Compiled by Umar Dalha. Copied by NAJA Mufeeda Mu'azu. 😰😰😰😰😰😰 AUREN DOLE 😰😰😰😰😰😰 *TALENTED WRITERS FORUM* *T.W.F* BOOK 2 Page 1 - 5 Story nd written By Mufeeda Muazu Bismillahir rahmanir raheem mosoyana ina ganin sakonninku ina godiya fatan alkhairi gareku Dedicated dis page 2 talent writers forum Bazan manta daku ba Classic feedoh Feedohm Sunera Basma er lele Halima Ameen Jin kara yasa su jidda juyowa Dalhat suka gani rike da Hudah tana kokarin kwacewa amma ta kasa saboda irin rikon da yayi mata sai kuka take tana kiran hajiya ganin zata tara masa mutane yasa ya dauketa cak ya shige da ita part dinsu Sumayya ta tintsire da dariya tace Allah ya kara Jidda tace kai keko baki da tausayi Sumayya ta harareta tace tunda ke kinada tausayi ai sai kije ki kwatota mata da mijinta jidda ta kai mata duka da gudu Sumyya ta shige part din su Jiddan tana yi mata gwalo dakin kasa suka shige dukkansu sukayi kwanciyarsu a gado Jidda kuwa falo ta wuce anan taga Radiya tana zaune tana kallo amma kwata kwata hankalinta baa tv yake ba Jidda ta zauna a one seater Radiya ta harareta ta tsuka tsaki Jidda dai ko kallonta batayi ba Wacece Radiya Radiya Ahmad tijjani yar kanwar Ummi ce wato Aunty Ramlat babanta yana da kudi sosai Radiya irin shagwababbun yaran nan ne wanda baa musu fada duk abinda sukayi dai dai ne tana son Dalhat sosai shi kuma sam batayi masa saboda shi a tsarinsa yafi son mace mai kunya da kawaici saboda hakene yasa basa shiri da Jidda ita gani take bata so dan uwanta ya aureta tafi son ya auri Hudah saboda kawarta ce Allah sarki Jidda baiwar Allah ba ruwanta Cigaban labari Jidda bata so taga Radiya a falo.ba saboda kada ta bata musu shirinsu don tasan halinta sarai ba mutunci ne da ita ba Jidda ta dauki remote ta kashe tv Radiya tazo ta fizge remote din ta hau mata masifa wai don mene tana kallo zata kashe mata don wulakanci Jidda tace bakiga dare yayi bane Radiya tace ina ruwanki koke kika kunna kuma wlh daga ke har Hudan sai nayi maganinku sai kun raina kanku nice na dace dana auri yaya Dalhat ba wata banza ba Jidda tace haba Radiya wai me kike nufi ne ka baki yarda da kaddara bane iyayen mu su suka hada auren itama baso takeyi ba Radiya tace dallah rufe mana baki Jidda tashi tayi ta shiga kitchen ta barta tana zage zage ita kadai A bangarensu Dalhat kuwa tunda ya dauketa bai direta ko ina ba sai kan gado sai ihu take tana birgima kamar karamar yarinya kallonta yayi fuska a murtike kiyiwa mutane shiru kafin inyi kasa kasa dake ganin ba wasa a fuskarsa yasa tasa hannu ta toshe bakinta toilet ya shige yana shiga ta diro daga kan gadon ta nufi kofa ta murda tajita a rufe waige waige ta fara tana neman makulli bata ganiba can kamar ance ta kalli sama sai ga key din a saman wardrob da sauri taje ta dauka ta bude kofar a hankali yadda bazaiji ba ta fita Tana xuwa main kofa ta fita aguje sai part dinsu Jidda ta baya dama tunda ta fito jidda ta hangota ta kitchen don haka ta bude kofar kafin ta iso Hudah na zuwa ta kama kofar zata kwankwasa Jiddah tace shigo da sauri Hudah ga yaya Dalhat can yana waige waige kuma na tabbar dake yake nema Hudah ta shigo da sauri da rufu kofar da karfi jin kara yasa shi juyoya da sauri tasa ma kofar key tana ajiyar zuciya Hudah ta kalli Jiddah,Jidda ka kalli Hudah ba wanda dai yayi ma wani magana suna tsaye basu bar kitchen din ba har ya kariso Hudah tana wurin windo tace gara ma ka koma ka kwanta dan wlh ba mai bude kofar nan inma ummi zaka kira tayi bacci tana sama Dalhat yayi kwafa yace zanyi maganinki daga ke har Jiddan wayarsa ya ciro daga aljihu yayi dialing numbern Ummi ya kara sau uku har ya gama riging bata daga ba............. 🌱🌱🌱🌱 Muffy 🌱🌱🌱🌱 😰😰😰😰😰😰 AUREN DOLE 😰😰😰😰😰😰 💦💦💦 *TALENTED WRITERS FORUM*💦💦💦 *TWF* BOOK 2 Page 6 - 10 *Story nd Written* *by* *Mufeeda Muazu* Bismillahir rahanir raheem Kwafa yayi ya juya Jiddah tace Hudah nidai gsky babu ruwana kada ki kuskura kisa sunana a ciki wlh ba ruwana Hudah ta harareta batace komi ba barin kitchen din sukayi a kofar kitchen din sukaci karo da Radiya tana musu labe Hudah ta zabga mata harara tare da tsaki tayi gaba abinta Jidda ne tace kedai wlh Radiya halinki baida kyau Radiya tace duk munafuncin da kuka kulla duk a kunnina kuma sai na fadawa Ummi Jidda tace ki fada mata mana sai me itama ta wuce ta barta anan tanata maganganu falo suka kwanta Jidda a 2seater Hudah ya 3seater Radiya tazo ta wuce su ta haura sama a nan dai bacci ya kwashe su Dalhat kuwa tunda ya tafi daki yake tufka da warwarar yadda zai wulakanta Hudah shima daya gaji kwanciya yayi nan da nan bacci ya kwashe shi saboda dama a gajiye yake lokacin daya kira Ummi idonta biyu amma wayar tana silent ne asuba nayi kamar a kunnen Hudah aka kira sallah a hankali ta tashi jidda tayi sallah saboda ita tana fashin sallah Jidda da kyar ta tashi saboda gajiya daki ta shiga ta tarar dasu sumayya sai baccinsu sukeyi tashinsu tayi sannan ta shige toilet tayo alola sannan ta dauki sallaya tafito falo anan ta tarar da Hudah zaune tayi zubga tagumi Jiddah tace lpy Hudah kikayi tagumi haka Hudah tace bkm Jiddah bari in tafi kafin ya dawo ya tara mun mutane Jidda tace to amaryan yaya sai mun shigo Hudah ta fita tana harararta da sauri ta fita lokacin gari bai gama wayewa ba a bude ta tarar da kofar tayi sauri ta shige dakinta ta shige ta shiga toilet ta gyara kanta sannan ta fito ta kwanta can karshen gado ta rufa da bargo tana jin lokacin daya shigo dakinsa ya shiga bai dade da shigowa ba taji fitar sa dada lafewa tayi side dinsu ya tafi baiga kowa a falo sai motsi dayaji a kitchen ya leka Ummi ne da Jiddah sai Radiya shiga yayi ya duka har kasa ya gaisheta da faraarta ta amsa har take tambayar ya Hudah shiru yayi bai ce komi ba Radiya da Jidda suka gaishe shi a tare fuska a daure ya amsa yace Ummi Hudah bata kwana a side dinmu ba Ummi ta ta juyo a firgice tace to a ina ta kwana Dalhat yace a tambayi Jidda Ummi tace jidda kuma Jidda dake fere dankali ta tsaya duk ta rude batasan wani irin mataki Ummi zata dauka ba Radiya tace eh Ummi jiya bayan sun dawo dasu Sumayya duk suka shige daki Jidda ta dawo falo ta zauna nima a lokacin ina zaune a falon ina kallo baa dade ba sai tashiga kitchen can naji ta bude kofar baya suka shigo nidai sama na haye bansan abinda ya faru ba Ummi ranta yayi matukar baci ta janyo Jiddah da karfi kyawawan mari ta zabga mata duka kuncin sai da taga wuta dafe wurin tayi tana kuka tace Ummi ni ba ruwana karyar Radiya ne Ummi tace in ita Radiya tayi miki karya Dalhat zaiyi miki karya ne yanzu ina Hudan take Jidda murya na rawa tace tana side dinta kuma ba anan ta kwana ba Dalhat yace zakiyi wa mutane shiru ko kuwa sai na babbala ki Ummi tace Dalhat muje side din mugani ba musu suka tafi side din har da Radiya A daki suka sameta kwance idonta a rufe kamar mai bacci jin maganar Ummi yasa tayi sauri ta tashi ta zauna ta gaisheta da kyar Ummi ta amsa ganin Jiddah na kuka yasa ta dukar da kai tana hawaye Ummi tace ina kika kwana jiya Hudah tayi shiru batace kom Ummi ta daga murya tayi bada ke nake magana ba murya na rawa tace anan na kwana Ummi Radiya tace karya ne wlh Ummi tace wayasa bakinki ciki shiru tayi Ummi tace tunda bazaku fadi gsky ba to zan fadawa Abbu yasan halin da kuke ciki Hudah tace Allah zamu fada a baa nan na kwana ba a side dinsu jidda na kwana amma ba ruwan Jiddah Ummi kiyi hakuri haka bazai kara faruwa ba Ummi tace to shikenan ya wuce nan dai tayi musu nasiha sosai sannan ta tafi Dalhat ma yabi bayanta dakin ya rage daga ita sai Jiddah da Radiya Hudah ta tashi tsaye ta isa inda Radiya ke zaune ta fincikota tace malama a fita mun a daki banda munafunci ina ruwanki damu harda sawa a mari Jiddah na wlh ki kiyayeni............. 🌱🌱🌱 Muffy 🌱🌱🌱 😰😰😰😰😰😰 AUREN DOLE 😰😰😰😰😰😰 💦💦💦 *TALENTED WRITERS FORUM*💦💦💦 *TWF* BOOK 2 Page 11 - 15 *Story nd Written* *by* *Mufeeda Muazu* Bismillahir rahanir raheem Radiya tace idan baa fita ba fah Hudah tace jikin mutum yanxu yayi tsami Radiya tace bazan fita ba inada ikon shiga ko'ina a gidan nan don ba gidan ubanki bane Hudah tace aike gidan ubanki ne ni gidan mijina ne inada iko ke kuma fah ashe maganar tayiwa Radiya ciwo daga hannu tayi zata mareta sai a lokacin Jidda tayi magana tace ke Radiya baki da hankali ko rike hannun Hudah tayi ta zabga mata mari ji kake tasssss!!! dai dai lokacin Dalhat ya shigo Radiya tana ganinsa ta kara narkewa ta dada rushewa da kuka bai tambayi meya faru ba kawai ya hau Hudah da duka saida yayi mai isar sa sannan ya kyaleta Radiya tana gefe tana mata gwalo fuska ba annuri yace su tafi side dinsu Jidda jiki ba karfi ta fita tana mai tausayawa Hudah Radiya kuwa ranta fes kamar ranar sallah Suna fita ya matso kusa da ita dama da kula guda biyu ya shigo idonta rufe tana share hawaye yace tashi kije kitchen ki dauko mana plate da flask akwai ruwan zafi a ciki ba musu ta tashi taje ta dauko ta aje masa a gabansa ta koma can nesa dashi ta zauna hararanta yayi yace waye kika aje wanda zai zuba mun ko kina nufin da kaina zan zuba jikinta a sanyaye ta tashi ta zauna a kasa kusa da shi kamshin turarenta ya daki hancinsa saida ya lumshe ido ruwan zafi ta zuba ta kalleshi idonta duk ya kumbura shi kanshi ta bashi tausayi kawar da kai yayi yace lpy kika tsareni da ido kaman na mujiya sunkuyar da kai tayi tace kana son sugar dayawa hararanta yayi yace ni ni sha zumami ne bata kara cewa komi ba ta hada masa ta tura masa gabansa sannan ta dauko plate ta zuba masa wainar fulawar ta koma gefe daya ta takure tsawa ya daka mata yace bani son munafurci kin wanije kin takure me kike nufi come on zokici abinci jiki na rawa ta taso ta zuba kadan ta hada tea din ta koma zata zauna yace dole sai dai ta zauna a gabansa bayadda ta iya haka nan ta zauna da kyar ta tuttura abincin bayan sun gama ta kwashe komai takai kitchen a falo tayi xamanta tana kallo Shiko yana daki yana jiranta dayaji shirun yayi yawa ne ya fito ya gani kota Kara guduwa ne sai ya ganta a falo daure fuska yayi yace ke wa kika aje dazai gyara miki daki kin wani dawo nan tashi tayi tana matsar kwallah ta rabe ta wuce ta gabansa sai da ya lumshe ido saboda daddan kamshinta tana shiga daki ita bataga wani datti ba gado ne kawai ya dan bacci tsaki tayi bata sani ba Ashe yana bayanta sai ji kawai taji yace wa kikewa tsaki matsawa tayi da baya tace Ina ruwanka dani duk kabi ka takurawa rayuwata matsowa yayi ta kara matsawa a haka a haka har saida ya kaita bango suna shakar numfashin juna yace ke ni zakiwa rashin kunya kasa tayi da kanta batace komi ba kugunta ya rike yace bada ke nike ba jitayi yarrr!! tace to shine don iskanci bazakai wa mutum magana ba sai ka taba shi girgiza kai yayi yace nine dan iska ko to yau kuma yanzu xan nuna miki ni dan iskane na gaske nan da nan gabanta ya shiga faduwa amma ta dake saboda kada ya rainata zip din rigarta ya zage ta rike rigar iya karfinta nan suka fara kokowa nan dai yafi karfinta ya cire rigar kuka ta farayi ya jefata kan gado daga ita sai bra hau gadon yayi da karfin tsiya ya ciremata kuka take kaman ranta zai fita..... 🌱🌱🌱🌱 Muddy 🌱🌱🌱🌱 😰😰😰😰😰😰 AUREN DOLE 😰😰😰😰😰😰 💦💦💦 *TALENTED WRITERS FORUM*💦💦💦 *TWF* BOOK 2 Page 16 - 20 *Story nd Written* *by* *Mufeeda Muazu* Bismillahir rahanir raheem Dedicated dis page 2 Muffy Hausa novels, Meenat hausa novels Rufaida ce ta shigo bako sallama su sumayya na bayanta da sauri suka juya shi kuma tashi yayi ya gyara rigarsa ya kalleta yace ki shirya zamu hadu anji zaki gane kurenki ita dai bata ce komai ta dauko rigarta ta saka fita yayi Daga dakin a falo ya wuce suna zaune yana fita sumayya ta shigo tana dariya harda tintsirawa Hudah dai tana kallonta ta takure tana hawaya su jidda suma duka shigo! Rufaida kuwa sai cika take tana batsewa kaman ance ta shigo dole Sumayya da JIdda ne suka zauna kusa da Hudah sumayya tace Amarya yaya jiki Hudah tai banza da ita kaman bata jiba ta Kara matsawa kusa da ita tace nace yaya jiki Hudah tai tsaki tace dallah malama ki kyaleni an gaya miki ciwo nikeyi Jidda tace kyaleta Hudah neman magana take Rufaida ce ta tsuka tsaki mtsw....... tace aikin banza munafukai kawai wlh sai kin bar gidan nan nice na dace da yaya bake ba yar qauye kawai Hudah zatayi magana su sumayya suka hanata Tashi sukayi suka koma falo suka barta anan tanata zage zage a falo ne Hudah take basu lbrn abinda ya faru tsakaninta Dalhat sumayya tace da zan baki shawara kiji da sai ince kiyi hakuri da kaddara ki rungumi mijinki kinga wata so take ta kwace Kuna ki daina fada masa irin maganganun da kike fada masa Jidda tace yawwa sumayya fada mata kila ke zataji naki Hudah ta goge kwallar daya zubo mata tace shima fah ba sona yake ba nidai mafita kawai nake nema yanzu Sumayya tace baki da wani mafita illa kawai kiyi hakuri idan Kuma kinki ke zaki sha wuya wlh Hudah tace jidda ki taimaka mun jiddah ta bude ido tace rufa mun asiri kiyi hkr kawai in ba so kike yaya ya karkaryani bane Bangaren Dalhat kuwa yana fita side din Abbu ya tafi a falo ya tarar dashi yana zaune yana karyawa cikin ladabi ya gaishe shi Abbu ya amsa cikin sakin fuska Dalhat yace Abbu na kawo karar Jidda ne saboda kada in dauki hukunci a hannuna kace nayi ba dai dai ba Abbu yace hakane me kuma autar tawa tayi Dalhat ya zayyane masa duk abinda ya faru Ran Abbu ya baci matuka yace kayi hkr Dalhat insha Allah zan dauki mataki Dalhat yayi godiya ya tashi ya tafi Gidansu Hudah kuwa hajiyace ta hana a shiga wurin Hudah wai sai dai in zasu tafi sai su shiga suyi mata sallama Aunty binta ce tace ita dai sai ta shiga ta duba lpyr yarta Suna zaune a falo Hudah sai kuka take sun sata a tsakiya sun rasaj yadda zasuyi da ita sai ga Aunty binta ta shigo tace lpy take kuka ku kuma kun tasata gaba kaman masu zaman makoki jiddah tace Aunty wlh tun daxu muke lallashinta amma taki yin shiru Hudah ta tashi da gudu ta rungume Aunty binta tana kuka tace Aunty don Allah ki tafi dani wlh yaya Dalhat kasheni zaiyi yace baya sona Aunty binta tace ki natsu Hudah Dalhat yana sonki kinji kiyi hkr nan dai taita lallashinta har tayi shiru Hudah tace Aunty binta muje daki kiji wata magana suka shiga daki zauna suka tarar da Rufaida..... 🌱🌱🌱🌱 Muffy 🌱🌱🌱🌱 😰😰😰😰😰😰 AUREN DOLE 😰😰😰😰😰😰 *TALENTED💦💦💦* *WRITERS FORUM*💦💦💦 *T W. F* Dedicated dis page 2 all talented members Www.Mufeedamuazu.blogspots.com BOOK 2 Page 21 - 25 *STORY AND WRITTEN BY* *MUFEEDA💦 MUAZU*💦 Bismillahir rahmanir rahim Zaune suka a bakin gado suka tarar da Radiya ta daura kafa daya kan daya tana chatting abinda hankali kwance kaman tana dakinta Jin karar bude kofa yasa ta dago da kanta Hudah ta kalleta ta watsar tace malam sai ki fita ki bamu wuri zamuyi magana nida uwata tunda dai ba dakinki bane Radiya tace idan baa fita bafa Aunty Binta tace yi hakuri baiwar Allah Radiya tace ina ruwanki haushi ya Kama Hudah da karfin ta figi hannun Radiya ta ingizata waje ta rufe kofar da key. Aunty binta tace Hudah sai kinyi hkr ba kowani Abu bane zaki ringa kulawa ba Hudah tace Aunty kinga wannan yarinya bata da mutunci bata ganin kowa da gashi wai ita dole son yaya Dalhat takeyi Ni wlh dama ita aka aura miki Aunty binta tace lallai baki da hankali wace magana zaki fadamun tafiya zamuyi Hudah idanunta suka cika da kwallah tace Aunty don Allah ki gudu dani wlh yaya Dalhat mugu ne wlh ban san wani abu kuma zaiyi mun ba idan ya dawo Aunty ta tausasa murya tace Hudah kiyi hkr ki kwantar da hankalinki kinji kiyi masa biyayya kinsan dai iyayenki baza su cutar dake ba kiyi hkr ki cigaba da addua kuma kiyi taka tsantsan da yarinyar nan Don na kula batada da tarbiyya zata iya yin komi akan mijinki don haka ki dage da addua muma iyayenki zamu tayaki Hudah cikin sanyin murya tace to Aunty ngd sosai tashi tayi ta bude kofar bata ga kowa a falon ba Sukayi sallama da Aunty har gate ta rakota tana kuka tana ganin gidansu kaman ta shiga Amma ba dama tana kuka suka rabu da aunty Side dinta ta koma ita kadai ta zabga tagumi tana tunanin Irin rayuwar da zatayi a gidan Radiya tana fitowa su sumayya ba Wanda ya ko kalleta cikin jin kunya ta tashi ta bar dakin! Bata dade da fita ba sumayya tace su zo su rakata ta hada kayanta anjima zasu tafi Hudah na zaune shiru ita kadai a daki wurin karfe 4pm ta jiyo muryar yan uwan mamanta Harda su sumayya sunzo yin mata sallama zasu tafi Nasiha suka dada yi mata sannan suka wuce rungume juna sukayi da sumayya Suna kuka da kyar suka rabu Jidda ta rakasu har mota sannan ta dawo Side din Hudah ta dawo gida duk an warwatse saura Radiya dataki tafiya wai sai ta Kara sati daya Hudah tace jidda gobe zakije skull ne Jidda tace eh zani insha Allah Hudah tace nima Inaso inje idan kin shirya ki biyo mun Jidda tace nidai ba ruwana kiyi hkr a dan kwana2 kin san yaya Dalhat bazai bari Idan an kwana2 sai kiyiwa ummi magana Hudah tace to shikenan bkm Suna zaune Suna hira har magriba Jiddah tayi sallah aka kawo abinci sukaci suka ajewa Dalhat nashi sai issha tayi mata sai da safe ta tafi Tashi tayi ta shiga wanka tai wanka ta gyara kanta ta sauya kaya ta fesa turare kayan bacci tasa mai kauri tayi kwanciyarta Bai shigo ba sai wurin karfe 9pm ya shigo yaji gidan Yayi shiru kaman ba kowa dakinsa ya wuce Yayi wanka yasa kayan bacci Sannan ya wuce dakin Hudah ya murda yajita a rufe dakinsa ya koma ya dauko extra key ba bude kallonta Yayi yanda take barcinta cikin nutsuwa saita burge shi Side bed din ya bubbuga a hankali ta fara bude idonta ganin ta bude ido yasa ya daure fuskarsa Yayi kaman bai taba dariya ba Tashi tayi ta zaune idonta ya cika da kwallah kallonta yayi ya watsar sannan yace ke ina abinci na a hankali tace yana dinning tsawa ya daka mata yace a nan zanci kije ki kawo ina jira saura ki dade....... 