AJALI Marubucin littafin Shafi'u Dauda Giwa Ebook creat by Shuraih Usman Ebook publish by www.hausaebooks.cf Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.cf Kuna ziyartar shafinmu don samun sababbin littatafai Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com AJALI Na Shafi'u Dauda Giwa Typing by Shuraih Usman Post by shuraih 99% @shuraih 99% Page 1 . BABI NA FARKO . "A gaskiya Nazifi sai dai ka yi haquri da abinda zan fada maka ni dai shawarar da zan ba ka ita ce, ka yi haquri ka manta da al'amarin wannan yarinyar domin kuwa a gaskiya ba abokiyar tafiya ba ce" . Nazifi ya dubi abokin hirar tashi cikin mamaki da kaduwa, "Kamar yaya in yi haquri Jamilu, ban gane abinda kake nufi ba." Jamilu ya muskuta a kan dogon bencin da suke zaune, "Ka gane ko Nazifi, ba wai ina nufin yarinyar ba ta da kyawawan halaye ba ne, a'a tana da halaye nagari. To amma, ni dai halayen babanta nake hango maka Nazifi. Na san halin mutumin domin kuwa tunda ka yi mini kwatancen yarinyar, na fara zulumin ka yi zaben tumun dare." . Nazifi ya sake duban sa cikin rudani. "Haba Jamilu wannan wace irin magana ce? Yaya ma za a ce in ga yarinya jiya-jiyan nan, sannan kuma in ji ina son ta a raina, har mu gama tattaunawa mu yi alqawari ni da ita, amma kuma ina fada maka ka ce da ni in rabu da ita. Kai ma kanka ka san cewa wannan magana taka Jamilu ba mai amsuwa ba ce." . "Ba ina qoqarin raba ka da yarinyar ba ne Nazifi. Abinda nake qoqarin nuna maka a nan shi ne wannan yarinyar ba baquwa ba ce a wurina. Na san gidansu domin kuwa mun taba zama a unguwar. Hakan shi ya sa na fahimci cewar ba za ka iya jurewa da halayen mahaifinta ba." . Samarin biyu suka qurawa juna idanu. Nazifi ya ce da shi, " To ai ni ban gane matsalar da kake so ka nuna mini na rabuwa da ita din ba ne, kuma ka qi ka sanar da ko wane ne mahaifinta, domin kuwa ni gidansu kawai ta kwatanta mini ba ta fada mini sunan mahaifinta ba." . Jamilu ya dan saurara sannan ya ce da shi, "Mahaifinta ba wai voyayye ba ne, sunansa Alhaji Dage, wataqila ma dai ba za ka rasa jin labarinsa ba." "Ban san shi ba, Jamilu, to amma dai tunda ka sanar da ni a halin yanzu, ina ganin kana iya ba ni taqaitaccen bayani game da halayen nasa don in fahimci irin matsalolinsa da kake magana a kai." . Jamilu ya kai ganinsa dama da hagun harabar qofar gidan, ya tabbatar babu wanda yake sauraron hirar tasu, sannan ne to ya dawo da hankalinsa kan Nazifi, wanda ya yi fakare yana sauraronsa. . "Ka gafarce ni Nazifi, zan fada maka halayensa gaba daya. A gaskiya Alhaji Dage ba ya baiwa talaka auren `ya`yansa, domin kuwa ya aurar da `ya`yansa aqalla guda biyar, amma kuma na ji an ce duk a cikin wadannan `ya`yan nasa, babu wacce ta auri talaka irinka Nazifi. Kuma a wata majiyar ma an ce wai idan har ka auri 'yar gidan Alhaji Dage, dole ne ka riqa samar masa da albashi kowanne wata. Ka ga dai kai talaka ne Nazifi, don Allah ka yi wa kanka qiyamul laili, kada ka jawowa kanka abin tsiya kana zaune lafiya. Kawai ka mance da zancenta, ka nemi wata budurwar daidai qarfinka." . Nazifi ya yi shiru yana tunanin maganar, zuwa can sai ya ce, "Amma fa al'amarin nan ya daure min kai Jamilu, domin kuwa jiya a wurin fatin nan kada ka so ka ga yadda yarinyar nan ta manne mini, duk inda na nufa tana liqe da ni kamar cingam. Kuma har ma mun yi alqawari da ita cewar zan kai mata ziyara a yau din nan." . Jamilu ya fashe da dariya. "To daga haduwar fari kuma kawai sai ka tsaya kana damun kanka Nazifi? Sai ka ce za ta kai ka qara idan ka ce ka fasa yin soyayyar? Ni dai ka ji shawarar da zan ba ka. Idan ka dauka ta yi maka amfani. Idan kuma ka yi kunnen uwar shegu da wannan shawara tawa, to wannan kuma ya rage naka. Ni dai na fita haqqinka a matsayina na abokinka, tunda dai ka tambaye ni gaskiya na gaya maka." . Koda ya kammala sanar da shi sai ya juyar da fuskarsa wani bangaren don ba shi damar yin tunanin maganganun. . Nazifi ya yi tagumi yana tunanin wadannan maganganu na wannan aboki nasa Jamilu. Sannan ya sake dawo da farkon haduwarsu da yarinyar a daren jiya sanda ake fatin wani abokinsa. . Tana daya daga cikin manyan qawayen amarya. Tana sanye da shudin gwaggwaro. dan saurayin ya yafito ta tun daga nesa cikin qwarewa da sabo da kiran kyawawan 'yan mata a wurin fati na yau da kullum. . Kyakkyawar yarinyar ta taso daga cikin qawayenta ta same shi, suka dan kebe, sauran jama'a kowa nata harkarsa. "Idan ba za ki damu ba 'yan mata, zan so ki ba ni 'yan mintuna koda biyar ne haka, domin kuwa ina da wata 'yar magana da ke." . Yarinyar ta yi masa fari, ga alamar wayayyiya ce, ta ce "In ban da abinka malam, ka taba ganin wanda zai damu da sauraron baqon shi? Ba komai kai dai yi bayaninka ina sauraron ka." . Nazifi ya yi mata murmushin farin ciki. "Na yi farin ciki da kika nuna mini yarda kuma na ji dadi sasai da sakin fuskar da kika nuna mini." . Ya dan saurara sannan ya ci gaba da cewa da ita. "Ni dai sunana Nazifi kuma dan asalin garin nan ne ni, domin kuwa iyayena ma a nan aka haife su. A zahirin gaskiya ni ba wani mai wadata ba ne, domin kuwa sana'ar kafinta nake yi, a nan nake ci in sha, sannan kuma in yin wasu 'yan buqatuna. Wannan shi ne dan taqaitaccen tarihina da zan sanar da ke. Na fada miki ne don ki san ko ni wane ne kafin ki ba ni amsar tambayoyin da zan yi miki." . "Wacce tambaya ce Malam Nazifi?" Ya yi mata murmushi, "Mhm! Tambayar ba wata boyayyiya ba ce. Da ma so nake yi na ji ko kina so na, sannan kuma za ki iya aure na? Ni dai gaskiya ina masifar qaunar ki malama, domin kuwa ba ki lura ba ne tunda aka fara wannan fati ke nake ta kallo?" . Zan cigaba Abokai AJALI Marubuci Shafi'u Dauda Giwa Typing by Shuraih Usman Post by Shuraih 99% @shuraih 99% Page 2 . Ta yi dariya, "Na ji bayaninka Malam Nazifi kuma ina yi maka albishir da cewar ka sami karbuwa a zuciyata, domin kuwa ni kaina ina matuqar sha'awar namiji irinka mai ban dariya." . Suka tintsire da dariya a lokaci guda. "Kada kuma ki ziga ni mana, in riqa fasa kaina a wurin 'yan mata." "Ba maganar ziga Nazifi, gaskiya nake fada." Ya sunkuyar da kansa sannan ya ce da ita yana murmushi. . "Ban san iyakar godiyar da zan yi miki ba wallahi, ga shi kuma ban san sunanki ba." Ta dan yi farin cikin kissa, sanna ta ce da shi. . "Kada ka damu Nazifi, kana iya kira na da A'isha." "Mhm! sunan naki akwai dadi wallahi, da ma wata rana na tava mafarkin zan auri wata kyakkyawar mace mai suna A'isha." . Suka sake yin dariya, ta ce da shi. "Kai dai Malam ba ka rabo da abin dariya wallahi." Abu kamar wasa a cikin 'yan mintoci biyar din da suka yi suka saba da juna sai ka ce sun shekara biyar da fara soyayya. Bayan ta yi masa kwatancen gidansu, shi ma ya sanar da ita inda gidansu yake. Sai ya ce da ita. . "Ina fatan dai daga wannan bikin ba mun rabu kenan ba, A'isha?" Ta sake duban shi ta ce. "Ni dai a bangarena ba mu rabu ba, amma idan kai ma haka abin yake a zuciyarka, me zai hana kai ka fara kawo min ziyara don in tabbatar da gaske kake yi." . Nazifi ya ce da ita. "Yaushe to zan zo in same ki, A'isha?" Ta jefe shi da wani sabon murmushin. "Ko gobe ma kana iya zuwa Nazifi, kowanne lokaci ina nan a gida ba inda nake zuwa." "Ki saurare ni da yamma A'isha, in Allah ya so za ki ganni." . Ta sake cewa da shi. "Don Allah ka zo Nazifi, wallahi ka shiga raina. Ba na gajiya da sauraron maganarka, kamar kada mu rabu." Suka yi dariya cikin farin ciki . Wannnan shi ne mafarin wannan al'amari. Har aka tashi fatin ya koma gida, bai daina tunanin 'yar budurwar ba. Duk ya qosa gari ya waye don yamma ta yi ya je ya same ta. . To amma ko a cikin ranshi, dama ya yi alqawarin kafin ya je wurinta sai ya shaida wa abokin sana'arsa Jamilu. Domin kuwa har suka bar wurin fatin a daren jiya bai sanar da shi abinda ya wakana a tsakaninsa da yarinyar ba . Tunanin Nazifi ya katse a yayin da ya ji Jamilu ya girgiza kafadarshi. Ya dube shi cikin tsananin kidimewa. . "Wanne irin tunani ne wannan Nazifi? Daga na dan ba ka mintoci biyu ka yi nazari amma ka share wajen mintoci goma?" . Nazifi ya yi ajiyar zuciya, sannan ya ce da shi. "Wallahi tunaninta nake yi Jamilu." "Tunanin wacce kuma?" Jamilu ya tambaye shi. "Maganar me muke yi da kai, Jamilu? Tunanin masoyiyata A'isha mana, ko ka mance ne" . Jamilu ya dube shi cikin rudani. "Au Wai da ma duk shawarar da na ba ka, ba ka dauka ba Nazifi? Ai ni na yi tsammanin ka mance da al'amarin. Ni wallahi da na ga ka yi shiru na dauka tunanin wani abun kuma kake." . Nazifi ya kawar da kansa cikin wani yanayi mai kama da damuwa, sannan ya dubi abokinsa Jamilu. . "A gaskiya ba zan boye maka ba Jamilu, ba na jin zan iya rabuwa da A'isha, tunda dai tana so na. Na san dai duk tsiyar baban nata ba dai zai kashe ni ba don na ce ina son 'yarsa." ************* Ya fito daga cikin dakinsa, a lokacin da ya ji Burarin 'yarsa A'isha, riqe da jarida a hannunsa, sanye da qaton farin tabarau a kan ramammiyar fuskarsa. A daidai wannan lokaci ne mafadaciyar matar ta ci wa kyakkyawar yarinyar kwalar riga ta girgiza da Karfi, sannan ta daka mata tsawa. "Don ubanki wane ne saurayin da kika canza, fada min?" . Yarinyar ta sake fashewa da kuka, ta dora hannayenta bisa kanta. "Lallai A'isha kin zama 'yar iska, ni zaki dubi tsabar idanuna ki sanar da ni cewar wai ba kya son Gali, kin samu wani sabon saurayin To ki fada mini ko dan gidan uban wane ne a garin nan ko in ci ubanki." . Ta sake cukuikuyarta ta kayar da ita a kan lallausan kujerun da ke zagaye da tsararren falon. , "Ya isa haka nan." Tsamurarren mutumin ya fada a sanyaye. Babu alamar damuwa ko farin ciki a fuskarsa. To amma dai da ganin guru-gurun idanunsa da ke cikin faskeken tabaran ka san cewar ba a son ranshi matarsa take dukan 'yar tasa Kwallin kwal da ya fi kauna a duniya ba, duk da yake dai bai san laifin da yarinyar ta yi ba. . Matar tasa mai suna Juma ta dago kai ta dube shi tana numfashi sama-sama kamar ranta zai fita, kwata-kwata ba ma ta san lokacin da Alhaji Dage ya shigo falon ba, sai dai kawai maganarsa da ta ji. "Laifin me ta yi miki kuma Juma, kike yi mata irin wannan mahaukacin duka? Irin wannan in tsautsayi ya ratsa ai sai ki karya ta a banza." . Ta sakar mata wuyan riga, A'isha ta miqe tana sharbar kuka. Ta nufi dakinta da gudu-gudu. Alhaji Dage ya bi ta da kallo, duk da yake idan yana sanye da farin tabaronsa ba kasafai mutum zai iya karanto wani yanayi a fuskarsa ba, to amma dai a wannan karon duk da wannan uban tabaron da ya tsare harabar kusan ramammiyar fuskarsa gaba dayanta, hakan bai hana bayyanar da alamomin damuwa ba a kan fuskar tasa. . "Wai laifin me ta yi miki ne, iye?" Juma ta dube shi cikin tsananin