[12/9, 4:30 PM] ~HUSSAIN YUSUF~: *ANAS MALEEK* Story&writing HUSSAINI YUSUF Whtspp number 07069475482. *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alƙalaminmu ƴancinmu* ________________________________ Page 1&2 Sa'eed bn Abdul'aziz azzalumin mutum ne, kuma ƙwararren ɗan ta'adda, yana ɗaukar matasa masu yawan gaske, daga mabanbantan ƙasashe. Yana koya musu ta'addanci, da sunan jihadi suke yi fisabilillah, haka kawai sai su shirya su hau kan babura su shiga ƙauyukan Fulani, su kashe na kashewa. Su bar wanda kwanansa bai ƙare ba, duk yawan shanun da Fulanin nan suka tara, sai sun kora su, sun tafi da su, komi yawansu kuwa. Yau ma kamar kullum, ƴanta'addan sai shiri suke yi za su kai wa wani garin fulani hari, bisa umarnin shugabansu Sa'eed bn Abdulazeez. Domin sun samu labarin garin suna da tarin, shanu da tumaki, har da awaki. Sa'eed ne ya kira wani mutum, cikin tantinsa domin babu wanda ya san inda maɓoyarsu take. Duk lokacin da suka aiwatar da zaluncinsu, cikin wani baƙin jeji suke shigewa da zarar sun shiga wannan jejin, babu wanda ya isa ya bi bayansu. Koda ya bi bayan nasu, ba isa ya gan su ba komi hatsabibancinsa kuwa. Yayin da mutumin ya shiga cikin tantin ya tarar da shugabansa, a kishiginɗe akan wani buzu yana jan casbaha. Sai ya tsugunna ya gaishe shi cikin ladabi, gyaran murya kawai yayi bai amsa sallamar da yayi masa ba, ballantana kuma gaisuwa. Murtuƙe fuska yayi yace "Ya kai Sahimu ya sunan ƙauyen da ka je ka gano a yankin najeriya?" duƙar da kai Sahimu yayi yace ya shugabana "Ba za mu kira wannan wajen ƙauye ba sai dai mu kira shi da gari." domin tarin albarkatun da suke da shi, ga su manoma ne sosai, sannan ga tarin shanun da Ubangiji ya albarkace su da su. Garin yana yankin jahar Taraba sunan shi Mambila. "Da yaushe kake ganin zamu farmake su, ba tare da sanin jami'an tsaron yankin ba?" Sa'id ya tambayi Sahimu "Ai ina ganin mu je musu a daren yau ɗin nan" don akwai wani shagali da ake yi a garin matar shugaban ƙauyen ce ta haifi ɗa namiji, shi yasa shugaban nasu ya shirya shagali na musamman, domin taya shi murnar samun ɗa namiji. Murmushin mugunta Sa'id yayi yace "Ka yi hanzari ka faɗa wa ƴan tawaga kowa ya zama cikin shiri don zamu iya tafiya a kowanne lokaci. Da sauri Sahim ya fice daga cikin ɗakin, ya sanar da saƙon shugaban nasu. *** Garin sai shagali ake yi ko'ina jama'a ne rututu sai faman ci ake ana sha. Wani dattijo na gani a zaune gindin wata bishiyar magwaro, wacce sanyinta yake ratsa ƙashi da ɓargo ya shiga cikin jiki ya haifar da kuzari gami da ƙarfin jiki. Wani yarone ya zo da gudunsa ya faɗa kan cinyar dattijon yana dariya, harara dattijon ya sakar masa yace "Anas har yanzu baka daina tsokanar ƙanwarka ba ki?" ka fi so kullum tayi ta raina ka ko?" A'a Baba ita ce fa ta fara tsokana ta, akan Inna ta aike ni in karyo itace a gona. Au! ashe ma Innarka ce ta aike ka karyo ice, shine zaka taho nan? Shiru Anas ɗin yayi yana kallon Baban nasa, daka masa tsawa yayi yace "maza ka tashi ka je ka karyo mata itacen. Da gudu Anas ya tashi ya nufi cikin jejin, yana barin wajen ƙanwarsa Safna ta iso wajen tana kuka. Faɗa masa abinda yayanta Anas yayi mata, haƙuri ya bata sannan ya kama hannunta suka nufi cikin gidan, dattijon yana shiga cikin gidan ya ga matarsa Inna Saratu tana ta faman aikin surfa dawa don ta ɗora musu sanwar rana. Zuwa yayi kama hannunta yace "Saro wallahi yau duk jikina nake ji babu daɗi, ina kyautata zaton akwai wani mummunan al'amari da yake shirin faruwa a garin nan ko kuma a kaina ko wani nawa. Cikin muryar fulatanci tace "Malam kai ka faɗa min duk lokacin da mutum ya ji fargaba tana ziyartarsa ya yawaita faɗin "Inna lillahi wa inna ilaiji raji'un". Idan ka manta yanzu na tuna maka, "ban manta ba Saro kawai dai na ji faɗuwar gaban nawa sai tsananta yake" to Malam Allah yasa mu ji alkhairi da amin ya amsa, sannan ya ɗauki buta ya nufi banɗaki. A kan wata bishiyar kanƴa yake, yana ta ɓallo itacen da ya bushe yana jefo shi ƙasa, ɗaga kansa yayi ya hango wasu mahaya babura yawansu sun kai su ɗari. Sun nufo ƙauyen nasu sai faman harbi suke yi da bindigu, suna wani irin ihu! na mugunta. Da gudu ya diro daga kan bishiyar, ya nufi cikin garin da gudu, Baffa yana alwala kawai ya ga Anas ya faɗo gidan da gudu. Yana zuwa ya tsugunna gaban Baffa, yana ta faman haki kai Anas lafiya kuwa? menene ya biyoka haka kake wannan gudun? Baffa ne ya jero masa waɗanan tambayoyin a jere, da kyar ya dubi Baffa yace "Baffa wasu mutane ne akan mashina, hannunsu riƙe da manyan bindigu suna ta harbi, Baffa wataƙila irin ɓarayin shanun nan ne da ka ba mu labari." Da sauri Baffa ya miƙe yace "Kuma nan garin suka nufo?" Wallahi Baffa nan suka nufo sai ihu suke tayi. Kafin Baffa ya samu damar furta harafi ɗaya, suka jiyo harbi a waje take ya kama hannun Anas da Safna, ya nuna musu wani tsohon rumbu ko murfi babu yace "su shige ciki kada su kuskura su fito sai sun daina jiyo harbi da ihun mutane sannan su fito su yi ta gudu su koma cikin Gembu. Da to Anas ya amsa yana kuka, ita ma Safna da ba ta cika wayo ba sai faman kuka take yi, ganin yayanta yana yi. Shafa kansu Baffa yayi yace Allah ya raya min ku ƴaƴana ya sanƴa albarka a cikin rayuwarku. Sannan ya juya kama hannun Inna Saratu yace "ita ma ta shige cikin rumbun su zauna ita da ƴaƴanta don baya so suyi maraicin uwa." Fashewa da kuka Inna ta yi, ta shiga cikin rumbun tana kiran Baffa shi ma ya zo ya shiga amma ko waigo su bai yi sai faman goge hawaye yake akan fuskarsa. Ɗakinsa ya shige ya ɗauko wata takobi sabuwa, da gudu ya nufi waje inda yake jiyo ihu gami da iface-ifacen mutane. #Comment #Share HUSSAINI YUSUF [12/9, 4:30 PM] ~HUSSAIN YUSUF~: *ANAS MALEEK* Story & writing HUSSAINI YUSUF Whtspp kimber 07069475482. *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* ______________________________ Page 3&4 Kisa kawai suke yi babu tausayi, ballantana imani a ciki. Ai sai da imani tausayi yake shiga, to su dai waɗanan babu ko ɗaya a tare da su (imani ko tausayin), yara sai kuka suke su da mata, duk wani namiji majiyin ƙarfi sai sun hallaka shi. Yayin da Baffa ya fito daga gidansa, hannunsa riƙe da wata zabgegiyar takobi, tsaye yayi yana zubar da hawaye takaici duk ya cika masa rai. Yanzu ace "saboda zalunci wasu su zo lallai sai sun raba ka da dukiyarka, bayan an raba ka da dukiyar taka ma baza'a ƙyale ka ba, sai an raba ka da rayuwarka?" Goge hawayen takaici yayi, dai-dai nan ya ga wani mugun ɗan ta'adda, ya ɗauki wani jariri ya cilla shi can sama, ya bushe da wata irin dariya mai kama da haushin kare, ya tsaya ya harɗe hannuwansa don yaga yadda jaririn zai faɗo. Cikin zafin nama, Baffa ya tafi da gudun gaske wanda bai taɓa yinsa ba, a iya tsawon rayuwarsa, kafin jaririn ya iso ƙasa Baffa ya je saitin da zai faɗo ya tare shi. Ji yayi alamun jaririn ko motsi babu a tare da shi, haka ta sa yayi zaton ya mutu sai ya ɗauke shi ya kai shi can gefen hanƴa ya ajiye shi, yana ajiye shi kafin ya juyo ya ji an buga masa wani ƙaton sanda. Bai san lokacin da ya faɗi ƙasa ba a matuƙar galaɓaice, yana fitar da numfashi sama-sama. Ɗanta'addan ne ya zo kan shi ya raba ƙafafun shi, yayi wani shu'umin murmushi wanda kai tsaye zamu iya kiran shi da kuka, domin ya fi kama da kukan. Damƙo gashin kan Baffa yayi yace "wato kai tsoho shine ina nishaɗina zaka zo ka katse ni ko?" waye kai ɗin ina iyalinka?" Shiru Baffa yayi yana ta kallon fuskar ɗanta'addan, ganin Baffan ba zai ba shi amsa ba ne ya zaro wata bindiga pistol, ya ɗamawa Baffa a ciki, nan take kuwa Baffa yayi shahada. Yayin waɗanan azzaluman ƴanta'addan, suka ga sun tarwatsa ƙauyen sun kashe na kashewa, sai suka tattaro duka shanun da suke garin, suka tare su a waje ɗaya. Sannan wasu daga cikinsu suka kora shanun suka yi gaba da su, su kuma sauran suka suka rinƙa cillawa ƙauyen wuta. Har yanzu Inna da ƴaƴanta biyu ANAS DA SAFNA, suna maɓoyar da Baffa ya ajiye su, sai faman haɗa gumi suke yi. Ji suka yi rumbun da suke ciki ya ɗauki zafi sosai, da sauri Inna Saratu ta fito ta leƙo gani ta yi ko'ina na gidan ya kama da wuta, sauri ta yi ta fito daga cikin rumbun sannan ɗaya bayan ɗaya ta zaro ƴaƴanta. Bayan sun gama fitowa, sai ta ɗauki Safna ta goya ta a bayanta sannan ta kama hannun Anas ta ja shi suka fita daga gidan da gudun gaske, banda gawarwakin mutane da suke haɗuwa da su a hanya babu abinda suke gani, sai gidajensu da aka cillawa wuta. Suna jiyo hayaniyar mata da ƙananan yara, a can tsakiyar garin, kuma har yanzu ƴanta'addan ba su tafi ba. Don daga inda suke suna jiyo, ihunsu da kururuwarsu, suna yiwa matan ƙauyen kashedi. Gudu-gudu sauri-sauri su Inna suke tafiya, a cikin garin, hango wani ɗanta'adda Inna ta yi ya nufo inda suke, gani ta yi alamun bai gan su ba, sai ta yi sauri ta ja hannun Anas suka shige cikin wata duhuwa, suka ɓuya. Cikin takun ƙasaita, ɗanta'addan ya zo dai-dai inda su Inna suka ɓuya ya tsaya. Nan take ya hau yiwa kan shi kirari, "Sai ni uban maza mai mayar da ƙananan yara marayu, sai ni mai mayar da mata zawarawa, sannan ya ƙwalla kabbara da ƙarfin gaske, har sau uku "Allahu akbar! Allahu akbar!! Allahu akbar!!!" dai-dai lokacin wani ɗanta'addan ya ƙaraso wajen, ya kawo masa wata bindiga ƙirar AK47, duban wanda ya kawo masa bindigar yayi yace "ya kai Sahimu aikinka yana yin kyau sosai don haka a cikin ganimar nan da aka samu kana da kaso mai tsoka." take Sahim ya tsugunna ya hau yin godiya, duk abinda yake faruwa akan idon Inna da Anas yake faruwa, ita kuwa Safna tana bayan Inna a goye kamar wata jaririya. Nan take tunanin Baffa ya faɗowa Inna, hawaye ta shiga zubarwa tana wani kuka marar sauti taso ta ɗaga muryarta tayi kuka ko zata ji sauƙin raɗaɗin da zuciyarta take yi mata. Sai dai ina? babu halin aiwatar da haka domin kada ƴanta'addan nan su jiyota, yanzu babban burinta bai wuce ƴaƴanta su rayu ba, saboda ta saka a cikin ranta duk rintsi sai ta tseratar da rayuwar ƴaƴanta abun alfaharinta. ƙarar bindiga ne ya doki dodon kunnensu, yadda wannan mutumin ya riƙe bindigar nan sai faman harbin sama yake yi da ita, ƙarar bindigar ce ta firgita su Inna Safna da take goye a bayan Inna ce ta ƙwala wani ihu! mai ƙarfin gaske, take kuwa ƴanta'addan nan mutum biyu suka jiyo ihun! yarinƴar take suka fara laluben inda suka jiyo Ihun! hango Inna suka yi tana ta faman tiƙar gudu hannunta riƙe da wani ƙaramin yaro bayanta kuma goye da wata ƙaramar yarinƴa, take kuwa suka ce "da wa Allah ya haɗa mu ba da ke ba?" Take su ma suka rufa mata baya cikin matsanancin gudu. Gudu sosai Inna da Anas suke yi, da ƙyar Inna take iya ɗaga ƙafarta domin ta yi mata nauyi sosai, ga goyon Safna a bayanta amma hakan bai hanata gudun ba domin ta tseratar da rayuwar ƴaƴanta koda ita zata rasa rayuwar tata. Gani tayi sun tserewa ƴanta'addan sosai haka yasa suka sake shiga wani lungun suka cigaba da gudun don kada ƴanta'addan su riske su. Da gawar Baffa Inna tayi karo a kwance a kan hanƴa, wata razananniyar ƙara ta saki, sannan ta sulale ƙasa sumammiya...✍️ COMMENT AND SHARE FANS🙏🙏🙏 HUSSAINI YUSUF [12/9, 4:32 PM] ~HUSSAIN YUSUF~: *🫐🫐ANAS MALEEK🫐🫐* Labari/Rubutawa HUSSAINI YUSUF Whatsapp number: *07069475482.* *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *________________________________* Page 5&6 Yayin da Anas ya ga Inna a kwance, a gaban gawar Baffa, sai ɗimauce zuciyarsa ta shiga bugawa da ƙarfin gaske. ƙoƙarin kwance Safna yake a bayan Inna, amma kwata-kwata ya kasa, domin ɗaurin da Inna ta yi mata ba na wasa ba ne, da ƙyar da siɗin goshi ya samu ya kwance ta, ganin har yanzu Inna ba ta tashi ba yasa shi fashewa da wani kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro sannan ya sa ka zuciya rauni. Tuno lokacin da Safna ta suma yayi, yadda ya ga ana watsa mata ruwan randa me sanyin gaske ta farfaɗo, yana gama wannan tunanin, bai tsaya wata shawara da zuciyar shi ba ya nufi wani ruwan sama da ya taru a gefen hanƴa.Da hannunsa ya ɗebo ruwan, kafin ya ƙaraso wajen Inna tasa ma rabin ruwan duk ya tsiyaye yana zuwa ya watsa mata a fuska, gani yayi bata motsa ba, ya sake komawa domin ɗebo wani ruwan, Safna ma biyo shi ta yi, don ta taya shi ɗebo ruwan su watsa wa Innarsu ta farka su tafi. Duk wannan abinda Anas yake yi sai faman kuka yake Mai sautin gaske, babban abinda ya fi ɗaga masa hankali shine ganin gawar Baffansu a kwance akan hanƴa a wulaƙance. Suna sake ɗebo ruwan, suka watsa wa Inna take ta farfaɗo daga suman da ta yi, tana ajiye ajiyar zuciya. Tashi zaune ta yi, ta rungume gawar Baffa ta fashe da kuka, su Anas ma sai suka fashe da kuka babu mai rarrashin wani a cikinsu. Sun shafe lokaci mai tsawo a haka, sannan Inna ta yi ƙarfin halin daina kukan ta dubi Anas. "Anas maza ka tashi, ka ja hannun ƙanwarka ku gudu daga wannan garin." ƙin tashi Anas yayi, shiru yayi yana kallon Inna "ba zaka tashi mu tafi ba ko so kake duk mu hallaka gaba ɗayanmu?" Inna ta daka masa wata razananniyar tsawa. Shi dai Anas a iya shekarun da yayi da mahaifiyarsa, ba ta taɓa ɗaukan wani madoki ta dake shi ba, ballantana ta yi masa wata tsawa. Amma yau ga shi da kanta take korarsa, akan ya tafi ya barta bai san halin da zata shiga ba idan ya tafi, sai dai ba shi da zaɓi, muddin yana son ya rayu to dole ne ya ja hannun ƙanwarsa su bar wajen. Harbi suka jiyo can nesa, daga inda suke, firgita Inna ta yi tace "Anas ka ja hannun Safna ku tafi, ni ta wa ta ƙare, ina yi maka nasiha ka rungumi ƙanwarka, ko kaɗan kada ka bari ta zubar da hawayen maraici. Jin harbin yana ƙara kusanto su, "Anas maza ka ja hannun Safna ku tafi insha Allahu babu abinda zai same ku" ina yi muku fatan alkhairi, juyawa Anas ya kama hannun Safna yana ta faman rusa kuka, ita ma Safnar ban da kuka babu abinda take yi. Tafiya suke yi, suna waigen mahaifiyar ta su, suna ta faman kuka, da ƙarfi Inna ta kira sunan Anas waigo wa suka yi a tare shi da Safna, "komai tsawon lokaci karka bar ɗayansu a raye, ka kashe su duka. domin ka ɗauki fansar ran iyayenka da jama'ar garinku." Da ƙarfi Anas yace "insha Allahu Inna duk sai na kashe su, ba zan bar ɗayansu a raye ba." Sannan ya ja hannun Safna, suka tafi da gudun gaske, suna cikin gudun suka ga jariri a gefen hanƴa yana ta faman tsala uban kuka, ga rana me zafin gaske sai gasa shi take yi. Har sun wuce shi da gudu, Safna tace "Yaya Anas mu koma mu ɗauki wancan jaririn da ganin shi, an kashe iyayen shi, mu taimaka masa wataƙila ta sanadiyyar sa mu ma Allah ya taimaka mana." Mamakin kaifin basira da hangen nesa irin na Safna, Anas yake yi, don shi ko kaɗan bai ji zuciyar shi ta raya masa ɗaukar jaririn ba, amma sai ga shi ƙanwarsa wacce ya shige ta a shekaru sosai ta yi wannan tunanin mai matuƙar amfani. Amma duk da haka sai ya dubeta cikin nutsuwa yace "yanzu Safna idan muka ɗauki jariri, me muke da shi wanda zamu ba shi?" mu ma kanmu ba mu sani ba ko zamu rayu, don haka kawai ki zo mu tafi, ki rabu da shi Allah zai kawo wanda zai taimaka masa. Yana faɗar haka ya kaɗa kai ya wuce gaba, yana mai yafito Safna da hannu alamun ta biyo shi, tafiya yake amma bai ji alamun ana bin shi a baya ba, waigowa yayi can nesa ya hango Safna ta ruga da gudu ta nufi inda suka ga wannan jaririn da babu uwarsa. Ai bai tsaya wata-wata ba, ya bi bayanta da gudu. Kafin ya riske ta har ta ƙarasa inda jaririn yake, ta ɗauko shi ta juyo. Anas yana zuwa inda take ya karɓi jaririn sannan yace "ta biyo shi da gudu su bar yankin garin nasu gaba ɗaya domin su tsira da rayuwarsu. Inna kuwa har yanzu tana kwance akan gawar Baffa tana ta faman rusa kuka mai tsuma zuciya, takun mutane ta ji alamun suna kusanto inda take, shiru ta yi ta daina kukan da take yi. ta rufe idanunta tare da ɗauke numfashinta, alamun ta mutu, suna zuwa suka ga gawar Baffa Inna tana kwance akansa, duk jikinsu ya ɓaci da jini. Bushewa da dariya suka yi, sannan ɗayan yace "oga dubi wasu ma'aurata saboda tsabar soyayya a lahirar ma ba za'a rabu ba. Shi ma ogan dariya ya saka sannan yace "rabu da jahilai ai a haka zamu ƙarar da su babu ruwan mu da wata soyayyar miji da mata domin mu bamu san ta ba." kisa kawai muka sani, sannan suka sake bushewa da dariya, suka taka ƙafar Baffa suka wuce, taɓa jikin Baffa Inna ta yi ta ji wata sharɓeɓiyar wuƙa mai kaifin gaske. Bata tsaya wata shawara da zuciyarta ba, ta zaro wuƙar ta riƙeta a hannunta na dama sannan ta ɗauki takobin Baffa a hannunta na hagu, ta bi bayan ƴanta'addan cikin wani irin gudu tamkar tauraruwa mai wutsiya. HUSSAIN YUSUF✍️ Comment Share fisabilillahi [12/9, 4:32 PM] ~HUSSAIN YUSUF~: *🫐🫐 ANAS MALEEK🫐🫐* Labari/Rubutawa HUSSAINI YUSUF Whatsapp number 07069475482. *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *___________________________* Page 7&8 Duk gudun da Inna take yi, domin ta tarar da su, Allah bai ba su ikon jiyo ko da takunta ba. Cikin ƙanƙanin lokaci Inna ta tarar da su, yayin da ta zo daf da su, sai ta ɗaga wannan sharɓeɓiyar wuƙar ta caka wa ɗayan mutumin a ciki, ta zaro ta ta sake caka masa. Nan take kuwa jini ya rinƙa fallatsi daga jikinshi, hancinsa da kunnuwansa suka rinƙa zubar da jini take ya sulale ƙasa matacce, idanunsa ƙur! akan Inna har ransa ya ƙarasa fita, daga gangar jikinsa. Mamaki ne ya hana ɗayan motsi, saboda bai taɓa ganin mace irin Inna ba. anƴa kuwa wannan mutum ce? ya tambayi zuciyarsa, take kuwa yace "kai wannan ba mutum ba ce" shi dai a iya saninsa da mata ko da sanda ba sa iya riƙewa ballantana kuma har ta kai su da kisa. Yana cikin tunaninsa ya ga Inna ta yo, kansa gadan-gadan da wuƙa a hannunta, sai ya ɗimauce ya zaro wata ƴar ƙaramar bindiga pistol daga aljihunsa ya saita Inna ya harba ƙin bindigar ta yi, babi harsashi ko ɗaya a ciki ballantana har ya harbi wani. Tuno wa yayi ashe babu harsashi a ciki, ɗazu ya ƙarar da shi wajen harbe wani mutum, bai ankara ba ya ji har Inna ta samu nasarar yankar shi a gefen wuyansa, kafin ya ƙara wani ƙwaƙƙwaran motsi ta caka masa wuƙar a kan cinyarsa, ta hagu. Wani uban ihu ya tsadara, dai-dai lokacin wasu ƴanta'addan sun ƙaraso wajen, ganin ogan na su suka yi a cikin jini male-male. Can nesa kuma suka hango Inna tana ta faman gudu domin tseratar da rayuwarta, daga hannun mugayen ƴanta'addan nan. Mamaki ne ya cika musu zuciya "wai mace ce ta yiwa ogansu wannan mummunan raunin, kuma ta kashe Saiham gaskiya wannan matar ta cika jarumar gaske, domin a iya zamansu da Sa'eed bn Abdul'aziz babu wanda ya taɓa ko da lakutar fatar jikinsa da sunan cutar da shi amma sai ga shi yau mace ce ta kai shi ƙasa. Suna cikin tunaninsu suka tsinkayo muryarsa yana cewa " ku bita sannan ku tabbatar kun kamo min ita a raye domin nasan irin hukuncin da zan yanke mata, take kuwa suka bi bayan Inna wasu akan mashina wasu kuma a ƙasa, suna ihu da ƙaraji irin na mugayen ƴanta'adda. Wasu ne suka yi sauri suka ɗauke Sa'eed suka ɗora shi mashin, suka tafi da shi don su yi masa magani. Anas da Safna sai tafiya suke yi a tsakiyar dokar daji, hannun Anas ɗauke da wannan jaririn da suka tsinta, Safna ce ta faɗi ƙasa tana kiran ruwa! ruwa!! ruwa!!! shi ma jaririn sai tsala wani uban kuka yake, da alama shi ma ruwan yake so. Tsugunna wa Anas yayi a gaban Safna yana ta faman rarrashin jaririn domin yayi shiru amma ya ƙi daina kukan, kallon Safna yayi yace "Safna ki taso mu ƙara yin gaba wataƙila za mu iya riskar wani ƙauyen a nan gaba, ko kuma mu tarar da wani kogin, sai mu sha ruwan anan." Inna sai faman gudu take yi, ta cikin ƙayoyi, ƙafafunta ko takalmi babu, ƙayoyin sai faman soke mata ƙafafu suke yi. Amma ko kaɗan bata damu da hakan ba, domin burinta kawai ta tseratar da rayuwarta, duk lokacin da ta saiga bayanta sai ta ga ba su daina binta ba, wasu akan mashina wasu kuma a ƙasa duk inda ta kutsa kai sai sun kutsa. Wata duhuwa ta shige, a cikinsu babu wanda ya ga shigarta cikin duhuwar, tana shiga duhuwar bisa mamakinta sai ta ga wata siririyar hanƴa kuma da alama mutane suna bin hanƴar, domin duk ga sawun ƙofatan dabbobi nan, ga kuma sawun takalma nan birjik ko'ina. Waigawa ta yi bayanta ta ga, mutanen ba sa biye da ita, wani farinciki ne ya ziyarceta take ta fara ɗingisa ƙafar tafiya don sai yanzu take jin zafin ƙayoyin da sossoketa. Sai da ta shafe awa ɗaya da rabi tana tafiya akan hanƴar sannan ta hango wani ƙaramin ƙauye a jikin wani ƙaton tsauni. Murmushin farinciki ta yi, sannan ta cigaba da tafiya, tana isa ƙauyen kowa hankalinsa ya dawo kanta, tana zuwa bakin wata rijiya ta ga mata da yara sai ɗiban ruwa suke yi, a rijiyar. Bata yiwa kowa magana ba, ta tsaya tana ƙarewa mutanen ƙauyen kallo, zubewa ƙasa ta yi bisa gwiwoyinta. A hankali take kiran ruwa! ruwa!! ruwa!!! wani tsoho ne ya kalli ƴan'matan da suke ɗiban ruwan ya daka musu tsawa yace "ba za ku taimaka mata da ruwan ba ne?" Nan take suka miƙo mata ruwan a cikin wani ƙoƙo mai ɗan girma. Tunda ta kafa kai a ƙoƙon ruwan, bata ɗaga ba sai da ta ga ya ƙare, sannan ta miƙa musu ƙoƙon tana ta faman sauke ajiyar zuciya. Wata tsohuwa ce ta zo ta kama hannunta tace "taso mu je gidan me gari kiyi masa bayanin inda kika fito babu musu kuwa Inna ta tashi ta bi tsohuwar a baya. Lokacin da su Inna suka isa gidan me gari, tarar wa suka ana ta faman fadanci, tsugunnawa tsohuwar ta yi ta kwashi gaisuwa, Inna ma ta yi koyi da ita, suka gaishe da megarin a tare. Tsohuwar ce ta yiwa me gari bayanin inda ta ga wannan baƙuwar matar wato Inna, me gari ne ya buƙaci Inna ta faɗa masa inda ta fito. Tana zubar da hawaye ta faɗa masa komai, hatta su Anas ƴaƴanta da ta tura su, su tafi domin su tseratar da rayuwarsu bata ɓoye musu ba. Gaba ɗaya jama'ar fadar sun tausayawa Inna, me garine da kansa ya umarci tsohuwar da ta tafi da Inna gidanta tunda ya lura kamar akwai shaƙuwa a tsakaninsu. Tsohuwa da murnarta ta kama hannun Inna suka nufi gidanta, dama ita kaɗai ce a gidan, yanzu ta samu abokiyar zama. ****** Al'amarin su Anas da Safna kuwa yayin da suka ci gaba da tafiya a wannan ƙungurmin dajin, suna ta neman ruwa amma ko alamun sa babu. Faɗuwa ƙasa Safna ta yi ta saki wani uban kuka mai karyar da zuciyar mai sauraro, wani gurnani suka rinƙa jiyowa yana kusanto inda suke, firgita suka yi gaba ɗayansu suna zazzare idanu. Gaba ɗaya sun ƙurawa inda suke jiyo gurnanin ido, a hankali suka rinƙa jiyo gurnanin yana kusanto su, babu wanda ya furta koda kalma ɗaya ballanta su samu damar guduwa daga wajen. Wani ƙaton murjejen zaki ne ya fito daga wata duhuwa, da kallonsa yunwa ce ta fito da shi daga maɓoyarsa. Kalle-kalle yake yi, yana bin ko'ina na dajin da kallo, karaf idanunsa suka sauka akan Anas da Safna, take kuwa yace "da wa Allah ya haɗa ni ba da ku ba?" Cikin wani irin gudu ya yo kansu domin ya hallaka su gaba ɗayansu, tsugunnawa ƙasa suka yi, suka rufe idanunsu suna jiran zakin ya afko musu, can gefe ɗaya kuma sun ajiye jaririn yana ta faman tsala kuka, kamar ana mintsinin shi a jiki. Kwatsam! ba zato ba tsammani suka ji ƙarar faɗuwar zakin, can waje ɗaya, da mamaki a idanunsu suka ɗago kawunansu suka ga zakin ya ƙurawa wani lungu idanu. Gani suka yi zakin ya ja da baya, sannan ya nufi cikin lungun da mugun nufi, gani suka yi an sake wurgo shi waje, mamaki ne ya cika musu rai. Waye wannan yake bugo zakin nan haka? ki kuma da aljanu yake faɗa? gani suka an cillo wani mashi mai tsinin gaske daga cikin lungun. Mashin bai tsaya a ko'ina ba, sai a jikin wannan murjejen zakin, nan take kuwa ya sulale ƙasa matacce jini yana fallatsa daga jikinshi. Ƙarar tafiya suka jiyo, daga cikin lungun duhuwar, ƙurawa wajen idanu suka yi domin su ga wanda zai fito daga wajen. Hussain Yusuf✍️ [12/9, 4:32 PM] ~HUSSAIN YUSUF~: *🫐🫐 ANAS MALEEK🫐🫐* Labari/Tsarawa HUSSAINI YUSUF My Whatsapp number 07069475482 *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *____________________* Page 9&10 Gani suka yi wani ƙaton mutum, ya fito daga cikin lungun, bayansa goye da kwari da baka. Tafiya yake amma ƙasar wajen, sai amsa amon takunsa take, yadda kasan wani basarake haka yake tafiya. Bai tsaya a ko'ina ba sai, akan mushen zakin nan, hannu yasa ya finciko mashinsa daga cikin zakin, sannan ya juyo ya nufo inda su Anas suke a tsaye. Yana zuwa wajensu, kai tsaye ya nufi inda jaririn nan yake kuka, sunkuyawa yayi ya ɗauke shi, yana rarrashinsa. Sannan ya kalli Anas yace "menene ya kawo ku wannan baƙin dajin?" Shiru suka yi suna kallonsa, babu wanda ya iya buɗe baki a cikinsu ya bashi amsa, har lokacin jaririn yana hannunsa yana ta aikin rarrashinsa amma ya ƙi yin shiru. Tafiya ya fara yi yace "ku biyo ni a baya" cikin hanzari kuwa suka rufa masa baya, tuni Safna ta manta da ƙishirwa da yunwar da take ji yayin da ta ga zakin nan, sai yanzu ne ta ji ta dawo jin matsananciyar ƙishirwa. Tafiya yake a hankali su ma sai faman bin sa suke yi, a baya su faɗa wannan surƙuƙi su fita su faɗa wancan. Da haka har suka ƙaraso, wajen wata bukka mai kyawun gaske. Yayin da suka iso ƙofar bukkar sai ya dakatar da su, ya shiga ciki shi kaɗai, ba jimawa sai ga shi ya fito da tabarmar kaba (karauni) ya shimfiɗa musu yace su zauna. Bayan sun zazzauna sai ya sake shiga cikin bukkar, sai ga shi ya fito da tulun ruwa me sanyin gaske a hannunsa, tsiyaya wa yayi ya bai wa jaririn Allah sarki bawan Allah sai da ya sha ruwan me yawan gaske, nan take barci yayi awon gaba da shi. Sake tsiyayawa yayi ya miƙa wa Safna, da sauri ta karɓa ta rinƙa sha, har sai da cikinta ya kusa ƙullewa sannan ta miƙa masa ƙoƙon, ya sake tsiyayo ruwan ya miƙa wa Anas shi ma ya sha da yawa yayi gyatsa ya godewa Ubangiji. Gani yayi duk hankalinsu ya dawo jikinsu, duban Anas yayi yace "menene ya kawo ku wannan dajin, kuna yara da ki?" Hawaye Anas ya fara zubarwa ita ma Safna ta shiga share hawayen. Labarin irin ta'addancin da aka je ƙauyensu aka yi musu suka ba shi, har saka