🌱🌱🌱🌱 *Muffy* 🌱🌱🌱🌱 😰😰😰😰😰😰 AUREN DOLE 😰😰😰😰😰😰 *TALENTED💦💦💦* *WRITERS FORUM*💦💦💦 *T W. F*💦💦 Dedicated dis page, 2 sis Asy khaleel Www.Mufeedamuazu.blogspots.com BOOK 2 Page 26 - 30 *STORY AND WRITTEN BY* *MUFEEDA💦 MUAZU*💦 Bismillahir rahmanir rahim Ba musu ta mike ta fita tana share kwallar daya zubo mata bata dade da fita ba ta dawo da tray a hannunta ta aje a gabansa Komawa tayi ta dauko lemu da cup shima ta aje a gabansa ta koma zata xauna yace wa kika aje da zaiyi serving dina Haka nan ta juyo ta duka a gaban ta dauko kusa dashi sai kamshin humra takayi gogan kuwa sai lumshe ido yake yaji kamshi mai sanyi Tuwon shinkafa ne miyar agushi ta zuba masa ta tsiyaya masa lemun a zuciyarsa addua yakeyi Allah yasa tayi zamanta kada ta tashi saboda bai gaji da jin kamshin ba Tana gama zuba masa kuwa ta miki ta koma gado tayi kwanciyarta ta dauki wayarta a bed side ta hau online jidda ta gani Jidda tace Amarya kin sha kamshi ina angon ya barki kina chatting Hudah tace gashi nan abinci yake ci Jidda tace to dan Allah ki aje wayar ki kular mun da yayana Hudah tace goya shi kikeso inyi ko mene Jiddah tace rufa mun asiri ni bance ba Abinda Hudah bata sani shine Dalhat yana tsaye a kanta yana kallonta yana tana danna waya tana smiling Ji kawai tayi an fisge wayar batayi wani yunkuri ba sbd tasan Dalhat ne yace ke dawa kike chating kike wani smiling dukar kanta kasa tayi batace komi ba Duba wayar yayi yaga swt sis budewa yayi ya krnta chat dinda sukayi murmushi yayi a zuciyarsa A fili kuwa daure fuska yayi yace ki kwashe tray dinnan ki kai kitchen ki dawo xamuyi mgn minti biyar na baki Idan kuma kika kara koda sec ne nida kene a cikin gidan nan Kwashe komi tayi ta gyara wurin tsaf yana kallonta yana kallon agogo 5mns dai dai ta gama ta dawo ta zauna Har yanxu fuskarsa a daure take yace kije ki alola kizo muyi sallah tana zaune ko motsawa batayi ba balle tai yunkurin tashi Tsawa ya daka mata har saida yan hanjin cikinta suka kada yace bakiji abinda nace ba kenan Duk ta daburce cikin rawar murya tace ba... ba... bana sallah kusa da ita ya matso yace karya kikeyi wannan shine dabaran da kuka shirya kenan zaki tashi ko sai na bata miki rai Hawaye ke zubo mata kamar an bude famfo tace Allah yaya ba karya nake da gske nake Girgiza kai yayi yace naji kwana nawa kikeyi kanta a kasa tace 5days to yaushe kika fara tace jiya yace to shikenan Ba damuwa Amma duk da haka sai na nuna miki Niba yaro bane Hudah tace dan Allah kayi hkr wlh wasa nake maka Dalhat yace ni abokin wasanki ne dama oya taso kixo nan ya nuna kusa dashi tayi kamar bataji ba tashi yayi yace tunda baxaki zoba ni sai inxo kuma xuwana wani karin hukunci ne a wurinki Mikewa tsaye tayi ta fara ja da baya yana binta harta kai bango tsugunnawa tayi ta fashe da kuka daukar ta yayi cak ya kaita gado nan ya dinga romancing dinta na hauka tun tana kokowa harta gaji ta kyaleshi sai hawaye da takeyi wani na bin wani Bai bari ta huta ba har asuba sannan ya tashi yayi wanka ya tafi masallaci ya barta a kwance da kyar ta iya tashi duk jikinta yayi tsami.... 🌱🌱🌱🌱 *Muffy* 🌱🌱🌱🌱 😰😰😰😰😰😰 AUREN DOLE 😰😰😰😰😰😰 *TALENTED💦💦💦* *WRITERS FORUM*💦💦💦 *T W. F*💦💦 Www.Mufeedamuazu.blogspots.com BOOK 2 Page 31 - 35 *STORY AND WRITTEN BY* *MUFEEDA💦 MUAZU*💦 Bismillahir rahmanir rahim Toilet ta shiga dama yau zata gama period dinta but tayi masa karya wanka tayi sannan tayo alola ta fito ta zauna gaban mirror ta goge kanta da karamin towel sannan tadan shafa mai ko powder bata shafa ba sai humra data goga wani gown ta dauko red mai ratsin baki ta saka kayan sunyi mata kyau sosai duk da ba wata kwalliya tayi ba saida tayi sallah sannan ta gyara dakin tsaf sannan ta kunna burner tasa turaren wuta dakin ya dauki kamshi da kyar ta fita falo duk ta gaji dakin Dalhat ta shiga ta wanke toilet sannan ta gyara dakin ta gyara koina a gidan, gida ya dauki kamshi Daki ta koma ta kwanta nan da nan bacci mai nauyi ya dauketa shiko Dalhat tunda ya tafi masallaci bai dawo ba sai 7am koda ya dawo ma side dinsu ya tafi a kitchen ya samu Ummi gasheta yayi ta amsa cikin kulawa Tambayarsa tayi ya Hudah ta kwana lpy klu yace mata Ummi ina Jidda me takeyi har yanxu bata tashi ba ta barki ke kadai a kitchen Ummi tace suna can daki ita da Rufaida bata dade da komawa ba zata fara shirin skull Kasan yau Monday Baice komi ba ya koma falo ya zauna yace Ummi wai me Rufaida takeyi bata tafi ba Ummi tace ina ruwanka komi ta tsare maka yata ce don haka babu ruwanka Dalhat yace Allah ya baki hakuri Ummi ina Abbu? Ummi tace ban saniba ka tashi ka tafi can wurin matarka kaxo nan da sassafe zaka dame mu Dalhat yace au korata ma akey Ummi tace eh ka girma murmushi yayi yace bari in tafi tunda korata akeyi tashi tayi Ummi tace ka gaisar mun da diyata murmushi yayi ya fita bai ce komi ba yana zuwa kofar side dinsu yaji kamshi ya daki hancinsa. Wani irin dadi yaji acikin ransa yana shiga yaga koina tsaf sai kamshi ke tashi dakinsa wow ya fada toilet ya shiga yayi wanka yayi brush Shiryawa yayi cikin white boyel ya fesa turarensa mai dadin kamshi wurin 8:30pm ya fito dakin Hudah ya shiga a kwance ya tarar da ita tana baccinta cikin nutsuwa Zama yayi kusa da ita ya kura mata ido a zuciyarsa yace to meye aibun Hudah tanada duk abinda yake bukata a wurin mace uwa uba ga tsafta saurin kawar da sannan tunani motsawa tayi saurin tashi yaya ya bubbuga gefen gado tashi tayi tana murmurxa ido a hankali ta bude idonta tsaf Daure fuska tayi a tsiwace tace malam lpy mutum na bacci dan wulakanci zaka tasheni bayan kai ka hanani baccin don zalunci Tsayawa kawai yayi yana kallonta yace lallai yarinya baki hankali ba Amma nan da 3days idan ance ki daga kai ki kalleni koda kudi bazaki iyaba balle har ki iya fada mun magana Irin wannan Ina breakfast dina Hudah tace ban girka ba kuma bazan girka ba don ba yar aiki aka kawo maka ba Daure fuska yayi yace kafin in dawo ki tabbatar kin gama breakfast in ba haka ba wlh ranki sai ya baci ya fita fuu...... Yana fita tace wlh bazanyi ba sai dai idan ka dawo ka kasheni komawa tayi ta kwanta abinda Bangaren su Jidda kuwa karfe 9:45am ta sauko kasa domin karyawa anan ta tarar da kowa Harda Rufaida Dama sun gaisa da Ummi ta gaisar da daddy taja kujera ta zauna nan daddy yayi mata fadan abinda sukayi hkr ta bashi Rufaida sai hararanta takeyi ko kallonta jidda batayi ba 10am suke da lecture ta makara sallama tayiwa su Ummi ta dauki key din motarta da tafi bata shiga side din Hudah ba sai ta dawo don tasan halin Hudah yanxu sai ta dama musu lissafi 10:30am Dalhat ya shigo gidan yaji shiru dakinsa ya shiga direct ya dauko belt sannan ya tafi dakin Hudah cikin bacin rai Bacci ya tarar tanayi iya karfinsa ya zabga mata a firgice ta tashi tana kuka tambayarta ina breakfast din tace ban girka ba Ba kuma zan girka ba sai dai ka kasheni.......... 🌱🌱🌱🌱 *Muffy* 🌱🌱🌱🌱 😰😰😰😰😰😰 AUREN DOLE 😰😰😰😰😰😰 *TALENTED💦💦💦* *WRITERS FORUM*💦💦💦 *T W. F*💦💦 Www.Mufeedamuazu.blogspots.com BOOK 2 Page 36 - 40 Dedicated dis page 2 my beloved sisters *Nafisa Muazu* *Aisha Muazu* *Hanifa Muazu* *Khairat Muazu* *Najaatu Muazu* Allah ya bar zumunci *STORY AND WRITTEN BY* *MUFEEDA💦 MUAZU*💦 Bismillahir rahmanir rahim Tashi tayi a guje zata fita sauri yayi ya rufe kofar tsayawa tayi tana kuka sai da Dalhat ya daketa san ransa sannan ya bude kofa ya tasata har kitchen ya tsaya a bakin kofa yace 15mns ya bata ta gama gas ta kunna ta daura ruwan zafi hade da kayan kamshi Sannan ta soya masa kwai ruwan na tausa ta juye a flask dinning ta kai masa dama jiya Jiddah ta kawo bread da daddare Ta kai masa yana zaune zata wuce ya riko hannunta yace zauna ki karya kema hawaye na bin fuskarta tace na koshi ko an gaya maka yunwa nakeji Da karfi ta saki hannunta tace malam sakar mun hannu belt dinsa ya dauko yace zaki zauna ko sai na fasa miki jiki share hawayen daya zubo mata tayi ta zauna Tea ta hada rabin cup da kyar ta iya shanyewa ta tashi ta shige dakinta ta kwanta taja bargo ta rufa tunani take kala kala a cikin ranta Husnah ke rokon Hajiya don Allah ta barta ta shiga wurin Hudah da kyar Hajiya ta barta Amma tace karta dade tace to da saurinta ta dauko gyalenta ta fito Saida ta shiga ta gaida Ummi sannan ta wuce side din Hudah a falo ta tarar da yaya Dalhat yana kallo gaishe shi tayi ya amsa cikin sakin fuska ya tambayi su hajiya tace duk lpy klu Dakin Hudah tashiga a kwance ta ganta Hudah najin motsi tai Sauri ta goge hawayen fuskarka husna tace Aunty lpy na ganki haka ko baki da lpy ne Hudah tace Haba Irin wannan tambaya sai kace yar jarida kuma sai yau kika daman zuwa ga baki ga hanci husna tace don Allah kiyi hkr wlh hajiya ce hanani shigowa wai zanzo in takura miki yanxu ma da kyar ta barni kuma tace kada in dade Hudah tace lallai aiko zaki dade don sai kinyi mun girki zaki tafi don bana jin dadi husna tace toh ki kirata ki fada mata kada tayi fada Hudah tace bazata yi ba husna tace to meza a dafa Hudah tace coconut rice sai Kuma sakwara da miyar agushi amma idan kin gama sakwarar kisa a babbar food flask ki barshi a kitchen din Sai kuma kunun aya don Allah kiyi mai dadi komi na nan a kitchen husna tace to naga yaya Dalhat a falo Hudah tace to ina ruwana kije kiyi abinda nasaki Husna tace to mayafin ta cire ta wuce kitchen bata ganshi ba Hudah kuwa komawa tayi ta kwanta nan da nan bacci ya dauketa husna ko tana kitchen sai aikinta takeyi Dalhat tunda husna tazo ya dauki key din motarsa ya fice karfe 1:30pm husna ta gama komi gidan sai kamshi yakeyi ta jera komi a dinning ta gyara kitchen din tsaf sannan tazo tayi alola ta tashi hudah Hudah tace wow har kin gama kenan husna tace eh na gama har nayi alola Hudah tace ngd nima bari inyo alolar toilet ta shiga tayo alolar itama taxo tayi sallah Hudah kinci abinci ne husna tace aa hudah tace ina yaya Dalhat din Husna tace baya nan Hudah tace yawwa zubo mana abincin kika kawo mana nan da kunun ayar Anan sukaci abincin su Hudah dai taki cire hijjabi saboda kada husna ta taga shedan bulala tayita mata tambayoyi Karfe 2:15pm Dalhat ya shigo gidan kamshine ya Daki hancin sa saida ya lumshe ido saboda dadin kamshin...... 🌱🌱🌱🌱 *Muffy* 🌱🌱🌱🌱 [3/11, 9:23 AM] Naja: 😰😰😰😰😰 AUREN DOLE 😰😰😰😰😰 💦💦💦 *TALENTED WRITERS FORUM*💦💦💦 *T. W. F* BOOK 2 Page 46 - 50 mufeedamuazu.blogspot.com *STORY AND WRITTEN BY* *Mufeeda Muazu* Bismillahir rahmanir rahim Shima wuri ya samu kusa da ita ya zauna matsawa tayi ya matso da taga ya kure wurin ta mike zata canxa kujera fixgota yayi ta fado jikinsa ya matseta mutsu mutsu take tana kokarin kwacewa ta kasa kwalla ne ya zubo mata tace malam ka sakeni mugu kawai Murmushi yayi yace lallai yarinya kin raina ni ammah zanyi maganin rashin kunyarki yace abinci nafa Hudah ta turo baki tace gashi can a dinning yace baa anan zanci ba kowo mun Tashi tayi ta dauko masa sai kallonta yakeyi duk da ta sanya hijabi duk sai ta tsargu sakwara ne miyar agusi ta kawo ta aje masa zata tafi yace ina zaki dawo ki zauna ya nuna mata kusa dashi ba yadda ta iya hakanan ta zauna tana kumbura baki Yace wannan hijab dinfa na menene common cire shi banza dashi tayi kamar bata jiba kyaleta yayi ya bude abinci aroma din abincin yasa shi ya lumshe ido yaci abincin sa ya koshi tana nan zaune ya hanata tashi saida ya gama Sannan yace ta kwashe Ta kwashe ta gyara wurin tsaf ta dawo ta zauna shiru ne ya biyo baya na yan mintuna Dalhat ne ya katse shirun da cewa yau kwana nawa da fara period dinki shiru tayi kamar bataji ba a tsawace yace bada ke nikeyi ba tace yau kwana 3 baice komi ba ya girgiza kai yace cire hijabin jikinki nace yanxu ko ranki ya baci turo baki tayi tace dan Allah ka kyaleni kananan kaya ne a jikina hararanta yayi yace me zan gani a jikinki zaki cire ko saina bata miki rai Tsaki tayi a hankali sannan ta cire Ashe yaji tsakin tasowa yayi yazo kusa da ita yace ni kikewa tsaki Tace ni bada kai nikeyi Dalhat yace dawa kike mara kunya janyota yayi jikinsa ya matseta bakinsa ya hada nata ya fara kissing dinta tun tana kokarin kwacewa ta daina jikinta yayi sanyi sai da yayi mai isar sa Sannan ya kyaleta Yace kada kiga haka ba wai na fara sonki bane kawai dai ina baki hakkinki ne kada ki kaini kara don na kula ke jarababbiya ne Tana jinsa batace komi ba suna zaune a haka yana rungume da ita dataga xaman bana kare bana kuma bacci takeji Ta dago Ashe ita yake kallo hada ido sukayi tayi sauri ta dauke kai tace don Allah ka kyaleni inje in kwanta Dalhat yace towa ya hanaki tace to ka sakeni inje daki in kwanta yace Ashe baki shirya yin bacci ba tundaga nan bata kara cewa komi ba nan dai tayi bacci a jikin shi sai da yaga baccin yayi nisa sannan ya kaita daki ya kwantar da ita sannan ya kula da shedar dukan da yayi ya tausaya mata Ashe haka jikinta yake baya son duka Shi yayi dukan amma sai baiji dadi ba ya dade a tsaye kafin Shima yaje dakinsa ya kwanta tunani yake Kala kala daga karshe yaga tunanin ba zai fisshe shi ba ya watsar da komi yayi kwanciyarsa Asuba karfe biyar na 5am Dalhat ya tashi ya tafi masallaci ba tasheta ba saboda a yadda ta fada masa bata sallah ita kuwa Hudah sai bacci take bata tashi ba sai wurin 5:45am Da sauri ta sauko daga gado ta shiga toilet tayo alola tazo ta shimfida sallayarta ta fara sallah abinda bata sani ba shine tana tayar da sallar Dalhat ya shigo yana tsaye a bakin kofa ya harde hannayensa yana tsaye harta idar Tayi adduarta juyowan da zatayi suka hada ido gabanta ne yace ras duk ta tsorata jikinta ya fara rawa Takowa ya farayi tana jada baya yace cool down tambayarki kawai zanyi hawaye na bin fuskarta tana girgiza kai tace to ina ruwanka dani da zaka shigo mun daki babu ko sallama Tsawa ya daka mata yace nace kizo ko Hudah tace wlh bazan zoba ni dai kawai ka fitar mun a daki kofar yayi da key ya koma ya zauna yace zo nan ki zauna ya nuna kusa dashi a hankali take takowa ta zauna hawaye duk ya wanke mata fuska....... 