damuwa. "Ba ka ji magana da muke ba ne da ita a lokacin da ka shigo?" "Ba wannan na tambaye ki ba. Ko na ji ko ban ji wannan ni ta shafa, ke dai ki fada mini abinda na tambaye ki." Mafadaciyar matar ta sake numfasawa, duk fuskarta ta yi sharkaf da zufa sai ka ce ta ci uban aiki. . "Wai Alhaji, wannan 'yar banzar yarinyar saura kwana takwas kenan fa a daura aurensu da Gali, shi ne don rashin albarka ta same ni har daki ta shaida mini cewar wai ba ta son shi, ta samu wano sabon saurayi wanda take so." . Alhaji Dage ya cire qaton tabaron cikin tsananin kaduwa da jin zancen matarsa Juma, saura qiris jaridar ta sullube daga hannunsa ta fadi qasa. Ya tambaye ta a tsorace. "Ta canza wani saurayi fa kika ce...? "Qwarai kuwa, idan kuma ka tababa sai in kira maka ita ka tambaye ta ta fada maka kai ma ka ji." . Ramammen mutumin ya ja doguwar ajiyar zuciya. Abu na farko da ya fara darsuwa a zuciyarsa shi ne, yanzu dai idan wannan 'ya tasa ta bijire har maganar auren nan ta lalace, a ina zai lalubo dubbban daruruwan kudin da suka cinye wa wannan saurayi da zai aure ta? wanda akalla ba akasara ba, in dai lissafi za a yi dalla-dalla to sun ci wa saurayin kudi ya kai miliyan guda, duk don kawai za su aurar masa da 'yarsu daya, sai kace 'yar zinare. Shi kuma da yake Allah ya jarrabe shi da son ta, haka nan yake ta bayarwa, tunda dai ya san in dai aka riga aka yi auren duk masifa dai kuma ba za a ce ya riqa ba da albashi duk wata ba. . "Amma fa wannan yarinyar tana neman dama mana lissafi, domin kuwa idan zancen auren nan ya lalace ban san yadda zan yi da wannan yaro ba." . Ya yi ta sambatu shi kadai matar tana tsaye tana kallon sa. . Abokai kuyi mani afuwa kwana biyu ina skul shi yasa kuka jini shiru Shuraih usman AJALI Na Shafi'u Dauda Giwa Typing by Shuraih Usman Post by shuraih 99% @shuraih 99% Page 3 . Duk da yake da ita ma irinsa ce, ba wai auki gare ta ba, to amma dai ta fi shi cika fuska, domin kuwa duk da tambarin da sunanshi ya yi a gari, wajen masifa da rashin hakuri, to idan ya dawo cikin gidansa kuma sai ya yi lagwaf kamar tsumma. . Domin kuwa matarsa Juma ta fi shi masifa nesa ba kusa ba. Kuma ko tsiyar tasu ta taso shi da ita, ba ya wani cin riba, don kuwa ta fi shi baki. Shi ya sa yake lallaba ta tunda dai ya san cewar jiya ba yau ba ce. . Da ace sanda yake da dukiya ne, kafin ya samu karayar arziki, ai itama ta san cewar ba abokiyar takawarsa ba ce. To amma tunda ta ga cewar dan abinda yake takamar ya kare, sai dai 'yan dabaru a gari, ita ma ta daina raga masa a cikin gida . "To wai a ina ma ta samu wani saurayin, kuma ma dan gidan wane ne a garin nan?" Alhaji Dage ya tambaye ta cikin karaya. . Juma ta turo baki a fusace ta ce da shi. "Ni fa ba ta fada mini ko wane ne ba. ta dai ce da ni ba za ta auri Gali ba. Kuma ni ina tsammanin duk yadda aka yi a wajen wannan tsinannen fatin bikin kawarta da ta je jiya, ta hadu da saurayin domin kuwa ba ta dawo nan gidan ba sai da talatanin dare." . Alhaji Dage ya warware jaridar ya soma fifita, domin kuwa a halin yanzu shi ma zufa- zufa yake ji. . "To in ban da abinki Juma me ya sa kike barin yarinyar nan tana zuwa wani fati? Kin san fa yanzu zamani ya canza. A wurin wannan fate-faten na alatsine, a nan 'yan mata suke lalacewa, su kangare a yi ta fama da su, ko kuma ma su je su kunsowa mutane abin kunya." . "To yanzu dai aikin gama ya gama." Juma ta ce da shi. "In dai kangarewar ne ita dai A'isha ta riga ta yi tunda har ta dube ni ido da ido ta ce a canza mijin aure, don haka yanzu ya rage namu mu nemi mafita, amma wannan cacar bakin da muke yi ba za ta fisshe mu ba." . Alhaji Dage ya sake jan doguwar zuciya, sannan ya ce da matar tasa. "Eh to ke ma a nan kin kawo shawara mai kyau Juma, domin kuwa ko da a ce al'amura sun lalace ita yarinyar ba ruwanta, mu za a tsare don haka lallai dabara ta rage tamu." . Ya sake numfasawa, zuwa can ya tattara hankalinsa wuri guda, ya ce da matar tasa a sanyaye. "Ina ganin abinda za mu yi shi ne mu zuba idanu mu ga sabon saurayin nan, babu mamaki yana da maiko-maiko. Idan zai iya ba mu naira miliyan guda mu biya Gali kudadensa da ya kashe, ina jin ai ba wata matsala ba ce, miliyan guda kawai zai ba mu sai a sallami Gali a daura auren da shi." ********** . Ta sami kimanin awa daya cur a kwance a dakinta, tana ta faman sharbar kuka ita kadai. Tunda take a duniya ba ta taba samun kanta a cikin matsanancin halin damuwa irin wannan ba. . (Shuraih 99% daga hausaebooks.cf) A'isha ta tsayar da kukan, ta mike ta zauna a kan gadonta, ta kurawa bangon dakin idanu, ko kiftawa ba ta yi. To amma a zahiri ba bangon dakin take nazari ba, hankalinta da kuma wani tunaninta kai gaba dayan zuciyarta ma ba ta kan komai sai a kan wannan dan saurayin da suka hadu a wurin fatin kawarta a daren jiya . Tun rabuwarsu bayan ta dawo gida, ta yanke shawarar ko dafa ta za a yi a tukunya ba za ta taba yarda a yi wannan aure nata da wannan saurayi mai suna Gali ba. . Domin kuwa har ga Allah matsa mata ake yi, amma ba ta kaunar sa ko miskala zarratin, to amma a yanzu tunda dai har Allah ya hada ta da Nazifi, to ta kwana gidan sauki. . A'isha ta dade da sanin wannan al'ada ta mahaifinta, domin kuwa ba akana ta ya fara yiwa `ya`yansa auren dole da, attajirai masu hannu da shuni ba. Duk yayyenta da aka aurar su kimanin biyar duk auran dole akayi musu, to amma ita lallai akwai alamar daga kanta za`ayita ta kare, . domin kuwa komai tsiya baza ta bada goyon baya ba, duk da yake kuwa ta san mahaifinta ya ciwa saurayin makudan kudi, duk kuwa da cewa saurayin nata Gali soja ne, da shi aka je kasar Saliyo. . Ita kanta wannan dukiyar da yake facaka ita, a dalilin wannan yaki ya same ta, domin kuwa an ce gwamnati ta basu miliyoyin kudi, wadansu kuma suna cewa daga can kasar ya samo wannan dukiya. To amma dai koma mene ne sanin kowa ne cewar saurayin ya samu kudi, , wadanda kuma ba su yi masa amfani wajen mallakar masa zuciyar `yar budurwa A`isha ba, domin kuwa ko da wurinta ya zo sai dai ya kari surutunsa shi kadai, amma ba za ta ce masa ci kanka ba . To amma kuma duk da wannan durama da suke yi wai a zahiri saura kwanaki kalilan a daura musu aurensu. A`isha ta share hawayen da ke gangarowa daga cikin idanunta, sannan ta yunkura gwuiwoyinta babu karfi . Ta sauka daga kan gadon, domin kuwa ta san cewar a kowane lokaci bayan yanzu, Nazifi zai iya zuwa ya same ta a cikin wannan hali. Don haka gara ta gaggauta ta kimtsa kafin ya zo. Nan da nan ta nufi bandaki, . ta yi wanka ta fito fes kamar babu wani abu da yake damun ta. Ta fiddo kayan kwalliyarta ta soma caba ado. Har kawo wannan lokaci zuciyarta ba ta daina tunanin masoyinta Nazifi ba. . Ta yi tunanin cewar duk don saboda ta ce tana kaunarsa aka lallasa mata shegen duka, ta yi wa kanta murmushi sannan ta ce a bayyane. "Ka da ki damu A`isha ba ki fadi kasa ba, in dai don soyayya za a yi miki wannan uban duka na kawo wuka. Ba ki fadi a banza ba A'isha, 'yar autar mata, soyayya ai ta fi gaban wasa." . Ta kammala shiryawa, ta dubi madubi, ta gamsu da abinda ta gani. Ta yi wa kanta murmushi domin kuwa ta san cewar wannan kwalliyar za ta biya kudin sabulu, tunda dai masoyinta na gaskiya ne zai ga kwalliyar. . Dadai a ce wannan wahalallen ne zai zo, to ba za ta tsaya bata lokacin inganta wata kwalliya ba. Domin kuwa ita da a ce ma akwai abinda za ta shafa, ko ta sanya a jiki, ya gani ya daina kaunar ta, to da tuni ma ta aikata sun rabu, don ta hutawa rayuwarta da wannan naci nasa. . Haryanzu dai kuna tare da Shuraih 99% cikin littafin AJALI na shafi'u dauda giwa Muje zuwa AJALI Na Shafi'u Dauda Giwa Typing by Shuraih Usman Post by shuraih 99% @shuraih 99% Page 4 . Tunda take ba ta taba ganin mutum da shegen nacin tsiya irin wannan saurayi da aka sa ranar bikinta da shi ba . Babu irin cin mutuncin da ba ta yi masa ba, amma kullum yana nan like da ita don tsabar masifar naci. . Don ma ta yi sa'a ne a halin yanzu ba ya nan,ya yi tafiya kafin ranar daurin aure ta zo Amma ba don haka ba da tuni har ya zo ya dame ta da surutun tsiya. . Tunanin A'isha ya yanke a yayin data ji sallamar wani karamin yaro, ta amsa sallamar yayin da yaron ya turo kofar dakin ya shigo . "Wani mutum ne ya ce in kira masa ke, yana can waje." A'isha ta ji gabanta ya fadi, ta ce da yaron. "Bai fada maka sunansa ba?" Yaron ya dan yi jim, sannan ya ce da ita. "Ya fada min, ya ce in fada maki Nazifi ne ke son ganin ki." A'isha ta rike numfashinta, ta yi murmushi sannan ta ce da yaron. "Don Allah ka je ka ce da shi ga ni nan zuwa yanzun nan." "To." Yaron ya fada cikin ladabi, ya fita. Ficewarsa ke da wuya ta bazama zuwa inda kayan sawanta suke, ta zabo wani uban leshi mai ruwan hoda, ta fara hanzarin sanyawa. . Duk Allah-Allah take yi ta je ta same shi, domin kuwa da tunaninsa ta kwana a zuciyarta . To sai dai kuma abinda 'yar budurwar ba ta sani ba shi ne ba ita kadai ce ke murna da zuwan saurayin ba, bayan ita hatta mahaifinta ma shi ma yana matukar murna da ganin saurayin, domin kuwa ya yi bakam a daki, . duk ya kosa su yi magana da sabon saurayin ya shaida masa kaulinsa na zunzurutun kudi naira miliyan daya, idan yana son a aurar masa da kyakkyawar A'isha. . BABI NA BIYU Ta fito daga cikin gida fuskarta wasai, sai sheki take yi, tana murmushin farin ciki. Kai da gani ka san cewar a boye, a bayan wannan kyakkyawar fuskar tata, akwai wani muhimmin albishir, wanda ga dukkan alamu kuma idan har ta furta shi daga bakinta, . To dole ne ma ya dadada wa wanda take shaidawa, tabbas zai dadada zuciyarsa. A'isha ta tsaya wuri guda, tana waige-waigen inda ya tsaya a cikin harabar gidan, wadda ke cike da shuke-shuke na alfarma da kuma tsirarun dawisu dake zirga-zirga nan da can $ jikinsu sai kyalkyali yake yi, a cikin dan abinda ya yi saura na hasken ranar da ke kokarin isa ga mafadarta. Duk da karayar arzikin da mahaifinta ya yi, da ganin dankareren gidansa, ka san cewar a wani zamani da ya wuce an yi tabara da naira. . Ba kasafai za ka samu wani mahaluki a harabar gidan ba, kullum wurin yana nan tsit kamar makabarta. Wani lokacin kuma idan Alhaji Dage ya bushi iska, yakan fito da kujera wajen harabar ya zauna ya yi ta karanta jarida. Mafi yawan lokuta samarin unguwar suna bakin ciki da wannan al'ada tasa, ta zama a waje, domin yana matukar takura masu wajen ganawa da 'yar kyakkyawar yarinya A'isha. . Bayan A'isha ta gama waigen kowanne bangare na harabar, sai ta hango Nazifi a can rakabe a jikin wata bishiyar dorawar turawa da ke kusa da babbar kofar shigowa cikin gidan. Yana tsaye a jikin bishiyar, ya jingine akwalar kekensa a gefe guda. Hannayensa a harde a kan kirjinsa, ya