An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels AWA 48 A ZIRIN GAZA Ibrahim Ahmad Daurawa Made:- Shuraih Usman Domin download na wasu kayatattun hausaebooks namu sai ku ziyarcemu a shafin yanar gizo gizon mu akan wannan adireshi http://shuraih.waphall.com Kuna iya ziyartarmu a shafinmu na facebook kuyi like http://fb.com/hausaebooks AWA 48 A ZIRIN GAZA Na Ibrahim akhatibi daurawa Littafi na daya 1 Page 1 Typing:- shuraih Usman Post shuraih 99% JAFFA . Allah daya gari ban ban nace a zuciyata bayan da iska mai zafi ta bugi fuskata a lokacin dana leko waje. Na tsaya karewa wajen kallo , tutar kasar izra'ila na fara hangowa tana filfilawa akan husumiyar filin jirgin saman , inda nan ake gudawar da zirga zirgar jiragen sama . Jama'a suna kaiwa da komowa a filin sannan na fara tako matakalar sauka daga jirgin , wani abu da bana mantawa da shi ne duk san da na dubi tutar izra'ila sai naji gabana ya yanke ya fadi ras . Da haka jakata a rataye a kafada ta muka yi dan tattaki zuwa falon karbar baki , wasu yan uwan su ko abokan harkansu sun zo tarar su cikin murna da annushwa . . Na kuma lura dda wasu ba taryar kowa suka zo ba babu wata walwala ko fara'a tare da su, idanunsu na kan kowa, kamar yadda kyanwa ke tare nutstuwa idan taji motsin bera. Ko ban fada ba kasan ko su waye su JAMI'AN TSARO NE . Wajen karban baki nan ne kuma ake duba fasgo da sauran takardun tafiye tafiye , gurin a tsare yake akwai kayan binciken muhimman takardu na zamani kamarsu inji mai kwalkwalwa da fitilun siddabaru wanda suke bayyana rubutun boye sirri . Kaman misali irin na takardar kudi, na bude baki ina kallon abubuwa har layi yazo kaina wani bayahude ya kalleni sama da kasa alokacin dana mika masa fasgodina a lokaci guda kuma gabana yaba da ras. Daga nan ya fara jeho tambayoyi barkatai iri iri kamar ruwa, kai ka cebai karanta fasgodina ba. . Abin dayai ba shi muhimmancin shine "me ya kai ka bosniya Hasgobina har tsahon wata biyar " don ya lura kan sarkin dayake jikin fasgon da kuma sabon da aka buga akwai tsahon kusan wata biyar a tsakani. . Azuciyar tana ce wannan bai shafe ka ba. Ina tunanin amsar da zan bashi yace "me ya kaika sayarebo" kai tsaye na bashi amsa "neman labari ya kaini" ya dubeni sosai kamar lokacin ya fara gani na "me ya zaunar da kai har tsahon wannan lokaci " ya bude ta ya kuma dubeni sosai " na so dawowa amma babu hanya saboda filin jirgin saman sayarebo yasha wata majalisar dinkin duniya ne ta rufeshi" yayi mini kallon ban gamsu ba . Ya gyada kansa cikin dabara hannunsa yanakan tebur ya gusa da shi gefen teburin ya danna wani dan kulltu wanda aka rufe gefensa da takardu, cikin ya aikata amma na lura da komai, don haka nasan cewa wani abu zai faru . Na kalleshi ido da ido yana shirin sake tambayata a cikin dakin dayake ciki kofa ta bude daga bayansa wani dogo kakkarfan bayahude ya fito ko'ina jikinsa an rubuce shi da jami'an tsaro ba sai ka tambaya ba duk da babu wata alama ko ta kayan sarki ,kallo daya kawai zaka yi masa ka tabbata jami'in tsaro ne ajin farkon babu wata tantama . Ya karbi fasgodina ya duba sukayi yaren yahudanci ya danna na'urar mai kwalkwalwa, yayi nazarin wasu bayanai cikin sauri "daga wacce kasa kazo nan" ya jeho min tambayarsa a lokaci guda kuma ya kura mini ido "daga Bosniya nake" na maida masa kai tsaye nima na kura masa ido " kai dan wacce kasa ce" ya sake tambaya ta . "Nijeria" na fada ba tare da na dauke idona daga kansa ba "Me ya kawo ka nan?" Nayi tunnani cikin sauri kafin na bashi amsa don na fara fahimta makircin da suke shirin kulla min kuma na san kasar izra'ila basa maraba da yan jarida kasan wanda yake da abin fada kum yason a afada bazai taba maraba da dan jarida mai kishin ba, sai dai yan abi yarima asha kida . Ni HADI sam ba irinsu bane ni dan jarida ne na hakika mai kishi, ina cikin wannan sake sake ne yace meye sana'arka na amsa "rubuce rubuce da neman labari" ya matso kusa dani "kana da sheda" na ciro katina daga aljihun rigata na mika masa ya duba ya kalleni ya sake kallona ya dauki kan talho yayi magana . . Ya ajjiye shi a hankali naga kamar yana tuna wani abu "me kazo yi nan" cikin sauri nace "yawon bude ido" ya tsira mini ido yasa hannunsa daya a aljihun wando ya kuma nuna ni da hannunsa na dama "bana son yan jarida a kasarmu sam bana maraba da ungulaye" . Yana rufe bakinsa wasu majiya karfi suka nufoni sun fito daga kofar kudu da inda nake ,kai tsaye suka nufo ni kamar kibiya,cikin sauri suka kewayeni daga nan suka ce na bisu inda suka fito na bisu ban yi wata gardamaba suka kai ni wani dakin bincike kwkkwara duk kayan jikina ba ain da basu duba ba hatta dunduniyar takalmina sai da aka kusa ballata bayan an gama bincike da wata yar na'ura mai kwalkwalwa da ake kira metal detector kwalar rigata ma bata tsira ba, babu inda ba'a bincike ba na share sama da sa'o'I ana yimin tambayoyi kala kala kamar mutumin daya fado daga duniyar wata . Daga karshe aka shige dani wani ofis inda na iske wani bayahude kato zaune akan kujera mai juyawa yana da kasumba da saje da gemu da kumatu luhu luhu yan idanunsa sun nutse ciki , akan teburin akwai talho zai kai biyar daya ajjiye wannan sai ya dauki wannan, ban ga sunan sa ba kamar yadda ake ajiye sunan mutum akan tebur ajikin dan katako ko roba , yana zaune yana busa tabar hanavana katuwa ahannunsa kamar yankan rake, muna shiga firgigit ya juyo da kujerar ya zuramin ido tamkar yana kallon wani dan kwaron da yake neman fada masa cikin shanyinsa ya gummtsi hayaki ya fesa sama, kumatunsa sukayi sama da kasa sai naji wani dan sauti kamar na kuya "Vulture are not welcome here and we think you have a hidden mission not tourism, even though we have nothing to incriminate you" Ma'ana ba a maraba da da ungulaye ,kuma muna tsammanin kana da wani boyayyen shiri ba yawon bude ido ka zo ba, ya sake busa sigarinsa na dube shi kawai cikin tsana da bacin rai don duk na gama galabaita da tambayoyi da bincike na wulakanci ga kallon kaskanci iri iri ya kalleni sosai "you are to deported back to where you come from" bansa dana yi subul da baka ba nace " tafi nono fari" ya dubi jami'an tsaron dake baya. Nan da nan suka bukaci dana fassara abin da na fada ya nace "shi kenan na gode" Toh anan zan dakata Tambayata anan shine MAI NE NE SUNAN MARUBUCIN LITTAFINNAN . AWANI SHEKARA YA WALLAFA WANNAN LITTAFI Bazan ga masu cika bakin cewa wai su suna karanta tsoffin littatafan hausa Daga naku shuraih 99% AWA 48 A ZIRIN GAZA Na Ibrahim akhatibi Daurawa Littafi na daya 1 Page 2 Typing:- shuraih Usman Post shuraih 99% . [kar ku manta dai kuna tare da shuraih 99% ne] Lokacin daya juya na naji yayi tsaki yace "we don't know who give you this pucking visas....." Na dan tsaya don naji karashen maganar jami'in tsaron ya rike kafada ya hankadani gaba "you are not welcome here" Turanci irin na amurka . Hankalina ya tashi gaba daya yayin da muka fito muka shiga dakin da akayi min bin cikie na zauna ina jiransu su tattaro min kayana . Raina ya gama baci matuka ainun don ba irin wulakancin da ban gani ba wajen binciken nan tambaya kamar wanda aka kama da laifin kisan kai . Aka garomin fasgo din akan tebur ya fado kan cinyata na yunkura na dauki jakata , don haushi ko budawa banyi ba na saka a ljihu, na figi jakata na saba a kafada nayi waje fuskata a daure rai na abace .inajin takun sahun mutun yana biye dan yana kokarin kwantar min da hankali wai ba sun yi min hakan don wulakanci ko kin bako bane sunyi ne don matakan tsaro .[kar ku manta dai kuna tare da shuraih 99% ne] Ni dai ko sauraransa ban yi ba da haka ya rakoni har tsakiyar filin jirgin saman abin dauya dameni kawai in rabu da wadannan yan wulakancin in dawo sayarebo wajen kausar ko hankalinta ya kwanta ni kuma inji sanyi a raina saboda ganin masoyiyata . Mutumin yayi min rakia zuwa kofar wani jirgin saman "swiss air" ina kokarin mika "boarding pass" dina na shige jirgin sai naji an rike min hannu ta baya , na juya a hankali na dube shi tsaf, dogo ne fatar jikinsa jajaja alamar ya zauna a kasa mai zafi , . Idonsa kanana masu launin toka toka , gashin kansa ruwan gitsawa yana da gashin baki ba gemu .[kar ku manta dai kuna tare da shuraih 99% ne] Ya mika mini hannu nine mr Ros ina son ganinka a ofis dina Wannan kalaman sun bata mini rai kwarai sai naji kamar ya kwaro min ruwan zafi, cikin sauri na nuna masa bodin pas "bana bukatar ganawa da kowa ba kun koreni ba na jefa masa maganar cikin gadara . Alokaci guda nayi kokarin shigewa ya rikeni gam " haryanzu kana cikin kasar izra'ila don haka dole ka mutunta dokokin karsa, ka biyoni kada kaji komai" . Naso nayi gardama koda na lura jami'an tsaro suna yimin muzurai kuma na san cewa ban shiga cikin jirgin ba dana shiga to nabar izra'ila kenan, ina cikin inuwar swizland" dole subarni ganin haka dole na rufawa kaina asiri na bishi duk jama'a suna kallona sun kuma san cewa da walakin goro amiya wannan shima ba karamin wulakanci bane , ace cikin dubbai an tasa ka gaba kamar barawo kowa na kallonka . mintina biyar a tsakanin ya miko min takardar iznin yawon bude ido a izra'ila amma banda wasu wurare daya kira "security zone" na duba takardun na ga babu iznin zama a telaviv da kewayanta sannan kuma an rubuta baro baro kada na shige kwana uku a kasar [kar ku manta dai kuna tare da shuraih 99% ne]. Na nutsu sosai wata tambaya tazo min me yasa yanzu aka bani izini bayan angama wulakantani an galabaitar dani an koreni kuma meyasa aka bani izni bayan da an mini cikakken bincike an gano ni hatsari ne ga tsaron izra'ila har an koreni don a huta da kaya sannan kuma