🌱🌱🌱🌱 Muffy 🌱🌱🌱🌱 [3/11, 9:23 AM] Naja: 😰😰😰😰😰 AUREN DOLE 😰😰😰😰😰 💦💦💦 *TALENTED WRITERS FORUM*💦💦💦 *T. W. F* BOOK 2 Page 51 - 55 mufeedamuazu.blogspot.com *STORY AND WRITTEN BY* *Mufeeda Muazu* Bismillahir rahmanir rahim Daure fuska yayi yace zakiyi mun shiru ko kuwa me akai miki shanye kukan tayi saboda yadda taga ya murtuke fuska yace ni zaki rainawa wayo kiyi mun karya ko girgiza kai tayi tace aa don Allah kayi hkr bazan sake ba Hijabin ya cire mata ya aje gefe guda jikinta sai rawa yake duk ta tsorata yace yau zan banbance miki tsakanin yaro da babba zumbur ta mike tsaye ta fara ja da baya yana binta harta kai karshen gado yazo daf da ita numfashin su na haduwa fizgota ta fado jikin sa hada bakinsa yayi da nata ya fara kissing dinta sai mutsu mutsu takeyi tana kokarin kwacewa amma ta kasa Saida yayi son ransa sannan ya kyaleta yace muje muyi alola ba musu ta miki don ta riga ta tsorata dashi a tare suka yo alola yaja su sallah bayan sun idar ne ya Kama kanta yayi addua kamar yaya addinin musulunci yace Ita ta fara tashi kan sofa taje ta zauna duk ta takure guri guda sai kwallah take sharewa ya dade yana addua sannan ya tashi har gurinta yazo ya tsugunna dai dai saitin fuskarta yace wannan hawayen na menene bayan ba ai komi ba Hudah tace don Allah yaya Dalhat kayi hkr wlh bana so Dalhat yace ni inason hakkina daukanta yayi cak bai direta ko ina ba sai a tsakiyan gado sata yayi ta cire hijabin ta aje a gefe rungumota yayi ta kwanta a kirjinsa gashin kanta data tufke ya warware Hannunsa yasa Yana ya mutsawa Yana jin kamshinta ita kuwa jikinta ba abinda yake sai rawa doguwar riga ne a jikinta jan rigar ya farayi ta rike tana kuka tace dan Allah yaya kayi hkr wlh bana so ko kulata baiyi ba ya cigaba da abinda yake Cire rigar yayi gaba daya kuka take kamar ranta zai fita babu mai taimako cire jallabiyar yayi ya rage daga shi sai boxers rumfa yayi mata da faffadan kirjinsa ni Mufeeda da naga haka sai nayi sauri na fita na rufo kofar na koma falo Can najiyo kukan Hudah kamar ana yankata anan dai na kwanta ban koma ba sai 9:45am dan gane ma idona abinda ya faru koda na shiga Hudah na gani kwance ita ba bacci take ba idonta a lumshe sai hawaye da yake zuba kamar an bude famfo Dalhat kuwa tunda ya samu nutsuwa kota kanta bai bi ba dakinsa ya wuce yaje yayi wankansa cike da farin ciki Hudah na kwance har 10:am ta kasa tashi data yunkura zata tashi sai ta kasa tashi duk jikinta yayi tsami sai kuka take ta rasa mai taimakonta Da taga dai ba wani sarki sai Allah yasa tayi kokari ta mike a hankali tana bin bango harta shiga toilet ruwan zafi tasa ta gasa jikinta sannan tayi wanka tazo tasa kaya doguwar riga ta gyara gadon ta koma ta kwanta ga yunwa datake ji kuka take mara sauti A haka Jidda tazo ta sameta jidda tace lpy Hudah meyafaru na ganki a haka Hudah ta runtse ido batace komi ba jidda tace Hudah magana nake amma kinyi banza dani don Allah ki fada mun abinda ke damunki ko sai na fadawa Ummi Hudah tace bkm yunwa nikeji dan Allah ki kawo mun abinci jidda tace tunda bazaka fadamun ba bari inje in fadawa Ummi Jiddah ta mike zata fita Hudah ta janyota tace dan Allah kiyi kada ki fada mata Jiddah tace to fada mun menene mayafaru Hudah ta runtse idanunta hawaye masu zafi suka zubo tace yaya Dalhat ne sai kuma tayi shiru jidda tace kiyi magana mana....... 🌱🌱🌱🌱 Muffy 🌱🌱🌱🌱 [3/11, 9:27 AM] Naja: 😰😰😰😰😰 AUREN DOLE 😰😰😰😰😰 💦💦💦 *TALENTED WRITERS FORUM*💦💦💦 *T. W. F* BOOK 2 Page 56 - 60 mufeedamuazu.blogspot.com *STORY AND WRITTEN BY* *Mufeeda Muazu* *Dedicated this page 2 all muslim ummah Happy sallah in advance* Bismillahir rahmanir rahim Hudah tace yaya Dalhat ne yayi mun fyade tana fadin haka ta fashe da kuka Jiddah tace haba Hudah ki daina fadin haka mijinki ne fah don Allah kiyi hkr ki share hawayenki Hudah tace dole inyi kuka Jiddah yaya Dalhat bashi da tsusayi karfinsa ya gwada akaina sannan ba wani nuna kulawa sai da ya samu abinda yake so yayi tafiyarsa Ban kara ganinsa ba da kyar na iya tashi nayi wanka na gyara gadon nan ga yunwa inaji ga bacci bai isheni ba jidda tace kiyi hkr Hudah Allah zai baki ladan hkrn da kikayi bari in fadawa Ummi ko akwai taimakon da zatayi miki wuyanta ta taba tace kinga jikinki ma yayi zafi Hudah tace nidai kada ki fadawa Ummi da wani ido zan kalleta ki barni kawai Jidda tace wlh bazan barki ba da gudu ta fita tana kwala Kiran Ummi Ummi......... Ummi.... Ummi dake kwance a falo ita da Rufaida suna hira taji kira ba kakkautawa tashi tayi zata fita sai ga jidda ta shigo da gudu Ummi tace lpynki kuwa Irin kwala kira haka Jiddah tace Hudah ce bata da lpy shine tace wai kar a fada miki Ummi tace ina Hudahn take Jiddah tace tana can daki a kwance Ummi tace muje tafiya sukayi Harda Rufaida a kwance suka sameta idonta biyu amma ta rufesu sbd kunyar Ummi Ummi ta tabi jikinta taji zafi rau kamar garwashin wuta tace meke damunki Hudah tace bkm zazzabi ne kawai Ummi ta kalleta tsaf ta girgiza kai alamar tausayi don ta gano ko meyafaru Tace Jiddah kije ki hado mata tea mai kauri da farfesun kaji sannan kije dakina a first aid box xakiga PCM ki dauko kiyi sauri Rufaida na tsaye sai tabe baki take Ummi tace rufaida ki kula da ita ina zuwa toilet ta shiga ta hada mata mai zafi sannan ta fito tace zaki iya tashi ko sai an kamaki Hudah ta cije baki sbd yadda take jin zafi tace zan iya Da kyar ta iya tashi Ummi ta kamata ta kaita har toilet din tace ta shiga ruwan ta gasa jikinta sannan ta fito dai dai tym din jidda ta dawo hannunta rike da basket a ciki ta hado kayan Ummi ta hada mata tea sannan ta zuba mata farfesun a plata Rufaida tace Ummi wlh yarinyar nan bata da kunya ta cika raki Ummi tace Waye Yarinyar saankice ita to wlh ki kuyayeni Hudah bata fito ba saida ruwan ya huce ta gargasa jikin kamar yadda Ummi tace a toilet din tasa kayanta sai kuma taji dadin jikinta sai dai tafiyarta daya canxa ta kasa hada kafa haka nan ta fito tana bin bango tana dingisa ka cike da kunya tazo ta zauna a sofa Ummi tace sannu kasa amsawa tayi Jiddah ce ta dauki plate din da tea ta aje mata a gaba tace gashi ki daure ki tuttura ko bakya jin dadi Hakanan taita turawa harta cinye Ummi ta ballo mata maganin ta bata da kyar ta hadiye kamar zatayi amai sbd ita ba gwanar shan magani bane Ummi tace ki kwanta ki huta Kada kice zakiyi girki zaa kawo miki Allah ya sawwake Da kyar ta karisa gado ta kwanta Jiddah ta gyara mata rufa Ummi na fita Rufaida ta tsuka tsaki mtsw..... aikin banza sai nayi maganinki sannan tabi bayan Ummi A kofar falo suka ci karo da Dalhat keya ya sosa yace inakwana hararanshi tayi ta amsa a dakile Rufaida dake bayan Ummi tace yaya ina kwana ya amsa mata ba yabo ba fallasa Wucewa sukayi shi kuma ya shige ciki direct dakin Hudah yaje ya tarar da ita a kwance Jiddah kuma a sofa tana zaune Hudah na ganinsa ta juya baya Jiddah ce ta gaishe shi ya amsa da kyar yace nasan kece kika kira Ummi wlh ki kiyayeni kuma fito da miji zakiyi zan sami Abbu zaman naki ya isa banga abinda kike ba sai gulma........ *Happy Eid-kabeer in advance* 🌱🌱🌱🌱 Muffy 🌱🌱🌱🌱 [3/11, 9:27 AM] Naja: 😰😰😰😰😰 AUREN DOLE 😰😰😰😰😰 💦💦💦 *TALENTED WRITERS FORUM*💦💦💦 *T. W. F* BOOK 2 Page 61 - 65 mufeedamuazu.blogspot.com *STORY AND WRITTEN BY* *Mufeeda Muazu* Bismillahir rahmanir rahim Dedicated dis page 2 *Ummah Shehu(First lady)* *Naseeba I Uba* Haka nan ya karaci fadansa ba Wanda ya kula shi Jidda kuwa tashi tayi abinta tace na tafi skull sai anjima Hudah kuwa juya masa baya tayi a cikin ranshi yana jin gsky bai kyauta ba amma dole ya tsare girmansa kada yarinya ta raina shi tsaki yayi ya fita tana jinsa bata dai tanka ba yana fita bacci mai nauyi yayi gaba ita. After four month Hudah ta koma mkrnt abinta Dalhat shima ya koma wurin aikinsa sai in yazo wkend haka dai zaman yake bai canxa ba amma dai ya rage wasu abubuwa tafi sakewa idan baya nan idan yazo ko duk ya takura mata da bukatarsa wani lokaci har mamaki yake bata idan yana tarairayarta ita kuma sai tayi kam bata san yanayi ba Wata rana yaxo wkend wani abokinsa yai masa waya yace zaizo shida family dinsa bai soba don yasan halin Hudah sarai zata iya jisgashi agaban kowaye tana zaune tana kallo yace abokina na kan hanya shida matarsa zasu kawo mun ziyara Hudah ta miki cike da masifa tace toni ina ruwana da wasu abokananka ba abinda zanyi musu ko ruwa wlh ranshi ya baci sosai yace ni zanje taro su wlh naga ba dai dai ba sai nayi maganinki Hudah tace maganina yafi karfin naka nufota yayi aguje ta shige daki ta turo kofa kwafa yayi ya wuce Tana shiga daki ta fada gado tana haki tanata tunanin abinda zatayi musu don tasan Dalhat zai iya dukanta wannan ba wani abu bane a gurinsa Wani tunani tayi murmushi tayi ta miki ta fito kitchen ta shiga jollof din indomie tayi sannan ta dafa kwai ta jera a sama batayi wani abin sha ba sbd sunada lemu a fridge gida sai kamshi yake a sha wani delicious food aka dafa suna shigowa yaji kamshi yaji dadi a ransa bai san tsiyar data shirya masa ba wuri ya nuna musu suka zazzauna yace ina zuwa dakin Hudah ya shiga ya tarar da ita zaune tana danna waya yace ga bakin namu can a falo ki fito ku gaisa ko dagowa batayi ba balle ta amsa yaji haushi amma ya danne yace bada ke nikeyi ba Hudah tace niba bakina bane bakin Kane don haka ka fitar mun a daki abinci na kitchen da kyar ya lallasheta sannan ta aje wayar ta sauki mayafi tare suka fito ba yabo ba fallasa suka gaisa daga nan ta wuce kitchen ta dauko tray din data jera abincin sannan ta bude fridge ta dauko musu ruwa da lemu ta aje musu ta koma ta zauna Matar ta taso zata zuba abinci tana bude kular taga indomie ita bata damuba saboda tana ci ita da danta mijinta ne baya ci kallon shi tayi shima ya kalleta Dalhat yace lpy murmushi yayi yace ah bkm matar ta zuba a plate ta mikawa dansu mai suna Ahmad ta zuba nata Dalhat yana gani yace meye haka nike gani indomie sbd yasan abokin nasa baya cin indomie tun suna skull ranshi yayi matukar baci zai fara fada abokin ya hanashi(Farook) hudah tace ai ina ce bakin naka turawa ne ta ya mutsa fuska ta tashi ta shige daki abinta Dalhat abin duniya duk ya ishe shi tashi yayi ya fita waje Jiddah ya kira yace don Allah idan da abinci ta kawo masa yayi baki ne batayi mamaki ba saboda tasan halin Hudah sarai bata jin magana dawowa yayi yana ba farook hkr ace mutum yazo tundaga nesa a rasa abinda zaa bashi sai indomie ai wannan wulakanci ne farook yace kasan mata sai hkr bilkisu(matar farook) tace kada ku daura mata laifi dayawa fah may be ko bata jin dadi ne yasa tayi indomie sbd shi zai zaifi mata sauki Baa dau lokaci ba Jiddah tashigo da sallama hannunta rike da tray gaishe su tayi ta aje tray din ta juya zata shiga dakin Hudah Dalhat yace ina zaki gulma ko to wuce ki tafi ngd kirikiri ya hanata shiga haka nan ta hakura ta juya cike da kunya a gaban mutane ya jisgata Farook yace ya zaayi ka hanata shiga Dalhat yace kyaleta ai duk halinsu daya bilkisu ta bude kular da Jiddah ta kawo rice nd stew with salad ne ta zuba masa Dalhat yace madam ke bazaki ci bane bilkisu tayi murmushi tace Alhmdllh tashi tayi tace bari in shiga gurin gimbiyar Dalhat ya kirkiro da murmushin karfin hali yace shikenan zaaje ayi kuskus ko Dakin Hudah ta shiga da sallama Hudah ta dago ba yabo ba fallasa tace sannu bilkisu tace yawwa dan Allah zanyi sallah Hudah ta nuna mata toilet kifin ta fito ta shimfida mata sallaya Dalhat da farook kuwa tare sukaci abincin suka kara sannan suka wuce masallaci harda Ahmad a hanyarsu ta dawowa ne Dalhat yake bashi labarin yadda aurensu ya kasance shida Hudah dayake anyi auren basa Nigeria Dalhat ya kara da cewa yanxu Allah ya jarrabeni da sonta amma ban san yadda zanyi in fada mata ba kona fada mata ma ba dole bane zata iya cewa karya nike yaudaranta zanyi farook ya numfasa yace abokina gsky kayi kuskure tun farko ya zaayi ka biye mata kuyita shirme kaifah namijine Dalhat yace kuskure dai anriga anyi yanxu meye shawara Farook yace shawara dayace ka rika nuna mata kulawarka sannan ka rika kawar da kanka a wasu abubuwan daga nan har akai mataki na biyu Wato lokacin daxaka furta mata kalmar so farook ya kara da cewa kaga kaman yanxu kada kayi mata magana akan abinda tayi dama tayi ne don ta bata ma rai Dalhat yace shikenan ba abokina ngd nidai fatana Allah yasa kada tayiwa madam wulakanci farook yace insha Allah bazata yiba da haka suka shigo gida Bilkisu kuwa tana fitowa daga toilet din taga har ta shimfida mata sallaya sallah tayi Hudah tace ga kayan kwalliya nan a dress mirror powder kawai ta shafa ta dawo kusa da ita ta zauna tace ni sunana bilkisu kefa tace sunana Hudah bilkisu tace nice name Hudah tace tnx bilkisu naso suyi hira Ammah Hudah taki sakin jiki sai cin magani take Hudah tace ya sunan yaron nawa bilkisu taji dadin karan datayi mata tace sunan sa Ahmad tashi tayi ta bude drower ta kwaso turaren wuta da humra masu kyau da tsada tun na aurenta ne tasa a leda tace gashi ba yawa bilkisu ta amsa tayi godiya sunyi shiru ba mai magana bilkisu tana tunanin hali Irin na Hudah kamar mai aljannu Dalhat ne ya shigo yace madam ki fito zaku tafi juyawa yayi bilkisu ta dauki mayafinta tace to Hudah sai anjima itama mikewa tayi sukayi exchanging no a tare suka fito a tsaye suka tarar dasu Hudah tace Ahmad zo mana mu gaisa da yake yana da wayau baiyi quyaba yaje 2k ta bashi tace gashi ka sha sweet Ahmad yace ngd Aunty farook yayi gdy har waje ta rakasu tana harar Dalhat duk suna kallonta murmushi farook yayi yace wannan madam din taka yar daru ce Ammah fah tanada taushin zuciya duk da haka kayita lallashinta haka sukayi sallama cike da begen juna saida yaga tafiyar su sannan ya dawo gida ya tarar ta kwashe kayan da sukaci abinci ta gyara wurin kusa da ita ya zauna yace my wife ngd sosai sunanda ya kirata dashi ya bata mamaki bata gama mamaki ba taji yace ki shirya anjima zamu fita shopping batayi musu ba saboda itama tana son fita Tace to don Allah inaso in shiga wurin hajiya yanxu yace to ba damuwa zuciyanta fari kal da gudu ta shiga daki ta dauko hijab dinta ta fito yana zaune tace sai na dawo Da gudu ta shiga tana kwada Kiran hajiya, hajiya tace ke wai yaushe ne zakiyi hankaili turo baki tayi tace nine banida hankali ko hajiya tace ya Dalhat din Hudahh tace yana gida yau bazan koma gida ba sai dare suna cikin hira shahid ya shigo ya kalli Hudah yace ke bakida mutunci ko Hudah tace me kuma nayi yace bansani ba zakiyi shiru ko saina fasa bakinki anan wurin hajiya tace lpy shahid yace daxu ina gidan Dalhat ya kira Jiddah wai insu nada ta kawo masa yayi bakine yanxu hajiya abinda takeyi ya dace kenan hajiya ranta yayi matukar baci Hudah batayi aune ba taji saukan mari rike wurin tayi don azaba ta bude baki zatayi magana shahid ya bige bakin zai daketa hjy ta hana tace baa asan kotana da juna biyu...... 