[7/30, 10:00 PM] Nanameera😍✌🏻: https://chat.whatsapp.com/LVwoOVW31kC9r0d7QRPZhP *BA ITA BA CE..💖💖💖* *MIKIYA WRITERS ASSO...* *Follow my account both arewabooks nd Wattpad.* *nanameera08*_arewabooks_. *@Nanameera08* _wattpad_. *Nanameera* # *SQUAD 2024*. ```PAGE 01``` *بسم لله الرحمن الرحيم* Wata iriyar tsawa mai firgitar da zuƙata aka yi wacce tayi daidai da sanda jaririyar data haifa ta tsala wani irin ihuu mai cika kunnuwa, ruwane ake yinsa bana wasa ba ruwan da duk wani mai hankali zai dinga jin tsoron zubarsa an daɗe sosai ba iya makamancin irin wannan ruwan ba cikin garin Damaturu, duhu ne mamaye da bukkar da suke ciki domin fitilar kwan gab take da mutuwa dan ko haskenta ba'a gani sai ɗan kyalli wanda shine zai tabbatar maka da cewa an kunna fitilar. Shirun da jaririyar ta yi ya yi daidai da ɗaukewar ruwan tamkar ba'a taɓa yinsa ba a hankali matashiyar matar take sauke wani wahalallen numfashi wanda take jansa dakyar, tsuroo magidancin mutumin ya zuba idanunsa yana kallon abinda matar tasa ta haifa sosai kuma ya yi mamakin yin shirun jaririyar. Above 20mins suna cikin wannan halin har sannan kuma babu wanda ya furta wata kalma a cikinsu, dakyar matar ta yunƙura dan ganin halin da abinda ta haifa yake ciki daidai lokacin da zuciyarta tayi wata irin kyakkyawar buguwa dalilin ganin ɗiyar tata da tayi yashe a gefenta ko ba'a faɗa mata tasan itama tabi sauran ƴan uwanta, runtse jajayen idanunta tayi wasu zafafan hawaye suka shiga zirarowa kan kuncinta tabbas taji babu daɗi kamar yanda ta saba jin babu daɗi ce eh.' a duk sanda ta haifa ɗa ko ƴa kuma ya mutu amma ya zatayi? tata ƙaddarar kenan jiki asanyaye ta janye gawar jaririyar bayan ta yanke cibiyar sannan ta ɗorata akan ƙirjinta bayan tsayin watanni data ɗauko tana ɗawainiya da cikin tasha wahala kamar yanda ta saba sha kowane lokaci sai gashi yanzu ma Allah ya karɓi abarsa. Miƙewa magidancin ya yi ya ɗauki wata ƙwarya wacce ke can gefe guda ya yi waje... Wani irin sanyin ake mai tsara ƙofofin jiki yayinda har sannan yayyafin bai gama zuba ba yanayin da ya yi wani irin daɗi banda ƙamshin ƙasa babu abinda ke tashi sai kuma kukan kwaɗi wanda ya samo asali dalilin taruwar ruwa a wajejen, daga can wani gefe inda ruwa ya taru yanayin wajen kamar pond ya ƙarasa yana tafiya a hankali. Tsugunawa ya yi sannan ya kafa kan tulun yana tarar ruwan da yake zuba a hankali yake sauke ajiyar zuciya wacce take nuni da halin da zuciyarsa take ciki saidai tsananin tsoron Allahnsa da kuma yarda da ƙaddara ya hanashi fallasa asirin zuciyarsa. Tamkar wanda aka tsikara haka ya juya gefensa daga can gefe guda ya hango wani farin abu mai ɗan faɗi kai tsaye bazai iya cewa ga abinda yake ciki ba. Ɗauke idanunsa ya yi daga wajen yana ambaton sunan Allah ya miƙe tsaye bayan ya gama ɗiban ruwan ya ɗora bisa kafaɗarsa. Gaba ya yi batareda ya sake kallon inda yaga wannan farin kyallen ba, da sauri yaja ya tsaya saboda wata irin bugawa da zuciyarsa ta yi a hankali kuma ya juyo yana kallon bakin pond ɗin tamkar wanda mayen ƙarfe ke jansa haka ya samu kansa da komawa wajen sosai sanyin asubar yake shigarsa wanda ya haifar masa da wani irin masassara mai kamada zazzaɓi, sake tsugunawa ya yi a karo na biyu amma wannan karon ya tsuguna ne gaban wannan farin yadin sosai ƙirjinsa ke dukan uku uku yayinda wata matsananciyar fargaba ta ziyarceshi a nutse bakinsa ɗauke da sunan Allah ya ɗora hannunsa kan yadin amma ga mamakinsa sai yaji wani irin laushi wanda bai taɓa jinsa a jikin wani nau'i na tufafi ba tamkar auduga saidai kuma yanada wani irin gashi a jikinsa kamar na jikin mage hannunsa na wata iriyar kakkarwa ya buɗe yadin wanda kai tsaye za'a iya kiransa da bargo ya subhanallahi!! da sauri ya yi baya sakamakon abinda ya yi arba dashi cikin wannan bargon cikin ransa yake furta duk wani sunan Allah da yazo bakinsa kuma iyaka iyawarsa kusan 2mins yana wannan halin kafin kuma ya yi ta maza saboda wata jarumta da yaji ta zo masa a hankali ya saka hannayensa duk biyun ya ɗauki bargon sannan ya miƙe tsaye kasancewarsa mutum mai cikar zati ya sanya ya ɗauki tulun da ɗaya hannunsa sannan ya cigaba da tafiya dan komawa inda ya fito. Yanda ya bar matar haka yazo ya tarar da ita har sannan kuma jaririyar tana kwancen bisa ƙirjinta tayi nisa cikin duniyar tunani dan kwata-kwata batasan ya shigo cikin bukkar ba lura da hakan ya sanya bai kulata ba ya ƙarasa can gefen tabarmar kabar ya shimfiɗar da halittar dake cikin bargon domin idan har ya ce yasan mene a ciki ya yi ƙarya ganin yanda bargon yake a jiƙe ya sanya ya yi saurin yaye shi daga cikinsa ya ilahy wani irin daddaɗan ƙamshi ne ya ratsa cikin hancinsa wanda lokaci ɗaya ya cika cikin ƴar ƙaramar bukkar tasu jinjina kansa ya yi cikeda al'ajab ya miƙe yana ƙarasawa wajen matar tasa dukda duhun dake bukkar hakan bai hanashi ganin kyallin hawayen dake fuskarta ba numfasawa ya yi sannan ya sanya hannayensa ya karɓi jaririyar hannunta sannan ya miƙe ya fice daga bukkar sai a sannan ta saki wani raunataccen kuka mai tafiya da imanin duk wani mai saurare kuka ne mai fitowa tun daga ƙawon zuciyarta kuka ne mai nuni da tsananin baƙin cikin da take ciki kanta ta matse tsakanin cinyoyinta ta cigaba da rera kukanta. Misalin ƙarfe 5:10am ya dawo cikin bukkar lokacin haske ya ɗan fara shigowa cikin bukkar da sauri ya ƙarasa wajen da ya yi ajjiya dan a wannan lokacin ji ya yi yana buƙatar mene ne shigowarsa ya yi daidai da ɗagowar matar a hankali kuma take binsa da idanunta wanda suka sauya launi daga fari zuwa jaa hannayensa ya sanya ya ɗaga halittar daidai nan kuma ta ƙaraso gabansa da wani irin sauri kallonsa take sai kuma ta kalli abinda ke hannunsa jaririyace mace kuma sannan kana ganinta kasan ɗanyen jego ce domin ba zata taɓa shige kwana ɗaya da haihuwa ba, da sauri ta karɓe yarinyar tana zuba mata idanu fara ce irin tass ɗin irin farin da ba'a fiye samun ƴaƴan hausawa dashi ba duk da kasancewarta jaririya hakan bai ɓoye asalin kyawun fuskarta ba idanunta a rufe suke yayinda gashin idanun ya kasance ya sakko har ya zo wajen kan gefen idanunta hannayenta a dunƙule suke kamar na kowace jaririya wacce take sabuwar haihuwa danshin da taji a jikinta da kuma lura da tayi kamar bata numfashi ya sanya ta yi saurin rungumeta kasancewar babu ko wando jikinta da sauri kuma ta kalli mijin nata a karo farkon bayan haihuwar tata ta ce "Ki kira sarkin ruwa yaya Gani" Bai ce komai ba ya miƙe tsaye yana tafiya da ɗan sassarfa ya fice daga bukkar, sake ƙanƙameta ta yi tana sauke ajiyar zuciya a hankali kuma wasu sabbin hawayen suka ziyarci kuncinta saidai wannan karan na zallar farin ciki ne duk da har sannan batasan daga inda mijin nata ya samo jaririya kuma ta tabbatar da cewa ba wacce ta haifa ba ce ba. Wata irin nannauyar ajiyar zuciya ta sauke lokacin da taji yarinya ta tsala ihu batasan lokacin da hawaye suke fara fitowa daga cikin idanunta ba sosai tayi murna dunƙule hannayenta ta yi wanda ke nuni da zallar farin cikin da take ciki miƙa masa yarinya Sarkin ruwa ya yi sannan cikin sakin murya ya ce"ina maka fatan Alkhairi Ya Gani Allah ya yara maka ita" tattausan murmushi ya yi sannan ya furta cikin kami'lalliyar muryarsa "Ameen ya rabbil alameen" fita Sarkin ruwa ya yi ita kuma ta ƙaraso da sauri tana duban kyakkyawar jaririya ta ce"Ya Gani ki bani shi" sai a sannan nagane ba bahaushiya ba ce domin asalin muryata ta Fulani ta bayyana cikin kalaminta koda yake daman da zarar kayi ido biyu da ita fuskarta taza shaida baka hakan kasancewarta kyakkyawar bafulatana sanye take da wasu kayan Fulani irin blue colour ɗin nan sai murjani wanda ta rataya a wuyanta, murmushi ya yi kawai sannan ya miƙa mata ita da sauri ta rungumeta a ƙirjinta tamkar wani ya ce zai kwace ta cikin kurɓattaciyar hausarta ta ce" wacece shi?, ko ɗiyata ne ya tashi?" gyara zamansa ya yi kan tabarmar kabar sannan ya kalleta a nutse kuma ya furta "*BA ITA BA CE ba!!*" sake kallon fuskarta ta yi ganin yanda take barcinta yasa ta kalleshi da ƴar damuwa a fuskarta ta ce" to waye shi?, kuma ina ka same shi?" Numfasawa ya yi sannan ya kama hannunta cikin sanyin murya ya labarta mata duk abinda ya faru, ya ce"saboda haka na yanke shawarar zamu kula da ita daga nan har ƙarshen rayuwarmu zamu riƙeta matsayin ɗiyarmu wacce ta mutu, tabbas na tabbata akwai wani ɓoyayyen al'amari a tareda wannan yarinyar wanda lokaci ne kawai zai tabbatar mana da hakan" yanayin yanda yake magana zaka gane cewa ba yare ɗaya suke dashi ba domin shi yana magana ne irin yanda mutanen garin ke magana musamman ma Kanuri wanda hakan ya tabbatar da cewa shi ɗin ya kasance Kanuri ne. Cikin sanyin murya itama ta ce" karki damu Ya Gani zan kula da ita kamar ɗiyata dana rasa nima naji ina sonshi sosai kuma ma yana kama dani kin gani" murmushi ya yi ganin da gaske nuna masa take ya gani jaririyar na kama da ita ya girgiza kansa sannan ya miƙe ya fice daga bukkar yayinda ita kuma ta ɗago fuskar yarinyar tana kallonta kallon da yake nuna irin ƙaunar da take mata ita kaɗai kuma take sakin wani yalwataccen murmushi haka har bacci ɓarawo ya saceta. *BA ITA BA CE...💖💖* *#Human trafficking* *#heart touching* *#destiny* *#Loyalty* *#pity* # *SQUAD 2024*. *Comments nd like*. [7/31, 3:29 PM] Nanameera😍✌🏻: *BA ITA BA CE!...💖💖* *MIKIYA WRITERS ASSO...* *Follow my account both arewabooks nd Wattpad* *nanameera 08* _arewabooks_ *@Nanameera08* _wattpad_. *Nanameera* # *SQUAD 2024*. ```Page 02``` *Rugar Jama'are* Durƙushe take gabansa ta zuba masa idanu tana kallonsa ƙaramar yarinya ce ba zata shige 4 to 5yrs ba tana sanye da kayan Fulani Blue colour as usual gashinta dake zube a gefenta wanda aka kalbaceshi irin manyan kalbar nan guda biyu yabi da kallon a hankali kuma ya sake lumshe idanunsa shi kaɗai yasan irin tsananin azabar da yake ji, kamar zatayi kuka take kallon mahaifin nata cikin wata siririyar murya mai Matuƙar zaƙi da ɗaukan hankali take cewa"Papina sannu zaka samu sauƙi kaji sannu dan Allah" bata rufe bakinta ba aka ɗaga labulen wanda ya kasance asabari ne suka shigo da sauri kuma cikin ɗaga murya Dada ta ce"Baba kura zo ki dubashi aradu mun higa uku ya Gani sannu Allah zai tashi kafaɗunki" da sauri wanda take cewa Baba kuran ya ƙaraso yana zuwa ya zube a gabansa hannunsa ya kai ya taɓa wuyansa sosai yaji zafi a jikinsa hakan yasa duk hankalinsa ya ƙara tashi a matuƙar razane kuma ya miƙe ya fice daga cikin bukkar, da kallo suka bisa kafin Dada ta kalleta da idanunta wanda suka sauya launi ta ce"kai Muhaira ɗebo ruwa a bashi yasha" da sauri ƴar ƙaramar yarinya ta miƙe ta ɗauki ɗan ƙaramin jallan ruwan tayi waje saidai kafin ta fita ta juya a hankali tana kallon fuskarsa ga mamakinta sai taga shima ita yake kallo wani tattausan murmushi ya yi mata dukda yanda bakinsa yake a bushe wanda ke nuni da asalin ciwon da yake ciki a hankali itama ta mayar masa da nata kyakkyawan murmushi ya ilahy wani irin sihirtaccen kyau ƴar yarinya ta yi tamkar wata ƴar aljanu haka ubangiji ya yi mata kyau kwayar idonta blue colour ce irin mai hasken nan sai wani irin sheƙi suke saɓanin na sauran mutane da suka kasance baƙaƙe. Da hannunsa ya yi mata alama da tazo hakan yasa ta ajiye jallan ta ƙara sa gabansa ɗan ƙaramin hannunta ya kama a hankali kuma ya buɗe bakinsa wanda yawo yake shirin ƙafewa daga cikinsa ya ce"Baddon Papi!" da sauri ta ɗaga kanta tana kallonsa wasu zafafan hawayene suka shiga gangarowa kan kuncinsa da sauri ta saka ɗaya hannun nata tana goge masa kwaɓe fuska ta yi cikeda shagwaɓa ta ce"Papi kadaina kuka kaji dan Allahhhh" shafa fuskarta ya yi hannunsa na kakkarwa ya gyaɗa mata kai dan bakinsa ya yi masa nauyi, Bani kura ne ya shigo bukkar shida wani mutum a bayansa da alama kuma mai magani ne. Bayan sun zauna ya kalli Papi sai kuma ya kalli Muhaira dake gefensa ya ce"Baddo maza jeki gidana ki karɓon ƙwarya" miƙewa Muhaira tayi ta fice tana tafiya da a sauri a hankali kuma take waiwayen bukkar tasu. Tafiya kawai take da sauri da sauri dan ko wasa bata tsaya ba haka har ta baro rugar tasu, kasancewar su a cikin gari suke ya sanya ta ɗan yi tafiya mai yawa kafin ta ƙaraso ƙofar gidan, "Wundo!! Wundo!! Wundo!!" turo baki Muhaira ta yi bata ce komai ba har sannan, da sauri ya'acca ta kalleta cikin ɓacin rai ta ce"ke kam Muhaira bakida mutunci ko?, banda iskanci ki shigowa mutane gida babu sallama sannan kuma ji ana waye kinyi tsif abinki ko?" sosai yarinyar ta tsorata da tsawar da tayi mata bakinta na rawa ta ce"unn...uhhhmm...dan...daman Bani kura ne ya ce a bashi ƙwarya" tsaki ya'acca ta yi ta ce"shine zaki tsaya kina mana shashanci" sunkuyar da kanta ta yi bata ce komai ba amma duk a tsorace take, shiga ɗaki ta yi ta ɗauko ƙwaryar ta mika mata, da sauri Muhaira ta karɓa sannan ta juya da gudu tayi waje, tsaki ta yi tana kallonta ta ce"shashasha kawai". Da sauri ta shigo cikin bukkar hannunta riƙe da ƙwaryar saidai me?, babu Bani kura wanda ya aikata haka zalika babu mai maganin da aka ɗauko sai Dada wacce ke zaune gefensa banda kuka babu abinda take yayinda Papi aka rufeshi da wani tsohon bargon, da sauri ta ƙarasa wajensa tsugunawa tayi gaban Dada tana cewa"Dadana Papi ya yi bacci?" kallonta Dada ta yi amma bata ce mata komai, sosai idanunta sukayi jajur ko ba'a faɗa maka ba kasan ba ƙaramin kuka tasha ba, kuka ta fashe dashi tana murza idanunta da kallo kawai Dada ta bita dan ita tama gagara magana ganin Dada bata kulata ba har sannan yasa ta kwanta a wajen tana birgima, Bani kura ne ya shigo shida masu maza a bayansa suna zuwa kai tsaye inda Papi ke shimfiɗe suka nufa ganin yanda take kuka yasa Bani kura ya ce"Aishatu ke dawa?" daga yanayin muryarsa zaki fahimci irin damuwar da take tare dashi, da sauri Muhaira ta tashi jin ya kira sunanta ta ƙarasa wajensa har Sannan kuma kuka take ta ce"Bani koba Dada bace" janta ya yi jikinsa ya rashe mata hawayen fuskarta sannan ya ce "to kiyi haƙuri zauna anan" shiru tayi ta zauna a gefensa tana kallon bargon da suka rufe Papi. Ƙarasawa suka yi bayan sun yaye bargon suka kamashi suka fita daga cikin bukkar duk wannan abun da ake banda kallo babu abinda Muhaira ke yi dan ita bata gane ba mene ne abinda ya faru ba, Dada kuwa ƙara sautin kukanta ta yi jikinta na wani irin kyarma, tashi Muhaira ta yi ta koma kusada ita ta zauna amma bata ce komai ba sai kallon mahaifiyar tata take, ita kuwa Dada tunanin yadda rayuwarsu zaka kasance take, tunanin rayuwar Muhaira take, zuciyarta cike take da tausayin tilon ƴar tata, tabbas ƙaddara ta riga fata domin Papi ya tafi ya barsu a lokacin da suka fi bukatarsa. Tunawa da wannan yasa ta sake rushewa da wani irin kuka mai tsuma zuciya ita kuwa Muhaira bata fahimtar komai ƙanƙantar shekarunta da kuma ƙarancin shekarunta sune suka yi tasiri wajen gazawa kwakwalwarta ta fahimtar da ita duk a tunaninta Papi ɗin wani waje zasu kaishi wanda zasu dawo mata dashi. Amma saidai abinda bata sani ba shine Papinta ya tafi kenan tafiyarda duk wanda ya yi ta baya taɓa dawowa,tun tana tambayar Dada ina Papinta har ta fahimci cewa Papinta ya bar duniyar a hankali mintuna ke komawa awanni awanni ke komawa kwanaki kwanaki ke komawa sattituka sukuma suke juyewa izuwa wattani wattani kuma ke juyewa izuwa shekaru, tafiya ta tafi a ƙalla Papi zai yi shekaru uku da barinsa duniya zuwa wannan lokacin kuma Muhaira tanada shekaru 8 a duniya. Wani irin sanyin ake mai ratsa ɓargon da jijiya sanyinne irin wanda ke haddasa cuttukan musamman Asthma, pneumonia, sickler dama wasu ciwukan, safiyar ranar juma'a ce gabaɗaya rugar Jama'are tayi tsit kowa yana cikin bukkarsa da iyalansa, tsugunne take gaban wata tukunya wacce aka ɗorata akan dutsuna guda uku wanda suka zama sune murhun da take girkin akai sosai take haɗe jikinta yayinda numfashinta ke wani irin fuzga ita kaɗai tasan azabar da take ji amma kuma burinta bai shige ta gama damawa Dada kokon ba. Cikin mintuna ƙadan ta kammala ta juyeshi cikin wani tsohon kofi sannan ta tashi da gudunt ta shige bukkar, tana nan yanda ta barta a kwance idanunta a rufe suke amma ba bacci take ba ajiye kofin hannunta ta yi sannan ta shiga kamata tana faɗin" Dada tashi, tashi kinji na dama miki kokon tashi kisha sai kisha magani" dakyar Dada ta buɗe idanunta ta kama hannun Muhaira ta miƙe daga kwancen ɗora kan Dadar tayi akan ƙirjinta dukda nauyin da tayi mata amma ko kaɗan hakan bai dameta haka ta ɗauki kofin kunun ta kai mata bakinta, girgiza kai Dada ta yi tana riƙe hannunta ta ce"A'a Muhaira bazan iya sha ba akwai abinda nakeson na faɗa miki tabbas wannan cutar tawa bata tashi ba ce saida... wani irin jan numfashi ta yi tana saukeshi a hankali runtse idanunta tayi hawaye suka shiga rige-rigen sakkowa kan kuncinta alama ta yi mata data bata kunnenta a hankali Muhaira ta kara kunnen nata kusada fuskar mahaifiyartata dan taji me zata faɗa mata. Above 5mins tana yi mata magana zuwa lokacin kuma banda hawaye babu abinda Muhaira ke yi gaba ɗaya tunaninta ya tsaya cak batada wata sauran dabara zuwa sannan kuma bata iya fahimtar abinda mahaifiyar tata ke faɗa mata. Shirun da taji Dada tayi yasa ta kalleta wata irin razananniyar ƙara ta fasa wacce ta yi daidai da shigowar Falmata cikin bukkar da sauri ta ƙaraso tana kallonsu duka ganin yanda Muhaira ta ƙamƙame Dadan har sannan kuma kuka take yi kallo ɗaya Falmata ta yi mata tasan cewa Ubangiji ya karɓi abarsa, ikon Allah kenan babu yanda mutum ya iya kamar yanda Papi ya mutu haka yanzu itama Dada tabi bayansa "Dadata! dan Allah dan Annabi ki tashi karki mutu ki barni banida kowa Dadaaaa...ki taimaka ki tashi Dada ko kinfi son nayi kuka har ƙarshen rayuwata?, banida kowa Dada kema kuma bakida kowa Papina ya tafi har yau bai dawo ba kema shine zaki bisa??? kenan duk baku sona? meyasa Dada?, me nayi muku?, ina zani yanzu? wane zai kula dani Dadaaaaa..." maganar ta tsaye a maƙoshinta sakamakon wani irin nauyi da zuciyarta tayi da gudu ta miƙe ta fita daga bukkar saboda wani irin amai daya tawo mata saidai me???? madadin amai na abinci ko kuma na ruwa wani irin guda-gudan jini ne ya shiga fitowa daga bakinta sai kuma ta faɗi nan ƙasa sumammiya. Allah sarki rayuwa tabbas babu abinda ke ɗorewa sai ikon Allah cikin ɗan lokaci ƙalilan Muhaira tarasa iyayenta guda biyu wanda hakan shine mafarin ƙaddararta, tabbas labarin rayuwarta akwai taɓa zuciya, musamman daya kasance tanada ƙarancin shekaru Hakazalika kuma babu wani wanda zata kama ta ce wannan danginta ne kasancewar iyayen nata Fulanin tashi ne, tarasa gatanta tun tana jaririya sannan kuma ta sake rasa waɗanda suka maye mata gurbin wannan gatan data rasa ya zatayi??dawa zata rayu?? wace irin ƙaddara ce ke bibiyar rayuwarta??... *17 years*. *Maitama district, Abuja* *No:113*. *Mai Zamani pov.* Wani zazzafan numfashi ya sauke bayan ya saki curtain ɗin, a hankali cikin tafiyarsa mai nuni da isa ya ƙaraso gefen kujerar dake gaban gadon ya zauna sanye yake da wata Polo T-shirt white colour sai kuma wani Cargon Three-quater black colour a jikinsa ba wani fari bane can haka zalika kuma ba baƙi bane yana dai da haskensa dai-dai misali, ɗan ƙaramin tsaki yaja sannan ya buɗe system ɗin gabansa ya shiga dubawa. Duba da irin yanda yake kallon system ɗin zaka fahimci tabbas wani abu mai matuƙar muhimmanci yake gabatarwa, turo ƙofar ɗakin tayi bakinta ɗauke da sallama a ciki ya amsata sannan ta ƙaraso gabansa zama tayi gefensa tana sanye cikin wani material black colour mai adon flower pink ɗinkin doguwar riga A-shape mug ɗin gabanta ta ajiye masa gefen table ɗin gabansa ta cigaba da kallon abinda yake, above tens minutes sannan ya kammala ya rufe system ɗin sai a sannan ya ɗago yana kallonta fara ce tass kuma asalin kyakkyawa dan ko ba'a faɗa maka ba kasan ita ɗin ba ta kasance cikin ƙabilar Hausawa ba ganin irin kallon da yake mata ya sanya ta sunkuyar da idanunta ƙasa tana wasa da fingers ɗinta masu ɗauke da zanen flower wacce tayi matuƙar amsar farar fatarta taɓe baki ya yi sannan ya ɗauki mug ɗin data ajiye a hankali kuma yakai tea ɗin bakinsa wani runtse ido ya yi saboda wani irin zaƙi da yaji har cikin kansa da sauri ya ajiye mug ɗin yana mata wani hargitsatsen kallo ya ce "Ma'eesha I'm play with you?" kallonsa ta yi fuska a kwaɓe ta ce" A'a yaya I'm sorry wlh banson sugar ya yi yawa ba I'm so sorry" kallonta ya yi from head to toe sannan ya yi tsaki ya tashi bai tsaya cigaba da jin abinda take faɗi ba ya ɗauki wayarsa ƙirar iphone 14pro max ya yi waje. Ajiyar zuciya ta sauke tana dafe ƙirjinta sanin halin yayan nata sai kuma ta miƙe itama tabi bayansa. A nutse take taka stairs ɗin benen har ta sakko gaba ɗaya, ya rabbi wani irin haɗaɗɗen parlon ne irin mai tafiya da imanin mutum ɗin nan komai na cikinsa golden colour ne tun daga kan kujeru, curtains, carpet, center table even bulb da suke parlon golden colour suke bayarwa banda sanyin A.C babu abinda ka keji a parlon sai kuma wani irin daddaɗan ƙamshin da yake fita daga kowace kusurwa ta parlon ko ba'a faɗa maka ba kasan wannan parlon bai yi kamada na ƙananan mutane ba ko kuma basu ji da ƙaramin arziƙi parlon ne irin wanda koda a cikin Villa yake sai ance ya haɗu iya haɗuwa, parlon ne na irin manyan nan wanda suka jiƙu da manyan kuɗaɗe, a hankali ta ƙaraso cikin parlon inda ta hangin iyayen nata. Zaune yake kan kujera Three seater yana sanye da wata dakakkiyar shadda Madam gezner blue black ɗinkin jamfa da babbar riga idanunsa maƙale da wani farin tabarau yayinda yake kallon jaridar dake hannunsa da alama kuma karantawa yake duba da yanda ya bada full attention ɗinsa a wajen magidancin mutum ne dan aƙalla zai kai irin 60yrs ɗin nan amma idan har kayi duba da yanayi na siffarsa zaka iya cewa bai fi 46yrs saboda kwarjini da kuma hutu wanda ya zauna masa. Major General Ibrahim Tijjani mai Zamani kenan wanda ke riƙeda muƙamin shugabannin sojoji na ƙasa kuma sanannen ɗan kasuwa mai tashen arziƙi mamallakin Companyn mai Zamani corture indai magana kake ta kuɗi to tabbas M.G Ibrahim ƙarshene sannan kuma uwa uba ya kasance mutum mai taimakon na ƙasa dashi wannan shine dalilin daya sanya yake da mabiya daga kowacce fuska. Da sauri ta zauna gefensa tana shagwaɓe fuska ta ce" Father narhhhh!!" murmushi ɗauke a fuskarsa yake kallon tilon ƴar tasa kallo mai nuna zallar so da ƙaunar da yake mata shafa kanta ya yi cikin kamilalliyar muryarsa ya ce" Shalelen Father what's wrong uhn" turo baki gaba tayi ta ce" Father ko ba yaya Farooq bane" da sauri Farooq wanda yake zaune kujerar dake opposite tasu ya ɗago yana kallonta amma bai ce komai ba, murmushi Father ya yi sanin halin rigimarta ya ce"keda yayan naki ne kuma yanzu?, To kiyi haƙuri bazai sake ba ya tuba" taɓe baki ta yi sannan ta ce"Father kace masa ya kaini saloon ɗin" dafe kansa ya yi yana zare glasses ɗin idanunsa ya ce" ohho!! Shalelen Father rigima ko?, Ki tambayeshi da kansa idan yaga zai rakaki fine idan kuma yanada wasu uzurin sai ki tafi da guards zasu jiraki" girgiza kai tayi ta ce"nooo! nasan ma zai rakani" kallon Farooq ta yi wanda yake kallonsu tun ɗazu ta ce"yaya zaka rakani ko?" da sauri ya gyaɗa mata kai ko babu komai ya samu damar da zai gasa mata aya a hannu, murmushi ɗauke a fuskarta ta kalli Father ta ce"yawwa Father kaji ko ya ce zai rakani" numfasawa Father ya yi ya jinjina mata kai sannan ya miƙe yana riƙe da hannunta ya ce"na tayaki murna amma karku daɗe zan fita byee" gyaɗa masa kai ta yi tana murmushinta mai kyau ta ce"ok Allah ya tsare hanya Father narh" kissing goshinta ya yi sannan ya yi waje. # *BA ITA BA CE* # *Human trafficking* # *Destiny* # *love*. # *SQUAD 2024* # *Nanameera ce!*. [8/1, 7:28 PM] Nanameera😍✌🏻: *BA ITA BA CE!..💖💖* *MIKIYA WRITERS ASSO...* *nanameera08* _arewabooks_. *@Nanameera08* _wattpad_. *Nanameera*. # *SQUAD 2024* ```Page 03``` Kallon Farooq ta yi ganin ya miƙe tsaye sai kuma ta ce" yaya bari na sauya kaya" taɓe baki ya yi bai ce mata komai ba ta juya tabar parlon, kwafa ya yi sannan ya yi waje. Haɗaɗɗen bedroom ne kana ganinsa kasan an kashe kuɗaɗe wajen haɗashi komai a bedroom ɗin purple colour ne coz ita ce favee colour ta Ma'eesha, kallon gefen bed ɗin ta yi sa kuma ta saki murmushi a hankali ta ƙarasa wajen ɗaukan Teddy bear ɗin ta yi wanda ita ce ta kasance purple colour ce sannan tayi waje. *Haj.Salma pov* Zaune take kan royal cusion ɗin dake zagaye da parlon idanunta bisa TV tana kallon show ɗin da ake haskawa a MBC Max turo ƙofar tayi hakan yasa ta ɗago dara-daran idanuwanta tana kallonta sai a sannan na ƙare mata kallo fara ce tass kuma asalin kyakkyawa kallon Ma'eesha nayi sannan na kalli Haj.Salma ko ba'a faɗa maka ba kasan Ita ɗin mahaifiyarta ce domin babu inda suka sha banban ta kammani zama tayi gefenta tana ɗora kanta a cinyarta ta ce"Mami zamu tafi"shafa kanta Mami tayi sannan ta ce"to Shikenan sai kun dawo Allah ya tsare hanya" Ameen Ma'eesha ta ce sannan ta miƙe dan fita daga parlon "Ma'eesha!" "Na'am Mami" Kallon fuskarta ta yi sai kuma ta ce"where is your mask?" langwaɓar da kai tayi sai kuma ta ce"Mami yana cikin jakana" harararta Mami ta yi ta ce"oh daman amfaninsa kenan?, Bring it out my friend!" turo baki gaba ta yi sannan ta buɗe ƴar ƙaramar jakar hannunta ta zaro mask ɗin "saka shi" Kallon Mami tayi taga ta haɗe fuska babu alamar wasa sai kawai ta maƙala face mask ɗin sannan ta fice daga parlon tana buga ƙofar, girgiza kai Mami ta yi sannan ta ce"Allah ya shirya ki Ma'eesha". Zaune ta sameshi a motar yana danna wayarsa murmushi ta yi ta ce"sorry yaya I kept yhu waiting" ɗan siririn tsaki ya yi sannan ya ajiye wayar ya juya yana kallonta, sanye take da wata turkish Abaya black colour tayi rolling veil ɗin a kanta sosai tayi kyau tamkar balarabiya. Zazzafan numfashi ya furzar kafin ya kama hannunta ya riƙe cikin nasa cikin cool voice ɗinsa ya ce"uhnn kinsan ai ina jiranki kika barni" langwaɓar da kanta tayi tana kallonsa idanunta rau-rau ta ce"I'm sorry yayana" girgiza kansa ya yi sannan ya saki hannunta ya kunna motar, akwai ƴar tafiya daga parking lot ɗin gidan zuwa gate dan kwalta ce aka shimfiɗa tamkar titi, tsaki tayi tana kallon sojojin da suke bakin street ɗin gidansu har zuwa cikin gidan, ita kam har ga Allah batasan irin wannan tsaron da ake musu. Kallonsa tayi ganin inda ya yi parking motar sai kuma ta ce"yaya naga ka tsaya anan?" banza ya yi mata ya ciro wayarsa ya shiga dannawa abinsa haɗe rai Ma'eesha ta yi ta kuma cewa"yaya Farooq kaga da wajen saloon ɗin can kuma kai kayi parking anan muƙarasa please kaga Father ya ce..." "Heyyyyyyyy! yimin shiru aku kawai bazan ƙarasa ba anan zan tsaya sauka kije ayi miki idan kin gama kizo mu tafi or else..." kallonsa tayi tuni hawaye ya fara sintiri akan kuncinta cikin kuka ta ce"dan Allah yaya kayi haƙuri kaga idan naje ƙafana ciwo zai yimin dan Allah ka ƙarasa dani" ba zaka taɓa cewa da Farooq take magana ba dan ko inda take bai kalla ba danna wayarsa kawai yake, sanin halinsa na kaifi ɗaya ya sanya Ma'eesha ta sauka daga motar tana tafe tana kuka har ta tsallaka ɗaya side ɗin, tafiyar wajen 5mins ce ta kawota bakin shagon a hankali ta tsaye ta goge idanunta sannan ta shiga ciki. Above 1hour kafin a gama gyara mata kan, kasancewar ba kuɗi take biya ba already an biya ya sanya ta fito dan su tafi gida saidai me??? tana zuwa inda tabar Farooq ɗazu taga babu shi babu alamarsa kuma babu motar ga wani irin ciwon ƙafa da take yi zama tayi gefen titin ta rushe da kuka tamkar jaririya tana yi tana jan numfashinta saboda asthmarta dake shirin tashi, ta ɗauki aƙalla awanni biyu zaune a wajen kafin ya dawo da sauri ya ƙaraso gabanta yana kallon yanda ta dunƙule waje ɗaya ya dafata, da sauri ta ɗago kanta ta kallesa sai kuma ta sake rushewa da wani kukan, kyakkyawan murmushi ya yi sannan ya kama hannunta cikin sigar rarrashi ya ce"ya isa tawo ƴar Babyn Father daina kuka kinji" ganin taƙi miƙewa yasa ya sanya hannayensa duk biyun ya ɗauketa kamar Baby ya sanyata a motar. Zama ya yi sannan ya ɗorata akan ƙirjinsa ya rungumeta tamkar wacce ake turata haka ta sake fashe da wani kukan, shafa kanta ya shiga yi cikin cool voice ya ce"I'm sorry naje unguwa ne amma bazan ƙara ba kidaina kuka kefa jaruma ce" ɗago fuskarta ya yi to see her reaction yaga sake haɗe ranta tana murza idanunta. Murmushi ya yi ya ce"shikenan muje na siya maki chocolate sai mu koma gida" da sauri ta ɗago ta kalleshi ya ɗaga mata gira ya ce"then you love it?" tura baki tayi sai kuma ta girgiza masa kai tana sake komawa kan ƙirjinsa, dariya ya yi ya ce"gulma ko?" murmushi tayi tana ɓoye kanta ta ce cikin wata murya irinta shagwaɓaɓɓun ƴaƴa "yaya ƙafana zai cire wayyo zafi yake minnnn!" a ɗan rikice ya kalli ƙafar tata sai kuma ya ce"I'm sorry bari muje gida sai a samiki magani sannu kinji" gyaɗa masa kai tayi tana matse hawaye shikuma ya yi motar key suka bar wajen. *MALAM DUDU POV* Cikin wata iriyar murya mai tsananin amo yake cewa"daman ai mun sanar dake lokacin zai ƙarato to yanzu gashi nan yazooo Hhhhhh!, Keee Hajiya yanzu lokacin daya dace ya auri wannan yarinya komai na ƙarƙashin kulawar mu karku wani damu ku bil'adama Hhhhhhhh!" cikin rawar murya matar gabansa ta ce"tooo yanzu zan yi masa maganar idan naje gidan amma ya za'a yi shi Alhajin ya yarda da auren nasu ba tareda ya yi tunanin wani abu ba??" haɗe rai bokan ya yi sai kuma ya ce" mantamu kika yi dolensa ya yarda da haɗin auren kuma shine wanda zai fi kowa farin ciki akan hakan Hhhhhhhh!, Ni Dudu nayi miki wannan alƙawarin" shiru tayi sai kuma ta ce"to me zan baka?" Wani mirmushin mugunta ya yi sai kuma ya ce"aikema kin sani" murmushin itama tayi sannan ta tashi ta shige bedroom ɗin dake kusada zauren, mikewa ya yi shima yabi bayanta, sai bayan 50mins sannan ta fito daga