sako wani farin yadi boyel, wanda ya dan fara zazzagawa . A'isha ta isa gare shi tana murmushi. Tun daga nesa da ya hango ta shi ma yake murmushi, har ta kawo inda yake. "Wallahi har na cire tsammanin zuwanka, Nazifi." . Soyayya da dadi jama'a Saide daga karshe....... Its shuraih 99% AJALI Na Shafi'u Dauda Giwa Typing by Shuraih Usman Post by shuraih 99% @shuraih 99% Page 5 . "Wallahi har na cire tsammanin zuwanka, Nazifi." Ya ci gaba da murmushi, ya ce da ita. "Haba A'isha, ai ke ma kin san cewar tunda dai har na daukar maki alkawarin cewar zan zo, ai ba zan karya ba." . Suka sake yi wa juna wadansu sabbin murmushi. "Gaskiya na ji dadi wallahi Nazifi, ka san yadda soyayyar ta koma yanzu. Wani lokacin sai ka ga an kulla alkawura sama da dari, amma da wahala ka ga an cika ko da goma ne a cikin darin. Kai dai ka san cewar da a ce yadda ake kulla alkawarin soyayya a duniyar nan, haka ake cikawa, to da yanzu babu sauran wani mutum wanda ba shi da masoyinsa." . Nazifi ya yi dariya. "Duk da haka dai A'isha, ai dole ne a samu nagari, kin san ba zai yiwu a ce duk an zama daya ba, duk da lalacewar da soyayya ta yi za a samu mutane nagari da ke cika alkawarinsu." "To za ki fara ke ma ko...?" Ta yi dariya. "Ba haka ba ne, wannan ai gaskiya ce Nazifi, domin kuwa ba wani zolaya don ka fadi halayen masoyinka nagari." . Suka sake tuntsirewa da dariya a lokaci guda. Nazifi ya fara cewa bayan sun gama dariyar. "A'isha akwai abun da ke tattare da zuciyata, wanda duk na kosa da ma in zo in amayar maki da shi. Wallahi A'isha jiya ban yi wani barcin kirki ba, domin kuwa ina komawa gida, tunaninki ya dabaibaye mini zuciya, sannan kuma ko da na samu damar yin barcin, mafarkinki ne ya buwayi kyakkyawan barcin nawa. Don haka nake so idan ba za ki damu ba, ina son mu yi maganar aure in dai har da gaske ne kina so na." . A'isha ta yi ajiyar zuciya sannan ta ce da Nazifi, "Na ji duk bayaninka Nazifi kuma na matukar farin ciki, to amma ina son ka yarda har zuciyarka. Nazifi wallahi ni ma duk duniyar nan babu wanda nake so sai kai. To amma da akwai wata 'yar matsala guda daya da ke tattare da ni. Ina son idan na fada maka kada ka karaya, domin kuwa wannan matsala ba za ta hana mu gudanar da soyayyarmu ba. Ta dan saurara sannan ta ce da shi. . "Nazifi saura kwana takwas kenan a daura aurena." Saurayin ya rike numfashinsa cikin kaduwa, sannan ya dafe kirjinsa, "Aurenki!! A'isha...ban fahimce ki ba." . Ta girgiza kanta "kwarai kuwa aurena Nazifi. To amma ina son ka sha kuruminka, domin kuwa ni da ma ba na son saurayin da za a daura mana aure da shi, kawai mahaifina ne ya takura min a kan al'amarin. To amma a halin yanzu, tunda har Allah ya hada soyayyarmu da kai, wannan zancen aure babu shi, ya lalace, in Allah ya so kai ne mijina Nazifi." . Nazifi ya yi ajiyar zuciya sannan ya ce da ita. "To amma kuma iyayenki kuma fa A'isha, kina jin za su amince?" "Sun riga sun san komai Nazifi, domin kuwa na fadawa mahaifiyata gaskiyar abinda ke zuciyata, to amma ban samu goyon baya ba. Domin kuwa a dalilin na ce ina kaunar ka Nazifi sai da ta lakada min dukan tsaiya, da kyar mahaifina ya yi mata magana ta rabu da ni." . Suka kurawa juna idanu cikin jimami. Nazifi ya ce "To amma kuma A'isha kina jin al'amarin nan zai yiwu? Tun yanzun fa kenan har kin fara fuskantar matsaloli, to ina kuma a ce tafiya ta yi nisa a tsakanina da ke?" "Me zai hana al'amarin yiwuwa Nazifi?" A'isha ta ce da shi. . "Ni dai na daukar maka alkawari, duk rigimar da za a yi ba zan amince a daura mini aure da wannan wahalallen ba, don haka na riga na gama tunanin komai a halin yanzu, kai kawai nake jira, don in ji ta bakinka. In kana jin za ka iya jurewa, kamar yadda ni ma zan jure, komai wahala mu rike juna." . Nazifi ya sake yin doguwar ajiyar zuciya, sannna ya ce da ita, "Kada ki damu A'isha, na daukar maki alkawari, komai wahala ni ma ina nan tare da ke, sai dai mutuwa za raba mu." . A daidai wannan lokacin ne da suke ta wannan doguwar hirar tasu ta masoya, kamar an jeho shi, sai Alhaji Dage ya fito daga cikin gida. Tun dazu yake zaman jira, yana tsammanin jin sautin dankareriyar mota ta yi fakin a kofar gidan, domin kuwa shi har yanzu tsammani yake yi, sabon saurayin da A'isha ta ce ta sake, wani hamshakin attajiri ne wanda ya rude ta da zunzurutun kudi. Fitowarsa ke da wuya, ya kai ganinsa inda A'isha ke tsaye tare da saurayin a gindin bishiyar. Alhaji Dage ya yi raunanannen murmushi da ya hango wanda ke tare da ita, domin kuwa ya dauka cewar masinjan masoyin 'yar tasa ne, ya zo fadawa 'yarsa A'isha cewar Alhajin ba zai samu zuwa ba. . Alhaji Dage ya nufi inda suke a tsaye. Ya hango tsohuwar akwalar keken saurayin a jingine da bishiyar, kamar dokin kara, nan da nan sai ya ji tausayin saurayin ya kama shi, domin kuwa yana matukar takaicin yadda attajirai da manyan ma'aikata ba sa kulawa da masinjojinsu, haka dai ya iske su suna cikin hirar . Nazifi ya rage tsawo ya gaishe da Alhaji Dage. Ya amsa cikin fara'a-fara'a akaici-takaici, kana ya ce da saurayin. "Allah sarki! Kai ya turo kenan, bai samu zuwa ba. In ka je ka ce da shi na yi zaman jiransa, domin ina son mu yi wata 'yar ganawa da shi a kan lamarin 'yata A'isha da ya ce yana so" . dan saurayin da 'yar budurwar suka kalli juna cikin tsananin mamaki. Ba su san me siririn mutumin yake nufi ba, to amma shi bai damu ba, sai ma ya ci gaba da zancensa kai- tsaye. "Idan ka gama fada mata sakon da ya aiko ka, don Allah ka yi saurin janye akwalar keken ka tafi malam, domin ina jin tsoron kada ka tsorata mini agwagi da dawisu da wannan tsohon keken mai shegen rakin tsiya." A'isha ta dubi mahaifinta cikin damuwa, ta ce da shi cike da kaduwa. . "Baba shi ne, ba aiko shi aka yi ba." "Ban fahimta ba, shi ne wa?" Ya zazzaro kwala-kwalan idanunsa da ke boye a cikin kwafcecen-tabaron. . A'isha ta ce da shi cikin ladabi. "Baba shi ne ai saurayin da nake so dama, shi ne masoyin nawa." Tuni jikinta ya soma kyarmar kaduwa. . Alhaji Dage ya kai hannu cikin razana, ya ciccibo katon tabaronsa kaya guda, ya rike a hannusa, ya kalli saurayin sama da kasa sannan ya ce a sanyaye. . "Lallai A'isha tubarkalla na ga saurayin, ya sunanka malam?" Nazifi ya sunkuyar da kansa kasa, domin kuwa ya tabbatar akwai matsala babba da ke shirin faruwa. To amma dai duk da haka, sai ya kokarta ya bude baki ya baiwa mutumin amsa. "Sunana Nazifi" Alhaji Dage ya dubi A'isha ya daka mata tsawa. "Shige cikin gida kafin in zo in same ki `yar banzar yarinya kawai" . A'isha ta juya cikin tsananin karaya, ta nufi cikin gidan. lokaci-lokaci ta kan waigo don ganin abin da zai wakana ga masoyinta. Nan da nan ta soma addu'ar Allah ya sa dai kada mafadacin baban nata ya buge shi, domin kuwa ta san shi wajen saurin hannu. . Wannan na daga cikin abin da ya sa shi yin kaurin suna a unguwar, domin kuwa ya sha marin samarin da ke zuwa wurin `ya`yansa, musamman ma idan a kasa mutum ya zo ba a mota ba . Shigewar A'isha ke da wuya, sai ya tattara hankalinsa gaba daya ya ce da dan saurayi Nazifi. "Ina son in yi maka gargadi na farko, kuma na karshe, wannan yarinya `yata ce, ni na haife ta, kuma saura kwana takwas kenan a daura aurenta, ka rufawa kanka asiri ka fita daga cikin harkokinta, domin kuwa A'isha a halin yanzu ko kai aka sayar ba za ka biya abinda za kai aurenta ba. Domin kuwa na san dai ba za ka kai naira miliyan guda ba, don haka kar ka jawo wa kanka bala'i dan saurayi." . Nazifi ya girgiza kai cikin gamsuwa bayan da ya ji mafadacin mutumin ya kai aya. Ya jawo akwalar kekensa cikin hanzari domin kuwa in ma tsautsayi ya ratsa ya ga alamar cewar jiki zai yi tsami, to ba zai bar akwalar keken a wurin ba, wacce ita kadai ya mallaka a duniya . Malam Nazifi abun tausayi Talakan masoyi ya hadu da ma kwadaicin siriki Its shuraih 99%AJALI Na Shafi'u Dauda Giwa Typing by Shuraih Usman Post by shuraih 99% @shuraih 99% Page 6 . Nazifi ya girgiza kai cikin gamsuwa bayan da ya ji mafadacin mutumin ya kai aya. Ya jawo akwalar kekensa cikin hanzari domin kuwa in ma tsautsayi ya ratsa ya ga alamar cewar jiki zai yi tsami, to ba zai bar akwalar keken a wurin ba, wacce ita kadai ya mallaka, a duniya. . Alhaji Dage ya sake cewa da shi a fusace,kafin ya tafi. "Ka rike a zuciyarka dan saurayi ba na magana biyu, haduwar mu da kai ta biyu babu dadin gani. Idan na sake ganin ko da inuwarka a nan gidan,kai ko sawunka na gani wallahi sai na aika polisteshan, an kulle min kai, shege beran masallaci." ________________________________ Wata dankareriyar mota mai tudun baya, ta garzayo a guje kamar kibiya, tana sheki a cikin hasken kwaleliyar ranar wacce ke ta faman gasa naman bil'adam. Jama'ar da ke zazzaune a bakin titin, suka bi motar da kallo, domin kuwa lokaci-lokaci sukan ga motar ta shigo cikin unguwar tasu, to amma kuma har yanzu babu wanda ya san takamaiman abin da ke kawo motar a kai- akai ba . Kamar kullum sai motar ta rage gudu sannan ta fara sigina, cikin abin da bai fi dakika biyar ba,har ta tsallako titi. . Saurayin da ke tuka motar ya daga musu hannu, wannan al'adarsa ce koda yaushe, da ma ya kan dago musu hannu in ya same su a zazzaune. Yawanci idan haka ta faru, su mutanen ba sa wani kula shi, ko a yanzun ma da ya dago hannu da kyar aka sami mutane uku da suka kula da shi, su ma kuma ba hannu suka daga masa ba, kai kawai suka gyada masa kamar kadangaru. . Me yiwuwa idan aka tona zuciyar mutanen unguwar watakila suna da gaskiya, domin kuwa tun ganin farko da suka yi wa saurayin ya shigo unguwarsu, duk da yake a cikin mota yake, ta gilashi suke hango shi, a matsayin suna kwararrun zauna gari-banza, sannan kuma masana akan ilimin sa-ido, sun fahimci cewar wannan saurayi duk inda ya fito ba mutumin kirki ba ne . Akwai wani mutum da ya taba cewa ma da ganin saurayin ya san cewar dan fashi da makami ne, shi yasa da zarar ya shigo unguwar suke hade masa fuska, kamar sun ga mutuwa. . Saurayin bai taba kula ta tasu ba, don kuwa ya san cewar wata rana ma ba za su sake ganinsa ba, neman aure ya jawo mishi shigowa wannan unguwar mai cike `yan sa-ido, dazarar an yi aure kuma ta kare . Saurayin ya yi murmushi da ya tuno cewa nan da kwanaki hudu za a daura auren sa da A'isha rabin ransa, Aisharsa da ya mace a kan kauna tsawon lokaci. . Ko da ya tsallaka titi sai ya shiga layin gidan su masoyiyarsa A'isha wacce yake ta faman ambatar sunanta sai kace mai bitar darasi. Ya ci gaba da murmushinsa sannan ya daki sintiyarin motar cikin farin ciki, . hakika komai yana da iyaka, ya ce a zuciyarsa. Ya dauki dogon lokaci yana nunawa A'isha soyayya, amma ta ki ta gane kullum sai dai kawai shi yake kidansa