[5/20, 10:01 PM] Ummu Amjad: _LITTAFIN ANDIZO NA KUƊI NE N300. +966577675904_ 16 Mutsu-mutsu ta dinga yi tana kawar da kanta dan ta kauce wa rungumar da yake son mata tana daga kwance, komawa gefe ya yi ya kwanta yana huci hakan ya ba ta damar faɗo wa daga gadon tana kuka wanda sautin shi baya fita dan bakin a manne yake, kafin ta yi wani ƙwaƙƙwaran motsi sai ganin shi ta yi a gaban ta yana ƙoƙarin kwanciya. Cikin maye ya fara maganar da ta sa numfashi Andizo ya ɗauke na wucin gadi. “Kin san tsawon shekaru nawa na ɗauka ina dakon soyayyar ki Khadija? Tun lokacin da kika fasa mini gilashin mota kallon farko naji na kamu da son ki, shekaru huɗu kenan ina ɗauke da cutar soyayyar ki. Hakan ya sa na dinga bibiyar ki ta yadda zan sa a kamo mini ke. Yanzu ga shi kin zama matata jiya aka ɗaura mana aure ni da ke.” Ya faɗa yana ɗago da ita ya zaunar. Idanuwan Andizo kamar su faɗo kasa saboda tashin hankalin da ta shiga, kalmar aure ita tafi hautsi ƴar jaririyar ƙwaƙwalwarta nan da nan kanta ya ɗauki zafi ganin ta ya tsaya na 'yan daƙiƙu. Sai da ya girgiza ta sannan ta buɗe ido tana kallon shi ta rasa me za ta faɗa masa, ita dai duk duniya ta san masoyinta ɗaya ne wato Saminu mai fanke, sai kuma Salim da a haukanta ta ce zai kaisu birni ita da Saminu su yi karatu in sun girma a musu aure. Sai yanzu take tunanin kenan Salim ma irin haka ne yake so a mata ita da shi? Girgiza kai ta yi ya ja mata hanci yana dariya ya ce “Sai kin haifi yara uku sannan zan kaiki ki gano danginki, kin ga lokacin za su fi farin cikin ganin ki da yaranki ba za su ce komai ba..” Ita dai kallon shi take hawaye na bin kuncinta, so take ta zazzage shi ko za ta samu sassaucin abin da take ji amma babu hali, cire mata gam ɗin ya yi yana wani irin shan yaji ya ce “Khadija yi magana na ji, nasan kina son ki ce wani abu.” Fashewa ta yi da kuka mai ƙarfi, gabaɗaya jikinta rawa yake tsoron shi ya kama ta musamman yadda ta ga jikinsa duk gashi ne kwance, sai da ta yi mai isar ta sannan ta tsagaita yana zaune yana surutan shi bai hana ta yin kukan ba sai ma dariya da yake mata. Tana shashekar kuka ta ce “Allah ya isa tsaknina da kai azzalumi ɗan iska marar albarka, uban wa ya ce ka aure ni? Ko ba ka san ba ina da masoyina Saminu mai fanke? Kuma shima mai hankali ya ce zai aure ni ya kaimu birni ni da Saminu mu zama 'yan gayu, shi ne ka tafi ka aure ni saboda kai sheɗan ne..” Ta faɗa tana huci.. Kasancewar ba ya cikin haiyacinsa dariya kawai yake yi yana tafa hannu tare da cewa “Very good beautiful girl, you are the best friend.” Matsawa ta yi dan ita dai ba ta san ba abin da yake faɗa, a masifance ta ce “To wa ya sani ma ko yaren su ne na 'yan iska yake faɗa mini dan nima na zama irin shi.” Yunƙurowa ya yi zai mata amai ta matsa da sauri tana nuna shi da tsaya sai kuma ta sa kuka tana faɗin “Waiyo Allah Saminu ina kake yau ga Dijanka wani ɗan iska ya aure ta, Allah ya fidda ni daga gidan nan..” Bacci ne ya ɗauke shi ta tashi tsaye tana kall-kalle ko za ta samu hanyar da za ta gudu kafin ya tashi, sai da ta gama duba ko'ina na ɗakin amma ba ta samu ƙofa ba dole ta dawo ta zauna a bakin gadon tana kallon waje ɗaya. Tana nan zaune ta ji ƙaran buɗe kofar, da sauri ta kalli wajen suka haɗa ido da ita, ta tashi da sauri ta tare ta tana zubar da hawaye ta ce. “Don Allah baiwar Allah ki fitar da ni daga gidan nan na koma ƙauyenmu, ki taimake ni..” Kallon ba ki da hankali ta mata ta wuce ta ɗauke kayan shaye-shayen da Sultan ya baje, sai da ta nufi kofar fita ta juyo ta kalli Andizo ta ce “Ai yarinya ke da fita daga ɗakin nan har abada, saboda ba a ƙasarku kike ba ballantana na taimaka miki ki gudu ki koma gida.” Dafe ƙirji ta yi ta ce “Na shiga uku ni Dije! To a wata duniyar nake.”. “Kina Abuja Nigeria, dan haka ki daina ma tunanin guduwa dan na san babu inda kika sani a cikin garin nan.” Tana gama faɗin haka ta kama kofar za ta fita Andizo ta yi saurin kama hannunta ta ce “Don Allah to ki nuna mini inda zan yo alwala rabon da na yi Sallah tun ranar da aka sato ni.” Fisge hannunta ta yi ta fice Andizo ya mara mata baya amma tana zuwa kan kofar ta ji an hankaɗo ta an dawo da ita cikin ɗakin kofar ta mayar da kanta ta rufe.. Jim kaɗan sai ga ta ta dawo, kama hannunta ta yi ta nufi wani dan lungu da ke cikin ɗakin sai ga su a bakin wata ƙofa, kamar sakarya haka ta saki baki tana kallon wajen dan ko kaɗan ba ta ga k'ofar ba sai yanzu.. Nuna mata komai ta yi ta yadda za kunna ruwan sannan ta fi ta yi tafiyar ta.. Andizo ta kasa kunna ruwan sai kallon banɗakin yake, da kyar ta iya kunnawa fitsarin ma a ƙasa ta yi saboda tsaron wajen da ta nuna mata take, alwalar ta ɗaura ta fito ta bi inda ta ga sun biyo ta dawo.. Shuru ta yi tana tunanin ina za ta ga kayan Sallah, bincike ta dinga yi a ɗaki har ta buɗe wardrobe ta samu wani dogon Hijabi da darduma a haɗe, cike da mamaki ta ɗauka ta shinfiɗa. Har za ta kabbara ta ji ta sake dawowa ɗakin, kallon ta ta yi ta ce “Anty ina ne alƙibila.” Nuna mata ta yi ta wuce banɗakin ta wanke ita kuam ta tayar da Sallah. Haka ta dinga jero salloli har sai da ta ji bacci na ɗibar ta sannan ta zame ta kwanta a nan.. _NIGER_ Suna isa asibiti aka fito da gado Ahmad ya fito a sukwane suka ɗaura shi aka yi ciki da shi, kasa rufe motar Ahmad ya yi sai da Hassana ta zagayo kashe ta biyo bayan su.. A bakin ƙofar suka zauna Mamma da Ahmad duk suka yi tsaye suna kallon ƙofar . Suna nan tsaye sai ga Aminatou ta shigo asibitin afujajan mayafi a hannu tana rusa kuka, taro ta Mamma ta yi suka ƙaraso ta zaunar da ita tana ba ta haƙuri. Ɗagowa ta yi ta kalli Ahmad cike da tsana ta ce “Kaine sanadin jefa shi cikin wannan halin, da ba ka je garin su waccan 'yar ƙauyen ba ai ba zai ganta ya ce yana so ba, har soyayya ta zame masa matsala. Ba shi da wani zance sai na Khadija kamar ita ce Autar matan duniya, Allah ya isa tsakani na da kai ban yafe maka ba na cutar mini da miji da ka yi.” Ta ƙarashe maganar tana goge hawaye.. Baki buɗe Hajiya Babba ke kallon Aminatou ita da Mamma, shi kuwa Ahmad runtse idanu ya yi yana jin wani mugun takaici ya mamaye masa zuciya, in da tasan irin tashin hankalin da yake ciki bai kamata ta faɗa mata irin waɗannan kalaman ba. Girgiza kai ya yi ya juyo ya kalle ya, gabaɗaya ta ƙara ɓata masa rai ya ce “Wace ce ke a wajen shi? Ke jininsa ce ko danginki ne shi? Ai iya miji ne a gareki ko? Kuma ko da mutuwa ya yi wani za ki sake aura ki manta da shafin rayuwar da kuka yi da shi ni kuma fa ? Jinina ne wanda ko da mutuwa ya yi ba zan taɓa samun kamar shi ba har abada, ki kama kanki ba na son tashin hankali a halin da nake ciki, da banzar maganarki zan ji ko da halin da yayana yake ciki? Ni kin san ba tsaran ki ba ne yanzu kike son na miki jahilci Wallahi.” Duk wannan maganar da yake faɗi in ba Hajiya babba da ke gefen shi ba babu wanda ya ji me yake faɗa mata, wani irin kallo ya aika mata ya ja tsaki ya ƙara da cewa “Zulwajahaini kawai, kamar wata ta Allah ke wai irin kina mutuwar son yaya Salim ko? To ki ci gaba da shiga gonata zan shata miki layi yadda ba kya tunani, ƴar rainin hankali in kin yi wasa da tunaninsu ni ba ki isa ki yi wasa da nawa tunanin ba dan na fi ki sanin duniyanci, kuma mu zuba ni da ke mu gani za ki gane Borno a gabas take.” Dafa shi Hajiya Babba ta yi ta girgiza masa kai tana masa nuni da ya rabu da ita, ita kuwa ta cika ta yi fam sai gyaɗa kai take kamar ƙadangaruwa.. Tun da aka shiga da Salim likitoci suka dukufa kanshi, sun shafe fiye da awa huɗu suna ƙoƙarin daidai bugun zuciyarsa amma abin ya gagara, sai da yamma ta yi lis sannan suka samu nasara ya farfaɗo, kalmar farko da ya furta yana kallon samar ɗakin ita ce Khadija. “Inna lillahi wa inna laihin raji'un! Ina Khadijana take? Don Allah ku ce ba da gaske ba ne tana gida, ina Ahmad yake? Ahmad zo ka ƙaryata mini abin da kunnena ya juyo mini ka ce wasa kake mini babu abin ya faru da Khadija..” Cike da tausayawa babban likitan ya fito waje dan ya kira Khadijar da ya ji yana kira, gabaɗaya suka yo kanshi suna tambayar shi ko ya farfaɗo. Cire galashi ya yi ya dube su ya ce “Don Allah wace ce Khadija a nan? Sannan waye Ahmad?” Da sauri Ahmad ya matso baki na rawa ta ce “N.. Ni ne likita, amma babu Khadija a nan.” “To ku biyun nan tun da ya farfaɗo yake kiran sunanku, ka fara shiga kai ɗaya ban da hayaniya.” To ya ce da sauri ya shige ɗakin. Yana shiga ya zauna a kusa da shi a sanyaye ya ce “Ka kwantar hankalinka Yaya in sha Allah za a same ta.” Runtse idanu ya yi yana jin zuciyarsa na masa ƙuna, da kyar ya iya cewa “Zan je na nemo ta da kaina.” To Ahmad ya ce yana ƙara kwantar masa da hankali tare da tabbatar masa za a ganta. Sai da aka ba su dama duk suka shigo ɗaya bayan ɗaya, lokacin da Aminatou ta shigo kuka ta dinga yi tana jero Allah ya isa ga waɗanda suka sace Andizo, da kanta ta taimaka masa ya tashi ya zauna ta dube shi tana share hawaye ta ce “Mijina ka daina tayar da hankalinka, nasan ma kafin a ba ka sallama za a ganta. Ni kaina hankalina ya kasa kwanciya a kan sace mana amarya da aka yi, amma ba komai ko ma waye Allah zai tona masa asiri. Yanzu ka daina wannan surutan kar hankalin su Mamma ya tashi a ɗauka ko ka zare ne, kai fa jarumi ne sojana ka nuna jarumta mana.” Ta faɗa tana jan kincinsa. Dogon numfashi ya ja yana jin sassauci ganin yadda Aminatou ta nuna damuwar ta a kan lamarin, albarka yasa mata ta amsa da amin tukun aka masa allurar bacci ko zai samu hutu.. Sai da ta tabbatar ya yi bacci ta fito ta samu su Mamma ta ce “An masa allurar bacci yanzu haka bacci yake, amma don Allah Mamma ki ba da cigiyar ta a ko'ina ko ya samu nutsuwa, babu abin da yake faɗa sai sunan Khadija..” Ta faɗa tana hararar Ahmad ta kasan idanu, sosai kishi ya turniƙe mata zuciya kawai ƙarfin hali take, wata muguwar tsanar Andizo ta ƙara samun gurbi a zuciyarta.. Tashi Ahmad ya yi ya dube su ya ce “To ku tafi gida ni zan tsaya a wajen shi in ya so gobe sai a kawo mana abinci.” Ba dan sun so ba suka tafi dan har Mamma ta ce ya bar Aminatou ta zauna amma ya ce sam ba za ta zauna ba ta koma gida kawai, hakan ya ƙara ƙular da ita ta wuce fu ta shiga motarta.. Kiran wayar Sabrin ta yi sai hura hanci take, tana ɗauka ta soma faɗa a kan abin da Ahmad ya mata. Shuru Sabrin ta yi har sai da ta kai aya sannan ta ce “To kenan shi kuma ta nan ya ɓillo? To ki bari shima za mu yi maganin shi, na fa lura in ba ki tashi tsaye ba wannan kucakar ta shigo gidan za ta kwace miki fada. Shi ya sa na ce miki a kashe ta amma kika ce gara a mata kurciya ta shiga duniya, yanzu ga shi ba ki rabu da baƙin cikin ta ba tun da mijinki yana magana.” Kwafa ta yi tana danna hon da ƙarfi, a kiɗime Maigadi ya fito daga banɗaki ya buɗe mata kofa, sosai mamaki ya kama shi ganin Aminatou ce mai wannan abin. Tana fitowa ta fice ciki suna ci gaba da tattaunawa da Sabrin har ta shigo palo, zama ta yi ta ƙure AC saboda ta haɗa zuba kamar wacce ta yi gudu a sahara lokacin zafi, ƙarshe ta tashi ta shige ɗaki tana ƙara jinjina kalar rashin mutumcin da za ta yi wa Ahmad da Khadija ko ta samu sassauci.. _NIGERIA_ Yau Monday hakan ya sa tun safe Andizo ba ta ga gilmawar Sultan ba, ta takure a waje ɗaya ga ɗakin ba shi da haske sosai, kuka ta ci ta ƙoshi sannan ta yi shuru ta ɗaga hannaye sama ta ce “Ya Allah ka kawo mini ɗauki na koma gida kar ka ba wa wannan mugun dama ya cutar da ni, nasan yanzu haka suna can ana cigiya ta ni kuwa gani a wata ƙasar.” Haɗa kai da gwiwa ta yi ta yi shuru tana tuna yadda take gudanar da rayuwarta cikin jin daɗi kafin a kawo ta wannan waje da ta yi wa laƙabi da baƙin ɗaki.. Kamar daga sama ta ji kiran Sallah ta zabura tana kallon ko'ina na ɗakin, yawo ta dinga yi har ta zo saitin taga inda ta nan ne kiran sallar ke zuwar mata, dafa ƙirji ta yi tana murmushi ta miƙa hannu ta buɗe taga dan ta ƙara jin sautin kiran Sallar. Kai ta miƙa sai dai ta ga daga bayar an kange tagar da karafuna, da sauri ta iso jikin kujera ta dinga turawa har ta kai bakin tagar, haka ta hau ta leƙa waje ai ba shiri ta yo baya ganin wasu manyan-manyan garada a farfajiyar gidan suna tsaye, dafe ƙirji ta yi tana zare idanu ta ce, “Ƙudun uban can! Yo wannan duk ƙauyenmu babu babba kamar irin su.” Shuru ta yi tana tunani can ta tashi tsaye ta kuma leƙawa, riƙe baki ta yi ganin yadda ta yi naisa sosai da ƙasa ta yi ƙuri tana kallon su wasu na kai-kawo wasu kuma suna nan tsaye kamar sojoji. Ƙaran motar da ta ji ta kallon bakin get tana son ganin wanda zai shigo, baƙar mota ce sabuwa dal ta sanyo kai ciki Maigadi sai gaishe da na ciki yake, Andizo ta taɓe baki ta ce “Tab ji wata lukutar masifar, ana gaishe da mutum amma ko ya tsaya ya amsa, ashe da gaske abin da muke gani a télévision yana faruwa a zahiri.” Ta faɗa tana kurawa motar idanu.. Wata hamshaƙiyar mata ce ta fito daga cikin motar, Sultan ma ya fito daga ɗayan gefen ya sha wankan ƙanana kaya sai wani shan ƙamshi yake, Andizo ta saki baki tana faɗin “Ji ɗan wahala kamar na Allah, ita wannan ɗin ko wace ce ita? Ƙila ma matarsa ce mugun.” Ta faɗa tana gyara zama. Tun da ya fito daga mota yana ɗaga kai sama ya hango an buɗe tagar ɗakin da Andizo take, sosai ya yi mamakin hakan amma a fili bai nuna ba ya zagayo ya kama hannun matar suka yi ciki, Andizo na kallon su har suka shige sannan ta janye kanta ta ci gaba da zama a nan. Zaman da ta yi a haka iska na fifitawa sai ta ji damuwar da take ciki tana gushewa, lumshe idanu ta yi tana shaƙar iskar, ƙaran buɗe kofa ta ji amma ba ta ɗago ba bare ta ji tsoron ya zo ya same ta a haka.. Da fito ya shigo ya daddana wasu lambobi ya kulle Ƙofar, yana juyowa suka haɗa idanu ya tsaya yana kallon ta ganin ta a can sama jikin taga, bai ce mata komai ba ya zauna a bakin gado sai ga mai kawo abinci ta shigo hannayenta ɗauke da faranti, itama ta yi mamakin ganin Andizo ta ɗane taga, haka ta aje tana wani kwarkwarsa ta kalli Sultan da yake ta daddana waya. “Sir food is ready.” Ta faɗa tana ɗan ranƙwafowa ƙirjinta duka rabi a waje, kanta dama ba ɗankwali sai kitson gashin doki da aka mata suka zubo har gadon bayan ta. “OK thanks.” Iya abin da ya faɗa bai ɗago ba bare ma ya ga abin da take masa. Yadda ya share ta sai ranta ya ɓaci, yatsarta ta tsoma a cikin cup mai ɗauke da black tea ɗin da ta haɗa masa ta kwashi ƙara tana yarfa hannu. Sororo Andizo ta yi tana kallon ta duk abin da ta yi tana gani, jin ƙaran da ta yi ya yi saurin ɗagowa ya kalle ta, ganin kalar shigar da ta yi sai ya shagala da kallon ta abin da ya faranta mata rai.. Ita dai Dijan ku ta gargajiya na kallon Ikon Allah, ta kawar da kai tana faɗin “Itama ashe ƴar iska ce.” Bai ankara ba ya ji ta ta faɗo jikinsa, a zaton shi Andizo ce ya sa hannu ya rungume ta, Andizo ta juyo ta ga sun manne da juna ta ɗaura hannu biyu a ka. “Inna lillahi wa inna laihin raji'un! Ihu kwartaye za su yi iskanci, jama'a ku zo na kama su.” Ta faɗa da iya ƙarfin ta tana dirowa daga taga.. A ruɗe ya buɗe idanuwansa ya kalle ta, wani irin hankaɗa ta ya yi ta faɗi ƙasa tim nan take goshinta ya fashe sai jini, a zuciye ya zare bel ɗin jikinsa ya shiga lafta mata tana kurma ihu, Andizo ta sheƙe da dariya ta ce “Shegiya gobe ma kike zuwa kina ɗanewa jikin ƙato, babu abin da ya dame ni ya miki dukan mutuwa ni dai burina na bar gidan nan.” Sai da ya ga ba ta motsi sannan ya rabu da ita ya, jikin bangon ɗakin ya isa ya matsa wani abu sai ga maza biyu sun shigo, nuna musu ita ya yo ya ce “Ku fitar da ita daga part dina sai na neme ta.” To suka ce tare da ɗaukan ta suka fita waje, ba a jima ba wani matashin saurayi ya shigo ya gyara wajen da jini ya ɓata, kayan abincin ya nuna masa cikin bada umarni ya ce “A canza mana abinci.” Jiki na rawa ya ɗauke abincin ya je ya kawo musu wani ya fita shi kuma mayar da code ɗin kofar ya rufe.. Tashi ya yi ya zauna a kasan carpet ya kalle ta, murmushi ya sakar mata tare da miƙa mata hannu ya ce “come here my wife.” Kallon shi kawai take sai kuma ta sauko ta tsaya a naisa da shi ta ce “To alƙur'an in ka kuskura ka zage ni tsaf zan rama kar ka ga dan ina ƙarƙashin ka.” Lumshe idanu ya yi yana jin muryarta kamar ana masa busar sarewa, ta kurame ya dinga mata alamar ta zo ga abinci ya samu ta zo ta zauna. Ruwa ya zuba mata a cikin wata ƙaramar roba da aka tanada dan wanke hannu ta wanke, abincin ya buɗe dambun kuskus ne ya sha kayan ƙamshi ya sa cokali ya ɗiba ya nufi bakinta da shi, da sauri ta ja da baya tana ɓata rai ta ce “An faɗa maka ni jaririya ce da zan tsaya ƙato kamar kai kana ba ni abinci a baki?” Tashi ya yi ya ɗauko wani ɗan ƙaramin kwali ya dawo ya zauna, “My wife ki tsaya in ciyar da ke abincin nan za ki fi ci da yawa.” Ya faɗa yana ƙara kai mata baki ta kauce tana murguda masa baki.. “Kai ni fa ba ƙaramin aikina ba ne in maka ɓalle-ɓalle a mazaunai da reza sabuwa fil.” Dariya ta ba shi amma ya gyumtse ya shammace ta ya kamo hananyenta duka biyun, da hanzari ya fito da gam din da ya ɗauko ya manne mata hannayen da shi da kyau , ta juya ta kasa raba hannun ai kuwa ta fasa ihu ta fashe da kuka tana faɗin “Allah ya t..” Next Fage _Maman Nusaiba ce_ [5/23, 7:39 PM] Ummu Amjad: *Arewabooks@saratalkasum88* _LITTAFIN ANDIZO NA KUƊI NE N300 KU TURO KUƊIN KU TA WANNAN ACCOUNT ƊIN._ _Account number 0003187186_ _Name account, khadija Salisu_ _Name Bank, Ja'iz Bank_ _Sai a yi screen shot a turo ta wannan number_ _🥏+966577675904_ Shafi 17 Kasa ƙarasa maganar ta yi sakamakon abincin da ya zuba mata a baki, furzar da dambun ta yi har da haɗawa da kakarin amai ai kuwa ya wuce mata ta kwaru. Tari ta dinga yi ga shi ba damar ta tashi, shi ko yana zaune yana kallon ta ko motsi bai yi bare ya taimaka mata, idanuwan Andizo suka yi jajur tana nishi kamar kadangaruwa ta ce “Ru. Ruwa zan sha.” Murmushin mugunta ya yi ya ɗauki ruwan a riƙe, kallon shi ta yi a galabaice ta yi abin tausayi, gyara zama ya yi ya ce “In dai har kina son shan ruwan nan sai kin amince da abin da na zo miki da shi.” Ba tare da tunanin komai ba ta ce “Na amince in dai za ka ba ni ruwan.” Gyaɗa kai ya yi ya miƙa mata ruwan sai kuma ya janye yana dariya, ganin da gaske makasar ta yake nema ta yi kukan kura ta yi facali da farantin abincin ta kurma ihu ta yo kanshi, da ƙafa ya dinga kai masa duka tana faɗin “Dama ai so kake ka kashe ni shi ya sa ka rabo ni da dangina, to alƙur'an kafin ka kashe ni sai na gajiyar da kai ko mu mutu tare.” Ko motsi bai yi ba yana jin ta ta gama dukan shi iya son ranta ta nufi hanyar banɗaki fuu, da sauri ta shigi banɗaki ta yi dabara da kyar ta kunna kan fomfo. Sai da sha ta ƙoshi sannan ta ɗago tana mayar da numfashi, kallon ko'ina take tana mamakin wai a ce duk kyan wajen nan banɗaki ne, jikin bangon ta shafa ganin yadda yake da sulɓi abin ya birge ta, bakin bahon wanka ta ƙaraso ta tsaya. “Shi wannan ɗin ko me ake yi a cikin shi? Inda bari na taɓa naji ko yana da kyan jikin bango.” Ta faɗa tana durkusawa ta taɓa a hankali ta ji shima sulɓi gareshi, ai kuwa ta sa ƙafarta a ciki sai ta kusa aje wa sai ta cire ta yi dariya ta ce “Kut na je na saka a lula mini da ƙafata..” Sai da ta yi haka ya fi sau biyar sannan ta saka ƙafar ciki, jin babu komai ta kuma saka ɗayar ai kuwa ta kama murna tana juyi a ciki. Kan fomfo ta kalla da ya yi sama ya lankwaso ƙasa, baki ta riƙe ta ce “Tab ji kamar maciji.” Haƙori ta sa ta dinga cirar gam ɗin da ya ɗaure mata hannu har ta cira shi, kallon hannun ta yi ta ce “Wallahi sai na ɗauki fansa ko min daren daɗewa, duk abin da ka mini bashi kake ɗauka da ni kake zancan..” Wani waje ta matsa ai kuwa sai ji ta yi shaa ruwa ya shiga yi mata feshi, ƙara ta fasa ta yi sufa sai ga ta bakin banɗakin tana zare ido, ruwan ya ci gaba da zuba tana tsaye tana kallo. Ganin dai ruwan ba zai daina zuba ba ta matso cikin sanɗa kamar mai son kama wani abu, riƙe ƙugu ta yi da hannu ɗaya dayan hannun ta miƙa ta taro ruwa ai kuwa ta ji ya fi na farko sanyi, dariya ta yi ta miƙa duka hannun ta dinga tarar ruwan tana wanke fuska cike da nishaɗi.. Sai da ta jiƙa kayanta har suna ɗigar ruwa tukun ta janye hannu tana son ta kulle amma ba ta san wajen ba, ganin ba zai tsaya ba ta nufi kofar fita ta kama za ta buɗe ta ji kam ta kulle.. Tsoro ne ya kama ta ta ci gaba da girgiza ƙofar tana faɗin “Kai dan giya zo ka buɗe ni mana.” Duk abin da take yi yana kallon ta cctv da ke cikin banɗakin, ganin ta fara kuka sai ya tashi ya zo ya buɗe mata. Da gudu ta fito sai ji ta yi ta afka kan mutum. Da sauri ta yunƙura za ta tashi ya yi saurin riko ta ta koma, kawar kai ta yi tana hura hanci ta ce “Malam dallah can ni sake ni na tashi.” Ƙin sakin ta ya yi sai ma juyawa da ya yi ya kwantar da ita suna fuskantar juna, jin ya matse ta sai ta daina mutsu-mutsu ta yi shuru tare da ƙura wa beauty face ɗin sa ido, shima kallon ta yake yana sakar mata kyakkyawan murmushi. Sosai ta shagala ta kallon shi tana yaba kyan shi a zuciyarta har ba ta san ba san da ta ce “Ashe 'yan iska ma suna da kyau kamar mai hankali?” Kunnenta ya ja ta fasa ihu tana ɗora hannunta a kan nasa, raurau ta yi da idanu ta sa ɗayan hannun ta riƙe hunnunsa wanda ya riƙe kunnen ta ce “Don Allah karka cire mini kunne.” Sakar mata ya yi ta yi saurin tashi tsaye tana shafa kunnen, kallon ɗan ƙaramin bakinta yake yadda take murguɗa shi, wato ita ko me za a mata ba za ta daina rashin kunya ba. Ajiyar zuciya ya sauke ya miƙe tsaye jin ƙaran ringing wayarsa ya nufi ɗaki, sum-sum ta bi bayan shi tana ƙara ƙare masa kallo, yadda yake tafiyar sai abin ya birge ta ga shi tsayayyen namiji mai jini a jika, gashin kansa da ya daure da rubam ta kalla tana gyaɗa kai, gabaɗaya sai ya mata kama da mata.. “Alƙur'an ya yi kama da Allu Arjun ɗan India.” Ta faɗa ƙasa-ƙasa tana murmushi. Juyowa ya yi ya ga shi take kallo ya yi murmushi ya ɗauki wayar, yana ɗagawa ta ji ya ce “No no Mom karki shigo gani nan zan fito.” Ya faɗa da sauri. Kafin ya sauke wayar ya gano ta ɗaga caméra tana tunkaro ɗakin, da hanzari ya buɗe wardrobe ya ɗauko wata riga da wando jins baƙi rigar ja ya nufi ta. Ja da baya ta yi tana faɗin “Meye haka?” Bai kula ta ba ya kamo ta tana zillewa ya shiga ƙoƙarin cire mata doguwar rigar da ke jikinta, kunce suka shiga yi ta dage ba zai cire mata kaya ba shi kuma ganin tana ɓata masa lokaci ya saka ta tsakanin kafafuwansa ya matse ta ya ɗaga hannayenta sama ya cire rigar, a ruɗe ta kwalla ihu tana faɗin “Waiyo zai mini tsirara na shiga uku!” Ta faɗa tana zamewa a ƙoƙarin ta na son zama a ƙasa ganin daga pant sai wata ƴar karamar farar riga a jikinta. Shi dariya ma ta ba shi sai wani rufe jiki take, a ransa yana cewa _'Ka ji wannan kwailar yarinyar yo me zan gani a jikinki?'_ Ƙararrawa aka dinga dannowa amma ya yi kunnen uwar shegu ya ƙi buɗewa, sai da ya sa mata kayan ya kamo gashin kanta ya ƙara daure mata shi. Ita kuwa sai zagin shi take tana jero masa Allah ya isa, ta kuma ce sai ta rama duk abin da ya mata ya ce ya ji ta rama ɗin. Jinkin madubi ya kawo ta ya ce “Beauty kalli ki ga yadda kika yi kyau.” Har ta ɗago za ta masa rashin mutumci ta kalli yadda kayan ya mata kyau, shafa fuskarta ta yi ta juyo ta kalle shi ya sakar mata murmushi.. Ƙofar ɗakin ya nufa ya buɗe sai ga wata ƴar karamar yarinya mai shekaru 8 kyakkyawa mai kama da shi ta shigo da gudu tana faɗin “Daddy I miss you?” Ta faɗa jikinsa. Rungume ta ya yi yana shafa bayan ta ya ce “Miss you too my darling.” Andizo ta saki baki tana kallon yarinya kyakkyawa, har za ta yi magana ta ga wannan matar ta shigo waya kare a kunnenta karaf idanuwanta ya sauka a kanta. Sauke wayar ta yi ta shigo daret ta iso har gaban Andizo cike da mamakin ganin ta, kallon Sultan ta yi ta ce “Son wannan black beauty fa? Wa ya kawo ta?” Tashi ya yi tsaye ya ruƙo hannun yarsa ya samu waje ya zauna, sai da Mom ta sake tambayar shi ya daure fuska ya ce “Ita ce na aura.” “What? Ka yi me ka ce? Son kana cikin hankalinka kuwa? Wannan ɗin ƴar ƙaramar yarinyar kusan sa'ar ƴarka ce ka aura? Waye ya aura maka ita?” Maƙale kafaɗa ya yi irin ko a jikin shi kai tsaye ya ce “Kawai ni naje aka ɗaura mana aure, na ga kin takura mini tun da Hibbat ta mutu ba ku da magana sai ta in yi aure, to ni kuma ban samu wadda nake so ba sai yanzu kuma ita ce wannan wadda nake matuƙar so.” Ya faɗa yana kallon Mom.. Sake da baki Mom ke kallon Sultan, duk da halin shi na rashin kirki amma ba ta yi tsammanin zai iya zuwa wani waje a ɗaura masa aure ba tare da sun sani ba, kuma auren ma da ƙaramar yarinya wadda ko ciwon kanta ba ta sani ba bare ta san me ake nufi da auren kanshi. Salati ta dinga tana dafe ƙirji in ta kalli Sultan sai ta juyo ta kalli Andizo da take kifkifta idanu, zama ta yi a bakin gado ta kalli Andizo ta ce “Come here.” Alamar da ta mata da hannu ne ya sa Andizo ta gane cewa kiran ta take, a hankali ta tako ta iso gaban Mom ta tsaya, sai da Mom ta ƙare mata kallo sannan ta ce “Ya sunanki?” A sanyaye ta ce “Suna na Khadija na malami amma a ƙauyenmu ana ce mini Andizo, shin ke ɗin babarsa ce?” Murmushin yaƙe Mom ta yi ta ce “Yes ni Mom ɗin sa ce.” “To don Allah ki faɗa masa ya mayar da ni garinmu in da ya sa aka sato ni, yanzu haka nasan an manta da ni ma sai su ɗauka ko mutuwa na yi namun daji sun cinye namana.” Ta faɗa tana matso ƙwalla. Ƙara tafa hannu Mom ke yi tana kallon Sultan da yake daddana waya, kwafa ta yi ta ce “Ina ne garin naku? Ƙauyen Kano ko na Katsina ko Kaduna ko Jigawa a wani state kike?” “Ki ma daina ɓata bakinki Khadija ba 'yar Nigeria ba ce.” Ya faɗa yana kallon Mom. “Inna lillahi wa inna laihin raji'un! Sultan mu kake son tozartawa a idanun duniya? Yanzu har za ka iya tsallake wata ƙasa ka sato yarinya ƙarama da sunan kana son ta wai ma har an ɗaura muku aure? Ina ne ƙasarsu?” “Inna ni 'yar Niger ce garinmu yana wajen Niamey, don Allah karki barni a wajen nan mugu ne yanzu fa sai da ya cire mini riga ya sa mini wannan kayan na 'yan iska, to amma dai duk da haka na yi kyau. Ni dai so nake in ganni a gida.” Andizo ta faɗa tana shafa kayan jikinta.. Tashi tsaye Mom ta yi cikin tsananin fushi ta ce “Maza tashi mu je ka kaini wajen malamin da ya ɗaura muku aure, kai na ma fasa tashi maza ka ciro mini ticket guda biyu yanzun nan na mayar da ita ga ahalinta, ban da kai shashasha ne kawai dan kana son ta sai ka sato ta haka ka auri Muhibbat da ka fara son ta? Ba gidansu muka je aka nema maka auren ta ba? To ka tashi kafin raina ya ƙara ɓaci na la'ance ka tun da abin da ka fi so kenan..” Da sauri ya ɗago ya kalle ta jin abin da ta faɗa, fuskar tausayi ya yi ya matso kusa da su ya kalli Andizo da itama shi take kallo ya ce “Beauty ai kina so na za ki zauna da ni ko? Kinga ga Farrah nan sai kuke zuwa makaranta.” Ya faɗa yana haɗa hannunayensu.. Farrah ta kalli Andizo ta ce “Za ki zama friend ɗina?” Kallon yarinyar Andizo ta yi ta kama kumatunta tana murmushi ta ce “ 'Yar yarinya mai kumatu irin na ƴar lukuta, mene ne friend?” Dariya Farrah ta yi itama ta kama kumatun Andizo ta ce “Aboki ko ƙawa.” “To na gane, amma ni garinmu nake so a kaini sai dai in za ki dinga zuwa Niamey a can za a mini aure da mai hankali shirin Allah, za ki zo wajen bikina ai ko?” Murna Farrah ta hau yi tana dariya ta ce “E ina so zan je tare za mu tafi na ga gidanku.” Ganin surutun nasu ba na ƙarewa ba ne Mom ta kama hanayensu ta ce “Mu je waje maza ina nan zuwa, Khadija riƙe hannun Farrah ku zauna a palo ku jira ni..” Bayan sun fita Mom ta tsatsara Sultan ta ce “Lokacin da aka ɗaura muku aure waye waliyin ka waye kuma waliyin ta? Sannan su waye shedun an ɗaura auren?” Hannu ya sa a aljihu yana murmushi tare da shafa kwantaccan sajensa ya ce “Mom Nazee ne fa ya ɗaura mana auren, kawai kuɗi na ba shi na ce ya ɗaura mana aure, sai ya ce sai an sayo halawa da goro kuma ya ji ana karanta fahita in za a ɗaura aure..” Ajiyar zuciya Mom ta sauke jin ba cikakken ɗaurin aure aka yi ba, kuma daɗin daɗawa ma Allah ya rufi asiri bai haƙe wa yarinyar mutane ba, kallon shi ta yi ta ce “wato saboda tsabar jahilci babu abin da ka sani game da addini sai Fatiha ko? Ka kyauta shi uban naka da ya ɗaura ka a kan wannan muguwar hanyar daga kai har shi sai kun yi kuka matuƙar ba ku canja hali ba banza kawai shashasha fi ce mu je ka sa a cire mana ticket ɗin, sannan ka haɗa mu da waɗanda suka sato maka ita su kai mu har garin su..” Baki ya buɗe zai yi magana ta daka mishi tsawa “Ba na son ka ce komai kawai ka yi abin da na ce maka!” Ba dan ya so ba ya hadiye maganar da yake son yi ya yi gaba ta bi shia baya.. Suna fitowa Mom ta kama hannunsu suka fito, a harabar gidan ta tsaya ta kalle su fuska daure ta ce “Kabir cikin ku su waye suka kawo yarinyar nan?” Sai da ya kalli Sultan Mom ta daka musu tsawa ya ce “Hajiya mu ai a airport muka amso ta a wajen wasu da suka kawo ta.” Tsaki ta ja ta sa su Andizo a mota itama ta shiga, direba na shirin shigowa ta dakatar da shi ta ce Sultan ya zo ya yi draving da kanshi, haka ya shiga jikinsa a sayayye.. Kafin su isa gidan Mom Sultan ya sa aka tanadar musu da ticket uku saboda Farrah ta kafe ta ce sai ta ga garin su Andizo tun da ta zama ƙawarta. Washe gari jirgin su Andizo ya ɗaga zuwa ƙasar Niamey, saboda murnar da take har rungume Mom ta yi tana mata godiya na fito da ita da ta yi daga wannan baƙin gidan za ta kai ta ahalinta... Ƙarfe 10:50am jirgin su ya sauka a Niamey, sosai ta dinga kalle-kalle har suka shiga mota, direban da ya dauke su can ya kaisu wata unguwa in da ya haɗa Mom da wasu matasa uku ya sanar da su Oga Sultan ne ya ce su mayar da yarinyar har cikin garinsu. Babu muso suka amsa da To.. Kasancewar sun gaji wani gida suka kai su suka huta suka ci abinci, Farrah sai cewa take “Khady ina gidanku yake wai.” Ita kuwa tana dariya ta ce “Ba nan ba ne mun kusa.” Sai da aka yi Sallar Azuhar sannan suka fito daga gidan, buɗe musu mota suka yi suka shiga suka wuce.. Da sauri ya fito daga motar yana kallon Ahmad ya ce “Ahmad Wallahi naji a jikina a cikin motar can akwai Khadijata, don Allah zo mu bi bayan su mu gani.” Girgiza kai Ahmad ya yi ya ce “Anya ba ka samu taɓin hankali ba Yaya Salim? Ta ya kawai daga ganin mota sai ka ce da Khadija a ciki? Ka ga shiga mu je gida..” Ba dan ransa ya so ba ya shiga motar Ahmad ya ce ya koma gefe shi zai ja su kar ya je ya kifar da su.... Next Fage. _Maman Nusaiba ce_ [5/24, 5:07 PM] Ummu Amjad: *_Arewabooks @saratalkasum88_* Littafin ANDIZO na kuɗi ne N300 ne, za ku turo kuɗinku ta wannan account ɗin. Account number 0003187186 Name account, khadija Salisu Name Bank, Ja'iz Bank. Sai a yi screen shot a turo ta wannan number. 🥏+966577675904. 18 Sai da suka tsaya suka sha mai sannan suka ci gaba da tafiya, Andizo da Farrah sai surutu suke Mom dai na kallon su, ita Andizo tana faɗa mata yadda suke yi a garinsu ita kuma Farrah na faɗa mata irin wajen shaƙatawa da Sultan kai ta da kuma sunan school ɗin da aka saka ta.. Sun yi nisa sosai da tafiya hanyar sai ta rabe musu gida biyu suka rasa wacce ce suka bi farkon zuwan su, ganin sun tsaya Mom ta kalli direban ta ce “Ya dai na ga kun tsaya?” Ɗaya daga cikin su ne ya ba ta amsa, “Mama hanyar ce ta rabe mana gida biyu mun rasa wacce ce muka bi a farkon zuwan mu..” Shuru Mom ta yi ta kalli Andizo da ko a kanta sai hira suke, kiran sunan ta yi ta ɗago kai ta kalli Mom tana sakar mata murmushi, ruƙo hannunta ta yi cikin nuna kulawa ta ce “Khadija shin ko za ki gane daga nan wacce hanya za ta kaimu cikin ƙauyenku?” Kallon gefe ta yi amma duhun glass ɗin motar ya hana ta ganin abin da yake waje ta ce “Mom to sai dai in ku buɗe mini na fita na gani ko zan iya ganewa.” Umarni Mom ta ba su suka buɗe motar, sai da Mom ta fita ta buɗe mata daga bayan ta fito Farrah na biye da ita. Kallon wajen ta dinga yi ko za ta gane sai dai ta ga wajen ba ta taɓa zuwa ba, a sanyaye ta kalli Mom ta ce “Mom gaskiya ni ban san ba wannan wajen, dama ban taɓa zuwa Niamey ba ina dai jin sunan ta.” Ganin lokaci na ƙure musu ɗaya daga cikin su ya danna wa Sultan kira. Lokacin Sultan na wajen motsa jiki ya yi shakaf da zuba, yana shirin fita ya ji wayarsa na ringing ya juyo ya ɗauka, ganin mai kiran ya yi saurin ɗagawa ya kara a kunne bai ce komai ba. “Hello Oga mun fa kasa gane kan hanyar ta rabe mana guda biyu, wacce za mu bi?” Lumshe idanuwansa ya yi wanda suke cike da bacci, gabaɗaya daren jiya bai yi bacci ba saboda abin da Mom ta masa na raba shi da matarsa a cewar shi, dafe saitin zuciyarsa ya yana hasko yadda take masa rashin kunya da lokacin da take saka shi dariya. Buɗe ido ya yi jin yana hello Oga, ajiyar zuciya ya sauke yana son yin magana amma ya kasa kawai ya saki wayar ta silalo ƙasa.. “Hello! Hello! Oga are you OK?” Yake faɗa amma ya ji shuru. Mom na cikin mota saboda iskar da ke kaɗawa da ɗan zafi shi ya sa ba ta san me ke faruwa a waje ba. Kashe kiran ya yi ya sake kiran shi take ya ɗauka, “Oga.” “Na'am.” Ya amsa yana saita nutsuwar shi, fita ya yi daga wajen motsa jikin ya nufi ɗakinsa yana faɗin “To kai kana ɗan wajen garin ai abin kunya ne ma a ce ba ka san hanya ba.” “Ba haka ba ne Oga, ni gaskiya ban taɓa zuwa wannan ƙauyen ba duk da a jaharmu yake.” Jinjina kai ya yi ya ce “Hanyar da ta bi hannun dama ita za ki, amma kafin nan kira Khadija ka ba ta wayar ina son magana da ita.” To ya ce ya ƙaraso wajen Khadija da ta yi ture ka ga tsiya ya miƙa mata wayar ya ce “Oga ne zai yi magana da ke.” A wulaƙance ta kalli hannnunsa sai kuma ta tuna ta ji suna cewa Sultan Oga. Da hanzari ta amsa, tsoron ta ɗaya kar ya canja ra'ayi su kuma mayar da ita wannan gidan da take fatan ko a mafarki ba ta son ganin shi. “Hello wai ka ce a ba ni waya? To gani me zan ba ka? Ni dai don Allah karka sa su kuma sace ni ina jiyo ƙamshin garinmu.” Ta faɗa tana sakin kuka marar sauti, saboda kewar su Hajja da ke addabar ta musamman da ta ji suna cewa sun kusa zuwa garin nasu sai ta ji zuciyarta ta karaya, ta ƙagara ta ga su Hamma da su Saminu abin kaunar ta.. Runtse idanu ya yi yana jin kukan ta har ƙasan zuciyarsa, in tana masa kuka gabaɗaya tayar masa da hankali take ya ji duk wani kuzarinsa na yin ƙasa. Cikin muryar rarrashi ya ce “Haba my wife ki daina kukan nan kin ji, kuma ba zan ƙara sace ki ba Mom ta ce da kanki za ki so zuwa ba sai na sato ki ba. Idan kuka je kar ki ce wa su Maigari komai kawai ki ce Mom ta tsince ki kin ji ki mini alfarmar.” Shuru ta yi tana jin saukar maganarsa mai haɗe da fitar numfashi a kunnenta har ya gama, har ta soma hura hanci za ta masa diɓar albarka ta tuna gara dai ta lallaɓa kar ya ƙara sace ta, cikin sanyin muryar da ita kanta ba ta san tana da ita ba ta ce “To ba zan ce komai ba, amma don Allah ni dai ba na son na sake ganin ka.” Ta faɗa tana murguɗa baki kamar tana gaban shi. Saurin janye wayar ya yi yana jin zuciyarsa na bugawa, sake mayarwa ya yi ya ce “Khadija ni kike cewa ba ki son ki sake gani na? Ni ne fa.” Hararar wayar ta yi sai kuma ta rufe baki tana kallon Mom da ke danna waya daga cikin mota, a hankali ta matsa daga inda take ta koma jikin bishiya ta duƙa. Murya ƙasa-ƙasa ta ce “Kai wai meye ma my wife ɗin nan da kake faɗa mini? Sannan ni ba suna na Beauty ba Khadija nake ko ka ce Andizo jikar Hajja ko ka ce Dijan mai hankali shirin Allah, kai ko uwar masu gari ka ce daidai ne saura na kuma ji ka ce mini Beauty kamar wata ƴar tagwaye.” Murmushi ne ya suɓce mishi har tana jiyo sautin shi, wani sanyi ya ji na ratsa shi zafin da ke addabar zuciyarsa na sauka, jin ta soma halin nata ya yi saurin faɗin “Ni dai ki mini alƙawari ko kin je babu ke babu wani saurayi, dama ina so na faɗa miki zan tafi Germany za mu buga wasa a can nan da sati ɗaya, daga can ma za mu yi gaba ina so ki tsare mini kanki karki bari kowa ya ce yana sonki, da zarar na dawo kawai bikinmu za a yi kinga ke mata ta ce. Na so na ɗauke ki mu tafi to Mom ta mini katanga da ke, ina sonki Khadija..” Ya faɗa cikin wani kalar yanayi mai narkar da zuciyar wanda aka furtawa. Da yake ita ba ta shi take ba tsaki ta ja ta ce “To sai me dan za ka tafi Germany? Ni fa na faɗa maka ba na son ma sake haɗuwa da kai, ka ce darajar ƙanwarka Farrah ita ƙawata ce in ba dan haka ba alƙur'an da sai na ɗan iskan duka kafin mu taho, ko kuma na sa Hammana ya buge mini kai da laggyar.” Ɗaiɗai ya yi a kan gado yana sauraron ta har ta dasa aya, buɗe idanuwansa ya yi ya janyo pilow ya rungume ya ce “Khadija ni kike cewa za ki a a buge ni?” A fusace ta ce “Yo kai ɗin a kayan miya mene ne?” Lura da in suka tsaya dare zai musu ya ce ta ba shi wayar ta miƙa masa tana kumbura baki, kallon ta Farrah ta yi ta ce “Waye kike magana da shi.” Kama hannunta ta yi suka nufi mota ba ta ce mata komai ba. Mom ta kalli Andizo ta ce “Khadija lafiya na ga kin ɓata rai?” “To ba shi ba ne yake mini daɗin baki, so yake ya sake sace ni.” Girgiza kai Mom ta yi suka ci gaba da tafiya.. Sai bayan La'asar suka iso garin lokacin Andizo na bacci ita da Farrah, da tambaya suka nufi gidan Maigari duk da Sultan ya musu bayanin koma amma ya ce su tambaya in sun shigo gari. Su Maigari suna zaune suka ga mota ta paka duk suka kalli motar, juyowa Mom ta yi ta tashi Andizo, buɗe ido ta yi ta kalli waje ai kuwa ta ga Maigari a zaune wani irin zabura ta yi tana dariya ta tashi Farrah ta ce “Tashi ƙawata ki ga garinmu kinga ga Babana can waiyo daɗi ku buɗe mini na fito.” Ganin yadda take murna sai ta ba wa Mom tausayi, buɗe wa Mom aka yi ta fito sannan suma ya zagaya ya buɗe musu, da mugun sauri ta fito ta kwasa a guje har tana faduwa ta nufi su Maigari sai kiran shi take da ƙarfi, “Maigari!Maigari!” Tashi tsaye Maigari ya yi yana kallon yarinyar da take tunkaro shi, sai da ta zo kusa ya ga Andizo ce ya saki baki yana kallon ta har ta iso ta rungume shi ta fashe da kuka.. Kowa na wajen sai hamdala yake, Maigari ya zauna ya janyo Andizo yana shafa jikinta kamar ya yi kuka ya ce “Uwata ina kika shiga mun yi neman ki har mun gaji mun zuba wa sarautar Allah ido.” Share hawaye ta yi ta ɗago ta kalli Mom da suka tsaya a ɗan naisa da su suna kallon su, har za ta faɗi inda aka kaita sai ta tuna da maganar Sultan ta yi saurin faɗin “Maigari waccan mata ta cece ni ta kawo ni gida ita da ɗiyarta.” Tashi Maigari ya yi ya kama hannun Andizo suka yo wajen su Mom, sannu da zuwa ya musu sannan ya musu jagora suka nufi ciki.. Suna isa bakin ƙofar gida Andizo ta kwace hannunta daga cikin na Maigari ta nufi gidan da gudu tana kiran su ɗaya bayan ɗaya.. Da sauri Hajja da Inna suka fito jin muryarta, tana dariya ta ƙaraso ta haɗa su ta rungume. Hamdala suka dinga yi Hajja ta ce “Uwar masu gari Allah ya kwace ki daga hannun azzalumai.” Dariya ta yi ta sake su ta ce “Wallahi fa Hajja kin ga da su Mom muke tare ga su nan a baya, amma ina su Hammana suke?” Sannu da zuwa Inna ke yi wa Mom ta ɗauko tabarma ta shinfida musu. Nan da nan gari ya ɗauka Andizo ta dawo ai kuwa yara suka dinga rige-rigen zuwa ganin ta, duk wanda ya zo sai ya ce ai Andizo ta zama mai kyau, ita kuwa sai murna take tana ba su hannu suna tafawa wasu har shafa jikinta suke wai jikinta ya yi laushi.. Ita dai Mom sai kallon Andizo take sai yanzu ta ji hankalinta ya kwanta da ta dawo da ita ga ahalinta.. Hayaniyarsu ce ta fito da su Giɗaɗo, yana isowa ya hango ta a tsakiyar yara tana ta murna, cike da wani kalar zallar farin ciki ya ce “Surbajon Hamma.” Juyowa ta yi suka haɗa ido ta nufo shi tana faɗin “Hammana gani na dawo gida na yi kewar ka sosai.” Ɗaukar ta ya yi yana juyi da ita sai dariya take shima ya yi, sai da Hajja ta musu magana sannan ya sauke ta ta nufo Umar duk ta rungume su suna ta farin cikin ganin ta.. Sai da aka dama wa Mom fura da nono aka kawo mata ruwa mai sanyi a cikin kofin sulba ta ɗan sha, ita kuwa Farrah sai ta ta ji ta ƙoshi sannan ta bari tana faɗin “Mom furar nan akwai daɗi.” Dariya Andizo ta yi ta ce “Yarinya haka muke yin ta.” Maigari ya ce “Gaskiya mun yi matuƙar farin ciki da kika ceci rayuwar yarinyar nan, Allah ya saka da alkhairi ba mu da abin da za mu biya ki sai dai mu yi miki addu'a. Uwar masu gari wai su waye suka sace ki?” Miƙe ƙafa ta yi ta ce “Nima ban san ko su waye ba kawai sai ji na yi an shaƙa mini wani abu daga nan ban sake sanin komai ba sai ganina na yi a wani gida ina tambayar mai aikin kawo mini abinci ta ce wai a Abuja Nigeria nake, to ina nan a tsare kawai sai ga Allah ya kawo Mom ta zo ta ceci rayuwata, shi ne ta dawo da ni gida..” Sake da baki Mom ke kallon Andizo, sosai ta yi mamaki kuma ta ji daɗi da ba ta ce Sultan ne ya sace ta ba. “Gaskiya Hajiya mun gode yanzu tun daga Abuja ta Nigeria kika zo har ƙauyen nan duk dan ki sada Surbajo da ahalinta? Wata ɗaya da rabi kenan da sace ta, Muna godiya sosai.” Cewar Giɗaɗo yana riƙe hannun Andizo.. Murmushi Mom ta yi ta ce “Babu komai ai ɗa na kowa ne, to mu za mu koma kar dare ya mana.” “Haba hajiya ai da kin tsaya kin kwana, yanzu yaushe za ku je Niamey sannan ku wuce Nigeria?” Cewar Umar. Girgiza kai Mom ta yi ta ce “Karku damu babu komai ai muna da masu tsaron mu, ga wannan kayan Khadija ne na rubuta mata number wayata tana ciki, idan mun je gida za suke gaisawa da Farrah.” Ta faɗa tana tashi ta kama hannun Farrah.. Godiya sosai suka mata, Maigari ya sa aka debo mata kwai aka kai musu bakin mota, Andizo na riƙe da hannun Farrah yara kuma na bin su a baya suna kallon su.. Da kyar Farrah ta saki hannun Andizo sai da Giɗaɗo ya matso ya ce mata wata rana zai kai Andizo har gidansu ta musu kwanaki, da haka aka shayo kanta ta sake ta suna shige mota Andizo na ɗaga musu hannu har suka ɓace wa ganin ta.. Bayan ta koma gida har za ta zauna ta tuna Hajaru, da sauri ta juya ta kalli Hajja ta ce “Hajja wai ina Hajaru take.” “Hajaru sun tafi wajen biki jiya yau za su dawo, ba ki ga yadda ta damu ba na rashin ki.” Cewar Hajja. Dawowa ta yi ta zauna ta rafka tagumi ta ce “Allah sarki Hajaru Allah ya dawo da ku lafiya.” Ta so ta tambayi ina Ahmad sai kuma ta fasa ta tashi ta fita suka shiga gari... Washe gari Maigari da kanshi ya kira Salim ya sanar da shi ai wasu mutane sun dawo da Andizo, sosai Salim ya nuna farin cikin shi ranar ko aiki bai tsaya ya yi ba ya dawo gida cikin ɗoki ya nufi part din Mamma da Sallama. Amsa mishi suka yi Mamma ta kalle shi tana faɗin “Da alama wani abu mai daɗi ya faru tun da na ga yau ka yi fara'a.” “Mamma an ga Khadija yanzu haka tana gida.” Da sauri Ahmad ya ce “Da gaske?” “Kwarai ma kuwa Maigari ya kira ni ɗazu ya ce wata mata ce tun daga Abuja ta ceci rayuwarta ta dawo da ita har gida jiya, ba na ce maka naji kamar Khadija ta kusanto ni ba kaƙi yarda da magana ta, to ga shi dai ta tabbata an ganta.” Ya faɗa yana faɗaɗa murmushin sa. Hamdala suka yi gabaɗaya, Hajiya Babba ta ce “To yanzu ni abin da nake son a yi, kun ga azumi ya kusa zuwa kawai a je a ɗaura auren nan a kawo ta gidan nan ko mun huta da yawan kiran ta da yake, ni ban taɓa ganin soyayya irin taka ba Salimu.” Wani sanyi ne ya ziyarci zuciyar Salim ya miƙe tsaye ya iso gaban ta yana ƴar dariya ya ce “To Hajiya ai sai ki sanar da su Abie ni gobe za mu tafi ni da Ahmad da Abdoul mu gano ta.” Mamma dai na kallon ɗan nata tana murmushi, sosai ta ji daɗin samun Khadija ko ba komai ɗanta zai samu nutsuwa.. Sai da ya jima suna ta tattaunawa a kan lefan da aka haɗa, sai tambaya yake ko akwai abin da ba a saya ba? Mamma ta ce “A'a mun sayi komai tashi je ka abin ka..” To ya ce ya tashi ya nufi part ɗinsa, shima Ahmad part ɗin su Abie ya nufa dan ya, sanar musu ganin Khadija.. Yana shiga ta tarbe shi da murna ta sha kwalliya, ganin yadda fuskar shi take dauke da fara'a sai, abin ya ba ta mamaki amma ta kawar ta ɗauko masa ruwa, sai da ya sha ya ruwan sannan ta dube shi ta ce “Mijina wannan fara'ar fa?” Hannayenta ya ruƙo ya ce “Alhamdu Lillah Khadija ta dawo gida jiya..” Wata irin zabura ta yi tana dafe ƙirji ta ce “Me ka ce? Da gaske ko wasa kake mini Salim?” Ganin yadda ta ruɗe ya kamo ta ya zaunar ya ce “Ya aka yi kika ruɗe? “To ba dole na ruɗe ba na yi farin ciki amaryarmu ta baiyana, kai gaskiya na yi matuƙar farin ciki da wannan albishir yanzu yaushe za ka kaini na gano ta?” Dariya ya yi yana girgiza kai ya ce “Ki bari dai a kawo miki ita tukun, gobe za mu je ni da Ahmad da Abdoul. Gaskiya ina ƙara gode wa Allah da ya ba ni ke a matsayin matata, Allah ya miki albarka yadda kike son abin da nake so na gode sosai Ma famme.” Murmushi ta yi ta miƙe ta kawo masa abinci ta ce “Bari naje na haɗa ma ruwan wanka kafin ka gama.” To ya ce mata sannan ta wuce ɗakinta da mugun sauri. Tana shiga kulle kofar ta haye kan gado ta zare wayarta da ke jikin caji ta danna wa Sabrin kira, tana ɗaura kafin ma ta ce wani abu ta ce “Hello Sabrin akwai matsala babba na tunkaro ni,wai kina ji yarinyar nan da na sa aka mata kurciya wai jiya ta dawo..” Sai da Sabrin ta yi ashar ta fi goma sannan ta ce “To amma ya aka yi haka ta faru? Ko dai kuɗin da muka kai masa ya yi kaɗan ne? Kinga maza-maza ki tanadi kuɗi gobe zan kaiki gidan wani boka aikinsa sha yanzu magani yanzu, ke har maganar haihuwar sai mu masa ki riga ta samun ciki..” Ajiyar zuciya ta sauke tana share hawaye ta ce “Ina jin zuciyata kamar za ta fashe Sabrin, amma dai ya ci amanar mu tun da har ya bari ta dawo gida, gobe za su tafi ki zo mu tafi ki kaini so nake wannan karon a kashe ta kowa ma ya huta..” Tana faɗin haka ta katse kiran ta miƙe tsaye tana zagaye ɗakin, gabaɗaya baƙin kishi ya rufe mata idanu sai tsine wa Andizo take tana shan alwashin daga gobe ta gama numfashi a duniya sai ta ga ta yadda za a kawo mata ita a matsayin kishiya... Next Fage _Maman Nusaiba ce_ [5/25, 1:36 PM] Ummu Amjad: *Arewabooks@saratalkasum88* *🥏+966577675904* 19 Washegari tun ƙarfe shida da rabi Salim ya gama shiryawa ya zauna zaman jiran Ahmad da Adoul, da am jima sai ya kalli agogo ya ja tsaki ji yake kamar ya yi fiffike ya ganshi a gaban sahibarsa. Sai da ƙarfe bakwai ta buga ya miƙe zai fita sai ga Aminatou ta fito, kallon shi ta yi cike da mamaki ta ce “Mon chéri ya kuma na ga ba ku tafi ba? Ai ni na ɗauka yanzu kun yi nisa da gari.” Tsaki ya ja yana sa hannu a aljihu bai ce mata komai ba, kallon shi take tana jin zuciyarta na ƙara tunzura ta a kan abin da take son aikatawa, kishin mijinta take na gaban kwatance. Lumshe idanu ta yi ta buɗe shi a kansa tana yaba kanshi, wankan da ya ɗauka ya matuƙar ƙara mata kishin sa a zuciyarsa. Ya sha ƙanana kaya t-shirt orange da baƙin wando kayan sun matuƙar ƙara fito da ainahin kyawunsa, hannnunsa tsadaddan agogo ne baƙi haka ma takalmin ƙafarsa baƙi ne, sumar kansa ya taje ta yo baya sai sheƙi take. Wani kalar fitinannan ƙamshi yake tashi a jikinsa, sai hura hanci yake saboda ɓata masa lokaci da suka yi.. A hankali ta ƙara matsowa gaban shi ta kai hannu ta shafo kwantaccan sajensa mai ƙara wa fuskarsa kyau, kallon ta ya yi cikin idanu ya sa hannu ya tallafo ta ganin tana son yi wa kanta masauki a jikinsa. “Ma famme ya aka yi? Ko akwai abin da kike buƙata?” Ya faɗa yana raba ta da jikinsa. Kasa ba shi amsa ta yi in ba dan tana son fita ba da ba za ta bari ya yi tafiyar nan ba, buɗe idanuwanta ta yi ta danne duk wani son zama a jikinsa ta wayance da cewa “Ba komai kawai naji kana wani ƙamshi na musamman ne, ba na so wata ta yaba wankan mijinmu.” Ta faɗa tana jan hancinsa.. Murmushi ya sakar mata cikin jin daɗin kalamanta ya ce “Haba ai kema kin sani ku biyu kun isheni, daga Khadija na rufe ƙofa, wannan ƙamshin da kika ji sabon turare ne na sayo jiya shi ne na saka, kinga naji oda a waje bari na je ko sun zo gabaɗaya sai mun dawo..” Ya faɗa yana fita daga palon. Bin bayan shi ta yi da kallo wani abu ya tsaya mata a maƙoshi, sosai ta ji haushin saka turaren da ya yi dan zai je wajen wata kucakar budurwarsa, kwafa ta yi ta zauna zaman jiran Sabrin.. A bakin mota ya same su suna jiran fitowar shi, Ahmad ya yi murmushi ya ce “Angon Andizo ba gaba da gaba ba ko da ta baya sai dai mutum ya zo da zamba dan Gyatumarsa, kai ka ji wani kalar ƙamshi da kake na musamman kamar an tsamo ka daga inda ake sarrafa turare? Dama nasan wannan wankan sai amarya ita kaɗai za ta kalla ta yaba a ji daɗi.” Ya ƙarashe maganar yana kallon ƙofar part ɗin Salim ganin Aminatou na tsaye tana kallon su, murmushi ya saki yana mata kallon ko da magana ne? Kwafa ta yi tana aiko masa da saƙon harara ta yi baya ta koma ciki zuciyarta kamar ta buga, ta rasa yadda za ta yi da Ahmad a gidan nan, shi ba shi da buri illa ya baƙanta mata zuciya kawai dan ba ya sonta da yayansa. A fusace ta fito ta shiga mota ba wanda ankare da ita sai ƙaran tashin motar suka ji duk suka juya suna kallon ta har ta fita.. Murmushi Ahmad ya yi ya kalli Salim ya ce “Yaya ina kuma matarka za ta tafi da safiyar nan? Kuma na ga kamar ranta a ɓace yake.” Girgiza kai Salim ya yi ya ce “E ta ce gidansu za ta je ta wuni tun da ba na gida yau, amma ba ta ce yanzu za ta fita ba sai wajen goma muka yi da ita, ina ga ko dai 'yan'uwanta sun fara zuwa ne aka soma kiran ta shi ya sa ta fita, ku shiga mu tafi ko ma meye in na dawo zan ji daga bakinta.” Ya faɗa yana shiga mazaunin direba.. Dariya Abdoul ya yi ya kamo shi ya fito da shi yana faɗin “A'a rufa mana asiri angon Nana Khadija kar ka je ta ce kana warin man mota kasan hali dai tsaf za ta faɗi..” Dariya shima ya yi yana hasko yadda za ta tare shi da murnar ta ta kira shi da mai hankali shirin Allah, babu abin da ya fi birge shi game da ita musamman irin yadda take yabon shi, lumshe idanu ya yi lokacin da ya ji sun fita daga gidan yana jin wani matsanancin fari ciki ba ƙara mamaye zuciyarsa. Maganganunsu na baya yake tunawa, ya yi missing rashin kunyar ta da ɗan ƙaramin bakinta wanda a kullum yake shan baƙin kwalli da mai ya yi ta maiƙo, idanuwanta farare tas masu narkar da zuciyarsa yana son ya yi ta kallon su tana masa fari da su musamman in tana sanar da shi lefin Ahmad, da yadda take riƙe ƙugu in za ta yi masa rashin kunya. Ajiyar zuciya ya sauke Abdoul ya taɓa shi yana dariya ya ce “Angon Dije wai duk tunanin ta ne ya hana ka cewa komai?” 'Yar dariya ya yi yana shafa ƙirjinsa irin farin ciki ya masa over ɗin nan ya ce “Ai Khadija ta musamman ce a zuciyata Abdoul, ba za ku gane hakan ba ko na faɗa saboda kun ganta ƙarama, ni kuma duk duniya ban ga wadda ta kai ta kwarjini da samun matsayi a zuciyata ba, ni kaina mamakin kaina nake yadda soyayyar ta take hana ni sukoni har na kasa gane komai lokacin da ta ɓata. Iya gaskiya ta nake faɗa muku ina son Khadija son da ban taɓa yi wa wata 'ya mace ba.” Dariya Ahmad ya yi ya ce “Gaskiya ka zauce a kan ɗalibar nan tawa, ya kamata kake gyara kalaman ka kar wata rana ka faɗa a gaban Aminatou ka haɗa fitina a gidanka nan gaba.” Ya faɗa yana kuma yin dariya saboda ya ji daɗin maganar. “Allah ya kiyaye, ai in sha Allah ba zan taɓa faɗa a gaban Aminatou ba, ko mutuwa ai tana tsoron ido ballantana Aminatou da ta nuna mini so da ƙauna, duk da dai ba ni naje na ce ina son ta ba ita ta kawo kanta ta ji matuƙar daɗi ranar da ta tare ni ta ce mini tana so na kuma so na aure, to don Allah me ya fi wannan daɗi a ɗaga baki a ce ana sonka?” Cewar Salim. “Gaskiya babu abokina, duk wanda zai ce yana sonka ai ba abin yadawa ba ne ka riƙe shi hannu bibbiyu.” Abdoul ya faɗa yana kallon hanya. Jinjina kai Ahmad ya yi yana wani yatsine fuskar dan shi gani yake ba tsari mace ta tunkari namiji ta ce tana son shi su yi aure, ya fi ganewa namiji ya je ga mace ya fara furta mata kalmar soyayya ya nemi su yi aure. Gyara zama ya yi ya ce “Ni kuwa a tsarina na fi gane dai namiji ya ce yana son mace.”. Tsaki Abdoul ya yi ya ce “Kai dama wa yake sa taka da ba ka da alƙibila, to Nana Khadija matar Manzon Allah (S. A. W) ita ta ce tana son shi, hamshakiyar ƴar kasuwa ce mai arziki amma da ta ji tana son ɗan gatan Allah ta ce a faɗa masa tana son shi, a lokacin ta girme shi nesa ba kusa a shekaru, shi yana matashi ɗan shekara 25 kuma ya aure ta. To meye aibu a ciki dan mace ta ce tana son ka? Ba haramun ba ne.” “Haka ne, amma ka sani 'yan matan yanzu sai sun samu mai kuɗi su dinga bibiyar shi suna cewa son shi suke, wasu fa ba son tsakani da Allah suke yi ba soyayyar ta dan yana da kuɗi ce.” Ya faɗa yana hura hanci kamar an masa lefi.. “Haka ne Ahmad, amma dai ai duk lalacewa ba za a rasa ta gari ba, kuma nasan Aminatou na ɗaya daga cikin mataye na gari waɗanda suke son mutum da zuciya ɗaya, in da dan kuɗi ta so Salim da tuni ya gano hakan ai.” Bai sake ba cewa komai ya soma danna wayarsa, jin ya yi shuru suma duk suka rabu da shi dan sun san shegen taurin kai irin na Ahmad a kan ra'ayinsa... Girki Maigari ya sa a yi na tarbar su Salim, Andizo sai murna take yau za ta ga mai hankali ta ba shi labarin abubuwan da ta gani. Ruwa ta ɗumama ta shiga wanka ta dirje jikinta tas da soso da sabulun da Mom ta sako mata a cikin kaya. Sabulun yana da ƙamshi sosai har lumshe idanu take tana shaƙa, buɗe ido ta yi ta tuna irin wannan ƙamshin sabulun ai a jikin Sultan ta ji shi, tsaki ta yi ta ci gaba da wanka tana cewa “Yo to ni ina ruwana ma ba Mom ta ba ni ba?” Tana fitowa ta shige ɗaki inda Hajaru ke jiran ta, suna ganin juna suka fasa ihun murna suka rungume juna cike da farin ciki, Andizo ta ce “Jiya na zo nake ta neman ki aka ce kun tafi biki.” Kallon ta Hajaru ke yi tana shafa jikinta ta ce “Ƙawata kin ga kuwa yadda jikinki ya yi kyau? Kai amma dai waɗanda suka sace ki abincin 'yan gayu suke ba ki?” Dariya Andizo ta yi ta shige lungun tsakanin gado da kayansu ta saka riga da siket ɗaya daga cikin kayan da Mom ta zubo mata, fitowa ta yi ta ce “Na yi kyau kuwa?” “Kai Alƙur'an ƙawata kin zama ƴar birni.” Hajaru ta faɗa tana taɓa kayan. Ledar ta janyo ta buɗe ta ce “To kema zaɓi guda ki saka ki raka ni in su mai hankali sun zo.” Ba muso ta ɗauki wata doguwar rigar abaya da mayafinta, sakawa ta yi ta ɗaura ɗankwali Andizo ta yi dariya ta ce “Alƙur'an kin ba da kala Hajaru.” Murmushi ta yi tana shafa kayan ta ce “Na gode ƙawata.. Su Salim na isowa ƙauyen aka kai su masauki, sai kallon ƙofa yake dan ya ƙagara ya ganta su Abdoul sai tsokanar shi suke yi. Giɗaɗo da Umar suka kawo musu abinci da ruwa da duk wani abin buƙata, amma Salim ya kasa cin komai dan shi ba ta abinci yake ba. Tun kafin su iso yake jin maganar Hajaru can kasa-kasa, murmushi ya yi yana gyara zama. Andizo na baya ta ɓoye a bayan Hajaru ta rufe fuska wai irin zuwan bazata za ta yi wa mai hankali sai cewa take “Ɓoye ni Hajaru.” Suna zuwa ƙofar ɗakin Andizo ta fito ta yi tsallen murna ta ce “Mai hankali shirin Allah.” Ta faɗa tana ruguwa a guje ya miƙe ya taro ta ya yi sama da ita yana juyi a tsakar ɗakin suna dariya. Gabaɗaya baki suka saki sunan kallon su, shi kuwa Ahmad waya ya ciwo yana musu video. Sai da suka ya gaji da kanshi ya sauke ta ƙasa ya ja ta suka zauna, ta matso kusa da shi tana faɗin “Ka rame.” Hannu ya miƙa mata jikinsa a sanyaye, miƙa masa ta yi ya kama da wani irin sauri ya rungume tsam a jikinsa yana sauke nannauyar ajiyar zuciya, dariya duk suka yi Ahmad ya miƙe tsaye ya ce “Abdoul ka ga tashi mu fita mu koma dakina waɗannan dai an gamu.” Tashi Abdoul ya yi suka fita har Hajaru itama tana dariya ta koma ciki.. Sun ɗauki lokaci a haka ya ɗago ta yana murmushi ya manna mata kiss a ƙoshi ya kuma mayar da ita jikinsa ya rungume ta kamar za a kwace masa ita, ita ko jin ƙamshin jikinsa da ɗumi suka sa ta yi luf tana ƙara yi wa kanta masauki, buɗe idanu ta yi a hankali tana jin wani iri a zuciyarta sai kawai ta fashe da kuka mai ƙarfi.. Hankali tashe ya ɗago da ita ya zaunar da ita yana faɗin “Khadija me ya faru ? Wani abu suka miki da suka sace ki?” Kasa magana ta yi sai kallon shi da take tana ci gaba da kuka, gabaɗaya ta ji wani irin yanayi na ratsa kowacce kusurwa ta jikinta wanda ta rasa mene ne shi, share mata hawayen yake yana rarrashin ta cikin wani kalar yanayi da yake jin shima ya tayata kukan. Sai da ta yi shuru ya sake tamayar ta, cikin muryar kuka ta ce “To ba kai ba ne ban ganka ba ina ta son na ganka.” Lumshe idanu ya yi ya tallafo fuskarta suka tsura wa juna ido, a hankali ta kai hannu ta shafi gefen fuskarsa ta ce “Shin da aka sace ni ka yi kuka ko?” Ta faɗa a shagwaɓe. Murmushi ya yi yana jin yadda take yawo da hannayenta a fuskarsa, murya a shaƙe ya ce “In da kuka ne ma ai mai sauƙi ne Khadija, har kwanciya na yi a gadon asibiti ban san wa ke kaina ba saboda ɓatan ki matata..” Zaro idanu ta yi sai kuma ta kalle shi ta ce “Waiyo Allah.” Ta faɗa tana koma tana bubbuga mishi baya a hankali ta ci gaba da cewa “Ka yi hakuri mai hankali yanzu ba ga shi Mom ta dawo da ni ba?” Sai a lokacin Andizo ta kalli kayan abincin ta kalle shi, “Mai hankali ba ka ci abinci ba ko?” Girgiza mata kai ya yi ta ɓata fuska ta janyo abincin ta buɗe ta tura masa ta ce “Bismillah.” Cikin nishaɗi ya ce “Sai dai in za mu ci tare.” Maƙale kafaɗa ta yi ta cuno bakinta da ya sha janbaki, janye abincin ya yi ya ce “To na ƙoshi tun da ba za ki ci ba.” Da hanzari ta sa hannu tana dariya ta ce “To mu ci.” Da kanshi ya dinga ba ta a baki tana ci itama tana ba shi, idan suka kalli juna sai su saki murmushi da haka har suka gama. Da kanshi ya wanke mata hannu itama ta wanke masa tana dariyar wai ƙato da shi ta wanke masa hannu ya ce ya ji.. Bayan sun gama ta ba shi labarin yadda aka sace ta da rayuwar da ta yi da yadda Mom ta kawo ta gida, amma ba ta sanar da shi abubuwan da Sultan ya mata ba kawai ta ce ba wanda take gani da aka kai ta sai mai kawo mata abincin, sosai Salim ya yi mamaki yana jinjina lamarin ɓarawon da yake son raba shi da numfashinsa a daidai lokacin da yake son gina wata sabuwar rayuwar.. Sai bayan La'asar suka shirya komawa gida in da suka sanar da Maigari saƙon su Abie Maigari ya ce ba matsala, amma dai kawai za a ɗaura auren bayan Sallah ta tare. Ba haka Salim ya so ba amma ya yi ƙudirin yi wa Abie maganar da an ɗaura a ba shi matarsa kawai ba sai an yi wani biki ba, da wannan tunanin suka kama hanya zuciyarta cike da bigen abar ƙaunar sa.. Washegari Andizo da Hajaru suna yawo a gari suka zo saitin wani gida, Hajaru ta kalli gidan ta ce “Ƙawata wannan fa gidan Iliya ne, tafiyarki da kwana uku aka masa aure da wata ƴar fulani mai kawo fura da nono nan, wai shi ne matar ta kama rashin aka ce aljannu gareta, kuma fa na ƙarya ne dan zai ƙara aure ne, kullum sai an mata ruƙiya amma abin sai gaba yake.” Dariya Andizo ta yi ta ce “Kenan dai na ƙarya ne? Ki bari da dare za mu zo mu mata ruƙiya.” Dariya suka yi suna tafawa, Hajaru ta ce “Shegiya sai wahalar da mijin take ya fasa auren amma ba ta daina cutar shi ba, kuma fa ko an zo ruƙiyar sai a ce sai ya ba da kuɗi mai yawa da ya bayar sai su raba da mai ruƙiyar in mijin ya fita.” Riƙe baki Andizo ta yi ta ce “Kut! Ka ji muguwa amma ke wa yake faɗa miki wannan labarin?” “Hmm ai ni babu abin da ban sani ba a gidan nan ko kin manta mijin ɗan'uwanmu ne?” Gyaɗa kai Hajaru ta yi suka yi gaba.. Da dare Andizo ta ɗauki wata babbar rigar Maigari fara sol guda biyu, a cikin kayan kwalliyar da Mom ta zubo mata har da farar fauda ta ɗauka ta zuba a leda ta ɓoye ta fita da sunan za su je dandali. A hanya suka haɗu da Hajaru nan suka nufi gidan. Sunan isa suka same shi a tsaye suka ce masa su masu ruƙiya ne za su fitar da aljannun da ke jikin matar yau din nan, jin haka sai ya musu iso har ɗakin da aka kulle ta, Andizo ta ce ya fita ƙofar gida duk abin da ya ji kar ya shigo, jiki na rawa ya ce to dan shi zaton shi aljannu ne yan'uwan aljannun jikin matarsa suka zo za su taimake shi. Sai da suka rufe ko'ina sannan Andizo ta maƙale murya ta ce “Keee!” Next Fage. Littafin ANDIZO na kuɗi ne N300 ne, za ku turo kuɗinku ta wannan account ɗin. Account number 0003187186 Name account, khadija Salisu Name Bank, Ja'iz Bank. Sai a turo shedar biya ta wannan number 🥏+966577675904 *Maman Nusaiba ce🤙🏻* [5/26, 11:29 PM] Ummu Amjad: _*AREWABOOKS@SARATALKASUM88*_ 20 Ƙin tashi ta yi sai ma gyara kwanciya da ta yi a zaton ta irin masu ruƙiyar da aka saba kawo mata ne, kallon juna Andizo da Hajaru suka yi ganin ba ta motsa ba, a fusace Andizo ta fito da bulalar da ta ɗauko tun daga gida, sai da ta taƙarƙare ta zabga mata. A firgice matar Iliya ta tashi tana fasa ihu idanuwanta ya sauka a kan su ta ja da baya, biyo ta Andizo ta yi tana zaro idanu ita kuma Hajaru tana haska fuskar Andizo da wayar Maigari rakani kashi, baki na rawa ta ce “Na shiga uku ni Laure ku kuke ganin mu ba mu muke ganin ku ba, don Allah ku yi haƙuri mutanen ɓoye karku kashe ni.” Tsawa Andizo ta daka mata tana nuna ta da bulalar ta ce “Ai yau kin yi bankwana da duniya sai kwanan lahira, tun da kika zama azzalumar mace dole mu azabtar da ke kafin ki isa gaban Allah ki masa bayanin cutar da mijinki da kike yi ba dare ba rana, in kuma kina son zaman duniya to da sharaɗi.” Ta faɗa tana wani irin juya idanu. Baki na rawa ta ce “Na. Na yarda ko ma meye kuke so in dai za ku rabu da ni.” Dariyar basawa Hajaru ta yi ta matso kusa da ita ta ce “Buɗe kanki mu miki ƙwal a kwabo dan ubanki, kinga in aka ga haka sai a san aljanun gaskiya ne a kanki sun miki aski, tun da kika shiga gonarmu mu aljannu daga yau kin dinga ganin masifa da bala'i matuƙar ba ki faɗi gaskiya ba.” Ta faɗa tana wanka mata mare, saboda mugun haushin ta take na wahalar mata da ɗan'uwa da take yi duk ya bi ya rame sai tagumi duk in da ka ganshi.. “Waiyo Allah na shiga uku na lalace! Ku taimake ni karku aske mini gashina, duk abin da kuke so zan yi yanzu ma zan kira Iliya na sanar da shi duk abin da nake ƙarya ce ni na tsara..” Kallon juna suka yi suka sa dariya da wata irin murya, riƙe kunne Andizo ta yi kamar mai sauraron wani abu can ta ce “E ina jinki yanzu, to ba damuwa kenan mu tafi da ita bangon duniya na arewa? To shi kenan da mun gama za mu zo da ita.” Ta faɗa tana sheƙewa da dariya, tana buɗe haƙoranta baƙi wuliƙ kamar da gaske haka suke, hakan ke ƙara sa matar Iliya ta tsorata da sun buɗe baki.. Durƙusawa ta yi a kan gwiwowinta tana kuka wiwi ta ce “Don Allah ku mini rai karku tafi da ni duniyar aljannu...” “Yo wa ya ce miki mu aljannu ne? Mu fatalwowi ne daga ƙabari muka fito.” Cewar Hajaru.. Kwalalo idanu waje ta yi tana kyarma gabaɗaya jikinta ya yi sharkaf da zuba, da na sanin abin da ta dinga wa mijinta ta mamaye ta, a ruɗe ta Kuma cewa “Don Allah ku yi mini rai karku tafi da ni Wallahi ina son mijina, dama sharrin sheɗan ne ya sa nake masa haka, ku taimake ni kun ga yau ɗin nan na gano ina ƙaramin ciki ko dan darajar shi ku barni zan gyara halina.” Ta faɗa tana dafe mararta.. Shuru suka yi Andizo ta sa hannu ta rufe hasken wayar da suke haskawa, kamo hannun Hajaru ta yi suka fito waje ta matso kusa da kunnenta ta ce “Hajaru kina ganin mu rabu da ita kar mu zane ta?” “Ƙila ma fa ƙarya take yi, amma dai in kin ce mu rabu da ita shi kenan mu ba ta kwana biyu mu gani idan ba ta canza ba ta haka za mu gane ƙarya ta mana..” Sai da suka gama shawara sannan suka dawo cikin ɗakin suka same ta ta takure a ƙuryar gado tana rawar jiki, gyaran murya Andizo ta yi ta canja muryna ta ce “To tun da kin ce ciki gareki za mu rabu da ke, amma bayan kwana biyu za mu dawo in dai muka ga ba ki canja hali ba to mun san ba cikin gaske ba ne. Sannan abu na ƙarshe ki ba wa mijinki haƙuri kuma ki miƙo wannan kuɗin da kuke cutar shi kuna amsa..” Da hanzari ta tashi ta ɗaga katifar gadon ta lalibo su ta miƙa musu, ganin idanuwanta a buɗe Hajaru ta ce “In ba ki rufe idanuwanki ba muna taɓa hannunki za ki ganki a dajin ƙare kukan ka.” Saurin rufe ido ta yi ta miƙa musu suka amsa, Andizo ta sake jadadda da mata in dai ba ta yi abin da suka ce ba za su dawo, ta amsa da to suka ce kar ta buɗe ido in ba ji ta yi Iliya ya shigo ba sannan suka fita.. Sanda Hajaru ta miƙa wa Andizo ta ce “Duƙa kike tafiya nima zan yi tun daga gida na zo mana da ita na aje a baƙin kofa.” Har ta buɗe baki za ta yi dariya sai ta tuna inda suke ta rufe bakin suka fito a duƙe kamar tsofaffin gaske.. Iliya da ya jingina da jikin katanga yana baccin wahala ya ji ana kiran shi da muryar tsafaffi ya yi saurin tashi, kallon kofar shiga ya yi ya ce “Malam har kun gama?” Gyaɗa kai Andizo ta yi tana rawar jiki irin an tsufa tukuf ɗin nan ta ce “E Wallahi yaro ai dama na faɗa maka mu za mu raba ta da aljannun, ka shiga babu wata matsala dama aljanun jikinta abokanmu ne mun zo mun tafi da su..” Zaro ido ya yi zai yi magana ta ɗaga masa hannu ta nuna masa kofar shiga, sai da ya zo zai shige ya ce “Gaskiya kuna da kirki sosai, yau zan yi barci hankalina kwance ba tarzoma..” Yana faɗin haka ya wuce da sauri suma suna ganin ya shige suka wuce.. Sai da suka je bakin dandali suka cire kayan Hajaru ta ba da ɗankwalinta suka goge fuskarsu, zama suka yi a bakin hanya suka dinga sheƙa dariya suna tafawa. Bayan sun gama Andizo ta fito da kuɗin ta haske fitilar waya suka buɗe kuɗin, sai da suka lisafa jika goma ce cif har da dala goma a kai Hajaru ta riƙe baki ta ce “Muguwa ji fa uban kuɗin da ta tara, gobe sai na kai masa abin shi.” Tashi Andizo ta yi ta ce “ Tab ki rabu da shi zan aje kuɗin in ta haihu sai mu kawo a matsayin gudumawa, mu je wajen Saminu tun da na zo ban ganshi ba, shi ko ya je ya ganni ma tashi mu isa sai na masa rashin mutumci..” Ta faɗa tana mayar da kuɗin ta ƙulle a jikin zaninta suka nufi in da Saminu ke zama.. Andizo ta riƙe kugu ta tsaya a gaban shi, a hankali ya soma bin ƙafafuwanta da ta mulke su da mai ƙasa ta baɗe su, saurin daga kai ya yi yana kallon ta. Murmushi ya sakar mata yana kallon gefe da gefe ya ga ba kowa, gefen shi ya nuna mata ya ce “Dije zo nan mana mu yi magana.” Ba muso ta dawo gefen shi ta zauna sai hura hanci take, Hajaru ta zauna a kusa da ita ta kalli Saminu da jikinshi ya yi sanyi sai wani irin kallo yake yi wa Andizo ita kuwa ko ba ɓangaren shi ba ta kalla ba.. “Gaskiya dai Saminu amana ba ta ce haka, yanzu masoyiyar taka ta ɓata na tsayin satuttuka, kuma ta dawo ka kasa zuwa ka gano ta? Anya ba munafukai sun shiga sun fita suna haɗa ka da ƙawata ta ba?” Ta faɗa tana riƙe ƙugu. Hannayensa ya haɗe waje ɗaya ya kalli Andizo da take cika tana batsewa, a sanyaye ya ce “Wallahi Dije ina matuƙar sonki kawai dai an hana ni zuwa wajen ki ne, ki yi haƙuri kar ki yi fushi da ni hakan ba zai mini daɗi ba.” Hararar shi ta yi ta ce “Mai ƙarya dai ɗan wuta ne Saminu, karka yi ƙarya dan ba na son ka zama ɗan wuta in, da gaske ne ka faɗa mini wanda ya hana ka zuwa inda nake mana.” Ta faɗa tana cuno baki gaba, sosai ta ji haushin rashin zuwan shi ganin ta.. “Wallahi Hammanki ne da wannan ɗan birnin suka ce kar na sake zuwa in da kike, shi Hamma Giɗaɗo cewa ya yi kar na sake kula ki in ya ganni da ke zai ɓata mini rai, shi ya sa kika ga ina yin baya-baya da ke ba wai dan ban damu da ke ba ne. Jiya har fanke na zuba da zafin sa na ba wa Talle ya kai miki sai ga shi ya dawo yana kuka, ya faɗa mini Hamma Giɗaɗo ne ya kwace fanken ya koro shi da bulala..” Ya ƙarashe maganar yana sunkuyar da kai. Tun da ya fara maganar Andizo ta saki baki tana sauraron shi, mamaki fal ranta jin wai Hammanta ne ya hana masoyinta zuwa inda take, a fusace ta miƙe ta dawo gaban shi ta durƙusa ta ce “Saminu!” Ɗago kai ya yi suka haɗa ido idanuwansa sun cika taf da hawaye, lumshe su ya yi dan kar ya bari su zubo amma ina ya makaro dan tuni Andizo ta gani, a ruɗe ta ce “Wallahi in ban rama maka abin da Hamma ya yi maka ba ka ce ni ba ɗiyar Hajja da Maigari ba ce, shi ne kake kuka dan ya hana ka gani na? Me ya sa ba ka faɗa mini ba tun wuri na masa kashedi kar ya sake shiga tsakani na da kai? Ka yi haƙuri yau Hamma ya taro bahar maliya, alƙur'an sai na sa shi kuka shima tun da har yake takura maka..” Ta faɗa a masifance. Murmushi mai ciwo Saminu ya yi, shi ya san ko giyar wake ya sha yanzu Andizo ta fi ƙarfin shi tun da har an sa mata rana, ita kuma a ganin ta tare za su tafi can birni su yi karatu da shi sai faɗa wa mutane take cike da kwarin gwiwa, shi kam in ta sanar masa kallon ta kawai yake ya rasa yaushe za ta gane wayo ne aka mata aure za ta yi ba karatu ba.. Tashi ya yi ya zuba mata fanke ya isa can gaba da su kaɗan ya sayo mata ranke guda huɗu ya haɗa ya miƙa mata, ƙin amsa ta yi ta maƙale kafaɗa, ya kalle ta ya yi murmushi komai nata tafiya yake da shi, sai dai in ya tuna ya kusa daina ganin ta sai ya ji gwiwarsa ta sace. “Ki amsa Dije in dai da gaske kina sona.” Jim abin da ya faɗa sai ta sa hannu ta amsa tana faɗin “Kar fa ka damu da zarar mun tafi birni ai ya huta da ganin mu ballantana ya takura maka.” To kawai ya ce mata suka masa sallama suka tafi.. Sai da suka kusa zuwa gida Hajaru ta ce “Andizo Wallahi Saminu tausayi yake ba ni, yanzu in aka ce ba za a tafi da shi birni ba shi kenan nan an raba ku ko?” “Kan uba! Ke ki bar faɗin wannan maganar ma, yo ai shi mai hankalin ya ce za mu tafi da Saminu har Maigari ya faɗawa, ki bar wannan batun ma zo mu cinye fanken nan gobe ko jibi mu je gidan Laure mu gani ta canja ko kuwa sai mun mata duka za ta daina ƙarya..” Ba ta sake cewa komai ba suka samu gefen hanya suka zauna ta baje musu fanken suka yi bismillah suka fara ci. Bayan sun gama Andizo ta ce “Ki zo mu je ki kwana a gidanmu yau.” Har za ta yi gardama sai kuma ta fasa dan ta san halin ƙawarta ta ba mutumci ba ne da ita tsaf za ta mata dibar albarka. Washegari Andizo bayan ta gwada kayayyakin da Mom ta kawo mata sai maganar Saminu ta faɗo mata a rai, ta haɗe kayan ta nufi ɗakin su Giɗaɗo da sauri tana kwada masa kira. “Hamma ! Hamma! Ka fito yau ni da kai a gidan nan ban ga ba mai raba mu sai Allah, kai alƙur'an daga yau ma zan iya fasa ce maka Hamma inga ta fankamar da kake kana takurawa masoyina..” Buba ya tashi zaune yana faɗin “To fa masifatu layar ƙanzo, yau kuma da Hamma Giɗaɗo za a yi? To bari na tashi na bar muku ɗakin kafin ta iso ta cika mini kunne.” Ko kallon shi Giɗaɗo bai yi ba sai ma gyara zama ya yi yana jiran zuwan ta. Ba ko sallama ta faɗo ɗakin, kanshi ta tsaya ta da hannu ta damƙo kwantacciyar sumarsa ta ɗago kansa da ƙarfi, tana hura hanci ta ce “Ina dai faɗa maka karka sake tare mini masoyi kana masa barazana, dan mugunta shi ne har da saka shi kuka ka hana ya zo inda nake? To ka fita idona na rufe tun kafin na ɗauki fansa a kanka. Ko dan ka ga ka hana ni rama abin da su Hajja suka mini kake tunanin na canja daga yadda ka sanni ne? To alƙur'an zan maka dukan tsiya in ga mai kwantar ka a gidan nan, ina ruwan ka da Saminu?” Ta sake shi tana huci ta kuma nuna shi da tsaya ta dora da cewa “Idan kunne ya ji gangar jiki ya tsira, kar ka ganka ƙato ka linka ni a tsayi tsaf zan maka duka babu abin da ya shafe ni da kai Hammana ne..” Sai da ta gama ya janyo hannunta da karfi sai ga ta yaraf a ƙasa ta yi zaman 'yan bori a gaban shi, kallon shi ta yi ganin yadda idanuwansa suka yi jajur kamar an watsa masa barkono, da kyar ya haɗiyi yawu ya ce “Surbajo ni kike faɗa wa magana a kan wani Saminu? To Allah ya ba ki haƙuri ba zan sake ba ai kin kusa daina gani na ki huta..” Kwafa ta yi ta miƙe tsaye ba ta ce masa komai ba ta wuce fuu tana faɗa har ta bar ɓangarensu.. Abie da Abba suka zo suka yi zama na musamman a kan buƙatar Salim, amma fir Hajja ta kafe ta ce gaskiya sai bayan azumi da kyar Umar ya shayo kanta ta amince su dawo sati mai zuwa a ɗaura auren su tafi da amarya. Cike da farin ciki Abba ya fito da sadaki 50,000F jika ƙamshin ya aje sannan suka koma zuciyyoyinsu cike da farin ciki.. Ko da suka koma gida suka sanar da Salim ranar kwana ya yi yana Sallah yana miƙa godiyar sa ga Ubangiji, duk abin da yake Aminatou na kallon shi tana mishi dariyar mugunta, za ta ga ta yadda amaryar za ta shigo. Ahmad kuwa cewa ya yi ranar da za a kawo amarya dole ne a harabar gidan ya haɗa gagarumar dinner ya gaiyato abokansa da na Salim a sha shagali, hakan ya ƙara kona zuciyar Aminatou dan ya gida ya zo ya sanar da Salim suna zaune a palo, in kuma ta tuna shirin da suka yi na musamman a kan Andizo sai ta ji wani sashe na zuciyarta ya yi fes, ƙarshe ma har baki ta sa a maganar amma Ahmad ya ƙi kula ta.. Ɗankwalinta a hannu ta isa wajen Maigari ta ce “Maigari ka ba ni wayarka zan kira Mom mu gaisa da Farrah ƙawata.” Babu muso ya miƙa mata ta koma ciki da sauri, waje ta samu in da babu kowa ta ɗauko number ta saka ta danna kira. Sai da ta yi ringing ba a ɗauka ba ta kuma kira, wannan karon ta kusa katsewa aka ɗauka. Murmushi ta yi ta ce “Mom ina wuni? Ya gida ina ƙawata Farrah? Ki ba ta za mu gaisa..” Daga can ɓangaren Mom na zaune a palo masu aiki na mata tausa ta yi dariya, kallon gefe ta yi ta ga Farrah ba ta kusa ta ce“Lafiya lau Khadija ya su Maigari? Farrah ba ta kusa tana ɗakinta bari na ba da a kai mata karki kashe.” “To Mom ai dama zan sanar mata aurena fa nan da kwana biyar ne, to ya kamata ta zo bikin tun da ta mini alƙawarin za ta zo a gaban ki aka yi haka ko?” “Kwarai ma kuwa ni ce shaida, ashe bikin ya zo ma? To bari a kai mata.” To Andizo ta ce Mom ta ba wa ɗaya daga cikin masu mata tausa ta kai wa Farrah. A kwance ta same su ita da Sultan suna ta hira ta yi sallama ya juyo, kallon ta ya yi ta sunkuyar da kai ta ce “Ranka ya daɗe Mom ce ta ce kawo mata waya wata ce ta kira tana neman ta.” Da sauri Farrah ta tashi ta duro daga kan gadon ta isa ta mashi wayar, a hankali ta ce “Hello wace ce?” Dariya Andizo ta yi ta ce “Khadija ce Farrah, dama na kira ne in faɗa miki yaushe za ki zo wajen bikin nawa? Kin ga yanzu saura kwana biyar dan har yau Hajja ta mini wankan lalle kin ji yadda nake ƙamshi kuwa.” Zaro idanu Farrah ta yi cike da murna ta ce “Wow nice one, Kenan Khadija auren naki har ya zo nan da kwana biyar? Ai kuwa za mu je ni da Mom k..” Ba ta ƙarasa ba ta ji an warce wayar ta yi saurin kallon shi, kara wayar ya yi a kunne yana huci ya ce “My wife me kika ce za ki yi nan da kwana biyar.” Jin muryarsa sai da gaban ta ya faɗi amma ta dake ta ce “Aurena mana ni da mai hankali za mu koma birni ni da Saminu.” Cikin ƙaraji ya ce “Khadijaa! Na rantse da Allah in kika bari aka miki aure da wani ba ni ba sai na kashe shi, waye shi da zai shigo gonata? Wallashi suma tallahi zan kashe shi har lahira in dai ya kuskure ya aure ki, waye ubansa a Niger ɗin?” Ya faɗa yana yin jifa da wayar Allah ya sa ta faɗa kan gado... *To fa jama'a Angon Andizo zai yi kisa🚶🏼‍♀️* *Mun kusa gama promote littafi zai dawo kuɗinsa na farko N500 daga nan zuwa ranar Alhamis.