ɗakin tana gyara ɗaurin zaninta sannan tayi waje. *MAI ZAMANI POV* Kallon doctor yake har ya kammala dubata sannan ya ce"doctor what's going up?" numfasawa ya yi sannan ya ce"sir ba wani abu bane kawai tayi stressing kanta ne nd kuma kasan yanayin lalurarta but nayi mata injection zata samu sauƙi in sha Allah" numfasawa ya yi ya ce"okay you can go we should talk later" okay doctor ya ce sannan ya ɗauki first eid box ɗin nasa ya yi waje daidai nan ta shigo tana kallonsu duka ta ce"yallaɓai ya jikin nata?" batareda ya juya ba ya ce" Alhamdulillah call Farooq" taɓe baki tayi sannan ta juya ta fita, zaune ta sameshi yana shan coffee ɗin nasa na ƙa'ida kallonsa tayi ganin kamar wani abun yake tunani ta ce"Farooq me kake tunani haka" furzar da wani zazzafan numfashi ya yi ya ce"Mommy wlh I'm tired!, nagaji!! I can't endure it anymore haba!" zama tayi gefensa da mamaki a fuskarta ta ce"then what happened?" a ɗan fusace ya kalleta sai kuma ya ɗauke kansa yana kwafa ya ce"Mommy Are you questioned me?, bama kisan meke damuna ba?, haba Mommy!!" Kama hannunsa ta yi cikin nata cikin son kwantar masa da hankali ta ce" Farooq kanada saurin ɗaukan zafi uhn, ƙoƙari fa nake ganin abubuwa sun tafi yanda mukeso meyasa kake damuwa?" zare hannunsa ya yi daga cikin nata ya miƙe tsaye yana zagaye parlon tamkar wanda ya yi wa Sarki ƙarya miƙewa itama ta yi ta ce"dan Allah ka kwantar da hankalinka kasan farin cikinka shine nawa, amma dole na iya takuna saboda kafini sanin halin General bashida kirki idan yaso" harɗe hannayensa ya yi a ƙirjinsa still looking at her ya ce"then mene ne abunyi Mommy?, Shekaru fa tafiya suke, mistakely idan General ya mutu yanzu zan fa tashi banida komai kema kuma haka amma kin ɗauki abun not serious" murmushin takaici tayi tana kallon ɗan nata ta ce" yanzu me kake so?" ajiyar zuciya ya yi sannan ya kama hannunta ya ce"good!, Mommy kije wajen General da buƙatar mu, tun kafin yarinyar nan wani a waje ganta labari ya sauya she's 17yrs fa yanzu kuma University take zuwa anytime zata iya cewa tana son wani kuma kinsan general bazai mata auren dole ba!" murmushi ta yi ta ce"Farooq ka kwantar da hankalinka indai wannan ne angama aurenka da Ma'eesha ka ɗauka anyisa, Ma'eesha takace kaima kuma kasan da wannan" sai a sannan ya saki fuskarsa ya yi murmushi ya ce"Mommy banson aurena da Ma'eesha ya wuce 2months kiyi iya bakin ƙoƙarinki please" shiru ta yi kamar me nazari sai kuma ta ce"in sha Allah za'a yi amma kafin nan akwai buƙatar na koma wajen Malam dan muji ta bakinsa" miƙewa ya yi ya ce"hakanma yanada kyau ko zuwa dare saina kaiki dan nima inason naji kanun labaran" dariya ta yi ta ce"mai zafi ma kuwa, yanzu dai kaje General na kiranka" okay ya ce sannan ya fita tana biye dashi. Da sallama bakinsa ya turo ƙofar ɗakin, zaune ya tadda Mami tana bawa Ma'eesha abinci sai General dake tsaye gefenta sauke idanunsa ƙasa ya yi sannan ya ƙaraso parlon Mommy na biye dashi, cikeda ladabi ya ce"Father gani" saida wasu ƴan daƙiƙu suka shige sannan ya kallesa fuskarsa babu alamun rahama ya ce"Farooq mene dalilin barin yarinyar nan tafi tafiya da ƙafarta bayan kasan meke damunta?, sannan idan kasan bazaka iya fita da ita ka kulamin da ita ba mene naka amsawa?, zan iya barin duk wani abu da nake na kaita inda zata sannan na dawo da ita domin duk duniya babu wacce nakeso sama da yarinyar nan, baka saba yimin haka ba tausayi da jiƙai ne tsakaninka da ita saboda haka ka tabbata ka cigaba da tafiya a haka idan ba haka ba zaka fuskanci zallar ɓacin raina get out of my side!" kansa a ƙasa ya miƙe yana kallonsa ya ce"sorry Father Allah ya wuci zuciyarka" sannan ya fice daga parlon, rai ɓace Mommy ta miƙe tana kallon General batace komai ba itama ta juya ta fita. Kallonsa Mami tayi ta ce"yallaɓai wannan abun bai dace ba koba komai kasan Farooq ba daga nan ba wajen kulawa da Ma'eesha yana iya bakin ƙoƙarinsa meyasa zaka yi masa haka?, ai sai ka saka yi dinga tunanin kodan bakai ka haifeshi ba yasa kayi masa haka" wani kallo General ya watsa mata sannan ya ce"ai daman ba nine na haifeshi ba bare ya yi tunani akan haka, lemme tell you something wlh indai akan Ma'eesha ne zan iya faɗa da kowa koda kuwa ace kece da kika haifeta hope you get me right?" ya fice daga parlon a fusace, tagumi Mommy ta zuba tama rasa me zatayi tabbas ba ƙaramin so General Kewa Ma'eesha ba kasancewar ita kaɗai ya haifa itama ɗin bayan shekaru masu ɗinbun yawa, bayan ya cire rai da sabon ƴaƴa kuma tun daga kanta bai ƙara ba wannan ne dalilin daya sanya yake mata wani irin so bashida burin daya shige yaga tana farin ciki haka duk lokacin da ciwonta ya tashi yafi kowa shiga tashin hankali domin kasancewarta AS kuma tana ɗauke da Asthma hakan yasa lokaci zuwa lokaci ciwon yakan tayar mata. *FAROOQ POV* "Kin gani ko Mommy, General ya fara gasamin magana akan ƴarsa kuma duk laifinki ne above one year Ina cewa ayi auren nan amma kin ƙi yarda dani, yanzu me kike tunani nan gaba kaɗan zai iya korata cikin gidan nan indai akan wannan shegiyar ƴar tasa ce sbd haka ni gaskiya bazan iya cigaba da lamuntar wulaƙanci ba gwara kawai ayi auren yanzu sai yanda nayi da Ma'eesha kafin nadawo kansa kuma!" ya ƙare maganar yana wani wuci kamar zaki, ita kanta Mommy ranta a ɓace yake dan General ya bata mamaki amma idan tayi duba da irin halinsa da kuma kasancewarsa soja sai gane zai yi abinda yafi haka ma dole ne su nemi mafita tun kafin ya juyo kansu, shiru sukai na wani lokaci sai kuma ta ce"shikenan Farooq ka shirya zuwa anjima zamu wajen Malam nan da 1months Ma'eesha zata dawo ƙarƙashinka sai yanda kaso zaka yi da ita" kallonta kawai ya yi sannan ya juya ya shige toilet dan idan ba shower ya sakarwa kansa ba bazai taɓa jin daɗin duniyar ba, kwafa Mommy ta yi sannan ta juya ta fita. *YOBE STATE* *Sabon fegi* *6:30am* *MUHAIRA POV* Yanayin lokacin sanyi ne sbd haka kowa yana cikin ɗaki shida ƴaƴansa, zaune take kan wata tsohuwar kujerar katako gabanta wani tulin wanke-wanke ne, yinsa take yayinda duk jikinta yake kakkarwa sanyin numfashi yana kai kawo wanke kayan take amma tuni hankalinta yabar wajen, dubban tunanunnuka ne ke yawo cikin kwanyar kanta, bakinsa ɗauke da sallama ya shigo cikin gidan cikin rawar murya ta ce "Sann..sannu da shigowa Baba" Sai a sannan nasamu sukunin ganin fuskarta tsarki ya tabbata ga ubangijin halitta wanda ya halicci wannan kyakkyawar budurwar tsayawa fasalta kyawu irin na Muhaira ɓata lokacine dan indai magana kake ta kyau to dazarar kayi ido biyu da ita magana ta ƙare tamkar ba mutum ba haka take da kyau saima ka saka idanunka cikin nata nan zaka gane Ubangiji ya yi baiwa. Kallo ya bita irin kallon tausayin nan duk ƴaƴan gidan sai ita kaɗai za'a saka aiki haka ma kuma cikin wannan sanyin ga yanayi na lalurarta, jiki a sanyaye ya ƙarasa gabanta cikin sanyin murya ya ce"Aishatu tashi kinji" batasan mene yiwa babba musu ba domin bata taɓa yi ba ta taso ne inda ko tanason abu ko bata so dole sai ta aikatashi, sosai ransa ya ɓaci hakan yasa ya fara kiran matan nasa "Falmata!! Falmata!! Ya'acca!! Ya'acca!!" Da sauri suka fito suna kallonsa da alama ma bacci suke ya ce"wai yaushe zaku fara imantawa wannan yarinyar ne?, me tayi muku haka da zafi?, kodan maraicinta ya kamata ace kuna tausaya mata sannan kuma ga yanayi na lalurarta wannan rashin imani ne kuke gwada mata kuma baku tunanin wata rana ayiwa naku haka" rai ɓace Falmata ta ce"haba mai gida idan bamu sata aiki ba kallonta zamu yi?, gaskiya ka wani daina nuna ka fifita yarinyar nan akan ƴaƴanka wannan ba daidai bane" baki buɗe yake kallonta sai kuma ya yi kwafa ya ce"A'isha tashi daga nan" dakyar ta iya yinƙurawa ta miƙe daga wajen jirin yana shirin ɗibanta da sauri Bani kura ya kamata ya ce"sannu kinji" tsaki Ya'acca tayi dan ita daman tun yarinyar na ƙarama ta tsaneta ashe zasu zauna tare da ita ga yarinya ce kyau kamar wata aljana. Bani kura bai sake bi ta kansu ba ya shige da ita ɗakin da take kwana. Ɗan ƙaramin ɗaki ne babu komai cikinsa sai wata tsohuwar tabarma da wani bargon mai kamada tsumma sai kuma Ghana most go ɗin da kayanta ke ciki, zaunar da ita ya yi sannan ya ce"sannu bari na samo miki ko kunu ne sai kisha muje asibiti" gyaɗa masa kai kawai tayi sannan ya juya ya fita, jingina tayi da garun ɗakin wasu irin zafafan hawaye suka shiga sakko mata ita ɗaya tasan irin zallar azabar da take ciki ga kuma yunwa da take ji dan rabonta da abinci tun jiya da rana tuwon daren da suka girka basu bata ba saboda Bani kura ya yi musu faɗa akanta haka ta kwana da yunwa yanzu kuma tana tashi da safe aka sanyata gyaran gidan gaba ɗaya. Kusan 10mins sannan ya shigo hannunsa riƙe da wani kofi sai leda zama ya yi gabanta ya miƙa mata kofin karɓa ta yi sannan ya buɗe mata ledar, ƙosai ne aciki da alama siyo mata shi ya yi, dakyar takai bakinta kan kofin kunun ta fara sha ko sugar babu ciki amma haka take sha daman inda sabo ta saba saida ta gama ci sannan ya ce ta shirya shima kuma ya fita dan shiryawar. Numfasawa likitan ta yi tana sake ƙare mata kallo sai kuma ta kalleshi ta ce"Baba yarinyar nan tanada buƙatar kulawa ta musamman dan a halin da ake cikin ciwon zuciyarta yana gab da shiga matakin ƙarshe gefe guda kuma Asthma bata samun kulawar taga dace da mai irin ciwonta yanada kyau ace an kula da rayuwarta yanda ya kamata idan ba haka ba nan gaba kaɗan labarin zai canza" sosai hankalinsa ya tashi cikin rawar murya ya ce"yanzu likita me zamuyi?, yarinyar nan marainiyace nikuma banida ƙarfi bansan ya zanyi da ita ba" kallonta doctorn ta yi ganin yanda ta matse jikinta guri ɗaya ga yarinya har yarinya amma babu kyakkyawar rayuwa Allah mai iko aranta tayi maganar sai kuma a fili ta ce"Allah ya rufa asiri yanzu zan rubuta mata magunguna ka tabbata ka siya mata dan tanada buƙatarsu" gyaɗa kansa ya yi yana kallon Muhaira shima. "Ke Muhaira!! Muhaira!!" Dakyar take buɗe idanunta wanda suka sauya kala wani irin ruwa kwance akansu, tsaki kulu ta yi sannan ta ce"kizo inji Umma" kallonta Muhaira ta sakeyi sai kuma ta fashe da kuka tana cewa"Papii! Papinaaa!!, wajen Papi zani banson nan gidan A'aaaaaa!!" da sauri Kulu tayi waje daidai lokacin da Bani kura ya shigo gidan hannunsa riƙe da magungunan Muhaira tana ganin ta ce"Baba Muhaira! Muhaira jikinta ya tashi" da sauri yabi bayanta suka koma ɗakin lokacin suma matan gidan suka fito. Kwance ya sameta tana birgima tana kiran iyayen nata harma da wasu sunaye da sauri ya ƙarasa gabanta hankali tashe ya ce"Aishatu ya isa haka za'a kirasu kinji ki daina dan Allah" ko saurarensa bata yiba ta cigaba da kukanta tana zallewa, rungumeta ya yi ajikinsa yana tofa mata duk addu'ar da tazo bakinsa duk mutanen gidan sunyi tsuru tsuru suna kallonta dan daman idan ciwon ya tashi haka ta keyi, sosai Bani yasha baƙar wahala kafin ya samu aljanun subar kanta wani nannauyan bacci ya ɗauketa. "Gaskiya mai gida a nemi mafita ya zamu dinga zama da mai lalurar aljanu acikin gida yarinya sai ciwoka kala kala gaskiya bazata saɓu ba" caraf Falmata ta karɓe tana faɗin"kema dai kin faɗa wlh wannan bazai taba yiwuwa ba haka kawai watarana ta shafawa ƴaƴanmu jaraba" Ko kallonsu Bani kura bai yiba ya girgiza kansa ya yi waje, suma suka fito suna maida zance. *ABUJA*. *MALAM DUDU POV* A matuƙar fusace Farooq ya miƙe tsaye yana yiwa malamin wani irin shegen kallo ya ce"bangane mai kake nufi ba?, Kai malam fito kayi mani bayani yadda zamu fahimta ka tsaya kana yiwa mutane wani zancen banza!" kallonsu Malamin ya yi sai kuma ya fashe da dariya lokaci ɗaya kuma ya haɗe rai ya ce"kai yaro ni ba abokin wasanka bane na baku aiki kuma baku yisa yanda ya kamata ba sannan kuma baku taɓa bibiyar maganar ba shiyasa nima nayi muku shiru kuma a halin yanzu banida wani abu da zanyi akai kamar yanda na faɗa muku wannan yarinyar *BA ITA BA CE!"* # *BA ITA BA CE!* # *Human trafficking* # *Destiny* # *Affection* # *SQUAD 2024* # *Nanameera ce!.* [8/2, 9:17 PM] Nanameera😍✌🏻: *BA ITA BA CE!..💖💖* *MIKIYA WRITERS ASSO...* *@Nanameera08* _wattpad_ *nanameera08* _arewabooks_. *Nanameera ce!* *Daga marubuciyar* *NAANAH* *TSAKANINMU* *SHEIKH HEESHAM* *FATTOMAH* *nd now* *BA ITA BA CE!* # *SQUAD 2024* ```Page 04``` Kallonsa Mommy take da tsananin tashin hankali kwata-kwata ta kasa fahimtar abinda yake faɗa kwakwalwarta ta tsaya cak!, Miƙewa tayi dan fita daga gidan saidai kafin takai kofar zauren tayi baya luuu zata waɗi da sauri Farooq ya tare ta hankali tashe kuma yake furta "Mommy!! Mommy!! Mommy" tuni jikinta ya saki hakan yasa kawai ya yi waje da ita, kallonta ya yi hannunsa riƙe da goran ruwan sai sauke numfashi take a hankali shi kansa dauriya kawai yake amma tabbas abun ya tabashi sosai, riƙo hannunsa Mommy ta yi murya bata fita sosai ta ce"Farooq ka fahimci abinda malamin nan ke faɗa kuwa? ni ban fahimta sosai ba, nufi yake duk abinda mukayi ya tashi a banza kenan?, muna tareda silar rugujewar burikanmu, nashiga ukuna Farooq idan General ya fahimta wlh mun kaɗe har ganyenmu ni wlh..." "Mommy dan Allah ya isa haka kina neman fasamin kai kema, please abar wannan maganar muje gida doctor ya dubaki maybe ma jininki ya hau baki sani ba, zamu yi maganar ko zuwa gobe ne" Batada wani zaɓin hakan yasa dole tayi shiru badan tagama faɗar abinda ke ranta ba sanin kuma halin Farooq na fusata yasa tayi shirun, fita ya yi ya koma front sit ɗin ya tayar ya motar, tafiya kawai sukai yana furzar da wani irin numfashi sai wuci yake haka har suka ƙarasa gida. *MAI ZAMANI POV* Kamar bazai magana sai kuma ya ce"meya sameta?" kansa ƙasa ya ce"wlh Father wai jininta ne ya hau" miƙewa General ya yi ya ce"okay Allah ya bata lpy zuwa anjima kazo zamuyi magana akan tafiyarka Paris" ya juya ya fita. Bin bayansa Mami tayi har bedroom ɗinsa, zaune ta taddashi yana waya hakan yasa ta zauna kan bedside drawer tana kallonsa saidai ya kammala sannan ya juyo yana kallonta yana murmushi ya ce"Madam ya dai?" shiru tayi bata bashi amsa ba hakan yasa ya miƙe cikin takunsa na isa ya ƙaraso inda take hannunta ya kama sannan ya koma ya zauna ya zaunar da ita bisa cinyarta yana kallon kyakkyawar fuskanta ya ce"Gimbiyata yau gida aka tuna ne?, Sarautar ce ta tashi?" da sauri ta rufe fuskarta a ƙirjinsa tana dariya ta ce"kai kam bakada dama wlh" dariya shima ya yi sannan ya ɗago fuskar tata yana kallonta cikin ido ya ce"kema ai kin sani banda ma yanzu kina hanani" turo baki tayi kamar wata ƙaramar yarinya ta ce"to ai kai bakasan ka girma ba" jan kumatunta ya yi ya ce" to kenan dan mutum ya girma bazai enjoying lfy ɗinsa ba?" girgiza kai kawai tayi sanin halin mijin nata ta ce"ai shikenan". *YOBE STATE* *BANI KURA RESIDENCE* Kallon Falmata ta yi da mugun mamaki ta ce"wai me kike nufi nifa bangane ba?" tsaki Falmata ta yi ta ce"ke daɗina dake rashin fahimta wlh, yanda nace miki haka zamuyi idan dare ya yi yau malam aikin dare zai yi kawai sai mu koreta ni a tunanina hakan shine kaɗai mafitarmu" "Aikuwa bazaku taɓa samun nasara ba Allah yafi ƙarfin ku" Da sauri suka juya suna kallon Bani kura wanda yake tsaye ya ɗage labule" a matukar razane suka miƙe tsaye suna kallonsa duk idanunsu sun fito waje, ƙarasowa ya yi yana kallonsu idanunsa sun rune na zallar ɓacin rai ya ce"kunji kunya wlh kuma kun bani mamaki, wace irin tsana kuka yiwa wannan yarinyar ne?, me tayi muku da zafi haka da har kuke shirin rusa rayuwarta?, idan tabar gidan nan ina take dashi inda zata zauna?, to wlh ku kuka da kanku ku sani duk abinda kuke aikatawa Allah na kallonku kuma da sannu zai yi maganinku sannan magana ta ƙarshe na yanke shawarar zan auri Aishatu saboda na inganta rayuwarta tunda akwai aure tsakanin mu daga nan babu wanda ya isa ya ce zau takata a cikinku dan itama sunan matata zata amsa". Da sauri Muhaira ta toshe bakinta tana girgiza kai inna'lil lahi wa ina ilayhi raji'uun Baba ne zai ce zai aureta?, kenan saboda batada gata haka rayuwarta zata kasance?, da sauri tayi ɗakinta saboda jin muryarsa yana ƙoƙarin fitowa daga ɗakin, tana zuwa ta faɗa kan tabarmar tana rushewa da wani irin kuka mai taɓa zuciya tabbas rayuwarta batada amfani kuma zuwa yanzu dole ta ɗauki matakin daya dace dan ko a mafarki bazata taɓa iya auren Bani kura ba bare kuma a gaske dole ta samu wata mafitar wacce zata ɓulle mata saidai batasan mene ne abinda zata yi ba!. Shi kuwa yana fitowa daga ɗakin ya yi waje dan zai je wajen Mai unguwane ya shaida masa idan yaso zuwa gobe da safe sai a ɗaura auren kuma ya yi hakan ne saboda ya samar mata da ƴanci cikin gidansa. *11:30pm* Wani irin baƙin hadari ne ya haɗo a sararin samaniya lokaci ɗaya garin yayi wani irin jaaa kasancewar lokacin damuna ne ga kuma dare, a hankali kamar wata ɓarauniya haka ta fito daga ɗakin tana sanɗa dan ko takalmi bata saka ba a hannunta ta riƙeshi babu kowa a tsakar gidan sai kukan gyare da kakeji ga kuma kukan iska wanda yake haɗe da ƙura da sauri ta fice daga gidan bayan ta zare sakatar ƙofar a hankali yanda wani bazai jiba, tana fita ta sanya takalmanta ta kuma sake riƙe jakarta sannan ta fara wani irin gudu kamar wacce ake binta. Gudun da take ya tsananta hakan yasa numfashinta ya fara janyewa saboda gudun da kuma ƙurar iskar dake tashi ta ko'ina, ƙarfinta ne ya fara ƙarewa a hankali ta fara rage gudun nata zuwa lokacin kuma an fara yayyafi, hakan yasa dole ta nemi waje ta tsaya sai a sannan ta lurada a cikin kasuwa take amma duk shagunan mutane a rufe suke hakan yasa ta samu rumfar wani shago ta shiga dan fakewa ruwan. *MAITAMA DISTRICT* *MA'EESHA POV* Kallonta Mami tayi sai kuma ta ce"then yaushe zakuyi tafiyar?" cikeda fara'a ta ce"ranar Friday Mami kuma kwana uku kawai zamuyi dan Allah ki bari naje" numfasawa ta yi ta ce"Ma'eesha bawai hanaki nake ba saboda banason ki fita A'a ina gudun abinda zai je yadawo ne kawai" turo baki gaba ta yi ta ce"Ayyah Mami wlh ba abinda zai faru kinga ai da ƴan department ɗinmu duka zamu tafi nidai kawai ki yarda tunda Father ya yarda" harararta Mami tayi ta ce"oh sai kin tura min baki gaba zan yarda?, ko shagwaɓar taki zaki min?" girgiza kai tayi tana murmushi ta ce"sorry Mami nidai please ki ce Eh" ganin yanda ta marairaice fuska yasa ta ce"shikenan Allah ya tsare hanya Amma ki kula sosai sannan banda shan ruwan sanyi Ma'eesha" rungume Mamin tayi tana dariya ta ce"yawwa Mamina Allah ya bar min ke" taɓe baki Mami ta yi ta ce" wa Allah ya bari da zai barni kedai ki yita shashancinki" dariya ta yi Mami ta ce" idan yaso bayan kin dawo sai ki shirya dan mai martaba yanata tambayarki" da sauri ta miƙe tana tsalle ta ce"yeee Mami zani masarauta?, harda ke Mami?" girgiza kai Mami ta yi ta ce" Allah ya baki nutsuwa, Maybe hardani maybe kuma ke ɗaya zaki" da sauri tayi waje tana cewa"bari na faɗawa yaya Farooq" murmushi Mami tayi tana nemawa ƴar tata addu'ar shiriya wajen ubangiji. *FAROOQ POV* "Mommy nace miki ki kwantar da hankalinki na tabbata ba za'a samu wata matsala ba domin nasan wanda nabawa aikin kawai yanzu zan nemo hanyar da zata fita ne amma ba tare dani ba yanda babu wani wanda zai yi zargina da zarar nasamu wannan to komai fa zai zo ƙarshe zamu gama da General cikin sauƙi batareda munsha wata wahala ba" ajiyar zuciya Mommy ta sauke tana sanye cikin wani less peach colour mai manyan zane ɗinkin Bubu tayi ɗaurin ture kaga tsiya, ga mata iya mata amma sai mummunar zuciya, cikin sanyin jiki ta ce"to Allah yasa muyi nasara dan ni wlh abun ya fara damuna koda wasa ban taɓa tunanin haka zata kasance ba, na ɗauka munyi abinda ya kamata kuma zamu samu sakamako mai kyau amma sai ta sauya zani" wani killer smile ya yi ya ce"Mommy nace miki ki saka a ranki cewa angama komai domin ni nasan halin wanda na bawa aikin nan wlh koda da wasa baza'a taɓa samun wani abu wai shi matsala ba, infact ma Mommy shi baya taɓa kuskure cikin aikinsa bayan haka kuma ya rigada ya turon kuɗaɗen kinga munci riba biyu kenan" murmushi ta yi daidai lokacin Ma'eesha ta turo ƙofar bedroom ɗin ta shigo, a ɗan tsorace suka kalleta amma sai sukaga tana murmushi hakan yasa Mommy ta ce"shalelen Father ce kuma?" murmushi Ma'eesha ta yi tana kallon Farooq ta ce"yaya guess what?" lumshe ido ya yi ya buɗe ya ce"Father ya siya maki chocolate" girgiza kanta ta yi tana murmushi ta ce"baka canka baaa" murmushi ya yi ya ce"shikenan naji I'm looser now tell me" rufe idanunta tayi sai kuma ta buɗe ta ce" ranar Friday zamu tafi excursion" baki buɗe da matukar murna ya ce"awwwn wane waje?" tana dariya tace "National museum Damaturu nd kuma Father ya yarda hakama Mami" wani ƙayataccen murmushi ya yi yana kama hannunta ya ce"wowww amma naji daɗi shalelen Father gaskiya zo mu fita let's celebrate" murmushi tayi sannan suka fita daga bedroom ɗin tana cigaba da bashi labarin. *YOBE STATE* *GASHUA MARKET* *MUHAIRA POV* Dakyar take tafiya cikin kasuwar duk jikinta ya yi weak, wajejen ƙarfe 12pm na rana ne duk mutane sun fito suna hada-hadarsu wata Irin yunwa take ji dan rabonta da abinci tun jiya da rana gashi ƙirjinta yana mata ciwo jikinta kuwa kamar wacce aka naɗawa duka haka takeji, wani mutum tagani yana gashin masara hakan yasa ta ƙarasa wajen, tsugunawa tayi cikeda ladabi ta ce"Baba ina yini" kallonta tsohon mutumin ya yi aikuwa ya saki baki dan shi bai taɓa ganin mai kyau irin haka ba duk zatonsa ma aljana ce, ganin bai amsa mata ba yasa ta ce"Baba dan Allah ka taimaka min da masarar nan yunwa nakeji" da sauri ya ɗauki guda uku ya sanya mata cikin leda ya miƙa mata dan shi ko magana ma ya gagara yi dan tsoro yake kar yaje ba mutun ba ce, sosai Muhaira tayi murna cikin sanyin murya ta ce"Allah ya biyaka da gidan aljanna Baba Nagode" kai kawai ya gyaɗa mata dan tsorone ya ƙara kamashi sanda yaji muryarta, miƙewa tayi ta cigaba da tafiya dan ta samu wani wajen ta zauna ta ci masararta hankali kwance, Wani tebur ta samu gefen wani mai kayan awo ta zauna a hankali tayi bismillah tafara cin masararta. Duk wanda ya zo shigewa sai ya kalleta ganin yanda tayi wani irin kyau dukda ita ba'a cikin nutsuwarta take ba, irinsu Muhaira ne idan suka samu hutu tofa basu ganuwa saboda kyau da kuma tsarin halitta. *BANI KURA RESIDENCE* Tsaye suke cirko-cirko kowa ya yi shiru shi kuwa Bani kura ya zauna kan dakalin ɗakinta ya zuba uban tagumi yama rasa ta ina zai fara, ko ina Muhaira ta tafi?, yaushe tabar gidan?, Allah shine masani, taɓe baki Falmata ta yi ta ce"wama ya sani ko yawonta data saba ta tafi daman ai duk irinsu ƙarshensu yawon banza" a fusace Bani ya ɗauketa da wani lafiyayyen mari yana kallonta ya ce"dallah rufe mana baki wama ya sani ko kune kuka koreta kamar yanda kuka shirya, ku sani zan fita neman Aishatu amma duk abinda ya samu rayuwarta Allah bazai barku ba jahilan banza kawai!" yana gama faɗin haka ya fice daga gidan kamar zai tashi sama, da harara Ya'acca ta Bisa sannan ta ce"can kaje gayyar tsiya kuma in sha Allahu bazaka taɓa ganinta ba mun rabu da wahala shegiyar yarinya tana gidan nan ubanma zai zo ya auri ƴaƴanmu ai gwara data tafi Allah yasa mota tabi ta kanta ta markaɗe" tuntsirewa sukai da dariya Kulu ta ce"wlh kuwa Umma rannan Salisu cemin yai wai shi wannan ta gidan namu yakeso" kwafa Falmata ta yi ta ce"yoo daman wannan ai annoba ce shiyasa shima baban naku yace zai aureta ai wai mu zaiwa duniyanci heheheheeeeeeee!" Tsaki Ya'acca ta yi ta ce"ai wlh da ya aureta ya jaza mata bala'i dan Allah watarana saina kasheta kowama ya huta, daman ɗiyar Fulani ai mugunta garesu ni bansan mema ya haɗashi abota da ubanta ba" Allah dai ya kyauta cewar Falmata sannan ta cigaba da wankin da take. # *BA ITA BA CE!* # *Human trafficking* # *Destiny* # *Unconditional love* # *SQUAD 2024* # *Nanameera ce!*. [8/3, 9:23 PM] Nanameera😍✌🏻: *BA ITA BA CE!..💖💖* *MIKIYA WRITERS ASSO...* *@Nanameera08* _wattpad_ *nanameera08* _arewabooks_. *Nanameera ce!* # *SQUAD 2024*. ```Page 05``` *MA'EESHA POV* Sanye take cikin wasu English wears white colour masu ɗan kama jiki sai kuma ta ɗora rap Abaya black colour akai tayi rolling fuskarta da veil ɗin rigar Masha Allah tayi kyau sosai abinta hannunta riƙe da mug na tea mai zafi tana sha, takun da taji abayanta yasa ta juya murmushi ta sakar masa saida ya sake kallonta dan ba ƙaramin kyau tayi masa ba tabbas badan bashida halin aurenta ba da ya mayar da ita mallakinsa yana matuƙar son kyakkyawar mace gashi kuma Ma'eesha Allah ya hore mata ga kuma kuɗi wanda shine yasa kyan nata ya sake fitowa fili cikin sanyin murya ta ce"yayana I'm gonna to miss you wlh" murmushi ya yi yana bata peck a goshi ya ce"same dear, da ace banida wasu ayyukan ai ni ne zan rakaki" turo baki ta yi tana langwaɓewa ta ce"toh yaya dan dai three days please mu tafi tare" cikin son kwantar mata da hankali ya ce"shalelen Father kenan, ai three days dayawa a wajena karki damu idan zaki Masarauta nida kaina zan rakaki" murmushi ta yi ta ce"yaya da gaske kake?" gyaɗa mata kai ya yi yana kwaikwayon muryarta ya ce"Eh da gaske nake babyn yaya" tuntsirewa ta yi da dariya ta ce"kai ko yaya hmmmm!" waro idanunsa ya yi ya ce"ni ko me?" girgiza kanta tayi tana rufe baki daidai nan suka ƙaraso parlon, General ne sanye cikin wasu kayan sojoji t-shirt da trouser sai jacket ya ɗora a sama sai Mami tana sanye cikin wani ubansu less blue colour mai ƙananun zane ɗinkin riga da zani ta ɗora mayafi pink akai idan ka kalli Mami ba zaka taɓa cewa ta haifi Ma'eesha ba tun daga yanayin fuskarta har zuwa jikinta Allah ya yi mata zubin halitta mai kyau hakama kuma ƴar tata, murmushi General ya yi idanunsa kan matar tasa sosai ta burgeshi dan yana matuƙar son ado da kwalliya shiyasa koda yaushe yake jin Mami kamar amarya a wajensa ko auren Mommy da ya yi saboda mahaifiyarsa ta matsa masa ne sai gashi itama ɗin bata samu haihuwar ba, fitowa Mommy ta yi cikin wata abaya ash colour tayi rolling veil kana kallon fuskarta zaka san ta fara manyanta dan Mami ta fita kyan jiki "Father mu tafi ana jirana please" Maganar Ma'eesha ce tadawo dashi daga tunanin daya tayi ya kalleta sai kuma ya yi murmushi ya ce"wato dai na fuskanci kin fison tafiyar nan ko?, mune kaɗai muke jin zamuyi kewarki ai Shikenan" ɓoye fuskarta tayi a jikinsa tana dariya ta ce"A'a Father nima wlh ina ji ai ba daɗewa zan yi ba" "Kina da tabbacin ba zaki daɗe ba?" Da sauri General ya kalli Mommy sai kuma ya ce"kamarya naga only three days zasu yi" duru-duru ta fara yi dan batasan sanda maganar ta suɓuce mata ba sai kuma ta ce kamar me koyan magana"uhmm...in daman nufina bata saniba ko a ƙara musu kwanaki" taɓe baki ya yi bai ce mata komai ba ya kama hannun Ma'eesha suka yi waje hakan yasa duk suka bi bayansu. Saida suka ga jirginsu ya tashi sannan suka koma gida sosai Ma'eesha ta yi kuka dan daman duk sanda zatayi wata tafiya sai tayi kuka kamar bazata dawo ba, wani killer smile Farooq ya yi sanda yaga jirgin nasu ya fara yawo a sararin samaniya cikin wata murya mai nuna zallar farin ciki ya ce"good bye lovely sister, I'm gonna to miss you shalelen Father" murmushi Mommy da take gefensa tayi dan taji abinda ya ce cikin ƙasa da murya ta ce"ka tabbata baza'a samu matsala ba?" kallonta ya yi sai kuma ya kama hannunta ya matse cikin nasa alamar Eh sannan ya saketa ya yi gaba, ajiyar zuciya Mommy ta sauke tana murmushi ko babu komai sun kusa samun abinda suka daɗe suna muradi. *YOBE STATE* *GASHUA MARKET*. Tsugune take ƙofar wani shagon mai saida abinci tana wanke-wanke jikinta sai rawa yake kasancewar garin damuna kuma jiya da daddare anyi ruwa sosai batada wani zaɓi daya shige tayi aikatau dan samun abinda zata sanya a bakinta dan kwata-kwata bata iya jure yunwa ba fitowa matar ta yi tana kallonta ganin har kusa gamawa ta ce"yawwa yarinya kiyi sauri ki gama kizo ki ci abinci nasan kina jin yunwa" gyaɗa mata kai kawai Muhaira tayi dan magana ma wahala take mata koda yaushe cikin tunanin mafita take tabbas bazata cigaba da rayuwa cikin kasuwa ba dolene ta fita daga ciki tsawan waɗannan kwanakin batada aiki sai tunane-tunane duk ta hargitsa kwakwalwarta ko ya zatayi?????. *MA'EESHA POV* Tana fitowa daga wankan sannan ta sanya doguwar riga pink colour sannan ta gyara gashinta wayarta ta ɗauka sannan ta zauna dan kiransu Father, Da sauri ta faɗo jikinta tana dariya tsaki Ma'eesha tayi sannan ta tureta ta ce"wai dan Allah Suhaila yaushe zaki yi hankali jifa yanda kika wani faɗo min a jiki salon ki karyani" miƙewa zauna tayi tana kallonta ta ce"ke banza ce wlh kinsan me??"girgiza kai Ma'eesha ta yi Suhaila ta ce" gobe zamu koma gida right?" gyaɗa mata kai Ma'eesha ta yi sannan ta cigaba da faɗin" to kafin mu tafi zamu shiga kasuwa haka sir ya ce kinga zamuga gari sosai daman duk an riƙemu" ihu Ma'eesha ta saki tana rungumeta ta ce"wayyoo Allahna daɗi kasheni, zan yi wa su yaya Farooq tsaraba kenan, daman wlh tun jiya nakeson mu fita, kai Allah ya yiwa Sir Ahmad albarka naji daɗi sosai wlh" tashi Suhaila ta yi ta ce"lemme take shower then muci abinci" girgiza kai ta yi ta ce"banza Acici kawai" gwalo ta yi tana shigewa toilet ɗin ta ce"naji ɗin". *MONDAY* *4:00pm* *GASHUA MARKET*. Wani irin farin ciki ne ya mamaye Ma'eesha da ƙawayenta both maza da matan tana sanye cikin wata Abaya purple colour sosai suke murna saboda ganin kasuwar gashua ɗin tunda take a rayuwarta bata taɓa shiga kasuwa ba saidai supermarket dan kome zasu siya anan suke siya hakama sauran ƙawayen nata kasancewarsu ƴaƴan masu faɗa aji, banda dariya babu abinda suke yayinda wasu suka shiga tiktok sunata ɗaukan vedio wasu kuma na hoto ko'ina kallonsu ake domin sun burge kowa duk abinda sukaga ana siyarwa wanda basu san shi ba sai sun tsaya sun tambaya sannan sunyi hoto da mai siyarda abun, murmushi ta yi tana kallon matar ta ce"Nagode Adda Allah ya ƙara arziƙi" rungume Muhaira ta yi ta