. Cikin kuka tace "Dan Allah goggo kiyi hakuri, wlh ban san mai nai miki ba" ta watsar da ita a kasa tace "yanzu zaki sani dan uban ki" dakin ta ta wuce ta fito da almakashi tace "bara na aske wannan shegen kan, sai inga ta karyar iskanci. Har ni zaki bazawa wani banzan gashin ki kina ji ina kira amma kika yi shiru" ta fara ihu ta tashi ta runtuma da gudu tayi hanyar zaure, goggo ma ko bata yi kasa a gwiwa ba ta daddage ta cafko ta, Deedo tasa hannuwan ta ta lullube gashin ta dasu, amma ena goggo ta riga ta damko wani gefe na gashin mai uban yawa, bata yi wata wata ba tasa almakashin ta datse. Deedo ganin gashin ta mai uban yawa a kasa yasa ta kurma wani gagarumin ihu, wanda hatta goggo saida ta razana. Malam Ilu ne ya shigo gidan da sauri, ganin abinda goggo ta aikata yasa ya karasa shigowa da gudu, sai da ya daddage sannan ya hankadar da goggo ta fadi kasa warwas! Cikin daga murya yace "Ke Batula kiji tsoron Allah, wlh ina jiye miki ranar da alhakin wannan yarinyar zai tambaye ki, ke yanzu duk uban dukan da kikai mata jiya bai ishe ki ba, dan bakin ciki shine yau har da aske mata gashi, ke baki tunanin wata rana zaki mutu ki bar abinda kika haifa? Ya zaki ji idan wani ya rinka cuzkuna musu irin yadda kike wa wannan marainiyar Allahn, in baki iya rike ta ki kai ta gidan marayu mana.." kafin mallam Ilu ya rufe bakin shi goggo ta daddage ta cilla mai almakashin da yake hannun ta, bai tsaya a ko ina ba sai a saman goshin shi, kafin yayi wani motsi jini ya riga ya wanke mashi fuska tasss! BA’A SHAN ZUMA… 15 NA LUBABATU MAITAFSIR & BENAXIR OMAR Ihu Deedo ta saka ganin jini ya wanke wa mal. Ilu fuska, da gudu ta ruga ta warto wani kallabi na goggo da yake shanye akan igiya tana kokarin daure mai wurin, cikin gadara da rashin nadamar abinda goggo ta aikata ta taso da sauri ta warce kallabin, tace "wato iskanci naki har da irin wannan kucakan kike yi? Mei zaki samu a jikin wannan tsohon? Lallai Deedo, daman na dade ina zargin ku, sai gashi zato na ya tabbata" ta juya ta kalli mal. Ilu da yake raba idanuwa tace "to wlh baku isa ba daga kai har ita, kuma idan ma kashe ta nake tana farkowa akwai abinda ya shalleh ka ne? Ince zama na take yi a gidan ko? Ko ko daman dan kuna labewa kuna iskancin ku shine har zaka zo ka tare mata, to ni Batula ba kanwar lasa bace, duk wanda yace zai ja dani wlh sai jikin shi ya gaya mishi, wannan ma da na maka kadan ne, dan a ciki na so in caka maka almakashin ka mutu kowa ma ya huta dan banga amfanin da kake tsinanawa wani ba a cikin gidan nan" tana kaiwa nan, ta bi ta gefen su, tasa kafa ta hanbare Deedo ta kara gaba abin ta.. Deedo wadda tausayin mal. Ilu yasa ta manta da tata larurar, tace "kayi hakuri baba, ka lallaba kaje chemist a gyara maka wurin kar wata cutar ta shiga" yace "kar ki damu Firdausi, dunia ce, ta ishi Batula riga da wando har ma da mayafi" ya mike dakyar yana ganin jiri, ya wuce ya fita ya bar gidan. Allah mai iko, ashe wannan fita ita ce fitar mal. Ilu ta karshe, yaje zai tsallaka titi ba tare da ya kula ba wani mai mota ya banje shi, nan take ya ce ga garin Ku nan.. Kulli nafsi za'katul maut! Allah ya jikan mal. Ilu da rahma amen! BA’A SHAN ZUMA… 16 NA LUBABATU MAITAFSIR & BENAXIR OMAR Hakika deedo taji rasuwan mal. Ilu , tana tuna kalmominsa na karshe akanta,gwaggo batayi nadama ko kadan ba, don taaziya ma sau daya ta leka, Deedo kuwa harta rame, tafada takara baki, asatin tafara zuwa makaranta, cikin ikon Allah saigashi wani malami yashigo ajin, yadebi masu kokari uku, ciki harda deedo sukaje ofishin principal, nan ya sanar dasu cewa gasa zasuyi wanda akwai baki daga kaduna zasuxo don su ga wannan gasa, akwai kyaututtuka masu tsoka dazaa raba, deedo tayi farin ciki sosai, nan da nan akabasu topic na debate FEMALE EDUCATION IS MORE USEFUL THAN MALE EDUCATION IN THE SOCIETY, inda ita zatayi supporting, zuwa tayi tasami malamin turancinn su tabashi don yarubuto mata hujja dazata kare kanta, yakuwa karba, Ranan da tadawo gida duk bakin cikin da gwaggo ke son tusa mata, deedo taki bata rai sai faraa take abun harya damu gwaggo, washegari dawurwuri tadebo ruwanta. Duk da bayanta baigama warkewa ba tanufi makaranta tanajira, hally tayi mamakin ganinta dawuri haka, malamin na isowa takarba, tafara haddacewa, har ajiye haly tayi tana koya agabanta, dahaka tahaddace komi akanta takuma yi murajaan yadda zata fita tabada tsokacinta Ran jumaa aka taru a hall na makaranta duk dalibai suntaru don ganin wannan ranan da zaaraba kyaututtuka, karfe takwas na safe aka bukaci suje, agyda kuwa tunda shehu yazo yasanar da gwaggo abunda zai faru , gwaggo ta tsiri aiki ranan, harda sa deedo wankin bango, deedo tanayi zata fita tadauko ruwan kayan miya tabata wai tafitar, tsabar nauyinsa saidaya bata mata kaya gashi batada wani uniform din sawa, dawuri tafice agydan don isa makaranta BA’A SHAN ZUMA… 17 NA LUBABATU MAITAFSIR & BENAXIR OMAR Hakika deedo taji rasuwan mal. Ilu , tana tuna kalmominsa na karshe akanta,gwaggo batayi nadama ko kadan ba, don taaziya ma sau daya ta leka, Deedo kuwa harta rame, tafada takara baki, asatin tafara zuwa makaranta, cikin ikon Allah saigashi wani malami yashigo ajin, yadebi masu kokari uku, ciki harda deedo sukaje ofishin principal, nan ya sanar dasu cewa gasa zasuyi wanda akwai baki daga kaduna zasuxo don su ga wannan gasa, akwai kyaututtuka masu tsoka dazaa raba, deedo tayi farin ciki sosai, nan da nan akabasu topic na debate FEMALE EDUCATION IS MORE USEFUL THAN MALE EDUCATION IN THE SOCIETY, inda ita zatayi supporting, zuwa tayi tasami malamin turancinn su tabashi don yarubuto mata hujja dazata kare kanta, yakuwa karba, Ranan da tadawo gida duk bakin cikin da gwaggo ke son tusa mata, deedo taki bata rai sai faraa take abun harya damu gwaggo, washegari dawurwuri tadebo ruwanta. Duk da bayanta baigama warkewa ba tanufi makaranta tanajira, hally tayi mamakin ganinta dawuri haka, malamin na isowa takarba, tafara haddacewa, har ajiye haly tayi tana koya agabanta, dahaka tahaddace komi akanta takuma yi murajaan yadda zata fita tabada tsokacinta Ran jumaa aka taru a hall na makaranta duk dalibai suntaru don ganin wannan ranan da zaaraba kyaututtuka, karfe takwas na safe aka bukaci suje, agyda kuwa tunda shehu yazo yasanar da gwaggo abunda zai faru , gwaggo ta tsiri aiki ranan, harda sa deedo wankin bango, deedo tanayi zata fita tadauko ruwan kayan miya tabata wai tafitar, tsabar nauyinsa saidaya bata mata kaya gashi batada wani uniform din sawa, dawuri tafice agydan don isa makaranta BA’A SHAN ZUMA… 18 NA LUBABATU MAITAFSIR & BENAXIR OMAR Angaji da jiranta hakan yasa aka fara kawai, dasauri tashigo tazauna, ruwan tumatur agefen riganta tana kokarin kakkabewa, kanta a kasa yayinda wacce tafarayi agefensu takeyi, kasancewar sune yan supporting, tana gamawa daga yan opposing , first speakernsu yafito yayi sannan yakoma anan aka kira sunanta Firdausi kabir sani, tafito a sanyaye ta tsaya, sannan takalli high table din tafara bayaninta "Mr.principal sir, honourable panel of judges, accurate timekeeper, co-debators, my collegue,ladies and gentlemen…….." Kanshi na kasa daga kan high table yadago dob ganinta, fararen idanunta yagani, yayinda take bayaninta, yadda take furta haruffanta bawanda zaiyi tunanin daga kauye take, tashin birni kawai, don tana fitar da kowanni kowanii hakki na kalamunta, yadda take Haka yata kallonta harta idar da batunta, wani tafi hall din yadauka kowa na tofa albarkacin bakinsa, yayinda alkalai suketa zuba mata mark, haka kowa yazo yayi nasa. Shikam hankalinsa yayi kanta, idonsa zur akanta har abokinsa nagefensa yadan sunkuyo sannan yace "Yadai lafiya naganka haka?" Yadan gyra murya don muryan takame ta ciki yace "Wacan yarinyan, second speaker" [10/12 01:16] Lubieee: BA'A SHAN ZUMA.. NA LUBABATU MAITAFSIR & BENAXIR OMAR Murmushi Faroukh ya saki, yace "kai ko meye hadin ka da ita? Ko ka santa ne?" Ya girgiza kai, yace "voice dinta ne exactly irin na ummi na, look at ha, hatta yanayin ta wlh" yace "haba abokina, ni kam banga kaman ba, ko dai ko dai?" Ya fada yana daria. Suna haka, aka fara kiran daliban don su anshi kyaututtukan da aka tanadar masu, aka kira 3rd position, sannan 2nd, sai daga karshe, principal ya anshi mic ya fara jawabi, wanda duk yawancin bayanan nashi yayi su ne akan namijin kokarin da deedo tayi, ya yaba mata, sannan daga karshe yace "I'll like to call on stage Dr. NAWAF KHAMIS!" Ya mike cikin takun shi na kasaita, kowa a wurin hankalin shi yayi kan shi, the most honourable nd young academic Dr. Ya karasa gaban principal ya mika mashi hannu, bayan sun gaisa ne principal din ya bashi mic, tare da wata yar paper ya koma wurin shi ya zauna. Ya buda papern cikin voice din shi mai wani irin zaki da girma, irin ta cikakken namijin da ya ansa sunan shi, ya kuma san abinda yake yi, ya fara jera tsararran turancin shi wanda ya tafi da imanin mutanen da suke wurin, most especially Deedo, wadda a duniya ba abinda take so irin taga hadadden namiji dan boko wanda ya iya tsara turanci. Ya gama jawabin shi, sannan ya kira FIRDAUSI KABIR SANI a matsayin dalibar da ta zo 1st a cikin daliban, nan da nan wuri ya kaure da tafi, ita kuma a natse ta mike, kanta a kasa ta karasa saman stage din. Nawaf wanda tunda ta taso ya zuba mata idanun shi, har ta karaso gaban shi, nan ya dauko gifts dinta, ya bata, haka duk abinda ake ya kasa dauke idon shi a kanta. BA’A SHAN ZUMA… 19 NA LUBABATU MAITAFSIR & BENAXIR OMAR A haka aka gama gabatar da duk abinda ya dace, sannan aka rufe taro da addu'a, kowa ya kama gaban shi. Ana fitowa Deedo tare da hally suka rungume juna,suna murna, nan da nan wasu hawayen farin ciki suka saukan mata, ta kalli hally tace "ina ma ina da wani wanda zaiyi proud dani a irin wannan ranar, ina ma iyayena suna raye suga wannan abin farin cikin da ya same ni" hally tace "kar ki damu Deedo, Allah yana tare dake, haka nima ina tare da ke 100%, iyayen ki kam ki dage da yi masu addu'a, shine babban abin da suke bukata daga gare ki" ta share hawayen, tace "in sha Allah hally, nagode miki da duk wani abun alkairi da kikai mun a rayuwa, bazan manta dake ba har abada" suka jero da niyyar tafiya gida, sun zo ta wurin staff room zasu wuce wani yaro yazo yace "Deedo ana neman ki a office din principal" bata tsaya bata lokacin komai ba, ta mika wa hally gifts din da suke hannun ta, sannan ta wuce zuwa kiran da ake mata. Tana shiga ya dago dara daran idanun shi masu matukar haske da sheki, bai aje su a ko ina ba sai saman kyakkaywar fuskar ta. Dam taji gaban ta ya buga, ta karasa da sallamar ta, ta samu gefe ta duka. Principal ya maida kallon shi ga Nawaf yace "Wannan kake nufi?" Ya girgiza kan shi alaman ita fa, principal din yace "no problem, ga ka ga ta ai" kafin Nawap ya buda bakin shi, wani teacher ya leko, yayi ma principal magana, haka ya mike ya fita, ya bar su a office din daga shi sai ita. Kallon ta yake, yana son ya karanci wani abu da ya gani tattare da ita, ba komai bane illa damuwa da rashin samun natsuwa tare da kwanciyar hankali. A hankali ya fara magana "Firdausi ko?" Kanta na kasa, dan ta kasa hada ido dashi, wani irin Kwarjini yake mata, cikin siriyar murya tace "yes sir" yace "yu did a good job today, kin fita kunyar makarantar ki, malaman ki tare da dalibai yan uwanki, I know they 're proud of yu" har cikin zuciyan ta abin yai mata dadi, dan har sai da wani murmushi ya bayyana akan fuskar ta! BA’A SHAN ZUMA… 20 NA LUBABATU MAITAFSIR & BENAXIR OMAR Ya cigaba da cewa "well, dalilin kiran ki ba komai bane illa ina son na san ko ke wacece, ba don komai ba sai don mugun kama da kike yi da ummi na, maganan ki, nd a lot of things" cikin tashin hankali ta dago fuskar ta, caraf suka hada ido, dan dama ita din yake kallo, sai da ta tattara natsuwar ta, sannan ta fara magana "ni kam ba kowa bace, ba kuma komai bace, asali ma, marainiya ce ni, ina zaune da goggo na, wadda ta kasance kanwar mahaifina, iyayena sun rasu tun ina shekara 5 a dunia" tana kai wa nan, taja bakin ta tayi shiru. Shiru na yan dakiku ya ratsa wurin, sannan ya saki ajiyar zuciya, yace "ehnn ina sauraren ki" ba tare da ta kalle shi ba, tace "shikenan ai" ya kura wa kyakkaywar fuskar ta ido, tabbas ya ga damuwa a tattare da yarinyar, amma ya rasa dalilin da yasa a lokaci daya yaji ta shiga ran shi, ya rasa dalilin da yasa yaji yana son ya san wani abu dangane da damuwar da ya gani bayyane a saman fuskar ta. Ya dan gyara zaman shi, sannan yace "a matsayina na psychologist, na karanci wani abu a tare da ke, wanda baki son ki sanar dani" ta dan firgita, sannan tace "bakomai fa" ya shafi tarin sumar da take saman kanshi, sannan yace "alright then, zaki iya tafia" bata kai ga mikewa ba principal ya dawo office din, a haka tayi musu sallama, tasa kai ta fita ta bar office din. Hally ta gani zaune a gefe ta karasa kusa da ita, tace "muje ko" ta mike suka jera,ta fara tambayar "me ya faru ne Deedo?" Ba tare da ta boye mata komai ba, ta fada mata abinda ya faru tsakanin ta da wanda taji an kira da Dr. NAWAP KHAMIS.. BA’A SHAN ZUMA… 21, 22 & 23 NA LUBABATU MAITAFSIR & BENAXIR OMAR A haka suka kawo layin su Deedo, inda suka yi sallama kowa ya kama gaban shi. Tana shiga gidan da murnar ta, sallama tayi, a lokacin goggo tana kofar daki, ta dago ta watsa mata wani kallo mai tattare da tsana da tsangwama, da sauri ta karasa gaban ta, tana "sannu goggo" ta dago fuskar ta a murtuke tace "uban mi zanyi da sannunki? Shine sai yanzu zaki dawo mun gidan nan ko? Kina can kina yawon naki na iskanci da kika saba" tayi kasa da kanta, tace "kiyi hakuri goggo, wlh a makaranta ne aka tsaida mu" tayi kwafa, sannan tace "uban miyye nan a hannun ki?" Tace "kyautar da aka bamu ce" goggo ta warce, ta farka wrapping sheet din, sannan ta fara fito da text books da math set, da note books da sabbin uniform gal, da sauran tarkace dai na students, ta kwashi uniform din tare da text books ta watsa mata, tace "wannan kadai zaki samu shegiya, wannan sauran kuma duk su shehu zan ba su" ta tattara ta tura su bayan ta, ta kara da cewar "wai ke nan a wannan shegen kan naki har wani kallon mai kokari suke maki, tashi wuce ki bani wuri, kin zura mun ido kamar na mujiya, kuma ga kayana nan, ki tattare su ki wanke tass" ta kwashe yan kayan da ta bata, ta shige daki, ita murna ma take yi, dan bata yi zaton zata samu wani abu daga cikin kyautar da aka bata ba. Dr. NAWAP KHAMIS, matashi ne mai kimanin shekarun da basu wuce 28 ba a dunia. Dogo ne sosai dan har ya dan rankwafa saboda tsabar tsawon shi, yana da kirji mai fadi wanda a kallo daya zaka ga bayyanannun 6-packs din shi. Yana da muscles a damtsen hannun shi, kasancewar shi masoyin gym ne na bala'i, yana da doguwar fuska wadda ke dauke da dara daran idanu tare da dogon hancin da ya dace da kyawawan lips din shi. In fact, Nawap namiji ne wanda ya ansa sunan shi namiji, yayi degree din shi na daya dana biyu a jami'ar Bayero da ke garin kano, inda daga bisani ya wuce England inda ya hada PhD din shi akan psychology. Shine da na farko a wurin mahaifiyar shi haj. Fatima wadda yake kira da ummi, mahaifin shi Alh. Khamis shaharraren dan kasuwa ne a garin kaduna, wanda Allah yai mashi rasuwa shekara biyu da suka gabata, kanwar shi kwaya daya Hafsat wadda take aure a garin Abuja. Yanzu haka yana aiki da federal ministry of education, wannan ne dalilin da ya bashi damar zuwa kauyen su Deedo, kasancewar su masu inganta ilimin matasa yan secondary skool. BA'A SHAN ZUMA… 2⃣2⃣ NA LUBABATU MAITAFSIR & BENAXIR OMAR Tun ranan da Nawap ya bar kauyen su Deedo bashi da abin tunani wanda ya wuce ta, babban tashin hankalin shi shine damuwar da ya gani shimfIda saman fuskar ta, gashi ya rasa gane menene ainahin dalilin damuwar ta a matsayin ta na yarinyar da duka duka bata wuce shekara 15 ba a dunia, idan zai iya tunawa principal din su yace suna 3rd term ne yanzu a ss2. Babu abinda ke mashi yawo a kan shi irin kalaman principal na karshe da yace "Deedo ta kasance yarinya hazika wadda zan iya cewa babu kamar ta kaf cikin makarantar nan, sai dai kuma yarinya ce wadda take bukatar taimako cikin gaggawa!" Dam! Gaban shi ya Kara bugawa, to wane irin taimako ne take bukata? Shine abinda bai tsaya ya samu cikakken labari ba. Mikewa yayi daga kan kujeran da yake zaune, ya tattara laptop din dake saman cinyan shi ya dora kan center table, sannan ya fara zagaya palon a hankali. Tunani ya fara yi shin me yasa ya damu da yarinyar bayan kuma ya kan hadu da cases sosai irin nata a yawancin makarantun da suke zuwa, a fili ya furta "nata is different! I saw the sorrow in ha, she's desperately in need of my help!" Ya sa hannu ya ciro wayan shi da ke ta faman ringing cikin aljihu, ya zaro wayan ya kaima screen din kallo, lokaci daya yayi wurgi da ita saman kujera har ta katse bai daga ba. Aka sake kiran wayan, a karo na biyu shima kaman ba zai dauka ba, can dai ya daga cikin muryar nan tashi mai kwantar da hankali, yace "Aysha ya akayi ne?" Ba tare da mun jiyo ansar da aka bashi ba, yace "I'm kinda busy yanzu gaskia, May be I'll call back later" bai jira ansar ta ba ya katse wayar yaja tsaki, tare da komawa kan kujeran ya lumshe idon shi, Deedo ya gani cikin kodaddun uniform dinta, fuskar nan ta ta cikin yanayi na damuwa da bukatar tallafin gaggawa, firgit ya bude idon, amma bai ganta ba, hakan ya sa ya cika bakin shi da iska sannan ya fitar, yace "I'll come 4 yu Deedo nd I promise I'll help yu" ya mike ya shige bathroom ya sakan ma kanshi shower… Katon bahon ruwan ta, ta doro a kai tana ta bunguza sauri kasancewar maghriba ta gabato, kayan jikin ta duk sun jike sai rawar sanyi take yi, kafar nan ta ta firi firi kaman tayi birgima cikin kasa, shehu ne tare da wasu yara suke binta a baya suna mata daria, bata ko damu da su ba, dan ta san idan ta tsaya yau kashin ta ya bushe wurin goggo. Hango shi tayi rungume da hannayen shi, ya zuba mata idanu kamar mai nazarin wani abu a tattare da ita. Kanshin turaren shi da ta shako daga inda take shi ya tabbatar mata da abin da take tunani! Cikin jin kunyar yanayin da take ciki tazo, ta raba ta gefen shi zata wuce ba tare da ta sake kallon inda yake ba, bai tanka mata ba, ta shige cikin gidan da saurin ta dan har an kwalla kiran sallah. Shehu ne ya shigo da sauri yana kwala wa goggo kira, ta fito daga daki zanin ta a hannu, tace "Shehu na Allah, yau kuma da waccen ka shigo?" Yace "wani mai mota ne wai a kira mai Deedo" ta zaro ido tace "mai mota da neman Deedo? Kai shehu ko dai dijangala yace?" Yace "wlh Deedo yace, har ma yace wai wadda ta shigo yanzu" goggo ta rafka salati tace "na shiga ukku, ubanwa kuma kika jawo? Wlh in masifa ce yau a kanki zata kare, dan ni dai ina zaman zama na baki isa ki jawo mun bala'i ba" ta dafe kanta tace "oh ni Batula! Wannan tsintacciyar mage na neman jefa ni cikin masifun ta" ta damko kunnen ta, ta wurga ta, tace "wuce kije ki san yadda zakiyi da bala'in da kika tattago, idan ma tafiya zasuyi dake wlh ko kofar zaure bazan je ba, tunda ban san sadda kika je yawon iskancin ki ba har kika jawo bala'in" Deedo tasa kara, tace "wlh goggo banje wani yawon iskanci ba, wlh ban ja kowa ba" goggo ta hankada ta, tace "ki wuce ki fita wlh jar ki ja tsinannun su shigo mun cikin gida, dan wlh duk wanda ya shigo sai na fasa mai kai da tabarya" Deedo ta share yan hawayen ta, taja lamusassun silifas dinta da suka ji wahalar dunia ta bi hanyar zauren zata fita, shehu kuma ya sa ihu yace "bari muje muga irin dukan da za a nakadawa shegiya, dama su tafi da ita mu huta" goggo tace "ka tsaya daga bakin zaure dai, dan kar su hada mun da dakai" bai bi ta kanta ba ya juya da gudu ya fita kofar gidan. BA’A SHAN ZUMA… 24, 25 & 26 NA LUBABATU MAITAFSIR & BENAXIR OMAR Koda ta fita baya kofar gidan, sai dai motan shi kawai, har ta juya zata koma ciki ta jiyo ana kwala mata kira, waigowa tayi, ta hango shi yana tahowa, da alama daga masallaci ya fito. Da sallama ya iso, ita kuma tana tsaye tana matse kwallan da suka taran mata, kallon ta yake cike da tausayin rawar sanyin da take yi, gata dai yarinya karama amma alamun damuwar da take tattare dasu sun bayyana karara akan fuskar ta, ba tare da yace komai ba. Dukawa tayi har kasa sannan tace "ina wuni" ya ansa a taqaice, sannan yace "kin gane ni kuwa?" Ta daga kai alaman eh, ya gyara tsayuwar shi, sannan yace "na tambaye ki labarin ki, amma baki fada mun komai, a yanzu kam, ba sai kince dani komai ba, domin yanayi da kike ciki ya sanar dani irin matsalar da kike fuskan ta a gidan nan" ta dago jajayen idanun ta da suka rine da kuka, tace "ni bana tare da matsalan komai" kallon ta yake yana nazarin yadda tayi maganar, murmushi yayi, ya juyar da kanshi ya ce "well, tunda baza ki fada mun matsalar ki ba, bara na shiga gidan sai inji dalilin da yasa kike daukan wannan katon bahon na ruwa a kanki, a matsayin ki na yarinya mai karancin shekaru" ya sa kanshi alamar zai shiga zauren, shehu na ganin ya nufo inda yake ya tashi ya runtuma da gudu cikin gidan, itama tayi sauri tasha gaban shi tace "kayi mun rai dan Allah, ba dan ni ba, yau muddin kaje ma goggo da maganar nan wlh sai ta kusan kashe ni" murmusawa yayi, sannan yace "zaki fada man ko ke wacece ko kuwa?" Ta girgiza kanta, "zan fada maka" ya ja da baya ya jingine jikin kofan zauren, yace "ina sauraren ki" ba tare da bata lokaci ba Deedo ta warware mashi komai, ta fada mashi duk halin da take ciki a gidan goggo, hatta da mutuwar mal. Ilu bata boye ma Nawap ba, ji yayi kafafun shi na neman kasa daukar shi, bai taba tunanin mutane marassa imani irin goggo suna rayuwa ba har yanzu a doron kasa, ya zata irin su sun gama karewa tun zamanin jahiliyya. Tausayin yarinyar ya kara shigar shi, ga wani irin kuka da take yi marar sauti, kallon ta yake a matsayin tilon kanwar shi Hafsat, har yana imagining idan ita ce wane irin mataki zai dauka. Kallon ta yayi, yace "kukan nan ya isa, ki shiga gida kinji, zan karasa cikin bauchi na kwana, zuwa gobe zan dawo in sha Allah" ta mike jiki ba kwari ta shige ciki, shi kuma ya shiga motan shi yai mata key ya kama gaban shi. Tana shiga ta tarar goggo da Hadiza da shehu sun jera sun zuba ma kofar ido suna jiran suga mei zai faru, damko ta goggo tayi tace "uban wanene wancan?" Deedo tasa kara tace "wani ne" goggo tace "wani wa?" Ta fara kame kame dan bata san ya za tai ma goggo bayani ba, ta daka mata tsawa tace "baza ki fada ba?" Tace "daga makarantan mu ne" goggo tace "naga alamar yau yan iskan ne a kanki, yanzu zanyi maganin ki idan baza kiyi magana ba" cikin tsoro da fargaba ta fada ma goggo yadda ta san Nawap, ta kara da cewar "yazo garin ne shine ya biyo ta nan" goggo ta sa salati, tace "ke Deedo ki fita a ido na wlh, yanzu ke yawon iskancin naki ya kai har da yan birni kike yi? Yau zaki gaya wa yan garin ku" ta damki yarinyar nan ta fara bugu, Hadiza ma ta mike ta debo ruwa a randa ta watsa mata, suka ci gaba da jibgar ta, shehu kam sai tsalleh yake yana jin dadi, dan duk dunia ba abinda ya ke so irin yaga goggo na kwalfar Deedo, saida sukai mata liiis,sannan suka shige daki suka barta a wurin. Dakyar ta lallaba ta shige dan akurkin dakin ta, kuka take yi sosai, ita kanta tausayin kanta take yi, wannan azaba ta ishe ta, neman hanyar da zata kubutar da kanta kawai take yi, ta lallaba tayi alwala tazo ta fara sallah ta gama, ta jawo littafin ta Geography tasha karatu sosai, abinka da mai sharp brain, dandanan ta kwashe komai da take bukata, ga yunwa ta addabe ta, ga kuma wani mugun bacci da yake figan ta, nan inda take ta dan shingida, kafin kace wani abu tuni bacci yayi gaba da ita, abin ka da ansha bauta da rana an gaji. Yau Allah ya taimaka ta kiran sallar farko a kan kunnen ta dan haka tayi zumbur ta mike, tashin ta keda wuya, goggo ta shigo da robar ruwan ta, tana haska fitila ta ganta a tsaye, tace "la'ananniya, da kar ki tashi mana" tayi kwafa tace, "kin wuce kin wanke kayan fitsarin can na shehu ko sai nasa kafa na hanbare ki?" Sum sum Deedo ta fito tana rawar sanyi, kayan fitsarin ta kwashe ta wanke, sannan ta doro alwala tazo ta gabatar da sallar asuba, sannan ta dauki bahon nan, ta wuce borehole. Bayan ta dawo tayi duk wani aiki da tasan nata ne, ta gama ta jawo uniform dinta, ta saka sannan ta fito ta karasa kofar dakin goggo. Ita daya ce zaune a bakin gado, dan su Hadiza sun dade da tafia makaranta. Tace "goggo zan tafi" ta watsa mata harara tace "na rike miki kafa ne? Ko wata tsiyar zan miki ne? Eyee?" Ta girgiza kanta, sannan ta mike ta fito daga dakin ta nufi makarantar. Tana isa har an fara exam, malamin ya kalle ta kaman wadda aka koro, yace "Firdausi Kabeer" dam taji gaban ta ya fadi, ta tsaya cak a inda take, yace "mei sa tunda aka fara exam kullun sai kinzo late?" Ta rasa abin cewa, sai can ta tuna da goggo ta fasa mata baki jiya wurin dukan ta har ma ya kunbura, tayi saurin cewa "I'm sorry sir, na taho ne na fadi a hanya saida na tsaya chemist na ansa magani" ya kare mata kallo, tabbas ga alama nan a tattare da ita, dan haka ya bata question paper yace ta wuce ta zauna, ta ansa da sauri ta wuce seat dinta ta zauna. Nawap kasa bacci yayi a daren jiya, yana tunanin ta ena zai biyo ma mace mai mugun hali da rashin imani irin goggo; shi dai yayi alkawarin taimakon yarinyar nan no matter what; amma ya rasa ta wane hanya zai bi dan ya kubutar da ita daga hannun azzalumar matar nan. Tunani ya fara yi ko court zai mika ta, sai kuma wata zuciyar tace "a matsayin ka na wa? In kaje gaban alkali kace me?" Yaja tsaki, ya watsar da wannan tunanin can kuma wata dabarar ta fado mashi, murmushi ya saki wanda ya kara mashi kwarjini, da sauri ya canja akalar motar shi yabi wani titi, ba tare da yasan ko ina cikin garin Bauchi ba, haka ya bi main road na cikin garin, nan ya samu wani katon mall, ya karasa yayi parking ya fito ya shige ciki. Duk wani abu da dan adam zai bukata akwai shi, haka ya zage yayi kyakkyawan shopping na dangin kayan abinci masu uban yawa, tarkacen man shafawa, sabulun wanka dana wanki, ya koma bangaren kayan sawa nan ma ya kwasa son ran shi, har da kayan yara maza ya kwaso, akai mashi total kudi wurin 150, 000, credit card din shi ya ciro ya basu suka cire, sannan aka kwashi kayan aka sa mashi a pickup ta shopping mall din, dan motar shi baza ta iya daukar lodin ba, ya shiga yana gaba masu motan na bin shi har cikin garin Ningi. A kofar gidan Hajia goggo suka tsaya, ya kira wasu almajirai suka taimaka ma masu motan suka shiga da kayan ciki. Goggo dake kofar daki tana sakacen hakori taga mutane da kaya niki niki, ta yi zumbur ta mike tace "kai malam daga ina wannan kayan?" Wani cikin su yace "wani ne yace mu shigo dasu yana nan waje" tana tambayar wanene amma bai bi ta kanta ba, suka juya suka fita. Saida aka gama shigo da kayan tsab, sannan Nawap ya shigo ya tsaya bakin zaure yayi sallama, goggo data kagara taga wanda ya kawo wannan kantin guda (inji ta tace wannan ai kanti ne guda ya kwaso) tayi