* _Maman Nusaiba ce🤙🏻_ [5/27, 10:20 PM] Ummu Amjad: _*AREWABOOKS@SARATALKASUM88*_ 21 Kallon shi Farrah ta yi a tsorace ganin yadda jijiyoyin kansa suka tashi sun yi raɗa-raɗa, bakin gadon ta iso ta sa hannu ta ɗauki wayar ta ga har yanzu Andizo na kan kiran, a hankali ta kara a kunne ta ce “Khadija wai me ya sa kuke faɗa da Daddy ne?” Tsaki Andizo ta yi tana murza idanu saboda firgita ta da y yi da karajin maganar da yake, sai da ta yi jim ta ce “Shi fa Daddy ce mini ya yi wai zai kashe duk wanda na aura, dama shi ɗan fashi ne ban sani ba? To alƙur'an ya shiga hankalinsa in yana tunanin zai iya rashin mutumci a Nigeria a kyale shi, to mu a nan Niger ya kashe mutum tsaf za a rataye banza ya mutu a wulaƙanci a kai shi a totse cikin ƙasa. To ma ni ina ruwana da shi? Ba kina ji ba Mom ta ce kar ya sake kulani?” Ta faɗa hawaye na zubo mata.. Zama Farrah ta yi ta yi shuru ita dai ba gane me Andizo ke nufi ba, dan haka ta kawar da maganar da cewa “Nan da kwana uku za mu je biki naki har da Abida mai kula da ni.” Gyara zama ta yi ta ce “To shi kenan amma ki faɗa masa kar ya sake amsar waya ya mini magana in muna hira da ke.” Dariya Farrah ta yi ta kalli Sultan da yake tsaye yana jin duk abin da suke faɗa dan speaker a buɗe take, hannu ya sa ya amshi wayar ya nufi ƙofar fita yana faɗin hirar ta isa haka zan kai na sa miki wayar a caji kin ji.” Ya faɗa yana wucewa. Ba dan ta so ba haka ta haƙura ta rabu da shi ta koma ta kwanta sai murna take za ta je bikin ƙawarta.. Daret ɗakinsa ya nufa, a hanya duk wanda ya haɗu da shi a cikin ma'aikatan gidan ya masa barka da rana ko samun arzikin ɗaga hannun da yake musu ba sa yi, hakan ya sa suak gane cewa lalle yau fa akwai matsala a tattare da Ogan nasu. Yana shiga ɗaki ya sa key ya ƙulle ya nufi wani lungu sai ga shi a kafataran Palo ya sha ado, gaba ya yi ya tsaya jikin wata kofa mai glas ya danna wasu numbobi da ke jikin Ƙofar ta yi ƙara sannan aka ce “Welcome to the room Mr Sultan.” Wani shan mur ya yi Kamar ya ga abin ƙi ya shige ciki, wani makeken gado ne a ɗakin royal an shifiɗe shi da kyakkyawan bedsheet fari tas sai adon dawisu da ke tsakiyar bedsheet ɗin. Zama ya yi yana huci ya kalli wayar ya ga ta kashe kiran, hanzari ya danna mata kira ta yi ringing ta gama ba a ɗaga ba ransa ya ƙara ɓaci, dafe kai ya yi ya sake danna kira ya ci sa'a an ɗauka. Dogon numfashi ya ja ya yi baya ya kwanta ya yi ɗaiɗai, ita kuwa can bayan dakunansu inda suke wasan tuwon kasa ta nufa a tunanin ta Farrah ce ta sake kira, ta samu waje ta zauna a ɗankaraminki na kayan wasa. Jin ba a ce komai ba ta ce “Ke Farrah wai ba za ki yi magana ba?” Murmushi ya yi yana haske yadda take maganar tana turo baki, buɗe ido ya yi murya a, shaƙe ya ce “My Dija.” Saurin ɗauke wayar ta yi daga kunnenta ta kalli wayar ta ga dai numéro ɗin da ta saka ne, mayar da wayar ta yi ta ce “Kai kuma me ya sa ka ɗauki wayar Mom? Dalla can Malam ka ba wa mai wayar abin ta ba na son kalan dangi, so kake na ce Farrah ta zo da kai bikina ko? To ba zan faɗi ba ka kuma ce mini my wife ɗin nan sai na faɗa wa Maigari duk abin da ka mini wanda na ɓoye..” Girgiza kai ya yi ya ce “To ai babu wanda zai aure ki in ba ni ba Sultan, dan haka ki ma daina maganar za a miki aure da wani ba ni ba, ni ne nan mijinki in kuma wani ya yi ƙoƙarin shiga gonata zan iya komai dan na fitar da shi daga ciki. Yanzu Khadija har za ki iya auren wani bayan ni? Ba ka yadda nake sonki ba za ki zaɓi wani a kaina?” Ya faɗa yana dafe saitin zuciyarsa tare da runtse idanu da karfi, gabaɗaya ɗan kuzarin da yake ji ya neme shi ya rasa sakamakon maganar ta.. “Kai can ta matse maka Malam ko ba ni da saurayi ne zan yi da wanda ko yadda zai bautawa Ubangijinsa bai sani ba, ka koma makaranta ƙila ko ka iya gane ciwon haukan da ya same ka.” Ta faɗa tana jan tsaki ta kashe kiran.. Kallon wayar ya yi cike da mamakin kalamanta, “To me take nufi da hakan? An faɗa mata ban je school ba ne?” Ya faɗa yana aje wayar.. Shuru ya yi yana kallon samar ɗaki, dole ne ya yi wani in ba haka ba akwai matsala, a hanzari ya miƙe ya nufi jikin wani table mai ɗauke computers har guda 3, ɗaya daga ciki ya buɗe ya sa code sannan ya ɗauko wani number ya sa kira. Eapis ya sa a kunne yana jiran a ɗauka, ana ɗauka ya soma magana cikin zafin zuciya.. “Ashu where is Bansh?” Daga can ɓangaren muryar mace ta amsa da cewa “Bansh is at Dubai, Oga what happing?” Tsaki ya ja yana faɗin “Ɗan iska shi ba zai dawo daga Dubai din nan ba? To ki sanar da shi akwai problem ne mai girma, idan kun yi waya ki sanar da shi zan tafi Germany yau da yamma, akwai wata kadarata da nake so ya luran mini da ita kafin mu gama buga bal ɗin can zan dawo, ko da ba a gama ba zan sa shi ya kawo mini ita in da nake.” “OK sir, amma naji kana cewa za ka sa a ka maka ita nan wace ce ita? Dama kana yin soyayya ne.” “Ke ban son hauka ki yi abin da na ce, kin je na ce miki mace ce? Idan har aka samu matsala a lamarin nan kin san hukuncin ki daga ke har shi ba sai na maimaita miki ba..” A ɗan tsorace ta ce “Yes sir na sani.” Katse kiran ya yi ya rufe computer ta tashi toilet ya nufa ya sakar wa kansa ruwa ko zai ji sanyi, mamaki da kalmomin da take faɗa masa sun hana shi sukoni, bai taɓa tunanin za ta ba shi matala ba ganin ita ba wata babba ba ce, ga shi yanzu sai wahalar da zuciyarsa take kuma tana ambaton za ta auri wani bayan da aurensa a kanta. Ajiyar zuciya y sauke ya kashe ruwan ya fito kamar marar lafiya.. Kaya ya saka ya fesa turare kaɗan ya fita, direba ya taso da sauri zai buɗe masa mota ya ɗaga masa hannu alamar yau ba ya son a raka shi. Komawa ya yi yana tambayar kansa ko mene ne ya sa Ogan nasu zam silent? Dan bai taɓa ganin shi a cikin irin wannan yanayin ba. Shiga ya yi ya ja motar a matsiyacin gudu ya bar gidan.. Andizo wunin ranar kalaman Sultan ne ke mata yawo a rai, ko da duka tafi Islamiya kasa samun nutsuwar ɗaukan karatu ta yi da an jima sai ta ja, numfashi ta tafka tagumi. Da dare ma kasa cin abincin kirki ta yi sai ta samu waje ta kwanta ta rufe ido kamar mai barci, tana jin Hajaru ta zo su tafi wasa amma ta yi ƙememe ta ce ita ba za ta fita ba yau ba ta jin ƙarfi a jikinta, dole ta haƙura ta rabu da ita ta koma gidansu... Kwanaki na ta tafiya bikin Andizo ya kankama, yayin da ita kuma ta tsage sai murna take za ta tafi birni tuni ta manta da shafin Sultan da kwana biyu da maganar su tunanin maganar shi duk ta hana ta sakat, amma da Salim ya zo ya ɗauke ta duka fita bayan gari ya yi ta lallaba ta yana sanar da ita irin makarantar da zai saka ta mai kyau ya dinga kai ta wajen wasa, hakan ya ƙara mata zumuɗi son auren... Ana ya gobe ɗaurin aure sai ga babbar mota ta faka a kofar gidan Maigari, Farrah ce ta fito sanye da riga da wando kanta ya sha gyara ga wani lalle da aka mata mai kyau baƙi da ja, fitowa direban ya yi ya tare wani yaro ya ce “Yaro nan ne gidan su Khadija amarya ko?” Gyada kai ya yi ya ce “E bari ma na kira maka ita yanzu aka gama waƙe suka shiga ciki.” Kafin ya ba shi amsa ya nufi gidan a guje. Bai fi sakan ashirin ba sai ga su a tare, hango wadda ke tsaye ya, sa Andizo sa ihun murna ta zo da gudu suka haɗe suka rungume juna suna dariya, ganin haka direban ya dauko mata akwatinta ya miƙa wa Andizo da take taɓa gashin Farrah. Amsa ta yi tana juya akwatin ta ce “Gaskiya naji daɗin zuwan ki ƙawata, muje ciki ki huta.” Dariya Farrah ta yo suka nufi gidan, har za su shiga direba ya mata kira ta dawo ya miƙa mata wayarta da ta manta... Washe gari aka ɗaura aure da safe ƙarfe goma da rabi, sosai kofar gidan Maigari ta cika taf ta al'umma, wasu daga makotan kauyukansu wasu daga ruga, ga kuma tawagar ango da iyayensa. Sai washe baki Salim yake ana ba shi hannu ana masa barka.. Bayan an yi Sallar Azuhar Ahmad shi da Abdoul suka ce suna son a ba su amarya tafi da ita da duk wanda zai je ganin gidan amarya, Maigari ya ce Hajja ta ce ba za a tafi da amarya ba sai gobe su zo da safe ko rana sannan sun gama komai. .. Suna barin wajen Ahmad ya dinga dariya yana kallon Salim da yake zaman jiran su, ganin dariya da suke Salim ya ce “Kai ba son hauka fa, lafiya la tafo kana dariya ?” Shiga ya yi ya zauna sannan ya ce “Hajiya Hajja ikon Allah ta ce ba za a ɗauki yau ba sai gobe.” Murmushi ya yi ya ce “To ai an yi mai wahalar dai ku jira ni naje mu gaisa sai mu tafi? Tsokanar shi suak dinga yi yana murmushi ya fi ɗakin da aka ba su ya zauna yana jiran zuwan ta.. R Takalmanta a hannu ta shiga, [5/28, 11:38 PM] Ummu Amjad: _*AREWABOOKS@SARATALKASUM88*_ 22 Ko rabin tafiyar ba su yi ba Andizo tana ta surutu bacci ya yi gaba da ita, ba ta farka ba sai da aka shigo cikin gari Ɗahare ta tashe ta tana faɗin “Surbajon Hamma tashi mun zo garin su mai hankali.” Idanuwanta ta buɗe ta soma murza su tana kallon ko'ina, kallon direba ta yi ta ce “Kai buɗe mini madubi mana.” Har zai yi magana sai kuma ya tuna kashedin da Salim ya masa, ya ce masa duk abin da ta ce tana so a yi mata su lallaɓa a zo lafiya kar ya bari ta yi kuka. Buɗe mata madubin ya yi hakan ya yi daidai da danger ta tsaida su, kanta ta miƙo waje tana ƴar dariya ta ce “Oh ni gyatumar masu gari, alƙur'an yau mai hankali zai ga samfurin jin daɗin kawo ni birni da ya yi, kalli ka ga wasu igiyoyin shanya da aka sa a kowanni titi ko ta ya ma za a shanya kayan?” Ta taɓe baki tana kallon su. Motar kusa da su ta kalla ai kuwa suka haɗa ido da wata kyakkyawar budurwa ta sha kwalliya har da glass, murmushi ta sakar wa Andizo tare da ɗaga mata hannu, itama ta ɗaga mata ta ƙara zuro kanta ta ce “Daga ina kike? Ni aure ni aka mini ga shi nan za su kai ni gidan mai hankali mutumin kirki, ke ina za ki je?” Dariya budurwar ta yi itama ta ƙara miƙo kai ta ce “Ni makaranta zan tafi, ke yanzu aure ne aka miki ko dai karatu ne kika zo yi?” Taɓe baki Andizo ta yi ta ce “A to ni dai daga gida aure aka mini, mai hankali ne ya ce zai saka ni a ècole ni da Saminu, ni suna na Khadija.” Jinjina kai ta yi tana shirin mata magana aka ba da hannu sai ɗaga mata hannu ta yi, itama Andizo ta ɗaga mata tana cewa “Kema da alama za ki yi kirki.” Janyo ta ciki Ɗahare ta yi ta ce “Haba meye haka? Kawai daga ganin mata sai ki dinga mata magana haka ake yi? To nan dai ba garinmu ba ne kina yiwa kowa magana za a sace ki.” Ɓata rai ta yi ta ce “Yo to kurma zan zama kawai dan na zo birni? Alƙur'an duk wanda ya mini magana sai na mishi.” Ta faɗa tana harɗe hannayenta.. Ba ta sake ce mata komai ba suka ci gaba da tafiya.. Sun shigo cikin gari sosai a jikin wani gida motar su Andizo ta tsaya direban ya kalli su Ɗahare ya ce “Hajiya a nan ku za ku sauka na tafi da amarya in da ango yake, daga can za su iso wajen dinner da ake yi..” Sanin an musu bayanin komai sai suka sauka wata mota ta zo da ban ta ɗauke su, ita kuma Andizo na kallon su ko motsi ba ta yi ba sai ma shafa warwaron da aka sa mata take tana yaba kyan shi. Sai da suka yi tafiyar minti goma sha biyar sannan suka iso wani madaidaicin gida mai kyau, hon ya yi aka buɗe masa ƙofa ya shiga harabar gidan. Yana gama packing ya fito daga motar ya zagayo saitin Andizo ya dan rusuna ya ce “Madam ki zauna karki fito Oga ne zai zo ya fitar da ke..” To ta ce masa ya juya ya fice a wajen.. Tun da suka yi hon yake tsaye jikin taga yana kallon motar ransa fes, ganin direban ya tafi ya nufi hanyar fita da sassarfa, sai da ya iso bakin ƙofa ya tsaya ya nutsu da kyau. Cikin takunsa irin na zaratan maza yake takowa fuskarsa kamar gonar auduga, yana isowa ya buɗe mata motar ya ɗan ja da baya yana jiran fitowar ta. Murmushi ta sakar masa sannan ta fito tana ƙare masa kallo, baki ta riƙe tana faɗin “Kai ma sha Allah, tubuli wayukulufullahu ta'ala, ka ga yadda ka yi kyau? Alƙur'an kayan ma irin nawa ne.” Ta faɗa tana zagaye shi. Hannu ya buɗe mata ya ce “Zo naji ɗumin matata.” Ba muso ta iso ya sanya ta a jikinsa ta yi luf kamar mage, cikin nuna zallar farin ciki ya ce “Alhamdu Lillah Khadija kin zama halaliyata matar aurena, Allah ya bar mu har gidan aljanna..” Shuru ta yi ba ta ce masa komai ba dan har wani bacci-bacci ta ji na son kama ta dama ta gaji, jin ba ta ce komai ba ya ɗago ta yana kallon yadda ta rufe idanu, a hankali ya hura mata iskar bakinsa. Turo baki ta yi ta ce “Babu kyau dai ina jin bacci kake busa mini iska a fuska.” Ta faɗa tana buɗe idanuwanta. Kama hannunta ya yi da nufin su tafi amma fir ta ce ita fa ta gaji ya ɗauke ta, dariya ya yi ya ce “Abu mai sauƙi matar Salim ai ko goyaki sai na yi ba ɗauka ba.” To ta ce ya ɗauke cak suka yi ciki.. Sai da ya zo tsakiyar palon ya aje ta yana faɗin “Hassana ga ta nan ki yi sauki ki shirya mini ita nima zan shiga wanka.” To ta ce tana dariya ganin yadda yayan nata yake ranar jiki a kan Andizo, ya juya zai tafi Andizo ta kamo rigarsa tana saɓa baki ta ce “To ni dai karka mini wayo ka tafi ka barni.” Duƙawa ya yi daidai tsayinta ya dafa kafaɗunta ya ce “Wanka kawai zan yi kema za a miki kwalliya ne mu tafi can gida wajen shagalin..” Jin bin da ya faɗa sai ta sake shi Hassana na kallon su cike da birgewa, hannunta ta kama suka nufi wata ƙofa shima ya nufi wata daban.. Ruwan wanka Hassana ta haɗa mata ta nuna mata yadda za ta yi amfani da komai na banɗaki sannan ta fita. Da yake ba wannan ba ne karon farko na ganin bahon wanka sai ta shige ciki tana lumshe ido jin wani ƙamshi na tashi a ruwan wankan. Bayan ta gama ta ɗaura towel ta fito suka haɗu a bakin kofa ta kama hannunta suka nufi ɗaki, ƙananan abin buƙata ta ba ta ta saka haɗi da wata doguwar riga sannan ta fara tsara mata special kwalliya irin ta manyan mata. Bayan ta gama ta ba ta rigar amare daidai ita mai masifar kyau pink colour ta ce ta sa, kasa sawa ta yi sai da ta taimaka mata ta sa aka ɗaura mata ɗaurin ɗankwali, ta ɗauko ƴar karamar jaka da takalmi masu tsini ta sa mata, ita dai sai kallon takalmin take tana tunanin ta yadda mutum za iya tafiya da wannan abin ɗonono a sama. Bayan an gama mata ta ce ta tashi ta gwada tafiya, a hankali ta tashi ta soma tafiya a hankali gudun kar ta faɗi sai abin ya birge Hassana ta tafa hannu ta “Très bien matar yaya kin iya tafiyar..” Daɗi ne ya lulluɓe zuciyar Andizo ta mata godiya, kama hannunta ta yi suka fito waje inda suka samu Salim tuni ya gama shirin sa su yake jira. Baki buɗe yake kallon ta ganin yadda ta yi masa kyau fiye da kowacce rana sai ma sha Allah yake furtawa, hannunta ya kama suka fita a tare har Hassana suka shiga mota zuwa gidansu.. Tun kafin su ƙaraso gidan suke jiyo sautin kiɗan da yake tashi, suna shigowa gidan MC ya ce “A dakata ango da amarya sun zo kowa ya je ya zauna.” Masu yin rawa kowacce ta koma wajen zaman ta tana son ganin fuskar amarya. Sai da suka ɗauki kunsan minti goma sannan Salim ya fito daga cikin motar ya zagaya ya buɗe mata, ita kuwa ta wani kame kamar babbar mace tana shan ƙamshi, duk wannan tsarin Hassana ne ita ta nuna mata yadda ake yanga in ana tafiya da ango in za a shiga fili, kallon ta ya yi zuciyarsa na ƙara narkewa da so da ƙaunarta, sosai ya ji daɗin ganin ta yi duk abin da aka koya mata kamar dama can ta iya, hannu ya miƙa tare da sunkuyawa ya manna mata kiss a kumatu ta bige masa kafaɗa ta ce “Ban son haka Nurul qalbi mu je mana.” Sumar wucin gadi ya yi jin sunan da ta kira shi da shi, jinjina ya mata da hannu yana mai faɗin “Ma femme kin biya ni ɗari bisa ɗari ko yanzu, taso mu isa mana ga su Ɗahare can na jiran mu.” A yangance ta miƙa masa hannu ya kama ya fito da ita, har za su fara tafiya sai ga Hussaina ta iso da sauri ta kama hannun Andizo ya yi saurin kallon ta. “Yaya Mamma ta ce sai amarya ta fara fitowa da yayyunta tukun za ta fito da ango, kawo ta mu je a canja mata kaya..” Ba haka ya so ba amma dole ya haƙura saboda ba ya taɓa muso da maganar Mamma ko da kuwa zai cutu ne, haka ya saki hannunta yana mata murmushi, ita kuwa har da ɗaga masa hannu ta yi hakan ya yi daidai da paka motar Aminatou ita da Sabrin.. Saurin kallon su Sabrin ta yi ta ce “Wai waccan ba ita ba ce amaryar?” Shuru Aminatou ta yi tana ƙare wa Andizo kallo ganin yadda suke sakar wa juna murmushi, Salim ta kalla ta ga ya ɗaga hannu ya juya ya rufe mota ya nufi ɓangaren Mamma in da aka yi da Andizo. Wani irin zafi zuciyarta ke yi sai huci take, dafa ta Sabrin ta yi ta ce “Ke fa wani lokacin hankalinki gushewa yake a kan wancan mijin naki marar amfani, ki nutsu kar su gano wani abu a yi taron nan lafiya a gama, hakan zai ba mu damar cimma burinmu a kansu..” Wasu zafafan hawaye ne suka zubo mata shar ta goge a hankali dan kar ta ɓata kwalliyar, fita suka yi tana dannar zuciyarta suka iso wajen 'yan gidansu da suka zo mata suka tarar ba ta gidan. Kallon ta mahaifiyarta ta yi ta nuna mata kusa da ita tana yi wa Sabrin wani irin kallo, sam ba ta son abotar ƴarta da Sabrin saboda hankalinta bai kwanta da ita ba, amma ita Aminatou ta nuna wa mamanta Sabrin ba ta da wata matsala.. Dafa ta ta yi ta ce “Aminatou ce a'uzu billahi minan sheɗani rashin sau uku, ki ƙara da cewa Hasbunallahu wa ni'imal wakil.” Sunkuyar da kai ta yi saboda kukan da ya zo mata, gabaɗaya ta rasa inda za ta saka kanta ta ji sanyi, Andizo da Salim kawai take gani a idanun zuci suna yi wa juna kallon soyayya, da kyar ta haɗiye kukan dalilin addu'ar da Ummin nata ke karanto mata tana mata nasiha ta umarce ta da ta dinga nanata, jin zuciyarta za ta yi bindiga ya sa ta dinga nanata addu'ar da Ummi ta faɗa mata, sai da ta ɗauki minti biyar tana yi sannan ta ji zuciyarta ta samu nutsuwa sai sauke numfashi take zuba na tsatsafo mata a goshi, jin ta samu sauki sai Ummi ta ce ta dinga karantawa ko mijinta ta gani ya fito da amarya kar ta bari sheɗan ya yi nasara a kanta zafin kishi ne take ji. To ta ce tana lumshe idanu.. Bayan an shirya amarya aka canja mata wasu kayan doguwar rigar shadda irin ta su Umar yellow, ɗakin da suke Husaina ta kai ta ta ce su taso. Andizo ta kalle su ta yi murmushi ta yi kyau matuƙa sai wani maƙale hannu take ɗayan hannu kuma jaka ce irin kalar shaddar. Hussaina ta ce “Kuna ji, mutum biyu za su tsaya a gefe su riƙe hannunta sauran su jeru, sai ku fito a haka.” To Umar ya ce yana gyara zaman hularsa, Buba da Giɗaɗo ne suka tsaya a gefen ta, har Giɗaɗo ya miƙa hannu zai riƙe nata ya yi saurin ja baya ya ce da Aliyu ya tsaya a gefen ta, shi da Umar da Iro suka tsaya a baya. Ana faɗin zuwan su aka sa musu waƙa, dukkan 'yan wajan kowa su ya zubo wa idanu sai cewa suke ma sha Allah lalle Salim ya auro ƴar Auta kuma ƙanwar maza biyar. Ahmad da Adoul tare da abokansu suna zaune suna kallon su cike da birgewa, ana tsayar da ita Ahmad ya zaro kudi sabbin kar ya shiga filin ya dinga liƙa musu yana murmushi, ita kuwa Andizo sai murmushi take tana ƙara riƙe hannun Aliyu.. Su Ɗahare da sauran waɗanda suka zo suma sun sha ankon atamfa suka ta so suka zo filin suna yi wa Andizo liƙi wasu na rawa. Aminatou tun da ta ƙura musu idanu sai da Ummi ta dafa ta sannan ta zabura ta ce “Ummi zan je na yi wa amarya liƙi ko na bari sai sun fito da ango?” 'Yan'uwanta suka ce ta bari ango ya fito tukun ta ce to. Bayan sun gama aka mayar da amarya aka sake yi mata canjin kaya tare da gyara mata kwalliyar sannan aka kira Salim ya zo, suna haɗa idanu ya ɗauke cak ya yi sama da ita yana juyi a palon suna ta dariya, Hassana ta ce “Don Allah Yaya ka sauke ta ku fita Mamma sai kira na take waya.” Sauke ta ya yi ya kama hannunta suka fita. Suna tunkaro wajen wasu mata suka tashi ana ta zuba musu fure aka sa musu waƙar share hawayen amarya ta Umar M Sharif. “Subhanallahi!” Aminatou ta faɗa ganin yadda suka yi mugun kyau, suna tsayawa ta dinga masa magana bai ji ba hakan ya sa ya ɗago duƙa daidai tsayinta yana kallon ta, kallo irin na wanda ake matuƙar so suna magana, Ahmad ya sa mai ɗaukan photo ya ce ya musu photo a haka ai kuwa sai ganin hasken camera suka yi, Salim ya ɗago kai ya kallo wajen suka haɗa ido da Ahmad ya masa alama da ya juya, ba yanda ya iya ya juya ya kama hannunta suka dinga rausayawa nan da nan dangi aka zo ana ta musu liƙi. Bayan an gama aka buƙaci uwar gida sarautar mata ta shigo fili, gyara mata mayafi Sabrin ta yi ta zaro ɗaurin kudaden da Salim ya ba su ta ce “Ki musu liƙi da kyau ƙawata karki bari a raina miki.” Murmushi ta yi ta miƙe ta kalli wajen zaman Ummi ta ga ba ta nan, da mamaki ta ce “Ashe da gaske Ummi take gidan ta tafi?” E kawai suka ce mata ta soma takawa tana nufar su kowa ya zuba mata idanu, Salim ma ita yake kallo yana sakar mata murmushi har ta iso, kallon Andizo ta yi tana murmushi ta iso daf da ita ta rungume ta ai kuwa aka ɗauki tafi da guɗa, Andizo ta yi murmushi ta sake ta ta iso ga Salim ta rungume shi tana faɗin “Félicitation mon mari Allah ya ba mu zaman lafiya.” Bubbuga bayanta ya yi cike da farin ciki, ya jinjina wa ƙoƙarin ta ya ɗago ta ta yi saurin wayancewa ta soma musu liken kuɗi, yan'uwanta suma suka gabata zo suka ding mata liƙi har da Andizo, sosai suka birge mutane.. Bayan an gama aka tashi lafiya kowa ya ci ya sha ya koma gidansa baƙi kuma aka kai su masauki, Andizo taƙi bin Salim ta ce a wajen Ɗahare za ta zauna, bai musa mata ba dan ya san washegari kamar war haka tana tare da shi, da kanshi ya kaita har ɗakin ya gaishe su sannan ya tafi.. Kasancewar ta mugun gajiya Sallah kawai ta yi ko abinci ba ta ci ba ta kwanta bacci.. Washegari bayan sun karya suka yi shirin tafiya, Ɗahare ta janyo Andizo gefe ta mata nasiha ta ƙara ja mata kunne, ita kuwa sai ma hilla hannayenta take tana cewa “To Adda ai Hajja ta faɗa mini komai, kuma zan yi duk abin da mai hankali ya ce.” “Yawwa yarinyar kirki haka nake son ji, yanzu mu za mu tafi sai wata rana ki kula da kanki, sannan Hajja ta ce duk abin da kike so iya mijinki za ki tambaya, in ba ya nan ki zo wajen Hajiya babba saboda amanar ki Hajja ta ba ta kina ji na da kyau ko?” “E Adda ku gaishe da Maigari da su Inna.” To ta ce mata tana ɗaga musu hannu har motarsu ta tashi, wajen su Umar ta iso da suma suke shirin tafiya ta ce “Hamma ku gaida gida.” Murmushi Umar ya yi ya ce “To Autar Hajja yanzu dai an girma a daina rashin ji irin na gida kin ji, ban da fita yawo ki yi zamanki a gidanki.” Dariya ta yi ta ce “Oh ashe nima, ina da gida ban sani ba? To Hamma ina Hamma Giɗaɗo yake?” Nuna mata shi ya yi cikin mota ya jingina kansa a jikin kujera kamar mai bacci, zagayowa ta yi saitin shi ta ce “Hamma am to a gaida gida.” Buɗe ido ya yi ya kalle ta da wani irin yanayi, da kyar ya iya cewa “To Surbajo am ban da tsokana kin ga nan ba garinmu kike ba, sannan ki kula da Sallah a kan lokaci har da dare ma in za ki kwanta kike yi kin ji.” To ta ce masa sannan ta ja baya suka bar gidan, juyawa ta yi suka haɗa ido da Sabrin da suka fito daga part ɗin Aminatou, kallon tsana ta yi wa Andizo. Andizo ta wani ɗauke kai tana jan tsaki ta yi gaba, kallon farko ta ji ba ta son matar hakan ya sa ta yi saurin shigewa part ɗin Mamma. “Kut! Ki ji fa Aminatou wannan kishiyar taki tsaki fa ta mini.” “To kema ban da abin ki meye na kallon ta yarinyar da ba ta fi a kaita gidan raino ba? Ba ki ga ni ban kalle ta ba girmana zan kama na riƙe ta yadda za ta mini biyayya haka Ummi ta ce na yi.” Tsaki Sabrin ta yi ta wucewar ta.. Da dare aka shirya Andizo aka kai ta ɓangaren su Salim, in da aka fitar mata da ɗakuna huɗu da Palo biyu babba da ƙarami sai banɗaki uku, sosai gidan ya tsaru duk wani kayan more rayuwa Salim ya zuba mata, saboda ya cewa su Maigari kar su wahalar da kansu shi zai yi mata komai. Hajiya Babba ta gama yi wa Andizo nasiha duk suka fita aka janyo mata kofar suka kulle ta ta baya. Tana nan zaune a tsakiyar gadon ta ji zaman ya ishe ta ta yaye mayafin ta fito Palo ta zauna a kan kujera, ruwan da Hajiya Babba ta kawo mata ta ɗauka tana sha ta ji ƙarar buɗe kofar, yi ta yi kamar ba ji ba. Da sallama ya shigo hannnunsa ɗauke da leda, mamaki ne ya kama shi ganin amarya a palo ta miƙe ƙafa ko ɗankwali babu a kanta, da dariya ya iso tsakiyar palon ya aje kayan ya tsaya yana kallon ta. Ɗago kai ta yi suka haɗa idanu ta sakar masa murmushi, hakan ya ba shi damar yin magana cike da tsokana. “Gaskiya ma femme ba ki da kunya, ke yanzu ko kukan rabuwa da dangi ba ki yi ba? Kuma ke da zan ganki a ɗaki sai kuma na zo na ganki a waje?” Murguɗa masa baki ta yi ta miƙe tare da rike ƙugu ta ce “Yo to so kake zafi ya mini illa? To alƙur'an dole ne ya fito yo ina dalili ni ba mayya ba a kimsa ni a ɗaki a rufe, ko an ce ma ni baƙuwar boka ce?” Tana gama faɗin haka ta sa kuka ta nufi ɗaki da sauri, cikin hanzari ya bi bayan ta yana kiran sunanta amma kafin ya zo tuni ta rufo kofar, da karfi ya tura kofar ta buɗe ya hango can tsakiyar gado ta yi ruf da ciki tana kuka. Gadon ya hayo ya ɗago ta ai kuwa ta birkice ta faɗin “Ba ni ba ce ba ni da kunyar? Alƙur'an in na kwana gidanka in zama karas..” _Maman Nusaiba ce🤙🏻_ [5/29, 2:07 PM] Ummu Amjad: _*AREWABOOKS@SARATALKASUM88*_ 23 Kallon ta kawai yake tana kai masa duka ta ko'ina, sai da ta gaji dan kanta sannan ta daina tana huci ta ce “Ni ka tashi ka kaini wajen Hajiya Babba ba zan kwana a nan ba..” Ta faɗa tana jan hunnunsa ta sauka daga kan gadon. Janyo ya yi ta yo baya ya zaunar da ita, a tausashe ya soma mata magana a daidai saitin kunnenta cikin kihima yadda za ta yi laushi. “Haba matar Salim meye na rigima da daren nan? Ba dai gidan Hajiya babba kike son komawa ba?” Gyaɗa masa kai ta yi tana turo baki gaba, hannu ya sa ya shafa bakin ya ɗora da cewa “Ai su gidansu ba shi da kyau irin nan, kinga fa duk girman wajen nan naki ne da duk abin da yake ciki har tv ga shi can a palo, idan kina so kike kallo ina kaiki makaranta ki daina rigima kin ji kuma ban da ƙin bin umarnina.” Ya ƙarashe maganar yana ɗago da ita jin ta saki jiki ta daina kukan, kallon ta ya yi itama ta kalle shi sai ta sa dariya tana tashi tsaye, gadon ta hau tsakiya ta soma tsalle tana faɗin “Kai Alƙur'an gadon nan akwai daɗin hawa, zan dinga haya abuna ina shan daɗin katifa.” Dariya shima ya yi ya tashi ya ce “To zo mu je mu yi Sallah mu gode wa Allah da ya ba mu ikon zama mata da miji.” Har za ta yi gardama ta tuna alƙawarin da ta yi wa Hajja sai ta sauko ta rike hannunsa suka nufi banɗaki.. Makilin ya ba ta ya ce ta goge bakinta, kallon shi ta yi tana cewa “Goga haƙorin zan yi ko na haɗa da ruwa na tofar?” Nasa ya ɗauko ya sa makilin ɗin ya nuna mata yadda ake yi, to ta ce ta goge itama ya ce ta yi alwala yana nan zuwa. Alwalar ta ɗaura tana kallon banɗaki domin ya birge ta kwarai da gaske, fitowa ta yi ta same shi ya shinfiɗa darduma yana jiran ta. Ba ta ce masa komai ba ya buɗe wardrobe ya ɗauko mata hijabi ta sa ya ja su Sallah, bayan sun gama ya dafa kanta ya dinga jero musu addu'oin samun zaman lafiya da kawar da fitina a tsakanin su. Tambayoyi ya mata game da addini ta dinga amsa masa tana wani kawar da kai, bayan ya gama suka yi addu'a suka shafa ta tashi ta cire hijabin har ɗankwali ta kalle shi. Murmushi ya mata ta ce “Mai hankali yanzu ni a nan ɗakin zan kwana?” Gyaɗa mata kai ya yi sai ta rausayar da kai ta ce “Kai fa ina za ka kwana?” Da hannu ya nuna gadon ta zaro ido ta ce “Gadon nawa ne za ka kwanan mini a kai? To ba zai yiyu ba ka sa katifar ta lomaƙe da wuri, kalle ka fa babba da kai..” Dariya ya yi ya girgiza kai ya tashi ya fita a ɗakin a tunaninta ya tafi inda zai kwanta ne, har ta haye gadon ta ga ya shigo da ledojin da ya shigo da su ɗazu, kallon shi ta yi sai ta ji ƙamshin kaza ya kawo mata ziyara ta yi saurin saukowa ta iso gaban shi ta sa hannu ta amshe ledar. Waje ya samu ya zauna ya ce “Nasan kina jin yunwa amma tashi muje ku gaisa da Aminatou sannan mu dawo.” Shuru ta yi tana tunani can ta kalle shi ta ce “To matarka kenan?” E ya ce mata ta samu gefen gado ta aje ledar ta ce “To mu yi sauri mu dawo ni dai bacci nake ji mai yawa.” To ya ce mata ya ce ta sa hijabi amma ta ce ita fa zafi take ji su tafi a haka kawai, ba yadda ya iya dole suka tafi kanta ko ɗankwali baki.. Aminatou na zaune a palo suna waya da Sabrin tana sanar da ita ai tun tuni Salim ya shige sashen amarya bai fito ba ko ya zo ya duba ta kafin ya shiga. Suna tsaka da maganar ta ji ana kwankwasa mata kofa, da sauri ta tashi ta ce “Sabrin ga shi nan ya zo.” “Yawwa ki san yadda za ki hana shi kwana a can wajen yarinyar.” Murmushi ta yi ta amsa da to sannan ta kashe wayar, buɗe ƙofar ta yi a hankali tana miƙa irin bacci ya soma ɗaukan ta, kallon su ta yi tana murmushi ta ce “A a haba ya za ka ɗauko amarya ka zo da ita bayan ta gaji? Wannan ai ɗaukan alhaki ne, da ganin ta bacci take ji ko Khadija?” Ta faɗa tana kallon Andizo da ta riƙe hannun Salim tana wasa da zoben da ke yatsarsa. Kallon ta Andizo ta yi ta ɗaure fuska ta ce “Ai sai da na ce masa bacci zan yi ya tafi wajen kwanan shi ya ce zai kawo ni mu gaisa.” Ta faɗa tana kumbura baki. “Gaskiya dai bai kyauta miki ba ƙanwata amma tun da kun zo ai sai ku shigo a gaisa ko?” Kallon su Salim ya yi yana murmushi ya ce “ To ai sai ki ba mu waje mu shiga ko.” Dariya Aminatou ta yi ta matsa suka shigo, a kan kujera suka zauna Salim ya gyara zama ya soma musu nasiha.. “Abin da ya sa na ce mu zo dan na ga lafiyarki kuma na miki godiya a kan namijin ƙoƙarin da kika yi a wannan lamarin, Allah ya miki albarka ya sa mu a gidan aljanna.” “Amin ya Rabbi, a haba dai meye kuma na godiya sai ka ce ni na ba ka kuɗin auren ko na biya sadaki?” “Haka nan ma naji daɗi yadda kika ba ni gwarin gwiwa, Aminatou ga Khadija nan ina so ku zauna lafiya nasan daga ke har ita babu mai matsala a cikin ku, amma Bahaushe ya ce yau da gobe ta fi ƙarfin wasa, kuma an ce zo mu zauna zo mu saɓa, Khadija yarinya ce duk yadda kika bi ta a haka za ta dauke ki, ki kama girmanki saboda ta dinga ganin ki da girma a ko'ina, sannan ki ba ta matsayin ta na ƙarama kema Khadija ki girmama ta ki ba ta matsayin ta na wadda ta girme ki, ba na son fitina ko wasu abubuwan da za su kawo rikici, Allah ya muku albarka..” Andizo da ta yi lamo a kan kafaɗarsa ta ce “In sha Allah zan ba ta girman ta, ai Hajja ta ce duk wanda ya girme ni na girmama shi na masa biyayya, amma in na ga yana zubar da girman shi na take na wuce, kuma ta ce duk abin ka umarceni kar na yi muso ko na ce ba za yi maka ba, har ita Aminatou Hajja ta ce na dinga zuwa ina gaishe ta da safe kuma na mata biyayya tun da ita ce uwar gida, kuma kar na mata rashin kunya kar kuma dan ina mata biyayya ta ce za ta mayar da ni baiwa, in tana mini haka to na daina mata biyayyar.” Ta faɗa tana turo baki gaba.. Duk da Aminatou ta ji haushin wasu daga cikin kalaman Andizo amma ta ji daɗi da aka ce ta mata biyayya ta ba ta girman ta na uwar gida, murmushin yaƙe ta yi ta ce “Karki damu Khadija in sha Allah ba mai jin kanmu kin ji.” To ta ce daga haka ba ta kuma cewa komai ba, Salim ya miƙa wa Aminatou ledar da ya shigo da ita ta amsa ta mishi godiya, ganin zai tashi sai ta dinga jan shi da hira.. Wasa-wasa ta hana shi tafiya sai narke mishi take ƙarshe ma kuka ta sa mishi ta ce za ta yi kewar shi na kwanakin da zai yi a ɗakin Andizo, shi kuwa da ba ya son ganin hawayenta ya dinga rarrashin ta yana ba ta haƙuri, yayin da ita kuwa Andizo ta daɗe da yin bacci kanta a kafaɗarsa ta zayaye hannayenta a cikinsa. Sai da ƙarfe 12 daidai ta buga ya kalli agogon palon cike da mamaki ya ce “Kai ashe dare ya yi bari mu wuce ita har ta yi bacci.” Tashi ta yi tsaye tana cewa “E Wallahi ka yi hakuri fa na hana ku tafiya hirar ce ta mini daɗi.” Ba komai ya ce mata ya ɗago da Andizo ya soma tashin ta, a hankali ta buɗe idanuwanta ya ce “Mu je ki kwanta.” miƙar da ita ya yi tsaye ya tashi ya kama hannunta suka nufi kofar fita Aminatou na biye da su, suna isa bakin ƙofa Andizo ta yi ƙasa ta jingina da ƙafar Salim ya yi saurin ɗago ta, ganin bacci ya ci ƙarfin ta ya sunkuya ya ɗauke ya saɓa ta a kafaɗa ya yi wa Aminatou sai da safe sannan ya fita ta rufe ƙofarta.. A jikin ƙofar ta tsaya tana tuna yadda Salim ya sunkuya a gaban ta ya ɗauki wata ya haɗa ta da jikinsa ya yi ficewar shi, fashewa ta yi da kuka ta isa kan kujera ta ɗauki pilo ta rungume tana tsine wa Andizo.. Suna shiga ya kwantar da ita ya je ya shirya cikin kayan bacci ya dawo, kayan bacci ya ɗauko ya cire mata na jikinta ya sa mata riga da wando farare sol, wandon bakin gwiwa rigar ƴar ƙarama ko cikinta ba ta ida rufewa ba. Tsayawa ya yi yana ƙare wa surar jikinta kallo, sosai ta masa kyau a cikin kayan ya hayo gadon ya kwanta tare da ɗauko ta ya kwantar da ita a kan ƙirjinsa ya lumshe idanu.. Bacci yake son yi amma ya kasa saboda yadda take juyi son ranta a kanshi, dole ya juya ya kwantar da ita ya rungume ta sai kusan asuba bacci ɓarawo ya kwashe shi, saboda ko runtse ido ya yi surar jikinta yake gani zuciyarsa na ingiza shi amma ya danna yana girgiza kai ya rufe ido da ƙarfi har ya yi bacci.. Kiran Sallah ne ya tayar farkar da Andizo, miƙa ta dinga yi tana salati ta buɗe idanuwanta ta ga mutum ya kanannnaɗe ta, kallon kayan da ke jikinta ta yi tana mamaki yadda aka yi aka canja mata wanda ta yi bacci da shi.. Tsura masa idanu ta yi tana kallon yadda yake fitar da numfashi yana zuƙa, a hankali ta kai hannu ta taɓa kwantacciyar girar idonsa. Tun da ta farka shima ya tashi amma ya yi shuru kamar bai tashi ba, tana ɗauke hannunta ya buɗe ido suka kalli juna ai kuwa ta juya fuska da sauri tana cewa “Kawai dai birge ni ne ta yi shi ya sa na taɓa.” Janyo ta ya yi ya mata kiss a goshi, cuno baki ta yi ta soma tirje-tirje ta ce “To ni dai ka daina mini wannan ab..” Ba Ta ƙarasa ba sakamakon bakinta da ta ji cikin nasa, ta zaro ido tana ƙoƙarin kwacewa amma ta kasa dole ta saki jiki kamar wadda aka zare wa lakka ta yi ɗaiɗai a jikinsa. Haka ya yi ta juya ta son ransa jin yana neman wuce gona da iri ta mirgino daga jikinta ta koma gefe ya biyo ta, da kyar ya iya controle kansa ya sake ta yana mayar da numfashi. Hannu ta sa ta rufe idanu tana shafa bakinta ta hankali ta ce “Ni dai alƙur'an karka cinye mini bakina, wannan ai maita ce mai lasisi.” Ta faɗa tana tashi zaune. Hannu ya sa ya janyo ta jikinsa ya tsura mata idanu, kumatunta ya shafa ya ce “Khadija wannan ai ba maita ba ce, komai naki nawa ne kar kike bijire mini kin ji.” “Yo to ni da ba maiya ba ta ya zan yarda da wannan abin, ai ƙazanta ce ma wannan kai ko kunya ba ka ji ma kake tsotse mini baki?” Dariya ya yi ya tashi da ita a jikinta ya saɓa ta a kafaɗa ya sauko ya nufi banɗaki. Har banɗaki ya kai ta ya ce shi zai tafi masallaci ta yi Sallah ta amsa da to sannan ya fita.. Bayan ta fito ta sa hijabi ta yi raka'atainun fajur, tana zaune tana lazimi ta ji an tayar da iƙama ta miƙe ta gabatar da Sallah. Bayan ta gama ta yi addu'oi ta shafa ta tashi ta cire hijabin ta faɗa gado saboda barci ba isar ta ya yi ba. Sai ƙarfe 7:am ya shigo ɗakin ya same ta ta yi ɗaiɗai tana sharar bacci, jallabiyarsa ya cire shima ya kwanta suka ci gaba da barci.. Ba su tashi ba sai ƙarfe goma ya ce su je ya mata wanka ai kuwa ta dinga dariya tana kallon shi, kama hannunta ya yi ya ce “To muje na miki wanka mana rana ta yi.” Maƙale kafaɗa ta yi ta ce “Tab haka kawai sai na yarda ka mini wanka da girma na da komai? To ni dai alƙur'an ba zan yarda da wannan abin ba sai ka ce wata ƴar is...” Shuru ta yi ta koma ta zauna tana murguda masa baki. Zama ya yi a gefen ta ya ce “To ai ba haramun ba ne dan na miki wanka, malaminku ba ki ji yana cewa tsakanin mace da miji babu kunya ba? Kuma ba lefe dan sun ga jikin juna?” Kai ta ɗaga sama alamar tunani, can ta kalle shi sai ta tashi ta ce “To muje.” Gaba ta yi ya bi bayan ta har banɗakin, da kyar da lallami ta yarda ta cire kayan ya mata wanka fes ya naɗo ta a towel ya kawo ta ya aje ya koma shima ya yi. Mai ta shafa tana ƙoƙarin yin kwalliyar da ta saba ya hana ta, da kanshi ya dauko fauda ya shafa mata kaɗan ya ce ta sa kwalli, amsa ta yi ta sa ta yi ɗigo ɗaya a goshinta ya ce ya isa haka.. Palo suka fito inda suka samu an kawo musu abinci daga gidan Mamma, janta ya yi suka zauna a ƙasa sai ya tuna kazar jiya ya tashi ya shiga ya ɗauko ya sa a freeze. Yana buɗe kular ya ga soyayyiyar doya ce da kwai sai kayan shayi, ɗayar kular kuma farfesu ne yana tururi. Andizo da son cin nama ta ce ita shi take so, plate ya ɗauko ya zuba mata ya haɗa shayi ya aje a gaban ta ya yi bismillah ya soma ba ta a baki ba muso ta dinga amsa.. Bayan sun gama ya ɗauke kwanukan ta taya shi ɗauke wa suka wanke wanda suka ɓata, kallon juna suka yi ya sakar mata murmushi itama ta mayar masa.. Suna zama ta ce ya kunna mata tv tana son yin kallo, ya kunna ya kawo mata arewa24 suna kan yin shirye-shiryen su ai kuwa ta gyara zama.. Sai da Andizo ta yi kwana huɗu ko nan da ƙofar gida bai barta ta fita ba, ba ta komai sai dai ta sha bacci in ta tashi ya mata wanka ya shirya ta su dawo palo ya kunna mata kallo, idan kuma yan rigimar sun tashi sai ta ce sai ya goya ta ba yadda ya iya haka yake goya ta ya yi ta zagaya palon da ita tana dariya.. Yau suna zaune aka kira shi wajen aiki kiran gaggawa, ganin tana kallo sai ya ce “Baby ki zauna zan je na dawo an kira ni wajen aiki, idan kuma na kaiki wajen Aminatou to tashi na kaiki ko wajen su Mamma.” Girgiza kai ta yi ta ce “A a sai ka dawo ni ban gama kallo na ba.” Ficewa ya yi ganin hankalinta gabaɗaya yana kan tv... “Hello sir na binciko maka gaskiyar magana game da girlfriend ɗin ka, da gaske ne an yi mata aure tana cikin garin nan, amma ba mu san a wani waje take ba sai dai in mun bincika..” Sultan da ba su jima da tashi daga buga kwallo ba ya yi sharkaf da zufa yana cire safar kafarsa jin maganar ya yi kamar saukar aradu, miƙewa ya yi tsaye ya ce “ What? Anya kuwa ka yi bincike da kyau, ni fa ban kama maganar Farrah ba ka ga ita yarinya ce duk da ta je ta yi kwana biyu a can.” Girgiza kai Bansh ya yi ya tashi tsaye ya ce “Ba ƙarya ta faɗa maka ba tabbas wajen auren aka kaita.” “Bansh ina so ka binciko mini ko ɗan gidan waye shi wanda ya aure ta, da auren nawa a kanta za ta bari a aura mata wani auren saboda Mom tana son ganin mutuwa ta? Wallahi in na ga wanda ya aure ta sai na binne shi a ransa, maza ina jiran ka, sati na ba ka ka gama binciko mini duk wani abu da shafe shi.” Ya gama faɗin haka aje wayar sai kaiwa da komowa yake yana ciza yatsa. Sam shi bai ɗauka da gaske Farrah take ba domin har labarin kyau da tsaruwar gidan Andizo take faɗa masa amma ya yi banza da ita, kallon shi Jamil ya yi ya ce “Man what happing?” Iska mai zafi ya fesar a yadda yake ji ba zai iya tsayawa yin doguwar magana ba, hakan ya sa ya wuce ɗaki duk taku tsaya ji yake ana zage masa lakkar jiki da kyar ya isa ɗaki yana dafe ƙirji. Freezer ya buɗe ya ɗauko kwalbar giya ta yi sanyi sosai ya buɗe ya ɗaga ta sama ya dinga kwankwaɗa, sai da ya kusa shanyewa sannan ya janye yana huci, a hankali ya miƙe yana tangaɗi ya faɗa kan gado sai bacci.. Sanye take da riga da wando ta yi fresh da ita, tana zaune a palo ba ta jima da dawowa daga sashen Mamma saboda can ta wuni kasancewar Salim ya koma bakin aiki. Kwankwasa ƙofar aka yi ta tashi da sauri tana cewa “Da aka jima ba ka zo ba da wajen hajiya babba zan koma.” Ta faɗa tana buɗewa. Ganin waɗanda suke tsaye sai ta matsa gefe tana cewa “Adda kune? To ku shigo.” Murmushi Aminatou ta sakar mata suka shiga ciki, zama suka yi ta tashi ta kawo musu ruwa da lemo ta zuba musu sannan ta koma ta zauna, Aminatou ta ɗauka ta kurba itama Sabrin ta sha, kallon ko'ina suke na palon can suka ga babban photon Andizo da Salim na ranar dinner su, Sosai suka shagala da kallon shi har sai da Andizo ta soma gaishe da su suka kawar da kai. Sabrin na yatsina fuska ta tashi ta ce “Bari mu je mu ga ɗakin kwanan amarya.” Amiantou ta yi dariya tana gyara zama, ita kuma ta wuce ba ta bari an yi mata izini ba ta nufi ɗakin. Da sauri Andizo ta sha gaban ta tana haɗe fuska ta ce “Ke kuma a su wa da kike son shigar mini ɗakina? Ai sai ki bari ma na miki izini ba ki yi gaban kanki ba kamar gidanki?” Baki Sabrin ta riƙe ta ce “Kan bala'i! Ke ni kike yi wa gorin gida? Banza ƴar ƙauye kucaka, in ban da ma namiji ga mata a gari nan na faɗi ya je ƙauye ya kwaso wannan jaririyar.” Andizo ta ji haushi ce mata kucaka da ta yi ta ce “Wallahi ke ce kucaka ba ni ba, na rantse dan kin ci darajar Adda Aminatou da ba dan haka da tuni na haɗa miki jini da majina, ki koma ba za ki shigar mini ɗaki ba..” Ta faɗa tana tura ta baya.. Zaburowa ta yi cike da haushin abin da ta mata ta ɗaga hannu za ta kifa mata mari ta ji an ce “Kika kuskura kika mare ta sai na ga uban da ya daure miki gindin shigowa har gida ki ce za ki ɗaki matar gidan..” Next fage _Maman Nusaiba ce🤙🏻_ [5/31, 12:14 AM] 577675904: _*AREWABOOKS@SARATALKASUM88*_ 24 A firgice Sabrin ta juyo jin muryar wanda duk cikin maza shi kaɗai take jin tsoro, wani irin kallo ya watsa mata yana takowa ya ƙaraso tsakiyar palon, a wulaƙance yake kallon ta har ya samu waje ya zauna. Ƙafafuwanta ne ta ji suna neman kasa ɗaukar nauyinta ta ja su a hankali ta matsa daga kusan Andizo jikinta na rawa, yadda take tsoron shi ko iyayenta ba ta musu kalar tsoron da take masa, baki na rawa ta ce “Babu abin da na mata kawai magana muke.” Baƙin glass ɗin sa ya cire ya kalli Andizo ya ce “Khadija Allah ya miki albarka tun da har kika san cewa ɗakin kwanan ku ke da mijinki sirrinku ne ba wanda yake da ikon shiga daga ke sai Yaya Salim, ke kuma ballagazar mata a tunaninki kowacce mace ma irin ki ce mai barin ƙawa tana shiga ɗakin baccinta? Wallahi duk iskancin da kuke ji zan sauke muku shi matuƙar kuka ce za ku shiga rayuwar Khadija ku takura mata, zai zo shi yaya Salim ɗin ko shi kansa sai na masa gargadi na kuma gindaya masa sharruɗa a Khadija, idan ya bari wannan banzan hannun naki ko na karuwar ƙawarki ya taɓa jikinta sai na kakkarya ku daga ke har ita, ke ko shi Salim ɗin ba zan bar shi ba sai na masa rashin mutumci..” Ya faɗa yana nuna su da tsaya.. Andizo da ta yi tsaye tana kallon su ya yafito ta da hannu ta yi saurin isowa kusan shi ta zauna a ƙasa, cikin ladabi ta ce “Ina kwana Yaya Ahmad? Ya makaranta?” Murmushi ya sakar mata ya ce “Lafiya ƙalau matar Yaya, tashi mu tafi mijinki ya ce na kaiki office ɗinsa ba zai dawo ba yau da wuri, kuma ba ya so ya yi naisa da ke.” 'Yar dariya ta yi tana tashi tsaye ta riƙe ƙugu ta ce “Kasan Allah dama ina so naga inda mai hankali yake aiki, bari na ɗauki mayafina sabon mu tafi, amma ni dai ka faɗa wa waccan ƙatuwar matar kar ta kuskure tsautsayi ya sa ta shigar mini ɗakin da muke bacci ni da mai hankali, domin Hajiya Babba ta ce ko ƙawa na yi kar na bari ta shigan mini ɗakin bacci, ballantana ita da ban san daga inda ta fito ba. Adda Aminatou tana ganin ta za ta wuce amma taƙi hana ta.” Ta faɗa tana kallon Aminatou da baƙin cikin gasa mata magana da Ahmad ya yi ya hana ta cewa komai, tsare ta ta yi da kallo tun daga sama har ƙasa, ta matso kuma da ita tana ƙanƙance idanu masifar ta taso ta ce “Amma ai tun da na zo gidan nan da muka je ɓangarenki sai da na faɗa miki abin da Hajja ta faɗa mini ko? To yanzu kin ɓata mini rai sau ɗaya ba komai, idan kika sake barin wannan ta zo in da nake zan daina miki biyayyar da aka ce na dinga miki tun da kin girme ni..” Wani abu ta ji ya tsaya mata a maƙoshi da kyar ta haɗiye ta kalli Sabrin ta juya da sauri itama ta mara mata biya suka fita fuu kamar za su tashi sama. Tsaki Ahmad ya yi yana cewa “Makira kawai in ba ki yi hankali ba sai ta kaiki ta baro banza kawai.” Ɗaki ta nufa da gudu ta ɗauko mayafi ta yafa, ganin yadda ta yi ya yi dariya ya ce “Nan fa ba ƙauye ba ne Khadija, Salim ya ce ki saka hijabi ba ya son kowa yake kallon masa matarsa..” Turo baki ta yi ta koma ta sako hijabi ya miƙe ya kashe wutar palon ya ce ta koma ɗaki ta kashe hasken ciki, kasancewar Salim ya kowa mata da gudu ta koma tana murna yau za ta ga gari ta kashe ta dawo suka tafi.. A fusace Aminatou ta shiga part ɗinta tana huci, Sabrin na isowa ta kalle ta cike da ɓacin rai ta ce “Haba Sabrin ya za ki ɓata mana shiri? Kawai daga zuwa sai ki ce mata za ki ga ɗaki yanzu ga shi za ki ja ganin girmana da take ya ragu a idanunta, Khadija fa mai sauƙin kai ce musamman in kika ja ta hira sai da na faɗa miki amma kika kwaɓa mana aiki,. Wallahi na tabbata da da hira kika ja ta babu abin da zai hana ta kaimu ɗakin mu gama abin da muke ba ta sani..” Ta faɗa tana zama tare da dafe kai ta sake ɗagowa ta dora da cewa “Nasan sai ta sanar da Salim abin da kika mata, ga shi yana ɗaukar maganarta da muhimmanci saboda ya ce ita ba ta ƙarya duk abin da za ta faɗa to an yi shi..” Maƙale kafaɗa Sabrin ta yi tana gyara zaman mayafinta ta ce “Ke kinga kar fa daga na zo na taimake ki ki mini rashin hankali, tun da haka ne daga yau na daina zuwa gidanki ki nemi wanda zai ci gaba da nema miki magani ba dai ni ba..” Tana gama, faɗin haka ta juya da sauri ta wuce. Tsaki Aminatou ta ja ta miƙe tsaye tana zarya, sam ba ta son Salim ya gano ba ta son Andizo saboda yardar da ya yi da ita ɗari bisa ɗari, ɗaki ta shige ta rufe kofar tare da dannawa Salim kira.. Yana ɗauka ta sa kukan ƙarya ya shiga tambayar ta, “Lafiya kike kuka? Ko wani abu ya faru bayan na fito?” Zama ta yi a bakin gado ta ce “Mijina ban san wani tsautsayi ya sa naje ɓangaren Khadija da Sabrin ba, shi ne fa suka samu matsala..” Da mamaki ya ce “Sabrin kuma? To ita me zai haɗa ta da Khadija daga zuwa?” “Kasan Khadija yarinya ce babu ruwan ta da ko mutum ya girme ta in ta yi niyar magana ba mai hana ta kaima kasan da haka, ita Sabrin ta dage sai mun je ta yi wa Khadija Allah sanya alheri na ce ta bari ka fita sai ka dawo, da ta takura dai muka shiga. Shi ne fa ta ce tv palona ya fi na Khadija kyau da komai nata, to shi ne fa Khadija ta fusata Allah ya kawo Ahmad ya ɗauke ta, ya ce mini wai ba za ka dawo da wuri ba yau kuna da aiki har dare..” Ajiyar zuciya ya sauke ya ce “Wallahi har kin tayar mini da hankali, yanzu saboda wannan abin ne kike zubar da hawayenki? Zan nuna mata in an zo ganin gida kar ta yi faɗa da kowa, amma itama ta ya za ta ce mata kayanki ya fi nata kyau a gaban ta? Wannan ai neman tada zaune tsaye ne, ba ƙaramin aikin Khadija ba ne yanzu da sun zo ta birkice ta ce sai na canja mata kayan palo na mata irin naki. Sai an jima ga Ahmad yana kirana ki kula da kanki..” Murmushin samun nasara ta yi ta ce “To mijina ina sonka sosai Allah ya tsare sai kun dawo..” To ya ce yana dariya ta kashe wayar, hamdala ta yi ta kwanta... Tun da suka fita Andizo da ta yi baya ta kwanta jikin kujera ba ta ce uffan ba, saboda Salim ya ce mata ko wane ne in dai namiji ne kar ta kuskura ta dinga magana da shi ko da kuwa Ahmad ne ta yi shuru. Kallon ta Ahmad ya yi cike da mamaki ganin ba ta ce komai ba, tunani ya yi ko dai akwai abin da suka faɗa mata wanda ya mata ciwo shi ya sa ta yi shuru, gyaran murya ya yi ya ce “Matar Yaya lafiya kika shuru?” Turo baki ta yi tana hararar shi ta ce “So kake na karya alƙawari?” Da mamaki ya ce “Wani, irin alƙawari kuma Khadija?” “Mai hankali ya ce kar na kuskura ko da kaine nake hira da kai rahamun ne tun da ni matar ce, dan haka ka rabu da ni kar ka ƙara yi mini magana, idan kuma kana son yin magana da ni to ka kira shi a telephone idan ya amince sai na yi magana da kai.” Dariya ya yi ya miƙa hannu ya ɗauki waya ya danna wa Salim kira, yana ɗauka ya ci gaba da dariya yana faɗin “Mai hankali shirin Allah Angon Andizo uwar masu gari.” Murmushi Salim ya yi yana gyara tsayuwar shi ya ce “Gani ba saƙo ba, da wa kuka yi gardama a raba muku? Ina Khadijar tawa take?” “Ga ta nan tana cika tana batsewa kamar fulawa, kai ka ce mata kar ta yi magana da kowa in dai mutum namiji ne? To a ba ni izini na tambaye ta abin da take son ci na sayo muku..” Shafa sajensa ya yi ya ja numfashi ya ce “To na ba ka, izini ka yi magana da ita, amma kar ta yi yawa dan ba na son kowa yake jiye mini muryar matata.” Kallon ta Ahmad ya yi yana cewa “To yaya sai mun ƙaraso.” To ya ce masa sannan ya kashe kiran.. “To matar yaya ya ce ya ba ni izini na yi magana da ke, me kike son ci?” “Ni marmarin masa da miya nake.” Zaro ido Ahmad ya yi yana yin packing a bakin Restaurant, kallon ta ya yi ya ce “Khadija nan fa ba ƙauye ba ne, ina za mu samu masa a nan.” “To sayo mini duk abin da ka gani.” To ya ce mata ya fita sai kuma ya buɗe mata ya ce ta fito su shiga ta ga yadda cikin yake, da sauri ta fito dama ranta na son ganin abin da yake ciki. Shawarma da kaza ya sayo musu, Andizo ta soma kalle-kalle Ahmad ya sunkuya a hankali ya ce “Karki dinga kalle-kalle a sace ki.” Da sauri ta dawo gefen shi tana kallon wani matashin saurayi, tun da ta sanyo kai cikin restaurant ɗin ya kafe da kallo, kalaman Ahmad ya sa ta ji tana tsoron wannan matashi. Yana gama biyan kuɗin ya yi gaba ta biyo shi da sauri suka fito, kafin ya isa ta riga shi ta buɗe motar ta shiga tana dafe ƙirji. Dariya ya yi ya ce “Matsoraciya kawai.” Murguda masa baki ta yi suka wuce.. Tun da suka fito Andizo ta dinga kallon waje, hakan ya sa Ahmad ya buɗe mata glass yana ce mata ƴar ƙauye ta zo birni ta ce eh ɗin ai ba shi ya kawo ta birnin ba. Kamar an ce ta kalli madubin jikin motar ta ga wata baƙar mota na bin su, ba ta kawo komai a ranta ba ta kawar da kai sai dai hankakinta bai kwanta ba. Sake dubawa ta yi ta ga duk in da suka bi motar na bin bayansu, ta dawo ciki tana cewa Ahmad “Ka ga wata mota na bin bayan mu tun da muka tafo daga wajen masu abinci..” Hannu Ahmad ya kai ya gyara madubin gefen shi ya hango motar na biye da su, gudu ya dinga yi amma still tana bun su, abin ya ba shi mamaki sai ya samu waje ya yi packing dan tabbatar da su ɗin suke bi ko kuwa dai rainin hankali ne irin na wasu matasan.. Yana kallon su suka zo wucewa madubin motar a buɗe yake, hakan ya ba shi damar ganin su biyu ne duk sun saka facemark haɗi da glas. Sai da ya tabbatar sun yi nisa sannan ya canja hanya, sosai yake mamakin kallon da suke mishi, ita kuwa Andizo takurewa ta yi a jikin kujera da ta runtse ido wannan gardi take gani yana kallon ta, sosai abin ya yi tasiri a zuciyarta tsoro ya baibaiye ta kafin su isa sai rawar ɗari take. Hankalin Ahmad bai kawo kanta ba saboda burinsa bai wuce ya kai ta wajen Salim ya dawo ya ƙara bincikar masu motar nan.. Yana gama packing a wani babban wajen shaƙatawa ya kalle ta, dariya ya yi ya ce “Matsoraciya tashi mu je.” Da kƴar ƙafafuwanta suka iya daukar nauyinta ta bi bayan shi sai waige take duk ta firgice, can ta hango shi cikin matasa sun kai goma kamar wadda aka tsikara ta kwasa a guje ta nufe shi. Abdoul ya matsa daga kusan Salim ya ce “Ku matsa daga nan ga amaryar Oga nan ta zo.” Kallon ta yake da kyau yana nazarin fuskarta, tashi ya yi tsaye ya taro ta suka haɗe da wani irin sauri ta faɗa jikinsa ta ƙanƙame shi ta fashe da kuka, ƴar dariya ya yi a tunaninsa kewar shi ce ta sa ta kuka, sai da ya ji kukan na gaske ne sannan ya ɗago ta ya ga yadda jikinta yake ɓari. “Subhanallahi! Ma femme lafiya kike kuka ? Waye ya taɓa mini ke ya amshi hukunci?” Saurin komawa ta yi ta kuma ƙanƙame shi idanuwanta a rufe sai kuka take, hakan ya sa Abdoul ya kalle su ya ce “Hmm ai amaryar can ta Salim ba dai rigima ba, ku kalla fa daga zuwa duk ta sa ya susuce kamar ba Soja ba..” Na gefen shi ya ce “Yo ita mace ina ruwan ta da wani muƙaminka in dai ta shirya rikita ka, ko kai shugaban ƙasa ne idan kana gaban ta kallon sa'anta take maka.” Dariya suka sa suna faɗin “Ai kuwa dai to muma Allah ya aurar da mu.” Ɗaukan ta ya yi suka koma ɗayar shinfidar da babu koma a kai, zaunar da ita yake ƙoƙarin yi amma sam taƙi yarda ya aje ta, hankalin Salim ya tashi dan bai taɓa ganin ta a cikin wannan yanayin ba sai yau. Ƙara rungume ta ya yi a hankali ya tashi ya saɓa ta a kafaɗa ya nufi motarsa, su Abdoul na tsokanar shi ya yi banza da su.. Saka ta ya yi a motar ya zagayo ya shigo ta yi saurin ruƙo hannunsa tana shasshekar kuka, cikin wani kalar yanayin damuwa ya ƙura mata idanu, hannunta ta ɗaga masa irin na yaro in yana so a ɗauke shi, ba yadda ya iya ya janyo ya ya rungume a cinyarsa ya tayar da motar suka bar wajen. Yadda take shigewa jikinsa duk ta hana shi yin tuƙin da kyau Allah dai ya kaisu lafiya bakin wani hôtel, ya fito da ita ya kulle motar ya nufi ciki. Masu tsaron wajen suka sara mishi kai kawai ya jinjina ya wuce, duk wanda ya haɗu da shi sai ya kalle su.. Sai da ya kaita har kan gado sannan ya aje ta, zama ya yi ta matso da sauri ta ɗaura kanta a kan cinyarsa murya na rawa ta ce “Ma.. Mai hankali don Allah ka kaini garinmu kar su sake sace ni.” Hannu ya sa ya cire mata hijabin ya gyara mata kwanciyar, a hankali ya shiga shafa kanta yana tofa mata addu'a lura da ba ta cikin haiyacinta. Ajiyar zuciya ta dinga saukewa ɗaya bayan ɗaya tana ƙara riƙe shi, har ya ɗauki waya zai kira Ahmad sai kuma ya fasa ya ci gaba da mata addu'a. Sai da ya tabbatar ta daina sumbatun sannan ya sunkuya saitin kunnenta ya ce “Dijan mai hankali.” Buɗe idanuwanta ta yi ta juyo da fuskarta suka yi facing ɗin juna, hannu ya sa ya share mata hawayen ya ce “Wani abu kika gani a hanyar ku ta zuwa nan?” Gyaɗa masa kai ta yi wasu hawayen suka zubo mata, rayuwar da ta yi a gidan Sultan ta faɗo mata ta yi saurin komawa jikinsa ta ce “Wallahi mugu ne shi har giya yake sha, kuma ba ya Sallah wai ya ce ni matarsa ce an ɗaura mana aure.” Mamaki da al'ajabi suka rufe Salim ya ɗago ta ya zaunar ya ce “Waye shi wanda ya ce ke matarsa ce?” “Shi ne wanda ya sace ni wai so na yake, labarin komai ta kwashe ta faɗa masa, amma ba ta faɗi sunanshi ba kuma ba ta ce Mom mahaifiyarsa ba ce.” Wani irin kishi ne ya turniƙe Salim jin har ya taɓa canja mata kaya, nan da nan idanuwansa suka yi jajur kamar an watsa mishi barkono, jijiyoyin kansa suka fito ran maza ya ɓaci. Saurin rufe idanunsa ya yi cikin karaji ya ce “No Khadija me ya sa kika bari ya taɓa jikinki? Me ya sa?” Gani yadda ya birkice sai ta fashe da kuka ta tashi tsaye ta haye kansa ta tallafo fuskarsa cikin kuka ta ce “Don Allah ka yi haƙuri mai hankali tsoron ka nake ji da ka yi haka, kuma fin ƙarfi ya nuna mini ban bari da kaina ba, ni to dama ban faɗa maka ba. Don Allah ni dai karka zama mugu irin shi, haka yake yi wa masu aikinsa ya yi ta shan giya...” Ƙanƙame ta ya yi yana fitar da numfashi fat! Fat! Fat! Gyara mata ruƙo ya yi ya kwanta ya ɗaura ta a kanshi gabaɗaya jikinsa rawa yake, da sauri ya janyo musu bango ya rufe su. Andizo ta yi shuru tana sauraron bugun zuciyarsa, sosai ta tsorata da yadda yake mata ta kalle shi a duhu ta ce “Mai hankali ba ka da lafiya ne?” Hannunta ya janyo ya ɗaura a saitin zuciyarsa yana huci ya ce “Khadija kin ji yadda zuciyata ke bugawa saboda tsananin kishin ki da nake? Wallahi ko waye shi a duniyar nan sai na binciko shi na hukunta shi, sai na sare masa hannanyen da ya taɓa jikinki, tabbas zai gane bakin rijiya ba wajen wasan makaho ba ne..” Ita dai shuru ta yi tana jin yadda yake sumbatu, haƙuri ta dinga ba shi tana cewa ya tashi su tafi asibiti jin jikinsa ya ɗauki zafi sosai, shi kuwa a yadda yake ji in ba Sallah ba da ta zama wajibi a gareshi ba ya jin akwai abin da zai tayar da shi daga kan gadon nan.. Jin tana masa kuka ya ce “Ki daina kukan ranar Litinin zan kaiki makaranta.” Murna ta maye gurbi kukan sai ta shiga fada masa kalar jakar da take so da kayan rubutu, ya ce duk zai saya mata da haka bacci ya dauke ta, shi kuma da kyar ya samu bacci ya ɗauke shi... “Sir da gaske nake maka yau ɗin nan mun ga wata mai kama da wadda ka ba mu photon ta, sai dai mun gansu tare da wani..” A zabure ya tashi daga kan gado ya saki murmushin da rabon da ya yi shi tun wayarsu ta ƙarshe, “Ina kyautata zaton ita kuka gani tun da kun ce nan cikin gari aka kawo ta, amma dai ku ƙara bibiyar su.” Ya faɗa yana nufar wata kofa inda matan turawa ne tsirara wasu daga su sai bra da pant suma da su da babu duk ɗaya suna wanka. Kashe wayar ya yi ya nufi wajen ruwan wankan sai yanzu ya ji nauyin da ya danne masa zuciya ya ragu, zama ya yi a bakin ruwan sai kuma ya faɗa ciki. Da sauri wata daga cikin matan ta biyo shi ta shiga ta same shi, ƙoƙari haɗa jikinta da nashi ta ke ya matsa ya ba ta waje, sake biyo shi ta yi ya ce “Stop Jennifer.” Kamar ba ta ji shi ba ta kuma biyo shi, hakan ya sa ya fita daga ruwan itama ta biyo shi kamar rakumi da akala. Gaban shi ta sha tana masa maganar wai ko bai ganta ba ne tana ƙoƙarin faɗa wa jikinta, tsawa ya daka mata. “He! Don't touch me Jennifer. ” Ya faɗa a zafafe yana nuna ta da hannu ya ƙara da cewa “I've got a wife.” Yana faɗin haka ya hankaɗa ta ta faɗi tim ya yi gaba, gabaɗaya hankalinsa ya tashi tun da suka sanar da shi sun ga mai kama da ita, ya ƙagara su gama buga wasan nan ko ya koma gida, saboda gani yake su Bansh ba sa yin aikin yadda ya dace, in shi ne da cikin sauƙi zai samo ta. Da wannan tunanin ya je ya hau mota ya bar wajen.. _Maman Nusaiba ce🤙🏻_ [6/1, 11:42 PM] Ummu Amjad: _*AREWABOOKS@SARATALKASUM88*_ 25 Wani katafaren super marking ya isa, cike da una izza ya fito yana sa glass ya ɗaga kai ya kalli sunan wajen sannan ya sa kai ya wuce ciki. Mutanen da suka zo sayayya suna ganin shi duk suka yo kanshi suna faɗi “Sultan! Sultan!” Tsayawa ya yi gefe yana bin su da kallo, ɓacin ran da yake ji ya ji ya sauka ganin duk mutanen wajen shi suke kira, cire glass ɗin ya yi ya saukar musu murmushin, sa mai tsada suka dinga ɗaukan shi photo da video. Wani ɗan ƙaramin yaro da ba zai wuce shekara 15 ba ya nufo shi da gudu, hannu Sultan ya miƙa mishi suka tafa yaron ya rungume shi yana faɗa masa ai shi fans ɗin sa ne, godiya Sultan ya masa ya hannu a aljihu ya ciro kuɗi masu yawa ya damƙa wa yaron amma yaƙi amsa, kallon shi ya yi ya ɗan sunkuyo ya ce ma sa me ya sa ba zai amsa ba? Buɗar bakin yaron sai ce masa ya yi shi ba kuɗi yake so ba, ya kai shi Nigeria so yake ya taɓa zuwa, murmushi Sultan ya yi ya ciro katinsa ya miƙa masa ya ce ya tamabayi iyayensa tukun in sun amince zai kai shi Nigeria ya gani, sosai yaron ya yi murna ya sake rungume shi sannan ya sake shi ya nufi wajen mamansa.. Gaba Sultan ya yi duk in da ya nufa sai ɗaukan shi ake yi, ganin haka ya sa masu tsaron wajen suka hana kowa ya dinga bin sa aka ba shi mutum biyu suka dinga bin bayan shi dan ya samu ya sayi abin ya zo nema. Wajen kayan sawa na mata ya nufa ya janyo wata sleeping dressing mai mugun kyau green colour, sosai rigar ta birge shi yana hasko yadda za ta yi kyau a jikinta, murmushi ya yi ya ɗauka mata kala daban-dabanhar guda 10 sannan ya yi gaba. Wajen takalma ya je ya dinga ɗiba mata yana faɗin “Wannan zai dace da Queen.” Duk abin da ya san na mata ne sai da ya saya mata shi sannan aka kawo masa aka mishi lissafi ya cake kuɗin ya ba su har ƙari ya musu suka dinga masa godiya. Kayan aka biyo shi da shi har mota suma masu ɗaukon kayan sai da ya ba su kuɗi sannan ya yi gaba.. Sai da aka kira Sallar La'asar sannan Salim ya motsa, a hankali ya soma buɗe idanuwansa yana addu'ar tashi daga bacci, hannu ya sa gefe yana laliben ta ya ji ba kowa ya yi saurin kallon wajen, tashi ya yi sai ya ganta can wajen ƙafafuwansa ta yi ɗaiɗai, dariya ya yi ganin ta cire kayan jikinta duka daga ita sai pant. Shi sai yanzu ma ya ji zafi ashe bai kunna musu AC ba bacci ya ɗauke su ita kuma zafi ya ishe ta ta cire kaya ta kwanta, tashi ya yi ya kunna AC ya ɗauko ta ya dawo da ita tsakiyar gadon ya kwantar da ita. Juyawa ya yi zai tafi ya ji ta riƙe hannunsa da ya ɗora a kan nata hannun, kallon ta ya yi ya ga ta buɗe ido sai ya dawo ya zauna ya ɗago ta. Kawar da kai gefe ta yi ta soma murza ido ya yi saurin faɗin “Zafi kike ji ko? Yi haƙuri ga shi nan na kunna AC ai yanzu za ki daina ji..” “To ba kai ba ne ka turo ni na faɗo.” Ta faɗa tana sa kuka. Baki buɗe yake kallon ta tsabar mamaki ya ma kasa cewa komai, tashi ya yi ya sauko ta yana faɗin “Ni ɗin ne na turo ki ƙasa?” Gyada masa kai ta yi tana nuna masa gadon bayanta ta ce “Zabura na ga kana yi shi ne nake kiran sunanka sai ji na yi ka juyo da hannu ka turo ni ƙasa na faɗo, shi ne bayana ya yi ciwo.” Hannu ya sa yana shafa mata bayan gabaɗaya mamaki ya kama shi, to shi da ba gagan bacci gareshi ba ta ya zai kado ta daga gado? Ɗaukan ta ya yi suka nufi banɗaki. Bai dire ta a ko'ina ba sai a cikin bahon wanka ya sakar mata ruwa mai sanyi, daina kukan ta yi ta dinga tarar ruwan shi kuma ya tsaya yana kallon ta, sosai ya shagala da kallon surar jikinta ganin yadda komai nata ya soma cikowa kamar ba cikin watan nan ba za ta cika shekaru 14, ita kuwa lamarin gaban ta take sai ta tara kumfa ta yi ta hurawa tana dariya. Sai da ta gaji sannan ta ɗago ta kalle shi, inda yake kallo a jikinta ta kalla sai ta hannu ta rufe tana ɓata fuska ta ce “Kai ba kyau fa ka ƙura mini na mujiya kamar wani maye, kuma ba a son ana kallon mutu ba kaya..” Ajiyar zuciya ya sauke ya matso kusa da ita ya ce “To ban da mijinki, wanda ba mijinki ba ne in ya kalla ya zama haramun, ni zan iya ganin komai naki halak ne kema za ki iya ganin komai nawa..” Baki ta riƙe tana buɗe hannunta da ta ƙanƙame jiki ta ce “Aww haka ne? To ni dai alƙur'an karka mini wayo ka ce ba lefi ba ne alhalin lefi ne.” Ta faɗa tana murguda baki. Girgiza kai ya yi ya fita waje ya bar ta, bai jima ba ya dawo sanye da towel ba ta kalle Shi ba saboda ta juya masa baya tana ci gaba da wankan ta, ba ta san lokacin da ya shigo ba sai ji ta yi an yi ƙasa da ita ta zabura sai ta ga shi ne, dariya ta yi ta daki ƙirjinsa ta ce “Mai hankali ashe ƙato ne kai.” Shima dariyar ya yi ya janyo shampoo ya soma wanke ta tana zillewa. Sai da ya gama yi mata ta ce ai kuwa shima bai isa ba sai ta cuɗa shi ya ce ta zo ta masa, sai da ta duba ta ga ba soson wanka ta kalle shi ta ce “To da me zan cuɗa maka bayan babu soso fa.” Idanuwansa a rufe ya ce “Ki min yadda na miki babu soso.” To ta ce tana ci gaba da masa har suka gama ya ɗauko ta ya dire à ƙasa suka yi alwala sannan suka fito. Sallar La'asar suka yi bayan sun gama ya yi waka aka kawo musu abinci lafiyayye sai ƙamshi yake, kallon farfesun ta yi ta kawar da kai tana wani yatsi fuska, da mamaki ya kalle ta ya ce “Ba za ki ci ba wannan ɗin?” Hararar shi ta yi ta tashi ta koma gefe tana kumbura baki ta ce “Yo me zan yi da wannan abin, haka ranar ka wani turo mini shi ko burodi babu kamar wata mayya zan sha roman kayan ciki, to alƙur'an da Hamma ya gano irin wannan abincin kake ba ni da sai ya maka duka, dan ma dai kai ɗin mutumin kirki ne ba zan bari ya dake ka ba tun da kana sona.” Dariya ya yi yana kallon farfesun, shi sai yanzu ma ya tuna ashe ranar da ya fara ba ta har ce masa ta yi wai ina masa ko ƙosai wanda za ta haɗa da farfesun? Ya ce ai za ta iya ci haka ita kuma ba dan ta so ba ta ci, tashi ya yi ya ce “Bari na je na sayo miki burodi sai ki haɗa ko.” Saukowa ta yi ta yi tsalle ta dire ta ce “Babba fa nake so irin wanda Hammana ke sayo mini in ya je lumo.” To ya ce mata ya fita ita kuma ta zauna a gaban abinci tana ƙare musu kallo. Mamakin abincin take dan ita dai wani kalar abinci ko nawa aka ba ta ba za ta iya ci ba. Bai ɗauki lokaci ba sai ga shi ya dawo hannunsa riƙe da baƙar leda, tw tashi da sauri ta amshe ledar ta buɗe ta ga burodi ne sai ta dinga murna tana masa godiya.. Bayan sun gama cin abincin ya ɗauke ta suka fita, waje dan ta gari.. Ba su dawo ba sai ƙarfe tara na dare, da kyar ya shigo da ita ɗakin kayan da ya sayo mata ya cire mata na jikinta ya sa mata riga da wando na bacci, tana kallon shi sai lumshe idanu take har ya gama ya kwantar da ita. Banɗaki ya je ya yo alwala ya yi Sallar shafa'i da wutiri sannan ya shima ya hayo gadon.. Gabaɗaya ta hana shi sukoni duk ta yi bake-bake a kanshi addu'a kawai yake dan ba ya son haƙurinsa ya ƙare a wannan dare, sai dai ina ya kasa ya sa hannu ya ƙara matse ta.. Can cikin bacci Andizo ta ji abin da ba ta taɓa jin shi ba tun da ta zo duniya, hakan ya sa ta zabura ta fasa kuka tana son sauka a gadon amma ta kasa. Duk 'yan gidansu babu wanda ba ta kira ba a wannan lokaci har bakin nata ya mutu ta yi ɗif, ba ta farka ba sai da ta ji a ruwan zafi ta buɗe ido a firgice tana ƙoƙarin tashi ya riƙe ta. Kuka ta sa ta ce “Ni ka kaini gidanmu Wallahi ba zan sake zama da kai ba.” Saurin rufe mata baki ya yi yana girgiza kai kamar shima zai sa kukan ya ce “Ki yi haƙuri kin ji ba zan sake ba wannan ma tsautsayi ne, da na san ba zan iya jurewa ba da ban zo da ke ba.” Duka ta kai mishi tana faɗin sai fa ya, dawo da ita gida ya ce in dai tana so ya kawo ta to ta yi shuru kar ta yi kuka, ba dan ta so ba ta yi shuru ya mata wanka a zuciyarta ta mishi zagi ya fi cikin kwando. Wunin ranar ko bakin ƙofa bai fita saboda rigimar da ta dinga yi, Sallah ma a ɗakin yake yi ga shi taƙi cin abincin sai kuka. Ganin abin yaƙi ƙarewa ya kwashe ta suka tafi asibitin da 'yan gidansu ke zuwa.. Ƙarin ruwa aka sa mata da allurori sannan likitan ya ja shi office, sai da ya gama rubuce-rubuce sannan ya ɗago ya kalle shi ya ce “Haba boss ya da haka? Wannan yarinyar gaskiya ka fi ƙarfinta ya kamata ka barta ta ƙara girma, in kuma ba za ka haƙura sai dai kake bin ta a hankali har ta saba tun da yarinya ce..” Haka ya ci gaba da yi masa faɗa haɗi da nasiha sannan ya ba shi takarda ya ce ya sayo maganin da ya rubuta, godiya ya mishi yana sosa kai ya tashi ya fita.. Sai Washegari ƙarfe 9:pm suka dawo gida inda Aminatou ta musu girkin tarba. Da kanta ta taro su daga bakin mota ta ce a ɓangaren ta za a ci abincin dare. Andizo ta tsaya tana riƙe da hannun Salim, kallon ta Aminatou ta yi zuciyarta na tafasa ta danne ta ce “Haba ƙanwata ɓangaren nawa ne ba ki son zuwa?” Girgiza kai ta yi ta ce “A a ni na gaji sosai jikina ciwo yake mini kamar an kakkarya ni, ni zanje na kwanta ba ni da lafiya ma..” Ta faɗa tana sakin hannun Salim ta soma tafiya a hankali tana layi kamar mai maye. Zaro idanu Aminatou ta yi tana kallon Salim a kiɗime ta ce “Salim me ka yi wa ɗiyar mutane?” Kallon ban gane ba ya mata ya nufi Andizo da ta doshi part ɗin Mamma tana tafiya tana rike bayanta. Tafa hannu ta yi kamar za ta fasa ihu sai kuma ta biyo su da sauri tana faɗin “Ka ga kawo ta nan muje ciki na mata ruwan ɗumi ta yi wanka za ta ji sauƙi.” Ganin Maigadi na kallon su sai ya miƙa mata ita ta ruƙo ta suka yo part ɗin ta, a kujera ta kwantar da ita ta ce “Khadija ina da ina yake miki ciwo? Meye ya faru da ke haka? Ko wani abin ya miki?” Kasa cewa komai ta yi sai nuna mata Salim ta yi da hannu, kallon shi kawai Aminatou ke yi tana jin kamar ta cinna musu wuta, ita ta rasa me Salim zai ji a jikin wannan ƙaramar yarinyar da ya ɗauke ta ya je ya yi abin da yake so. Hawaye ne suka zubo mata da ɗago da kyar ta ce “Mai hankali ka kaini wajen Hajiya babba.” Saurin kama ta ya yi ya ce “Kinga Aminatou ki bari na kai ta wajen Hajiya Babba sai na dawo, kin san dai halin ta in dai ta san ba ta da lafiya ba a faɗa mata ba yanzu za ta kama faɗa..” Wani kallo ta watsa mishi ta ce “Ba ta da lafiya ko kuma dai ka jaza mata rashin lafiya? Haba Salim kai fa ka ce mini rainon ta za ka yi har sai ta ƙara girma ka ɗauke ta a matsayin mace, amma me ya sa ka yi haka?.” Ƙawar da kai ya yi dan zuwa yanzu ransa ya soma sosuwa, gyara tsayuwa ya yi ya ce “To lefi ne dan na yi hakan? Ko akwai in da aka mini katanga da keɓewa da matata? Kinga ba na son irin wannan tambayoyin marar kai, haka kawai daga ganin yarinya a haka sai ki dinga tambayar ta me aka mata? Ba na son irin haka tun da dai ni ba zama na yi da ke ba na ce na miki alƙawarin yin hakan.” Yana gama faɗin haka ya wuce ya bar mata palon... Baki buɗe Aminatou ke kallon ƙofar palon, kasa zama ta yi sai kuma ta tashi ta nufi ɗaki da sauri, ko minti ɗaya ba ta yi ba ta fito ta shiga kitchen nan ma ta fito ta dawo palo tana nube-dube. Can ta hango abin da take nema wato wayarta, hannu na rawa ta danna wa Sabrin kira amma har ta gama ringing ba a ɗauka ba ta kuma kira, nan ma shuru. Jifa ta yi da wayar ta zauna jagwaf tana huci, kasa daurewa ta yi ta fashe da kuka tana sumbatu, “Wallahi Salim ba ka isa ba ka yi tarayya da wata 'ya mata kai nawa ne ni kaɗai, idan kuma wata ta yi kuskuren haɗa shinfiɗa da kai tabbas sai na ga bayan ta, sai ta gwammace gara mutuwar ta da rayuwa da kai a matsayin miji, na tsane ki Khadija! Na tsane ki! Tun da kuka yi kuskuren barin mijina ya kwana da ke gado ɗaya zan nuna miki iyakarki..” Haka ta dinga sumbatu tana jifa da duk abin da yake kusa da ita, kukan da ta yi har ya fi na ranar da aka kawo Andizo gidan... Suna isa Hajiya Babba suka samu a palo an yo mata shayi ta miƙe ƙafa tana sha tana kallon sunna tv hannunta riƙe da carbi tana ja.. Kallon su ta yi sai kuma ta kawar da kai tana faɗin “Allah na tuba dama ai sai da na faɗa miki za ku dawo ku same ni ina zaune, to yanzu daga gidan uban wa kuke?” Ta faɗa tana kallon Andizo da duk ilahirin jikinta ya soma rawa, gane hakan ya sa Salim da sauri ya ɗauke ta ya zaunar a kusa da Hajiya Babba yana zama shima. Da dabara Andizo ta zame ta kwato kanta a cinyar Hajiya Babba wasu hawaye masu zafi suka zubo mata, gabaɗaya ko'ina na jikinta ji take kamar ana yankan naman jikinta, kanta da yake mata ciwo ji take kamar an ɗora mata wani gingimeman abu mai nauyi. Aje shayin da ke hannun ta yi ta ɗan gyara zama ta kai hannu ta taɓa wuyanta, da sauri ta kalli Salim ta ce “Subhanallahi! Salimu zazzaɓi ne a jikinta ai, maza kira likita ya zo ya duba ta ina kuka je kuka zauna? Kana ganin yarinyar mutane ta kamu da cuta kaƙi miƙa ta asibiti? Wannan shi ne riƙe amanar da na ba ka? In ba za ka iya riƙewa ba ai sai ka faɗa mini na amshe ta na kula da ita..” Sunkuyar da kai