ce"karki damu yarinya kinyi kyau sosai, yanzu jeki ki yo mana cefane" da sauri ta karbi kuɗin sannan ta fita duk murna ta isheta barinma idan ta ƙara kallon Abayar dake jikinta dukda ƴar ɗinki ce amma zata iya cewa bata taɓa saka kaya mai tsadar wannan ba gashi kuma kalar purple ɗin ta karɓi farar fatarta duk inda tabi sai kallonta ake tayi wani irin kyau Masha Allah. Murmushi ta yi bayan ta ɗaga kiran tana kallonsa ta ce"yaya ka ganmu nan a kasuwar gashua zan tawo maka da tsaraba" murmushi ya yi ya ce"Allah ƙanwanta ki ce zan ci abun daɗi" gyada masa kai ta yi sannan ya ce"okay shalele I'll call you later" gyaɗa masa kai ta yi sannan ta katse kiran suka cigaba da kallonsu. *FAROOQ POV* A hankali yake sintiri a bedroom ɗin nasa kwata-kwata hankalinsa ya gaza kwanciya so yake kawai su kirashi su faɗa masa magana mai daɗi, ringing ɗin daya ji yasa ya yi saurin kallon screen ɗin wayar wani killer smile ya yi sannan ya ɗaga wayar "She's wearing Abaya purple colour" Sauke wayar ya yi yana sakin wani numfashi. *POV*. Kallon mutumin daya tsaya gefenta ta yi, sanye yake cikin wasu English wears ɓaƙaƙe ya rufe fuskarsa da face mask, kallonta ya yi sai kuma ya kalli wayarsa sannan ya ce" two pack of tomato" okay ya ce sannan ya juya dan ɗebo tumatur ɗin, matsowa ya yi kusada ita bata yi auneba taji ya ɗora mata wani hankaci a hanci nan take tayi baya zata waɗi da sauri ya riƙeta cikin hanzari kuma ya sanyata bayan motar ƙirar Honda Accord sannan ya shiga gidan gaba da wani irin speed drivern yaja motar suka bar filin kasuwar. Saida suka yi nisa sosai da kasuwar sannan ya ce"stop the car!" a hankali drivern ya yi parking juyawa ya yi ya ɗagota ya kalli fuskarta sannan ya kalli pic ɗin da ke kan wayar tasa daidai nan kira ya shigo ɗagawa ya yi daga ɗaya ɓangaren ya ce"what is going?" "I got her" Ajiyar zuciya Farooq ya sauke sannan ya ce "lemme see her" juyoda fuskarta ya yi, bai san sanda wani murmushi ya ƙwace masa ba ya ce"good job!," kashe wayar ya yi sannan ya koma inda yake ya zauna ya kalli drivern ya ce"Airport". *MAI ZAMANI POV* *6:30pm* Cikin son kwantar masa da hankali Mami ta ce"wai dan Allah General mene abun tashin hankali anan?, kasan fa inda Ma'eesha take kuma yau ta ce zasu dawo amma duk kabi ka rikice" wani banzan kallo ya watsa mata sannan ya juya ya fice daga bedroom ɗin, bayansa tafi har ya sauka main parlon na gidan dialing numbern Farooq yayi, suna zaune shida Mommy kowannesu da fara'a a fuskarsa ta ce"shiyasa nake alfahari dakai son nasan duk abinda ka sanya a gaba sai ka aiwatar yanzu mene ne nagaba?" buɗe baki ya yi zai magana kiran General ya shigo wayarsa, ɗagawa ya yi cikin ladabi sai kuma ya ce"ok gani nan" tashi ya yi yana kallon Mommy ya ce"kizo muje kisha labari, yau zanga yanda wasu zasu rikice" tuntsirewa tayi da dariya sannan ta miƙe tabi bayansa, hatta yanda suke sauke ƙafarsu a ƙasa zaka gane cewa cikin farin ciki suke, yana ya tsaya yana kallon General ganin yanda duk ya birkice ya ce"Father lafiya dai?" General ya ce"please gwada kiran Ma'eesha na kira har yanzu switch up gashi har ana shirin margib bata dawo ba" okay ya ce sannan ya shiga dialing numbern ta, still dai akashe take cewa, nan take tashin hankali ya bayyana a fuskar General ya ce" bari naje school ɗinsu na tambaya maybe ko wani abun ne" baki buɗe Mommy take kallonsa sai kuma ta ce"dan girman Allah ya yallaɓai ka nutsu, haka zakaje makarantar tasu duk ka fita hayyaci?, Ma'eesha fa da girmanta kuma i think kodai basu tawo bane" da sauri Mami tace"faɗa masa dai" kallonsu ya yi duk idanunsa sun yi jaa ya ce cikin ɗaga murya" bazan kwantar da hankalin nawa ba!, nace bazan kwantar ba!, ina naga wani kwanciyar hankali bayan ƴata bata dawo gida ba?, madadin ku tayani baƙin ciki da nuna tashin hankali shine ma kuke cewa na kwantar da hankalina you said I should come down saboda ba ƴarku ba ce kema kuma wai har da ke kina matsayin uwarta nonsense!" ya ƙare maganar yana kallon Mami, numfasawa Mami tayi sannan ta ce"Allah ya huci zuciyarka yallaɓai amma ni gani nai..." "Heyyyyyyyy!, Shout up!!" Shiru Mami tayi tana kallon mijin nata, itama kanta hankalinta a tashe yake amma General ya damata shiga tashin hankali kuma shi baya iya ɓoye nasa indai akan Ma'eesha ne. Cikin sanyin murya Farooq ya ce"Father dan Allah came down yanzu zan je school ɗin su na tambaya tunda..." Maganar ta maƙale a maƙoshinsa saboda sallamar Ma'eesha data daki kunnuwansa da sauri kuma a matuƙar razane ya juya mai zai gani?, Ma'eesha ce tsaye daga ɗan nesa dasu tana sanye cikin Abaya black colour hannunta riƙe da ƙaramar trolley ɗinta da gudu ta tawo tana zuwa ta rungume Father sai kuma ta saki wani irin raunataccen kuka, Farooq bai san sanda ya zauna kan kujera ba koma faɗawa ya yi bashida masaniya, Mommy kuwa jikinta sai rawa yake cikin sarƙewar murya ta ce"Ma..Maee.. Ma'eesha ke ce!" Kuka Ma'eesha ta cigaba tana ƙara shigewa jikin mahaifinta, General hannayensa yasa ya rungumeta ƙam shima a hankali yake sauke ajiyar zuciya Mami kuwa hamdala tayi a zuciyarta sannan ta nemi waje ta zauna, sun ɗauki lokaci mai ɗan tsawo a haka har saida Ma'eesha ta yi shiru sai ajiyar zuciya take saukewa, nauyin da yaji ta sakar masa yasa ya tabbatar bacci tayi hakan yasa ya ɗauketa kamar Baby ya rungumeta sannan ya haura sama without looking at anybody. Bayansa Mami ta bi hakan yasa Mommy tayi nata apartment ɗin da sauri tana zuwa ta faɗa kan gadon tana sakin wani kuka akaro na wajen uku kenan sun sake faɗuwa, anya kuwa zasuyi nasara??, Shigowar Farooq ya sanya ta miƙe zaune jijiyoyin kansa duk sun tashi idanunsa sunyi wani irin mugun ja ko ba'a faɗa maka ba kasan yana cikin tashin hankali mara misaltuwa, ko kallonsa Mommy bata yiba ta cigaba da rera kukanta wayarsa ya ɗauko ya yi dialing wata number wacce ta kasance international number ce, saida ya yi wajen 5missed call sannan aka ɗaga ana shiddan, cikin faɗa ya ce "Heeeee!! Daman haka mukayi daku??, Why zaku yaudareni?" a hankali mutumin yake buɗe idanunsa cikin wata iriyar murya ya ce"uhnnnnn!, Ahhhhh!!, Beb" cikin ɗaga murya Farooq ya ce" kaiiii au wani abunma kake daban?, ina yi maka magana kana harkar gabanka?, kace min kun saceta ashe ƙarya kake!!" da sauri ya ture yarinyar dake kansa ya miƙe zauna yana gyara zaman wayar a kunnensa ya ce"Hey guy bangane me kake cewa ba, wace yarinya kake magana akai?, ka siyar mana da yarinya mun biyaka kuɗinka sannan kuma yanzu kana mana wani maganar nonsense!" gaba ɗaya kan Farooq ya kulle ya kasa fahimtar komai, cikin sanyin murya ya ce" please Taj ka fahimtar dani wlh Ma'eesha tadawo gida yanzu haka tana wajen babanta ko kuma sakinta kuka yi bayan nan?" mikewa Taj ya yi yana zura wata bathrobe ya ce lemme show you" yana faɗin haka ya yi waje, wani bedroom ya buɗe sannan ya sake kiransa vedio call yana ɗagawa ya ce"look at her" "What!!!" Sake waro idanunsa ya yi waje, babu abinda ya rabata da Ma'eesha Allah mai halitta baki buɗe yake sake kallonta kwance take kan royal bed ɗin har sannan kuma bacci take bata farka ba, cikin ɗaga murya ya ce "Wannan ai *BA ITA BA CE!*" # *Incident* # *Human trafficking* # *Destiny* # *Unconditional love* # *BA ITA BA CE!* # *SQUAD 2024* # *Nanameera ce!*[8/4, 8:13 PM] Nanameera😍✌🏻: *BA ITA BA CE!..💖💖* *MIKIYA WRITERS ASSO...* *nanameera08* _arewabooks_ *Nanameera ce!* # *SQUAD 2024* ```Page 06```. Cikin ɓacin rai Taj ya ce"kai malam me kake nufi?, wane irin ba ita ba ce to wacece kenan?, kaine fa ka bamu pic nata nd bayan na ɗaukota na kiraka ka ce Eh ita ce then yanzu kuma ka zo kana yimin wani nonsense" bakin Farooq na rawa ya ce"ka fahimceni Taj wlh ba Ma'eesha ba ce coz yanzu ita ta dawo gida ma amma bansan mene ne abinda ke going ba, kawai tunda an yi haka ka saketa tunda bansan wace ba" wani killer smile Taj ya yi yana kallonsa ya ce"da alama kanada matsala a ƙwaƙwalwarka ko?, kana tunanin Zaki zai asarar kuɗaɗensa ne?, ko ita ce koma ba ita ba ce wannan matsalarka ce ba tawa ba kai bari ma na ƙarashe maka magana zuwa anjima zamu shiga Riyadh sbd haka karka sake kirana akan wannan maganar" yana faɗin hakan ya katse kiran cikin ɓacin rai ya ce"aikin banza ina cikin jin daɗi na zai takura min nonsense!" ya faɗa yana kallon kyakkyawar fuskar Muhaira sai a sannan na lura kamarsu ɗaya da Ma'eesha babu abinda ya raba tamkar twins haka suke lumshe idanunsa ya yi ya ce"wowww kaga yarinya da halitta ina ma Zaki ya bar min wlh I'll pay for her" murmushi ya yi shi kaɗai sai kuma ya juya ya fice daga ɗakin har sannan yana kallon fuskar Muhaira. Kallon screen ɗin wayar ya yi baki buɗe dan yama rasa abinda zai yi tabbas yasan Zaki bazai taɓa yarda da rainin hankali ba amma shi yanzu matsalarsa ɗaya idan ba Ma'eesha ba ce to kenan wacece wadda har take kamada ita haka harda shi kansa ya kasa ganesu tabbas akwai wani abu something fishy, ajiyar zuciya ya sauke sannan ya cilla wayar tasa kan bed ya shige toilet dan watsa ruwa. *MA'EESHA POV* Kwance take kan ciyar General yana shafa kanta har sannan kuma bata ce musu komai ba sai ajiyar zuciya take saukewa, cikin sanyin murya Mami ta ce" Ma'eesha tell us mene ya sameki uhn, meyasa kike kuka keda wa?" miƙewa zaune tayi tana kallon Mami ta ce"koba Sir Najeeb ne ya ce yana sona ba kuma wai aurena zai yi" tafaɗa tana sakin wani sabon kukan, murmushi Mami ta yi sai kuma ta ce"wait amma mene ya hanaki dawowa da wuri ɗazu sannan kuma ina wayarki?" turo baki ta yi ta ce"ai faɗuwa ta yi acikin kasuwa shine ta fashe kuma bamu samu jirgin da mukayi booking ba saida muka sake jira that's why ban dawo da wuri ba" ajiyar zuciya General ya sauke sannan ya ce"ok saboda malamin kike kuka?" gyaɗa masa kai ta yi tana turo baki gaba, murmushi ya yi ya ce"shikenan zan yi masa magana yanzu ki kwanta okay"gyaɗa masa kai tayi sannan ya a tashi yana kallon Mami ya ce"Fulani muje ko" miƙewa ta yi suka fita kafin ya rufe ƙofar ta ce"Fatherr" kallonta ya yi ganin yanda ta shagwaɓe fuska ya ce" mene?" "Father yaya Farooq nakeson gani" numfasawa ya yi ya ce" okay kwanta" ya ƙarasa rufe kofar sannan ya bar wajen. Lumshe idanunta ta yi tana tunanin jiya ta kasa mance abinda Sir Najeeb ya ce mata, ganin lokaci na tafiya yasa kawai ta tashi ta shige toilet dan yin wanka babu wanda takeson gani a wannan lokacin sai yaya Farooq hakan yasa tana fitowa ta zura wata long sleeve ɗin riga milk colour ta ɗora Baby hijab black akai ta yi waje. Murɗa handle ɗin ƙofar ta yi bakinta ɗauke da sallama lumshe idonta ta yi saboda wani irin ƙamshi daya ziyarci hancinta murmushi ta yi har saida dimful ɗinta ya loma ta ce"uhnnnnn yaya Farooq ɗan ghayu" ƙara sawa ciki tayi baya cikin parlon sai kawai ta shige bedroom ɗin batareda taji koda ɗar ba, waro idnaunta ta yi ganin nan ma baya nan hakan yasa ta zauna gefen bed ɗinsa tana jiran ya shigo juyawa zatayi sai ta hangi wayarsa da sauri ta ƙarasa wajen tana kallon wayar a fili ta ce"laa wayar ma akunne" ɗauka tayi tana kallon hoton dake kan screen ɗin, da sauri ta miƙe tsaye tana sake waro manyan idanunta sai kuma ta yi dariya ta ce"Allah sarki yaya Farooq ashe har hoto ya yimin jiya" ta faɗa tana dariya taɓe baki ta yi sai kuma ta ce"ko yaushe nayi bacci ohho" ajiye wayar tayi sannan ta koma ta zauna tana Kalle-Kalle cikin bedroom ɗin, murɗa handle ɗin ƙofar akayi ya shigo da mamaki yake kallonta ita kuwa da gudu tazo ta rungumeshi tana dariya ta ce"yayaaa nayi missing naka sosai" dakyar ya iya saka hannunsa ya rungumeta shima yana murmushi ya ce"same ƙanwata" ɗagowa tayi tana jan gemunsa ta ce"yaya na tawo maka da tsaraba"waro idanunsa ya yi ya ce" da gaske?" gyaɗa masa kai ta yi ya ce"okay ki bani" girgiza kai tayi tana haɗe hannayenta a ƙirji ta ce"inada condition" murmushi ya yi yana girgiza kansa ya ce"Ma'eesha rigima inaji" dariya ta yi ta ce"please ka siyomin ice-cream yanzu sai na baka" har ya buɗe baki zai faɗi wata magana sai kuma ya yi murmushi ya ce"Shikenan kamar angama don't worry" rungumeshi ta yi ta ce"yawwa yayana amma please kar ka bari Father ya sani"gyaɗa mata ya yi sannan ta juya ta fita daga ɗakin, tsaki ya yi yana kallon bayanta ya ce"Mumu" sannan ya ƙarasa ya ɗauki wayarsa ya fita shima. *WEDNESDAY* 9:00pm. *Saudi Arabia* *RIYADH* *Al-Olaya Residence* Zaune yake cikin wani katafaren haɗaɗɗen parlon mai tafiya da imanin mutane wani irin parlon ne wanda kana gani kasan a ƙasar waje kake ƙasar wajen ma kuma inda ake ji da ganiyar kuɗi wani irin sanyi ne irin mai ratsa jijiyar nan ne ke tashi a parlon zaune yake yana taunar cingam cikeda isa da jinkai yana sanye cikin wasu English wears t-shirt da trouser Black colour yana danna wayarsa aƙalla ya ɗauki kusan one hour yana jiransa amma har yanzu bashida alamun fitowa tsaki ya yi sannan ya tashi tsaye yana bin parlon da kallo sannan ya yi waje, buɗe wata ƙofa ya yi mai kamada ta zinare ya rabbi nan ma wani irin ƙaton parlon ne dan har ya fi wancen girma amma bai kai tsaruwar wancen ba wasu mazane majiya ƙarfi suna sanye cikin uniform black colour kana kallonsu kasan babu wasa a tare dasu ƙara sawa cikin parlon ya yi inda wasu mata ke zaune su biyar dukkaninsu farare ne kuma kana ganinsu kasan ƴaƴan manyane saidai suma ƙaddara ta faɗawa rayuwarsu, zaune suke duka sunyi shiru suna kallon Tv inda ake haska wani show babu alamar wahala atare dasu suna sanye cikin wasu banzar shiga wacce kwata-kwata batayi kamada shigar musulmai ba wata ƴar ƙaramar rigace irin mara hannun nan iya gwuiwa sun naɗe kansu da bandana kallonsu Taj ya yi sai kuma ya yi murmushi cikin sanyin murya ya ce" Tyha" da sauri wacce ya kira sunanta ta juya ta kalleshi sai kuma tayi murmushi da sauri ta taso tana kwarkwasa tana zuwa ta shige jikinsa rungumeta ya yi yana dariya ya ce"nayi missing naki sosai" ɗago kanta tayi tana kallonsa ta ce"nima haka kadawo amma?" gyaɗa mata kai ya yi ya ja hannunta ya ce"muje ki rakani" fitowa sukayi tana yi masa hira ganin inda ya nufa yasa ta waro idanunta tana kallonsa da kyakkyawar fuskanta ta ce"ina zamuje ne?" jan kumatunta ya yi ya ce" wajen Zaki" da sauri ta sakeshi ta ce"wait" sannan ta juya da gudu. Girgiza kai ya yi dan yasan me ta tafi yi ya tsaya yana jiranta not too long ta fito tana sanye da Abaya black colour tayi rolling veil ɗin murmushi ya yi ya ce"kuna matuƙar tsoran Zaki" dariya ta yi ta ce"ba dole ba kaima fa kasan halinsa" Taj ya ce"hmmm nima nan wani tym ɗin tsoransan nakejin mutum sai rashin mutunci" ta ce"kaga nidai babu ruwana wlh" dariya ya yi daidai lokacin suka zo bakin ƙofar murɗa handle ɗin ƙofar ya yi wani irin ƙamshin turaren Creed Aventus Eau de perfume spray shine ya daki hancinsu lumshe idanu suka yi a tare sannan ya shiga bakinsa ɗauke da sallama tsaye yake jikin wani ƙaton Enlargement na hoto ya zuba masa idanu yana sanye cikin wata armless Fara wacce takama jikinsa sosai sai Chinos Three-quater black colour gashi ne zube kan gadon bayansa tamkar na mace yasha Saloon duk ya kanannaɗe kamar macaroni ya sanya Prada brand black colour akansa hannunsa ɗaya cikin aljihun wandon ɗaya kuma yana riƙeda wani haɗaɗɗen mug, kusan mintuna biyu da shigowarsu amma bai juyo ba kuma badan bai ji shigowar tasu ba saidan wata irin halitta da ubangiji ya yi masa ta jin kai. Girgiza kai Taj ya yi sannan ya sake yin gyaran murya ya ce"Zaki" a hankali ya juyo cikin wani action mai ɗaukar hankali ya ilahy ubangiji ya yi halitta akan fuskar bawansa tamkar ba mutum ba saboda tsananin kyau tun daga girarsa wacce take cike da gashi baƙiƙƙirin da ita sai dogon hanci wanda yake har baka ga lips ɗinsa sunyi wani irin pink alamun yana yawan taunesu ganin yanda suka zuba masa idanu kamar basu taɓa ganinsa ba yasa ya haɗe rai yana waro musu manyan idanunsa masu matuƙar kwarjini hakan yasa suka sunkuyar da nasu taɓe baki ya yi bai ce komai ba ya nemi kujera ya zauna ya shiga girgiza ƙafa da kallo Tyha tabi ƙafarsa wata irin kyakkyawar gargasa ce kwance kan farar fatar tasa batasan sanda ta saki wata ajiyar zuciya ba tana lumshe idanunta ita inama wata rana Zaki ya nemeta ai da tafi kowa farin ciki saidai sanin shi ba halinsa kenan ba ya sanya ta kawar da tunanin daga cikin kwakwalwarta, riƙe hannunta Taj ya yi sannan ya jata suka zauna kan kujera ɗago kansa ya yi yana kallonsu sai kuma ya ce cikin hucky voice"Keee get out" da wani mugun sauri Tyha tayi waje har tana neman faɗuwa ko kallonta bai yi ba ya mayar da kansa gun Taj ya ce"where is she?" "Tana mota amma bata farfaɗo ba that's why na barta, nd then kuma naji Farooq yana mini wata magana wacce ban kai ga fahimtar ba" yana danna wayarsa ya ce"uhnn ina jinka" gyara zama Taj ya yi ya ce"cewa yake wai ba ita ba ce yarinyar daya siyar nd lokacin dana ɗaukota saida na kirashi ya tabbatar min da cewa ita ce amma yanzu ya ce wai ba haka ba" ajiye wayar ƙirar iphone 16 ya yi yana maida dubansa ga Taj ya ce"then what he mean, Taj kasan halina banason rubbish kuma ni bai dameni ba na rigada na biyasa dan hakan ko yau na samu wanda zai karɓi yarinyar nan zan bashi ne without second thought" murmushi Taj ya yi ya ce"to dan Allah na karɓeta hannu bibbiyu wlh zan biya yanda kayi mata kuɗi please Zaki kayi min wannan taimakon" wani kallo Zaki ya watsa masa ya ce"ɗan iska kawai kai bakada wani aiki sai na Sex ne kai kenan abu ɗaya, wait dan Allah mata nawa ka yiwa ciki tell me truth" tuntsirewa ya yi da dariya ya ce"kai bakada dama wlh ai inada kayan aiki da tsari nakeyin komai, nidai dan Allah kayi min wannan alfarmar wlh yarinyar ta haɗu" taɓe baki Zaki ya yi ya ce"bring her" okay ya ce sannan ya miƙe ya fita daga parlon, girgiza kai Zaki ya yi sannan ya cigaba da danna system ɗin dake gefensa, after some minutes ya dawo yana rungume da ita da kallo Zaki ya bisu har ya kwantar da ita kan ɗaya daga kujerun parlon zama ya yi yana kallonsa ya ce"gatanan kamar baka ɗauki Mutum ba ban taɓa ganin yarinya mara nauyi irinta ba kamar bata cin abinci" kallonta Zaki ya yi wanda hakan yasa ya miƙe tsaye cikin tafiyarsa da cikkaken namiji mai ji da kansa ya ƙarasa gabanta hannunsa zube cikin aljihu yake kallon kyakkyawar fuskanta taɓe baki ya yi sai kuma ya koma ya zauna yana kallon Taj ya ce"saboda kyanta kake sonta?" murmushi Taj ya yi ya ce"to wa yaƙi mace mai kyau?" "Ni" kallonsa ya yi sai kuma ya tuntsire da dariya ya ce"ai kai Aliyu banda kai a lissafi dan ba kai ɗaya bane, yanzu nidai zaka bani ita ko A'a" buɗe baki ya yi zai yi magana daidai nan ta buɗe idanunta kallon inda take ta yi sai kuma ta miƙe a birkice tana kallonsu ba Taj ba hatta Zaki saida ya sake kallonta, murmushi ya yi ya ce"woww what a prettiest girl" da sauri Muhaira ta miƙe tsaye ta kallesu duka sai kuma tayi waje da gudu bin bayanta Taj ya yi da gudu yayinda Zaki ya tsaya yana kallon ikon Allah taɓe baki ya yi sai kuma ya bi bayansu shima. Tsaye ya samesu a farfajiyar ƙaton gidan sunata kokawa da Taj harda wasu guards ɗinma nema take tafi ƙarfinsu dan turawa ɗaya take musu ta watsar dasu sannan ta ƙara nufar waje su bita da gudu su riƙeta, wani kyakkyawan murmushi ya yi wanda ya ƙara fito da zallar kyawunsa girgiza kansa ya yi yana kallon dramar da akeyi tamkar a cinema, kallonsa Taj ya yi cikin ɗaga murya ya ce "Zakiiiii dan Allah help me wlh tafi ƙarfina" Tsayawa ya yi na wasu seconds sannan ya taka har gabansu kallonsu ya yi duka sannan ya ƙarasa wajen Taj wanda ya cukwuikuyeta ya riƙe gam yana zuwa ya sanya tattausan hannunsa ya karɓeta hannun Taj wani wahalallen numfashi Taj ya sauke yana dafe ƙirjinsa zullo ta shiga yi a hannun Zaki hakan yasa ya yi wani murmushi sannan ya ɗauketa cak a kafaɗa ya shige ciki, bin bayansa Taj ya yi har sannan bai gama dawowa daidai ba ya shiga parlon bai ga Zaki a parlon ba hakan yasa ya nemi waje ɗaya ya zauna yana sakin wani Irin numfashi. Ganin da gaske aljanun kanta suke kuma koda wasa sunƙi magana yasa ya danneta akan gadon yana kallon fuskarta wacce tayi wani irin jaa girgiza kansa ya yi sannan ya ɗora hannunsa kan goshinta ya shiga murzawa da sauri ta saki wata irin ƙara cikin sautin kuka kuma ta ce"mu ka rabu damuuu ina ruwanka ka sakemu" taɓe baki ya yi cikin cool voice ya ce"bazan rabu daku ɗin ba me kuke a wajenta?" "batada kowa batada gata ta rasa duk wani farin cikinta tun ranar da tazo duniya babu wanda ya damu da ita rayuwarta cike take da ƙalubale dolene mu kula da ita mune kaɗai gatan ta ka rabu damu muyi aikin gabanmu kar kace zaka shiga tamm" yanda ta wani taune lips ɗinta wanda duk suka gama jiƙewa ya yawo sai ta bashi tausayi, ƙara yunƙurawa ta yi zata miƙe ya sanya hannunsa ya tokareta a hankali take sakin wani numfashi shiru ya yi na wasu mintuna sai kuma ya ce"uhnnn ku bar jikinta" tsaki ta yi ta ce"kai ne zamu ce ka rabu da ita amma mu babu wanda ya isa ya rabamu da ita" haɗe ransa ya yi ya ce"ohk rashin kunya zaku yimin?" girgiza kai tayi tana taɓe baki gyara kwanciyarsa ya yi ya sakar mata dukkan nauyinsa sannan ya kamo fuskarta a tafin hannunsa, cikin wata kamilalliyar murya ya shiga rera karatun Alkur'ani inda yake karanta suratul jinn kuka Muhaira ta sanya kuma duk abinda ake koda wasa bata buɗe idanunta ba cikin wata iriyar murya mai nuna fita hankali ta ce"kayi haƙuri wayyoooo zamu tafi kabari dan Allah zaka kashemuuuu!" ko saurarenta bai yi ba ya cigaba da karatunsa saida yakai inda ya yi niyyar sannan ya ɗago yana kallon fuskarta cikin sanyin murya ya ce"now leave her" cikin ƙaraji ta ce"wlh mun tafi amma zamu dawo kasa wannan a ranka" taɓe baki ya yi yana dungure mata kai ya ce"karku fasa dawowa nima bazan fasa ƙonaku ba" turo masa baki gaba tayi sannan ta ce"mun tafi muu" harararta ya yi ya ce"Allah ya raka taki gona" wata sassanyar ajiyar zuciya ta sauke sai kuma ta sake rufe idanunta a hankali shima yake sauke numfashi dan ya daɗe rabonda ya yi magana mai tsawon wannan tashi ya yi daga jikinta wanda ba daban aljanu ba da tuni ya illata ta bai sake saurarenta ba ya juya ya shige toilet dan watsa ruwa harga Allah ƙamshin turaren yarinyar bai masa ba duk da yasan ba wani ne ya sanya mata ba sai Taj. Fitowa ya yi daga wanka yana sanye cikin wata bathrobe ƙirjinsa a buɗe wani lafiyayyen gashi ne kwance a kansa tudun nononsa Kamar na mace saboda cika nipples ɗin kuma jajaye dasu, six pack ɗinsa ya fito raɗau ko ba'a faɗa maka ba kasance ba ƙaramin gym yake ba dan ko ɗan wristling albarka, bedroom slippers kawai ya saka ya juya ya fita gashin kansa na ɗigar ruwa kamar na Mace, cikin isa yake taka stairs ɗin benen wanda hakan ya sanya Taj juyowa kallonsa ya yi sai kuma ya ɗauke kai a hankali Zaki ya ƙarasa sakkowa sannan ya zauna kujerar dake facing tasa taɓe baki ya yi ganin yanda ya ajiye uban Cake a gabansa yana faman ci girgiza kai ya yi sai kuma ya ce"kwaɗayayye kawai" dariya Taj ya yi yana kai wani slice na chocolate cake bakinsa ya ce"naji ɗin" saida ya cinye tass sannan ya ɗauki water bottle ya sha ruwan ya ajiye yana gyatsa ya ce"Alhamdulillah" sai a sannan ya kalli Zaki ya ce"wlh yarinyar nan aljanu take" "wace yarinya??" harga Allah Zaki ya tambaya dan kwata-kwata ya manta da wata yarinya, harararsa Taj ya yi ya ce"banson rainin hankali ya kuka ƙare da aljanun" sai a sannan ya tuna ya taɓe baki yana faɗin"inada abinda yafi wannan yanzu ya kunyi magana da manager?" gyaɗa masa kai ya yi ya ce"Eh munyi an kammala komai, sannan akwai wasu yara guda biyu da Abrar ya yimin maganarsu zuwa anjima zanje naga idan zasu yi daman akwai wani wanda ya ce min yana son guda biyu idan naga sunyi sai kawai na miƙa masa" jinjina kai Zaki ya yi sannan ya ce"then we should talk later I'm so excited" miƙewa ya yi yana murmushi ya ce" a wuta lpy" sannan ya yi waje, da kallo Zaki ya bisa sannan ya tashi ya haye sama da ɗan sauri. Kai tsaye Taj ɓangaren su Tyha ya nufa yana zuwa ya samesu suna cin abinci da hannu ya yi mata alama da tazo ta tashi tana ɗaukan veil ɗinta sannan tabi bayansa kai tsaye kuma motarsa kirar Bugatti suka shiga ya bar gidan. Bayin Allah nagaji 😤😂. # *BA ITA BA CE* # *ZAKI* # *MUHAIRA* # *TAJ* # *TYHA* # *RIYADH* # *SQUAD 2024* # *Nanameera ce!* [8/5, 8:58 PM] Nanameera😍✌🏻: *BA ITA BA CE!..💖💖* *Ameenatou I Ibrahim* *Nanameera*. *nanameera08@arewabooks* *MIKIYA WRITERS ASSO...* ```Page 07``` Sheshsheƙar kukanta yaji sanda ya shiga cikin bedroom ɗin, zaune take ta haɗe jikinta waje guda ta tura kanta cikin cinyoyinta gashin kanta duk ya wargaje taɓe baki ya yi sannan ya ƙarasa gaban bed ɗin alamun shigowar mutum da taji ya sanya ta ɗago dara-daran idanuwanta wanda suka jiƙe da hawaye ta kalleshi, shima ita yake kallo kwarjinin nasa idanun ya sanya ta sunkuyar da nata sai kuma ta cigaba da rera kukanta Zaki bai sake saurarenta ba ya taɓe baki sannan ya juya ya fice daga ɗakin zaunawa ya yi nan parlon shi kaɗai yake yin tsaki da dukkan alamu Taj ya haɗashi da wahala, mikewa ya yi ya buɗe wani haɗaɗɗiyar Freezer ya ɗauko Apple guda biyu da dabinon ajuwa ya dawo ya zauna lumshe idanunsa ya yi saboda wani zaƙin zuma dana dabinon da suka dakeshi yana matuƙar son abu mai zaƙi a rayuwarsa that's why koda yaushe baya rasa cake, dabino da chocolate a fridge saida ya ci kusan guda goma sannan ya rufe robar water bottle ya ɗauka ya ɓalle murfin ya farasha sanyin ruwan ne ya sanya ya yi saurin ajiyewa dan lokaci ɗaya ƙirjinsa ya riƙe bandama rashin jin magana irinta Zaki da bazai sha ruwan sanyi ba, idanun da yaji yana yawo akansa yasa ya juya two eyes sukayi dashi ta ɗauke kanta tana turo baki ɗauke kansa ya yi shima ya cigaba da cin Cake ɗin gabansa wani takaici ne ya turnuƙe Muhaira kasancewar har sannan aljanun basu gama sakinta ba. Saida ya gama cin abubuwan daya ɗebo sannan ya miƙe ko kallonta bai yiba ya shige bedroom ɗin ya rufe ƙofar da kallo kawai Muhaira ta bisa haka kawai taji batasan ganinsa ko meyasa ohho??, tafiya tayi ta zauna ƙasan carpet ɗin parlon mai wani irin laushi kamar mage hannayenta ta ɗora kan carpet ɗin tana taɓawa dan ita bata taɓa jin abu mai laushin wannan ba abu kamar buredi. Gajiya tayi da zaman wajen hakan yasa ta kwanta nan ƙasa not too long kuma bacci ya ɗauketa dan a matuƙar gajiye take. A hankali ya buɗe idanunsa, da sauri ya tashi zaune yana kallon agogon dake gefensa babu kaya jikinsa daga shi sai wando Three-quater milk colour da alama tunda ya yi wanka bai saka kayan ba, ɗan siririn tsaki yaja sannan ya miƙe ya shige toilet ruwa kawai ya watsa ya fito yana ɗiga dryer ya ɗauka ya tsane kansa sannan ya sanya wani ribbon baƙi ya ɗauresa har kan gadon bayansa ya sauka dan gashinsa ko wata macen albarka wata V-neck t-shirt ya sanya coffee colour sai wandonta wanda ya kasance gajere shima coffee yarin diamond ya sanya a kunnensa ɗaya sannan ya fito, ƙamshin turaren Aventus Eau de perfume spray ne ya daki hancinta tana zaune gefen kujera sai baza idanu take idanunta sun faɗa sosai ko ba'a faɗa maka ba kasan yunwa takeji tsayawa ya yi a parlon yana gyara zaman farin Bluetooth ɗin kunnensa da kallo Muhaira ta bishi tunda take a rayuwarta bata taɓa ganin mutum mai kyawun Zaki ba ga iya kwalliya kamar ɗawisu "Keeee!" A ɗan firgice ta kalleshi sai taga ba ita yake kallo ba wayarsa yake dannawa kiran wayar ya shiga yi bayan an ɗaga ya ce"uhnnn sai ka zo" abinda kawai ya ce sannan ya kashe wayar wata kujera dake facing ɗinta ya zauna yana karkaɗa ƙafa wanda ke nuni da isa da taƙama kallonta ya yi from head to toe sai kuma ya taɓe baki cikin wata iriyar hucky voice ya ce"hyy come here" kasancewar tana zuwa makaranta dukda ba kullum hakan yasa ta gane abinda yake nufi, jikinta babu ƙwari ta ƙaraso wajen tana jan ƙafa zama tayi a gefen ƙafarsa ta sunkuyar da kanta cikin raunin murya ta ce"gagg...gani" idanunsa a rufe suke ya kifa kansa a jikin kujerar yana jinta saida ta faɗa sau uku sannan ya ɗago yana kallonta da mamaki take kallonsa ganin yanda idanunsa suka sauya kala zuwa jaa jijiyoyin kansa duk sun tashi ya haɗa zufa dukda AC dake kowace kusurwa ta parlon, sosai Muhaira ta tsorata hakan yasa ta fashe da kuka tana toshe bakinta, ya ilahy tamkar ɗigar dalma haka ya dinga jin kukanta akansa a hankali hannunsa ya fara kakkarwa ƙoƙarin yake ya yi mata magana amma bakinsa ya gagara furta komai gashin bashida wata mafita yasa ya kamo hannunta da sauri da miƙe tsaye dukda yanda takejin jiri harga Allah ita tsoro ya bata hakan yasa ta sake rushewa da wani irin kuka cikin zafin nama ya janyota ta faɗo kan ƙirjinsa sannan ya riƙe fuskarta gam a hannunsa iyaka rikicewa Muhaira tayi hakan yasa itama nata jikin ya shiga rawa batasan meke damunsa ba amma tasan duk abinda zai sa mutum ya dinga ha tofa ba mai daɗi bane ganin taƙi tayi masa shiru ya sanya ya janyota sosai jikinta har suna jin numfashin juna a hankali ya ɗora fuskarta akan tasa har sannan kuma ya gagara cewa komai sai zufa wacce ke sakko masa, ita kuwa Muhaira tsorone ya hanata yin komai sai kawai ta cigaba da rera kukanta ganin taƙi yi masa shiru ya sanya ya fashe da kuka shima kamar ƙaramin yaro tsabar mamaki batasan sanda ita tayi shiru ba ta zuba masa idanu tana kallon ikon Allah kamar wannan mutumin yana kuka taɓ ta faɗa a ranta. Saida ya yi mai isarsa sannan ya yi shuru yana sauke ajiyar zuciya kusan 5mins kafin ya janyeta a jikinsa ya tashi batareda ya kalleta ba ya shige bedroom ɗinsa, "taɓ babba da shagwaɓa taɓɗijan" Muhaira ta faɗa tana kallon ƙofar ɗakin nasa, wani irin murɗawa cikinta ya yi ta sanya hannayenta ta dafeshi tana sakin kuka yunwa take ji kamar ta mutu rabonta da abinci har ta manta dan batasan yau yaushe ba balle ta tuna ranar ita burinta ma bai shige ta tafi daga nan ba ko wama ya kawota?????. Ganin har kusan ƙarfe 12pm bai sake fitowa yasa ta share hawayenta ta kifa kanta gefen kujera