🌱🌱🌱🌱 Muffy 🌱🌱🌱🌱 [3/11, 9:27 AM] Naja: 😰😰😰😰😰 AUREN DOLE 😰😰😰😰😰 💦💦💦 *TALENTED WRITERS* *FORUM*💦💦 *T. W. F* Book 2 Page 66 - 70 Mufeedamuazuu.blogspot.com STORY And WRITTEN BY *Mufeeda Muazu* *Dedicated dis page 2* *Rahmat Nalele* *Husnah mb* Bissmillahir rahmanir rahim Hudah ta turo baki tace hajiya ki daina Irin wannan maganan Nifa banida komi kuma ma Allah ya kyauta in tsaya yayi mun ciki bana sonsa bana kaunarsa Shahid yace hajiya kinji abinda take fadi ko sbd taga kince a kyaleta mikewa tsaye yayi ya nuna kofan fita yace fita a gidan kafin in karkaryaki mara kunyar banza kawai hajiya kasa magana tayi lallai haryanxu Hudah batayi hankali ba Hudah tayi kaman bada ita yake ba saida taga ya zaro belt zai daketa sannan ta daka tsalle ta koma bayan hajiya tana kuka tace ya zaayi mutum da gidansu a rika korarsa hajiya kice ya kyaleni hajiya tace aini Kinfi Karfina duk abinda zaiyi miki bazan sake magana ba tana gama fadar haka ta tashi ta haye sama abinda ganin haka yasa Hudah ta mike tana goge hawayenta jikinta duk ya mutu ta kalli Shahid dake nuna mata kofar fita tace Allah ya isa mugu kawai ta fita a guje koda ta shiga gida side din su Jiddah ta wuce a falo ta tarar da Jiddah da Radiya kusa da Jiddah taje ta zauna tana haki Jiddah tace ke lpynki sai kace an biyoki Hudah tace yaya Shahid ne don wulakanci wai zai dakeni da aurena mtsw.....tsaki sukaji a tare suka dago don gane ma idonsu Waye mai tsakin Rufaida ce ba Wanda ya kulata ta taso tazo har gaban Hudah tace ke banza baki ganin mutanene da bazakiyi musu sallama ba Hudah ta mike tsaye cike da masifa ta kalleta sama da kasa tace ina mutanen suke waike wace Irin karya ce mara zuciya ance baayi dake amma kin nace Rufaida tace ai naga dai kema din ba sonki yake ba kuma ai kece karyar Hudah ta kai mata magigicin mari kikake tas! Rike wurin tayi tace ni kika mara Hudah tace an mareki din ke din banza ta murmushin mugunta tayi tace yanzu kam duk abinda zakiyi kiyi lokacinki ne nan da kwana kadan ba kya gidan nan wlh sai kin barshi Jiddah tace ke Rufaida mekike fada haka Hudah tace kyaleta ai ni nafison haka sbd nima dole akaimun kare yayar da zuciyarsa an dauka kullum ana gidansu saurayi don nasan ba don zumunci kike zuwa ba ai sai ki zauna a gidan ubanki yazo ya sameki sakarya kawai wadda bata da aji tana gama fadar haka taja hannun Jiddah suka haye sama suka barta a nan sororo A dakine Jiddah take fadawa Hudah ankawo goron sa rana da nata dana Husnah 6mnth zaa sa Hudah tace lallai ne shine ba wanda ya fadamun yanzu da ba danke da kika fadamun ba bazan sani ba koda yake yanzu na zama bare kwallah ne ya cika idonta Jiddah tace ba haka bane kene kinki ki kwantar da hankalinki ki natsu ki rungumi kaddara ba wanda bai sonki so ake kiyi hkr ki gyara komi mai wucewa ne watarana sai labari Hudah tace bazaki gane bane amma kinsan wani abu kuwa? Jiddah ta girgiza tace aa sai kin fada Hudah tace naga kwana biyu ya chanza sai wani kula dani yake yana tattalina kinga dazu da yayi baki ban dafa abinci ba da ace da ne da wlh raina sai ya baci Jiddah tace ni dama nasan yaya Dalhat yana sonki kene dai kike shirmenki Hudah tace rufe mun bakinki anan bani yake soba jikina yake so Jiddah tace kwaji da shi dai ku kuka sani Hudah ta mike tace ni kinga tafiyata magriba tayi Jiddah tace to muje in rakaki koda suka sauko ba kowa a falon Side dinta suka tafi anan sukayi magriba sukai issha sannan suka ci abinci suna zaune wayar Jiddah ta fara ringing dubawa yayi taga mai Kiran mikewa tayi tace matan yaya swtyna yaxo yana jirana gud nyt bata jira jin me zata ce ba ta fita da sauri kwallah ne ya kawo mata tace Allah sarki soyayya ni ban samu wannan daman ba Jiddah na fita ba dadewa Dalhat ya shigo sannu da zuwa kawai tace shi kuma gogan dadi yaji yau ta kulashi bai san sbd yace zasu fita bane yace yawwa ki shirya ko da sauri tace to ta tashi ta tafi dakinta shima dakinsa ya wuce tana shiga ta bude wardrop dinta taga kayanta ba yanda yake ba Dalhat harya shirya ya fito falo yaga bata fito ba dakinta ya shiga ya ganta tsaye tana fitowa da kaya yace ya dai madam juyowa tayi tace yaya bayan na fita waye ya shigo min daki Dalhat yace ba wanda ya shigo nima fita nayi lpy tace lpy bkm yace ko inzo in tayakine tace Aa ka barshi kawai nakusa gamawa ta janyo wani kaya kenan wani magani ya fado kallonsa tayi ta kalli maganin shima kallon maganin yayi ya kalleta ya duka ya dauka har an sha rabi karantawa yayi maganin family planning ne tsareta yayi da ido jikinta ya fara rawa ta bude baki zatayi magana ya bige bakin cikin zafin rai ya kaita bango ya matseta yace waya baki wannan maganin a ina kika samu bakinta na rawa tace Allah yaya bani na sha ba ni ban san wanda ya kawo mun ba ranshi ya dada baci wato shi zata rainawa hankali ga abu ya gani da idonsa...... 🌱🌱🌱🌱 Muffy 🌱🌱🌱🌱 [3/11, 9:27 AM] Naja: 😰😰😰😰😰 AUREN DOLE 😰😰😰😰😰 💦💦💦 *TALENTED WRITERS* *FORUM*💦💦 *T. W. F* Book 2 Page 71 - 75 Mufeedamuazuu.blogspot.com STORY And WRITTEN BY *Mufeeda Muazu* *Masoya littafin Auren dole ina mai baku hakuri na rashin jina da mukayi kwana2 fatan zamu kasance tare dani ngd Allah ya bar kauna* Bissmillahir rahmanir rahim Hudah da tuni hawaye ya wanke mata fuska tace don Allah yaya kayi hkr wlh bazan kara ba ammah don Allah kada ka fadawa su hajiya Dalhat ya koma gefe ya xauna cikin damuwa yace yanxu kin da kike mun har ya kai haka Hudah dai batace komi ba don ta san ita dai bata taba shan maganin family planning ba to waye ya kawo mata har cikin drawer koma waye Allah ya saka mun Dalhat ya daka mata tsawa yace ba magana nike miki ba Hudah tace Allah yaya ni ban san da shiba ba nawa bane hannu ya daga ya sharara mata mari yace ni zaki rainawa wayo banaki bane nawa ne ko Tashi yayi ya kwashe maganin ya fita a dakin don idan ya zauna zai iya zaneta sbd yanda zuciyarsa ke kuna yana fita ta dauko wayarta numbern Jiddah tayi dialing ring biyu aka daga tace jiddah don Allah idan bakya komi ina son ganinki jiddah tace lpy ba yanzu muka rabu ba Hudah tace don Allah ke dai kizo Jiddah tace to ganinan zuwa baa sauki wani lokaci ba Jiddah ta shigo Hudah ta rungumeta tana kuka ta kasa magana Jiddah ta dagota fuskarta cike da damuwa tace kince inzo gani kuma nazo kin tasani a gaba sai faman kuka kike ko in kira su Ummi ne Hudah dai ta kasa magana sai ajiyar zuciya takeyi da kyar tayi shiru tace jiddah don Allah ki taimaka kicewa Ummi tasa yaya Dalhat ya sakeni ni gsky nagaji da wannan auren Jiddah tace waike Hudah meke damunki ne yanzu me kuma akayi Abinda basu sani ba shine duk maganar da sukeyi Dalhat yana jinsu yazo wucewa yaji ana magana shine ya tsaya ji kawai sukai an bugo kofa da karfi cikin hargagi ya fara magana yace ke meya hana kije kice kin gaji tace in sakeki mara kunyar karya to bazaa sakeki ba sai dai ki mutu Jiddah duk ta tsorata ta tashi zata fita ya daka mata tsawa yace ina zaki munafuka kawai kashedi daga yau kada in kara ganin kafanki anan side in bada wani kwakkwaran dalili ba in ba haka ba yayi kwafa ganin ta fita a dakin Hudah ta tashi da gudu zata bita Dalhat yasa kafansa ta fadi dukawa tayi anan tana kuka mai tsuma zuciya shi kansa daurewa kawai yakeyi saboda kukanta har cikin zuciyarsa yake ji dukowa yayi inda take ya dagota ya zaunar da ita a sofa yana goge mata hawaye yace kiyi shiru kinji don Allah ina rokonki kada ki ra shan irin wadannan maganin kinji ba kya tunani zai iya cutar dake daga kai tayi alamar taji Dalhat yace to dan yi murmushi mana smiling tayi yace koke fah Tunani take anya wannan yaya Dalhat ne kuwa? ya kula da hankalinta baya wurin iska ya hura mata firgigit tayi kaman ta tashi daga bacci yace tunanin me kikeyi haka tace bakomi yace Anya kuwa tace bacci nikeji yaya yace kinyi wanka ne tace yanzu dai zanyi Dalhat yace muje in tayaki ba musu tace to sbd tana neman shiri kada yaje ya fadawasu hajiya abinda bataji ba bata ganiba tare sukai wankansu suka shirya tare ranar dai sun farantawa junan su kaman ba auren dole akayi ba Da asuba shiya rigata tashi saida yaje yayi alola sannan yaxo ya tasheta ya wuce masallaci ita kuma tunda tai sallah bata koma ba ta gyara gidan tsaf sannan ta shiga kitchen ta hada musu breakfast daki ta koma daki ta shiga wanka Bai dawo masallaci sai karfe bakwai na safe da kamshi ne ya daki hancinsa wani dadine ya ziyarci zuciyarsa yana jinjinawa lallai yayi saar mata mai tsafta da iya girki sai dai kash bata sonsa amma zan koya mata sona insha Allah ya fada a fili.......... 🌱🌱🌱🌱 Muffy 🌱🌱🌱🌱 [3/11, 9:27 AM] Naja: 😰😰😰😰😰 AUREN DOLE 😰😰😰😰😰 💦💦💦 *TALENTED WRITERS* *FORUM*💦💦 *T. W. F* Book 2 Page 75 - 80 Mufeedamuazuu.blogspot.com STORY And WRITTEN BY *Mufeeda Muazu* *Masoya littafin Auren dole ina mai baku hakuri na rashin jina da mukayi kwana2 fatan zamu kasance tare dani ngd Allah ya bar kauna* Bissmillahir rahmanir rahim Yana shigowa dakinsa ya shige anan yayi wanka ya shirya cikin shadda light blue sunyi masa kyau sosai kaman sun hada baki itama less tasa light blue tayi kyau sosai a dinning ya sameta tana hada tea cikin sakin fuska ya kariso kujeran dake kallon nata yaja ya zauna yace amarya kin sha kamshi murmushi tayi tace ina kwana yaya amsawa yayi yace fatan kin tashi cikin koshin lpy murmushi kawai tayi batace komi ba Tagama hada tea dinta ta fara sha yana kallonta yace madam kinta shan abinki ke daya bako tayi hudah tace ai gashinan ni ba hanaka nayi ba Dalhat yace to a hada mun mana tashi tayi da kofinta a hannu ta harare shi tace ai kanada hannu tayi gaba abinta kallonta yakeyi har ta shige daki yana mamakin hali irin na Hudah ga taurin kai ga kafiya Sauri yayi ya hada tea ya karya abinsa dakinsa ya koma ya dauko jakarsa don yau Monday zai koma wurin aikinsa dakinta ya shiga yayi mata sallama ba yabo ba fallasa tace masa a dawo lpy Allah ya tsare Dalhat yaji dadin adduar datayi masa yace ngd ko kinada bukar wani abu ne girgirza kai tayi tace babu komi bakin kofa ta rakoshi Bayan fitarsa ba dadewa ta kira jidda a waya tace idan ta shirya ta sameta a waje ba a dau mintoci ba Jiddah ta fito cikin shirinta daga nan suka dauki hanya sai mkrnta Da rana Rufaida tafi gidansu dama sbd Dalhat take zuwa kamar yadda Hudah ta fada Ansa ranar jiddah da Shahid Husnah da sir Haidar wata shida aka sa a skull su jiddah suka hadu da sir Haidar bayan su gaisa sai gdy yakewa Hudah sannan yayiwa jiddah fatan alkhairi Friday ranar ne kuma Dalhat zai dawo Hudah sai aikace2 takeyi jidda ta shigo tace matan yaya ki saurareni da kyau wlh gara ki cire taurin kan nan naki kinsan yau yaya zai dawo ko to gashi har Rufaida taxo tace wlh sai ta auri yaya kota halin kakane Hudah ta mike tsaye tace wlh bata isa ba kuma tayi kadan Jiddah tace abinda zaisa tayi kadan shine kawai ki rike mijinki da kyau kin san shi namiji yana son kulawa kisawa zuciyarki salama sannan ki yawaita addua Hudah da hawaye ya cika mata ido tace jiddah nasan duk abinda kike fadamun gsky ne kuma nasan ke mai kaunata ce da gsky kada ki manta yaya Dalhat ba sona yakeyi ba tayaya kike gani xaman mu zai dai daita tana kaiwa nan ta fashe da kuka Jidda sai lallashinta take tana bata hkr tare da shawarwari har dai ta samu ta shawo kanta da kyar Jiddah tace yanzu me zakiyi in tayaki Hudah tace nagama komi wanka kawai zanyi yanzu jidda tace to muje in zabo miki kayan da zaki sa Hudah dai bata ce komi ba suka shiga daki Hudah ta shiga wanka Jiddah ta dauko akwatin kana nan kaya a ranta tace lallai Hudah akwai wauta Wato ko jerawa ma batayi ba ta barshi a cikin akwati wani riga red da mini skirt black sai band black shima ta aje a gefen gado ta mayar da akwatin Hudah na fitowa jiddah tace iyyeh amaryarmu kinji kamshi yanda yake tashi tun kafin ma ki fito lallai yau yayana zai more Hudah ta kai mata dukan wasa tace dallah bani wuri in shirya kinzo kin cikani da surutu wlh yaya shahid zai sha fama dake Jiddah tace shikenan na daiji ga kaya nan don nasan yanzu yaya ya kusa isowa............ 🌱🌱🌱🌱 Muffy 🌱🌱🌱🌱 [3/11, 9:30 AM] Naja: 😰😰😰😰😰 AUREN DOLE 😰😰😰😰😰 💦💦💦 *TALENTED WRITERS* *FORUM*💦💦 *T. W. F* Book 2 Page 81 - 85 Mufeedamuazuu.blogspot.com STORY And WRITTEN BY *Mufeeda Muazu* Bismillahir rahmanir rahim Hudah tace uhmm ni kinxo duk kin dameni da surutunki kinsan dai ba auren soyayya mukayi ba Jiddah tace wai meyasa kike dawo da hannun agogo baya ne kuma nina san yaya Dalhat yana sonki kece dai baki bashi damar ya nuna miki ba Uhmmm kawai Hudah tace ta zauna a gaban mirror ta fara kwalliya ta shafa wancan ta goga wancan tayi kwalliyarta kaman ba ita ba gasu humra data shasshafa Jiddah ta miko mata kayan Hudah ta daga kayan ta kallah tace gsky bazan iya saka wannan kayan ba sai kace yar iska Jiddah tace wani irin iskanci ba mijinki bane wani dare ne jemage bai ganiba Hudah ta bata rai tace kinga kada ki bata mun rai yayi ta gani mana Jiddah tace maida wukar gyara kayanka ai bai zama sauke mu raba ba kuma ni bana son yaya ya kawo miki watane musamman ma Rufaida data nace ta like masa kamar cingum Hudah tace hakane kuma ya na iya kayan ta dauka ta saka Jiddah tace wow gsky ba karamin kyau kikayi ba anya yaya zai iya ganeki kuwa gsky kinyi kyau sosai Hudah tace uhmm kalli fah skirt din iyaka gwiwa fah kaman wata karuwa Jiddah tace shine fashion tashi tayi tace na barki lpy a sha soyayya lpy Hudah tace ina kuma zakije muna hirar mu Jiddah tace zan dawo ai tashi tayi ta fita Hudah ta bita a guje A bakin kofa sukai karo da Dalhat dago kai tayi suka hada ido taga ya kura mata ido kallon jikinta tayi taga ashe kananan kayane a jikinta juyawa tayi zata bar falon sauri yayi ya rikota ta fado jikinsa rungumeta yayi tsam a jikinsa dada lafewa tayi a fadadden kirjinsa sun dauki lokaci a haka kafin ya saketa tare da cewa kinyi kyau da gudu ta shige daki tana haki Murmushi yayi yaji dadi a ransa kuma yana fatan Allah yasa itama ta fara sonsa ne kamar yadda yake sonta dakinsa ya shige yayi wanka ya sauya kayansa kananan kaya ya saka koda ya fito falo bai ganta ba dinning area ya kalla yaga kuloli an jajera zama yayi a 3seater kiranta ya shiga saida ya kira sunanta sau biyu sannan ta amsa zunbulelen hijab ta saka tana tafe a hankali harta fito falon kallonta kawai yake nesa dashi ta zauna daure fuska yayi yace meye haka kuma mijinki ya dawo ai kamata yayi kizo kiyi masa sannu da zuwa ba Turo baki tayi cikin shagwaba kaman zatayi kuka tace sannu da zuwa yaya dariya ta bashi ma boye dariyar yayi sbd kada tayi fushi murmushi kawai yayi yace gimbiyata me kuma akai miki na kuka ke kullum kuka tasowa yayi yazo kusa da ita yace fada mun mai akayi miki goge mata fuska hijab din ya fara kokarin cire mata rikewa tayi kallonta ya tsaya yi ido cikin ido data ga kallon ya isheta dukar da kanta tayi Kokarin tashi takeyi ta kasa sbd yadda ya rungumeta da kyau Dalhat ya kalleta yace ina zaki bayan baki nuna min kwalliyar ba nasan kuma sbd ni aka yishi wani haushi ne ya kamata wai sbd shi tayi kwalliya Jikinta duk ya mutu ta kasa komi haka nan tana gani ya cire mata hijabin kissing dinta ya farayi kota ina kuka ta saka masa saurin dagowa yayi da idonsa da suka canxa kala yace mene ya saki kuka kasa cewa komi tayi sakinta yayi yace nasan baki sona kiyi hkr muje ki bani abinci ko kunyar tashi take sbd kayan dake jikinta.......... 🌱🌱🌱🌱 Muffy 🌱🌱🌱🌱 [3/11, 9:30 AM] Naja: 😰😰😰😰😰 AUREN DOLE 😰😰😰😰😰 Book 2 Page 86 - 90 Mufeedamuazuu.blogspot.com STORY And WRITTEN BY *Mufeeda Muazu* Ya kula da haka dukowa yayi kusa da ita yace ko in daukeki ne bazaki iya tafiya ba me kike boye mun a jikin naki wani dare ne jemage bai gani ba pillow din kujera ta jefa masa ta tashi a guje rufa mata baya yayi Kujera yaja ya zauna yana kallonta yakeyi cikin kauna inama da tun farko bai nuna mata baya sonta ba gsky tana da saukin kai ammah sai ka fahimceta wannan zancen duk a zuci yake yi ta zuba masa abincin tana ta magana bai san tanayi ba sai data hura masa iska yayi firgigit kaman ya farka daga bacci murmushi tayi taja kujeran dake kallon nasa ta zauna tayi tagumi Dalhat yana cin abinci yana lumshe ido sbd dadi cikin kuluwa yace lpy kike tagumi bayan gani kusa dake hararansa tayi tace sai me don kana kusa dani mutum da baya sonka don kana kusa dashi meye amfaninsa tsaki tayi ta ja kujera zata tafi rike hannunta yayi yace ina zaki bayan muna hiran mu mai dadi Kwallah ne ya cika mata ido aje abincin yayi ya rike mata hannu yace muje inji waya taba mun Mrs Dalhat ne falo suka koma suka zauna ya rungumeta yace fada mun meyake damunki shiru tayi batace komi idonta a rufe Dalhat yace bude idonki ki kalleni da kyau ki kalli kwayar idona wlh ina sonki ina matukar kaunarki da sauri ta bude idonta fuskanta cike da mamaki hawaye wani na bin wani tace yaya wlh karya kakeyi ni nasan baka sona kai ka fada da bakinka tayaya kakeso in gaskata ka yunkurawa tayi zata tashi ta kasa sbd irin rikon da yayi mata Dalhat yace haba Hudah wlh ina sonki don Allah kiyi hkr da duk abubuwan da suka faru ki daukeshi a matsayin kaddara kin san kuma ba wanda ya isa ya ketara abinda Allah ya rubuta masa girgiza kai tayi tace ni dai gsky bazan yarda ba yaudarata kawai kakeso kayi nidai kawai abinda na sani shine baka sona nima kuma bana sonka Dalhat yayi sauri ya rufe mata baki yace kada ki fadi haka my swt hrt wlh ina sonki ki yarda dani wlh bazan cutar dake ba ki daure ki soni koda rabin sonda nike miki ne ki bani dama in nuna miki irin sonda nike miki Tureshi tayi iya karfinta ta tafi daki aguje tana kuka baiyi yunkurin binta ba sbd kada ya matsa mata tashi yayi ya tafi side din su mama don ya gaishesu Hudah najin fitansa ta tashi ta zauna tana share hawayen da yaketa ambaliya a fuskarta ta dauki wayarta numbern Jiddah tayi dialing ringing daya ta dauka Hudah tace kina ina don Allah kizo yanzu Jiddah tace lpy yayan fah Hudah tace ya fita ita a tunaninta waje ya fita batasan ciki ya shiga ba Jiddah itama batasan ya shigo ba tana dakinta Jiddah tace to ganinan zuwa suna gama wayar ta sauko kasa ganinshi tayi shida Ummi suna hira a hankali ta kariso tace gaishe shi tashi tayi zata fita Dalhat yace ke ina zaki Jiddah tace gurin Hudah zani Dalhat ya sha mur yace inace yanzu kika dawo to bazaki jeba Ummi tace sbd me zaka hanata zuwa gurin yar uwanta Dalhat yace Ummi ita ke zugata yanzu tana zuwa zan rasa gane kanta Jiddah tace Allah Ummi ni ba ruwana Dalhat yace rufemun baki zaki koma ko kuwa bayadda ta iya haka nan ta hkr ta koma tana shiga daki Rufaida ta kwashe da dariya tace Allah ya kara uwar gulma ai sai Hudah ta bar gidan nan Jiddah tace tunda gidan ubanki ne ba Rufaida taji zafin maganar ta mike a fusace tace ni kike fadawa haka Jiddah tace ke din banza daga hannu tayi zata mareta Jiddah ta rike hannun ta zabga mata mari ta daga hannu kenan zata kai mata a daya kuncin taji an rike hannun Ashe Ummi ce Marinta tayi tace ashe ke wawiyace Jiddah ta bude baki zatayi magana Ummi tace yi mun shiru mara kunya kawai Ummi ta rike hannun Rufaida suka bar dakin Jiddah ta dauki wayarta takira Hudah ta fada mata Dalhat ya hanata shigowa Hudah tace to shikenan ina nan shigowa sukai sallama Dalhat kuwa suna gama gaisawa da hajiya Dalhat ya fita daga gidan Hudah kuwa suna gama waya da Jiddah ta dauki mayafinta ta rufe side dinta ta tafi side dinsu Jiddah bata tarar da kowa ba a falon kasa sama ta hau Ummi ta gani zaune ita day Rufaida kusa da Ummi taje ta zauna a kasa ta gaisheta mikewa tayi zata shiga dakin Jiddah Ummi tace ina fatan dai lpy Hudah tace lpy klu Ummi tace to shikenan A zaune ta tarar da Jiddah ta zabga tagumi Hudah tace lpy na ganki haka meyake faruwa Jiddah tace uhmmm wancan yarinyar mana yanzu tasa Ummi ta mareni Hudah tace kyaleta zamuyi maganinta...... 