saurin cewa "shigo mana" ganin tsayayyen namiji, jarumi, matashi, dan boko, wanda ya ji hutu, ya kuma ji bugun A.C, mai asalin zati da kwar jini! Yasa goggo tayi saurin ja da baya kamar wadda tayi karya, ta samu gefe ta rakube, bakin ta na rawa tace "yaro daga ena?" Yanayin da goggo ta shiga ya bala'in bama Nawap daria; haka dai ya gintse, yace "bari mu gaisa mana goggo ta".. BA’A SHAN ZUMA… 27, 28 & 29 NA LUBABATU MAITAFSIR & BENAXIR OMAR Goggo tana zara idanu ta mike da sauri ta dauko sabuwar tabarma daga daki ta shimfida mashi, ya zauna, ya gaishe da ita cikin ladabi, ta ansa bakin ta na kyarma, tace "ni fa har yanzu ban dau haske ba, daga ina kazo ne samari?" Ya saki lallausan murmushi, sannan yace "Sunana Nawap, dan asalin garin kaduna ne ni, yanayin aiki na ne ya kawo ni Bauchi state, daga nan kuma aka turo ni wannan gari" goggo tace "Ayyya, to wannan tulin kayan fa na menene?" Ya kara murmusawa, yace "naki ne Haj. Goggo" goggo ta zaro ido ta dafe kirji, tace "wannan uban kaya haka? To wai kai a ena ka sanni ma?" Nawap cikin zuciyar shi daria kawai yake, ya san hakon shi ya kusan cimma ruwa kasancewar yanayin da goggo ta shiga, ya san dama baza ta rasa son abin dunia ba. Yace "ina zaune da mahaifiya ta, ina kuma da kanwa kwaya daya, amma tayi aure, to mu kan samu masu aiki da dama, sai dai da yawan su basu zama sai su gudu, saboda aikin gidan yana da yawa. To jiya sai naga wata yarinya da katon baho na ruwa ta shigo gidan nan, hakan ya tabbatar mun da zata iya ko wane irin aikin wahala, shi yasa nace bara nazo naji ta bakin ki, ko zaki taimaka ki bani ita? Ke kuma ina turo miki da kudin aikin nata a ko wane karshen wata" goggo ta gyara zaman dankwalin ta, tace "ba dai wannan tambadaddiyar yarinyar kake nufi ba?" Yace "wa kenan?" Tace "Deedo mana, tsintacciyar mage, shegia mai mugun hali" har cikin zuciyan Nawap baya jin dadin zagin da goggo take ma marainiyar yarinyar nan, haka dai ya daure yace "ina ga ita din ce, ban dai san sunan ta ba" goggo ta dan matso da kanta dab dashi, kamar wani zaiji abinda zata ce, a hankali tace "nawa zaka na biya na duk wata idan na baka ita?" A takaice, yace "naira dubu hamsin" dan tsabar tsorata har sai da goggo ta hantsila baya daga kan yar kujerar tsugunnin da take kai, tace "dubu hansin?" Ya gintse dariyar shi yace "ko sunyi kadan ne goggo?" Tace "haba ina fa, ai ban taba kama ko rabin su ba, bari tsinanniyar tazo, ko zata mutu sai ta bika, kuma ko wahala zata kashe ta, kar ta sake ta dawo mun gidan nan, kai ni in ka tafi da ita ma ko ganin gida kar ta sake tazo" Nawap kallon ikon Allah kawai yake, tare da tsantsarar rashin imani na matar nan, ya muskuta, yace "ena yarinyar take ne?" Tace "ta tafi makaranta, ai tana dawowa ba abinda za a jira wucewa kawai zakuyi, daman ba wata kwalwar fahimtar karatun ne da ita ba, haka nan dai take zuwa makarantar" Nawap yace "bari dai muji ta bakin ta ko goggo" goggo tace "in dai ta bakin wannan shegiyar zamu tsaya ji ai ba yarda zata yi ta bika ba, dan haka kawai ba sai an mata wani bayani ba" Nawap wani irin kallo mai tattare da tsana yake watsa ma goggo, yanzu shi inda ace ba manufar alkairi gare shi akan yarinyar ba, da haka zata dauke ta ta bashi, ba tare da tunanin shi din ko wanene ba. A zuciyar shi yayi Allah wadaran hali irin na wannan matar, ya kuma yi mata addu'ar Allah ya sa ta dandanin kuncin rayuwa koda rabin wanda Deedo ta dandana ne. Sai da ya tattaro natsuwar shi, sannan ya saki murmushin yake, yace "to shikenan goggo, bara na dan zaga cikin gari zan dawo zuwa anjima" yasa hannu a aljihu ya ciro bandir na yan 500 ya mika mata, goggo hannu na bari, tayi saurin warcewa, sai da ta adana su cikin zanin ta, sannan tace "bayan wannan kantin guda daka kwaso, abin kuma har da wahala" yana tsaye yana kallon karfin hali da munafurci irin na goggo, ya girgiza kanshi, yayi murmushi, yace "wannan ai kadan ne goggo, kar ki damu" ta wangale bakin ta, tace "to shikenan Nawab, sai ka dawo din" yadda ta kira sunan nashi yasa ya kasa gintse dariyar shi, dan haka ya dan dara, sannan ya wuce ya fita. Yana fita skool din su Deedo ya zarce, direct office din principal ya nufa, bayan sun gaisa yake tambayar "Dr. Kaine a garin namu" Nawap ya shafi kyakkyawan sajen shi da ya kwanta luf saman fuskar shi, yace "wlh fa, ya students?" Yace "Lafia fa" nan suka cigaba da fira, inda yawancin firan nasu duk akan tabarbarewar ilimin yaran karkara ne, nan ya samu labarin su Deedo suna zana waec ne, wadda zasu gama sati mai zuwa, sannan kuma su fara neco. A haka yai ma principal din sallama, sannan ya fito. A kofar gidan goggo ya tarar da Deedo tare da hally, tana mika mata magani da ta ciro daga jakar ta, tace "wlh Deedo ki natsu, yanzu kinyi girman da za ace kin wuce duka, har ana kumbura miki baki, wlh idan nice ke tuni zan ture goggon gefe, sai dai ko mai zai faru ya faru" Deedo ta murmusa tace "hally ke dai ki gode ma Allah da yasa iyayen ki suna raye, amma baki san menene maraici ba, ni ina naga karfin halin da zan iya taba koda yatsan goggo ballantana kuma in samu halin ture ta, ke dai ki taya ni da addu'a kawai har Allah ya kawo karshen zamana a gidan nan" hally tace "Allah ya taimaka, bara na wuce" suka juyo a tare, nan suka ga Nawap jingine jikin mota, fuskan ba yabo ba fallasa, duk suka duka suka gaishe shi, sannan suka yi gaba ta dan taka ma hally, nan take fada mata yadda suka yi jiya, hally tace "Allah yasa ya zamo silar fitar ki daga kangin da kike ciki" Deedo tace "kaman ya? Ke ni ko ganin shi bana son yi wlh" hally tace "Ke dai yanzu je kiji da wacce yazo tukunna" sukai sallama ta wuce ita kuma ta dawo, amma bata ganshi ba dan haka tayi saurin shigewa cikin gidan, nan ta jiyo muryar goggo tana cewa "kaga gantalalliyar yarinyar nan har yanzu bata iso ba" jiki ba kwari tayi sallama cikin gidan ta shiga, ganin shi tayi zaune saman tabarma, dan da nan ta shiga tashin hankali, tasan yau karyar ta ta kare, Allah ne kawai zai raba ta da goggo da bala'in ta.. Dakyar ta karaso cikin gidan, a dai dai lokacin kuma goggo ta fito daga daki inda suke shiga da kayan da Nawap ya kawo masu. Harara ta watsa mata, sannan tace "ke dai Allah wadaran hali irin naki, shegiyar 'ya gantalalliya, ina kika je kika zauna kuma" ta karaso gaban ta, ta duka tace "kiyi hakuri goggo wlh ban tsaya ko ina ba" tasa kafa ta wurgar da ita, tace "daga yau dai gantalin ki ya kare, naga gidan uban da zaki kara yawon iskancin ki, dubi nan" ta nuna mata Nawap da yake zaune yana kallon goggo, Deedo ta dago ta kalle shi, sannan goggo taci gaba "to da shi zaku tafi, zaki je can kina masu aikatau, sauran kuma inji abinda ba shikenan ba, wlh na lahira sai ya fiki jin dadi" wani irin kuka ta saki, duk wanda ya kalle ta sai ya tausaya mata, kafar goggo ta rike tana "kiyi mun rai goggo, ki taimaki rayuwa ta dan Allah, wlh ban san shi ba, bazan bi shi ba, kila ma dan yankan kai ne, wlh zan yi miki ko mai kike so, amma kiyi mun rai kada ki kaini wurin yan yankan kai" saida goggo ta tattaro karfin ta gaba daya, sannan ta wancakar da Deedo, har saida ta bige da dogon karfe na baranda, sannan tace "kinsan Allah ko gawar ki ce sai bawan Allahn nan ya tafi da ita, kinji dai na rantse, baki isa ki sani kaffara ba kuma" tayi hanyar dakin Deedo da niyyar watso mata tsummokaran ta, Nawap dake gefe yana kallon abinda ke faruwa, cikin kunan zuciya wanda bai bari goggo ta gane ba, yace "ehnmm goggo" tayi saurin dawowa ta duka gaban shi tace "ya akayi ne Nawabu?" Saida yaja dogon numfashi, sannan ya tuna principal din su Deedo ya fada mashi suna exams, sannan ya tuno da ummin shi, at least ya kamata ya sanar da ita kafin ya kai mata Deedo, wata dabara ta fado mashi, ya dan gyara zama, sannan yace "naga alamar yarinyar nan tana da yan matsaloli, ga kuma yanayin jikin ta ba wani gyaran kirki, dan haka ina son a aje mun ita a nan zuwa nan da kamar wata guda, amma ina so duk wata wahala da take yi a da ta daina yin ta, ba don komai ba sai don idan na kaita can ta samu karfin yin aiyukan da muke dasu, irin dibar ruwan nan da sauran su, in yaso ko kofar gida kada a rinka barin ta tana fita, makaranta kawai na amince taje, wannan shima wani aiki ne, wanda zan biya kudin shi yanzu yanzun nan" goggo da taji maganar kudi, tayi sauri tace "to ai shikenan tunda dai kai ka bukaci hakan, amma dai naso ka tafi da ita yau din" yace "bakomai, zan dawo nan da wata 1" yasa hannun shi aljihu ya kara kwaso wasu kudin ya mika wa goggo, sannan ya mike yayi hanyar zaure, sai da ya kare ma Deedo kallo tsab, sannan ya sa kai ya wuce abin shi. Shehu ne ya rugo daga daki da sabbin kaya jikin shi, sai da yasa kafa ya hanbari Deedo sannan yabi Nawap har kofar gida yana cewa "Allah ya kiyaye hanya" Nawap wanda yake jin haushin su shi da uwar su, ko kallon shi bai ba, ya shige motar shi ya tada. BA’A SHAN ZUMA… 30, 31& 32 NA LUBABATU MAITAFSIR & BENAXIR OMAR Acikin Gida kuwa goggo takalli deedo sannan tace "kinji abunda yace!, tsintacciyar mage wacce bata gaji arziki ba, albarkacinki daya karna miki dukan tsiya kisamu illa yafasa daukanki, donhaka kije kina hutawa," takamo kunnenta sannan tace "saura kuma da gigin wasa kice bazakijeba, kokuma inkinje su koroki, wlh saina hallakaki" deedo dai shiru tayi, tana ganin goggo ta shige daki, itama ta mike ta shige akurkin ta, ta cire uniform dinta sannan ta fito tayi alwala ta koma ciki. Zuwan nawap gidan goggo ba karamin alkhairi bane yajawo a rayuwar kuncin da Deedo take ciki, domin kuwa tadenaa aiki,harta kai ko tsintsiya ta dauka, goggo ta fara zagin ta tana cewa zata janyo musu asaran arziki, hakan yabata daman yin karatu, hatta a makaranta sukansu sun lura da zuwa dawuri datakeyi, hally har zolayen ta takeyi, tana cewa " Allah ya yi abin, inji mafadin aure. kekuma aidole kidawo shalele, kudi saan kowa, mutuncin kowa, mu dai muna godewa Allah daya taimakemu yakawo karshen wahala duk da bauta zakijeyi" itadai Deedo ta kan rasa abin cewa, duk da tana son ta rabu da azabar goggo, amma kuma bata son bin mutumen da bata san daga ina yake ba. * **Nawap kuwa koda ya fito gidan goggo, gudu ya rinka yi sosai, har ya isa garin kaduna. Ta Alkali road ya bi, sannan ya shiga cikin Isah Kaita road, gida mai No. 55 ya danna horn mai gadin cikin uniform ya rugo da gudu ya bude mashi, bai jira komai ba ya kunna kan motar ciki. Parking yayi ya shiga gidan a gajiye, saida yayi wanka yayi sallah sannan yafito. Mahaifiyar tasa na zaune a falo yazauna yana sosa kai, kallon shi tayi, ta dan yi murmushi sannan tace "meya faru?" Ya dan gyara zama, ya dukarda kanshi kasa yace "Wlh ummi wata nasamu a wani kauye da aka taba kaini aiki, taban tausauyi sosai, yarinyar tana cikin wani hali, inason nataimaka mata, don Allah inason kawota nan, ko aiki tana dan tabawa" ummi tayi murmushi ganin cewan halin nan nashi na taimakon mutane da tausayi, bai canja ba, tace "bakomi, ai shi da' ai na kowa ne, kakawota mana" yasan daman ba zai taba samun matsala da ummin shi ba, kasancewar ita ta dora shi akan wannan kyakkaywar tarbiyya ta tausayi da jin kai. Dan haka cikin farin ciki ya wuce dinning ya ci abincin shi yayi kat, sannan ya koma side din shi dan ya dan huta.. BAYAN GAMA WAEC ND NECO….. Ranana da Deedo tagama exams dayamma tana zaune, wani murna takeyi tamkar zata shiga aljanna, ta godewa Allah sannan tanemi albarkan karatun agunsa, sallama taji saiga shehu ya rugo da gudu yana kiran goggo, da sauri tafito tana cewa "mei kuma ka samo mana yau?" Ya wangale baki yana cewa "Goggo nawabu ne yazo" Idonta ta zaro sannan tace "yana ina?" Yace"yana waje," da gudu gudu goggo ta koma tacanja zanin jikinta, ta jawo wani sabon mayafi ta buga sannan ta fito, yara ta gani sunata shigowa da carton carton da buhhuna da manyan ledoji, ta washe baki tana cewa "Nawabu sarkin kokari, baya gajiya da hidima, ku aje nan" tace da yaran, sannan dasauri goggo ta shige daki taciro wata atamfa sabuwa kal, dakin Deedo ta shiga tabata tare da cewa "ungo wannan, yi sauri kisa, yaganki fes fes abunki, kozamu samu da tsoka" ita dai ansa kawai tayi tasa ba tare da ta fahimci abinda goggo ke nufi ba. Da sallama ya shigo cikin gidan, goggo na jin shi tayi saurin fita suka gaysa, sai a sannan Deedo ta fahimci abinda ke faruwa, Dam taji gaban ta ya fadi lokacin data jiyo shi yana cewa yazo tafiya da ita ne. Goggota gyara zaman mayafin ta, tace "Ah itakam dasauki ai, kaga kuma yau tagama jarabawa sai farin ciki take" bai ce komai ba, dan bai yadda da goggo ba, burin shi dai yaga Deedo sannan ya tabbatar da abinda take fada, jin da tayi yayi shiru yasa ta kwala mata kira, Deedo ta fito jiki ba kwari, fuskan ta ba yabo ba fallasa, gashi kuma ta dan yi kumari, ga wani dan haske da tayi abin ta. Juyawa yayi ya kalla goggo, sannan yace "ai babu wata matsala ko?" Goggo ta wangale baki, tace "babu komai Nawabu, tafiya kawai ya rage muku" yasa hannun shi aljihu ya fito da kudi masu yawa ya mika mata, sannan ya mike tsaye yace "idan ta gama ta same ni a mota" yasa kai ya fice kofar gidan Goggo na ganin fitar shi, ta kwashe kudin da ya bata, ta kama bakin zanin ta ta daure su tam, sannan ta juyo inda Deedo take tsugunne bata da niyyar tashi. Kunnen ta ta damka, tayi daki da ita, tace "kinsan Allah, idan kika yi abinda mutumen nan yasa yace ya fasa tafiya dake, sai dai uwar ki ta dawo daga lahira ta haifa wata, dan wlh sai na hallaka ki, shegia wadda bata gaji arziki ba" ta wurga ta, ta ce "maza hada inaki inaki ki wuce ku tafi, kuma ko da ganin gida kar ki sake ki dawo mun nan" Deedo ta dan matse kwalla, ta shiga tattara yan kayan ta, ta daure a dankwali, ta matse a hammata, sannan ta fito. Shehu da goggo suna kofan dakin suna jiran ta, Hadiza kuwa tunda Nawap ya fita ta bi bayan shi tana karairaya wai ita dole don ya ganta ya kyasa, wanda shi bai ma taba tunanin Allah yayi halittan ta ba a wurin. Shehu ya buga ihu yace "yau zamu yar da dajar mangwaro mu huta da kuda" goggo tace "kai dai bari mana kar ya jiyo ka" haka suka tasa keyar Deedo gaba suna binta a baya, shehu har dan jawo mata kullin kayan ta yake yana cewa "tsintacciyar mage bata mage" sai ya kyalkyale da daria, a haka har suka iso gaban motar. Deedo ta bude gidan baya ta shiga, goggo kuma ta koma ta side din Nawap tana cewa "Allah ya tsare Nawabu, sai na ji sako na" wani kallo mai tattare da tsana ya watsa mata, sannan a zuciyan shi yace "zaki ga sako ganin idon ki" a fili kuma ya dan daga mata kai, alaman sai ta ji shi din, sannan yai ma motar key suka dau hanya. Suna fitowa layin gidan goggo, Deedo dake matse yan kwalla daga bayan mota, tace "dan Allah ina son in yima hally sallama" ba tare da ya kalle ta ba yace "ina me gidan?" Kwanar ta gwada mashi ya shiga, suka so har kofar gidan, sannan ta fita ta shige gidan su hally. Ta gaishe da maman su, sannan ta wuce dakin hally, ta same ta zaune ta gama sallan la'asar, ta zauna a gefen gado tace "nazo yi maki sallama ne, yanzu zan tafi" hally ta mike suka rungume juna suna dan kuka, a haka suka fito har bakin motan, suka yi sallama, tare da alkawarin baza su taba manta juna ba har abada. Tana shiga ko, ya ja motan sai garin kaduna.. BA’A SHAN ZUMA… 33, 34 & 35 NA LUBABATU MAITAFSIR & BENAXIR OMAR Gudu ya cigaba da yi, babu wanda ya ke ma wani magana, Deedo dai adduo'in matafiya take ta faman nanatawa cikin zuciyar ta. Shirun ya ji yayi yawa dan haka ya danna Suratul Room cikin qira'ar Sheikh Ahmad Sulaiman, ita kuma ta tattara hankalin ta baki daya, banda kallon titi ba abinda take yi, dan yau ne rana ta farko data fara barin kauyen Ningi. A sannu a hankali har suka shigo garin kaduna, Deedo idon ta kyar, ko alamar bacci babu, gashi lokacin kusan karfe 8 na dare, idanuwa ta baje ta fara kallon street light da yawan hold up, da kyawawan motocin da suke ta rafsa uban gudu a manyan titinan garin. Wani dadi taji ya ratsa mata zuciya, a hankali kuma ta fara samun natsuwa, dan tunda suka taho hankalin ta a tashe yake, hamdala ta yima Allah, sannan cikin zuciyar ta tace "ko bakomai ganin wannan kyawawan abubuwan ma wani abu ne a rayuwa" daga karshe tayi addu'ar Allah ya sada ta da dangin mahaifiyar ta, tunda dai ta san a garin nan suke. A haka taga sun shigo wata hadaddiyar unguwa wadda babu kowa sai kukan karnuka da yan tsiraran motoci da suke wucewa jefi jefi. A bakin wani makeken gida taga yayi horn, mai gadin ya fito da sauri ya bude tafkeken gate din, Nawap kuma ya tura kan motar shi hankali kwance. Ido ta cigaba da zarawa tana kallon flowers din da suka kayatar da tsararren ginin gidan. Wuri ya samu kusa da wasu jerin motoci ya parka, sannan yace mata ta fito suje ciki. Haka ta fito tana ta kalle kalle, yana gaba tana bin shi a baya, har suka iso kofar palon, ya tura kanshi da sallamar shi, babu kowa sai karan T.V an kunno tashar BBC WORLD. Deedo ma bata yi kasa a gwiwa ba ta biyo shi a baya ta shigo, sanyin A.C ne ya dake ta, sannan ta taka wani lafiyayyen carpet mai asalin taushi, gefe guda ta samu ta rakube ta zuba ma screen din tafkekiyar LED plasma idanuwan ta, yayin da shi kuma ya haura sama, ba tare da ta san abinda zai yi ba… * **Wata kyakkawar dattijuwa mai cikar kamala da kwarjini, ta gani tana saukowa a hankali daga stairs din yayin da shi kuma yake biye da ita a baya. Ido Deedo ta tsura masu, ganin asalin kamar da suke ne ya tabbatar mata da cewa matar jinin shi ce. A tare suka zauna a kujerun da suka yima palon ado, sannan matar ta gyara muryar ta, tace "ta so ki dawo nan mana yan mata" a hankali deedo ta mike, tana matse da dan kullin ta kamar wani zai kwace mata ta karasa tsakiyar palon ta zauna kasan carpet, ta dago domin ta gaishe da matar sai taga ashe tun da ta taso idon matar a kanta yake! Nuna ta matar ta fara yi da hannun ta, kamar zata ce wani abu, sai kuma ta fasa tace "ki saki jikin ki, kinji" ta dukar da kanta, ta gaishe ta, ita kuma ta ansa cikin fara'a da jin dadi, sannan kuma a hankali ta fara tambayar ta labarin ta, dana garin su da labarin karatun ta, da duk wani abu da ya shafi rayuwar ta. Hankali kwance Deedo ta rattaba mata tarihin ta, dana goggon ta, da irin rayuwar kaskancin da ta yi a kauyen Ningi! Dam gaban ummi ya fadi, mikewa tayi ta karasa gaban Deedo ta mikar da ita tsaye, kallon ta take kamar ta samu T.V daga bisani kuma ta rungume ta, wasu kwalla masu zafi suka gangaro mata, Deedo da bata fahimci komai ba, ta fara zara idanu, Nawap ma da yake gefe a zaune mikewa yayi, yazo gaban su yana cewa "ummi lafia?" Kuka sosai ummi ke yi, tace "Nawap ita ce wlh, yarinyar da nake kwana da tunanin ta nake tashi da shi a ko wace rana" tasa hannu ta kara rungume Deedo, tace "Firdausi dama kina raye? Ashe da rabon zamu gana dake" Nawap yace "ummi ban fahimce ki ba fa" sakin Deedo ta yi, sannan ta kamo hannun ta suka zauna a kan 3 seater, ta juya tana facing Nawap, tace "ita ce yarinyar da kanwa ta Rukayya ta rasu ta bari, wadda har naje dauko ta amma goggon ta ta hana, ashe dama don ta azabtar da marainiyar Allah ne" ta karasa maganar tana matse kwalla, Nawap kan shi sai da kafafun shi suka kasa daukan shi, karasawa yayi ya zauna sannan ya fara tunanin ashe dama yarinyar nan jinin shi ce, no wonder ya ji tausayin da yake mata ya banbanta da na sauran mutanen da yake taimakawa, Allah mai iko! Shine kawai abinda Nawap ya iya fada a bayyane.. * *Ummi ta kama hannun Deedo ta rike gam, kallon ta take tamkar marigayiyar yar uwar ta Rukayya, yarinya tubarkallah amma wahala ta kashe ta, cikin zuciyan ta take cewa zan kula dake Deedo, in maki gatan da banyi ma diyar dana Haifa ba, zan mayar da ke abin kwatance, in inganta rayuwar ki, sannan in tallafa maki har sai kin cika burin ki na zama kwararriyar likita. Deedo banda kuka babu abinda take yi, yau itace ta samu matar da ke consoling din ta, har ta yarda ta zauna kusa da ita! Ashe dangi ma wata rahama ce a rayuwar dan adam, Nawap ya katse su ta hanyar saukar da ajiyar zuciya, sannan yace "well, faduwa tazo dai dai da zama kenan, tunda dai yau ga diyar ki ta dawo hannun ki ai shikenan, ita kuma goggo akwai Allah, zai yi ma Deedo sakayya" ya mike, ya kara da cewar "bara na shiga ciki, ko sallan maghriba ba mu yi ba" ummi kai kawai ta daga mashi, dan yau wani farin ciki take ji, gata ga diyar ta. Kallon ta tayi, sannan tace "da izinin Allah, wahalar ki tazo karshe Deedo, ki saki jikin ki, dan baki da mahaifiyar da ta wuce ni, idan kin kwana biyu kin huta, zan kaiki kiga dangi su ma su ganki, zan baki duk wani farin ciki wanda ya kamata uwa ta bai wa diyar ta, kinji? Tashi muje in kaiki dakin ki, kiyi wanka kiyi sallah, sannan ki sauko muci abinci" dagowa tayi da jajayen idanun ta, tace "nagode ma Allah da ya nuna mun wannan rana a rayuwa ta, nagode ma Yaa Nawap wanda yayi silar sada ni da ku ummi, Allah ya yi maku sakayya da mafificin alkairi" hannu ummi tasa ta rufe bakin ta, tace "kyautata maki ya zama dole a gare mu, saboda mune dolen ki a rayuwar nan, kar na kara ganin hawaye a idanun nan kina jina?" Ta daga mata kai, sannan ta mike ta dauko kullin kayan ta, ummi na gaba tana binta a baya har suka haye sama, dakin da ke opposit na ummin ta bude mata, anyi painting dakin da pink nd purple, yayin da komai da yake cikin dakin ma pink nd purple ne, baki Deedo ta sake tana kallon haduwar wurin, hannun ta ummi ta ja ta gwada mata komai, haka ma toilet ta gwada mata, da yadda za tayi amfani da komai, ta dauko towel mai mugun taushi ta bata, tace ta daura ta shiga tayi wanka. Yayin da ita kuma ta juya ta fita, ta rufe mata kofan dakin. A bakin gado Deedo ta zauna tana kare ma dakin kallo, bata taba tunanin akwai irin jin dadin nan a wannan duniyar ba, hawaye suka yayyafo mata, tasa hannu ta share, sannan ta mike ta cire kayan ta, ta daura towel din ta shige wanka… BA’A SHAN ZUMA… 36, 37 & 38 NA LUBABATU MAITAFSIR & BENAXIR OMAR Tana shiga wankan takurawa bandakin kallo shima kansa wani duniya aka zuba, tadauko shampoo da sabulu ta ajiye akasa tazauna dirsham akan tiles din don yanda taganshi tsaftsaf tasan zata iyacin abinci aciki, takaranta jiki sannan tadauko soso tanufi cikin shower, murdawa taringayi harya kunnu taji ruwan sanyi dasauri takashe, takara kunna dayan saitaji ruwan zafi, murmishi yafito mata, tasanya tafara wanka, tafi awa biyu tana dirje jikinta, kafin ta wanke kanta ma, duk da Allah ya hore mata gashinta daidai gwargwado baya samun gyra, tafito tana goge kanta, itakanta wani iska takeji yana buso mata, tazauna gaban dressing mirror. Shafa wancan mulka wancan, dakarshe tashafa powder sannan ta leka wardrobe taga kaya azube , lalle yanzu duk wannan kayan ita zatasa?, set 4 takedashi a kauye, nan kuwa tanaga yafi dari, ga gun gyale daban, hijab daban, atamfa daban less da shadda ma haka, gefe kuma dogayen rigunane a tsaye. Taciro riga daya, ta maida ta rufe, sannan ta bude ta kasa nan taga inners, ta ciro shima tasaka sannan tadaure kanta ta tattara kayan da ta cire, ta zuba su aciki sannan tadauki sallaya tabiya sallahn dake kanta, tana nannadewa wata ta shigo tana murmushi daga gani saar Deedo ce, tace "inji ummi kisauko abincinki is ready" itama murmushin tayi sannan tabita suka sauka, Nawap na zaune yana mikawa cikinsa abinci takaraso, itama zama tayi sannan tafara kallon coolers din gabanta, Nawap yayi murmushi sannan ya kwala kiran saude, wacce takirata a sama sannan yace "zo ki diba mata abincin ko" ta amsa da "toh" Nan tafara zuba mata, ferfesun kayan cikin, agefe kuma jollof din shinkafa ne yaji busheshen kifi, tun tana kunyan ci anma tazage taci abunta, Nawap kuwa ganin zai takura mata yasa yamike yabar mata gun, itakuwa taci tayi nak, sunadan tadi sama sama da saude wacce take kimtsa gun, suna gamawa tai masu saida safe, ta haye sama, saboda wani bacci da yake figan ta. Haka Deedo ta kwana cikin farin ciki da jin dadin sauyin rayuwan data samu cikin dan kankanin lokaci. Da safe bayan ta tashi tayi wanka ta shirya tsab cikin wata royal blue din abaya, palon ta sauko domin taimaka ma Saude da aiyukan gida, amma abin mamaki har ta gama komai ta jera abinci a dining, suna cikin magana Ummi ce tashigo palon fuskarta kaman gonan auduga, Deedo ta karasa gaban ta da sauri, ta duka har kasa ta gaisheta. Cikin jin dadi ta ansa, sannan tace "Masha Allah, kinga yadda kikayi kuwa?, kuyi ku gama cin abincin nan na aike ku da Nawap ko kema zakiga gari," Jikinta narawa tamike don yanzu gani take kamar a aljanna take, Allah sa dai ba mafarki takeyi ba balle ta tashi, da sauri ta tuttura abincin, sannan ta koma sama, gyalen abayan ta dauko sannan ta fito, yana jingine ajikin mota, yasha brown shadda da hular zanna, kullum kwarjini yake kara mata, ta isa gareshi sannan tashiga. A hankali ta gaishe da shi, ya ansa ba tare da ya kalla inda take ba, ya cigaba da tukin shi har suka bar unguwan. Ido ta ware sosai ganin yadda mutane ke shawaginsu ba ruwan wani da wani, babban abinda ke kara sanya ta nishadi shine yadda take ganin kyawawan motoci suna rafsa gudu a titi hankali kwance. Ta cikin Malali suka shiga, sannan suka bi wani layi inda taga an rubuta Raba Road, ita dai bin ko ina take da kallo, ba tare da wata damuwa ba. Ba suyi wata tafiya mai nisa ba taga sun kawo gaban wata katuwar supermarket, wuri ya samu yayi parking mai kyau, sannan ya juyo yace mata "muje ko?" Fitowa tayi har tana dan tuntube, ta daga kanta sama wani tafkeken sign board ta gani mai dauke da manyan haruffa, an sa STOP AND SHOP! Jinjina kanta tayi, ganin haduwar wurin, ba tare da bata lokaci ba Nawap ya ja basket suka wuce ciki. Shopping ya cigaba da yi ba tare da ya bi ta kanta ba, kuma most of abubuwan da yake kwasa duk na mata ne, dangin cosmetics, native wears, handbags, takalma, jewelries da dai sauran su, sai da ya cika basket din dam, sannan ya tura zuwa inda zaiyi payment, ya biya kudin aka kwashi kayan aka sanya a boot din shi, sannan suka shige suka dau hanya. A tunanin ta hanyar da suka bi zasu koma, amma sai taga ya dau wata sabuwar hanyar. Emirate plaza ya nufa, inda ya shige ciki kai tsaye; sannan yayi parking a wurin da aka tanadarwa motoci. Ya fito yana bada fadi, a tunanin shi tana biye dashi, amma sai da ya juyo ya ganta zaune cikin motan sai kalle kalle take. Girgiza kan shi yayi, ya kara gaba inda ya shige wani katon shop mai kofa hudu, kuma babu komai a ciki dai zallan electronics. Gefen wayoyi yayi, inda ya zabo mata Samsung Galaxy s3, ya karasa ya biya kudin, sannan ya fito, yadda ya hango ta kura ma wasu kyawawan yan mata da suke ta kilbibi ido, sai abin ya bashi daria, inda cikin zuciyan shi yake cewa "kema very soon zaki zama abin kallo Deedo" da sauri ya karasa ya shige motan, yana shirin tadawa ne wayan shi dake aje a tsakanin seat din shi da na Deedo tayi ringing, ita ta dawo da Deedo daga duniyar da take, inda a tare suka kai kallon su kan screen din wayar… BA’A SHAN ZUMA… 39, 40 & 41 NA LUBABATU MAITAFSIR & BENAXIR OMAR Aysha shine sunan dake rubuce a saman screen din, sai