ya yi yana tsoron ta tona mishi asiri yau ya shiga uku a wajen Hajiya Babba, sosa kai ya yi ya ce “Mun je fa asibitin an ba ta magani har ruwa aka sa mata, shi ne ta ce nan zan kawo ta ba za ta zauna a can ba..” Dago ta ta yi tana ƙara rungume ta sai sannu take jera mata, mai aikin gidan ta kwallawa kira sai ga ta ta fito da sauri ta durkusa ta ce “Hajiya gani.” “Je ki haɗa wa jikata ruwan ɗumi a banɗakina, sannan ki ɗaura mata abincin mai ɗan ruwa-ruwa ba ta da lafiya.” To ta ce ta tashi ta nufi ɗaki da sauri, bayan ta haɗa ta fito ta ce ta haɗa ta ce ta kama Andizo ta kai ta banɗaki ga ta nan zuwa, ta amsa da to ta sunkuya a kusa da ita ta ce “Matar Oga tashi muje ki yi wanka.” Ba muso ta miƙa mata hannu ta tashe ta suka tafi, Hajiya Babba ta tashi ta ce “To kuma zaman me kake yi? Ba ni maganin sai da safe.” Miƙa mata ya yi a sanyaye jin ta ce masa sai da safe ya kuma gane yau dai ba za ta kwana kusa da shi ba. Amsa ta yi ta wuce tana mitar wai bai kaita asibiti da wuri ba shi ya sa zazzaɓin ya rufe ta har ta kasa yin magana, shi dai bai ce komai ya yi baya ya lumshe idanuwansa yana jin ba daɗi, anya zai iya barin ta ta kwana a nan tun da yau ma kwanan ta ne? Girgiza kai ya yi ya ci gaba da zama har Mamma ta fito daga ɗaki ta same shi sukuku.. “A'a, Salim lafiya dai ka zo ka zauna kai kaɗai a palo?” Gaishe ta ya yi sannan ya ce “Khadija ce ba ta da lafiya zazzaɓi mai zafi take, shi ne ta dinga kuka sai na kawo ta wajen Hajiya..” “Subhanallahi! Ko dai wannan wajen da kuke zuwa wanka ka kaita ta yi wanka har zazzaɓi ya kama ta? Kai fa yanzu ba yaro ba ne Salim bai kamata ba ka kaita can. Dama da kake ce mata za ka kaita ashe da gaske kake? To ni dai babu ruwana kai da Hajiya Babba Allah ya ba ta lafiya.” Amin ya ce sannan ya zame ya kwanta.. Can ciki Hajiya Babba ta samu Andizo ta shiga ruwan ta zauna har bacci ya ɗauke ta, cike da tausayi ta ce “Allah sarki kinga bacci ma ta yi a ruwan.” Tashin ta ta yi ta cuɗa ta da kyar take motsa jikinta, ruwan ta canja mata ta sake zuba mata wani ruwan ta ɗarwaye jiki sannan ta miƙa mata towel ta ɗaura suka fito, da kanta ta kwantar da ita ta lulluɓe ta da bargo mai kauri ta fita ta sa aka kawo mata dafa-dukar taliya da ruwan-ruwan ta, sosai ta ji daɗin abincin ta ci mai ɗan yawa sannan ta koma ta kwanta nan da nan wani bacci mai daɗi ya yi awon gaba da ita.. 1:am na dare Salim na nan kwance a palo ya kasa tafiya ji yake ba zai iya bacci ba in ba ta kusa da shi. Sai da ya tabbatar Hajiya Babba ta yi bacci ya yi sanɗa ya buɗe ɗakin ya ga Hajiya Babba ita ɗaya a kan gado, daɗi ne ya kama shi ya rufe ƙofar a hankali ya nufi ɗayan ɗakin ya buɗe. A lulluɓe ya same ta tana bacci hasken ɗakin ɗan kaɗan da aka bar mata shi ya ba shi damar kallon fuskarta sai yatsina ta take alamar baccin ba ya mata daɗi.. A hankali ya hayo gadon ya buɗe bargo ya shige, kamar jira take ta matso ya yi saurin janyo ta ya rungume har yanzu zazzaɓin na nan, ƙara ƙanƙame shi ta yi ta saki jiki ta ci gaba da bacci. Shi kuwa duk tausayin ta ya kama shi sai shafa kanta yake yana tofa mata addu'a har bacci ya ɗauke shi... _Maman Nusaiba ce🤙🏻_ [6/3, 12:33 AM] Ummu Amjad: _*AREWABOOKS@SARATALKASUM88*_ 26 Ƙarfe 3:am na bugawa ta yi motsi da nufin ta yi juyi ta ji da gam a an riƙe ta a firgice ta buɗe ido ta ganshi yana ta sharar baccin shi sai sauke ajiyar zuciya yake, fuskarsa ta kalla da ya cusa a ƙirjinta kamar irin na ɗa da uwa wanda ake shayarwa, dogon numfashi ta ja duk wata gajiya da ciwon jiki ba ta jin su sosai har zazzaɓin ya sauka. A hankali ta kai hannu ta shafa fuskarsa, hannnunsa da ya ɗora a in da ba ta so ta ɗauke tana turo baki gaba ta ɗaka masa duka a kafaɗa ta ce “Tashi ka saukar mini a gado nan dai ai ba gidanka ba ne, shi ne har ka wani lallaɓo ka zo ka kwanta mini a jiki ni fa ba ƴar is..” Kasa ƙarasa maganar ta yi sakamakon rufe mata bakin da ya yi. Lumshe ido ta yi tana amsar saƙon sa, hakan ya sa shi ya ɗago da ita ya kwantar da ita ai kuwa ta yi saurin tashi tana aika masa harara tuna abin da ya mata jiya, da hannu ta nuna masa ƙofa ta ce “Ni ka fita ka bar mini ɗaki ko na maka ihu ɓarawo..” Kanshi ne ya sara ya sa hannu ya dafe ya koma gefen ta ya kwanta, ganin yadda yake juyi yana cije lips sai ta yi gasaƙe tana kallon shi cike da masifa ta ce “To ba yarda ba zan yi ka kwanan mini a nan har da wani riƙe ciki, ni fa gobe ma zan ce wa Hajiya Babba ta kaini ƙauyenmu tun da ba za ka saka ni a ècole ɗin ba, kuma na ga har yanzu ba ka faɗa mini inda Saminu yake karatu ba ballantana ka kaini na ganshi..” Ta faɗa tana zuro ƙafafuwanta. Saurin buɗe ido ya yi yana kallon bayanta, gashin kanta da ya hargitse ya taɓa ta juyo a fusace tana hura hanci ta ce “Kai ban son a taɓa mini kai fa bori nake, idan kuma kana tantama ci gaba yau mai raba mu da kai sai Allah, alƙur'an idan ba ka kaini wajen Saminu ba sai na koma garinmu..” Dafe saitin zuciyarsa ya yi a tunaninshi ta manta da babin Saminu zuwa yanzu, wani irin zafi ya ji ya ziyarce shi sam ba ya son jin tana maganar wani namiji daban in ba shi ba. Ganin ba zai tashi ba ta daddage ta kuma ɗaka masa duka a gadon baya ta ce “Tashi na ce.” Lumshe ido ya yi yana murmushi domin ji ya yi kamar susa take masa a jiki, sam ya ji ba zai rabu da ita ba a wannan yanayin da yake ciki, da dabara ya dawo da ita ta kwanta suna facing ɗin juna, in ban da harara babu abin da take masa ya rasa ta ina zai shayo kanta su jone, can idear ta faɗo masa ya kalle ta yana huci kamar ba shi da lafiya, a hankali ya kamo hannunta ya dora a kan ƙirjinsa ya ce “Ma femme kina so ki rasa ni a daren nan?” Saurin girgiza masa kai ta yi tana zare ido, daɗi ya ji ya ƙara matso ta ya yi ƙasa da kai ya zo sautin kunnenta ya soma magana cikin raɗa. “Khadija in dai ba ki so na mutu ki yi duk abin da na ce, sannan kar ki yi kuka kuma karki ce komai duk abin da kika ji..” Kallon ka raina mini hankali ta yi mishi ta buge hannnunsa da ya ruƙo ta, sai da ta kusa sauka a gadon sai kuma ta dawo ta haɗe fuska ta ce “Amma dai ina faɗa maka karka zama mugu, idan kuma kaƙi jin maganata sai na koma garinmu.” To ya ce mata ya lallaɓa ya mata wayo ta yarje masa, sai da tafiya ta yi nisa ta ji abin ya fi ƙarfinta ta sa mishi kuka marar sauti ya yi saurin rufe mata baki ya ce kar ta ɗaga murya za a jiyo su,ba dan ta so ba ta yi shuru sai hawaye da ke ta zarya kan kuncinta tana kai masa duka. Tashi ya yi da sauri ya je ya haɗa musu ruwa ya dawo ya ɗauke ta suka shige banɗaki, sai da ta yi ta masa daru da kyar ya shayo kanta ya mata wanka ya gyara ta sosai sannan shima ya yi ya ɗauko ta suka fito, zaunar da ita ya yi ya gyara musu gadon ya sa sabon bedsheet ya kwantar da ita.. Jikinta ya taɓa ya ji zazzaɓin ya sauka ya sunkuya ya manna mata kiss a kumatu ta lumshe ido tana jin shi ba ta ce komai ba, sai da ya rufe ta da bargo kamar yadda ya ganta sannan ya mike zai fita ya ji ta riƙe hannnunsa ya kalle ta cikin wani irin shauƙi mai wuyar fassarawa, dawowa ya yi ya durkusa ya shafa fuskarta da ta yi fayau ya ce “So nake na tafi kar Hajiya Babba ta zo ta ganni ɗakin nan ta ci ubana” Sakin shi ta yi ba ta iya ce masa komai ba ya ɗago ta ya rungume ji yake kamar kar ya tafi ya bar ta ita ɗaya a ɗaki, to amma ya zai yi tun da Hajiya ta shiga lamarin? Sai da ta yi bacci sannan ya fita ya janyo mata ƙofa.. Yana zuwa palo ya kwanta kenan ya ji fitowar Hajiya Babba ya yi saurin kwanciya ya yi kamar mai bacci. Sai da ta zo saitin shi ta tsaya, riƙe baki ta so ma kiran sunansa. “Kai Salimu! Salimu! Tashi ka fitar mana a gida ka koma naka, ashe dama da na ce ka tafi ƙin tafiya ka yi ka zauna a palo har bacci ya ɗauke ga shi asuba ta gabato? To ni ba gantalalliya ba ce maza tashi.” Miƙa ya yi ya buɗe ido ya ce “Hajiya ƙarfe ɗaya ta yi kuwa?” Salati ta ɗauka ta watsa masa yatsu biyar tana cewa “Ungu nan dan butar uwaka, ni za ka tambaya ƙarfe ɗaya? To tashi ka tafi..” Murmushi ya yi ya tashi ya ɗauki wayoyinsa ya ce mata sai da safe ta raka shi da zagi har ya fita... Daret part ɗin ta ya wuce ya shige daki ya kwanta yana mai jin zuciyarsa wani iri. Sai da Andizo ta yi kwana biyar cif a ɓangaren su Hajiya Babba, idan kwanan ta ya zo sai ya bari sai hajiya Babba ta yi bacci ya lallaɓa ya je su kwana shi da matarsa, ita kuwa zuwa lokacin sai ta soma sakin jiki da shi saboda da yadda yake kulawa da ita tamkar flower da ke samun barruwa a kodayaushe, gabaɗaya ta soma canjawa idan yana waje ba ta yin magana sai dai ta yi ta satar kallon shi tana murmushi a ɓoye, yayin da shi kuma duk wani motsin ta a kan idanuwansa take yi,wata irin ƙauna yake mata wadda yake jin idan babu ita a gefen shi to rayuwarsa ta yi babban gyiɓin da ba za taba samun mai cike shi ba... Landi (Litinin) Sanye take cikin riga da sket 'yan kanti kayan sun mata kyau sosai, idan ka ganta yanzu za ka rantse ba Andizo ɗin da ka sani ba ce a baya, sosai ta canja ta yi haske jikinta ya murje ta ƙara girma, sai dai har yanzu rashin kunyar nan tata tana nan babu bin da ya canja sai ma abin da ya yi gaba, babu lefin tsaye ba na zaune za ta kira Salim yana tsaka da aiki ta yi ta masa kukan wai tsoro take ji ita dai ya zo ya ɗauke za ta zauna a wajen shi, idan ya ga ba ya da aikin kirki a ranar sai ya sa a zo a ɗauke ta ya kai ta wajejan shakatawa sai yamma su dawo. Ganin haka ya sa itama Aminatou in yana kwanan ta sai ta masa waya ta ce tana son su fita shan iska. Da farko bai gane ba saboda yana ɗaukan Andizo ne sai daga baya ya gane ya dage iyakar bakin ƙoƙarin sa wajen ganin ya musu adalci kar ɗaya ta ce ya fi fifita ɗaya a kanta, duk da kuwa yasan Andizo ba ta da matsala sai dai ita Aminatou in yana ɗakinta ta dinga bin hanyoyin da za ta hana shi zuwa ɗakin Andizo a daren ranar, shi kuma sai ya nuna mata wannan ba adalci ba ne ranar kwanan da ba nata ba ta hana shi zuwa inda yake. Wani lokacin sai sun yi faɗa sannan ya bar ɓangaren ta.. Da murna ta ta buɗe motar ganin ta a babbar makaranta, fitowa ya yi ya kama hannunta suka nufi ciki, duk inda suka nufa su ake kallo har suka isa office ɗin babban malamin makarantar.. Bayan sun gaisa Salim ya nuna mishi Andizo da ta yi ƙasa da kai ba ta ce komai ba tun bayan gaisuwar da suka yi. “Ga ta nan tun watan da ya wuce nake cewa zan kawo ta, to aiyuka sun mini yawa ne.” Murmushi ya yi ya ce “Ayya Allah sarki Allah ya taimaka ai kuna ƙoƙari ranka ya daɗe, ya sunan ƙanwar taka?” Kallon Salim Andizo ta yi ta murguɗa baki ta ce “Ka faɗa mishi ni ba ƙanwar ka ba ce, ni ƙanwa Hamma Giɗaɗo da su Hamma Umar ce, su Hassana su ne ƙannenka.” Da mamaki Malam ya kalle ta Salim ya yi saurin cewa “Malam matata ce ita, sunanta Nana Khadija Umar.” “Nana Khadija Maigari dai za ka ce.” Ta faɗa tana gyara zama. Kanta ya shafa ya ce “Kinga nan dai ba gida ba ne karki sake cewa komai in ba cewa aka yi ki yi magana ba, Maigari ai sunan shugabanci ne asalin sunanshi shi ne Umar, ba ki ga hammanki Umar magajin shi ba ne aka yi masa?” Baki ta saki tana kallon shi ita sai yau ma ta taɓa jin asalin sunan Maigari, saboda ita a can ƙauye da Khadija Maigari ake kiran ta a makaranta, shuru ta yi saboda ba ta son ɓata masa rai.. Sai da ya gama mata komai sannan aka yi mata tambayoyi ta dinga amsawa, sosai shugaban makarantar ya ji daɗi yadda take ba shi hamsa, hakan ya sa aka kai ta 6ème A (aji ɗaya secondary) har cikin classé ya raka ta, ganin da maza sai ya fito da ita waje ya sunkuya ya ce “Kina ji Khadija, kinga yanzu zan tafi na barki a nan inda baki san ba kowa, ban da neman faɗa ko wani namiji ya miki magana ki kula shi, karki kula kowa musamman maza ke matar aure ce haramun ne ki yi magana da namiji in ba ta kama dole ba, dolen ma sai malaminku idan kina buƙatar wani abu ki je wajen mutumin da na kaiki ya miki tambayoyi zai kira ni sai mu yi waya kin ji, ki dage ki yi karatu sosai zan sayo miki duk abin da kike so..” Jikinta ne ya yi sanyi ta ɗago da kai idanuwanta sun cika taf da kwalla, girgiza mata kai ya yi ta yi saurin faɗawa jikinsa ta sa kuka, shima rungume ta ya yi ya dinga rarrashin ta har ya samu ta daina kukan sannan ya ɗago da ita ya share mata hawayen yana lallaba ta har sai da ya ga ta yi dariya, babban Monsieur ya tarar da su a haka ya yi murmushi ya ce “Abin da za a yi ranka ya daɗe zan haɗa ta da ƙanwata su zauna a waje ɗaya, duk abin da ba ta gane ba zan sa take nuna mata..” Sosai Salim ya ji daɗi ya masa godiya sannan ya ciro kuɗi ya miƙa mata ya ce in an fito da su shan iska ta sayi abinci kar ta zauna da yunwa, to ta ce tana ɗaga mishi hannu har ya bar wajen sannan ta bi bayan Monsieur suka shiga ciki. Gabaɗaya ɗalibai suka tashi suka gaishe shi ya amsa, table na farko ya kalli wata yarinya ya ce “Ke tashi ki koma baya Khadija ta zauna a gaba saboda kin fi ta tsayo..” Kallon Andizo yarinyar ta yi fuska a damke ta tashi ta koma baya ita kuma ya ce ta zauna, zama ta yi ta kalli ɗayar ta mata murmushi itama ta mayar mata, matsowa kusa da su ya yi ya ce “Amira ga ƙawa na kawo miki, ki riƙe ta da kyau karki bari kowa ya takura mata saboda tana da kima a wajena. Ina dai ba ki manta Salim soja ba ko?” Gyaɗa masa kai Amira ta yi tana murmushi, ya ce “To matarsa ce ki kula karki kuskura wani namiji ya mata magana.” Zaro ido ta yi tana kallon Andizo sosai mamaki ya kama ta wai wannan yarinyar ce aka yi wa aure? Dafa ta Amira ta yi ta ce “Khadija daga yanzu ni ƙawarki ce za mu ke yin komai tare kin ji.” Kai ta gyaɗa mata tana wasa da kudin da Salim ya ba ta, kallon kuɗin Amira ta yi ta ce “To ki sa kuɗin a jakarki mana karki yada.” To ta ce ta sa kuɗin sannan duk suka mayar da hankali a kan darasi da aak fara musu... Bayan an tashe su shan iska suka fito a tare 'yan ajinsu sai kallon ta suke, ita kuwa duk jin ta take a takure duk yadda take da sakin jiki da wuri in ta je baƙon guri yau dai ta kasa sai ɗari-ɗari take da kowa, abincin Amira ta saya musu suka zauna amma ta kasa cin na kirki, saboda ta saba Salim ya ɓata ta ba ya bari ta ci abinci da kanta shi yake ba ta a baki har ta ƙoshi. Wasu zafafan hawaye suka zubo mata ta yi saurin gogewa tana kawar da kai da kar Amira ta gani, amma ina tuni ta gani ta dafa kafaɗarta ta ce “Khadija ki daina kuka kin ji, kinga Yayana ya ce na kula da ke kar na bari ki yi kuka, ki faɗa mini me kike so zan miki?..” Da kyar ta danne kukan da ya zo mata ta haɗiye yawu sannan ta samu damar yin magana, “Ban saba cin abinci ni kaɗai ba, shi yake cinyar da ni ga shi yanzu ba ya tare da ni.” Ta faɗa tana sakin kuka.. Dariya ce ta kama Amira amma ta daure ta ce “Ke Wallahi Khadija lamarin ki ba sauƙi, yanzu saboda haka ne kike kuka? Anya za ki iya zuwa wani garin ki yi sati ba tare da Yaya Salim ba? To bari ni na wakilce shi gyara zama na ciyar da ke kar ya zo ɗaukan ki ya ce an bar masa mata da yunwa..” Girgiza kai ta yi ta ce “A'a zan ci da kaina ai.” Amira ta janye abincin gaban ta ta ce “Ban yarda ba da wannan maganar, ki tsaya na ba ki kar a koma..” Dariya abin ya ba ta sai ta gyara zama Amira ta dinga diba da cokali tana ba ta tana ci, sai da ta ƙoshi sannan ta ce ta ƙoshi Amira ta yi hamdala ta miƙa mata ruwa ta sha ta wanke baki sannan suka koma ciki.. Ana tashi aka zo ɗaukan Amira ita kuma Andizo Salim bai zo ba, kallon ta yi ta ce “To yanzu ya za a yi Khadija? Ko za ki bini mu tafi gidanmu ne idan mun je sai Yaya ya kira shi ya zo ya ɗauke ki?” Shuru ta yi tana kallon gefe ta gaji sosai saboda yau darasin ya mata tsauri dayawa, sai da Amira ta sake yin magana sannan ta sauke jakarta ta ce “Da dai shi direban naku zai kaini gida sai in shiga.” Ɓata rai Amira ta yi ta ce “Kenan gidan namu ne ba za ki je?” Saurin girgiza kai ta yi ta ce “Ba haka ba ne bacci nake ji duk na gaji.” Za ta sake magana sai ganin mota suka yi ta paka a gaban su, da kallo suka bi motar har ya buɗe ya fito. Da sauri ta tashi tana murmushi ta ce “Amira ga Yaya Ahmad ma ya zo ɗauka na ba sai na bi ki ba.” Kallon shi Amira take tana yaba kyau da zubin halittar shi, ga shi ya ɗau wanka sai ƙamshi yake tashi a jikinsa. Yana isowa ya musu sallama suka amsa ya kalli Andizo ya ce “Matar yaya na zo ɗaukan ki, aiki ma nake aka ce sai na zo na ɗauke ki yanzu haka kina nan kina kuka ba a zo an, ɗauke ki ba.” Dariya ta yi ta miƙa masa jakar makarantar ta ce “Da ba ka zo yanzu ba da ƙawata Amira zan bi mu tafi gidansu.” “Ayya ya kike Amira?” Ya faɗa yana kallon ta.” Sunkuyar da kai ta yi ta ce “Alhamdu Lillah ya aiki?” Lafiya lau ya ce suka mata sallama suka tafi itama ta shiga mota suka direba ya ja suka tafi.. Ko da ta zo gidan sai ta ga wata mota da ba ta saba gani a gidan ba, kallon Ahmad ta yi ta ce “Yaya Ahmad ko baƙi aka yi a gidan?” Sai da ya fito daga motar sannan ya ce “Mamar Aminatou ce da 'yan'uwanta suka zo..” To kawai ta ce sannan ta wuce ɓangaren ta, tana isa ta kai jakar ɗaki ta aje ta fito palo, sosai ta yi mamakin ganin yadda aka hargitsa mata palon kamar yau ba ta gyara shi ba, cike da gajiya ta dinga gyara palon tana yi tana hutawa har ta gama, banɗakin palon ta shiga nan ma ta samu duk an yi fitsari a ƙasa sabulun wanke hannu a zubar da shi gabaɗaya a ƙasa, towel ɗin da suke goge fuska in sun wanke suma duka an yado su cikin fitsarin, mamaki sosai ya kama Andizo sai tambayar kanta take yaushe aka shigo mata palo har aka mata wannan ta'asar? Facemark ta ɗauko ta sa ta saka safar hannu ta shiga wanke banɗakin tana yi tana kakarin amai saboda tsamin kashin da banɗaki yake yi, bayan ta gama ta zuba abin ƙamshi mai yawa ta kwara a ƙasa ta zuba a ko'ina ta janye ruwan sannan ta ji banɗakin ya dawo yadda yake. A matuƙar gajiye ta fito duk ta haɗa zufa, duk son ta da kallo yau ji ta yi ya ishe ta ta nufi ɗaki, har za ta kifta kamar an ce ta kalli ɗakin baƙi ta ga an kunna hasken ɗakin, da mamaki ta nufi ɗakin tana karanto addu'a. Zaro ido ta yi ganin kujerunta gabaɗaya an hargiza su har carpet ɗin duk an yuye shi, rasa abin da za ta yi ta yi kawai ta fashe da kuka tana kallon ɗakin, sai da ta yi mai isar ta sannan ta shiga ta dinga gyara kujerun tana nishi saboda sun mata nauyi, da kyar ta gyara ta fito lokacin har an kira sallar la'asar, ɗakinta ta nufa ta wuce ta shige wanka. Bayan ta fito ta yi Sallah sannan ta shiga ta kunna gawayi, sosai yau take jin haushin yadda ta samu gidan nata a hargitse bayan sai da ta gyara ta yi masa turaren wuta sannan ta tafi makaranta. Turaren wuta ta kunna ta ɗauko 'ya'yan habbatussauta da Hajiya Babba ta ce da ta ga marece ya yi take turare gidan da shi saboda lafiyarta, har gyara gida sai da ta koya mata ita da Mamma domin sun ce mata in ba ta iya gyara gida da girki ba Salim zai daina sonta, hakan ya sa ta dage ta koyi komai ƙarfi da yaji har girki Mamma ta fara koya mata amma dai ba ta iya ba dafa indomie kaɗai ta iya.. Tunawa ta yi da Maman Aminatou ta shiga ɗaki ta yi simple kwalliya ta saka doguwar riga da ɗaura ɗankwalin ta ɗauki mayafi ta yaba ta nufi ɓangaren Aminatou, gabanta ne ya dinga faɗuwa dan ba ta san ba irin tarbar da za su mata, har ta juya za ta dawo sai ta tuna da maganar Hajiya Babba da ta ke ce mata indai kishiyar ta ki baƙi 'yan gidansu take leƙawa su gaisa sai ta dawo, ajiyar zuciya ta sauke ta aro jarumta ta yaba ta taka ta tsaya bakin kofar ta buga.. Su Aminatou suna cin abinci suka ji buga kofa, ta tashi da, sauri tana faɗin “Waye?” Ta ce ita ce ta yi saurin buɗewa tana dariya ta ce “A a 'yan makaranta har kin dawo? Amma dai ba Salim ya kawo ki ba?” Murmushi ta yi tana wasa da yan yatsunta ta ce “A'a ai shi rabon da na ganshi tun da ya kaini makaranta, na zo na gaishe da su Ummi ne Ahmad ya ce mini su ne suka kawo miki ziyara..” Matsawa ta yi tana kallon su ta ce “Ummi ga Khadija ta zo gaishe ku.” Ta faɗa tana kama hannunta.. Suna isowa ta durƙusa ta ce “Ummi sannun ku da zuwa, ya gida ya kwana biyu?” Cike da birgewa Ummi ta ce “Lafiya ƙalau Khadija yanzu Aminatou take ce mana kin tafi makaranta.” “E Wallahi sai ɗazu ma na dawo.” “Ma sha Allah to Allah ya ba da sa'a a maida hankali a yi karatu kin ji.” “To Ummi in sha Allah, bari na koma.” “A, haba dai ya za ki tafi bayan kinga muam, cin abinci ? Zo zauna mu ci abinci tukun.” Duk da yunwa take ji amma sam ba za ta ci abinci a cikin su ba, girgiza kai ta yi tana tashi tsaye ta ce “Wallahi na ƙoshi na ci abinci kafin na zo gida..” Tashi Aminatou ta yi ta ce “Haba girkin nawa ne ba za ki ci ba? Ko kunyar su Ummi kike ji? Da ai in kina jin yunwa ci kike tsaya na ɗauko miki dama nasan kamar za a yi haka shi ya sa na diba miki naki daban..” Ita dai ba ta ce komai ba sai wasa da take da hannunta, miƙa mata kula Aminatou ta yi ta ce “To ga shi tun dai kunya kike ji.” Amsa ta yi ta mata godiya sannan ta juya. “Wannan mayyar yarinyar kalli yadda take buɗewa ta girma ga haske da ta yi kamar ba ita ba ce aka kawo sai ka ce kazar mayu, ni Wallahi na tsane ta ma sani ne baki yi ba Anty, naji fa ana cewa ba a san ba ubanta, shi ne Yaya Salim ya je ya jajibo miki ita wa ya sani ko tsintar ta suka yi waɗanda suka riƙe ta..” Runtse ido Andizo ta yi da ƙarfi zuciyarta ta buga har ba ta san lokacin da kular ta subce mata ba sai ƙaran faduwar ta suka ji, da sauri duk suka ɗago suna kallon ta, Ummi da ba ta ji abin da ƙanwar Aminatou ta faɗa ta ce “Subhanallahi Khadija sannu ba ki dai ƙone ba ko?” Gyaɗa kai ta yi ta sunkuya ta dauki abincin ta dawo gaban ƙanwar Aminatou da suke kan kujera ita da Aminatou ta ɗaura kular a kan cinyarta ta ce “Ga abincin ki na faɗa miki na ƙoshi ƙamshin shi duk ya buwaye ni har zuciyata tashi take kamar zan yi amai..” Saurin kallon ta Aminatou ta yi tana zare ido, “Amai kuma Khadija? Ko ba ki da lafiya ne.” Wani irin kallo ta musu wanda ya ba su mamaki ta juya da sauri ta bar palon, Aminatou ta dafe kirji ta ce “Ke shegiya ko dai ta ji abin da kike faɗa a kanta ne?” Taɓe baki ta yi tana kawar da kai. Da gudu ta isa ɓangarenta ta faɗa kan kujera ta fashe da kuka, sosai maganganun ta ke mata yawo a zuciya tana nanata kalmar ƴar tsuntuwa. Da mamaki ya fito jin kukan ta, ganin yadda take kuka ya yi saurin isowa ya ɗago da ita, ganin shi ne ta faɗa jikinsa ta ƙarawa kukan ta mai, ta ce “Mai hankali da gaske ne ba ni da uba? Wai tsunto ni aka yi ba a san babana ba?” _*Maman Nusaiba ce🤙🏻*_ [6/4, 2:14 PM] Ummu Amjad: _*AREWABOOKS@SARATALKASUM88*_ 27 Saurin ɗago ta ya yi a ruɗe jin abin da ta faɗa, fuskarta ya ɗago yana girgiza mata kai ya ce “Wani mahalikin ne ya ce miki ba ki da uba? Kin taɓa ganin wanda aka haifa babu uba? Ki faɗa mini wanda ya ce miki haka..” Ya faɗa yana sake mayar da ita ya ci gaba da rarrashi ta. Dai da ta yi kuka mai isar ta sannan ta yi shuru tana sauke ajiyar zuciya, gabaɗaya ta ji tana son sanin waye ubanta indai har ba Maigari ba ne ya haife ta. “Khadija ki daina kuka kina da uba ke ba 'yar tsuntuwa ba ce, ɗiyar halak ce ke ba a titi aka yi tsince ki ba. In dai kina son na sanar da ke waye babanki to sai kin daina kuka, sannan kin faɗa mini wanda ya miki gorin ba ki da uba..” Wasu hawayen ne suka zubo mata ta sa hannu ta goge ta ɗago ta kalle shi, a sanyaye ta ce “To na daina don Allah ka faɗa mini indai ba su Maigari ba ne iyayena su waye suka haife ni?” Gyara zama ya yi ya ɗauko ta ya zaunar da ita a kan cinyarsa ya ce “Idan na faɗa miki ba za ki dinga kuka ba? Sannan ba za ki shiga damuwa ba za ki yi ta addu'a?” Gyaɗa mishi kai ta yi ya ce “Maigari da Hajja su kakanninku ne ba iyayenku ba k..” Saurin tarar numfashinsa ta yi ta ce “To kenan ina da 'yan'uwa waɗanda muke mama da baba ɗaya?” “Kwarai ma kuwa, yayunki su ne Umar, Buba, Aliyu, Ibrahim wato Iro uwa ɗaya ta haife ku..” Baki ta riƙe ta ce “To kenan Hamma Giɗaɗo ƙanen Innata ne shi da Adda Ɗahare? Tun da Inna matar Maigari ce.” Dariya ya yi yana riƙe hannunta ya ce “A a, Giɗaɗo ma yayanki ne amma ba uwa ɗaya uba ɗaya ba, su ne suka ceci rayuwarku ke da su Umar.” Kallon ban gane ba ta mishi shi kuma ganin ta nutsu ya soma faɗa mata labarin ranar da ta zo duniya da yadda 'yan bindiga suka hargitsa musu gari har mamanta da su Umar suka zo rugar su Inna, da yadda suka gudu har suka zo garin Tilaberi da yadda aka raine ta.” Tun da ya fara maganar take kuka har da majina, ashe mamanta da babanta duk an kashe mata su? Jikinta ne ya ɗauki rawa ta miƙe da sauri za ta bar palon jiri ya ɗauke ta kafin ya kai ga tashi sai faɗo masa ta yi a jiki sumammiya. Ɗaukan ta ya yi yana kiran sunanta ya nufi ɗaki da ita, ruwa ya fito ya ɗauka ya koma ya yayyafa mata. Dogon numfashi ta ja tana buɗe ido ta sa mishi kuka, rungume ta ya yi yana bubbuga bayan ta tare da yi mata nasiha har ta yi shuru ƙarshe bacci ya yi gaba da ita.. Kwantar da ita ya yi yana kallon ta cike da tausayawa, shima kwanciya ya yi yana jiran ta tashi ta sanar mishi wanda ya mata wannan gorin. Sai gaf da magariba ta tashi ya ja ta suka yi wanka, da kanshi ya shirya ta yana nuna mata kulawa duk dan kar ta sa damuwa a ranta. Bayan Sallar isha'i ya sake tambayar ta ta sanar da shi ƙanwar Aminatou ce ta faɗa mata tare da ba shi labarin duk abin da ya faru da ta je ɓangaren na Aminatou. Sosai ran Salim ya yi mugun ɓaci, ya kuma yi mamakin maganar, babu lefin wanda yake gani illa na Aminatou, tashi ya yi ya ce mata yana zuwa ta amsa da to sannan ya fita. Daret ɓangaren Aminatou ya nufa ko nocking bai yi ba ya murɗa ƙofar ya shiga da sauri, Aminatou ta ɗago tana kallon shi sai kuma ta haɗe rai ta ce “Haba Salim kamar ba musulmi ba ka shigo gida kai tsaye?” Wani irin kallo ya mata wanda ya sa ta sha jinin jikinta, kallon Abida ƙanwar Aminatou ya yi jin tana cewa “Yaya Salim tun da rana muka zo ba mu samu mun gaisa da kai ba, ina wuni ya gida ya dare?” Ko ci kanki bai ce mata ya kira Aminatou ɗaki suka zauna, ji yake jinin jikinsa na tafasa ya kalli Aminatou ya ce “Wallahi Aminatou kin ba ni kunya, ban taɓa tunanin har akwai lokacin da za ki canja daga mutuniyar kirki zuwa wata ta daban ba, ke yanzu kina ganin abin da kuka aikata kun yi daidai kenan?” Dafe ƙirji ta yi ta ce “Na shiga uku! Me kuma na yi haka Salim?” Ɗaure fuska sosai Salim ya yi wanda Aminatou ta hango zallar ɓacin rai ya bayyana ƙarara a fuskar, gaban ta ne ke dukan uku-uku tana ta saƙe-saƙe ta ƙagara ta ji me zai ce mata, ƙafa ɗaya ya dora a kan ɗaya ya ce “A tunanina duk wani abu da kika ga ina so za ki yi ƙoƙarin kare shi ko ina nan ko ba na nan ashe ba haka ba ne, tabbas yau kin ɓata mini rai da tun da muke da ke ba ki taɓa fusata ni irin na yau ba, yanzu har kina ji kina gani a gaban ki a ci wa Khadija mutumci ki kasa cewa komai? Kuma ba wani bare ba ne ƙanwarki ce ta ci mata fuska, shin ma na tambaye ki? Waye ya ce wa Abida Khadija ba ta da uba?” Ya faɗa yana zare mata idanuwansa da suka yi jajur saboda ɓacin rai. Jikinta ne ya ɗauki rawa ya daka mata tsawa tare da nuna mata hanyar fita ya ce “Je ki kira mini Abida yanzun nan.” Da sauri ta fita kamar wadda aka jefo Abida sai ganin ta ta yi a gaban ta, dafe ƙirji ta yi ta ce “Me ya faru?” “Ko ma me ya faru Abida ke kika ja mini, yau in dai Salim ya kora ni gidanmu ke ce sila da ba ki da kimtsin magana kin faɗi abin da ya fusata shi ga shi yau wai har ni Salim yake yi wa tsawa, ki maza ki tashi muje ya ce yana son ganin ki..” Tsaki ta ja tana tashi dan ita ba ta ga wani abin tayar da hankali ba dan ta ce wa Khadija ba ta uba, tana zuwa ta samu waje ta zauna ya ɗago ya kalle ta, kamar za ta saki fitsari ta ji ganin yadda Salim ya koma. Rai ɓace ya ce “Ke waye ya ce miki Khadija ba ta da uba? Sannan ma wa ya ba ki izinin shiga hurumin gidana ke ba matar gida ba? Kinga ina miki wasa da na fuskanci ke ba ki da kunya? To yau in ba ki faɗa mini wanda ya sanar da ke wannan maganar ba in kuma ke kika tsara kika faɗa sai kin kwana barikin sojoji, ita kuma 'yar'uwar taki da kike tinƙaho in ta bar mini gida sai na ga ta inda za ki zo har cikin gida ki faɗa wa matata maganar da za ta firgita mata lissafi..” A ruɗe Aminatou ta durƙusa ta ce “Don Allah Salim karka hukunta ni da barin gidanka, Wallahi ina sonka ba zan iya zama wajen da babu kai ba, ni iya gaskiyata nake faɗa maka ban san a ina ta ji wannan maganar ba, da ta faɗa ma sai da na yi ta mata faɗan me ya sa ta faɗa mata haka..” Kallon hadarin kaji ta musu Salim ya daka mata tsawa sai ga ta ta takure a waje ɗaya. “Za ki faɗa ko ba za ki faɗa ba?” “Wallahi nima a wajen Anty Sabrin naji tana faɗi, ita ta ce ta sa an bibiyan mata duk wani abin da ya shafi rayuwar Khadija an tabbatar mata ba ta da uba wasu mutane ne 'yan gudun hijira suka tsince ta, shi ne suka zo wannan ƙauye Maigari garin ya ba su mafak..” Tun kafin ya ƙarasa ma sai jin saukar mari ta yi tas! Tas! Aminatou ta wanke ta da maruka masu zafi, ƙafa ta sa ta yi bal da ita tana huci ta ce “To kenan so kuke ku kashe mini aure na dawo gida mu zauna ake lissafa mu ko? Ita Sabrin ɗin uban wa ya ba ta izinin yin hakan? Wallahi kika yi sanadin kawo saɓani tsakanina da mijina sai na illata ki ta yadda ba za ki moru ba..” Kuka Abida ta sa tana shafa kuncinta ta miƙe tsaye cike da rashin kunya ya ce “Saboda wannan juyan mijin naki ne kika mare ni ? Wallahi sai na rama ta in da ba ki tsammani ba tun da kika mare ni dan an taɓa waccan kucakar ya..” Sake ɗauke ta ta yi da mari za ta ƙara mata Salim ya ruƙo ta ya ja ta ya zaunar, hanyar waje ya nuna mata ya fita palo ki bamu guri..” “Kar ta kuskura ta zauna mini a gida tun da ita ta zama tawatsa watsa gida tana son ta watsa mini rayuwa, maza ki fita direba ya kaiki kar ma ya tafi gida zan zo gobe gidan daga ke har Sabrin ɗin sai na muku iyaka da gidana..” Ta faɗa tana huci.. “Gidan banza gareki ai nima ba daga sama na faɗo ba daɗin ta ma muna da gida, aikin banza da kina da 'ya'ya ne za ki yi tinƙaho da gidan, ke da ko kashi mai tauri ba ki taɓa yi ba shi ne kike fifita mijinki a kan ƙanwarki? To ki yi zaman duniya a gidan mijin ki gani juya kawai..” Tana gama faɗin haka ta fita fuu ta bar gidan.. Kuka sosai Aminatou ke yi kamar za ta shiɗe, sosai take jin raɗaɗi da azabar zafin gorin haihuwa da Abida ta mata, wai yau ita ce ƙanwarta take cewa juya to idan wani ya ce mata juya a gaban ta ai ba za ta ce komai ba.. Ruwa mai sanyi Salim ya ɗauko mata ya ba ta ta sha, ajiyar zuciya ta dinga saukewa ta rasa ma da me za ta ji ba ta so Salim ya ga lefin ta a kan wannan lamarin, durƙusawa ta yi har ƙasa ta riƙe ƙafafuwansa wasu hawayen na bin kuncinta ta ce “Don Allah mijina ka yafe mini kar ka ga lefina a wannan lamarin, Wallahi ban san me ya sa Sabrin ta sa aka mata wannan binciken ba..” Tausayi ta ba shi amma ya danne ya ce “Duk ke kika jayo komai ya faru, da da kike riƙe sirrinmu wa ya taɓa miki gorin haihuwa daga dangina har mutanen da kike hulɗa da su? Ke kika fara fitar da sirrin gidan aurenki shi ya sa har suka samu damar yin hakan kuma suke son dagula wa ƙaramar yarinya hankali da ba ta gama sanin rayuwa ba, idan kinga dama ki ci gaba da buɗe sirrin aurenki matsalar ke za ta shafa, ni dai ba za ki jefa ni cikin damuwa ba na rasa da wanne zan ji, in kin yi hankali daga yau sai ki gyara kuskuren ki..” Yana gama faɗin haka ya tashi zai wuce ta yi saurin tashi, da hanzari ta rungume shi ta baya kuma sa kuka tana roƙon shi. “Don Allah mijina karka hora ni da lefin da ba ni na aikata maka ba, Wallahi ba zan sake faɗin sirrin aurenmu ka yi haƙuri fushinka zai ƙara saka ni a cikin wani hali..” Ya so ya share ta amma yadda yake jin jikinta na rawa sai ya fasa ya juyo ya rungume ta yana bubbuga bayan ta, sai da ta yi shuru sannan ya ce “Ba komai ya wuce, kin san dama ai ba zan taɓa yin fushi da ke ba kawai dai raina ya yi matuƙar ɓaci, yanzu haka saboda abin da Abida ta faɗa wa Khadija ta ci kuka har zazzaɓi ya rufe ta tana can na baro ta na ce sai na zo naji dalilin faɗa mata wannan muguwar kalmar..” Ɗagowa ta yi daga jikinsa tana share hawaye ta ce “Inna lillahi wa inna laihin raji'un! Don Allah mu je na ga jikin nata, dama da ta shigo ta ce abincin da muka ba ta ƙamshin shi ya buwaye ta kamar za ta yi amai, muje ina so na nemi yafiya ta a kan abin da Abida ta mata..” Jinjina kai ya yi ya ce “Ki kasance a Aminatoun da na sanki matata, ka da ki bari zugar ƙawaye ko ta dangi ta sa ki canja daga mutuniyar kirki zuwa ta banza..” “In sha Allahu mijina na tuba ba zan sake biye musu ba su kaini su baro.” Fita suka yi a tare har part ɗin Andizo. A palo suka same ta ta rafka tagumi hannu bibiyu ta ƙura wa tv ido, kana kallon ta za ka san ta lula duniyar tunani Salim ya nuna mata ita da hannu ya ce “ Kin gani ko abin da nake faɗa miki, ba ta taɓa shiga damuwa da tashin hankali ba irin na yau..” Saurin isowa Aminatou ta yi ta zauna a kusa da ita, hannu ta sa ta janye mata tagumin ta yi firgigit za ta tashi ta ruƙo ta, kallon ta ta yi sai kuma ta janye hannunta da ke cikin na Aminatou ta tsaya tana kallon ta. “Khadija don Allah ki yi haƙuri kin ji, na zo ne na nemi yafiyar ki a kan abin da ƙanwata ta miki..” Dawowa ta yi ta zauna tana kumbura baki ta kalli Salim ta ce “Mai hankali ka faɗa mata ni ba 'yar tsuntuwa ba ce da ubana da uwata auren sunna aka yi aka haife ni, 'yan bindiga ne suka kashe mini su, itama ta kuka da kanta wani zai rama mini abin da ta faɗa a kaina..” Kamo hannunta ya yi ya zaunar da ita kusa da Aminatou, Aminatou ta ji ba daɗi ta kalli Salim ta ce “Da gaske 'yan bindiga suka kashe mata iyaye?” “Tabbas haka ne su suka kai wa garinsu farmaki. Labarin komai ya faɗa mata.” Sosai ta tausayawa Andizo ta kalle ta ta ce “Ki yi haƙuri Khadija ki dinga musu addu'a Allah ya musu rahama, in sha Allah hakan ba za ta sake faruwa ba..” Jinjina kai ta yi ta ce “To na yafe muku.” “Yawwa ƙanwata na gode ya jikin naki yanzu akwai zazzabin?” Ta faɗa tana taɓa gefen wuyanta, har yanzu akwai zafi ta kalli Salim ta ce “Ko mu kai ta asibiti ne?” “Nima dai haka nake tunani amma mu bari zuwa gobe in bai sauka ba sai na kaita..” “To shi kenan Allah ya ba ta lafiya bari ni in tafi na kwanta sai da safen ku..” Tashi ya yi ya raka ta suka shiga har ɗakin bacci, har za ta kwanta ya ce ta yo alwala tukun ta kwanta. Bayan ta fito ta zauna ta yi addu'ar kwanciya bacci ta kwanta ya lulluɓe ta tare da kissing ɗin goshinta sannan ya fito.. A ɗaki ya samu Andizo za ta kabbara Sallah ya kalle ta cike da birgewa ya ce “Matar tsaya na yo alwala nima mu yi Sallar tare..” To ta ce mishi ta zauna a baki gado, bayan ya fito suka yi Sallar shafa'i da wutiri sannan suka bi lafiyar gado. Yau yadda ya zo mata da wani sabon salon ƙauna sai ta samu damar ba shi goyan baya ɗari bisa ɗari, sosai hakan ya faranta masa rai ganin yadda ta saki jiki da shi ba kuka ba rakin da ta saba mishi in hakan ta haɗo su, itama a nata ɓangaren ta ji yau ba ta wahala ba kamar kodayaushe sai zuciyarta ta yi sanyi, wani abu take ji game da mijin nata wanda ba ta san ya za ta musalta shi ba kawai sai ta shige jikinsa. Kyakkyawar tarba ya mata yana murmushi ya ce “Yau dai a jarumta aka zo.” Duka ta kai mishi ya riƙe hannun yana dariya itama tana yi, ganin za ta yi bacci ya ɗauke ta suka yi wanka sannan suka koma bacci.. Washegari sun tashi ya taya ta ta shirya suka shiga part ɗin Aminatou itama lokacin ta tashi tana karyawa suka same ta, ruwan tea mai zafi ta haɗa wa Andizo ta ce “Amshi maza ki sha nasan ba ku kai ga karyawa ba ma..” Turo baki ta yi ta ce “To Adda wannan uban shayin duk ni kaɗai zan shanye?” “Sosai ma in ba ki sha ba kuma na ce Salim kar ya kaiki makaranta.” Jin abin da ta faɗa sai ta yi saurin amsa ta soma sha, Salim ya yi mata jinjina da hannu ta yi murmushi ta shige kitchen. Ba ra fi minti shida ba ta fito da soyayyan kwai a plate ta aje musu ta zauna itama, shima Salim shayi ya haɗa ya sha suka gama karyawa sannan suka tashi. Kallon Aminatou ya yi ya ce “Wannan ita ce mace tagari matata Aminatou kenan, Allah ya miki albarka.” Daɗi ne ya rufe ta ta ce “Amin mijina gara ku yi sauri ita Khadija har ma ta fita waje..” To ya ce mata ya fita tana ɗaga mishi hannu. A mota ya same ta tana jiran shi, ganin ta canja ya ce “Lafiya dai na ga kin ɓata rai?” “To ni sai yaushe za ka saya mini salula ne? Kai fa ka ce da na fara karatu za ka saya mini, ga shi ina so na kira ƙawata Farrah mun jima ba mu gaisa ba nasan za ta yi ta kira wayar Maigari a ce mata ban zo ba..” Dariya ya yi yana gyara zaman hularsa ya ce “Nana Khadija tawa ni kaɗai, ai yau nake cewa zan saya miki waya sabuwa dal a kwali..” Murmushi ta yi ba ta kuma cewa komai ba suka bar gidan. Yana aje ta sai ga Amira suka shiga ciki a tare, Amira ta ce “Ka ga matar soja.” Dariya Andizo ta yi tana rufe fuska, suna zama sai ga wani daga cikin ɗalibai ya iso gaban table ɗin su yana wani shafa kai, kallon shi Amira ta yi ta kawar da kai tana jan tsaki. Gyara tsayuwa ya yi ya ce “Yane Amira da dama? Wannan haɗaɗɗiyar yarinyar fa ƙanwarki ce?” A fusace ta juyo ta ce “Kai ka kama kanka wannan ba tsarar ka ba ce matar aure ce, idan kuma kana son kwana a hannun sojoji to ka ci gaba da abin da kake ka gani..” Dariya ya yi ya kalli Andizo ya ce “ 'Yan mata karki wani damu so ne take ta kashe miki kasuwa, saboda ni ba na son gajeruwar mace sai doguwa kamar ke..” Idan table ɗin da suke zaune ya tanka masa to Andizo ta ba shi amsa, haka ya gama surutan shi ya koma ya zauna ganin malam ya tafo cikin ajinsu.. Bayan kwana biyu Salim ya kawo mata waya da layi da komai ya buɗe mata, ranar tun da ta dawo daga makaranta ta tsare shi ya dinga kowa mata abubuwan da ba ta gane ba har dare sannan ta rabu da shi ya bar part ɗin saboda ranar kwana Aminatou ne. Washegari ta buɗe wata ƙaramar jaka ta fito da 'yar ƙaramar takarda, numéro ɗin Mom ta sa ta kira ta aka ɗauka. Da murna Andizo ta ce “Hello Mom ina wuni ya gida ya iyali? Don Allah ki ba ni ƙawata mu gaisa..” Mom ta riƙe baki tama faɗin “A a, wa nake ji kamar amarya? Kina nan ma Khadija? Farrah har ta gaji da kukan a nemo mata ke..” Fuskar tausayi ta yi ta ce “Ayya Allah sarki ƙawata alƙur'an na yi kewar ta sosai, kinga fa sai jiya ya saya mini waya shi ne na sa lambar na kira..” “Ai kuwa dai kin kyauta ga ta nan ma ta shigo bari na ba ta.” Miƙa wa Farrah wayar ta yi ta ce Khadija ce da sauri ta amsa tana dariya ta fita a ɗakin. “Hello Khadija ya kike ya angonki? na yi kewar ki sosai.” Dariya ta yi suka dinga hira ana labaran abin da ya faru tun bayan rabuwar su, sai da suka yi awa uku cif suna hira shima ba dan sun gaji ba katin Andizo ne ya ƙare kiran ya yanke, sake kira ta yi ta ji ba ta shiga sai ta aje tana jiran Salim ya zo. Yana zuwa ta miƙa masa wayar ta ce “Wannan wayar ba sabuwa ba ce ji fa daga kiran Farrah muna magana kawai ta fita, na sake kira kuma ba ta ƙara ta lalace ka kai a canja mini wata..” Kallon wayar ya yi sai kuma ya amsa ya shiga layin da ta kira ya ga adadin lokacin da suka ɗauka suna waya, dariya ya yi ya ce “Kai kai kai! Ai kuwa sai kin kawo kuɗi za a gyara miki ita tun da ke kika ɓata..” Dafe ƙirji ta yi ta ce “Waiyo yanzu kenan kana nufin ba zan sake yin magana da Farrah ba? A to bari na duba kamar dai ina da kuɗi da Hajja ta ba ni da zan tafo.” Ta faɗa tana wucewa ɗaki ya bi bayan ta da kallo yana lumshe idanu. Dala dari ta kawo mishi ta ce “To a kai a gyara mini ina so gobe na kira ta akwai labarin da ban faɗa mata na makaranta, itama ta ce za ta faɗa mini wani abu sai aka hana ta magana..” Ta faɗa tana zama.. Amsar kuɗin ya yi ya ɗauki wayarsa ya turo mata katin dala ɗari, ya ce mata kar ta taɓa wayar ta bari sai gobe har whatsapp zai buɗe mata w kafin safe wayar za ta gyaru da kanta, murna ta dinga yi tana mishi godiya ta tafi kitchen ta dafo masa indomie da ruwa-ruwa ta kawo mishi. Kallon ta ya yi yana murmushi ya ce “Sannu da ƙoƙari Allah ya miki albarka.” Amin ta ce ta ɗauke wayar ta kai ta can cikin kayan sawar ta ta duba tsakiyar kayan ta totsa ta tana jiran gobe ta yi ta fiddo ta, a cewar ta in wayar ba a ganin ta za ta fi gyaruwa da wuri.... _Maman Nusaiba ce🤙🏻_ [6/4, 11:35 PM] Ummu Amjad: _*AREWABOOKS@SARATALKASUM88*_ 28 Can cikin dare ta farka ta tashi tana kallon lokaci, ƙarfe 3:am daidai na dare ta riƙe kai ta ce “Oh ni Dije, alƙur'an na ɗauka gari ya waye ashe tsakiyar dare ne.” Tashi ta yi zaune tana kallon waje ɗaya, kallon fegen ta ta yi ta kai hannu ta shafa inda yake kwanciya, hawaye ne suka cika mata ido sam ba ta son ya yi naisa da ita, ko bacci ne in ba a jikinsa ba ta ji ta duk ji take kamar a waje ta kwanta. Dogon numfashi ta ja tana goge hawayen da suka samu damar zubowa, sauka ta yi a gadon ta nufi banɗaki ta ɗauro alwala ta fito duk sai ta ji ɗakin ba ya mata daɗin zama, kabbara ta tayar ta gabatar da nafila raka'a shida sannan ta zauna, addu'a sosai ta yi wa iyayenta tana yi tana kuka har cikin sujjada sai da ta musu addu'a, tun da ya sanar da ita iyayenta sun rasu sai ta zama wata kala, lokaci zuwa lokaci sai ta yi shuru tana tunanin itama da yanzu da mamanta watarana da sai ta kawo mata ziyara dan ta ga lafiyarta irin na Ummin Aminatou. Jikin gado ta jingina tana jan carbi har bacci ya yi gaba da ita.. Ɗakin ya shigo sanye da farar jallabiya bakinsa ɗauke da sallama, tsayawa ya yi yana kallon ta ya saki murmushi, wani matsayi take ƙara samu a can cikin lambu zuciyarsa saboda yadda take ruƙo da ibada, duk rashin jin ta da shirman magana da lokacin sallah ya yi za ta bar komai ta je ta gabatar. Tsugunnawa ya yi a gaban ta ya kai hannu ya shafo fuskarta yana faɗin “Ma femme tashi ki yi Sallah an kira sai ki koma baccin.” A hankali ta buɗe idanuwanta tar a kanshi, murmushi ta sakar masa ta miƙa hannu ta matso fuskarsa ta sumbace shi a goshi sannan ta ce “Barka da asuba mai hankali shirin Allah mijin Dijan Hamma.” Dariya ya yi ya ce “Yau kuma da salon gaisuwar da aka zo? Gaskiya kina ƙara shiga raina ma femme, Allah ya bar mu har gidan aljanna maɗaukakiya, tashi ki yi Sallah ni zan wuce masallaci kin san yau ba a école Samedi ce, to daga yau za ki fara zuwa Islamiyar da na je jiya na samar miki gurbin karatu..” Waro idanu ta yi ta miƙe tsaye ta ce “Waiyo daɗi ni uwar masu gari, Allah ya saka da alheri Ubangiji ya ƙara maka budi na alkhairi da ƙarfin imani, Allah saka ka a aljanna..” Cikin jin daɗin addu'ar ya amsa da amin yana miƙewa tsaye, sai da ya ga ta shiga banɗaki sannan ya wuce. Ƙarfe takwas ta shirya ta saka Unform ɗin da ya kawo mata, sosai kayan suka mata kyau ta ɗaura ɗankwali ta saka hijabin tana murna sosai, kallon ta ya yi ya kamo hannunta ya juya ta irin na 'yan India yana faɗin “A a matar tawa chass abinki, kinga kuwa yadda kika yi kyau kamar ba ke ba? Wai meye sirrin na ga sai wani ƙara zama lukuta kike kin yi fes kin barni?” Dariya ta yi ta yi tsalle ta dire ta yi juyi a gaban shi ya riƙe kwankwaso yana kallon ta suna dariya, shoki ta ɗauko ta dire sannan ta ce “Alƙur'an mai hankali ina sonka sosai, kaima fa ka haɗu kamar ba kai ba.” Ta faɗa tana gyara hannun hijabi. Ɗaukan ta ya yi ya ɗauki jakarta ya fito da ita har bakin mota, hakan ya yi daidai da fitowar Aminatou tan gansu a haka ta yi saurin dafe ƙirji kamar za ta faɗi, nan da nan kishi ya motsa mata ganin yadda suke ta wasa a bakin motar taƙi ya saka ta shi kuma yana mata magiya. Tuno maganar Umminta ta yi ta yi saurin faɗin “A'uzu billahi minan sheɗani rajim. Ya Allah ka sassauta mini wannan baƙin kishin nawa kar ya rinjaye ni wataran na cutar da wannan yarinyar, Wallahi ba na son ganin ki da mijina kawai dan babu yadda zan yi ke matarsa ce Allah ya halatta masa ya yi fiye da biyu ma, kuma na shaida mijina kana da adalci ba ka tauye hakkina..” Da sauri ta goge hawayen da suka zubo mata ta gyara zaman hijabinta ta dinga karanto lahaula wala ƙuwata ta doshe su tana mai ƙaƙalo murmushin yake.. Tsayawa Andizo ta yi ta ce “La ka ga Adda za ta fita itama, ai sai mu tafi tare ko?” Ta faɗa tana kallon Aminatou. Juyowa ya yi yana ƙare mata kallo, hannu ya miƙa mata suka yi musabaha yana murmushi ya ce “Gaskiya kin yi kyau matuƙa, yanzu wannan wankan ba ni za barwa na kalla na more ba gidan Ummi za a kai?” Murmushi mai sauti ta yi ko ba komai ya sanyaya mata zuciya da ruhi, juyawa ta yi ta ce “A a ku tafi abin ku na yafe ba na so na ɓata muku lokaci.” “Gaskiya ki zo mu tafi sai a fara kaini tukun ke sai ya wuce inda zai je.” Andizo ta faɗa tana turo baki. Dariya ta yi ta ce “To 'yar ɓaci naji zan shiga mu je to..” Yawwa Andizo ta ce ta je da sauri ta shige baya tana dariya ta ce “Dan in walala na yi kwanciyata kafin mu je.” Ita dai Aminatou wani lokacin in Andizo ta yi wani abin mamaki take kamar babbar mace, shiga ta yi ya ja suka bar gidan.. Tun da suka tafi hira suke yi ita da Andizo shi dai Salim yana sauraron su, Andizo ta miƙo kanta tsakanin kujerunsu ta ce “Adda idan kika haihu ki sa wa baby sunana, kinga sai in samu takwara.” Saurin kallon ta Aminatou ta yi, a sanyaye ta ce “To Khadija in sha Allah zan miki takwara, amma ki mini addu'a Allah ya kawo cikin ko a wannan satin ko a cikin watan nan sai na haifa miki takwara, kema ai watarana za ki haihu sai ki wa 'yar taki suna na.” Dafe ƙirji Andizo ta yi ta kalli Salim ta ce “Wai da gaske watarana zan samu ciki irin na haihuwa? Kai to ma ya kiyaye ni ai ba zan iya ba.” Ta faɗa tana taɓe baki, tun da ta taɓa ganin yadda ake naƙuda a ƙauyensu ta ce ita kuwa ba za ta yarda ta yi ciki ba tun da wahala ake sha.. Dariya Salim da Aminatou suka yi, Aminatou ta ce “To fa! Ji wata magana a wajen Khadija, to tun da ba ki so ai shi kenan za mu gani nan da wani lokacin.” Turo baki ta yi ta koma ta harɗe hannayenta a ƙirji ta ce “Haka kawai yo ina zan iya wannan abin da ake ai sai in mutu l..” Aminatou ta ce ai kuwa za ta haihu ta ce ta ji amma ai sai ta zama babba ta yi girma sannan ta haihu, Aminatou ta ce to shi kenan sannan ta daina mita tana Allah ya tsare ta da haihuwa. Suna tsayawa sai da Salim ya shiga ciki ya kaita wajen malamar ya ce ta kula mishi da ita da kyau ta amsa da ba, matsala sannan ya dawo.. Daret gidan su Aminatou ya nufa suna tafiya suna hira har suka isa, ko shiga bai yi ba ya ce kawai ta gaishe da Ummi sauri yake in ya dawo ɗaukan ta zai shigo, to ta ce masa suka yi sallama ta shige ciki shi kuma ya juya ya koma.. Tun da ta shiga ajin ba ta cewa kowa komai ba ta takure a waje ɗaya, sai da wata matahiyar mata da ke kusa da ita ta ɗan taɓa ta ta ce “Baiwar Allah ya sunanki?” Murmushi ta sakar mata mata ta ce “Sunana Khadija, ke fa?” “Ni suna na Aishatou, amma dai yau kika fara zuwa ko? Dan na ga kamar dai yau na fara ganin ki.” “E yau ya kawo ni.” “Ma sha Allah, to Allah ya, bamu ilimi mai amfani ga al'umma da da kawunanmu.” Amin Andizo ta ce suka ci gaba da amsar darasi, sai ƙarfe ɗaya aka tashe su.. Haka ta kasance ba ta hutu kullum tana makaranta, sosai take gane karatu yayin da Aishatou ta dinga koya mata wasu abubuwan tun da ta ce mata ita matar aure ce, da farko ba ta yarda ba sai da Salim ya zo ɗaukan ta ta janyo ta suka zo har wajen ta tambaye shi, murmushi ya yi ya ce tana aure shi ne ma mijinta, abin ya ba ta al'ajabi ta kuma, birgewa ganin yadda yake nuna mata tsantsar kulawa kamar zai mayar da ita ciki. Andizo ta manta da batun wayarta sai da watarana ta yi wanka za ta ɗauko kaya taki wani abu, da mamaki ta ƙara lalumawa ta zaro sai ta wayar ce, dafe kai ta yi ta ce “Ni har na manta da wayar nan Wallahi, ga shi kuma inanson mu yi magana da Farrah.” Kunna wayar ta yi ta samu waje ta zauna, kamar jira ake ta buɗe wayar sai ga kiran Mom ya shigo wayarta, ta washe baki tana faɗin “Allah sarki Mom ai dama yanzu nake shirin kira.” Ɗaga kiran ta yi tare da yin sallama Farrah ta amsa. “Haba Khadija ina ta kira sai a ce wayarki a kashe take ko lalacewa ta yi?” “Gyara zama ta yi ta ce “Ki bari kawai karatu ne ya ɓoye ni, to kuma ranar da muka yi hirar nan wayar ta lalace sai da aka gyara ta..” “Ayya to Allah ya kiyaye gaba, so nake na miki surprise ne..” “Da gaske?” Ta faɗa tana yin dariya.. “Sosai ma an jima za mu tafi Niamey tare da Antyna wajen Yayar Mom mu mata weekend..” “Ka amma ko da naji daɗi za ki zo gidana ai ko?” “Dama ai dan na zo gidanki zan biyo ta ba wai dan na ga wannan matar mai faɗan tsiya ba..” Ta faɗa tana haɗe fuska. Daɗi sosai Andizo ta ji suka ci gaba da labaransu na makaranta.. Yau da yamma sai ga Sabrin ta zo gidan Aminatou, ba yabo ba fallasa ta tarbe ta, ta kawo mata ruwa ta zauna ta ɗauki waya ta kira Andizo ta ce ta zo su ɗaura girki. Kallon ta Sabrin ta yi tana wani taunar cingam ta ce “Ƙawata wai wata Khadijar naji kina kira ta zo ku yi girki?” Daure fuska ta yi ta ce “Abokiyar zamana ko da wani abin dan na kira ta mu yi girki?” Cike da mamaki ta ce “Oh ni! Yaushe kika zama mai ƙwaƙwalwar kifi ban sani ba? Kishiyar taki ce kike yi wa haka? Anya ba ki fara shan kodin ba?” “A a uwar abin da ya fi kodin nake sha, dama neman ki nake dan na faɗa miki daga yau babu ni babu ke karki sake zuwa gidana, ke ko a hanya muka haɗu kika nuna kin sanni sai na miki rashin mutumci tun da na ga alama so kike ki ruguza mini rayuwar aurena, kina ɗora ni a kan keken ɓera ki kaini ki baro na koma ina zaman gida kamar ke, to daga yau na yanke alaƙar da ke tsakani na da ke. Saboda tsabar shisshigi da ya miki yawa kamar ke Salim yake aure kika sa ake bibiyar rayuwar yarinya duk dan ki tozarta ni ita kuma ki cusa mata baƙin ciki, ke Salim yake aure ko ni? Tambayar ki nake ko kun hada dangi da shi?” Tashi Sabrin ta yi rai ɓace ya kalli Aminatou ta ce “Yau ni kike faɗa wa wannan baƙaƙen maganganun? To kin yi da shegiya za ki gani, duk taimakon da na miki ina raka ki wajen malamai da bokaye duk dan ki samu fada a wajen mijinki shi ne yau za ki saka mini da haka? Daɗin ta ma daga ke har mijin naki dukkan ku juya ne ba haihuwa kuke ba bare ki yi gadara da shi, da ke ce mai matsalar waccan shashashar ai da yanzu ta samu ciki. Kin yi da ƴar halak Wallahi na rantse sai na rama wannan wulaƙanci, sai na tona duk wani ƙulli da muka yi ni da ke tun daga farko har ƙarshe mijinki sai ya san ke wace ce mai fuska biyu, tun da har kika yi kuskuren shiga gonata za ki ga abin da zan yi, kuma ni duk abin da nake yi ba dan ke nake ba ina da tagger ɗina daban, ke na ma fasa faɗa za ki gani a aikace.” Tana gama faɗin haka ta fita fuu. A hanya suka haɗu da Andizo za ta bangaje ta ta yi saurin matsawa ta ce “A'uzu billahi minan sheɗani rajim!” A kufule Sabrin ta kalli Andizo ta ɗaga hannu za ta mare ta sai kuma ta fasa ta wuce. Andizo ta yi dariya ta ce “Wallahi da wannan hannun naki mai bleaching ya taɓa naman jikina in duk garin nan gatan ki ne sai na sa an daure, shegiya mai baƙar zuciya dama ni tun da na miki kallon farko naji ba ki kwanta mini a rai ba ƴar wahala, in ma kika sake zuwa gidan nan tun da naji abin da kika ce wa Adda sa wa zan yi ta danne mini ke na miki balle-balle a mazaunai, ke har bille sai na miki irin na fullo..” Har Sabrin ta tsaya sai kuma ta sha kanwa ta wuce fu ta fita daga gidan, sosai ta ji zafin abin da suka mata musamman ma Aminatou ta kuma sha alwashin sai ta rama abun da suka mata.. Shugowa ta yi tana kumbura baki ya ce “Ki rabu da ita Adda, ai dama mai hankali ya faɗa mini ke mutuniyar kirki ce kina da biyayya ita ce take son mayar da ke wani abin..” Murmushi ta yi tana ƙara jin son Salim tabbas ta yarda shi ɗin jajirtaccan namiji ne, tun da har zai iya yaba halayenta a gaban abokiyar zaman ta. Kitchen suka nufa suka girka abinci mai rai da lafiya sai ƙamshi yake tashi, babu abin da yake damun Aminatou irin gorin haihuwar da soma mata, addu'a ta cigaba da yi Allah ya ba ta ciki itama ko za ta ga gudan jininta a duniya... Da gudu ta fito ta leƙa wajen Aminatou ta ce “Adda na tafi na taro ƙawata ta zo.” To ta ce mata ta fito ta nufi bakin get, budewa ta yi ta leƙa ta ga mota biyu a tsaye, har za ta koma saboda sun ba ta tsoro sai ta ga Farrah ta fito daga cikin motar ta nufo ta. Dariya ta dinga yi tana kallon ta har ta iso suka rungume juna suna murna da ganin juna, ciki ta ja suka shige part ɗin.. Kallon ta kofar gidan direban da ya kawo Farrah ya yi, ya yi saurin janyo waya ya kalli photon ya kuma hasko na Andizo, da sauri danna kira. “Hello oga yau dai mun ga gidan su yarinyar da ka ce mu nemo tun watannin baya, ashe ma ita ce ƙawar Farrah.” Shuru ya yi na 'yan daƙiƙu ya jinjina kai ya ce “OK sir wannan karon ba za mu bari a samu matsala za mu kawo maka ita..” _Maman Nusaiba ce_ [6/5, 5:53 PM] Ummu Amjad: _*AREWABOOKS@SARATALKASUM88*_ 29 Sauke wayar Sultan ya yi yana sakin wani shu'umin murmushi, taku biyu zuwa uku ya yi ya ce “Oh my wife ina matuƙar kewarki sosai da sosai, ban san dalilin da ya sa kika bari aka aura miki wani daban ba bayan ni da nake da matsayin mijinki, amma ba komai duk na kusa kawo ƙarshen komai ko kin daina azabtar da zuciyata.” Tashi ya yi da sauri ya fito palo inda ya samu Jennifer zaune tana kallo daga ita sai wani ɗan pant da bra, tana ganin shi ta saki murmushi ta matsa tana nuna mishi kusa da ita ta ce “Sweetheart come here.” Hararar ta ya yi ya koma ɗayar kujerar ya zauna yana kada ƙafa, cike da raini yake kallon ta yana jan tsaki, da idan ta yi irin wannan shigar gabaɗaya susuce mata yake har sai ya samu abin da yake so yake barin ta, wani lokacin ma sai su wuni a manne da juna suna shan soyayya, hakan ya sa Jennifer duk ta kori samarin da suke sheɗanci ta tsaya a wajen Sultan, domin ita a rayuwarta Allah ya mata mugun son namiji ɗan Africa musamman ma irin Sultan tsayayyan namiji ga kwarjini ga nuna izo, ga shi kakkarfan jarumi a fagen buga bal. Shi ya sa ta ƙudiri aniyar wannan karon da ita zai tafi Nigeria ta je ta ga ahalinsa, in daga can ma sai a ɗaura musu aure, yayin da duk wani motsin ta Sultan na gani yana mata mahaukaciya, shi yanzu gabaɗaya ta fitar masa a rai ba ya jin sha'awar zama da ita kwata-kwata, tun da ya haɗu da Andizo ya yanke alaka da duk wata mace daga kan turawa har na gida Nigeria in ya je da suke zuwa.. Tashi ta yi ta iso gaban shi ta zauna a kan cinyarsa tana shafa shi kamar yadda suka saba ya kawar da kai ya ce “Jennifer go.” Ƙin tashi ta yi ya sake mata magana amma taƙi tashi, a fusace ya hankaɗa ta ta faɗi tim ya zabga mata mari amma taƙi barin inda yake sai so take ta rungume shi, cikin hargowa ya ce “Jennifer na ce ba na so ki ƙara taɓa ni, oya get out of my house.” Gefe ta koma tana kuka saboda marin ya shige ta sosai, da yake ya koya mata Hausa tana ji sosai ta gane me ya faɗa mata, nuna ta ya yi da hannu ya ce “Na faɗa miki ni yanzu ina da mata na daina kula kowacce mace ki je can ki ƙarata da sauran 'yan iskan samarinki.” Ya faɗa yana juya mata baya. Tashi ta yi tana share hawaye murya na rawa ta ce “Babu inda zan je ina nan a tare da kai, ba ka isa ba Sultan sai ka aure ni babu ruwana da matarka, a baya ba ka ce mini addininku ya ba ku dama ku auri mata 4 ba? To ka zauna da mu biyu mana I really love you Sultan, ba zan iya rayuwa da kowanni namiji ba in ba kai ba. Kuma ina nan a gidan nan dole ka tafi da ni Nigeria, ko dan ka ga iyayena sun mutu ina hannunka shi ya sa har kake dukana? Ko mai za ka yi sai mun je tare har gidanku an mana aure..” Tana gama faɗin haka ta ja jikinta ta shige ɗaki ta banko ƙofar. Kallon ƙofar ɗakin ya yi ya ja tsaki ya wuce a gidan fuu, dan shi yanzu ba ta ita yake ba ta yadda zai dawo da abar ƙaunarsa yake. Ranar Andizo da Farrah wuni suka yi suna shirme, har girki Andizo ta zo ta musu na taliya fara da yaji da manja suka ci. Da yamma Salim ya dawo daret ya wuce part ɗin ta, tun kafin ma ya shiga ya dinga juyo dariyarsu ya yi murmushi ya ce “Oh su Dije ƙawa ta ƙaraso ashe, ko me suke yi?” Ya faɗa yana kwankwasa ƙofar. Da sauri Andizo ta tashi tana kallon jikinta ta ga ba komai, ɗaki ta nufa da gudu ta je ta ɗauki turaren da Aishatou ta ba ta ta ce in mijinta zai dawo daga office ta sa ta tarbe shi da shi, lumshe ido ta yi ta ce “Alƙur'an akwai ƙamshi mai daɗi.” Fita ta yi da sauri Farrah kuwa ta tashi ta shige ɗakin da aka kai mata kayanta, domin ta ɗauko wayarta ta kira Mom vidéo call su gaisa.. Buɗe ƙofar ta yi a hankali tana sakar mishi da murmushi, wani daɗin ƙamshi ne ya ziyarci Salim ya lumshe ido ya shaka. Hannu ta miƙa ta amshi jakar computer ta ce “Sannu da zuwa mijina.” Waro ido ya yi baki buɗe yana kallon ta cike da mamaki, far ta yi masa da idanu tana dariya, yau ɗin nan ta rantse duk wani abu da Aishatou ta koya mata sai ta yi wa Salim ta gani zai ji daɗi kamar yadda take faɗa mata maza na son irin haka. “Wow ma femme Wallahi je t'aime.” Ya faɗa yana jan hancinta. Dariya ta yi ta kama hannnunsa suka iso cikin palon, har za ta ja shi kan kujare sai ta yi jim ko me ta tuna sai ta ja shi suka yi gaba, shi kuma bin ta yake kamar raƙumi da akala. Inda ta ga yana aje computer ta kai ta aje, kallon shi ta yi ta ce “Wanka za ka yi ko kuma na zubo maka abinci? Yau kaima taliya da manja za ka ci..” Ƙara kashe shi ta yi da mamaki ya yi tagumi yana kallon ta, turo baki ta yi ta ce “To alƙur'an sai in fasa.” Murmushi ya yi ya ce “Haba ni na isa Khadija, zan fara yin wanka sai a kawo mini taliya da manja.” Ya faɗa yana dariya dan shi ya manta rabon da ya ci taliya da manja, in bai manta ba tun sun makarantar kwana ta aikin soja. Banɗaki ta shiga ta haɗa mishi ruwa sannan ta fito ta ce “To je ka yi wankan.” To ya ce mata ya zo cire kaya nan ma ta haye kan gado ta ce ita za ta taya shi ya fidda, bai mata muso ba ta taya shi ya cire kayan ya sa towel ya shige banɗaki.. Yana fitowa ta gama kawo masa abincin ta jera, bayan ya kimtsa ya zo ya zauna yana kallon abincin, daurewa dai ya yi ya juya taliyar ya kai baki dan kar ya ƙi ci yau ta hana shi bacci cikin nutsuwa, mamaki ya yi jin yajin ya yi daɗi. Kafin ya ankara ya cinye tas tana mishi hira yana amsawa da eh ko a'a bai san ya cinye ba sai da ya sa cokali ya ji ba komai, kallon juna suka yi Andizo ta sa dariya ta ce “Yee alƙur'an ya cinye duka taliyar, da har kake wani yatsina fuska kamar ka ga kashi.” Jinjina kai ya yi ya je ya wanke hannu da bakinsa ya dawo, ruwa mai sanyi ta miƙa mishi ya amsa ya sha.. Sai da ta tabbatar ya samu nutsuwar da yake buƙata sannan suka yi wanka a tare ta shirya shima ya shirya sannan suka fito palo. Zama ya yi yana kallon ta tana ƙoƙarin kunna tv, yau duk sai ya ji ta canja masa da irin tararrayar da ta nuna mishi ta ba shi kulawa kamar wata babbar mace, tagumi ya yi yana murmushi duk inda ta motsa bin ta yake da kallo yana ƙara gode wa Allah da matar tasa ta yi soma nutsuwa. Ɗagowa ta yi ta harare shi ta ce “Malam ya da kallo na haka ko na canja maka ne?” Girgiza kai ya yi bai ce mata komai, har za ta yi magana sai ga Farrah ta fito sanye da hijabi hannunta da waya tana faɗin “Mom Wallahi muka yi girki ni da Khadija bari ma ki ganta da mijinta sun sha kyau ga su nan a zaune a Palo.” Ta miƙa wa Andizo wayar, amsa ta yi tana gyara zama ta ce “Mom yau dai gani ga Farrah, ya gida ya Nigeria?” Dariya Mom ta yi tana zaune a katafaran palon ta ana mata tausa ta ce “Ma sha Allah, ai dama cewa ta yi ba dai sister na za ta je Niamey ba kawai gidanki za ta je har su gama hutu, ina Maigidan naki yake?” Matsowa ta yi kusa da Salim ta ce “Ga shi nan Mom.” Hannu Salim ya ɗaga wa Mom ya ce “Ina wuni? Ya gida ya yara?” “Lafiya lau mai hankali shirin Allah.” Cewar Mom tana dariya. Shima dariyar ya yi ya kalli Andizo ta ce “Kin dai ganshi dama ba ki taɓa ganin shi ba Farrah ce ta ganshi lokacin da aka kawo ni nan..” “Ai kuwa dai na ganshi, to ayi ta haƙuri dai Salim ita yarinya ce dole sai ka kawar da kai a kan wasu abubuwan da za ta dinga maka, ga kuma ƙarin abokiyar rashin ji nan kun samu ta ce sai ta muku sati za ta dawo.” Murmushi Salim ya yi yana faɗin “Haba Mom ai yanzu Khadija ta nutsu sanin da kika mata a da yanzu ba haka take ba, ai naji daɗin zuwan Farrah saboda kullum a ƙaramin kashi ta mini hirar ta sau bakwai, kuma naji daɗi da ta kawo mana ziyara Allah ya ƙara ƙarfin zuminci a tsakaninmu..” Amin Mom ta ce suka yi sallama ta kashe kiran, Farrah ta samu waje ta zauna ta ce “Amma dai za kuke kaini wajen shan iska ko? Domin ina son na ga gari..” “Ba ki da matsala gobe in sha Allah zan sa Ahmad ya kaiku koda ni ban samu damar kaiku ba.” Wayar Andizo ce ta ɗauki ringing ta tashi ta ɗauko, ganin me kiran sai ta yi saurin ɗauka ta kara a kunne, shuru ta yi tana sauraron abin da ake faɗa mata, can ta ce “E Adda ga shi ɗazu ya dawo daga aiki, to bari na sa.” Ta faɗa tana buɗe speaker wayar, daga can ɓangaren Aminatou ta ce “Mijina yau zan maka albishir da abin da ba ka taɓa zato ba.” Saurin matsowa ya yi kusa da Andizo ya ce “A haba dai? To ina jinki kin dawo ne?” “A a ban dawo ba gani dai a hanya, na kasa daurewa ne na zo, gidan shi ya sa na ce bari na kira ku na muku albishir mai daɗi.” Ta faɗa tana zubar da hawaye sannan tana murmushi. Andizo da ta ƙagara ta ji wannan labari ta ce “Adda ki sanar da mu Wallahi na zaƙu naji.” Dariya mai sauti Aminatou ta yi ta ce “Ƙanwata ina muku albishir da ina ɗauke da cikin wata biyu a jikina.” Wani irin tsalle Andizo ta yi ta sa kuwa tana dira a kan kujera, ta juyo ta kalli Farrah tana dariya ta rungume Salim tana faɗin “Alhamdu Lillah addu'ar da muke ta karbu, wow za yi mini takwara kai waiyo daɗi don Allah da gaske kike Adda?” Cikin muryar kuka ta ce “Da gaske ne Khadija nima zan ga gudan jinina a duniya gani nan na ƙaraso gida, na so ma na wuce gidanmu dan na fara yiwa Ummi wannan albishir ɗin amma na tuna ban nemi izinin shi ba.” “Kai gaskiya naji daɗi sosai Adda kuka ya ƙare, Allah ya inganta ya sa ki haifo mana yan huɗu maza biyu mata biyu..” Dariya Aminatou ta yi tana yin packing ta ce “To Khadija Allah ya kawo su lafiya..” Amin ta ce tana dariya ta kalli Salim da ya zama kamar gunki, sai da ta kashe wayar ta taɓa shi ya firgita yana kallon ta ya ce “Don Allah da gaske ne abin da Aminatou take faɗa?” Far ta yi da idanu ta ce “Sosai ma kawai ku tashi muje mu taro ta ta ƙaraso.” Zamowa ya yi daga kan kujera ya yi sujjadar godiya ga Allah yana yi wa Ubangiji kirari tare da gode masa da wannan gagarumar kyauta da ba su ka a lokacin da suke tsananin buƙatar ta, yana dagowa ya tashi suka bi bayan shi. Ta fito daga motar tana shirin rufewa ta ji an rungume ta ta baya ta yi dariya ta juyo, Andizo ta kai hannu ta taɓa cikin Aminatou ta ce “Adda sannu.” Murmushi ta yi tana kallon Salim da ya harɗe hannaye yana kallon ta cikin wani kalar yanayi na farin ciki har ma ya rasa me za ce mata, hannu ta miƙa mishi ya ƙaraso ya haɗa su ya rungume suna ta murna. Part ɗin ta suka nufa Andizo ta shiga kitchen ta ɗauko mata lemo mai sanyi na kwalba ta miƙa mata ta ce “To ki sha wannan ko kin ji sanyi.” Amsa ta yi tana mata godiya ta buɗe ta sha, kallon su take ganin yadda suke farin ciki da samun cikin sai ta ji sun ƙara shiga ransa, sosai ta ƙara yarda da Andizo tana kuma gode wa Allah da ya ta gane gaskiya tun guri kafin guri ya ƙure mata, da ta ci gaba da tafiya a kan keken beran da Sabrin ta dora da yanzu ba sa jituwa da abokiyar zaman ta.. Ranar har dare suna part ɗin ta Andizo ta ce ta faɗi mai take so za ta girka mata, ta ce ɗanwake take so Andizo ta ce “A abu mai sauki Adda ai yanzu zan yo miki shi tun a Ƙauye Hajja ta koya mini shi, sannan Mamma ta koya mini wani sabo daban..” Ta faɗa tana shigewa kitchen. Sai kusan karfe goma na dare suka bar ɓangaren ta ita da Farrah ta ce ta yafe sauran kwanan ta ɗaya ya haɗa wa Aminatou ya yi kwana uku a ɗakinta albarkacin cikin aka samu za a mata takwara. Da kallo Aminatou ta bi Andizo tana jinjina lamarin yarinyar, in ta yi wani abin har mamaki take ba ta, ta tabbata ba lalle ba ne in da Andizo ce ta samu ciki ta haƙura da kwananta ta bar mata, idanuwanta ne suka ciko da hawaye ta yi saurin mayar da su tana murmushi. Salim ya kalle ta ganin yadda ta bi Andizo da kallo, kamo hannunta ya yi ya ce “Kin gani ko Aminatou, dama na faɗa miki Khadija ba ta da wata matsala ko kaɗan, saboda son da take wa cikin jikinki har ta bar miki kwana duk dan na kula .. “Gaskiya na yarda Khadija ta daban ce a cikin mata ina mamakin yadda take wasu abubuwan kamar ba ta jin kishin ka, duba fa kwanaki a ɗakinta kake da za ka yi tafiya ta ce sai dai ni na bi ka ba za ta bar Islamiyar ta ba ta je ta yi sati a wani wajen, Allah ya ƙara haɗa kanmu ya kare mu da duk wani wanda yake son ganin ya raba kawunanmu..” Ta faɗa tana kwanto kanta kafaɗarsa. Amin ya ce mata sai ga kiran Ummi ya shigo wayarta ta ɗaga, sai da suak yi way gabaɗaya da 'yan gidansu kowa yana taya ta murna amma ban da Abida da ta ce ita fushi take da ita babu ruwan ta da wani sabon cikin da ta yi. Ba Ta ji daɗin abin da ta faɗa mata ba amma ta share ta ce to kar Allah ya sa ta mata barka mana ko haihuwa ta yi in ta ga dama ta zo in ba ta gani ba kar ta zo... Suna shiga ɗaki Farrah ta shige ɗakinta har za ta rufe sai kuma ta juyo ta ce “To amma ai za ki zo mu kwana tare ko?” “Sosai ma yanzu zan canja kaya na zo gani nan.” Ta faɗa tana shigewa ɗaki ta rufo har da datse ƙofa. Kan gado ta faɗa ta cuta kanta a jikin pilo ta fashe da kuka mai tsuma zuciya, sam ba ta son yin bacci ba tare da shi ba amma dole ta bar wa Aminatou kwananta, saboda yadda ta ga Aminatoun na buƙatar Salim a kusa da ita. Tashi ta yi zaune ta yi tagumi ji take kamar ta ce ta fasa ba da kwanan amma wani sashe na zuciyarta na tausar ta, hannu ta sa ta goge hawaye ta ce “Allah ka da kishin shi ya sa na kasa kyautata wa abokiyar zama na, ya Allah ka rage mini kishin da nake ji a kan Adda Aminatou.” Zuciyarta ce ta dinga mata saƙie-saƙe ta miƙe tana a'uziya ta shiga banɗaki ta ɗauro alwala, Sallar shafa'i da wutiri ta gabatar sannan ta zauna tana karanto addu'ar yayewar ƙuncin zuciya, hannu ta ɗaga sama tana karantawa kamar haka: ” لاَ إلَهَ إِلاَّ اللَّهُ الْعَظِيمُ الْحَلِيمْ، لآ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ رَبُّ العَرْشِ العَظِيمِ، لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهْ رَبُّ السَّمَوَّاتِ ورّبُّ الأَرْضِ ورَبُّ العَرْشِ الْكَرِيمُ.