*💖ABNUR💖* By maimoon🤓 Elegent Online writers *Free book* page 1 Bismillahi ar-rahmani ar-raheem_______ Hasken farin watan daya haske illarin garin shiyake bata daman ganin inda take sanya ƙafafuwanta gabaɗaya she is not in her right senses tafiya kawai takeyi ba tare da tasan inda ta nufaba Tafin hannunta ta sanya ta share hawayen da ya zubo mata a karo na ba adadi she really wish all dis was a dream cigaba da tafiyan kawai takeyi a ƙauyen da ko sunansa ma bata saniba Ita dai kawai burinta tayi nesa da inda ta fito A daidai kofar wani gida ta ja ta tsaya saboda batajin xata iya cigaba da tafiyan saboda galabaitan da take sake yi rabonta da abinci tun breakfast shima ba wani sosai taci ba gashi a yanda xata ƙiyasta saboda yanayin shirun garin da kuma duhun dare aƙalla ƙarfe 11:00 zai iyayi Guri ta samu ta zauna a ɗan dakalin dayake ƙofar gidan tare da kifa kanta tana cigaba da kukan da har takejin zuciyarta kamar ba'a jikinta yakeba batasan iya lokacin data share a zaune a wajen ba kawai dai taji idanunta na lumshewa alamar bacci takeji Muƙewa tayi a hankali akan dakalin tana jin zuciyarta na mata zafi batason tuno abinda ya rabo ta da gida a cikin wannan tunanin bacci ɓarawo yy nasaran fizgarta duk da ba ɗaɗin baccin takejiba sam Sanyin asuba tare da kiraye kirayen sallah a masallatan da suke ƙauyen yasata ɓuɗe idanunta a hankali waɗanɗa suka kumbura Sukayi jajir saboda tsananin kukan ta sha zaunawa tayi akan dakalin tana jin duk jikinta na mata wani irin ciwo ta shiga ƙare ma ƙauyen kallo tanason tuno inda take dafe kanta da ke tsananin ciwo tayi tana jingina da bango wasu hawaye Masu ɗumi suka sake gangaro mata Hannunta tasa da sauri da kare fuskarta saboda hasken fitilar daya haske mata fuska "Subhanallahi mutum ko aljan" mutumin ya tambaya da alamar tsoro a tare dashi yana tsaye daga ƙofar gidan da take zaune kasa cewa komai tayi sai hawayenta da ya ƙara ƙarfin gudu juyawa mutumin yy da sauri ya koma cikin gidan sai gashi ya ƙara fitowa tare da wani ɗan saurayi da alama shima alwala yayi na tafiya Masallacin "Kaganta nan wlhy nidai har na tsorata" tsohon ya faɗa yana nunama saurayin ita da alama ɗansa ne ƙarasowa kusa da ita yy ya tsaya ɗan nesa kaɗan da ita yana faɗin " baiwar Allah " ɗago kanta tayi a hankali tana kallonsa hawayen idanunta na cigaba da kwarara tsura mata ido kawai yy sai kuma ya juya ya kalli babannasa yace "baba ko xata shiga ciki kafin mu dawo daga masallaci lokaci na ƙurewa "wani kallo babannasa yy masa yana nuna ta yace "ta shiga ina wai, kasan wacece ita xakace ta shiga ciki "miƙewa yy yana sake kallonta sai kuma kawai yy wucewarsa baban ma ya bisa a baya suka nufi masallaci Har aka idar da Sallah gari ya soma haske tukun suka nufo gida tun daga nesa suka hangota still tananan zaune inda suka barta baba ya kalli kamal yace "anya wannan yarinyar mutum ce kuwa "murmushi kamal yy yace muƙarasa mugani "daidai kusa da ita ya durƙusa ya sake cewa "baiwar Allah" a karo na uku sannan ta ɗago kai ta kallesa murmushi yy mata yace "me ya sameki haka kike zaune anan da alama ma anan kika kwana ki faɗa min ko akwai taimakon da xan iya baki "nan ma shiru tayi ta sake miyar da kanta shiru yy kamar mai tunani sai kuma yace to ki tashi mu shiga ciki kiyi sallah nasan bakiyi ba ko kallonsa kawai takeyi kamar statue sai da ya sake maimaita abinda ya faɗa tukun ta miƙe a hankali jiri na ɗibarta saboda gaskiya tana buƙatar tayi sallolin da ake binta Kallonta yy tayi saboda baiga alaman yar ƙauyen bace ko duba da irin suturar da ke jikinta kaɗai to itakuwa me ya kawota ƙauyennan haka har suka shiga ciki ta tsaya a zaure tana raba ido baba da tunda yaga kamal ya tsaya wajenta ya shige cikin gida ya samu a tsakar gida zauren ya nuna masa yace "wannan yarinyar baba nace ta shigo ko xatayi sallah "saída baba yy shiru sai kuma yace "kamal mutum fah yanxu abin tsorone kuma kwata kwata batayi kamar yar nan ba bawai bana son taimaka mata bane" kamal yy murmushi yana komawa zauren tare da faɗin "karka damu baba banji ajikina mai cutarwa ce kuma mu ai dan Allah mukayi da kyakkyawar nufi idan ma ta cucemu Allah baxai barta ba A zauren ya sameta a rakuɓe yace baiwar Allah shigo yayi gaba tana binsa a baya har ƙofar ɗakin mahaifiyarsa sallama yy ta amsa sannan ya shiga itama ta bishi a zaune suka tarar da ita har lokacin akan abin sallan ta gaisheta yy ta amsa da fara'a tana kallon baƙuwar sai kuma tace " kamal wannan Fah a Ina ka samo ta" murmushi yy yana miƙewa yace" to muma dai a ƙofar gida muka ganta da alama ma anan ta kwana kuma taƙi magana shine nace mata ta shigo ko xatayi sallah" kallonta kawai umma takeyi sai kuma tace "to badamuwa bari tayi sallan idan mun karya sai muji daga ina take haka dan sam batayi kalar yan ƙauyennan ba" yauwa umma kamal ya faɗa yana ficewa daga ɗakin dan tafiya gona tare da baba dake jiransa a waje Abuja nigeria_ A haukace yake sauƙowa daga matakalan da yake haɗesu uku uku hurhuɗu hankalinsa a matuƙar tashe ƙofa ya nufa da azama yana sake dialling din number a wayarsa ɗaya daga cikin securities ɗinsa ne ya ƙaraso da sauri yana faɗin "morning sir" wani kallo da yy masa ya sashi shiga hankalinsa ya sake faɗin "sorry sir" juyowa yy gabaki ɗaya yana kallonsa yace "ina take" a tsorace guard ɗin yace "sorry sir we have tried our level best but still we are not able to reach to her" cakumo wuyansa yy a zafafe Yana faɗin "what the heck do you mean baku ganta ba wata sani ,ina xata je she has no one but me so na baku nan da awa ɗaya ku nemo min *NOOR* duk inda ta shiga a garin Abuja" hankaɗasa yy baya tare da sake faɗin "sorry sir" sake kallonsa yy sannan yace "don't u dare ,keep ur fucking sorry to yourself , just make sure lokacin da na baku kundawo min da noor gidannan "sai kuma ya juya a fusace ya nufi motarsa ya fice a gidan a guje To ABNUR has just started the story is yet to begin 🤓😇 *💖ABNUR💖* *By maimoon*🤓 *Elegant online writers* *Freebook* *page* 2 Tunda ya fito gidan yake yawo a cikin gari yama rasa ta ina zai fara neman NOOR ,ina zata je ,wata sani bayan shi, ya tabbata bata da inda zata je da ya wuce gidansa ,har yamma yana gararamba. Gefen titi ya samu yayi parking ya jingina kansa da steeryn motan, ya rasa ina zai nufa don neman ta, ɗago kanshi yayi da idanuwansa da suka gama rinewa sukayi jajir ya jingina kansa da seat ɗin motar . Why Noor? ,am I really that bad to you da kika zaɓi ki barni? ,do you have any idea halin da nake ciki yanxu ?please Noor ki dawo gareni i promise I will mend my ways ,na miki alƙawari zan gyara please Noor. Da ƙyar ya samu ya kai kanshi gida, har jiri yake ji dan rabonsa da abinci tunda ya fahimci Noor bata gidan . Baibi takan kowa ba har bodyguards ɗin da suke gaishesa, ko takalmansa bai cire ba ya faɗa kan gadon katafaren ɗakinnasa yana kallon saman ɗakin, yana sake zurfi a tunanin ina zata shiga a garin Abuja . Kamal ne ya fito daga ɗakin ,mahaifiyarsa na biye dashi ,zama tayi a tsakar gidan shima yaja ƙaramar kujera ya zauna yana fuskantar ta yace ,"umma da muka fita dama bata ce miki komai bane? ". Ďan shiru umma tayi kamar baxatayi magana ba sai kuma tace," wlhy kamal nayi iya tambaya amma batace min komai ba, banda kuka babu abinda takeyi, yarinyar tana da babbar damuwa sosai ,amma rashin sanin daga ina ta fito shine babbar damuwar ". Kamal yace ,"hakane amma gaskiya tana buƙatar taimako sosai ,kawai mu bari muga kwana biyu ko xata ji sauƙin abinda yake damunta, sai tayi mana bayani" . Shiru umma tayi sai kuma tace "toh Allah dai ya kyauta gata kyakkyawa wlhy kuma daga dukkan alamu yar gidan masu kuɗi ce ,"kamal ya miƙe yana faɗin," wlhy nima haka na gani". Fita yayi daga gidan dan yanaso ya je gidansu Abdul, dan yanaso ya amso kuɗin sa dake wajensa dan komai na gidannasu ya ƙare kuma gashi amfanin gona bai nuna ba bare , har ƙofar gidan yaje ya aika yaro ya kira masa shi, a ƙasan wani bishiya suka zauna Abdul ya kallesa yace "kuɗinka ko kamal" . Kamal yayi murmushi yace "saboda bana zuwa wajen ka sai idan inason kuɗi koh ",Abdul yayi dariya yace "wlhy ba haka bane kawai dai nasan halin garin ne yadda babu kuɗi", shiru kamal yayi sai kuma yace "wlhy Abdul banso na tambayeka ba amma wlhy ina matuƙar buƙatarsu ". Duk sukayi shiru kafin Abdul ya nisa yace" wlhy kamal bandashi nima ",shiru yayi sai kuma yace, "babu damuwa karka damu wlhy", daga haka ya miƙe yana faɗin "to sai mun haɗu anjima da daddare", Abdul ma ya miƙe yace "ba damuwa nagode kamal ". Daga haka ya juya yana ta tunane tunane har ya iso a tsakar gidan ya samu umma tana ƙoƙarin shiga kitchen kusa da ita yaje yace," umma dama naje wajen Abdul ne ko zan samu kuɗin wajensa amma bansamu ba ",umma ta nisa tace ," to Allah ya kyauta amma dai yau yaza ayi kenan, yanzu babanka ma ya dawo bai samuba ,wlhy gashi muna da baƙuwa " . D'an murmushi yayi yace "yanzu dai akwai wani ɗan canji a jikina idan na fita zan nemo mana abinda zamuci yau, amma dai gobe sai yadda Allah yayi da mu", duk juyawa sukayin jin motsin mutum a tsaye suka ganta tana kallonsu umma tace "ah ah Noor Kin fito ". Girgiza mata kai tayi tace ,"umma inaso zan shiga bayi ne," da sauri umma tace "ayya gashi can bari na saka miki ruwa a buta ",da sauri ta karɓi butan hannun umma tana faɗin "laa umma karki damu dan Allah". Ta wuce wajen randar ta ɗebi ruwan umma tace ."ga ruwan zafi idan zaki surka ,tace "toh" cup ta ɗauka ta ɗebi ruwan ta wuce bayi , Umma da kamal na nan zaune ta fito ta ajiye butan sannan ta nufi wajen tabarmar da taga sun shimfiɗa sun zauna. Itama zama tayi sai kuma tace "umma dan Allah kuyi haƙuri da shiga rayuwarku da nayi, amma ina neman alfarma a wajenku dan Allah ina so in zauna da ku na wasu kwanaki, nasan ya dace na faɗamuku abinda ya raboni da gida , amma na muku alƙwari zan fada muku insha Allahu ". Aai da ta ɗan yi shiru sai kuma ta sanya hannuta ta ciro ɗan kunnen gold ɗin dake kunnenta ta miƙama kamal tace "yaya kamal gashi ina so dan Allah ka siyarmin da wannan ɗan kunnen ". Sai da ya kalleta ya kalli ɗan kunnen sai kuma yasa hannu ya karɓa yana kallo yace," tabb Gwal ne fa". Tayi shiru tana kallonsa yace," sai dai bazan iya sayarwa a garinnan ba , sai dai gobe insha Allahu , tunda ranar kasuwan cikin garin kusa damu ne , su suna siya sai inje can na sayar miki ," ahankali tace "nagode sosai Allah ya saka muku da alkhairinsa ", duk suka amsa da ameen . Washe gari kamar yadda sukayi haka ya shiga cikin gari ya sayar , duk da dai an masa an siya ba yadda kuɗin sa ya keba ganin cewa ɗan ƙauye ne, haka ya ɗaure kuɗin a mayafi ya dawo gida, a tsakar gida ya samesu suna hira da umma ya zauna shima yana warware wa ya miƙa mata. "Yace gashi Noor ",ta karɓa tana murmushi ta ƙirga kuɗin sai kawai ta girgiza kai sannan ta kama hannun umma ta danƙa mata kuɗin. Dubu biyar kaɗai ta ɗauka a kuɗin umma ta zare ido tana kallonta girgiza kai tayi tana kallon umma tace "umma dan Allah karkice komai kiyi haƙuri jiya naji hirarku da kamal dan Allah ku karɓi kuɗinnan ,na baku ne a matsayin yan uwana saboda kunyi min taimakon da bazan taɓa mancewa daku ba, kunyi min taimako alokacin da nake tsananin buƙatarsa". Umma rungumeta kawai tayi tana sake jin son yarinyar har ranta, tana sake kwaɗaituwa da son jin dalilin ta na barin gida , a hankali ta share hawayen ta tace. " Ni ban san me ya raboki da gida ba Noor, amma ke ɗin alkhairi ce a wajenmu, kuma mungode Allah ya saka miki da alkhairi kuma ya fitar da ke a cikin duk matsalolin da rayuwarki ke ciki". Shidai Kamal kallonta kawai yakeyi sai kuma yace "Noor kuɗinnan", shhhh tace masa "yaya kamal pleaaaaase karkace komai". Nurmushi kawai yayi yace "to shikenan nayi shiru Allah ya saka", daga haka suka ci gaba da hirarsu tana samusu baki jefi jefi, but hankalinta da tunaninta gabaɗaya suna wani wajen daban. Wasu sabbin hawayene suka cika idanunta, she is sure baida buƙatarta a rayuwarsa, kuma bayida asara idan har bata tare dashi , he never loved her but tayima kanta alƙawari koda mai kama da ita bazai sake gani ba. zatayi nisa dashi irin nisan da bazai taɓa cinmata ba, a hankali ta sanya hannu ta share hawayen tana ƙaƙalo murmushi, ganin umma tana kallonta sai kuma ta miƙe ta nufi ɗaki duk suka bita da kallo . 🥱🥱🥱🥱🥱🥱 #maimoon 💖 **ABNUR**💖 *By* *maimoon* 🤓 *Elegant* *online* *writers* **Freebook** *Page* *3* Kwanci tashi asarar mai rai,yau kwanan Noor goma kenan a ƙauyen Marke dake jihar Kano. duk da cewa har yau ba tayi musu cikakken bayanin abinda ya rabota da gida ba,amma sun fahimci ita ɗin mutum ce mai matuƙar daɗin zama, sannan bata da son magana sosai. Hakan yasa suke zaune tare da ita, har zuwa sanda zata yanke shawarar sanar dasu ainihin abinda ya rabota da iyayenta , Umma tana matuƙar ji da ita, kuma hakan yasa basa ma ɗago maganar, saboda yadda daga an tambayeta, sai dai ta fara kuka, Sannan akoda yaushe maganar ta baya wuce"Umma kuyi haƙuri insha Allahu zan sanar daku ,har ma abinda baku tambaya ba". A bangaren ZANNUR kam babu sauƙi, yayi iya ƙoƙarin sa ,ya haukace da neman ta har gidajen Radio,but har yau shiru ,ga baki ɗaya ya fita hayyacinsa ,bai taɓa tunanin za tayi koda tunanin hakan a zuciyar ta ba, talkless of aikata shi a aikace Yau ma a gajiye ya dawo,bayan ya gama yawan nemanta kamar yadda ya saba ,duk da ya baza mutane sunfi a ƙirga da hotunanta ana nemanta, but shikanshi ya kasa daina wa. kullum gani yake idan ya fita yau zai ci karo da ita ,bazai taɓa manta yadda abubuwa suka kasance ba shekaru biyu da suka wuce,ɗakinsa ya wuce ya zauna akan kujeran dake ɗakin yana jingina da kujeran "i can never give up on you, har sai na ganki sannan kin tabbatar min da bakinki zaki dawo gida na, idan ba haka ba, ban san tayaya zan yafe ma kaina ba ,I know I will never be able to forgive my self idan har wani abu ya sameki". Da ƙyar ya miƙe daga kan kujeran ya zare rigar jikinsa,ƙirarsa na ƙarfafa ya bayyana, duk da yanzu rabonsa da workout ɗinma tun ranar da Noor ta bar gidan, wanda a da yake cikin morning schedules ɗinsa da baya iya tsallakewa, bayi ya wuce yayi wanka, yana fitowa kayansa kawai ya zura, yana jin yanda cikinsa ke kukan yunwa. A hankali yake sauƙowa stairs ɗin, gaba ɗaya ya canza kamar ba Zannur ba, 'the master of all' harta masu aikin gidan sun san baya cikin kwanciyar hankali, duk wanda yake tareshi yasan yana cikin matuƙar damuwa. Falon ya ƙaraso ya zauna yana rage ƙarfin ac, dan kamar sanyin zazzaɓi ma ya keji a jikinsa, Yasira ta ƙara so wajensa da sauri tana faɗin "Sir Should I serve your dinner?" Kallonta kawai yayi ,sai Kuma ya mayar da kansa ya jinginar, yama rasa me zai ce mata, bakinsa ya masa nauyi,sai da ta sake tambayan tukun ya ɗaga idanunsa,masu rikitarwa ya zuba mata su, sai kuma yayi gyaran murya yace "miss You Are fired!" Zaro ido tayi tana kallonsa, nan take tafara hawaye tana faɗin "Sir I am very sorry Dan Allah Kar ka koreni" "why shouldn't i?" ya katse ta a tsawace , "sanda ta tafi ta barni why don't you stop her ?" Ta buɗe baki zatayi magana, yayi saurin sanya yatsansa a baki , yace "shhhhh not another word, abinda nakeso dake yanzu shine,U Should get out of my sight immediately,before I lose my temper completely". Da sauri ta miƙe daga tsugunan da tayi, takoma kitchen da sauri! ,Ƴan matan da ke cikin kitchen ɗin suka kece da dariya ,Amina tace "sai da nace miki kar kije! ,kwanakin nan Sir neman inda zai huce haushinsa yake". Asabe da ke goge goge, tayi ƙwafa tana faɗin "sai kace sanda Madam ɗin takenan ya damu da ita" ,Ameena tace "Wallahi fah nima abin mamaki yakeban" ,Yasira dai bata bi ta kansu ba, ta wuce ta ƙofar baya dake kitchen ɗin, ta nufi shashen ma'aikatan gidan, a zuciyarta tana sake dana sanin zuwa tambayarsa da tayi. Shi kuwa ko a jikinsa, kawai burinsa ta inda Noor zata ɓullo ,wayarsa ce tafara ringing,a hankali ya ɗaga wayan yana kallon mai kiran "Maami" da ya gani ya shashi shafa yalwataccen sumarsa, he has been avoiding her since, dan baisan me zai ce mata ba sam, shahada yayi ya ɗau wayan "sallama yayi daga ɗayan ɓangaren ammi ta amsa tana faɗin "Habibi ina ka ajiye wayarka, I have been trying to reach you but baka picking calls ɗinka, I hope everything is fine there? " shiru yayi kafin ya samu ƙarfin halin haɗa kalmomin bakinsa "maami ya Dubai?" "lfy ƙalau habibi ina Noor" shiru yayi ya kasa cewa komai ,shirun da taji yayi yawa ya sata sake faɗin "Habibi are you there? "Umm...Maami" "are you okay my boy? mai yake faruwa me kake ɓoyemin? I hope you are not trying to hide anything!" "maami babu komai fah don't you believe me" "na yadda da kai mana my boy, to yanzu ina Noor? it has been long tunda mukayi magana da ita, kai mata wayan " A ɗan daburce yace "umm wai Noor ..in kai mata wayan? to ai tayi bacci,batajin daɗine shine sai ta kwanta" "ok shikenan maybe next time Allah ya sauwaƙe ka kira abbun ka, yace yakiraka baka picking " "a hankali yace "insha Allah Maami" daga haka yayi hanging Kiran yana sauƙe ajiyar zuciya. Da sauri kamal ya shigo gidan, hannunsa riƙeda jarida wanda hotonta ke jiki ɓaro ɓaro ,ita kaɗai ya samu a tsakar gidan tana wanke kwanukan da suka ɓata da safe ,yanayin da taga ya shigo ya sata saurin ɗauraye hannunta, tana ƙarasowa tsakar gidan dai dai umma ma ta fito daga ɗakin ta, tana faɗin "Noor Nikam Ina kikaga na ajiye goron da ke cikin ledannan ne? tsayawa tayi tana kallonsu yadda sukayi cirko cirko a tsakar gidan. "Lafiya?" Ta tambaya tana kallon Noor "umma nima wallahi bansani ba, haka naga ya shigo kamar ba lafiya ,umma ta karkata akalar tambayan nata ga kamal da ke tsaye yana kallonsu, miƙa mata jaridar yayi yana faɗin, Abdul ne ya shiga cikin gari ɗazu, shine nace masa ya siyomin jarida dan na karanta, shine fah kawai naga hoton Noor ajiki ,Umma ta karɓa tana dubawa, sai kuma tace to me aka rubuta ajiki? ko yan uwanta suke nemanta? ai dama dole su nemeta!! " Kamal kallonta kawai yake ganin tana ƙoƙarin wucewa ɗaki ya sa yace"Noor!" Ta juyo Amma Bata dawo ba, a hankali yace "bakya tunanin 'yan uwanki suna cikin wani hali na rashin ganinki? kuma haryanzu baki ga buƙatar ki sanar damu komai ba!?" shiru tayi ba tare da tace komai ba, a hankali umma ta ƙaraso inda take ta dafata tace"Noor bana miki kallon ƙasa da abinda na haifa, bakya tunanin idan ke 'ya tace kika bar gida irin haka, hankalin dole ya tashi to bare mahaifiyar ki, Yakamata ki faɗa mana abinda ya rabo ki da gida Noor, ko kina tunanin bamu kai musan damuwarki bane ? da sauri ta girgiza mata kai tana faɗin"umma dan Allah karkice haka, wallahi kun kai kuma har kunfi haka a gurina"ta share hawayen da ya zubo mata tace "insha Allah na muku alƙawari yau zaku san komai game dani, amma ina neman alfarmarku, ku bari zuwa baba ya dawo zuwa dare, ina so na baku labarina a gaban sa "umma ta yi murmushi tana faɗin Allah ya kaimu Allah ya muku albarka "suka amsa da ameen Maimoon# *💖*ABNUR**💖 *By* *maimoon* 🤓 *Elegant* *online* *writers* 📚📖 *Free* *book* *Page* *4* Kamar yadda ta faɗa kuwa, hakan ce ta kasance, bayan sallar isha duk suka taru a ɗakin Baba ,kasancewar Umma ta sanar masa komai , Kamal na shigowa ,Umma ta aikasa ya kira Noor,tunda ya zo ya kirata take jin faɗuwar gaba,shi kuwa dama bai tsayaba, yana kiranta yayi juyawarsa ya koma ɗakin,but zuciyarsa na cike da ɗokin jin labarin nata. Hijab ta sanya, tana karanto addu'a a ƙasan ranta ,tasan yanayin da take ciki yana da nasaba da tuno labarinta da zatayi. a hankali ta ƙarasa ɗakin kanta a ƙasa ,sallama tayi duk suka amsa suna kallon ƙofar ,a hankali ta ɗaga labulen ɗakin ta shiga ,can nesa kaɗan da su ta zauna tana fuskantarsu gabaki ɗaya, a hankali ta gaishe da Baba,ya amsa da fara'a yana tambayar lafiyanta ,ta amsa da ladabi ,kana Baba ya ƙara da cewa "Noor naji komai a bakin Aisha, tacemin yau Zaki faɗamana daga inda kika fito, da kuma dalilin fitowar taki ,naji daɗi matuƙa da kikayi wannan tunanin dan yana da kyau musan hakan ,saboda haka muna sauraranki kuma inaso ki faɗamana iya gaskiyarki". A hankali Kamal ya gyara zamansa yana kallonta ,Umma ma kallonta kawai takeyi,sai da ta share guntun hawayen idanunta, kafin ta fara da faɗin...... WAIWAYE (mafarin labarin) _Garin_ _BAULAWA_ _dake_ _ƙarƙashin_ _jihar_ __Kaduna_Nigeria_ Yarinya ce yar kimanin Shekaru 16 ,doguwa ce sosai ,fara tass kamar balarabiya, fararen ƙafafuwan ta da babu takalmi take tsalle dasu, tana caɓalasu a cikin ruwan daya kwanta a ƙasan saboda ruwan saman da ake kan yi a garin, Gaba ɗaya ta gama jiƙa jikinta,har gashin kanta da yake tare waje guda ta cureshi ,wani irin farin ciki take wanda fuskarta ya kasa ɓoyewa , Yara ne sun kai su shida a zagaye da ita,suna jiƙa jikinsu suna wasa ,ta biye musu kamar wata sa'ar su , duk wanda yake garin ya kwana da sanin wannan hali nata,tana matuƙar son ruwan sama, hakan yasa ko a ina take idan har ana ruwa to akanta yake ƙarewa, kuma abin mamakin shine ko irin zazzaɓin nan na mura batayi idan ta shiga ruwan. Malaman makarantarsu kuwa sunsha dukanta, akan ana aji tana shiga ruwa, amma inaaa gobe ma zata koma har sun haƙora sun ƙyaleta . Ɗaga kanta tayi sama ganin ruwan na shirin ɗaukewa ,ta ɓata fuska sauran yayyafin da ke sauƙa yana sauƙa mata a samar kyakkyawar fuskarta ,a hankali ta kama ƙasan rigarta tana matse ruwan, sannan ta nufi ƙasan bishiyan neem ɗin dake kusa da su ta zaro takalmanta ,ta sanya su ba tare da ta kula yaran da suke cigaba da wasansu,da ruwan caɓalin da ya kwanta ba kawai tayi hanyar gida. A daidai zauren ɗan ƙaramin gidan ta tsaya tana sake matse kayan jikinta ,sai kuma tayi sallama tana ƙarasawa tsakar gidan ,babu kowa hakan ya bata daman saurin faɗawa ɗakinta ta kwaɓe jiƙaƙƙun kayanta,ta canza wasu ,ta buɗe jakarta ta ciro littafan makarantarta ta zauna ta naɗe ƙafafu ta ajiyeshi a gefe, Jin alamar mutum na zuwa kusa da ɗakinnata ya sata saurin buɗewa ta fara karantawa ,ɗaga labulen Nenne tayi tana kallonta,sai kawai tayi murmushi tana faɗin "Noor!" Da sauri ta amsa "na'am Nenne" Nenne ta ƙaraso cikin ɗakin tace "ina jiƙaƙƙun kayan da kika jiƙa" shiru tayi tana kallon Nenne ta ƙasan ido ,a ranta tana addu'ar Allah yasa kar tayi mata faɗa, Ai kuwa kamar Nenne tasan miye a ranta ta soma faɗin "wai Noor meyasa baki san ciwon kanki bane sam,mutum bayi da aiki sai shiga ruwan sama, bakya tsoron sanyi ya kamaki?" Ita dai bata ce komai ba, sai ma wasa da ta shiga yi da takaddar hannunta ,idanunta na cika da hawaye ,dan Allah na gani batason faɗa sam ,tsorata ta yakeyi , Tsagaita wa Nenne tayi da faɗan,sanin halin ƴartata ta ƙarasa kusa da ida tana jawota jikinta,ai kuwa kamar jira take ta rungume ta ta soma kuka, shiru Nenne tayi sai kuma tace "Noor,bawai Ina miki faɗa bane dan bana sonki Ah ah ina miki faɗane saboda babu wanda ya kaini sonki, a yanzu ina tare dake ,watarana ba na nan Noor,banaso ki sha wahalan rayuwa ko bayan raina ,shiyasa nakeso ki san ciwon kanki tun yanzu,Noor ko babu komai watarana aure zakiyi ki tafi gidanki ,koh haka zaki je ki masa idan kunyi auren ?" ta tambaya tana murmushi jin bata amsa ba sai ajiyar zuciya da take sauƙewa ,yasa Nenne cigaba da magananta dan tasan ba amsawar zatayi ba , "Kina jina Noor"Nenne ta faɗa tana shafa kanta ,girgiza mata kai tayi ,Nenne tace"Noor ko babu aure Akwai mutuwa ,banaso na rigaki mutuwa ki shiga wani haali,da sauri ta ɗago tana rufe mata baki take wasu hawayen suka sauko mata ,ta sake rungume Nenne tana faɗin "Nenne bazaki barni ba, idan har kika mutu nidai binki zanyi,kuma Ni bazan yi aureba har abada". Murmushi kawai Nenne tayi tace "to shikenan naji ,yanzu ki cigaba da karatunki bari naje wani unguwa yanzu na dawo" ,da sauri tace Nenne zan biki ,nan take Nenne ta haɗe rai tace bazaki bini ba kuma idan kika kuskura kika fita a gidannan kafin na dawo zan saɓa miki" ,a hankali ta gyaɗa kai tana faɗin "insha Allahu Nenne " Nenne ta fice a ɗakin ,ita kuma ta cigaba da karatun ta tana tunanin," ina Nenne take zuwa kwana biyunnan da bataso ta sani?" Sai da ta tabbatar Nenne ta bar gidan sannan ta rufe littafin, ta mayar jakanta, ta ɗauko jiƙaƙƙen kayan taje ta shanya ,sannan ta dawo tayi kwanciyar ta a ɗan ƙaramin gadonta ,tana sake tunanin maganganun Nenne, Ita bazata yi aureba har abada, saboda bazata taɓa yadda ,wani yayi mata abinda mahaifinta yayi ma Nenne ba,kowa yasan mahaifinsa amma banda ita,ko kamanninsa bata saniba, sai sunansa da take anfani dashi ,alhalin yana raye ,yana birni yana cigaba da rayuwarsa ,kamar bai san da su ba. _ABUJA_ _NIGERIA_ Murza steery kawai yake, hankalinsa gabaki ɗaya yana kan tuƙin da yakeyi ,a hankali yayi horn a gaban wani babban Duplex house,mai gadi ya wangale masa gate ɗin yana ɗaga masa hannu,bai bi ta kanshi ba, sai ma cusa motar da yayi cikin gidan Yana driving a hankali ,fuskarsa ɗauke da wata ƙasaitacciyar murmushi,tafiya kamar na minti takwas a cikin gidan, ya kaisa parking space ɗin da aka adana dan motocinsa . A hankali ya ƙarasa ciki yayi parking, sannan ta fito daga motar, wani remote ya danna, nan take motar ta ɗagu sama ta jeru a cikin ƴan uwanta da suke hawa hawa ,anan take wata motar daban tayi replacing ɗin waccar, body guards ɗinsa su shida ya kalla yadda suka tsaya suna jiran umurni,bai ce musu komai ba, ya nufi main entrance ɗin gidan, yana taɓa bluetooth ɗin kunnensa ,a hankali cikin murya mai amo ya fara faɗin "then they are all fired" ɗan shiru yayi yana cigaba da tafiyarsa, alamar yana sauraron mai maganan sai kuma yayi ɗan murmushi yana faɗin,"then I will meet you in 3 hours time" daga nan ya kashe wayarsa ,daidai ya iso ƙofar da zai sada shi da main hall na gidan ,security ɗin ƙofar ya sanya sannan ya ƙara sa cikin parlorn yana zama a kan kujera , turarensa na _SHUMUKH_ shi ya kaima su Amina da ke kitchen saƙon dawowarsa, dan tuni ya karaɗe ko ina , da sauri Yasira ta fice daga kitchen ɗin ,kasancewar ita ce in charge na kitchen ɗin ,ɗan nesa dashi ta tsuguna tace " Sir lunch is ready , should I serve you!?" bai ɗago daga danna wayar da yakeyi ba, ya miƙe ya nufi bedroom ɗinsa Yana faɗin "maybe later" da kallo kawai ta bisa . wani ɗaki ya shiga ya jingina da bangon ɗakin yana bin ɗakin da kallo ,cameras ne kala kala ,da kuma hotuna iri iri na nature da na mutane iri iri ,murmushi kawai yayi ya nufi Camera ɗaya ya ɗauka, sannan ya ƙarasa balcony ɗin ya kai Camera ɗin idonsa, sannan ya ɗauki entire area ɗin a hoto ,yana jin matuƙar farinciki, ɗaukan hoto is his passion,he is very proud to be an explorer ,tunanin inda zai je next domin ɗaukan hotunansa yakeyi ,yana buƙatar zuwa guri that is full of nature, but still local, Yana son capturing al'adu da kuma sabbin abubuwa that's why yake neman inda zaije a cikin Nigeria ya gaji da capturing ƙasashe ,so yake ya fito da beauty na ƙasarsa ,ya kamata yayi research yaga ina zaije tourism this time a cikin Nigeria, fita yayi a ɗakin ya nufi ɗakinsa, ya zauna gefen gado yana dialling Numbern Maami, ringing biyu taɗaga tana faɗin "Habibi" a hankali kuma a shagwaɓe yace "Maaami " yadda yayi maganar yasa ta faɗin "and now ,me kake so kuma this time!?",wani murmushi yayi dan yasan Maami ta gama ganesa ,ya shafa yalwataccen sumarsa, da bayida maraba da ta asalin larabawan Dubai, a hankali yace"not much Maami ,kawai suggestion ɗinki nake nema akan wani abu" tace "ok am all ears Habibi, hope dai bawani abu bane ya dameka ko" murmushin ya kuma yi yana lumshe idanunsa sannan yace "not at all ,kawai dai so nake nayi exploring a ƙasata ,Ina so naje tourism somewhere very local but full of nature ,shine nace bana tambayi suggestion ɗin ki ,i know, no one will know better than you do" wani murmushi Maami tayi da har yana iya jiwowa tace " ok then why not Kaduna state well the state is full of nature just the way you like it" shiru yayi sai kuma yace " amma kin manta nace miki local ,Kaduna ai is too polished for what I want" dariya Maami tayi tana faɗin "and what about villages ɗin dake under Kaduna" ɗan shiru yayi sai kuma yace "kamar wanne kenan?" "Wannan kuma you have to research to find out " "okay Maami ,Abbu fah ?" "Abbu yaje finalizing deals da wasu companies a ukraine " "okay then I guess we will talk later" "okay Habibi take care" a hankali yace "sure" sannan ya katse wayar ,ajiyeta yayi ya jawo laptop ɗinsa ya shiga yin research akan Kaduna state , _BAULAWA_ ya sake maimaita sunan ,a hankali yayi murmushi yace "i guess I already got it!" Wayansa ya ɗauka yayi dialing Numbern personal assistant ɗinsa , Yana ɗagawa yace masa "we are going to Kaduna by Wednesday ,so prepare the needful " "yes Sir " taufeeƙ ya amsa ,kashe wayar yayi yana faɗawa kan gadon a hankali ya furta"its going to explore, Allah yasa na samu abinda nakeso a wannan ƙauyen" ,sai kuma ya ƙara murmushi yanajin kamar wani al'amari mai girma na tunkarosa Is it really going to explore!?me zai faru a ƙauyen BAULAWA ,zai samu abinda yake so kuwa !?