sannan kuma yake rawarsa, amma ita ba ma ta tasa ta ke ba. To amma dai yanzu ai wulakanci ya kare tunda dai ta kusa zama matarsa, ko da a ce ba ta kaunarsa, ai ya zame mata dole ne ta zauna da shi tunda dai ya saye iyayenta. . Saurayin ya ci gaba da murmushinsa na samun nasara, ya ce a zuciyarsa, "Hakika kudi suna da matukar amfani a rayuwa," domin ya san cewar da bai mallake su ba to da shi da A'isha kyakkyawa sai dai hange daga nesa. Da yawa daga cikin abokansa sun sha damun shi da surutai a kan wannan soyayya da ya ke yi wa A'isha domin kuwa ta sha ta kwabsa shi ko a gaban wanene ko da kuwa yana tare da abokansa ne . Akwai wani lokaci da wani abokinsa ya ce da shi. "Don Allah Gali ka rabu da yarinyar nan tun da dai ba ta kaunar ka, wai kai ina ma ka taba jin inda aka yi soyayyar dole ne? Ya kamata ka canza sheka haka nan, domin kuwa akwai `yan mata kyawawa a garin nan, ba A'isha ba ce kadai kyakkyawa" Gali ya yi murmushin ya ce da shi . "Abokina kada ka ga laifina don na likewa yarinyar nan, wani lokaci ni kaina nakan yi kokarin ganin cewar na cire son ta a zuciyata, don in huta wa rayuwata domin kuwa A'isha ta zame mini kamar maruru ko sartse a cikin zuciya, ba na minti daya a duniya ban yi tunaninta ba sannna kuma ba na iya daina son ta a zuciya ta." . Tun daga wannan rana mafi yawa daga cikin abokan Gali suka shafa masa lafiya, wadansu kuma suka ma bata da shi domin kuwa su a ganinsu ya ba da sojoji, ba haka aka san zuciyar soja ba. To amma kuma abin da ba su sani ba game da lamarin soyayya shi ne, ta kansa mutum ya makance ya dukufa akan son wani abu, wanda sauran jama'a ko da kudi aka hada su ba za su so wannan abu ba, . domin kuwa idan ba haka ba, babu abinda zai sa babban ba'askare a cikin sojoji, wanda ya shiga har kasashen turai, amma ya dishe da kaunar wata yarinya `yar cikin gida ba kirar waje ba, har kuma ta zo tana wulakanta shi, lallai abin dai kam akwai takaici. . Gali ya yi ajiyar zuciya da ya tuno walhalun da ya sha a baya na kaunar wannan yarinya A'isha, ya ce a bayyane cikin rada-rada. "Kin ba ni wahala A'isha amma ba komai na kusa ramawa" A daidai wannan lokaci ne ya karaso kofar gidan, ya yi fakin din dunkulalliyar motarsa mai tudun baya, ya fito yana sanye da dogayen kayan shudiyar shadda, dinkin ta- zarce, dogo ne kakkaura baki, yadda yake haka zuciyarsa take bakikkirin domin kuwa da ran mutum da na kiyashi duk daya suke a wurinsa. . Shekarunsa za su kai talatin da biyar koma fiye a duniya. Ya shiga zagayen gidan kai tsaye, ya tsaya a cikin harabar inda shuke- shuken alfarmar suke. Bai dade ba a wurin wata karamar yarinya ta shigo cikin gidan, ya tsayar da ita, ya ce da ita. . "Kice wa Ai'isha Gali yana jiran ta a waje" Ba a jima ba yarinyar ta fito ta ce da shi. "Ta ce tana zuwa" Ya zaro wazobiya sabuwa fil ya mikawa yarinyar. Ta amsa cikin doki ta fice a guje. . Gali ya yi ajiyar zuciya ya fara nazarin harabar gidan. dawisu da agwagin ruwa da suka fi komai ba shi sha'awa suna ta yawace- yawace, da kuma koke-koke abinsu. Ya yi mamakin yadda mahaifin A'isha rabin ransa ke matukar kulawa da wadannan halittu. Ba a jima ba A'isha ta fito. Tun daga nesa ta murtuke fuskarta da ta hango Gali tsaye kamar gunki . Ta ce a ranta "Wannan wahalallen banzan kuma yaushe ya dawo?" Ta karaso wurin da yake ta tsaya, ko sallama ba ta yi masa ba, ballantana kuma ta dube shi, to amma shi da yake ya saba da wannan dabi'a tata, bai damu ba sai kawai ya fara aikinsa na surutu. . "Ai'sha ya kamata yau dai rana daya ki saki fuskarki a gareni, domin kuwa ni da ke mun zama daya, kin ga fa yau saura kwanaki hudu kenan a daura mana aure . Bai kamata a ce mu yi aure kuma ya kasance ba wata kwakkwarar jituwa a tsakaninmu ba. A'isha ya kamata ki hakura haka nan, bakin alkalami ya riga ya bushe." . Ta juyo cikin izgili ta dube shi a yatsine ta ce da shi. "Kai da wacce kuma za a daura muku aure?" Gali ya dube ta cikin kaduwa. . Ku jira part 7 _________ Yan mata kudaina wulakanta samari Domin kuwa zai iya yiwuwa su zaku Aura Izan ya kasance Saurayin da ki ka wulakanta wajen neman aurenki ya zama mijinki sannan ki ka kamu da ciwon sonsa a yayin da shi kuma ya fara Rama wulakancin da ki ka masa . Mutane masu tsananin fushi, masu rike abu a zuciya, basa taba manta wulakanci . Wani mawaki yace = in aka furta so gareka sai kai na'am a zuciya karka zagi Kauna, = Masoyi yana da rana = Masoyi yana da Rana . Sai mun hadu gobe Its shuraih 99% AJALI Na Shafi'u Dauda Giwa Typing by Shuraih Usman Post by shuraih 99% @shuraih 99% Page 7 . "Kai da wacce kuma za a daura muku aure?" Gali ya dube ta cikin kaduwa. . "A'ah! ni da ke mana A'isha, ko ba ki gane ni ba ne? Ni ne Gali masoyinki." . A'isha ta yi murmushi, amma ko da ganin murmushin ka san cewar a boye a bayan sa akwai abubuwa marasa dadin ji bila'adadin. . "Wani lokacin ka kan ba ni mamaki Gal wai kai don Allah wanne irin mutum ne a duniyar nan? Ba tun yau ba na nuna maka a zahiri, na furta maka baki da baki ba na sonka, ba zan taba sonka ba kuma, to amma kai ka like mini. Yanzu kai saboda Allah har sha'awa kake yi ka auri matar da ba ta kaunarka a duniya?" . Saurayin ya yi ajiyar zuciya ya ce da ita cikin damuwa "A'isha kin dade kina wulakanta ni a lokacin da ni kuma nake ganiyar nuna miki tsantsar soyayya tagari. To amma kuma ke mene ne dalilin da za ki ce ba kya kauna ta? . Dole ne ma ki so ni A'isha, don kuwa babu dalilin da zaki ki so na. Me kike bukata ki mallaka a duniya wanda ba ni da shi? Ke kanki kin san cewar ina da abinda za ki so ni a duniya.." . Aisha ta tsayar da shi ta hanyar jifan shi da wani busashshen murmushi "Lallai ba ka da hankali Gali kuma ba ka san soyayya ba, tunda har ka iya bude baki ka ce wai kana da abin da zan so ka da shi dole . Na san cewar ba wani abu kake takama da shi ba face dukiyarka, to bari in fada maka ni ba dukiyarka ba ce a gaba na? Kai a haukanka shi kenan don kana da kudi dole ne mace ta soka wannan ba gaskiya ba ne ka sake tunani, domin kuwa kai ka mallaki kudi amma kuma ni ba na sonka. Ka ga kenan ashe ko wannan ma ya ishe ka darasi, don ka fahimci cewar kudi ba sa iya sayen soyayya." . Gali ya dubi `yar budurwar cikin harzuka, tunda suke ba ta taba kule shi irin wannan karon ba. Ya ce da ita a fusace "To ya isa hakan nan mu bar wannan zancen, yanzu mene ne shirye-shiryenki game da auren mu? Na san dai ba za ki rasa bukatar wani abu ba." . Tace da shi "Ina bukatar abubuwa da dama amma kuma ba wurinka ba. Ina da bukatar ne a wajen mijina da zan aura, ko ba ka san cewar wani zan aura ba ne Gali?" . Ya dube ta a tsorace "Wai me kike nufi ne? A'isha ni fa ban gane ba, duk kin ruda ni wallahi." . Ta ci gaba da murmushinta sannan ta ce da shi. "Abin da nake nufi shi ne saura kwanaki hudu a daura aurena da wani saurayi da nake kauna a zuciyata, amma ba kai ba." . Gali ya ce da ita cikin rudani. "To ai ni ma saura kwanaki hudu kenan mahaifinki ya daura aurenki da ni, kuma har ma na fara raba katin gaiyata, A'isha." . "Wannan matsalarka ce Gali, ni dai kasancewar ban taba cewa in kaunarka ba kuma ban taba amsar komai naka ba don haka idan an daura aure sai a kai maka wata amayar amma ba dai ni ba." . Tana gama furta kalaman sai ta juya ta shige gida tan kunkunai hade da yin tsaki. Saurayin ya bi ta da kallo har ta bace, maganganunta na ta faman amsa kuwa da kururuwa a kwakwalwarsa. Tuni har ya fara lissafo mutanen da ke bukatar a sai musu likkafani a cikin jerin wadanda zai aika barzahu, indai har ba a kai masa amaryarsa daki nan da kwanaki hudu masu zuwa ba _____________ BABI NA UKU . Ba kasafai Nazifi yake barcin rana ba, domin kuwa ko ba inda yake da bukatar zuwa, da wahala ka same shi a kwance da rana tsaka kai ko rashin lafiya yake yi bai cika kwanciya a daki da rana ba, . bar shi dai ya fito kofar gida ya zauna a dakali ya karanta mujallun fina- finai ko kuma littafan soyayya. To amma kuma sabanin wannan halayya tasa da aka san shi da ita shekara da shekaru, kwanaki biyu kenan Nazifi yana wuni a gida a kwance, ko lekowa waje ba ya yi . Mahaifiyarsa Tabawa ta yi iyakar kokarinta don ya fada mata dalilin canjin wannan halayya tasa amma kuma abin ya faskara, ya ki ya fada mata, sannan kuma babban abin da ya fi ba ta mamaki shi ne wai a cewarsa lafiyarsa kalau, ba inda ke yi masa ciwo. A cikin kwanakin biyun nan ko wurin sana'arsa ta kafinta bai leka ba, . wanda abu ne mai wahala ko ma kuwa menene dalilin a ce Nazifi ya ketare rana daya bai je wurin wannan sana'a tasa ba. To amma kuma abinda ya tsorata Tabawa shi ne, wani lokacin idan yana kwance yana barci idan ta leka dakinsa , sai taji yana ta sambatu a cikin barci, yana fadar sunan wata yarinya wai ita A'isha. Sannan kuma wani lokaci sai ta same shi yana ta murmushi . Ko da Tabawa ta lura da wannna bakon al'amari da ya sami danta Nazifi sai ta ce da shi a fusace a wuni na biyu . "Haba ai ni dama na san a rina ai ga irin ta nan kullum kwanan duniya yaron nan sai na yi fama da kai ka rika shan maganin miyagu da kuma na mutanen boye, amma taurin kan tsiyarku na `yan zamani ya hana ka Nazifi, ga shi nan ai ka yi gamo da aljana za ta sabautar da kai a banza." . Tun daga wannan lokaci Tabawa ta fara shirye-shiryen kaiwa bokanyarta ziyara, domin kuwa ta san cewar wannan aljana da ta cafi danta guda daya da take alfahari da shi a duniya, duk tsiyar aljanar in dai har ta kai ta wajen kwararriyar bokanyarta Iya mai dogari, to ko ba ta shirya ba sai ta fice daga jikin danta Nazifi . To amma kuma shi Nazifi ya san cewar ko sarakan bori na duniya ne suka taru a kan shi ba za su iya maganin wannan matsala tashi ba, domin kuwa duk kwarewarsu akan wannnan sana'a ba za su iya mallaka masa masoyiyarsa da ya kamu da ciwon so ba, wacce saura kwanaki biyu kacal a daura aurenta da wani saurayin can daban .... CIWON SO kenan ___________ MASOYA AKIYAYE Izan zaka so mutum to ka soshi daidai wa daida Haka nan yan mata kada ku dauki son duniya ku daurawa saurayi/budurwa, daga karshe kuma ku rasasu, rayuwarku ta fada cikin garari . Its shuraih 99% AJALI Na Shafi'u Dauda Giwa Typing by Shuraih Usman Post by shuraih 99% @shuraih 99% Page 8 . Kamar kullum a cikin kwanaki biyu yana kwance sai mahaifiyarsa ta shigo cikin dakin. Ya yi tsammanin zancen neman maganin ta zo yi masa, to amma sabanin haka sai ta ce da shi. . "Wata yarinya ce wai ta zo tana son ganin ka, shi ne na ce bari in zo in sanar da kai." . Nazifi ya mike zumbur cikin mamaki, domin kuwa inda haka nan ne banza sai a wuni ana fama da shi ba zai tashi ba, kai a cikin kwanaki biyun nan har lokacin sallah sai ya zo ya wuce yana kwance ba zai