🌱🌱🌱🌱 Muffy 🌱🌱🌱🌱 [3/11, 9:30 AM] Naja: 😰😰😰😰😰 AUREN DOLE 😰😰😰😰😰 Book 2 Page 96 - 100 Mufeedamuazuu.blogspot.com STORY And WRITTEN BY *Mufeeda Muazu* Bismillahir rahmanir rahim Kuka takeyi kaman ranta zai fita Ki jirani ina dawowa wlh sai nayi maganinki Dalhat ya fada tare da fita tunda ya fita tana zaune a inda ya barta ta kasa motsawa sbd bakin ciki gashi bata gane mai yake nufi ba Gidansu Hudah ya shiga a falo ya tarar dasu Hajiya da Alhaji kusa da Alhaji ya zauna a kasa ya kasa magana Hajiya ce tace lpy na ganka haka Dalhat ya dukar da kai yace Hajiya Hudah ce kasa magana yayi ya ciro maganin ya mikawa hajiya Alhaji yace wannan maganin fah na menene karantawa Hajiya tayi ta mikawa Alhaji tana salati Alhaji na gani ya tashi cikin bacin rai ya shiga daki ya dauko bulala ya boye a aljihu sannan ya fito Hanyar fita yayi baice wa kowa komi ba Dalhat yabi bayansa Da karfi Alhaji ya bude kofar Hudah na ganinsa ta tashi zata gudu daki tsawa ya daka mata yace ina zaki marajin magana Babu abinda take sai kuka tace Alhaji wlh ba nawa bane ni ban san wanda ya kawo ya aje mata ranshi ya dada baci Bulalarsa ya ciro daga aljihu tana ganin bulala kukanta ne ya dada karuwa zata gudu alhaji yace idan kika motsa daga nan zaki gane kurenki Dukanta yake baya ji baya gani kuka take tana ihu tare da bashi hakuri amma ina Dalhat ne daya ga dukan yayi yawa yaxo ya Kama bulalan ya rike yana bashi hakuri Ummi ce ta shigo sbd tun daxu take ta jin kuka bata san daga inda yake fitowa ba sai yanzu ta tabbatar da inda kukan yake Ummi tace lpy meya faru haka Alhaji don Allah kayi hakuri Yarda bulalan yayi ya fita batare da cewa komi ba Ummi ce ta karisa kusa da Hudah ta rikota tana lallashinta kallon Dalhat tayi tace me tayi maka kaje ka hadota da mahaifinta Nanan ya fadawa Ummi duk abubuwan da suka faru Hudah dake kuka tace Ummi Allah ni ban taba shan wani magani ba domin hana daukan ciki Allah shine shaidata ta karisa magana tana kuka Ummi ta jinjina maganar tayi musu Nasiha dukkansu Bayan Ummi ta tafi Dalhat ya shige daki abinsa ya barta anan sai kuka take gashi zazzabi ya fara kamata da kyar ta iya tashi ta shiga daki ta kwanta ta lulluba da bargo ranar dai batai bacci ba da Asuba ma da kyar ta iya tashi tayi sallga Dalhat kuwa ya dauki fushi da ita don koda safe daya tashi baibi ta kanta ba wankansa yayi ya fita Allah sarki Hudah baiwar Allah tana kwance sai rawar sanyi takeyi gashi kowa ya juya mata baya akan laifin da bataji ba bata gani ba Jiddah ce ta shigo dakin tanata sallama taji shiru kaman ba kowa Cikin daki ta shiga can karshen gado ta hangota rufe da bargo sai rawan sanyi takeyi da sauri ta karisa gurinta ta tabi jikinta taji zafi rau kamar garwashi Da yake Ummi ta fada musu duk abinda ya faru jiya Rufaida sai murna take Batai mamakin rashin ganin Dalhat ba Hijab ta dauko da takalmi ta saka mata ta rungumeta ta dauki key din motarta Asibiti suka tafi suna zuwa aka karbeta aka basu gado likita ya dubata sannan wasu nurses sukazo suka daura mata drip Ana gama sa mata tayi bacci Jiddah na zaune ta kura mata ido duk tayi wani fari ta rame ita tausayi ma take bata Doctor ne ya shigo ya tambayi Jiddah ina mijinta ko mamanta lallai yana son ganin wani a cikinsu Jiddah tace doctor ka fadamun meke damun yar uwata Doctor yace aa sai ta kira musa wanda yace yana son gani Wayarta ta dauko numbern Ummi ta kira bugu daya ta dauka muryarta na rawa tace Ummi Hudah bata da lpy muna asibiti yanzu haka doctor yace yana bukatar ganin daya daga cikin ku koke ko yaya Dalhat Cikin firgice Ummi tace meke damunta Jiddah tace nima ban sani ba doctor yace sai kunzo nan dai Jiddah tayi mata kwatancen asibitin Har lokacin Hudah bata farka ba Ummi cikin sauri ta shirya ta sami Abbu ta fada masa sannan ta kira Dalhat ta fada masa ya yanuna rashin damuwarsa sbd cewa ma yayi yanada uziri bazai samu damar zuwa ba sai da Ummi tayi masa tatas sannan ta kashe wayarta Dalhat fushi yake da ita haryanzu bai huce ba Ummi da Abbu ne suka tafi asibiti aka bar Rufaida a gida A kwance suka sameta tana bacci office din likita suka tafi suna zuwa saiga Dalhat shima a tare suka shiga Sun gaisa da likita sannan ya fara musu bayani kamar haka:bincike ya nuna tana dauke da ciki wata uku da sati biyu dukan da akayi mata shine ya kara mata ciwon jiki Allah ya tsare bai tabi cikin dake jikinta ba ammah gsky ya kamata a kiyaye nan dai ya basu shawarwari ya rubuta musu maganin daya kamata Ummi ce tace toh don Allah doctor a binciken da kayi bai nuna maka tana shan wani magani ba Doctor yace wani irin magani kuma? Ummi tace kamar na FP doctor yace aa ko kadan bamuga haka ba Godiya sukayi masa dakin da Hudah take suka shiga Abbu kuwa tafiya yayi Ummi da Dalhat kuwa mamaki ne ya cikasu Jiddah tace Ummi meyake damunta tun daxu bacci take haryanzu bata tashi ba Ummi tace kada ki damu zazzabi ne kawai insha Allah zata samu sauki Daga nan ta fita a dakin wayar hajiya ta kira ta fada mata wannan abin mamakin Abin ya bata mamaki lallai akwai alamun tambaya koma dai menene in sun dawo gida dole zaayi bincike daga nan sukai sallama..... 🌱🌱🌱🌱 Muffy 🌱🌱🌱🌱 [3/11, 9:30 AM] Naja: 😰😰😰😰😰 AUREN DOLE 😰😰😰😰😰 Book 2 Page 91 - 95 Mufeedamuazuu.blogspot.com STORY And WRITTEN BY *Mufeeda Muazu* Jiddah tace yar uwa meya faru kike ta nemana haka Hudah ta numfasa ta fada mata duk abinda ya faru yau tsakaninta da Dalhat Jiddah tayi shewa tace dama ai na fada miki yaya Dalhat yana sonki kinki sakin jikinki da shine shiyasa ya kasa fada miki Hudah tace uhmm ni ba wannan ba yanzu meye shawara Jiddah tace shawara daya ce ki bada kai kawai bori ya hau Hudah tace haba ya zaayi kice haka bayan irin wahalar daya bani gsky nima sai na rama sannan kuma inja ajina Jiddah tace nidai na baki shawara ta gsky kyaje garin jan aji yaje ya tsinke Hudah taja dogon numfashi tace naji zanyi shawara ni zan tafi sai nashigo anjima Jiddah tace ba sai kin shigo ba ki zauna Kusha soyayyarku Hudah ta harareta tace kyaji da shi ta bude kofa ita kuma Rufaida tazo kenan zata shigo bangajeta tayi zata wuce Hudah ta janyota tace wai ke wace irin karya ce ance ba ayi kin nace murmushin mugunta Rufaida tayi tace kin kusa barin gidan don dama yaya Dalhat ba saan aurenki bane nice na dace dashi bake ba tsaki Hudah tayi ta wuce abinta Dalhat yana fita gidansu Hudah ya shiga ya gaishe dasu hajiya sun dan taba hira kadan ya dawo gida ya tarar da side din a rufe baiji mamaki ba don yasan tunda ya hana Jiddah zuwa ita sai taje mamakin kawancen su yake jininsu ya hadu sosai basa boyewa juna sirrinsu A bude ta tarar da kofan tana shiga ta tarar dashi zaune a falo yana latse2 a wayarsa wuce shi tayi zata shiga daki Kiran sunanta ya kira bata amsa ba tsayawa tayi inda take yace ina kikaje ba izini banza tayi dashi saida ya sake maimaitawa sannan tace wurin Jiddah na shiga tunda kai ka hanata ta shigo wurina sbd wani tunani irin naka tana gama fadin haka ta shige daki abinta Ajiyar zuciya yayi tunanin yanda zai shawo kanta yake don gsky Allah ya jarrabeshi da sonta gashi ita kuma bata sonsa abinda bai saniba shine itama tana shiga daki tunaninsa ne fal a cikin ranta sai dai gsky tana kokonton son da ya fada mata yanayi mata don haka bazata yi saurin amincewa shiba koma zata amince masa to gsky ba yanzu ba sai taja ajinta yadda ya kamata Abinda basu sani ba shine Rufaida na biye da Hudah a baya saida ta tabbatar da babu kowa a falon sannan ta shiga ta boye bayan labule Dalhat yana shiga daki alola ya yo don an fara Kiran sallar magriba tunda ya tafi masallaci bai dawo ba saida akayi sallar issha Sanda ya dawo a falo ya tarar da ita tana sallah wuri ya samu ya zauna har sai da ta idar tayi addua suka shafa a tare kallonta yayi cike da kulawa yace baby ki shirya mu dan fita cikin jindadi tace toh tare da nade abin sallar daki ta shiga cikin yan mintoci ta fito sanye da zumbulelen hijabinta sai kamshi take zubawa yaji dadin shigar da tayi Murmushi yayi yace kinyi kyau taji dadi a ranta amma batace komi a tare suka fita saida sukayi nisa sannan ta kalleshi tace yaya ina zamuje dan kallonta yayi kadan sannan ya maida hankali ga tukinsa yace kisa ido zaki gani ba wanda ya kara magana cikinsu har yayi parking a gaban wani katon mall fita yayi yaga bata fito ba ta window ya leko yace madam ki fito mana ba musu ta fito yace muje ki zabi abinda kikeso siyayya sukayi sosai kananan kaya kuwa shiya zabar mata da kansa Daga nan restaurant sukaje a can sukaci abinci sannan suka Kama hanyar gida zuciyarta cike da farin ciki dama tana son fita irin haka Rufaida najin dawowar su tayi sauri ta koma bayan labule Dalhat ne ya shigo da kayan da suka siyo dakinsa ya wuce da shi itama daki ta shiga don yin shirin bacci Rufaida na ganin haka tayi sauri ta dauko ruwa da kofi ta tsiyaya ruwan a kofi ta aje tabs din FP a gefe tayi sauri ta fita a side din a kofar kitchen suka ci karo da Jiddah bata ce mata komi ba ta wuce zuciyarta cike da farin ciki Fitan ta ba dadewa Dalhat ya fito daga daki kaman ance ya kalli gurin hango magani yayi a center table zuwa gurin yayi ya dauki maganin iri daya dana rannan ransa yayi matukar baci Wato har yanzu bata daina sha ba kenan sai tayi kamar ta bari kiranta ya farayi bataji ba sbd ta fara bacci saida ya kira sau 3 sannan taji da sauri ta sauko daga gado ta fito tana mitsike ido almamun mai bacci yana yin data ganshi ya bata tsoro tace lpy meya faru Bata ankara ba sai jin Mari tayi dafe gurin tayi tana hawaye magana ya fara da kakkausar murya yace wato kin maidani banza kike tambayata abinda ya faru nuna mata maganin yayi yace Allah ya Kama ki kin dauko ruwanki zaki sha sai kika manta kuka take sosai tace Allah bani na ajeba ban san dashiba wani magigicin tsawa ya daka mata yace yi mun shiru daga ni sai ke a gidan nan kada ki raina mun hankali...... 🌱🌱🌱🌱 Muffy 🌱🌱🌱🌱 [3/11, 9:34 AM] Naja: 😰😰😰😰😰 AUREN DOLE 😰😰😰😰😰 Book 2 Page 101 Mufeedamuazuu.blogspot.com STORY And WRITTEN BY *Mufeeda Muazu* Bismillahir rahmanir rahim A hankali Hudah ta fara motsi da idonta tana budesu a hankali har ta bude su gaba daya Jiddah na ganin ta bude ido ta matso kusa da ita tace sannu ya jikin dai Hudah bata iya cewa komi ba sai hawaye dake bin fuskarta Dalhat da Ummi suna waje suka ga Jiddah ta fito a rude Ummi ta tareta tace lpy Jiddah tace ta farka ta kasa magana sai kuka take shine zanje in kira doctor Da sauri suka shiga dakin Jiddah kuma taje Kiran doctor Ummi ta zauna kusa da ita ta riko hannunta tana lallashinta yunkurawa tayi zata tashi Ummi tai sauri ta komar da ita tace kiyi hakuri kinga ruwa ake kara miki Dalhat na tsaye a gefe yana kallonta cike da kauna suna hada ido tai sauri ta runtse idonta ta mai jin zafin abinda yayi mata ya bude baki zaiyi magana kenan sai ga doctor ya shigo Jiddah na biye dashi a bayanta Likita ya duddubata sannan yayi mata wasu yan tambayoyi da yadda takeji a jikinta ta bashi amsa yayi rubuce-rubucensa yaba Dalhat yace yaje pharmacy ya siyo Jiddah tace sannu yar uwa tare da goge kwallar dake zubo mata tace yawwa ngd Hudah tace Ummi wai me likita yace ke damuna zazzabin yayi mun sauki yanzu zuciyata ke tashi ga matsanancin ciwon cikin dake damuna Ummi tace kiyi hakuri Hudah insha Allah zaki samu sauki yanzu zai kawo miki magani kinji Tun daga nan Hudah bata kara cewa komi ba lumshe idonta tayi kamar mai bacci har Dalhat ya dawo tare da magunguna a hannunsa Ya mikawa Ummi sannan yace bari yaje ya dawo Ummi tasa Jiddah ta hada tea mai kauri Sannan tasa ta kawo mata babban roba ta kuskure baki rungumeta tayi tana bata a baki da kyar ta iya shan rabin kofi sannan ta sha maganin nan da nan bacci ya dauketa Ummi tace jiddah ta kula da ita zataje gida ta dafa musu abinci zata turo Rufaida Jiddah ta bata rai jin an ambaci sunan Rufaida tace Ummi da kin kyaleta kawai ni zan iya kula da ita Ummi tace aa hakan bazai yiwu ba sai na dau Allah ya kara sauki Tafiyan Ummi ba dadewa Dalhat ya dawo hannunsa rike da leda kayan marmari ya siyo ajewa yayi akan drawer bude Jiddah ya tambaya ina Ummi tace masa ta tafi gida ta dawo Ya kalli Hudah dake kwance idonta a lumshe kamar mai bacci Dalhat yana kula da ita ba baccin take ba kallon Jiddah yayi yace dan bamu guri Tayi kamar bataji ba saida ya kara maimaitawa sannan tace yaya ai tana bacci yace ina ruwanki batace komi ba ta fita Tana fita yasa ma kofar key ya dawo kusa da ita ya riko hannunta yana murzawa har lokacin taki bude ido murmushi yayi yace nasan idonki biyu nine dai bakya son gani sbd laifin dana aikata a gareki ba tare da nayi bincike akai ba ina mai baki hkr akan abinda ya faru don Allah kada kiga laifina idona ne ya rufe kiyi hkr kinji ita dai jinsa kawai take bata gane inda maganarta ya dosa ba Hawayene ke zuba a idanunta ba tsayawa goge mata yakeyi yace Hudah bakice komi ba don Allah ki bude idonki kiyi mun magana kona samu sassauci a cikin zuciyata nan ma shiru Sakin hannunta yayi tare da mikewa yace shikenan tunda bazakiyi hakuri ki yafe mun laifukana ba shikenan bkm ammah ina rokon alfarma a gurinki don Allah ki kula da kanki da kuma cikin dake jikinki jin ya ambaci tanada ciki tayi sauri ta bude ido tayi farin ciki da Allah ya fitar da ita da zargi a daya bangaren kuma tana tunani bazata iya barin cikin ba sbd ta gaji da wannan auren na yaya Dalhat Kusa da ita ya dawo ya zauna yace banga kina farin ciki ba hararasa tayi ta kalleshi ido cikin ido tace bana farin ciki kuma ka daina wani rawar kafa don sai na zubar da cikin nan na fada maka bana sonka bana kaunarka ni ka kyaleni inyi rayuwata cikin farin ciki ka bani takardata ni bazan koma gidanka ba Maganganunta sunyi masa zafi matuka ammah ya danne don ya san yanzu tana cikin bacin raine kuma ga ciki lallabata zai tayi har Allah yasa ta sauko ta fahimceshi........ 