🤓the story has just begun🤝 *ABNUR* *By* *maimoon* 🤓 *Elegant* *online* *writers* 📚📖 *Free* *book* *Page* *5* *Wednesday* *Abuja Nigeria* Ƙarfe 7:30 dai dai, ya fito daga Gym ɗin dake cikin gidan ,gaba ɗaya ya gama haɗa zufa,Gym wears ne a jikinsa na kamfanin Nike,Wanda ya karɓesa matuƙa kamar dan kwalliya ya sanyasu, a tsanake yake haura steps ɗin duk da kuwa sauri ya keyi ,dan yau zai wuce Kaduna, Amina,Asabe,da kuma,Yasira da suka ɗan buɗe ƙofar kitchen ɗin ,suka bisa da kallon, ajiyar zuciya suka sauƙe a tare,ganin ya gama haurawa, Amina tace"wato kuɗi yayi ne Wallahi, shidai Sir a rayuwar sa ba shida matsalar komai,na farko ga kyau,ga kuɗi, ga iya shiga mai kyau,ke Ni komai yasa gani nake kawai dan kwalliya ya sa su" Asabe ta karɓe tana faɗin "hmm! kawai mata ta rage masa Wallahi shi ke nan ya cika cif-cif" Yasira tace"taɓ Sir kam ko zaiyi aure ba yanzu ba wallahi" Amina ta amshe "to sannu Maami!, kika sani?,wataƙila ma munkusa shan biki ko ba haka ba Asabe?" ta faɗa tana tafawa da Asabe , "aikuwa wallahi idan zaiyi ma ba sani zamuyi ba sai dai muji guɗar ƴan kawo amarya" Asabe ta faɗa tana ƙarasa wanke kwanukan dake cikin sink ɗin , Yasira dai bata sake cewa komai ba ta fice a kitchen ɗin tana wani ɓata rai ,Asabe ta sake tuntsirewa da dariya tana faɗin"kai kaji wahalalliya,wallahi wahala ce Bata isheta ba" Amina tayi ƙwafa tana faɗin "atoh ai ita taga zata iya" suka cigaba da wanke wanke suna taɓa hira. Wanka ya fito ,a gaggauce ya shirya cikin riga da wando na kamfanin _LOUIS_ _VUITTON_ sai da ya gyara sumarsa yanda ya keso,sannan ya gyara gemu da sajensa wanda duk wanda yasan larabawan Dubai yasan yadda Gemu da sajansu yake,sai da ya gama ɓata lokaci a gyaran sannan ya ɗau perfume ɗinsa na _SHUMUKH_ ya feshe jikinsa da shi ,wani button ya danna ,wani drawer ya buɗe wanda takalmansa suke jere ,na different companies _,WHITE ADRIAN ITALIAN SHOES_ ya zaro ya sanya a ƙafafunsa ,ya ƙara danna wani button ɗin wani mini drawer ya buɗe ,Agogo ya cire guda ɗaya ya sanya sannan ya kwashi wayoyinsa da jakan laptop ɗinsa ya fice a ɗakin, Da sauri bodyguard ɗinsa guda ɗaya ya ƙaraso ya karɓi kayan hannunsa yana gaishesa, Taufeeƙ dake tsaye ya ƙaraso shima tare da faɗin"morning Sir". "morning "ya amsa a taƙaice ,buɗe masa mota yayi ya shiga baya ,shikuma ya shiga gaba,ɗaya daga cikin bodyguard ɗin ya shiga mazaunin driver ,sauran kuma suka shiga wata mota daban ,suka fice a gidan, Amina,da Asabe dake leƙen window suka sauƙe Amina tana faɗin ,"to sai kuma sanda muka ganshi, Aljanun sun motsa " Asabe ta ce"kee bari a jiki babu ruwana wallahi" Amina tace "ke ma ai kinsani irin wannan fitar da yayi tunda kika ga Sir Taufeeƙ ,to zasu je yawon ɗauke ɗauke ne ,ai dama tunda naga Sir Taufeeƙ ya zo jiya ya haɗa abubuwan ɗaukan hoto da akwati da komai Na Sir ,nasan to sai kuma mun gansu" Asabe tace "to ai hutareren mu " Amina tace "wallahi Fah " suka koma kitchen, dan dama tun sauƙowar sa sukaji shine yana fita suka fito su leƙa . Kasancewar tsakanin Abuja da Kaduna ,ba wani nisa bane ya sa su tafiyan da mota, ƙarfe biyu saura suna cikin Kaduna, hotel suka wuce, wanda dama Taufeeƙ ya gama shirya komai ,sai da suka tsaya sukayi sallah ,sannan suka ƙarasa , a hankali ya juyo ya kalli Taufeeƙ yace"tomorrow by 8 "zamu tafi ,make sure by 7 waɗancan sun koma Abuja ," a ladabce Taufeeƙ yace "Sir your security matters, da dai anje da su for security purposes". "just do as are told mr" ya faɗa ba tare da ya juyoba , "pardon Sir ,your wish is always my command , za'a yi kamar yadda kace" bai sake cewa komai ba har suka iso ƙofar ɗakin nasa ,da sauri Taufeeƙ ya sa katin ,ƙofan ta buɗe ,sai da ya tabbatar ya gama masa duk wani abun da zai buƙata ,kafin ya bar ɗakin ,ya nufi nashi ɗakin dan shima yana buƙatar hutu. Washe gari tun bakwai ya sallami bodyguards ɗin suka koma Abuja, kamar yadda Zannur ya buƙata , ƙarfe takwas dai-dai ya fito daga ɗakin, ya shirya tsaf cikin ƙananan kaya, kansa sanye da facing cap sai shade a idanunsa , Snickers ne a ƙafansa na kanfanin Adidas ,a hankali yake tafiya Taufeeƙ na biye dashi bayan yaje ya yi checking out daga hotel ɗin ,har packing space ɗin, "pass the key" ya faɗa a taƙaice" Taufeeƙ ya miƙa masa key ɗin a zuciyarsa yana faɗin "shi zaiyi driving kenan" mazaunin driver ya shiga ,sai da Taufeeƙ ya gama saka jakansu da kuma jakan kayan cameras da zasu buƙata, a motan,sannan ya buɗe mazaunin mai zaman banza ya zauna , warming motar yayi sannan ya tada ya fice a hotel ɗin, map Taufeeƙ ya buɗe ya ajiye a gaban motan ,yana ganin directions ɗin daya kamata subi, suna fara shiga garin yayi parking motar ya sauƙa , Taufeeƙ ma ya sauƙa , makullin ya wurga masa ya caɓe ,shikuma ya buɗe bayan motan Camera ya ɗauka ya haɗa komai nata sannan ya koma wajen mai zaman banza , Taufeeƙ yayi murmushi yana shiga mazaunin driver ,a zuciyarsa yana tunanin da alama za'a samu abinda a ke so a wannan garin. Basu wani ƙara tafiya mai yawa ba sukaga hanya ta ƙare mota bazata iya bi ta shiga ba ,sauƙa Taufeeƙ yayi ya dudduba sai kuma ya dawo yana faɗin "Sir i don't think akwai hanya fah da mota zai ƙarasa, sauƙe Camera dake idonsa yayi yace "so!?" Taufeeƙ ya sosa ƙeya ,yace "I guess da ƙafa zamu ƙara sa ,ina ganin ƙauyen is just a little bit ahead, murmushi Zannur yayi ganin yayi capturing butterfly ɗin da yake ɗauka ,ba tare da yace komai ba ya sauƙa a motar da sauri Taufeeƙ yace "Sir zan kira faruƙ yana cikin Kaduna sai ya zo ya juya da motar ,gyaɗa masa kai kawai yayi yayi gaba yana sake kallon ɗan hanyan da zasu wuce ɗin. A firgice ta farka daga baccin daya kwashe ta a zaune ,ta miƙe da sauri tana leƙa tsakar gida ,hasken data gani tarr ne ya sata komawa ɗakin da sauri ta ɗauki jakan makarantar ta ,da roban abincinta tasa goran ruwanta a jaka ,sauri sauri ta fito dan tasan yauma tayi latti,tun asuba ta shirya dan kartayi latti amma gashi sai da tayi latti ,ɗakin Nenne ta leƙa ,taga bata ciki,"to ina Nenne taje da sassafe nan" ganin batada amsa gashi tana sake ɓata lokaci ya saka tai saurin fita a gidan , sauri sauri take tafiya ,dan dai makarantar da ɗan tazara,ganin saurin bazai mata ba yasata kwasa da gudu , Allah Allah take ta isa ,saboda yau ne za'a faɗi mutum ɗaya a duk cikin makarantar da ya samu scholarship ɗin zuwa cikin Kaduna karatu , gwamnati zata ɗauki nauyinsa saboda hazaƙarsa , Tun da ta shigo taga kowa na aji ,aji ta wuce tana sanɗa a ƙofar ajin ta tsaya ganin akwai Malama a ciki ,sai da taga Malamar ta fara rubutu tukun tayi sauri ta shigo , ta zauna a baya ,sannan ta miƙa ma na kusa da ita jakarta ,a haka sukayi ta passing passing ɗin jakar har kujeran gaba ,wanda shine wajen zamanta ,da dabara ta dinga canza wajen zama har ta iso gaba,tana shirin zama kawai Malaman ta jiyo , "Noor!" Malaman ta Kira sunan ta ,da sauri ta juyo " Malaman tace "You Are late again ,right!?" da sauri acikin harshen turanci ,dan kar ta ƙara ma kanta laifi idan tayi venacular tace, "dan Allah Malama kiyi haƙuri ,wallahi makara nayi" ,juyawa Malaman tayi ta cigaba da rubutu tana faɗin "zo ki tsaya a gaban Allo har sai na gama in faɗa miki hukuncinki" tsaya wa tayi tana marairaicewa ,Malama ta sake cewa " kafin na ƙirga uku na ganki a gaban Allo Noor,ɗaya.. ,biyu.." kafin tace uku tayi saurin ƙarasawa gaban Allon ta tsaya, tana kallon duka ƴan ajin, sai da Malama ta ƙara sa rubutun tukun tace "toh yanzu kafin a fara darasi, ina so in sanar da ku ,mutum ɗaya a cikin makarantar nan da Gwamnati ta ɗauki Nauyin karatunta ,bakowa bace face......." Duk ɗalibai suka zuba mata ido ,sai da ta ɗan yi murmushi kafin tace " _NA'IMA_ _RAZAƘ_ _ABDULKARIM_ wacce kuka fi sani da _NOOR_ " . Duk student ɗin suka hau murna dan dai sun san ,she deserve it ,itakam ta kasa ƙarasawa ma ,sai da Malamar tace mata "congratulations" tukun ta ƙarasa da sauri ta rungume ta kawai ta fashe da kuka, Malamar ta shafa kanta tace "karki damu You deserve it Noor,ni dama nayi tunanin haka" a hankali ta ɗago tace" Malama dan Allah ina so zan tafi gida" , "kije badamuwa gobe sai ki dawo congratulations once again" da sauri ta juya ƴan aji na ta mata murna ,tana binsu da murmushi , sai da ta fita daga makarantar tukun tayi wani tsalle tana faɗin "Nenne na samo scholarship zan tafi birni ,ita kaɗai take surutunta tana Allah,Allah ta isa wajen Nenne, "Baiwar Allah" taji an mata magana da sauri ta juya tana kallon wanda yake mata maganan ,saida ta runtse idanunta ta buɗe ganin ɗan birni ,a zuciyarta tana faɗin ,kar dai tun yanzu ne za'a tafi da ita karatun ,ah ah gaskiya ita fah idan ba da Nenne zasu tafi tare ba ,bazata je ba, "Baiwar Allah" Taufeeƙ ya sake faɗa yana kallonta yadda yaga ta wani rufe idanunta da sauri ta buɗe idanunta ta kallesa ,ta marairaice tafara faɗin ,"dan Allah ba yanzu ba ,ai Ni bansan yau za'a tafi ba ,na ɗauka sai na shirya dan Allah ku bari na fara ɗauko Nenne sai mu tafi tare, kallonta kawai yakeyi har ta gama tukun yace " baiwar Allah tambaya nakeyi, a garinnan ko akwai wani waje da za'a iya biya a kwana " shiru tayi sai kuma ta watsa hannunta tace "oho" "kina nufin baki sani ba" "Eh" ta faɗa tana juyawa ta cigaba da tafiya "keeeee" taji an faɗa da wata Muryar da ta tilasta mata juyowa tagako waye dan ta tabbata ba shi ne wanda ya tambayeta ba. #maimoon *ABNUR* *By* *maimoon* 🤓 *Elegant* *online* *writers* 📚📖 *Free* *book* *Page* *6* A hankali ta juyo, tana sauƙe idanunta a kansa,yana tsaye ,tun daga ƙafafuwan sa, take kallonsa, har takai kan fuskarsa,kallonsa kawai takeyi babu kiftawa, bata san yaushe ya ƙaraso kusa da ita ba,sai dai kawai ji tayi yace,"to ko zaki nuna mana gidan mai garin,garinnan?" Sai da ta saita kanta sannan tace "to nidai yanzu wallahi sauri nakeyi,saboda haka ku nemi wani ya rakaku, inada wani abu mai matuƙar muhimmanci a gaba na yanzu haka" bata jira abinda zai ce ba, tayi saurin juyawa tana cigaba da tafiya, Taufeeƙ ya sake baki, yana kallonta,lallai sai yau ya yarda, rashin sani yafi dare duhu,idan ba haka ba,the whole Sir Abubakar shuraim (Zannur)banda,sa kai wanda hausawa suke cewa ,yafi bauta ai ko ganinsa ma wannan bata isa tayi ba wallahi, Shidai ya na tsaye a wajen kamar wani statue, sai da ya kalli ko ina yaga babu alamar mutum sannan ya juya ya kalli Taufeeƙ,da sauri Taufeeƙ ya ce "Sir You don't have to worry, I will manage everything" daga haka ya yi saurin juyawa ganin wani matashi ya tsayar da shi, sai da ya tambaye sa ko akwai gurin kwana na kuɗi, matashin yace babu,kafin yace masa ko zai rakasu gidan mai gari, matashin yace babu damuwa, Sai da saurayin ya rakasu har gidan mai gari, Taufeeƙ ya ce "ɗan saurayi to ko zaka mana sallama da shi mai garin,kafin ya rufe bakinsa mai gari ya fito, yana gyara rawaninsa, matashin yace"gashi nan ma maigarin, Taufeeƙ ya masa godiya shikuma ya juya ya bar wajen,mai gari ya washe baki ganin Larabawa a ƙofar gidansa yana faɗin "ah ah baƙi mukayi,to to to sannunku da zuwa",cikin gidan ya koma ya fito da tabarma,ya shinfiɗa musu,sai da suka zauna sannan Taufeeƙ ya fara masa bayanin dalilin zuwan nasu. Mai gari yayi gyaran murya yana faɗin"dan dai wannan babu wata matsala,dan gurin da zaku zauna kam,amma sai dai fa zaku biya haya". Taufeeƙ yace babu "damuwa,zamu biya ko nawane", mai gari yace "to madalla sai ku tashi in nuna muku wajen". Sai da ya nuna musu inda zasu zauna, Taufeeƙ ya biya,sannan mai gari ya koma gida yana ta murna, ya samu kuɗi. Sai da Taufeeƙ ya gyara yadda zaima Sir Zannur daɗi sannan ya shigo musu da kayayyakin su, shidai bai ce komai ba, dan dai ya je wuraren da suka fi wannan complications, idan dai har zai samu abinda ya ke so, bare nan. A gajiye yake, hakan yasa wanka kawai yayi, ya kwanta, yanajin nishaɗi, daga gobe yakeso ya zaga garin ya gani idan har zai samu abinda yakeso duk da yaga alamar hakan tun daga shigowar sa garin. A take bacci ya ɗauke shi, Taufeeƙ da ya shigo ɗakin bayan shima yaje nasa ɗakin ya shirya, ya buɗe jakan kayansu ya ɗauko bargo,mai matuƙar kyau da taushi, ya lulluɓa masa, ya tsaya ya na kallonsa, "Sir is such a rare gem, samun kamarsa sai an tona gaskiya,yana fata da kuma addu'ar Allah ya bashi mata, wacce zata bashi farin ciki, wacce zata kula da shi,dan he really deserve that, Amma bai san meyasa sam batun aure baya cikin ajenda ɗin rayuwarsa. Fita yayi daga ɗakin, ya ja masa ƙofa ya fito waje, tafiya kawai yakeyi yana kallon garin mai cike da ni'imomi iri-iri,sai yamma ya dawo,a shirye ya gansa tsaf da alama fita zaiyi yace "Sir zakaga garin ne" "eh" kawai yace ya sa kai ya fice, shima ya bisa a baya, sai da suka zaga garin sosai, sai da sukayi sallar isha, sannan suka dawo gida,a gaskiya garin yayi masa ba kaɗan ba,yasan zai samu abinda yakeso a nan. Daga gidan mai gari aka kawo musu lafiyayyen abinci,har da su kaza, Taufeeƙ ne kaɗai yaci, shi kam kwanciya kawai yayi, daga haka bacci ya ɗauke shi Ita kam Noor tunda ta koma gida,tundaga tsakar gida take ƙwala kiran "Nenne,Nenne,burina ya cika,rayuwarmu ta kusa canzawa Nenne,ganin Nenne bata fito ba ya sata ƙarasawa ɗakin,da sauri Nenne dake kwance tana fitar da numfashi da ƙyar, ta juya mata baya,dan bataso ta fahimci halin datake ciki,amma inaa ta makara, Da sauri ta ƙara so ta tsuguna tana kallon Nenne,hankali tashe ta soma faɗin "Nenne baki da lafiya ne, me ya sameki Nenne na", cikin ƙarfin hali Nenne ta riƙe hannunta sannan ta shafa kanta tana faɗin,ki kwantar da hankalinki,babu komai fah kawai zazzaɓi ne yake damuna tun safe,kuma naji sauƙi sosai",Noor ta sauƙe ajiyar zuciya,tana faɗin Alhamdulillah, ai nazata ciwonki ya tashi", Gyara zama tayi ta riƙe hannuwan Nenne duka biyu tana faɗin "Nenne na samu scholarship,gwamnati zata ɗau nauyin karatuna a cikin gari", Nenne ta faɗaɗa murmushinta tana faɗin "masha Allah, Allah yayi miki albarka Noor,ya haɗaki da alkhairi ko bayan raina", Noor bata wani kula da batun Nenne ba ta miƙe tana faɗin, "Gobe ranar bikin shekara,dole ma na je na binciko abinda zan ci ado gobe dashi", ta faɗa tana miƙewa tabar ɗakin, Ai kuwa ranar batayi bacci da wuri ba,sai kai komo take tsakanin dakinta,da ɗakin Nenne, sai wajen ƙarfe sha biyu tukun tasamu bacci ya ɗauke ta a ɗakin Nenne, kallonta kawai Nenne takeyi yadda take baccinta,a nutse,tana fata da addu'ar Allah ya bawa ƴar ta kyakkyawar rayuwa,mai ƴanci ba irin nasu ba,shafa kanta tayi,sannan ta mata addu'ar bacci ta shafa mata,itama ta lumshe ido,take bacci ya ɗauke ta. Washegari tun safe ta shirya acikin uniform ɗin ta na boko,sai lokacin waɗannan mutanen jiyan suka faɗo mata,to me ya kawosu ƙauyen su,more especially ɗayan ma,yayi mata kwarjini da yawa,ko me zasu je yi a gidan mai gari, da wannan tunane tunanen ta gama shirinta tsaf ta yi ma Nenne sallama, ta fice a gidan,dan dai yau batayi latti ba, Tun safe Sir Zannur yake zaga garin, Taufeeƙ dai binsa kawai yakeyi,idan yaga abinda ya birgesa sai ya ɗauka a hoto,mutanen ƙauyen sai kallonsa sukeyi, wasu samari yaga sun zuba masa ido,ganin irin kallon da suke masa ya sa shi ƙara sa wa inda suke yace "sannunku" , da sauri ɗaya yace sannu bawan Allah,kafinma ya sake magana duk suka taso suka zo kusa dashi,suna masa sannu, murmushi yayi yace "in ɗauke ku hoto!? Ya tambaya yana ƙoƙarin sakewa da su,da sauri suka ce "eh" ai kuwa suka hau jeruwa, ya ɗauke su yana nuna musu, ai kuwa sai yaga mutane sunata ƙaruwa, wai suma a ɗauke su. abin har ya bashi dariya, harda tsofaffi gyarawa yayi yana ta ɗaukansu a hoto,yana ɗan yin baya,don ya samu capturing abinda yake so, buge mutum ɗin dayayi garin komawa bayanne ya sashi saurin juyowa yaga waya buge, bai sani ba, ita kam da har ta kai ƙasa, kasa ɗagowa tayi, a hankali ya ƙarasa wajenta ya miƙa mata hannu,ɗaga kai tayi ta kalleshi,tabi hannunsa da yake miƙa mata da kallo, miƙewa tayi ba tare da ta kama hannun nasa ba, tana karkaɗe jikinta, A hankali yace "meyasa kina tafiya bakya kallon gaban ki" Da batayi niyyan kulasaba, amma jin abinda yace ya saka juyowa ta kallesa da kyau sannan ta maimaita abinda ya faɗa sai kuma tace"malam sai kuma aka ce maka, kai ka dinga tafiya da baya da baya akan layin da ba siya kayi ba ko" Kallonta ya tsaya yi,sai yanzu ma ya gane ta da sauri Taufeeƙ ya ƙaraso,yana kallonsu, Bata sake cewa komai ba, kawai ta juya tayi wucewarta,baki sake suka bita da kallo, kafin yayi ƙwafa yana juyawa ya bar wajen, Tun da aka tashi school ta dawo gida take shirin bikin shekara da ƙyar ta samu ta gama shirya wa, duk da bata yi kwalliya irin na yan ƙauye ba, sai dai ɗigon kwalli da ta yi guda uku a ƙasan haɓarta,sai fararen lumsassun idanunta da ta sanya wa kwalli, ta fito rass da ita,sai da ta shiga tayi ma Nenne sallama, sannan ta fita a gidan ta nufi wajen bikin shekara wanda ake yinsa duk shekara a ƙauyen,duk wani al'adu nasu za'a yi a wajen. Tana isa wajen ta tarar har an fara, can nesa ta samu ta tsaya tana kalle kalle, Tun shigowar ta wajen ya lura da ita, ya tsaya da ɗaukan hoton da yakeyi yana kallonta,shi kansa bai san dalilin da yasa yake kallonta ba,samun kansa yayi da ɗaukan ta hoto ba tare da ta sani ba, yayi mata yakai kala uku, kafin ta juyo, karaf idanunta ya shiga nashi,kallonsa tayi taga yana ɗaukan ta hoto ai kuwa ta wani murguɗa baki ya ɗauka a haka, sai da ya kalli cikin camera ɗin sai ya samu kansa da yin murmushi kawai,bai sake kallonta ba ya cigaba da ɗaukan abinda ake yi, A ƙarshe aka kira ƴanmata,aikuwa ita da ƙawayenta suka shiga,waƙa aka saka musu na mutan ƙauye,suka hau yin rawar a nutse, a hankali, baya ya koma yana kallonsu, yadda suke rawar a tare suna juyawa, ba ƙaramin burgesa abin yayi ba, hoto ya shiga ɗaukan su,wanda duk nata ya fi yawa a ciki, Ba a tashi taron ba har kusan magrib, duk aka fara watsewa, Taufeeƙ ya ƙara so inda yake a tsaye ya jingina da wata bishiya, yana kallon hotunan, a kan nata ya tsaya yana kallo, yanda ta murguɗa baki da taga yana ɗaukan ta murmushi yasake yi, a zuciyarsa yana faɗin"she is just Soo naive". Taufeeƙ yace "Sir Are we leaving now,Yakamata ka huta fah,". Ɗagowa yayi yakallesa yana jin nishaɗi wanda ya daɗe baiji irinsa ba,ko dan bai taɓa ganin al'adu namu na ƙasar Hausa bane,shi kansa bai sani ba, Batare da ya kalle shi ba yace "kaje zan dawo anjima, ina son na yi wani abu first". Taufeeƙ ya buɗe baki zai yi magana ya ɗaga masa hannu kawai, bai sake cewa komai ba ya juya ya bar wajen. Tsayawa yayi yana tunanin to me ya hanashi komawa gida,what is he waiting for,shi kansa bai sani ba, kamar ance ya ɗaga kansa ya hangeta tana nufo inda yake,ita kaɗaice sai ɗan ƙaramin sanda,da ta riƙe a hannunta tana wasa da shi, tsayawa tayi tana magana da su lantana, sai dariya takeyi, Camera ya ɗauka ya cigaba da ɗaukan ta hoto, yadda take dariyan ya sa ya kasa ɗauke idanunsa a kanta, kamar ance ta juyo kuwa taga, yana ɗaukan ta, a fusace ta taho inda yake, tana kallonsa ta fara faɗin, "malam wai lafiya", sai da ya kalleta kamar bazai yi magana ba sai kuma ya gyara tsayuwa yace, "me kika gani,na Sanki ne da zaki tambayeni lafiya". Da mamaki take kallonsa sai kuma tace "baka Sanni ba, Ni ma ai ba saninka nayi ba, to meyasa kake ɗaukana hoto?, Wani kallo yayi mata sannan yace"sai kuma wa ya ce miki ke nake ɗauka?, saboda ke kaɗai ce, sai ke zan ɗauka?,ga kyawawan ƴanmata nan in rasa wa zan ɗauka sai ke". Sake baki tayi tana kallonsa sai kuma ta juya a fusace zata bar wajen ba tare da ta ce masa komai ba, riƙe hannunta taji anyi, da sauri ta juyo tana kallonsa da mamaki, da sauri ya sake hannun nata yana kallonta da idanunsa da suke sakata jin ta kasa nutsuwa, A hankali cikin lallaɓi yace, "ƙanwata me yake haɗa mu ne kam naga tunda nazo garinnan muke samun matsala da ke", jin a yadda yayi maganan ya sata faɗin"to waya sanine," murmushi yayi sai kuma yace to shikenan tunda baki sani ba, can we be friends? Da sauri ta kallesa sannan ta ce ƙasa ƙasa"Ni bana abota da maza" Kallonta ya ƙarayi,shi dariya ma take basa wallahi, sai kuma yace "kinga Ni baƙo ne a garinnan, ko a garinku bakwa son baƙi ne? Girgiza kai kawai tayi, yace yauwa ƙawata, to yanzu miye sunan ƙawar tawa a hankali ta ce "Noor" "Ni kuma Zannur" ya faɗa yana kallonta,murmushi kawai tayi,sai kuma yace to,yanzu kinga tunda mun zama friends shikenan nima sai ki nuna min garinku koh!?, Gobe insha Allahu zan jira ki sai ki zaga dani in ga garinku, ko bazaki nuna min ba? Ya tambaya yana kallonta, "Zan nuna maka " tafaɗa tana kallonsa, kawai mamaki takeyi daman ashe yana da sauƙin kai?,ai ita gani takeyi, yadda yake da kyau ɗinnan bazai ma kulata ba, A hankali tace "sai da safe dare nayi zan tafi gida, "To ƙawata sai goben zan jira ki anan" Bata sake cewa komai ba ta juya ta wuce abinta,tsayawa yayi yana kallonta, shi mamakin kansa ma yakeji, sai kuma yayi murmushi, yana shafa kansa ya juya ya bar wajen, a zuciyarsa yana tunanin maybe it's because the girl is too naive and tana da innocent face,bai taɓa tafiya da yayi masa daɗi irin wannan ba,yaje ƙasashe da yawa Amma the happiness daya samu a nan is something else, ɗakin Taufeeƙ ya buɗe yaga har yayi bacci, kawai ya ja masa ƙofan ya koma nasa ɗakin sai da wanka, yayi Sallah, sannan ya shirya acikin kayan bacci masu matuƙar taushi, ya kwanta bai daɗe ba bacci yayi awon gaba dashi. Itama hakan ce ta ɓangaren ta tunani tayi tayi dama haka ƴan birni suke da sauƙin kai, ko dai wannan ɗinne ya fita daban,sake shigewa jikin Nenne dake bacci tayi, itama bacci yayi awon gaba da ita. What will happen next is the unthinkable,ƙaddara a ko da yaushe dama akace ta riga fata🤗🤓 *💖 ABNUR 💖* *By* *maimoon* 🤓 *Elegant* *online* *writers* 📚📖 *Free* *book* *Page* *7* Washe gari,haka kawai take jinta cikin farin ciki,wanda har Nenne sai da ta fahimci hakan,amma da ta tambayeta,sai tace babu komai,bata sake ce mata komai ba,ita dai fatanta irin wannan farincikin ya dauwama akan fuskarta. Har taje makaranta ta dawo,murmushi bai gushe a fuskarta ba. Wanka tayi, ta ɗauko riga da zanin ta sanya,tayi ɗigon da ta saba,guda uku a ƙasan haɓarta,sannan ta ɗauko ɗan kwali ta ɗaure tulin gashinta,da bai samu wani isasshen gyara ba. fitowa tayi daga ɗakinta,ta shiga na Nenne,ta sameta, tana ninke kaya,wanda ƙarfin hali kawai takeyi, saboda bata so ta ɗaga ma Noor hankali, idan taci gaba da kwanciya. "Nenne zanje gidansu lantana",sai da ta kalleta da kyau,sannan tace"kar ki kai dare, ki gaishe min da baabarta, "Toh insha Allahu"ta faɗa tana barin gidan,a inda ya ce ta sameshi nan ta nufa, bataga kowa a wajen ba, ta lelleƙa bata ga ko wa ba,kawai taja tsaki tana diddire ƙafafunta. Juyawa tayi,tana ƙoƙarin barin wajen,a ranta tana faɗin, "dama can,ba zuwa zai yi ba, kawai dai ya raina mata wayo ne,itama ina ita ina abota da wannan balaraben, har tana jin ɗaɗi zai faɗa mata yadda birni yake kafin ta tafi karatun da gwamnati ta ɗauke ta" Kamar daga sama taga mutum a gabanta,har ta ɗan tsorata, ta ɗanyi baya,tana dafe ƙirjinta,tana kallonsa. "Kai ƙawata haka kike da tsoro daman?" ya faɗa yana kallonta yana murmushi. Kallonsa tai tayi daga sama,har ƙasa, shigar da yayi ba ƙaramar kyau yayi masa ba. Hure mata ido yayi, yana kallonta yace"kee wannan kallon fah,ko munina kike son ganine!?,ya faɗa yana ɗan dariya. Ai sai ya sake shagaltar da ita, ashe ma kyau ɗin sai yayi dariya ma, can kuma tayi ƙwafa tana kallonsa, tace "Ku a garinku malami ne yake zuwa ya jira ɗalibi dama? Ta faɗa tana wani ɓata rai, Kallonta yayi sannan yace toh"ashe Fah ke Malama tunda ke zaki nuna min gari, to afwan Malama,wannan ɗalibin bazai sake latti ba,ya faɗa yana kama kunnensa. Dariya tayi,sannan tace "shikenan an yafe maka na yau". Godiya yayi sannan yace "shall we" Suka jera suna tafiya suna hira. Taufeeƙ dake tsaye,yana kallonsu, mamaki ya kusa kasheshi a tsaye, Sir Zannur Ne ya sake haka da mace,macen ma ƴar ƙauye,tabbass akwai wani al'amari,amma yana fatan ko miye ne yazo da alkhairi,sannan yabi bayansu yana murmushi, Sun yawata sosai, tana nuna masa abubuwa na birgewa a garin, ko ina suka bi kallonsu ake ana mamakin, a ina Noor tasan wannan Balarabe mai ɗaukan hoton, Wani dutse ya samu ya zauna,yana faɗin"kee bakya gajiya da tafiya ne,gaskiya bazan iya cigaba ba" ya faɗa a shagwaɓe. Dariya ta dinga yi, tana nuna shi "to miye hakan kaman ba wani namiji ba, Ni da nake ƙarama ma kuma mace ban gaji ba sai kai". shagala yayi da kallonta kawai, ganin yana kallonta ya sa ta tsagaita tana faɗin, "to shikenan, in ya so gobe sai in ƙara sa nuna maka koh!? Ta tambaya tana kallonsa, kai ya gyaɗa mata, ita ma gefe ta samu ta zauna, tana kallonsa, sai kuma tace "nima ai na kusa komawa birni" "Haba" ya faɗa yana kallonta,"Allah da gaske gwamnati ta ɗauki Nauyin karatuna a cikin gari" Murmushi yayi yace "congratulations ƙawata". Taufeeƙ ya ƙaraso wajen da suke, da Camera a wuyanshi shima, yana kallon Zannur,gaishesa yayi, ya amsa yana miƙewa tsaye, "To ƙawata we shall talk tomorrow Koh?" Ya faɗa yana kallon ta, Ita ma miƙewa tayi tana faɗin, "Allah ya kaimu", sai lokacin ta gaishe da Taufeeƙ,ya amsa yana murmushi,sannan ya juya ga Zannur yace"Sir shall we?" Bai ce komai ba ya juya ya soma tafiya, shikuma ya bishi a baya. Itama gida ta wuce,kai tsaye,tana shiga gidan, ta samu Nenne a durƙushe a tsakar gidan, da sauri ta ƙarasa,tana faɗin "Nenne me ya sameki, Nenne bata iya cewa komai ba,sai girgiza kanta kawai takeyi,kuka ta soma yi, tana kiran sunan Nenne, sai kuma ta miƙe da sauri ta ɗebo ruwa tazo tana bata, da sauri Nenne ta karɓa tana sha da alama tana buƙatar ruwan, wanke mata fuska tayi, sannan ta taimaka mata suka shiga ɗaki, kuka ta ringayi tana kallon Nenne, Nenne dama baki da lafiya har haka shine kike ɓoyemin, tafaɗa cikin kuka sosai,girgiza mata kai kawai Nenne tayi. miƙewa tayi, da sauri Nenne ta riƙe hannuwan ta tana kallonta,"ki zauna da Ni Noor", "Nenne Ina nan tare dake,zan je in Nemo mai magani ne kar ki damu Nenne na". Duk yadda ta so taje, sam Nenne hanata tayi, haka ta haƙura,amma sam bacci ya ƙaurace mata, a zaune ta kwana riƙe da hannun Nenne da ta samu bacci da ƙyar, sallah kaɗai ta tashi tayi,ta dawo ta zauna. har aka kira sallah,ta miƙe ta ɗauro alwala, sai da tayi nafila tayi raka'a tanul fajr sannan ta gabatar da sallar asuba kamar yadda Nenne ta koyar da ita, tun tana ƙarama. Addu'a tai tayi , kan Allah ya bawa Nennen ta lafiya,sannan ta shafa ta miƙe. Ganin har lokacin Nenne bata farka ba,sai bata tashe ta ba, ta fita tsakar gida, ta gyara ko ina ta share tsakar gidan tsaf,sannan ta share ɗakinta, ta hura wuta ta ɗaura musu ɗumame, sannan ta koma ɗakin. a zaune ta samu Nenne akan sallaya, fuskarka looking so pale,a kusa da ita ta zauna, ta gaishe ta,Nenne ta amsa da ƙarfin Hali tana murmushi,tace yau bazaki je makarantar bane,sai da ta kalli Nenne, idanunta na cikowa da hawaye tukun tace "Nenne ta yaya zan iya zuwa makaranta, bayan halin da naga kina ciki jiya, Nenne jiya naji tsoro...",sai kuma ta kasa ƙarasawa, ta fashe da kuka. shafa kanta kawai Nenne tayi tace Noor Kar kiji tsoron mutuwa, mutuwa dolece, kawai ina fatan ki zama mai juriya akan duk abinda ya sameki. Noor ta katseta tana faɗin"Nenne mubar taɗin mutuwar nan,Nenne tace shikenan mun daina Noor" Ranar dai wuni tayi a gida, tana maƙale da Nenne, a zuciyarta tana tunani ko balaraben can yaje yayi ta jiranta,amma dai a yanzu batada abin da ya wuce kula da Nenne a wajenta. Kamar kuwa yanda tayi hasashe,tun ƙarfe 2 yake tsaye,tun yana tunanin zata zo, har ya fara cire rai, Taufeeƙ dai kallonsa kawai yakeyi. can da ya gaji da tsayuwar ya juya ya kalli Taufeeƙ,kamar zaiyi magana, sai kuma ya fasa, can kuma sai ya sake ɗagowa, yace "Taufeeƙ" da sauri Taufeeƙ yace "Sir" "Is this girl really going to come? Taufeeƙ yayi murmushi yace "ko zan bincika maka gidansu ne Sir" Ɗan shiru yayi sai kuma yace "uhmm... ok I think it will be better, we should check on her" Taufeeƙ ya ɗan gyara tsayuwar sa yace "Sir amma zan iya tambayanka please if u won't bother" ɗaga kai yayi ya kalleshi sai yace "go ahead" Taufeeƙ ya sosa kansa yace "Sir dama tambayan is too personal zan iya yi? Ya sake tambaya, Zannur daya zuba masa ido yana kallonsa yace "go ahead" "Sir do you have any feelings for the girl.....?" Wani kallo da ya masa yasa sauran magana ya maƙale ya kasa ƙarasawa, da sauri yace "Sorry sir" Sai da yayi ƙwafa alamar ransa ya ɓaci sosai kafin yace "how can You even think of that, dan kawai yarinya tana nuna min garinsu sai kace ko ina da feelings akanta. I think ko da wani ya ce maka zanso mace irin wannan, kai ne mutum na farko da zaka ƙaryata" da sauri Taufeeƙ ya sake faɗin "sorry Sir" bai sake ce masa komai ba but ga dukkan alamu ransa ya ɓaci sosai. Taufeeƙ yace "Sir bari na binciko gidannasu" Da sauri ya ɗagamasa hannu "No need, barta kawai, idan har kai zaka yi wannan tunanin,bansan kuma sauran mutane me suke tunani ba" daga haka ya juya ya bar wajen". Taufeeƙ ya bisa a baya,jikinsa duk yayi sanyi. sai da sukayi sallar isha sannan suka koma gida, but duk hankalinsa na kan me ya hanata zuwa Juyawa yayi ya kalli Taufeeƙ sai kuma yace "ummm...mr, can You look for the girl's house yanzu,Yakamata mu duba ko bata da lafiya ne?" da sauri yace "sure" sannan ya miƙe ya fice, shikuma Camera ɗin sa ya ɗauka yana kallon hotunan da yayi mata sanda tazo nemansa bata gansa ba. Taufeeƙ bai wani sha wahala ba ya gano gidan ya dawo ya sanar dashi miƙewa kawai yayi yace "muje" Taufeeƙ ya bisa a baya amma ya kasa daina kokon to a ransa, but yanzu ya yarda ba sonta yake ba maybe kawai, tausayinta yakeji,ganin bayi da amsa kuma bayi da hurumin tambaya ya sashi kawar da tunanin daga ƙwaƙwalwarsa. A ƙofar gidan ya tsaya,yana tunanin ta yadda zasu yi magana da ita, gashi har kusan 9 o'clock duk da garin har yanzu akwai sauran mutane,but babu yara da zai iya tura wa ciki Juyawa yayi ya kalli Taufeeƙ sai yace "jirani ina zuwa",daga haka ya kutsa kansa tsakar gidan,tsayawa yayi yana ƙare ma tsakar gidan kallo dake ɗauke da ɗakuna biyu kacal. Fitowa tayi daga ɗakin Nenne da kwanon da suka ci abinci,duk da da ƙyar Nenne taci kaɗan, idanunta duk sun kumbura saboda kukan da tai tayi, "wayyo Allah na!" ta faɗa tana ƙoƙarin komawa ɗakin da sauri ya riƙe hannunta yana faɗin "ke nine,babu wanda zan aiko ne shiya sa na shigo, abokinki ne". Tsayawa tayi da zille zillen da takeyi tana kallonsa, sai kuma tace "mai ya kawoka gidanmu" Tsura mata ido yayi yana kallonta,yadda idonta ya kumbura,duk da babu wadataccen haske,amma hasken farin wata na bashi daman ganinta , "me ya sameki,baki zo ba,nayi ta jiranki" Kuka ta fashe da shi tana faɗin "Nenne ne batada lafiya" "Ok stop crying, zata samu lafiya, me ya sameta" Nima ban saniba,tunjiya take wani irin numfashi,ɗazu har aman jini tayi" "Subhanallahi"muje na ganta Da sauri tace "ah ah.... " Bai saurari me zatace ba ya nufi ɗakin da ya ga ta fito,da sauri tabi bayansa. Akwance suka samu Nenne sai numfashi take yi da ƙyar,da sauri ya ƙara sa wajenta ya durƙusa kusa da ita yana faɗin "sannu mama" Kallonshi tayi a wahale,sai kuma ta juya ta kalli Noor,da sauri ta ƙaraso wajen kafin ma Nenne tace komai ta fara faɗin, "Nenne baƙo ne daga birni ya zo,shine yace in nuna masa gari, to shine yanzu da yaji baki da lafiya,yazo ya gaishe ki". Kallonsa Nenne tayi,sai kuma ta ƙura masa ido,kallon shi takeyi kamar wanda takeso ta gano wani abu,sai kuma tace "nagode" "Allah ya ƙara lafiya," ameen tace a hankali Yana ƙoƙarin miƙewa yaji ta riƙe hannunsa sai kuma tace "Noor ɗan bamu guri" Cike da mamaki, Noor tace "Nenne.." Kallonta yayi yace "kije mana" kamar bazata fita ba sai kuma ta juya a sanyaye ta bar ɗakin, kwanon da ta yar a tsakar gida ta ɗauka ta kai kitchen, ta fito ta zauna tayi shiru,tana tunanin wani magana Nenne zatayi da shi. Yakai minti fiye da 20 sannan ya fito a ɗakin,idanunshi sun kaɗa sunyi jajir. Da sauri ta tashi ta ƙara so inda yake bai tsayaba,sannan bai kalli inda take ba, yayi hanyar fita a gidan,tsayawa kawai tayi tana kallonsa, to me Nenne ta ce masa. Har ya kai ƙofa,sai kuma ya dakata yace "gobe ku shirya zamuje asibiti a cikin gari", daga haka ya fice. Tsayawa tayi tana bin hanyar da ya bi da kallo, ganin tsayuwar bazata fishsheta ba ya sa ta koma ɗakin,a kwance ta samu Nenne, idanunta a lumshe ta zauna a gefenta tana kallonta. Tunda ya koma gida,hankalinsa ya kasa kwanciya, miƙewa yayi ya nufi ɗakin Taufeeƙ,ya samu har yayi bacci, tashinsa yayi,da sauri ya miƙe yana mutsuka idanu ahankali yace "Sir is everything ok" A hankali yace "we will be leaving tomorrow, so ka shirya" da mamaki yake kallonsa amma bai basa daman magana ba ya fice a ɗakin. Cikin dare jikin Nenne ya tsananta, gashi ta ƙi bari Noor tayi Nesa da ita,ƙarfe 3 daidai na asuba Nenne ta cika, da kalmar shahada a bakinta, tana riƙe da hannun Noor. Tashin hankali da ba'a sa masa rana. Mafarin ƙaddara🤗 Maimoon# 💖*ABNUR*💖 *By* *maimoon* 🤓 *Elegant* *online* *writers* 📚📖 *Free* *book* *Page* *8* Innalillahi wa inna ilaihi raji'un,tashin hankali wanda ba'a saka mata rana. Sam Noor Bata fahimci cewa Nenne rai yayi halinsa ba, ganin jikinta ya saki,sannan ta daina motsi,sai ta matso kusa da ita, tana faɗin "Nenne kinji sauƙi ne!?,Nenne kiyi haƙuri da sassafe zamu tafi asibiti,wannan da ya zo ya gaishe ki,yace zamu je asibiti,insha Allahu zaki samu lafiya. Jin Nenne bata amsa ba,sannan bata motsa ba,yasa hankalinta sake tashi,kukan ta ya ƙaru, da sauri ta kama hannuwan Nenne duka