a kirayoni a bani iznin ba wani kace na ce , lai lai da sake wai mai kaza ya tashi da kai, don haka nace dole nayi taka tsantsan da mutanen nan sai maganar shugaban hizbulla a sarayebo ta fado min "zasu iya binka su halaka ka" ************************************** Rana ta raba sama gari ya dauki zafi sosai na duba agogona na ga shabiyu da rabi na rana , na shafe a sama da awa biyar kenan a filin jirgin saman ana yimin tambayoyi da binciken bin kwakwaf . Na fito harabar filin jirgin tare da dan rakiyata inda jama'a suke zirga zirga a wajen akwai wajen ajiye motoci masu zuwa filin jirgin. Akwai kuma wajen ajiye motocin haya da bas bas na alfarma sunyi layi , sai ka fadi inda zaka kuyi tsada da direba [kar ku manta dai kuna tare da shuraih 99% ne]. Kai tsaye ko kuma kaje ofis dinsu idan kana da kudi da yawa ka cashe musu kudinsu su baka direna ya kai ka duk inda kake son zuwa iya tsahon zaman ka a kasar, idan kuma kai sananne ka iya hayar motar har iya zamanka. . Na dauki hayar mota ajin masu kudi duk kuwa da cewa ba matsala bane a guna amma ina da wani abu araina . Muna shige shigen karge na jami'an tsaron filin jirgin sama na faa fahimtar halin kuncin da falasdinawa suke ciki. . Duk ina da naga ana aikin kaskanci ko aikin wahala idan na tambayi direna sai yace falasdinawa ne. Ina son tambayar dalilin daya sa falasdinawa ne kawai suke aikin kaskanci sai naji gabana ya fadi Ras. Don haka na kanne nace na bincika da kaina . Yayin da yake shigowa yakin cikin birnin telaviv lokacin na kuma ga wani abu daban wato taruwan jami'an tsaro da sojoji dauke da makamai kamar ana yaki, motocin yan sandan tarzoma suna zirga zirga ko'ina rike da bindigogi da rediyon walis a kugunsu suna lura da kowa suna muzurai kai kace jiya jiya ne akaci garin da yaki. . Gaba daya yanayin garin ya sauya ya koma irin yanayin filin daga , a gaskiya har yasa tunanin tuzla ya fado mini arai, naji na kasa jurea har zuciyata ta fara bugawa da karfi, na dubi wanda yake gefena wanda shine dan rakiyata "tourist guide " na kalleshi sosai "wannan jami'an tsaron haka lafiya kuwa?" Na tambayeshi tun daya shigo baice komai ba sai a lokacin "Sune dakarun zaman lafiya" ya dauke kansa yana kallon waje a daidai lokacin wata mota ta gifta mu na lura da ita ganin yadda ya kalleta, sabuwa ce mutum biyu ne acikinta daya yana magana ta rediyon walis dake cikin motar babu fallen rubutun lamba, bayanta kuma wata ta shigemu an rubuta "first class citizen" dan kasa mai daraja ta daya. Ba a jima ba kuma wata ta shige da lambar "third class" da fari dai banyi niyyar tambaya ba saboda yadda naga na kusa dani yana kallona amma cikin dabara sai na jeho tambayar"mai daraja ta daya" meye kuma haka ya dubeni zaiyi magana sai mukayi burki a shigen jami'an tsaro [kar ku manta dai kuna tare da shuraih 99% ne]. A gabanu jerin gwanon motoci suna tafiya a hankali zuwa kofar shingen sojoji da yan danda wasu dauke da bindigogi suna muzurai, wasu kuwa suna rike da na'urorin bincike irinsu na'urar sansanar bomb data binciken bindiga wasu kuma suna takardun mutane sunayensu da kuma gurin da zaus da lambar motar da matsayin mai motar wato bako ne ko dan gida ne, shi din ma wacce daraja yake da ita kuma wanne jinsi ne bayahude ne ko balarabe "kai wadannan mutane da rashin yarda suke" bansan lokacin da wannan furucin ya fito daga bakina ba sai dai nayi sa'a da harshen hausa nayi shi . Mutumin dake kusa dani ya kura mini ido ya kalleni sosai, adai dai lokacin kuma motarmu cikin sanda ta kai ga kofar shingen wani soja rike da bindigarsa kirar amurka m16 ya iso cikin sauri ya sunkuya tun kafin yayi magana direban ya bashi takardunsa sukayi magana, ga alama dai sun saba da shi na lura lokacin daya mika takardunsa sinyi musanyar alama ta cikin dabara cikin na lura da su ta wutsiyar idona . Wani ya karaso dauke da wani dogon karfe mai fadi daga karshen sa kamar shebur ya karasashe a karkashin motar sannan ya umarcemu mu fito ya kara mana na'urar binciken bindiga, ya bukaci fasgo dina na mika masa ya buda ya dubeni sama da kasa [kar ku manta dai kuna tare da shuraih 99% ne]. Yayi magana sojoji cikin sauri suka baibayeni kafin kace kwabo har wani ya doramin bindiga a wuya , sunyi mamaki da suka ga ko gezau banyi ba ni mamaki kawai suke bani ba tsoro ba, Na dubesu daidai cikin natsuwa "ka keta dokar kasar izra'ila "wata murya ta fada a bayana nayi kokari na waiwaya don yin tozali da mai maganai suka hanani motsawa "what is the hell with you" na fada cikin fushi "you are deported" murya ta mayar mini duk jami'an tsaro dake wajen suka juyo guri na cikin sauri suna jiran cika aiki kamar kare ya hango muzuru . Toh anan zan tsaya don na gaji Sai mun hadu ranar friday Daga shuraih Usman Inkiya shuraih 99% AWA 48 A ZIRIN GAZA Na Ibrahim akhatibi Daurawa Littafi na daya 1 Page 3 Typing:- shuraih Usman Post shuraih 99% . [kar ku manta dai kuna tare da shuraih 99% ne] Cikin hanzari na fisge fasgona daga hannunsa na buda wani shafin na nuna musu inda aka buga mini iznin shiga kasar kuma na cire "tourist visit permit" na nuna musu a daidai wannan lokacin wata mota jif patrol ta soja tayi birki a gabanmu akwai eriya doguwa a jikin motar . Wani manjo janar din soja ya dirgo kato ne mai katon ciki kamar tulu da walis a hannunsa fuskarsa kamar an aiko masa da mala'ikan mutuwa a turbune babu wani annuri Idanunsa irin na kyanwa kumatunsa kamar an sassaka, mai zagayyar fuska yana da saje da gemu buyya wanda ya maida shi tamka dattijon biri . Kafafunsa shafta shafta kamar dirka, kafarsa daya tafi daya tsawo abinda yasa tilas yake tafiya irin na kaguwa ya na dinkisawa a birkice . A kowane gefensa wasu matasa madaka kare suna biye da shi, kowane da karamar mashigan rike a hannunsa sun gama shirin tsaf suna shirin bude wuta jiransa kawai suke yace ket su cika aiki. Duk suna sanye da kayan soja mai rodi rodi , sauran kuma cikin motarsu suke suna masa rakiyta duk sunyi shirin kota kwana , yana karisowa gurin sauran sojojin a sauran jami'an tsaro suka sara masa sukayi cirko cirko wani kurtu ya fara masa bayani da yahudanci, ya dubi ne yayi musu magana da amon sautin jemage [kar ku manta dai kuna tare da shuraih 99% ne]. Nan take suka janye bindigoginsu daga saman sukayi sororo da su suna sauraransa cikin tsoro da girmamawa kai kace mala'ika neshi . Wannan girmama ta bani mamaki . Ya karen kallo tsaf ya karbi takarduna ya duba su a hankali cikin takama, kasaita da nuna isa ya gama ya sake kallona yayi magana daga cikin motar sai naga wal hasken fitilar daukan hoto na tabbata hoto na aka dauka , kawai sai naji sautin jemagen yana furta kalmomin turanci "be careful don't do anything wrong like gathering information or tres-passing into security zone or any no go area" yayi murmushin mugunta ya girgiza kansa "I will teach you a lesson that you will never forget throughout your life " Ya kalleni ya nuna ni da dan yatsansa cikin wani sauti mai tsoratarwa yace " kada ka tara ko ka rubuta mummunan rahoto akan kasar izra'ila kada ka kuskura ka aika da labarai a ciki ko a wajen izra'ila idan ka saba wannan ka'idodin yan yatsunka zasu baka amsa" . "I will cut this into pieces if you write mischief against us Mr goyim remember I am major dayin robert" ya kalleni sosai ya kada kai ya juya yana dingisawa ya shige motarsa suka rankaya a guje suka barni anan ina gumi ina yarfewa, sautin maganarsa yana kararawa acikin kwakkwalwata .[kar ku manta dai kuna tare da shuraih 99% ne] Mun karaso birnin telaviv da la'asar, yunwa da gajiya da zulmin major doyin yasa abun duniya ya dameni Na lura lallai nan ba wurrin da yan jarida suke da yanci bane , banayi binciken abubuwan da suke raina . Ko'ina jami'an tsaro da sojoji ne birjik kamar wani sansanin yaki, irin shingayen da na gani a hanya tamkar wani filin daga ne daya fada hannun abokan gaba , irin yadda ake binciken mutane daga inda suka fito da inda zasu da kuma abin daya fito da su sai ya tuna mini kasar afirka ta kudu alokacin wariyar launin fata inda bakin mutum bashi da iznin zuwa wani gari sai da takardar izni idan turawa sun amince da dalilin zuwansa a bashi kayadadden lokaci idan kuma lokaci yayi ya fice ko ya yabawa aya zakinta . Direba ya dauke hanya yaki shiga dani cikin birnin ya zarce dani wani gari a bayan telaviv JAFFA inda larabawa ne suke zaune a cikinsa . Dana nemi dalili yace wai ba bashi iznin kaini cikin birnin tel-aviv ba "doka ta hana shiga da bako sai da izni na musamman" . dana ji haka nace ya kaini otal mai saukin kudi ba wai don babu kudi isassu ne aguna ba , ina da kudi masu yawa wanda na samu daga wajen kaosar dalar amurka cinkus a jakata kuma duk binciken da akayimin ba wanda ya damu da kudina ina dauke da "america express card" don gudun sata ko shiga halin kaka ni kayi naso zama a otal mau saukin kudine don na samu cudanya da talakawa da sauran mutanen da ake samun labarai barkatai a gunsu . Sabo da yar gogayyar dana samu a aikin jarida , na lura mutane masu kudi ko fada aji basu cika fadar labaran rayuwansu ba, ko abinda jama'a suke da sha'awa akansa na halin zamantakewa ko halin musgunawa daga hukuma , su kullum suna boye labaransu suna kuma kaffa kaffa da abinda zasu fada a ko'ina suke, sannan kuma hukuma bata cika musguna musu ba, don haka basa sukarta , Bihasali ma ra'ayinsu shine ra'ayin hukuma amma ta zama cikin talakwa kuma larabawa zai kai ni na samu na kai ga bin da na zo nema ba tare da katsalandan din jami'an tsaro ba Matsala ta itace wannan dan rakiyar dole nasan yadda nayi na yarda shi cikin dabara .