❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️ 💕ALAƘAR YARINTA💞 ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️ NA MMN AFRAH FIRST CLASS WRITER'S ASSO... Page 1️⃣&2️⃣ JIGAWA STATE HAƊEJIA L.G *UNGUWAR K/AREWA* Sanye ya ke da kayan makarantar islamiya riga da wando ash colour sai hula dark blue, riƙe ya ke da jakar leda mai ɗauke da littattafai yaro ne ɗan kimanin shekara shida, tsaye ya ke a jikin bangon wani gida na ƙasa sai share hawaye ya ke wani na bin wani, ganin ƴan islamiyarsu sun zo za su wuce hakan yasa ya juya bayansa dan baya so su ga hawayensa su rainashi. "Kai kun ga Hizbullah prefect" Yaro ɗaya ya faɗa daga cikinsu. "Lah wallahi shine dama nan wajen ne gidansu" Yarinya ɗaya ta ce tana washe baki. "Aikwa ya juya bayansa kar mu masa magana dan dama shima baya yiwa mutane magana sai ya ga dama"Ɗayan yace suna ta bin Hizbullah da kallo dan ya basu baya kuma bai waiwayo ba dan duk maganganun da suke yana jinsu.Suna wucewa ya cigaba da hawayensa. "Hizbullah dama baka tafi makarantar ba Ikon Allah yanzu akan na ce Ridallah bacci take shine ka ƙi tafiya kake kuka?" Baba Habiba da fitowarta kenan daga gida ta ce tana riƙe haɓa. "Ai bazan tafi ba indai bata tashi na ganta ba sai dai na fasa zuwa makarantar" Yace yana share hawayensa. "Kai jama'a na ga ikon Allah wannan wace irin shaƙuwa ce tsakaninka da Ridallah, ace saboda tana bacci ba za ka tafi makaranta ba sai ta tashi, na ga ɗazun nan ka tafi gida ka yi shirin islamiyar shine bacci ya ɗauketa amma shine kake kuka kamar dai kwana kayi baka ganta ba" Shiru ya yi bai ce komai ba sai sheshsheka da yake ta faman yi. "Mu je ka ganta tana baccin sai ka tafi in yaso kafin a tasoku ta tashi daga baccin" Baba Habiba ta ce tana kama hannunsa domin su koma cikin gidan. "Au bai tafi makarantar ba?Ai dama nasan hali shi yasa na leƙo in tabbatar" Muryar Umma Sadiya ta katse musu tafiyar tasu. "Wallahi kwa ni zatona ma ya tafi shi yasa ban biyo bayansa ba dan da na ce masa bacci take to kawai yace ya juya ya fito daga gidan" "Hmmm ai Hizbullah da Ridallah sai Allah ki barshi ya ganta tana baccin ko ya samu ƙwarin gwiwar tafiya makarantar dan in ba haka ba ko an matsa masa ya tafi in yaje ma ba sakin jiki zai yi ba bare ya yi karatun kirki" Ummar Hizbullah ɗin tace ta juya domin komawa cikin gidan. "Bari na yi sauri kar ya makara"Baba Habiba tace tana jansa suka yi cikin gidan, dan shi ko uffan bai ce musu ba kansa kawai ya sunkuyar yana jin duk abin da suke cewa. Suna shiga cikin gidan ta kai shi har ɗaki, Ridallah yarinya ƴar kimanin shekara ɗaya tana baccinta hankali kwance.Baba na kai shi ɗakin ta tsaya a bakin ƙofa jakar hannunsa ya ajiye ya ƙarasa har kan katifar da aka kwantar da ita ya tsugunna a gabanta ya saki murmushi kallonta yake kamar yau ya fara ganinta sai kuma ya sanya hannu a aljihunsa na gaban riga ya fito da naira goma kuɗin makarantarsa yace. "Wannan kuɗin shi zan siyo miki alewa da carbin malam in kawo miki in aka taso mu" Yana gama faɗar haka ya tashi yana mata bye-bye ya ɗauki jakarsa ya fito ko ta kan Baba bai bi ba ya fice daga gidan dan ya kusa makara kuma da ɗan nisa dan dai kwalta kawai zai miƙe har makarantar ba tare da ya yi kwana ba. "Oh wannan yaro yana ƙaunar yarinyar nan ace kullum in zai je makarantar arabi ko boko sai ya shigo haka in ya taso ma, Allah raya ta, ta ga irin tarin ƙyautatawar da yake mata"Cewar Baba tana girgiza kai ta juya domin ta fita domin samun yaron da za ta aika siyan klin domin yin wanke-wanke. Yana isa makarantar ya nufi ofis ɗin malamai ya kirawo malamin Qur'an domin shine monita kuma duk ya haddace time table ɗin ajin nasu. A kujerar gaba yake su biyu da abokinsa Bilal yana shiga ya miƙawa Bilal hannu suka yi musabiha daga haka ya zauna bai kuma cewa komai ba ya fito da Qur'aninsa, tsit ƴan ajin suka yi saɓanin kafin zuwan Hizbullah ɗin da suke ta surutu dan shi da ido kawai yake kallonsu su yi tsit kamar babu kowa a ajin dan ko sunan ƴan surutu baya rubutawa yana musu kwarjini sosai dan ba shiga harkar kowa yake ba sai dai ya yi abin da ya kawo shi gashi da mugun ƙoƙari hakan yasa ya zama mai farin jini a wurin malamai. Malamin ne ya shigo ajin ya maimaita musu ɗorin da ya musu jiya sau uku sannan ya fara karɓar hadda daga kan Hizbullah domin shine a kujerar gaba kuma shine a farko.Tun da ya fara karatun kowa saurarensa yake yi ya iya ƙira'a gashi ko kakarewa ba ya yi har ya kai ƙarshen ayoyin da aka ɗora musu.Kabbara aka masa sannan malamin ya cigaba da karɓar hardar sauran duk cikinsu babu wanda ya bada harda irin ta Hizbullah. Ana fitowa break ya siyi alewa da carbin malam ya sanya a aljihu ko ɗanɗanawa bai yi ba, ana tashinsu ya kamo hanya ko gidansu bai kalla ba ya shige gidansu Ridallah dan dama maƙota ne katangarsu ɗaya.Da sallama ya shiga, Baba Habiba ta amsa masa Ridallah da ke tafiya tana ta dariya ganin ta ƙware a koyon tafiya, Hizbullah kawai wurinta ya nufa yana ta murmushi itama tana hangoshi ta nufoshi tana masa dariya dan ta matuƙar saninshi dan tun da ta buɗi ido take ganinshi. "Oyoyo ƙanwata" Yace lokacin da ya jinginar da jakarsa jikin bango ya ɗauketa sai murna take tana zillo, da yake yana da jiki dan in ka ganshi sai ka yi zaton ya yi shekaru goma ma saboda girman jikinsa. "Ga alewarki da carbin malam"Ya bata alewar a hannunta ta riƙe tana wasanta sai ya ɓare carbin malam ɗin ya sanya mata a baki. "Yanzu Hizbullah ace kullum ba zaka kashe kuɗin makarantarka ba in an baka sai dai ka siyo mata wani abun? Kake siyo abu marar zaƙi saboda kar rana ta kama ƙanwartaka" Cewar Baba tana kallonsu cike da sha,awa. "Ai ba zan iya cin abu ba ban kawo mata ba, amma zan ke siyo mata biskit dan kar rana ta kamata" Hizbullah ya ce yana zaunawa akan tabarma ya ɗora Ridallah a cinyarsa yana mata wasa Baba tana tuƙa tuwo.Sai da aka fara kiran sallar magriba sannan ya yi alwala ya ɗauki jakarsa ya yiwa Ridallah bye-bye ya tafi gida ya ajiye jakar ya wuce masallaci.Ridallah kwa daƙer Baba ta lallasheta ta yi shiru dan yana ficewa daga gidan ta fara kuka. Da daddare bayan an yi sallar isha'i ya ɗauki abincinsa ya tafi gidan Baba domin acan yake cin abincinsa tare da Ridallah, Baba ta yi ta cewa ya daina tahowa da abinci amma sai yace shi ya fi so ya kawowa Ridallah na gidansu sai shi kuma ya ci na gidan Babar.Sai wajen ƙarfe takwas da rabi idan Ridallah ta yi bacci sai shima ya tafi gida ya kwanta dan ko homework aka bashi a makaranta to a gidan su Ridallah yake yin kayansa. Washe gari da safe wajen ƙarfe bakwai da rabi ya shigo gidan Baba da sallama dama saboda zuwansa Baba take cire sakata ta bar ƙofar a kare dan ta san ba zai iya tafiya makaranta ba sai ya biyo ta gidan.Sanye yake da kayan makarantar boko jakar makarantarsa goye a bayansa, hannunsa da flask ɗin makarantarsa mai ɗauke da abincinsa sai leda a hannunsa mai ɗauke da biredi da ƙosai sai shayi a kofi ya kawowa Ridallah bayan ya gaishe da Baba ya yiwa Ridallah wasa ya ajiye mata abincin da ya kawo mata dan ita ma shegen wayo ne da ita dan dai siririya ce bata da jiki gashi dai akwai cin abinci dan babu abin da bata ci Baba da wuri ta koya mata cin abinci. Fita ya yi yana sauri dan ya kusa makara dan dai makarantar bayan layinsu ne. MMN AFRAH ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️ 💕ALAƘAR YARINTA💞 ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️ NA MMN AFRAH FIRST CLASS WRITER'S ASSO... Page 3️⃣&4️⃣ Bayan wasu shekaru Yaro ne ɗan kimanin shekaru goma sha ɗaya riƙe da hannun yarinya ƴar kimanin shekaru huɗu, sanye suke cikin kayan makarantar boko, shi riga da wando farare sai hula yellow ta prefect ita kuma riga da wando blue sai farin hijabi.Tafe suke suna hirarsu gwanin ban sha'awa,sai flask ɗin abincin Ridallah riƙe a hannunsa. "Ya Hizbu ni dai yau a ajinku zan zauna banaso ka tafi ajinku ka barni"Yarinyar ta ce tana turo baki. "Haba Rida kinsan dai ba ajinmu ɗaya ba kuma in malamin mu ya ganki a ajinmu ni zai yiwa bulala, ko kinaso a dukeni?" "A'a ni banaso" "To in mun je ki shiga ajinku ana fitowa break zan zo wajenki sai mu je in siya miki alewa ko?"Ya tambaya yana kallonta, kai ta gyaɗa masa alamar ta yarda. "Yawwa ƴar ƙanwata"Ya ce yana murmusawa, itama dariyar ta yi har haƙwaranta suka bayyana. A haka suka ƙaraso makarantar lokacin ana kaɗa ƙararrrawa za a shiga aji dan ƙarfe takwas dai-dai, prefect na ta kora yara ajijuwa, ajin su Ridallah ya shiga lokacin yara ke ta shiga ajin ganin Hizbullah kowa ya nemi wuri ya zauna ya yi ɗif, ko ta kan su bai bi ba ya nufi kujerar su Ridallah yara ne guda biyu a ciki dan haka Ridallah ta ce ita tsakiya take so ta zauna haka yaran suka matsa mata ta shiga ta zauna ba dan ransu ya so ba sai da ya lallaɓata sannan ta yarda ta zauna ya je ya ajiye mata abincin a inda suke ajiye kwanukan abinci sannan ya je class ɗin su ya ajiye scul back ɗinsa ya fito suka cigaba da kora yara ajijuwa da yake makarantar a haɗe take primary & junior scul sai dai kowane da ɓangarensu. Ana fitowa break ya je ya kamo Ridallah ya ɗakko abincinta ya zo ya zauna yana bata a baki, sai da ta ci ta ƙoshi sannan ya ci sauran, sai kuma suka je ya siyo ɓata abin da take so da kuɗin makarantarsa da nata ya haɗa ya kaso mata sai da suka zauna tana cin abubuwan da aka siyo ɗin sannan take ɗauka tana bashi a baki dan itama bata iya cin abu ta hanashi ko lokacin da ba a sanyata a makaranta ba idan aka bata abu yana makaranta sai ta ajiye masa har sai ya dawo ta ɗauka ta bashi abin da ta rage masa domin akwai shaƙuwa sosai a tsakaninsu bata san kowa ba sai shi sai Baba, daga ta ga bata ganshi ba za ta tafi gidansu nemansa idan kwa ɗaya bashi lafiya to ɗayan ma zai kamu da rashin lafiya. Bayan an taso su suka kamo hanyar gida suna zuwa gidansu Hizbullah suka fara shiga ya cire kayansa ya ɗakko abincinsa suka tafi gidan Baba itama Ridallah ta cire uniform ɗin ta sanya wasu kayan sannan suka zauna suka cinye abincin Hizbullah sannan Baba ta zubo musu wani suka ci tare dan haka suke yi basa yarda su ci abincin gida ɗaya wai su ciyayya suke yi. MMN AFRAH ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️ 💕ALAƘAR YARINTA💞 ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️ NA MMN AFRAH FIRST CLASS WRITER'S ASSO... Page 5️⃣&6️⃣ _BIRNIN TARAYYA ABUJA G.R.A_ Wani ƙaton gida mai tafkeken get na shiga, na tsaya ƙarewa gidan kallo girma da yanayin tsaruwar gidan gida ne da ya amsa suna gida, kana kallon gidan ka san mamallakan gidan sun amsa sunan manyan attajirai.Gini ne sashe -sashe ga motoci nan bila adadin a wurin da aka tanada dan ajiye motoci wasu a buɗe wasu kuma an rufe su. Girma da haɗuwar gidan yasa na saki baki ina bin gidan da kallo lallai wannan gidan shi ake kira da aljannar duniya! Tafiya na fara na doshi wata hanya da ta ɗan miƙe wacce idan ka kai ƙarshenta ne za ka ga ta rabu zuwa sashe -sashe, sai da na tsaya ina tunanin wane ɓangare ya kamata na fara zuwa sai kawai na nufi wanda ke gaba na.Ƙofar part ɗin na tura sai kuwa gani na shigo wani fili mai girma da wasu shuke -shuke na fulawoyi da abubuwa masu ƙawata wuri.Ƙarasa wa na yi na buɗe ƙofar da za ta sadani da babban falon. Wani sanyi da ƙamshi mai daɗi ne ya fara ziyartar hancina, ƙarasa shigowa na yi cikin falon tsaruwa da haɗuwar falo kaɗai abin kallo ne, ban gama ganin tsaruwa da haɗuwar falon ba idona ya kai kan dinnig area inda wata mata ke zaune akan dinnig ɗin tana danna wayarta sai wani yatsine-yatsine take tana harare -harare tana yi tana kallon agogon wayar ta dan ranta sai suya yake yadda har yanzu Alhaji ba su fito ba dama duk ranar girkin Hajiya Azima Alhaji ba ya son fitowa da wuri sai ta rasa uban me suke a ɗakin matar da ba haihuwa take ba menene abin ɓata lokaci a kanta. A hankali yake sakkowa daga upstairs ɗin sanye yake da cofee yadi mai ɗan haske ɗinkin tazarce hannunsa riƙe da agogon sa ƙirar Gucci yana ƙoƙarin ɗaurawa Hajiya Azima biye da shi riƙe da jakar office ɗinsa sai zance suke suna dariya abin su.Ƙaran takalma su shi ya maido da Hajiya Hauwa daga saƙar zucin da take.Yadda kan ta ke akan wayarta bata ɗago ba dan wani tuƙuƙin baƙinciki ne ya turnuƙe mata zuciya saboda sautin dariyarsu kaɗai sai da yasa ta ji kamar zuciyarta za ta buga.Amma da yake ta iya takunta sai ta danne abin da take ji ta ɗago kan ta tana kallonsu fuska sake. "Barkan ku da fitowa"Ta ce musu lokacin da suka ƙaraso dinnig area ɗin. "Yawwa barkan ki"Suka haɗa baki wurin faɗa. Alhajin ne ya jawa Hajiya Azima kujera ta zauna lokacin da ta dawo daga tsakiyar falon da ta je ta ajiye jakar office ɗin Alhajin akan kujera, kallonta yake fuskarsa ɗauke da murmushi har dai ta zauna kafin shi ma ya sanya hannu zai ja kujerar Hajiya Azima ta yi saurin sanya hannu ta ja masa kujerar ya zauna suna yiwa junansu murmushi tamkar dai sun manta da Hajiya Hauwa da ke zaune tana hararsu ƙasa-ƙasa. "Barka da safiya Alhaji" Cewar Hajiya Hauwa tana murmushin yaƙe dan ji take kamar ta rufesu da mugun duka tsabar takaici. "Kin tashi lafiya" Alhajin yace cikin sakin fuska. "Lafiya ƙalaw" Ta ce tana masa wani kallo na soyayya dan ta ɓatawa Hajiya Azima rai. "Masha Allah"Yace lokacin da ya sanya fork zai fara cin abincin da Hajiya Azima ta zuba masa. "Hajiya fatan kin tashi lafiya"Hajiya Hauwa ta faɗa cikin kissa. "Lafiya Alhamdulillahi fatan ke ma haka" "Lafiya nake" "Masha Allah" "Ina Iftihal ne ko har ta tafi school" Alhajin yace lokacin da yake kurɓar tea. "Bata tashi daga bacci ba ai" Hajiya Hauwa tace tana ɗan sanyaya muryarta dan kar ya yi mata faɗa. "Haba Hajiya sau nawa kike so na faɗa miki ki daina yiwa yarinyar nan wasa da karatun ta, ace an sanya yarinya a school amma ba za ta je ba to me kike so ta miki a gidan idan bata yi karatu ba haka jiya ma monday fa bata je ba, hatta islamiya ma bakya so ta je, gaskiya bana so kar a ƙara barinta a gida" Alhajin yace cikin ɓacin rai dan ya kasa gane Hajiya Hauwa wace irin mace ce da bata ƙaunar ƴarta ta je makaranta kullum ana ɓacin rai akan abu ɗaya. "Allah huci zuciyarka Alhaji hakan ba zai sake faruwa ba" Ta ce tana wasa da cokali a cikin plate ɗin dan tun da ya sako maganar karatun Iftihal sai ta ji gabaɗaya abincin ya fice mata a rai dan babu abin da ta tsana irin maganar zuwan Iftihal makaranta, shi kuma ya kasa gane wa cewa bata ƙaunar Iftihal ta yi wani karatu daga na bokon har na arabiya. "Haka kike cewa kullum amma kin kasa canjawa amma inaso ki sani akan maganar makarantar Iftihal za mu saka ƙafar wando ɗaya da ke" Ya kai ƙarshen maganar yana goge bakina da tissue, ita dai Hajiya Azima bata ce komai ba dan bata son sanya baki a abin da bai shafeta ba amma itama har ga Allah bata son sangarta Iftihal da Hajiya Hauwa ke yi musamman ma a ɓangaren karatu. "Hakan ma ba za ta faru ba" Ta ce tana marairaice murya. "Yanzu ma dan na ga lokaci ya ƙure har takwas da kwata kafin ace an mata wanka an shiryata amma da sai ta tafi yanzu ma" Yace yana miƙewa, domin tafiya office, Hajiya Azima ma miƙewa ta yi domin rakashi, wata uwar harara Hajiya Hauwa ta bisu da ita dan gabaɗaya haushin su take ji dan tun da ake cin abincin sai wani satar kallon juna suke kamar ba tare suka kwana ba. "Allah tsare" Hajiya Hauwa ta ce a takaice. "Amin "Shi ma yace ba tare da ya kalli ko inda take ba. Hajiya Azima jakar ta ɗauka take masa baya, suka fita, a ƙofar fita daga part ɗin suka samu Sa'idu direba yana jiran fitowar Alhajin, gaishe da su ya yi cikin girmamawa suka amsa cikin sakin fuska jakar hannun Hajiya ya karɓa ya jiya ya tafi ya bar su suna sallama, sai da ta ga tafiyar su tana ɗaga masa hannu shi ma yana ɗago mata duk da akwai ɗan tazara daga part ɗin zuwa parking space amma suna hango junansu ana wangale get motar na fita Hajiya Azima ta juya ta koma ciki domin ta gyara masa bedroom ɗin nasa na upstairs inda suka kwana dan bedrooms a saman ma guda huɗu ne sai dai ɗaya wanda suke kwana Alhaji da Hajiya Hauwa ɗaya kuma inda yake kwana da Hajiya Azima kowacce da ɗakin da ya zamana shine turakar da take kwana da miji dan basa sharing na turaka sauran biyun kuma kawai dai an ƙawata su ne da kayayyakin ɗaki amma ba wai ana kwanciya a ciki. Tana dawo wa bata tarar da Hajiya Hauwa a dinnig area ɗin ba ta koma part ɗin ta dan kowacce akwai ƙofar da za ta sada ta da part ɗin ta, sai kuku yana kwashe kwanuka, ya gaishe da ita ta amsa masa tare da hayewa sama domin yin gyaran dan ita a tsarinta bata yarda ƴar aiki ta gyara mata turakar mijinta ba saɓanin Hajiya Hauwa da mai aiki ke gyara mata. Hajiya Hauwa rai ɓace ta ƙarasa part ɗin nata dan har lokacin bata daina jin haushin faɗan da Alhajin ya mata a gaban Hajiya Azima sai dai ta sha alwashin sai dai ya yi falansa ya gama amma dai ba za ta taɓa yin abin da yace ba ko da ta fara ba zai ɗore ba.Mai aikinta Safiya ta samu tana ta faman goge -goge cikin girmama wa Safiya ta mata barka da dawo wa amma ko inda take bata kalla ba dama ita ma bata sanya rai cewa za ta amsa mata ba dan ta san hali, shegen wulaƙanci ne da ita. MAMAN AFRAH😍 ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️ 💕ALAƘAR YARINTA💞 ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️ NA MMN AFRAH FIRST CLASS WRITER'S ASSO... Page 7️⃣&8️⃣ Hajiya Hauwa upstairs ta nufa tana zuwa ta kama ƙofar ɗakin Iftihal ta buɗe kwance ta ganta akan gado tana cikin bargo fuskar ta ce kawai a buɗe sai baccin ta take hankali kwance.Wata uwar harara take bin Iftihal ɗin da ita daga ƙarshe ta doka wani uban tsaki tare da rufo ƙofar da ƙarfi ta juya ta koma nata ɗakin, Iftihal kwa da ke ta bacci bata san abin da ake ba.Tana shiga ɗakin ta ta cire ɗaurin ɗan kwalin da ta yi wanda ake kira ture ka ga tsiya wuri ta nema a bakin gado ta zauna har lokacin ranta na ƙuna ta rasa yadda za ta yi da Hajiya Azima kullum maimakon ace Hajiya Azima ta zama bora a wajen miji amma kullum ita ce mowa ita ce tauraruwa ita ce abar so ita duk faɗi tashin da take yana tashi ne a banza, kullum Alhaji cikin ganin laifinta yake a gaban Hajiya Azima sai ya tsinkata yana mata faɗa tabbas da sake dan ba za ta saɓu ba wai bindiga a ruwa. Miƙewa ta yi da sauri kamar wanda aka tsikare ta gaban mirror ta je ta tsaya tana ƙarewaa kan ta kallo tamkar dai yau ta fara ganin siffar kan ta a madubi.So take ta gano muninta so take ta hango makusar ta so take ta ga ta inda Hajiya Azima ra kere mata, kyau diri iya kwalliya ko me? Amma bata hango hakan ba duk da ta san cewa bata kama ko da ƙafar komai ba na Hajiya Azimar ba amma ta san ita ma tana da nata abin yabon, gashin kan ta, ta ƙurawa ido ganin shi iya kafaɗarta ko gama sakko mata bai yi ba sai kuma ta tuno gashin Hajiya Azima da ko ɗan kwali baya iya rufeshi har gadon bayanta yake sauka ga santsi da sheƙi, ai hakan da Hajiya Hauwa ta tuna sai kawai ta miƙa hannu wurin kwalaben turaruka da ke jere akan madubin ta ɗakko wata kwalbar humra ta ɗaga ta jefawa madubin a take ya tarwatse wani ƙara da gabaɗaya part ɗin ya ɗauka komawa ta yi ta zube akan gadon har lokacin zuciyarta na tafarfasa. Safiya da ke gyaran kicin ta jiyo ƙaran fashewar abu a hanzarce ta fara hawa step ɗin domin zuwa ta ga ko menene dan alamu sun nuna kamar ba lafiya ba.Tana gama hawa upstairs ɗin ta fara waige-waige tana son gano inda ƙaran ya fito amma bata gano ba kukan Iftihal ta fara jiyowa da sauri ta nufi ƙofar ɗakin ta tura ƙofar dan dama idan ranar girkin Hajiyar ne idan Hajiyar ta tafi part ɗin Alhaji to fa ita ke kwana da Iftihal amma a ɗakinta da ke kusa da na Iftihal ɗin da basa kwana a ɗaki ɗaya idan kuma ba girkin Hajiyar bane a ɓangaren su na ƴan aiki take kwana. Iftihal ɗin ta hango zaune akam gado ta duƙunƙune kan ta a cikin bargo tana takure a wuri ɗaya tana ta kuka, da sauri ta ƙarasa wurin Iftihal ɗin tana kiran sunan ta sannan ta sanya hannu ta yaye bargon aikwa Iftihal ɗin ta faɗa jikinta da sauri tana ƙara fashewa da wani kukan. "Wayyo Safiya dan Allah ki kai ni wurim Aunty tsorata ni ake da wani irin ƙara"Cewar Iftihal ɗin tana ƙanƙame Safiya. "Ki yi shiru babu komai anan ni ma na ji ƙaran amma da na zo ban ga ta inda ƙaran ya fito ba" "Ke ma kin ji kenan ni dai ki kai ni wajen Aunty tsoro nake ji" "To taso mu je tana ɗakinta" Sakkowa Iftihal ɗin ta yi sai da na duba da kyau sai ma na ga ba wata babba ba ce duka bata fi shekara huɗu ba, hannun ta Safiyar ta kama amma Iftihal ta ce ita dai ba za ta tafi da ƙafarta ba, sunkuyawa Safiyar ta yi Iftihal ɗin ta hau dan dama da wuya ka ga Iftihal na tafiya da ƙafarta rai da rai sai dai a baya, haka suka nufi ɗakin Aunty, nocking Safiya ta shiga musu amma abin mamaki bata bada amsa ba jin shiru yasa Safiya tura ƙofar dan dama haka take sai ka yi ta mata nocking ta ƙyaleka. Kwance suka sameta ta kifa kan ta a jikin filo da alama kamar tana cikin damuwa daga bakin ƙofar da Safiya ke tsaye da goyon Iftihal suka ga gabaɗaya madubin da ya tarwatse a ɗakin, da mamaki Safiya da Iftihal suke kallon madubin sai lokacin suka fahimci ƙaran fashewar madubin ne ya cika part ɗin har ya tsorata Iftihal. "Aunty"Iftihal ɗin ta kira sunan Hajiya Habiba tana ƙoƙarin sakkowa daga bayan Safiya. Shiru bata amsa mata ba "Kar ki sakko dan kar ki taka madubin"Safiya ta ce tana riƙe Iftihal ɗin dan yadda madubin ya ɓata ɗakin ko ina ya tarwatse Iftihal ɗin za ta iya takawa.Duk bidirin nan da ake Hajiya Habiba bata ko ɗago kai ta kalle su ba.A hankali Safiya ta bi ta gefen tana taka in da babu madubin har dai ta ƙarasa bakin gadon ta sauke Iftihal ɗin akan gadon, ƙarasa wa Iftihal ɗin ta yi ta faɗa kan Aunty ta tungumeta ta baya tare da kwantar da kan ta a bayan Auntyn.Ita dai Safiya daga haka ta fita ɗakin domin samo abin da za ta gyara wurin. "Aunty ke kika fasa madubi?"Iftihal ta jefa mata tambayar. A hankali Aunty ta zame Iftihal ɗin faga bayanta ta tashi zaune suka fuskanci juna.Iftihal ɗin kallon idon Auntyn take ganin ya yi jawur kamar dai kuka ta yi. "Haba Iftihal ya za ayi in fasa madubi abu na je ɗakkowa shi ne ya fashe" "Amma kuka kika yi?"Ta ƙara jefa mata wata tambayar. "Kai na ke ciwo shi sa kika ga ya yi ja" "Sannu kisha magani" "Yawwa na sha magani ma" Iftihal kan ta ta kwantar akan cinyar Auntyn, sai kuma Auntyn ke shafa kan nata , shiru suka yi babu wanda ya ƙara magana. "Aunty yau ma bazan je school ɗin ba?" Iftihal ta jefo mata tambayar.Auntyn na ƙoƙarin bata amsa Safiya ta turo ƙofa ta shigo ɗauke da tsintsiya da abin kwashe shara wurin ta shiga gyarawa sai da ta tabbatar ya gyaru babu sauran wani madubin sannan ta fita daga ɗakin. "Yanzu time na zuwa school ya wuce, ba a son mutum ya je makaranta a makare saboda bulala malam ke yi amma ki bari za ki je"Cewar Auntyn tana cigaba da shafa kan Iftihal ɗin. "To shikenan, amma dai gobe zan je" Shiru Auntyn ta mata har sai da Iftihal ɗin ta sake mata magana sannan ta ce. "Kar ki damu" "Zan je?" Ta sake jefa mata tambaya. "Ki bari yanzu bana son surutu kai na yana ɗan sara min" "Sannu " Iftihal ta ce tana tashi zaune daga kwancen da take tana kallon Aunty cike da tausayawa. "Yawwa ai kaɗan-kaɗan ne ma " Aunty ta ce tana ɗaukan wayar ta ta kira telephone da ke falon ƙasa, Safiya na ɗagawa ta ce. "Ki zo"Kawai ta ce ta katse kiran. Da sallama ta shigo ɗakin bayan ta yi nocking an bata izinin shiga. "Gani Hajiya" Safiya ta ce lokacin da ta durƙusa a gaban gadon da Aunty take. "Ki ɗauketa ki je ki mata brush ki mata wanka sannan ki bata abinci ta ci" Auntyn ta faɗa tana miƙa mata Iftihal . "To Hajiya an gama" Cewar Safiya tana juyo bayanta Iftihal ɗin ta hau suka fito daga ɗakin. Bayan ta mata brush ta mata wanka sannan ta shiryata tsaf cikin riga da wando ƴan kanti pink clour masu matuƙar kyau ta gyara mata kan nata sai sheƙi yake, haka ta goyota suka sakko ƙasa ta zaunar da ita da akan kujera, kicin ta shiga ta ɗakko mata soyayyen dankali da ƙwai sai soyayyen plantain.A kan center table ta ɗora ta ɗakko kayan shayi ta haɗa mata tea mai kauri ta zuba abincin ta shiga bata a baki, suna cikin haka sai ga Aunty ta sakko daga saman ta zo ta zauna ta ɗora ɗaya kan ɗaya dan zuwa lokacin ba ta ko so ta tuno da Hajiya Azima dan tun da ta yi kuka sai ta ji zuciyarta ta yi sanyi remote ta ɗauka ta canja tasha zuwa arewa 24 sannan suka sakarwa juna murmushi ita da Iftihal. Ita dai Safiya ba abin da ta ce tana baiwa Iftihal abinci har sai da ta juyar da kai gefe alamar abincin ya isheta.Ajiye fork ɗin Safiya ta yi ta ɗakko kofin me tea ɗin da ta haɗawa Iftihal a hankali ta shiga ƙoƙarin bata dan gudun yin kuskure dan kaɗan da aikin Hajiyar ta mareta koma ta hanata albashi wannan watan. "kar ki bani tea ɗin da kai na zan sha" Cewar Iftihal tana miƙa hannu ta karba, Safiya ganin an karɓeta sai ta shiga tattare kayan abincin, ta gama haɗawa za ta ɗago daga sunkuyen da take aikwa Iftihal ta ɗauki wannan shayin da ke hannunta ta watsawa Safiya a jikinta har fuskarta sannan ta ce "Bana shan abu mai zafi bayan haka bana son ana cika min madara " Wani haushi da mugun takaici ne ya mamaye Safiya ga tea ɗin da zafi bai huce amma sai ta cije sai dai ta yi ƙoƙarin damƙe hannun ta domin ta ayyana a ranta ko za ta rasa aikinta yau sai ta naushi Iftihal a bakinta domin sai ta nuna mata cewa bakin rijiya ba wurin wasan makaho bane, sannan ɗan adam Allah ya ɗauka ka shi dole ma ta nuna musu kuɗinsu ba shi bane tun da ba za su iya yiwa kan su abu ba dole dai talakan shi zai musu, hannu ta dunƙule tana duba in da ya kamata ta kaiwa mugun naushi a jikin Iftihal ɗin. MMN AFRAH😍🥰😘 ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️ 💕ALAƘAR YARINTA💞 ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️ NA MMN AFRAH FIRST CLASS WRITER'S ASSO... Page9️⃣ &🔟 Wata tsawa da Hajiya Hauwa ta dokawa Safiya ita ta dakatar da ita daga shirin dukan da take ƙoƙarin ta kaiwa Iftihal, wani tsoro ne ya ziyarci Safiya dan sai a lokacin ta ji a ranta cewa lallai da ta kaiwa Iftihal dukan to tabbas da ta yi babban kuskure, dan wataƙila kafin ta rasa aikin nata sai ta fara rasa ranta dan tsaf Hajiya Hauwa za ta mata dukan mutuwa akan Iftihal. "Wace irin marar hankali ce ke in ban da jakanci da jahilci maimakon ki yi saurin tafiya ɗaukan mopa da ruwa ki zo ki goge wurin shi ne kika tsaya kina kallon Iftihal ɗin sai ka ce wanda ta yi wani abu, ko dan baku san darajar kuɗi ba saboda baku da su shi yasa za ki bar min capet da ruwan shayi a jiki sai ya dafe yaƙi fita" Aunty ta ce tana wani zazzare ido tana bala,i. "Ki yi haƙuri Hajiya yanzu zan gyara" Safiya ta ce tana ɗaukan kanukan ta nufi kicin domin ta ajiye su, ga wani zafi da raɗaɗi da fuskarta da ƙirjinta ke yi dan shayin akwai zafi amma saboda rashin imani na Hajiya Hauwa maimakon ta tausaya mata shi ne take mata faɗa bayan Iftihal ya kamata ta yiwa faɗan amma saboda sangarci da kuma ganin suna da kuɗi za su iya taka kowa ma hakan ya sa ta zamar da ƴarta ta sangartacciya.Sai da Safiya ta tsaya ta share ƙwallar da ta zubo mata tana da na sani akan aiki a ƙarƙashin Hajiya Hauwa da bata da mutunci ko kaɗan bare tausayi, bata koyi da sobar zamanta Hajiya Azima mata mai kima da darajanta ɗan adam pan aikinta tamkar ƴaƴanta haka ta ɗaukesu ba kyara ba tsangwama. Tana ta saƙar zuci ta dawo falon ɗauke da mopa da burket da ta haɗo ruwa mai ɗauke da morning fresh, ta shiga goge wurin, lokacin Auntyn na lallashin Iftihal akan ta yi haƙuri za a haɗa mata wani tea ɗin marar zafi sosai marar madara da yawa.Wani haushi da takaici ne ya turnuƙe Safiya tana Allah wadaran naka ya lalace ace maimakon uwa ta zama turba na gina rayuwar ƴaƴanta akan hanya daidaitacciya mai ɓullewa wajen basu kyakkywar tarbiya amma shi ne ita Aunty ta zama mai bada gudunmuwa wajen taɓarɓarewar tarbiyar ƴarta, babu abin da yarinyar ta sanj sai sangarta. "Dalla malama ki yi sauri ki gama ki haɗa mata wani tea ɗin"Cewar Auntyn cikin zafin rai. "To Hajiya" Safiya ta amsa mata, bayan ta ɗakko freshner ta fesa a wurin saboda ƙarnin madarar sannan ta ɗauke kayan da ta yi amfani da su wajen gyara wurin, kicin ta koma ta ɗauki gishiri ta shafa a wurin da aka watsa mata shayin dan da alama ma kamar wurin zai tashi, bayan ta shafa sai kuma ta wanke hannunta ta sake haɗa shayin marar zafi sai dai yana da ɗan ɗumi sannan ta fito ta zo ta durƙusa ta miƙawa Iftihal ɗin, tun da ta ce da kan ta za ta sha. Ƙin karɓar shayin ma ta yi tana kallon tv, kamar ma ba ita ake baiwa shayin ba, Auntyn kwa tana kallo ko ta yiwa Iftihal ɗin magana. "Ga shayin na sake haɗa miki"Safiya ta ce da ta fahimci bata da niyyyar karɓa. Banza ta yi da ita, can kuma a shelaƙe ta karɓa, kurɓa ɗaya ta yiwa shayin ta ɗaga ta watsar da shi, ta yi jifa da kofin ya tarwatse dan dai ma akan tiles ne ba akan capet ba.Safiya kai ta sunkuyar tana jin a ranta cewa lallai neman halal da wuya musamman a ƙarƙashin wanda ba su san kima da darajar ɗan adam ba.Hatta Hajiya Hauwa ranta ya matuƙar ɓaci da abin da Iftihal ɗin ta yi amma saboda bata so ta nuna mata hakan duk da cewa ita ce ta ɓata yarinuar gashi bata son kwaɓarta sai kawai ta danne zuciyarta ta ce. "Wai Safiya baki san aikin ba? Komai sai an faɗa miki kenan? Ba za ki kula ki gyara wurin ba sai ki wani sunkuyar da ka kamar mai yin zaman tahiya yayin gabatar da salla. "Ki yi haƙuri Hajiya yanzu zan gyara" Haka Safiya ta share wurin wurin ta goge tas, sannan ta ɗore wasu ayyukan dan wuni ake ana aiki ba kama hannun yaro. Da daddare zaune suke su duka iyalin gidan a dinning area domin gabatar da dinner, Hajiya Azima sanye take da wani leshi purple colour an mata ɗinkin buba ta ɗaura ɗankwalinta ta sanya sarƙa da ɗankunne na gwal sai sheƙi suke ga warwaraye da zobuna sai zuba ƙamshi take tamkar dai mai shirin zuwa wani gagarumin biki ko suna. Hajiya Azima mace ce mai son ado da kwalliya gata da matuƙar tsafta, hakan shi ke ƙara wutar soyayyarta a wurin mijinta yake kuma ƙara rura wutar tsanarta a wurin sobar zamanta Hajiya Hauwa dan ta tsani duk wasu abubuwan da Hajiya Azima ke yi. Alhaji, Hajiya Azima sai Hajiya Hauwa su ne a wurin kowa zaune yake Iftihal kawai ake jira a fara cin abincin domin komai ya kammala dan kuku ya shirya musu komai da komai duk da kasancewar Hajiya Azima mai son take yin girki da kan ta amma fitinar da Hajiya Hauwa ke tadawa yasa Alhajin dakatar da ita, dan dama ita duk ranar girkinta ita ce ke yin girki, ita kuma Hajiya Hauwa sai dai aci girkin kuku dan dama bata wani ƙware a girki ba gata kuma da son jiki, to idan Hajiya Azima ta yi girki ranar girkinta sai Hajiya Hauwa ta ringa sanabe tana cewa gishiri ya yi yawa ko dai an cika yaji ita ulcer ta za ta tashi kuma duk gassada ce dan ta ga Alhajin yana ta yabon abincin idan ana ci.Irin fitintinun da take yasa ya dakatar da Hajiya Azima da yun girki akan a bar kuku yana yi domin shi ma kukun nasu gwani ne a wurin iya girki babu abin da bai iya ba. "Ke dai bakya gajiya da caɓa ado kamar mai shirin zuwa gidan biki"Alhajin yace yana yiwa Hajiya Azima wani kallo ƙasa-ƙasa. Murmushi ta yi kafin ta ce "Ai indai abu ne zan yi dominka bana taɓa gajiyawa da shi, bare kwalliya ai ni kai ne gidan bikin nawa, matuƙar na yi abin da ya birgeka to tabbas kwalliya ta biya kuɗin sabulu" "Ai ba ma kuɗin sabulu ba harda kuɗin soso" Yace suna dariya su biyun ban da Hajiya Hauwa da ta cika ta yi fam sai bin jikinta take da kallo sanye take da baƙar doguwar riga sai ɗankwalin rigar da ta ɗaura shi ya yi baya,ko ɗankunne babu a kunnenta, ita dama ta gaji da yin wata kwalliya duk shigar da za ta yi ko wacce irin sutura za ta sanya sai ta ga bata yi mata kyau kamar yadda kayan ke yiwa Hajiya Azima. Ji ta yi kamar ta tashi ta bar wurin saboda tsabar takaici kamar sun manta cewa tana zaune a wurin.Wata hararar ƙasan ido take bin su da ita su duka biyun. "Assalamun alaikum" Safiya da ke goye da Iftihal ta yi sallama. Hajiya Azima ce ta amsa mata sallama, ƙarasa shigowa ta yi sai da ta zo har wurin nasu sannan ta sauke Iftihal ɗin ta ja kujera ta zaunar da ita sannan ta juya ta fita dan idan Alhaji yana nan ba ya bari a baiwa Iftihal abinci a baki cewa yake a barta ta ci da kan ta. "Iftihal ɗina barkan ki da dare" Alhaji ya ce yana kallonta da murmushi. "Abie ina yini" Ta faɗa tana rufe fuska dan ta san ya fala mata cewa yaro ne yake fara gaishe da babba amma ita mantawa take in ma ba Abie ya faɗa mata ba idan sun haɗu, mantawa ma take akwai wani abu gaisuwa saboda Hajiya Hauwa bata koya mata gaishe da mutane. "Lafiya ƙalaw my daughter bakya gaishe da mutane sai sun roƙa ko?" Shiru ta yi tana rufe fuska da hannayenta. "To ni kaɗai za a gaishe dani ?"Abie ya jefa mata tambayar dan shi mutum ne shi mai son ya ga yaronsa ya tashi cikin tarbiya. "Momma ina yini" Iftihal ta gaishe da Hajiya Azima dan dama Momma take kiranta. "Lafiya law iftihal" Cewar Hajiya Azima tana sakar mata murmushi. "Aunty ina yini" Ta juya tana gaishe da Hajiya Hauwa. "Lafiya" Hajiya Hauwa ta amsa a taƙaice, a wani daƙile kamar an mata dole. Daga haka Hajiya Azima ta shiga zubawa kowa abincin amma Hajiya Hauwa da kan ta, ta zuba nata, aka shiga ci Iftihal na ci da kan ta ashe dama rainin wayo ne ace komai sai an bata a baki dan tsabar sangarta. A haka suka kammala cin abincin, Hajiya Hauwa ta riga kowa tashi ta bar part ɗin ma baki ɗaya, su kuma suka koma cikin falon suna hira abin su cikin farinciki Abie na tambayar Iftihal batun zuwa islamiya ta ce bata je ba anan take faɗa masa yadda suka yi da Aunty da safe da ra mata zancen zuwa school.Ran shi ta ɓaci sosai da ya ji bata je islamiya ba hakan yasa ya ɗauki alƙawarin gobe da wuri zai fito domin Iftihal ɗin ta tafi makaranta dan ya fahimci cewa Hajiya Hauwa da gaske ba ta son barin yarinyar ta raɓi ilimi kowane iri sai nuna mata soyayyar banza da shagwaɓata na wofi wanda hakan bashi da wani amfani. ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️ 💕ALAƘAR YARINTA💞 ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️ NA MMN AFRAH FIRST CLASS WRITER'S ASSO... Page 11&12 _Washe gari_ Tun wajen ƙarfe shida da rabi Abie ya sakko ƙasa, ko Hajiya Azima bata sani ba dan bayan ya dawo daga masallacin asuba da suka ɗan taɓa karatun qur'ani sai suka koma suka kwanta shi ne bacci ya ɗauketa.Part ɗin Hajiya Hauwa ya nufa, nocking ƙofar ya shiga yi amma shiru ba a buɗe ba dan babu alamar motsin mutum ma bare ya sa ran za a buɗe, wayarsa ya koma ya ɗakko sannan ya dawo ya shiga kiran Hajiya Hauwa, sai da ya kira sau uku amma ba a ɗauka ba. Hakan ya sa ya koma ya shiga ta ƙofar baya wacce ake bi ta cikin kicin sa'arsa ɗaya ƙofar ba a kulle take ba amma a rufe take.Yana shigowa ya kunna fitilun sannan ya haura sama, ɗakin Iftihal ya fara zuwa ya buɗe ya kunna ƙwan ɗakin kwance take tana ta bacci abinta, tashinta ya yi sai kuma ya kira telephone na ɓangaren ƴan aiki, yace a turo masa Safiya ta zo sashen Hajiya Hauwa yanzu.Ba a ɗauki wani lokaci ba sai gata ta zo ya umarce ta data yiwa Iftihal ɗin shirin makaranta. Yana fitowa ya nufi ɗakin Hajiya Hauwa a buɗe ya samu ƙofar bata sanya makulli ba, yana buɗe ƙofar ya kunna futilar ɗakin, sai bacci take gabaɗaya ta cika ɗakin da munshari filon da ta yi matashin kai dashi ya shiga bugawa amma ko gizau ba ta yi ba.Kallo yake ƙare mata da alama ma ko sallah ba ta tashi ta yi ba dan dama Hajiya Hauwa ibadar nan da sauƙi dan mace ce wacce bata damu da ibadah ba. "Hajiya, Hajiya, Hajiya"Sai da ya kira ta sau uku tana ɗan bubbuga kafaɗarta sannan ta yi wata miƙa tana, tare da saurin sanya hannu ta make masa hannu dan bata ma san wa ke tashin ta ba. "Wai ba da ke nake ba, kamar wacce ta suma ko kuma mai baccin mutuwa sai wani magagin bacci kike kamar wata yarinya" Cewar Abie a fusace dan gabaɗaya ransa a ɓace yake. "Alhaji kai ne" Ta ce tana mai tashi zaune tare da sakin wata hamma ko bakin bata rufe ba. "Ni ne mana kin zo kin kwanta kina ta faman bacci, babu sallah ba salati, sannan baki ji na ce yau Iftihal za ta je makaranta ba, amma maimakon ki tashi da wuri ki sanya a shiryata shi ne kika kwanta kina baccin asara sai ta makara ki ce ba za ta je makaranta ba" "Wai yanzu Alhaji akan shirin zuwan Iftihal makaranta kake waɗan nan maganganun?" "Ba dole na faɗa ba kina so ki koyawa yarinya ƙin makaranta tun tana ƙatamarta" Baki ta taɓe ta fara jan jiki ta sakko daga kan gadon ta nufi hanyar bayi tare da cewa "Koma dai makarantar neman lahira ce a barni in shiga bayi in fito in fara gaishe da ubangiji" Ta ce tana shigewa bayin ta banko ƙofar saboda ta tsani maganar zuwan Iftihal makaranta amma ta ga alama Alhaji ya kasa fahimta, dan gaka ma ta ƙudurta a ranta cewa sai ta ɗauki lokaci mai tsawo za ta fito daga bayi sannan ta san likaci ya ƙure dan bata da masaniyar Abie ya tashi Iftihal ɗin har ma ya sanya Safiya ta shiryata. Kai Abie ya girgiza ya juya ya fito daga ɗakin nata sai da ya bi ta ɗakin Iftihal ɗin ya ga har an mata wankan ana sanya mata uniform sai murna take yau za ta je makaranta. "Abie har an kusa gama shirya ni sai in yi sallah, ba sai na ci abinci ba ma dan kar lokaci ya ƙure"Cewar Iftihal dan bata son yau wani abu ya hanata zuwa makaranta. "Kar ki damu Iftihal har kya ci abincin ma dan da sauran lokaci yanzu 6:50" "Toh Abie" Ta ce lokacin da Safiya ta gama sanya mata ƙaramin hijab domin ta yi sallah.Tana yin kabbara sai Abie ya cewa Safiya idan ta gama sallah ta kawo ta part ɗin sa domin ta yi break fast acan saboda ba ya so Hajiya Hauwa ta sanya su makara.Amsa masa ta yi ya juya ya sauka ya nufi part ɗinsa, lokacin kuku har ya fara jera wasu abubuwan na break fast akan dinnig ɗin. Sama ya haura domin zuwa shi ma ya shirya sabida tafiya office. Safiya ce goye da Iftihal sai ta rataya school back ɗin Iftihal ɗin a kafaɗarta suka taho part ɗin Daddy, abin da take so ta zuba mata ta fara bata a baki. Hajiya Hauwa ta daɗe a bayi sannan ta fito ta yi sallah ko azkar bata yi ba ta tashi ta naɗe dardumar sannan ta koma ta kwanta, sai da ta ga ƙarfe bakwai da arba'in sannan ta taso domin zuwa ta tashi Iftihal ta san dai yanzu kafin ta kira Safiya ra shirya yarinyar har ta ci abinci lokaci zai ƙure sai dai a haƙura da zuwa makarantar. Tana zuwa ta tura ƙofar ta ga wayam babu kowa a ɗakin, kofar bayi ta buɗe shi ma ta ga Iftihal ɗin bata nan dan haka da mamaki fal a fuskarta ta fito daga ɗakin tana tunanimninda yarinyar take da sanyin safiyar nan.Ƙasan ta sauka nan ma bata nan, wayar ɓangaren ƴan aiki ta kira ta ce a turo mata Safiya domin ta je ta dubo ta a cikin gidan amma sai aka sanar da ita Safiyar ta fito domin amsa kiran Alhaji.A fusa ce ta kama hanyar part ɗin Alhajin tana fatan kar hasashen ta ya zama gaskiya tana zuwa kwa ta ga Iftihal riƙe da lunch box ɗin ta har direbanta ya zo za su tafi, Alhaji da Hajiya Azima kuma zaune a dinning area ɗin. Wani ƙaton abu ne ya tokare mata maƙoshi har yaushe ne Alhaji zai fahimci cewa bata ƙaunar Iftihal take halartar makaranta tana da ƙuduri mai girma akan yarinyar amma bata ƙaunat yarinyar ta yi wano abi wai shi karatu.Tana ji tana gani hwkw Iftihal ta fice ita da Safiya za ta rakata wurin mota, Iftihal ɗin sai ɗagawa Hajiya Hauwa hannu take amma ko ta kulata har sai da kowa ya fahimci hakan, shi kwa Alhaji ko ta kan Hajiya Hauwa bai bi ba ita ma Hajiya Azima banza ta yi da ita dan ta ga abin nata ya zama hauka, ace ƴar ƙwaya ɗaya amma ana hana ta zuwa makaranta ita ko kunya ma Hajiya Hauwar bata ji. Ganin kowa ya shareta yasa ta koma part ɗin ta ranta na suya tana yin wani ƙudirin akan lallai sai ta ƴara tashi tsaye dan ta ga abin na Alhaji ba ƙarami bane ita kwa ta sanya a ranta cewa sai dai su yi ta fafatawa. _ALHAJI HAMZA_ Ɗan asalin garin kano ne a unguwar zoo road, iyayensa shi kaɗai suka haifa,suna kiransa da Hamzan sa, ya tashi a garin kano tare da mahaifansa anan ya yi karatunsa tun daga primary har zuwa zuwa digree ɗin sa.Iyayensa basu da wani arziƙi sai dai suna da rufin asiri, bayan ya kammala karatunsa bai samu aiki ba sai ya fara ɗan sana'a har dai daga bisani Allah ya sa ya samu aiki a wani kamfani garin Abuja, hakan yasa ya fara zuwa wajen aiki yana dawo wa a week end, tafiya ta yi tafiya har ya samu ya samu ɗan gida madaidaici ya siya ciki da falo sai banɗaki haka ya dawo da mahaifansa kusa dashi suke zaune tare. Daga baya yana ƙara samun buɗi sosai domin Hamza ya kasance mutum mai gaskiya da riƙon amana hakan ya taimaka masa da wurin aikinsa suka riƙeshi da kyau sanadin gaskiyarsa, Har ake ƙara masa girma.Bayan ya sayi gida mai ɓangare biyu sai mahaifansa suka ce ya yi aure haka kuwa aka yi ya auri budurwarsa Azima ƴar garin Kano ce sun daɗe suna soyayya, da suka tare a sabon gidan su a ɓangare ɗaya iyayen Hamza ma a ɓangare ɗaya haka suke zaune lafiya dama Azima uarinya ce mai biyayya da kuma girmama na gaba hakan yasa zaman nasu yin ƙarƙo. Wata rana da ta zame musu rana mafi muni a cikin tarihi shine hatsarin da iyayen Hamza suka yi daga Kano zuwa Abuja domin sun je sada zumunci wurin ƴan uwa da abokan arziƙi hakan ne ya yi sanadiyyar rasa rayukasu.Haka aka yi zaman makoki aka tashi sai dai mu ce Allah sa mu yi kyakkyawan ƙarshe amin. Shekaru kusan bakwai kenan su Hamza Allah bai basu haihuwa ba, gashi a lokacin har ya je ƙasar India ya ƙaro karatu, ga buɗi na arziƙi ta ko ina amma kuma babu wani labari na haihuwa hakan yasa Azima ta ɗaga hankalinta amma shi Hamzan ke kwantar mata da hankali akan komai lokaci ne.Ya sake musu gida na gani na faɗa domin yanzu shi ma ya mallaki kamfano ni da dama sai dai ma wasu su ci abinci a ƙarƙashinsa.Yanzu ma yana aiki a ɗaya daga cikin kamfanonin sa kuma mutanen da ke tate da shi suna jin daɗin aiki da shi domin mutumin da ya san kima da darajar ɗan adam Watarana ya je Kano ziyara ya dawo sai motarsa ta lalace a Suleja, hakan yasa ya rasa yadda zai yi, wani gida da yake kan hanyar inda motarsa ta lalace mai gidan ya bashi tarbarma sannan ya bashi abinci har dai bakaniken da ya masa gyara ya kammala, sosai Hamza ya ji daɗin karramawar da mutumin ya masa hakan yasa alaƙa mai ƙarfi ta shiga tsakaninsu duk da cewa mutumin ya haifi Hamzan amma haka suka ƙulla alaƙa mai kyau, har ta kai Hauwa ta ƙyalla ido ta ganshi hakan yasa ta ɗauki alwashin sai ta aureshi duk da kasancewar mahaifinta talaka amma dai bata da buri da ya wuce auren mai kuɗi, shi yasa da ta ga Hamza ce sai ta aureshi ko ta halin ƙaƙa, haka suka shiga suka fita ita da mahaifiyarta, sai da Hamza ya auri Hauwa. Tun da ta tare a gidansa ta ga yadda yake ji da uwar gidansa hakan ya ƙara rura wutar kishi a ranta, ta ji duk duniya babu wacce ta tsana irin Azima haka ta sa a ranta ita ce za ta haifawa Hamza magaji dan ta zama tauraruwa kuma ta cusawa Azima haushi na rashin haihuwa. Makkah kwa sai da ta je sannan hankalinta ya kwanta,dan ta tsani ta ji ana kiran Azima da Hajiya. Zuwanta da wata biyar sai ciki ya ɓullo a jikin Hajiya Azima, hankalinta ya yi matuƙar tashi haka suka dinga shigi da fice akan kar ta haihu amma cikin hikimar ubangiji lokacin haihuwa na yi ta haifi ɗanta namiji a asibiti sai dai kwanan yaton ɗaya a duniya ya amsa kiran ubagiji.Murna a wajen Hajiya Hauwa ba a cewa komai sosai ta yi farinciki.Hajiya Azima kwa ta ji babu dali ganin yadda suka ƙwalla fa rai akan cikin har ma da ɗan lokacin da ya zo duniya ita da Alhaji Hamza da duk wani masoyinta, amma haka suka fawwalawa Allah komai. Sai da Hajiya Azima ta shekara shida da haihuwar ɗan da ya koma, sai kuma ciki ya bayyana a jikin Hajiya Hauwa, sai wani iyayi da sanabe take wai ita mai ciki za ta haifi magajin Alhaji ya gaji dukiya, shi ne fa da cikin ya isa haihuwa ta haifi Amina ana kiranta Iftihal.Hajiya Hauwa tun da ta haifi Iftihal take zaton Alhaji zai juyawa Hajiya Azima baya saboda bata haihu ba sai ta ga saɓanin hakan dan babu wani abu da ya canja hakan shi ne ke baƙanta mata tana ganin kenan dai duk da ta haihu bata samu martaba da kimar da Hajiya Azima ta samu ba a wurin Alhajin. sai kuma ta fara zargin ko Alhaji ya fi ƙaunar a haifa masa namiji, shi yasa take ganij bata samu wani matsayi da take son ta samu a wurinsa ba.Amma kuma daga baya dai ta fahimci Alhajin bashi da wani zaɓi sai abin da Allah ya bashi ko mace ko namiji duk yana so hakan yasa take fatan Allah ya ƙara bata haihuwa ta haifi namiji duk da tana jin tun da Hajiya Azima bata haihu ba babu yafda za ayi ta haɗa kan ta da ita duka da cewa mace ta haifa. wannan kenan. ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️ 💕ALAƘAR YARINTA💞 ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️ NA MMN AFRAH FIRST CLASS WRITER'S ASSO... Page 1️⃣3️⃣&1️⃣4️⃣ _Hizbullah_ Bayan shekaru biyar Shaƙuwarsa da Ridallah kullum ƙaruwa take, hakan yasa gabaɗaya bashi da wani wanda ya shaƙu da shi sai Ridallah, bayan iyayensa Umma Sadiya, da kuma mahaifinsa Malam Auwalu,babu wani wanda ya shaƙu dashi sai Ridallah Ita ma Ridallah haka ne a nata ɓangaren in ban da mahaifiyarta Baba Habiba dan mahaifinta ya rasu sai mahaifiyarta kaɗai ce a raye. A haka suka taso ko yaushe suna tare babu abin da ke raba su sai bacci, tare suke zuwa makarantar boko tare suke zuwa islamiya, tare suke cin abinci tare suke komai idan ɗaya bashi da lafiya to ɗayan ma haka zai wuni a kwance wani lokacin ma shi ma ɗayan kamuwa yake da jinyar da ɗayan ke yi wannan shi ne babban abin da ya ƙara sanya iyayensu ƙarfafa zumuncin maƙotaka a tsakaninsu dan un ban da maƙotaka babu wani abu da ke tsakanin su na ƴan uwantaka. Rayuwa na ta tafiya, da kaɗan -kaɗan ranaku ke rikiɗewa su koma sati, sati ya rikiɗe ya koma wata da sannu su ma watannin ke haɗuwa su bada shekara hakan ya kan sa shekarar ta haɗu da wata shekarar har su bada shekaru. Hakan ne yasa wucewar shekarun ya kawo mu lokacin da Hizbullah ya kammala karatunsa na secondry school, a lokacin Ridallah tana primary 5 dan dama lokacin da take primary 1shi kuma yana J.s.s 1. Yana zaman jiran fitowar jarabarwar su ta SSCE sai kuma wani mummunan abu ya faru, wanda ya yi sanadin wargaza gabaɗaya farincikin sa da ma sanya mahaifansa cikin damuwa saboda halin da ya tsinci kan sa a ciki. A wata ranar asabar ce aka tashi aka nemi Ridallah da mahaifiyarta Baba Habiba aka rasa babu wanda ya san inda suka tafi, dan ko kaya ma ba su ɗauka ba haka suka tafi gidan ma ko rufewa ba a yi ba. Sosai Hizbullah ya shiga damuwa da ƙunci na tashin hankali, dan yanzu ya daɗe da gano cewa ba wai shaƙuwace kawai tsakaninsa da Ridallah ba tabbas akwai wata ɓoyayyar soyayya a cikin zuciya, Umma Sadiya sun rasa yadda za su yu dashi sun yi lallashin sun yi faɗan sun yu lallamin amma dai Hizbullah ya yi nisa sosai baya jin kira.Da yake lokacin da Baba Habibabta dawo gidan da ke kusa da na su Hizbullah, lokacin Hizbullah yana ƙarami bai sani ba amma dai da wasu ƴan rani ne a gidan mata da miji da yaransu to da suka koma garinsu sai Baba Habiba ta kama gidan dan dama gidan haya ne me gidan yake bayarwa haya. Dan haka Umma Sadiya ta shiga masa bayanin duk yadda abun ya faru tun daga lokacin da Baba Habiba ta dawo gidan da zama lokacin Ridallah tana ƴar jinjira, sosai sabuwar haihuwa ce, to lokacin ne da Hizbullah ya ƙyalla ido ya ga Ridallah sai yake zuwa gidan wurinta.Ganin halin da ya shiga har ta kai ga kwantawa jinya dan duk inda suke zaton za su gan su sun cigita amma shiru kake ji wai malam ya ci shirwa.Hakan ne yasa Malam Auwalu ya nemi mai gidan da Baba Habibar ke zaune domin jin ko daga ina Baba Habibar take tun da shi ya bata hayar gidan, amma abin mamaki mutumin yace wallahi bai san daga inda take ba, shi dai kawai abu ɗaya ya sani maƙocinsa ne ya haɗa shi da ita, shi ma kuma maƙocin ba wai ya san ta bane kawai dai ta je wurinsa ne akan tana neman taimakon inda za ta zauna ko da gidan haya ne tana so wai mijinta ne ya rasu ya barta da tsohon ciki shine kuma bayan ta haihu ƴan uwan mijin suka koreta akan wai ba za su bata gado ba, hakan yasa ta baro garinsu ta dawo nan.Shi ma tausayinta yasa ya haɗani da ita na bata gidan ta zauna amma ko kuɗin hayar baya karɓa. Wannan jawabi da Malam Auwalu ya zo da shi, shi ya ƙara saka Hizbullah a cikin matsananciyar damuwa, dan dama yana tunanin a wurin mi gidan za a samu ɗan labarin garin da suka fito dan abi sawu to kuma sai aka samu akasin hakan.Da farko ma an yi tunanin ko kidnapers ne suka ɗauke su amma daga bisani an fahimci ba haka bane.Duk wanda ya ga Hizbullah sai ya matuƙar tausaya masa saboda rabuwa da abin da ka shaƙu ba ƙaramin abu bane, akwai damuwa sosai duk ya ƙare ya yi baƙi baya iya cin abinci kullum yana keɓance a ɗaki dama ba wani abokai gareshi ba Ridallah ita ce aboki ƙawa sannan ita ce komai nasa.Yanzu kwa da bata nan sai ya zama abin tausayi.Kullum yana ɗaki a rufe yana kuka rashinta ji yake zuciya da jijiyoyinsa ba za su taɓa iya jure rashinta ba, idan son ganinta ya ciyoshi haja zai fita ya yi ta yawo wuri-wuri yana nemansu gani yake kawai zai iya ganinsu idan ya gaji da yawo sai ya ya je bakin ruwa ya zauna masu kamun kifi suna ganin kamar zuwa ya yi domin yake kallon yadda ake kama kifi amma shi bai ma san me suke ba gangar jikinsa ce a tare da su amma zuciyarsa ta lula duniyar tunani da jimamin halin da ya tsinci kan sa a ciki na rashin abar ƙaunarsa ƙanwarsa wacce ya shaƙu da ita Ridallah. A wannan hali da yake ciki ne jarabawarsu ta fito ya yi ƙoƙari sosai, domin ya cinye jarabawar gabaɗaya, amma shi ko murnar hakan ba ya yi sai dai iyayensa ne ke ta murna da farincikin hakan.Ganin hakan da Malam Auwalu ya yi, ya samu abokinsa Malam Iro da maganar halin da Hizbullah ɗin ke ciki, dan yana jin tsoro kar damuwar da yake ciki ta shafi karatunsa.Malam Iro ya baiwa Malam Auwalu shawara akan ya sanya Hizbullah ya cike scholarship ko Allah zai sa ya samu idan ya samu ya fita wata ƙasar karatu zai fi maida hankali ga karatun nasa idan ya ga ya yi nisa da ƙasar ma baki ɗaya ba kamar anan ba ko yaushe zai ke tunanin zai ganta ko zai haɗu da ita.Wannan shawara ta yiwa Malam Auwalu daɗi sosai dan yana ganin hakan shi ne mafita dan ita damuwa a cikin zuciya take babu wani wanda zai iya cirewa wani daga zuciya sai ko a taya mutum da addu'a akan Allah ya cire masa. Duk da Umma Sadiya bata ƙaunar Hizbullah ya mata nisa domin kuwa shi kaɗai ne ɗan da Allah ya mallaka mata, amma saboda suna so ya samu kyakkyawar rayuwa da ilimi mai nagarta hakan yasa suka amince masa ya cike form ɗin schoolarship ɗin amma a ɓangaren Hizbullah shi dai bashi da wani zaɓi dan shi komai yanzu ba ya jin daɗinsa, sai dai baya so kwata-kwata ya bar ƙasarsa ta haihuwa saboda ya san akwai ɓarin jikinsa, mahaɗar rayuwarsa burin zuciyarsa a cikin Niger'a wato Ridallah. Cikin ikon Allah Hizbullah yana daga cikin wanda gwabnati ta biya wa karatu zuwa ƙasar china, iyayensa sun yi matuƙar murna da sanya albarka a cikin lamarin.Haka aka yi ta shirye-shirye aka yi passport sannan aka masa biza da komai da komai har Allah ya kawo ranar tafiyar, ta Dutse da ke Jigawa State za su tashi haka iyayensa suka masa rakiya har airport ɗin ya yi sallama da iyayensa suna masa fatan alkairi suna kukan rabuwa da shi, shi kuma kuka biyu yake ɗaya kukan rabuwa da iyeyen nasa ɗaya kuma kuka rabuwa da ƙasar da masoyiyarsa ke ciki tun da har yau babu labarin su Ridallah ɗin. Haka su Umma Sadiya suka tsaya har sai da jirgin su Hizbullah ɗin ya tashi sannan suka baro airport ɗin.Sun sauka lafiya a inda suka samu masaukin su da aka ba su acan ƙasar amma dai ba cikin makaranta suke ba gida ne wanda bashi da wani nisa da makarantar tasu, yawanci dama duk ƴan Nigeri'a ne wanda gwabnati ta biya musu schoolarship, da wanda suka kusa kammalawa da kuma wanda shekaru biyu ya rage musu da ma wanda su ne ƴan wannan shekarar.Gida ne mai tsari hawa -hawa wasu a sama wasu a ƙasa ɗakuna ne gasu nan kowa da nasa akwai kuma bayi a ciki har da kicin.A upstairs Hizbullah ya samu ɗaki bayan ya buɗe da makullin da aka bashi ya shiga ɗaki yana ƙare masa kallo akwai komai da komai a ciki haka ajiye jakarsa, yana leƙa ko'ina sai dai akwai ƙura dan ba kowa ke zaune a ciki ba. Yana tunanin yadda zai yi da gyara ɗakin domin yana buƙatar tsintsiya da mopa, gashi baya so ya fita ya tambaya dan ya ga kowa harkar gabansa yake, ɗakin da ke kusa da nasa kwa ban da kiɗa babu abin da ke tashi a ciki. "Barka da zuwa bro kai ma saukar yanzu ne?" Ya tsinkayi wata murya a bayansa.Juyowa ya yi domin ganin mai maganar, wani matashj ya gani wanda bai fi sa'an shi ba tsaye yana masa murmushi.Hizbullah duk da baya jin daɗin zuciyarshi gashi kuma baya son yawan hayaniya, amma haka ya daure ya ƙaƙaro murmushi ya ce. "Eh saukar yanzu" "Ayya sannu da zuwa mu kam mun ɗan wartsake gajiya, dan yau kwananmu biyu da zuwa"Matashin ya faɗa lokacin da yake ƙarasowa cikin ɗakin. Shiru Hizbu ya yi yana tunanin amsar da zai bashi dan shi bai saba da magana da abokai ba, babu wanda ya sani sai Ridallah, ita ce abokiyar hirarsa ita ce ke sanyashi nishaɗi tun bata san me zata ce masa ba ya saba da gwalan gwalantun ta tun tana ƙarama.Wata ƙwallah ce ta ciko masa idanunsa da bai shirya zuwanta ba dama tun a jirgin yake cike da damuwa da alhinin baro ƙasar da take.Haka yake ta tunani a jirgin har dai bacci ya yi nasarar ɗaukansa. "Haba mazaje ya da ƙwallah haka, ai fa dama rabuwa da iyaye sai an kai zuciya nesa but be a man kar kake yarda wani na ganin hawayenka, za ka saba ne dan nima nan haka na wuni na kwana da tunanin gida amma yanzu da mun yi waya shikenan" Cewar matashin yana dafa kafaɗar Hizbu. "Ba komai ba kuka nake ba ai, kawai dai na tuna wani abu ne" "Yawwa my bro sunana Abulkairi Abubakar ana kirana da AA ni ɗan garin Kano,a unguwar hotoro haka kawai tun da na ga zuwanka na ji kawai ka burgeni ga ɗakina can sai ka wuce shi za ka zo naka" "Thank u, sunana Hizbullah Auwalu ni ɗan jihar Jigawa ne a garin Haɗejia unguwar ƙofar arewa" "Masha Allah suna mai daɗi " Murmushi suka yi a tare, kallon ɗakin Abulkairi ya yi ya ce "Yanzu za ka ga mai gyaran wurin ya zo,kafin ya rufe bakinsa sai ga wani saurayi sanye da wasu kaya da alama ma,aikaci ne a wurin da tsintsiya da mofa ya musu sallama tare da gabatar da kansa a matsayin ɗaya daga cikin masu shara da goge -goge na gidan cikin harshen nasara. "Mu je ɗakina kafin ya gama gyara maka nan ɗin"Abulkairi yace yana kama hannun Hizbullah tare da ɗaukan jakar Hizbullah ɗin saboda kar ta yi ƙura suka fita daga ɗakin suka ba mai sharar damar yin aikinsa. Ɗakin Abulkairi suka shiga, gabaɗaya yanayin tsarin ɗakin irin na Hizbu ne sai dai wannan a gyare yake tsaf, saɓanin na Hizbu da babu gyara.akan ɗaya daga ckn kujerun suka yiwa kan su masauki, bayan Abulkairi ya ajiye jakar, frige ya buɗe ya ɗakko lemuka da ruwan roba ya ajiye a gaban Hizbu kicin ya wuce ya ɗakko kofi ya kawo masa.Ganin bashi da niyyar ɗaukan drinks ɗin ya sha hakan yasa Abulkairi ɗaukan ruwan ya buɗe ya tsiyaya masa a kofin ya miƙa masa tare da cewa. "Haba bro ka saki jikinka dan Allah sai wani ɗari -ɗari kake ka kasa sakin jiki dani" Ya faɗi hakan yana murmushi.Shi dai Hizbu bai ce komai ba ya miƙa hannu ya karɓi ruwan tare da kaiwa bakinsa yana mai ambaton Bismillah, ya kafa kai ya shanye ya ajiye kofin.Yana ajiyewa Abul ya ɗauki lemon ya buɗe zai tsiyaya masa a kofi. "Ka barshi haka ma " "Kana nufin ba zaka sha lemon ba?" "Eh "Kawai yace a taƙaice ya koma ya jingina da jikin kujerar ya lumshe idanunsa. "Ka koma kan gado ka kwanta in bacci kake ji" Da yake ɗakin kato ne daga can gefe akwai gado madai daici da wardrobe sai kuma kujeru guda biyu a tsakiya sai su frige kayan kallo da komai da komai na buƙata haka kowane ɗaki yake, da kicin da bayi duk a ciki. "Bana jin bacci" Hizbu yace cikin ƙaguwa dan ya fara gajiya da waɗannan tambayoyin. "Na lura dai baka fiya son surutu ba" Abul yace yana murmushi, shi dai Hizbu idanunsa kawai ya lumshe bai kuma cewa ƙala ba. Bayan mai gyara ya gama suka koma ɗakin Hizbu Abul na riƙe da jakar, suna zuwa komai tsaf sai ƙamshi ke tashi haka Abul ya zauna yana kallo shi kuma Hizbu ya shiga wanka.Bayan ya fito ya sanya kaya marar nauyi, ya fitar da sauran kayan ya jera a cikin wardrobe ɗin ya fito da wayarsa daga aljihun jakar, sai ya koma ya zauna a kujera yana ɗan danna wayarsa shi kuma Abul yana kallo dan da ya lura Hizbu ba ya son yawan magana sai ya ƙyaleshi dan a tunaninsa ko gajiya ce ta sanya yake hakan bai san ba abin a jininsa yake, surutunsa na tashi ne idan yana tare da Ridallah. _Bayan sati biyu_ Lokacin Hizbu har an zama ƴa gari domin yanzu har sun fara zuwa school, an fara karatu ba kama hannun yaro, yanzu abotarsu ta ɗan yi ƙarfi da Abul domin Hizbu ya lura yana da kyawawan ɗabi'u hakan yasa ya saki jiki dashi sai dai idan surutu ne ya yi yawa Hizbu bai biye mishi, shima kuma Abul da ya fahimci halin Hizbu ne rashin son magana sai yake ƙyaleshi idan ƴan kuramen suka zo.Yanayin zamantakewar su abin sha'awa basa shiga harkar kowa in ba gaisuwa ba bare kula ƴan mata kowa yana yin abin da ya kaishi. Duk da ba department ɗaya suke ba amma wani lokacin tare suke tafiya school, kowa sai ya nufi nasu ɓangaren domin aiwatar da abin da ya kaishi.Hizbu yana waya da su Umma amma duk lokacin da zai kira su sai ya ji zuciyarsa ta masa rauni saboda tuno Ridallah, sannan duk lokacin da suka yi waya sai ya tambayi labarin Ridallah ko zai ji an ganta amma magana ɗaya ce ko yaushe babu labarinsu hakan na sanya ya ji duk damuwa ta dabai baye masa zuciya dan ba ya jin dai-dai da second ɗaya zuciyarsa za ta manta da Ridallah domin ita ɗin a cikin jininsa take. MMN AFRAH😍🥰😘 ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️ 💕ALAƘAR YARINTA💞 ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️ NA MMN AFRAH FIRST CLASS WRITER'S ASSO... Page1️⃣5️⃣&1️⃣6️⃣ _Ridallah_ A ranar da za a nemi su a rasa da cikin dare, misalin ƙarfe biyu da wani abu Baba Habiba ta je bayi domin yin fitsari sai kuwa take jiyo muryoyi na maza suna magana ƙasa-ƙasa, duk da bata jin me suke cewa amma ta tsorata saboda a jikin katangar gidanta suke butar ta ajiye a hankali ta lallaɓa ta fito daga bayin ta je jikin katangar gidan inda za ta fi sauraren me suke cewa dan dai ta sana tabbas akwai wani abu tun da mai zai zaunar da mutane har wannan lokacin suna magana kuma raɗa-raɗa, tana kai kunnenta kwa sai ta fara jiyo me suke cewa. "Kawai mu haura ta katanga, tun da babu namiji a gidan daga ita sai ƴarta ta, na ci alwashin sai dukanmu mu ukun mun musu faɗe, dan ita yarinyar sai mun kasheta bayan mun mata fyaɗen saboda Hizbullah, a kanta ya ƙi amincewa da buƙatarmu yana ganin mutane a raine, to zamu gama da ita sai mu buɗe ƙofar gidan mu fice kafin asirinmu ya tonu. "Oga ka rabu dashi zai zo hannu ne dama saboda yarinyar nan da yake so shi sa bai amsa tayin ba, amma yanzu in ya ga an yi mata fyaɗe an kasheta ta bar duniyar dole zai ƙauna ce ka ya ke biya ma buƙatarka"Ɗayan shi ma ya amsa masa. "Yanzu ga wancan Alhajin can ya yi dare inaga daga Hotel yake kasan shi mayen mata ne, bari idan ya shige gida sai mu haura tun da yanzu ma bai gan mu ba" "Gaskiya ne yau akwai kwasar gara duk da ma dai mata ba wani damun mu suka yi ba, mun fi ƙarfi a neman ƴan uwanmu jinsinmu maza, amma saboda wannan mai taurin kan gwara mu afka musu tun d.... Cikin hanzari Baba Habiba ta baro jikin katangar jikinta sai mugun rawa yake, gabaɗaya ta susuce hankalinta a mugun tashe yake burinta kawai su bar gidan kafin mazan su duru, ɗaki ta nufa Ridallah da ke kwance tana baccinta hankali kwance, hannun Baba Habiba har karkarwa yake ta ɗago Ridallah tare da toshe mata baki, da yake Ridallah ɗin bata da wani magagin bacci ta buɗe idanunta amma tsoro sai ya kamata ganin Babarta ta toshe mata baki, hannunta kawai ta kama ta sakko daga kan gadon ganin hakan yasa Ridallah gane akwai wani abu da ke faruwa. Gani ta yi Baba Habiba ta nufi hanyar zauren ƙofar gida, duk cikinsu babu mai takalmi a ƙafarsa, a hankali Baba Habiba ta zare sakatar ƙofar gidan suka buɗe suka fita a hankali, suna fita suka zura da gudu babu kowa a titin saboda dare ne hakan ya basu damar gudu akan titi, gudu kawai suke ba su san inda suke saka ƙafafunsu ba.A can cikin gidan kuwa mazan sun sami nasarar haura katangar su duka uku, shigarsu gidan ke da wuya suka fara duba ɗakunan domin aiwatar da abin da ya kawo su, suna dubawa suka fahimci babu kowa a cikin gidan suka duba ƙofar gidan ganinta a buɗe yasa suka fahimci cewa masu gidan sun gudu ne da alama sun musu laɓe ko dai makamancin haka A take suka mara musu baya domin sun ci alwashin sai sun aiwatar da ƙudirinsu a yau ɗin nan! Ƙarfin namiji da mace ba ɗaya bane haka gudu da juriyar da namiji zai yi ba lallai ne mace ta yi ba.Wannan dalilin ne yasa mazan nan suka fara hango su Ridallah da ke sheƙa gudu, sai dai akwai tazara a tsakaninsu.Baba Habiba da yake suna gudu tana waiwayowa amma duk da layikan unguwanni da suka yi canjawa amma sai da suka lura suna biye da su hakan yasa suna shan wata kwana kafin mazan su ƙaraso Baba Habiba tasa suka shiga cikin wani kwalbati wanda babu ruwa a ciki suka kwanta rubda ciki yadda ba za a gansu ba suna fata da addu'ar kar Allah yasa su gansu domin babu mai cetonsu sai Allah, gashi talatainin dare kowa yana gidansa yana bacci. Mutanen nan na ƙarasowa kwanar nan su duka ukun suka tsaya, suna ta waige-waige sai haki suke na gajiyar gudun da suka yi kamar an sa su dole. Tafiya suke suna ɗan duba wa amma ba su gan su ba, haka suka zo har dai -dai kwalbatin nan suka tsaya, gaban Baba Habiba da na Ridallah sai bugawa yake da ƙarfi suna fatan kar Allah yasa su gansu.