biyu ta riƙe ƙam,tana kuka kamar ranta zai bar gangar jikinta,girgizata ta shiga yi tana cigaba da kiran "Nenne na ki tashi,Nenne ki taimaka min,ki tashi,idan baki tashi ba nima mutuwa zanyi. Wani tunani da yazo ranta, ya sa tayi sauran miƙewa ta fice a ɗakin da sauri. Ruwa ta ɗebo ta dawo da sauri tana shafawa Nenne,a tunaninta ko dogon suma tayi,but har lokacin Nenne bata motsa ba. Wani kukan ta sake fashe wa dashi da sauri ta miƙe,fice a gidan,har lokacin kuka take. Gidan Malam Habu,wanda yake maƙwabtansu ta shiga bugawa, duk da dare yayi amma ko tsoro bata ji, dan kusan asuba ne ma a lokacin. Ta ɗan jima tana bugawa, babu ƙaƙƙautawa, kafin Malam Habu,ya buɗe ƴar langa langa kofar yana faɗin "waye ne da talatainin daren nan" Cikin kuka sosai tace "Baba Noor ce". "Ha'a Noor lafiya da darennan me ya faru kike kuka" "Nenne, ce bata da lafiya, kuma ta ma suma,bata ko motsi, dan Allah ka taimaka min. Da sauri Malam Habu yace "subhanallahi muje muga abinda zamu iya yi". komawa ciki yayi da sauri ya taso matarsa Jummai, suka fito tare. A tsakar gida ta tsaya ta kasa ƙarasawa ɗakin,tana jin malam habu da matarsa suna ta salati, kasa gasgata abinda zuciyar ta ke sanar da ita tayi, a hankali tayi baya ta jingina da bango, tana maimata ma kanta "Nenne bata mutuba, batada lafiya kuma zata ji sauƙi". Jummai ta fito a ɗakin idon ta cike da hawaye, gurin Noor ta ƙara sa ta dafa ta tana faɗin"Allah ya baki haƙurin rashi Noor, Nenne rai yayi halinsa,Allah da ya fiki sonta ya karɓi abinsa" Ai bata ƙarasa jin abinda take sanar da ita ba ta yanke jiki ta faɗi a wajen sumammiya. Ƙarfe 7:00 na safe ya fito cikin shirinsa, Taufeeƙ na biye da shi a baya, bayan ya fitar musu da duk wani abu nasu trolley yake ja,yayinda shi kuma Taufeeƙ yake ɗauke da jaka na matafiya da kuma jakan kayan cameras ɗin su, A hankali yake tafiyar amma duk zuciyarsa a cunkushe, "do you really think this is a good idea!?, is this the right step daya kamata ka ɗauka!?" abinda zuciyarsa ke tambayan sa kenan. Da sauri ya furta "wannan shine right step ɗin da ya kamata na ɗauka, idan ba haka I will regret it for the rest of my life" Da mamaki Taufeeƙ ya kalleshi yace "Sir Are You ok" Sai lokacin ya gane ashe a bayyane yayi maganar "i am alright" ya faɗa a taƙaice yana cigaba da tafiya. Dai dai layinsu yaja ya tsaya, yana kallon cincirindon mutanen dake tundaga farkon layin, zuciyar sa ce ta buga da tsananin ƙarfi,da har sai da ya dafe ta, ya juya ya kalli Taufeeƙ ya ce "what's going on there?" Da sauri Taufeeƙ ya amsa da, "I have no idea Sir,but ko na bincika maka...?" kafin ma ya ƙara sa maganan, yaga ya sake trolley ɗin,ya nufi layin cikin sassarfa. Taufeeƙ ya bishi da kallo, shidai daga jiya zuwa yau,he is confused, ya rasa me ke faruwa da Sir Zannur. A dai-dai ƙofar gidan ya tsaya, yana kallon kowa, sai kuma ya ƙarasa wajen wani matashi da ke tsaye can gefe, hannu ya miƙa masa, suka gaisa, sannan ya tambaye sa abinda ke faruwa. cikin alhini saurayin ya fara faɗa masa "wallahi bawan Allah, matar gidan ne Allah ya mata rasuwa jiya cikin dare, abinda zai baka tausayin ma bazai wuce ƴar da ta bari ba. Dama can batada uba, gashi tana da ƙarancin shekaru, ga maman ma ta tafi ta barta,wallahi tun jiyan an kasa gane kan yarinyar, abin tausayi wallahi", ya ƙara sa faɗa yana matso hawaye. Baya yayi yana kallon matashin,kansa na wani irin juyawa,maganar da suka yi da ita jiya kawai yake tunawa,kenan wasiyya ta bashi ko me!? Ya juya ya nufi cikin gidan, bai damu da mutanen da ke kallonsa ba, mata ne birjik a cikin gidan,ya ma rasa ta ina zai fara nemanta,wata tsohuwa dake Zaune akan tabarma tace"yaro lafiya daga ina haka" da sauri ya russuna yayi musu gaisuwa,suka amsa. Kawai sai ya miƙe,dan ya rasa ma me zai ce,fitowa yayi waje ya koma can gefe ya tsaya. Taufeeƙ da ya mayar da kayan su ya dawo,dan yaga alama babu tafiyar,ya ƙaraso wajensa yana tambayansa abinda ke faruwa. "Taufeeƙ ta rasu,ta tafi ta barni da alƙawarin da bansan ta yaya zan fara cikasa ba,I thought zafin ciwo ne ashe wasiyya take bani,ya zanyi,tell me what exactly I should do!? Ya tambaya yana kallon Taufeeƙ,wanda ya sake shiga cikin duhu,dan bai fahimci komai ba a cikin maganganun Sir Zannur ɗin, amma ganin yadda hankalinsa yake a tashe,ya sashi dafasa ya ce "first of all,You have to calm down Sir,kasa a ranka komai muƙaddari ne daga Allah, sannan ko wani step zaka ɗauka, ka tabbatar kayi tunani mai zurfi akansa, though bansan abinda yake faruwa ba,but ina maka fatan ka ɗauki right steps,kuma Allah yana tare da kai, so Please ka kwantar da hankalinka". Shiru yayi,yana sauƙe ajiyar zuciya kawai,bai sake cewa komai ba, but yaji nauyin ya ragu a zuciyar sa, a hankali ya furta "Thank you" "No please Sir,it's always my pleasure,ban cancanci kamin godiya ba Sir,dan komai nayi maka ban biyaka ba" Murmushin ƙarfin hali yayi masa sannan ya juya ya bar wajen. Tare dasu aka kai Nenne gidan ta na gaskiya, har aka watse yana tsaye a kan kabarinta, Taufeeƙ ya ƙaraso wajen sa yace "Sir...." Da sauri ya katse sa " I will meet you outside" Juyawa kawai Taufeeƙ yayi ya bar wajen yana jinjina girman abinda Nenne ta faɗa ma Sir,da ya ɗaga masa hankali har haka. Zama Zannur yayi a hankali,dai dai kabarin, a hankali yace, "Meyasa kika zaɓeni, acikin duk mutane, bayan baki sanni ba,kuma kika tafi kika barni da responsibility mafi girma a rayuwata, Shiru yayi kamar mai jiran ta bashi amsa, sai kuma ya miƙe da sauri. Bai sake waiwaya wa ba, ya fice daga maƙabartar,yana jin wani nauyi a zuciyarsa. Gidan su Noor ya wuce kai tsaye, ga mamakinsa sai yaga babu kowa kamar ba gidan mutuwa ba,ƙarasowa yayi,yana kallon yadda har tabarmar an naɗe, bai gama mamaki ba sai da ya shiga cikin gidan, tsayawa yayi yana kallon tsakar gidan, nan ma babu kowa, mamakin sa yakasa ɓoyuwa. Tsohuwar ɗazu ce ta fito daga ɗakin Nenne tana faɗin "to Allah ya ƙara bamu haƙuri". Ganin fita zatayi yasa yayi saurin faɗin "Granny" juyowa tayi badan ta gane me yace ba,sai dan ganin su kaɗai ne a tsakar gidan, "yaro me ka dawo yi kuma"ta tambayesa tana kallonsa. Cike da mamaki yace"ina kuke tafiya kuma Granny?,naga babu kowa, masu karɓan gaisuwa" Tsohuwar ta kunce zaninta ta ɗauko jan goronta ta gutsura sannan ta kallesa tana faɗin "yaro zaman me kuma za'a yi?, a wannan ƙauye ai ba'a zama, ana kai mutum, shikenan kuma kowa zai kama gabansa,wanda ya mutu ai ya riga ya mutu koh? Ta faɗa tana kallonsa, Baisan sanda ya furta "to ita kuma yarinyar ya zakuyi da ita!?" Tsohuwar ta ƙara kallonsa tana faɗin "ya kuwa zamuyi da ita,wanda ya ga zai iya sai ya aiko mata da abinci, kafin dai ta warware, ai akwai inda Uwar yarinyar take aiki,gidan mai garin garinnan, Ni bance ma ƴar ta sani ba, ita ma sai taje ta dinga yi tana samun abinda zata ci,ah toh kowa ma fama yake da kansa" Ta faɗa tana juyawa tana ƙoƙarin barin gidan. "naga alama kai baƙo ne shiyasa har kake tambaya wai ya zamuyi da ita,to Ni kuwa me zan mata, ai kawai Allah ya bata haƙurin rashin uwa da tayi, ƴar makarantar da take zuwa ma ai yanzu kam ta ƙare". kallonta kawai yakeyi har ta fice tana cigaba da mita. Sai yanzu ya gano dalilin Nenne,shiru yayi yana tunanin wasu irin mutane ne su, sai kuma ya nufi ɗakin da tsohuwar ta fito, yana tafiya a hankali. A bakin ƙofar ya tsaya, yana kallon ɗakin,sai kuma ya ɗaga labulen a hankali ya ƙara sa ciki. A can dungu ya same ta a raɓe, idanun ta sun kumbura sunyi suntum, har lokacin basu daina tsiyayar da hawaye ba,gaba ɗaya ta fita hayyacinta, kallonta yayi na kamar 5seconds, sai kuma ya ɗauke kansa duk da tausayinta da yaji har cikin ransa, A hankali ya tako har gabanta ya tsuguna yana sake kallonta, sai kuma ya yayi gyaran murya, a hankali yace "Noor" Kin ɗagowa tayi, ya sake kiran sunan ta, nan ma bata ɗago ba bare yasa ran zata amsa, Sai da ya sake kira a karo na uku,tukun ta ɗago jajayen idanunta ta zuba masa, wanda sai da yaji har zuciyarsa tayi rawa, saboda yana iya hango tsananin ɗimuwa a idanunta. Cikin rarrashi ya soma faɗin "me yasa kike mata kuka?, kuka a gurin mamaci ba gata bane Noor!,babu abinda Nenne take buƙata a wajenki sama da addu'ar ki,ita kanta bazata so ta ganki a yanda kike ɗin nan ba. Ai kamar ya zuga ta,ta sake fashewa da wani sabon kukan, amma ta kasa cewa komai, rasa yadda zaiyi yayi,kawai sai ya jawota jikinsa ya rungume,Yana bubbuga bayanta,dan yasan she really need a shoulder to cry on, mutuwar mahaifiya ba wasa ba, he can't even imagine rasa Maami, yasan sai ya fita shiga tashin hankali, Sai da tayi kukan ta mai isarta, sannan ya ɗaga ta tsaye, hijab ɗin da ya gani ya sanya mata a saman ɗankwalin kanta,sannan ya kalleta a hankali yace "Nenne tace in tafi dake, zaki bini" ya faɗa yana kallonta. Ɗan dakatawa tayi da kukan tana kallonsa, ya girgiza mata kai. Sai lokacin ta iya buɗe bakinta a hankali tace "Nenne ce tace ka tafi dani?" a hankali ya gyaɗa mata kai. Sunkuyar da kanta tayi, batace komai ba, Shima bai jira ta e komai ɗin ba ya kama hannunta ya riƙe yace muje, yau zamu bar garinnan. ba musu ta bishi har suka fito waje,yana riƙe da hannunta, gida ya wuce da ita,still bai sake hannunta ba, kowa sai binsu yake da kallo, Taufeeƙ dake ƙofar gidan yayi saurin ƙarasowa inda yake yana tambayar sa abinda ya faru "Taufeeƙ pack our things we are leaving right Now" ya faɗa yana jan hanunta ya shiga cikin gidan, da sauri Taufeeƙ ya biyo bayansa yana faɗin,"ai kayanmu Are already packed bari in Kira faruƙ ya kawo mana mota", bai ce masa komai ba ya sake hannunta ya nufi ɗakinsa, Taufeeƙ dai kallonta kawai yakeyi,to me hakan yake nufi?, ganin babu amsa yasa ya shiga ɗakinsa, jakunkunansu ya fito da su ya fitar waje. dandazon mutanen da ya gani a wajen gidan ya sashi tsayawa kallonsu, ƙarasowa yayi yana faɗin "lafiya!?". Wani dattijo yace rufa mana baki, ba gurinka muka zo ba. Taufeeƙ ya buɗe baki da niyyar sake magana, amma sai yayi shiru, ganin Sir Zannur ya fito, hannunsa riƙe da na yarinyar,shima da mamaki yake bin mutanen da kallo, Aikuwa fitowarsa ke da wuya,wajen ya ɗau hayaniya,kowa na faɗan albarkacin bakinsa,shidai har lokacin bai gane me yake faruwa ba, da sauri Taufeeƙ ya ƙarasa wajensa yana faɗin "Sir bansan me ya kawosu ba, na tambayesu sunce wajenka suka zo" Juyawa yayi ya kalli mutanen yana sake haɗe ransa yace "ina sauraranku". wani dattijo ne ya fara magana yana faɗin"asirin ka ne ya tonu, daga mutuwar uwar ƴar nan har ka ɗakkota ka kawo ta gidan ka,ko kayi zaton bama saka ido akan ƴaƴanmu ne". Wani kallo yayi masa,sannan cikin takaici yace "saka ido akan yaranku?,shiyasa kuka barta ita kaɗai duk da ƙarantar shekarunta,abinda baku sani ba shine,a yanzun nan ba sai gobe ba, zan bar garinnan da ita, kuma babu wanda ya isa ya hanani tafiya da ita, saboda wannan wasiyyar mahaifiyar tace" Da sauri Taufeeƙ ya kalleshi kamar yadda kowa ya zuba masa idanu yana kallonsa. Wani tsohu yace"to a wani dalilin zaka tafi da ita,bayan babu abinda ka haɗa da ita,sannan ita ba muharramar ka bace, saboda haka ba inda zakaje da ita. Wani yawu mai ɗaci ya haɗiye kafin yace "to idan ta zama muharrama ta kuma Fah!?"ya faɗa yana kallonsu duka Duk shiru sukayi babu wanda ya masa. Ya nisa yace, yanzunnan ba sai anjima ba, ina so in cika alƙawarin da na ɗauka ma mahaifiyar ta, ina so a ɗaura min aure da Noor" Ba iya ƴan garin da Taufeeƙ ba, hatta Noor dake kuka sai da ta tsaya cak da kukan tana kallonsa, Taufeeƙ ya ƙara so da sauri yana faɗin "Sir" Bai bashi damar magana ba yace "that's my final decision". Jiki a sanyaye wani tsoho yace to ai shikenan, sai mu ɗunguma muje gurin mai gari,idan dai har an ɗaura, kuma mun shaida, babu wanda zai hana ka tafiya da matar ka. Hakan kuwa akayi,gabaɗaya suka nufi gidan mai gari, ba'a wani ɓata lokaci ba aka ɗaura auren _ABUBAKAR SHURAIM_ (Zannur)tare da _NA'IMA RAZAƘ ABDULKARIM_(Noor) akan sadaki Naira dubu hamsin lakadan ba ajalan ba. Gaba ɗaya wajen aka shaida,ita dai Noor bin kowa take da Kallo, meyake faruwa da rayuwar ta ne?,jiya mahaifiyarta ta rasu, yau an ɗaura mata aure, shin mafarki takeyi ko kuwa a zahiri komai yake faruwa?, Miƙewa Zannur yayi,sannan ya miƙar da ita, yana riƙe da hannunta yace "mun barku lafiya" Daga haka ya juya ya kalli Taufeeƙ wanda shima komai yazo masa a bazata, da sauri yabi bayansa,suka bar wajen, tafiya kawai sukeyi babu mai cewa komai,yana riƙe da hannunta yana janta tana binsa Taufeeƙ kuma na biye da su da kayansu, ya goya jakan yana Jan trolley ɗin, har suka iso dai dai inda suka bar motarsu. kasancewar Taufeeƙ ya riga ya kira faruƙ yasa basu jima a wajenba faruƙ ya iso da motar, bai kalli inda take ba ya juya ya shiga baya, Taufeeƙ kuma ya shiga gaba,tsayawa tayi tana kallonsu. Ganin batada alamar shiga motar, yasa Taufeeƙ sauƙa a motar ya buɗe mata baya yana murmushi yace"Madam shall we?" A hankali ta ƙara sa ta shiga Taufeeƙ ya rufe motar,ya koma gaba,faruƙ ya tada motar. shi kansa yasan ba lafiya ba ganin yanayinsu gaba ki ɗaya,amma bayida hurumin tambaya yasa yaja bakinsa yayi shiru, har suka fita a garin ba mai cewa komai sai ma faruƙ da ya gaishe da Sir Zannur, ganin bai amsa ba yasa bai sake cewa komai ba Jinginar da kansa yayi da jikin kujera, yana tunanin abubuwan da suka faru, itakam can dungu ta rakuɓe tana cigaba da kukan ta ƙasa ƙasa. Maimoon🤓# https://www.facebook.com/groups/1627491150723081/?ref=share 💖*ABNUR*💖 *By* *maimoon* 🤓 *Elegant* *online* *writers* 📚📖 *Free* *book* *Page* *9* Ƙarfe 12:40 suka shigo cikin Kaduna,har lokacin babu mai magana a cikin motan. Ɗan juyawa yayi ya kalli sashen da take, sai yaga ashe ma bacci takeyi,yadda take sauƙe ajiyar zuciyar zakasan ba daɗin baccin takeji ba . Ƙwafa yayi,yana juyar da kansa daga kallonta,ya maida kallonsa ga faruƙ da ke ƙoƙarin packing a packing space na hotel ɗin. Sai da duk suka sauƙa,ganin bata fito ba ya sa ya ɗan ja tsaki,a ransa yana faɗin "tun yanzu!? . Baibi ta kanta ba yayi wucewarsa ciki. Taufeeƙ ma da sauri yabi bayan sa,sai da ya gama yin all the needful ya rakashi har ɗakinsa, sannan ya dawo motar da sauri,wanda dama basu rufe da key ɗin ba ganin tana bacci. Buɗe ɗayan ɓangaren yayi,a hankali ya soma buga kujerar yana faɗin "Madam " A hankali ta buɗe gajiyayyun idanunta tana sauƙe numfashi,sai kuma ta juya a sanyaye ta kalli Taufeeƙ dake mata murmushi. Cikin girmamawa,yace "mun iso Ma,kuma Sir yace a ƙaraso da ke" Kallonsa kawai takeyi,yana maganan kamar wacce batasan me yake cewa ba, a hankali kuma wasu siraran hawaye suka sauƙo akan fuskarta,dan yanzu ta tuna ashe fa aure aka mata,sannan Nennenta ta rasu . Sauƙa Taufeeƙ yayi ya ƙara sa ya buɗe mata sashin ta,a hankali tace "nagode" Bai ce mata komai ba,yayi mata jagora tana biye dashi,har ƙofar ɗakin Zannur, sai da ya ɗan tsaya yana tunani,dan bai san ya Zannur ɗin zaiyi reacting ba idan ya kai masa ita,shima da gangan yaƙi kama mata ɗaki,dan yafi so as soon as possible su koyi zama da juna. A hankali yayi knocking a ƙofar ɗakin,sannan ya ɗan matsa ya tsaya yana jira a buɗe,dan dai ya san sau ɗaya ake masa knocking,Dan baya son hayaniya, Har kamar baza'a buɗe ba sai kuma yaji an buɗe ƙofan, kallonsa yayi ganin ya koma ciki,yasa ya dubeta ya ce "muje". Tana biye dashi a baya suka shiga ɗakin,yana zaune a kan gado,har yayi wanka ya canza kayansa zuwa three quarters da Riga na shan iska laptop ne a kan cinyarsa yana operating, ba tare da ya ɗago ba yace "is anything wrong? Da sauri Taufeeƙ yace "Sir, dama,ummm...Madam ce....." dakatawa yayi da danna keyboard ɗin ya ɗago manya manyan fararen idanunsa,aikuwa basu sauƙa akan kowa ba sai a kanta,tana rakuɓe daga bakin ƙofa kamar kace arrrr ta gudu. Maida kallonsa yayi ga Taufeeƙ sannan ya ɗan haɗe rai yace "what the hell is she doing here? me yasa baza ka Kaita room ɗin ta ba?me zata min anan?"ya sake tambaya. Da sauri Taufeeƙ yace "Sorry Sir,but am so sorry to say,all the rooms were booked,shiyasa na kawota nan,but kayi haƙuri,i can vacate my room,in yaso sai ta zauna a ciki". "Better" ya faɗa yana cigaba da danna laptop ɗin, jiki a sanyaye Taufeeƙ ya juya,ita dai kallon sa kawai takeyi,gabaki ɗaya ya canza mata,kamar ba abokinta na ƙauye ba. Har sunje ƙofa zasu fita,sai kuma ya ja tsaki,ya ajiye laptop ɗin sannan ya ce "Taufeeƙ" yadda zai ji shi,da sauri ya dawo yana faɗin "Sir" "Let her stay here" ya faɗa a taƙaice daga haka ya miƙe ya wuce toilet. Murmushi Taufeeƙ yayi,a zuciyar sa yana faɗin "I will try my level best,to unite you both". Koma wa yayi ya sake kiranta, dan har ta fita ita kam, har tsakiyar daƙin ta shigo ta tsaya,sannan Taufeeƙ ya juya zai fita,da sauri ita ma ta juya tana faɗin "umm...tafiya zakayi ka barni a nan". dan dai ita wallahi Zannur ɗin ya fara bata tsoro,dan lokacin da suke ƙauye sam ba haka yake mata ba. Taufeeƙ bai tsaya ba,bare tasa ran zai amsa mata,ganin da gaske fita zaiyi ya sata juyawa da sauri zata bisa,dan gani take gaskiya yafi Zannur ɗin kirki nesa ba kusa ba "Idan kika kuskura, kika sake ɗaga ƙafarki daga wajen, I will know how to deal with you" Taji an faɗa daga bayanta, cak ta tsaya,sannan ta kasa juyowa, lokacin Taufeeƙ har ya fice a ɗakin ya ja musu ƙofa. Bai sake cewa komai ba, shima yayi hanyar fita,hannunsa na ɗan ɗigan ruwa,sannan fuskarsa da leman ruwa,alama dai alwala yayi. Ganin shiɗinma fita zaiyi ya sata saurin biyosa da sassarfa,dan dai baza'a barta a ɗakin nan ita kaɗai ba. Jin alamun mutum a bayansa yasa ya tsaya da tafiyan da yakeyi ya juyo gabaki ɗayansa,fuskarsa a matuƙar ɗaure yake faɗin "where do you think you are going? a tsawace ya sake maimaita"Nace ina zakije da kike biyoni" Da sauri ta toshe kunnuwanta, dan babu abinda ta tsana a rayuwarta irin tsawa,jikinta har rawa yakeyi, ganin yadda tayi ɗin sai ya tsaya kallonta kawai,bai sake cewa komai ba ya juya,ya fice a ɗakin itama bata sake gigin binsa ba, tana ji ya rufe ƙofar ta baya. Sai lokacin ta samu daman ƙare ma ɗakin kallo,tana mamakin irin girmansa da ƙayatuwansa. A hankali ta samu waje a ƙasa ta zauna,wasu hawayen na ture turen zubowa daga idanuwanta, "Allah na gode maka,akan duk yadda ka so ka ga rayuwata, Allah ka jiƙan Nenne, Allah ka bani ikon cinye jarabawar da ka ɗauro min" abinda tayi ta maimaitawa kenan,tana jin zafin dake zuciyarta na raguwa. Tana zaune a wajen har ya dawo daga masallaci,bata ma ji shigowar sa ba,saboda yanda tayi nisa a tunani,ƙarar rufe ƙofan ne ya dawo da ita daga duniyan tunanin, ta bisa da ido. Ledan dake hannunsa ya ajiye a gabanta,sannan in a husky voice yace"kee,tashi kije kiyi wanka, ki cire waɗannan kayan na jikinki,kizo kiyi sallah". "To" kawai tace ta miƙe, amma sai ta rasa me ma zatayi?,ina zata shiga?,juyawa tayi ta nufi inda taga ya shiga ɗazu,har ta kai ƙofa taji yace, "kayan kuma fa" da sauri ta dawo ta ɗauka ta wuce toilet ɗin. Da kyar ta samu ta iya gane yadda ake amfani da toilet, ɗin,sai da tayi wanka da soson da ta gani a toilet ɗin, sannan tayi alwala,ledan ta buɗe tana kallon kayan ciki,zaro su tayi,tana dubawa. Nan ɗin ma da ƙyar ta samu ta saka shi dai dai,tanayi tana duba hoton matar da ke jikin ledan kayan. Gashinta ta warware,sannan ta sake dunƙuleshi kamar yadda ta saba,sannan ya warware ɗankwalin kayan, ba laifi yana da girma,ɗaure gashin tayi dashi sannan da ɗau hijab ɗin da ta cire ta saka. Tunda ta fito daga banɗakin yake kallonta ƙasa ƙasa,ganin ta maida hijab ɗin da ta cire,amma bai ce mata komai ba. Can gefe ta ja ta tsaya tana kallon ɗakin from every direction,ganin bazata iya ganewa ba yasa ta aro jarumta tace "umm dan Allah ina ne gabar,zanyi sallah" Ganin bai kulata ba yasa ta juya ta kalli gefe kawai,zata tada sallah. Miƙewa yayi ba tare da yace mata komai ba,sai da yazo dai dai da ita, sannan ya sa hannunsa a kafaɗunta ya juyar da ita,ta kalli gabar ɗin sannan ya miƙa mata sallaya. Ƙuri tayi masa da ido tana kallon sa ,har ya koma ya cigaba da danna laptop ɗinsa tukun ta shinfiɗa sallayan ta soma sallah. Tunda ta idar da sallahn tana zaune akan sallayan , Taufeeƙ yayi knocking ya tashi ya je ya buɗe ya karɓo abinci,a gabanta ya ajiye ya koma ya cigaba da abinda dake gabansa,da alama abin nada muhimmanci sosai. Amma gaba ɗaya rabin tunaninsa naga yadda zai faɗa ma Maami abinda ya faru, how will she react, shikansa bai sani ba. Har la'asar ya miƙe ya fice a ɗakin,ita ma sai da tayi sallan ganin bai dawo ba yasa ta ɗan jayo ledan abincin ta ɗan ci kaɗan,rufewa tayi ta ajiye a gefe sannan ta miƙe akan sallayan, nan da nan bacci yayi a awon gaba da ita. Bubbuga gefen sallayar da taji anayi shi ya tada ita, a tsugunne ta ganshi gefenta,yana ganin ta buɗe idonta ya miƙe,yana faɗin "ki tashi kiyi sallah", mutsuke idanunta ta shiga yi ta miƙe ta wuce toilet, sai da ta yi tsarki,sannan tayi alwala ta fito,karkaɗe sallayar tayi,ta sake shimfiɗawa sannan tayi sallah,duk abinda takeyi yana kallonta, sai da ta idar yace tashi "kiyi isha", kallonsa tayi sai kuma tace "anyi isha ne?", "Ban sani ba" yace a taƙaice yana zaro wayarsa ya fara dannawa, bata sake cewa komai ba ta miƙe ta yi isha sannan tayi shafa'i da wutiri, sai da tayi addu'a ta shafa sannan tayi kwanciyar ta akan sallayar, Shima bai ce mata komai ba ya gyara kwanciyarsa a kan gadon,sannan ya kai hannu ya kashe wutar ɗakin yana shafa addu'ar bacci(asuba ta gari🥱). Washegari da wuri suka ɗauki hanyan Abuja, duk da baiyi niyyan tafiya a mota ba amma ganin bata taɓa shiga jirgi ba ya sa yace su tafi a mota kawai, Tunda suka iso garin Abuja take kalle kalle, yau gata a birnin da take buri kullum, amma ba tare da Nennen ta ba, a take taji wasu hawaye na shirin zubo mata,kallonta yayi ta gefe, a zuciyarsa yana faɗin "wai Ni wannan yarinyar hawayenta anya bazai ƙareba kuwa". girgiza kai kawai yayi ya juyar da kansa yana kallon window ɗin shima. Tun kafin Taufeeƙ ya gama parking motar,bodyguards ɗin suka ƙara so da sauri, su ka tsaya, da sauri suka buɗe masa ƙofa, suna gaishe shi, a taƙaice ya amsa musu yayi shigewar sa ciki, Ganin basu lura da ita ba yasa Taufeeƙ ƙarasawa ya buɗe mata ƙofan yana murmushi dan yadda yaganta duk a tsorace. Ƙafafuwan ta zuro a hankali,waɗanda suke cikin flat shoes Wanda ya kawo mata tare da kayan jikinta,a hankali ta ƙarasa fitowa tana kallon ƙatoton mansion ɗin da aka kawota, a hankali take bin bayan Taufeeƙ ɗin har cikin main parlour na gidan,inda bodyguards suka riga suka shigo musu da kayayyakin su. Da gudu Asabe da Amina suka fito a kitchen ɗin suna rige rigen ƙarasowa wajen Taufeeƙ,kallonsu yayi yana murmushi yace " kukuma Fah " da sauri Amina tace " Sir Taufeeƙ yanaga kun dawo da wuri, Ni wallahi ban ma san ran dawowan ku nan da wata uku Bama wallahi" ta faɗa tana kallon Noor ta ke tsaye kawai tana kallonsu" "Sai kuma kika ganmu koh" Taufeeƙ ya faɗa yana hawa da kayan Sir Zannur steps ɗin. sai da ya kai ya dawo ya ɗau sauran sannan ya kalli Asabe da Amina yace "ga baƙuwa,ku gyara mata ɗaki a sama, anan zata zauna and ku kula da ita sosai fah, idan ba haka ba ku da Sir Ni dai babu ruwana" ya faɗa da sigar tsokana yana haurawa saman, Har rige rigen ƙarasowa wajenta sukeyi, Asabe tace "sannunki da zuwa baƙuwar Sir" ta faɗa tana murmushi. *💖ABNUR💖* *By* *maimoon* 🤓 *Elegant* *online* *writers* 📚📖 *Free* *book* *Page* *10* Ita dai kallon su kawai takeyi,ba tare da tace uffan ba, kallon juna suka yi sannan suka maida kallonsu gareta, Amina tace "Ni sunana Amina,wannan kuma......" "Asabe". Asabe ta faɗa tana tarar numfashin Amina. Murmushi kawai tayi musu ba tace komai ba. Taufeeƙ da ke sauƙowa ya kallesu yace "wai kun san waye ce ita kuwa kuka ajiyeta a tsaye, nace ku kaita ɗakin sama, baku Kaita ba kun tsaya kuna cika ta da surutu koh" ya faɗa yana ƙarasa sauƙowa "Sir Taufeeƙ dan Allah a ina kuka samu wannan kyakkyawar yarinyar son kowa ƙin wanda ya rasa,wallahi har ta shiga raina" cewar Amina tana murmushi. "Matar Sir Zannur ce" ya faɗa a taƙaice yana nufan ƙofan falon dan dai baya son tambayoyi, dan ya riga ya san halin su Asabe. a ranshi yana ayyana irin zaman da za'a yi a cikin gidan tsakanin Sir da kuma Madam ɗin sa. "Matar Sir ce", maganar daya doki ƙwaƙwalwar Yasira kenan wacce ke fitowa daga kitchen,dan yiwa su Amina magana suje su cigaba da aikinsu, kasa ƙarasowa falon tayi daga bakin kitchen ɗin ta ƙura ma Noor idanu, wacce ke tsaye duk tsayuwar ma ta isheta. Bata gama tantance abinda kunnuwanta suka jiyo mata ba taji Muryar su Asabe dake ta murna kamar waɗanda aka ma bushara da aikin hajji Asabe na faɗin "Sannu da zuwa Madam, wai da gaske ke matar Sir ce,ya ilahi,ina zansa kaina" ta faɗa tana sake kwashewa da dariya kamar taɓaɓɓiya, Duk yadda take jin zuciyarta sai da ta ɗan murmusa ba tare da ta shirya Ba. Amina tace"mun shiga uku, matar gida muka bari a tsaye, Asabe bazaki nuna mata ɗakin ba" ta faɗa cikin rashin sanin abinyi itama murnar ta kasa barinta. A hankali tace"Sunana Noor, kuma ina so in yi sallah, a ina zanyi" ta faɗa tana murmushi Da sauri Dukansu suka fara rige rigen yi mata jagora zuwa ɗakinta, tsaf ɗakin yake, hakan yasa suka barta tayi sallah,suka sauƙo suna cigaba da hirar abin, Asabe tace"anya Sir Taufeeƙ ba wasa yake mana ba kuwa, ya za'a yi Sir yayi aure babu sanarwa babu komai" Amina tace wallahi kamar kin shiga zuciyata,ko Maami ma bazata yarda da wannan auren ba". "Nima haka nake gani" cewar Asabe suna ƙara sa sauƙo wa daga matakalan. Hango Yasira da sukayi yasa suka canza hirar Asabe ta ɗaga murya tana faɗin"wallahi Fah matar Sir kyakkyawa, daga gani zatayi hankali" Amina ta karɓe "kuma wallahi ba ƙaramin dacewa sukayi ba, Allah dai ya barsu tare ya tsole idon maƙiya" ta faɗa tana kallon gefe. Har suka wuce ta bata ce musu komai ba, zuciyarta banda tafasa babu abinda takeyi. "ya za'a kayi min haka?, ya za'a yi ka auri wata ba Ni ba?, kai kaɗai na tanadawa kaina, kai nawa ne Ni kaɗai, dan Ni kaɗai aka halicceka Sir Zannur, bazan taɓa yarda ka zauna da kowace mace idan ba Ni ba,sai dai bayan raina" ta ƙara sa faɗa kamar mai shirin zarewa. Juyawa tayi a fusace ta wuce su Amina a kitchen ta bi ta ƙofar baya ta tafi ɓangaren su, tana tunanin yadda zata ɓullo ma lamarin idan har ya kasance gaskiya ne. Asabe da Amina suka bita da kallo sannan suka ƙyalƙyale da dariya ƙasa ƙasa suna faɗin "a sauƙa lafiya". Tunda suka fita suka barta, ta tsaya tana ƙarema ɗakin kallo, nan ɗin ɗakin ta ne kenan?, ita ce yau zatayi rayuwa a nan ba tare da Nennen ta ba, tabbas mutuwa bata barin wani dan wani yaji daɗi,idan ba haka ba da Nenne bazata mutu ta barta ba, hawayen idonta ta share sannan ta juya ta nufi ƙofan da ta gani wanda tafi tunanin shine banɗaki, shiga tayi ta tsaya tana kallon toilet ɗin. yafi na hotel ɗin da suka sauƙa a Kaduna kyau da girma da tsaruwa nesa ba kusa ba, bata wani sha wahalan yin amfani da toilet ɗinba kasancewar ta gane tun na hotel ɗin hotel ɗin, sai da ta yi wanka ta wanke tsefeffen gashin kanta da shampoos ɗin da ta gani a toilet ɗin,sannan ta ɗauro alwala, sai kuma ta tsaya tana tunanin kayan da zata saka, bathtub ta gani kala kala a banɗakin,haka kawai taji a jikinta shi ake sakawa idan anyi wanka, murmushi tayi ta jawo guda ɗaya mai kalar sky blue tana kallo, sai da ta saka sannan ta sake jiƙaƙƙen gashin kanta a bayanta, ya sauƙa har kusan ƙugunta duk da a jiƙe yake. A hankali ta buɗe ƙofan banɗakin ta fito tana rarraba idanu, da sauri ta ƙara sa wajen ƙofa ta murza key tana sauƙe ajiyar zuciya,a fili ta furta "hmm kawai sai wani ya shigo ya ganni a haka ai da kunya ta kasheni" sake kallon jikinta tayi sai ta rufe fuskarta da hannunta tana ɗan dariya, Duk abinda takeyi yana zaune yana kallonta, a cikin laptop ɗin sa, da yayi connecting da duka cctv cameras na gidan,murmushi kawai yayi ganin yadda ta rufe fuskarta a fili ya furta "silly girl" Amma a cikin ransa yana mamakin kyaun yarinyar ga ta da gashi abinda yake matuƙar so a wajen mace, sai dai shi baya ganin har gaban abada zai taɓa iya zaman aure da ita. rufe laptop ɗin yayi ya miƙe yana kai komo a ɗakin, babban damuwar sa a yanzu bai wuce yadda zai sanar da Maami da Abbu zancennan ba, waya ya ɗauka yayi dialling Numbern Taufeeƙ Yana ɗagawa yace " ina so zuwa gobe ka kai yarinyar can ka yi mata siyayyan kayan anfaninta and banaso ta nemi komai ta rasa i hope you understand" daga ɗayan ɓangaren Taufeeƙ ya amsa da "Yes Sir" katse wayan yayi sannan yayi cilli dashi a kan gado yana kai hannunsa ya ya mutsa lallausan yalwataccen sumarsa, a hankali ya furta "everything will be alright soon". juyawa yayi ya fice a ɗakin gaba ɗaya ba tare da ya ɗau wayan ba. Knocking ɗin da taji a ƙofar ɗakin ya sata saurin mayar da kayan da ta cire, ta ƙara sa bakin ƙofan tana faɗin "waye ne?" jin shiru ya sa ta ƙara sawa, ta murda ƙofan ta buɗe tana kallon wanda ke bakin ƙofar, kallon kallo suka shigayi kafin tayi murmushi tana faɗin "bismilla" daga haka ta koma ciki Sai da Yasira ta haɗiye wani mugun yawu kafin ta yi ƙarfin halin ƙarasawa ciki tana ƙoƙarin yin abin da ya kawota ba tare da ta kwafsa ba. Da murmushi ta dube ta tana faɗin "sannunki da zuwa, Sunana Yasira ni ce in charge na kitchen ɗin gidan nan gaba ɗaya" ta ƙarasa tana ƙura ma Noor ɗin ido A hankali tace "nagode". ɗan shiru Yasira tayi sai kuma tace ko zan iya sanin ke kuma wacece ta faɗa tana sake kallonta. "Bakida hurumin sannin wace ce ita!" da sauri dukkansu suka juya suna kallon mai magana, da mamakin Noor ke kallonsa yayinda Yasira cikin sauri ta shiga faɗin "Sorry Sir i just came to welcome her,am sorry Sir" ta faɗa tana raba idanu Bai ce mata komai ba yaƙarasa cikin ɗakin, zuwa lokacin ƙamshin turarensa na SHUMUKH ya gama cika ɗakin, fuskarsa babu yabo babu fallasa yace "ina so ki haɗa min duka staff ɗin da ke cikin gidannan by 6 o'clock", "Okay Sir" ta faɗa da sauri. "You may leave" ya faɗa ba tare ta ya sake kallon inda take ba. Da sauri ta fice a ɗakin tana waiwayensa. Sunkuyar da kanta Noor tayi tana wasa da yatsunta, zuciyar ta na wani irin bugu, dan gaba ɗaya ya canza mata daga wanda ta sani a da. Taku biyu ya ƙara yana kallonta yace " ƙarfe 6 yayi miki a falon ƙasa, i hope you understand!?. Girgiza kai kawai tayi batare da tace komai ba. Buɗe ƙofar da akayi ya sa duk suka juya suna kallon Asabe da ke ƙoƙarin shigowa, tana turo ƙaramin table ɗin da aka jera abubuwa daban daban akai, wani burki taci tana riƙe handle ɗin, tayan jikin table ɗin suka tsaya cak akan tiles ɗin da sauri ta juya tana dariya ƙasa ƙasa tare da faɗin "Sorry Sir",ai bansan kana tare da Madam ba". daga haka ta juya da sauri ta bar ɗakin, kallo yabi ƙofar da shi sai kuma yayi ƙwafa yana juya wa shima ya fice a ɗakin, ya barta a tsaye tana binsu duka da kallo Da gudu Asabe ta nufi kitchen tana dariya,Amina dake goge plates tace "kee Asabe lafiyarki " "Bari kawai Amina Nikam ai yau naga yadda ake love" ta faɗa tana satan kallon Yasira da ke duba time table ɗin girkin satin. Amina ta ajiye plate ɗin hannunta tana faɗin "fisabilillahi fah, a Ina kika gani" "Hmm ke dai bari wallahi, dana je kaima Madam abinci bansaniba ashe Sir yana ɗakin kekam dai abin ba'a magana " Ta faɗa tana ƙoƙarin ƙular da Yasira ai kuwa haƙar ta, ta cimma ruwa, dan