da ya ja dan siririn tsaki, sannan ya maida hankalinshi ga tukinshi. Reverse yayi, ya fita daga wurin, yayin da wayar ta cigaba da rera waka alamar kira yana kara shigowa. Deedo ganin bashi da niyyar dauka, tace "Yaa Nawap ana kiran ka" cikin halin ko in kula yace "ina ji ai" ganin bai damu da kiran ba yasa itama ta juya ta cigaba da kalle kallen ta har suka iso gida. Direct ya shige yayi parking kanshi tsaye, a gefe suka ga wata sabuwar Audi V10 baka, ba tare da tunanin komai ba ya fito, ya bude boot din ya cigaba da ciro kayan da suka siyo, yayin da Saude wadda ta fito tun lokacin da taji shigowa su ta cigaba da kwasa tana kaiwa ciki. Sauran da suka rage Deedo ta kwasa ta yi gaba yana binta a baya, da sallama suka shiga palon, inda suka tarar da Ummi da wata bakuwa a zaune. Sai da Deedo ta gaishe da su, sannan ta haye upstairs da kayan hannunta. Karasawa Nawap yayi ya zube a kujera yana kiran wash. Ummi tace "ya dai? Ko ka gaji ne?" Yace "Wlh yarinyar ki din can ta bani wahala Ummi" Ummi ta murmusa, sannan ta kara da "Ai sai hakuri dama, tunda dai ka riga ka zama babban yaya" ba tare da yace komai ba ya mike da niyyar barin palon, Ummi ta dakatar dashi ta hanyar cewa "wai baka kula da bakuwar mu bane?" Sai a sannan ya kai duban shi ga kyakkaywar budurwar da ke zaune, wadda tunda ya shigo ta tattara duk wata natsuwa, tare da hankalin ta, ta mika mashi. A kasalance ya juyo ya kare mata kallo, sannan ya shafi sumar shi mai tarin yawa, yace "Yaushe a gari?" Wani lallausan murmushi ta saki, sannan tace "inji maki' bako kenan" cikin halin ko in kula, yace "sorry naga call dinki, I was driving" ta gyara zaman ta, tace "no p" a dai dai nan, ta ja handbag dinta, sannan tayi ma Ummi sallama, ta mike da niyyar barin palon. Ita ma Ummi mikewa tayi, ta nufin wurin Deedo wadda hankalin ta ke wurin ta tunda suka shigo gidan. Shima juyawa yayi, ya bi hanyar da zata sada shi da part din shi, ba tare da ya kara bi ta kanta ba. Aysha ta juya ta bi bayanshi da kallo, tace "Nawap" Ya juyo hankali kwance, yana mata kallon fadi matsalarki.. Ta gyara tsayunwanta, tace "amma kasan saboda kai nazo gidan nan ko?" "Ban fahimce ki ba" ya fada, sannan ya jingine da bango ya nade hannayen shi yana kallonta. Takowa tayi a hankali zuwa gaban shi; tace "har yaushe ne ranar da zaka fahimci yadda zuciyata ke tafarfasa saboda sonka? Nawap yaushe ne ranar da zan samu farin ciki daga gare ka? Shin wai mei yasa baka tausaya ma zuciyar da ta dade tana azabtuwa da so da kaunarka ba? Plz Nawap kaji tausayi na mana" ta karasa maganar tana mai marairaice fuska kaman zata yi kuka. Kayataccen murmushinsa ya saki, sannan yace "look Aysha, ya kamata ace maganar nan ta wuce tsakanin mu, ya kamata ace a matsayin ki na mace kinyi facing reality yanzu, ki gane abinda kike so ba zai taba kasancewa tsakanin mu ba, in fact, kiyi hakuri ki bama masoyanki dama har a cikin su Allah yasa ki samu wanda zai kwanta maki, I'm sorry" yana gama fadin haka ya juya, ya cigaba da tafiyar shi.. Hawaye ne kawai Aysha bata yi ba, sai kukan zuci da take ta faman yi, zuciyanta yayi baki, ta rasa menene yake mata dadi. Juyawa tayi zata fita, a dai dai lokacin Deedo ta sauko daga sama, kujeran da Aysha ta tashi Deedo ta kaiwa kallo, nan taga iPhone6 dinta a yashe, da alama ta manta da ita ne, dan haka tayi saurin karasawa ta dauka wayan, sannan ta bi bayanta… Har ta shiga motan ta zauna, ta hada kanta da steering, wani irin zugi take ji a zuciyanta. Deedo ta karasa tayi knocking glass din, ta dago ta kare mata kallo, sannan ta zuge glass din ta watsa mata kallon raini, tace "ya akayi ne?" wayan Deedo ta mika mata, sannan tace "kin manta wayan ki ne" fisgan wayan tayi, sannan ta maida glass dinta ta zuge, ta fara kokarin tada motan. Ita kam Deedo da bata fahimci halin da take ciki ba, ta juya ta shige ciki abinta. WACECE AYSHA? Aysha Sabe Musa, 'ya kwaya daya tal a wurin iyayenta wanda suka kasance yan asalin garin Katsina, amma yanayin aiki ya dawo dasu garin kaduna da zama. Suna zaune a Galadima road inda ya kasance basu da nisa tsakanin su da su Nawap. Sunyi karatu tare da kanwar shi Hafsat a A.B.U zaria, inda daga bisani ta wuce Jordan inda ta kammala masters dinta, ta dawo gida yanzu. A kalla Aysha tayi shekara biyar tana dakon soyayyar Nawap, wanda son da take mashi ne ya kara kusancinsu da Hafsat har zuwa lokacin da tayi aure, amma saboda shi ta kan wanke kafa taje gidan su duk don ta ganshi, sai ta fake da cewar taje gaishe da Ummi ne. Sai dai tayi rashin sa'a, har inda yau take, Aysha bata samu karbuwa ba a zuciyar Nawap, asali ma bata jerin matan da Nawap zai iya so a rayuwanshi! BA’A SHAN ZUMA… 42, 43 & 44 NA LUBABATU MAITAFSIR & BENAXIR OMAR Cigaban Labari Cikin gida Deedo ta koma inda ta tarar da Saude tana jera abinci a dinning, taimaka mata tayi har suka gama, sannan ta wuce tayi sallah, ta gama ta shiga dakin Ummi ta sameta zaune saman sallaya, gefe guda ta samu ta zauna har ta gama, sannan ta juyo da murmushin ta, tace "auta ta ya aka yi ne?" Ta murmusa tace "lafia lau Ummi, abinci ne ya zama ready" ta kara fadada murmushinta, tace "kuma autar Ummi na jin yunwa ko?" Ta dukar da kanta tana 'yar daria, sannan tace "a'a nazo na fada maki ne kawai" daria Ummi tayi, tace "to tashi muje kasan" a tare suka mike, inda Deedo ta tattara hijab da sallayan da Ummi ta gama sallah ta ninke, ta mayar da su wurin su, sannan ta bi bayan ta suka sauka kasan. Nawap suka gani zaune da jallabiya a dinning area yana ta kwasan girki ba ji ba gani, Ummi ce tayi gyaran murya, sai a sannan ya lura da zuwan su. Daria suka sanya shi da Ummin, inda ita kuma Deedo ta dukar da kanta tana tata dariyar a boye. Karasawa sukai suka zauna, Ummi ce ta umarci Deedo da tayi serving dinsu, dan ta lura akwai abubuwa da dama da ya kamata ace Deedon ta iya, dan haka ma ta kalleta, ta kara da cewar "yau fa da girkinki zamu yi dinner, dan haka sai ki shirya" murmushi tayi, yayin da ta cigaba da zuba abincin, tace "to shikenan Ummi" Kallon ta Ummi ta cigaba da yi, tana mai tunano 'yaruwarta, wani so da tausayin yarinyar taji ya kara tsirga zuciyarta, wasu yan kwalla suka feso mata, inda tasa hannu ta share ba tare da ta bari sun lura da ita ba. Kallonta, ta mayar kan Nawap wanda ya tada plate din fried couscous yana korawa da kunun aya mai gardi, tace "wai kai yaushe zaka koma office ne? Ko har yanzu hutun bai kare ba?" Yayi gyatsa tare da hamdala, sannan ya dan shafi sumarshi yace "Jibi zan wuce in sha Allah" tace "ai gara kazo ka tafi dan ka kusa cinye mana abincin gida" yace "kin dai gaji da ni tunda kin samu diya yanzu" tace "har ma da hakan" yace "yawwa yanzu naji batu Ummi" haka suka cigaba da firan su cikin jin dadi, Deedo da bata cika saka baki a firan ba, sai dai tayi dan murmushi kawai. Jin ta take a wata duniya ta daban, yay ita ce ta samu 'yanci. Hamdala tayi sannan ta yima Allah godia da ya nuna mata wannan kyakkaywar rana… A tare suka mike bayan sun kammala con abincin, inda Deedo ta tattara wurin ta kimtsa komai, sannan ta wuce da kwanukan kitchen. Tana kokarin shigowa palon taji Ummi na cewa "yanzu Nawap kana ganin rayuwa zata yi a haka? Ka tuna kai fa ba yaro bane, ya kamata ace yanzu ka aje iyali fa, kuma ni ita yarinyar can Aysha ban ga abinda ta rasa ba da baza ka so ta ba, ko dai kana da wata matsala ne?" A hankali ya fara magana, "wlh bata da komai Ummi, kawai dai ba zan iya rayuwa tare da ita bane, amma kar ki damu in sha Allah zan nemo mata in dai hakan zai faranta maki rai" tace "shikenan, Allah ya taimaka" ya ansa da amen, sannan ya mike ya bar palon. Karasawa Deedo tayi, ta zauna a kasan carpet tana dan matsa kafan Ummi. Kanta Ummi ta dafa tace "auta ya akayi ne?" "Lafia lau" ta fada tana dan murmushi, ita ma Ummi murmushin tayi, tace "gobe dai in sha Allah zamu je kiga danginki, kiga yar tsohuwar kakarki da kowa da kowa" dadi ne ya ratsa ta, ta rasa abinda zata ce ma Ummi, nan da nan hawaye suka fara bin fuskarta, a hankali ta fara magana "Ummi kinyi mun komai a rayuwa, kin mayar da ni mutum a lokacin da kowa ya ke kyamata, bani da bakin yi maki godia, sai dai ina addu'ar Allah yayi maki sakayya da mafificin alkairi, ya sa ki gama da dunia lafia" Nan take itama Ummi hawayen suka gangaro mata, mikar da ita tayi ta rungume ta sosai, tana shafa bayanta alaman rarrashi. A sannu a hankali ta daina kukan, mikewa duk suka yi zuwa sama domin gabatar da sallan la'asar. Suna gamawa suka wuce kitchen, inda Ummi tare da Saude suka cigaba da taimaka ma Deedo har ta gane yadda zata yi amfani da abubuwan kitchen din, cikin raha da annashuwa suka gama komai suka jera a dinning, sannan suka wuce domin bada farali.. Misalin karfe sha daya na safe Deedo ta fito daure da towel a jikinta, a hannunta dan karamin towel ne tana tsane yalwataccen gashinta. Gaban mirror ta zauna, ta shafa mai tare da Dan simple makeup. Ta gyara gashinta sannan ta mike zuwa wardrobe domin ta samu kayan sakawa. Daya bayan daya take bin lodin kayan da kallo har ta rasa wanne zata saka a ciki. A karshe ta jawo wata super peach nd coffee brown dinkin skirt and blouse ta saka, ta buda kallabin tayi mashi wani mugun dauri kamar ta kifa turmi. Kallon kanta tayi a mirrorn dake jikin wardrobe din taga kaman ba ita ba, a fili ta furta "lallai sutura ita ce mutum" murmushi tayi, sannan ta jawo bakin gyale ta buga abinta. Wurin takalma ta matsa taga duk high hill ne, ita kam ta san ko za a sa mata wuka ba zata iya tafia da su ba. Wani maroon ta gani shine mai dan tudu kuma bai cika tsawo ba dan haka ta jawo abinta, ta dora ta sauka zuwa palo inda Ummi ke jiranta. Nawap ne ya fara kallonta, daria taso kwace mashi, amma ya fuske yace "Ummi ga fa autar ki ta faso" Juyawa Ummi tayi ta kare mata kallo, gata dai tubarkallah, kaya sun ansheta sai dai wani bahagon daurin kallabi da tayi da kuma color riot din da ta buga. Murmushi tayi sannan ta mike tace "eyyeh! Lallai auta ta tayi kyau, sai dai matsala daya" taja hannun ta suka koma sama. Wardrobe din ta bude ta dauko mata peach din gyale, ta bata peach din takalmi, sannan ta dauko mata handbag coffee brown, ta zaunar da ita ta gyara mata daurin kallabin sannan tace "tashi ki gan ki" mikewa tayi ta kare ma kanta kallo, lallai gyara shine mace, ta dan rufe fuskanta alaman kunya, Ummi tace "tashi muje kar muyi rana" ta mike ta bi bayanta, a hankali take takawa kasancewar bata iya tafia da high hill ba, amma abin sai ya bada wani style na daban… Dagowan da Nawap zaiyi, tsab suka hada ido, da sauri ta dukar da kanta, inda shi kuma ya kasa dauke idonshi a kanta, Tubarakallah Masha Allah ya dinga furtawa a zuciyanshi, lallai yarinyar mai kyau ce. Ummi ce ta katseshi da cewa "muje mana" cikin jin kunya ya dan sosa kai, sannan ya mike suka wuce, amma hankalin shi kaf yana gun yadda Deedo ke takawa a kasaitance.. BA’A SHAN ZUMA… 45&46 NA LUBABATU MAITAFSIR & BENAXIR OMAR Da dan sauri ya karasa wurin ajiyar motocin, inda ya darzo wata dark blue din Audi R8, reverse yayi, sannan ya gyara tsayuwar motar, inda su kuma a lokaci daya suka bude suka shiga. Deedo ce a gaba, yayin da Ummi ta kame a owner's corner. Wuta ya ba motar, sannan suka lula saman titi hankali kwance. Tafiya suka yi mai dan nisa, Deedo har ta fara tunanin ko garin zasu bari. Daga karshe dai ta ware idanunta ta cigaba da yan kalle kalle, cikin hikima Nawap ke satar kallonta yana ganin yadda farin ciki ke bayyane a fuskanta, yanayinta kawai, zai sanar da kai cewar bata da sauran damuwa. Murmushi ya saki wanda bai san lokacin da ya sufce mashi ba, a haka suka iso main house din su Ummi da yake Hayin Banki. Ba tare da bata lokaci ba ya samu wuri yayi parking, sannan duk suka fito suka shige ciki. Zaune suka tarar da mai gidan a cikin wata yar baranda, idon shi sanye da medical glass yana duba jaridar Daily Trust. Inda yake zaune suka karasa duk suka kwashi gaisuwa, sannan suka mike gaba dayansu zuwa cikin gidan. Kallon Deedo yake kaman ya taba sanin mai irin fuskarta, sai dai bai ce komai ba har suka shige ciki. Ita ma tunda suka shiga take kallon dattijon mai cikar kamala da kwarjini, kamar shi sosai ta gani da Nawap, sai dai yanayin tsufa kawai da yake tattare dashi. A palon suka samu Inna zaune da yar casbaharta tana lazumi. Kallo daya tai wa Deedo taji gabanta ya fadi, a take kuma ta yardar wa kanta cewar duk yadda akai wannan yarinyar jininta ce. A daddafe suka gaisa, yau ko tsokanar da ta saba yiwa Nawap ba ta mai ba, cikin zakuwa ta kalli Ummi tace "ke kam ina kika samo mai kama da ke?" Murmushi Ummi tayi, ba tare da bata lokaci ba kuma ta warware masu komai dangane da Deedo, ta kara da cewar "amma yanzu ta dawo nan da zama kenan in sha Allah" Salati Inna ta kwasa, sannan ta saki kuka, tana cewa "yaki nan Firdausi, ashe dama kina wannan duniyar?" Matsawa Deedo tayi, suka rungume juna, inda Malam ya kallesu fuskarshi dauke da murmushin dattako yace "to ke banda abinki wannan ai abun farin ciki ne, menene abun kukan?" Nawap kallon Inna yake yana daria, Ummi kam itama sai da ta dan matse kwalla, nan fa wuri ya kaure da murna, yan tsofaffin sai nan nan suke da Deedo, gani suke kaman Rukayyar su ce ta dawo. Hamdala suka yi, suka yima Allah godia da ya dawo da yarinyar cikin danginta. Itama Deedo taga gata, banda hamdala babu abinda take yi. Godia tayi ma Allah daya sada ta da dangin mahaifiyar ta, jinta take tamkar yau ce ranar da aka haifeta.. Nawap tsintar kanshi yayi a yanayi na mugun farin ciki, ganin Deedo cikin walwala da jin dadin rayuwa. Sai da suka yi sallan azahar sannan suka yi haramar tafia, daga nan ma gidajen kannen Ummi suka je, duk wani dangi na nesa da na kusa babu inda basu kai Deedo ba, a nan ta tabbatar ma kanta lallai ita mai gata ce, sannan ta kara tantancewa dan uwa rahma ne, ko ba komai wannan soyayyar da zai nuna maka ma wani abu ce a rayuwa. Wurin karfe shidda na yamma, sannan suka dau hanyar gida, a nan Ummi ke ce ma Nawap "ya kamata ace Deedo tayi jamb fa, don bana so ta bata lokaci, so nake da result din su ya fito ta wuce makaranta" Sai da ya saci kallon Deedo wadda tsananin farin cikin da take ciki yasa sai faman murmushi take, murmushin yayi shima, sannan yace "nima nayi wannan tunanin sai dai kaman an gama jamb yanzu fa" Ummi tace "ba naga sun bullo da wani sabon system na computer base ba?" Yace "haka ne, zan bincika gobe kafin na wuce in sha Allah" ta ansa da "amen" inda a dai dai lokacin kuma suka kawo gida. The next day kamar yadda Nawap yayi alkawari haka ya gudanar da duk wani bincike, inda bai bar Kaduna ba sai da ya tabbatar ya gama mata duk wani abu da ya kamata. Misalin karfe biyu na rana suka dawo gida, wanka kawai yayi, yayi sallah ya ci abinci, sannan ya dau hanyar Abuja, yana mai cike da tunani da maraicin Deedo da Umminshi.. ***** Haka rayuwa ta cigaba da tafiyan ma Deedo cikin jin dadi da walwala, weather garin ta anshe ta sosai, tayi fresh tayi das das abinta, gashi Ummi tana kokarin koya mata abubuwa, in ka ganta baza ka taba gane ta ba, balle har kayi zaton ita ce Deedon Goggo ta kauyen Ningi.. BA’A SHAN ZUMA… 47,48,49 &50 NA LUBABATU MAITAFSIR & BENAXIR OMAR Ranan wata Juma'a da misalin karfe biyar da rabi na yamma Deedo ta fara takowa a hankali zuwa babban palon gidan, sanye take da wani blue skinny jeans, tare da wata armless tshirt yellow mai dan fadi, an rubuta LISTEN TO YOUR MUSIC & SONGS. kunnenta makale da earpiece, ta tattara yalwataccen gashinta tayi parking dinshi a tsakiyar kai. A hankali take bada step, tana dan latsa wayanta yayin da take saukowa zuwa kasa. Duk wanda ya kalleta sai ya kara, saboda asalin kyaun da tayi, tayi fes fes abinta, kaman irin tashin birnin nan tun asali. Karasawa tayi inda ta samu Ummi zaune, a gefenta kuma matar nan ce ta ranan nan, wadda ta tabbatar da cewar itace taji Ummi ta kira da Aysha. Karasawa tayi ta zauna a kasan carpet dai dai inda Ummi take, dagowa tayi da niyyar ta gaishe da bakuwar amma taga idonta kyam a kanta har lokacin da ta zauna. Cikin siririyar muryanta, ta kara duban Aysha tace "aunty ina wuni" Kallonta Ayshan ta kara yi, sannan ta saki wani dan murmushi yayin da tace "kina lafia?" "Lafia lau" ta bata ansa a takaice, inda ta maida hankalinta akan game dinta da take yi na candy crush. Kanta Ummi ta shafa, sannan tace "auta ya akayi ne?" Sai da ta murmusa sannan tace "lafia lau Ummi na" "Masha Allah" Ummi ta fada, inda ta maida hankalinta kan wayanta da take ringing a gefenta. Wayan ta daga da sallamarta, tace "ai mun zata laifi muka yi, yau kusan kwana ukku kenan babu kai babu labarin ka" Daga dayan gefen Nawap ya dan yi daria, sannan ya gaishe da ita, ya kara da "Ummi ai kin yaye ni yanzu tunda kinyi sabuwar 'ya" tace "to kai banda abinka, ina zan tuna da kai ina busy kula da autata" ta kara da cewar "idan ka ganta baza ka gane ta ba yanzu" cikin raha da jin dadi suka cigaba da firan su ta da' da mahaifi, inda daga karshe ya shaida mata cewar principal din su Deedo ya mashi waya cewar result din su ya fito, dan haka zuwa Monday zai je ya an so mata, daga nan zai biyo ta kadunan. Hamdala Ummi tayi, sannan tace "to Allah ya sa muga alkairi" "amen" ya fada, sannan ya kara da "a gaishe da kowa" tace "ga autata nan, bara ta gaishe ka" Ummi ta mika mata wayar, ta ansa ba don ranta ya so ba, a kunnenta ta kara wayan, tace "Yaa Nawap ina wuni" Sai da ya ja wani gauron numfashi, sannan ya ansa da "kina lafia Autan Ummi?" Tace "lafia lau, ya aiki?" Yace"Lafia, Ummi ta fada maki result dinku ya fito ko?" Tace "a'a, tana da bakuwa ne yanzu, nasan anjima zata fada man" yace "ok, zanje Ningi on monday, ko zaki je ne?" Ya fada cikin sigar wasa, murmushi ta dan yi, sannan tace "ka manta goggo tace kada na koma koda ganin gida ne?" Daria yayi sosai, sannan yace "to shikenan, zanje in ce kina gaishe da ita" tace "to shikenan, amma ina da sako dan Allah" yace "ki kira ni idan na fita office sai ki fada man" A haka suka yi sallama ta mika ma Ummi wayan, sannan ta mike tace "Ummi bara na taya Saude girki" yayin da take tafia zuwa hanyar kitchen din. Wani kallon tsana Aysha ta bita da shi, har saida ta daina ganinta sannan ta kyaleta, juyon da zata yi karaf, suka hada ido da Ummi wadda take kallon duk abinda ke faruwa. Murmushin yake tayi, sannan ta dan fara kame kame, tace "Ummi wai dama Hafsat na da sister ne?" Murmushi Ummin tayi itama, sannan tace "mai kika gani?" Tace "naji kina kiran yarinyar can da autarki, kuma ni ban taba saninta a gidan nan ba, ko ba nan take zaune bane?" Ummi ta dan muskuta, tace "owh wai Deedo kike nufi? 'Ya ta ce 'yar kanwata, amma Allah yayi wa maman nata rasuwa, shine ta dawo hannuna da zama" Wani malalacin murmushi ta saki, sannan tace "Allah sarki, Allah ya jikan musulmi" Ummi ta ansa da "amen" yayin da Aysha ta kimtsa inata inata ta kara ma bujenta iska. Tana fita gidan, wayan Nawap ta kira ya kai sau biyar amma bai ansa ko daya daga cikin calls din ba, haka ta hakura, ta shilla kan motarta saman titi, ta bata wuta.. Deedo na gama sallan maghriba, tana zaune saman sallaya taji wayanta ya fara ringing, hannu tasa ta zaro wayan, sannan ta kalla number da take kiranta, Yaa Nawap ta gani a rubuce dan haka tayi saurin dagawa ta gaishe da shi, cikin baby voice dinta mai dadin sauraro. Kwance yake saman 3seater, bai san lokacin da idonshi ya lumshe ba, a hankali ya bude su, sanna yace "ya muka yi dake? Ko kin fasa bada sakon ne?" Yadda yayi maganan duk sai ya daburtar da ita, ta fara magana tana in'ina, "ehmm, wlh, I'm sorry Yaa Nawap, na shiga kitchen ne ban dade da fitowa ba shi yasa" yadda tayi maganan ya bala'in birge shi, nan take idanuwan suka kara lumshewa, ba tare da ya bude su ba yace "idan kin gama abinda kike zaki kwanta, ki kira sai ki fada mun, sauran kuma ki kara mantawa, kiga yadda zanyi dake" Da sauri tace, "ba zan manta ba in sha Allah" ba tare da ta jira abinda zai ce ba ta kashe wayan, sannan ta mike tayi sallan isha'i wadda taji an kira a masallacin kofar gidan.. Rungume wayan yayi a kirjinshi, wani irin abu ne ke mashi yawo gaba daya jikinshi, ya rasa tantance wane irin yanayi yake ciki, a hankali fuskantan ya fara yi mashi gizo, muryanta yake ji cikin tsararren turancinta ranan da suke debate, a hankali ya hango fuskanta mai cike da damuwa a ranan da ya fara magana da ita, sannan ya hangota ranan da ta buga daurin kallabin nan mai kama da turmi, sannu a hankali kyakkaywar fuskanta tai mashi walkiya a ranan da suke dawowa daga unguwa, yanayin farin cikin da take ciki, da yanayi na gushewar duk wata damuwa da take tattare da ita, shi ya bashi damar sakin wani yalwataccen murmushi. A hankali ya furta, "Alhamdulillah Allah daka cika mani burina, Allah nagode maka daka bani damar cika alkawarin dana dauka na samowa marainiyar ka farin cikinta… " Kira ne ya shigo wayanshi, wanda yayi sanadiyyar katsewar tunaninshi. Da sauri ya jawo wayan dan a tunanin shi Deedo ce, ganin sunan Aysha a rubuce yasa gwiwoyin shi sakewa, inda ya daga wayan a kasalance. "Kina lafia?" Ya tambaya, inda daga bangarenta, ta fashe da wani irin matsanancin kuka mai tsuma zuciya. Mikewa yayi daga kishingidar da yayi, sannan ya fara tambayar "Aysha lafia? Ya akayi ne?" Tambayoyi ya dinga jera mata, amma ta ki ta bashi ansar ko daya, kuka kawai take yi kaman wadda aka fada ma sakon mutuwar uwa ko ta uba! Jin kanshi yayi ya mashi nauyi, duk da ba son Aysha yake ba amma yana jin kukanta har cikin zuciyarshi, kasancewar shi mutum mai tsananin tausayin mace, wanda ko kadan baya son yaga mace a cikin wani hali. Haske wayan ta fara yi call waiting na shigowa, dago wayan yayi daga saman kunnenshi inda yaga sunan Deedo a rubuce saman screen din… BA’A SHAN ZUMA… 51, 52 & 53 NA LUBABATU MAITAFSIR & BENAXIR OMAR Da sauri ya katse wayan Aysha, inda ya daga kiran na Deedo kai tsaye, a hankali kwance ta fara magana, inda ya nemi tunaninshi gaba daya ya rasa, jin muryanta yake har cikin bargonshi, lumshe idanuwanshi yayi inda a lokaci guda ya nemi damuwar da take tare dashi ya rasa, cikin kunnenshi ya tsinkayi muryanta tana cewa "kaji Yaa Nawap?" Firgigit, ya dawo daga duniyar da yake, yace "mei kika ce ne?" Tace "zan bada sako wurin Hally ne" "go ahead ina jinki" ya fada, ita kuma ta cigaba da cewa "kace ina gaisheta, kuma dan Allah ka bata number ta kace ta kira ni" duk a tsorace take maganan, gani take kaman zai ce ta raina shi ne, dan haka take maganan cikin wani salo na yarinta da neman afuwa. Wani numfashi ya ja, sannan yace "shikenan sakon naki?" Kai ta girgiza kaman yana kallonta, sannan ta ansa mashi da "eh shikenan, sai da safe" da sauri ta katse wayan, inda shi kuma ta barshi da tsananin tunani da muradin sauraren muryanta mai dadi. Yana cikin wannan hali wayan Ayshan ta kara shigowa, wanda dama kiran take ta faman yi tun yana cikin magana da Deedo. Daga wayan yayi, ba tare da yace komai ba, a tunaninshi kukan zata cigaba da yi, sai yaji ta buda murya tace "Nawap na gano dalilinka na wulakantani, yanzu nasan menene dalilinka na kin ansar soyayyata, abinda nake so ka gane shine, bazan taba rayuwa ba tare da kai ba, sannan kuma wata yar ficiciyar yarinya bata isa tazo ta wargaza mun plans din da na dade ina shiryawa shekara da shekaru ba Wata tsawa ya daka mata, wadda tasa ta shiga taitayinta lokaci guda, cikin wata kakkausar murya ya fara magana "who do yu think yu re? Nd where all this ur nonsense are heading to?" Kasa ansa shi tayi, inda shi kuma ya cigaba da cewar "thou, ban san ina maganan ki ya dosa ba, amma ina so ki gane ba wanda ya isa ya juya ni, ni nake da ikon kaina kuma ba wanda ya isa ya sani yin abinda ba shi nake so ba, shin wai ke yaushe ne ranar da zaki farka daga dogon mafarkin da kike yi? Yaushe ne zaki gane abinda kikeyi is so old fashion? Ya kamata ki neman ma kanki Mafita Aysha, me nd yu ain't belong to each other, plz ki barni naji da rayuwata, ki fita harka ta plz.. " Bata bari ya karasa fadar abinda yake son fada ba, ta katse shi da cewar "lallai kana da aiki Nawap, idan har kana tunanin akwai ranar da zan daina sonka, ina mai tabbatar maka da cewar na bar dunia a wannan ranan, sannan kuma duk wulakancin da kake ganin ka iya, bazan hana ka yi mun ba, amma ka sani, wannan fitsararriyar yarinyar daka baro a gida, a kanta abin zai kare, so yu better becareful.." tana gama fadin haka ta katse wayan tayi wurgi da ita, a lokaci guda kuma ta fashe da wani matsanancin kuka, ta rasa wane irin so take ma Nawap wanda ta kasa cire shi daga cikin ranta shekara kusan biyar kenan! Sai a lokacin ya gane inda maganan Aysha ya dosa, amma babban abinda ke bashi mamaki baya wuce yadda take neman kulla wata alaka ta daban tsakanin shi da Deedo, yarinyar da tausayinta yasa yake bata duk wani muhimmanci da yake bata, yarinyar da ya dauka a matsayin kanwarshi, shin wai menene dalilinta na yin wannan exaggerating din? Amsar da ya rasa inda zai samo ta, mikewa yayi jiki ba kwari ya karasa cikin bedroom, a lokaci guda ya cire jallabiyan jikinshi yaja towel ya daura sannan ya wuce bathroom… Ranan Monday da misalin karfe 5 na asuba Nawap ya mike, bayan ya dawo masallaci bai jira komai ba ya fara shiri, duk wani abu da zai bukata ya gama tattarawa. Karfe 7 dai dai ya isa office din su, anan ya samu yayi breakfast inda daga bisani ya karasa nashi office din, anan ya tadda reply na letter da yayi na son yin tafiya ta sati daya. P.A dinshi ne ya shigo ya gaishe da shi, sannan ya ke fada mashi cewar dazu aka kawo lettern daga office din director. Godia yai mashi, inda ya koma kan wata 2seater da ke aje a tsakiyan office din ya zauna. Zaro lettern yayi, ya fara dubawa, nan da nan murmushi ya bayyana a kan fuskanshi, cikin hanzari ya mike yayi kiran P.A din yai mashi bayanin duk abinda ya kamata, sannan ya tattara laptop dinshi da sauran documents din da zai bukata yai mashi sallama ya fito .. Inda yayi parking mota ya nufa, ya zuba tarkacen a baya, sannan ya shiga ya tada motan ya fito. Gudu sosai ya rinka yi hankalinshi kwance, jin zuciyanshi yake fari tass kaman anyi mashi albishir da wani babban abun alkairi. Cikin ikon Allah ya shigo garin Ningi, bai jira komai ba ya wuce skool din su Deedo, cikin kankanin lokaci yayi duk wani abu da ya kamata, sannan ya anshi result din yai masu sallama ya fito. A hankali ya fara shiga cikin garin yana tunanin ta ina zai gano gidan su Hally, hanyar gidan Goggo ya dosa, dan ya san ta can ne kawai zai iya samun damar da zai gane gidan su yarinyar… BA’A SHAN ZUMA… 54, 55 & 56 NA LUBABATU MAITAFSIR & BENAXIR OMAR Tun daga nesa ya fara hango taron mutane, wuri ya samu yayi parking, sannan ya fito daga motan, a kafa ya karasa, nan ya tarar da yan sanda har guda ukku, biyu mata da namiji guda. Hannuwan Goggo matan suka kama suka rike ta gam kamar wadda tayi kisan kai, tirjewa take tana kuka kaman ranta zai fita, amma matan nan kokarin tura ta suke cikin motarsu. Da sauri Nawap ya karasa gabansu yana tambayar abinda