Ɗaya daga cikinsu ne yave zai yi fitsari dan haka ya ƙarasa bakin kwalbatin da su Ridallah suke, daga tsaye ya shiga yin fitsari a cikin kwalbatin, su Ridallah fuskokinsu suka sanya a tafukan hannayensu suka rufe suna jin yadda mutumin nan ke tsula fitsari a jikinsu domin fitsarima ba wai a wuri ɗaya yake yi ba kawai wasa yake da fitsarin yana watsawa ko ina, har sai da ya gama fitsarin sannan ya gyara wandonsa, sai ya juya ga sauran yace "ina ga fa sun bi wancan layin" Ya faɗa yana musu da hannu.A guje suka tafi dan duk a tunaninsu su Ridallah suka marawa baya. Suna tafiya, jin su Baba basa jin motsin kowa alamar sun yi nisa haka suka tashi suka fito daga cikin ramin, basu damu da fitsarin da ke jikinsu ba dan burinsu kawai su tsira da mutunci da rayuwarsu.Hanya suka canja suka cigaba da gudu har sai da suka yi nisa sosai, dan gabaɗaya ma hanyar barin garin suka ɗauka dan sun tsorata sosai haka suke gudu ga tsananin gajiya sai da suka yi nisa da gari sosai sannan suka samu wata ƴar siririyar hanya suja bi hanyar ga tsananin duhu haka suka shiga wurin a ƙarƙashin wata bishiya suka yada zango suna ta haki saboda gudun da suke yi.Haka suka kwana a wurin cike da tsoro da fargaba, da asubar fari suka yi taimama suka gabatar da sallar asuba, da duku-duku suka cigaba da tafiya dama saboda kar wanda ke nemansu suje tashar mota shi yasa suka ƙi zuwa tashar sannan yanzu ma suna iya biyo bayansu, sai da suka yi tafiya mai ɗan nisa sannan suka tsaya a hanya bakin titi suka tsayar da motar haya suka shiga direban ya tambayesu garin da za su sauka Baba Habiba ta ce garin Gumel. Sai da suka yi tafiya mai ɗan nisa sannan hankalin Baba Habiba ya ɗan kwanta, ita kwa Ridallah dama tun da ta ɗora kan ta akan cinyar Baba sai wani bacci mai nauyi mai cike da tarin gajiya ya ɗauketa saboda basu runtsa ba.Har sai da suka shia cikin garin Gumel sannan ne Baba ta tasheta, a nato aka sauke su Baba ta kunce gefen zaninta da akwai kuɗin da ta ƙulle ta ɗauka ta baiwa mai mota.Napep suka tare suka shiga Baba ta ce a kai su unguwar ɗantanoma, a dai-dai wani gida aka saukesu ta sallami mai napep ɗin suka sannan suka shiga cikin gidan. Sallama Baba ta yi, aka amsa musu tare da basu izinin shiga, suna shiga matar gidan ta ce "Habiba?" Ta faɗi hakan cike da mamaki akan fuskarta. Murmushi Baba ta yi ta ce "Na'am Rahma" Cikin kulawa ta musu iso har cikin ɗaki tana ta faman musu sannu da zuwa tare da nuna jin daɗinta da ganinsu.Ridallah ce ta fara gaisheta ta amsa cikin sakin fuska da nuna jin daɗinta.Sannan suka shiga gaisawa da Baba Habiba cikin kewa da yaushe gamo.Ruwa ta gabatar musu duk da akwai tarin tambayoyi birjik a bakinta dan ganinsu da ta yi wujiga-wujiga ko takalmi babu. Bayan sun ɗan huta Rahma ta ce Ridallah ta shiga wanka, ba musu kwa ta shiga dan lokacin kusan sha biyu na rana dama watan buƙatar watsa ruwa a jikinta.Bayan shigarta wanka Baba ta shiga yiwa Rahma bayanin dalilin barowarsu hadejia , Rahma ta jimanta abin tare da yiwa Baba jaje akan abin da ya so samun su tare da murna akan tsallake rijiya da baya da suka yi. A nan Rahma ta shiga yiwa Baba bayani akan tun bayan mutuwar mijinta aka bata timunin takaba take zaune a gidan sai ƴan siye d siyarwa da take da kuma aikin abinci a wata makarantar kwana ta mata da take cikin garin Gumel ɗin. MMN AFRA😍😘 ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️ 💕ALAƘAR YARINTA💞 ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️ NA MMN AFRAH FIRST CLASS WRITER'S ASSO... Page1️⃣7️⃣&1️⃣8️⃣ _Hajiya Hauwa_ Zaune take a bakin gado ta haɗa hannaye biyu a kumatun ta, ta yi tagumi kamar wacce aka aikowa da saƙon mutuwa, abubuwan da suke faruwa ba ƙaramin ɓata mata rai suke ba ace kullum magana ɗaya yanzu tun da class mate na Iftihal suka kammala primary school Alhaji ya sakota a gaba wai da gangan take hana Iftihal ɗin ziyartar makaranta yanzu gashi nan tana neman ta mata asara. Iftihal ɗin ce ta shigo ɗakin ko sallama babu bare neman izini, sanye take da wata doguwar riga ƴar kanti wacce tsayinta iya gwiwarta ne, sai phone ɗinta riƙe a hannunta tana jin waƙa, headphone ɗin ta zare daga kunnenta, sannan ta ɗan buga jikin Auntyn nata a ɗan firgice ta ɗago domin kwa ta yi nisa cikin tunani, kallonta Auntyn ke yi tana ƙarewa gabaɗaya jikin Iftihal ɗin kallo kamar dai yau ne ranar farko da ta fara ganinta sosai yarinyar halittar ta da surorinta ke haɓaka kamar wacce ta ke shirin kammala secondry school kallonta take daga sama har ƙasa tana hasasho yadda idan ta kasa hajarta za ta samu ciniki sosai da kuma riba mai tarin yawa, wani murmushi ne ya maye gurbin ɓacin ran da take ciki wanda hakan yasa Iftihal ɗin cewa "Aunty yanzu nan fa kika yi shiru tare da yin nisa a cikin tunani amma kuma yanzu gashi kina kallona kina murmushi" "Iftihal kenan akwai dalilin da ya sani shiga cikin damuwa, wanda ba komai bane hakan illah yadda Abienki ke takura min akan rashin zuwanki makaranta, amma nasan ba komai ke sanyashi yin hakan ba sai rashin sani wanda ya fi dare duhu! Baisan irin ƙudurin da nake da shi akan ƴata ba shi yasa yake faɗan rashin zuwanki makarantar.Amma kuma dana kalleki sai na tuna da wani abu wanda wannan abun shi ne ya sanyani murmushi" Aunty ta kai ƙarshen maganar tana dafa kafaɗar Iftihal ɗin da ta zaunrta kusa da ita tana murmushi. "Hakane Aunty amma kuma sai in ke ganin kamar koma menene a bayan karatuna yake domin ilimi shi ne ginshiƙin rayuwa kuma shi ne sinadarin zaman duniya har ma da lahirar baki ɗaya domin ba fa boko kaɗai kika hanani zuwa ba har da islamiya, kuma kullum in na tambayeki menene kudurin naki a kaina bakya faɗa min" "Kar ki damu Iftihal ni dai nasan babban abin da ke sanya mutane neɓan ilimi a wannan zamanin shi ne kuɗi! To kuwa indai kuɗi ne tabbas babu makawa har sai kin taka naira da ƙafafunki, kuma batun ilimi gishirin koma menene duk wannan bai taso ba domin a wannna ƙasar tamu masu yanzu idan da za a ce a lissafo wanda suka kammala karatunsu amma basu samu aikin yi ba yo wallahi lissafasu ma kaɗai aiki ne, dan haka ki kwantar da hankalinki kuma indai kudurina ne a kan ki zan faɗa miki nan ba da daɗewa ba domin na hango lokacin na nan tafe ya ma kusa zuwa" "To shikenan Aunty na yarda domin kuwa uwa ba za ta taɓa yin abin da za ta cutar da ƴarta ba" Wani murmushin Auntyn ta sake yi domin Allah kaɗai ya san kudurin da ke ranta, kafin ta ce "Yawwa Iftee na shi sa bani da tamkar ki" "Ni ma haka Aunty shi sa ma kika ga na fi bin umarninki fiye da na Abie na" Wani daɗi ne yasa Auntyn sanya hannu ta rungume Iftihal ɗin suna dariya a tare. Bayan sun ɗan tattauna Aunty ta shiga koyar da Iftihal ɗin tafiya, da kwarkwasa da dai abubuwa duk da Iftihal ɗin bata san manufar hakan ba amma dai tana jin daɗi a ranta ganin mahaifiyarta na koya mata abubuwa da kan ta. _Momma_ Misalin ƙarfe biyar na yammacin ranar laraba, zaune take akan sallayarta tana karatun qurani mai girma tun da ta yi sallar la'asar take karatun, bayan ta gama ta rufe qur'anin tare da ɗaga hannunta sama tana ta addu'a wanda ba a jin me take cewa sai dai hawaye na ta kwaranya daga idanunta har ta kammala ta shafa.Qur'anin ta ɗauka ta mayar dashi ma'ajjinsa sannan ta linke hijabin da sallayar ta ajiyesu, kan gadonta ta koma ta kwanta idanunta a sama har lokacin hawaye na kwaranyowa a idanun nata, ita kaɗai ta san me take ji a zuciyarta game da abin da take tunawa Allah ne kuma kaɗai ya san damuwarta domin duk duniya babu wanda ta taɓa faɗawa damuwarta.Amma dai ta san kullum idan ta tuno shi tana jin damuwa a ranta kuma in ba kuka ta yi ba bata samun sassauci a zuciyarta, idan kuma ta rufe idanunta shi take gani lokacin da ya faɗo daga jikinta, da kuma lokacin da aka gama gyarashi aka miƙo mata shi, Allah sarki idan kuma ta tuna lokacin da aka ce ya mutu aka sanyashi a kwali aka ce gida za a je ayi suturarsa sai ta ji zuciyarta ta yi rauni da yawa.Gashi yau tsawon shekaru goma sha shida kuma bata sake samun wani cikin ba bare ayi zancen sake haihuwa bata sani ba ko za ta haihu a gaba ko kuma shi ne kaɗai rabonta. "Ya Allah kai kaɗai ne ka san damuwata Allah ka kawo min mafita, ya Allah ka bani wani rabon kafin na bar duniya, idan kuma shi kaɗai ne rabona ya Allah ka...kafin ta ƙarasa sai kuka ya ƙwace mata.Haka dai tana nan tana tunani har dai Suhailat mai mata aiki ta faɗa mata cewa Alhaji ya dawo haka ta wanke fuskarta ta gyara fes kamar ma ba ita ke cikin damuwa da yin kuka ba ta shafa powder da lipstick ta fito abinta sai tashin ƙamshi take. Tana zuwa kwa ta ga Abie tsaye yana jiranta dan ko upstairs ɗin ma ya kasa hawa "Welcome back"Ta ce tana sakar masa murmushi tare da ɗaukan jakar office ɗin nasa. "Ni na yi fushi" Ya ce yana juya mata baya. Wani murmushi ne ya suɓuce mata. "Ai wanda ya yi fushi ba shi yake faɗa ba, wanda aka yiwa fushin ne ke fahimtar haka" "Koma dai menene ni bana kulaki" "Ni ce fa" Ta faɗa lokacin da ta zo inda ya juya ɗin.Ƙara juyawa ɗaya side ɗin ya yi.Ita ma komawa ta yi tare da ajiye jakar hannunta ta ce "Ni ko? Afwan" Ta faɗa tana haɗe hannayenta wuri ɗaya alamar roƙo. Da murmushi ya juyo suka fuskanci juna, sannan ya ce "Ba ke ce ba kika ƙyaleni ina ta jiranki, kuma kinsan ba zan iya haurawa sama ba matuƙar dai baki fito ba gashi na gaji ba zan iya zuwa ɓangarenki ba" "To ka yi haƙuri ka ji? Ina can ina ɗan maka kwalliya ne" "To me yasa baki yi min kafin dawo wa ta ba?" "Afwan wani ɗan abu ne ya riƙe ni har na shagala da hakan, amma ai ka san ina ji da kai" "To shikenan na huce, ai ni na ma fi ji da ke" "Godiya nake"Ta ce tare da ɗaukan jakar ya riƙo ƙugunta suka haura sama abinsu suna zantukan soyayya. _JIGAWA STATE_ _GAGARAWA L.G_ Tafe ta ke a gefen titi sai sosa kan ta take tana dariya ita kaɗai, sanye take da kaya wanda suka yi wani datti kan ta babu ɗankwali gashin kan nata mai tsawo da yalwa ya bazo har gadon bayanta, ga ƙura da datti a jikin gashi da suk canja masa kama daga baƙi zuwa wani ja, kyakkyawar mace ce duk da yanayin jikinta ya nuna baya samu kulawa kasancewarta a cikin hali na hauka. Ƙarasowa ta yi wajen wani maina inda mai shayi da kuma mai tsire a gefe da ma masu sayar da abubuwa da dama a wurin, tsayawa ta yi tana bi tana miƙa hannu a bata, da alama abinci take buƙata. "Ke dalla kauce ki ba mutane waje sai kin je kin sakawa mutane wannan dattin jikin naki ko kim saka mana gashi kij kashe mana kasuwa"Cewar mai tsiren cikin zafin rai.Cikin sauri ta matsa dan har tsorata ta yi yadda ya zafice ta, tana tafiya tana waiwayen dan gani take biyota zai yi ya daketa, bata gani ba ta bige wa wata mai siyar da abinci kwanan miya ds yake ta tafi wurin wasu samari ta karɓo kwanukan ta da kuɗin, daga can ta hango mahaukaciyar ta mata ɓarin jar miya ai kuwa da cikin sauri ta taho tana zuwa ta sanya hannu ta damƙo gashin mahaukaciyar ta juyo da ita suka fuskanci juna da yake ita ko da ta ɓarar da miyar ma bata kawo aka ta yi wani abu ba da yake a halin rashin hankali. "Wane ɗan iskan ya ce ki ɓarar min da miya?" Cikin tsoro mahaukaciyar ke kallonta tana tattakurewa, ai kuwa mai abincin nan ta ɗaga hannu ta ɗauketa da wani mari, cikin gigicewa ta dafe kuncinta tare da ƙoƙarin ƙwace kan ta daga gashinta da ta riƙe mata da hannu ɗayan, nan dai mutane suka taru wasu na bata haƙuri wasu na cewa bata kyauta ba tunda bata da hankali daƙer dai matar nan ta ƙyale mahaukaciyar bayan wani mutum ya biyata kuɗin miyar, sannan ya siyawa mahaukaciyar abinci a wurin wata aka zuba mata a leda dan sun ce ba za su bata a kwano ba. Karɓar abincin ta yi ta juya cikin sauri dan dama yunwa take ji tun jiya rabonta da abinci, ƙarƙashin wata bishiya ta koma can nesa da mutane ta zauna ta bule abincin nan taliya da miya ce amma ba ruwanta da cakuɗawa haka ta shiga ci babu ƙaƙƙautawa wani sa'in ta ɗakko wurin miya wani lokacin kuma ta ɗakko inda babu miya, sai da ta cinye tas sannan ta kwanta a ƙasan wurin a take bacci ya ɗauketa. Mmn afrah😍🥰😘 ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️ 💕ALAƘAR YARINTA💞 ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️ NA MAMAN AFRAH FIRST CLASS WRITER'S ASSO... PAGE 1️⃣9️⃣&2️⃣0️⃣ _Jigawa state Dutse gadawur_ Gidan Alhaji Sagiru sarkin yaƙin Dutse, Alhaji sagiru ne zaune a bakin gado ya yi tagumi fa duka hannayensa, da alama dai ya yi nisa a cikin tunani sai dai shi kansa bai san takamaimai tunanin me yake ba.Kullum ya kan tsinci kansa a irin wannan halin idan har ya keɓance kansa daga mutane yana ji ya rasa sukuni yana jin damuwa da tunani sun addabi zuciya da ƙwaƙwalwarsa, amma kash sai dai baya taɓa tantance tunanin me yake, sai dai ya gaji ya haƙura da tunanin da ke addabarsa wani sa'ilin ma har sai ya zubar da ruwan hawaye sannan yake samun sauƙi a ransa. Hajiya Suwaida ce tafe cikin wani tsadadden lashi da aka mata ɗinkin buba sai zuba ƙamshi take yi abinta, upstairs ta haura domin dubo mai gidan nata saboda ta ga shiru bai sakko ba.A hankali ta tura ƙofar ɗakin da ta san za ta sameshi, ta maida ƙofar ta rufe amma har ta ƙaraso cikin ɗakin da alama ma bai san ta shigo ba, inda yake kallo ta kalla sai ta ga idanunsa na kan wani ƙaton hotonsa da ke manne jikin bango, hoton an ɗaukesa ne a ranar da aka naɗashi sarkin yaƙin garin Dutse yanzu kusan shekaru ashirin kenan.Sanye yake da kufta da aka yiwa aikin irin na sarauta sai alkyabba da da aka ɗora akan kayan yana riƙe da sanda irin ta sarauta, ya kafe hoton da ido ga kuma idanun nasa sun masa jajawur.Yatsina fuska ta yi tare da taɓe baki, dan ta san zancen gizo baya wuce na ƙoƙi shi kullum yana tunani kuma in ka tambayeshi sai yace shi kansa bai san danuwarsa ba hasalima sai yace bai san me yake tunawa ba ita har gajiya take da tambayarsa. Bakin gadon ta ƙarasa ta zauna, a kusa dashi amma har lokacin bai san tana wurin ba, hannu ta sanya ta dafa kafaɗarsa, shiru bao san tana yi ba har sai da ta ɗan jijjiga kafaɗar tasa sannan ya juyo a ɗan firgice. "Hajiya" Ya kirata da ɗan ruɗewa a muryarsa saboda ya ɗan razana da ta taɓashi sanadin nisan da ya yi a cikin tunani. "Na'am Alhajina, tunanin nan ne da har yanzu kake yi haba sarkin yaƙi mai takobin zinare kaifin takobinka zai sa kowa ya watse" Ta ce tana wani murmushi a fili a ranta kuma tana ayyana cewa ƙaryarka dubu ka tuno abin da kake son tunowa wannan ɓoyayyen sirri ya rufu har gaba da abada babu mai tunowa bare har ya fallasa. Murmushi ne ya kuɓuce masa na kirarin da ta masa, duk da bai wani dawo daidai ba daga halin da ya shiga ba, dan har wani sarawa ya ji kansa na masa sannan yace "Wallahi Hajiya ni kaina inason na daina tunanin nan amma bansan lokacin da yake zuwa min ba saidai in tsinci kainana ciki dumu-dumu"Ya faɗa yana dafe goshinsanda hannu. "Ka yi haƙuri za ka daina ai da kaɗan-kaɗan zai barka tunda yanzu ba kamar da babya ragu" "Ke kike gani ya ragu amma ni nasan bai ragubba saboda kullum sai na yi babu adadi, ni abin da ke damuna bai wuce ba rashin rashin sanin takamai man abin da nake tunawa ba sai dai fa in ƙari tunani amma tunanin nawa baya kaiwa inda nakeso ya kai saidai na gaji na haƙura" Haka kwa za kake gajiya har abada dan babu wani abu da ƙwalƙwalwarka za ta tuna, saidai ka gaji ka haƙura, ta faɗi hakan a ranta a fili kuma sai ta ce "Allah sarki Alhajina nima bana jin daɗin halin da kake kasancewa wallaho saidai dan ba yadda zan yi ne, amma ka yi haƙuri zaka daina watarana" "To Hajiya Suwaida shi sa nake alfahri da kasancewarki mata ta" "Ni ma ina alfahri da kasancewarka miji a gareni" A haka ta lallaɓashi ya shiga wanka ya shirya suka sakko ƙasan tare, lokacin ma'aikatan gidan na ta hidima kowa ya kama aikinsa. Alhaji sagiru ɗan asalin garin Dutse ne, kuma ɗa ne ga mai martaba sarkin Dutse, shi kaɗai iyayensa suka haifa sai ƙanwarsa da aka haifa a ranar ta mutu, yana da matar aure Hajiya Suwaida ita ma ƴar cikin garin Dutse ce sai dai Allah bai basu haihuwa ba. Gidan Alhaji Sunusi Hajiya Sakina ce zaune a falonta ta sanya kayan marmari a gaba sai tuffa a hannunta wanda ko gutsira bata yi ba, ta yi nisa cikin tunani sai tv da ke ta faman aiki.Hawaye ne ke kwaranya a idanunta amma saboda nisan da ta yi a tunanin ko share hawayen bata yi . Hafeez ne ya shigo cikin falon sanye yake da t.shirt da wandon jeans baƙi sai ƙamshi yake abinsa.Da sallama ya shigo falon mahaifiyar tasa, amma kuma sai jikinsa ya yi sanyi ganin halin da ya tsinci mahaifiyar tasa a ciki, cikin sanyin jiki ya ƙaraso cikin falon har ya zo gabanta ya durƙusa amma bata ma san da zuwansa wurin ba.Da ido ya bi plate ɗin kayan marmarin da ke ajiye wanda tun lokacin da zai fita daga falon ya hangi Na'ima mai aikinsu ta fito daga kicin da ta yayyanka mata za ta kawo mata amma abin mamakin gashi har ya je ya yi wanka ya shirya duk ɓata lokacin da ya yi amma har yanzu babu wani abu da ta ci daga cikin kayan marmarin sai tunani da ta tsunduma, a ciki shi yasa kwata-kwata ba ya so ta kaɗaice ita kaɗai saboda yawan tunanin nan gudun kar ma ya yuwa lafiyarta illa.Wata ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya sanya hannu ya ɗan taɓa ta tare da cewa "Ammi!" Jin taɓa ta da aka yi da kuma sunanta da aka ambata shi ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta kai ziyara. Dubanta ta kai ga Hafeez ɗin, sai kuma ta yi saurin kawar da kan ta gefe jin lemar hawayen da ke kan kumatun ta, da sauri ta ajiye tuffar a kan plate ɗin sai kuma ta sanya hannayen nata ta goge hawayen tare da ɗan jan hanci kaɗan sannan ta ƙaƙalo murmushi tare da cewa "Hafeez wai kana nufin har ka yi wankan ka shirya, ko dai jiƙa-jiƙa ka yi baka fita ba shi yasa ka yi saurin fitowa" Ta ce cikin zolaya dan kar ya mata zancen halin da ya tsince ta a ciki, saboda ko da zai tafi wankan sai da ya sha lallaɓata akan dan Allah kar ta yi wannan tunanin, har da kunna mata tashar arewa 24 suna shirin mata a yau dan su ɗauke mata kewa amma shi ne ya dawo ya same ta dumu-dumu tana aikin nata da ta saba wato tunani. " Haba Ammi yanzu duk maganar da muka yi a gefe kika ajiyeta, kinsan ko kaɗan bana son ganinki cikin damuwa, domin damuwa tana sanya ciwo, shi yasa in dai ba makaranta zan je ba ko wani uzuri mai muhimmanci ba na son na yi nesa da ke dan kar ki ke yawan tunanin nan"Hafeez ya ce lokacin da yake zaunawa daga tsugunnon da ya yi. "Hafeez kenan sau nawa kake so na faɗa maka cewa nima ba a son raina nake tunanin nan ba, kuma ma bana sanin lokacin da nake yin tunanin sai dai na tsinci kaina a ciki, dan Allah kake min uzuri mana wannan tunanin ya zame min jiki koma in ce ya zame mini abokin rayuwa!" Cewar Ammi tana sanya hannu ta share ƙwallar da ta kwaranyo mata yanzu. "Ki yi haƙuri Ammi, nasan da haka tun da abin nan ba ke kaɗai ke yi ba nima ina yi haka Abba ma sai dai naki ne ya fi yin tsauri, Allah ne kaɗai ya san dalilin wannan yawan tunaninnda yake nema ya zame mana kamar gado kuma abin al'ajabin ma babu wanda cikin mu zai ce ga wani abu da yake tunawa a lokacin da yake tunanin, sai dai idan wani tunain ne da ban za ka yi kuma ka tuna abin da kake son tunawa har ma ka yanke hukunci ko sharar idan akan hakan ka yi tunanin..Amma shi wannan dogon tunanin fa da ya zama kamar ibada sji baka taɓa gane inda ka dosa bare ka san inda ka je sai dai ka gama bulayinka, ya tafi ya barka da damuwa a ranka.Tunani ne da ya sha ban -ban da wanda kowane tunanin da mutum zai gane irinsa sai dai mu cigaba da addu'a akan Allah kawo mana mafita" "Amin ya rabbi" Ammi ta ce tana bin ɗan nata da kallon so da ƙauna tabbas kowacce uwa idan ta samu ɗa mai biyayya irin Hafeez to tabbas ta yi dace. Ganin kallon da take masa ya sakar mata murmushi tare da miƴa hannu ya ɗakko tuffa ɗin da ta ajiye ya miƙa mata, karɓa ta yi cikin jin daɗi itama tana sakin murmushin ta kai bakinta ta gutsura, haka suka cigaba da hirarsu har aka kira sallar magriba, sannan Hafeez ɗin ya tafi masallaci itama ta shiga domin yin alwala ta gabatar da sallar tana so ta damawa Abban Hafeez kunun gyaɗar da ya ce ta dama masa zai sha idan ya dawo domin ya je gidan abokinsa kuma ta san a gida zai ci abincin dare domin baya iya cin abinci a ko'ina sai a gidansa. Maman Afrah🥰😍😘 ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️ 💕ALAƘAR YARINTA💞 ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️ NA MMN AFRAH FIRST CLASS WRITER'S ASSO... PAGE 2️⃣&1️⃣2️⃣2️⃣ _Ridallah_ Tun komawarsu garin Gumel rayuwarsu ta sauya, Mama Rahma kamar yadda Ridallah take kiranta, ita ta sanar wa shugaban Boarding pri & Junior scul da take aikin abinci, akan ya mata alfarma za ta kawo wacce za ta maye gurbinta, cikin ikon Allah kuea sai ya ce dama akwai wacce ta rasu ba' a maye gurbinta ba dan haka ta bashi lokaci zai yi ƙoƙari ya bada sunan Baba Habiba idan Allah ya sa tana da rabo ta za ta samu haka suka masa godiya da ƙoƙarin da ya musu suka dawo gida cikin farinciki. Bayan mako biyu kwa aka nemi Baba Habiba akan ta fara zuwa wurin aikin, duk da wasu masu aikin acan makarantar suke kwana amma Mama Rahma da yake tana da kula da aikinta tana zuwa akan lokaci ga kuma cika ƙa'idoji hakan yasa idan ta gama aikinta take tafiya gida ta kwana.Ita ma Baba Habiba ta nemi wannan alfarma kima da darajarsu da shugaban makarantar ke gani ya basu dama suke zuwa suna tafiya tun da a cikin gari suke, wannan ya sa su ma suka bada himma da kuma ganin basu yi duk wani abu da zai ruguje duk wata yarda da kuma dama da aka basu ba. Kullum idan su Baba Habiba suna kicin suna aiki sai Ridallah ta samu wuri ta zauna ta rinƙa kallon ɗalibai idan suna tafiya ajijuwa, gwanin sha'awa kowa sanye da uniform da socks da sandal sai abin ya rinƙa birgeta tana jin inama ita ce, dan tana da son karatu amma gashi sun baro garinsu, hakan ya sa Ya Hizbunta ya faɗo mata yadda suke tafiya makaranta ya kama hannunta ya yi ta siya mata duk abin da take so.Amma yanzu gashi wasu sun shiga tsakaninsu da shi, sun sanya sun baro garinsu sun dawo wani garin da bata ma jin daɗin garin saboda babu Ya Hizbu a cikin garin. "Kasan me Ya Hizbu?" "A'a sai kin faɗa " "Inaso in yi karatu mai zurfi idan na gama in samu aiki" "Allah sarki Ridallah, insha Allahu sai kin yi karatu har ya isheki, ni nan zan tsaya tsayin daka har sai kin cimma burinki, sannan in Allah ya yarda za ki samu aiki" "Nagode Yaya na" Ta ce tana murmushi, shi ma murmushin ya mata. Maganar da suka yi ana gobe za su baro Hadejia ta faɗo mata, hawaye ne suka zubo mata ta sanya hannu ta share tana jin kewar Ya Hizbunta har cikin ranta, ashe burinta ba zai cika ba. "Ridallah! Baba Habiba ta kirata da ta fito domin shanya gawayi.Da sauri ta ɗago kan nata ta kalki mahaifiyarta ta da ke kallonta cike da mamaki, duk da dama tun da suka dawo Gumel tana kamata tana kuka idan ta tambayeta sai ta ce Ya Hizbu ta tuno.To itama Babar tana mata uzuri tun da ta san irin shaƙuwar da suka yi, yo kuma abu ne mai wahala ace ta yakice tunaninsa lokaci guda duk da ta san dai ba lallai ne ta manta da shi ba har abada amma dai ta san mawuyaci ne ace sun ƙara haɗuwa ma, sai dai bata taɓa ganin tana yin kuka a wajen da jama'a ke kai kawo ba, ko a gidan takan kamata ne a ɗaki ta ɓoye kan ta tana kuka. Ajiye ƙaramin buhun hannunta ta yi wanda ra zubo gawayin a ciki, ta ƙarasa wurin da Ridallah ke zaune ta zauna akan dakalin ita ma, hannun Ridallah ɗin ta kama da hannayenta biyu ta ce "Haba Ridallah, har sai yaushe ne zaki daina yin wannan kukan kina zubar da hawayenki? Bayan kinsan cewa Hizbullah mun baro shi a Haɗejia sannan bai san ma inda muka taho ba, bare ya biyoki amma sai ki zauna ki yi ta zubar da hawaye, abun har ya kai kina kuka a inda mutane suke ficewa kuma za su iya ganinki? Dan Allah ki sanyawa ranki haƙuri da dangana duk da nasan da wuya hakan amma daurewa za ki yi ko nima na daina tunanin halin da kike ciki idan da rabon ganawa wata rana sai ki ga kun gana ke da shi" Baba Habiba ta kai ƙarshen maganar cikin sanyin murya tana kallon Ridallah da hawayen suka cigaba da sirarowa daga idanunta. "Hakane Baba, amma ni yanzu ba wannan ya sanya ni kuka ba" "Menene?" "Kawai saboda na ga... "Baba Habiba waye ya taɓa ƴar lelen naki na ga kina ta faman lallashi?" Maganar principal ɗin makarantar ta katse Ridallah daga abin da take so ta faɗa. "Wallahi shugaba ka ganni da ita nima ban kai ga jin wanda ya taɓo ta ba"Baba ta ce cikin jin nauyin shugaban makarantar saboda mutum ne shi mai kirki da girmama mutane. Wurin ya ƙaraso yana murmushi tare da cewa "Ƴar lelan Baba wa ya taɓa ki?" Shiru ta yi tana wasa da yatsun hannunta. "Ba magana ake miki ba?" Baba Habiba ta faɗa tana kallonta. "Dama fa..."Sai kuma ta yi shiru. "Dama me?" Ya ce cikin lallashi. "Dama da na ga uara suna tafiya aji shi ne ni ma na ji inason karatu" Ta kai ƙarshen maganar tana goge hawayen idanunta. "Kai! Allah sarki Ridallah dama akan karatu ne kika shiga damuwa, ni ma da na yi tunanin cewa Babar taki a sanyaki a makarantar nan maimakon kike zaune, to kuma sai nake tunanin ko bata da ra'ayi, amma yanzu tun da har kina so babu abin fa zai hanaki shiga aji in har ta amince" Ya ce yana goya hannayensa a bayansa. "Na amince shugaba, ai ni dama daga ni har ita ba mu da burin da ya wuce haka, saboda Ridallah yarinya ce mai matuƙar son karatu, gata da hazaƙa tun da take ko ta biyu bata taɓa ɗauka ba a makaranta kullum ita ce ke ɗauka na farko a ajin su" "Allah sarki! To insha Allah za a sanyata a J.s 1 ɗin idan an mata interview mun gani, Allah jiƙan mahaifin nata" Principal ɗin ya ce yana mai jin tausayinsu, dan Rahma ce masa ta yi mijinta ne ya rasu ƴan asalin Malam madori ne sanadin mutuwar tasa ce suka dawo Gumel ɗin da zama dan Baba ta hana ace daga Haɗejia suka taho dan bata so kowa ya san daga inda suke saboda wani dalili nata daban wanda ita ce kaɗai ta san hakan. "To mun gode ƙwarai Allah sa ka fi haka, Allah ɗauka ka, ka ya albarkaci zuri'a" Baba ta faɗa cikin farinciki. "Amin ya Allah nagode ni ma da addu'a, kuma babu komai ai yiwa kai ne, ni zan mata komai kama daga litattafai da komai da komai" "Nagode Baba shugaba Allah saka maka da alkairi, ya sanyaka a aljanna" Ridallah da ta tsugunna har ƙasa ta haɗe hannayenta a wuri ɗaya ta ce cikin murna da farinciki. "Ba komai ƴa ta taso mu je" Ya ce yana kama hannunta suka tafi can office ɗinsa. Baba Habiba kwa tsabar farinciki ma ta rasa bakin magana, haka ta tsaya tana kallonsu har suka ɓacewa ganinta sannan ta ɗauki buhunta ta kama hanyar kicin. Dan so take ta je ta baiwa Rahma labarin wannan abin arziƙi da aka musu. Sosai Mama Rahma ta ji daɗi da wannan albishir Principal ɗin office ɗinsa ya wuce da ita ya yi mata register da komai da komai, sannan ya ɗakko mata uniform set biyu daga cikin uniforms ɗin da gobnati take bayarwa a rabawa ɗalibai.Ridallah sosai daɗi take ji a ranta baki yaƙi rufuwa sai kallon uniform ɗin take yi tana murmushi sai faman godiya take yiwa shugaba shi kwa sai cewa yake ta daina godiya, wani Malami ya kirawo yasa ya mata interview sosai suka yi mamaki daga Malamin har principal ɗin saboda yadda take bada amsoshi a nutse ko gaga ba ta yi sun gamsu da amsoshinta sosai dan haka principal ɗin ya ce ta je ta sanya kayan makarantar ta dawo, haka ta je ɗakin su Baba da ke can inda ɗakunan ma'aikatan kicin yake, duk da su, su Babar basa kwana a makarantar amma dai akwai ɗakin da suke hutawa, haka ta je ta sanya kayan tana ta murna ta linke wanda ta cire ɗin ta nufi kicin ɗin. Da murna ta je ta rungume Baba ita ma Babar rungumeta ta yi cike da farinciki dan ji take kamar yau take sallah tana son farincikin Ridallah haka kuma ta tsani baƙinciki ko ɓacin ranta.Kowa a wurin sai dariya yake musu ganin suna murna gwanin sha'awa.Haka ta ce musu ta tafi aji, office ɗin shugaban ta je ya kalleta yana murmushi ya ce "Ridallah an zama ƴan makarantar kwana" Cike da kunya ta sanya hannu ta rufe fuskarta tana murmushi dan duk daɗi ya cikata ta ƙosa ta ganta zaune cikin aji tana ɗaukan darasi. "To ga wannan" Ya ce yana miƙo mata wata jaka mai ɗauke da dukkan littattafan da ake amfani da su a ajin da za ta je sai biruka guda biyu da mathset da komai da za ta buƙata har test buke duk a ciki. Idanu ta ɗan zaro dan ita tsabar ruɗewa da kuma murna ta ma manta da wasu abu littattafai. "Gaskia shugaba ko dai ni za a baiwa nima in shiga ajin"Malamin nan ya ce cikin zolaya yana murmushi. "Nawa ne waɗannan" Ta ce tana miƙa hannu cike da ladabi ta karɓa, tare da buɗawa ta leƙa ganin abin da ke ciki sai farincikinta ya ƙaru akan wanda take ciki da. "Allah saka maka da alkairi, ya faranta maka kamar yadda ka faranta mini" Ta ce tana kallon Principal ɗin cike da girmamawa. "Amin ya rabbi, shugaba da da Malamin suka hala baki wajen faɗa. "Mu je na raka ki ajin " Malamin ya ce yana yin gaba ta juya ta bi bayansa. "Allah bada sa'a" Ta tsinkayo muryar Principal ɗin lokacin da ta kai bakin ƙofar fita. "Amin" Ta ce tana sanya kai ta fita daga cikin office ɗin. Principal ɗin komawa ya yi ya jingina da jikin kujerarsa yana jin wani irin daɗi da nishaɗi a ransa dan a rayuwarsa yana son ya ga ya taimaki mutane, musamman yara, yaran ma marayu yana son sanya farinciki a zuciyar maraya, kasancewarsa maraya ya san zafi da raɗaɗin maraici hakan yasa yake ta ƙoƙari domin ganin ya cire su daga wani ƙunci ko baƙinciki ya sanya su a farinciki. _Hizbullah_ Zaune yake a ɗakinsa yana riƙe da handout yana karatu, sai kofin shayi ɗan ƙarami da ke kan ɗan ƙaramin faranti, jifa-jifa yana ɗauka yana kurɓa ya maya ya ajiye, yana cikin karatun sai ya ji Ridallah ta faɗo ɓasa a rai da sauri ya ajiye handout ɗin kamar wanda aka tsikara ya dafe kansa da hannu biyu saboda jin da ya yi ya sara