kuwa dangwarar da schedules ɗin girkin tayi, ta bar kicin ɗin tana danne kukan da ke shirin zuwa mata. Amina tace tana ƙoƙarin kwaikwayon Muryar Yasira "Wallahi Sir bazai yi aure yanzu ba" duk suka tuntsire da dariya. Ƙarfe 5:00 dai dai ya shigo ɗakin nata, ganin bai ganta a ciki ba yayi tunanin tana banɗaki, a jiye ledar hannunsa yayi sannan ya zaro takadda a aljihunsa ya ɗaura akan ledan ya juya ya fice a ɗakin. Tunda ta fito take kallon babbar ledan dake kan gadon, ƙarasowa tayi ta na kallon farar takaddar da aka linke ta tsaf, a hankali ta ɗau takaddar tana warwarewa, "Don't make the mistake Of making me wait,make sure 6 ta miki a ƙasa" Ƙara maimaita karantawa tayi sai kuma ta jawo babban ledan tana kallo kayan dake ciki. Dress ɗin take kallo babu ko ƙiftawa, a hankali ta kalli agogon ɗakin ƙarfe 5:31 Da sauri ta warware kayan tana ƙoƙarin sanya su,doguwar rigace irin ta princesses ɗin nan blue colour, sai da ta saka kayan sannan ta warware gashinta da ya riga ya bushe, ta sake naɗeshi kamar yadda ta saba, sannan ta ɗau gyalen kayan mai ɗan girma amma ba sosai ba ta sanya, kallon kanta ta tsaya yi ganin bata da maraba da princess ɗin da take gani a littafan makarantar ta murmushi tayi, nan take hawaye ya kawo idanunta, tayi iya ƙoƙarin ta na ganin ta mayar da su, a hankali ta zura flat shoes ɗinta tana fitowa ɗakin da sauri, ganin six ɗin ya kusa, a hankali take sauƙowa daga kan steps ɗin idanunta nakan inda take sanya ƙafafuwan ta, dress ɗin ta ne ya harɗe ta da sauri tayi baya tana rutse idanunta, jinta a jikin mutum yasa tayi saurin buɗe idanunta tana kallonsa, yayinda ƙamshin turarensa na _SHUMUKH_ ya ke mata maraba a duk ƙofofin hancinta. Da sauri ta miƙe daga jikinsa tana kallon dukkan ma'aikatan gidan da suka zubo musu idanu suna kallonsu, wani kunya taji ya rufe ta, shikam ƙara tsumewa yayi, ba tare da ya sake kallonta ba ya ƙara sa sauƙa a matakalan, itama binsa tayi a baya tana tattare dress ɗinta, Ma'aikatan ne suka shiga gaishesa cikin matuƙar girmamawa, Asabe da Amina da gulma ya kusa kashe su kasa jurewa sukayi sai da suka yi ƙus ƙus ɗinsu,suna dariya ƙasa ƙasa. Yasira kam fashe wa ne kaɗai batayi ba amma ta kumbura tayi suntum, sai ƙwafa takeyi. A hankali ta ƙara so ta tsaya a gefensa tana kallonsa, "have a seat" ya faɗa ba tare da ya kalleta ba, a hankali ta zauna a kujeran dake kusa da nashi tana wasa da hannunta, da sauri duk ma'aikatan suka shiga gaisheta, murmushi kawai takeyi amma ta kasa amsawa, Sai da yayi gyaran murya kafin ya soma magana............. Maimoon🤓# Maimoon🤓# *💖ABNUR💖* *By* *maimoon* 🤓 *Elegant* *online* *writers* 📚📖 *Free* *book* *Page* *11* Do anyone of you have any problem? tambayan da ya fara yi kenan, cikin girmamawa duka suka amsa da "No Sir" "Good" sai da ya ɗan kalle gefen da take, kafin ya mayar da kallonsa a kan dukkan ma'aikatan gidan dake gabansa, "Let me go straight to the point, wannan da kuke gani" ya juya ya kalleta, suma duk juya wa sukayi suka kalleta, kafin suka mayar da kallonsu gareshi. "Amana ta ce!,so ina so ku bata dukkan wani respect she deserves,I hope you understand?" "Yes Sir" suka haɗa baki wajen faɗa. "You may introduce yourselves to her" ya faɗa yana komawa ya jingina da kujera yana latsa wayarsa. Ɗaya bayan ɗaya suka shiga gabatar da kawunansu, tun daga bodyguards ɗin gidan, zuwa masu kula da flowers, masu gadi,masu kula da motoci,masu kula da tsaftace gidan, sannan su Asabe waɗanda sune suke da ragamar komai da ya shafi kitchen ɗin gidan. a dai dai nan Taufeeƙ ya shigo falon, da sauri ya ƙarasa yana faɗin "Sorry Sir, I was late,wallahi..." Ɗaga masa hannu yayi bai ce komai ba, yana cigaba da abinda yake yi a wayarsa, ganin abinda akeyi yasa Taufeeƙ yin shiru,har last person ya gama introducing kansa kafin Taufeeƙ ya karɓa da faɗin "And I am Taufeeƙ Muntasir, his personal assistant, Ni nake kula da duk wani abu na Sir Zannur,kama daga kayan sakawarsa,inda zaije, waɗanda zai haɗu dasu, da sauransu". Ya kai ƙarshen maganan yana murmushi,kallonsu tayi tayi,ba tare da tace komai ba, can kuma ta nisa tace, "Nagode sosai da gabatar da kanku da kuka yi a gareni, Ni sunana Noor, kuma Ni ma...." "What the hell are you trying to say", ya faɗa da sauri har yana ƙoƙarin ƙwarewa yana zare mata ido. Da sauri tayi baya, tana kallonshi itama,ta kasa cewa komai,to miyene a ciki idan ta faɗa musu cewa ita matarsa ce. Taufeeƙ ma da mamaki ya ke kallonsa, da sauri ya juyo ya kalli staffs ɗin sa yace "You may all leave" juyawa sukayi suka fara ficewa a cikin falon suna tunanin to wacece wannan ɗin a wajensa, Taufeeƙ ya bisu da ido har suka gama ficewa, kafin ya juya ya kalli su Amina ya musu alama da ido, da sauri suma suka tashi suka nufi kitchen,Amma harga Allah sunason sanin me ke faruwa. Yasira da ta kasa nutsuwa, ta maƙale dan taji abinda yake faruwa, ganin bata shigo ba yasa Asabe leƙowa tana ɗaga murya tare da Faɗin, "Wallahi Laɓe dai ba kyau ne dashi ba fisabilillahi" da sauri Yasira ta ƙarasa kitchen ɗin, tana tsinewa Asabe a zuciyarta dan tasan Sir ya ji abinda Asaben ta faɗa. Duk da yaji amma bai damu ba, mai da kallonsa yayi ga Noor dake tsaye tana kallonsa a tsorace, "WHO do you think you are? ya tambaya yana matsowa kusa da ita Ɗan matsawa bawa tayi itama ba tare da tace komai ba. Cikin kakkausar murya ya sake faɗin "ki bani amsata, ke wayece a cikin gidannan". Cikin matuƙar shakka da tsoronsa da taji ya shigeta tace "Ni matar....." "Darn it!" ya faɗa yana buga kujerar gefensa, sannan ya ɗago jajayen idanunsa yace "don't ever make that mistake,a duk rayuwarki kar ki kuskura ki taɓa furta ke matata ce, ke amana tace da Nenne ta barmin bayan haka baki da wata matsayi a zuciya ko kuma rayuwata,ina fatan kin fahimta?" da sauri ta gyaɗa masa kai idanunta na kawo ruwa, ta ɗaga kai ta dubi Taufeeƙ da ya sunkuyar da kansa yana jin ba daɗi, he is sure Sir will regret this one day. "Ke me ce ce a wajena?" ya sake jefo mata tambayan yana kafe ta da ido, da sauri tace "Ni amanar kace da Nenne ta baka, bayan haka bani da gurbi a rayuwarka" "Good, from now on, duk abinda kike buƙata ki tambayi Taufeeƙ,I don't think I have anything to do with you". Daga haka ya juya yayi wucewarsa sama ya barta a nan a tsaye. Ƙarasowa Taufeeƙ yayi yana kallonta kafin cikin matuƙar girmamawa yace, "Madam kiyi haƙuri, komai zai wuce, i am sure shi kansa bai san me ya ke so ba,but Ni na san ko shi waye,ba zai taɓa wofintar da rayuwar ki ba. A hankali ta ɗaga idanunta da suka ɗan yi ja kaɗan tana kallonsa sai kuma tayi murmushin ƙarfin hali tana faɗin, "babu komai,Ni kaina bana so na zama komai a rayuwar sa,iya amanan da ya riƙe ma Nenne na ya ishe Ni, kuma bazan daina gode masa ba, bisa taimakon sa a gareni" Daga haka ta juya da sauri tana tattare rigarta ta haura saman ta barshi anan tsaye yana tunani,shima juya wa kawai yayi ya nufi main kitchen na gidan. Karo yaci da Amina dake fitowa daga kitchen ɗin da manya manyan warmers zata kai dining hall, Da sauri ta ja baya tana faɗin"Sir Taufeeƙ kana buƙatar wani abu ne". Murmushi yayi yace "jeki shirya table ɗin sai ki kiramin Asabe, ku sameni a garden akwai maganar da zamuyi Ni da ku". "Ok Sir Taufeeƙ angama, Allah dai yasa da ɗumi ɗumin ta zaka bamu" "Idan kunzo zakuji ai" ya faɗa yana juyawa ya bar wajen. Tunda ta shiga ɗakin ta saka key tafaɗa gadonta tana jin kuka na taho mata amma bata so tayi, dan bata ga dalilin yin su ba, ita kanta sai yanzu take ganin wautar ta da har take ƙoƙarin nuna kanta a matsayin matarsa. Miƙewa tayi ta zare rigar jikinta tana yin cilli da ita "Bazan sake saka rigar Bama,to ma wa yace ya bani rigar, mtsww,ta sake hararar rigar. Miƙewa tayi ta tsaya hankalinta a kwance dan dai ta san ta kulle ƙofar babu mai shigo mata, daga ita sai white clean bra ɗin jikinta da kuma gajeren wando iya gwuiwarta, a hankali ta ƙara sa cikin toilet ta sako bathtub fari tass ta dawo tayi kwanciyarta tana sake tura baki. Rufe laptop ɗin yayi yana jingina da gado,a hankali ya furta "wato ga mai da bathrub kaya" sai kuma yayi murmushi yana lumshe idanunsa,fararen ƙafafuwan ta zuwa gwuiwarta da kuma fararen cikakkun breast ɗin ta da ke cikin bra kawai idanunsa suke hasko masa, Da sauri ya buɗe idanunsa da har sun fara canza kala daga farare tass zuwa ja, hannunsa ya sa ya shafa sumarsa,sannan ya gyara kwanciyarsa a kan gadon yana sauƙe numfashi. Ƙarar wayar sa yasa ya janyota a hankali yana ɗagawa "Habibi me ya ke damunka ne,what's keeping you this busy?" Abinda Maami ta fara faɗi kenan. Cikin kwantacciyar murya mai nuna akwai abinda ke damunsa yace "Maami na!" take Maami ta rikice ta soma jero masa tambayoyi "son are you alright?,am sure you are not, me ya faru? faɗa ma Maami kaji, ko nazo Nigeria?," Cikin son ya kwantar mata da hankali yace "Maami, babu komai fa, but akwai wani magana da nake so nayi dake, a very serious one" Ya faɗa yana lumshe idanunsa "Ina jinka Habibi tell me" "Ba ta waya ba,zanzo Dubai" When? "Next week" "Allah ya kaimu,but you are sure babu abinda ya sameka koh" "Maaamiiiii" Ya faɗa yana jan sunan, Dariya tayi kafin a hankali tace "Habibi bazaka gane ba,I won't be able to do without you, you are my life Habibi". "I know Maami, and you are mine too,Abbu ya dawo daga ukraine?" Ya tambaya da kulawa, "Bai dawo ba but Gobe insha Allah Zai dawo" "Ok Allah ya kaimu" "Ameen" "I guess I will hang up now Habibi, we will talk later okay" "Uhm" ya faɗa ƙasa ƙasa "Okay bye Maami loves you" Bata jira amsar sa ba ta katse wayar ta. Ajiye wayar yayi yana miƙewa dan tafiya masallaci. Yadda suka yi tagumi suka ƙura masa idanu yasa Taufeeƙ ɗan murmushi yana kallon su Amina yace "kai haba duk kallon na me ne ne haka" Cire tagumin Asabe tayi tana faɗin "to Sir Taufeeƙ ba dole ba, tun ɗazu ka kasa faɗa mana maganan da ka kiramu a kai, kuma kasan waccar jarababbiyar yanzu zata fara nemanmu a kitchen". Murmushi yayi sannan ya ce "okay tom kuna jina" suka amsa da "eh" kafin ya cigaba da magana Sai da ya faɗa musu duk abinda ya sani ga me da auren Sir Zannur kafin ya ɗaura da faɗin "Kunsan me yasa na faɗa muku" Girgiza masa kai sukayi mamaki ya ƙi sake su, "Ok,so nake ku ja ta a jiki, ku nuna mata komai,kunga Ni namiji ne, sannan bana tunanin Sir zai nuna mata komai,dan Allah kar ku bari tayi kaɗaici, and kamar yadda kuka sani, mu biyar kaɗai muka sani banda ƴan ƙauyensu, please Kar ku faɗa ma kowa matar Sir ce kunji?" Asabe ce ta sauƙe ajiyar zuciya tana faɗin "ai kuwa akwai shidan mu wallahi". Taufeeƙ yace "waye?" Waye kuwa banda Yasira itama tasan Matar Sir ce, dan sanda ka faɗa mana,ina kyautata zaton taji. Shiru yayi sai kuma yace babu damuwa, na san yadda zanyi da lamarinta ku dai kuyi abinda nace . "Baka da damuwa Sir"suka faɗa a tare. Miƙewa yayi yace "I know I can count on you both nagode sosai" Haba haba Sir Taufeeƙ, ya kana haka, ai duk taimakon kai ne ko ba haka ba Asabe? "Haka take"Asabe ta faɗa tana dariya. Shi dai bai sake cewa komai ba ya juya ya bar garden ɗin, suma miƙewa sukayi suka bar garden ɗin suna jinjina maganan. Yasira dake laɓe ta fito tana murmushi, a fili ta furta, "Sir Zannur zan tabbatar da na mallakeka, kuma wannan shine mataki na farko da zan mallakeka, tabbass na san yanda zanyi anfani da labarin nan in samu abinda nake so". daga haka ita ma tabi bayansu Amina dan dama tun fitowarsu ta biyo su dan tace musu su koma bakin aiki amma ganin inda suka nufa yasa ta bisu taga me zasuyi a wajen. Washegari kamar yadda Zannur yayi umurni haka Taufeeƙ ya ɗauke ta, ya kaita sukayi shopping ɗin duk abinda zata ɓuƙata, kama daga kayan sakawa,zuwan kayan shafa,da ma duk wasu kayan anfani na mata. ganin bata san wasu abubuwan ba yasa ya haɗata da ma'aikatan wajen kasancewar babban supermarket ne na manya, yasa matar ta zage ta kwasa mata komai kamar mahaukaciya, and daɗin daɗawa ce mata da Taufeeƙ yayi she is important to Sir Zannur, kuma shi ya turo su, ai kuwa sun sha shopping kamar na hauka har yamma tukun suka dawo gida. Su Amina su suka shirya mata komai, sannan suka nuna mata yadda ake anfani da komai, duk da yawanci kafin ma su faɗa take karantawa ta gane miye ne sai dai a nuna mata yadda ake anfani da shi. Haka suka saka ta, ta shirya suka zagaya da ita gaba ɗaya gidan, a ranar ta sha mamaki ganin irin girman gidan,wani irin mutum ne shi kuwa? tambayar da ta yi ta yi ma kanta kenan. Zuwa yanzu ta gama sabawa da gidan dan kuwa kwananta shida kenan,amma har ranan bata sake sakasa a ido ba, Taufeeƙ ma sai jifa jifa take ganinsa, su Amina sune abokan hirarta, har kitchen take zuwa ta zauna, suna hirarsu, Yasira kam tsakaninta da ita gaisuwa,idan ta gaisheta ta amsa shikenan babu abinda ke sake haɗata da ita. What? Maami ta faɗa ta ƙarfi tana miƙewa, me kike nufi?, You must be out of your senses, do you want to tell me Habibi yayi aure ba tare da nasani ba!?,wannan ma ai maganar banzace, Shiru tayi tana sauraron mai maganan daga haka ta katse wayanta tana kallon farin balaraben dake gefenta da laptop akan cinyarsa yana operating, idanunsa sanye da fararen medicated glasses. Abbu, kanajin wata maganar banza, wallahi i won't take it,I am leaving for Nigeria tomorrow morning. Ta faɗa zama kusa dashi,ɗagowa yayi ya dubeta sannan cikin kulawa yace "What happened Hilwa!" Wai Habibi yayi aure,ake faɗamin, zancen banza, zancen hofi,Ni nasan hakan bazata taɓa faruwa ba da amincewata ba, saboda haka zan tafi Nigeria,dama ina so inga Habibi, jikina Yana bani Yana cikin wata damuwa. Janyota yayi yana manna mata kiss a forehead kafin yace "ok but ki kwantar da hankalinki,Zannur yana lafiya,and bazai yi aure bada yardar ki ba, so now smile" Murmushi ne ya suɓuce mata,ya shafa kanta yana murmushin shima,shigewa jikinsa tayi tana faɗin "Abbu what if da gaske yayi auren?,kasan Habibi Yana da Zurfin ciki. "Ki kwantar da hankalinki everything that happens is for the best okay,zan sa ayi miki booking flight ɗin don't worry". Ta gyaɗa masa kai tana sake kwantar da kanta a ƙirjinsa, tana tunanin Allah yasa ba da gaske bane dan kuwa bazata taɓa yadda da hakan ba. *💖ABNUR💖* *By* *maimoon* 🤓 *Elegant* *online* *writers* 📚📖 *Free* *book* *Page* *12* _Washegari_ Tun safe Zannur yake jinsa wani iri,ya kasa fita,ko nan da can. ganin ya kasa nutsuwa ya sa ya jawo laptop ɗinsa,yana kallon ta, yadda ta shige cikin bargo ta rufe har kanta. sai kuma ya ja tsaki yana faɗin, "mutum yayi ta bacci tun safe". Yana ƙoƙarin rufe laptop ɗin yaga tayi miƙa tana yaye bargon daga jikinta, sai ya fasa rufewa, ya cigaba da kallon ta, miƙewa tayi zaune a kan gadon tana mutsuka idanunta,sai kuma ta zuro ƙafafuwan ta ƙasa, slippers ɗinta ta sanya kafin ta miƙe, har ta shige banɗaki,kafin ya sauƙe ajiyar zuciya yana shafa sumar kansa a fili ya furta "Ke amana tace, saboda haka dole ne in sa ido akanki" sai kuma yayi murmushi yana rufe laptop ɗin, dan har yaji mood ɗinsa ya canja, yana jin sa cikin nishaɗi, duk da wani sashi na zuciyar sa na fargaba wanda bai san fargabar miye ba. Agogo ya kalla, ganin ƙarfe goma saura minti goma, ya sashi miƙewa shima ya wuce toilet. sai da yayi daɗe a banɗakin kafin ya fito ɗaure da towel a ƙugunsa, cikin abinda bai fi 30 minutes ya shirya tsaf cikin riga da wando na *_Louis Vuitton_* Agogo ya sanya da pcap a kansa duka na *_Louis Vuitton_* sannan ya feshe jikinsa da mayen turarensa na *_shumukh_* slippers ya sa a ƙafan sa shima na *_Louis Vuitton_* sannan ya koma gefen gadon ya zauna,ya jawo laptop ɗinsa Yana dubawa, dan baya tunanin zai fita ko ina. Iska da fara sauƙan yayyafi ya shashi miƙewa yana leƙa waje, ai kuwa sai ruwa ya tsuge kamar da bakin ƙwarya, saurin matsawa yayi daga jikin window,aransa yana tunani yadda za'a yi wasu da basu san ciwon kansu ba har su bari ruwa ya jiƙasu idan ba tsautsayi ba. Komawa yayi ya zauna ya sake jawo laptop ɗin,kai tsaye ɗakinta ya duba ganin bata ciki yasa yayi ƙwafa yana kashe laptop din gabaki ɗaya, ya miƙe ya fice a daƙin, Ɗakin hoto ya shiga yana ƙarasawa ya ɗauki Camera,saboda yana son yin capturing ruwan yanda yake sauƙa, a hankali ya yaye labulen balcony ɗin yana saka Camera ɗin a idanunsa,iskan ruwan na kaɗawa yana sa rigar jikinsa haɗewa da jikinsa . Abinda ya gani ta cikin Cameran ya sashi saurin janyewa daga idanunsa yana ƙura mata idanu, tabbass ba gizo idanunsa ke masa ba, ita ɗince a cikin ruwan sama, baki a sake yake kallonta, yanda take juyi tana nishadi a cikin ruwan, shagala yayi da kallonta, tundaga sama har ƙasa yake yake kallonta, riga da wando ne a jikinta masu laushi na *_Dior_* kanta ta saka band Wanda ya Bama gashinta daman sauƙa ta bayanta, *_Stuart weitzman Cinderella slippers_* ne a fararen ƙafafuwan ta, yanda take dariya ya sa shi mayarda Cameran idanunsa ba tare da ya sani ba. hotuna yayi ta mata ba tare da tasan ma yana gun ba,Dan kuwa babu wanda yake zuwa ta bayan balcony ɗin,shiyasa ma ta je can dan bazata iya ƙin shiga ruwa ba. Ajiye Camera ɗin yayi a hankali ya fice a ɗakin. Hannuwanta ta tara a ruwan ya cika ta watsa a fuskarta,ta sake tara hannun tana shirin watsawa taji an riƙe hannuwan nata, a tsorace ta ɗago, idanunta suka shige cikin nasa,fuskarsa babu alamar wasa,gaba ɗaya ya gama jiƙe jikinsa,ƙirarsa na ƙarfafa ta sake bayyana saboda yadda ruwan yasa kayan ya manne da ƙirjinsa, Kallonta kawai yakeyi ba tare da ya ce komai ba, da sauri ta ƙwace hannunta tana shirin barin wajen dan batasan sam zaizo wajenba, ita bata mayi zaton yana gidan ba,dan rabon ta da shi tun ranan da ya kawota, da sauri ya sake riƙe hannunta, yana jawota gabaki ɗayanta zuwa jikinsa,kasa koda ƙwaƙƙwaran motsi tayi,cikin Muryar da shi kansa bai san yana da ita ba ya soma faɗin "me yasa kike shiga ruwa,bakya tsoron mura ya kamaki?" Ɗagowa tayi ta kalleshi,sai kuma ta sunkuyar da kanta,ta kasa cewa komai, "Tambayar ki nake"ya faɗa a hankali yana dubanta. "To ai Ni ina so,kuma ko a Baulawa ma ina shiga" ta faɗa tana turo baki. "To nan ba Baulawa bane, nan ba'a shiga ruwan sama, idan dai baso kike ki ƙarar min da kuɗina a asibiti ba". "Ni ruwa baya sani rashin lafiya" ta faɗa a shagwaɓe, "I see"ya faɗa ya na sake ta Ai kaman jira takeyi da gudu ta bar wajen,ya bita da kallo yana shafa jiƙaƙƙen sumarsa, su Amina da Asabe da ke leƙe ta kitchen sai tafawa sukeyi duk da basa jin me suke faɗa, Asabe ta ɗaga hannu sama tana faɗin"Allah ka aurar da mu"Amina ta amsa da "Ameen ya Allah muma dai muji me ake ji" suka sake ƙyalƙyalewa da dariya, Yasira da ke tsaye itama ta ɗayan ɓangaren ta ja tsaki, sai kuma tayi murmushi a zuciyarta tana faɗin "komai ya kusa zuwa ƙarshe". kallon jikinsa yayi, yaga yadda yayi sharkaf da ruwa,a hankali ya furta "Yuk" Yana ɓata fuska,sai kuma ya ja tsaki, sam ba abinda yake son ce mata ba kenan, so yayi ya mata faɗa, amma bai san ya akayi harshen sa ya kasa bashi haɗin kai ba,shima juyawa yayi ya bar wajen yana sakin attishawa. Ƙarfe 3:00 ya fito daga ɗakinsa ya sake shiryawa cikin wasu ƙananan kayan,but ya ƙara rigar sanyi akai, sauƙowa yayi falon ƙasa ya zauna yana danna wayarsa. a hankali itama take sauƙowa ta canza kayanta zuwa doguwar rigar abaya ƙafafuwan ta san ye cikin flat shoes na *_Miu Miu_* kitchen ta nufa batare da ta lura da shi ba, a hankali yace "tea" Cak ta tsaya,sai kuma ta juya ta kallesa,ganin idanunsa a lumshe yasa kawai ta juya ta nufi kitchen ɗin, Amina da Asabe na ganinta suka soma gulma ƙasa ƙasa suna dariya, "Ku kuma fa" ta faɗa tana murmushi itama, "Ina kwana Madam" suka haɗa baki wajen faɗa,murmushi kawai tayi. "Ina kwana" Yasira ta gaisheta a daƙile, itama ƙasa ƙasa ta amsa, tana faɗin "Yasira ki haɗa tea, ki saka kayan ƙamshin a ciki, da citta, yanzu ina jiranki ki kawomin parlour". Yasira ji tayi kamar ta fashe ƙasa ƙasa tace"ok ma" Daga haka ta juya ta bar kitchen ɗin. Asabe da Amina suka tafa suna faɗin "wannan irin shiga ruwa na masoya ai dole su sha shayi saboda sanyi" Amina tace "haka abin yake" suka sake kwashe wa da dariya. Ita dai Yasira ko takan su bata bi ba,ta haɗa shayin,ta jera a kan tray mai matuƙar kyau sannan tace "Amina kikai mata" "In kai mata ina?,Ni rufa min asiri, matar gida tace ki kai mata kice in kai mata, ah ah wallhi" Yasira tayi ƙwafa ta suri tray ɗin ta fito, ganin Sir Zannur a falon ya sa ta saita kanta da fuskarta ta gyara tafiyarta, a yangance ta ajiye a kan Centre table ɗin tana kallon sashin da Noor take zaune, itama kallonta takeyi,kawar da kanta tayi tana kallon Zannur tace " Sir should I serve you tea" Itadai Noor kallonta kawai takeyi "don't worry,ki barshi, ki je ki cigaba da aikin ki" ya faɗa ba tare da ya dube ta ba, "ok sir" ta faɗa badan ran ta ya so ba, ta miƙe ta bar wajen, da ido Noor ta bita kawai, Ɗago wa yayi daga danna wayar yace "Are You waiting for me to ask you to serve the tea" Da sauri ta sauƙo daga kujeran tana ɗaukan cup ɗin ta shiga tsiyaya masa shayin. Satan kallonta kawai yake yi yadda take yin komai a nitse,har ta gama ta miƙa masa, yana shirin karɓa wayarsa tayi ƙara, Ganin Maami haka kawai yaji gabansa ya faɗi, ɗagawa yayi tare da yin sallama, "Habibi come and pick me up at the airport" Da sauri ya ajiye cup ɗin daya karɓa yana faɗin "what!!, Maami, wani airport ɗin" "Nnamdi Azikwe International Airport" ta faɗa a taƙaice tana katse wayar ta. Wayar hannun sa ya bi da kallo, sai kuma ya juya ya kalli Noor, ba tare da yace komai ba kawai ya juya ya nufi ƙofa, kallo ta bishi da shi,a ranta tana tunanin anya lafiya kuwa, shayin da ya bari ta ɗauka,sannan ta kira landline na kitchen, tace suzo su maida tea ɗin. daga haka ta haura da nashin a hannunta tana tunanin abinda ya ɗaga masa hankali haka. Maimoon# 💖ABNUR💖 By maimoon🤓 Elegant online writers📚📖 Free book📚 Page 13 Har ya isa Airport ɗin, bai dai na tunanin mai ya ka wo Maami Nigeria all of a sudden ba. A hankali ya ƙaraso in da ta ke tsaye,ta na sanye da abaya, fuskar ta da glass mai kyau,ta fito a Mrs shuraim ɗinta. Rungume ta ya yi ba tare da yace komai ba, sai lokacin ta lura da shi,da sauri ta ɗago kansa ta na kallon sa "Habibi are you Ok?" murmushi ya yi ya ce "babu kawai am happy saboda zuwanki ne" ya faɗa ya na murmushi. Cikin matuƙar farinciki,ta manna masa kiss a both chicks ɗinsa da forehead ta na faɗin "I missed you so much Habibi,mu je gida". Bai ce komai ba ya ɗago daga jikinta,ya na Jan trolley ɗinta,kasancewar bai fito da bodyguards ba. Sai da ya sa a mota, kafin ya zagayo ya buɗe mata ƙofan motan, "my Queen,shall we?" ya faɗa yana nuna mata motar Dariya tayi sosai tana kallon shi, kafin ta shiga ta zauna, shima ya zagaya ya shiga motar, amma gabaɗaya tunaninsa na ga abinda zai faru idan Maami ta haɗu da Noor. Ganin he is carried away ya sa Maami shafa furkarsa ta na faɗin "Habibi are you hiding anything?" Da sauri ya girgiza mata kai,yana faɗin "Maami kin san na ce miki ina son muyi magana idan nazo Dubai!, so tunda kinzo, I will explain everything to you Amma sai kin huta" Ƙura masa ido tayi tana kallonsa,sai kuma ta ce, "nima kai na akwai abinda nake so in tambayeka that is very important, Dan kusan ma shi ya kawo Ni Nigeria, duk da nasan ba zaka taɓa yin hakan ba da amincewa ta ba". shiru yayi yana sauraranta, dan bai kawo ko a ransa ta san da aurenshi ba, to wa ma zai faɗa mata idan ba shi ɗin ba. Motar ce ta kusa kufce masa saboda tambayar da ya jita a bazata "Habibi wai kayi aure ba mu sani ba?" Da sauri ya ja burki da ƙarfi yana duban ta "Who told you this Maami?" "Kar ka damu nasan ba gaskiya bane, wata ce kawai ta kira ni wai ka yi aure but I didn't believe her" ta faɗa tana murmushi "Maami zan faɗa miki komai idan mun je gida" Shine kaɗai abin da ya iya furtawa, zuciyarsa na tafasa, tabbass da ya san waye ya faɗa ma Maami zancennan, sai ya sashi yayi regretting, but yasan yanda zai ɓullo wa Maami, fatan shi kawai Allah ya sa kar Maami ta ɗauka da zafi, dan ya san ta, tana sonshi sosai, amma tana da matuƙar kafiya akan abinda ba ta so. Har suka iso gidan ba wanda ya sake cewa komai, da sauri bodyguards suka buɗe musu ƙofa suna yi ma Maami sannu da zuwa cikin matuƙar girmamawa, hannu kawai ta ɗaga musu, ta wuce, shima ya bi bayanta jiki a sanyaye, A falo ya sameta tana tsaye ta na ƙarema ko ina kallo, "Ƙarasowa yayi yace Maami ki huta sai muyi maganan kinji!" Bata ce masa komai ba ta nufi bene, tsayawa tayi cak,ganin wata kyakkyawar matashiyar budurwa tana sauƙowa,ja baya tayi tana kallon Noor,sai kuma ta juya da sauri tana kallon Zannur Har ta ƙarasa sauƙowa kafin ta lura da waɗanda ke falon, kasa wucewa tayi,sai ta tsaya kawai tana kallonsu, "Ina wuni"ta faɗa cikin in-ina dan dai daga ganin matar kasan itace mahaifiyar Zannur duk da ba wani kama yake da ita sosai ba. Kallonta kawai Maami keyi,tama kasa amsawa,sai kuma ta juya da sauri ta na kallon Zannur "and who is she?"ta faɗa a ƙausashe "Maami pleaaaaase na ce miki za muyi magana idan kin huta please" Cikin tsawa ta katse shi tana faɗin "Habibi who is she?,don't you dare lie to me, wayece wannan?,kuma daga ina take?,me takeyi a sama?" Sunkuyar da kansa yayi dan ya san irin ɓacin ran Maami, idan har bai faɗa mata ba to tabbass ranta ƙara ɓaci zaiyi wanda zai sake ɓata komai. Cikin inda inda yace "my w..i..f.e" "You Are Mad Habibi, ka haukace, how could you? ta faɗa tana zare ido, da sauri kuma ta juya ga Noor da duk a tsorace take da ita. Cikin faɗa tace "me kika yi ma yarona, tell me before I deal with you personally" Ta faɗa tana tunkaro Noor, Da sauri Zannur ya sha gabanta yana faɗin "Maami listen to me,zan faɗa miki komai, pleaaaaase muje ɗakin ki" "Out of my way Zannur" ta faɗa tana kallon cikin idonsa. With suprise Shima yake kallonta, rabonta da ta kira sunansa har ya manta, ya tabbata yau ranta ya kai matuƙa wajen ɓaci. Cikin sauri yace "Maami ki saurareni, she is my wife, but I promise bana sonta, ban taɓa sonta ba, kuma bazan taɓa sonta ba, I only helped her, kuma ke kika ce in dinga taimako Maami!" Wani kallon ka raina min wayo Maami ta ke masa, kafin ta sa hannu ta matsar da shi daga gabanta ta na nufan Noor Ai da gudu Noor ta juya ta koma sama ta shige ɗakinta ta rufe ƙofar da key, dan wallahi ta tsorata ainun da matar, amma maganganun sa sun fi mata ciwo fiye da fushin mahaifiyarsa saboda ta san fushin Maami is justified, dole ranta ya ɓaci. A hankali ta ƙarasa gefen gadonta tana toshe bakinta da tafin hannunta saboda kukan da ke ƙoƙarin cin ƙarfinta Juyowa Maami ta yi ta kallesa sai kuma ta haura sama, ba tare da ta sake cewa komai ba Shafa kansa yayi,dan abin ya wuce yanda ya yi tunani, a hankali shima ya haura ya nufi ɗakin Noor, jinsa a rufe yasa ya wuce ɗakin Maami shima a kulle, bai san sanda yayi murmushi ba ya juya ya wuce ɗakinsa ya na kiran layin Abbu Yasira da ke jin komai, ta yi saurin wucewa ɗakin su ta na jin wani farin ciki, burinta ya kusa cika, Zannur ya kusa zama nata, ta kusa tashi daga in-charge na kitchen, itama ta zama Mrs Zannur Shuraim, da sauri ta rufe ƙofar dan tasan su Asabe suna can baya suna wanke kayansu yau, rawa tayi ta tiƙa tana juyi a ɗakin sai kuma ta faɗa gadon ta na ƙyalƙyalewa da dariya. ***** "Son, meyasa kayi haka, kaima kasan Hilwa batada wanda take so fiye da kai, da baka ɓoye mata ba tun farko zata fahimceka, but zan mata magana,make sure You apologise" Cikin sauri yace "i will Abbu,Wallahi i will,but please talk to her she shouldn't be angry,it hurts" Okay I will talk to her insha Allah, kaje ka samu matarka kuje tare ku bata haƙuri, kasan tayi burin aurenka but ka ɓata mata komai dole tayi fushi" A hankali yace "toh Abbu" duk wannan maganan cikin harshen larabci suke yin sa, Sai da Abbu ya ƙara yi masa nasiha, da nuna masa kuskurensa kafin sukayi sallama,kasa zuwa ya yi sai kawai ya kwanta a dakin ya na jin a little bit of relieve. **** "Hilwa!!" Shiru tayi daga masifan da take ta yi tana mayar masa abinda ya faru, "Hilwa!" ya sake maimaitawa "Abbu bazaka gane ba..." bai barta ta ƙarasa ba yace "na gane i understand you wifey, kawai ina so ne kiji other side of the story, ki tsaya kiji dalilin sa please for me" ya faɗa yana marairaicewa "Why are you blackmailing me emotionally" ta faɗa tana murmushi Shima murmushin yayi dan da alama ta ɗan sauƙo, a hankali yace "cause I know exactly the type of wife I am married to" dariya tayi tana zama akan gadon ba tare da tace komai ba A hankali yace "i missed you hilwa!" "Tun yanzu ai kuwa bazan dawo ba sai nan da 2 month" "You are joking" ya faɗa da ƙoƙarin sata ta manta da duk ɓacin ran ta. "Am serious...." shiru tayi jin ana knocking sai kuma taja tsaki tana faɗin "Ɗan ka da ka turo gashi nan har ya iso" Cikin harshen larabci shima ya mayar mata, "ɗanki dai, Habibi ne Fah kin manta" Batace komai ba ta miƙe ta buɗe ƙofan ta dawo bakin gado ta zauna tana ɓata fuska , A hankali kamar wani Maraya ya ƙaraso ɗakin yana kallonta da fuskar tausayi, har abin ya kusa bata dariya, amma ta gimtse ta ƙi kulawa. Zama ya yi kusa da ita ya kwantar da kansa a kan Cinyarta, har ta ƙarasa wayan ta kashe ta ajiye ba tare da ta kula shi ba, a hankali ya soma magana "Maamiii" bata kula ba Ya cigaba da magana "Maami pleaaaaase an so sorry, please Maami listen to Habibi" Juyar da kanta tayi tace ina sauraron ka Da sauri ya miƙe ya zauna daman he trust Abbu shi kaɗai yasan yanda ya ke sauƙo da Maami duk tsananin fushin da tayi kuwa. A hankali ya soma bata labarin abinda ya faru tun zuwansa Baulawa har kawo yanzu. With shock ta juyo tana kallonsa, sai kuma ta sake haɗe rai tana faɗin "none of my business, Yanzu abinda nake so da kai, kaje ka kira min waccar da kake ikirarin matar kace, kuzo nan yanzunnan" A sanyaye ya buɗe baki zai yi magana ta ɗaga masa hannu tana nuna masa ƙofa, Miƙewa yayi ya fice a ɗakin yana jin kamar ya kurma ihu, ya zaiyi ya mata bayani ne wai. A ƙofar ɗakin ya tsaya, sai da ya ɗan yi jim sai kuma ya soma knocking a hankali, sai da yayi sau huɗu kafin ta buɗe ƙofan Kallonta yayi tayi ganin Yadda idanunta suka yi jajir suka kumbura, Tana haɗa ido dashi tayi saurin juyawa ta koma ɗakin shima shigowa yayi ya jingina da ƙofa ya harɗe hannuwansa yana kallonta, sai kuma yace "kukan me kike yi?" Bata kula shi ba, ta share hawayen da ya zubo mata, ƙwafa yayi a hankali yace "taso ki biyoni" Da sauri ta kallesa, Bai sake kallonta ba ya juya har yakai bakin ƙofa ya juyo yace "zo ki wuce" A hankali ta miƙe ta biyo bayansa, har ɗakin Maami. Maami na ganinsu ta haɗe girar sama da ƙasa tana karkaɗa ƙafanta, Noor kam ta gama tsurewa, ƙirjinta sai dukan uku uku yake. Da sauri ta ƙaraso ta durƙusa, tana faɗin "Maami dan Allah kiyi haƙuri wallahi bazan sake ba" Dariya ce ta kusa kufce wa Maami sai ta miƙe kawai tana faɗin "keee tashi ki tsaya" A hankali ta miƙe ta tsaya tana share hawayenta, Sai da Maami ta ƙara taku biyu zuwa gabanta kafin ta jawota ta rungume gabaki ɗaya tana murmushi, Buɗe idonsa yayi a hankali dan yayi zaton marinta Maami zatayi, da kuwa bazai iya jure gani ba. Da mamaki yake kallon Maami, sai kuma ya sauke wani wawan ajiyar zuciya a ransa yana faɗin "You Are the best Maami na" "Me ya saka ki kuka daughter,is this how to welcome your mother in law?" Ta faɗa tana