“ Sai da ta ji ta samu nutsuwa da kyau sannan ta tashi ta canja kaya ta nufi ɗakin Farrah. A zaune ta same ta tana rubutu, ganin waya a aje sai ta gane waya take, zama ta yi a ɗaya gefen ta ce “Ke kuma da wa kike waya da daren nan?” Dariya ta yi ta ce “Daddy ne sai yau ya ga damar kira na, ya ma ce na gaishe ki ko Daddy.” Ta faɗa tana kallon Sultan da ke zaune yana shan tea. Jinjina kai ya yi ya ce “E ina gaishe ta ko kuma tare n?” Ya tambaye ta saboda so yake ya ganta. Juyo wayar ta yi ta ce “Ga ta nan ta juya baya ma, juyo Khadija Dad na miki magana.” Gyara ɗankwali ta yi Sam ba ta son yin magana amma dan kar Farrah ta ga ta mata wulaƙanci ta juyo ta murmushi a fuskarta ya ce “Barka da dare Daddy.” Waro idanu ya yi bai san ba lokacin da ya tashi tsaye ya ce “Wow Khadija ke ce kika zama babba haka?” Kawar da kai ta yi ta sauka a gadon ta zauna a ƙasa, saboda yanzu ta san ciwon kanta ita matar wani ce magana da wani namijin haramun ce a gareta in ba ta zama dole ba. Washegari ta shirya tsaf ta tafi ècole ita kuma Farrah ta tafi gidan sister Mom, yau ko Salim ba ta gani ba da idonta itama ta basar ta ci gaba da lamuran ta.. Da yamma gidan ya cika da dangin Aminatou sun zo taya ta murna, ko da wasa ba ta yi gigin zuwa ba duk da kuwa kiran ta da Aminatou take a waya amma ta ƙi ɗauka, gabaɗaya yau sukuku ta wuni ba ta son ganin kowa tana son ta keɓe kanta.. Bayan sati biyu da faruwar haka Andizo ta dinga ciwon kai mai tsanani har ya hana ta zuwa makaranta, kullum a ɓangaren ta Aminatou take tana zaune da ita har Salim ya dawo. Ganin abin ba na ƙarewa ba ne Hajiya Babba ta sa aka kira likitansu ya turo nurse ta zo har gida ta duba ta. Sai ta gama mata gwaji ta ce ta yo fitsari ta kawo mata, da kyar aka tashe ta saboda ko buɗe ido ba ta iya yi. Tana yi ta kawo mata ta musu Sallama ta ce gobe za ta zo da sakamakon duk abin da yake damun ta.. Washegari dai ta dawo ɗauke da takardar Andizo na da cikin wata biyu da sati biyu cif, murna sosai Hajiya Babba ta yi da samun ƙaruwa har biyu a lokaci ɗaya, ranar Salim kuɗi mai yawa ya dauko ya miƙa wa likitar ya ce goron albishir ne. Ita kanta Andizo ta ji daɗin samun cikin amma ciwon kan na damun ta. Sai da ta yi sati sannan ta samu sauƙin ciwon kan ya tafi, Allah ya taimake ta ba ta yin laulayi mai wahala kawai kwadayi take ji ga cin abinci kamar gara, da ta ci abinci an jima za ta ci kamar an mata sata sai ta ƙara ci, hakan ya sa Salim ya jibgo musu sayayyar kayan maƙulashe ita da Aminatou. Gabaɗaya da gari ya waye sai su tafi part ɗin Mamma a can za su wuni sai lokacin girkin abincin dare ya yi su dawo.. Next Fage _Maman Nusaiba ce_ [6/6, 11:43 PM] Ummu Amjad: _*AREWABOOKS@SARATALKASUM88*_ 30 Sanye take da doguwar rigar abaya ta ɗora ɗankwalin a kan kafaɗarta, hannunta ɗaya riƙe da plate ɗin Indomie ta ciko shi taf har baki yayin da ɗayan hannun shi kuma gorar ruwa ce babba ta riƙe. Kallon ta Aminatou ta yi ta girgiza kai, sai da ta aje a gaban ta ta ce “Adda za ki ci Indomie?” Done hanci ta yi tana yi fifita da hannu, kallon Indomie ta yi ta miƙe da sauri ta nufi banɗaki, Andizo ta bi da kallon tausayi tana faɗin “Allah sarki Adda Allah ya ba ki lafiya ki daina aman nan.” Sai da ta gama amayo duk abin da ta samu ya ɗan zauna a cikin sannan ta wanke bakinta ta fito tana nishi, baki ta buɗe kamar sakarya tana kallon Andizo da take shanye ruwan Indomie ta cinye tas, waje ta samu ta zauna tana huci ta ce “Gaskiya Khadija kin ji daɗin ki babu ruwan ki da amai irin nawa.” Gyatsa ta yi ta ɗauki ruwa ta sha sosai sannan ta aje, murmushi ta yi ta kalle ta ta ce “Gaskiya ni kam ina tausayin ki sosai Adda, kalli fa ki ga yadda kika rame kamar ba ke ba kin ƙara koɗewa kamar ana miki wankan farar fauda, I'm ba dan ba ma shi ne da na ci kamar kuturu ai da sai ya bari ki tafi gida dan ki samu kulawa ta musamman, to yaƙi daɗi nima na yi kukan na gaji a kan ya kaini na ga gida amma ya ce ba za je ba wai sai na haihu, yanzu fisabilillahi sheraka ta biyu fa har da watanni a gidan nan ban taɓa zuwa garinmu ba, ko wani nawa babu wanda ya zo na ganshi naji daɗi, Farrah ce kawai ta kawo mini ziyara.” Ta faɗa tana goge hawayen da suka gangaro kan kuncinta, sam yanzu ta ji ba ta son zaman gidan duk ya ishe ta musamman cikin jikinta da ta iya bacci kusan a tsaye take kwana.. Dafa ta Aminatou ta yi ta ce “Karki damu Khadija duka saura wata nawa mu haihu ma, nan da wata uku fa duk mun haihu kinga sai ki tafi ki ga gida da ɗiyarki ko ɗanki gwanin sha'awa. Ni kaina da nake ciki garin kina gani dai yau wata na 4 da ɗoriya ban je gidanmu ba ya hana ni fita, kina ce y ce wai ba ya so a wahalar masa da yara kamar ba mu muke ɗauke da yaran nasa ba..” “To shi kenan Adda amma dai ke ya kamata ki je gida ko kwana biyu ne ki yi dan Wallahi kina buƙatar kulawa ta musamman, shi ba a gida yake ba bare ya kula da ke kuma ya hana wani ya kula da ke, da a ce ni bani da komai sai na dinga kula da ke har ki haifo takwara ta..” Murmushi ta yi ta ce “Zan sa Mamma ta mishi magana ko zai bari, Ian so na samu hutu sosai duk da a nan ɗin ma ba wani abu mai wahala muke ba iya girki ne.” To Andizo ta ce mata suka ci gaba da tattaunawa domin samo hanyar da zai bar kowacce ta tafi gaban iyayenta a kula da ita... Washegari Salim ya dawo daga wajen aiki bayan Sallar isha'i Mamma ta ce tana son ganin shi, sai da ya ci abinci ya huta sannan ya nufi part ɗin su. Da sallama ya shiga suka amsa shi Hassana ta yi dariya ta ce “A a ga Abban 'yan biyu.” Murmushi ya yi yana shafa gemu in aka ce masa Abban 'yan biyu jin kansa yake a sama, zama ya yi yana gaishe su suka amsa da lafiya. Mamma ce ta fito daga ɗaki ta kalle shi yana gaishe ta ta amsa tana tambayar shi wajen aiki ya ce Alhamdu Lillah, sai da suka yi hira sosai sannan Mamma ta kira sunanshi, hakan ya sa ya gyara zama ya tattara duk wata nutsuwar shi ya miƙa mata. “Salim me ya sa ka hana Aminatou ta je gidansu ta yi kwana biyu? Haba wannan ai taushe haƙƙin ne wata nawa ba ta sa iyayenta a ido ba ka gana ta? Kuma gara ma ita a kan Khadija ita da tun da aka kawo ta ba ka taɓa cewa kai bari na kai Khadija ta je ta ga iyayenta da 'yan'uwanta ta sada zuminci, kawai ka kime su a gida kuma ba wanda ya kawo musu ziyara ai damuwar sai ta yi yawa. Ina so ka barsu su je su ga iyayensu, Aminatou ta je gobe ta ta yi kwana biyu saboda Umminta kullum sai ta kira ta tambaye ni ya jikin nata, ta ce tana so ta zo gida k hana ta ita kuma da ta faɗa mata ta ce ta haƙuri ta bi umarni mijinta za su dinga waya. Haka su Hajja da an yi kwana biyu sai Maigari ya kira yana tambayar ba dai matsalar komai a game da jikarsa? Na ce masa ba komai sannan ya kashe waya, wannan son kan naka ya yi yawa ka tausaya musu mana.” Ta faɗa tana kallon shi.. Sunkuyar da kai ya yi yana sosa ƙeya, shi fa ba ya son su matsa daga inda yake. Ɗagowa ya yi ya kalli Mamma ya ce “To Mamma in sha Allah gobe sai ta je ta musu kwana biyu ko uku ta dawo, ita kuma Khadija nan da sati ɗaya zan kai ta itama ta yi kwana biyu ko ukun naje na dawo da ita.” “Kai na ci butar ubanka Salimu, yarinyar ta shekara biyu cir har da ɗoriya ka ce wai ka kaita ta yi kwana biyu ko uku ka ɗauko ta ba ka kirki ashe ban sani ba? To ba ka isa ba sati za ta yi ko sati biyu ko kai ka haifa musu ɗiyar da za ta yi kwana biyu ta dawo kamar wadda ake kora daga garin? To ba na son wannan rashin kunyar taku ta sojoji, kuma su kansu sun matsu su ganta ko da za ka auro ta ciniki aka yi suka sayar maka da ita?” Ta faɗa tana dungure mishi kai.. Dariya Hassana ta yi ta ce “Kuma fa haka ne Hajiya ai in da a ce ni ce a zaman Khadija Wallahi summa tallahi idan na dinga ma kuka da buri dole ka kaini na ga iyayena, yo ina zan iya shekara biyu gari ba wani nisa mai yawa ba ban ga dangi ba..” Duka ya kai mata ta yi saurin komawa bayan Hajiya Babba, nuna ta ya yi ya ce “Idan manya suna magana kika ƙara sa baki sai na kakkarya ki.” “Kai dallah gafara daga nan, ita ba mutum ba ce da za ka ce ba za ta sa baki a al'amuran da suka shafi rayuwarka ba?” Shuru ya yi bai sake cewa komai ya ɗauki wayarsa ya miƙe ya musu sallama ya tafi. Ko da ya dawo bai samu Andizo ba a part ɗin ta sai ya wuce part Aminatou, a palo ya same su Andizo na yi wa Aminatou tausa sai sannu take jera mata, kallon su ya yi ya tsaye yana faɗin “Lafiya dai Khadija?” “Wallahi tashi ne ta yi za ta shiga banɗaki ta zame za ta faɗi, Allah ya taƙaita ina nan na taro ta shi ne ta ce kafaɗar ta sage na matsa mata.” Zaro ido ya yi ya matso kusa da ita yana jera mata sannu, a sanyaye ya ce “Don Allah ku dinga bi a hankali wajen tafiya musamman ma banɗaki kunga shi dai kasan shi ba ya rasa digon ruwa, to kuke tafiya a hankali karku ji wa kanku ciwo da Baby's ɗin mu..” To Andizo ta ce dan ita Aminatou zazzaɓi ne ya rufe ta, tashi ya yi ya ɗauki tarkacan kayan maganin ta ya zo ya ɓallo kowanne ya ba ta ta sha. Da kanshi ya dauke ta ya kaita ɗaki ya kwantar ya lulluɓa mata bargo sannan ya fito, yana fitowa ya ga ba kowa tuni Andizo ta tafi part ɗin ta. Dawowa ya yi ɗakin ya buɗe fuskarta ya ce “Bari naje na yi mata sai da safe, sannan gobe zan kaiki gida ki musu kwana biyu..” Duk da tana jin jiki amma albishir din da ya mata ya sa ta ji kwarin jikinta, murmushi ta mishi da kyar ta iya cewa ta gode ta mayar mata da bargon ya wuce... Zaune ya same ta tana shafa cream a hannayenta, kallon shi ta yi tana murmushi ta ce “Allah ya taimaki Abban 'yan biyu.” Dariya ya yi ya zauna a bakin gado ya ce “In sha Allahu sati mai zuwa za mu je garinku, ita kuma Aminatou gobe zan kaita da safe haka wajen ƙarfe takwas.” Saurin kallon shi ta yi ya jinjina mata kai alamar tabbatarwa, daɗi sosai ya rufe ta ta ce “Na gode sosai da ka amince na je na gado su Maigari, Wallahi ina matuƙar kewar su kamar ba gobe, amma zan raka ka mu kaita.” Tausayi ta ba shi sai yanzu ya gane ashe duk tsayin lokacin nan juriya kawai take tana masa biyayya da ya ce ba za ta je garinsu ba, sai ta kwanta ya ja mata bargo ya tofe ta da addu'oi sosai sannan ya rage mata wutar ɗakin ya ja k'ofar yana ɗaga mata hannu. Gari na wayewa duk suka shirya Aminatou sai washe baki take tana haɗa kaya a cikin ƴar ƙaramar Jakarta, kala huɗu ta zuba da duk abin da za ta buƙata. Andizo ta shirya itama ta shigo ta ɗaukar mata jakar suka fito a tare, hakan ya yi daidai da fitowar su Mamma su duka har da Hajiya Babba. Kallon su Hajiya Babba ta yi ta ce “Yanzu don Allah kalle su gwanin birgewa, ai zaman lafiyar kishiyoyi ba ƙaramin kawo ci gaban miji yake ba, da farko Salim har wani baƙi ya soma yi saboda abubuwan da waccan duguwar matar tasa ta tsiro, yanzu da ta gane Allah ɗaya ne ta dawo kan hanya ba ga, shi suna zaman su kamar yaya da ƙanwa ba..” Murmushi Mamma ta yi tana bin su da kallo, ita kanta suna matuƙar birge ta sosai musamman yadda suke taimakon junansu, Ahmad ma gyaɗa ya yi ya ce “Wato Hajiya Allah ne ya dubi Aminatou da idanun rahama ta gane gaskiyar abin da take ba daidai ba ne, kuma abin da ya birge ni ma da ta rabu da wannan muguwar ƙawarta ta mai yawon dare, duk ita ce ta dinga ɗora ta a hanya marar kyau tana duga ta ta tayar wa da mijinta hankali ta kuma bi kowacce hanya wajen ganin ta zauna ita kaɗai a gidan yaya Salim. Ba su san duk wani motsinsu a tafin hannuna yake ba, har wuraren bokaye da malaman da suke zuwa duk ina sane..” Shiga motar suka yi ya ɗayar suka bar gidan, sai da suka yi nisa Mamma da ta riƙe baki saboda mamakin abin da Ahmad ya faɗa ta ce “Wai da gaske kake ko wasa Ahmad? Aminatoun ce ta je gidan boka?” “Kina mamaki da lamarin ku na mata musamman aka ce za a muku kishiya in ba ku aje yaro ba, gani fa suke kamar za a zoa kore su daga gidan ne. Ku ne ba ku san Aminatou a baya irin ta'asar da ta aikata ba dan ma ina yawan nuna mata na fa san komai duk abin da take, to Alhamdu Lillah tun da ta gane gaskiya ta tuba ta koma ga Allah, yanzu ita kanta in ta tuna abubuwan da ta yi a baya sai ta ji ta muzanta..” Turo baki Hassana ta, yi ta ce “Kai Yaya tonon asiri fa ba kyau, tunda dai ta tuba meye amfanin faɗa mana abin ya wuce? Ai, da ka yi shuru da bakinka kawai..” Hararar ta ya yi ta madubi ya ce “Wallahi ki fita idona Hassana, saboda ƴar wajen ki ce shi ya sa ba ki son a faɗi abin da ta aikata na cutarwa wa ɗan'uwanki?” “Ba haka ba ne yaya, na ga dai ai ta tuba sai ka rufe mata sirrin ta wanda ba kowa ya sani ba daga ita sai ƙawarta sai kai sai kuma mahaliccinmu, kai yanzu za ka rasa lefin da kake aikatawa ne nima sai na faɗi ka ji in da daɗi, yanzu da a ce maganar da ake tana ji za ka kashe mata kwarin gwiwa ta dinga yin ɗari-ɗari da shiga part ɗin mu, amma dai ba komai Allah ya yafe mana bakiɗaya.” Ta faɗa tana kawar da kai gefe, saboda ba ta so ya faɗa wa su Hajiya Babba abin da ba su sani ba marar kyau game da Aminatou, sarai halin hajiya babba watarana za ta iya mata gori da maganar kaɗan daga aikin ta ne.. Tsaki ya ja yana cewa babu ruwan ta tun da ba ita ya faɗawa ba, ta ce koma meye ai ta tuba ka manta da maganar kawai, sai da Hajiya Babba ta musu magana sannan suka daina musayar magana. Mamma ta sauke tagumi ta ce “To Allah ya sa mu dace ya shirya mana zuri'a..” Amin suka ce daga haka babu wanda ya sake cewa komai.. Su Aminatou na isa gidansu suka fito gabaɗaya suka shige gidan. Da murna Ummi ta tarbe su tana faɗin “Maraba lale sannun ku da zuwa.” Murmushi Andizo ta yi suka zauna Ummi ta sa aka kawo musu ruwaai sanyi suka sha sannan suka gaisa, sai da suka jima Salim ya miƙe ya ce “To Ummi mu za mu koma gida nan da kwana uku zan zo na ɗauke ta.” Ga in Andizo ta tashi ta ce “To ai da ka bar mana har Khadija a nan in yaso ka taso daga aiki sai ka zo ka ɗauke ta, ko ba haka ba Aminatou.” Dariya ta yi tana kallon Salim domin ta san ba lalle ba ya bar Andizo ta zauna ba, ruwa ta kurɓa ta ce “E Wallahi Ummi sa mun wuni muna hira.” Sosa kai Salim ya yi ya ce “Ummi kar nauyin ya miki yawa ga Aminatou kuma ga Khadija, ita fa Khadija ba ta ɗaukan lokaci take cin abinci ai ba, za ki iya, wannan wahalar ta girki ba Ummi.” “Kai dai ba ruwan ka in dai za, ka barta girki ai ba mai wahala ba ne zan musu duk abin da suka so.” Ba dan ya so ba ya amince ya fita ya bar musu gidan. Hira sosai suka dinga yi Andizo na faɗa wa Ummi ta yadda aka shayo kan Salim har y barsu su zo gida, dariya Ummi ta yi ta ce “Salim akwai ɗan rigima Wallahi, ashe duk lokacin nan ba ki taɓa zuwa gida ba? Sai jiya Aminatou ke faɗa mini na yi ta mamaki.” Turo baki ta yi ta ce “Wallahi fa Ummi kuma kullum so nake na ga su Hajja amma ba dama sai dai a waya.” Suna tsaka da hira Abida ta dawo daga makaranta, b ba ta kalli inda suke ba sai da Ummi ta daka mata tsawa ta ce “Anya Abida ba a mini musaya ba a asibiti ba da na haife ki? 'yar'uwar taƙi ta zo ki kasa mata sannu da zuwa har ki dinga wani kawar da kai kamar kin ga kashi.” Ɗaure fuska ta yi ta ce “Ni fa babu ruwana da ita Ummi, a gaban mijinta ta mare ni har sau biyu saboda wannan banzar kishiryarta ya ita ƴar miji daɗi, shi ne dan sun zo dan kula su? To babu ruwana da su ko ni na ce su zo mana gida?” Tana gama faɗin haka ta wuce fuu. Da kallo suka bi ta Andizo ta ce “Ki rabu da ita Ummi watarana za ta gane abin da take yi wa Adda kuskure ne.” “Amma dai da ciwo ƙanenka ya nuna ba ya son ganin ka.” Ba komai Aminatou ta ce suka ci gaba da hura. Sai bayan La'asar Salim ya zo ya ɗauke ta suka tafi gida. Tun da Aminatou ba ta nan hidimar Salim ta yi wa Andizo yawa, wani hali ma da ya tsiro ya ce da zarar ƙarfe 12 ta buga na rana zai turo a kai masa abinci, haka take ɗin hidimar da ta ga ƙarfe 10:30am ta yi take tafiya daga part ɗin su Mamma ta je ta ɗaura girki, da haka har sai da Aminatou ta yi kwana biyar sannan ta dawo. Ta dawo da kwana biyu itama suka ya shirya suka nufi ƙauye, sosai Andizo take murna yau dai za ta ga su Hammanta.. _Maman Nusaiba ce🤙🏻_ [6/10, 12:58 AM] Ummu Amjad: _*AREWABOOKS@SARATALKASUM88*_ 31 Tun da suka kama hanya surutu take mishi tana ba shi labarin rayuwarta ta baya, shi in banda eh ko a'a babu abin da yake ce mata saboda ransa bai so tafiyar nan ba. Ita kuwa ko a jikinta ƙarshe ma bacci ta yi abin ta har sai da suka zo kofar gidansu ya tsayar da mota ya soma tashin ta. “Khadija tashi mun zo yau dai ga ki ga Maigari.” Saurin buɗe ido ta yi ta kalli waje daga ta ga su Maigari a zaune suna kallo motar, zabura ta yi za ta fita ya yi saurin kulle motar yana kallon ta cikin yanayin damuwa. Ɗago kai ta yi suka haɗa ido ta turo baki tana kawar da kai, ruƙo ta ya yi ta kwanto kanta a jikinsa sai ta yi saurin tashi tana kallon shi, da mamaki ta ce “Shin ba ka da lafiya ne?” Girgiza mata kai ya yi bai ce komai ba, ta kai hannu ta dafa saitin zuciyarsa ta ce “Haba ni dai ban yarda ba mu sauka mu gaisa da su Maigari ka wuce asibiti a duba lafiyarka, ji fa yadda ƙirjinka daga ciki da yake bugawa kai ba ka jin ciwo ne?” Ta faɗa tana ɗaga rigarsa ta leƙa wai ko za ta ga abin da yake sa wajen bugawa da sauri-sauri.. Dariya ce ta subce mishi ya riƙe hannunta, shi wani lokacin mamaki da al'ajabi take ba shi in ta yi masa wani abin kamar babbar mace, wani lokacin kuma in ta yi wata maganar shirmen sai dai y yi gum da bakinsa ko kuma ya yi dariya, idan kuma ya ce zai yi dariya mai yawa ta hau sama ta tayar da rigima. Cire glass ɗinsa ya yi da ya dora a goshi ya aje a gefe, murmushi ya yi ya ce “Khadijana kenan, Allah ya nuna mini ranar da za ki gama gane komai na rayuwa ki zama babbar mace, yanzu ke ba ki san yadda zuciya ke bugawa ba a jikin ɗan'adam? Lalle da sauran ki har yanzu.” Hararar shi ta yi ta ce “To dama haka zuciya ke bugawa?” “E mana to ke ba ki taɓa jin taki zuciyar na bugawa kamar haka ba?” “Kai Alƙur'an a'a, ni kam ai ba ni da wannan.” Kyale ta ya yi ganin in ya biya ta sai su wuni a motar, buɗe mata ya yi ta fito shima ya fito, Andizo da murna ta nufo su Maigari tana faɗin “Maigari ba za ka tashi ka mini barka da zuwa ba?” Dariya ya yi ya kalle ta yana yaba kiwon Salim ganin yadda ta yi shar abin ta ga cikinta da ya girma kamar ya kai wata bakwai, tashi ya yi ya ce “A'a, lale maraba da uwar masu gari uwata ta kaina ni kaɗai a duniya sannun ku da zuwa.” Dariya ta yi ta rusuna saboda ta so ta durkusa sai ta kasa ta ce “Ina kwanan ku? Barkan ku da rana Liman ya gida ya su Goggo?” A tare suka amsa suna washe baki dan ta birge su, ga ta ta samu kulawa ta musamman sai ka rantse da girman Allah ba Andizo ba ce mai wuni tana neman fitina. Ciki suka nufa har Maigari yana gaba suna biye da shi, a farfajiyar gidan ya hango Ɗahare shanya kayan wanki ya kira sunanta, saurin juyowa ta yi ai kuwa suka yi ido huɗu da Andizo ta zaro ido ta ce “La Surbajo Hamma ce nake gani ko kuwa dai gizo5ne idanuwana ke mini kamar kullum?” Ta faɗa tana murza ido dan tabbatarwa. Dariya Andizo ta yi ta iso gaban ta ta ce “Adda Ɗahare ni ce dai ba gizo ba ne nake miki.” Rungume juna suka yi suna ta murar ganin juna, jan ta ta yi suka iso bakin rumfa ta shiga ɗaki ta tashi su Hajja tana sanar da su zuwan Andizo. Duk da mamaki suka fito suka ganta tsaye da ƙaton cikinta tana dariya, da sauri ta nufe su Hajja ta yi saurin taro ta tana faɗin “Ke ki bi a hankali ba ki gani ba ke kaɗai ba ce? Har yanzu kenan ba ki daina wannan shirman naki ba?” Rufe fuska ta yi tana dariya dafa cikin ta kalli Inna ta ce “Innata ina su Hamma?” Mirmu Inna ta yi ta kamo hannunta suka zauna ta wuce ta kawo mata ruwa mai sanyi, sai bayan ta sha sannan Inna ta ce “Su Hamma sun kusa dawowa Maigari ya aike su nan ƙauyen kusa da mu wajen ɗaurin auren ɗiyar abokinsa.” Ɓata fuska ta yi kamar za ta sa kuka ta juyo ta kalli Salim da ke gefen ta zaune, fakar idon su Inna ya yi ya taɓa hannunta suka haɗa ido ya kashe mata ido ɗaya ta banka mishi harara. Bayan sun gaisa sun ci abinci Salim y musu Sallama zai tafi ya dubi Hajja ya ce “Hajja ga ta ba na kawo ta ta muku sati ɗaya, zan dawo rana itayau na ɗauke ta saboda nan da kwana goma zan yi tafiya..” Riƙe baki Hajja ta yi ta ce “To amma ai da ka barta a nan har ka je ka dawo daga tafiyar, ka ga cikin jikinta ya tsufa haihuwa yau ko gobe gara tana wajen manya a dinga lura da ita, duk da nasan a can ɗin ma akwai Hajiya Babba.” Murmushi ta yi ya sassa kai ƙasa, dsam ya san za a rina wai a saci zanin mahaukaciya, a sanyaye ya ce “A a Hajja, idan tssn nan ba za take kula tana zuwa awon ciki ba, amma a can ita da abokiyar zaman ta tare suke zuwa a yi musu komai su dawo, sannan makaranta take zuwa boko da arabi idan tana nan karatun nata zai ja baya. Idan zan tafi a wajen Hajiya Babba za ta zauna har na dawo, kai ko na dawo ɗin ma ba lalle ba ne ta dawo ɗakinta sai bayan ta haihu, sannan ma Hajja cikin ai bai kai lokacin haihuwa ba..” Kallon Inna Hajja ta yi irin me za ta ce game da hakan, Inna ta ce “A to shi kenan in dai a wajen Hajiya Babba za ta zauna, Allah ya sauke ta lafiya shi ne fatan mu.” Godiya sosai ya yi ya musu sannan ya miƙe ya fita, ɗaka mata duka a cinya Ɗahare ta yi ta ce “Shashasha mijin naki zai tafi ba za ki je ki masa Allah kiyaye hanya ba? Maza tashi ki je ki masa sallama.” Kuka ta sa saboda dukan ya shige ta, kama ta Ɗahare ta yi ta tashi tsaye ta yafa mayafi ta nufi waje tana faɗin “Sai na haɗa ki da Hamma da ya zo in ce mishi dukana kika yi daga zuwa na, dama ai Mai hankali ya ce ba wata kewa ta da kuka yi naƙi ji yanzu ga zahiri na gani.” Fuska haɗe Inna ta ce “Haba Ɗahare ya za ki ɗaka mata duka haka? Ba ki ganin ba ita kaɗai ba ce.” “Yo ai gara da ta mata haka, ka zo da mutum ya ce zai koma ta kasa tashi ta mishi Allah kiyaye hanya?” Cewar Hajja. Shuru Inna ta yi jin Hajja ta sa baki a maganar. Har zai kunna motar ya ganta ta fito daga gida tana share hawaye, kallon ta yake yana murmushi a tunaninshi kukan rabuwa da shi ne take, sai da ta zagayo saitin da yake ya buɗe glass ya kalle ta da wani irin yanayi ya ce “Ma femme ko ba ki son zama mu koma?” Girgiza kai ta yi ta ce “Adda ce ta dake ni a cinya wajen sai zafi yake mini.” Da mamaki ya kalle ta sai kuma ya kawar da mamakin ya ce “Yi haƙuri da zarar na zo ɗaukan ƙi zan rama duk abin da ta miki kin ji shalele.” Gyaɗa mishi kai ta yi ya ɗauko kuɗi ya miƙa mata ya ce ya tafi ta ɗaga masa hannu, sai da motarsa ta ɓace wa ganin ta sannan ta koma ciki, ranar har dare ba ta sake yi wa Ɗahare magana ba ta ce sun ɓata sai bayan kwana biyu za su shirya. Da dare su Giɗaɗo suka dawo daga wajen biki nan suka samu Andizo, ai kuwa ta yi ta murna tana rungumar su ɗaya bayan ɗaya tana faɗin “Alƙur'an na yi kewar ku su Hamma.” Dariya Iro ya yi yana cire babbar rigarsa ya jefa wa Ɗahare ya ce “Kai su Andizo an zama manya iyye, Adda don Allah ki wanke mini kayan nan yanzu ki shanya mini shi va ne so su kwana a haka.” Hararar shi ta yi ta wurgo mishi rigar ta ce “Wallahi babu wanda zan yi wanki da daren nan, jaka kuka mayar da ni da za kuke kawo mini kayan wanki duk lokacin da kuka ga dama? To ba zan wanke ba.” Ta faɗa tana tashi ta bar musu wajen. Dariya Umar ya yi ya ce “Yawwa ƙanwata karki sake musu wanki tun da ke baiwarsu ba ce.” “In ka sake ce mini ƙanwarka sai na masga maka mari, saboda ka raina ni ni ce ƙanwar taka?” Tashi Inna ta yi ta karkade zaninta ta ce “Yo Umar ai ya fiki da shekara ɗaya dole kuwa ya ce miki ƙanwarsa.” Dariya suka sa ita kuma Ɗahare taƙi fitowa daga ɗaki sai cika take tana batsewa saboda maganar Inna, Hajja ce kawai ta goyi da bayanta ta ce kar ya kuma ce mata ƙanwarsa.. Washegari rana na ɗagawa Andizo ta fita gari yawo ganin gari, ai kuwa duk inda ta bi yara cu sai sun bi bayan ta ana faɗin “La ga Andizo ta zama ƴar gayu har ta kusa haihuwa.” Ita kuwa in ba dariya ba babu abin da take yi in ta ji sun ce mata haka, sai da ta zo saitin da Saminu yake sayar da fanke ta yi saurin jan hijabinta ta gyara, kallo wajen ta yi sai ta ga sai Lado a zaune a wajen kayan, nufar shi ta yi tana wani haɗe fuska. Lado na ganin ta ya saki baki yana kallon ta, yau Andizo ce yake gani ko kuwa dai gizo ne take magana ga ta ta zama babba har da hijabi a jikinta? Sake murza ido ya yi ya ga dai da gaske wannan fuskar ta Andizo ce. Tana isowa bakinta ɗauke da sallama ya amsa, kuɗi ta miƙa mishi ta ce “Lado a ba ni fanke a talatin, amma ina Saminu yake ne?” “A a sannu da zuwa Andizo mutanen birni, Saminu ai tun da kika bar garin nan shima ya bar gari, shi ne da zai tafi ya bar mini kayan sana'arsa nake yi.” Fuskar damuwa ta yi ta ce “Allah sarki Saminu, amma dai neman ilimi ya tafi ba yawon duniya ya tafi saboda da rashina ba ko?” Girgiza kai ya yi ya ce “Gaskiya neman abu biyu ya tafi, ya haɗa kudaɗensa bakiɗaya jika ɗari da tamanin ya tafi da su, ya ce zai je can birni ya fara neman sana'a sannan zai koma makaranta boko da arabi, amma ya ce duk wata uku zai ke zuwa ganin gida..” Ya faɗa yana miƙa mata fanken da ya ƙulla. Amsa ta yi tana faɗin “Allah sarki Saminu, to Ubangiji ya ba shi abin da ya je nema.” Amin Lado ya ce ta sake miƙa mishi kuɗin ya ce “Ki barshi ai ko ba komai kina da daraja a wajen abokina ba zan karɓi kuɗinki ba.” Godiya ta mishi sannan ta juya ta yi gidan su Hajaru. Wanki ta samu Hajaru na yi ai kuwa ta zo a guje za ta rungume Andizo Innar Hajaru ta yi saurin shiga tsakanin su ta ce “Ke meye haka? Ba ki ga yadda take ba ne?” Ja baya Hajaru ta yi tana kallon Andizo, ganin ta da ƙaton ciki sai ta sa dariya ta matso kusa da ita tana fadin “Ƙawata ashe mun girma? Kai Allah sauke ki lafiya zan sake zuwa Niamey a karo na biyu.” Dariya Andizo ta yi ta kama hannunta Innar Hajaru ta shinfida musu tabarma suka zauna, ita kanta mamakin Andizo take ganin yadda take magana a nutse kamar ita ba. Ganin Innar Hajaru ta tashi Andizo ta matso kuma da Hajaru ta ce “Wai Hajaru ashe Saminu ya bar gari.” “Hmm bari kenan ƙawalliya, Wallahi ba ki ga ba yadda Saminu ya koma abin tausayi duk wanda ya ganshi sai ya yi kamar ya zubar masa da hawaye, bayan tafiyar ki rashin lafiya ta kwantar da shi ashe ciwon sonki ne ke addabar zuciyarsa kuma ya hana Lado ya faɗawa kowa, har asibiti aka kwantar da shi a nan ne ma suka ce yana gaf da kamuwa da ciwon zuciya matsawar bai daina zurfafa tunani ba, amma yaƙi hi kullum photonki a ƙirjinsa yake kwana da shi ciwo ya sake dawowa, sai da ya ga Innarsa na kuka tana rokon shi ya rufa mata asiri shi kaɗai gareta kar ya mutu ya barta sannan ya rage abin da yake, to ƙarshe dai ta yanke shawarar tura shi wajen wani abokin babansa da ke can Niamey yana kasuwanci, ke har ma da makaranta ta ce idan ya je duk ya koma ya samu ilimi mai inganci dan wasu abubuwan da yake har da rashin ilimi ma..” Goge hawaye Andizo ta yi tana jinjina irin son da Saminu yake mata, addu'ar samun nasara ta mishi sannan suka ci gaba da hira. Ba Ta dawo daga gidan su Hajaru ba sai kusan magariba, gabaɗaya labarin Saminu ya sa jikinta ya yi sanyi jin yadda ya sha wahala duk saboda da ita, ranar ko Salim bai samu fuskar yin waya da ita ba da ya kira sai ta yi shuru sai ya ɗauka network ce ya kashe y sake kira, sai da suka yi haka kusan sau goma sannan ya gane yau 'yan surutun ba sa kanta ya haƙura ya barta. Shi ɗin ma dama Aminatou ce ta takura mishi sai ya kira mata ita sun gaisa ta ji ya ta sauka shi ya sa ya kira.. Kwanci tashi ba wahala wajen Ubangiji har Andizo ta yi sati a garinsu, tun safe aka haɗa mata kayanta kamar sun san Salim zai zo da wuri. Ƙarfe goma na safe sai ga shi ya iso, ba ta wani ja da nisa ba duk ta musu sallama suak ce sai sun zo suna tana rufe fuska ta shiga motar, tsarabar da suka mata aka jibge mta ita a bayan mota suka tafi su Maigari na ɗaga musu hannu.. Tun da suka kama hanya da suka gaisa ta soma ba shi labarin abubuwan da ta tarar a ƙauyen sai bacci y yi gaba da ita, kallon ta ya yi ya girgiza kai ya ce “Nana Khadijana kenan ke bacci ba ya miki wahala ba ruwan ki.” Ko da suka iso gida ba ta tashi ba ya kashe motar ya fito, zagayowa ya yi ya buɗe set ɗin ta ya ɗauke ta cak suka yo part ɗin ta. Aminatou da ta fito ta sa dariya tana faɗin “To ke kuma sai bacci ina nan ina ta jiran ki, to tashi maza.” Buɗe ido Andizo ta yi ganin ta a gidanta ta waro idanu ta ce “Kai, wai har mun zo kenan?” “Ga, zahiri kin gani.” Cewar Aminatou suka yi part ɗin ta. Zama suka yi suka dasa hira Salim ya yi tagumi yana kallon su sai murmushi yake, ganin kallon ya yi yawa Aminatou ta ce “Haba mijinmu ko mun canja maka ne wai? Na ga tun da yau ta yi ka sa ni a gaba kake kallo, yanzu kuma Khadija ta dawo ka saka mu duka a gaba ka yi tagumi kana kallo lafiya dai?” Sauke tagumin ya yi ya ce “Wallahi ba na so na tafi na barku har na kwanan wata ban ganku ba, da za su ɗauki wani a madadin hakan da ya mini daɗi.” “Haba dai Mai hankali shirin Allah, ai sati ɗaya kamar kwana ɗaya ne a wajen Allah nan da nan za ka ga ya yi ka dawo gida. Fatan mu dai Allah ya kaiku cikin sa'a ku dawo da tarin nasara..” Cewar Andizo. Dariya ya yi ya ce “Ke wai ba za ki daina ce mini mai hankali shirin Allah ba?” Dariya suka yi a tare Andizo ta ce “To ai gaskiya ce mai hankali ne kai ɗin.” Tashi ya yi ya fita su kuma, suak ci gaba da zama.. Da dare bai bari sun yi girki ba ya ɗauke su suka tafi wajen cin abinci suka ci a can, har da takeaway ya yo musu ya ce ko ya tafi da safe su cikar su yi girki, su dai da ido suke bin shi ya ja su suka nufi wani babba shagon sayayya, duk wani abin da yasan za su buƙata sai da ya sayo musu wanda har ya je ya dawo zai ishe su sannan suka dawo.. Gajiyar da Andizo ta yi tasa yau da ya zo mata ta yi kamar gawa ta bar shi shi kaɗai ya yi komai da kansa, da kyar ta tashi ya taimaka mata suka yi wanka sannan suka koma bacci. Washegari ƙarfe takwas ya shirya suka fito bakin mota duka 'yan gidan suka mishi rakiya, Ahmad shi ya ja motar zai kaishi airport din su da duk wani sojan da yake cikin wannan tawagar tafiyar ta su tuni ya je, shi ne ma ya ɗora minti biyar a kan lokacin da aka diba musu, sai da Ahmad ya ga tashin jirginsu sannan ya dawo gida. Ko da ya zo Andizo tana kuka wiwi da ta ganshi ta miƙe da sauri ta ce “Har ya tafi ko?”. Dariya ya yi yana zama ya kalli Aminatou ya ce “Ke ba ki kukan ba Aminatou, ai sai da suka tashi sama sannan na dawo gida.” Addu'ar sauka lafiya suka mishi sannan suka ci gaba da lamuransu, ita kuwa Andizo wuni ta yi ranar tana kuka da an jima sai ta danna mishi kira sai a je wayar a kashe take, gabaɗaya ta hana su sukoni Ahmad y samu ya lallaɓa ya ɗauki wayar Salim ɗayar da ya ba shi ya ce ya dawo da ita gida, text message ya turo mata ya ce _“Ma femme Idan muka huta zan kira ki video call kin ji, kuma in naji labarin kin yi kuka zan daina kiran ki har na dawo.”_ Gani suka yi kawai ta sa dariya hawaye na bin kuncinta ta kalli Aminatou ta nuna mata saƙon ta ce “Kin gani ko Adda ya ce zai kira video call da ya huta.” Ta faɗa tana zama a kusan Aminatou. Murmushi ta yi ta kalli Ahmad ya mata ƴar ido ta kawar da kai, ta ga lokacin da yake tura mata saƙon. Tun da ta samu, wannan saƙon sai ta ji zuciyarta ta samun salama ta kwanta bacci y ɗauke ta.. Har kusan La'asar ba ta farka ba, ana kira Sallah ta zabura a firgice ta tashi tana salati, Hajiya Babba ta yi saurin riƙe ta ta ce “Subhanallahi me ya faru Khadija?” Dafe ƙirji ta yi ta ce “Ina wayata take?” “Ga ta can a caji da kika sa.” Saurin sauka ta yi daga kan kujera ta je kan wayar ta miƙa hannu za ta ɗauka kamar jira ake ta tsaya sai ga kiran Salim ya shigo, da hanzari ta ɗauka cike da farin ciki ta ɗaga kiran ta ce “Hello mai hankali an je lafiya ya gajiya?” “Ba shi ba ne... _Maman Nusaiba ce🤙🏻_ [6/10, 11:08 PM] Ummu Amjad: _*AREWABOOKS@SARATALKASUM88*_ 32 Baya ta yi a ta faɗi Hajiya Babba ta yi saurin taro ta tana faɗin “Subhanallahi! Me ke faruwa Khadija?” Jikinta né ya ɗauki rawa amma ta riƙe wayar gam tana kokowa da numfashi da yake ƙoƙarin rabuwa da gangar jikinta, da gudu Hassana ta je ta ɗebo ruwa ta kawo Mamma da ke tsaye kanta suna tambayar ta ta amshi ruwan ta shafa mata a fuska tana salati. Dogon numfashi ta sauke baki na rawa ta ce “Mamma zan mutu ki taimake ni ya dawo ni ba na son tafiyar nan da ya yi.” Zama Mamma ta yi a gefen ta ta amshi wayar ta ga an kashe, Andizo ta ɗora hannu biyu a ka ta fashe da kuka tana miƙa wa Mamma hannu ta ce “Don Allah ki bani wayar na kuma kira naji, Wallahi zuciyata za ta buga in ban ji muryarsa ba..” Ganin yadda ta birkice sai Mamma ta ba ta wayar tana kallon ta cike da tausayawa, saurin danna mishi kira ta yi kafin ma ya gama ringing farko aka ɗaura. Ƙaran bindigar da ta ji ya sa ta ƙara miƙewa tsaye ta ce “Hello don Allah kai waye? Kuma ina mai wayar yake?” A ruɗe ya amsa da cewa “Abdoul ne.” Dafe ƙirji ta yi ta ce “Alhamdu Lillah har naji sanyi ina yake mai hankalin! Ba shi na masa magana.” A wannan lokacin fuskar Abdoul ta yi baƙi kamar an zuba mishi gawayi, yana cikin wani rami wanda bishiyoyi biyar suka kewaye ramin, ɗago kai ya yi ya leƙo waje ya ga abokan aikinsu sun gama kashe 'yan ta'ada sai mutum ɗaya da suka kama aka ɗaure shi a jikin wata bishiya. Sauke kai ya yi ya miƙe tsaye ya fito, ganin shi ya sa da gudu suka nufo shi ɗaya daga cikin su ya ce “Ina Oga yake? Fatan dai komai lafiya ko?” Girgiza musu kai ya yi yana musu alama da su yi shuru, gane hakan ya sa duk suka koma gefe wasu suna harhaɗa bindigun 'yan ta'adda da duk wasu muyagun makamai. Dawowa ya yi cikin ramin ya kira mutum biyu suka fito da Salim da jini ke ta zuba ta gefen cikinsa, kansa ma duk ya ɓaci da jini dai runtse ido yake yana cije lips. Kwantar da shi suka yi a filin wani ya buɗe jakar da ke goye bayanshi ya fito da maganin wanke ciwo ya iso gaban Salim, kama shi suka yi suka cire rigar wadon ma suka cire sai na ciki suka bar mishi nan aka shiga ƙoƙarin wanke masa ciwuka. Dogon numfashi Abdoul ya sauke ya koma gefe ya sauke wayar jin yadda Andizo ke ta rusa kuka ana rarrashin ta, girgiza kai ya yi ya kashe kiran ya sake kira ta ɗauka, a murya can ƙasa ya ce “Khadija ki kwantar da hankalinki Salim yana nan da ransa ciwo ne ya ji a ƙafa ana wanke masa ne, idan suka gama zan kira ki na ba ki shi ku gaisa kin ji ki daina kukan kar ciwo kema same ki, kinga idan kika yi haka ba zai ji daɗi ba idan ya samu labarin kukan da kika yi..” Ɗankwali ta sa ta goge fuskarta wadda ta yi kaca-kaca da majina da hawaye, tana ajiyar zuciya ta ce “N.. Na fasa kukan ka ji Hamma Abdoul karka faɗa mishi na yi kuka, amma don Allah ku dawo gida yau ni ba na son wannan tafiyar taku.” Ta faɗa wasu hawayen na silalowa daga kwarmin idanuwanta. Wani abu mai ɗaci Abdoul ya haɗiye ya kalli in da Salim yake magashiyan sai aiki ake a kanshi, wayarsu ta ma'aikata ce ta soma ƙara Abdoul ya kalli ɗaya daga cikin su ya ce ya ɗaga shi kuma ya dawo ga Andizo. “Khadija ki ba wa Mama waya ba mu da lokaci duk cikinmu wayar wannan ta Salim kaɗai ce aka ba mu izinin kunnawa, to yanzu da an jima za ki ji ta a kashe bani Mamma na mata magana.” Jiki a saɓule ta miƙa wa Mamma wayar ta kwanto kan cinyarta, har yanzu jikinta bai daina rawar sanyi ba. Kara wayar Mamma ta yi ta ce “Abdoul wai don Allah me ke faruwa ne da ku? Ina fatan dai lafiya ko?” Zama ya yi ya jingina da bishiya ya ce “Mamma gamu nan za mu dawo gida ƙila gobe da safe mu sauka, amma dai gaskiya..” Ya yi shuru dan bai san wani yanayi za ta shiga ba. “Amma dai me Abdoul ? Ka sanar da ni komai karka wani damu ni fa musulma ce nasan ƙaddarar Ubangiji a kan bawansa..” Hakan ya ba shi ƙwarin ya soma magana cikin wani kalar yanayi. “Mamma mun yi nasara kama waɗannan 'yan ta'adar da shekarun baya suka addabi ƙauyukan da ke kewaye da mu ciki kuwa har da ma haifar su Khadija, yau dai mun ci nasara da kansu duk mun kashe shegu mutum ɗaya muka bari da rai shima dan ya yi bayani ne da ya gama mu kashe shi, amma maganar gaskiya Mamma Salim sai addu'a.” Gaban Mamma ne ya buga da ƙarfe ta ɗan runtse ido dan kar Andizo ta gane akwai matsala, gyaran murya ta yi ta ce “To ina jin ka Abdoul ci gaba” “Ba zan iya ce miki komai ba Mamma sai mun je gida, yanzu dai ga su nan ana ƙoƙarin tsayar mishi da jinin amma yaƙi tsayuwa, saura minti ɗaya su ɗauke connexion ɗin wayar ki faɗa wa Khadija Salim ya ce zai dawo tun da ba ta so.” Ajiyar zuciya ta sauke ta ce “To shi kenan Abdoul Allah ya kaimu goben sai an jima.” Ta faɗa tana kashe wayar. Kallon ta duk suka yi ta danne kukan da ke ƙoƙarin zo mata da kyar ta ce “Khadija ki daina kuka Salim ya ce zai dawo tun da ba ki son tafiyar..” Murmushi ta yi ta amshi wayar ta ce “To Mamma gara dai ya dawo dan ni gabaɗaya hankalina bai kwanta da tafiyar nan tasu ba..” Sai da Hajiya Babba ta lallaɓa ta ta raka ta banɗaki ta sa mata ruwan wanka ta ƙulle kofar ɗakin sannan ta dawo palo, Aminatou da tuni jikinta ya ba ta mijinta ba lafiya ba ta yi tagumi tana kallon su, so take ta yi kuka ko za ta ji sauƙin abin da take ji a zuciyarta amma kukan ya ƙi zuwa, kallon da Mamma ta yi ta ruƙo hannayenta ta ce “Nasan ke kin san me ake kira da ƙaddara da kuma haƙuri da juriyar abin da kake so in wani abu ya same shi, ke ba kamar ita ba ce kina da hankali da hangen naisa shi ya sa na ce ma ki zauna, domin ko na miki dabara ba za ki yarda ba irin na Khadija ke babba ce, mijinku dai ya samu raunika sosai a jikinsa shi ya sa gobe za su dawo, amma a yadda Abdoul yake mini magana da wahala ma in mutuwa Salim ya yi ya ƙi ya sanar da mu sai dai ya zo mana da gawarsa, amma dai Allah ya kaimu goben karki damu kin ji ki yi ta addu'a karki saka tashin hankali a ranki.” Wani irin abu ne mai nauyi ya danne wa Aminatou ƙirji ta runtse ido tana faɗin “Lahaula wala ƙuwata illa billahil aliyun azim! Allahuma ajurni fi musibatee wa'akalifili khairan minha! Allah ya ka dubi marayun Allah ka tashi kafaɗun mijinmu, shi ne gatanmu Allah ya dube mu kar ya tafi ya bar mu a lokacin da muke tsananin buƙatar shi, Allah sarki ashe shi ya sa tun shekaranjiya ya sa mu a gaba yake kallo kar mai mana kallon ƙarshe, waiyo Allah ni Aminatou ni ba kaina nake ji ba halin da Khadija za ta shiga in ta ganshi a mawuyacin hali..” Ta sa kuka marar sauti ta ƙunshe bakinta da gefen mayafinta, Husaaina ta ruƙo ta tana rarrashin ta itama kukan take. Haka suka zauna jugum-jugum har dare Abba ya dawo daga kasuwa ya same su a haka, tambayar su ya yi ko akwai abin da yake faruwa, Hajiya Babba ta ja shi ɗakinsa ta sanar da shi komai. Shi kansa ya firgita da wannan labarin abin sai ya tuna mishi da shekarun baya ya yi baya ya zauna yana ta salati, nasiha Hajiya Babba ta dinga mishi ya samu sassauci sannan ta fito.. Ranar a gidan ba, wanda ya yi baccin kirki kusan a zaune suka kwana sun ƙagara gari ya waye. Ƙarfe takwas daidai Abdoul ta kira Mamma ya sanar mata sun iso amma su same su a asibiti dan an yi gaba da Salim, to ta ce mishi ta kashe wayar ta ɗauko hijabi suma su Hajiya Babba duk suka shirya, so suke su tafi kafin Andizo ta farka sai dai suna gama shiri ta fito itama sanye da hijabi tana kumbura baki ta ce “Shi ne za ku tafi ku barni?” Kamo hannunta Hajiya Babba ta yi suka nufi harabar gidan. Babbar motar gidan suka shiga Ahmad ne ke ja shi kuma Abba tuni ya riga su tafiya.. Babbar asibitin garin suka isa inda tun daga bakin asibitin sojoji ne a kewaye da motocinsu, zaro ido Andizo ta yi tana leƙawa ko za ta ga Salim a cikin waɗanda suke tsaye amma har suka zo shiga ciki ba ta ga mai kama da shi ba ma. Suna paka motar wani soja ya buɗe musu suka fito yana gaishe su suka amsa, shi ya musu jagora suka isa har bakin ƙofar ɗakin da yake ciki. Zama suka yi suna jiran a ba su izinin ganin shi, Abba ya kira Abie yake sanar mishi suna asibiti Salim ne ya samu jikkata, hankalin Abie a tashe ya ce zai dawo Niger Abba ya ce a a ya zauna tukun kar ya dawo, ba dan ya so ba ya haƙura.. Ƙarfe 11:am likitocin da suka dukufa a kanshi suka fito ɗaya bayan ɗaya, na karshen ne ya tsaya a wajen su ya ce “Su waye iyayensa.” [6/11, 2:25 PM] Ummu Amjad: _*AREWABOOKS@SARATALKASUM88*_ 33 Da sauri Mamma da Abba suka amsa a tare “Mu ne iyayensa likita.” Kallon shi su ya yi sannan ya ɗora da cewa “Ku biyo ni ina buƙatar ganin ku.” Ya faɗa yana yin gaba. Su uku suka bi shi Mamma, Abba, Ahmad har office ɗin sa, takardun da ke ɗauke da result ɗin Salim yake kallo yana girgiza kai, hakan ya sa gaban Mamma ke bugawa da mugun sauri ta kai hannu ta dafe saitin zuciyarta, Ahmad ya riƙe mata hannu yana nuna mata ta nutsu. Bayan ya gama ya yi gyaran murya ya soma musu jawabi, “Maganar gaskiya wannan bawan Allah yana cikin mawuyacin hali, duk wanda yake ɗauke da irin wannan raunukan da su karaya gaskiya ba lalle a kawo shi har asibiti yana cikin haiyacinsa ba, amma shi tun da aka ƙare mishi aiki sunan wata ya dinga kira wai ita Khadija, ko kuma ya ce ko Amina ko wa..” Ajiyar zuciya Ahmad ya sauke ya ce “Likita yanzu wani irin raunika da karaya ne ya samu haka masu muni?” Takardar ya ɗauka yana kallo ya ce “To abu na farko dai ƙashin haƙarƙarinsa biyu sun karya, ga harsashi da aka fitar masa a fegen cikinsa guda biyu, sannan ya samu buguwa a kansa sosai in da har wajen ya yi rami mai zurfi amma Alhamdu Lillah ƙwaƙwalwarsa ba ta taɓu ba, ƙafarsa ta ji 'yan raunuka, abu na ƙarshe kuma muna buƙatar jini mai yawa wanda zai yi leda uku, domin ya zubar da jini fiye da tunaninku a yi maza-maza a nemo jini a fara sa mishi, tukun ku sayi wannan magungunan da allurori wanda za a sa mishi su kashe masa raɗaɗin ciwo da zugin da jikinta zai yi in ya farka..” In ban da Inna lillahi babu abin da Mamma ke faɗi hawaye na bin kuncinta, godiya suka mishi Ahmad ya amshi takardar ya kama Mamma suka fito, daret shi ya wuce wajen amso magani da kuma inda za a dibi jininsa su kuma suka koma inda suka baro su Hajiya Babba. Yana zuwa ya miƙa takarda take suka miƙo masa domin likitan ya kira ya musu bayanin komai shi ya sa suka haɗa mishi da ya zo suka ba shi, da mamaki ya amsa ya zaro kuɗi ya miƙa musu ya yi saurin nufar ɗakin ɗaukan jini, har ya kusa zuwa wani tunani ya faɗo mishi ya ciro wayarsa ya kira Abdoul ya ce ya same shi a ɓangaren ɗaukan jini, Abdoul ya ce to ya sauke wayar ya sake gargadin sojojin da su kula kar su yarda wani ya zo ya ce zai shiga suka amsa da to sannan ya tafi. A bakin ƙofa ya same shi suka shiga tare, Abdoul ya fara shiga shi ya zauna yana jira ya ji me za su ce, gabaɗaya jikinsa ya yi sanyi sai yanzu yake Allah wadai da shan sigarin da ya dinga yi a shekaru biyu baya da suka wuce, tunani kala-kala suka dinga fareti a ƙwaƙwalwarsa, addu'a kawai yake yana fatan jinin Abdoul ya zo ɗaya da na Salim in kuwa ba su zo ɗaya ba to sai dai su saya.. Fitowa Abdoul ya yi jiki a sanyaye ya kalli Ahmad ya ce “Sun ce nawa bai zo daidai da nashi ba kawo maganin kai ka shiga.” Miƙa mishi ya yi ya shiga da sallama ta amsa, zama ya yi a kan kujera aka zuƙo jininsa aka ɗauki na Salim aka fara aunawa, shuru ya yi yana jin faduwar gaba Allah-Allah yake yana fatan kar a ce jininsu bai zo ɗaya ba, ko kuma ya zo ɗayan su ce shi yana shan sigari wanda tuni ya gane kuskuren da yake aikatawa ya daina ya tuba, amma yau ya ƙara jin tsanar shaye-shaye fiye da kowacce rana ba ya so a ce jininsa da Salim sun zo ɗaya kuma su gano ya taɓa shan wani abu.. “Yawwa Alhamdu Lillah naka da nashi sun zo ɗaya yanzu za mu ɗauki leda uku, domin na ga kana da jini sosai.” Da sauri ya buɗe ido yana kallon nurse ɗin cike da farin ciki ya ce “Ko ya fi haka kuke so likita ku ɗauka.” To ta ce mishi ta nemo jijiyar ɗaukan jini ta soma ɗauka, bayan ta gama ta sa mishi auduga a wajen ta ɗauki jinin suka fito tare. A bakin kofa ta dakatar da su Abdoul ta miƙa mata maganin da suka sayo ta yi ciki da shi.. Tun da suka zo Andizo duk son ta da kuka kasawa ta yi, saboda idanuwansa sun soye sai kukan zuci take, burinta bai wuce ta ga Salim ya fito daga ɗakin ba yana mata murmushi tare da buɗe mata hannaye kamar yadda ya saba ta zo su rungume juna, juyar da kai gefe ta yi tana sauke ajiyar zuciya. Suna nan zaune sai kusan La'asar aka ba su damar ganin Salim shima sun ce da bibbiyu za suke shiga kar su yi yawa a ɗakin, sun samu ya yi bacci kuma kar hayaniyarsu ta tashe shi. Abba da Mamma da Hajiya Babba suka fara shiga, yadda suka ga an jona mishi na'urori abin ya girgiza su sosai iya fuska da hannnunsa ne kawai ba a sa mishi bandeji ba, Mamma ta matso kusan gadon da sauri tana zubar da hawaye ta shafa fuskarsa da ta yi fayau, addu'oʼin samun lafiya ta dinga tofa mishi tana shafa mishi a fuska, bayan sun gama suka fito Hassana da Hussaina suka shiga, da kyar suka tsayar da kuka suka mishi addu'a ganin halin da yayan nasu yake ciki abin ya mugun ɗaga musu hankali matuƙa, bayan sun fito Ahmad ya shiga shi da su Aminatou har Abdoul.. Tana hango shi ta kwace hannunta da ke cikin na Aminatou ta nufo shi da sauri, har za ta sa kuka ta tuna batun likita sai ta rufe bakinta ta dinga kuka tana kallon shi, a hankali ta matso kusa da gadon ta kai hannu ta taba fuskarsa tana faɗin “Allah ya ba ka lafiya mai hankali, wannan wani irin ciwo ne haka duk aka naɗe ma jiki da bandeji? Ya Allah ya dubi maraicina ka ba wa wannan bawan naka lafiya, Allah kaine gatan kowanni bawa amma akwai wanda a duniya yake jiyar da kai daɗi har ka kira shi da gatanka to wannan shi ne gatanmu ni da Adda da ma sauran 'yan'uwansa Ubangijin talikai ka ba shi lafiya.” Ta ƙarasa tana goge hawayen da suka zubo mata, gabaɗaya duniyar ta mata zafi fiye da jiya ganin shi a wannan halin. Aminatou ta tsaya a ɗayan gefen itama kamar yadda Andizo ta yi addu'a haka ta mishi tana kallon shi cikin alhini da damuwa mai yawa. Bayan sun gama Ahmad ya ce su fito ai kuwa Andizo ta ce ba ta san wannan zancen ba ita a nan za su zauna ita da Aminatou su yi jinyar mijinsu, da kyar da dabara ya fito da ita tana kuka.. Sai ƙarfe 10:pm Ahmad ya ce su tafi gida da safe sun dawo, ba dan sun so ba suka shiga mota Abdoul ya sa ɗaya daga cikin sojoji ya kaisu gida. Tun da suka isa gida mai aikin su ta kawo musu abinci ba wanda kalli ko wajen da abincin yake bare ma su ji za su iya ci, ƙarshe ma duk ɗaki suka shige ta bi su da kallo ita kanta yau wuni ta yi a gidan tana tunanin halin da Salim ɗin yake ciki, abincin ta ɗauka a kula ta nufi ɗakin Andizo ta kai mata sai ta samu ba ta ciki, ajewa ta yi ta fita tana jin tausayin ta.. Ranar a gidan babu wanda ya yi baccin kirki kusan kwana suka yi suna jera nafila suna mishi addu'a, Andizo kuwa tun da ta kwanta a gado kasa tashi ta yi saboda zazzaɓi da ciwon kai sun mata rufdugu, idan ta ci kuka ta gaji ta yi shuru tana kallon samar ɗakin tana tuna yadda yake ririta ta kamar ya mayar da ita ciki, da tunanin hakan ya zo mata sai ta fashe da kuka ta kudundune a cikin fargo, sai da ƙarfe uku ta yi ta lallaba da kyar ta sauka a gadon, da bin bango ta shiga ta ɗauro alwala tana hucin zazzaɓi.. Jiki na rawa ta tayar da iƙama, tun tana yi a tsaye har ta kasa jure tsayuwar ta zauna tana yi daga zaune, sai da ta ji alarm ɗin wayarta ya buga ƙarfe huɗu da rabi sannan ta yi raka'ar ƙarshe, a sujjadar ta dinga jero wa mijinta addu'ar samun lafiya tana yi tana kuka. Bayan ta salamce ta ci gaba da jan carbi har aka kira Sallah ta gabatar, bayan ta gama ta ji yunwa na neman illata ta babyn cikinta sai motsi yake, hannu ta sa ta dafe cikin tana zubar da hawaye tuna duk asuba kafin ya tafi masallaci sai ya dafa cikin ya yi mata addu'a.. Tashi ta yi ta kyar tana bin bango ta buɗe abincin ta ga ciwo ne da miyar taushe, yau duk san ta da tuwo ji ta yi ba za ta iya ci ba ta rufe nufi waje. Da kyar ta haɗa ruwan tea ta ɗauko fito ta shige ɗaki, shayin ta shanye ta sha magani sai ta ji kamar za ta iya cin abincin ta janyo ta buɗe, loma uku ta yi ta ji amai na neman zuwa ta haƙura ta rufe abincin tana nishi ta wuce banɗaki, wanke baki ta yi fito tana jin cikints na wani irin juyawa ta dafe ta iso kan gado ta kwanta.. Hayaniyar su Hassana ce ta tashe ta ta sauko ta je ta wanke baki da fuska ta sako hijabi ta fito, kowa ya shirya suka dunguma zuwa asibiti.. Yau ma har suka gama zama bai farka ba hakan ya kara tayar wa da Andizo hankali ta yi ta kuka suna rarrashin ta, ita kuwa Aminatou su Ummi suka zo ta zauna a wajen su Ummi na rarrashin ta. Dangi da 'yan'uwa na zuwa duba Salim har da makotan su Mamma duk sun zo. Sai da Salim ya yi kwana uku sannan ya farfaɗo, ranar har sun haƙura za su koma gida wata nurse ta fito ta tsayar da su duk suka dawo, kallon su ta yo ta ce “Ya farka yana kira wasu mutane amma dai za ku iya shiga..” Su duka suka shiga ciki kowa so yake ya ganshi, zaune suka same shi ya jingina da gadon an tallabo kansa da pilo idanunsa a kan kofar yana murmushi, suna shigowa ya hango su ya lumshe idanu yana godiya ga Allah da ya ba shi ikon ganin su, sannu suka dinga mishi yana masawa. Andizo ta zauna a kusa da shi ta riƙe hannnunsa tana faɗin “Alhamdu Lillah mun gode wa Allah da ya farkar da farin cikinmu.” Kallon su yake yana murmushi a hankali ya ce “Nana Khadijana kenan ai na faɗa miki zan dawo in sha Allah, gashi kuma kin gani na dawo ɗin.” Ya faɗa yana kallon ɗayan gefen da Aminatou take zaune itama ta riƙe hannnunsa. A hankali ya ce “Matar Salim ya yarana suke? Fatan dai duk ba ku ɗaga hankalinku ba kuka yi ta wahalar mini da yara ko? Dan nasan ita wannan rigimammiyar ko shakka babu ta sha kuka.” Murmushin jin daɗi Aminatou ta yi ta ce “Kuka ai ya zama dole mijin Aminatou da Khadija, musamman ma ita ai ba a magana amma tun da ka tashi Alhamdu Lillah mun gode Allah.” Jinjina kai ya yi Mamma ta kalle shi tana goge hawaye ya ce “Haba dai Mamma meye na kuka ba gashi na tashi ba? Ka da ki yi tunanin abin da ya faru shekeru goma ne zai sake faruwa yanzu, in sha Allah ba komai ba na so ma kike tuna wannan lokacin..” Girgiza kai ta yi ta ce “Haba yarona ai ba zan taɓa manta wannan baƙar ranar ba mai ɗauke da baƙin dare, naji daɗi matuƙa da ka farka Allah ya ba ka lafiya.” Amin ya ce yana kallon su Hassana suma ya ce su daina kuka suka ce to, Hajiya Babba ta ce “To yanzu ku tashi mu tafi gida dare ya yi sai mu dawo gobe tun da ga Ahmad nan da Abdoul suna tare da shi.” Duk tashi suka yi amma Andizo ta ce ita sam ba ta san ba zancen tafiya gida, da suka takura mata ma kuka ta sa ta riƙe hannun Salim ta ce “Ni ba inda zan je muna nan ni da Adda za mu kula da shi ai.” Ganin yadda ta kafe sai Aminatou ta ce “Khadija ki yi shuru ba wanda zai mayar da ke gida kin ji, ki zauna a nan ni zan tafi idan kika yi kwana biyu nima sai na zo na yi kwana biyu.” Goge hawaye ta yi tana dariya ta ce “To Adda sai da safe.” Kallon Salim Aminatou ta yi ya ɗaga mata gira ɗaya, juyowa ta yi ta ga duk sun fita Andizo ma ta shiga banɗaki, matsowa ta yi ta manna masa kiss a ƙoshi da kumatu ji take itama ta tsaya ɗin amma ta ɗaure saboda ganin yadda Andizo ke kuka gara ita ta zauna da farko. Yadda ta tsura mishi ido sai da ya hura mata iska ta rufe tana dariya ta mike tsaye ta ce “To sai da safe ko.” Hannu ya ɗaga mata ta fita da hanzari.. Tana fitowa Sallah ta yi ya kallon ta, bayan ta gama ta ɗaga hannu a bayyane take jero mishi addu'oʼi yana amsawa da amin har ta gama ta shafa, cire hijabin ta yi ta dawo ta zauna tana faɗin “Sannu mai hankali, yanzu ma kana jin ciwo ko?” Ta faɗa tana riƙe hannnunsa. Girgiza mata kai ya yi ya dafe cikinta ya yi masa addu'a sannan ya ɗauke ya ce “To tashi ki je ɗayan gadon can ki kwanta na ga kin fara hamma.” Babu muso ta tashi ta isa gadon ta hau ta kwanta ta yi facing ɗin Shi, ƴar dariya ya yi ganin yadda take kallon shi, itama dariyar ta yi zuciyarta na ƙara sanyi ta tashi ta haɗe yatsu ta masa alamar zuciya, ta nuna mishi yana cikin ranta tana sonshi sosai ba kaɗan ba. Dariya ya yi shima ya nuna mata yana matuƙar ƙaunar ta ita da babyn da ke cikinta, alamar godiya ta mishi tana rufe ido. Gyaran murya ya yi ya ce “Allah sauke ku lafiya Nana Khadija, ina so ki haifa mini yara dozin shida su yo kamar ki shida su yo kama da ni, zan sa sunan su Mama da su Hajiya Babba.” Buɗe ido ta yi ta ce “Kai haba dozin kuma kamar wata kaza?” Dariya yi ya ce “To ai ba yanzu ba, da ɗaiɗai za ki haifo mini su.” “To Allah ya kaimu lokacin.” Amin ya ce daga nan ba ta sake cewa komai ba. Ganin haka ya sa shima ya rufe ido ba dan yana jin bacci ba.. Sai da ya ji ta yi bacci ya buɗe ido yana kallon ta ba ba ko ƙiftawa har shi ma bacci ya ɗauke shi. Kiran Sallah ne ya tayar da shi ya kalli gadon ta ya ga ba ta nan, can ya hango ta tana zaune tana jn carbi ya lumshe ido. An gama Salla sai ga Ahmad ya shigo suak gaisa ya dube shi ya ce “Ahmad Sallah nake son na yi, tun da dai kafata lafiya take riƙe ni na shiga banɗaki.” “To shi kenan bari na kira likita ta cire maka wannan abin.” Fita ya yi ya je ya zo likita ya cire mishi ƙarin ruwan da ake mishi, kama shi ya yi a hankali suka tafiya har suka shiga banɗaki, ruwan alwala ya diba mishi sannan ya fito waje. Ledar da ya zo da ita ya ɗauko ya fito da wando ya kai mishi, Andizo na zaune tana kallon su. Bayan ya gama ya fito ta shinfida mishi abin sallah ya zauna ya yi Sallah. Bayan ya gama likitan ya dawo ya mayar mishi da ƙarin ruwan, kallon Ahmad ya yi ya ce “Idan Abdoul ya zo ka ce mishi ya ba ka abin da na ba shi ya aje maka.” To ya ce ya fita ya zo da kayan abinci ya haɗa mishi shayi mai kauri da soyayyan kwai da doya ya miƙa mishi, itama ya tura mata Kwandon kayan abincin ya ce “Matar yaya ki samu ki ci abinci.” Godiya ta mishi ta ɗauki kamar yadda ta ga Salim yana ɗan ci, sai da ta dan ci mai yawa ta aje Salim ya kalle ta ya ce “Ba dai har kika ƙoshi ba ?” Turo baki gaba ta yi ta ce “Ba zan iya ci ba na ƙoshi.” Bai takura mata ba ya dan shima bai ci sosai ba ya aje. Yana gama ci ta ɗauko mishi ruwa ya wanke hannu Ahmad ya ba su waje ya fita ta zauna a kusa da shi, hannunta ya riƙe ya ce “Khadija kin san kuwa irin son da nake miki?” Girgiza kai ta yi ta ce “Ni kuwa na sani sosai kamar yadda nake sonka.” Murmushi ya yi ya lumshe ido ya ce “Alhamdu Lillah.” Baki ya buɗe zai yi magana sai ta ga ya yi shuru yana kallon ta fuska ɗauke da murmushi, itama sai ta yi tagumi ta zuba mishi ido. Zabura ta ga ya yi ta yi saurin riko shi tana faɗin “Subhanallahi lafiya dai?” Girgiza mata kai ya yi ya ce “Khadija Allah ya muku albarka.” Amin ta ce tana murza hannnunsa, salati ta ji yana yi yana sauke ajiyar ajiyar zuciya hakan ya sa ta zauna tana riƙe da hannnunsa, can dai ta ji shuru ta ɗago kai ta kalle shi ta ga yana kallon gefe, taɓa shi ta yi ta ce “Juyo mana.” Ta ji shuru ta taɓa shi ta ji bai motsa ba, a rude ta kwaɗa wa Ahmad kira sai ga shi ya shigo afijajan. Nuna mishi ta yi ta ce “Na yi ta mishi magana ya yi shuru.” taɓa shi ya yi ya ji jikinsa ya saki, nan take jiri ya ɗauke shi kamar zai fadi ya daure ya kai hannu ya sa a saitin wiyanshi, idanuwansa ya rufe mishi ya fita da sauri yana ce mata bari na kira likita.. A tare suka dawo lokacin su su Abba sun ƙaraso suma suka shigo, auna shi ya yi da ya gama sai gani suka yi ya cire duk wata na'ura da ke jikinsa ya janye gefe ya ja zanin gadon ya rufe mishi fuska. Kallon shi suka yi suna tambayar me ke faruwa, girgiza kai ya yi ya ce “Ku yi haƙuri wanda ya fi mu son shi ya karɓi abinsa.” Wani dum Andizo ta ji kunnenta ya yi kamar jinta ya ɗauke, kallon su kawai take sai ta ta ji Abba na faɗi “Inna lillahi wa inna laihin raji'un! Allah ya jiƙan ka Salim..” Wani irin ƙara ta fasa ta yi lu za ta faɗi Mamma ta yi saurin taro ta ta sume a hannunta, itama Aminatou a jikin Hassana ta suma. Hankali tashi aka kira likita aka zo aka ɗauke su zuwa ɗakin taimakon gaggawa.. Gabaɗaya kuka suke sun rasa da wanne za su ji da mutuwar Salim ko da matansa da suka sume, gawar aka fito da ita aka sa ta mota har za su tafi su bar su Hassana su kula da su Andizo sai ga Aminatou ta fito a firgice, riƙe ta suka yi ta dinga rusa kuka tana faɗin “Ina mijina yake? Don Allah karku ce mini ya mutu waiyo Allah na gode maka, ina Khadija takeda?” Da kyar suka rarrashe ta suka sa ta a mota kamar haɗin baki itama Andizo ta farka ta tsige ƙarin ruwan da ake mata ta fito. Kamo ta Hajiya Babba ta yi ta sa ta mota suka nufi gida.. Suna zuwa gida motar Abie ma na isowa suka shigo gidan tare, sai da aka rufe su Andizo a ɗaki sannan aka shigo da gawar Salim ɗakin Mamma a nan aka mishi wanka aka shirya shi, bayan sun gama suka zo ɗaya bayan ɗaya suna mishi addu'a. Ana buɗe su Hajiya Babba da wata makociyarsu suka shigo da su ɗakin, rungume gawar Salim suka yi suna ta kuka duk da ana hana su yin kukan, Andizo kamar za ta yi hauka da aka zo ɗauke gawar za a fita da ita, ƙarshe daga ita har Aminatou sake suma suka yi ba su san ba lokacin da aka fitar da gawar.. _Maman Nusaiba🤙🏻_ [6/12, 2:13 AM] Ummu Amjad: _*AREWABOOKS@SARATALKASUM88*_ 34 A harabar gidan aka aje gawar Salim suka sallace shi, Ahmad da kyar ya iya tsayuwar sallar duk dauriyar da yake nunawa ana salamcewa kuka ya subce mishi, Abdoul ya bubbuga kafaɗarsa shima hawaye na bin kuncinsa, sosai yake jin mutuwar Salim har ƙasan zuciyarsa gabaɗaya ya ji aikin soja ya fitar masa a kai. Jan shi ya yi gefe ya danne nashi kukan ya daure a kyar ya ce “Ahmad ka yi haƙuri mana ka masa addu'a ba kuka ba, za kake yi wa mamaci kuka bayan kasan ba a so wannan aikin ai sai mata aka sani da kuka mai sauti ba maza ba, ka daure mu tafi in kuma ba za ka iya zuwa ba ka zauna a gida mu je mu dawo.” Girgiza kai ya yi ya goge hawaye ya ce “Dole na yi kuka Abdoul mutuwar Salim kamar mutuwar wani sashe na jikina ne.” “Ba komai ka yo mishi addu'a kawai.” Hannunsa ya kama suka shiga ɗaya daga cikin motocin da suke ɗaukan mutane zuwa maƙabarta, Abba da Abie su ne suak sa gawar Salim a tsakiya da limamin unguwarsu da wasu daga cikin malamai. Tun da Abba ya sunkuyar da kai kukan zuci yake yana tuna nagartaccan ɗansa wanda duk cikin yaransa ya fi jin sa a ranshi, iska ya fesar yana ta salati yana karanto addu'a yana tofawa.. Bayan sun isa an gama komai daam su ake jira, aka ɗauko gawar masu binnewa suka ce makusantan mamaci su matso, Abba, Abie, Ahmad, Abdoul da biyu daga cikin 'ya'yan Abie da suka zo tare suka matso su duka. A kansa Ahmad ya saka gawar Salim a rami shi da Abdoul, runtse ido ya yi yana ta addu'a ya matsa daga bakin ramin yan kallo suka gama rufe ƙabarin, bayan an gama duk aka tsaya ana ta yi wa mamaci addu'ar neman afuwa a cikin makwancinsa sunan amsawa da amin har aka gama. Kowa ya tafi ya bar Ahmad har su Abba sai da suka gama yin addu'oin da za su yi suka bar shi a wajen, Abdoul ya koma jikin mota yana jiran shi.. Hannu biyu ya ɗora a kan ƙabarin hawaye sun cika masa ido ya shanye su yana sauke ajiyar zuciya, a hankali ya ce “Ɗan'uwana zan yi kewar ka sosai, Allah ya yi maka rahama aiyukan da ka yi na alkhairi da ɗawainiyar da ka yi da mu Allah ya biya ka, ina kyautata maka zaton samun aljanna mafificiya Yaya Salim, Allah haskaka wannan gida naka matanka da ka bari da ciki Allah ya sauke su lafiya su haifa mana masu kama da kai sak ko za mu samu sassauci, ba zan gaji da yi maka addu'a ba har gaban abada, zan ci gaba da ziyartar ka in sha Allah ɗan'uwana bissalam..” Tashi ya yi a hankali ya miƙe yana kallon ƙabarin, girgiza kai ya yi ya juya ya tafi yana kukan zuci.. Ana dawowa aka kafa runfuna a harabar gidan aka soma karɓar gaisuwa. Tun da Andizo ta Aminatou suka sume sai da suka kwana suka wuni ba su farfado ba, har sai da Hajiya Babba ta ce likitar da aka kawo tana duba su su tafi asibiti kar a yi rashi da yawa sai kuma Aminatou ta farfaɗo, tana buɗe ido babu abin da nema sai kallon su take, ganin Ummi a kusa da ita ta soma ƙoƙarin mikewa za ta fita suka ruƙo ta aka zaunar da ita, addu'a Ummi ke yi mata tana mata nasiha a kan haƙuri da dangana yayin da aka yi maka mutuwa, sai a lokacin ta samu damar kuka ta dinga yi ba wanda ya hana ta, har wata ƙanwar Ummi za ta hana ta Hajiya Babba ta ce ta barta ta yi kukan za ta samu sassaucin radadin da take ji a zuciyarta mutuwar miji ciwon ta ya fi gaban kwatance. Sai da ta yi mai isar ta sannan ta kalli Ummi ta ce “Ummi ina Khadija take? Ku kaini wajen ta don Allah.” Tashi Hassana ta yi ta kama ta ta ce “Muje na kaiki ki ganta.” Da kallon tausayi suka bi ta har su soam tafiya Mamma ta ce su dawo za a kawo Khadija nan itama ta farfado, dawowa suka yi Aminatou ta zuba wa kofar shigowa ido tana share hawaye, tafi jin tausayin Andizo fiye da kanta. Inna da Ɗahare suka shigo da Andizo da ta zama kamar kurma sai kallon mutanen ɗakin take, har kusan Aminatou suka kawo ta aka zaunar da ita Aminatou ta rungume ta ta sake sa sabon kuka ta ce “Ki yi haƙuri kin ji Khadija Allah ya fi mu son Salim shi ya sa ya ɗauke mana shi, kar ki yi kuka kin ji ki daure..” Kowa da ɗakin sai da kalaman Aminatou ya saka shi zubar da hawaye, Andizo ta ɗago kai ta kalli Aminatou ta ce “Yanzu Adda shi kenan ba za mu sake ganin mai hankali ba? Waiyo Allah ni Dije ya zan yi da rayuwata babu kai a cikin mijina? Adda hannuna cikin nasa ya rasu fa, jiya da dare har kusan ƙarfe ɗaya muna hira ya ce so yake ya ga mun haifa masa yaransa ashe ba zai gansu ba, yanzu ina gawar tashi take ina so zan yi mishi addu'a tashi ki kaini Adda na ga fuskarsa gani na ƙarshe..” Ta ƙarasa tana sakin kuka mai tsuma zuciyar.. Girgiza kai Aminatou ta yi ta ce “Ki yi haƙuri Khadija ai tun jiya aka kai shi gidansa na gaskiya, nima sai yanzu nake ji labari a wajen su Ummi.” Kanta ta kwanto a kafaɗar Amiantou suka ci gaba da kuka suna ta surutai kamar sun fita daga haiyacinsu, da kyar aka shayo kansu suka daina kukan. Haka aka yi ta karɓar gaisuwa har aka yi sadakar uku, Andizo da Aminatou kuwa a gado ɗaya suke kwana saboda dukkan su in suka kwanta daban-daban ba sa iya bacci suna kuka domin tuna mijinsu kowacce tana faɗin da yana nan tare za su yi bacci rungume da juna cikin nishaɗi. Da farko an so a raba musu su kowacce take kwana a gado ita ɗaya amma suka ƙi dole aak haƙura aka rabu da su. Sai ranar sadakar sati mutanen da suka rage suka tafi aka bar 'yan gidan, sai a lokacin Ahmad ya samu damar shigowa cikin gida da yamma. Saurin kallon shi Andizo ta yi sai ta ga kamar Salim ne ke nufo ta, gane hakan ya sa Ahmad ya zo har gaban ta ya durƙusa amma ba ta daina kallon shi ba, ganin daga ita sai Aminatou a palon ya hura mata iska yana faɗin “Khadija ya dai? Wannan kallo haka ko dan kin kwana biyu ba ki ganni ba.” Hawaye ne suka zubo mata ta kalle shi still dai fuskar mijinta take gani a fuskar Ahmad, runtse ido ta yi yana faɗin “Allah ya jiƙan ka da rahama.” Ta buɗe ido ta ta sake kallon shi, a hankali ta ga yana canja mata har fuskar Salim ta ɓace a ganin ta, ajiyar zuciya ta sauke ta ce “Ka yi hakuri.” Iya abin da ta faɗa daga haka ba ta sake cewa komai ba.. Girgiza kai ya yi ya kalli Aminatou ya ce “Ya jikin naku fatan dai komai lafiya babu inda yake muku ciwo?” Kai ta gyaɗa mishi ta nisa ta ce “Alhamdu Lillah ba ma jin komai.” Tashi ya yi tsaye ya sa hannu a aljihu ya juya yana fadin “To Alhamdu Lillah idan sati ya zagayo likita za ta zo ta duba lafiyarku, amma don Allah kafin lokacin ku yi ƙoƙari ku rage yawan tunani kar hawan jini ya kama ku, ku cika wa Yaya Salim alƙawarin da kuka ɗauka.” In sha Allah Aminatou ta faɗa ya fita ya bar palon. Washegari Inna ta ce su za su tafi da Andizo gida a kula da ita Hajiya Babba ta dube ta ta ce “Kar ku tafi da ita ƙauye, za mu ci gaba da kula da ita har ta haihu ita da ƙauye sai ziyara dan in ta gama takaba mu za mu aurar da ita ga duk wanda take so, domin Maigari ya ba ni ita amana.” Murmushi Inna ta yi tana jinjina kirki irin na wannan dangi, gyara hijabi ta yi ta ce “Ayya to ai ban san kun yi haka ba, to shi kenan Allah sauke ta lafiya za mu sake dawowa in an samu kwanaki biyu haka.” Allah kiyaye hanya suka musu Andizo tana kallo suka fita da kyar ta iya ce musu su gaida gida, sai da Dahare za ta tafi ne ma ta yi kuka ganin ita kaɗai a ɗakin, rarrashin ta ta yi ta ƙara yi mata nasiha sannan ta tafi.. Giɗaɗo ya so ganin Andizo amma bai samu dama ba sai haƙura ya yi suka tafi gida.. Kwanci tashi babu wuya a wajen Ubangiji har Salim ya yi wata ɗaya a kabari, a ranar ne kuma Mom da Farrah suka diro garin Niamey. Kasancewar Farrah ta san sunan Unguwar suka dinga tambaya har suka iso kofar gidan, hon suka yi aka buɗe musu suka shigo.. Ahmad ya shigo fito shi da Mamma suka taro su, a palo suka zauna aka kawo musu ruwa da lemo suka sha, Mom ta gaishe su tare da musu gaisuwa sannan ta ce “Ina Khadija da abokiyar zaman nata?” Hajiya Babba ta sa aka kira su, ba ta lura da su ba dan ba ta san za su zo ba shi ya sa ko kallon wajen ba ta yi ba kanta a ƙasa, sai da ta iso kusa da su Farrah ta miƙe hawaye sun cika mata ido ganin yadda ta rame ga cikin ya kere ta yanzu sun shiga watan haihuwa, a hankali ta kama hannunta ta ce “Khadija.” Saurin juyowa ta yi suka haɗa ido, da hanzari ta iso gaban Mom ta kama hannunta ta ce “Mom kece nake gani da Farrah ko gizo ne kuke mini irin na mai hankali?” “Ba gizo ba ne Khadija ni ce da Farrah muka zo miki ta'aziyya, ba mu san Salim ya rasu ba sai yau da asuba na kira Maigari muam gaisawa y sanar da ni, shi ne na sa aka cira mana ticket muka ci sa'a jirgin safe ya ɗauko mu, sannu kin ji Khadija Allah ya jiƙan Salim da rahama, ku kuma Allah y ba ku haƙurin rashin shi.” “Amin Mom Allah ya saka da alheri na gode sosai, kina da kirki Mom kin ɗauke ni kamar Farrah duk wani abin da ya shafe ni sai kin shiga ciki, Allah ya bar zumunci..” Ta faɗa tana zama kusan Farrah “Babu komai Khadija ga Farrah nan an musu hutu ta ce za ta taya ki zama har sai kin haihu.” Guntun murmushi Andizo ta yi ta ce “Ke ɗin ƙawar kwarai ce Farrah Allah ya barmu tare, kuma ko ba komai kin sa naji farin cikin da rabona da shi tun ranar da zai rasu.” Murmushi Farrah ta yi ta kama ta suka koma ciki. Mom ta musu Sallama ta tafi suka mata rakiya har bakin mota suna mata godiya. Ƙarfe biyar daidai na asuba Aminatou ta tashi da naƙuda, hankali a tashe Farrah ta fita ta buga wa Mamma kofa, dama ba bacci take ba kwanakin nan saboda halin da su Andizo ke ciki. Da sauri ta zura Hijabi ta fito ganin Farrah ya sa ta nufi ɗakin da hanzari, hankali tashe ta kama ta suka fito palo ta je ta bugawa hajiya babba kofa ta fito. Mota suka fito da ita Hassana ta ja su zuwa asibiti, suna isa aka amshe suka, shigar da ita ɗakin haihuwa. Suna nan tsaye har Ahmad ya zo ɗaya daga cikin likitocin ta fito da baby tana murmushi ta ce “Alhamdu Lillah ta sauka lafiya ga ƴarta mace ta haifa.” Mamma ta amshi Jaririyar tana kallon ta sak Salim, miƙa wa Ahmad ta yi ya amsa ya zauna yana kallon ɗiyar ba ko kiftawa. Sai da aka gyara ta tukun su Ummi suka iso asibitin kowa sai ɗaukan Jaririyar yake ana ta murnar game da lahini. Ita kanta Aminatou da ta ga jaririyarta sai da ta yi kuka sosai, da aka yi Sallar Azuhar aka sallamo su suka yo gida, Ummi ta so su tafi gida amma Mamma ta ce sam ta bari ta ƙarasa ladan ta, ba yadda ta iya ta haƙura suka nufi gidan.. Andizo da ga ta yarinyar ta ɗauka tana kallon ta ta kalli Aminatou tana murmushi ta ce “Dama na faɗa miki za ki haifo mini takwara to G shi dai addu'ata ta karbu dan haka a cika alƙawari..” Murmushi ta yi ta ce “, Ai ba zan manta ba Khadija tun a asibiti Ahmad ya rada mata suna da Nana Khadija kin samu takwara.” Zama ta yi ta murmushi hawaye suak cika mata kwarmin ido ta ce “Na gode Adda haƙiƙa ke abokiyar zama ce ta gari, kin kasance mace mai kirki mai son abin da mijinta yake so, Allah ya saka da alheri da wannan takwarar ta kika mini naji daɗi sosai ba zan taɓa manta halakcin ki a gareni ba..” Murmushi Aminatou ta yi ta ce “Karki damu Khadija ai ke kika fi dacewa da a kira ki da abokiyar zama ta gari, tun da nake da ke ba ki taɓa nuna mini kishi ba a duk wasu lamuran mu, kin sha sadaukar mini da kwananki yayin da ba ni da lafiya, kin sha min wa'azi da dora ni kan hanya madaidaiciya, duk da a lokacin kina, yarinya ƙarama amma duk wasu ɗabi'unki na manyan mutane ne, dan haka karki ji komai zan miki abin da ya fi haka ma in dai ina raye a duniyar nan.” Ta ƙarashe maganar tana dafa ta.. Kallon su su Ummi suka yi suna yaba hali irin nasu, sai da ta ji bacci na ɗaukan ta ta ba da ɗiyar ta tafi ta kwanta. Jaririya na ta kuka aka ce Aminatou ta shayar da ita ta amshe ta, aka nun Mata yadda za ta yi ta rungume ta doam shayar da ita. Kwana biyu har ruwan nono ya zo kamar almara ya ɗauke, ranar jaririyar ta wuni tana kuka sai madara aka ba ta ta sha. Washegri ranar itama ta tashi da daƙuda, kafin ma a yi ƙoƙarin kaita asibiti daga za tw yi fitsari sai jin kuka suak yi a banɗaki, da sauri Ummi ta shiga ta ta haihu, janye babyn ta yi ganin tana wata naƙudar ta kalli Mamma ta ce “Ta saura fa.” Kamar minti goma ta sake haifo namiji, murna a gidan ba a magana aka gyara ta ita da yaran suka kaita asibiti aka duba ta duka ce ba matsalar komai.. Yaran da aka zo rada musu suna Andizo ta ce namijin a sa mishi sunan mahaifin Aminatou macen kuma a sa sunan Mamma, hka kuwa Ahmad ya sa rada musu suna. Ranar Aminatou ta dinga wa Andizo godiya ta ce ba komai ai za ta mata fiye da haka ma.. Washegari da kukan ɗiyar Aminatou ya yi yawa Andizo ta tashi ta ɗauke ta ta soma shayar da ita, tuni ta kama tana sha Aminatou ta yi tagumi tana kallon ta, ta rasa da wani irin alkhairi za ta saka wa Andizo, su kansu su Mamma sun ji daɗin abin da ta yi bayan ta gama shayar da ita yarinyar ta yi bacci har da dogon numfashi take ja.. Hajja ta ce tun da har ta sha nonon Andizo ita za ta ci gaba da shayar da su duka ukun, Ummi ta ce da an ba ta madara Andizo ta sa kuka ta ce“Haba Ummi ina nan a raye za a ba wa takwara ta madara? Ki barni na, shayar da su ai duka yarana ne.” Albarka ta dinga sa mata tana amsawa da amin.. _Maman Nusaiba ce_ [6/14, 1:31 AM] Ummu Amjad: _*AREWABOOKS@SARATALKASUM88*_ 35 Taron suna aka haɗa shi rana ɗaya tun da kwana biyu ne tsakanin su, hakan ya sa aka shirya walima duk da wannan haihuwa ta zo musu a baibaiye ne, sosai Salim ya ci buri a kan wannan haihuwar sai ga shi an yi haihuwa shi kuma ba ya duniyar.. Ana gobe suna 'yan ƙauye suka diro Niamey har da su Salame su Hajaru duk wasu ƙawayen da suka yi wasa tare Andizo cewa ta yi kowa ba ta ɗauke mishi ba sai ya zo wajen bikin yaranta za ta biya masa kuɗin mota da suturar da za su suka kala bibiyu, sosai hakan ya yi wa ƙawayen nata daɗi kowacce ta sha wanka aka turo mota huɗu ta zo har kofar Maigari aka kwashe su. Su Salame sai ƙauyenci ake nunawa har da shafa bangon ɗakin Andizo ta ce “Jakka uban nan! Yanzu Andizo a nan kike rayuwa? Kai mutuwa mai yankan ƙauna Allah ya jiƙan Salim ɗan gayu mai fara'a.” Fara'ar kan fuskar Andizo ce ta rage ta yi ƙasa da kai tana amsawa da amin tana kallon yaran nata musamman ma namiji tafi ganin kamannin shi da Salim, tana gama shayar da su ta miƙa wa Inna aka kwantar da su a kan gadonsu mai kyau, nan ma Salame ta ce “Kenan yara ma suna da gado kamar na manya?” Wannan karon dariya ta ba wa Andizo ta yi murmushi ta ce “Salame kenan, ke komai kika gani sai kin yi magana? Ni kuwa ina jikar Iya take? Ko Iyar ta hana ta zuwa?” Gyara zama Salame ta yi tana dariya ta ce “Gaskiya na yarda yanzu Andizo kin soma manta mutane, jikar Iyar da ga ta nan a gefen ki amma kike tambayar ina take.” Saurin kallon gefen ta ta yi jiyar Iya ta yi dariya ta sha kwalliya bakin nan sai maiko yake, dariya Andizo ta yi ta ce “Alƙur'an kin haɗu jikar Iya mai koko da ƙosai.” Su duka suka sa dariya Farrah ta riƙe ƙugu tana kallon su, turo baki ta yi ta ce “Khadija shi ne dan kin ga ƙawayenki kika manta da ni ko? To bari na tafi wajen Anty Aminatou wajen ta zan kwana.” Fuskar tausayi Andizo ta yi ta ce “Haba my friend am so sorry kin ji.” Juyawa ta yi tana faɗin “To bari dai ina zuwa dama Daddy ya ce zai miki barka zan kira shi ku gaisa. To kawai Andizo ta ce tana kallon ta har ta bar ɗakin. Hajaru ta kalli kofar ɗaki ta ce “Andizo wannan kamar dai na santa a wani waje.” “Wai ba ki gane ta ba? Farrah ce fa ƙawata da na yi lokacin da aka sace ni mamanta ta ceci rayuwata.” “Haba ni fa kamar na santa ashe ita ce har ta girma haka, Allah mai iko.” Suna ta hira sai ga wata daga cikin dangin Aminatou ta shigo ɗakin da sallama hannunta riƙe baby tana ta kuka, amsa mata suka yi ta iso tsaya ta miƙa wa Andizo ta ce “Ɗiyar albarka kinga yarinyar nan taki kuka take yi ko yunwa ce take damunta” Bakin gado ta matso ta amshi shi tana murmushi ta ce “Allah sarki yarinyata ai dole ta ji yunwa, rabon da na shayar da ita fa tun da La'asar ai ta yi ƙoƙari ma.” Ta rungume shi ta soma shayar da shi. Murmushi matar ta yi ta ce “Bari to na zauna ta gama sha sai na koma da ita ko?” “A'a Mama, ki tafi kar na tsayar da ke idan ta yi bacci ko ta ƙoshi zan kaita da kaina.” “To shi kenan na wuce dama aiki nake duk ya buwaye mu da kuka na ce bari na kawo shi wajen uwarsa mu huta.” Ta faɗa tana dariya ta yi gaba. Itama Andizo dariyar ta yi tana cewa ai ta yi ƙoƙari ma. Duk kallon ta suka yi cike da mamaki, dan su yara biyu aka ce musu ta haifa mace da namiji, sai ga shi sun ga wani jaririn an kawo mata. Salame ta nisa ta ce “Hmm wai dama Andizo yara uku haifa? Mu fa biyu aka ce kin haifa ba uku ba.” Murmushi ta yi tana kallon yarinyar ta shafa kanta, sosai take jin son babyn har ƙasan zuciyarta ji take kamar ita ta haife ta, kallon Salame te yi ta ce “Ke dai kin cika magana Salame to ɗiyar Adda Aminatou ce abokiyar zamana, uwar ba ta da ruwan nono ni ke shayar da su. Wallahi ni tausayi Adda take ba ni kullum sai ta yi ta kuka, sun je asibiti sun nemi na gargajiya a kwanakin nan amma shuru har yanzu ba ta iya shayar da ita.” Fuskar tausayi duk suka yi suna yi wa Aminatou addu'ar samun lafiya tana amsawa da amin. Sai da ta yi bacci sannan ta janye ta daga shayarwar ta saɓa ta a kafaɗa ta ce “Zo mu tafi Hajaru ki raka ni.” Tashi ta yi Salame ta ba za a barta a baya ba suka tafi Inna ta girgiza kai tana kallon su. Suna isa suka samu Aminatou tana zaune ta yi tagumi, a hankali Andizo ta zauna a kusa da ita ta sauke baby ta rungume ta ce “Adda ki daina zurfafa tunani dayawa karki jayo wa kanki wani ciwon kuma, ke fa kike mini faɗan yin tunanin mai zurfi sai kuma na ganki yau kina yi, ga takwara ta yi bacci a samu a kwantar ta ita..” Abida da ta iso hannunta riƙe da cup da magani ta ce “Faɗa mata dai Khadija ƙila ke da yake tana ganin girman ki ta ɗauki maganarki da muhimmanci.” Sauke tagumin ta yi ta amshi maganin ta sha ta yi baya ta lumshe ido ta ce “Ku yi haƙuri Wallahi na kasa daina tunanin ne, ko na ce zan, kasa da na zauna ni kaɗai musamman a nan palon gani nake kamar zan ji Salim ya yi sallama ya kira suna na.” Ta faɗa tana goge hawaye. Dafa ta Andizo ta yi ta ce “Haka ne, dama ai ba zai yiyu a ce ka cire wanda kake so a zuciyarka a lokaci ɗaya ba dole sai a hankali za ka rage tunanin shi, amma dai ki rage karki kamu da wani ciwon..” “Zan rage Khadija in sha Allah, ni yanzu damuwa jaririyar nan da shayar da ita Allah bai ba ni iko ba, ga shi ke an dora miki nauyi a barki ma da yara biyu su kansu kina ƙoƙarin shayar da su ballantana kuma a ƙara miki da wata ɗiyar, Wallahi ina matuƙar ganin girman ki Khadija ban san da me zan saka miki ba da wannan hidimar da kike wa jaririyata, Allah barmu tare..” Murmushi Andizo ta yi ta ce “Karki damu Adda ai nima ɗiyata ce zan mata duk abin da zan yi wa yaran da na haifa, ko kin manta mun yi masa alkawarin cewa za mu tarbiyantar mishi da yaransa tamkar uwa ɗaya uba ɗaya?” “Ban manta ba kuma ke ce kika fara cika wannan alƙawari, Allah ya ba mu ikon cika mishi duk alƙawarin da muka ɗauka..” Amin suka faɗa ta ba ta ɗiyar ta tashi har za su tafi Abida ta kira Andizo ta dawo ta zauna tana kallon su. Saukowa ƙasa Abida ta yi ta kalli Andizo ta ce “Don Allah ku yafe mini ke da Anty abin da na aikata muku a baya, Wallahi sharrin zuciya ne da na sheɗan.” Dariya Andizo ta yi ta ce “Haba Abida ai ni tuni na riga da na yafe miki ya wuce.” Godiya ta mata sannan suka tafi.. Washegari gida ya cika, da 'yan'uwa da abokan arziƙe aka yi hidimar suna lafiya, da Yamma aka yi taron walima a harabar gidan. Ahmad shi ya yi anko iri ɗaya da su Andizo ya amshi namijin su kuma kowacce ta ɗauki ɗaya suka fito ya rako su har wajen zama. Tun daga naisa Mamma ta kafe su da ido hawaye na bin kincinta, Salim kawai take gani a tare da matansa suna tunkaro ta. Taro ya tashi lafiya waɗanda za su tafi gida suka tafi, masu kwana kuma suka tsaya. Washegari 'yan ƙauye suka shirya aka gama musu sha tara ta arziƙi suka tafi gida aka bar Inna dan take kula da Andizo.. Sosai aka kula da Andizo duk wani nau'in abinci da gina jiki sai an yi mata shi daga na gargajiya har na zamani, hakan kuma ya sa ta yi haske ta murje har wata ƙiba ta yi kamar ba ita take shayar da yara uku ba. Sai da suka gama arba'in sannan aka shirya zama har lokacin Farrah tana nan dan ta ce ba ta shirya zuwa gida ba, har Mom ta kira ta ta ce an kusa gama hutu ta dawo ta su je kasuwa ta yi sayayyar komawa ta ce ita sam ba yanzu ba sai ya rage saura kwana biyu a koma za ta diro Nigeria, ba yadda Mom ta iya dole ta rabu da ita, shaƙuwar su da Andizo har mamaki yake ba ta. Da misalin karfe 10:am na safiya duk aka taru a palo, suna nan zaune Abba da Abie suka shigo tare da Limamin unguwar. Bayan sun gaisa Abie ya buɗe taro da addu'a sannan ya fara magana. “Allah gafarta malam dama mun kira ka ne ka yi mana bayani game da rabon gadon dukiyar da marigayi Salim ya bari, sannan ya matsayin takabarsu yake ko na ce idda?” Gyara zama Liman ya yi ya ce “Iddar mace mai ciki ta na zuwa karshe ne da sauke abin da yake cikinta kawai, shin rabuwar saboda rasuwa ne ko saboda wanin haka ne, Allah mai girma yana cewa: (Mata masu ciki wa’adin iddarsu shine su haifi abin da yake cikin mahaifarsu) [Aldalaq:4] wannan ayar ta kunshi hukuncin macen da mijinta ya rasu ko wanin haka. Allah madaukakin Sarki ne mafi sani. Sannan kamar yadda kuka sani shi rabon gado idan har mamaci yana da yara maza da mata to fa kason namiji linka na mace, idan an ba wa mace kaso biyu a gado to namiji yana da kaso huɗu ne, idan kuma an ba wa mace kaso ɗaya namiji kuma yana da kaso biyu, dan haka sai ki haɗa duniyar waje ɗaya daga kan fili kuɗi gida da duk wani abu da kuka san nashi ne, sannan in ana bin marigayi bashi ku diba a cikin dukiyar da ya bari ku biya mishi bashin sannan a raba gado..” “Ma sha Allah mun fahimta yanzu kenan su matansa za su iya yin aure sun gama takaba?” Cewar Abie. “Haka ne Alhaji ko yanzu miji ya fito za su iya yin aure.” Tashi Ahmad ya yi ya ɗauko wata baƙar jaka ya buɗe, takardu ya fiddo ya aje a gaban su ya ce “Wannan takardun sun ƙunshi duk wasu kadarori na Yaya Salim, har bashin da yake bin mutane ya rubuta kuma da sa hannun wanda ya ci bashin da nashi sa hannun, yana da filaye guda huɗu da manyan shaguna uku a grand marché, da kudinsa da suke banki wanda zuwa yanzu ban san ko nawa ba ne sai dai a yi tattaki muje banki a duba tun da na san code ɗinsa.” “To shi kenan yanzu abin da za a yi ku gama sanin adadin kuɗin in ya so gobe ko jibi sai a raba gadon kowa a ba shi haƙƙinsa.” Da to suka amsa sannan liman ya tashi ya musu sallama zai tafi Abdoul ya dakatar da shi, juyowa ya yi ya dawo ya zauna ya dubi Abdoul ya ce “Abdoul shin ko kana da bin cewa ne?” “Kwarai kuwa Allah gafarta Malam, lokacin da Salim ya kusa rasuwa ya yi wani rubutu ya ba ni ya ce na ba wa Ahmad, ya kuma yi guda biyu ya ce na bai wa matansa kowacce ɗaya. To ganin yadda suka shiga yanayin baƙin ciki da tashin hankali shi ya sa ba wanda na yi wa maganar saƙon, sai jiya da na kwanta na yi mafarkin Salim ya zo mini fuska ɗauke da damuwa yana sanar da ni cewa “Ya kai aminina kuma ɗan'uwana shin me ya sa ba ka isar da saƙon da na ba ka ba?” Na firgita sosai na tashi a daren na ɗauko takardun na aje su a kusa da ni na ce yau da na fito zan kawo su dan na cika alƙawari.” Ya faɗa yana fito da takardar ya miƙa wa kowacce tata. Dafe kai Ahmad ya yi ya ce “Ni kaina lokacin bai fi saura minti goma ya mutu ba ya ce na zo wajen ka na karɓi saƙo, to gabaɗaya na manta kwata-kwata..” Hajiya Babba ta ce “To kowa ya karanta ya faɗa mana abin da takardar ta kunsa.” Kowa buɗewa ya yi ya karanta duk suka ɗago a firgice suna kallon su, Mamma ta ce “Me aka rubuta Ahmad?” Miƙa mata takardar ya yi bai iya ce mata komai ba. Amsa ta yi ta soma karantawa a hankali. _“Ɗan'uwana wannan rubutun da nake maka Ian cikin tsananin ciwo tsakanin mutuwa da rayuwa, don Allah Ahmad ka kula da yaran da za a haifa mini, ka ba su tarbiya mai kyau ka musu duk abin da suke so matsawar bai saɓa wa addini da shari'a ba, sannan ina mai roƙon ka wata alfarma Ahmad idan su Khadija sun gama idda ka aure su gabaɗaya saboda ka kula da su dan ba na son su bar gidanmu ka ji ɗan'uwana.”