masa. "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un" Ya ce yana wani runtse idanunsa da ƙarfi jin yadda zuciyarsa ke buga masa da mugun ƙarfi tamkar wacce ke neman agajin gaggawa, kan nasa ya saka ya sanya hannun nasa a ƙirjinsa saitin zuciyarsa ya dafe tabbas Ridallah ita ce bugun zuciyarsa amma yanzu bai ma san inda take ba bare ya san halin da take ciki ba. Da sauri ya miƙe kamar wanda aka tsikara ya nufi inda ya sanya wayarsa caji ya ɗakko ta maimakon ya dawo ya zauna a kan kujerar sai ya tsaya a jikin bango tare da jingina bayansa da bangon, a hanzarce ya shiga contact ya nemo lambar wayar Ummarsa ya shiga buguwa amma har ta tsinke ba'a ɗauka ba, bai yi wata-wata ba ya sake danna wani kiran a karo na biyu burinsa kawai Umma ta ɗauki wayar cikin sa'a kwa sai aka ɗaga wayar. "Assalamu alaikum" Umma ta yi sallama daga can ɓangaren. "Wa alaikumus salam" Ya amsa "Hizbu na kai ne akan layi" "Ni ne Umma, ina yini " "Lafiya ƙalaw, ɗan albarka ya karatu" "Alhamdulillahi! Umma ina lafiya ƙalaw" "Masha Allah, ina Abulkairi" "Yana lafiya" Nan dai suka suka shiga hira ya tambayi Babansa ta ce ya fita, so yake ya tambayeta labarin su Ridallah amma kuma ba ya so ya ji labarin da ya saba ji kullum dan ya san da ace an samu labarinsu to da tun kafin ya kira da sun kira shi aun shaida masa hakan dan ya san sun san halin da yake ciki na buƙatar jin labarin. "Hizbu na baka ji na" Muryar Umma ta katse masa tunani. "Umma ina jinki, dama...dama..." "Dama me? Ka faɗi abin da kake son faɗa mana" "Dama ina so in ce miki ya labarin su Ridallah" Ya ce yana maida kan sa ya jingina a jikin bangon tare da ɗaga kan sa sama ya sauke akan ɗaya daga cikin ƙwan fitilun mai kyau da walwali da aka masa wata walkiya da wani abun walkiya mai ƙyalƙyalin ruwan gwal, tare da sanya haƙori ya danne gefen leɓensa na ƙasa yana jiran jin amsar Ummar. "Haba Hizbu kullum a rinƙa magana ɗaya? Kasan dai da ace an samu labarinsu sai mun fara kiranka mun sanar maka kafin ka kira ka tambaya amma ace kullum sai ka kira ka tambaya wataran ma sai ka kira ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba, ka kwantar da hankalinka ka dage da karatunka insha Allahu Allah zai bayyana su muna nan muna addu'a kai ma ka cigaba da yi" "To Umma nagode sai an jima a gaishe da Baba" Ya faɗi hakan cikin raunin da zuciyarsa ta masa. "To Hizbullah ka gaishe da Abulkairi" Da to kawai ya iya amsa mata ya kashe wayar ya tako yana jan ƙafafunsa dakyar ya ƙaraso ya zube akan kujerar ya saki wayar ta faɗa kan handout ɗin da yake karatu.Idanunsa a rufe yana jin wani ɗaci a cikin zuciyarsa tamkar ya sanya magani paracetamol a ciki haka yake ji, a hankali ya buɗe idanunsa zuwa lokacin sun yi jawur kamar wanda ya kwana yana kuka, cikin sanyin jiki ya tashi ya tafi ya buɗe wardrobe ɗinsa, ya ɗakko wani ɗan ƙaramin kit ya koma ya kwanta akan gadon tare da ɗora kansa bisa filo, ɗan kit ɗin ya buɗe ya saya hannu ya fiddo wata flower da ɗankunne wari ɗaya ya riƙe su akan tafukan hannayen sa tare da zuba musu jajayen idanunsa a hankali maganarta ta shiga dawo masa a ranar da ta bashi waɗannan abubuwan. " Ya Hizbu wannan flower a jikin flower Baba na ciro a ɗakinta, saboda jiya ina ganin film ɗin kwana casa'in sai na ga Yawale da durƙusa ya baiwa Rayya flower, shi ne nima na ciro na kawo maka" Haka ta durƙusa kamar yadda Yawalen ya yi ta baiwa Hizbullah flower, cikin murna ya karɓa sannan ta miƙe suke dariya su duka, tun daga wannan ranar yake ajiye da flower dan wataran ma idan ta shiga gidan su Hizbullah ɗin sai ta ce "Ya Hizbu ina flower da na baka" Har sai ya ɗakko ya nuna mata sai kuma ta ce "Dan Allah ka jaiyeta kar ka jefar" "Babu abin da zai sa na jefar da ita" Ita ce amsar da yake bata. Ɗankunnen ya ɗago da yatsunsa biyu yana kallonsa duk da ɗankunnen ya daɗe amma babu abin da ya yi kasancewar sa azurfa, nan take ya shiga tuno da ranar da ta bashi warin ɗankunnen yana zaune a ɗakinsa yana gyaran littattafan makarantarsa yana sanya su a jaka ta shigo da ɗankunnen a hannunta.A kusa da shi ta zauna ta ce "Ya Hizbu ɗankunne na kawo maka" "Ɗankunne kuma Rida ni da ba mace ba mai zanyi da ɗankunne?" "Dama Baba ce ta siya min sabo ta sanya min saboda ɗayan wannan ya faɗi shi ne na kawo maka, tun da maza ba kwa sanya ɗankunne ba sai ka ajiye ba" Ta faɗa tana nuna masa ɗankunnen da aka siya mata sabo a kunnenta. Jakar ya ajiye a gefe ya miƙo hannunsa ta basa ɗankunnen yana ta murmushi itaɓa tana yi. "Yawwa to godiya nake" Ya faɗa yana buɗe zip ɗin Babbar akwatinsa ya fito da ɗan kit ɗin da ya siya ya sanya flower da ta bashi, ya buɗe ya sanya ɗankunnen a ciki. Bai ankara ba sai jin hawaye ya yi suna gangarowa a kumatunsa, tabbas ya yi kewar Ridallah, kewar da shi kan sa bai san yawa da adadinta ba kewar da ya san babu ranar da zai daina har sai ranar da ya sanya Ridallah a idanunsa.Juyawa ya yi, ya koma ribda ciki ya shiga yin kukan yana jin zafi da raɗaɗin rashinta na ratsa dukkan sassa da gaɓoɓin jikinsa, tabbas shaƙuwa wata aba ce mai wuyar fita daga rai, shaƙuwa tana yin zama a cikin zukata tamkar yadda kayana kayan ciki ke zaune cikin jiki, tana haɗuwa a zukata har ta zama abin da bai rabuwa wato hanta da jini. ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️ 💕ALAƘAR YATINTA💞 ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️ NA MMN AFRAH FIRST CLASS WRITER'S ASSO... PAGE2️⃣3️⃣&2️⃣4️⃣ "Wallahi duk abin da kike ganin za ki yi sai dai ki yi, dan tafiya babu fashi dole Iftihal ta je china ta yi karatu tun da na ga abin naki babu hankali a ciki.Kamar ba ke kika haifeta ba ƴar ƙwaya ɗaya amma ace ta tashi babu arabi ba boko sai yawon banza da kike sanyata da bin gidajen ƙwaye" Abie ya kai ƙarshen maganar tare da buga kan kujerar da yake zaune da hannunsa dan ya lura abin na Hajiya Hauwa ba na ƙare bane sai an zage dantse an nuna mata iyakarta. "Dan Allah Alhaji ka yi haƙuri kar ka kai min ƴata karatu ƙasar waje, na yarda zan barta take zuwa makarantar anan amma ya za a yi ace kamar Iftihal har nawa ma take da za ace an fitar da ita karatu har wata ƙasa" "Da can baki san da karatun nata ba kika ƙi kullum muna magana ɗaya amma kin ƙi ji yanzu ban da shegen yawo da yarinyar ke fita ba tare da sani na ba, ni ma yanzu ban yarda da ke ba akan zaki barta ta yi karatu kuma da kike maganar nawa take zan aikata ƙasar waje karatu ai na faɗa miki gidan abokina Alhaji Sani Habu da yake zaune acan zan kaita acan za ta yi karatun ta dan haka kisa Safiya ta haɗa mata kayanta dan bizarta tana fitowa za ta tafi" "Alhaji ka yi haƙuri a sasanta mana tun da dai yanzu ta amince ka haƙura da kaita chaina"Momma ta faɗi hakan cikin sanyin murya da lallashi. Idon Abie Hajiya Hauwa ta faka ta aikawa da Momma wata uwar harara me nuni da ke kika sani munafuka, sai zare ido take kamar idanunta za su faɗo ƙasa.Ita dai Momma yi ta yi kamar ma ba ta san tana yi ba dan ita tsakaninta da Allah take faɗar abin da ke ranta dan ita ma bata ƙaunar hana Iftihal ɗin zuwa makaranta da take sannan ta tsani yawon da aka buɗewa yarinyar idanu da shi, dan ta san shi Abie bai ma san har samari suke kawo Iftihal ɗin gida a mota ba, abin na damunta amma ba ta so tayi magana ace baƙinciki take saboda ba ita ce ta haifeta ba, dan akwai wata rana da ta fara ganin an sauke Iftihal ɗin a mota wani mutum ne babba da shi, a lokacin Momma ta dawo daga unguwa direba ya kai ta lokacin da hancin motarsu Momma ya danno ƙofar gjdan ita kuma Iftihal ta buɗe ƙofar ta fito suna ɗagawa juna hannu ita da na cikin motar, baki sake Momma ke kallonsu dan kwata-kwata hankalinta bai kwanta ba Iftihal ɗin na ganin su Momma ta yi saurin tura ƙaramar ƙofar get ɗin ta shige cikin gida. Horn direban ya yi aka wangale musu get ɗin suka shiga dan ko da Momma ke tambayar direban ko ya san mai motar cewa ya yi ai yanzu motoci ne kala-kala ke kawo Iftihal ɗin gida su ajiyeta a bakin get. Dan haka tana tana fita daga motar hankali tashe ta yi part ɗin Hajiya Hauwa dan ta yi alƙawari ko me Hajiyar za ta ce mata sai ta faɗa mata abin da idanunta ya gani dan ta sani dan ta san idan ta sanar mata ko nan gaba ta fita ko a girin Allah ko da wani abu ya faru duk da ba a fatan hakan.Tana kaiwa dai -dai ƙofar da zata sada ta da falon Hajiya Hauwa sai jin wata magana ya dakatar da ita daga shiga ta tsaya tana sauraron maganar hankali tashe. "Yanzu Alhajin da ya dawo da ke gida shi ne ya baki wannan maƙudan kuɗin Iftihal"Cewar Hajiya Hauwa muryarta cikin farinciki. "Wallahi kwa Aunty shi ya bani dan da kuɗin da ya bani bai kai haka ba, aikuwa da muka fito daga Hotel ɗin zai kawo ni gida na marairaice murya kamar yadda kika koya min ina kashe masa ido ai nan da nan ya ƙara buɗe aljihunsa ko irgawa bai yi ba ya zuge jakata ya zuba mini"Iftihal ɗin ta ce tana dariya.Momma bata ankara ba sai jin ƙaran tafawar hannayensu ta yi alamar sun tafa dan jin daɗin halin da suke ciki. Saurin sanya hannu ta yi ta rufe bakinta gudun kar aji ta dan abin da take saurara ya wuce hankali da tunaninta ace ƴarka ta cikinka ka zama sanadiyyar lalacewar rayuwarta sai ka ce a mafarki ko kuma a film, lallai zamanin nan da muke ciki ya ƙazanta ta ce a cikin zuciyarta. "Ai sai kin zama abar kwatance a kaf faɗin Abuja sai an san da zamanki, ke bake ba ma hatta ni sai na yi sunan saboda za mu tara kuɗaɗen da za a yi ta kwatance da mu"Maganar Hajiya Hauwa ta katsewa Hajiya Azima tunani, a hanzarce ta bar ƙofar falon tare da baro part ɗin ma gaba ki ɗaya cikin tashin hankali dakyar take iya ɗaga ƙafafunta saboda sanyi da suka mata tana jin wani ƙunci da tashin hankali na maganganun da kunnuwanta suka jiyo mata. "Hajiya Azima dan Allah kar ki ɓata bakin ki dan na gama yanke hukunci, babu wani abu da zan sauya daga haka" Muryar Abie ta dawo da ita daga tunanin da take. Wani tashin hankali ne ya ziyarci Hajiya Hauwa tana ganin Alhaji Hamza zai datse mata hanyar samun maƙudan kuɗaɗen da take samu wanda shi ba zai taɓa iya bata su ba, dan idan har ya kai Iftihal China to haƙiƙa ya ɗauke mata jarinta dan ita yanzu bata ga wata sana'a ba da ke saurin kawo kuɗaɗe sama da wacce Iftihal ɗin ke musu. "Iftihal ki tabbatar kin haɗa komai da zaki buƙata Safiya kuma ta shirya miki kayanki dan tafiya za ta iya kasancewa ko da wane lokaci"Abie ya ce yana kallon Iftihal da take ta zubar hawaye amma shi ko a jikinsa wai an tsikari kakkausa tun da ta sna wannan shi ne babban gata da zai mata. "To Abie" Shi ne kawai abin da ta iya furtawa dan ta san dai ita a da tana ƙaunar karatu amma yanzu ko sh'awar shiga aji bata yi bare ya yi sha'awar ɗaukan karatu musamman yanzu da idanunta suka buɗe da samun kuɗi ta hanyar sai da mutuncinta da mahaifiyarta ce ummul aba'isin hakan tana ƙaramarta amma ta san bin maza amma ta san ba ta isa ta ja da amaganar Abie ba shi yasa ma ta aminci amma ba wai dan ranta ya so ba. Hajiya Hauwa ce ta tashi buguzun-buguzun ta bar falon tamkar za ta tashi sama, tana fita ita ma Iftihal ɗin ta miƙe cikin sanyin jiki za ta tafi daga ɓangaren Abie. "Kin dai ji abin da na gaya miki, kuma ki sani ko kin shirya ko baki shirya ba biza na fitowa za ki tafi" Maganar Abie ta katse Iftihal da ke bakin ƙofa za ta fita. "Zan yi ƙoƙarin yin hakan kafin lokacin" Tana gama faɗar haka ta sanya kai ta fita. Ran Momma fari tas jin wannan hukunci na Alhaji wai a hakan ma aho Alhajin bai san cewa Iftihal ɗin har maza take bi ba.Nan dai suka cigaba da yin hirar su dan yau Momma ce da girki yau Auntyn ta fita daga kwananta sai Momma ta karɓa, to dama a dinner ne da aka zo aka ci a part ɗin A bie shi ne ya ce idan an kammala yana da magana, shi ne suka tattaru a falon ashe da wannan maganar Abie ke tafe wannan kenan. Iftihal na fita ta koma part ɗin Auntyn ta ɗakinta ta buɗe ta shiga, ta kwanta akan gado ta ɗakko wayoyinta har guda uku kowacce ta doshi 300k ta shiga waya da ƙawayenta na banza da suka haɗu a harkar bariki da kuma samarinta na wofi. Hajiya Hauwa cikin fushi ta koma part ɗin ta, wayarta ta ɗakko cikin ɓacin rai ta zauna a bakin gado ta shiga laluɓo number ƙawarta aminiyarta Hajiya Suwaida, Hajiya Suwaida aminiyarta ce tun ta ƴanmatanci, Hajiya Suwaida ƴar garin Dutse ce da ke Jihar Jigawa sai dai tana zuwa Suleja hutu wurin ƴan uwan mamanta, to acan suka haɗu da Hajiya Hauwa suka ƙulla ƙawance da yake ta su ta zo ɗaya sai ƙawancen na su ya yi armashi har yanzu. Har kiran ya katse ba a ɗauki wayar ba, ƙara kiran ta yi ranta baƙiƙƙirin kamar ta saki kuka ko ta samu sassauci.Wani kiran ta shiga doka mata har sai da ya kusa tsinkewa sannan ta ɗaga cikin murnar ganin aminiyarta ta. "Aminiyata kin fi ta kowa" Cewar Hajiya Suwaida tana neman wuri ta zauna akan kujera dan fitowarta kenan daga bayi ta jiyo ƙaran wayarra ta shi ne ta zo domin kawo wa wayar ɗauki sai kuma ta tarar da kiran ma na aminiyarta ne. "Suwaida dan Allah ki saurara ki jini wannan kiran ba na lafiya bane, akwai gagarumar matsala da ta tunkaro ni" "Ikon Allah ya na ji muryarki haka? Allah sa dai ba sakin ki Alhaji Hamza ya yi ba zai tona mana asiri" "Ba saki na ya yi ba amma abin ba ƙarami bane wallahi ina cikin tashin hankali" "To ki nutsu ki mini bayani ko menene domin mu san yadda za mu yi mu shawo kan matsalar, dan babu wani abu da zai tunkaro mu face mun yi maganinsa" "Wai Alhaji ne zai kai Iftihal karatu ƙasar Chaina, wallahi yana neman ganin bayan samun kuɗina yana kuma ƙoƙarin karya jari na" Wani mugun wuntsilowa Hajiya Suwaida ta yi daga kan kujerar, sai ga ta a ƙasa tsabagen ruɗew da ta yi, dan duk tunaninta matsalar ƙarama ce sai ta ji girman matsalar na neman wuce gona da iri. "Shi Alhaji Hamzan ne ya yanke wannan ɗanyan aikin, saboda shi bai san burinmu akan yarinyar ba" "Wallahi kema dai kya faɗa amma hankalina ya tashi dan kin ga gabaɗaya so yake ya karya ƙudirinmu akan ta" "Lallai kuwa dole a nemi mafita dan babh yadda za a yi mu haƙura da burinmu ya ma za a yi mu da bama ƙaunar yarinyar ta yi karatu shi ne zai wani ce har ƙasar waje zai kai ta ta yi karatu ba ma a Nigeri'a ba" "Wallahi kuwa ni kai na duk ya kulle amma ki samo mana mafita" Shiru Hajiya Suwaida ta yi tana nazari da tunanin yadda za ta samo musu mafita akan haka tun kafin haƙƙar Alhaji ta cimma ruwa. "Yawwa akwai wata ƙawata a ƙasar China, ƴar nan Nigeri'a ce aiki ne ya kai mijinta China ina ganin za mu samu mafita a gunda dan itama shegiyar kan ta ce" "Ta yaya? Kinsan fa shi Alhajin ya ce ba a makaranta za ta zauna ba, bare ki ce za a ruɗeta, ya ce gidan abokinsa zai kai ta" "Mun shiga uku asirinmu zai tonu na samun kuɗi lallai da alama burinmu na zama hamshaƙan mata ba zai ciku ba" "Ni ma shi ne damuwata wallahi da ace makaranta zai kai ta da mun samu mafita amma kuma gida ne zai kai ta" Runtse idanu Hajiya Suwaida ta yi tana ta saƙa da warwara tana son gano mafita, can sai cewa ta yi. "A Nigeri'a a ina abokin nasa yake ɗan wane gari ne?" "Ɗan Kano ne... "Haba dan Allah ya sunansa ina fatan ma ya kasance mijin ƙawar tawa dan ita ma ƴan Kano ne?" "Sunansa Alhaji Sani Habu ana kiransa da... "Ana kiransa da Soja" Hajiya Suwaida ta katse Hajiya Hauwa ta hanyar ƙarasa mata sunansa dan ta fahimci shi ne mijin ƙawarta Wasila da suka yi F.U.D anan Dutse. Wani ihu mai ƙarfi Hajiya Hauwa ta sanya, jin am samo mafita.Ita ma Hajiya Suwaida sai wata dariya take ta mahaukata jin komai ya zo da sauƙi. "Yadda za a yi zan kira ta mu yi magana nasan babu abin da zai gagara, in yaso sai a ɗora neman kuɗin a can Chinan a ɗora daga in da aka tsaya dan ai ko'ina ma akwai kalar mutanen da kake son rayuwa da u wla na banza wala na kirki" Cewad Hajiya Suwaida suna dariya cikin farinciki. Haka suka ƙarƙare maganar su, cikin jin daɗi suka yi sallama akan cewa Hajiya Suwaida za ta kirata Hajiya Hauwa ta sanar da ita duk yadda suka yi da Wasilar haka suka yi sallama. Sosai Hajiya Hauwa ta ji daɗin a ranta ta ajiye wayar tana furtawa a fili cewa "In kasan wata ai baka san wata ba wallahi Alhaji da ni kake zancen mu zuba mu gani" Wayar ta ƙara ɗauka ta kira Iftihal ɗin cikin yan sakanni sai gata ta turo ɗakin ta shigo tana shigowa ta faɗa jikin Auntyn nata tare da sakin wani kuka.Bayanta Hajiyar ya shiga bubbugawa tana lallashinta har sai da ta samu ta yi shiru sannan ta shiga kora mata jawabi kamar haka. "Ki daina kuka Iftihal babu abin da zai faru kuma ma gidan da zai kai ki na san matar gidan kuma ƙawar Hajiya Suwaida aminiyata ce dan haka ba za ki takura ba za ki yi duk abin da ranki ke so, dan kin san su dama maza ba mazauna gida bane bare ya takuraki shi abokin Abien naki.Hajiya Suwaida za ta kirata ta mata jawabi dalla-dalla. Wani daɗi ne ya ziyarci zuciyar Iftihal ɗin ta rungume mahaifiyarta ta cikin farinciki dan dama ita a rayuwarta ta tsani takura bare yanzu da idanunta suka buɗe ba ta jinnza ta ɗauki kulle a gida kamar wata matar aure.Haka dai su ka yi ta tsara yadda komai zan kasance idan Iftihal ɗin ta je Chaina maimakon a gan su suna ɓacin rai sai aka ga saɓanin haka saboda aun riga sun samo mafita basu da matsala. A ɓangaren Hajiya Suwaida ma ta kira Hajiya Wasila ta rattaba mata bayani, aikuwa ta ji daɗi dan dama mijin nata ya faɗa mata cewa abokinsa zai kawo ƴarsa ɗaya tilo gidansa domin ta yi karatu.Jin cewa kuma ƴar gidan aminiyar ƙawarta ce kuma ga ƙudurinsu kuma ita ma fama ƴar harka ce dan haka kwa suka ƙudurta neman kuɗi sai sun ga abin da ya turewa buzu naɗi. Suna gama wayar Hajiya Suwaiba cikin azarɓaɓi ta kira aminiyarta ta labarta mata yadda suka yi, daɗi a wurin Hajiya Hauwa kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha. ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️ 💕ALAƘAR YATINTA💞 ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️ NA MMN AFRAH FIRST CLASS WRITER'S ASSO... PAGE2️⃣5️⃣&2️⃣6️⃣ _Umma Sadiya_ Zaune take akan tabarma bayan magriba, Malam Auwalu ne ya shigo ɗauke da sallama amsa masa ta yi tana masa sannu da zuwa, zaunawa ya yi akan tabarmar ita kuma ta tafi ta kawo masa abincinsa tuwon masara da bushashshiyar kuɓewa.Ruwan da ta ɗakko masa a wata ƴar roba mai faɗi ya wanke hannayensa, miƙa masa ta yi ya yi Bismillah ya fara ci suna ɗan taɓa hora yana ta yabon daɗin da girkin ya yi. "Wallahi lamarin yaron nan yana ɗaure min kai, duk da dai nasan halin da zai tsinci kan sa a ciki sanadin ɓatan su Ridallah amma yadda na ga ya ɗauki abin ya girmama kar abin ya taɓa karatun sa" Ta ƙarasa faɗa tana kallon Malam ɗin da ya dage sai cin abincinsa yake da alama daɗin ya wuce inda ake zato. Sai da ya kai lomar ƙarshe ya ture kwanon da ta zuba masa a ciki gefe sannan ua wanke hannunsa da bakinsa ta miƙa masa ruwan da ta zuba masa a ƙaramin kofi ya karɓa ya sha sannan ya fara bata amsa. "Duk maganganun ki haka suke amma sai dai babu yadda za a yi Hizbullah ya ki maida hankali a karatu sanadin damuwar da yake ciki, ke kan ki kin san halinsa baya wasa da karatu duk da yana da damuwa a ransa amma haka ba zai sanya ya yi watsi da abin da ya kai shi ba" "Hakane Malam amma yadda ya damu ne abin ke tsoratani wallahi kullum fa sai ya kira ya fi a ƙirga yana tambayar an gan su ko an samu labarin su" "Wannan duk ba wata matsala ba ce kuma ke kan ki kinsan irin yadda ya shaƙu da yarinyar a yadda ma ya yi ai ba ƙaramin yaƙi ya yi da zuciyarsa ba kuma kiran da yake yana tambaya kar ki ɗauka wani abu yana yin hakan ne da ya samu sauƙi da salama a cikin zuciyarsa saboda Allah kaɗai ya san yadda yake ji abin da nake so kawai mu ƙara dagewa da addu'a akan Allah ya bayyana su, kuma duk lokacin da ya kira ki rinƙa kwantar masa da hankali" "Wannan haka yake, kuma insha Allah za mu cigaba da addu'a kuma zan cigaba da kwantar masa da hankali dan ya samu nutsuwa ya yi karatun" "Yawwa to Allah mana jagora su kuma Allah bayyana su" "Amin amin" Ta faɗa tana tashi ta shiga kwashe kayan da ya ci abincin. _GAGARAWA L.G_ Tafiya take wasu dandazon yara biye da ita suna tafi suna mata waƙa. "Mahaukaciya ta ɗan Bala,mahaukaciya ta ɗan Bala" Haka suke ta faman faɗa suna tafi suna dariya haɗe da tsalle-tsalle ita dai bata musu komai ba hasalima kamar ba da ita suke ba dan ita dama bata faɗa bare kuma yanzun da take tafiya kamar a gabaice ma take da alama wani abu na damunta, a daidai wata kwana kawai sai gani suka yi ta yanke jiki ta faɗi cikin razana da tsoro yadda suka ga ta yi yasa yaran ja da baya suna cewa. "Ta mutu!!! " Suna ta maimaitawa, a guje duk suka fara watsewa suka barta anan yashe da yake layin babu mutane sosai shi yasa babu wanda ya gan su bare ya san mai ya faru. Malam Idi mai almajirai ne tafe shi da wasu almajirai guda huɗu daga gonarsa suke suka yi aiki shi ne suka taso ganin magriba ta kawo kai, dan dama da yamma ne suka koma gonar saboda daman sun je da safe.Kwanar da suka shawo sai ganin mace suka yi kwance a ƙasa cikin hanzari Malam Idi ya yi kan ta tare da almajiran nasa, haka yasa almajiran suka kamata da yake matasa ne da ɗan girmansu kuma dama a layin gidan nasa yake.Haka yasa suka kai ta har cikin gida yasa matarsa Malama Zainab ta shimfiɗa tabarma da yake ita ma mace ce mai kirki ko yadda jikin mahaukaciyar yake bata ƙyamata ba bare ta ce ba za a ɗora mata ita ba akan tabarma. Gabaɗaya Malama Zainab ta ruɗe da ganin mahaukaciyar dan duk tunaninta ma mutuwa ta yi, Malam Idin ne ya shiga kwantar mata da hankali akan ba mutuwa ta yi ba haka aka watsa mata ruwa Malam ɗin ya shiga tofa mata addu'a cikin iko da hikimar ubangiji sai ta kawo hankali.Tun da ta falka take ta bin su da ido, amma bata ce komai su kuma dama sun san mahaukaciya ce dan suna ganinta a layin duk da ba wata hauka tuburan take ba sai dai kana ganinta kasan tana da gushewar hankali. Ganin alamomin yunwa a tattare da ita yasa Malama Zainab zubo mata abinci ta kawo mata, Malam Zainab na ƙoƙarin ajiye mata abincin sai ta sanya hannu ta warci kwanon abincin, cikin sauri ta sanya hannu tana ci hannu baka hannu ƙwarya, Malam sai jijjiga kai yake alamar tausayi Malama Zainab kwa ban da hawaye babu abin da ke zuba daga idanunta saboda tsabar tausayi da kuma ƙara godewa Allah da take da ya iyota cikin masu hankali lallai komai Allah ya baka yana daga cikin baiwar ubangiji. Dan mutane da dama ba sa gane baiwa da ni'imar da Allah ubangiji ya musu ba wani kullum bashi da burin da ya wuce suke kallon wata ɗinbin dukiya da gidaje da tarin motoci da Allah ya baiwa wasu, suna mantawa da hatta lafiya da Allah ya basu babban arziƙi ne.Lafiya idan aka karɓeta daga bawa aka jarabceshi da rashinta, sai ki ga duk tarin dukiyarsa ya ƙarar da ita a neman magani amma lafiyar bata samu ba shi yasa idan Allah ya baka rai da lafiya to ka gode masa duk wani abun duniya samamme ne kuma ƙararre matuƙar kana da rai da lafiya da rufin asirinka ka ɗauke idanunka daga kan abin duniyar mutane Allah kai ma yana sane da kai wani ma abin da zai ci gagararsa yake amma kullum cikin godewa Allah yake Allah sa mu da ce. "A gaskiya Malam sosai wani imani ya ƙara shiga ta ganin halin rashi na hankali da matar nan take ciki, lallai rai da lafiya, hankali ji da kuma gani su kaɗai Allah ya baka to ya baka babban kyauta! Duk da waɗan nan abubuwan da na lissafa abin tambaya ne ga duk wanda aka baiwa su" Ta faɗi hakan ƙwalla na cikowa daga idanunta ganin yadda mahaukaciyar ke cin abincin ko na bakinta bata cinyewa ba take ƙara tura wani. "Wannan haka yake Zainabu amma mutane ba ma la'akari da hakan kuma wasu ba sa amfani da abubuwan wajen gyaran lahirarsu, suna duk abin da suka ga dama da su" "To Allah ya ganar da mu gaskiya, ya bamu ikon amfani da baiwar da ya mana ta hanya mai kyau" "Amin" Cewar Malam yana sauke wata gwauruwar ajiyar zuciya, tare da kallon mahaukaciyar da ta kammala cin abincin ta yi wurgi da kwanon, ta shiga waige-waige da alama ruwa take nema. "Zainabu ki ɗakko mata ruwa " "To Malam" Zainabun ta ce tana tashi ta ɗakko ruwan a wani kofi mai ɗan girma ta miƙa mata madadin ta sha ruwan sai kawai ta karɓa ta ajiye sai kuma ta sanya ƙafa ta ture ruwan ya zube gabaɗaya a ƙasa.Kallan kallo aka shiga yi tsakanin Malam da Malama Zainabu dan ita Malamar har wani tsoro ta ji ya ɗarsu a ranta, ita kuwa mahaukaciyar ko a jikinta ta tashi ta nufi randar da ta ga Malama ta kwalfo mata ruwa har ta buɗe sai kuma ta rufe da ƙarfi har murfin ya yi ƙara da yake wani farantin silba ne ƙarami aka rufe randar dashi. Sai da ta je kan randar ta ƙarshe da yake randunan uku ne ta buɗe ta sanya kofin da aka kai mata ruwan da shi ƙasan sa ma akwai ƙasa haka ta dulmiya ta kwalfo ruwan da ta fito da hannun nata gabaɗaya ya jiƙe dan har hannun ta sanya a randar ta ɗakko ta kafa kai ta sha sai da ya ishe ta, sannan ta dangwarar da kofin a wurin ta juyo ta dawo inda ta tashi ta zauna. Su Malam dai kallonta kawai suke. "Uhmmm Malam tun da ta warware kuma ta ci abinci dama ina ganin yunwa ce ta sanya ta faɗi, ai sai a nuna mata ƙofa ta tafi ko?" Cewar Malama Zainab tana kallon Malam ɗin da ya yi shiru kamar mai wani nazari. Shirun dai ya yi bai bata amsa ba har sai da ta ƙara maimaita masa maganar sannan ya huro da iska daga bakinsa, sai kuma ya ce. "Hakane Zainabu amma ba wai na ƙi ta taki bane sai dai ni ma akwai abin da nake hange wanda nake ganin kamar ke baki hango ba, inaso dan Allah ki bani haɗin kai mu riƙe matar nan a gidan nan" Ya ce yana kallon Malama da ta yi saurin miƙewa tsaye cikin kaɗuwa. "Me kake faɗa haka Malam? Mahaukaciyar kake cewa ta zauna a gidan nan, haka kawai ba sanin halinta ba muka yi yo da Allah na tuba mahaukaci ma ai ba a saka shi a lissafi ba son ta je ta cutar da mu" Malama Zainab ta ce tana kallon inda mahaukaciyar ke zaune tana ta wani kurta layi da yatsanta a ƙasa sai wani maganganu take da baka gane ko fahimtar me ma take cewa. "Haba Zainabu ya kamata ki fara saurarata ki ji manufata kafin ki yanke hukunci, kuma insha Allah za mu ajiyeta ne dan mu taimaka mata mun yi hakan da kyakkyawar niyya da yardar Allah babu abin da za ta mana" "To ina sauraranka Allah kuma ya sa haka"Ta faɗa tana komawa ta zauna. "Amin" Ya ce kafin kuma ya ɗora wata maganar. "Hakiƙa Allah yana baiwa bayinsa baiwa haka kuma yana jarabtarsu ta duk inda ya ga dama, amma cikin iko da hikimar ubangiji na gano wani sirri tattare da matar nan, Allah ya bayyana tare da nuna mini wani ɓoyayyen al'amari a tattare da ita" "Me kake so ka ce ne Malam" Malama ta katse shi. "Inaso in ce miki wannan matar ba wai da haukar nan aka haifeta ba, asalima ba mahaukaciya ba ce daga baya abin nan ya sameta, tabbas akwai wani sihiri a tattare da ita" Malam ya faɗa idanunsa kafe a kan mahaukaciyar da zuwa lokacin kuma kawai ɗaga kai take yi sama tana saukewa ƙasa. Ƙanƙance idanu Malama Zainabu ta yi ta kalli matar tana son gano abin da Malam ɗin y faɗa amma kuma bata ga komai ba dama ta yi zaton hakan dan tasan bata da baiwar da mijin mata yake da shi"Yanzu Malam kana nufin ka ce min matar nan da asali ba mahaukaciya ba ce, kenan ta taɓa zama da hankalinta?" "Tabbas haka nake nufi, kuma na ƙudurci taimaka mata insha Allahu za a dace za ta dawo ras kamar bata taɓa yin haukar ba" "Amin ya Allah, kai duniyar nan abin tsoro ce wallahi wannan wane irin rashin tsoron Allah ne da kuma son duniya za a mayar da mutum mahaukaci kawai yake yawo a gari kai Allah ka karemu sharrin mutum da aljan"Malama Zainabu ta ce tana jijjiga kai. "Amin, ke dai bari rayuwar yanzu sai a hankali" "To Allah tayamu riƙo ya bata lfy" "Amin, yanzu abin da nake so da ke wancan ɗakin da ake sanya kayayyaki, za a kirawo almajirai guda biyu ko uku su kwashe su haɗa a ɗaya ɗakin, sai a gyara mata ta zauna a ciki" "To Malam, amma wani hanzari ba gudu ba kan ganin za ta yadda ta shiga ɗakin kwa?" "Eh za ta shiga yanzu kafin su gama gyarawa akwai wani magani da zan yayyafa mata a jikinta zai taimaka wajen shigarta ɗakin" Da "to" Malama ta amsa masa. Kafin meye wannan almajiran Malam sun shiga gyara ɗakin, ita kwa mahaukaciyar tana nan kwance a inda take da Malam ya watsa mata maganin anan ta ɓingire tana bacci, har sai da ɗaki ya zama tsaf sannan aka shimfiɗa tabarma da ƙaramar katifa, tana falkawa Malama Zainab ta nuna mata ɗakin cikin ikon Allah kwa babu abin da ta yi kawai shiga ɗakin ta yi ta zauna tare da miƙe ƙafa duk da baccin dama ba wani isarta ba ya yi da alama, ɗakin kawai take bi da kallo. _Bayan sati biyu_ Jiki ya yi kyau sosai dan har sai da Malam ya mata addu'a ya kafeta a cikin gidan dan gudun fita saboda tana ta yunƙurin a barta ta fita, yanzu ma duk haukar ta yi sauƙi sai dai ta zauna ta yi shiru, ko aiki Malams Zainab take a tsakar gida sai ta fito ta zauna a ƙofar ɗaki take ta bin Malamar da ido duk inda ta yi. Yanzu jikinta ma fes yake saboda hatta kan ta sai da Malama Zainab ta wanke mata shi ta gyara mata ta tufke mata, saboda ta fahimci bat son kitso da an kama kan sai ta rinƙa jijjiga kai alamar bata so.Kayan Malamar ne yanzu ma a jikinta dan har wanka take mata sosai sauƙi ke samuwa shi kwa Malam kullum ciki haɗa rubutu da maganin ita ce gashi yana jin daɗin yadda Zainabun ke yiwa matar ba kyara ba tsangwama. ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️ 💕ALAƘAR YATINTA💞 ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️ NA MMN AFRAH FIRST CLASS WRITER'S ASSO... PAGE2️⃣7️⃣&2️⃣8️⃣ _Ridallah_ Karatu ya kankama sosai ta maida hankali a karatun ta dan yanzu duk class ɗin nasu babu wacce ta fita ƙoƙari Malamai har mamakin irin ƙoƙarinta suke saboda iliminta har nema yake ya zarce ajin da take.Ko yaushe cikin nazari da duba litattafai take babu ruwanta da shirme ko biya ƙawaye ƙawarta gida ɗaya Anisa Bello ƴar garin Dutse ce ita ma yarinya ce mai ƙoƙari da hazaƙa shi yasa ma tasu ta zo ɗaya da Ridallah. Shugaban makarantar shi ne ya mata siyayyar madara cornflakes da makamantan su, tabbas Principal ya yi musu alkairi da ba za su taɓa mantawa ba saidai Allah ya biyashi. Baba da inna Rahma suka mata sauran siyayyar kayan yaji da mai da sauran abubuwan buƙata yanzu ta zama ƴar makaranta, hankalinta kwance dan kullum sai ta ga su Baba hakan ke sa ta ji kamar ma ba boarding school take ba. Da yammaci ne garin ya yi luf kamar akwai haddiri saboda lillimi da ake yi, zaune suke a ƙarƙashin wata bishiyar maina suna kan sallayar da suka shimfiɗa ga litattafan da suka ɗakko nan domin yin karatu, saidai Ridallah ta buɗe nata littafin a zahiri idan ka ganta zaka ɗauka karatun take amma a baɗini ba wai karatun take ba kawai dai tana kallon littafin ne amma ko rubutun bata iya karantawa sai hoton Ya Hizbullah kawai take gani yana mata murmushi hakan yasa idanunta suka ciko da ƙwalla saboda kwana biyun nan sosai tunaninsa ke addabarta tana ta ƙoƙari ta yakice tunaninsa da son ganinsa daga zuciyarta amma hakan baya samuwa.Anisa da ta ga wani wuri bata fahimta ba a cikin littafinta tana so Ridallah ta mata bayani ta ɗago tana mata magana tare da nuna mata rubutun. Amma duk maganar da take mata bata ko da kalli inda take ba bare kuma ta san ran za ta bata amsa. Sororo ta tsaya tana kallonta ganin hawaye na ɗiga a kan littafin da ke hannunta, hannu ta sanya ta taɓota, figigit ta yi tana kallon Anisa tare da sanya hannu ta goge hawayenta. "Haba ƙawata mai yake damunki ne haka har da kuka, ko Babanki kika tuno da ya rasu?" "Allah sarki! Addu'ar da nake yiwa Babana ba ta bari na masa kuka, sai dai kawai idan na tuna da Yaya na ina jin a jikina yana can cikin damuwa kamar yadda nake jin damuwar rashin sa" "Dama kina da Yaya amma baki taɓa bani labarinsa ba? To yana ina?" "Ya Hizbullah ba iyayen mu ɗaya ba, maƙotanmu ne sai dai na shaƙu da shi yadda bakya zato" "Allah sarki ! Amma wata rana zai zo ki daina damuwa ki maida hankali muke karatun mu" "To shikenan nagode" Ridallah ta ce tana goge hawayen nata, ta nunawa Anisa inda bata gane ba suka cigaba da yin karatunsu abin sha'awa dan basu da wata damuwa kuma ma da yake su ƴan J.s 1 ne babu mai takura musu komai ma musu ake barw da aka san Ridallah akwai mahaifiyarta a makarantar ba a takura mata ga kuma an ga Malamai da Shugaban makarantar suna ji da ita saboda ƙwazo da kuma girmama mutane. _Aunty_ Gobe ne jirgin su Iftihal zai ɗaga zuwa ƙasar Chaina ita da Abie za su je idan ya kaita akwai wani abu da zai gabatar sai ya dawo.Dan haka sai shirye-shirye ake tsakanin uwa da ƴa, saboda tsabar dabbanci irin na Auntyn har kayan mata ta haɗawa Iftihal ɗin domin ta gyara kan ta na kasa gane Aunty wace irin uwa ce da ta zama mabuɗin lalacewar ƴarta da hannunta saboda aon abin duniya. Ita kuma Iftihal saboda Auntyn na nuna mata wannan ita ce hanya mai ɓullewa hakan yasa take ganin kamar daidai ne ga kuma uwa uba yarinta da ke damunta ga rashin ilimi hakan yasa ta kasa gane gaskiya kamar yadda mahaifiyarta ta kasa ganewa. Dama tun anan tana bata kayan mata tasha domin Alhazan da ke nemanta su ke bata kuɗaɗe marar misali su kuwa da yake ƴan akuyoyi ne haka suke more yarintarta da kuma kayan matan da ke ƙara musu armashin wajen yin saɓon Allah, Allah ka tsaremu ka tsare mana zuri'a baki ɗaya amin.Komai ta sanya mata a jakarta sannan ta ƙara koya mata abubuwan da za take ɗauke hankulan maza dan haka sai da ta shirya komai sannan kuma sun yi magana da Hajiya Suwaida akan Hajiya Wasila za ta ɗora daga inda aka tsaya. Washe gari haka su Aunty suka raka su Airport basu dawo ba har sai da suka ga tashin su, sosai Aunty ke cike da farinciki dan tana ganin wannan wani cigaba ne da ya shigo rayuwarsu tabbas tana ganin nasara yanzu a duk abubuwan da ta sanya a gaba bata ganin duhu saidai haske!. Sun sauka a Chaina lafiya, a inda Alhaji Sani da da Hajiya Wasila suka je taryensu Airport ɗin, sun yi murnar ganinsu saboda sun ga yarinya kyakkyawa duk da ita Hajiya Wasila haihuwarta biyu amma sun rasu sai ƴar mijinta da take a hannunta ita ma kuma ba wai tana mata riƙo bane na tsakani da Allah, ita ma ta maida yarinyar jarinta ba tare da sanin uban ba.Sun ƙaraso gidan a inda aka nunawaSun ɗakkosu sosai Amal ke murna ganin ta samu ƙawa sai janta take da hira da yake motoci biyu suka je da su ɗaya mai gidan ne a baya direba yana jan sa, sai Abie ya shiga baya, ɗayar motar kuma Amal ce a gaba sai Hajiya Wasila a baya ita da Iftihal ta kwantar da Iftihal ɗin a gefen kafaɗarta murna fal ran Hajiya Wasila da ta ga Iftihal ɗin ganin tsantsar kyau kamar ita ta yi kan ta ko ina a cike hakan yasa take hango ɗinbin nasara a tafiyar tasu dan ta lura tabbas yarinyar za ta kawo haske sosai sama da hasken da ta samu a tafiyarta da Amal tun da tana ga manyan mutane sun fi son ƙananun yara a Barker bariki hakan ya kan sanya su fitar da kuɗaɗe dan biyan buƙatarsu. Iftihal sai ƙarewa ko ina kallo take tana mamakin yadda kowa yake sabgar gabansa ba tare da ya damu da kowa baDuk da cewa ba wannan ne karonta na farko ba zuwa China amma lokacin da ta taɓa zuwa tana ƙatama sosai suka zo, shi yasa bata iya tuno komai game da ƙasar dan ko umra ma da suka taɓa zuwa yanzu ba z a ta ce ga yadda saudiyya take ba shi yasa yanzun ma take ganinta a China kamar a cikin mafarki.Ta shagaltu da ganin garin sosai har dai suka ƙaraso gidan Alhaji Sani Habu ƙayataccen gida ne dan haka irin tsarin ginin ya burgeta, tun tsayuwar motocin mai gadin yana buɗe get ɗin ta shiga ƙarewa gidan kallo dan lokacin da ta taɓa zuwa China a Hotel suka sauka kuma ko ma a nan gidan suka sauka to babu abin da za ta iya tunawa duk da yanzun ma ba wani girma gareta na azo a gani ba amma dai tana jin kan ta kamar yadda kowacce mace ke jin kan ta. Part ɗin da aka sauki Abie da ban ita kuma Amal ta kai ta wani ɗakin da ke ɗauke da komai na buƙata, bayan ta ɗana watsa ruwa ta shirya Amal da ke zaune kan gado tana ta danna waya ta kalleta ta ce "Masha Allah rigar nan da kika sanya ta matuƙar miki kyau kamar dama dan ke aka ƙerata" Tsayawa Iftihal ɗin ta yi, tana bin Amal da kallo kafin daga bisani ta ɗan yatsina fuska cikin halin ko in kula ta ce "Thanks" Murmushi Amal ta yi dan ita har ran ta take jin ƙaunar Iftihal dan haka bata ga laifinta ba. "Ya gajiyarki" "Bani da gajiya" "Haka ake so" Wayar Amal ce ta ahiga ruri tana dubawa ta ga Mummy, ɗauka ta yi. "Ku fito aci abinci" Ta tsinkayi muryar Hajiya Wasila. "To Mummy gamu nan fitowa" Tana gama faɗin hakan Mummyn ta katse wayar kallonta ta maida kan Iftihal da ke gyara ribbon ɗin kan ta ta ce "Mummy ta ce mu je mu ci abinci" "Okay" Ta ce tare da miƙewa tsaye tana ɗaura ɗankwalin doguwar rigar a kan ta, ta kama hanyar ƙofa Amal ta bi bayanta suka fito. A dinnig area suka samu gabaɗaya mutanen gidan har da Abie kowacce kujera ta ja ta zauna kowa ya zuba abin da yake so Mummyn kuma ta zubawa su Abie itama ta zuba nata aka shiga cin abincin, bayan sun kammala Abie da Daddy Alhaji Sani suka fita domin su ɗan zagaya gari sai murna suke domin sun ɗan kwana biyu basu haɗu ba.Suna fita Mummy ta kira su Iftihal ɗin falonta ta shiga kora musu bayani kamar haka. "Amal ga ƙawa nan kuma ƴar uwa inaso ku zama tamkar abu ɗaya, bana so wani abi marar daɗi ya shiga tsakaninku dan sai kun haɗe kan ku sannan komai zai tafi kamar yadda nakeso na tsara" Cewar Mummy tana bin dukkanninsu da kallo. "To Mummy insha Allah babu wata matsala da za a samu dan ni tun da na ganta na ji ta shiga raina sosai" Amal ta ce tana murmushi. "Yawwa Amal haka nake son ji"Mummy ta ce tana maida hankalinta kan Iftihal da babu alamun za ta ce wani abu ta lura yarinyar ƴar rainin wayo ce kuma da ganin idonta ta wanke a bariki dan kar take kallon mutane. "Babu abin da zai haɗamu"Iftihal ta ce tana maida hankalinta kan wayarta.Shiru ne ya ɗan biyo baya Mummy kuwa a ranta tana cewa "Yarinya za ki shigo hannu ne, dole na moreki tun da a hannu na za ki zauna dole na samu kuɗaɗe ta dalilinki. "Mummy ina son na ɗan huta" Amal ta ce cikin girmamawa, dan dama Amal yarinya ce mai biyayya duk da yanzu Mummy ta yi nasara wajen kassara mata rayuwa ba tare da sanin mahaifinta ba amma dai ha yanzu tana girmama na gaba da ita. "To Amal ku je maza ku huta "Mummy ta ce tana murmushin yaƙe, haka suka tashi suka juya suka bar falon Mummy na bin su da ido tana girgiza kai tare da yin ƙwafa. Sati guda Abie ya yi ya dawo Nigeri'a dan sai da aka gamawa Iftihal komai da komai na makaranta sannan ya taho dan har lesson teacher aka ɗaukar mata dan yake koya mata karatu a gida saboda duk babu abin da ta iya saboda rashin halartar makaranta da ba ta yi. A makarantar da aka sanyata ma ta su Amal da ƙer suka yarda suka sanyata a J.s 1 shima dan su Abie sun ɗan musu magiya akan za su ɗaukar mata da wanda zai ke koya mata a gida dan da suka mata interview duk ba ta ci ba, gashi kuma duk ta fi ƴan sauran ajijiwan bayan girma da yake tana da girman jiki doke dai haka aka sanyata a J.s 1 ɗin. Tun da Abie ya tafi shi kuma Daddyn Amal ya koma wurin aiki dan dama shi baya dawo wa daga office sai magrib in ya fita tun safe, hakan ne ke baiwa Mummy damar cin karenta babu babbaka.Dan haka yanzu ma ta cigaba da nuna musu hanya marar ɓullewa sai yaran suka ɗora daga inda suka tsaya dan dama kowaccen su ta tsufa a harka yaran ƙanana da su amma an ɓata musu rayuwa, sosai suke samo kuɗaɗe wanda Mummy ke haɗasu da manyan mutane suke sheƙe ayarsu, idan suka basu kuɗi sai ta ɗauki kasonta ta basu nasu sauran kuma ta aikowa Aunty su raba da ita da ƙawarta Hajiya Suwaida sosai Auntyn ke siyan kadarori da kuɗaɗen tana jin daɗin irin yadda harkar ke tafiya dan koyaushe idan suka yi waya da Iftihal sai tana jaddada mata akan ta maida hankali wajen janye ra'ayoyin abokan tarayyarta dan dama batun karatu ma ba ta shi suke ba duniya ce kawai a gaban su.Shi kwa Daddy bai san wainar da suke toyawa ba bare kuma Abie da ke can hankalinsa kwance yana ganin ƴarsa tana can tana karatu da yace ko hutu aka yi ba za ta zo ba sai dai su je su gan ta dan baya so ta zo Aunty ta tsiro da wani abun da ban. Mummy hatta mai lesson ɗin da aka ɗaukarwa Iftihal ta ja masa kunne akan kar ya kuskura ya faɗawa Daddy cewar ba a karatun sai take bashi kuɗi ta toshe bakin, dan Aunty ta ce ko mai koya musu karatun addini ma da ake koyawa a maƙota Daddy yace suna zuwa dan kamar islamiya ce wata mata take koya musu karatu amma haka suka hana yaran zuwa, ni kwa na ce Allah wadaran naka ya lalace. ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️ 💕ALAƘAR YARINTA💞 ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️ NA MMN AFRAH FIRST CLASS WRITER'S ASSO... *Alhamdulillah godiya da yabo sun tabbata ga Allah maɗaukakin sarki da ya bani ikon sake zuwa da wani sabon littafina mai suna ALAƘAR YARINTA yadda na fara lafiya Allah sa na gama lafiya, Allah bani ikon rubuta abin da mutane za su amfana da shi amin* . Wannan littafi daga farkonsa har ƙarshensa sadaukarwa ne ga aminiyar ƙwarai Meenatu mmn muhibba Boy & sadiq , alkairin Allah ya kai muku a duk inda kuke Allah ya bar ƙauna tsakaninmu❤️ Page 29-30 Haka rayuwar Iftihal da Amal ta cigaba da kasancewa cikin ƙazantacciyar rayuwa kullum idanunsu na buɗewa ashe mai makarantar da aka sanya Iftihal ɗin ma inda acan aka sanya Amal ita ma dai da ba zuwa take ba ba a ce makarantar su ba shi ma ɗan hannu ne dan haka suna lasa masa zuma a baki hakan yasa ya rufi bakinsa bai taɓa sanar da Daddy cewa basa zuwa makaranta ba sai dai akwai ranar tonon asiri. *Bayan shekaru uku.* Iftihal girma ya ƙaru kai ya ƙara fashewa idanu sun ƙara buɗewa, ta ƙara zama babbar yarinya kuɗi ya zauna, dan yanzu hatta motar da suke yawo a ciki wacce Daddy ya siya musu sun canja ta, amma Daddy kamar ma bai sani ba dan yanzu da Mummy ta sanar da Aunty yana neman ya harbo jirginsu sai suka sanya aka rufe masa baki ruf daga shi har Abie ɗin dan haka ynzu babu wani ɓoye-ɓoye dan babu wani abu da ya isa ya yi, iya shekarun nan da ta yi Abie bai ƙara ziyartar ta ba sai dai Aunty ta zo ita ma dan ta kawo musu kayan mata na gyara dan hatta zuwan ma Abie riƙe masa ƙafa aka yi.Momma ce dai ke ta addu'a domin tana lura da komai da yake faruwa sai dai bata tantance me ke faruwa a Chainan ba, amma dai rashin gaskiya ya bayyana a tare da Aunty da kuma irin maƙudan kuɗaɗen da take fantamawa da su, har mota gareta amma gamin Abie ma bai kawo komai ita ma ta ja nata bakin ta yi shiru dan akwai lokacin da ta ce za ta bi Auntyn China domin su gano Iftihal ɗin amma Auntyn ta mata gori akan cewa ba ƴarta ba ce ta bari idan ta haifi ɗiyarta ta je amma ba Iftihal ba hakan yasa Momma ba ta ƙara cewa za ta bita su kai wa Iftihal ɗin ziyara ba. Sanye take da wasu fararen kaya riga da wando wandon ya matuƙar kama mata jiki, sai dogon takalmi mai tsini, babu ɗankwali a kan ta sai dai gashin nata ya sha gyara sai sheƙi yake jelar gashin na reto a gadon bayanta.Idan ka kalleta ba zaka taɓa zaton ta haɗa iri da Hausawa ba bare kuma ka yi tunanin tana ɗaya daga cikin musulmai.A dai dai ƙofar da za ta shigar da ita ƙayataccen Restuarant ɗin ta samu wajen da aka tanada dan yin parking ɗin motoci ta faka motarta kiɗa sai tashi yake tamkar dai motar za ta taka rawa saboda yadda ƙaran bugun kiɗan ke ɗawainiya da motar. A hankali ta buɗe ƙofar motar cikin yanga da aji tana wani yatsina fuska, bayan ta sanya glases ɗinta ta kashe motar ta ɗakko ƙaramar jakarta, ƙafafunta ta sanyo su ƙasa ta fito tana ɗan bin wajen da kallo kafin ta maida ƙofar ta sanya makulli ta kulle motar.Jakarta ta rataya kafin ta fara takun ta cikin izza da jan hankali, taku ɗaya biyu ta yi wayarta ta shiga ruri tana neman agaji har kiran ya katse bata ma fito da wayar daga jakar ba, sai a karo na biyu da kiran ya sake shigowa ta fiddo wayar sunan Alhajin da Autynta ta turo mata no sa ta gani, daga Nigeri'a yake ya zo ganin likita China shi ne suka yi magana da Autynta akan zai je wurin Iftihal ɗin su haɗu, sunan Restuarant ɗin ya tura mata tare da mata kwatance ashe ma ta san wurin shi ne za su haɗu a nan kafin su gama daidaitawa su wuce Hotel. Bayan ta ɗaga ya faɗa mata ɓangaren da za ta sameshi, wayar kawai ta kashe ba tare da ta bashi amsa ba, ta nufi ƙofar domin shiga wurin domin ba ƙaramin wuri bane. " Akwai ƙofa daga damanki ki shigo zaki hangoni zaune wurin bishiya"Ta tsinkayi muryar Alhajin da ya ƙara kiranta waya.Wani haushi da takaici ne ya kama ta wato ma ba cin abincin zai yi ba yana can ciki da yake wurin daga can ciki sai aka ware wurin hutawa haka dai da ƴan shuke-shuke a wurin, wato ma ya ɗauketa wata bagidajiya irin bata san wurin ba har wani kwatance yake mata, ƙwafa kawai ta yi a ranta ta kashe wayar ba tare da ta bashi amsa ba, kai tsaye ta turo ƙofar gilashin ta shiga wurin mutane ne gasu nan birjik suna cin abincin wasu kuma yanzu ake kawo musu abincin kowa dai yana sabgar gabansa. Cikin takunta ta shigo wurin direct wurin wani farar fata ta nufa ta miƙa masa kuɗi ya ɗauki wata takarda ya yi signing a jiki ya miƙa mata tana karɓa ta juya ta buɗe ƙofar nan ta shige. Zaune suke akan kukeru a can ƙasan wata bishiya hira suke taɓawa jefi-jefi dan kwata-kwata Hizbullah ba ya son yawan magana, Abulkairi ne ke masa hiran shi kuma iyakarsa "Eh, a'a, hakane" "Wai Hizbullah kai wane irin mutum ne dan Allah, ya kamata kake sakewa da ni ko da ba za kake sakewa da wani ba, saboda ni abokin ka ne amma kullum da ka saurareni mu yi magana ka gwammace ka rinƙa tunani?" "Ba haka bane, dama can ni ban fiye son yin magana sai in dai da Ridallah ne, ya kamata ace ka fahimci bani da yawan magana a iya zaman da mu ka yi na shekaru" "Hakane ni ma na fahimci hakan amma dai a ƙalla kake magana akan shiru dan shiru na haifar da illah ga lafiyar ɗan adam" "To zan ƙoƙarta in ke yin hakan amma abin da ya ƙara sanyani na ƙara zama shiru-shiru tin hutun da na je gida na ƙara tabbatar da cewa Ridallah ta ɓata babu labarinsu tun daga nan na ƙara jin bana jin daɗin komai wallahi" "Maganarka hakane ka ga ko lokacin da ka je Kano ka kai min ziyara lokacin da mu ka je hutun na ga ka rame akan zuwanmu, kuma ni ma da na je Haɗejia na kai maka ziyarar na ji Umma na cewa nake maka faɗa ka canja hali daha shiru-shirun nan kake sakewa a jama'a" "Ai ita Umma ko yaushe laifina take gani, tana tunanin kamar da gangan nake sanya kaina a damuwa bata san ba abin daga zuciyata ya... Shirun da Abulkairi ya ji yasa ya ɗago kai yana kallon Hizbullah domin ya ga abin da ya katse masa maganar ya kasa ƙarasawa, ai kuwa yana ɗagowa ya yi tozali da Hizbullah ya miƙe tsaye daga zaunen da yake ya maida hankali ga kallon wani waje bakinsa a buɗe.Hizbullah kwa hangota da ya yi shi ne abin da ya dakatar da shi daga maganar da yake ya miƙe tsaye yana hangota tana nufowa inda suke, fosta ya yi dan hatta numfashinsa ji ya yi yana barazanar barin gangar jikinsa saboda ɗimaucewa da kuma wani mugun bugawa da zuciyarsa ke yi da ƙarfi kamar ya yi tseran gudu na kilo miter masu yawa.Idanunsa kwa ko ƙiftasu ba ya yi har ruwa taruwa ya yi a cikinsu dan ba ya so ya ƙiftasu ya nemeta ya rasa duk da yana ganin kamar a mafarki yake ganinta. Abulkairi dai ya tsaya shi ma cikin mamakin abokin nasa sai ya kalli Hizbullah sai ya juya ya kalli wacce ya ga Hizbullah ɗin na kallo cikin tsantsar ruɗewa, abin da ke baiwa Abulkairi mamaki wacce Hizbu ke kallo mace ce kuma Hizbu maza ma bai damu da kallonsu ba bare wasu mata ma da ya tsani zancen mace in ba zancen Ridallah ba ko na Ummarsa ba dan ko Abulkairi na yiwa Hizbu zancen tasa budurwar Bilkisu sai ya ce shi fa ba ya son surutu amma yau shi ne ke kallon mace ba Ridallah ba macen ma wannan mai kama da arnan dan gabaɗaya jikinta babu alamar da za ta nuna akwai muslunci a tare da ita. Tana dab da ƙarasowa saitin inda suke Hizbullah ya dawo daga shork ɗin da ya shiga, cikin zafin nama ya tafi gareta yana zuwa kawai ya sha gabanta cikin wata iriyar murya ya fara magana. "Ridallah dama kina raye? Ya aka yi kika zo ƙasar nan? Yaushe kika yi watsi da tarbiyarki kike irin wannan shigar Ridallah, yanzu ace ko tunani na ma bakya yi kin manta da ni ina nan ina cikin damuwar rashin sanin takamai man inda kike, a raye ko a mace amma kina nan lafiya ƙalaw hankali kwance kin... "Wai ƙwalƙwalwarka ta taɓu ne? Ya daga ganin mace ka zo kana mata wasu surutai cikin gushewar hankali, shin ka manta ba a Nigeri'a kake ba? Ko kuwa wannan ta maka kama da bahaushiya dan Allah ka rufa mana asiri Hizbu" Abulkairi da ya ƙaraso gabansu ya ce yana bin Hizbu da kallon takaici, ita kwa Iftihal da ta langaɓar da kai gefe idanu kanne fuska a yatsine dan ita takaici ne ma ya hanata magana dan tana jin komai su ne ke mata kallon kamar ba bahaushiya ba. "Wai ni kake yiwa eaɗannan maganganun? Shin ka ɗauka bana cikin hayyacina to Ridallah ce wannan kuma ni nasan tana jin hausad shi yasa ka ga ina mata magana, kai... Ƙaran wayar Iftihal ɗin ne ya katse Hizbu daga maganar da yake ƙoƙarin ƙarasawa.Kallonsu ta yi tare da banka musu wata uwar harara kafin ta buɗe baki ta ce "Dallah malamai ku ja jikinku a nan, ko an faɗa muku nan ma Nigeri'a ce inda kuka saba yaudarar ƴanmata to ko a Nigeri'a ai na wice ajinku da gani ma wannan gwabnati ce ta biya muku karatu kuka samu damar ketowa hazo" Ta faɗa tana gyara glases ɗin fuskarta.Baki sake Abulkairi ke kallonta jin hausa a bakinta kamar jakin garinsu Kano dan bai taɓa tunanin ta san inda hausa ma take ba ganin hasken fatarta da kuma yanayin shigarta duk da musulman ma na irin shigarta a nan ɗin ma amma ko hula suna sanyawa su rufe kan su ko ɗankwali amma ita haka gatsal kamar inyamura. "Au bahaushiya ce ke ashe, to koma menene waye ma zai so mace irinki ko a ƙafa aka ɗaura mana ke sai mun kunce, shi ma wannan dan bashi lafiya ne amma mai zai yi da ke ba zia taɓa ƙaunark...Hannu Hizbu yasa ya rufewa Abulkairi baki yana jin kamar ya hau shi da duka. "Wai me yake skaa kake min haka ne ya za a yi macen dana fi ƙauna duk duniya bayan uwata ka ce bana ƙaunar... Hannun da Iftihal ta ɗaga za ta ɗauke Hizbu da mari Abulkairi ya yi saurin damƙe hannun shi ya dakatar da Hizbu daga maganar da yake yi MMN AFRAH Page3️⃣1️⃣&3️⃣2️⃣ "Ridallah ni za ki mara?" Hizbu ya ce cikin mamaki yana ƙanƙance idanu, dan shi ganin abin yake kamar almara, yana gani wai Ridallah ɗinsa ce ke nuna bata san shi ba har tana ɗaga hannu za ta mareshi taɓɗi lallai akwai lauje cikin naɗi kenan dama ba son shi take ba? Kenan dama so ne na yarinta yanzu ta girma idanunta sun buɗe ta manta da shi ta barshi shi yana fama da tunaninta kullum cikin kallon ɗankunne da flower da ta bashi yake ba ya son ko kaɗan ya manta da ita ko da na second ɗaya ne dan yana ganin ya ci amana ya ci amanar ƙaunar da take masa da ma wacce yake mata baki ɗaya. Kallon shi ta yi a raine tare da buga wani uban tsaki, ta fido wayarta da ke ta faman ƙara daga kiran ya katse sai wani ya shigo, tana dubawa ta ga Alhajin nan ranta ya ƙara ɓaci dan tana ganin duk shi ya jaza mata wannan bala'in da sun wucewarsu Hotel da duk haka bata faru ba yanzu gashi nan ya sanya wannan mai kama da mahaukatan yana kiranta da wani suna da bata ma taɓa jin mai irinsa ba. "Ina jinka" Shi ne kawai abin da ta ce. "Ya na jiki shiru ko dama baki taho ba?" Alhajin ya tambayeta daga ɗaya ɓangaren. "Ka taho wajen hanyar fita ina wurin wani ya hanani tafiya" Ta ce dan bayan ta ɗaga wayar ma ta yi ƙoƙarin tafiya amma Hizbu ya janye Abulkairi daga gabansa ya je ya sha gabanta zai cigaba da jefa mata tambayoyi marar kai da ƙafafu.Tana kashe wayar ta kalli Hizbu cikin takaici ta ce "Za ka gane shayi ruwa ne dan sai nasa an kulleka an koya maka karatun da baka da ilimi a kan sa tun da baka da hankali" Ta ce tana ɗauke idanunta daga kallonsa. "Shikenan Rida na ji baki sanni ba kamar yadda kika nuna amma inaso ki faɗa min ina Baba take shin tana raye? a nan ƙasar take ko tana Nigeri'a?" Wani kallon baka da hankali ta masa ta ɗauke kai dai dai nan Alhajin ya ƙaraso dan ta tura masa hotonta yana hangota ya ganeta. Babban mutum ne dan da ganinsa ma ya haifi Iftihal ɗin sanya yake da wandon jeans da riga mai dogon hannu sai wani uban ƙaton tunbinsa tari guda yana reto kana ganinsa kasan kuɗi sun sami wuri sun tare. "Baby Iftee menene hakan me ke faruwaa ne?" Ya jefa mata tambayar idanunsa a kanta dan yana ganinta ya ji wata kasala ta baibayeshi, ganin irin shigar da ta yi mai bayyana surorin jikinta. "Kalli wannan baƙauyen ne yake kirana da wani suna ya kafe dole ya sanni bayan ni ko a mafarki ban taɓa ganin ko da mai kama da shi ba" Ta kai ƙarshen maganar tana wani karkaɗa jiki dan Alhajin ya ji daɗin ɗaukan mataki. Wani haushi da kishi ne suka turnuƙe zuciyar Alhajin lokaci guda ya kalli Hizbu da ya babbake a gaban Iftihal ya ce "Malam halan daga turu ka fito ko? Ka taɓa ganin yadda ake niƙe mutum a maidashi dambun nama? To akan wannan yarinyar zan sanya a dandaƙa ka har sai cikinka ya haɗe da bayanka, dan haka ka fita harkarta ko a mafarki babu kai babu ita" Yana kai ƙarshen maganar yasa hannu ya hankaɗa Hizbu gefe guda sannan ya kama hannun Iftihal suka juya suka fara tafiya dan maimakon su shiga ciki hanyar fita suka nufa, ya maida hankalinsa kwacakwam kan ta ita kwa sai wani rausaya jiki take dan ƙara ɗauke masa hankali dan tana so ta samu kuɗaɗe masu yawa daga wurinsa dan Auntynta ta faɗa mata cewa ta tabbatar ta yi iya yinta dan ta wanki gara. Hizbullah ganin Alhajin nan ya ƙara saka masa damuwa kenan Ridallah ta ma wuce inda yake tunanin wato shigar jikinta kaɗai da kuma yadda Alhajin nan ya kamata ya tabbatar da ta sanya kan ta a wata rayuwa dan da gani ba mijinta bane dn da mijinta ne da yace masa mai ya haɗashi da matar aure? Yana hango sun shige ƙofar ta rufo cikin hanzari ya fara taku zai bi bayansu dan yau sainya ga abin da ya turewa buzu naɗi ba zai taɓa barin Ridallah ba, taku ɗaya biyu Abulkairi ya yi ya damƙi rigarsa dan shi abin na Hizbullah ya fara bashi tsoro dan ya tabbata dai Ridallah ta fara masa gizo.Duk da dai bai taɓa ganin yarinyar ba ko a hoto bare ya ce ita ce ko ba ita ba ce dan Hizbullah memorinsa mai ɗauke da hotunansu ya faɗi a ranar da zai baro Nigeri'a dan haka yanzu ko hotonta bashi da shi, amma abin da ke baiwa Abulkairi mamaki me yasa bata taɓa masa gizo akan duk mutane ba sai akan wannan lallai akwai ayar tambaya tun da dai yarinyar bahaushiya ce alamu sun nuna ƴar Nigeri'a duk da a yadda Hizbu ke bashi labari ba ya jin yarinyar za ta yiwa Hizbu haka amma kaidin mata yawa gareshi kuma rayuwa da burika suna canja mutum. "Ka saka ni kar su ɓace min"Hizbu ya ce cikin ɓacin rai. "Haba abokina ka dawo hayyacinka mana me yasa kake hakane, shin ƙauna da tunanin Ridallah har zuciyarka ta fara ɗakko fuskarta tana ɗorawa a gangan jikin wata kana yiwa wata kallon Rifallah?" Abulkairi ya faɗa yana kama duka hannayen Hizbu da ƙarfi ya riƙe dan ya ga sai fisga yake yana so ya ƙwace ya bi bayansu. "Abulkairi ka sake ni na ce idan suka ɓace min sai ka gwammace baka sanni ba"Hizbu ya ce yana zazzare idanu dan ya kasa ƙwace riƙon da abokin nasa ya masa saboda rauni da damuwar da ya tsinci kan sa a ciki sai ya ji gabaɗaya ƙarfinsa ma ya bar gangan jikinsa *Gumel* Ridallah har an shiga Senior secondry scul yanzu haja tana S.S 1 sun yi hutun first term dan haja yanzu tana gida hutu ake yi.Sanye taje da doguwar rigar jar atamfa an mata manyan fulawoyi baƙaƙe da la'asar sakaliya ne, share tsakar gidan take cikin nutsuwa.Sai da ta gama sharewa tas ta kwashe sannan ta wanke ƙafafunta da hannunta sai kuma ta je ta iza wutar da take dafa miya dan har ta gama tuwo, da ta gama wanke -wanke sai ta kwashe tuwon shi ne ta yi shara. Ɗakinsu ta nufa inda Baba Habiba take dan Mama Rahma ba ta nan ta fita unguwa gidan barkar haihuwa, zaune ta samu Babarta ta ta yi shiru shigowar Ridallah ya katse mata shiru da take yi. "Wai Baba ko zafi bakya ji kin zauna a ɗaki ga tabarma can na shinfiɗa miki a inuwa ki fita kisha iska amma kin zauna a ɗaki kamar boka" Cewar Ridallah tana murmushi ta samu wuri ta zauna a kan katifar da ke lailaye da shinfiɗar wankekken zanin gado dan Ridallah ba dai tsafta ba komai nata tsaf gwanin sha'awa. "Kawai dai na fi son zaman ɗakin ne"Baba ta faɗa cikin sanyin murya. Ɗago kai Ridallah ta yi tana kallon mahaifiyarta ta dan kwata-kwata amsar ba ta gamsheta ba dan ba haka Babar ta saba mata magana ba musamman ma ta kan mata barkwanci su rinƙa dariya abinsu. "Baba wai ko bakya jin daɗi ne yau tun safe nake ganinki cikin damuwa?" Ridallah ta ce tana matsowa kusa da Baba ta ɗora hannunta a kan cinyar Baba, hannu Babar ta sanya ta riƙo hannun Ridallah ta ce "Ridallah babu abin da yake damuna, kawai dai wani lokacin na kan tsinci kai na a cikin damuwa idan na tuno da mahaifinki" Ta faɗa tana sanya hannu ta goge ƙwallar idanunta.Ita ma Ridallah ƙwallar ce ta ciko mata idanu jin maganar ta Baba ta sosa mata inda yake mata ƙaiƙayi dan duk lokacin da aka yi zancen mahaifi sai ta tuna nata bare kuma aka yi magana a kan mahaifinta ta kan tsinci zuciyarta cikin rauni hakan yana tuna mata cewa ita marainiya ce ba ta mahaifi a raye dan ita ko a hoto ba ta taɓa ganin mahaifinta ba kawai dai ta san Baba ta ce mata kamarsu ɗaya da mahaifin nata babu abin da ta bari na mahaifinta to idan ta kalli kan ta a madubi ta hakan take ganin fuskar mahaifinta a jikin fuskarta. "Ki yi haƙari Baba kawai mu cigaba da masa addu'a Allah lulluɓesa da rahamarsa" "Amin Ridallah" Baba ta ce tana rungumo Ridallah jikinta cikin tausayinta dan ita ba wannan tunanin mutuwar bane kaɗai damuwarta akwai wata damuwar da ita kaɗai ta san da ita ko Ridallah ba ta san da hakan ba. Haka dai Ridallah ta cigaba da lallashin mahaifiyarta a haka har Iya Rahma ta dawo lokacin dab da magriba ne ta kaɗa miyar sannan ta shinfiɗa musu sallayoyi akan tabarma ta ajiye musu carbinsu aka sannan ta wuce ta yi alwala.Bayan sun gabatar da sallah suka ɗore hirarsu har sai da aka yi sallar isha'i suka yi sannan Ridallah ta zubo musu tuwon su ka ci. Haka suka yi hirarsu har wajen ƙarfe goma ganin an kawo wuta sai Ridallah ta sanya musu gidan sauro a ɗaki da yake ita Iya Rahma a nata ɗakin take kwana su kuma a ɗaki ɗaya, hakan ya sa ta shiga ɗakinta su ma suka mata sallama suka shiga nasu ɗakin.Bayan sun yi addu'a suka kwanta suna ƴar hirarsu har bacci ya yi awon gaba da su. Cikin dare wasu samari guda uku suka diro daga saman katanga, sun tsaya suna ƙarewa gidan kallo. "Baaba ka san fa ba mu san ɗakin da yarinyar take ba kar fa mu je ka hakewa tsohuwa" Ɗaya daga cikinsu ya faɗa yana kallon wanda ya kira da suna Baaba. "Kai fa gara ne wa ya ce maka a duhu za a aiwatar dole ai a haska fitila kuma ko ma ba a haska fitila ba ai babu yadda za a yi na kasa banbance tsohuwa da yarinya sai ka ce wani kai" Baaban ya bashi amsa. "Mu shiga nan ɗakin ka ga takalmi biyu da alama wannan ƙaramin na yarinyar ne ka ganshi na soso mai ɗan tudu" Ɗaya ma ya faɗa yana washe baki, gabaɗayan su suka bushe da dariya dan da alama ma ƴan shaye-shaye ne dan daga maganarsu ma ana iya fahimtar su waye su. "Fito da bindigar nan" Ɗaya ya faɗa cikin raɗa-raɗa "An gama Oga" Ya faɗa yana ɗaga rigarsa ya fito da bindiga daga inda ya soketa a ƙugunsa. Karɓar ya yi ya jujjuyata a hannunsa yana dariya, su ma dariyar suka yi kafin suka ɗunguma suka shiga ɗakin da su Baba Habiba suke dan ƙofar buɗe take hatta da labulen a ɗage yake saboda zafi sai ƙaran fanka da ke ta aikinta suka sai baccinsu suke hankali kwance. Da fitilar wayarsu suka yi amfani suka gano makunnar ƙwan ɗakin suna kunnawa kwa haske ya gauraye ɗakin, hango su Ridallah suka yi cikin net suna ta bacci Ridallah sanye da rigar bacci mai ƙaramin hannu. ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️ 💕ALAƘAR YARINTA💞 ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️ NA MMN AFRAH FIRST CLASS WRITER'S ASSO... *Alhamdulillah godiya da yabo sun tabbata ga Allah maɗaukakin sarki da ya bani ikon sake zuwa da wani sabon littafina mai suna ALAƘAR YARINTA yadda na fara lafiya Allah sa na gama lafiya, Allah bani ikon rubuta abin da mutane za su amfana da shi amin* . Wannan littafi daga farkonsa har ƙarshensa sadaukarwa ne ga aminiyar ƙwarai Meenatu mmn muhibba Boy & sadiq , alkairin Allah ya kai muku a duk inda kuke Allah ya bar ƙauna tsakaninmu❤️ Page3️⃣2️⃣&3️⃣3️⃣ Hannu ɗaya daga cikinsu ya sanya ya ɗauki ruwa a wani jug ya zuba a hannunsa ya watsawa su Baba Habiba da ke bacci, gabaɗaya suka tashi suna dube-duba Ridallah tana murtsuke idanu, a tare suka sauke idanunsu akan ƙartan mazan da ke tsaye suna rarraba jajayen idanunsu sai wani wari ke tashi a jikinsu. "Baby ya kike kallonmu a tsorace wurinki fa muka zo" Ogan nasu da ke riƙe da bindiga ya faɗa yana washe baki. "Subhanallahi! Dan Allah ku yi haƙuri ku rufa mana asiri" Baba ta faɗa tana ƙoƙarin gyara ɗaurin zaninta dan har sun fito daga cikin net ɗin nasu. "Tsohuwa idan ba so kike a haɗa da ke ba ya kamata ki yiwa bakinki mukulli ki fito ki jira oga a waje ya kammala aikinsa" "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un! Dan Allah ku taimaka min"Ridallah ta ce a kiɗime tana ɗora hannu aka, dan lokacin ta fahimci abin da suke nufi dan har Ogan nasu ya cirw belt ɗinsa. "Dan Allah ku yi hakuri ko me kukeso na baku zan baku amma kar ku keta haddin marainiyar Allah" Baba ta faɗa tana durƙusawa a gabansu hawaye na zuba a idanunta. "Ko ki fita ko mu fitar da ke da ƙarfin tsiya, in kuma kina son gani akan idanunki a karɓi amarcin kyakkyawar ɗiyarki to zaki iya neman wuri ki zauna dan muma fita za mu yi"Ɗayan ya faɗa yana karɓar bindigar hannun Ogan nasu ya nuna Baba da ita, dan Ogan nasu ya raja'a da son ɓalle maɓallin jikin wandonsa dan so yake su yi su gama dan gudun kar a samu matsala. Cikin tsananin tsoro Ridallah ta kai kallonta kan bindigar da aka saita Baba Habiba da ita, wani abu ne ya ɗarsu a ran ta lokacin da ta kafe bindigar da ido, dan dama da ganin samarin nan ta san da wuya su mallaki bindiga dan kawai kana ganinsu kasan kawai ƴan iskan unguwa ne irin masu dira gidajen mutane su saci waya da sauransu ba wasu riƙaƙƙun ɓarayi bane.Fakar idon su ta yi dama a tsugunne take ta kai hannu ta janyo ledar yajin daddawa da suka ci tuwo cikin hikima ta ware ledar da hannu ɗaya ba tare da kowa ya kura da abin da take yi ba tana gama warewa ta shammacesu ta miƙe tsaye ta watsawa Ogan nasu a ido, wani ƙara ya saki kafin ka ce me ta ƙara watsawa ɗayan ma, shi ma ihu ya saki mai mugun ƙara, a take ɗayan da ke riƙe da bindigar ya saki bindigar ya fita a guje yana cewa sai kun taho Oga, da gudu ya bi hanyar ƙofar gida ya buɗe ƙofar a cikawa rigarsa iska ya barsu suna dawur wurin neman hanya sai miƙa hannu suke kamar makafi. Ƙaran nan ne ya tashi Rahma da ke ɗakinta, a tsorace ta ƙudundune a bargonta gabanta na faɗuwa dan ta tabbatar ƙaran a cikin gidan ne kuma muryar ƙartin maza lalai yau ɓarayi sun ziyarci gidan.Ridallah kwa wata sanda ta ɗakko a bayan ƙofa ta shiga dukansu da ita suna ta ihu ga yajin ba kaɗan bane ya shiga idanunsu haka suka shiga kuka suna bata haƙuri cikin halin ko in kula ta fara magana. "Ku kama hanya ku fitar mana a gida, kuma daga yau idan kuka sake zuwa sai na muku wanda ya fi wannan dan da aljannu na zan haɗa ku su kai min ku birnin sin" "Wallahi ba za mu sake zuwa ba, ko wani gidan mun daina shiga da sunan sata ko fyaɗe daga yau ɗin nan" "Ku yi yamma kuke tafiya zan ke faɗa muku inda za ku bi" Haka suka rinƙa tafiya suna lalume tana faɗa musu inda za su yi, idan kwana za su yi ta faɗa musu dan ko buɗuwa idanun basa yi saboda tsananin yaji, a haka har suka fita ƙofar gida dan har karo suke yi da juna suna fita ta banka ƙofar gidan ta sanya sakata tare da komawa ta jingina da jikin ƙofar tana sauke wata nannauyar ajiyar zuciya dan ta san ba ƙaramin jarumta ta yi ba yau dan dukan maza kamar wannan gaskiya ta yi ƙoƙari duk da tana ganin hakan kamar ganganci amma kuma idan ta tuna ba wasu ɓarayin kirki bane illah ƴan jagaliya ne sai warin kayan maye suke dan kawai ƴan shaye-shaye ne na unguwa.Tunowa da ta yi da abin da ya bata ƙarfin gwiwa har ta aikata hakan shi ya sanya ta taho cikin gidan cikin sauri, Baba ta gani da Rahma suna tsaye suna maida yadda aka yi. Dan suna fita Rahmar ta fito daga ɗakin dan jin ana dukan ana ihu ya fargar da ita me ke faruwa, shigowar Ridallah ya sa suka nufota suna murna, ita kuwa murmushi kawai ta musu tare da shiga ɗakinsu ta ɗakko bindigar da suka bari ta nufo su Baba da ita. "Innalillahi wai anan suka bar mana bindigar dama? Mun shigesu "Rahma ta ce tana kama baki da mamaki. "Bari ku ga bindiga"Cewar Ridallah tana kama kunamar bindigar ta matsa, sai kawai suka ji ƙaran bindigar yara har danjar jiki tana kawo wa.Ƙyalkyalewa Ridallah ta yi da dariya ta ce. "Kun san ya akayi na gane ba bindigar gaske ba ce" "Ja'ira sai kin faɗa"Baba ta ce ita ma tana dariyar. "Kawai fa lokacin da Ogan ya miƙa masa bindigar sai na hango batiri dan wurin batirin ba murfi, shi ne na fahimci bindigar wasan yara ce" "Ikon Allah kawai Allah ne ya cecemu ya kuma ceci mutuncinki Ridallah, amma da bindigar yaran ce za ta musu amfani dan da ita za su yaudaremu mu tsorata har su ida nufinsu a kan ki sai kuma Allah ya kawo hanya mai sauƙi ido ya juye da mujiya dan gashi nan sun ɗanɗani kuɗarsu"Baba ta ce tana karɓar bindigar daga hannun Ridallah take ƙarewa bindigar kallo. " Wallahi kawai dama ƴan iskan unguwa ne, in ba haka ba ina na taɓa jin an tafi ko sata da bindigar wsan yara"Rahma ta ce tana jimanta abin. Haka sai suka shiga jajanta abin daga ƙarshe kowa ya koma ɗaki amma b wai dna bacci ba Baba Habiba da Ridallah alwala ma suka yi suka gabatar da sallar nafila suna addu'a tare da godiya ga Allah bisa nasara da ya basu a kan azzalumai MMN AFRAH😍 ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️ 💕ALAƘAR YARINTA💞 ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️ NA MMN AFRAH FIRST CLASS WRITER'S ASSO... *Alhamdulillah godiya da yabo sun tabbata ga Allah maɗaukakin sarki da ya bani ikon sake zuwa da wani sabon littafina mai suna ALAƘAR YARINTA yadda na fara lafiya Allah sa na gama lafiya, Allah bani ikon rubuta abin da mutane za su amfana da shi amin* . Wannan littafi daga farkonsa har ƙarshensa sadaukarwa ne ga aminiyar ƙwarai Meenatu mmn muhibba Boy & sadiq , alkairin Allah ya kai muku a duk inda kuke Allah ya bar ƙauna tsakaninmu❤️ page 3️⃣4️⃣&3️⃣5️⃣ ABUJA Zaune Aunty take a falonta ta ɗora ƙada ɗaya kan ɗaya tana danne waya, da hannu ɗaya ɗayan hannun kuma riƙe da ayaba tana gutsira a hankali Safiya ce ta shigo falon ɗauke da sallama sai da ta zo har gaban Auntyn ta durƙusa har ƙasa ta ce "Hajiya gashi " Cewar Safiya tana miƙa mata leda mai ɗauke da atamfofi, ta ajiye a gabanta sannan ta ɗora mata mukullin motar motar a kan center table ɗin da ke gabanta. "Kin kulle min motar?" Auntyn ta tambayeta hankalinta a kan waya. "Eh na kulle, da na ga na kasa kullewa ma direba nasa ya kulle miki" "Gaskiya ƙauyencinki ya yi yawa Safiya kullum ke bakya gane abu sau nawa na loya miki buɗe mota da rufewa saboda irin haka idan na yi mantuwa ki ɗakko min, amma ba laifinki bane babu a house shi sa" Ta faɗa tana juyowa ta kalli Safiyar irin kallon raini.Shiru Safiyar ta yi duk da maganar ta mata ciwo amma babu yadda za ta yi tun da aiki take a ƙarƙashinta kuma ma ai gaskiga ta faɗa tun da ba su da ko keke a gidansu bare a yi zancen mota.Amma ita ma Autyn ai ƴar talakawan ce kawai dai samun wuri ne ya sa ta manta da baya. "Ɗauki ki kai min ɗakina sai ki gyara min gadon dan ɗazu na kwanta aka duk shimdiɗar ta ɓaci" Muryar Aunty ta katse mata tunani "To Hajiya an gama" Safiya ta faɗa tana ɗaukan ledar atamfofin da ta ɗallowa Aunty a mota ta hau sama da su. Tana shiga ɗakin ta jefar da ledar kayan a ƙasa ta shiga ƙarewa ɗakin kallo tana ƙada jin wani haushin Auntyn na tokare mata maƙoshi. "Matar nan baki da hankali amma da sannu nasan za ki gane shayi ruwane, kin bar ƴar cikin ki tana karuwanci saboda tsabar jahilci da son duniya tana aiko miki kuɗi kina bishasharki kin ɓanta cewa amana Allah ya baiwa iyaye ta ƴaƴansu kuma sai ya tambayesu kamar yadda ya faɗa amma ke baki tanadi amsar baiwa ubangiji ba kina hauka sai ranar da aka maƙuraki a kabari mala'iku su shiga jibgarki" Safiya ta faɗa iyo jifa da filillikan kan gadon ta shiga ɗame zanin gadon, dan ita Aunty gani take ba a san me take ba duk da ta fi ƙarfin mijin mata amma kuma bata san gabaɗaya takunta a kan idon Safiya yake ba tana sane da ita ko wayar da take da Iftihal ko Hajiya Wasila tana mata laɓe ko kuma idan Hajiya Suwaida ta kawo mata ziyara duk maganar da za su yi a kan kunnen Safiyar suke ba tarw da sanin suna yin shuka a idon makwarwa ba. Aunty na ganin Safiya ta haye sama ta kamo number Hajiya Suwaida ta doka mata kira, sai da ta kusa tsinkewa Hajiya Suwaida ta ɗauki kiran. "Hello ƙawata"Cewar Hajiya Suwaida cikin wata murya. "Na'am aminiyata fatan kina lafiya" "Lafiya ƙalaw wallah i fatan kema kina lafiya" "Lafiya ƙalaw, sai na jiki shiru kuma ban ji alert ba" Hajiya Suwaida ta faɗa tana dariya. "Haba ƙawata ke kwa akwai gajen haƙuri, ai kin san da kuɗin sun shigo da tuni na hankaɗo miki naki kason dan babu sanya kawai dai ni ma ina jiran tsammani ne" "Bangane jiran tsammani ba, kina nufin ita Iftihal ɗin basu haɗu da Alhajin ba? Ko dai ita ma ta fara sanin kan ta ne ta riƙe kuɗin ba ta baiwa Hajiya Wasila ba bare a turo mana namu?" "Ba haka bane kinsan dai Iftihal sai abin da na ce take yi kuma ba za ta taɓa riƙe kuɗi ba ko da za ta samu kaɗaɗe malala gashin tinkiya in miki ta yara" Ta faɗa tana dariya. "To a ina matsalar take?" "Sai fa yau za su haɗu da Alhajin dan mun yi waya ma ɗazu ta ce min tana hanyad zuwa inda za su haɗu da shi, kinsan kwa komai na kankama za a sanar da ni" "Yawwa yanzu na ji batu, amma da na ji shiru " " A haba ƙawata ai kin fi ƙarfin komai a wurina" A tare suka kyalkyale da dariya, suka faɗa wata hirar daga ƙarshe suka yi sallama a kan idan kuɗin sun sauka da zafinsu za ta tura mata kasonta.Tana ajiye wayar ta shiga magana ita kaɗai tana murmushi. "Ke ma dai ƙawata da wasa kike amma ke da kika ɗorani a hanya ya za a yi na manta da ke ko na yada ki ai in na yi haka na yi butulci ba na fatan faruwar hakan ma."Ta faɗa tana faɗaɗa murmushinta *MOMMA* "Assalamu alaikum" Suhaila take sallama daga bakin ƙofar ɗakin Momma, amsa sallamar Momma ta yi sannan ta mata izinin shigowa, shigowa ta yi ta ce. "Hajiya na kammala aikin" Kauda kai gefe Momma ta yi dan ba ta so Suhaila ta ga idanunta saboda ta sha kuka duk sun yi ja sannan saman fatar idanun ma duk ya kumbura. "Yawwa dama ɗakin can nake so ki tayani mu gyara kamar yadda muka saba" "To Hajiya ai sai abin da kika ce, sai dai kuma ina da shawara" "Ina sauraronki Suhaila ki faɗa kan ki tsaye dan kin san ba ƴar aiki na ɗauke ki ba na ɗauke ki tamkar ƴar da na haifa" "To Hajiya dama gani na yi ɗakin can ba fa datti yake yi saboda gabaɗaya window da labulayen ɗakin a rufe suke, sannan kuma babu wani wanda yake shiga ciki amma ace duk ƙarshen wata sai mun gyara ɗakin mun juya jeran ɗakin sannan kayayyakin da babu wanda ya taɓa sanyasu kuma yadda muka ajiye haka suke amma sai mun hargitsasu mun sake jerawa?" Shiru Momma ta yi, wannan karon ta maido kallon ga Suhaila tana nazarin kalamanta kalaman da suka ƙara sosa mata inda yake mata ƙaiƙayi, wanda hakan ya ƙara sanadiyyar cikowar ƙwalla daga idanunta, hannu ɗaya ta sanya ta rufe fuskarta ta ɗan jima a haka sannan ta murza fuskarta dahannun ta zubawa Suhaila idanu ta ce "Suhaila shin iya shekarun da muka ɗauka da ke muna aikin nan baki taɓa min wannan tambayar ba sai yau? Sannan kuma baki taɓa tunanin dalilin da ya sanya muke aikin ba sai yau?" "Ba haka bane Hajiya kawai dai yau ne na ce bari na gwada sa'a ta ko za a dace, domin na san tun daga ranar da kika fara buƙatar na tayaki gyara ɗakin nake yiwa kaina tambayoyi duk da acan baya ke kaɗai ke yin kayanki kafin daga bisani ki sanya nake tayaki muna gyarawa.Ba komai ke bani mamaki na har ya ɗaure min kai irin yadda kike siyan kaya kina jibgewa ba tare da ana amfani da su ba, iya gani na tun daga ranar da aka haifi yaro kawo ya zama saurayi akwai kayan da zai sanya a cikin ɗakin, kayan jarirai, kayan wanda ke rarrafe, kayan mai koyan tafiya kayan yayayyen yaro kawo shekara uku huɗu kai har kawo kayan matashi akwai a ɗakin a tawa fahimtar kayan ne kike siya tun daga jarai har girman yaro akwai kayan da zai sanya a ɗakin jibgi-jibgi, sai dai inaso ki yi haƙuri da tambayar da zan miki, na san dai baki da ɗa, iya sani na dai kin taɓa haihuwa ɗan ya rasu, to shin yaron ne kike siyawa kayan nan kike ajiyewa, ko kuma dai taro ne kike yi abin da bahaushe kan kira kafi ɗa wuya?" Suhaila ta kai ƙarshen maganar tana ɗagowa ta kalli Momma ganin gabaɗaya hawaye ya wankewa Momma fuska jikin Suhaila ne ya yi sanyi har tana ji a ranta bata kyauta ba domin ta shiga hurumin da ba nata ba gashi har ta sanya uwar ɗakin nata kuka wannan dalilin ne yasa tun daɗewa shekara da shekaru ta riƙe tambayar nan bata yiwa Momma ba. "Suhaila na ji duk tambayoyinki sai dai inaso ki sani duk duniya babu wanda ya san da abubuwan da ke cikin wancan ɗakim daga ni sai ke sai kuwa Allahn da ya haliccemu, ko Abie bai san da komai na cikin ɗakin ba, ke ma dan na yarda da ke shi yasa na sanar da ke, tabbas bani da ɗa kamar yadda kika sani kuma haihuwata ɗaya kuma kamar yadda kowa ya sani yaron baya raye, sai dai ni dalilin da ya sa nake ajiye kayan nan Allah ne kaɗai ya sani, kuma ba zan sanar da ke ba kuma ba dan ban yarda da ke ba sai dai na barwa kai na sanin sirrin zuciyata, sai dai zai iya kasancewa taro nake ta bahaushen wato kafi ɗa wuya" Momma ta faɗa wasu hawaye masu zafi na kwaranyo mata, a lokaci guda kuma tana sakin murmushi mai ciwo. Wata ajiyar zuciya Suhaila ta sauke tana jin dana sani a kan tambayar da ta yiwa uwar ɗakin nata, dan ta ga ta shiga damuwa sosai wajen bata amsa. "Dan Allah Hajiya ki yi haƙuri da tambayar da na miki, insha Allah ba zan ƙara miki makamanciyar tambayar ba" "Ba komai Suhaila taso mu je mu fara kar lokaci ya ƙure mana" Cewar Momma tana miƙewa Suhala ta mara mata baya. Suna zuwa Momma ta sanya mukulli ta buɗe ɗakin ta tura ƙofar suka shiga, wani sanyi ne ya ziyarcesu irin na ɗakin da ya yake a rufe kowane lokaci, ga kuma wani ƙamshi na freshner. ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️ 💕ALAƘAR YARINTA💞 ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️ NA MMN AFRAH FIRST CLASS WRITER'S ASSO... *Alhamdulillah godiya da yabo sun tabbata ga Allah maɗaukakin sarki da ya bani ikon sake zuwa da wani sabon littafina mai suna ALAƘAR YARINTA yadda na fara lafiya Allah sa na gama lafiya, Allah bani ikon rubuta abin da mutane za su amfana da shi amin* . Wannan littafi daga farkonsa har ƙarshensa sadaukarwa ne ga aminiyar ƙwarai Meenatu mmn muhibba Boy & sadiq , alkairin Allah ya kai muku a duk inda kuke Allah ya bar ƙauna tsakaninmu❤️ Page 3️⃣6️⃣&3️⃣7️⃣ *DUTSE GADAWUR* HAJIYA SUWAIDA Hajiya Suwaida ce cikin kicin bayan masu aikin abinci sun kammala ta zo ta dakatar da su daga ɗauka domin su kai su jera akan dinning, cewa ta yu su je uzurinsu ita za ta jera, cikin girmamawa ta suka fita daga cikin kicin ɗin suka barta ita kaɗai amma a ransu auna mamaki dan ba ta son yin aiki ko kaɗan ta fi so komai a mata amma kuma yau gashi ta buƙaci su bar ta za ta yi. Suna fita sai da ta bari suka ɗan jima da fita ta daina jiyo motsinsu da takun tafiyarsu, sannan ta sanya hannu a cikin aljihun doguwar rigarta ta ɗakko ƙullin magani guda biyu kowanne ƙulle a leda sai dai ledar ɗaya fara ce ɗayar kuma baƙa wannan bambancin ledar ne abin da zai sa ba za ta manta da aikin kowanne maganin ba.Kallon maganin take tana dariya, saboda farincikin da ya baibaiye zuciyarta domin tana ganin ta samo maganin sauran matsalarta dan ba komai bane matsalarta yanzu ba sai riƙe aljihu da Sarkin yaƙi ya tsiro mata da shi kwata-kwata ba ya so yake sakin aljihu da kuɗi ko dubu ɗari nawa take so yana bayarwa amma kwanan nan ta fara ganin canji daga gareshi to maganin da ke cikin farar leda maganin sakin aljihu ne na baƙar ledar kuma na wani sirri ne da ta daɗe da haƙa rami ta binne, amma yanzu tana ganin kamar sirrin na neman barin jikin Alhajin wannan dalili yasa ba ta yi ƙasa a gwaiwa ba wajen samo maganin matsalarta dan dole Alhaji Sagiru ya dawwama a halin da yake ciki kuma sirrin nan da ta binne ya cigaba da bunnuwa har abada! Na farar ledar ta kunce ta buɗe flask ɗin miyar ta barbaɗa a ciki ta sanya spoon ta gwauraya sosai, sannan ta kunce na baƙar ledar ta buɗe flask ɗin farfesun kayan ciki ta juye a ciki ta juya har maganin ya haɗe da romon ta mayar ta rufe ta jefa ledojin cikin shara, kan ta ta ɗaga sama ta kalli agogon bangon da ke manne jikin bangon kicin ɗin 12:00 pm ta yi wani shu'umin murmushi dan ta san ƙarfe 12 aka ce za a gama taron naɗin sarautar da ake a fadar mai martaba Sarkin Dutse, tabbas ta san yanzu nan da mintuna ashirin Alhaji Sagiru zai ƙaraso gidan.Fitowa ts yi daga cikin kicin ɗin ta ƙwalawa masu aikin nata kira suna ƙarasowa ta musu umarni a kan su ɗakko kayan abincin su kai kam dinning ɗin, cikin bin umarninta suka nufi kicin ɗin ita kuma ta wuce abinta. Misalin ƙarfe 12:30 ta kiyo tsayuwar motar mai gidan nata tasowa ta yi ta fito ta nufo ɓangarensa domin tarɓarsa, Tana shigowa falon ta ƙofar baya Shi ma yana shigowa amma sai ta gan shi a wani firgice kamar wanda za a ce kamoshi ya gudu.Direbansa ne riƙe da rawaninsa sai zaginsa (Bafadensa) Riƙe da alƙyabbarsa, cikin mamaki ta ƙaraso ganin suna masa sannu har ya zauna a kan kujera yana wani sauke numfashi sama-sama. "Ikom Allah mai ke faruwa ne?" Ta jrfa musu tambayar tana bin su da kallo ɗaya bayan ɗaya. "Eh dama, dama... "Dama me? Na ce dama me ina tambayarku mai yake samesa kana min wani kame-kame?" Ta katsewa direban hanzari cikin ƙaraji. "Kawai fa a wajen taron wannan ne shi ne ya ga wani Hakimi Ɗan buran shi da ɗansa Hafiz to suna ƙoƙarin gaisawa ne dukansu kowa ya fara karkarwa su duka ukun har Hafiz ɗin suka dafe kan su, dama bayan an gama taron ne ana ɗan gaggaisawa, sai kawai Sarki ya ce a saka su a mota kowa ya tafi gida" Bafaden ya faɗa cikin girmamawa. Wani murmushi ne ya sauka a kan fuskar Hajiya Suwaida jin wannan daddaɗan labari amma babu wanda zai iya ganin murmushin nata saboda cikin hikima da gwanancewa da kissa ta yi.A hanzarce ta nufi Alhajin hankali tashe tana salati, tana jero masa sannu shi dai bai iya cewa komai ba dan gabaɗaya sai wani gumi ne ke tsatssafo masa ko ta ina ga wani karkarwa da yake kamar mai zazzaɓi. "Kai Allah kaɗai ya san mai hakan ke nufi" Ta faɗa cikin sanyin murya. "Wallahi Hajiya kowa ma mamaki yake hatta mai martaba ya jinjina al'amarin" Direban ya ce cikin jimanta abin. "Allah dai ya yaye masa ya karesa daga azzalumai da sharrin duk wani mai sharri" Bafaden ya ce yana ɗora alƙyabbar a kan ɗaya daha cikin kujerun. "Amin ya Allah, alfarmar annabi da alqur'ani" Direban shi ma ya ce yana ajiye rawanin a kusa da alƙyabbar. Shiru Hajiya Suwaiba ta yi ba ta ce amin ba. "Hajiya bari mu je sai ya tashi ko" Suka haɗa baki wajen faɗa. "To to to, sannunku da ƙoƙari" Suna fita ta bi bayansu da harara a ranta ta ce "Amma na ji daɗin faruwar hakan, ai ba za ku taɓa gane junanku ba, duk wanda ya tarki tuno ɗaya daga cikinku to tabbas ya tarowa kan sa aradu da ka" Ta faɗi haka a cikin zuciyarta tana maida hankalinta ga Alhaji da bacci ya ɗaukeshi a jigace.Haka ta ɗan gyara masa kwanciyad da ke doguwar kujera ce ya ɗan kishingiɗa aka a duk da kasancewarsa babban mutum amma hakan bai hana kujerar ɗaukansa ba saboda irin manya -manyan nan ne. Sai wajen ƙarfe huɗu da wani abu ya farka, kamar ma bashi ba dan ya dawo dai dai, sai da ya yi wanka ya yi sallar azahar da la'asar sannnan Hajiya ta gabatar masa da abinci, haka ya ci abincin mai maganin nan da ta barbaɗa, yadda bai mata zancen haɗuwarsa da Ɗan buran ba haka ita ma ta wagarar da zancen dan dama ba ƙaunar zancen take ba shi kuma da alama ma ya manta da komai da ya faru. Bayan sun kammala suna nan suna ɗan taɓa hira a take Hajiya Suwaida ta bijiro da buƙatar kuɗi domin gwada sa'arta saboda tana so ta tabbatar da ingancin maganin. "Alhaji dama inaso ka bani wasu kuɗi saboda inaso in yi siyayya dan duk wasu abubuwam buƙata ta sun ƙare" Ta faɗa tana masa wani kallo ƙasa -ƙasa. "Cikin ɗan ruɗewa ya ce miƙo min wayata a kan Tv stand " Cikin ɗan sauri ta tashi ta ɗakko wayar a ranta tana jinjina aikin Malamin.Tana kawo masa ta tsaya jiran tsammani dan so take ya tambayeta adadin kuɗin da zai mata buƙatun ta, dan bata so ya bata kuɗi kaɗan dan an ce in zaka roƙa ka roƙa da babban masaki... "Kamar nawa kike buƙata" Ta tsinkayi muryarsa ya jefa mata tambayar. "500k ne " " Kina ganin za su isheki?" "Sun isa" Cewar Hajiya Suwaida tana jin wani itin daɗi a ranta dan tabbas magani ya fara aiki, dan tun da maganin ya karye ko 100k bai sake bata ba bare kuma har 500k. Ƙaran shigowar saƙo wayarta ne ya ƙara tsundumata cikin gogin farinciki, tana dubawa ta ga alert ɗin transper da ya mata. "Godiya nake Ranka ya daɗe" "Ai babu komai" Ya xe yana tashi domin hawa sama dan yin alwalar magrib, yana hawa saman ta tashi ta koma part ɗinta, no Hajiya Hauwa ta kira a nan ta shig bata labarin abubuwan da suka faru, dariya suka kwashe da ita . "Kina lokacinki ƙawata" Cewar Hajiya Hauwa tana dariya. "Ke dai bari ƙawata ai da sannu zai gane shayi ruwa ne" "Ina yinki ƙawata kin san ta kan tsiya, gaskiya kina wuta muna binki da fetur" "Eh mana amma bar kani wutar na da baki kar mala'iku su ce amin" "To na bari" "Yawwa ko ke fa ai gwara dai ki ce ina aljanna ko" "Hakane kam fatana nagari lamiri duk da baɓa aikin aljannar' " Za mu tuba ai" "Allah ba mu iko" "Amin" Haka dai suka cigaba da tattaunawa daga ƙarshe suka yi sallama. *GIDAN ƊAN BURAN* Hajiya Sakina ce tsaye a gaban freezer ita da ƴar aikinta tana fitar da kayan marmari waɗan da za a yanka, tana warewa domin mai aikin nata ta je ta ƙara wankesu ta kawo mata ta yayyanka, saboda ta gama haɗa komai na abinci yana dining dan ta san mai gidan nata da tilon ɗan mata yanzu suna tafe daga dawow daga wajen naɗin da suka je fada.So take daga ta kammala ta je ta yi sallah dan ga lokaci ya kusa fan ta san suma idan sun dawo sai sun je masallaci sun dawo sannan za a ci abincin. Bayan ta gama yayyankawa ƙanana dan fruit salad ne ta haɗa tana gamawa ta zuba a kwanon flastic mai zurfi ta sanya madara da ƙanƙara sai ɗan sugar kaɗan, ta sanya murfin ta rufe, sannan ta markaɗa mangwaro ta haɗa lemon mangwaro bayan ta kammala ta zuba a jug tasa ƙanƙara ta kai kan dinning ta ajiye sannan ta wuce domin zuwa ta ɗan ƙara watsa ruwa saboda zadin da take ji, sai ta yi sallar, bayan ta kammala wankan tana ƙoƙarin yin alwala ta tsinkayo muryar mai aikinta ta shigo ɗakin tana kiranta, jin yanayin kiran da take mata da alama kamar akwai matsala hakan yasa ta suturta jijinta ta fito, aikuwa ta ga ƴar aikin nata na nuni da hannu ta ma kasa furta komai.Da sauri Hajiya Sakina ta sanya dogon hijabinta na sallah da ke ajiye tare da sallaya a kan ƙaramar loka, dan ba ta da nutsuwar da za ta tsaya sanya kaya. Bayan ƴar aikin ta biyo dan gabaɗaya ma ganinta neman gushe mata yake Ta ruɗe ta ma kasa tambayar ƴar aikin takamaiman abin da ke faruwa, ita ma kuma ƴar aikin ba ta san abin da ke faruwa ba kawai dai ta hango wasu dogarai guda biyu sun riƙo Alhaji, sannan direba da mai gadi sun riƙo Hafiz dan duk sai da aka shiga kafaɗarsu. A can part ɗin Alhaji Sunusin an zaunar da Hafiz da Alhajin a kan kujerar sai aka jinginar musu da bayansu a jikin kujerar, a dai dai nan Hajiya Sakina suka ƙaraso ita da mai aikinta. "Subhanallahi! Me ke faruwa da su ne? Ko guba aka zuba a cikin abubuwan da aka ci a wurin taron ne?" Hajiya Sakina ta faɗa cikin gushewar hankali dan gabaɗaya ta tsorata da yanayin da ta gan su. "Wallahi Hajiya ba haka bane, bayan an kammala taron ne ma suka haɗu da Sarkin yaƙi daga haka kar ki ƙara kar ki raga, shi ne gabaɗaya suka kasance a cikin wannan halin har gwara ma shi Sarkin Ƴakin a kan su dan su sai da mai martaba ma ya bada umarni dogaran nan su tayamu mu kawo su gida" Direban ya mata bayani ai ambaton sunan Sarkin Yaƙi da ya yi sai da kan ta ya sara mata da mugun ƙarfi har sai da ta dafe da hannu ɗaya sannan a hankali ta zauna.Ganin halin da ta shiga yasa ƴar aikin nata yin sauri tana mata sannu.Shiru ba ta yi magana ba sai zuwa can ta ce "Yawwa" Sai ta maida hankalinta kan mai gidan nata da ɗan nata, ta taso ta zo garesu tana tambayar mai je damunsu dan har ta manta da labarin da direban ya bata hakan ne ya sanya kan nata ma ya saka mata. Daga dogaran har direban da mai gadin kallon kallo aka shiga yi jin tambayar da ta fito daga bakinta, babu wanda ya sake wata magana dan su ma sun lura kamar akwai halin da ta shiga lokacin da aka faɗa mata dalilin da ya sanya suka shiga wannan halin.Sallama dogaran suka musu tare da musu fatan samun sauƙi, shi ma direban fitowa ya yu shi ma mai gadin ya koma bakin aikinsa. Sun ɗauki tsawon awa guda sannan suka dawo hayyacinsu, dan dama ba dai bacci suke ba amma yanayinsu kamar na wanda suka sha abin maye suka bugu.Ganin sun farfaɗo yasa ƴar aikin nata ta fita ta koma bakin aikinta, ita kuma sannu ta shiga musu dan daga ita har su sun riga da sun manta takamaiman abin da ya faru. Sun dawo kamar ma babu abin da ya faru dan abin kamar wani shafar aljannu, alwala suka yi suka yi sallah Alhajin ne ya ja su sallar har Hakiya Sakina dan lokacin har an riga da an idar da sallar azahar ɗin, bayan sun idar suka ci abincinsu cikin kwanciyar hankali suna taɓa hira cikin farinciki da barkwanci. "Sannu da zuwa Baba Malam Baiwar Allah ta faɗa cikin girmamawa. "Yawwa sannu Baiwar Allah, wanki ake" "Eh" "Ke dai bakya gajiya da aiki" Ya ce yana murmusawa. "Kai ma dai ka faɗa Malam ni ma yanzu na gama faɗa" "To ai shikenan tun da tana son yin aikin ai shikenn" "Wlh kwa dan yanzu ma ta gama kwashe tuwo ta ɗora miya, ni ce ma na ce zan ƙarasa miyar daker ta yarda shi ne ta ƙara tsirar wanki" Malama Zainab ta ce tana ɗaukan ledojin da Malam ya iyo tsaraba, daga wani ƙauye da ya je wurin wani babban Malami abokinsa domin su haɗa wani magani da za a haɗawa Baiwar Allah. Bayan ya ci abincin dare suna hira a tsakar gida ya ce Malama Zainab ta ɗakko masa wata baƙar leda da ya zo da ita a hannunsa ɗazu da ya dawo ya faɗa mata inda ledar take dan ɗazu ma da ya zo da ita a cikin aljihun babbar rigarsa dan maganin ne sanadin tafiyarsa tun bayan sallar asuba. Bayan ta ɗakko ya buɗe ledar ya fito da gora mai ɗauke da rubutu, sai kuma wani ƙullin magani ya ce "Wannan rubutun da kike gani, idan aka zuba maganin nan ta sha na tsawon kwana uku to duk wani abu da ta manta za ta tuno da shi, ba ma ita kaɗai ba matsawar sihirin mantuwar nan ya bar jikinta to duk su ma wanda aka musu tare sai ya bar jikinsu, domin su biyar ne aka yiwa sihirin duk da ban san sauran ba amma nasan ba za su wuce makusantan da ba saboda su manta da ita ba za su tuna da ita ba ma bare har su nemi inda take amma cikin ikon Allah komai ya kusan zuwa ƙarshe kamar yadda haukar ta bar jikinta da izinin Allah haka ma mantau ɗin zai bar su" Cewar Malam Idi yana buɗe gorar ya since maganin ya shiga zubawa a ciki. "Alhamdulillah! Na yi matuƙar farinciki da samun wannan magani Allah ƙara muku sani da basira Allah kuma ya taimakeka ya baka ladan abin da ka yi" Malama Zainab ta faɗa cikin farinciki dan tana jin Baiwar Allah tamkar ƴar uwarta ta jini iya zaman da suka yi na kusan shekaru uku da wani abu. "Ai nake faɗa miki maganin ne samun sassaƙensa akwai wahala, shi yasa gashi ba mu da bishiyoyin a nan wajen a can ma da na je sai da muka yi tafiya mai nisa kafin mu je ga inda muka samu bishiyoyin muka sassaƙa, na daɗe ina neman inda zan samu sassaƙen amma ki ga cikin hikimar Allah yanzu da lokacin ya yi na samun lafiyar warakar mantau ɗin nata sai a abokina da na tambaya ya ce akwai a wajen ƙauyensu ana samu, gashi dai mun haɗo mun kuma rubuto ayoyin da za su taimaka sai da ya tayani duk muka rubuce sannan aka wanke aka ɗiga nonon jikin bishiyar saboda kafin azo nonon ya ƙame, hatta sassaƙen ma sai da ya sanya matarsa ta daka min" "Kai gaskiya an gode Allah bar zumunci ya barku tare" "Amin, ki mata magana ta fito ta sha maganin" "To bari na kirawo ta tun da ta shiga ta yi sallar isha'i da ta idar ba ta fito ba ko kwanciya ta yi, ka san ba ta sakewa idan kana nan tana ganin girmanka" Malam Zainab ta faɗa tana tashi ta kwashe kwanukan tuwon ta shiga ɗaki ta kira Baiwar Allah, bayan ta fito ta zauna a kan tabarmar da Malama Zainab take zaune, Malam ne ya tsiyayo maganin a ƙaramin kofi ya miƙawa Malama Zainab ta miƙawa Baiwar Allah, Bismillah ta yi ta kafa kanta ta shanye dan ko ɗanɗano maganin bashi da shi babu ɗaci babu komai haka ta shanye ta ajiye kofin tare da musu godiya, cikin jin daɗi suka ce ba komai dan an zama ɗaya babu batun godiya sai dai fatan dacewa maganin ya yi aiki. MMN AFRAH ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️ 💕ALAƘAR YARINTA💞 ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️ NA MMN AFRAH FIRST CLASS WRITER'S ASSO... *Alhamdulillah godiya da yabo sun tabbata ga Allah maɗaukakin sarki da ya bani ikon sake zuwa da wani sabon littafina mai suna ALAƘAR YARINTA yadda na fara lafiya Allah sa na gama lafiya, Allah bani ikon rubuta abin da mutane za su amfana da shi amin* . Wannan littafi daga farkonsa har ƙarshensa sadaukarwa ne ga aminiyar ƙwarai Meenatu mmn muhibba Boy & sadiq , alkairin Allah ya kai muku a duk inda kuke Allah ya bar ƙauna tsakaninmu❤️ Page 3️⃣8️⃣&3️⃣9️⃣ *HIZBULLAH* "Dan Allah Hizbullah ka nutsu ka saurareni, bana so ka sanya kan ka a cikin matsala, wannan yarinyar da ganinta ba yarinyar arziƙi ba ce bare kuma shi mutumin da suke tare zai iya maka komai idan ka bisu dan Allah abokina ka dawo hayyacinka" Abulkairi ya ce lokacin da ya ƙara riƙo rigar Hizbu daga baya da ya yi yinƙurij bin su Iftihal.Wani ruwa ne ya ciko cikin idanun Hizbu saboda bai san da kalaman da zai yi amfani da su ba Abulkairi ya bar shi ya bi bayansu kuma ba ya so su ɓacewa ganinsa gashi duk kan sa ya kulle baisan ta ina zai fara tsayawa yiwa Abulkairin bayanin cewa ita ce Ridallah ɗinsa da da yake kwana da rashinta yake tashi yake cike da damuwa a cikin zuciya da ruhinsa wanda babu wanda ya san hakan sai shi sai kuma Allah da ke ganin zukatan bayinsa. " Ka yiwa iyayenka ka barni bana tsoron komai ya faru da ni matsawar zan cimmu su kafin su ɓacewa gani na, ka bari zan maka bayani daga baya, saboda kasan dai idan har ta ɓacewa gani na bani da tabbacin ƙara ganinta amma idan na bi bayansu a ƙalla zan san inda take zaune" Shiru Abulkairi ya yi yana nazarin halin da abokin nasa yake ciki, sosai tausayinsa ya kamashi domin ya ga rauni sosai a tare da shi bayan kuma ya san abokin nasa akwai dagewa da kuma jajircewa ba ya taɓa bari mutum ya ga gazawarsa amma kuma yau gabaɗaya rauninsa ya bayyana duk da dai dama ba abin mamaki bane a ga komai a tare da shi in dai a kan Ridallah ne, shi ya ma kasa gane takamai man inda batun ya dosa dan ya dai san wannan ba Ridallah ba ce duk da bai santa ba amma ya yadda yake bashi labarin Ridallah da irin soyayyarsu bai kamata ace ta nuna bata san shi ba ma tabbas akwai lauje cikin naɗi akwai wani abu a ƙasa da yake ganin kamar shi kan sa Hizbullah ɗin bai sani ba bare kuma shi d... "Ka sakar min riga" Muryar Hizbu ta katse masa tunaninsa.Kafin ya ce wani abu Hizbullah ya ƙwace rigarsa da ƙarfi ya tafi.Sho ma bashi da wani zaɓi da ya wuce bin bayan Hizbullah ɗin, lokacin da ya zo inda mutane ke cin abinci ya tsaya waige-waige ko zai ga Hizbullah ɗin dan kan meye wannan har ya ɓacewa ganinsa amma bai ga ko da alamarsa ba hakan yasa ya bi ƙofar fita daga wurin ya fito waje, yana ta dube-dube bai ga Hizbullah ɗin ba tafiya ya lan fara yi aikuwa ya hangoshi can wajen parking space ya tsaya hankali tashe yana ta dube-dube. Cikin hanzari ya nufi wurin abokin nasa, yana zuwa ya ga Hizbullah na zubar da hawaye yana ta magana shi kaɗai "Ridallah dan Allah kar ki min haka, ina sonki a hakan ma, babu wani hali ko yananyi da za ki tsinci kan ki a ciki wuya ko daɗi kyakkyawan hali ko akasin haka babu wani bau da zai ragu daga cikin ƙaunar da nake miki, ganinki da na yi yau ya ƙara rura min wutar son ki a cikin tai da zuciyata, amma ya aka yi kika ƙara tafiya kika barni bayan ni ba zan iya barinki ko da na lokaci ƙanƙani ba amma ke kin tafi kin barni tsawon wasu shekaru yanzu kin dawo amma kika ƙara guje min? Shin kin san wani irin hali zan sake shiga ta dalilin hakan? Haba Ridallah mai ya sa za ki guji wanda ya fi ƙaunarki fiye da kan sa a rayuwarsa? Wanda ya fifita son ki a kan kowacce mace bayan mahaifiyarsa a rayuwarsa, wanda ya ƙudurta zamar miki bango abin jingina a rayuwarki, wanda zai riƙe miki maraicinki ya kyautata miki ya zamar da ke sarauniya har iya ƙarshen numfashin da Allah ya ɗaukar masa, mai yasa Ridallah, mai yasa zaki min haka, mai yasa bakya tausayin mai ƙaunarki da gaskiya!!! " Yana kaiwa ƙarshen maganar ya durƙushe a wurin yana sakin wani kuka mai tsuma zuciya, dan gabaɗaya sai yau ya ƙara sanin ba zai iya rayuwa in ba Ridallah, haƙiƙa ƙaunar gaskiya wata aba ce mai wuyar ƙanƙaruwa daga zuciya sai dai kullum take ƙaruwa tana hauhawa a zukatan masu yin ƙauna dan Allah ba masu yin soyayyar yaudara ba soyayyar da babu komai sai sha'awa da tarin yaudara. (TSOKACI ki nutsu da kyau ki gane mai ƙaunarki da gaskiya, wanda ke son ki da aure ba waɗannan samarin ba wanda babu komai a ransu sai yaudara ba komai yake so ba sai jikinki bashi da buri kullum sai yadda zai yi amfani da kalamai da kuma kaifin harshe wajen jan hankalinki ki mallaka masa kan ki da zarar kuma ya samu abin da yake so da ke da bola duk ɗaya.Mutuncinki shi ne ribarki shi ne ribar iyayenki kada soyayyar shan minti tasa ki siyar da darajarki ta ƴa mace darajar iyayenki da ta ahalinki bakiɗaya.Bayan nan darajarki ita ce mutuncinki da ta ƴaƴanki domin kema uwa ce wata rana ki zama wacce ƴaƴanki za su yi alfahri da ke a matsayin uwa domin duk abin da kika yi ƴaƴan nan naki fa zasuyi kin ga kin jefa rayuwarsu a matsala, saurayin da zai ke taɓa miki jikin ki wallahi wallahi ba mai ƙaunarki bane! Allah tsaremu daga azzalumai). Tausayin Hizbullah ne ya shiga zucouar Abulkairi ji yake ina ma yana da iko da ya cikawa Hizbullah burinsa ko dan kasancewarsa mutumin kirki amma tabbas rangwame irin na raɗaɗin soyayya sai wanda ake yin soyayar domin shi, shi ne zai iya faɗawa masoyin kalamai wanda za su tausasa zuciyarsa, haƙiƙa wannan aikin Ridallah ne sai dai shi ya masa addu'a akan Allah warware wannan ƙullin da ya sake tunkaro rayuwar Hizbullah.A hankali ya ƙarasa kusa da shi hannu ya sanya ya dafa kafaɗarsa ya ɗan ranƙwafo ta gefensa ya ce "Haba Hizbullah ka zama namiji mana" "Wane namiji kuma kasan zafin so kwa Abulkairi? Kasan yadda nake ji kwa yanzu, kasan halin da zan cigaba da kasancewa yanzu da na yi tozali da wacce soyayayarta ta rayu a cikim zuciyata tun ALAƘAR YARINTA, soyayyarta ta girma a raina ina bege da muradinta, duk da bana ganinta amma hakan bai rage ko kaɗan na daga soyayyar da nake mata ba, ka sanya kan ka a matsayin ni yau gashi na gan ta amma ta nuna bata ma sanni ba har tana iya ɗaga hannu za ta mareni, Ridallah nutsatstsiyar yarinya kamila wacce tun tana ƙarama nake rainonta da ɗabi'u masu kyau amma yau na ganta a wani yanayin marar kyan gani ko wannna kaɗai ya isa tashin hankali a gareni" " Na sani Hizbu, na sani bu ne mai ciwo abu ne mai girma amma haƙuri da dangana shi ne babbar mafita... " Haƙuri da dangana su kaɗai ba zan samu sauƙin a zuciyata ba sai dai addu'a kaɗai ce za ta sanya na samu salama" Ya katse Abulkairi ta hanyar yin maganar cikin ƙaraji tare da fashewa da kuka mai ciwo. Zagayowa gabansa Abulkairi ya yi gaban Hizbu shi ma ya zauna a ƙasan, tare da zuba masa idanu shi ma a take nasa idanun suka ciko da hawaye tausayin abokin nasa ya tsarga masa a cikin ƙoƙon zuciyarsa ji yake ina ma bai riƙeshi ya hanashi tahowa wajensu ba, dama ya barshi ya cim musu da duk hakan bai faru ba duk da yana ganin da ya barshi ya tarar da su Allah kaɗai ya san abin da zai faru, dan ba ya so Hizbun ya je ya yi abin da zai taɓa masa karatunsa. Zabura Hizbu ya yi, ya miƙe tsaye shi ma Abulkairin miƙewa ya yi ya sha gabansa da ya ga yana ƙoƙarin bin wata hanya da ban "Wai ina za ka je ne?" "Taxi zan samu na tafi gida, so nake kawai na jini a kwance jj nake ƙafafuna ba za su iya ɗaukana ba saboda halin da zuciyata ke ciki, idan aka jima ma zan iya faɗuwa ka rabu da ni dan Allah' " Wane irin gida kuma Hizbullah mu da za mu koma scul, ka san fa ba mu gama da scul ɗin ba yunwar da kake ji yasa muka baro makaranta saboda ka ce ba ka son siyan abincin restuarant makarantar ba sai dai mu zagayo wannan Restuarant ɗin ka ga ganin babu nisa da scul ɗin muka zagayo kuma maimakon mu koma sai ka ce gida za ka tafi?" " Ka bar maganar scul ɗin nan kawai" Shiru ya yi yana nazarin halin da abokin masa ke ciki tabbas ko shi ya fahimci ko da sun koma scul ɗin Hizbu babu abin da zai iya taɓukawa, hakan ya sa ya tare musu taxi suka shiga dan shi ma ba ya jin zai iya barinsa a halin da yake ciki ya tafi gidan shi kaɗai gwara dai ya kasance a kusa dashi ko zai samu sassaucin a cikin zuciyarsa kuma idan yana kusa da shi ɗin zai rage zurfin tunani a maimakon idan shi kaɗai ne tunanin zai yi yawa sosai. Suna zuwa gidan ya hau sama da sauri ya buɗe ɗakinsa ya shiga ya rufo ƙofar ya sanya mukulli, dan haka Abulkairi na hawo wa saman ya murɗa ya ji ƙofar a kulle cikin sanyin jiki ya koma ya buɗe nashi ɗakin ga shige, sai a lokacin ma ya tuno sun bar handout ɗin a Restuarant ɗin kai kawai ya kaɗa ya shiga yin wasu hidimomin. Hizbullah kwa na shiga ya wuce ya ɗakko ɗankunnen da flower da Ridallah ta bashi ya shiga kallon su yana maganganu shi kaɗai dan shi duk gani yake kamar ya rasa Ridallah dan shi duk tunaninsa Ridallah ce Iftihal ɗin. MMN AFRAH😍🥰😘 ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️ 💕ALAƘAR YARINTA💞 ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️ NA MMN AFRAH FIRST CLASS WRITER'S ASSO... *Alhamdulillah godiya da yabo sun tabbata ga Allah maɗaukakin sarki da ya bani ikon sake zuwa da wani sabon littafina mai suna ALAƘAR YARINTA yadda na fara lafiya Allah sa na gama lafiya, Allah bani ikon rubuta abin da mutane za su amfana da shi amin* . Wannan littafi daga farkonsa har ƙarshensa sadaukarwa ne ga aminiyar ƙwarai Meenatu mmn muhibba Boy & sadiq , alkairin Allah ya kai muku a duk inda kuke Allah ya bar ƙauna tsakaninmu❤️ Page 4️⃣0️⃣&4️⃣1️⃣ *IFTIHAL* Suna fitowa ita da Alhajin daga Restuarant ɗin ta ja ta tsaya, shi kuma ganin tana wani shan ƙamshi tana haɗr rai sai duk ya ji ba daɗi, amma hakan bai sanya ya ji kp da haushinta ba shi dai kawai so yake buƙatarsa ta biya. "Kinsan fa wani abokina da ke zaune a nan ne ya sanya direbansa ya kawoni yanzu kuma sai dai mu shiga taxi mu je Hotel ɗin in kama mana ɗakin da za mu huta ko baby?" Ya faɗi hakan yana wani murmushi tare da washe haƙora sai wani lasar baki yake kamar wani tsohon maye.Ƙasa ta yi da glases ɗin nata ta masa kallon up nd down ta sauke idanunta a kan ƙaton tumbinsa tari guda kamar mai cikin wata tara, ɗauke kai ta yi gefe tare da maida glases ɗin nata yadda yake ta ɗago wayarta ta duba time. "No kar ma ki yi la'akari da wannan cuki ba wai tsufa bane ya sanya y yi girma hakan tsabar cin daɗi ne da kwanciyar hankali kinsan idan akwai kuɗi to mutum bashi da matsala sai wacce ba a rasa ba" "Ok ni ai ka san daga gidan talauci na fito" "Ba haka nake nufi ba baby, inaso na sanar da ke yau idan ki ka tashi tafiya za ki tafi da maƙudan kuɗaɗe wanda kowa sai ya san kin yi tarayya da wanda ke matashin kai da kuɗi" Ya faɗa yana washe baki. Jin ba ta ce komai ba ya sanya ya ƙara cewa "Mu je ko muna ɓata lokaci" Dan shi gabaɗaya wannan shan ƙamshin da take burgeshi take yi sabod yana son ya ga mace mai aji ya fi son hakan dan an fi daidaitawa da shi. Ita ta fara yin gaba, ganin ta nufi wajen wata mota da ke fake a wurin ya gane cewa da mota ta zo, hakan ya ƙara tabbatar masa da babban yarinya ce saboda har mota gareta ta kan ta.Suna isa ta sanya mukullin ta buɗe ta shiga wurin direba ta zauna sai dai ƙafafunta a waje suke, jakarta ta jefa kan ɗaya sit ɗin mai zaman banza, shi kuma cikin sauri ya nufi ɓangaren mai zaman banzan zai buɗe ya shiga sai washe haƙora yake kamar gonar auduga. Iftihal na ganin ya gewayo ta maida ƙafafunta cikin motar ta rufe ƙofar, gabaɗaya ta kulle motar Alhajin na kama ƙofar zai buɗe ya ji ta a kulle, ƙwanƙwasawa ya yi amma maimakon ta buɗe sai ta sauke glass ɗin ta sanya hannu ta yi ƙasa da glases ɗin fuskarta ta masa wani kallon ƙasƙanci ta ce "Malam ka bar min jikin mota tun kafin in tasheta in yi gaba in kuma yi reverse in kwasheka kuma na kwashe banza wallahi" "Haba baby wace irin magana kike haka? Idan ma wasa kike ki bari kar kisa ruwana ya hau, dan na gama ɗora rai a kan ki wallahi" "Za ka ga wasa da zarar na take ka, kuma sai dai hawan jininka ya tashi ba wai hawan ruwa ba" "Dan Allah ki buɗe in shigo mu tafi... "Kai na fasa zuwa ko ina da kai" Ta katse shi. "A haba dai haba baby ya zaki min haka" "Bani da lokacinka" Tana gama faɗar hakan ta ɗaga glass ɗin motar, ta mata key, Alhajin kuwa ya daddafe motar har sai da ya ji ta fara tafiya, ya ja baya ganin ta fisgeta da sauri ya tare taxi ya bi ya ce mai taxi ɗin ya bi bayan motar, tun suna bin bayansu har suka nemi inda motar ta yi suja rasa aikuwa Alhajin kamar ya cinye direban taxi ɗin sai masifa yake masa da turanci dan ba jin hausa yake ba daga chinanci sai ko turanci.Shi dai haƙuri yake bashi yana faɗa masa cinkoson motoci ne ya sanya motar ta ɓace masa, haka dai ya kaishi wani hotel ya yiwa wata waya dan ya rage zafi da ita saboda ɗora rai Allah sa mu fi ƙarfin zukatanmu. Iftihal kwa da ta lura da bin da su Alhajin ke mata dan dama tana ganinsa ta mudubi lokacin da ya tsare taxi ɗin, a haka ta yi ta yaudararsu har ta yanke ta wata hanya inda ta ɓacewa ganinsu.Gida ta nufa tana jin zuciyarta ba daɗi, tana yin parking ta nufi ɗakinsu ta shiga ta samu Amal zaune tana a kan gado tana waya jefa jakarta ta yi a kan gadon ta cire kayan jikinta ta ɗakko wata yaloluwar riga iyakar ƙwaurinta ta sanya ta kwanta rubda ciki ta jin ranta na mata wani zafi wanda ta kasa gane dalilin hakan dan ta rasa mai ke damunta, dan ita yau ɗaya kawai ji take duk ta tsani rayuwar da take yi, tun da ta gane saurayin da ta haɗu da shi a restuarant ya gane ta masa kama da wata a fuska amma ba a halayya ba kenan ita halayyarta marar kyau ce? Kenan ita ba dan kama da take masa da wata ba a fuska da bata da wani kyan hali da har zai sa a tunkareta, tabbas ta ji a yau tana sha'awar a ce ita ma wani zai iya yin abin da ta ga saurayin nan na yi a kan wata wato soyayyar gaskiya lallai hali mai kyau shi ne jigo a rayuwa shi kima da kuma martaba, amma ita mai ya sa babu wata hanya da aka nuna mata mai ɓullewa? Sai dai gurɓatacciyar hanya kuma matar da ita ce mahaifiyarta ita ya dace ta sanyata a hanya madaidaiciya amma kuma sai aka samu saɓanin hakan, shin ina mafita a ina amsar tambayarta take mai yasa Aunty ta zaɓa mata wannan rayuwar akan ta sanyata a hanyar da za ta zama abar kwatance kuma abar sha'awa ga kowa da kowa? Wasu hawaye ne suka shiga zubo mata, bayan hannunta ta sanya ta goge shin mai yasa bata taɓa jin ƙyamatar halayyarta ba sai yau ɗin nan? Mai yasa bata taɓa jin abin da take aikatawa ba dai dai bane sai yau ɗin nan tabbas an sanyata a a hanyar marar ɓullewa.Tana a haka har aka fara kiran sallar magriba. Wayarta ce da ke cikin jakarta ta shiga ringing amma har kiran ya katse bata ɗauka ba, Amal da ta kwanta bayan ta gama wayar da take ta juya mata baya tana chart ta ce "Wai malama bakya jin wayarki ta cikawa mutane kunne in ba za ki ɗauka ba ya kaɓata ki kashe dan ni ƙaran ya gundureni" Shiru ta mata bata tanka mata ba, mamaki ne ya cika Amal jin Iftihal ɗin bata ce komai dan ta san dai Iftihal ba ta taɓa barin ta kwana kana faɗa mata mafana za ta baka amsa dai dai da kai, amma kuma abin mamaki yanzu ta shareta.Juyowa ta yi dan ta tabbatar idonta biyu ko kuma bacci take, amma kuma mamakinta bai ƙaru ba sai da ta ga idanunta biyu buɗe. A dai dai nan wayar ta sake wanj wani ƙaran da alama wani kiran ne ya shigo bayan na farkon ya katse. "Iftihal ni kam ko dai baki da lafiya ne?" Amal ta jefa mata tambayar tana tsareta da ido dan ita bata ma lura da hawayen da ke ƙara kwaranyowa daga idanuna Iftihal ɗin ba.Baki ta taɓe ta juya ta yi kwanciyarta, ita kuma Iftihal ɗin jin ba a da niyyar daina kiran wayarta ta ne ya sanya ta tashi zaune dan kiran na katsewa wani ke shigowa kuma ta san babu mai mata wannan kiran a kai- a kai sai Auntyn ta dan samarinta da abokan hulɗarta kowa ya sani ba ta son damu dan in ka dameta da kira ma tana iya yanke alaƙa da kai saboda ita ƙa'idarta ce idan har ka mata kira ɗaya biyu ka ga bata ɗauka ba to ka bari idan ta ga dama za ta bi kiran. Cikin sanyin jiki ta tashi ta buɗe jakarta ta ɗakko wayar, tana shirin danna ok kiran ya katse sai ga wani koran ya shigo a take, kamar yadda tunanin nata ya bata kuwa Aunty ce tana kallon sunan sai da wasu hawaye masu zafi suka zubo mata.Ɗaukan kiran ta yi ta kai wayar kunnenta amma ba ta ce komai ba. "Iftihal haba ina kika shiga tun ɗazu sai kiranki nake amma shiru babu amsa, shi ma Alhajin na masa kira ya fi goma amma bai ɗauka ba daga ƙarshe ma wayar aka kashe, ko har yanzu baku baro Hotel ɗin bane kuna hutawa?" Wani takaici ne ya rufe gabaɗaya zuciyar Iftihal jin wai mahaifiyarta ce ke mata tambaya a kan cewa har yanzu tana Hotel tana hutawa tare da dadironta, shin mai yasa bata taɓa jin zafin tambayar nan ba sai tau tun da ba yau ne ta fara mata makamanciyar tambayar nan ba? Shin ita wace irin mahaifiya gareta shin anya kuwa Aunty ta cancanta ta zama uwa, duk da an ce mahaifiyarka ko mahaukaciya ce uwa ce a gareka amma maj yasa ita tata mahaifiyar na da hankali amma ba na tunani ba tun da duk wata uwa ta gari ba za ta so ta ga rayuwar ƴarta ta lalace ba, lallai kowacce uwa mahaifiya ce amma ba kowa ce mahaifiya ba ce ke zama uwa ta gari ga ƴaƴanta. "Wai Iftihal ya kika yi shiru ina ta sauraren ki fara min bayanin yawan kuɗaɗen da kika cafko mana a wurin Alhajin Allah, amma sai in ji kin yi shiru" Aunty ta katse mata tunanin. "Ni fa ba ma tare da shi" Ta bata amsa a taƙaice. "Allah sarki my Ifti ki ce har kin koma gida wato kun rabu da shi kowa ya kama gabansa, yo ai dama tun da kowa ya samu abin da yake so sai a raba garun, shi ya samu biyan buƙatarsa ke kuma kin samo mana kuɗi, wato kasuwa ta watse ɗan koli ya ci riba" Ta ƙarasa faɗa rana wata dariya. "Ni fa Aunty ba mu aiwatar da wani abu ba, dan ni ko Hotel ɗin ban je ba kawai dai na fasa yi... "Ke! Dakata dallah ya ina miki magana kina sako min wani zancen banza da wofi" Auntyn ta katseta cikin ƙaraji. Shiru Iftihal ɗin ta yi ba ta ce komai ba. "Wato duk yadda na shirya wannan haɗuwar taku sai da kika yi yadda kika yi kika ruguzata, wato duk irin yadda na so mu samu abin arziƙi mai tarin yawa sai da kika yi fatali da damar da kika samu, shin kin san waye wannan mutumin kin san irin tarin dukiyar da yake da ita, shin wai ma wace mai hure kunne kika haɗu ta hure miki kunne dan tana baƙinciki ko kuwa Amal ɗin ce ta hanaki dan tana ganin bata da irin waɗannan Alhzan?" Saurin juyawa ta yi ta kalli Amal da ke danne- danne a wayarta ba ta ma san me ake yi ba. "Ni fa babu wanda ya hanani ni ce kawai na ga hanyar ba ta da ƙofar da za a bi a ɓulle shi yasa na fasa ... "Shin yau shaye-shaye kika yi Iftihal? Ni kike faɗawa wannan maganar?" "Aunty abin nan fa ba na zafi bane, kawai dai ni yau na duba lamarin nan ne na ga babu wani alfanu a ciki sai ɓata tarihin rayuwa yanzu na gane babu wani abu da ya dace da ƴa mace sai ɗakin mijinta, ga uwa uba neman ilimi da ni ko cikin cokali ban samu ba shin ni a haka rayuwata za ta dawwama? Shin ni haka zan zauna cikin jahilci babu arabi babu boko? Sai dai in bayar da kaina a biyani kuɗi na zama kamar wata motar haya sai dai a hau a biyani? Shin bakya jin ciwo a kan halin da nake ciki ko kuwa bakya hango mana da na sani a gaba, ko kuma bakya tunanin maganin hana ɗaukan cikin da nake sha wataran Allah zai iya jarabta ta da samun ciki shin idan cikin yaƙi zubuwa na haihu ya kike so na yi? Haka yaron zai tashi babu wani tsayayyen uba, babu wani kyakkyawan tarihi a rayuwarsa da tawa baki ɗaya mai zan cewa yaron?" Amal da ke kwance ba ta san lokacin da ta tashi zaune ba, ta ajiye wayarta ta maida hankalinta kwacakwam kan Iftihal da ke wasu maganganu da ta kasa gane inda ta samo su, duk da ba ta jin mai ake faɗawa Iftihal ɗin amma tana jin mai Iftihal ɗin ke faɗa, maganganu masu ɗinbin kyau da dacewa maganganun da ya dace a ce fala musu su ake ba wai Iftihal ɗin ke faɗa ba, ba komai ya fi tafiya da gabaɗayan hankalinta ba sai kukan da Iftihal ɗin ke yi yayin da take maganar waya, a hankali ta ƙaraso kusa da ita ta miƙa hannu ta dafa kafaɗar Iftihal ɗin tana jin tausayin su ita da Iftihal ɗin dan yadda rayuwar Iftihal ɗin ke dabaibaye da tarin ƙalubale da aikin da na sani haka ita ma tata rayuwar ke a ƙudundune babu komai sai abin Allah wadai. Aunty kwa da ke ƙoƙarin haɗo kalmomi da haruffan da za ta yi amfani da su wajen shawo kan Iftihal ɗin dan gabaɗaya ta ma rasa ta inda za ta fara, ta rasa mai za ta faɗa wanda zai jawo hankalin Iftihal ɗin kar ta ɗora zargi a kan ta a matsayinta na mahaifiyarta, gabaɗaya zufa ta gama wanketa sai wani zazzare idanu take tana wani kame-kame take. "Aunty ki bani amsoshin tambayoyina" "Uhmm haba Iftihal kinsan dai ai ba zan taɓa sanyaki a hanyar da babu wata mafita ko kuma hanyar da za ki cutu ko ki samu kan ki cikin halin da na sani, kar fa ki manta ni mahaifiyarki ce ba zan taɓa son wani abu da zai cuceki ba bare har... "Wato yanzu wannan soyayya ce?" "Ina zuwa bari in shiga bayi" Aunty ta faɗa cikin rawar murya dan ta san bata da amsar tambayoyin da Iftihal ke mata idan kuma suka cigaba da magana to tabbas za ta ƙureta ta yadda ma ba za ta samu bakin magana ba, tana gama faɗar hakan ta kashe wayar da sauri. Kallon wayar kawai Iftihal ke yi hawaye na kwaranya daga idanunta, dan ta san da gangan Auntyn ta kashe wayar dan ko amsarta ba ta jira ba a kan neman uzurin shiga bayin da ta yi na ƙarya.Ajiye wayar ta yi jikinta sanyi ƙalau, ta juya ta kalli Amal da ke dafe da kafaɗarta wacce ita ma tuni hawayen sun wanke mata tata fuskar. Rungume juna suka yi suna kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro.Sai da suka yi kukan su suka ƙoshi sannan Iftihal ɗin ta ce su tashi su yi sallah, sallar da duk cikinsu babu wacce za ta iya tuna rabonta da ta yi sallah dan a taƙaice ma ba yin sallar suke ba. Haka suka yi alwala suka zo yin sallah abin takaicin duk su biyun babu wacce ta iya karatun sallar dan babu ilimi dan dama ba a san a je makaranta ba sai tsantsar jahilci.Bayan sun duddugura suka zauna suka yi shiru kamar daga sama sai ganin Mummy suka yi ta hankaɗo ƙofar kamar an jefota, tana shigowa ta maida ƙofar ta rufe ta tsaya tare da kama ƙugu ta ce "Wai dama Iftihal kin dawo gidan nan amma shi ne saboda tsabar kin raina ni shi ne baki neme ni ba, wato ni za ku rainawa wayo daga ke har uwar taki, shi ne kuka riƙe kuɗin ita ma ko kirana ba ta yi ba shi ne ke ma kika shigo ɗaki har da wani yin sallah da ban da munafurci sallah kuke? Ki tashi ki ɗakko nawa kuɗin ki bani kaso na" Tashi tsaye Iftihal ɗin ta yi ta cire mayafin doguwar rigar da ta sanya tare da doguwar rigar ta gabatar da sallah, ɗaurawa ta yi a kan ta ta tako har gaban Mummyn ta tsaya ta ce cikin ƙaraji da ɗaga murya. "Kowa kuɗi, maganarku ɗaya kuɗi, baku da magana sai ta kuɗi, shin ku bakwa tunanin yadda rayuwarmu za ta kasance ku dai burinku ku saku kuɗi" Baki sake Mummyn ke kallonta dan gabaɗaya kalaman yarinyar sun kusa sanyawa ta nuna rashin gaskiyarta a fili "Wace magana kike yi ne wai Iftihal?" "Ba kuɗi kika zo in baki ba wanda na samo a yawon karuwanci!" MMN AFRAH🥰😍❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️ 💕ALAƘAR YARINTA💞 ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️ NA MMN AFRAH FIRST CLASS WRITER'S ASSO... *Alhamdulillah godiya da yabo sun tabbata ga Allah maɗaukakin sarki da ya bani ikon sake zuwa da wani sabon littafina mai suna ALAƘAR YARINTA yadda na fara lafiya Allah sa na gama lafiya, Allah bani ikon rubuta abin da mutane za su amfana da shi amin* . Wannan littafi daga farkonsa har ƙarshensa sadaukarwa ne ga aminiyar ƙwarai Meenatu mmn muhibba Boy & sadiq , alkairin Allah ya kai muku a duk inda kuke Allah ya bar ƙauna tsakaninmu❤️ Page 4️⃣0️⃣&4️⃣1️⃣ *IFTIHAL* Suna fitowa ita da Alhajin daga Restuarant ɗin ta ja ta tsaya, shi kuma ganin tana wani shan ƙamshi tana haɗe rai sai duk ya ji ba daɗi, amma hakan bai sanya ya ji ko da haushinta ba shi dai kawai so yake buƙatarsa ta biya. "Kinsan fa wani abokina da ke zaune a nan ne ya sanya direbansa ya kawoni yanzu kuma sai dai mu shiga taxi mu je Hotel ɗin in kama mana ɗakin da za mu huta ko baby?" Ya faɗi hakan yana wani murmushi tare da washe haƙora sai wani lasar baki yake kamar wani tsohon maye.Ƙasa ta yi da glases ɗin nata ta masa kallon up nd down ta sauke idanunta a kan ƙaton tumbinsa tari guda kamar mai cikin wata tara, ɗauke kai ta yi gefe tare da maida glases ɗin nata yadda yake ta ɗago wayarta ta duba time. "No kar ma ki yi la'akari da wannan cuki ba wai tsufa bane ya sanya y yi girma hakan tsabar cin daɗi ne da kwanciyar hankali kinsan idan akwai kuɗi to mutum bashi da matsala sai wacce ba a rasa ba" "Ok ni ai ka san daga gidan talauci na fito" "Ba haka nake nufi ba baby, inaso na sanar da ke yau idan ki ka tashi tafiya za ki tafi da maƙudan kuɗaɗe wanda kowa sai ya san kin yi tarayya da wanda ke matashin kai da kuɗi" Ya faɗa yana washe baki. Jin ba ta ce komai ba ya sanya ya ƙara cewa "Mu je ko muna ɓata lokaci" Dan shi gabaɗaya wannan shan ƙamshin da take burgeshi take yi sabod yana son ya ga mace mai aji ya fi son hakan dan an fi daidaitawa da shi. Ita ta fara yin gaba, ganin ta nufi wajen wata mota da ke fake a wurin ya gane cewa da mota ta zo, hakan ya ƙara tabbatar masa da babban yarinya ce saboda har mota gareta ta kan ta.Suna isa ta sanya mukullin ta buɗe ta shiga wurin direba ta zauna sai dai ƙafafunta a waje suke, jakarta ta jefa kan ɗaya sit ɗin mai zaman banza, shi kuma cikin sauri ya nufi ɓangaren mai zaman banzan zai buɗe ya shiga sai washe haƙora yake kamar gonar auduga. Iftihal na ganin ya gewayo ta maida ƙafafunta cikin motar ta rufe ƙofar, gabaɗaya ta kulle motar Alhajin na kama ƙofar zai buɗe ya ji ta a kulle, ƙwanƙwasawa ya yi amma maimakon ta buɗe sai ta sauke glass ɗin ta sanya hannu ta yi ƙasa da glases ɗin fuskarta ta masa wani kallon ƙasƙanci ta ce "Malam ka bar min jikin mota tun kafin in tasheta in yi gaba in kuma yi reverse in kwasheka kuma na kwashe banza wallahi" "Haba baby wace irin magana kike haka? Idan ma wasa kike ki bari kar kisa ruwana ya hau, dan na gama ɗora rai a kan ki wallahi" "Za ka ga wasa da zarar na take ka, kuma sai dai hawan jininka ya tashi ba wai hawan ruwa ba" "Dan Allah ki buɗe in shigo mu tafi... "Kai na fasa zuwa ko ina da kai" Ta katse shi. "A haba dai haba baby ya zaki min haka" "Bani da lokacinka" Tana gama faɗar hakan ta ɗaga glass ɗin motar, ta mata key, Alhajin kuwa ya daddafe motar har sai da ya ji ta fara tafiya, ya ja baya ganin ta fisgeta da sauri ya tare taxi ya bi ya ce mai taxi ɗin ya bi bayan motar, tun suna bin bayansu har suka nemi inda motar ta yi suja rasa aikuwa Alhajin kamar ya cinye direban taxi ɗin sai masifa yake masa da turanci dan ba jin hausa yake ba daga chinanci sai ko turanci.Shi dai haƙuri yake bashi yana faɗa masa cinkoson motoci ne ya sanya motar ta ɓace masa, haka dai ya kaishi wani hotel ya yiwa wata waya dan ya rage zafi da ita saboda ɗora rai Allah sa mu fi ƙarfin zukatanmu. Iftihal kwa da ta lura da bin da su Alhajin ke mata dan dama tana ganinsa ta mudubi lokacin da ya tsare taxi ɗin, a haka ta yi ta yaudararsu har ta yanke ta wata hanya inda ta ɓacewa ganinsu.Gida ta nufa tana jin zuciyarta ba daɗi, tana yin parking ta nufi ɗakinsu ta shiga ta samu Amal zaune tana a kan gado tana waya jefa jakarta ta yi a kan gadon ta cire kayan jikinta ta ɗakko wata yaloluwar riga iyakar ƙwaurinta ta sanya ta kwanta rubda ciki ta jin ranta na mata wani zafi wanda ta kasa gane dalilin hakan dan ta rasa mai ke damunta, dan ita yau ɗaya kawai ji take duk ta tsani rayuwar da take yi, tun da ta gane saurayin da ta haɗu da shi a restuarant ya gane ta masa kama da wata a fuska amma ba a halayya ba kenan ita halayyarta marar kyau ce? Kenan ita ba dan kama da take masa da wata ba a fuska da bata da wani kyan hali da har zai sa a tunkareta, tabbas ta ji a yau tana sha'awar a ce ita ma wani zai iya yin abin da ta ga saurayin nan na yi a kan wata wato soyayyar gaskiya lallai hali mai kyau shi ne jigo a rayuwa shi kima da kuma martaba, amma ita mai ya sa babu wata hanya da aka nuna mata mai ɓullewa? Sai dai gurɓatacciyar hanya kuma matar da ita ce mahaifiyarta ita ya dace ta sanyata a hanya madaidaiciya amma kuma sai aka samu saɓanin hakan, shin ina mafita a ina amsar tambayarta take mai yasa Aunty ta zaɓa mata wannan rayuwar akan ta sanyata a hanyar da za ta zama abar kwatance kuma abar sha'awa ga kowa da kowa? Wasu hawaye ne suka shiga zubo mata, bayan hannunta ta sanya ta goge shin mai yasa bata taɓa jin ƙyamatar halayyarta ba sai yau ɗin nan? Mai yasa bata taɓa jin abin da take aikatawa ba dai dai bane sai yau ɗin nan tabbas an sanyata a a hanyar marar ɓullewa.Tana a haka har aka fara kiran sallar magriba. Wayarta ce da ke cikin jakarta ta shiga ringing amma har kiran ya katse bata ɗauka ba, Amal da ta kwanta bayan ta gama wayar da take ta juya mata baya tana chart ta ce "Wai malama bakya jin wayarki ta cikawa mutane kunne in ba za ki ɗauka ba ya kaɓata ki kashe dan ni ƙaran ya gundureni" Shiru ta mata bata tanka mata ba, mamaki ne ya cika Amal jin Iftihal ɗin bata ce komai dan ta san dai Iftihal ba ta taɓa barin ta kwana kana faɗa mata mafana za ta baka amsa dai dai da kai, amma kuma abin mamaki yanzu ta shareta.Juyowa ta yi dan ta tabbatar idonta biyu ko kuma bacci take, amma kuma mamakinta bai ƙaru ba sai da ta ga idanunta biyu buɗe. A dai dai nan wayar ta sake wanj wani ƙaran da alama wani kiran ne ya shigo bayan na farkon ya katse. "Iftihal ni kam ko dai baki da lafiya ne?" Amal ta jefa mata tambayar tana tsareta da ido dan ita bata ma lura da hawayen da ke ƙara kwaranyowa daga idanuna Iftihal ɗin ba.Baki ta taɓe ta juya ta yi kwanciyarta, ita kuma Iftihal ɗin jin ba a da niyyar daina kiran wayarta ta ne ya sanya ta tashi zaune dan kiran na katsewa wani ke shigowa kuma ta san babu mai mata wannan kiran a kai- a kai sai Auntyn ta dan samarinta da abokan hulɗarta kowa ya sani ba ta son damu dan in ka dameta da kira ma tana iya yanke alaƙa da kai saboda ita ƙa'idarta ce idan har ka mata kira ɗaya biyu ka ga bata ɗauka ba to ka bari idan ta ga dama za ta bi kiran. Cikin sanyin jiki ta tashi ta buɗe jakarta ta ɗakko wayar, tana shirin danna ok kiran ya katse sai ga wani koran ya shigo a take, kamar yadda tunanin nata ya bata kuwa Aunty ce tana kallon sunan sai da wasu hawaye masu zafi suka zubo mata.