ɗago ta daga jikinta, kasa cewa komai Noor tayi A hankali Maami ta miƙa masa hannu tana faɗin "come my boy" Ƙara sawa ya yi ya shige jikinta, ta haɗa su duka ta rungume ta na shafa sumar kansa Da ƙyar ya buɗe bakinsa da yayi masa nauyi yace "thank you Maami naa" Ɗago kansa tayi tana kallonsa tace "You know I love you Habibi,so dole ne naso duk abinda ka ke so!, but gaskiya You both have to apologise to me Dan kun rage min burina akan aurennan" Da sauri suka haɗa baki wajen faɗin "We are so sorry Maami" Dariya Maami tayi tana faɗin "You Are pardoned " Sake rungumeta yayi yana ƙara jin tsantsan ƙaunar ta . Ita dai Noor Satan kallonsa kawai takeyi Maimoon🤓# *💖ABNUR💖* *By* *maimoon* *Elegant* *online* *writers* 📚📖 *Free* *book* *Page* *14* Ɗagowa yayi karaf suka haɗa ido da ita, da sauri ta sunkuyar da kanta, sakamakon hararar da ya watsa mata, miƙewa yayi yana faɗin, "Maami, You really scared me"ya faɗa yana ɓata fuska, dariya Maami tayi tana faɗin, "You know Bai kamata na sauƙo yanzu bama, but I have no choise, tunda kun haɗani da Abbu" Dariya yayi sosai yana faɗin, "i trust Abbu shiyasa right away na faɗa masa, gashi komai ya wuce cikin sauƙi" Ita dai Noor ta kasa ɗauke idanunta akansa, yadda ya ke dariyan sai ya sa ta shagala sosai da kallon sa, dan bata taɓa ganin ya na farinciki haka ba. Sake haɗa ido sukayi dashi, ganin ta na kallonsa ya sa shi jan kumatun ta ya na faɗin, "kallon Fah baby!" Sai da ta kusa ƙwarewa, saboda yadda abin ya zo mata a bazata, Maami tayi murmushi tana faɗin, "Wayene ɗazu ya ke cewa 'bana sonta kuma bazan sota ba nikam" sosa kai ya yi yana murmushi, "so you take me as a fool, ta ya ma za'ayi ba zaka so wannan kyakkyawar yarinyar ba, she is more like Arab don't you see? Itadai ta kasa cewa komai, sai kallon sa take da zallar mamaki. Miƙewa ya yi ya na faɗin, "Maami, seriously am starving" ya faɗa ya marairaicewa, Maami ta kalli Noor da ke jikinta har sannan,tace "daughter your husband is starving" a hankali ta ɗago ta kalleshi, sai ya kashe mata ido, ya shafa cikinsa. Miƙewa kawai ta yi ta ce"Maami i will arrange the table sai mu ci abinci, kema bakici komai ba" tana faɗin haka ta juya ta fice a ɗakin, da ido ya bita sai kuma ya shafa kansa ya yi murmushi. Maami ta ce, "zauna Ina son magana da kai" Zama ya yi a ƙasa dai dai ƙafafuwan ta, ya kwantar da kansa akan cinyar ta, a hankali ya furta "ina jinki Maami na" Hannunta ta sa a kansa ta na masa head massage a hankali,lumshe idonsa ya yi saboda yadda yakejin ɗaɗin yadda takeyi ɗin A hankali ta ce "what about her family Habibi,ya zamuyi kenan" Shiru ya yi sai kuma yace "Maami i don't know much, but ita zata faɗa mana ai koh?, Ki bari idan kin huta sai muyi maganan da ita" Jinjina kai tayi ta na faɗin "Ok I think it will be better" Sallama tayi ta shigo ɗakin, Maami tace "daughter sannu fah" Girgiza kai kawai ta yi tana faɗin "the table is ready Maami." Bai so ya kalleta ba, but Sam zuciyarsa ta kasa bashi haɗin kai, ɗagowa yayi ya na kallonta suna haɗa ido ya sake galla mata harara da yasa tayi saurin juyawa zata bar ɗakin Maami ma miƙewa tayi tabi bayanta kafin shima yabi bayansu zuwa dining hall ɗin. Sai da ta yi serving Maami, sannan ta saka nata ta ja kujera ta zauna, dan tana tsoron ta saka masa, ya gwaleta a gaban Maami Har ta saka spoon, zata fara ci, ta ji ya ce "Baby kin manta da Ni ne,I told you am starving" Da sauri ta ajiye spoon ɗin tana kallonsa, Maami dai abincinta kawai take ci, bata kula su ba, Plate ta ɗauka zatayi serving ɗin sa ya yi saurin riƙe hannuwan ta, ya ce "barshi kawai I will eat with you" Ya faɗa ya na matso da kujerar sa kusa da nata, baki a sake take kallonsa ita iya saninta ko a guri ɗaya basu taɓa cin abinci ba bare plate ɗaya. Ba tace komai ba ta koma ta zauna, tana tsakuran abincin, shima kaɗan yaci ya ajiye spoon ɗin, itama ajiye nata spoon ɗin tayi, ta tsiyaya masa ruwa, ƙarba yayi ba tare da yace komai ba, sai da yasha kaɗan ya ajiye cup ɗin sannan ya miƙe "Habibi har ka gama kenan" Maami ta tambaya itama ta na zarar tissue "Yeap Ina so zan ɗan fita but I won't be long" "Okay take care" Bai ce komai ba ya juya ya fice, ita dai Noor da ido take binsa, ta gagara gane shi wani irin mutum ne, sai ta yi ƙoƙarin gane halinsa sai ya sake canzawa completely. Landline ɗin kitchen ta Kira akan suzo suyi clearing ɗin table ɗin kafin tabi bayan Maami da ta wuce sama. ɗakinta ta wuce dan yin sallah, sannan ta bar Maami ta huta, a hankali ta zauna a gefen gado bayan ta idar da sallah, tana tunanin abubuwan da yayi ta yi ɗazu, sai kawai tayi murmushi, miƙewa tayi taje gaban madubi ta na kallon kanta, wasu hawaye taji sun cicciko idanunta, cikin kukan ta shiga furta "Abba ina ka tafi ka barmu Ni da Nenne, gashi Nenne ta rasu ta barni Ni kaɗai, Nenne ta rasu ba tare da ka nemi gafarar ta ba, me ya hanaka dawowa garemu Abbana." Sai kuma ta share hawayenta ta na sake faɗin, "bana buƙatarka har abada, dan dama bansan soyayyarka ba ban taso naji ɗumin kaba, sannan bansan koda kamannin ka ba," Kuka ne ya sarƙe ta ta zube a wajen tana cigaba da kukan gwanin tausayi. Yasira jin shiru shiru, bata sake jin wani hayaniya ba ya sata fitowa falo, a lokacin taga Sir Zannur yana fita a gidan, da sauri ta ƙara sa ƙofar dining hall ɗin tana leƙawa, ganin Noor da Maami suna cin abinci tare, ba tare da wani alama na tashin hankali ba, ya sata ja da baya, a hankali take ja da baya kafin ta ruga da gudu ta koma ɗakinsu, durƙushewa tayi a wajen tana sakin kuka mai sauti, sai kuma ta shiga sumbatu cikin kukan tana faɗin, " wallahi tallahi ina sonka, kuma bazan taɓa yarda na rasa ka ba, kai ne rayuwata, Allah ne ya ɗaura min sonka, kuma bazan taɓa haƙura da kai ba, kamar yadda bazan zauna da kai tare da ko wace mace ba, zan iya aikata koma miye ne dan na mallake ka, koda kuwa ta kama da wani ya bar duniyan nan ne" sai kuma ta share hawayenta tana murmushi ta cigaba da sumbatu kamar zautacciya "ai nayi zaton zai zo min da sauƙi ne shiyasa na kira Maami na faɗa mata, amma yanzu naga alama babban shiri kake buƙata Sir Zannur wallahi, wallahi, wallahi, duk wanda ya shiga tsakanina da farin cikina kwanan shine ya ƙare ta faɗa tana miƙewa a zabure kamar mahaukaciya. Su dai su Asabe basu san me ake ciki ba, suna can baya suna wanki, suna hirar su, gabaɗaya basu ma san da zuwan Maami ba bare haukar Yasira. ******* *_*_ AL RAJWA VILLA'S, AJMAN, DUBAI_*_* Zaune yake a katafaren falon, ya jingina da kujera, da alama yayi matuƙar zurfi a tunani. dafa shi da yaji anyi yasa ya ɗago idanunsa da har sun kaɗa sunyi jaa, farin Balarabe ne kyakkyawan gaske mai cikar kamala sosai. Ammi, cikin harshen larabci, ta soma faɗin, "me yasa bazaka daina uzura ma kanka ba mijina." kallon farar balarabiyar yayi ba tare da ya ce komai ba ya miƙe tsam ya bar mata falon, wani ɗaki ya shiga inda kana gani kasan na zane zane ne, ƙara sawa yayi gaban board ɗin zanen, ya ɗau brush ɗaya ya saka a paint, a hankali ya lumshe idanunsa sai kuma ya buɗe ya shiga zane, wasu siraran hawaye na sauƙa a kan fuskarsa, Ammi ce ta sake shigowa ta tsaya ranta a ɓace ta ke faɗin "yanzu a tunaninka wannan shine abinda ya dace ka dinga yi koh?, ka zana hoto ɗaya a iya lissafina yafi ɗari, kullum sai ka zana, meyasa bazaka sauwaƙema kanka, nima ka dube Ni ba?" Ɗagowa yayi, ya kalleta sai kuma yace "Please nadiya, I need a break" Daga haka ya fice ya koma ɗakinsa yana rufewa da makulli Ƙwafa tayi,tana jin zuciyarta na suya, a fusace ta ƙarasa gaban allon ta yi wurgi dashi, tana faɗin, "na tsaneki, ya zan yi da ke?, kin zame min annoba, kin kasa barina in ji daɗin rayuwata." sai kuma ta juya a fusace ta bar ɗakin tana huci. Falonta ta wuce, inda ƴan mata biyu da namiji ɗaya ke zaune suna video game, babbar cikinsu bazata fi 15 ba sai mai bi mata wacce ita ma bazata fi 10 ba namijin kuwa bazai fi 7 ba, A fusace tace, "farhaana, ku wuce falonku, ku barmin falona bana son hayaniya yanzu" Da sauri farhaana tace, "Ammi Are You ok, ke da papi ko?" Bata kulata ba, sai zama da tayi ta riƙe kanta da duka hannuwanta, da sauri farhaana ta kora ƙannen nata suka wuce part ɗin su, tana tunanin sai yaushe papi zai koma kamar kowa?, sai yaushe zai zauna tare da su kamar yadda ko wani uba yake zama da ƴaƴansu? ************ Tunda Maami ta zo, Zannur ya canza mata, gabaɗaya Noor ta rasa gane ina ya dosa, a gaban Maami kulawa yake bata da har take jin dama har zuciyansa yake mata hakan, amma inaa, bayan idon Maami banda harara babu abinda ke haɗashi da ita, a rashin sanin ta kuwa duk wani shiga da fitanta akan idanunsa takeyi, dan kuwa yana iya yini yana kallon ta a laptop ɗin sa, Taufeeƙ ya tafi Bangaladash saboda wakiltar Zannur akan wasu ayyukansa,hakan yasa bata ganinsa, Asabe da Amina kuwa, kullum cikin ɗebe mata kewa da sakata dariya suke, Yasira ta sake kamar babu komai a zuciyarta, but ita kaɗai ta san gagarumin abinda take shiryawa wanda zai ruguza farin cikin duka ƴan gidan. Satin Maami biyu ta koma Dubai, da kewan Habibi da kuma Noor, dan kuwa shaƙuwa sosai ya shiga tsakaninsu, ta sake wayar mata da kai akan abubuwa da dama, sannan kafin ta tafi ta sa an nemo mata malamai har biyu na islamiyya da boko tana cigaba da karatunta, a halin yanzu Noor Bata da wata damuwa da ya shige ta Zannur, amma shiɗinma sam bata saka shi a rai ba bare ya hanata walwala. 12 ga watan August dai dai da cikar Noor shekara ɗaya da wata huɗu a gidan, shine ranar da abubuwa suka fara canzawa, ƙaddarar da bazata taɓa mantawa ba, da duk wani wanda yake gidan ya faru wanda yayi sanadiyar ruguza duk wani hasashen farincikin Noor................. Kuyi haƙuri page ɗin yau yayi kaɗan, bana ɗan jin daɗi ne shiyasa, Amin uzuri Maimoon# *💖ABNUR💖* *By* *maimoon* *Elegant* *online* *writers* 📚📖 *Free* *book* *Page* *15* I DEDICATE THIS PAGE ENTIRELY TO MY NIMCYLUV, I LOVE YOU SO VERY MUCH, THANKS ALOT FOR THE SUPPORT, AND I WONT FORGET TO THANK DUK MAI KARANTA ABNUR, I REALLY APPRECIATE THE LOVE, MORE ESPECIALLY ABNUR GROUP, I CAN'T LOVE YOU GUYS LESS, AND YOUR PRAYERS ALWAYS GOT ME, BAN MA SAN ME ZANCE BA, YOU GUYS ARE THE BEST, ****** 12 ga watan August,ya kama ranar Laraba, tun safe ta ke jin matsanancin bugun zuciyan, da batasan dalilinsa ba, tunda ta yi breakfast tare da Zannur, ba ta sake sakashi a idonta ba, har wannan lokacin, wanda agogon dakin ya nuna mata karfe 3:30 kenan. Littafin umdatul ahkam ɗinta da ta ke biyawa ta ajiye kasancewar muallimar bata jima da tafiya ba, a hankali ta dafe ƙirjinta da ke bugu. Akan laɓɓanta ta furta "hasbunallahu wa ni'imal wakil,auzubillahi minashaiɗani rajeem, Allah kasa inga Alkhairi." Sai kuma ta miƙe, ta nufi kitchen gurin su Asabe, nan ma bata iya zama ba, duk da yadda suke janta da hira amma ta kasa sake jikinta, daga ƙarshe takoma ɗakinta, kwanciya tayi taja bargo tayi shiru ko zata samu bugun zuciyar nata ya ragu. A hankali ya buɗe ƙofar ɗakin nata ya shigo, zurfin da tayi a tunani, yasa bata ma ji shigowar sa ba, harɗe hannuwansa yayi a ƙirji ya na kallonta a inda take kwance. zuwa yanzu ya gama gasgata ma kansa, ya na matuƙar so da ƙaunar Noor, sake ware idanunsa ya yi a hankali a kanta, ya na jin yanda zuciyarsa ke bugawa, a cikin shekara ɗaya da wata huɗun da suka zauna waje ɗaya da ita, baya shiga harkarta, shi kaɗai yasan irin azabtuwar da zuciyar sa keyi bazai iya jurewa ba, ya gaji da kallonta daga nesa ko kuma ta cctv,dole ya sanar mata tsantsan soyayyarta dake zuciyarsa. A hankali ya ƙarasa, kasancewar barci har ya fara ɗibanta, sam bata ji alamarsa ba, har ya hayo gadon, bargon ya shiga sannan ya jawota ya rungume ta sosai a ƙirjinsa, sai lokacin ta lura, ai kuwa ta buɗe baki zata kurma ihu yayi sauri toshe mata baki da hannuwansa, zare ido ta shiga yi, dan bata ma gama tantance waye bane, duk da ƙamshinsa na SHUMUKH da ya karaɗe ko ina, amma sam ta kasa nutsuwa, dan ta tabbatar Zannur, dai bazai taɓa hawa gadonta ba, balle har ya rungumeta haka, ganin ta gagara ihun ya sa ta fara shure shure, ta ƙi nutsuwa. Dariya ma ta bashi, ita a dole ga mai ƙarfi, a cikin kunnenta ta raɗa mata "Baby, mijinki ne fah" Wani banbaraƙwai taji zancen, amma sai ta rage shure shuren ta na ɗago idanunta ta kallesa, ganin ta nutsu yasa ya sake mata bakinta, ya lumshe idanunsa, sannan ya buɗe. Tashi yayi da ita a jikinsa, ya zaunar da ita akan ƙafafunsa,sannan ya juyo da ita tana fuskantar sa, cikin murya mai nuna kulawa da tayi daban da na Zannur ɗin da ta sani yace "Noor!" Kasa amsawa tayi, saima sunkuyar da kanta da tayi, tana wasa da yatsunta, dan gaba ɗaya a takure take, kasancewar basu taɓa kasancewa very close irin na yau ba. Jin bata amsaba, sai shima bai damu ba, ya cigaba da maganan sa, "Noor, nasan Zaki yi mamaki, abinda ya kawo Ni ɗakinki har kan gadonki, but ba abin mamaki bane, idan kika yi la'akari da matsayina a wajenki, sannan yau yayi daban da duk ranakun da muka kasance tare da ke, a yau ina so in faɗa miki wani abu mai matuƙar muhimmanci da yafi komai muhimmanci a rayuwata yanzu, sai da ya ɗan yi shiru kasancewar yayi maganan da yawa sai kuma ya nisa kafin ya furta kalma mai matuƙar nauyi a wajensa wato 'Please' dan dai banda Abbu da Maami, baya tunanin ya taɓa cewa wani please. A hankali yace "pleaaaaase Noor, Ina so kiyi min kyakkyawar fahimta, sannan kar ki hukunta Ni akan laifuka na a gareki." Jin yayi shiru ya sata ɗagowa suka haɗa idanu, da sauri ta sunkuyar da kanta, dan ta kasa gane inda maganganun sa suka nufa, sannan ita bai mata laifin komai ba, hasali ma bata da wani wanda take matuƙar darajawa da kuma so da ƙauna kamar sa, dan shi ya tsamota sannan ya tallafa mata bayan Nennen ta, Amma ita tasan ya fi ƙarfinta har abada, bazata taɓa samun shi ba, cigaba tayi ta wasa da yatsunta, dan ta rasa me zata ce masa. zagayo da hannuwansa duka biyu yayi akan cikinta, batasan sanda ta sauƙe ajiyar zuciya ba tana sake sunkuyar da kanta dan wani irin kunyarsa ce ta kamata lokaci ɗaya, muryarshi taji dai-dai kunnenta da har sai da tsigar jikinta ya amsa, cikin raɗa ya ce, " kin bani dama in faɗa miki abinda yake raina da zuciyata, and you promise you won't judge me?" Ya faɗa da sigar tambaya dan so ya ke ta buɗe baki tayi masa magana. girgiza masa kai alamar Ah ah, da sauri ya ɗago fuskarta yana kallonta, "why" ya faɗa yana ƙoƙarin cigar da ƙwayar idonsa nata,amma ta ƙi. Cikin inda inda tace "saboda lokacin sallah yayi, ka bari ka dawo daga masallaci" Wani ɓoyayyen ajiyar zuciya ya sauƙe yana jan hancinta, sai kuma yace, "ok wifey your wish will always be my command." daga haka ya ɗaga ta daga jikinsa, ya sauƙa a kan gadon. A bayan gidanta ya yi alwala, sannan ya fice a ɗakin, Ita dai da ido kawai take binsa, yau gabaɗaya ya canza mata, sai kuma tayi murmushi itama ta miƙe ta wuce toilet dan yin nata alwala ******** "Ka saurareni Sir Taufeeƙ, wallahi idan har ban samesa ba mutuwa zanyi, dan Allah ka taimaka min, pleaaaaase" ta faɗa tana kuka wiwi kamar ranta zai fita Wani irin kallo yayi mata na tsana, kafin ya soma magana cikin matuƙar ɓacin rai "Yasira ke wace irin mara tunani ce, taya zakiyi tunanin Sir zai taɓa sonki, bare har ya zauna tare dake, kin manta irin taimakon da ya mana, a lokacin da namu dangin suka wofintar da mu, tayaya ma zaki fara tunanin rama alkhairi da sharri." shiru yayi yana furzar da numfashi, kafin ya cigaba "Wallahi tallahi, ni Taufeeƙ Muntasir, idan har ina raye bazan taɓa bari ki ruguza farincikin Sir Zannur ba, idan baki sani ba ki sani, Noor itace kaɗai wacce Sir zai iya rayuwa da ita, saboda shi kanshi ya fara sonta ne batare da ya sani ba, kuma idan har ina raye zai zauna da wacce zuciya, ruhi da gangar jikinsa keso ne, ba son raina ba, ko kuma son ran ƴar uwata Yasira Muntasir ba." Daga haka ya juya yana shirin barin gun, da gudu ta ƙara so ta riƙe ƙafafuwan sa tana faɗin, "yaya wallahi bazan iya rayuwa babu shi ba, mutuwa zanyi, ita Noor ɗin mai ka haɗa da ita, da ka zaɓe ta akaina, wallahi zan iya kasheta akan na mallaki Sir Zannur, Ni kaina bansan wani irin so nake masa ba, pleaaaaase Yayana ka taimaka min" Dakatawa yayi yana kallonta sai kuma ya naɗe hannuwansa a ƙirji yana faɗin "ok to yanzu me kike so in yi miki" hawayenta ta shiga gogewa cikin sauri tace "yaya so nake Noor ta bar duniyan nan, ko kuma ta yi nisa da mu, yadda zan samu daman rayuwa da Sir Zannur Ni kaɗai" Wani kallo da yake binta da shi yasa ta gagara ƙarasa zancen tana kallonsa "Yasira when did you turn to be a monster ban saniba, how could you even think of that, kin San me kike faɗi kuwa, wallahi billahi, kiyi hanzarin cire wannan banzan tunanin daga kanki, sannan yanzunnan ba sai anjima ba zan je na sanar da Sir Zannur duk abinda kike shiryawa, yasan yanda zai yi dake, bana son yayi la'akari da cewa ke ƴar uwata ce, don kuwa kin zama guba a cikin mutane, idan har zaki iya tunanin kisa" daga haka ya juya ya fice a ɗakin yana huci. kamar zautacciya haka ta miƙe daga durƙuson, tana faɗin "Zaka faɗa ma Sir, wallahi babu wanda ya isa ya rabani da Sir koda kuwa uban da ya kawoni duniya ne bare kai da muke ƴan uba, badai idan har kana raye ba to wallahi yanzu zaka bar duniyan nan." daga haka ta fice da sauri, har tana haɗa wa da gudu ta nufi kitchen, su Asabe da ke aikin girki, basu ma lura da ita ba, da sauri ta zari wuƙa ta cusa cikin zaninta, ta fice a kitchen ɗin da sauri. A tsakar gida ta riske shi, shi kaɗai yana Safa da marwa, tunanin abinda ƙanwar tasa take shirin aikatawa ya hanasa sukuni, ƙarasowa tayi ta na faɗin "yaya" Idanunsa da suka kaɗa suka yi ja,ya ɗago ya zuba mata, yana mata wani irin kallo "yaya dan Allah kayi haƙuri, wallahi nayi dana sanin abinda na furta tun farko dan Allah yayana" Juyowa yayi sai kuma ya kasa cewa komai. "yaya dan Allah muje garden muyi magana,na maka alƙawarin, zanyi duk yadda yace." Wani ajiyar zuciya ya sauƙe yana faɗin "ok muje" Har cikin garden ɗin suka shiga sai da ta tabbatar su kaɗai ne kafin ta soma kukan ƙarya tana faɗin "yaya dan Allah, yanzu bazaka tausaya min ba ka duba halin da nake ciki" Cikin ƙunar rai yace "kina kan bakan ki kenan, ai nayi zaton kin haƙura ne shiyasa ma na biyoki nan, kuma banga amfanin zama na a nan ba, tunda bazaki ji magana ta ba, kiyi duk abinda zuciyarki ta raya miki, nima kuma ina mai tabbatar miki, zanyi duk abinda zuciyata ta raya min dan ganin ba abinda ya samu Sir Zannur ko kuma Madam Noor." Daga haka ya juya zai bar gurin. Cikin ƙaraji ta nufe sa da wuƙar, juyowa yayi da sauri, amma ko kafin ya farga, ta luma masa wuƙar a cikinsa, tana kuka, tana faɗin "meyasa baka barni da zaɓi ba yaya, dan Allah ka yafe min amma bazan iya zuba maka ido ka ruguza min farin ciki na ba" sake luma wuƙar tayi tana jujjuyasa a cikinsa, wani irin murmushin takaici yayi, amma ya gagara ko da motsi saboda azaban dake ratsa shi, sannan bakinsa ya gagara furta komai, Dafa shi tayi ta zare wuƙar ta sake caka masa ita, dan bata so ko kaɗan ya tsira, tanayi tana kuka wiwi, daga ƙarshe ta hankaɗa shi ya faɗi a wajen. Da sauri ta bar wajen tana bar masa wuƙan a cikinsa, ɗakinsu ta wuce, ta shiga banɗaki tana ƙoƙarin dai dai ta nutsuwarta, wanke hannunta tayi da fuskarta, sannan ta fito a bayin, sai data gyara fuskarta, sannan ta fito ta nufi ɗakin Noor, wacce ta idar da sallah kenan, tana jiran Zannur, dan ta ƙagu ta ji abinda yake son sanar da ita. Knocking tayi, cikin sauri tace "come in." A zatonta Zannur ne, ganin Yasira yasata ɗan haɗe fuska ba tare da tace komai ba, cikin in ina, ta soma faɗin "Ma, daman Sir ne yace ki samesa a Garden yanzu" ta faɗa tana sunne kanta, Kamar bazata kula ba sai kuma tace "kice ina zuwa" "Ok Ma" ta faɗa tana barin ɗakin da sauri, miƙewa tayi ba tare da ta cire hijab ɗin da tayi sallah ba, ta naɗe sallayan ta ajiye sannan ta zura takalman ta ta fice a ɗakin, dan gudun kar ta ɓata masa lokaci. Yasira da ke tsaye, tana kallonta ta wuce, ta sauƙe ajiyar zuciya, duk ac ɗin dake gurin, amma gumi take haɗawa, tana tsaye sai ga Zannur zai wuce ɗakin Noor, da sauri ta fito daga inda ta maƙale tana mai shan gabansa, dakatawa yayi ganin ta a gabansa, "lafiya" shine abinda ya furta yana kallonta yadda duk take a birkice "Uhm babu komai Sir, dama ce maka zanyi, Madam bata ɗakinta, tun fitarka naga ta tafi Garden, da alama akwai abinda suke tattaunawa da Sir Taufeeƙ." Shiru yayi yana karantar ta sai kuma yace "Taufeeƙ?" Da sauri tace "eh" Bai sake cewa komai ba ya juya ya nufi Garden ɗin yana tunanin to me suke tattaunawa kuma da Taufeeƙ. Cak ya ja ya tsaya, numfashin sa na ƙoƙarin fin ƙarfinsa, ganin Taufeeƙ cikin jini mala mala, ita kuma tana tsugunne a gabansa tana kuka wiwi, da wuƙa a hannunta, sannan duk hijab ɗin ta ya ɓaci da jini. Kasa gane tunanin da zaiyi yayi, dan dai ya gagara gane me ke faruwa a wajen Taufeeƙ dai, personal assistance ɗinsa,Wanda yake gani kamar ɗan uwansa, wanda ya riƙe da amana, yake jinsa a cikin jininsa, shine a kwance a cikin jini. yayinda matarsa, wacce yake jin bazai iya rayuwa ba tare da ita ba, wacce ya gama gasgatawa kansa ta cancanci ta zama mahaɗin rayuwarsa, itace a durƙushe akan Taufeeƙ da wuƙa, no it's not possible. Da sauri ya ƙarasa wajen yana ɗagota Faɗawa jikinsa tayi tana sake fashewa da wani irin matsanancin kuka, "Wallahi a haka na zo na gansa, bansan wa ya masa haka ba, mu kaisa asibiti kar ya mutu." Kasa cewa komai yayi, saima ɗaga ta da yayi daga jikinsa, cikin tsananin tashin hankali, ya sunkuya ya rungume Taufeeƙ tsam a jikinsa sai kuma ya ɗauke sa cak, ya nufi barin Garden ɗin dashi, yana iya ƙoƙarin sa ganin ya hana kansa hawaye, gudu gudu ya fito dashi, daga cikin Garden ɗin jikinsa na wani irin rawa, Da sauri bodyguards ɗin sa suka ƙara so, amma sai ya ƙi basu shi, ɗaya daga cikinsu ya buɗe masa mota ya kwantar da shi a baya, ya gagara furta komai a bakinsa, zagayawa yayi ya shiga mazaunin driver. Noor da ta biyosa ganin zai tafi ya barta, ya sa tayi saurin buɗe motar ta shiga, bai ce mata komai ba, ya tada motar, ya fice a gidan, bayan ya hana bodyguards ɗin binsa. Gudu kawai yake shararawa, akan titi, amma gani yake baya sauri sam, ita kam banda kuka babu abinda take, satan kallon sa tayi, taga yadda fuskar sa tayi jajazir, amma babu ko ɗigon hawaye, kana ganinsa zata fahimci tsantsan tashin hankalin da yake ciki. Tafiyar minti talatin ne zuwa asibiti, amma a minti sha biyar ya isa, da sauri ya fito, ya ma rasa mai zai yi, cikin asibitin ya nufa har da gudunsa, ita dai tana, zaune a motan, taga sun fito daga cikin asibitin tare da nurses da gado. Buɗe motan tayi ta fito, nurses ɗin suka ƙaraso, suka ciro Taufeeƙ aka kwantar da shi a gadon suka nufi cikin asibitin dashi. Daƙyar Zannur ya samu suka yi attending ɗinsa, kasancewar sun sansa, dan cewa sukayi sai an saka police a cikin lamarin. Tunda aka shiga da Taufeeƙ ɗakin, yake Safa da marwa ya gagara, zama, ita kanta ta gagara daina kuka. A hankali ta ƙara so inda yake tana faɗin "Kayi haƙuri insha Allahu zai samu lafiya" Wani irin kallo da ya watsa mata ya sata saurin yin baya, dan bata taɓa ganin yayi ma wani irinshi ba, bare kuma ita. Cije lips ɗinsa, yayi, amma ya kasa cewa komai, Likitan da ya fito ne ya sashi, saurin ƙarasawa yana faɗin "Doctor ya ɗan uwa na yake" Dafa shi Doctor ɗin yayi sai kuma ya girgiza kai kawai" Da sauri ya sha gaban doctor ɗin dake ƙoƙarin wucewa yace "tell me is he alive" Shiru doctor ɗin yayi sai kuma yace "He is alive, but bayan nan babu abinda zan iya ce maka saboda cause he is in a very critical condition, dan he may slip into a coma" Daga haka ya juya ya bar wajen. Baya yayi jikinsa na wani irin rawa, sai lokacin yaji hawaye na sauƙa akan fuskarsa....... Maimoon# *💖*ABNUR💖** *By Maimoon* *Elegant online writers*📚📖 *Free book* *Page 16* Itama durƙushe wa tayi a wajen tana kuka, ta ma rasa tunanin me zatayi, wani irin tsana ne da har zai sa mutum yayi ƙoƙarin kashe mutum ɗan uwansa, wannan wani irin ƙaddara ce da ta faɗa musu. A hankali ta ɗago idanunta, tana kallonsa, yadda ya samu guri can gefe ya zauna, yayi shiru, kai tsaye bazaka taɓa gane me ya ke tunani ba, sam sai taji batason ganinsa a haka, zuciyarta bazata iya ɗauka ba. A hankali ta nufe sa, har tazo dab dashi bai ɗago ba, kansa a sunkuye yake, gashin kansa ya sauƙo ya rufe fuskarsa, saboda sunkuyar da kan da yayi. Tsugunnawa tayi dai-dai ƙafafunsa, ta lalubo hannuwansa ta riƙe gam. Sai lokacin ya ɗago kansa, yana sauƙe idanuwansa a kanta, yadda idanuwansa suka kaɗa sukayi jajir, har sai da gabanta ya faɗi, amma sai ta dake. Cikin ido take kallonsa, kafin a hankali ta soma magana, cikin muryarta mai matuƙar sanyi. "Dan Allah kayi haƙuri, ka zama musulmin na ƙwarai, mai yarda da ƙaddara, yau koda ace Taufeeƙ ya mutu ne, babu yadda muka iya, saboda Allah ya riga ya rubuta kwanansa ya ƙare, bare yana raye, kuma insha Allahu zai farfaɗo, kamar yau zai tashi akan ƙafafuwan sa, nasan yana da muhimmanci a wajenka, but dan Allah ka masa addu'a, kar ka kasance cikin waɗanda basa komawa ga Allah idan masifa ta samesu, kuma na yarda da kai, ɗari bisa ɗari, zaka nemo duk wanda ya aikata masa hakan kuma ka hukunta shi, hukuncin da ya dace dashi." A hankali hawayen da ta ke ta ƙoƙarin dannewa, ya sauƙo a kan fuskarta, dan ita kanta ba juriyar ce da ita ba, but ganin haalin da yake ciki yasa dole ta danne nata raunin. Kallonta kawai yakeyi, ya kasa cewa komai, a hankali ya sa hannunsa yana share mata hawayen da ya zubo a samman kyakkyawar fuskarta, sai kuma ya ɗagota gabaki ɗaya daga tsugunnen da tayi a gabansa, kusa da shi ya zaunar da ita, yana sauƙe numfashi, ɗago idanunta tayi, suka haɗa ido dashi har lokacin hannuwansu na cikin na juna, a hankali kuma ya kwantar da kansa a kan kafaɗar ta, yana ajiyar zuciya, Zare hannunta tayi daga nasa, ta maida a kansa tana shafa gashin, gyara masa sumar tayi, tana cigaba da shafa kansa, tana jin zuciyarta na ƙara tsananta bugu. Har kusan magrib, suna zaune a haka, sai lokacin ya ɗago kansa, gani yayi ta jingina bayanta da kujeran, ta lumshe ido, alamar bacci ya ɗauke ta, tashi yayi ƙoƙarin yi, amma sai yaji ta sake damƙe dayan hanunsa da ke cikin nata, bai san sanda yayi murmushi ba, yana sake kallonta, irin kallon da bai taɓa nutsuwa yayi mata ba, kallo yake mata ma ƙurilla. Juyar da kanta tayi tana ɓata fuska dan sam baccin kawai ya ɗauke ta ne, amma ba dan tana jin ɗaɗinsa ba, lips ɗin ta ta motsa a hankali, kamar zatayi magana, sai kuma ta maida su tana tsotsan na ƙasan, ƙuri yayi ma lips ɗin nata da ido, yana kallonsu, sai kuma yayi saurin juyar da kansa, yana shafa sumarsa, wacce ta ke ɗabi'arsa. A hankali ta buɗe idanunta, sai kuma ta ɓata fuska tana gyara zamanta akan kujeran, motsinta da yaji, yasa ya juyo yana kallonta, sai kuma ya mata murmushi yana faɗin, "Zaki tafi gida yanzu!" Cikin innocent and calm voice ɗinta tace " tare zamu tafi?" Ta faɗa da sigar tambaya, kwaikwayon yanda tayi maganan yayi yana faɗin "ke kaɗai zaki tafi" Sai da ya ɗan nisa kafin ya sake damƙe hannunta yana faɗin "bazan iya tafiya na barshi ba, Taufeeƙ yana cikin mutane masu muhimmanci a rayuwata, zan iya cewa he is my only friend, saboda bani da aboki, but ya fiye min kowani irin aboki, for the past 16 years, da nake tare dashi, bai taɓa bani ƙofar da zanyi complain ba, he was with me tun Ƙanwarsa Yasira tana da shekara biyar, shine ƙadai gatan ta, duk da kasancewar ba ciki ɗaya suka fito ba, but sukaɗai suka taso, cikin maraici, da rashin gata, a lokacin babansu was a drunkard, mashayin giya ne, wanda bai damu da iyalinsa ba, hakan yasa iyayensu mata suka bar gidan. Taufeeƙ Yana son Yasira sosai hakan yasa da ya yanke shawarar barin gida, ya taho da ita, dan yana ganin she can't handle all that alone. tunda na haɗu dashi nake matuƙar jinsa a jikina, saboda mutum ne shi mai amana, Maami kanta tasha faɗa min Taufeeƙ mutum ne in riƙesa, haka zalika Abbu, sai kuma yayi shiru, kallonta ya kuma yi sai kuma kawai ya jawota ya rungumeta sosai a jikinsa, kamar wani zai raba sa da ita, ita ma bata hanashi ba sai ma kwanciya da tayi shiru a jikinsa tana jin yadda zuciyarsa ke bugawa da ƙarfi. Cikin ɗacin rai ya cigaba da magana " bazan taɓa yafewa duk wanda yayi masa haka ba, koda kuwa waye ne shi a wajena, sannan zan gano ko waye ne, kuma zan hukuntasa da mafi raɗaɗin hukunci," sai kuma ya sake yin shiru yana sauƙe ajiyar zuciya. Itama shiru tayi ba tare da tace masa komai ba, tana fatan Allah ya sassauta masa zuciyarsa, ya bashi daman yanke hukunci, cikin nazari, dan idan rai ya ɓaci, hankali gushewa yakeyi. Ɗagowa tayi daga jikinsa, tana sake kallonsa tace " ba zaka tambaye Ni me nakeyi a kusa da Taufeeƙ ba " Da sauri ya juyo yana kallonta, sai kuma ya shiga girgiza mata kansa, ba tare da yace komai ba. Kuka ta shiga yi a hankali, kafin ta buɗe bakinta tana ƙoƙarin faɗa masa abinda ya kaita Garden ɗin, har ta riski Taufeeƙ a haka Da sauri ya saka yatsansa a bakinta yana kallon tsakiyar idonta "Shhhhhh not another word, ko ki faɗa min, ko karki faɗa min, nasan a haka kika samesa, bazaki taɓa koda tunanin kisa ba, bare har ki aikata, i trusted you after so many trials, so baki da buƙatar yi min bayanin komai" Kallonsa kawai takeyi, itama ta kasa cewa komai. "Yanzu ki tashi, za'a kaiki gida, nima zan dawo idan na tattauna da Doctor ɗin kinji?" Hawayenta ta share, kafin ta miƙe a hankali tana kallonsa, shima miƙewa yayi, har ta kai ƙofa, sai kuma ta dawo da sauri ta rungume sa, tana sakin sabon kuka Shafa kanta yayi, yana raɗa mata a daidai kunnenta "everything will be alright, ba ke kika ce in bar damuwa ba" Ɗago idanunta da suka kaɗa sukayi jaa tayi tana dubansa, sai kuma tayi murmushi tana faɗin " dan Allah ka dawo, zan jiraka, kazo ka faɗa min abinda kace zaka faɗa min dazu" Murmushi yayi shima, wanda kana gani kasan a iya fuska ya tsaya, "kina son in fada miki ne!?" Gyada kai tayi alamar eh "To ki jirani komin dare zan faɗa miki" "Do you promise?" "I do" ya faɗa yana sakin hannunta da ke cikin nasa. A hankali ta juya ta nufi barin wajen duk jikinta a sanyaye. Da ido kawai ya bita, yana kallon irin baiwar kyau da Allah yayi mata, wanda shi bai taɓa lura ya gani ba sai yau, yanda take tafiya a hankali, cikin sanyi yake kallo har ta fice kafin ya sauƙe idanunsa yana sakin ajiyar zuciya. Tana fitowa, da sauri bodyguard ɗin dake jiranta, ya fito yana zagawa ya buɗe mata motan yana gaisheta, shiga tayi ta zauna, tana kallon compound din asibitin, har suka fice, fuskarta ta juyar daga kallon window ɗin, ta mayar tsakanin cinyoyinta, tana sake tunanin wa yake son kashe Taufeeƙ a cikin gidan,kuma me ya musu. Har suka iso ta kasa gano komai, yana yin parking, bata jira ya buɗe mata ba, ta buɗe motan ta fita, tana tafiya a hankali, a falo ta samu su Asabe, duk idanunsu sunyi jajir saboda kuka, Amina har lokacin kuka takeyi wiwi, suna ganinta suka nufo ta sauri, "Madam ya jikin Sir Taufeeƙ" kasa ce musu komai tayi. Yasira da ke gefe tana jira a ce mata ya mutu, sai zare ido takeyi, ta kasa nutsuwa, da sauri ta bi Noor da ke ƙoƙarin haurawa sama "Ma dan Allah ki faɗa min halin da yayana yake ciki, shikadai nake dashi, ya mutu ne?" ta