haka wani baccin rashin abinyi ya sake ɗauketa. *2:30am* Wani irin sanyin ne ke ratsa ƙashinta wanda hakan ya nemi ɗaukewar numfashinta batasan sanda ta miƙe zaune ba tana fashewa da wani kuka gwanin ban tausayi yunwa takeji, ga wani zazzaɓi daya kawo mata farmaki duk jikinta ciwo yake mata sake kallon ƙofar bedroom ɗin tayi sai kuma ta tashi da sauri ta koma ta zauna saboda kanta da ya yi wata irin sarawa ganin batada zarafin tafiya ya sanya sakko daga kan kujerar ta shiga tafiya da rarrafe kamar ƙaramar yarinya saida taje bakin ƙofar sannan ta miƙe tsaye dakyar tana lumshe idanu, murɗa handle ɗin ƙofar ta yi ta tura kanta ciki saurin jingina tayi da jikin ƙofar tana toshe bakinta saboda wani irin ƙamshi da sanyi da suka cure waje guda, sanyin ya yiwa fatarta yawa wasu hawayene suka shiga zarya akan fuskarta kamar ta juya ta fita amma kuma yunwar da takeji bazata barta tayi haka ba. Tafiya tafara kamar wacce babu laka a jikinta har ta ƙaraso gabansa kwance yake kan gadon ya rufe duk jikinsa da duvet. Shashshekar kukanta ce ta sanya ya farka dan kwata-kwata baya iya bacci waje da hayaniya a hankali ya yaye bargon dake jikinsa kamar ɗazu yanzuma babu kaya jikinsa da alama haka ya saba baya kwanciya da kaya, kallonta ya yi sai kuma yaja siririn tsaki ya ce"kee I'm ur mate da har zaki shigo min ɗaki?" girgiza masa kai tayi sai kuma ta sake fashewa da kuka tana kifa kanta gefen gadon, da mamaki Zaki ya kalleta dan bai saba ganin mace mai yawan kuka irin haka ba, tsaki ya ya sannan ya sanya hannunsa zai tureta wani zafi yaji a hannunsa hakan yasa ya ƙara taɓa wuyanta cikin sanyin murya ya ce"are you sick?" gyaɗa masa kai ta yi ya haɗe rai ya ce"bakida baki?" tashi zaune tayi tana murza idanunta cikin kuka ta ce"zazzaɓi nakeyi kuma yunwa nakeji" harararta ya yi ya ce"to tunda yunwa kikeji cinyeni" sunkuyar da kanta tayi tana safe Fashewa da wani sabon kukan, baki buɗe Zaki yake kallonta dan shi a zatonsa ma ko aljanun ne suka dawo banda haka yarinya ta dinga kuka babu dalili, haɗe ransa ya yi ya ce"kee wato ke shagwaɓaɓiya ce ko?" Ita dai kukanta take bata kallesa ba ya ce"rufemin baki ko na kwaɗa miki mari" haɗiye kukan nata tayi tana jan numfashi. Tsaki Aliyu ya yi sannan ya janye duvet ɗin jikinsa ya miƙe tsaye bai sake bi ta kanta ba ya fice daga parlon, turo bakinta ta yi tana binsa da kallo sai kuma ta jingina da prame ɗin gadon mai taushi kamar kujera, lumshe idanunta ta yi tana sauke ajiyar zuciya, shigowa ya yi hannunsa riƙeda robar dabino sai wani pack na biscuits ajiyewa ya yi gefen gadon sannan ya juya wajen Freezer ya ɗauko mata fresh milk ajiye mata ya yi ya ce"to mayunwaciya eat" kallonsa Muhaira tayi ya watsa mata wata harara sai ta sunkuyar da kanta tsaki ya yi sannan ya buɗe wata ƙofa ya shige ciki, da sauri ta shiga ƙoƙarin buɗe bottle ɗin robar saidai kwata-kwata batada kwari hakan yasa ta sake rushewa da kuka turo ƙofar ya yi yana kallonta ya ce"kee mene kuma?" nuna masa robar tayi fuskarta shaɓe-shaɓe da hawaye ta ce"nakasa buɗewa" wani takaicine ya turniƙeshi ya girgiza kansa ya ƙaraso wajen fizgar robar ya yi ya buɗe sannan ya miƙa mata ya juya yabar wajen, dolema gobe ya rabu da yarinyar nan idan ba haka ba sai ta saka masa ciwon zuciya. Cikin sauri ta shiga cin biscuit ɗin tana korawa da madarar har ta cinye tass dukda babba ne sannan ta buɗe robar dabinon wani irin lumshe idanu tayi tana taunawa saida ta cinye na bakinta sannan ta buɗe idanunta tana kallon robar wani kyakkyawan murmushi tayi barinma da taga zuma kwance akansa a hankali ta sake ɗaukan wani ta ci tana murmushi haka har ta cinye na robar tass sannan ta ajiye robar sauke robar da ledar biscuit ɗin tayi a gefenta ta gyara zamanta kan gadon ta kwanta bargon taja ta lulluɓa ta saki wani kyakkyawan murmushi har saida beauty point dinta suka loma ta ce"ƙamshi" ta faɗa tana rufe idanunta nan da nan wani bacci mai matuƙar daɗi ya ɗauketa. Kiraye-kirayen sallar asuba da aka fara ya sanya ya fito da mamaki ya ƙaraso yana kallon yanda ta ƙugundune cikin lafiyayyen bargonsa tana bacci ɗora hannunsa ya yi a ƙugu tana kallon zallar rainin hankali irin na yarinyar tsaki ya yi har zai tasheta sai kuma ya rabu da ita da mamaki ya kalli robar dabinon sai kuma ya tuntsire da dariya mara sauti ganin da ya yi tass ta cinye komai babu abinda ta rage kallonta ya yi ya ce"witch" sannan ya shige toilet dan ɗauro alwala. *Nigeria* *MAITAMA DISTRICT* *MA'EESHA POV* Lumshe idanunta ta yi tana kai chocolate ice-cream ɗin bakinta cikin jin daɗi ta ce"yaya may god bless yhu" murmushi ya yi ya ce"Ameen Shalele, yanzu dai ina tsarabata zan tafi kinga dare nayi" murmushi ta yi ta ce"yaya kenan wait for me nagama shan ice-cream zan ɗauko maka" buɗe baki ya yi zai yi magana wayarsa ta shiga ƙara kallon sunan dake kan screen ɗin ya yi sai ya ce"kinga idan kin gama kin kawomin ɗaki bye" mikewa ya yi ya fice ta bishi da kallo sannan ta cigaba da shan ice-cream ɗinta hankali kwance, saida ta shanye tass sannan ta tura robar ƙasan bed gudun kada Mami ta shigo ta tashi ta zuge trolley ɗinta sannan ta ɗauki wata leda wacce ta zubo masa kayan ta fice da sauri. Tana ƙoƙarin buɗe handle ɗin ƙofar taji Mami ta ce"Ma'eesha!" a ɗan firgice ta juyo sai kuma ta saki ajiyar zuciya tana tace a shagwaɓe"Mami yhu scared me" Mami ta ce"ina zaki je a wannan daren?" turo baki ta yi ta ce"yaya Farooq zan kaiwa tsarabarsa" wani kallo Mami ta yi mata Wanda yasa ta sunkuyar da kanta ta ce cikin kakkausar murya"koma ɗaki" sanin halin Mami wani lokacin yasa ta bi gefenta ta shige apartment ɗinta da gudu tana sakin kuka, girgiza kai Mami ta yi sannan ta shige daman General ta fito ɗaukarwa wani File. Yana duba file ɗin gabansa ya ce"kenan me kike nufi?" numfasawa Mami ta yi ta ce"zuwa yanzu ya kamata ace Ma'eesha ta daina shigewa Farooq coz kasan alaƙar dake tsakaninsu bayan nan kuma duk sun fara girma akan me zata dinga zuwa apartment ɗinsa da daddare wannan bai dace ba yallaɓai" zare glasses ɗin fuskarsa ya yi yana kallonta ya ce" # *BA ITA BA CE* # *MA'EESHA* # *FAROOQ* # *General* # *SQUAD 2024* # *Nanameera ce!*. [8/6, 5:50 PM] Nanameera😍✌🏻: *BA ITA BA CE!..💖💖* *Ameenatou I Ibrahim* *Nanameera* *MIKIYA WRITERS ASSO...* _Hauwa'u Omar writer of A WANI COMPANY Allah ya baki lafiya Masoyiya 😢, pray for my twinkle wish yhu speedy recovery, Allah ya baki lafiya mai ɗorewa 🤲._ ```Page 08``` *RIYADH* *Al-Olaya Residence* *8:30am* Taɓe baki Tyha tayi tana kallon Abra ta ce"wai dan Allah me kike nufi ne?, nifa inason Taj kuma zanyi duk abinda ya umarceni then what's ur problem?" girgiza kai Abra ta yi ta ce"ke ai saboda bakida hankali yasa kk gama yarda dashi kwata-kwata bakisan kanki ba bakiga gatan da Zaki ya yi mana ba, yaƙi siyar damu kamar yanda ya saba siyarda mata ya killacemu cikin gidansa sannan ya sakamu a makaranta dan mu samu kyakkyawar rayuwa amma ko kaɗan bakiga wannan ba kin gwammace ki cigaba da iskanci nidai wlh yanda Allah ya rufa mini asiri ya rabani da wannan rayuwar na barta har abada zan cigaba da karatuna dan nasan watarana zai amfaneni" tsaki Amrish ta yi ta ce"ai sai kiyi ta yin karatun mukam saidai idan bamu samu masu tayawa ba amma muddin muka samu wlh sai munji daɗin rayuwarmu" murmushi Tyha ta yi tana kallon Amrish ta ce"faɗa mata dai ni kunsan wane a target ɗina?" girgiza kai suka yi ta yi wannan murmushi tana cije baki ta ce"Zaki!" da sauri duk suka kalleta sai kin suka tuntsire da dariya haɗe rai ta yi Khady ta ce"lallai bakida hankali taɓ ke a ganinki Zaki zai kulaki?, to ni tunda nake a tarihi ban taɓa jin ya kula wata mace bama iya kaci shidai akawo masa ya siyar ko ya bada haya amma bansani ba ko sai dare ya yi tashi take zuwa" dariya suka yi duka ta ce"aikuwa ku zuba idanu kuga in sha Allah sai haƙata ta cimma ruwa sai nayi rayuwa a apartment ɗin Zaki" mikewa Abra ta yi ta ce"na fuskanci bakuda abunyi shiyasa kunga tafiyata school" da harara suka bita har ta fice daga parlon sannan Amrish ta ce"wai ke nawa Taj yake baki ne?" haɗe rai Tyha tayi ta ce"ina ruwanki banson gulma ke" murmushi tayi ta ce"nifa ina son guy ɗin nan dan shima ya haɗu" wani kallo Tyha tayi mata kafin ta miƙe batace komai ba ta shige bedroom ɗin. Ganin yanda take binsa da kallo yasa ya haɗe rai yana kallonta ya ce"bar kallona" murguɗa masa baki ta yi ta ce"to kai ya akayi kasan ina kallonka", baki buɗe Zaki ke kallonta da alama sai ya koyawa yarinyar nan hankali, ajiye turaren hannunsa ya yi ya ƙaraso gabanta yana kallonta sai kuma ya nemi waje ya zaune da hannu ya yi mata alama da tazo aikuwa ta tashi babu musu ta ƙarasa har zata zauna a ƙasa ya riƙe hannunta ya zaunar da ita kan cinyarsa turo baki ta yi cikin gunguni ta ce"nidai Allah kabari banason iskanci" ware idanunsa ya yi ya tamke fuska kamar bai taɓa dariya ba, tattausan hannunsa ya sanya kan lips ɗinta sosai ya yi laushi taɓe baki ya yi sannan ya murza da ƙarfi kuka ta saki tana yarfe hannunta ƙara murɗewa ya yi da duk ƙarfinsa. Kuka take son yi amma yaƙi bata damar hakan aƙalla yakai wajen 5mins sannan ya saki bakin yana jingina da jikin kujerar, rushewa tayi da kuka jin yanda bakinta yake raɗaɗi yayi wani irin jaa lumshe idanunsa ya yi above two minutes yana jin kukan nata ganin tana son rikita kwakwalwarsa yasa ya jawota ya matseta a faffaɗan ƙirjinsa luf tayi kamar bai rufe komai ba dan kwata-kwata Muhaira batada ƙiba, a hankali kamar mai koyan magana ya ce"shii...shiiiiiii ya isa haka" tura baki tayi gaba tana hawaye ɗago fuskarta ya yi ya ce"what's ur name?" shiru tayi masa ya haɗe ya ce"I'm ur mate?" girgiza kanta ta yi cikin shashshekar kuka ta ce"Muhaira" harararta ya yi ya ce"Malama ur real name" zumɓura baki ta yi ta ce"A'ishah" sakinta ya yi ya ce"ɗagani" ƙuri tayi masa da idanu ya ce"ta Allah ba taki ba kike wani kallona witch kawai" harararsa tayi ta ce"wlh ni ba mayya ba ce" girgiza kansa ya yi yana murmushi ya ce" rashin kunya kike min ko?, zanyi maganin bakin rashin kunyar" turo baki gaba tayi ya kai hannu zai riƙe bakin da gudu ta tashi daga jikinsa takoma can bakin ƙofa ta tsaya. Murmushin mugunta ya yi ya ce"zan kama kine yarinya sai kin raina kanki" gwalo tayi masa tana dariya, kallonta ya yi tayi yadda dariyar tayi mata wani masifar kyau taɓe baki ya yi ya ce"aljana" sannan ya miƙe bai sake bi ta kanta ba ya yi waje. *9ja* *Prime University, kuje, FCT Abuja* *10:40am* Tafiya suke tana basu labari sai dariya suke banda Ma'eesha wacce ta haɗe ranta kamar bata taɓa dariya ba, lura da haka yasa Fateema ta ce"takwara what's wrong with you?" numfasawa Ma'eesha ta yi ta ce"bakomai kawai bana jin daɗi ne, nd inason naje gida" murmushi Fateemah ta yi ta ce"kedai ki daina zurfin ciki wlh, ko zaki ɓoyewa kowa wani abu ai ni nayi zaton zaki iya faɗamin dan Allah talk to me dear" kallonta Ma'eesha tayi hawaye kan fuskarta ta ce"Takwara ina cikin matsala bansan ya zanyi ba kuma bansan wa zan faɗawa ba hankalina a tashe yake" tsayawa Fateemah tayi tana kallon Ma'eesha ta ce"kin barni cikin duhu Ma'eesha faɗa min mene ne ya dameki?" share hawayen fuskarta ta yi ta ce"bari muje gida dan Allah" numfasawa tayi ta ce"to shikenan" suka cigaba da tafiya dan fita daga makarantar. Da sallama ta shigo parlon babu kowa gidan shiru kamar ruwa ya cinye da alama Mami ma ta fita ne, riƙe hannun Fateemah tayi suka shige apartment ɗinta, saida ta rage kayan jikinta sannan ta zauna da sauri Fateema ta ce"yanzu faɗa min" ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ce"wlh nakamu da soyayya ne kuma da ɗan uwanmu gashi bansan taya zan tunkareshi da maganar ba, Fateemah bantaɓa jin son wani ɗan adam irinsa ba nikaina bansan yaushe nafara sonsa ba tun ina ƴar ƙaramar yarinya rabonsa da ƙasar nan, kuma har yanzu bai dawo ba amma ana saka ran nan bada jimawa ba zai dawo yanada mata harda ƴa yanzu ma anyi masa kucciya ne shine yabar ƙasar gaba ɗaya rannan Mami ta nuna min hotonsa tun daga ranar ban sake bacci mai daɗi ba kullum shi nake mafarki bansan ya xanyi ba takwara dan Allah ki taimakeni..." Ta ƙarashe maganar tana sakin wani kuka mai ban tausayi. Riƙe hannunta Fateemah tayi tana goge mata hawayen fuskarta ta ce" ya isa haka ƙawata, insha Allah za ki zauna dashi matsayin mijin aurenki karki sanyawa kanki damuwa kinsan yanayin lalurarki, kinada buƙatar kulawa ta musamman Ma'eesha dan Allah karki sanya komai cikin ranki yanzu yaushe ne ake saka ran zai dawo?" numfasawa ta yi ta ce"Mami bata faɗa min ba amma ni inason kafin ya dawo naje Masarauta dan inada buƙatar haɗuwa dashi" murmushi Fateemah tayi ta ce"shikenan karki damu zan taimaka miki in sha Allah kawai abinda ke zaki yi yanzu shine kiyi ƙoƙari ki gano sanda zai dawo ƙasarnan daga nan komai zai zo da sauƙi in sha Allah" rungumeta Ma'eesha tayi tana dariya ta ce"Nagode sosai takwara Allah ya barmu tare" tana murmushi itama ta ce"Ameen takwara, yanzu dai ba wannan ba kenan bazaki bawa Sir Najeeb dama ba?" harararta ta yi ta ce"nifa koda wasa bai taɓa burgeni ba wlh kuma har ma Father ya ce zai sameshi ya faɗa masa ya rabu dani akanme taɓ" dariya Fateema ta yi tana kallon ƙawarta ta ta ce"taɓ lallai ma ke ɗin nan maganar har wajen Father taje lallai abun naki ya girmama" miƙewa Ma'eesha tayi ta ce"uhnn naki wasane bari na kawo mana abinci". *FAROOQ POV* Murmushin takaici ya yi ya ce"Mommy nifa abun nan ya isheni nagaji kuma haba dan Allah duk sanda mukayi attempting nayi wani abu sai aikinmu ya ɓaci yanzu dan Allah ya zamuyi Mommy nifa nagaji da zama ƙasan General sonake duk dukiyar ta dawo ƙarƙashin ikona, sannan ya zamuyi da Ma'eesha? yarinya nema take tafara bamu ciwon kai bansan wace mai kama da ita wacce har ni kaina banganesu ba amma dole akwai wani abu a ƙasa saboda haka yakamata tun wuri musan abunyi idan ba haka ba zamu tashi a tutar babu." shiru Mommy tayi dan itama abun ya fara fin ƙarfinta tsawon shekaru sun kasa cimma komai kullum sune suke faɗuwa yaushe zasu yi nasara akan General ne??, ganin taƙi cewa komai yasa ransa ya fara ɓaci ya ce"Mommy naga baki ɗauki abun nan serious ba to bari ni zan ɗauki matakin daya dace tunda ke kin gaza" ya juya ya fice yana buga ƙofar, da kallo Mommy ta bisa sai kuma ta girgiza kai kwata-kwata tarasa me zatayi akan al'amarin duk wata dabararta ta ƙare idan mallaka ce ta saba da mallake General kuma Allah da ikonsa ya fita shiyasa ma ita tabar layin malamai dan da ace zasuyi aiki da ba'a kawo wannan lokacin ba da wannan tunanin ta kwanta dan gaba ɗaya agajiye take. "Ma'eesha!! Ma'eesha!! Ma'eesha!!" "na.. na'am Mami" Kallonta Mami tayi ta harɗe hannayenta a ƙirji sunkuyar da kanta tayi tana wasada fingers ɗinta, ƙarasowa Mami tayi ta dafata tace"kedawa Ma'eesha?" rungume Mami tayi tana fashewa da kuka, shiru Mami tayi tana shafa mata bayanta sosai tayi kuka jikin mahaifiyar tata sannan ta ɗago Mami ta ce"now tell me meyake damunki kwana biyu?" murmushi ta yi tana goge hawayen nata ta ce"kawai ji nayi inason nayi kuka Mami" wani kallo Mami tayi mata wanda ya sanya tasha jinin jikinta. Kama hannunta Mami tayi ta jata gefen royal bed ɗin suka zauna cikin sanyin murya ta ce"Ma'eesha kinsan bakida wacce ta fini duk duniyar nan, ni ce ya kamata nazama abokiyar hirarki da kuma shawararki saboda haka kar kiji komai ki sanar dani damuwarki please" riƙe hannun Mami tayi ta ce"Mami kinsan da akwai wani abun zan sanar daku wlh babu komai kawai nima banajin daɗi ne amma babu abinda aka yimin wanda zai sa ku shiga damuwa kawai ku tayani da addu'a" numfasawa Mami tayi ta ce"tunda kin ce haka shikenan Ma'eesha Allah ya yaye miki abinda yake damunki" murmushi tayi ta ce"Ameen Mamina". *RIYADH* *Al-Takhasosi Residence*. Wani irin haɗaɗɗen parlon ne mai Matuƙar girma komai na cikinsa silver ne sai sheƙi yake parlon ne mai kamada faɗa kana ganinsa kasan wasu ishasshun mutanene ke rayuwa a ciki zaune suke sunyi da'ira akan wani katafaren dinning table mai kyau abincine baje a gabansu sai wanda kaga damar ci, manyan masu kuɗi ne amma ba larabawa ba kana ganinsu kasan zamane ya kaisu ƙasar, dan larabawan basuda yawa sosai a cikinsu, wani babban mutum ne ya kalli Zaki wanda ke zaune kujerar dake facing tasa yana sanye cikin wasu suit black colour ya ɗora Glass akan fuskarsa ya yi wani sihirtaccen kyau cikin isa ya ce"Lion" ɗagowa Zaki ya yi ya ce"Yes sir" ajiye cokalin hannunsa ya yi ya ce"mata nawa ne yanzu a hannunka?" cikin sanyin murya ya ce"only 5 remains" murmushi ya yi ya ce"zuwa dare ka bawa Taj ya kawosu" ajiyar zuciya Zaki ya sauke sannan ya ce"amma Sir da an nemi wasu cox waɗannan sun ɗan daɗe a ajiye" gyaɗa kansa ya yi ya ce"Eh kuma hakane amma ai naji Taj yana maganar wata yarinya da ka siya right" da sauri Zaki ya kalleshi kafin ya ce"hakane" murmushi ya yi ya ce"kawai ka bawa Taj ita ya kawomin da daddare hope virgin ce?" gyaɗa masa kai kawai Zaki ya yi yana sauke wani numfashi ya miƙe without looking at anybody ya yi waje, da kallo suka bisa sannan wani daga cikinsu ya ce"wannan yaron ɗan zafin kaine yanada wahalar sha'ani" murmushi ya yi ya ce"haba Bala ai Zaki ba daga nan ba shiyasa nakeson mu'amala dashi above 5yrs muna tare dashi anan amma koda wasa bai taɓa yimin abinda ba daidai ba. Yasan aikinsa sosai shiyasa duk cikin yarana both na nan dana 9ja nafi sonsa kuma bakowa yakewa aiki ba" murmushi wanda aka kira da Balan ya yi ya ce"ai naga alama gashi yasan takan mata idan ya kawo maka mace kamar karka rabu da ita shiyasa nake son aikinsa" murmushi ogan ya yi ya miƙe ya ce"bari naje na shirya yau inada sabon jini" tuntsirewa sukayi da dariya ɗayan ya ce" kaifa Dmash bakada kyau kuma baka wasa da kaya" sunkuyowa ya yi ya ce"wazai yi wasa da abinci ai babu" yana faɗin haka ya haye sama suka bisa da dariya. Shigowa ya yi parlon hannunsa zube cikin aljihu yana tafiya yana furzar da wani irin zazzafan numfashi, zaune ya samesu ita da Taj yana bata labaru kanta a ƙasa dan bata san shi ba kuma batada saurin sabo, miƙewa ya yi yana kallon Zaki ya ce"sai yanzu?" gyaɗa masa kai kawai ya yi sannan ya haye sama, miƙewa Muhaira tayi Taj ya ce"A'a beauty ina za ki kuma?" turo baki gaba tayi tana wasada fingers ɗinta masu tsayi ta ce"to ba wajensa zan je ba" murmushi ya yi ya ce"shi wa?" da sauri ta kallesa da idanun ya kashe mata ido ya ce"kinsan shi ne?" kwaɓe fuska ta yi ta ce"Papina ne ai to" dariya ya yi ya ce" su Zaki Papi are you Fulani?" gyaɗa masa kai ta yi ya ce"enyeee kuma kin iya fulden?" gyaɗa masa kai nan ma ta yi ya ce"to yimin naji" buɗe baki ta yi zatayi magana suka ji ƙarar taku da sauri duka suka juya suna kallonsa. Sanye yake cikin wata armless maroon colour ya sanya Three-quater Maroon colour shima ya sanya Gucci brand fara akansa gashinsa ya sauka akan bayansa hannunsa riƙe da mug ɗin coffee. Taɓe baki ya yi bai kulasu ba ya zauna kan wata kujera ya zauna komawa suka yi suka zauna suma duk sunyi shiru kamar waɗanda akawa dole, a hankali yake sipping coffee ɗin hannunsa har ya shanye sannan ya ajiye mug ɗin a table ɗin gefensa ya juyo yana kallonsu, murmushi ya yi yana kallon Taj ya ce"munafiki" dariya Taj ya yi ya ce"naji ɗin, wai Sir Dmash ya ce nazo na tafi da yarinyar nan" haɗe rai Zaki ya yi bai ce masa komai ba ya kalli Muhaira wacce take kallon Taj ya ce"kee come here" miƙewa tana tafiya a hankali ta ƙaraso gabansa ta tsuguna kallon fuskarta ya yi for some minutes sai kuma ya ce"jeki bedroom ɗina ki ɗaukan wayana" miƙewa tayi ta haye sama, sai a sannan ya kalli Taj ya ce"zan kai masa ita da kaina kawai kayi tafiyarka" kallonsa Taj ya yi da mamaki ya ce"da kanka kuma amma why?" haɗe rai ya yi ya tashi ya miƙe tsaye daidai lokacin Muhaira ta sakko hannunta riƙe da wayar tasa, kallonta ya yi sanye take da wata riga long sleeve amma bata ƙarasa saukar mata ba ta tufke gashin kanta ya sauka har wajen ƙugunta, miƙa masa wayar ta yi ya karɓa sannan ya yi waje yana jan hannunta. Kai tsaye part ɗin ƴan matan gidan yana nufa har sannan kuma yana riƙe da hannunta ita kuwa sai binsa take kamar wata doluwa suna zuwa ya tura ƙofar bakinsa ɗauke da sallama wacce ba lallai bane su jita, zaune take a parlon tana karatun littafinta da sauri ta miƙe cikin rawar murya ta ce"bar...barkaaa da fitowa yallaɓai" kallonta ya yi from head to toe sai kuma ya ɗauke kansa ya ce"uhnnn ina suke sauran?" cikeda ladabi ta ce"suna bedroom bacci suke" bai ce komai ba ya juya ya bar wajen Muhaira ta bita da kallo. Cikin wata mota Fererri ash colour ya sanyanta sannan ya zagaya wajen driver da sauri guards ɗinsa suka tawo ya ɗaga musu hannu sannan shiga motar ya yi mata key bakinsa ɗauke da addu'a. A hankali ya sanyo ƙafarsa waje bayan ya kashe motar kusan 2mins yaga bata fito ba hakan yasa ya koma side ɗinta yana yi mata wani kallo ya ce"jira kike saina fito dake ne?" zumɓura baki ta yi ta ce"to ni nasan yanda ake buɗewa ne da zaka yimin faɗa" kwafa Zaki ya yi sannan ya buɗe motar yana harararta ya ce"baƙauyiya kawai" fitowa ta yi sannan itama ta galla masa harara cikeda tsiwa ta ce"naji ɗin kai kuma mai yiwa mutum iss..." maganar ta maƙale saboda wani mugun kallo da taga ya watsa mata ta haɗe rai itama tana ɗauke kanta tsaki ya yi sannan ya ce"Mumu kawai witch" wasu hawayene suka shiga sakko mata na baƙin ciki ita kwata-kwata batasan mutumin nan saboda ko kaɗan bashida kirki a hankali ta shiga murza idanunta tana shashshekar kuka dafe kansa ya yi ganin yarinyar na son tara masa mutane ya ce a fusace"idan baki yimin shiru ba saina kwaɗa miki mari wlh" banza ta yi masa ta nemi waje ta zaune kasancewar duk ƙasan garin kamar glass yake ko'ina tsaf, kallon agogon rollex ɗin hannunsa ya yi sai kuma ya kalleta ya ce" shikenan tashi kiyi shiru kinji" turo baki ta yi tana murza idonta ta ce"to ka maidani gidanmu ni, banason nan ni banasoo!!" ta faɗa tana sake fashewa da kuka. Ganin da gaske Muhaira bazata tashi ba yasa ya yi gaba cikin wata iriyar murya mai ban tsoro ya ce"gasu nan ku kamata" da gudu tabi bayansa tana riƙe masa hannu kyakkyawan murmushi ya yi ita kuwa ta riƙe shi gam gudun kada ya tafi ya barta. *Olaya Aqua park* shine sunan dake saman haɗaɗɗen ginin cikin tafiyarsa ta isa ya shiga ciki tana riƙe da hannunsa. *ZAKI HAKA ZAMU YI DAKAI😢😭😂* # *LOVE* # *DESTINY* # *POWER* # *TRAFFICKING* # *SQUAD 2024* # *NANAMEERA CE!✍️* [8/7, 1:58 PM] Nanameera😍✌🏻: *BA ITA BA CE!..💖💖* *Ameenatou I Ibrahim* *Nanameera* *MIKIYA WRITERS ASSO...* ```Page 09``` *Olaya Aqua park* Kallon wajen kawai Muhaira take kamar idanunta zasu faɗo iyaka haɗuwa wajen ya haɗu park ne mai ɗauke da swimming pool amma rufaffe akwai wadataccen haske a wajen dan bazaka taɓa cewa ba rana ba ce ba jan hannunta Zaki ya yi suka shiga wata ƙofa sai a sannan tagane ashe da ba taga komai ba inda suke tsaye yafi inda suka shiga da farko haɗuwa tsayawa ya yi gaban swimming pool ɗin wanda yake bada feshin ruwa mai matuƙar sanyi murmushi tayi tana cire hannunta daga nasa ta ƙarasa wajen tana shirin zura ƙafafunta taji an riƙeta. Kwaɓe fuska tayi tana kallonsa taga ya haɗe rai sai ta sunkuyar da kanta cikin sanyin murya ta ce"dan Allah Papi nashiga?" girgiza mata kai ya yi ta langwaɓar da kanta cikin sigar roƙo ta ce"wlh bazan yi wasa ba" taɓe bakinsa ya yi sannan ya ja hannunta zuwa wasu kujeru wanda suka zagaye wajen zama ya yi ya zaunar da ita gefensa bai ce mata komai ba, sosai ranta ya ɓaci dan ita a rayuwarta tana matuƙar son wasan ruwa dukda illar da hakan ke mata wata waiter ce tazo ta ajiye musu ice-cream a table ɗin gabansu sannan tabar wajen, kallon ice-cream ɗin Muhaira ta yi amma bata ɗauka ba wayar hannusa ya mayar aljihu sannan ya ɗauki ice-cream ɗin guda ɗaya ya fara sha sosai yake lumshe idanu saboda daɗin ice-cream ɗin hakan yasa Muhaira ta sanya hannunta zata ɗauki ɗayan, buge mata hannu ya yi yana harararta har sannan kuma bai ce mata komai ba. Turo baki ta yi cikin shagwaɓa ta ce"toh ni bazan sha ba?" banza Zaki ya yi mata ya cigaba da abinda yake aikuwa ta fashe da kuka yana jinta har ya shanye na hannunsa sannan ya ɗauki ɗayan ma ya fara sha ganin da gaske shanyewa zai yi bai bata ba yasa ta ƙara volume ɗin kukanta wani killer smile ya yi sannan ya kalleta ganin yanda duk ta ɓata fuskarta da hawaye ya ce" then you like it?" saurin gyaɗa masa kai ta yi ya dungure mata kai ya ce"kwaɗayayiya kawai" hannunta ta sanya tana dafe goshinta ta ce"ohhccccc zafi wayyo" harararta ya yi sannan ya miƙa mata ragowar na hannunsa karɓa tayi tana cigaba da kukanta har ta shanye sosai ice-cream ɗin ya yi mata daɗi dan yau ne shanta dashi na biyu miƙewa ya yi yaje wajen swimming pool ɗin ya zauna a nutse ya zura sangalin fararen ƙafafunsa cikin ruwan a hankali yake furzar da wani zazzafan numfashi gabaɗaya tunaninsa ya kwance abubuwa nason fin ƙarfinsa rauninsa nema yake ya fito fili wanda hakan ne yake gudu. Ƙarar ruwan da yaji shine ya dawo dashi daga duniyar tunanin daya tafi a hankali ya kalli gefensa ganin yanda wajen yake kwai alamar wanda ya faɗa yana numfashi, da sauri ya juya inda yabar Muhaira amma sai yaga wayam babu ita da sauri ya mike tsaye yana sake kallon ruwan, kenan yarinyar cikin ruwan ta faɗa??, Furzar da nunfashi ya yi yana dafe kansa sai kuma ya juya wajen wani table ya ajiye wayarsa sannan ya koma wajen without second thought kuma ya faɗa ruwan shima ji kake "tsundummmmm" saida ya fara iyo cikin ruwan sannan ya hangota can daga ƙarshen swimming pool ɗin kasancewar bashida wani zurfi yana zuwa ya jayonta ya rungume jikinsa sannan ya fito gaba ɗayan jikinsu sai ɗigar ruwa yake ajiye ya yi gefen wajen ganin ko numfashi batayi yasa ya matse cikinta da sauri ta fara tari ruwa na fitowa ta bakinta saida duk ruwan ya fice sannan ta sauke ajiyar zuciya idanunta sun rune sunyi jajur dasu tsaki ya yi sannan ya miƙe ya ɗauki wayarsa yana kallonta ya ce"tashi" shiru tayi masa tana kallonsa dan batajin zata iya tashi, ganin tana son ɓata masa lokaci yasa ya sunkuya ya ɗauketa kamar Baby suka fice daga wajen kai tsaye kuma motarsa ya nufa da ita. Wani irin sanyi ne ya shiga ratsa duk wata ƙofa ta jikinta sai rawar sanyi take hakan yasa ya kashe AC motar amma dukda haka bata daina ba, wani shahararren gudu ya shiga yi cikin ƴan mintuna suka ƙaraso gida. Suna shiga ya kamo hannunta ya fito da ita taka ƙafarta tayi wanda yasa ta fashe da wani irin kuka da sauri ya kalleta sai kuma ya ce"mene?" cikin kuka ta ce"wayyo ƙafata zai cire wayyo Allah nashiga uku Papi ka taimakeni" ganin yanda take kuka da gaske yasa ya sunkuya ya ɗauketa, suna zuwa ya kwantar da ita kan gadon yana kallon fuskarta ya ce"next time idan kika sake irin wannan shashancin saina zaneki" yana gama faɗin haka ya juya ya fice daga ɗakin, tura bakinta tayi sannan ta miƙe zaune ganin duk kayan jikinta a jiƙe suke gashi sun kama mata jiki, dakyar ta iya miƙewa ta shiga toilet tana hawaye saboda zafin da ƙafar ke mata. "Zaki mene haka ka aikata?, inata jiranka ka kawomin yarinya amma naji shiru kasan halin daka sanya ni?, akanme zaki yi haka?, raina ya ɓaci sosai zuwa da safe lallai ka tabbata ka kawomin yarinyar nan or else..." Kallon screen ɗin wayar ya yi sai kuma ya ajiye yana taɓe baki ya gyara kwanciyarsa nan da nan bacci ya ɗaukeshi. Wajejen 2am ta farka saboda tsananin ciwon da jikinta ke mata ga ƙafarta kamar ana sassara mata ita haka takeji ganin bazata iya cigaba da zama ba yasa ta miƙe zaune tana sakin wani sabon kuka babu wanda zai taimaketa dan ko tafiya bazata iya yi ba ganin ciwon na neman hallakata yasa ta sauka daga gadon ta shiga rarrafe kamar Baby haka har ta fito daga ɗakin kai tsaye kuma ɗakin Zaki ta shiga kwance ta sameshi yana baccinsa batayi wani tunani ba ta hau kan gadon cikin son samun ceto ta kwanta gefensa a hankali kuma ta shige jikinsa tana sakin wani irin numfashi. Above 5mins sai kuma wani wahalallen bacci ya ɗauketa tana sake rufe fuskarta cikin naked chest ɗinsa, duk abinda take Zaki na jinta dan tun sanda ta shigo ɗakin ya farka jin yanda jikinta ya ɗauki zafi yasa ya rabu da ita a hankali kuma zafin jikin nata ya dinga shiga nasa jikin lumshe idanunsa ya yi dan shima ba daɗin jikin nasa yake ji ba haka har bacci ya sake ɗaukeshi. *FCT, ABUJA* Sanye take cikin shigar atamfa Holland maroon colour ta ɗora veil fari akai dukda ba wani babba bane amma tayi kyau sosai, kallonta Najeeb ya yi ganin yanda ta haɗe rai ya ce"Ma'eesha" batareda ta kalleshi ba ta ce"na'am" "naga kamar baki saurarena" kallonsa tayi da manyan idanunta sai kuma ta tura baki ta ce"ai naga kunnene ki ji kuma ina jinka" numfasawa ya yi ya ce"shikenan na baki lokaci kije kiyi tunani da kanki ina fatan za ki yanke shawara mai kyau" kallonsa tayi har zata yi magana sai kuma tayi shiru ta juya tabar wajen kawai, girgiza kansa ya yi idan ba soyayya ba ai ya shige ajin yarinya ta dinga wulakanta shi. Kallonta Fateemah tayi ganin yanda take ta haɗe rai ta ce"wai daman Ma'eesha mene haka?, bakison mutumin nan fine amma haɗe ran na mene ne?" kwafa ta yi ta ce"wlh idan har bai yi a hankali ba sai na yi masa rashin mutunci nifa banason irin haka ya fara takuramin wlh" murmushi Zeey ta yi ta ce"nima dai abinda nagani kenan, ni wlh ban taɓa tunanin ma zai yarda ki dinga yi masa irin wannan wulaƙancin ba mutum mai hankali da aji" a hasale Ma'eesha ta ce"to ni na kawo shi ai shi ya kawo kansa inda za'a wulaƙanta shi wlh idan bai yi wasa ba saina yi masa abinda har ya koma da Allah bazai manta dani ba" girgiza kai Fateemah tayi ta ce"to Allah ya wuci zuciyarki shalele" harararta tayi ta ce"ni dai ku taso muje wajen sir Ahmad na bashi assignment ɗina" okay suka ce sannan suka tashi. Zaune suke a main parlon na gidan banda ƙarar cokula babu abinda ke tashi Mommy ce ta