_ Ɗago kai Mamma ta yi ta kalli su Andizo, hannu ta miƙa musu ta ce “Ku kawo taku na gani.” Miƙa mata suka yi ta amsa itama ta soma karanta ta Andizo. _“Nana Khadijana damo sarkin haƙuri, a yayin da nake miki wannan rubutun ban sani ba ko za mu sake yin rayuwa da ke a nan gaba ba, ba na jin wannan kwanciyar da na yi zan tashi har na yi rayuwa da ku, hakan ya sa na yanke wani hukunci wanda ban san ya za ku kalle shi ba, ko bayan na mutu Khadija ina son ku ci gaba da kasancewa a gidanmu, saboda ku ɗin mata ne da kowanni namiji zai yi alfaharin samun su a zaman shi na duniya, tabbas ni na kasance mutum mai sa'a da na same ku Khadijatuna, hakan ya sa nake so ko da a ce na mutu ke da Aminatou ku auri ɗan'uwana Ahmad dan ku haɗu ku tarbiyantar mini da yaran da za ku haifa nan gaba. Amma fa Khadija van takura muku ba idan har kuka ji zuciyarku ba ta aminta da wannan hukuncin nawa ba karki bari ayi auren nan ku auri waɗanda kuke so hakan shi ne daidai, idan kuma kun aminta da hakan iyayena za su fi kowa jin daɗin hakan har ma da naku iyayen, amma don Allah kar dan kuna ganin girmana a matsayina na mijinku ku sadaukar da farin cikinku, ba na haɗin ya zama dole idan da haka ma ku ɗauki lokaci kafin auren dan ku shaƙu da juna har ma soyayyar ta ƙullu a tsakaninku. Bissalam daga mijinki abin ƙaunar ki mai tsananin sonki Salim."_ Buɗe ta Aminatou ta yi itama kamar yadda ya yi wa Andizo bayani haka itama Aminatou ya mata jawabi ɗaya bayan ɗaya. Fashe wa da kuka Andizo ta miƙe tsaye ta saɓa jaririyarta tana kallon su, cikin muryar kuka ta ce “Wallahi ni dai ko Adda Aminatou ta amince ni dai ba zan taɓa yarda na auri Ahmad ba, ni yaya yake a wajena babu maganar aure a tsakani ba da shi, duk wani namiji wajena kallon mace nake masa in dai ba Salim ba, tuni na cire maganar yin aure a babin rayuwata har abada zan raini yarana na ci gaba da zama na kula da su har su girma. Dan haka yau zan bar gidan nan zan muku nisa ta yadda ba wanda zai ganni bare ya haɗa ni da wani namiji da sunan miji, domin ni mijina ɗaya ne dal a duniya shi ne Salim kuma ya mutu ya bar duniyar, dan haka zan zauna na ci gaba da jiran lokacin da zan tarar da shi.” Tana gama faɗin haka ta wuce ɗaki har tana haɗa da gudu. Itama Aminatou tashi ta yi ta ɗauki 'yarta ta ce “Mamma ki yi haƙuri da abin da zan faɗa, ko ni ba zan iya auren Ahmad ba gaskiyar magana kenan, ina ganin idan na auri Ahmad na ci amanar Salim. Za mu ci gaba da karatu ni da Khadija don Allah karku tayar da maganar nan iyayenmu su ji.” Ta juya itama ta bar wajen.. Gabaɗaya palon kasa motsi suka yi kalamansu duk ya kashe musu jiki, Liman ne ya yi ƙarfin halin faɗin “To abin da zai fi kyau shi ne ku bar maganar nan Alhaji, tun da shi marigayi da y yi wasiƙar nan bai takura ba ya ce dama in suna son hakan, to sun nuna ba sa so a yi haƙuri a rufe maganar zuwa nan da wasu watanni. A yanzu dama ba za su taɓa yarda da wannan hukuncin ba duka watan shi nawa da rasuwa? Ciwon mutuwa bai gama sakin su ba dole ku musu uziri.” Jinjina kai Abba ya yi ya ce “Tabbas haka ne, in sha Allah za mu bi komai a hankali.” Sallama ya musu ya tafi. Suna zaune duk sun yi shuru suka ga ta fito Sanye da hijabi ta goyi Nour shi kuma Aiman ta saɓa shi a kafaɗa tana jan babbar akwati, gabaɗaya kallon ta suka yi, Hassana ta yi saurin tashi ta sha gaban ta ganin za ta wuce, a rude ta ce “Khadija ina za ki tafi kika ɗauko akwati?” Gyara tsayuwa ta yi ta ce “Zan tafi ƙauyenmu ne.” Tashi Mamma ta yi ta amshi Aiman, kamo hannunta ta yi ta ce “Babu inda za ki tafi Khadija kina nan gidan, indai dan wannan maganar ce za ta sa ki tafi to ki dawo an fasa, shi wanda yake so ayi hakan dama ai ya ce bai muku dole ba, Hassana mayar mata da jakar nan ciki.” Lumshe idanu ta yi ta juya ta koma ciki, gabaɗaya hankalinta ya bala'in tashi, ta kuma ƙuɗiri aniyar ko ina za a je ba za ta taɓa yarda ta auri Ahmad ba.. _Maman Nusaiba_ [6/20, 2:11 PM] Ummu Amjad: _*AREWABOOKS@SARATALKASUM88*_ 36 Gabaɗaya shuru palon ya yi bayan sun samu Andizo ta koma ciki, Hajiya Babba ta sauke tagumin da ta yi ta kalli Abie ta ce “Saddiƙu kunga wannan maganar a barta kar yaran nan su shiga wani hali, musamman ita Khadija da take shayar da yara uku dole a lallaɓa ta dan kar ta sa abin a ranta a samu matsala, idan aka samu nan da shekara ɗaya nasan za su gane abin da Salim yake son su yi zai zame musu alkhairi.” Tashi Ahmad ya yi ya ce “Hajiya don Allah kamar yadda suka buƙata ku rabu da su, ni kaina abin ya mini girma gaskiya ba zan iya ba ku yi haƙuri.” Ya wuce fuu saboda tsabar kiɗima ko gabanshi ba ya gani da kyau. Har ya zo zai gifta ta ƙofar ɗakin Andizo ya ji tana kuka sai sumbatu take. “Wallahi ba zan iya wannan cin amanar ba, haba mijinmu ya za ka ɗora mana wannan abin mai girma wanda kai kanka kasan daga ni har Adda ba mai yarda da wannan ɗanyan hukuncin, idan har yaranka kake tunanin rayuwar da za su yi nan gaba ina so ka kwantar da hankalinka, domin na yi alƙawarin ni da aure sai dai na lahira in ana yi, kai kaɗai nake so a duniyar nan kuma ka tafi ka barni, dan haka babu maganar na sake haɗa jikina da wani namiji in ba kai ba, da kai na saba kaine ka gyara rayuwata. Allah ya jiƙan ka da rahama ina fatan ka kasance cikin hasken rahama a makwancinka kamar yadda Allah yake ba ka damar ka yi sanadin haska rayuwar mutane da dama, ina matuƙar sonka mijina.” Girgiza kai ya yi ya murɗa ƙofar ya shiga, a durkushe ya same ta Nour na nutsu-musu a bayanta saboda ta matsu. A hankali ya tsugunna ya sa hannu ya soma kunce goyon, ram ta riƙe hannnunsa ta ce “Karka kunce mini ita.” “Pordon matar yaya kin fa matse ta sosai ba ki ji ne? Ki ba ni ita mu tafi ɗakina.” Make mishi hannu ta yi ta miƙe tsaye tana haɗe rai, sauke Nour ta yi ta kwantar a kan gado yarinyar ta soma kuka, zama ta yi tana hararar shi ta gyara zaman hijabi ta ɗauki Nour ta saka ta ciki ta soma shayar da ita. “Malam ka fitar mini a ɗaki da ba ka da kunya, kana gani zan shayar da yarinya ka wani tsare ni da ido kamar maye.” Ta faɗa gyara lulluɓin hijabi. Hassana ce ta shigo da Khadija tana kuka sai jijjiga ta take, ganin Ahmad tsaye sai ta raɓa ta gefen shi ta iso gaban Andizo ta ce “Anty Khadija ga takwarar ki nan ta addabe mu da kuka a ba ta abincinta.” Ɗago kai ta yi suka haɗa ido da Ahmad ya juya da sauri ya fice, tsaki ta ja tana hura hanci ta cire hijabin tana faɗin “Dan shegen shigigi za ka wani zo ka tsaye mini a ɗaki ga shi nan Nour har ta haɗa zufa.” Murmushi Hassana ta yi ta ɗora mata Khadija a cinya ta gyara zama ta soma shayar da ita, harde hannu Hassana ta yi tana jinjina wa ƙoƙarin Andizo, ga ta yarinya ko shekaru 17 ba ta cike ba amma tana shayar da yara uku. Ajiyar ta sauke tana goge hawayen da suka zubo mata tuna yadda Salim yake yi wa Andizo, ko fita ya yi in ya kira ta ya ji ba ta ɗauka ba zai kira Hassana ya ce sai ta je ta ga a wani hali Andizo take ciki ya kira ba ta ɗauka ba, wucewa ta yi ta bar ɗakin. Da kallo Andizo ta bi Hassana, sai da suka ƙoshi Khadija har ta yi bacci ta kwantar da ita a gadon Nour ta kwanta tana kallon su har bacci ya ɗauke ta.. Ahmad yana shiga ɗaki wayarsa ta ɗauki ringing ya ƙi ɗaukan kiran har wayar ta katse, sake kira aka yi ya ja tsaki ya janyo wayar yana kallon screen ɗin wayar. Ganin mai kiran ya saki baki yana zaro ido, cike da mamaki ya ce “Mr J! Tab lalle za a yi ruwa da ƙanƙara yau.” Ya ƙarashe maganar yana ɗaga kiran ya kara a kunne yana faɗin “Number wa nake gani kamar 'yan ƙasar waje?” Daga can ɓangaren ya sa dariya ya ce “Wallahi fa nine aboki abubuwa ne suka yi mini yawa, ga damuwa ta hana ni sukoni na kasa samun nutsuwa.” Riƙe baki Ahmad ya yi ya ce “Iko sai Lillahi wahidul ƙahar! Yanzu kai har akwai damuwar da za ta hana ka sukoni?” “In sha Allah ina nan tafe zan diro Niger, wannan karon ta can zan bi saboda da ina da wani aiki mai muhammanci a garin nan naku.” Murmushi Ahmad ya yi ya ce “Allah sarki aboki wai ni ko sai yaushe za ka yi aure ne? Zan fa zuga Mama ta taso ka a gaba ko kuma na samo maka wata a nan garinmu, yanzu dai a ƙalla ka kai kusan 40 years kana zaune ka zama tuzuru ƙarfi da yaji, kai duk matan duniyar nan ka kasa samun mace ɗaya da ka ji kana so a zuciyarka? Kuma nasan ba wai masu sonka ba ne ka rasa kaine dai kaƙi yarda ka aura.” Tsaki Mr J ya yi ya ce “Kai fa ɗan iska ne wani lokacin Ahmad, so kake ka ɓallo mini ruwa kenan? To ka kwantar da hankalinka in sha Allah ba zan sake yin shekara cikakkiya ba zan yi aure, ba na taɓa ba ka lamarin wata kyakkyawar budurwata ba?” “Kwarai kuwa an yi haka.” Cewar Ahmad. “To ita ce take ba ni ciwon kai, ka bari sauran labarin sai na zo zan maka bayanin komai.” “To Allah ya nuna mana lokacin aboki, ni kaina yau na shiga wata matsananciyar damuwa mai girma, amma ka bari in ka iso sai mu tattauna ko za mu samu mafita daga ni har kai.” Sallama suka yi Ahmad ta girgiza kai ya tashi ya shige banɗaki.. BAYAN SHEKARA ƊAYA Su Nour sun yi wayo suna gudun su ko'ina Mamma ta ce za ta yaye su amma Andizo ta hana, ta ce sai sun kai lokacin da kowanni yaro yake kaiwa kafin a yaye shi dole ta rabu da ita. Sanye take da riga da sket na atamfa kayan sun zauna a jikinta, idan ka ganta ba za ka taɓa cewa ta san meye rayuwar aure ballantana a kai ga haihuwa, ta ƙara tsayi da jiki ga wani kyau na musamman da ta yi fatarta sai sheƙi take, duk wata cikar halitta da ake nema a jikin mace Andizo ta same ta ma sha Allah, ita kanta ta san yanzu take cikakkaiyar mace saɓanin baya da take kwaila. Aiman ne a kafaɗarta sai jijjiga shi take saboda rigimar da yake mata, ganin Aminatou a zaune sai ta iso ta saka mata shi tana kumbura baki ta ce “Wallahi Adda wannan ɗan naki ya cika rigima, tin safe nake fama da shi kamar na sabga mishi mari nake ji, ga Nour can ta yi luf abin ta amma shi ban da saka ni zarya babu abin da yake.” Dariya Aminatou ta yi ta saɓa shi a kafaɗa ta soma jijjiga shi ai kuwa ya yi shuru yana sauka ajiyar zuciya, kallon juna suka yi ta riƙe baki ta ce “Ka ji yaro ɗan nema.” “Ki ba shi abincinsa kafin ki tafi, ni da kin yarda ma sai a samo mai raino take bin ki ècole ɗin idan sun kuka sai ki fito ki kula da su, dama kuma Aiman ne ya fi kowa rigima a cikin su.” Zama ta yi tana turo baki ta amshe shi tana faɗin “Kai Wallahi ba zan tafi da su ba, haka kawai su addabe ni su hana ni karatu musamman shi wannan mai kama da wancan ɗan wiwi ɗin.” Ta faɗa tana dungure kan Aiman ai kuwa ya sa kuka. “Kai Khadija wannan dai cuta ce ya za kike masa rankwashi a ka kamar wani babba? Ki ba shi ya sha zan goya shi.” Bayan ta gama ta tashi tana gyara rigarta ta saka mayafin da ta fito da shi, kallon ta Aminatou ta yi ta ce “To a dawo lafiya nima na kusa komawa ai.” Amin ya ce ta goya jakarta ta sa kai ta wuce, a bakin ƙofar fita suka ci karo da shi ya zo shigowa, riƙe kai ta yi ta ce “Kai kai kai!” Saurin kallon ta ya yi ya ce “Yi haƙuri dama ke na zo kira ai, mu je na kaiki kar na makara wajen aiki.” Harara ta banka mishi ta wuce gaba fuu tana turo baki, gani take duk dan a takura wa rayuwarta ne Mamma ta ce shi zai ke kaita makaranta, tsaki ta ja ta tsaya tana jiran ya iso ya buɗe mata ƙofa. Kallon ta ya yi ya girgiza kai, ya san haka take yi wa Salim dole shi ne zai buɗe mata mota in dai za su fita, a hankali ya buɗe ya ce “Bismillah matar yaya.” Baya ta kama ta buɗe za ta shiga ya yi saurin rufewa ya ce “Na rantse da Allah in kika shiga baya sai dai yau ki fasa zuwa ècole ɗin, dan kin raina mini hankali direbanki kika ɗauke ni da za ki shiga baya?” Baki ta murguda tana hura hanci ta ce “To ai dama ban ce ka kaini ba malam, ai kasan ina da direban da mijina ya ɗauka mini yake kaini, idan kuma ba ya komai shi yake ɗauko ni ko ka taɓa ɗauko ni daga makarantar in ba sau ɗaya ba? Ni ba na son wannan baƙin halin naka..” Ran Ahmad ne ya ɓaci amma ya danne saboda da kashedin da Hajiya Babba ta mishi, da hannu ya nuna mata gaba ta ja tsaki ta buɗe baya ta shiga. Zagayawa ya yi ya shiga ransa a matuƙar ɓace ji yake kamar ya yi ta zabga mata mari saboda sabon rainin da ya shiga tsakaninsu. Yana kaita ya ciro 1000F (dala ɗari) ya miƙa mata yana wani shan ƙamshi ya ce “Mamma ta ce a ba ki saboda sayan abinci kafin ku taso.” Da har ta kalle shi a wulaƙance jin Mamma ce ta ba da ba ta sai ta amsa ta wuce da sauri ya bi bayanta da kallo. Tana shiga suka gaisa da 'yan ajinsu, sai da ta jima a zaune tana tunanin rashin zuwan ƙawarta Amira. Dafa ta ta ji an yi ta yi sauri juyowa suka haɗa ido da wata matashiyar budurwa, murmushi ta sakar mata ta ce “Yane Sadiya da dama?” Tashi ta yi ta dawo kusa da ita ta zauna ta kalle ta sannan ta ce “Lahiya lau Wallahi ya gida? Ina su Aiman ?” Kwafa ta yi ta ce “Cewa za ki yi ina sarkin rigima, ai yana can ya gama kuka na samu ya yi bacci sannan na fito.” Dariya ta yi ta ce “Khadija ina jinjina miki matuƙa Allah ya ba ki ƙoƙari da juriya, kalle ki fa yarinya ƙarama amma kina da yara biyu ga ɗiyar abokiyar zaman ki ta uku, Allah dai ya raya miki su.” Itama dariyar ta yi ta ce “Amin Sadiya na gode da addu'ar da kika yi wa yarana, amma ban da abin ki wa yake ja da ikon Allah? Ai ko ke aka yi wa aure a shekaruna za ki iya duk abin nake wanda kike ganin kamar na yi ƙarama na yi su.” “Tab! Alƙur'an ba za iya rainon yara biyu ba, ke ni fa ko ɗaya ne sai na samo mai raino tana tayani.” Cewar Sadiya tana ƙifƙifta idanu. Dariya Andizo ta yi ta gyara zama hango malaminsu ya nufi aji, hakan ya sa itama Sadiya ta gyara zama.. Bayan sun taso suka fito a tare suna tafiya sai ga wannan saurayin mai suna Arma da yake damun ta ya tare su, kallon shi ta yi cike da mamaki ganin yadda ya ƙara girma ko dan ta jima ba ta ganshi ba ta ga ya yi saurin girma. Murmushi ya yi ya ce “Nana Khadija Maman Aiman da Nour barka da dawowa, ya kuma haƙuri Allah ya jiƙan mijinki ya raya ɗiyanku, lokacin da aka yi rashin mun je har sau biyu amma ba mu samu damar ganin ki ba.” Sunkuyar da kai ta yi ta ce “Amin ya Rabbi na gode sosai.” Gyara tsayuwa ya yi ya ce “Ba komai dama na zo ne in ba ki haƙuri a kan abin da na miki a baya na bibiyar ki da nake, Wallahi ban ɗauka da gaske ke matar ba ce sai da Monsieur ya sanar da mu Allah ya yi wa mijinki rasuwa, ashe ma nasan mijin naki sosai. Amma don Allah yanzu zan iya zama ami ɗinki sai muke karatu tare har Sadiya da Amira?” Ya faɗa yana haɗe hannu biyu alamar roƙo. Kallon Sadiya Andizo ta yi ta gyada mata kai, juyowa ta yi ta ce “To ba matsala amma wai ina Amira ta shiga ne? Tun da na dawo ban taɓa gani ta zo ècole ba ko lafiya? Kuma ina kiran layinta sai a ce mini a kashe, ga shi ba ni da spécial numéro ɗin ta ta so ta ba ni lokacin da na yi zuwan ƙarshe ècole, to sai aka zo ɗauka n doek na haƙura na tafi.” “Amira ba ta jin daɗi ne rashin lafiya ta yi, ai ta jima rabon ta da ècole yanzu haka ni zuwa gobe nake so naje har gidansu na duba ta in kina son zuwa ki zo mu je.” Fuskar tausayi ta yi ta ce “Ayya Allah sarki ƙawata, to shi kenan goben sai mu tafi ko kana da sabuwar numéro ɗin ta?” “To Allah ya kaimu ki ba ni number ki idan isa gida zan tura miki whatsapp, goben in shan Allah in na fito sai na kira ki mu haɗu kin san ni yanzu na bar ajinku.” Numéro ta ba shi ya mata godiya sannan ya wuce.. Tun da suka tsaya Ahmad ya iso yana kallon su cike da takaici, kallon saurayin ya yi har ya shige mota yana yin kwafa. Sallama kawai ta mishi ta shiga ya amsa ciki-ciki ya ha motar suka tafi.. Washegari bayan sun taso daga makaranta ta fito bakin get tana jiran shi ya fito, har ta gaji ta samu waje ta zauna tana jira sai ga jira ya shigo wayarta ta duba ta ga sabuwar number ce, ɗauka ta yi tare da yin sallama ya amsa sannan ya ce “Ina mai baki haƙuri Khadija gani nan zuwa yau mun sha karatu ne ba sauƙi.” “Ayya Allah sarki to sai ka zo.” To ya ce mata sannan ya kashe kiran. Tashi ta yi ta isa wajen Ahmad ganin ya iso, kankwasa glass ɗin ta yi ya zuge, wani daddaɗan ƙamshi ne ya ziyarce ta har sai da ta lumshe ido ta buɗe su a kanshi, kallon ta ya yi sannan ya ce “Shiga mu tafi sauri nake karki ɓata mini lokaci, ina da abin yi karki ce za ki mini wannan rashin kunyar taki.” Wani irin kallon raini ta mishi ta ɗora hannunta a bakin ƙofar ta ce “Dama zuwa na yi na ce maka ka tafi gida yanzu ina da wajen zuwa, ina so zan je gidan su ƙawata Amira ba ta jin daɗi zan duba ta da jiki.” “OK to shi kenan sai kin dawo.” To ta ce mishi sannan ta juya cikin nutsuwa ta wuce ya bi bayanta da kallo yana jinjina kai.. Yana zuwa ya yi packing a motarsa ya buɗe ya fito yana faɗin “Afuwan fa Khadija kina ta jira ko?”.. “Ba komai ina Sadiyar take?” Nuna mata mota ya yi sai ta zagaya za ta shiga baya ya ce “Ki shiga gaba mana Khadija.” Murmushi ta yi ta shiga ya rufe sannan ya zagaya ya shiga suka bar wajen duk a kan idanun Ahmad, kwafa ya ja ya ja motarsa ya wuce, yana jinjina rainin da Khadija ta mishi yaro ƙarami wanda bai kashi ba ta shiga gaban mota shi, da shi sai ta masa ɗibar albarka kuma taƙi shiga. Iskar bakinsa ya fesar yana kallon hanya, a fusace ya ce “Yarinyar nan sai na koya miki hankali tukun za ki daina mini rashin kunya, ni za ki mayar kamar ƙanenki? Wallahi da na ce na fasa aurenki saboda tausayinki da nake ji amma yanzu na daina dole ma na aure ki na ladaftar da ke yadda ko suna na kika ji sai kin rusuna, sai na nuna miki ni Ahmad sanin da kika mini a farkon haɗuwarmu haka nake babu abin da ya rage sai ma ƙaruwa ya yi..” Suna isa gidan su Amira ya yi hon aka buɗe mishi get ya sa kai ciki, a tare duk suka fito ya tsaya tare da sa hannu a aljihunsa ya fito da waya, kiran Amira ya yi ya ce mata sun zo ta ce ga ta nan zuwa. Suna nan tsaye sai ga ta ta fito, tana hango Andizo ta haɗa da gudu ta iso suka rungumi juna suna murna, ɗago ta Andizo ta yi ta ce “Ƙawata ashe ba ki da lafiya?” “Hmm ki bari kawai muje ciki tukun.” Ɗakin baƙi ta kaisu ta fita ta kawo musu abinci da ruwa da duk abin buƙata, zama ta yi tana faɗin “Arma 'yan ècole gaskiya naji daɗi da ka zo mini da ƙawata, da ina cewa sai na ƙara jin sauƙi zan je na gano yarana.” Murmushi Arma ya yi ya ce “Itama ba ta san ba ki da lafiya ba sai jiya nake sanar da ita da zuwan da zan yi, shi ne ta ce to za mu zo tare.” Ya faɗa yana kallon ta. Dafa Andizo ta yi ta ce “Nasan ni mai laifi ce a wajen ki ƙawata ina ba da haƙuri, an yi mutuwa ban je ba an kuma samu ƙaruwa nan ma ban je duk ina kwance ba lafiya, ƙarshe da abin ya fi ƙarfin nan sai da aka fitar da ni waje fa.” Zaro ido Andizo ta yi tana kallon Amira, tagumi ta yi ta ce “Allah sarki Wallahi ban sani ba dukkan mu kowa yana cikin yanayi, ashe har waje aka fitar da ke Allah ya ƙara lafiya ya su Mama.” “Wallahi wani yayana da ya kira waya aka ce masa ba ni da lafiya gani a kwance ko motsi ba ne yi, shi ne ya mana kuɗin jirgi da komai aka kaini ƙasar da yake, yana da kirki sosai ba ki ga yadda yake kula da ni ba kamar 'yar da ya haifa. Da za mu dawo ya ce zai biyo mu ya kawo ziyara wa Mama saboda ba mu je tare da ita ba da Yaya muka je da wata likita da aka haɗa mu da ita tun daga nan. Mama kuma tana nan lafiya lau idan mun gama ta ce ku shiga a gaisa, ya karatu Sadiya?” “Alhamdu Lillahi Amira ya ƙarfin jiki? To Allah ya ƙara lafiya.” Jinjina kai Andizo ta yi ta ce “Kai gaskiya ya cika mutumin kirki, Allah ya saka mishi da alkhairi yadda ya taimake ki Allah ya ba shi duk abin da yake nema duniya da lahira.” Cikin jin daɗi Amira ta amsa da amin sannan suka ci gaba da hira. Su Arma da suka jima suka ce su za su wuce Amira ta hana Andizo ta tafi ta ce za ta sa a kaita kar ta bi su Arma tun da ba hanya suke ba, ba dan ta so ba ta zauna tana faɗin “Haba Amira yo ai da sai in hau motar haya babu komai.” Hararar ta Amira ta yi ta kama hannunta ta kaita ɗakinta ta zaunar a bakin gado, hira suka fara amma duk hankalinta yana kan su Nour kar su fara kuka, kallon ta yi cike da damuwa ta ce “Ke Amira gaskiya ki sa a kaini gida yaranki lokacin tashin su ya yi, gabaɗaya ba na jin nutsuwa gida zan tafi.” Tashi Amira ta yi ta ce “To shi kenan ina zuwa bari naje na sanar da direban ga shi can yana ba wa flower ruwa.” To ya ce mata ta wuce, ko minti ɗaya Amira ba ta yi da tafiya ba aka kwankwaso kofar, miƙewa Andizo ta yi ta isa bakin kofar ta ce “Amira ba ta nan ta fita.” Ta faɗa tana buɗe ƙofar. Tun daga kan kyakkyawan ƙafafuwanta ta soma kallon shi har zuwa kan fiskarsa wadda ƙasunba ta cika ta, kallo ɗaya za ka mishi ka gane yana cikin damuwa. Zaro ido ya yi ya juya gefe da gefe ya ga ba kowa, kallon shi kawai take tana tunanin a ina ta taɓa ganin mai kama da wannan fuskar, ba ta ankara ba ta ji ya kama hannunta ya tura ta cikin ɗakin ya kulle. Zaro ido ta yi ta soma ja da baya gabaɗaya jikinsa rawa yake so yake ya kira sunanta amma ya kasa sai nuna ta yake da hannu, zamewa ta yi ƙasa ta kankame jikinta tunaninta ya ba wannan mutumin mai larurar ƙwaƙwalwa ne ba a cikin haiyacinsa yake ba... _Maman Nusaiba ce_ [6/22, 1:34 AM] Ummu Amjad: _*AREWABOOKS@SARATALKASUM88*_ 37 Tsugunnawa ya yi a gaban ta sai a lokacin ya iya cewa “Kha.. Khadija !” Ya faɗa fuskarsa na bayyana tsantsan farin cikin da yake cikin zuciyarsa na ganin ta a wannan lokacin. Saurin buɗe fuska ta yi ta saki baki galala tana kallon bakinsa da yake rawar sanyi, sam ta kasa gane a ina ta san wannan fuskar sai ta ja baya ta zauna, shima gyara zama ya yi yana sauke ajiyar zuciya kamar ya yi gudun ceton rai, sai zuwa can ya ce “Khadija wai ba ki gane ni ba? Ni ne fa masoyinki wanda yake sonki fiye da kowa a duniyar nan, ke ko waɗanda suka kawo ki duniya da kaɗan za su fini sonki, ina kika shiga tsayin shekara uku ko labarinki ba na ji? Kin san kuwa irin hali da na shiga sakamakon rashin labarinki da na yi? Ina mijin da naji an ce an aura miki?” Ya ƙarashe maganar yana kamo hannayenta ya soma murzawa a hankali yana kallon ta cikin yanayin damuwa mai tarin yawa. Sororo Andizo ta yi tana kallon ikon Allah ta rasa yaushe suka san juna da shi da yake jero mata wannan tambayoyin, tagumi ta yi ta ce “Malam ni fa ban sanka ba ka tsare ni da tambaya kamar ina cikin ƙabari, a ina muka taɓa zama da kai har muka ƙula soyayya? Ka matsa ka ba ni guri in fita yarana suna can yanzu sun fara kuka.” Zaro ido ya yi ya ce “Wai har haihuwa kika yi?” Cike da ƙosawa ta miƙe tsaye ta ce “E yarana uku ma.” “Kai ƙarya ce duka yaushe aka miki auren da har za ki yi yara uku.” Tsaki ta ja ta iso bakin gadon Amira ta ɗauki hijabi ta saka saƙala jakarta ta harare shi za ta yi gaba sai ga Amira ta shigo, ganin shi a ɗakin ya sa ta faɗaɗa murmushin kan fuskarta ta ce “Uncle kaine a nan? Dama ina cewa yanzu zan je na kai ƙawata ku gaisa wadda nake ba ka labarin an mata ga ta ƴar ƙarama.” Tashi ya yi tsaye ya sa hannu a aljihunsa ya saki fuska ya ce “E ni ne na shigo na duba ki sai na haɗu da wadda na kwashe shekaru uku ina neman ta, ga shi Allah ya sa na ganta.” Da mamaki Amira ta kalle shi ta ce “To dama Uncle ka san Khadija ne?” “Sosai ma, ai ita ce mace ta biyu da na fara so a duniya amma ta ɓace mini.” Andizo ta cika ta yi fam ta kalli Amira ta ce “Kinga ni fa ban taɓa ganin shi ba in ba yau ba, sai dai in wata ce mai kama da ni da irin suna na ya sani ba dai ni ba, zan wuce dan ba ni lokacin shi yarana nake son gani?” Ta faɗa tana yin gaba za ta fita Amira ta yi wuf ta kare bakin ƙofar. Kallon ta ta yi zuwa yanzu ita kanta Amirar haushi take ba ta, ya daga zuwa dubiya sai kawai wani sangameman mutum ya ce wai sun san juna da ita? Tsaki ta ja ta ce “Don Allah ki matsa ki ba ni waje na tafi gida.” Girgiza mata kai Amira ta yi ta ce “Da gaske Khadija ke ce wadda Uncle ɗina yake dakon soyayyar ki a zuciyarsa? Don Allah ki saurare ni in miki bayani ƙila za ki tuna da shi.” Ta faɗa tana haɗe hannu alamar roƙo. Dafe kai Andizo ta yi ta sa hannu ta janye Amira daga bakin buɗe ta fita suka rufa mata baya, har harabar gidan suka biye da ita Amira na kiran sunanta amma ta yi kamar ba ta ji ba ta wuce za ta buɗe get Amira ta sa maigadinsu ya hana ta shiga, tsayawa ta yi ta riƙe ƙugu tana kallon su. “Don Allah Khadija ki tsaya direba ya kaiki, ni ba zan hana ki tafiya ba daga baya mun waya tun da na ga ranki ɓaci amma ki yi haƙuri.” Yadda take roƙon ta sai ta yarda ta tsaya, direba ya ɗauko mota ya ta shiga ko sai an jima ba ta cewa Amira va saboda tsabar takaicin da ta shaƙa. Hannu Amira ta ɗaga mata har suka bar gidan, juyowa ta yi tana kallon shi a sanyaye ta ce “Uncle ka yi haƙuri muje ciki ka bi komai a hankali, Khadija fa mijinta bai fi shekara da wata ɗaya da rasuwa ba, ba ta son a mata maganar aure.” Mamaki sosai ya bayyana kan fuskarsa ya sai ya juya yana ta nazarin maganar Amira ya shige ciki.. Maman Amira na ganin su ta ce “Lafiya dai kuka shigo jiki ba lakka?” Wayancewa suka yi Amira ta ce “Ba komai Mama na raka Khadija ne da sai muka haɗu da Uncle.” Da kallo kawai ta bi su har kowa ya shige ɗakinsa.. Babu irin kiran da Amira ba ta yi wa Uncle ɗin nata ba dan ya mata bayanin yadda aka yi ya san Andizo amma ya ki ɗauka, haka ta lalibo numéro ɗin ta ta kira ta ji wayar a kashe dole ya haƙura ta zauna da tarin tambayoyi fal zuciyarta. Suna sauka ta fito ta mishi godiya sannan ta nufi ciki, ta kusa isa ta ga an sha gaban ta ta ɗago kai suka haɗa ido da shi, takaici ne ya rufe ta matsa za ta raɓa gefen shi ya yi saurin jan ta ya shiga wata ƙofa da ita. Da ido kawai take bin shi dan ta ga iya gudun ruwan shi, ganin su ta yi a wani katafaran palo mai girma sosai an cika shi da kayan ado. Kujera ya nuna mata yana haɗe rai ya ce “Zauna a nan mu yi magana ta fahimta.” Kallon ka raina mini hankali ta mishi tana turo baki, kwafa ya yi yana tsare da idanu ji yake kamar ya rufe ta da duka saboda raina shi da ta yi, sai da ya daka mata tsawa ta zauna a kiɗimi tana rawar jiki, in akwai abin da ke hargitsa mata lissafi to bai wuce a mata tsawa ba nan da nan za ta rasa nutsuwarta. Hararar ta ya yi yana kaɗa ƙafa ya ce “Shi wancan yaron da na gani kina wani sakar mishi fuska waye shi? Sannan ina kuka je da kika shiga motarsa.” Da mamaki take kallon shi nan da nan ranta ya ɓaci ta miƙe tsaye tana riƙe ƙugu ta ce “To ina ruwan ka da inda muka je? Ni fa ba na son shisshigi a lamurana ka fita a rayuwata tun da ban gaiyato ka ba malam, ko ka ɗauka yanzu ma kamar da ne da ka kake mini wulaƙanci son ranka? Ni ba tsarar ka ba ce daga yau karka sake ƙoƙarin taɓa jikina tun da kai ba Salim ba ne.” Ta faɗa a fusace tana yin hanyar da ya biyo da ita. Har ya je bakin kofa ta ji muryartmsa, “Idan na taɓa jikin naki me za ki ?” A kufule ta juyo ta nuna shi da yatsa ta ce “Tabbas zan koya maka hankali in dai ka yi kuskuren sake taɓa jikina, idan kana tantama ko ganin ba zan iya ba ka sake taɓa ni ka ga me zai faru.” Fuu ta wuce ta bugo mishi ƙofar. Tashi ya yi tsaye yana zagaye kujerun palon cike da tsananin mamakin ta, yatsa ya ciza ya shaƙi iska ya ce “Ni kuma zan nuna miki Ahmad ba Salim ba ne Khadija, idan har kika mini abin da hankalina ya ki ɗauka tabbas zan miki aika-aikar da za ki ji dama ba ki zo duniya ba.” Wata ƙofa ya bi daga cikin palon yana sauri. Tana shiga ta samu yaran suna wasa Khadija ce kaɗai take kuka tana kiran “Mama! Mama!” Cike da tausayin yarinyar ta yi saurin cire mayafi ta ƙaraso ta durƙusa a gaban ta tare da buɗe mata hannu ta ce “Ɗiyar Mama zo gani na zo.” Jin muryar wadda take nema sai ta juyo da sauri sai kawai ta kama murna, sai a lokacin su Aiman suka ganta sua duk suka yo kanta suna murnar ganin ta shafa kansu ta dinga yi tana ba su haƙuri kamar wasu manya. Dariya Hussaina ta yi ta ce “Anty Khadija uwar son ɗiya, tun da kika tafi ba wanda ya yi kuka a cikin su sai takrawar ki ita ce duk ishi kowa a gidan nan, yaya Ahmad da ya dawo ya ɗauke ta amma ta ƙi yin shuru dole ya dawo da ita, ga shi Anty Aminatou ba ta dawo ba itama bare ta goya ta duk wanda ya ɗauke ta ba ta yarda sai mama take kira.” Murmushi ta yi ta ce “Uwarta kaɗai take so ta gani ba ku ba, kai ku matsa wannan ta fiku buƙata.” Ta faɗa tana janye su Nour ta gyara zama tana shayar da Khadija.” Kuka suka sa Aiman ya dinga ƙoƙarin janye Khadija shi ya maye gurbin ta Andizo ta hana shi, ganin za su ƙara rikita mata lissafi ta kalli Hussaina ya ce “Don Allah ɗauke mini Aiman idan suka gama shi sai a ba shi.” Ɗaukan shi Hussaina ta yi suka wuce ɗakin Hajiya Babba, kallon su take musamman Khadija da take sauke ajiyar zuciya duk da bacci ya soma ɗaukan ta, hakan ya sa ta ji yarinyar ta ƙara ba ta tausayi domin ta lura ta sha kuka ba kaɗan ba. A hankali ta matso kusan kujera ta kwantar da Nour itama ta kwantar da ita ai kuwa ta buɗe ido za ta fara kuka, saurin ɗaukan ta ta yi ta goya ta da mayafi tana jijjiga ta.. Hajiya Babba ce ta fito tana jan carbi sai yi take tana tofawa a gefe da gefen ta, kallon ta Andizo ta yi tana murmushi ta ce “Hajiya lafiya dai na ga yau ana tofe mana gida.” Ba ta kuka ta ba har sai da ta zauna sannan ta ɗago ta kalle ta ta tofar da yawu, zama itama ta yi tana riƙe baki ta ce “Yau kuma ni kike tofar wa yawu Hajiya?” “Ke da Allah matsa ki ba ni guri salbiya, kalle ki da kin ciko sosai amma yanzu kin fara ramewa, an ce a yaye yaran nan amma ƙememe kin ƙi bari a yaye su, ni fa tausayin ki nake ji shi ya sa ma na ce a yaye su amma tun da na ga kin soma zama shashasha gobe zan sa matar Saddiƙu ta zo ta ɗauke su ta tafi da su can sabon gidansu su yi sati sai a dawo da su..” Shuru Andizo ta yi tana kallon Hajiya Babba, sam ita ba ta so a raba ta da yaranta ko da na wuni ne, kuka ne ya tafo mata ta danne da kyar tana kallon Nour ta kawar da kai gefe ta ce “To shi kenan Hajiya Allah y kaimu goben, nima ina son naje ƙauye na gano su Hajja idan an dawo da su sai mu tafi a gansu har Khadija za mu tafi..” Murmushi Hajiya Babba ta yi tana faɗin “A to madalla Allah ya kaimu lokacin, haba ko ke fa yanzu a ce yara uku sun kai shekara da wata biyu sai ya yaye su ai kema ki huta ko?” Gyaɗa mata kai Andizo ta yi ta tashi jiki ba ƙwari ta wuce ɗakinta. Wanka ta yi ta saka kaya marar nauyi ta fito ta ɗauki abinci ta koma ɗaki, gabaɗaya duk haushin 'yan gidan take ji gani take kamar su suka zuga hajiya Babba take son a yaye mata yara lokacin yaye su bai yi ba, sai da ta gama cin abinci ta ji an kira La'asar ya tashi ya yo alwala ta gabatar. Tashi ta yi ta hau kan gado ta ɗauki wayarta da ji ƙaran shigowar text message, ganin numéro ɗin Amira ce ya sa ta ja tsaki tana tuna wannan mutumi da yake ikirarin wai ya santa a baya, tagumi ta yi ta soma karanta saƙon. _“Ƙawata don Allah ki yi haƙuri a kan abin da Uncle ɗina ya miki, gabaɗaya ke da shi kun rikita mini lissafi na rasa wa zan fara tambaya, shi ya ce ya san ki ke kuma kin nuna mishi ba ki, taɓa ganin shi. Amma don Allah ki, bari mu haɗu ko da ècole ne mu tattauna.”_ Tana gama karantawa ta ja dogon numfashi, tunani take to wai a ina ma ta san wannan mutumin mai kama da masu allurar ƙwaƙwalwa? Shuru ta yi tana so ta tuna inda ta san shi amma ina, tashi ta yi ta fito gadin ɗin gidan ta samu ɗaya daga cikin kujerun da aka tanadar a wajen ta zauna. Whatsapp ta shiga, tana amsa saƙonni har da na Farrah tana faɗa mata ta yi kewar ta sosai na tsayin shekara guda da ba su ga juna ba, kasancewar Farrah ta bar Nigeria ta ta fi America karatu. Murmushi ta yi tana mayar mata da reply sai ga kiran Farrah ya shigo, cike da zumudi ta ɗauka tana faɗin “Mutanen ƙasar waje kenan Allah ya ba ni kuɗi na hau jirgi ma kawo miki ziyara.” Daga can ɓangaren Farrah ta yi dariya ta ce “Kai amma kuwa da naji daɗi, zan sa Daddy ai ya biya mini kuɗin jirgin sai ki zo gani na kuma ki zo mini da su Aiman rabona da ganin tun suna jarirai, ke kin kasa musu pictures ki turo mini na gansu.” “A to mayar da wuƙaƙen Wallahi sam mantawa nake shi ya sa ban tura miki ba, amma da mun gama zan tura miki su har vidéo su.” “Wow to na gode, yawwa dama ina so mu yi wata muhimmiyar magana da ke Khadija, amma ina so ki ba ni hankalinki ta yadda za ki fi saurin fahimtar in da na dosa..” Duk da ba ta jin son yin magana sosai amma ba za ta ƙi ba wa ƙawarta ta lokaci ba ta ji me take son faɗa mata, gyara zama ta yi ta ce “To Farrah ina sauraron ki.” “Yawwa dama na sanar da Mom ne na ce me zai hana ta ɗauko ki ki dawo gidanmu da zama, sai kuma na ga ba lalle wannan gidan surukan naki su yarda ki tafi da yaran nan ba, amma idan aka yaye su na sanar da Daddy ya biya miki kuɗin karatu ya kawo ki nan mu yi karatu tare, domin ina son mu kasance a waje ɗaya, sannan akwai w..” Ji ta yi an warce mata wayar ta miƙe da sauri tana juyowa, ganin shi ne ta fusata ta ce “Wai kai wani irin baƙin mugu ne Ahmad? Ya za ka zo ka warce min waya ina muhimmiyar magana? Bani wayata tun da ba da kuɗinka na saya ba.” Ta faɗa tana miƙa mishi hannu.. Murmushin gefen baki ya yi ya kashe kiran ya sa wayar a aljihunsa, kallon ta ya yi da wani irin salo ya ce “Ki shirya abokina zai zo jibi ki shirya mishi abincin nan mai daɗi da kika taɓa girka mini can kwanakin baya kafin ki raina ni, sannan ki zo ku gaisa zan gabatar mishi da ke a matsayin matar da zan aura ban da wata ɗaya, ki shirya zama da ni a matsayin miji dan Wallahi aure ni da ke babu fashi..” Yana gama faɗin haka ya juya cikin takunsa na 'yan gayu ya wuce.. Sake da baki Andizo ta bi bayan shi da kallo tana nanata kalmar aure nan da wata ɗaya, jikinta ne ya musu murus ta ja ƙafa ta koma ciki. Da dare suna cin abinci ta kalli Hajiya Babba kamar za ta sa kuka ta ce “Hajiya don Allah ki ce masa ya ba ni wayata.” Tsayar da cin abincin Hajiya Babba ta yi ta kalli Andizo ta ce “Waye ya amshe miki waya?” A hannu ta nuna mata Ahmad da ya yi kamar ba da shi suke ba sai cin abincinsa yake hankali kwance, hannu Hajiya ta miƙa mishi ta ce “miƙo mini wayar yarinya, me ma ya sa ka amshe mata waya?” Tashi ya yi tsaye yana ɗaukan cup mai cike da lemo mai sanyi ya sa ɗayan hannnunsa a aljihu, sai da ya kurɓa sannan ya ce “Hajiya ki rabu da yarinyar nan wannan faɗan tsakanin ni da ita ne, wani ƙato fa naji suna waya shi ne har take wani kashe mishi murya tana kwatanta mishi nan gidan wai ya zo zance, shi ne nake tambayar ta waye shi nan ta dinga mini rashin kunya ni kuma na amshe wayar na ga ta inda zai zo gidan. Idan kuma kina son wayarki ki biyo ni tana ɗaki ki ba ni haƙuri sai ki ɗauki wayar abin ki.” Baki Andizo ta saki tana jin ƙaryar da yake sharara mata, kallon su suka yi sauran Mamma ta yi murmushi ta ce “To kai meye naka dan ta yi magana da wani? Amma dai tun da ka ce faɗan ku ne bari mu yi shuru ku je can ku ƙarata.” Ta tashi ta bar wajen. Hajiya Babba ma kasa cewa komai ta yi, amma dai ta yi mamaki sosai tana jinjina wa wanda har yake da gagarumar sa'ar samun Khadija. Yana tafiya ta tashi a zuciye ta bi shi ɗakinsa, tana buɗe ƙofar ya damƙo ta yana faɗin “Wa na kama? Ƙaramar marar kunya ke da wayarki sai kin mini duk abin da na sa ki sannan zan ba ki ita.” Ƙoƙarin kwacewa ta fara yi amma ta kasa, sai da gaji yana kallon ta sannan ya sake ta kafin ya yi wani kwakaran motsi ta wanke shi da mari, da sauri ya ɗago yana kallon ta ta ɗaga hannu za ta sake marin sa sai kuma ta fasa tana huci ta ce “Kai wani kalar jahili ne ina matar yayanka kake cakuma ta? Ko zuwa Islamiyar da ka yi ya tashi a banza? To ka shiga hankalinka ni ba irin wannan shashashun matan ba ce da kuke taɓa jikinsu da sunan wayewa, zan koya ma hankali na ba da jimawa ba.” Ta faɗa tana jan tsaki ta buɗe kofa ta fita. Da kallo ya bi ta yana murmushi ya shafa kuncinsa ya ce “Kin ci bashi yarinya lokacin ramuwa na nan zuwa.” Kamar yadda ya faɗa mata bayan kwana biyu Mamma ta same ta ce ta daure ta yi masa girki ba dan halinsa ba ko dan darajar baƙon da zai zo, ba dan ta so ba ta tashi tun ƙarfe goma na safe ta dora girkin shinkafa fara da miya, gefe ɗaya kuma ta haɗa musu kunun aya. Sai ƙarfe ɗaya daidai ta gama aiyukan ta fito tana runtse ido jin cikinta na murɗa mata, ɗaki ta shiga ta faɗa banɗaki ta yi wanka ta shirya cikin doguwar rigar atamfa pink colour. Mai da kwalli kawai ta sa hau kan gado ta kwanta tana riƙe da cikinta, jin ciwon na ƙaruwa ta tashi ta buɗe loka ta ɗauko maganin ciwon ciki ta ɓalli biyu ta sha tana tuna su Nour, hawaye ta ji ya zubo mata ta rungume pillow sam ta kasa cin abincin tun da sassafe da aka ɗauke mata su ta kasa fita balle su yi kuka in sun ganta ta yi zaman ta, amma da ta ji suna shirin tafiya ta tashi da sauri ta leƙa ta taga a kan idanunta suka bar gidan. Har bacci y fara ɗaukan ta sai ga Hassana ta shiga tana tashin ta, tashi ta yi zaune kafin ma ta ce komai ta miƙa mata waya ta fice. Kara wayar ta yi a kunne ta ji saukar nunfashinsa, “Khadija please kin ji.” Lumshe ido ta yi tana jin yadda katararta take mugun ciwo, a hankali ta ce “Me zan yi maka?” “Ya zo baƙon ki zo ki kawo mishi abinci sai ku gaisa, amma don Allah karki disga ni a gaban shi dan na faɗa mishi kina da hankali da nutsuwa, ki a je faɗan da ke tsakanin mu ki fidda ni kunya please matar yaya.” Ya faɗa cikin sayayyar murya. Kashe kiran ta yi ta sauka daga kan gadon, banɗaki ta shiga ta wanke fuska ta gyara ta sako hijabi ta fito. Daret kitchen ta shiga sai ta ɗauki kayan abincin da tuni ta haɗa ta aje. Kamar wadda kwai ya fashewa a ciki haka take tafiya, nan da nan ta ji zazzaɓi mai ƙarfi yana neman yi mata rufdugu, a bakin kofar ta tsaya jin jiri na neman ɗaukar ta. Sai da ta jima sannan ta sa kai cikin palon bakin ɗauke da sallama. Amsa mata suka yi Ahmad ya tashi da sauri ya amshi kayan yana faɗin “Sannu da ƙoƙari.” Murmushi yaƙe ta mishi ta durƙusa ta zuba musu ruwa da lemo gabaɗaya jikin sai wani kyarma yake sakamakon ƙamshin turaren da ta shaƙa, da kyar ta gama zuba musu ta ɗago kai a hankali ta dube gefen baƙon ta ce “Sannu da zuwa, ya hanya?” Saurin janye wayar ya yi suka haɗa ido, zaro ido ya yi sai kuma ya kalli Ahmad ya ce “Abokina anya kuwa ban haukace ba?” Da mamaki Ahmad ya ce “Ban gane ka haukace ba?” “Ahmad tsananin son da nake mata ya sa har fuskarta da muryarta naje gani da ji a jikin wata macen, Kahdijata fa nake gani tana mini gizo..” Itama tun da ta ƙura mishi ido jikinta ya ba ta kamar ta san shi, sai da ta daɗe tana kallon shi sannan ta gane shi ne, ajiyar zuciya ta sauke ta ce “Ni ce Khadijar da kake nema ba gizo ba ne nake maka.” Miƙewa ya yi ya iso gaban ta ya rasa me zai ce mata kawai ya miƙar da ita tsaye, kasa tsayuwa ta yi saboda ba ta da ƙarfi ga jiri na son kayar da ita. Wani irin duhu ta ga ya mamaye mata ganinta ta yi baya luu.... _Maman Nusaiba ce🤙🏻_ [6/23, 1:16 AM] Ummu Amjad: _*AREWABOOKS@SARATALKASUM88*_ 38 Ta kusa kaiwa ƙasa ya yi saurin taro ta ta faɗo jikinsa sai ga su sun zube a kan kujera, ƙoƙarin tashi take yi amma ya hana ta. Tsananin mamaki ne ya hana Ahmad tashi ya ƙame a kan kujera kamar sojan da ke filin fareti, a wannan lokacin zuciyarsa ce kawai take bugawa amma ban da gangar jikinsa. Sai da yi second fiye da arba'in sannan ya ja dogon numfashi yana kallon su, sam ya kasa gane inda abokin nasa ya dosa dama macen da yake yawan ba shi labari a kanta ashe Khadijar da yake son aura ce? To taya ma suka haɗu har suka san juna bayan shi ba mazauni ba ne? Sannan ita Khadija ba ta taɓa fita wata ƙasar ba ballantana a ce can suka haɗu har suka ƙulla soyayya? Girgiza kai ya yi ya runtse idanu ganin yadda yake share mata hawayen da ke fareti kan fuskarta. “Sweetheart dama a nan gidan kike? Aka ce an miki aure ko dama Mom ta faɗi haka ne dan ta saka ni à damuwa? Kin san kalar tashin hankalin da na shiga lokacin da Farrah ta sanar da ni ta je gidanki hutu tana ba ni labarin yadda mijinki yake kula da ke? Har fa kwanciya na yi a gadon asibiti a can London wannan karon sai da aka buga bal sau biyu ban da ni. Yanzu tun da na ganki nasan ƙarya ce Farrah take ba a miki aure ba.” Ya ƙarashe maganar yana ɗago hannunta ya ɗora a kan fuskarsa, ji yake kamar ya mayar da ita ciki saboda tsananin kewar ta da ya yi, so yake ya rungume ta ya ji ɗumin jikinta amma ganin yadda take yatsine fuska ya sa ya haƙura. Hannu ya sa ya ɗago fuskarta ya ce “Ki yi magana mana.” Buɗe idanunta ta yi a kan fuskarsa tana ƙare mishi kallo, a hankali ta ce “Hali zanen dutse, shi ya sa Hausawa ke cewa idan ka jima ba ka ga mutum karka tambaye shi labari tambaye shi halinsa, ke ko yaushe za ka canja hali Daddyn Farrah? Sannan meye haɗin ka da Amira da na ganka a gidansu? Duk da naji tana ce maka Uncle.” Murmushi ya yi ya kalli Ahmad da ya yi shuru yana kallon ikon Allah, shi maganar ma ta gagare shi sai ido kawai, tun da yake da Sultan bai taba jin ya furta wa wata 'ya mace kalmar so ba sai a kan Khadija, jinjina kai ya yi ya yi gyaran murya ya ce “Wai Mr J ban fahimci inda kuka dosa ba dama ka san Khadija ne?” Kallon ta ya yi ya dawo da kallon shi kan Ahmad ya ce “Ni kuwa nasan Khadija fiye da kai kanka, domin duk wani motsin ta a tafin hannuna yake, ko makaranta ta je ana bin mini diddigin ta.” Baki Ahmad ya saki yana juya magana can ya tuno ranar da wata mota ta biyo su, da sauri ya kalli Sultan ya ce “Dama yaranka ne can baya suka taɓa biyo mu naje ɗaukan Khadija zan kai ta wajen Yaya Salim?” Gyaɗa kai ya yi yana murmushi tare da cewa “Tabbas haka ne, amma ban taɓa tunanin Khadija tana tare da kai ba, na fasa bibiyar rayuwarta ne sakamakon Mom da ta mini katanga da ita, kai har fushi Mom ta yi ta daina amsa gaisuwa ta dole na haƙura na koma London na fasa bin duk wani motsin ta, amma a zuciyata ina cutuwa domin ban yarda Khadija aure aka mata ba tunanina ya fi ba ni danginta ne suka ɗauke ta ta dawo birni da zama.” Kishi ne ya rufe Ahmad amma ya danne yana rarrashin zuciyarsa kar ta tunzura shi ya ci mutumcin abokinsa da ya tashi tun daga wata ƙasa ya kawo mishi ziyara, sauke kai ƙasa ya yi ya ce “Abokina to ai Khadija ita ce matar Yayana Salim da ya rasu, kuma har suna da yara biyu a tsakanin su. Abu na gaba kuma yayana ya bar wasiyyar na aure su dan na kula mishi da yaransa, sai dai kuma dukkan su kowacce ta ce ba za ta taɓa yarda ta aure ni ba musamman ita wannan fitinanniyar mai bakin rashin kunya.” Ya ƙarashe maganar yana nuna ta tare da kirkiro murmushin yaƙe dan ya kawar da abin da yake ji a zuciyarsa.. A hankali ta tashi tsaye tana riƙe kai ta ce “Ba ka ba ni amsa ba kuna da dangantaka da Amira ne?” Cikin jin daɗi ya gyaɗa mata kai ya ce “Sosai ma, da mamar Amira da Mom uwa ɗaya uba ɗaya suke, ko lokacin da Farrah ta zo nan hutu ai gidanta ta fara zuwa ta ce ba za ta zauna ba wajen ki za ta zo, dalilin zuwana Niamey dan na sake binciko ki na san a wani hali kike ciki, idan na ganki na ɗauke ki mu bar ƙasar..” Duk da tana jin ciwo amma sai da ta harare shi ta haɗe fuska ta ce “Tab wace ce za ta bar ƙasar ba dai ni Khadija ba?” Tana gama faɗin haka ta yi ta maza ta sa kai za ta wuce ta ji muryarsa yana faɗin “Shin da gaske ne wai kin haihu naji shima Ahmad ya faɗi?” Kai kawai ta gyaɗa mishi ta yi gaba gabaɗaya ya cagula mata lissafi. Sai da ya ga ta rufo ƙofar sannan ya juyo kan Ahmad yana murmushi tare da matsowa kusa da shi yana riƙe hannunsa ya ce “Gaskiya naji daɗin ganin Khadija ta girma sosai, ashe zuwa na gidanku alkhairi ne.” Ahmad dai sai yaƙe yake yana bin shi da eh ko a'a, sai da ya ci abinci sosai yana yaba daɗin girkin hakan ya ƙara ƙular da Ahmad. Bayan ya gama suka fito ya masa jagora ya shigo ciki suka gaisa da su Mamma, Hussaina ta kalli Sultan tana murmushi ta ce “Yaya wannan ne Mr J ɗin da muke ji kana ambata?” Kallon ta Sultan ya yi ya ce “Ƙanwata ya kike?” Da sauri ta amsa da “Lafiya lau ya ƙasar turai?” Alhamdu Lillah ya ce mata sannan ya a je wa Mamma da Hajiya Babba leda guda-guda, da yake ba shi da ta ido kai tsaye juya ya yi wa Hussaina alama da hannu ta biyo shi, can harabar gidan suka fita ya tsaya yana sakar mata fuska ya ce “Yawwa please je ki kira mini Khadija ki ce Farrah ta ba da saƙo a ba ta.” Kallon shi ta yi tana mai ci gaba da murmushi ta ce “Dama ka san Farrah ne?” “she is my daughter.” Ya ba ta amsa. Waro ido tana yi ashe dama yana da ɗiya kamar Farrah? Da sauri ta juya ta shige ciki dan kiran Andizo. A bakin ƙofar ɗakinta ya tsaya bayan ya buɗe, ko kallon shi ba ta yi ba saboda ta kanta take sai da ta ga abin nashi ya wuce gona da iri ta ce “Don Allah ka rufe mini ƙofa ina son zan kwanta na gaji.” Rufe ƙofar ya yi ya ƙaraso in da take zaune ya tsugunna fuska haɗe ya ce “Ki faɗa mini a ina kuka kula soyayya da abokina? Sannan dama ƴarsa da yake ba ni labari ita ce ta zo miki hutu a baya?” Tsaki ta ja tana mishi kallon banza ta ce “To kai meye naka a ciki ɗan sa'ido? Da Duk zaman ka da shi ba ka taɓa ganin ƴar tasa ba dan ƙarya?” Dafe kai ya yi ya rasa me ya sa take faɗa mishi magana son ranta ba, idanuwansa ne suka yi jajur ya ɗago ya kalle ta ya ce “Na rantse da Allah idan kika sake yin magana da shi sai na, saɓa miki.” “To sannu Hamma Giɗaɗo ko Maigari ko kuma mamata, kai har ka isa ka hana na yi magana da baban ƙawata? Meye haɗin ka da ni?” “Saboda ni ne zan aure ki dole kuma ki bi duk wani umarni da zan ba ki matuƙar kina son ki ji daɗin zama da ni.” Kallon ba ka da hankali ta mishi tana hura hanci te ce “Allah ya sauwaƙe na aure ka Wallahi, ai ko da kuɗi aka haɗa mini da kujerar Makkah ba zan yarda na haɗa alakar aure da kai ba, da alama sai na dawo maka Andizo ɗin da ka sani tun a Ƙauye kafin mu daidaita da kai, kai a su wa da har kake wani tsaƙewa? To ka fita sabga ta ban sayo da kai ba daddyn Farrah kuma dole ne na kula shi tun da baban ƙawata ne.” Tashi ya yi tsaye a fusace ya ce “Haka kika ce?” Itama a zafafe ta ce “E haka na faɗa.” Kwafa ya yi zai fita suka ji ana buga ƙofar duk suka kalli wajen. Muryar Hussaina suka jiyo tana faɗin “Anty Khadija Daddyn Farrah ya ce ki zo zai ba ki saƙon da Farrah ta ba shi ya kawo miki.” Dan ta ba wa Ahmad haushi ta saka mayafi ta nufi ƙofar tana faɗin “Gani nan zan, fita yanzu.” Ta buɗe ta fita suka, wuce da Hussaina. Har gaban shi ta kai ta ta ce “Yawwa ga ta na kawo ta.” Godiya ya mata sannan ta juya ta koma, sunkuyar da kai ta yi tana mamakin kiran da ya mata, leda ya miƙa mata yana sa ɗayan hannunsa a aljihu ya ce “Ga shi wannan ce kyauta ta a gareki ta farko Khadija.” Kallon ƴar ƙaramar akwatin ta yi ja an ɗore jar flower a kai Mai ƙamshi, ɗago kai ta yi tana kallon shi baki sake za ta yi magana ya yi saurin faɗin “Kar ki ce komai please my wife ba a mayar da hannun kyauta baya.” Karaf maganar a kunnen Ahmad da yake can gefe yana kallon su, ya yi kwafa yana jiran Sultan ya tafi ya bi ta har ɗaki ya ga abin da ya ba ta. Ganin yadda yake mata magiya dai ta amsa har ta ɗan juyo sai ta ga Ahmad ta yi kuyo tana murmushi ta ce “Na gode da wannan kyautar da ka mini, gaskiya naji daɗi flower na da ƙamshi irin na turaren jikinka.” Ta faɗa tana kallon Ahmad da wutsiyar ido. Ƙayataccan murmushi ya sakar mata sannan ya ɗago ya kalli Ahmad ya masa alama da ya zo, fuska daure ya iso yana bin akwatin da kallo hakan ya sa Sultan ya ce “ Ya dai ko ta birge ka ne na sayo maka ka kai wa budurwarka.” Murmushi ya yi ya ce “Gaskiya ta yi kyau sosai, muje na kaika gida tun da na ga direban naka bai riga da ya zo ba.” Kallon Andizo ya yi ya ce “Khadija please ki ɗauki Kiran Amira ta dame ni tun jiya har kuka ta yi ta ce na haɗa ta faɗa da ke kina fushi da ita, sannan ki zo gidan su Amira sai na nuna wa Mama ke.” Duk da ba ta son zuwa amma ganin Ahmad ya sa ta ce “Ai kuwa zan zo sai dai ba ni da waya bare na kira Amira na ce mata zan zo, amma ba komai zan ari ta Hassana sai na sa numéro ta na kira..” Har zai shiga mota ya fasa jin abin da ta faɗa, “Haba Khadija kamar ke a ce ba ki da waya a hannunki kina babbar yarinya? Gaskiya abin kunya ne dole ki yi waya an jima zan turo Amira ta kawo miki.” To kawai ta ce ta mishi sallama ta juya ta wuce.. Suna tafiya a hanya Sultan ya ce “Ashe dai nine zan auri Khadija Shi ya sa ta ƙi amincewa da kai.” Kallon shi kawai Ahmad ya yi yana saƙa da warwara, murmushi ya yi yana gyaɗa kai ya danna wayarsa ya shiga gallery ɗin wayar, photon su Nour ya taɓo ya nuna mishi. “Wannan su ne yaran Khadija jiya aka yaye su.” Amsa ya yi yana kallon yaran, sosai suka birge shi yana faɗin “wow so beautiful.” Haka ya dinga kallon su yana yaba kyaun yaran, sai da ya shiga whatsapp ya tura photon yaran ya fi ashirin a kan number shi sannan ya a je masa wayarsa. Shi dai Ahmad bai sake cewa komai ba sai murmushi da yake yana gyaɗa kai. Ɗakin Aminatou ta shiga ta same ta tana haɗa kaya, da mamaki ta zauna a bakin gado ta ce “Adda ina zuwa haka?” “Zan koma gida ne zaman ai ya isa haka a gidan surukai, su ba sa so mu bar gidan nan suna so su haɗa mu da wannan ɗan rainin hankalin ni kuma ba zan taɓa yarda na zauna da Ahmad a matsayin miji ba, tun farko ba ma ga maciji da shi dan haka ni gidanmu zan tafi can zan fi sakewa dama ai dan yaransu ne suka hana mu bar gidan, to an ɗauke su in sun dawo a kai mini Khadija gidanmu, idan kuma sun ce su za su riƙe ta zan haƙura na bar musu ita tun da gari ne zan ke zuwa ina ganin ta akai-akai..” Jinjina kai Andizo ta yi ta ce “Wallahi Adda kamar kin shiga raina, na zauna na yi tunani na ga zaman da muke a gidan nan ba shi da amfani, shekara da wata biyu ai gara mu koma gaban iyayenmu.” Sai da ta gama haɗa kayan sannan ta zauna a kusa da Andizo ta ruƙo hannunta ta ce “Ko da mun bar gidan nan Khadija kar mu yanke zumunci, sannan muke ziyartar yaranmu.” “In sha Allahu, nima nan da kwana uku zan, tafi ƙauyenmu sa..” Kasa ƙarasa maganar ta yi jin kamar ta yi fitsari, da sauri ta miƙe tana riƙe ciki cikin tsananin ciwo ta ce “Waiyo Adda zan mutu cikina da ƙuguna.” Saurin ruƙo ta Aminatou ta yi tana jero mata sannu, kan gadon ta kalla sai ta kalle ta da sauri ta ce “Khadija dama haka kike fama idan ƙarshen wata ya yi?” Lumshe ido ta yi ta ce “A a Adda ni ban taɓa yin irin wannan ciwon ba.” Da mamaki take kallon ta, kama hannunta ta yi ta nufi banɗaki da ita. Ruwa mai ɗumi ta haɗa ta ce “Shiga ki gyara jikinki zan miƙo kaya ki sa.” Hijabin ta ja ta cire sai ta ga jini a jiki, a rude ta kalli Aminatou Kamar za ta sa kuka ya ce “Kin gani fa wani ciwon ne ya same ni?” Dariya ta yi ta amshe hijabin ta ce “Wallahi ban taɓa ganin macen da ta haihu ba ta taɓa yin al'ada ba sai ke Khadija, ina jin labarin irin ki na ɗauka ƙarya ce ashe da gaske akwai irin ku? To gyara jikin ba wani ciwo ba ne sai yanzu kika girma.” Ta faɗa tana fita. Sai lokacin ta ji kunya ta rufe ta ta zauna, ita ta manta da wai mace tana jini duk ƙarshen wata, ajiyar zuciya ta sauke ta tashi tsaye ta gyara jikinta ta fito ta tsaya tana jiran ta kawo mata kayan. Tana kawo mata kayan ta sa ta fito kanta a ƙasa da sauri ta gudu ta bar ɗakin, dariya Aminatou ta yi tana faɗin “Ki dawo na ba ki abin amfani karki zauna a haka.” Amma taƙi juyowa ta fita.. Sai da ta gama shiryawa ta ɗauki pant ta kai mata har ɗaki suka rungume juna har da kuka, haka ta lallaɓa suka fito tare Mamma na faɗin “Yanzu yaran nan duk tafiya za ku ba za ku zauna ba har ku yi wani auren? To ba komai hakan ma mun gode.” Sunkuyar da kai Aminatou ta yi ta musu sallama ta ce in an kawo su Khadija a sanar da ita za ta zo ta dauke ta, Mamma ta ce ba matsala za a sanar mata. Har bakin mota suka raka ta suna ɗaga hannu, Andizo ta dawo ta bar su a harabar gidan dan ta gyara jikinta kamar yadda Aminatou ta nuna mata. A bakin ɗakinta suka ci karo ta matsa gefe ta buɗe ƙofar ta shiga za ta rufe y yi karaf ya shigo kallon shi ta yi a fusace ta ce “Fitar mini a ɗaki Malam ba na son kawo ciwon kai ta kaina nake.” “Ki fito da wannan ƴar akwatin da Mr J ya ba ki na ga wacce tsiyar ce a ciki.” Kallon banza ta watsa mishi ta ce “Idan kuma aka ƙi fa?” “OK bari ki gani.” Ya faɗa yana yo wa kanta gadan-gadan, da sauri ta matsa gefe tana hararar shi, ganin zai taɓa ta ta hankaɗa shi ya faɗa kan gado ta nufi banɗaki da gudu ta datse kofa... _Maman Nusaiba ce🤙🏻_ [6/25, 8:57 PM] Ummu Amjad: _*AREWABOOKS@SARATALKASUM88*_ 39 Tsaye ya yi a tsakar ɗakin yana wurga na mijiyarsa ko zai ga inda ta aje akwatin, gaban wardrobe ɗin ta ya isa ya buɗe. Yadda ta jera kayanta da na su Nour sai ya birge shi, hannu ya kai ya soma buɗa kayan ko zai gani, wata ambulan ce ta faɗo fara ya sunkuya ya ɗauka. Buɗewa ya yi ya fito da abin da yake ciki, photon Salim ne sun fi talatin wani shi da ita sun rungumi juna suna dariya, wani kuma ta turo baki gaba ta harare shi aka ɗauki photon. Shagala ya yi da kallon photunan ba ƙaramin birge shi suka yi ba sai murmushi yake, a hankali ta buɗe banɗakin ta fito tana kallon ƙofar ta ga baya nan, ajiyar zuciya ta sauke tana faɗin “Mutum sai shegiyar mugunta ya sa a gaban shi, to Wallahi ko me za ka yi ba ka isa na ba ka wannan akwatin ba, daga kai har shi babu wanda ya ishe ni kallo shima har wani cewa yake zai kaini ƙasar waje ya ɗauka zai rude ni da kuɗi na yarda,to ko Salim da ya aure ni ba dan kuɗinsa nake son shi ba saboda ya iya soyayya da bada kulawa ga sanin darajar iyali.” Hannu ta sa ta goge hawayen da suka zubo mata tunawa da masoyin nata ta ɗora da cewa “Allah ya jiƙan ka mijina ba zan taɓa mantawa da kai ba a rayuwata.” Duk abin da take yana jin ta shi sam ya rasa me ya sa ta kasa sassauta wa zuciyata a kan soyayyar Salim wanda kasa ta rufe idonsa, a hankali ya tako ya iso kusa da ita tare da sa hannu ya dafa kafaɗarta. Da sauri ta juyo suka haɗa ido, hararar shi ta yi ta bige hannun ta yi gaba ta zauna a kan gado, kallon ta ya yi da wani irin yanayi yana jin ciwon furta masa kalmar da ta yi jiya, zuciyarsa ce take bugawa da sauri-sauri kamar ana turo shi ya ƙaraso ya tsugunna a gaban ta, kallon shi ta yi da ta ga idanuwansa sun cika taf da ruwa ya yi kalar tausayi sai mamaki ya kama ta. Hannunsa ya ɗora a kan cinyarta cikin wani kalar voice ya ce “Khadija ki yarda da ni.” Kallon ban gane ba ta jefa masa duk da ya ba ta tausayi amma ba ta jin har akwai ranar da za ta ba wa Ahmad yarda. Zama ya yi da kyau a ƙasa ya kamo kafarta yana ja mata 'yan yatsu, lumshe ido ta yi dama ƙafafuwan nata sun kumbura kamar na mai tsohon ciki, ganin yadda take lumshe ido sai ya ƙara da matsa mata ƙafar a hankali yana jera mata sannu. Shuru ta yi tana jin shi babu abin da take tunawa sai lokacin da duk ta tayar da rigimar jikinta ciwo Salim zai zauna ya yi ta matsa mata jiki. Can kuma ta buɗe ido da sauri ta janye ƙafarta tana yin istigifari, kallon ta ya yi ya sakar mata murmushi mai ƙayatarwa sannan ya miƙe tsaye, sai da ya kusa kaiwa ƙofar fita ya juyo ya ce “Khadija ki yi haƙuri ki a je komai mu yi auren nan, nasan ba kya sona amma mu yi hakan ba dan kanmu ba sai dan yaran nan su tashi tare da uwa da uba.” Juya mishi baya ta yi ta ce “Ka bar ma wannan maganar ba zan taɓa yarda da hakan ba.” Bai sake ce mata komai ba ya buɗe ƙofa ya wuce. Sai da ta ji fitar sa sannan ta gyara kwantaciyar ta tana sauke ajiyar zuciya, gabaɗaya duk ya bi ya takura wa rayuwarta ta ja tsaki ta janyo bargo ta rufa. Sai da ta yi kwana biyu ba ta je ècole ba saboda yadda take kwana da zazzaɓi har garin Allah ya waye ba ya sauka sai rana ta, Mamma ta ce likita ya zo ya duba ta amma sam ta ƙi ta ce ai ta samu sauƙi ma, ganin ba za su daina maganar zuwa asibiti da kiran likita ba washegari ta shirya ƙarfe 7:30am zuwa makaranta. Tana fitowa palon gaisawa suka yi da Hajiya Babba da take sababi ita kaɗai a palon, zama ta yi tana faɗin “Hajiya waye ya taɓo mana ke kike faɗa da safiyar nan?” Gefen kitchen ta kalla ta tofar da yawu ta ce “Da ni da wancan ɗan butar uwar mana, ya zo yana faɗa mini maganar banza ni sa'ar shi ce da zai ke faɗa mini duk wata maganar da ta zo bakinsa? To ni ba ƴar banza ba ce bari uban nasa ya dawo zai ga me zai faru, ko kuma zan haɗa shi da Saddiƙu.” Dariya Andizo ta yi ta miƙe tana faɗin “To wa zai shiga tsakanin ku ke da ɗan lelen ki? Ni na tafi sai na dawo.” Kwafa ta yi tana faɗin “Daɗin ta ma kema ba barin ki ba ya yi har da kika ƙi tayani yi mishi faɗa, za ku dawo ku same ni yau a gidan nan ba mai yin girki kowa ya girka nashi ya ci.” Dariya Andizo ta kuma yi tana gyara zaman hijabin jikinta ta wuce. A harabar gidan ta same shi ya yi tsaye hannayensa cikin aljihu yana kallon gefe, ƙura mishi ido ta yi tana ƙare mishi kallo, yadda yake a tsaye ƙyam sak Salim ga shi ɗan wanka sai ta ga ya mata wani kalar kwarjini, sai take ganin kamar Salim ne take tunkara hakan ya sa ta dinga sakar masa sayayyan murmushi irin na masoya, sanjensa da yankwanta luf a fuskarsa ta bi da kallo tana faɗin “Wannan shi ne mijina.” Karaf maganar a kan kunnensa ya juyo cikin jin daɗin abin da ta faɗa ya miƙa mata hannu ganin ta kusa zuwa da nufin ta ba shi jakar makaranta, sai da suka haɗa ido ta ga ya juye ya dawo Ahmad nan da nan annurin kan fuskarta ya ɗauke ta ja tsaki ta kauce, hawayen da suka cika mata ido ne suka samu damar zubowa ta kai hannu ta goge, shi kuwa da kallo ya bi ta ganin yadda lokaci ɗaya ta haɗe rai. Wajen direba ta duba yana ganin ta ya ƙaraso tare da rusunawa ya ce “Madam barka da fitowa.” “Yawwa barka dai baba ècole nake son zuwa.” Ta faɗa tana yatsina fuska. Kallon Ahmad ya yi hakan ya sa ta gane sai ya ba shi umarni abin sai ya ɓata rai, ba ta son ta makara dan haka ta juya ta nufi ƙofar fita da sauri. Murmushi ya yi ya ce “Baba ka rabu da ita karka ɗauke ta ni zan ke kaita.” Jinjina kai ya yi ya koma inda ya zauna shi kuma ya shiga mota ya fita, sai da ya bar unguwarsu sannan ya hango ta can naisa da shi bakin hanya tana ƙoƙarin tsayar da motar haya, dafe kai ya yi ya ce “Oh Khadija rigimar ki ba ta ƙarewa, shi ya sa Yaya Salim yake cewa zai ga lokacin da za ki yi hankali.” Har ta tsayar mota tana sanar da shi inda zai kai ta sai ga wasu motoci biyu sun paka a gefen su, wani ƙaƙƙarfan namiji ne ya fito daga mazaunin direba ya iso wajen su, da kallo Andizo ta bi shi sai kuma ta kawar da kai tana yin tsaki, cike da gadara ya ce “Kai ɗan sahu wuce abin ka wannan ba kalar hawa irin motarku ba ce.” Da mamaki Andizo take kallon mutumin har mai motar ya wuce, cike da girmamawa ya ɗan rusuna ya ce “Madam mu je oga yana jiran ki a mota.” Kallon ba ka da hankali ta mishi tana jin kamar ta zabga mishi mari, agogon da ke daure a tsintsinyar hannunta ta kalla ta ga ƙarfe 7:45am rai ɓace ta kalle shi ta ce “Waye wani Oga? Kawai daga gani na sai ka ce wai na je Oga na jira na ka sanni ne?” Girgiza kai ya yi cikin girmamawa ya ce “No Madam mu je dai ki ganshi karki makara ya ce mini makaranta kike son zuwa.” Banza ta mishi ta ci gaba da tsayuwa tana ƙoƙarin tare mota, amma duk wanda ya yi ƙoƙarin tsayawa sai wannan mutumin ya kalle shi dole ya ƙara wa motarsa gudu, dafe kai ta yi kamar za ta fashe da kuka ta ɗago kai sai ta ga Amira a gaban ta, da mamaki ta ce “Amira!” Ba ta amsa ba sai hannunta da ta kama ta ja ta suka nufi motar, kamar raƙumi da akala haka ta dinga bin ta har ta buɗe ɗayar motar ta saka ta ta rufe sannan ta dawo ta gaba da su ta shiga suka soma tafiya. Ahmad yana kallon su sai ya tuna abin da Andizo ta faɗa lokacin da ta ga Sultan, “Mene ne haɗin ka da Amira.” Ya nanata maganar take ya gane Sultan né ta ɗauke ta, kwafa ya yi ya juya kan motar ya nufi wajen aikinsa. Kasa yin tuƙin motar ya yi ya koma bakin hanya yana sauke ajiyar zuciya, kishin ta yake ji sosai wanda har yake barazanar ɗaukewar numfashinsa kamar mai ciwon asma, dafe saitin zuciyarsa ya yi da karfi jin yadda take bugawa da mugun gudu. Ya jima a haka sai addu'a yake ta karantowa ko zai samu sassauci, sai da ɗauki kusan minti shabiyar sannan ya dawo daidai amma kana ganin shi kasan yana cikin ɓacin rai, wayarsa ya ciro daga aljihu ya lulibo wata number ya danna mata kira, ana ɗauka ya ɗan saki fuska ya ce “Assalam alaikum Maigari Angon Hajja barka da safiya.” Daga can ɓangaren Maigari da yake hanyar dawowa gida daga masallaci ya ce “Wa alaikum salam Ahmadu ya kuke kun tashi lafiya? Ya wajen su uwar masu gari?” “Tana nan lafiya maganar ta ce ma nake so mu yi shi ya sa na kira.” “A to ba damuwa in ce dai lafiya ba wani abu ba ne marar kyau ya faru ko? Dan ni na ce ma ta dawo gida zaman haka ya isa ta samu ta yi aure.” Wani kalar murmushi Ahmad ya yi yana shafa kai ya ce “In ko haka ne ka kwantar da hankalinka faɗuwa ta zo daidai da zama, dama maganar auren ce nake so na sanar da kai kafin su Abba su zo. A taƙaice dai mun daidai ta kanmu ni da ita za mu yi aure, dama kuma in ba ka manta ba wasiyar da mijinta ya bari kenan ko da mutu kar ta auri wani na aure ta dan mu kula da yaransu.” Cike da farin ciki Maigari ya iso ƙofar gidansa ya zauna yana faɗin “Kai amma dai wannan batu naka da daɗin ji yake Ahmadu, gaskiya na yi murna na yi farin ciki da jin hakan kuma nasan Hajja sai ta fini jin farin ciki saboda ƙawancansu ita da Hajiya, ina fatan dai tana sonka kaima ba dan cika wasiya za ka aure ta ba harda soyayya ma ko? Saboda idan ba ka sonta ba zan aminta ba duk da na jima ina, addu'ar Allah ya daidai tsakaninku hakan zai fi mana daɗi.” Shima cike da kin daɗi ya ce “Haba ai Maigari sani ne ba ka yi ni na fara son Khadija kafin ma Yaya Salim ya ganta, to lokacin na yi zurfin ciki ne kuma kasan muna ƴar tsama da ita sau ta raina ni, to kuma da yake akwai rabo tsakanin ta da yayana shi ya sa duk ba wanda ya gane ina sonta ko ita kanta ba ta sani tun da lokacin ba hankali gareta ba. Yanzu dai mun gama fahimtar juna zan sanar da su Abba yau da an jima in na dawo zuwa nan da kwana biyu sai su zo a yi maganar auren.” Jinjina kai Maigari yake yana murmushi har ya gama maganar sannan ya ce “Ka yi gaskiya Ahmadu hakan za a yi, gaskiya ina farin ciki Allah ya muku albarka itama zan yi magana da ita naji daga ɓangaren ta.” Saurin tarar numfashinsa Ahmad ya yi ya ce “Ai ko ka tambaye ta ba za ta iya ce maka komai ba, ta ce min kunya take ji ba ta so ta ce komai a kan lamarin nan har a yi a gama ita dai ta amince mini.” “A to shi kenan sai an jima bari naje na sanar da Hajja wannan daddaɗan labarin.” “To na Hajja ikon Allah na gode sai an jima.” Kashe wayar ya yi yana jinjina wa kansa tare da cewa “Idan kin san wata ai ba ki san wata ba, kaima Sultan zan yi maganin ka shi ne har da wani zuwa ka ɗauke ta a mota ina son na ɗauke ta, sai dai ka ji labarin an saka ranar bikinmu lokaci kusa.” Ya ja tsaki ya kunna motar ya hau kan hanya. Tun da suka fara tafiya ba ta ɗago ba duk da tana jin ƙamshin turarensa mai sanyaya mata zuciya amma ta yi kamar ba ta ji ba, kallon ta ya yi ya ce “Khadija rigima.” Jingina kanta ta yi da jikin kujera idanuwanta a rufe tana jin shi ta yi shuru, sai da ta ji sanyi a kumatunta sannan ta buɗe idanu ta sauke shi a kansa. Ido ɗaya ya kashe mata yana matsowa kusa da ita ya janyo ta ya manna mata kiss a goshi ta yi banza da shi sai kallon shi kawai da take, ganin haka ya sa ya ɗago da ita ya ɗora kanta a kafaɗarsa ya zagaye ƙugunta da hannu yana sauke ajiyar zuciya. Kasa taɓuka komai ta yi domin jikinta ya yi sanyi ta kasa gane Sultan wani irin mayen kiss ne, ga shi ba shi da kunya a gaban kowa ma zai iya taɓa jikinta abin na damun ta har mamakin kanta take ranar da ya zo gidansu ba ta masa rashin mutumci ba da ya rungume ta, ajiyar zuciya ta sauke tana danganta hakan da kara ƙawarta take ji shi ya sa ba ta iya masa rashin mutumci kamar Ahmad. “Princess wai ba za ki yi min magana ba? Ko duk fushin ne kike da ni da na saɓa alƙawari?” Ya faɗa yana ɗago ta daga jikinsa, ƙoƙarin haɗa fuskarsa da tata yake ta kawar da kai tana turo baki, hannu ya sa ya shafo bakin cikin wani kalar shauƙi ya ce “Oh my god! Kina tafiya da imanina my wife.” Sai a lokacin ta ji za ta iya magana ta ɗago tana hararar shi, “Wace ce wife ɗin taka? Dama kai kana da imani ne” Nuna ta ya yi da hannu yana gyara zaman glass ɗinsa sannan ya kamo hannayenta ya ce “Kin taɓa ganin mutumin da ba shi da imani ko da ɗigo ne? Ya kamata a ce yanzu kin gane inda muka dosa na sanar da Mom a yi bikinmu ko na ɗauke ki mu tafi next month.” Kasancewar yanzu tana jin turanci ta gane me yake nufi, tsaki ta ja ai kuwa ya damƙi bakin ta yi ƙara ya saki, wani irin kallo ya mata irin na mashaya waɗanda suka kai ƙarshe a buguwa, jikinta ne ta ji ya yi yam ta yi saurin rufe ido tana faɗin “Dalla can ni ka daina mini irin kallon nan ba kyau.” Murmushi ta yi ya ce “To in ban kalli matata ba wacce mace zan kalla naji sanyi?” Ya faɗa yana gyara mata jakarta. “Kai ka sani dai, a hakan ne kake tunanin za ka aure ni da ko Sallah ba ka yi.” Saurin kallon ta ya yi da mamaki, maganarta sai ta tuna mishi lokacin da ya sato ta ta ce mishi baya Sallah, girgiza kai ya yi ya ce “Wa ya faɗa miki ba na sallah? Ni fa musulmi mai zai hanani yin Sallah da lafiyata da komai, jam'i ma nake zuwa masallaci tun shekarun baya da kika ce in dai ba na yin Sallah ba za ki so ni ba, na canja abubuwa da yawa da kika sanni da su Khadija, yanzu ko giya sai na yi wata biyu uku ban sha ba idan ma kika ga na sha to an ɓata mini rai ne na rasa wanda zai kwantar mini da hankali sai na sha na kore damuwa.” Ya ƙarashe maganar cikin yanayin damuwa ƙarara a kan fuskarsa. A zuciyarta ta ji daɗi da yake Sallah, amma a fili sai ta yatsine fuska ta ce “Kana saya wa kanka cuta dai ba kore damuwa ba, jiya da sauran kayan shaye-shaye suna lalace kayan ciki kamar su huhu ƙoda, zuciya, kai har ma da ƙwaƙwalwa ita ce take fin komai samun matsala, idan ma ka faɗa dan naji daɗi ne ba ka birge ni ba sai na gani a, zahiri, ko yanzu wannan motar taku warin kayan maye take kamar kodin kamar giya.” Ta faɗa tana murguɗa baki daidai sun zo get din makaranta. Za ta fita ya yi saurin ruƙo ta ya marairaice fuska kamar ƙaramin yaro ya ce “Please kiss me one.” Kallon banza ta watsa mishi ta ce “Kai ni fa ba ƴar iska ba ce da har kake ƙoƙarin nuna mini iskanci, ba za, a yi kiss ɗin ba.” Kwantar da kansa ya yi a jikin kujera kuma ya ƙi sakin ta, ɗayan hannun ya sa ya ce “Idan ba ki yi mini ba a baki ba za ki tafi ba sai ki zaɓa na wuce da ke hotel mu wuni a can ko kuma ki mini one kiss mai sugar.” Dafe kai ta yi kamar ta sa kuka ta ce “Don Allah Daddy Farrah ka rabu da ni na makara ni ba na son iskancin nan naka.” “Ai kuwa sai kin so ko ki mini ko mu wuce.” Banza ta mishi ga Amira a tsaye a gefen motar tana jira ta fito, danne dariyarsa ta yi ya ce “Oya to yi mini a kumatu.” Gabaɗaya tsoro ya rufe ta gani take kamar zai sake sace ta a karo na biyu, ba dan ta so ba ta miƙa fuskarta ya yi saurin ruƙo ta, runtse ido ta yi za ta mishi kamar ya faɗa a kunci amma sai ta ji saɓanin hakan sakamakon ɗumi da ta ji ya ratsa mata baki, kwalalo ido waje ta yi tana ƙoƙarin kwacewa amma ya riƙe ta kam kamar zai ƙarya ta, inna lillahi kawai take faɗa a zuciyarta ganin ya ƙi sakin ta, sai da ta daddage ta minti ne a hammata ya sake ta ta dinga mayar da numfashi, buɗe motar ya yi ya fito ya za gaya itama ya buɗe mata da kyar ta fito tana sunkuyar da kai gani take kamar Amira ta gane abin da Uncle ɗin nata ya mata. “Haba Khadija kuma shi kenan sai ku zauna kuna ta hira alhalin kin san mun makara.” Ta kalli Sultan ta ce “Duk lefin ka ne Uncle nan fa makaranta ce muka zo ga shi ƙila ba za mu samu haiga ba sai malamin da ya shiga ya gama ya fito za mu samu shiga.” Murmushi ya yi yana shafa gemunsa da yake sheƙi ya kalli Andizo ya ce “Ƙawar taki ce ta cika neman rigima, wai so take na kai ta wajen Farrah ni kuma na ce ta bari sai kun yi hutu lokacin za mu yi aure sai mu koma can da zama.” “Kai!” Ta faɗa tana kallon shi jin sharrin da ya mata, kwafa ta yi ta kama hannun Amira ta ce “Muje kinga ba na son doguwar magana.” Kuɗi ya zaro a aljihunsa ya kamo hannunta ya damƙa mata ya ce “Wannan tukuici ne da aka kula da ni yau.” Ƙin amsa ta yi sai da Amira ta yi magana sannan ta amsa ta mishi godiya suka yi gaba, sai da suka ɓace wa ganinsa sannan ya juya ya koma cikin motar suka tafi.. Arma ne ya tare su yana ɓata rai ya ce “Ku kuma shi kenan sai ku shanya ni ina ta jiran ku, wai lafiya ? Tun karfe 7:30am Khadija ta ce mini ga ta nan za ta fito daga gida, amma yanzu kalli ki ga lokacin 8:30am ina kuka tsaya?” Taɓe baki Amira ta yi ta ce “Ga wadda nan ta tsayar da mu tun ɗazu muka zo amma taƙi fitowa daga mota sai da aka rarrashe ta ta fito.” Tsaki Andizo ta yi ta yi gaba ta samu waje ta zauna suma suka biyo ta, sai da suka zauna Andizo ta ce “Ina Sadiya?” “Tana ciki ita ai ta riga mu zuwa.” Arma ya ba ta amsa yana kallon ta ganin yadda take wani ciccin magani.. Sai da malamin ya fito sannan suka samu damar shiga cikin classé ɗin, Andizo ta fara copy rubutu tana gamawa wani ya shigo sai suka ake. Bayan sun fito suka wuce restaurant suka sayi shawarma amma Andizo ta kasa ci, da ta shinshina bakinta sai ta ji ƙamshin jikinsa sai ta tofar da yawu tana jin kamar ta yi amai, ƙyanƙyamin shi da take ya sa ta kasa cin abincin ta ce ta goshi. Bayan sun tashi motar gidan su Amira ta zo ta ɗauke su aka kai ta har gida, tana shiga ɗakinta ta wuce banɗaki da gudu sai amai, iya ruwan da ta sha a wunin ranar shi ta amayo, tana gamawa ta yi brosh ya fi sau biyar sai da ta soma jin za ta faɗi saboda yunwa sannan ta haƙura ta watsa ta fito . Bayan ta fito kaya ta canja sannan ta fito ta wuce Denning table ta dibi shinkafa fara da miya ta dawo palo wajen Hajiya Babba ta zauna. Kin Kula ta Hajiya Babba ta yi har ta gama cin abincin ta kai kwanon ta a je ta sha ruwa sannan ta dawo, dariya ta yi zauna tare da kwanciya a cinyar Hajiya Babba ta ce “Haba Hajiya wai duk fushin ne kike ba ki huce ba?” “A a uwaki ce nake.” Dariya ta kuma yi sai kuma, ta tashi ta zauna ta ce “Yawwa wai ni ko Hajiya mene ne ya faru a gidan nan shekarun baya da suka wuce? Lokacin da Salim yana kwance a asibiti naji ya ce kar ta tuna da abin da ya far shekarun ba da suka wuce, shin wani mummunan abu ne ya faru?” Ta faɗa tana kallon Hajiya. Jinjina kai Hajiya ta yi sai ga hawaye sun soma zarya hakan ya sa Andizo ta ce “Haba Hajiya ya da kuka?” “Khadija gyara zama zan sanar da ke abin da ya faru shekarun baya har kika ji Salim na cewa kar mahaifiyarsa ta tuna. A wata ranar asabar...” Ƙaran banko ƙofar da aka yi ya sa Hajiya da Andizo suka ɗago da sauri, ganin shi duka yi kamar wani kumurcin maciji ya iso gaban Andizo rai ɓace ya ce “Uban waye wanda ya ɗauke ki a mota ?” Ya faɗa kamar zai kai mata duka duk da ya san wanda ya ɗauke ta. Tsoro ne ya kama ta ta ja da baya tana ƙara mannewa da jikin kujera, hakan ya sa ya biyo ta tare da damƙar hannunta ya miƙar da ita tsaye, sunkuyawa ya yi ya mata ɗaukan akuya ta fasa ihu tana faɗin “Hajiya don Allah karki bari ya tafi da ni Wallahi dukana zai yi mugu ne mugunta zai mini, ki cece ni Hajiya waiyo Mamma zai ƙarya ni...” *Maman Nusaiba ce* [6/26, 11:10 PM] Ummu Amjad: _*AREWABOOKS@SARATALKASUM88*_ 40 A tare Mamma da su Hassana suka fito a firgice jin ihun Andizo, ganin abin da yake faruwa sai sai suka zari ido suna kallon Ahmad da yake ƙoƙarin barin palon, ita kuwa sai ihun neman taimako take tana dukan shi a gadon baya amma ya yi kamar bai ji ba. Haɗe rai Mamma ta yi ta ce “Kai Ahmad ba na son hauka meye haka? Sauke ta na ce kafin na iso na zabga maka mari.” Sauke ta ya yi yana huci kamar kumurcin maciji ya riƙe ƙugu ya ce “Mamma to kin san me ta yi ne kika hana na mata hukunci?” To ko ma meye ta yi tun da ba kisan kai ta yi ba ko abin kunya ai bai kamata ka mata irin wannan ɗaukan ba.” Cewar Hajiya tana zaune da mamakin Ahmad ya hana ta tashi daga kan kujera. Tsaki ya ja ya dawo ya zauna a kusa da Andizo ta yi saurin matsawa tana kallon shi a tsorace, harara ya aika mata ya ce “Na rantse in kika sake matsawa sai na ɗauke ki ni na san abin da zan miki, ba dai dan na sa miki ido ba ne har kike yin duk abin da kika ga dama? To daga yau kin gama duk wani ɗan iskan da na sake gani ya tsaya da ke da kaina za zane ki, amanar ki Maigari ya ba mu ba zan zuba ido na ga kina kula tantiran 'yan iska ba na yi shuru amana ta ci mu. Saboda ba ki ɗauke ni mutum ba shi ya sa kika kama hanya kika fita har wani ƙato ya zo ya ɗauke ki, me ya faɗa miki da kika shiga motar?” Duk maganar da yake mata murya can ƙasa yake yi ba mai ji daga ita sai shi, a hankali ta ɗago ta kalle shi baki na rawa ta kuma sunkuyar da kai sannan ta ce “Don Allah Yaya Ahmad ni ka rabu da ni na yi rayuwata cikin salama, kai ka takura mini shima Daddyn Farrah ya addabe ni so kuke ku haukata ni ne? Wallahi na ma fasa zama zan koma ƙauye na yi gaba da rayuwata kawai.” Ta faɗa wasu hawaye masu ɗumi suka silalo daga kwarmin idanuwanta. Kwafa ya yi cikin ba da umarni ya ce “Tashi ki tafi ɗaki zan je na same ki magana za mu yi, kuma idan kika kuskura wani ya ji maganar nan sai na yanka wuyanki da wuƙa.” Saurin kallon shi ta yi tana zare ido, da hannu ya nuna mata hanya ta tashi sumaƙai kamar munafuka ta wuce. Da kallo suka bi ta Hajiya ta ce “Ni dai ina ga rayuwa a gidan nan, ban taɓa ganin jarababbe irin ka ba Ahmadu duk ka bi ka takura wa rayuwar yarinyar nan, ta ce za ta je ganin gida amma ka bi duk wata hanya ka hana ta tafiya ta haƙura, yanzu kuma ɗan karatun da take shima ba za ka bari ta yi cikin kwanciyar hankali ba? Ni fa ba ƙanwata ba ce ta yaye ni ballantana bari ka sa wa marainiyar Allah ciwon zuciya, a haka kake so ta so ka har a muku auren?” Ci gaba ya yi da daddanna wayarsa yana jin ta ya yi shuru, hakan ya sa Hajiya ta ɗauki pillow ta buga mishi tana faɗin “Ɗan banza futsararre tashi ka ba mu guri.” Sai lokacin ya ɗago kai ya kalle su, Mamma dai na zaune ta kawar da kai ko bi ta kanshi ba ta yi ba ta ci gaba da kallon tv, amma kuma hankalinta yana kan maganar da Hajiya ta yi. Dariya ya yi ya tashi tsaye ya ce “Hajiya wannan ɗiyar taki idan ba a sa mata ido ana tsawatar mata sai ta haɗu da abokan banza su ɓata mata rayuwa, kuma kinga dai amana ce a garemu bakiɗaya, idan wani abu ya same ta da mu Maigari zai yi kuka. Kuma aure ni da ita ai ba fashi ba ki ga mun daidai kanmu ba ne? Shi ya sa na hana ta kula kowa tun da ta amince za ta aure ni.” Yana gama faɗin haka ya juya ya wuce da sauri. Murmushi Hajiya ta yi ta ce “Aha ashe dai kishin ne ya motsa dan ka gata da wani ko?” Juyowa ya yi ya sakar mata murmushi ya juya ya wuce, daƙuwa Hajiya ta yi wa bayansa tana faɗin “Ja'iri kawai.” Kuka sosai ta ci da ta shiga ɗaki ta rasa me ya sa suka takura wa rayuwarta musamman ma shi Ahmad da duk wani motsi in ta yi sai ya samu abin da ya ce ta yi, jin ƙaran takun tafiyarsa ta yi saurin tashi ta sa wa kofar ɗakin makulli ta kulle. Banɗaki ta shiga ta gyara jikinta sannan ta fito, tana ji yana mata magana amma taƙi buɗe kofar, kan gado ta zauna ta buɗe jakar makarantar ta ta fito da takardu ta fara dubawa. Bayan ta gama ta buɗe za ta mayar sai ta ga wata leda fara mai kyau a ciki, da mamaki ta ɗauko ledar ta buɗe, zaro ido ta yi ganin sabuwar waya iPhone 15pro, juya wayar ta dinga yi tana mai nuna al'ajabin yadda aka yi waya ta zo cikin jakarta, buɗewa ta yi kalar wayar ya tafi ta imaninta pink color. Murmushi ta yi ta kunna har da layi a ciki Artel ta sake juya waya, sai ta jima tana dudduba cikin wayar abin da ya ba ta mamaki photunanta ne sun fi ɗari a ciki lokacin tana ƙarama, gyara zama ta yi ta sake duba wani photo da ta ga ba nata ba ne, Farrah ta gani da Sultan da ita ta yi tsai tana tuna yaushe suka yi wannan photon kuma? Ajiyar zuciya ta sauke tana ƙare wa photon kallon, in ta kalli Farrah sai ta kalli Sultan saboda yadda suke kama kamar ya yi kaki ya tofar, hannu ta kai ta shafa fuskar Farrah ta ce “Ma belle chérie.” Lumshe ido ta yi tana jin wani matsanancin farin ciki na mamaye lungu da kusurwar zucyarta, ji ta yi duk wani haushin sa da take yana raguwa ta sake kallon photon, yadda ya yi mata wani kalar kallon love a photon har sai da ta yi tagumi tana faɗin “Marar kunya shi ko a photon ma sai ya nuna ko yaushe aka yi wannan photon?” Ta yi murmushi tana ƙare wa surar jikinsa kallo. Tabbas Sultan ya cika duk wani mataki da ake buƙata a miji, ga shi ɗan gayu mai ji da izza kamar jinin sarauta , ga kuɗi ga iya soyayya, ga kyau ga class Ko takun tafiyarsa abin kallo ne, dogo fari kyakkyawa zubin jaruman maza. Ɓata rai ta yi ta ce “Sai dai kuma ai ɗan iska ne ga shaye-shaye, wa ya sani ba ko mayaudari yan yaudarar 'yanmata da kyan da Allah ya ba shi da kuma kuɗi.” Ta sake kallon shi sai kuma ƙara da cewa “To duk da haka dai na ji daɗi da ya saya mini wayar nan tun da shi wancan mugun ya kwace tawa ya ƙi ba ni.” Har ta gyara za ta kwanta ta ji shigowar saƙo ta yi saurin ɗaukan wayar ta shiga text message. _“My wife ina fatan Kim buɗe wayar kuma kin ga kalar ta yi miki? Idan kuma ba ta birge ki ba gobe idan za ki tafi makaranta sai ki zo da ita ki faɗi kalar da kike do sai a sayo miki, I love you so much my darling. Please Idan kinga saƙona ki daure ki dawo mini da reply duk da nasan da wahala ki kula saƙon ma bare ki ba ni amsa, nasan ni mai lefi ne a gareki amma ki yi haƙuri ki yafe mini mu yi aure zan ba ki kulawa fiye da wadda kika samu a wajen Salim ina mai tabbatar miki, ke kanki kin san tsananin son da nake miki ne ya sa har na sato ki aka ɗaura mana aure a shekarun baya, ki daure ki ce kina so na ko da sau ɗaya ne Khadijata, yanzu haka Farrah na sanar mata da abin da yake tsakaninmu da ke ba ki ga yadda take murna ba har da kuka ta yi na farin cikin za ki zama matar mahaifinta..”