tambaya tana matsar kwalla Dafa ta Noor tayi sannan tace "kar ki damu bai mutu ba, kuma insha Allahu bazai mutu ba, yana nan da ransa kuma za'a gano duk wanda ya aikata masa hakan." Dakatawa tayi da kukan da takeyi, hawayen ya ƙafe jin Taufeeƙ bai mutu ba, batasan sanda ta furta "Bai mutu ba?" da ƙarfi tana zare ido Da mamaki Noor take kallonta, kafin tace, "kina so ya mutu ne?, nace miki bai mutu ba, kuma insha Allahu kwanannan zai dawo akan ƙafafunsa" Da sauri ta sake fashewa da wani irin gigitaccen kuka, tana faɗin shikenan na shiga uku, yayana shi kaɗai nake dashi, Abinda bakinta ke furtawa kenan amma zuciyarta tana raya mata, idan har bai mutuba ai kuwa ta kaɗe, ta shiga uku, Ganin kukan da takeyi yasa Noor faɗin "Yasira ki yarda da ƙaddara yayanki ya shiga coma, but insha Allah zai tashi da yardar Allah kiyi masa addu'a" Kasa cewa komai Yasira tayi da sauri ta juya ta bar wajen, duk suka bita da kallon tausayi. Sai da Noor tayi wanka sosai, duk da haka daga zaran ta tuna yadda jini ke malala daga jikin Taufeeƙ sai ta runtse idanunta, wasu hawaye na sake taruwa a idanunta. har ƙarfe goma babu Zannur babu alamar sa, tun tana jiransa, har bacci ya fara ɗaukan ta, a kishigiɗe haka tayi bacci, dan bataso ta kwanta bacci ya ɗauke ta batare da ya dawo ba. A bangaren Zannur, tun bayan fitowarsa daga asibiti, kasancewar asibitin basa barin kowa a wajen majinyaci su suke kula da shi da kansu, tun da ya fito yake tunanin abinyi, tunanin cctv daya zo masa yasa shi nufar gida kai tsaye, Ɗakin sa ya wuce ba tare da ya bari kowa yasan da shigowar tasa ba. ƙuri yayi ma na'urar yana kallo, ganin babu footage ɗin Garden kwata kwata, da mamaki yake sake kallon computer, ya maimaita dubawa ya kai sau biyar, Amma still babu wannan footage ɗin, a hankali ya shiga duba sauran gurare na gidan, yana so ya gano taka maimai abinda ya faru. Cak ya tsaya akan inda Yasira ta fito tana kuka, ta samu Taufeeƙ a compound, baya iya jin me suke faɗa, amma da alama faɗa sukeyi, sai kuma yaga sun nufi Garden dukansu, baiga fitar Yasira ba sai kuma yaga Noor ta shiga, pulsing yayi, ya miƙe da sauri ya fita a ɗakin. Ƙasa ya sauƙo, sannan ya ɗau landline ya Kira ɗakin su Yasira, Amina ce ta ɗau wayan, a taƙaice yace "Yasira ta sameni a falo immediately" daga haka ya kashe wayar. "Ni kuma?, meyasa yake nema na?" Yasira ta faɗa tana kallon Amina da ta isar mata da saƙon Zannur, "Idan kinje sai ki tambayesa Ni kawai cemin yayi kije" Miƙewa tayi zuciyarta na wani bugu ta fice a ɗakin, A zaune ta samesa, ita ma ta samu waje can ƙasa ta zauna, tana shirin gaishesa ya ɗaga mata hannu, fuskarsa babu alamun wasa ya soma faɗin "Me ya haɗa ki da yayanki ɗazu?" Ɗago ido tayi ta kallesa, kafin tace "Ni.. babu komai" ta faɗa tana kame kame "Babu komai?"ya sake tambayan yana kafe ta ido Daburcewa tayi, sai ta soma inda inda, "eh dama, au babu Fah, Amma dai kawai cemin yayi zai kaini gurin baba, shine nace masa bazan je ba, shine yake min faɗa, sai kuma yace muje can muyi magana, muna cikin magana sai Madam ta zo, ranta a ɓace, shine sai ya ce min in tafi, shikenan kawai sai muka ji wai an kashesa." tana kaiwa nan ta fashe da matsanancin kuka, harda shesheƙa. Kallonta kawai yakeyi, kamar mai ƙoƙarin gano wani abu, kafin a hankali ya furta "Yasira kina jina?" Gyaɗa masa kai kawai tayi, tana cigaba da kukan "Yayanki zai samu lafiya, ki kwantar da hankalinki, kina jina?, na miki alƙawarin duk wanda yayi masa wannan abun, da kaina zan bincikosa, sannan in hukuntasa, ki cigaba da yi masa addu'a kinji?" "To" ta faɗa tana fyace majina "Tashi kije" ya faɗa a taƙaice, yana jingina kansa da kujera. Miƙewa tayi, ta wuce, tana sake waiwayowa ta dubesa, a hankali kuma tayi murmushi, a zuciyarta tana faɗin "Kaɗan ya rage na mallakeka Zannur, kuma nayi alƙawarin, duk wanda ya kawo min cikas wallahi sai na kawar dashi" sai kuma tasa yatsa ta share guntun hawayen idanunta, sannan ta wuce ɗakinsu. Miƙewa yayi daga kan kujeran, yana jin gabaɗaya kansa ya kulle, ta yaya ma Yasira zata cutar da ɗan uwanta, bazai yiwuba, har ya koma ɗakin sa ya faɗa kan gadonsa yana cigaba da tunani, to me ya kai Noor wajen Taufeeƙ?, kuma ranta a ɓace, me ya mata?, dole ne ta amsa masa waɗannan tambayoyin nasa, shin ko dai yayi kuskuren amincewa da ita ne?, wata zuciyar ta raya masa, da sauri kuma ya girgiza kansa, yana maimaita "Allahummu ajirni fi musibati." Gabaɗaya ya manta da wani tana jiransa, har bacci ya dauke sa. Mun kusa dawowa kan labari🤓so get ready, gumurzun yana gaba Maimoon# *💖ABNUR💖* *By maimoon* *Elegant online writers* 📚📖 *Free book* *Page 17* Da safe ma kiran doctor ne ya tashe sa, akan yana nemansa da gaggawa, a gaggauce ya shirya ya bar gidan, ba tare da ya ma Noor sallama ba. Noor kam, tunda tayi sallah, ta gagara koma wa bacci, tunani takeyi meyasa bai zo ba?, bayan ya mata alƙawarin zai zo komin dare. "to ko bai dawo bane jiya" abinda zuciyarta ta raya mata kenan, Definitely bai dawo ba, tasan da zai shigo, to ko jikin Taufeeƙ ɗin ne, ya hanashi dawowa, wani zuciyar ta sake raya mata, haka tayi ta tunane tunane, kafin daga bisani ta miƙe ta wuce toilet. Wanka tayi, ta fito ɗaure da pink towel mai kyau, fararen ƙafafuwanta, sanye cikin room slippers pink, jiki a sanyaye ta ƙarasa ta buɗe sif tana kallo, riga da skirt ta zaro na atampa, ɗinkin riga da skirt, ta ajiye akan gadon, kafin ta ƙara sa gaban mirror ɗinta, dake shaƙe da abubuwan anfaninta. Mai ta ɗauka tana shafawa akan lallausa fatar ta mai santsi, amma duk tunaninta na wani wajen daban, a haka har ta ƙara sa, kayan da ta ajiye ta ɗauka ta sanya, yadda suka zauna ajikinta tubarakallah masha Allah, kallon kanta ta tsaya yi a madubi, sai kuma ta ɗan yi murmushi, dan ko ba'a faɗa mata ba tasan ita ɗin mai kyau ce, akan laɓɓanta wanda suke pink shar, sannan kamar ta shafa musu lip gloss, saboda yadda suke koda yaushe da santsi da yalƙi ta furta "Alhamdulillah" Gefen gado ta koma ta zauna, tana kallon agogon hannunta, ƙarfe takwas saura, da sauri ta miƙe tsaye a ranta tana faɗin "bari kawai na dubo shi, anya ma ya kwana a gidannan." Daga haka ta fice a ɗakin, tana tafiya a hankali, turus tayi a bakin ƙofan tana kallon Yasira, da ta fito daga ɗakin, daga ita sai kayan bacci wanda ko Cinyarta basu gama rufewa ba, idanunta da alamun, tana ganinta itama tayi saurin yin baya, tana kallon ta, sai kuma ta zo zata gilma ta, Hannu Noor tasa ta dawo da ita, tana kallonta cikin ido tace "Yasira me kike yi a ɗakin Zannur" Ta faɗa tana zare mata ido, kamar zasu faɗo ƙasa Cikin nuna tsoro da kuma kuka Yasira ta soma magana "Madam dan Allah kiyi haƙuri, ba komai bane, kawai Sir yaga halin da nake ciki jiya saboda rashin lafiyan Yayana, shine yace nazo, to shine bacci ya ɗauke Ni a nan, ba komai bane" Noor kallonta ta tsaya yi kafin cikin tsawa tace "ƙarya kikeyi, aka gaya miki shi jahili ne da zai gayyaceki ki kwana a ɗakinsa, alhalin ke ba muharramarsa bace" Cikin kuka wiwi, Yasira ta soma faɗin, "wlhy da gaske nakeyi Ma" "Ok to da ya kiraki ke kuma sai kikazo, saboda ke munafuka ce harda sako kaya irin waɗannan" Ta faɗa tana nuna jikin Yasira, rai a ɓace idanunta sun gama canza kala "Ma kiyi haƙuri Sir ne ya bani yace in saka, nima bansan dalilinsa ba, kuma Ni bazan iya yi masa musu ba shiyasa nasaka" Girgiza kai kawai Noor takeyi, kafin ta sake Yasira ta juya a fusace ta nufi ɗakin ta, wato abinda ya hanashi zuwa gareta jiya kenan! me yasa zuciya ta yaudareta da har take ganin kodai Zannur ya fara sonta ne, gadonta ta faɗa tana cigaba da rusa kuka wiwi. Da sauri Yasira ta zaro dogon hijab ɗinta, a inda ta ɓoye ta zura, sannan ta koma ɗakin Zannur cikin sassarfa, inda tasan yana ajiye laptop ɗinsa ta nufa, kasancewar babu security yasa ta buɗe da sauri, sai da ta tabbatar ta goge wannan footage ɗin kamar yadda ta goge na Garden, kafin ta shiga tafa hannunta tana murmushin mugunta, "Yaya Taufeeƙ, kayi kuskure, da har kake ƙoƙarin rabani da rayuwata, dan kuwa Zannur rayuwa ta ne, zan iya komai dan na mallakesa, amma bazan ƙi gode maka ba, saboda makarantar computer da ka sakani, har na zama computer guru, idan ba haka ba, da tuni asirina ya tonu, sannan ina mai tabbatar maka bazan taɓa bari ka farfaɗo ba,bare har ka tona min asiri, har sai Zannur ya Zama nawa." Daga haka ta fice a ɗakin tana murmushi, da jinjina ma kanta. ****** "Congratulations, gaskiya dan uwanka, yana da matuƙar Sa'a, ba kowa bane ya ke shiga coma ya dawo da wuri, but da izinin Allah jiya ya motsa, kuma daga nan zuwa ko wani lokaci, zai iya farkawa." Da sauri Zannur ya ɗago yana kallon likitan, jinjina masa kai doctor yayi alamar tabbatarwa, "But saboda lafiyarsa, yasa bazamu bari ya gana da kowa ba, har sai bayan kwana uku" Likitan ya ƙara sa faɗa yana gyara glass ɗin idanunsa, da murmushi a kan fuskarsa. "Alhamdulillah, Alhamdulillah, alhamdulillah" shine kaɗai abinda Zannur ke iya faɗa, ko babu komai, Taufeeƙ zai faɗi wanda ya aikata masa hakan da kansa. Miƙewa yayi yana miƙa ma doctor ɗin hannu, suka yi musabaha, kafin ya fice a office ɗin yana jin matuƙar farin ciki, bai zarce ko ina ba sai gida. Ɗakin Noor ya nufa, dan yana so ta amsa masa tambayoyin da ya kwana dasu, Tunda ya shigo ɗakin taji shigowar sa, amma sai tayi kamar tana bacci, ƙarasowa yayi ya zauna a gefen gado yana kallonta, kafin a hankali ya sa hannuwansa duka biyu ya ɗago ta gabaɗaya, yatsine fuska tayi kafin tace "miye hakan?" Bai kulata ba ya zaunar da ita a tsakiyar gadon yana kallonta da fuskar da babu wasa yace " " " Noor! " Tone ɗin da yayi maganar dashi, ya sata nutsuwa ta tsura masa ido tana saurarensa, duk da matuƙar haushinsa da takeji. A hankali ya cigaba da magana "Noor ina so ki faɗa min, me ya haɗa ki da Taufeeƙ, da har kika aikata masa haka" Zaro idanunta tayi duka tana kallonsa kafin tace "Me kake nufi na aikata masa haka, meyasa zan masa haka?, me ya min?" Cikin ɓacin rai yace "Noor na riga nasan komai, ina so ne ki faɗa da bakinki, miye Taufeeƙ ya aikata miki daya cancanci haka?" Idanunta da suka ciki da hawaye, ta rintse ,kafin tace "Wallahi tallahi, a haka na gansa, nima..." "Ƙarya kikeyi", ya faɗa a tsawace yana miƙewa tsaye, gabaɗaya fuskarsa ta gama canzawa, hannunsa yasa a gashin kansa ya birkita kafin yayi ƙwafa yana faɗin "nayi zaton zan iya amincewa dake, saboda kamilalliyar fuskarki, ashe zuciyar ki baƙa ce, Ni ina da shaidan cewa lokacin da kika shiga kika samesa da ransa, sannan babu wanda ya ƙara shiga bayan ke, wace irin zuciya ce dake, azzaluma mara imani" Kasa haƙura tayi, idanunta ya rufe, a fusace ta sauƙo daga kan gadon tana kallonsa, hawaye wasu nabin wasu Cikin Muryar kuka ta shiga faɗin "abinda yasa ka kawo Ni gidanka kenan?, meyasa baka bar Ni a can na mutu ba, meyasa ka ɗauka ma Nenne alkawarin da bazaka iya cikawa ba?, nagode wa Allah, kuma bana buƙatar kowa ya yarda dani saboda Ni nasan kaina, Ni ba azzaluma bace, kuma Ni ba mai kisan kai bace, sannan Ni ba fasiƙa mai zina bace" ta faɗa da ƙarfi tana rushewa da kuka. Da sauri ya ɗago fuskarsa ya kalleta, a hankali ya tako dai dai inda take, fuskarsa tayi jajazir "Waye fasiƙi mazinaci?" ya tambaya yana kallonta. Ƙin dagowa tayi da ƙarfi ya ɗagota yana kallonta "nace miki waye fasiƙi mazinaci?" Da zafin rai take kallonsa kafin tace "ka ɗauka zan ji tsoronka ne in kasa maimaitawa, kai fasiƙi ne kuma mazinaci, kuma Allah bazai Barka ba" Ɗif ta ɗauke wuta sakamakon wani shahararren marin da taji a fuskarta har sai da jinta da ganinta ya ɗauke na wasu sakonni "Ni ne mazinaci?, Ni?" sai kuma ya furzar da iska mai zafi, yana faɗin "nayi dana sanin baki dama, nayi dana sanin tunanin kin cancanta na so ki, nayi da na sanin saninki, kuma ina mai tabbatar miki da kaina zan hukunta ki,bana buƙatar kowa, zanmiki mafi munin hukunci wanda bazaki taɓa mantawa da Ni a tarihin rayuwarki ba, yanzu zakisan waye Abubakar shuraim a baya Zannur kika sani " daga haka ya juya ya fice a ɗakin, kai tsaye gidan ya bari, dan gidan ya masa baƙiƙirin ba zai iya zama a cikinsa ba, so kawai yakeyi Taufeeƙ ya tabbatar masa da bakinsa cewa Noor itace ta caka masa wuƙa, daga nan kuma zai yanke mata duk hukuncin da ya dace da ita. Ɗurkushewa tayi tana wani irin kuka, ta shiga uku, shin dama fuska biyu yake dashi, sai da ya nuna mata ɓangarensa mai kyau, kafin ya nuna mata mafi munin ɓangarensa, "Bazai yiwuba" ta faɗa tana miƙewa tsaye, Sai kuma ta nufi sif ɗinta kamar zararriya, birkito kayan tayi, amma ta kasa ɗaukan ko ɗaya, jakanta ta nufa ta buɗe ta ciro atm dinta, ta zura hijab ɗinta tana rusa kuka kamar ranta zai fita. Fitowa tayi daga ɗakin bata ko ganin gaban ta, da sauri Asabe da Amina da ke tsaye cirko cirko suka nufo ta, dan suna jiyo hayaniyansu daga sama, amma basa jin me suke faɗa, sai kuma sukaga Sir ya fita ranshi a ɓace, "Madam lafiya, ko jikin Sir Taufeeƙ ne ya tashi?" Ko kallonsu batayi ba ta nufi ƙofa, Da sauri Asabe ta sha gabanta "ina zakije please madam, ki faɗa mana Please" "Out of my way" tafaɗa tana zare dukkanin idanuwanta, Da sauri Asabe ta matsa tana matsar kwalla, dan dai ta tabbatar ba fitan lafiya Noor zatayi ba yanzu Ko dai jikin Taufeeƙ ne ya tashi, to ko Taufeeƙ ɗin ya mutu ne, da sauri ta juyo da nufin ta tambayeta, amma inaa har ta fice a falon, da ƙafa ta taka har gate, ba tare duk ma'aikatan gidan sunyi yunkurin hanata ba, dan babu wanda bai san Madam bace, dan Taufeeƙ da kansa ya sake tara su kamar yadda ya tara su a baya, ya shaida musu, matarsa ce, kuma subi dukkan umarnin ta. Mai gadi dake tsaye jikin gate da sauri yace "Hajiya meke faruwa?, ko jikin Taufeeƙ ɗinne? naga yallabai ma ya fita a fusace" Ba ta basa amsan sa ba sai cewa da tayi "baba buɗe min ƙofa" Yadda yaga babu alamun wasa a tare da ita yasa shi saurin buɗe ƙofan yana faɗin "Hajiya a dawo lafiya, Allah ya ƙara bashi lafiya bawan Allah." Bata kulasa ba, tayi ficewarta, tafiya kawai takeyi, da kafa burinta kawai ta bar Area din gidan gabaki ɗaya, Sai da ta iso main junction kafin ta samu abin hawa, yana tsayawa, Shiga kawai tayi ba tare da ta ce masa komai ba. Sai da ya fara tafiya kafin yace "Hajiya ina zan kaiki?" Rasa inda zatace tayi, dan babu inda ta sani a faɗin Abuja, ahankali tace "ka kaini guri mai nisa daga nan ko nawa ne zan baka" ta faɗa tana kifa kanta, shiru mai adaidaita yayi har suka iso inda yake ganin tayi nisa sosai da inda ya ɗauko ta. Juyowa yayi yace "Hajiya mun iso" idanunta ta ɗago ta kallesa kafin tace "bari in cire kuɗi sai na baka." Dayake indaya kawota kusa da kasuwane, bata sha wahala ba ta cire a P.O.S ta bashi, godiya yayi ganin ta bashi fiye da kuɗin sa, yaja mashin ɗin sa yayi gaba. Guri ta samu can gefe ta zauna, tana kallon área din, sai kuma ta miƙe, gurin wani mai sai da kati ta nufa a hankali tace masa, malam dan Allah akwai tashan mota anan, nuna mata yayi yace gashi can a gaba kaɗan A hankali ta masa godiya kafin ta juya ta nufi tashan, dan gani takeyi har yanzu batayi nisan da ya kamata ba tunda suna gari ɗaya. Tana shiga tasha, yaran tasha suka soma tambayanta inda zataje, "inda yafi nisa" kawai ta iya furtawa tana share hawayen da yaƙi tsayuwa a fuskarta Yaron motan da ke son motan kano ya cika, yayi saurin faɗin, "aikuwa Kano ne inda zakije, dan dai kam akwai nisa daga nan" ya faɗa yana ƙoƙarin janta dan karta fasa tafiyan, miƙa masa ATM dinta tayi tace "sai na cire kuɗin mota" da sauri yace "babu damuwa Madam, ga p.o.s nan ma" sai da ta sake cirewa ta biya kuɗin motan, kafin ta soke sauran canjin, har mota ya cika tana jingine da window hawaye na sauƙa a fuskarta, sai da suka hau hanya sosai kafin ta lumshe idanunta a hankali ta furta "Dama yaudarar kaina nakeyi, U never loved me,kuma zanyi nisa da kai, nisa na har abada." (wannan shine dalilin Noor na barin gida har ta haɗu da su khamal) Zannur kam tunda ya fito a gidan, direct hotel yayi booking, yana shiga ɗakinsa ya rufe kofar yana faɗawa kan gadon ɗakin, yana jin zuciyarsa na suya, shi zatace ma mazinaci, sai kuma ya yi ƙwafa, yana jaddada ma kansa, bazai koma gidan ba har sai Taufeeƙ ya amsa masa tambayoyinsa nan da kwana uku, a lokacin zai kamata da hujja, daga haka ya miƙe ya wuce toilet. Ranar da Taufeeƙ ya cika kwana uku, a ranar Zannur ya samesa a asibiti, da ƙyar Doctor ɗin ya bashi daman ganinsa. Yana shiga, ya zuba ma Taufeeƙ idanu, yanda ya rame, oxygen ne a hancinsa, dan baya iya numfashi yadda ya kamata, Kujera ya ja ya zauna kusa da shi ya riƙe hannuwansa, ga mamakin sa, sai yaga hawaye na gangarowa a fuskar Taufeeƙ. Shafa hawayen yayi, kafin yace "ka kwantar da hankalinka, ka sanar da Ni waya maka haka, duk da na riga na sani amma inaso inji daga bakinka, shin Noor ce ta caka maka wuƙa?" Ya tambaya a ƙagauce Zaro ido Taufeeƙ yayi sai kuma ya shiga girgiza kansa da sauri, sauƙe masa oxygen din yayi dan ganin kaman Yana son cewa wani abu "Ba ita bace.. batasan komai akai ba.. watace daban..." kasa ƙarasawa yayi, jin an murɗa ƙofan ɗakin an shigo, Yasira ce ta shigo, da basket a hannunta tana kallon yayannata, wanda shima ya ke kallonta, hawayen idanunsa na ƙara zuba, juyowa yayi da niyyar cema Zannur ita ce, amma sai yaga Zannur ɗin ya miƙe, a hankali ya ƙara so ya maida masa oxygen ɗin, dan bayason suyi maganan a gaban kowa, shafa kansa yayi yace "we will talk later ok" Sai kuma ya juya ya kalli Yasira "waya kawoki nan" Da sauri tace "Sir dan Allah kayi haƙuri, na kasa jurewa, ina so inga yayana, shiyasa nazo" "Babu komai" ya faɗa yana juyawa yabar ɗakin, dan hankalinsa gabaɗaya yana ga Noor a halin yanzu, dan kuwa ya tabbata ya mata laifin da zaiyi wuyan kankaruwa, duk da Taufeeƙ bai faɗa masa wacece ta caka masa wuƙa ba, amma ya tabbatar masa ba Noor bace, hakan yana nufin zargin da yake mata ba daidai bane, fitowa yayi a gaggauce ya nufi motarsa, dan yana buƙatan magana da Noor ya wanke kansa. Wlhy na gaji, naso mu dawo kan labari yau,amma dai saura ƙiris, mudawo. Maimoon# *💖ABNUR💖** *By Maimoon* *Elegant online writers* 📚📖 *Page 18* A hankali cikin taku ɗai ɗaya, Yasira ta ƙaraso gaban Taufeeƙ, sai da ta sunjuyo dai dai fuskarsa, kafin tasa hannunta ta shafa fuskarsa. "Yaya ya jikin?, Me kake faɗa ma masoyina?", ta faɗa tana kallon cikin idonsa. Juyar da kansa yayi daga kallonta, yana jin ƙunar zuciya. Sai da tayi ƙwafa, tana wani murmushi kafin tace "Wato kana kan bakanka ko?, To bari kaji, Na rantse da Allah baka isa ba, yanzu zan ƙarasaka saboda bazaka ɓata min shiri ba". Daga haka ta saka hannu ta cire oxygen ɗin, pillow ta ɗauko ta ɗaura akan fuskarsa, ta danna da iya ƙarfin ta. Wani numfashi ya shiga fitarwa, yana miƙewa da kakkarwa a kan gadon, amma ko ajikin Yasira, sai ma sake dannawa da take da ƙarfi. Jin numfashinsa na ƙoƙarin barin jikinsa, yasa ya ɗaga hannunsa yana bugawa a jikin gadon, cikin Sa'a kuwa hannunsa ya tabo madannin da mara lafiya yake dannawa idan yana buƙatar wani abu. Ai kuwa ɗakin ya ɗau kuwwa, da sauri ta cire pillow ɗin tana mayar masa da oxygen ɗin cikin ruɗewa. Nurses ne suka shigo,su kusan uku, da sauri suka ƙara so suna kallon Yasira, da ke gyara masa kwanciya. "Madam wa ya baki daman shigowa nan?" Daya daga cikin nurses ɗin ta tambaya tana kallon Yasira cikin tuhuma. Cikin in ina tace "dama yaya na ne, shine nazo na gansa, kuma...uhm" Sai ta kasa ƙarasawa. "Ok ke relative ɗinsa ce?" Da sauri tace "eh nice kaɗai Ƙanwarsa." "Ok to but ba lokacin ganin mara lafiya bane yanzu!, saboda haka ki dawo right time." "Eh dama abinci na kawo masa, dan Allah ku barni in bashi." Ɗaya daga cikin nurses ɗin tace bakiji "me akace bane, ki dawo lokacin da ake ganinsa Please" Babu yadda ta iya haka juya ta fita, a ranta tana faɗin "babu damuwa akwai wani lokacin, amma ina mai tabbatar maka bazan taɓa bari ka haramta min muradin zuciyata ba." Daga haka ta fice tana murmushi. Tunda Zannur ya shigo gidan, bai bi takan duk masu gaishesa ba, ya nufi sama, da sassarfa, Allah Allah,yake ya gansa a gaban Noor. Murɗa ƙofan ɗakin yayi ya shiga, tsayawa yayi daga bakin ƙofan yana kallon kayan da ta zubo dasu daga cikin sif ɗin, ba tare da tunanin komai ba ya ƙaraso cikin ɗakin, ganin bata ciki yasa shi ƙarasawa ƙofar bandaƙin, dan ya tabbata tana ciki, jiki a sanyaye ya soma magana "Noor, bansan me zance miki ba, wallahi ina matuƙar kunyar ki, Taufeeƙ ya tabbatar min zargina ba daidai bane." sai kuma yayi tsaki "Mtseewww me ma nakeyi?" Ya faɗa yana dafe kansa, sai kuma ya cigaba "Noor please ki fito ki saurareni, bakin ce kina so kiji abinda nake so na faɗa miki ba rannan?, to yau zan faɗa miki na miki alƙawari." Jin bata fito ba ya sashi, ɗaura hannunsa akan handle ɗin Yana shirin magana yaga ƙofar ta buɗe, alamar ba'a rufe da kyau ba, a hankali ya ƙarasa tura Kofar, Wayam yaga banɗakin babu kowa. Zuciyarsa ce tayi wani irin wawan bugun da ya sashi dafewa da sauri, kafafuwansa da sukayi nauyi, ya ja da sauri ya juya ya nufi ɗakinsa, laptop ɗinsa ya nufa. Kai tsaye kitchen ya duba, bata ciki, ya duba duk wani guri a gidan amma babu ita, cikin sauri ya shiga tariyewa baya 3days ago tun sanda ya bar gidan. Wani irin miƙewa yayi yana faɗin "shit" Landline ya ɗauka yana kiran securities ɗin gidan Yana ɗagawa yace "where is Noor? Why do you let her out? akan me ya sa kuka barta ta fita a gidannan ba tare da izinina ba." ya faɗa a tsawace. "Sorry Sir" "Shut up, na baku 30 minutes ku nemo min matata, idan ba haka ba..." sai kuma yayi ƙwafa yana katse wayan. Dafe kansa yayi, yana riƙe ƙugunsa Sai kuma ya durƙusa a wajen yana jin idanunsa na masa matuƙar raɗaɗi "Why Noor, meyasa baki jirani na gano gaskiya ba?, Noor you are my life, Please ki dawo gareni, I promise to trust you completely, wallahi bazan sake kuskuran fahimtar ki wifey." Sai lokacin, hawaye mai zafi ya sauƙa masa, bazai yafewa ko waye yayi sanadiyyar rabasa da Noor ɗinsa ba. Bai san tsayin lokacin da ya kwashe a wajen ba trying to calm himself, kafin ya miƙe da sauri ya nufi downstairs cikin sassarfa. (Finally we are back, and the story continues.....) Numfashi ta sauƙe a hankali tana share hawayen idanunta, bayan ta gama basu labarin abubuwan da ta sani. A hankali umma ta taso ta zo kusa da ita tana shafa kanta. Kamal kam kallonta kawai yakeyi sai kuma ya sunkuyar da kansa, yana murza hannunsa, dan ya gagara cewa komai. Baba ne yayi gyaran murya kafin ya fara magana "Noor, munji labarinki, kuma a gaskiya kin yi haƙuri, kuma Allah ya jiƙan Nenne, yanzu abinda nake so dake kije ki kwanta insha Allahu zamuyi magana gobe, muga ya zamu samo mafita, Allah ya miki albarka." "Ameen" umma ta amsa dashi, tana shafa kan Noor dake cigaba da kuka. Jin kiran sallan Asuba, yasa Baba faɗin "subhanallahi, ashe ma garin har ya waye, mun kwana a zaune fah kenan, to Allah ya kyauta, kamal tashi muyi haramar tafiya masallici, A'isha sai kuyi sallah kafin ta kwanta koh?." "Insha Allah Malam" Umma ta faɗa tana miƙar da Noor suka fice a ɗakin. Sai lokacin khamal ya miƙe shima, suka fice da Baba, Dan tafiya masallaci kafin a shiga sallah. ************ Ƙarfe 1:30 daidai, jirgin *Emirate Airlines* daya taso daga *Dubai* ne ya sauƙa a babban filin jirgi na Kaduna wato *Kaduna international Airport.* A hankali mutanen ciki ke sauƙowa, ɗaya bayan ɗaya a gajiye. Farhaana ce ta fara sauƙowa, sai sudais da namra a bayanta, duk fuskarsu a jagule, daga bayansu kuma Ammi ce, sai papi a bayanta. Haka suka jero suna sauƙowa abin sha'awa, sai dai fuskokinsu babu wanda yake walwala, idan ka cire sudais kasancewar bai ma san me akeyi ba shi. Sai da suka gama yin all the formalities, kafin suka zarce gidan da papi ya saya a garin Kaduna wanda ke unguwar GRA, har suka isa babu mai cewa komai. Suna shiga, Farhaana taja su Namra suka wuce shashinsu, Ammi ma nata ta wuce suka bar papi a tsaye, shafa sumar kansa yayi, a zuciyarsa yana faɗin "Na gaji da zama da haƙƙinki, a wannan lokacin babu wanda zai hanani nemanki, dan tabbatar miki da alƙawarina a gareki, ina fatan zaki yafe min, sannan kimin kyakkyawar fahimta". Daga haka ya wuce shashensa shima yana jin matsanancin gajiya a tattare dashi. ********** Zannur ne a zaune kusa da Taufeeƙ da ke barci ƙura masa ido yayi yana kallonsa, bai san miye dalilin Taufeeƙ na ƙin faɗan wanda ya aikata masa haka ba, yayi iya ƙoƙarin sa, amma Taufeeƙ yaƙi cewa komai. Miƙewa yayi ya ƙarasa jikin window yana jin zugi a ransa, meyasa ƙaddara ta zo masa a haka?, da wanne zaiji?, da ɓatan Noor ko kuwa da rashin lafiyar Taufeeƙ?. Taufeeƙ ɗan amanarsa ne, da bazai iya barinsa ba kuma sai ya hukunta ko waye ya aikata masa hakan, Gashi ya kasa sanar da Maami abunda ke faruwa. A hankali ya juya ya bar ɗakin yana jinsa kamar bashi ba. Taufeeƙ daya buɗe idanunsa yana kallonsa, dan dama ba bacci yakeyi ba, hawayen da ya ciko idanunsa suka bi gefen fuskarsa, suna sauƙa akan gefen kunnensa. A hankali ya buɗe bakinsa da yake a bushe, ya furta "bazan taɓa bari a cutar da kaiba Sir, koda kuwa hakan na nufin ƙarewar rayuwata, hakan yasa na yanke shawaran ƙin faɗa maka, kayi haƙuri zan faɗa maka, amma sai a lokacin da ya dace, sannan nayi alƙawarin zaka zauna da Noor har karshen rayuwarka, sai dai idan kai kace baka sonta Sir, bazan taɓa manta halaccin ka a gareni ba, duk da Ni ba kowa bane, amma ka nuna min zallar soyayyah da kulawa." Sai kuma ya juyar da kansa yana jin ɗaci a ransa. Maimoon# *💖*ABNUR💖** *By Maimoon* *Elegant online writers* 📚📖 *Page 19* *Two days later* Noor ne ta fito daga kitchen, hannunta ɗauke da kofin roba, tana sanye da abaya kalar baƙi, wanda khamal da kansa ya shiga cikin gari ya siyo mata da ATM ɗin ta, dan dama ta manta da shi ne ya sa har ta siyar da ɗan kunnenta. Waje ta fito, ta samu waje ta zauna, a kusa da umma dake tsintar shinkafa, ajiye cup ɗin tayi ta shiga taya umma tsintan suna hira sama-sama. Khamal ne ya shigo, da sallama, ya ja kujera ya zauna yana faɗin "Sannu da aiki Umma" "Yauwa sannu khamal ya gonan dai?" "Alhamdulillah wallahi, ya gida?" "Lafiya ƙalau" A hankali Noor tace "ina wuni yaya khamal" "Lafiya" ya amsa a taƙaice kafin ya miƙe yana faɗin "Umma bari naje wajen Abdul" "To sai ka dawo" Sai da ya fice a gidan, kafin umma da maida dubanta ga Noor dake cigaba da tsintan shinkafan. "Noor!" "Na'am Umma" ta faɗa with full concentration. Bakya kewan mijinki?, bakya tunanin kina so ki gansa?, Noor zaman aure da kika gani, wani abune mai matuƙar buƙatar haƙuri, da soyayyah, Noor ke mace ce, bakida inda yafi gidan mijinki daraja a wajenki. Kuka Noor ta fashe da shi ba tare da ta bari Umma ta ƙarasa magananta ba. Umma Ni bana sonsa, Umma ko ina sonsa zan hakura da shi, saboda idan har babu yarda to babu soyayya, me yasa bazai yarda da Ni ba?, meyasa zai yi tunanin zan iya aikata hakan ga Taufeeƙ?, laifin me yamin da har zan aikata masa haka?, umma na riga na yanke hukunci, banason komawa garesa har abada, idan kuma har kun gaji da zama da Ni ne please kuyi haƙuri." ta faɗa tana cigaba da kuka "Batun mun gaji da ke bai taso ba Noor, kawai ina faɗa miki ne a matsayinki na ƴata, dan ko da ace Ni na haife ki haka zan faɗa miki." Cikin kuka Noor tace "nagode Umma, amma dan Allah banaso na koma ga Zannur, please ki barni a nan." Daga haka ta miƙe ta wuce ɗaki, Umma ta bita da kallo tana jinjina kai. Baba da shigowar sa kenan ya tarar suna maganan, bai ce komai ba ya wuce ɗaki. Miƙewa umma tayi tabi bayansa, a zaune ta samesa akan ɗan gadonsu yana matsa ƙafarsa da take ɗan masa ciwo. Da sauri ta ƙaraso ta tsuguna ta sa hannu tana matsa masa ƙafafun, "sannu Malam, ƙafar ce take ciwo har yanzu?" "Eh wallahi Aisha, Amma ba sosai ba, Allah ya miki albarka." "Ameen." ta faɗa tana cigaba da matsa masa duka ƙafafuwan. "Yauwa Aisha naji kuna magana da Noor!" "Wallahi Malam taƙi saurarata, kuma kasan halin yaran yanzu, tsoro na kar taga kaman zamu takurata mu neme ta mu rasa yanda mijinnata ya rasa ta." Numfashi Baba yaja kafin yace "hakane, amma duk da haka ai bazamu biye mata ba, yarintace kawai ke damunta, amma shima yaron dole na zauna dashi, kafin na bashi Noor, dole ne a aure ya zama akwai cikakken yarda da aminci, ai ba'a haka, yanzu so nake mu cire anfanin gona, idan mun siyar, kuɗin sai muyi anfani dashi mu maidata gidan mijinta, dan shine mutuncinta." "Hakane kam Malam, Allah dai ya saka maka da alkhairi." "Ya saka mana gaba ɗaya uwar ƴaƴana" ya faɗa yana kallonta da murmushi. Itama Murmushin tayi tana miƙewa tace bari "naje na ƙarasa girki." Daga haka ta fice a ɗakin. *********** *_Kaduna Nigeria*_ What? Papi ya faɗa yana miƙewa tsaye, "banganeba, me kake nufi?, papi ya faɗa yana ja da baya, "Abinda kunnuwanka suka jiye maka nake faɗa." Mai gari ya faɗa yana miƙewa shima. "Yarinyar nan da ka gudu ka bari, ta rasu shekara biyu kenan sannan ƴarta tayi aure, ta auri wani ɗan Balarabe ɗan birni da ya zo garinnan, ya tafi da ita mu kan mu bamu san ina ya tafi da ita ba." Girgiza kai papi ya shiga yi idanunsa sun kaɗa sunyi jajir "Kana nufin Fatima tana ɗauke da cikina sanda na tafi na barta?, kana nufin ina da wata ƴar bayan su farhaana?, pleaaaaase ku faɗa min ina ƴata take ɗan Allah, ita ɗin jinin Fatima ce, matar da nafi so fiye da kowa a duniya." A fusace Ammi ta miƙe tana faɗin, " ba sai ka cigaba da maimaita cewa baka sona a gaban kowa ba razaƙ Abdulkarim, laifina ne dana so ka, sannan na biyoka Nigeria." Daga haka ta miƙe daga kan tabarmar da take, tana riƙe hannun sudais,ta bar wajen. Kasa cewa komai papi yayi, sai wasu zafafan hawaye dake sauƙa akan fuskarsa. Farhaana ce ta ƙaraso inda yake, a hankali tace "Papi zamu sameta insha Allahu, zamu nemo ƴar uwata a duk inda take a duniya, kuma Ammi zata sauƙo, but Please papi Kar kayi kuka." Rungume ta kawai yayi, baice komai ba, shi kaɗai yasan me yake ji a cikin ƙirjinsa. A hankali ya ɗago jajayen idanunsa, yana kallon mai gari, "Dan Allah ko kuna da koda hoton ƴa ta ne, zan nemo ta duk inda ta shiga a duniya." ya faɗa yana share hawayen da ya sauƙo masa. Shiru mai gari yayi kafin yace, "ai kuwa kayi matuƙar Sa'a, dan kuwa yaron da ya aure tan yana ɗaukan hoto, kuma bikin shekaran da akayi, a shekaran da yazo garinnan ya musu hotunan, ina tunanin Noor ɗin na ciki, kuma ya kawo min wasu daga cikin hotunan, bari dai na duba, dan kuwa na adanasu dan tarihi ne." "Noor!" papi ya maimaita sunan, *kenan sunan ƴata da Fatima ta haifamin Noor" sai kuma ya lumshe ido, sabbin hawaye na zirya akan farar kyakkyawar fuskarsa. Miƙewa mai gari yayi, ya nufi cikin gida, can kuma sai gashi ya dawo da hotuna a hannunsa, sai da ya kalli hoton yaga da Noor kafin yayi wani Murmushi, "aikuwa harda ita a ciki amma dai kam sai ka siya, dan bazan baka kyauta ba." Da sauri papi yace "zan siya ko da ace da dukkan kuɗin dana mallaka ne, pleaaaaase ka bani inga ƴa ta." "Ah ah sai na fara ganin kuɗin" da sauri ya miƙe yana zaro dukkanin kuɗin aljihunsa yana zube su gaban mai gari "Idan basu isa ba, zan ƙara maka, akwai wasu a mota, a can mukayi parking sai naje na ƙaro maka." papi ya faɗa yana miƙewa tsaye da alama baya cikin hayyacinsa. Zaro ido mai gari yayi ganin bandir ɗin kuɗi har huɗu, ai baisan sanda ya watsar da hoton ba ya rungumi kuɗaɗe, tsugunnawa