kalli General ta ce"yallaɓai daman inason zan tambayeka idan babu damuwa" ajiye spoon ɗin hannunsa ya yi ya ce"uhnn inaji" numfasawa tayi sai kuma ta ce"idan babu damuwa inason zanje gida zuwa gobe" yana riƙeda glass cup ya ce"ohk Allah ya kaimu" murmushi tayi ta ce"daman idan babu damuwa inason zan tafi da Ma'eesha" kallonta ya yi for some minutes sai kuma ya girgiza kai ya ce"tana zuwa makaranta saboda haka bazatayi fashin skull ba saidai idan anyi hutu" Okay ta ce amma har cikin ranta bataji daɗi ba, tura baki Ma'eesha tayi tana jin haushin General daya ce ba zata jeba dan ita tanason zuwa wani waje kodan tayi yawo. Mikewa ya yi bayan ya goge bakinsa da tissue ya ce"zanje Villa" okay sukace ya kalli Ma'eesha wacce take kallonsa ya ce"Shalele zo ki rakani" da sauri ta miƙe tana murmushi ta ce"yawwa muje Father" girgiza kai Mami ta yi ta ce"ƙafar yawo shige ki ɗauko veil to". Buga ƙafarta tayi tana ƙunƙuni ta haye sama da gudu dan kada General ya tafi ya barta, murmushi ya yi kawai tun daga sama take cewa"Father baka tafi baaa" dariya suka yi duka har ta sakko tana haki kama hannunta ya yi ya ce"ki daina gudu kar wani abun ya sameki dear" gyaɗa masa kai tayi sannan sukai waje Mommy ta ce"au ko sallama ba zakiyi mana ba?" ɗaga musu hannu tayi tana dariya, miƙewa Mami ta yi ta ce"Allah ya shiryaki Ma'eesha" Mommy ta ce"Ameen". *FAROOQ POV* Murmushi Abeed ya yi ya ce"kai baba kanada sanyawa kanka damuwa wlh, wai me kake nema da har zaka bari ranka ya dinga ɓaci nifa idan ni ne kai wannan yarinyar tasa zan shiga na fita na aura sai nayi amfani da ita wajen kwato abinda yake hannunsa karka manta yana mutuwar sonta sai ka dinga tilastata tana karɓar kuɗaɗe a hannunsa haka har ka ja naka kasan" furzar da wani irin numfashi ya yi yana ajiye drink ɗin hannunsa ya ce"kai daɗina dake rashin tunani, idan da zan iya auren yarinyar ai da tuni nayi hakan bama sai kaji ba, ni yanzu kawai neman hanyar da zan kawar da yarinyar nake idan nayi hakan nayi rabin aikin" dariyar mugunta Abeed ya yi ya ce"to saika ɗaura ɗamara dan ni ba ɗan kowa ba bazan shiga ba haka kawai ta kwaɓe azo a kamani ubanwa zai fito dani, kaima kuma zan baka shawara kayi komai a sannu kasan dai ubanka mahaifi ba kowa bane idan ka jawo abinda soja zai ɗaureka kaga kayi ba wan ba ƙanin" miƙewa Farooq ya yi yana buga table ɗin gabansa ya ce"kai a wa ka faɗamin magana wlh har abada nafi ƙarfin a kulleni dan ko a yanzu inada abinda zai isheni rayuwata saboda haka maintain ur words!" ya ƙarashe maganar yana nuna shi da yatsa, tashi Abeed ya yi shima yana murmushi ya ce"Farooq kenan idan har da kanada abinda zai isheka kayi rayuwarka so why kake neman dukiyar wasu?, kayi rayuwarka da abinda ubangiji ya raba ya baka mana kadaina hangen dukiyar wasu ka zauna matsayinka na agola wanda aka kula da rayuwarsa kamar ɗan gida, saboda girman Allah wlh sai kayi mamakin yanda zakaci gaba a rayuwarka" tsaki Farooq ya yi sannan ya ɗauke wayarsa da car key ɗinsa yabar wajen girgiza kai Abeed ya yi sannan shima ya ɗauki mukullinsa ya yi waje. *Asokoro Villa* Sake riƙe hannun General tayi ganin wasu mahaukan jami'an tsaro dukda ta saba ganin na gidansu amma waɗannan sunfi nasu yawa, har suka shiga main parlon na gidan Ma'eesha bata saki General ba sai kwaɓe fuska takeyi saida shugaban ƙasa Muhammad Sani Tanka ya fito sannan suka zauna bayan sun gaisa ya kalli Ma'eesha ya ce"ƴar Baba kin girma ko?" kasancewar General abokinsa ne tun suna yara yasa sunsan juna sosai murmushi ya yi ya ce"daman jiya Khaleel ya dawo kije yana second parlon ɗin nan" to kawai ta ce sannan ta miƙe tana tafiya a hankali har ta buɗe ƙofar parlon. Haɗaɗɗen parlon ne wanda aka kashe iyayen kuɗi wajen haɗashi ƙamshin turaren Parfums De marley Layton ne ya daki hancinta ta lumshe idanunta kafin tayi sallama, zaune yake ya harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya black beauty ne yanada cute round face da siririn hanci sai beard ɗinsa mai kyau kana kallon fatarsa kasan kuɗi ya zauna. Ƙasa ƙasa ya amsa sallamar tata kafin ta zauna kujerar dake gefensa waro idanunsa ya yi ya kalleta sai kuma ya ce"eesha" murmushi ta yi ta ce"ya Khaleel ina yini?" girgiza kansa ya yi ya dawo gefenta ya ce"ashe dai ban manta ki ba, ykk yasu Mami?" tana wasada fingers ɗinta ta ce"suna nan klao, ashe ka dawo" ya ce"Eh nadawo jiya shekaru sun tafi eesha kin girma abinki" rufe fuskarta tayi da hannu tana murmushi ta ce a shagwaɓe"kai yaya ai kaima ka ƙara girma sosai ji beka fa kafi ya Farooq" haɗe ransa ya yi ya ce"har yanzu wannan guy ɗin na gidanku?" sunkuyar da kanta tana gyada masa kai dan tasan ko kaɗan basa shiri da Farooq, ɗaga kafaɗarsa ya yi ya ce"amma mene yake har yanzu a gidan i think ya isa ace ya yi aure ya bar gidan" ɗaga kafaɗarta ta yi alamar bata sani ba ya ce"then yana shiga harkarki" ji tayi gabanta ya yanke ya faɗi ta yi shiru bata bashi amsa ba, hannunsa ya sanya ya ɗago fuskarta kallonsa tayi taga fuskarsa babu alamar wasa hakan yasa ta fashe da kuka tana faɗawa jikinsa. Wata nannauyar ajiyar zuciya Khaleel ya sauke yana riƙe da ita above 3mins kafin ya ɗagota yana kallonta ya ce"baki amsa min tambayata ba eesha" tura baki tayi gaba ta ce" to ai naga a gidanmu yake kuma..." kallon da taga ya yi mata ne yasa tayi shiru bata ƙara sa abinda zata faɗa ba shiru ya yi na wasu seconds tuni idanunsa suka sauya kala wani ruwa ya kwanta a kansu lura da hakan yasa tayi sauri miƙewa tsaye cikin sigar rarrashi ta tsuguna a gabansa tana haɗe hannayenta biyu ta ce"dan Allah yaya Khaleel kayi haƙuri bazan sake ba wlh dan Allah" ta faɗa tana shashshekar kuka miƙewa tsaye ya yi bai ce komai ba ya kama hannunta hakan yasa ta miƙe itama tabi bayansa har suka shiga wani ƙaton parlon. Parlon ne babba nan ma ya sake buɗe wata ƙofar inda suka shiga wani haɗaɗɗen waje kamar stadium ko'ina anyi zane duk bangon ɗakin an yi kaca-kaca dashi hannunta ya ja har gaban wani bango wanda duk akayi zane iri-iri a jikinsa wani ansa Ma'eesha, wani eesha, wani kuma Khalil wani kuma Tanka wasu kuma heart aka zana a ciki an saka *Khaeesh* batasan sanda ta rungumeshi ba tana kuka kamar ranta zai fita hannayensa ya sanya ya zagayeta ajikinsa yana jin yanda duk ta jiƙa masa ƙirji da hawaye saida tayi kuka mai isarta sannan ta ɗago ta kalleshi cikin kuka ta ce"ya Khaleel meyasa kaci amanata?, ya Khaleel meyasa kayi aure ka barni?, ka manta sanda kake cewa ni zaka aura Father zai bar maka ni shine kaje kayi aurenka a wata ƙasar ya Khaleel baka sona ni kaɗai nake sonka kuma nima yanzu nadaina sonka bana son..." da sauri Khaleel ya haɗe bakinsa da nata yana bawa lips ɗinta wata amintacciyar tsotsa yayinda hawaye suka shiga gangarowa kan kuncinsa shima sun ɗauki lokaci mai tsayi a haka jikin Ma'eesha ban rawa babu abinda yake a hankali ya zare bakinsa daga nata yana kallon kyakkyawar fuskanta wacce tayi face-face da hawaye ya ce" # *Khaleel* # *eesha* # *Zaki* # *Muhaira* # *love* # *SQUAD 2024* # *Nanameera ce!✍️* [8/8, 11:33 AM] Nanameera😍✌🏻: *BA ITA BA CE!..💖💖* *NANAMEERA* *MIKIYA WRITERS ASSO...* ```Page 10```. # *The war* "I'm sorry eesha amma ya kamata ace kin tsaya kin fahimci abinda zan faɗa miki wlh isn't my fault banida zaɓi na auri Ramlah ne saboda babu yanda zanyi ni ne nake kula da ita nd kuma yanayin lalurarta dole idan ta ce tanason abu ayi mata shi idan ba haka ba za'a ga ba daidai ba wannan shine dalilin kawai" girgiza kai tayi tana raba jikinta da nasa ta ce"A'a yaya Khalil kaima kana sonta yasa ka aureta idan ba haka ba bazaka mance alƙawarinmu cikin sauƙi ba, karka damu nima yanzu inada wanda nakeso kuma nake shirin aure saboda haka..." hannayensa ya sanya yana rufe mata baki cikin zafin rai ya ce"wlh baki isaba eesha ke tawace ni kaɗai kuma babu wanda ya isa ya aureki ina raye kuma na barshi nasan kin gane abinda nake nufi"ture hannunsa ta yi tana harararsa ta ce"da kenan amma yanzu na shige wannan level ɗin kuma har abada zan cigaba da kallonka matsayin marayaudari wanda yaci amanata" ta ƙarashe maganar tana rufe bakinta saboda wani kuka daya zo mata da gudu ta fice daga ɗakin. Jingina ya yi da wall ɗin ɗakin yana dafe kansa gabaɗaya ya ji duniyar tayi masa zafi furzar da wani irin zazzafan numfashi ya yi sannan ya juya ya fita. Zaune ya tadda ta kan royal cusion ɗin parlon sai kuka take kamar ranta zai fita, hannayensa zube cikin wandonsa ya ƙaraso gabanta sannan ya tsuguna ɗago fuskarta ya yi cikin sanyin murya ya ce"eeshana" kallonsa tayi da idanunta da suka sauya kala zuwa jaa bata ce komai ta cigaba da kukanta cikin son ya rarrasheta ya ce"now tell me kina sona?" da sauri ta ɗago ta kalleshi sai kuma ta janye hannunsa daga kan fuskarta ta miƙe tana kallonsa ta ce"a baya dai na soka yaya Khalil naji kamar bazan iya rayuwa idan babu kai ba nayi mararin kasancewa matarka kamar yanda ka kwaɗaitamin" numfasawa ta yi sannan ta cigaba da faɗin"amma yanzu na haƙura dakai na barka kayi rayuwa mai daɗi da matar daka aura nima ina fatan nasamu wanda zai soni sona har ƙarshen rayuwa"ta ƙarashe maganar tana goge hawayen kan fuskarta, miƙewa tsaye ya yi yana kallonta zuciyarsa fal tausayinta ya ce"Ma'eesha nasan nayi kuskure amma dan Allah karki ɗauki haka matsayin makamin da zaki cutar da rayuwata har yau har gobe ina sonki kuma inada burin aurenki ƙaddara ce ta rabamu amma nayi miki alƙawarin wannan karan bazan bari ta rabamu ba" "Aikuwa kayi kaɗan kuma kayi ƙarya domin ƙaddara ta rigada ta gifta tsakaninku babu kai babu ita har abada matuƙar ina numfashi wlh Khalil bazan bari ka zauna da ita ba ko a baya ina faɗa maka balle kuma yanzu da ka rigada kayi aure" hankali tashe yake kallon Mommy bashi kaɗai ba hadda Ma'eesha wacce tazama kamar statue a wajen kenan har i Wannan lokacin Mommy bata daina tsanarta ba?, har yanzu tana nan akan bakanta na son ganin bayanta?, a baya ta saba da cin zarafin Mommy a gareta tun bata san tsanarta Mommy tayi ba har tayi girman da ta fahimci komai amma tsananin so da ƙaunar da takewa Khalil ya sanya bata iya fushi koda yaushe tana hanyar zuwa inda suke. Bakinsa na rawa ya ƙarasa wajen Mommy yana kallonta ya ce"haba Mommy i think ai mun shige wannan level ɗin mene haka please?, mene ne aibunta da kika tsaneta har haka?, ya kamata ace ko dan saboda ni ki daina yi mata irin waɗannan abubuwan yanzu fa ba da bace Ma'eesha ta girma tasan kanta zata fahimci duk abinda kike mata dan Allah Mommy stop it" juyowa ya yi da niyyar yiwa Ma'eesha magana saida ko inuwarta babu tun sanda ya bar gabanta ta fice daga parlon, dafe kansa ya yi sannan yabi bayanta. Tsaye ya sameta jikin corridor tana goge hawayen fuskarsa gudun kada General ya gani, rungumeta ya yi ta baya hakan yasa ta sake fashewa da wani sabon kukan na takaici jan hannunta ya yi bai ce mata komai ba ya buɗe wata ƙofa suka shiga kai tsaye kuma waje suka fito motarsa ya buɗe ya zurata ciki sannan shima ya shiga ya yi mata key suka bar gidan, kwafa Mommy tayi tana sakin curtains ɗin ta ce"dani kake zancen wlh" ta shige bedroom ta ɗauki wayarta ringing ɗaya matar ta ɗauka Mommy ta ce"kina ina Hajiya?" daga ɗaya ɓangaren ta ce"kin ganni nan ina gida lafiya?" girgiza kai Mommy ta yi ta ce"gobe ki zo zaki rakani unguwa" okay kawai ta ce sannan ta kashe wayar ta shiga safa da marwa cikin ɗakin sai kuma ta fita. Tura ƙofar tayi ta shiga wani haɗaɗɗen bedroom ɗin ya yi kyau sosai zaune ta hangeta tana danna wayarta hankali kwance tsaki Mommy ta yi sannan ta ƙara sa gabanta tana fincike wayar ɗago kanta tayi tana turo baki sai a sannan na kalleta fara ce tasa amma ba wata kyakkyawa ba kana ganinta kasan idanunta a buɗe suke tasan duniya zama Mommy tayi gefenta ta ce"shashasha kina nan kina danna waya bakisan halin da ake ciki ba" turo baki tayi ta ce"to dan Allah Mommy me zanyi ai bansan meya faru ba kuma kinzo kina min faɗa" girgiza kai Mommy tayi ta ce"to idanma zaki daina wannan shashancin ki daina idan kuma ba haka ba nan da ƴan kwanaki kiji ance mijinki ya ƙara aure" da sauri ta miƙe zaune tana kallon Mommy da manyan idanunta ta ce"Mommy kamarya mijina?, mene ya samu mijin nawa aure kamarya?" ajiyar zuciya Mommy ta sauke ta ce"kamar yanda kika ji na faɗa miki dan Khalil na gab da ƙara aure" miƙewa tayi tsaye tuni attachment ɗin kanta ya wargaje ciki tashin hankali take cewa"dan Allah Mommy ki daina yimin irin wannan wasan haba, ina Khalil ɗin yake?" kama hannunta Mommy ta yi ta zaunar sannan ta ce"bari kiji na faɗa miki kinsan yarinyar da yake so da can baya har na sanya yabar ƙasar saboda kada ya aureta to yanzu daya dawo tazo gidan nan ɗazu da babanta kuma Khalil ya nuna har yanzu yana sonta kuma yanda ya nuna ma nan gaba kaɗan zai aureta" ɗora hannunta tayi a ka cikin tashin hankali take cewa"nashiga uku Mommy wayyo Allahna dan Allah ki hanashi wlh bazan iya zama da kishiya ba" tsaki Mommy tayi ta ce"ke amma anyi shashashar yarinya Macen kikewa kuka?, kishiyar da ba'a yi miki ba?, to ni bazan lamunci kiyi kishi da wata ba bare kuma Ma'eesha dana tsaneta tun tana ƙarama kibar komai a hannuna daga wajenki kawai inason ki tubure ki nuna ke ciwonki ya tashi karki kuskura ki bari ya gane ba ciwon gaske bane ya tashi nikuma duk sauran zanyi" jikinta na rawa ta miƙe tsaye zata yi waje Mommy ta ce"gidan ubanwa zaki?" "Mommy zanje na kwanta ne kafin ya dawo" murmushi Mommy tayi sannan itama ta miƙe ta fice. *Riyadh* *Al Olaya residence* Yana gama breakfast ɗin ya fito cikin cikin wata jallabiya ash colour gashinsa ya sakeshi ya kwanta kan bayansa kallonta ya yi ganin yanda take hawaye har sannan, girgiza kai Zaki ya yi sannan ya ƙaraso gabanta yana kallonta ya ce"tashi tsaye" girgiza masa kai ta yi tana yarfe hannu ya ce"bazaki tashi ba?" kamar zatayi kuka ta ce"ni to bazan iya tashin ba ƙafana yana zafi sosai" dan ƙaramin tsaki ya yi sannan ya sanya hannunsa ya ɗauketa ya fice daga parlon. Kallonsa Muhaira tayi sai kuma ta kalli doctorn kawai ta fashe da kuka haɗe ransa ya yi ya ce"zakiyi min shiru ko saina bige bakin?" ko saurarensa bata yiba ta cigaba da kukanta tana ganin likitan ya gama haɗa allurar ta miƙe da gudu tana rungume Zaki tana sakin wani irin kuka gaba ɗaya sun rigada sun gama gano abinda ya sanyata kukan hakan yasa Zaki ya ce"kidaina wannan abun ki fito ko ranki ya ɓaci" sake zagaye hannayenta tayi a jikinsa ta ce"dan Allah kar ayimin allura wlh naji sauƙi babu zafi yanzu" cikin son shawo kan rigimarta ya ce"babu zafi?" gyaɗa masa kai tayi ya ce"to zo naga" da sauri ta dawo gabanshi ya sanya hannunsa ya jawota jikinsa ya rungume ya ce"to faɗamin mene yake damunki da?" cikin sanyin murya ta ce"ƙafata ce tana ciwo sai kuma kaina, gashi ƙirjina yana min zafi sosai kuma..."maganar ta tsaya sakamakon allurar da taji an tsaka mata da sauri ta sake shigewa jikinsa tana sakar masa cizo murmushi kawai ya yi sannan ya ajiye sringe ɗin yana shafa bayanta ya ce"shhhh ki daina kukan ya isa haka" kamar yana sake tura ta haka ta cigaba da yi masa kuka ya ce"Shikenan kiyi shiru zan siya maki chocolate da ice-cream" cikin shashshekar kuka ta ce"ni a'a banso ka maidani gurin Baba banason nan Papi" shafa kanta ya yi bai ce komai ba yana ji har ta fara sauke numfashi a jikinsa alamar bacci ya ɗauketa. Cikin nutsuwa likitan yake masa bayani ya ce"Sir yarinyar nan tana ɗauke da cutar Asthma sannan kuma reason ɗin dake sawa ta dinga ciwon ƙafa jininta AS ne babbar matsalar kuma ita ce tanada ciwon zuciya wanda yake gab da kaiwa matakin ƙarshe" da sauri Zaki ya kalleshi sai kuma ya kalli Muhaira wacce take rungume ƙirjinsa Allah mai iko wannan ƴar ƙaramar yarinyar da ciwon zuciya abun akwai tausayi sai a sannan maganganun aljanun jikinta suka dawo kansa kenan idan da gaske suke ita ɗin batada kowa kenan?, amma kuma ai a wajen ɗan uwanta ya siyeta something fishy!. Maganar likitan ce ta dawo dashi daga tunanin daya tafi ya ce"Sir akwai buƙatar a dinga kulawa da ita da abinda zata ci da wanda zata sha sannan kuma kada a dinga yawan ɓata mata rai dan hakan zai iya haifar da matsala" duk wannan maganar da ya faɗeta ne da harshen labarci, gyaɗa kai Zaki ya yi sannan sukayi sallama ya fito daga asibitin kai tsaye kuma gida ya nufa da ita. *FCT, ABUJA* Hannunsa riƙe cikin na Ma'eesha ya ce"idan Allah ya kaimu gobe zan zo dan Allah eesha ki cire komai daga ranki karki bari wani abun ya samu lafiyarki" gyaɗa masa kai kawai tayi sannan ta sauka daga motar ta shige gida, saida ya daina hangota sannan ya juya ya bar gidan zuciyarsa har sannan cike take da ɓacin rai koda wasa bai taɓa zaton abun zai zama haka ba da bazai taɓa barin Ma'eesha ba a wancen lokacin. Kallonta Farooq ya yi har ta ƙaraso gabansa tana shirin shige shi ya ce"Ma'eesha!" yanda ya faɗi sunan nata ne tagane something not good hakan yasa ta dawo ta tsaya amma bata ce komai ba, miƙewa tsaye ya yi yana kallonta ya ce"uban wane ya kawoki gida?" shiru Ma'eesha tayi masa dan idan ranta yana ɓace to bata iya magana, sosai shirun nata ya tunzura Farooq hakan yasa cikin ɓacin rai ya ce"kee dan ubanki ni nake miki magana kina jina?" wani kallo tayi masa sai kuma ta haye sama da sauri batareda ta bashi amsa ba, kwafa Farooq ya yi ya tsaya for some minutes sai kuma ya bi bayanta. Kwance ya tarar da ita sai rusa kuka take kamar wacce aka cewa Mami ko General ya mutu, cikin ɓacin rai Farooq ya ce" bari na sanar dake wani abu duk ranar dana sake ganinki da wannan guy ɗin wlh sai na lahira ya fiki jin daɗi sai na ɓata miki rai fiyeda tunaninki ki dinga kula ɗan iska yaro saboda kinason jawo mana abun magana" a fusace ta mike tana kallonsa cikeda tsiwa take cewa" wlh saina kulashi babu ruwanka da wanda zan kula da kuma wanda bazan kula ba abinda nakeso shine wanda zan yi ba wanda kai ka zaɓamin ba tunda kai ba ubana bane nayi maka biyayya a baya wacce hakan ta jefani cikin wani hali har yanzu kuma ban fita daga cikinsa ba saboda haka wannan karon bazan ji maganarka ba indai akan Khalil ne" ta shige toilet tana buga ƙofar da ƙarfi. Kwafa ya yi sannan ya juya shima ya fita daga dakin yana buga ƙofar, jingina tayi da kofar banɗakin ta fashe da wani sabon kukan inama bata bi Father ba, inama tayi zamanta a gida wataƙila bataga abinda zai tayar mata da hankali ba inama ace mafarki take wanda zata farka yanzu nan, ganin lokaci na tafiya yasa ta ɗauro alwala ta fito tayi sallah sannan ta kwanta kan gado ko zata samu sauƙin abinda takejin yana yi mata yawo cikin ranta. *Al Olaya residence* Da mamaki Zaki yake kallon tarin motocin da suka yi parking harabar gidan taɓe bakinsa ya yi sai kuma ya ɗauko Muhaira wacce har sannan take bacci ya shiga takawa da ita cikeda isa. Turus ya yi sanda ya shiga parlon saboda idanu biyu da sukayi da Dmash wanda yake zaune kan kujera shida tawagarsa a gefe, yana ganin ya shigo ya miƙe tsaye kana ganin fuskarsa kasan ransa a ɓace yake yana zuwa bai yi wata wata ba ya sauke masa lafiyayyen mari a fuska ji kake tassssss, runtse idanuwansa ya yi lokaci ɗaya jijiyoyin kansa suka tashi above 2mins kafin ya buɗe idanunsa yana kallon Dmash wanda yake tsaye gabansa da sauri Muhaira wacce ƙarar marin ya tasa ta fashe da kuka tana rungumeshi ta ce"Papinaaaa" gam Zaki ya riƙeta a jikinsa yana kallon Dmash ya ce". *Dommmmmmmmmmm😂*. # *Unconditional love* # *Trafficking* # *Incident* # *Destiny* # *SQUAD 2024* # *Nanameera ce!✍️*.[8/8, 8:11 PM] Nanameera😍✌🏻: *BA ITA BA CE!..💖💖* *Nanameera*. *MIKIYA WRITERS ASSO...* ```Page 11``` # *The incident* Da sauri Taj ya girgiza masa kai yana yi masa nuni da kar ya ce komai, furzar da wani zazzafan numfashi ya yi kana ya ɗauke kansa, ganin kamar bashi a mara ba yasa Dmash ya ce"kai har kanajin ka isa da kake aikata abinda kayi niyya?, wane kai ɗin?, har ni zaka dinga rainawa hankali ina yi maka magana ka kawo min yarinya amma ka mayar dani ɗan iska yaro wato kawota ne bazaka yiba ko me?" da sauri Muhaira ta sake shigewa jikin Zaki tana rufe fuskarta a ƙirjinsa dan ba ƙaramin tsorata tayi da Dmash ba. Ganin har sannan bai ce komai ba kuma bashida niyyar yin magana yasa Dmash ya sanya hannunsa yana ƙoƙarin fizge Muhaira daga hannunsa, girgiza kai Zaki ya yi sannan ya janye yarinya yana mayar da ita bayansa cikin wata iriyar murya ya ce"Sir ya kamata ka tsaya iya matsayarka kasan irin abinda zaka dinga yimin or else..." ya ƙarashe maganar yana taune lips ɗinsa baki buɗe Dmash ke kallonsa dan koda wasa bai taɓa jin Zaki ya yi masa makaman iyar wannan maganar ba yana bin duk maganar daya faɗa masa da muhimmanci amma yau daga ganin yanda yake ɗaga muryarsa zaka gane ba lafiya yake ba, Taj ne ya ƙaraso yana kallon Dmash ya ce"Sir please sorry maybe akwai abinda ke damunsa dan Allah ka koma zan tawo maka da yarinyar" "Stop joking Taj billahil Azeem bazan bada yarinyar nan ba sbd haka ma kasan abinda zaka yi masa alƙawari amma banda ita mark my words" juyawa ya yi ya haye sama cikin zafin nama Muhaira na biye dashi. Kwafa Dmash ya yi sannan ya ce"ka gargaɗi abokinka idan ba haka ba zan yi masa abinda bai taɓa tsammani ba, ba'a faɗa dani a samu nasara" ya juya ya fice daga parlon sauran suka mara masa baya, girgiza kai Taj ya yi sannan ya haye saman yana kiran sunan Zakin. Zaune ya sameshi kan kujera ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya sai huci yake kamar wani mayunwacin Zakin, zama Taj ya yi jikin hannun kujera yana dafashi ya ce"please Zaki kayi haƙuri da abinda ya yi maka sannan kuma ka ɗauki yarinyar nan ka bashi kodan lafiyarka kada wannan mutumin wanda ka tabbatar da babu Allah a ransa ya cutar dakai dan Allah" cikin ɓacin rai ya janye hannunsa daga kafaɗarsa ya ce"dalla can cikani wlh kome zai yi saidai y yi amma bai isa na bashi yarinyar ba zan ɗauki kowace kasada akan rayuwarta saboda haka leave me alone" da mamaki Taj yake kallonsa dan yasan halin Zaki da kafiya amma bai ɗauka zai kafe akan yarinyar ba ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce"to faɗa min meyasa bazaka bada ita ba?" miƙewa tsaye ya yi yana kallonsa ya ce"saboda haka nayi niyya" ya juya ya bar wajen "Kana sonta ne?" Taj ya faɗa yana kallonsa, tsayawa ya yi cak ya saki handle ɗin ƙofar sannan ya dawo yana kallonsa ya ce"wa ni?, God forbid! bazan bada ita bane saboda yarinyar ta bani tausayi tabbas akwai wani abu cikin rayuwarta wanda ba daidai ba tanada buƙatar mentor wanda zai dinga kulawa da ita sbd haka nayi alƙawarin kulawa da rayuwarta muddun ina numfashi kamar yanda ta iya kirana da sunan mahaifinta zan tabbatar mata da wannan muradin nata bayan wannan babu wata alaƙa dake tsakanina da ita sbd haka kasan me zaka dinga cemin" yana gama faɗin haka ya juya ya shige bedroom ɗin yana buga ƙofar da ƙarfi. Miƙewa Taj ya ya sai kuma ya girgiza kansa ya ce"jarababbe kawai". *Next day* Da sassafe ta tashi bayan tayi sallar asuba ta zauna tana karatun Alkur'ani mai girma wajejen 6:30am ya shigo gidan daga masjid haka kawai yaji yana son ya ganta, shiga ɗakin ya yi bakinsa ɗauke da sallama ga mamakinsa sai yaga wayam babu kowa waro idanunsa ya yi yana sake kallon ɗakin ko ina ta shiga?, fitowa ya yi yana ƙoƙarin shiga bedroom ɗinsa ya juyo ƙamshi na tashi hakan yasa ya tafi zuwa direction ɗin da yake jiyo ƙamshin, turus ya tsaya ƙofar kitchen ɗin yana mamakin wanda yake girki a ciki bai sake mamaki ba saida ya shiga ciki ya ganta ta taƙarƙare tana ta faman aiki ƙarasawa ya yi inda take tsaye ya zuba mata idanu yana kallonta, cikeda ladabi ta sunkuya ta ce"ina kwana Papi?" bai amsa mata ba kawai ya gyaɗa mata kai sanye yake cikin wata embroidery Jallabiya Black colour ya ɗora hula akansa hannunsa riƙe da cazbaha yana ja. Yana kallonta ta ɗauki kwai tafasa sannan ta sanya masa species ɗin data gani a wajen takunna wuta tana shirin kunna gas ya kalleta ya ce"be careful" da sauri ta juyo tana kallonsa sai kuma ta ce"please Papi ka kunna min zafi inaji" ɗauke kansa ya yi sai kuma ya ƙaraso wajen, dakyar ta daidaita numfashinta saboda wani irin ƙamshi daya taki hancinta a hankali ta lumshe idanunta. Tsayawa ya yi a bayanta ya zuro hannayensa ta tsakanin hammatarta sannan ya karɓi letar ya kunna mata sannan ya ɗora pan ɗin akai ya matsa yana kallonta tagama komai kuma yaƙi fitane saboda kada wani abun ya sameta saida ta zuba a plate sannan ya fice daga kitchen ɗin ya shige ɗakinsa. Bai fito ba sai wajen ƙarfe 11am yana sanye cikin wasu English wears wata deep V-neck t-shirt sai kuma Cargon Three-quater gashin nan nasa yasha gyara gwanin sha'awa kwance ya ganta kan kujera one seater ta dunƙule jikinta waje ɗaya girgiza kansa ya yi sannan ya ƙarasa inda take yana zuwa ya ja ƙafarta a razane ta buɗe idanunta tana kallonsa sai kuma ta tura baki tana cewa"to ba na ajiye maka naka ba ai ban cinye ba kuma" taɓe baki ya yi dan baima fahimci akan abinda take maganar ba ya juya yabar wajen kai tsaye fridge ya nufa yana zuwa ya ɗauko dabino pack ɗaya sai yogurt roba ɗaya ya dawo ya zauna. Da kallo ta bisa sai kuma ta haɗe rai ta miƙe tana tafiya a nutse ta koma kitchen ɗin, kallon plate ɗin data ajiye masa ya yi sai kuma ya kalleta ta ce"ai na ajiye maka naka" abincin ya nuna sai kuma ya nuna kansa ta gyaɗa masa kai ya galla mata harara ya ce"ni ne zanci abincin ki ƙazama dake" turo baki tayi gaba tuna kwalla ta taru a idanunta ta ce"to meyasa bazaka ciba?, Bani kura yana cin abincina idan na dafa" taɓe baki ya yi yana kai dabinonsa baki lumshe idanunsa ya yi saboda zaƙin zumar daya dakeshi saida ya cinye sannan ya kalleta ya ce"saboda ke ƙazama ce Mumu witch that's why bazan ci abin hannunki ba" fashewa tayi da kuka ta kwanta tana birgima akan lallausan carpet ɗin wajen girgiza kansa ya yi yana murmushi ya cigaba da cin abincinsa saida ya gama sannan ya goge bakinsa da tissue. Taj ne ya yi sallama ya shigo ya amsa masa can ciki, zama ya yi yana kallonta ya ce"subhanallahi ke dawa beauty?" cikin shashasha kuka ta faɗa masa abinda ya faru, murmushi ya yi ya ce"sorry dear taso kiga abinda na kawo miki" tashi tayi tana goge hawayen fuskarta ta zauna a ƙasan ƙafarsa ya miƙa mata wata takarda. Karɓa tayi ta kalla sai kuma ta miƙa masa yana murmushi ya ce"kinsan ta mene?" girgiza kanta tayi ya ce"admission later ɗinki ce gobe zaki fara zuwa makaranta" miƙewa tayi tsaye cikeda murna tahau tsalle a parlon kamar wata ƙaramar yarinya saida tayi mai isarta sannan ta juyo tana kallonsu hararar da taga Zaki ya watsa mata ya sanya ta shiga taita yinta ta sunkuyar da kanta tana murmushi. Dawowa tayi ta zauna cikin sanyin murya ta ce"Nagode sosai" murmushi ya yi ya ce"bani zaki godewa ba Zaki ne yasa a kaiki" da sauri ta kalleshi taga ba ita yake kallo ba hakan yasa ta miƙe ta ƙarasa inda yake a tsugune ta zauna a cinyarsa ware idanunsa ya yi yana kallonta da alama tafara sabawa da zama a cikinsa cikin sanyin murya ta ce"Allah ya ƙara maka arziƙi ya baka abinda kake nema Nagode sosai" wani kyakkyawan murmushi ne ya suɓuce masa ya shafa kanta yana gyaɗa mata kai cikeda da murna ta shige bedroom ɗinta tana rawa kamar wata Baby. Murmushi Taj ya yi yana kallonta ya ce" gaskiya yarinyar nan zero tension ce ji yadda take murna dan zata fara zuwa makaranta" girgiza kai Zaki ya yi bai ce komai ba ya miƙe yana karɓar takardar ya shige bedroom ɗinsa. *FCT, ABUJA* "Ma'eesha!! Ma'eesha!! Ma'eesha!" a firgice ta buɗe idanunta tana kallon Mami sai kuma ta tashi zaune kallonta Mami tayi ta ce"mene y sanya ki bacci haka? har wajen 9am bakiyi sallar asuba ba?" hamma tayi ta ce"wlh Mami kaina ne yake ciwo tun jiya to banyi bacci da wuri ba shiyasa na makara sorry" girgiza kai Mami tayi ta ce"gashinan idanunki sun kumbura hala kuka kika yiwa ciwon kan?" turo baki tayi Mami ta girgiza kai ta ce"Allah ya shiryeki, maza kiyi sallah ki fito ki ci abinci sai a kira doctor yazo ya dubaki" gyaɗa mata kai tayi sannan ta tashi ta shige toilet ita kuma Mami ta yi waje. Kasancewar ranar Saturday ya sanya babu makaranta tana zaune wajejen 2:30pm Mommy ta fito, kallonta ta yi sai kuma ta ce"Mommy har za ki tafi?" gyaɗa mata kai Mommy tayi tana murmushi ta ce"General ya hana da mun tafi tare" Ma'eesha ta kwaɓe fuska ta ce"ai yau babu school kuma ba kwana zaki yiba ko?" gyaɗa mata kai ta yi ta ce"please zan biki" girgiza kai Mommy tayi ta ce"A'a tunda ya hana ki haƙura kinsan halin babanki ki bari next idan zani sai mu tafi tare" buɗe baki tayi zatayi magana Farooq ya fito yana sanye cikin wata dakakkiyar shadda black colour ya sanya hula zanna akansa sai zuba ƙamshi yake, shiru tayi da bakinta sai kuma ta miƙe ta ratsa ta jikin Mommy ta haye sama. Da mamaki Mommy take kallonta har ta haye sama sai kuma ta kalli Farooq wanda shima ya bi Ma'eeshan da kallo, taɓe baki ya yi sannan ya ce"Mommy muje" "lafiya dai meya haɗaka da ita?" bai cewa Mommy komai ba ya yi waje hakan yasa dole itama tabi bayansa. Da mamaki yake kallon wanda yake tsaye jikin motar ya harɗe hannayensa a ƙirji sanya yake cikin wata dakakkiyar shadda Madam gezner ash colour ya ɗora zanna ash akai hannunsa maƙale da rollex ya sanya Glass baƙi a fuskarsa hannayensa zube cikin aljihu da alama akwai wadda yake jira, tsayawa ya yi a wajen kamar statue can kuma yaji an buɗe ƙofsr entrance ɗin gidan Ma'eesha ce ta fito cikin wata Eigypt Abaya purple colour mai manyan flower a jiki white colour ta yi rolling fuskarta da veil ɗin Abayar hannunta riƙe da wayarta iphone 13pro max. Ta gabansu ta shige ta ƙarasa inda yake tsabar baƙin ciki yasa Farooq ya shiga binsu da kallo kamar wani dolu can kuma ya ƙarasa wajen yana tafiya kamar wani damisa. Tsaye ya gansu yana mata magana cikin ɓacin rai ya ce"kee dan ubanki zo ki shige gida" wani kallon sheƙeƙe tayi masa sai kuma ta ce" bazan shiga ba wlh kuma karka sake zagin ubana" sakar baki ya yi yana kallonta sai kuma ya kalli Khalil wanda ya nuna baima san dashi a wajen ba ya ce"kai kuma idan kanaji da tashen iskancinka kasan inda zaka dinga zuwa kana yi saboda akwai inda idan kayi ranka zai ɓaci, ka fita a harkar yarinyar nan idan ba haka ba wlh sai na saka kayi dana sani mara amfani babu ruwanka da ita kaji na faɗa maka idan kuma kaƙi jin abinda na faɗa maka ta lallami to ka sani zanyi maka Yaren dana tabbatar zaka fahimta kuma..." "Haba yaya Farooq maganganunka sun fara tsauri kasan irin abinda zaka dinga furtawa idan ba haka ba kuma wlh nima zan yi maka abinda bakayi zato ba ni ba baiwar ka bace inada ƴancin nayi abinda nakeso ko mahaifina bai takura min ba balle kuma kai ka fita a harkata" Girgiza kai Farooq ya yi ya ce"ke ai banida lokacinki yanzu amma ki bari anjima na dawo saina baki mamaki" yana faɗin hakan yabar wajen kamar zai tashi sama. Da harara ta bisa sannan tayi kwafa kallonta kawai Khalil ya yi sai kuma ya furzar da nunfashi ya ce"eesha wannan bai dace dake ba, da hankalinki ki dinga ihuu kowa yana jinki" wani kallo tayi masa tana kwace hannunta daga nasa ta ce"ni cikani!" yanda tayi maganar cikeda tsiwa ya sanya ya yi murmushi ya ce" to laifin kaina ya dawo?" harararsa ta yi ta ce a zafafe"karka sake zuwa gidanmu dan ni bazan auri ragowar wata ba kaje ka kula da matarka wlh" baisan sanda ya tuntsire da dariya ba yana girgiza kai ya ce" # *Ameenatou ce✍️* # *BA ITA BA CE!