yi ba. . Amma yanzu daga jin an ce wata ta zo nemansa, duk da dai bai san ko wace ce ba, amma a can cikin zuciyarsa sai ya ji ya dokanta da ya fita din. . Ya tashi da sauri kamar ba shi ne ke wuni a nannade a gado ba, kamar wanda ake yiwa karin ruwa. Lallai dai sha'anin yaran zamani sai dai a bar su, Tabawa ta fada a zuciyarta, ita ma ta fice daga dakin. . Fitar sa ke da wuya ya cikaro da ita a tsakar gida tana sanye da atamfa shudiya da kuma dan fingilin gyale. Hakika zatonsa ya zama gaskiya domin kuwa wacce yake tsammani ce ya gani. Suka yiwa juna murmushi, Nazifi ne ya fara yi mata magana. . "A'isha da ma ashe ke ce...?" Ta jefe shi da murmushin Allah kashe ni don dadi, sannan ta ce da shi. "Kai da wa kake tsammani?" "Ban yi tsammanin ki ba, domin kuwa na dauka cewar tuni kin mance da ni A'isha." Ta sake jifan shi da wani murmushi. . "In ban da abinka Nazifi ka taba ganin inda mace ta mance da mijinta? Ko ba ka san cewar ni a matsayin mijina nake daukarka ba, ko ka mance da alkawarin da na daukar maka ne in dai ina da miji a duniya ai kai ne Nazifi." . Ya lumshe idanu don farin ciki, a zuciyarsa ya ce Allah ya sa haka ya zama gaskiya A'ishata, sannan ya ce da ita. . "Zo mu shiga daga ciki A'isha nan ba wurin da za mu tattauna matsalolinmu ba ne." Suka shiga cikin dakinsa, rufin kwano doron zabuwa amma kuma babu silin babu komai a ciki idan aka tsame dan tsurkun gadonsa na katako mai kama da makara da kuma wata kujera daya ita ma ta katako mai kafa uku da rabi. A'isha ta yi wa kujerar kallon nutsuwa kafin ta sami mazauni a kanta, domin kuwa tunda suka shigo cikin dakin ta dubi rubabbiyar kujerar ta fara zullumin cewar da wahala kujerar ta iya daukar nauyin mutum dukansa . To amma kuma cikin sa'a sai kuma ta dauke ta gaba daya, duk da yake dai takan nemi ta turgude a dalilin nakasar da ta yi na gutsurewar rabin kafa guda. Nazifi ya fada kan gadon katako . Da farko A'isha ta yi tsammanin gadon zai baje a kasa, to amma abin mamaki sai ta ga shi ma gadon taurin rai gare shi irin kujerar, bai yi komai ba sai dai burari da raki domin kuwa ko'ina a jikinsa ihu yake yi da zarar an motsa. . Saurayin da budurwar suka kalli juna cikin nutsuwa, Nazifi ya fara magana "A'isha ina fatan ba ki samu wata babbar matsala ba a wurin mahaifinki, domin kuwa ransa ya baci sosai a dalilin ganina da ya yi tare dake." . Ta ce da shi "Kai zan yiwa wannan tambayar ka riga ni Nazifi, domin kuwa tun rabuwarmu nake faman zullumin ina fatan bai doke ka ba Nazifi." Ya yi ajiyar zuciya. . "Bai doke ni ba amma kuma gara ma a ce duka na ya yi da abin da ya sanar da ni. Ya gargade ni kada in sake kusantar inda kike A'isha. Wannan kalami da ya yi ya sosa zuciyata, a dalilin haka ne na sami kaina a cikin wani hali mawuyaci. Tun wannan lokaci ban sake fita ko waje ba kullum ina nan a daki ina jimamin rabuwata da ke domin ni ban ma yi tsammanin zan sake ganin ki ba har abada, A'isha." . Ta yi murmushin karfin hali. "Duk wannan bai kamata a ce sun sa ka tsorata ba, domin ni kaina ya sha yi mini wannan barazanar, don haka ka kwantar da hankalinka Nazifi, aski ya riga ya zo gaban goshi." . Ya dube ta cikin rashin fahimta, "Kamar yaya ban gane ba?" Ta sake yin murmushin. "Abin da nake nufi shine wahalar mu ta zo karshe in dai ka shirya, kuma da gaske kana kauna ta har cikin zuciyarka kamar yadda ni ma nake kaunarka" Ta dan saurara sannan ta ce da shi a sanyaye. ''Nazifi ka shirya gobe mu je a daura mana aure.'' . Saurayin ya ji gabanshi ya fadi ras da kalaman suka dira a cikin dodon kunnen shi a bazata, kadan ya rage ya fado kasa don tsananin razana. . ''A`isha aure fa kika ce?'' Ta dube shi har cikin idanunsa ta ce da shi. ''Aure mana Nazifi ko ba ka shirya ba ne, dama yaudarata kawai kake son yi ban sani ba." . Saurayin ya dubi kwayoyin idanin `yar budurwar da ke zaune akan kujera ta sa shi a gaba, ya tabbatar lafiyar ta kalau ba tabin hankali ta samu ba, ya ce da ita cikin mamaki. . "A'isha kin taba ganin inda saurayi da budurwa kawai suka ware kansu suka aurar da kansu ba wasu shaidu ko waliyyai, sannan kuma ya za a yi a ce gobe-gobe ba wani shirye-shiryen komai." . `Yar budurwar ta ce da shi "Ni ba cewa na yi ka sayo min akwatuna ba, sadaki kawai nake so a wurinka, shi ma don ya zama dole ne, da ba zan bukaci komai a wurin ka ba kuma shi din ma sai abinda ka kawo ka ba ni. Malamin da zai daura mana aure da shaidu, kai ko ma mene ne ake bukata ba za mu sha wahalar samu ba. . Wannan alhakin ka ne ka nemo mana malami wanda zai daura mana aure cikin sirri daga mu sai mu sai shi. Daga nan kuma sai ka samar mana wurin zama na sirri . Duk wadannan abubuwan ne da ya kamata a ce ka shirya su a gobe domin kuwa idan abin ya wuce gobe, to mun rasa juna kenan har a bada." . Shiru bai ce da ita komai ba domin kuwa maganganun da take fada duk sun gama sa shi tsurewa. Zuwa can sai ya ce da ita cikin in- ina "To ai ni a gaskiya A'isha wallahi abin ne ya zo mini duk a kurarren lokaci, kuma bayan haka kin dai gani da idanunki wallahi ba wani wadata ne da ni ba kuma ba wata kwakkwarar sana'a nake yi ba. sannan...." , Ta katse shi cikin damuwa. . "Duk da haka dai na tabbatar a matsayinka na namiji indai har ka yi niyya duk wadannan abubuwan ba za su gagare ka ba, in dai har kana sona da gaske to bai ma kamata ka tsaya ka kawo mini wadanan matsalolin ba, kasancewar dai ko rance ka nema a wurin abokan sana'arka ba za ka rasa samu ba. Ba wasu kudin ba ne masu yawa za ka tanada ba Nazifi, sadaki kawai fa na ce ina bukata, daga nan kuma sai 'yan kudin da za a baiwa limamin da zai daura auren, don mu rufe bakinsa kada ya tona mana asiri. Haba Nazifi ka yi tunani fa ka gani, akwai wanda ya kashe miliyoyin kudi a kaina, amma na ce ba na kaunar shi sai kai Nazifi, amma kuma kana nema ka ba ni kunya, ka kware mini baya." . Ya yi saurin cewa da ita "Ba haka ba ne A'isha, ke kina ganin kamar ba na son al'amarin ne, wallahi ina so. To amma matsalolin da ke tattare da al'amarin nake hangowa. Idan fa muka yi auren nan a boye, muka nemi wurin zama dole ne a yi bincike don a gano inda kike a garin nan, kuma abin duniya ba ya boyuwa, dole ne asirin mu ya tonu wata rana, don aure ba abin wasa ba ne." . "To sai me don an gane daga baya in dai mun yi auren? Ai shi kenan, ka san dai duk duniyar nan idan an taru ba mai raba mu, tunda muna son juna. Kuma wai kai tsoron me ma kake ji? Sai ka ce ba namiji ba. Rigima wa ta kashe a duniya? Mu yi auren nan shi ne mai wahala, komai zai biyo baya ya ma biyo. Ni fa mace ce Nazifi amma har in ce na ji na gani a kan soyayyar mu, amma kai kana namiji ka tsaya kana fargaba. Ni wallahi ka fara ba ni kunya Nazifi." . Ta kura mishi idanu a yayin da ya yi shiru yana mis-mis da baki, yana kokarin fitar da tunani daya tsakanin amincewa da kuma sabanin haka, daga nan sai ta cigaba da ta ga bai ce komai ba. . "Idan kuma kana ganin ba zai yiwu ba, shi kenan ba matsala sai in tashi in yi tafiyata, ka nuna mini kenan da ma ba kauna ta kake yi ba, sai in je in rungumi kaddara in auri wancan saurayin da ba na kauna a zuciyata, wanda shi kuma yake sona kamar ya hadiye ni. Ba komai Nazifi, dama an ce son maso wani koshin wahala."Ta mike daga kan musakar kujerar da niyyar ficewa. Nazifi ya yi farat ya ce da ita, bakin sa na rawa. . "Ki gafarce ni A'isha, abin bai kai mu ga haka ba. In dai don wannan maganar ce kina bukatar komawa ki zauna, na amince zan yi duk abin da kika ce da ni. Ni dai a halin yanzu ko sisi ba ni da shi a aljihuna, to amma kuma tunda kin ce da ni rigima ba ta kashe uban kowa, to ni ma zan jarraba yin ta, don na san ba za ta kashe ni ba. Domin kuwa ba karamar rigima ba ce mutum ya tunkari aure awoyi ashirin da hudu masu zuwa sannan ya nemi gidan haya, da kuma kudaden limamin daurin aure duk kwana daya kacal, amma kuma bai tanadi ko ahu a aljihunsa ba, ke ma kin san wannan katuwar rigima ce, A'isha." . ___________ Tab malam Nazifi kwarankwasa maganarka dutse ce, Don da rigima na kisa, da wannan typing din bai zo gareku ba sakamakon rigimar dana jajibo ma kaina shekaran jiya, sai de dakyar na sha yayin da fuskata ta suntuma suntum, idanuwa na sukai luhu luhu, sakamakon dukan da na ci wajen ......... Kaga su o'o da o'o an kasa kunne don jin tsurku to na fasa bada labarin, its shuraih 99% . Part 9 is loading AJALI Na Shafi'u Dauda Giwa Typing by Shuraih Usman Post by shuraih 99% @shuraih 99% Page 9 . Washegarin ranar tun da sassafe misalin karfe bakwai, Nazifi ya fara zirga-zirga a cikin garin yana fafutukar nemo rancen isasssun kudin da zai rike , kafin nan da wadansu awoyi in dare ya yi, domin kuwa a yadda suka rabu da 'yar budurwar ta ce da daddare za ta zo ta same shi su wuce wurin daurin aure. . To amma kuma tun a jiya din bayan sun rabu yake ta faman cuku-cukun inda zai sami kudin da yake bukata, amma kuma shi dai a iyaka kokarin sa bai san inda zai samo wadannan kudi ba. . Sannan kuma bugu da kari ba shi da wata tsohuwar ajiya ko kuma wadansu kadarori ballantana ya daga su ya makar don ya sami kudaden da yake bukata. Ya san cewa in dai ba tsohon kekensa ba to da wahala ya sami wani abu da zai sayar, wanda kudinsa za su kai dubu daya, ko suturunsa ya daga ya sayar ya san cewar ba za su samar masa kudin ba. . Don haka ya kasance cikin rashin kwanciyar hankali ko wani barcin kirki bai yi ba. Duk mutanen da Nazifi yake tsammanin zai sami kudi a wurinsu, da kuma abokansa duk ya bi su daya bayan daya amma kuma Allah bai sa ya dace ba . Da rana ta take misalin karfe sha biyu sai Nazifi ya zauna a makarin wata kwalbti dake bakin titi, yana tunanin inda zai sake dosa kuma gashi lokaci kara kurewa yake yi. . Nazifi yayi ajiyar zuciya, sannan ya mayar da hankalin shi kan motocin da ke wucewa ta gabashi ya yiwa kansa murmushi, da ya yi tunanin cewar wai saura bai fi awoyi takwas masu zuwa ba ya zama ango, amma kuma babu ko ahu a aljihunsa, . gashi kuma wata azababbiyar yunwa ma yake ji, ko abin da zai sa a cikin shi bai mallaka ba amma kuma wai a yau ne zai tare da sabuwar amarya, wacce wani ya kashewa kusan miliyan guda don a mallake ta, lallai wannan shi ne daukar dala ba gammo. . To wai shin me zai sa ma in dami kaina ne? Nazifi ya tambayi kanshi lallai fa bai kamata ba ma ya tsaya yana damun kanshi, domin kuwa ita ta ce ta ji ta gani, ko ba shi da ko sisi, ya san cewar za ta san inda za ta samo masa kudaden tun da dai ta riga ta mutu akan kaunarsa. . Ya sake yiwa kansa murmushi sannan ya ce a bayyane. "Kada ka damu Nazifi, ko baka da ko sisi yau sai ka zama ango a duniyar nan, kuma sai ka tare a dakin kyakkyawar amarya, wacce farashinta ya zo