ke faruwa amma babu wanda ya tanka shi. Namijin dan sandan ne ma ya juyo yace "idan kana bukatar jin ba'asi zaka iya biyo mu station malam" a dai dai lokacin su kuma suka yi nasarar tura kan Goggo cikin motar suka shige suka bata wuta. Ba tare da bata lokaci ba shima ya shige ta shi motar ya bi bayan su har zuwa police station din. Suna isa suka fito da ita hannunta sagale da handcuffs suka tusa keyarta gaba, tana kuka tana komai, amma ko tausayin tsufanta basa yi, haka suka tura ta cikin cell suka jawo shi suka rufe. Da saurinshi ya karasa wurin dan sandan yana tambayar abinda ke faruwa, sai da officern ya gama wasu 'yan rubuce rubuce sannan ya dago yace "malam ya kuke da matar nan ne?" Nawap ya gyara tsayuwarshi, yace "kanwar mahaifi na ce, plz ka fada mun abinda tayi" dan sandan ya cigaba da jawabi kamar haka "ita kam babu abinda tayi, amma kasan dan kuka ya kan ja ma uwarshi jifa, dan haka shafin danta ne ya shafeta.." "Ban fahimce ka ba" Nawap ya fada yana kallonshi. Dan sandan ya cigaba "yaronta Shehu ne ya karya kafar wani yaro, sannan kuma ya caka mashi wuka a ciki, kuma an nemeshi sama da kasa a cikin garin nan an rasa, gashi kuma iyayen wanda aka yi ma raunin sunce baza su taba hakura ba, saboda yaro yana can a asibiti tsakanin rayuwa da mutuwa, yau kuma kusan kwana hudu kenan muna neman Shehu amma babu wani labari, dan haka muka yanke shawaran kama uwashi, idan yana sonta ya bayyana kanshi, sai mu saketa" Wani irin gumi ne ya yayyafo ma Nawap, a lokaci guda kuma ya fara karanto innalillahi wa inna ilaihir raji'un… Komawa yayi da baya, ya samu wani dan benci ya zauna, hannuwan shi duk biyun ya sa ya tallabi kanshi, yana mai cigaba da karanta innalillahi wa inna ilaihir raji'un. Tunanin abinda Goggo tai ma Deedo ya fara yi, har wata zuciyar tace ya tafi ya barta anan, amma tunowan da yayi da ko bakomai kanwar mahaifin Deedonshi ce, shi ya bashi damar mikewa ya koma gaban dan sandan yace "abokina yanzu menene abin yi?" Officer yace "abin yi anan shine kaje kaga dangin yaron a asibiti, duk yadda kuka yi sai ka dawo kai mana bayani" Nawap yace "ka taimaka muje tare mana" sai da yayi jim, kaman ba zai je ba, sai kuma yace "ok muje mana." A tare suka fito suka shiga motan Nawap din, sannan suka doshi asibitin kai tsaye. Dakin da akayi admitting yaron suka nufa, nan suka tarar da baban yaro yana matse kwalla. Bayanin abinda ke tafe da su dan sandan yai mashi, baban ya dago yace "Allah dai ya tsinewa yaron nan, Ian zaman zamana ya jawo mun masifa, yanzu gashi nan ance sai an mishi aiki a ciki, kuma wai sai na bada kudi naira dubu saba'in, ni yanzu ina na gansu?" Ya karasa maganan yana matse hawayen da suka taran mashi. Dukawa gaban shi Nawap yayi, yace "Baba kayi hakuri ka daina kukan nan, alfarma zan roke ka, kasa a saki mahaifiyar Shehu da aka kama, ni kuma zan biyawa yaronka kudin aiki har ma dana magani, su kuma yan sanda zasu cigaba da neman Shehu har zuwa ranan da za'a ganshi" dan tsohon ya dago yace "in dai kayi wannan alkawarin to zan sa a sake ta, amma fa bazan taba yafewa Shehu ba, dole ne alkali ya raba mu" Nawap yace "na maka alkawari baba, muje in biya maku kudin aikin, daga nan mu wuce police station kasa a saki Goggon" mikewa duk sukayi, saida suka biya ATM Nawap ya cire 100, 000 yaba dan tsoho, sannan suka karasa station aka gama rubuta statements, daga nan aka fito da Goggo ido yai mata gwale gwale kaman danyen nama saboda kukan da tasha, Nawap bai bari ta ganshi ba, ya shige motarshi ya kara gaba. Unguwan ya koma, dakyar da tambaya ya samu wani dan matashi ya kai shi gidansu Hally, a hanya ne yake tambayar yaron abinda ya faru da su Goggo, yaro da yaji sanyin A.C, nan da nan ya baje baki ya fara bashi labari yana cewa "shi ai Shehun ne kasan yanzu wasu mutane ne yake bi, ni a yadda naji ma haka ake cewa wai kashe yaron suka so suyi, Allah ne bai basu sa'a ba, sai dai suka caka mai wuka a ciki kuma suka karya mashi kafa saboda wata kungiya ce garesu, shi kuma yaron ya fita daga cikin su shine fa sukai mai wannan danyen aiki." "Allah ya kyauta" Nawap ya fada, yaro ya cigaba da cewa "amin fa, amma al'amarin Shehu sai addu'a, gashi nan yanzu ya ja ma uwar tashi ai" a haka suka karaso kofar gidan, ba tare da Nawap ya kara tanka mashi ba, 1k ya zaro ya mika mashi, sannan yace "shiga ciki kace ana sallama da Hallyn" yana kyarma ya anshe dubun ya fara rafka godia, sannan ya wuce cikin gidan yana ta murna. A tare suka fito, yana tsaye jikin motan ya nade hannayenshi yana dan kalle kalle. Tana ganinshi ta gane, dan haka ta karaso da dan sauri ta gaishe shi, ya ansa fuskanshi sake, cikin zakuwa ta fara tambayar "ya wajen su Deedo? Tana lafia?" Murmushin shi mai tsada ya saki, yace "tana nan lafia lau, nazo ansan mata result dinta nema, tace na biyo nace tana gaishe ki, kuma na baki number ta" a dai dai lokacin ya duka cikin motan ya samo wata yar paper ya rubuta mata number, ya dago ya mika mata. Hannu biyu tasa ta ansa tana ta washe baki, ta san ko bakomai, Deedo tana cikin jin dadi tunda gashi har waya gare ta. Godia tai mashi, sannan ta juya zata koma ciki, kudi ya ciro ya bata, amma taki ansa, dakyar ya samu ta ansa, yai mata sallama ya shige motan ya bar kofan gidan. Sai da ya hau titi sosai, ya fara tafia, sannan ya jawo wayanshi da niyyar kiran Ummi don ya shaida mata ya taho, missed calls din Aysha ya gani kusan guda 5. Wani mugun tsaki ya jaa, inda a lokaci guda kuma yayi wurgi da wayan a seat din dake kusa dashi.. BA’A SHAN ZUMA… 57,58,59&60 NA LUBABATU MAITAFSIR & BENAXIR OMAR Gudu sosai ya cigaba da yi kaman wanda zai tashi sama, ya rasa abinda ke mashi dadi, gurin shi daya, ya saita idanunshi kan yar kanwarshi wadda yake ta faman tunani da son jin muryanta. Ba shi ya shiga Kaduna ba sai wurin karfe biyar da rabi na yamma, dan haka bai tsaya bata lokaci ba, gida straight ya wuce ko dan ya samu natsuwar zuciyanshi. Da sauri mai gadi ya bude mashi bakin gate din, inda a lokaci guda ya tura kan motarshi ciki, mikewa yayi sosai da niyyar ya samu wurin parking, amma numfashinsa ne ke shirin daukewa lokacin da ya hango ta zaune saman wasu fararen kujeru. A gabanta wani dan table ne fari, tana sanye da bakin skinny jeans da wata red din t-shirt mai dan tsawo, saman kanta wani royal blue din veil ne, tayi daurin torchlight.. Kunnuwanta makale da earpiece, ta dora kafanta saman table din dake gabanta, idanuwanta a lumshe, da alama wakar da take sauraro tana shigarta yadda ya kamata. Wani gwauron numfashi Nawap ya ja, a lokaci guda kuma ya fara yan kalle kalle, daga gefe ya hango Idi dake ta faman gyaran flowers din shi, can gefe kuma Mal. Habu driver ne zaune yana sauraron radio. Wani mugun abune ya ji ya cakan mashi zuciya cikin dan kankanin lokaci, yaji numfashinshi na shirin daukewa, tunani ya fara yi ko Deedo ta samu tabin hankali ne, tana ganin gardawan mazan nan amma take zaune a haka, lallai yau zata yaba ma aya zakinta! Da sauri ya balla murfin motan ya fito, har yanzu tana nan yadda take. Wurin da take zaune ya dosa, bai yi wata wata ba ya fincike earpiece din dake kunnenta, cikin kaduwa da razana tayi saurin bude idonta, tana shirin artawa a guje, ganin mutum tayi kamar wanda aka jefo daga sama yana ta faman huci kamar mayunwacin zaki.. Idanuwan nan sun canja launi zuwa jaa, yanayin data ganshi ya bala'in firgitar da ita, dan haka ta mike da gudu tayi hanyar cikin gidan, mikewan da ta yi, yaji kaman an caka mashi kibiya a kahon zuciyarshi, ashe da tana zaune bakomai ya gani ba kenan, lallai yarinyar nan zata gane kurenta. Bai yi kasa a gwiwa ba shima ya bi bayanta da gudunshi. A palo ya cimmata, kunnenta ya damka ya murda tun karfinshi, ihu ta saka wanda yasa Ummi karasowa cikin palon da sauri. Ganin halin da suke ciki yasa tayi saurin matsawa ta warce Deedo daga rikon da Nawap yai mata, kallonshi take cikin fushi, tace "malam lafiya daga zuwan ka zaka hau dukan mun yarinya?" Idonshi sunyi zuru zuru sai huci yake, yace "watau Ummi ke baki ma ga laifin da tayi ba kenan?" Tace "me tayi fa, ince a zaune ka sameta a waje, ko wani abun tayi?" Kara kallonta yayi, gyalen da ta daura ya sabule, gashinta ya bazo saman fuskanta, gani yayi tayi wani mugun kyau kamar aljanna, yadda ta rakube a bayan Ummi tana raba ido abin sai ya birge shi, nan da nan yaji kunyar abinda yai mata, Ummi ce ta katse mai tunani da cewa "ina saurarenka inji laifin da tayi" Cikin borin kunya ya dan shafi sumarshi da ta kwanta luf luf, kallonta ya kara yi, sannan ya dan tsuke fuska yace "kar na kara ganin kin fita haka ba tare da kinsa hijab ba, baki ganin akwai gardawa a cikin gidan ne?" Kara kallon kanta tayi, ita dai bata ga matsalan shigan ta ba, asali ma lokacin da ta fita babu kowa a wajen, ba tare da ta kara kallonshi ba tace "kayi hakuri, ba zan kara ba" wani murmushi ne ya kwace mashi, bai san lokacin da yace "that's my lil sis" Ummi kam tabe baki tayi, tayi gaba tana banbami "mutum daga dawowa ko hutawa bai yi ba amma ya fara takura mana" a haka ta shige kitchen ta bar su nan tsaye kaman bishiyar da aka dasa.. Dukar da kanta tayi, ta rasa menene abinda ya kamata tayi, shin ta tafi ko ta tsaya? Bata yanke shawaran abinyi ba, taji ya tako zuwa inda take, a hankali ya fara magana yana kallonta, har yanzu dai kanta a kasa yake, "I'm sorry lil sis, nayi laifi ko?" Bata ce komai ba, sai kanta da ta girgiza alaman a'a, murmushi ya saki kaman tana kallonshi, yace "kece ai baki ji, wato tunda na tafi haka kike fita gaban masu gadi ko?" Da sauri ta girgiza kanta, "wlh yau ne kawai, kuma lokacin da na fita ba kowa a wajen.." Yace "issokay to, kada ki kara kinji?" Dagowa tayi, da niyyar bashi hakuri, idanuwanshi kyam akanta, da sauri ta juyar da fuskanta, tace "I'm sorry, bazan kara ba" "kalle ni" yace da ita, ta juyo idanuwanta masu tafiyar da imaninshi ta dora su kan nashi, wani abu yaji ya tsirga saman kanshi, ya sauka har zuwa babban yatsanshi na kafa, sai da ya tattara natsuwar shi, sannan yace "promise?" Wani dan murmushi ta saki tace "promise Yaa Nawap…" Murmushin ya saki shima yace "that's my dearest sis" da sauri tana yar dariya ta juya ta ansa foodflasks din da suke hannun Ummi ta jera su a dinning, shi kuma ya karasa gaban Ummin yana dariya, yace "na sameku lafiya Ummi?" "Lafiya lau" ta fada a takaice, sannan ta karasa cikin palon ta zauna saman 3seater, nan ma kara biyo ta yayi ya zauna a gefenta, yace "Ummi duk gajiyan da nasha na kula baki murnan zuwana ma" juyowa tayi ta kalle shi tace "ina fa zanyi murnan zuwanka, kazo ka hau mun 'ya da jibga" "Ayi hakuri Ummi, bazan kara ba, kuma ma har mun shirya da 'yar taki fa" kallon Deedo tayi wadda take jera plates, tace "wai haka auta?" Murmushi tayi, tace "haka ne Ummi" sai a sannan Ummi ta sake, suka cigaba da firansu, inda daga bisani ya mike ya wuce side din shi, dan ya samu yayi wanka, ya sauke sallolin da suke kanshi.. Shiryawa yayi tsab cikin kananun kaya, black jeans nd white t-shirt, kirarshi ta fito sosai, hannunshi daure da makekiyar agogo mai tambarin GUESS anyi mata ado da stones din diamond, kafarshi daure da bakaken sneakers. Sumar nan tayi kwance luf sai sheki take, a haka ya karaso cikin palon, hannunshi rike da doguwar envelope kalar ruwan kasa. Saman dinning ya karasa, nan ya ja kujera ya zauna, sannan ya dubi Deedo yace "taimaka mun da abinci" ba tare da tace komai ba, ta mike tayi serving dinshi, ta mika mashi, duk abinda take idonshi a kanta ko kyaftawa baya yi, murmushi ya sakan mata yace "thanks my lil sis" itama murmushin tayi, ta koma ta zauna ta cigaba da cin abincinta. Envelope din da ya shigo da shi ya mika ma Ummi, yace "kinga rashin kokarin da autarki tayi" ya fuske ya ci gaba da kwasar abincinshi. Ummi bata ce komai ba ta ansa ta aje a gefenta, saida suka gama cin abincin sannan ta buda, ga mamakin ta, taga ko C babu a result din Deedo, daga A sai B, da murmushinta ta mika mata, ta kalli Nawap tace "ai dama nasan auta ta ba daga nan ba" inda ta kai dubanta kan Deedo tace "you deserve to be a Doctor my dear, Allah yi maki albarka ya sanya alkairi a rayuwanki" Wani mugun farin ciki ne ya lullube Deedo wanda yasa ta fara hawayen jin dadi, ta dade tana neman wanda zai na appreciating dinta a duk lokacin da tayi wani abun kwarai, Allah mai iko yau itace ake sama albarka saboda ta samu sakamako mai kyau, bata ma san da bakin da zatai ma Ummi godiya ba. Mikewa tayi ta fada jikinta, tana kukan farin ciki, Ummi ma kwalla ne suka yayyafo mata, tasa hannu ta share, tace "ya isa haka, bana son kukan nan kina jina" murmushi ta saki ga kuma hawaye na bin fuskanta, sannan ta fara daga kanta alaman baza ta kara kukan ba. Nawap dake gefe kallon su yake yana mai jin wani farin ciki na yawo a jikinshi, dan haka ya tako zuwa inda suke, Deedo ya kalla yace "lil sis shirya ki raka ni unguwa" cikin zakuwa ta mike ta haye sama, inda Ummi ta kalleshi tace "ina zaka kai mun ita kuma muna tsaka da jin dadin mu?" Murmushi yayi, yace "zamuje duba jamb dinta ne Ummi" tace "aiho, na zata yawo zaka kai mun ita ai" a haka Deedo ta sauko sanye da bakar abaya yar Dubai, ta tattara gashinta a tsakiyar kanta ta daure, sannan tayi rolling gyalen abayan, kafanta sanye da bakin plat shoe na Gucci, sai wani kanshi mai dadi yake tashi a jikinta. Ido Nawap ya kura mata kamar zai cinye ta, ya rasa mai yasa yake ganin kyaun yarinyar yanzu, wanda shi a da bai taba sanin tana da shi ba, gashi ta wani goge ta waye kaman wadda ta shekara goma a birni. Karasowa tayi cikin palon tace "Ummi zamu tafi" "sai kun dawo auta" Ummi ta fada, ta juyo tana "Yaa Nawap na shirya fa" nan taga yadda ya ware idanunshi yana kallonta kaman bai santa ba. Basarwa yayi, yace "muje mana" inda yayi gaba tana bin shi a baya. Zaune take a gefenshi, shi kuma yana seat din driver, sunyi bala'in kyau abin ba'a cewa komai. Dai dai lokacin da yake kokarin fita gate din gidan, motar Aysha ta kunno kai, ganin Nawap tare da wata, yasa ta saki wani uban full light wanda ya kashe masu idanu gaba dayansu.. BA’A SHAN ZUMA… 61, 62 &63 NA LUBABATU MAITAFSIR & BENAXIR OMAR Cikin kankanin lokaci idanuwan nan suka juya, suka sauya launi daga fari zuwa jaa, da sauri zuciyarshi take harbawa, Deedo da take zaune a gefe hankalinta yayi kololuwa wurin tashi, a tunaninta wani mugun abun ne ya faru ganin mood din Nawap ya canja lokaci guda. A zuciye ya balla murfin motan ya fita, inda a hankali Aysha ta fara rage full light din da tayi, cikin isa da gadara itama ta buda murfin tata motan ta fito, sannu a hankali ta fara takowa zuwa inda yake. Kallonta yayi cikin tsananin bakin ciki yace "so it's yu?" Murmushi ta saki mai tattare da rainin hankali, ta nade hannuwanta, ta jingine jikin motarshi, sannan ta kalleshi tace "yup, it's me" wata muguwar harara ya watsa mata, sannan ya juyar da kanshi yace "dame kike son a kira sunan abinda kika yi?" Murmushi ta kara saki, tace "duk abinda ka kira shi" sai da ya dai dai ta tsayuwanshi, yayi facing dinta yadda ya kamata, sannan yace "Aysha abinda kike shirme ne, kauyanci ne, kuma rashin wayewa ne! I told yu ki fita hanya ta, otherwise zaki gane kurenki, dan na lura abin naki na neman ya zama raini, ni bana ciki da rainin hankalinki.. " Wata kibiyar bakin ciki ce tayi suka ta caki zuciyar Aysha, kallonshi kawai take don ta rasa ta cewa, babban bakin cikinta shine Deedo tana sauraren duk abinda sukeyi, kasancewar a bude ya bar motan, wasu yan kwalla suka yayyafo mata, juyawa tayi cikin salo na gogaggun yan mata ta dan share, a lokaci guda kuma ta cigabada kallon Nawap tana dan murmushi, sannu a hankali ta taka zuwa gabanshi tace "Nawap sonka a cikin jinina yake, dashi nake rayuwa, idan har kana tunanin akwai ranar da zan daina sonka, to ka tafka babban kuskure, domin da sonka nake numfashi, da shi nake kwana da shi kuma nake tashi a ko wacce safiya, harkanka kuma da kake magana, yanzu na fara shigarta, dan haka mu zuba nida kai.. " Juyawa tayi da sauri da niyyar ta shige motan ta, hannunta ya finciko tun karfi, ta dawo da baya, kallonta yayi ido cikin ido yace "idan mafarki kike gara ki farka Aysha, domin bakya jerin kalar matan da zan iya so a rayuwata, baki da quality kwara daya da zan iya so a wurin mace, sannan kuma rashin kunya na daya daga cikin abubuwan da nafi komai tsana a tsarin rayuwata, dan haka ki natsu, ki gane cewa ruwa ba sa'an kwando bane!" Yayi wurgi da hannun sannan ya koma ya shige motan, yayi reverse ya koma cikin gidan. Wani tiririn bakin ciki ne ya cigaba da fita daga zuciyan Aysha, kallon motan tayi, inda wasu hawayen bakin ciki suka gangaro saman fuskanta, a hankali ta furta "zaka san ka wulakanta ni Nawap, ba dai akan wannan tsinanniyar yarinyar bane kake yi mun abinda kaga dama, wallahi sai tayi dana sanin shigowa gonata da tayi" dakyar ta ja kafanta ta koma cikin motan, gidan da bata shiga ba kenan, domin jin zuciyanta take kaman ana tafasa ruwan zafi a ciki. Parking Nawap yayi, ya juyo ya kalla Deedo wadda itama shi din take kallo, ji yayi tamkar an zuba mashi ruwan sanyi, kyawawan idanunta kadai, sun tafiyar da kunci da bakin cikin da yake ciki, murmushi ya sakan mata, wanda na tabbata bai san lokacin da ya subuce mashi ba, a hankali yace "ki shiga ciki, da safe zan je na duba maki jamb din kinji?" Ba tare da tace wani abu ba, ta buda motan ta fita, shi kuma ya bita da idanu har sai da ta shige ciki. Ummi ta samu zaune tana kallon Sunnah T.V da murnarta, tace "ba dai har kun dawo ba?" Sai da ta zauna, sannan tace "bamu je bama, yace da safe zai je ya duba mun, wai dare yayi" tace "ba laifi ai, Allah yasa dai muga alkairi " "amin" ta fada, sannan ta mike ta haye sama, zuciyarta fal da tunanin wannan bala'i irin na Aysha. Namiji yace baya son ki amma ke kin nane mashi sai kace mayya! A fili ta furta "Allah dai ya kyauta wannan rayuwar wahalar." Alwala tayi sannan ta gabatar da sallan isha'i, tana gamawa ta cire kayan ta da niyyar shiga wanka, wayanta ne ya fara ruri, karasawa tayi inda wayan take taga bakuwan number, da sallama ta daga wayan ta kara a kunnenta, daga dayan bangaren taji ance "dan Allah ina neman Deedo ne" wani mugun dadi ne ya ziyarci zuciyanta, domin ko a mafarki, baza ta taba manta mai wannan muryan ba. Nan da nan suka barke da fira ita da Hally, ba tare da bata lokaci ba ta zayyana mata dangantakar dake tsakaninta da Ummin Nawap, ta kuma bata labarin result dinta da yadda rayuwa ke tafiyan mata cikin jin dadi. Murna sosai Hally tayi, ta kara da cewar "mahakurci mawadaci Deedo, dama ai haka rayuwa take, idan wani ya kika wani zai so ka" da haka suka yi sallama, inda Deedo tai mata alkawarin kiran ta da safe in sha Allah Nawap ya dade zaune cikin motan yana tunanin abinda ya faru kaman a mafarki, daga karshe dai ya fito ya shiga palon bai ga Deedo ba sai Ummi kawai a zaune, kunnuwa ya baza yana sauraren yaji abinda zata ce game da abinda ya faru tsakaninsu da Aysha amma yaji tsit, don a tunaninshi ko Deedo ta fada mata. Haka ya karaci zaman shi, inda daga bisani ya mike yayi mata sai da safe ya wuce side dinshi. Da safe kamar yadda yayi alkawari, haka ya fita around 10, cafe din da yayi mata registration ya nufa ya siya scratch card ya duba mata, yaji dadi sosai ganin ta ci kusan 250, bai bata lokaci ba yayi printing result din ya fito, straight KASU (Kaduna State University) ya wuce, gaban faculty of medicine yayi parking, sannan ya ciro wayanshi ya kira wata number. Cikin yan mintuna wani matashi wanda shekarunshi basu wuce 30 ba ya fito ya karaso gaban motan Nawap. Fitowa yayi, ya mika mashi hannu suka gaisa, sannan suka jera zuwa cikin faculty din. Office din mutamin da naji ya kira da Kashim Yarima suka nufa, bayan sun gaisa ne Kashim ke ce mashi "wlh baka da kirki Nawap, zumuncinka yayi karanci ko?" Nawap yace "kasan abubuwa sai a hankali, yanzu ma wata sis dita ce nazo yima follow-up, ta cika nan skool din ban sani ba ko zaku dauketa" Dariya Kashim yayi, yace "me zai hana indai nan din ta cika, kuma tana da abubuwan da muke bukata, zuwa end of this month ma zamu fitar da 1st list na admission in sha Allah" Nawap yace "plz kayi mun kokari, komai tana dashi, medicine take son karantawa, dan Allah kar ku bata course din da ba shi take so ba" ya kara da "bara na baka sunanta idan kun fitar da admission din sai ka duba mun please" wata paper ya mika mashi ya rubuta details din Deedo ya bashi, sannan sukai sallama, inda yai mashi alkawarin kiran shi da zaran sun fitar da list din.. BA’A SHAN ZUMA… 64, 65 &66 NA LUBABATU MAITAFSIR & BENAXIR OMAR Yana karasawa gida wanka yayi yanufi masallaci, bayan ya fito ne yashigo cikin gida anan ya ga feedo kwance akan doguwan kujera, sanye take da riga da wando, kanta ba dankwali ta tattare gashin ta baya ta daure, sai da ya kare mata kallo kafin yayi sallama, da sauri ta mike ta zauna tana kokarin nemo hulanta wanda dama ya fadi ne ta baya, "ina wuni"tace dashi, ya ansa, ya kauda kansa sannan yace "ki shirya gobe muje in kaiki saloon" ta ce "toh, dama dazu ummi ta gama maganan" ruwa ya dauka a fridge sannan ya fice. Washegari karfe goma ta shirya tsaf tana jiransa, yazo suka gaysa da ummi inda ya mata bayanin cewa yaje maganan admission din Deedo, taji dadi sosai sannan yace Deedo ta fito su wuce, ta shiga motan sannan ta rufo, yajasu suka fice, bai tambayeta inda zai kaita ba kawai taga ya nufi wani saloon da ita, Tripple D Beauty and Care saloon taga an rubuta, saloon din ya hadu sosai domin babu abinda basa yi ajikin board din takaranta, nan ya ciro dubu biyar ya mika mata tare da cewa "inkin gama ki kirani" shigewa saloon din tayi, tasamu mutane biyu agabanta don haka tazauna jira, har akazo kanta, anwanke mata kai ana kokarin sata a dryer saiga Aysha da kawarta sunshigo, da farko murmushi take tana dariya, ganin Deedo yasa ta dauke annurin fuskanta tamkar taga malaikan mutuwa, taja wani mummunan tsaki sannan tanemi gu tazauna, hankalin mutane ya nufi kanta jin tsakin da tayi, Deedo ma ganinta yasa tagane da itane, anma kasancewar tasan ta girmeta, sai bata nuna alaman ta ji bama, nan ta ce "ina wuni?" Bata amsa ta ba, hakan yasa itama ta kauda kanta, kawarta ce take kokarin cemata ana mata magana, nan cikin fadin rai da iko tace "itace munafukan danake miki bayani" habawa tuni kawar ma ta daure fuska "awh! Ai sai kice min ga snatcher, lallaima ina zaki kai wannan abun?" "Tayani ji dai inbanda namiji da ruwan ido da rashin sanin daidai, Allah wadaran tsiya inji arziki" Deedo duk tana jinsu bata tanka ba, hatta yan saloon din ma kowa dai yayi shiru ne don yadda suke maganan zai tabbatar dacewa da dayansu akeyi Aysha takalli kawar ta sannan tace "kinsan wani abu ma kuwa?" "A a saikin fada" "Ita fa take binshi, sai shishigewa take, matsiyaciya tazo tashiga arziki, ta kainane, a zatonta yatsu tsayinsu daya, dontaga ita yar uwa ce" Kawar ta tabe baki sannan tace "ji munafukar kamar ba da ita ake ba" kafin Aysha ta amsa tanufi kan Deedo taja gashinta , matan ta fara bada hakuri yayin da Deedo tamike tare da cewa "kuyi hakuri, anma duk abunda kuke fada bahaka bane" bata idar ba taji anwanke ta da mari, hannu tasa tarike fuskan alokacin yan saloon din suka mimmike don kawowa mata agaji, tuni Aysha da kawaarta suka hau dukan Deedo har sai da suka yaga mata riga. Wayanta taciro da kyar takira Nawap, batayi magana ba yana kokarin cewa hello yaji hayaniya yayi yawa, dama baiyi nisa ba nan da nan yajuyo yataho, yana isowa ya bude kofan motan ya manta baima kulle ba yashiga saloon din ganin Aysha da Deedo ko baa fada masa ba yasan abunda suka aikata mata tunda ga riganta ayage tana kokarin rufe jikinta, idonshi tuni ya canja kala yayi jajur ya kalli mai saloon din tare da cewa "meya faru?" Ta mayar masa da komi kamar yadda ya faru, alokacin yaji kamar ya shako Aysha ya kashe don bakin ciki, ya ruko Deedo ya sanyata a mota bai ce komi wa Aysha ba wacce jikinta sai bari yake, Rufo motan yayi yabawa mai saloon kudinta sannan ya tuka suka fice, kuka take tayi anma yarasa ta yadda zai fara bata hakuri, danne zuciyansa yayi tareda cewa "kiyi hakuri duk abunda ke faruwa saboda ni ne, Aysha tadauka nemanki nakeyi, kiyi hakuri ahankali zata gane gaskiya" bata ce komi ba har suka isa, tuni tabude motan tashige gida, daki tanufa saboda ta canja kaya, Nawap kuma yana tunanin abunda zaifada idan Ummi ta tambayeshi meya faru, duk da yasan Deedo zata fada. Bai shiga gidan ba sai dare inda yaga Deedo sai dariya take suna tadi da Ummi, kuma da ya zauna baiga sauyi ba don anhada dashi ana tadin, nan ya tabbatar da cewa Deedo bata sanar da ummi abunda yafaru ba. Cikin zuciyanshi mamaki yake ita wace irin yarinya ce, bai ce komai ba, haka ya daure ana dan tadi dashi, daga bisani ya mike ya wuce part dinshi inda ya cigaba da tunanin abun da zai yi ma Aysha ko dan ta fita hanyarsa.. Ranan da zai koma Abuja ya gama shirinsa tsab, ya saka kayanshi a mota, ya shiga cikin gidan yayi ma Ummi sallama, amma bai ga Deedo ba, fitowa yayi zai wuce, a dai dai nan ya hade da ita zata shiga kofan palon, hannunta ya jawo suka bar wurin zuwa bakin motanshi, yana kallon kwayan idonta yace "ni zan wuce lil sis, ba lallai ina nan admission dinku ya fito ba, amma zan hada ki da Dr. Kashim phrnd dina ne, nasan zai maki komai in sha Allah, dan haka abinda nake so dake shine ko kinje skool ba ruwanki da samarin banza bata gari, wanda basu da aikin yi sai hure ma yara kunne, ki natsu, kiyi abinda ya kaiki, kina jina? Nd ina mai kara baki hakuri akan abinda Aysha ta miki, I promise yu hakan ba zai sake faruwa ba kinji?" Murmushi ta saki, tace "in sha Allah zan cika umarninka Ya Nawap, Allah ya tsare hanya" ta juya zata wuce, sai ya ji kamar kada ya tafi ya barta, da sauri yace "baza ki jira kiga tafiyana bama" bata ce komai ba, sai murmushin data saki, hannayenta ta harde, ta tsaya tana kallonshi, hakan da tayi ya bala'in yi mashi kyau, ba tare da bata lokaci ba ya zaro wayanshi, ya kyalla mata hoto, dariya tayi, ta rufe fuskanta, haka ya cigaba da daukanta har sai da yaga yana niyyan makara, sannan yace tazo, ta matso kusa dashi, dan haka ya daukesu tare, sunyi bala'in kyau, sai a lokacin yaga ashe har kama suke yi. Ba don ya gaji da ganin Deedo ba, yai mata sallama ya shige mota, inda ya cigaba da jaddadada mata cewar ta kula da kanta, tana murmushi ta daga mashi hannu har sai da ya fita gate din gidan, sannan ta shige ciki. Yana fita, gidansu Aysha ya zarce, a bakin gate ya hade da ita, da alama office zata fita, parking yayi ya fito daga motan ya karaso gabanta. Yanayin da ta ganshi ta san ba mutunci, kuma dama ta dade tana jiran wannan ranan, dan haka ta kama kanta, ta fara raba idanu, kaman shege a rabon gado. Nuna ta yayi da hannunshi, yace "this shud be last warning, ki fita hanyar yarinyar mutane, idan ba kina so fita daga cikin gidanku ya gagareki ba, na fada maki bana son ki, to menene na yi mun shishshigi a rayuwa, ki tsaya matsayinki, if