*. [8/9, 12:19 PM] Nanameera😍✌🏻: *BA ITA BA CE!..💖💖* *Nanameera*. *MIKIYA WRITERS ASSO...* ```Page 12``` # *Love* "Narasa yaushe kika koyi tsiwa eesha da dai ba halinki bane" turo baki ta yi ta ce"sanda ka yaudareni sannan nikuma na koya" girgiza kansa ya yi dan yasan rigima take nema, kusan two minutes sannan ya ce"munyi magana da Dad jiya kuma ya ce zai yiwa Father magana" zaro idanu ta yi tana dafe ƙirjinta ta ce"nashiga uku wace magana kenan?, ban fahimta ba?" murmushi ya yi ya ce"maganar aurenmu mana koda kinyi zaton wasa nake?" haɗe rai ta yi ta ce"yaya Khalil ka daina yimin irin wannan wasan wollah banaso" cikin tafiyarsa ta isa ya ƙaraso gabanta ya kama hannunta yana murzawa ya ce"eesha stop joking kinji kinsan Ina sonki nd kuma ni ne wanda Father ya yiwa alƙawari sbd haka dan Allah ki furamin asiri kar kice a'a" girgiza kanta ta yi tana zare hannayenta ta ce"A'a ya Khalil yanzu kai ba tsarana bane kada ka manta a wancen lokacin ba kayi aure ba sannan baka kai matsayin daka taka yanzu ba jiya ban samu nayi bacci ba saboda tunane-tunane dan Allah karka sake karyamin zuciya ka barni da abinda yake damuna yaya Khalil" ta ƙarashe maganar tana haɗe hannayenta alamar roƙo. Hankalin Khalil ya tashi dan abinda take faɗa daga zuciyarta yake fitowa tuni jijiyoyin kansa suka tashi cikin rawar murya ya ce"ees... eeshana dan Allah karki barni karki jiyamin baya ki taimaka ki kasance dani a karo na biyu ki bani dama nayi miki alƙawarin bazan yaudare kiba dan Allah ki taimaka" kallonsa tayi sai kuma ta girgiza kanta tana dariya mai haɗe da hawaye ta ce" wlh bazan iya ba yaya Khalil kamar yanda na faɗa maka yanzu zuciyata akwai wanda take muradi saboda haka leave me mu cigaba da kasancewa matsayin ƴan'uwa wannan ya wadatar please" tana gama faɗar haka ta juya ta koma gida da gudu sbd kukan da yaci ƙarfinta. Dafe kansa ya yi cikin tsananin tashin ya ce"inna'lil lahi wa ina ilayhi raji'uun Allah ka taimakeni ka sassauta zafin zuciyar Ma'eesha ko na samu salama" ganin yana ɓata lokaci kuma tayi tafiyarta yasa ya shiga motarsa ƙirar Honda Accord ya bar gidan. Girgiza kai Mami tayi cikin son rarrashinta ta dafata ta ce"mene ne nayin kuka Ma'eesha?, tunda har Khalil ya baki haƙuri ya kamata ace kin haƙura kinsan halinsa bashida wani mummunan hali to me kike nema wajen namiji?" ɗagowa tayi daga cinyar Mami cikin kuka ta ce"Mami bazaki gane irin zafin da zuciyata ke yimin ba, Mami inaji kamar zan mutu yaya Khalil ya auri wata bani ba bazan taɓa samun kwanciyar hankali ba idan na aureshi saboda bazan iya jurar ganinsa da wata Macen ba" murmushi Mami tayi tana goge mata hawayen fuskarta ta ce"Ma'eesha kenan karki kuskura ki saka a ranki cewa ke mijinki naki ne ke ɗaya yanada damar aurar wacce yakeso matuƙar yanada halin riƙeta kuma daga gidanku kake fara koyar abu ni kaɗai ce a gidan nan?" girgiza mata kai ta yi, Mami ta ci-gaba da faɗin"saboda haka kima daina kawo wannan tunanin a ranki ki maida komai ba komai kinsan babu abinda zai hana babanki ya bawa Khalil aurenki sai ikon Allah sbd haka ki daina wannan damuwar matuƙar kin riƙe mijinki yanda ya kamata to bazai taɓa kufce miki ba koda ace ku huɗu ne a wajensa" shiru tayi tana sauke ajiyar zuciya Mami ta miƙe ta fita a ranta tana jinjina yarinta irinta Ma'eesha. Da mamaki ya ƙara sa gaban gadon yana kallon yanda duk ta naɗe cikin bargo ya ce"Ramlah!! Ramlah!! Ramlahhh" da sauri ta miƙe daga kwancen tana murza idanunta sai kuma ta langwaɓar da kai ta ce"wlh doctor banajin daɗi zuciyata zafi take yimin" zama ya yi gefen gadon sai kuma ya ɗora hannunsa kan ƙirjinta dan jin yanda zuciyarta ta ke bugawa, janye hannunsa ya yi yana miƙewa tsaye ya ce"bari na kawo miki drugs ɗinki da ruwa sai kisha" gyaɗa masa kai tayi sannan ya juya ya fita murmushi ta yi sannan takoma ta kwanta. Zaune ya samu Mommy tana kallon wani series da ake haskawa bai ce mata komai ba ya shige parlonsa ko minti biyu ba ayi ba ya fito hannunsa riƙe da ledar drugs kallonsa Mommy ta yi sai kuma ta ce"subhanallahi wace babu lafiya?" yana duba ledar drugs ɗin ya ce"wai Ramlah ce bata jin dadi shine zan bata magani" okay Mommy ta ce sannan ya juya ya koma bedroom ɗin, kwafa Mommy ta yi tana cewa"yaro baisan wuta ba sai ya taka jira zakaga abinda na aikata" sai kuma tayi wani kyakkyawan murmushi ta cigaba da kallonta cikeda nishaɗi. Sai bayan sallar isha'i sannan suka shigo gidan babu kowa a parlon daman kuma haka suka so kawai kowa ya yi part ɗinsa, taɓe baki Ma'eesha tayi dan tana kallo suka shigo suna sanɗa kamar wasu munafukai haka kawai taji yanzu bata sonsu musamman ma Farooq wanda take jin da tanada dama da tuni ta koreshi daga gidan murmushi tayi tana sipping coffee ɗinta Saboda tunawa da yaya Khalil da tayi idan ta ce bata sonsa to kowa zai gane ƙarya take dan ita kanta tasan tana mutuwar son Khalil kawai tana jin haushin auren da ya yi ya barta ne. Saida ta shanye tass sannan ta fito daga kitchen ɗin a hankali ta shiga tafiya saboda duhun daya mamaye parlon haka kawai taji tsoro ya rufeta. Numfasawa ne ya kusa ɗaukewa saboda jin abu da tayi agabanta cikin tsananin tashin hankali ta buɗe baki zaka kwalla ƙara, da sauri ya toshe mata baki yana yi mata alama da tayi shiru, kusan five minutes kafin ya ɗago ya kalleta da idanuwansa da suka sauya kala cikin wata iriyar murya ya ce" Ma'eesha! da sauri ta kalleshi dukda ba ganin fusakarsa take yi ba ya ce"naji I'm sorry amma bazan sake ba bazan sake yi miki abinda nayi yanzu ba dan Allah forgive me my lil sis" da sauri ta faɗa jikinsa tana kuka mara sauti, murmushi Farooq ya yi sannan ya dafa kanta ya ce"Nagode sosai ƴar albarka dare ya yi shige ki kwanta" gyaɗa masa kai ta yi sannan ta juya ta haye sama ta barshi nan tsaye yana saƙa da warwara. *RIYADH* *Al Yesmin international school* Fitowa tayi daga cikin makaranta tana kallon yanda ake ta zuwa ɗaukan yara gaba ɗaya a gajiye take ga wani irin ciwo da ƙirjinta ke mata tura baki tayi ganin har sannan ita babu wanda ya zo ɗaukanta waje ta nema ta zauna ta miƙe ƙafarta saboda wani irin ciwo da take mata tun daga nesa yake kallonta ganin yanda duk ta kwaɓe fuska kaɗan ya rage bata fashe da kuka ba, fitowa ya yi daga motar yana sanye cikin Jallabiya Black colour idanunsa maƙale cikin sun glasses kasancewar akwai rana a garin kwata-kwata Muhaira bata lura dashi ba har ya ƙaraso gabanta girgiza kansa ya yi sannan ya ja kunnenta da sauri ta ɗago tana kallonsa sai kuma ta fashe da kuka bai ce mata komai ba ya kama hannunta suka bar wajen saida ya sanyata a motar sannan ya kalleta ganin yanda take kuka kamar wacce aka yiwa wani abu ya ce"za ki yimin shiru ko sai ranki ya ɓaci?, sbd ke kike da bakin kuka duk abinda aka yi miki sai ki fashe da kuka?" tura masa baki ta yi tana shashshekar kuka. Siririn tsaki yaja sannan ya ja motar suka bar wajen, a bakin ƙaton gate ɗin gidan ya yi parking ba tareda ya kalleta ba ya ce"sauka" kallonsa ta yi sai kuma ta buɗe motar ta fita shi kuma ya bar wajen kallonta suke har ta shigo gidan suna zaune kan wata kujera suna hira shigewa ta zo yi Tyha ta ce"keee zo nan" juyowa Muhaira ta yi ta kalleta sai kuma ta tura ƙofar ta shige batareda ta amsa kiran da tayi mata ba baki buɗe Tyha ta bita da kallo sai kuma ta yi kwafa ta ce"wai wannan wace ce?" ɗaga kafaɗa Amrish ta yi ta ce"nima nasani maybe dai itama siyanta akai ko kuma aka satota" Zeey ce ta ce"kenan ita ba a cikinmu take ba naga tana kwana part ɗin Zaki?" Tyha ta ce"tunda kikaga haka ko Zaki ɗin ne ya riƙeta maybe dan ya ganta da kyau ne kuma daga gani yarinyace sosai" murmushi Amrish ta yi ta ce"aikuwa amma duk da haka yarinyar batada kunya" numfasawa Tyha ta yi ta ce"aikuwa zan yi maganinta saidai idan ba zata fito ba" tsaki Zeey ta yi ta ce"ke daɗina dake rashin tunani to da gani kike tana fitowar?, yau ɗin ma bakiga school taje ba" wani kallo Tyha ta yi mata ta ce"dalla Malama karki sake cemin mara tunani zan miki rashin mutunci wlh" ganin abin nasu na neman zama faɗa yasa Amrish ta ce"dan Allah ku saurarawa mutane wannan ai ba daidai bane ku dinga abu kamar wasu yara" buɗe baki tayi zata yi magana sukaga Zaki ya shigo gidan da motarsa sunkuyar da kansu sukai har ya fito daga motar hannunsa riƙe da ledoji. Wani guard ya miƙawa ledojin sannan ya yi gaba, yana zuwa suka sunkuya cikeda girmamawa suka ce"sannu da zuwa yallaɓai" bai basu amsa ba ya yi gaba, har ya riƙe handle ɗin ƙofar sai kuma ya juyo yana tafiya hannunsa zube cikin aljihu ya ce" ina sauran?" Tyha ce ta ce"sunje school" "then ku mene ya hanaku zuwa?" kasa bashi amsa suka yi ya ce"idan ba zakuyi karatu ba kunfi son ɗaya rayuwar fine zanyi maganinku" yana faɗin haka ya juya ya shige parlon. Dafe ƙirji Amrish ta yi ta ce"mun shiga uku wlh tun wuri musan abunyi nidai zan koma school gobe" Zeey ta ce"nima haka wlh dan nasan idan ya waiwayemu abun bazai yi da kyau ba" kallonsu Tyha ta yi sannan ta ce"sai abinda Taj ya ce min" tsaki Amrish tayi ta ce"banza kawai" tashi suka yi suka barta a wajen saida taga sunyi nisa sannan itama tabi bayansu. Da sauri ya ƙarasa inda take kwance ɗin idanunta har sun fara ƙaƙƙafewa ɗagota ya yi jikinsa yana kallon fuskarta ya jijjigata ya ce"keeee! keee!" ganin tana neman rasa rayuwarta gashi babu inhaler a gidan yasa ya zauna yana gyara zamanta akan cinyarta a hankali yayi coping face ɗinsu ya ɗora bakinsa daidai nata cikin nutsuwa ya zura bakinsa cikin nata sannan ya saki wani zazzafan numfashi da sauri ta riƙeshi tana sauke wani irin numfashi saida ya yi mata haka wajen sau uku sannan numfashin nata ya dawo zare bakinsa ya yi daga nata yana kallonta har sannan wasu hawayene suka shiga sakko mata na zallar azabar fitar numfashi, sosai ta bashi tausayi dan yasan azabar cutar numfashi dan har yanzu idan Asthmarsa ta tashi sai ya yi kamar ya rasa ransa. Saukar numfashinta ya ji a ƙirjinsa hakan yasa ya kalli fuskarta gani ya yi tayi bacci ya shafa kanta sannan ya miƙe da ita ya shiga bedroom ɗinta yana kwantar da ita ya juya tayi saurin riƙe masa hannu cikin wata iriyar murya ta ce"karka barmu ka zauna a nan tsoro muna ji" kallon fuskarta ya yi yaga ta kwaɓe fuska hakan yasa ya zauna gefen gadon ya zuba mata idanu yana kallonta wata iriyar ƙara ta saki sai kuma ta miƙe zaune tana sauka daga kan gadon da sauri cikin zafin nama ya riƙota ya haɗata da ƙirjinsa ya rufeta ruf yana jin yanda take ƙoƙarin guduwa ya sake rufeta yana haɗe face ɗinsu waje guda cikin wata iriyar murya mai amo tashiga furta" mu ka kyalemu tafiya zamuyi da ita ka rabu damu ka daina riƙemu" shiru ya yi yana sakin ajiyar zuciya ya ce"au kune?" sake yunƙurawa tayi ya yi saurin rungumeta yana sakin murmushi ya ce"meyasa zaku tafi da ita to?" ta ce"saboda ita ɗin amanarmu ce babanta ya barma amanarta kafin ya mutu sbd haka dole sai ta bimu ka rabu damu" haɗe ransa ya yi yana dungure mata kai ya ce"ƙarya kuke" "mu ba ƙarya muke ba munsan Allah ai" murmushi ya yi ya ce"au da gaske?" gyaɗa masa kai ta yi ya ce"shikenan muyi abu guda, naji ku tafi amma ku barmin amanarta ni zan riƙe muku nayi alƙawarin bazan bari wani abu ya cutar da ita ba" tura baki tayi gaba ta ce"kayi alƙawari?" gyaɗa kansa ya yi ta sake cewa"to amma bazaka bari kowa ya taɓa ta ba, duk randa wani abu ya sameta to ka karya alƙawarinmu kuma zamu zo mu tafi da ita" numfasawa ya yi ya ce"na yarda" murmushi ta yi tana miƙo masa hannunta ta ce"to kayi mana alƙawari" girgiza kansa ya yi sannan ya ɗora hannunsa akan nata, waya sassanyar ajiyar zuciya ta sauke sai kuma jikinta ya saki kallon fuskarta ya yi sai kuma ya kalli hannunta wanda yake cikin nasa ya ɗauki ƴan mintuna a wajen kafin ya kwantar da ita ya rufa mata duvet ya fice daga ɗakin. Kai tsaye kuma ɗakinsa ya shiga yana zuwa ya ajiye wayarsa sannan ya shige bathroom ya sakarwa kansa shower saida ruwan ya dakeshi sosai sannan ya dafe kansa wanda ya kejin ya yi masa nauyi tunani ne kala-kala cikin ransa lokaci ɗaya kuma ya tuna da maganar Dmash furzar da wani irin numfashi ya yi sai kuma ya yi tsaki kawai ya yi wankansa, fitowa ya yi cikin wata bathrobe fara dryer kawai ya saka a kansa saboda jiƙewar da ya yi sannan ya kwanta yana rufe jikinsa nan da nan bacci ya ɗaukeshi. Sai wajen 6:20pm sannan ta farka daga baccin da sauri ta shiga toilet tayi wanka ta ɗauro alwala sannan ta fito wata jallabiya ta sanya mai ƙaramin hannu ta gyara gashinta sama-sama dan ita a rayuwarta ta tsani a taɓa mata kanta ko da itace kuwa parlon ta fito saboda wata irin yunwa da take ji da sauri tayi hanyar kitchen, dube-dube ta shiga yi dan ganin ko zata samu abinci tura baki tayi ganin babu komai a kitchen ɗin kuma tsoron kunna gas take gudun kar abinda ya faru da ita ɗazu ya sake faruwa, fitowa tayi tana jan ƙafa da sauri ta ƙarasa wajen ledojin da tagani tana zuwa ta shiga buɗewa takeaway ne guda uku a ciki na farkon ta buɗe taga jallof rice ce wadda taji wadatattun kayan haɗi ƙamshinta ne bai yi mata ba hakan yasa ta buɗe ɗaya takeaway ɗin fried rice tagani a ciki tayi murmushin jin daɗi sannan ta ɗauko ɗayan ta buɗe taga gasasshiyar kaza da sauri ta ɗauko sannan ta dawo ƙasan carpet ɗin ta baje ta hau cin abincinta hankali kwance tass ta cinye shinkafar kazar kawai ta rage amma itama taci tafi rabi sannan ta ɗauka ta mayar ledar ta buɗe fridge ta ɗauki ruwa tasha sannan ta koma ɗaya parlon tayi zamanta tana kallo. Fitowa ya yi cikin wata t-shirt da 3quater kai tsaye wajen ledojin ya nufa saboda wata irin yunwa da yake ji buɗe ledar ya yi yaga empty takeaway a ciki da mamaki ya kalli take away ɗin sannan ya buɗe ɗayan jallof rice ya gani itama kuma da alama taci dan ba haka ya ajiye ba yana buɗe ɗayan yaga babu kazar sai ƴar kaɗan a fusace kamar zai yi kuka ya yi ɗaya parlon yana wuci da sauri ta ɗago kanta jin yanda ya buga ƙofar yana kallonta ransa a haɗe kamar hadari ya ce" # *Unconditional love* # *Destiny* # *SQUAD 2024* # *BA ITA BA CE!* # *Ameenatou I Ibrahim* # *Nanameera ce!✍️*. [8/10, 11:19 AM] Nanameera😍✌🏻: *BA ITA BA CE!..💖💖* *Nanameera ce ✍️* *MIKIYA WRITERS ASSO...* ```Page 13``` # *DESTINY* "Keeeee!" a ɗan firgice Muhaira ta kalleshi sai kuma ta turo baki tana cigaba da kallonta kwafa ya yi sannan ya ce"ubanwa ya ce kije ki cinyen abinci ko ke kika siyamin? nabaki permission ne?" kallonsa tayi da manyan idanunta sai kuma ta zumɓura baki tana wasada fingers ɗinta a tsawace ya ce"ba dake nake magana ba!" sosai ta razana sai kuma ta fashe da kuka tana murza idanunta sakar baki ya yi yana kallon ikon Allah tsakanin shi da ita kowane ya dace ya yi kuka??, ƙarasowa ya yi cikin takunsa na isa ya zauna kujerar da take fuskarsa babu alamun rahama ya ce"tell me meyasa kika cinyemin abinci?" cikin shashshekar kuka ta ce"koba yunwa nake jiba shiyasa naci amma kana yimin faɗa to zan biyaka" wani kallo ya yi mata sai kuma ya ce"da gaske?" gyaɗa masa kai ta yi tana murza idanunta. Girgiza kansa ya yi yana murmushi ya ce"shikenan biyani abincina tunda bake kika siyamin ba" kallonsa ta yi da idanunta wanda ruwa ya kwanta akai ta ce"to zan dafa maka wani" gyaɗa kansa ya yi ya ce"hurry up" sannan ya tashi ya fita, tura bakinta tayi wanda sukai jajur dasu sannan ta miƙe kamar wacce aka yiwa dole tayi waje kai tsaye kitchen ta nufa tsayawa tayi tana tunanin abinda zata dama masa sai kuma ta yanke shawarar tayi masa shinkafa tunda ita ta cinye masa dakyar ta iya kunna gas ɗin dan gaba ɗaya ta tsorata dashi, cikin sanyin take yin aikin dan lokaci ɗaya jikinta ya fara yi mata ciwo amma kuma tsoron faɗan da zai yi mata yasa ta daure ta cigaba above 2hrs kafin ta kammala dafa shinkafar da bata shige 1cup ba ko kaɗan batada saurin aiki kuma hakan ya samo asali ne dalilin ciwonta zuwa lokacin idanunta sun kumbura sosai gabaɗaya jikinta rawa yake da sauri ta kwashe a plate sannan ta fito parlon. Zaune ta sameshi yana danna system ɗinsa yanda ya bada attention ɗinsa zaka gane abu yake gabatarwa mai muhimmanci a gaban table ɗinsa ta ajiye masa plate cikin sanyin murya ta ce"gashinan na biyaka" kusan 5mins sannan ya kalleta ya kuma kalli plate ɗin ya ce"ni abokin wasanki ne?" sunkuyar da kanta tayi ya ce"za ki ɗauke daga gabana ko saina ɓata miki rai shashasha kawai" da mamaki Muhaira ta kalleshi cikin rawar murya ta ce"amm.. amma kaine kace na biyaka kuma dakyar nadafa wlh" rufe system ɗin ya yi yana yi mata wani kallo ya ce"wai ke bakida tunani ne what are u thinking ni ne zanci abinda kika dafa kina ƙazama are you mad?" tuni hawaye suka fara ambaliya akan fuskar Muhaira cikin kuka ta ce"wl..wlh banyi ƙazanta ba kaci kaji" "Tassssssssssss" A matuƙar razane ta kalli plate ɗin abincin wanda ya fashe duk abincin ya tarwatse a parlon cikin tsananin ɓacin rai fuskarsa har wani jaa ta yi ya ce"get out of my side!!" da gudu Muhaira ta shige bedroom ɗinta tana kuka, faɗawa kan gadon tayi ta fashe da wani raunataccen kuka an daɗe ba'a ɓata mata rai irin na yau ba wani irin kuka ta dinga yi tana jan numfashi a hankali kuwa jikinta ya fara rawa sai kakkarwa sanyi take wani irin amai taji ya taso mata da gudu ta tashi ta shiga toilet tana zuwa ta fara yunƙurin amai madadin tayi aman wani abun sai wani guda gudan jini ya fara fitowa daga bakinta dafe kanta tayi sai kuma ta tafi luuuuu ta faɗi a ƙasa sumammiya. Murmushi Taj ya yi ya ce"karka damu Sir nayi maka alƙawarin kawo maka yarinyar nan har gida kawai kabani 24hrs" numfasawa Dmash ya yi ya ce"nayarda dakai Taj sbd haka go on" sunkuyar da kansa ya yi alamar girmamawa sannan ya juya ya fita, furzar da numfashi Dmash ya yi ya ce"Zaki taka ta ƙare". Ƙarfe 8:20am ya fito daga bedroom ɗinsa sanye yake cikin wasu suit coffee colour ya tufke kansa da ribbon fari kunnensa ɗaya ɗauke da yarin diamond kallon parlon ya yi wanda yake tsaf dashi kamar ba wanda ya ɓata ba jiya sai wani irin ƙamshi mai daɗi ne ke tashi a parlon taɓe baki ya yi yana ƙarewa parlon kallo da mamaki ya kalli agogon hannunsa ganin lokaci yaja har haka gyara zaman Bluetooth ɗin kunnensa ya yi cikin wata murya ya ce"yarinyar nan ta fita school ne?" "No sir she didn't come out at all" gyaɗa kansa ya yi sannan ya murɗa handle ɗin ƙofar ya shiga ƙarewa parlon ya yi ganin komai tsaf dashi kamar ba yarinyace a ciki ba taɓe baki ya yi sannan ya ƙarasa bedroom ɗin da mamaki yake kallon kan bed ɗin ganin babu kowa da alama ma ba'a kwanta akansa ba, kallon kofar toilet ɗin ya yi sai kuma ya ƙarasa ya yi knocking yana faɗin"keee! keee come out" shirun da yaji ne yasa ya murɗa handle ɗin without second thought kuma ya tura kansa cikin toilet ɗin. Cikin hanzari ya ƙarasa inda ya ganta kwance yana zuwa ya ɗagota da mamaki ya kalli wajen ganin gudan jini wanda ya daskare a wajen sosai hankalinsa ya tashi amma ko kaɗan babu hakan a kan fuskarsa da sauri ya ɗauketa yana miƙewa tsaye idanunsa ya sauka kan sink ɗin ganin duk daskararren jini yasa ya yi waje da sauri ya yi waje tun kafin ya ƙarasa driver ya buɗe masa motar yana shiga shima ya shiga kai tsaye kuma asibiti suka nufa, rungumeta ya yi sosai a jikinsa jin yanda jikinta ya yi sanyi klao da alama ta daɗe da sumewa dan duk jikin nata ya saki sosai kiran Taj ne ya shigo wayarsa gyara Bluetooth ɗin ya yi daga ɗaya ɓangaren Taj ya ce"Zaki kana gida?" girgiza kai ya yi ya ce"no" Taj ya ce"daman..." "Please Taj I'll call you back" da mamaki Taj ya kalli screen ɗin wayar sai kuma ya taɓe baki ya shige toilet, har suka ƙarasa asibitin bai ɗauke idanunsa daga kanta ba. *Asokoro Villa*. Murmushi Dad ya yi yana kallon Khalil ya ce"General ya amince da aurenka da Ma'eesha sbd haka yanada kyau ka fara shiri dan ba wani lokaci za'a ɗauka ba" murmushi ya yi ya ce"wowww Dad thank you I really appreciate naji daɗi sosai" girgiza kansa ya yi dan ba tun yau ba yasan irin son da Khalil yakewa Ma'eesha ko sanda zai bar ƙasar saida ya zubar da hawaye sbd zai rabu da ita gashi cikin ikon Allah kuma zai aureta bayan wasu shekaru, da sauri Mommy tabar wajen ta shige bedroom ɗinta zaune ta samu Ramlah tana kallo a TV tsaki ta yi sannan ta ce"keee maza-maza tashi zamuje wani waje" da mamaki Ramlah ta ce"Mommy ina zamu je da yammacin nan?" tsaki Mommy tayi tana yafa veil ɗinta ta ce"idan bazaki tawo ba ki zauna kina tambayata shashasha kawai" tana faɗin hakan tayi waje, buga ƙafarta tayi aƙasa sannan ta miƙe tabi bayan Mommy tana sauke veil ɗin dake kanta kasancewar Abaya ce ajikinta. Convey ɗin da sukaji yasa Dad ya ce"ina kuma ta sake fita da yammacin nan?" taɓe baki Khalil ya yi ya ce"Maybe ko wani abunne ya taso mata urgent, nima zuwa anjima nakeson mu tafi gida" girgiza kai Dad ya yi ya ce"but kafara tsayawa ta ƙara samun sauƙi sbd kaga can idan ka koma babu mai kulawa da ita" gyaɗa masa kai ya yi sannan ya miƙe tsaye ya ce"zan je asibiti" ohk Dad ya ce sannan ya juya ya fita. Shiru General ya yi yana saurarenta har ta kammala maganar sannan ya ce"then me kikeso nayi akai?" murmushi Mommy tayi ta ce"A'a kawai daman naga ya kamata ace na sanar maka ne shiyasa" bai ce mata komai ba ya cigaba da sipping coffee ɗinsa, sakkowa tayi daga saman tana kallonsu ɗaya bayan ɗaya murmushi Mommy tayi ta ce"Shalele an tashi" shiru Ma'eesha tayi mata tana zuwa ta zauna gefen General ta ɗora kanta a cinyarsa shafa kanta ya yi sannan ya ce"Shalelena meya faru?" shiru tayi masa hakan yasa ya leƙa fuskarta ƙuri tayi masa da idanu ya sake cewa"ƴar gidan Father tell me kedawa?" ganin tayi banza yasa Mami ta kalleta cikin ɓacin rai ta ce"ke bakijin ana yi miki magana ne kikayi shiru Ma'eesha ki kiyayeni fa!" ko kallonta Ma'eesha bata yi ba hakan yasa General ya sake kallonta idanunta a buɗe suke balle ace bacci take ɗago kanta ya yi ya ce"ƴar Baba meyasa kika yi shiru" a hankali ta ɗora hannayenta bisa fuskarsa ta shiga shafawa sai kuma tayi murmushi da tsananin mamaki duk suke kallonta General ya ce"faɗa min mene ke yi miki ciwo?" bakinsa tabi da kallo sai kuma ta girgiza masa kai miƙewa tsaye ya yi yana riƙe da hannunta ya ce"Ma'eesha bazaki magana ba?, ni abokin wasanki ne? Ma'eesha I'm ur mate da nake miki magana nd u remain silence?" da kallo kawai Ma'eesha ta bishi sai kuma ta faɗa jikinsa tana sakin wani kuka mai sauti" da sauri General ya kalleta sai kuma ya durƙusa yana kallon kyakkyawar fuskanta ya ce"Ma'eesha baki jin abinda nake faɗa miki ne ko kunnenki na yi miki ciwo ne?" bakinsa ta ƙalla sai kuma ta girgiza masa kanta da hannu ta nuna masa bakinta sai kuma ta nuna masa kunnenta da sauri Mami tace"Ma'eesha baki jin abinda muke faɗa, tell us Ma'eesha" ta faɗa tana jijjigata fashe tayi da kuka tana rungume Mami, cikin tashin hankali Mami ta ɗago fuskarta ta ce"Ma'eesha kinji abinda na faɗa?" kallon bakinta tayi sai kuma ta girgiza mata kai tana goge mata hawayen dake zuba a fuskarta. Cikin kuka Mami ta ce"inna'lil lahi wa ina ilayhi raji'uun Ma'eesha wane yayi miki haka?, Wa ya kurumtaki?, me kika yiwa wani? Inna'lil lahi wa ina ilayhi raji'uun mun shiga uku" da sauri Mommy ta rufe mata baki tana kuka itama ta girgiza mata kai ta ce"ki daina cewa an shiga uku zaki ƙara wata masifar kawai muyi mata addu'a koma wane ya yi mata wannan abun Allah ya saka mata kuma ya bi mata haƙƙinta" fashewa Mami ta yi da kuka tana dafe kanta ta ce" me tayiwa wani?, yarinyar da bata shiga harkar kowa babu ruwanta da mutane wane mara imanin ne ya cuci rayuwarmu" ta ƙarashe maganar tana sakin wani kuka mai gunji. Miƙewa General ya yi wanda idanunta suka kaɗa sukayi wani irin jaaa waje ya yi ko gabansa baya gani sake tashi Mami tayi ta koma inda Ma'eesha take zaune tana kuka ta kama hannunta ta ce"Ma'eesha kinyi faɗa da wani ne ko akwai wanda ya ce zai yi miki wani abu?" girgiza mata kai Ma'eesha ta yi takama hannun Mami tana ɗorawa akan bakinta ta girgiza mata kai rungumeta Mami tayi tana sake fashewa da wani irin kuka mai tsuma zuciya ita kaɗai ce ƴar data mallaka kuma take burin taga tayi aure kodan su samu ƙarin zuri'a tunda su basuda yawa sai gashi an samu wani mara imanin ya kurmantata dan babu shakka wannan abun ture akai mata ko jifa. Shigowa Farooq ya yi da mamaki yake kallonsu duka dan shi tunda sassafe ya fita ƙarasawa ya yi ganin yanda suke kuka kamar waɗanda aka yi mutuwa ya kalli Mommy ya ce"Mommy what happened?" kasa bashi amsa Mommy tayi saboda kuka da yaci ƙarfinta hakan ya sa ya ce"Mami dan Allah ku sanar dani abinda yake faruwa" kallonsa Mami tayi da idanunta wanda suka yi wani irin jaa ta ce cikin kuka"Farooq sun kurmantata sun cucemu Ma'eesha bata jin abinda muke cewa kuma bata magana" cikin tsananin tashin hankali ya ce"what!!!?" ƙarasowa gaban Ma'eesha ya yi ya kama hannunta ya riƙe cikin nasa cikin wata iriyar murya mai nuna zallar tashin hankali ya ce"Shalelen Father ki cemin ba haka bane abinda Mami tafaɗa ki yimin magana dan Allah Ma'eesha kice wani abu ko naji sanyi a raina nasan halinki da wasa dan Allah Ma'eesha stop joking tell me the truth kar zuciyata ta buga kiyimin magana naji muryarki kinji shalelen ƙanwata" da idanu kawai Ma'eesha ke binsa da kallo dan yawan maganar da ya yi mata yasa ta gaza fahimtar koda magana ɗaya abu ɗaya kawai tasani shine yana magana ne akan abinda ya sameta hakan yasa ta nuna masa bakinta da kunnenta sannan ta girgiza masa kai. Durƙushewa Farooq ya yi kamar ƙaramin yaro ya shiga rera kuka wanda ya daɗe bai yi irinsa cikin rayuwarsa ba kuka ne wanda yake fitowa tundaga zuciyarsa yana matuƙar son Ma'eesha bashida burin daya shige ganin farin cikinta koda yakeson ya rabata da iyayenta yana yine sbd hakan ya kasance ƙudirinsa amma bazai taɓa mance Alkhairin Ma'eesha a gareshi ba bazai manta irin so da ƙaunar da take nuna masa ba tabbas duk wanda ya yi mata wannan aika-aikar to ɓa ƙaramin maƙiyinta bane. General ne ya shigo cikin sauri gabaɗaya ya fice hayyacinsa wasu doctors ne guda biyar suka shigo sai Farooq da His Excellency Muhammad Tanka da sauri Khalil ya ƙarasawa wajenta ya kama hannayenta cikin sanyin murya mai nuna rauni ya ce" _Ƙaddara a bace wacce bawa baya iya tsallaketa kowa da kalar tasa ƙaddarar kuma kowa da akwai silar tasa ƙaddarar ba'a iya guje mata domin ita ta kasance rubutacciyar aba ce tamkar zanen dutse haka take duk yanda zakayi bazaka iya gogeta ba no matter who are you or what you have nobody can change his/her destiny either good or bad ya rabbi ka bamu ikon cinye duk wata jarrabawar da zaka yi mana😭🤲🤲_. # *Love* # *Destiny* # *Manifestation* # *SQUAD 2024* # *Nanameera ce ✍️*.https://chat.whatsapp.com/BghAYLLnNSvK6y3XpGoE9I *BA ITA BA CE!..💖💖* *Nanameera ce ✍️* *MIKIYA WRITERS ASSO...