daidai da naira miliyan..." . Bai gama tunanin ba ya ji dirar zukekiyar motar a gabanshi, ya dawo hayyacinsa cikin kaduwa a lokacin har gilashin motar ya sauka kasa , suka dubi juna shi da dogon saurayin dake cikin motar, shi kadai sanye da bakar kwat, yana murmushi. Da farko Nazifi bai gane shi ba, domin kuwa rabon da a ce sun hadu da wannan saurayi tun a makarantar sakandire, inda suka gama tare, to amma a halin yanzu ya kara girma da kiba da ba don tun a wancan lokaci sun shaku ba, to har ga Allah da Nazifi bai gane babban abokinsa Gali ba. . "Nazifi me kake yi a nan zaune, lafiya" Nazifi ya mike ya dafa tagar motar ya ce dashi cikin mamaki "Gali ashe dama kana duniyar nan" Saurayin ya yi dariya. . "Ina nan a raye Nazifi, ina nan a garin wallahi" Samarin biyu suka gaisa cikin farin ciki nan suka tuna da tsohuwar abotarsu tun suna makaranta. . "Wallahi Gali na cire tsammanin za mu sake haduwa, domin kuwa tun shekara da shekaru na neme ka har na gaji." Amma kuwa har yanzu tunanin awoyin da suka rage ta zo ta same shi ne zuciyarsa. Gali ya ce da Nazifi ya bude bangaren mai zaman banza ya zauna suka sake gaisawa da Gali babban aminisa. Gali ya ce da shi. . "Na san cewar dole ne ka yi mamakin bacewar da na yi shekara da shekaru Nazifi, ba na kasar ne domin kuwa tun bayan gama makaranta ni ban ci gaba da karatu ba, sai na shiga aikin soja, aka turani kudancin kasar nan, daga baya kuma da za a je sasanta rigimar kasar Saliyo aka diba har da ni. . Tun wancan tsawon lokacin muna can sai bara aka dawo da mu, shi ne na dawo gida a halin yanzu don in yi aure, domin kuwa wallahi abokina mun sami alheri sosai a dalilin wannan yaki da muka je." . Nazifi ya ce da shi cikin yake-yake, dariya- dariya. "Ai na ga alama wallahi mutumina ka sami hutu, mu muna nan har yanzu a rabe muna ta `yan buge-buge, amma ba wani canzawa kullum muna guri guda." . "Tun bayan gama makarantarmu me ka yi Nazifi?" Ya yi ajiyar zuciya sannan ya ce da shi. . "Ba na aikin komai Gali, kawai dai ina dan taba sana'ar kafinta wacce nake dan samun na batarwa a cikinta" . Gali ya dan nuna damuwarsa a fuska sannan ya ce da shi. . "Rayuwa kenan Nazifi sai hakuri, ka san cewar kowa rabon shi yake samu a duniya mutum bai wuce rabon shi Nazifi." . Nazifi ya yi murmushi a zuciyarsa yace "Ni kuwa na san haka tunda gashi ba ni da ko ahu amma zan auri kyakkyawa wacce wani miloniyan ke burin ya aura a duniya." . "Yanzu zaman me kake yi a nan kai kadai cikin rana, Nazifi?" Ya sake yin ajiyar zuciya, "Wallahi wannan zaman da ka ga na yi Gali ina cikin wata katuwar matsala ce wacce ta fi karfina." . Gali ya yi masa murmushi ya ce da shi. "Ni kuwa ban yi tsammani cewar a wannan halin da nake ciki har akwai wanda zai ce ya fi ni shiga matsala ba, matsalarka ba ta kai ko rabin wacce nake ciki ba" . Nazifi ya ce dashi. "Haka dai ka ce Gali amma da a ce za ka ji matsalata, kai da kanka za ka san cewar ta fi taka matsalar" fada min matsalar taka na ji ni kuma zan fada maka tawa matsalar." Nazifi ya kurawa gilashin motar idanu ko kiftawa ba ya yi sannan ya ce da abokin nasa . "A halin yanzun da ka ganni a nan Gali, yau ne za a daura aure na kuma a yau ne zan nemi gidan da za mu zauna ni da amarya, amma kuma ko sisin kwabo ba ni da shi a aljihuna . Ka san cewar ina cikin matsala maigirma, Gali" Gali ya tuntsire da dariya. . "To kai Nazifi ya aka yi ka daukowa kanka wannan rigimar, ka san cewa ba ka da ko sisi? sai ka ce za ka auro `yar tsana ba mutum ba?" . Nazifi ya dube shi sosai ya ce. "Wallahi rigima ce kawai Gali, bari ka ji yadda abin ya faru. Tun farko yarinyar ce ta like mini na rasa yadda zan yi da ita shi ne ta ba ni zabi ko dai in nemo kudi a daura auren a yau din nan ko kuma mu yi hannun riga ma'ana mu rabu , to ni kuma ina bala'in son yarinyar nan Gali, kullum tana raina, shi ne na yi mata karya zan nemi kudin amma har yanzu da ka same ni a nan ko kwabo bai zo hannuna ba, kuma anjima za a daura aurenda daddare" . Gali ya yi ajiyar zuciya sannan ya ce. "Eh, to kai ma kana cikin matsala Nazifi, to amma kuma dai har yanzu ina jin matsalata ta fi taka domin kuwa ni ma gobe ne za a daura aurena da wata yarinya, na kashe kudi sun kusa miliyan daya a kan wannan yarinya, . to amma kuma ba ta kauna ta ko nan da can. Ko jiya da na je wurinta da zage-zage muka rabu amma kuma gobe ne za a daura mana aure domin kuwa tuni har na gama rarraba katin gayyata, Nazifi." . Nazifi ya ce da shi "Ina ban da abinka Gali me ya ja maka yin wannan tabargaza? Yaya za a yi bayan kasancewar yarinyar ba ta kaunar ka amma kuma ka kashe mata wadannan uban kudade sai ka ce za ka auri `yar zinariya, ba wacce take da jini irinka ba?" . "Wallahi Nazifi ni ma dai rigima ce kawai ta sa ni yin wannan aika-aikar domin kuwa irin ciwon son yarinyar nan da nake shi ya sa na turawa iyayenta wadannan makudan kudade, domin kuwa na san cewar duk tsiyarsu dai ko ba sa so dole ne su ba ni yarinyar, tunda dai ba za su iya biyana kudin da na kashe ba." . Abokan biyu suka tuntsire da dariya a lokaci guda hade da tafa hannuwa. Nazifi ya ce da abokin nasa. . "Kai rigima dai ba ta karewa a wannan duniyar Gali, in kana duniya ka ga tsiya iri-iri, wato in da za ka san cewar ni dan tsiya ne, bani da kirki abokina, wani miloniya ne fa ke son yarinyar nan tawa amma kada ka ga yadda take kwabsa shi . An ce wai da motoci yake zuwa wurin ta zuka-zuka, amma kuma na kwace mishi ita." Suka sake fashewa da dariya Gali ya ce . "Ai ni har yanzu ban ma gano nawa abokin karawar ba, wallahi na rasa dan iska da ke hurewa tawa budurwar kunne a garin nan. To amma ina nan ina zuba idanu sai na gano dan banza." . Ya rage fara'a sannan ya ce da abokin nasa. "Ka san abin da zan yi masa kuwa Nazifi?" Nazifi ya girgiza kai cikin rashin fahimta. Gali ya dan yi busasshen murmushin mugunta sannan ya ce da shi. . "Harbe shi zan yi da `yar kaunar bindigata." Suka sake yin dariya a lokaci guda, amma shi Nazifi yake-yake yi ba dariya ba, domin kuwa bai taba tsammanin irin wannan tunani na kashe mutum a zuciyar abokin nasa ba. . To amma kuma abin da bai sani ba, shi ne abokin nasa yafi jin tausayin kashe kiyashi fiye da kashe mutum. Gali ya tattara hankalinshi wuri guda sannan ya ce da Nazifi. . "Kada ka damu Nazifi zan magance maka matsalarka gaba dayanta, daga nan kuma sai mu dawo ni ma ka taya ni don mu magance tawa matsalar. . Yanzu dai da farko zan ba ka gida da zaka zauna kai da amaryarka domin kuwa ina da sababbin gidaje har guda uku a garin nan duk gaba daya na ginasu, sannan kuma zan ba ka isassun kudin da za ka yi hidimar komai da komai na wannan aure." . Nazifi ya ji numfashinsa ya dauke, don tsananin murna, "Na gode sosai Gali, wallahi ka yi bala'in `yanto ni mutumina" . Gali ya jawo wata bakar jaka da ke bayan motar, ya dorata a kan cinyar Nazifi, sannan ya danna wani kwado murfin jakar ya bude. Nazifi ya some a zaune, jakar dankare take da 'yan dari biyar-biyar sabbi fil da su, suna ta daukar idanu. Gali ya dafa kafadarsa cikin tsokana sannan yace da shi. . "Kai banza na ga duk ka bi ka wani rude sai ka ce ka ga wasu kudin arziki Ka da ka damu Nazifi ba su da yawa rabin miliyan ne, da ma yanzu na je banki na amso su, Allah ya sa rabonka ne, ka je ka yi hidimar aurenka da su." . Nazifi ya dubi abokin nasa a rude ya ce da shi cikin kidimawa "Duka ka bar mini Gali? Rabin miliyan fa ka ce...?" Gali ya daga masa girar idanunsa sannan ya ce da shi. . "Eh, rabin miliyan ne Nazifi, ko sun yi maka kadan ne in kara maka kamarsu su zama miliyan guda?" . Nazifi bai gasgata kunnuwansa ba. ________ Hehe Rikici bata kisa amma da alama zata fara takan Nazifi SOJA GALI yayi tabargaza, shin meye tunaninku alokacin daya gano budurwarsa daya rage saura kwana biyu a daura masu aurene, Nazifi zai aura, kuma zasu zauna cikin gidansa, me zai faru . GWARAMA KENAN Its shuraih 99% ________________ BABI NA HUDU| . Dogon malamin wanda ke sanye da dogayen kaya farare rike da dogon carbi a hannunsa ya gyara zaman katon nadinsa, wanda ya mike tsawon bayan sa ya kwanta, kamar wutsiyar doki, ya dubi saurayin da budurwar, wadanda ke zaune a gaban shi suna sauraronsa kamar wadanda ke daukar darasu ya ce dasu cikin girmamawa, . "Yara me yake tafe daku?" Nazifi da A'isha suka dubi juna a sannan lokaci guda suka yi ajiyar zuciya, domin kuwa shi dai Nazifi tun kafin su zo wurin malamin da ma yana shakkar da wahala idan za su yi nasara, to amma dai a yadda ya ji ana kishin- kishin tabbas ya ji an ce wai wannan malami dan tsubbu ne shi ya sa ya zabi su zo wurin sa, domin kuwa ya san cewar zai dan fi saukin kai in dai suka nuna mishi makudan da ke hannusu . Nazifi ya dan yi masa murmushi sannan ya ce da shi. "Mhm. da ma malam wata `yar matsala ce ke tafe da mu zuwa wurinka." . Malamin ya sake gyara zaman a kan tafkeken buzu, sannan ya gyara zaman nadinsa mai kama da mushen jimina, domin kuwa tun zuwan wadannan yara biyu saurayi da budurwa, ya ji kansa yana dan sarawa kamar zai yi ciwo, domin kuwa duk ya rasa kansa kamar ba mutane ba. . "Ni fa a gaskiya ban gane abin da kuke nufi ba, ban san me yake tafe da ku ba. Ina jin da za ku fito fili ku fada mini matsalarku da zan fi son haka, amma kuna ta wasa da hankalina sai ka ce wani karamin yaro." . Nazifi ya sunkuyar da kan shi cikin ladabi ya ce da malamin. "Ka yi hakuri malam lamarin ne yana da dan wahala shi ya sa ka ji muna fargabar fada maka." . Malamin ya shafi dogon gemunsa ya ce da su "Duk da haka dai tun da kun rigaya kun zo ai sai ku fada mini in ji domin kuwa ina da aiki da yawa a gabana, kun ga yanzu dare ne lokaci ne da muke aiki da rauhanai, ba lokacin tsayawa wasa ba ne." Wannan karon yana magana yayin da yake dan zazzare ido don barazana. . Saurayin da budurwar suka sake kallon juna. `Yar budurwar tana sanye da burmemen hijabi, tana sauraron diramar da ake yi tsakanin saurayinta da kuma malamin mai kama da rauhani, domin kuwa ya mafi kama da rauhanin fiye da mutane. Nazifi ya ce da shi kai tsaye.. . "Alagafarta malam ka gafarce mu, ba wani abu ya sa muka zo wurinka ba ni da wannan masoyiya tawa sai kawai don wata `yar bukata wacce muke son ka share mana hawaye a kan ta." . Nazifi ya dan saurara sannan ya cigaba. "Alagafarta malam mun zo gurinka ne don ka daura mana aure a boye, ma'ana ba ma son kowa ya san da faruwar wannan al'amari." , Dogon malamin ya zaro idanunsa cikin rudani kana ya yi saurin dafe kan shi. A wannan karo ji yake kamar zai rabe gida biyu domin kuwa duk shekarun da ya dauka yana wannan sana'a ta tsubbu ya hadu da attajirai da talakawa, `yan kasuwa, da kuma `yan siyasa, kai har da `yan fashi