not, zaki ga abinda zai biyo baya" ya juya a fusace, yana fadin "maran zuciya kawai" ya shige motanshi ya bata wuta. Aysha saboda bakin ciki bata ce komai ba sai mazurai da take, nan take hawaye suka cika mata ido, kuka ta cigaba da yi kaman an bude famfo, cikin kunan zuciya tace "baza a rabu da kai din ba, sai an soka din, kuma in dai wannan shegiyar yarinyar ce yanzu na fara takura mata har sai wahala tasa baza ta taba sonka ba, wanda bai son abinda ya dace dashi ba kawai, wannan har wani abun so ce" ta ja tsaki ta share hawayen, tace "bari dai kawata ta dawo daga tafiyan da tayi, wallahi sai mun koya ma yarinyar can hankali" ta jawo mirror cikin jakanta ta gyara fuskanta, sannan ta yi ma motar key ta bar gun.. BA’A SHAN ZUMA… 67-69 NA LUBABATU MAITAFSIR & BENAXIR OMAR Haka rayuwa ta cigaba da tafiyan ma Deedo hankalinta kwance, bata da sauran matsala, gashi kuma ta kan kira Hally su sha labarin duniya amma ko ta tambayi ya su Goggo, Hally zata shashantar da maganar bata ma son ko kadan Deedo na tunawa da Goggo, yau ma kwance take a daki suna waya da Hally take ce mata ta samu admission a ATBU, har ma ta fara registration, Deedo ta mata murna sosai, inda take tambayar "ya maganan naku admission din?" "Muna kan jira muma, in sha Allah" "Allah ya taimaka" ta fada, haka suka cigaba da tadinsu cikin jin dadi, daga karshe tai mata sallama ta mike, domin gabatar da sallahn azahar. Bayan ta gama sallah tana zaune kan sallaya taji wayanta yayi kara, ta dauko ta duba, email ne ya shigo daga KASU, sun bata admission a faculty of Medicine and Surgery. Murna sosai take yi, da gudu ta mike da niyyar zuwa dakin Ummi, wayan Yaa Nawap ce ta katse mata hanzari, cikin sauri ta daga wayan tare da gaishe shi cikin zakuwa, shiru yayi yana imagining farin cikin da take ciki, nan da nan ya ji inama yana da iko da sai dai su ganshi a gida kawai. Murmushi yayi yayin da ta katse mashi tunani ta hanyar cewa "Yaa Nawap dama yanzu zamu kira ka" "ni da na fi damuwa daku ai gashi na riga ku kira, kuma da babban albishir na zo" Cikin zakuwa tace "nima albishir ne zan maka, amma ka fara fada mun naka 1st" murmusawa yayi, yadda take maganar duk ta tafi mashi da wata kasala da yake tare da ita, idonshi a lumshe, yana juyawa a kujerar office dinshi, yace "yanzu Dr. Kashim yai mun text sun baki admission" murmushi ta saki mai taushi, kaman yana gabanta, tace "shine albishir din da zan maka nima, yanzu email ya shigo mun" "congratulations, sai ki shirya on monday, kuje tare da driver, zan hada ki da Dr. Kashim ki fara registration ko" "nagode Yaa Nawap Allah ya saka da alkairi" "issokay" ya fada, inda a lokaci guda yai mata sallama ya koma bakin aikinshi. Dakin Ummi ta wuce da murnarta ta shaida mata yadda sukai da Nawap, Ummi ta rungume ta suna ta jin dadinsu, tace "tashi mu wuce kasuwa, ai zama bai ganni ba auta zata tafi jami'a" murmushi tare da hawayen farin ciki ne suka gangaro a fuskar Deedo, ta share, sannan ta mike ta wuce daki ta fara shiri. Siyayya sosai Ummi tayi ma Deedo, dangin kayan sawa, takalma, jakunkuna da sauran tarkace na 'yan matan jami'a. A gajiye liss suka dawo gidan wurin karfe biyar na yamma, wanka tayi, tayi sallah, sannan ta gangaro palon don ta samu damar hutawa, Ummi ta tadda tana bude kayan da suka siyo, inda ta zauna itama suka cigaba da budawa tare, daga karshe Ummi tayi ma tailansu waya, domin yazo ya anshi kayan dinki. * ** A daddafe Nawap yake rayuwa a garin Abuja don wani matsanancin kewar Deedo da ke damunshi, wadda ya rasa tantance ko menene dalilin. Pictures dinta kawai yake kallo ya samu natsuwa cikin ranshi. Ga aiki ya sakashi gaba sosai, bashi da wani lokaci balle yayi tunanin samun damar zuwa ya ganta. Da misalin karfe biyar na asubar ranar litinin, wadda tayi dai dai da daya ga watan February, 2016 (1st Feb, 2016) Deedo ta tashi, wanka tayi, sannan ta doro alwala ta fito. Sallah tayi, ta zauna a wurin ta cigaba da azkar har wurin karfe bakwai na safe, daga bisani tayi addu'ar neman sa'a a karatunta, da kuma rayuwarta, ta kara da neman tsari daga dukkan wani sharri na rayuwa. Daga karshe tai ma Ummi addu'ar da ta saba, sannan ta nema ma iyayenta gafara a wurin mai kowa mai komai. Gaban dressing mirror ta isa ta shafa mai tare da designers din turarukan da suke zube a wurin, simple make up tayi, sannan ta matsa gaban wardrobe din ta buda tana tunanin wane kaya ya dace ta saka a wannan farar rana. Wata super java ta dauko, mai kalar light orange nd purple, dinkin skirt nd blouse ta saka, wasu round dankunnen ta sanya masu kalar gold, ta daure hannunta da agogon Vintage, itama dai kalar gold din ce, bracelets ta sanya a dayan hannunta na hagu, sannan ta dora zobuna na isassun yan mata, wanda duk a cikin siyayyar da Ummi tayi mata suka siyo da su. Lafiyayyan daurin yan zamani tayi, sannan ta jawo gyalenta purple, takalmanta da handbag dinta kirar Jimmy Choo wanda suka kasance reddish brown, ta sanya, ta dauko handbag din, ta kara feshe jikinta da turaruka na alfarma, sannan ta fito. Karfe tara lokacin har da minti biyar, dakin Ummi ta shige, inda ta same ta tana breakfast. Dukawa tayi har kasa ta gaisheta, Ummi kam binta tayi da kallon mamaki, anya wannan autarta ce? Da murmushinta ta ansa, tace "wannan duk kyau ne Deedo?" Kanta a kasa tana dan murmushi, ta zauna kusa da Ummi ta fara hada tea. A gurguje tayi breakfast din ta gama, Ummi dai sai yaba kyau da gayun Deedo take, bayan ta gama fitar da kwanukan, ta dawo tayi ma Ummi sallama, inda tayi mata nasiha mai ratsa jiki kan ta kula da mutuncinta, ta kuma tsare martabar gidansu. A haka suka sauko palon tare da Ummi, ta dauka kudi ta bata, sannan tayi kiran driver, tace ya kaita skool, idan ta gama sai tayi waya, yaje ya daukota. Cikin zakuwa ta rungume Ummi, tayi mata bye, ta wuce ta shige motan. Tana shiga wayan Nawap ya shigo, da murnarta ta daga ta gaishe da shi, sai da yaja numfashi, sannan ya ansa, tambayarta ya fara "kin shirya ne?" Tace "gamu zamu tafi ma" yace "ina fatan dai bakiyi wani kwalliya ba, dan karatu zakije ba fashion parade ba" murmusawa tayi, sannan ta kalla mirrorn gaban motan, tace "ban yi ba fa Yaa Nawap" yace "idan kina son na yadda ki mun snapping kanki, ki tura mun ta whatsapp yanzu" "to" kawai ta fada, yai mata bayanin yadda zata ga Dr. Kashim, dan shine zai mata komai ya kuma hada ta da wannan zai taimaka mata wurin registration. Daga karshe cikin wata irin murya mai sanyi yace "I wish ina tare dake a irin wannan ranar lil sis" kasa magana tayi, saboda yanayin da yayi maganan bata san ya zata fassara shi ba, murmushi kawai tayi, tace "thanks for everything Yaa Nawap, sai na kira idan naje skool din" ta kashe wayan lokaci guda, sannan ta dauka selfie ta kunna datan ta tura mashi, tayi bala'in kyau kamar aljana, ta kashe datan ta jefa wayan cikin jaka. Suna shiga office din Dr Kashim ta nufa direct, ko da bata fada mashi ba ya san ita ce sister Dr. Nawap, saboda asalin kamar da yaga suna yi. Gaishe dashi tayi, sannan ta samu wuri ta zauna, bayan ya ansa, yace "Firdausi, ryt?" "Yes Sir" ta fada, yace "ina fatan kinzo da credentials dinki baki daya?" "Eh na zo da komai" "ok, lemme call someone who will assist yu" "Ok Sir" ta fada, yayin da ta dukar da kanta, ta cigaba da wasa da 'yan yatsun hannunta. Wayanshi ya dauka ya kira wani, yace ya sameshi a office yanzu. Cikin mintunan da basu wuce sha biyar ba, aka turo kofar office din aka shigo, kanshin wani lafiyayyan turare ya daki hancin Deedo inda a lokaci guda taji zuciyarta ta buga da karfi, kafarshi ta fara kallo ta ganta lullube cikin lafiyayyun sneakers black nd white kirar Tommy Takkies, a hankali take dago kanta, sanye yake da bakin pencil jeans, da white t-shirt ta Ralph Lauren, hannunshi daure da agogon fata baka kirar Orlando, kasa dauke idonta tayi lokacin da ta yi arba da kyakkyawar fuskarshi, gashin kanshi ya kwanta luf, sai kyalli yake kaman na jarirai, kallonshi take kaman yau ne rana ta farko da ta fara ganin bil adama. Kallonta yake shima, inda cikin zuciyarshi yake nanata "tsarki ya tabbata ga Allah, ubangijin da ya tsara wannan kyakkyawar halitta!" Murmushi ne ya subuce mashi, inda itama a lokaci guda ta sakan mashi nata kayataccen murmushin… BA’A SHAN ZUMA… 70-72 NA LUBABATU MAITAFSIR & BENAXIR OMAR Dr. Kashim ne ya katse su da cewa "yawwa Affan ka zo ne? Karaso ciki mana" cikin jin kunya ya dan shafi sumarshi ya karasa cikin office din ya mika gaisuwarshi ga Dr. Kashim, inda shi kuma a hankali kwance ya ansa, ba tare da ya dago ba, ya cigaba da typing din da yake akan laptop dinshi. Kujeran da ke kallon ta Deedo ya zauna, kura mata ido yayi, inda a bangarenta itama ta kasa tantance dalilin da yasa take jin dadin kallon da yake mata. Dr. Kashim ya dago daga kallon laptop din gabanshi, yace "yawwa, Affan plz, wani taimako za kai mun dan Allah" ya maida dubanshi ga Dr. Yace "na me fa? Hope dai ba aike bane, cuz ina da class karfe sha biyu" ya fada yana duban kayataccen agogon hannunshi. Dr. Yace "kai fa problem dina da kai kenan, ka cika laziness kaman, mace" murmushi Affan yayi, ba tare da yace komai ba, inda Dr. ya cigaba da magana.. "Wannan sister phrnd dina ce, tazo registration ne, nd as yu can see bani da time da zanyi guiding dinta, kuma ba zai yiwu na hada ta da Secretary dina ba, plz ka taimaka mata komai da za'a bukata tana dashi, zaku je kuyi clearance ku ansa admission, then sai ku fara reg, plz my Lil bro" ya fada yana kallonshi, inda shi kuma ya dan dage giranshi tare da kafada irin na big boys, yace "alright then, I'll try my best" sannan ya mike, ya cigaba da kallon Deedo, yace "let's go beautiful" murmushi tayi kawai, ta mike ta yi wa Dr. godiya, sannan ta fita. Dr. Kashim ne ya kwala ma Affan kira a yayin da yake kokarin bin bayan Deedo, yace "plz, ka kula da yarinyar nan, amanan Dr. Nawap ne kana ji na?" Juyawa yayi yana dan bouncing yace "have no probz bro.." yana dariya ya bar office din, Dr. Ya girgiza kanshi, sannan cikin zuciyarshi yace "Affan the trouble maker" Tare da taimakon Affan Deedo ta kammala clearance dinta tsab, ta anshi admission letter dinta. Bayan sun fito ne tayi deciding kiran Nawap ta fada mashi, nan ta ci karo da 3 missed calls dinshi, sai da ta duba taga ashe wayan silent ta shiga lokacin da ta jefa ta cikin jaka. Da sauri ta fara kiran number har kuma ta katse bai dauka ba, ta kara kira a karo na biyu, nan ma shiru kake ji. Ba tare da wata damuwa ba ta maida wayan cikin jaka, sannan ta cigaba da yan kalle kallen yadda students suke shawaginsu hankali kwance. "Hey beautiful" taji an fada cikin muryar nan tashi mai dadin sauraro. Juyowa tayi dauke da murmushi ba tare da tace komai ba. Ya karaso ya zuba mata idanu, sannan yace "zamu je inyi lecture, idan na fito sai muyi wani abun, zuwa gobe kuma sai mu karasa ko?" Ya fada yana mai cigaba da kallon kyakkyawar fuskarta. Bata iya yi mashi gardama ba, dan haka suka mika zuwa wurin da yayi parking suka shige motan, sannan ya fara k'ok'arin tadawa. Bayan sun shiga motan sun zauna ne, har ya tada, amma sai bai tafi ba, kallonshi tayi tare da alamar tambaya, nan ta ci karo da shanyayyun idanuwanshi na aiko mata wani sako wanda har sai da zuciyarta ta buga lokaci guda. Dakyar ta daure tace "muje mana" cikin wata irin murya ya langab'ar da kanshi yace "Feedo I can't hold it, to be honest, you're beautiful nd you've a beautiful smile too" murmushi ne ya kwace mata, inda tasa gyalenta ta dan rufe fuskanta, a hankali ya furta "OMG look at ha dimples, I love them" ya dan ciji leb'enshi, sannan ya daure yayi ma motan key suka bar wurin. Zaune take a gefenshi, inda ya tattara hankalinshi gaba daya yana kallonta ba tare da sanin ta ba, kasancewar hankalinta na kan game din da take yi a wayanta. Wasu phrnds dinshi ke ta tambayar inda ya samo ta, amma yana ta basarwa, shi a dole kada su samu fuskan yi mata magana. WANENE AFFAN? Affan Taufiq, matashi ne mai shekaru ashirin da biyar a duniya, namiji dan gayu wanda ya saba da hutu mai asalin zati da kwarjini a wurin jama'a. Kyakkyawa ne dai dai misali, sai dai yana da wasu idanuwa masu haske da walk'iya wanda sune suke rikita duk wata mace da tayi arba da kallonshi. Iyayenshi Alh. Taufiq, da Haj. Maryam yan asalin garin mak'arfi ne ta jihar Kaduna, amma Allah yayi masu rasuwa tun Affan yana shekara goma a duniya, wannan yasa rik'onshi ya dawo hannun yayan mahaifinshi, wato Daddyn su Dr. Kashim. Affan ya kasance masoyin karatun likitanci kamar Deedo tun daga k'uruciyarshi, wannan yasa ya zama zakaran gwajin dafi a gaba daya department dinsu, tun ranar da ya fara har izuwa yanzu da yake a final year dinshi. * * Misalin karfe biyar na yamma a gajiye liss Deedo ta koma gida, a palo ta zube inda ta tarar da Ummi, nan ta gaisheta, cikin yanayi na tausayawa Ummi ta ansa, sannan tace "makaranta ba dadi ko auta?" Murmushi Deedo tayi tace "a hankali zan saba Ummi" ta mike saman 2 seater, can kuma tace "Ummi ko Yaa Nawap ya kiraki?" "A'a bai kira ba, ya akayi ne?" "Munyi magana kafin na isa skool, to na manta waya na silent ashe ya kira, na kira kuma bai dauka ba" Ummi tace "may be aiki yake, idan ya gani zai kira" bata kara cewa komai ba, ta koma ta kwanta luf, fuskan Affan ce ke dawo mata, yadda yake tsokananta da yadda yake magana, abin na bala'in birgeta murmushi ta saki, a dai dai lokacin kuma wayanta ya fara ruri,hakan yayi sanadiyyar yankewar tunaninta. Yaa Nawap ta gani, dan haka tayi saurin dagawa, tana kokarin gaishe da shi, taji yace "haka muka yi dake? Wane irin abu ne ban fada maki ba kafin na tafi? Haka nace ki rink'a dressing idan zaki je skool? Wato kin raina ni ko? Ni ban isa ince ga yadda zakiyi ba, kin tashi kinyi uban kwalliya kin tafi skool, a haka zaki karatun?" Kyarma hannunta ya fara yi, a karon farko kuma ta saci kallon kujeran da Ummi ke zaune amma bata ganta ba, cikin murya mai alaman ta kuka tace "I'm sorry Yaa Nawap, wallahi banyi dan na b'ata maka ba, bazan sake ba in sha Allah" wata muguwar tsawa ya daka mata wadda ta sa yan hanjinta motsawa lokaci guda, nan da nan hawayen da suka mak'ale suka gangaro saman fuskarta, ba tare da ya jira me zata ce ba ya datse wayan, sannan yayi wurgi da ita saman kujerar dake gefenshi.. BA’A SHAN ZUMA… 73-75 NA LUBABATU MAITAFSIR & BENAXIR OMAR Zubewa shima yayi a kujeran, ya rasa dalilin rasa natsuwarshi tun lokacin da ya ci karo da pic d'in da Deedo ta tura mashi ta whatsapp. Zuciyarshi da take wani tuk'uk'i yake dan bugawa a hankali yana fadin, "why! Why this for my lil sis?" Ya dad'e yana k'aryata zuciyarshi akan abinda take fada mashi, amma ina, ya riga ya gama yardan ma kanshi cewa yana cikin yanayi na soyayya! Soyayyar ma mai mugun tsanani, wadda take tattare da wani mugun kishi wanda har ya kan rasa inda zai tsoma ranshi a duk lokacin da ta taso mashi. Cikin k'unar zuciya ya furta "I love yu Deedo, why can't yu understand? Me sa baza ki kulan mun da kanki ba? Me sa kike neman halaka ni da soyayyarki" ba tare da ya tantance ba ya ji wata zufa ta karyo mashi duk kuwa da A.C dake palon, babu abinda yake tunani sai hanyar da zai je Kaduna, tunanin Deedo tare da son ganinta yana bala'in azabtar da shi da rayuwarshi. Kuka sosai Deedo ta cigaba da yi, ta rasa wannan wace irin rayuwa ce, ace a matsayinta na mace kuma 'yar jami'a amma bata da wani 'yanci nata na kanta? Tana tunanin tun da ta bar gidan Goggo tayi bankwana da bak'in ciki, ashe ba haka abun yake ba, mutum baya nan ma amma ya sama rayuwarta ido, shin wai ya yake so tayi ne? Jin alamar mutum na tunkaro palon daga hanyar kitchen yasa tayi saurin mikewa ta haye sama, Jan gado ta fada ta cigaba da rera kukanta inda a zuciyarta tana fadin baza ta k'ara bashi hak'uri ba, tunda dai ba wani abu tayi ba. Ta k'ara da cewar "kuma abinda nake in ba mai kyau bane ai Ummi baza ta barni nayi ba, dan haka taje can ta matse mashi mutum sai fad'an tsiya" a haka har aka kira maghriba, sannan ta mik'e ta shige toilet ta d'oro alwala. Tana gama sallan taji text ya shigo wayanta, sai da ta gama duk abinda take sannan ta dauko wayan, ga mamakinta taga ashe Yaa Nawap ne, gwiwa sake ta bud'a text din "text me the registration fees" taga ya turo, shiru tayi tana k'ara kallon wayan, inda take tambayar kanta "wai shi wane irin mutum ne?" Wurgar da wayan tayi ta mik'e ta sauka k'asa ba tare da ta mashi text din kud'in registration din ba, nan suka ci abinci, sannan suka cigaba da firarsu da Ummi. Jin shirun da Nawap yayi yasa ya kira number ta har sau biyu amma shiru, dan haka ya kira Ummi yana tambayar ko ina Deedon take. Bayan sun gama gaisawa da Ummi ta mik'a mata wayan, sannan ta wuce sama domin gabatar da sallan isha'i. Gaisheshi tayi ciki-ciki, haka shima ya ansa mata yace "baki ga text dina bane" "Ban gani ba na bar wayan a daki" "Oya kije ki duba, ki mun reply yanzu, ok?" "Ok zan duba" Ba tare da ya kara cewa komai ba ya kashe wayan, inda zuciyarshi ta cigaba da jin haushi da kuma son yarinyar da bata san ma yana yi ba. Mik'ewa tayi ta koma d'akin, ta d'auko wayan, nan tayi arba da missed calls dinshi, shiru tayi tana tunanin rashin kyautawar da tayi wa yayanta mai burin faranta mata a koda yaushe. Admission letter dinta ta d'auko ta duba kud'in registration din, ta rubuta, sannan daga k'arshe ta sa "I'm so sorry big bro, bazan k'ara ba" ta tura mashi. Yana kwance ya ji alamar text, da sauri ya duba wayan, nan ya ci karo da text din Deedo, wani lausassan murmushi ya saki, nan da nan kuma ya nemi damuwar da yake tare da ita ya rasa. Bai b'ata lokaci ba yayi mata mobile transfer ta kud'in registration din, sannan ya k'ara mata da 20k, yayi mata text cewar "in case idan kina da buk'atar wani abu" Washe gari ma da wuri ta shirya cikin turquoise blue din abaya ta yafa gyalen abayar ya zauna mata d'as, ta zaro handbag dinta mai tarkacen takardunta, ta sanya takalminta sannan ta k'arasa dakin Ummi. Ta zauna a gefe ta gaishe da ita, ta ansa tana mai sanya mata albarka, tayi mata sallama, suka wuce tare da driver. Ko da suka shiga skool tunanin abinda zata yi ta fara, bata san kowa ba bata san ko ina ba kuma, gashi bata da number Affan, dan haka ta wuce office din Dr. Kashim ba tare da wata damuwa ba. Abin mamaki tana isa kofan office din ta jiyo k'anshin turaren nan da ta ji jiya, ba tare da saninta ba ta lumshe idanu ta, sannan ta saki wani kyakkyawan murmushi, a dai dai lokacin shi kuma ya bude kofan ya fito. Kallonta yayi, ya tabbatar tana cikin nishadi, dan haka yayi saurin fadin "Hey beautiful" kaman daga sama taji muryanshi, hakan yasa ta kara sakin wadataccen murmushi, sannan ta gaisheshi, sai da ya k'are mata kallo sannan ya ansa yace "me kika zo yi nan?" "Neman wanda zai raka ni registration" ta fada kanta tsaye. Murmushi yayi, yace "ga wani kin samu, muje ko?" Ba tare da tace komai ba, tabi bayanshi suka fara tafiya. Suna yi suna dan fira jefi-jefi. A haka dai da taimakon Affan da kuma sanayyarshi da mutane ta samu ta kammala registration dinta, sai dai 'yan abubuwan da baza a rasa ba, wanda koda tana cikin lectures ne zata iya k'arasa su. Affan ne yayi mata rakiya zuwa bakin mota lokacin da driver ya zo d'aukanta, sai a sannan kuma ya anshi wayanta, yayi dialling number shi, sai da ya tabbatar ta shiga sannan ya mik'a mata, cikin wani salo yace "I'll miss you for a while" ba tare da tace komai ba, ta d'an saki murmushi, dan ta san itama har zuciyarta zata missing dinshi, saboda yan kwanakin nan da suke yawan kasancewa tare ta shak'u dashi da yawan zolayarshi. BA’A SHAN ZUMA… 76-78 NA LUBABATU MAITAFSIR & BENAXIR OMAR Kwanakin da tayi tana fita zuwa makaranta registration yasa tafara jin kad'aici da bata fita yau ba, zaune take tana karyawa da dankali soyayye da k'wai, wanda ta lafta ketchup akai, wayanta a hannunta tana game d'in candy crush, message ne ya shigo mata, cikin hanzari ta fita sannan ta duba, Affan ne ya turo mata "hey, ya gajiya?, sannan ya shirin fara lectures?" Tayi murmushi sannan ta ajiye fork d'in ta masa reply da "ga munan, munata shiri" Message taji ya k'ara shigowa, da sauri ta d'auka zata duba a zatonta Affan ne sai kuma taga sunan Ya Nawap, cikin sanyin jiki ta bud'e ta karanta "kin gama registration d'in ko da saura?" Ta mayar masa da "nagama Yaya, Allah bada lada" Murna yake ji da walwala idan yana musayar txt da ita, don haka sai yafara tunanin me zai kara ce mata, don yanzu so yake ya jata ajiki kasancewar yasan inda zata je, jami"a ba gidan wasa da dama bane, kar wani yaje ya hure mata kunne duk shukan da yayi wani k'ato ya girbe, ita kuwa tattara abincin tayi sannan takai kitchen ta nufi d'aki ta fara gyran wardrope d'inta wanda bata samu tayi ba saboda fita data keyi kwana biyu. Affan na k'ok'arin jan hankalinta wanda itama ta tattara hankalinta ta mayar gunsa, k'arshe yaga message d'in bazai yiwu ba don haka kawai ya kirata, murmushi tayi ta jawo earpiece ta saka sannan ta saka wayan a aljihun riganta ta cigaba da gyaran yayin da suke magana. Shikuwa Nawap ya mata text yana jira ta mayar masa da martani yaji shiru, ya fara tunani me yarinyan nan take yi tana gida yau kuma babu wani aiki da takeyi, baya son kiranta akan message d'in don haka ya kira Ummi ya fake da gaisheta yake yi sannan ya tambaya ina Deedo?, tace "tana d'aki" Sallama yai ma Ummi, sannan ya kira numbanta, sai kuma ya kashe, sai da ya samo abin cewa sannan ya kirata, number busy yaji, domin bata sa wayanta a call waiting ba balle ta san yana kira, tuni yaji gabanshi ya fad'i ganin sai kira yake yi amma bai shiga ba, har lokacin wayan take yi, tuni yaji zuciyarsa ta tokare, numfashinsa na neman guduwa gagara zama yayi yana jan tsaki, a kalla yakai minti talatin yana kira yana jin busy, bai san Affan da Deedo sunyi nisa a tad'insu na duniya ba. Wanda muka rasa gane shin soyayya ce ko kuma tsabar shak'uwa ce? Deedo da Affan suna cikin nishad'i domin kuwa wayan da sukeyi kowanne acikinsu najin kamar kada su rabu, sai taji tana Allah Alah afara lectures ko zasu na had'uwa da Affan sosai, siffarsa na mata gizo, tana tunanin halittarsa, duk da cewa bai manyanta sosai ba, anma namiji ne wanda ko wacce mace zata so ya kulata, don haka har ta gama aikinta, ta wanke toilet duk suna wayan, ta kunna ruwan wanka, sannan ta zauna akan gado, tanason cemasa zata shiga wanka tanajin kunya, don haka kawai sukayi ta tad'in makaranta yana bata labarin abubuwan dariya da al'ajabi dake faruwa acikin makarantan, Can dai ya dan nisa, yace "bari naje na karb'i aiki, zan kiraki anjima" suna sallama ta ajiye wayan, bata lura da text din daya shigo ba kai tsaye toilet ta shiga tafara wanka, tana shiga taji wayan na kara, Nawap ne yake kira akalla awa daya da minti sha biyar suna waya, jin wayan ta shiga yasa shi jan numfashi yana jira ta d'auka ya sauke mata kwandon masifa, sai kuma ikon Allah yana ta kira shiru, feedo kuwa jin kukan wayan ya tsananta tafara tunanin waye, don dai ita tasan Affan bazai kira yanzu ba, toh ko ma waye ya jira ta ta gama kammalawa. Sai da ta gama wankanta tafito, har lokacin wayan na kara, ta duba kawai ta d'auka gabanta na fad'i ganin sunan Yaa Nawap, a hankali ta saka a kunnenta sannan tace "ina wuni Yaya?" "Dawa kike waya for more than one hour?" Shiru tayi bata bashi amsa ba, wanda hakan ya kara kular dashi "Me kike so ki mayar da kanki?, daga fara makaranta tun kafin muje ko ina har kin fara tara maza?, ba na hanaki ba?, ko so kike na kwace wayan?, ki kiyayeni fa!, ki gaya mun da wa kike waya kuma!" Duk fad'an da yake yi bata bashi amsa ba, sai ma kukan da ta saka, a duniya babu abunda ya tsana ji kaman kukanta, a take ya rud'e sannan yace "Ji fa, fisabililah daga miki magana kin fara min kuka ke kinfi kowa yawan ruwan hawaye ne?" Bata amsa shi ba sannan ba ta daina kukan ba, zuciyanta na kunci, ta rasa meke mata dad'i, kashe wayan tayi alokacin ta ga missed call 42, ga messages guda hudu, duk nashi ne, sai taji wani iri ta tabbata yayi ta kirane yaji shiru yasa yake fad'a, batason taji yana mita ko fad'a , don haka saida ta ida hawayenta a lokacin text d'in affan ya shigo "Yh, how far r u done?" Saitayi shiru tana tunani, ta tabbata ita bata ce masa zata yi wani abu ba, shi yace bari yayi abu anma sai gashi yana tambayanta, murmushi tayi ganin cewa ya gane akwai uzuri agabanta har ya saurara mata, tuni ta manta da batun Nawap, yayinda shikuwa gogan yana zaune yana jira yaga text d'in ban hakuri, Ba tare da bata lokaci ba ta yi reply wa Affan da "ae am done" Aikuwa sai gashi ya kira, aka cigaba daga inda aka tsaya, Nawap ganin bata turo masa komai ba yasa yayi tunanin ko kuka take har lokacin don haka sai ya kara kiran numban don yaji ko lafiya, number busy da ya ji yasa ya daki teburin dake gabanshi, sannan yaja wani mugun tsaki! Wanda muma sai da muka tsorata.. Wayansu suke hankalinsu kwance, domin kuwa yadda Affan ke fada mata kalamai masu kwantar da hankalin mai sauraro yasa ta manta da batun fad'an da Nawap ke mata kwata kwata, cikin wani irin salo na karya murya yace "Feedo na yaushe zan ganki dan Allah?" Wani irin abu taji har cikin zuciyarta, dak'yar ta gyara murya tace "ni ba sunana Feedo ba, ka kira ni Deedo yadda kowa ke kira na" kaman yana gabanta ya mak'ale kafad'anshi yace "no, ni ba kowa bane so zan na kiranki Feedo cuz ya fi mun dadi" Bata k'ara cewa komai ba sai wani farin ciki da take ji yana ziyartanta, haka suka yini suna wayan nan inda ta b'angaren Nawap kuwa, fashewa ne kawai bai yi ba saboda bak'in ciki. Ana gab da kiran azahar sannan Affan yayi mata sallama, ba wai dan sun gaji da juna ba, kawai dan ya bata daman aiwatar da abubuwan da suke gabanta hankali kwance. Suna gama wayan ta d'an mik'e rigingine a gado sannan ta rungume wayan a k'irjinta, ta rasa me sa take jinshi har cikin jininta, saboda ita dai bata tab'a shiga irin yanayin nan ba. Mik'ewa tayi da niyyar ta d'oro alwalla, amma taga wayanta yana blinking alaman tana da sak'o murmushi ta saki, inda cikin zuciyarta tace "Affan baya gajiya shi kam" toilet din ta zarce tayi alwalanta ta fito ta tada sallah ta gama, ta shirya tsab, sannan ta dauka wayan ta sauka k'asa. Dinning ta wuce ta zuba abinci, sai da ta fara cin abincin sannan ta duba wayan, gabanta ne ya fad'i dam! Kasancewar karo da tayi da text din Ya Nawap kamar haka "are yu insane? Kin maida ni k'aramin yaro ko? Shi yasa ina maki magana kika share kika cigaba da wayanki. Ki shiga hankalinki tun kafin na iso garin nan" Ture plate din tayi a gefe ta dafe kanta, "wai shi meye nashi da yake neman matsa ma rayuwata?" BA’A SHAN ZUMA… 79&80 NA LUBABATU MAITAFSIR & BENAXIR OMAR Wani fanni na zuciyarta ne yake fada mata "ya damu da ke ne da kuma al'amurranki, kuma ko bakomai Yayanki ne wanda ya cancanci kiyi mashi biyayya a kowane irin hali" girgiza kanta tayi, alaman ta gamsu, a karo guda kuma ta fara kiran numbershi amma shiru. Saida ta kira har sau hudu, amma bai dauka ba, hakan ya tabbatar mata cewar lallai