* ```Page 14``` "Eeshana da gaske baki jin abinda nake faɗa? eeshana ki ce ba gaskiya bane abinda ake faɗa min talk to me please" ya faɗa yana jijjigata, fashewa tayi da kuka ta rungumeshi tana girgiza masa kai Dr Sabo ne ya ƙaraso wajen yana kallonsu ya ce"aje da ita asibiti maybe agano abinda ke damun nata" okay kawai Khalil ya ce sannan ya miƙe tsaye yana riƙe da hannunta sukayi waje ajiyar zuciya Mami ta shiga saukewa tana binsu da kallo har suka fice sannan ta tashi da sauri ta haye sama da kallo Mommy ta bita sannan ta tashi itama ta shige nata apartment ɗin, cikin tashin hankali take cewa"wlh Fulani bazan iya jurewa ba zuciyata bazata iya ɗauka ba tashin hankalin ya yimin yawa Ma'eesha fa dan Allah" daga ɗaya ɓangaren ta ce"haba Asma'u mene haka?, ki yarda da ƙaddara mana babu wanda ya isa ya sauyata koma wane ya yiwa Ma'eesha mugunta ai Allah yana ganinsa kuma zai yi maganinsa saboda haka karki sake cewa zaki damu kanki ku tayata da addu'a Allah ya bayyana asirin koma wane idan kuma Allah ne ya ɗora mata to shi zai yaye mata zuwa gobe ko su Jakadiyane zasu zo sai su tawo da Aleema" gyaɗa mata kai Mami tayi saboda kuka da yaci ƙarfinta girgiza kanta tayi tana ajiye wayar ta ce"Allah dan girmanka da buwayarka Allah dan zatinka ka bayyana koma wane ya aikatawa Ma'eesha haka Allah ka bata lafiya ka yaye mata ka kuma bamu ikon cinye jarrabawar" ta ƙarashe maganar tana kuka kamar ranta zai fita gabaɗaya duniyar tayi mata zafi rabonda ta shiga tashin hankali irin wannan tun ranar da Mai martaba ya rasu girgiza kanta ta yi tana jinjina mugunta irinta ɗan Adam ko me Ma'eesha ta aikata?????. Sai wajen 5pm suka dawo gida lokacin tayi bacci Khalil ya ɗaukota duk irin wasu gwaje-gwaje da aka yiwa Ma'eesha ba'a ga wata alamar ciwo wanda zai hana majiyanta aiki ba manyan likitoci na gidan president ne suka dubata amma basuga komai ba haka suka dawo babu wani result mai kyau har bedroom ɗinta Khalil ya shiga ya kwantar da ita sannan ya fito babu wanda ya yiwa sallama ya yi waje dan gaba ɗaya baya cikin nutsuwarsa. Allah sarki General gaba ɗayansa ya fita hayyacinsa kana ganinsa kasan Akwai tashin hankali mara misaltuwa a tare dashi idanunsa duk sun zurma dan rabonsa da abinci tun daren jiya tunda ya shiga bedroom ɗinsa bai fito ba har akayi sallar isha'i dan ko masjid bai jeba, wajejen 9pm Mami ta tura ƙofar ta shiga zaune ta sameta kan gadon tana sanye da baby hijab da alama sallah tayi zama Mami tayi a gefenta da sauri ta dora kanta akan cinyar Mami ɗumin hawayenta Mami taji shafa kanta tayi kawai dan itama ɓoye nata hawayen take numfasawa tayi sannan ta ɗogata tana mata nuni da abinci, girgiza kai Ma'eesha tayi Mami ta ce"A'a Ma'eesha tun jiya babu abinda kikaci kar kuma wani ciwon na daban ya sameki" tana faɗin haka ta buɗe plate ɗin gefenta wainar shinkafa ce a ciki sai zuba ƙamshi take miyar taushe aka yi mata wadda taji wadatattun kayan haɗi da nama a hankali ta gutsuro ta kai mata bakinta a hankali ta buɗe bakinta ta karɓi abincin haka Mami ta yita feeding ɗinta saida ta tabbatar da cewa ta ƙoshi sannan ta rabu da ita ruwa ta bata tasha sannan ta ce taje tayi wanka, Mami na zaune a ɗakin har saida tagama wankan ta shirya cikin wata sleeping dress fara ta kwanta saida Mami ta tabbatar bacci ya ɗauketa sannan ta gyara mata kwanciyar ta rufeta da duvet tabar ɗakin. Da sallama tashiga ɗakin zaune ta sameshi kan kujerar dake gefen gadon ya zuba uban tagumi gefensa al-qur'ani ne da alama karatu ya gama a sanyaye Mami ta ƙarasa ciki ta zauna gefensa shiru bedroom ɗin ya ɗauka na wasu mintuna sannan Mami tayi breaking silence ɗin ta hanyar faɗin"yallaɓai bakaci abinci ba tun jiya kar ciwonka ya tashi" ɗago idanuwansa ya yi wanda sukayi wani irin jaaa ya kalleta sannan ya ce" Asma'u ko kaɗan banajin yunwa yama za'a yi naji yunwa Asma'u? kin manta halin da ƴata ke ciki? Ma'eesha fa dan Allah karki karyamin zuciya ki barni kawai" girgiza kai Mami ta yi ta ce"bawai zan karya maka zuciya bane a'a zan ƙarfafa maka ita ne ka tuna cewa Allah shine wanda ya azurtamu da Ma'eesha bayan tsawon lokaci bayan mun yanke tsammanin zamu samu haihuwa sannan kuma muka kusa rasata a yayin haifarta nanma Allah ya sake bamu dama kada ka manta kowane bawa akwai irin tasa jarrabawar mu wannan ita ce tamu dukda zuciyata a karye take amma naji zan dogara da Allah kuma zan cigaba da roƙonsa har sanda zai bawa Ma'eesha lafiya kaima dan Allah dan Annabi karka saka wannan abun a ranka ka cire komai mu fawwalawa Allah haƙiƙa shi ɗin mai jin kukan bayinsa ne idan kana shiga damuwa Ma'eesha bazata samu salama ba kullum zata kasance cikin tashin hankali dan Allah General kayi mani wannan alfarma" numfasawa ya yi sannan ya kalleta ganin tana hawaye. Hannunsa yasa ya goge mata sannan ya ce"shikenan Asma'u Allah ya bamu ikon juriya da haƙuri da ƙaddara amma tabbas kowane ya yi wannan abun bazan taɓa yafe masa ba da sannu kuma Allah zai bayyana mana shi" gyaɗa masa kai Mami ta yi ta ce"dan Allah ka daure kaci abinci ko yaya yake kar ulcer ya tayar maka" bayason ya sake nuna mata damuwarsa hakan yasa ya gyaɗa mata kai kawai da sauri ta tashi ta fita dan kawo masa abincin yanda ta sanya Ma'eesha a gaba haka shima ta sanya shi a gaba saida ta tabbatar ya ƙoshi sannan ta rabu dashi tashi tayi zata fita ya ce"Asma'u" da sauri ta juyo sai kuma ta dawo ta zauna wainar shinkafar ya gutsuro ya kai mata baki batayi musu ba ta karɓa kawai dan itama rabonta da abincin tun jiya. Khalil na zaune ya yi shiru hannayensa bisa kumatunsa ya tafi can duniyar tunani his Excellency ne ya shigo ya zauna gefensa dafashi ya yi wanda hakan ya dawo dashi daga duniyar tunanin da ya tafi gyara zamansa ya yi ya ce"na'am Dad" numfasawa ya yi ya ce"Khalil tunanin me kake?" jiki a sanyaye ya ce"Dad Ina tunanin Ma'eesha ne ina tunanin halin da take dan Allah Dad kayi magana da Father a sakko da maganar aurenmu ya dawo nan kusa zuciyata zata iya bugawa idan na cigaba da ganinta cikin wannan halin dan Allah Dad" kallonsa ya yi sai kuma ya dafashi ya ce" ka yarda zaka zauna da ita a haka?" "Dad koda makancewa Ma'eesha zatayi zan zauna da ita domin ni ita nakeso kamar yanda nasan da ace ni ne na shiga wani hali to babu abinda zai rabani da ita" murmushi Dad ya yi ya ce"kayi abinda ya dace Khalil I'm so proud of you nagode sosai" girgiza kansa ya yi ya ce"karka godemin Dad wannan yiwa kai ne" dafa kafaɗarsa Dad ya yi alamar jinjina sannan ya tashi ya shige ciki, da sauri ta koma bedroom ɗin tana zuwa ta faɗa jikin Mommy tana sakin wani irin kuka hankali tashe Mommy ta ce"ke Ramlah ke dawa?? meya sameki?" cikin kuka ta ce"Mommy kina ji ya ce zai aureta a haka Mommy Doctor ya ce zai zauna da ita koda ta kurumce dan Allah Mommy help me wlh ina cikin tashin hankali ki taimaka mini banason na rasa mijina kuma na tabbata ya aureta shikenan bashida lokacina" ajiyar zuciya Mommy ta sauke sannan ta ce" Ramlah karki wani damu kanki nasan abinda zanyi yanda na faɗa miki Khalil bai isa ya yi miki kishiya ba indai ni ce na haifeki saboda haka ki daina kukan nan" goge hawayenta tayi dan tasan tunda Mommy ta faɗa to ya zauna tashi ta yi ta ce"bari naje wajensa" okay Mommy ta ce har takai baƙin kofa ta ce"karki kuskura ki nuna masa kinji abinda suka tattauna ko kuma ranki ya ɓaci" gyaɗa mata kai Ramlah ta yi sannan ta fita. Tsaye yake jikin ƙaton Enlargement ɗin hoton ya zuba masa idanu wasu hawayene suka shiga zirarowa kan kuncinsa cikin sanyi murya ya ce"Mom why?why? meyasa kika barsu Mom? kin barni Mom banajin daɗi Mom yaushe zaki dawo ne? I really need you" ya ƙarashe maganar yana goge hawayen fuskarsa komawa ya yi ya zauna gefen bed ɗinsa a hankali ya fara recalling abinda suka shige some years back tabbas Mommynsa tabar baya da ƙura babu Irin neman da ba'a yi mata ba amma har i Wannan lokacin basu sake jin lbrnt ba dukda an tabbatar da asiri akayi mata na kucciya baisa sun hakura da nemanta ba aƙalla ankai wajen shekaru 30 da ɓacewarta ganin lokaci na tafiya yasa ya miƙe ya shige bathroom gudun kada ya makara. *Riyadh* *Al hammadi international hospital* Zaune yake kan kujerar dake facing gadon idanunsa a lumshe suke ya yi matuƙar gajiya har zuwa sannan kuma Muhaira bata farfaɗo ba duk da sunyi mata allurar bacci "Papi" Da sauri ya buɗe idanuwansa yana kallon inda yaji an kirashi idanunta a rufe suke ƙarasawa ya yi ya zauna gefen gadon ya riƙo hannunta cikin sanyin murya ya ce"yarinyar Papi kin tashi?" gyaɗa masa kai kawai tayi har sannan kuma idanunta a rufe suke ta ce"ka mayar dani gida please ni bazan sake kwana anan ba wajen Papina zani ka mayar dani garinmu dan Allah" hawayen da yaga suna zuba daga idanunta yasa yaji jikinsa ya yi sanyi yasan shine wanda ya jawo komai ko kaɗan bai ji daɗin abinda ya yi mata ba hannunsa yasa ya goge mata hawayen sannan ya ce"kidaina kuka kinji ki bari ayi discharging naki" girgiza masa kai tayi cikin kuka ta ce"ka mayar dani gida ni banason nan banson zama dakai ni na tsanek..." da sauri ya rufe mata baki yana girgiza mata kai buɗe idanunta tayi wanda suka sauya kala wani irin ruwa ya kwanta a cikinsu batace masa komai ba ta fashe da kuka tana ɗauke kanta daga kallonsa dafe kansa ya yi ya ce"ki yiwa Allah ki daina kukan nan haira naji zan mayar dake gida" da sauri ta kalleshi sai kuma ta ce" da gaske?" gyaɗa mata kai ya yi kawai daidai nan Taj ya shigo ɗakin yana kallonsu ya ce" # *BA ITA BA CE!* # *Haira* # *Zaki* # *SQUAD 2024* # *Nanameera ce ✍️*.[8/11, 7:55 PM] Nanameera😍✌🏻: *BA ITA BA CE!..💖💖* *Nanameera ce ✍️* *MIKIYA WRITERS ASSO...* ```Page 15&16``` "Ya jikin nata?" numfasawa Zaki ya yi ya ce"da sauƙi Alhamdulillah" zama ya yi kan kujera yana kallonta ya ce"Muhaira" buɗe idanunta ta yi ta kalleshi amma bata ce komai ba, murmushi ya sakar mata itama ta mayar masa tsayawa Zaki ya yi yana kallonsu sai kuma ya ɗauke kai daidai nan Dr ya shigo ɗakin sake duba jikin nata ya yi sannan ya yi discharging nasu kallonsa tayi ganin yanda ya juya baya tura baki tayi gaba ya yi murmushi ya ce"hau na goyaki mana" ɗauke kanta tayi sai kuma ta hau bayan nasa tana riƙeshi sosai dariya ya yi mara sauti ya ce"tunani kike zan ya dake?" batace masa komai ba ya girgiza kansa sannan ya fice daga asibitin zaune suka sami Taj a mota yana jiransu sauketa ya yi ta shiga back seat sannan shima ya buɗe gaba ya shiga. Sunyi nisa sosai Taj ya ce"Dmash fa yana gidanka nd kuma yana jiran ka dawo ya karɓi Muhaira ne kuma ba shi kaɗai bane sunada yawa gabaɗaya ma dai abun nasu da akwai alamar rashin gaskiya saboda haka kar kaje gidan yana tunanin ya haɗa baki dani ne domin na ce masa zan kawo masa Muhaira without ur permission" kallonsa Zaki ya yi sai kuma ya yi murmushi ya ce"daman nasan dole haka zata iya kasancewa kada ka damu ka kasance a tare dashi komai ya kusa zuwa ƙarshe in sha Allah anjima zan yi magana da Sir" gyaɗa masa kai Taj ya yi sannan ya kalli Muhaira wacce tayi tsuru da idanu tana kallonsu murmushi ya yi ta mudubin ya ce"Baby lafiya?" turo baki tayi tana fashewa da kuka harararsa Zaki ya yi ya ce"wannan ma ai rashin mutunci ne kasan da anyi mata magana kuka take amma zaka kulata ni wlh nagaji da jin kukan nan" dariya ya yi ya ce"to na tuba please ki daina kuka kinji" cikin shashshekar kuka ta ce"ni gida zani" Taj ya ce"to kiyi shiru za'a mayar dake kinji" girgiza kai Zaki ya yi bai sake cewa komai ba har suka ƙarasa gidansa dake Al Hamra. Haɗaɗden gidana amma bai kai wancen girma ba kallon gidan kawai Muhaira tayi ganin ba gidan da ta saba zama ba jan hannunta Zaki ya yi ya haura da ita upstairs wani parlon ya buɗe mata ta shiga sannan ya ce"oya kiyi sallah zan kawo miki abinci sai kisha drugs ɗinki" gyaɗa masa kai tayi sannan ya juya ya fita ita kuma ta shige bedroom, zaune ya tararda Taj yana danna wayarsa yana ganin ya fito ya miƙe ya ce" ya kamata na tafi yanzu" numfasawa Zaki ya yi ya ce"inason na tambayeka wani abu daman" Taj ya ce"ina jinka" "a ina ka samo yarinyar nan ne?, sannan wane ya siyar da ita kaine ka sanshi ni bansan wane ne ba please ka nemo min information nasa" gyaɗa masa kai Taj ya yi sannan suka jera suka fita. Kwance ya sameta amma ba bacci take ba tana ganinsa ta miƙe zaune har sannan kuma fuskarta a kumbure take zama ya yi a kan carpet ɗin parlon da hannu ya yi mata alama da tazo ta taso a hankali ta zauna gefensa kamo hannunta ya yi ya zaunar da ita kan cinyarsa ya ɗora kansa bisa wuyanta cikin sanyin murya ya ce"ke dawa? wane ya sakaki kuka?" riƙe hannusa tayi sai kuma ta sake fashewa da wani sabon kuka dafe kansa ya yi ya rungumeta ya ce"ya isa kidaina kukan okay" sosai tayi kuka a jikinsa sannan tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya shafa bayanta ya yi ya ce"now tell me mene yasa kike kuka?" cikin shashshekar kuka ta ce"ni gida zani banason nan ka mayar dani gida" murmushi ya yi ya ce"shine kike rigima?" da sauri ta kalleshi sai kuma ta ɗauke kanta tana turo baki gaba tattausan hannunsa ya sanya ya juyo da fuskarta kallonsa tayi sai kuma tayi saurin rufe fuskarta da hannunta tana faɗawa jikinsa cikin shagwaɓa ta ce"Allah ni bansoo!" murmushi ya yi ya ce"to naji bakiso me kike so?" "Ni kawai ka mayar dani gidanmu Allah" shafa kanta ya yi ya ce"i promise you zaki gida sooner or later" "to ni yanzu yanzu nakeso naje ai" tafaɗa tana ɗago kanta daga jikinsa jan kumatunta ya yi ya ce"to yanzu so kike nazama fly na kaiki gida?" murmushi tayi tana jan cute beard ɗinsa ta ce"to nan a ina muke?" waro idanuwansa ya yi tayi saurin kautar da fusakarsa cikin shagwaɓa ta ce"ni kadaina kallona da wannan idanun naka abun tsoro" dariya sosai Zaki ya yi rabonda ya yi dariya mai yawan haka har ya manta Muhaira kuwa zuba masa idanu tayi kamar ta samu Tv bata taɓa ganin mutum mai kyau da cikar zati irinta Zaki ba yanada wani irin halitta mai matuƙar ɗaukan hankali yanayin jikinsa zaka irin zaton balarabe ne dan ko kaɗan baya kamada hausawa dukda ya iya hausan sosai. Ganin yanda take kallonsa kamar ta samu Tv yasa yakai hannunsa wajen idanunta da sauri ta ture hannunsa ta ce"A'aaaaa kabarni ni" murmushi ya yi ya ce"idanun nawa ne suke baki tsoro?, da idanuna da naki wannan ya kamata ace anji tsoro ke baki kalli naki idanun bane kamar wata mage?" wani kyakkyawan murmushi tayi tana riƙe da gemunsa ta ce"ai kai naka manyane kamar na dodo" "dodo kuma mene ne haka?" ta ce"abun tsoro mana wanda Dadata take bani lbr a tatsuniya" murmushi ya yi yana kama hannayenta ya ƙura musu idanu kamar wanda yake kallon wani abu kallon hannun nata tayi itama sai kuma ta janye su daga hannunsa ajiyar zuciya ya sauke ya ce"in tambayeki?" gyaɗa masa kai tayi ya ce"bani labarin inda kike sannan a ina Taj ya ɗaukoki ina iyayenki?" turo baki ta yi lokaci ɗaya jikinta ya yi sanyi ta ce"Papina ya tafi ya barni Dada tayi ta cemin zai dawo amma bai dawo ba sai kuma Dadata ta mutu tabarni duk sun tafi sun barni banida kowa sai Bani kura shine kawai ya ɗaukeni sannan..." katseta ya yi ya ce"eat ur food first sai ki bani lbrn" gyaɗa masa kai tayi sannan ya miƙa mata plate ɗin abincin kwaɓe fuska tayi bata karɓa ba girgiza kansa ya yi kawai sannan ya ɗauki spoon ɗin ya fara bata abincin a baki lumshe idanunta tayi saboda daɗin da abinci ya yi mata gyaɗa kanta tayi ta ce"unnnn daɗi" murmushi kawai ya yi bai ce mata komai ba dan shi a ƙa'idarsa idan yana cin abinci baya magana sbd haka ne itama ya yi mata shiru. Sosai ta ci abincin ta ƙoshi sannan ya bata drugs ɗinta dakyar tasha hardasu kuka tana gama sha kuma bacci ya ɗauketa a wajen wani zazzafan numfashi ya sauke sannan ya tashi ya fice daga parlon. Kai tsaye ɗakinsa ya shiga yana zuwa ya faɗa bathroom ya yi wanka sannan ya fito shiryawa ya yi cikin wata jallabiya ash colour ya tufke kansa da ribbon ash colour sannan ya ɗauki turaren Creed Aventus ya fesa ƙarar da yaji wayarsa nayi ne yasa ya kalli inda take a hankali ya ƙarasa wajen ya ɗauka shiru ya yi yana kallon sunan dake kan screen ɗin wayar har sannan kuma bai ɗaga kiran ba yana ji har ya katse mamaki ne sosai kan fuskarsa duk da yasan zai iya kiransa amma ko kaɗan bai kawo yanzu ba ƙarar kiran ya sake ji a karo na biyu dafe kansa ya yi kamar wanda aka yiwa dole ya ɗaga shiru ya yi yana sauke wani numfashi daga ɗaya ɓangaren ma haka cikin sanyin murya ya ce"good afternoon sir" cikin kamilalliyar murya mai nuni da kamewa aka ce"Aliyu duk inda kake ka dawo gida" buɗe bakinsa ya yi zai magana yaji wayar ta katse kallon screen ɗin wayar ya yi sai kuma ya ajiyeta yana dafe kansa abubuwa nasan kwaɓe masa dole ne yayi azama ya yi abinda ya kawo shi ƙarar kiran wayar ne ya dawo dashi daga tunanin daya tafi kallon wayar ya yi sai kuma ya ɗaga cikin girmamawa aka ce"sir gamu nan kai muke jira" okay kawai ya ce sannan ya kashe kiran ya tashi ya fice kallon ƙofar apartment ɗinta ya yi sai kuma ya fice daga gidan. Bata farka ba sai wajen ƙarfe 5pm a hankali ta buɗe idanunta tana ambarta sunan Allah tashi tayi daga kan bed ɗin ta shige toilet tayi wanka tayo alwala shiryawa tayi cikin wata abaya data gani black colour ta ɗaura veil ɗinta tayi sallah shiru tayi tana tunani sai kuma ta tashi ta fice daga ɗakin babu kowa a parlon sai kawai tayi waje wata ƙofa ta gani tana facing tata da sauri taje ta buɗeta dan ita tsoron gidan take ji, babu kowa a parlon sai ƙamshi da dake tashi ko'ina tsaf yake bedroom ɗin ta shige da sauri taja wani irin numfashi saboda wani irin ƙamshi dake tashi a ɗakin ga wani irin sanyin AC wanda ya gama ratsa ɗakin a hankali ta cigaba da taka ƙafafunta har taje bakin gadon ta zauna tana bin ɗakin da kallo komai na ɗakin fari ne ta haka tagane yana matuƙar son kala fara dan duk inda zai zauna zagaka farin abu ko coffee wani ƙaton Enlargement tagani a kafe a ɗakin da sauri ta tashi taje wajen ta zuba masa ido tana kallonsa haka kawai kuma ta yi murmushi ta ɗauki lokaci mai ɗan tsayi kafin ta koma ta zauna kallon gefenta tayi taga wata ƙofa aikuwa da sauri ta tashi taje ta buɗe ƙofar, ƙofar ta glasses ce daga ciki kuma wani wajene wanda aka ƙawata shi da kayan kiɗa masu matuƙar kyau da tsada sai wasu kifaye da aka zuba cikin wani glass suna motsi gwanin ban sha'awa da gudu ta ƙarasa wajen ta tsuguna tana zuba musu idanu hakan ba ƙaramin faranta mata rai ya yi ba. Wata drawer tagani daga gefenta haka kawai taji tanason ta buɗe taga mene ne aciki ƙarasawa wajen tayi ta buɗeta wani ƙaton Enlargement ne amma an rufeshi da wata ledar raping da alama ana matuƙar ji da hoton turo baki tayi ta ce"to ya kuma a rufe ni so nake nagani" ajiye tayi ta sake ɗauko wani shima dai kamar wancan ɗin an rufeshi ba'a ganin fƙarfe sake kwaɓe fuska tayi kamar tayi kuka ita kaɗai ta ce"nidai wlh sai nagani meyasa za'a rufesu to?" gyara zamanta tayi a nutse tashiga ɓare hoton kamar an sakata tana gamawa ta juyo dashi tana kalla wowww hotonsa ne cikin wasu riga ɗinkin jamfa da babbar riga sai alkyabba irinta sarakai akansa hannunsa riƙe da wata ƙaramar yarinya kallon yarinyar tayi sai kuma ta ce"kaiiiii wlh sunyi kyau dama ni ce" ita kadai take murmushi dan ba ƙaramin kyau hoton ya yi mata ba ajiyeshi tayi a gefe ta ce"yawwa sauran ɗayan" daga haka ta shiga ɓare wancan shima kamar ɗayan shi ne dai a jikin hoton amma wannan karon shida wani babban mutum ne anyi masa naɗi irin na sarakai fari ne shima kuma kyakkyawa ajin farko dukda ya fara manyanta amma hakan bai hana kyansa fitowa ba wannan karon ɗin ma da wannan yarinyar tsaye a gabansu tana murmushi kana ganinta kaga kyau da kuma zallar hutu tana sanye cikin wata doguwar riga iya gwuiwarta an raba mata gashin kanta gida biyu anyi mata kalba dashi kowanne ɗaya ya zubo kan kafaɗarta sannan an jera stones jajaye akai shafa hoton tayi sannan ta lumshe idanunta batasan ko suwane waɗannan ɗin ba amma duk inda suke sun kasance jininsa ne domin duk kama suke yi dashi abu ɗaya takeson yanzu ta sani shine wane shi???. Haka ta ƙarasa yininta a ɗakin har akayi kiran sallar magrib sannan ta mayar da komai inda ta ganshi ta fice daga wajen anan toilet ɗinsa tayi alwala tayi sallah sannan ta fito parlon ta zauna tayi shiru tana tunane-tunane, har tayi sallar isha'i Zaki bai dawo gidan ba zuwa sannan kuma ta fara tsorata da zaman nata ita kaɗai ganin har 9pm tayi yasa ta fashe da kuka ta takure kanta jikin kujera tana kallon ƙofa tana cigaba da kuka. *FCT, ABUJA* *MAITAMA DISTRICT* Da gudu suka shigo parlon suna zuwa suka rungumeta murmushi Mami ta yi tana kallonta ta ce"ke daɗina dake Aleema wauta" turo bakinta tayi ta ce"kai Mami dan Allah to menayi kuma?" dungure mata kai ta yi ta ce"bansani ba" kallon bayanta tayi sai kuma ta ce"A'a inasu jakadiyar?" taɓe baki Aleema ta yi ta ce"wai Granny ce ta ce su fasa zuwa nazo ni kaɗai ina maee?" girgiza kai Mami ta yi ta kalleta ganin tayi upstairs da gudu, tana shiga ɗakin ta rungumeta cikin jin daɗi ta ce"naji daɗi ganinki sister" shiru Ma'eesha tayi mata tana murmushi tunawa da abinda Granny ta faɗa mata yasa ta fashe da kuka daidai nan Mami ta shigo kallonta ta yi ta ce"Aleema mene yasa kike kuka?" kallon Mami tayi cikin kuka ta ce"Mami da gaske Ma'eesha batajin abinda ake faɗa kuma bazata iya bani amsa ba?" gyada mata kai Mami ta yi ta ɗora hannu aka ta ce" mun shiga uku wlh Mami duk wanda ya yi mata wannan abun Allah ya isa bamu yafe ba kuma wlh sai naje har wajen boka ya tona masa asiri shima kuma ya kurumce" girgiza kai Mami ta yi sannan halin Aleema da shirme ta ce"Aleema ki dinga yin abu irin na mutune kinji" turo baki tayi ta ce cikin shashshekar kuka"haba Mami ya za'a yi a cucemu kuma ace bazamu rama ba wlh duk inda ake nemo boka sai naje na nemoshi ya yi mana maganin duk wanda ya cutar da ita sai inda ƙarfina ya ƙare har mai martaba ma nafaɗawa" girgiza kai kawai Mami ta yi ta ce"yanzu dai ba wannan ba ki tashi kiyi wanka sai ku sakko da ita kuci abinci" okay ta ce sannan ta tashi ta shige toilet ita kuma Mami ta dawo kusada Ma'eesha ta riƙe hannunta ta ce"zaki ci abinci?" gyaɗa mata kai ta yi sai kuma ta ce mata"Khalil zai zo ki shirya" kallon bakinta Ma'eesha ta yi sai kuma ta yi mata alama da hannu tana tambayar wa? "Khalil" Mami ta sake faɗa gyaɗa mata kai tayi sannan ta tashi ta fita. Zaune suke a parlon ya zuba mata idanu yana kallonta ita kuwa ta sunkuyar da kanta kullum son Ma'eesha sake shiga zuciyarsa yake musamman yanzu da son ya haɗa da tausayi yana matukar tausayinta ko kaɗan baya jin daɗi rashin maganarta da kuma jinta amma ya yi alkawarin da zarar an ɗaura musu aure to duk inda magani yake sai yaje ya nemowa Ma'eesha har zuwa sanda ubangiji zai yaye mata bazai gajiya ba. Dukansa ta yi wanda yasa ya dawo daga duniyar tunanin daya tafi da hannu ta tambayeshi mene girgiza mata kai ya yi ta haɗe ranta tana dungure masa kai murmushi ya yi ya kamo hannunta ya riƙe cikin nasa ya ce a hankali"sauran 1week a ɗaura mana aure" tagane abinda ya faɗa hakan yasa tayi dariya har Saida beauty point dinta ya loma sosai yaji daɗin ganin tayi farin ciki ya ce"ki rubuto mana ƙasashen da zamuje" kasancewar a hankali yake maganar yasa take fahimtar abinda ya faɗa gyaɗa masa kai ta yi daidai lokacin Aleema ta shigo parlon zama tayi kujerar dake facing tasu ta ce"wato shine aka tawo ake cin soyayya ko a kirani mu gaisa ko?" murmushi Khalil ya yi ya ce"haba wa ya isa kawai daman jira nake nagama da ita sai na kira ki" harararsa ta yi ta ce"haka fa" murmushi duka suka yi sannan suka cigaba da hirarsu gwanin ban sha'awa wani abun Ma'eesha tana tayasu da sabon yarenta. *MOMMY FOV* Murmushi ta yi tana kallon Farooq ta ce"ni banga abin ɗaga hankali ba bayan in Sha Allah nasara na tare damu" girgiza kansa ya yi ya ce"Mommy u can't understand what I'm talking about Mommy ina magana ne akan Ma'eesha fa, kina gani fa aure zatayi nan da one week kuma kinfi kowa sanin ni ba ƙaunar wannan guy ɗin nake ba kamar yanda shima baya ƙaunata ko kaɗan" tsaki Mommy ta yi ta ce"kai daɗina dakai shashasha ne wlh bakasan abinda kake yiba ina ruwanka da wanda zata aura?, mene haɗinka dashi idan tayi aurenta tayi nesa damu ai shikenan daman ita kaɗai ce matsalarmu kaga idan babu ita komai zai zo mana da sauƙi ita wannan zamu iya sakawa a kaɗata kawai kaga idan muka kashe General duk abinda ya mallaka zai dawo hannunmu mu kaɗai tunda danginsa ba anan garin suke ba kafin su yi tunanin yin wani abu tuni mun bar ƙasar" miƙewa ya yi ya ce"Mommy naji duk wannan amma ni abinda baki sani ba shine indai ina raye to Ma'eesha bazata auri Khalil ba yanda banida damar aurenta haka shima zan haramta masa ita" sakar baki Mommy ta yi tana kallonsa sai kuma ta ce"lahhh kaji shashashan yaro" ko saurarenta Farooq bai tsaya ya yi ba ya yi waje abinsa haɓa Mommy ta kama tana jinjina hali irin na Farooq. Tun kafin ya sakko yake jin dariyarsu yana zuwa ya kallesu ko inda yake Khalil bai kalla ba hakan kuma ba ƙaramin ƙona masa rai ya yi ba dan yaso ya tanka masa ne suyi tashin hankali ganin sunyi kamar basu san da inuwarsa a wajen ba yasa ya juya ya fice yana buga ƙofar da ƙarfi da sauri Ma'eesha ta kalli ƙofar dan ita bata ma ganshi ba ganin babu kowa kuma yasa suka ci-gaba da hirarsu tana binsu da kallo. Shafa kanta Mommy ta yi ta ce"ki daina wannan kukan ke wai wace irin shashasha ce nafada miki shida zaman aure da ita saidai a lahira amma anan dai duniya ya yi kaɗan bai isa ba sbd haka ki kwantar da hankalinki kamar tsumma a randa" cikin kuka ta ce"haba Mommy kullum haka kike cewa amma gashi har yau sauran kwana 6 ɗaurin auren banga ana niyyar fasawa ba ni wlh bazan iya sharing miji da wata ba watar ma kuma kurma wacce koda naci mutuncinta ba jina zatayi ba dan Allah Mommy ki taimaka minnnn!" ɗago fuskarta Mommy tayi ta ce"kawo kunnenki na faɗa miki wani abu" miƙa mata kunnen tayi ta raɗa mata da sauri ta kalli Mommy tana murmushi ta ce"dan Allah Mommy da gaske kike?" gyaɗa mata kai Mommy tayi ta rungumeta tana dariya ta ce"kaiiiii amma naji daɗi sosai Mommy" da sauri Khalil ya saki handle ɗin ƙofar gaba ɗayansa ya jike da gumi kana kallon fuskarsa kasan hankalinsa a tashe yake "Khalil lafiya?" Da sauri suka kalli ƙofar sai kuma suka miƙe tsaye dafe ƙirjinta ta yi ta ce"mun shiga uku Mommy badai sunji ba?" shiru Mommy tayi tana kallon bakin ƙofar murɗa handle ɗin akayi suka shigo suna kallonsu duka His Excellency ne ya ce" _Free pages sun kusa ƙarewa ƴar uwa only 4 pages remain isn't free it's 500# via 9086030007 Hauwa lawan adamu Opay digital service evidence via 08106608363 or 07041901078 ki biya ki karanta cikin kwanciyar hankali akwai special group posting sau biyu a rana with is 1k only karku manta zaku iya fara payment yanzu ƙofa a buɗe take🥳🥳_ _Bamu fara komai ba cikin littafin BA ITA BA CE akwai abubuwan da karantawa kaɗai zai iya fahimtar dakai karku bari a baku labari_ # *BA ITA BA CE* # *Destiny* # *Unconditional love* # *Power* # *SQUAD 2024* # *Nanameera ce ✍️!*. [8/12, 9:18 PM] Nanameera😍✌🏻: *BA ITA BA CE!...💖💖* *Nanameera ce ✍️* *MIKIYA WRITERS ASSO...