[kar ku manta dai kuna tare da shuraih 99% ne] Tafiyar kamar mil shida daga tel-aviv muka yi kwana zuwa dan gari mai girma da ake kira jaffa, abubuwan danagani sun bani mamaki kwarai , gidajen larabwa falasdinawa wasu sun rushe wasu kuwa sun dade da zama kango, wasu kuma ga suna ,rabi a rushe rabo a tsaye , babu wani gyara kamar wani sansanin bayi , Jami'an tsaro da suke safa da marwa sun maida garin kamar garin da aka fafatawani yaki . Abinda zaka fara fahimta shien talauci yayiwa mutanen farin kanta na tambayi direba dalilin da gidajen wasu suke a rushe "basu da iznin gyara gidaje" ya fada mini . Wannan amsar ta bani mamaki mutum da gidansa wai sai ya sami iznin gyarasa, zan sake tambayar naga dan rakiyata yana kallona sai kawai na kanne dana tuna da maganar mr doyin , muna dada ratsa garin jami'an tsaro suna kara yawa suna tsaida abin hawa suna bincikawa suna buda kaya sannan su caje mutum tsaf . Da kayi wata gardama sai su kama mutum su garkame shi acikin wata shiga ba biya. Wannan abubuwan din bani mamaki da tsoro da haushi alokaci guda, domin wannan babu wata maraba da mai mutane fursononi a garinsu ko daurin talala mai kamar sake .[kar ku manta dai kuna tare da shuraih 99% ne] Mun isa babbar kasuwar garin karfe biyu da rabi na yamma munje don nayi saye saye sannan ya wuce dani gidan saukar baki Tun kafin na fito daga motar naga matan larabawa suna saye da sayarwa cikin fara'a wasu suna sai da kayan marmari da yayan itace . . Alokacin guda kuma wani abu ya bata mini rai matasa sanye da wandon kaki rin na soja da fara singileti sanye da wata hula yar karama mai kama da yar madina shudaye mai ratsin fari suna rike da mashigan suna bi layi layi , rumfa rumfa kamar duba gari kasancewar su agun sun mai da kasuwar kamar kurkuku [kar ku manta dai kuna tare da shuraih 99% ne]. Can na hango wata katuwar rumfan sai da kayan mar mari iri iri kamar su tuffa lemon tsami dana zaki kala kala, akwai dabino da inibi kala kala da sauran yayan itatuwa ,yawuna ya guda don haka na dauko jakata na rataya na doshi rumfar "ina kuma zaka" direban ya tambayeni " zan sayo kayan marmari a wancan rumfar" na maida masau . Nayi sallama a kofar rumfar wata balarabiya sanye da dogon siket har kasa ta sanya riga mai dogon hannu ta yafa mayafi kato ya rufe tun daga kanta zuwa kaurinta tana fara'a ta tareni "ahlan wasahlan" tayi min nuni dana shigo ciki"marhababika ya akhi" Ta nuna min kujera na zauna ina shiga kanshin yayan itatuwa suka bigi hancina sha'awa ta motsa ,kanshin ni'ima na kayayyakin marmari ya kaure rumfar .[kar ku manta dai kuna tare da shuraih 99% ne] Cikin fara'a ta tambayeni sunana da kasar dana fito na gaya mata ni dan najeriya ne sai kawai cikin sauri ta bani ruwan sha ta jinjina min "nayi farin ciki da ganinka saboda dan uwana yana kasuwanci acan " ta fada cikin larabci . Sannan ta dauko jakar saye syae ta cika mini da kayan marmari ina kokarin ciro kudi na biyata ta riken hannu tace "kyauta na baka dan uwa na, saboda ina son musulmin Nageriya " Na gode mata na gaigaisa da sauran mutanen da ke rumfar na fito kofar rumfar ta biyoni "ina ne masaukinka kwana nawa zaka yi " na bude baki zan bata amsa kenan sai wata kara mai karfi da fashewa ta abku, wuta da hayaki a lokaci guda suka watsu cikin sauri na saki ledar da ke hannunsa na watsar da jakata na rumbace ta muka zube a kasa , nayi haka don gudun kada tararratsin bomb ya same ta . TOH FA DAN JARIDA YA FADA HATSARI Daga shuraih usman Inkiya shuraih 99% AWA 48 A ZIRIN GAZA Na Ibrahim akhatibi Daurawa Littafi na daya 1 Page 4 Typing:- shuraih Usman Post shuraih 99% . [shuraih usman inkiya shuraih 99% ke magana] Daga kowacce kusurwar kasuwar sai mutane ne ke runtumawa a guje , daga nan kuma sai harbi da bindigogi masu sarrafa kansu ya biyo baya abin da yakara yamutsa gun kasuwar ta yamutse , . Hayaki ya turnuke sama kura ta tashi hargowa ta cika ko'ina mutane da gudu suna tsallake rumfunansu ko rufe su basu yi ba wasu sunyi karfin hali sun tsaya rufe kofofinsu . Cikin sauri na samu naja jiki na rakube a jikin gyaren rumfar ita ma tayo ciki, cikin sauri muka rufe kofar ta matse matsen kofar na samu wata yar kafa data bani daman kallon abun da yake faruwa acikin kasuwar . Matasar dana gani suna kaiwa da komowa a cikin kasuwar rike da bindigogi suna harbin mutane na tabbata falasdinawa suke harbewa . Cikin mintina biyar kasuwar ta yaye ba kowa sai jami'an tsaron yahudu suna zirga zirga wasu a kasa wasu acikin landorobobi . Suka shiga kama wanda aka harbe suna jefawa acikin motocinsu wasu kuma suna bin falasdinawa da gudu suna kamasu izan sunyi gardama sai su harbesu wasu kuma suna kofofin rumfunansu suna kamo mutanen da suke ciki wannan yasa na gane dalilin dayasa wasu suke guduwa daga rumfunansu . Matan ta mike ta janye katakon da ake leken waje nan da nan ta rude ganin suna ta jifgar mutanen da suka kama , na lura da inda motarmu ta tsaya ba komai sai karikiceta dai-dai da direbanmu cikin jini, hannunsa ya cire idonsa ya fita sai kafarsa ce take dan motsawa ganin wannan ya tayar min da hankali sosai bansan lokacin dana fara kyarma ba zufa na keto mani , "wai da ban fito sayen lemo ba da yanzu bani " nace a raina . Motar asibiti tazo tana jiniya tazo ta kwashe gawarwakin mutane ban san kowane bane , akwai wasu mutum hudu da suka rasa sassan jikinsu motar janwai motocin da bomb yayi kaca kaca da su . . Ko mintina goma sha biyar ba ai ba an kwashe gawarwakin an janye mushen motocin an wanke jinin . Wama ya nuna cewa lallai yahudawa sun shirya da irin wannan ranar sosai kuma basa son kowa yasan irin barnar da suke [shuraih usman inkiya shuraih 99% ke magana] . Ina shirin cewa ta bude kofar ganin kura ta lafa sai naji hayaniya da kawar mutane sai na hango mutumin da muka shigo mota tare ya shiga motar jami'an tsaro ya tafi da fari nayi mamaki amma dana tuna akasar yahudawa nake ko ince kasar da su ka kwace da karfin tsiya banyi wani mamaki ba . Alokacin da motar shiga-ba-biya take shirin ficewa daga kasuwar a lokacin hayaniyar jama'a ta karaso cikin kasuwar wasu matasa a guje suna kabbara suna jifansu da duwatsu suna tunkararsu, . Batare da ko bindiga ba kowani kwakkwaran makami ba , ganin haka ban sana lokacin dana wangame kofar ba na fito don na kashe kwarkwatar idona ba . Rannan naga ikon Allah matasan falasdinawa suka taho gadan gadan ba wani tsoro ko fargaba a guje a daya barin soja da yan sandan izra'ila cikin sauri suka dinga dirgowa daga cikin motocinsu wsu suka durkusa wasu suka sunkuya wasu kuwa suna harbi suna gudu da haka suka tarbi falasdinawa masu jefa da duwatsu kamar soja yayi karo da abokin gabarsa soja afilin daga [shuraih usman inkiya shuraih 99% ke magana] , Mamaki da al'ajabi ya kamani ,ina mamakin yaya soja da muggan bindigogi zai harbi farar hula da bashi da makami, alokaci guda kuma ina al'ajabin yadda akayi mutum ba komai a hannunsa ya tunkari mai bindiga , . Aka ja daga daya barin karar bindiga daga daya barin kuma kabbara gurin ya kaure .an shafe sama da mintina ashirin ana dauki ba dadi falasdinawa suyi kora soja da bindiga kaga ya ruga da gudu har yana fadiwa, in anjima kuma kaga falasdinawa suna gudu abin kamar al'mara , . An harbi falasdinawa da yawa an jikkata wasu wani abu daya bani mamaki shine duk wanda aka harba yana faduwa na bayansa zai zo da gudu ya daukeshi [shuraih usman inkiya shuraih 99% ke magana] . Sannan kuma wani nan take zai maye gurinsa, don haka babu wata gawa ko masu rauni da sojan yahudawa suka kama . Ana cikin haka sai wasu falasdinawa suka hau saman rumfunan suna kabbara , suna jifansu da duwatsu wasu kuma suka biyo ta bayansu ganin za'a yi musu kofar rago sai suka jefar da wadanda aka kama suka tsere a guje n nan da nan kasuwar ta rude da kabbara da sowar falasdinawa suka mamayeta . Wannan shine abu na farko daya bani mamaki a saukata a cikin falasdinu . Na kirata falasdinu saboda shine sunan halal ba izra'ila ba kamar yadda yahudawa yan kaka gida suke kiranta .[shuraih usman inkiya shuraih 99% ke magana] Tambayar da nake yiwa kaina kuma na rasa amsar ta shine wane abu ne ya ingiza mutum ba makami ya kori mai bindiga har ya gudu yana faduwa yana barin bindigarsa . Me ya baiwa falasdinawa karfin guiwa har suka fuskanci yahudawa rike da bindigogi duk da sun san cewa harbesu zasuyi ga kuma sheda agansu sunga an kashe da damansu, . Sannan kuma wane daliline yasa mutum yana gani an harbe dan uwansa zai tsallake gawarsa ya shige gaba ya kuma tabbata shima harbeshi za'ayi sannan kuma me yasa suke dauke gawan wanda aka harbe . Wannan tambayoyin da wasu irin kamar son jin dalilin da ko'ina aka saka jami'an tsaro suna gadin dauka cin garin kamar anci garin da yaki kuma na ajin tsoron kwace shi koda wane lokaci, me yasa aka tsaurara matakan tsaro bayan kuwa su falasdinawa ba su da makamai da zasu iya yaki da yahudawa, . Kai kona kare kai basu dashi sannan wata kuma me yasa duk matakan tsaron nan ba su hana falasdinawa yunkuri da yin bore a kasuwa ba ? .