Nawap yayi fushi da ita, daga k'arshe da taga zaman ba zai kaita ba, dan haka ta yanke hukuncin tura mashi text na ban hak'uri, inda take bayyana mashi cewar ba wai abinda yake tunani bane. * **** Wasa wasa har ta suka fara lectures, amma Nawap bai k'ara bi ta kan Deedo ba, dan ko waya suke da Ummi da ta bata wayar yake kashewa. Bata damu da irin abinda yake yi ba, dan a tunanin ta ko ya bata freedom dinta ne, dan haka ta ba Affan dama suka fara shimfid'a nagartacciyar soyayya mai asalin dad'i da kuma tsafta, hakan yasa har aka fara sheda su a cikin makaranta, dimin ko da yaushe suna manne da juna, idan bashi da lecture haka yake rakata har sai ta gama lectures, yayin da itama hakan yake a wurinta, basa iya rabuwa ko kadan sai abinda ya zama dole. Yau ma kamar kullun zaune suke gaban faculty suna tad'insu na masoyan da suka zurfafa a cikin son junansu, wata bak'ar mota k'irar Corolla S ce tayi parking daga gefen da suke. Kamar ance ma Deedo ta kalla wurin, cikin firgici tayi arba da fuskar k'awar nan ta Aysha wadda suka nad'a mata duka a saloon. Cikin yanayi na mamaki matar take kallon Deedo, bata gaskata abinda take gani ba saida tayo tattaki har zuwa inda suje, a dai dai lokacin ita kuma Deedo tace ma Affan ya tashi su bar wurin. Mik'ewar da zasuyi taji caraf matar ta damk'e hannunta gam, cikin fargaba ta zare ido tana kallonta, can murya dashe tace "ina wuni aunty" wani malalacin murmushi matar ta saki, sannan ta matso daf da kunneta tace "hey you lil bitch! Nan kika dawo kenan? Kin bar mu muna shan wuyan nemanki. Ina mai yi maki albishir da ki shirya taranmu nida k'awata, domin muna nan zuwan miki, domin ke baki kai matsayin fa za'a ci mana mutunci saboda ke ba" tayi wurgi da hannun sannan ta dafa kafadarta tana murmushi tace "see you 'yan mata" ta juya ta cigaba da tafiyan ta. Sai a lokacin Affan ya kula shi kadai yake tafiya, bai wani b'ata lokaci ba ya dawo, yace "meke faruwa ne? Kin bar ni ina tafiya ni daya" Murmushin yak'e ta k'ak'alo, tace "I'm sorry, ina gaisawa da mutane ne, muje mu tafi" a dai dai nan drivernta ya iso, dan haka sukai sallama ta wuce gida, zuciyanta fal da tsoro da tunanin abinda zai biyo baya. Lokaci na tafiya, yayin da abubuwa da dama suke shud'ewa, rayuwar Deedo ta zama sabuwa, ta inda in ba wanda yayi mata cikakken sani ba, ba lallai ya gane ta ba, ta zama cikakkiyar budurwa mai madaidaitan shekaru kusan goma sha bakwai, (17) kenan, ta waye ta goge, tayi clean abin sai dai wanda ya gani. Da sauri take ta shiri dan tana da exams k'arfe biyun rana, kasancewar sun fara exams d'in first semester, gashi kuma tana son ganin burin ziciyarta kafin ta shiga exams din. Duk wannan abu da ake, har yau Nawap bai shigo Kd ba, ta inda ya daina kiran ta kwata kwata, ya kuma daina chatting da ita ta ko ina. Wannan ya bata damar sakankancewa ta cigaba da b'arje gumin soyayyarta, ita da Affan. Hakan bai k'ara komai ba, sai asalin so da kuma k'aunar Deedo wanda suka cigaba da wanzuwa a cikin zuciyarshi, suke kuma azabtar dashi. Kasancewar yau Juma'a, da wuri ya tashi ya fara shiri, jakunkunanshi guda biyu babba da k'arama ya jawo ya cika su dam, da kayanshi, ya tattara takalmanshi, da duk wani abu mai muhimmanci, sannan ya wuce toilet yayi wanka, ya fito. Fuskarshi babu yabo, babu fallasa, haka ya fara shiri, ya gama tsab, ya fito cikin shaddar Gezna fara k'al, ya d'ora hularshi zanna mai kwalliya bak'i da ash, ya sanya bak'in takalmin ALDO, sannan ya d'aure hannunshi da lafiyayyar b'akar agogon fata, ta Promado Royal. Dan da nan ya fito tass dashi kamar sabon ango, ya feshe jikinshi da turaruka, sannan ya fara kwasar kayan shi yana sanyawa a boot din motarshi. Gudu yake yi sosai, domin baya son ya tsaya ko ina sai a cikin garin Kaduna. BA’A SHAN ZUMA… 81&82 NA LUBABATU MAITAFSIR & BENAXIR OMAR Cikin ikon Allah Nawap ya iso Kaduna k'arfe d'aya da yan mintuna, bai b'ata lokaci ba ya wuce massallacin Juma'a yabi jam'i, sannan ya wuce gida. Ummi tana zaune ta ganshi kamar wanda aka jefo daga sama, da murnanarta, ta tarbe shi tana mashi lale marhabun da mutanen Abuja. Cikin jin dad'i ya zauna suka gaisa, sannan suka cigaba da tad"insu na d'a da mahaifiyar da suka dad'e basu ga juna ba. Ido ya ware yana ta jiran saukowar Deedo, amma shiru kake ji, Ummi ce ta so ta fahimci halin da yake ciki, kasancewar yadda yake yawan kallon stairs din benen, dan haka tace "wai baka ce ina auta ta ba" Yace "ina niyyan tambayarta inda take ai Ummi" "tana skool, kasan har sun fara exams" nunawa yayi kaman bai sani ba, yace "eyya, abin ba wuya kenan, to Allah ya taimaka" Ummi tace "amin." Har ya mik'e zai wuce side dinshi, ya juyo yace "k'arfe nawa zata gama exams din na yau?" "K'arfe biyar" Ummi ta bashi ansa, bai k'ara cewa komai ba, ya wuce domin ya samu damar hutawa. * ** K'arfe hud'u da kamar minti ashirin, Aysha tare da k'awarta mai suna Baby Labo, suka yi parking motarsu gaban faculty of medicine & surgery. Baby ce ta fara fitowa kasancewar ita ta san kan makarantar, saboda anan take masters dinta, itace kuma ta binciko cewar Deedo tana da exams yau, da misalin k'arfe biyu zuwa biyar na yamma. Bayan Nawap ya dan huta, ya tashi yayi sallan la'asar, sannan ya shirya, ya zari key din motarshi, ya fito. Wurin Ummi ya k'arasa yace zai je ya d'auko Deedo ba sai driver ya je ba. Allah ya kiyaye Ummi tai mashi, sannan ya sa kai ya wuce, zuciyarshi duk a dagule, ya rasa abinda yake mashi dadi.. Kasancewar basu da nisa sosai yasa ya isa wurin da misalin k'arfe biyar saura kwata. Gefe guda yayi parking ta inda zai iya hango duk wani mai shiga da mai fita a harabar wurin. Cikin jin dad'i Deedo ta fito daga exam hall tana ta faman fara'a, kasancewar ta rubuta komai da aka tambayeta, murmushi ta saki a lokacin da ta hango abar k'aunarta rungume da hannayen shi, a gaban hall din yana jiran k'arasowanta. Wayarta dake cikin jakar hannunta ta fara ruri, ta fito da ita ta duba, Hally ce ta kira ta, da sauri ta d'auka suka fara gaisawa, tayi mata ya exams, ta ansa da "lafia lau 'yan mata, ya skool" "ina gida ma wlh, kinsan an sa ranan bikina" "amma baki da kirki, shine baki fadi mun ba" "jiya ne fa aka sa, kuma naga kina da exam yau, shi yasa nace idan kin fito zan kira na fada miki" murmushin jin dadi Deedo tayi, tace "Bauchi dai ta aureki kenan, ai nasan dama baza ki bar Mubarak din nan ya wuce ki ba" duk suka sa dariya, tayi mata fatan alkairi, sannan tace "say hi to my boo" ta mik'awa Affan wayar, ya ansa suka gaisa, kasancewar ya san labarinta tsab a bakin Deedo. Ansar wayar tayi bayan sun gama gaisawar, tace "zamuyi waya anjima" "ke ban gane ba, ina Ya Nawap din?" Hally ta tambaya, "ke ki share, bakomai fa tsakanin mu" "ni dai nafi son ki da shi Deedo, wannan daga ji ma dan yaro ne, irin chewing gum guys din nan wallahi" murmushi tayi, tace "zamuyi waya anjima" ta kashe wayar ta jefa a jaka, suka jera da Romeo dinta, suna tafe suna firansu abin gwanin ban sha'awa, sai dai wanda ya gani. Gaban faculty suka isa, saman wasu kujeru suka zauna suna ta zabga soyayyarsu, su Aysha da suke gefe suna jiran fitowarta ne suka hango kamar ita, dan haka duk suka fito a motar, a dai dai lokacin wani abu yazo zai fada idon Deedo, Affan yace ta rufe idonta ya cire mata, hannunshi da ya sa zai cire abun, yayi dai dai da d'agowar Dr. Nawap ya kawo kallonshi kan kujerun da suke. Daaaaaaam! Yaji zuciyarshi ta buga a lokaci guda, wani bak'in kishi ne ya ya kai mashi ziyara, yayin da a karon farko yaji k'wanyarshi na shirin d'inkewa! Da sauri ya fito, a dai dai lokacin kuma su Aysha suka k'arasa wurin inda Baby tasa hannu ta finciko gashin kan Deedo wanda ta daureshi a baya, gyalen kanta ta fara k'ok'arin warewa, amma Allah ya bata sa'a ta rik'e shi gamda hannunta. Affan yayi saurin mik'awa yana fadin "what the hell are you doing? Ke wacece?" Isowar Nawap yayi dai dai da shiga hankalin kowa da yake wurin in banda Affan wanda bai taba ganinshi ba, bai kuma san daga ina yake ba. Deedo dake lab'e bayan Affan tana raba idanuwa tuni tayi saurin fitowa, ganin Idanun Nawap sun sauya kala daga fari zuwa jaa, ta san cewar yau k'aryarta ta gama k'arewa. Hannunta ya finciko tun k'arfinshi ba tare da ya cewa kowa komai ba, shima Affan bai yi k'asa a gwiwa ba yasa hannu cikin izza yana jawota daga hannun Dr. Nawap!… BA’A SHAN ZUMA… 83&84 NA LUBABATU MAITAFSIR & BENAXIR OMAR Nan da nan hankalin mutanen da suke wurin ya dawo kansu, kafin kace wani abu wuri ya cika mak'il da mutane iyayen son jin k'wak'waf. Juyowa Nawap yayi idon shi ya k'ank'ance, kallon Deedo yayi cikin wani irin yanayi yace "I'm disappointed in you, abinda kika koma yi kenan? Irin tarbiyyar da aka baki kenan? Who's this guy?" Ya fada da wata irin tsawa, wadda tasa 'yan cikin Deedo kadawa a lokaci guda. Cikin muguwar tsawar da tafi ta dazu yace "I'm talking to you, kin tsaya kina mun shirme, me sa kika zubar da k'ima da darajarki ta 'ya mace? Me sa kika yi watsi da hudubar da na dade ina yi miki? Me sa baki fahimci abinda nake ji game dake ba? Me sa baki kulan mun da kanki ba? Me sa kika kasa gane cewar duk abin da nake ina yin shi ne sabo da SO da K'AUNAR da nake miki? I LOVE YOU DEEDO y can't you understand!?" Numfashin Deedo ne ya fara k'ok'arin sark'ewa, cikin tashin hankali ta d'aga kai ta kalle shi, sai a sannan abinda ya fad'a ya fara yawo a kanshi, "damn it" ya fad'a tun k'arfinshi, sai kuma a lokacin Affan ya samu bakin magana, ya k'araso gabanshi, ya kalle shi ido cikin ido, yace "malam kai kuma daga ina? Me hadinka da matar da zan aura?" Wani mugun kallo Nawap ya watsa mashi, a yayin da ya dunk'ule hannunshi yana shirin kai wa bakinshi naushi, ko me kuma ya tuna, kawai ya saki hannun ya juya, a fusace ya fara tafiya. Aysha da kuka ya k'wace mata, ta bi bayan shi, da sauri ta tari gabanshi tace "Nawap nice mai sonka, wadda take k'aunarka, zan iya jure ko wane irin cin fuska in dai daga gare ka ne, me sa baza ka bani dama na nuna maka irin yadda nake son ka ba? Ka taimaki rayuwa ta Nawap!" Gefenta ya bi, ba tare da yace mata uffan ba, ya shige motarshiya tada da wani irin k'arfi, ya wuce ya bar wurin.. Kuka sosai Deedo ta saki ganin Nawap ya ja motarshi ya tafi, Affan ya matsa gabanta ya fara lallashinta, yana fad'a mata kalamai masu dad'i wanda suke tafiya da ita da imaninta. A sannu a hankali ta samu natsuwarta, ta kalleshi tace "ka fitar dani bakin gate na samu abin hawa, nasan driver ba zai zo ba" "no, bazan iya barinki ki tafi ke daya ba, muje na kaiki gida" dak'yar ya lallabata, ta tashi, inda yayi parking motar shi suka isa, ya bude mata gaba ta shiga, sannan ya maida murfin ya rufe, ya zagaya ta mazaunin driver ya shiga ya tada suka tafi. Baby Labo da akaje da niyyar dambe, can na hange ta, taja k'afafun nan nata masu kama da na sauro ta k'arasa gaban k'awarta, tana bata baki, dak'yar Aysha ta mik'e saboda kukan da take, haka dai ta kamata suka shige motarsu suma suka kama gabansu, ta inda suka fara tunanin canja shiri akan na dukan Deedo da suka zo dashi. Har sai da Nawap ya kawo gida, sannan ya fara tunanin halin da ya baro Deedo, amma dakewa yayi, ta inda yake ganin koma me yayi mata, itace ta ja wa kanta, dan haka bai shiga gidan ba, yayi parking nesa kadan da gidansu, yana jiran yaga yadda za ai ta dawo gida. Kusan mintuna ashirin ya share yana jiran zuwanta amma shiru, dan haka ya tada motar da niyyar ya shige gida, sai kuma ya hango wata ash din Toyota Supra na k'ok'arin danna kanta a gate din gidan su. Dakatawa yayi, har motar ta shige, sannan ya bi bayan ta shima ya shigar da tashi, nan ya ci karo da Affan ya fito, ya bude wa Deedo k'ofa yana aika mata da wani sak'on kallo mai tattare da so da kuma k'aunar juna.. BA’A SHAN ZUMA… 85&86 NA LUBABATU MAITAFSIR & BENAXIR OMAR Fitowa yayi zai shige kaman bai san da halittar mutane agun ba, a zahiri kuma zuciyarsa tafasa takeyi, tana ingizashi da yaje ya kama Affan da duka, can kuma har zai shiga daga ciki wanda Affan jikinsa yayi sanyi ganin cewa cikin d'aya ko yayanta ko dan'uwanta bai ankara ba yaji Nawap na cewa maigadi "yaushe ka fara barin samari suna shigo mana cikin gida?" Dasauri mai gadin ya nufi inda Affan yake tare da cewa "mai gida don Allah kad'anyi hakuri" Wani k'ullutun bak'in ciki yaji a zuciyarsa yana kallon Nawap anma rashin sanin wayeshi yafi komi 6ata mishi rai, ya kalli Deedo wacce duk ta rikice tana neman madafa yace "ki shiga zamuyi waya" tayi shiru kaman zatayi magana saikuma ta shige, motarsa yaja yafice yayinda shikuma Nawap yashige palo ya zauna, yana ajiyar zuciyar kamar wanda yafito daga filin daga. A hankali take tafiya zata wuce yace "zo nan" jikinta na bari ta zo ta tsuguna kanta a kasa, cikin mugun gushi yace "Inaso kigayamun wanda yabaki izini kiyi saurayi" shiru bata amsa ba illa hawaye da yake kokarin zubowa, ganin hawayenta yafi komi cimasa rai anma haka yarufe ido ya fara zuba mata yayyafin masifa ta inda yake shiga ba ta nan yake fita. Muryarsa Ummi tajiyo tafito, a yadda yake masifan kaman uba ya kama 'yarsa tana zina, abin ya matuk'ar bata mamaki sanin cewa bata taba ganinshi awannan yanayin ba, idonsa yayi jajur ya cicciko, ya kalli Ummi sannan yace "Ummi da wani fa na ganta" Sai da ta nemi wuri ta zauna sannan tace "toh daka ganta da wani shi ne yazama laifin me? Wayeshi kekuma?" Kuka take sosai yayinda ta goge hawayenta tace "wanda ya tayani registration ne" Nawap ya katseta da cewa "ohhhh shine kuka hau soyayya, Ummi can u imagine har yana ce mun ni waye meya had'ani da matar da zai aura" Abun yabawa Umma dariya ganin yadda Nawap karara yake nuna kishinsa. Anan tace wa Deedo ta tashi ta shiga ciki, shikuma tace " kamata yayi in sonta kakeyi ka fad'a mata, baka fito kana takura mata ba, zata tsaneka, mu mata bama son takuri munfi gane lallab'i inka bincika lallab'ata yakeyi shima wancen din" fuskarshi cike yace "Ummi yaro ne fa, irin chewing gum boys din jami'a" Dariya tayi sannan tace "ahaka kuma ya take ka agun nema ba, dole ka koyi sassauci ka koyi danne zuciyarka idan mace kakeso, kacire maganan dizgi da takuri karka kara yiwa y'ata tsawa haka, ji yadda ka sata zubar da hawaye" tana gama fad'in haka ta mike ta bi sawun Deedo wacce ko da taje d'akin ma fad'awa tayi akan gado tana kuka, har ranta bataji dadin yadda Nawap ya mata ba, sai dai ta wani fannin kuma ji tayi kaman ansauke mata dutse a ranta ganin yau ya furta mata da kanshi cewa yana sonta.. BA’A SHAN ZUMA… 87, 88 & 89 NA LUBABATU MAITAFSIR & BENAXIR OMAR Da murmushi Ummi ta shiga d'akin, wuri ta samu a bakin gado ta zauna, sannan ta kai dubanta ga Deedo wadda take kuka bil hak'k'i da gaskiya. A hankali ta furta "oh, auta ba dai abinda wancen yayi miki bane kike kuka?" Sai a sannan Deedo ta san da shigowarta, kasancewar kanta na kasa tayi ruf da ciki. Ba tare da ta jira ansarta ba ta cigaba "ke manta mun da shi auta, babu wanda zai miki dole kinji 'yar albarka, dan haka tashi maza, ki wanke fuskar nan taki bana son ganin bacin ranki 'yar auta ta" cikin jin kunya, Deedo tana sum sum da kai ta mik'e ta shige toilet, wanka tayi sosai, sannan ta fito, amma bata tarar da Ummi ba. Shiryawa ta cigaba da yi dan lokacin maghriba ta gabato, kasancewar tana hutun sallah, ga wani yunwa da yake addabar cikinta yasa tayi gaggawan sauka kasa domin ta samu abinda zata ci. Zaune ta tarar dashi a kujerar da ta barsa ya k'ura wa halittar t.v ido, amma daga dukkan alamu, bai san abinda ke faruwa cikin t.v din ba. Sad'af-sad'af tayi ta shige kitchen, shi kam jin kanshin turarenta yasa yayi zumbur, ya dawo daga dogon tunanin da yake. Mik'ewa yayi yabi hanyar kitchen din, can ya hango ta tana faman daga manya manyan food flask din da su kan zuba abinci. A kofan kitchen din ya harde hannayrnsa, ya zuba mata idanu wanda bata ma san Allah yayi ajiyarsa a wurin ba. Ta gama dibar abincinta, tana k'ok'arin fitowa, amma ya kare hanyar ta yadda baza ta iya wucewa ba matuk'ar bai bata hanya ba. Ido ya k'ura mata sosai ta yadda ba wani motsi da zata iya yi. Take ta daburce, ta nema natsuwarta ta rasa, bata ta6a tunanin Nawap na da kyau haka ba, ga wasu irin idanunshi masu kamar yana jin bacci, dak'yar ta sauke idonta a kansa, cikin k'arfin hali tace "zan wuce Yaa Nawap" bai ce komai ba, sai ma gyara tsayuwarsa da yayi, ya fuskance ta sosai. Har ya daga baki zai fara masifa, sai kuma ya tuno da kalaman Ummi wanda tace "mu mata mun fi son lallami" sumarsa ya shafa, cikin boron kunya ya daure yace "Lil sis, yanzu haka kike ganin ya dace ace munyi dake?" Bata ansashi ba, dan haka ya cigaba "ban son yadda akai na kamu da soyayyarki ba, haka na tashi na tsinci kaina a cikinta, amma a tunanina, baza ki ta6a gujewa duk wani abu da ya shafe ni ba, matuk'ar ba sa6on Allah bane." Ya ja gauron numfashi sannan ya cigaba "soyayyarki ta riga ta yi mani mugun kamu, wanda in har ban samu goyon bayanki ba, komai zai iya faruwa, amma idan kina ganin zan takura ki, fine, kina da 'yancin da zaki zabar ma kanki dukkan abinda kike so, amma kafin kiyi saurin yanke hukunci, ina son kiyi nazari, duk shawarar da kika yanke, zan aminta da ita, matuk'ar abin zai zama farin ciki a gare ki." Ya gyara mata hanya, yace "zaki iya wucewa" bata ce uffan ba, ta bi gefensa ta wuce palon, yayin da shi kuma ya fito ya kwashe wayoyinsa, sannan ya wuce part dinshi. Juyawa spoon din hannunta kawai ta cigaba da yi, ita dai ta san bata k'in Yaa Nawap, dan shine mutun na farko da ya daga darajarta a lokacin da bata da wani gata balle kuma 'yanci, shine wanda ya inganta rayuwarta da farin cikin da ta dade tana mafarkin samu. To amma ya zata yi da Affan wanda ko wane bugun zuciyarta yake fita da son shi da k'aunarshi? Ya za ta yi da shak'uwa da karamcin da ya nuna mata a cikin dan k'ank'anin lokacin da ta san shi? "Ya Allah ga ni gare ka" shine abinda ta furta, tare da ture plate din da yake gabanta zuwa gefe. Wayanta ne ya fara ruri alamar text yana shigo mata, hannu ta sa ta ciro shi a aljihun dake jikin rigarta, text din ta fara dubawa kamar haka "Hope you're fine Feedo na?" Murmushin k'arfin hali ta saki, sannan ta fara typing mashi ansa "I'm good, kayi hak'uri da abinda ya faru dazu fa" Take ta ji ansar shi ta dawo mata, "never mind dear, but wanene shi a wurin ki?" "Cousin dina ne" ta maida mashi ansa itama. Dam! Zuciyar Affan ta buga, ba don komai ba sai don jin dangantakar dake tsakanin Nawap da Deedo, shi dai yana son ta, har cikin ransa, amma ya san aure tsakanin su abu ne mai matuk'ar wahala, domin ko ga Dr. Kashim nan har yanzu bai yi aure ba, ya san da kunya ya kai batun nashi auren daga gama skool dinshi, sannan yanayin da Nawap ya shiga a yau, ya tabbatar mashi da cewar yana k'aunar Feedo fiye da yadda yake son ta, kuma ko bakomai zai so mata abinda yake mafi alkairi ne a gare ta, dan haka yana jin zai iya sadaukarwa Nawap da soyayyar da yake wa Feedo ba don komai ba sai dan cancantar shi da ya gani. Jin shiru bai dawo mata da ansa ba yasa ta k'ara tura mashi "are you there?" Shigowar message din ne ya katse tunanin shi, a hankali ya share zufanda ta karyo mashi, sannan ya fara rubuta mata ansa "ki fada mun gaskia kina son shi ko?" Kamar daga sama ta ji tambayar, haka dai ta daure tace "I can't say Affan, but, shine mutumin da ya 'yanta ni, ya mayar da ni abinda nake a yau" "Ok, na fahimce ki, ki kwantar da hankalinki, zamu yi magana anjima kinji?" "Alright, take care" ta tura masa, sannan ta mik'e a 3seater ta cigaba da tunanin halin da take ciki. Number Hally ta fara kira amma har ta katse shiru bata daga ba, dan haka ta shafa mata lafia, don ta san indai ta gani, to zata kira ta. BA’A SHAN ZUMA… 90&91 NALUBABATU MAITAFSIR & BENAXIR OMAR Tunani kam tayishi harta gaji, ta rasa me zatayi, don tasan ba karamin butulci bane tace taki jinin ummi, Shikuwa acikin kwanakin yakara daburcewa yadawo wani iri har Ummi tagane saidai bata ce masa komi yadawo baya ko kulata ayayinda shikuma Affan yariga da ya cire abun aransa yasawa kansa cewa ya hakura kawai, tunda tamishi bayanin komi na rayuwanta da nawap, randa taje makaranta lectures ma sun zauna anan yace mata "ina ga zan baki zabi ne, kije kiduba kiga wa kika fi so, zanzama mai farin ciki da bayaninki, zan kuma yarda da kaddara, saidai kisani cewa inasonki ba kuma zan hadaki da wata ba, niyyata na aureki" Har ya idar da bayaninsa batace komi ba, ita dai ta shiga rudani gashi shareta da nawap keyi yakara sata awani damuwan. Nawap a gida yasamu ummi ya ce yana son magana da ita, ta ce "toh" sannan ta zauna yafara sosa keya sannan yace "Ummi na zauna nayi tunani ne, wlh inason Feedo ba kadan ba, don Allah ummi ki mana aure" tunda ya fadi kalmomin sa tasan cewa tabbas dagaske yanason feedo din tunda tasan shi mutum ne mai balain kunya, bai taba tunkararta da magana shige irin wannan ba tayi murmushi sannan tace "Ai dole sai yar tawa ta Amince, zan mata auren dole ne aka gaya ma?" Yayi shiru don bai tabbatar tana sonshi ba yace " zata cemiki tanason wani ne, wlh ummi kar ki yarda, yaro ne yaudaranta zaiyi" itadai ta zura mishi ido aranta kuwa kaman ta juye ruwa a kasa tasha don murna, tadade tana adduan Allah yanuna mata wannan rana da zata hadasu aure, shikenan tuwonta maiyanta, Feedo kuwa bayan tagama tunaninta duk ansa daya ta kare dashi, wato nawap takeso, takira Affan tace inta gama lectures suhadu nan ya amince, ko da yazo yazauna akan kujera a dept dinsu datake jiranshi, ta ce "ni dai nasan randa nafara soyayya dakai, bantaba yi don ranka yabaci ba, banyi don na yaudareka ko na rabu dakai daga baya ba, ban yi da zuciya biyu ba, anma kasan dan adam ajizi yau an wayi gari bakai din zancigaba da so ba, maganan gaskiya yaa nawap nafara so arayuwata, shi ya maidani mutum har ka ganni kakeso, shi ya taimakamin kuma yana kai, mahaifiyarsa ita tarikeni da zuciya daya, ban mata adalci ba ace dan cikinta guda yace yana sona naki yarda, ba zata ji dadiba duk da zata nunamin ba komi anma danka naka ne, kayi hakuri ka gafarceni" tana fada ta share hawayenta, shima kallonta yake har ransa tausayinta yake ji, yace "bakomi wallahi, na fahimceki sosai ubangiji Allah ya sa hakan shiyafi alheri, nima Allah hadani da wata" nan suka danyi tadi sannan ta mike don komawa aji BA’A SHAN ZUMA… 93,94&95 BA'A SHAN ZUMA… 93 NA LUBABATU MAITAFSIR & BENAXIR OMAR ®NWA Gida ta dawo zuciyarta wasai, tana jin tamkar ta sauke wani gagarumin nauyin dake kanta. Bayan sun gaisa da Ummi ta wuce sama, don ta shirya ma wannan rana, domin alkawari ta yi yau zata fada ma Yaa Nawap ta ansa tayin soyayyarsa, don haka take son tayi surprising dinshi ta hanyar kawata mashi kanta da ado na ban mamaki da daukar hankali. Number sa ta laluba ta kira amma a kashe, ba tare da wata damuwa ba tai mashi text "I need to see my big bro" ta tura, amma bai yi delivery ba, hankali kwance ta gama shirinta tsab, ta sauko kasa amma ba kowa a palon, ga wani shaukin son Yaa Nawap da yake fisgarta, bata da buri a lokacin wanda ya wuce mata ganin fuskar shi. Ko ina ta dudduba amma babu kowa a cikin gidan, ba tare da wata fargaba ba ta zarce part dinshi, a hankali ta tura kofar palon, amma ga mamakinta ta jita a datse gam. Cikin natsuwa take kwankwasa kofar amma shiru, dukawa ta yi ta dan leka ta inda ake sanya key, nan taga jam lock, cikin rashin jin dadi ta juyo ta dawo cikin gidan, a palo tayi arba da Ummi, nan ta fara kame-kame, amma Ummi ta basar tace "ina kika shiga ina ta kwala kiranki?" "Na dan zagaya nan baya ne in sha iska Ummi" tace "to, wuce ga abinci can" dining area ta nufa ta zuba abincin ta ci gaba da juya spoon din tana tunanin inda Yaa Nawap ya nufa, domin shi dai yawo ba al'adarshi bace matsawar yana gari to fa kullun yana gida kaman mace. Ummi tana hankalce da yanayinta amma ta basar, don bata son ta takura mata sai taga kamar don ba ita ta haifeta bane. Spoon biyu kawai tayi a abincin ta taso ta dawo gefen Ummi ta zauna ta kurawa wayanta ido tana jiran taga delivery na sakon da tayi wa Yaa Nawap. Can dai zuciyarta ta kasa daurewa, tace "Ummi ni kam ina Yaa Nawap ya shiga? Rabon da na ganshi tun shekaran jiya" murmushin jin dadi Ummi tayi a fakaice, ta san ko bakomai d'an nata ya fara samun kar6uwa a zuciyar Deedo. Ta kalleta tace "jiya tun kafin ki tashi bacci ya koma Abuja an mashi kiran gaggawa" ta dan saci kallon ta taga yadda hankalinta ya tashi lokaci guda, sannan ta cigaba da magana… BA'A SHAN ZUMA… 94 NA LUBABATU MAITAFSIR & BENAXIR OMAR ®NWA "Bayan ya isa kuma wurin karfe shidda na yamma ya kira ni yake sheda mun cewar yau da misalin karfe biyar na asuba zasu tashi zuwa London, an tura su yin wani course na shekara ukku" tana kawowa nan taja bakinta tayi shiru, tana mai cigaba da kallon akwatin t.v. Mikewar da Deedo zata yi taji wani mugun jiri ya kwashe ta, kukan da take makalewa a take ya subce mata tagal tagal tayi, tana me kokarin faduwa, nan Ummi ta kwashi salati tana kwalawa Saude mai aiki kira, cigaba da jijjigata tayi tana fadin "lafiya Deedo? Menene abin kukan?" Cikin rashin sani Deedo take magana "Yaa Nawap me sa kai mun haka, bayan kasan kaine buri na, kaine farin cikin rayuwa ta" kuka ta kuma fashewa da shi ta koma kaman zararriya, ta kalli Ummi da tausayin Deedo ya cika ta, tare da jin dadin kalamanta, tace "Ummi da gaske Yaya ya tafi ya barni? Ummi ya zan yi da DAKON SO (Na KAUSAR LUV) na Yaa Nawap da nake fama dashi?" Ta k'ara fashewa da wani kukan mai ban tausayi.. Dak'yar Ummi ta lallaba Deedo a wannan rana, banda kuka ba abinda take yi, haka dai Ummi ke kwantar mata da hankali, yayin da wutar soyayyar Nawap take faman kara ruruwa cikin zuciyarta tamkar ana watsa mata fetur. * ***–****** Da sallama suka shigo palon ba kowa sai Deedo da ta kurawa wani makeken hoton Yaa Nawap dake mak'ale a palon ido, wanda ya kasance sana'arta kullun da ta dawo daga makaranta bata da sauran aikin da ya wuce ta zauna gaban wannan hoto tayi ta kallonshi, wani lokacin har da yan sambatun da baza a rasa ba. Aysha ta karasa ta dafa kafadar Deedo, sai a sannan ta dago a razane dan ko alama bata ji shigowar mutun ba. Kallonta tayi a tsorace, inda ita kuma ta sakar mata murmushi tace "Ina Ummi fa?" Murmushin k'arfin hali ta mayar mata, tace "ku zauna mana, taje unguwa ta dawo" su Baby Labo aka ja yan kafafuna aka karasa cikin palon aka zauna a kujera ana aika ma Deedo sakon murmushi. Ita kam abin ya bata mamaki, mutanen da suke neman ta su daketa sune suka dawo kamar ba su ba, anya babu wani kulli a kasa? Ta dai daure ta kwala kiran Saude ta kawo masu dan abin motsa baki, yayin da Aysha ta fito da I.V na guda ukku ta mik'awa Deedo, tace "da naki, da na Ummi, wannan kuma na daurin aure ne ki bama Nawap" [18/04 23:41] Nty Lubiee: BA'A SHAN ZUMA… 95 NA LUBABATU MAITAFSIR & BENAXIR OMAR ®NWA Ansa tayi idonta waje ta duba da kyau, tabbas bikin Aysha za ayi, cikin zuciyarta tace "har ta hakura da Nawap din kenan" tunani ta fara itama ko hakura za tayi dashi, tunda bai damu da ita