su a rumbu da Baffa yayi domin su tsira da rayuwarsu sai da suka ba shi.Da irin wahalar da suka sha a hanƴa kafin su iso nan duk sai da suka faɗa masa, ba su ɓoye masa kome ba har zuwa lokacin da wannan zakin ya ritsa su sai da suka faɗa masa. "To a ina kuka samu wannan jaririn?" Safna ce ta faɗa masa yadda aka yi suka tsince shi yana ta kuka kuma babu uwarsa a kusa da alamu ita ma an kashe ta. Hawaye maharbin ya shiga zubar wa, haƙiƙa ya tausayawa su Anas ba kaɗan ba, nan shi ma ya shiga ba su na shi labarin kamar haka. Sunana Aisar ni haifaffen garin Katsina ne, na dawo nan yankin Taraba ne sakamakon ƴanta'addan da suka addabi yankinmu. Lokacin ina yaro mu na zaune, ni da iyayena mu ka ji ƙarar harbin bindigu, nan take mahaifina ya ɗauke ni, a kafaɗarsa ya ja hannun mahaifiyata mu ka fice daga ƙauyen namu ta ɓoyayyiyar hanƴa, ba tare da ɗaya daga cikin ƴanta'addan ya gan mu ba. Sai da muka share awa uku muna tafiya, sannan muka iso wata mararrabar hanƴa. Sauke ni mahaifina yayi daga kafaɗarsa, yace mahaifiyata ta ɗauke ni. Sunkuyawa ta yi ta ɗauke ni, cikin nutsuwa mahaifina ya dubi mahaifiyata ya nuna mata wata hanƴa da ta yi yamma. Yace "ta bi hanƴar akwai garuruwa da ƙauyuka sosai akan hanƴar" duk garin da ta je kada ta tsaya, da ta samu ruwa da abinci ta sha to ta ƙara gaba, domin a kowanne lokaci ƴanta'addan za su iya riskar ɗaya daga cikin garuruwan. Sannan yace wa mahaifiyata ta bani tarbiyya dai-dai gwargwado. Sannan ya sake cewa ta saka ni a makarantar boko da islamiyya, kada ta barni na zama mutumin banza. Ya ciro wani zobe daga hannunsa, ya miƙawa mahaifiyata yace "idan na girma ta ba ni shi a matsayin gadon da mahaifina ya bar mini." Juyawa yayi zai tafi, mahaifiyata ta yi wuf, ta riƙe rigarsa ta saki wani kuka mai tsuma zuciya tace "Abban Aisar don Allah kar ka tafi ka bar ni!" Hawaye Abbana ya goge, sannan ya dubi mahaifiyata yace "Binta dole ne na koma wajen mutanen can, domin na ɗauki fansar ran iyayena" kuma na kare rayukan mutanen garinmu. Bai tsaya sauraron abinda Ummata za ta faɗa ba, ya juya ya fara tafiya domin ya koma garin ya tari ƴanta'addan. Kama hannuna Ummata ta yi, muka fara tafiya, sai faman kuka Ummata take yi tana waigen Abbana. Har suka daina hango juna, Ummata ba ta daina hangen Abbana ba. Da kyar Ummata take iya ɗaga ƙafarta, tana tafiya ita kaɗai cikin yashi. Sai da muka shafe sama da awa uku muna tafiya, sannan Ummata ta tsaya a gindin wata bishiya, ta sauke ni ta ba ni nono nan take kuwa na riƙe na fara sha. Barci mai nauyi ne ya ɗauke ni, Ummata ta shimfiɗa mayafinta a ƙasa ta kwantar da ni a kai. Ita ma ta kishingiɗa, take kuwa barci ɓarawo yayi gaba da ita, mun daɗe a gindin bishiyar muna barci, sai wajen doshin faɗuwar rana Ummata ta farka daga barcin, bakinta ɗauke da salati duban ta takai inda nake kwance, gani na tayi har lokacin ban farka ba, ajiyar zuciya ta sauke ganin babu abinda ya same ni. Ɗauka ta tayi ta goya ni a bayanta, sannan ta cigaba da tafiya, cikinta ban da ciwo babu abinda yake yi, ƙirjinta yana yi mata zafi, sakamakon tana ciwon ulcer kuma ga shi bata samu abinci ta ci ba tun safe. Yayin da Ummata ta ga duhu yana ƙoƙarin mamaye sauran hasken ranar da ya rage, sai ta samu waje a gefen hanƴa ta zauna ba tare da ta kwance ni daga bayanta ba. Jim kaɗan da zamanta, sai ta fara jiyo wani irin gurnani, marar daɗin sauraro, da sauri ta tashi ta shige cikin wani kogon dutse da yake gefen hanƴar. Hussaini Yusuf✍️ Comment and share [12/9, 4:33 PM] ~HUSSAIN YUSUF~: *🫐🫐 ANAS MALEEK🫐🫐* *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* Labari/Rubutawa HUSSAINI YUSUF *______________________________* *Page 11&12* Lokacin da Ummata ta shiga cikin kogon, sai ta ga cikinsa duhune sosai, haka yasa ta tsaya daga wajen ƙofa. Ta rakuye jikin wani ɗan ƙaramin dutse, jikinta ban da rawa babu abinda yake yi, sannu a hankali ta fara hango hasken wuta a can cikin kogon. Tafiya ta fara yi a hankakli, cikin sanɗa tana nufar cikin kogon, domin ta ga wanda ya hura wannan wutar, addu'a take yi a cikin ranta Allah yasa kada na farka daga dogon barcin da na koma. Daga inda take ta hango wani mutum, sanye da kaya irin na mafarauta, yana gasa nama da alama ci zai yi, domin sai faman jujjuya naman yake yi akan wutar yana barbaɗa wani abu a kai, ko ba'a faɗa maka ba ka san gishiri ne. Hamdala Ummata tayi sannan ta nufi wajen mafaraucin, tun daga nesa ya hangota, mamaki ne ya cika mi shi rai har yake tantama a cikin ran shi anƴa kuwa wannan mutum ce? Amma bai razana ba kasancewarsa gwarzon jarumi, kuma ba haka kawai yake shiga irin wannan dajin ba. Bai ɗauke idanunsa daga kanta ba, har ta ƙaraso inda yake, ta yi tsaye akansa tana muzurai, kallonta yayi yace baiwar Allah mutum ko Aljan? Cikin sanƴin murya irin ta wanda ya sha wuya sosai Ummata tace "Ni mutum ce kamarka." Miƙewa tsaye yayi yace "idan ke mutum ce ya aka yi kika zo nan?" Zaunawa Ummata tayi a ƙasa tace ka taimake ni da ruwa, idan na samu nutsuwa sai na ba ka labarina, miƙa mata wani ƙaramin ƙoƙo yayi cike da ruwa, karɓa Ummata ta yi ta kafa kai sai da ta ji ya ƙulle mata ciki sannan ta ajiye, tare da yin wata ƙatuwar gyatsa. Bayan ta samu nutsuwa, sai ta kwance ni daga bayanta ta ajiye ni akan cinƴarta, har lokacin sharar barcina nake yi, ba abinda ya dame ni. Kallon mafaraucin nan ta yi, tace ka shirya yanzu zan baka labarina, da na dalilin zuwana wannan dajin mai matuƙar ban tsoro. Cikin ƙanƙanin lokaci ta ba shi labarin abinda ya barota da garinsu da gidansu har da mijinta da ya koma domin yaƙar ƴanta'addan bata ɓoye masa ba. Har hawaye sai da mafaraucin ya zubar, saboda tausayin Ummata da ya cika mishi zuciya yace "kash! dama mijinki bai yi gangancin komawa garin ba, tunda har ya riga ya gudo ba tare da sun gan shi ba." Amma yayi namijin ƙoƙari, tunda har ya tseratar da rayuwar iyalinsa, ko ba komai ai ya bar baya. Wuƙa ya ɗauko ya miƙawa Ummata yace "ta yanki naman zomon da yake gasawa ta ci iya cinta ta ƙoshi." Yankar naman zomon Ummata ta rinƙa yi, tana ci har sai da ta ji ta ƙoshi. Sannan ta miƙa masa wuƙar shi ma ya fara yanka yana ci, har ya ƙoshi sannan ya sake miƙowa Ummata ruwa ta karɓa ta sha, sannan shi ma ya sha. Miƙewa tsaye yayi yace Ummata ta biyo shi a baya, take kuwa ta bi shi, wata siririyar hanƴa ya bi da ita, nan take kuwa hanƴar ta kai su har wata bukka wacce aka yi ta da itatuwa. Tsayawa yayi a ƙofar bukkan yace "Ummata ta shiga ciki ta kwanta washegari, shi zai kwanta a waje." Ummata ta kalle shi tace "Me zai hana nima na dawo wajen mu kwana tare?" Wani kallo ya watsawa Ummata har sai da ta firgita, yace "ke ba musulma ba ce?" Kinsan dai Addinin musulunci ya hana mutum ya keɓe da matar da ba muharramarsa ba ko? To gaskiya ni ina kiyaye addinina don haka ki shiga ciki ki kwanta ni zan kwanta anan. Idan kuma ba zaki iya kwanciya a ciki ba, ki fito ki kama hanƴa ki tafi ya faɗa a fusace, ba yadda Ummata ta iya ta shiga cikin bukkar ta kwanta, tunowa ta yi da Sallolin da bata yi ba, don a yau iya Sallar Asuba ta yi. Bata samu damar aiwatar da sauran sallolin da suka wajaba akanta ba, firgigit ta tashi ta fito waje tambayar inda zata samu ruwa tayi zata yi Sallah, nuna mata wani tulu yayi da yake cike da ruwa, ta ɗauko wani ɗan ƙaramin ƙoƙo ta tsiyaya, bayan ta kamo ruwa ta zo ta ɗaura alwala ta koma cikin ɗakin ta tayar da Sallah. Sai da ta rama duk sallolin da ake bin ta a ranar, sannan ta ɗora da Sallar nafila, a takaice dai sai misalin ƙarfe ɗaya da rabi na dare Ummata ta gama Sallar. Lokacin ni kuma na farka daga dogon barcin da nake yi, zuwa tulun nan me ruwa ta yi ta tsiyayo ruwan ta zo ta bani, ba kaɗan ba na sha ruwan sannan ta bani nono na sha na koma barci. Ita ma nan ta ɗare gadon karan da yake cikin ɗakin, tunani ne kala-kala ya cika mata rai, tunanin mijinta da iyayenta da sauran jama'ar garinsu ne, ya cika mata rai, hawaye ne ya rinƙa sintiri a kan fuskarta a haka har barci ɓarawo ya zo yayi gaba da ita. Duk abin nan da Ummata take yi, yana kallonta ganin yadda ta zage tana ta Sallah ne ya burge shi sosai, bayan ta barci ya ɗauke ta shi ma ya tashi ya ɗaura alwalar ya tayar da Sallah. Bai idar da sallar ba har doshin asuba, sannan yayi sallama ya ɗan kwanta ya runtsa kafin alfijir yayi. Washe gari da safe ya ɗauko gurasa da gasashshen nama, ya bai wa Ummata yace ta ci. Bayan ta gama ci, sai ya kalleta yace "yau zai koma garinsu don haka ta shirya sai su koma tare." Ɗauko jakarsa yayi irin ta ƙwararrun mafarauta, ya rataya ta a kafaɗa yace Ummata ta biyo shi a baya. Tafiya suke sosai, tun da sassafe har rana ta take, saboda tausayin Ummata da yake yi yasa ya tsaya ta huta sannan suka cigaba da tafiya sai can wajen yamma suka fara hango wani ɗan ƙaramin ƙauye a tsakanin duwatsu. Bayan sun ƙarasa ƙauyen ne, wani gida ya nufa da ita yayin da suka shiga gidan, sai wata tsohuwa ta taso da murnarta tare shi tana cewa "sannu da zuwa babana." Sai da ta ɗago idanunta, karaf! ta sauke su akan Inna, tambayar shi ta yi inda ya samo wannan matar yayi bai ɓoye mata kome ba, game da labarin Ummata. Wannan tsohuwar ta tausayawa Ummata ba kaɗan ba, tun daga ranar suka zama ƴan'uwan juna da Ummata, kullum a wajen wannan tsohuwar nake wuni. Sannu-sannu har Ummata ta samu labarin mutuwar Abbana a hannun ƴanta'addan nan, haƙiƙa ta yi kuka sosai, na rabuwa da Abbana da kyar tsohuwa da Mafaraucin nan suka rarrasheta tayi shiru. Lokacin da tayi idda sai Habib wato mmafaraucin nan ya nuna yana son auren Ummata, da kyar dai ya samu ta amince zata aure shi. Lokacin da ya auri Ummata sai ya mayar dani ɗansa, ya saka ni a makarantar boko a can wani gari nesa da ƙauyen da muke sosai, kafin na yi wayo kullum shi yake rakani har makarantar sannan idan an tashi da kansa zai zo ya ɗauke ni. Kuma kullum da yamma da daddare ina zuwa makarantar allo da take cikin ƙauyen, idan kuwa aka yi hutu tare muke zuwa farauta, da haka har nima na koyi farautar. Wata rana kwatsam! lokacin ina aji shida a primary, muka tashi da Abbana ciwon ciki ya turnuƙe shi, kafin mu yi wani yunƙuri rai yayi halinsa. Mun sha kuka sosai, musamman ma ni ba ƙaramin shaƙuwa muka yi da shi ba. Tun daga ranar nima na ware rana, duk wata sau uku nake zuwa farauta, saboda na gaji Abbana. Sannu a hankali har na zama ni ne shugaban mafarautan ƙauyenmu, saboda kaf ƙauyen babu wanda ya kai ni iya farauta. Shikenan na watsar da duk wani karatun boko sai na allon nake ɗan taɓawa, wani lokacin. kunji taƙaitaccen labarina, don haka kuma zan taimaka muku iyakar ƙarfina. Safna ce tayi murmushi tace "Abba labarinka wallahi akwai daɗi murmushi yayi ya shafa kanta, yace kina son labarai? gyaɗa masa ta yi yace "To karki damu kullum zan rinƙa baki labari Mai daɗi. Anas ne ya katse musu zancen da cewa "Abbanmu zaka kai ni in zama babban soja? [12/9, 4:33 PM] ~HUSSAIN YUSUF~: *🫐🫐 ANAS MALEEK🫐🫐* Labari/Tsarawa HUSSAINI YUSUF *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘Yancinmu* *Page 13&14* Murmushi Aisar yayi ya shafa kan Anas yace "Anas me yasa kake son zama soja?" Saboda na ɗauki fansar ran iyayena da mugayen ƴanta'addan can da suka kashe iyayena, kuma na kawo ƙarshen ta'addanci da zalunci a ƙasata. Sosai Anas ya burge Aisar, saboda yana matuƙar son yaro marar tsoro saboda haka ya sha alwashin ko zai rasa kome na shi, sai ya taimakawa Anas ya cika burinshi na zama soja. Kallon Safna yayi yace "ke kuma ƴan'mata me kike son ki zama anan gaba?" Kwantar da kai ta yi tace "ni burina na ga Innata sannan na faɗa mata abinda nake son zama, don Allah ka kai ni wajen Innata na ganta." Sosai ta bai wa Aisar tausayi, rarrashinta yayi yace "gobe da safe zai kaita wajen Innar ta ta." Washe baki Safna ta yi tace "Nagode Abbana daga yau ka zama Abbana tunda Baffa ya mutu kai ne Abbana" Murmushin jin daɗi yayi ya dubi Safna yace "Da yau to ki rinƙa kirana da Abbanki." Da sauri tace "to Abba" tana sakin wani murmushi da ya saka dimple ɗinta lotsawa. Haƙiƙa Safna yarinƴa ce don a shekaru ba ta fi shekara takwas ba, shi kuma Anas zai yi shekara goma sha huɗu shi yasa yake da wayo da kuma hankali. Shi kansa Anas ya san Aisar ya faɗawa Safna zai kaita wajen Innarta ne, don kawai ya kwantar mata da hankali, amma shi yasan yanzu Innarsu ta daɗe da mutuwa. Shiga cikin bukkar Aisar yayi, bai daɗe ba ya fito da wata jaka a hannunsa, kunce ƙullin jakar yayi gurasa ce da busashshen kifi a ciki. Ruwa ya ɗebo ya jiƙa gurasar da kifin, har suka yi laushi, sannan ya ɗauko ya zo ya hura wuta, ya sake gasa kifin da gurasar har suka yi ɗumi, damƙawa kowa gurasa uku kifin da ya kasance manya ya ba su bibiyu. Ci suke yi suna nishaɗi abinsu, dama ba ƙaramin yunwa suke ji ba yanzu sun samu wanda zai taimaka musu a rayuwa, da santi ya ɗebi Safna bata san lokacin da ta dubi Anas ba tace "Yaya Anas dama na faɗa maka mu taimaka wa jaririn can, mu ma Allah zai kawo me taimaka mana, kuma ga shi mun samu da ba mu taimaka masa ba da yanzu mu ma Allah bai taimake mu ba. Dariya Anas da Aisar suka saka, sannan Aisar ya dubi Safna yace "A'a Safna ko da ba ku taimake shi ba, Allah zai kawo wanda zai taimaka masa, kuma zai taimake ku saboda kuna buƙatar taimakon, ai Allah shi ba azzalumin bawansa ba ne." Yana kai wa nan a zancensa, ya tashi ya shiga cikin bukkar. Bai daɗe a ciki ba, sai ga shi ya fito rungume da jaririn ya rufe shi da wata busashshiyar fatar Damisa, saboda zafin rana. Sannan ɗaya hannunsa riƙe da jakar farautansa, kallon su Anas yayi yace "ku taso mu tafi cikin gari, da sai gobe na so mu tafi saboda wannan jaririn nace mu tafi yau. Tashi suka yi Anas yace "Abba kawo jakar na riƙe maka" a'a Anas ku ji da tafiyar ma da zamu yi don da ɗan nisa kafin mu isa ƙauyen namu. Saka su a gaba yayi shi kuma ya rinƙa bin su a baya, sai da suka fita daga surƙuƙiyar nan sannan suka faɗa wata babbar hanƴa. Hanƴar tana da faɗi sosai ga shi cike take da yashi, amma a haka suke ta tafiya, idan ya ga sun gaji sai ya tsaya su huta sannan su cigaba da tafiya, sai doshin magariba suka isa wani ɗan ƙaramin ƙauye. Murmushi Aisar ya saki ya dubi su Anas da Safna yace "kun ga ɗan ƙauyen namu ko?" dariya Anas yayi yace "Abba ai nan yafi ƙarfin a kira shi ƙauye." Tafiya suke yi a cikin ƙauyen, har suka ƙaraso ƙofar wani gida, wanda aka zagaye shi da dangar kara daga gaban gidan kuma aka yi shi da bulon ƙasa, har da zaure da kuma ɗaki a cikin zauren. Lokacin da suka shiga cikin gidan, babu kowa a tsakar gidan motsin mutum, suka ji a cikin banɗakin da yake tsakar gidan. Nuna musu wani itace yayi yace su zauna akai, shi kuma ya shiga cikin wani ɗaki ya ajiye kayan farautarsa ya fito ya zauna kusa da su ya ƙurawa fuskar jaririn da yake ta sharar barci abinsa idanu. Ba daɗewa sai ga matar gidan ta fito daga banɗakin, sai faman yarfe ruwa take yi a jikinta, hankalinta bai kai inda su Anas suke ba. A hankali ta ɗago idanunta, ta sauke su akan su Anas da Safna sai kuma mijinta riƙe da jariri yana ta aikin kallonsa. A hankali tace *"Abu Nisreen* lafiya na ga ka dawo, ba lokacin da ka saba dawo ba? Da sauri ya ɗago da kansa ya kalleta ya sakar mata wani murmushi mai taushi yace "haba *Ummu Nisreen* ga dalilin da yasa na dawo yanzu, ya faɗa yana nuna su Anas da Safna. Ta daɗe tana kallonsu, kafin ta mayar da hankalinta wajen jaririn da yake hannunsa tace "Abu Nisreen wannan jaririn fa ko shi ma tare ka same su" haka yace mata kwantar da hankalinki zan baki labarin komai, idan na samu nutsuwa. Ni tunda na shigo ma ban ga Nisreen ba, ina ta tafi ta zo na samo mata ƴar'uwa murmushi Ummu Nisreen ta yi tace "Wallahi tun yamma ta tafi gidan Iya kuma har yanzu ba ta dawo ba." Murmushi ya saki yace "Ai kin san Nisreen da Iya idan suka haɗu basa son rabuwa ko kaɗan, yanzu dai ki ɗumama wa waɗannan yaran ruwa su yi wanka, miƙa mata jaririn da yake hannun sa yayi yace "ungo wannan jaririn in anjima kaɗan zai farka insha Allah." Har ƙasa ta durƙusa ta karɓi jaririn tare da ƙura masa idanu. Shi kuwa Abu Nisreen, roba ya ɗauka ya nufi rijiya domin ya ja ruwa ya watsawa jikinsa ko zai ji ɗan daɗi a jikinsa. Shiga da jaririn Ummu Nisreen ta yi cikin ɗaki ta ajiye shi, sannan ta fito ta ɗauki bokiti ta nufi rijiya za ta ɗebo ruwa, da sauri Anas ya tashi ya riƙe bokitin yace "Umma kawo na ɗebo miki ruwan" murmushi ta yi tace "ka bar shi kawai, zan ɗebo kai da gajiya a jikinka." Ƙin sakin bokitin yayi, a bisa dole ta bar shi ya tafi rijiyar domin ya jawo kata ruwan, a zuciyarta kuwa addu'a take Allah yasa kada Abu Nisreen ya gani tace ita ta saka shi ransa ya ɓaci, ita kuwa ta tsani ta ga ran mijinta ya ɓaci. Anas yana cikin jan ruwan, sai ga *Nisreen* ta shigo gidan da gudu tana kiran Umma! Umm... Shiru ta yi yayin da ta ga Safna a zaune kuma ta hango Anas yana jan ruwa, a bakin rijiya. Bata daɗe da shigowa ba, sai ga Iya ta shigo gidan da alama tare suke da Nisreen ɗin. Idanun Iya ne ya kai Safna da take zaune, da Anas da ɗauko bokitin ruwa, dai-dai lokacin kuma Ummu Nisreen ta fito daga cikin ɗaki, hannunta riƙe da ashana. Tana ganin Iya ta yi sauri ta ɗauko mata kujera ƴar tsugunne, ta kai mata ta zauna sannan ta dubeta tace "Rahila baƙi kuka yi ne?" murmushi ta yi tace wallahi iya Abu Nisreen ne ya zo da su daga wajen farautarsa, ni ma bai yi bayanin inda ya samo su ba. "Ikon Allah ashe ya dawo?" "E, wallahi bai daɗe da dawo wa ba, wanka ma yake yi, shine yace na ɗumama musu ruwa su ma suyi wanka, har da wani jariri ma yana ɗakina yana barci. Ita dai Iya riƙe baki kawai ta yi, Nisreen ce ta je wajen Safna ta kama hannunta tace "ke ma ƙawata ce?" gyaɗa mata kai Safna ta yi sannan ta sakar mata murmushi, ita ma Nisreen murmushin ta sakar mata, sannan ta kama hannunta tace "zo mu je ki ga kayana da Abbana ya siyo mini." Miƙewa Safna ta yi ta bi Nisreen ɗin a baya, Ummu Nisreen da Iya sai dariya suke yi na shirmen da Nisreen take yi yana burge su. Iya ce tace "Ummu Nisreen ta je ta ɗauko mata jaririn ta gan shi, bayan ta tafi ɗauko mata shi sai ta mayar da kallonta wajen Safna nan take ta ganta tana tsananin kama da matar da ta taimakawa jiya, kuma ta tuno matar ta bata labarin tana da ƴaƴa yanzu haka bata san inda suke ba. Dai-dai lokacin Ummu Nisreen ta fito daga ɗaki hannunta rungume da jaririn, shi ma Abu Nisreen (Aisar) ya fito daga wankan da ya shiga. Zuwa yayi gaban mahaifiyar ta shi ya tsugunna har ƙasa ya gaishe ta, kafin yayi wata magana Iya ta riga shi da cewa, Aisaru a ina ka samo waɗannan yaran? Kafin ya bata amsa ta riga shi da cewa, abinda yasa na tambayeka jiya wata mata tazo garin nan, a firgice tace wai wasu ƴanta'adda ne suka kashe mata miji shine ita ma Allah ya bata nasarar kashe ɗaya a cikinsu ƴanta'addan da suka biyota sai Allah ya jefo ta nan garin, ni ce nan na taimaka mata bayan mun je gidan me gari yace "ta zauna a gidana. Tun jiya ta ƙi cin abinci sai faman kiran sunan ƴaƴanta take yi, kuma ina zaton duk yadda aka yi wannan ƴarta ce domin suna tsananin kama da juna, ta faɗa tana mai nuna Safna. Anas ne ya zo da gudu ya riƙe ƙafafun Iya yana kuka yake cewa "Don Allah a ina kika ganta ta so mu je ki nuna mana ita Allah yasa Innarmu ce. Hussaini Yusuf Comment Share Fisabilillahi [12/9, 4:33 PM] ~HUSSAIN YUSUF~: *🫐🫐 ANAS MALEEK🫐🫐* Labari da Rubutawa HUSSAINI YUSUF *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *Page 15&16* Aisar ne ya zo ya kama hannun Anas yace "Anas ba mu tabbatar Innarku ba ce, har sai mun je mun gan ta. Wataƙila ma a irin ƴan garinku ne waɗanda su ma suka yo gudun hijirar, yanzu ka je ka yi wanka magriba ta kusa idan mun yi sallah sai mu je mu gano ta. Gaba ɗaya mutanen wajen sai da suka tausaya wa Anas da Safna, musamman ma Iya har hawaye sai da ta zubar ta rinƙa cewa "wallahi yanzu ƙasar nan babu adalci ko kaɗan, haka kawai kana zaune lafiya wasu su zo har cikin gidanka su hallaka ka amma gwamnati ta kasa ɗaukar mataki akai, wannan wanne irin rashin imani da tausayi ne? Ummu Nisreen ce ta kama hannun Safna ta ja cikin banɗaki, ta yi mata wanka bayan ta gama yi mata ta fito sai Anas ma ya shiga, ba ƙaramin daɗi ya ji a jikinsa ba yayin da yake watsa ruwan zafin a jikinsa, saboda ko'ina na jikin nasa tsami yake yi masa. Bayan ya fito daga bayin, sai ya ɗauki buta ya ɗaura alwala domin an fara kiraye-kirayen sallar magriba. Bayan Ummu Nisreen ta gama yiwa Safna wankan, sai ta jawo cikin ɗakinta ta shafa mata mai ta yi mata kwalliya, sannan ta ɗauko kayan Nisreen ta sanƴa mata a jiki, masha Allah shine abinda na faɗa yayin da naga Safna ta yi wani irin kyau duk da yarinƴa ce, amma idan ka kalleta sai ka sake kallinta saboda Safna ba baya ba ce wajen kyau da cikar halitta irin ta ƴa mace. Lokacin da Nisreen ta ga Safna sanƴe da kayanta, kuma ta yi kyau sosai kamar ɗiyar larabawa, sai ta cika da farinciki ta rinƙa jan Safna da zance tun ba ta kula ta har ta zo ta riƙa mayar mata, daɗi yasa Nisreen tace ta bar wa Safna kayanta da aka sa mata. Bayan Anas ya gama ɗaura alwalar, sai suka tafi masallaci tare da Abu Nisreen, ita ma Ummu Nisreen sai ta ɗebowa Iya ruwa tace ta yi alwala ita ma ta ɗauki wata butar ta fara alwalar. Su Nisreen da Safna kuwa sai faman wasansu suke yi, Nisreen sai faman zagaya gidan take yi ita da Safna tana nuna mata abubuwa. Allah -Allah Anas yake yi a idar da sallah su je su gano matar da Iya ta faɗa, idan kuwa Innarsu ce bata mutu ba babu wanda zai kai su farinciki da ganinta. Bayan an idar da sallar an shafa addu'a sai Abu Nisreen ya kamo hannun Anas suka fito daga masallacin, yayin da suka shigo cikin gidan su Iya Ummu Nisreen sun idar da ta su sallar, gaba ɗayansu suka ɗunguma suka tafi gidan Iya, har da su Nisreen da Safna. Sosai Safna take jinta a cikin farinciki ta samu ƙawa me mutunci, a cewarta wato *Nisreen* a hanƴa ma hannunsu yana sarƙe da na juna, cike da nishaɗi da walwala suke tafiya, duk inda Nisreen ta ga ƙawayenta sai ta kira sunansu ta nuna musu Safna tace kun ga sabuwar ƙawata haka ko wanda ta sani idan ta gan shi sai ta nuna masa Safna. Cikin ƙanƙanin lokaci suka iso gidan Iya, take kuwa Anas ya ji gabansa ya tsananta faɗuwa sosai fargaban kada ya ga wata ba Innarsu ba yake yi cikin ran shi. Yayin da suka shiga cikin gidan gaba ɗayansu, Inna tana cikin banɗaki daga ciki take jiyo muryar Safna da Nisreen, domin ta daɗe da sanin Nisreen don a gidan take yini kullum. Murje idanuwanta ta yi don ta tabbatar ba'a mafarki take jin muryar Safnar ta ba, sauri ta yi ta kammala abinda ya kaita banɗakin sannan ta nufo ƙofar fitowa. Idanunta sai ƙaiƙayi suke, sun matsu su yi tozali da ƴaƴanta abin alfaharinta, zuciyarta tana ta muradin sake ganinsu, yayin da ƙafafunta suka ƙagu a taka su domin su ga farincikin rayuwarta. Lokacin da ta gama fitowa daga cikin bayin, ta hango su a zaune a ƙofar ɗaki kan tabarmar da Iya ta shimfiɗa musu, tana gama fitowa karaf! idanun Safna suka sauka a kanta ba ta tsaya wani jinkiri ba ta tafi da gudu tana kiran Innaaaa! da sauri Anas ya ɗago da kansa da yake a sunkuye tun shigowarsu cikin gidan. Innarsu ya gani, ya murza idanunsa don ya tabbatar ba'a mafarki ya ganta ba, ai bai jira wani abu shi ma ya nufe ta da gudu ya rungume ta, gaba ɗayansu suka fashe da kukan farinciki. Anas yace "ashe Inna ba ki mutu ba? zamu sake ganinki, Safna ma tace "Inna me yasa kika ce mu gudu mu bar ki, kuma ina Baffamu yake a can kika baro shi?" Tambayar Safna ta sake karyarwa Inna da Anas zuciya, suka sake fashewa da kuka, mai tsuma zuciya. Su Abu Nisreen da Iya da Ummu Nisreen, sai faman zubar da hawaye suke yi, na tausayin su Inna da ƴaƴanta, Allah sarki! Yanzu da Allah bai sake haɗa su, ko yaya za su yi da rayuwarsu? don tsakanin ɗa da mahaifi sai Allah. Har *Abu Nisreen* ya yunƙura zai je ya rarrashe su, da sauri Iya ta hana shi tace me yasa zaka je ka hana su kukan farincikin sake ganin juna da suka yi? Dakatawa yayi ya zauna ya ƙurawa su Inna idanu, cike da tausayinsu. Dai-dai lokacin jaririn da su Safna suka tsinta ya farka daga barcin da ya shafe awanni yana yi, kukan shi ne ya dakatar da su Inna, da sauri suka ɗago kawunan su, suka kalli inda suka jiyo kukan jaririn da yake goye a bayan Ummu Nisreen. Da sauri Iya ta karɓe shi daga hannun Ummu Nisreen, ta je ta ɗebo ruwa a wani ɗan ƙaramin kofi ta bai wa jaririn, kowa a wajen sai da yayi mamakin ruwan da jaririn ya sha. Shigewa ɗaki Ummu Nisreen ta yi domin ta ɗauko tabarma ta shimfiɗa musu, fitowa ta yi daga ɗakin Iya hannunta riƙe da wata ƙatuwar tabarma sabuwa dal. Shimfiɗawa ta yi a ƙofar ɗakin Iya, Abu Nisreen yace "kowa ya zo ya zauna, gaba ɗayan su suka zo suka zauna akan tabarmar har Inna da su Anas da Safna sun zo sun zazzauna akan tabarmar. Nisreen kuwa tun da ta ga ƙawarta Safna tana kuka, sai jikinta yayi sanƴi ta samu waje ɗaya ta zauna ta yi shiru tare da ƙurawa su Safnar idanu. Bayan kowa ya zauna a kan tabarmar sai Abu Nisreen yayi gyaran murya, yayi wa Allah godiya tare da addu'a ga fiyyayen halitta Annabi Muhammadu (S.A.W) sannan suka yi addu'a suka shafa. Anas ne ya fara bayar da labarin irin wahalar da suka sha, shi da Safna har tsintar jaririn da suka yi, da yanda Safna ta kafe akan dole sai sun ɗauko, da lokacin da zaki ya ritsa su a dokar daji zai hallaka su, Allah ya kawo Abu Nisreen ya taimaka musu. Sosai kowa ya ji tausayin su Anas, Iya har da zubar da ƙwalla sai da ta yi, haka Ummu Nisreen ma sai da ta zubar da hawaye na tausayin su Anas. Inna ma nan take ta shiga bayar da nata labarin da irin wahalar da ta sha bayan ta cewa su Anas su tafi, su rabu da ita, bayan kowannen su ya gama alhinin da zai yi sai Abu Nisreen yace "ita Ummu Nisreen ta ruƙe jaririn ta raine shi tunda Allah bai sake bata haihuwa ba tun haihuwar Nisreen. Ita kuma Inna ta zauna a gidan Iya sai a bata Safna da Nisreen, Nisreen ta zauna hannun Iya ita kuma Safna ta zauna a hannun Inna yayin da shi kuma Anas zai zauna a hannun Abu Nisreen, sai su rinƙa zuwa farauta da neman kuɗi tare. Nan take kuwa kowa ya amince da wannan kyakkyawar shawarar da Abu Nisreen ya kawo, miƙewa tsaye Abu Nisreen yayi yace "Ummu Nisreen ta tashi su tafi, domin an kusa yin kiran Isha'i, su kuma su Nisreen da Safna su zauna anan su kwana da safe za'a kawo musu kayan sakawar su." Daga ƙofar gida suka ji ana bugun gidan kamar za'a karya ƙyauren da ke maƙale a ƙofar gidan da sauri Abu Nisreen ya fice domin ya gano lafiya ake buga masa gida haka. To be continue.......... Comment and share🙏 Hussaini Yusuf✍🏻 [12/9, 4:33 PM] ~HUSSAIN YUSUF~: *🫐🫐 ANAS MALEEK🫐🫐* Labari/Rubutawa HUSSAINI YUSUF *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *_____________________________* *Page 17&18* Yayin da Abu Nisreen ya fito ƙofar gidan, sai ya iske ɗan aiken me gari a tsaye yana jiransa, ya fito. Yana ganinsa yace "yawwa Allah dama kai me gari ya aiko ni ba kira ka" cike da mamaki Abu Nisreen yace "Lafiya me gari yake nema na? ni da ban daɗe da dawo wa garin ba." Koma menene idan ka zo zaka ji, iska Abu Nisreen ya furzar daga cikin bakinsa yace "ka je ka ce masa ina zuwa amma sai na yi sallah zan zo." cike da mamakin maganar Abu Nisreen ɗan aiken me garin ya dube shi yace "Yanzu saboda ka raina yallaɓai yace ka zo kace sai kayi wani uzuri sannan ka zo? Abu Nisreen yace "kiran me gari ya fi kiran Allah ne" don haka ka je ka ce masa ina yin sallah zan zo, bai jira abinda ɗan aiken megarin zai ce ba ya juya ya shige cikin gidan ya bar shi a tsaye, riƙe da baki na mamakin Abu Nisreen. Yana shiga cikin gidan, ya ga su Iya da Inna duk hankalinsu a tashe, sakin fuskarsa yayi yace "Ummu Nisreen taso mu tafi gida" miƙewa ta yi haɗe da goya jaririn a bayanta, da sauri lya ta sha gaban Aisar (Abu Nisreen) tace "ba ka faɗa mana menene yake faruwa ba zaka tafi gida, bayan tun tafiyarka muke nan muna jiran ka dawo mu ji abinda yake faruwa. Murmushi yayi yace "Iya ba wani abu ba ne dama me gari ne yace na zo yana kirana, shine nace sai na yi sallah zan je." Da sauri Iya ta dafe ƙirji tace "me gari fa kace Aisaru" to me yasa yake nemanka? wallahi Iya sai na je can fadar sai in ji dalilin kiran amma yanzu ni ban san kome ba akai, an ce dai yana kirana. Ajiyar zuciya Iya ta sauke tace "Allah yasa dai mu ji alkhairi, da amin gaba ɗayansu suka amsa, sannan Aisar ya ja hannun matarsa suka fice daga gidan. Rahila (Ummu Nisreen) zuciyarta fes yau ta samu ɗa, kuma ɗan ma namiji, abin da ta daɗe tana mafarkin samu idan ta yi aure wato ɗa namiji, amma cikin hukuncin Allah sai ya bata ƴa mace. Amma hakan bai sa ta ƙyamace ta ba ko taƙi ta hasali ma soyayyar da ta nunawa Nisreen, Aisar har kishi ya rinƙa yi, saboda ba ya samun kulawa daga wajenta kamar da, kafin ta haihu, amma yanzu da ta haihu duk kulawar da take bashi ta koma kan ƴar ƙaramar ƴarsu wato Nisreen. Yau shekararta takwas da haihuwar Nisreen, Allah bai sake ba ta wani cikin ba, ballantana ta saka ran samun namijin, har ta fitar da rai sai ga shi Allah ya kawo mata ɗan har gida, ita kuwa me zata yiwa Allah ba godiya ba? domin ya cika mata burinta na rayuwa ya kawo mata ɗa namiji har gida. Don haka a cikin ranta ta ɗauki alƙawarin sai ta yi azumi uku don nuna tsantsar godiyarta ga Allah (S.W.T), suna cikin tafiya Aisar ya fahimci halin da take ciki, ya kalli fuskarta, ya ga sai faman murmushi take saki kamar gonar auduga. Cike da jin daɗin ganin matarsa a farinciki ya tambayeta abinda ya sakata murmushi haka, kamar wacce aka yi wa albishir da gidan aljanna.