* ```Page 17&18``` "Lafiya na ganku tsaye?" wata ɓoyayyiyar ajiyar zuciya suka sauke sannan Mommy ta yi murmushi ta ce"daman fita zanyi sai naji an turo ƙofar" kallonta Khalil ya yi sai kuma ya kalli Ramlah wacce take ta binsu da ido ya ce"ki shirya zamuje asibiti" gyaɗa masa kai tayi sannan ya juya ya fita his Excellency ma yabi bayansa dafe ƙirji Mommy ta yi ta ce"Allah nagode maka" numfasawa Ramlah ta yi ta ce"bari naje Mommy" okay ta ce mata sannan ta buɗe ƙofar ta fita ita kuma ta nemi waje nan ta zauna tana tunane-tunane. Kwance ta tarar dashi kan bed ya rufe idanunsa ƙarasawa tayi ta zauna gefen gadon a hankali ta ce"doctor gani" shiru Khalil ya yi mata kuma ba bacci yake ba saida ta maimaita sau uku sannan ya tashi zaune yana kallonta da idanuwansa wanda sukayi ja da Mamaki ta ce"bakada lpy ne?" girgiza mata kai kawai ya yi sannan ya tashi ya shige toilet taɓe baki ta yi sai kuma ta tashi ta fita dan daman bata gama abinda take ba, fitowa ya yi cikin wani yadi maroon colour mai shara-shara ɗinkin jamfa da wando ya ɗora hula zanna akansa fuskarsa maƙale cikin glasses kamar koda yaushe gaba ya yi tana ganin haka tabi bayansa zaune ta sameshi a motar yana danna wayarsa gidan gaba ta buɗe ta shiga sannan ya ajiye wayar yaja motar suka bar gidan. Murmushi Aleemah ta yi ta ce"wlh kuwa Mami nifa na ƙagu ayi auren nan nasan ma gobe ko jibi su Fulani zasu zo" Mami da take tajewa Ma'eesha kanta ta yi murmushi ta ce"ke kam Allah ya shiryaki Aleema in banda abinki ai auren nufine na Allah kuma naga Zahrah ba wani shekaru ne da ita ba, abun da kamar wuya Fulani tazo kinsan dai halinta" taɓe baki Aleemah ta yi ta ce"wlh Mami ita take jawowa kanta bakiga yanda take wulaƙanta samari ba duk kuɗin mutum idan ya ce yana sonta sai ta nemi ta ci masa mutunci kowa ya kasa gane kanta kuma taƙi ta faɗi wanda take so" girgiza kai Mami ta yi ta ce"Allah sarki to Allah ya shiryata maybe Gani take basu yi mata ba ko kuma akwai wanda takeso amma idan ba haka ba ai Zahrah tanada hankali kuma tasan me take" murmushi Aleemah ta yi ta ce"ai ni wlh kullum addu'a nake mata insha Allah sai ta rasa wanda zata aura tunda ita ruwan ido ta tsaya" girgiza mata kai Mami ta yi ta ce"ba'a faɗar haka ki dinga yi mata addu'a tagari" turo baki gaba ta yi batace komai ba har Mami ta kammala abinda take tashi tayi ta kalli Ma'eesha wacce tayi tsuru ta ce" taso muje kici abinci zamuje unguwa" maƙale kafaɗa ta yi alamar bazata jeba tunda ta tashi daman babu wanda ta kula hatta General daya shigo dubata bata kulasa ba, kamo hannunta Mami ta yi suka fice daga wajen sanin inda ta ita ne bazata tashin ba. Kallon Aleemah ya yi wacce take sanye cikin wata doguwar riga ta atampa me ɗan kama jiki kallo ɗaya ta yi masa ta ɗauke kai dan ita daman bata wani ƙaunarsa duk sanda tazo gidan batason abinda zai haɗata dashi har tayi gaba taji ya ce"Aleemah" tsayawa tayi amma bata juyo ba takowa ya yi cikin tafiyarsa ta isa ya tsaya a gabanta haɗe hannayenta tayi a ƙirji ta zuba masa idanu ɗan cute smile ya yi ya ce"ya kike?" "Lpy" cewar Aleemah numfasawa ya yi ya ce"daman inason magana dake idan babu damuwa please" ta ce"ina jinka" Farooq ya ce" mu ɗan zauna mana please" ɗaga kafaɗa tayi sannan ta zauna kan ɗaya daga kujerun da akayi ado dasu a garden ɗin zama ya yi shima yana facing ɗin ta ya ce" na daɗe inason na samu damar faɗa miki abinda ke cikin raina amma sai nake ganin kamar bazaki aminta dani ba, wlh Aleema ina matukar sonki tun ba yau ba dan Allah kar kiyi rejecting soyayya ta please leema" tunda ya fara magana Aleema take kallonsa with so much surprised koda wasa bata taɓa tunanin haka daga gareshi ba duba da yanda yake maganar zaka fahimci har cikin zuciyarsa haka yake nufi miƙewa ta yi ta ce"I'm so sorry amma ni ban taɓa soyayya ba and kuma banajin zan iya farata yanzu coz karatu shine abinda nake focusing yanzu dan Allah ka fahimceni" tana gama faɗin haka ta juya tabar wajen da kallo kawai Farooq ya bita sannan ya girgiza kansa wani killer smile ya yi ya ce"karki damu yarinya da sannu zaki zo hannuna" ya tashi ya yi waje dan daman fita zai yi "Me kika tsaya yi?" numfasawa ta yi ta ce"wlh Mami na ɗan tsaya magana da Farooq ne" "Farooq kuma mene ya haɗaki da magana dashi?" murmushi ta yi ta ce"Mami karki damu" taɓe baki Mami ta yi ta ce"kije ku ci abinci zuwa anjima Khalil zai zo ku fita nima yanzu fita zanyi" okay Aleema ta ce sannan ta shige ciki, Da sallama ta shiga zaune ta tarar da Mommy tana danna wayarta da alama magana mai muhimmanci take tana ganin Mami ta tashi tana murmushi ta ce"sannu da zuwa" zama Mami ta yi ta ce"yawwa " "ya jikin Ma'eesha?" murmushi Mami ta yi ta ce"da sauƙi Alhamdulillah yau ne dai ta tashi da abun dan taƙi kula kowa" girgiza kai Mommy ta yi ta ce"Allah sarki ubangiji ya yaye mata cikin sauƙi" "Ameen" cewar Mami, Mommy ce ta ce"yawwa daman munyi magana da talatu ta ce za'a samu kayan" "Nima daman abinda ya kawoni kenan zuwa anjima idan kin shirya zamuje siyan ragowar wanda akayi order kuma sun zo to za'a je jere in sha Allah" murmushi Mommy ta yi ta ce"Allah sarki Ma'eesha da yanzu tana ta surutu kala-kala ta ce wannan ta ce wancen, to Allah ya kaimu anjiman daman babu abinda nake" okay Mami ta ce Sannan ta tashi ta fita. Murmushi Mommy ta yi ta ce"dani kike zancen Asma'u". Ƙarfe 5pm Khalil ya iso gidan har parlon ya zo ya kama hannun Ma'eesha suka fita shida ita suna gidan gaba Aleema kuma na gidan baya har suka isa mall ɗin babu wanda ya ce komai a cikinsu kowanne da abinda ya dameshi. Siyayya sosai suka yo duk wani abu na nau'in kaya babu wanda Khalil bai siyawa Ma'eesha ba wani abun ita take nunawa wani kuma shi yake zaɓar mata hatta Aleema saida ya siya mata sai wajejen 6:30pm suka bar wajen kai tsaye kuma wani park ya kai su wajene wanda aka ƙawatashi da kayan wasan yara irinsu lilo, swimming pool da masu kayan wasan sannan akwai nau'i na abinci kala-kala a wajen zama sukayi kan kujeru suna Kalle-Kalle ya yi hakane kuma sbd ya ɗauke hankalin Ma'eesha dan Mami ta faɗa masa halin da take ciki dukansa ta yi hakan yasa ya juyo yana kallonta ya ce"mene ne?" turo baki ta yi sannan ta nuna masa can gefe inda akayi wani waje ana siyarda ice-cream kallonta ya yi sai ya ce"za ki sha?" da sauri ta ɗaga masa kai dungure mata kai ya yi ya ce"kinsan ai bakida lafiya ko sbd haka bazan siya miki ba" kuka ta sanya masa amma ya yi mata banza dan daman shi haka halinsa yake inda ya ce bazai abu ba to kome za'a yi bazai yi ɗin ba babu irin kukan da Ma'eesha batayi amma ya yi funfurus popcorn kawai ya siya musu suka bar wajen ana kiraye-kirayen sallar magrib ya yi parking fita Aleema ta yi ta shige cikin dan duk a gajiye take, murɗa handle ɗin ƙofar tayi taji a rufe hakan yasa ta juyo ta kalleshi da idanunta da suka yi jajur alama tayi masa daya buɗe motar ya girgiza mata kai jawota ya yi yana gyara zamanta a kan cinyarsa ya ɗago fuskarta hannu tasa ta tureshi tana fashewa da kuka yasan fushi take dashi murmushi ya yi yana haɗe jikinsa da nata ya rungumeta yana shafa kanta sosai tayi kuka a ƙirjinsa kafin ya sake ɗago fuskarta ya yi coping da tasa suna sauke numfashi a tare saurin janye fuskarta tayi saboda wani iri da taji a jikinta murmushi Khalil ya yi ya juyo da fuskarta ya kama kunnensa alamar ta yafe masa ɗauke kanta tayi hawaye na zirarowa kan kuncinta dafe kansa ya yi ya ce a hankali"I'm sorry eeshana" kallon bakinsa tayi sai kuma ta nuna masa ƙofa alamar ya buɗe mata da hannu shima yayi mata alama da ta yafe masa saurin gyaɗa masa kai tayi dan Allah Allah take tabar motar buɗe mata ya yi yana gani ta sauka da sauri ta shige parlon daidai nan Farooq ya fito da kallo yabi motar yana gani har securities suka gama kwashe kayan dake motar suna shiga dashi gidan sannan ya juya ya bar gidan taɓe baki Farooq ya yi yana kallon uban kayan da suke shigowa dashi ko ba'a faɗa masa ba yasan ba ƙananan kuɗi aka kashe ba furzar da wani zazzafan numfashi ya yi sannan ya buɗe motarsa ƙirar coralla ya shiga da wani irin speed ya bar gidan. "Haba Aleema wannan kayan ai sunyi yawa" Turo baki ta yi Fulani ta ce"babu wani yawa da sukayi daman haka akewa kowace ƴa idan za'a aurar da ita" murmushi Mami ta yi tana kallon mahaifiyartata sai kuma ta ce" to shikenan ai" dariya Aleema ta yi ta ce"Fulani kice ta ɗaga ki" kallonta matar tayi kyakkyawace sosai kuma sannan kamarsu ɗaya da Mami dan harma tafi Mami kyau kana ganinta kasan ta manyanta sosai amma kuma kuɗi da mulkin daya zauna musu shine abinda ya ɓoye tsufan nata Fulani kenan mahaifiya a wajen Mami kuma matar sarkin Katsina marigayi Alhaji Aliyu ɗan sarari ya yi tashen kuɗi a lokacinsa dan babu wani sarki wanda ya kai shi a arziƙi a lokacin yanzu kuma ɗansa Alhaji Ahmad Aliyu shine wanda yake karagar mulkin mace ce mai faran faran da jama'a musamman jikokinta suna matuƙar jin daɗin zama da ita kasancewar sunanta aka sawa Ma'eesha yasa take matuƙar sonta duk cikin matan sarki na wannan lokacin babu wacce ta kaita ƙarfin iko dan ita ce wacce mai martaba yafi so kasancewar da ita ya yi aure tun saurayi da budurwa kuma ita ƴar sarki ce wannan kenan. Hararar Aleemah ta yi ta ce"ai sai kizo ki sanya ta ɗagani ja'ira kawai" gwalo Aleema ta yi ta ce"ke kam kin fiye rikicin tsufa wlh ko mema kika zo yi nan ohho!" Cikin kunfar baki Fulani ta ce"ubanki Mahamuda shi nazo yi nan ja'irar yarinya kawai" buɗe baki ta yi zata sake magana Mami ta ce"ke shiga hankalinki uwartawa kika mayar abar wasanki" da sauri Fulani ta ce"a'a kekam Asma'u banson ƙin Allah idan banyi wasa da jikokina ba dawa zanyi wasa kinsan dai su kaɗai gareni" girgiza kai Mami ta yi dan ta fuskanci rikicinta ne ya tashi hakan yasa ta miƙe ta ce"to Mama bari na kawo miki abinci" ta ce"ai da nayi zaton babu abinci a gidan ne nasa a kiramin janar din naji dalilin da zai barki da yunwa" tuntsirewa Aleema ta yi da dariya ta ce"to ke Fulani idan baya basu abinci ina ruwanki" banza Fulani tayi mata tana shafa kan Ma'eesha wacce bacci ya ɗauketa. Daren ranar basu kwanta da wuri ba sbd hirar Fulani hatta Ma'eesha da ba jin abinda take cewa tayi ba saida ta zauna tana kallonta idan taga tayi wani abun tayi dariya saida Mami ta zo ta lallaɓa Fulani sannan ta kwanta, da sassafe kuma masu gyara jiki suka dira a gidan part guda Mami ta ware musu aka basu abinci sannan aka kai Ma'eesha wacce take ta kuka dan harga Allah baso take ba yinin ranar bata fito ba dan hanata suka yi sai wajen magrib sannan ta sanya kuka dole suka barta ta tafi tana zuwa ta kwanta jikin Fulani wacce take ta mita ta gyaran jikin wai an ɗauke mata ita Ita dai Mami batace mata komai ba sai Aleema ce take janta. Haka aka dinga yi mata gyaran jikin har ya rage sauran kwana uku a ɗaura aure kasancewar ba wani fita zasu yi ba tunda batada lafiya yasa aka ɗauko mai henna tazo har gida tayi musu ita da Aleema washegari da azahar tawagar Mami suka iso gidan ciki harda matar sarki Hajiya A'isha mace mai karamci da Mutane ba bahaushiya bace ta kasance balarabiya dan lokacin da sarki yaje Makkah gidansu abokinsa ya ganta ya ce yana sonta bai baro ƙasar ba saida aka ɗaura musu auren da ita. Tuni gidan General Ibrahim Tijjani mai Zamani ya cika maƙil da manyan mutane kowa sai hada-hadarsa yake a cikin gidan Ma'eesha kuwa tana part ɗin General dan ko kaɗan batason taron mutane ranar da akayi mata henna da rana aka ɗauko photographers aka dinga ɗaukanta hotuna tayi kyau cikin lufayar da aka ɗaura mata purple colour gashin nan yasha gyara ya zubo har gadon bayanta sai sheƙi yake yi ƙunshi mai matuƙar kyau aka yi mata sai murmushi take musamman sanda taga su Fateemah sun zo hakan ba ƙaramin faranta mata rai ya yi ba. *RIYADH* *AL HAMRA RESIDENCE* Kallonta ya yi ganin yanda take faman kuka kamar ƙaramar yarinya a kwana biyun nan gaba ɗaya ta hanashi sukuni gashi yanzu ko kaɗan baya samun lokacin kansa abubuwa duk sun sha masa kai gajiya ya yi da jin kukan kawai ya kashe light ɗin daƙin duhu ya mamaye ko'ina cikin wata iriyar murya ya ya ce"ga dodo nan"da gudu Muhaira ta taso tana zuwa ta shige cikin blanket ɗin ta cukwuikuyeshi tana sakin kuka shafa kanta ya yi a hankali ya ce"ya isa to kiyi shiru karya kamaki" ajiyar zuciya ta shiga saukewa tana sake shigewa jikinsa dan gaba ɗaya a tsorace take cikin kuka ta ce" ni ka kaina gida Papi banso nan ka tafi dani Allahhhhh!" numfasawa ya yi ya ce"bana faɗa miki xan kai ki ba gidan wa zamu ce idan munje garin naku?" turo baki tayi ta ce"ni banida gida kawai kasuwa Gashua zaka kaini wajen Mama mai abinci anan nake kwana" da mamaki ya kalleta cikin duhun ya ce"wace haka?" turo baki ta yi ta ce"ni duhuuu" murmushi ya yi sannan ya kunna dum light hakan yasa ɗakin ya yi wani irin blue ya kalleta ya ce"now tell me wace ita?" Numfasawa tayi sannan ta fara bashi lbrn rayuwarta tun daga farko har zuwa sanda Taj ya saceta ba ƙaramin tausayi ta bashi ba dan bai yi zaton hakan zai iya kasancewa da mutum ba cikin kuka ta ce" dan Allah Papi karka kaini wajen Bani kura wlh banaso bazan iya aurensa ba dan Allah Papi kasuwa zaka kai ni" rungumeta ya yi ya ce"ya isa haka stop crying sleep kinji" yana ji tana shashshekar kuka har bacci ya ɗauketa shafa kanta ya yi sannan ya gyara mata kwanciyarta ya rufeta da duvet ya kashe AC ya fito parlon kai tsaye kitchen ya shiga ya haɗa coffee sannan ya fito ya shiga wani daƙi gaba ɗaya bangon ɗakin an rubuceshi wani wajen kuma an maƙala hutuna babu haske a ɗakin hakan yasa ba komai ake iya gani ba zama ya yi akan wata kujera da table a gabansa ya buɗe system ɗin ya shiga dannawa a hankali yana sipping coffee ɗinsa sai wajen 3am sannan ya tashi daga wajen ya rufe system ɗin ya fito kai tsaye kuma toilet ya shiga ya yi wanka ya ɗaura alwala sannan ya shirya cikin wata embroidery Jallabiya Black colour ya shimfiɗa prayer mat ya shiga sallolinsa na nafila har lokacin kiran asubahi ya yi saida ya tasheta sannan ya fita dan gabatar da sallar a masjid bayan ya idar kuma ya zauna karatu bai shigo gidan ba sai wajen 6am kai tsaye kuma kan kujera Three seater ya kwanta ya lumshe idanunsa nan da nan bacci ya ɗaukeshi. Ringing ɗin wayarsa ne ya farkar dashi yana ɗagawa ko sallama bai yiba ya ce"ohk I'm coming" ya ajiye wayar ya shiga bedroom kai tsaye bathroom ya shiga ya yi wanka sannan ya fito ya shirya a gurguje kallonta ya ya ganin yanda take bacci hankali kwance kasancewar ranar weekend yasa bai tashe ba ya yi waje. Murmushi Dmash ya yi bayan yaga shigewar motar Zaki ya yiwa drivern magana suka shiga gidan kasancewar gidan babu wasu securities sai mai gadi yasa ya ce masa wajensa yazo sanin yasan yana zuwa wajen nasa yasa bai hanasu shiga ba, shiga cikin gidan ya yi mutanensa na biye dashi kana ganinsu kaga marasa mutunci da imani kallon parlon ya yi ganin babu kowa a ciki yasa ya haye upstairs kai tsaye kuma bedroom ɗin ya nufa yana shiga hangota kwance tana sharar baccinta hankali kwance lumshe idanu ya yi yana cije baki sai kuma ya yi wani killer smile ya ƙarasa gabanta cikin takunsa na isa yana zuwa ya sanya hannunsa ya yaye bargon jikinsa runtse idanuwansa ya yi ganin surar jikinta dan ƴar ƙaramar sleeping dress ce a jikinta wata dariya ya saki sannan ya. _Free pages sun kusa ƙarewa only two pages remain 😂 you can start making ur payment via 9086030007 Hauwa lawan adamu opay 500# for normal group 1k for VIP posting sau biyu a rana ki biya sister bazakiyi dana sani ba nayi muku alqawarin haka🤝😍_ _BA ITA BA CE!_ # *SQUAD 2024* # *Power* # *Unconditional love* # *Trafficking* # *Nanameera ce ✍️!* [8/13, 11:43 AM] Nanameera😍✌🏻: *BA ITA BA CE!...💖💖* *Nanameera* *MIKIYA WRITERS ASSO...* ```Page 19&20``` *Last free pages* A firgice Muhaira ta farka tana kallonsu ɗaya bayan ɗaya sai kuma ta saki wata razananniyar ƙara hawa kan gadon ya yi ya riƙe hannunta cikin sanyin murya ya ce"hyyy I'm not here to hurt you kinji" gyaɗa masa kai ta yi da sauri dan gaba ɗaya a tsorace take murmushi Dmash ya yi sannan ya ce"tawo muje" cikin rawar murya ta ce"in...ina?" bai ce mata komai ba ya kama hannunta suka sauka daga kan gadon tsorone fal fuskar Muhaira sai dube-dube take ko za taga Zaki amma bata ganshi ba suna fitowa compound ɗin gidan ta zare hannunta daga nasa tana kwaɓe fuska kallonta ya yi sai ya yi murmushi cikin sanyin murya ya ce"mene ne?" "ni Papi zani" numfasawa ya yi Sannan ya ce"to ai nima wajensa zan kai ki" langwaɓar da kai ta yi ta ce"nidai mu jira shi a nan" dafe kansa ya yi ya ce"to ai shima yana can yana jiranmu Muhaira kinga let's go" turo baki tayi sannan ta zauna kan wata kujera tana haɗe rai ta ce"ni dai ya ce na dinga jin magana kuma ai bai cemin na fita ba kaga idan na fita faɗa zai yimin kawai ka kirashi shi ya zo" shiru Dmash ya yi yana saurarenta ya fuskanci bazata taɓa yarda ya fita da ita ba dan da alama tanada kafiya da gardama da idanu ya yiwa wani yaronsa magana gyaɗa masa kai ya yi sannan ya ƙarasa ta bayanta wani gyaɗa ya rufa mata a fuska nan da nan idanunta suka rufe baya tayi zata faɗi ya yi saurin tare ta tunda mai gadin yaga haka ya yi saurin kiran wayar Zaki amma baya picking hakan yasa ya rasa yanda zai yi yana kallon sun ɗaukota ya ƙarasa wajen duk da tsoron da yake ji cikin dakkakiyar murya ya ce"Sir ina zaku tafi da ita" kallonsa yaran sukai dan tuni Dmash ya shige mota girgiza kai ya yi ya ce"aikuwa babu wanda ya isa ya fita cikin gidan nan har sai mai gidan ya dawo" taɓe baki Dmash ya yi ya kalli Drivern ya ce"what are you waiting for?" girgiza kai ya yi a nutse ya ce"shot him" ƙarar bindigar da naji shine yasa na kalli wajen amma me sai naga gateman ɗin a kwance cikin jini yanata kokawa da numfashi ko second ɗaya basu ƙara ba a cikin gidan suka fita, Above 10mins kafin Zaki ya ƙaraso gidan cikin wani irin speed ya ƙarasa wajen mai gadin tsugunawa ya yi ya riƙeshi dan tun sanda ya tura masa msg hankalinsa yake a tashe dukan kumatunsa ya yi ya ce"si... Sir I'm sorry nakasa cetonta" girgiza kai Zaki ya yi"don't worry john isn't ur fault" wani irin jan numfashi ya yi yana rike hannun Zaki ya ce"Sir na sanka karka barshi kar ka rabu dashi kada ka bari yallaɓai nasan zaka iya kaji..."tari ne ya turnuƙeshi ya yi saurin sakin hannunsa riƙo fuskarsa Zaki ya yi ya ce"don't worry john yanzu zan kai ka asibiti kaji zaka samu lpy" kallonsa ya yi da idanuwansa wanda suka sauya kala sun rine sunyi jajur dasu ya girgiza masa kai yana murmushi a hankali kuma ya sauke wani wahalallen numfashi kansa ya yi baya runtse idanunsa Zaki ya yi for some seconds kafin ya buɗe su ya kalli fuskar John wacce a yanzu ta zama gawa daidai nan securities suka shiga shigowa gidan da guards ɗinsa bai ce musu komai ba ya shige gidan su kuma suka ɗauke John daga wajen. Kai tsaye bathroom ya shiga yana zuwa ya sakarwa kansa shower ta ruwan sanyi yana jin yadda ruwan ke ratsa kowace ƙofa ta jikinsa hannayensa ya tura cikin gashin kansa wanda shima ya gama jiƙewa da ruwan ya jima sosai a haka kafin ya kashe showern ya yi wanka sannan ya fito sanye da bathrobe Acn ɗakin ya kunna nan da nan wani irin sanyi ya mamaye ɗakin kai tsaye kan royal bed ɗin ya kwanta yana lumshe idanunsa above 10minutes kafin wani baccin wahala ya ɗauke shi. A firgice ta farka tana bin inda take kwance da kallo kafin kuma ta fashe da wani irin kuka mai gunji nan take ta fara birgima a ƙasa tana kiran sunan Papi buɗe ƙofar a kayi ya shigo hannunsa riƙeda mug da sauri ya ƙaraso gabanta ya ajiye mug ɗin a kan table sannan ya kamo hannunta turewa tayi cikin kuka ta ce"ka barni ni karka sake riƙeni ni wajen Papina zani" ta ƙarashe maganar tana fashewa da kuka janyota Dmash ya yi ya shaƙe wuyanta cikin kakkausar murya ya ce"keee I'm not ur mate duk ranar da kika sake yimin tsawa saina kasheki" iyaka tsorata Muhaira ta tsorata hakan yasa ta haɗe jikinta waje guda sai rawar sanyi take tuni fa fara ficewa hayyacinta tsaki ya yi sannan ya juya ya fice daga ɗakin kai tsaye kuma nasa ɗakin ya nufa dan yau babu abinda zai hanashi karɓar budurcinta. Ƙarar Alarm ce ta farkar dashi a hankali ya buɗe idanunsa ya ɗauki aƙalla awanni 3 yana baccin kuma ba ƙaramin daɗin hakan yaji ba tashi ya yi bakinsa ɗauke da addu'a ya shige toilet wanka ya sake yi sannan ya fito ya shirya cikin wasu suit black colour ko tsayawa gyara gashinsa bai yi ba ya juya ya yi waje, yana zuwa aka buɗe masa mota ya shiga gidan baya kafin drivern ya ja motar da gudu suka bar wajen tun a mota ya buɗe system ya shiga dannawa a hankali kuma tym to tym yake magana da mutane a waya a haka har suka ƙaraso gidan nasa yana shiga ya yi apartment ɗin su Tyha zaune ya samesu suna hirar cikin sanyin murya suka gaishe shi gyaɗa kansa ya yi sannan ya ce"get ready" ok sukace masa sannan ya juya ya shige apartment ɗinsa zaune ya samu Taj ya shirya cikin wasu English wears murmushi kawai ya yi masa sannan suka gaisa babu wanda ya sake cewa komai a Cikinsu shi ya yi sama shi kuma Taj ya yi waje. *ASOKORO VILLA* *RAMLAH POV* Cikin shashshekar kuka ta ce"ni Mommy nagaji da jin wannan maganar da kike faɗa min kina gani fa gobene ɗaurin auren amma babu wani abu da kika yi wlh Mommy zan iya mutuwa idan Khalil ya yimin kishiya ni bazan jure ba mutuwa zanyi Mommy" ta ƙarashe maganar tana rushewa da wani sabon kukan murmushin takaici Mommy tayi ta ce"kenan Ramlah kina ganin kamar na gaza ne ko?, kina tunanin zan bari Khalil ya yi aure kenan ko?, kenan duk baki yarda da abubuwan da nake miki ba kenan idan ba daban ni ba babu yanda za'a yi Khalil ya aureki dan ko mahaifinsa bazai yarda ba amma yanzu akan wannan ɗan ƙaramin abun kike ɓata ranki nima nawa yana ɓaci bari kiji indai aka ɗaura auren Khalil da Fateemah gobe to na yadda ki sauyani a matsayin uwa!" da sauri Ramlah ta kalleta ta gyaɗa mata kai rungume mahaifiyartata tayi tana goge hawayen fuskarta ta ce"thank you Mommy" murmushi tayi sannan ta ɗago fuskarta ta ce"tashi ki tafi ki kwanta dare ya yi sosai" gyaɗa mata kai kawai tayi sannan ta tashi ta fice daga ɗakin ajiyar zuciya Mommy ta sauke sannan itama ta tashi ta fita. *MAITAMA DISTRICT* *MA'EESHA POV* A hankali take tafiya a cikin gidan ko ina ya yi shiru kowa ya kwanta bacci dan lokacin wajejen 12am ne tura ƙofar tayi a hankali kwance ta samesu suna bacci ƙarasawa tayi ta tsuguna wajen General ta dakeshi da hannu da sauri ya buɗe idanunsa kallonta ya yi da mamaki sai kuma ya tashi zaune hasken ɗakin ya kunna yaga ta zuba masa idanu tana kallonsa murmushi ya yi ya ce"meya faru?" tura baki tayi gaba batace masa komai ba, Mami wacce ta farka sannan ta kallesu ta ce"lafiya?" ɗaga kafaɗa ya yi ya ce"i don't know kawai ganinta nayi" da hannu Mami tayi mata alama da tazo tasowa tayi ta zauna gefenta Mami ta kalleta ta ce"mene ne?" girgiza mata kai Ma'eesha tayi sai kuma ta nuna mata bacci za tayi Mami ta ce"muje na rakaki ɗaki ki kwanta" tura baki tayi sai ta nuna mata kan gadon General ne ya ce"a nan zaki kwanta" da sauri ta gyada masa kai ya yi ya ce"common" tashi tayi ta kwanta kan cinyarsa yana shafa kanta not too long bacci ya ɗauketa tashi Mami tayi ta ce"bari a mayar da ita ɗaki" girgiza kai General ya yi ya ce"barta ta kwana a nan ɗin tunda haka take da buƙata" shiru Mami tayi sai kuma ta koma ta kwanta kasancewar gadon babba yasa ya ishesu suka kwanta duk su ukun rabonda su kwana tare da ita tun kafin ta fara zuwa makaranta sai gashi yau tarihi ya maimaita kansa. *RIYADH* *Al takhasosi residence* A hankali ya kalli mudubin dake maƙale a bangon wani killer smile ya yi sannan ya juya ya fita yana murɗa handle ɗin ƙofar wayarsa ta fara ƙara ɗan siririn tsaki yaja kafin ya kalli screen ɗin ganin sunan Taj yasa ya ɗaga ya ce"ya akayi Taj?" daga ɗaya ɓangaren Taj ya ce"sir da alama yau kana cikin farin ciki dan naji a muryarka" murmushi Dmash ya yi ya ce"tunda kabani farin ciki ai dole nayi" Taj ya ce"Sir ina gidan yanzu please kazo it's something important nd ka tawo da Muhaira dan kowane lokaci Zaki na iya kawo maka farmaki ina wajen da aka saba gudanar da taro kowa ya hallara kai kaɗai ake jira" okay Dmash ya ce sannan ya kashe wayar tura ƙofar ya yi ya shiga dakin zaune ya sameta inda ya barta gaba ɗaya idanunta sun kumbura saboda kuka dan murmushi ya yi sannan ya kamo hannunta bin bayansa Muhaira tayi tana Kalle-Kalle dan ita gaba ɗaya a tsorace take dashi tunda yace zai kasheta burinta bai shige taga Papinta yazo ya rabata da wannan wajen ba. Babban ɗakin taro ne mai matuƙar kyau da haɗuwa kana kallon wajen kasan an kashe iyayen kuɗi wajen haɗashi wasu manyan mutane ne zaune a parlon kowannesu yana sanye da suit ko ba'a faɗa maka ba kasan ba talakawa bane dan kana ganinsu kaga kuɗi, tashi Taj ya yi yana murmushi ya ce"welcome Sir" jinjina kai ya yi sannan ya nemi guri ya zauna da kallo Muhaira ta bi Taj amma sai taga ko kallonta bai yi ba hakan yasa ta sunkuyar da kanta hawaye na zubo mata, tattauna suka shiga kan abinda ya shafe su Taj ya ce", yanzu ma na tawo muku da wasu ƙarin matan ai" dafa kafaɗarsa Petor ya yi ya ce"weldone Taj" murmushi kawai ya yi sannan ya miƙe ya ce"I'm coming" ya juya ya fice daga parlon kallonsu Tyha ya yi ya ce"come out" okay sukace sannan suka fito daga motar suka bi bayansa miƙewa tsaye sukai duka ɗan daso ya ce"wowwwww wannan tayi min kyau sosai" ya faɗa yana kallon Zeey, sunkuyar da kansu suka yi Taj ya ce"Nima nasani sir shiyasa na samo muku latest waɗanda nasan zaku ji daɗinsu fiye da ƙima" wata dariya suka yi sannan Dmash ya ce"Taj aikinka yana kyau akwai wata kwangila da nakeson na baka" murmushi ya yi ya ce"okay sir Ina ji" Dmash ya ce"ina son ka kashe Zaki idan kayi haka nikuma nayi maka alƙawarin baka ragamar daularmu wacce yanzu take hannun Zaki" miƙewa Muhaira tayi cikin kuka ta ce"a'a wlh bazai karɓa ba hamma Taj nasan ai bazaka kashe Papi ba ko?" ta faɗa tana riƙe hannun Taj wata kyakkyawar tsawa Taj ya yi mata wacce ta sanya tayi baya tana fashewa da kuka kallonsa Dmash ya yi ya ce"why zaka mata tsawa sai ka ce mata Eh" girgiza kai Taj ya yi yana miƙewa tsaye ya ce"i can't Sir coz bana ƙaunar yarinyar nan na tsaneta kamar yanda na tsani Zaki" tashi Dmash ya yi yana kallonsa ya ce"wannan ba hujja bace karka sake irin haka" murmushi Taj ya yi ya ce"idan kuma nasake fa?" da mamaki duk suke kallonsa Petor ya ce"Taj kaji abinda ka faɗa kuwa" kallonsu ya yi sai kuma ya dafe kansa ya ce"oh I'm sorry sir I thought da Zaki nake magana" okay sukace daidai lokacin suka fara jiyo ƙarar harbi da mamaki duk suke kallon ƙofa Dmash ya ce"what happened?" girgiza kai Taj ya yi alamar bai sani ba turo ƙofar da aka yi ne ya sanya suka kallo ƙofar da sauri sanye yake cikin wasu uniform na sojoji wanda sukayi matuƙar yi masa kyau baki buɗe duk suke kallonsa da sauri su Tyha suka sara masa irin yanda akewa babba idan anganshi da sauri Dmash ya kalli su Petor wanda yaga sunyi the Same irin abinda su Tyha sukai ciki harda Taj takowa ya yi cikin parlon yana taku na isa da taƙama hannayensa zube cikin aljihun kayan jikinsa baki na rawa Dmash ya ce"hii...hy..you" murmushi Zaki ya yi ya ce"kayi mamakine?, ai banyin tunanin zakayi mamaki ba Sir Fahad Dmash nayi zaton ai kanada dakakkiyar zuciya" girgiza kai Dmash ya yi ya ce"ya akayi ban ankara da wuri ba?, meyasa na yarda dakai Zaki?" ɗaga kafaɗa Zaki ya yi ya ce"call my real name" kallon tag ɗin jikin rigarsa ya yi sai kuma ya ce"General Aliyu Ahmad Aliyu" "Yes it's my name ka ɗauka duk tsawon lokacin dana bata tare dakai sbd ina son harƙalla dakai ne?, koda wasa baka taɓa burgeni ba gabaɗaya na tsaneka ina rayuwa dakai ne kawai sbd hakan ya zame mini dole ka gagari mutane dayawa an turo sojoji babu adadi amma ƙarshe saidai su rasa rayuwarsu a banza sbd haka nayi alƙawarin na daina aiken kowa da kaina zanyi maganin abun. A duk sanda muka haɗu dakai ina jin kamar na fasa kwanyar kanka a wannan lokacin saidai wata zuciyar ta hanani ban shigo rayuwarka ba saida nagama sanin komai naka a tunaninka kai ne ka jawoni cikin rayuwarka amma kayi kuskure dan ni ne wanda na jawoka cikin tawa rayuwar kuma yanzu zan miƙa ka ga hukuma" wata dariya Dmash ya yi sannan ya ce"haba kai ma kayi irin wannan dabarar ballantana ni" yana faɗin hakan ya ɗora bindiga kan Muhaira yana shaƙeta ya ce"ko ku rabu dani ko kuma na harbeta" murmushi Zaki ya yi yana tsaye inda yake ya ce"taya zaka yi harbi bayan babu komai a cikin bindigar?" kallon gun din Dmash ya yi shidai yasan ya zuba bullet a ciki amma ya kasa yarda da abinda Zakin ke faɗa masa cikin zafin nama Zaki ya ƙarasa gabansa ya finciketa yana buga masa kan gun aka riƙe kansa ya yi yay baya zai faɗi Taj ya tareshi yana murmushi ya ce"haba sir naga zaka fadi har kayi give up?" girgiza kai Dmash ya yi daidai lokacin yaransa suka shigo parlon without second thought kuma suka fara buɗe wuta hannun Taj Zaki ya kama ya danƙa masa Muhaira ya ce"go" girgiza kai Taj ya yi ya ce"mu bar ka anan sir?" gyaɗa masa kai ya yi Taj ya ce"no sir I can't" "Taj!! ba shawara nake baka ba" sara masa ya yi sannan yaja hannun Muhaira suka fita daga parlon. Duk yawancinsu saida Zaki ya harbesu duk ba baya harbin inda mutum zai mutu dan a raye suke buƙatarsu yana yi Petor na tayashi saida suka rage sai su biyu sannan suka tsaya taɓa shi Petor ya yi ya joyu ya ce"Sir ka tuna?" girgiza kai Zaki ya yi ya ce"sanda ka kashe Smallo he's my brother sbd shi na shiga hukumar sojoji kawai dan na ɗaukar masa fansa" buɗe baki Zaki ya yi zai magana ji kake tassssss ƙarar shigar bindigar cikin ƙirjinsa da gudu Taj suka ƙaraso da wasu tarin sojojin garin Saudiyya Petor na ganin haka ya dasa gun din akansa ya kashe kansa zubewa Muhaira tayi awajen tana zunduma ihu ta shiga jijjiga Zaki wanda yake kwance baya ko numfashi sai jini ne yake zuba a ƙirjinsa rungumeshi tayi tana kuka kamar ranta zai fita take kiran"Papi!! Papina ka tashi ka tashi dan Allah kaima tafiya zaka yi ka barni?? kaima su Dada zaka bi?? Papi wake up ka tashiiiii don't leave me alone please Papinaaaa!" ko alamar motsi Zaki bai yiba har sannan kuma banda jini babu abinda ke gudu a jikinsa gaba ɗaya ta bata jikinta da jininsa da sauri Taj ya zo ya janyeta yana girgiza mata kai cikin kuka ta ce"hamma Taj ka cewa Papi ya tashi ya tashi mu gudu" shiru Taj ya yi mata dan bashida amsar bata koda ace shi ba likita bane zai iya faɗa cewa kai tsaye Zaki ya tafi domin duba da inda aka yi masa harbin balle kuma shi da yake likita wasu zafafan hawayene suka shiga sakkowa kan fuskarsa tabbas ya yi rashin aboki domin Zaki abokinsa ne tun na yarinta. Kallonsa Muhaira tayi daidai lokacin da wasu likitoci suke ɗauke Zaki daga wajen da idanu Taj ya yi masa magana ya girgiza masa kai alamar he's gone juyowa ya yi zai yiwa Muhaira magana yaga ta sulale ƙasa nan ta faɗi ƙasa sumammiya. *Nmandi azikewe Airport* Furzar da wani irin zazzafan numfashi ya yi yana sake duba rollex ɗin hannunsa misalin ƙarfe 3am ne ɗan siririn tsaki yaja daidai lokacin motar tayi parking da sauri ya fito ya ƙaraso cikin ladabi ya ce "I'm sorry sir" taɓe baki ya yi bai ce masa komai ba ya yi gaba shi kuma yabi bayansa Saida ya sanya trolley ɗinsa a bot sannan ya dawo wajen driver seat ya tayar da motar da wani irin speed suka bar airport ɗin. A firgice ta farka tana Kalle-Kalle kallonsu Mami wanda suke bacci ganinsu tayi tamkar wasu dodanni hakan yasa ta runtse idonta da gudu kuma ta fice daga ɗakin kai tsaye stairs tayi tana zuwa ta buɗe ƙofar entrance ɗin gidan ta fita da gudu, buɗe gate ɗin da tayi shine ya farkar da gatemans ɗin wanda bacci ya ɗaukesu da sauri suka kalli ƙofar sukayi wajen Kofar da gudu saidai me sam ƙofar taƙi motsi gabaɗaya ta cije tana fitowa ta yi kan titi tana gudu kamar mahaukaciya wani irin wawan birki drivern yaja, ɗago kansa ya yi ya kalleshi kafin yayi Magana yaga mace a gabansu tsaki ya yi sannan ya fito daga motar kallonta ya yi da gudu ta ƙaraso wajensa ta riƙe hannusa tana nuna masa bayanta waro idanuwansa ya yi da mamaki ya ce "Muhaira?" shigewa jikinsa tayi tana sakin kuka rungumeta ya yi ya shige motar da sauri drivern yaja suka bar wajen buɗe gate ɗin ya yi daidai da farkawar General fitowa ya yi saman bene sbd hayaniyar mutanen da yaji hangosu ya yi sunata kokawa da ƙofa lokacin sojojin suka fito wani soja ne ya ja ƙofar da ƙarfi aikuwa ta buɗe da gudu sukayi waje suna nemanta sakkowa ya yi da sauri yana zuwa ya kalli sauran waɗanda basu fitan ba ya ce"what's going on?" cikin inda inda ya ce"sir.. sir...daman Ma'eesha ce ta... fita" "what?" da sauri General ya buɗe ƙofar ya yi waje shima yabi bayansu. Har akayi sallar asuba suna waje saidai babu Ma'eesha babu alamarta dawowa gidan suka yi yana shigowa parlon ya tarar dasu kowa yayi cirko-cirko a tsaye kallonsa Mami tayi ganin yanda idanunsa suka faɗa cikin rawar murya ta ce"yallaɓai tana....tana ina?" girgiza mata kai General ya yi hawaye na zirarowa kan fuskarsa duk dauriya irin tasa "Tassssssssss" Da sauri suka juya suka kallon Mami wacce ta faɗi ƙasa sumammiya girgiza kai General ya yi sannan ya yi hanyar upstairs saidai ko stairs biyu bai taka ba ya haɗo shima nan ƙasa a sume. Wani irin tashin hankali ne ya mamaye a halin da gudu Aleema tayi kan Mami tana fashewa da kuka ta ce"Mamiiiiiiiiiii!!" *SHIN WANENE ZAKI?* *INA MA'EESHA TA TAFI?* *SHIN DA GASKE ZAKI YA RASU KO A'A?* *WACE IRIYAR RAYUWA MUHAIRA XATAYI IDAN YA KASANCE ZAKI YA TAFI YA BARTA?* *SHIN WANE WANDA YA YIWA MA'EESHA KURCIYA?* *WANE NE WANDA YA KIRAYETA DA SUNAN MUHAIRA?* *MENE NE HAƊIN MUHAIRA DA MA'EESHA HAR SUKE KAMA ƊAYA?* *INA MAHAIFIYAR KHALIL TAKE?* *SHIN MUHAIRA ƳAR WACE KUMA MENE NE DALILIN DAYA SANYA AKA YARDA ITA TUN TANA JARIRIYA?* *SHIN MEYASA AKE CEWA BA ITA BA CE! IDAN BA ITA BA CE TO WACECE?* *DUK WADANNAN TAMBAYOYIN DAMA WASU DA DAMA ZAKU SAMU AMSARSU SU NE A YAYIN DA KUKA BIYA ONLY 500# FOR NORMAL GROUP 1K FOR VIP VIA 9086030007 HAUWA LAWAN OPAY EVIDENCE OF PAYMENT VIA 08106608363 OR 07041901078 KI BIYA KI KARANTA CIKIN SAUƘI DA NISHAƊI SISTER* *FOR MORE INFORMATION A YIMIN MAGANA VIA MY NUMBERS* _TAKU HAR KULLUM NANAMEERA MU HAƊU A PAID GROUP_.