ba, gashi yau kusan wata daya da tafiyarsa amma ko a waya bata jishi ba, Ummi ma in zai kira ta sai yayi hiding number sannan, tasan kuma duk don saboda ita yake hakan. Aysha ce ta katse mata tunani ta hanyar cewa "ya dai? Naji kinyi shiru ko congrats babu" murmushin dole tayi, tace "I'm so happy 4 yu, sai dai kuma Yaa Nawap baya nan, yaje yin wani course London, amma in sha Allah zaki ganmu ni da Ummi" "Allah ya sa"ta fada, sannan suka mike a tare, ta d'an taka masu zuwa inda sukai parking sannan ta dawo ciki, tana me cike da mamakin sauyawan da Aysha tayi lokaci guda. * *–**** Cikin yarda da hukunci irin na ubangiji, aka yi bikin Aysha da angonta Saifullahi, wanda dak'yar Ummi ta lallaba Deedo ta leka wurin dinner. Haka ma aka sha bikin Hally, aka kaita Bauchin Yuguda, amma Allah bai ba Deedo ikon zuwa ba, kasancewar rashin Yaa Nawap wanda ya kasance wani jigo na rayuwarta, tafiyarsa ta zama wani gi6i a rayuwar Deedo, domin tana jin tamkar ta rasa shi ne har abada, ga wani irin son shi da ya bi ya addabi zuciyarta, gani take ashe son da tayi wa Affan ba soyayya bane shak'uwa ce kawai, amma asalin so na zahiri Nawap take yiwa shi, sai dai bata gane hakan ba, sai yanzu. Idan tana tunanin shi ta kan zubar da hawaye domin shine kawai abinda take yi ta samu sassauci a cikin birnin zuciyarta. Ummi ce ma take dora ta akan yawan addu'oi domin kuwa addu'a takobin mumini ce kuma ta kan taimaka ma bawa a kowane irin yanayi. Shawarar Ummin dai ta bi, idan abun ya dameta ta kan yi salloli tare da addu'oi, sannu a hankali ta fara samun natsuwa, ba wai don ta daina jin DAFIN SO (coming soon) na harbin zuciyarta ba, sai don fawwalawa Allah dukkan lamurranta da tayi, ta maida hankalinta ga karatun ta, wanda take ganin shine kawai abinda zata yi ta farantawa Yaa Nawap dinta. BA’A SHAN ZUMA… 96,97&98 BA'A SHAN ZUMA… 96 NA LUBABATU MAITAFSIR & BENAXIR OMAR ®NWA BAYAN SHEKARA UKKU A hankali yake saukowa daga matattakalar jirgin janye da dan madaidaicin trolley, yana shakar iskar da take busawa mai cike da ni'ima tamkar za'a saki ruwan sama a dai dai lokacin. Waige-waige yake alamar yana neman wanda ya zo daukarshi, can ya hango ta sanye da wata light purple d'in abaya, ta yafa gyalen, ta nade hannayenta duk biyun ta zuba mashi idanu tana murmushi. Sosai ya wara idonshi yana kare mata kallo, tabbas Deedonshi ce, ta canja sosai, ta zama cikakkiyar budurwa, fatar jikinta ta goge sosai, ga wani annuri mai haske tattare da ita. Wani mugun dadi ne ya tsirga zuciyarsa, nan take soyayyarta ta dawo masa sabuwa fil, tayi masa famin ciwon da yake fama da shi shekara da shekaru, sai dai kuma ya san ta riga ta mashi nisa, ya san son da take ma Affan ba irin wanda zata yi fatali da shi ne ba, ya san ba zai taba samun kar6uwa a wurin zuciyar da ya hallakar da tashi zuciyar domin ta ba, dan haka dole ya kama mutuncinshi tun kafin ya zube a idonta. Gintsewa yayi, ya karasa gaban ta, dariya take mai cike da wani salo, tana kallonshi, a lokaci guda tace "sannu da zuwa Yaa Nawap" Kaman ya nitse a wurin, kasancewar muryarta da ya ji, shekara ukku cif cif rabon da ya ji wannan zakakkar muryar. Dakyar ya dawo daga duniyar da yake, yace "na sameku lafiya lil sis?" "Lafia lau" ta fada, yayin da ta anshi trolleyn da ke hannunsa tayi gaba, shi kuma ya bita a baya. Inda tayi parking suka k'arasa, fuskanta lullu6e da wani farin ciki wanda ba zai iya 6oyuwa ba, bayan motan ta buda ta jefa jakan hannunta, sannan ta zagaya driver seat ta zauna ta daura seat belt, duk idanun Nawap na kanta, mamakin ta yake yi sosai, yadda take abu komai a waye, kanta ya gama fashewa kamar ba Deedon Goggo ba, kallonshi tayi ta saki murmushi wanda ya rasa ko na menene sai dai ya kawar da kanshi, ita kam ta yi ma mota key suka kara gaba. BA'A SHAN ZUMA… 97 NALUBABATU MAITAFSIR & BENAXIR OMAR ®NWA Har suka je gida ba wanda ya tanka ma wani, illa Deedo da lokaci zuwa lokaci ta kan kai dubanta gareshi sannan ta saki murmushi, wanda ya rasa gane ko na menene, daga k'arshe tasa ya tsargu da kanshi, har yana tunanin kodai wani abu ne a jikinsa wanda yake sanya ta dariya? Nan da nan ya hade rai, ya juyar da kanshi yana ta faman shan kanshi, har suka isa. Wucewa ciki yayi bayan tayi parking, inda ita kuma ta fito da jakarsa, ta ja zuwa cikin gidan. Da murna Ummi ta tare shi tana mashi barka da zuwa, cikin jin dadi da girmamawa ya isa suka gaisa, sannan suka mike gaba dayan su zuwa dining table, kamar sun san da yunwa ya iso. A haka suka gama cin abincinsu hankali kwance, suna yi suna yar fira jefi-jefi ta yaushe gamo. * **—-****** Tun bayan da Nawap ya dawo kwata-kwata Deedo ta rasa gane kanshi, baya shiga harkan ta ko kadan, haka zalika ko shigowa yayi ya tarar da ita, to fa baya zama zai bar wurin, inda a bangarenta take fama da so da kuma k'aunar shi wanda su kan tunzura zuciyarta. Hanyar da zata sanar dashi yadda soyayyar shi ke azabtar da ita take nema, amma ina, babu fuska ta bangarensa, domin kuwa ya dade da sallamawa da ita, ya shafa ma zuciyar sa ruwan sanyi, ya daukan ma kanshi alkawarin ba zai taba takurata ta so shi ba. Ganin halin ko in kula da Nawap yake gwada ma Deedo, yasa Ummi ta kira shi, tana tambayar "ni kam Nawap ina maganar ku ta kwana kai da auta ta?" Ba tare da ya kalleta ba yace "Ummi wannan magana ai ta wuce, ita da take da wanda take so" murmushi Ummi tayi, ganin yadda yayi kicin-kicin da ido, tace "me zai hana ka kara jarraba sa'ar ka, ka sani ko ka samu kar6uwa yanzu" bai ce komai ba, sai ma mikewa da yayi ya wuce part dinsa… BA'A SHAN ZUMA… 98 NA LUBABATU MAITAFSIR & BENAXIR OMAR ®NWA Yana shiga ya mike a kujera yana jin wani tiririn son Deedo na tokarar zuciyar sa, anya zai iya jure rashinta? Ko dai shawarar da Ummi ta bashi zai yi amfani da? Cikin azama ya mike ya jawo wayarsa, ya cire screen lock din, nan da nan hotonsu shida ita da suka dauka wata rana dazai koma Abuja ya bayyana, sosai ya kura ma hoton ido yana ganin yadda take dariya, ga dukkan alamu bata da wata damuwa a wancan lokacin. A fili ya furta "i can't let yu go Deedo, cuz yu belongs to me" ya shafa fuskan wayan, sannan ya lalubo number ta a sabon layin mtn din da yake amfani da shi. Sai da ya kira har ta katse bata daga ba, inda ya k'ara kira a karo na biyu, nan ma shiru kake ji. Text ya tura mata "Ina fatan lokaci yayi da zan samu ansar tambayar da na maki shekaru ukku da suka wuce" ya tura ba tare da ya sanar da ita ko wanene ba. Kwance take tana sana'ar tata, wato tunanin halin da zata shiga in ta rasa Nawap, tana kallo aka kira har ta katse amma bata ko motsa yatsanta ba, shigowar text din ne yasa ta gane mai kiran yana bukatar wani abu daga gare ta. Hannu tasa ta janyo wayan ta buda text din, sai da ta gama karantawa sannan ta duba number, amma bata san mai ita ba, tunani sosai ya cika kwanyar ta, daga k'arshe dabara ta fado mata, inda ta sanya number a TrueCaller, nan ta ci karo da sunan DR. NAWAP KHAMIS har ma da pic dinshi.. Yadda kasan an mata albishir da gidan aljanna, haka Deedo ta tsinci kanta cikin farin ciki. Zumbur ta mike daga kwanciyar da take ta kara murza idonta, tabbas ba gizau sunan yake mata ba, cikin zazzodi ta fara rubuta mashi ansa "I'm just waiting for this day to come" can kuma wata zuciyar ta bata shawaran ta dan jaa class mana, tunda dai har yanzu yana son ta. Murmushi ta saki sannan ta goge text din, ta rubuta wani "nd who's this?" Ta tura masa ba wai don zuciyarta ta so ba. Jin shigowar text yasa yayi saurin duba wayar, bayan ya karanta, yayi murmushin takaici, sannan ya rubuta "someone who can't live without yu" ya senda mata… Ganin text din yasa ta taka rawar disco, domin ta gama sarewa Nawap ya guje mata, ashe ba haka abin yake ba, ashe kallon kitse ne su ke wa rogo. Wasu hawayen jin dadi suka gangaro ga bakinta kunshe da murmushi, ta shafa idonta taji tabbas hawaye ne, nan ta kara fadada murmushinta, domin duk duniya ba yanayin da ya kai wannan dadi, kana hawaye a lokaci guda kuma kana murmushi, wannan ya nuna farin cikin ya kai k'arshe BA’A SHAN ZUMA… 99&100 BA'A SHAN ZUMA… 99 NA LUBABATU MAITAFSIR & BENAXIR OMAR ®NWA Cikin sigar shagwaba kamar wanda yake kallon ta ta turo dan bakinta, sannan ta fara rubuta ansar da zata bashi "if yu really mean ur words, me zai hana ka bayyana kanka?" Ta tura, yayin da ta rungume wayar tana jin sabon yanayi na daban a cikin jikinta. Murmushi yayi wanda har sai da kyawawan hakoransa suka bayyana, a lokacin da yayi arba da sakonta, ba tare da wata fargaba ba, ya mayar mata da ansar "ok, ki shirya gani na da misalin karfe bakwai na daren yau." Ihun murna ta saki, inda ta fada da baya ta kwanta, ta k'ank'ame wayan tana tunanin abinda ya dace tayi kafin lokacin haduwarsu. Da sauri ta mike ta wangame wardrobe dinta, sannu a hankali take bin kayan ciki da kallo, amma bata ga wanda ya dace da ita a rana irin ta yau ba, rufewa tayi, sannan ta bude dayan gefen wanda yake dogayen riguna ne zallah jere a cikin wardrobe d'in, a hankali take duba su daya bayan daya, inda a k'arshe ta sauke idonta akan wata English gown kalar lemon green, murmushi ta saki sannan ta zaro rigar, wuyanta irin rufaffen nan ne (tuttle neck) yayin da hannun rigar yake dogo, sai dai ya matse daga k'arshe, doguwa ce har k'asa, in banda kyakkaywan (shape) da aka yi mata daga sama. A samar gado ta aje rigar, sannan ta bude inda gyaluluwanta suke, ta samo wani madaidaicin jan gyale wanda ta san tabbas zai hau da rigarta, haka ta gama hada duk wani abu da zata sa, sannan ta sauka kasa zuwa kitchen. Saude ta tarar tana aiki, ta kalleta tace "je ki huta Saude, bar ni da aikin kitchen din nan yau" godiya Saude tayi ta wuce, duk da ta fuskancin yanayin farin cikin da uwar dakin nata take ciki. Tana tsaka da aiki, ta juya bayan ta Nawap ya shigo kitchen din, ya buda fridge ba tare da ya san ita ke aiki wurin ba. A hankali ta dago idanunta, inda ta sauke su a kan nasa, amma yayi kicin-kicin da fuska shi dole ga big bro, baya son ta gane da shi tayi musayar text dazu. Murmusawa tayi, sannan tace "har ka tsorata ni wlh, me zaka dauka na kawo maka?" Basarwa yayi, yace "eyya, ban san kina nan bama ai, ruwa ne, na riga na dauka ma, kiyi aikin ki kedai" tana kallonshi tana dariyar yadda yake faman bonewa, tace "ok, ehnmm" ya juyo yace "ya dai?" "Daman zan ce ne anjima ina da bako, yace zai zo nan dan kada kace ban fada maka ba" ta karashe maganan tana mai karantar yanayin da yake ciki. Cikin borin kunya ya shafi kanshi, "lokacin da kika fara soyayyanki dama kin nema izinina ne?" Ya fada yana fita a kitchen din, biyo shi tayi tana fad'an "ni fa ba wani soyayya Yaa Nawap, aboki ne kawai" da murmushi ya juyo, sai kuma ya daure yace "naji, kije kiyi aikinki" "to bakon nawa fa? Baka ce komai ba" Ido ya kura mata, yana mata kallon kece rayuwa ta, nan da nan yake neman sanya ta a wani hali, domin bugun zuciyar ta taji ya karu, ba tare da tace komai ba, ta juya ta koma kitchen din zuciyarta fal da so da k'aunar Yaa Nawap. [20/04 20:56] Nty Lubiee: BA'A SHAN ZUMA… 100 NA LUBABATU MAITAFSIR & BENAXIR OMAR ®NWA Lokacin da ta gama girkinta har karfe shida saura kwata, a gurguje ta jera komai a dining table, lokacin Ummi na saukowa ta kalleta sai zuwa take tana dawowa tsakanin kitchen da dining area, ga fuskanta a sake da alama tana cikin farin ciki sabanin kwanakin baya da ko kasan ta daina saukowa, kullun tana daki kaman bokanya. "Ba dai ke kika yi girkin yau ba auta" Ummi ta fada dai dai lokacin da ta karaso gabanta. Da murmushi ta kalla Ummi tace "yau special na hada mana Ummi, har sai kunne yayi motsi idan aka ci" bubbuda coolers din Ummi take yi, inda wani kanshi ya daki hancinta, tace "lallai naga alama, amma menene sirrin?" Ta fada da sigar tsokana. "Ba komai fa Ummi" Deedo ta fada tana rufe fuskanta da hannu, "sai dai ehnmmm" "mene?" Ta tambaya tana kallon ta. "Ina da babban bako anjima Ummi, idan ya zo zai zo ya gaishe ki ma" ta fada tana dariya. "Bako Deedo?" Ummi ta fada cikin karaji, girgiza kai Deedo tayi, "zaki ganshi Ummi, kuma in sha Allah zaki yaba dashi" "Allah yasa" ta fada yayin da take wucewa zuwa palo ba tare da ta ji dadin maganar Deedon ba. "Yanzu shikenan yaron nan yana gani zai yi rashin mace kamar Deedo? Duk dan saboda dan banzan kishi irin nasa, kuma yana son ta ba wai baya son ta ba." Sababin da Ummi ke ta faman yi kenan a cikin zuciyarta, har aka kira maghriba, ta mike ta haye sama domin bada farali. A bangaren Deedo ko bayan ta fito wanka ta bada sallar maghriba, sannan ta cigaba da yan shafe-shafenta, sassaukar kwalliya tayi kasancewarta ba ma'abociyar dam6are-dam6are ba, sannan ta ja rigarta ta sanya, ta gyara gashinta ta faka shi a tsakiya, inda tayi amfani da jajayen kananan yan kunne, ta daura bracelet ja, tana kokarin feshe jikin ta da turare, taji alaman message ya shigo mata, da sauri ta duba "Ina cikin gidan ku, zaune a palon baki, just waiting for my princess" shine abinda ta gani rubuce a message din. BA’A SHAN ZUMA… 101-103 BA'A SHAN ZUMA… 101 NA LUBABATU MAITAFSIR & BENAXIR OMAR ®NWA Dariya mai sauti ta saki, a fili ta furta "Yaa Nawap kenan" sannan ta rubuta mashi ansa "hmmmm, ina zuwa yanzu" ta tura masa, sai da ta karasa duk abinda zata yi, ta janyo wasu red plat shoes ta saka, ta yafa gyalenta sannan ta fita. Dakin Ummi ta fada, ta tarar da ita zaune tana jan casbaha, ta zauna gefen gado tana wasa da hannunta. Har sai da tayi addu'a duk suka shafa a tare sannan Ummi tace "har ya iso ne?" Kanta a kasa ta girgiza kai alaman "eh" "To ki tashi kije, ki dai kula da kanki da mutuncinki" "in sha Allah Ummi" Deedo ta fada lokacin da take mikewa, a zuciyarta tana mai cewa "Ummi da ta san ko waye da ba wanda zai kaita jin dadi, shaaa, zanyi surprising dinta ne" ta wuce hankalinta kwance, domin yadda take jin son Nawap yasa ta rage fargaban haduwa dashi. Zaune yake ya bama kofa baya, in banda kanshin turarensa na Tom Ford Velvet Orchid, babu komai da yake tashi a wurin sai fa sautin T.V inda ake nuna labaran kasa a tashar TVC. Da sallama ta shigo, kanta a kasa ba tare da fargaba ko mamakin ganinsa ba, haka ya dago kansa yana kallon yanayinta, me sa bata yi mamakin ganin shine ba? Anya babu wani abu da ta sani tuntuni? Kawar da tunanin da yake yayi, sannan ya ansa sallamar yayin da take karasowa tsakiyar palon. Kallonta yake tamkar yau ce rana ta farko da ya fara ganinta, tayi mashi kyau sosai wanda bai taba tunanin tana da shi ba. Nesa dashi ta zauna, ta dago a hankali tace "Ina wuni Yaa Nawap" Cikin rashin kuzari ya ansa ta, nan wani dogon shiru ya ratsa tsakaninsu, muskutawa Nawap ya yi, cikin k'arfin hali, sannan yayi gyaran murya yace "ke haka ake taran bako ko ruwan sha babu?" Shiru tayi kaman baza ta ansa ba, can dai ta nisa tace "bakon nazo nema, but unfortunately sai na ganka, kunya ce ta hana ni tambayar ko ka kasan inda yake?" Ido ya tsare ta dashi har saida ta gama maganarta, inda ya cika bakinsa da iska, a karo guda ya furzar dashi, ya rasa ta ina zai fara mata bayani, ga so da k'aunarta na matuk'ar azabtar dashi, amma yana tunanin halin da zai tsinci kanshi matuk'ar bata ansa tayin soyayyar shi a karo na biyu ba. Fuskantarta yayi, yayin da ya dawo daga duniyar tunanin da yake, cikin wata irin murya ya kira sunanta "Firdausi" ta dago a hankali ta yadda taga fuskarsa ta san he's damn ready nd serious. Domin tunda take dashi sau daya ya taba kiran ta da ainahin sunanta, ranar da ta fara ganinsa a duniya. Kwantar da kai yayi, sannan ya fara magana "Bazan so na zama mai son kai ba, haka zalika kada kiyi tunanin dangantar dake tsakaninmu, ina son ki dauka baki taba sani na ba, ta yadda baza ki sha wahala wurin yanke hukunci a kaina ba. Shekaru ukku da suka wuce na nemi sanin takamaiman abinda ke zuciyarki dangane da ni, amma Allah bai nufa zan samu ansa ta, ta inda tafiyar gaggawa ta same ni, gashi kuma nayi alkawarin bazan neme ki ba, har sai ke da kanki kin neme ni da ansar tambayar da na miki" sai da ya dan tsagaita, yana mai cigaba da kallon yadda ta dukarda kanta, tana wasa da yatsun hannunta, sannan ya cigaba… BA'A SHAN ZUMA… 102 NA LUBABATU MAITAFSIR & BENAXIR OMAR ®NWA "Ina mai rokon Allah yasa yau ta kasance rana ta k'arshe da zan san matsayina a wurin ki" yayi shiru yana mai cigaba da kallon ta yana kuma rokon Allah yasa ya dace a wannan rana. Shirun da tayi har na tsawon mintuna kusan bakwai yasa ya cigaba da magana "idan har na saka ki a rudani, ina son ki gafarci zuciya ta wadda take bugawa a ko wacce sa'a da so da k'aunar ki, wadda take azalzala ta, ta ke kuma hana ni sukuni a duk tsawon shekarun dana sanki, ba laifi na bane Deedo, ba kuma ni na dorawa kaina ba, Allah ne ya jarabce ni da son ki, me sa baza ki taimaki yayanki ba? Me sa baza ki gane farin cikin da zan samar maki ba, matuk'ar kika yarda da ni a matsayin uban ya'yanki, ina son ki sosai, wanda bazan iya dainawa ba, domin kuwa kece mace ta farko da na fara so, haka kuma kece ta karshen da zan tafi ga mahaliccina da k'aunarta koda baki yarda kin so ni ba." Yana gama fadar haka ya mike da niyyar fita, domin zuciyarsa ta gama karyewa, gashi Deedo ta ki tace komai, asali ma ko kallon yanayin da yake ciki bata yi. Har sai da ya kai bakin kofa sannan ta samu damar dago da jajayen idanunta, wanda suka rine da ruwan hawaye tace "Yaa Nawap" juyowa yayi da sauri jin raunanniyar muryarta na kiran shi, ganin hawaye na zuba daga kyakkyawar fuskarta yasa yayi saurin dawowa da baya yace "no please lil sis, don't be like this kinji, na fahimci kina son Affan ko? Me sa zan shiga rayuwarku, na hakura zan danne son da nake maki, amma bazan iya jurar ganin hawayenki ba, it's ok kinji" yayin da yasa hannu ya zaro handkerchief ya mika mata. Ansa tayi ta toshe bakinta dashi, sannan ta saki kuka mai sautin, wanda ya gigita Nawap, har ma ya rasa ta ina zai lallasheta, da ya san haka ne da bai zo mata da maganar nan ba. Katse mashi tunani tayi ta hanyar cewa "Yaa Nawap kaine mutun na farko wanda ya kalle ni a matsayin mutun kamar kowa, kai ka daga darajata, ya cika mani gurin rayuwa ta, sannan kaine mutun na farko wanda zuciya ta ta mace saboda son shi, ban taba son wani kwatankwacin son da nake maka ba, amma na rasa me sa baka fahimci hakan ba, har kayi fushi da ni, tsawon shekaru ka barni ina dakon sonka ka manta da ni, me sa Yaa Nawap? Kasan halin tashin hankalin da na shiga?" Ta k'ara fashewa da kuka mai tsuma zuciyar masoyi, wanda yasa Nawap dafe kanshi da duk hannayensa biyu. Ya ma rasa menene yanayin da yake ciki, shin farin ciki ne ko kuma haushin kanshi yake ji yadda bai fahimce ta ba tun asali. Kasan carpet din ya zauna shima ya dago fuskanta ya share mata hawayen, sannan yace "I'm so sorry lil sis, azaban kishi ne ya hana ni fuskanta inda kika sa gaba, I promise baza ki taba da na sanin kasancewa tare da ni ba, zan faranta maki dai dai gwargwadon iko, zan kula dake, in tarairaye ki fiye da yadda ARCH. SADDIQ ya tarairayi LAILA (Rabon ka ko yana bakin kura na Chuchun Gaye) zan shayar dake madarar farin ciki fiye da yadda FU'AD ya shayar da MEELA (WATA RAYUWA) ki yarda da ni my lil sis, ki bani aron zuciyarki, ni kuma na maki alkawarin I'll never ever let yu down…." BA'A SHAN ZUMA… 103 NA LUBABATU MAITAFSIR & BENAXIR OMAR ®NWA Murmushi ta sakan mashi yayin da hawayen suka cigaba da zarya akan kuncinta, "shhhh.." ta fada lokacin da take dora dan yatsanta akan bakinta, nan take yayi tsit, tare da aika mata sakon kallo mai alamar nayi missing dinki, langabar da kai tayi, itama tana kallonsa, sannan a tare suka sa dariya kamar ba ita ce wadda tasha kuka yanzu yanzu ba. Cikin dan k'ank'anin lokaci suka dinga aika ma juna da kalamai masu dadi da kwantar da hankalin masoyi, har sai da suka gama aminta da junansu, inda daga k'arshe Nawap ke tambayar ya akai bata yi mamakin ganin shi yake aika mata sakon text ba, nan ta fada mashi tayi amfani da TrueCaller ta gane shine. Dariya yayi, sannan yace "Ooops, na manta akwai wannan fa" dariyan tayi itama, gani take kaman ba Yaa Nawap din da ta sani ba, ashe dama ya iya soyayya? "Tashi muje ka nema izini wurin Ummi, dan idan ba kai mata ba nima zan hakura da kai" wara idanunsa yayi "da zaki hakura ai da yanzu kin mance dani, yarinya ko Ummi bata yadda ba ni ba yadda za ayi dani, dole a so ni," Sannan ya mike ya bi bayanta tana dariya suka fito, suka k'arasa cikin gidan. Ummi zaune saman dining table suka shigo fuskokinsu dauke da murmushi, kallon Nawap tayi tace "Kai kam ina ka shige ina nemanka ka taya ni cin abinci?" Sosa kai yayi, yace "naje neman aure ne" Ummi sake da baki tace "to fa! Babbar magana" Ganin Deedo na bin shi a baya tace "ke kuma ina bakon? Ko har ya tafi?" Dariya ta kwace mata, ta karasa kujerar da take kusa da ta Ummi ta zauna, yayin da shi kuma ya zauna a wadda take kallonsu, tana kallon Ummi tace "ga bakon na kawo ya gaisheki" tana yi tana nuna Nawap da yatsa. Shiru Ummi tayi, yayin da take k'are masu kallo duk kowannensu da fara'a dauke a fuskarsa, tace "kai ku dakata, ban fa gane ba" duk suka sa dariya, inda Nawap yace "Ummi zaki bani autar taki ko na nema wata?" Duk da kanta ya kulle da sha'anin yaran zamani, amma matuka tayi farin ciki, taji dadi fiye da misali, inda ta kai kallonta ga Nawap tace "akwai sharudda dai, wanda matuk'ar ka kiyaye su to zan baka ita" Ya buda ido yana kallon Ummi, yace "tohm a jero su ina ji" ya fada lokacin da yake sai ta kunnensa garesu. Dariya ya basu, dan haka suka kyakyale gaba dayansu, sannan Ummi tace "banda yawan takuri, sannan bana son yawan la6e, ana kiraye mun auta, kuma idan ka shirya ka turo da magabatanka dan dama na gaji da ciyar da gauro a gidan nan" Sosai ya ji dadin maganganunta, "zanyi yadda kike so Ummin mu" ya fada yana kallon Deedo da ta dukar da kanta tana murmusawa… BA’A SHAN ZUMA… 104-106 BA'A SHAN ZUMA… 104 NA LUBABATU MAITAFSIR & BENAXIR OMAR ®NWA Deedo wadda tunda aka fara maganar kanta yake kasa, tana jin wani sabon canji a jikinta, domin yanayinta na yau, yasha ban ban dana kullun. Mik'ewa tayi ta zuzzuba masu abincin cikin jin kunyar mugun kallon da Nawap ya tsare ta dashi. Bayan sun gama Ummi taga abin nasu ba mai k'arewa bane, dan haka ta wuce sama, inda a zuciyarta take cewa "oh ni Fatima, yaran zamani sai a bar su, ko dan kunyar idona ba'a ji, uhunmm" ta haura sama, ta haye dan gadonta tana tunanin yadda zata aurar da ya'ya har biyu. Deedo da Nawap wanda soyayya tasa suka manta ko sallar isha'i basuyi ba ne suka ankare da lokaci, yayin da ta sauke idanunta kan tafkekiyar agogon bangon dake manne a palon, k'arfe goma har da minti ashirin da biyu (10:22pm). Mik'ewa tayi ba wai dan ta so ba, ta kalli Nawap wanda ya marairaice fuska kaman zai saki hawaye yana mata kallon ban gaji da ganin ki ba. Alama ta mashi da ido, abin nufin ya kalla agogo. Wadda ke daure a hannunsa ya duba, bai ma san lokaci ya ja haka ba, dan haka ya dan wara idanunsa, sannan ya mike, hannuwansa duk biyun cikin aljihu, ya kalli Deedo yace "it's ok yan mata na, ki shiga ciki, I'll call kafin ki bacci" Murmushin itama ta sakan mashi, sannan ta juya tana tafiya, sai da ta hau stairs din, kafin ta juyo tace "don't keep me waiting plz" cikin shagwaba mai narkar da zuciya tayi maganar, dan haka Nawap ya sandare a wurin, ya kasa motsa koda yatsan k'afarshi, har ta haye tana mai dariya. Girgiza kansa yayi, sannan ya juya ya wuce side dinsa, inda a zuciyarsa yake cewa "tabbas ka so a so ka ma wani babban abu ne mai tattare da farin ciki a duniyar masoya" * ***—-****** Soyayyar Nawap da Deedonsa soyayya ce wadda suka shimfid'a a kan gaskiya da amana, soyayya mai cike da so, tattali, da kuma kula da junansu, wanda hakan ya basu damar sanar da magabatansu domin cika burin masoya. A ranar yau, wadda tayi dai dai da juma'a ishirin da ukku ga watan ifirilu (23 Apr,) aka sanya ranar auren Deedo da Nawap dinta, wata ukku cif cif, wanda ya kama sati daya dai dai gama jarabawarta ta aji hud'u (400L). Bayyana farin cikin da masoyan suke ciki, b'ata baki ne, domin ko suna cikin tsananin farin cikin da ni Lubiee ba zan iya fasalta shi ba, lokaci kawai muke jira mu sakata mu wala, sannan kuma mu 6arje guminmu. BA'A SHAN ZUMA… 105 NA LUBABATU MAITAFSIR & BENAXIR OMAR ®NWA BAYAN WANI LOKACI A gajiye liss ta shigo gidan, ta zube akan kujera tana kwala kiran Saude wadda ta rugo da dan saurinta tana cewa "sannu da zuwa uwar dakina, ya jarabawar?" Idonta a lumshe tace "Alhamdulillah, taimaka mun da abu mai sanyi, baki ji ranar da na kwaso ba" "to, to bari inzo" Saude ta fada, sannan ta mik'e ta koma kitchen din, ta dawo hannunta dauke da dan tray, da jug, da kuma cup a sama. A gaban Deedo ta dire shi, tace "kinyi sa'a ko, dazun nan muka hada zo6on nan ni da Hajiya, kinga har ya dau ra6a kuwa" tsiyayawa Deedo tayi, ta kai bakinta yayin da taji wata nutsuwa ta sauko mata, ga wani gard'i da dad'i da zo6on ke da shi, sai da ta kara cika wani cup din, ta sha kaman rabi, sannan tace "lallai zo6on nan yayi dad'i Saude, wai ina Ummin take ma?" "Tana ciki, ga dukkan alamu sallah take" "Ok, bara na shiga, nagode Saude" Yayin da ta mik'e ta haye saman, ta wuce dakin Ummin straight. A zaune ta tarar da ita tana duba wani littafi mai sunan (You can be the Happiest Woman in the world) na Dr. A'id al-Qarni. Saida ta gama karanta bayan littafin, sannan tayi murmushi, ta zauna gefen ta. "Sannu da gida Ummi" Da fara'arta ta dago, ta cire medical glass din da yake idonta, sannan ta kalle ta, "Yawwa auta, ya exams din?" "Alhamdulillah Ummi, amma fa ta yau sai hamdala, ku dai taya mu da addu'a" "Ana ta yi ai, Allah dai ya baku sa'a" Tace "amin" sannan ta dukar da kanta bakinta na motsi, da alama akwai abinda take son fada. "Ya akayi ne amarya?" Ummi ta tambaya, tana kallon ta da alamar tsokana. Rufe idonta tayi da duk hannunta, tana dariya, sannan tace "ehnmm, Ummi dama zan ce ne dan Allah idan na gama exams ina son zuwa ganin Goggo, in masu bankwana" Murmushin jin dadi Ummi tayi, tace "Ahaf, kin hutar da ni kenan, dan ni ina nan na shirya irin lallashin da zan maki akan kije kuyi bankwana, dan ba dadi haka kawai suji an miki aure, ashe 'yar tawa mai hankali ce da hakuri da kuma maida komai ba komai ba, amma naji dadin kasancewarki haka, domin haka ake son dan Adam ya kasance, duk wanda yayi maka sharri, kai kuma ka saka mashi da alkairi, sai kiga kai kuma Allah yayi maka sakayya ta wani 6angaren" Hannunta ta rike, "Allah yayi maki albarka Deedo, ya kuma kare ki daga ko wane irin sharri kinji" Da murmushinta, ta ansa da "amin Ummi, Allah yayi maku sakayya da gidan aljanna kuma" "Amin, kinga next week zanyi tafiya, kuma Hafsat (kanwar Nawap) tace mun jibi zasu zo, sai ku zauna dasu, ga Saude kuma, idan kin gama exams, ke kuma sai kuje da driver, nasan kafin nan na dawo, zan zo sai mu dawo tare, da su din ma, tunda na san zasu zo bikin suma" "To shikenan, Ummi, duk yadda kika ce haka za'ayi" "yawwa autalle, tashi kije ki danyi wanka ki huta