Ƴar dariya ta saka tace "haba Abu Nisreen akwai abinda ya saka ni farinciki fiye da wannan gagarumar kyautar da kayi mini? Da mamaki a fuskarsa yace "ni kuma wacce gagarumar kyauta na yi miki da har take saka ki farinciki haka? nuna masa jaririn da yake bayanta ta yi, tace "akwai kyautar da tafi wannan a wajena?" Girgiza kai yayi yace "babu domin na san yadda ki ke matuƙar son ɗa namiji" amma bari na yi miki wata tambaya, yi tambayarka kowacce iri ce insha Allah indai na sani zan baka amsarta. Me yasa lokacin da na shigo da jaririn nan, ban ga fara'a da walwala a fuskarki ba kamar yanzu? Sake sakin wani murmushin ta yi tace "abinda yasa lokacin ba ka ga fara'a a fuskata ba, gaskiya ba zan ɓoye maka ba, abu ɗaya ne zuwa biyu. Na farko shaiɗan ne yaso yayi wasa da zuciyata wajen saƙa mini mugayen abubuwa a cikin raina, lokacin da na ganka da jariri, sai na rinƙa tunanin ko ba farauta kake zuwa ba, shashancinka kake zuwa shine har ka samo ɗa ka zo ka ce tsinto shi kayi, abu na biyu kuma shine bayan na kawar da tunanin da shaiɗan yake ta aikin saƙa mini game a wannan jaririn, sai na ji ƙaunar yaron ta shiga cikin raina, na tuna ina masifar son ɗa namiji amma tun da ga shi na samu zan yi sake da damata, sai na ji tsoron kuma kada ka kai shi gidan me gari ya ƙwace shi ya bai wa wata matar ni kuma a bar ni da baƙin ciki, to ka ji abinda yasa ka ga ban yi maraba da yaron ba tun wuri. Sosai ya jinjinawa matar tasa bisa wannan ƙoƙari da ta yi, kuma ya godewa Allah da ba ta bi son zuciyarta ba da ruɗin shaiɗan. Cike da nishaɗi suka isa gidan, suna shiga buta Aisar ya ɗauka domin an fara kiran sallar Isha, bayan ya gama alwalar ya miƙe tsaye yace "Ummu Nisreen ni zan tafi masallaci, kuma daga can zan wuce gidan me gari, domin na ji kiran da yake yi min sannan ya dubi Anas yace idan ya gama ta shi alwalar ya same shi a masallaci." Murmushi ta saki tace "To Abu Nisreen Allah ya dawo min da kai lafiya, cike da jin daɗi ya amsa da amin sannan ya fice daga gidan. Bayan ya fita Ummu Nisreen ta dubi Anas tace "idan ka dawo daga masallacin ka zo ka karɓi abinci, amsawa yayi da to sannan shi ma ya fita daga gidan domin zuwa ya samu jam'i. Bayan an idar da sallar Abu Nisreen ya cewa Anas ya koma gida ya ci abinci, shi zai je domin amsa kiran me gari, babu musu Anas ya nufi gida, shi kuma Aisar kai tsaye ya nufi gidan me gari domin ya ji dalilin kiran shi da aka yi. Yayin da ya iso fada sai ya ga fadar cike da jama'a, sun kewaye me gari da yake zaune akan wata kujera, wacce aka haɗata da katako. Yana iso wa jama'ar wajen suka dare, suka buɗa masa hanƴa ta tsakiyarsu, ba tare da tunanin komai ba ya shige yaje har gaban me gari ya tsugunna ya kwashi gaisuwa, a wajen dagacin. Amma ko ci kanka babu wanda yace da shi a wajen ballantana yasa ran za'a amsa masa gaisuwarsa, gaba ɗaya jama'ar wajen shiru suka yi suna sauraren su ji abinda me gari zai ce.......akan Aisar. Sai da aka ɗauki dogon lokaci sannan me gari yayi gyaran murya, yace "wato yanzu kai Aisaru abin naka har ya kai ga haka?" Cike da mamaki Aisar yace "ranka ya daɗe me na yi kuma?" Cikin ɗaga murya me gari ya fara faɗa yana cewa "yanzu in ban da ka raina mu, mu tashi ɗan aike mu ce ya faɗa maka ka zo yanzun nan ana son ganinka a fada, amma saboda ba ka ganin girmana na shugaban ƙauyen nan, ka ƙi zuwa har sai da ka kammala abinda kake sannan ka kwaso wasu shegun ƙafafunka ka zo. Sunkuyar da kai Aisar yayi cike da ladabi yace "Allah ya baka yawan rai, ba ƙin amsa kiranka na yi ba gani na yi lokacin sallah yayi shine nace idan mun idar da sallar sai na zo. Rufe min baki ja'iri kawai ni zaka nunawa sallah? me yasa ba ka zo nan mun yi sallar tare da kai ba? me gari ya faɗa a hasale. Murmushin takaici Aisar ya saki yace "yallaɓai a yi haƙuri na tuba" mtssss! me gari ya ja wani dogon tsaki yace. "Dama abinda yasa na aika a kiraka ba komai ba ne, sai dangane da wani zargi da mutane suka fara yi akan ka, kai da mahaifiyarka, da sauri Anas ya ɗago da kansa ya kalli me gari yace "yace Yallaɓai me mutanen suka ce mun yi musu ni da Iyata?" Ni dai a iyakar sanina ina zaune da kowa lafiya. Me gari ne ya cigaba da cewa "zarginka suke yi wai idan ka fita farauta, matan banza ka ke bi shine har ka samu ƴaƴa ka ɗauko su ka kawo su garin nan, yau ɗin nan ance ka zo da wasu yara har da jariri. Ita kuma mahaifiyarka ana zarginta da taimakawa ƴanta'adda domin an shaida min cewa " matar nan da mahaifiyarka ta taimakawa ƴar leƙen asiri ce, ta zo ne domin ta ga yadda ƙauyen namu yake ta shaidawa ƴanta'adda su farmake mu su kashe mu su ƙwace dukiyoyinmu, sannan su raba mu da rayuwarmu. Ƙarya take domin an shada mana a ƙauyen da ta baro, babu ko mutum ɗaya da ya tsira da rayuwarsa ƙarya ta faɗa mana domin kawai ta samu damar da za ta aiwatar da aikinta ba tare da wani ya gano shirinta ba, ballantana ya tona mata asiri, da yake Allah ya riga ya karemu sai ya tona mata asiri shirinta ya watse cikin ƙanƙanin lokaci...... To be continue....... Comment and share Hussaini Yusuf✍🏻 [12/9, 4:34 PM] ~HUSSAIN YUSUF~: *🫐🫐 ANAS MALEEK🫐🫐* Labari da Rubutawa HUSSAINI YUSUF *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *_________________________________* *Page 19/20* Tunda me gari ya fara magana, ran Aisar ya rinƙa ɓaci zuciyarsa ta rinƙa tafarfasa har wani ɗaci ya ji zuciyarsa tana yi masa, a fusace ya dubi me gari yace "Yallaɓai na san dai ka san ko ni wanene, kuma ka san mahaifiyata ita ma ko wacece. Yakamata me gari idan an kawo maka irin wannan zancen, ka rinƙa bincike kafin ka yanke hukunci. Kaiii! rufe min baki wawa kawai, shashasha kai har ka isa ka faɗa min gaskiya? me gari ya faɗa ransa a ɓace. ya cigaba da cewa "dukkanmu nan da kake gani babu sa'an mahaifinka a cikinmu, da har ka ke ɗaga mana murya, ko shi marigayi mahaifinka malam Habibu bai isa ina faɗa yana faɗa ba. Kuma da kake cewa mun san kai wanene ta yaya muka sani? In ce malam Habibu ne a yawon farautarsa ya tsintoka, kai da mahaifiyarka, waye ya san daga inda kuka fito? Nan take jama'ar wajen suka ɗauka dama tsintacciyar mage ba ta mage, fashewa da kuka Aisar yayi yace "yanzu Yallaɓai da kan ka kake tozarta ni a cikin jama'a? Rufe min baki, kuma na ƙara jin ka kira sunana, yanzun nan sai in keta maka rigar mutunci, me gari ya faɗa a fusace yana mai duban Aisar. Shi ma Aisar cikin fushi yace "Wacce rigar mutunci ce kuma baka keta mini ba?" wallahi me gari ka ba ni mamaki da har ka ɗauki ƙarairayin mutane a kaina. Ban taɓa zaton haka daga gareka ba me gari, a zatona kai uba ne a gare ni, duba da yadda kuka yi zaman aminci da mahaifina. Ashe yadda na ɗauke ka, kai ba haka ka ɗauke ni ba, nagode da wannan sakayyar da ka yi mana. Shiru me gari yayi domin ba shi da abin cewa, jikinsa yayi sanƴi haƙiƙa har a zuciyarsa bai taɓa ganin wani aibu na Aisar ba, da har za'a yi Allah wadai da shi. Amma saboda shaiɗan ya riga ya mallake zuciyarsa, sai yayi sauri ya kawar da wannan tunanin daga zuciyarsa, ya dubi Aisar yace "Yanzu zaɓi biyu zan baka, dole ne ka zaɓi ɗaya daga ciki. Zaɓi na ɗaya da zan baka shine gobe da safe ka je ka mayar da waɗannan yaran da ka zo da su inda ka ɗebo su, zaɓi na biyu kuma idan har ka nuna ba za ka mayar da su ba, to sai dai duk ku bar min garina gaba ɗaya, bana son na sake ganinka a garin nan idan har kace ba za ka mayar da su ba, to har mahaifiyarka ban yarda ta zauna a garin nan ba, tun da nawa ne ni nake da iko na bar mutum ya zauna ko kuma na kore shi. Wanne ka zaɓa daga ciki? me gari ya tambaya yana kallon inda Aisar yake tsugunne, ya sunkuyar da kansa ƙasa. Ɗagowa yayi da rinannun idanun shi, ya kalli me gari yace "Na zaɓi na bar garin nan akan na mayar da waɗannan yaran dajin da na tsinto su, ka sani me gari ƙasa ta Allah ce haka gari da kake ikirarin naka ne to ka yi kuskure, domin garin nan da kake gani na mutanen da suke zaune a cikinsa ne. Ka sani a yanzu idan na bar garin nan ba zan rasa inda zan zauna ba, tunda duniya ce Allah yayi ta da girma, kuma mutanen ƙwarai masu tausayin jama'a ba su ƙare ba, ba zan rasa wanda zai ji ƙaina ya taimaka mini ba. Kai dakata ɗan samari Liman ya faɗa ransa a ɓace yace "ban taɓa zaton ba ka da wayo ba sai yau ɗin nan, yanzu akan waɗansu yara da ka tsinto a cikin daji ka yarda ka bar garin da Allah ya rufa maka asiri a cikinsa?" Ni dai shawarar da zan baka, tun lokaci bai ƙure maka ba kayi gaggawar canja shawara, domin idan ka bar nan ba lallai ka samu kamar sa. Dakata liman Aisar ya faɗa a hasale "wallahi liman ka ba ni mamaki da har ka biyewa son zuciyarka, kake faɗan son ranka akan wani ɗan abin duniya da za'a baka wanda bai taka kara ya karya ba. Sannan ya kalli me gari yace "Yallaɓai ni na yarda zan bar garin nan, amma ina roƙon wata alfarma guda a wajenka. Kallon shi me gari yayi sannan ya kalli liman yace "malam liman ya kake gani mu yi masa alfarmar?" A fusace Liman yace "kawai ka yi abin da ya dace, yaron da akan idonka ya gama ci mini mutunci amma ka kasa cewa komai shine yanzu zaka hau tambayata wai ayi masa alfarma? kawai idan ka ga zaka yi masa kayi masa idan kuma baza ka iya ba kace kai tsaye ba zaka yi ba." Kallon fuskar Aisar me gari yayi gani yayi ya masa wani irin kwarjini, take yace "faɗi alfarmar da kake son nayi maka idan zan iya sai na yi maka." Dama alfarmar da zan nema ita ce ka bar ni na zauna tsawon sati biyu idan na kammala shirye-shiryena sai na tafi gaba ɗaya. Ɗaga kai megari yayi sama yana nazari, sai da ya ɗauki tsawon minti biyu a haka sannan ya kalli Aisar yace "na yarda babu matsala ko wata guda ka ce zaka yi na yarda. Godiya Aisar yayi wa me gari sannan ya tashi ya nufi gida, zuciyarsa ban da suya babu abinda take yi, ji yake kamar ya koma ya shaƙe me gari ya kashe shi kawai don ya huce haushin kiran mahaifiyarsa da ƴarta'adda da yayi. Shi ba korarsa ne yafi ɓata masa rai ba, kawai cin mutuncin mahaifiyarsa da aka yi ne yake ƙona masa rai. To wai wanne munafikin ne ma ya ganni lokacin da na shigo da su Anas garin nan? har yayi min sharrin zina, a zuciyarsa ya ƙudiri aniyar zai yi bincike ya gano kowane, idan kuwa ya gano shi sai ya keta masa rigar mutunci kafin ya bar garin. Ya saƙa wannan ya kwance da haka har ya ƙaraso gida, yana shiga ya tarar da Rahila (Ummu Nisreen) sai faman zarya take yi a tsakar gidan, ta kasa zaune ta kasa tsaye, tana ganin Abu Nisreen ta yi ajiyar zuciya. Tambayar shi ta shiga yi, me ya faru ake kiran shi a gidan megari? bai yi mata magana ba, ya kama hannunta suka je wata tabarma da take shimfiɗe suka zauna, Anas ma ya zo ya zauna ya zuba tagumi gabanshi sai faman faɗuwa yake yi, kamar ana daka shi da taɓarya, yana bayar da wani sautin duf!duf!!duf!!! Addu'a yake yi Allah yasa ba akansu bane me gari ya kira Aisar, shi damuwarsa ɗaya idan suka bar wajen bai san inda za su je su zauna ba, cikin aminci da kwanciyar hankali. Shi a nasa tunanin ko'ina ƴanta'adda ne, duk inda ya je sai sun gan su sun hallakasu gaba ɗaya, ballantana kuma Inna tace suna nemanta saboda ta yiwa ogansu rauni. Shi yasa ko da wasa ba ya son su bar wannan ɗan garin da Allah ya jefo su ta hannun Abu Nisreen. Shiru ne ya wanzu na ɗan lokaci, shi Abu Nisreen yayi shiru yana tunanin ta yadda zai faɗawa matarsa abinda yake faruwa ba tare da hankalinta ya tashi ba, gaba ɗaya ya rasa yadda zai yi ya faɗa mata an kore shi daga garin, kan shi ya kulle sosai, ya rasa yadda zai yi. Ita kuma Ummu Nisreen ta yi shiru tana sauraron ta ji abinda mijin nata zai faɗa mata, gani ta yi yayi shiru ya ƙi magana sai faman tunani yake yi, magana ta fara yi masa amma sam bai jiyo muryarta ba ballantana ta saka ran zai amsa mata, saboda ya tafi can wata duniya daban da wacce muke ciki(wato duniyar tunani). Gani ta yi gaba ɗaya hankalinsa da nutsuwarsa basa tare da shi, sai ta haɗa hannuwanta waje ɗaya ta tafa, firgigit! ya dawo daga duniyar tunanin da ya tafi, ya hau sosa kai alamun rashin gaskiya. Kallon shi kawai take yi kamar tana son gano wani abu game da shi, amma ta gagara hakan, marairaice murya ta yi tace "Haba Abu Nisreen me yasa kake son ɓoye mini damuwarka ne? Bayan ka san indai ka faɗa mini zan san yadda zan shawo kan matsalar? Shafa kai yayi yace "wallahi Ummu Nisreen kaina ya kulle ne gaba ɗaya, me gari ne yace da ni gobe da safe na mayar da su Anas inda na tsinto su, ko kuma na bar garin gaba ɗaya. A firgice Anas ya dubi Aisar ya saka kuka mai sauti, ya taso daga inda yake ya zo har gaban Aisar ya tsugunna yace "don Allah don Annabi Abba karka mayar da mu wani wajen, wallahi idan muka bar nan kashemu za'a yi, don Allah ka taimaka mana. Kama kafaɗunshi Anas yayi yace "taso ka zauna anan kusa da ni babu musu kuwa ya taso ya zauna, sannan Aisar ya dube shi yace "ka kwantar da hankalinka Anas ban zaɓi na mayar da ku inda na tsinto ku ba hasali ma na zaɓi na bar garin nan gaba ɗaya duk don saboda ku. Kallon Ummu Nisreen yayi yace "haƙiƙa a tarihin rayuwata ba a taɓa ci mini mutunci ba kamar yau ɗin nan a fadar megari, sun kira ni mazinaci, kuma sun kira mahaifiyata da ƴarta'adda sai ya fashe da kuka. Nan take ita ma Ummu Nisreen ta fashe da kukan, haka shi ya karyarwa da Anas zuciya shi ma ya saka kukan, sun daɗe suna yi aka rasa me rarrashin wani a cikinsu. Shi Abu Nisreen abinda ya saka shi kuka, tozarta mahaifiyarshi da aka yi ne kuma bai samu dama ya rama ba, shi yasa zuciyarsa take yi masa wani irin zafi kamar ana ƙona masa ita da garwashi wuta. ita kuma Ummu Nisreen abinda ya sakata kuka, tunanin halin da za su shiga take yayin da suka bar garin, don dole ne ta bi mijinta duk inda zai shiga a duniyar nan, domin bata da kamarsa a tarihin rayuwarta, domin shine ya zamar mata uwa da uba, duk da mahaifinta yana raye amma bata samu wani gata da kulawa daga wajensa ba, kamar yadda kowanne ɗa yake samu daga wajen ubansa. Mahaifiyarta kuwa ta daɗe da mutuwa, don bata fi shekara biyar ba a duniya Allah ya karɓi ran mahaifiyartata. Tun tasowarta ba ta san wani abu wai shi gata ba, sai da Allah ya haɗa ta da Aisar ya rinƙa bata kulawa a matsayinta na matarshi, duk da ba wani soyayya suka yi ba, an aura masa ita ne, kawai don a ƙuntatawa rayuwarta, bisa umarnin matar babanta, sai ga shi kuma cikin ikon Allah da tayi haƙuri sai mijinnata yake tsananin jin tausayinta fiye da kowa, kuma yake tallafawa rayuwarta fiye da yanda take tunani. Saɓanin ƴaƴan Goggo (wato matar babanta) da aka aura musu waɗanda suke so, sai labari ya sha bambam domin kullum su a cikin tashin hankali suke, kullum suna hanƴar gida kai ƙarar mazajensu ko kuma su yo yaji, babu wanda zai zo bikonsu sai dai su gaji don kansu su koma....... To be continue......... Comment and share _*Hussaini Yusuf ✍🏻*_ [12/9, 4:35 PM] ~HUSSAIN YUSUF~: *🫐🫐ANAS MALEEK🫐🫐* *Story and writing by:* HUSSAINI YUSUF *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *_______________________________* *Page 21/22* Ita kuwa Ummu Nisreen tana zaune a gidanta lafiya, haka yasa suka ɗauki karan tsana suka ɗora mata, sai su zo har gida su zazzageta tas idan ta yi magana su yi mata ɗan banzan duka su tafi, amma ko da wasa ba ta taɓa faɗawa Aisar ba. Lokaci zuwa lokaci sai sun zo sun yi mata rashin mutunci, a cewarsu asiri ta yi musu shi yasa suka ƙi zaman aure, ita kuma da suke zaton ba zata zauna a gidan auren nata ba, sai ta basu mamaki, take zaune da mijinta lafiya ba ta taɓa zuwa gida yaji ba, ballantana ma har ya kai ga an saketa. Shi yasa suka sakata a gaba banda hassada da ƙyashi, babu abinda yake tsakaninsu. Wata rana suka zo suka tarar da ita, tana wanke-wanke suna shigowa babu wacce ta yi mata magana a cikinsu kawai suka hau ta da duka babu sassauci balle tausayi, ihu take yi tana neman taimako amma saboda zalunci suka rufe mata baki ko ta yi ihun babu wanda zai ji ballantana a kawo mata ɗauki. A haka Aisar ya shigo gidan ya tarar da su, ai kuwa bai tsaya wani jinkiri ba, ya koma ya rufo gidan ya ɗauko wani ƙaton icce ya rinƙa jibgarsu suna ihu suna bashi haƙuri, amma saboda ransa ya riga ya ɓaci ko sauraronsu ba yayi kawai dukansu yake. Sosai jama'a suka taru a ƙofar gidan, sun rasa ta yadda za su shiga domin su taimaka musu, da ƙyar dai wasu suka ɗare katangar gidan suka haura sannan suka zare sakatar gidan sauran jama'ar suka shigo da ƙƴar jama'a suka ƙwace su daga hannunsa. Aikuwa ana ƙwatarsu suka fice daga gidan a guje, suna ihu da kururuwa, saboda ba ƙaramin wahala suka sha a wajen Aisar ba. Tun daga ranar ba su ƙara zuwa gidan Aisar ba, kuma ita ma Rahila ba ta ƙara zuwa gidansu ba, saboda ko ta je ta san sai sun rama dukan da mijinta yayi musu, shi yasa tayi zamanta a gidanta bata damu da zuwa gidansu ba.Ko mahaifinsu idan hanƴa ta biyo da shi, yana zuwa su gaisa sannan ya wuce, saboda ba ƙaramin daɗi yake ji ba da yaga Rahila tayi zamanta gidan mijinta, duk da ba zaɓinta aka bata ba amma a haka ta yi haƙuri ta zauna, tana yiwa mijinta biyayya dai-dai gwargwado. Haka ne yasa take tsananin ƙaunar Aisar fiye da komai, ko mahaifinta bata yi masa son da take yiwa Aisar, domin kuwa Aisar ba baya bane wajen iya soyayya da tarairaya, duk abinda take so ya sani. Yana iya ƙoƙarinsa wajen sauke nauyinta a wuyansa, bai rageta da komai ba na rayuwa shi yasa take jin bazata iya rabuwa da shi ba, sai dai idan mutuwa ce ta raba su, ko kuma shi yace baya sonta. Don haka ta ɗauki alƙawari a cikin ranta duk inda Aisar zai shiga a duniyar nan indai ya amince tare zasu shiga. Kallonta Aisar yayi ya ga tayi shiru, gaba ɗaya bata tare da nutsuwarta, kama hannuwanta yayi firgigit ta dawo daga duniyar tunanin da ta tafi, kallonta Aisar yake yi kamar yana son gano wani abu dangane da ita. Cikin sanƴin murya yace "Ummu Nisreen ki cire duk wani tunani a cikin ranki, Allah yana tare da mu, kuma insha Allahu ina ji a jikina barin garin nan shine yafi zama alkhairi a gare mu. Yanzu ki tashi ki gyarawa Anas wancan ɗakin ya kwanta, da safe zan je na sanar da su Iya abinda yake faruwa, daga nan sai mu samu mafita mu san garin da ya kamata mu koma. Da kyar ya samu ya rarrashi Anas yayi shiru daga kukan da yake yi, da kansa ya raka shi har cikin ɗakinsa ya kwanta, sai da ya tabbatar yayi barci sannan ya bar ɗakin ya nufi na Ummu Nisreen. Sosai ya mantar da ita duk wata damuwa da irin soyayyar da ya nuna mata a cikin wannan daren, sai wajen ƙarfe uku na dare sannan ya barta ta huta, shi sai da yayi wanka sannan ya zo ya kwanta. Ita kuwa Ummu Nisrin barci ne yayi gaba da ita, sai da safe ta yi nata wankan. 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 Washe gari da sassafe Aisar ya fita daga gidan, ya nufi gidan su Inna, domin ya sanar da su abinda yake faruwa. Yana shiga cikin gidan ya ga babu kowa a tsakar gidan, ɗakin Iya ya nufa yana shiga ya tarar da ita akan sallaya tana lazimi, zaunawa yayi akan wata tsohuwar kujera, ya jira har ta gama laziminta ta shafa addu'a. Juyowa tayi ta kalli inda Aisar yake zaune, tace "lafiya Aisaru na gan ka da sassafen nan?" ji tayi yayi shiru kiran sunan shi ta ƙara yi "Aisaru! Aisaru!!" firgigit ya dawo hayyacinsa, yana sosa kai yana wani murmushi domin ya ɓoye damuwar shi, gudun kada Iya ta fahimci halin da yake ciki ita ma hankalinta ya tashi. "Aisaru wai me yake faruwa da kai ne? ina ta yi maka magana amma hankalinka baya tare da kai" lafiya kuwa? Zaunawa yayi kusa da Iya fuskarsa cike da damuwa ya gaishe da ita, amsawa tayi tana tambayarsa abinda yake faruwa, domin ta matsu ta ji abinda ya saka Aisar cikin wannan damuwar da bata saba ganin shi a ciki ba. Labarin abinda ya faru jiya da daddare a gidan me gari ya baiwa Iya, bai rage mata komai ba. Sosai ta shiga cikin tashin hankali, nan da nan ta nemi nutsuwarta ta rasa. Tunani ta fara yi a cikin ranta, dama mutanen garin nan a matsayin ƴarta'adda suke ɗaukarta duk tsawon shekarun da ta ɗauka a garin, ashe su mutanen garin a banza suke ganinta? Ashe duk mutanen da take mu'amala da su, a ƴarta'adda suke ɗaukarta? ita kuwa ya zata yi da rayuwarta? ko da me gari bai ce su bar garin ba, ya zama dole su bar shi. Ko don su tsira da mutuncinsu, duban Aisar ta yi tace "Aisaru yanzu je ka kira min Innar su Anas na sanar da ita abinda yake faruwa..... Tashi yayi ya fice daga ɗakin, yana shiga ɗakin ya ganta a zaune tana jan carbi, har ƙasa ya durƙusa ya gaisar da ita, sannan ya sanar da ita Iya tana son ganinta a ɗakinta yanzu...... Ba ta wani ɓata lokaci ba ta biyo shi a baya har ɗakin Iya, basu ɓoye mata komai ba, sosai Inna ta shiga tashin hankali, fashewa da kuka ta yi tana neman yafiyar su Iya da Aisar akan baƙin jinin da suka jawo musu ita da ƴaƴanta..... Aisar bai baro gidan ba, sai da suka tsayar da garin da yakamata su koma, Inna ce tace "Kawai su koma Kano domin can yafi daɗin zama da kwanciyar hankali, duk da tarin Jama'ar garin amma hankalinsu a kwance yake, domin Baffa lokacin da yake da rai yana zuwa har can ya siyo kaya yazo nan ƙauyensu ya siyar....... Babu musu Aisar da Iya suka amince da shawarar Inna, domin shi ma Aisar yana jin labarin garin duk da bai taɓa zuwa ba amma yaji hankalinsa ya kwanta da garin na Kano......... Tashi Aisar yayi yace "bari yaje ya sanar da Ummu Nisrin inda suka yanke za su koma, sannan ya je ya siyar da dabbobinsu don su tanadi guzuri da kuma kuɗin da zaiyi sana'a idan sun koma can Kanon........ Tun daga nesa ya hango mahaifin matarsa yana ta faman zuba masifa shi kaɗai, kamar wani mahaukaci sai faman zarya yake yi a ƙofar gidan ya je nan ya je can, kana kallon shi zaka gano rashin nutsuwa a tattare da shi, yana ganin Aisar ya nufo gidan nutsuwa yayi ya ƙurawa Aisar ɗin idanu yana cewa "Alhamdulillahi.......... Tsayawa yayi har Aisar ɗin ya ƙaraso kusa da shi, har ƙasa ya durƙusa ya gaishe shi amma ko kallon inda Aisar ɗin yake bai yi ba, maimakon ya amsa gaisuwar sai ya fara masifa yana cewa...... Aisaru dole ne ka sakar min ƴata Rahila, babu inda ka isa ka je da ita, ban yarda ba, yau da safen nan naje fadar me gari naji yana cewa wai an koreka daga garin nan akan wasu shegun yara da ka tsinto, kuma ana zargin mahaifiyarka da ta'addanci, ina jin haka ban tsaya wani jinkiri ba na zo nan domin ka bai wa ƴata takardar sallamarta in saka ta a gaba mu tafi saboda kar ku je can wajen ƴanta'adda da ita, ita ma ta koyi ta'addancin don ni insha Allahu ba zan taɓa haifar ƴanta'adda ba a cikin zuri'ata.......... Miƙewa tsaye Aisar yayi yace "Baba kai ne kaɗai zaka zo har ƙofar gidana kayi min irin wannan cin mutuncin na ƙyale ka ka tafi lafiya ba tare da nayi maka wani abun ba......... Ka sani muddin Rahilat ta yarda zata bi ni duk inda za ni, babu wanda ya isa ya hanata bi na, yanzu Aisar rashin kunƴarka har ya kai ina faɗa kana faɗa a matsayina na surukinka? To muddin ka ce bazaka sakar min ƴata ba, zaka ga waɗanda zan turo su tilasta dole ka bata takardarta ko kuma su yi maka lahanin da baza ka moru ba ballantana kuma ka samu ƙwarin gwiwar barin garin........ Sannan ya juya ya tafi a fusace, ya bar Aisar a tsaye yana ta mamakin yadda mutanen garin nan suka juya musu baya karo ɗaya, dole akwai munafikin da ya haɗa duk wannan abin, kuma ya zama dole na nemo kowaye kafin na bar garin nan Aisar ya faɗa a cikin zuciyarsa, sannan ya nufi cikin gidan nasa.............. To be continue.......... Comment and share HUSSAIN YUSUF [12/9, 4:35 PM] ~HUSSAIN YUSUF~: *🫐🫐 ANAS MALEEK🫐🫐* *Story and writing by:* Hussaini Yusuf *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *_________________________________* *Page 23/24* Yana shiga ya tarar da Rahila (Ummu Nisri) a zaune ta zuba tagumi, ko sallamar da yayi bata ji ba, ballantana ta amsa zuwa yayi kusa da ita ya tsugunna a gabanta, ya sauke mata hannuwanta daga haɓarta....... Murmushi ta sakar masa amma kana gani ka san yaƙe ne kawai ta yi don bai kai cikin zuciyarta ba, shi ma zama yayi a kusa da ita yace "Haba farin cikin rayuwata, annurin zuciyata wacce nake kalla a koda yaushe na ji farinciki marar misaltuwa, menene ya saka ki a cikin wannan damuwar har nayi sallama ba kiji ni ba.........? Murmushi ta sakar masa tana ƙoƙarin ɓoye damuwarta tace "Babu komai mijina kawai ina tunanin inda zamu koma ne, ba mu san kowa ba, kuma babu wanda ya san mu" karkaɗa mata kai yayi yace "Ba wannan ne ya saka ki cikin damuwa ba, ki faɗa min gaskiya kin ji abinda mahaifinki ya faɗa ko........? Fashewa ta yi da kuka cikin muryar kukan take cewa "wallahi ko da wasa bana son rabuwa da kai mijina, ko a mafarki bana tunanin rabuwar mu, don Allah karka tafi ka bar ni a garin nan, domin baƙin ciki ne zai kashe ni, ba zan taɓa iya rayuwa babu kai ba, don Allah ka taimaka karka ɗauki zantukan mahaifina, domin umarnin Goggo ne ita ce ta saka shi ya zo yace bai yarda na bika ba. Domin ta samu damar da zata muzgunawa rayuwata, son ranta........... Kama hannunta Aisar yayi ya ja ta cikin ɗaki, ita kuwa sai bin shi take yi, kamar raƙumi da akala, bakin gado ya zauna ita ma ta zauna kusa da shi, ido cikin ido suka ƙurawa juna idanu, sun daɗe a haka kafin Aisar yayi ƙarfin halin cewa......... Rahila kin san ina sonki ko? shiru tayi ta ƙura masa idanu, kuma kema kina so na, anan ma shiru tayi tana kallonsa ta kasa furta koda kalma ɗaya cigaba yayi da cewa......... Tunda har kina sona to ki saka a ranki babu wanda ya isa ya rabamu, sai mutuwa ki cire duk wata damuwa daga cikin ranki na fargaban rabuwa da ni, domin duk inda zani tare za mu tafi kaf faɗin garin nan gaba ɗaya babu wanda ya isa ya hana ni tafiya tare da ke tunda har kin amince za ki bini mu tafi........... Jiyowa suka yi daga waje ana dukan ƙyauren gidan kamar za'a karya shi, sakin hannun Rahilat Aisar yayi ya fito da sauri, ganin su yayi a tsaitsaye a tsakar gidan, hannunsu ɗauke da makamai........ Suna ganin shi ya fito kallon rainin wayo wani daga cikinsu yayi masa yace "Sarkin dawa Aisar an turo mu ka bamu matarka da takardarta a hannu mu tafi da ita, idan kuma kayi taurin kai ance muyi maka lahani idan ya kama ma mu kashe ka mu tafi da ita......... Fashewa da kuka Ummu Nisrin ta yi, ta lafe a bayan Aisar jikinta ban da tsuma babu abinda yake yi...... Cike da ƙwarin gwiwa Aisar ya dube su yace "Ku je ku faɗa wa wanda ya turo ku, kuce masa ya rasa waɗanda zai turo su tafi da matata sai ku? Kuyi maza ku faɗo masa, na fi ƙarfin nayi faɗa da ku sai dai ya turo na sama da ku....... Maganar ta yiwa shugaban ƴan'daban zafi, cikin fushi ya dubi wani daga cikin yaransa yace " zaki maza ka je ka gwada masa ko mu su waye ya daina raina mu"........ Cikin fushi wanda aka kira da zaki ya nufo Aisar da mugun nufi a cikin ransa, yana zuwa ya ɗaga wata ƙatuwar adda zai sari Aisar a kafaɗa, cikin zafin nama Aisar ya tare saran sannan ya kama hannun da ya riƙe addar ya murɗa ji kake ƙarararas! hannun ya karye wurgar da shi yayi a gefe yana ta faman ihu da ƙaraji na raɗaɗin karayar da ya samu a hannu..... Sauran ƴan'dabar tsorata suka yi, suka tsugunna suna baiwa Aisar haƙuri, ogansu ne kawai ya ƙi ja da baya, duban Aisar yayi yace "Ni nan da ka ganni ba zan taɓa tafiya ba sai da Rahila, kuma an yi min alƙawarin indai ka sake ta ni za'a aurawa ita, ta zama matata ta har abada..... Cikin fushi Rahila ta dube shi tace "ƙarya kake wallahi kai baka isa na zama matarka ba, sai ko idan bana numfashi, sannan sai ka auri gawata..... Cikin fushi ya taho wai zai doke Rahila, riƙe shi Aisar yayi yace "Ka yi kuskure da har ka yarda ka kawo kanka waje na, kuma wannan furucin da kayi kace Rahila ta zama matarka to sai ka yi nadamar yinsa..... Yana gama faɗar haka ya dube shi ya wanka masa wani gigitaccen mari a fuska, take kuwa haƙorinsa ya fito daga bakinsa ya faɗi can waje ɗaya, amma duk da haka Aisar bai bar shi ba ya kwarfe shi ya faɗi ƙasa ji kake tim wata ƙara ya saki, kana ji ka san ta irin wanda ya sha wahalar nan ne...... Ɗaga ƙafa yayi zai taka shi, da ƙyar ya iya ɗaga hannunsa alamun Aisar yayi haƙuri fasa taka shi yayi, ya dubi sauran ƴan'daban, duk sun tsure sai muzurai suke yi jikinsu yana rawa, a fusace Aisar ya dube su yace " waye ya turo ku ku raba ni da matata.......? Cikin muryar tsoro suka ce "Goggo ce da me gari da malam Inusa (mahaifin Rahila) suka ce kar mu dawo sai da Rahila, kuma sun yi wa Ƙaura alƙawarin indai ya dawo da ita za su aura masa ita, dama tsohuwar budurwar shi ce ada....... Kaiiii! Aisar ya daka musu tsawa yace "yi min shiru ko na yanke harshenka, wawa kawai yanzun nan ku je ku shaida musu tare da Rahila zan bar garin nan, tun da har ta yarda zata bini mu tafi babu wanda ya isa ya hanani tafiya da ita....... Tashi suka yi jikinsu yana tsuma, za su bar wajen, dakatar da su yayi yace "ku zo ku ɗauke waɗannan banzayen ku tafi da su, ko kuma anan za ku bar min su.......? Cikin sanƴin jiki suka dawo suka ɗauke su ranga-ranga rai a hannun Allah suka fita da su banda huci babu abinda Aisar yake yi.. Suna fita Aisar ya dubi Rahila yace "ki fara haɗa mana kayanmu yau zamu bar garin nan, yanzu zan je na faɗawa su Iya suma su shirya sai mu tafi domin na ga kawai ana son hallakamu a garin nan yafi kyau mu bar shi cikin lumana tun kafin mu zo muna nadamar ƙin barinsa da wuri..... Fita yayi daga gidan ya nufi gidan Iya domin ya faɗa musu su shirya, yana cikin tafiya a kan hanƴa tunani kala-kala sun cika masa ransa, ya rasa yadda zai yi da rayuwarsa, a ransa yake ji barin garin shi yafi alkhairi fiye da zama a cikinsa.... Kamar daga sama ya ji ance "Aisar sannan aka bushe da wata mahaukaciyar dariya, waigawa yayi domin ya ga me dariyar wani mutum ya gani, yan nufo shi abokin zuwa farautarsa ne, ba tun yanzu yake takun saƙa da Aisar ba, kullum burinsa shine ya ga Aisar a ƙasa, ko kuma ya rushe masa zaman lafiya a garin.... Yana ƙarasowa kusa da Aisar ɗin, sai ya bushe da wata dariya, ya dafa kafaɗar Aisar yace "Aisar a zatonka waye ya haɗa maka wannan munafurcin aka tsane ku a garin nan? Girgiza kai Aisar yayi yace ban san waye ba, amma kafin na bar garin nan ina son na gano ko waye, domin na ɗauki fansar abinda yayi min.... Bushewa da dariya yayi yace "Aisar kenan ban taɓa ganin kasawa a tare da kai ba, kullum zuciyarka a dake take, irin zuciyar mazan jiya ce da kai Aisar, ka sani ba kowane ya haɗa maka wannan cakwakiyar ba, face ni ɗin nan da kake gani a tsaye a gabanka, kuma kafin ka bar garin nan sai na haɗa maka wata cakwakiyar da zata saka mutanen garin nan suyi maka bore kafin ka.......Ji kake fauuuu! cikin fushi Aisar ya dunƙule hannunsa da iyakar ƙarfinsa ya daki bakin mutumin....... Take kuwa haƙorinsa yayo fitar burgu daga bakinsa, jini ya cika masa baki, amma haka bai sa Aisar ya ƙyale shi ba, ya hau shi da duka da bugu ya rinƙa tattaka ruwan cikinsa, tun yana ihu yana neman taimako, har ya daina motsi sannan Aisar ya ja shi cikin wata duhuwa ya wurgar da shi yayi tafiyarsa abinsa..... Babu wanda ya ga lokacin da yayi masa wannan abin domin hanyar ba mutane ne suke binta sosai ba, shi yasa tun lokacin da ya fara dukansa babu wanda ya zo wajen ballantana ya cece shi daga wajen Aisar ɗin..... Sauri kawai Aisar yake domin ya isa gidan Iya, zuciyarsa fes ya ɗauki fansa akan wanda ya haɗa shi da ƴan garin, ko kaɗan bai yi nadamar abinda ya aikata ba domin ya tsani munafiki, tsana ba ta wasa ba, da wannan tunanin ya ƙaraso gidan Iya, shiga yayi ya gaishe su bai jira sun amsa ba yace " Iya kuyi sauri ku haɗa kayanku yanzun nan domin so nake mu bar garin nan kafin wani abun ya faru da mu..... Tambayar shi abinda ya faru Iya ta yi, cike da zaƙuwa yace "Iya yanzu ba mu da lokaci, ku dai kawai ku shirya mu tafi, idan mun samu nutsuwa zan faɗa muku komai.... Nan take kuwa suka hau shiri, dama ba wasu kayane masu yawa da su ba, nan da nan suka gama shirinsu suka biyo bayan Aisar suka fice daga gidan.... Gidan Aisar suka nufa, akan hanƴarsu ta komawa ne suka haɗu da wani abokin Aisar a firgice ya dubi Aisar yace "Yawwa Aisar dama neman ka nake yi ruwa a jallo, kuyi sauri ku bar garin nan domin naga matasa yaran Ɗanliti sai wasa makamansu suke yi wai me garine da mahaifin matarka Rahila suka turo su, su hallakaka du ɗauki matarka su tafi da ita, ba ka ga shirin da suke yi ba, wallahi so suke su kashe ka a cewarsu kai ɗanta'adda ne.... Fashewa da kuka Iya da Inna suka yi, shi kuwa Aisar ransa ne ya ɓaci matuƙa, ba don yana son ya tseratar da rayuwar su Iya ba, da sai ya tsaya ya koyawa me gari da sauran mutanen garin hankali. Cikin sauri ya ke tafiya su Iya suna bin shi a baya, su Nisreen da Safna ma, su har gudu-gudu sauri-sauri suke yi, hannuwansu sarƙe da na juna, addu'a yake yi a cikin ransa Allah yasa ba su je gidansa ba. ******** Farkawa yayi daga dogon suman da shafe awa ɗaya yana yi, ganin shi yayi a cikin ciyawa a kwance, an jefar da shi kamar mushe da sauri ya tashi zaune, nan take ya rinƙa tuno abinda ya faru tsakaninsa da Aisar, shafa bakinsa yayi yaji jini, hawayen baƙinciki ne ya zubo masa kamar an tsikare shi ya miƙe tsaye ya kurma wani uban ihu. Ihuuuuuuuu! Aisar gani nan bisa kan ka, falfalawa yayi da gudun tsiya cikin garin domin ya je ya shirya yaransa su yi wa Aisar kisan wulaƙanci...... To be continue............ Comment and share Hussain Yusuf [12/9, 4:36 PM] ~HUSSAIN YUSUF~: *ANAS MALEEK* *NA* *HUSSAIN YUSUF* *______________________________* *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *_______________________________* *Page 25/26* Shi kuwa Aisar yana zuwa gida ya tarar har Rahila ta gama haɗa musu kayansu, ita da Anas suna tsaye suna jiransa. Yana shigowa ya gansu, yace su zo sai su biya ta gidan su Iya su tafi, lokacin wani abokinsa ya shigo gidan a firgice. Ya dubi Aisar yace "Alhamdulillahi Aisar dama kai nake nema, kuyi sauri ku bar garin nan tun kafin a hallaka ku," kallon shi Aisar yayi yace "me yake faruwa ne, a firgice yace "wallahi Aisar ga su can a fadar me gari sai faman wasa makamansu suke yi wai za su zo su yaƙe ka tun da kai ɗanta'adda ne, don haka kuyi sauri ku fita daga garin nan, tun kafin su zo su iske ka suyi maka wata illar." Aisar nunawa yayi ko a jikinsa, Rahila da Anas kuwa ban da kuka babu abinda suke yi, kallon abokin nasa Aisar yayi yace "Mu'az zan baka amana idan har baza ka ci mini ba, cike da tausayawa Mu'az yace "Aisar bani duk amanar da zaka ba ni insha Allah zan riƙe maka ita hannu biyu." "Alhamdulillah" shine abin da Aisar yace sannan ya dubi Mu'az yace ga dabbobi na nan, don Allah ka ɗauke su ka mayar da su gidanka ka cigaba da kula min da su, har lokacin da zan buƙace su, idan kuma baza ka iya kula min da su ba, to ka kai min su kasuwa, idan na koma inda za ni sai muyi waya. Haka yace "to Aisar ni dai na karɓi wannan amanar taka hannu biyu," saboda haka yanzu zan kunce su na mayar da su gidana zan cigaba da kula maka da su insha Allah har zuwa lokacin da zaka buƙace su daga hannuna, godiya sosai Aisar yayi wa Mu'@z sannan ya ja hannun Anas da Rahila suka fita daga gidan suka nufi gidan su Iya. Suna zuwa suka tarar su ma har sun gama haɗa kayansu, nan da nan suka fito suka bi wata siririyar hanƴa, wacce zata sada su da bakin titi. Tafiyar minti talatin suka yi sai ga su, a bakin titi kasancewar titin motoci basa binsa sosai, sai faman jiran mota suke yi ta zo amma shiru har suka shafe awa guda suna jiran mota amma babu wacce ta zo zata wuce, sai wata guda ɗaya ita ma kaya ne ta ɗebo saboda haka babu damar shigarta. A cikin garin kuwa zugar ƴan'daba ne hannunsu riƙe da mugayen makamai, sun nufo gidan su Aisar sai faman wasa kansu suke yi, suna zuwa suka daki ƙyauren gidan da sandunan hannunsa nan take kuwa ƙyauren ya kakkarye, suka kutsa kansu cikin gidan, suna shiga suka tarar babu kowa, sai da suka lalube kowanne ɗaki na cikin gidan, amma ko motsin su Aisar basu ji ba. Saboda haka suka fito suka nufi gidan Iya, nan ma dai ba su tarar da kowa ba, ba su tsaya wani ɓata lokaci ba, suka nufi bakin titi don su riski Aisar ɗin a can. Har yanzu shiru babu motar da ta zo wuce wa, har sun ga ji da tsaiwa su Iya sun tsugunna, daga tsugunne Inna ta hango zugar ƴandaba sun nufo inda suke hannuwansu riƙe da makama. A firgice ta muƙe tsaye ta nunowa Iya su, Aisar ma yana waigowa idanunsa suka yi tozali da su, a firgice yace "su Iya su tashi su bar wajen. Har sun tashi za su gudu, sai suka hango wata mota ƙirar golf ta nufo inda suke, tun daga nesa Aisar ya rinƙa ɗaga wa motar hannu, su kuma ƴan'daban koda suka hango motar tana niyyar tsayawa domin ta ɗauki su Aisar, sai suka rinƙa gudu domin su tarar da su kafin su hau motar. Me motar yana zuwa dai-dai su Aisar sai ya ja burki ya tsaya, ya dubi su Aisar yace "Ina zaku je ne?" Cike da zaƙuwa Aisar yace "cikin Jalingo zaka kai mu" murmushi me motar yayi yace gaskiya kuna da sa'a, dama can na nufa yanzu kuyi sauri ku shigo. Da sauri Aisar ya buɗe motar, sai da ya tabbatar kowa ya shiga. Sannan shi ma ya shiga gaba, me motar kuwa ya ja suka tafi, ƴan'daban kuwa dai-dai lokacin da motar ta tashi suka ƙaraso wajen, wasu daga cikinsu suka ɗauki duwatsu, suka rinƙa jifan motar, amma ko kusa da motar jifan bai kai ba, na gaba yayi gaba na baya........Gudu sosai direban yake yi da su Aisar, kallon Aisar yayi yace "daga Jalingo ina kuma zaku nufa?" Murmushi Aisar ya saki yace "za mu nemi motar Kano ne, don na ji an ce can ɗin yafi daɗin zama shi yasa na ɗebo iyalina zamu koma can da zama." Murmushi direban ya saki yace "gaskiya ne ka iya zaɓan wajen da zaka koma, don Kano indai ka tashi ka nema to insha Allahu zaka samu, yanzu a nawa zan kai ku can Kano ɗin, saboda nima haifaffen Kano ne, yanzu da ka ganni a Taraba, wasu fasinjoji na kawo, shine na shigo nan yankin Mambila domin na wasa idanuna, sai kuma Allah ya haɗa ni da ku, ka ga yanzu na huta zuwa tasha in jira lodi. Shi ma Aisar ɗan murmusawa yayi yace "Yanzu kenan kana nufin har can Kanon zaka kai mu?" Gyaɗa masa kai direban yayi kafin yace "ƙwarai da gaske ma kuwa, don yanzu ma can na nufa da ku. Hamdala Aisar yayi, sannan yace "to direba kana ganin a kamar nawa zaka kai mu can Kano ɗin?" Ko kallon Aisar ɗin bai yi ba, yace "ni ko nawa ku ka bani Allah yasa musu albarka" dubu biyar Aisar ya miƙa masa, karɓa yayi har da godiya. Ana kiraye-kirayen sallar magriba su Aisar suka iso Kano, ba su san inda za su nufa ba, saboda haka direban da ya ga haka, sai ya ji tausayinsu kai tsaye ya yace bari ya kai su gidansa, da safe sai ya nemo musu inda za su zauna.Godiya sosai Aisar da su Iya suka yi masa, saboda halin kirkin da ya nuna musu, a unguwar Darmanawa gidansa yake, saboda kai tsaye can ya nufa da su.Lokacin da suka isa, sai ya tsayar da motar a ƙofar wani gida, ɗan madaidaici, sannan ya fito su ma gaba ɗayansu suka fito daga cikin motar. Tsayar da su yayi a ƙofar gidan, sannan shi ya shige ciki domin yayi musu iso a wajen matarsa, yana shiga da sallama da gudu wata yarinƴa da ba tafi shekara biyar ba, ta fito ta tarye shi tare da rungume shi tana kiran ga Baba ga Baba, shi ma rungume ta yayi, tare da ɗaga ta sama yana dariyar farinciki, ita ma yarinyar sai faman dariyar take yi.Dai-dai lokacin wata tsohuwa ta fito daga wani ɗaki tana cewa "Aah Sa'idu an dawo kenan?" ajiye yarinyar yayi ya durƙusa har ƙasa, ya gaisheta, lokacin matarsa ta fito da banɗaki, ita ma murmushin ta saki tace "me gida an dawo kenan" shi ma murmushin ya saki cikin sigar zolaya yace "da ban dawo ba zaki ganni ne?" Murmushi kawai ta yi tace "sannu da zuwa amsawa yayi tare da zaunawa" ya dubi tsohuwar nan wacce ko ba'a faɗa maka ba ka san mahaifiyar shi ce, sannan ya dubi matarshi yace "Ammi Husna a tare suka amsa suna mai ƙura masa idanu, ya cigaba da cewa akwai wasu bayin Allah da na ɗauko daga Jalingo, na kawo su nan Kano, za su nemi gida su zauna, to kuma mun iso dare yayi ban ta inda zan fara nema musu gidan ba, shine nace me zai hana na kawo su nan gidan su kwana idan yaso da safe sai na je na nemo musu gidan da za su zauna. Wani kallo Ammi ta watsa masa tace "yanzu kai Sa'idu dama da baƙi ka zo shine ka shigo kamar ba tare da kowa kake ba?" Husna ma cewa tayi me gida me zai hana sai su shiga wancan ɓangaren tun babu kowa a ciki, ka ga kenan ba sai ka tafi wahalar nemo musu gida ba, indai mutanen kirki ne to nan ma ai gida ne. Godiya yayi wa Allah da ya bashi uwa ta gari da mace ta gari, Ammi ce tace "maza ka tashi ka je ka shigo da su, ban da abinka Sa'idu ka san ni dai ba zan ƙi saukar baƙo ba, amma ka tsaya ka bar bayin Allah a waje haka? Tashi yayi ya fita daga gidan, domin ya je ya shigo da su Aisar cikin gidan....... To be continue........ Comment and share _Hussain Yusuf_ [12/9, 4:36 PM] ~HUSSAIN YUSUF~: *ANAS MALEEK* *NA* *HUSSAIN YUSUF* *_______________________________* *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *______________________________* *Page 27/28* Koda ya fito ya iske su a tsaye suna jiransa, murmushi yayi yace "kar ku ga na daɗe don Allah kuyi haƙuri akwai abin da ya tsare ni. "A'a babu komai kar ka damu" Aisar ya faɗa yana mai sakarwa Sa'id murmushi.Koda suka shiga gidan, sai ya nuna musu wani lungu me ɗauke da ɗakuna uku, sai kitchen da banɗaki, nuna musu yayi yace amma ɗakunan sun yi ƙura sai sun gyara. Murmushi Aisar yayi yace "kar ka damu babu komai wallahi zamu gyara." Tashi Sa'id yayi ya fita don ya ba su damar gyara wajen sosai, zuwa yayi ya ga Ammi tana alwala, Husna kuma tana ta fama da hura wuta zata ɗora abinci, da mamaki ya kalleta yace "Husna har yanzu ba ki gama girki ba ne har magriba?" Murmushi ta yi ta kalle shi tace "gani nayi mun yi baƙi shine naga abincin da na dafa ba zai ishe mu ba, shi yasa na sake ɗorawa domin ya isa, murmushin jin daɗi yayi yace "Allah ya saka miki da gidan Aljanna matata, kina son duk abinda nake so haka kuma kina ƙin duk abinda nake ƙi, kuma kullum burinki shine ki gan ni a cikin farin ciki. Rufe fuskarta ta yi da hannayenta, alamun jin kunƴa ɗaukar buta yayi zai shiga banɗaki yace "ta ɗauko bokiti a kai wa baƙin ruwa su yi alwala domin lokacin sallar magriba yayi. Da sauri kuwa ta tashi ta je ta kitchen ɗin su, ta ɗauko wani sabon bokitin Ƙarfe, ta kunna famfo ta tari ruwa, ta haɗa da butoci guda biyu, tare da kofi, ta ɗauka ta nufi wajen su Aisar don ta kai musu su yi alwala. Tana shiga ta tarar da su Ummu nisreen tana shara, su Inna kuma suna fito da kayansu, suna shigar da su cikin ɗakin. Har ƙasa ta tsugunna ta gaishe da su, cike da kulawa suka amsa, fuska a sake sannan tace "ga ruwa nan kuyi alwala" bata jira me za su ce ba ta tashi ta nufi hanƴar fita, sai jero mata godiya su Iya suke yi amma ko kaɗan bata waigo ba balle ta amsa. Inna ce ta dubi Iya tace "gaskiya ashe ba ƙarya ake yi wa mutanen kano ba, suna da karrama baƙo, sosai abin nan da suka yi mana ko wajen ƴan'uwanmu muka zo iyakar abin da za suyi mana kenan. Iya ta ajiye ajiyar zuciya tace "ke dai bari, ai na gama tsinkewa da al'amarin Kanawa ashe da gaske ne da ake cewa mutane ne masu karrama baƙo, ki kalli irin karramawar da aka yi mana. Aisar ne ya ɗauki ɗaya daga cikin butocin, ya ɗebi ruwan da Husna ta kawo musu, ya shiga cikin banɗaki, bayan ya fito ya ɗaura alwala, don lokacin sai kiran sallah ka ke ji a masallatan da suke cikin unguwar. Bayan ya gama alwalar ya nufi ƙofar gida, a hanƴar fita ya haɗu da Sa'id shi ma zai tafi masallacin, murmushi Sa'id yayi da ya ga Aisar yace "kai ma masallacin ka nufa kenan?" Aisar yace "E wallahi can na nufa, duk da ban san ma inda masallacin yake ba. Murmishi Sa'id yayi yace "ka ji ka, ko babu ni idan ka fita ai zaka ga mutane suna tafiya masallacin" dariya suka saka gaba ɗaya sannan suka fice daga gidan, cikin sauri suke tafiya don har an fara tayar da iƙama. Bayan an idar da sallar an yi addu'a an shafa, Aisar tare da Sa'id suka fito daga masallacin, suka nufo gida, da suka zo ƙofar gidan, sai Sa'id yace "Aisar ya tsaya za su yi magana" babu wata jayayya Aisar ya tsaya, nuna musu wani ɗan dakali yayi yace su je su zauna anan. Bayan sun zauna Sa'ad ya dubi Aisar yace "haƙiƙa tun da nake ban taɓa haɗuwa da mutumin da ya shiga raina, nake kuma matuƙar jin tausayinsa fiye da kai ba, ya nuna Aisar sannan ya ci gaba da cewa. "Batun neman inda zaka zauna ka daina, inda na sauke ku na ba ku shi ku zauna, har lokacin da Allah zai hore maka kai ma kayi naka. Aisar ya rasa da bakin da zai gode wa Sa'id, saboda tsananin murna, ji yake kamar Sa'@d ɗin ɗan'uwansa ne na jini. Nan dai suka zauna, suna ta hira har aka gama abinci, Sa'ad da kan shi ya je ya fito musu da abinci, tare suka ci, suka ɗan taɓa hira lokacin har an fara kiran sallar Isha. Bayan an idar da sallar sai suka yi wa junansu sai da safe sannan kowa ya nufi ɓangarensa. Yayin da Aisar ya shiga cikin gidan, sai ya iske su Iya har sun yi barci, a ɗakinsu da suka zaɓa, kai tsaye ɗakin matarsa Rahila ya nufa. Yana shiga ya gan ta akan sallaya tana sallah, samun waje yayi ya zauna ya zuba tagumi. Bayan ta idar da sallar, ta yi addu'ointa ta gama, sai ta juyo ta kalli inda yake, kan shi a sunkuye. Cikin sanƴin murya tace "Abu Nisreen lafiya kuwa ka yi tagumi?" A hankali ya da kanshi ya dube ta yace "wallahi ina tunanin sana'ar da ya kamata na yi ne." Murmushi ta yi tace "ka kwantar da hankalinka gobe idan Allah ya kai mu, sai ka tambayi me gidan nan, sai yayi maka bayanin sana'ar da ya kamata ka yi tun da shi mazaunin garin ne." Sai da yayi tunani sosai, sannan yace "na amince da wannan shawarar ta ki matata insha Allahu zan jarraba na gani." Daga nan suka yi addu'a suka kwanta, sosai suka samu farinciki a wannan daren, sun daɗe suna shan soyayya, sai wajen 2:30am suka samu barci ya ɗauke su. Washe gari da sassafe Aisar ya je ya gaishe da su Inna, sannan ya fita ya je ya gaisar da Ammi, sosai Ammi ta yaba da hankalin Aisar ta ji ya burge ta sosai. Bayan ya gama gaida su, sai ga Sa'ad ya fito daga ɗaki, yana ganin Aisar ya saki murmushi tare da miƙa masa hannu suka yi musabaha. Bayan sun gama gaisawa, Husna ma ta fito daga ɗakinta, ta tsugunna har ƙasa ta gaisar da Aisar, cike da kulawa ya amsa mata, sannan ya juyar a kallonsa kan Sa'ad, yace "ina son idan baza ka damu ba zamu yi magana." Wani ɗan madaidaicin falo Sa'ad ya ja hannun Aisar suka shiga, kowanne ya samu kujera ya zauna, suna masu fuskantar juna, cikin nutsuwa Aisar ya dubi Sa'ad yace "abinda yasa na zaɓi na zauan a Kano shine saboda na ji labarin suna da sana'oi da yawa sannan kuma ga tarin albarka idan ka kasa zaka sayar. Shi yasa nace zan shawarce ka ka bani shawarar sana'ar da ya kamata na fara yi a yanzu, domin muna ɗora maka nauyi, jiya zuwa yau ɗin nan. Murmushi Sa'ad ya saki yace "me yasa zaka faɗi haka? bayan ka san baƙunta ku ka yi, ka ga kuwa dole ne na ciyar da ku domin nauyin ku ya hau kaina, kuma Hausawa sun ce baƙonka Annabinka.Sannan batun sana'ar da yakamata ka fara, idan har kana da jari, to ka zo na kai ka wajen wani abokina, a Wambai yana sayar da kaya gwanjo, sai na haɗa ka da shi ka sara kaje ka shiga cikin kasuwa ka sayar, ita ma wannan sana'ar ta gwanjo, indai ka shigeta a sa'a to akwai albarka sosai a cikinta. Nan take kuwa Aisar yace ya amince da wannan shawarar, ba su bar wajen ba sai da suka tsaya akan suna yin breakfast idan Sa'ad zai fita to tare za su fita ya kai shi wajen abokinsa domin ya fara jarraba sana'ar gwanjo. Sosai Aisar ya rinƙa zubawa Sa'ad godiya, sannan ya sake cewa "yana son kuma ya kai su Anas makarantar boko da Islamiyya, Sa'ad yace "wannan kar ka damu insha Allahu ina da niyyar kai su, amma ka bari sai ranar monday sabida yanzu ka ga ƙarshen sati ne. Sosai Aisar yayi murna nan take kuwa ya tashi ya nufi wajen Rahila (Ummu Nisreen) domin ya shada mata abin da suka tsara shi da Sa'ad mutumin kirki don haka suke kiransa........... To be continue........... Comment and share _Hussain Yusuf_ [12/9, 4:36 PM] ~HUSSAIN YUSUF~: *ANAS MALEEK* *NA* *HUSSAIN YUSUF* *______________________________* *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *_____________________________* *Page 29/30* Yana shiga ya tarar da su gaba ɗayansu a zaune a kan tabarma suna karyawa da shayi da bread, zama yayi yana tambayar su inda suka samu shayi, Iya ce ta bashi amsa da cewa "ai ɗiyar albarkar can ce ta kawo mana, da sassafen nan, kai ma zauna a zuba maka." Samun waje Aisar yayi ya zauna, Rahila ce ta zubo masa shayin, a wani a kofi sannan ya karɓa yana godiya, biredin iri me yanka-yankan nan ne, saboda haka karɓa yayi ya ɗebi guda uku yace sun ishe shi. Nasreen na hango a gefe ita da Safna, sai faman shan shayin suke yi, ko irin surutun nan, da suke yi idan suna cin abinci yau babu shi, ban da santi babu abinda suke zubawa. Sosai suka bai wa kowa dariya a wajen, Anas ma bai saba shan shayi da madara ba, yana jin daɗin shi sosai, amma shi ko kaɗan bai nuna yana santi ba, saboda kar ayi masa dariya, don ya tsani ya ga ana yi masa dariya to yanzu ransa zai ɓaci. Bayan kowa ya gama breakfast ɗin, sai Aisar ya dube su cikin nutsuwa yace "Alhamdulillahi rabbil alamin, dukkan godiya ta tabbata ga Allah (S.W.A) tsira da amincinsa su ƙara tabbata ga Annabi Muhammadu (S.A.W) kamar haka muka fito daga garinmu ana bin mu za'a kashe mu, cikin ikon Allah da ƙudurarsa ya kawo mana Sa'ad ya taimaka mana, sanadinsa yau ga mu dukanmu a cikin farin ciki. Nan ya kwashe labarin yadda suka yi da Aisar da safiyan nan, ya faɗa musu bai rage musu komai ba, ya cigaba da cewa "ni yanzu babu isassun kuɗaɗe a wajena, amma zan fara da waɗanda nake da su, kafin na yiwa Mu'az waya, ya siyar min da dabbobina ya aiko mini da kuɗin sai na ƙara jari, ko ya kuka gani? Rahila ce ta yi gyaran murya tace "ni ina da wasu kuɗi da na siyar da saniyar nan da babata ta bar min, to kuɗin suna nan ko biyar ban taɓa ba, saboda haka bari na je na ɗauko maka su, sai ka haɗa da na wajenka ka fara, Allah ya sanƴa albarka a cikin sana'ar. Nan kowa ya amsa da amin, sannan Iya ma tayi masa addu'ar farawa lafiya, nan dai kowa yayi ta masa addu'a, nan suka zauna suna hira, sosai har lokacin fitar Sa'ad yayi. Da kansa ya shigo ya gaisar da su Inna, sannan yace "shi zai fita aiki, ban da aikin godiya babu abin da su Iya suke yi masa, shi ko sai cewa yake babu komai ai yiwa kaine. A motarsa ya ɗauki Aisar suka nufi kasuwar Wambai, kai tsaye rumfar abokin Sa'ad malam Ɗahiru suka nufa, suna zuwa suka iske shi yana ƙirgar kuɗi sauri yayi ya ɓoye, sannan ya dubi Sa'ad rai a ɓace yace "haba Sa'adu ya zaka shigo mini rumfa kai tsaye baka tsaya nayi maka iso ba?" Murmushi kawai Aisar yayi saboda ya riga ya san halin Malam Ɗahiru akan kuɗi, ba shi da mutunci sai son kuɗi amma kuma ba zai iya siyan wani abun ya saka a cikinsa ba. Haka yasa yake tsoron ƴaƴansa, kada suyi masa sata, shi yasa idan zai yi irgar kuɗi sai ya shige can cikin rumfarsa ya hana kowa shiga. To yau ma irgar kuɗin yake yi, su Aisar suka same shi, a zatonsa wani daga cikin yaransa ne, ya shigo shi yasa ya firgita sosai, da yaga su Sa'ad ne sai ya fasa faɗan da yayi shirin yi amma duk da haka sai da ya sauke wa Sa'ad wani faɗan. Samun waje suka yi suka zauna akan wani benci, sai da ya gama irga kuɗinsa tas, sannan ya saurari su Sa'ad yace me yake tafe da su, nan take Sa'ad yayi masa bayanin komai, take ya yarda malam Ɗahiru akwai son customer, suna nan zaune ya kira wani yaronsa ya kawo wa su Sa'ad ruwa da abinci. Sai da suka ci suka yi masa godiya sannan Sa'ad yayi masa bayanin duk abinda ya kawo su, nan take kuwa ya ɗauko wasu gwanjuna masu yawan gaske ya bai wa Aisar. Godiya Aisar yayi, sannan yace zai nemo masa wajen da zai rinƙa zama yana kasa kayan, ba sai ya fita yawo ba tun da bai san cikin garin sosai ba, bayan Aisar ya karɓi kayan gwanjon sai malam Ɗahiru ya haɗa shi da wani yaronsa ya nuna masa inda zai kasa kayan, kuma yace yaron ya tsaya ya rinƙa koya masa yadda ake siyarwa, kafin ya saba shi ma ya fara siyarwa da kansa. Tare da Sa'ad suka fito suka kira wani baro ya daukar musu kayan har rumfar da aka baiwa Aisar ɗin ya zauna, bayan sun je Aisar ya ga akwai masu gwanjo da yawa a wajen, a ransa yake tunanin zai siyar kuwa, amma sai yayi shiru bai ce komai ba, bayan sun sauke kayan, sai suka kakkasa su a gefen hanƴa inda mutane suke wucewa. Suna gama kasawa kuwa mutane suka kewaye su ana zaɓa, yaron ne me faɗar farashin kayan, shi kuwa Aisar yana kula da duk wanda ya ɗauka gudun kar gudar musu da kaya, ciniki suke yi sosai yamma tayi sannan suka haɗe kayansu suka nufi shagon Malam Ɗahiru, suna zuwa kuwa Aisar ya zauna a cikin rumfar ya lissafa kuɗinsa, bisa ga mamakinsa sai ya ga ya mayar da kuɗinsa, har da riba ma akai, wajen dubu huɗu da ɗari biyar kuma yana da sauran kayan ba su ƙare ba. Kiran yaron da ya taimaka masa yayi ya sallame shi, Malam Ɗahiru ya kalle shi yace "da fatan dai yanzu ka ga yadda ake yi? gobe ko kai kaɗai ma zaka iya zuwa ko?" Shafa kai Aisar yayi yace "na gani Baba insha Allah gobe ko ni kaɗai ne, zan iya kula da komi, ashe ma harkar babu wuya sosai. Nan dai yayi wa Malam Ɗahiru sallama ya nufi gida, duk hanƴar da suka biyo shi da Sa'ad lokacin da za su zo Wambai ɗin, yana riƙe da ita a ransa bai manta ba, don haka shi ma nan ya rinƙa bi, har ya fito bakin titi ya tari napep yace Darmanawa zai kai shi, faɗa masa kuɗin yayi yace "su je babu matsala". Lokacin da iso cikin Darmanawan Allah yasa suka fito dai-dai unguwar da Aisar ɗin suke, da suka kusanto layin nasu sai ya dakatar da me napep ɗin yayi yace zai ƙarasa a ƙafa. Bayan ya sallami me napep ɗin sai ya nufo gidan, yana zuwa ya iske Nasreen da Safna da kuma Basma suna ta wasa a ƙofar gidan, suna ganin shi suka tashi da gudu suka tarye shi, har da Basma duk da bata san shi ba amma sabida ba ta da wuyar sabo nan ita ma ta zo ta rungume Aisar kamar dai yanda ta ga su Safna sunyi. A tare suka shiga cikin gidan, ya fito da tsarabar da taho musu da ita ya damƙawa kowa nasa, har da Basma sai da ya baiwa. Da gudu kuwa ta je ta nunawa Ummanta, harararta tayi tace "wato Basma ba ki jin magana ko?" bana hanaki roƙo ba? Marairaice murya ta yi tace " wallahi Umma ni ban roƙe shi ba, Abban Safna ne ya ganmu muna wasa shine da ya basu sweet ɗin nima ya bani. Kallonta Husna tayi tace "shikenan amma kar na ƙara ganin kina roƙo, idan ki ka ga Abban su Safna ya dawo to kiyi sauri ki taho gida kin ji, kar ki kuskura ki je kema a baki sweet ɗin, idan kika faɗawa Abbanki zai siyo miki kin ji. Da murnarta tace "to Ummata kiyi haƙuri ba zan ƙara ba, na je na mayar musu da wannan sweet ɗin yanzu?" Sai da ta baiwa Husna dariya tace "a'a ban ce ki mayar musu ba, amma kar ki ƙara zuwa a baki kin ji ko. Aisar kuwa yana gama rabawa su Safna da Nasrin sweet ɗin, sai ya ɗauki bocket ya nufi famfo zai ɗebi ruwa domin ya watsawa jikinsa, da sauri Rahila ta karɓe bokitin da kanta ta tara masa ruwan, ta ɗauka ta kai masa banɗakin sannan ta fito tace ya shiga yayi wankan. Kafin ya fito har an fara kiran sallar magariba, saboda haka ta ɗauko buta ta zuba masa ruwan kafin ya fito, yana fitowa kuwa yayi maza ya ɗaura alwalar ya shiga ɗaki ya saka kayansa masu kyau, ya nufi masallaci. Su Iya kuwa suna can ɓangaren Ammi sai hira suke faman sha, domin Ammi macece mai son jama'a kiran sallar da suka ji ne yasa suka tashi suka taho lungunsu domin su gabatar da sallah. Aisar kuwa akan hanyarsa, zai fito ya haɗu da Sa'ad ya dawo daga kasuwa, yana ganin Aisar ya saki murmushi yace har ka dawo kenan, Aisar yace "wallahi na daɗe da dawo wa ma har nayi wanka yanzu masallaci zan je, idan na dawo zamu yi magana, shiga cikin gidan Sa'ad yayi shi ma ya ɗaura alwalar ya fito ya nufi masallacin, don har an kai raka'a ɗaya raka'a biyu ya samu, haka ma ya godewa Allah da ya nufe shi da zuwa masallacin don Sa'ad ba baya bane wajen ƙokarin ibada....... To be continue.......... Comment and share *_HUSSAIN YUSUF_* 07069475482[12/9, 4:37 PM] ~HUSSAIN YUSUF~: *ANAS MALEEK* *NA* *HUSSAINI YUSUF* *_______________________________* *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *______________________________* *Page 31/32* Bayan an idar da sallar a tare suka fito daga masallacin, a ƙofar gidan suka zauna Aisar ya shiga ba wa Sa'ad labarin yadda kasuwar ta kasance yau, fatan alkhairi Sa'ad yayi masa, hira sosai suke yi har aka yi kiran sallar Isha'i suka tafi masallaci. Bayan sun dawo Sa'ad ya shiga ya fito musu da abinci, shi ma Aisar ya shiga ciki sai ga shi da nasa abincin.Da mamaki Sa'ad ya kalle shi yace "Aisar abinci ka bayar aka dafa maka ne?" murmushi Aisar yayi yace "E wallahi gani nayi nauyin zai yi maka yawa, ga su Ammi ga mu ai abin da yawa, shi yasa nace daga yau ba zan sake barin ka da wannan nauyin ba. Ɗan ɓata fuska Sa'ad yayi yace " me yasa kake haka ne Aisar? na riga na shaida maka ku baƙina ne har yanzu baku zama ƴan gari ba, to wai ma kwata-kwata nawa ka samu daga fara sana'arka zaka fara kashe kuɗi haka? so kake ka cinƴe jarin da wuri haka?" Murmushi Aisar yayi yace "gani nayi kai ma samunka ba wani ƙarfi ne da shi ba, mota fa kake ja wata ran ka samu fasinja wataran kuma ba zaka samu.....waya gaya maka? Aisar ya faɗa yana mai duban Aisar, ya cigaba da cewa "Ai ni nan da ka ganni ina da motoci sama da guda biyar kuma duk haya na bayar da su, har wannan da na ke ja guda shida, duk wata ake kawo min balance, kuma a haka zaka ce samun mu ɗaya? Ka ga kenan tun da na fika samu dole ne na taimaka maka, yanzu ma abinda nake so da kai shine, ƴaƴan nan naka zan kai su makarantar boko da Islamiyya, kuma ni zan ɗauki nauyin karatunsu har su gama insha Allahu na ɗauki alƙawari, insha Allahu. Aisar ne yace "Haƙiƙa tun da nake a rayuwata ban taɓa ganin mutum mai karrama mutane da ganin darajarsu kamar ka ba, kana da mutunci ƙwarai da gaske. Ka duba tunda Allah ya kawo mu nan gidan, ba ka taɓa tambayar labarinmu da abinda ya baro mu daga gida ba, haka mahaifiyarka da matarka ma ban taɓa ganin wani a cikinsu ya nuna mana tsangwama ko kyara ba, kullum cikin kokarin kyautata mana suke yi.Ba mu da bakin da zamu gode muku, sai dai muyi ta yi muku addu'a, har ƙarshen numfashinmu, kuma Allah ya bamu ikon saka muku da abin da kuka yi mana, fiye da shi ma Allah ya ba mu mu saka muku. Dafa kafaɗar shi Sa'ad yayi yace " Aisar duk abin da ka ga nayi muku, nayi muku ne saboda Allah don haka bana neman wata sakayya daga gare ku, a wajen Allah nake neman sakayya ta. Nan dai suka cigaba da hira har suka cinƴe abincin, suka tattauna akan sana'ar Aisar wato gwanjo, bayan sun gama cin abincin kowa ya tashi ya tafi lungunsu. Yayin da Aisar ya shiga sai ya tarar da Rahila ta idar da sallah, nan da nan kuwa suka hau yin hira, sai wajen sha ɗaya da rabi na dare sannan suka kwanta. Washe gari da safe kowa ya tafi sana'ar shi, Husna kuwa bayan ta gama duk wasu ƴan ayyukanta, sai ta taho wajen Rahila suka hau hira sai wajen sha biyu na rana ta tafi domin ta ɗora abincin rana. Wata rana bayan sallar Isha gaba ɗayansu sun haɗu a wajen Ammi suna ta hira, idan ka gan su a wannan lokacin sai kayi zaton family ɗaya ne, idan ba'a faɗa maka ba. Anan ne Aisar ya shiga bai wa su Sa'ad labarin abin da yasa suka baro garinsu suka tahi Kano. Ammi da Rahila sai da suka yi kuka sosai na tausayin su Inna, nan take kuwa Sa'ad ya ɗauki alƙawarin zai ɗauki nauyin Aisar har zama soja ya cika burin shi na ɗaukar fansa akan ƴanta'adda. Su Ammi kuwa mamaki suke yi da aka ce Aisar da Anas ba dangi ɗaya suke ba, amma idan ka gan su sai ka rantse dangi ɗaya suka fito. ****** **** ******* Washe gari yau ta kama monday, da sassafe Sa'ad yace "idan su Anas sun gama breakfast su shirya zai kai su makaranta. Murna a wajen Anas kuwa bata faɗuwa, saboda zumuɗi ya kasa cin abincin karyawar ma, Safna kuwa ita bata yin wata murna, don dama can a ƙauyensu bata yin makarantar Aisar ne kaɗai mai yi, shi yasa yake jin daɗi da aka ce yau za'a mayar da shi. Nasreen ma sosai take murna yau za'a kaita makaranta, bayan sun gama karyawa Sa'ad ya ɗauke su a motarsa ya nufi makarantar da su. *ABIDDEEN NURSERY AND PRIMARY SCHOOL DARMANAWA* naga an rubuta jikin wata makaranta, me kyawun gaske horn yayi me gadin makarantar ya zo da gudunsa ya buɗe masa, sai da ya bincike motar tsaf sannan ya bar shi ya shiga ciki. Bayan yayi parking ya buɗe musu suka fito gaba ɗayansu, riƙe hannunsu yayi suka nufi cikin makarantar. Wani masinja suka gani a zaune yana jin rediyo, ƙarasawa wajensa Sa'ad yayi, sallama yayi masa cike da kulawa ya amsa. "Don Allah malam ina ne ofishin shugaba makarantar nan? Sa'ad ya tambayi masinjan, tashi tsaye yayi yace ku biyo ni a baya. A hankali suke bin sa har ya kawo su office ɗin bayan ya nuna musu sannan ya juya yayi tafiyarsa. Da sallama suka cikin office ɗin. Tunda suka shiga cikin office ɗin, su Anas da Safna suke ta faman kalle-kalle, musamman ma hotunan da ke manne a jikin bangon office ɗin, suka fi mayar da hankalinsu akai.Hoton wani Soja ne sanye da kaki irin na jajurtattun sojojin nan, shine ya tafi da Anas can wata duniya, ya rinƙa jin sanyi a cikin zuciyar shi tare da fatan Allah yasa shi ma ya zama fiye da wannan sojan. Shugaban makarantar yana zaune a wata kujera ta alfarma, gabansa ga wani tebur nan me girman gaske, ga takardunan masu yawa zube a kansa. Bayan su Sa'ad sun gama samun wajen zama, sai shugaban makarantar ya dube shi yace "Malam barka da zuwa" da fara'a Sa'ad ya amsa "barka dai yallaɓai, dama yara ne na kawo ko za su samu gurbin zama a wannan makarantar?" Da fara'arsa yace "me zai hana? mu kullum burinmu ai shine mu ga ana ta kawo mana ɗalibai ko da yaushe mu kuma muna karɓewa" ya karashen maganar da salon zolaya, murmushi Sa'ad yayi yace "masha Allah to ga ƴaƴana nan suma a ba su aji." Kallon Anas shugaban makarantar yayi yace "ɗan samari ya sunanka?" cikin sanyin murya Anas yace "sunana *ANAS ABDUL MALEEK* masha Allah shine abin da shugaban makarantar ya faɗa, sannan ya rubuta a jikin wata paper, ya sake duban Anas yace "ka taɓa yin makaranta?" "E na taɓa yi a can kauyenmu" good ajinka nawa a can kauyen naku? Ajina huɗu zamu shiga na biyar shine muka baro kauyen. "Masha Allah yanzu ka iya karatu da rubutu?" "E na iya" ɗauko wata farar paper yayi ya ajiye akan desk ɗin da yake gabansa yace Anas ya rubuta masa A, B, C, D, cike da nutsuwa ya rinƙa rubuta masa har ya gama tsaf. "Good hand writing" shine abin da shugaban makarantar ya faɗa, sannan yace ya rubuta masa sunansa nan ma ya ga Anas ba baya bane, wajen iya rubutu, da karatu, anan dai yayi ta faɗo masa sunayen abubuwa da turanci yana rubuta masa, ko kuskure ɗaya bai yi ba. Sosai Anas ya burge shugaban makarantar da Sa'ad, tun da aka fara yi wa Anas screaning ya ke ta faman murmushi, nan take ya ji yana alfahari, ya rinƙa jin sa tamkar ɗansa na jini. Kallon Sa'ad shugaban makarantar yayi yace "hakika na yaba da kokarin Anas Abdul Maleek, don haka naga yafi dacewa da primary six (class 6) anan zamu saka shi, shekara tana kewayowa sai su zana jarrabawar common interest ya shiga secondary school. Murmushi Sa'ad yayi yace "haka yayi wallahi ni ban yi zaton kokarinsa ya kai har haka ba." sannan ya dubi Safna da Basma yace "yan mata ku kuma ya sunanku?" Safna ce ta fara cewa "Ni sunana Safnatu Abdul Maleek" ƴar dariya shugaban makarantar yayi yace *"Safnat za ki ce ba Safnatu ba kin ji ƴan mata?"* girgiza kai tayi tace "to malam" sannan yayi mata wasu ƴan tambayoyi har dai ya gane ita ba ta taɓa shiga aji ba Nasreen ma dai ba ta taɓa shiga aji ba saboda Aisar yana niyyar kai ta makarantar sai kuma suka bar garin, haka ne yasa ba'a samu damar kai ta ba sai a birnin Kano Allah yasa za'a kaita, Basma kuwa mahaifinta yana kusa bai bari ma an yi wasu tambayoyi ba, yace "yau ya fara kawo ta makaranta". Nan dai bayan an gama abin da za'a yi aka kai kowa ajinsa Anas shi aka kai shi class 6 Safna da Nasreen da Basma aka kai su primary 1 a cewar shugaban makarantar sun yi girma a nursery. Nan take Sa'ad ya biya kudinsu gaba daya, aka damkawa kowanensu uniform da littattafai na karatu da na rubutu dai-dai ajinsu, sannan yace tomorrow su fara zuwa makaranta...... To be continue......... Comment and share Hussaini Yusuf 07069475482. [12/9, 4:37 PM] ~HUSSAIN YUSUF~: *ANAS MALEEK* *NA* *HUSSAIN YUSUF* *_______________________________* *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *______________________________* *Page 33/34* Bayan sun dawo gida, Anas da Nasreen da Basma sai faman murna suke yi, gani suke yi kamar su janƴo gobe saboda zumuɗi. Aisar yana dawo wa daga kasuwa Safna ba ta bar shi ya huta ba, ta shiga ba shi labarin makarantar da aka kaisu. Haka Nasreen ma Anas shi kuwa da ya zamana yafi su wayo, ko kaɗan bai nuna wa Aisar ya matsu gobe ta yi ba, har sai da Aisar ya tambaye shi sannan yayi masa bayanin komai har class ɗin da aka saka shi sai da ya faɗawa Aisar, ba ƙaramin daɗi Aisar ya ji a cikin ransa ba, kullum burinsa da fatansa shine ya cika wa Anas babban burinsa na zama soja. Washe gari da sassafe su Anas suka tashi, da wuri Rahila ta ɗora musu tea, domin su yi breakfast da wuri kafin lokacin tafiya makarantar yayi. ƙarfe bakwai da rabi dai-dai, Sa'ad ya shigo lungun nasu, hannunsa riƙe da Basma ta sha uniform ɗinta, sun yi mata kyau sosai, ga school bag a bayanta, ban da kallonta babu abin da Anas yake yi, tunda ya zo gidan nan Basma take burge shi, kome tayi shi a wajen shi dai-dai ne, haka kawai ya ji yana ƙaunar yarinyar sosai a cikin ransa. Amma saboda Anas irin mutanen nan ne, marasa yawan magana, ba za ka taɓa fahimtar wani abu game da shi ba, bashi da surutu irin na sauran yara, ko da yaushe a nutse yake komai na shi yana aiwatar da shi ne cikin sanyi da nutsuwa, kana kallonsa zaka tabbatar a jininsa sanyi da nutsuwa suke. Amma fa idan aka ɓata wa Anas rai, to mai rarrashin shi ya hakura sai yayi da gaske, domin idan yayi fushi yana daɗewa bai huce ba, amma kafin yayi fushin ne a wahala. Kallonsu Anas Sa'ad yayi yace "wai ba ku gama breakfast din ba ne?" da sauri Nasreen tace "Mun gama" Aisar yace "Kuyi sauri ku shirya kun ga yana ta faman jiranku, kada ku makara a makarantar". Anas tashi yayi ya shiga cikin wani ɗaki, da alamu dai anan ne yake kwana, bai daɗe a ciki ba sai ga shi ya fito a cikin shirinsa na makaranta, kayan sun yi masa kyau sosai, su Safna ma ba su daɗe ba, Rahila ta gama shirya su, fitowa suka yi fuskokinsu dauke da murmushi na farinciki yau za'a shiga school. Kama hannunsu Sa'ad yayi suka fita, kai tsaye motar shi ya bude musu suka shiga, Safna da Nasreen da Basma, a baya shi kuma Anas Sa'ad yace "ya shiga gaba." Aisar yana tsaye yana ta sakin wani murmushi, yana ta aikin ɗaga musu hannu har Sa'ad ya tashi motar ya tafi, Aisar bai daina murmushi ba, burinsa ya cika babu abin da zai ce da Sa'ad sai dai yayi ta masa addu'a, domin ya cika masa burinsa a ransa yake ji Anas zai cika burinshi ya zama babban soja a kasar nan. Sai da ya daina hango motar sannan ya juya ya shiga gida, don ya shirya shi ma ya tafi neman abincin shi. ***** ******* ***** Yayin da suka shigo cikin makarantar, kai tsaye office ɗin Headmaster suka wuce, suna shiga da murnarsa ya tare su yana musu barka da zuwa. Nuna masu kujera yayi yace su zauna, bayan sun gama zaunawa, sai ya dauki waya ya kira wani, two minute sai ga wasu matasan malamai sun shigo cikin office din, kallonsu Head master din yayi yace "Kabir ga sabon dalibi nan na kawo maka ka kai shi cikin ajinka, sunan shi Anas Abdulmalik." Murmushi malamin yayi yace "masha Allah sannan ya kalli Anas yace "Anas ta so mu tafi na gabatar da kai a ajin" tashi Anas yayi ya bi shi a baya, suka fita, sannan ya sake kallon daya malamin yace "kai kuma ga sababbin dalibai nan, murmushi malamin yayi ya kalli su Safna yace "yan'mata ya sunanku?" Kafin su yi magana Nasreen ta riga su, tace "ni dai sunana Nasreen Aisar" Safna ma tace "ni kuma Safnat Abdul maleek" sannan ya kalli Basma yace "ke kuma fa ƴan'mata kin yi shiru" ranta a ɓace tace "Lailat Sa'ad" kallonta Sa'ad yayi yace "Basma me yake damunki ne?" kamar zata yi kuka tace "ba sune suka ƙi bari na na faɗa wa Malam sunana ba; ta faɗa tana nuna Safna da Nasreen, kowa a wajen sai da Basma ta ba shi dariya, sosai ta burge Malamin nasu, a ransa yake jin yarinyar zata yi kai sosai ko daga maganarta zaka gane hakan. Tafiya da su malamin yayi, suna shiga class ɗin gaba daya ƴan class din suka mike a tare suka ce "good morning Uncle!" kallonsu yayi yace "Morning student, how are you?" hade baki suka yi a tare suka ce " We are fine Uncle" sai bayan kamar minti biyar sannan yace "sit down student" anan ma a tare suka ce "Thank you Uncle" sannan kowanen su ya zauna. Yanayin yadda ɗaliban suka gaisar da malaminsu ne burge su Safna, sai faman sakin murmushi suke yi, suna fatan su ma su iya wannan turancin da ƴan ajin suka yiwa Malam. Kallon sauran yan ajin malam yayi yace "Alhamdulillah mun samu ƙarin new commers, a cikin wannan class din namu, ina fata zaku karɓe su hannu bibbiyu ku ba su wajen zama?" A tare suka ce "insha Allahu Uncle" sannan ya kalli su Safna yace "yanzu za su faɗa muku sunayen su ɗaya bayan ɗaya domin yanzu sun zama abokanku kuma yan'uwanku. Nuna Safna yayi yace "ƴan mata kalli ƴan aji ki fada musu sunanki" muryarta na rawa saboda bata saba magana a cikin mutane haka ba tace "Sunana Safnat Abdul Maleek" nan da nan kuwa ta ji malam yace "clap for her" nan da nan ajin ya ɗauki sautin raf! raf!! raf!!! haka ba ƙaramin yiwa Safna da su Nasreen dadi yayi ba. Sannan ya kalli Basma yace "ƴan'mata ke kuma fa yaya sunanki?" kallon yan ajin Basma ta yi tace "sunana Lailat Sa'ad" nan ita ma aka tafa mata, sannan Nasreen ita ma tace "sunana Nasreen Aisar" nan take ita ma class din suka yi mata tafin. Sannan malam yace "monitor ya basu wajen zama" wani desk ya nuna musu wanda babu kowa akai, zuwa suka yi suka zauna, sannan malam ya juya board din ajin ya fara rubutu. •••••••••••••••• Anas kuwa bayan sun shiga cikin ajin, sai malamin ya umarce shi da ya bayyanawa sauran daliban sunansa, amma da turanci zai faɗa, murmushi Anas yayi sannan ya kalli yan ajin da suke zaune yace "my name is Anas Abdul Maleek" tafi suka yi masa sannan malam ya nuna masa wata kujera yace "ya je ya zauna akai kafin, a samo masa na sa, tun da me ita baya nan. Zuwa yayi ya zauna kusa da wani yaro, kallon shi yaron yayi ya sakarwa Anas murmushi yace "abokina mu gaisa mana" cikin sanyin jiki Anas ya mika masa hannun suka yi musabaha, sannan yaron ya sake cewa Anas"sunana Ammar da fatan za mu zama abokan juna" sai a sannan Anas ya saki murmushi yace "ba matsala Ammar tun da yanzu mun zama daya, tun da ka zama maƙwabcina, dole ne mu ƙulla zumunci. Hira ce sosai ta ɓarke tsakanin Anas da Ammar, idan ka gan su sai kayi zaton dama can sun san juna. Su Nasreen ma an yi sababbin ƙawaye a makaranta, sosai Nasreen ta zage sai zuba musu surutu take yi, kamar dama can ta san su, Safna da Basma kuwa su ba su fiye yawan magana ba, sai ta kama su yi magana sannan kake jin bakinsu, sai dai kome Nasreen ta tambaye su, sai dai su bita da E ko a'a da haka dai har malam ya shigo, ya kira su Safna ya shigar da sunansu cikin register. Ƙararrawar tashi aka buga, nan da nan kuwa naga ɗalibai ta ko'ina suna fitowa, Anas sai hangen su Safna yake, amma ko kaɗan bai hango su ba, kai tsaye sai ya tafi bakin gate ya tsaya, yana ta kallon masu wucewa ko zai ga su Safna a ciki amma bai gan su ba. Sai da kowa ya gama fita daga makarantar, amma bai ga ko alamun su Safna ba da sauri yayi cikin makarantar, yana kiransu, amma shiru babu su babu alamun su.......... To be continue........ Comment and share _*Hussain Yusuf*_ 07069475482. [12/9, 4:37 PM] ~HUSSAIN YUSUF~: *ANAS MALEEK* *NA* *HUSSAINI YUSUF* *______________________________* *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ƴancinmu* *______________________________* *Page 35/36* Sosai Anas ya ruɗe sai faman zagaya cikin makarantar yake, amma babu su Safna, wani malami ya hango zai hau kan babur ɗinsa, da gudu ya karasa wajen malamin. A gigice ya dubi malamin yace "Malam ka taimaka min na rasa ƴan'uwana" kallon shi malamin yayi yace "ni ban san ka ba ma anan makarantar amma yau kuka fara zuwa ko?" da sauri Anas ya ɗaga masa kai yace "E yau Abbanmu ya kawo mu." Murmushi malamin yayi sannan ya sauka daga kan babur ɗin ya kafe shi, ya dubi Anas yace "biyo ni a baya" da sauri Anas ya bi bayansa, har ɗan gudu-gudu yake yi, don kada malamin yayi masa nisa...... A can waje kuma Sa'ad ya kai wajen 30 minute, yana jiran su Anas su fito ya ɗauke su amma shiru, akan idonsa gaba daya ɗaliban suka gama fitowa, amma bai ga alamun su Safna ba. Bai tsaya wani ɓata lokaci ba, ya kutsa kai cikin makarantar, domin ya gani ko wani abun ne ya hana su fitowa. Wani lungu malamin ya kutsa, da sauri shi ma Anas ya bi bayanshi. Wajen ya burge Anas sosai, ɗan ƙaramin lambu ne mai ɗauke da shuke-shuke, kamar irin su Mangwaro, Gwanda, Lemo da sauransu.... Hango Safna Anas yayi tana ta faman kokarin ciro wani mangwaro, da wani dogon sanda amma ta kasa, har suka karaso wajen ba su san sun zo ba. Cike da jin haushi Anas ya daka musu tsawa, a firgice suka juyo suna niyyar guduwa, don ba karamin tsorata suka yi ba. Kallonsu yayi yace "wato ku saboda rashin hankali, ina can bakin gate ina ta faman jiranku amma shine za ku zo nan wajen ku hau cirar wani mangwaro ko?" Yanzu ma na san Abba yana can yana jiranmu, tsuru-tsuru suka yi da ido, gaba dayansu sun sunkuyar da kansu ƙasa. Kallonsu malamin yayi yace "ku kuwa me yasa kuka aikata haka? na ga ba'a zuwa nan wajen sai a lokacin break muke bari a zo" me yasa ba ku zo da break ba sai da aka tashi? ga shi duk kun bi kun dagawa ɗan'uwanku hankali. To daga yau idan na ƙara ganin wani anan bayan an tashi sai na zane shi, ku mu je ku fita dag...... hangota yayi a ɓoye a bayan wata bishiyar gwanda, sai faman leƙo su take yi, haka ne ya hana shi furta abinda yake shirin faɗa. Nunawa yayi kamar bai ganta ba, ya dubi su Basma yace "naga ku baƙine anan makarantar waye ya kawo ku nan wajen tun da dai baku san shi ba ?" zazzare ido suka fara yi wannan ta kalli wannan an rasa wanda zai ba wa malam ɗin amsa a cikinsu. Murmushi malam yayi kai tsaye ya nufi wajen bishiyar gwandar da ya hangota a bayanta, tana tsaye jikinta ban da rawa babu abinda yake yi, daga bayan gwandar ya tsaya ya miƙa hannu ya kamo hannunta. Firgita tayi ta saki wata ƙara! nan take ta saki kuka tana roƙon malam ya saketa. "Don Allah Uncle Jamil ka yi haƙuri ba zan ƙara ba, na tuba na bi Allah na bika, kayi min rai ba zan ƙara ba" dariya ta so ba shi amma sai ya sha kunu, a ransa yake cewa "Bilkisu kenan sai fitinar tsiya, amma akwai ɗan banzan raki, kamar wacce za'a yanka". Daka mata tsawa yayi yace "indai ba ta yi shiru ba sai ya zaneta" ɗif kamar ɗaukewar ruwan sama ta daina ihun da take yi, duban su Nasreen Uncle Jamil yayi yace "wannan ce ta kawo ku nan wajen ko?" da sauri Nasreen tace "E ita ce tace mana idan muka zo zata cira mana mang..... shiru tayi sakamakon hararar da Anas ya aika mata, sosai ta tsorata don bata taɓa ganin Anas a cikin ɓacin rai kamar yau ba. Kallon Anas Uncle Jamil yayi yace "me yasa zaka hanata faɗar abin da yake bakinta?" rai a ɓace Anas yace "Uncle mu zamu tafi don na san yanzu Abbanmu yana can yana ta aikin jiranmu" duban Bilkisu Uncle Jamil yayi yace "maza ki tsugunna ki bai wa yayansu hakuri na ɓata masa lokaci da wahalar da shi ɗin da kika yi". Zuwa tayi gaban Anas ta durƙusa, da sauri Anas ya dubi Uncle Jamil yace "ni ai na hakura kuma ba ita ce tayi min laifi ba, ka ga wadanda suka yi min laifi" ya faɗa yana nuna su Safna da hannu. Bai tsaya jin wani abun da Uncle Jamil zai ce ba ya ja hannun ƴan'uwan na shi suka fice daga cikin garden ɗin. Shi kuwa Uncle Jamil kallon Bilkisu yayi yace "ke Bilkisu me yasa ba ki da hankali ne" haka kawai zaki jawo yara cikin school garden bayan an tashi daga makaranta ko? don kuyi ta'adinku son ranku da safe sai a nemi wanda yayi a rasa, alhali kuma ke ce me janyo yara kuna yi ko? duk ta'adin da ake yi ashe kece ki ke kawo yara kuna yi ana ɗorawa masu gadi akan ba sa kula ko? to yau asirinki ya tonu gobe zaki ci ubanki kuwa a cikin makarantar nan, don a kanki sai na haɗa assembly na zane ki a gaban ɗalibai. Da sauri ta kama ƙafafunsa tana kuka tana cewa "don Allah malam ka yi haƙuri daga yau ba zan ƙara ba" murmushi yayi yace " ke dai ki bari gobe kiyi bayani a gaban sauran student, ga shi nan saboda fitinarki kullum ba kya cigaba a makarantar nan, ƙannan ƙannanki sun zo sun tafi sun bar ki saboda tsabar rashin ƙokarinki. An kai ki ajin yara sai kiyi ta saka su suna aikata laifi, kina zare kan ki ko? da sauri ta girgiza mai kai tace "wallahi malam bana saka su" murmushi yayi yace to me yasa da na shigo kika ɓuya a bayan bishiya? wato so kike sai na fita sannan ki fito ki gudu ko? to tun daga ƙofa na hango ki a ciki..... Su Anas suna fita suka ci karo da Sa'ad yana ta faman neman su, kallonsu Sa'ad yayi yace "ina kuka tsaya ne ina ta nemanku? tun ɗazu na zo nan ɗaukarku amma har ɗaliban suka gama fita ban gan ku ba lafiya?" murmushi Anas yayi yace "idan mun je gida zan faɗa maka Abba mu tafi kawai". Girgiza kai kawai Sa'ad yayi sannan ya wuce gaba suka bi shi a baya. A hanya Anas ya bayyanawa Sa'ad dalilin da yasa suka daɗe, bai ɓoye masa kkomai ba amma maimakon ransa ya ɓaci, sai ya saki murmushi yace "yarinta ce insha Allah za su daina" a haka dai da suka koma gida, Sa'ad tara su yayi ya musu faɗa sosai, ya nuna musu ɓacin ransa akan haka. Kuma yace "daga yau idan an tashi su za su rinƙa jiran Anas a ƙofar gate" Rahila da Husna ma sun yi musu faɗa sosai daga baya dai da nasiha suka gama yi musu faɗan. Washe gari ko da suka je makarantar, ƙin kula Bilkisu suka yi, sai faman shishshige musu take yi amma ko kallonta ba su yi ba ballantana ta saka ran za su kulata. Sosai suka mayar da hankali akan abinda ya kawo su makarantar, sai ga shi cikin ikon Allah sun fara fahimtar abubuwan sosai. ****************************** A kwana a tashi babu wuya a wajen Allah, yau Anas ya kammala secondary school, yayin da su Safna suke Js.s two. Akwai wani abokin Anas da suka haɗu a makarantar, shi ma ra'ayinsa irin na Anas ne, ma'ana shi ma soja yake son zama, zuwa yayi ya sanar da Daddyn shi a samo masa admission a makarantar horar da sojoji ta Kaduna, kuma yace tare da Anas yake son a samo musu. Saboda Daddy ya san ko wanene Anas a wajen Ammar bai ɓata masa wani lokaci ba yace zai samo musu tare, kuma ya je ya shaidawa Anas ɗin shine zai ɗauki nauyin karatun na shi,har su kammala kuma ya ɗauki alƙawarin shine zai tsaya musu har sai sun zama manƴan sojoji a ƙasar nan. Ai da gudu Ammar ya fita daga gidansu ya nufi gidan su Anas domin ya shaida masa wannan albishir ɗin, yana zuwa ya tarar da Anas a ƙofar gida, ya zuba tagumi hannu biyu kallonshi Ammar yayi cike da zumuɗi yace da shi...... Anas albishirinka da sauri ya ɗago ya kalli Ammar din don sai lokacin ma ya san da zuwan shi, sake maimaitawa Ammar yayi yace "Anas albishirinka" da sauri Anas yace goro........... To be continue........ Comment and share _*Hussaini Yusuf*_ 07069475482. [12/9, 4:37 PM] ~HUSSAIN YUSUF~: *ANAS MALEEK* *NA* *HUSSAINI YUSUF* *______________________________* *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *______________________________* *Page 37/38* *Z* ama Ammar yayi yace "to bani goron sai na faɗa maka" murmushi Anas yayi yace "idan kuma albishir ɗin bai yi min daɗi ba fa?" "ai wannan albishir ɗin da zan yi maka ba'a taɓa yi maka irin shi ba" kallon shi Anas yayi yace "don Allah kayi sauri ka faɗa mini indai yayi min daɗi ni na san kyautar da zan yi maka". Murmushi kawai Ammar yayi yace "Anas ka godewa Allah domin burinka yana gab da cika, Daddy na yace tare da kai zai nemo mana admission a makarantar horon sojoji ta Kaduna" a zabure Anas ya miƙe tsaye yana yi wa Ammar kallon tuhuma, zama yayi ya kalli Ammar ɗin yace "ta yaya Daddyn ka ya san ni da har zai samo min admission?". Murmushi Ammar yayi yace "Anas kenan ai kullum idan na zauna da Daddy na babu labarin da nake ba shi face naka" da haka har ya san ka a baki amma bai taɓa ganinka ba, kuma nace kaine kake taimaka mini a makaranta, sosai kana da kirki. Haka ne yasa duk lokacin da na yabe ka, sai Daddy ma ya yabe ka, kuma na ce masa burinmu ni da kai iri ɗaya ne, ma'ana ni da kai duk sojoji muke son mu zama. Da yace min zai nemo mini admission na shiga makarantar horon sojoji, sai na dage nace tare da kai za'a nemo mana, idan kuwa ba haka ba na fasa yin sojan gaba ɗaya. Dole Daddy ya haƙura zai nemo mana a tare ka ga sai mu wuce ko? har hawaye sai da Anas ya zubar don murna. Duban Ammar yayi yace "Ammar tashi ka raka ni na je na yiwa Daddynka godiya." Da sauri Ammar ya dakatar da shi ya ce "Yanzu Daddy na baya gida, sai dai ka bari a ƙarshen satin nan yake zaman gida, da kaina zan zo na raka ka wajen shi ka yi masa godiyar, yanzu ni dai ka bani goron albishir ɗin da ka ce zaka ba ni." Murmushi Anas yayi yace "jira ni anan ina zuwa" sannan ya shige cikin gidan, kai tsaye ɗakinsa ya nufa, dube-dube yake ta yi ya rasa me zai ɗauko ya kawo wa Ammar ɗin, saboda ya matuƙar burge shi ba kadan ba. Wani hoto ya ɗauko wanda shi da Ammar ɗin ne a jiki sun yi kyau sosai, kamar ƴaƴan Larabawa. Fitowa yayi ya samu Ammar ɗin a ƙofar gida yana jiransa, yana zuwa ya miƙa masa hoton yace "ungo wannan hoton da ban yi niyyar ba ka ba amma saboda wannan albishir ɗin da kayi mini na mallaka maka shi. Karɓar hoton Ammar yayi yana sakin wani murmushi, ya dubi Anas yace "a ina ka ɗauki hoton nan? don ni ban da shi ba gaskiya". Murmushi Anas yayi yace "yanzu kai har ka manta wajen da muka yi hoton nan?" gyaɗa masa kai Ammar yayi "ka tuna lokacin da muka tafi yawon shaƙatawa a makaranta?" da sauri Ammar yace "wallahi na tuna, a wajen TIGA DAM ko?". Dariya Anas ya saki yace "ashe ba ka manta ba, to a lokacin da aka ta yi mana hotunan nan, anan aka ɗauke mu. Inda na samo hoton kuwa wata rana na shiga office ɗin Principal ina share masa shi, babu kowa a ciki sai naga wannan hoton, ni kuwa da naga mune a jikin hoton kuma mun yi kyau sosai, sai na ɗauke shi na ɓoye shi a cikin jakata, da so nake sai mun girma in nuna maka shi na san zaka yi farinciki idan ka gan shi. Dariya Ammar yayi yace "ai ba zan raba ka da wannan hoton ba, yanzu ka je ka ajiye shi idan na samu lokaci zan zo ka raka ni mu kai shi a wanko mana wani su zama biyu kaga kenan ni ɗaya kai ɗaya kowa a cikinmu ya mallaka. Bayan tafiyar Ammar Anas wuni yayi da farinciki, ya matsu Abban shi ya dawo ya shaida musu, ko kadan bai yi gangancin faɗawa su Inna ba don yana tsoron kada su riga shi faɗawa Abbansu. Bayan sallar Isha'i sai ga Aisar ya dawo daga kasuwa, dama yayi sallarsa kafin ya shigo ciki, yana shigowa abincin Rahila ta kawo masa zama yayi ya fara ci. Yana cikin cin abincin Anas ya shigo, har ƙasa ya tsugunna ya gaisar da shi yayi masa sannu da zuwa, cike da kulawa ya amsa yana mai shafa kan Anas ɗin. Bayan ya gama cin abincin, ya wanke hannunsa, sannan ya dubi Anas yace "ya karatun naku?" sunkuyar da kansa ƙasa yayi yace Alhamdulillah Abba, dama akwai albishir ɗin da nake son nayi maka. Da sauri Aisar ya kalli Anas yayi murmushi yace "to ina jin ka Anas" kansa yana ƙasa ya fara magana dama ina so na faɗa maka Daddin Ammar yace zai samo min admissin a makarantar horar da sojoji ta Kaduna. Da sauri Aisar ya tashi daga kishinhiɗen da yake, ya kalli Anas ya ce; "Waye Ammar kuma waye Daddinsa da har zai biya maka kuɗi alhalin ni ban san shi ba." Murmushi Anas yayi ya ce; "Ai abokina ne a makaranta, kullum idan na kawo shi ku gaisa ba na samun ka a gida, sai dai na kawo shi wajen su Inna da Iya su gaisa sannan ya tafi. Amma ya ce; "In an jima zai zo ya raka ni wajen Daddynsa na yi masa godiya a bisa abin alkhairin da yayi mana, ka ga ai sai mu tafi tare ko." Murmushi Aisar yayi ya ce; "Masha Allah yanzu kenan su Innarka sun san shi Ammar ɗin? E mana Abba duk sun san shi mutumin kirki ne, duk faɗin makarantar nan shi kaɗai ne abokina, su Safna ma duk sun san shi." Girgiza kai Aisar yayi ya ce; "Allah ya kai mu goben sai mu je mu yiwa Daddinnasa godiya ko?" Murmushi Anas yayi ya ce; "Na gode Abbana Allah Ubangiji ya nuna mana goben lafiya" Amin summa amin Anas ayi maza aje a kwanta ka ji, Allah yayi maka albarka. Bayan Anas ya tafi ɗakinsa ya kwanta, sai ga Abban Basma ya dawo daga wajen neman abincinsa, a ƙofar gida ya ajiye motarsa, sannan ya shigo cikin gidan. Bayan ya shiga wajen iyalinsa, jim kaɗan ya fito, ya nufi wajen Aisar, shi kaɗai ya tarar a wajen a kishingiɗe akan tabarma yana sauraron rediyo. Yana ganin Sa'ad ya tashi zaune yana sakin wani murmushi, ya nunawa Sa'ad tabarmar da yake kai a zaune ya ce; "Bismillah zauna mana" babu musu kuwa Sa'ad ya zauna kusa da Aisar ɗin suka fara hirarsu irin ta abokai, waɗanda suka yarda da junansu. A cikin hirar tasu ne Aisar yake faɗawa Sa'ad mahaifin abokin Anas zai samo mishi admission a makarantar horon sojoji ta Kaduna, sosai Sa'ad yayi murna har da hawaye duk da ba shine ya haifi Anas ba, yana matuƙar so da ƙaunar yaron tamkar shine ya haife shi. Dubansa ya kai wajen Aisar ya ce; "A ina mahaifin abokin nasa yake gobe idan Allah ya kai mu sa mu je mu yi masa godiya?" Girgiza kai Aisar yayi ya ce; "Wallahi ban taɓa ganin shi ba, kai ni ban san ma yana da wani aboki ba sai yau ɗin nan na dawo daga kasuwa ya faɗa mini." Amma ya ce; "Wai abokin nasa zai zo gobe ya raka shi wajen mahaifin nasa yayi masa godiya, ka ga idan ya zo zai raka shi sai mu tafi tare ko ya ka gani?". Washe gari da safe ta kama Asabar ɗin ƙarshen wata, saboda haka zaka samu duk kusan ma'aikata manya da ƙanana suna gida. Mahaifin Ammar ne a zaune a wani ƙayataccen falonsa da yake hutawa a irin wannan lokacin, kallon wani wa'azi yake yi a tashar SUNNAH TV. Gaba ɗaya ya tattara hankalinsa da nutsuwarsa akan wa'azin da wani shahararren malami yake gabatarwa, akan ta'addanci da illolinsa. Kwatsam! Ya ga Ammar ya faɗo cikin falon a guje, yana zuwa bai zame ko'ina ba sai akan cinƴar Mahaifinsa. Kallon shi Mahaifin nasa yayi ya ce; "Haba Ammar sai yaushe za ka girma ne, ko so kake ka karya mini cinyoyina tun da sauran ƙwarina?" Murmushi Ammar yayi ya ce; "Wane ni Daddy ai ban isa na karya ka ba, idan kuwa har na karya ka to nima sai na karya kaina." Dariya sosai Daddy yake yi barkwancin Ammar yana matuƙar burge shi, idan yana gida ba shi da abokin hira da ya wuce tilon ɗansa wato Ammar. Kallon Ammar Daddy yayi ya ga bakinsa yana motsi, da alamu dai akwai abin da yake son cewa, murmushi ya sakar wa Ammar ya ce; "Me kake son faɗa ne Ammar?" Sosa kai yayi in ina ya fara magana "dam...dam.....dama, sai kuma yayi shiru ya sunkuyar da kansa ƙasa." "Ammar kenan sarkin kunya, ka buɗe murya ka faɗa min abin da yake cikin ranka, to kai yanzu Ammar idan ba ka faɗa min ba wa ka ke da shi da zaka faɗa masa? Maza ina sauraron ka." Muryarsa har rawa ta rinƙa yi nan take ya fara magana "Dama Daddy Anas ne da na shaida masa, za ka nemo mana admission tare shine ya ce idan kana gida, na faɗa masa zai zo yayi maka godiya, murmushi Daddy yayi ya ce; "Akan wannan abun ne kake ta faman sunne min kai, kamar ka ga wata budurwarka?" to maza ka je ka shaida masa ina gida, dama ina son na ga wannan Anas ɗin da ka ke ta faman bani labarinshi. Da gudu Ammar ya fita daga cikin falon, kai tsaye ƙofar gate ya nufa ya fita, yana zuwa bakin titi ya tari Napep sai unguwar Darmanawa domin ya shaidawa Anas yanzun nan ya zo ya ga Daddynsa yayi masa godiya....✍️ To be continue......📝📝📝 Comment and share _*Hussain Yusuf*_ 07069475482. [12/9, 4:37 PM] ~HUSSAIN YUSUF~: *ANAS MALEEK* *NA* *HUSSAINI YUSUF* *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* _Kuyi haƙurin rashin ji na da kuka yi kwana biyu, wata ƴar matsala ce amma insha Allahu yanzu komai ya dai-dai ta_ *Page 39/40* Har ƙofar gidan su Anas aka kawo shi, kuɗi ya ciro a cikin aljihunsa ya sallami me napep ɗin, ba tare da wata fargaba ba ya kutsa kansa cikin gidan su Anas ɗin. A ƙofa yayi karo da Basma zata fito, kallonta yayi ya ce; "Ke Anas yana nan kuwa?" Girgiza kai ta yi ta ce; "Yana nan breakfast yake yi, murmushi Ammar yayi ya ce; "Don Allah je ki kira mani shi zamu yi wata magana". Komawa cikin gidan ta yi, Anas kuwa yana zaune akan tabarma yana shan shayi, nan kuma ga su Aisar da su Inna gaba ɗayansu dai an haɗu ana karyawa. Basma ce ta shigo da sallamarta, tana zuwa ta ga Safna da Nasreen suna cin ƙosai, ba ta jira sun yi mata tayi ba, ta zura hannu ta fara cin ƙosan. Harararta! Nasreen ta yi ta ce; "Ke haka ake yi da shigowar ki, ba kiyi kowa magana ba, sai kawai ki fara ci mana abinci? Wallahi kika yi wasa ba ki isa ki ƙara ci ba." Ko kallonta Basma ba ta yi ba ta cigaba da cin ƙosanta, gaba ɗaya ta manta da saƙon da aka aikota ta zage tana ta cin ƙosanta har da kora koko, sai da ta ji tayi nak sannan ta ɗago da kanta, tana wani kalle-kalle karaf! Idanunta suka sauka akan Anas.Nan take kuwa ta tuno da aiken da Ammar yayi mata, kallon Anas ta yi ta ce; "Yaya Anas abokin nan naka yana waje ya jiranka mantawa na yi ban faɗa maka ba." A fusace ya kalli Basma ya ce; "Yanzu dama ke aiko ki aka yi shine kika kasa faɗa mini har sai da ki ka ci kika ƙoshi ko? Yanzu yana can yana jirana sai ya ce nayi masa wulaƙanci alhalin ni ban san ma yana jirana ba." Mtsssss! ya ja wani dogon tsaki sannan ya ɗauki takalmansa ya fita waje, Ammar ya gani a zaune akan wani ɗan ƙaramin dakali, yana ta aikin zaman jiransa, sallama Anas yayi masa da sauri ya juyo ya kalli Anas sai ya saki wani murmushi. "Don Allah Ammar ka yi haƙuri, wallahi yarinyar da ka aiko sai yanzu ta faɗa mini kana jirana, amma wallahi kwata-kwata ban san da zuwanka ba. Ko da yake ba komai ai duk laifinka ne" da mamaki Ammar ya kalle shi ya ce; "Laifina kuma Anas bayan jiran da nayi maka? Laifinka mana me yasa da ka zo ba ka shigo daga ciki ba ka tsaya a ƙofa sai ka ce ka zo gidan ƴan yankan kai." Murmushi Ammar yayi ya ce; "Wallahi ni bana son shiga gidan da ba na mu ba, sai naji ni duka a ɗaɗɗaure, na kasa samun sukuni shi yasa wallahi, har zan shiga sai na haɗu da wannan ƙanwar taka Basma za ta fito shi yasa nace ta kirawo min kai sai ka shigar da ni. Amma yanzu tun da gashi ka fito ai kawai sai mu tattauna anan ba sai na shiga ba." "Ohhh! kana nufin nan ba gidanku ba ne shi yasa baza ka sake ba idan ka shi ko?" Murmushi Ammar yayi ya ce; "No Anas ba haka nake nufi ba, kawai dai ba na jin daɗin shiga gidanne kawai" miƙewa tsaye Anas yayi ya dubi Ammar da yake zaune ya ce; "To bari ka ji ba zan taɓa tsayawa na saurare ka ba, indai ba za ka shiga cikin gidanmu ba." Yana gama faɗar haka ya juya ya nufi cikin gidan da sauri kuwa Ammar ya miƙe ya bi bayansa a tare suka shiga cikin gidan. A tare suka ƙarasa shiga ciki, kallon Anas Aisar yayi ya ce "Anas wannan kuma wanene?" Murmushi Anas yayi ya ce "Ammar kenan Abba ya zo ne ya raka ni mu je mu yiwa Daddinsa godiya" murmushi Aisar yayi ya ce "Masha Allah ai tare zamu je don nima nayi masa godiya, akan abin da yayi mana." Murmushin yaƙe Ammar yayi ya ce "A'a Abba ai ba sai ka je ba, tunda Anas za shi kawai ka yi zamanka. Dariya Aisar yayi ya ce "Ai dole ne na je na yiwa Daddinka godiya, domin abin da yayi mana kafin a samu wanda zai yi mana irin shi za'a daɗe sosai. Duk yadda su Anas suka so hana Aisar ya bi su, sai da ya kira Sa'ad suka tafi gidan su Ammar ɗin tare. Cikin falon da ake ajiye baƙi Ammar ya kai su Aisar, shi kuma ya shiga cikin gidan, domin ya shaidawa Daddinsa baƙin da yayi. A falonsa ya zo ya iske shi yana ta faman danna laptop, zuwa yayi ya zauna kusa da shi, ya ce "Daddy ga Anas ɗin ya zo amma......." Kallonshi Daddy yayi ya ce "Amma me?" sunkuyar da kai yayi ya ce "Amma tare da Abban shi muka zo, wai shi ma zai yi maka godiya." Murmushi Daddy yayi ya ce "Masha Allah da bai zo ba ma sai nasa an kirawo min shi, tashi mu je kada su ce an bar su an ƙi kula su." Tashi yayi ya dubi Ammar ya ce "maza ka je ka cewa Lami tayi sauri ta kawo musu ɗan abin taɓawa" tafiya Ammar yayi domin ya faɗawa me aikinsu Lami saƙon Daddinsa. Shi kuma Daddy ya nufi ɗakin baƙin domin ya haɗu da su Aisar. Da sallama ya shigo cikin falon, suna ganin shi suka miƙe tsaye suna mai barka da shigowa. Murmushi Daddy yayi ya ce "Ku zauna mana" zama suka yi, sannan shi ma Daddy ya zauna, dai-dai lokacin Ammar ya shigo shi da Lami hannunta ɗauke da plate da ruwan gora akai, ajiye wa tayi sannan ta tashi ta fita. Shiru ɗakin ya ɗauka na ɗan wani lokaci, Aisar ne yayi ƙarfin halin ce wa "Alhamdulillah Alhaji kamar ba ka san mu ba, mu ne iyayen Anas abokin ɗanka Ammar; mun zo ne domin mu yi maka godiya akan abin alkhairin da kayi mana, ka ce zaka samowa Anas aikin soja" murmushi Daddy yayi ya ce "Ai har na samo musu aikin ma, ƙarshen satin nan ma nake son su tafi domin a fara ba su horo" da gudu Ammar ya tashi ya je da gudu ya rungume Daddy yana ce wa "Nagode Daddyna Allah ya cika maka burinka kai ma, da sauri ya ce "Amin amin ɗana, gobe insha Allahu zaku fara shirin tafiya." Kallonsu Daddy yayi ya ce "Wai ina Anas ɗin ni fa har yanzu ban gan shi ba, kafin Ammar yayi magana Anas ya riga shi ya ce "Ga ni nan Daddy" murmushi Daddy yayi ya ce "Taso mana ka zo kusa da ni ai kaima ka zama ɗana daga yau, cikin sanyin jiki Anas ya miƙe ya je ya zauna kusa da Daddy. Cike da jin daɗi Daddy yake kallonsa, yana sakin wani murmushi ji yake kamar Anas ɗin jininsa ne. Mayar da kallonsa wajen su Aisar yayi ya ce "Insha Allahu a satin nan su Anas za su tafi makarantar horon sojoji ta Kaduna, ba za su dawo ba har sai sun gama karɓar horo. Saukowa su Aisar suka yi daga kan kujerar da suke a zaune, suka dubi Daddy suka ce "Alhaji yadda ka faranta mana kai ma Allah Ubangiji ya faranta maka, Allah ya ji ƙan iyaye da kakanni, murmushi Daddy yayi ya ce "Kai haba don Allah ku tashi mana, da ni da ku ai mun zama ɗaya ta sanadiyyar yaranmu, yanzu abin da nake so da ku shine ku tashi ku je ku shirya domin a satin nan nake son su Ammar su wuce don su karɓi horo da wuri." Tashi tsaye suka yi "To Alhaji mu zamu wuce Allah ya saka da alkhairi" kallonsu Daddy yayi ya ce "To yanzu zaku wuce?" "E wallahi Alhaji zamu fita neman abinci ne" "To ku tsaya ina zuwa" shiga cikin gidan yayi bai daɗe ba, sai ga shi da kuɗi ɗauri biyu ya miƙawa Aisar ɗaya ya miƙawa Sa'ad ɗaya, sannan ya ce "Allah ya kiyaye ya bayar da sa'a" saboda jin daɗi su Aisar kasa yin magana suka yi, suka rasa da bakin da za su yiwa Daddy godiya, domin samun irinsu sai an tona. Murmushi Daddy yayi "Daga yau na ɗauki nauyin karatun Anas, insha Allahu har ya gama ba za'a nemi komai daga wurinku ba." Godiya suka yiwa Daddy sosai sannan suka yi masa sallama suka tafi, amma ba su tafi tare da Anas ba, domin Daddy ya ce "A bar shi tare da Ammar idan yamma ta yi sai ta taho." _*WAYE DADDY*_ Asalin sunansa shine Abubakar, haifaffen jahar Kaduna ne a ƙaramar hukumar Rigasa. Ya gaji dukiya mai yawa a wajen mahaifinsa, kasuwanci ne ya kawo shi garin Kano. Har Allah ya haɗa shi da Aminatu ta je wani ƙaton Mall ɗin shi sayayya, anan ya ganta ya ji ta burge shi, bai tsaya wani ɓata lokaci ba ya tunkare ta, bai sha wahala sosai ba wajen shawo kanta. Ba su ɗauki wani lokaci ba manya suka shiga cikin maganar, aka daidaita sai ga Aminatu ta zama matar Alhaji Abubakar. Shekararsu biyar da yin aure sannan Allah ya albarkaci Amina da samun juna biyu, murna a wajen Alhaji Abubakar ba ta faɗuwa domin sai da yayi ta yiwa ma'aikatansa kyatuttuka saboda burinshi ya cika zai samu zuri'a tare da Aminatu, ƴar Aljanna, domin haka yake kiranta saboda tsananin biyayya da kuma kyautata masa da take yi. A ranar wata Juma'a da safe Amintu ta tashi da matsanancin ciwon mara, tun tana jurewa har ta gagara, tana cikin kitchen tana haɗa musu breakfast Alhaji Abubakar yana zaune a falo ya jiyo ihunta! Ba tare da tsayawa ɓata lokaci ba, yayi cikin kitchen ɗin a guje, a kwance ya tarar da ita jini yana bin ƙafafunta. Da taimakon wata ƴar aikinsu suka canja mata kaya, sannan suka saka ta a mota sai Asibiti, da sauri likitoci suka hau kanta don ceto rayuwarta. Sai da suka ɗauki dogon lokaci sannan babban likitan ya fito, ya ce "Alhaji ya biyo shi office" da sauri Alhaji Abubakar ya bi shi, domin ya matsu ya ji halin da matarshi take ciki, bayan likitan ya zauna sai ya dubi Alhaji Abubakar ya ce "Ka daina damuwa haka Alhaji, ba wata matsala ce babba ba haihuwa ce ta zowa matarka amma ta zubar da jini da yawa, don haka muna buƙatar jini yanzu cikin gaggawa" da sauri Alhaji Abubakar ya ce "Likita me kake jira ba gani ba a ɗauka a jikina mana" murmushi likita yayi ya ce "Ai sai mun gwada idan yayi dai-dai da nata sai mu ɗauka." An gwada jinin Alhaji cikin ikon Allah yayi dai-dai dana matarsa Aminatu, aka saka mata, jinin yana ƙarewa wata naƙudar ta sake zuwar mata. Bata daɗe tana yi ba ta haifo santalelen jaririnta, mai kama da ita sak, Alhaji Abubakar saboda tsananin murna rasa inda zai saka kansa yayi, bayan an kaita ɗakin hutu ya je ya ganta ga jaririn a gefenta cikin tawul yana ta barci abinsa. Cike da zumuɗi Alhaji Abubakar ya sunkuya ya ɗauke shi ya sumbace shi a goshi...... To be continue......📝📝📝 _*Hussaini Yusuf*_ [12/9, 4:37 PM] ~HUSSAIN YUSUF~: *ANAS MALEEK* *NA* *HUSSAINI YUSUF* *______________________________* *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *______________________________* *Page 41/42* Alhaji Abubakar ya sunkuya ya ɗauke shi, ya sumbace shi a goshi, harararsa Amina ta yi ta ce "Wato ta ɗanka ka ke yi ko kula ni" da sauri ya juyo ya kalleta ya sakar mata wani lallausan murmushi ya ce "Kiyi haƙuri matata wallahi zumuɗine ya ke ɗibana kiyi haƙuri kin ji" ita ma yayi mata kiss a goshi, sannan ya samu waje gefen gadon da take zaune ya zauna. Ƙura mata ido yayi ya daɗe yana kallonta kafin ya ce "Yanzu dai da fatan babu inda yake yi ciwo" gigiza masa kai ta yi ta wani ɗan yatsina fuska ta ce "Ni babu inda yake yi min ciwo, na gaji ma da zaman asibitin nan ka je ka kira likita ya bani sallama." Murmushi Alhaji Abubakar yayi kafin ya ce "Haba ke kuwa Ƴar Aljanna me kike faɗa haka? ki bari ka sake warwarewa mana sai mu karɓi sallamar, kawar da kanta gefe ta yi kamar za ta yi kuka ta ce "Ni dai ka je ka kirawo min likita ya sallame ni, don na tsani zaman asibiti gaba ɗaya wallahi." Ba yadda ya iya tashi yayi ya nufi office ɗin likitan, a zaune ya same shi yana duba files, sallama yayi masa kafin ya samu wurin zama, bayan ya zauna ya dubi likita ya ce "Likita Madam ce wallahi ta damu a bata sallama wai ita ta matsu ta tafi gida" murmushi Likita yayi ya ce "Ko kwana fa bata yi ba ta ke cewa haka" ƴar dariya Alhaji abubakar yayi ya ce "Likita ka san halin Madam ɗin da rigima" numfasawa Likita yayi ya ce "Ok to bari na je ba duba ta idan babu matsala sai na baku sallamar. A zaune suka zo suka sameta riƙe da jaririnta yana kan cinƴarta tana ta sakar masa murmushi, zuwa Likita yayi ya ce "Haba Madam ki bari ki ƙara warwarewa mana sai na baku sallamar sannan kin gama warwarewa gaba ɗaya. Ɗan ɓata fuska ta yi ta kalli Alhaji Abubakar ta kawar da kai, da sauri ya kalli Likita ya ce "Kawai ka ba mu sallamar tun da ta matsa, sai ta sake warwarewa a gida" sai da Likita ya ƙara duba ta sosai, sannan ya rubuta mata takardar sallamar, tare da wasu ƴan magunguna. Bayan sun dawo gida ƴan'uwa da abokan arziƙi suka yi ta zuwa suna yi musu barka, kowa idan ya zo sai ya yaba da kyawun jaririn. Abokan Alhaji Abubakar suka yi ta kawo masa kyaututtuka masu yawan gaske, Amina ma ta samu kyaututtuka daga wajen matan abokan mijinta, da ƙawayenta da kuma danginta. Da satin haihuwar ya zagayo aka raɗa wa yaron suna KAMALUDDEN amma ana kiransa da AMMAR saboda sunan mahaifin Amina aka saka masa. An sha shagali sosai har walima aka yi, an ci an sha sosai abokan Alhaji sun zo sun taya shi murnar samun ɗa namiji da yayi. Bayan suna sosai suka mayar da hankalinsu wajen kula da tilon ɗansu na fari, lokacin kuma arziƙin Alhaji Abubakar ya ƙara bunƙasa, har company ya gina sosai ga manyan shaguna a cikin kasuwanin cikin Kano. Lokacin da Ammar ya cika shekara biyu da rabi, har an saka shi a makaranta irin ta ƙananun yaran nan, sosai yake samun kulawa daga hannun iyayensa ko kaɗan ba sa barin shi yayi kukan rashin wani abu da suka fi ƙarfinsa. Wata rana da safiyar Juma'a, Amina ta tashi da wani irin matsanancin ciwon ciki, Alhaji Abubakar bai jira wani abu ba, ya ɗauke ta yayi asibiti da ita, anan Likita ya shaida masa tana ɗauke da wani sabon juna biyun, sosai Alhaji ya rinƙa murna kamar wannan ce haihuwarsa ta farko. Sosai Amina ta rinƙa samun kulawa daga wajen Alhaji Abubakar, duk da farko Amina ta nuna ƙin amincewarta akan cikin domin ba ta daɗe da yaye Ammar ba ta kuma samun wani juna biyun, ta nunawa Alhaji a zubar da cikin, fir ya ƙi amincewa kuma ya ce "Indai ta kuskura ta zubar da cikin nan sai ya ɗauki mummunan mataki akanta" ba yadda ta iya haka ta haƙura ta cigaba da rainon cikin, har ya cika wata tara. A safiyar wata Juma'a ne Amina ta tashi da naƙuda, babu ɓata lokaci aka kaita asibiti, likitoci ne suka taru akanta domin bata taimakon gaggawa, bayan an ɗauki tsawon mintina. Sai ga ɗaya daga cikin likitocin ya fito yana share zufa, tamkar wanda ya shafe awanni a cikin ɗaki mai zafin gaske, kallon Alhaji Abubakar yayi ya ga yadda duk ya bi ya fita daga hayyacinsa, kamar wanda aka yiwa alƙawarin barin duniya. Shi ma Alhaji Abubakar idanu ya ƙurawa likita, bakinsa yana ta motsi alamun yana da magana a baki amma ya kasa furta ta. Alama likita yayi masa da ya biyo shi office, bai tsaya wani ɓata lokaci ba, ya tashi da ɗan sassarfarsa ya bi bayan likitan, bayan likita ya zauna shi ma Alhaji Abubakar ɗin ya nemi waje ya zauna yana mai fuskantar likita tamkar ɗalibi a gaban malami. Wani gwauron numfashi likita ya ajiye, tamkar wanda ya daɗe bai shaƙi iska ba, ko kuma wanda aka shaƙewa wuya ya ɗan daɗe bai shaƙi iska ba. Cike da ƙwarin gwiwa ya shiga yi wa Alhaji bayani "Maganar gaskiya Alhaji matarka ba za ta iya haihuwa da kanta ba, har sai an yi mata aiki" wani matsiyacin kallo Alhaji ya jefi likita da shi, ya ƙura masa manyan idanunsa da suka firfito waje tamkar na mujiya. "Yanzu likita kana nufin sai kun yiwa Aminata ƴar Aljanna aiki sannan za ta iya haihuwa da kanta? ƙwarai da gaske kuwa Alhaji domin mun yi iyakar bakin ƙoƙarinmu amma ta kasa haihuwa." Ajiyar zuciya Alhaji Abubakar ya ajiye, shiru office ɗin ya ɗauka na mintuna kamar maye ya ci shirwa, likita ne yayi ƙarfin halin ce wa "Alhaji lokaci fa yana tafiya amincewarka kawai muke buƙata, domin maganar gaskiya matarka tana mawuyacin hali" da sauri Alhaji Abubakar ya dubi likita ya ce "Na amince likita indai za ta haihu lafiya" wata farar takarda likita ya ajiye masa ya ce ya saka hannu, ba tare da wani ɓata lokaci ba Alhaji ABUBAKAR ya sanya hannu a farar takardar. Nan take kuwa aka shiga da Amina cikin ɗakin tiyata, tun da aka shiga da ita gaban Alhaji ya rinƙa faɗuwa gani yake yi kamar baza'a fito da ita da rai ba, zuciyarsa raya masa take kamar ya rabu da matarsa, rabuwa ta har abada. Shaiɗan sai faman wasa yake yi masa da zuciyarsa wajen saƙa masa abubuwa marasa daɗi game da aikin da ake yi wa matarsa. Bayan kamar awanni biyu, sai ga likita ya fito daga ɗakin tiyatar yana ta faman share zufa, bai daɗe da fitowa ba sai ga nurses sun fito da Amina akan gado tamkar gawa cikin hanzari suka tura gadon zuwa wani ɗaki. Da gudu Alhaji Abubakar ya yunƙura zai bi bayansu, riƙe hannunshi likita yayi ya ce "Haba Alhaji ka tsaya na yi maka bayani mana za ka tafi ka barni a tsaye" sosa kai ya shiga yi tamkar wanda ba shi da gaskiya, muryar likita ce ta doki dodon kunnensa yana ce wa "Alhaji ka yi haƙuri ɗan bai zo da rai ba, sannan ita ma Aminar tana matuƙar shan wahala" yunƙura Alhaji Abubakar yayi ya nufi ɗakin da aka kwantar da Aminar, da sauri likita ya sake dakatar da shi a karo na biyu, ya ce "Haba Alhaji ka tsaya mana na je na sake dubata sannan sai na ba ka izinin ganinta. Ba yadda ya iya juyo wa yayi ya nemi kujera anan reception ya zauna ya zuba tagumi, gaba ɗaya kewar matarsa ta dame shi, so yake ya ganta ko sau ɗaya ne amma likita ya hana shi, shi da matarsa. Yana sunkuye da kansa tunani kala-kala sun cika masa zuciya, ya rasa yadda zai yi ya kasa controlling ɗin kansa akan abun da yake ji game da Amina kewarta ta dame shi sosai, yana cikin tunanin shi ya ɗago kansa karaf! idanunsa suka sauka akan ƴar aikinsu Lami tana ɗauke da Ammar a hannunta, ɗayan hannun kuma ɗauke da kula ta abinci......✍️ To be continue.....📝📝📝 *Hussaini Yusuf✍️* [12/9, 4:37 PM] ~HUSSAIN YUSUF~: *ANAS MALEEK* *NA* *HUSSAINI YUSUF* *______________________________* *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu Ƴancinmu* *______________________________* *Page 43/44* Ammar yana gano mahaifinsa, ya kama mutsu-mutsu dole Lami ta yarda ta sauke shi, aikuwa tana sauke shi ya tafi da gudu wajen Mahaifinsa. Shi ma kuwa da ɗan gudunsa ya zo ya rungume ɗan nasa a ƙirjinsa, yana jin wata ƙaunarsa tana ratsa sassan jikinsa. Ɗaukar shi yayi ya nufi inda yake zaune, ya zauna ya zaunar da Ammar ɗin akan cinyarsa, dai-dai lokacin Lami ta ƙaraso wajen har ƙasa ta durƙusa ta gaisar da Alhaji fuska a sake ya amsa mata. Ajiye abincin ta yi ta ce "Abban Ammar abinci ne na kawo muku" murmushi yayi ya ce "Haba Lami da kin bar abincin nan yanzu ba tashi muke yi ba, har yanzu ban san a halin da Amina ƴar Aljanna take ciki ba" tsinkayo muryar Ammar suka yi yana cewa "Daddy ina Ummata take?" Kafin Daddy ya bashi amsa sai ga wata nurse ta zo a gigice ta dubi Daddy ta ce "Kai ne mijin waccan marar lafiyar wacce aka yiwa operat........Kafin ta ƙarasa ya riga ta ya ce "E nine, to kayi sauri ka zo tana son ganin......" Ai kafin ta ƙarasa ya ɗauki Ammar yayi cikin ɗauki da gudu. Cikin sanyin jiki Lami ta bi bayansu zuwa cikin ɗakin, a kwance take akan gado idan ka ganta baza kayi zaton tana tare da numfashinta ba, bata iya yin ƙwaƙƙwaran motsi ko hannunta ba ta iya ɗagawa. Da kyar da siɗin goshi ta juyo da kanta ta fuskanci mijinta da ɗanta, da suka daɗe a tsaye suna kallonta, wasu zafafan hawaye ne suka kwaranyo daga cikin shanyayyun idanunta, cikin ƙarfin hali ta miƙo hannu alamun ɗanta Ammar ya je kusa da ita, da sauri Alhaji Abubakar ya miƙa shi, ƙaƙalo wani murmushi ta yi ta shafa kansa ta ce "Allah yayi maka albarka Ammar, Allah ya raya ka cikin Addinin Musulunci". Sannan ta juyar da idanunta akan mijinta, da ya ƙura mata idanu ya kasa furta ko da kalma ɗaya ne, ya tafi can wata duniya daban ta tunani, tun da ya ga matarsa a cikin wannan halin gaba ɗaya ya nemi nutsuwarsa ya rasa, tunani ne kala-kala suka cika masa rai, ba ya so ya rabu da matarsa abar alfaharinsa, mace ɗaya tamkar da dubu tun da ya aureta ba ta taɓa ɓata masa rai ba, idan ma ta yi masa wani abun da ransa bai so ba, idan ta kalli fuskarsa ta ga alamun bai ji daɗin abin da ta yi masa ba, to nan take ba shi haƙuri hankalinta ba ya kwanciya har sai ta gan shi ya dawo cikin nishaɗi da walwala. Muryarta ce ta dawo da shi daga can wata duniyar da ya tafi, "Alhaji don Allah ga Ammar nan na bar maka shi amana, ka kula min da shi ka yi ƙoƙari ka ba shi tarbiyya irin ta Addinin Musulunci, domin ni yanzu tawa ta ƙare na tabbatar ba zan tashi daga wannan ciwon ba." fashewa da kuka Alhaji Abubakar yayi tamkar wani ƙaramin yaro, Ammar ma ganin Daddinshi yana kuka sai shi ma ya fashe da kukan, aka rasa mai rarrashin wani a tsakaninsu. Sunkuyawa Alhaji Abubakar yayi dai-dai fuskar Amina, hannayenta ya kamo ya riƙe su sosai. Sai faman matsa su yake yi, bakinsa yana ta motsi alamun magana yake son furtawa amma bakinsa yayi masa nauyi. Cikin raunin murya ya fara magana yana ce wa "Haba Aminatu bai kamata zafin ciwo yasa ki rinƙa faɗin irin waɗannan kalaman ba." "Ki sani cuta ba mutuwa ba ce sai kwana ya ƙare, ke kuwa na ki kwanan bai ƙare ba. Hawaye ne ya zubo daga idanunta, da ƙyar ta iya buɗar baki ta ce "Don Allah mijina ka kula min da ɗana ka riƙe duk abin da na faɗa mak......" Tana kai wa nan muryarta ta sarƙe, ta kasa cigaba da furta kalma ɗaya sai Kalimatush-shahada kaɗai Allah ya bata ikon furtawa. Tana kammala biyawa kuwa tace "Ga garinku nan". Da gudu Alhaji Abubakar ya tafi kiran likita, ba su wani dogon lokaci ba sai ga su sun shigo a tare. Likita yana ƙarasawa kanta, ya ji jikinsa yayi sanyi. ɗaga hannunta yayi ya ga ya dawo, bayan ya gama aune-aunen da zai yi ya gama sai ya ja mayafi ya rufe mata fuskarta. Ya juyo ya kalli Alhaji Abubakar ya ce "Alhaji sai dai haƙuri fa domin Amina ta riga mu gidan gaskiya" Tashin hankali......Wanda ba'a saka masa rana. Zubewa Alhaji Abubakar yayi a wajen, yana ta wani irin haki abin tausayi. Da sauri likita ya riƙe shi ya buɗa fridge ya ɗauko ruwa ya bashi kaɗan ya kurɓa sannan ya ji zuciyarsa ta fara yi masa sanyi. Da kyar ya samu ya rarrafa kan gawar Aminar, rungume ta yayi ya fashe da wani irin kuka mai ban tausayi. Ammar ma da yake yaro bai san komai ba a lokacin, ganin mahaifinshi yana kuka shi ma sai ya rushe da kuka. Da kyar likita ya rarrashi Alhaji ya daina kukan. Wayarsa ya ɗauko daga cikin aljihu, ya kira ƴan'uwa da abokan arziƙi ya sanar da su rasuwar Amina. Kowa idan ya samu labarin sai ya girgiza, saboda Amina mace ce mutunci da kima a wajen mijinta da dukkan wanda ya santa. Tana da hali mai kyau, babu ruwanta da shiga abin da bai shafe ta ba, iyakar kyautatawa tana yi wa mijinta shi yasa yake jin ba zai taɓa samun kamarta ba. Cikin ƙanƙanin lokaci aka yi mata wanka da sallah. Aka ɗauketa aka kaita gidanta na gaskita, ya Allah ka sa mu cika da imani don alfarmar Annabinka sallallahu alaihi wasallam. Bayan rasuwar Amina Alhaji ya sa a ranshi, ba zai sake yin aure ba har sai Ammar ya girma ya mallaki hankalin kansa. Babu yadda ƴan'uwansa ba su yi masa ba, akan ya ƙara aure amma ya ce musu ba yanzu ba. Sai Ammar ya girma domin ba ya son ya je ya auro wacce za ta wahalar masa da tilon ɗansa Ammar. Tun Ammar yana yaro yake da burin zama soja, kullum idan suka zauna shi da mahaifinsa ban da zancen sojoji babu abin da yake yi masa. Shi kuwa ya ɗauki wannan buri na ɗansa ya sanya a ransa da ƙudurin sai ya cika masa shi. Wannan shine labarin Ammar abokin Anas. CIGABAN LABARI Shirye-shirye su Anas suke yi sosai, Aisar da kansa ya shiga kasuwa yayi ta siyowa su Anas abubuwan da ya kamata ya tafi da su. Da ranar tafiya ta zo, Inna har kuka ta saka. Ji take kamar kar ta bar Anas ya tafi, tana matuƙar son su shi da Safna fiye da kowa a rayuwarta. Aisar ma ji yayi duk duniyar babu daɗi domin ya shaƙu da Anas shaƙuwa mai tsanani.Nasiha mai ratsa jiki Inna da Aisar suka yi masa har ma da Sa'ad sai da yayi masa tasa nasihar. Gaba ɗayansu suka ɗunguma suka tafi raka shi gidan Alhaji Abubakar, suna zuwa kuwa suka iske har Ammar ɗin ya gama shiryawa yana zaune Alhaji Abubakar yana ta yi masa nasiha da jan hankali. Bayan Daddy ya gama yi wa Ammar tasa nasihar, da kansa ya ja hannunsu shi da Anas. Bakin wata mota suka zo suka tsaya, da gudu wani direba ya zo ya buɗe musu suka shiga. Sannan ya nunawa su Aisar wata motar, suka shiga wani direba ya zo ya ja suka tafi. AMINU KANO INTERNATIONAL AIRPORT suka nufa kai tsaye. cikin ƙanƙanin lokaci kuwa suka isa, bayan sun yi parking kowa ya fito. Inna ce ta kirawo Anas yana zuwa kusa da ita, kallon shi ta yi, ta kasa magana. Wuf ta yi ta rungumeshi ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya. Da kyar ya samu Inna ta sake shi, aikuwa tana sakinshi ya ɗauki jakarsa ya nufi inda jirgin yake a ajiye. Tunda Alhaji Abubakar ya ƙyalla idanu ya ga Inna, nan take ya ji ta burge shi, cikin salo da dabara ya tambayi Aisar ya ce "Waccan ita ce mahaifiyar Anas?" Amsa masa Aisar yayi, nan ya shiga ba shi labarin haɗuwarsu da Anas da kuma ita Innar tasu. Bayan su Anas sun gama shiga cikin jirgin, ba tare da ɓata lokaci ba ya tashi ya nufi Kaduna. Su Anas kuwa sai murna ake yau za'a shiga NIGERIAN DEFENCE ACADEMY (N.D.A) cikin kankanin lokaci suka isa nan Kadunar. Neman mai taxi suka yi, ya ɗauke su ya kai su cikin makarantar. Daddy kuwa tun da ya koma gida, tunanin Inna ne ya hana shi sukuni. Tabbas ya ji zuciyarsa ta gamsu da halayen Inna, yadda ya ga ta rungume ɗanta tana kuka ya san idan ya aureta baza ta wulaƙanta masa Ammar ba. Kasa daurewa yayi, ya ɗauki waya ya kira Aisar ya ce "Ya zo gida ya same shi za su yi wata magana mai muhimmanci." Ba tare da ɓata wani lokaci ba, Aisar ya nufi gidan Alhaji Abubakar, yana zuwa kuwa ya buɗe ya shiga mai gadi bai yi yunƙurin hana shi saboda har sun yi sabo a ɗan zuwan da yake yi. A wani ƙayataccen falo ya samu Alhaji Abubakar a zaune, yana kurɓar juice a cikin kofi. Sallama yayi masa sannan ya samu wuri a ƙasa ya zauna, da sauri Alhaji Abubakar ya ce "A'a tashi mana ka dawo kan kujera". Tashi Aisar yayi ya koma kan kujerar ya zauna yana mai fuskantar Alhaji Abubakar, wani ɗan murmushi ya saki ya ce "Aisaru wata muhimmiyar magana za mu yi ni da kai, shi yasa na kirawo ka." Gyara zama Aisar yayi ya ce "To Alhaji ina sauraronka" gyaran murya yayi kafin ya fara ce wa "Aisaru ya sunan mahaifiyar Anas?" murmushi Aisar yayi ya ce "Alhaji sunanta Saratu amma muna kiranta da Inna." Murmushi Alhaji Abubakar yayi ya ce "Masha Allah" sannan ya cigaba da ce wa "Maganar gaskiya Aisaru ba zan ɓoye maka ba, daga lokacin da naga wannan matar na ji ina son ta kasance a matsayin matata." Murmushi Aisar yayi ya ce "Amma na ji daɗi sosai Alhaji amma kafin nan ta ina kake son na taimaka maka?" "Yawwa Aisaru an zo dai-dai wajen da nake so, yanzu so nake ka shawo min kanta ta amince da ni kafin na fara zuwa wajenta mu fahimci juna." "Indai wannan ne Alhaji ba ka da damuwa, yau ɗin nan insha Allahu zan isar mata da saƙonka mu ji yadda za ta amshe shi." Da sauri Alhaji Abubakar ya ce "Yawwa Aisar ka daure ka faɗa mata mu ji yadda zata amshi wannan ƙudurin nawa." "Baka da damuwa Alhaji zan faɗa mata duk yadda muka yi da ita zan sanar da kai ta waya" miƙewa Aisar yayi ya ce "Alhaji ni zan koma" godiya sosai Alhaji Abubakar ya rinƙa yi wa Aisar kamar wanda ya ba shi wata gagarumar kyauta. A hanya kuwa Aisar sai faman tunanin yadda zai tunkari Inna da wannan labarin yake yi. Domin yana matuƙar jin kunyarta da nauyinta don haka kawai ya yanke shawarar zai sanar da Iya sai ta sanar da ita. Su Safna da Nasreen da Basma da suka dawo daga makaranta aka shaida musu Anas ya tafi makarantar horon sojoji. Safna da Nasreen wuni suka yi suna kuka, Basma ce ma ta saki ranta don bata yi wani sabo mai yawa da Anas ba. Haka suka ƙari ƙuncinsu suka gama, har kewar Anas ɗin ta sake su sosai suka saki ransu, sai kuma suka hau lissafin kwanakin tafiyar Anas. Da dare yayi Aisar ya je har ɗakin Iya, ya sanar da ita saƙon Alhaji Abubakar, ya roƙi da ta sanar da Inna idan ya so da safe sai ta sanar da shi amsar da ita Innar ta bayar. Yana gama faɗa mata ya tashi ya fita, yana fitowa sai ga Inna ta fito daga banɗaki, gaisar da ita Aisar yayi sannan ya nufi ɗakin Ummu Nasreen. Inna tana shiga ta tarar da Iya tana shirin kwanciya, fasa kwanciyar ta yi ta ce "Saratu zo nan ina son magana da ke" zuwa ta yi kusa da Inna ta zauna tana mai fuskantar ta. Gyara zama Iya ta yi ta ce "Saratu a yanzu idan ki ka samu miji zaki yi aure kuwa?" Duƙar da kai Inna ta yi tayi shiru............✍🏻 To be continue.......📝📝📝 *Hussaini Yusuf✍️* [12/9, 4:38 PM] ~HUSSAIN YUSUF~: *ANAS MALEEK* *NA* *HUSSAINI YUSUF* *_______________________________* *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *______________________________* *Page 45/46* Sai da Iya ta maimaita tambayar sannan Inna ta yi gyaran murya ta ce "Me zai hana Iya idan na samu mijin da ya dace da ni." "Yawwa yanzu nima gani na yi da zamanki haka gara ace kin yi aurenki, shine zai ƙara fito miki da darajarki da kimarki" Iya ce ta cigaba da ce wa "A yanzu haka da nake yi miki wannan zancen, akwai wanda ya aiko yana neman aurenki idan kin amince." Zaro idanu Inna ta yi ta ce "Ni kuma? ni da ba na fita yawo ko ina, a ina ya gan ni har ya ce yana so na da aure?" Murmushi Iya ta saki ta ce "Sai na faɗa miki sunan mutumin ma sannan zaki yi mamaki" da sauri ta ce "Waye wannan Iya?" Iya ce ta cigaba da ce wa "Ni dai abu ɗaya nake nema a wajenki Saratu, don Allah ki amshi maganar mutumin nan hannu biyu, domin mutumin kirki ne. Ba wani ba ne ya aiko yana neman aurenki sai Alhaji Abubakar mahaifin Ammar." Domin yayi miki kyakkyawar shaida ya ce yana da yaƙinin ke ce kaɗai zaki iya riƙe masa tilon ɗansa Ammar. Shiru Iya ta yi tana sauraron Inna domin ta ji amsar da zata bata, sai da Inna ta ɗauki dogon lokaci sannan ta ɗago da kanta ta ce "Iya ina son ki bani lokaci domin in yi shawara da zuciyata." Babu yadda ta iya dole ta bar ta domin ta yi shawarar, amma sai ta ce "Kafin gobe da safe ta tabbatar ta yanke shawarar da zata yi, domin ta sanar da ita amsar." Tashi Inna ta yi ta shige cikin ɗakin da yake cikin falon, kwanciya ta yi amma tunani kala-kala sun cika mata zuciya. Tsakaninta da Allah har yanzu ba ta daina son tsohon mijinta ba, mahaifin su Anas har yanzu zuciyarta ba ta daina tunani da begenshi ba duk da yanzu ba ta tabbatar yana raye ba. **** **** **** Su Anas sosai suke karɓar horon da ake ba su, sun sha wahala sosai kafin jikinsu ya saba da horon. Cikin ƙanƙanin lokaci jikin Anas da Ammar ya fara murɗewa, suka fara tara damtse, idan ka gan su sai kayi zaton irin manyan mutanen nan ne masu ƙirar samudawa. Har wata ƙasumba Anas ya tara, ƙirjinsa ya kumbura sosai kamar na mace. Anas irin mutanen nan ne, da ba za ka ga ƙirar da Allah yayi musu ba idan suna sanye da kaya, amma idan babu kaya a jikinshi ka gan shi sai kayi zaton kamar dutse aka cusa masa a damatsansa, saboda ƙirar da Allah yayi masa. Haka Ammar ma yake idan ka gan shi jikinsa duk ya murɗe, shi ji yake ma kamar ya gama karɓar horo kawai ɓata musu lokaci ake yi. Yau za'a fara koya musu harbi da bindiga, sosai Anas yake murna saboda babban burinsa a aikin soja shine ya gan shi ya riƙe bindiga yana harbi. Anas bai sha wata wahala ba wajen koyon harbin, domin da can ma yana harbin tsuntsaye da danƙo don haka ya iya saiti sosai. Haka Ammar ma shi ya ɗan sha wahala kafin ya gama koya, kafin wasu watanni sun ƙware a harbi sosai, yadda ba ka zato. *BAYAN SHEKARA BIYU* Sanye su ke cikin kakin soja, sun yi layi irin na sojoji suna jiran umarni. Wani babban soja ne ya zo ya tsaya a gabansu. Bayani ya shiga yi musu, "Yanzu dai ku ne zaɓaɓɓu kuma horarrun sojojin da zamu yi aiki da su, ina fatan zaku ba mu haɗin kai?" Gaba ɗayansu suka amsa "Insha Allahu yallaɓai" murmushin jin daɗi babban sojan yayi ya ce "Za mu je yaƙar wani hatsabibin ɗanta'adda ne a can jahar Taraba a yankin Mambila, mai suna Sa'id bn Abdul'aziz" ko da Anas ya ji sunan ɗanta'addan nan take tsigar jikinsa ta tashi. Kowanne gashi da ya je jikinsa ya miƙe, jikinsa ya hau tsuma tamkar wanda ya ke jin sanyi, saboda tsananin ɓacin ran da ya shiga. Ba zai taɓa mantawa da fuskar ɗanta'addan nan ba. Shine silar barin garinsu, shine ya kashe masa mahaifinsa, sannan ya mayar da yara sama da ɗari biyu marayu a ƙauyensu. Don haka duk yadda zai yi sai ya yi wa Sa'id bn Abdul'aziz kisan wulakanci wanda ba'a taɓa yi wa wani mahaluƙi a bayan ƙasa ba. Muryar shugaban nasu ne ya katse masa tunaninsa.... "Don haka yanzu zamu bar ku ku je gidaku huta, sosai sannan ku dawo da niyyar fita filin daga. A tare suka haɗa baki suka ce "Thank you sir" sannan suka juya da fareti suka bar filin taron. Sai faman haɗa kaya Anas yake yi, zuciyarsa cike da farinciki yau zai je ya ga danginsa wanda rabonsa da su yau shekara biyu da watanni, amma musababbin murnar ta shi ita ce yau zai yi tozali da fuskar da ya daɗe yana mafarki, tunaninta ya hana shi sakat gaba ɗaya ba shi da walwala ko kaɗan. Amma da zarar ya tuno da kyakkyawar fuskarta sai ya ji nan take zuciyarsa ta yi fari sai ya ji tamkar an shiga zuciyarsa an saka hannu an zare masa duk wata damuwarshi. Yanzu ma sai faman murmushi yake zubawa kamar gonar auduga. Ammar ne ya shigo ɗakin ya gan shi yana haɗa kaya yana murmushi, zama yayi kurum ya zubawa abokin nasa idanu yana mamaki. "Wannan wacce yarinya ce da take hana Anas sakewa?" Shi kaɗai yake yi wa zuciyarsa waɗannan tambayoyin, amma ko kaɗan bai samu amsar su ba. Ganin wankin hula yana niyyar kai su dare sai ya kada baki ya ce "Anas don Allah wace ce wannan yarinyar da take yawan shiga cikin tunaninka tana hana maka walwala da jin daɗi?" Murmushi kawai Anas yayi ya ce "Me kake ci ba baka na zuba? Idan ka yi haƙuri da zarar mun koma gida zaka ga ko wacece wannan yarinyar, da take sanyani nishadi da walwala a koda yaushe....." Shi ma Ammar ɗin kawai yayi ya ce "Idan ta yi tsami ai zamu ji" daga haka bai ƙara cewa komai ba shi ma ya duƙa ya fara haɗa kayansa a cikin jakarsa, domin ƙarfe huɗu da rabi jirginsu zai tashi zuwa Kano. ***** ******** ***** Gaba ɗaya gidan murna suke yi yau Anas zai dawo, sai faman girke-girke ake yi. Safna da Nasreen ma sun fi kowa murna domin ba ƙaramin kewar Anas suke yi ba, tun suna irga kwanakin da yake yi har suka dawo irga sati sai watanni ga shi yau shekararsa biyu baya tare da su dole ne su yi kewarsa. Ita kuwa Basma ko a jikinta domin a cewarta "Kada Allah yasa ma Yaya Anas ɗin ya dawo" domin tun yana nan haushi yake bata ba kaɗan ba, akan yana yawan yi musu faɗa. Ƙarfe 6:00pm dai-dai gaba ɗaya ƴan gidan suka shirya suka nufi AMINU KANO INTERNATIONAL AIRPOT domin taron Anas da ya shaida musu jirginsu ya taso. Ko kaɗan Safna ta kasa ɓoye murnarta, ji take kamar ta je can Kadunar su dawo tare da Anas ɗin saboda zumuɗi. Zaune suke a reception sun zubawa sararin samaniya idanu, jira kawai suke yi su ga dirar jirgin, ƙarfe shida dai-dai sai ga shi na ya keto gajimare yana yin ƙasa-ƙasa alamun sauka yake son yi.....Ba'a ɗauki wani dogon lokaci ba, jirgin ya gama sauka, a hankali aka buɗe murfin jirgin nan da nan mutane suka fara sauka...... Gaba ɗaya dangin Anas sun zuba ido su ga Anas, can suka hango shi shi da Ammar kowanne riƙe da jakarsa a hannu yana ja, ai da gudu Safna da Nasreen suka tafi suna rungume shi, suna ce wa "Yaya Anas sannu da dawo wa". Hango Basma yayi can wajen su Aisar a tsaye ta haɗe rai, ko kaɗan babu alamun fara'a a fuskarta, gani yayi gaba ɗaya ƴan'matan sun ƙara girma sun zama cikakkun ƴan'mata. Ƙurawa Basma ido yayi ya ga ta yi wani haske, ta ƙara kyau sai a lokacin ya gama ƙarewa Basma kallo kyakkyawa ce ajin farko. Wannan ɗan ɓata ran da ta yi, sai ya ƙarawa fuskarta wani irin sihirtaccen kyau. A hankali ya ƙarasa wajensu, ya gaisa da Aisar da Sa'ad sannan ya je ya gaisa da su Inna da Iya. Dai-dai lokacin Alhaji Abubakar ya aiko da motoci biyu domin a kwashe su, gaba ɗaya aka kwashe su sai gida. Maimakon Anas ya ga an nufi gidansu da ya sani, sai ya ga an nufi cikin unguwar Hausawa estate. A ƙofar wani ƙerarren gida na gani na faɗa motar tayi parking, danna horn direban nasu yayi sai ga shi nan da nan gate man din ya zo ya wangame gate ɗin. Shi kuwa Ammar tuni direban shi ya wuce da shi can gidan mahaifinsa amma ya ce wa Anas zai zo su gaisa da mutanen gidan. Motsi bakin Anas yake yi, alamun yana son tambayar wanne gida ne wannan, da sauri Aisar ya dakatar da shi ya ce "Ya tsaya sai sun zauna." Bayan sun shiga falon kowa ya zauna, Aisar yasa Safna ta kawo wa Anas ruwa mai sanyi, karɓa yayi ya sha, sannan ya ajiye ajiyar zuciya. Kallon Inna yayi ya ga ta warware ta ƙara haske, ainihin haskenta na bafulatanar usuli ya fito, ta ƙara yin ƙiba sosai. Wani irin daɗi ne ya ziyarci zuciyar Anas saboda ya dawo ya iske ahalinsa a cikin walwala da kwanciyar hankali fiye da yadda ya tafi ya bar su. Aisar ne yayi gyaran murya ya ce "Da fatan dai Anas an samu abin da aka fita nema?" Sunkuyar da kansa ƙasa yayi ya ce "Insha Allahu Baffa mun samu, yanzu mun gama karɓar horo, kuma kafin a gama hora mu ma, wajen sau biyar muna fita yaƙi kuma cikin ikon Allah duk muna cin nasara. Yanzu ma an ba mu hutu ne, na wata biyu kacal, idan mun koma zamu fita wani babban yaƙi wanda ba iya tawagar mune kaɗai za su je ba. Murmushi Sa'ad yayi ya ce "Yanzu ɗana kenan ya zama babban soja" sunkuyar da kai Anas yayi yana murmushi ya ce "A'a Abba zamu zama dai" gaba ɗaya suka saka dariya. Sai a sannan Inna ta yi magana ta ce "Yanzu Anas kana nufin nan da wata biyu zaku koma wani yaƙin? E Inna idan mun huta mun koma zamu fita, girgiza kai Inna ta yi ta ce Allah ya ba da sa'a" gaba ɗaya suka amsa da amin. A can gidan su kuwa yana isa Alhaji Abubakar ya gan shi, take ya shiga yi wa Allah godiya da dawo masa da ɗansa lafiya, domin tun bayan tafiyar Ammar aikin soja, ya daina barci mai daɗi abinci ma idan yana ci baya jin daɗinsa, kawai yana ci ne da kada ya zauna da yunwa. Rungume Ammar yayi a ƙirjinsa wani sassanyan farinciki yana ratsa zuciyarsa, ji yake kamar kada ya sake barin shi yayi nisa da shi. Falo suka shiga Daddy ya ce "Ammar ɗin ya je ya yi wanka, sannan ya dawo ya bashi labari" cike da ladabi Ammar ya ce "To Daddyna bari na shiga ciki, to Ammar ɗina kayi sauri domin ina nan ina jiranka." Su Anas ana zaune sai faman hira ake sha, amma duk wannan hirar idanun Anas suna kan Basma, ya ƙura mata idanu, tun ba ta ankara yana kallonta ba har ta zo ta kula, gaba ɗaya sai ta ji ta takura tashi ta yi ta tafi part ɗinsu domin gaba ɗaya ta tsani wannan kallon da Anas yake binta da shi. Kiran sallah aka fara yi a Masallacin unguwar, gaba ɗaya suka tashi suka shiga ciki suka ɗauro alwala suka nufi Masallaci. Su ma su Inna da Iya miƙewa suka yi, suka tafi domin su gabatar da tasu sallar. Bayan sun dawo daga Masallacin, Aisar ya ce "Anas ya je yayi wanka ya kwanta ya huta, da safe sai suyi magana, tashi yayi ya nufi ɗakin da aka nuna masa nasa ne.......✍️ To be continue.....📝📝📝 *Hussaini Yusuf✍️* [12/9, 4:38 PM] ~HUSSAIN YUSUF~: *ANAS MALEEK* *NA* *HUSSAINI YUSUF* *______________________________* *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *______________________________* *Page 47/48* Bayan ya shiga cikin ɗakin, sai ya ga komai tsaf-tsaf, komai na ɗakin sabo ne har da air condition, ga wani tamfatsetsen gado a shimfiɗe a ɗakin. A hankali ya zo ya buɗe haɗaɗɗiyar wardrobe ɗin da ya gani a manne jikin bangon ɗakin, kaya ya gani dai-dai shi, an shirya su tsaf cikin wardrobe ɗin. rufe ta yayi ya dawo gefen gadon ya zauna, tunani ne kala-kala ya cika masa zuciya, to "A ina su Aisar suka samu kuɗi har suka gina irin wannan gida haka?" Shi kaɗai yake yi wa kansa wannan tambayar, amma ba shi da amsarta dole sai wajen su Aisar ɗin zai ji komai. Ganin wankin hula yana niyyar kai shi dare, sai ya tashi ya nufi toilet ɗin da ya gani a cikin ɗakin. A hankali ya buɗe ya shiga, "Masha Allah" shine abin da ji ya faɗa, a hankali ya rufe ƙofar bathroom ɗin, sannan ya shiga yin wanka, wani daɗi ne yake ratsa jikinsa jin sa yake tamkar an yaye masa duk wata damuwarsa. Bayan ya gama wankan, sai ya ɗauki ɗaya daga cikin tawul ɗin da ya gani a cikin banɗakin ya ɗaura shi ya ɗauki wani kuma yana tsane ruwan jikinsa. A jikin wani irin dressing mirror ya tsaya, wanda ban taɓa ganin irinsa ba a rayuwata. Kayan shafe-shafe ne sun fi gaban a ƙirga, ga perfumes nan wajen kala ashirin sai wanda ya ga damar zaɓa. Just vasselin ya shafa, sannan ya buɗe wardrobe ɗin ya ɗauko wata baƙar jallabiya ya sanyata a jikinsa. Wow! ba ƙaramin kyau Anas yayi ba a cikin rigar nan, zuwa yayi ya zauna a gefen gado ya shiga tunani, nan da nan tunaninta ya faɗo masa. Shi kaɗai ya rinƙa sakin murmushi, tamkar gonar auduga yadda ta haɗe ranta ba ƙaramin burge shi ta yi ba. A ransa ya saka kafin ya koma bakin aiki sai ya bayyana soyayyarsa a gareta, ko da baza ta amince da shi ba. Kamar an tsikare shi ya tashi ya fita daga ɗakin, kai tsaye ɗakin Inna ya nufa. Tarar da ita yayi ta idar da sallah tana shirin kwanciya, ganin Anas ya shigo sai ta fasa kwanciyar ta zauna a gefen gado, shi kuma Anas ya zauna a ƙasa. Cike da ladabi ya sake gaisheta, ita ma da nuna kulawa irin ta uwa ta amsa masa gaisuwar tana mai shafa kansa tana sakin wani tattausan murmushi. Shi ma ban da sakin murmushin babu abin da yake yi, domin babu abin da ya fi so a duniya fiye da ya ga mahaifiyarsa a cikin walwala da farinciki. Ƙasa-ƙasa yayi da muryarsa ya ce "Inna wai a ina ku ka samu kuɗin da har kuka gina wannan katafaren gidan?" Dariya Inna ta yi ta ce "Ka kwantar da hankalinka ba Baffanka ya ce da safe zai sanar da kai komai ba? To ka jira safiyar mana idan Allah ya kai mu." Ba ta jira abin da zai ce ba ta cigaba da magana "Ni kuwa Anas akwai maganar da nake son mu yi ni da kai, dama ina son a kirawo min kai kafin ka kwanta. Amma sai na yi tunanin ka gaji, sai na bar ka ka huta, idan Allah ya so da safe muyi maganar, amma tun da ga shi ka shigo shikenan sai muyi maganar ta mu. Gyara zama Anas yayi ya ce "Ina sauraronki Inna" murmushi ta yi ta ce "Ta so ka dawo nan kusa da ni sai ka fi fahimtata" tashi yayi ya koma kusa da ita ya zauna yana mai fuskantarta. "Tun bayan da ka tafi neman aikin soja, Alhaji Abubakar yake ta yi min aike wai yana son ya aure ni domin yana da yaƙinin zan iya riƙe masa Ammar na kula masa da shi. Na bashi taimakon da duk wata uwa take bai wa ɗanta, kuma ya ce idan na aure shi sai na haɗa da ku da Ammar ɗin na riƙe ku, ni na zama tamkar mahaifiyar Ammar da ta rasu tun yana yaro. Shi kuma ya zama tamkar mahaifinku da kuka rasa. Kullum idan ya aiko min haka nake faɗa masa, sai ka dawo na yi shawara da kai, tun da hankalinka ya kai a saurare ka a ji ra'ayinka a cikin wannan magana. Shiru Anas yayi ya ɗaga kansa sama yana tunani, sai da Inna ta dafa shi, kamar an soka masa allura ya dawo hayyacinsa. Duban Inna yayi ya ce "Inna a iyakar sani na ba mu daɗe da rasa Baffa ba, muka samu madadinsa" da sauri Inna ta gyaɗa kai alamar gamsuwa da maganar Anas cigaba yayi da ce wa "Baffa Aisar shi ya zamar mana kamar Baffanmu da muka rasa, akanmu ya rabu da garinsu, akanmu aka ci masa mutunci aka nemi ya mayar da mu inda ya tsinto mu ko kuma ya bar garin, amma ya zaɓi barin garin akan ya mayar da mu inda ya same mu." Ban da hawaye da yake zuba a idanun Inna babu abin da take, domin ta tuno irin wahalar da suka sha kafin su baro ƙauyen nan da yake yankin Mambila a can Jahar Taraba. Muryar Anas ce ta doki dodon kunnenta, in da yake ce wa "Inna ni a gani na babu wani uba da zamu samu bayan Baffanmu fiye da Baffa Aisar" shiru Inna ta yi tana nazarin maganar Anas tabbas gaskiya ya faɗa ita bata taɓa yin wannan tunanin ba ma, nan take ta shiga mamakin kaifin hankali gami da hangen nesa irin na Anas. Cigaba yayi da ce wa "Inna ke kin sani da a ce Baffa Aisar yana da damar kai ni makarantar horon sojoji, ba zai taɓa barin Abban Ammar ya kai ni ba, da kansa zai so ya kaini." Da sauri Inna ta girgiza kai alamar gamsuwa har yanzu ta kasa magana saboda a baya duk ba ta yi wannan tunanin ba, sai yanzu da Anas ya ankarar da ita sannan ta gane irin halaccin da Aisar yayi musu a rayuwa. "Haka Inna idan muka duba Daddin Ammar yayi mana halacci a rayuwa, da bai kamata mu watsa masa ƙasa a ido ba" ita dai Inna ta yi shiru tana sauraren ɗan nata ta kasa furta ko da kalma ɗaya "Don haka Inna ni na amince ki auri Daddin Ammar, amma ke kaɗai zaki koma wajensa mu muna tare da Baffa Aisar, tun da shine ubanmu na ainihi bayan Baffanmu da ya mutu. Amma kafin ki sanar da shi ki fara faɗa wa Baffa Aisar mu ji shi kuma abin da zai ce akai" murmushi Inna ta yi ta ce "Haƙiƙa na daɗe ina nazari akan maganar auren nan amma ban taɓa yin kwatankwacin wannan tunanin da kayi yanzu ba." "Amma game da maganar na sanar da Baffanka Aisar, ai tun kafin na sani ma shi ya rigani sani. Domin ta hannunsa saƙon ya iso gare ni, kuma shi ya rinƙa roƙona akan na amince da maganar auren, ni na ƙi amincewa na ce sai na yi shawara da kai na ji ta bakinka sannan na amince. Yanzu ka tashi ka je ka kwanta, idan Allah ya kai mu gobe zan sanar da su ce wa na amince da auren." Tashi Anas yayi ya ce "To Inna sai da safe" murmushi ta yi ta ce "Allah ya kai mu" sannan ya fice tare da jawo ƙyauren ɗakin. Tun da ya je ya kwanta tunaninta ya sake faɗo masa a rai, Allah-Allah yake gari ya waye domin yayi tozali da kyakkyawar fuskarta, mai sanyaya masa zuciya, nan take kuma ya koma tunanin hanyar da zai bi domin sanar da ita muradin zuciyarsa, amma sam ya rasa da wannan tunanin barci yayi gaba da shi. *WASHE GARI* Misalin ƙarfe 8:30am kowa ya hallara a dining area, abincine kala-kala sai wanda mutum ya zaɓa sannan zai ci. Dubawa Aisar yayi bai ga Anas ba, nan ya tashi Basma ya ce ta je ta kira wo shi yayi break fast. Fuskarta a murtuƙe ta tashi ta nufi ɗakinsa, domin ko kaɗan Basma ba ta son abin da zai haɗa ta da Anas ko kaɗan, kwata-kwata ba ta son haɗa wata mu'amala da shi, amma yanzu wai a rasa wanda za'a tura kiranshi sai ni kaɗai?" A hankali ta tura ƙofar ɗakin, shi kuma Anas lokacin ya fito daga bathroom yana tsane jikinsa da wani ɗan ƙaramin tawul, ji yayi an shigo ɗakin ba tare da neman izini ba. Da sauri ya waiga domin ya ga wanda ya shigo, numfashinsa ne ya nemi ɗaukewa yayin da yayi tozali da kyakkyawar fuskarta, mai ɗauke da wani haske mai sanyaya zuciya, dara-daran idanuwanta da dogon hancinta da kyawun dirin da Allah ya bata sune suka fi ruɗar shi ya ji tamkar Basma ta kasance tauraruwar ƴan'mata ko kuma kai tsaye za'a iya kiranta da autar mata, saboda irinsu kaɗan ne a cikin al'umarmu ta Hausawa. Yayin da ta gama buɗe kyauren ɗakin sai ta koma da sauri saboda tun da take a rayuwarta bata taɓa ganin namiji a haka babu riga a jikinsa ba. Murtuƙe fuska yayi cikin dakakkiyar murya ya kira ta "Ke zo nan" kamar kar ta koma haka zuciyarta ta rinka raya mata, amma da ta tuno irin muguntar da yake yi musu tun kafin ya tafi soja, to yanzu da ya dawo muguntar ai sai ta ninka ta da, tana gama wannan tunanin ta kutsa kanta cikin ɗakin. Kanta a sunkuye ta ƙarasa shiga ciki, tana ta faman wasa da ƴan yatsun hannunta, murtuƙe fuska yayi kamar ba shi ba ya ce "Me ya kawo ki ɗakina?" cikin harɗewar harshe ta fara magana "Dam....dam...dama me min tsaya kina wani Kame-kame" da sauri ta ce "Dama haka aka ce na kirawo ka ka zo ayi breakfast" tana gama faɗar haka ta juya da sauri ta bar cikin ɗakin tare da jawo murfin da ƙarfi, alamun ranta ya ɓaci. Bayan ya gama shiryawa ya ɗauko wata dakakkiyar shadda fara ya sanya ta a jikinsa, ba ƙaramin kyau Anas yayi ba dama ga shi asalin bafulatanin Mambila. Ya ɗauko wani agogo mai tsadar gaske ya ɗaura shi a tsintsinyar hannunsa na dama, sannan ya ɗauko wasu zobuna masu ɗan karan kyau da tsada ya zura su a zara-zaran yatsunsa, buɗe wardrobe ɗin cikin ɗakin yayi ya ɗauko wata hula kalar milk, ya ɗorata akansa wow! ba ƙaramin kyau Anas yayi ba sai ma kun gan shi musamman mata sai kun ƙyasa wallahi lol. A hankali ya buɗe ƙofar falon ya fito, ɗaya bayan ɗaya yake take stairs ɗin kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki, ko kuma kamar wanda tafiya take wahalarwa. Yana ƙarasowa cikin falon, sai ya hango su a wani keɓantaccen waje wanda iya wani dogon dining table ne a wajen a jera abinci kusan kala goma, kowa sai dai ya zaɓi abin da zai ci hankalinsu kwance kowa sai faman zura lomarsa yake abinsa. Samun ɗaya daga cikin kujerun da suka zagaye table ɗin yayi ya zauna, bayan ya gaishe da kowa a wajen, sannan su Safna da Nasreen har da Basma ma suka gaishe shi, Safna ce tayi saving na shi zaunawa yayi ya fara cin abincin har sai da ya ƙoshi. Aisar ne yayi gyaran murya ya ce su Safna su tashi su shiga da ciki, babu musu kuwa su duka ukun suka tashi suka shiga, bayan sun tafi Aisar ya juyo ya kalli Anas ya ce "Yanzu zan faɗa maka dalilin da yasa ka gan mu a wannan ƙerarren gidan. Gyara zama Anas yayi ya ce "To Baffa ina sauraronka" numfasawa Aisar yayi sannan ya cigaba da cewa. "Bayan tafiyarka neman aikin soja, mahaifin Ammar ya nuna yana son auren mahaifiyarka, ita kuma ta ƙi amincewa ta ce "Har sai ka dawo ta ji ra'ayinka sannan ta amince." Amma duk da haka mutumin nan bai daina yi mana hidima, da na faɗa masa sana'ar da nake yi ta sayar da gwanjo sai ya haɗa ni da wani babban dealer, ya ara mini kuɗi masu yawan gaske. Sannu a hankali kasuwancina ya rinƙa haɓaka, da ni da ke bai wa sarin kaya na dawo ni ne mai bayarwa, har na zo duk faɗin kasuwar Wambai babu inda ba'a sanni ba" "Na gina manyan shaguna na gani na faɗa, wasu ina kasa kayana wasu kuma na bayar da su haya ana kawo min balance ko wacce shekara." Wata rana na je na saro kaya da yawa, na zo shago ina ta duddubawa kwatsam na ga wata ƴar madaidaiciyar jaka a ciki, ban yi wani jinkiri ba, na ɗauko ta ina dubawa kawai sai na ga dalolin kuɗi a ciki, a zatona ko me bamu kayanne yayi mantuwa amma sai na ga wata ƴar ƙaramar takarda ce wa "Zakka ce duk wanda ya samu rabonsa ne kuma halak ɗinsa ne" ai kuwa da sauri na ɗauki jakar na nufo gida da ita, da na nunawa Sa'ad ya ce "Wannan ba ƙananan kuɗi bane, nan da nan muka ɗebi kaɗan daga ciki muka je wajen canji, nan muka ga an bamu kuɗi masu yawan gaske wajen 30 million naira, nan muka shiga murna, da mamaki don ni ban taɓa ganin dala ba sai a wannan lokacin. Nan da nan kuwa kasuwanci ya bunƙasa, a hankali muka rinƙa canjar da kuɗin, har suka ƙare mun samu kimanin naira biliyan ɗaya a kuɗin Najeriya. Yanzu haka ina da manyan shaguna da nake sayar da atamfofi da kayan sakawa a kasuwar kantin kwari. Kuma kai ma na gina maka ƙaton mall na mallaka maka shi halak malak, kuma akwai wasu kuɗi da na tanadar maka, idan ka gama zama sojan zan baka su ka rinƙa ɗan taɓa kasuwanci. Kuma wannan gidan da kake gani da ribar da na samu a shekara ɗaya na gina shi, amma insha Allahu zan gina wanda ya fishi nan gaba kaɗan. Numfasawa Anas yayi ya ce "Baffa haka Allah yake yin lamarinshi, idan ya soka da arziƙi yanzu ne zaka fi kowa, haka idan ya soka da talauci babu wanda ya isa ya fitar da kai daga ciki idan ba shi ba" "Wannan gaskiya ne Anas" cigaba Anas yayi da cewa "Amma Baffa shi kuma Baffa Sa'ad me ka yi masa?" murmushi Aisar yayi ya ce "Ai na gina masa ƙaton gida, a can unguwar Ƴar akwa kuma na bashi naira miliyan ɗari yayi jari, yanzu haka ma ya samu labarin dawowarka yana hanya zai zo ku gaisa...... Hussain Yusuf✍🏻 [12/9, 4:38 PM] ~HUSSAIN YUSUF~: *ANAS MALEEK* *NA* *HUSSAINI YUSUF* *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu 'yancinmu* *Page 49/50* Murmushi Anas yayi ya ce "Baffa da ka ce masa ma ya zauna sai na je har gidan nasa na gaida shi". "Anas kenan ka san halin mutumin naka da gardama, wallahi sai da na faɗa masa haka amma furr ya ƙi amincewa lallai sai dai ya zo da kansa ya sameka, a cewarsa kada a wahalar da kai. Kafin Anas ya furta wani abun suka ji sallamar Sa'ad ya shigo cikin falon, da gudu Aisar ya je ya tare shi yana ce wa "Baffana sannu da zuwa da ka bari ma ai sai na zo da kaina mu gaisa ba sai ka zo ba" murmushi Sa'ad yayi ya ce "Ai zuwan da nayi yanzu, don na matsu na ganka ne shi yasa, amma ai na san zaka zo inda nake Anas ɗina." Dai-dai lokacin su Nasreen da Safna da kuma Basmah suka fito daga ɗakinsu, cikin shirin tafiya school. Basmah ce ta hango Abbanta da Momynta a zaune, da gudu ta ƙarasa wajensu ta rungume su tana tambayarsu yaushe suka zo. Sa'ad ne ya daka mata tsawa ya ce "Ke har yanzu ba ki daina wannan rashin hankalin ba ko? Ko haka ki ka ga sauran ƴan'uwanki sun yi?" "Haba Sa'ad me kuma yarinyar nan ta yi fisabilillahi, murna fa take yi da ganinku amma sai ka hau ta da wannan faɗan kamar za ka dake ta?" Cewar Aisar yana mai jin haushin Sa'ad akan takurawa Basma da yake yi, shi yasa ma ta zaɓi ta zauna da su Safna don ta daina fuskantar faɗan da take sha a wajen mahaifinta. Kamar ba shine ya haifeta ba haka yake rufeta da faɗa kullum ita da gidansu bata da sukuni, wannan halayya ta Sa'ad tana matuƙar ɓatawa mahaifiyar Basma rai, musamman idan ta kalli yadda Aisar yake tarairaiyar su Safna da Nasreen sai ta ji ina ma a ce haka mijinta yake yi wa tilon ƴarsu Basma, da ta fi kowa farinciki da jin daɗi, kullum idan sun zauna ban da aikin faɗa masa illar da abin da yake yi wa Basma take yi amma ya ƙi fahimta kwata-kwata. Bayan Baffa Sa'ad ya zauna Baffa Aisar ya fuskance shi ya ce "Wai mene ne dalilin da yasa ka ke yawan yi wa Basma wannan kyarar kamar ba kai ne ka haife ta ba?" Numfasawa Sa'ad yayi ya ce "Ba wai ina kyararta ba ne don ba na son ta, a'a sai don ba na son na nuna mata gata irin wanda ake nunawa wasu kuma ƙarshensu ya zama marar kyau." "A kan idona lokacin ina gidan haya tare da wani mutum, ya rinƙa nunawa ƴarsa gata yana ririta ta ko kaɗan baya son ganin laifinta, ko mahaifiyarta ba ta isa ta tsawatar mata ba, ƙarshe wannan yarinyar cikin shege ta je ta samo. Mutanen unguwa suka rinƙa tsangwamarsu daga ita har mahaifin nata, kuma shi duk ɗan abin da ya ke da shi yanzu duk ya ƙare. In taƙaice maka labari wannan yarinyar ta sanadinta ya haɗiyi zuciya ya mutu da baƙin cikinta, wannan shine dalilin da yasa ba na son yawan nuna mata gata, ba wai sonta ne ba na yi ba, kawai ina jiye mata tsoron ka da ta faɗa irin mummunar rayuwar waccan yarinyar da muka zauna da su a gidan haya ɗaya. Murmushi Aisar yayi ya ce "Ai ba da tsangwama ake bayar da tarbiyya ba, kulawa da yabawa su ma duk hanyar bayar da tarbiyya ne, shi wancan mutumin da kuka zauna tare gata ya nunawa ƴarsa wanda ya wuce kima, kuma ga shi ka ce ba ya son laifinta. Wannan shine dalilin da yasa ta lalace, amma don Allah ka daina nunawa ƴarka irin wannan tsangwamar kamar ba kai ne ka haifeta ba?" Ba ƙaramin daɗi Husna ta ji ba, jin mijinta ya ce ya daina nunawa tilon ƴarsu tsangwama, a zuciyarta kuma tana yabawa Aisar akan ƙoƙarin da yayi wajen shawo kan matsalar da ta daɗe tana son magancewa sai ga shi a ɗan ƙanƙanin lokaci ya magance komai gaskiya dole a yaba masa. Su Safna ne suka ɗauki tashi suka ce su za su tafi makaranta, don yau suna da lacture, Sa'ad ne yayi kiran Basma ya ɗauko kuɗi ya bata yana sakar mata murmushi dubu uku ne ya ce "Ta bai wa Safna da Nasreen dubu ɗai ɗai sannan ta riƙe dubu ɗaya ita ma" da murnarta ta karɓa tana ta yi masa godiya saboda tana matuƙar son Abbanta sai dai tsangwamar da yake nuna mata ne yasa bata sake wa da shi ko kaɗan. Wata mota ce ƙirar prado tun sassafe take tsaye a ƙofar gidan su Anas, da alama akwai abin da suke jira domin sun ƙi tafiya ko kaɗan. Su Safna ne suka fito za su tafi school ɗinsu, kawai wani mummunan mutum ya fito daga motar ya sha gabansu ya tsaya ƙiƙam kamar gunki. Safna ce ta daka mai tsawa ta ce "Malam lafiya zaka xo ka sha gaban mutane suna cikin tafiya?" shiru yayi mata kafin kiftawar ido suka ga wasu manyan ƙarti majiya ƙarfi sun zagaye su, sun ritsa su da bindiga tare da nuna musu motarsu alamar su shiga. Kurma ihu Nasreen tayi ai kuwa kamata ɗaya daga cikin ƙartin yayi ya hankaɗa ta cikin motar har goshinta ya fashe, su Safna da Basma kuwa babu musu suka shiga motar suna kuka. Suna gama shiga suma gaba ɗayansu suka shiga sannan suka jefo wata farar takarda waje, nan take suka ja motar da gudun gaske suka bar unguwar gaba ɗaya. Wani matashi ne da yake laɓe yana kallon duk abin da yake faruwa, da ya ga sun tafi sai ya fito daga maɓoyarsa ya ɗauki takardar ya nufi gidan su Anas da gudun tsiya, kamar kura ta biyo kare. Yana zuwa bai tsaya wani tambayar izinin mai gadi ba, ya kutsa kansa cikin gidan, ai kuwa me gadin ma ya bi shi a baya yana cewa ya dakata amma inaaa! sai da ya dangano da falon gidan. Suna cikin karyawa kawai suka ga mutum ya shigo falon kamar an jefo shi daga sama, Anas ne ya daka masa tsawa ya ce "Kai lafiya ka shigowa mutane babu sallama?" Daidaita nutsuwarsa matashin yayi ya ce "Yallaɓai wasu mutane ne suka zo da wata baƙar mota suka ɗauke wasu ƴan'mata da su uku da suka fito daga nan gidan" da sauri Anas ya miƙe tsaye da ƙarfin gaske ya ce "Whattt". Aisar ma tuni hankalinsa ya tashi, ya dubi matashin ya ce "Su nawa ne suka zo suka ɗauke su?" "Wallahi ban ko du nawa ba ne domin wasu ba su fito daga cikin motar ba," Su Iya da Inna kuwa tuni sun fara zubar da hawaye, Husna kuwa gigicewa ta yi tana kiran sunan ƴarta Basma. Sa'ad kuwa har yanzu ya kasa furta komai akai yayi shiru haɗe da dafe kanshi da yake barazanar tarwatsewa. Sai a wannan lokacin matashin nan ya tuno da takardar da suka jefar ya tsinta, fito da ita yayi ya miƙa wa Anas ya ce "Su ne suka jefar da wannan takardar amma ban karanta ba" da sauri Anas ya karɓa hannunsa yana karkarwa ya fara karanta rubutun kamar haka: _Saƙo daga wajen shugaban ƴanta'addan Najeriya, CAPTAIN ANAS ABDUL-MALEEK ka sani ina sane da duk shirye-shiryen da ku ke yi a kaina._ _Ka sani kome kuke shiryawa ina da labari, yanzu haka an barku ku zo gida ku huta sannan ku dawo da shirin yaƙata. To burinku ba zai taɓa cika ba, domin ina da masu bani bayanan kome kuke shiryawa ina da labari, amma ku sani burinku ba zai taɓa cika ba._ _Ni ne nan shugaban ƴanta'adda Sa'eed bn Abdul'aziz, ka sani ni ne nan na kwashe ƴan'uwanka, matuƙar ka cika kai cikakken soja ne ka zo ka ƙwace su daga hannuna._ _Kuma ka sani idan zaka zo ka zo kai kaɗai, kuma ban yarda ka zo da makami ko ɗaya ba, muddin kuwa ka kuskura ka yi ɗaya daga cikin sharuɗan nan to zan yi wa ƴan'uwanka gunduwa-gunduwa sannan ka zo ka kwashe su. Muna nan a cikin dajin Falgore ka sani ka kaɗai ne ka san inda nake amma ka kuskura ka taho da wani to rayuwar ƴan'uwanka tana cikin haɗari sai ka zo muna jiranka, domin akwai wani aiki da muke so ka yi mana._ _Sai ka zo muna jiranka._ Anas yana gama karanta takardar ya kurma wani uban ihu, da gudu ya haura sama ɗakinsa ya shiga, yana shiga wayarsa ya ciro da take caji, lambar ogansu ya lalubo nan take ya danna masa kira. Bugu ɗaya ya ɗauka ya ce "Anas ya aka yi ne?" nan take Anas ya faɗa masa komai, ya ƙare da cewa "Oga umarni na ke jira daga gareka ka barni na tafi yanzu haka ma shirya wa zan yi domin na je na karɓo ƴan'uwana. Shiru ogan nasu yayi har sai da Anas yayi zaton ya katse kiran ne, can ya ji muryarsa yana cewa "Anas ba ka san wani Sa'eed ba labarinshi kawai ka ke ji amma wannan mutumin ba shi da imani da tausayi ko kaɗan." Ni a tunanina abin da yasa yayi maka haka, idan ba ka manta ba mun taɓa artabu da wasu tawagar ƴanta'adda to shugaban y'anta'addan nan shine babban yaron Sa'eed kuma kaine ka kashe shi. Don haka ni a ganina da tunani na ya kafa maka tarkone da ƴan'uwanka yadda zaka kai kanka har wurinshi domin yayi maka hukunci dai-dai da abinda ka yi masa, na kashe masa babban yaronsa da ka yi. Don haka ni a shawarata ka tsaya dama akwai shirin da muke yi masa ka ga sai mu farmake shi ta inda bai yi zato ba, amma akwai haɗari idan ka tunkari mutumin nan kai kaɗai. Domin hatsabibancinsa ya wuce duk inda ka ke tunani, ka tsaya sai mu haɗa ka da tawagarmu ku je ku farmake shi duk da ba mu san shirin da yayi mana ba. Da sauri Anas ya ce "A'a oga ni kaɗai ya zaɓi na je kuma yanzu zan je izininka kawai nake Nema." "Anas ba ka san irin mutanen nan ba ne shi yasa ka yarda zaka kai kanka wajensu, ka sani yaudararka zai yi sannan ya kashe ku kai da ƴan'uwan naka." "Oga ka sani ni kome zai yi min ba zan taɓa bari rayuwar ƴan'uwana ta salwanta ba, duk kokarin da yakamata na yi zan yi shi kawai abu ɗaya nake nema a wajenka izini." Sanin taurin kan Anas da kafiyarsa ya sa ogan nasu ya amince da ya je amma za'a saka sojoji su kewaye dajin don tabbatar da tsaro, nan ma Anas ya ce baya buƙata ya bar shi kawai shi yasan yadda zai yi ya ceto rayuwar ƴan'uwansa. Babu yadda ogan ya iya dole ya ƙyale shi, amma yana jinjina abin a cikin ransa yana tunanin ta yadda Anas zai kawo ƙarshen wannan mugun kuma hatsabibin ɗanta'addan, duk da yarda da Anas ɓangaren jarumta da sa'a a duk abin da yasa a gabansa, amma yana jiye masa tsoron Sa'eed domin ba ƙaramin makiri ba ne. Ba Ƙaramin daɗi Anas ya ji ba da hukumarsu ta sojoji ta amince ya tunkari Sa'eed, nan take kuwa ba tare da ɓata wani lokaci ba ya fara shiri cikin ƴan mintuna ƙalilan ya gama kimtsawa ya fito cikin shigarsa ta sojoji. A hankali ya rinƙa saukowa ƙasa har ya gama saukowa su Aisar ya gani a tsaitsaye suna jiranshi ya sauko, kallonsu yayi ɗaya bayan ɗaya sannan ya ce "Yanzun nan zan je domin dawo da ƴan'uwana ku taya ni da addu'a." Yana gama faɗar haka ya juya zai fice daga falon, "ANAS" muryar Aisar ta daki dodon kunnensa, juyowa yayi a hankali fuskarsa tana zubar da hawaye ya dubi su Inna ya ce "Ku gafarce ni Inna idan na mutu ku yafe min don Allah domin ban sani ba ko ba zan dawo a raye ba. Inna na yarda ki auri Daddin Ammar ko da ba na raye, domin ina da yaƙinin zaki samu farinciki da walwala a wajensa." Kowa a wajen zubar da hawaye yake yi, Aisar ne ya buɗi baki cikin raunin murya ya fara magana "Anas ta yaya kake zaton za mu barka ka tafi kai ma ka hallaka? So kake mu rasa ku gaba ɗaya ne, me kake faɗa haka ka, tsaya a bi komai a sannu mana, ka sani gaggawa aikin shaiɗan ce." Murmushi Anas ya saki duk da ba wai murmushin murna ba ne, kana ganin murmushin ka ga murmushin takaici gami da alhini amma haka bai hana fuskar Anas haskawa ba, domin Anas irin samarin nan ne da mata suke mafarkin samu a rayuwarsu, ga ilimi ga kyau ga kuɗi sannan kuma jarumta, sai kuma babban abin da yayi wa rayuwarsa ado shine tausayi, Anas yana matuƙar tausayawa mace a rayuwarsa ko kaɗan ba ya so ya ga abin da zai ɓata mata rai kome ƙanƙantarsa kuwa. Share hawaye Anas yayi daga idonsa ya ce "Baffa ba su Safna suke buƙata ba, ni suke buƙata na kai musu kaina shi yasa suka yi garkuwa da ƴan'uwana domin su same ni cikin sauƙi kuma ga shi sun samu." "Ka sani da zarar yanzu na kai kaina zasu dawo da su har nan gida a yadda suka yi alƙawari ba za su cutar da ko ɗaya ba, indai ban karya musu dokokinsu ba. Don haka yanzi ni na tafi ba insha Allahu idan su Nasreen ba su dawo yau ba to gobe za su dawo wannan alƙawari ne na yi muku." Yana gama faɗar haka ya juya zai tafi, sake dakatar da shi Aisar yayi ya ce "Ungo wannan ka ɗaura shi a damtsen hannunka na dama insha Allahu babu abin da suka isa suyi maka" ya faɗa yana mai miƙa masa wani kambu wanda aka naɗe shi da fatar zaki. Karɓa Anas yayi da sauri ya fice daga falon don kada su sake tsayar da shi, ya zo dai-dai ƙofar gidansu ya ga Ammar shi kuma ya zo gidan. Da sauri Ammar ya fito daga motarsa yana tambayar Anas ko lafiya, shiru Anas yayi hawaye yana kwararowa akan kyakkyawar fuskarsa sai da ya daidaita nutsuwarsa sannan ya dubi Ammar cikin nutsuwa ya ce........................✍🏻 To be continue.............📝📝📝 HUSSAINI YUSUF✍️