🌱🌱🌱🌱 Muffy 🌱🌱🌱🌱 [3/11, 9:34 AM] Naja: 😰😰😰😰😰 AUREN DOLE 😰😰😰😰😰 Book 2 Page 102 Mufeedamuazuu.blogspot.com STORY And WRITTEN BY *Mufeeda Muazu* Bismillahir rahmanir rahim Su jiddah ne suka shigo su uku da Husnah da Rufaida ganin Haka yayi sauri ya fita suna gaishe shi bai tsaya amsawa ba yayi gaba abinsa Hudah sai kuka take Mara sauti ganin haka ya sanya Rufaida jin dadi a ciki ranta ita bata San abubuwan da suke faruwa ba da batai farin ciki ba Husnah da Jidda suka matso kusa da gadon da hudah ke kwance Husnah ta riko hannun yayarta tana mata sannu tare da share mata hawaye da yake duk ta San abubuwan da Duke faruwa tanata bata hkr Allah sarki Dan uwa rabin jiki Rufaida kuwa sai kallon banza take mata ko ya jiki ta kasa ce mata Jiddah tace Hajiya tace a gaisheki daga kai kawai tayi alamar taji ba wai don bazata iya amsawa ba aa maganar ce kawai bata so tayi sbd yanda takejin zuciyarta kamar ta fito ta fashe sbd bakin ciki da damuwa ta san idan harta bude baki to ba Abu mai dadi zai fito ba Dalhat tunda ya fita bai dawo yan uwa da abokan arxiki sai zuwa ake ana gaisheta da yamma da likita yaga jikin nata da sauki sosai ya rubuta musu sallama Jiddah da Husnah suka har hada kaya suka kai mota Rufaida na zaune tana kallon su saida suka gama kwashe kayan kaf sannan Jiddah ta kira Dalhat ta sanar masa likita ya sallamesu da har yace ta tsaya gashinan zuwa sai ce masa tayi gasu har sun fito bakin asibitin zasu taho gida Dalhat yace to shikenan su hadu a gida Husnah da Jiddah ne suka taimaka mata sbd jikinta ba karfi sosai Jiddah ta kalli Rufaida tace idan kinga dama ki fito mu tafi sukai gaba abinsu Sunxo gate zasu shiga gida Hudah tace Jiddah don Allah danyi parking a nan Jiddah tace me kuma zakiyi a nan gaskiya bazan tsaya ba baba maigadi yaxo ya bude gate suna tsayawa ta bude kofa ta fito da sauri ta fito Jiddah na magana tai banza da ita tana tafiya kamar zata fadi sbd jikinta ba kwari ta bude gate zata fita shi kuma Dalhat yana dawowa yana ganinta yayi sauri yayi parking motarsa ko kafin ya zo inada take ta bude gate din gidansu Biyota yayi da sauri tana ganin ya shi ya shigo ta kara da sauri ta shiga falo tana shiga ta fada a kujera tana maida numfashi kaman tayi gudu ita bata ma kula akwai mutum ba Dalhat shima shigowa yayi ta tashi zata shige daki jiri ya debeta ta koma ta zauna Shahid yace lpy kuwa yaya Dalhat meya faru ba ance tana asibiti bane Dalhat yace nima ban sani ba Jidda dai ta kirani tace an sallamesu nima yanzu dawowata kenan na ganta zata shigo nan Hudah dai tana kwance tana jinsu Shahid ya dauko wayarsa ya kira Jiddah ya tambayeta lpy kuwa ta fada masa duk yadda sukayi Hade rai yayi ya fadawa Dalhat yadda Jiddah ta fada masa Shahid ya daka mata tsawa yace ke......... tashi kibi mijinki kafin in bata miki rai Tashi tayi ta zauna tace wlh yaya bazan koma ba saidai a kasheni Hajiya ce ta fito jin hayaniya Tambaya tayi meke faruwa Shahid ne yayi mata bayanin abinda ya faru Hajiya tace Hudah kefa bakida kunya ko tashi kibi mijinki hawayene yake bin fuskarta zatayi magana amai yazo mata da gudu ta shiga toilet tayi ta wanko bakinta ta fito jiki ba kwari tana hawaye ta zauna kusa da hajiya tace wayyo cikina zan mutu Hajiya tace kiyi hkr bazaki mutu ba kinji hakuri ake kina shan magani zaki samu sauki Hudah tace hajiya bacci nakeji alhat yace hajiya ki barta tayi baccin anjima zanzo mu tafi hararansa tayi sallama yayiwa hajiya tare suka fita da Shahid..... 🌱🌱🌱🌱 Muffy 🌱🌱🌱🌱 [3/11, 9:34 AM] Naja: 😰😰😰😰😰 AUREN DOLE 😰😰😰😰😰 Book 2 Page 103 Mufeedamuazuu.blogspot.com STORY And WRITTEN BY *Mufeeda Muazu* Bismillahir rahmanir rahim Suna tafiya Hajiya ta taimaka mata ta kaita daki ta kwanta ta lullubeta da bargo sannan ta rufe mata kofa tana fitowa Alhaji na shigowa tayi masa sannu da zuwa ya wuce daki saida ya huta sannan tayi masa bayanin abinda ke faruwa Alhaji addua yayi Allah ya sawwake Hajiya tace tana daki tana bacci Alhaji yace wani dakin tace dakin Husnah Alhaji yace don me zatazo nan bayan ga gidanta can kira mun ita hajiya tace tana bacci Alhaji yace tasota taxo ta wuce gidanta tun wuri wannan ai sakarci ne sai fada yakeyi Hajiya dai hkr taketa bashi Alhaji ya rufe idonsa yace wlh sai an tasota ta tafi gidanta hakanan hajiya taje ta tasota da kyar ta tashi tana goge ido alamar bacci bai isheta ba tace hajiya don Allah ki kyaleni inyi bacci hajiya tace Alhaji ne yace a kiraki idan kuma baza kije bane to tashi tayi tana ya mutsa fuska tace ganinan zuwa wai meyasa akace masa ina gidan nan ne hajiya tace ke dai kika sani tana gama fadar haka ta fita a dakin Hajiya na fita Hudah ta shiga toilet ta wanke fuskarta sannan ta fito tana tafiya a hankali har ta isa falo a kasa kusa da hajiya ta zauna kanta a kasa tace gani Alhaji yace me kikaxo yi gidan nan bakinta na rawa tace banida lpy ne shine nazo idan naji sauki sai in koma Alhaji yace to baki isa ba da izin wa Hudah tayi shiru yace to maxa ki tashi ki dauko mayafinki ki koma gidan mijinki turo baki tayi tace Alhaji don Allah kayi hakuri inci abinci idan anyi sallar issha sai in koma alhaji yace idan an gama abinci zaa kawo miki tana kuka ta tashi dama anan falo aje gyalenta ta dauka zata tafi hajiya ta tsayar da ita ta kira Husnah tace ta rakata tare da Husnah suka tafi Suna fita Alhaji yace wa hajiya kada kiga nayiwa Hudah haka ki dauka ko bana sonta ne aa ko daya ba haka bane ina sonta sosai inayi mata hakene sbd ta rungumi kaddara ta gane cewa ba komai bane mutum ke nema ya samu ba Hajiya tace hakane na fahimceka Allah dai ya basu zaman lpy Alhaji ya Amsa da Ameen Suna fita Hudah tacewa Husnah kinga ni ko su Alhaji basa sona kina ganin yadda ya koreni bayan kuma banida lpy Husnah tace ba haka bane Aunty suna sonki kuma suna matukar kaunarki so suke suga kin saki jiki da mijinki kun zauna lpy Suna tafe a hankali suna hira gunin ban shaawa har suka shiga gidan a falo suka tarar da Dalhat yana zaune yana kallo Hudah na ganinshi tai tsaki ta shige dakinta Husnah ce ta gaisheshi itama tabi bayan yayarta Murmushi Dalhat yayi ya cigaba da kallonsa amma acikin zuciyarsa tunanin Hudah ne kawai yana mamakin irin sonda yake mata gashi tana so ta bashi wahala yana cikin tunanin ne yaji kiran sallah ya tafi masallaci Side dinsu Jiddah kuwa Ummi ce take ta aikin girki tana dafa abincin marmari sbd Hudah Saida ta gama hada abincin ta kira Jiddah tace taje ta kaiwa Hudah Koda ta shiga bataga kowa a falon ba sai ta aje basket din abincin a falo ta shiga daki a kwance ta tarar da Hudah Husnah kuma zaune a gefenta suna hira kadan kadan don baa cikakken minti 10 zataji amai yazo mata Jiddah ta gaisheta da jiki sannan ta shaida mata ga abinci nan ta Kawo mata tazo taga in akwai wanda zata iya ci Hudah tace Jiddah bazan iya cin komiba bakina ba tests kuma cikina ciwo yake Jiddah tace hakuri zakiyi kici saiki sha magani insha Allah zaki samu sauki Hudah tace uhmm nida samun lpy kuma sai nan da wata tara Jiddah tace [3/11, 9:34 AM] Naja: 😰😰😰😰😰 AUREN DOLE 😰😰😰😰😰 Book 2 Page 104 🌐🔰 HAJOW 🌐 🌐HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITTER🌐 mufeedamuazuu.blogspot.-com STORY And WRITTEN BY *Mufeeda Muazu* Bismillahir rahmanir rahim Jiddah tace bangane me kike nufi ba Hudah tace duk abinda ake baki sani ba to wai ina dauke da ciki wata 2 ne ko uku ni nama manta cikin farin ciki Jiddah tace wai ne ma wannan ai abin farin ciki ne kuma kinga ai kin fita daga zargin dasu Abbah suke miki Hudah tace hakane ammah ni gsky bani son wannan cikin zubarwa zanyi ni bazan iya da wahala ba Jiddah ta bata rai tace nagane abin naki iya tsiya ne wlh gara ki kama kanki tun wuri kada garin kallon ruwa kwado yai miki kafa wata tazo ta kwace miki miji kina ji kina gani sai yafi karfinki kuma kin san babu saki a tsakaninku gara kiyi hkr ku zauna lpy nidai shawara nike Baki Hudah tace naji kuma ngd tayi murmushi tace me kika Kawo mun Jiddah tace uhmm nima ban sani ba Ummi ce tace in kawo miki nifa naji mamaki Ashe tana tattalin jikanta ne kafin yazo Hudah dai murmushi kawai tayi don ta san idan ta biye mata zataita tsoka nanta ne Ta bude kula taga tuwon shinkafa ne miyar agushi sai dayan kulan kuma dan-wake ne yaji mai da yaji da sauran kayan hadi Plate ta dauko ta zuba dan-waken ta zuba yaji mai yawwa sosai Jiddah irin wannan yaji haka kadafa yayiwa danmu illah Hudah ta harareta Husnah dai na gefe tana kallon su Hudah ta manta Ashe Husnah tana dakin sai zuba takeyi Hudah ta juya ta kalleta tace wlh saura inji wannan maganar wlh ranki sai ya baci Dakin yayi shiru kowa yayi shiru sai Hudah dake ta cin dan-wake Dalhat ya shigo da murmushi dauke a fuskarsa yace hira kukeyi haka Hudah hararansa tayi ta cigaba da cin dan-wakenta bai damu ba don ya san neman rigima take Jiddah da Husnah suka tashi zasu tafi Hudah ta bata rai tace bana son munafunci daga ya shigo sai ku wani tashi tsaya sukayi suna kallonta Dalhat yace kuje abinku kunji saida safe sallama sukayi mata suka tafi kusa da ita yazo ya zauna bata kula shi ba ta cigaba da cin abincinta Hannunsa yasa a cikin plate din ta bige hannun tace malam meye haka wannan abincin ba naka bane ga tuwo nan a kula Murmushi yayi yace dama nasan ba nawa bane irin wannan yaji haka ai da gani kasan na masu ciki ne bata rai tayi ta dauki plate dinta ta bar masa dakin ta koma falo . Shima fitowa falon yayi ya zauna a kujeran da yake fuskantarta yace Hudah sarkin fushi daga magana sai ki taso ki barni to Allah ya baki hkr don Allah kiyi hkr akan abinda ya faru. Ko kallonsa batayi ba balle yasa ran zata tanka shi tashi yayi ya matso kusa da ita ya saka gwiyoyinsa a kasa yana cigaba da bata hkr sai da yayi kaman zaiyi kuka sannan tace shikenan na hkr komi ya wuce Cikin farin ciki ya tashi ya rungumeta yace ngd sosai Allah ya barmu tare Sakinta yayi ya kalli fuskarta yace don Allah kice kina sona wlh ina matukar qaunarki murmushi tayi ta mike tsaye ta nufi hanyar dakinta saida ta kai kofa sannan ta juyo ta kalleshi shima ita yake kallo tace *I LUV U TOO Yaya DALHAT* tana fadar haka tayi sauri ta shige daki sbd kunya Dalhat kuwa yana zaune ya kasa motsawa sbd farin cikin daya mamaye shi shi abin har mamaki yake bashi Ashe Hudah zata so shi yana cikin wannan tunanin ne Husnah tayi sallama ta shigo hannunta dauke da kula Dalhat ya taso ya amshi kulan tace hajiya tace a kawo ma Hudah bude kulan yayi yace amarya ma aka Kawo mana kunya ya kamata tayi sauri ta juya dambu ne sai kamshi yake Dakin Hudah ya shiga da kulan a hannunsa tana ganinsa ta koma gado taja bargonta ta rufe fuskarta wai tana jin kunya....... ... 🌱🌱🌱🌱 Muffy 🌱🌱🌱🌱 [3/11, 9:34 AM] Naja: 😰😰😰😰😰 AUREN DOLE 😰😰😰😰😰 Book 2 Page 105 🌐🔰 HAJOW 🌐 🌐HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITTER🌐 mufeedamuazuu.blogspot.-com STORY And WRITTEN BY *Mufeeda Muazu* Bismillahir rahmanir rahim Kusa da ita ya karisa ya yaye mayafin data rufe fuska,hannunta tasa ta dada rufe fuska rike hannun yayi rufe ido tayi ta kasa kallonsa murmushi yayi yace ikon Allah yau kuma ni akejin kunya fuskarta dauke da murmushi tace nidai ka kyaleni tayi maganar ne cikin shagwaba shi kuma sai abin ya burgeshi kwaikwayonta yayi yace ni gsky bazan tafi ba sai an bude mun wannan kyakkyawan idon naki mai kama da zinare Dariya ma ya bata hakanne yasa ta bude idonta kallon juna suke cikin so da kauna ita ta fara kawar da idonta Sannan tace yaya meka Kawo mun ne a kula Dalhat yace aike yar gatace dambune Hajiya ta aiko miki dashi Bata rai tayi tace saida na koshi sannan zaa Kawo mun yamutsa fuska tayi ta janyo kulan ta bude kamshine ya cika mata hancj nan da nan taji amai yazo mata da sauri ta shige toilet sai kwarara amai take duk ta galabaita da kyar ta fito tana tangadi kamar zata fadi Dalhat yayi sauri ya tare ya rungumeta yayi a jikinsa dada shigewa tayi kamshin turarensa yayi mata dadi sosai Dalhat sai sannu yake jero mata tun tana iya amsawa har ta gaji tambayarta yayi ko tasha maganinta na dare girgiza masa kai tayi alamar aa Kwantar da ita yayi ya tashi ya dauko maganin tare da ruwa kusa da ita ya dawo ya zauna ya tallabota ya bude magungunan ya bata da kyar Tasha tana yamutsa fuska yana gama bata ya kwantar da ita ya rufeta da bargo sannan ya fita yaje ya rufe kofa daga nan dakinsa ya koma yayi wanka sannan yayi shirin kwanciya dakin Hudah ya koma Koda ya shiga ya tarar tayi bacci gefenta ya kwanta ya janyota jikinsa dada shigewa tayi sai baccinta take cikin kwanciyar hankali Dalhat kuwa fadawa yayi cikin kogin tunani yadda sukayi zaman doya da manja ammah wai yanzu sune a haka cikin soyayyar juna tana sonsa shima yana sonta ajiyar zuciya yayi lallai dole yayiwa Allah godiya kuma yayiwa iyayensu godiya da suka zaba masa mata tagari mai hakuri Da yaso ya cuci kansa saboda wani shirme dada rungumeta yayi tare da manna mata kiss a goshi yace I really luv u Hudah Ranar dai yayi baccinsa mai dadi Da asubah ya rigata tashi don har lokacin tana jikinsa sai baccinta take a hankali ya zameta daga jikinsa yaje toilet ya dauro alola sannan ya tasheta da kyar ta iya tashi tana goge ido alamun baccin bai isheta ba saida ta shiga toilet sannan ya tafi masallaci da kyar ta iya alola duk jikinta ya mutu bata jin karfi A zaune tayi sallah tana addua ya shigo kusa da ita yaje ya zauna harta gama addu'ointa a tare suka shafa kallonsa tayi a kunyace tace INA kwana yaya amsawa yayi cikin jin dadi sannan ya tambayeta mezata ci shiru tayi nadan lokaci sannan yace dan-Wake Dalhat yace ba jiya kika ci ba kamar zatayi kuka tace ni shi kawai nike so inci bana shaawar komi in bashiba Dalhat yace yi hkr ranki ya dade bani minti kadan tashi yayi ya tafi kitchen Allah yasa ya iya girki dan-waken yayi [3/11, 9:34 AM] Naja: 😰😰😰😰😰 AUREN DOLE 😰😰😰😰😰 Book 2 Page 106 🌐🔰 HAJOW 🌐 🌐HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITTER🌐 mufeedamuazuu.blogspot.-com STORY And WRITTEN BY *Mufeeda Muazu* Bismillahir rahmanir rahim Yayi mata dan-waken sannan ya dafa ruwan zafi ya zuba a flask har daki ya Kawo mata ya zuba mata a plate sannan ya zuba nasa ya hada tea Tana kaiwa bakinta tayi sauri ta fito dashi kallonta yayi cikin kulawa yace lafiya? Kaman xatayi kuka tace ni ba irin wannan Nike so ba irin na Ummi nikeso Dalhat yace wani iri ne na Ummi ai duk da fulawa ne itama dashi tayi Kuka ta fara yi masa tana cewa Allah ba iri daya bane rigima take tayi masa duk ya rasa yadda zaiyi da ita tashi tayi zata fita tambayarta yayi ina zata turo baki tayi tace wurin Ummi zani Dalhat yace haba Hudah kiyi hkr kici wannan din mana duk iri daya ne kallonsa tayi tace gaskiya bazan ci ba Idan bazakaje ka samo mun ba ni zanje da kaina shiru yayi na dan lokaci shi gaskiya yanajin kunya yaje wurin Ummi yace tayiwa Hudah dan-wake ganin ya tsaya shi bai barta taje ba shi kuma bai tafi ba Kuka ta saka masa hakuri ya bata yace bari yaje ya samo mata fita yayi gidan gaba daya restaurant yaje ya siyo mata dan waken yana dawowa kitchen ya shiga ya zuba dan-waken a kula sannan ya kai mata tana kaiwa baki ta tofar tace wlh wannan ba Ummi tayi ba tashi tayi ta koma gado ta kwanta tana kuka kusa da ita yaje ya zauna yana lallashinta ammah ina fir taki yin shiru Ganin ba sarki sai Allah yasa yasa ya tashi ya shiga side dinsu Ummi a kitchen ya sameta tana hada breakfast dukawa yayi ya gaisheta yana sosa keya Ummi ta fahimci akwai magana a bakinsa tambayarsa tayi lpy Cikin jin kunya yace dama Hudah ce sai kuma yayi shiru Ummi tace mai ya samu Hudah Dukar da kai yayi yace wai dan-wake takeso irin na jiya murmushi tayi tace dama shine ka kasa fada yanzu zanyi mata insha Allah Jiddah zata Kawo mata Dalhat ya yiwa Ummi godiya sannan ya tambaya ko Abbu ya tashi Ummi tace bai tashi ba side dinsu ya koma a falo ya tarar da ita gidan tsaf sai kamshi yakeyi ta gyara ko ina tayi wanka tana kwance a doguwar kujera zuwa yayi ya dago kanta ya zauna ya kwantar da ita a cinyarsa sai kamshi take zubawa Dalhat yace yan mata ansha kyau sai kamshi kike zubawa murmushi kawai tayi tace uhmm waye yan matan bayan saura kwana kadan ta zama mummy Dalhat yace ni kullum yan mata kike a wurina Hudah tace gara da kace a wurinka don nasan yanxu da yawan mutane a tsohuwa suke kallona rufe bakinta yayi yace kul kada ki kara fadan irin wannan maganar a gabana idan ba kina so muyi fada bane Hannunsa ya kai cikinta yana shafawa yace bari inji lafiyar baby nah cire hannunsa tayi tace ni don Allah kabari wannan ai rashin kunya ne Dalhat yace wani irin rashin kunya kuma bayan matatace ke kuma cikina kike dauke dashi.......... . Masoyana ina mai baku hkr na rashin jina da kukayi kwana2 ngd sosai da kulawarku Muffy ce yar mutan Zazzau👌🏼 [3/11, 9:38 AM] Naja: 😰😰😰😰😰 AUREN DOLE 😰😰😰😰😰 Book 2 Page 107 🌐🔰 HAJOW 🌐 🌐HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITTER🌐 mufeedamuazuu.blogspot.