_ Tagumi ta yi tana sake bin text ɗin tana ƙara karantawa, murmushi ta yi ta aje wayar tana jinjina son da ƙawarta ta take mata, tana ta tunane-tunane har bacci ya ɗauke ta.. Washegari ta shirya ta fito palo inda ta ga duk sun hallara ita suke jira ta gaishe da Mamma da Abba da Hajiya, hararar inda Ahmad yake ta yi suka gaisa da su Hassana, kasancewar tana kusa da shi ya miƙa ƙafa ya take mata 'yan yatsu. Da sauri ta kalle shi suka haɗa ido ya sakar mata da murmushin mugunta ya ƙara danna yatsun, ƙara ta sa jin wani mugun zafi har tsakiyar kanta. Hajiya ta kalle su ta ce “To kin fara ko gari ya waye? To kin ji da shi babu wanda zai kula ku tun da kun zama 'yan drama.” Idanuwan Andizo ne ya ciko taf da hawaye amma ganin yana mata dariya ƙasa-ƙasa sai ta daure taƙi bai wa hawayen damar zubowa, ɗayar ƙafa ya kai ya sake murza yatsun ta kuma yin ƙara tana faɗin “Mamma ƙi masa magana zai karya mini yatsun ƙafa dan mugunta.” Ta faɗa tana sakin wani kalar kuka gwanin ban tausayi saboda zafin da yatsotsinta suke mata kamar ba a jikinta suke ba, ganin hawayen ta sai ya yi dariya ya janye ƙafafuwansa ta yi saurin ɗago ƙafar da kyar. Kuka ta sa tana faɗin “Mugu azzalumi sai Allah ya saka mini cuta ta da kake yi yi.” Abba ya kalli Ahmad ya ce “Kai tashi ka ba mu guri kafin na saɓa maka, wacce irin mugunta ce haka za ka dinga take mata 'yan yatsu dan rashin imani?” Daure fuska ya yi ya ce “Ƙarya ce fa take Abba babu wani take mata ƙafa da na yi, ita ce ma ta take mini tawa ƙafar Allah ya sa ina da takalmi ƙafa ciki.” Da hannu ya nuna mishi hanya ya ce “Da wasu ne waɗanda ba 'yan gidan ba in la faɗa musu za su yarda ba mu da muke ganin artabon da kuke kamar za ku ga hanjin juna.” Andizo ta ɗago ƙafar ta ce “Ƙarya ce yake Abba shi ne ya take min ƙafa da wannan takalmin nashi mai tauri, kalli ki ga har jini suke yatsun nawa.” Ta faɗa wasu hawayen na zubo mata. Salati Hajiya Babba ta ɗauka tana taɓa ƙafar, a fusace ta kalli Ahmad da ya yi kitsin-kitsin da fuska ya tsare gida yana harare-harare ta ce “Anya kuwa Ahmadu za ka ga daidai a rayuwarka? Yanzu saboda Allah sai ka illata mata ƙafa dan kafi ƙarfinta? To Wallahisai na ci ubanka Musalle ga shi nan a zaune, ni za ka mayar tsohuwar banza? To bari Saddiƙu ya zo zan haɗa mata kayanta ta koma can ƙasar waje ta ci gaba da karatu tun da kai so kake ka kashe ta. Kai kuma Musalle idan ba ka yi masa kashedi ba a kanka zan fanshe duk iskancin da yake mini.” Abba ya ɗan sunkuyar da kai ya ce “In sha Allahu zan mishi kashedi, ni kaina na yi tunanin ta koma wajen Saddiƙu saboda matarsa ta takura sai sun zo har su Hassana sun kawo musu ziyara, to na ce mata sai sun yi hutu da kaina zan kai su har can.” Goge hannu Hajiya ta yi ta kama hannun Andizo ta ce “Ya dai fi maka dan Wallahi ba ƙaramin aikina ba ne na maka rashin mutumci a gidan nan matsawar bai daina cin zalin ta ba.” To Abba ya ce ita kuma ta janyo Andizo suka dawo palo, tissue ta sa ta goge mata ƙafar sai sababi take tana zagin Ahmad ta sa mai aikin gidan ta ɗauko mata roof ta shafa mata ƙafa, godiya Andizo ta mata ta tashi ta wuce zuwa ècole. A harabar gidan ta ganshi tsaye ta wuce tana ɗingisa ƙasar a hankali ta nufi hanyar fita, kallon ta ya yi ya juya ya koma ciki. Tana fitowa sai ga su Amira sun iso yau ba muso ta shiga motar saboda yadda ƙafarta ke mata zugi, sunkuyar da kai ta yi ta ce “Good morning Daddy.” Lumshe ido ya yi bai amsa gaisuwar ba sai ce mata ya yi “Daga yau na hana daddy ɗin nan ki kira ni da kowanni suna na masoya.” Turo baki gaba ta yi ta ce “Yo to ba mahaifin ƙawata ba ne kai meye a ciki dan na ce maka daddy? Thank you na ga waya Allah ya ƙara arziƙi.” Wani Sanyin daɗi ne ya ratsa zuciyar Sultan yadda ta sakar masa da murmushi mai ƙayatarwa ya san wayar ta birge ta, ajiyar zuciya sauke ya ce “Ai ni da ke babu godiya a tsakanin mu tun nine mijinki ma gobe in sha Allahu. Amma ba ki ga saƙona ba?” Kawar da kai ta yi gefe tana kumbura baki ta ce “Na gani mana.” “To amma me ya sa ba ki ba ni amsa ba?” Hararar shi ta yi tana tsuke ɗan ƙaramin bakinta da ya sha man lips sai sheƙi yake, lumshe ido ya yi yana ciza lip ɗin sa na ƙasa, gabaɗaya yarinyar tana rikitar da tunaninsa ya ƙagara ta ba shi amsa ko zai samu Mom da magana a yi auren nan ko hankalinsa ya kwanta ya samu nutsuwa. Ba ta ko kalle shi ba sai marmatsa ƙafa da take saboda zafin takalmi da zafin ciwo sun haɗe mata, ganin tana yatsina fuska sai ya kalli ƙasa ya ga yadda take yi da kafar, cike da kulawa ya kalle ta ya ce “My wife ko ciwo ƙafar take miki ne?” Girgiza kai ta yi tana kumbura baki ba ta yi magana ba, ganin hakan ya sa ya ɗago ƙafar ya cire takalmin ai kuwa ya ga yadda ƙafar ta ɗauki kumburi, a ruɗe ya ƙara ɗagowa ta dora ta a kan cinyarsa yana kallon ta da kyau. Runtse ido ta yi da ya dan danna ƙafar ta yarfa hannu ta ce “Please ka bari akwai zafi.” Bakinsa ya kai kan ƙafar ya dinga hura mata isa, shuru ta yi tana jin saukar iskar bakinsa sai ta ji zafin ya ragu hakan ya sa ta saki jiki ta jingina kanta da jikin kofar motar tana kallon shi. “Sannu my wife ya aka yi kika ji ciwo har ƙafar ta fara kumbura ba ki je asibiti an duba miki ba?” A shagwaɓe ta kalle shi idanuwanta sun cika taf da ruwa, gira ɗaya ya dage mata yana mata wani irin kallo mai wiyar fassarawa, yana tsaka da hura mata suka iso makaranrar ta soma ƙoƙarin janye ƙafarta amma ya riƙe ya hana ta motsi. “Kinga mu je asibiti a duba miki ƙafar nan kar ciwon ya miki yawa.” Maƙale kafaɗa ta yi ta ce “Zai daina ai sake mini ƙafa kar in makara irin na jiya da ka hana ni fita.” Ba dan ya so ba ya sake mata ƙafar ta buɗe motar za ta fita ta juyo a hankali cikin Sanyin murya ta ce “Thank you.” Jinjina mata kai ya yi yana bin ta da kallo kamar kar ya bar ta ta fita, tana fitowa Amira ta iso suka nufi ciki inda suka samu Arma da Sadiya suna jiran su. Gaisawa suka yi Arma ya ce “Wallahi yau wani Monsieur ne mai zafi aka kawo shi zai fara shiga classé ɗin mu, dan haka ku zo mu shiga daga ciki.” Tashi suka yi suka shige ciki suka ci gaba da tattaunawa a kan darasin da zai musu har ya zo. Suna gaf da tashi ƙafar Andizo ta ƙara kumbura take zazzaɓi ya rufe ta, da kyar ta lallaɓa suka fito Amira na riƙe da ita suka samu waje suka zauna. Number Sultan ta kira ringing ɗaya a na biyu ya ɗauka, ko hello bai ƙarasa faɗa ba Amira ta taru numfashinsa ta ce “Uncle akwai matsala fa don Allah ka yi maza ka zo jikin Khadija ya rikice zazzaɓi mai ƙarfi ya rufe ta.” Daga can ɓangaren Sultan da yake yin Sallama da Mama zai wuce airport zai koma Nigeria ya yi saurin faɗin “Subhanallahi! Gani nan zuwa yanzu karki kuskura ku shiga motar haya.” To Amira ta ce sannan ya kashe Mama ta dube shi ta ce “Lafiya dai yaron?” Cikin damuwa ya ce “Wai Khadijata ce zazzaɓi mai ƙarfi ya rufe ta suna can a makaranta da Amira, na fasa tafiya zan je na kai ta asibiti zuwa gobe in na ga jikin da sauƙi sai na tafi.” “A to in kuwa haka ne bari mu tafi tare.” Mota ya buɗe mata yaransa biyu da ya zo da su suka iso za su shiga ya ɗaga musu hannu ya ce “Ba sai kun biyo mu ba idan ina buƙatar ku zan kira ku.” To suka ce suna matsawa daga kusan motar ya shiga mazaunin direba ya ja suka bar gidan.. Andizo sai rawar sanyi take Amira ta cire hijabinta ta rufa mata ita kuma ta warware ɗankwalin kanta ta yafa sai sannu take jera mata, suna nan zaune sai ga su Sultan sun iso, yana gana packing ya fito da sauri ya kamo ta zai ɗauke ta Mama ta ce “Ka bari mu shigar da ita ni da Amira.” Ba dan ya so ba ya sakar musu ita suka kama ta yana biye da su har bakin mota, buɗe musu ya yi suka saka ta a baya suka shiga sai asibiti.. Kasancewar Sultan na da aboki babban likita hakan ya sa ya kira shi, yana ɗauka ya ce ga shi nan zai zo da mara lafiya ya amsa da to. Suna isa aka amshe ta suka yi ciki da ita, tsaye ya yi yana kallon kofar sai da Mama ta mishi magana sannan ya iya zama. Amira ta kira Hassana ta sanar mata Andizo ba lafiya sun asibiti, a ruɗe Hassana ta ce “Inna lillahi! Gamu nan a wani asibiti kuke?” Kwatance ta yi mata sannan ta kashe kiran. Suna zaune sai ga su Mamma sun iso asibitin hankali tashe, tambayar Amira Hassana ke yi meye ya samu Andizo ta ce zazzaɓi ne mai ƙarfi.. Ƙofar aka buɗe likitan ya iso gaban su, saurin tashi Sultan ya yi ya ce “Friend me ke damun ta ne bayan zazzaɓin?” Murmushi ya yi ya ce “Ka, ga ka kwantar da hankalinka iya zazzaɓi ne sai kuma da alama tana yawan yin tunani zuciyarta ta fara kumbura, ya kamata ku kula kar ciwon zuciya ya kama ta. Yanzu mu je na rubuta maka maganin da za take sha amma dai kar ake barin ta tana zurfafa tunani.” Salati suka ɗauka Ahmad ya yi shuru yana jin maganar likita wani iri, “Zuciyarta ta fara kumbura?” Ya nanata maganar yana bin bayan Sultan, a hanya suka haɗu zai wuce amsar magani da aka rubuta, hannu ya miƙa mishi ya ce “Ba ni takardar ni zan sayo maganin da kuɗi na mun gode ma da ɗawainiyar kawo ta asibiti da kuka yi Allah y bar zumunci.” Ya faɗa yana haɗe rai. Kallon ban gane ba Sultan ya mishi sai kuma ya ja tsaki ya ce “Kema fa Ahmad mugun ɗan rainin hankali ne, ya ina son na kyautata wa masoyiyata kana ƙoƙarin hana ni matsa ka ba ni guri naje na sayo maganin.” Ya faɗa yana raɓawa gefen shi zai wuce Ahmad ya yi saurin janyo shi ya dawo baya, a kausashe ya ce “Ka ga wasa a idanuna? Yarinyar nan ɗiyar ruƙo ce a wajen mu amana aka ba mu shi ne har kake nema ka faɗa mini maganar banza? Babu wanda ya kamata ya kula da ita fa ce ni da nake a matsayin yayanta na kusa.” Wani irin kallo Sultan ya mini ya buge hannun Ahmad da ke kan kafadarsa ya wuce fuu, kwafa ya yi ya juya shima ya wuce. Bayan ya sayo maganin ya koma office ɗin doctor ya miƙa mishi ya amsa suka fito tare, suna isowa ya shige ciki ya ce kar su biyo shi ba su gama ba. Allah-Allah Ahmad yake a ba su damar ganin Andizo ya shiga ya nuna wa Sultan ƙarfin ikon da yake da shi a kan ta, sai ciza lip yake yana jinjina kai gabaɗaya kishi ya rufe mishi ido har ya fara ganin lefin Andizo da ta yarda su Sultan suka kawo ta asibiti, “Wa ya sani ba ko shi ya ɗauko ta a jikinsa da za su saka ta a mota tun da Amira ta ce kasa tafiya ta yi?” Ya faɗa can ƙasan maƙoshi yana jin wani irin ɗaci ya mamaye masa maƙoshi. Duk abin da yake Sultan na ankare da shi, murmushi ya yi bin shi da kallo. Bayan ya fito aka ba su damar ganin ta duk suka shiga b kamar Ahmad ma shi ne a gaba-gaba ya ƙwaryar sallah, a zaune suka same ta a rufe ido kamar mai bacci duk suka jeru suna mata sannu. A hankali ta buɗe ido ta ga Ahmad a daf da ita yana mata sannu, kawar da kai ta yi tana amsawa ta juyo ɗayan gefen suka kalli juna ita da Sultan murmushi ta mishi tana kallon Amira da ke kusa da shi tana mata sannu, a hankali ta ce “Na gode sosai ƙawata Allah ya saka da alheri, na gode daddyn Farrah.” Zama ya yi a kujerar da ke wajen ya ce “Ni fa godiyar nan taki ta fa isheni Khadija, ke ba dama a miki abu sai kin yi ta godiya? Ai in na taimake ki kamar kaina na taimaka tun ke ɗin tawace ni kaɗai.” Shuru ta yi ba ta ce mishi komai saboda kalaman nasa sun sa ta ji kunya ga kuma su Mamma a wajen duk da tasan ba ji mai ya faɗa ba, Ahmad na jin su ya cika ya yi fam yana jan numfashi da kyar, a fusace ya fita suka bi shi da kallo. Tare suka dawo da likita ya miƙa wa Sultan takarda ya ce “Idan ruwan da aka sa mata ya ƙare za ku iya tafiya gida ga takardar sallama nan.” Ya juya zai tafi Sultan ya miƙe ya ce “To friend my je mu tattauna kafin mu tafi.” Fita suka yi a tare Amira da Mama suka musu sallama suka tafi Hajiya na ta musu godiya, sai da su Mamma suka fito waje ya ga daga shi sai ita ya hayo kan gadon ya zauna a can gefe ya tsare ta da idanu, kawar da kai ta yi ta ce “Kai mutum ba shi da lafiya ma sai ka nuna mishi halin naka?” “E haka za ki ce mana dama tun da har wani ƙato ya ɗauko ki ya kawo ki asibiti. Zan yi maganin ku daga ke har shi.” Banza ta mishi ba ta ce komai ba har Hajiya ta, shigo da likita aka cire mata allurar ƙarin ruwa ta sauko da ita daga kan gadon, a hankali take takawa sosai ta ji daɗin ƙafar ganin kumburin ya huce zafin ma ba sosai ba take ji. A harabar asibitin suka isko Sultan ya tari Hajiya ya ce “Hajiya zo mu je ku shiga motata wannan motar ta muku kaɗan.” Fuska a sake ta ce “To Sultan ai da ka bari ma mun tafi a haka ɗawainiyar ta yi yawa, amma to ina su mamar taka?” Shafa sajansa ya yi ya ce “Ai sun tafi gida wata motar ta zo ta ɗauke su suka tafi.” Motar ya buɗe musu suka shiga su kuma su Mamma suka shiga ta Ahmad suka bar asibitin. Sun fara tafiya Andizo ta ɗago kai ta ce “Hajiya ba ki sanar da ni ba wannan maganar, kinga nan wancan mugun ba ya nan ki ba ni labarin kafin mu je gida.” “Haba Khadija ke da kike fama da rashin lafiya ina ke ina son jin labari?” “Ni kam dai ina so ki faɗa mini.” Sultan ma ya kasa kunne yana jin wani labari ne ta kafe sai an ba ta shi daga tasowar ta daga gadon asibiti? “Kamar yadda na fara faɗa miki Alyasa'a babban ɗa a wajen Musalle, da kuma ɗan autana Ziya'ulhaƙ da mahaifin Zulai da ƙanenta. Sun kasance dukkan su sojoji ne mahaifin Zulai shi ne general a wajen aikin su Alyasa'a kuma mataimakinsa, Ziya'ulhaƙ da ƙanen Zulai su ne kasa da su, sun kasance sojoji ƙasa da ƙasa ne. A wannan rana ta asabar aka tura su can jahar Tahoua cikin wani daji da 'yan ta'adda suka addabi wajen, haka muka yi sallama da su suka tafi muna ta musu addu'a, kamar Alyasa'a yana ganin wani abu sai sun shiga mota sai ya dawo ya rungume ni ya rungume uwarsa Zulai ya ce zai yi kewar mu, sai da ya yi haka ya fi sau biyar sannan na ɗaka mishi duka na ce ya tafi jiran shi fa suke sannan ya shiga mota. Haka muak dinga ɗaga musu hannu muka dawo ciki, a wannan lokacin Salim yana makaranta sai da ya kira aka ce mishi su tafi kamar yaro ƙarami ya yi ta kuka sai da na rarrashe shi ya yi shuru.. Bayan sun sauka muka yi waya da su wadda ita ce ta farko kuma ta ƙarshe..” _Maman Nusaiba ce_ [6/27, 11:38 PM] Ummu Amjad: ADZ 41 Saurin kallon ta Andizo ta yi Sultan kuma ya ja birki a ƙofar wani babba shopping mall mai kyau, Hajiya ta dago hawayen da suka zubo mata ta dubi Sultan ta ce “Ya kuma ka tsaya?” Juyowa ya yi yana murmushi sannan ya ce “Hajiya ki zauna za mu shiga na sayo mata ɗan kayan marmari irin na marassa lafiya ko ta warware da wuri, kinga kuma likita ya ce ake kula da ita kar a bari ta shiga damuwa, to nasan tana son irin kayan wajen nan shi ya sa na tsaya.” Turo baki gaba ta yi tana yin fuskar tausayi jin abin da ya faɗa, ita sam ba ta son jerawa da shi amma ganin Hajiya na kallon ta ya sa ta buɗe motar ta fita. Hannunta zai kama ta maƙale kafaɗa ta ce “Don Allah ka bari ni ba na son kake kama hannuna tun da ni ba muharramarka ba ce.” Murmushi ya yi kamar bai ji mai ta faɗa ba sai da ya kai hannu ya ja kuncinta sannan suka jera suka nufi ciki. Suna shiga wasu daga cikin masu sayayya suka dinga kallon su suna magana ƙasa-ƙasa, ƙara ɗaure fuska ta yi domin ita ta tsani kallo ya yi yawa duk sai ta daburce. Wajen kayan marmari ya ja ta suka ya dinga ɗiba mata su apple ayaba da sauransu, ta yi tsaye tana kallon ikon Allah ganin yadda yake kwasar kayan kamar ba kuɗi zai ba da ba, gaba ya yi ta bi bayan shi suka iso wajen su chocolate ya kalle ta, saurin sunkuyar da kai ta yi dan kar ya ga abin da take kallo ya ɗauko mata, murmushi ya sakar mata ya ɗauko mata duk abin da ya san tana so sannan suka wuce wajen biyan kuɗi. Yana biya suka sa mishi a leda aka dauka ya nuna musu motar da za su saka, ɗago kai ta yi za ta mishi magana sai ga wata matashiyar budurwa ta iso wajen su, farin cikin ne ya bayyana kan fuskar budurwar ta dafe ƙirji ta ce “Mr J! Kai nake gani ko dai mafarki nake?” Annurin fuskarsa ta ga ya ɗauke suka haɗa ido sai ya saki fuska ya kalli budurwar yana murmushi ya ce “E ni ne dai.” Kamar za ta faɗa jikinsa ta matso kusa da shi sosai ta ce “Don Allah ka ba ni number ka ni ɗin nan da kake gani babbar masoyiyarka ce ta haƙiƙa, in ba damuwa ka ba ni number ka sai mu yi magana ka taimaka.” Ta faɗa kamar za ta yi kuka, kallon Andizo ya yi ya ga tana kallon budurwar da wani irin yanayi, murmushi ta yi yana jinjina kai ya ce “Kawo wayar na sa miki number.” Miƙa mishi ta yi zai karɓa ta yi saurin amsa ta daddana ta sa mata number ta miƙa mata, da kallo budurwar ta bi Andizo sai kuma ta amsa tana faɗin “Merci beaucoup, amma ke ƴarsa ce ko?” Ko kallon ta ba ta yi ba dan mugun haushin budurwar ta ji, Sultan ya ji daɗi ya rufe shi ganin Andizo ta nuna kishi a kanshi, gyaran murya ya yi ganin budurwar ba ta tafi ba ya ce “To sai an jima mu za mu wuce..” “Don Allah Mr J ƴarka ce Ko ƙanwarka?” Budurwar ta faɗa domin ita tuni ta tabbatar wa kanta tsuntsunta ya kama tarko tun da har ta samu number Sultan cikin ruwan sanyi, abin da ta ɗauki sama da shekara biyu tana neman wanda zai haɗa ta da shi amma aka yi ta damfarar ta ƙarshe dai ta haƙura, sai yau kamar daga sama ta ganshi. “A a ba 'yata ba ce she is my favourite wife.” Zaro ido ta yi sai kuma ta wayance ta ce “Ayya yi haƙuri madam ai ban sani ba mu fans ɗin mijinki ne, ni suna na Halisa ɗiyar gwamnan Niamey.” Kallon ta ya yi ya jinjina kai ya ce “Wow ashe ku ke riƙe da garin? To na gode sosai da ƙauna sai an jima mun wuce.” Har sun juya ta kira sunansa ya juyo ta ƙaraso ta ce “Please one minute zan ba ka wani abu kar ka ce ba ka so.” Ta faɗa tana ciro wani babban turare na maza mai shegen ƙamshi sabon fitowa, miƙa mishi ta yi tana murmushi ta ce “Ga kyauta ta a matsayina na fans Allah ya sa ban ɓata ran madam ba.” Amsa ya yi ya mata godiya Andizo ta kalle ta ce “Mun gode Halisa sai an jima.” Tafiya suka yi suka bar ta a nan tsaye tana sakin murmushi kamar wata sakarya. Wasu 'yanmata biyu ne suka iso wajen da take tsaye, ɗayar ta ce “Wai ke ina kika shiga muke ta duba ki?” Lumshe ido ta yi ta ce “Yau dai na ga abin ƙauna ta.” Kallon mahaukaciya suka mata ɗaya ta ce “Haba dai Halisa ai ba abu ba ne mai sauƙi ki ga Mr J a nan garin, da a Nigeria ne ba zan miki gardama ba in ya zo hutu za ki iya ganin shi a wani wajen.” “Wallahi da gaske nake Bishira ku yarda da magana ta kunga har number shi na amsa, sannan wannan turaren da na saya dama dan shi na saya idan Allah ya haɗa ni da shi na ba shi sai ga shi kamar daga sama na haɗu da su a nan.” Hararar ta Bishira ta yi ta ce “To in dai da gaske ne mu fita ki nuna mana shi.” Da hanzari ta ce “Ku yo sauri ga motarsu can ana sa musu kaya.” Suna fita suka ganshi tsaye shi da Andizo ana sa kayan da suka saya, kallon juna suka yi Bishira ta ce “Kan uba! Alƙur'an shi ne bari mu je mu gaisa.” Ta faɗa tana shirin tafiya Halisa ta damƙo hannunta ta ce “Kar ki je tare fa suke da waccan yarinyar wai ya ce mini matarsa ce.” Kallon Andizo Bishira take tana tafa hannu, sai kuma ta ce “Ke Wallahi faɗi ne yake ba matarsa ba ce ko kin manta a binciken da muka sa aka mana an ce ba shi da aure amma yana da matashiyar budurwa? Ko kin manta uwar ɗiyarsa rasuwa ta yi?” Dafa ƙirji Halisa ta yi ta ce “Wash Wallahi sai yanzu naji zuciyata ta yi sanyi, yanzu haka ji nake kamar na faɗi saboda ganin waccan ƙaramar yarinyar a zaman matar masoyina.” dariya suka yi suna tafawa har motar su Andizo ta bar wajen sannan suma suka tafi.. Bayan sun kama hanya Andizo ta sauke ajiyar zuciya ta ce “Hajiya ki ci gaba da ba ni labarin dama ban bi shi ba sai zafi nake ji na haɗa zufa..” Ta faɗa tana murguda baki, shi kuwa yana kallon ta ta madubi ya yi murmushi. Gyara zama Hajiya ta yi ta ce “Tun daga wannan rana ba mu sake yin waya da su ba har aka shafe sati ɗaya sai abin ya fara damun mu, Zulai ta ƙara kiran babanta amma sai a ce mata wayar a kashe dole ta haƙura muka zuba wa sarautar Allah ido, sai da aka cika kwana goma sai ga Salim ya dawo daga Maraɗi wajen karatu, yadda muka ga ya shigo abin sai ya ba mu mamaki domin da shigowar shi da yin kukan sa duka lokaci ɗaya ne. Hankali a tashe na tarbe shi ina tambayar shi lafiya ko bai samu jarabawar ba ne shi ya sa yake kuka? Nan yake sanar da mu baƙin labari, “Hajiya su yaya ne aka ce za a kawo su gida suna hanya, wai sun samu raunika su duka shi ya sa za su dawo gida.” Salati muka dinga yi Zulai har ta fara kuka muka zauna muna jiran mu ji sun kira sun ce an kai su asibiti,amma har yamma ba a kawo su ba har sai bayan magariba aka kira Salim suka sanar da shi ga su nan shigowa unguwarmu. Tun kafin ma su iso ƙaran jiniyar motocinsu ta sanar da mu zuwan su muka fito harabar gidan duk muka yi tsirko-tsirko, ko 'yan unguwar sai da suka tabbatar ba lafiya ba duk da sun saba jin jiniyar motar su Alyasa'a idan za su fita, amma na wannan karon sai ya ba, su mamaki yara suka fito suka biyo motar hr cikin gida. Wasu daga cikin sojoji suka fito aka buɗe mota suka kama suja fito da ɗaya, yadda muka ga an rufe su tuni jikina ya ɗauki rawa muka ƙarasa wajen su, hannuna na rawa na buɗe wanda yake kusa da ni, fuskar Alyasa'a na gani kamar yana murmushi gabaɗaya gefen kansa ya yi raga-raga an rufe wajen amma duk da haka jini bai daina zuba ba, tun daga nan naji kamar zan kurma ihu saboda na tabbatar Alyasa'a ya riga da ya mutu na rufe na yi gaba na buɗe ta kusa da shi. Ziya'ulhaƙ autana shi na gani cikin jini fuskarsa ta ɓaci da jini, na rushe da kuka ina kiran sunansa ina jijjiga shi amma ina rai ya yi halinsa, kamar ana tura ni na yi gaba ma buɗe na kusa da shi na ga ƙanen Zulai ne shima babu kyan gani na buɗe ta ƙarshe in da baban Zulai ne, ranar a gidan babu wanda bai suma ba saboda tashin hankalin da muka shiga musamman ma Zulai sai da aka ɗaure ta kamar mahaukaciya ta koma sannan aka ɗauke su aka shiga da su ciki, Musalle da Saddiƙu da kyar aka rarrashe su suka wanki Alyasa'a da Ziya'ulhaƙ da ƙanen Zulai da babanta, ranar mun ga tashin hankali wanda ba mu taɓa gani ba, domin Salim da ya yi arba da gawar yayansa da ƙanen mahaifinsa tun da ya suma har dare bai farka ba, haka sallace su aka kai su gidansu na gaskiya, su kansu mutanen unguwar nan sun sha kuka suna ta faɗin alkhairin Alyasa'a, sai bayan kwana biyu Salim ya farfaɗo nan ma wai tashin hankali muka ƙara shiga, ya ƙi cin abincin ya ƙi shan ruwa sai cewa yake shi dai a kai shi wajen yayansa ba mutuwa ya yi ba, da kyar Saddiƙu ya rarrashe shi ya ɗauke shi daga gidan ya kai shi can wai waje da ban saboda yadda yake sa mutane kuka da kalamansa, Zulai si ta dawo kamar kurma sai sai an, kwantar da ta sai an tayar ba cin abinci da kyar ake samu ta ci loma ɗaya shima sai ƙanwata ta yi da gaske take yarda ta amsa, ƙarshe ma kamar ciwon hauka ya so samun ta ta dinga surutai tana faɗin “Yarona da ƙanena da babana Wallahi ba su mutu ba dan ba ku sansu ne y sa kuka binne su da ransu.” Surutai dai makamantan haka ta dinga yi, sai da muka sa malamai suka dinga mata addu'ar dangana da kyar ta taimakon Allah muka samu ta dawo haiyacinta. Har aka yi shekara da mutuwar su Alyasa'a amma kullum sai Zulai ta yi kuka da zarar ta fito palo ta ga photonsa shi da Salim, hakan ya sa Musalle ya cire photon har na ɗakinta, duk wani abu da ya, san zai tayar mata da hankali game da Alyasa'a duk ya ɗauke ya ɓoye, muna ji ta dinga nema muka yi shuru har ta gaji ta haƙura. Da Salim ya gama karatu ya ce shi aikin soja yake so yana son ya kashe waɗannan 'yan dajin da suka kashe mishi ahali, Zulai ta yi rantsuwa da girman Allah ta ce in dai Salim ya ce sai ya yi soja to sai dai ya rama mata nononta da ta shayar da shi kuma babu si babu ita, hakan ya sa hankalinsa ya tashi ya ba ta haƙuri ya aje maganar ba dan ya haƙura ba. Bayan shekara ya sake tayar da maganar yana lallaɓa Zulai ta barshi ya yi aikin soja dan ya ɗauki fansar abin da aka yi wa su Alyasa'a nan ma taƙi, sai da ya haɗa ta da mamanta ta zo har gida ta mata nasiha ta nuna mata suma din kawai kwanansu ne ya ƙare shi ya sa suka mutu ta rabu da shi ya yi aikin tun da yana so, a ranar ƙin amincewa ta yi sai da mamanta ta yi zuwa uku tana rarrashinta sannan ta haƙura ta bar Salim ya yi aiki, ranar ya yi farin ciki ya zo ya mata godiya sai kawai ta sa kuka tana faɗin “Wato kai dai ka dage sai ka yi aikin sojan nan Salim ko? Kaima so kake a kashe ka kamar yadda aka kashe su Baba ? Ni dai Allah ya gani hankalina ya kasa kwanciya da aikin nan naka Salim, amma ba komai Allah ya dafa maka ya sa ka yi nasara a kan abin da kake son yi.” Ya ji daɗi sosai ya mata godiya, bayan kwana biyu suka tafi tirenin ɗin aikin soja. Kullum sai ya kira a ƙalla sau biyar yana faɗa mana duk abin da aka musu, amma da zarar sun shiga aiki ba a samun shi, da ya zo shekarar ƙarshe in ba hai ya kira mu ba ba a iya samun shi Zulai ta so ta ɗaga hankali sai da Ahmad ya mata bayani sannan ta yi shuru. Haka ya dawo gida cike da tarin nasara an ɗauke shi aikin soja, muka taya shi murna ya kama aiki cikin nasara da sanin makamar aiki. Shekarar shi biyu da fara aiki aka aika su inda su Alyasa'a suka je ba su dawo a raye ba ranar Zulai ta tashi hankali ta ce ba zai je ba sam, da kyar aka rarrashe ta ya tafi. Sanin halin da ya baro ta da ya sauka ya kira ta ya ce ta mishi addu'a za su shiga daji yanzu daga nan ma'aikatar sojoji, sosai muka mishi addu'a sannan ya kashe. Bayan kwana biyu sai ganin shi muka yi ya dawo Zulai ta yi murna sosai ganin ɗanta ya dawo a raye, sai washegari ya sanar da mu sun yi nasarar kashe duk yan ta'addar da ke cikin dajin da suka addabi ƙauyukan yankin, mun ji daɗi sosai inda daga wannan tafiyar ne aka mishi ƙarin matsayi, wannan shi ne abin da ya faru.” Ta faɗa tana kallon Khadija, hawaye ta gani suna ta zarya kan fuskarta ta ce “Nasan dole ki yi kuka Khadija game da wannan labarin.” Ajiyar zuciya ta sauke ta ce “Gaskiya na tausaya muku musamman Mamma mutuwar mutum uku a lokaci ɗaya, shi ya sa ashe ta dinga kuka da ta ga Salim an nade mishi jiki da bandeji ba ta sani ashe shima tafiyar zai yi kamar su.” Ta ɗora kanta a kan kafaɗar Hajiya tana tuna shi.. Shi kanshi Sultan duk dauriyar shi sai da hawaye suka zubo mishi, irin wannan mutuwar tsayawa a rai gareta, hon ya yi aka buɗe mishi get ya shiga ciki. Suna fita Hajiya ta sa Maigadi ya ɗauko kayan su kuma suka nufi ciki, kiran sunanta ya yi sai ta tsaya taƙi juyowa, ganin haka sai ya girgiza kai ya iso inda take. Turaren da Halisa ta ba shi ya miƙa mata ya ce “Ki bai wa Ahmad wannan turaren ni ba irin wanda nake fesawa ba ne.” Ɗago jajan idanuwanta ta yi ta zabga mishi harara ta ce “Ba zan kai, ba kai ka ba shi mana ba abokinka ba ne? Dan naje ya ƙara yi min muguntar da ya saba.” “Ba sai kin je inda yake ba ki ba wa Hajiya sai ta ba shi, yanzu ni gobe jirgin safe zan bi na tafi Nigeria don Allah ki kula da kanki karki ƙara yin tunani mai zurfi, sannan kike cin abinci kinga yadda kika rame wuni ɗayan nan? Zan ke kiran ki amma ki kula idan na samu lokaci zan dawo lokacin da zai, zama na ƙarshe dan zan zo, da Mom da kuma kawuna a yi maganar aurenmu, yanzun ma dan kawai kin ƙi ba ni amsa ne da kafin na koma za a yi komai a gama na ɗauke ki mu tafi na kula da ke. Bye bye sai wani lokacin ko?” Sunkuyar da kai ta yi ta amshi turaren ta ce “Na gode idan ka je ka gaishe mini da Mom da Farrah.” Jinjina kai ya yi ya ce “Na manta kawo hannunki kuma ki rufe idanuwanki.” Ji ta yi ba za ta iya mishi muso ba a wannan karan ta miƙa mishi hannun ta runtse ido tana addu'ar kar wani ya gansu, yatsarta ta kusan babbar ta ji a sa mata wani abu ta yi saurin buɗe ido, zobe ce sabuwa dal a cikin ƴar akwatin ta ruwan gold sai sheƙi take, baki sake take kallon shi sai kuma ta kalli zoben har ba ta san lokacin da ta saki murmushi ba sai da ta ji karan camera ya ɗauke ta a photo, ƴar dariya ta yi ta ce “Thank you so much zan wuce ina jin jiri.” Hanya ya ba ta yana bin da kallo har ta shige ciki sannan ya koma motarsa ya wuce. Duk abin da suke a kan idanun Ahmad yana ganin su daga tagar dakinsa kwafa ya yi ganin ta shigo shima sai ya fita daga ɗakin ya yo palo.. Tana miƙa wa Hajiya turaren da Sultan ya ba ta ya iso ya tsaya a kanta ƙerere, kallon shi ta yi ba ta ce mishi komai dan ta lura sam ba shi da tausayi, a wannan halin da take ciki ma sai ya ƙuntata mata. Dogon numfashi ta ja ta miƙe tana yatsina fuska ta ce “Mamma zan je na kwanta idan Umma ta kira ku ce mata ina gaishe su an jima zan kira ta na ga su Khadija.” Ta faɗa tana yin gaba Mamma ta amsa da cewa “To kar dai ki kwanta da ba ki son cin abinci in ba ki da lafiya yanzu zan sa a kawo miki abinci, sannan ai kin ji me Sultan ya faɗa miki bayanin likita dai ko?” Gyara kai ta yi tana runtse ido har yanzu kafar zafi take mata ta yi gaba, da kallo ya bi ta sai kuma ya ɗauki ledar maganinta da ta manta ya ce “Bari na kai mata kinga har ta fara halin nata, gara na je na sake jadadda mata shan magani a kan lokaci kar ta yi wannan sakarcin nta da ta saba.” Ba wanda ya ce mishi kalzil har ya bar palon domin Hajiya ta ce kar wanda ya sake shiga sabgar su wata ƙila ta hakan sai Allah ya sa wa Khadija son Ahmad, shi ya sa kowa ya bi shi da kallo. A hanya suka haɗu ya ce “Ina za ki je?” “Maganin ne fa na manta zan je na ɗauko.” Ta faɗa tana kallon maganin da ke hannunsa. “Mu je ciki ki sha na yamma kuma ban da sakaci dan na san halinki.” Turo baki ta yi kamar za ta yi kuka ta ce “Yaya Ahmad maganin ne akwai ɗaci fa.” Murmushi ya sakar mata wanda rabon da ta ga ya mata irin wannan murmushi har ta manta, hanya ya nuna mata ta juya ya bi bayan ta har ɗaki, zama ta yi tana maida numfashi ya kalle ta yana dariya ya ce “Raguwa kawai wannan ƴar tafiyar da kika yi ai ne har kike huci kamar wata ƙatuwar mace wadda take tashi da kyar zama da kyar.” Sunkuyar da kai ta yi ta ce “To ai ƙafata ce ta riƙe ciwon har cikin ƙwaƙwalwarta nake ji, ba ni maganin na sha zan kwanta ko ciwon ya ragu.” Duk da ya ji tausayin ta amma bai nuna ba maganin kawai ya ba ta ya dawo kitchen ya ɗibi ruwa ya kawo mata ta sha maganin, sai da ta kwanta sannan ta ce “Merci.” Tun da yake da ita bai taɓa mata abun arziƙi ta ce mishi ta gode ba sai abin ya ɗan ba shi mamaki, amma tuna shirinsa a kanta sai ya yi murmushi ya kai hannu ya shafa kumatunta duka biyun ya ce “Meye na godiya kuma Khadija? Ni ba na son muke yin faɗa da ke ya kamata mu shirya muke girmama juna.” Ɗago kai ta yi ta kalle shi ya kanne mata ido ɗaya ta kumbura baki, sai da ya sake kiran sunanta sannan ta ce “To ai dama kaine kake zalin ta ta ni me nake maka wanda yake cutar da kai?” Jim abin da ta faɗa sai ya samu gefen gadon ya zauna ya ce “Khadija kina so mu daina faɗa?” Kai ta gyaɗa mishi ya gyara zama ya ce “To inda kina so mu fasa faɗa sai dai ki yi wani abu ɗaya wanda zai kashe duk wata rigimar da ke tsakani na da ke.” Kallon shi ta yi sai kuma ta ce “In dai za ka daina mini mugunta zan yi matuƙar bai saɓa wa addini da al'adata ba.” Ta faɗa a sanyaye kallon shi domin ta gaji da cutar da ita da yake yi a kullum kamar jikan Fir'auna. Kallon ta ya yi sai kuma ya kalli gefe ya yi murmushin da shi kaɗai ya bar wa kansa sani sannan ya ce “Ina so ki daina kula Sultan idan ya zo zai ɗauke ki, ke gabaɗaya ma ko magana ba na so ta shiga tsakanin ku dan bai cika sharruɗan mijin aure ba, musamman idan kika duba yadda mata suke bin shi yan iska rikakku ke har turawa kansu Sultan bai bari ba sheƙe ayarsu suke, kinga kuwa ai ba abin ki tsaya kina sauraron shi ba ne ni fa ba ni da tabbacin Sultan yana yin Sallah, kayan maye kuwa babu abin da ba ya sha me za ki yi da irin wannan namijin?” Zaro ido Andizo ta yi cike da al'ajabi ta ce “Dama har neman mata yake ashe? Ashe ɗan iska ne? Ni dai nasan yana shaye-shaye a gaban idona ya sha giya ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba, amma yanzu ya ce mini duk ya tuba yana Sallah ya rage shan kayan maye..” Haushi Ahmad ya ji a zuciyarsa da Sultan ya sanar da Andizo ya tuba, amma a fili sai ya daddage ya nuna mata sam bai daina ba ya ce kuma in ta yarda yana taɓa jikinta wata rana zai iya cutar ita ya mata faɗe, tsoro ya kama Andizo ta ce ta daina kula shi har abada. Murmushi ya yi ya ce “Yawwa ba na son wani ya cutar da ke kinga ke amana ce a wajen mu ki tayamu ruƙon amanar ki don Allah Khadija.” Kamar wata ƙadangaruwa ta gyaɗa mishi kai ta ce “To in sha Allah.” Ta faɗa tana kwanciya shi kuma ya fita ya bar ɗakin ransa fes tun ya samo lagon ta zai raba su cikin ruwan sanyi.. _Maman Nusaiba ce_ [6/30, 12:13 AM] Ummu Amjad: ADZ 42 Sai da ta tabbatar ya fita sannan ta tashi zaune ta tafka tagumi hannu biyu, tunani ta dinga yi yadda Sultan ya dinga kula da ita a wannan 'yan kwanakin, sannan tun da suke haɗuwa ba ta taɓa ganin alamar har yanzu yana shan kayan maye ba, ajiyar zuciya ta sauke ta kalli zoben da ya saka mata. Har ta kusa cire zuben sai kuma ta fasa amma sam hankalinta ya kasa kwanciya game da maganar da Ahmad ya faɗa a kan Sultan ɗin, girgiza kai ta yi ta ce “Zan tambayi Amira naji idan har na tabbatar bai daina ɗabi'ar da na sanshi da ita ba to zan yanke duk wata alaƙar da za ta haɗa ni da shi har abada, ba zan yarda ya cutar da ni ba.” Komawa ta yi ta kwanta tana ta saƙe-saƙe har bacci ya yi gaba da ita. Misalin ƙarfe 11:00am Ahmad ya sauka a ƙauyen su Andizo, ya samu kyakyawar tarba daga wajen Maigari da sauran jama'a, hatta ɗaliban da ya koyawa karatu sai da suka yi comba guda suka zo gaishe shi har da masu kawo mishi girki, hakan ya faranta mishi rai matuƙa ganin yadda yaran ke ƙaunar shi wasu ma daga cikin 'yan matan har an musu aure har da masu haihuwa, mamaki sosai ya sha ganin su Salame an musu aure har da yaronta jariri ɗan wata biyu, yana kallon ta ya miƙa hannu ya amshi yaron tsaf-tsaf da yaron sai ƙamshin mai jarirai yake. Addu'a ya yi wa yaron yana murmushi ya ce “Allah mai girma su Salma an zama Mama.” Dariya Salame ta yi tana rufe fuska ta ce “Monsieur ai har yanzu ban fasa makaranta ba ina yi, yanzu ma hutu muka samu na kwana goma shi ne na zo gida ziyara.” “A haba dai? To shi mijin naki yana ina?” Ya faɗa da mamaki kan fuskarsa. Nuna mishi ta yi ta ce “Shima karatun yake ai tare muke a can Niamey, akwai danginsu a can shi ne muke zaune da su, na so a ce na san gidanku da sai na kai muku ziyara to ban sani ba, har numéro ɗin Andizo na nema ban samu ba amma tun da ka zo don Allah ka taimaka ka ba ni numéro ta ina so na kai mata ziyara mu ga juna.” Jinjina kai Ahmad ya yi sosai Salame da mijinta suka birge shi, numéro Andizo ya ba ta sannan ya miƙa mata yaro ya sa hannu a aljihu ya ciro 'yan jika biyar guda huɗu ya miƙa mata ya ce “Ga shi a saya wa bèbè(Baby) madara.” A kunyace ta amsa ganin kuɗi mai ƴar dama ta mishi godiya ita da mijinta sannan suka tafi. Bayan kowa ya watse Ahmad ya huta ya ci abinci sannan ya nufi su Maigari domin gabatar da abin da ya kawo shi, sai da ya gama tsara duk maganar da zai fara tukun ya shiga cikin ɗakin Maigari. Murmushi Maigari ya yi yana nuna mishi wajen zama, zama ya yi ya gaishe da Maigari ya amsa yana faɗin “Ya su Musan da fatan duk kuna lafiya? Ya, wajen Hajiya ?” Sunkuyar da kai ya yi ya ce “Duk suna nan cikin ƙoshin lafiya sun ce a gaishe ka har Khadija.” “To ma sha Allah ina amsawa ita uwar masu gari yaushe za ta zo ne? Ta ce mini fa za ta zo mana ziyara kuma naji shuru.” Murmushi ya yi yaba rausayar da kai ya ce “E jarabawa garesu a makaranta shi ya sa ba ta zo ba, amma da an musu hutu ni da kaina zan kawo ta.” “Madalla.” Cewar Maigari, gyara zama ya yi sannan ya fara gabatar da maƙasudin zuwan nashi. “Maigari dama na zo ne a kan maganar da muka fara da kai ta waya kwanakin baya, to yanzu mun gama komai su Abba sa su zo a su nema mini auren Khadija.” “Kai madalla gaskiya naji daɗin wannan abu sosai, ai dama tun tuni na fara maka babu wata matsala in dai kun shirya a tsakanin ku za mu fi ku ma jin daɗin haɗin, yanzu abin da za a yi idan ka je gida ka sanar da s Musa sai su sa lokaci ko nan da sati ɗaya ne sai su zo a ɗaura aure, ba ba son a sa bikin ya yi nisa.” Daɗi sosai ya mamaye zuciyar Ahmad ya ce “In sha Allahu Maigari zan sanar da su, amma ya kamata a sa ko wata biyu ne saboda a yi gyare-gyare a gidan nawa, idan sun zo kawai ka sa wata biyu.” Jinjina kai Maigari ya yi ya ce an gama hakan za a yi tun da ya fi so a kai bikin nasu har nan da wata biyu,godiya sosai ya yi wa Maigari ya aje mishi kuɗi mai yawa sannan suka fito. Sai da ya shiga ciki suka gaisa da su Hajja suna ta wasa sai ga su Umar, gaisawa suka yi suna ta tambayar su Andizo da yaranta ya amsa musu da lafiya lau suke suna nan zuwa su kawo musu ziyara. Har bakin mota suka raka shi Giɗaɗo ya dubi Ahmad bayan su Umar sun wuce ya ce “Ungo ka sa mini numéro ɗin Surbajo ina son yin magana da ita.” Sai da ya kalli shi ya kuma kalli sabuwar wayar da yake miƙa mishi sannan ya ce “To shi kenan bari na sa maka.” Sa mishi numéro ɗin ya yi suka sallama ya tafi shima ya ja motarsa ya bar ƙauye cike da farin ciki. Yana komawa gida ya sanar da Abba maganar, sanin yanzu suna ganin tsakanin su har hira suke sai ya yi farin ciki da wannan maganar, ya ce in sha Allah za su je shi da Abie. Bayan kwana biyu suka shirya tsaf har da abokansu suka isa ƙauyen su Andizo in da suka samu kyakkyawar tarba, sai da suka huta suka ba da duk wani abu da ake yi na neman aure sannan aka sa bikin nan da wata bi kamar yadda shi mai gayya mai aiki ya ce, haka suka dawo gida cikin farin ciki suna jinjina halin dattijantaka irin ta Maigari akwai son jama'a. Da dare duk bayan sun gama cin abinci sun dawo palo Abba ya yi gyaran murya ya ce “Khadija su Maigari suna gaishe ki.” Murmushi ta yi tana wasa da 'yan yatsun ƙafarta sam yau ta kasa samun kwanciyar hankali tun da Ahmad ya sanar da ita jiya ya je neman izinin auren ta wajen su Maigari, da kyar ta yi bacci domin ita Allah ya ga zuciyarta babu soyayyar Ahmad a ciki duk da kuwa yanzu yana nuna mata soyayya da kulawa, idan kuma ta tuna da ta auri mazinaci dan shaye-shaye wanda ko sallah ba ya yi gara dai ta zauna da Ahmad ɗin shi nashi mai sauƙi ne ta san halayensa.. Taɓa ta da Hassana ta yi ya sa ta firgita tare da ɗago kai ta ce “Abba me ka ce?” Ƴar dariya ya yi ya ce “Tunanin me kik haka muna ta miki magana kin yi shuru?” “Ba komai Abba kawai dai ina son ganin su Khadija ne da su Hajja, ina so na tafi da su can idan mun samu hutu.” Murmushi Abba ya yi yana faɗin “To Allah ya kaimu su kuma yara zan sa Ahmad gobe ya tafi Diffa ya kawo miki su sai ku tafi tare, dama ina sanar da ke an sa ranar bikin ku ke da Ahmad wata biyu masu zuwa, da fatan babu wata matsala ko? Idan kuma akwai ki sanar da ni karki ɓoye mini komai ni ɗin tamkar mahaifinki nake karki duba sukunta kin ji, ko ba ki aure ɗana ba zan riƙe ki saboda mun zama dangin juna.” Sunkuyar da kai ta yi ƙasa nan da nan idanuwanta suka cika taf da ruwa ta yi jarumtar riƙe su, zuciyarta ta kasa aminta da maganar auren nan amma sai ta dinga jero addu'o'i ko za ta ji sauƙi, idan ta ce ba za ta auri Ahmad ba gani take tamkar ta yi wa su Abba butulci, ita kuma ba ta son a ce yau ita ce ta ɓata ran mutanen da suka gyara rayuwarta. Da kyar ta haɗiyi yawu sakamakon maƙoshinta da ya bushe, a hankali ta ce “To Abba Allah ya kaimu.” Tana faɗin haka ta tashi da sauri ta wuce ɗaki Ahmad ya bi bayan ta. Dariya Hassana ta yi suna tafawa ita da Hussaina ta ce “Kan bala'i! Tom and jerry za a zama miji da mata wai.” Dariya duk suka yi Mamma ta j dogon numfashi ta ce “Wallahi ni duk na fi ku ji farin cikin wannan haɗin, a baya da ta ƙi ina ta tunanin wacce yarinya Ahmad zai je ya kwaso mana? Ya halayenta suke? Amma yanzu Alhamdu Lillah naji daɗi matuƙa Wallahi.” Kowa murna yake ana ta sa albarka. Tana shiga shima yana shiga ya dafa kafaɗarta a sanyaye ya ce “Khadija mene ne yake damun ki? Kin san dai abin da likita ya ce ki daina yawan tunani ko? Nasan Yaya Salim kike tunawa kina ganin kamar kin ci amanar, ki kawar da wannan tunanin babu abin da ya yi kama da cin amana a auren da za mu yi, kinga zan ɗauke ke ki mu tafi Diffa can Abie ya samo mini aiki kinga za kike zuwa gidan Umma kullum ni zan ke kaiki ma.” Hawayen da take riƙewa ne suka samu damar zubowa, gaban ta ya dawo yana kallon ta da wani irin yanayi ya ce “Ki yi haƙuri kin ji na takura miki da surutu ko?” Girgiza kai ta yi ta tsayar da hawayen tana rarrashin zuciyarta ta ce “Ba komai kawai dai naji abin ne banbarakwai wai na auri ƙanen mijina.” “Ki daina irin wannan tunanin Khadija ba shi da amfani, ina so ki ba ni dama kafin lokacin auren mu zan saka ki cikin farin ciki ta yadda za ki yarda da cewa ba auren cin amana muka yi ba, kin ba ni dama daga yau?” Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ce “E na ba ka Yaya Ahmad.” Ta ƙarashe maganar tana sakin marayan kuka, hannunta ya janyo ya rungume ta abin da ba ta yi zato ba har za ta ture shi sai kuma ta kasa. Bubbuga bayanta ya dinga yi yana nusar da ita irin son da yake mata tun ma kafin Salim ya ce yana son ta, da yadda ya shiga damuwa bayan auren ta da Salim har ya samu ya kawar da komai ya ci gaba da harkar gaban shi. Sai da ya ga ta yi bacci sannan ya bar ɗakin ya ƙudiri aniyar zai faranta mata rai sosai ya ba ta kulawa kafin wata biyun su cika, ya watsar da duk wani musguna mata da ya ce zai yi idan ta shigo gidansa. Tun daga wannan lokacin Ahmad ya daina yi wa Andizo mugun ta sai nuna mata kulawa da soyayya, ita kuma ganin ya daina mata duk wani nau'in cuta sai ta saki jiki da shi suke wasa suna dariya da shi ya kaita makaranta idan sun tashi ya je ya dawo da ita gida, har wani sabon yawo ya tsiro musu da zarar maraice ya yi rana ta yi sanyi zai ɗauke ta su fita sha ice cream ya kai ta wuraren shaƙatawa sai sun kai wajen ƙarfe tara na dare sannan su dawo, su kansu su Hajiya abin ya birge su ganin mafaɗatan sun shirya kansu. Yau bayan sun taso daga makaranta ita da Amira suna da Sadiya da Arma, tsayawa suka yi dingin wata bishiya suka samu waje suka zauna. Arma da ya gaji ya tashi ya musu sallama ya tafi itama Sadiya ta tafi ya rage saura su biyu, kallon Amira ta yi ta ce “Amira ina so na sanar miki an sa bikinmu nan da wata biyu ni da Yaya Ahmad.” Da sauri Amira ta zabura tana kallon Andizo ta ce “Ban gane an sa ranar bikinku ke da Ahmad ba Khadija? Da don Allah va na son irin wannan wasan in ma da wasa kike ki fasa please ba na so.” Da mamaki Andizo take kallon ta ta ce “Wallahi da gaske nake miki yanzu haka ma an yi kwana biyar a cikin wata biyun, da a yi hutu za tafi gida.” Gyara zama Amira ta yi tana hura hanci kamar za ta kai wa Andizo duka ta ce “Amma dai kin san ba ki yi wa Uncle adalci ba ko? Duk wani motsin shi Khadija ko wani abu ya gani na mata zai ce wannan zai miki kyau ya saya ya aje ya ce in kin zo gidansa zai miki surprise, ashe ke kina can wancan mai ciccin maganin ya hure miki kunne, yanzu da wani ido zan kalle shi na ce masa an sa miki rana? Ki faɗa mini Khadija me kike so na ce masa idan ya tambaye ni mun haɗu da ke a ècole?” Ta faɗa rai ɓace, Andizo ta kafe ta da ido tana mamakin yadda ta fusata a kan ɗan giya, girgiza kai ta yi ta ce “To ke wa ya ce miki dama ina son Uncle ɗin ki? Tun farko dama na faɗa masa ni ba zan auri ɗan shaye-shaye ba manemin mata, amma sai ya mini ƙarya ya ce wai yanzu ya na yin duk wani aikin masha'a kayan mayen ma duk ya rage sha a hankali zai fasa ashe duk ba da gaske ba ne?” Wai irin kallo Amira ta jefa mata ta ce “Wallahi kin ba ni mamaki Khadija, ba ki san waye Uncle ba ne shi ya sa har kika ƙaryata maganarsa, idan da bai fasa aikata duk waɗannan abubuwan ba Wallahi ko kashe shi za ki ba zai miki ƙarya ba, Uncle mutum ne mai magana ɗaya idan har ya ce eh to haka ne idan kuma ya ce a'a to ba haka ba ne. Tsohuwar magana ce wannan ni kaina shaida ce Uncle ya kimtsu zama na da shi a London da lokacin Sallah ya yi sai ya je ya bi jam'i, ya daina komai duk saboda da ke Khadija. Da farko da ban san ke ba ce na jinjina wa Khadijar da ta yi sanadiyar shiryuwar Uncle ɗina bayan na so na gane ke ce farin cikin da na yi ya fi na baya, ina son na ga ranar aurenku domin ki ƙarasa ladan ki a gaban idona abokansa yan bal in suka zo duba ni a gidansa za su zo da giya amma sai ya ce musu shi Khadija ta hana shi shan komai ta ce cutar da lafiyarsa suke ba zai sake sha ba, su kansu sun sha mamaki matuƙa lokaci ɗaya da ya daina biye musu a kan mace har sukan ce mishi ya kamata ya maza ya auro Khadija ko sun zo sun ga wannan mai sa'ar da ta sace zuciyar Mr J, Idan suka faɗi haka har kyauta yake musu tare da tabbatar musu lalle zai kawo Khadija a matsayin matarsa su ganta su kansu sai sun yaba da zaɓin zuciyarsa, ashe ke kina can ki watsar da shi har an sa miki rana da ƙanen mijin ki. Allah ya sanya alkhairi ya ba ku zaman lafiya amma ki sani ba zan je wajen aurenki ba kar ma ki sa ran za je Uncle ɗina nake tayawa kishi.” Ta faɗa tana miƙewa tsaye ta wuce fuu. Da sauri Andizo ta tashi har tana haɗawa da gudu ta isko Amira ta janyo hannunta ta yo baya, suna haɗa ido ta fashe da kuka ta faɗa jikinta tare da cewa “Don Allah Amira ki yi haƙuri karki ga lefina a wannan lamarin, Wallahi ko ni kaina zuciyata ta kasa aminta da auren Yaya Ahmad kawai dai na amince ne saboda iyayensa, sun mini halicci kuma suna son su ga auren nan saboda ba sa son na bar gidansu, ni kansu su Maigari tun farkon maganar Maigari ya ce a ɗaura a rabu da ni idan na nutse zan gane gata Salim yake nema mini sai Abba ya ce sam ba zai yi ba a tauye mini haƙƙi a ba ni wanda ba na so, a bari idan har Allah ya sa akwai aure a tsakanin mu za mu fahimci juna gaba, ni kuma ganin yadda kowanni suke son haɗin sai na dangana domin farin cikinsu musamman Maigari..” Ɗago da ita Amira ta yi ta ce “Yanzu kina nufin ba son Ahmad kike ba kawai dan farin cikin su Maigari za ki yi?” Gyaɗa mata kai ta yi tana share hawaye ta ce “Kuma ba na son a ce na rayu a inda babu su Nour ba, ina son na riƙe yarana su girma a tare da ni.” Hararar ta Amira ta yi ta kai mata bugun wasa ta ce “Ke dai ga babban dalili masifar son yaranki da kike ne ya sa kika amince da auren wanda ba kya so.” Dariya mai haɗi da hawaye ta yi ta ce “Ke dai ki tayani da addu'a Allah ya sa na iya yi masa biyayya.” “To shi kenan Allah ya ba ki ikon yi masa biyayya, amma dai ni ba zan iya cewa Uncle an sa miki aure ba sai dai ke za ki faɗa mishi idan ya kira ki, dan haka ni kinga tafiya ta sai mun yi waya.” Da haka suka, yi sallama Andizo na bai wa Amira haƙuri har ta shiga mota ita kuma ta koma gefe tana jiran zuwan Ahmad. Ba ta jima da tsayuwa ba sai ga shi ya iso, da kallo ta bi motar har ya fito ya iso inda take tsaye ya haɗe hannu biyu yana marairaiwa ya ce “Ina mai ba da haƙuri a kan abin da na yi, nasan na barki kina jira a mini afuwa matata.” Harara ta banka mishi ta jefa mishi jakar makarantar ta wuce ta shiga mota, murmushi ya yi ya bi ta da sauri ya shiga suka tafi. Tun a hanya ya ga ta yi shuru tana kallon gefen hanya ba magana irin yadda suka saba, jikinsa ne ya yi sanyi ya kai hannu ya shafo fuskarta cikin sassanyar murya ya ce “Khadija ya dai? Ko ba ki da lafiya ne?” Lumshe ido ta yi ta juyo ta ce “Yaya zazzaɓi nake ji.” Da sauri ya ce “Subhanallahi tun yaushe ya same ki ba ki kira ni kin sanar da ni ba?” Ƙasa ta yi da kai ta ce “Ɗazu ne da muka fito fa in naje gida zan sha magani.” “A'a ba na son wasa da lafiya muje asibiti a duba ki.” Ƙi ta yi ya yi juyin duniyar nan amma sam ta ce ba za ta je asibiti ba dole ya haƙura ya rabu da ita. Bayan sun je gida ta yi wanka ta ci abinci ta shige ɗaki ta kulle dan kar ma ya zo ya dame ta da hira ita kuma yau ba ta jin yin magana. Kwanciya ta yi ta lulluɓa har baccin ta ya fara nisa ta farka a firgice, dafe kanta ta yi tana karanto addu'ar mummunan mafarki cikin wani kalar yanayi irin na masu rashin lafiya _*“آعوذ با كلمات الله المامات من غضبه و عقابه و شر عباده، و من همزات الشياطين و أن يحضرون*_“ Shuru ta yi bayan ta gama addu'a tana mayar da numfashi, ƙarshe dai ta tashi ta canja kaya dalilin kiran da Ahmad yake mata a waya yana so su fita waje, a harabar gidan ta same shi ya dinga tsokanar ta ita kuma ta yaƙe dan kar ya gane tana cikin damuwa haka dai suka tafi. Wajen wani sabon cin abinci ya kaita wanda bai fi sati da buɗewa ba, sosai wajen ya ɗebe mata kewa ta ɗan saki jiki suka dinga hira yana nuna mata kalar atamfofi da shaddojin da za a kai mata lefi ta zaɓi kalar da take so, haka dai ta zaɓa wani kuma sai ta ce shi ya zaɓa sai ya nuna ya aje ta. Suna dawowa da gida da kyar ta isa ɗaki ƙafafuwanta sun yi sanyi sosai sai da Ahmad ya ɗauke ta ya kwantar jikinta sai rawa yake. Ganin abin na ƙasuwa hankalinsa ya tashi fita ya kira Hajiya Babba ta zo ta ce su tafi asibiti. Ko da suka je allura kawai suka mata ta maleriya suka dawo gida, da kyar ta samu bacci. Ihun ta ne ya tayar da su ƙarfe uku da rabi na dare, ta fito a guje ta nufi ƙofar palo tana son fita Mamma ta iso wajen ta tana salati, ruƙo hannunta ta yi ta ce “Ke Khadija lafiya ina za ki je.” Ƙoƙarin kwacewa take tana faɗin “Fita zan yi ki sake ni na tafi.” Ta kwace ta ƙarasa buɗe kofar Mamma ta juya da sauri tana kiran Ahmad, can cikin bacci ya ji kiran hakan ya sa ya buɗe ido ya yi zaton ko mafarki ne yake amma ya ƙara jin kiran, da sauri ya mike ya fito ya ga Mamma a firgice tana ganin shi ta ce “Don Allah maza bi ta Khadija ce ta fita da gudu yi sauri na rike ta ta kwace har da ture ni ta yi.” Kafin ma ta ƙarasa ya wuce da sauri ya fito waje ya same ta ita da maigadi suna ta fama, ƙarasowa ya yi ya kamo hannunta tana turjewa tana kai masa duka sai fadi take ya rabu da ita za ta fita, ganin abin na neman fin ƙarfinsa ya daddage ya ɗauke ta cak ya dawo da ita ciki. A palo duk suka zauna tana matse a jikin Ahmad sai kuka take tana son kwacewa, Abba ya matso ya dinga mata karatu yana fito mata, tun tana mutsu-mutsu har ta saki jiki bacci ya ɗauke ta, kowa ajiyar zuciya ya sauke yana kallon fuskar Andizo yadda ta yi kaca-kaca da ruwan hawaye da majina,Hajiya Babba ta nisa ta ce “Ni dai ban taɓa ganin Khadija ta yi irin wannan abin ba, ko ma meye ke son samun ta Allah ya yi mata katangar ƙarfe da shi.” Amin suka ce a tare Mamma ta ce Ahmad ya kaita ɗakin Hajiya babba ya amsa da to. Yana kaita ya hau kan gadon ya kwantar da ita, gabaɗaya duk sai ta ba shi tausayi yana ta mata addu'a, zama ya yi a bakin gadon ya zuba mata ido har sai da Hajiya ta shigo ɗakin ya fita ba dan ransa ya so ba.... _*Maman Nusaiba ce*_ [7/3, 5:26 PM] Ummu Amjad: ADZ 43 Daren ranar Ahmad bai sake komawa bacci ba har aka kira assalatu ya miƙe ya shiga banɗaki ya ɗauro alwala, bayan ya gabatar da raka'a tainun fajur ya zauna yana yi wa Andizo addu'ar samun sauƙi, domin ya matuƙar firgita da ganin abin da ta yi yau da kyar ya iya sarrafa ta duk ji da yake shi cikakken namiji ne mai ƙarfi. Ajiyar zuciya ya sauke ya tashi ya fice domin zuwa masallaci, a hanya suka haɗu da Abba suka wuce a motarsa. Ƙarfe 7:am na bugawa Andizo ta farka tana miƙa, kallon inda take a kwance ta yi tana zaro ido cike da mamakin yadda aka yi ta zo ɗakin Hajiya Babba, ba ta gama shan mamakin ganin ta a ɗakin ba sai da ta ga duk yan gidan sun shigo ɗakin kowa yana jero mata sannu, kallon su kawai take har sai da Mamma ta zo kusa da ita ta taɓa jikinta ta ji ba zafi, murmushi ta sakar mata ta ce “Sannu Khadija yanzu ina yake miki ciwo?” Girgiza kai ta yi ta ce “Kaina kawai yake ciwo Mamma amma me ya kawo ni ɗakin Hajiya?” Ba wanda ya ba ta amsa sai kama ta da Mamma ta yi ta sauko ta raka ta har banɗaki tana sanar ta ita ta yi Sallah har ƙarfe bakwai ta yi, sosai ta sha mamaki domin ita ba ta makara har ta kai bakwai ba ta yi sallah ba, haka dai ta yi alwala ta yi sallah ta yi zaune tana tunani ko za ta tuna yadda aka yi ta zo ɗakin Hajiya tun da su sun ƙi ba ta amsa amma sam ta kasa tunawa. Ƙamshin turarensa ne ya kawo wa hancinta ziyara ta ɗago kai ta kalli ƙofa karaf idanunsu ya sarke da na juna, murmushi yake sakar mata yana takowa zuwa gareta, itama murmushi ta mishi bai taɓa yi mata kyau da kwarjini ba irin yau ta kasa ɗauke idanunta daga kallon shi kamar yadda shima yake a ɓangarensa. Sai da ya iso ya durƙusa gwiwowunsa har ƙasa ya yi magana murya can ƙasa, “Bonjour ma belle comment vas tu aujourd'hui ?” Sunkuyar da kai ta yi cike da jin kunyar kallon da ta mishi, a hankali ta amsa da “Alhamdu Lillah.” “Ma sha Allah naji daɗin haka, yanzu ki tashi mu tafi asibiti a duba lafiyarki, duba ki ga daga jiya zuwa yau yadda kika zabge kamar kazar mayu.” Turo baki gaba ta yi ta ɓata rai ta ce “Ni fa na samu lafiya ba sai mun je asibiti ba.” “Ai kuwa ba ki isa ba sai mun je, tashi maza ki ɗauki hijabinki mu tafi kar na makara wajen aiki.” Kallon shi ta yi ta ce “Wai Yaya aikin me kake yi? A baya fa ka ce ba ka son koyarwa kaima sojan kake son zama, ni dai ina tsoro don Allah karka tafi aikin soja ba na son kaima wani abu ya faru da kai.” Ta faɗa tana goge hawayen da suka zubo mata. Murmushi ya yi ya kamo hannayenta ta ce “Haba Khadija ai ba zan yi aikin soja ba yanzu, da dai ina da ra'ayi amma yanzu ba ma za a bar ni ba saboda abubuwan da suka faru, ba wia kuma muna yiwa Allah dabara ba ne kawai dai naji a raina aikin ya fice mini a rai, yanzu ni 'yan jami'a nake koyarwa.” Murmushi ta yi ta ɗaga baki za ta yi magana sai kuma ta fasa ta miƙe a hankali ta koma bakin gado, ganin hakan ya sa ya wuce yana ƙara jidadda mata kar fa ta jima ta amsa da to tana hararar bayan sa. Ba dan ta so ba ta fita daga ɗakin ta nufi nata ta ɗauko hijabi ta fito, kiciɓus suka yi da shi a bakin ƙofa ya yi saurin taro ta ganin ta yi baya za ta faɗi ya haɗa ta da jikinsa, shuru ta yi tana jin sautin bugun zuciyarsa da sauri-sauri can kuma da ɗago sauri, kallon ta ya yi ya mata alamar me ya sa ta tashi, sunkuyar da kai ta yi za ta raɓa ta gefen shi ta wuce ya ruƙo ta suka fito a tare. Buɗe mota ya yi ya saka ta ya rufe sannan ya zagaya ya shiga suka tafi, sai da suka yi nisa ta ɗan kalle shi kamar wata munafuka ta ce “Yaya ba ka da lafiya ne?” Murmushi ya sakar mata bai ce komai ba, itama daga hakan ba ta kuma faɗin ko kalma ɗaya ba ganin ya ƙi ba ta amsa. Suna isa daret wata ƙofa ta ga ya kwankwasa aka ba su izinin shiga, da sallama suka shiga inda suka samu wata babbar mace a ciki ta hakimce a kan kujera tana ta rubutu, suka zauna Ahmad ya gaishe ta ta ɗago kai tana murmushi ta ce “A'a sannun ku da zuwa yau kaine da kanka ɗan Abie?” Sosa kai ya yi sannan ya kalli Andizo da ta kusan dawowa kansa sai rawar sanyi take ya kai hannu ya ɗago ta yana ƴar dariya ya ce “Matsoraciya daga ganin likita sai ki kama rawar sanyi tun ma ba a duba ki ba?” Saurin komawa ta yi kan cinyarsa ɗaya ta kwanta tana lulluɓa da hijabin jikinta, kallon su likitar ta yi tana murmushi ta ce “Ko ita ce Khadijar da aka sa muku rana?” “Ita ce Mami ba ta da lafiya ne jiya ta hana mu bacci shi ne na kawo ta a duba mini ita, tun da aka sa bikin nan namu duk ta taƙi sakin jikinta musamman shekaranjiya da jiya.” Ya faɗa fuska ɗauke da damuwa. Girgiza kai matar ta yi ta miƙa hannu ta ce “Zo nan 'yata karki ji tsoro kin ji zan duba ki ne.” Maƙale kafaɗa ta yi nan da nan idanuwanta suka cika da ruwa baki na rawa ta ce “Ni dai ba na so gida zan koma.” Dariya Ahmad ya yi yana ɓamɓare ta daga jikinsa ya ce “Ai kuwa ba ki isa ba sai an duba ki tun da mun zo har cikin office ɗin Mami.” Kuka ta sa musu tana ƙara ƙanƙame Ahmad, hakan ya sa Mami ta kalli Ahmad ta ce “Riƙe ta a haka in duba ta.” Ɗauko ta ya yi cak daga kan kujera ya rungume ta sosai ta yadda ba za ta subce masa ba, da haka Mami ta fara auna ta ta ɗibi jininta kaɗan ta koma can fege, allura ta ɗauko ta fasa kwalbar ta zuƙa ta nufo su, ai kuwa ƙara ta sa tun kafin ma a tsira mata allurar Mami ta yi murmushi tana faɗin “Kai ko Ahmad wannan mata taka akwai mugun tsoron allura.” Dariya shima ya yi ya ce “Kuma fa ta taɓa haihuwa amma take tsoron allura.” Riƙe ta ya ƙara yi sannan aka mata allura guda biyu, bayan an gama ta yi rubutu a kan wata takarda ta miƙa masa ta ce “Gaskiya tana fama da zazzaɓi da ciwon kai mai zafin gaske amma dai ta rage tunani, wannan maganin da na rubuta su za ku saya take sha ko sun ƙare a ƙara sayo mata domin zai taimaka mata matuƙa.” Ta faɗa tana kallon Andizo da take murtsika ido. Godiya ya mata ya tashi ya kama hannun Andizo suka tafi, da kyar ta isa mota da ƙafarta saboda allurar da aka mata ta ɗan riƙe mata ƙafa. Da yamma tana kwance a kan gado tana amsa kiran da Umma ta yi mata su Nour sai kwaranci suke mata tana ganin yadda suke ta guje-guje, gyara wayar ta yi ta tashi zaune ta ce “Khadijata kina so ki zo wajena?” Dariya Umma ta yi ta ce “To ita da ba magana ta iya ba taya za ta ce miki eh ko a'a?” Murmushi ta yi ta musu sallama ta kashe wayar, kanta ne ya ƙara nauyi ta dafe kan tana runtse ido, kira ne ya shigo wayarta ta ɗago da wayar, ganin mai kiran ta ja tsaki ta aje wayar amma kafin ma ta ɗauke hannu aka sake kira nan ma taƙi ɗauka, bayan ta gama ringing sai ƙarar shigowar saƙo ta dafe kai ta ɗauki wayar tana duba saƙon. _“Khadija ni kike katse wa kira? Me na miki haka? Tun da na dawo kin ƙi ɗaukan kirana Allah ya sa dai ba wani abu marar kyau ba ne ya faru, please ki ɗauka ina so zan nuna miki wani abu ne.”_ Tsaki ta ja gani take duk ya bi ya takura mata, kiran video call ne ya shigo ta gyara ɗaurin ɗankwali sannan ta ɗaga kiran tana ɗaure fuska ta kalle shi. Babu riga a jikinsa gashi ne kwance a faffaɗan ƙirjinsa baƙi ya yi luf-luf sai iskar AC ke fifita shi. Da wani irin yanayi ta yi saurin runtse idanuwanta tana kawar da kai gefe, dariya ya yi ya tashi zaune ya ɗago mata hannu ya ce “Hello.” “Wannan ɗin wani irin abu ne ka sa riga in kana so na ci gaba da riƙe waya.” Singlet fara ya ɗauko ya saka ya yi baya da gashin kansa kamar na mata har ma yafi na wata macen, gyara zama ya yi ya ce “My wife ina son na nuna miki kofin da muka ci jiya da na kira ki amma kika ƙi ɗauka, yanzu zuwa nan da sati biyu zan tafi Nigeria kinga sai mu zo da Mom har can garinku ayi maganar aurenmu.” Ƙara kallon ta ya yi ganin yadda ta rame ya ɗora da cewa “Ko ba ki da lafiya ne? Me yake damun ki?” Kasa ce masa komai ta yi sai kallon shi da take, yadda ya yi magana cike da fara'a sai ta ji jikinta ya yi sanyi sunkuyar da kai ta yi ta ce “Please ba na jin daɗi yau ma an kaini asibiti sai an jima zan kwanta na huta, zan tura ma text yanzu da na kashe.” “A'a tsaya ina so na nuna miki wani abu da na sayo miki nasan zai miki kyau sosai.” Tagumi ta yi tana jiran ta ga me zai nuna mata, tashi ya yi ya fita bai ɗauki lokaci ba sai ga shi ya dawo hannunsa ɗauke da leda. Zama ya yi yana murmushi ya ce “Kinga wannan abayar jiya da na fita sayayya na ga ta mini kyau, shi ne na ce bari na ɗauko miki tabbas za ta dace da ke ya kika ganta?” Kallon a bayar ta yi black colour mai masifar kyau sosai ta ji abayar ta birge ta, amma tuna yanzu tana gaf da shiga gidan wani sai ta ɗan ɗaure fuska, ganin yadda ta canja fuska sai ya yi saurin faɗin cewa “My wife ba ta miki ba ko? To kwantar da hankali zan bayar da ita na sayo miki wadda ta fi wannan kyau.” Ya faɗa yana kallon ƙofa jin ana kwankwasawa, kallon Andizo ya yi da take yi shirin kashewa ya ce “One minute zan kira ki abokina ne ya zo ni kuma ba na son ya ganki har sai lokacin da na kawo ki nan.” Ya faɗa yana tashi. Tsaki ta ja ta kashe wayar ta tura mishi saƙon da ta faɗa masa ta aje wayar ta kwanta gaban ta na dukan uku-uku, wani irin gudu zuciyarta take ba ta san ba wani kalar hauka zai yi mata yanzu. Kamar ya san me take tunani sai jin kira ta yi ta duba ta ga shi ne sai taƙi ɗauka, jin sanyi yana shigar ta ta janyo bargo ta lulluɓa tana jin saukar ɗumin ruwan hawaye kan kumatunta. Kasa daurewa ta yi da kiran dan yau so take a yi ta ta ƙare ya kamata ta sanar da shi gaskiyar abin da ke faruwa ko zai fita daga rayuwarta ta huta. A hankali ta yi picking call ɗin ta yi shuru ta ji me zai faɗa, saukar numfashinsa ta fara ji a majiyarta ta yi saurin runtse ido, wani irin yanayi take ji gabaɗaya neman rasa nutsuwarta take tun ma kafin ya yi magana. “Kha.. Khadija.. Khadijaaaa!” Ya ja sunan da wata kalar murya da ba ta taɓa jin irin ta ba a gareshi, ƙara runtse ido ta yi tana addu'a ita dai burin ta ya taimaka ya rabu da ita, numfashi ta ji yana fitarwa da ƙarfi so yake ya mata magana amma sam ya ƙasa, can ta ji muryar wata mace tana faɗin “Mr J are you OK?” Can kuma ta ji macen tana ruri ta ɗan yi nisa da wayar, shuru ta yi jin ba kowa sai motsin Sultan, can kuma ta fara jin muryoyi dayawa suna tambayar Sultan me ya same shi? Daga haka ba ta tsaya jin komai ba ta kashe wayar ta yi jifa da ita ta kwanta. Idan ta tuna yadda yake kula da ita sai ta ji ba ta mishi adalci ba, amma idan ta tuna ɗabi'unsa sai ta ji hankalinta ya rabu gida biyu, ajiyar zuciya ta sauke tana dafe kanta da ya yi mata nauyi kamar an ɗaura mata dutse hake take ji. Nan da nan zazzaɓi da ciwon kai irin na dare suka dawo mata ta ƙara lulluɓa da bargo rawar sanyi.. Har bayan sallar isha'i ba ta fito ba sai dai su zo su leƙo ta daga bakin kofa su gani tana bacci sai su koma, yayin da ita kuma ta tsinci kanta a wani yanayi bacci take amma kamar tana farke, so take ta tashi amma wani abu mai mugun nauyi ya danne mata ƙirji da ta yunƙura ta tashi sai ta ƙasa, jikinta ji take kamar ana zuba mata tafasashshan ruwan zafi idanuwanta ne kawai take suke aiki yadda ya kamata. Ƙarfe 8:am Hajiya ta gaji da rashin ganin Andizo ta tashi ta nufi ɗakinta, kwankwasa ƙofar ta yi ta ji shuru hakan ya sa ta tura ta sa kai ciki, yadda suka bar ta jiya a lulluɓe haka ta same ta ko juyi ba ta yi ba daga wajen sai mamaki ya kama Hajiya, a hankali ta yaye bargon tana faɗin “Khadija wannan ɗin wani irin bacci ne tun jiya har yanzu ba ki tashi ba?” Da kyar ta iya buɗe idanuwanta da suka yi jaju, bakinta ya buɗe ta kalli Hajiya sai hawaye shar, Hajiya ta kama ta ta tayar da ita tana jera mata sannu jin jikinta da zafi, ruwan da ke can gefe take kallo tana son ta ce za ta sha amma maganar ta gagara. Kallon inda take kallo Hajiya ta yi sai ta ga ruwa ta jingina ta da jikin gado ta isa ta ɗauko ruwan ta buɗe ta iso ta kafa mata a baki, bismillah ta yi a zuciyarta ta soma sha har ta shanye duka ruwan gorar. Kallon ta Hajiya ta yi sai kuma ta ce “In da buɗe bakinki Khadija mu gani.” Da kyar ta buɗe Hajiya ta ga duk ƙuraje sun cika mata baƙi ga su nan felas, saurin fita ta yi ta nufi ɗakin Ahmad tana kiran shi ta ji shuru sai ta tuna ya tashi wajen aiki. Palo ta iso ta samu Abba na shirin tafiya ta ce “Tsaya Musalle karka tafi.” Juyowa Abba ya yi ya ce “Hajiya lafiya na ganki duk a firgice?” “Ina fa lafiya yarinyar nan Khadija ce rai a hannun Allah, ga ka yadda ta kara ramewa? Yanzu haka bakinta cike yake da ƙuraje kamar wata yarinyar goye, muje maza a mayar da ita asibiti.” A tare suka shiga ɗakin Abba, Hajiya, Mamma Har da su Hassana. A ƙasa suka same ta ta kifa kanta ƙasa hakan ya sa Hajiya ta yi sauri ta kama ta tana faɗin “Ka gani ko faɗowa ta yi daga kan gadon.” Hijabi Mamma ta saka mata suka ɗauke ta su duka suka nufi waje Abba na biye da su, sosai hankalinsa ya tashi ganin yanayin da ƴar amanar tasu take ciki. Mamma da Hajiya da su aka tafi su Hassana suka koma ciki jiki ba daɗi, suna zama a palo Hussaina ta dubi Hassana ta ce “Gaskiya ni fa ban yarda Khadija Wannan ciwon nata ba na zuwa asibiti ne, ki duba ki ga daga jiya zuwa yau yadda ta koma kamar ƙashi anya ba aljannu ba ne suka shafe ta ba mu sani ba muke kaita asibiti?” Tagumi Hassana ta yi tana gyaɗa kai ta ce “To nima dai abin da na gani ba za a gwada yi mata ruƙiya ba, bari Abba ya dawo shi za mu samu da maganar ko kuwa na Hajiya za ta yarda da maganarmu nan take fiye a Abba.” To Hussaina ta ce suka ci gaba da zama. Suna zuwa asibitin Mami ta ƙarbe su suka shiga cajin lafiyar Andizo, sun kusan minti talatin sannan Mami ta fito ta nemi da su bi ta office su duka suka bi bayanta. Bayan ta ɗan yi rubuce-rubuce a kan takardar da ke gaban ta ta kalle su ta ce “Hajiya gaskiya na gama cazar lafiyar Khadija ban ga ba komai ba sai abin da na musu bayani jiya da safe, sai ƙurajen baki kaɗai yanzu na mata allurar bacci an jima za ta farka za ku iya tafiya Allah ya ƙara lafiya.” Duk shuru suka yi suna ta mamaki yadda suka kawo ta nan a galabaice wai a ce ba komai sai dai zazzaɓi da ƙurajen baki duk wannan firgitar da ta dinga yi tana mimmiƙewa kafin su iso asibitin? Godiya suka mata suka fito suka zauna suna ta jero wa Andizo addu'ar samun lafiya. Wasa-wasa Andizo ta shafe sama da sati uku amma babu abin da ya canja sai ma ƙaruwa da ya yi, ba ta iya cin abinci sai dai a yi koko a ba ta shima da kyar take sha, saboda ƙurajen bakin da wasu sun mutu wasu za su kuma kadowa maganar ma da kyar take, kwana take tana kuka tana faɗin jikinta zafi yake, maganin gargajiya Ahmad ya dinga amso mata ana mata amma kamar ƙara mata ciwon ake, wani magani da ya amso yau da kwana biyu a kasuwa da yaji ana tallar sa ya kawo aka mata wanka da shi gabaɗaya jikinta ya ƙara rikicewa, ƙuraje ƙanana kamar na zafi suka kaɗo mata ta dinga kuka tana sosawa, ranar babu wanda ya yi bacci a cikin su a kanta suka kwana suna tofa mata addu'a har asuba tukun ta samu bacci ɓarawo ya yi sace ta. Ganin lamarin na ƙara girmama Hajiya ta kira su Maigari ta sanar da su duk abin da ke faruwa, hankali tashe Maigari ya ce ga su nan zuwa garin.. Da safe suka sauka, suna shigowa gidan ya yi daidai da ta kaɗo a guje daga ciki sun biyo ta, da wani irin tashin hankali Giɗaɗo ya taro ta yana kiran sunanta amma tana zuwa saitin shi ta kauce ta yi gaba. Zari uku ya yi ya damƙo ta ta dinga ƙoƙarin kwacewa amma ya riƙe ta gam. Da kyar ya iya riƙe ta suka shiga har cikin palon Hajja sai kuka take tana salati. Zama duk suka yi Giɗaɗo ya kalli jikin Andizo ya ga duk ta yi baƙi ta koma ƴar ficiciya kamar ba ita ba, cike da tausayin ta ya ɗago ya kalli su Hajiya ya ce “Wai tun yaushe ta fara wannan rashin lafiyar ba mu sani ba?” Cire tagumi Hajiya ta yi tana share hawayen da suka zubo mata ta ce “Gaskiya ta kusa wata ɗaya tun bayan sa bikinsu da sati ɗaya ta soma wani irin zazzaɓi mai zafin gaske, to muna kaita asibiti. Nan dai ta kwashe komai ta faɗa.” Sake kallon ta Giɗaɗo ya yi ya girgiza kai ya ce “Wannan fa ba ciwon asibiti ba ne Hajiya.” Ya ƙarashe maganar a sanyaye. “Ai tun da muka gane haka muka dinga nema mata na Hausa, duk inda muka ji magani sai mun amso an yi mata amma Wallahi ga ta nan kamar ƙara mata ciwon ake duk safiya. Ni kunyar haɗa ido nake da ku kun ba mu amana amma ga abin da ya faru yarinya kar ku ga kamar mun yi sakaci ne da ruƙon ta.” Hajiya ta faɗa tana share hawaye. Maigari ya ce “Haba Hajiya sai ka ce mu ba musulmai ba ne za mu ce kun kasa riƙe amanar uwata? Ai duk abin da ya faru da bawa muƙaddari ne daga Allah, nasan kun riƙe da kyau fiye ma da yadda mu za mu riƙe ta Allah dai ya bar zumunci.” Tashi tsaye Giɗaɗo ya yi ya sunkuya ya ɗauke ta ya saɓa ta a kafaɗa ya ce “Za mu tafi da ita gida a nema mata magani a can ko Allah zai sa a dace, ku shiga ku ɗauko mata tufafinta ko da kala uku ne.” “Haba ɗan nan daga zuwan ku sai ka ce ku tafi da ranar nan? Ku zauna a shirya mata kayanta ku ɗan huta sai ku tafi an jima kaɗan.” Cewar Mamma tana kama Andizo ya sauke ta suka kwantar da ita ba dan ya so ba.. Ahmad duk ya kasa nutsuwa ko magana ya kasa yi jin sun ce za su ɗauke mishi ita su tafi ƙauye. Da kyar suka bari aka yi La'asar aka haɗa wa Andizo kayanta suka raka su direban gidan tare da Ahmad suka yi mota biyu suka nufi ƙauye.. Suna tafiya a hanya wayar Andizo da ke hannun Giɗaɗo ta yi ringing ya kalli wayar, ganin an rubuta Amira sai ya ɗaga kiran, sautin kuka ya masa sallama a kunne ya yi shuru yana jiran jin me za a faɗa, sai da ta dan ɗauki sakanni sannan aka fara magana. “Hello Khadija yanzu kin kyauta kenan ? Wallahi abin da kika faɗa wa Uncle kin ganshi nan yanzu ma an sake shiga emergency room da shi da ya farfaɗo sunanki ne kawai a bakinsa, yanzu haka ba na tunanin yana raye saboda yadda ya dinga aman jini ba lalle ba ya rayu, ni yanzu ban san me ya kamata na yi ba Khadija.” Ta faɗa tana ƙara fashewa da kuka mai tsuma rai.. Ajiyar zuciya ya sauke ya kalli Andizo ya ce “Ki yi haƙuri na ga an sa Amira ko? To itama kanta Khadijar ga ta nan rai a hannun Allah mun je mun ɗauko ta za mu koma ƙauye..” Ya kashe kiran yana tunanin me ya faru tsakanin Uncle ɗin Amira da Khadija har take ce mata abin da ta yi ta kyauta?... *Maman Nusaiba ce* [7/4, 3:15 PM] Ummu Amjad: ADZ 44 Sake kira Amira ta yi Giɗaɗo yaƙi ɗauka yana kallo har ta yi ringing ta katse, ba a fi minti ɗaya ba ta sake kira ya girgiza yana ɗaukan wayar tare da faɗin “Hello baiwar Allah ba ki ji ba abin da na faɗa miki?” Kukan da take ne ya ci ƙarfinta ta kasa magana shi kuwa Giɗaɗo sai ya yi shuru yana sauraron ta, tabbas duk wanda ya ji kukan Amira ya san tana cikin tashin hankali musamman yadda take kiran sunan Khadija, sai da ta tsagaita sannan ta ce “Bawan Allah don Allah kai waye? Kuma ina Khadijata take da Yaya Ahmad? Na kasa yarda da abin da ka faɗa mini.” Shuru ya yi bai ba ta amsa a take ba sai da ya ɗauki second goma sannan ya kalli Andizo da take daf da shi ya kai hannu ya gyara mata zaman hular kanta ya ce “Ni yayan Khadija ne yau muka zo daga ƙauye muka tafi da ita ba ta lafiya ga ta nan ba ta gane wa ke kanta, idan kuma ba ki yarda ba ki kira ta caméra sai na nuna miki ita ki ga zahiri.” Baki na rawa ta ce “To amma ai Khadija tana da yayu har biyar amma tafi ambaton Hamma Giɗaɗo kai wanne ne daga cikin su?” Ta faɗa tana sharce majina. Numfashi ya ja saboda duk ya ji ta takura mishi da tambaya, gefe ya kalla ya ce “Hamma Giɗaɗo be.” “To nuna mini ita Wallahi hankalina a tashe yake da naji abin da ka ce, nan Uncle ga shi can ya mutu ba ko yana da rai Allah masani kaima ka ce mini ƙawata na kwance ba lafiya.” Gyara wayar ya yi ya nuna mata Andizo a kwance fuskar nan ta yi baƙi ƙananan ƙurajen da suka fito mata sun mutu dai fuskar ta yi wata kala kamar an shafa mata gawayi, zaro ido Amira ta yi ta nufi wajen Mom tana kuka wiwi ta ce “Mom kalli itama Khadijar halin da take ciki.” Mom ya gani nan take ya gane ta amma bai ce komai ba yana kallon yadda itama take kuka tana salati, da ya gaji ya yi gyaran murya ya ce “To zan kashe sai an jima.” To suka ce suna ta jero mata addu'ar samun lafiya yana amsawa da amin har ya kashe.. Tagumi ya yi yana hasko fuskar Mom a zuciyarsa sosai ya ga matar tana cikin matsananciyar damuwa, janye tagumin ya yi ganin sun iso ƙofar gidansu. Sauka duk suka yi ya rage saura shi da ita, shima ya sauka ya ɗauko ta yana ƙara lulluɓe mata jiki ta hijabin da aka sa mata ya yi saurin shigewa gida, yaran da suka fara tsayawa sai duk suka bi Giɗaɗo da kallo ganin ya ɗauko mace a lulluɓe ya shige ciki sai suka bi bayan shi. A rumfa ya kwantar da ita shima ya zauna ya ɗago yana kallon yaran da suka yi tsaye suna son ganin fuskar wadda aka rufe, wani yaro daga cikin su ya ce “Giɗaɗo wannan ɗin waye ya mutu?” Haɗe rai ya yi ya nuna musu hanyar fita da hannu ya ce “Maza kowa ya fita ba mutuwa aka yi ba ba ta da lafiya ne uwar masu gari ce.” Gabaɗaya yaran sai suka kalli Giɗaɗo da mamaki ba wanda ya ce ƙala har suka fita daga gidan, kowanne yaro gidansu yake nufa a guje ya je ya kai labarin an kawo Andizo tana nan kamar ta mutu ma, tuni gari ya ɗauka Andizo ba lafiya matan aure duk suka nufi gidan Maigari ana zuwa ganin ta amma ba wanda aka yarda ya ganta suka sa ta ɗaki. Ahmad ya sa aka kira mishi Giɗaɗo ya zo, kallon shi Giɗaɗo ya yi ya ce “Yaro ya ce kana kirana?” Gyara tsayuwa ya yi yana fuskantar shi ya ce “E ina so ka ba ni wayar Khadija zan tafi da ita.” Girgiza kai Giɗaɗo ya yi ya kalli wayar da ke hannunsa sai ma ya saka ta a aljihu ya ce “A a ba zai yiyu ba na ba ka wayar Surbajo, nasan ƙawata da sauran abokanta na makaranta za su kira ta idan wayar ba ta kusa da ita ai ba za su san halin da take ciki ba, ɗazu muna mota ma wata Amira ta kira ba ta san ba ta lafiya ba sai da n sanar mata, da farko taƙi yarda sai da ta kira caméra ta gani da idanuwanta sannan ta yarda, nan dai ya kwashe labarin komai ya faɗa masa.” Zaro ido Ahmad ya yi yana faɗin “Inna lillahi wa inna laihin raji'un! Shima Sultan ɗin ba shi da lafiya har da aman jini? Subhanallah! To shi kenan bari mu koma za dawo jibi in sha Allah.” Ya faɗa yana shiga mota shima direban ya shiga ɗayar suka bar wajen, shi ne Giɗaɗo da ido ya bi shi ganin yadda shi ɗin ma ya firgice da ya faɗa masa wancan ba lafiya, tunani ya yi ko sun san juna ya juya ya koma ciki.. _NIGERIA_ Can ɓangaren Sultan tun da suka shiga da shi emargercy ba su fito ba har sai da suka shafe awa biyu suna faman ceton rayuwarsa, bayan sun fito suka buƙaci yun magana da Mom ta bi bayan babban doctor ita da Amira da Farrah zuwa office ɗin sa, bayan sun zauna gama duba sakamakon da suka samu na rashin lafiyar Sultan ya aje a gefe ya fuskance su, Mom ta tattaro 'yar sauran nutsuwar da ta rage mata ta fuskanci doctor domin ya ji wani halin ɗan nata yake ciki. “Hajiya gaskiya yallaɓai yana cikin mawuyacin hali ƙodarsa na gab da kamuwa da ciki, zuciyarsa dama tun zuwan ku farko na sanar da ku ya kamu da ciwon zuciya, ya kamata ku nemo mishi abin da yake buƙata tun kafin abin nasa ya ƙara girmama, daga ya farfaɗo sunan wata yake kira ni ban ma riƙe sunan ba amma dai koma meye wannan mai sunan ita yake son gani a kusa da shi..” Hawayen da suka zubo mata ta sa hannu ta goge tana girgiza kai ta ce “Ba zai taɓa samun wannan mai sunan ba domin an riga da an aura wa wani ita, kuma ita ɗin ma yanzu haka ta ma fi shi jin jiki ba ta da lafiya.” Shuru Doctor ya yi yana kallon su Amira ta ce “Gaskiya ba a yi wannan auren ba Mom, ni zan je na sanar Yaya Ahmad komai har garin nasu zan nema na tafi domin na ga halin da yake ciki kuma na sanar da su abin da suke son aikatawa za su kashe rai biyu ne, na tabbatar Mom Khadija tana son Uncle kawai dan babu yadda za ta yi ne ya karɓi auren Ahmad, ko an ɗaura auren nan nasu zan roki alfarma su warware.” Ta faɗa tana gunjin kuka. Dafa ta Mom ta yi ta ce “Kin tabbatar ba a ɗaura auren nan ba?” “E Mom ba a ɗaura ba ai da sauran kwanaki, kuma ma tana cikin wannan yanayin taya za su ɗaura mata aure?” Kallon su Doctor ya yi ya ce “To ku dai yi ƙoƙarin kawo masa wannan yarinya yana farkawa ya ganta kar aikin da muka masa ya sake dawo da mu baya.” Godiya suka mishi suka fita a office ɗin, ɗaukan handbag ɗin ta ta yi ta rataya ta ce “Mom ki sa a nema mini ticket ko na dare ne ba na son na kwana a garin nan zan wuce.” Kallon ta Mom ta yi ta ce “Yanzu ke ba za ki zauna ba sai kin tafi? Ki bari ya samu sauƙi sai mu tafi har da ni zan je har ƙauyen nasu na nemi alfarma.” Girgiza kai ta yi ta ce “Ba za ki gane ba Mom Khadija ta sanar da ni Maigari yana son wannan haɗin mai Hajja tun farkon abin, to kinga kuwa da Ahmad ne kawai za mu fara idan har ya janye to komai ya zo da sauƙi, shi ya sa na ce miki shi zan fara tunkara da maganar, idan kuma Mama ta dawo sai mu je tare har gidansu mu sanar da su komai.” Ba yadda Mom ta iya ta kira ɗaya daga cikin yaran Sultan ta sanar da shi ticket take so na zuwa Niger na mutum ɗaya, an gama ya ce sannan ta kashe. Gida ta sa aka kaita ta ce da direban in ya je ya isa airport ya ɗauko Farrah ta kusa sauka ya amsa da to.. _NIGER_ Bayan kwana biyu da kai Andizo ƙauye Maigari ya sa duk malaman ƙauye su dukufa da yi mata addu'a, Liman ya ce za su gwada yi mata ruƙiya su gani ko za ya dace, bai musa ba yau da rana ta yi Liman da wasu baƙin malamai biyu da suka zo suka shigo gidan tana kwance jikin Inna ana ba ta kunu, ganin su ya sa ta kankame Inna tana ɓoye fuskarta. Zama suka yi suka gaisa suna tambayar me jiki suka ce da sauƙi, bayani Maigari ya musu ga abin da za a yi wa Andizo sai suka ba su waje aka bar Umar da Giɗaɗo suka riƙe ta. Karatu malaman suka fara yi mata suna tofawa har kusan minti ashirin amma shuru, ɗaya daga cikin baƙin malaman ya kalli Liman ya ce “Gaskiya da akwai babbar matsala Liman, aljannun jikin yarinyar nan mugaye ne ba sa ma yin magana amma bari ka ga zan sa su yi magana dolen su.” Shi dai Liman yana gefe yana kallon su yana tofa tashi addu'ar, ruwa ya sa Umar ya ɗauko ya tofa addu'oi shima ɗayan ya amsa ya tofa sannan suka aje a gefe suka ci gaba da karatu, sai da suka ɗauki lokaci sannan malam ya ɗauki ruwan addu'ar ya zuba mata a fuska. Wata irin zabura ta yi tana ƙoƙarin kwacewa daga hannun su Umar malam ya ce su riƙe ta da kyau suka ƙara riƙe ta, sake ɗaukan ruwan ya yi ya zuba mata ta sa ƙara tana buɗe idanu malam ya yi murmushi ya ce “To daga kuma wa ya turo ku.” Kuka ta hau yi har da rufe fuska Maigari ya kalli Malam ya ce “Akarramakallah ya kuma take kuka?” Hannu malam ya ɗaga wa Maigari ya ce “Kar wanda ya sake kuma, ina jin ku me ya sa kuke cutar da baiwar Allah.” Tsayar da kuka ta yi ta haɗe rai tana kallon Malam kamar ba ita ba ce take kuka yanzu, fuskar tausayi ta yi ta ce “Malam ka daina ƙona ni nifa babu ruwana ba ni nake cutar da ita ni iyaka ta kawai mai tsaro ne.” Jinjina kai Malam ya yi ya ce “To idan ba kai kake cutar da ita ba me ya sa sai kai muka samu? Ka faɗa mana gaskiya tun kafin na ƙona ka.” Kara murtuke fuska ta yi aljanin ya ce “To idan har ka yi gangancin ƙona ni to tabbas wannan yarinyar ba za ta taɓa samun lafiya ba har abada za ta zauna a haka.” Ganin abin na shi da wasa da hankali malam ya kuka fesa mata ruwan ta sa ihu tana ƙoƙarin kwacewa suka ƙara riƙe ta gam, Malam ya kuma cewa “Za ka faɗi ko kuma sai na ƙona ka maƙaryaci?” “Zan faɗa Malam ni ina tsaron inda aka binne sihirin ne, waɗanda suke shan jininta suna cutar da ita suna nan guduwa suka yi.” “To maza ka kira su su dawo yau sai kun faɗa mana wanda ya sa ku aikata wa baiwar Allah wannan ɗanyan aikin.” Ɗayan malamin ya faɗa a fusace. A galabaice aljanin ya ce “Sun gudu ni kaina tsoron su nake ji amma zan sanar da ku komai, wata mata ce ta je har ƙasar India aka mata wannan aikin a kan Khadija, da farko cewa ta yi kashe ta bokan ya ce ba zai yiyu ba shi ne ta ce a sa mata ciwon da kowa zai tsane ta, ƙarshe ta dinga ɗoyi tana wari koya ya gudu ya bar ta har 'yan'uwanta kowa ya tsane ta ta ruɓe ƙarshe ta mutu. To yanzu maganar da nake maka sun gama sa mata dukkan cutar da matar da nema daga gobe wasu ƙuraje za su fito mata a cikinta masu wari wanda zai dinga fitar da koran ruwa mai tsami har' yan hanjinta su fatattake su ruɓe, idan an gama wannan kuma an hana ta gane kowa a makantar da ita ta yadda babu wanda za ta gani kuma ba bakin magana ballantana in tana da buƙatar wani abu ta iya magana. Kun taki sa'a da kuka fara nema mata maganin cutar ta yau, da kin bari sai gobe to ba zan ce ba za ta warke ba amma da wahala, kai ko yanzu illar da suka mata ta wuce misali dan haka ku bari su zo sai ku sa su warware..” Shuru su Malam suka yi sai kuma ya ce “To yanzu kai ka nuna mana in da aka binne sihirin mana.” Girgiza kai ya yi cike da tsaro ya ce “Idan na nuna muku za su kashe ni, yanzu haka ni kaina ban san takaimaiman in da maganin nan yake ba domin jiya sun canja mishi waje, a nan inda nake a tsaye yake amma ban san ta wani ɓangare yake ba, da za au binne aikina aka yi wajen wani boka na kai saƙo kafin na dawo sun binne sun sanar da ni a nan yake amma ba za gani ba sun mishi muguwar ajiya..” Malam ya gyara zama ya ce “To kai ya sunanka?” Dariya ya yi sannan ya ce “Ni ne Najibu.” Da mamaki malam ya ce “Amma kuma sai naji sunan musulmai gareka, kai kuwa kana musulmi me ya sa kake cutar da ɗan'uwanka musulmi.” “Ni ba musulmi ba ne malam kawai na zaɓi sunan ne dan ina so.” “To shi kenan yanzu kai Najibu ba za ka ji tausayin wannan baiwar Allah ba ka tone wannan sihirin?” “Gaskiya ba zan iya ba, amma taimako ɗaya zan muku.” Malam ya ce “To muma jinka wani taimako ne?” “Idan kuma son samun su ku zo da dare. Ko da yamma kusan magariba.” Malam ya haɗe rai ya ce “Ka tabbatar da gaske kake? Idan fa muka kasa samun su zan ƙona ka da ayar Allah kuma ka san dai ai zan iya ko?” “Na yarda Malam.” Yana faɗin haka sai gani suka yi ta yi atishawa mai ƙarfi ya koma jikin Umar ta kwanta. Maigari ya kalle eu ya ce “Amma Malam za su dawo kuwa? An ce fa aljannu mugun wayo né da su ga ƙarya.” Girgiza kai Malam ya yi ya ce “In sha Allah dai sun dawo, idan ma kuka ƙi dawowa da ƙarfin ikon Allah zan sa su dawo kuma su tone sihirin da suka binne.” Godiya suka mishi ya miƙa musu sauran ruwan ya ce su shafe mata jikin ta da shi za ta samu sassaucin ciwon da take ji a jikinta, godiya sosai Maigari ya musu sannan suka fita. Amira na ta ƙoƙarin ganin ta samu Ahmad a waya amma ko ta kira ba ya ɗauka, hakan ta tuna lokacin da Andizo ta sanar mata yana dawowa daga aiki ta saici lokacin ta nufi gidansu. Bayan ta shiga gidan ta gaishe da su Mamma tana tambayar su ya labarin wajen jikin Andizo suka ce da sauƙi ɗazu suka kira aka ce ta samu bacci, gyara zama ta yi ta ce “Mamma ina Ahmad yake?” Kafin Mamma ta ce wani abu sai ga shi ya iso palon sanye da ƙananan kaya na zaman gida, kallon shi ta yi tana miƙewa tsaye ta ce “Yaya Ahmad ina wuni?” Sai da ya zauna sannan ya ce “Lafiya lau Amira ya gida?” “Alhamdu Lillah, dama wajen ka na zo.” “OK to muje ɓangarena.” Gaba ya yi ta bi bayan shi tana ta addu'ar Allah ya sa kar ya ƙi amincewa buƙatar da ta zo mishi da ita... _Maman Nusaiba ce_ [7/5, 3:39 PM] Ummu Amjad: ADZ 45 A palo ya mata masauki ta zauna tana bin ko'ina da kallo, wajen fes-fes da shi sai ƙamshin turaren wuta ke tashi mai Sanyin daɗi, lumshe ido ta yi ta shaƙi ƙamshin sai kuma ta yi saurin buɗe ido tuna abin da ya kawo ta. Gyara zama ta yi sai ga shi ya kawo mata ruwa a gora ya zauna tare da miƙa mata fuska a sake, amsa ta yi itama ta mishi murmushi ta ce “Merci.” Kawar da kai gefe ya yi sai da ta gama sha ya juyo ya fuskance ta ya ce “Amira me ke tafe da ke?” “Alfarma na zo nema a wajen ka yaya Ahmad, duk da nasan da wahala ka mini ita saboda girman ta.” Da mamaki ya ce “To wannan ɗin wata irin alfarma ce mai girma haka Amira? Kawai ki faɗa naji in dai ba ta fi ƙarfina ba in sha Allah zan miki, ko kin manta ke ƙawar matar da zan aura ce wadda take ji da ita sosai?” Ya faɗa yana ƙare mata kallo. Sunkuyar da kai ta yi ta sa hannu ta goge hawayen da suka zubo mata, shi ne kallon ta yake har ta zame ƙasa ta durƙusa a gaban shi tare da haɗe hannaye waje ɗaya ta ɗago kanta hawaye sun wanke mata fuska kuka ya kwace mata. Zaro ido Ahmad ya yi yana faɗin Subhanallahi! Amira Wai me ke faruwa? Ki sanar da ni don Allah.” Tsayar da kukan ta yi ta ce “Ban san da wata fuska za ka kalle mi ba yaya Ahmad, amma idan har za ka mini wannan alfarmar ka ɗauke ni da kowacce irin siffa ma na yarda in dai a kan buƙatar da na zo maka da ita ne.” Tagumi ya yi yana jiran ya ji wannan buƙata ta Amira da ta saka ta kuka, goge hawaye ta yi ta ɗora da cewa “Don Allah ka ji tausayin Uncle ɗina Yaya Ahmad har ita kanta Khadija ka musu rai kar ta dalilin ka a yi gawa biyu a lokaci ɗaya, Khadija tana matuƙar son Uncle nasan kaine ka hure mata kunne ta fasa kula shi har aka kai ga sa muku rana, idan da za ka ga halin da Uncle Sultan yake ciki Wallahi ko wata irin ƙiyayya kake mishi dole ka tausaya mishi. Abin da ya kawo ni wajen ka ina so ka janye maganar auren ka da Khadija ka bar wa Uncle ita don Allah, ni ban san da wata kalma zan yi amfani ba wajen fahimtar da kai irin raɗaɗin da zuciyar Uncle take ciki ba tun ranar da ta sanar da shi an sa muku rana kar ya sake kiran ta, tun daga lokacin ba a kuma gane kanshi ba ko da ya farfaɗo sunan Khadija ne a bakinsa yana mai roƙon ta kar ta rabu da shi, sanin da ta mishi a da daban ne yanzu ya dawo mutum kamar kowa ta dalilin wa'azin da take mishi, ka yi hakuri don Allah ka je can ƙauye ka ce musu ka janye auren ka da ita shi zai aure ta..” Baki Ahmad ya saki yana kallon Amira jin abin da take faɗa masa, ta ya zai ce ya fasa auren Khadija a yayin da take cikin matsananciyar rashin lafiya? Dogon numfashi ya ja yana kaɗa kai ba ya ji akwai abin da zai sa shi ya fasa auren ta, idan kuma ya tuna irin halaccin da Sultan ta mishi a rayuwa sai ya ji gwiwarsa ta yi sanyi, ɗago kai ya yi zai yi magana Amira ta yi saurin tarar numfashinsa ta ce “Ina so ka kalli wannan photuna da video ka ga halin da yake ciki, idan har ka kalla ba ka tausaya mishi ba ka mishi sadaukarwa, to ba zan sake bibiyar ka ba a kan wannan maganar zan ce mishi ya haƙura idan kuma ya mutu To Allah ya jiƙan shi..” Jiki ba kwari ya amshi wayar da Amira take miƙo mishi, a hankali ya kunna video nan take Sultan ya bayyana a video, an sa mishi na'urori hanci da hannu da saitin zuciyarsa ya rame sosai fuskarsa hanci kawai kake gani a miƙe, cikinsa ya faɗa kamar na macen karya yadda kasan ba a taɓa zuba mishi wani abu mai suna abinci ba haka yake, magana yake amma ba a ji sai ya ga Amira ta iso kusa da shi tana mishi magana tana shafa kansa hawaye na bin kuncinta. Ɗayan vidéo ya kunna in da ya ganshi a zaune Mom na ba shi shayi yana sha da kyar, Amira ta amshi shayin Mom ta fita ya kalle ta ya ce “Thank you Meera.” Girgiza kai ta yi ba ta ce mishi komai ba ya ɗora da cewa “Amira ki je ki kawo mini Khadijata kin ji, ni nasan ƙarya ta faɗa mini kawai dan ta ga na dame ta da kira ne ta ce an sa mata rana da abokina, shi fa da kansa ya ce ta ce ba za ta taɓa auren shi ba tun da ya kasance ƙanen mijinta, yanzu kuma sai ta ce wai shi ne za ta aura ba ni ba? Nasan Khadija tana sona.” Ya ƙarashe maganar yana dafe ƙirji Amira ta yi saurin miƙa mishi ruwa, sai da ya sha ya kuma ce mata ta je ta gano masa Khadija kuma su dawo tare, to ta ce ta taimaka mishi ya koma ya kwanta, har ta miƙe tsaye ya ce “Idan kuma da gaske abokina ne zai aure ta bai kyauta mini ba, domin na ɗauki shekaru ina sanar da shi irin son da nake mata shi kansa a lokacin kallon mahaukaci ya dinga mini, har cewa yake wa ya sani ba ko Khadijar tawa aljana ce na ce naji watarana zan kawo mishi ita ya ganta ashe ma a gidansu take rayuwa, bayan ya san ita ce me ya sa ai mini haka?” Ya faɗa yana juyar da kai gefe, haƙuri Amira ta ba shi tana kuka ta sanar mishi za ta tafi ta zo mishi da Khadija har cikin asibiti sai ya saki murmushi yana kallon ta daga nan vidéo ya ƙare. Ɗago da kai ya yi idanuwansa sun yi jajur ya kalli Amira da ta sunkuyar da kai ƙasa tana jira ya gama ta ji me zai faɗa a kan ɗan'uwanta, idan har wannan video bai sa ya ji tausayin shi ba ta yi alƙawarin ba za ta kuma zuwa gidansu ba abotar ma da Khadija za ta daina ta koma ta ci gaba da rarrashin ɗan'uwanta. “Amira in dai saboda da maganar an sa bikinmu ne abokina ya shiga wannan halin na janye auren Khadija na bar mishi ita, Wallahi ban san abin ya kai har haka ba da ba za akai wannan lokacin Sultan bai auri Khadija ba, zan sanar da kowa na fasa auren Khadija na sadaukarwa mishi da ita har abada tashi muje.” Wani irin matsanancin farin ciki ne ya lulluɓe zuciyar Amira ta ɗago da sauri tana dariyar murna hawaye na zubo mata, kafafuwansa ta dafa kamar wata zautacciya ta ce “Da gaske kake yaya Ahmad ka bar wa Uncle Khadija? Kai waiyo Allah Alhamdu Lillah, na gode sosai yaya Ahmad Allah ya saka maka da alheri lalle ka cika abokin kwarai.” Murmushi ya yi ya ce “Da gaske ne mana tashi mu tafi.” Tashi ya yi ta miƙe ta bi bayan shi bakinta ya ƙi rufuwa, a palo suka samu Hajiya ta mata sallama suka fita waje. Har bakin mota ya raka ta ya sanar da ita gobe ta zo su tafi ƙauyen su Khadija ta ganta, cike da farin ciki ta amsa da to ta ja mota ta wuce, da kallo ya bi motar yana girgiza kai har ta fita sannan ya dawo.. Da dare bayan sun ci abinci ana hira Ahmad ya dubi Hajiya ya ce “Ina so zan faɗa muku wata magana ban san da mai za ku ɗauke ta ba, amma duk abin da kuka ji da gaske nake kuma na yi shi ne dan sadaukarwa.” Duka palon suka kalle shi Hajiya ta ce “To kai kuwa Ahmadu mene ne shi haka wadda kake tunanin za mu kalle ta ta wata fuskar?” Gyara zama ta yi ya yi ƙasa da kai ya ce “Daga yanzu na janye aure na da Khadija.” Hajiya ta matso kusa da shi da sauri tana tafa hannu ta ce “Wannan ɗin wacce irin magana ce Ahmadu? Anya ba ka fara shaye-shaye ba?” “Babu abin da nake sha Hajiya ina cikin hankalina, nima ba da son raina zan yi hakan ba sai dan na yi saukarwa ga abokina Mr J.” Shuru suka yi suna kallon shi, Hassana ta nisa ta ce “Wallahi Yaya dama ni na jima da ganin soyayyar Mr J a idanun Khadija, musamman lokacin da ya kaita asibit, na tabbata ta fi son shi sama da kai a zuciyarta kawai dai faɗa ne ba za ta yi ba.” Hussaina ta amshe maganar da cewa “Tabbas haka ne domin na taɓa jin ta wata rana tana waya tana kuka tana sanar da Anty Aminatou, auren ka da za ta yi kawai dan farin cikin su Maigari da su Hajiya za ta ba dan tana jin ka a zuciyarta ba, amma ita Sultan take so kawai dai dan ba shi da hali mai kyau shi ya sa ta dangana ta zaɓi ta faranta muku rai ita ta ba wa zuciyarta haƙuri, da aka ce zuciyarta ta fara kumbura na karo na biyu na so na sanar da ku abin da naji tana faɗa sai kuma na yi gum da bakina, amma dama can Sultan take so ba kai ba Yaya kuma naji daɗi da ka haƙura ta auri wanda take so, Allah dai ya ba ta lafiya.” Ta ƙarashe maganar tana goge hawayen da suka zubo mata. Shuru palon ya yi Abba ya girgiza kai yana nazarin maganar ya rasa ta ina zai fara sanar da Maigari Ahmad ya janye auren Khadija, Mamma ta janye tagumin da ta yi ta ce “Allah ya sa hakan shi ne mafi alkhairi a gareka, kuma ka kyauta da ka yi hakan.” Murmushin yaƙe Ahmad ya yi ya ce “Dan ma, ba ku ga halin da yake ciki ba da sai kun miahi kuka. Nan ya kwashe komai ya sanar su har vidéo da ya gani da bayanin Amira, gabaɗayan su jikinsu ya yi sanyi da jin labarin Sultan suka mishi addu'ar samun lafiya. “Gobe ni zan je na fara fahimtar da Maigari komai ba sai ka je ba Abba.” Ya faɗa yana tashi ya wuce.. Washegari ya shirya ya nufi gidan su Amira da ta miahi kwatance, yana isa suka fito ita da Mama ya fito ya buɗe musu mota suka kama hanya.. Kamar yadda aljani Najibu ya yi alƙawari da su Malam suka dawo ya dawo shima ya kuma kawo abokan aikinsa, sai da aka yi dambarwa da su sosai sannan wani daga cikin su ya ce “Mu za mu tone sihirin da muka binne, amma ba fa iya wannan ba ne sihirin da ke jikinta akwai baƙin sihiri da aka yi mata, shi ne wanda bakinta yake cika da ƙuraje a zare mata kuzari ta kasa tashi, idan ta kwanta a danne mata ƙirji ta kasa tashi sai lokacin da suka ga dama su rabu da ita, kowanne daban-daban ne.” Malam ya yi tasnima yana kallon Khadija ta aka birkice ta ƙafafuwanta a lauye bakinta ya karkace, jinjina kai ya yi ya ce “To su ina suke?” Dariya aka yi sannan ya ce “Ku nemo su kamar yadda kuka nemo mu.” Malam ya kalli liman ya ce “Lalle yarinyar nan ko su waye suka mata wannan ɗanyan aikin sun cika azzalumai na ƙarshe. To shi kenan ku tone ku lalata shi idan kuma kuka, mini ƙarya dukkan ku sai na ƙona ku daga ku har waɗanda suka buya.” “Haba Malam ai mun yi maka alƙawarin hakan yanzu haka ma ɗaya daga cikin mu ya tone ga shi can yana lalatawa, idan muka fita a jikinta za ta yi amai baƙi hakan shi ke nuna ta amayar da cutar da ke cikinta saura ɗayan.” Suna faɗin haka sai gani suka yi ta maƙure a waje ɗaya ta dinga jero attishawa, sai da ta yi bakwai sannan ta soma tari sai amai ya biyo baya mai wani, sai da ta gaba tas Umar ya ɗauko ruwa ya zuba mata a bakin ya ce ta kuskura bakinta ta zubar, sai ta wanke har fuskarta sannan ta ɗago kai tana kallon su. Liman ya kiran sunanta ta amsa tana bin su da kallon mamaki, gefe Umar ya janye ta Maigari ya ce su canja wajen zama su koma can gefe a gyara wajen, ita dai kamar raƙumi da akala haka take bin su tana jikin Umar sai sannu yake jera mata. Bayan, sun zauna Malam ya ƙara gyara zama ya fara karatu yana yi yana fes mata ruwan addu'ar da ke gefen shi. Sai da aka ɗauki lokaci mai tsayi sannan aka samu nasarar samun su, ɗaya daga cikin su ya ce “Malam ka yi haƙuri karka ƙona mu za mu faɗa.” Gyara zama Malam ya yi ya ce “To ina jin ku me ya sa kuke cutar da baiwar Allah?” “Ka yi haƙuri Malam muma saka mu ne aka yi amma za mu rabu da ita, duk sihirin da muka mata za mu warware.” Sai da Malam ya jigatar da su sosai sannan ya umarce su da su warware komai kuma su fita daga jikinta, cikin ladabi suka bai wa Malam haƙuri sannan suka ce sun warware komai tukun ya ba su izinin fita, haka ta dinga jero attishawa har sai da Umar ya riƙe ta saboda ƙarfin attishawar sai da ta yi kamar za ta kifa. Hamdala suka yi suna yin kabbara tare da yi wa Allah kirari da ƙarfin ikonsa an yi nasara yau sun fita gabaɗaya. Ruwan addu'ar Malam ya ba da ya ce ya dinga shafe mata jiki da shi in za ta kwanta, godiya sosai suka mishi Maigari ya rasa da me zai saka wa wannan baƙin malaman masu ɗinbin tarin albarka da suka zama sanadin warakar jikarsa mafi soyuwa a zuciyarsa, shi ya sa ake cewa baƙo raɓa ne kuma rahama ne.. Ƙarfe 1:20pm suka iso garin in da aka musu jagora har cikin gidan. Sai da suka gaisa sannan Ahmad ya gabatar musu da Amira da mamanta sun zo ganin Khadija, sosai Hajja ta ji daɗi ta musu jagora zuwa ɗakin da Andizo ke kwance tana baccin wahala, shi kuma Ahmad ya nufi wajen Maigari domin faɗa masa abin da ya kawo shi ko sun koma a kan lokaci. Suna shiga ɗakin a zaune suka same ta tana murza ido, da sauri Amira ta isa in da take ta ce “Alhamdu Lillah Khadija.” Saurin buɗe ido ta yi sai ganin Mama da Amira ta yi a gaban ta, sake murza ido ta yi ta ɗauka ko gizo ne suke mata sai da ta ji Amira ta rungume ta ta fashe da kuka, itama kukan take sai suka ba wa Mama tausayi ta same waje ta zauna tana kallon su.... _Maman Nusaiba ce_ [7/9, 12:06 AM] Ummu Amjad: ADZ 46 Sai da suka gama kukan ganin juna sannan Amira ta fara ɗago da Andizo daga jikinta tana ƙare mata kallo, wani irin tausayin ta take ƙara ji na shigar ta ganin yadda ta koma kamar ba ita ba, itama kallon ta take tana tuna maganar su ta ƙarshe da ita. Sai da Mama ta gaji da abin nasu ta ce “Khadija sannu ya jikin naki?” Dogon numfashi ta sauke ta juyo ga Mama tana gaishe ta har tana tambayar baban Amira Mama ta ce yana lafiya. Bayan sun huta sun ci abinci Hajja ta zo ta fita da Andizo Amira har za ta bi su Mama ta riƙe ta tana dakatar da ita, “Ki tsaya su dawo mana kika sani ko magani ne za a ba ta?” Turo baki ta yi ta zauna tana faɗin “Ni ba na so ta haɗu da yaya Ahmad har sai na sanar da ita komai, kinga ko da ya yi mata maganar za ta fi fahimtar shi.” Hajja ba ta zarce ko'ina da Andizo ba sai ɗakin Maigari wanda suke tare da Ahmad. Tun da ta sako ƙafa yake kallon ta cike da tsananin tausayin ta, tuna ya sadaukar da soyayyar da yake mata sai ya ji zuciyarsa ta ƙara karaya nan da nan idanuwansa suka cika taf da ruwa ya yi saurin sunkuyar da kai yana dafe saitin zuciyarsa, ita kanta sai ta ga Ahmad ɗin ya rame sosai sai ta danganta hakan da rashin lafiyar da ta kwanta, zaunar da ita Hajja ta yi itama ta samu waje ta zauna Maigari yana mata sannu ta sunkuyar da kai ƙasa ta ce “Yaya sannu da zuwa, dama tare kuka zo da su Amira?” Murmushi ya sakar mata ya amsa, “Yawwa Khadija ya jikin naki? Tare muka zo da su.” Maigari ya gyara zama ya kalli Andizo ya ce “Uwata waye Sultan?” Saurin ɗago kai ta yi ta kalli Maigari sai kuma ta juya akalar kallon mata ga Ahmad idanuwanta suna mishi kallon ya aka yi Maigari ya san Sultan, alama ya mata da ta amsa mishi kawai ya kawar da kai gefe yana jin wani kalar zafi da raɗaɗi na sukan heart ɗin sa. Sai da Maigari ya sake tambayar sannan ta ita ba shi amsa a sanyaye, “Maigari shi ne mahaifin Farrah ƙawata kuma ɗa ga Mom.” Da mamaki Maigari ya ce “To ikon Allah! Wai dama ɗan hajiya ne?” Gyaɗa mishi kai ta yi shi kuma ya ci gaba da magana, “Ahmad ne ya zo da maganar ya janye maganar auren ki ya haƙura.” Saurin kallon Ahmad ta yi cike da mamakin abin da ya sa Ahmad ya janye maganar auren nasu, ta san yana matuƙar son ta ita ce dai ba ta jin son shi kamar yadda shi yake nuna mata, ajiyar zuciya ta sauke ta yi ƙasa da kai saboda da wani sanyin daɗi da ya mamaye zuciyarta, amma duk da haka ta ji babu daɗi saboda yanzu ta fara son shi tun lokacin da ta danni zuciyarta ta ba ta haƙuri musamman yanzu sai ta ga ya ƙara mata kyau da kwarjini a idanu duk da ya ɗan rame. Maigari ya ƙare musu kallo sannan ya kwashe duk maganar da Ahmad ya sanar da shi ya faɗa mata, sannan ya ƙara da cewa “Na tabbata Ahmad ba zai bari wani wanda ba mutumin kirki ba ya aure ki, kuma mahaifiyarsa tana da kirki za ta riƙe ki kamar ɗiyar da ta haifa. Yanzu ke ya kika gani kina son shi ɗan nata kin amince na sa a ƙara mini bincike da kansa duk da bayanin da Ahmad ya ba ni game da shi? Za ki aure shi uwata? Yanzu haka yana can kwance a gadon asibiti rai a hannun Allah, Ahmadu ya ce mini shi kaɗai ne ɗanta namiji sai mace ɗaya.” Hankalin Andizo ya tashi matuƙa duk saboda da ita ne ya kwanta a gadon asibiti, amma da ta tuna ɗabi'u da halayensa sai ta haɗe rai tana kumbura baki ta kalli Ahmad suka haɗa ido, tausayi ya ba ta ta gammace gara farin cikin wannan ahali da nata farin ciki, za ta sadaukar da soyayyarta saboda da su domin sun yi mata halaccin da ba kowanni ɗan'adam ba ne zai iya yi. Maigari ya gyara babbar rigarsa ya ce “Uwata ba ki komai ba shin kina son shi ko kuwa ba ki son shi? Ki ba mu amsa ɗaya mu ba za mu yi miki dole sai kin aure shi ba.” Shuru ya ratsa ɗakin na wajen sakan talatin duk sun zuba mata ido suna jiran jin abin da za ta faɗa, ita kuma maganar ta ke kan harshenta take son faɗa amma zuciyarta na gargaɗin ta a kan kalmar da take son fitarwa, runtse ido ta yi da ɗan ƙarfin da ya rage mata ta cije lip ɗin ta na ƙasa sannan ta ce “Ku ɗin kun kasance bango abin jingina a gareni Maigari, matuƙar akwai abin da zan yi na saka ku cikin farin ciki to komin wahalar shi in dai bai saɓa wa shari'a ba to zan yi muku shi, Salim shi ne fitilar da ya haske rayuwata ta zamo ingantacciya, duk wani abu na rayuwa in dai ya shafi ilimi zai kaini na koya ko kuma shi ya kowa mini har na iya.” Ta ɗago ta kalle su ta ga duk sun zuba mata ido baki sake, sharce majina ta yi tana zubar da hawaye zuciyarta na ƙara limka ciwon da take ji har numfashi in ta ja sai ta ji kamar za ta kurma ihu, amma ta daure ta cije tana huci ta ɗora da cewa, “Yanzu kuna ganin wannan mutumin ya cancanci na ƙi duk wani wanda ya haɗa alaƙar jini da shi? Shi ne fa wanda ya kashe maƙudan kuɗi ya saka ni à makaranta da rayuwata gaba ta zama mai kyau, yanzu kuma babu shi sai na nuna ba zan auri ɗan'uwansa ba? A da ciwon mutuwarsa ya sa na tsani maganar aure, sannan yadda muka zama abokan faɗa ni da Yaya Ahmad ya sa naji ba na so shi, amma yanzu ni yaya Ahmad nake son ƙarashe rayuwata da shi ba Sultan ba, dukkan ku ba ku san waye Sultan ba shi ya sa kuke ƙoƙarin ba ni shi a matsayin abokin rayuwa, ba ya Sallah, ba shi da tausayi, duk wani abu da ya shafi addini Sultan bai sani ba a haka kuke so na zauna da shi? Shin kun san wani irin lefi ya aikata mini? Wannan ni kaɗai na bar wa kaina sani sai kuma shi da ya yi abin, amma tun da na ga kuna jin tausayin shi yau zan faɗa muku abin ya haɗa ni da shi.” Ta sake ɗagowa tana kallon su a karo na biyu.. Baki buɗe Ahmad ke kallon Andizo zuciyarsa na mugun bugawa da ƙarfi har sai da ya sa hannu ya dafe, tabbas ya san in me Khadija ta faɗa shi ne sila tun da ya faɗa mata aibun Sultan har sai da ya ga tsoro a idanuwanta sannan ya rabu da ita, yanzu kuma ga shi an zo lokacin da yake son su haɗu su ceto rayuwar abokin nasa amma ya ga wankin hula na neman kaishi dare. Maigari ya sauke ajiyar zuciya ya ce “To ke wani mugun abu ya miki haka da kike aibata shi? Ko kin manta shi ɗa ne ga hajiyar nan da ta ceto rayuwarki daga hannun mutanen da suka sace ki?” Goge fuskarta ta yi ta ce “To ai shi ne mug..” “Surbajo ya isa haka! Tashi ki tafi tun da dai Ahmad kika zaɓa ba mai miki dole.” Suka jiyo muryar Giɗaɗo daga bakin ƙofa duk suka bi shi da kallo har ya iso cikin ɗakin ya zauna. Kallon ta ya yi ya nuna mata hanya da hannu ya ce “Je ki kwanta ki huta kin ji, so samu ma ki yi bacci ko kin ƙara jin ƙarfin jikinki.” Duk da tana jin jikinta wani iri amma hakan bai hana ta hararar shi ba tukun ta yunƙura za ta tashi Maigari ya dakatar da ita ya ce “Idan kin je ki kira mini Innarki.” Kai kawai ta gyaɗa ta ɗago suka haɗa ido da shi, murmushin yaƙe wanda ya fi kuka ciwo ya yi ya ce “Na gode Khadija idan kin je ki kira Mama.” A hankali ta tashi Hajja ta ce “Ko na raka ki?” Girgiza kai ta yi ta fita ɗakin tana goge hawayen da suka zubo mata, kicibus suka yi da Umar ta kalle shi ganin yadda idanuwansa suka yi jajur, a hankali ta ce “Hamma za ka shiga ciki ne?” E kawai ya ce mata ya yi gaba ya shige ciki itama ta wuce. Tana isa ɗaki ta sanar da Mama Maigari na son ganin ta ta tashi da hanzari ta fita, bayan ta fita ne suka dasa hira da Amira in da take sanar da ita irin yadda Sultan yake ambaton sunanta yana son ganin ta, ita dai murmushi kawai take tana faɗin “Allah sarki Daddyn Farrah Allah ya ba shi lafiya.” Amira sai ta amsa da amin har Mama ta dawo ta same su, Mama ta ƙara yi mata Allah ya ba da lafiya sannan ta ce da Amira ta tashi su tafi Ahmad yana bakin mota. Gabaɗaya suka fito har Andizo suka iso bakin motar ta yi wa su Mama godiya sannan ta matso kusa da Ahmad ta turo baki gaba ta ce “Shi ne ko ka ce mini ya jiki?” Ƴar dariya ya yi ya ce “Haba ji ne dai ba ki yi ba, amma na faɗa a ɗakin Maigari yanzu kuma sai ranar biki za ki dawo birni?” Kai ta gyaɗa mishi ya ɗaga hannu ya juya ya shige mota, tana tsaye sai da suka bar wajen sannan ta juya ta koma ciki. Zama ta yi a cikin ɗaki tana karanta wasiƙar jaki har bacci ya ɗauke ta. Sai da Andizo ta yi sati ɗaya tana shan rubutun da Malam yake aiko mata kafin ta samu kuzarin ta ya soma dawowa, sosai Inna ke kula da ita tana jiƙa mata wani tsumi ta haɗa mata da zuma ta ba ta ta shanye, idan za ta kwanta ta tafasa bagaruwa da lalle da ganyan magarya ta shiga ciki ta zauna har sai ya huce sannan ya fito, gyara na musamman irin na gargajiya Inna ke yi wa Andizo, kaji da zabo kuwa kullum sai an dafa mata su ta ci nan da nan ta maida jikinta hasken fatarta ya fara dawowa. Tana cika kwana goma aka daina ba ta komai sai kanumfari da ake jiƙa mata shi Inna ta ce ta mayar da shi ruwan shan ta zai taimaka mata sosai, da farko sam ƙin shan ta yi sai da Inna ta zaunar da ita ta faɗa mata kanumfari shi kaɗai gayya ne yana maganin infection, basir, ɗaurewar marar yayin al'ada, wanke ciki, da sauransu. Bayan ta ji wannan bayani game da kanumfari sai ta dinga sha kamar ba gobe.. Kwanakin da aka ƙara na biki sakamakon rashin lafiyar amarya sun karato ya rage saura sati ɗaya, a ranar dangin aka kawo lefin Andizo tare da su Hassana da ƙawayen Mamma da 'yan'uwanta, ranar mata har gida suke zuwa suna ganin kayan lefen da aka kawo wa Andizo a karo na biyu, wasu cewa suke wannan lefen ya fi ma na auren farko yawa akwati goma sha biyu cif a jere kowacce cike da kaya na alfarma. A kawo kaya da kwana ɗaya Amira ta kira Andizo a waya tun daga sallamar ta gane ƙawar tata a fusace take, can ta shige ƙuryar ɗaki ta zauna a bakin gado sannan ta ce “Ƙawata ya dai naji ki haka me ya faru?” Daga can ɓangaren Amira ta hayayyaƙo mata kamar za ta fito daga wayar ta rufe ta da duka. “Ai ko me ya faru ke ce sila Khadija, na ɗauka ke ɗin ƙawa ce ta amana ashe ba haka ba ne, yanzu Khadija kin zaɓi Ahmad a kan Uncle? To ba komai kin kyauta kuma na gode kin ji Khadija, amma ina so ki sani ba ke kaɗai ba ce 'ya mace a duniya akwai mata bil'adadin da suke bin kan Uncle ya aure su amma ya kafe ya ce ke yake so, sai ga shi kin ƙi shi kin zaɓi wani a kansa. Khadija ina so ki sani ni Amira in sha Allah zan auri Uncle kuma na zame mata komai a rayuwa, zan nuna mishi soyayya da tattali da kulawa saboda da shi ɗin jinjina né shi ba zan sake bari ya ambaci sunanki ba balle har ya ji ba daɗi a ransa, dan haka sai an jima dama abin na kira ki na sanar da ke an sa mana aure da shi sai an jima.” Wayar ta bi da kallo tana nanata sa rana, shuru ta yo tana kallon gefe. Can Farrah ta faɗo mata a rai ta tuna yadda suke son juna da yadda yarinyar ke nuna sha'awar ta zama matar mahaifinta, amma ita kuma ta ji ba za ta iya zama da shi ba a matsayin miji saboda ba ya Sallah, haka dai ta karaci tunaninta ƙarshe ta kawar da komai tana maƙe a fili ta furta “To ni ina ruwana dan za ta aure shi? Ita ta ga za ta iya sai ta runguma.” Fita ta yi daga ɗakin ta nufi cikin yan matan da suka zo mata zaman wuni har da wadda za ta mata lalle da kitso a cikinsu. Zama ta yi aka fara yi mata suna mata waƙa ita kuma tana dariya.. Biki ya kankama ana ta hidima yau ta kasance saura kwana ɗaya ɗaurin aure, Ahmad ya kira ta a waya bayan sun gaisa ya ce “Khadija na tura miki saƙo ta whatsapp ban ga kin ɗaga ba, kayan fitar gobe nake so ki zaɓa mana a cikin waɗanda na tura miki.” Lomar da ta sa a baki ta haɗiye sannan ta ce “To bari yanzu zan shiga na duba ban gani ba ne duk na shiga hidima ne.” “Hidimar ai daga ta gobe ta gama, sannan dama ina so na faɗa miki daga nan daret Diffa za a wuce da ke, ni gobe idan aka gama ɗaura aure da su Abdoul za mu huce can mu zauna.” Ya faɗa yana buɗe dinkin shadda blue ya sha zubin zare. “Allah sarki Yaya Abdoul na kwana biyu rabon da mu gaisa, zan nuna maka wadda na zaɓa yanzu sai an jima.” To ya ce sannan ya kashe, daret ta shiga whatsapp ba ta tsaya buɗe saƙon kowa ba ta zarce kan nashi duk da kuwa sakonnin da ta gani rututu, bayan ta ɗaga ta duba kayan can dai ta nuna mishi farar shaddar ita za su saka gobe ya amsa da cewa “To shi kenan Allah ya kaimu lokacin.” Amin ta faɗa sannan ta aje wayar. Masu iya magana na cewa rana ba ta ƙarya sai dai uwar ɗiya ta ji kunya, a yau ne aka cika a babban masallacin juma'a da ke ƙauyen aka zauna domin ɗaura auren mutum uku, bayan Andizo akwai wasu yan mata biyu da bikin masu ya rana ɗaya, hakan ya sa aka haɗa ɗaurin auren a waje ɗaya. Sai da aka ɗaura auren Andizo sannan aka ɗaura na sauran, duk in da ka nufa a garin baƙi ne wasu daga Niamey wasu maƙotan ƙaiyukan da suka gaiyato har ma da fulanin yankin duk Maigari ya gaiyato su, su sauran amaren da yake duk Maradi za a kaisu mutanen Maradi dayawa sun halarci ɗaurin auren, kasancewar ɗaya daga cikin yan matan ɗan mai kuɗi ne ta aura babansa ɗan kasuwa ne sananne, ga kuma na su Ahmad suma Daddy ya gaiyato mutane manya-manyan yan kasuwa. Tun daga farkon titin da zai sada ka da masallaci har kofar gidan Maigari motoci ne sun fi ashirin, su Ahmad sun kawo motar kusan goma yayin da ɗan mai kudi ya kawo motoci fiye da goma, ɗayar amaryar ce aka zo da mota uku.. Bayan an gama ɗaurin aure aka fara shirin kai amarya gidanta. Wankan turare Andizo ta fesa duk in ta ta ɗaga a jikinta ƙamshi yake, sosai aka tsantsara mata kwalliya ta gani ta faɗa, ita kanta ta san chocolate ɗin fatarta ta haska sai sulɓi take ga ƙamshi na tashi daga jiki. Ana yin Sallar La'asar Andizo ta ce sai ta wanke kwalliya ta yi Sallah, Ɗahare ta ce ba za ta wanke ba tun da ta yi alwala kawai ta yi Sallah, amma ta ce ita fa sam sai ta wanke kwalliyar nan dama ba ta ce a yi mata kwalliya ba a bari a yi La'asar su ne suka matsa mata ta yo alwala a yi in an gama ta yi Sallah. Ba yadda suka iya dole suka rabu da ita ta shiga banɗaki ta sa sabulu ta wanke tas ta ƙara watsa ruwa sannan ta yi alwala ta fito ta gabatar da Sallah, bayan ta gama Ɗahare ta dube ta ce “Sai ki zo a sake Angonki dai shi zai yi biya biyu ai.” Baki ta murguɗa ta ce “Tab! Wace ce za a yi wa kwalliya? To ba dai ni ba fauda kawai za ta sa mini na sa kwalli ni ba na son kwalliyar nan, kafin ma mu je ai ta lalace.” Kyale ta Ɗahare ta yi ta wuce mai kwalliya ta mata simple kwalliya Sosai ta yo kyau, haka dai aka shirya aka yi mata nasiha sosai tana kuka wiwi da kyar aka banbare ta daga jikin Maigari aka sa ta mota, sauran masu rakiya suka shiga aka kama hanya. Maimakon ta ga an kama hanyar Diffa sai ta ga sun kama hanyar Niamey ta yi shuru tana kallon gefe, da an jima Ahmad sai ya kira ta yana tambayar a in suke ta sanar da shi. Suna isa daret airport suka nufa ta bi wajen da kallo karo na biyu kenan da ta taɓa zuwa airport, ba su fi minti arba'in da zuwa ba jirgin da zai kaisu Diffa ya sauka nan suka fito suka nufi inda zai sada su da jirgin. Bayan sun shiga sun zauna da yan mintoci jirgi ya cika suka tashi.. Zuwa cikin dare suka yi inda Abdoul da wasu matasa guda uku shi na huɗu suka zo da motoci manya suka kwashe su zuwa gidan amarya. A wani katafaren gida suka fara hon maigadi ya zo ya buɗe musu get suka kutsa kai ciki, babbar harabar gidan duk da dare ne amma an ƙawata ta da shukokin flowers masu kyau, gidan hawa huɗu ne. Bayan an fito da amarya suka wuce ciki, faɗin tsaruwa da girman palon ɓata baki ne, ya rakiyar amarya kowa sai kallon gida yake yana faɗin “Ma sha Allah gaskiya gidan nan ba dai tsaruwa ba.” Wasu mata suka zo suka musu sannu da zuwa da gabatar musu da abinci da in da za su kwanta haƙarƙarinsu su huta, sosai suka yaba da kirkin matan suak wuce ciki, Ɗahare da Andizo da babar Hajaru su ku za su kwana a ɗaki ɗaya, sauran kuma suma suka shiga dakuna uku suka rabu, Sallah suka rama magariba da isha'i suka ci abinci sannan suka bi lafiyar gado. Andizo kasa bacci ta yi sai juyi take tana kallon gefe, a hankali ta janyo wauarta ta shiga whatsapp ta yi wa Ahmad saƙo. Ba a jima ba sai ga kira ta yo saurin danne ƙaran ta ɗaga ta ƙara a kunne tana sauke ajiyar zuciya. A hankali ya ce “Khadija duk gajiyar ce ta sa kika kasa bacci? Ki je ki yi wanka za ki ji daɗin jikinki, idan kuma wani abu kike buƙata ki sanar da ni.” Ƙasa-kasa ta yi da murya sannan ta ce “Yaya shi ne ko ka zo na ganka ka ɓoye kamar kai ne amaryar?” Ƴar dariya ya yi ya ce “Ba ɓuya na yi ba, nima ina son ganin ki to kinga akwai mutane a tare da ke shi ya sa ban ko leƙa b sai gobe da safe za mu je mu gaisa mu raka su su tafi gida.” Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ce “Shi kenan sai an jima.” To ya ce mata sannan suka aje waya, ba ta ɗauki lokaci ba bacci ya yi gaba da ita.. Washegari da safe bayan sun tashi a kawo musu abinci sun karya su Ahmad suka shigo da abokansa suak gaishe su, bayan an gaisa suka tafi ce su shirya jirgin ƙarfe ƙarfe 6 na yamma za su bi suka ce ba matsala. Haka suka wuni a gidan Andizo ta ji daɗin ganin 'yan'uwa da abokan arziki sun cika gidanta sai ta ji kamar kar su tafi. Ƙarfe 5:30pm suka gama shiryawa manyan suka ƙara yi mata nasiha sannan suka fito, tana tsaye suka fara shiga mota sai ta ji zuciyarta ta karye ta sa musu kuka ita sai ta bi su, hararar ta Ɗahare ta yi tana faɗin “Uwar kilbibin tsiya jiya fa ina ji kike cewa ya ƙi zuwa shi ne dan kin raina mana hankali har kike kuka sai kin bi mu ? Matsa ki ba ni hanya na shiga kafin na bangaje ki angonki ya ga baƙina.” Dariya suka sa har ita ta goge hawayen tana ɗaga musu hannu har suka fita sannan ta juya ta koma. Ji ta yi gidan ya mata girma amma tana jin maganar wasu daga sama kamar yara, murmushi ta yi da ta tabbatar yara ne sai ta tuna su Nour, zama ta yi a kan kujera ta ce “Allah sarki yarana, ai kuwa wannan maƙociyar tawa zan sa yaya Ahmad yake kawo mini yaranta suna ɗebe mini kewa.” Bayan Sallah isha'i ta yi wanka ta ɗan yi kwalliya ta zauna, har tsoro y fara kama ta sai ta ji maganar su Ahmad suna doso ciki, gyara zama ta yi ta janyo mayafi ta rufe fuska tana jiran zuwansu. Sun Kai su goma suka shigo duk suka zauna a palo, Ahmad ya leƙa ɗakin yana murmushi ya ce “Khadija fito mana an zo yi mana nasiha.” Ya faɗa yana washe baki. Murmushi ta yi ta sauko a hankali ta biyo bayan shi ta samo waje ta zauna a ƙasa kusa da ƙafafuwansa, gaisawa suka yi da yan rakiyar ango suak dora da nasiha, bayan sun gama Ahmad ya ce ta koma ciki zai raka su yanzu zai dawo ta ce to ta shige ɗaki. Tana jin yadda yake rufe ƙofar palo ya kashe wuta ya ɗauki ledar da ya zo da ita ya nufo ɗakin, kwankwasawa ya yi sannan ya murɗa a hankali bakinsa ɗauke da sallama ya shigo, ta sauri juya baya ta yi kafin ya ƙarasa shigowa tana amsa sallama. Tana ji ya cire babbar rigarsa da hula ya aje a gefe sannan ya hayo gadon ya ƙaraso inda take ya sa hannu daga baya ya yaye nayafin, hannu ya sa ya juyo da ita fuskarsa ɗauke da murmushi ya ce “Amaryata ai kuma kunya ni da ke ta ƙare tun da muka zama miji da mata, ɗago ki kalli mijinki ke kaɗai Allah ya mallakawa.” Ya faɗa yana ɗago da fuskarta.. Runtse ido ta yi jikinta ya ɗauki rawa, murmushi ya yi a karo na barkatai ya ƙara matso da ita daf da shi, buɗe ido ta yi karaf suka haɗa ido sai kawai ta ɗora hannu biyu a ka ta fashe da kuka tana riƙe hannnunsa...” *Ku ji ni kwana biyu shuru Wallahi ina cikin damuwa ne Yayuna da ke Libiya a zaune aka kwashe su yanzu haka babu wanda ake samu a, waya. Da kyar aka samu mutum ɗaya shi ne ma har na samu nutsuwar yin rubutu. Don Allah ku taya mu da addu'a Allah ya fito mana da su daga hannun mugayen nan🤲🏻* _Maman Nusaiba ce_ [7/12, 2:55 AM] Ummu Amjad: ADZ 47 Baki ya saki yana kallon ta kamar yadda itama shi take kallo, matsowa ya yi ta yi saurin yin baya sai da ta haɗa da ƙarshen gado ta takure a waje ɗaya tana bin shi da kallon tsoro ƙarara a kan fuskarta. Girgiza kai ya yi ya cire hula ya gyara zama sannan ya ce “Nasan hakan za ta faru Khadija, ki matso ki zauna a kusa da ni zan sanar da ke abin da ya faru.” Ya faɗa yana janyo kafarta. Ihu ta sa tana faɗin “Nan ɗin ma ka biyo ni ne dan ka sace ni kamar yadda ka saba? Ina mijina yake? Me ka mishi har ka samu damar shigo mini har cikin uwar ɗaka? Ka sake mini ƙafa ko na yi maka ihu ɓarawo.” Ƙin sakin ta ya yi har sai da ya dangana ta da jikinsa, ta taƙarƙare ta gatsa mishi ciwo a ƙirji dan ya sake ta amma sai ji ta yi ya ce “Na gode Khadija ki ci gaba da cizo na in dai za ki bari na rungume ki.” Ganin dai taƙi tsayawa sai ya sake ta ta zabura ta sauka a gadon, da mugun gudu ta isa bakin ƙofar ɗakin ta buɗe ta fita duk yana zaune ko motsi bai yi ba yana kallon ta. Tunawa ta yi da wayarta tana son komawa amma tana tsoron shiga, gabaɗaya jikinta rawa yake sai safa da marwa take a palon, ta juya za ta koma ta ganshi a bayan ta ya miƙo mata wayar ya ce “Ki kira abokina.” Wartar wayar ta yi tana hararar shi, kawar da kai gefe ya yi yana isa bakin kujera ya zauna. Kiran number Ahmad ta yi ringing ɗaya ya ɗauka tana jin ya ce hello ta fashe da kuka tana faɗin “Yaya Ahmad ina kake ka ganshi nan ya shigo mini gida, kawai daga cewa za ka raka abokanka kuma sai na ga ƙato ya shigo saɓanin kai.” Sautin dariyarsa ta ji hakan ya sa ta tsayar da kuka tana hura hanci ta ce “Dariya ma na ba ka ? Ka yi maza ka zo ka ganshi kar ya sace ni.” Ahmad da ya yi tsaye a tsakiyar ɗaki ya ce “Gani nan zuwa Khadija yanzu.” To ta ce sannan ta kashe kiran ta isa bakin ƙofa tana jiran ta ji ya kwankwasa. Kamar da minti biyar sai suka ji ana buga ƙofa, da sauri ta murɗa sai ta ji a kulle ta juyo ta kalle shi, idanuwansa a rufe suke amma yana jin duk abin da take, sai da ya ji ƙaran murɗa key an buɗe kofa tukun ya buɗe ido yana kallon su. Baki ta saki tana kallon su cike da mamakin ganin su a tare, dariya Ahmad ya yi ya ce “Yar rainin hankali matsa ki ba mu hanya mu wuce mana.” Ba ta san lokacin da ta matsa daga bakin ƙofar ba sai jin muryarsa ta yi a gaba da ita, juyowa ta yi da sauri ta iso gaban shi tana shirin kama hannunsa ya yi saurin tarewa, hararar shi ta yi ta kalli Ahmad ko zai ce wani abu amma sai ta ga ya yi murmushi hakan ya ƙara saka ta a kogin tunanin anya Ahmad yana da hankali kuwa? Taya kana ganin wani ƙato yana taɓa hannun matarka amma ka yi shuru ba ka ɗauki ƙwaƙwƙwaran mataki ba? Ko dai ya koma shaye-shayen ne ba ta sani ba? Ajiyar zuciya ta sauke jin ana jijjiga ta ta kalle gefen ta, tuna maganarsu ta ƙarshe ya sa ta juyo tana faɗin “Amira kinga abin da nake faɗa miki game da ɗan'uwanki ko? Na faɗa miki ba zai canja ba kawai sai dai wani ikon Allah taɓa jikin mace shi ba wani abu ba ne a wajen shi, to ki ɗauke shi ku bar mini gida kar ya kashe min aure, ko da yake ai shi kansa wanda nake ganin zai ji ba daɗi in wani ya taɓa ni dariya ma ya yi.” Ta faɗa goge hawayen da suka zubo mata. Dafa ta Amira ta yi ta ce “To ai shi Uncle ɗin shi ne mijinki ni kuma yaya Ahmad na aura, ina fatan ku yi rayuwa mai albarka da samun zuri'a ɗayyiba ƙawata. Nasan kin shiga ruɗani ko? To idan kika kwantar da hankalinki in muka huta zan sanar da ke duk abin da ya faru har aurenki ya dawo kan Uncle, ya kamata mu tafi mon mari na ga Uncle yana harara ta.” Ta faɗa tana dariya. Baki Andizo ya saki tana kallon Amira jin maganarta ta yi tamkar saukar aradu, wai ita ce aka aura wa Sultan? Anya ba mafarki ba ne? Runtse ido ta yi da ƙarfi ta ce “Amira don Allah ki sabga mini mari ko zan tashi daga wannan baccin da nake mai cike da ruɗani.” Dariya suka sa Ahmad ya miƙa wa Sultan hannu ya ce “Aboki ya kamata ku kwanta ku huta ka ga gobe za ku koma Nigeria, daga nan kuma ku wuce London za ku sha wahala sosai in ba ku yi bacci yanzu ba. Khadija sai da safe gobe za mu dawo ki ji komai daga bakina ba daga bakin Amira ba, wanda kike dakon soyayyar sa a zuciyarki shi kika aura ba zaɓin tsohon mijinki ba, don Allah ba na son jin komai daga gareki ki kwantar da hankali ku yi bacci cikin salama da safe za ki ganmu.” Kamar gunki haka ta zama sai in ta juya ido ta kalli Ahmad ta kalli Amira da Sultan, har suka fita Sultan ya dawo ba ta motsa daga inda take ba, tunani barkatai take ta rasa wanne za ta ɗauka ta yi amfani da shi. Ƙarasowa ya yi tare da sunkuyawa ya manna mata kiss a kan laɓɓanta ta yi saurin kallon shi, hannu ya sa ya ɗago ta jiki ba kwari ya ce “Ki yi haƙuri na ɓoye miki da aka yi my wife, mu je ɗaki mu kwanta gobe za ki ji komai.” Ba dan ta so ba ta saki jiki ya ruƙo ta suka nufi ɗaki ya zaunar da ita bakin gado, ƙugu ya riƙe yana tuna irin kalar wahalhalun da ya sha kamar zai sheƙa kafin ya same ta a matsayin mata, murmushi ya sakar mata ya ce “Kin wahalar da jaririyar zuciyata my wife yanzu da sai dai ki ji labarin na mutu, yake Allah ni ya kira a matsayin mijinki sai ga shi kin zama tawa har abada, tashi ki yo alwala nima zan je na yo mu yi Sallah mu gode wa Allah da ya nuna mana rana mai ɗunbin albarka.” Ya faɗa yana fita daga ɗakin. Ita dai umarnin Ahmad take bi da ba dan haka ba da tuni ta tayar da aljannu dan dolen sa ya mayar da ita inda suka ɗauko ta, ta matsu gari ya waye domin ta ji yadda aka shirya wannan badaƙalar ba tare da ta ankara ba, miƙewa ta yi ta shige banɗaki. Bayan ta fito sai ga shi ya dawo da jallabiya milk haɗe da hula fara a kansa, kallon shi ta yi a zuciyarta ta furta “Ma sha Allah.” Ba ta san ta fito fili ba sai da ta ji ya ce “Yaya ta mini kyau ko?” Sunkuyar da kai ta yi cike da jin kunyar maganar da ta yi a zuciya ta fito fili, darduma babba ya shinfiɗa irin wadda ake shanfiɗawa idan an fita yawon shan iska, gaban wardrobe ya isa ya buɗe ya fito mata da red ɗin hijabi, tsayawa ya yi a gaban ta ya buɗe ya sa mata sannan ya kamo hannunta ya iso da ita kan dardumar shi kuma ya yi gaba kaɗan da ita, iƙama ya tayar suka soma gabatar da Sallah kamar yadda addini ya tanadar. Bayan sun gama ya juyo ya dafa kanta ta ji wani abu mai sanyi ya mamaye zuciyarta, lumshe ido ta yi tana shaƙar ƙamshin turaren da ya sa, firgicin da ta shiga ne ya sa ko kaɗan ba ta ji ƙamshin da ke tashi a jikinsa ba sai yanzu. Addu'oʼi ya yi ta jero musu na samun zaman lafiya, ita kuwa ta kasa kunne tana jin daɗin sautin muryarsa da yadda yake yin addu'ar cikin kwarewa, sosai ta yi mamakin hakan domin a sanin ta da shi a baya ya ce mata shi ko Sallah bai ma san yadda ake yi ba. Bayan ya gama ya yi mata tambayoyi game da addini ta ba shi amsa ya ja kumatunta ya ce “Ustaza Khadijatu.” Duk da tana jin haushin shi amma sai da maganar ta ba ta dariya ta yi murmushi tana kai hannu ta ɗora a kan nasa, a hankali ya zare mata hijabi ya tashi ya fita ta bi bayan shi da kallo, gabaɗaya ya rame sai tsawon kawai ta girgiza kai tana kawar da kanta gefe. Bai ɗauki lokaci ba ya dawo hannunsa ɗauke da plate da ledoji biyu, a gaban ta ya dire ya cire jallabiyar ya zauna, saurin runtse ido ta yi tana faɗin “Meye haka kuma?” Dariya ya yi ya miƙa hannu zai taɓa ta ta kauce ta ja baya, cikin zafin nama ya damƙo ta ya ɗora ta a kan cinyarsa, shuru ta yi jin bugun zuciyarsa ta ɗago ta kalli ƙirjinsa, ɗinki ta gani a ƙirji wajen ya yi huce ta ɗago kai suka haɗa ido, so take ta tambaye shi amma ta kasa hakan ya sa ya kai hannu ya shafa wajen ya ce “Ai ya warke yanzu sabon aiki za a mini nan da kwana biyu, amma zan sanar da likitan ya bari sai nan da sati ɗaya in na gama hutawa sai mu tafi ki raka ni, kuma dama ƴarki ta matsa sai ta zo na ce ta bari zan kawo ki har inda take sannan ta haƙura.” Tausayin shi ne ya lulluɓe ta amma ba ta ce mishi komai ba, kazar ya diba ya kawo bakinta ta kauce ya kalle ta yana dafe kai ya ce “Oh my wife! Ki yi haƙuri fa na ce ki ci kazar nan mu kwanta.” Ganin yadda ya narke mata kamar mai shirin yin kuka sai ta amsa tana wani yatsina fuska, haka ya dinga ba ta har ta ƙoshi sannan ya saukar da ita daga kan cinyarsa ya zuba milk ya ba ta ta sha, goge hannnunsa ya yi ya ce “To nima a ba ni.” Zaro ido ta yi ya ɗage mata gira ɗaya ta sunkuyar da kai, ta rasa me ya sa Sultan sam shi ba shi da kunya ko ta sayan gishiri. Zamewa ya yi ya ɗora kansa a kafaɗarta yana faɗin “Yunwa fa my wife Kar ta illata miki miji, yau fa ko breakfast ban ci ba.” Saurin kallon shi ta yi ya gyaɗa mata kai ya ce “Yes da gaske zamuɗin ganin ki ya sa naji duk ba na jin yunwa, sai yanzu naji kamar an mini yasa.” Murmushi ta yi ta janyo kazar ta dinga ba shi yana ci yana mata wani irin kallo wanda ya sa har sai da ta dara ta ce “Wannan kallon fa?” “Wallahi ji nake kamar na fi kowani namiji sa'a a duniya, yau dai ga ƴar kwailata ta zama babba kuma na auri abuna, ɗazu ma sai da Ahmad ya ce mini mijin kwaila na ce ai tafi matarsa hankali.” Murmushi ta yi tana girgiza kai ta ci gaba da ba shi abincin har ya ƙoshi. Bayan sun gama ta ɗauke dardumar shi kuma ya ɗauke kayan abincin ya mayar, yana dawowa ya ɗauko towel ya cilla mata ta cafe tana kallon Shi da alamun tambaya, hanyar banɗaki ya nuna mata ta maƙale kafaɗa, bai ce mata komai ba ya wuce ciki bayan kamar minti uku ya fito ya yo wajen ta. “Mu je mu yi wanka za mu fi jin daɗin kwanciya.” Ja baya ta yi ta ce “Tab! Da kai zan yi wankan?” “Kwarai da gaske da mijinki za ki yi wanka.” Ƙin yarda ta yi ganin tana ɓata mishi lokaci ne ya ɗauke ta cak ya shige banɗaki, duka take kai mishi amma ya ƙi aje ta sai jin ta ta yi a cikin ruwan ɗumi. Rasa me za yi ta yi a wannan lokacin ganin ya soma cire mata kayan jikinta, ta kulle ido gam tana jin shi ya gama wanke ta tas ya saka mata towel ya dauko ta suka fito. A gado ya aje ta ya dauki ƙaramin towel ya goge mata kanta da jikinta tana zaune tana ji, bayan ya gama shirya ta shima ya ja ya zauna a gaban madubi ya shafa mai ya feshe jikinsa da ture mai daɗin ƙamshi wanda ya sa ta buɗe ido ta kalle shi a sace amma ta kasa ɗauke idanuwanta. Bayan ya gama ya juyo suka haɗa ido ya ƙaraso bakin gadon ya hau ya janyo ta ta takure a waje ɗaya, bai matsa mata ba ya rabu da ita ta kwanta yadda take so, ƙarshe ma can ƙuryar gado ta koma ya yi ta magana amma ta yi mirsisi ta kyale shi. Kasa haƙuri ya yi sai da ya dawo da ita jikinsa a haka ya rufe su a bargo babu jimawa bacci ya ɗauke ta, shi kuwa kasa baccin ya yi yana kallon yadda take juyi a kansa tana sharar baccin ta son rai, sai karfe ɗayan dare sannan bacci ya ɗauke shi. Kiran Sallar assatu ne ya tayar da shi ya buɗe ido yana ƙaranto addu'ar tashi daga bacci, a hankali ya zame ta daga jikinsa ya sauka a gadon ya dauro alwala. Bayan ya fito ya jima a kanta a tsaye yana son tashin ta amma ya ga baccin ya mata daɗi, sai da ya ji ana tayar da iƙama sannan ya soma tashin ta. A hankali ta buɗe ido ya kai hannu ya bubbuga kumatunta Sanyin ruwa ya sa ta wartsake ta tashi zaune. “My wife tashi ki je ki yo Sallah ni na wuce masallaci.” Ya faɗa yana wucewa. Sauka ta yi ta dauro alwala ta soma gabatar da Sallah.. Sai ƙarfe bakwai ya dawo ya tarar da ita tana bacci ta jingina kanta da jikin gado, sanin jirgin ƙarfe shaɗaya za su bi ya sa shi ɗaukan ta ya cire mata hijabin ya kwantar da ita, shima cire rigarsa ya yi ya hayo gadon ya, kwanta yana shinshinar gashin kanta da ya sha gyara sai wani sihirtaccan ƙamshi yake fitarwa har bacci ya ɗauke su. Ba su farka ba sai karfe 10:20am ya sauko ya ɗauke ta ya yayo mata wanka idanuwanta cike da bacci ta saki jiki kamar marar lakka a jiki, shi kuwa daɗi yake ji saboda zai ɗauke ta su wuce salin alin kafin ta tayar da fitina. Bayan ya shirya ta shima ya shirya ya kama hannunta suka fito zuwa palo, daret kan dinner table suka nufa ya haɗa mata tea ya ba ta tana sha tana mishi mitar wai bai iya haɗa tea ba, dariya ya yi ya ce ya ji ta dai sha. Kular da ke gaban su ya buɗe ya ga soyayyar doya ce wadda aka haɗa da kwai ya juyo ya kalli Andizo ya ce “My wife za ki ci wannan abincin?” Kallon abincin ta yi ta ystsina fuska ta kawar da kai gefe, ganin haka sai ya rufe ya tashi ya wuce ɗaki ya janyo akwati ƴar madaidaiciya ya aje a Palo, ɗakin ya sake komawa tana nan zaune jim kaɗan ta ga ya fito cikin wata dakakkiyar shadda kalar kayan jikinta pink colour, dinkin Kamar a jikinsa aka zana ya masa kyau sosai duk da ya rame. Kasa ɗauke ido ta yi a kansa har ya ƙaraso gaban ta sai jin iska ta yi a idanuwanta, saurin rufe ido ta yi ya kama ta ya miƙar ya ce “Mu je kar jirgi ya zo ba mu isa ba.” Har ta yi taku ɗaya sai kuma ta tsaya cak ya juyo ya kalle ta, “Ya kuma kika tsaya?” Kamar za ta sa mishi kuka ta ce “To ba sun ce za su dawo da safe ba me ya sa har yanzu ba su zo ba?” Fuskantar ta ya yi ya ce “Am sorry kina bacci Ahmad ya kira ni ya ce su bacci suke Amira ba ta jin daɗi gajiyar zirga-zirgar ce da ta sha.” Baki ta turo ya harde hannayensa a ƙirji yana kallon ta da wani irin yanayi, in tana mishi shagwaɓa sai ya ji kamar tana tafiya da numfashinsa ne, gaba ta yi ta zauna a kan kujera ta kafe ta ce sai ya kira su sun zo, ya yi ta rarrashin amma taƙi yarda su tafi ita lalle sai an zo an sanar da ita yadda aka yi wannan badaƙalar. Sai da ya kira Amira ta sharara mata ƙaryar suma za su je Nigeria nan da kwana biyu sannan ta yarda suka tafi. Sun isa filin jirgin aka sauke su suka nufo inda za su zauna su yi jira na minti goma, wasu kattai ta gani su shida suna nufo su masu kama da bodyguard ai da sauri ta maƙale a bayan Sultan, dariya ya yi ya janyo ta ta dawo gefen shi ya ce “Ki nutsu my wife yarana ne fa.” Ajiyar zuciya ta sauke tana dafe ƙirji ya sa hannu yana ruƙo ta har suka iso. Hannu suka dunƙule aka yi gaisuwar yan gayu ta kalle su tana mamaki ganin yadda suke wasa da dariya, bayan shi ta koma komawa har sai da suka gama tattaunawa suka bar wajen sannan ta fito, dariya ya yi ta mata tana hura hanci sai ga jirgin da za su hau ya sauka.. Bayan sun shiga suka miƙa can gaba in da sai manyan mutane suke zama wato special kujera, sun kusa isa sai ga ɗaya daga cikin ma'aikatan jirgin ta fito, ganin Sultan ya sa ta faɗaɗa fara'arta tare da cewa “Welcome Mr J.” Ta ƙarashe maganar tana miƙa mishi hannu alamar su gaisa. Saurin shiga tsakanin su ta yi ta fuskanci Sultan idanuwanta cike da ruwa ta saɓa baki, gab take da fashewa da kuka ya kamo hannayenta ya ce “Mene ne faɗa mini naji?” Ya yi maganar cike da tsananin kulawa irin ta masoyan da suke ƙaunar junansu kamar ba gobe. Hannu ta ɗaga mishi murya na rawa ta ce “Ni ka ɗauke ni ƙafafuwana ciwo ba zan iya tafiya ba.” Murmushi ya yi ya ɗauke ta cak ya mata rungumar jarirai ya ce “Abu mai sauƙi hakan ya miki?” Gyaɗa kai ta yi tana kwantar da kanta a ƙirjinta ta kalli wannan mata ta gefen ido. Sultan ya gyara tsayuwa ya ce ta ba su waje, har sun wuce sai ta kasa haƙuri ta bi su har kujerar da suka zauna, takaici ne ya rufe Andizo amma ba ta ce komai ba tana son ta ga iya gudun ruwan matar. “Mr J wannan yaronka ne?” Ta yi maganar da Hausar ta wadda ba ta gama shiga bakinta ba. Girgiza kai ya yi ya ce “Amaryata ce.”