kinji" ta mik'e ta wuce dakin ta, sannan Ummi ta maida tabaranta ta cigaba da karatun ta. BA'A SHAN ZUMA… 106 NA LUBABATU MAITAFSIR & BENAXIR OMAR ®NWA Tana shiga, kiran Nawap ya shigo mata, da murmushi ta ansa wayar, suna firarsu ta masoya, nan take shaida masa zata je ganin su Goggo, yace "yaushe kuma keda kike exams" "Sai na gama fa, kuma Ummi ma tace naje ai" ta fada tana tura bakinta gaba, kamar yana kallon ta. "To ke banda abinki, Ummi ce mijinki ko ni? Idan nace a'a fa, ya zakiyi?" "Tafiya zanyi mana, tunda dai Ummi ta barni, kai kuma sai ka bari idan na zo gidanka ka juya ni yadda ka so" Dariya mai sauti ya saki, yace "Yarinya kina da aiki, ai tun yanzu zan fara ba sai kin zo ba" Ba tace komai ba, tayi shiru tana saurarensa. Sai da ya gama tsokanarta sannan yace "I'm just kidding kinji, na san by then na samu hutu, kinga idan na zo sai muje tare kawai. "Thanks hun" ta fada, bakinta kunshe da murmushi, nan suka cigaba da firan su har suka gama, sannan ta mike ta fada toilet. * —**** Ranar da Ummi tare da kanwarta zasu wuce Dubai, domin hado lefen Deedo, da kuma siyayyar wasu abubuwa daga cikin kayan dakin ta, kiran ta tayi, sukai sallama, inda ta kara da cewar "duk in mun dade, to sati guda ne, ke kam ai jibi kike gama jarabawan ko?" Deedo ta girgiza kai, Ummi tace "yawwa, kinga washegari sai ku wuce da driver, idan na dawo na dan huta, zan zo sai mu dawo tare" "Ya Nawap yace zai zo sai muje tare wai" "To ai shikenan ma, amma abinda za ayi shine, to ku tafi da Hafsat da yaranta, su sai su dawo tare da shi, ke kuma su baro ki can" "To shikenan Ummi, Allah ya tsare, ya kuma dawo daku lafia" Tace "amin" yayin da ta mika mata kudi, tace "kya yi masu tsaraba." Gaba dayansu suka fito domin yi masu rakiya, yayin da driver ya dauki su Ummi zuwa Abuja, kasancewar ta can zasu tashi. Bayan sun shiga Abuja, waya sukai ma Nawap, yaje ya samesu, nan sukai bankwana, yayin da shi kuma ya dauko hanyar Kd, tare da driver, zuciyarsa fari kal yana ta faman sharta gudu kaman zai tashi sama. Deedo wadda tuni suka saba da Hafsat, tare suka shiga kitchen suka cigaba da tanadar mashi dad'ad'an abincin kala kala. BA’A SHAN ZUMA..107&108 BA'A SHAN ZUMA… 107 NA LUBABATU MAITAFSIR & BENAXIR OMAR ®NWA Bayan sun gama ta wuce ta fesa wanka, ta dau gayu na musamman domin taryar rabin ran nata. K'arfe biyu da kwata dai dai suka iso gidan, da sallamarshi ya shigo palon babu kowa sai Mahmoud yaron Hafsat yana kallon cartoon a MBC3. Da gudu ya taso ya rungume Nawap yana cewa "ga Uncle ga Uncle." D'aga shi sama Nawap yayi, yana fadin "my boy, ka zama babban mutum" Dariya ya kyalkyale da shi, "sosai ma, har na kai nursery 2 fa uncle" "Smart boy" Nawap ya fada yana dariya, sannan ya sauke shi, ganin Deedo na saukowa fuskarta kunshe da wani murmushi na ban mamaki. Karasawa yayi inda take tsaye ta nannade hannayenta, ya kalleta yace "yan mata na, yakike?" "Ina wuni" ta fada, yayin da ya ansa a daburce, "na same ku lafia?" "Lafia lau, ya hanya?" "Alhamdulillah, ina ta sauri na zo nayi tozali da abin k'aunata " Rufe fuskarta tayi, alamar kunya, tayi gaba tana cewa "muje ka ci abinci, dan na san yanzu haka ko breakfast baka yi ba" Bayanta ya biyo yana cewa "banda abinki waye zai ba gauro abinci" Dariya tayi lokacin da suka iso kan dining table din, sai da ta rage muryanta, sannan tace "just two weeks ya rage, ka daina zama da yunwa in sha Allah" Ta juya ta cigaba da serving dinshi, inda shi kuma yana murmushi yace "I trust my baby doll" Ta kalle shi ta murmusa, sannan ta mika mashi plate din abincin, ta wuce kitchen domin kwaso drinks. A haka Hafsat ta tarar dasu yana cin abincin, yayin da Deedo ke zaune gefenshi suna tadinsu cikin jin dadi. Suka gaisa dashi, yana tambayar "ina mama small" tace "dak'yar na lallabata, tana sama tana bacci." Sannan ta wuce cikin palon inda Mahmoud yake a zaune. Tunda Nawap yazo kullun suna manne da Deedo, shi ke kaita skool, sannan ya jirata office din Dr. Kashim, har sai ta fito exams, sannan ya dauko ta su dawo gida kullun, har zuwa yau da take gamawa. A hanya take ce mashi "Ummi ta fada maka da su Yaa Hafsat zamu tafi?" "Me zasuyi mana ne in mun tafi dasu? Me sa Ummi take mun haka, bata son ina ke6ewa da matata" ya dan ja tsaki, ya kara gudun da yake, yace "ke kuma me kika ce mata?" Dariyar da take ta dan tsagaita, tace "ni har na isa ince wani abu ne bayan Ummi ta gama yanke hukunci, lallai ma" "Duk ke kika ja mana ai da kika fada mata" "Zan bi wani ne ba tare da sanin Ummi na ba aka fada maka" tana yi tana kallon yadda yayi kicin kicin shi dole ga wanda aka shiga hakkinsa. "Zaki maimaita ranar da kika zo hannuna yarinya, dan sai kinyi wata biyu baki ga Ummin taki ba" ya fada a dai dai lokacin da suka iso kofar gida, ya fara danna horn kamar wanda ya d'auko majinyaci. Ita dai dariya kawai take, yana yin parking ta fito zata shige, yace "wa kika bar ma wannan tilin books din naki?" "Wa fa in ba mijin yar auta ba" ta shige tana ta dariyar mugunta. Yayi kwafa, ya kwashi k'atin- k'atin din text books din har guda ukku, shi kanshi sai da hannuwansa suka k'age, ya zube mata su a palo, yana banbami "koma ya ake tana daukan books din nan, gata dai abu kamar a karya ta" Mahmoud yace "uncle kai da wa kake fada?" Yace "wannan yar siririyar auntyn taka mana, ta sanya ni daukar books masu nauyi" Yayi dariya, yace "ai idan ta dauka zasu fadar da ita ne shi yasa, kai kuma kana da k'arfi kaga" Shafa kanshi yayi, ya wuce kitchen ya dauka robar ruwa, sannan ya wuce side dinsa. [24/04 21:45] Nty Lubiee: BA'A SHAN ZUMA… 108 NA LUBABATU MAITAFSIR & BENAXIR OMAR ®NWA K'arfe goma dai dai na safe, kowa ya gama shiryawa tsab, suna zaune a palo suna jiran fitowar oga Nawap wanda yake ta faman cika yana batsewa shi dole an takura masu, za'a hana su sakewa shi da Deedo. Karasowa yayi, ya dau wanka cikin farar gezna, hularshi da takalminshi har ma da agogo duk bak'ak'e, yana ta kanshin Tom Ford Velvet Orchid, Mahmoud kawai yai ma dariya, ya kama hannunsa suka fita. Deedo da Hafsat da suke kunshe dariya suka kyalkyale, sannan Deedo ta sa6i mama small suka fito, yayin da Saude take kwaso kayan da zasu tafi dasu tana lodawa a boot. A gaba suka zauna ita dashi, sai mama small a hannunta, yayin da Mahmoud da Hafsat suke a baya. Haka suka fara tafiyar kamar kurame, in banda Mahmoud da mamah da suke yan surutansu na yara. * ******** K'arfe d'aya na rana Nawap yayi parking motarsa a kofar wani kwarmad'ad'd'an gida wanda yake da tabbacin tabbas nan ne gidan Goggo, domin ko ba zai taba manta gidan da ya fara ganin mamallakiyar zuciyarsa ba. Kallon Deedo yayi, yace "kamar munyi batan kai ko?" "Anya kuwa?" Bari dai in shiga mu ga" Ta 6alla murfin motar ta fito, yayin da shi ma ya bude nashi kofar ya bita a baya. Cikin gidan wanda ga dukkan alamu rabon da ya ga shara akalla anyi shekara hud'u, domin ko yadda kasan kango, haka bola ta samu wuri ta basar, suka kutsa kansu, Nawap ya kalle ta "Bana tunanin akwai dan Adam din da yake rayuwa a irin wannan wurin, fito mu shiga makwabta mu tambaya ko sun koma wani wuri ne" Basu ankara ba suka tsinkayi murya daga cikin dan akurkin dakin da Deedo take da, wanda shi kadai yayi saura a cikin dakunan da suke gidan, domin kuwa sauran duk sun rufta, kana iya hango komai daga inda suke a tsaye. "Wane dan banzan ne nan? Iyii? Ko bakwa ji na ne la'anannu" Ta fara laluben sandarta, dakyar ta dafa bango ta mik'e tsaye, tana bin bangon ba tare da sanin ta ba ta taka wani kwano, aiko ba tare da 6ata lokaci ba ta fadi kasa, ji kake wani rigijib!!! Nawap da Deedo da suke tsaye bakin dakin suka yi saurin kutsa kai ciki, amma wani mahaluk'in k'arni tare da wani gagarumin wari ne suka yi ma hancinsu sallama nan da nan suna rige-rige suka yo waje da gudun bala'i, Nawap ya rik'e cikinshi wanda yake murd'a mishi, nan take ya fara shek'a amai ba k'akk'autawa… "Allah dai ya tsine muku, wai su uban waye a nan?" Ta cigaba da laluben inda ta wurga sandar, ko Allah zai taimaketa ta fita ta warci daya a cikin irin yan iskan yaran da suke shigowa suna tsokanarta ko wacce rana. (Nayi iya kokarina na karasa labarin nan yau, amma hakan bai samu ba, I promise yu zuwa gobe in sha Allah. Thanks y'all for the love. I love yu too) BA’A SHAN ZUMA… 109-111 BA'A SHAN ZUMA… 109 NA LUBABATU MAITAFSIR & BENAXIR OMAR ®NWA Hawaye masu azabar zafi suka gangaro a fuskar Deedo ganin halin da kanwar mahaifinta ke ciki. Hannu tasa ta share, ta juya tana kallon Nawap wanda yake goge bakinsa da handkerchief, karasawa tayi, gabanshi "Sannu Yaa Nawap" ta fada yayin da take waige waige ko me take nema, "Kaje waje, bari nayi magana da ita" Goggo wadda ta rarrafo ta turo kanta kofar dakin, tace "Wai muryar su waye nake ji nan? Iyii? Ko baza kuyi magana bane tambadaddu ya'yan fata, Allah dai ya tsi… " Nawap ya katseta ta hanyar cewa, "Goggo Nawap ne, wannan kuma Deedo ce, dago ki ganta" "Deedo? Nawabu? Ku ne? Ko dai tsinannun ya'yan unguwa ne suke tsokanata" Ta fada yayin da ta dago kanta, ko Allah zai sa ta hango kyallin wani abu wanda zai tabbatar mata da cewar su din ne. A tare suka toshe bakinsu da hannu, suna fadin "innalillahi wa inna ilaihir raji'un! Goggo!" Ganin kwantsa mai kama da mugunya, har da wasu yan tsutsotsi suna fita daga idanun Goggo, idon ya ca6e, ya cakwale, Allah kadai ya san iya shekarun da ta dauka tana tare da wannan azabar. Lalube ta cigaba da yi, inda ta jawo 'yar k'afarta guda daya da tayi mata saura, ta fito da ita wajen dakin dak'yar, "'Ya'yan nan ku fada mun gaskia, Deedo ce wannan a gaba na da gaske?" Tasa hannu tana lalube ko zata samu damar ta6a Deedon. "Nice Goggo, wai me yake faruwa da ke ne? Bakya gani ne ko ya akayi?" Kuka mai sauti Goggo ta saki, sai dai kash, kukan babu ko alamar hawaye, amma duk wanda ya ganta zai tabbatar kukan nadama Goggo take rerawa. "alhakinku ne yake bibiyata Deedo, dake da malam Ilu, wanda bakin cikina yayi sanadiyyar barin shi duniya, na shiga ukku ni Batula," Abinda Goggo take nanatawa kenan, yayin da ta dauki hamnuwanta ta dora bisa kai, tana kurma ihu kamar mahaukaciya. Ihun da Goggo ta kurma, shi ya jawo hankalin su Hafsat, da Mal. Labarin makwabcin Goggo wanda shi kadai ne mutumen da ya rage wanda ke taimaka mata a unguwar, kasancewar kowa ya san bakin hali da bala'i irin na Goggo, shi yasa babu mai kallon inda take, anan inda take a zaune zata yi kashin ta da fitsari, haka kuma idan malam Labaran ya miko mata dan abinci, anan din dai zata cinye shi, ba tare da wanke hannu ko kashin da yake jikinta ba. Da azama suka yo cikin gidan, ganin yanayin yadda wurin yake yasa Hafsat dakatawa, hannunta rik'e da na Mahmoud, yayin da Mal. Labaran ya karasa yana fadin "Samari daga ina? Lafiya kuwa?" "Lafiya lau mal., ina wuni" Cewar Deedo, inda shi kuma ya cigaba da kare mata kallo kamar ya santa. "Deedo ce" ta fada tana kallon goggo, Nan ya fara salati yana sallallami "Deedo? Ina kika shiga? Wanene wannan din shi kuma?" Anan suka gaisa da Nawap, yai mashi bayanin kanshi, mal. Ya kara da tambayar "kai kuma ina ka santa?" Nawap wanda baiyi kasa a gwiwa ba ya labartawa mal. Yadda akai ya san Deedo, har ma da yadda akai ya tafi da ita. Goggo wadda ta daskare tun lokacin data tabbatar da Deedo din dai ce a wurin, ta kara kurma wani sabon ihun, a yayin da Mal. Labaran ya kwashi sabon salati yace "Eh lallai dole kike shiga wannan halin Batula, ka ganta nan" ya fada yana kallon Nawap tare da nuna Goggo da yatsa, yace "Wannan matar bayan tafiyar Deedo, duk wanda ya tambayeta ina yarinyar nan take, ce mashi take ta tafi yawan karuwanci, ashe ke da hannunki kika dauki diya kika bayar, chabdi! Lallai Allah yana son ki Batula, tunda har ya baki damar sake ganin Deedo don neman gafararta" Cigaba da jinjina kai yayi, ko a film bai taba jin irin wannan tsantsan rashin imanin na Goggo Batula ba. [26/04 01:21] Nty Lubiee: BA'A SHAN ZUMA… 110 NA LUBABATU MAITAFSIR & BENAXIR OMAR ®NWA Deedo wadda take shar6ar kuka domin jin bayanin mal. Labaran nan da nan taji wata sabuwar tsanar Goggo ta karyo mata, ba don kanwar ubanta bace, da babu wani abu da zai kara hada su, duk uwar azabar da ta gana mata bata isheta ba, har sai da ta zubar mata da duk wani mutuncinta daga idon mutanen garin. Nawap ne ya lallabata har tayi shiru, sannan ya kai dubansa ga mal. Labaran wanda har yanzu bai daina mamakin makirci da mugun hali irin na Goggo ba, "Mal. To ita menene musabbabin dawowarta haka? Ina yaranta suke ne basu kula da ita?" "Chabdi! Dogon labari kenan," Cewar mal. Labaran, sannan ya cigaba "Abinda yayi sanadin dawowarta haka baya rasa nasaba da dan ta shehu, wanda tun yana dan shekara sha biyar ya zama tataccen dan daba, inda ya shiga wata kungiya ta wasu mutane masu yanka mutun su gudu. Haka ta faru da shi bayan ya soka ma wani yaro wuka a ciki, ya gudu ya bar garin, yan sanda suka nemeshi suka rasa, har suka kame ita Batular, inda wani bawan Allah da bata san ko wanene ba yayi belin dinta, to bayan an sako ta daga caji ofis din ne ta taho gida mota tayi ciki da ita, wanda hakan yayi sanadiyyar rasa kafarta guda ta dama" Mal. Labaran ya dan tsagaita, sannan ya dora, "To ita kuma waccen Hadizar, babbar 'yar tata kenan, da tana kula da ita, daga k'arshe sai abin ya dawo kamar ta dan samu ta6in hankali, kullun in banda kuka da kiran shehu bata da wani aiki, nan zata yi kashi, tayi fitsari, bata iya motsawa ko kadan, ana haka duk Hadizar na taimaka mata, kwastam, sai aka wayi gari aka ga Hadiza da katon ciki wanda babu wanda ya san inda ta yo shi, kuma ita dai ba aure akai mata ba, nan fa yaran unguwa suka dinga jifarta, suna zaginta, itama daga nan aka nemeta aka rasa. To ni dai a ganina kukan rashin ya'yanta, da kuma iftila"in da ta jefa mutane, shine yayi sanadiyyar rasa ganinta, ana haka kowa ya watse babu ko wanda yake kallonta, sai fa ni din nan, nima dan dai kawai in sauke hakkin makwabtaka, amma in ba haka ba, babu abinda zai sa na kalli mai mummunan hali irin na wannan matar" Ya karasa maganar, yana mai nuna ta da yatsarsa. "Hasbunallahu wa ni'imal wakil" Shine abinda Nawap yake maimaitawa, yayin da yayi saurin dauke idonsa akan Goggo, wadda yake jin kamar ya shaketa ya hada da bango ta mutu kowa ma ya huta. "Sai ki nemi yafiyar yarinyar nan, tunda Allah ya taimaka miki gata a gabanki a karo na biyu" Cewar mal. Labaran kenan yayin da yake kallon Goggo. "Na yafe mata ni kam, mal. Ko yadda Allah ya mayar da ita ai ya isa ishara gareta, da duk wani mai hali irin nata, fatan dai Allah ya yafe mana baki daya" Deedo ce take wannan jawabin a lokacin da take share kwallan idanunta. "Amen" duk jama'ar wurin suka ansa da. Goggo dai banda wasu surutai, da wasu yan bige bige kamar wadda sauro ke cizo babu abinda takeyi, sai kuma lokaci zuwa lokaci kaji ta kurma wani gagarumin ihu, babu Allah, bare kuma salatin annabi a bakinta. Kofar gidan suka fito gaba dayan su, in banda ita da bata iya takawa sai dai rarrafe. Gaban mota Nawap ya bude, ya fito da kudi wanda bansan adadinsu ba, mik'awa mal. Labaran yayi, "A taimaka a gyara mata ginin nan da ya rufta, sannan a dinga sai mata abinci, inda hali a samu wanda zai rinka tsabtacce mata wurin, ni zan rinka biya in har an samu wanda zaiyi hakan, mun gode mal., Allah ya kara girma, ya kuma baku ladar abinda kuka yi" "Amin" ya fada, sannan sukayi musayar number shi da Nawap, ya wuce zuwa cikin gidan shi, inda shi kuma ya kai kallonsa ga su Deedo da sukai jugum, "Sai ku shiga mu wuce" Babu gardama, duk suka shige suka dau hanyar komawa. Sai da suka shiga Bauchi sannan suka tsaya, domin neman abinda zasu ci, anan Deedo ta kira hally, tai mata kwatacen gidanta suka je, nan ta tarar da ita har da dan yaronta mai shekara daya da rabi, suna cikin fira take shaida mata halin da Goggo take ciki, addu'a dai sukai mata, inda daga bisani ta fada mata bikinsu kwana goma masu zuwa. Hally kuma tai mata alkawarin zuwa in har Allah mai kowa mai komai ya bata iko, sukayi sallama, sannan suka dau hanyar Kaduna. [26/04 02:05] Nty Lubiee: BA'A SHAN ZUMA… 111 NA LUBABATU MAITAFSIR & BENAXIR OMAR ®NWA Har suka iso gida firar da suke ta irin mutane masu halayya irinta Goggo ce, Hafsat wadda abin ya zama sabo a wurinta tace "Allah kenan, buwayi gagara misali, yanzu ji yadda matar nan ta dawo, ko duniyar da take ma hadama ta juya mata baya, suma ya'yan da ta musguna ma wasu saboda su sun gudu sun barta, kai Allah dai ya sa mu cika da kyau da imani," "Amen" suka ansa da shi, lokacin da suka iso kofar gidan, ana ta faman kwalla kiran sallar maghriba. * ******* Kwana ukku da dawowarsu, su Ummi suka dawo, inda tayo siyayya ta ban mamaki, sun hado mata lefe dai dai gwargwado, babu karya, babu kuma karanta a ciki, sai dai san barka, haka kayayyakin daki ma sun siyo dai dai iyawarsu, inda suka karasa siyen sauran anan gida Nigeria. Bayan Ummi ta natsu, ta huta duk hankalin kowa ya dawo jikinshi, anan take tambayar Deedo yadda akai bata je Ningin ba, ta kara da cewar "Ba dai mutumin can ne ya hure maki kunne ba?" Ta fada tana kallon Nawap, Murmushi Deedo tayi, tace "ko daya Ummi, munje ai" Nan ta labarta duk abinda ya faru, bata rage komai ba, Salati Ummi tayi, sannan ta kara da "Allah kasa my gama da duniya lafia" Suka ansa da amin gaba dayan su, inda suka d'auko wata firar, wadda yawanci duk labarin yadda za'a tsara bikin ne suke. Biki dai sai matsowa yake, inda yau rage kwana hud'u a fara. Kasancewar Deedo bata da tarkacen kawaye, hakan ya bata damar kammala duk wani rabon invitation da zata yi, wanda dama duk course mates dinta ne ta gayyato, sai fa yan mutanen da baza a rasa ba, wanda suke gaisawa a makaranta. Hakan ya bata damar natsuwa wuri guda, tana daukar gyara a wurin matar da Ummi ta dauko takanas, daga Niger republic. Haka Hafsat ma ba a barta a baya ba, itama da nata sinadarin gyaran na daban, wanda ya kasance tsakanin ta da Deedo ne, sirrin kissa da kisisina, da iya rik'e miji kawai take dora mata, yayin da Deedo take kwashe su a kwakwalwarta kamar tana rubutawa. Domin ko zamanin nan dai sai da kissar, amma sai kaga mace a harbutse, ko magana bata iya ba, sai kuma idan mijin ta ya kyallo wata abun ya zama bala'i, a daure a koyi sirrikan mazan aure yanuwana. Rana bata karya, wai sai dai uwar diya taji kunya! Inji Hausawa. Haka aka fara bikin Deedo da Yaa Nawap dinta, amarya sai kyalli take tasha dilka, tayi kyau har ta koshi da shi. Daga su sai su suke bikin nasu, dangin Maman ta ne, sai kuma dangin baban su Nawap, sai 'yan gayun kawayenta wanda duka duka basu wuce mutun sha biyar ba, biki ne suke hankali kwance ba tare da hayaniya ba, babu wata bidi"a, illa kyakkyawar dinner da za suyi a gobe, sai kuma daurin aure. Amarya ce ta fito cikin light brown din gown mai asalin kyau, wadda ta dace da kirar jikinta, yayin da KHADY'S MAQUILLAGE ta gwangwaje ta tsararran make up mai daukar hankali. Tayi kyau dai dai misali, haka angon ya fito a cikin danyar farar shaddar Sheraton, wadda taji lafiyayyan aiki da light brown din zare, hularshi da takalmansa, gami da agogonsa duk light brown din, sunyi kyau kamar a sace. Bayan sun shigo hall din Kabir Gymnasium, inda ya kasance can ne aka tanada domin gabatar da dinner, nan fa aka fara sakin flash, masu video coverage suma suka cigaba da dauka, yayin da zaka hango farin cikin da yake kwance a fuskar Ummi domin ganin wannan kyakkyawar rana. Haka aka cigaba da rakashewa, ana gwangwajewa yadda ya kamata, har aka gama lafia, kowa ya kama gabansa. Washe gari da misalin k'arfe 1 na rana aka Daura auren Dr. NAWAP KHAMIS, & FIRDAUSI KABIR SANI, akan sadaki mafi daraja, wanda ya ta'allak'a akan koyarwa ta ma'aiki (S.A.W). Bayan daura auren da misalin karfe shidda na yamma aka dauki amarya sai gidanta dake Sultan Road. Komai ya ji, babu abinda Ummi bata yi ba, sai kuma fatan zuri'a mai albarka. Kwanansu biyu a Kd, sannan suka tattara suka wuce Abuja, kasancewar hutun da Nawap ya dauka ya kare. Rayuwarsu abin sha'awa, soyayya suke ta ban mamaki, kowa kokari yake yaga ya faranta ran dan uwanshi, dan haka suke zama na jin dadi da salama. Satinsu biyu a Abuja su deedo suka koma hutu, bata da yadda zata yi, dole ta dawo Kd, da sabuwar Mercedes-AMG dinta wadda Nawap ya bata tukwicin amarci. BA’A SHAN ZUMA… K’ARSHE BA'A SHAN ZUMA… 112 NA LUBABATU MAITAFSIR &BENAXIR OMAR ®NWA Shi da kanshi ya tuko su, gidansu suka zarce ko da suka shigo Kd, wanka sukai suka gabatar da sallar maghriba wadda tai musu a hanya, Deedo ta fito cikin wani skinny long skirt, da yar top dinta, gashinta, ta tara shi wuri daya ta daure, kitchen take k'ok'arin shiga domin ta sama masu abinci, a dai dai lokacin Nawap ya fito palon shima cikin blue din jeans da red din t-shirt, gabanta ya karaso, ya mika mata agogon dake hannunsa, sannan ya miko hannun, yana kallon ta. Ansa tayi, tana tura baki tace "Abinci fa zan girka mana, kuma ka zo zaka tsaida ni" Dariyar yadda tayi da bakinta yayi, "Gobe kaman haka baza ki ganni ba, balle har na tsaida ki" Ya fada yana langabar da kai, Itama fuskan tausayin tayi, tunowar da tayi gobe fa ita kadai ce; babu yayan ta. "Yi sauri dauko hijab dinki muje gaishe da Ummi, can sai mu samu abinda zamu ci" Ya fada yana kallon console mirror din dake makale a palon, yana gyara collar rigarsa. "Da gaske Yaa Nawap?" Ta fada cikin zumudi. "Zan ce na fasa ko ki wuce kizo mu tafi" Da dan gudu ta shige daki tana fadin "I'm sorry Mon amour", Bata wani dade ba ta fito sanye da dogon hijab har gwiwanta, suka rufe gidan suka shige mota sai gidan Ummi. Taji dadin ganinsu sosai, sun kuma yi sa'a tana zaune a dining table tana cin abinci, dan haka ba tare da bata lokaci ba suka zauna suma, Deedo ta zuba masu, suka cigaba da ci suna fira. Sai wurin goma da rabi, sannan suka yi mata sallama suka wuce gida. A palo suka zauna, firar yadda zasu yi missing juna suke ta yi, a haka har sha daya da rabi, inda Deedo ta fara hamma, bata ankara ba ta bingire a wurin ta cigaba da bacci. Juyowar da Nawap zai yi ya ganta sai bacci take, murmushi yayi, don ya zata baccin karya ne, saboda haka take mashi, sai ya dauke ta ya kaita daki sannan ta mik'e. Shigewa yayi ya gama shirin baccinsa, ko da ya fito dai a haka ya tadda ta, dan haka ya sa6i abinshi suka wuce dakin baccinsu. Tun karfe biyar na asuba suka tashi, wanka suka yi, tare da alwallah sannan ya ja su sallah, bayan sun gama suka yi adduoin da suka saba, Nawap ya mike ya koma gado, inda ita kuma ta wuce kitchen ta shirya breakfast mai sauki, sannan ta shirya jikinta da jeans wanda ya matse ta tsaf, ta samo top dinta mai fadi ta dora, tayi kyau sosai, sannan ta matsa inda yake a kwance, lokacin karfe bakwai dai dai, fuskarsa take shafawa har ya buda idonsa, "7:am har yayi kana bacci, ka manta akwai aiki yau ne? Nd flight din karfe takwas zaka bi" Ya mike tare da salati, "Ai duk lefinki ne" Ya fada yana cire kayan jikinsa, Ta mika masa towel, "je ka shirya idan ka fito sai kayi banbanmin" ta fada tana fita daga dakin. K'arfe takwas saura suka fito, jikinta sanye da doguwar abaya, ta yane kanta da gyalen, ita ta kaishi har airport, sannan ta dawo, tana mai cike da kewa da maraicin mijin ta. Daga nan ita ma skool ta wuce domin sun fara lectures tun satin da ya wuce. BAYAN SHEKARA HUD'U Deedo ce ta fito daga babban asibitin gwamnati na garin Kaduna, atamfar super wax ce jikin ta dinkin riga da skirt, sai dogon hijab dinta, hannunta na dama sagale da farar riga ta likitoci (lab coat), yayin da dayan hannun yake dauke da jaka, da kuma katon littafin (text book) mai hoton kwakwalwar dan Adam a jiki. Gaban motar ta kirar BMW M4 ta isa, ta juye tarkacen hannunta a baya, sannan ta bude bangaren driver ta shiga ta bata wuta, ta wuce hankalinta kwance. Cikin unguwar rimi ta nufa dai dai kan alkali road, naga tayi parking gaban wani asibiti wanda aka rubuta TAIMAKO SPECIALIST CLINIC, lab coat dinta ta buda bayan motar ta dauka, yayin da ta shige cikin asibitin kasancewar wayar da aka mata kan tayi sauri tana da marassa lafia. Cikin k'warewa take bin gadajen marassa lafiyar, a bayanta kuma nurse ce tana dauke da file na kowanne patient a wurin. Gadon wani dan tsoho ta isa, wanda yake fama da ciwon zuciya, ta duba file dinshi, ta juyo da kallonta gare shi "Baba akwai gwaje gwaje da zanyi maka, akwai kuma na jini, sannan kuma zan duba bugun zuciyarka, amma sai kayi hakuri fa" Cikin ciwo tsohon yace "Kuma duk a nawa zakuyi wannan aikin? Ni fa wlh ba kudi ne da ni ba, sai da nace su kaini na gwamnati, amma suka kawo ni nan, ni ban san ya zanyi ba 'yar nan" Da murmushinta, ta kalle shi "Kar ka damu Baba, domin kuwa babban dalilina na bude asibitin nan ba komai bane, sai dan na taimakawa marassa hali irin ka, in sha Allah za ayi komai, ba kuma tare da ko sisinka ba" Ta mik'awa nurse din file dinshi, sannan ta wuce zuwa gado na gaba, haka har ta gama round dinta, ba ita ta bar asibitin ba sai misalin karfe biyar na yamma. [26/04 09:40] Nty Lubiee: BA'A SHAN ZUMA… 113 NA LUBABATU MAITAFSIR & BENAXIR OMAR ®NWA Tana shiga gidan ta zube a palo saboda tsabar gajiyar da ta kwaso, hannuwanshi taji ya ziro ta kafadarta yana danna mata su a hankali, lumshe ido ta fara yi, tana jin tamkar a mafarki, "Likita bokan turai" shine abinda ta ji an fada, wanda yasa tayi firgigit ta juyar da kanta tana kallonsa. "Yaushe a gari?" Ta fada tana kare mashi kallo, murmusawa yayi, "Ko 30 mins banyi da shigowa ba, na gaji da missing matata bazan iya daurewa har sai Friday kafin na ganta ba" Ya zagayo inda take a zaune ya zauna a gefenta, hannuwansa cikin nata. Bude bakinta zata yi magana wata kyakkyawar yarinya mai asalin kama da Nawap, ga dan banzan wayo, duk da shekarunta basu wuce biyu ba, ta rugo da gudu ta fada kanta, tana shashshekar dariya. "Mammy sannu da zuwa" ta fada cikin maganarsu ta yara, lokacin da ta mik'e ta rungumo wuyanta, tana mai nuna farin cikin ganin Mammyn tata. Sama Deedo ta daga ta, tana fadin "Thank you Ummina " Nawap ya jawosu jikinshi yace "Ummi har kin manta da ni ko, dan kinga mammy ko? Gobe ma zan koma bazan kara wasa dake ba" Suka kyalkyale da dariya ita din da Deedo, yayin da ta zaunar da ita a tsakaninsu, ta mika hannu ta rungumo Nawap, shima haka yasa hannunsa ya k'ank'amesu yana jin soyayyar matarshi, da tilon 'yar tasa, har cikin birnin zuciyarsa. ALHAMDULILLAH, anan na kawo karshen wannan labari, kuskuren da nayi Allah ya gafarta mana, Allah kuma ya amfani abinda na fada dai dai, ya bamu ikon amfani da darasin da yake ciki. This is a dedication to a sis from another mother (FEEDO- DEEDO) thank you 4 been there always. Special thanks to Aysha Chuchu, Jam33la & Ummu Ahmad, 4 loving this story like no one. Nagode kwarai da hakurinku akan jinkirin da aka samu kafin kammaluwar wannan labari. Ku cigaba da kasancewa tare dani a labarina na gaba wanda ya ansa sunan K'ADDARAR AURENA! Lubabatu Maitafsir & Benaxir Omar muke yi maku fatan alkairi a koda yaushe. Complied by Princess Aysha Muhammad