[shuraih usman inkiya shuraih 99% ke magana] Hakika wadannan tambayoyi ne da suke bukaar amsa wanda duk wani dan jarida mai kishin aikinsa zai so ya gane bakin zaren abin da na kuduri niyya kennan duk kuwa da cewa ba neman labari na zo ba , na zo ne neman yar uwar NAGIS don na bata sarkar wuyanta to amma yaya za ace ni HADI dana shiga cikin runtsi a bosniya lokacin da ban san komai ba a dabarun yaki, yaki ta rutsa da ni na fito lafiya cikin ikon Alla . Sannan ga wata dama ta samu ta aikin jarida na hakika na kiyin wani abu sam-sam ba zan iya hakuri ba idan kuwa na hakura ban bincika na , to ba sunana hadi hantsi leka gidan kowa ba, neman labari ya zame mini jini da tsoka don haka naji ba zan iya barin wannan damar rubuta halin kunci da kuntatawa da yan uwana musulmin falasdinu suke ciki ba. . Wannan shiya sauya mini makasudin tafiyata, shu'urin aikin jarida ya motsa sai dai kuma na san cewa nan fa ba a maraba da yan jarida domin yahudawa sun san tasirin yada labarin abun da suke aikatawa, don haka basa yiwa yan jarida da suke aiki bil hakki da wasa , saboda basa son duniya taji labarin irin danne hakkin dan adam din da sukeyi . . Kawai sai na gabana ya fadi ras dana tuna da gargadin mr. Doyin . Har kullum dai nine Shuraih Usman Inkiya shuraih 99% AWA 48 A ZIRIN GAZA Na Ibrahim akhatibi Daurawa Littafi na daya 1 Page 5 Typing:- shuraih Usman Post shuraih 99% . [shuraih usman inkiya shuraih 99% ke magana] Na bude kofa zani wajen da aka fafata matar nan ta riken hannu " kai bako ne kada kaje su kamaka bari in rufe muje gida in saukeka" ta fada mini sunanta "ismi zulaikha" ta fara hada kayanta cikin sauri "motar ku aka sawa wa bomb ko" ta tambaya tana kallona na gyada kai sauran mutanen da suke cikin rumfar kowa yayi ta kansa . Ta shige gaba ina bunta muna gudu-gudu sauri sauri ta kurda can ta kurda nan . Da haka muka fice daga kasuwar jami'an tsaro suna yiwa kasuwar tsinke , tafiya mai dan nisa ta kai mu wani dan gida a cikin rukunin wasu jerin gidajen talakawa, duk unguwar larabawa ne acikinta idana kaga bayahude toh babu shakka jami'an tsaro ne babu ja wai kare ga mutu a saura , sai da cikin unuguwar babu jami'an tsaro a ciki sosai . Tayi sallama ta kwankwasa kodar wani karamin gida bayan yan mintina wata yarinya doguwa budurwa mai matsakaicin kauri ta bude kofar, gashin kanta har kirjinta tana da fararen idanu kamar madara a koko ga dogon karan hanci har baka , tana da siraran lebba da yalwar gashin gira shekarunta zasu kai goma sha bakwai ko sha takwas , muna hada ido ta rufe kanta da mayafi. . [shuraih usman inkiya shuraih 99% ke magana] A hankali ta bude kofar ta karbi kayan zulaikha sannan ta kalleni tayi min barka da zuwa kuma ya karbi jakata muka shiga dakin saukar baki, shine na farko da cikin gidan daga hannun dama ta bude kofar tace na shiga na zauna a cikin akwai kujeru guda uku tsofaffi da dan karamin teburin shan shayi, sai kananan kofuna na shan shayi a gefe guda na wani gadon katako tsoho. . Na zauna kenan yarinyar ta shigo da butar shayi ta daureye kofunan dake kan teburin ta zuba min shayi ta fice tana tafiya cikin nutsuwa, sannan ta shigo da yayan itatuwa irir iri da ruwan sha ta fita,shayin dana sha ya sana ji karfina ya dawo na kuma wartsake yayan itacen da sha sun gusar min da yunwa . Ni dinne dai Shuraih 99% ke typing . Alokacin ne na nutsu sosai na shiga hayyacina na dauke takarda na tsara abubuwan daki daki, wannan al'adace a gareni duk sanda zanfara wani aiki sai na zauna a tsanake na tsara komai dalla dalla , saboda kashin bayan cin nasara a kowace irin harka ta duniya kota lahira shine kyakkyawan tsari, da shiri mai inaganci , . Domin kuwa duk wanda bai tsara al'amarunsa ba to kuwa ya dauki matakin ruda kansa. . Abu na farko shine lokacin dana ke da shi kankane ne ,kuma abin da yake gabana yana da yawa, ga kuma wahala ba kamar yadda ba zata ba, yadda jami'an tsaro suke ta safa da marwa babu wani yanci walwala, ga tashin hankali iri iri ga harsashi na yawo. . Akwai hatsarin na shiga neman yar uwar nagis kai tsaye don ban san matsayinta ba agun jami'an tsaro ko taba cikin wadanda ake nema ruwa a jallo ,sannan jin cewa ina nemanta kuma na taso tun daga sarrayebo, wannan zai bada haske ga jami'an tsaro su tasani a gaba don su halakamu gaba daya, . Sannan kuma ban san waye jami'an tsaro waye da leken asiri ba, sannan na tuna da wanda muke tafiya tare na tabbata dan leken asiri ne , nayi hamdala da Allah ya raba mu cikin sauki . Nagode nine dai Shuraih 99% . Babban abinda yake damuna nake son kuma sanin bakin zaren shine dalilin da falasdinawa suke cikin wannan kunci da takura, koma meye harzukasu, suke dauki ba dadi da su haka, Na tsara komai cikin dabara da yadda zan sami amsoshin wadannan tambayoyi ba tare da wani jami'in tsaro ya sansano wani abu ba, kuma ba tare da mai bani labarin yasan cewa yana fadamini wani muhimmin abu labari ba, . Zan lullube komai da sunan ni dan yawon bude ido ne da san jin tarihi ne wannan abu ne mai sauki wajaen kwararren dan jarida musamman idan ya samu kansa cikin hatsari, Amma ba abu ne mai sauki ba Izra'ila . Kuna tare ne dai da Shuraih 99% . Zulaikha ta shigo tare da wani saurayi da wannan yarinyar suka zauna"wannan yayana ne " tace "sunansa Abduljalil shine wanta ita ana kiranta zakiyya shi yana karatu a jami'ar jaffa , ita daliba ce a kwalejin yan mata ta jaffa . Bayan shirin yan mintuna sai na jeho musu tambaya cikin dabara "ko kun san labarin sarkin Ramalla na karshe?" Na zuba musu ido , wannan ne karo na farko dana fara aikin daya kawoni, ya kalleni sosai yasa hannunsa a aljihun kirjinsa ya fito da kwalin taba ya kasta ashana sai zakiyya ta fice waje "ban san labarinsa ba" ya gumtsu hayaki ya fesar "wani tsoho abokin babanmu yasan komai na labarin falasdinu kafin a mamayeta da bayan an mamayeta da irin yake yaken da akayi tun kafin a haifemu, duk sanda nake da wani aiki daya shafi tarihi shi nake ziyarta ya bayyana mini komai" ya dube ni ya kalleni mahaifiyarsa " idan bazaka damu ba dana hada ka da shi mutum ne mai son bakon da yake son sanin tarihinmu zai gamtsar da kai da duk wani bayani da kake bukata" . Shuraih 99% ke cewa . Nayi murna da jin haka don haka nace " muje na ganshi mana yanzu "ya dubeni yayi murmuishi "Ba a nan garin yake ba sai gobe zan kaika wajensa a nablus ne " na duba agogona naga lokacin da nake dashi bashi da yawa "ina son ganinsa yau don sauri nake akwai wani uzuri da nake da shi" Ya kada kafadarsa " banda hali zuwa nablus a yau , ina son zuwa jami'an ina da jarabawa kuma kafin agama dare yayi, kasan nan ba'abari ayi tafiya da daddare daga wani gari zuwa wani garin , karfe shida zuwa bakwai na dare dole kowa ya koma garin da yake da zama ko ya fuskanci tuhuma . Shigewar zakiyya da farantin abinci ta ajiye a agabana tafice " zan biyo ka jami'ar nace masa bayan da yayi mini bismillah . Jami'ar jaffa tana daya daga jami'ar da larabawa suka gina suke gudanar da ita da harkokinta, akwai falasdinawa da yawa suna karatu wasu kuma suna koyarwa, Haka zalika akwai yahudawa har ma da turawa dalibai da malamai . Hukumar yahudawa ce ke lura da tsara tsaren makarantan da manhaja da ake amfani da ita , tana da shashen karatu mai zurfi akan ilimin kimiyya da aikin likita, tarihin da aikin injiniya . Abduljalil yana koyan aikin likita yana da sekara ta biyu muna shiga ya shiga aji bayan ya kaini dakin karati, ina shiga na dukufa binciken littatafai, da kasidun tarihi daban daban akan kasar izra'ila amm banga abin da nake son gani ba , labarai ne wanda ko agida najeriya na iya samu, sai dan abin da ba a rasa ba, . Wanda ya karamin haske akan binciken dana ke son yi Kuna dai tare ne da shuraih 99% . Bayan ya gama yazo muka fita zuwa gida a tahowar mu mun shafe kasa da mintuna goma sha biyar , amma akan hanyar komowa mun shafe sama da mintuna arba'in saboda cunkoson da jerin gwanon abun hawa "me ya kawo wannan Jerin gwanon" na tambayeshi "abduljalil yace "larabawa da yawa suna aikin leburanci a da sauran aikin karfi a tel-aviv da saura garuruwa na yahudawa da suka mamayee in sun kwana a gidajensu da sassafee kuma su sake neman iznin shiga garuruwan domin neman abun da zasu ci, wannan yasa duk safiyar Allah da kuma La'asar hanyoyi suke cika makil da abin hawa saboda kowa yana kokarin zuwa gida kar lokacin fara tare mutanee yayi . Nayi shiru kawai ina kallon jama'a a cikin dogayen motocin bas da sauran ababan hawa makare da mutane , . Yauwa anan zan tsaya na dan huta sai mun hadu a page 6 . Dan Allah ku saka ni acikin Addu'anku AWA 48 A ZIRIN GAZA Na Ibrahim akhatibi Daurawa Littafi na daya 1 Page 6 Typing:- shuraih Usman Post shuraih 99% . [Shuraih 99% nake cewa daku] . Toh jama'a sai daikuyi hakuri don kuwa fallayen littafin sun babbale, a saboda hakanne zamu danyi tsallake , . Amurka da sauran kasashen turai sun tara musu dimbin makaman yaki na zamani wasu ma ba'a taba jarabasu ba sai a lokacin, yahudawa suna da cikakkiyar masanaiya game da duk wani motsi da sojojin larabawa sukeyi , domin suna samun bayanan sirri kai tsaye daga ma'aikatar tsaro ta amurka kada ka manta kuma shugabannin wasu kasashen labarawa munafikaine . "Wannan nasarar ta basu daman waftar kasashen larabawa, don haka min sake fafatawa da su ashekarar 1967, wannan shine yakin kwana shida, kwanan bakin ciki" Abuja'afar yayi shiru banyi wani kokarin tambayarsa ba don na lura fuskarsa ta sauya idanunsa sun kada sun yi jawur don haka na lura abin daya ke son fada ne yake masa ciwo matuka zuwa can sai hawaye ya dinga tsattsafowa daga idanunsa yana bin kumatunsa a hankali . Ni dinne dai shuraih 99% . Cikin murya mai rauni tana rawa cike da sauti mai ban tausayi ya labarta mini labarin yakin kwana shida " yakin kwana shida yakine yakine da larabawa ba zasu taba mantawa da shi ba har abada, domin kuwa mun tozarta acikin kwana shida mun kaskanta mun ga wulakanci , munyi asaran filayen mu, an kashe mana mata da yaya iyalai masu yawa bazasu sake gaini juna ba. . Domin iyalai da yawa an watsasu acikin duniya suna yi gudun hijra cikin kaskanci da yawa sun halaka matayenmu da yawa sun ga wulakancin da basu taba zata ba domin kuwa an yiwa da