Ɗaukan kiran ta yi ta kai wayar kunnenta amma ba ta ce komai ba. "Iftihal haba ina kika shiga tun ɗazu sai kiranki nake amma shiru babu amsa, shi ma Alhajin na masa kira ya fi goma amma bai ɗauka ba daga ƙarshe ma wayar aka kashe, ko har yanzu baku baro Hotel ɗin bane kuna hutawa?" Wani takaici ne ya rufe gabaɗaya zuciyar Iftihal jin wai mahaifiyarta ce ke mata tambaya a kan cewa har yanzu tana Hotel tana hutawa tare da dadironta, shin mai yasa bata taɓa jin zafin tambayar nan ba sai tau tun da ba yau ne ta fara mata makamanciyar tambayar nan ba? Shin ita wace irin mahaifiya gareta shin anya kuwa Aunty ta cancanta ta zama uwa, duk da an ce mahaifiyarka ko mahaukaciya ce uwa ce a gareka amma maj yasa ita tata mahaifiyar na da hankali amma ba na tunani ba tun da duk wata uwa ta gari ba za ta so ta ga rayuwar ƴarta ta lalace ba, lallai kowacce uwa mahaifiya ce amma ba kowa ce mahaifiya ba ce ke zama uwa ta gari ga ƴaƴanta. "Wai Iftihal ya kika yi shiru ina ta sauraren ki fara min bayanin yawan kuɗaɗen da kika cafko mana a wurin Alhajin Allah, amma sai in ji kin yi shiru" Aunty ta katse mata tunanin. "Ni fa ba ma tare da shi" Ta bata amsa a taƙaice. "Allah sarki my Ifti ki ce har kin koma gida wato kun rabu da shi kowa ya kama gabansa, yo ai dama tun da kowa ya samu abin da yake so sai a raba garun, shi ya samu biyan buƙatarsa ke kuma kin samo mana kuɗi, wato kasuwa ta watse ɗan koli ya ci riba" Ta ƙarasa faɗa rana wata dariya. "Ni fa Aunty ba mu aiwatar da wani abu ba, dan ni ko Hotel ɗin ban je ba kawai dai na fasa yi... "Ke! Dakata dallah ya ina miki magana kina sako min wani zancen banza da wofi" Auntyn ta katseta cikin ƙaraji. Shiru Iftihal ɗin ta yi ba ta ce komai ba. "Wato duk yadda na shirya wannan haɗuwar taku sai da kika yi yadda kika yi kika ruguzata, wato duk irin yadda na so mu samu abin arziƙi mai tarin yawa sai da kika yi fatali da damar da kika samu, shin kin san waye wannan mutumin kin san irin tarin dukiyar da yake da ita, shin wai ma wace mai hure kunne kika haɗu ta hure miki kunne dan tana baƙinciki ko kuwa Amal ɗin ce ta hanaki dan tana ganin bata da irin waɗannan Alhzan?" Saurin juyawa ta yi ta kalli Amal da ke danne- danne a wayarta ba ta ma san me ake yi ba. "Ni fa babu wanda ya hanani ni ce kawai na ga hanyar ba ta da ƙofar da za a bi a ɓulle shi yasa na fasa ... "Shin yau shaye-shaye kika yi Iftihal? Ni kike faɗawa wannan maganar?" "Aunty abin nan fa ba na zafi bane, kawai dai ni yau na duba lamarin nan ne na ga babu wani alfanu a ciki sai ɓata tarihin rayuwa yanzu na gane babu wani abu da ya dace da ƴa mace sai ɗakin mijinta, ga uwa uba neman ilimi da ni ko cikin cokali ban samu ba shin ni a haka rayuwata za ta dawwama? Shin ni haka zan zauna cikin jahilci babu arabi babu boko? Sai dai in bayar da kaina a biyani kuɗi na zama kamar wata motar haya sai dai a hau a biyani? Shin bakya jin ciwo a kan halin da nake ciki ko kuwa bakya hango mana da na sani a gaba, ko kuma bakya tunanin maganin hana ɗaukan cikin da nake sha wataran Allah zai iya jarabta ta da samun ciki shin idan cikin yaƙi zubuwa na haihu ya kike so na yi? Haka yaron zai tashi babu wani tsayayyen uba, babu wani kyakkyawan tarihi a rayuwarsa da tawa baki ɗaya mai zan cewa yaron?" Amal da ke kwance ba ta san lokacin da ta tashi zaune ba, ta ajiye wayarta ta maida hankalinta kwacakwam kan Iftihal da ke wasu maganganu da ta kasa gane inda ta samo su, duk da ba ta jin mai ake faɗawa Iftihal ɗin amma tana jin mai Iftihal ɗin ke faɗa, maganganu masu ɗinbin kyau da dacewa maganganun da ya dace a ce fala musu su ake ba wai Iftihal ɗin ke faɗa ba, ba komai ya fi tafiya da gabaɗayan hankalinta ba sai kukan da Iftihal ɗin ke yi yayin da take maganar waya, a hankali ta ƙaraso kusa da ita ta miƙa hannu ta dafa kafaɗar Iftihal ɗin tana jin tausayin su ita da Iftihal ɗin dan yadda rayuwar Iftihal ɗin ke dabaibaye da tarin ƙalubale da aikin da na sani haka ita ma tata rayuwar ke a ƙudundune babu komai sai abin Allah wadai. Aunty kwa da ke ƙoƙarin haɗo kalmomi da haruffan da za ta yi amfani da su wajen shawo kan Iftihal ɗin dan gabaɗaya ta ma rasa ta inda za ta fara, ta rasa mai za ta faɗa wanda zai jawo hankalin Iftihal ɗin kar ta ɗora zargi a kan ta a matsayinta na mahaifiyarta, gabaɗaya zufa ta gama wanketa sai wani zazzare idanu take tana wani kame-kame take. "Aunty ki bani amsoshin tambayoyina" "Uhmm haba Iftihal kinsan dai ai ba zan taɓa sanyaki a hanyar da babu wata mafita ko kuma hanyar da za ki cutu ko ki samu kan ki cikin halin da na sani, kar fa ki manta ni mahaifiyarki ce ba zan taɓa son wani abu da zai cuceki ba bare har... "Wato yanzu wannan soyayya ce?" "Ina zuwa bari in shiga bayi" Aunty ta faɗa cikin rawar murya dan ta san bata da amsar tambayoyin da Iftihal ke mata idan kuma suka cigaba da magana to tabbas za ta ƙureta ta yadda ma ba za ta samu bakin magana ba, tana gama faɗar hakan ta kashe wayar da sauri. Kallon wayar kawai Iftihal ke yi hawaye na kwaranya daga idanunta, dan ta san da gangan Auntyn ta kashe wayar dan ko amsarta ba ta jira ba a kan neman uzurin shiga bayin da ta yi na ƙarya.Ajiye wayar ta yi jikinta sanyi ƙalau, ta juya ta kalli Amal da ke dafe da kafaɗarta wacce ita ma tuni hawayen sun wanke mata tata fuskar. Rungume juna suka yi suna kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro.Sai da suka yi kukan su suka ƙoshi sannan Iftihal ɗin ta ce su tashi su yi sallah, sallar da duk cikinsu babu wacce za ta iya tuna rabonta da ta yi sallah dan a taƙaice ma ba yin sallar suke ba. Haka suka yi alwala suka zo yin sallah abin takaicin duk su biyun babu wacce ta iya karatun sallar dan babu ilimi dan dama ba a san a je makaranta ba sai tsantsar jahilci.Bayan sun duddugura suka zauna suka yi shiru kamar daga sama sai ganin Mummy suka yi ta hankaɗo ƙofar kamar an jefota, tana shigowa ta maida ƙofar ta rufe ta tsaya tare da kama ƙugu ta ce "Wai dama Iftihal kin dawo gidan nan amma shi ne saboda tsabar kin raina ni shi ne baki neme ni ba, wato ni za ku rainawa wayo daga ke har uwar taki, shi ne kuka riƙe kuɗin ita ma ko kirana ba ta yi ba shi ne ke ma kika shigo ɗaki har da wani yin sallah da ban da munafurci sallah kuke? Ki tashi ki ɗakko nawa kuɗin ki bani kaso na" Tashi tsaye Iftihal ɗin ta yi ta cire mayafin doguwar rigar da ta sanya tare da doguwar rigar ta gabatar da sallah, ɗaurawa ta yi a kan ta ta tako har gaban Mummyn ta tsaya ta ce cikin ƙaraji da ɗaga murya. "Kowa kuɗi, maganarku ɗaya kuɗi, baku da magana sai ta kuɗi, shin ku bakwa tunanin yadda rayuwarmu za ta kasance ku dai burinku ku saku kuɗi" Baki sake Mummyn ke kallonta dan gabaɗaya kalaman yarinyar sun kusa sanyawa ta nuna rashin gaskiyarta a fili "Wace magana kike yi ne wai Iftihal?" "Ba kuɗi kika zo in baki ba wanda na samo a yawon karuwanci!" MMN AFRAH🥰😍 ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️ 💕ALAƘAR YARINTA💞 ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️ NA MMN AFRAH FIRST CLASS WRITER'S ASSO... *Alhamdulillah godiya da yabo sun tabbata ga Allah maɗaukakin sarki da ya bani ikon sake zuwa da wani sabon littafina mai suna ALAƘAR YARINTA yadda na fara lafiya Allah sa na gama lafiya, Allah bani ikon rubuta abin da mutane za su amfana da shi amin* . Wannan littafi daga farkonsa har ƙarshensa sadaukarwa ne ga aminiyar ƙwarai Meenatu mmn muhibba Boy & sadiq , alkairin Allah ya kai muku a duk inda kuke Allah ya bar ƙauna tsakaninmu❤️ Page4️⃣2️⃣&4️⃣3️⃣ *AUNTY* Bayan ta kashe wayar sanadin rashin makamar amsar da za ta baiwa Iftihal, da sauri ta kamo sunan Hajiya Suwaida hannunta sai karkarwa yake a hanzarce ta doka mata kira amma har ta katse ba ta ɗauka ba, wani kiran ta ƙara mata dan ji take kamar dai ta zama tsuntsuwa ta gan ta a gaban Hajiya Suwaida ta faɗa mata wannan gagarumar damuwar ko kuma gagarumar matsalar da ta tunkaro kai. Sai da kiran ya kusan katsewa sannan ta ɗaga tana washe baki dan ta ɗauka ko za ta tambayeta ne ta ga alert dan ta san wani lokacin ba ta fiye ganin alert ba idan kuɗi ya shigo accaunt ɗin ta sai dai idan ta yi chacking blance cikin farinciki ta ce "Hello ƙawata ƙawar arziƙi kin ma wuce ƙawa kin zama aminiya kuma ƴar uwa kin turo min... "Dan Allah ki ajiye waɗannan kalaman a gefe ki ji mai ke tafe da ni" Hajiya Hauwa ta faɗa cikin tashin hankali. Wani takaici ne ya cika Hajiya Suwaida jin abin da Hajiya Hauwa ta faɗa kuma da alama ma akwai mtsala dan ta ji muryarta wani iri kamar akwai damuwa. "Wallahi kar dai ki yi zaton akwai wasu kalamai da za ki yi amfani da su wajen yaudarata a kan maganar kuɗin nan, dan babu wani uzuri da zan miki dan na ga alama neman kike ki canja hali" "Wai mai kike son cewa na zo da magana hankalina a tashe ke kuma kina wani maganar kuɗi" "Wai ma dan dai kar ki yi zaton zan yarda da wata magana in dai ba dumus na ji ba, faɗa min abin da ke tafe da ke" "Akwai gagarumar matsala fa" "Matsalar me fa" Ta tambaya hankali kwance dan ita magana in har ba ta kuɗin nan ba kawai ba za ta ɗauki wani rainin hankali ba. "Iftihal fa ba ta haɗu da wannan Alhajin ba" "Hahaha lallai ma, ni za ki rainawa wayo kin manta ɗazu kika gama cewa suna tare" "Eh amma babu abin da ya shiga tsakaninsu suka rabu cewa ta yi ba za ta je Hotel ɗin ba, dan haka ma ko ƙwandala bai bata ba, ba ma hakan bane damuwata yarinyar nan da alama ta fara gane cewa ba a kan hanya mai kyau aka ɗorata ba dan idan da kin ji irin maganganun da take fala min wanda hakan ya sanya na kashe wayar sai kin mamaki har tuhumata take yi a kan hanyar da na ɗorata" "Wai Iftihal ɗin ce ta fara gane hakan har ta ƙi zuwa su keɓe a Hotel, to ƙawaye ta sake ne suka nuna mata hakan ko kuwa?" "Gaskiya ba na jin hakene tun da ko kafin ta koma gida da mu ka yi waya suna tare ko a muryarta babu wata alama da za ta nuna hakan, amma da na kirata ɗazu daƙer ma ta ɗauka sannan kuma da ta ɗauka babu wata magana mai daɗi" "To ko dai al'amarin ya lalace ne?" " Ni ma abin da ya tada min hankali kenan tunanina bai wuce ko asirin jikinta ne ya bar jikin nata ma'ana ya karye" "Tabɗi lallai akwai lauje cikin naɗi, tabbas da alamar hakan lallai sai an sake sabon shiri, gobe zan je wurin boka in ji bayani" "Yawwa ai gwara ki je ƙawata shi yasa na kiraki dan nasan ke kaɗai ce za ki min wannan abun" "Kar ki damu ki kwantar da hankalinki, dama na ɗauka kuɗin kike so ki haɗa da nawa ki riƙe shi yasa kike min hanya-hanya ashe ke babbar magana ce ta taso" "Ke dai bari ƙawata wannan maganar ma ai bai dace kike faɗa ba, dan ni mai haƙura da abu ne in bar miki" "Ni ma wasa nake miki" "Da sauƙi to" Haka dai suka yi sallama Hajiya Hauwa na jin ɗan dama-dama a zuciyarta ganin an samo mafita. *MOMMA* Labulayen ɗakin Suhaila ta shiga bubbuɗewa, ɗakin ya yi haske nan suka shiga bubbuɗe drawer ɗin na kayan jarirai suka fara da shi sai da suka fito da su gabaɗaya suka jibgesu kafin aka fito da gabaɗayan sauran aka ware kowanne a waje guda dan ba a haɗa su wuri ɗaya ba.Haka suka shiga juya jeren ɗakin komai suka canja masa mazauni sai da suka ga ɗakin ya yi yadda suke buƙata sannan suka shiga maida kayayyakin, duk abin nan da ake Momma sai share hawaye dan gabaɗaya raunin zuciyarta ya bayyana a tattare da ita. Bayan sun gama sanya kowanne a ma'ajjinsa sai Momma ta aika Suhaila ɗakinta ta ɗakko wasu kaya ɗinkakku a cikin wata ganamasgo ƙatuwa, tanankawo mata ta karɓa ta shiga fito da su sababbin ɗinkakkun shaddodi ne da yadika masu tsada aka yiwa ɗinki mai kyau da tsaro irin na zamani wanda ake yayi da huluna kowanne kalar kaya da hularsa da wata ƙaramar jaka a ciki mai agoguna da zobunan azurfa na matasa masu kyau, haka suka ware kowai suka shirya a wardrobe sai da komai ya yi dai dai sannan aka share ɗaikin tas duk da ba wani datti ya yi ba sannan aka yi moping ɗinsa aka feffesa freshners masu ƙamshi da ke danƙare a kan mirror ɗin ɗakin sai da ko'ina ya ɗauki ƙamshi sannan Momma ta yiwa Suhaila umarni da ta tafi haka Suhailar ta fita daga ɗakin ta rufo mata, bed sheet ɗin ta cire ta shimfiɗa wani mai kyau sai da ta gama sannan ta samu wuri ta zauna daga bakin gadon wani kuka ne mai cin rai ya sarƙeta, tana jin ina ma akwai mai ɗakin nan a cikin ɗakin da kuwa damuwarta ta kau har abadah. Sai da ta yi kukanta ya isheta har zuciyarta ta mata sanyi sannan ta tashi ta ɗauki bedsheet ɗin da ta cire ta fito da shi daga ɗakin domin a wanke shi, ta sanya mukulli ya ƙulle ƙofar. *GAGARAWA* *BAYAN KWANA UKU* A yau ne Baiwar Allah za ta gama shan maganinta na mantau dama oya kwanaki uku ne, da la'asar sakaliya ne Malam ɗin bayan ya tashi almajiransa daga makaranta ya shigo cikin gidan bayan ya ɗakko maganin Malam Zainab ta kirawo Baiwar Allah tana ɗaki tana ta faman linke kaya.Da sallama ta shiga ɗakin na Malam dan a can ɗakin suke dan dama Malama Zainab ɗin can ta ce mata ta je. "Wa alaikumus salam" Malama Zainab ta masa mata sallamar. Wuri ta samu ta zauna a kan tabarmar Malam ɗin na bakin yana tsiyaya maganin a kofi bayan ya haɗa ya miƙowa Malama Zainab ta miƙa mata da hannu biyu. "Kafin ki sha, bayan kin yi bismillah sai kin karanta ayatul kursiyyu da falaƙi da nasi, idan kin sha kuma sai ki karanta ƙulhuwallahu ƙafa ɗaya" Malam ya faɗa yana kallonta. "To" Ta amsa tare da fara karantawa cikin natsuwa tana gama karantawa ta shanye, sannan ta karanta suratul iklas ɗin, tana kaiwa ayar ƙarshe sai kuwa ta ji kan nata ya mata wani dumm ya yi nauyi kamar an ɗora mata dutsi a kan nata, da hannu biyu ta dafe kan jin yana barazanar rabe mata a biyu, Malam dai bakinsa bai yi shiru ba tun da ya ga yanayinta ya fara canjawa ya shiga karanto sunanyen Allah.Malama Zainab kuwa sai karanta duk abin da ya zo bakinta take, Baiwar Allah kwa tana dafe da kan nata ta fara zamewa hat sai da ta kwanta a wurin dafe da kan ta, sai jujjuyawa take idan ta juya nan gefen sai ta juya nan gefen. Ganin haka sai Malam ɗin ya taso ya dawo gabanta ya shiga karanto ayoyin qur'ani yana ta tofa mata. "Bana so! Ka daina ƙonani" Baiwar Allah ta faɗa da wata irin murya kai da ji ka san ba muryarta ba ce. Maimakon Malam ya dakata da karatun kamar yadda muryar ta faɗa sai ma ya cigaba. "Wayyo ka daina zan fita daga jikinta" Malam cigaba ya yi, aljanin kwa ya cigaba da ihu da kururuwa a kan a daina ƙonashi sai da Malam ya lura ya jigata sosai yadda duk umarnin da zai bashi ba zai yi musu ko gardama ba. "Mai ya zaunar da kai a jikinta ka sanya mata cutar mantau? Ni duk tunanina babu wani sihiri a jikinta ashe kai kana jiki ka maƙale" "Ba yin kaina bane aikoni aka yi, ba ma jikinta ita kaɗai ba ni na sanya musu mantau su biyar sama da shekaru goma sha wani abu, amma yanzu zan fita kuma za ta tuna komai da ta manta" "Saboda rashin imani ka rabota da kowa nata saboda ba za ta iya tuna su ba, su ma ka sanya ba za su iya tuna su ba" "Ka yi haƙuri yau zan fita yanzu ma kwa" "Zan ƙyaleka ka fita amma sai na sanya maka sharɗi" "Wallahi zan bi kowane sharaɗi" "Inaso ka fita daga jikinta kuma ko da wasa kar ka sake dawo wa , sannan si ma sauran ka sake su a yau ɗin nan idan ba haka ba wallahi sai na ƙonaka ƙurmus yadda ko gawayi sai ya fika kyan gani" "Na yi alƙawari zan bi dukkan sharuɗɗan, kuma su duka zan sake su, ko kanaso in faɗa maka wanda ya sanya aka aikoni jikinsu?" "Bana son jin komai daga gareka kun saba haɗa husuma to ni bana son jin komai koma wanene ya je dan kan sa Allah na ganinsa"Malam na gama faɗin haka ya cigaba da karatunsa, take Baiwar Allah ta shiga karkarwa kamar wata mai zazzaɓi tana wani abu kamar mai farfaɗiya, cikin lokaci ƙanƙani ta fara wata atishawa sai da ta yi sau uku sannan ta daina karkarwar da take, a hankali ta shiga buɗe idanunta da suka yi wani ja kamar wacce ta daɗe tana kuka, da kallo ta fara bin saman ɗakin da yake a kwancen take reran, haka ta dinga sauke idanunta a kan gabaɗaya ɗakin lafin daga bisani idanun nata suka sauka a kan Malama Zainab, sannan ta maida kallon nata kan Malam, fuska ta yatsina irin na ka ga wanda baka sani ba, kafin ta fara ƙoƙarin tashi daga kwancen da take tana musu kallon ban san ku ba, su waye ku. "Ina ne nan?" Ta jefa musu tambayar tana kalle-kalle tana musu kallon rashin sani. "Ki kwantar da hankalinki kina cikin kulawarmu ne kin jima a tare damu kusan shekaru uku" Malam ya faɗa yana kallonta. "Shekara uku kuma? A nan ɗin, ina Alhajina" Ta tambaya idanunta na kawo ƙwalla. "Ki yi haƙuri ba mu san kowa naki ba mun taimaka miki ne" Malama Zainab ta faɗa tana kama hannunta. Da sauri Baiwar Allah ta kalli cikinta tana zare ido ganin babu komai, tsaye ta miƙe a razane tana cewa "Ina cikin da ke jikina???" To ni ma dai jiran ta inda amsar za ta fito nake ku kasance tare da ni dan jin yadda za ta kaya. MMN AFRAH😍😘🥰 ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️ 💕ALAƘAR YARINTA💞 ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️ NA MMN AFRAH FIRST CLASS WRITER'S ASSO... *Alhamdulillah godiya da yabo sun tabbata ga Allah maɗaukakin sarki da ya bani ikon sake zuwa da wani sabon littafina mai suna ALAƘAR YARINTA yadda na fara lafiya Allah sa na gama lafiya, Allah bani ikon rubuta abin da mutane za su amfana da shi amin* . Wannan littafi daga farkonsa har ƙarshensa sadaukarwa ne ga aminiyar ƙwarai Meenatu mmn muhibba Boy & sadiq , alkairin Allah ya kai muku a duk inda kuke Allah ya bar ƙauna tsakaninmu❤️ Page 4️⃣4️⃣&4️⃣5️⃣ *DUTSE* *Hajiya Suwaida* Zaune take a part ɗin Alhaji a falon ƙasa tana danna waya, zaman jiran fitowar mai gidan nata take saboda ba ta son hawa saman dan ta san yanzu zai sakko, dan magriba ta gabato ta san kwa dab yake da sakkowa ya tafi masallaci idan an kira sallah.Sanye yake da farar jallabiya da hula a kansa sai carbi baƙi mai ƙyalƙyali, a hankali yake sakkowa daga matattakalar benen sai da ya zo tsakiya kawai sai ya ja ya tsaya jin ƙafafun nasa na riƙewa kamar an ɗaure masa su da hanzari ya dafe ƙarfen da ke gefen matakalar dan har jiri da ya ji ya ɗaukesa kan sa na juyawa tamkar zai cire bai san lokacin da ya zaune a wurin ba tare da dafe kan nasa da ke sara masa yana ambaton Allah. Hajiya Suwaida sai a lokacin hankalinta ya kai wajen dan bata ma san ya taho ba hankalinsa a kan wayarta tana karanta wasu saƙonni, ganin abin da ke fatuwa ta taso da saurinta ta nufoshi tana kiran sunansa dan ita gabaɗaya ta tsorata da yanayinsa. "Lafiya dai Alhaji" Ta faɗa lokacin da ta zo wurin nasa hankalinta a tashe. Bai ce da ita komai ba sai ƙara riƙe kan nasa yake, yana ta karanto addu'o'i ya jima a hakan zuwa can ya yi shiru kamar ruwa ya cinyeshi, Hajiya kwa sai bin sa da ido take hannayen nasa ya cire daga kan nasa sai kuma ya tsaya yana kallon Hajiya Suwaida kamar dai yau ya fara ganinta. "Alhaji sannu ka dawo dai dai?" Ta jefa masa tambayar tana miƙewa tsaye daga sunkuyon da ta yi a kan sa. Shiru ya yi bai yi magana ba, jim kaɗan sai ƙwaƙwalwarsa ta jefa masa wata tambaya. "Ina Ruƙayya???" A zabure ya tashi tsaye yana waige-waige kamar dai yana son ganjn wani. "Alhaji mai kake dubawa ne" Hajiya Suwaida ta jefa masa tambayar cike da son jin amsar da zai bata. "Ina Hajiya Ruƙayya?" Ta tsinkayi muryarsa a kunnuwanta ya jefo mata tambayar da ta sanyata rikicewa lokaci guda a maimakon ya bata amsar tambayarta. Idanu ta zaro jin wata tambaya mai rikitarwa da rikita lissafi, tambayar da ta kaɗa mata hanjin cikinta tambayar da ta ruɗata tare d sanyata cikin wani zulumi marar misaltuwa saboda ita rabon da ta ji wannan sunan ma a bakin Alhajin sama da shekaru goma sha wani abu amma yau gashi da bakinsa cikin hayyacinsa yana ambaton sunan Hajiya Ruƙayya tare da neman inda take. "Ina Afrah na ce miki amma kin tsaya kina wani abu da ban" Ya ƙara jefo mata tambayar da ta katse mata gabaɗaya saƙar zucin da take, tare da fara ƙoƙarin haɗo kalmomin da za ta bashi amsar tambayarsa saboda jin tambayar tasa cikin wani amon muryarsa wanda ya ɗauki shekaru aru-aru bai yi amfani da muryar ba. "Ban...gan...ta...ba" Ta faɗa muryarta na karkarwa hakan ne ya sanya maganar daddatsewa ta fito a ciccire. Wani kallo Alhajin ya mata kafin ya fara takawa cikin izza da sarauta da ta gama ratsa jijiyoyi da jinin jikinsa, da sauri Hajiya Suwaida ta sha gabansa duk da a mugun tsorace take tana cewa. "Alhaji ina zaka je ne? Ba ka ganin yanzu nan kan ka ke maka ciwo" Hannu ɗaya ya sanya ya maidata gefe guda, ya cigaba da sakkowa daga step ɗin yana gama sakkowa ya nufi ƙofar fita daga falon, Hajiya Suwaida cikin ruɗewa da fargaba ta biyo bayansa tana fatan Allah ya sa masallacinzai tafi duk da ta ji har lokacin ba a kira sallah ba.Cikin sanɗa take biye da shi tana son ta ga inda ya nufa, abin da ta gani ne ya sanya ta ji wata irin muguwar faɗuwar gaba wacce tafi wacce ta ji lokacin da ya ambaci sunan Ruƙayya (Afrah) ba komai ta hango ba wanda ya sa ta ji fitsari na bin ƙafafunta saboda ruɗewar da ta yi, Alhajin ba ko ina ya nufa ba illa part ɗin Hajiya Ruƙayya. Bugun zuciyarta ne ya ƙaru gabaɗaya yawun bakinta ya ƙafe, hatta numfashinta kokawa suke da ita saboda tsananin ruɗewa.Part ɗin sa ya zama tamkar maƙabarta saboda yadda ya koma tamkar wata bola. Daker take iya ɗaga ƙafafunta tana bin bayansa shi kuwa tafiya yake cikin marari da son ya ga ya ƙarasa part ɗin masoyiyar tasa domin ya yi tozali da ita. Tana zuwa dai dai wani ƙarfe da ke jikin wani bango hanyar da za ta sadaka da part ɗin Hajiya Ruƙayya ta kama ƙarfen ta tsaya saboda barazana da ƙafafun nata ke mata na kasa ɗaukarta da suke neman yi.Nan ta tsaya tana kallon yadda zaninta ya jiƙe da fitsari ta ma kasa sanin takamaiman tunanin da za ta yi bare har ta samu makamar abin yi, daga inda take tsaye tana hango shigar Alhajin part ɗin Hajiya Ruƙayya. Alhaji kwa na zuwa part ɗin tun daga waje ya fara ganin sauyi dangane da part ɗin, kamar dai babu alamar ana rayuwa a wurin.Cikin fargaba ya fara dosar ƙofar da za ta sadashi da falon farko da ke cikin part ɗin Hajiya Ruƙayya. Yadda ya ga ƙofar a rufe amma ba ruf ba ba a ƙarasa rufeta ba bare a yi tunanin an sanya mukulli, hannu ya sanya ya tura ƙofar amma ya ji ta ƙi buɗuwa alamu sun nuna ta daɗe a haka dan kamar ɓa ƙasa ta tokare bayan ƙofar. Sai da ya zage ƙarfinsa ya dinga tura ƙofar sannan ta buɗu, kallon falon yake da mamaki ganin irin tarin ƙurar da ke danƙare a falon hatta kayan kujerun da na kallon baka iya ganin komai sai ƙasa da ta baibayesu, kafet ɗin ma tamkar ƙasa ce a wurin dan ko alamarsa ba a gani, cikin ɗacin rai da fargaba ya sanya ƙafafunsa cikin falon hakanya shigo yana bin ko ina da kallo, ganin babu kowa sainkawai ya nufi upstairs da gudu ya hau faɗuwar gabansa na tsananta dan ba ya so ya je bai tarar da ita ba domin ba ya fatan hasashensa ya zama gaskiya, domin a iya tunaninsa ya kasa tuna rabon da ya sanya Ruƙayya a idanunsa, ya manta rabonsa da ita jiya ne ko kuwa yau ne? Yana hawa ya shiga bubbuɗe ɗakunan amma gabaɗaya babu kowa a ciki yana fitowa daga ƙofar ƙarshe ya durƙushe a wurin cikin ƙurar nan ya dage ƙarfinsa ya ce "Ruƙayya!!!" Gabaɗaya ɓangaren ya ɗauki amsa kuwwar muryarsa. Amon muryarsa ne ya doki kunnen Hajiya Suwaida da ke riƙe gam da ƙarfe tana ganin kamar idan ta saki ƙarfen faɗuwa za ta yi.Saboda yadda take a tsorace, tana cikin wannan ruɗanin ta tsinkayo takun tafiyar Alhajin, tana ɗago kanta ta hangoshi a firgici ya nufota, idanu ta fara zazzarewa tana ganin kamar ya gano cewa da sanya hannunta, kamar dai ya san ita ce ummul aba isin faruwar komai, tabbas idan har hasashenta ya zama gaskiya to yana ƙarasowa shaƙeta zai yi har lahira. "Ina kika kai min Ruƙayya???" Ya jefo ɓata tambayar tun kafin ya ƙaraso inda take ido ta ƙwara masa tana hango tsantsar tashin hankali a tare da shi da alama ma baya cikin hayyacinsa. MMN AFRAH😍🥰😘 ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️ 💕ALAƘAR YARINTA💞 ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️ NA MMN AFRAH FIRST CLASS WRITER'S ASSO... *Alhamdulillah godiya da yabo sun tabbata ga Allah maɗaukakin sarki da ya bani ikon sake zuwa da wani sabon littafina mai suna ALAƘAR YARINTA yadda na fara lafiya Allah sa na gama lafiya, Allah bani ikon rubuta abin da mutane za su amfana da shi amin* . Wannan littafi daga farkonsa har ƙarshensa sadaukarwa ne ga aminiyar ƙwarai Meenatu mmn muhibba Boy & sadiq , alkairin Allah ya kai muku a duk inda kuke Allah ya bar ƙauna tsakaninmu❤️ Page 4️⃣&6️⃣4️⃣7️⃣ *GIDAN HAKIMI ƊAN BURAN* Hajiya Sakina ce tsaye a dining area tana jera kayan abincin dare, ta gama jerawa tsaf tana ɗan goge kujerun dining ɗin, Mai gidan nata ne shi da Hafiz suka shigo cikin shirinsu na zuwa masallaci dan har an fara kiran sallah ma a wasu masallatan. "Ammi wai har abincin ya kammala" Cewar Hafiz yana dariya. "To acici ka dai bari ai ku dawo daga masallacin dai ko, kai ne sarkin ci" Ammi ta ce tana kallonsu da murmushi. "Barshi ya ci ai dan shi nake nemowa" Abban nasa ya faɗa cikin barkwanci. "Yawwa Abba ci dama ai ba laifi bane" Hafiz ya ce yana kallon Ammi. "Wato ma dan shi kake nemowa" Ammi ta ce tana kafe mai gidan nata da idanu. "Har da ke mana" Ya faɗa yana dariya ganin yadda ta yi dan ya ce dan Hafiz yake nemowa. "Ka ce fa, ai da dan shi kaɗai kake nemowa ni ma sai in daina dafa muku abincin in ga ko kwa ci abincin ɗanye" "Dafa abinci aiki ne dama" Ya faɗa ckn sigar zolaya. " Ba aiki bane bacci ne, shi yasa ma na ga baka iya cin abincin masu aiki" "To gaki mai zanyi da abinci wasu masu aiki, ai zaƙin hannunki kaɗai bai barin mutum ya ji ɗanɗanon abincin kowa sai... Kafin ya kai ƙarshen maganar sai kawai suka ga fuskarsa ta sauya, yana yatsina fuska sai kuma suka ga ya dafe kansa. Da sauri Ammi da Hafiz suka nufoshi, kafin su ƙaraso har ya durƙushe a wurin Hafi ma na zuwa sai kawai ya yanke jiki ya faɗai, wani ƙara Ammi ta fasa ganin su duka biyun sun shiga wani yanayi marar kyan gani dan a take ta fara tuniwa da yanayin da suka shiga lokacin naɗin da suka je a fadar Sarki da aka maido mata da su basa hayyacinsu.Ai ita ma bata gama tantancewa ba sai jin kan ta ta yi yana juyawa take ita ma ta kwance a wurin. Ƙaran da ta saki shi ne ya janyo hankalin ƴar aikinta da direban gidan da wani mai ban ruwan fulawa, dan koea ya ji ƙaran ya san ba na lafiya bane. A kusan tare suka shigo dan dama ɗabi'ar gidan ce masu aikin gidan tamkar ƴan gidan haka suke.Sun same su kowa dafe da kai sai dai kowa da abin da ke fitoww daga abakinsa na addu'a da ambaton sunayen Allah, wannan yanayi da suka samesu ya ɗaga musu hankali dan haka suke ta ƙoƙarin yadda za su tafi da su asibiti amma kuma ba a ɗau wani lokaci mai tsawo ba suka dawo hayyacinsu sai dai su duka daga farfaɗowarsu mutum ɗaya suke ambato wato Ruƙayya.. Daker Abban ya umarcisu da su gabatar da sallah kafin su tafi gidan Ruƙayyar dan su duka sun zaƙu su ganta dan sun kasa gane ko tuna rabon da su ganta, dan ko a waya basa son kiranta ita kawai suke son gani.Bayan sun idar da sallar dan a gida suka yi Abban ya ja su dan an fito daga masallaci lkcn, haka suka ɗunguma direba yana jan motar Hafiz a gaba Ammi da Abban a baya. Abba sai cewa direban yake ya yi sauri domin ganin ɗiyar tasa yake son yi ji yake kamar ya fi su Ammi da Hafiz ɗin son ganinta ma.Suna zuwa direban ya yi horn mai gadi da hankalinsa ke kan radio yana saurara ya ajiyeta a kan bencin nasa da sauri ya leƙa ganin motar gidan sirikin mai gidansa ya wangale musu get ɗin suka shigo yana ɗaga musu hannu.Ko gama parking direban bai yi ba suka fara buɗewa suna fitowa kowa hankalinsa na ga son ganinta. Hanyar part ɗinta suka nufa su duka, suna tahowa suka fara jiyo hayaniyar mai gidan yana ta amboton ina Ruƙayya.Mamaki da al'ajabi ne suka cika su jin su ma ita auka zo nema amma gashi nan shi ma yana nemanta to ina take? Kowa ya jefawa kansa tambayar a zuciyarsa.Tun kan su ƙaraso suka ashe da shi da matarsa Hajiya Suwaida ne, gabaɗaya fuskokinsu cike da tarin tambayoyi ganinsu yasa Alhaji Sagiru ya nufosu tun kan su ƙaraso yana tambayarsu ina Afrah??? "Mu ma wurinta maka zo" Abba ya faɗa yana kallon Alhaji sagirun.Dan dama abokai suke shi ne ya auri ɗiyarsa dan zumuncinsu ya cigaba da ɗorewa. "Ni da ina zan san inda take da zai sanyani a gaba yana cewa sai na nemota" Hajiya Suwaida da ee ta faman share hawaye take faɗa, dan zuciyarta kamar ta faso ƙirjinta ta fito saboda baƙinciki dan ita kukan daowarsu hayyacinsu take dan ganin dangin Ruƙayyar suna nemanta ya ƙara tabbatar mata da karyewar asirin, gashi so take ta keɓe ta yi waya dan ta kamata a ce ta fara shirin ɗaukan mataki tun kafin Ruƙayyar ta bayyana dan ta san ita ma duka inda take in har tana raye to ta dawo hayyacinta, gwara tun kafin ta jiƙa mata aiki ta sanya a ƙara matar da su kan su, su duka a ƙara nisanta tsakaninsu idan ma ta kama a kashe Ruƙayyar gabaɗaya. "Wai dama bata nan ne" Ammi ta jefa wa Hajiya Suwaida tambayar. "Da safe fa ta fita unguwa shi ne fa har yanzu bata dawo ba, ni kaina bansan ina ta tafi ba" Hajiya Suwaida ta faɗa cikin kissa da kisisina. Shiru kowa ya yi, Hafiz kwa sai hararar Hajiya Suwaida yake dan ya san bata ƙaunar ƴar uwarsa ko kaɗan dama bai zama lallai kishiya ta ƙaunaci kishiyarta ba kuma ma ba kowace mace ba ce za ta ce tana ƙaunar kishiya sai dai ana samun masu zama da kishiya tsakani da Allah ba cuta ba cutarwa sai dai ita Hajiya Suwaida tsanarta da ban take ƙiri-ƙiri take nuna tsanarta a fili dan ba zai manta ba duk da ba wani wayo ne da shi ba amma kuma tabbas ya san lokacin da take nunawa ƴar uwarsa tsana a fili har da shi ma idan ya zo wajen Aunty Afrah. "Ya aka yi kika san unguwa za ta je?" Hafiz ya jefa mata tambayar. Idanun mutanen ta faka ta jefa masa harara kafin ta bashi ams da cewa. "Na dai hangota ne za ta fita" "Amma yanayin yadda na ga part ɗinta babu alamar akwai wata halitta da ta rayu a yau a cikinsa dan ko a shekaru bana jin ɗan adam ya shig sashen , dan haka ya akayi bansan bata nan ba? Ya aka yi kuma kika ce yau ta fita da safe? Shin mai kike ɓoyewa dan nasan kin san komai dan haka ki faɗa min gaskiyar ina take, tunda iyayenta ma ba su san inda take ba, da alama su ma a yau suka nemi inda take kamar yadda ni ma a yau na nemeta, ki faɗi gaskiya idan ba haka ba kuwa in har na gano gaskiya na gane da sa hannunki sai na ɗaureki har igiya ta yi saura" Cewar Alhaji Sagiru yana nunata da yatsa. "Billahillazi huwar rahmanu bansan komai ba, wato ni kamar bani da kowa shi ne za a ce da sanya hannu na a ciki" Ta faɗa tana fashewa da kukan makirci. Ammi kwa sai share hawaye take jin wai sashen Rauƙayyar ma babu alamar ana rayuwa a ciki, kenan ƴarta ta ɓata ta yi ko kuma mutuwa ta yi ko kuma kasheta aka yi. "Hafiz kira min mai gadi" Alhaji Sagiru ya faɗa rai ɓace. D a sauri Hafiz ya juya tun kafin ya ƙarasa wurin mai gadin yake ƙwalla masa kira, mai gadi jin ana masa kiran mafarauta ya taso da sauri ya nufo Hafiz tun kan ya ƙaraso Hafiz ɗin ya juya ba tare da ya ce masa komai, bin bayansa ya yi cikin ruɗani dan sai yake ganin ko garin buɗe musu get ɗin ne ya yi laifi yana tsoron kar ya rasa aikinsa. Suna ƙarasowa Alhajin ya jefawa mai gadin tambaya. "Mai gadi yaushe Hajiya Ruƙayya ta bar gidan nan? Kai ne a bakin ƙofa dan haka nasan kasan duk mai shiga da mai fita a gidan na domin sanin hakan ya rataya a wuyanka, yaushe rabon da ka ganta yaushe ta fita da wane lokaci ta fita tau tsawon wane lokaci? Ido mai gadin ya fara rarrabawa jin duk tambayoyin nan shi ake jiran amsar su daga gareshi, ta ina zai fara bayanin wannan dan baya so shi ma ya shiga ciki mace mai tsohon ciki tana ɗauke da cikin hakimi kuma jikokin sarki sannan babanta hakimi ƴar gata gaba da baya amma matuƙar ya shiga cikin cakwakiyar nan babu mai fitar da shi sai Allah amma tabbas zai faɗi gaskiya ko dan karamcin matar a gareshi. "Ana tambayarka ka yiwa mutane shiru?" Abba ya faɗa yana kallon mai gadin ganin duk ya tsorata hakan na nuna masa akwai wani abu. Hajiya Suwaida kwa fakar idanunsu ta yi take yiwa mai gadin gargaɗi tare da nuna masa za ta bashi kuɗaɗe masu yawa in bai faɗi gaskiya ba dan ta san ya san lokacin da Ruƙayya ta bar gidan amma kuma ba zai taɓa ambata wani abu ba har sai an nemi hakan saboda wanda za su nemi sanin haka an mantar da su ba sa cikin hayyacinsu. Mai gadin kallon Hajiya Suwaida yake yana kuma bin fuskokin sauran mutanen da ke wurin yana tunanin mai ya dace ya faɗa gaskiya ko ƙarya? MMN AFRAH🥰😍😘