papi yayi ya ɗau hoton yana kallo. "Subhanallah, laa haula wala ƙuwwata illa Billah." Babu inda Noor ta barsa, sai dai yanayi na Fatima data ɗauko. Wasu hawaye Masu ɗumi ne suka wanke masa fuska, kafin ya miƙe, ba tareda yabi ta kan mai gari ba ya juya ya bar wajen Farhaana na biye dashi. A jikin mota suka tarar da Ammi, ta cika tayi pam. Bai bi takanta ba ya shiga Mota, suma shiga sukayi kafin ya tada motar ya bar garin gabaki ɗaya, a zuciyarsa yana tunanin ta inda zai fara neman Noor!. ************ Idan akwai abinda yafi tashi hankali, Zannur ya shigesa, gaba ɗaya ya rasa sukuni, ya rame, kamar ba Zannur ba, sai suma da ya tara har ya masa yawa. Aƙalla yau watan Noor uku kenan babu ita babu labarin ta, yayi Neman har ya fara cire rai. An sallami Taufeeƙ a asibiti, bayan jinya da yayi, a yanzu ya warke rass, sai dai baya cewa komai, sai an daɗe yake buɗe baki ya ce wani abu, gaba ɗaya Zannur ya fita hayyacinsa, a yanzu ya ma daina neman wanda ya yi yunƙurin kashe Taufeeƙ, gabaki ɗaya hankalinsa naga inda zai ga Noor. Yasira kam, komai ya jagule mata, dan kuwa Zannur ya koreta a aiki a matsayin chief staff na kitchen, hakan yana nufin, batada hurumin zuwa inda yake, sai dai zata zauna a gidan albarkacin Taufeeƙ, sai dai batada hurumi da mai gidan, dama da hakan take fakewa tana kallonsa tana jin sanyi a ranta, gashi yanzu Taufeeƙ ya toshe duk wata hanya da zata gansa, kwata kwata, gabaɗaya tá rasa mai zatayi, tsoronta kaɗai kar ya faɗama Zannur, duk da a halin da Zannur yake a yanzu, bazai saurari kowa ba, dole ne tayi gaggawan ɗaukan mataki, kafin lokaci ya ƙure mata. Yauma, a zaune Zannur yake a dakin Noor, Wanda ya jima da tarewa anan, Camera ne a gabansa, ya zuba ma hotunan ta ido yana kallo ko ƙiftawa bayayi. Gashin kansa ya sauƙa gefe da gefen fuskar sa, he look pale, but duk da haka ya ƙara haske da wani irin kyau kamar wanda yake cikin kwanciyar hankali, ramar dayayi ne kaɗai zai tabbatar maka da halin da yake ciki. "Habibi!" yaji an faɗa da ƙarfi Ɗagowa yayi yana kallon Maami with suprise Dan baisan zatazo ba, Abbu da ya gani a kusa da Maami sai ya sake basa mamaki, amma sai baice komai ba, ya mayar da kansa wasu hawaye na taruwa a idanunsa. Da sauri Maami ta yasar da jakanta, tana ƙarasowa gabansa, ɗago fuskarsa tayi "Habibi talk to me, miye duka hakan?, Taufeeƙ ya kira mu yace muzo bakada lafiya me ya sameka, kaga yanda ka rame kuwa rabin raina?, meyasa bazaka faɗa wa Maami ba?." Kasa cewa komai yayi, kawai dai ya rungume ta sosai yana sauƙe ajiyar zuciya. A hankali ya buɗe bakinsa daya ƙafe yana faɗin "Maami Noor ta tafi ta barni, Maami bansan ta ina zan fara nemanta ba, Maami where can I find Noor?, I need to apologise, idan wani abu ya sameta bazan yafewa kaina ba. Shafa kansa tayi tana faɗin "Habibi calm down, Taufeeƙ ya faɗa min komai, zamu sameta da izinin Ubangiji, ka kwantar da hankalinka." cigaba tayi da shafa kansa, har taji sauƙar numfashinsa alamun bacci ya ɗauke sa, a hankali ta gyara masa kwanciyarsa a kan gadon. Hannunta ta sa a cikin na Abbu dake miƙa mata hannunsa. A hankali ya miƙar da ita suka fice a ɗakin, suka nufi ɗakin Maami, sai da suka isa ɗakin kafin Maami ta fashe da kuka "Abbu ka ga Habibina kuwa?, meyasa Noor ta tafi tanar min yarona a haka?, kashe min shi takeso tayi ne?. Ta faɗa tana sake fashewa da kuka. rungumeta Abbu yayi yana shafa kanta, karki damu Hilwa, Zannur will be alright, kuma za'a sami yarinyar, ki kwantar da hankalinki Please." Haka Abbu yayi ta rarrashin Maami, har sai da yaga ta samu nutsuwa kafin shima nashi hankalin ya kwanta. ************ Khamal ne ya shigo gidan yauma da saurinsa, da jarida a hannunsa, tun daga tsakar gida yake ƙwala kiran "Noor! Noor! Ina kike? A tare suka fito da umma, jin kiran yaƙi ƙarewa "Khamal lafiyanka?" Umma ta tambaya tana kallonsa. "Umma bayan mijin Noor da ke nemanta, yau kuma wani ne yake nemanta, wanda yake ikirarin shi mahaifinta ne, gashinan dai hotonta ne ɓaro ɓaro akan jaridar, sannan yasa kuɗi mai tsoka ga duk wanda ya san koda labarinta ne." Ya karashe zancen yana mikawa umma hoton. A hankali Noor ta jawo ƙafar ta ta ƙara so gaban Umma, hannu ta saka ta amshi jaridan tana kallo sai kuma tayi wani murmushi tana tafa hannunta "Kai a tunaninka kana da wayo ko?, umma ba fa mahaifina bane, Zannur ne zai raina min wayo, shine kaɗai yake da wannan hoton, shine ya ɗaukeni, ta yaya za'a yi mahaifina da koni kaina bansansaba zai samu wannan hoton, a tunaninsa idan yace mahaifina zan dawo ne hmmm." sai kuma ta ajiye jaridar ta yi wucewarta ɗaki Daga khamal har umma da kallo kawai suka bita, kafin khamal yace, "Ummah kina ganin a barta kawai?, a gaskiya Nikam zan kira numbar da aka saka dan nemanta, in sanar dasu inda take, idan ma mijinnata ne gwara yazo a sasanta komai ta koma gidanta ko ya kuka ce." "To khamal me zance maka, ka dai jira Malam ya dawo muji ta bakinsa koh?" Bai sake cewa komai ba ya juya ya bar gidan. Maimoon# *💖ABNUR💖* *By Maimoon* *Elegant online writers* 📚📖 *Page 20* Kamar yadda Umma tace kuwa, Baba na dawowa, khamal ya zo ya samesa da maganan "Khamal gaskiya kayi tunani mai kyau, amma kaɗan jira kaɗan,yarinyar tana cikin damuwa, kuma nima ina tunanin mijin nata ne yace mahaifinta, dan yasan zata so haɗuwa da mahaifinta." "Shikenan Baba, babu damuwa, duk sanda kuka ga ya dace a sanar da su, sai a sanar dasu." "Yauwa khamal Allah yayi maka albarka." "Ameen Baba" daga haka yayi ma Baba sallama ya bar ɗakin. ********** "Abdul kaji yadda mukayi da Baba, Amma gaskiya ya kamata ta koma ga mijin ta, bana tunanin zamanta anan shi yafi" khamal ya faɗa yana kallon Abdul da ke zaune a gefensa ya zuba masa ido. Gyara zama Abdul yayi kafin yace "to kai miye damuwarka ne, tunda ba akanka take ba, ka barta mana ai zasu maidata koh?" "Bazaka gane ba, ni nafiso ta koma kawai, nima kaina bansan meyasa ba, ina mata kallon ƙanwata na jini, kuma ai kaga zanso ta zauna a gidan mijinta, kuma idan ka duba yarintace kawai yasa ta baro gida, idan ba haka ba ai alkhairinsa yafi cutarwarsa yawa a gareta." "Hakane kam to mai zai hana kawai idan mun shiga cikin gari anjima, mu nemi waya mu kira kawai mu sanar da shi mahaifinnata, idan ma mijinnata ne ke ƙaryar mahaifinta, duk dai mu sanar musu, kaga da kansu zasu zo har nan su dauke ta, sai kace ba ka san ta yaya suka sani ba, ko ya ka gani." Shiru khamal yayi kamar mai tunani, sai kuma yace "kana ganin babu wata matsala?" "Kaji ka da wani zance, ai taimakonta kake son yi ba cutar da ita ba." "Shikenan to, Allah ya kaimu, sai muje mu kira ɗin." "Yauwa abokina, Allah ai yaga nufinka" Daga haka suka miƙe suka jera suna cigaba da tattauna maganan. *_Kaduna Nigeria___*_ Papi ne a zaune a falonsa, ya ƙura ma hoton Noor idanu, yayi zaton abin zai zo masa da sauƙi wajen neman Noor, Amma yanzu ya gane aiki ne babba a gabansa idan har yana so ya gana da ƴarsa. Miƙewa yayi da hoton, ya nufi ɗakin zane zanensa, a hankali ya zauna a kan kujerar zanen, ya shiga zana Noor, idanunsa na kawo ruwa, Fatima kaɗai yake tunawa, ta rasu ba tare da taji uzurinsa ta yafe masa ba. Wayar sa dake gefensa ce tayi ƙara, a hankali ya juya ya kalli screen ɗin ganin babu suna ya sashi cigaba da zannen, wani kiranne ya sake shigowa, a hankali ya kai hannu ya ɗaga yana faɗin "Assalamu alaikum" Mai shagon kiran jin an amsa ya mikawa khamal wayan yana faɗin "gashi kayi magana" Karɓa khamal yayi a nutse yana kallon Abdul dake gefensa yana gyaɗa masa kai alamun ya faɗa kar yaji komai. Cikin sanyin murya ya amsa sallaman sannan ya ɗaura da faɗin "Ina wuni?", ba tare da ya jira amsa ba ya cigaba "sunana khamal, kai ne kake neman ƴarka data ɓata?" A zabure papi ya miƙe yana faɗin "Ni ne!, eh Ni ne, ka ganta ne?, ka san inda take?, faɗa min a ina take please zanzo yanzu" "Uhm..eh Noor tana wajenmu, kuma yanzu haka mu muna Kano ne, a wani ƙauye mai suna Marke, Noor tana tare da mu a can" "Alhamdulillah, Alhamdulillah ya Allah, pleaaaaase ka min wannan taimakon, kar ka bari ta bar inda kake, zan nemi Flight zuwa Kano yanzu, Please ku jirani." Shiru khamal yayi kafin yace "ranka ya daɗe ka bari zuwa gobe mana, idan ya so sai mu zo mu jiraka, ta yanda zamu iya yin waya da kai, dan wayar ba namu bane, na wani ne muka ara." "Kar ku damu, dan Allah ku jira Ni zanzo bazan iya kai gobe banga Noor ba", ya faɗa yana fitowa da sauri daga ɗakinsa cikin sassarfa. "To yallaɓai zamu gwada jiranka sai kazo." Abdul da ke kallonsa bayan ya kashe wayar, yace "wai jiransa zamuyi?" "Haka dai yace" "Tabb, ko da yake ba zai fi awa ɗaya ba zuwa da rabi, sai mu nemi waje mu zauna, sai kace wani abin yaƙi ya bari gobe mana." "Nima haka nace amma yace kawai mu jira sa." Papi na kashe wayan ya fito da sassarfa, Farhaana da Ammi dake falon ƙasa, suka miƙe suna kallonsa. ganin yana shirin fita a falon yasa Ammi faɗin "Ina zakaje haka?, ina fatan lafiya!" Batare da ya juyo ba yaje, "na samu ƴata, zanje in zo da ita." Bai jira amsar su ba ya fice a gidan, ko driver bai nema ba yayi driving kansa zuwa airport, bai wani ɓata lokaci ba ya gama duk abinda zai buƙata, jirgi ya tashi da shi zuwa Kano. A cikin awa daya jirgi ya sauƙa a Kano. Layin da suka kirasa da shi yayi ta kira amma ba'a ɗauka, rasa yanda zaiyi yayi, idanunsa har sun kaɗa, Sake dialling yayi a karo na bakwai, kafin mutumin wanda dama su khamal sun sanar dashi ko da an kira basa nan, ya kirasu dan babu wajen zama a wajen, ya ɗaga yana faɗin "ranka ya daɗe sunje suci abinci" da sauri papi ya ce, "dan Allah a ina kuke, zanzo yanzu na samesu a nan" "To babu damuwa bari na maka kwatance." Da ƙyar papi ya samu ya isa inda suke masa bayani, dan ma mai motan da yayi shata ba inda bai sani ba a garin Kano. Motan na parking yayi saurin fitowa, da sauri mai shagon yace "ranka ya daɗe kai ne muke waya da kai?" "Eh nine Ina khamal din yake? wanda ya kira Ni ɗazu" "Eh suna zuwa ai, ina ganin bayan sunci abincin sun tsaya Sallah ne." Bai rufe bakinsa ba sai ga khamal da Abdul suna tahowa. "Yauwa gasu can ma, sune suka kiraka." Ya faɗa yana nuna su khamal. Suma tun daga nesa suka kallonsa, "Tabbass wannan shine mahaifin Noor, ko kokonto banayi" khamal ya faɗa yana dafa Abdul "To mu ƙarasa mana" Sai da sukayi musabaha, kafin yace "wayene khamal wanda ya kirani yace min yasan inda Noor ɗina take a cikinku?" Da sauri Abdul ya nuna khamal yana faɗin "ai a gidan su noor ɗin take." Rungume sa papi yayi, ba tare da tunanin komai ba, "Nagode khamal, dan Allah ka kaini wajen ƴata yanzu ina so in ganta." "Babu damuwa yanzu zan kaika, zakaga ƴarka insha Allahu" kamal ya faɗa yana ɗagowa daga jikin papi. Sai da suka ma mai shago godiya kafin papi ya basa kuɗi masu yawa, ai kuwa ya zube yana ta godiya. A motar da papi ya zo da ita suka nufi cikin ƙauyen, kasancewar mota kan shiga yasa har ƙofar gidan su khamal suka zo. Sai lokacin khamal yayi tunanin, me su Umma zasuce masa?, amma sai ya share ko ma me zasu ce, shi ya haɗa ƴa da mahaifine. Noor da ke tsakar gida tana kwasan shanya, taji zuciyarta ta buga da ƙarfi, da sauri ta dafe ƙirjinta tana faɗin "inna lillahi wa inna ilaihi raji'un" "Lafiya Noor" Umma ta faɗa daga zaunen da take a tsakar gida tana kallonta. "Zuciyata ce ta tsinke Umma, babu komai" daga nan ta cigaba da Abinda takeyi. Baba da ya fito daga ɗakin Umma yana shirin fita, sai ga khamal ya shigo jiki a sanyaye. Sunkuyar da kansa yayi kafin yace "Baba mun yi baƙo yana neman izinin shigowa" Da mamakin duk suke kallon sa kafin, Baba yace "wayene?" Khamal bai amsa ba hakan yasa Baba faɗin "kace masa ya ƙaraso, tunda kai ka kasa faɗan wayene." Sai kuma ya juya ga Noor Yana faɗin "Noor ɗauko wani tabarmar a shinfiɗa masa." "To Baba" ta faɗa tana sake jin yadda zuciyarta ke bugawa. Sallamar da taji ya sata saurin ɗagowa dan taji ta kwaɗaitu da ganin mai sallaman. Cikin idon mahaifinta idanunta suka faɗa, da sauri ta dafe ƙirjinta tana kallonsa babu ko ƙiftawa. Shikam hawayen idanunsa ne suka kasa tsayuwa, suka shiga sauƙa akan fuskarsa. Da sauri ya ƙara so ya na faɗin "Noor!" Da kokonto, wai gashi ga ƴar Fatima kuma ƴarsa, ko dai mafarki yakeyi ne? Itama tuni hawaye ya jiƙa fuskarta, dan tabbass bata buƙatar ace mata wannan mahaifinta ne, kamar da takeyi da shi ma kaɗai ya wadatar. Da sauri ya nufe ta, yana faɗin " yarinya ta ashe kina nan?, ina ta nemank...." Hannu ta ɗaga masa da sauri idanunta na kwararar da hawaye, "Kar ka ƙaraso kusa dani, Ni ba ƴarka bace, kuma bazan taɓa zama ƴarka ba, da ace Ni ƴarka ce bazaka taɓa wofintar da rayuwata da ta mahaifiyata ba, bana son ganinka Dan Allah ka tafi ka barni, in cigaba da rayuwa kamar yanda na faro." With shock yake kallonta, amma ya gagara ƙara ɗaga ƙafan kamar yadda ta faɗa "Noor ki saurareni, ban wofintar da ku dan son raina ba, hasalima bansan da akwai cikinki ba Noor, kuma wallahi duk duniya babu wanda ya kaini sonku ke da Fatima." "ƙarya kakeyi kai ba mahaifina bane, kuma bazan taɓa ɗaukan ka a matsayin mahaifina b........" Tass!, sauƙar Marin da taji a fuskarta, ya sata haɗiye sauran maganan da ke bakinta, tana kallon Umma da shock, Jawota Umma tayi ta rungume, tana kuka itama tana faɗin, "Noor mahaifinki ne shi, ko me yayi miki bai cancanci ko wani irin magana daga bakin ki ba, ki sauraresa kiji dalilinsa, daga nan sai ki yanke duk hukunci da kika ga ya dace dashi." Fashewa tayi da kuka tana sake rungume Umma, "Ummah baya so na, bayason Nenne, shiyasa ya tafi ya barmu, kowa baya sona, Zannur baya sona, wani irin rayuwace irin tawa." Ta faɗa tana ɗurkushewa a wajen, tana cigaba da wani irin kuka mai taɓa zuciya. Da sauri papi da ya gama daskarewa a tsaye, shima ya kai ƙasa ya riƙo ta gabaɗaya, fuskarsa ta gama yin jajazir. 'Wayace miki banasonki Noor" ya faɗa jikinsa har rawa yakeyi, "wallahi Noor nafi kowa sonki, pleaaaaase ki yafe ma papi kinji daughter." Rungumesa tayi tana sake fashewa da sabon kuka, shi kanshi ya kasa daurewa, hawaye kawai ke fita daga idanunsa, ya rungumeta sosai a jikinsa yana jin kamar ya maida ita cikinsa ya sake haifo ta, saboda tsananin son da yake ji yana mata. Sun ɗauki tsawon lokaci, kafin kowa ya dawo nutsuwarsa. Baba da ke tsaye har lokacin yayi gyaran murya yana faɗin, "To masha Allah, Allah mai hikima" Umma da ta ƙarasa shinfiɗa tabarmar da Noor ta yasar tace, "Alhaji bismilla." Khamal kam da Abdul kallon ikon Allah kawai sukeyi. Kafin kowa ya sami waje ya zauna, Noor kam tana jikin papi, Dan shi kanshi ya ƙi bari ta matsa daga kusa da shi. Sai da kowa ya nutsu kafin Baba ya faɗa ma papi komai da ya faru, daga haɗuwarsu da Noor zuwa yanzu. Jinjina kai kawai papi yakeyi kafin yace "nagode, nagode, bansan da wani kalma zan yi anfani in gode muku ba, dan kun riƙe min yata mafi soyuwa a gareni, bani da abinda zan biyaku da shi, sai dai ina muku addu'ar Allah ya saka muku da mafificin alkhairinsa." Ameen duk suka amsa dashi kafin papi ya ɗora da fadin, "kuma ina neman alfarmarku, ku barni in tafi da Noor yau, dan Allah." Da sauri Umma tace "Alhaji da dai an bari zuwa gobe, yanzu yamma tayi", ta faɗa hawaye na ciko idanunta dan sam batason rabuwa da Noor. "Ah ah Aisha ki barshi ya tafi da ƴarsa, ai da nan da can duk ɗaya ne, kuma ai zumunci ba yanke wa zai yi ba, Noor ƴarkice har abada." Da sauri papi yave "wannan haka yake, har abada zumuncin ku da Noor ba zai taɓa yankewa ba na muku alƙawarin hakan." "Shikenan Alhaji mun gode sosai", Umma ta faɗa tana matsar hawaye. Babu abinda Noor ta ɗauka, daga ita sai kayan jikinta, sai gyalen abayar a kanta suka fito daga gidan, su Umma suka musu rakiya har bakin mota, Zare hannunta Noor tayi daga na papi, da sauri taje ta rungume Umma tana kuka, A hankali Umma tace "Noor ki kwantar da hankalinki, insha Allahu zamuzo muga inda kike bada jimawa ba kinji." Gyaɗa kai tayi kafin taje gurin Baba dake tsaye shi kansa daurewa kawai yakeyi "Baba zan tafi' ta faɗa tana rufe fuskarta saboda kukan da ya ci ƙarfin ta, "Allah ya miki albarka Noor, sai munzo." Ya faɗa yana shafa kanta, juyawa tayi zata shiga motar, khamal yace "Wato Ni kadai ne baza'a ma sallama ba koh Noor?" Da sauri ta juyo tana kallonsa Murmushi yayi yana faɗin ba "laifinki bane wato anga Baba, an manta da yaya ko?" Kuka ta fashe da shi, da sauri Baba yace "khamal ka kiyayeni fah." Dariyar ƙarfin hali khamal yayi ya matso kusa da ita yana faɗin "wasa nake miki ƙanwata, Allah ya kiyaye hanya ya kai mana ke lafiya Noor, sai munzo." Ɗago idanunta tayi kafin a hankali tace "nagode" Bai ce mata komai ba ya buɗe mata baya ta shiga, papi ma sallama yayi musu ya shiga motar, driver ya tada motar suka bar ƙauyen suna ɗaga ma juna hannu. Maimoon# *💖ABNUR💖* *By Maimoon* *Elegant online writers* 📚📖 *Page 21* Har suka isa Airport, babu mai cewa komai a motan, daga Noor har Papi, kowa da irin tunanin da yake a zuciyarsa. Juyowa Papi yayi ya kalleta, yadda ta matsa can jikin window, ta jingina kanta, idanunta a lumshe, sai kayi tunanin bacci takeyi. Amma a bangaren Noor tunani kawai takeyi, gwara ma tayi nisa da Zannur, idan ta tafi tare da mahaifinta, bazai sake ganinta ba, bazai sake jin ɗuriyarki ta ba, ta fita daga rayuwarsa na har abada. Tsayuwar da motar yayi, shi ya dawo dasu daga tunanin da suka lula, a hankali suka sauƙo daga motar, kowannen su jikinsa a sanyaye yake. Har papi ya gama duk abinda zasu buƙata, hannunsa na cikin Noor, haka suka shiga jirgi yana riƙe da hannunta. Duk da Noor bata taɓa shiga jirgi ba, but ta daure sosai, har jirgin ya daidaita a sararin samaniya. Ƙarfe 8:00 na daren ranan Papi ya shigo da Noor cikin gidansa, a matsayin ƴarsa halak malak, wacce zai iya nunawa duka duniya with proud yace "Noor ƴatace." A Falon ƙasa suka sami Sudais da Namra, suna hide nd seek, suna ganinsa suka nufosa da gudu suna faɗin "papi" Ɗaga sudais yayi yana dariya kafin yace "kazama ƙatoto kaima fa" duk suka tuntsire da dariya, Namra tace "papi you are welcome" ta faɗa tana kallon Noor. Jawo hannunta yayi yace "oya common, greet your elder sister" What's her name? Namra ta tambaya tana cigaba da kallonta, dan ganin tsananin kaman da sukeyi da papinta. "Noor"ya faɗa yana murmushi. Ƙarasowa tayi gaban Noor kafin tace "Ina wuni anty Noor" Wani sanyi Noor taji tundaga tsakiyar kanta har babban yatsanta, Yanzu waɗannan ɗin ƙannen ta ne? Wani irin sonsu taji ya shiga ranta fiye da tunaninta, Ta tsura ma Namra ido bata ko ƙiftawa. Ammi dake sauƙowa daga sama, Farhaana a biye da ita, suka ƙaraso Falon, fuskar Ammi babu yabo babu fallasa, tace "sannunku da zuwa." cikin harshen larabci. Da sauri Farhaana ta ƙaraso tana kallon Noor, sai kuma ta juya ta kalli papi da sauri. Gyaɗa mata kai yayi yana murmushi. Ai da gudu ta ƙaraso ta haye jikin Noor tana faɗin "ukhty, Finally mun sameki, muna ta nemanki up and down, Ina kika shiga kika sa Papi kuka" Dariya kawai Noor tayi, sannan tace "gani ai na dawo" ta faɗa tana matsar da Farhaana daga jikinta ta nufi Ammi dake Zaune, tsugunnawa tayi a hankali tace, "ina wuni Nenne" Wani kallo Maami tayi mata, kafin tace "point of correction, Ammi, Ni ba Nenne bace, Ni Ammi ce." Ta faɗa tana miƙewa ta bar falon. Da ido duk suka bita, kafin papi ya ƙaraso ya riƙe hannun ta "don't worry daughter, that's how she is, but zata sauƙo kinji, muje in kaiki ɗakin ki kiyi wanka kiji abinci, kiyi bacci, kin gaji, gobe sai ayi introducing ɗinki ga kowa duk dama kowa ya sanki,kece dai baki san kowa ba." Batace komai ba tabi bayansa, har ya fara hawa steps ya juyo ya dubi Farhaana, kafin yace "kuje ku kwanta dare yayi" "Night Papi" duk suka faɗa a tare "Night Papi's Angels" Daga haka ya ja hannun Noor suka haura sama, sai da ya kaita wani katafaren ɗaki, da ya gaji da haɗuwa, kafin ya ce mata "Daughter kiyi wanka akwai kaya a cikin siff ɗin, kafin zuwa gobe muje muyi shopping, za'a aiko miki abinci, sai kici ki kwanta kinji rabin raina?" Kallon sa kawai takeyi, har ya miƙe ya je bakin ƙofa ya tsinkayo muryarta tana faɗin "Meyasa ka tafi ka bar Nenne na,sannan ka kasa dawowa har sai bayan bata raye" ta faɗa idanunta na ciko wa da hawaye. Cak ya tsaya da tafiyan, kafin ya juyo a hankali, dawowa yayi ya shafa kanta shima nasa idon na cika da hawaye "daughter kin gaji, ki samu ki huta, zamuyi maganan gobe alright?" Ya faɗa yana kallonta, dan dama ko bata tambaya ba gobe dolene ya sanar da ita. Daga haka ya juya ya fice a ɗakin yana jin sanyi a ransa. Sai da ta yi wanka, sannan ta shirya cikin kayan bacci masu laushi, riga da wando, band ta sa ma kanta, kafin ta juya ta kalli tray ɗin dishes ɗin da aka ajiye akan ɗan madaidaicin dining table dake ɗakin, ƙarasawa tayi ta zauna ta buɗe abincin. Bata wani ci sosai ba, ta dai ɗan tsatsakura, kafin ta miƙe, taje ta ƙarayin brush, tare da alwala, sallah tai-tayi tana godiya ga Allah da ya sada ta da mahaifinta, cikin lafiya da kwanciyar hankali. A bangaren papi ma haka ne, ya kasa bacci, shima alwalar yayi, ya hau sallaya, yana ƙara gode ma Ubangiji da ya haɗa sa da ƴarsa sannan yayi ma Nenne addu'o'i sosai yana jin he is relieved from a very big burden. A daidai wannan lokaci kuwa a garin Abuja, Zannur ne akan sallaya, babu abinda yake roƙo da addu'a akai sai Allah ya sa dashi da Noor. Har ƙarfe 2:00 kowannensu na kan sallayarsa, kafin dukaninsu suka miƙe kamar suna ganin juna, kowa ya kwanta tare da addu'an bacci, da tunani iri, iri acikin ransa (Asuba ta gari 🌝). Washegari Noor ta tashi cikin matuƙar farin ciki, tare sukayi breakfast da duka ƴan gidan, kafin papi ya faɗa mata sunayensu da shekarun su,sannan suka zaga da ita ko ina a gidan, ita dai murmushi kawai takeyi. Ammi kam daman suna gama cin abinci tayi wucewarta ɗakinta. Kamar yadda papi ya faɗa kuwa haka akayi, shopping suka tafi har da su Farhaana. Noor taga gata, wanda ake kira gata, dan daga ƙarshe fashewa tayi da kuka kawai na tsantsan farinciki. A gajiye suka dawo da kaya niƙi niƙi, kamar masu buɗe supermarket, tare duk suka shirya kayan tsaf, kafin Papi yace "Noor kiyi wanka sai ki sameni a ɗakina." Noor tace "toh papi" Fita yayi ya bar su, ya koma part ɗinsa. Sai da ta gama duk abinda zatayi kafin ta nufi part din papi, a can ta samu Ammi, da alama Papi ne ya kirata, waje ta samu ta zauna, kafin papi yayi gyaran murya ya fara faɗin "Noor, nasan zakiso kiji, miye dalilina na barinku danayi, a yanzu zan sanar dake." Gyaran murya yayi kafin ya cigaba. "Ni asalina ba ɗan ƙasar nan bane, mahaifina da mahaifiyata duka ƴan Dubai ne, ƙaddara ita ta haɗani da Yusuf a makaranta, ɗan Nigeria ne da yake karatu a Dubai, sakamakon scholarship da ya samu, tunda na haɗu da Yusuf, muka shaƙu sosai, har ya zamana kamar shine best friend ɗina, sannan ina matuƙar sha'awar Yaren Yusuf wato Hausa, da Yusuf yaga ina so, sai ya fara koya min, kasancewar ina da saurin koyan abu, cikin lokaci ƙalilan na fara gane Yaren Hausa, amma sam iyayena basason abota na da Yusuf, a ganinsu shi bak'ar fata ne, ɗan Nigeria, wanda Ni sam bai dame Ni ba. Kullum Idan Yusuf ya tashi zuwa Nigeria ganin iyayensa, sai naji kamar na biyosa, saboda yadda nakeson ƙasar a raina, amma ina tsoron iyayena. Ana haka sai muka gama makaranta, Yusuf yace min idan ya tafi ba lallai ne ya sake zuwa ba, alokacin na masa alƙawarin zanzo Nigeria gurinsa, Yusuf ya dinga jin daɗi. Bayan tafiyan Yusuf, sai na rasa me zan ce ma iyayena, su barni na zo Nigeria, kasancewar Ni architecture ne yasa nace musu na samu wani contract, da zai iya ɗauka na aƙalla wata shida, a wata ƙasa, amma banyi kuskuren ce musu a Nigeria ba. A zatona, wata shida ya isheni, in San Nigeria, da komai nata, in iya yarenta, sannan in zauna da Yusuf Abokina. Iyayena basuyi kokonto ba, suka barni na tafi, tunda nazo Nigeria na ringa mamakin irin gidan da Yusuf ke ciki, gida ne ƙarami, mai ɗakuna biyu kacal, kuma a unguwar talakawa, hakan yasa na kama mana apartment guda muka zauna, a cikin garin Kaduna. Kullum sai mun je mun zaga gari, mun ga abubuwa iri-iri, farinciki nakeyi sosai, kasancewar wannan shine abinda nake so. Ana haka Yusuf yace min zaije ganin iyayensa, amma bazan iya zuwa ba, saboda a ƙauye ne, ai kuwa nace bai isaba, ko a jejine sai naje. Haka muka shirya, muka nufi Baulawa, wanda shine ƙaddarar haɗuwa ta da Fatima. Yusuf ɗan mai gari ne,hakan yasa muka sauƙa a gidan mai gari, amma kullum sai mun fita, ganin gari, saboda yadda garin keda matuƙar kyau. Tun ganin farko da nayi ma Fatima a wani bikin shekara da ake yi a ƙauyen, Allah ya ɗaura min matuƙar sonta, har mamaki nakeyi, tayaya za'a yi na so ɗan Nigeria, iyayena baza su taɓa amincewa ba. Amma babu ruwan zuciya, tun ina binta bata yarda, har itama ta fara kulani, soyayya mai matuƙar tsafta ta shiga tsakani na da ita, duk da sati ɗaya mukazo yi da Yusuf,amma sai nace masa Ni bazan tafi ba, Yusuf yayi ta min dariya, yana faɗin "ka dai ga ƴar fara kyakkyawa" sai dai kawai nayi murmushi. Babu yadda na iya bayan mun cika kwana goma, haka na tafi na bar masoyiyata Fatima, tare da alƙawarin zan dawo idan Yusuf zai sake zuwa, dan kuwa makarantar da Yusuf ke koyarwa sun nemesa. Hankali na bai tashi ba, sai da na yi waya da mahaifiyata, kwana biyu bayan dawowan mu daga Baulawa, ita take sanar dani wai kar nakai wata shida na dawo, za'a haɗani da ƴar uwata Nadiya aure, saboda yadda take mutuwar sona. A take nace mata, Ni bana sonta, amma sai ta ce min, ai sun riga sun amince. Ƙarshe sai ce mata nayi, ai bazai yiwu in dawo ba tunda contract ne, su jira six months ɗin. Haka suka aminci badan ransu ya so ba. Ni na uzura ma Yusuf, muka sake komawa Baulawa. tunda naga Fatima, nasa a raina, bazan iya rayuwa babu ita ba, kasancewar a hannun matar mahaifinta take, sam bata samun kulawa. Ai kuwa ina zuwa na zame mata cingam, ko ina zata je sai na bita, har mutane suka fara saka mana ido. Ranar da bazan taɓa mantawa ba, a rannan ina zazzaɓi, hakan yasa banje ko ina ba, tun safe bamu haɗu da Fatima ba. Yusuf kuma yaje gurin mai gari, ina kwance, sai naji an buga ƙyauren a hankali, miƙewa nayi da ƙarfin hali, na buɗe, ga mamakina sai naga Fatima. Dana ce ta shigo, sai naga kaman tana tsoro, sai nace mata babu komai ta shigo, idan bata shigo ba bazan kulata a wajen ba, dan jiri nakeji bazan iya tsayuwa ba, hakan yasa ta shigo, kwanon abinci ta ajiyemin, tace wai ta kawo min inci, murmushi nayi na ɗauka ina ci muna hira da ita, amma duk ta kasa sakewa. Can kuma sai ta miƙe tace min, ita zata tafi, hakan yasa nima na rakota ƙofa. Mutanen da muka gani a bakin ƙofa ya sani matuƙar mamaki, dan kuwa kusan rabin ƴan garin suna bakin ƙofar mu. Haka suka ƙeƙashe suka ce wai ɓata mata tarbiyya nakeyi ai sun jima da ganin take-takena, abun ya bani mamaki, alokacin sai ga Yusuf, shima yayi iya ƙoƙarinsa ya fahimtar da su amma sam suka ƙi fahimta, a nan take suka ce sai dai muje a ɗaura mana aure, dan su ba'a ɓata musu yara a zauna lafiya, Bayan ɗauki ba daɗi da akayi tayi, ganin Fatima na kuka, kuma nasan Ni na janyo mata, kuma ina sonta yasa na amince, ai kuwa ba'a ɗau lokaci ba aka ɗaura mana aure wanda nake jinsa yamin banbaraƙwai, su wasu irin mutane ne, babanta bai damuba, haka ma kishiyar mahaifiyarta, washe gari muka bar ƙauyen, muka taho cikin Kaduna, anan muka zauna. Wani irin tsabtataccen soyayya muke shimfiɗawa, wanda har nakejin rayuwata tafi ko yaushe daɗi, bana son tuno cewa wata shida nayi da mahaifana. Kwanci tashi, har wata shida, ya wuce, amma bana tunanin komawa gida, iyayena sunyi kira har sun gaji bana ɗauka, a wata na takwas na samu mail daga baba na, yayi bincike ya gano ina Nigeria, kuma idan har ban koma ba a cikin sati na gaba, shikadai yasan abinda zai min. Nasan halin mahaifina, yana da matuƙar zuciya, hakan yasa na yanke shawaran komawa, but zan je in shayo kan iyayena, in dawo in tafi da Fatima. Na yi ma Fatima bayanin komai, ta amince, amma ta sa nayi mata alƙawarin zan dawo gareta. Nayi iya yi na, inga na fahimtar da iyayena, amma sam suka nuna basu san da maganar ba, har ƙoƙarin tsine min sukayi idan har na cigaba da wannan maganan. Sannan basu ɓata lokaci ba suka ɗaura min aure da Nadiya, sannan sai da mahaifina ya tabbatar ya goge duk wani abu da zai haɗa Ni da Yusuf, bare har inji lafiyan Fatima, bayan haka, mahaifina da mahaifiyata, suka ce, idan har na taka ƙafa na a Nigeria, to wallahi bazasu taɓa yafe min ba. na shiga wani hali, har sai da na kwanta a asibiti, amma kasancewar bani da mafita ya sa na hakura na auri Nadiya, Wanda Alhamdulillah yanzu muna da ya'ya har uku da ita. Yusuf kam ganin kuɗin gida ya ƙare, kuma bazai iya sake biyaba, yasa ya tattara Fatima ya mayar da ita Baulawa, amma acikin kuɗi mai yawan da na bashi kafin na tafi, sai ya siya mata gida, sannan yace musu nayi tafiya ne kuma zan dawo. Sam bansan akwai cikinki ba, ita kaɗai tayi renon cikinki ta haife ki. A yanzu haka da nake faɗa miki, mahaifiyata da mahaifina, sun rasu a wani plane crash a hanyar su ta zuwa Iraq, Amma kafin tafiyarsu sun tabbatar min zan iya zuwa Nigeria. Naji matuƙar daɗi ashe sune zasu barni, dan tafiyan da basu dawo ba kenan. Sai dai kash, ina zuwa sai mai gari ya sanar da Ni Fatima ta rasu, ke kuma kinyi Aure. a wajensa na samu hoton ki, na bazama nemanki, amma na rasa ki, sai bawan Allah khamal ya kirani yace kina wajensa." Ya faɗa ya share hawayen idanunsa. Itakam Noor kuka take wiwi, ita kanta Nadiya kuka takeyi, dan bai taɓa bata labari ba, kenan Nenne yake zanawa duk kwanan duniya? A hankali ta taso ta ɗago Noor tana faɗin "kiyi haƙuri Noor, insha Allah zan maye miki gurbin Nenne." Da mamaki yake kallonta, kafin yayi murmushi yace "Nadiya na gode." Sai da suka ɗan lafa, kafin ta sake basu labarin tasowarta da rasuwar Nenne, zuwa aurenta da Zannur har kawo yau. Duk shiru sukayi suna jinjina al'amarin, kafin Noor tace "To papi Ammi da su Farhaana kuma a ina suka iya Hausa?" Murmushi Ammi tayi tana faɗin "ai kowa ya zauna da shi sai ya iya Hausa, sai da ya tabbatar mun iya" ta faɗa tana dariya, Shima dariyar yayi. A ranan sun wuni cikin farinciki a gidan, jifa jifa takan tuno Zannur, amma sai ta kauda a ranta, dan bataso tana tunoshi. Rayuwar Noor a gidan iyayenta, rayuwa ce mai cike da kulawa, gata, da soyayyah, babu abinda ta nema ta rasa, hakan yasa ta sake kyau, ta sake zama ƴar gayu, dan kuwa, Ammi basuga wannan shopping center ɗin, basuga wannan. Zannur kam....... Maimoon# *💖*ABNUR*💖* *By Maimoon* *Elegant online writers* 📚📖 *Page 22* Zannur kam, gaba ɗaya ya rasa me ke masa daɗi, ya canza kamar ba shine Zannur the master of All ba, tun Maami na ɗauka da wasa, har hankalinta ya soma tashi, kwata kwata ya daina walwala, ko magana ba yayi sai dole. sometimes Maami har kuka takeyi, sai dai Abbu ya rarrasheta, zuwa yanzu shima abin ya fara damunsa. Yasira ta rasa yanda zatayi, gabaɗaya komai ya kufce mata, ita sam ba haka ta so ba, to yaushe ma Zannur ya soma son Noor har haka?, lallai tayi mugun sake. Amina da Asabe kansu sun rage walwala, da yake yanzu Amina ce chief of kitchen staffs, kullum ta gansa, cikin damuwa take ganinsa, duk da cewa a da ma ba wani shiga harkarsu yakeyi ba, sai dai Taufeeƙ, amma yanzu daga shi har Taufeeƙ sun zama wasu iri, hakan yasa gidan kowa