damansu fyade, . Yi tunani a ranka cewa matar da bata taba fita waje ba ko kuma wacce wani namiji bai taba ganin fuskarta ba , balle kirjinta, rana daya ta samu kanta cikin fasikai sui mata tsirara suna lalata da ita a gaban ya yanta ko danginta , sannan a yasar da ita a filin Allah bako sutura, . Tuna yaya zakaji izan matarka ko yarka ko mahaifiyarka ce a kayi wa a gabanka, abubuwa munana mafi muni kuma awannan yakin ne yahudu ya kwace kudus gaba daya har masallacin al'aksa . Kai gaskiya na tausayawa larabawa, ehm Shuraih 99% . Amurka ta gina rundunar sojan izra'ila ta kuma sabunta kayan yaki ta da na zamani mafi inganci, tun a shekaar 1948 duk shekara suna wasu wasu makudan kudade na musamman da suna "development Aid" da kuma "military Aid" domin gina kasar da rundunar sojanta, suna kuma ba su kayan yaki wanda basa sayarwa kowacce kasa irinsa . Sannan suna ba sojansu horo na musamman ga kuma bayana da rahotanni na sirrin na watan dan adam . "Kwatsam izra'ila ta farwa kasashen larabawa don cimma burinta na kafa izra'ila babba , acikin kwanaki shida akayi mummunar fafatawa a tsakanin larabawa masu tarin kayan fada marassa inganci ga sojoji mara kwarewa cikin kankanin lokaci suka yi mana kaca kaca, sojojin mu suka zubar da kayan yakinsu su suka gudu, suka bar mu da abun fada ana dariya . Izra'ila ta mamaye lardin sinai mai tarihi na kasar masar, sun mamaye rabin jodan wanda ya hada da gabanshin gabar kogin jodan sun wafci wani bangare na kasar siriya bayan anyi kazamin yaki a tuddan golan . Nidinne dai shuraih Usman inkiya shuraih 99% Sun mamaye ilahirin ZIRI GAZA da sauran gabar kogin jodan (west bank) sun kuma kame daukacin darussalam (jerusalam) suka kwace masallacin kudus suka keta alfarmar masallacin suka kashe daukacin mata da yaran da tsofaffin da suka fake a cikinsa jini ya malala cikinsa kamar ruwa, suka kuma sake kwace wani bangare na kasar larabawa . "Acikin kwana shida sun yiwa larabawa wulakancin da ba a taba yi musu ba , tun bayan zuwan Annabi muhammaduu (SAW) mun ga tasku da wulakanci iri iri a hannun yahudawa har ta kai mun rasa inda zamu sa kanmu an kashe mata iyaye an yi lalata da yan mata , an kakkaraya mana matasa an zuba su a rami an rufesu da ransu, matayenmu,yayanmu a gabanmu akayi musu fyade, an wasashe dukiyarmu an kone an kuma rusa mana gidaje an mayar da mu yan gudun hijra a cikin kasarmu, Ta gado Shuraih 99% ne din dai . Falasdinawa da yawa sun watsu a duniya da sauran kasashen larabawa suna shan wulakanci iyalai da yawa sun halaka, iyaye basu sain inda yayansu suke ba , dangi sun warwatse yanzu akwai akwai faladinawa yan gudun hijra sama da milyan daya a cikin duniya basa ko tunanin dawowa kasarsu ta gado sai dai a mafarki...... . Abduljalil ya fashe da kuka yana fadin babana ko yana ia oho.." Can kuma sai ya dinga fadin wallahi zamu rama sai mun dauko fansa komai dadewa sai mun kwace kudus ko duk zamu kare" . Na lura duk ya sake jikinsa yana tsuma yana karkarwa, bayan ya nutsu abuja'afar yaci gaba . "Yakin kwana shida yasa larabawa sun farka sun shiga cikin hankalinsu sosai sun san kuma duniya ta canja, sun gane cewa ba wani shirin daukan fansa da dawo da martabarsu a idon dunia. . Ashekarar 1973" cikin kukan abujafar muryarsa a karye yadan saurara sannan yaci gaba "kasahen laraba sun nunawa duniya sun dauki darasin abubuwan da suka fari sannan an kuma samu sabbin shugabannin masu jini a jika masu kishin larabawa, wadanda sukayi aiki tukuru sukayi shiri na musamman acikin watan azumin wannan shekarar yakin da ake kira "yakin october" ya faru . Yahudawa suna da wata rana da suke kira "yom kippur" a wannan ranar basa aikin komai hatta jiragen sama basa tashi ko sauka balle wani aiki , muna zaune a unguwanmu dan ba damar shiga garuruwan yahudawa ranar hutu . "Na bude rediyo sai naji anacewa "meat pie" sea wolf and woll stringl wannan kalmomin sojane na siddabaru ana kiran sojan kota kwana da su dawo bariki cikin sauri" . Cikin sauri na katseshi "ya akayi ka gane kiran soja akayi musamman da kace kalmomin siddabaru "code word" na lura abduljalil bai ji dadi dana katseshi ba "nasan hakane saboda na shiga wata kungiyar karkashin kasa ta fada da manufofin izra'ila na mamaye palasdinu kuma ina aikawa da labarin sirri ga wasu kungiyoyin leken asiri don haka na san wannan dama wasu kuma wasu bayan da za fada maka a gaba na sansu ta irin wannan hanya ina fatan ba zaka tambayeni hanyoyin dana bi na sani ba, . Da kuma hanyar dana kebi na sanar da nawa bayanan asiran" nayi shiru bance masa komai ba. . "Bayan wannan sai muka ga motocin sojoji cike da sojoji da kayan yaki sun doshi bakin iyakokin da suka shatawa kansu, misalin goma na safe manyan rundunonin sojan izra'ila ssu dinga motsawa bakin daga cikin sauri, . Jirafe saman yakinsu suka dinga shawagi kasa kasa a cikin gari ko'ina daga nan kuma sai muka ji muryan firmiyan lokacin "golda meir" a redio tana cewa "bama wata tantama game da nasararmu, an yiwa abokan gaba mummunar barna" daga nan kuma muryar dan ta'adda moshe dayan yana cewa "larabawa ba zasu ci moriyar wannan yakin ba kafin a tsagaita wuta, kuma mutane birnin telaviv zasu samu suyi barci sosai" . Rugogin jiragen saman yaki yasa mutane gudu cikin gidajensu abin daya sabawa al'adar "yom kippur" ranar hutu da zaman jagwab, ta koma ranar yaki zazzafa, . Ranar da yahudu ba zai manta da ita ba domin a wannan rana sun dandana kudarsu, tunanin da suke nacin nasara cikin sauki ya koma kokarin kwatar kai ta kowane hali. . Yauwa hakann na keso shuraih 99% ke magana . "Ayakin ramadan ko yom kippur ko black october" Kamar yadda yahudawa suke kiransa an gwabza shi sosai anyi gumurzu kuma kazamin yaki mafi muni a taihi yakin zamani tun yakin duniya na biyu anyi kazamin gumurzu a guraree guda biyu da yakin sinai da daya kewaye na tudda golan . "Kasar masar sanadiyar kwace mata sinai tayi shiri sosai sai a kewayen sinai, ta sawo kayan yaki sabbi daga kasar rasha, wanda ya hada makamai masu linzami samfari sam 6, sam 3 da sam 2 da rokoki da bindigogi kakkabo jiragen sama na zamani, . Sun hada da garkuwan sararin samaniyar mai sarkakiyar a yakin sa sinan , sun tara tankoki masu inganci da saukin sarrafawa a cikin hamada da sauran bindigogin atilare na zamani masu amfani da na'urar mai kwakwalwa. . Wanda kwamandojin kasan rasha suka hada masu . . HMM LALLAI ZA'AFAFATA KAZAMIN YAKI . Kafin nan dai nine Shuraih Usman Inkiya shuraih 99% Nake cewa daku muhadu a page 7 AWA 48 A ZIRIN GAZA Na Ibrahim akhatibi Daurawa Littafi na daya 1 Page 7 Typing:- shuraih Usman Post shuraih 99% . . Cikin dare wasu kwale kwale dauke da masu nutsu suka haura gabar ta suwiz (suez canal) suka dasa nakiyoyi a bangaren izra'ila ,cikin sauri a lokacin da sojan izra'ila suka motsa nakiyoyin suka tashi suka watse ramikan karkashin kasa na boyar soja . Hayaki ya turnuke kura tayi sama,kafin kura ta lafa sojojin tanka sun haura da tankoki sama da uku ta kwalekwalen katakon da suka hada su saki wuta armuka ginin karkashin kasan maboyar soja da kayan yakinsu , gurin ya hautsine wuta ta kama , gine-gine da sauran tantunan sojoji suka kone kurmus . Sojojin da suka taso don hana sojan misira haurawa cikin kankanin lokaci aka gama da suwajen guda dari sukayi saranda, sauran aka kashe su, daga nan larabawa suka yiwo kora, suka kame sansanin mai girma a yankin. .[Kada ku sha'afa ni dinne dai Shuraih 99%] Ta amfani da gurnati da yollar wutar aka kone yahudawa da kayan yakinsu. Kafin yammar wannan ranar jiragen yaki masu saukar ungulu suka yi ta jigilar sojoji da kayan yakinsu. . Sojan kasa dauke da makaman atilare suka mamaye yankin sinar sun keta sinar ta wajeje biyar sukayi kaca kaca da sojan izra'ila suka lalata barakokinsu da kauyukan yahudawa , sun kama da yawa a masayin fursunoni, wajejen da suka fi barna mai yawa shine bakin gabar fu'ad da ismailliya an yiwa izra'ila barna mai yawa a Qatara . Sojan misira sunyi kokarin haurawa da jiragen saukar ungulu a Ras da sudr, sunyi asarar jirage goma kuma kowanne yana dauke da mutum 30 zuwa 40, kwamandoji sun yi kokarin katse hanyar samun kayan sojan izra'ila amma basuyi nasara ba sun harbo jiragen izra'ila sama da arba'in 40 sun yi asara nasu sama da goma, . Yahudawa sun lugudan wuta Shuraih Usman inkiya shuraih 99% mai tsanani ta sama da tankoki, Amma bai yi tasiri ba . Rundunar sojan izra'ila tayi kokarin karya sojan misira Amma duk shirinsu ya zama a abanza jiragen yakinsu , abin da suke mana zarra, sun gamu da garkuwar makamai masu linzami wadanda ake harba su daga kasa "surface to air missile" duk jirgin daya shigo cikin yakin sinai sai yayi karo da mizal ko Roka ya kone, . Ko bindigogin harbo jiragen sama ,jiragen amurka kirar phantom da hawk da sauran jiragen masu saukar ungulu sun sha lugudan wuta da ruwan mizayal da rokoki, ko ina ka duba a sama sai kaga jirage na faduwa kasa suna ci da wuta , wasu kuwa a sama zasuyi bindiga su watse hayaki ya cika sama kaman gajimare mizayal sam 6 yana harbo duk jirgin daya tashi sama sosai kamar kafa 40,000 a sama wanda yayi kasa kasa domin yin bomb akan tankoki zai ci karo da sam 3 ko sam 2 wanda aka saita su don harbo jiragen da yake kasa kasa Shuraih usman 99% . Tarun ayarin tankokin yakin da izra'ila ta turo a yakin sinai sun sha wuta sun yi dai dai suka watse a cikin hamada suna cin wuta, saboda sun gamu da sabon makamin kone tanka, don haka tarun tankoki sama da dari hudu basuyi komai ba . Illa zama kaskon suya yahudawa, tilas sojan suka fita daga tankokinsu suna jifa da makamansu da hulunan kwanansu suna zubawa aguje