-com STORY And WRITTEN BY *Mufeeda Muazu* Bismillahir rahmanir rahim Rufe idonta tayi don ita kunya takeji Dalhat yace ni kike jin kunya lallai ashe zaki wahala gara ma tun farko ki cire wannan kunyar don yanzu ne zamu fara cin amarcin mu nasan su hajiya sun fada miki zaman aure babu kunya a ciki Hudah tace ni ba wannan ba ina dan wakena? Dalhat yace Jiddah zata kawo suna cikin maganar saiga Jiddah ta shigo hannunta rike da basket ganinsu haka yasa tayi sauri ta aje basket din zata juya Dalhat yace kinzo kin aje abu bako magana dukar da kanta tayi tace Ummi tace in dawo yanzu ne shiyasa Hudah kuwa duk kunya ya kamata sai kokarin tashi takeyi ammah ya hana Jiddah dai tana tsaye tana ganin ikon Allah ya tsayar da ita yana rashin kunya a gabanta tafiyarta tayi basu ma san lokacin da tafi ba suna can suna rikicin su kuka ta fara yi masa shiyasa ya kyaleta basket din ya janyo tare da dauko plate ya mika mata kusa da ita ya koma ya zauna amsa yayi zai bata abaki da farko kin amsa tayi sai daga baya dai taga bazai bari taci da kanta ba sannan ta Amsa haka yai ta bata a baki har saida ta koshi Maganinta ya dauko ya bata sannan shima yaje yayi breakfast dinsa yayi wanka koda ya fito ya tarar ta fara bacci gyara mata kwanciya Jiddah kuwa tunda ta tafi take mamakin abinda ta gani lallai yaya Dalhat bashida kunya ammah kuma taji dadi data ga sun fara zaman lpy gaskiya abin ya burgeta Rufaida kuwa duk ta kasa sukuni bata ji labarin abinda take sonji ba suna zaune a falo da Ummi Jiddah da Rufaida Jiddah tace Ummi kin san wani abu? Ummi tace aa Jiddah tace gaskiya yau su Hudah sun burgeni Ummi tace da akayi mene? Jiddah tace wlh bakiga yaddah yaya Dalhat yake tattalinta ba bazaki taba cewa ga yadda aurensu ya kasance ba da abubuwanda suka faru gsky naji dadi Ummi tace Alhmdllh haka ake so Allah ya basu zaman lpy tare da zuria dayyiba Jidda ta amsa da Ameen Rufaida kuwa wani bakin ciki ne ya kamata Jiddah na kula da hakan hararanta tayi tare da yi mata gwalo Rufaida taji haushi tace Ummi kinga Jiddah ko wlh ta kiyayeni Ummi tace Jiddah INA kula dake fah kin rainata ki fita a idona in rufe Jiddah tace to Ummi ai saita fada miki abinda nayi mata Ummi tace Rufe mun baki ni ban san meya hadaku ba sam ba kwa taba zama inuwa daya sai kunyi fada nan dai tayi musu nasiha mai ratsa jiki duk jikinsu yayi zanyi Jiddah tace dama itace bata son zaman lpy sbd wani dalili nata Ummi tace to yanxu dai komi ya wuce kada in kara gani kuma na kula ba kwa magana da Hudah don Allah ku gyara Rufaida tace insha Allah komi ya wuce Ummi tace to Allah yayi muku albarka duk suka amsa da Ameen Jiddah tace kuma akwai abinda nikeso in fada mata tuntuni Ummi tace wani irin magana ne haka Jiddah tace na farin ciki ne Ummi ammah tsakaninmu ne jan hannun rufaida tayi tace kinji yar uwata taso muje Ummi tayi murmushi tace sannu mai yar uwa ina kuma zaku ana hira Jiddah tace wurin Aunty Hudah zamu Ummi tace to adawo lpy fita sukayi rike da hannun juna Ummi taji dadin ganin sun shirya side din Hudah suka shiga a kwance tana barci suka tarar da ita Jiddah taje dai dai kunnenta tana yafi firgigit ta tashi shagwabe fuska tayi kaman zatai kuka Jiddah tace ke dallah malama bashi bane da zaki shagwaba Hararanta tayi tace bana son gulma Jiddah tace mai ciki Hudah tace wlh ki fita idona in rufe nifa Auntynki ce Jiddah tace nima haka ai kinga duk sai mu girmama junan mu Rufaida tana zaune tayi shiru tana kallonsu zuciyarta cike da tsoro da fargaban abinda zata fada don a zahirin gaskiya tana son ta nemi afuwar Hudah akan abinda tayi mata ammah kuma gsky tana jin tsoro Hudah kuwa tun shigowarsu ta kalleta ta dauke kanta Jiddah tace baku gaisa da Rufaida ba Hudah tace wacece kuma haka Jiddah tace meye haka kuma bana son wulakanci Rufaida ta matso kusa da Hudah ta tsugunna a gabanta ta kamo hannuwanta fisge hannunta tayi tace waike lpy ina ruwanki dani da har zaki wani rike mun hannu kin wani tsuguna kamar mai karban gaisuwa Rufaida tace don Allah kiyi hakuri da duk abinda ya faru ki yafe mun laifukan da nayi miki Hudah ta bata rai tace ni bakiyi mun komi ba idan ma kinyi keda Allah Jin haka yasa Jiddah tace haba Hudah kiyi hkr ki yafe mata Allah ma daya haliccemu munayi masa laifi ya yafe mana balle mu yan Adam..... Muffy👌🏼 [3/11, 9:38 AM] Naja: 😰😰😰😰😰 AUREN DOLE 😰😰😰😰😰 Book 2 Page 109 🌐🔰 HAJOW 🌐 🌐HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITTER🌐 mufeedamuazu.blogspot.com STORY And WRITTEN BY *Mufeeda Muazu* Bismillahir rahmanir rahim Shiru yayi na dan lokaci kafin yace shikenan kije ammah kada kiyi magriba da sauri tace to tare da bude kofa zata fita riko hannunta yayi ta dawo ta zauna yace ba muyi sallama ba zaki tafi kanta a kasa tace wani sallama kuma bayan Wanda mukayi kissing din hannunta yayi sannan yace sauran ice-cream dinki fah sai da ta fita a motar ta leko ta windo tace ka aje mun a freezer don Allah kada ka sha mun kai kawai ya gyada mata gate din gidansu ta bude ta Shiga sai da yaga shigewarta sannan yayi horn aka bude masa gate ya shige Da sallamarta ta shiga Shahid kawai ta tarar a falon wuri ta samu ta zauna gaishesa tayi mamaki ne ya kamashi sosai sbd tunda aka fara maganar aurenta da Dalhat ya daina samun ko kallon arxiqi balle ya san zaa gaishi sa amsawa yayi cikin kulawa tambayarsa tayi hajiya Shahid yace tana falon Alhaji Shahid ya tambayeta fatan dai lpy don naga jiya a gidannan kika yini yau kuma kin dawo Hudah tayi murmushi tace lpy klu yaya,Shahid yace to Allah yasa tashi tayi ta barshi a wurin cike da mamakin canxawarta lokaci guda falon Alhaji ta shiga da sallamarta cikin nutsuwa ta shiga kusa da hajiya taje ta zauna gaishesu tayi cikin girmamawa Alhaji yace ince dai ko lpy murmushi tayi sannan tace lpy klu dama nazo ne in gaisheku kuma in nemi gafararku akan duk abubuwan da suka faru don Allah kuyi hkr ku yafe mun insha Allah bazaku kara jin wani matsala daga gareni ba zamu zauna lpy kuma ngd da zabin da kukayi mun hakika da naso in tafka babban kuskure na bijirewa umurnin ku sai Allah ya soni ya hadani da yan uwa masu sona kuma masu son suga nabi hanya mai dacewa yanzu nasan duk wanda yabi zabin iyayensa bazai taba yin nadama ba ko Kadan Hannun hajiya ta riko duka biyun tana kuka tace don Allah ku yafe mun goge mata hawaye tayi tana lallashinta tace ki daina kuka mu dama can bamu rike ki da komi ba kullum addua mukeyi miki da fatan shiriya to Alhmdllh yanzu tunda kin gane gaskiya Allah yayi miki albarka ya baku zaman lpy Alhaji ma godiya yayiwa Allah sannan ya sanya mata albarka tare da nasiha mai shiga jiki Tun daga wannan rana take ganin gata wurin iyayenta da yan uwanta bata da damuwa ko kadan mijinta kaman ya hadiyeta don kauna tayi kiba tayi haske abinta gashi cikinta ya fara fitowa wata shida kenan Ya rage saura kwana biyu bikinsu Jiddah,Hudah itace kirjin biki sai kaiwa da komowa ake bata gidansu bata gidanta duk ta zama busy ga ciki Dalhat tunda ya dawo bata side dinsu gashi cikin gida cike yake da mutane kunyar shiga yake wayarta ya kira yaji tana ringing a kan kujera tsaki yayi ya jefar da wayar ya fito waje cikin kawayensu ya hangota sai hirar su suke abinsu ko a jikinta bata da damuwa Sumayya ce ta shigo zata wuce ya kirata yace don Allah ta kira masa Hudah Sumayya na zuwa wurin tace Maman twins ana kira Hudah tace wane ke kirana nuni tayi mata Dalhat ta hango a tsaye ya harde hannuwansa yana kallosu tashi tayi zata tafi Jiddah yace saura kuma ki dade Hudah tace ai dole in dade kema kinsan dole in kula da mijina Sumayya tace eh lallai masu miji inace yaushe aka gama guje-gujen baa so muna dawowa fake muna baki hkr kin tuna ranar da aka kawoki idan kin manta bari in tuna miki hararanta tayi tace na daiji duk abinda zaki fada sai dai ki fada tana gama fadar haka tayi gaba abinta....... ,...... Muffy👌🏼 [3/11, 9:38 AM] Naja: 😰😰😰😰😰 AUREN DOLE 😰😰😰😰😰 Book 2 Page 110 🌐🔰 HAJOW 🌐 🌐HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITTER🌐 mufeedamuazu.blogspot.com STORY And WRITTEN BY *Mufeeda Muazu* Bismillahir rahmanir rahim *Ina ba masoyana hakuri na rashin jina kwana 2 ina fatan zaku gafarceni* *Dedicated dis page 2 my friend Sumayya Umar Dalhat Kebbi* Dariya sukayi mata tana tafiya a hankali harta isa gurinsa tana zuwa ya bata fuska yace kinsan yau zan dawo ammah shine zaki tafi kiyi zamanki kin San zan nemeki murmushi tayi tare da riko hannunsa tace yi hakuri zo muje binta yake kamar rakumi da akala har suka isa falonsu ta zaunar dashi kitchen ta shwayam a dauko ruwa da kofi tsiyaya masa tayi tare da mika masa kin amsa yayi wai sai dai ta bashi a baki ba yadda zatayi hakanan ta bashi a bakin yana gama sha ta hada masa ruwan wanka kafin ya fito wanka ta jera masa kayan da zai sa sannan tabar dakin Wannan karon gidansu ta shiga kowa yaji msmakin ganinta yadda tayi kyau gashi cikin yayi mata kyau Aunty Asiya ce ta kirata tace Hudah ina kiyayyar take yanzu nuna mata cikin dake jikinta tayi kunya ne ya kama Hudah tayi sauri ta fita a dakin Dalhat koda ya fito daga wanka bai ganta ba sai kayan da ta aje masa a gefen gado shiryawa yayi ya fita daga gidan bai dawo ba sai bayan sallar isha bai ganta a falo ba ya shiga bedroom nan ma bata toilet ya bude yaga wayam falo ya dawo yaga an jera abinci a dining ranshi ya baci ammah ya zaiyi dole ya hakura tunda biki ake kuma bikin Jidda dole yayi hakuri don tsakanin Hudah da Jiddah sai Allah Ya gama cin abinci ya koma falo ya zauna yana kallo shiru-shiru har karfe tara bata dawo ba wayarsa ya ciro zai kirata sai ganin wayar yayi a center table tsaki yayi wannan wani irin wulakanci ne kwana 2 naya gari tasan yana bukatarta kusa da shi shine ta tafi tayi zamanta shi yanxu ina zai ganta ta ina zai fara nemanta wayar Jiddah ya kira har sau uku baa daga ba tashi yayi ya shiga cikin gidan ko zaiga wani ya aikeshi ya nemo masa ita bai ga wani yaro ba Ummi ne a falon kasa da yan uwanta gaishe su yayi ya zauna yayi shiru Ummi ta fahimci akwai magana a bakinshi tambayarsa tayi meya farune Dalhat dukar da kai yayi yana sosa keya sannan yace Ummi Jiddah nike nema Ummi ta fahimci matarsa yake tambaya a fakaice murmushi tayi tace inajin suna gidan babanku tunda ta fadi haka ya san gidansu Hudah take nufi sallama yayi musu ya tafi duk kunya ta kamashi Gidansu Hudah ya shiga a farfajiyar gidan ya hadu da Jadeed tambayarsa Yayi ina Hudah take Jadeed ya tabbatar masa suna ciki Dalhat yace ya kira masa ita a corido ya gansu ita da Sumayya Jadeed ya fada mata sakon mijinta bata rai tayi tace ni wallahi duk ya takura mun daga dawowarsa bayan na hada masa abinci me kuma yake da bukata oho masa Sumayya tace ke yake da bukata aje a kula da oga Tsaki tayi kaman zatayi kuka don ta San jarabar tsiyarsa ne ya tashi ciki suka shiga ita da Sumayya tayiwa su Hajiya sallama su Jidda sai dariya sukeyi mata duk ta kule harda kwallarta a compound din gidan ta tarar dashi da Shahid gaishe da Shahid tayi ta Wuce su tana wucewa Dalhat yayiwa Shahid sallama yabi bayanta hannunta ya rike yace shine zaki tafi kiyi zamanki ki barni ni daya Shiru tayi batace komi ba har suka shiga gida rufe kofa yayi hijab kawai ta cire tayi kwanciyarta a kujera kusa da kafanta yaje ya zauna yana mata tausa duk ta gane nufinsa banza tayi dashi da yaga shirun yayi yawa ne yace hala dai kin gajine dagowa tayi Kadan tace kaman ka sani wallahi ji nake kaman anyi min duka........tashi yayi yace taso muje in gasa miki jikin yadda zakiyi baccinki mai dadi ba musu ta tashi ta bishi daren ranar dai sun raya shi bisa sunna da safe da kyar ta iya tashi sbd tsabar gajia Muffy..... 😰😰😰😰😰 AUREN DOLE 😰😰😰😰😰 Book 2 Page 111 🌐🔰 HAJOW 🌐 🌐HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITTER🌐 mufeedamuazu.blogspot.com STORY And WRITTEN BY *Mufeeda Muazu* Bismillahir rahmanir rahim *Wannan shafin sadaukarwa ce ga dukkanin masoyana ngd sosai da soyayyarku gareni nima ina sonku* Sai da tayi musu breakfast sannan tace masa zata tafi cikin gida yau zaayi lalle Dalhat yace mai lallen taxo nan tayi miki babu inda zaki tafi ki barni rokonsa ta farayi ammah Sam ya shafawa idonsa toka yace bai yadda ta fita ba suna cikin rigimar ne Sumayya da Jiddah suka shigo yana ganin sun shigo ya tashi ya fita daga gidan kwallane ya zubo mata sauri tayi ta goge Sumayya tace lpy meyafaru kuna soyayyar ku abin shaawa kowa mamaki yake Hudah tace wai cewa yayi ko nan da kofa bai bani izinin in taka ba Jiddah tace kodai kinyi masa wani jiya Hudah tace wallahi banyi masa komi ba sbd kawai na kai dare sai kace wani wuri naje wai sai dai mai lallen tazo tayi min anan Jiddah tace shikenan kiyi hakuri ki daina kuka idan ta gama mana zatazo tayi miki Ki cigaba da hakuri kin san halin Yaya sai a hankali wani lokacin idan yayi abun kamar bashi ba share hawayen fuskarta tayi tare da jan dogon numfashi sannan tace ai dole yayi mun wulakanci dama ba sona yake ba cikin dake jikina kawai yake so Nine dai da banida zuciya kullum nike manne masa inaso inga farincikinsa Uhmmm Sumayya tace ba haka bane Kawai kiyi hakuri tunda dai zaa zo ayi miki meye abin damuwa tashi sukayi sukace dama mun jiki shiru ne shiyasa mukazo mu gani ko lpy sai anjima ki shirya zatazo tayi miki tana ji tana gani suka tafi daki ta koma ta kwanta nan da nan bacci mai nauyi ya dauketa bata tashi ba sai wurin karfe daya da rabi 1:pm sallah ta farayi sannan ta shiga kitchen shayi ta dafa ta soya plantain ta zuba nata a plate ta zuba masa nasa a kula sannan ta jera a dining table bai shigo ba sai wurin 2:30pm a falo ya sameta tana kallo tunda ta amsa sallamarsa bata kara cewa komi ba shima baice mata komi ba ammah yaji dadi a zuciyarsa tabi umurninsa dining ya nufa ya duba kula plantain ya gani ga kuma flask din ruwan xafi dariya yayi yasan tayi ne don ta bata masa rai Zama yayi ya hada tea din ya zuba plantain din a plate sai da ya kusan gamawa sannan tazo ta zauna a kujeran dake kallon nashi a hankali tace anima za'ayi kamu zakaje ne kallonta yayi sama da kasa yace kinga nayi miki kama da mai zuwa kamu girgiza kai tayi tace to nidai zani Dalhat yace umurni kike bani kome to babu inda zakije da wannan cikin aje a wahalarmun da yaro kallon mamaki takeyi mass sannan tace don Allah kayi hakuri ta barni inje kasan fa nice babbar kawa dariya yayi sannan yace babbar kawa yanxu kam sai dai ta samu wata ke kin riga kinyi nauyi jan kujeran tayi da karfi ta tashi abinta ta barshi anan. Wurin karfe 3:10pm mai lalle taxo tayi mata mai kyau kamar itace amaryar lokacin Dalhat baya gidan har aka gama lallen bai dawo ba don haka ana gamawa ta tashi ta shiga wanka tana fitowa tasaka ankonta mayafinta da Jakarta ta fito ta rufe side din da key cikin gida ta shiga inda akewa amare kwalliya itama akai mata Sannan akayi mata dauri tayi kyau sosai kamar itace amaryar karfe 4:30pm suka tafi wurin kamu [4/9, 9:33 AM] Naja: 😰😰😰😰😰 AUREN DOLE 😰😰😰😰😰 Book 2 Page 113 🌐🔰 HAJOW 🌐 🌐HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITTER🌐 mufeedamuazu.blogspot.com STORY And WRITTEN BY *MUFEEDA MUAZU* Bismillahir rahmanir rahim Dis page is Dedicated 2 HAYAT BABA ZUBAIRU.Happy birthday wishing u long lyf nd prosperity🎂🎂🎂🎂🎂 Ana kiran sallar magriba su Jiddah suna shigowa sannan su Ummi suka fita sunyi mamakin ganin Hudah a dakin tare dasu Ummi Sumayya ce ta tambayeta lafiya muka ganki anan Hudah tace lpy klu wallahi basu labarin abinda ya faru ta kara da cewa yanzu shida ganina a side dinmu sai bayan an gama biki Jidda tace kiyi hkr kada kiyi masa haka tunda dai ya hakura to meya rage kuma Hudah tace abinda ya rage shine ban son takura ina komawa duk zaibi ya takura min Jiddah tace nidai banga abin takura ba Hudah tace Alhmdllh ai kema kina kan hanya gobe ana daureki ai zaki gane Sumayya tace kudai kuka sani ni kunga tafiyata tashi tayi ta bar dakin Hudah da Jiddah suma suka suka yo alola bayan saisha Ummi ta shigo a kwance ta tarar da Hudah tambayarta tayi jikin Hudah ta marairaice tace jiki da sauki Ummi tace Jiddah taso ki rakata side dinta tunda dai taji sauki Hudah bataso haka ba ammah ba yadda ta iya dole ta tafi Asabar :yaune dubban mutane suka shaida auren HAUWA' U ALIYU(JIDDAH) Da Angonta OTHMAN ABUBAKAR SADIQ(SHAHID) Da RADIYA AHMAD TIJJANI tare da Angonta HAIDAR ALIYU Da kuma Amarya ASMA'U ABUBAKAR SADIQ (HUSNAH) Tare da Angonta ALIYU HAIDAR AHMAD An daura aure cikin farin ciki da kwanciyar hankali kowa ka gani zaka San cewa yana cikin farinciki musamman amare da Angwayen nima Mufeeda cewa nayi Allah ya bada zaman lafiya Ameen Yamma yayi anata shirin kai amare gidansu saida aka kaisu wurin iyaye akai musu fada Jiddah aka fara kaiwa gidanta dake G.R.A sannan Husnah kuma gidanta na Bello Khaliel sai Radiya da aka kawota gida kafin a wuce da ita giant a dake Dutsen Tanshi Hudah na daki sai kuka take Dalhat ya hanata zuwa gidan Jiddah lallashinta yake ammah sam taki hakura daya gaji da lallashin yayi kwanciyarsa ya kyaleta tashi tayi ta koma falo tayi kwanciyarta a kujera can dare ya laluba bai jita ba haske ya kunna yaga bata nan tashi yayi ya fito a falo ya ganta a kujera tana baccinta da har zai tasheta kome ya tuna oho sai ya fasa daki ya koma da asuba da zai tafi masallaci ya tasheta sannan ya wuce yana fita ta tashi tayo alola tayi sallah bai dawo gidaba sai da gari yayi haske a lokacin duk ta gama aikin da zatayi tayi wanka ta jera breakfast a dining daki ta shige tana jiransa ya dawo da sallama ya shigo a ciki ta amsa sallamar sannan ta gaishe shi ba yabo ba fallasa Kusa da ita yazo ya zauna ya janyota jikinsa tare da amsa gaisuwarta yace madam gaskiya kinyi kyau sosai kokarin kwacewa take ammah yaki sakinta murmushi yayi yace Gimbiya baa huce ba kenan ayi hakuri ranki shi dade ayi mun afuwa bazan kara ba bata san lokacin da tayi murmushi ba tace shikenan ya wuce dariya yayi tare da shafa cikinta yace Babynah Allah ya saukeki lpy amsawa tayi Ammen................ Muffy😘 [4/9, 9:34 AM] Naja: 😰😰😰😰😰 AUREN DOLE 😰😰😰😰😰 Book 2 Page 114 🌐🔰 HAJOW 🌐 🌐HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITTER🌐 mufeedamuazu.blogspot.com *STORY And WRITTEN* *BY* *MUFEEDA MUAZU* Bismillahir rahmanir rahim *Dedicated this page 2 Aisha Gombe(Autan Mama)* A kunnensa ta rada masa *I luv u* murmushi yayi sbd jin dadin maganar fuskan tausayi tayi sannan tace don Allah yaya ina neman izini ne Dalhat yace izinin mene kanwata Hudah tace dama so nake inje gidajen amare shiru yayi baice komi ba gabanta ne ya fara faduwa kada dai ya hanata sai can yace shikenan kije ammah kada kiyi dare bana son kina kaiwa dare a anguwa Mayafinta ta yafa tare da daukar key din motarta tayi masa bye bye harta kai kofa yace zaki tafi baki bani breakfast ba Hudah tace lah don Allah kayi hakuri mantawa nayi ga abincinka can a dining sai na dawo fita tayi da sauri don kada ya kuma tambayar wani abun shima ya fahimci hakan dariya yayi ya tashi ya tafi dakinsa don yin wanka Hudah kuwa tana fita motarta gidan Radiya ta fara zuwa bata wani dade ba ta tafi gidan Husnah ta dade a can anata hira sai bayan sallar azahar wurin 2:30pm sannan tayi musu sallama da gidan Husnah Sumayya ce ta biyota tare suka tafi gidan Jiddah Sumayya sai tsokanar Hudah takeyi a hanya wai Allah yasa yan biyu zata haifa tun tana kulata harta gaji ta kyaleta a daki suka sameta taci kukanta harta gode Allah Hudah na zuwa ta maka mata duka a baya da sauri ta tashi ganin Hudah ne yasa ta koma ta kwanta tana hararanta tace sai yanzu ne kikaga daman zuwa ai da kin sani bakizo ba Hudah tace ai yanxu ma bata baci ba sai in koma tunda baki bukatar ganina tashi tayi zata fita Jiddah tayi sauri ta riko hannunta tace haba yar uwa baki San wasa bane Sumayya tace kyaleta ta tafi mugani Hudah tace ke kuma waya sakoki ciki zama sukayi a gefen gado Hudah tace kinsan da yaya na fito kuwa da kyar ya barni kuma yace kada magriba tayi mun a waje Jidda tace aiko bazai yiwu ba ace bazaki kai dare ba Hudah tace to yaya zanyi abinda yafi karfina dole sai hakuri Jidda ta dauko wayar ta dialing no Ummi tayi bugu daya ta dauka bayan sun gaisa Jidda tace Ummi don Allah kice yaya Dalhat ya bar Hudah sai dare sai yazo su tafi tare Ummi tace eh to bazan ce eh ko aa ba don bai kamata in shiga hurumin da ba nawa ba kuma idan nayi masa magana zai ga kaman itace ta fada mun kinga zasu iya samun matsala kuyi hakuri kawai Sallama sukayi Jidda bata so haka ba hawayene ya gangaro mata a fuska Hudah ta goge mata tace kiyi hakuri nima ba haka naso ba ammah ba yadda muka iya Jidda tace shikenan yanxu zumuncin mu zai yanke Hudah tace ki daina fadan haka xumuncinmu bazai taba yankewa ba har a bada kamar yadda muka taso mukaga iyayenmu nayi haka muma insha Allah mutuwa ce kawai zata raba mu Jiddah tace ba gashi ba yanzu yaya yana so ya yanke ba Hudah tace wane mutum ai bai isa ya yanke mana zumunci ba Sumayya tace Allah sarki Allah ya bar zumunci dukkansu suka amsa da Ameen daga nan kuma sai hira ya tsinke Wurin karfe 6:30pm sukayi shirin tafiya Jiddah kuwa kwalla ne ya cika mata ido Hudah tace hakuri zakiyi kowa da kika ganshi haka aka tafi aka barshi ina nan zuwa kada ki damu kinji yar uwa goge mata hawaye tayi rakosu tayi har wurin da sukayi parking din mota Hudah tace to amarya sai munzo gashi gone kallon Sumayya tayi tace ko ba haka ba . . Sumayya tace kinji Jiddah kyaleta dadin abin ma baa kaiki kina guduwa ba wai ba kyaso sai kuma gaki da ciki ina kiyayyar take Hudah bata ce komi ba ta bude mota tayi shigewarta sannan tace kwaji dashi ke kuma Sumayya idan kin gama shirmen naki sai ki shigo mutafi sallama sukayi mata suka dauki hanyar gida Jiddah ta koma gida jikinta a sanyaye....... Muffy😘 [4/9, 9:34 AM] Naja: 😰😰😰😰😰 AUREN DOLE 😰😰😰😰😰 Book 2 Page 115 🌐🔰 HAJOW 🌐 🌐HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITTER🌐 mufeedamuazu.blogspot.com *STORY And WRITTEN* *BY* *MUFEEDA MUAZU* Bismillahir rahmanir rahim Bayan wata uku Hudah ce ta fito da tsohon cikinta tana kiran Dalhat shiru bataji motsinsa ba dukawa tayi sakamakon matsanancin ciwon mara tana cikin wannan hali Aunty Mufeeda ta shigo da sauri ta karisa wurinta tana tambayarta meyafaru kasa magana tayi sai ciki da take nuna mata kamota tayi a hankali suka fito a mota ta sata sannan ta zaga mazaunin direba ta shiga maigadi ya bude musu gate suka fita asibitin da take awo ta kaita don haka suna zuwa aka amsheta labour room suka shige da ita don suna ganinta suka gane haihuwa CE Aunty Mufeeda fitowa waje tayi tana nema layin Dalhat Koda Dalhat ya dawo yayi sallama yaji shiru ya duba ko ina bai ganta ba ya tafi side din Ummi nan ma shiru yaji ba kowa a falo dakin Ummi ya shiga ya tarar tana bacci wayarsa ne tayi kara Aunty Mufeeda ne karan wayar ne ya tashi Ummi daga bacci dauka yayi tare da yin sallama daga can Aunty Mufeeda ta amsa sannan suka gaisa anan ne ta fada masa suna tare da Hudah a hospital tana labour sannan tace masa ya duba dakinta ya dauko kayan da ta hada na haihuwa Hankalinsa duk ya tashi ya fadawa Ummi da sauri ya fita Ummi kuwa toilet ta shiga tayi brush ta wanke idonta zani kawai ta daura ta dauki hijab dinta ta sauko kasa da sauri lokacin harya fito da mota shiga tayi sai asibiti Tun safe har yamma bata haihu ba hankalin kowa duk ya tashi Doctor ne ya fito daga dakin duk yayi xufa yace Dalhat ya biyo shi office Ummi tace lpy kuwa Doctor baice komi ba Dalhat yabi bayansa Doctor ne ya fara bayani kamar haka a gaskiya munyi iyaka kokarin mu ammah har yanxu d only solution kawai shine ayi mata C.S wani takarda ya dauko ya bawa Dalhat yace yasa hannu Dalhat yace C.S kuma Doctor? Doctor yace eh don aceto rayuwarta da abinda ke cikinta Dalhat cikin sanyin jiki ya daura hannu akan takardar kenan sai ga wata nurse ta shigo da sauri tace Doctor kan dan ya fara fitowa da sauri ya tashi suka tafi dakin dukkansu dakatar da Dalhat nurse din tayi dawowa yayi sai safa da marwa yakeyi yakasa zama Ummi sai baki take bashi Doctor na shiga dakin Da na fitowa kato dashi sak irin babansa dan wani lokaci kadan nakuda ya dawo sabo wannan karon macece bayan 10mins saiga wanni nakudan lokaci kadan haifo yarta mace ba dadewa mahaifar ya fito saida suka gama gyarata tsaf aka gyara jariran sannan wata nurse ta fito hannunta rike da namijin da fara'arta tazo ta mikawa Ummi babyn sannan tace congratulations Dalhat yace ya mahaifiyar fa nurse din tace tana lpy ta haifa maka jarirai guda uku congratulations once again Dalhat bai jira ba yayi sauri ya shiga dakin sbd tsantsar farin ciki su Ummi suka mara masa baya Doctor dinne ya mika masa hannu yayi masa murna nurses suka mika masu jariran Dalhat hunnunsa rike da mace daya yaje kusa da Hudah inda take kwance ya riko hannunta yana jin sonta a ransa bacci take don anyi mata allurar bacci sbd ta huta nurse tace idan ta tashi likita yace zaa sallamesu don sun dubata sun tabbatar da lafiyarta kalau Aunty Mufeeda ta kira Hajiya ta fada mata alokacin Husnah na nan tazo ganin gida da sauri Hajiya ta dafa ruwan zafi ta juye a flask ta hada kayan shayi ta hada mata a basket tace tayi sauri ta kai musu cikin lokaci kadan labari ya watsu cikin dangi Hudah ta haifi yan uku Dalhat ya karbi yaran yayi musu huduba ammah bai fadawa kowa sunan daya sanya musu ba....... Muffy😘 [4/9, 9:34 AM] Naja: 😰😰😰😰😰 AUREN DOLE 😰😰😰😰😰 Book 2 Page 116 🌐🔰 HAJOW 🌐 🌐HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITTER🌐 mufeedamuazu.blogspot.com *STORY And WRITTEN* *BY* *MUFEEDA MUAZU* Bismillahir rahmanir rahim Dedicated dis page 2 *Muffy online Hausa Novels* *Muffy & Maryam Ahmad paki* *Feedoh online Novels* *First lady Hausa Novels* *Da sauran groups din Novels wanda ban ambata ba* After four hours Hudah ta farka Ummice a gefenta sai kuma Dalhat dake tsaye a gaban gadon Ummi tace sannu Hudah rufe ido tayi sbd kunya Dalhat yace baki tambayi abinda kika haifa ba shiru tayi batace komi ba daya na hannun Ummi biyun kuma an kwantar dasu a gadon yara dake kusa da nata Dalhat yace yara uku kika haifa biyu mata daya namiji Hudah dai shiru tayi batace komi ba Ummi ta mika mata yaron dake hannunta kin amsa tayi wai tana jin kunya Ummi ta mika wa Dalhat yaron tace bari in tashi nasan ni kikejin kunya tana fita Dalhat ya dawo kusa da ita ya daura mata yaron akan cinyarta kurawa yaron ido tayi cikin so da kauna duka yaran ya dauko mata duk tayi musu addu'a kallonsu tayi tace ammah yaran nan dakai suke kama fah Dalhat yace aa dake suke kama Wani suna kasa musu Hudah ta tambaya Dalhat yace wani suna kikeso a saka musu Hudah tace duk sunan da ka sanya musu nasan bazaka zaba musu suna mara maana ba Dalhat yayi murmushi tare da shafa kanta yace Masha Allah Allah yayi muku albarka Ameen ta amsa Dalhat yace namijin nasa masa Hibban matan kuma Kausar da Wahida murmushi hudah tayi tace masha Allah.Allah ya raya manasu Bayan 1hr likita yaxo ya dubata lpynta kalau sannan ya sallamesu tun kafin su dawo mutane suka fara zuwa barka Dama sun yake shawarar gidanta zaa barta wata kanwar Hajiya zatazo ta zauna da ita Dalhat yaji dadin haka don gidanta aka dawo da it a Sumayya da Jiddah Suna zaune a gefenta Sumayya tace kinga Allah ya amsa adduata ko harda kari ma Hudah tayi murmushi tace aike zan bawa guda daya inba Jiddah daya Jiddah tace ai muna so wannan babbar kyautace kinga Sumayya ta samu dan zaman daki dariya sukayi dukkansu. Hibban ne ya fara kuka Jiddah ta miko mata shi don ta bashi nono Hudah tace wlh bazata bashi ba sai dai bashi madara ya cika tsotso dayawa Sumayya tace aiko dole ki bashi tunda babansa ya riga ya biya abu kamar wasa taki bashi Husnah dake gefe zaune da laulayin cikinta wata biyu ta mike zata fita Sumayya tace ina zakije ana zaune ana hira Husnah tace kaina ke ciwo zanje in dan kwanta ne Hudah tace Uhmm manya Husnah dai batace komi ba tayi tafiyarta gidansu tana shiga ta fadawa Hajiya duk abinda ke Faruwa baa jima da fitar Husnah na ba saiga Hajiya ta shigo sai fada take tundaga kofa tana shiga dakin ta amshi Hibban a wurin Jiddah dake kuka tana lallashinsa ta ajiyewa Hudah a cinyarta tace ta bashi nono da kyar tana hawaye ta ciro nono ta bashi tana cije baki wai zafi yake mata Ranar suna Dalhat rago hudu ya yanka da Sa guda daya gida ya cika da mutane sai murna ake mai jego kuwa sai shiga da fita take cikin kaya na alfarma kayan suna ko da aka tara baa magana saboda tsadarsu da yawansu anyi suna lpy kowa ya watse bayan suna da wata uku akayi bikin Sumayya lokacin Jiddah,Husnah da Radiya wata biyar Bayan shekara biyar Hudah na gani da Dalhat tare da yan ukunsu sun fito daga wata hadaddiyar mota haduwarta ita ke bayyana tsadarsa duk wanda ya gansu sai yaji sun burgeshi sun kara kyau da haske wani katon super market suka shiga duk inda suka bi kowa saiya kallesu sunyi siyayyarsu mai yawa sannan suka fito don komawa gida Hibban ne yace mummy don Allah akaimu gidan Hajiya kausar tace mudai gidan Ummi zamu Hudah tace to saiku fadawa Daddy ai Dalhat yace babu inda zakuje ku barmu mu kadai a gida ba tunda mummy taki ta bamu wasu twins din........ Muffy😘 [4/9, 9:34 AM] Naja: 😰😰😰😰😰 AUREN DOLE 😰😰😰😰😰 Book 2 Page 117 last page 🌐🔰 HAJOW 🌐 🌐HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITTER🌐 mufeedamuazu.blogspot.com *STORY And WRITTEN* *BY* *MUFEEDA MUAZU* Bismillahir rahmanir rahim *Dedicated dis page 2* *Aishatu Shuibu Adamawa kawar kirki ngd sosai Allah ya bar Zumunci Ameen* *Bazan Manta daku ba* *Maryam Ahmad paki* *Zainab Nijer(Maman Ramla)* *Ummi Nijer* *Ummah Shehu(First lady)* *Jinjina Gareku HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS ALLAH YA KARA BASIRA DA HADIN KAI AMEEN* Hararansa tayi cikin wasa tace nine ma zan bawa kaina Dalhat yace bari mu sauke su Hibban insha Allah yau zan baki baby murmushi kawai tayi Tambari suka nufa gidandu Hudah suka fara shiga Hajiya da Alhaji duk suna falo a kasa su Dalhat suka zauna gaishe da iyayen nasu sukayi cikin girmamawa Hibban yana zuwa ya hadu da yaron Husnah mai sunan Alhaji (Abubakar)ana kiransa da Muhseen sai tsalle-tsalle sukeyi abinda yakeso kenan Hudah tace Hajiya ina Husnan take Hajiya tace taje asibiti kinsan ta kusa haihuwa Hudah tace Allah ya raba lpy suka Amsa da Ameen Hajiya tace Hudah Allah yasa dai ba kwayoyin hana daukan ciki kike sha ba Kunya ne ya kama Hudah ta dukar da kai tace bana shan komi Hajiya Allah ne bai Kawo ba Hajiya tace Allah ya kawo masu albarka daga nan sukayi musu sallama nan suka bar Hibban gidansu Dalhat suka shiga anan suka tarar da Jiddah da Radiya kowa da yaranta biyu duk mata nan wasa ya kachame dasu kausar dama abinda sukeso kenan bayan sun gaisa da Ummi ne Hudah ta dawo falo wurinsu Jiddah sai hira sukeyi Jiddah tace kinga yayanki ya hanani aiki wai sai dai inyi business Hudah tace nima haka ai ya zamuyi sai hakuri haka dai cigaba da hirarsu har na dan wani lokaci Dalhat yazo ya dauketa yabar su Wahida Abbu da Ummi sai albarka suke sa musu da fatan Allah ya shirya musu zuria Sun koma mansion house dinsu dake G.R.A cike da jin dadin yadda iyayensu suke musu addua A falo suka zauna Hudah ta dauko musu lemu mai sanyi da kofuna guda biyu ta zuba musu kusa da ita Dalhat ya dawo yana bata a baki itama har suka shanye Dalhat ya kalleta cikin so da kauna yace rabin raina kin san wani abu kuwa girgiza kai tayi alamar aa murmushi yayi yace duk sanda na kalleki sai inji nutsuwa sai nike ganin duk duniya ba wanda ya kaini Saar samun mace tagari gaskiya yiwa iyaye biyayya yanada matukar mahimmanci a wurin Da don a duniya ba wanda yakai iyaye son Dansu don haka bazasu taba zaba masa abinda zai cutar dashi ba duk Dan da yake so yaji dadin rayuwar duniya to yabi Allah da manxonsa sannan yayiwa iyayensa biyayya matukar ba sabon Allah sukace yayi ba koba dadi yayi hakuri a gaba sai yaga ribar biyayya da hakurin da yayi kinga dai misali akan mu rugumeshi tayi tace hakane mijina fatana Allah ya barmu tare nima ganin nike a duk duniya ba macen data fini Saar miji nagari godiya da fatan alkhairi ga iyayenmu Allah ya saka musu da aljannar fiddausi Dalhat yace Ameen Daga mata gira yayi yace Madam it's tym fah insha Allah yau kwallona zai shiga raga dariya tayi ta tashi zata gudu nan suka fara zagaye falo daga karshe yayi nasar kamata dagata yayi cak tana dariya suka shige daki ni Mufeeda dake gefe na jah musu kofa nace sai anjima. *Tammat Bihamdulillah* *Dukkan godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki data bani ikon kammala wannan Littafi na AUREN DOLE lpy* *Masoyana ako ina kuke a fadin duniya a ina godiya sosai Allah ya bar kauna Nima ina sonku* *Ina fatan zaayi amfani da darussan dake cikin wanna littafi Wanda na batawa rai kuma ya gafarceni kunsan Dan Adam ajizi ne inayiwa kowa fatan alkhairi* *MUFEEDA MUAZU*😘