. Ya ba ta amsa. Zaro ido ta yi cike da mamaki tana tunani, kenan zuwan da ya ce mata zai yi Niger aure ne ya yi? Jinjina kai ta yi ta ce “Congratulation.” Kai kawai ya gyaɗa mata dan ya matsu ta ba shi guri da matarsa su huta, jiki ba ƙwari ta bar wajen ta fice da sashen ta koma baya. Kwafa Andizo ta yi can ƙasa ta ce “Shegiya futsararriya wai har da wani miƙa mishi hannu, Wallahi duk sai na ci muku uwa ɗaya bayan ɗaya sai na raba ku da shi ko a hanya kuka ganshi sai kun canja wata.” Gum Sultan ya yi da bakinsa ko motsi bai yi ba dan kar ya nuna alamun ya ji maganar da ta yi, zuciyarsa ta ƙara narkewa a login ƙaunar ta ya sa mata bel ya yi baya ya lumshe idanu yana shafa kanta... *Ina matuƙar godiya da addu'oinku Allah ya saka muku da alkhairi* _Maman Nusaiba ce_ [7/14, 10:49 PM] Ummu Amjad: ADZ 48 Tana jin yadda yake taɓo mata gashi ta yi luf a jikinsa kamar mage, sai da suka kusa zuwa Nigeria sai ga wannan matar ta iso fuska ba yabo ba fallasa, ɗago kai ya yi ya kalle ta ta aje musu cake da ruwa da duk abin buƙata wanda in ka shiga jirgi musamman manyan mutane ake kawo musu, murmushi ya sakar mata itama ta mayar masa da martani, kallon Andizo ya yi ya ga ta yi kicin-kicin da fuska tana kallon abincin, ɗago da ita ya yi ya ce “My wife Ko akwai abin da kike buƙata a kawo miki?” Turo baki gaba ta yi tana dora hannunta ɗaya a ƙirjinsa, sai da ta ɗago ta ga tana nan a tsaye ta kawar da kai gefe ta ce “Ruwa kawai zan sha.” “To nima dai ruwa kawai nake so tun da ba za ki ci komai ba.” Kallon shi ta yi ya jinjina mata kai alamar tabbatarwa, kayan abincin ya ce ta mayar ruwa suke buƙata, sororo take kallon shi cike da takaicin canja mata da ya yi daga jiya zuwa yau, idanuwanta ne suka ciko da hawaye ta yi saurin ɗauke kayan ta fita. Da kallo ya bi ta yana jin ba daɗi ganin hawaye a fuskarta, ita kuwa Andizo tana ganin ta tafi ta sauke ajiyar zuciya a ɓoye ta koma jikinsa ta kwanta babu jima bacci ya yi gaba da ita.. Ƙarfe ɗaya daidai jirginsu ya sauka a airport ɗin Abuja, kallon yadda take fitar da numfashi tana zuƙowa yake, a hankali ya fara hura mata iska a kunne ta yi saurin buɗe ido tana kallon waje ta taga. Ji ta yi an miƙar da ita ba ta ce komai ba sai ma saki jiki da ta yi jin ta a jikinsa, ganin yana shirin fita da ita haka ta yi saurin faɗin “Daddyn Farrah ka sauke ni a nan mana zan fita da kaina.” Dariya ya yi yana sauke ta kalle ta sai sunne kai take yi, mayafin ya gyara mata ya riƙe handbag suka nufi kofar fitowa. Tun kafin su ƙarasa saukowa ta hango wasu manyan mata su uku masu kama da shi sak kamar an tsaga kara, kowacce ta sha material tsadadde na gani na faɗa, kallon su ta sake yi sai ta ji jikinta ya yi sanyi, abin da take tunani a kan Sultan ya tabbata lalle ya fi ƙarfin ta, ita ɗin ba ta kai ta zama matarsa ba tana ɗiyar talakawa shi kuwa duk Africa ba wanda bai san shi ba a harkar kwallo. Taɓa ta ya yi ta ɗago kai ta kalle shi da sauri, fuska ɗauke da damuwa ya ce “Me kike tunani Wife? Tun ɗazu nake magana ba ki ji ba.” Ajiyar zuciya ta sauke ta sake kallon mata ta ga suna mata murmushi si ta ji zuciyarta ta ɗan samu nutsuwa, a hankali ta miƙa masa hannunta ya kama suk ƙaraso wajen su. “Welcome to Nigeria Khadija.” Cewar ƙaramar cikin su wadda tafi tsananin kama da Sultan. Sunkuyar da kai ta yi murya ƙasa ta ce “Thank you Anty.” Dariya matar ta yi ta rungumi Sultan tana faɗin “Yaya ka faɗa wa matar nan taka mu fa ba ma son kunyar nan da take sunkuyar da kai, mu ƙannenka ne ba yayu ba ka sanar da ita ta saki jikinta Mom ta ƙagara ka kai mata ɗiyarta.” Kuncin Andizo ya shafo ta yi murmushi mamaki fal ranta wai yanzu wannan manyan matan masu aji da class duk ƙannen mijinta ne? Ajiyar zuciya ta kuma saukewa ta saki fuska tana murmushi ta isa gaban sauran suka rungume ta, ɗaya ta ce “Ina miki murna da samun Yaya J a matsayin miji Allah ya ba ku zaman lafiya da zuri'a ɗayyiba.” A kunyace ta ce “Amin ya Rabbi.” Daɗi sosai ya rufe Sultan ganin Andizo ta saki jiki da 'yan'uwansa, mota suka shiga aka nufi gidan Mom. G R. A. Suka iso jikin wani babban get motar ta yi hon aka buɗe musu suka shiga, da sauri ɗaya daga cikin masu tsaron shi ya iso ya buɗe musu ƙofa, matan suka fara fitowa sannan shima ya fito ya zagaya ya buɗe mata ƙofa ta fito a kunyace. Ba ta lura da Mom ba sai da suka kusa isowa daf da ita ta ji saukar sautin muryarta. “Barka da zuwa ɗiyata.” Da sauri ta ɗago kai suka haɗa ido da Mom, fisge hannunta ta yi daga na Sultan ta nufi Mom ta sauri itama ta taro ta suka rungume juna, tafi suak sa Sultan ya kalli Mom ya ce “Yanzu abin ya zama na son kai ashe, an yasar da ni an kin ga ƴarki.” Daƙuwa Mom ta mishi tana dariya ta ce “To dama wa kake tunanin zan tara? Ai 'yata na taro ba kai ba matsa ka ba mu guri mu wuce ciki.” Dariya ya yi ya matsa Mom ta kamo hannun Andizo suka wuce ciki, wani tantsameman palo na alfarma suka shigo, faɗin tsaruwar palon ma ba ta lokaci ne, kujerun palon kansu abin kallo ne can gefe wani harɗaɗɗan dinner table ne babba Mai ɗauke da kujeru goma shabiyu, idan ka shigo da palon da photon Sultan za ka fara cin karo wanda aka manne a jikin bango, yana sanye da kayan bal hannnunsa riƙe da kofi ya ɗaga shi sama ya yi murmushi aka yi photon, ɗaya gefen na photon shi kuma dukkansu family ne har da mahaifina, can gaba kaɗan photon Farrah ne ita da shi ya goya ta suna dariya aka yi photon.. Sama aka haura da ita cikin wani ɗaki, zaunar da ita ta yi ta ce “Matar Yaya nan ne ɗakinsa ki yi wanka ki sauko mu ci abinci sai ku kwanta ku huta.” Murmushi ta sakar mata ta ce “Don Allah ya sunanki?” Har ta juya ta dawo ta zauna ta ce “Ni sunana doctor Rahama ni nake biyawa Sultan, sai ƙanwata wannan wadda ta fimu girman sunan ta Barrister Safna, sai Autarmu doctor Sultana.” Waro ido ta yi tana yar dariya ta ce “To gaskiya ni Antys zan ke kiran ku tun da kun fini shekaru.” Ta faɗa tana yaye mayafin jikinta. “Tab rufa mana asiri, so kike Yaya ya ce mun raina masa mata? Ki kira mu da sunan mu.” Ɓata rai ta yi ta ce “Lalle ma, to ni kam gaskiya ba zan iya kiran ku da sunanku ba, ko ba komai ai kun girme ni naisa ba kusa ba zan dinga kiran ku da doctor's ita kuma Barrister ya yi ko?” Kumatunta ta shafo ta ce “Yawwa beautiful ɗin Yaya hakan ya yi tun da kin ce ba za ki kira mu da sunanmu ba, bari na wuce kar ki yi wanka ki fito mu ci abinci.” To ta ce tana kallon ta cike da birgewa ganin yadda ta saki jiki da ita kamar dama can sun taɓa zama da ita, tashi ta yi ta je ta kulle ƙofar ta dawo ta cire kaya ta nufi ƙofar da ta gani a cikin ɗakin. Tana buɗewa maimakon ta ga toilet sai ta ga saɓanin haka, wani babban ɗaki ne babu komai a ciki sai kayan motsa jiki kala-kala, riƙe baki ta yi ta mayar ta rufe ta rasa duba ko'ina amma ba ta ga wata ƙofar ba, buɗe handbag ta yi ta ɗauko waya ta lalibo number shi ta danna masa kira. Yana ɗauka ta ce “Wanka nake son yi ka zo.” Miƙewa ya yi tsaye ya ce “OK gani nan zuwa.” Kallon shi Doctor Sultana ta yi ta ce “Yaya ina kuma za ka je daga zuwan ku?” Mayar da wayar ya yi aljihu ya ce “My Wife ta ce tana son yin wanka na je, da alama ta gaji matuƙa zan je na gani.” Dariya ta yi ta ce “To masoya sai an fito.” Hararar ta ya yi ya yi gaba suna tsokanar shi ya ce zai rama idan ya dawo. Ƙofar ya burda ya ji ta a kulle sai ya kwankwasa, da sauri ta tashi ta leƙa ta wata ƙaramar ƙofa da ke jikin ƙofar ta ga shi ne, buɗe mishi ta yi ta matsa ya shiga ta rufe ta kuyo da nufin mishi magana sai ji ta yi ya yi sama da ita yana juyi a tsakar ɗakin. Zaro ido ta yi ta ce “Sauke ni please hajijiya za ta kama ni yunwa fa nake ji.” Saurin aje ta ya yi yana dariya ya kama zanin gadon da ta rufe jiki da shi ya yaye yana faɗin “Daga ni sai ke za kike rufe jiki.” Make hannunsa ta yi tana turo baki gaba ta ce “Kai fa ba ka jin kunya.” Dariya ya yi ya ce “Ai har yanzu ba ki ga rashin kunyata ba sai nan gaba, sai na mayar da ke kamar ni.” Gum ta yi da bakinta ba ta kuma cewa komai ba, kayan jikinsa ya cire ya ɗauki towel ya sa idanuwanta a rufe, itama ɗauko mata ya yi ya fisge zanin gadon ya sa mata ya nufi wata ƙofa da ita. Jin suna tafiya sai ta buɗe ido tana kallon wajen, sai da suka bar ɗakin kamar za su shiga wani bangare sannan ta ga ya buɗe wata ƙofa sai ga su a toilet. Wanka ya mata sannan shima ya yi suka yo alwala suka fito, bai tsaya ɓata musu lokaci ba shirya ta ya yi cikin wata riga da sket na shidda kamfala, sosai ta yi mamakin ganin kaya a jere tun daga sama har ƙasa kaya ne kala-kala ba mace da na namiji, tunani ta yi ƙila ko na maman Farrah ne sai kawai ta tsaya turus tana kallon shi. Kallon ta ya yi da alamun tambaya ta juya mishi baya tana kumbura baki, ta ya ma zai sa mata kayan matarsa da ta mutu? Dafa ta ya yi ya ce “My wife Mom fa na jiran mu ki zo mu fita kar ta dinga kira, yanzu ta kira ta ce na sauko da ke ki ci abinci kar na bari ki yi bacci.” Kamar za ta fashe da kuka ta juyo ta kalle shi a hankali ta nuna mishi kayan jikinta ta ce “To amma wannan ɗin kayan waye ka ba ni na saka?” Shuru ya yi yana jinjina lamarin ta, shi ya sa ta yi kicin-kicin da fuska dan ta ga kayan mace a jikin wardrobe ɗinsa? Hannunta ya ruƙo ya ce “Ki daina tunanin kowacce mace a cikin rayuwata in ba ke ba my wife, wannan ba kayan kowa ba ne naki ne wanda nake saya ina ajewa.” Ji ta yi zuciyarta ta samu nutsuwa ta saki fuska ya kalle ta cikin tsona ya ce “Wannan matar tawa akwai kishi.” Murguɗa mishi baki ta yi, darduma ya shinfiɗa suka gabatar da Sallar da ke kansu sannan suka fita.. Daret dinner suka nufa Mom na ganin su ta kalli Sultan da ya ƙi sakin hannunta sai mutsu-mutsu ya sake ta ya ƙi, hararar shi ta yi ta ce “Wai ba za ka sake mata hannu ba?” Sakin hannun nata ya yi ya ja mata kujera har za ta zauna sai ta fasa ta dalla mishi harara ta dawo kusan Mom ta ce “Mom ni a kusa da ke zan zauna.” Baki ya saki yana kallon ta cik da mamaki Sultana ta sheƙe da dariya ta ce “An gaishe da Anty amarya.” Kujerar kusa da ita Mom ta ja mata ta zauna, ɗaure fuska ya yi ya zauna suka fara cin abinci. Kasa cin abincin ya yi sai cokalin yake juyawa yana kallon ta ta gefen ido, duk abin da yake tana lura da shi ta sunkuyar da kai ta ci gaba da cin abincinta. Mom ta fara tashi ta wuce gabaɗaya ma ta bar palon, ganin Mom ta tashi ya dawo kujerar da ta tashi ya tura mata abincinsa, Doctor Rahama ta miƙe tsaye tana goge baki ta kalli su Sultana ta ce “Kunga ku tashi ku bar masoya su ci abinci.” Tashi suka yi suna tsokanar su Andizo ta yi shuru har suka bar wajen, wani kallo ta mishi da ya sa shi lumshe ido ta ce “Daddyn Farrah me ya sa ba ka ci abinci ba?” Ƙara tura mata abincin ya yi kamar wani ƙaramin yaro ya ce “Ni ke za ki ba ni.” Waro ido ta yi sai kuma ta turo baki a shagwaɓe ta ce “Gaskiya ni ka yi ƙato dayawa.” Tashi ya yi tsaye ya ce “OK to ba zan ci ba.” Da kallo ta bi shi ya juya nufi sama, janye idanunta ta yi daga kallon shi tana mamakin yadda yake mata wasu abubuwan kamar ƙaramin yaro daga jiya zuwa yau. Tashi ta yi ta nufi sama, har ta yi nisa sai kuma ta juyo tana tunanin anya ta kyauta wa mijin nata kuwa in ta bar shi ya kwanta bai ci abinci ba? Girgiza kai ta yi ta ɗauki plate ɗin abincin ta wuce. A hankali ta buɗe ƙofar ta shiga da sallama, a kan gado ta ganshi kwance ya yi ruf-da-ciki ta aje abinci a kan carpet ta tsaya a kan shi. “Daddyn Farrah tashi ka sauko in ba ka abincin da hannuna ba ma da cokali ba.” Yana jin ta ya yi kamar mai bacci sosai ya ji daɗin yadda ta biyo shi da abincin, ganin ya ƙi motsawa ta hayo kan gadon ta leƙa fuskarsa ta soma bubbuga mishi kumatu, “Daga shigowa har ka fara bacci ka tashi mana.” Miƙa ya yi irin kamar mai bacci gaske ya matso ya kwanta a kan cinyarta, hannunta ya kamo ya ɗora a kansa yana yawo da shi, gane abin da yake nufi sai ta shiga shafa sumar, a sayayye ta kuma cewa “Abincin fa.” Sai a lokacin ya iya cewa da ita “Tea kawai zan sha.” Ture shi ta yi tana sauka daga kan gadon ta ce “Tea? Ba dai yanzu ba sauko ni bacci nake ji.” Ta faɗa irin ba wasa ɗin nan, dariya ta so ba shi ya fisge ya tashi ya sauko ta harare shi. Zama ta yi ta wuce toilet ta wanke kannunta ta dawo ya gyara zama, abincin ta dinga ɗiba tana ba shi a baki idan ta sa mishi sai ya haɗa har da yatsunta ya tsosa son ransa sannan ya sakar mata yatsun, banza ta yi da shi ta ci gaba da b shi har ya ƙoshi ta miƙe ta dauki plate ɗin za ta fita ya yi saurin ruƙo ta. “Ina za ki je?” “Zan mayar da plate ɗin ne.” Ta ba shi amsa a taƙaice tana ƙoƙarin kwace ruƙon da ya mata. “No dawo ki aje mu kwanta ba yanzu ba.” Har za ta ce ba za ta dawo ba sai kuma ta tuna irin jan kunne da doguwar nasiha mai ratsa jiki da Umma matar Abie ta yi mata a waya, haka ma Mamma ta yi mata nasiha sosai game da yi wa miji gardama ko faɗa mishi magana kai tsaye, ta so ta botsare ta ce ta fasa auren ta gudo, amma ganin yadda Mom da 'yan'uwan Sultan ke tarairayar ta sai ta ji jikinta ya yi sanyi. Ajiyar zuciya ta sauke ta dawo ta aje plate ɗin ta bi shi zuwa toilet, tsaye ta same shi yana sa makilin a broch ta yi shuru kamar ba ta shigo ba. Sai da ya gama goge ya juyo ya ganta murmushi ya sakar mata itama ta mayar masa da martani, hannunta ya kamo ya kawo bakin famfo ya wanke mata ya ɗauko broch sabo ya sa mata makilin ya nufi bakinta ta yi saurin kaucewa. “Ya kika kauce My wife broch ba za miki.” Wani kallo ta mishi ta ce “To shi kenan komai sai ka ce sai ka mini har broch ɗin ma?” “Sosai ai duk wani abu ni zan ke miki shi kema kina yi mini, hakan zai ƙara mana so da ƙaunar junanmu kuma wannan shi ake kira da kyautata a zamantakewa, matso na miki kar mu tsawaita magana a toilet.” Matsowa ta yi ya ce ta buɗe bakinta, sai da ta harare shi sannan ta buɗe ya goge mata. Bayan sun fito ya ciro mata Sleeping dressing ring da wando, rigar iya ciki wandon bakin gwiwa, ta yi sororo tana kallon kayan sai Salim ya faɗo mata a rai, ba za ta manta ranar da ya taɓa ba ta sleeping dressing irin wannan ta ce ita ba ƴar iska ba ce ba za ta sa ba, ya yi ta dariya yana rokon ta ta amsa ta sam ita fa ba ƴar iska ba ce, haka suka dinga zagaye ɗaki har ya ci sa'ar damƙo ta ya sa mata ai kuwa ta tayar ta aljannu dole ya cire mata ya barta da wanda take so. Kumatunta ta ji ana shafewa ta ɗago kai suka haɗa ido, girgiza mata kai ya yi ganin hawayen abar ƙaunar tasa duk sai ya shiga damuwa, a sanyaye ya soma tambayar ta, “My wife why are you crying?” Ya faɗa yana ƙara share mata hawaye. Ajiyar zuciya ta sauke tana ƙoƙarin mayar da kukan da yake son kubce mata amma ta kasa, fashewa ta yi da kuka mai ƙarfi ta faɗa jikinsa, hankalin Sultan ya yi matuƙar tashi sai ƙara rungume ta yake yana bubbuga bayanta, ganin tsayuwar ba za ta musu ba ya ja ta suka koma kan gado ya kwanta ya dora ta a kanshi yana rarrashin ta kamar shima zai yi kukan. “My wife don Allah ki daina kukan nan yana tayar mini da hankali, idan wani abu ne na miki wanda ya ɓata miki rai ba kuka ya kamata ki yi ba faɗa mini za ki sai na gyara, ko ba ki da lafiya ne?” Ya ɗago da ita. Ganin yadda ya damu sai ta tsayar da kukan ta yi shuru ba ta mishi ko uffan ba, sake mayar da ita ya yi jikinsa. “Am sorry kin ji ki faɗa mini abin da yake damun ki, kinga ke amana ce a hannuna babu irin kashedin da Ahmad bai mini ba a kan na kula da ke fiye da kaina kar na bari ki yi kuka sai ga shi daga zuwan mu kin fara kuka me ya faru ?” Tashi ta yi zaune ta shafe fuskarta shima ya tashi ya fuskance ta, a hankali ta ce “Wani abu ne na tuna shi ya sa ni yin kuka, sannan ina son ganin yarana tun da aka ɗauke su ni da su sai dai a waya don Allah ka sa Yaya Ahmad in za su zo su kawo mini su na gansu ko na kwana ɗaya ne.” Ta ƙarasa maganar murya na rawa. Tausayi ta ba shi ya ya kama hannunta ya ce “In sha Allahu in dai dan su Nour ne za ki gansu da zarar sun shirya zuwa nan zan faɗa masa ya je ya kawo miki su ki gansu, ki daina tunanin komai na miki alƙawarin zan faranta miki fiye da tunaninki, ban sani ba ko tunanin marigayin mijinki kika yi har kika yi kuka, amma ba komai zan kyautata miki iyakar iyawata ko na ce fiye da Salim ma.” Saurin kallon shi ta yi ya jinjina mata kai ya dora da cewa “Yes ba lefi ba ne dan kin yi tunanin Salim in ya faɗo miki a rai, mutumin da ka rayu da shi na sati ko wata ya kyautata maka ba za ka taɓa mantawa da shi ba, ballantana kuma wanda kuka kasance a karkashin inuwa ɗaya ai ba abin mantawa ba ne, amma don Allah karki cika yawan tunani irin haka gudun ya kawo miki matsala a zamanmu.” Shuru ta yi tana sauraron shi har ya dasa aya, gyara zama ta yi ta ce “In sha Allahu hakan ba za ta sake faruwa ba, nima zan yi ƙoƙarin yin maka biyayya iya bakin ƙoƙarina duk da har yanzu hankalina ya kasa kwanciya a kan zamana matarka.” Dariya ya yi ya ce “Y kamata na sanar da ke komai kar ki kasa yin bacci.” Gyara zama ta yi domin ta ƙagara ta ji yadda aka yi.” “Lokacin da su Mama suka samu labarin kin ce Ahmad kike so sai ran Amira ya ɓaci amma a lokacin ba ta nuna miki ba da za su tafo, bayan sun dawo da yan kwanaki na dami Amira yaushe za ta kawo mini ke ta sanar da ni abin da ya faru, to a lokacin ne na zabura na faɗo daga kan gadon asibiti na faɗo a kan glass cup ɗin da Mom ta zuba mini juice, na zubar da jini sosai domin cup ɗin ya fashe har ya shiga jikina sai da aka cire mini, shi ne taɓo da kika gani a ƙirjina.” Ya faɗa yana buɗe mata towel ɗin, wani irin tausayin shi ta ji ta sunkuyar da kai shi kuma ya ci gaba da ba ta labarin ɗaya bayan ɗaya. “Mom ta ce a ranar sai da aka mini allurar bacci saboda sumbatun da nake yi ina kiran sunanki, kwana biyu tsakani na farfaɗo na sa Rahama ta kira mini Ahmad, yana ɗauka na ce mishi yanzu Ahmad kaine za ka aure mini abin da na fi Ƙauna? Anya akwai amana ?” A nan ne yake sanar da ni na kwantar da hankalina ai Khadija tawa ce domin ya riga da sadaukar mini, sun shirya komai ta yadda ba ki gane ba Ahmad ba ne Angon, hakan da ya yi Amira ta ce ita kuma za ta maye mishi gurbinki a zuciyarsa a sa bikin kamar yadda aka sa bikin, sosai naji daɗi matuƙa sai naji na samu lafiya duk da an ce in na gama shan magani za a yi mini aiki ƙodata ɗaya ta lalace, haka na dinga shan magani har bikin ya matso nasa Mama ta sayo kayan lefe da duk abin da ake buƙata, idan kuma na ɓangaren abokai ne zan tura wa Ahmad komai ya sayi duk abin da ake buƙata har angon bikin na ce mishi ya ɗinka wa abokansa ko sun kai ashirin, domin naji daɗin yadda ya mini sadaukarwa. Ana saura kwana biyu biki Mom suka yi nasu bikin a nan duk da ba ta gaiyaci kowa ba iya family ne suka zo, ranar ɗaurin aure har ƙauyenku muka je na sa Ahmad ya ba ni turaren da kika san shi da shi nasa na kuma saka facemark na rufe fuskata, ina zaune aka ɗaura mana aure mutane suka dinga ba ni hannu ina amsawa ni da Ahmad domin sun kasa gane ba Ahmad ba ne Angon kasancewar sunanmu ɗaya da shi, kuma su Abba su suka amsa mini aurenki. Bayan mun ta so na kasa nutsuwa sai da na sa Ɗahare ki muka gaisa ba ki gane ni ba saboda kanki a ƙasa yake kin kasa kallon mu, ni kuwa a lokacin kallo ɗaya na miki na gane kika cikin damuwa, sai a lokacin na ƙara tabbatar wa kaina kina masifar sona kawai kin danne ne kika zaɓi Ahmad dan ki faranta ran iyayenki. A tare aka kawo ku ke da Amira aka yi sama da ita ke kuma aka barki a ƙasa, na so naje amma Ahmad ya hana ni dole na haƙura sai washegari muka je, a nan ma dai ba ki kalli kowa ba har aka gama komai muka fito. Bayan mun fito sai da muka raka abokanmu har mota sannan na koma ɗakin da na sauka na canja kaya na sa turaren da kika sanni da shi na zo gareki. Ahmad da Amira su suka yi komai, ba dan Ahmad ya haƙura ba da yanzu ina kwance ko a mace ko a raye. Amma fa Ahmad sai da ya kwanta rashin lafiya har na kwana uku tukun ya warware, ganin shi a wannan hali ne Amira ta ce da shi in dai har zai iya ta amince su yi aure, Wannan shi ne abin da ya faru.” Tun da ya fara maganar ta yi lamo a jikinsa tana jinsahar ya sada aya, tashi ta yi ta ce “Gaskiya mun gode wa Ahmad har da Amira, ni ai lokacin an kuma biki ta kira ni ta mini tas ta ce kai za ta aura ta share maka hawaye, ƴar rainin hankali ashe ƙarya take, na jima ina dakon soyayyarka a gangar jiki da ruhina kawai ina dannewa ne domin ba na son ɗora wa kai son wanda ya fi karfina ta kowanni ɓangare.” Kunnenta ya ja ta sa ƙara tana yarfa hannu ta ce “Akwai ciwo fa Daddyn Farrah.” “Sai na murɗe wannan bakin da yake kirana da daddy, ke ba irin ki kira ni da sunan masoya sai wani Daddyn Farrah kamar wata suruka ta?” Kwafa ta yi ta ce “Zan rama ai.” “Sai dai ki rame yarinya oya zo mu kwanta.” Kyale shi ta yi suka kwanta nan da na bacci ya ɗauke su... Washegari da yamma ƙarfe 4:10pm su Rahama suka shirya musu dinner a harabar gidan, kowacce ta gaiyato ƙawayenta da abokan aikinta gidan ya cika taf kamar a lokacin ne ake bikin. Wani tsadaddiyar atamfa Andizo ta saka shi kuma ya sha ƙanana kaya sai ƙamshi suke zubawa, haka aka dinga musu liken kuɗi wasu daga cikin masu zuwan sai mamaki suke ganin matar da Sultan ya auro yarinya ce sosai, wasu kuma suka birge su sai ɗaukan su suke a waya ana musu tafi. Karfe shida da rabi aka tashi kowa ya tafi gida. Wannan satin da suka yi ba su samu damar yin baccin kirki ba saboda zuwan da ake yi ana taya Mom murnar auren Sultan, sai ana gobe za su tafi London suka kwanta da wuri.. Washegari suka shirya tafiya zuwa London, tun da ta tashi ta yi sanyi domin ta ji labarin yadda ake yin aikin cire ƙoda sai ta ji sam ba ta son tafiya, amma ta danne zuciyarta su Mom suka raka su har airport, sai da suka ga jirginsu ya tashi sannan suka dawo gida.... _Maman Nusaiba ce_ [7/17, 1:18 PM] Ummu Amjad: ADZ 49 Cikin takunsa na ƙasaita ya fara saukowa daga cikin jirgin hannunsa cikin nata, ya manna baƙin glass sai wani shan ƙamshi yake, Khadija ta yi lakwas a gefen shi tafiya ma ƙarfin hali take saboda da yadda ta ga irin motocin da suka zo ɗaukar mijin nata, ashe ba ta ga komai ba a Nigeria da motoci shida suka zo tarbar su, domin nan iya wanda ta gani a jere su goma duka baƙaƙe kala ɗaya, ta jinjina kai tana yi wa Allah tasbihi wai ita ce aka zo ɗauka a irin waɗannan motocin da a film kawai take gani. A hankali ta ɗago kai ta kalle tsayinsa iya haƙarƙari ta zo mishi ga ta ƙarama ita ba wani jikin a zo a gani ba, amma ba za ka kira ta da sirriya ba, murmushi ya sakar mata tare da tsayawa ya duƙa ya ce “My wife ya kika ga London?” Ajiyar zuciya ta sauke ta rasa me za ta faɗa masa sai juya kalaman bakinta take tana taunasu gudun ta faɗi ba daidai ba, ƙara matso da ita ya yi jikinsa ga mutane sun soma taruwa suna ɗaukan su a waya, wasu kuma suna faɗin “super star Mr J.” Lumshe idanu ta yi a hankali ta ce “Je t'aime mon amour.” Cak ya ɗaga ta sama ya mata ɗaukan jarirai ya nufi wajen mota, kafin ya ƙaraso da sauri ɗaya daga cikin bodyguard ɗin ta buɗe masa mota tare da yi masa welcome back, murmushi kawai ya sakar mishi ya shige mota. Motocin na tafiya sai ga Jennifer ta shigo Airport ɗin cikin motarta, packing ta yi ta fito da sauri ta nufi wata matashiyar budurwa da ke zaune kan kujera, tana isowa ta ce “Ruby ina suke?” Tashi tsaye Ruby ta yi tana yatsina fuska ta ce “Ai kin makara ɗazu suka wuce, ba ki ga yarinyar da ya zo da ita ba kyakkyawa ce sosai kuma ƙarama dan kin yi biyun ta a girma, yadda yake mata magana da nuna mata tsananin kulawa ya sa na fahimci tabbas akwai wani abu a tsakanin s..” Ɗaga mata hannu Jennifer ta yi tana dafe ƙirji cikin tashin hankali da firgici ta fara magana irin ta wanda ya fita daga haiyacinsa. “Ruby ina jin zuciyata Kamar ta fashe zan mutu, ina mai tabbatar miki in dai yarinyar da kike ba ni labari girlfriend ɗinsa ce sai na kashe ta, duk macen da ta raɓi my start sai ta yi nadama.” Ta ƙarashe maganar da ɗaga muryar hakan ya janyo hankulan mutanen da ke wajen, ganin za ta tara musu mutane Ruby ta kama ta sai sumbatu take ta saka ta a mota suka wuce.. Tun da suka shiga mota ba ta ce komai ba domin ta matuƙar gaji sai lumshe ido take tana buɗewa, shi kuwa Oga waya kawai yake amsawa ta abokinsa yana sanar da su alƙawarin da ya musu gobe zai cika domin ya kawo Khadijarsa da yake faɗa shekaru da dama. Tana jinsa ta yi kamar ba ta ji ba sai yanzu ta tuna maganar Amira lokacin da ta sanar da ita an sa mata rana da Ahmad, murmushi ta yi tana ƙara jin son ƙawartata. A ƙofar wani gold ɗin get suka hon maigadi ya buɗe musu suka shiga, ba ta ɗago ba har ya fita ya zagayo ya buɗe set ɗin da take ya sa hannu ya fito da ita, wari idanu ta yi ganin girman gidan ya fi na Mom ga kyau ga shukoki kala-kala a harabar gidan, ganin ta tsaya kallo ya kama hannunta suka nufi wata ƙofa. Duk in da suka bi masu aikin gidan sai sun rusuna suna mishi welcome back sir shi Kuma ya tsaya su gaisa sannan su yi gaba, sosai ta ji daɗin ganin yadda yake kula da masu yi masa hidima, idan suka gaishe ta murmushi take ta ce thank you tana ganin abin take kamar almara, wai yau ita ce turawa ke gaishe ta cikin girmamawa suna kiran da ta ma'am? Babban palon gidan suka shiga komai tsaf-tsaf sai ƙamshi da yake tashi, jan ta ya yi zuwa wata ƙofa ya tsaya ya danna wasu numbobi, murya ta ji daga jikin kofar tana faɗin “Welcome back Mr J.” Kallon shi ta yi a tsorace suka haɗa ido ya yi ƴar dariya y ce “Daɗina da ke shegen tsoro kamar farar kura, kin manta irin wannan ƙofar kenan?” Numfashi ta ja ta ta ce “Allah na manta sai yanzu na tuna lokacin da ka yi kidnapping ɗina in da ka sakani irin wannan ƙofar ce.” Ta faɗa tana bin bayan shi ƙofar ta maida kanta ta rufe ruf, suna isa bakin gado ya faɗa kai buduf ya ce “My wife ƙi taimaka ƙi mini tausa please.” Baki ta murguɗa ta zauna a kusa da shi ta ce “Kai kuwa Amour ka cika neman magana daga zuwa sai na yi maka tausa? Ni kam a gajiye nake ina son na huta.” Tashi ya yi ya tsura mata idanu kamar yadda take kallon shi, daɗi ne ke ratsa zuciyarsa ya ga shi ga Khadija a matsayin matarsa ta sunna, ya janyo ta jikinsa ya ci gaba da kallon ta.ganin kallon ba zai ƙare ba ta ɓata rai ta ce “Alƙur'an kuruwata ɗaci ne da ita ato.” Dariya ce ta kwace mishi ya ƙara matse ta itama sai ta taya shi, bakinta da yake matuƙar so ya sumbata ta lumshe ido, sake kai fuskarsa ta yi ya manna mata kiss mai tsayawa a rai har sai da ta zagaye ƙugunsa saboda da yadda ta ji jikinta ya ɗauki rawa, murmushi ya yi ya haɗe bakin nasu.. Sun fi minti goma a haka ta sakar masa komai ya dinga sarrafa ta yadda yake so, ganin zai wuce gona da iri ta tura shi tana mayar da numfashi, girgiza kai ya yi yana matsowa kusa da ita kamar mayunwacin zaki ya ce “No my wife karki mini haka Wallahi ji nake kamar na mutu.” Saurin matsawa baya ta yi a tsorace ganin yadda ya koma mata cikin ƙanƙanin lokaci, bin ta ya yi ta ƙara matsawa hawaye suka cika mata kwarmin ido ta ce “Am sorry Amour Wallahi ni tsoron ka nake ji kuma ga shi na gaji bacci nake ji.” Ta faɗa tana sakin kuka. Bai ji maganar da take mishi da kyau domin ya riga ya rikice ya matso ya damƙo ta ta sa ƙara ta ce “Wallahi bacci nake ji na gani.” A galabaice ya haɗa ta da jikinsa yana wani irin huci da ya ƙara tsoratar da ita ya ce “Please ki yi haƙuri da baccin.” Ya ƙarasa faɗa yana yin tafali da tufafin jikinta. Duk yadda ta kai ga hana shi kasawa ta yi, wani irin salo yake mata mai wuyar fassarawa yana tafiyar da ita a hankali kamar yadda ya dinga kuka tana faɗa mishi, sai ta tafiya ta yi nisa ta fara jin azaba a nan ta dinga kukan da gaske ba wai na shagwaɓa ba.. Bayan ya samu kansa ya birgina gefe yana sauke numfashi wanda fitarsu yake jin yana ƙara jin nutsuwa, sosai ya yi mamakin 'yar ƙaramar yarinya ta ɗauke nauyinsa, ko Jennifer a baya da suke tsakar holewarsu duk jarabarta wani lokacin sai ta gudu ta bar shi, wannan shi yake haɗa su faɗa ya ce zai nemi wata macen su zama biyu amma ta haukace mishi ta ce za ta kashe duk macen da ta raɓe shi, ta gwammace ta dinga mishi kuka da ya haɗa jiki da wata bayan ita, a lokacin faɗa suka yi sosai har ya lakaɗa mata dukan tsiya jikinta ya yi kaca-kaca da jini, kuma a hakan sai da ya sauke abin da yake kansa sai da ya sumar da ita saboda tsabar mugunta sannan ya rabu da ita ya kira likitarsa ta duba ta, amma duk da haka ba ta daddara ba ta ci gaba da zama da shi saboda ba ta inda za ta je da ya fi gidansa. Wata rana ya je Nigeria ya dawo ya tarar ta kawo wani abokinta ya same su ranar mutuwa ce kawai ba ta yi domin dukan da ya lakaɗa mata ya yi biyun wanda ya mata na baya da kyar abokinsa da suka shigo tare ya raba su, amma da yake tana masifar sonshi ana janye da aka gama gyara mata jiki ta dawo gaban shi ta kama ƙafafuwansa tana ba shi haƙuri ta ce ba za ta sake yin hakan ba ta kasa jure rashin sa ne na tsayin sati ɗaya, maganarta ta ƙarshe ta fusata shi ya wanka mata mari ta kwalla ƙara amma taƙi tashi sai haƙuri take ba shi, sai da ta yi kwana biyar tana ba shi haƙuri sannan ta samu kansa ya sauko suka jone. Tun daga lokacin ta daina kula duk wani friend in dai namiji ne suak ci gaba da rayuwar farin ciki. Shigowar Andizo rayuwarsa shi ya kawo taɓarɓarewar alƙarsu musamman lokacin da ta mishi wa'azi mai kashe jiki, tun daga lokacin ya nisanta kansa da Jennifer ko ta zo ba ya kula ta, ƙarshe dai ya, saya mata motoci biyu da gida babba ya sa mata kuɗi masu yawa a account ɗinta ya ce shi ya daina yin zina addininsa ya yi hani da hakan, idan kuma mutum bai basa ba in ya mutu zai shiga wuta, ranar hauka tuburan Jennifer ta yi ta ce dole sai ya aure ta shi kuma ya ce mace ɗaya yake da ra'ayin ita ce Khadija, duk wata hanya da za bi ta ganshi ya kulle ta dinga zuwa gidan har ta gaji ta haƙura, idan har ta samu nasarar ganin sa to sai dai in sun shiga filin bal ne suna bugawa a nan ne za ta ganshi idan sun ci ta dinga murna haɗi da kukan yanke alaƙarsu da ya yi. Ajiyar zuciya ya sauke bayan ya dawo daga duniyar tunanin da ya lula, a fili ya firta “Astagafurullahi wa atubu il aika?” Kallon shi Andizo ta yi tana son, tashi amma ta ƙasa sai cije lips take ta nisa ta ce “Amour zan shiga toilet.” Saurin kallon ta ya yi sai kuma ya tashi ya sunkuya ya ɗauke ta suka wuce toilet, gasata ya yi sosai tana mishi kuka har ya gama ta yi wanka shima ya yi ya naɗo ta a towel suka fito. A kan carpet ya aje ta ya canja shinfiɗar ya sa wani sabo dari sol, wata ƙaramar riga ya ɗauko mata iya gwiwa ya sa mata shima ya ƙanana kaya na zaman gida ya dora jallabiya a kan kayan duk tana zaune a takure sia rawar sanyi take. A daddafe suak yi sallar azahar da la'asar suna gamawa ta jingina kanta da jikin gado tana jin yadda ƙugunta ke mata zugi. Juyowa ya yi ya ga tana gyangyaɗi ya tashi ya cire jallabiyar ya ɗauke ta ya kwantar, da sauri ta buɗe ido za ta tashi ya mayar da ita jikinsa ya ja musu blanket, goshinsa da nata ya haɗa cikin muryarsa mai daɗin sauraro ya fara yi mata daɗaɗan kalaman soyayya masu fasa kwanya. “My wife baki ya yi kaɗan na firta miki kalmar godiya, tabbas ke ɗin kin kai na kira kira da sarauniyar zuciyata kum uwar 'ya'yana da za mu haifa nan gaba kaɗan, ban taɓa jin son wata mace ba wanda ya hana ni sukoni na rasa nutsuwa da hankalina sai a kanki Khadija, ke ɗin ta musamman ce a zuciyar Sultan my wife kin gama mini komai da kika zama matata abar samun nutsuwar nutsuwa da gangar jikina, ina matuƙar sonki Khadija zan miki duk abin da kike so komi wahalar shi matuƙar bai saɓa wa addinin Musulunci ba, ke ɗin tawa ce ni kaɗai ba iya a duniya ba har ma a gidan aljana. In ƙaunar ki da dukkan zuciyata wife I love you so much matar Sultan.” Hajiya Khadija kalaman soyayya sun tsuma ta ba ta san lokacin da ta ƙara shegewa jikinsa ba, shi kuwa abin nema ya samu ya ƙara ba ta masauki ya ji gaba da fallasa mata sirrin zuciyarsa har bacci ya ɗauke ta, murmushi ya yi ya shafa lips ɗinta wanda shi yafi tsokane mishi idanu a fuskarta har bacci ya ɗauke shi.. Washegari misalin karfe 10:00am suka tashi daga baccin da suka koma bayan Sallah asuba, wanka suka shiga a tare wanda ya ɗauke su fiye da minti talatin, domin wasan ruwa suka dinga yi kamar wasu yara ya biye mata, idan ya watsa mata itama ta watsa mishi sai da suka gaji tukun suak yi wankan suka fito. Suna fitowa suka samu an jera musu lafiyayyan abinci sai ƙamshi yake, Andizo ta shafa cikin da ya ke a ɗame kamar ba ta kayan ciki, nasa hannun ya kai ya shafa ya yi fuskar tausayi ya ce “Ya aka yi wife?” Narke mishi ta yi a jiki domin yadda ya yi maganar da wani salo sai da wani irin shok a jikinta, “Amour yunwa.” Ta faɗa tana turo baki gaba, daukan ta ya yi da hanzari suka wuce wajen cin abinci. Zaunar da ita ya yi sai ga mai aiki ta iso ta gaishe su suka amsa ta haɗa musu tea mai kauri, kula ta buɗe farfesun kayan ciki ne ta zuba musu ta sake buɗe ɗayar kular ita kuma shinkafa da kaza ce sai tashi ƙamshi take, lumshe ido Andizo ta yi yawunta ya tsinke tana jikinsa a kwance mai aikin ta gama yin saving ɗin su ta wuce. Ɗago da ita ya yi ya fara ba ta tea ɗin, sai da ta shanye tas sannan ta janyo farces shima ya fara ba ta, ba ta ci mai yawa ba ta kawar da kai gefen ya kalle ta da mamaki ya ce “My wife ba dai Kim ƙoshi ba?” Gyaɗa mishi kai ta yi sai ya aje cokali ya kwantar da kanta a ƙirjinsa ya ce “Na hutar da ke ciyar da ni yanzu dan na lura sai mu kwashe lokaci ba ki ba ni na ci na ƙoshi ba, ga shi kuma Taufik yana kirana a waya wai yaushe zan zo gidansa madam ɗinsa ta takura sai na kai mata ke.” Ɗago da daradaran fararen idanuwanta ta yi ta kalle shi, yadda yake tauna abinci sai tsji ya birge ta ta kai hannu ta shafa sajansa mai ƙara mishi kyau da kwarjini ta ce “Amour.” Aje cokalin ya yi ya sunkuyo gabaɗaya ya ji abincin ya fita kanshi saboda yadda take shafe shi ga shi kuma tana kan cinyarsa sai mutsu-mutsu take taƙi zama ɗam, haɗiye abincin ya yi ya ce “My wife karki sa mu fasa tafiyar nan fa.” Ƙara shigewa jikinsa ta yi ita kanta ji take kamar su dauwama a haka, gabaɗaya ta ji sam ba ta son barin jikinsa sai ma ci gaba ta yi da taɓa shi dole ya bar cin abincin gabaɗaya ya miƙe tsaye tana maƙale a jikinsa, baki ya buɗe zai yi magana ya ji shashshekar kukan ta ya ciro ta daga jikinsa a ruɗe ya ce “Me ya faru? Wani abu kike so?” Ya jero mata tambaya biyu a jere. “Nima ban sani ba Amour.” Ta ba shi amsa tana komawa jikinsa. Ɗaki suka koma ya cire mata kayan tafiyar ya kwantar da ita yana rarrashin ta, kasa jurewa ya yi da jin laushin fatarta ya rufe su da banket. Sai ƙarfe 12:am suka sake yin wanka yana ta tsokanar ta in ta gaji ta sa mishi kuka ya rarrashe ta da kyale ya ci gaba. Suna fitowa tuni an fito da motar da za su shiga, baya aka buɗe musu suka shiga sai gidan Taufik. Suna zuwa suka samu Taufik da matarsa da yaransa biyu a harabar gidan suna jiran zuwan su, da kanta ta iso ta buɗe set ɗin Andizo fuska ɗauke da murmushi ta ce “Oyoyo madam J.” Ta faɗa tana son ganin ta. Andizo har za ta fito sai ta tuna maganar Sultana da sabuwan da ta koya mata yadda za ta ke tafiya da magana irin na masu class, musamman ita da take matar shahararren dan kwallo dole ta kame ta nuna ita babbar mace ce mai aji. Sai da Sultan ya zagayo yana faɗin “Matsa daga nan in ɗauko abata dan na ga ba mu kuka zo tarba ba.” Riƙe baki matar Taufiƙ ta yi tana nuna zallar mamaki ta ce “Kai bro yau kuma ni kake yi wa haka?” Bai kula ta ba ya kamo hannun Andizo ya fito da ita ta saki fuska ta sa hannunta a cikin na Sultan ta dubi matar, mara ce tana yanayi da Sultan kuma ba lefi tana da kyau, sai dai ba ta kai Sultan dinta ba. Dariya ta yi ta ce “Matar bro zo mu je karki tsaya sai man ƙwabrinki ya ƙame, waɗannan in suka haɗu sai a hankali.” Ta faɗa tana kama hannunta suka ci gaba. Sultan ya gyara tsayuwar shi yana bin Andizo da kallo yadda take tafiyar a yangance abin ya tafi da imaninsa, sai da suka shige sannan ya janye idanuwanta daga wajen ya kalli Taufiƙ tare da miƙa mishi hannu suka yi musabaha. Dukan wasa Taufiƙ ya kai wa Sultan ya ce “Angon Dije uwar masu gari ba gaba da gaba ba.” Dariya Sultan ya yi yana shafa ƙirji ya ce “Faɗi ka ƙara nine nan.” Dariya suka yi a tare suna tafawa sannan suka shiga ciki.. A palo suka same su zaune suna magana kamar dama can sun san juna, Sultan ya riƙe ƙugu ya ce “Limart kar fa ki koyawa matata rashin mutumci irin naki, na ga sai wani magana kuke ƙasa-ƙasa.” Kallon mijinta ta yi ta miƙe tsaye ta ce “Ka ga bro ba ruwan ka ku tafi in da za ku je ka bar mini ita a nan, kuma ni wani rashin mutumci ne nake da shi da har zan koya wa wani? Khadija zo mu je ciki mu bar su a nan tun da abin sa'ido ne.” Sai da ta fakaici idon Limart da Taufiƙ ta yi wa Sultan gwalo, kanshi ya nuna ya mata alamar da shi take? Ta gyaɗa kai ta juya suka wuce. Duk abin da suke a kan idanun su Taufiƙ gudun Sultan ya ce musu magulmata suka yi kamar ba su gani ba.. Ganin tafiyar da Andizo take kamar ba daidai ba ce Limart ta shiga toilet ta haɗa ruwan ɗumi, wardrobe ta buɗe ta ɗauko wata baƙar leda ta wuce Andizo dai na zaune a bakin gado tana jin yadda zazzaɓi ke nuƙurƙur ta, gabaɗaya ta gaji musamm da safe wanda ita ta janyo wa kanta. Tana fitowa hannunta ta kama suka shige toilet ta nuna mata ruwan tana murmushi ta ce “Ki shiga ki gasa jikinki za ki ji daɗi sosai ganyan magarya ne da bagaruwa za su taimakawa miki sosai, bari zan kawo miki towel.” To ta ce ita kuma ta fita ta kawo mata sabon towel a ledarsa ita da kanta ta buɗe, fita ta yi ita kuma ta cire kayan jikinta ta shiga cikin ruwan ta zauna. Sosai ta ji daɗin jikinta sai da ta ji ya yi fara yin sanyi ta fita ta ɗarwaye jikinta ta sa towel ɗin ta fito kanta a ƙasa. Kaya ta gani a kan gadon ta gane ita aka ajewa ta ɗauka ta sa, tana zama Limart ta dawo hannunta ɗauke da wani cup mai ɗan girma ta ciko shi taf da kunu, miƙa mata tashi ta ce “Kin shanye shi tas karki bar saura.” To ta ce duk da ba yunwa take ji ba amma ta ji tana son shan kunun, kurɓa ta yi ta ji wani mugun daɗi har tsakar kanta ai ba ta san lokacin da ta shanye ba sai jita yi babu komai a cup ɗin. Sai bayan sallar Isha'i su Sultan suka dawo gidan, da za su tafi Limart ta sa Andizo a ɗaki ta dinga koya mata yadda za ta janyo hankalin mijinta cikin ruwan sanyi, ta haɗa mata turaruka da na gida da na jiki da kuma na wanka har da ganyan magaryar duk ta haɗa ta zuba mata a leda, godiya sosai Andizo ta yi mata suka fito. Suna haɗa ido da Sultan ta sakar murmushi mai kwantar da zuciya, domin Limart ta ce ta fara gwada abin da ta koya mata daga yanzu ita kuma ta sa a ranta komai sai ta aiwatar. Sai da suka zo tafiya Limart ta ce “Bro a ba wa madam izini ta ba ni number wayarta.” Dafe kai ya yi ya ce “Oh my god! Ba ta da waya amma gobe idan mun dawo daga hospital za mu biya na sayo mana har ni, idan kuma kina son magana da ni ki amshi special number na sai ku yi magana.” To ta ce ta ɗaga musu hannu direba ya ja suka tafi. A daren ranar ma ba ta samu bacci kirki ya takura mata sai da ta dinga mishi kuka sannan ya rabu da ita, zafafan kalaman soyayya babu irin wanda bai faɗa mata, ji yake kamar ya mayar da ita ciki dan so da ta yi motsi dai ya ƙara kankame ta yana rarrashin ta. Washegari da safe karfe goma da rabi suka shirya zuwa hospital inda za a yi mishi aiki, tun da suka shigo mota tana maƙale a jikinsa ban da kuka babu abin da take, gabaɗaya tsoro ya mamaye mata zuciya gani take kamar in ya shiga ɗakin tiyata shima sai dai a fito mata da gawar shi. Suna packing a harabar asibitin ya ɗago ta fuskarsa ɗauke da damuwa ya ce “My wife kukan ya isa haka kina sagar mini da kwarin gwiwa, ki yi min addu'a ayi aikin nan lafiya karki sa nima na fara kukan.” Ya ƙarashe maganar yana share mata hawaye. Daina kukan ta yi ta riƙe fuskarsa tana kallon shi wasu hawayen suka zubo ta fara magana cikin raunanniyar murya. “Amour Wallahi tsoro nake ji ba na son kaima ka tafi ka barni, ka yi mini alƙawarin za ka fito lafiya.” Kai kawai ya jin mata yana mayar da hawayen da suka cika mata idanu, fita suka yi yana riƙe da ita har office ɗin babban likitan in da ya musu tarba ta musamman. Suna zaune aka koma haɗa komai na aiki wata doctor ta shigo ta sanar da babban doctor komai da ya zama ready su ake jira, Sultan na tashi ta miƙe ta riƙe shi tana kuka ya yi ta rarrashin ta amma taƙi yarda ta sake shi, sai da aka kira ɗaya daga cikin nurses ta riƙe ta ƙarfi sannan suka fita. Jiki ba kwari suka shiga wani ɗaki aka ba shi kayan marassa lafiya ya saka, zama ya yi aka fara mishi allura biyu a kowanni hannu sannan suka fara mishi gwaje-gwaje. Da sauri doctor ɗin ke duba Shi ta ɗago ta kalli babban doctor, tambayar tw ya yi me ke faruwa ta dakata daga aikin da take? Kai ta girgiza sai kuma ta sake mishi gwaji ta ja baya ta zauna a kan kujera, gabaɗaya duk sai ta sa likitocin jikinsu ya yi sanyi suka tambayar ta abin da ta gani game da gwajin da ta yi. Ba ta ba su amsa ba ta cire mishi duk wata na'urar da aka jona mishi, abin da ta gani ta nuna wa babban doctor Shi kansa ya girgiza da ganin abin da gwajin ya nuna, umarni ya ba su su janyo gadon da Sultan ke kwace wanda tuni bacci ya ɗauke shi,suka fita da shi zuwa wani ɗaki wanda ya fi wannan kayan aiki aka ɗora shi a wani baƙin gado tare da sa mishi wata hula mai aiki da lantarki duk suka koma gefe suka bar babban doctor.... _Maman Nusaiba ce_ [7/20, 12:06 AM] Ummu Amjad: ADZ 50 A kan idanunta aka fito da shi daga ɗakin tiyata zuwa ɗayan ɗakin sai ta muƙe zumbur za ta bi su, har ta kusa zuwa ta ji an kira sunanta ta tsaya cak a wajen har sai da aka sake kiran ta sannan ta juyo. Limat ta gani ita da Taufiƙ tsaye a inda ta tashi, a hankali ta tako ta iso har gaban su ta kalli Limat idanuwanta sun cika da ruwa, baki take motsawa tana son yin magana amma ta kasa, hakan ya sa ta kama ta ta zaunar cikin sigar rarrashi ta dinga magana. “Am sorry kin ji babu abin da zai same shi in sha Allah za a yi aiki lafiya, ki yi mishi addu'a.” Kasa riƙe kukan da ya zo mata ta yi ta rufe baki dinga yin shi marar sauti, sosai ta ba su tausayi Taufiƙ ma ya zauna suka ci gaba da rarrashin ta har suka samu ta daina kuka amma idanuwanta a kan kofar ɗakin da yake ciki. Zuwa can sai ga Doctor ta fito ta yo inda suke, ta miƙe da sauri jikinta na ɓari tun kafin ma ta fara magana ta riga ta, “Doctor kar dai ki ce mini ya rasu? Idan ya mutu nima bin shi zan yi don Allah ki taimaki rayuwar marainiyar Allah.” Janyo ta Limat ta yi ganin ta fara fita daga haiyacinta suka bi bayan Doctor zuwa office ɗin babban likita. Suna isa duk suka zauna ya dube su yana murmushi sai ta saki baki tana kallon shi, bayan ya gama rubuce-rubuce a kan takardar da ke ƙunshe da bayanan cutar Sultan ya ɗago ya kalle su, duk zuba mishi ido suka domin sun ƙagara su ji me zai faɗa musu ita kanta Limat jikinta ya yi sanyi, gyara zama ya yi sannan ya fara musu bayani. “Gaskiya na yi matuƙar mamaki game da Mr J ban taɓa jin karo da majinyaci irin shi ba.” Saurin katse shi Taufiƙ ya yi, “Doctor me yake faruwa da abokina? Ka mana bayani kai tsaye domin zuƙatanmu su samu sauƙi. Murmushi ya yi a karo na biyu ya ɗora da cewa, “A wancan satin da ya zo na faɗa mishi ya yi maza ya dawo London domin ƙodarsa ɗayar ta lalace, da farko ya ƙi yarda da abin da na fara mishi sai da ya je Nigeria ya kwanta ciwo nan suka tabbatar mishi matuƙar ba a cire ƙodarsa ɗaya ba to za ta iya harbar ɗayar itama ta kamu da cuta, idan hakan ta faru kuma akwai gagarumar matsala. To yanzu yau da ya dawo mun kai shi ɗakin tiyata har an gama mishi allurori an haɗa komai na aiki, da doctor Julie ta yi gwaji sai abin ya firgita ta, ni kaina da na gani sai na kamu da mamaki ta ya mutumin da ƙodarsa ta lalace a zo za a mishi aiki kuma a samu lafiyar su ƙalau babu wannan cutar ko ƙwaya ɗaya, shi ya sa muka fito da shi zuwa ɗakin miƙe gwaji na musamman amma duka abu ɗaya ya nuna mana lafiya yake babu komai a jikinsa.” Kallon juna Taufiƙ da Limat suka yi a tare suka ce “To ya aka yi haka?” Girgiza kai ya yi ya miƙa musu takardar ya ce “Ni kaina ban sani ba amma abin ya girgiza ni sosai.” Andizo ta ɗaga hannu tana dubar da hawayen farin ciki ta ce “Alhamdu Lillah Allah na gode maka da addu'a ta ta karɓu, Allah ka ƙara wa mijina lafiya ka kare shi.” Amin suka ce suka tashi cike da farin ciki suka nufi ɗakin da yake kwance. A tare suka shiga ɗakin duk ta ƙagu ta ganshi, kwance suka same shi ta yi saurin ƙarasawa bakin gadon tare da sunkuyawa ta manna mishi kiss a goshi ta sa hannu tana shafa kwantacccan gashin kansa, Limat ta ja mijinta suka iso ta ce “To Laila da Majnun sai ki daina kukan tun da ba a farke miki cikin miji ba.” Dariya mai sauti ta yi tana goge fuskarta da hijabi za ta yi magana ta ga ya fara motsawa, hannunsa ta riƙe tana faɗin “Sannu Amour.” A hankali ya fara buɗe idanuwansa tun yana ganin dishi-dishi har ya washe, Taufiƙ ya matso kusa da shi yana jera mishi sannu. Taimaka mishi ya yi ya tashi zaune cike da mamaki yake kallon jikinsa sai shafa ciki yake, Andizo ta ruƙo masa hannu tana mai nuna tsantsan farin ciki ta ce “Amour ya kake jin jikin naka yanzu?” Lumshe ido ya yi Taufiƙ ya ce “Ka yi mamaki da ba ka ji alamar ciwo a jikinka ba ko?” Buɗe ido ya yi ya ce “Sosai ma Taufiƙ wai me ya faru ne? Ko lokacin fara aikin ne bai yi ba? Amma kuma ai ni da kaina na shiga ɗakin tiyata na kwanta a kan gado aka mini allurori daga nan dai ban san komai ba sai yanzu.” Zama ya yi a ɗaya daga a ɗayar kujera ya zayyano mishi duk abin da Doctor ya sanar da su, baki ya buɗe yana kallon Taufiƙ sai kuma ya juya ya kalle ta, kama hannun Limat ta yi ya ce su sun tafi gida ya bi su da kallo har suka bar ɗakin. “Amour ka ga ikon Allah ko? Mu kanmu mun yi mamaki ko na ce mun ma fi ka Allah ne ya dube mu da idanun rahama amma dai abin akwai ɗaure kai duk da ba a ja da ikon Allah.” Ajiyar zuciya ya sauke ya sa hannu ya ɗago ta ta taimaka mishi ta hayo gadon, kallon juna suka dinga yi na ɗan wasu second sannan ya ce “Gaskiya ina ta al'ajabi My wife, yau fa da safe ji na yi kamar ana yankan naman jikina har muka iso asibiti, a lokacin dauriya nake ganin yadda kika ruɗe amma kuma yanzu sai a ce wai lafiya ta ƙalau? To duk da haka dai Alhamdu Lillah.” Murmushi ta yi ta sauka a gadon ta kama shi ya sauko sun nufo ƙofa sai ga doctor ya shigo, kallon juna suka yi ya miƙa mishi hannu ya ce “Congratulations.” Murmushi ya yi suka fita tare yana ƙara mishi bayanin dukkan abin da suka gani har ya gamsu. Har bakin mota ya rako su sai da ya ga tafiyar su sannan ya dawo. A hanya suka tsaya jikin wani Restaurant, kallon ta ya yi hannunsa cikin nata ya ɗan murza ta turo baki tana kallon gefe, gefen wuyanta ya sumbata ya ce “Me kike son ci?” Girgiza kai ta yi ya janyo daf da shi ya ce “Me ya faru na ga kin canja fuska?” Ya faɗa yana kallon in da take bi da ido, wata matashiyar budurwa ya gani ita da mahaifinta da mahaifiyarta sun saka ta a tsakiya suna ciyar da ita, idan wannan ya ba ta wannan ya ba ta sai shagwaɓa take zubawa son ranta. Fuskarta ya juyo gareshi ya ga hawaye na yin fareti a bisa kumatunta, cikin damuwa ya kwanto da ita jikinsa yana bubbuga mata baya. Sai da ya ji ta daina shashshekar kukan sannan ya ɗago da ita cikin tsananin kulawa yana share mata hawaye. “My wife ƙi Kwantar da hankalinki don Allah ba na son ki saka damuwa a ranki har wani abu ya same ki, ba gani ba a tare da ke ni zan zame miki uwa, uba, miji, yaya, dangi, duk abin da kike so zan miki shi komin wahalar shi in dai kuɗi yana sayan shi.” Komawa ta yi jikinsa ta ƙara fashewa da kuka murya na rawa ta fara magana. “Amour ba za ka gane ba, Idan na ga iyaye na kulawa da ɗiyansu sai naji inama ni ce da nawa iyayen, sai kuma na tuna ni ɗin marainiya ce gaba da baya duk da na, samu gata da kulawa a wajen kakannina sun aurar da ni a in da aka ci gaba da kula musu da ni har na gane ni wace ce, lokacin da na gane ba su ba ne iyayena na shiga firgici da tashin hankali marar musaltuwa, a yadda Salim ya sanar da ni labarin mahaifana ba ƙaramar girgiza na yi ba, mamata ta ɗanɗani azaba biyu a lokaci ɗaya ta yi naƙuda ta haifi iya runguma ta kawai ta yi ta sadaukar da rayuwarta domin ta tseratar da tamu rayuwar, a wannan yanayi na ciwon haihuwa suka kashe ta. Babana kuma ni ban sani ba sun kashe shi ko sun tafi da shi ne? Har yanzu ina jin a jikina wata rana zan ga mahaifina domin a yadda na samu labari fantsama suka yi lokacin da aka kawo wa ƙauyenmu hari kowa yana gudun ceton rai, mamana ta tafi da yayuna da kuma ni da nake ciki tana tsaka da naƙuda ta, ya Allah ka jiƙan ta da rahama ka haskaka ƙabarin ta, babana idan yana raye Allah ya nuna mini shi kafin numfashina ya tsaya.” Ta ƙarashe maganar tana sa sabon kuka, ganin budurwar nan da iyayenta ya ƙara karyar mata da zuciya.. Wani mugun tausayin ta ne ya mamaye mishi zuciya, rarrashin ta ya dinga yi ya fara mata nasiha. “My wife ƙi ɗauka wannan ita ce ƙaddararki ki rayu ba tare da ganin fuskar iyayenki ba ko da sau ɗaya ne, ki gode wa Allah da kika samu gata aka kula da tarbiyarki sannan kika auri miji jajirtacce kamar Salim, bayan Allah ya ɗauke miki shi kin yanke hukunci ba za ki ƙara aure ba har abada, a tunaninki ba za ki samu miji kamar Salim ba amma da yake Allah maji ƙai ne ya ba ki ni a matsayin miji na biyu, ko ta hana ai ya kamata ki daina kukan maraici domin Allah haskaka rayuwarki da ni'imomi kala-kala, dan haka ki ce Alhamdu Lillah.” Ya ƙarashe maganar yana yin kissing lips ɗin ta ya tsotsa kaɗan ya saki yana bin ta da kallo. Dogon numfashi ta ja sosai ta ji hankalinta ya kwanta ta ɗago kai za ta yi magana ya dora hannunsa a kan bakin hakan ya sa ta hadiye abin da take son faɗa. Fita ya yi ya zagaya ya buɗe mata ƙofa ta fito tana gyara zaman hijabinta, bodyguard ɗin sa suka firfito su shida biyu a gaba huɗu a bayan su haka suka shiga restaurant ɗin. Wajen da aka tanada domin cin abinci suka nufa mutane har sun fara ɗaukan su a waya, ita dai taƙi sakin jikinta sai manne mishi take tana ɓoye fuskarta dan kar su ɗauke ta, gane hakan ya sa ya buɗe handbag ɗin ta ya cire mata niƙaf ya kare ta ta ɗora, sai a sannan ta iya zama da kyau. Masu kawo abinci suka zo su biyu suna tambayar su me za a kawo musu? Kallon nau'ikan abincin Sultan ya yi ya nuna wani gasashen nama, miƙa mata daftaran ya yi a hankali ya ce “My wife me kike so bayan gasashen naman?” Wani juice wanda aka haɗa da madara ta nuna ta ce “Shi kadai nake so.” To ya ce mata ya faɗa musu adadin da suke buƙata. Suna zaune Andizo ta kalli mutanen da ke wajen can ta hango wasu mata biyu na son zuwa in da suke amma bodyguard sun hana su, da mamaki ta kalli Sultan ta ce “Amour su waye ke son zuwa in da kake ake hana su?” Ɗago kai ya yi suka haɗa ido da Jennifer ita da Ruby, haɗe fuska ya yi ya sa aka sanar da masu restaurant ɗin su musu takeaway ba za su ci abincin a wajen ba, hakan ya yi mata daɗi domin ita Allah ya mata kishi mai tsanani musamman a kan Sultan, ji take ta ma fi jin kishin sa fiye da lokacin da ta yi rayuwa da Salim. Bayan an gama musu komai suka biya kuɗin sannan suka wuce, sai da ya saka ta a mota ya juyo ya ji ta damƙo rigarsa ta baya, sarai ya gane ita ce sai ya juyo tare da faɗin “A'uzu billahi!” Wani irin kallo ya mata wanda ya sa ta yi saurin sakin shi, bai ce da ita komai ba ya juya ya wuce ya shiga mota suka bar wajen. Wani irin zafi ta dinga ji ƙirjinta na mata sai hasaso Jennifer take tana mamaki tsaurin idon ta, can kuma sai ta ce ƙila ko sun san juna ne shi ya sa hakan ya sa ta daure fuska tashi daga jikinsa ta koma can gefe tana hura hanci.. Ranar kasa gane kanta ya yi abincin da suka sayo ta ce ta ƙoshi ta shige ɗaki ta rufe, babu kalar rarrashin ta da bai yi ba amma taƙi buɗe mishi ƙofa sai shi kaɗai ya kwana a ɗakinsa. Washe gari bayan Sallar Isha'i tana zaune tana kallon wani move wayarsa da ke aje a caji ta ji an kira, tashi ta yi da nufin ta kai mishi wayar amma, ganin sunan Jennifer ɓaro-ɓaro a kan screen ɗin wayar ya sa ta yi jifa da wayar ji kake tasss! Zama ta yi jagwab a kan kujera tun kafin sun zo gia jiya take ganin kiran Jennifer na shigowa a wayarsa. Tsaye ya yi a kanta cikin wani irin yanayi ya rasa me take so ya faɗa wanda za ta yarda yanzu ba sa tare da Jennifer, ga shi Jiya ta azabtar na nisanta kanta da shi da ta yi da kyar ya yi bacci yana ta juyi. Ji ta yi kamar ana kallon ta ta ɗaga kai suka haɗa ido da shi, tashi ta yi da sauri ta wuce ya bi bayan ta yana faɗin “My wife please ki tsaya mu yi magana.” Kafin ma ya ƙarasa faɗa tuni ta faɗa ɗaki ta datse ƙofar da kye, bugawa ya dinga yi tana ji ta yi banza da shi har ya gaji ya dawo palo yana kallon yadda wayar ta yi ɗaiɗai, girgiza kai ya yi ya sunkuya ya dauki sim ɗin ciki ya kira mai aiki ya ce ta share gurin shi kuma ya wuce daƙinsa.. _Maman Nusaiba ce_ [7/22, 2:11 AM] Ummu Amjad: ADZ 51 Abu kamar wasa yau dai sun kwashe sati uku suna zaune a irin wannan yanayin, ta daina mishi komai idan ma ta ji motsin shi a palo ba ta fitowa sai ta yi zaman ta a ɗaki, gabaɗaya ta ji garin duk ya ishe ta saboda ko waya ba ta ita ballantana ta kira wani ko ta yi kallo, ga shi ba ta san yadda za ta kunna tv da ke cikin ɗakin ba. A ɓangaren Sultan kuwa ba ƙaramar azabtuwa yake ba, ya bi hanyoyi da dama domin su haɗu amma bai yi nasara ba, yana son ya fahimtar da ita su yi magana a nutse amma fir taƙi daɗi idan ya matsa da buga mata ƙofa sai ta tayar da aljannu tana ihun ya matsa mata daga bakin ƙofa, ganin abin na son fin ƙarfinsa sai ya tattara ta gefe ya zuba mata ido. Sanye take da riga da sket na atamfa orange colour ta kafe ɗauri a gaban goshi, gashin kanta da ya sha gyara ta daure shi ta yo baya da shi, ba ta yi wata kwalliya me yawa ba hoda ta shafa ta sa kwalli sai man kaɗan da ta sa lip, sosai ta yi kyau ta ɗauki mayafi mai ɗan girma ta ɗora a kafaɗa tana kallon kanta a madubi. Ji ta yi ba za ta iya fita da mayafi ba dama can ita ba ma'abociyar sa shi ba ce, amma dan ta ba shi haushi dai ta zari handbag ɗin ta ta yo waje tana ɗora wani ɗan sirrin agogo a hannunta na hagu, ɗayan hannun kuma wani babbar warwaro ne mai kyau sai kyalli yake haka ta fito fuska daure tana taku ɗaiɗai kamar wata sarauniya. Tun kafin ta ƙaraso ƙamshin turaren da ta sa ya kawo wa hancinsa ziyara ya lumshe ido cikin wani irin yanayi ya ce “Oh my wife kina son kashe bawan Allah.” Miƙewa ya yi yana sakar mata murmushi ita kuma tana aiko mishi da harara har ta iso ta tsaya, sam ba ta son su fita tare amma ba yadda ta iya tun da kiran Limat ne, a gaban ta ya tsaya yana bin mayafin da kallo cike da mamaki. “My wife ya kuma na ga kin ɗauko mayafi?” Wani irin kallo ta mishi ta kawar da kai gefe tana hura hanci, kai ya girgiza ya juyo da fuskarta ya ƙura mata ido, fisgewa ta yi ta dawo kan kujera ta zauna. Wayarsa ce ta ɗauki ruri ya duba ya ga Taufiƙ ne ke kira, ɗagawa ya yi kafin ma ya yi magana shi ya riga shi yin. “Malam idan ba za ku zo ba sai ka sanar da ni, ka shanye mu kamar kayan wanki kuma kasan gobe ne za a fara buga wasa kana sanya yankin gara.” Hannu ya sa aljihu ya nisa sannan ta ce “Mayar da wuƙaƙen gamu nan fita madam ce ta ɓata mana lokaci.” Yana faɗin haka ya ɗauke wayar daga kunnensa ya sa a aljihu, kallon ta ya yi sai wani basarwa take tana hararar shi ta gefen ido, gaba ya yi yana mata alama da a biyo shi ba muso ta bi bayan shi suka yo harabar gidan. Har suka isa babu wanda ya cewa wani ƙala, shi kam ya shiga damuwa na wannan ɗaukan Allah gangamon da ta yi da shi alhalin ba ta tsaya ta bincika ta gano gaskiyar lamari ba, a palo suka same su ko zama Sultan bai yi ba Taufiƙ ya kalli agogo ya ce “Oya muje.” Kallon Limat ya yi gaba ta biyo shi, a bakin mota suka tsaya ya dube ta da yanayi tausayi ya ce “Ƙanwata don Allah ki taimaki yayanki, Khadija yau sati uku kenan ba ta mini magana komai da kika sani na mata da miji ba ta yi, na rasa gane kanta wani lokacin sai na ga kamar aljannun da suka shiga jikinta ne suka dawo.” Da mamaki ta kalle shi har da riƙe baki domin yadda suke waya da ita tana fallasa mata sirrin zuciyarta irin son da take mishi sai ta ji maganar tashi ta mata banbarakwai, gyara tsayuwa ta yi ta kalli Taufiƙ da ya juya musu baya ya yi kamar ba ya jin me suke faɗa, kallon Sultan ta yi ta ce “Bro ka tabbata babu abin da ka yi mata? Anya Khadija za ta kwashe kusan wata ɗaya tana fushi da kai ba tare da wani ƙwaƙƙwaran dalili ba? Ka dai faɗa mini abin da ka mata ta hakan ne zan samu damar shayi kanta ta sauko, idan kuma ba ka faɗa ba ni ba zan iya ba gaskiya.” “Madam shi ne da lefi ba Khadija ba, wannan fitinanniyar yarinyar ce take son dawowa cikin rayuwarsa, shi ne ta gano abin da ke faru hae hka ta faru amma ki same ta ku yi magana.” Taufiƙ ya ƙarashe maganar yana shige da wa mota. Zaro ido Limat ta yi sai kuma ta juya tana faɗin “Bro ka kwantar da hankali zan shayo kanta.” Jiki a sanyaye ya shiga motar suka bar gidan. A inda ta zauna a nan ta same ta, zama ta yi ta kira mai musu aiki ta sa aka kawo mata lemo mai sanyi da cake, babu abin da ta taɓa sai murmushin yaƙe da take har Limat ta gama shirya yaranta suka fita za a kaisu wajen wasa, bayan ta dawo ne ta dube ta ce “Khadija wai lafiya na ga kin rame shima ya rame kamar kuna shan ruwan zafi? Me ke faruwa?” Hawaye ne suka zubo mata ta sa hannu ta goge Limat ta matso kusa da ita ta dafa ta cikin nuna kulawa ta ce “A tunanina na zama 'yar'uwarki uwa ɗaya uba ɗaya duk abin da ya ke damun ki za ki zo ki sanar da ni, ashe ke ba ki ɗauke ni a matsayin yayarki ba shi ya sa kike ɓoye mini abin da yake damun ki.” Kuka take sosai har da ja numfashi Limat ta zuba mata ido duk sai ta ba ta tausayi, sai da ta yi mai isar ta sannan ta riƙe hannunta ta ce “Ki sanar da ni abin da ya sa kika rame.” Baki na rawa ta fara magana “Anty ina jin kishin sa kamar na mutu, Wallahi ba zan juri na ga wata mace a, waje tana bibiyar shi ba in dai ba auren ta zai yi ba, amma a kan kullum za take kiran shi ba dare ba rana text message ya fi a lissafa wanda take mishi a kodayaushe, wai har ce mishi take ta yi kewar kwana a jikinsa da ƙamshin turaren da ya saka wa yaushe zai zo su gaisa? Wata kalmar ta yi mini girma ba zan iya faɗa miki ba ni ba zan iya zama ba gara ya mayar da ni ƙasarmu.” Kuka ta kuma sakawa Limat ta girgiza kai tana dariya, jin hakan ya sa ta tsayar da kukan tana kallon ta cike da mamaki, gyara zama ta yi ta fuskance ta ta ce “Ba ki san waye Sultan ba har yanzu Khadija, shi mutum idan ya ce ya bar abu to fa ya bar shi har abada ba zai ƙara waiwayar wannan abin ba, da ta dinga turo mishi da message kin taɓa gani ya mata reply ko da sau ɗaya ne?” Girgiza kai ta yi ita kuma ta ɗora, “To ki farka daga nannauyan baccin da kike ki dawo haiyacinki, ke za ki dage ki kwace mijinki ki zame mishi mace guda ɗaya tilo a zuciyarsa, wannan fushin da kike duk ba shi zai sa Jennifer ta rabu da Sultan ba, shi ya rabu da ita tun lokacin da kika shigo rayuwarsa ya watsar da duk wani abu marar kyau ya koma makarantar addinin islama neman ilimi.” Ji ta yi kaso tamanin bisa ɗari ta gamsu da bayanin ta, a hankali ta buɗe baki kamar mai koyon magana ta ce “Anty dama can tun asali yana neman mata? Ko kuwa da ya dawo nan ƙasar ne ya buɗe ido da su?” Girgiza mata kai ta yi sannan ta ce “Sultan ya taso cikin gata da sangarta irin na wasu 'ya'yan masu kuɗi, mahaifinsa ba ya son ganin ɓacin ransa shi ya sa yake lallaɓa shi tamkar shi kaɗai ne ɗan da ya samu bayan akwai wani namiji kafin shi, kasancewar sunan mahaifinsa aka sa mishi sai ya fifita shi a kan yayansa Rudwan, bayan shi kuma aka haifi su Doctor Rahama nasan kin gansu. Kwanci tashi har suka zama samari baba ya haɗa su lokaci ɗaya ya musu aure da matan da suke so, tun ya taso yake da burin yin kwallon ƙafa baba ya goya masa baya duk da Mom ta nuna ba ta so, haka ya dinga ƙoƙarin cika mafarkinsa. Bayan shekara da aurensu ya zama shahararre a fanni kwallon ƙafa in da ya dawo nan London da zama, mata dayawa sun kawo kansu gare shi amma shi sam ba sa gaban shi ta matarsa yake har Allah ya sa ta samu ciki ta haifi 'yarta mace wato Farrah, sosai muka yi murna da samun ƙaruwa suka dawo gida aka ci gaba da kulawa da matarsa da jaririya, wata uku da haihuwar Farrah wata ranar Lahadi da ba za mu taɓa mantawa da ita ba wadda familynmu ke kira baƙar rana, sun shiga jirgi su duka za su zo wajen aurena suka yi hatsari wasu suka mutu wasu suka jikkata haka aka yi asibiti da su. Waɗanda suka mutu sun haɗa da Rudwan da matarsa, Baba, mahaifiyar Farrah, su kuma su Sultan su ne suka ji ciwo. Kowa sai da ya tashi aka bar Sultan a doguwar suma har na tsayin wata ɗaya, bayan ya farfaɗo aka sanar da shi mutuwar matarsa ranar sai da aka kulle shi a ɗaki, domin hauka tuburan ya dinga yi yana fashe-fashen kaya ya ce shi matarsa da su baba ba su mutu ba, sai da aka kusa shekara sannan ya dawo cikin nutsuwarsa ya dangana. Shi yake kula fa Farrah tare suke kwana duk abin da uwa take wa ɗa shi yake yi mata, Mom ta yi faɗan ya bari ita ta ci gaba da kula da ita amma sam ya ƙi dole ta rabu da shi, Farrah ta cika shekara biyu amma kullum in ya duba wani abu na mamanta sai ya shiga kunci dole ta sa ya dawo nan London gabaɗaya da zama.. A cikin wannan yanayin ne ƙaddara ta haɗa shi da Jennifer, wata rana ya fito zai zo nan gidan ya buge ta da mota sai ya kai ta asibiti, bayan ta farfaɗo sai ya nemi sanin gidansu ta faɗa mishi ya ɗauke ta suka tafi. To da kaɗan-kaɗan yana zuwa ya zubo ta ko ya sa yaransa su kai mata kayan abinci kasancewar iyayen Jennifer ba masu ƙarfi ba ne talakawa ne, shi ya sa yake jin tausayin ta har ta samu ya ba ta number shi suke gaisawa idan ya samu time, ƙarshe dai suka kulla soyayya har ya faɗa mata matarsa ta rasu, ta tausaya mishi sosai ta dinga ba shi kulawa da kyautata mishi iya iyawarta, bayan ta samu shiga sai ta nemi kusanci da shi sosai ƙarshe dai suka zama kamar miji da mata, na yi baƙin ciki ganin ɗan'uwana ya zama mazinaci amma babu yadda na iya. Ita ta canja mishi rayuwa a baya da iya kwaya yake sha a gida sai ya zamana duk wani nau'i na kayan maye babu wanda ba ya sha, ita koya mishi zuwa club iri-iri da dare ba shi da aiki daga zuwa yawon banza sai buga kwallo, komai nashi ya canja har Mom ta gano ɗanta ya zama rikakken ɗan shaye-shaye, ke in taƙaice miki Jennifer ba ƙaramar makira ba ce kaɗan ya rage Sultan ya bar musulunci saboda da ita, sai Allah ya shigo da ke cikin shafin rayuwarsa daga nan ne ya dinga neman ta yadda zai ɗauko ki. Labarin auren ki da ya ji a nan ya yi jiyar jikinsa a cikin gidan nan ko buga kwallo ba ya zuwa ya ɗauki hutun sati biyu, da kyar ya dawo daidai a lokacin ya yanke alaƙarsa da Jennifer.” Ta ƙarasa faɗa mata yadda suka rabu da yadda ta dinga bin hanyoyi wajen ganin ya dawo gareta, a ɗago suka haɗa ido da ita ta ce “Wannan shi ne ɗan taƙaitaccan tarihin Sultan, shi ne za ki bari mijinki ya ƙara faɗa wa tarkon waccen sheɗaniyar?” Jinjina kai kawai take tana bin Limat da kallo, ashe haka yake son ta? Goge hawayen da suka zubo mata ta yi nan take ta ji wani nadama na shigar ta na ƙin tsaya ta saurare shi. “In sha Allahu ni zan gyara mata zama tun da ta shigo gonar ni uwar masu gari, za ta ɗanyan aikin jikar Hajja yaushe ne ma za su buga wasa?” Ta faɗa tana huci. Murmushi Limat ta yi ta mata jinjina da hannu ta ce “Yawwa ƙanwata ki zama jaruma, gobe ne za a buga wasan kuma nasan za ta zo domin in sun ci ta rungume shi kamar yadda ta saba a baya, musamman ma yanzu da ta san ba za ta iya ganin shi ba sai ta wannan hanyar.” Kwafa ta yi ba ta sake cewa komai ba tana ta shawara da zuciyarta me ya kamata ta yi a goben. Sai yamma suka dawo ya ɗauke ta suka wuce gida, tun a hanya ya ga canji daga gareta sosai ya cika da farin ciki, gira ya dage mata ya ce “My wife me kike son ci na biya na mana takeaway?” Wani irin kallo ta mishi irin na masoya tare da sakar mishi tsadaddan murmushi ta ce “Amour ni ba na son komai mu je gida zan mana girki mai daɗi da ya fi da waje komai.” “Allah da gaske my wife.” Kai ta gyara mishi tana dariya, shi ma ya taya ta. Daren ranar ya nuna mata shi ɗin masoyinta ne na haƙiƙa, ita kanta ta aminta da son da yake mata babu algus a cikinsa. Washegari ya shirya ta shima ya shirya suka fito sai filin buga wasa, a mota ya ba ta rigar irin ta jikinsa mai lamba takwas a baya taƙi ta saka, sai da ya lallaɓa ta sannan ta saka ta yi rolin kanta da mayafin abayar jikinta. Wasa aka fara bugawa bugun farko aka ci su Sultan, ita kuwa tana zaune a gaba tana kallon Jennifer da ke can gefe sai kiran sunan Sultan take kamar yadda sauran jama'a suke kiran shi ganin kwallo ta zo hannunsa, kawar da kika ta yi ta mayar kan su. Ana ta fafatawa a filin daga har Sultan ya samu saka kwallo a raga har su uku su kuma waɗancan sau huɗu a haka aka tafi hutun rabin lokaci. Wasu dakuna ta gani ya kama hannunta suka shiga ɗaya daga ciki ya faɗa kan gado buduf, haki ya dinga yi AC ba dukan shi sai jera mishi sannu take tana shafa kansa, ji ta yi ya ba ta tausayi sai gani ta yi ya tashi ya hau kan wani inji ya dinga motsa jiki sai da ya yi sharkaf sannan ya sauko ya zauna duk tana zaune tana kbin shi da na mujiya. Kwankwasa ƙofa aka yi ya ba izinin shigowa, wani kalar juice aka kawo mishi ya amsa ya shanye nan take ya koma ya zauna, fuska a haɗe ta ce “Ina fata dai ba giya ba ce ka sha?” Miƙewa ya yi tsaye ganin time ɗin komawa saura minti biyu, kiss ya manna mata a goshi ya ce “Ki yarda da mijinki ya zama Ustaz.” Murmushi ta yi ta miƙe ta rungume shi ya ce “Karki fara my wife muje, idan kuma za ki huta ni zan wuce in kin fito akwai wanda zai kaiki har wajen zaman ki.” Ce mishi ta yi ita ba yanzu za ta fita ba ya yi gaba ita kuma ta zauna, ya fita kenan ta ji ana buga ƙofa ta tashi ta buɗe. Kafin ma ƙarasa buɗewa ta ji an hankaɗo ta ta yi taga-taga za ta faɗi ta tsaya, kallon su take cike da tsaurin ido ta ɗaga kai ta kalli samar ɗakin ta ga ba cctv sai ta matsa ta shigo. A wulaƙance take kallon Andizo har ta zauna a kan gado, tsaki ta ja ta ce “Kin yi kuskure Khadija da kika yi sanadin raba alaƙa ta da Mr J.” Dariya Andizo ta yi ta cire rigar da ya sa mata ta yi tsukiya da mayafin abaya ta ce “Ke zan cewa kin yi kuskure da kika shigo ɗakin nan, dama neman hanyar da za same ki nake sai ga shi kin kawo kanki cikin ruwan sanyi, yau sai na rarrabe miki tsakanin aya da tsakuwa.” Kanta ta yi ta rufe ta da duka ta ko'ina, duk da Jennifer na ramawa amma ƙarfi wadda ta girma a afirca ba ɗaya ba ne da na wadda ta taso a turai. Sai da ta galabaitar da ita sannan ta juya tana neman abin duka, can ta hango cazar Sultan ta isa da gudu ta ɗauko ta dinga tsula mata, sai da ta ga da kyar take numfashi sannan ta daina dukan ta ta ja ta ƙiii ta zaunar ta jingina ta a jikin gadon, kunnenta ta damƙa ta murza da ƙarfi ta saki ƙaran azaba, a fusace ta ce “Za ki ƙara takura wa rayuwarmu?” Girgiza kai ta dinga yi ta daka mata tsawa ta ce “Idan ba ki faɗa da bakinki sai na kakkarya miki ƙafafu, shegiya mai kama da ƙosai ke har kin isa ki ja da ni? Za ki sake bibiyar mini miji?” Ta sauke mata dundu a gadon bayan. A wahalce Jennifer ta ce “Am sorry Khadija ba zan sake ba daga yau.” Rankwashi ta kai mata a ka ta ce “Ki ma ƙara ki gani wannan zan miki gaba sai an kasa gane hatsari kika yi ko faɗowa kika yi daga bene mai hawa talatin, ai susar jiki na miki matuƙar ba ki kama gaban ki kin rabu da rayuwarmu ba, maza tashi je ki wanke fuskarki da hannu, kuma duk wani motsin ki a tafin hannuna yake duk in da za ki shiga akwai masu bibiyar ki.” Da kyar ta tashi za ta bar ɗakin ta kara daka mata tsawa dole ta shiga toilet tana tsaye ta wanke fuska da hannu ta goge da towel suka fito, sai da suka nufo wajen ta riƙe hannunta suka ƙaraso. Sai da ta kai ta har wajen zaman ta ta zaunar da ita a gefen Ruby Sannan ta dawo ta zauna a kusa da Limat. Kallon ta Limat ta yi ganin yadda take huci, “Khadija ya na ganki ke da Jennifer kuma kina huci?” Dogon numfashi ta ja ta ce “Zan miki bayani daga baya Anty.” Ta ƙarashe maganar tana murmushi ta mayar da hankalinta ga wasan. A ranar su Sultan suka cinye kofi mabiyan su suka dinga ihu ana tafi, Andizo sai ta ga turawa na rungume ta ana taya su murna. Bayan kwana biyu Andizo ta sanar da Limat abin da ta yi wa Jennifer, dariya ta dinga yi tana jinjina rashin tsoron ta ya ce “Lalle Khadija ba ki da tsaro, kuma kin ga ba ta shigar da ƙara ba.” Dariya itama ta yi ta ce “Ta shigar mana ta ga yadda zan sake zuwa har gidanta na mata ɓalle-ɓalle a mazaunai.” Dariya suka kuma sa wa suka ci gaba da hira. A kwana a tashi su Andizo suka yi wata biyar a London suna shiga na shida ta kwanta rashin lafiya a lokacin ne kuma Farrah ta diro ƙasar, sun yi murna da ganin juna Farrah ta zama big girl ga class a daren ne zazzaɓin da ke zubo mata duk dare ya tsananta suka yi asibiti da ita, gwajin farko aka tabbatar musu tana ɗauke da ciki har na wata uku, ranar du kansu ma'aikatan asibitin sun san ɗan da zai fito a cikin Khadija ɗan gata ne, domin Sultan rabon kuɗi ya dinga musu yana ta yin sujjada yana gode wa Allah da ya albarkace shi da damun ƙaruwa, ganin yadda suke murna har tausayi suka mata Farrah har da kuka ta yi itama za ta samu ƙane ko ƙanwa.. Tun daga asibitin ya dinga kiran abokansa yana sanar da su matarsa n da ciki, sun taya shi murna waɗanda ba su samu damar ganin ta ba suka ce ai kuwa za su shirya walima suka sa rana, ita dai Andizo in suna wani abin tagumi take ta dinga kallon su, Farrah zuwa take ta dafa cikin ta dinga yin magana wai tana hira da ɗan'uwa ko 'yar'uwarta. Ranar da abokansa suka zo kowa gift ya dinga ba ta, wasu kayan baby wasu sarƙa mai tsada wasu warwaro, wasu kuɗi haɗi da flower Mai ƙamshi an naɗe kuɗin a jiki, ranar sai da ta yi kukan kyautar da abokan mijin nata suka mata. Bayan kwana biyu matayensu suka zo taya murna tun abin na mata mamaki har ta daina ji ta shiga cikin su wasu turawa ne wasu kuma Hausawa irin ta, da za su tafi duk suka amshi number ta aka saka ta a group ɗin manyan mata masu class da aji matan manyan mutane. Cikin ta na cika wata tara ta haifo ɗanta namiji fari sol mai kama da ubansa sak da yamma aka ba su salama, bayan sun dawo Mom ta ce dole ya tarkata su dawo gida a kula da ita ba dan ya so ba ya cira musu ticket har da Limat suka nufi Nigeria. Ranar suna an ga ɓarin kuɗi, masu rabo har da wayoyi suka samu gift din uban jego, canjin kaya kuwa sun yi ya fi kala shida shima dan ta ce ita ta gaji da canja kaya ne ya haƙura, yaro dai ya ci sunan Rudwan sunan yayansa wanda Andizo ce ta ce a sa wa jaririn, sosai ya family suka ji daɗin karar da ta musu. Sai bayan kwana goma da zuwan su ya koma London cike da kewar su, ita kuma Mom ta ci gaba da gyara ta. Bayan sun gama arba'in ta shirya ta nufi Niger ganin dangi. A Niamey ta fara sauka suka haɗu da Amira da katon cikinta har dare suna hira, sai washegari ta nufi Tilaberi inda dangi da 'yan'uwa suka dinga ɗaukan Rudwan har sai da Maigari ya hana kowa ɗaukan shi. Kwana uku ta yi tana zaga gari ta je gidan su Hajaru ta samu ba kowa, cikin jimami ta dawo ta tambayi Hajja. “Hajja ni kuwa lafiya na ga gidan su Hajaru ba kowa? Kuma har dabobinsu duka babu me ya faru?” Aje mata ɗumamen tuwo ta yi a gaban ta ya sha man shanu da daddawa, sai da ta zauna sannan ta ce “Ai sun tashi shekara ɗaya kenan da tashin su, sun koma can jahar Zander mahaifin Hajaru ya je can yin kasuwanci Allah ya buda mishi, shi ne ya dawo ya kwashe iyalinsa suka koma can, ita Hajarun shekaranjiya Maigari da su Liman suka je ɗaurin auren ta.” Zaro ido ta yi sai kuma ta yi dariya ta ce “Kai, don Allah? Kuma shi ne ba ku faɗa mini ba?” “To yanzu ba ga shi kin ji ba, yayunki ma an sa bikinsu saura sati uku, Maigari ya ce ya sanar da mijinki a faɗa miki tun kafin ki haihu ma.” Wani farin ciki ne ta ji ya ziyarce ta ta rungume Hajja tana faɗin “Gwaurayen yayuna bana sun shirya aure kenan? Kai naji daɗi Alhamdu Lillah ina nan har a yi biki.” Da dare ta kira Sultan suna tsaka da musayar kalamai ta shigar da ƙorafin ƙin sanar mata da ya yi a sa bikin su Giɗaɗo, haƙuri ya ba ta aka wuce wajen sai da za su sallama ta ce “Amour ina son zan je Zander.” “Yin me ?” Ya tambaye ta. “Kasan ƙawata Hajaru? To sun koma can da zama an yi an mata aure ina son na ganta, please kar ka ce mini ba zan je ba don Allah ka dubi girman abota.” Ta faɗa murya na rawa. “Babu komai zan sa a nema miki ticket daga Niamey sai ki isa can, amma please da an gama biki in kika, je can Zander kwana ɗaya za ki ki dawo Niamey wahsegarin ranar ki dawo Nijeriya, gabaɗaya kewar ki ta addabe ni gaskiya ina jin ba lalle na jure ba a ce nan gaba sai kin yi kusa wata ɗaya kafin ki dawo.” Haƙuri ta dinga ba shi tana mishi kalaman soyayya mai ratsa zuciya, sai da ta ji yana dariya har da ƙyaƙyatawa sannan suka yi sallama. Biki ya kankama su Andizo ana ta shige da fice, sosai Sultan ya sakar mata bakin aljihu ta dinga bacaka da kuɗi, kafin ta tafi sai da ta bi duk dangi ta musu kyauta matasa masu zuwa makaranta ta saya musu machine. Bayan ta je Zander Mama ta yi murna da ganin yadda ta koma babbar mace, Hajaru har da kuka ta rungume Rudwan sai yanzu ta ƙara tabbatar da cewa lalle abotarsu tana nan ita da Andizo sun riga da sun zama 'yan'uwa. Washegari ta koma Niamey. Da dare Abie ya duro garin tare da su Nour sun ƙara girma da wayo ga surutu, Andizo har da kuka daɗin ni'imomin da Allah ya mata wai yau ita ce da yara uku, a tare suka kwana tana sa su a gaba cikin so da ƙauna. Da safe sai ga Aminatou ta wasu mata biyu sun lulluɓe jikinsu da hijabi, bayan sun gaisa ne sai duk suka ji wani irin ɗoyi na tashi a palon sai suka fara done hanci, Aminatou ta ce “Munafukai sai ku mata bayani ai ko, ai duk wanda ya ce zai ka da ikon Allah sai ƙarshensa ba, zai yi kyau ba.” A tare suka ɗago suka durƙusa a gaban Andizo ta yi saurin toshe hanci, kuka suka sa ɗayar ta ce “Don Allah ki yafe mana Khadija a kan cutarwar da muka miki.” Da mamaki duk suke kallon su Andizo ta kalle su da kyau sai ku. A ta kalli Aminatou ta ce “Su waye wannan Adda?” Kwafa ta yi ta ce “Ai, dama ba za ki gane su ba, Sabrin ce da Halisa.” Kwalalo ido waje ta yi ta ce “Subhanallahi! Me ya same su?” “Su ne suka haɗe baki suka miki asiri kika zama abar tausayi, yanzu kuma ƙaiƙayi ya koma kan masheƙiya shi ne suka rasa in da za su saka kansu sai neman ki suke, ko ni sai da Ummi ta sa baki na ce in naji kin zo zan kawo su su nemi yafiyar ki, amma Wallahi da ni ce ba za yafe musu ba irin halin da suka jefa ko maƙiyi ya ganki a wannan yanayi dole ya zubar da hawaye. Ita wannan da ta yi ƙaryar ƴar gwamna ce ashe ƙarya take babanta ɗan kasuwa ne.” Ta karashe maganar tana nuna Halisa. Kuka suka sa suna ruƙon ta yafe musu abin da suka aikata mata, Ahmad ya zaburo zai yi magana Hajiya Babba ta hna shi, duk da sun cutar da ita amma sai ta ji sun ba ta tausayi ta share hawaye ta ce “Me na muku kuka cutar da ni?” Halisa ta ce “Ni saboda ina son Mr J Shi Kuma ya ce ke ce zaɓinsa, kuma daga ke ba ƙari ya rufe zuciyarsa da makulli, na shiga hanyar da zan samo kanshi amma na rasa, kwatsam muka haɗu da Sabrin dama mun yi Ècole da ita nan nake sanar da ita damuwata, ta ce da ni ai ita ta tsane ki domin ta yi ta bin hanyoyi kala-kala dan ta fitar da Aminatou daga gidan Salim ta aure shi ke kika ruguza mata komai, ƙarshe suka yi rabu da Aminatou shi ya sa ta ji ta tsane ki. Sai ga shi ta ji labarin an sa muku rana da Ahmad gefe ɗaya kuma ta ji labarin son da Mr J yake miki, shi muka je wajen wani boka kowacce aka mata aiki aka turo miki baƙaƙen aljannu suke wahalar da ke, shima Sultan Sabrin ta ce a sa mishi ciwon ƙoda duka biyu su lalace ƙarshe kuma a kashe shi.” Salati duk suka ɗauka Andizo ta girgiza kai ta ce “Ashe haka kike ƙi na Sabrin? Kawai dan na hana ki kashe aure? Ashe dama can zuwan da kike yi gidan nan Salim kike so? Alhamdu Lillah da Allah ya nuna muku iyakarku ko iya haka aka bar ku da shi ya isa ya hana ku sukoni, kun cuci kanku ku tashi mun yafe muku ni da mijina Allah ya sa mu dace.” Ahmad ya ce “Tab Wallahi Khadija kina da ƙarfin imani da kika yafe musu, maza ku bar mana gida tun da ta yafe muku.” Tashi suka yi suka fita Aminatou ta ce “Gaskiya Sabrin muguwa ce ashe lokacin da take zuga ni so ne take Salim ya sake ni ita kuma ta aure shi? Sai ga shi ma mai gajeran kwana ne ya bar mana duniyar, Allah ya jiƙan shi da rahama.” Amin suka ci aka ci gaba da hira. Bayan kamar awa ɗaya suka kaita filin girji ita da su Nour, sai da suka ga tashin su sannan suka dawo gida.. Tana isa Abuja kwana biyu ta yi suka koma London, ranar ta ga soyayya ya nuna mata irin kewar ta da ya yi itama ta nuna mishi tata kewar. Haka suka ci gaba da rayuwa Sultan harkoki sun ƙara buɗewa ya ƙara girma da cikar zati, Rudwan sai ƙara wayo yake. _BAYAN SHEKARA BIYAR_ A cikin wannan shekaru abubuwa da dama sun faru ciki har da rasuwar Inna da Maigari, Andizo ta yi kuka kamar ba gobe da kyar da addu'a ta dawo haiyacinta, a lokacin yaranta uku da Sultan namiji da mata biyu, an yi auren su Hassana aka kai su Diffa, itama Farrah an aurar da ita ɗan abokin Sultan ta aura. Suna zaune a palo Farrah ta kawo musu ziyara ga su Rudwan sun cika palon da hayaniya, sai da ta gaji ta daka musu tsawa sannan suka yi shuru. A hankali yake saukowa daga matakalar bene idanuwansa sanye da glass ɗan sirri, da sauri Farrah ta miƙe ta taro shi ta rungume shi ya shafa kanta ya ce “My daughter ke dai har yau ba za ki girma ba, ba kya gani yanzu kin zama babba?” Turo baki ta yi suka, ƙaraso ya zauna a kusa da Andizo tana musu dariya. Kiran sunanta ya yi ta juyo suka yi fecing ɗin juna, a sanyaye ya ce “Na sa an gudanar da bincike a kan baba ɗazu suka gama suka kira ni, am so sorry Shekaranjiya sojojin Niger sun gama ɗaya daga cikin shugaban 'yan bindiga, garin su tsairatar da mutanen da suka ɗauko wasu suka mutu, a ciki akwai baba wanda ciwon zuciya ya kashe shi, likitoci sun ce ya jima da ciwon damuwa da ta maye gurbin farin ciki ita ta yi sanadiyar mutuwar sa.” Wani irin ƙara ta yi sai ta zube a jikinsa, da gudu Farrah ta ɗauko ruwa ya yayyafa mata ta farfaɗo. Kuka sosai ta sha ta ce dole ya dakar da duk wani abu sai ta ga fuskar mahaifinta kar su binne shi yanzu, haka ya kira Giɗaɗo ya sanar da su suka ce dama ba an ce sai gobe za a ba su gawar. A ranar ya nema musu ticket suka yo Niger, saukar yamma suka yi a Niamey ko ruwa ba su sha ba suka wuce Tilaberi. Kusan kwana ta yi tana jera nafilfili tana roƙa wa iyayenta da su Maigari gafarar Ubangiji, washegari aka kawo gawar babanta ta sa ta gaba ta mishi addu'a, yau ce rana ta farko da ta ga fuskar mahaifinta wanda kullum take fatan ta gani, amma ganin ya zo mata ba yadda ta so ba. Sai da Umar ya je ya janye ta tana kuka wiwi, haka aka kai shi gidansa na gaskiya . Bayan sati suka koma London Andizo ta fauwala wa Allah lamarinta suka ci gaba da shinfiɗa rayuwa mai kyau da tsafta... _Alhamdu Lillah a nan na kawo karshen wannan littafin mai suna *ANDIZO* Kuskuren da ke ciki Allah ya yafe mini, darasin da ke cikin Allah ya ba ni ladan. Ku kasance da Maman Nusaiba nan gaba kaɗan in sha Allahu zan zo muku da zazzafan littafi mai sun *ZAWAJUL MUWADDA* Daga jin sunan labarin kun san akwai abubuwa kala-kala a, ciki. Ina sonku masoya one love 🫶🏻_ *Taku har kullum Maman Nusaiba ce🤙🏻*