suna ihu Wasu sun bace a hamada wasu sun haukace wasu sun kurmance ko'ina takalma da hulunan da belt da bindigogi kirar amurka zaka gani birjik . Sojan kasar siriya sun kai farmaki daga barin gabas takan tudun golan sun share sojojin izra'ila acikin AWA 48 suka danna har wasu kauyuka sun kone gevel kibbuts da heamek. . Wayewar gari jiragen izra'ila sun kai hari kan garuruwan fararan hula sun kone gidaje da asibitoci da makarantu sama da mutum 1000 sun mutu a rummaneh. . "Mummunan yakin atilare da tankokin yaki ya fara da misalin karfe biyu na yamma bayan da suka sha kashi a shuraih Usman inkiya 99% Hannun siriya, tankoki samfurin cneturions da patton suka dirkako zuwa tuddun golan nan suka yi karo da tankokin siriya aka gwabza yakin tanka mafi muni da tsanani a tarihi . Hayaki da wuta ko'ina ga rugugin bom da manyan harsasai da inji tanka kawai zaisa kunnen mutum ya kurmance, anyi kare jini biri jini ko'ina karekican konannun tankoki da gawarwakine suke yashe kamar kasa . Can kuma jiragen saman amurka na phantom suka dinga ruwan boma bamai kamar ruwan sama akan tankokin siriya sun yi lugudan wuta mai tsanani na lokaci mai tsawo,anyi daga sosai mutum da kansa zai bude tankarsa ya fito ya ruga da gudu, sama wuta kasa wuta tsakiya masifar zafi . Kashe gari da taimakon jiragen yakin amurka da bayanan sirri na watan dan adam daga amurka, izra'ila sunyi raga raga da tankokin siriya sun kuma lalata garkuwar makamai masu linzami da suka hada jiragen izra'ila suka karya Shuraih Usman inkiya 99% rundunar sojan siriya suka sake kama tuddan golan an sake fafatawa sosai akan golan sama da tankoki 1500 suka gwabza aka yi kazamin yakin tanka a tarihi . Hakazalika wayewar gari a lardin suwiz sojan izra'ila sunyi nasarar karya sojan misira da suka hauro cikin hamadar sinai, saboda sun kai tankoki masu yawa , sun kumayi nasarar lalata cibiyar makamai masu linzami da suka hana jiragensu haurawa. . Wannan ya baiwa yahudawa damar raunaa ragowar tankokin da suke hamadar sinai ba tare da wata kiryar mizayal ba , rashin sabbin tankoki da zasu ci gaba musu da raunatesu. . Rundunar sojan izra'ila sun keta garkuwan jiragen saman yaki ta yankin sinai sun lalata rumbunan rokoki da mizayal da taimakon amurka da kayan yakinta da bayanan sirri na watan dan adaam, sun lalata cibiyar bada umarni ta makamai masu linzami sam 6 sam 3. Amma haka bai faru ba sai da amurka ta shiga kai tsaye . AMma dai kafin wuta a tsagaita larabawa sun kwato Shuraih Usman inkiya Shuraih 99%. Da dama daga filayensu da izra'ila ta mamaye a yakin kwana shida 1967. Martabarmu ta dawo a idon duniya, mu larabawa ba abin da muka tsana face ayi galaba da mu kuma a din ga kallonmu a mutanen banza, . Abin dayasa muka samu nasara bai wuce cewa sojanmu sun samu kyakkyawan horo da ingattattun kayan yaki na zamani irin wanda izra'ila take tinkaho da shi ba, kuma sojojinmu sun shiga fagen daga da niyyar ko cin nasara ko su mutu, Amma ba su gudu kamar yadda sukayi a yakin kwana shida ba, mun nuna wa izra'ila cewa mu ba kanwar lasa bane" . Matarsa ta shigo tare da wani mutum suka gaisa ni da abduljalil muka yi sallama da shi bayan nayi masa godiya mai "nine zan gode maka da ka taho tundaga wata kasa don binciken yadda rayuwarmu take da halin da muke ciki, ka nunan kana kaunarmu kwarai" . Ya saki hannuna nayi masa alkawarin zan dawo muci gaba da shira akan halin da aka jefa falasdinawa a ciki . Har na juya zan tafi sai na tuna da maganar neman gidansu Nagiz nayi masa maganar sarkin ramalla yace " sai na dawo ma ci gaba "tayaya zanje gidan " na tambayeshi . "An rushe gidan tuntuni don mu daina tunawa da shi, ba komai yanzu sai fili kawai, amma yana da 'ya'ya ya mike tsaye ya dauki Shuraih Usman 99% kwagirinsa ya rakoni kofar ya sunkuya kamar zai sumbace ni " yana da diya sunan ta Nagis taana da kanwa Ikram dukkaninsu suna cikin kungiyar hamas, bansan inda nagis take ba yanzu kada kaje nemansu . Ba mamaki jami'an tsaro su halakaka don kowacce ana nemanta ruwa ajallo" Ya dafa ni kamar yana bani shawara sai ya fadi wasu kalmomi da sunan wani layi a cikin ramalla yace na tambayi wani mutum na fada masa abin daya fada mini "zai taimaka maka kaga daya daga cikinsu na gaya maka ne don na amince da kai maga alamar kai mujahidi ne" . Muka fito da abduljalil ya shiga mota zuwa gida ni na tafi cikin Ramalla . . Anan zan tsaya sai mun hadu bayan kwana biyu Nine naku akoda yaushe Shuraih Usman Inkiya 99% . Abun dayasa kukaga bana post kullum kuma banayi da yawa shine Nafi ga ne nayi post kadan mai amfani AWA 48 A ZIRIN GAZA Na Ibrahim akhatibi Daurawa Littafi na daya 1 Page 8 Typing:- shuraih Usman Post shuraih 99% . . ZIRIN GAZA --------------------Na shiga garin ramalla a wa daya bayan rabuwar mu da abduljalil kai tsaye na shige masallaci nayi sallar azahar bayan sallama limamin masallacin ya mike yayiwa masallata wa'azi yana fadakar da su abin da yake gabansu na fafatawa da yahudawa . "Dole ne mu sauke nauyin daya hau kanmu dole mu kwato kanmu daga kan gin bautar 'yan kaka gida , falasdinu ta falasdinawa ce kuma masallacin kudus na musulmi ne" . Kabbara mai karfi tama sallata ta katse shi da aka lafa yaci gaba "duk musulmin duniya ya haukansu suyi yaki don yantar da masallacin daga hadarin da yake ciki, . To amma mune makwabtan masallacin don haka mune zamu fara nuna kin yardarmu , da bijirewarmu sannan muyi tawaye , mu yi fito na fito mu fafata, mu hautsina da yahudawa don mu nuna wa sauran musulmin hanya" . Aka sake kabbara mai karfi har sau uku, da haka yayi bayani na zaburar da matasan dake cikin masallacin ya kuma kare da "Allah ya tsinewa masu danne hakkin mutane, ALLAH YA TSINE WA 'YAN TA'ADDA" masallacin ya kaure da kabbara yayin da ya ce "ALLAH YA TSINE WA IZRA'ILA, ALLAH YA TSINEWA AMURKA" (Nima shuraih 99% nace Allah ya tsinewa yahudu, jama'a kuyi comment da Allah ya tsine masu) . Cikin dabara wasu matasa suka sashi a tsakiyarsu suka fice da shi daga masallacin suna kabbara suna daga hannuwa, wannan lamarin ya farkar dani samun wani kuzari a ruhina, duk da labarin yakin da abuja'afar ya bani wanda yasa jikina yayi sanyi bakin ciki kuma ya rufeni wannan bayanan da kuma kumaji da kuzarin da ruhin gwargwarmayar dana gani tare da matasan Ramalla ya bani kwarin guiwa da farin ciki a raina, domin naga alamun daukan fansa a tare da matasan . Kai tsaye na tafi inda akayi min kwatance bayan na gama nazarin gurin a taswirar matafiyata dana saya na nablus, na sauka daga bus na yi tattaki mai dan nisa , kwatsam sai (shuraih usman inkiya 99% bazan taba daina fadin Allah ya tsinewa Izra'ila ba ) jikina ya bani kamar ana bina cikin hanzari na waiwaya naga wani mutum dogo dan tsattsama yana sauri yasa bakaken kaya da hula hana sallah. . Ina ganin sa gabana ya fadi na sassauta tafiyata na saurara ya cimmini ya dan bangajeni ya shige . Ganin haka sai na koma baya ina isa bakin hanya wata motar limousine mai kofa shida , gilashin motar bakine yana daukar ido ta tsaya a gabana a hankali, ganin ta tare hanya sai na kauce zan gifta sai naji wata murya kamar na taba jinta amma na manta inda na taba jinta , nayi kamar ban jiba sai na sake ji " may I give you a lift " . Muryar mace matashiya mai taushi lokacin na tabbata na taba jin muryar, don haka na waiwaya sosai na sunkuya don inga mai maganar, ban iya ganin ta ba, sai gabana ya fadi ras, don haka ban amince na shiga ba naci gaba da tafiyata .(Shuraih Usman inkiya 99% Na fara tafiya amma ban san inda zan nufa ba ganin ina kokarin ciro taswira daga aljihuna sai motar tayo gaba ta cimmin "can I help you" har zance a'a sai kofar motar ta bude wata yarinya ta fito sanye da siket iya cinya da tabarau baki a idonta tasa takalmi mai tsini rigarta shara shara wacce ta bayyana dukkan surinta kusan mamanta a waje suke, hannun ta akwai agogon gwal . Ta tsaya a gabana tana kanshin turare kana ganinta kaga ba Amurkiya, hakika na san cewa akwai inda na taba ganinta amma saboda halin da nake ciki na kasa gane ta "Kai bakone anan ko" tace dani na dubeta "Ni dan yawon bude idone " ina gama fada mata nayi kokarin tafiya tayi murmushi "Ina kake son zuwa ne in kaika "ta duben tayi dariya "kana jin tsorone" jin haka na gaya mata inda zani . Ta girgiza kanta "bana shiga nan akwai hatsari garemu" Tai mun kwatance na kama hanyar shiga motar tayi gaba har da dago min hannu . Na shiga unguwar datai mani kwatance, nayi ta shiga lunguna har nakai ga fadar sarkin ramalla ba komai sai fili kato an kewayeshi wayar mai kugiya sojoji suna Shuraih Usman inkiya 99% gadin filin suna dauke da bindigogi masu sarrafa kansu, a gefe daya akwai wata yar rumfar soja an kewaye filin . Ban aune ba sai naga wani soja a gabana rike da wani jifgegen kare mummuna yana haushi sun tsaya a gabana "no tresspassing mister" Sojan ya fada cikin fusata na rufawa kaina asiri nayi gaba . Na isa masalacin ramalla don nayi sallar la'asar ina sallama ba shida nisa da filin , shine masallacin sarkin ramalla , baban nagis ne ya gina kafin yahudawa su kasheshi, bayan na idar da salla na tambaye wani dattijo ko yana da labarin filin can da sojoji suke gadinsa, . "Wani yace maka wani abune game dashi" nayi shiru zuwa can nace masa "ni dan yawon bude idone , ina dai son jinko yana da wani tarihi" . Yadubeni sosai "daga wacce kasa kake" cikin sauri nace masa "nazo daga Nijeriya" ya nade carbinsa "zo na kai ka wajen wanda zai baka labarinsa" . Yana gaba ina binsa a baya cikin ladabi muka shiga wani dan karamin gida a cikin wani lungu a tsakiyar unguwar, muka shiga can kuryar gidan, muka iske wani