da makamai, amma ko sau daya bai taba jin wani ya zo masa da tatsuniya irin wannan ba, sai a wannan karon. . Ya gyara zamansa sannan ya muskuta baya kamar yana tsammanin za su haushi da duka a cikin dan tsurkun dakin nasa na ganawa da baki. . "Ku gafarce ni yara a gaskiya ba ni jin zan iya wannan aikin, ina jin sai dai ku lalubi wani malamin amma dai ni ba na irin wannnan aika-aikar." . Nazifi ya dubeshi cikin damuwa. "Ka taimake mu malam, wannan ba wai abin assha ba ne domin kuwa kai ma za ka samu lada, tun da dai raya sunnar fiyayyen halitta ce." . Malamin ya ce "Ba wai taimakon naku ne bana son yi ba, to amma shi aure ba haka nan ake yin sa kawai ba wani bincike ba, domin kuwa ni yanzu ba zan iya sani ba ko da aure a tsakaninku ko babu ba, tunda dai ban taba ganinku ba. Sannan kuma ban san da wacce manufa za ku yi auren ba." . Nazifi ya sake marairaicewa. "Wallahi malam ba wata manufa, muna so ne kawai mu yi aure, wadansu matsaloli ne suka sa za mu yi a boye." . "To me ya sa ba za ku sa iyayenku a gaba su wakilci maganar ba? Ko ba ku da iyaye ne a nan garin?" . Masoyan biyu suka sake duban juna, kana saurayin ya ce, "Muna da iyaye Malam, to amma dai wannan wani sirri ne a tsakaninmu da kai. Mun wakilta ka ka zama iyayenmu, sannan kuma ka zama waliyi a tsakaninmu duka, kuma kai ne shaida." . Malam ya tattara carbinsa wuri guda kamar `ya`yan goriba sannan ya dubi masoyan biyu ya ce da su. "Aure irin wannan ba shi da kyau, ko kuma in ce yana da matsala domin kuwa babu mamaki ma kun sha nono daya." . Nazifi ya ce a marairace. "Wallahi malam ba mu sha nono daya ba, masoyiyata ce ba kanwata ba ce." Malam ya sake hade fuska duk ya yi zufa sharkaf ya ce da su "Kai ni fa ban taba yin wannan aika-aikar ba, a gaskiya sai dai ku gafarce ni ba zan aikata wannan tabargazar ba, domin kuwa shi aure ba haka kawai ake..." . Maganar ta makale a makogwaronsa, bai samu damar karashewa ba sakamakon abinda ya hango a hannun saurayin. Sababbin `yan dari biyar ne dami guda suna daukar idanu. Saurayin ya ajiye kudin a gaban malamin sannan ya ce da shi . "Amincewarka muke bukata ba wa'azinka ba Malam, domin kuwa ba haka nan za mu barka ba. Idan ka amince ka dauki wannan duk naka ne ladan aiki. Idan kuma ba ka amince ba shi kenan sai mu dauke kudinmu muje gaba wani malamin ya daura mana auren. To amma dai me ka gani?" . Malamin ya sake gyara zama kamar wanda yake zaune a kan kunama, ya sake duban kudin a halin yanzu bayan ciwon kan da yake ji har wani abu kuma yake ji yana tsikarar hakarkarinsa da cikin zuciyarsa. Ya yi ajiyar zuciya sannan ya ce da saurayin. . "Kada ku damu yara zan dan yi shawara. Mu gani, ni dai a gaskiya ban taba irin wannan ba, to amma dai tunda kun ce a taimaka muku ai dole ne a taimaka muku din. Ina ganin ba wata matsala ta yanka maka sadaki ka biya, yanzu nan ma sai a daura muku auren, ku yi tafiyarku." . Yana gama fada ya warce damin kudin, ya bankada karkashin tafkeken buzunsa ya watsa su ciki. Duk fa wa'azin da ya yi musu a baya duk ya mance. . _____________________________________ Shuraih 99% . "Ku yi hakuri Gali, wallahi ni kaina ban ji dadin faruwar wannan mummunan al'amari ba. To ka san zamani ya canza. Wallahi ni kaina ban san lokacin da yarinyar nan ta lalace haka ba, ban taba tsammanin zata iya guduwa ta bar gida a kan wannan maganar ba." . Gali da ke sauraron Alhaji Dage ya hade fuskar shi. ''Agaskiya Alhaji ba zan yarda da duk abinda za ka fada mini a kan wannan al`amari ba. Ta yaya ma za a ce in gama raba katin gayyata, anjima nan jama`a fa za su fara zuwa kofar gidan nan don daurin aurena da yarinyar nan, amma ka ce da ni wai tun daren jiya ba a san ma inda take ba . Dole ne a nemo mini matata, in dai ana son zaman lafiya.'' Alhaji Dage ya gyara zaman faskeken tabaronsa, wanda ya fi fuskarsa sai ka ce wazirin akun magana jari. "Bai kamata a ce ka yi saurin fushi haka ba Gali, domin kuwa wannan yarinyar dai ba za ta bata ba a garin nan. Koda bayan an daura auren dole ne a nemo ta, dole ne a gano inda ta shiga." . "Haba Alhaji, to amma saboda Allah yaya za a ce an daura mana aure ba amarya? Kai ma ka san cewa wannan ba karamin tonon asiri ba ne a gare ni. Ya kamata dai a san abinda ake ciki kawai." . Siririn mutumin ya share zufa de ke kan dokin wuyansa. "Wallah ni kaina ban san me yake damun wannan yarinyar ba. To ka san bai yiwuwa ka haifi yaro sannan kuma ka haifi halinsa, wannan hali nata ni ban san inda ta samo shi ba, domin kuwa daga ni har uwarta duk mutanen kirki ne wallahi." . Gali ya harari mutumin a fakaice, a zuciyarsa ya ce "Kana matsayin mutumin kirki amma ka damfare ni kusan miliyan guda, don kawai za ka ba ni 'yarka?" To amma dai a zahiri cewa ya yi da shi, "Ni dai ka ji bayanina Alhaji, in dai har ba a gano mini amaryata ba, to ina jin mu duka sai kawai mu yi hakuri da maganar. Domin kuwa jiya aka daura auren abokina, muna so ne mu hada bukukuwanmu rana daya da aurenmu, amma kuma ni a ce wai ba a ga tawa amaryar ba. Wannan ai tonon silili ne ake nema kawai a yi mini." . dan motsattsen mutumin ya yi ajiyar zuciya, jikinshi ya soma kyarma domin kuwa a yadda ya lura da kwayoyin idanun saurayin ya san cewar abubuwan da yake fada har cikin zuciyarsa abinda yake nufi kenan. . "To ni yanzu don Allah me kake son in yi maka? Ai'sha dai ni na haife ta, kuma ta kwashe kayanta ta gudu ta bar gidan nan, me kake so yanzun in yi maka, tunda ka ce ba ka yarda ba?" . Saurayin ya sake hade fuska sannan ya ce da shi. "Ai ba wani abu ba ne mai wahala, ina ganin Alhaji, in dai ban takura maka ba, ai ina gani ban yi laifi ba idan na ce ka shiga cikin gida ka tattaro min kudadena da na kashe tun farkon soyayyata da 'yarka A'isha. Domin kuwa idan har za ka iya tunawa ka amshi manyan kudade a wajena, kuma kai ma ka san dai ai ba kyauta na ba ka su ba, domin kuwa inda a ce ni talaka ne ba ni da kumbar susa, na tabbata daidai da rana daya ba za ka taba barina in zo kofar gidanka har in furta ina neman 'yarka ba . Don haka ni ma na rika ba ka kudaden da kake bukata, na san dai ba ka mance ba da su ba." Saurayin ya dan yi murmushin takaici sannan ya ci gaba da shaidawa ramammen tsohon . "Tun fara neman auren A'isha na fara lissafin abubuwan da nake kashewa a dalilinta, kai hatta man da nake zubawa a motata in zo wurinta, da kuma kudin da nake baiwa yara su kira min ita, duk ina rubutawa. A halin yanzu lissafi ya yi kauri, domin kuwa kullum sai na ciro doguwar takardata ta lissafi, na yi bitar kudaden da ke cikin akawun dina da wurinka . Don haka na ba ka awowi goma ka tattaro min kudadena. In ba haka ba, ka ji na rantse maka da Allah, sai na dankara ma ka harsashin bindiga, tsohon banza makwadaici kawai macuci!" . Gali ya bude kofar motar a fusace ya shiga ya tashe ta. Ya juyo ya dubi motsattsen mutumin, wanda a halin yanzu ko'ina a jikinsa kyarma yake yi hatta fuskarsa da ke dakon faskeken tabaron ita ma kyarma take yi, duk da uban kayan da aka jibga mata, . "Kada ka damu Baba, na ga ka rude, ai kudin ba wasu masu yawa ba ne, miliyan daya da dubu dari bakwai da hamsin kawai, sai naira dari uku da talatin da biyar." Ya fizgi motar ya fice a guje daga kofar gidan . Motsattsen mutumin ya bi kurar motar da kallo. A daidai lokacin ne faskeken tabaron ya kubuce daga 'yar mitsitsiyar fuskar tasa, ya fadi kasa. Tuni har ya fara tsammanin hawan jini. . ___________ Shuraih 99% Iyaye ayi hattara da amsar kudi ko wani abu a hannun siriki kafin Aure . Duniya ta lalace da cin hanci wai har MALAMAN ADDINI suna RASHAWA ._____________ AJALI Na Shafi'u Dauda Giwa Typing by Shuraih Usman Post by shuraih 99% @shuraih 99% Page 11 . ____________ Tsawon mintuna biyar mafadaciyar matar na ta faman yiwa mijin nata banbami. Yana tsaye kawai yana duban ta, sai zufa ke ta faman kwararo masa, tana wanke masa fuska, kamar ana yi masa sakiya . Ya rasa da me zai ji tsakanin masifar da kuma gargadin da surukinsa ya zo ya yi masa. Ya san cewar wannan saurayin dan bindiga-dadi ba hankali ya cika ba, kamar yadda da ma ya dade yana jin ana cewa ba duk soja ne ke da cikakken hankali ba . Hakika yana iya aikata duk abubuwan da ya fada, ga shi kuma yanzu Juma ta tuso shi a gaba da tata masifar. . Duk ya rasa abinda ke masa dadi a duniya. "Kawai aikin banza Malam, ka jawo min 'yata kwalli kwal da nake alfahari da ita a duniya ta tattara kayanta ta gudu, da ma haka kake so sai ka zuba ruwa a kasa ka sha, burinka ya cika." . Alhaji Dage ya yi shiru, bai ce da ita kala ba, domin kuwa ya san cewa yanzu ba lokacin tankawarsa ba ce, don kuwa har ga Allah matar tasa ta tunzura. Ya san cewa idan ya biye mata, tana iya kama shi da kokawa, kuma ba ya kokwanto ya san cewa shi za ta kayar . Shi ya sa ya rufawa kansa asiri ya rabu da ita, in ta yi ta gaji dai ai dole ne ta bari. Juma ta sake cewa da motsattsen mutumin cikin kwarmato kamar za ta hadiye shi. . "Wai me kake nufi ne Alhaji, ba ka ce komai ba. Ko kuwa kana nufin shi kenan, kai ka cinyewa mutane kudi, ni kuma ka bar ni da asarar 'yata. To ai sai ka sake tunani, don kuwa ba kyale ka zan yi ba, duk inda 'yata ta shiga sai ka je ka kwakulo min ita, in dai kana son zaman lafiya a duniyar nan, to wallahi ka nemo min A'isha domin kuwa duk kai ka jawo mana wannan masifar." . Ramammen mutumin ya yi ajiyar zuciya, a karo na farko ya ga cewar ya kamata dai ya dan ce wani abu. Don kada ta ga ya ki tabuka komai, ta sake haye masa yadda ta ga dama. . "Ba na son rashin albarka, Juma." Ya ce da ita, "Ni kike yi wa wannan tsagerancin ko kuwa kin fi ni son 'yar tawa ce, da kike fada min wadannan maganganun? Ko kuwa ni ne zance ta gudu ta bar gidan? Wannan tsinanniyar yarinya ina amafaninta, duk ba halinki ta kwaso ba? Ke din a da can me ye ba ki yi ba? Ba don yanzu an mance, ba a tone- tone, shi ne har kin samu bakin magana. Kada in sake jin muryarki a kan maganar nan Juma." . Ya zazzaro mata idanunsa da ke cikin fasasshen tabarau, a tsammaninsa watakila ta dan ji tsoro ta lafa. To amma kuma cikin rashin sa'a sai ya ga ta yi shewa, sannan ta yi tafi ji kake fas, ta ce da shi. . "Lallai yau da tone-tone a gidan nan. Au kai nan har gori zaka yi min? Ka mance da abubuwan tsiyar da ka kuntuka a baya? Haka fa kawai nake zaman hakuri da kai. . Shi ne yanzu har ka samu bakin da za ka yi tonon silili. To ai sai mu fara a ji ni da kai wa ya fi wani mugun tabo, ba tsoron ka nake ji ba Alhaji, mu yiyar tonon asiri." . Alhaji Dage yayi saurin tsayar da ita, da ya ga ta sake hayewa. "Duk wannan ba ta taso ba, ni dai gaya miki na yi dama don maganar da ya dace ki rika fada, ai ba cewa na yi za mu yi wani tone- tone ba, don kuwa mu dai ba yara ba ne, ya isa a ce mun mallaki hankalinmu a halin yanzu." . Juma ta yi guda sannan ta ce da shi. "Ashe ka ji tsoro mai gida. Ai na so mu jarraba tonon silili da kai wallahi da ka ga dan biki da cika yau a gidan nan. In ana fadin abin kunya kai har ma ka sa baki a gidan nan. In ba abin kunya ba mene ne amfanin karbarwa mutane dukiya don za su auri yarka? Haka fa ka yi ta yi wa ragowar yayan danginka da ka rika a gidan nan. Ka aurar da yan mata sama da biyar duk a bisa zalunci. Yanzu suna can dakunan mazajensu suna shan wahala ana yi musu gori da wulakanci, tunda dai ka saida musu da mutunci. To ni ba mai yi wa yata A'isha wannan mulkin mallakar, mu zuba ni da kai a gidan nan tun da kai ba ka gudun abin kunya." . Mutumin ya yi ajiyar zuciya, ba shi da ta cewa domin kuwa duk abin da matar ta fada gaskiya ne duk ya aikata. Yana jin ta ta ci gaba da cewa da shi. . "Duk wanda ya sa ranshi a kwadayin abin duniya dole ne ya ga wulakanci mai gida, amma ina amfanin a ce a matsayinka na babban mutum wanda zai yiwa wani nasiha a ce kana rigima kai da surukanka kana amsar musu dukiya? Yanzu ga abin da ka jawo mana, wannan mutunci ne?" . Ramammen mutumin ya girgiza kan shi kamar uwa na wa danta fada "To ai laifin yarinyar ne ni wannan tsinaniyar yarinyar wallahi ta cuce ni.." . "Ka da ka tsinewa yata a banza domin kuwa ba ta da laifi, kai ka jawo mana wannan rigimar muna zaman zamanmu lafiya. Ka san cewar A'isha ba ta kaunar yaron nan ka nace a kan maganar nan don ka gan shi da kumbar susa, ga shi yanzu kana jin tsoron fita waje ka da surukinka ya harbe ka . Ina na taba jin irin wannan abin tsiya ma a duniya, ni Juma." Alhaji Dage cikin nadama ya ce. . "Kin ga laifina ne a banza Juma, amma a matsayina na magidanci saboda Allah ba ni da yanci zabarwa yata mijin da na ga ya fi dacewa da ita? Wani zamani dai Allah ya kawo mu inda yara ke kangarewa su fi karfin iyayensu. . Mu a zamaninmu wane yaro ya isa ya ce shi zai yiwa kansa zabi sai wanda ya ke so, mu kuma mutane sai mu bar abu ya lalace da kanmu, mu ce ai zamani ne, da gangan ake kyale yara suna wannan iya shegen da fitsarar ana kallon su." . "Ba haka ba ne maigida" Juma ta ce da shi "Ko ka ki ko ka so al'amura suna canzawa, kuma zamani ya kan zo da abubuwa iri-iri dole kuma mutum ya bi abinda zamani ya zo da shi matsawar bai sabawa shari'a ba. Ai ba haramun ba ne don yaro ya zabi wanda ya ce yana so ya aura. Kuma da ka ce a naka zamanin ba haka ake yi ba, kai zamaninka ka sani, ba ka damu da zamanin yayanka ba. A zamanin naka ai bante ake daurawa ba sutura ba, me ya sa ba za ka cigaba da daura bante a wannan zamanin ba, tun da ka ce ba ka amince da canjin zamani ba, sai ka koma tafiya tsirara da bante, don kuwa shi ake daurawa zamaninka na baya." . "Yanzu dai mu bar wannan maganar" ya ce da ita abin da ya faru dai ya riga ya faru, dole ne in sanar da jami'an tsaro su shiga cikin maganar don a kawo karshen wannan rigima, kafin abin ya kai mu ga kashe-kashe don na ga alamar abin da wannan mahaukacin sojan ke nufi kenan, in ya so daga baya sai in sayar da gidana na sabuwar unguwa in biya shi kudadensa, ita kuma A'isha sai a nemo ta a bata wanda take so." . Juma ta dan saki ranta ta ce da shi. "To yanzu da ka yi haka kai kanka ba ka fi jin dadi a ranka ba? Ai wannan shi ne datattako maigida, yanzu to ka nemi a zauna lafiya." Kamar aikin budar idanu cikin yan tsararun mintuna mafadanta ma'auratan biyu suka dawo cikin raha kamar ba su ba. Shekaru sama da talatin kenan, suna wannan halayya, an ce a cikin minti daya sai su hautsine da fada, kafin kiftawa da bismillah sai kuma a ga sun dawo suna dariya. . To sai dai kuma a wannan karon da sun san cewar akwai wani shu'umin saurayin da ya cika bindigarsa da harsashi, sannan kuma ya saya musu likkafani jana'iza da ba su sake yin wata raha ko dariya ba. _____________ A'isha ta dubi angonta Nazifi cikin farin ciki sannan ta ce da shi "Nazifi 'darling' yau dai Allah ya cika mana burinmu, mun zama mata da miji. Duk duniya babu mai raba mu ni da kai masoyina." . Nazifi ya dube ta shi ma duba na so da kauna yana kwance a kan doguwar kujerun da ke cikin tsararren dakin da suke ciki, ya ce. "Ai ni A'isha ba ma abinda zan iya cewa sai dai kawai in godewa Allah da kuma wannan abokin nawa domin kuwa wallahi ni dai ya gama yanto ni, ya yi min komai na alheri." A'isha da ke zaune a kusa da shi ta ce cikin mamaki "Wai da gaske bayan ya ba ka rabin miliyan har kuma wannan gidan duk shi ya ba ka, Nazifi?" . "To ga zahiri ma kin gani A'isha tun da har ga shi kuma na shigo da ke kin tare a ciki, ko kuwa ke a da kin ga na yi miki kama da wanda zai iya mallakar wannan tsantsareren gidan?" . A'isha ta yi dariya farin ciki. "Mun gode masa wallahi. Don Allah sai yaushe zai zo don in gan shi mu yi masa godiya ta musamman akan wannan abin alheri da ya yi mana?" . Nazifi yace da ita "An jima nan kadan za ki ji ya zo ya kwankwasa mana kofa domin kuwa shi ma yau ake daura aurensa da wata yarinya a nan garin kuma mun yi da shi zai biyo min ya dauke ni mu wuce wurin daurin aure tare." . A'isha ta sake lumshe idanu cikin murna ta ce. "Mun gode wallahi, Allah ya bar zumunci tsakanin mu da shi. Yaya sunan tasa amaryar Nazifi?" . Nazifi yayi farat ya ce. "Ai abin namu ni da shi ya zo daya domin kuwa saboda tsabar shakuwa da muka yi da shi, har ankon sunan amare muka yi, cikin sa'a ita matar tasa sunanta A'isha." . Suka yi dariya, A'isha ta ce. "Lallai abin yayi min dadi Nazifi, ka ce kun samar min kawa kenan ni ma" Suka ci gaba da dariya abin gwanin ban sha'awa. Suka fito da naman kaza suka tasa a gaba, dama tun tarewa su gidan a daren jiya Nazifi ya sawo dakwalen kaji soyayyu har guda uku. Tun a jiya suka cikye biyu saura ragowar daya wacce suka baje a halin yanzu. . Ba abin da ya dame su, kudine dai sun samu abin kamar daga sama, dole ne su godewa wannan abokinsu mai farar aniya. A daidai wannan lokaci ne Gali ya karaso kofar gidan fuskarsa a murtuke kamar wanda aka yiwa albishir da mutuwa. Lokaci-lokaci yakan kai hannusa cikin aljihu ya shafi bindigarsa. Kamar yadda ya tsara a ransa, . daga nan idan ya gama gaisawa da ango da amarya, to farauta zai wuce abinsa. Ba farautar namun daji zai fita ba, farautar amaryarsa A'isha zai fita da kuma saurayin da aka ce ya sace masa ita sun gudu. Kuma ya sha alwashin muddin ya yi ido biyu da A'isha da wannan saurayi da ya sace ta, to ba wani bata lokaci duk aikawa da su zai yi barzahu . Gali ya yi murmushin mugunta sannan ya sake mika hannu ya shafo bindigarsa wacce ke boye a cikin aljihu. Ya daga hannu ya kwankwasa kofar gidan a sanyaye. A'isha da Nazifi da ke cikin gidan suna baiwa juna naman kaza a baki, suka dubi juna cikin farin ciki a dai dai lokacin da suka jiyo sautin bugun kofar "Kin ji dan halak!" . Nazifi ya ce "Shi ne yake kwankwasa kofa, Gali ne abokina. Je maza ki bude masa kofa ki rako shi, A'isha." . Amayar ta ce da angonta a sanyaye. "Wata kila ma wasu miliyoyin kudin ya sake kawo mana 'darling'." Nazifi ya ce "Babu mamaki, A'isha ai na fada miki abokin nan nawa yana bala'in sona, ke dai je ki bude masa kofa, ki tarbo shi ya shigo." . ___________ YAU KAM RIGIMA ZATaYI KISA . Ya kuke ganin zata kaya Ku biyoni Shuraih 99% a littafin AJALI Nazifi ya ce "Babu mamaki, A'isha ai na fada miki abokin nan nawa yana bala'in sona, ke dai je ki bude masa kofa, ki tarbo shi ya shigo." . A'isha ta mike cikin farin cikin tana rangwada ta nufi kofar gidan. Hakika sun yi dace ita da angonta Nazifi, Allah ya hada ta da mai sonta kuma ita ma take kaunarsa. Ya raba ta da wannan wahalallen da a da ya nace mata, A'isha ta ce a zuciyarta tana murmushin farin ciki. . Ta kama kofar gidan da hannayenta biyu, ba tare da wani fargaba ko zullumi ba TA BUDE MASA kOFAR! ****====****** Dankareren kayataccen gidan ne da ya kai matuka wajen tsaruwa. Jama'a da dama kan dakata don yiwa kyakkyawan gidan kallon tsaf! saboda ginuwarsa. Mutane da dama kan tuna da kayataccen gidan saurauniyar ingila dake "BUCKINGHAM PALACE" a duk lokacin da suka dubi tsararren gidan. Wani dadin abin da ke matukar jan hankalin jama'a ga hadadden gidan shi ne daddadan kamshin furanni dake gewaye da gidan. dan tsamurmurin dattijon maigadin da ke zaune akan bencin a gefen katotuwar kullalliyar kofar gidan mai fasalin fuka-fukan dawisu, ya dan yamutsa fuska gami da gyara rikon jaridar da ke hannusa tamkar mai tsammanin shekowar wani a guje ya wafce ta, cikin zakuwa ya soma bude shafukan cikin ta, a shafi na biyar ya yi ido hudu da labarin da yayi matukar jan hankalinsa mai taken KADDARA KO FANSA! . A hanzarce ya muskuta gami da gyara zama, kana ya sake kafa kwala- kwalan idanunsa akan hotunan gawarwakin wasu mutane biyu mace da namiji da ke gefen rubutun, cikin zakuwa ya soma karantawa. . A safiyar jiya ne yan sanda suka tsinci gawar wani saurayi Nazifi tare da masoyiyarsa A'isha. . An tsinci gawarwakin ne yashe a cikin wani sabon gida bayan an harbe su da bindiga har lahira. Tuni jami'an tsaro sun cafke wanda ake zargi da aiwatar da kisan gillar wanda ya kasance wani matashin soja wanda shima yake kaunar budurwar, wanda kuma har an sa ranar bikin su da ita amma kuma ita ba ta kaunarsa. . Mahaifin yarinyar mai suna Alhaji Dage ya yi nadamar afkuwar mummunan al'amarin sannan kuma ya tabbatarwa da wakilinmu cewar dukkan wannan al'amari da ya afku laifinsa ne sakamakon tilastawa diyar tasa da ya yi a kan sai ta auri wanda ita ba shi take so ba. A karshe ya yi kira ga iyaye a kan su dinga mayar da hankali a kan dukkan abin da `ya`yansu ke bukata matsawar dai hakan bai sabawa addini ba. . Sannan kuma ya yi doguwar addu'a gami da bayyana matukar alhininsa ga mamatan . Don jin yadda zata kaya mu hadu a cigaban littafin nan mai suna A’ISHA don jin karshen sarkakiyar sarkakakken labarin. Na gode, naku Shafi’u Dauda Giwa. ......................... Anan kuma ayau muka kawo karashen littafin AJALI amma da yardar Allah daga nan zuwa wani lokaci zan saka maku cigabansa . AJALI Na Shafi'u Dauda Giwa Typing Shuraih Usman 99% .... JINJINA GA Shafukan Shuraih 99% Zauran labarai Home of Littatafan yaki and Hausa novels . Ina mika sakon gaisuwata ga ahalin kungiyar TSANGAYAR MARUBUTA TASKAR GIDAN LITTAFI ..... Nine naku a kullum da ko yaushe Shuraih Usman 99% Ku tareni a littafin A'ISHA AJALI Marubucin littafin Shafi'u Dauda Giwa Ebook creat by Shuraih Usman Ebook publish by www.hausaebooks.cf Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.cf Kuna ziyartar shafinmu don samun sababbin littatafai Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com