baya cikin farinciki. ******* "Habibi wai meyasa yanzu baka jin maganata ne?, rabonka da abinci tun yaushe?, Please Habibi kaci abinci kaji?" ta faɗa da alamun damuwa a tattare da ita Bai ɗago ba, bare tasa ran zai tanka, hakan yasa ta ajiye tray ɗin akan center table na ɗakin ta juya ta bar ɗakin tare da ja masa ƙofa. Tray ɗin abincin ya ƙura ma ido, yana jin zuciyarsa na bugawa da sauri, bai taɓa sanin yana ma Noor irin Wannan matsanancin son ba, har sai da tayi nisa dashi. Ɗaga idanunsa yayi yana kallon saman ɗakin, kafin ya shafa kansa, yana gyara kwanciyarsa a kan gadon Noor. *********** "Abbu ya zanyi?, yarinyar nan ta cutar min da yarona, me yasa in the first place zata tafi ta barsa?" Maami ta faɗa tana fashewa da kuka. Jawota Abbu yayi ya rungume, shi kansa daurewa yakeyi, a hankali yace "Hilwa, listen to me, ki kwantar da hankalinki, idan har tana raye za'a sameta." Ya faɗa yana shafa sumar kanta, ɗayan hannun kuma yana share mata hawaye Shiru tayi tana kallonsa, kafin tace "Abbu ya zamuyi mu taimaka ma Habibi ya sami yarinyar nan?, don itace kwanciyar hankalin mu duka." Shiru Abbu yayi kafin yace, "ga shawara" Da sauri ta miƙe daga jikinsa tana faɗin "Dan Allah Abbu faɗa min, zan yi ko miye ne" Murmushi yayi yace "Me zai hana mu siyi gaban mujallar gobe, mu da kanmu on behalf of Zannur, mu roƙi Noor ta dawo." Shiru tayi sai kuma tace "Shikansa Zannur ɗin ya sa an buga mujalla ana nemanta, but ba'a sameta ba." "Nasani Hilwa, but still zai iya yiwuwa, shi tana jin haushinsa, amma ai mu zata ji kunyar mu ta dawo, mu dai kawai ba burinmu Noor ta dawo ba?" Shiru Maami tayi, kafin tace "Allah ya sa mu dace, wannan yarinya dai ta taimake Ni ta dawo." Kamar yadda Abbu yace, haka mujallar washegari ta fita da jawabin Abbu da Maami, da hoton Noor ba tareda ko shi Zannur ɗin ya sani ba. Papi dake karatun jaridar safiyar ne ya ci karo da hoton Noor da kuma bayanin su Abbu, wanda duk banbaki ne, da kuma sanar da ita haalin da Zannur ke ciki akan rashin ta. Murmushi yayi a hankali ya furta akan laɓɓansa "Daughter kinyi punishing ɗinsu enough, it's time ke ma kiyi rayuwa kamar kowa da mijinki" Daga haka ya juya ya fito a ɗakin, Ammi ya samu a ɗakinta tana shirya siff ɗin ta, a hankali ya ƙaraso da sallama, kafin ya samu guri a gefen gadonta ya zauna yana kallonta Ƙarasawa tayi, itama tazo kusa dashi ta zauna tana faɗin "Is anything wrong?" Murmushi yayi mata yana jan kumatunta, "Babu komai Fah, look how you are worried for reason" Murmushi tayi itama tana faɗin "dole na damu na ganta kamar abu na damunka." Shiru yayi sai kuma yace "Ina Noor?" "Tana ɗakinta, I think bacci ma takeyi." "Ok", ya faɗa yana ɗaura mata jaridan akan ƙafarta Sai da ta gama karantawa kafin tace "to yanzu kai me ka yanke akan hakan?" "Zata koma gidan mijinta mana, babu abinda yafi mata daraja kamar wannan, sannan ai sun gane kuskurensu, and am sure they won't repeat" "Ok but da munji ta bakinta" "Nope ki ce mata ta shirya zamuyi tafiya, i will return her myself, sannan in yi magana da mijinnata" "Ah ah sai dai mu tafi tare Please Papi, Ina so in kai ƴata da kaina gidanta." "Ok babu damuwa, zan kira su a waya tunda sun bada Number ɗin da za'a yi contacting ɗinsu, in yaso zuwa Next week sai mu tafi." "Allah ya kaimu" Daga haka ya miƙe ya fice a ɗakin Waya Ammi ta ɗauka ta kira wata balarabiyar ƙawarta, kayan gyaran jiki irin na amaren larabawa take só ta haɗa mata, and tana so ta turo mata zuwa gobe please it's urgent. Sai da ta tabbatar mata babu damuwa, kafin ta kashe wayan, ta sake kiran wata ƙawarta wacce suka haɗu a Nigeria, watannanin da suka wuce, matar shuwa Arab ce, itama dai kayan gyaran jikin ta tambayeta, aikuwa matar tace mata zuwa gobe da safe ɗan ta zai kawo mata, a taƙaice dai Ammi sai da ta kira mutum kusan uku. Washegari kuwa kaya suka iso, na Dubai ne kaɗai sai zuwa yamma. Noor da bata san abinda ake ciki ba, washegari sai gani tayi Ammi ta saka ta a gaba da gyara, daga a mata wannan sai a mata wancan, daga a bata wannan sai a bata wancan, da ta tambaya sai Ammi tace, so take ƴarta tafi ta kowa kyau, ita kuwa Noor ta yarda ta zage tana karɓan duk abinda aka bata. Zuwa kwana uku, Noor ta koma wata sabuwar halitta, wani irin glow da skin ɗinta keyi kaɗai har abin mamaki ne. Ita kanta har tsayawa take tana kallon kanta, Farhaana kam tasa ta take a gaba, tayi ta kallo sai dai kawai tayi murmushi. Papi sunyi magana da Abbu, dan har ya sanar ma Maami, amma ko da wasa, basu sanar da Zannur ba, dan so suke suyi masa abinda ake kira suprise. Da yamma Zannur na sauƙowa daga sama, dan yau yana so ya ɗan fita, kasancewar ya kwana biyu baya fita ko ina. Maami da Abbu dake magana sukayi saurin yin shiru, suka zuba masa ido suna kallonsa, Maami na sake gode ma Allah a ranta, wai wannan kyakkyawan cikakken namijin ɗan ta ne. yana sanye da riga da wando na Louis Vuitton, Dan dai shi baya anfani da kowane kanfani idan ba wannan ba, sai dai gabaɗaya ya gama yin sanyi. Ƙarasowa yayi falon yana kallonsu, sai kuma ya samu waje ya zauna yana faɗin "Maami, Abbu me kuke cewa ne?, naga kunyi shiru da na zo, Ku cigaba da maganan mana, ina so inji" Ya faɗa yana kallonsu "Ehm dama batun komawa mukeyi, mun yanke shawara zamu tafi tare da kai Ko ba haka ba Abbu?", ta faɗa tana ƙiftawa Abbu ido. Murmushi kawai Abbu yayi ba tare da yace komai ba. Cikin rashin damuwa da maganar yace "Maami i don't wanna leave, ku tafi kawai ku barni." Shiru Maami tayi Jin yadda yayi maganan, he sound very worried, sai taji kamar tace masa jibi iwar haka Noor tana tare da shi. Cikin sanyi itama tace "meyasa?, saboda Noor ne bazaka bi mu ba?" Ta tambaya tana kallon fuskarsa Kallonta yayi sai kuma yayi ƙwafa yana faɗin "not at all since ita ta zaɓi ta barni, ba yanda zanyi da ita, I guess zan haƙura kawai, i won't force her into anything she don't wan't to, I will move on with my life, bana buƙatar in cigaba da tauye rayuwata a kanta, zan yi iya ƙoƙarina inga na saba da rashin ta." Daga haka ya miƙe ya bar falon gabaɗaya. Da ido duk suka bisa, Maami kam baki sake take kallonsa, kafin ta juya ta kalli Abbu, gyaɗa mata kai yayi tare da faɗin "kar ki damu idan ya ganta komai zai dai-daita." "Allah yasa" ta faɗa cikin sarewa. Mutanen Kaduna sun gama shirin tafiya, wanda sam Noor bata san inda zasuje ba, dan ko da wasa babu wanda ya faɗa mata komai. Tun a Airport take jin wani irin tsinkewar zuciya, a hankali ta kama hannun Papi ta riƙe tana maimaita duk addu'ar ta tazo bakinta. Tunda aka kira passengers ɗin Abuja ta sake jin ƙirjinta ya buga, juyawa tayi ta kalli su Farhaana da Ammi da har sun wuceta. Jan hanunta da akayi ya sata dawowa cikin hayyacinta, tana kallon Papi "Daughter what are you thinking?, muje Mana" ya faɗa yana murmushi "Papi zuciyata ce ke tsinkewa" ta faɗa idonta na ciko wa da hawaye ""Common not now Noor!, kiyi addu'a babu komai sai alkhairi, kinji?" "To" tace, kafin Papi yaja hannunta suma suka bi bayan su Ammi. Har jirginsu ya tashi, ta kasa samun nutsuwa. In less than 30 minutes jirginsu ya sauƙa a Abuja, waya Papi yayi da Abba, akan sun iso, wanda dama tuni driver na jiransu a Airport ɗin. Tunda suka ɗauko hanya daga Airport Noor ke zare ido, ganin in da suka nufa yasa Noor fashewa da kuka, janyota Ammi tayi tana faɗin "miye hakan Noor?", Kasa cewa komai tayi, sai shesheƙa da takeyi. A hankali ta ɗago kanta, tana ƙare ma compound ɗin parking space ɗin kallo, tabbass su Papi gidan Zannur suka dawo da ita. Body guards Ne suka ƙaraso tareda buɗe musu ƙofan motan, gaba ɗaya zama tayi kamar doluwa, tana bin kowa da kallo, a hankali ta zuro ƙafafunta ƙasa, tana jin wani iska na kaɗa ta, ta ko ina a jikinta. Cikin nutsuwa ta sauƙo tana kallo su Papi da su Farhaana da har sun yi gaba abinsu. Riga da wando ne a jikinta na *PRADA,* sai kimono da ta sanya a zamansu kalar maroon, veil ɗin kanta shima kalar maroon ne, sai karamar jakar dake rataye a kafaɗanta, gashin ta ya kwanta lub lub har gaban goshinta, da gefen fuskarta, fuskarta looks natural, Dan babu komai a fuskar, lips ɗinta sun yi pink shar suna shining kamar ta saka lip gloss, Wanda sam babu abinda ta saka, haka suke naturally, ƙafafunta sanye cikin flat shoes na *GUCCI* . Papi jin baiji alamar ta ba, ya sa shi juyowa, sai kuma yayi murmushi yana dawowa inda take, siririn hannunta dake sanye da agogo na *CHANEL* ya janyo yana faɗin "Ya kika tsaya anan daughter?, mu ƙarasa Mana." Binsa kawai takeyi kamar wata sokuwa. A ƙofar main parlour suka ci karo da Abbu da Maami, ai kuwa Maami na ganinta, da sauri ta ƙaraso ta rungumeta tana faɗin "Noor, marhaban Noor, you are welcome back", ta faɗa wasu hawaye na cika a idanunta. Abbu ne yayi ma su Papi iso zuwa babban falon. Zannur dake Zaune yana danna wayarsa, gaba ɗaya ya gagara nutsuwa, danna wayar kawai yakeyi, shi kansa bai san me yakeyi a wayan ba. Jin hayaniyar shigowar mutane, ya sashi miƙewa da niyyar haurawa sama, dan sam baya don hayaniya, kuma Maami batace masa zatayi baƙi ba, da bazai ma zauna a falon ba. Cak ya tsaya da haurawa steps ɗin da yakeyi, jin ihun su Asabe dake faɗin "Oyoyo Noor, oyoyo Noor" In slow motion yashiga juyowa, har ya juyo gabaki ɗayansa sa, yana sauƙe idanunsa akan Noor, wacce ke tsaye jikin Maami, Cikin idanunta, idanunsa suka shige, kasancewar itama shi take kallo.............. Maimoon# *💖ABNUR*💖 *By maimoon* *Elegant online writers* 📚📖 *Free book* *Page 23* Kallon kallo suka shiga yi ma juna, babu ko ƙiftawa, kallonta kawai yake yi, kamar ya samu tv, yama rasa me za iyi. Juyar da kansa yayi, kafin yayi wani Murmushi yana shafa kansa, da sauri ya shiga sauƙowa daga steps ɗin, bai damu da Papi, Abbu, Maami, Ammi, da kowa dake falon ba. Wani irin kyakkyawar runguma ya bata, da har sai da Dukansu suka sauƙe ajiyar zuciya, gaba ki ɗaya ya manta da wani fushi da yake da ita, ita kanta ta manta wai tana jin haushinsa, dan dama ita kanta tasan ƙarya take ma kanta, amma tasan tana matsanancin son Zannur, kuma tayi kewansa fiye da misali. Ɗaga ta yayi yana juyi da ita a tsakar falon, gabaki ɗaya ya rasa ma me zai mata ya tabbatar mata da irin farincikin da yake ciki. Dariya ta shiga yi, tana wuntsula ƙafafunta, shima kansa dariyar kawai yakeyi, yana jin kamar kar wannan moment ɗin ya taɓa wucewa har abada. Direta yayi a hankali, yana faɗin "Noor, Ina kika je?, inata nemanki, meyasa Kika yanke min the worst hukunci da za'a taɓa yankewa wani ɗan Adam?, Noor me yasa baki jira na gane gaskiya ba?, wallahi yanzu na gane komai, I will never misunderstand you ever again, please ki yafe min" Ya faɗa yana kamo dukkanin hannuwanta. Kowa a ɗakin kallonsu kawai yakeyi kamar suna cinema, Abbu da ya buɗe baki da niyyan magana da sauri Maami ta girgiza masa kai tana murmushi, Shima murmushin yayi kawai, suka tsaya ganin ikon Allah Shi kansa Papi murmushi yakeyi haka Ammi da su Amina. Shiru Noor tayi ba tace komai ba, sai hawaye daya ciko idanunta, "Noor!" Ya Kira sunanta, Kawar da kai tayi taƙi kallonsa. Da sauri ya juyo da fuskarta, "Don't do that Noor it hurts, Please kimin magana, what do you want me to do, me kike so inyi miki, so kike inyi kneeling in baki haƙuri" Ƙin magana tayi amma a zuciyar ta dariya take yi tana faɗin "bazan kulaka yanzu ba ko me zakace." Ɗurkushewa yayi akan gwuiwowinsa, yana faɗin "Noor please ki yafemin I won't repeat my mistake." Da mamaki take kallonsa, bata taɓa tunanin zai iya hakan ba, da sauri itama ta ɗurkushe a ƙasan tana faɗin "Miye haka kake yi?" hannuwansa ta lalubo duka ta riƙe tana kallon cikin idanunsa "Na yafe maka, na jima da yafe maka, kuma har abada baka min komai ba, nima ka yafe min Please" Tana kaiwa nan ta fashe da kuka, rungumeta yayi tsam tsam a jikinsa, ya lumshe idanunsa, yana jin wani relieve na sauƙa masa tun daga kansa har ƙafafunsa. "Awnnnnn🤗" Amina da Asabe suka faɗa a tare suna ƙyalƙyalewa da dariya. Sai lokacin yayi saurin sakinta, Dukansu suka miƙe tsaye, Noor kaman zata mutu dan kunya, shikam shafa kansa kawai yayi, kafin yayi magana Maami ta riga sa tana faɗin "To idan kun gama, sai kabar ta tazo ta zauna, daga tafiya take, ai ka barta ta zauna ta huta ko?" Murmushi yayi kawai bai ce komai ba, saima ƙarasowa falon yayi ganin baƙin fuska, wanda ɗaya yayi matuƙar kama da Noor ɗinsa Maami ma kama hannun Noor tayi, suka ƙarasa cikin falon, itakam sai sunkuyar da kanta takeyi. Yasira dake tsaye a gefe, idanunta sun kaɗa sunyi jajir, ta share hawayen idanunta tana jin ƙuna a zuciyarta. Taufeeƙ ne ya shigo falon, ganin mutanen da ke ciki ya sashi faɗin "sorry I will come back later." Da sauri Abbu yace "ah ah Taufeeƙ a ƙaraso Noor ne ta dawo tare da mahaifinta." Sai lokacin ya lura da Noor, Itama ido ta zuba masa, ganin ya warke rass kamar ba shi ba, sai kuma ta sunkuyar da kanta ƙasa. Da sauri ya ƙaraso cikin falon da fara'a sosai akan fuskarsa "Alhamdulillah, mun godema Allah da ya dawo da Madam Noor cikin ƙoshin lafiya, congratulations Sir ya faɗa yana dariya." Zannur dai kasa amsawa yayi, sai murmushi da yake yi kawai, wanda ya daɗe rabonsa da fuskarsu gabaki ɗaya. Asabe da Amina ne suka ƙaraso da sauri suna faɗin, "Our Madam, Sannu da dawowa, wallahi bakiji yadda gidan ya zama ba da bakya nan" Murmushi tayi musu, dan dai kamar an sace Mata kalaman bakinta ta kasa furta komai. Kowa ka kalli fuskarsa cikin farinciki yake a falon, banda Yasira da ta rakuɓe can gefe tana tsiyayar da hawaye. Juyawa tayi zata bar falon, da sauri ta dakata jin Muryar Taufeeƙ da tayi yana faɗin "Yasira bazaki ma Madam Barka da dawowa gidanta ba, her rightful place, gurin da babu wani mahaluki da yake da iko sai ita kaɗai." Turus tayi, sai kuma ta share hawayen da ya zubo mata, ta juyo a hankali. Gani tayi gabaki ɗaya mutanen falon idanunsu na kanta, jiki a saluɓe ta ƙaraso cikin falon. A gaban su ta tsaya kafin cikin ƙarfin hali tace "Sannu da dawowa Madam" Ta faɗa tana ƙoƙarin danne shahararren kukan dake zuwa mata. Ko kallonta Noor batayi ba, bare ta sa ran zata amsa mata, hakan yasa Papi faɗin "Daughter sannu da zuwa take miki" "Na ji ta, Papi" "To meyasa baki amsa ba?" ya tambaya yana kallonta da kulawa Turo baki tayi tana shirin magana suka ji ance "Saboda bata cancanci Zama a gidannan ba, talkless of amsa gaisuwarta" Duk juyawa sukayi suna kallon Taufeeƙ Cikin tsananin takaici ya soma faɗin "Sir ka tambayeni several times, wanene yayi yunƙurin kasheni to ba kowa bace face ƙanwata Yasira." Duk miƙewa suka yi tsaye, har shi kanshi Zannur ɗin. "What Are You saying Taufeeƙ?, me yasa Yasira zata yi yunƙurin kasheka, bayan bata da kowa a duniya da ya wuce kai." Zannur ya faɗa with disbelief yana kallon Taufeeƙ Murmushi Taufeeƙ yayi kafin yace "tabbass Yasira ita ce tayi yunƙurin kashe ni kuma ba komai ya sata aikata hakan ba face soyayya, soyayyarma naka Sir Zannur." Gaba ɗaya ɗakin salati suka sanya, da Sallallami. Taufeeƙ ya cigaba, "saboda nayi yunƙurin hanata, hakan yasa ta gwammace in bar duniyan, har asibiti ta bini dan ta ƙarasa ni, Amma Allah bai bata iko ba" Ya ƙarashe zancen yana jin wasu hawaye Masu ɗumi. Cikin kuka sosai Yasira ta nufi Sir Zannur, akan gwuiwowinta ta zube tana kama ƙafafunsa "Dan girman Allah Sir ka tausayamin, wallahi na aikata duka hakane saboda tsananin son da zuciyata ke maka, bazan iya rayuwa idan babu kai ba, wallahi kaine rayuwata" ta ƙarashe da wani irin kuka har shiɗewa takeyi. Noor da idanunta suka gama rufewa, sai yanzu ta fahimci komai, tabbas tayi wauta da ta tafi ta bar Zannur, wato wannan duk sharrin Yasira ne, Ƙarasowa tayi, ta sa hannu ta ɗago Yasira sai ji kake tassss ka wanke ta da mari, kafin ta farfaɗo ta sake wanke ta da wani marin, Marinta ta rinƙa yi har sai da Zannur ya riƙe ta, nan take fuskar Yasira tayi fulu fulu yatsun Noor ne akwance a fuskarta ta ko ina. "Allah ya isa tsakani na da ke, kuma wallahi sai dai ki mutu, amma mijina yafi ƙarfin ki" Ta faɗa tana ƙoƙarin kwacewa daga riƙon da Zannur ya mata gabaki ɗaya idanunta sun gama rufewa. Asabe da Amina al'ajabi ya kashe su a tsaye. Papi ne yayi gyaran murya kafin yace "kowa ya samu waje ya zauna." Duk zama sukayi, sai Yasira dake tsugunne tana cigaba da kuka Papi yace "to bansan me zance akan wannan al'amari ba, abu dai ya riga ya faru, saboda haka dan Allah kukai zuciya nesa, Ke kuma Yasira kike ko waye?, kije, duniya ta isheki riga da wando, bazan bari su miki Allah ya isa ba saboda ko a yanzu zuciyarki baƙace ina ga kuma kina ɗauke da Allah ya isan jama'a." Abbu dake jin zafin abinda Yasira tayi shima ya ɗaura da faɗin "Yasira i didn't expect that from you, ɗan uwanki, Taufeeƙ ya ma fi uba a wajenki, babu abinda ya nuna miki sai tsantsar soyayya, amma abinda kika saka masa da shi kenan, saboda haka na baki 20 minutes ki tattaro duk abinda yake naki a gidan nan ki fice ki bamu guri, kinci Sa'a bamu haɗa ki da yan sanda ba saboda kinci darajar Taufeeƙ amma ina mai tabbatar miki idan har kika wuce wannan lokacin, nan ne zakisan cewa bawai tsoronki mukeji ba zamu iya yanke hukunci akanki." Kuka ta sake rushewa da shi, kafin ta rarrafa ta je wajen Maami "Maami ki taimakeni, bani da wajen zuwa please ki roke su?" Juyawa Maami tayi ta dubi Abbu kafin tace "Abbu idan har na buɗe idona, naga yarinyar nan a gabana, wallahi duk abinda na aikata mata kar kowa ya sake ya min magana." Yasira na jin haka ta miƙe da sauri ta nufi su Asabe tana faɗin "please ku taimaka min" Matsawa Amina tayi da sauri, tana jawo Asabe "Ke Asabe matsa a kusa da wajen kar ta shafa miki zuciyar kafirai" Asabe kam kallonta takeyi cikin ido kafin tace "Wallahi Yasira, ba tun yau nasan cewa zuciyar ki baƙa bace, amma ban taɓa tunanin ya kai haka ba, Yasira Taufeeƙ Fah, Yasira ko kin manta waye Taufeeƙ a wajenki ne?, sannan kuma ki rasa wa zaki so sai Sir, ki ruguza masa rayuwarsa da matar da yake so, wallahi Yasira ko a hanya bana fatan na sake haɗuwa da ke." Da gudu Yasira ta nufi ɗakinsu jin Abbu na ƙirga lokaci, ko abu ɗaya bata dauka ba, taji Abbu na faɗin 'ku shiga ku fito min da ita, idan taƙi fitowa ku ɗauko ta aka ku yasar min da ita a wajen gidannan." Bodyguards ne har guda huɗu suka shigo, ganin da gaske suke yasa ba tareda ta musu gardama ba, ta biyosu suka fito, da kallo tabi Zannur, wanda ke rarrashin Noor da banda kuka babu abinda takeyi, har suka fice a falon, sai raba ido takeyi ganin bataga yayanta ba. Sai da suka rakata har bakin gate,kafin suka rufe ƙofan, suka yi shigewarsu, a gurin ta ɗurkushe tana wani irin kuka. Handkerchief ɗin da taga an miƙo mata ya sata ɗaga kai ta kallesa Da sauri ta miƙe tana faɗin "yaya!" Ba tareda ya kalleta ba yace "tashi ki shiga Mota muje." Miƙewa tayi ta shiga motan, shima Taufeeƙ ya zagaya ya shiga ya tada motar ya bar unguwan. Kuka kawai takeyi da ƙyar ta buɗe baki tana faɗin "Yaya dan Allah ka yafemin, Ni kaina bansan meyasa na aikata hakan ba, wallahi soyayya ce ta rufe min ido dan Allah yayana ka yafe min." Ta ƙarasa da kuka Bai ce komai ba, sai da ya yanki kwana kafin yace "Yasira Ni ɗan uwanki ne, ko me kika aikata a duniya bazan so inga kin tagayyara ba, amma Ni kaina bazan iya zama da ke ba, saboda ke guba ce a cikin mutane, saboda haka yanzu zan saka ki a mota, ki koma ƙauye wajen Baba, Allah ya sadamu da alkhairinsa." A daidai lokacin yayi parking a bakin tasha, fita yayi, itama ta sauƙo tana jin wani irin kuka na taso mata kamar zata haɗiye ranta. Babu yadda ta iya, haka Taufeeƙ ya sata a mota, sannan ya bata dubu ashirin ta riƙe a hanunta, daga haka bai sake kallon ta ba ya juya ya bar wajen. Tana kallonsa har ya tada motarsa ya fice a tashan gabaki ɗaya kafin ta sake rushewa da wani matsanancin kukan. Maimoon# *💖ABNUR*💖 *By Maimoon* *Elegant online writers* 📚📖 *Page 24* Kwanan su Papi uku, suka tattara suka koma Kaduna, cike da kewar Noor, bayan Papi ya zaunar da su gabaɗaya ya musu nasiha sosai. Duk da yadda Abbu da Maami, suke kula da Noor, amma sai da tayi kewar Ammi da Papi, da su Farhaana, daƙyar suka rabu a Airport, tana kuka kaman zata shiɗe. Rungumeta Zannur yayi, yana aikin rarrashi, amma sam Noor taƙi yin shiru, har suka shiga Mota Noor kuka take, ya rasa yanda zai yi da ita tayi shiru, ya yi rarrashin, yayi daɗin bakin amma duk a banza. Har suka iso Noor taƙi yin shiru, yana yin parking tayi saurin ficewa daga motan, da gudu ta ƙarasa cikin gidan ta haura sama tare da shigewa ɗakinta har da murza key. Murmushi yayi kawai, tare da shafa sumarsa, a ransa yana faɗin "Zakiyi bayani yarinya." Bai bi takanta ba yayi wucewarsa ɗakinsa, shiryawa yayi ya fice a gidan tare da Taufeeƙ. Sai da ta gaji dan kanta tayi shiru, har bacci ya ɗauke ta. Ƙarfe 12 dai-dai ta farka, a hankali ta miƙe daga kan gadon, tare da yin miƙa. "Hmm" Zannur ya faɗa yana gyara zaman laptop ɗin dake kan cinyarsa. Miƙewa tayi daga kan gadon, ta wuce toilet, Yana kallonta har ta fito, ta gama shiryawa cikin riga da wando band ta saka a kanta, kafin ta ɗauki hijab ɗinta ta zura, sai da tayi sallah, tayi addu'o'inta kafin ta miƙe ta naɗe sallayan, ta zame hijab ɗin ta naɗe ta ajiye. Gadon ta sake haurawa, ta ja bargo tayi kwanciyarta. Murmushi yayi, a zuciyarsa yana faɗin "kin gaji da kukan kenan?" A hankali ya rufe laptop ɗin, kafin ya ɗau wayarsa ya kira kitchen. Asabe yasa ta kai mata abinci kafin ya kashe wayarsa. Har yamma kafin ya dawo, a falo ya sami Maami, da Abbu, wanda suma zuwa jibi suke shirin komawa Dubai. Kasancewar Maami ta gama zaga danginta, dama abinda ya jinkirta tafiyan nasu kenan. Zama yayi a falon yana ɗan hira sama sama da su Maami, amma gabaki ɗaya hankalinsa na ga Noor. Daga ƙarshe miƙewa yayi kawai ya nufi sama. Ƙofan ta da yaji a kulle ya sa shi yin murmushin da bai shirya ba, kenan fushi takeyi da shi. Juyawa yayi ya nufi ɗakinsa, laptop ɗinsa ya bude yana kallonta, ganin tana cin abinci da aka kai mata ya sashi shafa kansa, a fili ya furta "Silly girl." Bai sake ganinta ba, sai ranan da su Maami zasu tafi, kasancewar tare zasu kaisu Airport ya sa ta shiryawa cikin abaya kalar ja da fari, da yayi mata matuƙar kyau. Har suka isa Airport, taƙi kallonsa, ita a dole fushi take dashi, ai yana ganin tana kuka amma ya shareta. Shidai satan kallonta kawai yakeyi ta mirror, idan suka haɗa ido sai dai yayi murmushi, ita kuma ta galla masa harara. Nan ma dai bata fasa kukan ba, ganin su Maami zasu tafi, dan ta saba da Maami sosai. Kallonta kawai yakeyi, a ransa yana tunanin ina zata kai saurin kukanta. Sai da jirginsu Maami ya ɗaga kafin suka bar Airport ɗin, amma sam Noor taƙi kulasa. Shima bai kulata ba har suka iso gida, buɗe motar tayi a fusace ganin ya ƙi tankanta ta bugo murfin da ƙarfi, ta nufi cikin gida. Girgiza kansa kawai yayi, shima ya fito daga motan, sannan yayi mata key ya nufi cikin gidan. Har dare babu wanda ya kula wani, Noor kam ta cika tayi fam. ********* Ƙarfe 12:00pm Zannur ya rufe laptop ɗin, kasancewar ya gama aikin da yakeyi. Miƙewa yayi ya nufi ɗakin Noor, jinsa a rufe ya sashi komawa ya ɗauko spare key, a ransa yana addu'ar Allah yasa ta cire makullin jiki. Cikin Sa'a kuwa Kofar ta buɗe, wani ajiyar zuciya ya sauƙe, kafin ya ƙarasa cikin ɗakin a hankali, ya maida ƙofar ya rufe. Kallonta ya tsaya yi, yadda ta duƙunƙune a bargo, ta ɓata fuska, sai kawai yayi murmushi tare da ƙarasawa, botiran rigan baccin sa ya buɗe gabaki ɗaya, kafin a hankali ya haura kan gadon, tare da jawota gaba ɗaya jikinsa. Wani ajiyar zuciya suka sauƙe a tare, cikin bacci Noor ta jita a jikin mutum, hakan yasa ta sake gyara kwanciyar ta a kan bare chest ɗinsa, tana turo baki. Hannunsa yasa ya zare band ɗin kanta, gashin ta ya barbaje, kafin ya sa hanunsa a cikin sumar, yana shafawa, a hankali. Buɗe idanunta dake cike da bacci ta shigayi, kafin ta miƙe da sauri, fahimtar da tayi ba mafarki takeyi ba, a jikin mutum take da gaske. Da sauri ya maida ita ya matse a jikinsa yana hura mata, iska a fuska. Ɓata fuska tayi, tana faɗin "Miye hakan ka shigo min ɗaki?, ta ina ma tukunna ka shigo bayan na rufe ƙofar?" Murmushi yayi a hankali ya raɗa mata "Dama baki san cewa mijinnaki aljani bane, ɓullo wa kawai nayi" "Hmm" kawai tace tana sake yunƙurin tashi daga jikinsa. Ƙin saketa yayi, a hankali yace "Baby, meye na?" ya faɗa yana marairaicewa Dukansa ta shiga yi a ƙirjinsa, kafin ta fashe da kuka, "Ni bansani ba, baka damu da Ni ba, ka mayar da ni wajen Papi, baka so na!" Da sauri ya birkito da ita, ya koma Samanta, yana kallon cikin ƙwayar idanunta. "Don't ever say that again, wallahi ina sonki kaɗai yayi kaɗan, akan abinda nake ji tattare dani akanki, ina sonki, irin son da babu wani namiji da kema matar sa irinsa, Ina sonki fiye da duk yanda wani mai kwatance zai kwatanta, i never knew you were the reason I live, sai da kika barni Noor." Ajiyar zuciya kawai Noor take sauƙe wa, tana kallonsa, yadda yake confessing soyayyarsa a gareta, da sauri ta sa yatsanta a bakinsa tana faɗin " Shhhh, Its enough, ya isa haka, na yarda mijina, nasan kana sona, ko da ace baka furta komai ba." Ta faɗa hawaye na sauƙa a gefen idanunta. Sai da ta yi shiru kafin ta cigaba "Wallahi nima ina sonka, fiye da yadda zaka iya misaltawa, bansan sanda na fara sonka ba, amma abinda na sani a yanzu shine, bazan iya rayuwa ba tare da kai ba..." Kasa ƙarasawa tayi jin bakinsa a cikin nata, wani hot kisses ya ke bata, da ƙwaƙwalwarta ta gagara ɗauka, jikin sa har rawa yakeyi, gabaɗaya ya gigata mata lissafi." Sun shafe tsawon lokaci a haka, kafin a hankali,ya mirgina ya koma gefe yana sauƙe numfashi, idanunsa sun kaɗa sunyi jajir, batare da ya ce mata komai ba ya sauƙa a kan gadon, zagayowa yayi, a hankali ya riƙe hannuta yana kallon ta, "Zo muje" Zuciyar ta ce ta tsinke da sauri cikin in Ina tace "Ina..za..mu je..? Bai bata amsa ba, ya sunkuyo tare da ɗaga ta cak, Nutsuwa ta samu kanta da yi a kan faffaɗar ƙirjinsa, a hankali ya juya da ita, ya bar ɗakin. Har suka shiga nasa ɗakin bata daina jin bugun zuciya ba, a hankali ya sauƙe ta a tsakiyar daƙin yana kallonta kafin ya juya ya nufi toilet. Gefen gado ta samu ta zauna, tana ƙare ma ɗakin nasa kallo, ba ƙaramin kyau ɗakin yayi mata ba,kasancewar bata taɓa shiga ba, mayen turarensa na *_SHUMUKH_* ya gama kama ɗakin. Fitowa yayi daga toilet ɗin, yana daure da towel da alama, wanka yayi, a hankali ya dubeta kafin yace, ki shiga nan kiyi wanka, ki haɗo da alwala. Da sauri ta girgiza masa kai tana faɗin, Ah ah, zanje inyi a ɗakina. Bai kulata ba ya ƙarasa jikin Kofar ya rufe da key, sannan ya zare key ɗin ya ƙarasa jikin mirror, yana gyara sumar kansa. Babu yadda ta iya haka ta ƙarasa toilet ɗin. Mamaki ta tsaya yi, yadda toilet ɗin sa yake abin sha'awa, kamar ba bayi ba. A haka ta ƙarasa, sai da ta zare kayan jikinta, tayi wanka, sannan ta ɗauro alwala, bathrub ta sanya a jikinta, kalar skyblue kafin ta fito a hankali, tana leƙawa cikin ɗakin. A zaune ta gansa a bakin gado yana operating system ɗinsa. A hankali ta fito, cikin sanɗa, har ta iso tsakiyar daƙin, kafin ya ɗaga kansa yana kallonta. Tura baki tayi, cikin shagwaɓa ta ce "to Ni ai babu kayan da zan saka a ɗakinnan" Shafa kansa yayi kafin ya juya ya fice a ɗakin, can sai gashi ya dawo, da kayan bacci, har da hijab. Miƙa mata yayi, ta karɓa, sai da ta gama shiryawa tsab, kafin ya gabatar musu da sallah raka'a biyu. Addu'o'i yayi musu sosai, kafin a hankali ya zare hijab ɗin jikinta, linkewa yayi da kansa ya ajiye yana mata murmushi. A hankali ta miƙe, dan bacci take ji, ta nufi gadon, kwanciya tayi tare da shigewa bargonsa mai tsananin laushi. Sai da ya gama abinda yake yi duka, kafin ya hauro gadon shima, a hankali ya janyota jikinsa, tareda yi Mata raɗa a kunne. Zaro ido tayi waje tana kallonsa, ta buɗe baki da niyyar magana, bai bata daman maganan ba ya haɗe bakinsu waje ɗaya yana jin wani shaukin sonta na ɗibarsa. Tun Noor na ganin kamar wasa, har abin ya fara wuce tunani da lissafinta, sai lokacin kuka ya zo mata, ta shiga magiya amma ina, Zannur ya riga yayi nisa, ya sha alwashin mayar da ita cikakkiyar mace, sannan Mrs Zannur Shuraim. Ba ƙaramin wahala Noor ta sha ba a wannan daren, har sai da kukan ma ya daina fita. sai bayan komai ya lafa kafin ya janyota jikinsa wasu hawaye Masu ɗumi na bin fuskarsa, albarka kam ta shasu kwando kwando. Ita kam Noor banda kuka babu abinda takeyi, sai sake birkita masa lissafi takeyi. A ranar ya tabbatar yana ma Noor son so, irin sonda baya tunanin wani ya taɓa hasashensa. ***_10 years Later_* Mrs Zannur Shuraim ce a zaune, a babban falon da ya ji komai na rayuwa, a hankali ta miƙe tare da yaron da ke kan Cinyarta wanda bazai wuce shekara ɗaya da watanni ba. Daƙin yara ta kaisa, tare da kwantar da shi a kan gadonsa, tana lallaɓa shi, dan ta tabbata idan har ya farka, rikici zai saka mata, a hankali ta zare hannunta, tare da fita daga ɗakin. Ƙasa ta sauƙo, ganin babu kowa a falon ya sata ƙarasa wa ɗakin hoto dan ta tabbatar duk suna can. Daga bakin ƙofa ta tsaya tana kallonsu, yadda Zannur ya sa ƴaƴansu guda biyu a gaba, Fatima, da Shuraim, yana koya musu ɗaukan hoto Fatima wacce suke kira da, Nihal tace "daddy na ɗauka, wallahi i clicked it right! Adnan ka gani!" ta faɗa tana tsalle tare da nuna ma Shuraim da ya kasa ɗaukan ko ɗaya. Murmushi Zannur yayi yana faɗin "shima yanzu zai ɗauka ki bar yi mishi dariya" Ƙarasowa tayi cikin ɗakin a hankali tana murmushi, "Daddy saura Ni" Ta faɗa cikin shagwaɓa da sigar zolaya. Juyowa sukayi Dukansu suna kallonta, kafin Shuraim yace "daddy ni Ummi zan ɗauka, bazan ɗauki mimi ba, tunda ta min dariya" "To shikenan, but is daddy allowed to join Ummi? Ya tambaya yana murmushi "Eh kai kaɗai amma" Matsawa kusa da ita yayi yace "to my boy" Ai Yana shirin ɗauka Mimi tayi saurin shiga ya ɗauka da ita, nan fa suka shiga rikici. Noor ce ta ƙarasa tare da karɓan mini câmeras ɗin hannunsu, to ya isa haka, kuje lesson teacher ɗinku na hanya, don't keep her waiting. "Toh Ummi" suka faɗa a tare, Da sauri suka juya suka fice a ɗakin dan ɗauko littafan makarantarsu. Janyota Zannur yayi yana faɗin, "me kikace ɗazu?, kikace saura ke? To muje in koya miki naki" Turo baki tayi tana faɗin Nikam "ah ah yanzu fa na samu sadeeq yayi bacci" bai jira mai zatace ba, ya ja hannunta suka fice a ɗakin. Yasira kam zuwa yanzu, ƴaƴanta huɗu, dan kuwa tun komawarta, Baba yayi mata aure da wani dattijo, mutumin yana da hankali sosai, kuma yana son Yasira sosai, a yanzu ta kwantar da hankalinta, ta riƙe mijinnata da ƴaƴan sa tana zaune lafiya da su. Taufeeƙ da Amina duniya sabuwa, dan kuwa yanzu ƴaƴansu biyu, suna zaune cikin kwanciyar hankali da soyayyah. Asabe tayi aure Ita ma, har tana da ya'ya biyu. Papi da Ammi, suna zuwa Nigeria, duk sanda suka ji kewan su Noor, haka Abbu da Maami, kamar yadda suma suke zuwa musu duk sanda suka samu hutu daga wajajen aikinsu. A yanzu ana shirin auren Farhaana, da saurayinta ashraf acan Dubai kenan, Noor ana ta shirye shiryen zuwa, dan kuwa itace ƙirjin biki. Tammat bi hamdillah, anan na kawo ƙarshen littafin ABNUR, kuskuren da nayi ina roƙon Allah ya yafemin, da Ni da ku baki ɗaya,na taƙaita labarin saboda wasu dalilai nawa. Alhamdulillah, Alhamdulillah Alhamdulillah. Maimoon#