mutum yana zaune akan wata darduma mai alfarma irin ta da matasa majiya karfi sun kewayeshi, muka Shuraih Usman inkiya 99%. Gaisa bayan dattijon ya gabatar dani na gaya masa labarina . "Ni ina daga cikin 'yan gidan sarautar Ramalla sunansa abdullahi ya fada mini kai tsaye, "Wacce sheda za ka nuna mini" na tambayeshi yayi murmushi "wannan sune shaiduna" dattijon daya kawoni ya katse mu shi dan jinin sarautar gaba na baya" . Wannan yasa nayi farin ciki gani ban sha wahalar da na zata zan sha wajen neman kanwar Nagis don haka cikin zakuwa nace "ina son ganin 'ya'yan sarkin Ramalla yanzu" . Wani matashi a gefe yacee "ba shi da 'ya'ya" na kalleshi "yana da su mana "na mayar masa . Wani abu kake da shi muhimmi haka da kake sin ganinsu" , Dan gidan sarautar ya fada yana kallona "kwarai kuwa ina son ganin Nagis binta Taziz da kanwarta" sai nayi kallamar da abuja'afar ya fada mini gaba dayensu suka kura mini ido, can yace bani da labarin Nagis Shuraih Usman inkiya 99% yanzu na samu labarinta jiya amma ban tabbatar ba ance dan aike zai zo yayi min bayani . Amma kanwarta tana cikin zirin gaza, suna kiranta da sunan bintul jihad a gaya mini layi har da gidan da zan same ta . . Cikin murna da farin ciki na barsu, kamar cewa aka yi gata nan, ashe dala dashi da shiga biirni bane, nayi sallama ko labarin dalilin girke sojoji a filin ban tambaya ba . *** *** *** Gaza birni ne mai girma yana da fadin kilomita mirrabba'in 350 yana kuma da fadin kilomita 40km, birni ya fada hannun sojan izra'ila a lokacin yakin kwana shida a shekarar 1967 ,kafin lokacin yana hannun misra tun daga yakin shekara 1948 har zuwa 1967, . noma da kasuwanci shine sana'ar mazauna birnin, akwai mutane wajen miliyan daya mazauna birnin , sannan akwai unguwannin yahudawa 'yan kama guri zauna da suka yi kaka gida aduk gurin da yake da wata ni'ima an yi musu barkoki sojoji suna gadinsu dare da rana cikin shigar yaki . Gaza duk sauran garuruwan Shuraih Usman 99% nake da tarin sojoji cikin kayan fada sabodaa cibiya ce ta tashin hankali . Doguwar bas din dana ke cike tayi birki a gaban wani katon shingen binciken shigi da ficen sojoji da karnuka masu sansanar bom, . Da na'urorin sansanar bom sun bin cika gurun akwai matsanancin tsaro agun sosai zaiyi wahala mutum ya shige da ko allura batare dako na'ura ko karnuka sun ganoshi ba, haka dai muka shige . Muna isa cikin garin na fara ganin kayan abinci iri iri da yayan itatuwa baja baja a ko'ina an baza sana saidawa kamar yadda zakaga shagunan sai da kayan tireda idan ka shigo birnin kano . Mutane birjik suna harkokinsu na yauda kullum , sai dai kuma dole mutum ya tsorata idan bakone kamar ni irin yadda sojan izra'ila da yan sanda da sauran jami'an tsaro suke kaiwa da komowa layi layi, . Matasa kuma suna cikin halin harzuka da shirin fito na fito da jami'an tsaro kamar an yi musu allurar yaki, kafin na shiga cikin garin Gaza na sha bin cike da caje caje barkatai da tambayoyin yaya kazo duniya........ . Yo ana zan tsaya Nidinne dai Shuraih Usman Inkiya 99% Mamallakin shafin hausaebooks da Keffians News Teller nake cewa ALLAH YA TSINE WA IZRA'ILA Kai/ke ma ku tsine masu AWA 48 A ZIRIN GAZA Na Ibrahim akhatibi daurawa Littafi na daya 1 Page 9 Typing:- shuraih Usman Post shuraih 99% . . Karfe biyar da rabi na yamma daidai na shiga cikin garin gaza, jami'ar tashin hankali makarantar koyon gwagwarmaya da daki ba dadi , fagen daga kwami filin yada kanin wani . Na duba agogona naji kausar ta fado min arai na yanzu saura sa'o'I goma sha biyu alkawarin da na yiwa kausar na komawa ya su cika, kuma shine yayi daidai da sauran sa'o'I araba'in da takwas na lokacin da aka diba mani na zama kasar izra'ila ya kare gashi ban ga kanwar nagis ba . Amma nasa araina nan da sa'o'I biyu ko uku komai dare na gama abin da ya kawoni. Gobe na kai ziyara masallacin kudus na kammala komai na koma sarayebo wajen kausar kafin mako guda na koma gida najeriya Shuraih Usman inkiya 99% ina tawa Allah na tasa kuma ta Allah ce mai tabbatar ko ina so ko bana so . Alokacin da muka ratso ta bazar din gaza na ga shaguna duk a rufe na za ci har sun rufesu ne haka da wuri, na tambayi abokin zamana cewa da wuri ake rufe kasuwa ne?" . Ya dubeni "kai bakone ko" na amsa masa maimakon yayi wani bayani sai yayi shiru kawai zuwa can wani agefe yace " intifada ta shigo kasuwa kenan" sai yayi kabbara munzo daidai da wasu yan sanda, wani matashi a kujerar gaba, . Yana sanye da suwaita fara mai tmabarin pLO da wando baki yasa tabarao shima baki ya yafa makawuya mai rodi rodi fari da baki , kakkarfa dashi ya mike ya leko ta taga yace " al mautu lil izra'ila" ya fada da karfi cikin motar suka amsa masa . Kafin kace kwabo sun durkusa kasa suka dinga yo mana harbi gadan gadan gilas din baya na motar ya zube shar kamar ruwa na gaba yayi caba caba da hudojin Shuraih Usman inkiya 99% arsahshi . Direba ya take kwano, cikin motar maimakon ya rude da kara da hargowa kamar yadda zai abku inda ace a sarayebo ne cikin sauri sai kowa ya kwanta cikin motar wasu akarkashin kujera wasu a karfen motar suna kabbara suna AL MAUTU LIL IZRA'ILA . Ni kadai na rage a zaune ina son ganin kwakwaf na dauka abin wasa ne , wata mata mace agefena tana yi mini ishara na kwanta naki, koda gilas din gefena ya zube ya tarwatse , tartsatsinsa ya same ni a fuska cikin rabin dakika daya nai tsalle nabi lafiyar kwano . A guje muka ratsa bazar din , muna gab da fita wasu sojan izra'ila suka ja daga suka durkusa kowanne ya dana bindigarsa ya saito mu, abin dana iya gani kenan na sake bin lafiyar karfen motar, . Dakikoki biyu ko uku a tsakani sai gilas din gaba ya zube, direban yayi kara ya saki matukin motar ya fadi a gefe jini yana zuba ta kansa, motar tayi sartu damu a guje ta tunkuyi wasu jerin rumfunan kayan marmari ta shige ciki tayi karo da bango gao! . Shuraih Usman inkiya 99% tana tsayawa na nemi inda kofa take na laluba gun da nasa jakata na jawo ina tsima nayi waje na taka mutane cikin jini na bazama da gudu ban san inda nake ba . Nabi ta bayan rumfunan na bullo ta wani kwararo dogo ina kaiwa tsakiyarsa, sai na hango yan sandan izra'ila guda biyu da bindigogi a gabana suna muzurai suna jiran na karasa, cikin sauri na waiwaya baya na hango soja da bindiga ya biyoni da gudu, nayi tunani cikin kankanin lokaci na rasa mafita gaba kura baya siyaki nace araina . Halt halt, sojan ya kwalan tsawa na tsaya cak. "Am a tourist don't shoot me please"na fada cikin kaduwa kafin na rufe bakina har yayi harbin iska guda biyu, na tsaya na kama salati a cikin zuciyata . Yan sandan suka kariso "hands up" suka ce dani na daga hannuwa sama gabana yana faduwa , lungun shiru ba motsin komai, mari mai karfi cikin sauri ya sauka a fuskata har sai danaga walkiya ta gifta, . Dan sandan ya kufuteni a baki dayan kuma ya hada mani Shuraih Usman inkiya 99% naushi da mangari, daga nan sai mari, naushi da kutifo da managari ta ko'ina ya dinga sauka ajikina . "Ku saurareni kuji matsayina mana" na dinga fada ina rokonsu, amma kememe suka ki saurerena sai duka suke min kamar Allah ya aikosu, . Sojan yana karisowa ya tabe iya karfinsa yakai min duka da gindin bindigarsa bai fi taki daya ba bindigar ta sauka akaina na lura cikin sauri da hanzari na ban mamaki na kauce cikin dabara na hankada dan sandan dake gabana nayi tsalle gefe guda, bindigar na sauka akansa yayi kara kafin ya fadi idonsa ya juya yif ya fadi kasa kamar itace . Ganin haka daya dan sandan yaja da baya ya fito da bindigarsa daga kugunsa a cikin rigarsa, kamar na rumbacceshi ta irin salon da aka koya mini yadda ake kwace bindiga in an rutsa mutum, . Amma ganin bayana akwai soja da bidiga, naji gabobina sun tsaya cak kamar an zaren min laka, sanyin karfen bindiga akeyata shi ya karyan lago Shuraih Usman inkiya 99% . "You are under arrest" sojan ya fada da kakkausar muryarsa, na daga hannuna sama "kayi amfani da karfi akan jami'an tsaro" na bude baki zanyi magana sai naji kakat yana shirin harbi don haka na tsaya kam bana ko motsi . A hankai suka bincike jakata suka dauken american express card dina da kudina sam dala dubu ashirin dina na takardar dala dari dari acikin sin kinsu, suka dauki fasgo dina suka bincike kasar jakar suka dauko sarkar wuya ta nagis, suka duba sosai "ancient atiquity" dan sandan ya mikawa sojan, yadaga sosai precious jewellery of the middle age " ya saka a aljihunsa yasa dariya . Naji kamar an cire mani zuciyana koda nayi kokarin magana sai "zamu kashe ka yanzun nan" suka sa dariya cikin kankanin lokaci nayi tunanin sarkarnan ita ta kawoni nan , sannan ga alkawarin dana yi wa Nagis gashi nazo garinsu mintuna kadan ya rage na kaiga mai sarakar, . can na tana ai jiya ba yau bane ,yanzu ina da Shuraih Usman inkiya 99% horon soja na kuma kware a fagen dabarun yaki naga kuma yaki nayi shi na shiga hatsari daban daban , don haka dole na kwace sarkar nan ko da zan mutu kuwa, wannan shine abin da zanyiwa Nagis bayan ranta . Na saki jikina nakama rokonsu na marairaice har da hawayen karya, mai bindigar yana dan waiwaya don duba wanda ya suma cikin hanzari na shammaceshi ni kai na nayi nayi mamakin irin saurin danayi nasa hannuna na bige bindigar da karfi . Kafin dan sandan dayake gabana ya danna kuna man bindigarsa ne na dauke shi da kafata tayi sama cikin sauri da azama na sunkuya kasa, yayin da sojan ya kawo harbi harsashi ya sami dan sandan aka yayi tsalle ya fadi kasa tum . Nakai kasa Shuraih Usman inkiya 99%cikin sauri nayi kwabo na kwashe kafafunsa ya saki bindigar ya zube da baya cikin sauri da azama nayi tsalle na hau ruwan cikinsa , muka kaure da kokawa naiya kokawa don ni gwanin kokawane tun ina yaro . Ganin nayi biji biji da shi kuma bazai iya galaba da ni ba, ya zaro wuka a kugunsa ya kai min suka nayi tsalle na goce gefe, ya sake kai mun wani wawan suka Allah ya kiyaye na sake gocewa . Ganin na daga shi sai ya tashi idonsa a rufe ya nufi bindigarsa ina share kafafunsa , ganin zaici da baka dole ya saki wukar don ya ceci hakoransa daga zubewa ban san ya akayi ba sai naji ya kurma ihu, wukarsa ta nutse a cikinsa jini na zuba hanji waje . Cikin sauri na kwashe kudina da sarkar da katuna na na harhada kayana cikin hanzari na rataye jakata, ina ratayawa motar yan sanda ta gifta kwararon tana jiniya ban san lokacin dana daka wani wawan tsalle ba na hau katangar rumfar kasuwar nayi sulu a bangon gini, Na dire waje na rarimi jakata na kama cin gudu . Matsanancin gudu kamar raina zai fita ya kaini cikin wani lungu inda palasdinawa suke karfina ya kare na yanke jiki na fadi, cikin murya mai taushi akayo mini sallama wasu hannuwa suka ci cira ni zaune na bude ido na duhu ya fara yi "ina ne wajen saukar baki" . Na fada ina haki, wani ya karbi jakata yabani dabino, wani kuma ya kuma ya mika mani jaka cike da tuffa da inibi da lemon zaki . YOH KAGA MUSULMAN DUNIYA KENAN . Anan zan tsaya maci gaba a page 10 Nidinne dai Shuraih Usman Inkiya 99% mamallakin shafin hausaebooks da Keffians News Teller ke cewa ALMAU'TU LIL IZRA'ILA AWA 48 A ZIRIN GAZA Na Ibrahim akhatibi daurawa Littafi na daya 1 Page 10 Typing:- shuraih Usman Post shuraih 99% . . Mun isa wani gida wasu matasa rike da bindigogi masu sarrafa kansu suka kewayeni, sun rufe fuska da makayuwa idonsu kawai ake gani, a kusurwar gidan akwai wasu dauke da "rocket propelled launcher" . Kowanne yana rike da madubin kawo nisa kusa ,muna isa daya ya dirgo yasa sauko yana bani mamaki, kuma ya tuna min da yadda yan hamas suke dirga yabani hannu muka gaisa . "Na hango yadda kayi da la'annun can ka birgeni ko ka taba yaki ne" ya saki hannuna na bashi labarin zuwana da kuma gaskiyar cewa ni dan jarida ne" Muka shiga wani dan ofis a kuryar gidan ya saka aka kawo min ruwan sha "nine aba yusuf mataimakin shugaban Hamas reshem zirin gaza da kewayenta, jin haka murna ta rufeni sosai , don wannan shine mutumin da Abuja'afar yace na nema a zirin gaza Shuraih Usman inkiya 99% . Naji kamar nazo gida , nayiwaa Allah godiya daya saukaka min abubuwana haka , amma duk da haka ban saki jiki da suba don gani nake kamar basu bane . Wayewar gari da sanyin safiya unguwar jeninta cike da matasa birjik , na fita daga layinmu na ktsa cikin jami'an tsaro cikin tsoro, na isa wani dan banki da ake canjin kudi na dade ina bin layi, . Ina gaf da zuwa kanta suka samu umarnin tsaida harkokin banki kai tsaye,dana nemi dalili matar da take kanta tace "sabon tashin hankali ya barke a zirin gaza yanzu ba shiga ba fita an rufe ko'ina" . Gabana ya fadi Allah yasa dai ba abin da ya sameni a sarayebo bane za'a maimaita ba nace araina "waya bada umarnin " na tambayeta "Peoples committee" tace dani sai na gane kwamitin jama'a na palasdinawa na ya bada wannan umarnin ba gwamnatin izra'ila bace . Kamar yaddaa na fara fashintar abubuwan tun daga jiya a wajen Abu yusuf Shuraih Usman inkiya shuraih 99% ke typing . Jama'ar cikin gari suka harzuka suka hau kan titi suna zangar zangar lumana na fice daga harabar bankin ina tafiya ina waige waige, na shiga wani shagon sai da shayi don na karya, kuma naji tsegumi . Na fara shan shayin kenan sai naji kabbara ta kaure akan titi, motocin yan sanda suna kawa da jiniya daban daban cikin sauri na kurbe shayin na fito na tsaya a bakin titi don na kashe kwarkwatar idona . Matasa mata da maza , yara da manya dauke da kwalaye an rubuta tsinuwa da la'anta ga mamayar yahudawa, wasu anyi rubutun ayoyin jihad, wasu kalmar shahada aka rubuta . Suna tafe suna kabbara suna tsinuwa yahudawa da gwamnatinsu, sahun gaba ya kunshi matasa majiya karfi da kuma wasu yara kanana cikin jan kaya, matasan suna sanye da bakaken kaya dun suna rawa irin ta soja na gabansu ya rike wata jar tuta an rubuta INTIFADA, Shuraih Usman inkiya 99% . Gefensa matasa suna zarya suyi gaba suyi baya cikin azama da kumari a bayansu wasu suna dauke da tutar palasdinu da kwalayen da suke kira ayi tawaye, wasu an yi kalmomin masu daraja da ayoyi masu tsarki . Suna tafiya cikin jin karfi suna buga takalmansu a kasa da karfi kasa tana rawa bayansu wasu matasa sunyi shiga mai ban sha'awa suna jan tutar izra'ila a kasa wani na dauke da kwali a bayansu an rubuta death to izra'ila . Haka suka ringa shigewa kungiya kungiya sahu sahu cikin tsari gwanin ban sha'awa, nan da nan jiki na ya dau tsima kamar an yimini allurar karfin jiki . Kawai ina tsaye sai naji kafata tana tsima kamar an kada mini gangi, koda wani ayarin cike da matasa majiya karfi yan bana bakwai wanda suke sanye da bakin wando da farar riga da jajayen kyalle a goshinsu , suna waka suna rawar soja suna zarya suyi gaba da gudu su dawo baya Shuraih Usman inkiya 99% suna fadin; . Shahada maganin mutuwa Allah bamu shahada Allah a gaza mana Allah karya yahudu Allah karya amurka!!! . Wannan wakar na sha jin yan hizbullah suna rera ta alokacin dana ke bosniya, ban san lokacin dana amsa musu ba, ban yi aune ba sai na tsinci kai na a tsakiyar yan zanga zanga cikin yan mintuna sai na ganni a sahun gaba . Ina rawa ina waka ina juyi ina buga kafata a titi, kamar ba ni ba duk hatsarin da nake ciki na manta cewa bafa a kasarmu nake ba, na mance kasar izra'ila nake, na manta a bin daya faru jiya atsakanina da jami'an tsaronsu, bana shakka kuma ana nemana, dadin dadawa kuma lokacin da aka kayade min saura kadan kuma yana cika akan dole na fice ko su shiga farautata, . Amma gaskiya duk wanda ya saba shiga rawar sojoji ko zanga zanga ta fito na fito yasan cewa duk wani hatsari ko tsoro bacewa suke yayin da kaga ayarin masu zanga zanga na ficewa tya gabanka, komai mantawa zakayi dashi har sai ka shiga sannan hankalinka zai kwanta, . Tun ina jami'a Shuraih Usman inkiya 99% na sha karanta babin zanga zanga da ake kira Mob Action amma ban fahimci ainashin sa ba sai dana samu kaina a gaban sahun matasar zanga zangar INTIFADA . Can mun zo tsakiyar wani fili ban yi aune ba kawai sai ga motocin sojoji dana yan sandar kwantar da tarzoma cikin mugun shiri, sunyi sahu sun shirya sosai mu suke jira mu karaso . Bayansu motocin daukar gawa sun layi kai kace yaki za'ayi tsakanin rundunoni, masu karfi kuma karfinsu yazo daya, ban taba zaton za'ayiwa farar hula masu zanga zangar lumana wannan mummunan tanadin ba , ganin yadda suka zo da motocin daukar gawa ya nuna cewa sun zo da nufin halaka mu gaba daya . Ina tsaye ina kallon wannan shirin kisan gilla sai wani matashi ya tabani "kafita daga sahunnan, kai bako ne, sa kuma sheda ka, kuma kai baka zo ne saboda gumurzu ba ka Shuraih Usman inkiya 99% barmu mune muka gaji fafatawa da yayan da Allah ya tsinewa . Naki matsawa ko'ina, wani na yazo ya gaya mini haka, toh don na sami daman kallon komai ba don naji tsoro ba, don har wannan lokacin jikina tsima yake , sai na koma gefe na tsaya ina kallon yadda mara bindiga zai fafata da mai cikakkun kayan wuta, wanda ya tanadi duk wani makami na kisa ko tsoratarwa da gallazawa dan adam . Akayi cirko cirko sojojin sun shirya tsaf sun saka hulunan gwano maganin iskar tiya gas, sun sanya wasu rigunan roba suna rike da garkuwar karfe, motocin asibiti na jiniya shiga baya sunyi layi, palasdinawa Shuraih Usman inkiya shuraih 99% masu zanga zanga suna kabbara sun a hailala suna rokon Allah yabasu juriya da nasara . "Wata doguwar mota na tabbata tankar ruwar zafi ce tayi birki, daga baya a daidai lokacin da wasu matasa dauke da bindigogi suka karasa cikin masu zanga zanga, kamar a film wani kyaftin din sojan izra'ila ya karaso fili a cikin wata mota mai sulke, ya fito da kasan daga cikin motar yayi magana ta lasifika daaga nan ya daga hannunsa alamar umarni sojoji suka karba, karar bindiga da kabbara a lokacin guda suka abku, wani abu kamar abu kamar ruwa kamar hayaki yayi tsiri sama daga dogon bututn dake gaban tankar ruwan zafin..................." . Anan muka kawo karshen littafi na daya Marubucin yace zai cigaba a AWA 48 A ZIRIN GAZA na biyu Ibrahim akhatibi daurawa nagode , wassalam . Ammafa jama'a sai dai kuyi hakuri don bani da littafi na biyun Shurarih Usman inkiya 99% . DIRAR MIKIYA Yakin basasa yayi kaca kaca da kasar somaliya , Yunwa na kashe mutane yan tawaye da sauran yan ta'adda suna cin karensu ba babbaka , gefe daya sojojin Amurka suna kokarin mamaye kasar gaba daya , sun shiga fasadi da mata da yada gurbatattun Al'adunsu . Daga ibrahim akhatibi daurawa SANARWA Wannan labarin kago shi akayi, amma akwai abubuwa da yawa a cikinsa wanda suka faru a tairhi ka bincika sosai zaka karu . Alura sosai ba fim bane, an rubutashi sakamakon bincike mai zurfi na lokaci mai tsaho Ba'a yarda a juya shi ta kowacce irin hanya ba, sai da rubutaccen iznin marubucin . DAGA IBRAHIM AHMAD DAURAWA Sarayebo. 1,2,&3 Dirar Mikiya Baradan Chechen Kundunbala Hadirin Kasa Kowane Allazi. 1&2 Tarnaki Gidan Rina Awa 48 A Zirin Gaza 2 . P.O. Box 5055, kano Anfara bugawa a 2000 INAD Publisher Al-khatibi, 2000 . Kada ku manta zaku iya downloading wannan littafi zuwa kan wayoyinku ta hanyar ziyartar shafinmu na yanar gizo gizo Hausaebooks . Ko kuma kuyi searching nashi a google ku downloading . Daga Naku Shuraih Usman Inkiya 99% Littafinmu na gaba shine TARAR ARADU Littafina Uku 3 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels