[3/4, 11:35 PM] Maman Maryam: *_Abinda Ke Cikin Zuciya_* ©®_Hafsat Rano_ (1) ****Yara ne yan kasa da shekara biyar masu yawan gaske cike da harabar babban gidan marayun, kowanne na harkar gaban sa wanda mafiya yawancin su wasa suke daidai da karancin shekarun su. Kasancewar yau asabar ce babu karatu sai na yamma, yasa harabar ta zama iya yaran ne kawai inda manyan cikin su ke chan baya suna wanki da gyare gyaren da ya zama kamar al'adar gidan a kowanne mako.    Zaune yake jikin ginin dakunan kwanan su ya tattare kafafuwan sa sama yana kallon su, yaro ne shi mara son hayaniya da rashin ji irin na sauran sa'oin sa, mafiya yawancin lokuta zaka ganshi zaune ya zura musu ido kawai yana kallon su ba tare da ya shiga wasan ba. Duk kuwa yadda Maman Yara take kokarin ganin ya sake a cikin sauran yara sam yaki, sai dai duk da haka wayon sa daban ne, yana da kaifin basira da saurin daukar abu, kokarin sa har mamaki yake basu, duk wani abu da anyi shi yake zama daram akan sa. Babban abinda ya zamar masa jiki shine tausayi, duk da rashin son hayaniyar sa, amma yana da mugun tausayi da kaunar duk wani yaro da yake cikin gidan nan.    A hankali gate din gidan ya shiga budewa,chak yaran suka tsaya da wasa suka zubawa kofar ido cikin son ganin me zai faru. Mota ce karama ta shigo cikin harabar gidan, ta samu gefe ta tsaya, da sauri duk yaran sukayi wajen motar da murnar su, mikewa yayi shima yana murmushi ya nufi motar har da dan gudun sa, kafin ya karasa sun fito, wani mutum ne da a kalla zai yi shekara arba'in ya fito hannun sa rike da dan karamin Yaron da bazai wuce shekara hudu zuwa biyar ba, yadda yaran suka zagaye shi zaka gane cewa ba karamin muhimmanci yake dashi a wajen yaran ba. Wata leda ya ciro a motar sa ya fara raba musu sweet yana shafa kansu d'aya bayan d'aya, duk wanda aka bawa sai ya tafi yana murna. Haka yayi ta raba musu har ya sallame su dukka kafin ya juyo wajen yaron dake tsaye gefe ya saka hannun rigar sa a baki. "Sultan..." Ya kira sunan sa yana mika masa hannu, da d'an sauri ya karasa garesa yasa hannu ya daga shi sama. "Baka saki jikin ka ba har yanzu my boy, me yasa ne wai?" Ya fad'a yana kallon Maman Yara data iso wajen "Alhaji Sultan halin sa sai shi, baya son mutane gashi nan dai tun muna damuwa har mun hakura dan babu me chanja shi." "Daddy waye shi?" Dan karamin yaron da suka zo tare ya tambaya yana kici-kicin bude ledar sweet din sa, rankwafawa Daddy yayi ya sauke Sultan a gefen sa, sannan ya kamo hannu yaron "Sunan sa Sultan, abokin ka ne daga yau kaji?" Sai ya daga kai kamar me tunani kafin yace "Zamu tafi dashi toh muna wasa tare?" Girgiza kai yayi sannan ya shafa kansa "Zan dai dinga kawo ka wajen sa duk Sunday's sai kuyi wasan ko?" Mak'e kafadar sa yayi irin yadda yara keyi, ya turo baki gaba kamar zaiyi kuka yace "Ni dai yanzu nake so, dan Allah kaji Daddy." "Alhaji mu je ciki ko?" Maman Yara ta katse maganar da zai yi, sai ya kama hannun su dukka suka nufi cikin gidan... Takardu ta baje masa a gaban sa da bayanin duk abinda ya faru daga satin da ya wuce zuwa yanzu, karin yaran da suka samu da kuma karin NGO's din da suka sake hada kai dasu. Sosai yayi farin ciki ya kuma dauki Numbers din su da address domin su samu lokaci su sake zama sosai. Ya jima sosai a gidan yana aikace aikacen sa, da sauraron matsalolin da suke ciki da yin yadda za'a kawo saukin su. Da kyar aka nemo masa Safwan da zasu tafi ya shige cikin yara ana ta wasa kasancewar sa yaro me son mutane da faran faran. Sai dai duk in da yayi yana rike da hannun Sultan wanda a kalla zasuyi kusan sa'anni. A haka sai gashi ya dan saki jikin sa har yana dan shiga wasan. Ganin haka ba karamin mamaki ya bawa ma'aikatan gidan ba, musamman yadda kowa yasan waye Sultan da yadda yake. Har wajen mota ya raka su still suna rike da hannun juna Safwan har da kuka sai da Daddy yayi masa yawo sannan ya yarda ya tafi yana daga ma Sultan hannu. **** *_(SMM OPANAGE)_* Shine sunan gidan marayun, babban gidan marayu ne na wani bawan ALLAH wanda babu wanda yasan shi balle ya taba haduwa dashi sai mutum daya Alhaji Sulaiman (Daddy) , tun farkon kafuwar gidan Daddy ne yake kula da gidan har kawo yanzu da ya bunkasa sosai har kungiyoyin sa kai da yawa suka saka shigo ciki ake gudanar da komai tare. Zaka sha mamaki ganin irin yaran da gidan ya tara wanda mafiya yawansu tsintar su akayi wasu ko cibiya ba'a yanke musu ba gasu nan dai abun gwanin tausayi. Karatu da duk rayuwar su a cikin gidan suke yin ta, babu me fita waje daidai gwargwado basu nemi komai sun rasa ba, har su kan fi wasu yaran dake zaune gaban iyayen su.    Sultan yana d'aya daga cikin yaran da suke wannan gida, sai dai kamar sauran yara, akwai banbance banbance masu yawa a tsakanin su, tun daga zuwan sa gidan har kawo yanzu da yake ciki komai nasa daban Maman yara take masa. Bata yarda da kowa wajen kula da al'amuran sa ba,ita take masa komai da duk wani abu da zai nema tun kafin ma ya nema ta samar masa, hakan na bawa sauran ma'aikatan gidan mamaki sai dai babu me Ikon tankawa saboda itace shugaba kuma babu wani abu na rashin gaskiya ko rashin adalci da take wa sauran yaran. ***Kwana uku da tafiyar Daddy ya dawo, sai dai wannan karon ba kamar sauran zuwan da ya saba bane, muhimmin abu ne ya kawo shi, abun da zai zama mabudin dukkan wata kofa, kofar da zata zama alkhairi ga wasu ta kuma zama sharri ga masu sharri. Sun jima suna tattaunawa da Maman yara da manyan masu kula da gidan kafin a samu daidaita wa, hannu ya saka a gurguje bayan ya amsa kiran matar sa ya tabbatar mata yana kan hanya.     Ciki Maman yara ta shiga, ta dauko wata madaidaiciyar jaka ta bud'e tana bin komai na ciki da ido kamar me neman wani abu, ta dan dau wasu sakanni a haka kafin ta sauke ajiyar zuciya me karfi ta rufe ta maida ita ma'ajiyar ta ba tare da ta dauki komai ciki ba.   In da tasan zata samu Sultan ta wuce kai tsaye, ta riko shi har in da Daddy ke tsaye ya goya hannayen sa a baya yana kai wa da komawa, ganin su yayi saurin bude motar yana murmushi me bayyanar da tsantsar farin ciki. "In sha Allah zan rike shi kamar yadda zan rike Safwan." Yace tun kafin tayi magana dan ya ga sanda take motsa baki tana tattaro maganar da zata fad'a. Daga kai kawai tayi ta zaunar da Sultan a kujerar gaba sannan ta dafa kansa tace "Allah yayi maka albarka ya tsare ka a duk in da kake." Sai ta kalli Daddy tace "Yaran nan Amana ne a wajen mu, ina fatan zaka cika alkawarin daka dauka duk da bani da kokonto akan hakan." "In Sha Allah." Yace da sauri sannan ya zagaya ya tada motar ya fita da dan sauri yana kallon wayar sa dake neman agaji, dagawa yayi ya kara a kunnen sa "Muna hanya..." Kawai yace ya kashe ya bawa motar wuta. *_Premier Clinics_* A reception ya tarar da ita tana magana da staff din wajen, wuce ta yayi rike da hannun Sultan suka haura sama, kai tsaye dakin da aka kwantar da shi ya wuce ya tura, Dr na tsaye kansa yana gyara masa abin oxygen din inda wata nurse ta rike hannun sa daya tana shafa kansa, da sauri Daddy ya karasa shiga dakin ya tsaya gaban gadon yana kallon yadda tilon d'an sa yake battling da numfashi. Girgiza kansa yayi zuciyar sa na zafi still yana damke da hannun Sultan daya zubawa Safwan ido ganin abinda ake masa, sai da suka gama sannan bacci ya dauke shi, sai a lokacin Dr din ya bawa Daddy hannu suka gaisa sannan ya fita zuwa sauran ayyukan dake gaban sa.     Kujerar daya tashi Daddy ya zauna yana kamo hannun Safwan dake bacci a nutse alamun numfashin ya daidata, sai ya juya ya kalli Sultan dake tsaye ya kamo shi ya zaunar a gefen sa. "Ka ga abokin ka ko? Bashi da lafiya yana ta cewa sai an kawo shi wajen ka, ina fatan idan ya farka ya ganka zai dawo daidai, komai tare zakuyi ka zama danuwan sa shima haka." Kallon sa Sultan yake ba tare da ya fuskanci inda maganganun nasa suka dosa ba, ganin ya zura masa ido yasa ya d'an dafa kansa a hankali yace "Na manta he's just a child, Allah yasa abinda nayi ya zama ya cike gurbin da muka rasa na farin ciki, Allah ya hada min kansu ya raya su ya bamu ikon tarbiyyartar dasu, Allah kar ya kawo abinda zai raba kansu." "Amin..." Tace tana karasowa dakin, sai ya dago da sauri ya kalli inda take, karasowa tayi ciki tana kallon Sultan kafin ta kamo hannun sa ta dora shi a saman kafarta tana jin wani iri yanayi mara misaltuwa. Tana fatan hakan ya zama alkhairi a garesu baki daya. Nace Allah yasa. *** Tun da Safwan ya farka ya ga Sultan sannan Daddy da Mahmah suka tabbatar masa da ya dawo gidan su baki daya sai ya sake, ya hau wasa da tsalle tsallen sa kamar ba mara lafiya ba, Sai kawai suka nemi sallama suka wuce gida.   Tun daga lokacin komai ya sauya a familyn, duk in da kaga Safwan toh zaka ga Sultan, komai tare suke, haka ma iyayen komai tare suke musu dan ko sun so yiwa Safwan shi kadai ba zai yarda ba, sai yace ina na Sultan. Ajinsu daya a makaranta, daya daga cikin manyan makarantun da ake ji dasu a birnin Kano. Haka ma islamiyya komai daya, idan suka dawo daga school zaka samesu a dakin su suna wasa, rayuwar Sultan ta chanja gaba daya, duk Sunday's suna kai ziyara _SMM OPANAGE_ tare da Daddy sai kuma su wuce chan family house din su Daddy din, sai dare suke dawowa. ***Watarana Daddy na zaune bayan ya dawo daga office da yamma aka turo ana sallama dashi, fita yayi ya dan jima sai gashi ya dawo, ya zauna yana kallon Mah-Mah. "Makocin nan namu ne da suka tare kwanaki ashe Dr ne a Bayero University, shine yazo neman alfarma, wai zai chanja wa yaron sa makaranta yana so yasa shi a ta Sultan sai su dinga tafiya tare, idan matar sa ta kaisu sai ke kuma ki dauko su, ko kuma ke kaiwa ita dauko wa, yace idan har mun amince sai ya turo matar tasa ta shigo ku daidata." "Ok me kace masa?" Ta tambaya "Eh nace babu komai amfanin zaman taren kenan, kinga dama muna tunanin neman driver saboda aikin ki da nawa, kinga shikenan idan zamu fita sai mu mika su idan yaso ita tunda yace house wife ce business take a cikin gida sai ta dauko su da yamma." "Good idea, toh Allah ya bamu ikon sauke nauyin juna." "Amin." Yace sai kuma suka shiga hirar iirn halin iyayen dah da yadda ake daukar makoci kamar danuwa amma banda yanzu da komai ya baci, sai ka dade a unguwa ma baka san makocin ka bam Da yamma kuwa sai ga Matar ta shigo rike da hannun yaron taa wanda yake sa'ansu Safwan din, da fara'ah Mah-Mah ta karbe ta, suka d'an taba hira da tsara yadda zasuyi kafin ta kira yaron nata me suna Adnan da ya shige wajen su Safwan sukayi musu sallama suka tafi.    Tun daga lokacin zumunci me karfi ya kullu tsakanin gidajen biyu, tuni matan suka dinke dan dama Mah-Mah bata da kawa a unguwar, yaran ma ko yaushe suna tare da juna. ***Rayuwa ta cigaba da garawa cikin hukuncin Allah, har zuwa lokacin da yan samarin suke shirye shiryen gama primary school dinsu, a lokacin ne kuma Umman Adnan ta samu ciki, farin cikin da both families din suka shiga ba kadan bane, Safwan, Adnan da Sultan basu da magana da magana sai ta kanwar da za'a haifa musu, Mah-Mah ta kusan fin kowa murna dan yadda take son haihuwa ba'a magana, gashi tun bayan Safwan ko batan wata bata sake ba, shi ma tazo ta haife shi da ciwon zuciya tun ranar da ya iso duniya, ga matsalar numfashi da ta zamar masa asthma, sai ya zama dukkan rayuwar su suna yin ta ne da farin cikin Safwan, duk abinda ya nema in dai be fi karfin su ba suna yi masa, duk da haka basu sangartashi ba. Zuwan Sultan rayuwar su ya kara musu kwanciyar hankali, kadaitar da Safwan yake fama da ita duk ta tafi, hakan yasa Suke son sultan kamar yadda suke son Safwan. Ranar wata juma'ah Mah-Mah na zaune bayan ta dawo daga aiki da wuri, yaran na daki suna shirya zuwa masallaci da zuwa gidan Hajiya kakar Adnan, kiran Umma ya shigo wayar ta, da sauri ta dauka don tasan haihuwar zata iya tasowa ko yaushe, aiko tana daga wa taji yadda take magana da kyar tayi saurin daukar hijab dinta ta shiga gidan, tana zuwa ta tarar har Umman ta soma shiga cikin mawuyacin hali, a rikice ta kira Daddy ta sanar masa yace gashi nan zai shigo layin nasu, a daidai lokacin kuma Dr ya shigo kamar an jego shi, ya taimaka suka saka ta a Mota, sannan suka barwa Daddy yaran suka tafi.   Isar su asibitin kenan ta sauka, ta haifo kyakkawar yarta cike da koshin lafiya, da sauri Mah-Mah ta dauki waya ta kira Daddy ta fad'a masa, tana jiyo ihun yaran ta wayar lokacin da Daddy yake fad'a musu sunyi kanwa, sai kawai ta kashe ta koma wajen Maijegon! *_ZAFAFA BIYAR 2021_*🔥 _*SUKAR BAYA*_💚 _BILLYN ABDUL_ ( _kwai cikin qaya_ ) ( _raina kama_) ( _wutsiyar raqumi_ ) *_SIRADIN RAYUWA_*💛 _SAFIYYA HUGUMA_ ( _alqawarin Allah_ ) ( _daurin boye_ ) ( _Dangantakar zuci_ ) 💙 _*KIBIYAR AJALI..*_💜 _MISS XOXO_ (Sulke baya tsare ta sai ta wuce) ( _Igiyar zato_) ( _Kaimin halacci_ ) ( _Naufal_ ) *_ABIN DAKE CIKIN ZICIYA_*🧡 _HAFSAT RANO_ ( _ruhi daya_ ) ( _Sauyin qaddara_ ) ( _Daurin goro_ ) *_MIN QALB_*❤️ _MAMUHGEE_ ( _buri daya_ ) ( _tarayya_ ) ( _eznah_ ) Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇  0903 234 5899 IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 09033181070 Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥 [3/4, 11:35 PM] Maman Maryam: *_Abinda Ke Cikin Zuciya_* ©®*_Hafsat Rano_* Amrah (2) _Wannan littafin na kudi ne, bamu yarda da sharing ba, idan kina bukata ki tuntubi numbobin dake kasan littafin._ ***Ganin both uwar da jaririyar lafiya lou suke sai aka sallame su sukayo gida, tun kafin su karaso gida Hajiya ta iso da kayan ta, suna zuwa suka tarar da ita har ta dora ruwan wanka, nan danan gidan ya soma ciki da yan uwa da abokan arziki kowa da son nuna farin cikin sa, kasancewar tun bayan Adnan sai yanzu Allah ya kawo haihuwar yasa kowa yake jin kamar itace ma ta farkon.     Tun da aka kwantar da jaririyar a daki Sultan da Safwan babu wanda ya motsa daga wajen, duk motsin da zatayi suna kallon ta, chan tasa kuka sosai kuka irin na jarirai sabbin haihuwa, da sauri Sultan ya mike ya koma wajen kofa ya tsaya yana rarraba ido cikin yanayin damuwa, kallon sa Umma tayi ta yi murmushi ta cigaba da hada formula saboda rashin ruwan nono, shigowa Mah-Mah tayi dakin ta tsaya da mamaki tace "Wai dama yaran nan suna makale anan Adnan na chan yana neman su." Dariya Umma tayi tace "Suna nan muna jegon tare." "Lallai kam, toh Hajiya tace an kai ruwan." Sai ta mike ta bata madarar ta fice ta barsu, hannu Mah-Mah tasa ta kirawo sultan ya dawo ciki suka sata a tsakiyi ta shiga feeding Little angel din da zuwan ta ya zama wani tsani na cikar bururruka da yawa.    Tun daga ranar har zuwa ranar da akayi suna Safwan da Sultan basu bar umma ta huta ba, idan wannan ya dauke ta sai wannan ma yace sai shi, haka zata sa musu ita a kafarsu suyi ta kallon ta suna jin dadi.    Ranar suna taci suna Fatima sunan Hajiyan Dr, a take Mah-Mah tace Amrah zasu dinga ce mata saboda shine sunan da ta jima tana so, umma bata ki ba, tun daga lokacin sai rainin Amrah ya zama tsakanin Hajiya da bata tafi ba da Mah-Mah, idan ta dawo aiki take karban ta ta goye sai ta gaji tayi kuka sannan take bawa sabuwar mai'aikinta ta mika tah. Haka yaran ma suke faman jeka ka dawo tsakanin gidan nasu da gidan su Adnan, duk yadda wataran Adnan yake musu gori akan Kanwar sa ce ba tasu ba basa kin zuwa.     Shekarar Amrah daya cif Umma ta sake haihuwa, sai dai haihuwar tazo da matsala dan sai da akayi mata aiki, sosai ta galabaita saboda haka tun kafin ma su baro asibitin Hajiya ta sa kanwar Umman me suna Safiyya ta hada mata kayan Amrah ta tafi da ita, hakan be wa kowa dadi ba musamman Mah-Mah da yan samarin ta,wanda basu nan ma suna makaranta. Ko da suka dawo suka tarar da abinda ya faru sun nuna bacin ransu sosai, haka dai Mah-Mah tayi ta lallaba su da alkawarin ana yayentan zata dawo nan da sati Bayan Sati biyu Dr yaje amma sai Hajiya tace a bari Umman ta sake samun karfin jikin ta, ta kuma kula da yar jinjirar me suna Afrah. Haka Dr ya hakura ya dawo gida ya kara bada lokaci Amma sam Hajiya taki.    Ko da lokacin sata a makaranta yayi Dr (Abba) yazo tafiya da ita sai Hajiya ta daka tsalle tace sam tazo kenan, babu yadda Abba ya iya a haka ya sata a makarantar ya kuma samar mata mai adaidaita sahu da yake kaita ya dauko ta kullum, ajinsu daya da Afrah saboda makaranta daya Abban ya sasu, tare suke komai hatta abinci na mutum biyu umma ke zuba musu haka ma Hajiya.     Bangaren Yan samarin kuwa sun kara girma suna aji uku a secondary, sosai shakuwar su da Amrah ta ja baya, sai ya zama idan ba ranar Friday ce tayi ba suka zo gaida Hajiya ba basa ma haduwa.      Amrah bata son mutane shiyasa ko sunzo bata sakewa dasu sai ta makale a gefen Hajiya har su tafi bata musu magana, ita kuwa Afrah sai ta zama me faran faran da surutu ga wayo sosai.     ***Rayuwa ta cigaba da garawa cikin hukuncin Allah har zuwa lokacin da Amrah suka shiga primary 4 a lokacin ne kuma Abba ya samu invitation daga wata babbar university dake Canada, har lokacin Amrah na wajen Hajiya dan bata ma son zuwa gidan su sam saboda yadda umma ke mata fad'a saboda sangarcin ta, abu kadan sai ta bare baki tayi ta kuka, hakan ba karamin kona wa Umman rai yake ba, sai ta tattara ta, ta maida wa Hajiya ita.    Sana'ar snacks da foods Umma take, Babar caterer ce, sosai take samun manyan orders na biki, suna da manyan tarukan gwamnati, sai ya zama ta kara zama babbar mace da ake damawa da ita, amintar su da Mah-Mah bata chanja ba sam, sai ma kara karfi da tayi.   Haka yaran su ma komai tare sukayi, Duk wannan amintar Mah-Mah bata taba fadawa Umman cewa Sultan ba dan ta bane, kuma iya zaman su Umman bata taba ganewa ba sbaoda babu wani abu da zai nuna ma hakan. Da daddare Abba ya dawo a gajiye saboda wani meeting da ya dauke su tsawon lokaci a Senate,wanka kawai yayi ya kishingid'a yana kallon news umma na jera masa kayan abinci a saman carpet din dake tsakiyar dakin. "Ummah..." Ya kirata yana maida hankalin sa kanta, sai ta ajiye cup diñ hannun ta, ta nufe shi ta zauna a gefen sa tana tattara dukkan hankalin ta akansa don tasan maganar me muhimmancin ce . "Na'am." Ta kalle shi, shiru yayi yana dan juya kansa sai kuma yace "Ina ganin tare zamu tafi gaba daya da Mamana da Afrah, idan yaso Adnan ya zauna gidan Alhaji Sulaiman ko wajen Hajiya ya karasa shekara dayan data rage masa sai ya biyo mu, saboda gaba daya an samu change of plan ashe ba contract zan musu na two years ba, aiki ne na wasu shekaru masu yawa, kinga kuma tarbiyyar yaya mata sai da uba." "Masha Allah." Tace tana murmushi "Gaskiya ne, nima ina ta tunanin hakan sai dai Hajiya ko zata yarda, kaga ta shaku sosai da Amrah." "Zanje na sameta zata yarda in sha Allah." "Allah yasa." Tace tana murmushi, sai ya mike ya isa inda ta ajiye masa abincin, dawowa tayi gefen sa ta zuba masa suka cigaba da hirar yana ci. *** Zaune yake yà kalmashe kafarsa yayi irin zaman dirshan din nan yana sauraren ta, yadda take magana kadai ya isa ka gane ranta ba daidai yake ba, be tanka ba har sai data dire sababinta ta d'anyi tsaki kadan tana kallon gefe, murmushi yayi yana sake fuskantar ta yace "Kiyi hakuri Hajiya, dama saboda karatun chan yafi na nan shiyasa nake so mu tafi dasu din, a cikin kankanin lokaci ake gama wa a chan mukuwa nan ga yajin aiki ga abubuwan da zasu biyo bayan nan." "Kudai dai kawai kuce kuna son yarku a kusa da ku, shikenan ya zanyi? Kira ta zan ku wuce yanzu kenan ko?" Sai ya sake matsowa sosai yana son tabbatar da ya kwantar mata da hankali... "Kiyi hakuri Hajiya, ai da saura ma tafiyar dama zamuje ayi musu passport ne gobe muna dawowa zata dawo ai." "Shikenan! Bari na sa ta fito." Tace tana mikewa. Da sauri ta saki labulen data makale a jiki tayi cikin dakin tana bubbuga kafarta irin na shagwababbun yara,  shigowa Hajiya tayi ta dauki yar karamar jaka ta zuba mata kaya set biyu sai pants da vest ta mika mta "Kwana biyu kawai zakiyi, duk wanda yayi miki ko kallon banza ne ki fad'a min." Turo baki tayi ta karba, sai hajiyan ta sa mata dan madaidacin hijab suka fito, Abba na ganin su ya mike yana sallama da wanda suke magana a waya, ya kama hannun ta yana murmushi, dauke kai Hajiya tayi ta zauna tana son sakin ranta. "Allah ya kiyaye, a gaida mutanen gidan." "Amin Hajiya sai mun dawo." Yace sannan suka fito zuwa inda ya ajiye motar sa. * A kofar gidan yayi parking suka fito a tare, hannun sa cikin nata suka shiga ciki har lokacin yana amsa wayar da tun da suka tawo yake yinta wadda duk akan tafiyar ce, suna shiga Afrah ta taho da gudu ta d'ane ta,ganin ta yasa ta saki jiki ta dane ta suka sa dariya a tare suka shiga ciki, umma na zaune rike da wani littafi tana dubawa ta tashi tana wa Abba sannu da zuwa,. "Ta yarda da biyo ka kenan." Ta fad'a tana kallon Amranbbayan ta amsa gaisuwar ta, da kai ya amsa mata ya zauna cikin kujerar falon yana ajiye hular sa a saman hannun kujerar tare da cigaba da wayar da yake. Hannun ta Afrah ta kama suka tafi dakinta, suka hau labarin makaranta da kawayen su na aji, da haka Umma ta shigo ta tadda su, hannun ta rike da kibiya da comb ta mika Amrah tace "Ungo taya ta ku tsefe kannan idan yaso sai ta tayaki kema." Karba tayi suka hau tsifar suna cigaba da hirar su, chan Umman ta leko tace su bar tsifar su ci abinci, rufe kan tayi muka koma falon, muka ci abinci sannan Umman ta karbi kibiyar ta karasa mata, nima tace zatayi min idan an yi sallar magriba ganin lokacin ya gabato.   *** Muna idar da sallah Umma ta kwala mana kira, muka zauna ta soma yi min tsifar sai aka turo kofar, daya bayan d'aya suka shigo Ya Safwan ne a gaba sai Ya Adnan sannan ya Sultan a karshe, kamshin turaren su ne ya cika falon suka zauna suka gaishe da Umman sannan suka zauna zaman cin abinci. Mikewa umma tayi ta shiga ciki, da sauri Amrah ta dago kanta da tun dazu take son ganin su, a kan Sultan ta fara sauke idon ta yana kokarin kai abinci bakin sa, sai ya kware sosai ya shiga tari babu kakkautawa, da sauri Safwan ya balle ruwa ya bashi yasha still yana cigaba da tarin da sauri da sauri, fitowa umma tayi hannun ta dauke da plate da akayi rufe tayi saurin cewa "Lafiya dai Sultan?" "Kwarewa yayi umma." Safwan yace sounding kamar zai fashe da kuka Sannu tayi masa ta tashi Adnan ya mikawa me delivery order da akayi mata dazu sannan ta dauko musu damammiyar fura a fridge. Sultan dai ne sha ba, sai ma ya mike ya fice da dan sauri *_SMM OPANAGE_* *_ZAFAFA BIYAR 2021_*🔥 _*SUKAR BAYA*_💚 _BILLYN ABDUL_ ( _kwai cikin qaya_ ) ( _raina kama_) ( _wutsiyar raqumi_ ) *_SIRADIN RAYUWA_*💛 _SAFIYYA HUGUMA_ ( _alqawarin Allah_ ) ( _daurin boye_ ) ( _Dangantakar zuci_ ) 💙 _*KIBIYAR AJALI..*_💜 _MISS XOXO_ (Sulke baya tsare ta sai ta wuce) ( _Igiyar zato_) ( _Kaimin halacci_ ) ( _Naufal_ ) *_ABIN DAKE CIKIN ZICIYA_*🧡 _HAFSAT RANO_ ( _ruhi daya_ ) ( _Sauyin qaddara_ ) ( _Daurin goro_ ) *_MIN QALB_*❤️ _MAMUHGEE_ ( _buri daya_ ) ( _tarayya_ ) ( _eznah_ ) Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇  0903 234 5899 IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 09033181070 Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥 [3/4, 11:35 PM] Maman Maryam: *_Abinda Ke Cikin Zuciya_* ©®*_Hafsat Rano_*   Free page (4) *** Tashi yayi da sauri ya shiga contact yayi dailing number Sultan, ringing tayi, tayi be daga ba, sai ya ajiye yana jin wani feeling me karfi na shigar sa, text message ne ya shigo wayar ya duba sai ya ga Sultan ne ya turo masa message "Ina tare da supervisor dina ne, call back if it's urgent." "No take care." Yayi masa reply ya ajiye wayar a saman mirror din dakin ya fad'a toilet, wanka yake yana murmushi shi kadai, ya sameta ya gama yasan, shiyasa ba zai yi k'asa a guiwa ba wajen xuwa ya samu Hajiya da maganar ba. Ko da ya fito ya shirya tsaf cikin kananan kaya da sukayi masa kyau ya fesa perfs masu kamshi ya rufe dakin ya bi corridor zuwa shashen iyayen su.  Mah-Mah na bawa me aikin ta sautu ya shigo yana d'an kad'a kansa kadan cikin farin ciki, kallon sa tayi, ta zauna tana bin ba'asin mood din sa da ta gani. "Wannan farin cikin kamar wanda akayi wa kyautar mata." Tace tana kallon sa, sosa kansa yayi ya saki dariya kadan yace "Gidan Hajiya zani na gaishe ta, rabona da gidan tun kafin Adnan ya tafi, kar tace dan baya nan ne muka dauke kafa." "Ka kyauta, shi sultan ya zama agogo sarkin aiki, yace min yau sai dare ma zai shigo gida saboda wani abu da zasuyi a clinic ko me ma yace ne? Yaren nasu ne sai su." "Eh haka yace min, na kirashi ma yana tare da supervisor din sa." "Ok Allah ya taimaka wannan karatu me wahala, ko da yake da an gama shikenan." "Balle ma nasu, sai dai k'wari irin sa dama ba irin namu na masu small brain bane." Sai ya mike "Bari naje Mah-Mah, dan Allah yau da daddare ayi mana tuwo miyar zogale, irin na Umma dan Allah Mah-Mahn mu." "Toh ai ban iya irin nata ba sarkin iyayi." Tace tana dariya "Please please sai na dawo, yau a farin ciki nake matuka, I can't wait Sulty ya dawo na siyar masa da jaridar." Yace yana yin gaba, daga murya tayi tace "Idan tayi wari maji ai, magulmata." Dariya yayi ya fice yana jin shi on top of the world baki daya. Motar sa ya shiga ya bata wuta bayan ya kunna wakar soyayya ya nufi gidan Hajiya domin isar da sakon zuciyar sa. Ta fito tsakar gidan kenan tana kwashe shanyar da tayi ya shigo, da sauri ya karba ya karasa ya bi bayan ta suka shiga ciki suna tsokanar juna, ruwa ya dauko a fridge yasha ya koma ya zauna yana maida hankalin sa kan ta sosai ya ce "Hajjaju me ran karfe wajen ki nazo fa." "Ja'iri ai nasan ba takanas dan ka gaishe ni kazo ba, ko da yake kafi dayan dan uwan naka mara kirki." "Wanne dan-uwan nawa a ciki?" Yace yana dariya "Wanene idan ba adunanu ba? Ja'iri jiya ya kira ya gama kare min tanadi, harda wai ya sami baturiya ba shi ba dawowa." "Kai be kyauta ba, ni ai ba haka nake ba." Yace yana guntse dariyar sa "Kaji dashi, Muhammadu ne kawai na kirki a cikin ku, ko jiya sai da ya biyo ya bani man ciwon kafa." "Allah sarki ai da tare fa zamuzo, sai kuma Allah be yi ba." "Kanka akeji, kace waje na kazo, ya akayi?" Zamowa yayi ya zauna a kasa ya sosa kansa yayi murmushi "Dama... Dama kamun kafa nazo hajiyar mu." "Na sani ai, ja'iri." "Allah Hajiya, kin ga gida be koshi ba ai ba za'a bawa dawa ba." Washe vaki tayi cikin gamsuwa tace "Amratu ce ko afiruwar?" Shafa kansa yayi "Amrah ce hajiya." "Toh Masha Allah, wannan abu yayi min d'adi sosai, kaga dama na matsu ya tattaro su ya dawo dasu nan, dan idan suka cigaba da zama dasu a chan wa zai gansu har yace yana so? Ga ka yanzu hankali na sai ya kwanta,saura itama Afran Allah ya kawo mata nata, duk sai mu hada ku rana daya musha biki." "Allah yayi muku Albarka." Amin yace yana jin a ransa kamar yace Sultan kuma Afrah, idan yaso sai asha bikin rana daya, amintar su sai ta kara kulluwa gashi sun auri yan gida daya, har ya bar gidan yana sakawa da kwancewa akan yadda zai bullo wa Sultan akan maganar Afrah dan baya so maganar sa tayi karfi ba tare da ta Sultan din ba.    Yana xuwa gida ya tarar dashi ya dawo,yana cin abinci hannun sa dunkule da wani abu, be bada muhimmanci akai ba ya zauna suka karasa cin abincin sai dai ya kasa bashi labarin kamar yadda yayi niyya, ji yayi ba zai fad'a masa ba sai dai yayi suprising nasa sanda zasu zo Kano dan Hajiya tace da sun gama secondary school zasu zo gida za kuma su dan dade, a lokacin xai bayyanawa kowa, kafin nan kuma zai ta nunawa Sultan hotunan Afrah ko Allah zai sa a dace shikenan burin sa ya cika.      Fitar Safwan ya bawa Sultan damar bude bracelet din hannun sa, shafa shi yayi ya saki murmushi me kayatarwa "Allah ka taimake ni, ka tsare min zuciyar ta, har zuwa lokacin da zan bude na shigar da soyayyar ta a ciki na sa mukulli na rufe ruf ba tare da ta samu space din kowa ba komai kankatar sa." "Amin." Ya amsa da kansa sannan ya maida shi cikin dan box din da yayi masa musamman domin ajiye shi ya daga kasan kayan sa ya saka shi. ***Da safe suna chan bayan gidan Sultan na motsa jiki, Safwan na zaune a saman kujera yana chatting ya bada hankalin sa sosai akai har Sultan yayi masa magana be ji ba, tasowa yayi ya fisge wayar yana hararar sa "Ohhh! Ina kokarin samo kan wata beb ne wallahi, sorry me kace?." "Aikin kenan, Allah ya shirye ka kai da Adnan shegen ruwan ido." "Kaga kuma hoton ka na tura mata wallahi, har kuma tayi falling ganin ka rataye da stethoscope tasan guy din hot ne." "What? Wallahi amma kai ko? Toh ni an bada ni ma dan kaji." Yace yana balle murfin ruwa ya kafa kansa yasha sosai sannan ya kalli Safwan da yake ta faman masa dariya "Ha'a...What's funny kuma?" "Kai mana, ji yadda ka wani ce an bada kai, ko uban waye ya bada kai? Tsaya ma... Aina ake bada namiji ne a garin nan? Idan ma hakan ne ai ni zan bada kai." "Madallah." Yace yana gid'a kansa "Bani wayata toh, naji reply dinta." "Kasha maganin ka?" Ya bata rai ya ki basa wayar "Na shiga uku ni wai kamar wani karamin yaro sai ance nasha magani ko ban sha ba? Katon magidanci dani haba, idan beb dita taji ai sai ta raina ni wallahi." "Baka son wayar ka kenan, kasha ko baka sha ba?" Yace yana sosa saman girar sa "Nasha wallahi." "Good." Sannan ya bashi wayar shi kuma ya shiga ciki domin gyara jikin sa. Wannan shine irin soyayyar dake tsakanin Sultan da Safwan, soyayyar tsakani da Allah da babu komai a cikin ta sai tausayi da girmawa a tsakanin su. Karbar wayar Safwan yayi ya cigaba da yiwa Adnan magiya ya sake turo masa wasu pictures din, sai da ya gama wanashi sannan ya turo masa wasu da sukayi a wani eatery tana murmushi hankalin ta na kallon wani abu chan da be san menene ba, sai ya zuba mata idanuwa yayi ta kallon ta kamar ya samu tv,wunin ranar da hotunan yayi su, yana jin duk wata damuwa da matsalar sa na fita kadan kadan, yana jin sa so strong da yake son rayuwar sa tayi tsayin da zai nuna mata tsantsar soyayya cike da kulawa. Adah ya kan yi tunanin yadda kullum idan ciwon sa ya tashi kowa yake kawo masa mutuwa saboda masu irin matsalar sa ana musu kallon basu da rayuwa me tsawo, duk da haka be taba rok'ar Allah ya bashi tsawon rai ba sai yanzu da yake jin yadda soyayyar ta, take bin kowanne kusurwar gangar jikin sa tana maye gurbin duk guraben da suka bude saboda nauyin ciwon da yake dauke dashi.    Kasa bacci yayi daren ranar ya dukufa rokon Allah ya ara damar da zai nuna mata gata ya maida ita sarauniya a fadar zuciyar sa. *** Gida ne babba da ya zama islamiyyar tasu, wata baiwar Allah ce da suke kira da Aunty Muhsina yar asalin kasar Saudiyya da tayi karatun ta tun daga matakin primary har zuwa degree a bangaren addinin islama ta bude makarantar bayan dawowar ta kasar, hakan ba karamin taimaka wa musulmai mazauna garin yayi ba, sosai suke karatun su na addini tamkar suna gida, su Amrah sun yi nisa sosai a karatun nasu dan sun gama littattafai da yawa Qur'ani kuwa sun sauke shi har sun fara hadda, zaman su a kasar masu jajayen kunnen be sasu sun bar dabi'ar su ta Hausa Fulani ba, Umma a tsaye take akan su, haka ma Abba baya yarda da shigar banza suna kokari sosai wajen ganin sun kula da tarbiyyar su. Afrah ce ma me rawar kai, shiyasa ma iyayen suka fi saka mata Ido sosai domin su turawan babu ruwan su, balle yadda suke kyawawa dasu TubarkAllah Masha Allah.      Sha biyu suke tashi daga islamiyyar tasu sai kuma gobe Idan asabar ce idan lahadi ne kuma shikenan sai wani satin, da yake babu nisa tsakanin su da gidan a kafa suke takawa.    A kitchen suka tarar da Umma tana shiryen shiryen lunch, jakar su kawai suka ajiye suka sameta a kitchen din, suna aikin suna hira har suka kammala sannan suka tafi yin sallar azahar ganin lokacin yayi.       Yan matan umman kyawawa ne na karshe, abin ka da Fulani da suke da kyau me sanyi, skin colour din su ba fari bane kal, ya dan sirka da duhu kadan sai suka kara yin wani irin kyau me sanyi da sai ka zauna dasu zaka kara ganin sa, musamman Amrah da take da manyan idanuwa farare tas, da dan madaidacin baki da dimple a both side din kumatun ta wanda ko bata yi magana ba in dai ta motsa fuskar sai sun loba saboda girman su.    Tafi Afrah tsayi da kadan sannan ta fita cika, duk da ba wasu manyan yanmata bane amma sun yi saurin girma sosai, jikin su ya murje kallo daya zakayi musu ka tabbatar da tsantsar hutu da gayu sun samu matsuguni a jikin nasu.     **** Dukkanin fitar numfashin shi na fita ne da soyayyar ta, haka ma duk wani abu yanayin sa ne da ita a makale a zuciyar sa, tsawon shekarun nan be taba tashi ba tare da ya tuna ta ba, sai dai bashi da sukuni sanin cewa shi kadai yake kidan sa yake kuma rawar sa,Idan ya tuna sai duk tunanin sa ya kulle ya kasa katabus. Ya rasa irin son da yake mata, tun tana zanin goyon ta, tun ranar data fara zuwa duniyar nan, tun be san me yake ji akan ta ba, tun shi kansa be gama sanin shi din waye shi ba, me yake so mene baya so, be gane irin tasa kalar soyayyar ba sai da ya mallaki hankalin kansa, sannan ya tantance irin soyayyar da yake mata, yake kuma jin tsoron abinda zai biyo baya idan har ta zabi wani bashi ba.     Ranar da ya ga hotunan su a status din Adnan, be runtsa ba ko kadan, yana tunanin yadda zata karbe shi. Zuciyar sa takan yi zafi idan ya tuna waye shi, maraya wanda bashi da UWA balle UBA bare azo maganar dangi, ya sani a aure nasaba na da matukar muhimmanci, toh shi be san kowa nasa ba ma bare azo maganar ma baki daya. Tunanin sa yakan katse idan ya tuna zai iya yiwuwa ma ba ta hanyar aure aka sameshi ba, da sauri yake neman tsari da haka duk sanda tunanin ya gifta ta kansa.    Idan kuma ya tuna Daddy da Mahmah da gatan da sukayi wa rayuwar sa, sai yaji ya samu kwarin guiwar da zai nemi soyayyar ta, su kuma tsaya masa kamar yadda xasu tsayawa Safwan. Wannan kenan!   ***Graduation gowns ce maroon colour sanye jikin su, fuskar su kadai zaka kalla ka shaida tsanar farin cikin da suke ciki, taro ne akeyi a cikin tsari babu hayaniya wajen. Gefe Adnan ya samu ya fara Skype shi da Safwan yana nuna masa duk abinda ke faruwa a wajen, tun farkon fara gift ga students din da suka chanchanta, daga Amrah har Afran suna ciki, haka aka kirasu aka basu kyaututtukan su gwanin sha'awa.     Kwance yake a daki ya rufe ko ina yana more kallon komai kamar yana wajen, turo kofar Sultan yayi cikin shirn fita, ya tsaya yana kallon yadda yake kallon waya yana murmushi, zuwa yayi da niyyar lekawa Safwan ya tashi yana boye wayar yana dariya "Kai matsalar ka kenan, Idan ana shirin suprising naka sai ka bata plan din, Allah yaso baka ga komai ba." Yace yana sake boye wayar, tabe baki Sultan yayi ya dauki jakar sa ya rataya. "Idan tayi wari zamuji ai, na lura da take taken ka yaro." "Karka damu, nayi alkawarin kai ne na farko da zan fara sanarwa komai da zarar an dace, kai dai ka taya ni da Addua ina neman abu me muhimmanci a rayuwata, infact idan na same shi ma zuciya ta zata samu sauki da kaso hamsin cikin dari, kaga kai ma saukin ka ne ba kayi ta fama dani ba bayan kai ma kana da life ahead of you." Yanda yayi sounding a karshe kana ji kasan abun na taba shi, sai ya ajiye jakar ya matso ya dafa kafadar sa kafin yace "I promise to give you my maximum support, karka manta lafiyar ka itace priority dina, zan yi duk abinda zanyi wajen ganin ka cika burin zuciyar ka." "I trust you." Yace yana murmushi Musabiha sukayi ya fice shi kuma yayi dialing number Adnan dan ya kashe kiran tun da suka fara magana da Sultan, jin be daga ba sai kawai ya ajiye wayar ya fita daga dakin. ****Toh masu karatu, me kuke tunanin zai faru? Akwai chakwakiya ko nace chakwakiyoyi a gaba. Abin da ke Cikin Zuciya littafin kudi ne, daya daga cikin jerin littafan Zafafa Biyar, domin mallakar naki sai ki tuntubi wadannan lambobin 0903 234 5899 Or 09033181070 Not edited Rano 👌💞     [3/4, 11:35 PM] Maman Maryam: *_Abinda Ke Cikin Zuciya_* ©®*_Hafsat Rano_*   Free page (3) *** *_SMM OPANAGE_* Juya aikakkiyar wasikar take a hannun ta, zuciyar ta a jagule kamar ta dora hannu aka ta saka ihu ko taji saukin zafin da take mata, sai da tayi mata duban tsanaki sannan ta ninke ta, ta hada da sauran kayayyakin da take tarawa, ta ajiye su a ma'ajiyar su, sannan ta fito wajen yaran dake jiran ta.    Ranar a kasalance tayi komai, daga karshe ma sai ta shige ciki da niyyar ta kwanta ta huta ko ta samu zuciya da gangar jikinta su samu nutsuwar da suka rasa.     *** Da sauri Safwan ya bi bayan shi, har ya kai gate zai fita ya tsaida shi da d'an gudun sa "Lafiya kuwa?" Yace sanda ya fuskance shi, sai ya ga kamar idon sa yayi ja "Babu komai kaina ne ya dan yi dum, sai kuma na tuna sakon Daddy, kasan fa time na kurewa bamu ma gama hada kan kayan ba balle mu kai." "Shine duk ka damu haka? Chill guy muje mu karasa shan furar chan sai mu karasa hade kayan gobe da wuri sai mu kai musu." Girgiza masa kai yayi "Karka damu, bari na je gida idan ka gama sai ka sameni." "Shikenan tunda ka dage, bari naje sai na shigo.". Sai ya juya shi kuma ya fita yana jin wani irin emptiness da besan na menene ba, ya san dai kawai ba normal yake jin sa ba. Daki kawai ya wuce direct ya kwanta rigingine ya daga kansa sama yana tunanin yadda rayuwar sa take, idan ya tuna shi din maraya ne, bashi da kowa da zai nuña a matsayin jinin sa, sai yaji duk komai ya kwance masa, amma idan ya tuna gatan da kuma Allah yayi masa ya tsamo shi ya inganta masa rayuwa sai yaji duk tunanin ya kau, baya fatan ganin iyayen sa domin Mah-Mah da Daddy sun cike dukkan gurbin da iyayen nasa suka bar masa shi open, sannan ga dan uwa amini da zai iya cewa bashi da kamar sa duk fadin duniyar nan, soyayyar da yake masa daga Allah ce, Allah ne ya hada su cikin Ikon Sa, ya kuma saka kauna a tsakanin su,kauna me tsanani da ta zama wani jigo na rayuwar sa.      Bashi da wata matsala da su, haka kuma iyaye ya dauke su, ba kuma ya fatan Allah ya kawo ranar da zai butulce musu. Daya daga cikin abinda yasa ya zabi bangaren lafiya, kuma bangaren zuciya saboda ya riga yasan Safwan ne rayuwar iyayensu, Shima kuma haka, duk lokacin da ciwon sa ya tashi su kan rasa sukuni, har sai sun ga ya dawo daidai sannan komai yake komawa daidai.     Safwan mutum ne shi be faran faran da jama'a da son duk wani da zai rabe shi, fuskar sa a sake take da wuya ka ga bacin rai a fuskar sa while Sultan bashi da fara'ah sai dai fuskar tasa a sake take ba irin a daure nan ba. Yana da kazar kazar shiyasa ma Daddy yafi dora shi akan duk wani abu kafin yace Safwan sau daya ya kira Sultan sau goma.    Yana kwance yana sakawa da kwancewa aka kira sallah, sai ya mike ya dauro alwala ya wuce masallaci. A chan suka ya tarar da su adnan bayan sun idar sai suka samu waje a nan bakin layin sukayi zaman su suna hira irin wadda maza samari ke yi galibi, hirar siyasa, kwallon kafa sai kuma hirarrakin yan mata. Safwan da Adnan sune akan gaba wajen kawo tactics din saye zuciyar mace, inda sultan sai dai yayi musu dariya kawai idan abin dariya ne. Chan Adnan ya zungure shi ya bata rai yace "Kaifa wallahi dan rainin class ne, kana yin kamar baka san komai ba, kamar wani uztaz." "Toh da menene?" Ya amsa masa yana dariya Wani abokin su Mubarak yace "Gaskiya ne ya sheik, irin ku ne soyayya ke wa kamun kazar kuku, kuzo kuna ciwo kamar ba zakuyi rai ba." "Allah ya kiyaye wallahi.". Safwan yace yana mikewa "Sultan yafi karfin yace yana so a wulakanta shi wallahi, gaye iya gaye ga nutsuwa ga aji, ai sai na zaba na darje kafin na yarda ya kula koma wace." "Kai ne ma zaka aurar dashi kenan." Adnan yace yana buga tsaki "Kusan haka ne ko bro?" "Hakan ne ma." Ya amsa yana murmushi Sai sauran suka sa ihu da shewa irin ta samari masu jini a jika. *** Da safe bayan Umma ta tashi su Amrah tasa su sunyi wanka sun shirya sai ta shiga gidan Mah-Mah kafin lokacin da Abba yace zasu tafi yayi. Gaisawa sukayi sai ta dauko mata maganar tafiyar tasu, sosai maganar ta daki Mah-Mah, dan batayi zato ko tsamammani ba, musamman yadda aka saba sosai rana daya mutum ya tafi wata uwa duniyar, dole abin zai taba ka, hakuri dai Umman ta bata da alkawarin zumuncin su ba zai yi komai ba, sannan ma sun yanke shawarar barin Adnan awajen su saboda ya karasa zuwa lokacin sai ya biyo su.    Har gate ta rakota tana sake jaddada mata yadda tafiyar tasu ta zo mata a bazata, da yadda zasuji ita da yaran idan basa nan. Ita dai umma hakuri tayi ta bata sannan sukayi sallama ta tafi.     Su Sultan na tsaye Umman ta fito, suka gaishe ta, ta wuce ciki. Tana shiga ta tarar da wayar ta Abba na kira, dagawa tayi yace su sameshi a chan immigration office din zai wuce daga nan dan kar a bata lokaci. Adnan tasa Afrah ta kirawo ya fitar da mota, lokacin Safwan ya shiga gida sai yace Sultan yazo suje.    Suna zuwa basu wani dau lokaci ba  akayi musu komai saboda wani abokin Abban da yake aiki a wajen suka juyo gida.    Da yamma Abba ya saka Adnan ya maida Amrah kafin Hajiya ta sake kira, tare suka tafi su dukka har da Afrah da tace itama sai tayi rakiya. Sultan ne yake driving din, Adnan a gefen sa sai su kuma a baya tare da Safwan da yake ta tsokanar Afrah tana biye masa, ita dai Amrah bata ce komai ba tana ta juya set din earing da Umma ta bata ta kai wa Hajiya har suka iso, kama kofar tayi zata bude ta kasa, da sauri Sultan ya balle murfin kofar sa ya bude mata, fitowa tayi tayi kicin kicin da fuska ta kalle shi, murmushi yayi mata ya mika hannu ta bashi dan kunnen, noke kafada tayi ta wuce shi, karar fadowar abu yaji, ya kalli inda ta bari, dan karamin bracelet ne golden and red me kyau yasa hannu ya dauka yana kallo, sai yayi murmushi ya zura shi a aljihun sa ya bi bayan su dan tuni duk sun shige ciki.     Yana shiga ya ganta a tsaye gaban Hajiya ta rike kugu tana maida labarin abubuwan da suka faru, komai sai data fad'a mata bata rage komai ba, mamakin ta sukayi tayi ashe tana nad'e komai tana jira ta dawo ta amayar, dungure mata kai Adnan yayi ta hau bubbuga kafa Hajiya ta kai mishi bugu da muhucin hannun ta ya goce yana dariya.     Har dare suna gidan, sai da Abbaya kirasu ya fara fad'a sannan suka tafi suka bar Afrah a chan dan tace ba zata tafi ba.      A hanya duk suna ta hira Amma Sultan be sa musu baki ba, zuciyar sa ta lula a tunanin abinda ke nukurkusar ta, ya rasa dalilin da yasa yake jin irin feeling din da yake ji idan ya ganta. Yarinya ce karama just 9years amma yana jin wani irin shock duk sanda ya kalli kwayar idon ta, zai iya cewa idanun ta kadai ke sashi jin kamar yayi ta tafiya ba tare da ya tsaya ba, ya kan ji wani irin strong attachment idan kwayar idonta ta sauka a cikin tasa, gashi dai shi din ma nawa yake? He's not ready for any relationship dan karatun da yake shirin tunkara ba na raguwar zuciya bane, yana so ya zama cardiologist, cardiologist consultant saboda Safwan, saboda ya zama babu wani matsala tasa da zata taso har a rasa me tsaya masa, ya yarda ko da shi kadai karatun nasa zai amfana bashi da damuwa akai, bashi da matsala hakan kadai ya wadatar.    *** Shirye shiryen tafiya ya kankama, komai ya zama ready sai rana kawai ta rage musu, Hajiya da Amrah, Mah-Mah da yan samarin ta basa son tafiyar ko kadan, amma babu yadda zasuyi din sai fatan hakan ya zama alkhairi a garesu baki daya. Daren ranar tafiyar mutane da yawa basu runtsa ba, ciki harda sultan da yake jin kamar some part of him is leaving him, juye juye yayi tayi kafin a soma kiraye- kirayen sallah ya tashi zuwa toilet.    Jirgin karfe goma zasu bi saboda haka tun kafin lokacin yan uwa da abokan arziki suka cika gidan, aka dunguma aka tafi raka su airport. Bayan komai ya zama cleared jirgin su ya daga cike da kewar mutane dan da kyar aka raba Hajiya da Amrah dake ta faman kuka. *Bayan shekara* *(6)* ***Abubuwa da yawa sun chanja rayuwa ta cigaba da garawa cikin hukuncin ubangiji, shigar Safwan, Adnan da Sultan jami'ah ya kara taimaka musu wajen sake sanin rayuwa. Bangaren da kowa ya zaba yake karanta, inda Safwan ya zabi bangaren law Sultan kuma medicine sai Adnan da yake karantar Criminology, da taimakon Abba kowa ya samu dream karatun sa. ***Sallama suka yi a kusan tare suka shigo gidan, Daddy na zaune yana cike wasu takardu ya dago ya sauke idon sa akan yaran nasa, har suka karaso be dauke kansa daga kallon su ba, yana nazarin su sosai, Mah-Mah na lura da irin kallon da yake musu tasan bazai wuce na mamakin yadda suka girma suka zama manyan samari ba, Safwan ya gama law yana shirye shiryen tafiya law school inda Sultan yake level 500, Adnan kam har yayi service din sa ya bi su Abba chan da niyyar zai dan huta kafin ya dawo kuma a fara maganar aiki.   Sai da suka zauna a gaban sa sannan ya sauke boyayyiyar ajiyar zuciya yana fad'ad'a fara'ar fuskar sa. "Barka da gida Daddy." Suka fad'a a tare "Barka dai my boys, likita bokan turai ya karatun?" Yace yana maida hankalin sa kan Sultan "Alhamdulillah wallahi, muna ta fama kamar mutum ya zura da gudu." "Ayi hakuri kar a zura din, wataran sai labari." Dariya suka saka gaba daya, ya tambayi Safwan shirye shiryen da yake, ya amsa masa suka cigaba da hirar har sanda lokacin sallah yayi suka tashi. **** G*idan shiru babu alamun akwai wanda ya tashi a cikin su kasancewar weekend ne, tsaye take a babban kitchen din dake daura da kofar fita daga shahen baki daya, wuka ce a hannun ta tana aikin ferayar dankali inda hankalin ta ya rabu gida wajen biyar cikin son ganin ta gama komai ta kammala kafin cikar lokacin data d'iba wa kanta, a k'aidar ta bata wuce karfe tara bata gama hada komai ma. Duk da aikin ba me yawa bane amma kasancewar sa kashi-kashi yasa yake ci mata lokaci.   Hannun ta ta wanke a gaban sink ta sa dan karamin towel ta tsane su tana sake duba komai, mutum ce ita me matukar tsafta da kyankyami, hakan yasa take aiwatar da komai cikin tsantsani da takantsantsan had'e da zallar kwarewa. A saman dining ta jera musu komai bayan ta zuba nata ta wuce zuwa dakin su.     Jan bargon da Afrah ta rufe kanta dashi tayi, ta kai mata duka a baya, a rikice ta tashi ta hau sosa wajen tana ware idon ta, ajiye plate din hannun ta tayi ta dauki towel ta wuce toilet tana jan siririn tsaki, Afrah tasan suna da islamiyya amma ta kwanta tana bacci dan wulakanci, bata son a komai a bata mata lokaci tafi son komai tayi shi cikin tsari, bata da hayaniya har yanzu koman ta a nutse take yin sa, zaka dauka yanka ce da ita sai dai ko kusa haka nature dinta.    Ware gashin kanta tayi ya bi bayan ta ya kwanta har kusan rabin bayan nata, shampoo masu kamshi ta matsa ta wanke kan tas sanñan tayi wanka a gurguje ta fito, ganin Afrah nannade a bargon still yasa taje a fusace ta fizgeshi "Amrahhhhg..." Taja sunan tana lumshe idon ta, duka ta sake kai mata da yasa ta mike da sauri. "Allah kika bari na gama sai dai ki hakura dan bazan jira ki ba." Tace cikin harshen turanci tana komawa gaban mirror, kunkuni Afrah tayi ta wuce toilet din ta barta tana shiryawa a nutse.      Black abaya duk suka saka Amrah ta yane kanta da orange veil da zanen black ita kuma Afrah tasa yellow. Ashirye suka fito suka tarar da Ya Adnan a saman dining yana breakfast, zama Afrah tayi suka karasa tare suna dan taba hira, Amrah na gefe tana kallon su dan ita tayi nata, a tsarin ta bata son zama a saman dining shisa ko yaushe take cin nata daban. Sun tashi zasu tafi Adnan ya tsaidasu ya dauke su hoto sannan suka tafi. Komawa daki yayi ya shirya sannan ya dauke wayar sa, misscalls din Safwan ya gani, yabi kiran yana zama a cikin cushion din falon. "Hello..." Yace sanda akayi picking call din, sai dai baya jin komai alamun network din chan bashi da kyau, kashewa yayi ya hau whatsapp, ya ganshi online sai kawai ya masa magana. Hira sukayi sosai da zasuyi sallama yace ya tura masa hoton kannen su dan rabon sa dasu tun ranar da suka tafi. Gallery Adnan ya shiga ya tura masa wanda sukayi tare dazu sannan ya kashe datar ya sa wayar a aljihu ya fita walk. Da wani irin sauri Safwan ya tashi zaune daga kwanciyar da yayi yana sake kallon hoton, zuciyar sa na wani irin bugawa da sauri da sauri. Sake kalla yake yana son gasgata abinda ya gani, haka yaran suka kara girma da kyau ko kuwa idon sa ne? Kamar wasu twins haka suka koma masa, bin su yayi tayi da kallo kafin ya tsaida kallon sa akan Amrah yana sake zooming sosai. "Ya Rabb!" Yace yana fadawa baya "Qurratul ayn." Ya furta yana shafa kansa, murmushi me kyau ya subuce daga bakin sa zuwa saman lips din sa. A hankali ya sake furta "Itace wallahi.!*_Abinda Ke Cikin Zuciya_* ©_Hafsat Rano_ Free page 5 *** Tana kwance bayan ta gama duba gifts din da suka karba tana jiran dawowar Abba da wayar da yàce zai siyo musu a matsayin gift dinsa na grad da sukayi, duk da bata da tarin kawaye balle ace zasu dinga waya ko chat, amma tana so taga yadda duniya ta zama, tana so itama ta zama social ta shiga kowanne lungu da sako na social media taga me ake yi, me ake ji, plus abubuwan da suka shafi harkar chefs, girke girken dishes na kashashe daban daban da ya kasance passion dinta, idan da wayar zata kara samun experience na abubuwa da yawa, gashi tana da sha'awar karatun novels na manyan marubuta online both na turancin dana hausan ma.     Da sauri ta tashi jin maganar Abban a falo, ta fito da sauri har tana neman tuntube, boxes biyu ne a hannun sa an rufe su, hasken fuskar ta ya karu, ta karasa da d'an gudun ta suka saka Abban a tsakiya, sai da ya gama yi musu nasiha sosai sannan ya basu sabbin wayoyin hade da gargadi da ya fi yiwa Afrah, sunyi masa godia da alkawarin babu abinda zai faru in Sha Allah. Dakin su suka tafi suka hau kan wayoyin sukayi ta fama har dare yayi suna aikin abu daya, sai da Adnan ya shigo sannan ya taimaka ya tayasu yin wasu settings din shima sai da yayi ta ja musu aji.   Shirye shiryen tafiya Nigeria ya kankama, suna ta murna da dokin zuwa, ranar da daddare Abba ya dawo a gajiye ya shigo lokacin ma suna dakin su suna sabon aikin wayar da ya same su, ya same su man dan tun da wayar tazo basu huta da hidimar ta ba.    Bayan Umma ta gabatar masa da abinci da ya kasance snacks ne da milk shake, be iya ci ba yace ya koshi ya karbi black tea kawai yasha sannan yace "School din nan da na taba yiwa Amrah applying sun fitar da circular zasu fara classes next week, akan girke girke da gyaran jiki da abubuwa dai, yanzu ne opportunity din da zata samu tayi kafin su shiga university." Dan bata fuska umma tayi dan har ga Allah bata son abinda zai katse mata tafiyar ta, muryar Abba ta katse mata tunani "Ba zan iya hanaku tafiya ba, dan kunsa rai bayan haka ma ya kamata kuje din, dole dai ita Amrah ta zauna sai na hakura ni dama akwai ayyukan da nake son karasawa." "Toh yanzu ba yadda za'a yi kenan?" "Eh hakan za'a yi, idan kuka dawo mu sai mu sa lokaci muje in Sha Allah." "Toh Allah yasa haka ne mafi alkhairi, ita na su Afran basu fara ba kenan?" "Eh su sai nan gaba, sune batch din da zasuyi bayan mamana sun gama." "Okh Allah ya kaimu." Tace tana tunanin yadda Amrah zata ji idan aka ce babu tafiya *** Duhu ne sosai da ya mamaye kowanne lungu da sako na dakin, karamin daki ne na gaske babu komai a ciikin sa sai ta wata yagalgalalliyar katifa data cinye kusan gaba daya dakin, daga chan kuryar dakin take kwance ta zuba wa saman rufin kwanon da rana ta gama dukansa duk ya bule hakan yasa haske rana ke shigowa ciki musamman idan ana tsananin ranar.    Sha biyu da wasu dakiku na dare, shiru kake ji garin yayi babu karar komai sai chan k'asa k'asa zaka dinga jiyo haushin karnuka da karar injinan gidan masu hannu da shuni dake chan kasan unguwar.     Juyi take ta tana aikin tunanin yadda rayuwar su ta zama yanzu, idan baka dashi shikenan rayuwar ka ta gama tagayyara, mutane a wannan zamanin kowa kansa ya sani, daga shi sai iyalin sa. Shisa gaba daya rayuwar tayi wahala ainun, babu me jin kan na kasa dashi balle ya taimaka masa, sake gyara kwanciyar ta tayi, ta cigaba da tunanin sana'arta ta kosai da take yi a kullum, abinda suke samu su rayu kenan ita da yayanta biyu mace da namiji Muhammad da Aisha, sosai Muhammad yake fafutuka akan su,tasan yana iyakar kokarin sa wajen ganin ya kyautata rayuwar su, ya inganta musu ita, sai dai komai baya tafiyar musu a daidai, babu me kula su da sunan abota, babu me hulda dasu saboda wani dalili da take ganin sa mara tushe, dalilin da be kai a wulakanta dan adam akan sa ba, musamman idan baka da masaniyar ainihin abinda ya samu rayuwar mutum har ya zama abinda ya zama. Allah da kansa ya ce ya karrama bani Adam, toh me yasa wasu mutanen suke wulakanta wannan darajar da Allah ya basu? Gidan da suka zaune gidan haya ne irin babban nan, yana kunshe da dakuna a kalla guda asharin masu falle falle, sai kuma irin nasu me ciki da falo da ya kasance guda biyar irin sa a cikin gidan, kar kayi tunanin idan ance ciki da falo ana nufin hadadden daki, babu wani banbanci tsakanin nasu da sauran masu falle dayan, banbancin kawai guda biyu ne aka hade su suka bada ciki da falo. Suma da chan a guda dayan suke, amma sai aka fara juya magana ganin Muhammad ya girma ana musu mummunar fassara har ta kai maganar ta dawo kunnen su, ran shi ya baci sosai haka ya kara kai mi wajen yar sana'ar da yake ya samu suka kama daki biyun,shi yana falo su kuma su na ciki. Duk da haka basu tsira da maganar mutane ba, sai kawai suka tattara su suka watsar suka cigaba da rayuwar su yadda Allah ya hukunta musu.    Shekaru sun ja sosai haka ma rayuwa ta sauya wa mutane da yawa, ciki har ta wannan baiwar Allah me suna Safiyya, Wanda yayan ta suke kira da Ammi, mace ce jarumar gaske, da wuya ka gane wani abu a tattare da ita da zai iya yi maka fashin baki akan halin da take ciki, tana da kuzari da kazar kazar sosai wanda idan ba samun ta kayi a irin lokutan da take warewa musamman don tunawa da rayuwar ta ba, zakayi tsammanin bata da wata damuwa da irin rayuwar da suke yi, a zahiri ko yaushe cike fuskar ta take da farin ciki da annashuwa, Sai dai a bad'ini zuciyar ta  ba haka bane, a chunkushe take da manya manyan kaddarori masu wuyar fassarawa, tabbas abinda ke cikin zuciyoyin mutane baki ba zai iya fidda su ba, wasu zakutan dankare suke da matsaloli masu yawan gaske. Duk da bahaushe kan ce labarin zuciya a tambayi fuska,  amma a gurin wasu tsirarun mutane irin Ammi zai yi wuya ka iya gane ainihin abinda suke ciki, mace ce jarumar gaske, ta kowanne bangare tana iyakar kokarin ganin ta tsaya da kafar ta da rayuwar ta, tayi kuma kokari wajen manta baya! Da yin assalatu take soma aikin sana'arta, ta gyara komai ta kimtsa shi waje guda, ba karamin karbuwa tayi da sana'ar tata ba, shiyasa bata k'asa a guiwa wajen kula da sana'ar tata.    Tashin Aisha taje yi ganin har rana ta soma fitowa bata ji motsin ta ba, sai ta same ta a dunkule waje daya tana motsa kafarta alamun idonta biyu "Aisha?" Ta kira sunan ta, tana kokarin kai hannu jikin ta, juyowa tayi sai ta yi salati "Baki da lafiya?" Tace tana matsowa kusa da ita 'Daga mata kai tayi tana ciccije baki irin na marasa lafiya, kama ta tayi ta zaunar sannan ta fita, sai gata ta dawo da kofi da ta jika kanwa, ta mika mata tasha lokacin har Muhammad ya shigo ciki yana yi mata sannu. Amsawa tayi ta koma ta kwanta a hankali sai cikin ya saki, ganin haka yasa Ammi ta koma wajen sana'arta ganin lokacin har ya fara shurawa. Wajejen karfe sha daya bayan Ammi ta gama ta dawo da komai ciki, sai ciwon cikin ya kara tsananta, dole suka dunguma suka tafi asibiti da ita ganin yadda take murkususun ciwon kamar zata mutu. ***Ranar a gajiye yake, ga wani mugun ciwon kai daya addabeshi, ya takura masa har baya gani sosai, magani ya dauka yasha sannan ya koma bakin aiki, yau itace busiest day dinsu a clinic, shiyasa ma ko waya baya dagawa sai ta zama dole.    Kiran Dr Ahmad (Ruhi Daya)  ya shigo masa a lokacin da yake kokarin maida wayar silent, da d'an sauri ya daga yace "Sir." "Kazo office ka same ni." "Okh." Yace ya katse kiran ya fita da sauri, sauran wanda suke tare suka bishi da kallon tambaya, be bi ta kansu ba ya haye kan doguwar barandar da zata sadaka da ofishin Dr Ahmad, hannun sa sakale da bayan a bayan sa, yazo daidai wajen wani x-ray room yaji gaban sa na tsananta faduwa, tsayawa yayi ya dan waiga kamar me neman wani abu, babu kowa sai wani mutum da yake nufo shi, cigaba da tafiya yayi yana jin wani strong attachment da wajen, ganin babu komai yasa ya hakura ya karasa office din Dr Ahmad yana jin kamar ya bar wani abu me muhimmanci a wajen da ya baro.    Ba kowa ke samun damar ganin Dr Ahmad ba, ba kuma wai dan yana da wulakanci ko wani abu ba, sai dai kasancewar sa mutum me kwazo da iya aiki, baya gajiya kamar agogo haka yake shi yasa duk yadda kaso ganin sa, sai ka hada gumi ka share kafin ka samu ganin sa. Sultan ya kasance me tsananin sa'a dan shi har mamakin yadda ake zuzuta wahalar ganin Dr Ahmad yake, iya zaman sa a asibitin ya ganshi yafi sau nawa, da kansa ma ya karbi number sa yace zai neme shi, gashi kuwa ya neme shin duk da be san dalilin kiran ba, sai dai yana jin ko menene yana da muhimmanci.    Knocking yayi aka bashi Izinin shiga, sai ya yi sallama ya shiga cikin tsantsar nutsuwar sa dake kara masa girma a wajen mutane.   Fuskar Dr Ahmad a sake ya amsa sannan ya nuna masa wajen zama bayan ya amsa gaisuwar sa "Muhammad Sultan Sulaiman." Ya kira sunan shi yana kallon allon computer "Yes sir." "Ka gode wa Allah domin yana sonka, lately mukayi magana da Prof Mudi head of department dinku akan kokarin ka da kwazon ka, hadi da irin course din daka zaba da ya zama ba kowa ne yake yi ba, muna lacking Cardiologist a kasar nan bama a garin nan ba, abun mamaki sai ga invitation daga Babbar University, University of Medicine Canada (My university thou 😁 I don't know ko akwai ta ko babu, just my imagination) suna neman hardworking and talanted students zasu dau nauyin sa yayi wani course na 3years akan Brain, so babu bata lokaci muka tura sunan ka da details naka, to cut the long story short, ka samu admission, duk wasu shirye shiryen sun gama, tafiya kawai ta rage maka." Cikin tsantsar farin ciki yake kallon Dr Ahmad din har ya dire bayanin sa, àlhamdulillah ya ambata a fili yana jin kamar matsalar Safwan din sa ta kare, abin da yake tunanin yi kenan, abinda yake buri kenan, Sai gashi Allah ya kawo masa a daidai lokacin da yake bukata, godiya kam ranar Dr Ahmad ya sha ta, har sai da yace ya isa haka Allah zai gode wa, a take ya karbi mail dinsa yayi updating komai sai gashi sun turo masa admission letter din a take, da form din da zai cike for sauran abubuwan da zasu biyo baya.    Fuskarsa ta gaza boye halin da yake ciki, sauri sauri ya dinga yi ya kira Safwan ya bashi labari, yana fita ya tsaya jikin wata kofa ya danna masa kira yana jera godiya ga Allah da yayi masa wannan gatan.    Yana jin ya daga yayi wata dariya da shi kansa Safwan din sai da yayi sensing Sultan yana cikin tsantsan farin ciki "Ya akayi? Daga jin muryar ka nasan akwai kyakkyawan labari, share it." "Kana ina?" Yace "Gani na je airport dauko Umaima, ya akayi?." "Umaima!?" Ya fadi sunan yana son tuno ina yasan sunan "Amma kai dan rainin wayo ne Yarinya Antyn Lagos fa." "Ohh na tuna, wallahi sunan ne ya kwanta min." "Haka kake ai, gashi ita bata manta da kai ba, sai tambaya take kana nan." "Nima na tuna ta, an jima rabon da suzo kasan, anyways idan ka fito ku biyo nan sai mu wuce, akwai babban albishir." "Sai ka dai ja min aji sannan zaka fada min ko? Shikenan gata nan ma ta fito tana zara ido, sai munzo." Ya katse kiran, maida wayar yayi aljihu ya taka a hankali ya koma wajen aikin su, yana zuwa kai tsaye ya nemi izinin team leader dinsu akan zai je gida, be tambayi ba'a si ba yace shikenan sai gobe tun da dama be fiya daukar excuse ba. Kayan sa ya tattare ya zuba a jakar system din sa ya fito bakin wajen ya zauna yana jiran Safwan yana danna waya. ***Tun da suka tawo hanya take masa surutu, duk son magana irin ta Safwan sai data kure shi yaji ya gaji, ya fara amsa mata da eh ko a'ah, har suka iso asibitin be kara wata doguwar magana ba, kallon gate din tayi ta karanta abinda aka rubuta, sai ta fad'ad'a fara'ar ta tace "Wajen Ya Sulty zamu?" "Umm." Yace mata dan gaskia ta bashi haushi "Yes! Rabo na dashi an dade, kamar kasan shi nake son fara gani kafin kowa ma, thanks so much." Da mamaki ya dube ta, hadda su thanks so much, sai ya girgiza kansa kawai, bata san waye Sultan ba, zai iya share ta ya bawa iska ajiyar ta wallahi, dan ya tuna wani zuwa hutu da tayi lokacin ana gyaran kitchen cabinets Sultan din ne tare da me yin aikin, shi kuma Safwan yana daga kan fridge yana danna waya ta shigo kitchen din tana iyayi, tana tambayar sa ina aka ajiye plate da spoons zata ci abinci, be amsa mata ba sai kawai yaje ya dauko komai da yasan zata sak tambaya ya dire mata a wajen ya fice ya bar mata kitchen din, ba karamin dariya Safwan yayi a lokacin ba, tunowar da yayi yanzu ya kara sashi dariya sosai yana hasaso drammar da za'a sha idan ta nemi matsa masa.    A bakin wajen yayi parking tayi saurin balle murfin motar ta fito, a daidai lokacin Ammi da Aisha sunzo wucewa, tana budo kofar ta bugawa Ammi a kafa, da sauri tace wash tana dan durkusawa saboda yadda taji zafi, a yatsine ta kalle su, irin kallon wulakancin nan kafin tace "Ku baku san mota bane ko babu ita a kauyanku? Ba zaku dinga dubawa ba aikin banza." Da sauri Safwan ya fito ransa a bace ya daka mata tsawa "Wanne irin wulakanci ne ki bige mutum ki kuma bishi da cin mutunci huh?" "Dan Allah Mama kuyi hakuri." "Ba komai." Ammi tace suna yin gaba, ran Safwan ya baci sosai, yayi mata wani kallo kafin yace "Wannan ba halin kirki bane, mutum daraja ne dashi baki san su waye ba." "Baka ga laifin da sukayi bane? Ko basu da ido basu ga mota ta tsaya ba, zasu zo su makale a jiki." "Ya isa! Ki koma mota ki jira na kirawo shi, ba shiga zakiyi ba ai." Ranta ya baci ta juya a fusace ta shige ta zauna hade da bugo kofar da karfi, be ko juyo ya ga me tayi ba ya wuce ciki. Kafin ya karasa Sultan ya hango shi ya taso suka hadu a hanya, hannu ya mika masa suka gaisa sannan suka tawo still hanayen nasu sarke da juna zuwa wajen motar. **** Toh masu karatu, ga Safwan na jiran zuwan sahibar zuciyar sa, sai dai gashi tafiyar ba zata yiwu da ita ba, gefe daya ga tafiyar da Sultan zai yi wadda zata zama budar mukullin labarin zuciyar mutane da yawa. Wacece Ammi? Wacece Umaima? Me zai faru Idan sultan ya tafi Canada, akwai soyayya me tsayawa a zuciya da ruhi Akwai riguntsumi sosai da zai biyo bayan wannan sai dai amsar tana cikin littafin ABIN DA KE CIKIN zuciya Domin mallakar naka sai ka tuntubi wadannan lambobin 0903 234 5899 Ko*_Abinda Ke Cikin Zuciya_* ©_Hafsat Rano_          Last free page (6)    *** Yana shigowa motar ya ji an kira sunan sa, ya juyo da dan sauri dan be ma lura da ita ba, murmushi yayi mata ya amsa sannan ya juya, sai ta fara masa surutu, dafe kansa yayi ta hannu daya yana jin wani haushi na kamashi, har suka zo gida bata yi shiru ba, haka suka fito suka shiga ciki still tana cigaba da surutun da babu me kulata a cikin su, sai ma kara sauri da Safwan yayi ya shige bangaren su yana daga waya.    Jerawa sukayi har falon Mah-Mah, kana kallon yadda yake amsa mata zaka gane ba son hirar da take masa yake ba, zama yayi Mah-Mah ta fito kenan daga kitchen da sauri Umaima taje ta rungume ta suka saka dariya a tare "Yanzu muka gama waya da Amina tace min kin iso? Nace dai Safwan yaje daukar ki ashe tare ma kuke da Sultan." "Tare muke, sai da muka bi muka dauko shi." "Sannu da zuwa toh, ki shiga ciki ki huta Hauwa zata kawo miki abinci." "Ok Mah." Taja jakar ta ciki bayan ta juyo ta sakar ma Sultan murmushi, girgiza kansa yayi ganin irin kalar tata tarbiyyar, be ji lokacin da ta gaida Mah-Mahn ba kuma ko a jikinta,Allah ya kyauta kawai yace ya dan zamo ya ce "Barka da gida Mah-Mah." "Barka Sultan, ya aikin?" Ta zauna tana rage karar tv, "Alhamdulillah." "Ina dan uwan naka ya tsaya?" "Ya shiga ciki." "Owk sannun ku, abinci fa?" "Um sai dan anjima, ni wani kyakkyawan labari nazo dashi ma Mah-Mah, yaushe Daddy zai dawo gida?" "Ah Alhamdulillah, ko nayi sirika ne?" Sosa kansa yayi ya girgiza shi yana dariya "Scholarship na samu akan course din da nake." "Alhamdulillah, alhamdulillah kai amma naji dad'i." "Abin da ya dawo dani ma gida yanzu kenan, kin ga har sun turo komai." Ya bude mail box din sa ya mika mata, karantawa tayi, sannan tace "Wannan labarin yanzu zaka kira Daddy ka sanar masa, naga abin ba zai dau lokaci ba sai ka fara shiri." "Shirin me za'a fara?" Ya karaso ciki yana kallon Sultan, sai ya mika masa wayar yana murmushi, layi bayan layi yabi ya karanta sannan da sauri ya dago yana nuna farin cikin sa "Amma gaskia baka kyauta min ba, da wannan good news din amma muka tawo all the way from asibiti har gida baka fad'a min ba." 'dage kafadar sa yayi yana murmushi yace "Uwa ce gaba da dan'uwa ko baka gane ba?" Ya kanne masa ido daya yana kallon Mah-Mah "Haka ne." Mah-Mah tace tana dariya "Kaci bashi wallahi, akwai abinda nake son fad'a ma nima amma na fasa Wallahi, sai komai ya kankama zaka ji." "Kar muyi haka dakai dan Allah, dan fesa min mana." "Zaka bushe ka fado kamar ganye aikuwa, idan lokacin jin naka yayi kaji Malam." "Kai kuwa Sultan kyale shi, dole dai zaka sani din, tashi kaje kaci abinci sai ka kira baban naku, kasan yafi so ku yayan sa ku fad'a masa abu kai tsaye ba wai yaji ta waje na ba." "Toh Mah-Mah, bari na kirashin dan bana jin yunwa yanzu sai ko anjima." "Allah ya kaimu anjiman." "Amin." Suka fad'a a tare. Tashi tayi ta shiga ciki ta barsu suna cigaba da hirar tasu, ***Da safe Abba ya kirasu ya sanar dasu yadda tafiyar ta zama, sai dai kafin lokacin Umma ta chanja shawara zata zauna din kawai bayan tayi tunanin yadda zata barta ita kadai har tsawon wasu watanni, Amrah har da guntun hawayen ta, amma jin cewa idan su Afrah suka dawo suma zasu je sai ta hakura ta saki ranta, abinda zatayi yanzun burin ta ne, ta jima tana so da kauna, haka Allah ya tsara shiyasa ma hakan ta faru.    Sun shirya tsaf ranar da zasu tafi, tayi kokarin kwantar da hankalin ta sukayi musu rakiya har airport ita da Adnan da Umma, sai da suka ga tashin su sannan suka koma gida.    Ranta a jagule ta wuce dakinsu ta kwanta kawai tana jin gidan yayi mata fadi sosai, sun saba komai tare suke yi da Afrah, suyi fad'a su shirya basu taba nisa da juna ba tun bayan sun dawo kasar. Ranar bata ci abincin dare ba,haka tayi kwanciyar ta a daki har bacci ya dauke ta wanda bata tashi ba sai da gari yayi haske, duk lokacin da bata sallah takan makara sosai ta rasa dalili ko dan bata kwanciya da niyyar tashi da wurin ne shiyasa, haka ta fito lokacin su Umma sun gama breakfast suna zaune suna kallo a tv ita da Ya Adnan, joining dinsu tayi bayan ta dauko breakfast din ta, ta dawo tsakiyar falon, tana ci suna kallo had'e da hira har zuwa lokacin da ta tashi ta koma daki ta dauki wayar ta,ta kwanta tana game cikin kwanciyar hankali. Suna ta sa rai da kiran su Abba, sai dare kiran ya shigo, tana daki umma ta shigo da wayar a kunnenta suna magana, sai ta mika mata ta zauna gefen gadon. Da Abba suka fara gaisawa sannan Hajiya ta karba, sai Afrah, sun dan yi hira da Afran tana bata labarin tafiyar tasu, sai da umma ta karbe wayar ta sannan suka hakura, rufo mata kofar tayi suna cigaba da magana da Abban.WhatsApp ta hau suka cigaba da maganar su, sai gashi hira ta mika kamar ma suna tare da juna. Sati d'aya tsakani ta fara zuwa makarantar, da farko ta kasa gane yadda tsarin yake, sai a hankali ta fuskanci komai sai gashi ta ware tana ganewa sosai, ba kadan take jin dadin makarantar ta da yadda ake gudanar da komai cikin tsari da kwarewa. Da safe kafin ta tafi sai ta gwada abun da aka koya musu, sannan ta dauka ta kai wa malamar tasu ta gani, ba karamin mamaki malamar take ba ganin yadda take da kwazon dauke komai da anyi musun, bata san cewa duk abinda ya zama kana da passion akai ba, zaka bada dukkan nutsuwar ka wajen koyan sa. *** Da tsananin murna Safwan ya shigo gidan jin labarin saukar su, a tunanin sa harda gimbiyar zuciyar sa tun da Adnan be fad'a masa yadda tafiyar ta sauya ba, turus yayi ganin Afrah ita kadai sai Umaima dake gefe tana faman danne danne a waya fuskar ta a chunkushe ta juya tana kallon gefe kamar bata yi maraba da zuwan na Afrah ba. Da murna ta tare shi "Ya Safwan." "Wa nake gani kamar yar afiriri, Innalillahi gaskia an kwana biyu, Masha Allah." Rufe fuskar ta tayi da tafin hannun ta, tasa dariya tunowa da sunan da yake fad'a mata da tana karama. "Ya Safwan baka chanja ba, kana nan da tsokanar ka wallahi." "Kema nasan baki chanja ba ai, surutun yana nan." Sai ya dan rage murya kadan yace "Ina dunkum din, na ganki ke kadai." Fashewa tayi da dariya sosai shima yana tayata "Wai dama baka manta da sunan nan ba, tab ai kuwa nasan Amrah yanzu da zata ji sunan nan sai ta kusan sumewa saboda haushi." "Ina kika barta?" Ya tambaya cike da zak'uwa "Ai nida Abba kadai muka zo, ita da umma sai mun koma." "Shit!" Yace yana jin duk farin cikin sa na barin sa, Umaima da ta maido hankalin ta wajen hirar su ta dan tab'e baki ta cigaba da bin wakar ta, dan ita har ga Allah yarinyar batayi mata ba, dadcin d'ad'awar ta daji daga in da tazo, sai taji wani abu me kama da tsanar ta ya shiga zuciyar ta nan take, ya bata mata happy mood din ta baki daya. Ba'a son ransa ba, ya zauna suka cigaba da hirar ganin Mah-Mah bata nan kuma Umaimah bata da niyyar kulata, sai dai kaso tamanin na hankalin sa yana chan wajen tunanin yadda ya sa rai da ganin ta a yau, sai dai kash. Kansa a kasa bakin sa dauke da sallama ya shigo falon, da sauri Umaima ta tashi kamar dama zaman jiran sa take, gaishe shi tayi ya amsa kirjin sa na wani irin bugu, da Afrah ya fara yin tozali sai da zuciyar sa tayi wani irin tsalle, tunanin sa zai ganta zaune kusa da Afran, be shirya ganin ta a lokacin ba, sai dai a take yaji babu abinda yake son ganin kamar ita. Da kyar ya ja kafar sa a kasalance ya karasa shigowa falon ba tare da ya lura da Umaimah dake faman washe mishi 32teeth dinta ba, iyakar shak'a ta shak'a musamman yadda taga gaba daya daga Sultan din har Safwan din sun bada attention dinsu a kan bakuwar, a zuciye ta wuce ciki tana sake jin wata irin tsanar ta. Da Mah-Mah ta dawo ta tarar da Afrah murna sosai tayi, ta rasa inda zata sata saboda farin ciki, har zuwa dare ana abu daya, hira sosai tsakanin su har basu san lokaci ya ja haka ba babu wanda ya nemi abinci, ba kuma su bi takan Umaima dake chan daki tana kunci ba. A tare suka shigo da Abban da Daddy, suka zauna a falon, Sultan da Safwan kowa na kokarin gaida Abba a kunyace kowa da tasa manufar a zuciyar sa, ya amsa musu a sake had'e da yan tambayoyi, tare suka ci abinci da iyayen nasu sannan suka tafi suka basu waje don su samu damar tattaunawa. Zancen tafiyar Sultan Daddy yayi Abba inda ya roki alfarmar zai xauna a tare dasu har ya kammala, Abba be ji dadin alfarmar da yace ba, dan shima ai Adnan anan din ya zauna bayan sun tafi kuma har ya karasa karatun sa Abban be taba biyan ko sisi ba. Sai wajen tara Abban ya tafi bayan Daddy yasa su Sultan sun maida shi gidan Hajiya sannan suka dawo gida. Daga nan gidan Afrah ta fara yawon zagaya dangi, Safwan ne ya dauki nauyin yawon nata duk inda zata bata da matsala. Zaman ta da Umaimah be dame ta ba, bata ma san me ne ne game da ita a zuciyar ta ba, a tunanin ta ma haka yanayin ta yake shiyasa ta debe ta, ta watsar ta cigaba da harkokin ta kamar tana gaban Ummanta. Dama chan ita bata da duhun kai balle yanxu da suka waye suka goge da rayuwa, hutu da gayu ta kowanne bangare, ga uwa uba kyawun da Allah ya basu. ***Kafin ranar tafiyar Sultan Abba ya riga ya kira Umman ya sanar mata, tayi farin ciki da zuwan nata dan ita har ga Allah tana son yaron da nutsuwar sa, ta dade tana yiwa daya daga cikin yaran nata sha'awar sa, idan Allah ya kaddara yace yana son daya daga cikin su zata tsaya masa da dukkan support dinta, bayan haka ma Mah-Mah ta chanchanci aso zuri'arta, mace ce me kirki da sanin ya kamata. Shirye shiryen zuwan sa kuwa kamar wanda zasuyi bakon da babu irin sa, Amrah tasa ta gyara masa daki guda anan cikin gidan, ta kuwa yi masa gyara sosai irin yadda take kara koya, yadda ta gyara gadon ma kad'ai ma abin kallo ne, sannan ta kawo wasu flowers masu kyau ta jera su akan gadon ta rubuta welcome home dasu ya bada wani irin tsari me kayatar wa Bayan ta gama umma tasa tayi wanka, ta shirya cikin shigar simple doguwar riga na atamfa da Adnan ya tawo musu dashi da zaizo, ta daura dankwalin kamar yadda take bin wani tutorial na daurin dankwali a YouTube, sai ta yafa dan madaidacin mayafi ta bi ta feshe kowanne lungu da sako na jikinta da turaren fantasy me sanyin kamshi. Tana fitowa Umma ta kalle ta, a zuciyar ta tana adduar Allah yasa abinda take hasashe ya kasance, Allah ya tabbatar musu da alkhairi. Ita kanta Amrah sai ta dinga jinta so empty, tana jin wani irin nervousness kamar zata shiga dakin jarabawa, bata san me yasa take jin wani irin attachment da Bakon da zaizo yau, bakon da Umma taki fada mata ko waye ne, sai dai ta tabbata da irin matsayin da yake dashi wajen Umman ta. Kai tsaye airport suka wuce kamar yadda ta san inda zasu tun kafin su bar gida, sanda suka je jirgin be sauka ba, waje suka samu suka zauna chan sai Adnan yayi excusing kansa ya bar ta ita kad'ai, tana nan zaune chan ita ma ta mik'e ta fara takawa a hankali tana kallon tsari da kyawun wajen, daga chan gefe ta tsaya ta harde hannayen ta biyu tana kallon yadda mutane ke kaiwa da komawa tun daga kan mazauna kasar da ma masu shigowa, chan gefe wani ruwa ne yake tashi da d'an karfi yana jik'a wasu fulawowi masu ban sha'awa, a hankali ta soma takawa har ta isa wajen ta tsaya tana kallon wajen sosai cike da birgewa, ta shagala sosai wajen kallon ruwan har bata san lokacin da suka iso wajen ba, maganar Ya Adnan ta riska a saman kanta sai ta juyo da sauri, idon ta ne ya sauka a cikin nasa da ya bude su sosai yana duban ta, kallo irin na tsanaki me tattare da ma'anoni da yawan gaske, bata shirya ganin shi ba, ba kuma ta dauka haka yake ba sai da idanun ta suka dauke ta zuwa duniyar nasa idanun dake cigaba da yawo akanta, kasa dauke idon yayi ya manta da komai da kowa balle ya tuna da Adnan dake magana a gefe. Kanta tayi saurin saukewa kasa jin yadda zuciyar ta ke wani irin bugu da karfin gaske, kokari take ta tattaro maganar da zata yi tun kafin ma taji muryar sa, tana cikin kokawa da kwakwalwar ta muryar sa ta sark'i numfashin ta, ta sauka har zuwa tafin kafarta "My Amrahhhh...'" ya kira sunan a hankali yana lumshe idon sa, bata iya dagowa ba sai dai ba karamin jin yadda ya kira sunan nata tayi har chan cikin kwanyar ta. "Ya kuka tsaya anan ne Sultan, mu wuce gida." Adnan yace yana juyawa yayi gaba ba tare da ya fuskanci komai ba, ashe tun kafin su karaso wajen ya tsaya daga baya suna magana da wani bature. Baya ya ja sannan ya nuna mata hanya tare da furta "Ladies first." Wucewa tayi gaba da dan sauri ya bi bayan ta yana jin komai na warware masa, tamkar duk wata matsalar sa ta kau, tamkar don shi kadai akayi ranar, ya ganta fiye da yadda yayi tunanin ganin nata, tayi masa fiye da tunanin me tunani. "Hayatii." Ya furta a chan kasan makoshin sa bayan ya maida kansa ya kwantar a jikin kujerar cab din da suka dauka zuwa gida. Suna isa gida tayi sauri ta wuce ciki tun kafin su taddo ta dan ba zata iya da idanun nan nasa da suka birkita mata tunani ba, tana bukatar lokaci da zata zanta da kwakwalwarta, ta samu damar tuna komai. Wani irin yanayi da bata taba fuskantar kanta a ciki ba take jin ta a yanzu, bata san wanne irin abu ne haka me karfin gaske yake sake ingizata ba. Tana kwance tana juyi a gado ita kad'ai ta tashi kamar an tsikare ta, a hankali ta bud'e kofar dakin ta fito zuwa dan corridor da zai sadaka da main falo in da take juyo maganganun su tare d Umma. Muryar sa kamar kida haka take keta kofifin cikin kunnenta kai tsaye zuwa birnin zuciyar ta, labewa tayi tana hangen sa, magana yake da Umma cike da girmamawa da nutsuwa, sai da maida kallon ta wajen umma, farin cikin da yake kan fuskar ta kadai ya isa ya tabbatar mata da yadda Sultan yake da muhimmanci a wajen Umman. Da baya da baya ta dinga tafiya har ta fad'a saman gadon ta,ta fad'a kai tana dora hannun ta a saitin zuciyar ta. Sai dai, a daidai wannan ranar , a daidai wannan lokacin, Abba na zaune tare da Daddy, suna tattaunawa akan maganar Safwan bayan ya sami Daddy a daren ranar ya sanar dashi bukatar zuciyar sa, shi kuma Daddy be yi kasa a guiwa ba wajen samun Abba har gida ya isar da sakon Safwan, a take Abba ya karbi maganar, yayi na'am da ita don dama tun zuwan sa Hajiya tayi masa maganar, jira dama yayi su neme shi da maganar shi kuma ya amsa, sanin cewa yaran nasa babu wanda suke kulawa yasa be wani ja maganar ba ya amince a tunanin sa babu wata matsala da zata taso. Ba karamin farin ciki Daddy yayi ba, dama su burin su tilon dansu ya samu abinda yake so, tun bayan tasowar sa suke yi masa sha'awar yaran Abban musamman Amrah data kasance tafi Afrah nutsuwa da hankali duk da itama Afran bata da wata matsala. Kash!!!💔💔💔💔 Ina ganin tun daga nan ya kamata mu fara raba team  ______________________ KUNA BUƘATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA'ARKU A PAGES ƊIN BOOKS ƊIN ZAFAFA BIYAR 2021?. To kuzo ga dama ta samu💃🏻💃🏻.         Ina ma'abota son a tallata musu hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?. Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon haziƙan marubanku ƴan biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da saƙo ta dalilin shafukan littatafai. Ga duk mai buƙatar a saka masa tallan kayan sana'arsa a shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntuɓar waɗan nan Numbers 0903 234 5899 or 09033181070 ta WhatsApp, idan har agama buks ɗin kana buƙata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauƙi. Idan kuma wasu adadin pages kake buƙata koda ɗaya ne duk zamu saka maka akan farashi mai sauƙin gaske🤓. Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike neman sauƙi😻😻😄🤗. ______________________ _ZAFAFA BIYAR 2021_*🔥 _*SUKAR BAYA*_💚 _BILLYN ABDUL_ ( _kwai cikin qaya_ ) ( _raina kama_) ( _wutsiyar raqumi_ ) *_SIRADIN RAYUWA_*💛 _SAFIYYA HUGUMA_ ( _alqawarin Allah_ ) ( _daurin boye_ ) ( _Dangantakar zuci_ ) 💙 _*KIBIYAR AJALI..*_💜 _MISS XOXO_ (Sulke baya tsare ta sai ta wuce) ( _Igiyar zato_) ( _Kaimin halacci_ ) ( _Naufal_ ) *_ABIN DAKE CIKIN ZICIYA_*🧡 _HAFSAT RANO_ ( _ruhi daya_ ) ( _Sauyin qaddara_ ) ( _Daurin goro_ ) *_MIN QALB_*❤️ _MAMUHGEE_ ( _buri daya_ ) ( _tarayya_ ) ( _eznah_ ) Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 0903 234 5899 IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 09033181070 Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥_*Abinda Ke Cikin Zuciya_* Hafsat Rano 7 *Wannan littafin na kudi ne, idan kina so ki karanta ki tuntubi numbobin dake k'asan littafin* *** Tsaye yayi yana kallon yadda aka tsara da kawata dakin, kamshin da yake fita me dadi da saka nishad'i, lumshe idon sa yayi ya bude su a hankali yana tariyo komai, ganin da yayi mata yanzu bayan wasu shekaru ya sake tada tsohuwar ajiyar zuciyar sa. Yanzu ne daidai lokacin da yake jira, lokacin da zai bude mata birnin zuciyar sa, ya bata dama ta shiga ciki tayi yadda take so ba tare da wani abu ya gifta ta ciki ba. Zuwan sa kasar da yadda Allah ya chanja tsarin tafiyar ta ya tabbata wani plan ne da Allah ya tsara hakan ta faru, sai dai yana ji a ransa kamar Adduar sa da ya jima yanayi ce Allah ya karba, adaidai lokacin da ya dace dasu dukka. Mission dinsa biyu ne yanzu, kuma sune cikar burin sa, sune rayuwar sa, ba zai iya rayuwa babu daya ba, zai yi duk yadda zaiyi yaga komai ya tafi masa daidai. Juyi kawai take itama tana jin yadda Innocent zuciyar ta ke budewa a hankali tana jin tasirin idanun sa na occupying kowanne lungu da sakon na ciki. Sosai suka samu tasiri me yawa akanta, sai taji tana son sake ganinsu, ta sake sasu a cikin nata tayi analysing komai akansu ko ta gano dalilin da yasa suka daddaure ta haka. Mirginawa tayi ta dauko wayar ta, ta hau whatsapp ta nemo kan sunan Afrah, sannan ta ajiye mata message ganin bata online "Kece kike karatun novels, idan mutum ya ji wani irin feeling daban da wanda be taba ji ba, akan wani me kenan?" Duk wajen mintuna sai ta duba ta gani ko tayi mata reply, har ta gaji ta kashe wayar gaba daya ta kwanta. Bata san sanda bacci ya dauke ta ba, sai farkawa tayi ta ganta tayi d'aid'ai iska na kad'a ta. A guje ta fad'a toilet ganin har ta fara makara ta dauro alwala tazo tayi sallah a dakin sannan ta fita zuwa kitchen. Baccin da yayi ranar zai iya cewa ya dade beyi irinsa ba, jin sa yake so complete ba karamar yadda yake jin sa a dah ba. Ko da ya tashi ta karfin sa ya tashi, ya hau shiryawa a tsanake saboda zuwa ya fara abinda ya kawo shi. Yana juyo maganar Umma a falo da alama waya take, fitowa tayi ganin sa ta katse kiran tana sake fad'ad'a fara'ar fuskar ta, ya zame k'asa ya gaishe ta cike da girmamawa, ta amsa a sake.     Amrah na Kitchen jin maganar sa sai ta tsaya chak tana murmushi ita kad'ai, tana ji ya zauna bayan Umma tace ya zauna yayi breakfast kafin ya fita, sai kuma ta dan bude muryar ta kirata, wani irin zillo taji zuciyar ta tayi, taji kamar ba zata iya fitowa ba, sai data fara wanke hannun ta, ta goge sannan ta jero komai akan dan madaidaicin tray ta dauko ta nufi falon. Yana zaune yana facing hanyar kitchen din, idonsa tsaye k'em akan hanyar, tana fitowa ta soma ganin sa, shigar kananan kaya ce a jikin sa sun karbe shi sosai sai kamshin turaren sa daya cika wajen. Kamar zata hard'e haka ta daure ta karaso ta ajiye masa a gaban sa, ta dago zata mike yayi mata murmushin da ya saka ta kusan narkewa a wajen. "Go...ood..morn..ing." Ta hadu su da k'yar tana yin gaba tayi hanyar kitchen din "Goodmorning." Ya amsa yana sakin siririn murmushi da ya dan fitar da sauti kadan, tana kokarin shiga kitchen din ta tsinkayi muryar sa a tsakiyar kanta "Thanks My Amrah." Juyowa tayi ta kalle shi da d'an wasu dakiku,sai ta juya ta shige ciki da sauri. A jikin kofar kitchen din ta jingina tana maida numfashi, "Me yake faruwa dani?" Ta tambayi kanta tana dafe gefen zuciyar ta. Ta jima a tsaye har sai da umma ta shigo tana kare mata kallo, saurin barin wajen tayi ta hau wanke kayan da ta bata tana son daidaita kanta. Bayan ya gama tana ji yayi ma umma sallama ya tafi, ajiyar zuciya ta sauke ta fito ta wuce dakinsu. Tana zuwa ta taga wayar ta na haske, ta sauri ta kai hannu zata dauka ta katse, Afrah ce, sai kawai ta bud'e whatsapp din ta dan tasan kila magana tayi mata taji shiru shiyasa ta kira, dama kuma ta matso tayi mata reply dan ta kasa gane kanta baki daya. _"Yeeeeee, someone has fallen so deep._  Afrah tace da wani dan Emoji na tsokana _"Is this Love?"_ tayi reply tana hasaaso abinda Afran zata ce, katse mata tunani tayi da dogon bayanin exactly yadda takeji, a karshe ta hada da tsokana. Kashe datar tayi ta ajiye wayar ta kwanta a hankali tana jin zuciyar ta bata yi mata adalci ba, daga ganin sarkin fawa sai miya tayi zaki? Idan kuma har abinda Afrah ta fad'a akan one side love gaskiya ne fa, Idan ta kasance shi bashi da feelings akanta fa? Ya zatayi kenan? Yadda take jin sa daga jiya zuwa yau wani babban al'amari ne me wuyar fassarawa.     Wunin ranar sukuku tayi shi, ta rasa abinda yake mata dad'i, duk sanda taji za'a bude kofa sai tayi tunanin ko shine, zuciyar ta na fisgarta zuwa son sake ganin sa. Har dare be dawo ba, da ta gaji da zaman sai ta koma daki tayi kwanciyar ta. *Wannan littafin na kudi ne, idan kina so ki karanta ki tuntubi numbobin dake k'asan littafin* "Idan nace ban taba ganin Safwan a irin farin cikin yau ba, banyi karya ba,kaga yadda yayi bayan na bashi labarin yadda kukayi da Prof." "Ai nasan dole ne yayi farin ciki, ni kaina bazan iya misalta yadda na ke ji ba, Allah dai ya tabbatar da alkhairi ya nuna mana." "Amin." Mah-Mah ta amsa tana cike da farin ciki. A daki Umaimah na zaune gaban Mirror tana makeup, Afrah ta gama hada kayanta waje d'aya, dan a yau take son komawa gidan Hajiya, dan ta fara mata korafin ta ki zama anan ta gudu gidan yan gayu, dole ta sanarwa Mah-Mah zata tafi, duk da bata so ba amma da tayi mata bayani sai tace shikenan. Da kallo umaiman ta bita ganin taja jakarta zata fita "Tafiya Zakiyi?" Ta tambaye ta, tana sauke brush din hannun ta "Yeah, kina murna ne?" "Mesa zanyi murna?" "Naga kamar baki so zuwa na ba, yadda kike ta had'e min rai." Sai ta share maganar tace "Kina da number Ya Sultan ne? Ina so na kirashi nayi masa ya hanya." Girgiza mata kai tayi tace "Dama nasan bukatar ki ce ta kawo ki,bani da ita idan kin matsu ki tambayi Mah-Mah." Tayi gaba abinta tana tsaki, ta tsani rainin hankali,bata kulata dan iskanci sai da ta ta, ta kawota. Idan itace ma Sultan ba zata iya da irin Umaimah ba, ba aji sam gashi bata da kunya ko kadan.   ***Pheeewww....Long chapter😂😂😂😂 Read more goma⛹️⛹️⛹️⛹️⛹️⛹️⛹️ zamu hadu idan Allah ya kaimu gobe Afwan!!! KUNA BUƘATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA'ARKU A PAGES ƊIN BOOKS ƊIN ZAFAFA BIYAR 2021?. To kuzo ga dama ta samu💃🏻💃🏻.         Ina ma'abota son a tallata musu hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?. Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon haziƙan marubanku ƴan biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da saƙo ta dalilin shafukan littatafai. Ga duk mai buƙatar a saka masa tallan kayan sana'arsa a shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntuɓar waɗan nan Numbers 0903 234 5899 or 09033181070 ta WhatsApp, idan har agama buks ɗin kana buƙata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauƙi. Idan kuma wasu adadin pages kake buƙata koda ɗaya ne duk zamu saka maka akan farashi mai sauƙin gaske🤓. Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike neman sauƙi😻😻😄🤗. ______________________ _ZAFAFA BIYAR 2021_*🔥 _*SUKAR BAYA*_💚 _BILLYN ABDUL_ ( _kwai cikin qaya_ ) ( _raina kama_) ( _wutsiyar raqumi_ ) *_SIRADIN RAYUWA_*💛 _SAFIYYA HUGUMA_ ( _alqawarin Allah_ ) ( _daurin boye_ ) ( _Dangantakar zuci_ ) 💙 _*KIBIYAR AJALI..*_💜 _MISS XOXO_ (Sulke baya tsare ta sai ta wuce) ( _Igiyar zato_) ( _Kaimin halacci_ ) ( _Naufal_ ) *_ABIN DAKE CIKIN ZICIYA_*🧡 _HAFSAT RANO_ ( _ruhi daya_ ) ( _Sauyin qaddara_ ) ( _Daurin goro_ ) *_MIN QALB_*❤️ _MAMUHGEE_ ( _buri daya_ ) ( _tarayya_ ) ( _eznah_ ) Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 0903 234 5899 IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 09033181070 Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥*Wannan littafin na kudi ne, idan kina so ki karanta ki tuntubi numbobin dake kasan LITTAFIN*              Page 8 ©Hafsat Rano       ***Duk yadda Safwan yaso ya samu Sultan ya waya ya kasa samu, ya matsu ya bashi labari ya tayashi farin ciki, cigaba yayi da gwadawa har ya gaji ya ajiye, ya shirya ya nufi gidan Hajiya. A chan ya zauna har dare suna ta hira da Afrah, da zai tafi ya karbi number Amrah a wajen ta yayi saving. Allah Allah yayi ya isa gida ya kirata, yaji muryar ta me sanyi, yana isa ya fito ya zauna a saman motar sa, sannan ya fara kiran Sultan,cikin sa'a kuwa bugu daya ya d'aga, "Ina ka shiga ne, wayar ka taki connecting tun rana nake trying." "Ta samu ne? Ina chan na shiga school aiki ya rik'e ni, mutanen nan da gaske suke so suke sai sun karar da ruwan kai na tas, boko suke hadda na masifa wallahi." "Kace kuna karbar gashi kenan." "Daidai yadda ta kamata, abun ba sauki." "Allah ya taimaka ya bada sa'a." "Amin ya Allah, addu'ar kenan." "Ya kaga kasar? Ji nake kamar nayi tsuntsuwa na biyo ka wallahi." "Da komai yayi min yadda nake so, kana shan maganin ka ko? Kasan dai na ja maka kunne akan magani sosai bfr na tafi ko?" "Ina Sha Oga Sir." Ya fad'a yana sara masa kamar yana ganin sa "Good boy, mene labari? Yasu Mah-Mah da kowa da kowa?" "Akwai latest news, amma wait su waye kowa da kowa? Baka tambayi kanwar ka Umaimah ba." Ya karashe da sigar tsokana "Tasan tana lafiya ai, kasan munyi magana dazu da ita, nasan kai ka bata wannan number ko?* "Matsa min tayi wallahi, da gaske fa take yarinyar nan." "Toh Allah ya bata sa'a." "Haka zaka ce?" "Me zance? Bayan ni kai zaka aurar dani, idan ita ka zaba min ai shikenan Baba." Dariya sosai Safwan yayi sannan yace "No ba irin ta nake so ba, ina nan ina searching zan samo wadda ta dace da dan uwa na, wadda zata iya da I don't care attitude din ka." "Best of luck." Yace yana kallon Adnan da ya shigo dakin da tab a hannun sa yana dannawa, gadon ya dane ya kwanta yana cigaba da abinda yake yana sauraron wayar da suke. "Kamar kace akwai labari, kuma kayi shiru da maganar, sai ka gama wana ni zaka fad'a min ko?" "At first da na kira da intention din fad'a maka nazo, sai dai bansan me yasa ba, nake jin ba yanzu ba, may be later..." "May be never..." Ya amsa masa yana dariya "No zan fad'a maka dole ne, amma ina so ka sake bani time, ka kuma tayani da addu'a." "Karka damu, take your time ina kyautata zaton zata yi accepting dinka, babu macen da zata ce dan uwana be mata ba, ba'a haifeta ba kaf duniyar nan." "Wait... Yaushe nace maka maganar mace ne?" "Karka manta nasan ka fiye da yadda kasan kanka, bayan haka ka ma tuna kana magana ne da heart doctor." "Umm, sannu heart doc." "Yawwa, shawara daya kawai kabi komai a sannu, karka zurfafa da yawa kazo ka fad'a ciki, kasan condition dinka dai." "Yes boss." Dariya sukayi gaba daya sannan sukayi sallama. Ajiyar zuciya Sultan ya sauke bayan sun gama wayar yana addu'ar sa komai ya tafi wa Safwan,be san yadda zata kasance ba idan har abinda ya ke tsoro ya faru.      Suna zaune suna shan coffee me zafi shi da Adnan ta fito, kanta a kasa ta wuce kitchen, da kallo ya bita har ta shige shi, sannan ya maida kansa kan abinda yake yi yana ayyana yadda take koman ta a nutse ba baragada, idan kaji hirar ta me tsayi toh waya take da Hajiya, Afrah ko magana suke da Umma, ya lura ko Adnan din ba wata hira suke ba sannan yana lura da ita, bata da wajen zama da ya wuce kitchen, tun anan ya gane yadda take da son girke girke, hakan yayi masa dadi dan yana d'aya daga cikin abinda yake so wajen mace kenan, iya sarrafa kalolin abinci. Tashi yayi ya dauki mugs din da suka gama,ya nufi Kitchen din, tana tsaye a gaban sink tana wanke abu a cikin dan basket da be lura da mene ba, ya shiga da sallama. Chak ta tsaya da abinda take tana jan numfashi kadan kadan, takun tafiyar sa taji abayan ta, tayi kamar ta zura da gudu sai ta dake tayi kokarin tattaro nutsuwar ta kafin ya gane yadda yake samun tasiri akan ta a duk sanda taji shi kusa da ita, a dan gefen ta kan wani babban table ya ajiye mugs din, turaren sa na hugo boss ya bige hancin ta, ta bude su a hankali ta shak'e shi sosai yabi ya shiga kowanne sashe na hancin ta. "Sannu da aiki." Yace yana komawa jikin fridge sannan yayi folding hannun sa yana karewa kitchen din kallo. "Uhmm." Kawai tace sannan ta juya ta saka kitchen gloves a hannun ta, ta sauke tukunyar da ke saman wuta. Shiru babu wanda yayi magana a cikin su, shi be fita ba, ya kuma ki barin ta, ta sake tayi aikinta, kadan kadan take jan tsaki tana jin haushin tsayawar da yayi dan har ga Allah ya shiga rayuwar ta. Dan satar kallon sa tayi taga ashe ma shi danna wayar sa yake hankalin sa kwance, yana kuma murmushi, murmushin da zata iya cewa babu abinda tafi so bayan idanun sa kamar su. "Yadai?" Yace yana dariya, fuska tayi ta cigaba da abinda take pretending as if ma ba ta san yana wajen ba. Matsowa yayi kusa da ita sosai yace a hankali yace "Please a zuba min abinda aka yi mana,ko so ake kamshi ya kashe mutum da ransa ne a gidan nan." "Toh." Tace ta sauri tana yin wajen plates din har ga Allah ya takura wa rayuwar ta, ta dauko ta zuba masa da yawa ta mika masa, taki bari su hada ido. "Yanzu fa muka gama shan wanchan abun ya ma sunan sa? Um? Um tuna min dan Allah." "Coffee." "Yawwa shi, toh aina zan zuba wannan kuma, sai dai idan tare zamu ci" Da sauri ta kalle shi, sai ya kanne mata ido daya, tayi saurin kasa da kanta tana murmushi "Idan zamu ci tare kinga ya ishe mu." "Bari a rage toh." Ta dauko wani plate din da zuba masa wani daban daidai daidai, tana gama wa ta mika masa sai ya makale kafadar sa yaki karba "Menene?" Tace tana kallon abincin sannan ta kalle shi "Yayi min kadan wannan, daga cewa ki rage sai ki kwashe fiye da rabi." "Toh ni bansan ya kake so ba, gashi ya zuba da kanka toh." Tace tana ajiye masa akan wajen zata juya, da sauri ya sha gabanta, ya marairace fuska, "Dan Allah karki tafi,ki karasa aikin ki, zan koma gefe na tsaya,nidai kawai ki yi ta min magana karki yi shiru kinji, zan ci wannan din yayi min.* "Toh ai na gama, shiryawa zan na tafi school." "Zan je nima." Yace da sauri "Amrah..." Umma dake nufo kitchen din ta kira sunan ta, da sauri tayi gaba, shi kuma ya daga murfin freezer din pretending kamar wani abu zai dauka, kafin Umman ta shigo Amrah ta fita sun hadu a hanya, magana tayi mata ta koma falon itama kuma Amrah ta wuce dakin su.   Dauke da abincin ya fito da bottle din ruwa me sanyi ya zauna, ya fara ci Adnan ya dauko spoon suka ci tare, kunnen sa kamar zai cire saboda yadda abincin yayi dadi sosai, yana ci yana lumshe ido be san sanda ya fara yiwa umma santi ba, tayi ta mishi dariya Adnan na tayata, sai da suka cinye abincin tas sannan suka tashi kowa yayi nasa waje. ***Wayar ta tayi haske, ta dauka tana duba sakon da ya shigo, karo na shida kenan da irin wannan sakon na shigowa wayar ta, babu suna sai number waya, daga Nigeria ne ta sani, amma bata san waye ba, ta kuma kasa tunanin kowa dan babu wanda ta sani da zai mata hakan, sake maimaita karantawa tayi,sannan ta ajiye ta shiga wata sabgar. ***Zufa ce ta rufe shi, numfashin sa na kaiwa da komowa a tsakanin kirjin sa, yau ne karo na wajen biyar da yake irin wannan mafarkin, me cike da firgitarwa. Duk sanda ya farka bayan hakan yakan samu kansa da shiga tsananin firgice me yawan gaske, wanda har yake hanashi aiwatar da komai. Yana ji aka d'an taba kofar dakin nasa, ya mike da kyar ya nufi kofar ya bude, tana tsaye ta harde hannunta a kirjin ta, idanun ta sun fad'a ciki, kallo daya yayi mata yasan tayi kuka, kukan da ba ka iya boyeshi a cikin idanun ka, gefe ya matsa mata ta gifta shi ta shiga ciki tana dan kallon yanayin dakin, a gaban gadon ta tsaya, ta yaye bargon da yake hargitse akai ta ninkeshi ta maida shi wajen ajiyar sa, sannan ta hau gyara dakin. Toilet ya wuce ta ya shiga, yayi alwala ya fito, a shinfid'e ya tarar da abun sallah, gefe jallabiya da yar karamar counter, wai gawa yayi ya kalle ta na d'an sakanni sannan ya tada sallar.    Bayan ta gama gyara ko'ina ta yi hanyar fita daga dakin, ya dakatar da ita. "Ina bukatar hutu, kwakwalwata a chunkushe take da tunani kala kala, bazan samu fitowa ba yau." Kallon sa tayi sai tasa kai ta fice ba tare da tace komai ba. Da jikin gadon ya jingina, ya rufe idon sa yana tariyo abubuwan da suka faru, yaushe Maryam zata daina ganin laifin sa, yaushe ne zata gane abinda ya aikata shine kawai mafita, mafita a gare su baki daya.   Zuciyar sa ce ta dauke shi zuwa lokaci chan baya, a sanda komai yake tafiyar musu daidai basu da wata matsala a duniya, sai kuma ta sake daukar shi zuwa wata ranar. Ranar da ba zasu iya mantawa da ita ba, ranar da ta zame musu ta musamman a cikin rayuwar su, ana tsuga ruwan sama ne, me karfin gaske, gari yayi duhu sosai, ko ina yayi shiru kamar babu sauran me numfashi a doron kasa. A daidai lokacin ne...     Kalmashe kafarsa yayi yana murza goshin sa da yan-yatsun sa, yana jin kamar a lokacin komai yake faruwa, kaddara na da suna daya, sai dai tana da fuskoki masu yawan gaske, wanda baki ba zai iya lissafa su ba. Breakfast din sa ya kalla, dake shirye a saman dan madaidacin teburin dake cikin dakin nasa, ya dauke kansa yana komawa saman kan tafkeken gadon da ta gama gyarawa yanzu ya mike kafafuwansa,sannan ya jingina da fuskar gadon yana cigaba da bitar rayuwa da yadda take zuwar ma mutum da fuskoki mabanbanta. Kira ne ya shigo wayar sa, sai a lokacin ya tuna har ita wayar ya kamata ya kashe dan da gaske yau hutawa yake so yayi, ya jawo ta da nufin kashe kiran sai dai ganin me kiran yasa shi fasawa, shine mutum na karshe da zai k'i amsa wayar sa ko a wanne hali yake. Ya jima yana magana dashi, sannan ya kashe gami da danne power off ya ajiye ta anan saman bedside drawer.      Be fito ba sai chan yamma, lokacin yaji karfin jikin sa, duk da haka yana bukatar ganin likita, domin yadda yake jin jikin sa da k'yar idan ba jinin sa ne ya hau ba, yana tsoron ciwon da zai kwantar dashi a yanayin da yake ciki yanzu, ga girma ya fara kamashi ga abubuwa da yawa da yake fatan su daidaita. Yana ji lokaci ya kusa da zai fuskanci kowa da komai, ya bayyana wa duniya kansa da ya jima yana boyewa.     Sai dai abu daya ne yake dakatar dashi da cikar burin sa, ta ina zai fara neman ta? Bayan be san inda ta nufa ba tun wannan ranar. Bashi da madogara sai Allah, dan haka addua ce kad'ai zata iya dawo masa da farin cikin da ya rasa,ko yace da suka rasa baki daya.    Yau ma kamar sauran ranakun, hawayen bakin ciki ne ke fita daga idanun ta, tana kaichon irin rayuwa da son zuciya tana jin dama za'a dawo da baya da ta goge duk wani shafi na cikin rayuwar ta ta baya. Rufe idon ta tayi tana hasko komai kamar a lokacin ne yake faruwa ***Durkushe take a gabanta, kanta a duke a k'asa, kirjinta cike yake da tsoron abinda zata ce mata. A tunanin ta laifi tayi, shiyasa ma da kiran ya riske ta, ta dora hannu aka tayi ta zunduma ihu har sai da Yabi ta tsawatar mata, fadawan dake tsaron bangaren gimbiya maryama ne, su aka aiko kiran ta, suka kuma tusa k'eyar ta har katafaren bangaren na gimbiyar sai da basu bi duk wata hanya da zata hadasu da mutane ba har suka isa, suka kuma isar da sakon zuwan ta, izini akayi mata ta shiga, shine ta samu gefe ta rabe tana rarraba idanuwa, duk da sanyin A.C dake busa ta, ta ciki jike take da zufa tana lissafin hukuncin da za'a yanke mata idan har wani laifin tayi. Wajen mintuna nawa gimbiya bata ce komai ba, tana ta kare mata kallo sama da k'asa, kallon sauran bayin dake durkushe a gefe tayi sannan tace su basu guri, duk suka fita har amintacciyar baiwar ta, kafin ta kalli yarinyar gaban nata, wadda ba zata wuce shekara goma sha bakwai ba tace; "Zaki yi min rakiya zuwa wani waje, wanda nake so ya zama sirri tsakani na dake, ya zama babu wanda zai sani, Idan har kika kasa rike min sirri zan dauki mummunan mataki akanki da dukkan ahalinki." "In Sha Allah ranki ya dade zaki same ni me bin umarnin ki." "Shikenan. Ke kad'ai nake son gani, haka ma bana so ki fad'a wa kowa abinda mukayi magana akai." "Tashi kije, ki zama cikin shiri zan aiko miki da kayan da nake so ki saka,bayan magriba zamu fita." Tashi tayi, tayi godiya ta fita, zuciyarta na ta sakawa da warwarewa a dalilin kiran da gimbiya ta yi mata, ta kuma dauko maganar rakiyar ta dawo dashi gaban tunanin ta, duk cikar fadar babu wadda gimbiyar ta nema sai ita, me yasa? Me yasa haka? Sukuku ta shiga bangaren nasu, ta samu Yabi a zaune ta yi Tagumi, ganin ta yasa ya tashi da sauri ta riko ta "Me kika aikata yanzu?" "Babu abinda nayi fa Yabi, wai anjima da magriba zan koma wajen gimbiyar akwai aikin da zata sani." "Ita gimbiyar? Bata da wanda zai mata aikin sai ke? Ki fad'a min gaskiya idan akwai wani abu." "Babu komai fa Allah." Ta wuce ciki, shiru Yabi tayi tana auna abin a ma'aunin hankali, me zai sa gimbiya ta nemi jikar ta ta duk mutanen dake zagaye da masarautar, hankalin ta be kwanta ba sam, tabbas akwai babban dalili.      Da magriba kuwa sai ga Aiken gimbiya nannade a cikin wata leda, daki ta shiga ta shiga ta saka ta fito, tayi wa Yabi sallama tabi bayan baiwar da aka turo.      Chan wani waje a bayan masarautar in da motocin mai martaba ne cike a wajen babu wanda ake bawa Izinin shiga sai wanda ya zama amintaccen masarautar, nan taga sunyi da baiwar, daga d'an nesa baiwar ta tsaya sannan tace "Gimbiya na ciki tana jiranki." Bin kofar wajen tayi da kallo sannan ta sa kai ta shiga, wani bafade dake tsaye yayi saurin bude mata wata mota yace ta shiga, tsoro ne fal zuciyar ta amma haka ta daure ta shiga, ya maida kofar ya rufe ya cigaba da tsayawa a wajen.     Yabi na zaune ta tafka tagumi jakadiya ta shigo, dan tashi tayi tana gaida ta, kasancewar tun farkon zaman su a masarautar bata taba ganin jakadiyar haka ba, sai gashi ta tako har cikin gidan su, har dakin ta inda ta bata bayanin sakon gimbiya, ta kuma fito ta barta yayin da tayi mutuwar zaune.     Kuka ta saka sosai tana jin kirjin ta yana zafi, Aminatu ita kad'ai ce take gani zuciyar ta, tayi sanyi. Me yasa zasu zabi tauye mata rayuwa? Saboda su masu mulki ne? Sbaoda su sune mutane su kuma ba komai ba?wannan wacce iri yar rayuwa ce muke ciki? Me kudi shine kawai mutum talaka ba bakin komai bane. Bata da yadda zatayi, ba zata iya hana su abinda sukayi niyya ba, sai dai zata kai karar su wajen Allah, shine kadai abinda tasan zata iya kuma tasan zai bi mata hakkin ta Jin tashin motoci tayi daga chan nesa, kafin daga bisani taji wadda take ciki ta tashi itama, tafiya sukayi me dan nisa a cikin masarautar kafin su fita daga ciki su hau titi sosai. Tsayawar da motar da take ciki tayi shi ya dawo da ita daga tunanin da ta tafi, ta kalli kofar dake budewa a hankali har ta gama budewa kafin yayi mata Izinin fitowa.     Fitowa tayi ta tsaya, tana kallon wajen da yafi yi mata kama da tashar jirgin sama, wurga idanuwan ta, tayi tayi awajen tana son gane in da take, bafaden dake tsaye kusa da ita ta dan matsa daf dashi sannan tace "Dan Allah Ina ne nan?" "Filin jirgi." Ya amsa a takaice Kanta ne ya daure ta sake yinkurin tanbayar sa, amma sai ya dakatar da ita ta hanyar yin gaba yace ta biyo shi. Bin sa ta shiga yi har suka dangana da wata kofa, daga nan kuma sai gasu a harabar tashi da saukar jiragen, jikinta ne ya fara rawa, kanta ya fara juyawa taji tana neman zubewa amma sai wata baiwa da bata san da ita a tafiyar tasu ba, ta tareta, ta kuma riketa har zuwa sanda suka haura saman matattakalar da zata kaisu cikin jirgin, sannan kuma ta cigaba da rik'e ta har zuwa sanda jirgin ya daidai ta a sararin samaniya, ta kuma taimaka mata sanda suka isa inda zasun. Suna fitowa mota na jiransu, ta dauke su zuwa wani babban waje da sai data nutsu sosai ta gane asibiti ne. Jikin ta ya kara yin sanyi sosai, sanda suka fara haurawa zuwa wani shashe dake chan gefen cikin asibitin tsoro ya kara kamata, ita dai tun farkon tasowar su zuwa yanzu da suke nufar wata babbar kofa bata ga gimbiya ko wani alamu da zai nuna tare suke, toh me hakan ke nufi? Suna isa kofar baiwar ta dakata sannan ta nuna mata hanya "Gimbiya na ciki na jiran ki." Kasa motsawa tayi, ta tsaya idonta na kawo ruwa, tace wa baiwar "Dan Allah inane nan din da muka zo." "Asibiti ne mana, baki ga alama ba?" "Na gani, amma garin nake son sani." "Kinsan Ikko? Birnin Legas? To nan ne, kiyi maza kar ta gaji da jira tare suke da maimartaba kuma." Jan kafafuwan ta tayi da kyar ta tura kofar ta shiga, bakin ta dauke da addu'a, bata yarda da maganar baiwar nan ba da tace har da maimartaba sai da ganin ta ya sauka akansu, shida gimbiya zaune a gaban likitan suna magana k'asa kasa. Yau ne rana ta farko da ta taba ganin sa haka a zaune babu Taron mutane babu wani me tsaran sa, sai taji dakin ya karayi mata girma, durkushewa tayi a wajen ta chusa kanta a cikin kafafunta "Wannan ce yarinyar ranka ya dade? Kana ganin zata iya dauka kamar tayi karama." Likitan ya fad'a cikin harshen turanci, amsa masa sukayi sannan yayi rubuce rubuce a jikin takarda sannan yace ta taso su shiga ciki. KUNA BUƘATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA'ARKU A PAGES ƊIN BOOKS ƊIN ZAFAFA BIYAR 2021?. To kuzo ga dama ta samu💃🏻💃🏻.         Ina ma'abota son a tallata musu hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?. Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon haziƙan marubanku ƴan biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da saƙo ta dalilin shafukan littatafai. Ga duk mai buƙatar a saka masa tallan kayan sana'arsa a shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntuɓar waɗan nan Numbers 0903 234 5899 or 09033181070 ta WhatsApp, idan har agama buks ɗin kana buƙata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauƙi. Idan kuma wasu adadin pages kake buƙata koda ɗaya ne duk zamu saka maka akan farashi mai sauƙin gaske🤓. Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike neman sauƙi😻😻😄🤗. ______________________ _ZAFAFA BIYAR 2021_*🔥 _*SUKAR BAYA*_💚 _BILLYN ABDUL_ ( _kwai cikin qaya_ ) ( _raina kama_) ( _wutsiyar raqumi_ ) *_SIRADIN RAYUWA_*💛 _SAFIYYA HUGUMA_ ( _alqawarin Allah_ ) ( _daurin boye_ ) ( _Dangantakar zuci_ ) 💙 _*KIBIYAR AJALI..*_💜 _MISS XOXO_ (Sulke baya tsare ta sai ta wuce) ( _Igiyar zato_) ( _Kaimin halacci_ ) ( _Naufal_ ) *_ABIN DAKE CIKIN ZICIYA_*🧡 _HAFSAT RANO_ ( _ruhi daya_ ) ( _Sauyin qaddara_ ) ( _Daurin goro_ ) *_MIN QALB_*❤️ _MAMUHGEE_ ( _buri daya_ ) ( _tarayya_ ) ( _eznah_ ) Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 0903 234 5899 IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 09033181070 Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥   Ignore the typos *Wannan littafin na kudi ne, idan kina so ki karanta ki tuntubi numbobin dake kasan LITTAFIN* Page 9 ©Hafsat Rano ***Da jan kafa ta isa inda likitan ya shiga, ta tsaya daga gefe kanta na sarawa,wata nurse dake gefe ta matso ta kama hannun ta suka shiga ciki, dakin daukar jini ne, haka tana ji tana gani aka dauki jinin ta, aka shiga gudanar da gwaje gwaje akan jinin. Sannan suka wuce wani daki inda za'a mata gwajin STD da sauran tests da zasu tabbatar da lafiyar ta. Fitowa likitan yayi ya dubi maimartaba yace "Ranka ya dade yarinyar nan ta kai 20years kuwa?" "Ta kai." Inji gimbiya maryama "Ok, but she looks very young,sannan kamar bata taba haihuwa ba, an fison wadda ta taba haihuwa shine ka'idar." Kallon juna sukayi, ta marairace fuska tana kallon maimartaba, "Babu damuwa Dr, you can carry on with your work." "Owk." Yace ya juya ya shige ciki Sai kuma ya dawo da baya yayi wata magana sannan ya koma ciki... (Mu ajiye wannan zaren, zamu bukace shi nan gaba wajen hade labarin) ***Bata san tsawon lokacin da ta shafe a asibitin ba, kuma tun bayan zuwan su bata sake saka shugabannin nata a idonta ba, baiwa daya ce hade da wani bafade suke kula da ita, duk da bata san me ya faru da ita ba, bata san me akayi mata ba,tana jin wani irin yanayi a tattare da ita, wanda ba zata iya fassara shi ba. Watarana tayi bacci me tsawo, sai ta farka data yabi a gefen ta, tana matsar kwalla, ganin ta farka tayi saurin tasowa wajen ta, tana jera mata sannu...   ***Gyara zama tayi tana sake jin zafin abinda suka aikatawa marainiyar Allah, tana kuma cigaba da tuno fuskar yan kananan jariran cikin shigar fararen kayan sanyin data zaba musu, ta kuma sanya musu a ranar da suka iso duniya, soyayyar da take musu daban ce, ta bi jini da jijiya ta zagaye ko ina. Yan biyu ne dukka maza, wanda ta kwallafa rai akan su tun ranar da aka sanar musu da abinda yake cikin Aminatu, ta kuma tanadi kalolin gatan da zata yi musu, sai dai tun ba akai ko ina ba, ta rasa wannan babban burin nata, tun daga ranar har yau bata sake samun farin ciki me suna farin ciki ba a rayuwarta, tun ranar da yaran suka iso duniya komai ya lalace musu, komai ya chanja musu ciki harda rasa abu mafi soyuwa a wajen maigidan ta, Mulkin Masarautar Saji. A wannan ranar, a wannan yinin komai ya baci, komai ya zama ba a muhallin sa ba, basu da iko ko hurumin bin ko da gefen masarautar ne, balle akai ga shiga ciki. Ta sani, kuma kowa ma dake da kusanci dasu sun san cewa alhaki ne ke bibiyar su, kuma suna da burin ganin ta kafin su har duniya, ko ba dan yaran ba, ko dan su bata hakuri su kuma samu sassaucin nauyin da ke dauke a wuyan su wanda son zuciya ya kaisu da aikata abinda suka aikata din, amma sai dai ta ina zasu fara neman ta? Bayan tun bayan wannan ranar babu wanda ya kuma jin ko da labarin ta ne.    Muskutawa tayi kadan tana share hawayen da ya zama abokin ta a kullum, duk sanda tayi irin wannan tuna bayan takan rasa sukunin ta, har sai dai ta zubar da hawaye sannan zata ji dad'i.    Da daddare ya shigo, ya zauna a falon sannan ya dauki landline ya kirata, sai data dau lokaci sannan ta fito, ta sameshi a zaune yana kallon network news, bata yi magana ba ta zauna gefen sa, ta maida kanta tana kallon gefe, murmushi yayi me ciwo,ya rasa me yasa ta kasa mantawa da komai bayan shi kanshi ba daidai yake ji ba, yana tunanin ma ya fita cutuwa da abinda ya farun. Girgiza kansa kawai yayi, sannan ya shiga yi mata bayani a hankali yana fatan kuma ta fahimta, ko da bata fahimta din ba,yana fatan ya rage mata wani abu kadan daga cikin abinda take ji a ranta. ***Shigowar da Aysha tayi yasa Ammi tayi saurin boye abinda ke hannun, tayi kokarin daidai ta kanta, dan kallon ta Aysha tayi, tasan halin Ammin tasu ko da ta tambaye ta me yake damun ta, ba zata taba fad'a ba, shisa ma kawai sai ta share tayi abinda ya kawo ta dakin ta fita,tana fita Ammin ta tashi ta maida komai yadda yake, ta gyara fuskar ta,ta fito waje domin kammala aikin waken gobe.    Tana aikin tunanin yana sake dawo mata a cikin kwakwalwar kanta, duk yadda taso ta yakice shi ta kasa, har sai ta ya shafi kuzarin ta, wanda Muhammad na shigowa ya gane bata jin daidai, ya kuma san ba zai rasa nasaba da abinda ya baro dasu daga gida ba, sai dai rashin son ayi maganar yasa basa matsa mata da zancen, da sun ga irin haka basa matsa wa, sai dai suna iyakar kokarin su wajen taimaka mata ta dawo daidai.    ***Karar message ne ya shigo wayar ta, ta ajiye rubutun da take ta dauka ta duba, sakon ne kamar ko da yaushe, sai dai na yau ya dauki hankalin ta sosai, sai kawai ta danna kiran number tana fatan samun kowaye suyi magana.    Safwan na zaune kiran ya shigo, kirjin sa ya buga sosai dan be yi zato ba, kura wa wayar ido yayi kamar me nazari ya kasa dauka har sai da yaji zata katse sannan yayi saurin mika hannun sa, ya daga ya saka a kunnensa. Sallamar ta, ta doki kunnen sa, tabi jini da jijiya ta zagaya ko ina sannan ta dawo saman zuciyar sa. Ya lumshe ido ya bude a hankali sannan yace "Wa'alaikisalam." Tsaya wa tsak tunanin ta yayi, jin muryar sa, idan har abinda taji gaskia ne, kenan Ya Safwan ne, dan tayi waya dashi a wayar Ya Adnan farkon zuwan sa, a zuwan zasu gaisa suna kuma gaisawar ta bashi wayar sa tayi tafiyar ta, kenan shine ke turo mata sakonnin kenan tsawon wannan lokacin? Me hakan ke nufi?" "Amrah, kina jina kuwa?" Yayi karfin halin cewa yana jin dukkan sauran karfin halin sa na barin sa, da gaske ne da ake cewa wasu mazan basu da liver, liver da zasu iya tsaida mace har su tsarata, da bai yarda ba idan suna tare da abokai ana musun, gani yake ai yana da baki dan haka komai lafiya Lou, sai dai yanzu ya karyata kansa, wani abu me kamar tsoro tsoro ma yake ji yana sake kanannade shi, yana jin kamar ace masa kyet ya ruga a dari, gashi dai damar da yake ta jira ce, amma baya jin yana da confidence din da zai iya. "Ina ji ya Safwan, ina wuni ya gida ya aiki?" "Lafiya Lou, ya makaranta, ya kowa da kowa?" "Alhamdulillah." Sai sukayi shiru gaba daya, ita tana tunanin abinda zai ce mata da bata fatan hasashen da take ya zama gaskiya,shi kuma yana tsara yadda zai fara,dama zata taimaka masa ta dauko masa zancen messages din da yake mata da ta bud'e masa hanya, amma sai yaji tayi shiru alamun shi take sauraro, "Umm.. umm, dama toh... Ya karatun?" Ya samu bakin sa da furtawa bayan ba haka suka tsara shi da zuciyar sa ba, ajiyar zuciya ta sauke dan har ga Allah bata shirya abinda zai ce matan ba, ta amsa da lafiya lou sannan suka sake yin shiru, sai kawai ta kashe kiran gaba d'aya sannan ta kashe wayar ta kwanta rigingine tana kallon saman dakin. "Damn it!" Yace yana buga hannun sa a jikin fuskar gadon, dama iya dama ya samu amma yayi wasa da ita, haushi ne ya kamashi, haushin kansa da zuciyar sa, ta k'asa fitar da abinda yake cikin ta. ***Daga chan bayan gidan akwai wasu resting chairs guda biyu da d'an karamin table, mafiya yawancin lokuta Abba ke zama a wajen idan yana gida, anan yake zama yayi bitar littafan sa idan zaman Library ya ishe shi. Tun bayan tafiyar sa Amrah ta maida wajen, wajen zaman ta da yamma nan take zuwa ta zauna kusan kullum.    Yau ma kamar yadda ta saba yi, bayan ta gama taya Umma komai ta dauko wani wani littafi na 200 recipes ta fito ta zauna tana dubawa, ya budo kofar ya tsaya yana dubanta, ta dago suka hada ido ya shiga takowa har ya kawo in da take, sai yayi folding hannayen sa a kirjinsa  yana kallon littafin hannun nata, gaishe shi tayi, ta maida kanta abinda take yi, a zahiri ta bada attention dinta baki daya akan littafin, sai dai a bad'ini ba haka bane, ta kasa kara ko da kalma daya ce akan inda ta tsaya kafin shigowar sa, yana tsaye still a inda yake, tana jin idanun sa akanta, sai dai bata yarda ta dago ma. "Taimaka min da ruwa please." Taji yace yana zama a daya kujerar, sai a lokacin ta lura da katon littafin dake hañnun sa, ya ajiye saman dan table din, tashi tayi ta ajiye nata littafin ya awajen zaman ta, sannan ta shige cikin gidan, da sauri ya dauki littafin ya bude page din tsakiya ya saka mata dan karamin note sannan ya ajiye. Ruwan ta kawo mishi ta ajiye ta dauki littafin ta, ta shige ciki dan ko giyar wake tasha ba zata iya cigaba da zama dashi a waje guda ba, wajen ma haka so close da babu wata tazara me yawa a tsakanin su, da yasan yadda take ji idan taji alamun tahowar sa wajen da take da be dinga kawo kansa so close haka da ita ba, ji take kamar jijiyar dake taimakawa wajen rarraba jini a sansan jikin ta na tsitsinkewa.     A saman gado ta ajiye littafin ta jona wayar ta a charge ta rufo dakin, zaman ya fara isar ta haka nan, ta matsu Afrah ta dawo gidan ya dawo kamar yadda yake, so take ma ta dan fita amma ta k'asa, duk sanda zata fitan idan ba makaranta ba sai taji bàzata iya ba dan bata saba ita kad'ai ba.     Duk'ufa yayi sosai akan littafin dan karatun nasa ya fara daukar zafi sosai, yanayin wajen yayi masa daidai da karatun sa, be tashi barin wajen ba sai da lokacin sallah yayi, ya koma ciki yayi alwala yayi sallah sannan ya dora karatun ba tare da tunanin komai ba, ciki kuwa harda abincin da ya kamata ya sawa cikin sa.   Chan wajen sha biyun dare cikin sa ya fara salati, ya mike da k'yar ya fito, Sai a lokacin ya tuna be saka komai cikin ba yana ta faman boko, a gaban dining din ya tsaya ya duba babu komai, ya rufe ya nufi kitchen din yana saka ran samun ko da fresh milk ce dan da gaske yunwar yake ji, babu in da be duba ba, be samu komai ba, ya dafe kansa da hannu kamar ya fasa ihu, ya juyo bayan ya dauko ruwa ya wuce daki.     Tana kallon sa ya gama dube dube akan dining din, sannan ya shiga kitchen, lokacin ta gama kallon wani movie ta fito kenan zata saka charge din system dinta a main falon saboda dakin babu wajen sata ta hange shi, sai ta makale a jikin labule har ya gama ya tafi. Sai data ga shigar sa sannan ta nufi kitchen din, ta dora noodles tayi sauri ta gama, ta had'a masa tea a cup me murfi ta dora akan tray ta kai kofar dakin ta ajiye, tayi knocking a hankali sau biyu, jin ya taso yasa tayi saurin barin wajen, yana budewa yaga tray a ajiye, ya dudduba be ga kowa ba, ya dauka ya shiga ciki ya zauna yaci sosai yasha tea din, yana ci yana blushing, tasan yunwa yake ji,shine ta dafa masa abinci a lokacin da yafi bukatar sa akan komai, yaji dadi sosai hakan kuma ya kara masa akan yadda yake jin ta a zuciyar sa, bashi da tantama ko haufi, yasan zata kula dashi idan sukayi aure ba zata barshi da yunwa ba. Tunanin hakan kawai ya kara sa mishi jin baya da bukatar sanin ainihin waye shi, Allah yayi mishi gatan da ba kowa yayi wA ba, ya kuma hada shi da mutanen da yake da yakinin ba zasu taba barshi ya wulakanta ba. Sai yaji ya kara tattara maganganun Maman Yara ya tura su chan bayan kansa, maganganun da tayi mishi a ranar da yaje gidan isar da wani sakon Daddy, be daukesu da muhimmanci ba tun a lokacin, har yanzu kuma baya jin suna da Wani Amfani a gareshi. Afwan dan Allah, wayata ce ta dan samu matsala shisa kuka ji ni shiru. Manage pls,ignore typos banyi editing ba. KUNA BUƘATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA'ARKU A PAGES ƊIN BOOKS ƊIN ZAFAFA BIYAR 2021?. To kuzo ga dama ta samu💃🏻💃🏻.         Ina ma'abota son a tallata musu hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?. Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon haziƙan marubanku ƴan biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da saƙo ta dalilin shafukan littatafai. Ga duk mai buƙatar a saka masa tallan kayan sana'arsa a shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntuɓar waɗan nan Numbers 0903 234 5899 or 09033181070 ta WhatsApp, idan har agama buks ɗin kana buƙata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauƙi. Idan kuma wasu adadin pages kake buƙata koda ɗaya ne duk zamu saka maka akan farashi mai sauƙin gaske🤓. Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike neman sauƙi😻😻😄🤗. ______________________ _ZAFAFA BIYAR 2021_*🔥 _*SUKAR BAYA*_💚 _BILLYN ABDUL_ ( _kwai cikin qaya_ ) ( _raina kama_) ( _wutsiyar raqumi_ ) *_SIRADIN RAYUWA_*💛 _SAFIYYA HUGUMA_ ( _alqawarin Allah_ ) ( _daurin boye_ ) ( _Dangantakar zuci_ ) 💙 _*KIBIYAR AJALI..*_💜 _MISS XOXO_ (Sulke baya tsare ta sai ta wuce) ( _Igiyar zato_) ( _Kaimin halacci_ ) ( _Naufal_ ) *_ABIN DAKE CIKIN ZICIYA_*🧡 _HAFSAT RANO_ ( _ruhi daya_ ) ( _Sauyin qaddara_ ) ( _Daurin goro_ ) *_MIN QALB_*❤️ _MAMUHGEE_ ( _buri daya_ ) ( _tarayya_ ) ( _eznah_ ) Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 0903 234 5899 IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 09033181070 Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥*Wannan littafin na kudi ne idan kina so ki karanta ki tuntubi numbobin nan* *0903 234 5899* Or *09033181070* © Hafsat Rano Page 10 * Daga littafin tayi da nufin chanja masa waje takardar ta fado, yar karama ce me dan fadi, jikin ta da zanen heart kalar red, daga sama an rubuta _Amrah_, zama tayi ta bud'e a hankali, tabi rubutun da kallo yadda ya tsaro kamar ba da pen aka rubuta shi ba. _The first time i saw you, I can see we are made for each other, your eyes so gentle, your smile so true._ _You are soul, my heart, my eternal peace of mind, my oneness._ _please accept this as a token of my love for you_ _#With love Sultan💓_ Sake maimaita karantawa tayi, zuciyar ta na budewa kadan kàdan har ta gama budewa gaba daya, kalaman sa suka samu matsuguni me yawan gaske a cikin ta, sai ta lumshe idon ta, ta bud'e su tana shakar sanyayyiyar iska da taji lokaci daya ta chanja mata baki daya. Ita kad'ai tayi ta faman murmusawa tana sake kallon takardar da wani shauki da bata taba jin irin sa ba. Wasan buya suka fara ita dashi, taki sam su hada hanya ma balle har ta kaisu ga yin magana, sosai hakan ke wahalar da zuciyar sa, amma kasancewar ba a gidan yake wuni ba sai ya zama ya kasa samun chance din da yake ta nema, yasan zuwa yanzu taga sakon sa, ya kuma tabbatar da samun karbuwar sa, saboda yadda take boye masa, hakan yasa ya samu peace of mind ya cigaba da karatun sa yana fatan haduwar su nan kusa. Umma na lura da ita, tana kuma fatan hasashen da take ya zama gaskiya, ta matsu Abban su ya dawo suyi magana, dama yace mata akwai maganar da zasuyi shima amma yafi so suyi ta gashi gata, ga kuma Amrah, sai ita ma ta ajiye komai ta barshi zuwa sanda zasu dawo din. Watarana Amrah taji shigowar Sultan falon, sai kuma taji hirar su da Adnan da alamun sun kwana biyu basu yi irin zaman ba tunda shima ya Adnan din ya fara masters dinsa Sai ya zama haduwar a zauna irin haka tana musu wuya, suna cikin hirar taji umma na kiran ta, dogon wando ne a jikin ta da katuwar rigar sanyi data xo mata guiwa sannan ta saka hula me girma data sauko ta bayan keyar ta sosai, ta kalli kanta a mudubi ta ga babu inda jikinta ke nuna wa, amma tasan umma sai tayi mata fad'a indai ta fito hakan musamman da Yan samarin suke gidan, dan madaidaicin veil ta ciro ta dora a saman kanta ya sakko har kirjinta ta fito, direct dakin yake kallon saboda haka tana fitowa dashi ta fara cin karo, ido daya ya kashe mata tayi saurin sauke kansa k'asa kirjinta na bugawa, ta wuce su ta shiga wajen Umman, chan ta fito ta wuce su taje kitchen, ta hado musu komai akan tray ta kawo inda suke ta ajiye musu, zata tashi Adnan ya tsaida ta. "Amrah sultan zai yi magana dake." Sai ya tashi, sannan yace "Minti biyar na baka dan I'm very hungry wallahi." "An gama babban yaya." Yace yana dariya. Zama tayi a dan gefe ya kira sunan ta, ta amsa a ciki sosai, "Har yanzu ba'a gama wasan yar buya buyan bane? Na fara shiga situation fa." "Ni ba buya nake ba, kaine baka zama agidan yanzu." "Karatun ne Amrah, akwai wahala da daukar time shiyasa." "Best of luck." Tace tana waasa da fingers din ta "Thanks, dama ina so naji if you ok, shisa ma na nemi alfarma wajen Adnan, tun da naga boye min ake." "Uhmm." Tace tana murmushi. "Shikenan bari muci abinci, sai dai a taimaka min a daina hanani ganin ki ko daga nesa ne pleaseeee." Tashi tayi tana murmushi ganin Adnan ya dawo ta shige ciki. Tun daga lokacin komai ya chanja tsakanin ta da Sultan, ta bud'e masa birnin zuciyar ta sosai ya shiga ya yi wa kansa waje da zai yi wahalar fiddowa. A lokacin kuma suka hau shirye shiryen tarbar su Afrah, Amrah tafi kowa murna dan ita bata labarin soyayyar da suke sha tafi so tazo ta gane wa idon ta, soyayya me tsafta ba irin soyayyar zamanin yanzu ba, basa taba kebewa idan zasuyi magana, sai da ma Adnan ya fara yi wa Umma maganar tayi kuma na'am da hakan sannan suka samu dama, sai ga Amrah ta ajiye kunya ta manta da nauyin baki, hira sosai suke da Sultan,komai zatayi sai ta fad'a masa shima haka, cikin kankanin lokaci suka shaku da juna sosai shakuwar da rabuwar su zatayi wuya. **Abin duniya yayi wa Safwan yawa, har ya fara jin chanji sosai a tattare dashi, wanda yake tunanin zai iya shafar lafiyar sa, sam Amrah ta daina daga kiran sa ko ya kira, text messages din kuwa bashi da TABBACIN tana gani ko bata gani tun da ba reply take masa ba, Mah-Mah ta lura da yanayin sa,ranar ta zaunar dashi tana tanbayar sa me yake damun sa, ganin ta damu sosai yasa ya fad'a mata gaskiya ya kasa samun yadda zai shawo kan Amrah ne, lallaba shi tayi, tace zasuyi magana da Daddyn su, shima idan yaso ya tuntubi Sultan da maganar ko zai bashi wasu shawarwarin. Basu fiya magana yanzu da Sultan din ba sbaoda dukkan su sun zama busy, shi da karatu shi kuma aikin da ya fara a Federal High Court ya kara sashi ya zama so busy, gashi yana under wajen kamfanoni uku a matsayin private lawyer dinsu. Bari yayi gari ya waye daidai lokacin da yasan zai same shi a waya sai ya kira. Gari na waye wa ya kira Sultan, he badly need him dan idan be fallasa asirin zuciyar sa ba, zata iya farfashewa a zo a tarar da ita ta zama pieces a k'asa, babu dogon zance kamar yadda suka saba yana dagawa yace "Akwai matsala." "Subhanallah, are you sick?" Ya tambaya yana mikewa daga zaman da yake yana bitar karatun aa "I'm about to be, so soon kuma dan wallahi ina jin zuciya ta na zafi, idan ban fad'a mata ba komai zai iya faruwa,please help me ina cikin damuwa." "Me kake cewa? Me yasa ka kasa fad'a mata? Who is she? Ni ka bani number ta, na kirata na fad'a mata yadda dan uwana ya damu da ita, nasan dole ta karbi soyayyar ka." "Bansan me yasa ba, bani da confidence sam, kuma har nayi ma su Daddy magana har an gama magana da su Abba." Abban da ya ambata yasa gaban sultan ya dan buga, sai kuma ya share da ya tuna ai kowanne Baba ma zai iya zama Abba.. "Amma me yasa ka saka su Daddy a maganar ba tare da kun daidai ta ba, kuma tun yaushe akayi haka amma baka fad'a min ba." "Ka gane, ina jin tsoron kamar zan rasata, shiyasa nayi saurin fada musu, nasan idan suka shiga maganar na same ta na gama, saboda babu yadda za'a yi Abba yaki, toh kuma kaga abinda ya faru, wallahi tama ki bani dama balle na yi mata bayanin kaina." "Baka kyauta ba, kasan mata basason irn haka, shiyasa ma kila taki sauraron ka, tana ganin kamar zaka sa ayi mata dole ne." "Toh ya zanyi yanzu? Wallahi idan ban sameta ba rayuwa ta na cikin matsala." "Safwan!!! Get hold of your self,kasan condition dinka, kasan komai amma kana so ka jefa kanka a cikin matsala muma ka jefa mu, ya kake so su Daddy suyi idan wani abu ya sameka, kana tunanin Mah-Mah kuwa? Kasan irin tashin hankalin da take shiga duk lokacin da wani abu ya faru da kai? Kayi tunani first kafin ka shiga ramin da mu kanmu ba zamu iya ciro ka ba dan Allah." "Sultan! Ya zanyi!? Kasan abinda nake ji kuwa? Kasan soyayya da yadda take da zafi kuwa? Ka sani? Ba yin kaina bane, kuma bansan yadda zanyi na rage ba wallahi." "Ok ok, I understand, dan Allah ka kwantar da hankalin ka, ka nutsu zan yi kokarin ganin komai ya zo da sauki. Yanzu idan mun gama magana ka tura min number ta, zan kira ta, zan yi kokari wajen convincing dinta in sha Allah." "Zaka iya? Ka tabbata zaka mata magana? Zaka iya mata magana face to face amma idan kafi son number zan tura maka, please kayi iya kokarin ka dan Allah, ka fini kusa da ita yanzu idan ma face to face din ne zaka fi saurin convincing dinta." Sultan be gane kan abinda Safwan ke nufi ba, shi da ke wata uwa duniyar amma yake ma maganar face to face, sai ya share kawai dan kar ya kuma sashi dogon tunani yace "Zan iya yin komai for you, I promise you ko bata so ka ba at the beginning zata so ka a karshe, i promise you this." Ajiyar zuciya ya sauke yana jin kamar matsalar sa ta kau, yana jin kamar bashi da sauran matsala ko damuwa, yasan Sultan zai yi komai domin ganin ya bashi dukkan abinda yake so. Ta ina zai fara gode masa? Kaf rayuwar sa a tsaye yake akan sa, koman sa shine, bashi da wani buri sai na ganin shi ya samu abinda yake so ko da shi zai rasa, ta ina zai fara saka masa? Anya yayi daidai daya dora masa alhakin kula da komai nasa ciki harda abinda ya kamata ace shi yayi wa kansa? Toh amma be san yadda zai yi ba, he's too weak akan komai, shi tashi kaddarar kenan, tun da yazo duniya yake struggling da komai ciki harda iskar numfashin da yake shak'a. Sultan is a blessing to him, Allah kadai yasan dalilin da yasa shi turo shi cikin rayuwar sa. Be tura masa number a lokacin ba, ya bari a matsayin zai bi komai a sannu yaga abinda Allah zaiyi. *** Ranar da su Afrah suka dawo murna wajen Umma da Amrah ba'a cewa komai, text tayi wa Sultan yana school ta fad'a masa dawowar tasu, ya kirata sukayi magana sannan ta kashe. A makare yake dawowa ranar, saboda haka sai da ya fara tsayawa wani shopping mall ya siyo musu chocolate da yawa sannan ya nufo gidan, a falo ya tarar dasu dukkan su suna hira da Abba, takalman sa ya cire ya karaso ya zauna a gefen Adnan ya gaida Abba cike da girmamawa yayi masa sannu da zuwa sannan ya gaida Umma, Amrah da Afrah suka gaishe shi, ya d'an tsokani Afrah ya tashi ya shiga ciki, yana zama Adnan ya shigo ya kirashi inji Abba, rigar saman kawai ya cire ya same shi falo, cups ne guda uku a jiye da coffee me zafi, abba ya dau daya ya basu suka dauka shida Adnan sannan suka shiga hirar karatu yana musu tambayoyi, sai wajen sha d'aya sannan yayi musu sai da safe ya wuce dakin sa. Umma na zaune ya shigo, ya zauna a gefen gadon sannan yace "Menene labarin da kika ce zaki bani da zarar na dawo, dan nima tafe nake da labarin da nasan zaki so sosai." "Nima kam nasan zaka so so labarin." "Toh ina jinki." Yace yana gyara zama. "Dama maganar Amrah ce..." "Nima maganar tace din, amma inaga nawa zaifi naki saboda haka ni zan fara." Yace yana dariya "Shikenan, ina sauraron ka." "Nayi wa Mamana miji." Kamar saukar aradu haka Umma taji maganar, zaro ido tayi da sauri tace "Miji kuma Prof? Waye shi?" "Kwantar da hankalin ki, Danki ne ma ai." "D'ana? Wanne kenan?" "Safwan!" Da sauri ta mike ta kuma dora hannun ta akan chest dinta "Safwan ko Sultan?" "Sultan Kuma? A ah Safwan ne dai mukayi magana da Alhaji Sulaiman kuma har ma nayi musu alkawarin basu sanin da nayi babu wanda yaran nan suke kulawa " Jagab umma ta koma ta zauna kamar wadda aka tura, "An samu matsala Prof, Sultan da Amrah suna son junan su, chan gefe kuma Safwan har ya kai maganar wajen iyaye, na tabbata iyayen nasu basu san da maganar Sultan ba, yanzu ya kenan?" "Kina nufin shi Sultan din ne yake son mamana?" "Kwarai kuwa, itama kuma tana sonshi, bansan ya akayi haka ba." "Toh gaskiya ni iyayensu Safwan suka ce min, kuma bama haka ba tun kafin suyi min magana Hajiya tayi min maganar dan yaje ya sameta da zancen, kinga kenan babu kuskure a maganar kenan." "Toh, akwai matsala." "Kinga Ina zuwa." Abba yace yana mikewa, dakin ya wuce yayi musu knocking, Sultan ne ya bude, ganin Abba yasa shi dan ja baya, tsayawa yayi yana kallon sa sai kuma ya fasa magana yace yazo falo ya same shi ya juya zuwa dakin su Amrah, nan ma knocking yayi, Afrah ta bud'e masa, yace Amrah ta same shi a falo ya wuce yana kokarin had'a maganganun waje daya. Rano KUNA BUƘATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA'ARKU A PAGES ƊIN BOOKS ƊIN ZAFAFA BIYAR 2021?. To kuzo ga dama ta samu💃🏻💃🏻.         Ina ma'abota son a tallata musu hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?. Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon haziƙan marubanku ƴan biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da saƙo ta dalilin shafukan littatafai. Ga duk mai buƙatar a saka masa tallan kayan sana'arsa a shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntuɓar waɗan nan Numbers 0903 234 5899 or 09033181070 ta WhatsApp, idan har agama buks ɗin kana buƙata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauƙi. Idan kuma wasu adadin pages kake buƙata koda ɗaya ne duk zamu saka maka akan farashi mai sauƙin gaske🤓. Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike neman sauƙi😻😻😄🤗. ______________________ _ZAFAFA BIYAR 2021_*🔥 _*SUKAR BAYA*_💚 _BILLYN ABDUL_ ( _kwai cikin qaya_ ) ( _raina kama_) ( _wutsiyar raqumi_ ) *_SIRADIN RAYUWA_*💛 _SAFIYYA HUGUMA_ ( _alqawarin Allah_ ) ( _daurin boye_ ) ( _Dangantakar zuci_ ) 💙 _*KIBIYAR AJALI..*_💜 _MISS XOXO_ (Sulke baya tsare ta sai ta wuce) ( _Igiyar zato_) ( _Kaimin halacci_ ) ( _Naufal_ ) *_ABIN DAKE CIKIN ZICIYA_*🧡 _HAFSAT RANO_ ( _ruhi daya_ ) ( _Sauyin qaddara_ ) ( _Daurin goro_ ) *_MIN QALB_*❤️ _MAMUHGEE_ ( _buri daya_ ) ( _tarayya_ ) ( _eznah_ ) Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 0903 234 5899 IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 09033181070 Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥[3/16, 7:39 AM] Maman Maryam: *SULE BAYA TARE TA SAI TA WUCE* *NANA HAFSAAT* *WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE! KI DUBI GIRMAN ALLAH KI SAYA DA KUDIN KI, KADA KI SHARING, TEMAKA KI SIYA NAKI A NAMBOBIN MU DAKE KASA* *All characters/ some places/ Incidents, Portrayed in this novel are fictitious.. * *(Duk mutanen ciki da sunayen wasu guraren da na saka, Da wasu abubuwan da suka faru, Duk tatsuniya ce, Idan yayi shige da rayuwar wani ko wata to akasi aka samu.) Consider it as synchronization👌🏾* *XII* *KANO STATE* **Abin ka da rashin sabo ga kauyanci da yake dawainiya dani, tunda muka fara tafiya ina kalle-kalle har bacci ya dauke ni. Ban farka ba sai da aka shigo garin kano, na gane mun shigo ne ta hanyar kokarin da nayi na karanta symbol da aka rubuta *'Welcome to kano'*. Na gyara zama ina ta kalle-kallen abubuwa na burgewa dake kan titi, ga tituna lafiyayyu babu ramuka, hakika birni lafiya ce. Yadda kwaryar birnin kano ta cika shine zai tabbatar maka da cewa wani abun ake yi mai matukar muhimmanci, saboda din bin mutane ta ko'ina ba masa tsinke. Na kasa yin shiru tun ina lekawa ta glass din window har nace da drive ya zuge min na dinga lekawa kafin na tambaye shi me ake yi yace min. “Mantawa nayi da wannan na’din (turbaning ceremony) da bamu biyo ta wannan hanyar ba, wallahi wani matashin saurayi za'a nada sarki, shi yasa kowa ya fito ya ganewa idanunsa ba sai an bashi labari ba, gashi nan duk an cika mana garin.” Cikin mamaki nace. “Kai..! Sarki fa kace?” “Kwarai kuwa, ke ba kiji bushebushen abin sarauta ba?” “Walle banji ba kadan-kadan dai kamar ake yi, dan Allah ka kai ni na gano na din.” Ya yi saurin cewa. “Kai..! Yo kafin mu kutsa cikin mutanan nan ai aiki ne, ballantana kuma karasawa wajan rumfar nadin. Kiyi hakuri wata rana zaki ganshi idan ya fito koda sallah ne.” Na jijjiga kai alamar na gamsu. Bandamu da ganin saba dama mu kai wucewar mu gidah, Na san dai irin nad’in sarauta ne kamar na kauyen mu, Lokacin da aka nada sabon hakimin Alfundi, Bazan mantaba har can muka tafi a kasa. Ganowa idanun mu sabon hakimi da yazo daga birni, Sannan mai unguwa jamilu ma sanda mahaifin sa ya rasu aka nada shi haka akaita bushe bushe algaitu a karakar mu. Muna tafe akan titi ina karanta signboards din kan hanya, Kai birni da girma take, Na bawa idanu na hakkin su sosai, Kafin mu karasa gida *DR ISMA’EL MUHAMNAD SINGA RESIDENCE* Kai tsaye wata unguwa naga mun nufa mai matukar tsari, gine-gine ne wannan yana cewa d'an uwansa bani guri. Dr Isma'il Muhammad singa resident nan ne inda drivern ya shiga, ya yi horn a kofar wani katafaran gate wanda ya amsa sunan sa, mai gadi ya bude muka shiga. Compound d'in kadai abin kallo ne yadda aka kawata harabar gidan da shuke-shuke na burgewa, ga manya da kananun motoci tamkar kamfanin su aka zo kala kusan shida. Baki na saki ina kallon aljannar duniya, ina mamakin wai dama muna da wani dan uwa mai dukiyar da zai iya yin wannan muhallin, amman aka barmu a kauye muna ta shirme. Muryar driver ne ya katse min tsantsar mamakin da ya addabi kwakwalwa ta inda yace. “Muje cikin gidan.” Ya yi gaba ina bin bayan shi kamar wata jelarsa. A bakin wata rantsatsiyar kofa muka tsaya, naga yasa yatsan sa tare da danna wani abu ya yi kara, ba dadewa muka ga an bude kofar. “Yauwa shiga da bakuwar wajan Mami.” Drivern ya yiwa wadda ta bude kofar maganar wacce yar aiki ce a cikin gidan. Tunda na saka kafata a ciki naji wani sanyi yana bude kayan jiki na ya na shiga cikin tsoka ta, ta matse jiki ina sake kundundinewa dan ban saba jin irin sa ba. Katon parlor tamkar a film din indiyawa, mai dauke da kujeru da suka sake kayata shi, tare da talabijin kamar mutanan ciki zasu fito waje saboda tsabar girmanta. Bene ta hau ni kuma na tsaya ina kallon yadda take hawa da sauri da sauri bama ta tsoron fadowa ita, sai da ta haye sannan ta juyo taganni tsaye ina hangenta tace. “Taho mana muje.” Cikin zaro ido nace. “Ni..!?” “Eh mana da wa nake yiwa maganar.?” Na hadiyi miyau tare da sunkuyar da kai kasa, da alama yar uwar su ce ganin tana da fadin rai. “Ni dai bazan iya ba.” “Ba zaki iya mene ba?” “Hawa inda kike so nazo.” “Oh so kike nazo na goya ki na doroki ne?” Nayi saurin girgiza kai nufin a'a amman har lokacin banji zan iya hawa ba saboda tsananin tsoro. Ta juya a fusace tana masifa tamkar wacce na yi mata mugun laifi, ni kuma tsakani da Allah ji nayi ba zan iya hawa ba, ina ganin tamkar zan gangaro saboda santsin tiles da yake ta sheki. Ina tsaye sai gata sun fito da matar gidan wacce naji suna kira da Mami, ta kalleni tare da cewa. “Dije hawo mana.” Na hadiyi kakkauran miyau saboda shiga tashin hankalin yadda zan iya hawa benan. “Ba zan iya ba wallahi.” Nayi magana a sanyaye. “Okay Jummai jeki riko mata hannunta.” Ta taho tana zuba min harara ta rike min hannun dama na, ya yin da ni kuma na rike karfen binan da hannun hagu muna hawa da kyar. “Ki saki jikin ki Dije babu abin da zaki ji.” Cewar Mami, haka na hau ina rike da Jummai wace ke ta faman yi min dariya kasakasa. Ina hayewa kuwa na zauna ina sauke numfashi da kyar. Mami ta riko hannu na muka karasa parlorn tana ta dariya itama ganin yadda nake ta kallon tsarin parlorn ya matukar firgita ni dan yaci uban na kasa komai da komai. Muna nan zaune sai muka ji muryar mutane suna hawowa benan da gudu ko tsoro basa ji. Yan mata ne su biyu sanye cikin dogayen riguna na larabawa, sunyi kyau a ciki ba karya, suna shigowa suka haye kan cinyar Mami suna furta. “Wassh Mami mun gaji.” Tace dasu. “Gajiyar ce ta hanaku ganin bakuwa ko?” Duk sai suka tashi suna kallo na a tare, na yi saurin sunkuyar da kai na ina wasa da mayafin jikina. “Dije ko?!” Suka yi maganar cikin alamun tambaya suna sake kallon Mami, ta gyada musu kai tana murmushi. “Ayya! Allah sarki Dije, ya hakurin Baffan ki.?” Hawayen da yake shirin zubo min sukai saurin komawa saboda bana son zubar su, Dara'ifa tace min kuka na azaba zai karawa iyayen nawa, addu'a zan dinga yi musu, nace dasu. “Alhamdulillahi na gode.” “Haba Dije meye na godiya, munso zuwa gaisuwa Allah be yi ba. Sai kuma Daddy yace ai dakko ki zai yi gabaki d'aya ki dawo nan gida. Welcome Khadija, munyi farin cikin zuwan ki cikin mu kinji?” Daya daga cikin su tayi maganar cikin nuna kulawa, ta kare maganar da cewa. “Ni suna na Hameedah, nice babba a gidan nan. Sai sister dina wato Shukrah yar auta kenan. Ba tare aka haife mu ba, na bata shekaru biyu amman kinga kan mu ɗaya saboda tsahon kafa gare ta.” Duk aka yi dariya yayin da ni kuma murmushi na saki dan ji nake wata iri da ni. Duk baki na da rashin kunya ta ji nayi ina mugun shakkar mutanan gidan. Gashi dai basu nuna min kyama ba, suna nuna kulawa a gare ni. Amman a lokacin na kasa sakin ciki kamar wacce aka yiwa ture na rashin walwala. Daga nan Mami tace su tafi dani dakin su nayi wanka nazo naci abinci. Shukrah itace ta kama ni muka nufi dakin su, a nan naga aljannar duniya, wato yaran yan gata ne na bugawa a jarida. Komai na cikin dakin guda biyu ne kuma cikin tsari ta yadda tsarin ya kawata dakin matuka. “Toh Dije ga toilet nan ki shiga, akwai ruwan zafi a heater.” Ban san mene heater d'in ba kuma ban tambaye ta ba, haka na ajiye carbin hannuna dama na Baffa ne na dauka domin ya zame min madubi da zan dinga gani ina tunawa da shi a zahirance. Na bude kofar da suka nuna min sai dai na kasa shiga dan banga ya yi min alamar cewar bandaki bane. “Dije shiga mana.” Tamkar wacce zata saki kuka haka nayi magana. “Banga bandakin ba ai.” “Ikon Allah, gaki nan a kusa da kofar kin bude.” “Daki ne fa.” Ai sai kawai naji sun kwashe da dariya abin ya bani haushi na dawo na zauna akan wata kujera da na gani a cikin dakin ina ta turo baki, Hameedah ta juyo tana kallo na tace. “Bandaki ne wallahi Dije, ya za'ai mu kai ki daki muce kiyi wanka a ciki? Zo ki gani na nuna miki.” Ta shiga sannan na bi bayanta, Shukrah na daga bakin gado tana ta dariya ta kasa yin shiru saboda keta. Hameedah ta kunna wani guri ruwa ya zubo cikin wani abu mai dan zurfi da kuma tsaho da alama ruwa ake tana da a cikin sa, naji tana cewa. “Idan ya kusa cika sai ki kashe nan wajan zaki ga ruwa ya dena zuba, sannan sai ki cire kayanki ki shiga cikin ruwan nan kiyi wankan. Ga sabulu nan da soso kiyi amfani dashi.” “Jakar uban can kayyasa! Cikin wannan uban ruwan zan shiga sai kace wata kifi ko kwad'on ruwa?” Dukan su kuma sakin dariyar suka yi, dan ita Shukrah har da hawayen ta tsabar dariya. Na kallesu cike da jin haushi ina turo baki tare yin gunguni ina zagin su a rai na. Meye na dariya bayan maganar gaskiya na fada, banda rainin hankali su kawo guri harda madubi da mayuka shegen jarkokin da malama Mardiyya take matsowa ta shafa shine zasu ci min toilet ne? Hameedah ta fita ta kira Mami suka taho tare. “Kinga kira ni kina ta faman dariya menene wai?” “Mami wallahi Dije dai taki shiga cikin toilet wai daki ne, kuma ta ya zata shiga cikin ruwa kamar wata kifanya ko kwaduwa.” Itama Mami sai ta saki bakin tana rike habarta idanunta a kai na take cewa. “Dije ai wannan ba daki bane, cikin nan inda muke shine daki. Nan da suka nuna miki toilet ne da ake bayan gida ko wanka, ki dena damuwa a hankali zaki fahimci komai, yanzu dai ki taimaka ki shiga kiyi wankan duk yadda kika ga dama.” Na sake komawa ciki na tsaya ina kallon yadda aka kawata shi, ni da naga na malama Mardiyya ina ganin shi aljannar duniya, ashe ga aljanna na ban sani ba. Na duba naga sam babu bokiti a bandakin kuma bana son kuma yin abinda zasu min dariya sai kawai na cire kaya na dauki wani kofi da na gani sai na dinga dibar ruwan da Hameedah ta tara cikin kwami ina tsaye ina wanka na. Abin da ya sake daure min kai a ciki shine, da na waiga sai naga kai na a cikin madubi na hango kumfa a inda hannu na baya kai wa sai nasa ruwa na watsa a gurin, na kuma matsawa wajan madubi ina duddubawa ko akwai inda bai fita ba. Ashe amfanin shi kenan a ciki, ikon Allah gaskiya yan gayu komai nasu daban yake. Ina gamawa na saka skirt dina tare da jansa sama wato har kirjina sannan na fito sai faman muzurai nake kamar bani da gaskiya. “OH my God Dije, maimakon ki dauro towel kawai sai ki sako skirt ɗin da kika cire.” Shukra ta yi maganar tana yatsina fuska da murmushi a fuskarta. “Ai ban ganhi Au ban ganshi ba.” “Kai! Ohh Dijeh, daman har yanzu ana hi da hah a duniyar nan?” “An dena walle.” Ta kuma sakin wata dariyar. “Kin kuma ai Dije, mu bar wannan maganar kawai zo ki shafa mai kisa kaya muci abinci.” Na amsa mata sannan duk suka fita ni kuma na janyo jakar kayana da Jummai da shigo min dasu, na ciro basilin dina na shafa sannan na ciro riga da zani nasa tare da zauniya a kasa na zabga tagumi ina tunanin yadda rayuwa ta zata kasance a cikin wannan gidan. “Dije ki fito muci abinci ma, kin zauna anan kina ta tunani?” Hameedah ta leko tana min maganar. Na tashi nabi bayan ta muka nufi dining da gurin kansa abin kallo ne bare kuma yadda aka kawata kan table d'in da abincika kala-kala. Kamar yadda naga sun zauna haka nima naje na zauna ina ta raba ido. “Dije maimakon ki sako kaya mararsa nauyi shine kika jibgo wata atamfa?” Nayi murmushi kawai ban ce komai ba saboda ko tace naje na saka mararsa nauyin to bani dasu dan haka shiru kawai shine a wajan. Shukarah ta fara zubawa kowa wanda yace yana so, ni kuwa daman bama sanin abubuwan nayi ba bare nima fadi nawa ra'ayin, koda aka tambaye ni ma cewa nayi a bani koma menene zance dan ni babu abinda bazan iya ci ba indai naci din ne. Ai kuwa ta zuba min farfesu na naman kaji da ya sha kayan kamshi na lashi lebe na sama da kasa yo yaushe rabon da a hadu? Ta miko min harda sako min wani cokali mai yatsu na kuwa cire na ajiye shi a gefe na zura hannu ina dakko tsokar kazar nama ina dannawa cikin bakina. Ana ta hira amman ni sam bana sauraron su nama na kawai nake ci ina korawa da lemon kwakwa mai dan karan sanyi da yasha madara har wani gardi-gardi yake yi alkuran. Haka muka gama ci kowa ya yi harkar gabansa, ni kuma tunda na samu tv na zauna ina ta kallo shirye-shiryen su yana dada bani sha'awa da kara karfafin gwiwa wajan son yin aikin jarida. Sallah ce kawai take iya tayar dani daga gaban talabijin d'in nan. Koda nayi sallah isha'i dawowa nayi naci gaba da yin kallon, su kuma mutanan gidan kowa ya tafi yin harkar gabansa, a nan bacci ya dauke ni, koda uncle Isma'eel ya dawo anan ya ganni ina ta bacci kan kafet nayi rashe-rashe tamkar wacce tasha abin maye. Kawu yace a mai dani daki kan gado, Jummai tazo ta dinga tashi na amman ina naki tashi saboda wani irin nauyin bacci da Allah ya sakko min a ranar. Haka Mami da kanta tayi ta tashi na nan ma shiru sai kyale ni suka yi sai da uncle ya gama cin abinci ya tashi da kanshi ya dauke ni ya kai har kan gadon Shukarah yace mu kwanta kafin nima a siyo min nawa. Muna bacci na dinga yarbawa Shukrah kafafuwa na a jikinta, tun tana min kawaici har ya zamana ta dawo tana duka na wanda ban san tana yi bama saboda tsabar bacci dana’urar sanyi abinka da basabin ba, Da asuba take bamu labari, kuma ni dama ba gwanar iya ba da hakuri bace tun ina karama ballanta kuma da na fara girma. “Wai Dije ba zaki ban hakuri ba.?” Na kalleta da mamakin jin abinda take fada, sai kuma na shiga yatsina fuska alamar bafa zan bada ba. “Dije tazo inji Mami a kasa.” Cewar mai yiwa su Hameedah gyaran daki da wasu aiyukan da suka shafe su wato Lamtana. Na tashi da sauri nabi bayanta dan ba hakurin nan zan bayar ba komai zata yi min. A zazzaune na tarar dasu, na duka har kasa duk na gaishe da su sannan cikin murna da murmushi kawun nawa yace dani. “Dije ki saki jikin ki a cikin gidan nan saboda kema ya ta ce kamar yadda suke ya ya na babu banbanci. Duk abin da kike so ki gaya min ko Mami ga ta nan a zaune, uwa ce a gareki ina son ki bi umarninta kamar yadda su Hameedah suke yi mata. Sannan insha Allahu zan samar miki makaranta ki ci kaba tunda kin kammala secondary, me kike son ki karanta ne Dijeh? Dan kar naje na yi miki shisshigi cikin rayuwarki.” Na dinga soshe soshe saboda wata kunya da nauyin sa da suka kama ni a lokacin, ina murza idanuwa nace. “Kawu ni dai ina son naga nayi aikin jarida.” Yace. “A'ah a'ah a'ah! Kice zamu samu mai jiyo kwakwafa a duniya kenan? Masha Allah Dije, toh Allah ya tabbatar da alkairi insha Allahu zan yi kokarin ganin kin cika burinki na rayuwa. Tashi kije Allah ya taimaka.” “Amin kawu na gode.” “Yauwa bana son wannan kawun da kike kirana dashi, ki kirani da sunan da kikaji mutanan gidan nan suna kira na wato daddy..” Nayi dariya ina rufe fuska da tafukan hannayena tare da tashi na tafi, na tsani hawa bene saboda tsoronsa nake ji, duk sanda zan hau ji nake kamar za'a turo ni na gangaro ko nayi baya idan ina hawa. Har na kusa gama hayewa sai kuma na dawo na sakko, na koma parlor sai na tarar basa nan. Fitowa nayi dan har ga Allah bana son zama guri d'aya dan bahaushe yace zama guri d'aya tsautsayi ne. Lamtana na gani zata shiga mota, da sauri naje na tambaye ina zata je, tace cefane zata yo, na hade hannuwa ina rokonka akan dan Allah ta tafi dani na raka ta, aikuwa tace to na shiga muka tafi ina ta sake ganin birni da suke abubuwan su cike da burgewa. Ina biye da ita har ta kammala siyayyar muka dawo mota driver ya dawo damu. A farfajiyar gidan muna shiga da mota na hango matar Kawu Isma'il wato Hajia Abeedah (Mami) da kawarta suna zaune akan fararen kujerun dake zagaye da yar balcony’ din farfajiyar. “‘Mami mun wuni k’alau, Ina yini Hajia?” Na gaishe da Mami da kawarta cikin ladabi, Mami ta amsa da fara’a, Kawar kuma ta debe ni ta watsar, Mik’ewa nayi na shige ciki abuna. Ina shigewa nabi kofar dana rufe da kallo ina harararta tamkar ita taki amsa min gaisuwar. “Abeedah! Wacece wannan? Karki cemin sabuwar mai aiki kika dauka haka? Bakya tsoron abunda zaije ya dawo?” “Hmm! Hajia ba yar aiki bace. D’iyar mai gidan nan ce, Yar kanwar suce data rasu shekarun baya.” “Ayyo to! Ai kuwa tamkar ita tayi kanta. Tab ni fa bana son rikon ya'yan yan uwa n miji, Akwai su da kisisina ga shiga tsakanin ka da mijin ka.” “Anya kuwa? Wannan fa yar kauyen kayau ce fitik. Kawai dai dan tana da zubin manyan mata ne, Ga kyau tamkar ita ta kera kanta. Ai babanta ance bafulata ni ne, Shima bai jima da rasuwa ba.” “Allah sarki! To amman dai kiyi takatsan tsan.” “Insha Allahu!” Dakin mu na shige ina mai yage hijabin jiki na, Ya Shukrah ce kawai a ciki Ya Hameedah bata nan. “Assalamu Alaikum!..” “Wa’alykm Salam Oganniya Dije!” Na murtuke fuska ina gatsine baki, “Ya Hameeda an tsine wannan sunan fa...” “Inji wa? Karya kike bayan ke kika bamu labarin? Aina aka tsine? Jia ko shekarn jia?” Na sheke da dariya ina kallon kai na a mudubin su mai tsaho, Zaka iya ganin kanka gaba ki dayan ka a tsaye. “Sunana Nana Khadija.. Ko Ummi na yadda Baffa na ke gayamin sanda yana raye.” Ya Hameeda tayi murmushi kawai tana gyad’a kai, Bandaki na shige nayo wanka sosai, Kafin na sauya kayan jiki na zuwa doguwar riga marar nauyi, irin tsarabar makkan nan. Jefi jefi mukan taba hira da Ya Hameeda har Kawu ya dawo yace akirawo mu duka, “Kawu Sannu da zuwa..” “Yauwa yar kawu duk da dai nace bana son ana ce min haka! Ba dai matsala ko?” “Babu Kawu!” “Yauwa munyi magana da wani Professor anan jamiar da zaki fara, Yace suna shirye shiryen ranar da zasu sanya ku fara lectures, Saboda haka kafin sannan nidai na yanko miki form a center din da su Hameeda suka koyo British English, Saboda ki sake wayewa da ilimin sa. Ai h..” “Alhaji Wai British eng learning centre dai?” “Ita! Meya faru?” “Uhm! Alhaji gani nai tayi tsada, Haj Luba ma kasa sa yarta tayi.” “Toh sai akai yaya? Ina ruwana dan ta kasa sa yar ta. Ni Khadija ba ‘yata bace? Kafin na samu nawa ‘yayan wana fara samu a duniya? Mahaifiyar ta Jamila daga ni sai ita, Kuma duk duniya babu wanda nakeso sama da ita duk cikin yan uwana, Kuma gudan jininta wadda itama ‘ya ce agare nin zan ki kyautatawa? Shekara nawa ina rokon abani ita na rike hakan bai samu ba sai yanzu. Karki batamin rai hajia. Yauwa Khadija monday zaki fara attending classes dinsu, Na tsawon watanni uku ne kacal. Hameeda ga MasterCard dina da safe ki kaita shopping ki sauya mata da irin shigar mu tanan, Ku bawa tailor dinku dinkunan ta, Ki kaita saloon a gyaro mata kan ta amata manicure..” Ni dai shiru nayi ina sauraron Kawu tamkar a mafarki, Mami tayi kwafa tana kada kafa, “Alhaji wannan yawon ai ba na Hameeda bane sai dai ko driver ya kakkaita. Amma ya za’ai ta katse schedules dinta ta kaita koina?” “Toh Hajia ai gidan ki ne, Ya’ya kuma naki ne ko? Shikenan yayi kyau! Khadija ki shirya da sassafe ni zan kaiki ko’ina. Jeki debi abinci kici ki kwanta.” Kada kai nayi na silale na gudu da’ki, Ina jiyo sanda ya koma parlorn sa, Mami nata tsaki tana mita, Hameeda ma na taya ta. Jiki na gaba d’aya ya saki yayi sanyi, A darare Na fita na shiga kitchen na zuba abinci naci acan, Na koma daki na kwanta. Saboda Banda nauyin Bacci ina jiyo sanda Ya Shukra ta dawo suka hau bata labari . A haka bacci yai awun gaba dani, Bansan sanda suka dena magana ta ba. *WASHE-GARI* Da wuri na tashi na shirya, Na wanke bandaki, saboda na fara gane kanshi da amfanin wasu abubuwan dake cikin sa. Sunata kumbure fuska a haka na bisu na gaggayshe su, Ranar Kawu ko abincin safe bai ciba yace muje, Gurare sosai ya kai ni ya narkomin kayan yan gayu da atamfofi da laces da materials, Abayoyi suma fal da takalma da jakankuna Harda kayan kwalliya dana man shafawa. Ya biya ya bawa tailor ya gwada ni, Daga nan muka je salon aka wankemin kai na, Aka gyaramin kafata da farata na. Wallahi tamkar ba ni ba. Daga nan ya biya dani kasuwar waya, Ya siyamin dalleliyar waya ta zamani. Wallahi tsabar farin ciki Bansan sanda nasa hawayen dadi ba, Na shjga kwararawa Kawu addua. Ranar dai gaba d’aya cinyeta mukai a bukatu na, Sannan ya dire ni a gida ya wuce kasuwa. ______________________ KUNA BUƘATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA'ARKU A PAGES ƊIN BOOKS ƊIN ZAFAFA BIYAR 2021?. To kuzo ga dama ta samu💃🏻💃🏻.         Ina ma'abota son a tallata musu hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?. Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon haziƙan marubanku ƴan biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da saƙo ta dalilin shafukan littatafai. Ga duk mai buƙatar a saka masa tallan kayan sana'arsa a shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntuɓar waɗan nan Numbers 0903 234 5899 or 09033181070 ta WhatsApp, idan har agama buks ɗin kana buƙata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauƙi. Idan kuma wasu adadin pages kake buƙata koda ɗaya ne duk zamu saka maka akan farashi mai sauƙin gaske🤓. Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike neman sauƙi😻😻😄🤗. ______________________ ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥 [3/16, 7:39 AM] Maman Maryam: *Wannan littafin na kudi ne idan kina so ki karanta ki tuntubi numbobin nan* *0903 234 5899* Or *09033181070* © Hafsat Rano Page 11 ***A kusan tare suka isa falon, Abba ya zauna a saman kujera, shi da ita kuma suka zauna a k'asa, ya kalmashe kafar sa cike da girmamawa kansa na k'asa, satar kallon sa Amrah tayi sai kuma ta sauke kanta itama jin Abba ya fara magana "Labari ya same ni, Umman ku ta fad'a min abinda ke faruwa tsakanin ku, dukkanin ku namu ne, kai d'an mu ne kamar yadda Mamana take a wajen mu,dan babu abinda zan cewa Alhaji Sulaiman sai godia, dan haka ko da na samu labarin naji dad'i, amma kuma akwai abinda ya bani mamaki, munyi magana da shi Alhaji Sulaiman, sai dai kuma labarin ya sha banban da wanda naji yanzu, kayi magana da su ne akan maganar?" "A ah Abba, dama ina so ne a d'an kara lokaci." "Toh... Toh shikenan dai, zanyi magana da shi muji." "Toh Abba." Ya amsa. "Shikenan zamuyi magana idan Allah ya kaimu, ke kuma Mamana, jeki ki sami Umman ku." Tashi sukayi a tare, ya wuce dakin su ita kuma tayi ma Umma knocking, tana shiga tayi saurin tashi "Amrah...Kun taba wata magana da Safwan ne?" Shiru tayi, sai da Umman ta sake maimaitawa sannan tace "Yana yawan yimin text messages amma bayan haka bamuyi wata magana ba." "Kin sani? Amma kuma baki taba fad'a min ba? Har sai dai mahaifin ku ya karbi maganar shi? Ya kuma amince." "Ummah!" Ta zaro idon ta "Eh sunyi magana kuma har ya amince musu, sai dai duk wannan ba matsala baçe, tun da ko an daura aure ma ana iya fasawa, matsalar itace, ta yaya kike so mu aura miki k'ani bayan ga wansa kuna soyayya? Kinsan me hakan zai haifar? Sannan ni tun da nake ma ban taba ganin yan uwa masu kaunar junan su kamar yarannan ba, me kike tunanin zai faru?" Kuka ta saka sosai, ta fara girgixa kanta tana matsowa cikin dakin sosai "Kuma wallahi Umma ni Ya Sultan nake so, bana son Ya Safwan." Dafe kai Umma tayi, wannan shi ake kira gaba kura baya siyaki, tayaya zasu warware wannan abun? Wa zasu bawa a ciki su hana? Hakan zai iya kawo matsala sosai da iya hasashen ka ba zaka hasaso me zai faru ba, ta lura da yadda suke son junan su ita da Sultan, ace kuma an bawa kanin sa ita ya zata kasance kenan, rarrashin ta tayi, sannan tace "Kije ki kwanta zamuyi magana da Abban ku, komai zai zo da sauki in Sha Allah." Daki ta wuce da sauri ta fad'a kan gado, ta saka kuka sosai, Afrah ta taso tana tambayar ta menene amma ta k'asa amsa mata, zuciyarta zafi take mata sosai, ga wani irin tsanar Safwan da take ji, dan me yasa zai kai maganar wajen iyayensu bayan shi da ita basu taba wata doguwar magana ba, me yasa xai mata haka? Wayar ta dake ajiye a gefe ta shiga kara, tayi saurin tashi ta dauka, ganin shine yake kira ta daga da sauri, babu sallama babu komai tace "Ina ganin girman ka, tun kafin nayi maka abinda baka taba tunani ba ka koma ka samu su Mah-Mah kace ka janye maganar auren daka je musu, dan bana son ka, bana son ka ko kadan!"  Bata jira komai ba ta kashe kiran ta sake fashewa da kuka. _"Bana son ka, bana son ka ko kadan!!!._" Wata murya a bayan kansa ta shiga amsa kuwwa a cikin kunnensa, runtse idon sa yayi ya dafe kansa da hannayen sa, ya fara ganin dishi dishi, a hankali a hankali dakin ya soma juya masa, sunan Allah ya shiga ambata yana jin yadda numfashin sa ke sarkewa, kafin duhu ya mamaye ganin sa baki daya. Kuka take sosai da k'yar Afrah ta bata baki tayi shiru sannan ta bata labarin abinda ya faru tun farko har xuwa karshe, ta kuma rufe da bata son shi ko kadan ita Sultan take so, mamaki ma ta bawa Afrah dan bata taba tunanin soyayya zata kama Amran haka ba. Haka suka kusan raba dare suna maganganu sai wajen asubah suka kwanta. Da safe Ummah ta kirata bayan Abbah ya fita, suka kara tattauna maganar ta kuma kwantar mata da hankali da cewa kila Abba ne yayi mistaken sunan ya dauka Safwan sukace, Amma yace xai kira Alhaji Sulaiman din sai ya karaji. Jin haka ya saka ta kwantar da hankalin ta, ta kuma cigaba da walwalarta tana ji a ranta tasan babu wanda zai mata auren dole. **** Tun yana hanya yake ta kiran wayar sa amma ba answer,yana zuwa kai tsaye bangaren su ya wuce dan yana da yakinin zai same shi a chan, sai dai yana bude kofar ya ganshi a yashe a k'asa, da sauri ya karasa ya hau jijjigashi, yana kiran sunan sa da karfi, ganin zai bata lokaci yasa ya fita da sauri ya kira wani yaro dake musu aiki ya taimaka masa ya shashi a mota, sannan suka wuce asibiti, suna zuwa aka karbe shi, aka shiga bashi taimakon gaggawa.Mah-Mah bata san me yake faruwa ba, tana chan family house dinsu ana bikin yar cousin dinta, Mubarak ya kirata da wayar Safwan, matsawa tayi daga wajen hayaniya sannan ta d'aga, bata iya karasa jin abinda yake cewa ba ta kashe kiran, tayi saurin kiran Daddy tana jin kwalla na taruwa a idonta, yadda Mubarak ya fad'a mata haka ta fad'a masa sannan tayi sallama da yan bikin bayan ta fad'a musu Safwan ne babu lafiya, addu'a akayi ta masa sannan wata sister dinta ta karbi driving din suka nufi asibitin da wasu daga cikin yanuwan ta, suna tafe tana kuka dan tasan yadda yake jin jiki idan ciwon nasa ya tashi, ya jima rabon sa da ya samu irin attack haka shiyasa ma suka shiga tashin hankalin jin a sume ma aka kaishi asibitin, wajen lokaci daya suka isa ita da Daddy, suka dunguma zuwa dakin da aka bashi hankalin su a tashe, lokacin an samu numfashin sa ya dawo daidai sai dai he's still unconscious, kukan Mah-Mah ne ya karu ganin yadda lokaci daya ya zabge kamar ba shi ba, yana kwance sambal oxygen a makale a saman hancin sa, yanayin yadda girjin sa ke kaiwa da komowa zaka gane ba daidai yake ba, gefen gadonta zauna ta kama hannun sa cike da tausayawa, ko me ya sa shi shiga wannan yanayin ba karamin abu bane. ***Har ya gota su sai ya dawo da baya ganin hausawa ne tun daga yanayin shigar su, daga dan nesa dasu ya tsaya yana kallon babban mutumin dake zaune yana magana da wani, da dukkan alamun yadda yake magana yasan baya jin daidai, wata mace ce babba a gefen sa, tasa doguwar riga ta yane kanta da mayafi sai dai kanta a duke yake a k'asa baka ganin fuskarta, wani abu me kama da mayen karfe yaji yana fizgar sa wajen su, takawa ya shiga yi da d'an sauri ganin suna kokarin barin wajen. "Babah..." Ya samu kansa da kiran mutumin, chak suka tsaya a tare, suka juyo, matar ta kura masa ido tana jin wani abu na zagaya wa a saman kanta, sunan da yayi amfani dashi yasa fuskar dattijon tayi fadi, ta haska da wani irin murmushi, sai ya dan rissina yace "Barka da rana Babah, ya jikin?" Hannun sa dattijon ya kama, ya saka cikin nasa sannan ya girgiza kansa "Ya akayi ka kirani da Babah? Ko kana neman wani ne?" Girgiza kai Sultan yayi alamar a'ah, sannan yace "Zan wuce ne na ganku a zaune, na kuma ji ina son sanin halin da kake ciki, saboda ganin da nayi kuma hausawa ne kamar ni, a kasar da ba tamu ba, nasan watakila akwai abinda zan iya taimaka wa dashi, Babah kuma sunan duk wani babba ne, nasan idan na fadi haka zaku gane saboda ba a kasar da ake amfani da sunan bane." "Allah yayi maka albarka, lallai iyayenka sun yi kokarin baka tarbiyya, jiki alhamdulillah kasan idan abu ya hada da girma." "Haka ne, Allah ya sauwake ya kara lafiya, nima ina karatu ne anan bansani ba ko akwai abinda zan iya yi." Jinjina kai yayi ya sake damke hannun sa, sannan yace "Zakayi alfarma,ka zo gida?" "Zanzo Baba, zanzo in Sha Allah." Yace yana murmushi Sai ya kalli matar cikin tsananin farin ciki yace "Gimbiya Allah ya bamu d'a." Sai yaga fuskar ta tana washewa a karon farko tun dawowar su kasar, ta matso sosai sannan ta kama hannun Sultan tace "Bless you my child." Murmushin da tayi masa ya tsaya sosai a ransa, ya kasa barin tunanin sa, he feel so attached, yana jin kamar akwai wani abu me karfin gaske tsakanin shi da wadannan bayin Allah, sosai yaga farin ciki a fuskar su da ya nuna sun jima rabon su dashi, address suka bashi, tare da rokon shi akan ya cika alkawari kamar yadda yace zai zo. Wunin ranar baki dayan ta a tunanin mutanen yayi, daya tsaya da abinda yake fuskokin su zasu fado masa, sai ya bar hakan a matsayin yadda suka yi masa da kuma kasancewar su yan uwansa hausawa kuma yan k'asa daya, shiyasa yake jin kamar dama chan ya sansu. Da haka ya bar tunanin ya cigaba da abinda yake ganin shine daidai. Yana hanya a cikin mota kiran Daddy ya shigo, ya kalli wayar sai tunanin maganar da Abba yayi masa ta fado masa, ko dai Abba ya kira Daddyn ya fad'a masa abinda yake tsakaninshi da Amrah ne shiyasa ma yake kiran sa yanzu? Sai yaji kunya ta kamashi yayi murmushi yana fatan hakan ya zama gaskiya. Da sallama ya daga wayar, sai dai muryar Daddyn kadai ta sanar dashi akwai matsala. "Sultan kana ji na? Safwan ne ya samu attack... "Subhanallahi... Me ya same shi? Garin yaya?" Yace a rude, yadda yayi maganar kad'ai zaka san ya rude iya kar rudewa "Bamu san me ya faru ba Mubarak ne ya ganshi a sume, kuma Likita yace zuciyar sa ta fara kumbura, komai zai iya faruwa dashi, gashi munyi munyi ya fad'a mana abinda yake damun sa yaki, kayi kokari ka kirashi kaji dan Allah." Ya karashe muryar sa na karaya "In Sha Allah Daddy, zan kirashi yanzu, ku kwantar da hankalin ku babu abinda zai faru." "Shikenan Sulthan, Allah sa muji alkhairi." Da sauri Sultan ya shiga neman Layin Safwan hannun sa har rawa yake, yana dagawa ya rude ya fara masa fad'a ya manta ma lallabashi ya kamata yayi "Me kake so kayi? Kana so ka kashe rayuka hudu hadda aka? Akan mace? Akan mace? Me yasa Safwan? Me yasa? Na dauka mun gama maganar nan tuntuni, kasan halin da kake jefa zuciyar ka duk sanda irin wannan abun ya faru? Kana rage mata karfin tane." "Ya zanyi Sultan? A kunnena take fad'a min bata son na, tace ta tsaneni, bata so na ko kasan, bayan bani na sawa zuciya ta son ta ba, da nasan yadda zanyi dana cire son ta daga zuciya ta da nayi tun ranar,i just can't, I love her so much da ni kaina bansan wanne irin so bane." "Then dolen ta ne ta soka, ko tana so ko bata so sai ta soka Safwan, I can't risk loosing you akan mace, ko wacece yau zan kirata, zan mata magana zan fad'a mata condition dinka." "Nasan zata amince, karka damu zan yi kokari na kaji, just stay calm ka kwantar da hankalin ka please komai yazo karshe, ka bani number ta da sunan ta yanzu zan kirata ba sai anjima ba." "Number ta baida amfani ina ganin gwara kuyi magana face to face zaifi." "Ta yaya zan iya magana da ita face to face Safwan? Ka manta bana nan ne?" "Kuna tare ai..." Dam kirjinsa ya buga ya tsaya da tafiyar da yake yi, yace a d'an tsorace "Muna tare?" "Eh." "Bangane ba Safwan,kana nufin itama tana kasar nan kenan?" "Sultan Amrah ce fa, Amrah ce." "Amrahhhhhh!" Ya ambata da d'an karfi, da sauri ya jingina da fence din wani gida yana jin hajijiya na neman kaishi k'asa, daga nan be sake fuskantar abinda Safwan yake fad'a masa ba, jin sa da ganin sa ne suka dauke da wani lokaci, komai ya zama baki kirin a gaban sa, da k'yar bayan jin sa ya fara dawowa kàdan kadan yace "Shikenan zan kiraka." Yayi saurin kashe wayar, tafiya ya shiga yi ba tare da yasan inda yake sanya kafar sa ba, yasan dai ba hanyar gida ya dauka ba sai dai be san ina ya nufa ba, besan me zaiyi a lokacin dan komai ya tsaya masa ne chak, hatta bugun zuciyar sa ya daina bugawa daidai, gani yayi gidajen na koma masa upside down, ganin da gaske zai iya samun matsala idan ya cigaba da tafiya a haka yasa ya samu wajen wasu kujeru ya zauna sannan ya dafe kansa dake masa wani irin sarawa kamar zai rabe da gangar jikin sa.. KUNA BUƘATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA'ARKU A PAGES ƊIN BOOKS ƊIN ZAFAFA BIYAR 2021?. To kuzo ga dama ta samu💃🏻💃🏻.         Ina ma'abota son a tallata musu hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?. Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon haziƙan marubanku ƴan biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da saƙo ta dalilin shafukan littatafai. Ga duk mai buƙatar a saka masa tallan kayan sana'arsa a shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntuɓar waɗan nan Numbers 0903 234 5899 or 09033181070 ta WhatsApp, idan har agama buks ɗin kana buƙata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauƙi. Idan kuma wasu adadin pages kake buƙata koda ɗaya ne duk zamu saka maka akan farashi mai sauƙin gaske🤓. Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike neman sauƙi😻😻😄🤗. ______________________ _ZAFAFA BIYAR 2021_*🔥 _*SUKAR BAYA*_💚 _BILLYN ABDUL_ ( _kwai cikin qaya_ ) ( _raina kama_) ( _wutsiyar raqumi_ ) *_SIRADIN RAYUWA_*💛 _SAFIYYA HUGUMA_ ( _alqawarin Allah_ ) ( _daurin boye_ ) ( _Dangantakar zuci_ ) 💙 _*KIBIYAR AJALI..*_💜 _MISS XOXO_ (Sulke baya tsare ta sai ta wuce) ( _Igiyar zato_) ( _Kaimin halacci_ ) ( _Naufal_ ) *_ABIN DAKE CIKIN ZICIYA_*🧡 _HAFSAT RANO_ ( _ruhi daya_ ) ( _Sauyin qaddara_ ) ( _Daurin goro_ ) *_MIN QALB_*❤️ _MAMUHGEE_ ( _buri daya_ ) ( _tarayya_ ) ( _eznah_ ) Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 0903 234 5899 IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 09033181070 Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥   Wannan littafin na kudi ne idan kina so ki karanta ki tuntubi numbobin nan* *0903 234 5899* Or *09033181070* © Hafsat Rano Page 12 ***Bazai iya tantance tsawon lokacin daya dauka a wajen ba, ya dai san yana jin dukkan burarin da wayar sa take yi tana yankewa da kanta, bashi da karfin halin da zai iya daga wayar balle ya kai ga amsawa masu faman jera masa kiran, sai ya kashe ta gaba d'aya ya tura ta aljihun gaban dogon wandon sa. Hannayen sa ya hade waje d'aya suka bada sautin k'as, ya sake maida idon sa ya rufe su ruf yana jin dama komai be faru ba, dama za'a iya komawa baya a goge abinda yake a yanzu, idan yace dama komai yana nufin komai din, ciki har da kaddarar data kawo shi kasar, ya kuma shak'u da ita har yake jin rabuwar su zai masa wuya ainun, sai dai ya zamar masa dole, ya rabu da ita ya kuma toshe duk wata kofa da zata bar wani gibi da har Safwan zai sani, baya fatan hakan ta kasance, ba kuma ya fatan wani ma ya sanar dashi. Zai cika masa alkawarin da yayi masa, zai nemar masa soyayyar Amrah ko da hakan na nufin katsewar nasa numfashin.     Tashi yayi bayan shafe dogon lokaci, ya duba address din zuciyar sa na jaddada masa cewa nan ne kad'ai in da zai je a yanzu, yana jin kamar idan ya gansu dukkan damuwar sa zata tafi, be damu da ko karfe nawa bane, burin sa kawai ya isa garesu. Har kofar katon gidan ya tsaya, ya daga kansa yana duban gefe da kewayen gidan, yana kuma nazari, nazarin da ba zai iya cewa shi kad'ai yasan me yake yawo a saman kansa. Hannu yasa ya taba kofar, yana saran wani ya fito ya ganshi, a hankali yaga kofar ta bud'e, sai kuma yaga matashiyar yarinya ta tsaya a gabansa, cikin shigar kayan da yayi kama dana masu aiki, matsawa tayi baya kad'an cikin maganar ta, ta bahaushiya tace "Wa kake nema?" Sama ya kalla, cikin tunanin abinda zai ce mata, be san wajen wa zai ce mata ba, dan baya jin bayan hirar da sukayi ya tambayi sunan dattijon, ganin ta tsire shi da idanu sai ya dan shafa gefen fuskar sa, sannan yace "Wajen Babah nazo, idan yana ciki kice wanda suka hadu dazu ne." Bata ce komai ba, ta bi wata doguwar hanya ta haura saman wata baranda, yana tsaye ya zuba wa hanyar da ta bi ido yana kallon tsari da yanayin gidan. Bata jima ba ta dawo, ta kuma yi masa jagoranci har zuwa hadadden falon nasa, yana gishingid'e, fuskar sa tana kallon kofar yana dakon shigowar sa, kamar wanda k'wai ya fashewa a ciki ya shiga ciki, bakin sa dauke da sallama kansa a duke yana kallon k'asa "Yaka Muhammadu." Yace yana mika masa hannu ganin yana neman zama daga nesa da inda yake, matsawa yayi da jan jiki ya zauna daf dashi, ya gaishe shi a sanyaye "Karka yi mamakin kiran ka da nayi da Muhammad, duk wani namiji Muhammad ne." "Haka sunan yake ai dama Baba." "Ah toh Masha Allah." Sai ya dora "Ban sa rai da zuwan ka ba kwata-kwata ma fa, sai kaga a lokacin da banyi tsammani ba." "Zanzo dama Baba." "Naji dad'i, da kasan yadda zuwan naka zai faranta rai na dana Gimbiya, da tun dazun zaka biyo mu, sai dai yanzu ma naji dadi sosai." A jere suka shigo su uku dauke da tray kowanne su kansa a k'asa suka ajiye a gaban wajen sannan suka d'an rissina kad'an suka juya, har sun kai kofa ya dakatar dasu "Ina take?" Da baya da baya d'aya daga ciki ta dawo, ta rabe a gefe sannan tace "Ta gargad'i kowa akan shiga shashen ta yau, tace tana bukatar hutu." Kallon Sultan yayi, sannan yace "Ka ci wani abu ina zuwa kaji?" Ya mike da d'an k'yar sannan ya soma takawa a nutse, yabi wata kofa daga chan gefen falon. Bayan ya rakashi da ido ya sauke idonsa akan trays din, baya jin a halin da yake ciki zai iya saka ko da ruwa ne a makogoronsa, balle wani abu me suna abinci. Karar AC da karar Tv suka dauke shi suka wurgashi chan wani bigire, farkon rayuwar sa kawo yanzu da ya zama mutum, cikakken mutum me cikar Iko, sai kuma ya dauki tunanin shi ya koma baya, rayuwar sa a orphanage din nan, da kuma abubuwan da suka faru kafin zuwan sa gidan da bashi, be ji shigowar su ba, sai jin maganar ta yayi a gefen sa, ya rasa me yasa, yake jin abinda yake ji a tattare dashi a tare da wadannan bayin Allah, yana jin kamar wanda yayi aiki ya gaji matuka ya iso gida cikin familyn sa,ko wanda yayi doguwar tafiya yana bukatar hutawa a inda ya zama kamar shine final destination dinsa.    Gaishe ta yayi yana ayyana abinda yake faruwa da ita, kallo daya zaka mata ka gane akwai abinda yake damunta me girma, wanda yayi nasarar dakushe kaso sabanin cikin d'ari na walwalarta, guzarin ta dama yadda take abubuwan ta, yaji yana son tambayar ta abinda yake damunta,sai dai bashi da wannan hurumin, be kuma ma san da wacce fuskar zata dauki abun ba.      Sallama yayi musu, ba a son ransu sukayi bankwana ba, yana shiga gidan ya tarar da Adnan a falo, da sauri ya mike "Lafiya kuwa? Kira babu wanda ba'a yi maka ba amma no answer daga karshe ma sai aka kashe ta baki daya." "Mun shiga wani aiki ne tare da manyan docs na asibitin, dole muka kashe wayar saboda yadda aikin yake." Ya amsa masa da haka dan be shirya fadawa kowa abinda ke zuciyar sa ba, ya wuce daki ya barshi tsaye yana rarrabe kalmomin "Something is wrong." Yace yana bin bayan sa, yana shiga yaji karar ruwa a toilet, sai ya zauna yana jiran fitowar sa dan ya tabbata akwai babban abinda ya same shi din. Daya fito be yarda sunyi wata magana ba, yayi kwanciyar sa gami da jan duvet ya rufe har saman kansa, yana bukatar time yayi nazarin abinda ya kamata yayi, kafin Safwan ya nemi jin yadda aka kwana. Be runtsa ba har aka kira sallah, ya tashi dak'yar ya dauro alwala yayi nafila sannan ya fita inda suke jam'i dasu Abba suka yi sallah sai kawai yayi zaman sa awajen yana tilawar karatun Al-Qur'ani me girma, sai yaji zuciyar sa ta washe, nauyin da yake ji ya ragu sosai, karatun Qur'ani babban magani ne dake tafiyar da damuwa da kunci ya kuma sake tabbatar da haka. Tashi yayi ya koma ciki ya shirya a gaggauce dan baya son haduwar sa da Amrah, sai dai yana zuwa kofa ya tarar da ita a jingine jikin ginin tana rike da dan madaidaicin basket mai kyau, fuskar ta babu walwala, yana jin sanda ta sauke ajiyar zuciya, bata ce komai ba ta mika masa basket din ta wuce shi ta shige ciki, gaban kansa ya murza da karfi ya had'e bakin sa waje daya ya taune da karfi yana jin wani iri, ta yaya zai iya bawa zuciyar sa hakuri akan abinda ta jima tana burin mallaka? Ta yaya zai iya wannan babban aikin da shi kansa ganin ta yanzu ya sake jin kamar ba zai iya din ba, kamar bashi da karfin zuciyar. Da kallo yabi basket din, takarda ce fara daga d'an gefe yasa hannu ya ciro ta ya karanta _"Karka manta kaci please, jiya gaba daya baka ci komai ba."_ Amrah Sai ya kundundune takardar, ya chusa ta aljihun sa, ya tsuguna ya dauki basket din ya fita da d'an sauri, sakin labulen data makale a jiki tayi ta fad'a kan kujera zuciyar ta na harbawa da sauri, me yake faruwa? ***Har ya kusan gama aikin ranar be samu kwakkwaran idea abinda ya kamata yayi ba, yana jin jiki dan kansa yayi wani irin daure masa jijiyoyin na amsawa Kamar zasu ballo da jini amma be daina matsawa kan da tunanin mafita ba, mafitar da zata zama matakin farko na cika alkawarin da yayi masa. ***Waya Abba ya daga da niyyar kiran Daddy akan maganar, sai dai labarin rashin lafiyar Safwan din ta hanashi dauko masa maganar, yayi masa fatan samun lafiya sannan sukayi sallama. Ya kalli Umma dake gefe tana jiran jin yadda za'a yi, yace "Kinji ashe Safwan din ne ciwon sa ya tashi, suna asibiti ma." "Subhanallahi, yaron nan na shan wuya wallahi." "Wallahi,baki ji muryar Alhaji Sulaiman din bama, abun tausayi." "Allah ya bashi lafiya." "Amin." Ya amsa sai kuma yace "Shiyasa watakila sultan jiya bashi da walwala yaron, kuma da yake miskilin kansa ne kinga ai be fad'a wa kowa ba." "Allah ya kyauta, zan kira Mah-Mahn anjima idan Allah ya yarda." "Ya kamata gaskiya." "In Sha Allah zan kira, ni yanzu wani tunani ma na tafi, Idan ace yaran nan su dukka biyun babu wanda yasan da zuciyar dan'uwan sa, ya kake ganin zamu warware wannan abin?" "Muyi addu'a Allah ya zaba mana abinda yafi zama alkhairi." "Haka ne, Allah ya kawo komai cikin sauki." "Amin." Ya amsa. *** *Masarautar Saji* Babbar masarauta ce, wadd take dauke da mutane masu yawan gaske, gari guda ce babu abinda ba'a saidawa a cikin ta,sannan akwai manyan makarantu da asibiti a cikin ta, babu abinda dai mutum zai nema a ciki be same shi ba. Shiga yayi sak irin ta mutanen da ake kira da bararoji, kansa rufe ruf da wani yadi me kaurin gaske, baka ganin komai sai idanun sa wanda idan ba tsananin sani kayi masa ba, ba zaka iya ganeshi ta farat daya ba. Kamar yadda ya saba, haka yayi ta gifta mutane yana ratsawa ta tsakiyar masarautar har zuwa babbar fadar sarkin da ke kan mulki, Sarki Muhammad Bello Moddibo Saji, babu wanda yayi yunkurin tsaidashi, har ya dangana da tsakiyar fadar, ganin sa yasa sarki sallamar kowa dake fadar, aka barsu su biyu, bayan an rufe kowacce kofa da zata iya daukar magana ko mai kankantar ta, ta fitar da ita. Nadin kan nasa ya cire, kansa da babu ko gashi ziri daya ya bayyana yana ta kyalli kamar wata a daren sha biyar, kamar sa ta sha banban da ta mutanen da yayi irin shigar su, baki ne kakkaura, kuma gajere, be zauna ba, dan bashi da sukunin zaman, a hanya yake dole ce ta sashi ratsowa, ya fiddo wani abu kamar mudubi, ya ajiye a k'asa sannan ya haske shi daidai saitin Sarki, yan kananan danjoji ne guda biyu jajaye masu matukar haske suka bayyana, sai wata daga chan gefe guda d'aya da ta rabe gida biyu, hasken ta yayi matukar dishashewa sai ka kalla sosai zaka gane shi. Sai kuma wata itama daga gefe da babu ko haske a tattare da ita. "Ranka ya dade, matsala tana sake gabatomu, ya kamata ayi wani abu." Yace yana kallon sarkin daya zurawa mudubin Ido, babu ko kiftawa, kansa ya jinjina a hankali sannan cikin muryar sa me amo da sauti mara karfi yace "Idan har kun k'asa gane inda suke ku nemo su lallai akwai tangard'a a aikinku, idan har wannan karamin aikin zai hana mu sukuni toh lallai kun gaza, gazawa irin ta faduwar bakar tasa, babu sauran abinda zan ce muku, ina bukatar a tabbatar min da in da take, da kuma inda yaran suke, daga yau zuwa karshen sati, idan har hakan bata samu ba, zan chanja ku,da wanda zasu maye gurbinku suyi aiki na kwarai." Da sauri ya zube a k'asa, cikin kasa da girmawa yace "Ranka ya dade, gazawar mu ba tana nufin kasawa ta har abadah ba,ba tana nufin shikenan komai ya baci ba, aikin ne yake cike da sarkakiya da bamu san menene Allah ya lullube ba, su waye taurari biyun nan da suke haskawa ako da yaushe, kullum hasken su kara karfi yake kusancin su da masarautar nan na sake matsowa, me suka taka? Me suka sani game da wani abu daya shude, aka kuma rufe babin sa tun shekaru masu yawan gaske." "Ko su waye su, ko me suke takama dashi, muna nan muna jiran su." "Akwai karfi a tattare dasu ya mai girma, karfin da mutum ko aljanna basu isa su gane komene zasu zo dashi ba." "Aiki ya rage naku, a kwanakin da muka baku, idan kun so kunyi abinda ya dace, idan kuma kunki kun cigaba da wasa da damar ku..." "Hakan ba zata faru ba ranka ya dade." "Madallah da kai, zaka iya tafiya." Nannade komai yayi, ya maida nadin nasa ya saka sannan ya bi ta kofar baya ya fice gaba daya daga gidan. ***Ya riga yasan inda zai sameta, tun da ya duba bata nan a inda ya zame mata office din ta, sai ya nufi chan din yana sake tattaro courage din sa, kafin ya karasa ya riga ya gama tsara yadda xai mata magana, yana kuma fatan ta fahimta yadda ya zauna ya dau tsawon lokaci yana tsara abinda zai ce mata. Jiñ an bud'e kofar yasa ta dago da idonta dake saman fence din wajen ta sakala hannayen ta ta makalo shi jikin hannun nata,guiwar hannun na saman fence din, kayan dake jikinta sunyi matukar amsar ta, ta yi rufe kan ta turban. Sanyayyen kamshin turaren ta na Jadore da Prada ya bigi hancin sa, ya rufe su da wani irin yanayi sannan ya bud'e su a hankali, suka sauka acikin nata, da ta d'anyi k'asa dasu har kana iya ganin yadda gashin idon ya kwanta a saman fuskar ta. Ita ta fara janye idon ta, ta maida su wajen balcony din tana bin wasu couples da kallo. A daf da ita ta tsinkayi muryar shi, ya dora hannayen sa a saman fence din kamar yadda tayi, "Naga alama kina son yanayi irin wannan, me kika fi tunawa a duk sanda kika kebe kanki ke kad'ai dan bana raba daya biyu tunani ne ke tsare ki har a manta da inda kike mafiya yawan lokuta." "Lokuta da yawa nafi son na ji ni ni kad'ai." "Umm, da gaske?" Daga masa kai tayi alamar eh, "Me yasa ka chanja kwana biyun nan? Bana jin dadin yadda kake acting." Tace a hankali, gefe ya kalla, ta ina xai fara ce mata su hakura da juna bayan yasan su din suna kaunar junan su da gasken gaske, ta yaya zai ce mata ta bawa dan uwan sa dama, suyi soyayya bayan yana duniyar ba mutuwa yayi ba, anya zata fahimci yadda abin yake kuwa? Ba zata zarge shi da rashin adalci ba? Daga chan bayan kansa yaji wata murya na tunasar dashi waye Safwan, halin da yake ciki a yanzu da ma wanda zai iya shiga idan har be samu abinda zuciyar sa ke muradi ba, kenan shine yake da dama da Ikon da Safwan zai zauna lafiya, idan kuma ya samu matsala shine mutum na farko da zai fara zargin kansa da rashin sadaukarwa. Kansa yayi fadi, fadin da yake jin kamar an saka abu an kwashe komai da ya ke cikin kan, babu abinda yayi saura sai fanko. Samun kansa yayi da sauka akan kafafuwan sa, ya had'e hannun sa waje daya, kana kallo zaka ga yadda Adam Apple dinsa ke kaikawo a tsakanin wuyan sa, sai kuma fuskar sa da tayi fayau kamar farar takarda, yawun bakin sa ne yaji ya kafe, ya kasa hado kalma daya da zai fad'a mata, bin sa tayi itama ta durkusa a kusa dashi, kwalla na taruwa a idon ta, ko menene zai gaya mata tasan ba me dadin ji bane. A hankali kamar wanda ya shekara guda ba tare da ya furta kalma daya daga bakin sa ba maganar ta fito, yanayin yadda ta Fito din zaka gane kwacewa tayi ta bayyana kanta "Ple..eseee ki ba...wa S..a..f..w..an dama." "Na'am?" Ta dago da sauri Sai ya daga kansa cikin tabbatarwa yace "Kinsan condition dinsa, yana kwance yanzu haka a gadon asibiti saboda abinda kika fad'a masa, yana shan wahala sosai, Safwan mutumin kirki ne, he deserve the best, shi ya chanchanta da ya same ki, nayi masa alkawarin zan yi kokari na wajen ganin na daidaita komai." Girgiza masa kai take har ya gama maganar, ya kuma karashe kamar zai fashe da kuka, sai dai dakiya irin tasa da jarumta sun shanye komai. "Dan Allah karka yi min haka ya Sultan, karka barni dan ALLAH." "Amrahhhhhh..." Ya kirata ganin yadda take kuka sosai, "Karka yi breaking heart dina, kayi min alkawarin zaka zauna always by my side, yanzu kuma kake cemin na bawa Safwan dama, ni ba toy bace da zaka gama playing da ita ka turawa Safwan shima ya buga, nima mutum ce da zuciya a kirjina." "Na sani, nafi kowa sani, kuma ki sani this the hardest thing da zan taba yi a rayuwa ta, I love you so much kin sani, but Safwan deserve you fiye dani, kun dace da juna, kuna da wani abu mai muhimmanci a neman aure da ni na rasa shi, saboda haka ban cika ba, ina da wani gibi a rayuwa ta da babu abinda zai cike shi." Sai ta mike tace "Bazan taba son Ya Safwan ba, na tsane shi na tsane shi. I hate him!!!" Ta shige da sauri tana kuka sosai, kukan da wanda aka taba balla wa zuciya ne kawai zai iya fuskanta. Idon sa ya kada yayi jajur, ya kalli wayar ta sake yashe a wajen, ya sa hannu ya dauka, zuciyar ta ta shiga raya masa abinda ya kamata yayi, ya kuma yi na'am da hakan, babu bata lokaci ya dauki matakin farko na ruguje dukkan farin cikin su. RanoWannan littafin na kudi ne, AMANA CE, duk wanda yayi mana sharing dinsa shi ALLAH! Idan kina/Kana so ki/ka karanta ki/ka tuntubi numbobin nan* *0903 234 5899* Or *09033181070* Page 13  *ANNUR PERFUMES*  MASARAUTAR KAMSHI KENAN, MUNA BADA TURAREN MU AKAN FARASHIN SARI DA KUMA SAYI ‘DAI-DAI, SHIN NA LISSAFO MUKU ABUBUWAN DA MUKE SIYARWA KUWA?_ _TURAREN WUTA (NA KAYA/ GIDA/ JIKI/ DA TSUGUNNO. KHUMRAH, KULACCAM,_ _MUSK(AL MISKI THAHARA/AYSHA/BLACK AND RED MISKI)_ _DECORATIONS (NA GIDA/OFIS/ KAMFANI DA SAURAN SU/ MUNADA INGANTATTUN KAYAN INFECTION (HERBAL WANDA BA ZAI SAKI WANI SIDE EFFECT BA, MUNADA DANA MATSI (STEAMING)_ _ANNUR PERFUMES NA GARIN *KANO* ADIRESHIN MU: GAIDA LAYIN MASALLACIN IMAMU MALIK!. LAMBOBIN TARHON MU: 07086341096//07069037534. MUNA TURA KAYAN MU A KO’INA A FADIN NIJERIYA. SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA SAI ANNUR PERFUMES_ _WANNA SCENT EXOTIC??HEY.. WHICHEVER WAY YOU WANT IT WE’VE GOT YOU COVERED AT *ANNUR PERFUMES(CASTLE OF SCENTS)* FOR YOUR MIND/ YOUR SOUL.. AND YOUR HOME.. BE THE CENTER OF ATTRACTION WITH ANNUR PERFUMES.. WE ARE YOUR SCENT PLUG..TANTALIZE YOUR SENSE OF SMELL AS YOU SINK INTO BLISS. SAY NO!! TO DAMP SMELL LOVELIES. OUR DUKKANS LAST’S LONGER AND LINGER. VERY AFFORDABLE... DELIVERY IS NATIONWIDE ******* *Sosai yaji karfin jikin sa tun bayan maganar da sukayi da Sultan, sallamar sa akayi daga asibitin suka wuce gida, kamar zai fadi haka yake jin sa ya samu da k'yar ya isa daki, ya kwanta, yana kwance Mah-Mah ta shigo, ta zauna daf dashi sannan tace "Inaso muyi magana ne." Tashi yayi da k'yar yana fuskantar ta "Ka fad'a min gaskiyar abinda yake damun ka,ni mahaifiyar kace don haka Ina bukatar sanin halin da tilon d'ana yake ciki." Tausayi ta bashi, tun bayan da yaxo duniya take dawainiya dashi, dawainiya irin ta duk d'an da aka haife shi da wata tawaya, yadda iyaye suke fadi tashi akan da, suna burin ace shima ya zama kamar sauran yara masu lafiya. Bata chanchanci boye mata abinda yake ciki ba, watakila zata iya masa wani taimako Akai, duk da yana ji a ransa ba zai taba so ayi wa Amrah dole ba, yana dai fatan kawai za'a iya shawo kanta har ta amince dashi, maganar da sukayi da Sultan da alkawarin da yayi masa ya kara bashi kwarin guiwa , yasan Sultan zai yi iya kokarin sa. "Mah-Mah..." Ya matso yana dora kansa a saman kafadarta, hannu tasa ta shafa kan nasa sannan ya cigaba, ya bata labarin komai tana sauraron sa, bata kuma katse shi ba har ya gama, sai daya kai karshe. Murmushi tayi masa ta mike sannan tace "Ka kwantar da hankalin ka kamar ka sameta ka gama ne." Kallon ta yayi a hankali yace "Kar ayi mata dole dan Allah Mah-Mah." "Karka damu." Tace "Ka sanar da Sultan ko?" Daga kansa yayi alamar eh sai tace "Shikenan...Bari na samo maka abinda zaka ci." Fita tayi ya maida kansa baya ya runtse idon sa a hankali ya furta "Ya Allah! Tana fita ta isa wajen da ta ajiye wayar ta, ta dauka sannan ta kira Umma, gaisawa sukayi sannan ta sake tambayar lafiyar Safwan din, tace mata an sallame su ma sun dawo gida, shiru suka d'an yi kafin Mah-Mah tace "Ai ashe wai rashin lafiyar ta Amrah ce." "Ta Amrah kuma?" Ta tambaya da mamaki "Wallahi, kinsan yaran yanzu da saka soyayya a rai,wai ce mishi tayi bata sonshi shine shi kuma ya hau ciwo." "Toh subhanallah." Umman tace tana jin ya kamata tayi mata maganar "Wallahi, sai dana matsa masa sannan ya sanar dani." Sai kuma tayi k'asa da muryar ta "Dan Allah Umman yara alfarma nake nema, kasancewar Safwan shine kad'ai d'an da muka mallaka a duniyar nan, ga kuma lalurar da yake dauke da ita tun yana tsumma, shine nake neman alfarma wajenki, dan Allah ki bawa Amrah hakuri ta taimaka masa ta bashi dama, na tabbata ba zatayi dana sani ba, dan Allah." Sosai umma ta lula tunani farkon maganar Mah-Mah, shine kadai d'an da suka mallaka, idan haka ne kenan? Toh ko sun san da maganar Sultan amma suka zabi ta Safwan din suka kyale tashi? "Kina kan layi kuwa?" Mah-Mah ta tambaya jin tayi shiru "Ya hakuri ina kai, na tafi wani tunani ne,naji kince Safwan ne kad'ai d'an da kuka mallaka, kenan Sultan..." "Kiyi hakuri dole ce tasa ni fad'ar haka, amma dai wannan maganar ta wata ranar ce daban ba yau ba. Ki taimaka dan Allah,ke UWA ce kinsan yadda iyaye suke ji a duk lokacin da d'an su ya shiga wani hali." "Shikenan ki kwantar da hankalin ki, ki kwantar wa Safwan din ma nasa, matar mutum kabarin sa, ko munso mu bawa Safwan idan Allah beyi Matar sa ce ba bamu Isa ba, saboda haka mu cigaba da addu'a Allah ya zaba mana mafi alkhairi." "Haka ne, shikenan Allah ya taimaka mana." "Amin ya Allah." Tace sannan sukayi sallama. Ajiye wayar Umma tayi cikin tsananin mamaki, bata taba ganin ko da alamar da zai nuna cewa basu ne suka haifi Sultan ba, tayi niyyar yi wa Mah-Mahn maganar Sultan din amma jin abinda tace yasa ta fasa dan hakan na iya jawo masa wata matsalar, bata san me yasa ba take jin shi sosai a ranta take kuma yi wa Amrah sha'awar auren sa fiye da Safwan din ba duk da shima Safwan din bashi da wani nakasu. Tun da aka fara maganganun nan shikenan ta rasa sukuninta, sai a lokacin ta gane yadda iyaye keji idan aka fara maganar auren yaransu, zaka ga sun shiga damuwa sosai ashe ire-iren wadannan matsalolin ne ke tasowa, bata da wani zabi dan bata masan ya zatayi ba, kawai sai ta dukufa rokon Allah ya kawo musu koma menene cikin sauki. ***Tun bayan abinda ya faru tsakanin Sultan da Amrah wani abu me kuma faruwa ba, basu sake haduwa sunyi magana da juna ba, wayar ta dake hañnun sa ma Adnan ya bawa ya bata ya kuma sake dedicating kansa gaba daya a school baya dawowa gidan sai dare. Kallo daya zaka yi masa ka ga tsantsar rama da rashin kwanciyar hankali, duk sanda Abba yayi masa magana sai yace makaranta ce, a haka suka cigaba da tafiya babu abinda ya sauya dan Amrah na nan a kan bakanta ba kuma ta sake daga wayar mayen nata ba duk yadda yake kiran ta wanda tasan sarai Sultan ne ya cire shi daga block list data sashi, sashe daya na zuciyar ta na tausaya masa idan taga yana jera mata kira babu kakkautawa, takan tausaya masa tayi masa message da words biyu zuwa uku ta tura masa. Hakan da take shine yake kara masa hope har yake ganin watarana komai zai iya chanjawa.    Kamar ko yaushe idan ya dawo zai tarar da abinci me rai da lafiya a daki an ajiye masa wanda yasan aikin Amrah ne, duk sanda ya gani sai yaji wani iri, yana jin kamar ya dau waya ya kira Safwan yace masa yayi hakuri ba zai iya cika masa alkawari ba, kamar ya dauke loudspeaker ya fad'a yadda kowa zaiji wala'alah hakan zai sa abinda ya danne masa zuciya yayi sauki , sai dai ya riga ya gama making mind dinsa, ya kuma yi alkawarin duk runtsi bazai taba chanjawa ba, not now not ever.     Kadan yaci abinci ba wai dan bayajin yunwa ba, ba kuma don abincin babu dad'i ba, sai dan baya cikin abubuwa masu muhimmanci yanzu a rayuwar sa, yana ci ne kawai dan ya faranta mata rai, sannan ya saka wani abu ko yaya ne a cikin nasa ko dan lafiyar sa.    Kudade sosai yake samu a duk watan duniya, dama scholarship din tasa 100% ce tayi covering komai,sannan suna biyan sa wasu kudade na karatun da yakeyi, ganin babu abinda zai yi da kudin yasa ya tuntubi Mubarak akan ya nema musu fili shi da Safwan, bayan an samu an siya ya kuma dora masa alhakin kula da komai ba tare da ya sanar da Safwan ba dan so yake kawai yayi masa bazata.      Karatun nasa ma ya matse shi sosai baya ko hutawa saboda so yake yayi yayi ya tattara ya bar kasar dan zama waje daya da Amrah kara masa nauyi yake a zuciyar sa. Wani yammaci ya dawo da wuri ranar, yayi wanka ya chanja kayan sa yana so ya kai musu ziyara, kusan kullum sai mutumin ya kirashi akan yaushe zaizo, shiyasa da yaga ya gama da wuri yau sai kawai ya shirya ya fito. Suna zaune ita da Afrah suna solving wani puzzle, ya shigo falon, bata dago ba har ya iso daidai kujerar da take kai, ya tsaya yana kallon abinda sukeyi, duk da babu yadda rana zatazo ta fadi be saka ta a idon sa ba ko da daga nesa ne, amma sai yaga yau ta chanja masa baki daya, kamar an sake sabunta ta ta ko yace an musanyata da wata daban, muryar Afrah ta katse shi "Ya Sultan fita zakayi ne?" "Eh kina da sako ne?" Yace "No Amrah ce dai tun dazu take jiran ya Adnan wai zai rakata ta ina kika ce ma?" Ta kalle ta "Bansani ba." Tace tana bata rai, harde hannayen sa yayi yana kallon ta, ta dago suka hada ido kawai ta harare shi ta cigaba da abinda take dan har ga Allah haushin sa take ji sosai. "I'm Sorry." Yace a hankali, taji shi sarai sai tayi kamar bata ji ba, gaba ya d'an yi kamar zai tafi sai kuma ya tsaya ya juyo "Dan Allah minti biyu." Ya langabe kai tare da hade hannun sa waje daya alamar roko, tashi tayi kamar zata sai kawai ta wuce shi tayi shigewar ta ciki. Be ji dad'i ba, ya kuma san tana da right din reacting fiye da yadda tayi, toh amma ya zai yi? Da tasan yadda yake ji da bata kara masa akan abinda yake ji din ba. Guiwa a matukar sake ya fita ya nufi gidan. Afrah na duba messages din ta na whatsapp taga Mah-Mah tayi mata magana tun jiya ama ashe, shiga tayi sai ta ganta online ma, da alamar recording take, jira tayi ya shigo ta kunna tana sauraro. Bayan ta gama shi ta danna itama ta shiga recording, recording din daya yi sanadiyyar chanja alakar mutane da yawa! ***Yau kai tsaye ya shiga gidan ya kuma wuce kai tsaye ya danna door bell, ya rungume hannayensa a bayan sa yana jiran a bud'e. Yarinyar ranar ce yau ma ta bud'e, ganin shine yasa tayi gaba bayan ta ce ya biyo ta, suka wuce falon farkon da suka zauna ranar suka shiga chan cikin gidan, waje ta nuna masa ya zauna sannan ta shiga ciki, jim kadan ta fito ta wuce shi. Kansa a k'asa yana tunanin abinda ya faru kafin ya tawo ta fito, yau ma kamar wanchan ranar fuskarta babu walwala, sai dai tana ganin shi tayi kokarin daidaita yanayin ta, ta maye damuwar dake shinfid'e saman fuskarta zuwa murmushi me fadi,me dauke da ma'anoni masu yawa. Zamowa yayi ya gaishe ta, ta amsa a sake sosai fiye da duk ganin da yayi mata, sannan da kanta yaga tabi wata kofa sai gata ta dawo da dan karamin plate da cup da Lemo alai ta ajiye masa sannan ta zauna, godiya yayi mata sannan ya ce "Yau Baba baya gida?" "Baya nan, ya dan fita amma nasan zaka iya ganin shi ya shigo yanzu ma." "Allah sarki." Yace yana kisissima abinda ke masa yawo a zuciyar sa, yana jin idan be ji wani abu daga garesu ba kamar ba zai iya cigaba da komai ba, yana son sanin damuwar wadannan bayin ALLAH da yake jin su sosai a ransa, dan gyara zaman sa yayi kad'an yace "Dan Allah Mamah, ko zan iya sanin dalilin daya dawo daku nan kasar kuke zaune kuna rayuwar ku ba tare da dangin ku ba? Ranar da mukayi magana da Baba ya fad'a min wata magana data tsaya min a rai, yace "Ba ko yaushe ne rayuwa take tafiyar wa mutum a yadda yaso ba, sau da dama abubuwa na chanja salo da alkibla daga inda bakayi zato ko tsammani ba, kuma yace min zuciyar mutum birnin sa, sannan yace min Abinda Ke Cikin ZUCIYA, baki ba zai iya furta shi ba, haka kuma yafi gaban a tona, ya kuma kare da cemin mutum mugun icce, kar nayi saurin yarda da mutum domin akwai cuta me muni da girma tsakanin mutum da mutum." "Tun daga ranar nake bitar wadannan kalaman nasa, na kuma yi musu waje na musamman a cikin zuciya ta, na kuma auna su na dora su a mizanin abinda nake tunanin shine makasudin zuwan ku nan." Da gefen dankwallin kanta tasa ta share hawayen da suka fito tunowa da tayi da abubuwan da suka faru a baya, abubuwan da suka kasa barin birnin tata zuciyar suke cigaba da nakastata suka yi mata raunin da warkewarsa zai yi matukar wuya. Sai dai bata cire mijinta a cikin mutanen da suka taimaka wajen rugujewar rayuwar ta ba, duk kuwa da ya bata TABBACIN bashi da hannu akan duk abinda ya farun ya kuma yi iya kar kokarin sa wajen son tabbatar mata da gaskiyar sa, sai dai har xuwa yanzun bai xo mata da gamshashiyar hujja ba! "Idan har ka shirya sauraron labarin mu, zan sanar dakai, ko hakan zai taimaka wajen rage abinda nake ji." "In sha Allah." Yace cike da zakuwa **** *Masarautar Saji* *Tuna baya* Duhun da ya mamaye sararin samaniya ne ya shiga yayewa yana maye gurbi da hasken asubah, mirza idanun ta tayi, ta mik'e ta sauke kafafuwanta a hankali suka sauka a lallausan carpet son din dake ajiye a gaban gadon, agogo ta fara kalla, sannan ta wuce zuwa toilet ta dauro alwala, ta fito ta shinfida abin sallah tayi sallah, ta zauna tana azkar har rana ta d'aga, tashi tayi ta zauna saman gadon sannan ta daga waya tayi kira, kofar ta bud'e sannan suka shigo su uku, suka zube suna diban gaisuwa "Barka da tashi tauraruwa me haske, gimbiya me tashe, Allah ya ja da kwanan ki, ki dade kiyi karko gimbiyar masarautar Saji." Dan murmusawa tayi, yana cikin abinda take so a al'adar masarautar, wannan kirarin da ake mata tun bayan da sahibin ta ya d'ane kujerar Mulkin Masarautar take amsa sunan gimbiya sarauniya. Shekarar ta, ta biyar kenan a cikin masarautar, tun bayan da ya aurota ya kawo ta, abubuwa da yawa sun faru a shekarun nan, sai dai bata taba daga kai ta kalle su balle har su daga mata kai, kai tsaye take abubuwan ta kasancewar ta wadda tazo daga nahiya daban da tasu, karatu ne ya had'a su, daga nan suka fad'a soyayya har ta kaisu da aure ya kuma dauko ta ya kawo ta nan din, daga dangin ta har nasa babu wanda yaso auren, sai dai tun da suka samu albarkar iyayen su suka rufe idon su, suka cimma burin su na zama a inuwa daya. Bata fuskanci wani abu a zaman ta da sirikinta saboda yana kaunar ta a matsayin ta na Matar babban dansa, wanda ya kasance sarki a lokacin har zuwa yanzu da Allah ya karbi ransa, matan sa uku na aure wanda ya mutu ya bari, sai mahaifiyar Usman da ta rasu tun yana yaro, be taso da ita ba, haka kuma be taso cikin masarautar ba har sai ya kammala karatun sa baki daya ba kuma akasar yayi ba, a lokacin kuma yan uwan sa da suke uba daya kowa ya kawo karfi, kuma dukkaninsu kowa yana da burin gadon mahaifin nasu, da farko sun dauka dadewar da Usman din yayi a kasar waje ya sauya masa tunanin sa akan sarautar, sai dai yadda ya dawo da karfin sa tare da maganar aure yasa jikinsu yayi sanyi. Tun da ya dawo kullum suna tare da mai-martaba mahaifin nasu suna tattaunawar da babu wanda yasan me suke cewa, haka har akayi auren kowa kuma yayi tunanin a lokacin sarkin zai yi murabus ya bashi amma sai akaji shiru, hakan ya kwantar musu da hankali har aka kawo yanzu da babu ran mahaifin nasu kuma ba tare da wani dogon tunani ba aka nad'a shi ya haye kujerar.    Juya ruwan take tana wasa da hannun ta, sosai ruwan yayi mata matukar dadi ga wani kamshi na musamman dake tashi, sai data dau dogon lokaci tana wankan sannan ta fito, ta shirya cikin shigar manyan mata yan kwalisa, sannan baiwa guda ta taimaka mata wajen saka alkyabbar da ta zama mata kamar dole daga satin da ya wuce zuwa yanzu. Katafaren falon ta ta isa,tare da jagorancin bayi masu yawan gaske da aka kara yawansu a shashen nata tun bayan nadin sarautar, suke mata dukkanin hidima daidai da magana da suna da yadda zasuyi su karbar mata da tabbas ba zaà barta tayi ba, abinci ne birjik kala kala aka jere mata, ta kishingid'a kadan dan bata da muradin cin su a halin da take ciki, burin ta d'aya ta ganshi, ta kuma zauna dashi kamar yadda suka saba kafin satin da ya gabata komai ya chanja ciki harda ganin sa da yayi mata wuya, da farko ta kasa sabawa da hakan sai dai a hankali ta fara sabawa tunda ta riga ta gane hakan shine mulkin, shine sarautar Kuma shine girman da mutane da yawa da suka shigo yi mata Allah sanya alkhairi suke fad'a mata. Amma dole ne ta ganshi dan gaskiya ba zata iya rike abinda ke cikin zuciyar ta ba na tsawon wani lokaci. Baiwa guda ta tasa ta aika zuwa wajen jakadiya tayo mata iso ta sanar da ita tana bukatar ganin sarkin a yanzu. Sakon da baiwar ta dawo mata dashi ya bata mata rai sosai, ba zata samu ganin sa ba saboda wani muhimmin tattaunawa da suke da manyan fada, ranta a bace ta koma ciki tana jin kamar mijin nata be chanchanci sarautar ba idan har hakan zai hana mata ganin sa a duk sanda taso ta kuma yi muradi.    Wunin ranar gaba ki daya ta kasa sukuni, tun bayan data tabbatar da juna biyun dake jikinta bayan shekara biyar da sukayi da aure,burin ta kawai ta ganshi ta bashi kyakkyawan labari, sai dare sannan jakadiya tazo tafiya da ita zuwa shashen nasa, tana shiga ya taso da sauri ya tare ta, ta dan bata rai ta zauna a gefe, sai da yayi ta ban baki sannan ta sanar dashi labarin cikin, yadda tayi tunanin zai je sai ma taga kamar yafi hakan, farin ciki sosai ya nuna yayi ta gode wa Allah.     Sai dai, a lokacin da suke cike da farin cikin wasu mutane dake ciki da kewayen masarautar na cikin bakin ciki, bakin cikin abinda zai faru watan watarana.     Kasancewar cikin ta bame laulayi bane sai ya zama bata shan wahala,babu kuma wanda yasan da maganar cikin tun da tsohuwa Hajja ta kirawo su ta hanesu da d'aga zancen, dukkan su basu kawo komai ba, dan basuyi tunanin akwai wani abu da zai iya shiga rayuwar su, da zuciya daya suke zaune da kowa musamman ma ita da bata san kan dawar garin ba.     Tana kwance daga gefen sa, hannun ta a saman cikin nata tana ta jujjuya shi, ta rasa dalilin da yasa take mafarke mafarke sosai yanzun wanda da batayi, wani lokacin har idan tayi irin mafarkin bata sha'awar sake komawa baccin saboda tsoron kadda ta sake yi, hakan ce ta faru yanzun ma, bayan ta farka sai ta kasa komawa ta cigaba da juyi, gefe ta kalla ta ga yana baccin sa hankali kwance, sai ta muskuta ta cigaba da aikin tunani kafin a hankali ta fara jin kamar ana motsa window din d'akin da suke ci, kallon wajen tayi sai taga kamar inuwar mutum ta jiki, damke idon ta, tayi taja jikinta ta matsa sosai kusa dashi, tana tunanin waye zai zo wajen a wannan daren, bayan haka ma kewaye wajen yake da masu tsaron su, tana kwance luf taji magana k'asa-k'asa, tayi kokarin gane me aka cewa ta k'asa, sun d'an jima suna tattaunawa a wajen kafin taji an bar wajen. Da safe ta tashi da wata irin kasala, ta k'asa mikewa daga gadon, har ya gama shiryawa ya fita idonta na kulle tana jin wani abu yana mata yawo aka, wajen goma na safiyar ciwo ya turketa, kafin Sha d'aya jini ya balle mata, da k'yar aka samo kanta dan ba karamin galabaita tayi ba, sai dai cikin dake jikin ta ya lalace.    Ko da ta farfado aka fad'a mata cikin ya zube tayi kuka sosai dan ba karamin son yara take ba, ta kwallafa rai da cikin sai dai dole ta hakura tayi tawakkali. Haka rayuwa ta cigaba da garawa duk sanda ta samu ciki toh sai ya lalace, sosai hakan yake damun su,sai dai basu kawo komai ba a ransu balle su zargi wani akan hakan ba.    KUNA BUƘATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA'ARKU A PAGES ƊIN BOOKS ƊIN ZAFAFA BIYAR 2021?. To kuzo ga dama ta samu💃🏻💃🏻.         Ina ma'abota son a tallata musu hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?. Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon haziƙan marubanku ƴan biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da saƙo ta dalilin shafukan littatafai. Ga duk mai buƙatar a saka masa tallan kayan sana'arsa a shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntuɓar waɗan nan Numbers 0903 234 5899 or 09033181070 ta WhatsApp, idan har agama buks ɗin kana buƙata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauƙi. Idan kuma wasu adadin pages kake buƙata koda ɗaya ne duk zamu saka maka akan farashi mai sauƙin gaske🤓. Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike neman sauƙi😻😻😄🤗. ______________________ _ZAFAFA BIYAR 2021_*🔥 _*SUKAR BAYA*_💚 _BILLYN ABDUL_ ( _kwai cikin qaya_ ) ( _raina kama_) ( _wutsiyar raqumi_ ) *_SIRADIN RAYUWA_*💛 _SAFIYYA HUGUMA_ ( _alqawarin Allah_ ) ( _daurin boye_ ) ( _Dangantakar zuci_ ) 💙 _*KIBIYAR AJALI..*_💜 _MISS XOXO_ (Sulke baya tsare ta sai ta wuce) ( _Igiyar zato_) ( _Kaimin halacci_ ) ( _Naufal_ ) *_ABIN DAKE CIKIN ZICIYA_*🧡 _HAFSAT RANO_ ( _ruhi daya_ ) ( _Sauyin qaddara_ ) ( _Daurin goro_ ) *_MIN QALB_*❤️ _MAMUHGEE_ ( _buri daya_ ) ( _tarayya_ ) ( _eznah_ ) Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 0903 234 5899 IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 09033181070 Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥*K..........* *NH* *WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE! KI DUBI GIRMAN ALLAH KI SAYA DA KUDIN KI, KADA KI SHARING, TEMAKA KI SIYA NAKI A NAMBOBIN MU DAKE KASA* *All characters/ some places/ Incidents, Portrayed in this novel are fictitious.. * *(Duk mutanen ciki da sunayen wasu guraren da na saka, Da wasu abubuwan da suka faru, Duk tatsuniya ce, Idan yayi shige da rayuwar wani ko wata to akasi aka samu.) Consider it as synchronization👌🏾* *15* Gabaki d'aya sai hankalin mutane ya dawo kan Dije dake yashe a kasa. Shi kuwa sarki Salman tuni motarshi ta bar gurin taron tamkar ba sune suka jaza wannan ta'asar ba. Basu tsaya sunji me yake faruwa ba bare su san halin da yarinyar mutane take ciki. Kafin kace menene tuni aka dauke ta aka sa a mota sai asibiti domin bata san inda kanta yake ba. Kasan cewar akwai manyan jami'ai hakan ya sanya suna zuwa asibiti babu wani bata lokaci aka shiga bata taimakon gaggawa. Mas'oud dake kan hanyar shi ta zuwa gidan radio saboda yaje gida ya maida mahaifinsa kenan, kawai yaji labarin cewar Dije na can asibiti bata san inda kanta yake ba. Ya juyo da motar ya nufi asibitin cikin tashin hankali da tunanin abinda ya sa har hakan ya afku a kanta. Koda yaje kasa shiga cikin asibitin ya yi, yan sanda sun hana kowa shiga. Ya ciro id card d'in sa ya nuna musu amman duk da haka suka hana shi shiga, dama duk sauran yan jaridar da suka biyo su suna tsaye a bakin gate an hanasu shiga, saboda so ake a boye maganar cewa bafaden sarki ne ya yi sanadiyyar hakan. Aka fara cewa ai cikowar mutanan gurin ne yasa numfashin ta ya dauke ta zo faduwa shine ta buge. Tuni labari yaje wajan Alhaji Isma'il yana kan hanyar shi ta zuwa filin sauka da tashi na malam Aminu Kano zai je birnin Lagos. 'Innalillahi wa'ina ilaihir rajiun' ita kawai yake furtawa tare da juyo da motarsa ya nufi asibitin cike da tashin hankali. Yana hanya ya kira Mami ya sanar da ita cewa tayi maza-maza taje asibitin shima gashi nan zai je. Cikin mamaki duk kuwa da cewa tana cike da tsantsar mamakin jin cewar Dije na kwance a asibiti tace dashi. “Toh bari na shirya naje, amman kai ya zaka ce ka fasa yin tafiyar bayan ka riga kayi booking d'in tafiyar.?” “Hajiya wannan ba wata matsala ba ce, jin lafiya marainiyar Allah shine kawai burina. Karki manta Dije amanace a gare ni, kuma ya ce a waje na kamar yadda su Shukrah suke.” Yana gama maganar ya katse kiran yana jin mamakin matarsa da sam ba ta son ganin yana kyautatawa yarinyar nan. Ta kasa fahimtar cewa wata rana itama zata rabu da nata ya'yan kuma ba ta san waye zai kular mata da su ba. Mata duk lissafin su guda d'aya ne wato za'a riga su mutuwa, duk kuwa da cewa sun sha ganin Allah yana dauke wanda yaso a lokacin kuma yaga dama. Ita kuwa bayan taji ya katse wayar sai ta rike habarta, abin da mijin ta yake yi sam bata jin dadin shi. Haka ta mike taje ta shirya tasa driver ya kai ta bayan ta tambayi wane asibiti ne, aka sanar da ita. Alhaji Isma'il na zuwa ya sanar da yan sandan dake tsare da gare cewar shine mahaifin Dije, suka barshi ya shiga inda suka bar yan jarida guda uku suka bi bayan shi ciki kuwa harda Mas'oud. Mami ma tana zuwa aka barta ta shiga ta tarar da Alhaji Isma'il ya fito daga wajan likita yana gyaran babbar riga. Ta karasa suka hadu a center, kallon da ya yi mata shine kawai ya tabbar mata da cewar tayi masa laifi wanda ba zai rasa nasaba da nuna cewa aikin shi yafi Dije da ta nuna masa. “Ashe zaki zo?” Ya tambaye ta yana mai lasar lebensa da ya fara bushewa saboda kaduwar da ya shiga. Kanta yana kasa tana murza zoben zinarin ta tace. “Me zai hana Alhaji.?” “Naga kamar baki damu ba ne shi yasa, har na fara tunanin dakko wacce zata kular min da ita.” Kamar tace ai yanzu ma ba ita zata zauna ba, sai kuma ta hadiye kasan cewar yaki sakar mata fuska ta kasa ganin walwalar shi kamar yadda ya sabar mata. “A a zan zauna mana Alhaji, yanzu me yaje faruwa da ita?” Yaja numfashi yace. “Yanzu likitan ya kira ni yace ta farfado, gefen goshinta ya fashe. Dole sai ta d'an kwana ko biyu ne a asibitin dan bata kulawar likita.” “Daman ban da fitina ina Dije ina aikin jarida tsakani da Allah fa. Duk irin karatukan duniyar nan ta rasa wanne za ta yi sai shi saboda kawai taso ta dinga shiga cikin ridan-ridan maza. Gashi nan yanzu taje an....” “Ya isa haka Hajiya naji. Duk da haka ma dai zan kawo wacce zata kula da Dije, ke sai ki koma gida saboda yara.” Ta fi nono fari daman ba so take ta zauna d'in ba kawai fushin sa ne bata so shi yasa ta yadda cewa zata zauna. Yanzu kuwa da yace ta tafi idan ta gama abin da zata yi bata ja ba saboda kar taje yace ya fasa dole ita zata zauna. Ya nufi room din da aka kwanta da Dije wacce ke ta faman bacci tamkar babu abinda ya same ta. Sunkuye suka tarar da Mas'oud a gefen ta yana sharar hawaye, Alhaji Isma'il ya tambayi waye shi suka tabbatar masa da cewa abokin aikin ta ne, gidan radio d'in su d'aya. “Allah sarki, hakuri zaka yi muma duk shi zamu yi. Dubi goshinta duk da cewar an rufe kasan cewar ciwon ba kadan bane ba. Allah ya baki lafiya Dije, yasa kaffara ne.” Sun jima sosai a dakin kafin su fito dan gabar da sallah. Addu'a kam Dije tasha a gurin Alhaji Isma'il da Mas'oud wanda ya kasa bayyana mishi alakarshi da ita. Mami ta zauna akan kujera suna waya da Hameedah tana sanar mata da abin da ya faru wanda taji a bakin wani d'an jarida da abin ya faru a gaban su. “Kinji yarinya Mami, ko tayi zaton har yanzu a kauye take ne?” “Kema dai kya fada.” Cewar Mami. “Sarki fa! Taya Dije zata ce zata yiwa sarki interview banda dai ta latsawa kanta tunani. Ai gashi nan ta jawowa kanta an ji mata ciwo a banza. Kuma ance masarautar bata yi wani abu ba akan lamarin ko?” “Uhmmm! Kin san dai ba sarauta bace ta kauye, kuma yanzu ma rufe maganar aje son yi saboda kar a batawa masarautar suna.” Haka Mami ta zauna a gurin Dije babu wata alfarma da take yi mata saboda tsabar wulakanci, Allah ya taimaka ma bacci take ta yi, da watakila sai tayi hawaye da idanunta. Suna idar da sallah Alhaji Isma'il ya lallaba Mas'oud ya tafi kar ya damu zata ji sauki harma ta koma aiki da ikon Allah. Ya tafi ba dan yaso ba sai dan kar Alhajin yaga kamar bashi da kunya ko sabanin haka. Gabaki d'aya Alhaji Isma'il ya kasa samun sukuni ko fita ya yi yanzu zaka ga ya dawo har dare lokacin da Allah yasa Dije ta farka. Da Mas'oud ta fara yin karo da idanuwanta, kasan cewar ya sake dawowa asibiti da aka yi salla magariba, ya kasa zama sam shi yasa ya dawo. Dishi-dishi haka ta dinga ganinshi, ta gane shi tsab sai dai bata iya ganinshi tar-tar kamar yadda ta saba kallon abu. Ya mike tsaye tare da karasawa gurin ta yana cewa “Alhamdulillahi ta farka Allah mun gode maka.” Alhaji Isma'il ya shigo da sauri cike da tsantsar farin ciki juyowa da ya yi cewar Dije ta farka. Kallon mutane kawai take ba baki taki koda motsa shi bare a saka ran zata yi magana. Nurse ta shigo wacce ita ce ya bawa kwangilar kular masa da Dije. Sannu a hankali ya taje ta gyara mata inda ya kamata cikin haka ne ma suka ji ta furta. “Kawu daddy.” Tamkar ta tsira masa wani abun, haka yaji ya nufe ta ya riko hannunta, hawaye suka biyo ta cikin kyawawan idanuwanta, yasa hannu d'aya da yake kusa da fuskar ya share mata yana cewa. “Bar kukan nan Dije, dena kuka zaki warke da ikon Allah.” Still bakin ba wai budewa ya yi da yawa ba wajan son yin magana, ta kuma cewa. “Kawu daddy sarki ne ya harbe ni ko? Wallahi ba bu abin da nayi masa kawai daga tam......” “Yi shiru Dije, tsautsayi ne kawai da kuma kaddara suka fad'a kanki. Allah ya riga ya kaddara cewa hakan zata faru dake tun farko. Kiyi hakuri zan tsaya tsayin daka, da ikon ubangiji zaki dawo kamar baki yi ba kinji yarinya ta?” Lumshe ido kawai tayi saboda yadda take jin kanta ya yi mata wani irin kato tamkar an dora mata duniya haka take jinsa, saboda raunin da yake a goshin ta shine ya yi sanadiyyar hakan. Ta sunkuyar da kanta kasa ba tare da ta kuma cewa komai ba sai zuciyar ta da ta addabeta akan ganin rashin imani da rashin mutunci a gurin bafaden da ya ce mata yar talakawa. Bata taba zato ku tsammanin cewa haka suke ba, ashe ba su da kirki kansu kawai suka sani. Amman ban da haka ba ta ga dalilin da zai sanya su dinga yiwa mutane abin da suke yi ba. Mas'oud ya dinga kallanta yana son su sake had'a ido ko zai ji sassauci akan zugi da rada din da yake zuciyar shi, yana son ta nuna masa wata alama da zata tabbatar mishi da cewa a kowane yanayi take ciki zata iya gane shi da kuma matsayin da yake a gurin ta. Ganin tsawon lokaci taki dagowa ya sanya shi juyawa zai fita daga dakin, kamar an ce ya kuma kallon ta sai yaga ta dago ta kalleshi tana rausayar da kai alamar damuwa. Ya koma tare da cewa. “Sannu kinji?” Ta kifta idanuwa alamun ta amsa gashi yaga taki kawar da ido daga kansa yace. “A kawo tea ko?” Tayi shiru ba ta ce komai ba dan magana da kyar take iyawa. Nurse d'in tace ya bari a had'a mata suma zasu so ganin ta d'an ci wani abun ko ya ya ne. Alhaji Isma'il da kanshi ya dinga bata a hankali kasan cewar da kyar take iya daga lebeanta har a samu tea ɗin. Kadan tashi ba ne yawa ba sannan aka kuma kwantar da ita. Haka taci gaba da kwanciya a asibiti tana samun kulawar likitoci. Yan dubiya kuwa ba'a magana, ta ko'ina zuwa ake ana duba ta, har ta fara samun lafiya fuskarta tasabe kumburin ya baje sai gurin ciwon kawai. Mas'oud kam kullum yana asibitin tun safe har dare, hakan ya kuma tabbatarwa da Dije cewar Mas'oud shine farin ciki da walwalarta a rayuwa. Soyayyarsa ta kuma ninkewa a duk wasu sassan jikinta masu motsi da kai sakonnin gamsuwa ga abin da aka hakikance akan shi. Su Hameedah da Shukrah ma kullum sai sunje, a wannan zuwan ne kuma Shukrah ta fara nanikewa Mas'oud, ko be kulata ba sai ta kula shi saboda Mas'oud ba baya ba wajan tsarin halitta. Duk da cewa Dije ba ta da lafiya hakan be hanata jin kishi ba, yadda Shukrah take nanikewa abin alfaharinta abin yana mata ciwo dan yafi raunin goshinta zafi da radadi. Yau kwanaki biyar kenan wajan karfe hudu suna zazzune ana ta hira, duk da cewa shi baya kula su amman wata maganar idan an sako shi yana magana, yanzu ma hakan ce ta faru, Shukrah tace. “Abokin aiki gaskiya kana da kirki.” Ba tare da ya kalleta ba yace. “Da nayi mene?” Shukrah ta saki murmushi tare da cewa. “Gani muka yi tunda wannan abin ya faru da Dije kullum kana nan har ka fimu zama a gurin ta.” Mas'oud ya juya ya kalli Dije wacce itama shi take kallo, hakan kuma ya tayarwa da Shukrah hankali tayi saurin katse su ta hanyar cewa. “Kaga wasu jakunkuna da nayi order jiya.” Sai ya waiga ta miko masa wayarta yana kallon jakunkuna, ba karya sunyi kyau, kuma zasu yiwa Oum Waleedah kyau. “Sunyi kyau sosai kamar na siyawa madam, tana warkewa sai ta rataya a barta ko.?” Ya fada yana kallanta da murmushi. Turo baki tayi tare da mai da idanuwa ta rufe ba tare da ta ce komai ba, abin da yake sake jan ra'ayinsa akan ta kenan wato yanga. “Kana nufin Dije zaka siyawa?” Shukrah ta tambayesa cikin mamaki. “Eh mana na murnar ta tashi lafiya ba.” “Cab, ai duk an riga an siye su. Jira kawai masu su suke su dauki abubuwan su, sai dai next time.” Shi ma daman ba wai da gaske yake zai sai mata ba, koda zai siya mata abu baya jin zai sai mata a gurin wanda ta sani bare kuma yar uwarta. Duk iya surutun da Shukrah take yi masa besa shi ya fuskance ta ba, sai rubuce-rubuce da yake ta faman yi tamkar besan abin da take cewa ba. Haka suka yini har Mas'oud d'in ya fito zai tafi tayi saurin biyo bayan shi. Dije na kallon ta fita gabanta ya dinga bugawa, gani take tamkar wani makircin zata ta yi masa, gaba daya bata yadda da Shukrah ba sam. Cikin ranta ta dinga addu'a dan tasan babu mai tsare mata Mas'oud sai Allah, shine ya had'a zukatan su a lokacin da basu sani ba, haka suna fatan ganin Waleed da Waleeda a tsakanin su. °°°°°°°°°°° °°°°°°°°°°°° °°°°°°°°°°°°°° *MASARAUTAR BASANNABAS* Tun a ranar da wannan tsautsayin ya affku ya ke cikin jimami, ko da suka shiga mota yaso ya daure ya tsaya dan yaga abinda zai faru da yarinyar da bafadansa ya rafkawa sanda. Amman ya kasa saboda shi baya san hayaniya, wannan dalilin ne yasa ko kallon gurin be sake yi ba bare asaka ran zai yi wani abu akai. Har suka je gida bai dena ganin jarumta irin ta wannan zakwakurar yar jaridar ba, da take son taji wani abu daga gare shi. Sashensa na musamman ya nufa kowa ya tsaya daga bakin kofa dan wannan ka'ida ne da indai ya shiga cikin wannan dakin to babu wanda yake shiga sai matarsa ko mahaifiyarsa. Cikin isa da kasaita ta nufo sashen nashi, Bayan jakadiya ta mata iso. dan a kan kunnanta motocinsa suka shigo masarautar, bayin ta suna biye da ita sun sha kaya iri d'aya. Tana zuwa wajan kofar bayin nata suma suka tsaya yayin da ita kuma ta karasa ciki kamar yadda ta taho cikin tinkaho mai nuni da cewar ita d'in matar sarki ce. A zaune ta tarar dashi kansa a kasa ko glasses d'in dake manne a fuskar shi be cire ba. Daman idan da sabo ta saba da duk wasu dabi'unsa, musamman na shariya da kin kallon mutane tamkar wani makaho. Banda wani fitinannan kamshe babu abinda take yi, ta zauna can nesa da shi idanunta a kanshi tace masa. “Sannu da dawowa, shin me yake faruwa ne naji ko'ina ya dauki zance nama kasa gane abinda yake faruwa. Shin me ya faru da kai?” Ya yi shiru tamkar tana magana da gunki da aka sassaka da dutse. Taja tsaki a can kasan ranta dan tasan ko mahaifiyarshi ce a nan gurin take tambayarsa ba amsa mata zai yi ba bare ita da taga wajan baccin shi. “Anyway! Nasan daman ba magana zaka yi. Amman ko da kane ina son ka yi min alama yadda zan fita daga cikin shakkun da nake ciki. Shin kun bige wani ko wata ne a wannan fitar da kuka yi?” Ashe yaji duk abinda take ta fada, sai gashi ya daga mata kai ba tare da bata lokaci ba. Ta jujjuya idanuwa tare da tabe baki. “Ance ai ta mutu ma, Allah ya taimaka ba kai zaka sha azumi sittin ba driver ne da ya yi sanadiyyar mutuwar ta. Sai dai kuma kai ne zaka ba da diyya, tunda kasan dai kai za'a sanyawa ido kaji ko?” Kamar wata uwarsa haka ya kuma daga mata kai alamar 'eh' yaji. Tayi shiru dan tasan ta gama magana dashi ba kuma daga kan zai yi ba. Kusa dashi ta d'an matsa tasa hannu zata zare masa dark shade d'in da ya yi mata shamaki da ganin fuskarshi, ya yi saurin sanya hannu ya rike nata da take shirin cirowa alamar ba ya so. Sai ta kai bakin ta kan hannun nasa tare da sumbatar shi tana cewa. “Yau ma ba zanga fuskar ka ba ko? Shikenan.” Mikewa tayi tabar parlorn dan dama zuwa tayi taji tabbas daga bakin shi kuma taji. Abin da kawai za ta yi shine tasan yadda kudin diyyar da za'a kai sun biyo ta hannunta. Shi kuma abin ne ya yi matukar bashi mamaki jin cewar yar jaridar ta mutu. Ya dinga yin hasbunallahu a cikin zuciyar shi, a ranshi yana jin ashe daman mutuwa za ta yi shi yasa Allah ya ba shi iko da damar daga ido ya kalleta? Rabon da ya yi irin kallon nan ya manta, dan ko mahaifiyar sa ba zai iya tuna rabon da ya kalli kwayar idanunta bare ya gane a wane hali take ciki. Abinda ya sani kawai shine muryar ta da kuma yadda take tafiya. Ranar da kyar ya rintsa saboda abin da yaji na cewar badanshi ya kashe wata yar jarida daga yin tambaya. Duk kafafan watsa labarin da ya kunna da daddare labarin ake yi, sai dai su sunyi sabanin abinda yake jiyo wa a bakunan mutane wato. Yarinyar tana karkashin kulawar likitoci, mutane kuma suna cewa ta mutu rufe maganar ake yi dan kar ace mutanan sarki ne. Sai da safe bayan ya fito fada su waziri suke sanar dashi cewar yarinyar ta farfado kar a damu nan ba da jimawa ba zata koma bakin aikin ta. Be ce komai ba sai da yaji duk wannan firgicin da yake ji duk ya ware baya ji yanzu. •••• A ranar da Dije ta cika kwanaki biyar a asibiti ne yasa sarki Salman ya kirawo wani amintaccen bafadanshi yace yaje ya binciko asibitin da aka kwantar da wacce aka buga, baya son kowa ya san cewar zai yi wannan binciken saboda idan suka ji hanawa zasu yi, sunfi son su ji ana zagin shi a duniya ana cewa bashi da mutunci. Haka aka yi yaje da daddare har asibitin, wanda ya gano shi ne dalilin binciken da yayi na gidan rediyon da take aiki, yaje can suka sanar dashi, shi yasa besha wahala ba wajan ganowa. Lokacin da yaje ya tarar Mas'oud ya fito Shukrah na biye dashi, bafade ya tambayi nurses d'in dake reciption dakin da aka kwantar da ita. Daga nurse din da take kula da ita sai Hameedah dake zaune tana danna waya. Dije kwance idanunta akan kofar tana jiran taga shigowar Shukrah sai kawai taga kayan fadawa irin na jikin wanda ya yi sanadiyyar kwanciyar ta a asibitin yanzu haka. Cike da tashin hankali tayi saurin rufe idanuwa da alama yanzu mugun tsoran shi take ji. Sallamar da ya yi ne tasa Hameedah dagowa nurse din kuma amsa masa tana mai tasowa dan jin abinda yake tafe dashi. “Wani abun ya faru ranka ya dade?” Nurse d'in ta tambaya dan sanin karin bayani. “Daga masarautar Basannabas ne aka umarce ni da nazo naga halin da yarinyar take ciki.” Cikin sauri Hameedah ta taso, tsayawa tayi tana kallon bafaden tare da cewa. “Okay sannu da zuwa, ni Yayar tace.” “Masha Allah, ko zan samu ganin mahaifin ku dan na kara bashi hakuri akan abinda ya faru, da kuma jinkirin rashin zuwan wani daga cikin masarautar Basannabas ?” Wayar ta dago ta shiga kiran daddyn su amman sam taki shiga not reachable. Ta sanar masa ta kasa samun wayar shi amman idan yazo zata gaya masa. Ya kuma kallon Dije wace har lokacin bata bude ido ba saboda haushin su da take ji, ya juya ya tafi. Yana tafiya babu jimawa Alhaji Isma'il ya dawo, suka bashi labari ya jinjina kai, kuma sannan haushin su shima da yake je na rashin nuna kulawarsu akan lamarin ya ragu. Gwamna ne kawai da shugaban yan makarantar da suka yi saukar sune kawai suka yi wani abu akan lamarin sai kuma yanzu da sarkin ya yo aiken dubiya, hannu na dukan cinya ba wani ihsani, a matsayin su na wadanda sune silaaa.. ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥Wannan littafin na kudi ne, AMANA CE, duk wanda yayi mana sharing dinsa shi da ALLAH! Idan kina/Kana so ki/ka karanta ki/ka tuntubi numbobin nan* *0903 234 5899* Or *09033181070* Heart 💓Page 14💓 *** Bayan tsawon lokaci sai ga wani cikin, tayi mamaki sosai dan ta fara tsorata da lamarin cikin nata musamman tun da tsohuwa Hajja kakar su Usman din ta taba ce mata tana zargin akwai sa hannu a yawan barin da take samu, tun daga lokacin sai ta dage da addu'a ba dare ba rana ta kuma yi kokari wajen karantar kowa dake kusa da ita har ma da na nesa, a hankali ta fara gane wannan shine yanayin gidan sarauta,akwai abubuwan da baki ba zai iya fayyace su ba, sai ta sake kame kanta da rage duk wani abu da take yi da. A hankali sai fuskanci komai, ta gane yadda mutanen cikin gidan zasu iya salwantar da rayuwar duk Wanda suka so a kuma lokacin da suka so, hakan yasa ta daina wasa ta zama me kamewa da aiwatar da komai cikin nutsuwa da takatsantsan.    Watarana da daddare bayan tayi ma maimartaba sallama bayan ya bata labarin yadda sukayi da yan uwan sa su Bello akan lallai sai ya kara aure kamar yadda yake a tsarin masarautar shi kuma ya fafure yace sam ba haka zai ba,dan shi akwai boko a tattare dashi dama chan kuma yana son matar sa so ba na wasa ba wanda ya lura kamar hakan na bata ran yan uwan nasa. A kasalance ta dawo daki ta kwanta dan bata jin dadin jikinta, tana jin ta haka sakayau kamar an cire wani abu me muhimmanci a tattare da ita,tana kwance ta saman curtains din dakin ta hangi inuwar mutum,lokacin cikin jikinta ya kai wata bakwai har da doriya, tayi matukar kokari wajen boye cikin dan idan ba kallon ta kayi sosai ba ba zaka gane ba, duk wasu abubuwa da zasu hada ta zama waje daya da mutane har su gane ta daina, ta kuma rok'i Usman akan kar ya sanar wa kowa su jira suga abinda Allah zai yi,da be yarda ba ya dage akan sanin dalili dan shi be ga amfanin boyewar ba tun da abin farin ciki ne amma sai tak'i, ta yi kokari tayi convincing dinsa.    Iska ce ta shiga da karfin gaske, alamun tasowar hadari a lokaci daya, yadda iskar take kad'awa da kuma yadda lokaci d'aya duhu ya mamaye dakin har bata iya ganin komai, tashi tayi a d'an firgice ta shiga kiran sunan amintacciyar baiwar ta, sai dai babu motsin kowa kuma babu alamun akwai wanda yake jin ta ma, ta sani yadda kofar bangaren nata ke cike da masu kula da bangare, sannan a ciki akwai bayi a kalla su bakwai da suke kwana a ciki, biyu daga ciki na zama daf da kofar ko da zata bukace su cikin dare. Mamaki ne ya kamata dan a yadda taji shiru ta tabbata babu kowa kenan a bangaren,toh ya akayi haka?    Takawa ta shiga yi a hankali da nufin fita, wani abu me yauki da bata san da zaman sa a wajen ba ya kwashe ta, tayi wata irin mummunar faduwa da azaba tasa ta kwalla gigitaciyar k'ara kafin a hankali idanun ta su rufe ruf ta daina sanin in da take.     Farkawa tayi ta ganta a kwance, hannun ta sakale da ruwan drip dake shiga a hankali, bin doguwar robar tayi da kallo har zuwa tsintsiyar hannunbta sannan tabi jikin ta da kallo zuwa saman cikin ta, babu komai kamar an shafe shi, da sauri tasa hannu a saman cikin nata. "Sannu da tashi kinji?" Tabi inda akayi maganar ta sauke ganin ta akan ta, karo na farko kenan da tazo in da take tun bayan da tayi aure, kasancewar akwai nisa da tazara sosai a tsakanin su yasa babu wanda ya taba leko tan ita kuma zuwan ta biyu kenan. Idan har lissafin ta ya zama daidai kenan ba yau abinda ya dawo mata aka ya faru da ita ba kenan? Bayan faduwar da tayi bata san me ya faru ba sai yanzu data farka ta ga babar Yayarsu Yaya Muhsina. "Alhamdulillah sannu Maryam." Ta sake cewa, bata iya amsa sannun ba sai tace "Yaya yaushe kika zo? Ina cikin dake jiki na kuma?" "Ciki Kuma? Ai kwana na uku anan sai yau kika farfado babu kuma wanda naji yayi maganar ciki ne dake dan likitan ma naji tana cewa kin auna arziki da baki rasa ranki ba." A hargitse ta kalleta, kafin tayi magana aka bada sanarwa shigowar sa, yana sanye cikin shigar alkyabba fuskar sa a rufe ruf da nadi irin na sarakai, sai d'an siririn glass daya toshe idon sa dashi, a gaban gadon ya tsaya sannan ya yi mata sannu, sai taga kamar an chanja shi, kamar ba Usman din ta ba, me son ta da kula da ita, yadda ya tsaya da yadda yake bin komai da kallo ya nuna mata kamar yau ne zuwan sa na farko, ture tunanin komai tayi dan a lokacin so take kawai ta ji ina cikin jikin ta, sai dai abinda ya bata matukar mamaki be wuce yadda ya zura mata ido kamar a lokacin ne ya fara jin sunan ciki ma, sake tanbayar sa tayi lokacin da likitan ta shigo,ya kalli likitan yace "Ina tunanin bata cikin hayyacin ta, ayi mata allurar bacci kafin ta farka ta dawo hayyacin ta." Sai ya juyo gareta yace "Ina tunanin mafarki kikayi Maryama,baki da ciki dama faduwa kikayi bayan kin zame a toilet, ki kwanta ki huta kinji? Allah ya baki lafiya." Cikin karaji tace "Kamar ya babu komai aciki na? Ni dakai mun san akwai har ma yayi girman da ko da haifar sa akayi zai iya rayuwa amma kace min haka?" Be amsa ba, sai kawai yayi gaban kansa ya fice ba tare da ya gama jin me take cewa ba, tayi yunkurin tashi taji wani azababben ciwo a k'asan cikin ta, runtse ido tayi dan yadda zafin ya shige ta, tana ji tana gani aka sake mata wata allurar.    Bata farkaba sai cikin dare, inda tunanin abinda ya faru ya dawo mata akanta daki-daki, me ya sami mijin nata? Ina danta ko yarta? Idan ma ya mutu ne ai sai ya fad'a mata bawai ya nuna be masan abinda take nufi ba. Tunanin ya taba ta sosai har taji kamar kanta zai cire, kuka take sosai Yaya Mas'udah na bata hakuri bayan ta tabbatar mata da ciwon da take ji a k'asan cikin ta yanka ne, alamun an bud'e wajen an cire abu. Abun da bata san menene ba sai bayan shud'ewar wasu lokuta! Kallon Sultan tayi daya bada nutsuwar sa baki d'aya yana tattara abubuwan da take fad'a masa a kansa kamar yadda yake haddace karatun da yake yi, d'an girgiza kai tayi cikin jin ba dadi tace "Wannan labarin ba labarin kowa bane sai nawa,kadan daga cikin rayuwa ta, wannan shine shafi na farko a cikin abubuwa da na fuskanta, wanda har gobe suke hunting dina down, suka hanani duk wani farin ciki, an zalunce ni ta fuskoki daban daban, an raba ni da abinda ko dabba ce aka rabata dashi takan fita hayyacin ta, har tayi kamar zata zauce, balle ni da akayi min ta inda bani da ikon magana bani da ikon tambayar dan me? Saboda wanda zai tsaya min har yau shima bashi da gamshashiyar amsar da zai bani da zata gamsar dani" Sai ta cigaba "Bayan sati in fama da jinyar kaina da zuciya ta, saboda yadda nake ji a duk lokacin da nayi kokarin yi masa magana akan abinda ke ciki na, amsar sa daya ce be san me nake magana akai ba, nakan had'a kaina nayi kuka na share, har Yaya Muhsina ta tattara ta koma bayan na roke ta akan karta sanar da iyayenmu halin da nake ciki.    Ina kwance bayan na dan samu saukin jikina, hankali na yakai kan wata takarda dake ninke a k'asan kujerar dake fuskantar gadon da nake kai, na tashi da sauri na tsuguna na dauka, na bude ta ina bin rubutun da kallo, da Hausa akayi rubutun sai dai kafin ka fuskanci yadda rubutun yake a harhade sai ka sake karantawa, _"Hakika Allah baya son zalunci, saboda haka addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi, an zalunce ki ta hanyar cire abinda ke cikin ki saboda wani kuduri nasu, aka koma so a halaka shi, sai dai Allah ba Azzalumim Sarki bane,Yayi ikon Sa akan Abinda kika haifa ba tare da sun iya aikata komai ba, Ina fatan watarana, zai zamar musu ciwon idanu, hakan zai yi sanadiyyar bayyanar Abinda Ke Cikin ZUCIYA, komai zai bayyana sannan kofofin zalunci zasu rufu ruf, watarana, ranar da komai zai bude, ban san yaushe ba, amma nasan akwai ranar, zata zo komai daren dadewa!"_ "Na maimaita karatun takardar nan har sai da na dinga jin kalaman na amsa kuwwa a kaina, har sai da na koma ina rayuwa akan abinda takardar nan ta kunsa, zan iya cewa har yau ina rayuwa ne da burin bayyanar Abinda Ke Cikin Zuciyar mutanen da suka wargaza min rayuwa, suka raba uwa da d'an ta, suka kuma ingizata ta aikata abinda har yanzu nake cikin dana sani,nake tsoron haduwa ta da Allah. Ina burin ganin ta, ina so na tabbatar mata da duk abinda ya faru ya faru ne bisa kuskure, rami me matukar zurfi suka hak'a mana suka kuma tabbatar mun fad'a ciki chan k'asa, suka kuma saka k'asa suka rufe mu a ciki ba tare da sun bar wata shaida da zata nuna gaskiyar mu ba. Ta ina zan fara neman ta Muhammad? Ta yaya? Bayan tun ranar babu wanda yace mana ko me kama da ita. Tabbas mutum mugun icce ne, mutum abin tsoro ne Muhammad." "Wacece ita?" Ya tambaya tausayin ta na ratsa shi, sai yake jin kamar yana da wata gudummawa me girma da zai iya bata, amma ta yaya? "Ka shirya jin zalunci mafi girma da muka aikatawa marainiyar Allah, zaluncin da ya kawo mu inda muke yanzu ya ajiye mu ba tare da wani ya sake waiwayen mu ba." "Muhammad kai likita ne, kasan abinda ake nufi da Surrogacy, kasan illar sa, haka kasan hukuncin sa a addinin mu. Idon mu ya rufe, haihuwa kawai muke nema bayan da likita ya tabbatar da mahaifata ta lalace, lalacewar da ba zata iya daukar ciki ba har abadah, tun bayan dana samu labarin na shiga kunci, na daina walwala na kuma chanja komai ya daina min d'adi, na daina farin ciki na zama mafad'aciyar karfi da yaji, ana haka sai maimartaba yazo da shawarar da ta ruguza dukkan komai, bansan wanda ya bashi shawarar ba, idona ya rufe ban iya tsayawa bin diddigi ba na amince da Abinda na san ba daidai bane, haramun ne Allah ya hana, muka shirya da babban likitan da ya kware a aikin wanda shine likita na farko da ya fara irin wannan aikin na dashe a kasar mu, muka kuma samo yarinya bayan dogon bincike da nazari akan yaran dake cikin masarautar da basu da wani galihu, muka kuma samo wadda muke ganin itace daidai,muka kuma aiwatar da kudurinmu akanta." Hawayen take fitar wa sosai, hawayen dake rage mata rad'adin abinda take ji, samun kansa yayi ta zaro handkerchief a aljihun sa,ya mika mata yana jin kukan na taba shi sosai, kallon agogo yayi be san lokaci ya ja sosai haka ba. Murmushi tayi masa bayan ta goge fuskar tace "Na bata maka lokaci ko? Naji ni sakayau bayan dana amayar maka wani shashe na abinda ke cikin zuciya ta, yau zan yi baccin da ban taba yin irin sa ba, nagode da bani damar da ka bani." Folding hannun sa yayi, yana jin at that instant matsalar ta, ta zama tasa, zai kuma yi iyakar kokarin sa ganin ya dawo mata da farin cikin da take cewa ta rasa, zai nuna mata cewa tana da damar da zata fara rayuwa afresh, ta manta da komai da kowa, sai dai yana bukatar yayi dogon tunani akan labarin ta , ya yi masa filla filla yadda zai gane inda matsalar take. Sallama yayi mata ya fito, ya dan yi turus ganin Baba a falon yana jan tasbah "Nagode sosai Muhammad, ina saka ran Maryam zata manta da komai nan kusa ta dawo da rayuwar ta kamar yadda take, ka taimaka min wajen cikar buri na." Ya tare shi da magana tun kafin ya karasa gaishe shin da yake "Karka damu Baba, in Sha Allah zan yi kokari na akai." "Allah yayi maka Albarka." Yace yana gyad'a kansa kamar komai ya kare. ***A kafa yake takawa yana tuna komai daki-daki, yana kuma so ya fitar da daidai da akasin haka a cikin labarin nata, wayar sa dake hannun sa tayi kara kad'an, ya duba da sauri sai yaga kiran Mah-Mah ne ya shigo ya yanke, da sauri ya bi kiran yana tunanin ko Safwan ne ba lafiya, sai dai tun kafin ya gama daidaita wayar a kunnensa abinda be taba tunani ko hasashe ba.    Da sauri ya karasa gidan, dan tsananin tashin hankali be san inda yake wurga kafarsa ba, ba damuwar sa bace abubuwan da zasu je su dawo, damuwar sa daya abinda mutanen da ya dauke su rayuwar sa zasu shiga idan komai ya kwabe. "Ya Aallah!" Yake ta ambata sanda ya tura kofar da yaji ta a bud'e ba tare da ya danna door bell ba, suna zaune su uku, ta dora kanta akan kafar Umma tana kuka sosai, sai yaji ya k'asa garasawa ciki, ya jingina da kofar ya jin wani iri, rana ta farko da ya ji bashi da confidence din fuskantar mutane, be san me zasu ce masa ba, haka be san amsar da zai basu ba a yanzu da shi kansa be san waye shi ba. KUNA BUƘATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA'ARKU A PAGES ƊIN BOOKS ƊIN ZAFAFA BIYAR 2021?. To kuzo ga dama ta samu💃🏻💃🏻.         Ina ma'abota son a tallata musu hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?. Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon haziƙan marubanku ƴan biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da saƙo ta dalilin shafukan littatafai. Ga duk mai buƙatar a saka masa tallan kayan sana'arsa a shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntuɓar waɗan nan Numbers 0903 234 5899 or 09033181070 ta WhatsApp, idan har agama buks ɗin kana buƙata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauƙi. Idan kuma wasu adadin pages kake buƙata koda ɗaya ne duk zamu saka maka akan farashi mai sauƙin gaske🤓. Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike neman sauƙi😻😻😄🤗. ______________________ _ZAFAFA BIYAR 2021_*🔥 _*SUKAR BAYA*_💚 _BILLYN ABDUL_ ( _kwai cikin qaya_ ) ( _raina kama_) ( _wutsiyar raqumi_ ) *_SIRADIN RAYUWA_*💛 _SAFIYYA HUGUMA_ ( _alqawarin Allah_ ) ( _daurin boye_ ) ( _Dangantakar zuci_ ) 💙 _*KIBIYAR AJALI..*_💜 _MISS XOXO_ (Sulke baya tsare ta sai ta wuce) ( _Igiyar zato_) ( _Kaimin halacci_ ) ( _Naufal_ ) *_ABIN DAKE CIKIN ZICIYA_*🧡 _HAFSAT RANO_ ( _ruhi daya_ ) ( _Sauyin qaddara_ ) ( _Daurin goro_ ) *_MIN QALB_*❤️ _MAMUHGEE_ ( _buri daya_ ) ( _tarayya_ ) ( _eznah_ ) Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 0903 234 5899 IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 09033181070 Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥Onar Tasfah 15💓 ***Ajiye wayar tayi tana kallon Hajiya Ummah "Abinda nayi kuwa ya dace?" Mah-Mah tace tana zama a kusa da ita "Kinga matsalar ki ai, kun dauko yaro kun ajiye shi a gidanku wai ku tausayi, gashi nan kina kallo idan baki yi wasa ba zaki rasa d'an naki k'waya d'aya tal a duniya, ke kin samu dayan ma mu kuwa fa? Idan nice da Safwan sai in da karfi na ya kare wajen ganin na masa abinda yake so, bare yaron nan bashi da kowacce matsala zuciyar sa fes take yana kaunar duk wanda ya rabe shi, amma ni dama sam Sultan be min ba, kawai kar kayi magana ne ace dan baka haihu bane baka san zafin d'a ba, amma ni kallo daya nayi masa nasan a karshe shine zai zamar muku matsala." "Amma Ya Ummah Sultan bashi da wata matsala tun tasowar su, ina jin kamar ban kyauta ba abinda na gaya masa." "Sai kiyi ta ganin rashin kyautawar kinji, ita fa wannan rayuwar kowa kansa fa ya sani, ina laifi ma abinda kukayi masa, gata dai daidai gwargwado ai kun masa, wanda nasan ba dan ku ba toh da har ya bar duniya ba zai taka inda ya taka a yanzu ba." "Haka ne." Tace tana son d'ora zancen Hajiya Umman a mazaunin da take kokarin dora mata shi Abinda ya faru shine, mahaifiyar Umaimah ce ta kira Mah-Mah tayi mata maganar a matsayin wanda ita Umaiman take so, bayan sun ajiye wayar ne Mah-Mah tayi ma Afrah magana a WhatsApp dan duk tunanin ta Sultan da Afran sun daidai ta kansu dan a yadda taga suna yi kafin ya tabi tayi ta adduar hasashen ta ya zama gaskiya, shiyasa ma da Safwan yazo da maganar Amrah taji dadi tayi kuma yiwa sultan fatan samun Afran, maganar Umaimah tasa ta son jin wani abu daga bangaren Afran kafin ta tuntubi shi sultan din, idan tasan akwai wani abu tsakanin su toh zata san yadda tayi ta bawa Anty Aminan hakuri ba tare da Sultan din ma yasan abinda ke faruwa ba balle yaga rashin kunyar Umaiman da mahaifiyar ta. Sai dai kuma abinda taji wanda yasha banban da abinda take tunani yasa zuciyar ta, ta kad'a tsoron abinda zai samu Safwan dinta ya shige ta, ta tabbata idan ya samu labarin Sultan ke soyayya da Amrah daya kwallafa rai zai iya hakura, hakan kuma na nufin me? Tayi ta faman sakawa da kwancewa akan abinda ya kamata tayi, kafin komai ya kwabe musu, sai dai abu daya da yayi mata zafi ainun shine tasan tabbas Sultan yasan da maganar Safwan din tunda tasan babu yadda Safwan zai yi wani decision a rayuwar sa ba tare da sanin Sultan din ba, ta kuma tuna da kanta ta tambayi Safwan din bayan an sallamoshi daga asibiti, ta kuma bashi shawarar ya sanar da Sultan , kenan ya san komai amma yayi gaban kansa ya manta da komai yake kokarin kafa kansa,bayan yasan halin da Safwan din zai shiga idan komai ya bayyana? Wannan tunanin ne ya kara bata mata rai ainun, a haka Hajiya Umma wata yar uwar ta da suke kusan sa'anni a dangi ta shigo ta sameta, ta manta ma shaf sunyi waya tace zatazo, sai da ta ganta ta tuna, ta kuma kasa rike abinda yake cikin zuciyar ta, sosai Hajiya Umman ta shiga ingizata, da kalaman da suka sata aikata abinda zai iya zamar mata dana sani anan gaba. Farko dai shiryawa tayi a gurguje suka fita a motar Hajiyan Umman da drivern ta, zasu fita daga layin Safwan ya shigo, ya tsaya suka gaisa da Hajiya Umman sannan Mah-Mah tace masa yanzu zasu je su dawo. Adawo lafiya yayi musu ya wuce cikin layin su kuma suka fita. Kwatance Mah-Mah ta dinga yiwa drivern har suka isa kofar gidan, ya faka daga chan gefen gidan, Hajiya Umma ta kalli Maman tace "Ta sanki ne?" "Eh ta sanni." Ta amsa tana jin wani shashi na zuciyar ta na yin rauni, tana jin kamar abinda zata suke shirin yi be kamata ba,sai dai da ta tuna saboda Safwan zatayi, saboda samar masa lafiya sai taji wannan bangaren na Zuciyar ta na danne wanchan. "Ki zauna anan, bari naje ni nasan me zanyi." Sai ta bud'e kofar ta fita,ta nufi gidan. Kamar an dasa Mah-Mah a wajen ta k'asa cewa komai har ta shige ciki, kamar tace ta dawo amma sai ta hau karfafa kanta da tunanin abubuwan da Hajiya Umman tace mata. Da sallama ta shiga gidan, Hajiya na na zaune tana kallon Arewa 24 ta amsa tana mata maraba sannan ta nuna mata wajen zama, maimakon ta zauna sai ta yi zaman dirshan gaban Hajiya cikin girmamawa ta gaida ta, ta amsa mata a sake duk da bata gane ta ba, lankwashe murya tayi cike da son tura sakon da tazo dashi cikin kan Hajiyan "Hajiya magana ce me matukar muhimmanci ce ta kawo ni, kinsan yadda zamanin nan ya zama, shiyasa mutane yanxu basa taimako, domin idan ka taimaki mutum ka dauko shi daga rana ka kawo shi inuwa, sai yayi kokarin turaka ranar." "Haka ne kam." Hajiya tace cike da gamsuwa. "Toh abinda ya kawo ni Hajiya akan jikar ki ne Amrah." Gyad'a tayi ta sake gyara zama jin an ambaci tauraruwar zuciyar ta "Wani abun Amratun tayi ko ya akayi?" "Ko d'aya Hajiya, wato abinda ke faruwa shine..." Sai ta dauko labarin dauko Sultan daga orphanage din nan,da kawo shi gidan da duk abubuwan da suka faru da yadda aka rike shi tamkar Safwan, sannan sai ta gangaro kan rashin lafiyar Safwan din, ta karkare da cewa "Toh kinji duk wannan alkhairin da akayi wa yaron nan, ashe shi sam ba haka bane a cikin zuciyar sa, babu wanda yake son ganin baya irin Safwan da iyayensa ba kuma ya san cigaban Safwan din ko k'ad'an, hakan tasa da yaji maganar dake tsakanin Safwan din da Amrah sai da yasan yadda yayi ya shiga tsakani, ance ma Amrah bata son shi da farko tunda dama chan ita Safwan take so, toh ba'a san ya akayi ba sai gashi yanzu ta k'ek'ashe k'asa tace sam shi take so, ta kuma ciwa Safwan mutunci har ta kaishi da kwanciya asibiti, wanda likita yace Zuciyar shi daf take da daina bugawa idan har be sami abinda yake so ba..." Sai ta saka kuka kamar gaske tace "Baki ga yadda yar'uwata mahaifiyar Safwan din ba ta fige ta lalace saboda tunani, gashi taki yarda ayi ma Sultan din magana a tsawatar masa saboda Zuciyar musulunci irin tata, ni tsoron da nake ma Allah yasa ba asirce miki jika yayi ba tun da kinga yana chan tare dasu." Sai kuma ta hau girgiza kai "Ai babu wani dogon tunani ma tabbas abinda yayi kenan, gashi baka san asalin yaro ba ma karka dau yarka ka bashi azo gaba akeji, tunda kinga su iyayen da suka rikeshi tsakani da Allah ma be barsu ba ballantana kuma matar da take ikon sa idan ya aureta, ai sai abinda yayi." Iyakar baci ran Hajiya ya baci, a rayuwar ta ta tsani cin amana da duk wani abu da xai shafe ta, iya zaman su da mutanen nan basu taba ganin wani abu da zai nuna cewa ba sune suka haife shi ba, amma ya rasa ta inda zai saka musu sai ta kashe musu d'an nasu k'waya d'aya,aiko in dai tana numfashi hakan ba zata taba faruwa ba, aure da Safwan da Amrah kamar anyi an gama indai ita ta haifi Abban nasu. Mikewa tayi tsaye ta ce "Nagode sosai da wannan labarin da kike zo dashi, a yau ba sai gobe ba zan nuna mishi ni ke da iko da d'ana da jikokina, zan kira iyayen Safwan din suzo a tsaida maganar rana, dan bazan yarda jikar tawa mafi soyuwa a gareni ta fad'a hannun da zamu zo muna dana sani. Shiyasa aka ce tsintacciyar mage... Allah ya kyauta." "Amin." Tace tana sakin murmushi ba tare da ta bari hajiyan taji ba, sai ta mike ta gyara zanin ta sannan ta bud'e jakarta ta ciro kudi duhu biyar CIF ta ajiye a gefe "Gashi Hajiya aci goro." Kallon kudin Hajiya tayi ta girgiza kanta "Gaskiya ba zan karbi kudinki ba a wanne dalilin?" Ta kura mata ido da kallon dake nuna kamar tana son karantar yanayin ta, da yake gogaggiyar mace ce sai tayi saurin wayance wa tace "Haba Hajiya karki dauki wannan kudin da wata manufa, ko daya ba abinda kike tunani bane, tun kafin na zo nayi niyyar siya miki goro dan ni wallahi daya na dauke ki da Hajiya ta, dan idan ba me son ka ba, babu me zuwa ya sameka akan abinda ya shafi ahalinka, ki dauki wannan kudin a matsayin kyauta daga d'aya daga cikin yayan ki ki samin albarka dan Allah." Jinjina kai Hajiyan tayi dan bata da bakin magana kuma sai kawai tace "Allah yayi albarka nagode." "Amin." Ta amsa sannan tayi mata sallama ta fita. Mah-Mah na hango ta, ta bud'e kofar motar, tana jiran ta karaso dan har ga Allah hankalin ta ya kasa kwanciya akan abin, da hannu ta nuna wa driver alamar ya shigar da kayan sannan ta zauna a wajen zaman ta "Albishirin ki?" "Goro." Mah-Mah ta amsa sai dai kana jin yadda muryar ta,ta fita zaka gane kamar akwai d'an tsoro, tsoron abinda kunnuwan ta zasu jiyo mata. "Komai dai an gama dan Hajiya ta tabbatar min a yau zata kira mahaifin yarinyar sannan zasu aiko wakilan sa suzo asa musu rana kinga kowa ya huta kenan." Kada kai Mah-Mah tayi, sannan tace "Me kike fad'a mata da ya fusata ta haka?" "Me na fad'a mata kuwa? Bayan gaskiya, na fad'a mata waye Sultan a wajenku, na kuma bata LABARIN komai, na tabbatar da ban bar gurbi daya a cikin kanta da zai bata damar tunanin ko sharri aka masa ba..." Sai ta bawa Mah-Mah labarin komai ba tare da ta rage komai ba, ta rikice sosai ta fara fad'a "Haba Yaya Umma ya zakiyi haka, wannan sam be kamata ba." "Kinga dalilin da yasa ake cutar ki ko? Ke saukin kai shikenan kina kallo za'a kashe miki d'an kina wannan tsoron naki." "Amma ai da ba ta haka akayi ba." "Ta yaya za'ayi kenan? Lokaci fa ta fiya yake, kinga idan fa baki koyi yadda zaki tackling problem tun da wuri ba wallahi a ciki zaki dinga kwana, ni dai nayi Abinda nake ganin shine daidai, kuma ba komai yasa ni yin hakan ba sai dan naga hakan shine daidai, sannan kuma na dauka Safwan nima d'ana ne zan iya zartar da komai akansa..." "Amma idan hakan be miki ba, toh Allah ya baki hakuri da na shiga Abinda bani da iko akai." Ta karashe tana kallon window alamun bata ji dadi ba "Kiyi hakuri ni ba da wata manufa da fada ba." "Shikenan." Tace ta kuma cigaba da zuzuta abin har sai da Mah-Mah ya yarda hakan shine daidai. Da suka koma gida ta saka ta, ta kira Sultan akan ta tambaye shi, ta kuma kira,sai dai amsar daya bata kai tsaye tasa ta sake gasgata maganar Hajiya Umman. Da farko ta tambaye shi ya karatu,sannan tace ko yasan abinda ke tsakanin Safwan da Amrah, kai tsaye yace mata Eh dan shi be gane komai ba, aikuwa ta rufe shi da fad'a ta kuma fad'a mishi abinda be taba tunanin zata iya fad'a mishi ba, ba sunayen da ta kirashi dashi bane suka fi damun sa, cewa da tayi baya son Safwan yana so yaga bayansa ne yafi d'aga masa hankali, yayi kokarin fahimtar da ita abinda take tunani ba haka bane amma sam ta maki bashi damar hakan, tace kuma yaje dan ta tabbata sako ya riski gidan su Amrah tunda hakan ya zaba. Hankali a tashe a Isa gidan, ya kuma tsaya ya kasa motsawa yana jin yadda sautin kukan ta ke fita a hankali. Jin kamar motsi yayi ya dago kansa da sauri,Umma ce a tsaye gaban sa, fuskar ta babu yabo babu fallasa tace masa "Kayi hakuri Sultan, kowanne bawa da ka gani a duniyar nan da tashi kalar jarabawar,wannan yana cikin taka kalar jarabawar, ina fatan zaka karbe ta hannu biyu ba tare da ka matsa da tunanin me yasa hakan ta faru dakai ba, hakika Allah ne shaida ta, naso tarayyar ku da Amrah, ina kuma so har yanzu ba wai na daina bane, sai dai dukkanin mu a karkashin ikon Hajiya muke, dole ne duk abinda ta yanke mu bi idan har muna son ganin daidai a rayuwar mu, ba wai kuma dan mun yarda da abinda aka samu wasu suka je suka fad'a akan ka ba, sai dan kasancewar ta uwa a garemu." Sai ta juya ta fara kokarin barin wajen "Kayi hakuri watarana sai labari." "Nagode Umma." Yace yana murmushi sannan yace "Komai aka fad'a akai na gaskiya ne umma, bani da kowa hasalima bansan waye ni ba, sai dai ban taba jin hakan a matsayin wani abu da zai hanani rayuwa me inganci ba, nasan ubangijin da ya halicceni Ya fini sanin dalilin da yasa Ya kaddara min rayuwa ta a haka,ina kuma gode Masa bisa ga ni'imomin da ya lullube rayuwa ta dasu." "Madallah da kai, Allah yayi maka albarka." Ciki ta wuce ta dangana da dakin ta na kwana dan tana bukatar hutawa, tun bayan kiran Hajiya da tayi wa Abba, ta kuma jaddada masa akan lallai lallai duk abinda ya rage masa a kasar nan ya kammalashi nan da d'an lokaci kad'an ya tattaro ya dawo gida sannan ta kuma jaddada masa auren Safwan da Amrah ba fashi ta kuma bashi LABARIN abinda aka ce akan sultan din, yayi mamaki sosai sai dai daga shi har Umman basu yarda Sultan zai iya aikata cutar wa ga kowa ba balle Safwan da duk suka shaida da irin yadda suka shaku da junan su. Saboda haka ya tara yaran nasa ya sanar dasu abinda mahaifiyar sa tace ya kuma bawa Amrah hakuri ya roke ta da tayi musu biyayya in Sha Allah zata ga daidai a rayuwar ta. KUNA BUƘATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA'ARKU A PAGES ƊIN BOOKS ƊIN ZAFAFA BIYAR 2021?. To kuzo ga dama ta samu💃🏻💃🏻.         Ina ma'abota son a tallata musu hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?. Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon haziƙan marubanku ƴan biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da saƙo ta dalilin shafukan littatafai. Ga duk mai buƙatar a saka masa tallan kayan sana'arsa a shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntuɓar waɗan nan Numbers 0903 234 5899 or 09033181070 ta WhatsApp, idan har agama buks ɗin kana buƙata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauƙi. Idan kuma wasu adadin pages kake buƙata koda ɗaya ne duk zamu saka maka akan farashi mai sauƙin gaske🤓. Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike neman sauƙi😻😻😄🤗. ______________________ _ZAFAFA BIYAR 2021_*🔥 _*SUKAR BAYA*_💚 _BILLYN ABDUL_ ( _kwai cikin qaya_ ) ( _raina kama_) ( _wutsiyar raqumi_ ) *_SIRADIN RAYUWA_*💛 _SAFIYYA HUGUMA_ ( _alqawarin Allah_ ) ( _daurin boye_ ) ( _Dangantakar zuci_ ) 💙 _*KIBIYAR AJALI..*_💜 _MISS XOXO_ (Sulke baya tsare ta sai ta wuce) ( _Igiyar zato_) ( _Kaimin halacci_ ) ( _Naufal_ ) *_ABIN DAKE CIKIN ZICIYA_*🧡 _HAFSAT RANO_ ( _ruhi daya_ ) ( _Sauyin qaddara_ ) ( _Daurin goro_ ) *_MIN QALB_*❤️ _MAMUHGEE_ ( _buri daya_ ) ( _tarayya_ ) ( _eznah_ ) Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 0903 234 5899 IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 09033181070 Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥         Abinda Ke Cikin Zuciya Page 15 Hafsat Ranowww.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac. _*ASSALAMU ALAIKUM SISTERS..!_* _*INA MASU NEMAN INDA ZASU SAMU INGANTATTUN: _* _*HERBALS APHRODISIAC MA’ANA NA GARGAJIYA BANA HADIN BATURE BA MAI SIDE EFFECT..?_* _*TO KU MATSO, DOMIN NESA TAZO KUSA.._* _*ZEE HERBALS APHRODISIAC_* _*ZEE HERBALS APHRODISIAC_* _*ZEE HERBALS APHRODISIAC_* _*MUNZO MUKU DA INGATTTUN KAYAYYAKI WANDA ZASU GYARA KI CIKI DA WAJE_* _*MUNADA SUPPLEMENT MASU GYARAN JIKI DANA FATA, WANDA ZASA SAKI KIYI SHEKI FATAR KI TAYI LAUSHI. TAYI LUWAI LUWAI TAMKAR TA JARIRAI_* _*AKWAI SUPPLEMENT NA KAYAN MATA WANDA ZASU GYARA KI, KIJI KI TAMKAR BUDURWA, SUPPLEMENTS DINMU BASU DA SIDE EFFECT, DOMIN AN HADO SU NE DAGA INGATTATTUN ITATUWA, WATO NATURAL PRODUCTS NE ACIKI._* _*KAI BA ANAN KADAI MUKA TSAYA BA, MUNA DA INGATTUN KAYAYYAKIN MATA WANDA KESA KISHIYA KWAFA, WANDA DUK INDA SARAUNIYA TAKAI KIN WUCE, WANDA ZASU TSATSO MIKI MARTABAR KI DA KIMAR KI_* _*AKWAI INGATTATTUN MAGUNGUNA, NA CUTUTTUKAN DA SUKA SHAFI DAN ADAM DAMA JINNU.. KAI DAMA WANDA BAMU AMBATA BA.. ZEE HERBALS APHRODISIAC (MASARAUTAR INGATTATTUN MAGUNGUNA KENAN)_* _*KYAU, ARHA, INGANCI, RAHUSA... SAI ZEE HERBALS APHRODISIAC_* _*MANHAJOJIN MU NA SOCIAL MEDIA: KAMAR INSTAGRAM DA WHATSAPP DAMA NAMBAR TARHON MU: DOMIN SHIIGA KUGA IRIN KAYAYYAKIN MU TUNTUBE MU TA_* _INSTAGRAM LINK DIN MU:_ www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac _WHATSAPP LINK DIN MU:_ https://Zeeherbalsaphrodisiac.whats.bz _NAMBAR TARHON MU_ 08169380189 _*DA A BAKA LABARI GWARA KA BAYAR.. KIZO A DAMA DAKE YAR UWA, KI ZAMO DAYA DAGA CIKIN KASAITATTUN MATA MASU AJI.. MUNA GARIN KATSINA, SANNAN KAYAN MU MUNA BADA SU AKAN FARASHIN SAYA ‘DAI DAI KO SARI.. MUNA TURA KAYAN MU A KO’INA A FADIN NAJERIYA._* _*BE YOUR OWN BOSS, BUILD YOUR OWN EMPIRE, BE THE WHOLE WORLD OF HIS MAJESTY( YOUR HUBBY) BE THE ONLY CENTER OF ATTRACTION WITH ZEE HERBALS APHRODISIAC. OUR PRODUCTS LASTS LONGER AND VERY EFFECTIVE. NO SIDE EFFECTS. AVAILABLE N WHOLESALE/ RETAILS.. DELIVERY IS NATIONWIDE. 100% TESTED AND TRUSTED_* _*17/18_* *MASARAUTAR BASANNABAS* Bashi da wata dama ko karsashi da zai kaiwa wani kukansa bare a ashere mishi. Kiri-kiri yana son bayyana abu a zahirance amman sai ya kasa, yaji tamkar ana shake masa wuya. Tsaye yake jikin taga yana hangen duk wani motsin masu yawo a can harabar gidan, sannu a hankali ya hango mahaifiyarsa tana tafiya jikin ta sanye da mayafi, wanda alama suka nuna daga wani wajen ta dawo. Salman ya dauke fuskar sa daga kallon ta tare da takawa a hankali yaje ya zauna daga kan kujerar da ya taso. “Assalamu alaikum.” Cikin ransa ya amsa be ce komai ba bare ya dago dan ganin wace ce, muryar ta kawai ta shaida masa cewar jakadiya ce. “Allah ya taimaki sarkin sarakuna, an buga an barka mazan fama. Uwar gida kuma gimbiya tace a yi mata iso wajan ka.” Kamar yace a'a saboda shi a yanzu yana da bukatar nazari akan abin da yake shirin yi na auran da zai yi, yana so ya zurfafa tunaninsa ta yadda zai yi ya ware inda zai sanya amaryar idan an daura aure an kawo ta gidan, saboda yasan dole azo a nemi muhallin da zai ajiye ta. Da yake Jakadiya tasan halinsa na shariya, hakan yasa ranta be baci ba har lokacin da ya ga dama yace mata. “Kice bacci nake ji.” Ta kuma russunawa tare da sunkuyar da kai cike da girmamawa tace. “Gyaraaa kintse sarkin sarakuna, zanje na gaya mata kamar yadda kace.” Shi dai be kuma cewa komai ba har ta fita daga dakin, yana zaune ya rasa wane irin tunani zai yi. Jakadiya ta kuma dawowa da alama ma dai ita kanta uwar gidan nashi tana bakin kofa dan yaga Jakadiyar ba ta jima da fita ba yaga ta dawo, yaja tsaki a cikin ransa, zuciyar shi tana zugi saboda wasu mutum biyu da kwakwalwarshi take ta son tuna masa ko su waye a gurin shi amman ya kasa tantance ainahin su. “Allah ya ja da ran sarkin Basannabas, uwar gida tana neman afuwa dai akan son ganin nan naka. Tace kanta bisa wuya, ka tausaya ka bata damar shigowa ciki.” Hannunsa kawai ya daga kuma Jakadiyar ta fahimta dan tashi kawai ta yi taje ta sanar da ita sai gata ta shigo. Tana shiga Jakadiya ta yi sauri ta nufi sashen Gimbiya Jaleela wato kishiyar mahaifiyar sarki Salman. Hango ta tayi tana sakkowa daga bene cikin shiga ta alfarma, tana hango Jakadiya ta kuma tsuke fuska dan dama bata sakar mata fuska duk kuwa da irin yadda munafincin da take kawowa daga lungu da sakon cikin masarautar. “Takawarki lafiya farin cikin marigayi sarki Aliyu, uwar marayun masarautar Basannabas, farin ciki da walwalar bayin Basannabas. Allah ya kara miki lafiya da nisan kwana uwar daki na mai share min kuka.” Sai da tazo ta zauna ta gyara zama sannan ta kalli Jakadiya cike da iko tace. “Jakadiya meke tafe dake? Ina fatan dai kin zo min da labarin da zai sanyaya min zuciya ta.” “Ina neman afuwarki uwar daki na, sai dai wannan labarin da nazo miki dashi ban san yadda zaki dauke shi ba.” “Ina jin ki Jakadiya.” “Dama yanzu Gimbiya Shaheedah tasa nayi mata iso wajan maimartaba sarki, yanzu haka tana can gurin sa zasu yi ganawa ta musamman tsakanin su.” A fusace Gimbiya Jaleela ta kalli Jakadiya tana hararata tace. “Me nace miki game da cewa Salman sarki?” “Ki gafarce ni Uwar daki na tuba nake Allah ya huci zuciyar ki, sha'afa nayi wallahi ki yafe min.” “Shikenan amman ki kiyaye gaba. Ina so kuma ki binciko min abinda taje suka tattauna, bana kuma son kuskure kin sani dai.” “Insha Allahu uwar daki na ba za a samu wani kuskure ba, Allah ya ja zamanin ki.” Daga haka ta mike ta fita tana rawar jiki. Bata wuce ko'ina ba sai sashen Gimbiya Najwa wato kishiyar Gimbiya Jaleela, wace ita ce matar marigayi sarki Aliyu Salman ta uku, yar Galadima ce. Ita kuwa tana kishingide a tsakiyar katafaran parlorn ta, hadimanta suna ta faman yi mata fifita, wasu na matsa mata kafafuwa yayin da wata ke gefe tana yanka mata kayan marmari d'aya bayan d'aya tana sha. Gimbiya Najwa na ganin Jakadiya ta yi saurin sallamar hadiman nata, dan tasan tabbas labari ne ta kawo mata game da Sarki Salman ko Gimbiya Shaheedah ko kuma mahaifiyar sarki Salman d'in wato Gimbiya Sa'adatu. Jakadiya daman tasan halayen ko wacce mata dake gidan, saboda duk itace munafukar su, wajan kai gulmar ko wacce a gurin d'aya. Tasan daman Gimbiya Najwa ba zata tambaye ta komai ba har sai idan ita ce ta fara yin magana, wani lokacin Jakadiya takan jinjinawa irin girman kanta da takamarta saboda kawai tana yar Galadima, da ace a yar gidan sarkin kacokam Allah ya yi ta bata san me zata yi ba, duk da cewa a wannan lokacin su Waziri da shi Galadiman sune suke jan ragamar sarautar Sarki Salman, sai abin da suka ce shi za'a yi. “Na gaisheki ta gaban goshin marigayi sarki Aliyu... Jinjina da ban girma gareki shalelen Baba Galadima, uwa ga magajin sarki wato yarima Ilyas(junior). Nazo miki da wani labari.” Kamar ba zata amsa ba tsawon lokaci, sai da ta mulu ta mulmule sannan ta kalli Jakadiya karo na biyu tace. “Idan kin san maganar ba ingantacciya bace karki sanar dani, ki bari idan kin tabbatar da ingancinta, sai kizo ki gaya min.” “Na kuma gaisheki ta gaban goshi, tabbas bani da gamsashiyar magana akan abin da nazo miki dashi. Kamar yadda kika ce, zan koma idan na gama tabbatar da ko menene zan dawo. Na barki lafiya, farin cikin yarima kuma sarkin gobe, shalele Ilyas.” Tufa d'in dake hannunta taci gaba da ci ba tare da ta sake bi ta kan Jakadiya ba, saboda ita Gimbiya Najwa tana da wasu munafukan bayan Jakadiya, dan ita a cewar ta idan wata taga wani abun, wata be zama lalle ta gani ba. Hakan yasa ta rarraba kafa ta baza masu gano mata sirrikan duk wata mata dake cikin gidan. Shi yasa Galadima yafi waziri sanin duk wani abu da ya shafi Gimbiya Shaheeda da kuma sirrin mahaifiyar sarki Salman. Can kuma bangaran Sarki Salman da uwar gidan sa wato Gimbiya Shaheeda, tana shiga ta zauna gefen shi tana tsotsar alawar da take cikin bakin ta tace dashi. “Wani lokacin kakan yi min abin da sam be dace ba a gaban kaskantattun mutane, wato hadimai. Ya za'ai kamar ni nace ina son yin magana da kai kace a ce min bacci kake yi? Karka manta ban da ni babu wacce zata iya zama da kai bayan kowa yasan cewar ba da kwan haihuwa, ba zaka iya bawa Basannabas magaji ba kamar yadda marigayi ya bar maka gadon mulkin sa wanda kake a kai yanzu.” Jin kalamanta yasa ransa fara tafarfasa saboda zafin su da yaji, bata da wani abu da take yawan yi masa gori irin rashin haihuwar sa. Amman saboda tsabar shakkarta da yake yi sai bai ce mata komai ba har ta kuma yin magana. “Ni wallahi kasan ba da ban soyayyar da nake yi maka ba, da tuni nasa ka sauwake min naje nayi wani auran na haihuwa. Amman saboda na san babu matar da zata iya auran ka yasa nake daurewa ina lallashi zuciya ta akan ta hakura ta zauna tare da kai.” Ta yi shiru na dan wani lokaci, shi kuma wata irin tsanarta ce take sake zama sabowa a zuciyar shi. Shi be ki ta ce ya sauwake mata ba indai har tana da bukatar yin haka, baya jin komai a game da ita sai zallar shakka da son bin duk wani abu da take so. Kansa a kasa dan ko da ta shigo be dago ya kalleta ba sai ji ya yi tace. “Honey dago ka kalle ni.” Ta na rufa baki kuwa ya daga yana kallanta, ta yatsina fuska tare da mika hannu ta zare bakin glasses d'in idan shi yadda zata ganshi sosai. “Haba Honey, ba na hanaka kallo na da wannan glasses d'in naka ba? Na yi na yi da kai ma ka dena saka baki amman ka kasa bari, idan ka sashi kamar wani tsohon makaho wanda bashi da d'an jagora.” Da yasan wannan maganar ce zata kawo ta da duk yadda zai yi sai ya hana su hadu, sai dai ance rashin sani yafi dare duhu. Kuma idan da sabo yaci ace ya saba da duk wasu abubuwa da ake yi masa a masarautar. Ita kuwa kallon shi kawai take yi tana jin wata zazzafar kaunar shi, hakan ne yasa bata son taji ana cewa ya kara aure shi yasa take kuma rike shi ta hanyar da zuciyarta ta aminta. “Sannan kullum nice nake nema ka kai babu wani abu da yake damunka. Ina tunanin rashin haihuwar nan taka tana da nasaba da rashin sha'awa da baka da ita. Ko kai kayi zaton sarakuna basa mu'amala da matan su?” Salman ya yi shiru dan shi sam ba wani farin ciki yake ji ba idan suna yi. Shi kawai yana yi ne ko Allah zai sanya ya samu rahama, ya kuma fita a hakkin ta na aure. Ganin ba zai yi magana ba yasan yata tashi tana murmushi ta wani jujjuya ya masa kugu ya kawar da kai, ba burgeshi take yi ba, hasalima ji yake tamkar ya fashe da kuka dan haushi da takaicin abin da take yi. Tana fita ya sauke ajiyar zuciya tare da rintsa ido kawai ya hangi Dije tana ta yi masa murmushi a wajan fuskar shi. Sai ya samu kansa da kin bude idon yana jin wani dadi a yadda yake ganin ta. Kiran sallar magariba shine ya tayar dashi daga gurin, ya shiga toilet ya daura alwala daga nan ya shirya ya fito zuwa masallaci dan kagabar da sallah. °°°°°°°° °°°°°°°°° °°°°°°°°°°° Tun da ta idar da sallah ta mayar da goshinta kasa bata sake dagowa ba, addu'a kawai take yi tana zubar da hawaye. Cikin kaskantar da kai take gayawa Allah muradanta duk kuwa da cewa tasan yasan tana cikin halin bukatar taimakonsa. Sannu a hankali ta dago fuskarta sharkaf da hawaye, tasa bayan hannunta tana sharewa. Gimbiya Sa'adatu kenan wato mahaifiyar sarki Salman, mace mai tsantsar hakuri da juriya tare da kawar da kai. D'an ta ne, amman ba ta da wani iko akan shi, daga nesa kawai suke hango junan su amman basa haduwa face to face saboda an riga an janye mata shi daga gareta. °°°°°°° °°°°°°°° °°°°°°° Kishingid’e gimbiya shaheeda take a doguwar kujera dake tafkeken parlorn ta na alfarma. Wanda komai na cikin parlorn kirar samfarin kayan sarauta ne wanda turawa kewa laqabi da ‘Royal design’. Kai hatta salular da ke saqale ajikin da bango itama ta Royal ce. Bayinta biyu ne a zaune kowanne yana mata tausa a kafa d’aya d’aya. Sai lumshe idanu take ahankali tana mai cigaba da taunar tufar dake hannunta, Wanda take gutsira ahankali cikin k’asaita. Wayar tace dake kusa da ita tayi haske alamar saqo ya shigo, Sai data mula tasha iska tukun sannan ta daga wayar ta duba. Ta jima kafin ta daga musu hannu alamar su dakata, Sannan ta mike ta gyara zaman wani hadadden mayafin jikin ta mai beza. Bayin guda biyu suka bi bayanta kowacce kanta a kasa. Sashen su ta nufa, Dake dare ne, Tarwar masarautar take da hasken lantar ki. Tsuntsaye nata kuka. Shiga tayi cikin wani babban parlor. Duk sun hallara aciki, Kowacce tana hakimce a kujera tana jin kanta. Kallo d’aya zakai musu kasan manyan mata ne masu aji, Wanda ke watayawa a duniyar masu kudi. Gaishe su tayi. Ta samu waje ta hakimce itama. Bayin dake wajen duk suka basu wuri. Babbar matar ta tsakiya dake hakimce ta mike kafafun ta akan center table itace tafara magana, “Shin ya sanar muku da halin da ake ciki kuwa....?” “Hmm! Ki bari kawai.. Mun fara sanya fa. Yacemin kwana biyu ya kasa gane kansa.” Cewar Haj Huwaila ta bawa Haj Jaleelah amsa tana tana jijjiga kafafu. “Shin Gimbiya Shaheeda kin fara ganin alamun canji kuwa?” Haj Najwa ta tambayi Gimbiya Shaheeda dake kallon su baki d’aya. Gimbiya Shaheeda taja majina tana jujjuya zobunan daham din hannun ta. “Toh.. Gashi nan dai.... Ba wani matsala gaskia. Yanzu ma wanka nakeso nayi ayimin iso wajen sa.” “Karki sakaci da maganin nan Gimbiya. Wallahi Malam ya rantse da abinda zai kashe shi wannan maganin babu na biyun sa..” Haj Jaleela tace da Gimbiya Shaheeda data mike lokaci guda tana Yatsina fuska, “Duk yadda ake ciki...” Sallama ta musu ta dauki hanyar sashen ta. Kallo d’aya tayi wa sashen mai babban daki tayi gaba tana sake daure fuskar ta. Su kuwa ko bayan fitar ta sa zancen ta suka yi a gaba. Sunata shewa suna tafawa. Tamkar ba kishiyoyi ba ada. Aminan juna ne na qut da qut. Gimbiya Jaleela ce ta gyara zama tana faman jujjuya ido tace. “Ni wallahi so nake a fara bawa mata sarauta a kasar nan. Ina ji a jiki na zan iya duk wani abu da ake yi a cikin sarauta. Kuma nayi mafarki nan gaba kadan mata zasu dawo sune suke jan ragamar mulkin masarautar Basannabas.” Ta gama maganar tana dora kafa daya kan daya tare da juyawa ta kalli sauran one by one. Cike da tsantsar dariya irin ta rainin hankalin nan Gimbiya Najwa ta mike tsaye tare da yin taku daya biyu zuwa uku ta tsaya a tsakiyar su tana gyara kafadun rigar jikinta tace. “Kwarai kuwa Hajjaju, ina jin kuma ni aka bawa damar karasa yin wannan daddadan mafarkin naki da kika fara. Domin kuwa ni na hango kai na akan wannan kujerar ta sarauniyar Basannabas. Kuma a cikin d'in bin halacci na har na baki mukamin Baba na, wato waziriya ta. Ke kuma..” Ta Nuna Gimbiya Huwaila wato yar ciroma tare da cewa. “Ke kuma na yi miki mukamin Baban Hajjaju Najwa, wato Galadima. Na san dai wan.....” Bata karasa ba Gimbiya Najwa tayi saurin da katar da ita ta hanyar cewa. “Ya isa dan Allah, wannan ai shirme ne. Idan zaku dawo cikin serious d'in ku toh ku dawo, amman ta ya zaku zauna kuna ta yi mana wasu zantuka na shirme. Yanzu mu maida hankali wajan ganin yarinyar nan ta yi aikin da muka bata, Salman d'an girman kai ne, ko uban shi be yi wannan jiji da kan ba wallahi.” “Haka ne kam, dan naga kwanan nan itama ya fara yi mata gardama, juya dashi amman sai shigen fadin rai.” Duk suka yi dariya tare da yin tafi da hannayensu. Gimbiya Huwaila ta ce. “Sa'adatu ce ma ni take bani mamaki, matar nan Sam taki yadda da cewa yaran nan baya son ganin ta, amman kullum cikin wahalar da kanta take wajan koke koke da wasu addu'o'in ta na shirme. Ai gara ka yiwa kanka maganin matsalar ka, amman kace zaka jira ai sai ka dade, koma ka mutu baka cimma burin ka ba.” “Ai Baba (Madaki) yace abu d'aya ne yasa shi barin matar nan. Shine baya daukar ta a matsayin mutun mai rai, amman da tuni yasa anyi shekara lahira.” “Gaba d'aya manta ta nake a cikin tsarin rayuwa ta.” Jaleela ta fada cikin yatsina fuska. Haka suka zauna suna ta shirya makircin su kamar yadda suka saba. Ita kuwa Sa'adatu tana sashen ta tana kukan zuci da na idaniya. Kuncin da take shiga wani lokacin har mutuwa take roko tazo ta dauketa saboda wahalar da ranta yake yi. Amman tasa a ranta komai daga Allah yake zuwa, yasan kuma lokacin da zai warware mata wannan masifar da take ciki. Tsab ya yi shirin bacci, yaje ya kwanta akan gado sai gata itama ta shigo cikin shigar kayan bacci masu santsi gasu shara-shara. Gadon itama ta hau tare da rungume shi ya kawar da kai, tunda tasa hannunta ta shafi kirjinsa shikenan ya nemi nutsuwa ya rasa. Kansa ya yi girma yaji kamar an dora masa duniya da abinda ke cikin ta. Wani barin na zuciyar shi kuma yana kusanto masa ita akan ya yi mu'amala da shi. Kafin kace menene ya firgice sun zama abu d'aya, koda suka dawo cikin hayyacin su wani gigitaccen bacci ne ya dauke shi. Ta tsaya tana kare masa kallo mai cike da fassarori kala-kala. Kanta ta dora saman kirjinsa take itama bacci ya dauke ta a jikinsa. Garin ya yi shar gwanin dadi, sarki Salman ya fito akan farin doki da aka kawata shi da ado mai daukar hankali. A hankali yake tafiya har ya isa wajan wani ruwa inda wata tsohowar mata tana durkushe sai kuka take yi. Ya tsaya tare da sakkowa yaje kusa da ita cikin sassanyar murya yake mata magana. “Baiwar Allah lafiya? Me yasa ki kuka a cikin mulki na?” Ba tare da ta wai go ba ta gyara yagaggen mayafin da ke jikin ta tana share hawaye tace. “Yara na duk sun guje ni, ba su san gani na bare ganin fuskata.” “Suna raye kuma?” Tace, “Ban sani ba ni, sai dai ina ji a jikina tabbas suna raye. Me ye amfanin yaran da zaka haifa da cikin ka amman su guje ka? Me ye amfanin wahalalliyar nakudar da zaka haifi yara amman su gaza sanya ka farin cikin rayuwa? Kaico da irin wannan duniyar mai cike da tsantsar hasara....” Ta wai go a fuska sai kawai yaga fuskar mahaifiyarsa, ta riko kafafunsa ta riƙe gam tana cewa. “Zan tafi, zan kuma yin nisa da yara na da suka kasa gane matsayina a gurin su. Ka tausaya min ka dawo min da yara na, gwara mu zauna cikin talauci tare da su akan su yi arzikin da za'a raba mu. Karka tafi ka bar ni ya shugaba, ka tuna yadda ake ji idan aka rasa wani bangare na jiki. Ka tausaya min ya......” Sarki Salman dake kwance kan katafaran gadon shi, ga matarsa kwance a jikin sa, kawai sai ji ya yi ya tashi a gigice yana sakin wata firgitaacciyar kara. Jikin shi kuwa sharkaf kamar an tsamo tsumma daga cikin mai.... *KHADIJA* ____Wajen Aisha kawata naje, Wadda muka yi British da ita, yanzu ta kai matakin lecturer a jami’a. Mun sha hira sosai kafin na dau hanyar dawowa gida. Ta babbani shawarwari sosai akan rayuwa, Da yadda zan cigaba da gudanar da ita. Kasancewar garin damina ne tuni hadari ya hadu aka shiga kwarara ruwa tamkar da bakin kwarya. Gashi na sallami TK driver tun dazu nace yaje ba komai zan dawo idan na kammala. Adaidaita sahun da nake ciki sai tangadi take a titi tamkar zata kifar damu saboda yadda iskar damina ke kad’a ta. Ganin gamu ga gidan rediyon mu hakan yasa na tsaida shi na falfala da gudu na tsaya a rumfar motoci, Waya na lalubo na kira Mas’oud nasan shi kullum yana nan, Baya da day off Saboda kasancewar sa babban ma’aikaci awajen, Na sheda masa ina waje ruwa ya tsare ni. Cikin barin jiki kuwa sai gashi Da lema a hannun sa ya karo yai saurin rufamin ita akai, “Sannu Habibaty.. Ya akai haka, Ina kika je?” “Hmm bari dai Habiby.. Wai zuwa nayi na gayda Aisha da naje wankin kai, Kasan kusa da jami’ar sune shine na biya.” “Ayyah sannu, Muje ciki ki huta, Dama wannan damina da ake marka marka..” “Allah yasa mu wuce Lapia..” Nace dashi, Muka shiga ciki, Kowa yagan mu sai ya tsokane mu, musanman ni. Wai na biyoshi wajen aiki na kasa hak’uri. Office dinsa muka shiga. Sai rawar sanyi nake.Rigar sanyi ya dakkomin acikin kayan custume da ake ajiyewa. Muka shiga hirar soyayya hankalin mu kwance, “Kyanta ace Ruwan nan da ake ni da ke muna matsayin mata da miji. Mezesa mu wani fito aiki.. Ai sai dai ragargazar soyayyah da..” Katshe shi nayi. Domin sai ina taka masa birki, Kunya ce ke lullube ni duk sanda yai wadannan kalaman, “Wai love sai Yaushe zaka zo ka gayda Kawu daddy ne?” “Zanzo Insha Allahu! Banason zuwa ne batare da komai ya kammala ba. Kinga akwai gini da kawo kudi da sauran su. “ “Gini kuma love?” “Oum waleeda gwara ace son samu komai na rayuwar da zamuyi ya zama na is ready . Banason muyi wahalalliyar rayuwa.” Kullum dai zancen kenan. Na ka’da kai kawai ina mai mamakin kalaman sa. Ni fa wallahi Saboda rin k’aunar da nake masa ko lefe zan iya yafe masa . “Shikenan Mine! Amman da ba sai ka wani wahalar da kanka ba, Ko da irin haya sai mu fara ko..?” “Shi kenan Oum Waleed zan samu alhajin mu da maganar, Kinsan suna ganin Ya Haysam bai aure ba gani zasu yi nayi kankanta.” Cuno baki nayi gaba na masa gatsine, “Ai. Ai.. Ni dai nai dai nima ba canai nima ayi auren ba. Kawai dai saboda Kawu daddy yasan da kai ne.” “Haba tawaje na.. Ai ke tawa ce. Nine mallakin gangar jikin ki da soyayyar ki Insha Allah. In Shaa Allahu zaki ji..” Banbashi amsa ba saboda nasan yanzun sai ya kauce hanya. Mikewa nayi na saqale jakata. Ganin ruwan ya tsagaita. “Zan tafi gida...” “Okay muje na sauke ki..” Gaba nayi yana biye dani abaya muka shiga mota ya tayar. Tunda ya fara tuki na juya masa baya ina kallon waje. Yanayi na damina gari yayi shar-shar dashi. “Oum Waleeda fushi ake dani..?” “Haba ni na isa? Kawai Ina kallon sarautar Allah ne.” “Ina son ki.. Ina miki son so tawan..” Rufe fuska ta nayi da tafin hannaye na da suka sha kunshi na sudan, Sunyi maroon gwanin sha’awa. “Lallen ki Yayi kyau...” “Godia nake Habiby..” Har k’ofar gida ya kai ni, Dai dai lokacin da Kawu Daddy ya dawo Shima. Ganin na fito yasa Mas’oud fitowa Shima ya rissina ya gayshe da Kawu daddy daya futo da sauri da alama mantuwa yayi, “Kawu daddy sannu da zuwa..” “Yauwa Sannun mu Khadija..! “ “Yallabai Barka da rana...” “Barka kadai... Ya aiki?” “Alhamdulillah!” Mas’oud ya bashi amsa yana sosa kai, Kawu daddy ya kalle ni ya kalle shi, “Kamar na san shi ko?” “Abokin aikinta ne ni yallabai..” Cewar Mas’oud, Na juya na galla masa harara, “Abokin aiki kuma?” Na tambaye shi ina hade girar sama data Kasa, “Oganta ne ni.. Naga garin da lema shine na sauke ta..” Mas’oud ya bani amsa yana kallon Kawu daddy. Nayi k’wafa kawai ina galla masa harara, “Ah Allah sarki, ai na gane ka yanzu. Kai ne mai jinyarta a asibiti. Angode sosai. Tukur driver baya nanne?” “Eh nace ya dawo gida dazun.” Musabaha sukai da Kawu daddy ni kuma na shige cikin gida da sauri, Kawu na biye dani. Ya dauki brief case dina a parlor da alamun shi ya manta, Har ya kai kofa, Ya juyo, “Khadija..” “Na’am Kawu daddy..!” “Idan kin samu Lokaci zuwa gobe haka zamuyi magana Insha Allah.” “Toh.. Kawu...daddy..” Na bashi amsa a rarrabe saboda yadda cikina ya soma hautsinewa, Kodai ban kyauta bane yadda Mas’oud ke kawo ni gida? Wata zuciar tabani amsa da ‘Kwarai baki halacci ba Khadija. Driver sukutum guda da mota fa aka baki.. “Kawu kayi hak’uri ..” “Kin cika Shirme! Wayace lefi ki kai? Magana kawai zamuyi ta hankali. Alkhairi ne In Shaa Allahu.” Yana gama magana ya fice da sauri, Ni kuma na haye sama ina hada hanya. To maganar me zamuyi? Oho..... . ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥.   [3/30, 9:40 PM] Maman Maryam: www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac. _*ASSALAMU ALAIKUM SISTERS..!_* _*INA MASU NEMAN INDA ZASU SAMU INGANTATTUN: _* _*HERBALS APHRODISIAC MA’ANA NA GARGAJIYA BANA HADIN BATURE BA MAI SIDE EFFECT..?_* _*TO KU MATSO, DOMIN NESA TAZO KUSA.._* _*ZEE HERBALS APHRODISIAC_* _*ZEE HERBALS APHRODISIAC_* _*ZEE HERBALS APHRODISIAC_* _*MUNZO MUKU DA INGATTTUN KAYAYYAKI WANDA ZASU GYARA KI CIKI DA WAJE_* _*MUNADA SUPPLEMENT MASU GYARAN JIKI DANA FATA, WANDA ZASA SAKI KIYI SHEKI FATAR KI TAYI LAUSHI. TAYI LUWAI LUWAI TAMKAR TA JARIRAI_* _*AKWAI SUPPLEMENT NA KAYAN MATA WANDA ZASU GYARA KI, KIJI KI TAMKAR BUDURWA, SUPPLEMENTS DINMU BASU DA SIDE EFFECT, DOMIN AN HADO SU NE DAGA INGATTATTUN ITATUWA, WATO NATURAL PRODUCTS NE ACIKI._* _*KAI BA ANAN KADAI MUKA TSAYA BA, MUNA DA INGATTUN KAYAYYAKIN MATA WANDA KESA KISHIYA KWAFA, WANDA DUK INDA SARAUNIYA TAKAI KIN WUCE, WANDA ZASU TSATSO MIKI MARTABAR KI DA KIMAR KI_* _*AKWAI INGATTATTUN MAGUNGUNA, NA CUTUTTUKAN DA SUKA SHAFI DAN ADAM DAMA JINNU.. KAI DAMA WANDA BAMU AMBATA BA.. ZEE HERBALS APHRODISIAC (MASARAUTAR INGATTATTUN MAGUNGUNA KENAN)_* _*KYAU, ARHA, INGANCI, RAHUSA... SAI ZEE HERBALS APHRODISIAC_* _*MANHAJOJIN MU NA SOCIAL MEDIA: KAMAR INSTAGRAM DA WHATSAPP DAMA NAMBAR TARHON MU: DOMIN SHIIGA KUGA IRIN KAYAYYAKIN MU TUNTUBE MU TA_* _INSTAGRAM LINK DIN MU:_ www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac _WHATSAPP LINK DIN MU:_ https://Zeeherbalsaphrodisiac.whats.bz _NAMBAR TARHON MU_ 08169380189 _*DA A BAKA LABARI GWARA KA BAYAR.. KIZO A DAMA DAKE YAR UWA, KI ZAMO DAYA DAGA CIKIN KASAITATTUN MATA MASU AJI.. MUNA GARIN KATSINA, SANNAN KAYAN MU MUNA BADA SU AKAN FARASHIN SAYA ‘DAI DAI KO SARI.. MUNA TURA KAYAN MU A KO’INA A FADIN NAJERIYA._* _*BE YOUR OWN BOSS, BUILD YOUR OWN EMPIRE, BE THE WHOLE WORLD OF HIS MAJESTY( YOUR HUBBY) BE THE ONLY CENTER OF ATTRACTION WITH ZEE HERBALS APHRODISIAC. OUR PRODUCTS LASTS LONGER AND VERY EFFECTIVE. NO SIDE EFFECTS. AVAILABLE N WHOLESALE/ RETAILS.. DELIVERY IS NATIONWIDE. 100% TESTED AND TRUSTED_* *1___9* _Zakuga canjin sunan masarauta daga BARNABAS... zuwa BASANNABAS. Ko ince tun d’and’ano ma na canza. Na manta ban sanar ba.. My baddd! So dai komai yana bukatar sanarwa. Bayan nayi bincike nagano BARNABAS. Wani suna ne ko ince abu ne daya danganci ma’abota littafi. Sunan yazo acikin bible ma sunce: The Gospel of Barnabas is a book depicting the life of Jesus😅so BARNABAS din Joseph dinsu ne acikin bible.. To avoid consequences 😂💔salin alin se muka koma da BASANNABAS. Duk kuwa da kirkirarren labari ne gara a canza din🤤 case closed ko? .. To acigaba da gashi🤗😉_ *MASARAUTAR BASANNABAS* *Yadda* taga yana ta waige waige kamar yana neman wani abu a kusurwoyin dakin yasa itama ta tsorata tare da rike shi. Nan take taji ya yi wancakali da ita yana kuka mai firgitarwa, hannayensa dafe a kai yana ihu. Tabbas akwai abin da yake damun sarki Salman wanda ta kasa fahimta, da tana tunanin ko maganin da tasa masa a cikin pillow ne, wanda su Gimbiya Najwa suka bata suka umarce ta da ta sanya masa, ko shine yasa shi yin wannan abun cikin talatainin dare? Babu mai ba ta wannan amsa, har sai taji abin da ya sanya shi yin wannan abun. Gimbiya Shaheeda ta riko gaban sleeping dress d'in ta da botiran suke a bude, ta sake matsowa kusa da shi a tsorace dan gaba daya ya canza sai faman cije baki yake yi da hakoransa. Leka idanunsa tayi taga yana zubar da hawaye, abin da ta dade bata gani ba a tare da shi. Sai ta marairaice tana share masa kwallar saman kirjinsa, murya a sanyaye ta fara masa magana. “Na tsorata da ganin ka cikin wannan yanayin, nasan mafarki kayi, kuma da alama bashi da dadi duba da yadda kake zubar da hawaye. Shin me ka gani a cikin mafarkin naka?” Ya yi shiru ba tare da ya kalleta ba, ga wani irin azababban sanyi da yaji yana huda duk wata kofar gashi dake jikin shi. Zare hannunsa ya yi daga rikon da ta yi masa, ya janyo jarkar ruwa tare da budewa ya kafa kai yana sha. Tun da ya fara sha bai sauke ba sai da ya kusa shanyewa taji ya ja wani dogon numfashi tare da saukewa yana lumshe ido. “Ko mafarkin Ammie ka yi?” Sai tambayar ta ta tayi matukar daure masa kai, ya dago tare da kallon ta da jajayen idanunsa. Take yaji wani faduwar gaba, sai ya sunkuyar da fuska yana girgiza mata kai. “Idan mafarkin ta kake yi ya kamata ka dena, domin Ammie sam bata kaunarka. Ka manta sanda za'a nada ka matsayin sarkin Basannabas ita tazo ta dinga gayawa mutane cewar kai juya ne baka haihuwa kar a baka? Ka manta?” Salman ya yi shiru kafin daga bisani ya daga kai alamar haka aka yi. Shaheeda ta yi murmushi sannan ta sake matsawa jikin shi ta shige tana faman shafa shi, cikin tsantsar makirci tace masa. “To ka dena damuwa da duk wanda be damu da san ganin abinda Allah ne ya mallaka maka shi. Ni zan kasan ce da kai a duk yanayin da kake ciki, zafi rana da damuna ba zan taba rabuwa da kai ba.” Cikin matukar farin ciki Salman ya jinjina kai, sai kuma ya matsa ya kwanta akan pillow still tana jikin shi sai lailaya shi take kamar ta samu jariri sabuwar haihuwa. Daga haka ya manta da wannan mafarkin da ya yi da mahaifiyar shi, bacci ya kuma daukar shi. Gimbiya Shaheeda ta mike zaune lokacin da ta tabbatar da cewa ya yi bacci da gaske. Sakkowa ta yi daga kan gadon ta ciro wani farin zare daga cikin gashin kanta tana kare masa gani kafin ta yi murmushi wanda ita kadai ce tasan matsayin shi. Boyewa tayi sannan ta shiga toilet ta tsarkake jikinta ta fito ta shirya ta kwanta tana jin farin ciki. Basu farka ba sai wajan karfe shida, ya bude ido da kyar sai yaga Shaheeda a kusa da shi, ya fara duba jikin shi. Gabaki d'aya bai san sunyi wani abu ba sai yanzu da yaga yanayin shi, ya duba agogo yaga lokacin sallah har ya wuce. Da sauri ya tashi ya tashe ta sai tace masa ai tayi wanka tun dare. Yaji haushi kuwa sai dai ko a fuska kasa nunawa ya yi, kawai ya wuce bathroom shima ranshi a bace. *KHADIJA (Dije).....* Tun da na idar da sallah nake jiran kiran kawu daddy da yace zai ganni da anjima amma naji shiru, sai na fito daga daki naje parlor na koma kitchen amman shiru yana daki be fito ba. Hakura na yi na koma daki na zauna ina duba wani littafi. Kamar jira ake na zauna sai ga kiran shi ya shigo waya ta, na daga yace na sakko na same shi a parlorn kasa. Jiki na rawa na dauki hijab nasa na fito dan na kagu naji abin da zai sanar da ni, wanda sam na kasa kawo ko meye a cikin zuciyata. Yana zaune rike da waya yana dannawa nayi masa sallama ya dago ya kalle ni, kafin na zauna ya ce yace na rufe kofar naje na rufe sannan na dawo na samu gefen kujera nesa dashi na zauna. Ya yi gyara murya tare da aje wayar a gefen sa ya dan matso daga gefen kujerar yace. “Alhamdulillahi Khadija a kullum na kalli yadda rayuwar ki ta dawo na kanji dadi da farin ciki. Gashi cikin ikon Allah ya sake daga daraja da mutuncinki ta hanyar da bamu tunani ba, yanzu bani da wani buri irin naga na mika ki zuwa dakin mijin ki, wannan shine buri na na biyu akan ki Khadija. Ina fatan zaki ci gaba da kulawa da kanki kamar yadda kike yi a koda yaushe. Na ga yanzu Allah ya baki miji wanda nake saka ran insha Allahu shine fitila na gaba da zai ci gaba da haskakawa a cikin duniyar ki. Ni dai ya yi min, tarbiyarsa, dabi'unsa da kuma kalamarsa duk ba bu wanda ban duba ba. Kema nasan zai yi miki, naga yaro ne matashi mai jini a jika, Allah ya daukaka shi a cikin tarin ni'imomin da yake da su.” Kai na a kasa farin ciki ya mamaye ni, ashe kawu daddy kallon takun mu kawai yake yi nida Mas'oud bamu sani ba? Lallai babba-babba ne inji bahaushe da yace yaro ko ya hau rimi ba zai iya hango komai ba. Wayyo Allah dadi sai na hango gashi har an daura mana aure an kai ni gidan Mas'oud birnin zuciya ta muna ta shan soyayyar mu. “Nan da dan wani lokaci za'a daura auran ku insha Allahu. Duk da cewa bani ne wanda zai bada auran ki ba, amman na dauki alkawarin zuwa can dangin mahaifinki da kai na nayi musu bayani yadda zasu fahimta. Allah ya yi miki albarka Khadija tashi kije daki ki kwanta nasan gobe akwai aiki.” Ciki da jin kunya na tashi na ruga da gudu, farin ciki da nishad'i na suka dadu ba. Kan gado na fada ina tsalle tamkar wata yar shekara uku, na kagu Mas'oud ya kirani dan na kyankyasa masa wannan zazzafan labarin wanda nasan idan yaji ko bacci ba zai iya yi ba saboda murna. Wani ikon Allah sai be kira ba sai sako da ya turo min na text message cewar suna tare da Abban su ba zai samu damar kira ba mu hadu gobe a gurin aiki. Banji komai ba saboda ina cike da murna na je kitchen na zuba abinci naci sannan na dawo na kwanta cike da zakuwar ganin gobe. *WASHE GARI* Yau kam na fi koda yaushe saurin shiryawa dan zuwa gurin aiki saboda zumudi, na shirya tsab na dauki jakata Tukur driver ya dauke ni sai gurin aiki. Babu kowa sai wadanda suka yi aikin kwana, na shiga muka gaisa sannan na wuce office na zauna dan jiran lokacin da zan yi program dina. Bamu hadu da Mas'oud ba sai wajan karfe goma sha d'aya dalilin rashin zuwan sa da wuri. Sai da na jira har karfe d'aya lokacin da ya gama nashi sannan mukai sallah nace ina son yin magana dashi. Yana ta zolaya ta ganin yadda na cika da nishad'i ba kamar kullum ba, ya samar mana gurin zaman muka zauna. “Ko ranar da aka daura mana igiyoyin aure sai haka madam, irin wannan murna da farin ciki haka, meye sirrin a ban nasha nima.” Na yi dariya tare da rufe ido da hannayena, na bude ina wasa da zoben yatsa na nace. “Albishirin ka?” “Goro Oum Waleedah.” “Fari ko baki?” “Ahhh! Sai ma an jani tukunna? Toh na zabi uhmmmm... Uhmmmm... Zabar min dai da kanki.” Ya yi maganar cike da shagwaba, ban san lokacin da na saki dariya ba ina cewa. “Gaskiya kai zaka zaba, ai ni zan gaya ma albishir d'in.” “Toh shi kenan na zabi fari tartar.” “Yauwa jarumi na kasan me?” “Sai kin gaya min da bakin ki sweetheart.” “Kawu daddy ya gano cewa muna soyayya, jiya da kanshi ya kira ni yace ya yaba da hankalin ka ya amince za'a yi auran mu nan ba da jimawa ba.” Mas'oud ya bude baki tare da zaro ido cike da tsantsar mamaki, ya kasa ma magana saboda yadda abin ya zo masa daga sama. “Wai kina nufin kice min min daddy da kanshi ya gano cewa soyayya muke yi?” Na gyada kai ba tare da na yi masa magana ba sai dariya nake yi. Kasan cewar a cikin office din su muke, kuma babu kowa a ciki sai kawai ya taso tare da yin juyi yana rawa ina dariya. Kusa dani na ji ya matso tamkar zai hade jikina da nashi nayi saurin rintsa ido saboda na riga na saddakar da faruwar hakan, sai naji yace. “Ina ma ace ina da wannan damar, dana nuna miki irin tsantsar farin cikin da na shiga ta hanyar baki lafiyayyan runguma. But ya zama bashi, Allah ya kai mu lokacin da zamu zama abu d'aya zan biya ki harda na yau.” Sai ya d'an matsa daga kusa da ni ya zauna akan kujerar da ya taso, sannan ne na samu damar bude idanu na. “Kin fiye jin tsoro Oum Waleed, ya kamata kuma na rage miki yawan shi.” “Ai ni wani lokacin wallahi tsoranka nake ji, dubi yanzu fa kana kokarin taba ni.” “Ban taba ba ai Oum waleedah, but soon zan yi miki abin da yafi tabawa ma.” Na share shi dan idan na biye masa tsab zai sanya ni cikin wani yanayin da ban shirya zuwan sa ba. Muka ci gaba da hira saboda zakewa harda yadda bikin zai kasance muke ta tattaunawa hankali kwance. Tun daga wannan lokacin muka sake d'in kewa ni da Mas'oud saboda ganin zamu mallaki juna. Daga ni har shi bamu taba kawowa cewar kawu daddy ba junan mu ya mallakawa ba, saboda bai fito fili ya bayyana mana cewa ga yadda yake nufi ba. Haka muka ci gaba da rayuwa lokaci yana ta tahowa, Mas'oud yana ta hada kudin da zai turo gidan mu dan nema masa aure na kamar yadda ake yi. *FADAR BASANNABAS* Tunda yai mafarkin nan yake jin jikin sa yana rawa, Tunani ne dankare a kirjin sa. Amma ya kasa samun nutsuwar yadda zai warware shi. Dafe kansa yai ya rintse idanun sa. Yana zaune a fada amma bai bada damar aiwa kowa iso ba. Jakadiya sai zarya take tana sanar masa isowar mutane. Dakyar ya bari tabawa waziri dama ya shigo, “Allah yaja zamanin sarki adali. Allah ya Kara Maka lapia da nisan kwana mai amfani ranka ya dade!” Hannu sarki Salmaan ya daga masa yana dafe da habar sa, “Allah ya tausasa ran sarki! Allah yakara maka dattako baban kowa. Shin akwai abunda ke damun Sarkin mu ne? Sanar min ko menene shi shugaba na.” Sarki Salmaan ya d’anyi murmushin jin dadi. A duk duniya waziri na cikin sahun mutanen farko da yake so. Saboda a kullum sai ya tambayi abinda ke damun sa yana kuma k’ok’arin ganin ya yaye masa matsalolin sa, “Waziri... Nayi mafarki irin na kwanaki. Menene gaskiyar al’amari?” “Allah ya karawa sarki lapia. Tabbas shakka babu zamu iya fassara hakan da cewar sharri ne na mafarki. Amma kuma idan aka auna abun a mizanin hankali za’a gano akwai kullalliya ko makircin bil adama..” “Menene mafita to...?” “Kamar dai yadda na nemo maka hayakin nan da ka yiyyi kwanaki? Yanzun ma zan koma wajen Malam din na karbo maka wani..” Kada kai SAS yayi kafin su cigaba da magana data shafi fada. Mikewa sarki yayi. Dogaran sa suka rufe shi ya wuce sashen sa jin yadda yake wani irin jiri mai gigita kwakwalwa, ga ciwon kai da yake kuma barazanar faduwa. Waziri ne ya cigaba da zaman fadar, inda ya zauna dasu Galadima, ciroma, wambai da sauran su. Ya sanar da su rashin lafiyar sarki Salman tare da umartar wani babban hadimin sa da cewar yana son ya kuma karbo masa wannan hayakin a wajan malam kamar yadda ya taba karbowa kwanaki. Galadima ya kalli ciroma suka saki wani murmushi ta cikin rawanin su, da alama wata damar ce zasu samu wajan kuma yiwa sarki Salman wani makircin. Nan dai suka nuna jimami da alhinin rashin lafiyar, amman a zukatan su ba haka abin yake ba, wata muguwar manufa ce a rasu. Ciroma da kanshi yaje ya karbo wasu kayan tsibbun wanda yake dauke da tsana mai karfi tsakanin sarki Salman da mahaifiyarsa, ganin ya fara mafarki da ita sun tabbatar zasu iya shiryawa, wanda shirin zai iya wargaza musu duk wani shiri da suka yiwa masarautar. Shi kuma tunda ya shiga daki ya kwanta yake wani irin bacci mai nauyi da ko wane irin ihu ba zai iya farkar da shi ba. ____Cikin wasu furanni masu launin shudi da rawaya yake hangenta, sanye da kaya na alfarma sai faman murmushi take yi. Shi kuma yana daga gefe zaune da jarida yana dubawa sai idanunsa suka sauka akan ta, ya dinga kallon ta yana son kuma ya gano wa take yiwa wannan fara'ar mai tsadar gaske. Ya mike cike da kasaita yana isa gurin da take sai yaga shi take yiwa dariyar, ya kuma kallon ta tare da kamo hannunta sai kawai ta shige jikinsa tana kankamewa, murya a raunane yaji tana cewa. “Nagode ya kai annurin da yake haskaka min zuciya ta, tun dazu nake nan ina jiran zuwanka.” Shafar bayanta kawai ya yi ba tare da ya yi magana ba. Shan kamshin nan nasa yana sake sanya ta cikin begen sa, ta dago fuskarta tana kallon tashi tace. “I love you my hubby.” Sai ga Shaheedah tazo gurin, gabansa ya yi mugun bugawa, amman sai yaji Dijen ta rike shi tana cewa. “Kadena jin shakkarta saboda ita ba komai bace face azzaluma, ba ta son ka shi yasa take cin zalinka. Allah ya fita babu abin da ta isa ta yi maka ina tare da kai my hubby.” Ya samu kansa da tsayawa a gurin na ta duk da tsoran da yake tattare da shi na Shaheedah. Daga gefe ta tsaya itama tama miko masa hannu wai yaje, sai ya kalli Dije ya kuma kallon Shaheedah yana tunani yadda zai yi. Zuwan wani saurayi gurin yana kuka shine yasa Shaheedah barin gurin, Dije kuma ta kama shi suka tafi daki. Sai ya kuma jin nutsuwa yana yiwa Allah godiya da ya bashi Khadija matsayin mata abar alfahari. Sam be yi zaton a bacci yake ganin hakan ba sai sa ya farka ya ganshi a tsakiyar gadon sa yana juye-juye a kai. Tabbas yaji a jikinsa Khadija itace zabin zuciyar shi, dole ne ya ci gaba da farautar neman auran ta koda kuwa yin auran zai janyo abubuwa da dama a cikin masarautar. Sai da ya yi wanka ya shirya sannan ya nemo amintaccen bafadensa wato Al-hassan, suka kebe yace masa yana son a ci gaba da shirye-shiryen auran sa kamar yadda suka fara. Ya amsa sannan ya sake komawa wajan Alhaji Isma'il wanda ya tabbatar da cewar zai je dangin mahaifin Khadija ya sanar dasu, idan yaso yana dawowa sai ya sanar da a shirya daurin auran. Haka kuwa aka yi Alhaji Isma'il be sanar da su Mami zai je ba, sai shiryawa ya yi da shatara ta arzikinsa ya je ya sanar dasu komai, suma dai be gaya musu wanda zata aura ba, ya ce musu dai ya amince da tarbiyar yaron dan gidan mutunci ne iyayensa masu daraja ne. Suka amince tare da bashi ragamar aurar da Khadija, a cewar su ai shine uwa da uba na ta dan haka babu wani abu da zasu ce sai fatan Alkairi a cikin auran. Bayan ya dawo ne yake sanar da Mami cewa yaje can sun gama komai sannan ya kira yan uwansa suma ya gaya musu sunce idan lokacin yazo yasu bar komai su zo ayi dasu. Bata damu ba dan bata yi zatan wani mai daraja za'a aurawa Khadijan ba. Tunda aka fara wannan abun Dije da Mas'oud basu yi zaton ba junan su zasu aura ba, basu zaci hangen da kawu daddy ya yi ba akan su yake ba, sai da abin yazo gab har ana sauran sati daya biki sannan ne yace da Dije zai kuma yin magana da ita idan ya gama komai. Kasan cewar da yamma ne ta gaya mata kuma Jumma'a ce yana ganawa da mutane yan kasuwa, shi yasa ta bari zuwa gobe idan Allah ya kaimu. °°°°°°°°°°° °°°°°°°°°°°°°° °°°°°°°°°°°° *WASHE-GARI* Tunda Kawu daddy yace zamu yi magana daren ranar ban runtsa ba har wayewar gari. Kasan cewar asabar ce, Ina malale akan gado gaba na sai dukan uku-uku yake. Shin akan me zamu tattauna? Nasan tabbas lefi nayi. Kuma duk yadda akai akan bana bari TK ya dakko ni wani lokacin idan na fita. Ko kuma su Mami ne suka qulla min qullalliya a gurinsa? Ko kuma zancen iyayen Mas'oud zai min kila yace nace ya turo. Ganin sha biyu ta kusa ban ci abincin safe ba hakan yasa na diro daga gado ina mika, Band’aki na shige nayo wanka na canza kaya cikin doguwar rigar A line marar shape. Na taje kai na dakyar saboda inayi yana zamewa saboda santsi da cikar sa, Na d’aure da ribbon. Dauri me sauki nayi na shafa man baki na sauka kasa. A dinning area na tarar da Mami dasu Ya Shukrah suna cin abinci suna hira. “Mami ina kwana..? An tashi lapia.” “Lapia lou..” Ta bani amsa a tak’aice tana mai cigaba da kurbar tea dinta. “Ya Shukra ina kwana? Ya Hameeda ina kwana.” Kowannen su ya amsa babu yabo babu fallasa. Ganin haka na mike na daddebi abinda zan ci a plate na koma k’arshen parlorn nakeci acan. Sai bayan na kammala ina zaune ina karanta wani book na wajen aiki sai ga Kawu daddy yafito. Sanye cikin jallabiya. “Kawu daddy...Barka da safiya Kawu daddy! An tashi lapia?” “Alhamdulillah Khadija.. Muje ko?” “Toh Kawu..” Su Mami suka bimu da kallo, Yana gaba ina biye da shi ya shiga parlorn sa ya zauna akan babbar kujera ni kuma na tsakure a gefe, “Hau kujera ki zauna mana.” “Nan ya isa Kawu....” Gyaran murya yai. Ya rage volume din CNN dake faman yi, “Kafin dai mu fara magana ina son tabbatarwa kai na Kamar yadda kika sani, wannan maganar da muka yi dake a baya na aure ita ce ta kuma tasowa. Amman Shin ki na da saurayi ne dake zuwa neman ki gidan nan? Kai bama wannan ba. Akwai wanda ya taba yi miki zancen aure? Dan ni dai nasan da akwai zan sani ko kuwa..? Dan naje munyi magana da dangin mahaifinki, sun kuma bar min komai a hannuna cewar na yi komai da komai a game da auranki.” Wani daskararren abu naji ya tokare min a wuya. Shin menene yake shirin faruwa dani.? Ko wani sharrin aka kullamin? “Magana nake miki Khadija kin yi shiru...” “Kawu daddy.. Ba.. babu!” Na samu kai na da bashi amsa haka! Kawu daddy ya sake yin shiru na dan wani lokacin kafin yace, “Tun wannan dai wanda nazo nace miki na yaba da hankali da tunaninsa, gashi kai tsaye ni ya nema kinga kenan da gaske yake yi ko?” Sake samun Kai na nayi da kada kai. To me zance? Shi kansa Mas’oud din yana namiji ya boye alakar mu bare ni Mace? “Toh shikenan! Alhamdulillah tunda babu wata magana tsakanin ku da wani. Kinsan babu kyau neman aure akan aure. Wannan yaro me hankali da dattako ne, ya fito daga gidan mutunci. Yana neman auren ki.. Kuma azahirin gaskia ma nace na bashi. Saboda ko da kina da wanda kike so din a matsayina na mahaifi agare ki. Babu wanda ya zo ya same ni. Manya basu shigo ciki ba, Dama already blood sample/genotype dinki sunyi kyau. Kowa zaki iya aura, Kuma Khadija...” Ai bai karasa magana ba na fashe da kuka, Me yasa su Ya shukra da Hameeda su ba za’ai musu auren ba sai ni? Okay! saboda ni ba yar gidan bace ba ko kuwa? Ko dan banda gata ne? Tsana ce wannan kome? Wayyo Allah na ni Khadija..Ashe daman ba Mas'oud aka zaba min ba? Kuka Sosai nake yi ina rike kai na. Duk duniya babu d'a namijin da nake so, gangar jiki na keson mallaka irin Mas'oud ba. Ina son Mas’oud saboda shine first love dina. Ina son Mas’oud saboda shi ya koya min so har nasan menene so? Ina son Mas’oud saboda shi ya rai ni zucia ta ya koya mata abinda take so. Ina son Mas’oud saboda yana so na so mai wuyar fassarawa. “Innalillahi wa inna ilaihir raji’un...” Shi naketa nanatawa a fili ina bubbuga kai na ajikin kujera, Kawu daddy ya sauke zuciya ina jiyo sautin ta, “Kiyi hak’uri Khadija. Na rantse da Allah ban amince da aura miki shi ba don na cuce ki. Wallahil azim ba zan kai ki inda zaki wahala ba don na lalata miki rayuwa ba Khadija. Wallahi Khadija wannan auren ni inaji ajiki na alkhairi ne a gareki damu gabaki d'aya. Saboda Ina ji ajiki na nan gaba zaki ya ba min wannan rana..” Kuka nake sosai shabe shabe ina fyace majina da kasan dankwali na. “Kawu Mas'oud fa.. Mas’oud Kawu! Ina son Mas’oud.” “Wanene haka kuma Khadija.?” “Kawu shine wanda ya ke sona. Tun service dina muke tare Kawu daddy. Munyi alk’awarin aure dashi wallahi Kawu daddy..” “Khadija me yasa be zo ya same ni da zancen ba? Akalla kafin ya fara neman ki sai ya nemi yarjewa ta kamar yadda wannan ya yi. Amman Me yasa bai turo Manya sunzo ba idan har da gaske yake yi Eh?” Shiru nayi ina ajiyar zuciya. “Yace ne.. Ko wansa bai yi aure ba kuma shine karami. Sannan bai gama ginin sa ba..” “Sai Yaushe kenan zai fadawa manyan ki Uhm!? Ko kuwa zama za kiyi tayi kina jiran sa kina faman tsufa agida? Shi kuma yana bata miki lokaci? Daga karshe ma yazo yace miki an hada shi aure da yar uwar sa! Uhm? Shikenan tunda baki dauke ni amatsayin uba ba Khadija. Na ky’ale ki sa..” Riko kafafun sa nayi ina Kuka, Ni din banza zan ki amincewa da maganar Kawu daddy? Mutumin da ya mayemin gurbin uwa da uba? Halacci d’aya zanyi shine na amince. Ba Wai don ina son wanda za’a daura min aure dashi ba. Kawai dai saboda Kawu daddy ne. A duniya banida mafiyin sa idan ka tsame sauran yayyun Umma ta. “Bar Kuka Khadija.. Na kyaleki wallahi. Zan ku..” “Na amince Kawu daddy.. Na amince wayyo Allah karkai fushi dani.” “Allah ubangiji ya miki albarka. Ya biya miki bukatun ki na alkhairi, Allah yasa wannan auren ya zamo wanzuwar farin cikin ki, Yasa ki zama wata aba a rayuwa, Allah yasa ayi a sa’a. Nan da sati d’aya wato mai kamawa za’ayi in Shaa Allah!..” Kasa magana nayi, Ni wallahi ji nake tamkar bacci nake yi. Gaba d’aya bana gane me kawun yake fada. Na sandai nace na amince amma gaba d’aya wani dishi dishi ma nake gani. Zucia ya da idanu na Mas’oud kawai suke nuna min, Sanye cikin kananun kaya yana rataye da ID card dinsa na wajen aiki. Cikin haka Mami ta banko kofa ta shigo, “Meye haka ne? Koke-koken me aketayi ne uhm? Tun daga karamin parlor nake juyowa, Me akai ne?” Tana magana tana sakace hakorin ta da toothpick. “Babu komai ya akai..?” Kawu daddy ya tambayeta yana duban ta da kyau . “Koke koken da muketa jiyowa ne shysa na shigo ganin Lapia? Kar ma’kota su fara lek’owa suna tambaya.” “Lapia Alhamdulillah Hajia. Ba kukan wani abun bane na farin ciki ne.” “Toh faa! Tooo” Mami tace hakan tana mai zama a gefen sa. “Tashi kije Khadija. Allah ya miki albarka Khadija!” “Aamin Kawu daddy..” Mikewa nai dakyar ina tafiya. Ina jiyo mami nata tambayar sa menene? “Wai meke faruwa ne alhaji. Alkhairin menene?” “Hajia.. aure ne! Wani bawan Allah ne ke neman auren ta ya biyo ta kai na.” “Aure..” Mami tafada tana dafe da kirjin ta, Ni kuwa sauri nayi Na fita na jawo musu kofar. Ina fita na haye sama ina mai bude sabon shafin wani kukan. Mami ta muskuta kusa da Kawu daddy, “Alhaji bangane me kunnuwa na suke jiye min ba, aure? Aure fa kace? Waye zai auri wa?” “Hajjaju da hausa fa nake miki magana. Nace neman auren ta akazo waje na.” “Au ashe da saninta ma shine take kukan munafurci kuma?” “A’a Hajia wanda takeso daban. Wanda kuma yai tambaya daban.” “Toh fa! Alhaji Kai wa ka bata kenan..?” “Wanda ya fara magana mana.” “Shi din wanene shi! Wai ka na nufin bada masaniyar ta ka bayar da auren nata ba? “ “Eh ban isa bane? Ni ba mahaifin ta bane.?” Yatsina fuska Hajia Abeeda tayi tana sosa idon ta, “Toh shi wannan Waye manemin kenan? Dan wanene?” “Wallahi wani bawan Allah ne kawai nutsatstse ya kwanta min arai kuma.” “Ya'yan abokan ka Wai..?” “Ko d’aya wallahi.. wani ne daban. Marainiya ce gwara na aurar da ita hankali na yafi kwanciya.” “Dankari Makari.. Ai shikenan! Toh su Shukra Alhaji ka nemo musu mana acikin yaran abokanan ka. Ko Yayan commissioners dinnan da kukayi makarnta.” “Ai nagaya miki inde sai dan wane da wane zaki bari su aura ni babu ruwana na tsame hannu na, Muyi ta zama ana k’irga mana shekaru tare.” “Wai dan anbiyo takan ka ance anason Dije? Tab Alhaji ai wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa, Dai dai ruwa dai dai tsaki. Su ana ganin kai ne mahaifin su babu kasakantaccen da zai biyo takan ka yace yana neman auren su.. “ Dr. Ismael yayi daria yana kurbar ruwan hannun sa, Yasan halin matar sa sarai, Shi yasa bazai taba gaya mata gidan da dije Zata shiga ba sai an daura aure ko kuma an kawo kayan aure abu ya kusan tabbata. Yasan kuma Zata titsiye Dijen da tambaya shiysa bai sanarwa Dijen bama, Duk ya tattara ya rufe su a fai-fai. Mami ta jima tana neman bugar cikin Dr. ismael don jin waye? amma tsabar zurfin ciki irin nasa duk nacinta haka ta hakura bataji Waye manemin na dije ba. Data dame shi ma sai ya rufe fuskar sa da jarida wai kansa ciwo yake. Tashi Tai ta fice ta kyale shi. “Mami ya akai kuma..?” “Kukan me take Mami.?” Shukra da Hameeda suka tasata a gaba da tambaya ganinta fito daga wajen Dr. Ismael “Hmm! Makira algunguma aure Zata yi fa..” “Aure! Wa Zata aura Mami..?” Hameeda ta tambaya tana raba idanuwa. “Ba dai Mas’oud ba?”Shukrah ma ta tambayi Mami tana dafe kirji. “Waye Mas’oud kuma? Du basu bane. Wani ne daban yazo neman auren ta. Shine take wannan kukan batasan wanene ba..” “Kuma Daddy ya yadda?” “Kwarai kuwa.. Yace ma afara shiri sabon sati me kamawa zaayi bikin.” Hameeda ta tabe baki, “Allah ya raka taki gona..” Shukra ma jin ba Mas’oud bane sai ta samu kanta cikin jin dadi, “Masha Allah! Allah ya kai mu.” Harara Mami ta dankara mata. Tanemi waje ta zauna, “Gwara kuma ku fito da mazajen aure...” “Soon In Shaa Allah!” Cewar Shukra tana murmushi. Hameeda khma ta shiga raba idanuwa. Haka dai suka tasa zancen auren agaba sunata ta kwashewa dije albarka. Musanman Mami dake bakin cikin auren dw zatai. Amma Idan ta tuno kila ba auren jin dadi bane sai ta shiga murmushi kuma tana k’ada k’afa. Ni kuwa inacan d’aki ina kuka. Ba kalar wanda ban ba. Kai har karamin hauka sai da nayi. Naita buga kai na ajikin bango duk ya daddauje. Naita bori. Ina tunanin ko hada kayana zanyi na gudu ne yadda ake a film. Wata zuciar tace bakisan halacci ba. Dole nayi hak’uri zuciya mai halacci bata manta alkhairi komai girman sharri . Kawu daddy ya zamar min uba ya zamarmin uwa. Shine gatana. Yana gatantani fiye da tunani. Me yasa zan bijirewa abinda yake so ya kuma nuna isa akan sa? Wacece Ni? Dole na hakura. Illa dai koma wanene ya yankemin buri na na auren Mas’oud saiga rayuwa. Wallahi sai ya bambancewa aya zakinta na shiga hurumin soyayya da yayi. Ina ruwan sa? Lallai ni na hadu da sharrin late comer mai datse farin cikin zukatan masoya biyu . Bansan ka ba, Dan jaraba da kalata kace ni kakeson aura? Wannan wacce irin bahaguwar kaddara ce? Wata zuciar tace taki kaddarar kenan Khadija. Zaki shiga wata ukubar rayuwar kenan ta uku. Na bigi wajen kirjin nawa inda zuciar take tamkar dai zaucacciya. Ni kadai nace ah k’arya kike wallahi sai dai shi ya shiga uqubar rayuwa. Ba shine ya ce yaji ya gani yana so ba? Ai kuwa zai San ya tafka babban kuskure. Mas’oud sai kira na yake na kasa dauka. To me zance masa? Koma menene shi ya janyo mana wallahi. Ni dai ranar gaba d’aya haka na yita rabi kuka rabi zancen zuci, rabi magana ni kadai. Wani lokacin kuma na bubbuga kai na a jikin gado. Wayata kuwa daga karshe kashe ta ma nayi gaba d’aya. Oh ni dije. Wai ni za’aiwa auren dole da wanda bansani ba? Kuma cikin wata d’aya jal aka gama komi. Nashiga uku sau dubu uku. Haka nayita sallolin nafila ina wa Allah kuka a sujjada kan ya tarwatsa wannan auren da za'a yi min koda kuwa anzo daurawa ne...... ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥. [3/30, 9:40 PM] Maman Maryam: Hafsat Rano 17 www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac. _*ASSALAMU ALAIKUM SISTERS..!_* _*INA MASU NEMAN INDA ZASU SAMU INGANTATTUN: _* _*HERBALS APHRODISIAC MA’ANA NA GARGAJIYA BANA HADIN BATURE BA MAI SIDE EFFECT..?_* _*TO KU MATSO, DOMIN NESA TAZO KUSA.._* _*ZEE HERBALS APHRODISIAC_* _*ZEE HERBALS APHRODISIAC_* _*ZEE HERBALS APHRODISIAC_* _*MUNZO MUKU DA INGATTTUN KAYAYYAKI WANDA ZASU GYARA KI CIKI DA WAJE_* _*MUNADA SUPPLEMENT MASU GYARAN JIKI DANA FATA, WANDA ZASA SAKI KIYI SHEKI FATAR KI TAYI LAUSHI. TAYI LUWAI LUWAI TAMKAR TA JARIRAI_* _*AKWAI SUPPLEMENT NA KAYAN MATA WANDA ZASU GYARA KI, KIJI KI TAMKAR BUDURWA, SUPPLEMENTS DINMU BASU DA SIDE EFFECT, DOMIN AN HADO SU NE DAGA INGATTATTUN ITATUWA, WATO NATURAL PRODUCTS NE ACIKI._* _*KAI BA ANAN KADAI MUKA TSAYA BA, MUNA DA INGATTUN KAYAYYAKIN MATA WANDA KESA KISHIYA KWAFA, WANDA DUK INDA SARAUNIYA TAKAI KIN WUCE, WANDA ZASU TSATSO MIKI MARTABAR KI DA KIMAR KI_* _*AKWAI INGATTATTUN MAGUNGUNA, NA CUTUTTUKAN DA SUKA SHAFI DAN ADAM DAMA JINNU.. KAI DAMA WANDA BAMU AMBATA BA.. ZEE HERBALS APHRODISIAC (MASARAUTAR INGATTATTUN MAGUNGUNA KENAN)_* _*KYAU, ARHA, INGANCI, RAHUSA... SAI ZEE HERBALS APHRODISIAC_* _*MANHAJOJIN MU NA SOCIAL MEDIA: KAMAR INSTAGRAM DA WHATSAPP DAMA NAMBAR TARHON MU: DOMIN SHIIGA KUGA IRIN KAYAYYAKIN MU TUNTUBE MU TA_* _INSTAGRAM LINK DIN MU:_ www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac _WHATSAPP LINK DIN MU:_ https://Zeeherbalsaphrodisiac.whats.bz _NAMBAR TARHON MU_ 08169380189 _*DA A BAKA LABARI GWARA KA BAYAR.. KIZO A DAMA DAKE YAR UWA, KI ZAMO DAYA DAGA CIKIN KASAITATTUN MATA MASU AJI.. MUNA GARIN KATSINA, SANNAN KAYAN MU MUNA BADA SU AKAN FARASHIN SAYA ‘DAI DAI KO SARI.. MUNA TURA KAYAN MU A KO’INA A FADIN NAJERIYA._* _*BE YOUR OWN BOSS, BUILD YOUR OWN EMPIRE, BE THE WHOLE WORLD OF HIS MAJESTY( YOUR HUBBY) BE THE ONLY CENTER OF ATTRACTION WITH ZEE HERBALS APHRODISIAC. OUR PRODUCTS LASTS LONGER AND VERY EFFECTIVE. NO SIDE EFFECTS. AVAILABLE N WHOLESALE/ RETAILS.. DELIVERY IS NATIONWIDE. 100% TESTED AND TRUSTED_* *Nigeria* Aikawa Hajiya tayi wajen su Daddy akan su zo asa musu rana wanda wani k'anin Abba ta wakilta akai shi kuma ya kirasu ya sanar dasu, murna wajen Safwan da Mah-Mah ba'a magana, Daddy ya aika wani abokin sa da k'anin sa suka je, aka saka ranar bayan an lissafa daidai lokacin da zasu dawo da wata daya cif, sannan Hajiya ta kira Abban ta gaya masa yadda akayi, yace duk yadda akayi yayi daidai, albarka tayi ta shi masa zuciyar ta fes zata yiwa Amrah abinda take so, dama kuma ta gama shiryawa da ta dawo za'a soma yi mata magungunan musulunci wanda zai taimaka kafin auren ta dawo hayyacin ta, kamar yadda baiwar Allah nan ta fad'a mata. Kuma itama dama taga alamun hakan dan yadda iyayen Amrah din ma kad'ai suke nunawa zai tabbatar maka da ba haka ya bar su ba, dan Abban ya fara yi mata zancen ta katse shi dan bata ma son ji balle ranta ya kai ga baci.    Duk abinda ke faruwa Safwan na kiran Sultan ya fad'a masa, duk da be boye masa gaskiyar abinda ke faruwa tsananin sa da Amrah din ba na rashin daukar wayar sa da takeyi, amma sakon da take turo masa duk safiya duniya shi kad'ai ya isheshi, sai kawai ya bar komai a haka ya dauka ko wayar ce bata so, duk da sakon baya nuna kai tsaye kalaman soyayya amma shi hakan ma ya isheshi. Da wannan kawai ya dogara yake kuma fatan zata chanja, idan ma bata chanja ba shi yasan yadda zai ya chanja ta idan komai ya tabbata. A duk sanda ya fad'a masa wani abu daya danganci Amrah ranar wuni zaiyi yana shan maganin ciwon kai, dan yadda kan zai ta sara masa kamar zai raba haka yake ji, tun yana daukar abin wasa har ciwon kan ya kwantar dashi, yayi wajen sati yana jinyar kansa da zuciyar sa kafin ya sake mikewa ya koma abinda yake ganin shine k'adai gatan sa a yanzu. Mafiya yawan lokuta yakan kin daga kiran Safwan da gaske dan shi kad'ai yasan kalar tashin hankalin da yake shiga, daga baya ma sai ya bashi uzurin karatun yayi zafi ya kashe wayar baki dayan ta yayi concentrating a karatun sa. Komawar sa makaranta ya karasa shi ya dukufa sosai akan karatun nasa, a tunanin sa hakan zai mantar da shi komai sai dai ya kasa cire ta daga zuciyar sa ko da na sakan daya ne, duk kuwa da yadda be sake zuwa gidan ba amma babu wani chanji, haka ya cigaba da gurgurawa har zuwa ranar daya kammala, yasha wuya sosai dan idan ka ganshi zaka rantse bashi bane yadda ya rame ta fuska kad'ai zaka gane akwai damuwa a tattare dashi ga rashin samun abincin da yaka mata yaci hakan ya kara taimakawa wajen lalacewar tasa, sai dai yanayin jikinsa da yake kurman jiki ne dashi ba nuna komai ba, yana nan a ingarman namijin sa. Ranar daya gama ya had'a komai waje d'aya sai ya nufi gidan, yana zuwa ya tarar da suma sun kammala duk shirye shiryen tafiya, ya jima sosai a gidan amma be ga ko gilmawar ta ba duk da Afrah har inda take tazo ta gaishe shi, tun yana saka ran xata fito har ya hakura yayi haramar tafiya. Da yazo tafiya Abba ya fad'a masa yayi duk shirye-shiryen da zai yi ya gama ya fad'a masa ranar da zasu yi grad daga nan sai su ga sanda ya kamata su siya flight ticket don tare yake so su bar k'asar baki daya har Adnan, idan yaso shi sai ya dawo ya karasa karatun sa. Ya amsa masa da toh yayi musu sallama ya tafi. Kai tsaye gidan ya wuce dan suma rabon su dashi tun zuwan da yayi sukayi magana da ita, sai dai suna haduwa da Baban dan wani lokacin takanas yake zuwa asibitin ya same shi har inda yake idan ya shigo check-up, sai ya zama yana jin komai a kanta dan sosai ya damu da ita dan lokuta da yawa tunanin halin da take ciki kan dameshi har ya dinga jin yana son zuwa ya sameta ko zai iya rage mata abinda take ji. Yau a zuwan na musamman yayi, yana so ya fad'a musu tafiyar da zai yi sannan ya karasa jin labarin su ko dan yana jin da gaske zai iya yin wani Abu akai, Idan ya koma gida. Kamar yadda ya yi tunani zasu ji idan suka ganshi hakan ce ta kasance dan yadda suka nuna tsantsar farin cikin zuwan nashi kad'ai ya isa ka gane yadda ya shiga zuciyar su, Baba ne ya kalle shi kallon tsanaki sannan ya soma magana. "Muhammadu ya akayi ka rame haka, me yake damun ka?" "Na'am Babah?" Yace yana son boye abinda baban Ke kokarin hangowa "Wannan damuwar dake kan fuskar ka ba damuwar karatu bace, damuwa ce irin ta wanda ya rasa wani abu muhimmi a gareshi, me yake damun ka?" Me zai ce? Ya shiga tunani, babu abu daya a labarin sa da zai taimaka wa Baban Idan yaji, haka kuma babu wani abu da zai iya yi masa, ba kuma yason fad'an abinda zai sa a ga laifin Mah-Mah ko Safwan balle har a fadi wani abu mara dadi akansu, sai ya girgiza kai "Babu komai Baba, karatun ne wallahi akwai wahala, amma yanzu tunda na gama nasan komai zai tafi yadda ya kamata." "Toh Allah ya bada sa'a, gashi zaka gudu ka barmu, Gimbiya ba zata ji dadi ba, idan ta fito karka fad'a mata maganar tafiyar, ka barni zan mata bayani daga baya." "In sha Allah, dama Baba nace idan babu damuwa ina so naji karshen labarin ku, idan yaso sai naga ko akwai abinda xan iya akai Idan na koma." Da sauri yace "Kul Muhammadu, karka soma saka kanka a sha'anin nan, ni kaina babu abinda zan iya akai dan da zan iya wani abu da baka ganni anan ba, hatsabibancin mutanen cikin masarautar nan yana da yawa, na roke ka karka shiga abinda zai zamar maka matsala." "Babu abinda zanyi Babah, kawai da wai na zata ko zan iya wani abu akai ne shiyasa.' Murmushi me ciwo yayi sannan ya kamo hannun sa ya nuna masa wani tangameman hoto dake makale a saman falon,be taba lura da hoton ba sai a lokacin, tashi yayi ya isa wajen hoton ya tsaya yana kare masa kallo, mutum biyu ya gane a cikin hoton sai ya dawo ya zauna kusa da baban yana masa kallon son jin karin bayani "Labarin da Maruama ta baka ba komai bane akan wanda zai sanar dakai a yanzu, anan zaka tantance abinda nake fad'a maka, labarin cike yake da sark'akiya wadda duk iyakar hasashen ka ba zaka hasaso wanda yake mana zagon k'asa ba." Nannade kafar sa yayi ya tankwashe ta, ya jingina da jikin kujerar yana bawa Baban dukkan attention din da yasan yana dashi dan da gaske akwai wani abu me kamar maganad'isu da yake fusgarsa akan labarin nasu. (Idan kun shirya, mu waiwaya mu shiga Masarautar Saji muyi wani abu da ake cewa waiwaye adon tafiya, karku manta akwai zaren labarin mu da muka ajiye a baya, kowa ya dauko shi domin had'e shi.) ***A hankali karatun suratul Al-Khaf ke tashi a dakin, daga chan gefe yana sanye da short da singlet ya hargitsa dakin baki daya yana gyara tun bayan da ya samu labarin dawowar su sati me zuwa, shiyasa tun yanzu ya soma gyara dakin dan gaba daya komai aka fitar na dakin aka yi sabon fenti me kyau, aka sauya komai hatta curtains da komai na dakin, yana aikin yana bin karatun a hankali yana jin dadin yanayin, Mubarak ne ya shigo kasancewar jum'ah ce a shirye cikin shigar farar shadda kafad'ar sa rataye da sallaya, da mamaki ya dubi Safwan din "Wai karfe nawa ne?" Yace tun kafin Mubarak din ya samu damar yin korafi, agogon hannun sa ya saito daidai fuskar sa, da sauri Safwan din ya dafe bakin sa, sai ya ajiye abinda ke hannun sa yayi saurin zarar towel yayi hanyar toilet "Wallahi bansan lokaci yaja haka ba, two min bari na watsa dan Allah." "Kayi sauri toh." Yace masa ya zauna yana kare kallon dakin. A gurguje yayi wankan ya fito ya shirya cikin manyan kayan shima suka fita. Sun ci sa'a sun samu complete raka'oin sai bayan da aka gama aka watse sannan suka nufi gidan Hajiya. Da fara'ar ta, ta karbe su tana tsokanar ga angon ta ga angon ta, sunne kai kawai Safwan yake dadi fal ransa suka gaishe ta, sannan aka gabatar musu da tuwon shinkafa miyar taushe da ya zama al'adar gidan Hajiyan tun suna yara duk jum'ah tuwon ake suzo suci suna santi, hakan ce ta kasance yau ma, bayan sunci sun koshi sannan suka taba hira zuwa la'asar sukayi mata sallama suka tafi bayan sun ajiye mata kudi. Satin nan Safwan jinsa yake kamar shekara, kullum da sabon abinda xai yi na shiryawa ranar, sababbin dinkuna yayi musu shida Sultan din iri day kala biyar, ya had'a musu da takalma da set din turarukan da yasan Sultan din na so, komai ya zama ready ranar kawai yake jira, ranar da zata zamar masa daban da sauran ranaku, ranar da zasu sake haduwa da ita bayan tsawon lokaci, yasan akwai abubuwa da yawa dangane da ita da basa bayyana a hotunan ta da yake gani, he's eager to see her, irin eagerness din nan da mutum shi kad'ai yasan yadda yake ji. Gidan su Amrah ma yasha gyara sosai, dama yan haya aka saka a ciki da zasu dawo aka tashe su aka gyara shi tare da sauya komai na gidan hatta da Windows duk sai da aka sauya su. Sai gidan ya dawo sabo fil sai jiran masu gidan kawai. Ranar da sassafe ya tashi ya hau shiryawa, kamar wani mace haka yake ta bin komai daki-daki, a karshe yayi wanka, ya bata lokaci wajen kayan da zai saka, kowanne idan ya dauka sai yaga kamar be ba, haka yayi ta sawa yana cirewa har ya samu daidai wadda yayi masa, ya fito sosai kamar wata a daren sha bakwai, sai shining yake kamar wani Ango fuskar sa dauke da madaukakin murmushi. Cikin gidan ya shiga ya sami Mah-Mah da mai aikinta da Umaimah da tazo a satin jin zuwan Sultan din suna ta aikin girke-girken tarbar su Umman, sosai Mah-Mah take farin ciki da dawowar su dan dama tayi kewar Umman da kawancen su, shiyasa take cike da farin ciki a gefe kuma Safwan dinta zai hadu da abin da zuciyar sa keso. Da kallo tabi Safwan din yadda yayi kyau sosai, ya fito a cikakken mutum, sai ta hau gode wa Allah tana kuma addu'ar samun cikar burin sa. Ganin ya shigo kitchen din sai ta kasa hakuri sai data magantu "Kayan nan sun karbe ka sosai." Tace tana murmushi "Allah Mah-Mah?" "Allah kuwa, kamar wani ango." Dariya yayi yana shafa kansa, Umaimah dake gefe tace "Hala dai gasar kyau zaka je ba wai airport ba ko?" "Duk yadda kika dauka haka ne." Yace yana hararar ta a wasa, sai ya maida kallon sa wajen Mah-Mah yace "Zanje Mah-Mah, mota biyu zamuyi data Mubarak kar su karaso suyi ta jiran mu." "Shikenan Allah ya kiyaye." "Amin." Yace ya juya ya fita yana jin kamar yayi fiffike ya ganshi a airport din, sha d'aya jirgin zai sauka amma gashi tun 10 ya gama ya fito yaje yasa Mubarak a gaba shima ya shirya suka dauki hanyar airport din. ***Sallama sukayi fa kowa da suka saba, sannan suka dauki hanyar airport din cikin wani irin yanayi da ya kasu kashi kashi, farin cikin komawa kasarsu cikin yan'uwansu da kuma bakin cikin barin mutane masu kirki da nagarata musamman Anty Muhsina da family dinta da suka zama kamar wasu yan'uwa dan sosai suka shaku da ita har sukan fad'a mata damuwar su daga ita har Afrah, bangare daya kuma tunanin abinda zasu tarar a chan din ya saka Amrah jin kamar tace ta fasa tafiya, tana jin kamar tana barin wani abu me muhimmanci behind her, kamar komai ya kare ne a lokacin da ta dora kafar ta a kan matattakalar jirgin tana jin iska na hudata ta ko'ina, yana bayan su shida Adnan sai dai fuskar sa a toshe take da bakin glass baka ganin ko kwayar idon sa saboda duhun sa, a wajen bincike suka hadu amma sai yayi kamar be ganta ba har aka gama musu komai suka wuce zuwa jirgin suka shiga, ita da Afrah na gaba shi da Adnan na take musu baya, a wajen zaman ma shi ya zauna a daidai saitin bayan ta, muryar sa da yake ma Adnan magana da ita ta saka jinin ta daskarewa, dunkulewa tayi a kujerar ta lafe tana shakar kamshin turaren sa na hugo boss da ya zama kamar dan shi kawai kamfanin ke yin shi. Tafiyar sai ta zama masa kamar fami akan ciwon da yake son rufewa wanda ya gaza rufuwa har yanxu, ganin ta so close to him ya kara taimakawa, dake wa yayi yana kokarin saita kansa lokacin da Adnan yayi mata magana ta juyo idon ta ya sauka a nasa,duk da ya lullube su acikin bakin gilashi amma sai da wani abu kamar mayen karfe ya makale shi har ya kasa dauke idon nasa. "Ya Allah." Ya furta yana shafa sajen fuskar sa, yana jin yadda zuciyar sa ke bugawa da sauri da sauri kamar wanda yayi gudun tsere, ko da yake shi dinma ai gudun tseren akeyi between zuciyar sa da soyayyar Amrah, be san wanne ne zai tsare wa wani ba, dan yanzu sam zuciyar tashi bata bashi hadin kai kamar farko, gaban kanta takeyi ba tare da shawara ko neman zabin sa ba, balle akai ga ta dauki command din da yake bata na cire soyayyar Amran ta karfin gaske. Filin tashi da saukar jiragen sama na Malam Aminu Kano cike yake da mutane, daga gefe Safwan ne tsaye suna d'an taba hira da Mubarak duk da hankalin sa kusan rabi baya wajen ya kafa wa wajen da aka rubuta arrival ido, yana so ya zama idonsa na wajen sanda zasu fito,wani ne yazo giftawa ta kusa dasu yaji yana waya yana cewa jirgin ya sauka, wani irin tsalle zuciyar sa tayi kamar zata fito, yasa hannu wajen, taba shi Mubarak yayi ya juyo adan firgice "Man ya kamata ka nutsu fa, get hold of your self." Bece komai ba, shi kad'ai yasan abinda yake ji da kuma abinda yake tunani. So sorry 😐 nayi typing ya goge gaba d'aya wallahi Da kyar na yi wannan. Ignore the typos 😸 Abinda Ke Cikin Zuciya Page 18 ©® Hafsat Rano Wattpad @HafsatRano instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac. _*ASSALAMU ALAIKUM SISTERS..!_* _*INA MASU NEMAN INDA ZASU SAMU INGANTATTUN: _* _*HERBALS APHRODISIAC MA’ANA NA GARGAJIYA BANA HADIN BATURE BA MAI SIDE EFFECT..?_* _*TO KU MATSO, DOMIN NESA TAZO KUSA.._* _*ZEE HERBALS APHRODISIAC_* _*ZEE HERBALS APHRODISIAC_* _*ZEE HERBALS APHRODISIAC_* _*MUNZO MUKU DA INGATTTUN KAYAYYAKI WANDA ZASU GYARA KI CIKI DA WAJE_* _*MUNADA SUPPLEMENT MASU GYARAN JIKI DANA FATA, WANDA ZASA SAKI KIYI SHEKI FATAR KI TAYI LAUSHI. TAYI LUWAI LUWAI TAMKAR TA JARIRAI_* _*AKWAI SUPPLEMENT NA KAYAN MATA WANDA ZASU GYARA KI, KIJI KI TAMKAR BUDURWA, SUPPLEMENTS DINMU BASU DA SIDE EFFECT, DOMIN AN HADO SU NE DAGA INGATTATTUN ITATUWA, WATO NATURAL PRODUCTS NE ACIKI._* _*KAI BA ANAN KADAI MUKA TSAYA BA, MUNA DA INGATTUN KAYAYYAKIN MATA WANDA KESA KISHIYA KWAFA, WANDA DUK INDA SARAUNIYA TAKAI KIN WUCE, WANDA ZASU TSATSO MIKI MARTABAR KI DA KIMAR KI_* _*AKWAI INGATTATTUN MAGUNGUNA, NA CUTUTTUKAN DA SUKA SHAFI DAN ADAM DAMA JINNU.. KAI DAMA WANDA BAMU AMBATA BA.. ZEE HERBALS APHRODISIAC (MASARAUTAR INGATTATTUN MAGUNGUNA KENAN)_* _*KYAU, ARHA, INGANCI, RAHUSA... SAI ZEE HERBALS APHRODISIAC_* _*MANHAJOJIN MU NA SOCIAL MEDIA: KAMAR INSTAGRAM DA WHATSAPP DAMA NAMBAR TARHON MU: DOMIN SHIIGA KUGA IRIN KAYAYYAKIN MU TUNTUBE MU TA_* _INSTAGRAM LINK DIN MU:_ www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac _WHATSAPP LINK DIN MU:_ https://Zeeherbalsaphrodisiac.whats.bz _NAMBAR TARHON MU_ 08169380189 _*DA A BAKA LABARI GWARA KA BAYAR.. KIZO A DAMA DAKE YAR UWA, KI ZAMO DAYA DAGA CIKIN KASAITATTUN MATA MASU AJI.. MUNA GARIN KATSINA, SANNAN KAYAN MU MUNA BADA SU AKAN FARASHIN SAYA ‘DAI DAI KO SARI.. MUNA TURA KAYAN MU A KO’INA A FADIN NAJERIYA._* ***Akan idon sa suka soma fitowa, itace a gaba sai Adnan, Afrah sai Sultan, karshe Umma da Abba, da sauri ya isa karesu tun kafin su gama fitowa gaba daya daga wajen, ya rungume Sultan da dukkan karfin sa, fuskar sa na bayyana tsantsar farin cikin ganinsu. "Welcome back bro." Yace yana sakin sa "Thanks d'an-uwa, kai kad'ai?" Yace yana dubawa "Nida Mubarak ne fa, baka ganshi ba." "Ina zai ganni, ai ba zai ganni ba." Ya amsa yana hararar Sultan "Allah ban ganka ba sai da kayi magana, kasan mutum ya jima be ga dan uwansa ba." "Kwaji dashi, da an kwana biyu zamu fara jin kanku." "In your dreams." Yace yana dariya Matsawa Safwan yayi kusa da Adnan ya taba shi "Kaga yadda kayi kiba kuwa? Anya kana ma karatun nan da gaske?" "Sai daka gama ganin shi sannan ka ganni kenan." "Na ganka mana Ta gefe ya saci kallon ta, ta wuce wajen yan uwan Umma da suma suka zo tarar su, hannun sa sarke cikin na sultan din suka karasa inda su Umma suke yayi musu sannu da zuwa sannan suka dunguma  suka tafi gida, Sultan da Afrah suka shiga motar Safwan, Amrah ta shiga ta Mubarak ita da Adnan ba tare da ta kalli ko bangaren dasu sultan din suke ba duk da ta kama shi yana satar kallon ta, haushin yadda Safwan keta rawar kai taji, shiyasa ma da aka zo tafiya tayi saurin shiga motar Mubarak din Umma kuma suka bi motar yan uwanta ita da Abba.   Ana zuwa kofar gida tayi saurin fita ta riga kowa shiga gida, yan'uwan Abba da Umma ne cike da gidan ganin su ya mantar da ita abinda take ciki, aka shiga nan nan dasu, ga abinci masu rai da lafiya gefe kuma ga na gargajiya nan, sai ta manta da bakin cikin da take ciki aka shiga hirar yaushe gamo. Da murna Ammi ta tare shi, aka shiga gabatar masa da abinci, sannan ta aika Umaimah da mai aikinta suka kai gidan su Amrah, tace suyi musu sannu da zuwa kafin ta shigo. Wanka ya fara yi, kafin ya fito Safwan ya ajiye masa kaya komai sabo, iri daya da na jikin sa, ya shirya sannan yaci abincin yabi lafiyar gado dan sosai yake bukatar hutu. Daga shi sai dogon wando da singlet ya ware fanka a kansa ya rufe idonsa bacci me karfin gaske ya dauke shi.    Fita Safwan yayi ya barshi a dakin bayan ya jawo masa kofa, a hanyar shiga cikin gidan suka hadu da Umaimah zata bangaren nasu, dakatar da ita yayi yace mata bacci yake, kamar ba zata koma ba sai kuma ta juya tana jin haushin Safwan din, kwalliya tayi sosai da zata zo gashi yanzu dole komai ya baci. Amma bata karaya ba zata dawo anjima.    Rabon da yayi irin wannan baccin ya manta, dan sosai yasha bacci sai da Safwan ya matsa masa ya tashi da k'yar ya yi Sallah ya sake cin abincin da aka aiko masa daga gidan Umma, sannan ya fito suka nufi harabar gidan inda abokansu suke a zazzaune akan fararen kujerun roba, aka dasa hira me dadi har wajen magriba sannan suka watse. Da daddare Daddy ya dawo, suka sameshi a falon sa,da fara'ar sa ya hau cewa "Shiyasa naji gidan ya kara haske ashe likita na ne ya dawo, welcome home son, sannu da hanya." "Yawwa Daddy,mun sameku lafiya?" "Lafiya lou wallahi, ya aka kammala karatun? Ina fatan dai an samu abinda ake so." "Sosai kuwa." Safwan yace "Ai shine ma best student dinsu na shekarar." "Ah Masha Allah, Allah ya sanya wa karatun albarka." "Amin." Suka fad'a a tare. "Toh alhamdulillah, tunda an samu abinda ake so sai kaima ka kawo wadda kake so, idan yaso sai aje a samu iyayenta a yi magana ko." Dariya Safwan yasa, yayi caraf yace "Dama maganar da muka fara kenan daxu Daddy, soon zai turo ni da maganar." "Da yake kaine suda ko? Sarkin labari toh ban saka ba." Dariya Sultan ya saka yana kallon Safwan da yayi kicin kicin da fuska,  duk da yadda yaji da Daddy ya ambato maganar,amma sosai Safwan din ya bashi dariya har sai da sautin dariyar tasa ta fito. "Zan rama ne." Yace yana barin falon. Tattaunawa suka cigaba da yi da Daddy akan karatun da kuma yanayin banbance banbance da suke tsakanin kasar mu Nigeria da ma sauran kashashen da suka cigaba, da haka suka shafe lokaci me tsawo suna tattaunawa sai wajen goma sannan yayi ma Daddyn sallama. Yana shiga ya tarar da Safwan na kaiwa da komowa hankalin sa a tashe, nazarin sa yayi na d'an sakanni sannan ya jawo hannun sa ya zaunar dashi ya zauna a gefen sa. "Menene?" Yace yana balle links din hannun sa "Anya ban yi garaje ba Sultan?" "Na me fa?" "Na kai magana ta da Amrah gaban iyaye tun kafin mu sasanta kanmu, da gaske Sultan Amrah bata sona ko k'ad'an, wani daban ne a zuciyar ta..." "Kamar ya?" Sultan ya fad'a hankali a tashe "Ya kai kasan akwai wani a zuciyar ta dan kawai bata sauraron ka." "Ita ta fad'a min da kanta, tace bata sona dan Allah na barta ta auri wanda take so yake son ta." "Ta fad'a maka waye suke soyayyar?" Ya fad'a kirjinsa na bugawa, girgixa masa kai yayi alamar a ah sannan yace "Tace idan na bata dama zata sanar dani ko waye, amma bana jin ina da karfin zuciyar da zan iya tsayawa na saurareta,Ina cikin matsala Sultan." Ajiyar zuciya Sultan ya sauke da karfin gaske, wanda har yasa Safwan din kallon sa,yayi saurin waskewa tare da dora hannun sa a saman kafadar Safwan din "Mubi komai a sannu, karka takurawa kanka da tunani kasan abinda hakan zai haifar, Ina so dai kawai ka sa a ranka babu wanda ke auran matar wani, idan kaga baka aure ta ba toh ba matar ka bace, mu cigaba da addu'a." Sai ya mike ya cire kayan jikin sa a fad'a saman gadon sa yana fatan kar Safwan ya gane komai. ***Sati biyu da dawowar su, babu abu daya daya sauya na daga yadda Amrah take ma Safwan, tun bayan da taje ta samu Hajiya da maganar tayi kokarin ganin ta wayar mata da kai amma fafur taki fahimta sai ma hado ta da tayi da wasu turaren hayaki da tulin magungunan sha, hakan ya kara bata mata rai ta watsar da komai ta kuma kuduri aniyar sai ta san yadda tayi aka fasa auren wanda take ji a bakin su Umma saura sati biyu banda uban shirye shiryen da ake, komai baya mata dad'i, kowa haushin sa take ji shiyasa ma ta kara janye kanta daga harkar kowa ta sake zama introvert din gaske, a haka Anty Fatima yayar umma ta kawo wata mai gyaran jiki,ba karamin baci ranta yayi ba, tayi ta mita tana kunkuni babu wanda ya kulata. Hadari ne sosai ga garin sai dai a lokacin be taso ba, tana kwance a daki tana lissafin yadda ranakun suke guda wanda har gashi ana maganar saura sati daya bikin wanda bata ga alamun fasa shi ba, duk yadda tayi babu wanda ya saurare ta, gaba daya Hajiya tayi brainwashing din duk wanda zata samu da maganar duk kallon wadda bata cikin hayyacin ta suke mata, tashi tayi jin wani tunani ya d'arsu a ranta, ta sauya kayan jikin ta zuwa doguwar riga, ta saka d'an karamin hijabi akai, ta fito, babu kowa a falon gidan sai tv dake ta faman yi ita kad'ai, kai tsaye ta fita daga gidan nasu ta nufi gidan dake kallon shi wanda ya kasance na su Safwan, tura gate din tayi, taga motar sa a fake a gefe alamun yana gida kenan, kai tsaye ta shiga takawa sai dai tun kafin ta karasa main entrance din suka yi kicibis dashi yana sauri zai fita, wani irin birki yaja dan saura kadan su gwaru da juna, kusancin da suka samu ya saka kowanne su a cikin wani irin yanayi mara misaltuwa, kasa janye idon sa akanta daga kanta, rabon da ya ganta tun watarana da ya shiga gaida umma, tun ranar be yarda sun sake haduwa ba musamman yanzu da abubuwan bikin suka kara matsowa ya zama busy sosai, Yanzu ma fita zasuyi da Mubarak yayi wata mantawa shine ya dawo ya dauka dan ko motar sa achan ya barta ya hawo napep,ja da baya yayi kad'an yana bata hanya sai dai maimakon ta wuce sai ta tsaya ba tare da ta motsa ba, bakin ta na rawa tace "Ya sultan." "I'm so sorry." Yace yana girgiza mata kai Sai ta fashe masa da kuka, da sauri ya ciro handy ya mika mata "Karki yi kuka Amare basa kuka fa." Kin karba tayi ta cigaba da kukan da take yi, sosai kukan yake taba san dan dama kukan ta na daya daga cikin weakness dinsa, zai yi magana Mah-Mah ta fito kamar ana tunkud'ata, da sauri ya d'an ja baya sai dai kallon da take masa kad'ai yasa hantar çikin sa kad'awa. "Lallai ban taba sanin baka da kirki ba sultan sai yau, bayan duk abinda na fad'a maka, amma dan rashin kirki ka rasa aina zaka yi soyayyar ka sai a cikin gida, a cikin gidan ma gidan su Safwan, wanda ya kasance bashi da wanda yake gani sai kai, be yadda da kowa ba sai kai, kai kad'ai ya iya Kaine kake daidai a koyaushe..." "Mah-Mah ba abinda kike tunani bane Wallahi..." "Rufe min baki!" Tace a dan tsawace "Wannan shaidar kad'ai ta ishe ni." Tace tana haska masa hoton dake jikin fuskar wayar, hoton sa ne da Amrah sanda suka kusa yin gware, ba'a dauki hoton ba sai da aka tabbatar duk wanda ya gani kai tsaye zai ce rungume ta yake shirin yi,ji yayi kansa ya sara, ya dafe shi yana jingina da bango, sai ta cigaba "Dama ance tsintacciyar mage bata mage, ka bani kunya,kuma na tabbatar kai ba dan halak bane dan baka san halacci ba, shiyasa su kansu iyayen naka suka wofintar da rayuwar ka, tir da hali irin naka na manta Alkhair." Runtse idon sa yayi, yana ji ta cigaba da jifan sa da munanan kalaman da zuciyar sa ta gaja dauka. ***Sakin labulen tayi a hankali ta fito falon ta zauna a k'asa, da sauri Muhammad ya dube ta, yace "Ta samu baccin?" Daga masa kai tayi, idanun ta da yayi ja sosai yabi da kallo sannan ya mike "Bari naje chemist din Bala na samo mata ko paracetamol ne." "Ok." Tace tana zagba tagumi, fita yayi ita kuma ta koma ciki ta duba ta sannan ta fito ta had'a charcoal ta dora ruwa, ta dawo ciki ta zauna tana duba lokaci. Dogon bacci tayi sosai da ta jima bata yi irin sa ba, har akayi magriba akayi Isha'i sannan ta farka, tayi sallolin da suka tsere mata sannan tasha magani bayan ta d'an taba shinkafa da waken da Aysha ta dafa musu. Suka d'an taba hira ta koma cikin daki ta bar Muhammad yana kara ma Ayshan karatun wani littafin addini.    Zagaye dakin ta hau yi tana tariyo abinda ya faru dazu da ta fita kasuwa, tabbas idan har ba gizo idonta yake mata ba toh tabbas shine, dan ba zata taba mantawa da fuskar sa ba duk kuwa da shekarun da aka dauka da kuma nad'in dake lullube a saman kansa.    Tasan idan har ya tabbata ya ganta toh tabbas ya biyo bayan ta, kuma yaga gidan da take,ya zamar mata dole ta yi abinda ya kamata kafin komai ya lalace.    Sak'a abinda ya kamata tayi ta kwana tanayi, Idan ta lalubo wannan hanyar sai taga ba me bullewa bace dan mutanen nan sun wuce duk inda hasashen me hasashe ya kai, idan tace zata gudu dole ne zasu san in da take tun da tasan ba zasu taba barin ta ba tun da suka gano tana raye bayan rufe babin ta da take tunanin sunyi da suka samu labarin hatsarin da ya auko ranar, wanda ba dan mutum daya a duniya ba da tuni tasan rayuwar ta, ta kare daga ita har yayanta. Shine ya taimaka mata ya karbe ta a mawuyacin halin da take ciki, duk da a lokacin ashe shima da nashi kudurin a kanta sai dai hakan be dame ta, tun da ya taimaka mata ya tseratar da ita daga mummunan hannu. Tunawa da tayi dashi duk da dama bata manta dashi ba ko da na sakan daya ne saboda abinda yake a tsakanin su da ba zai taba barin ta mantawa dashi din ba, tsawon lokacin nan tasan in da yake, amma bata taba neman sa ba, sai yanzu da wani tunani ya d'arsu a zuciyar ta, taji tilas tana bukatar ganin sa, ta kuma nemi taimakon sa a karo na biyu.   Yadda taga rana haaka taga dare bata ko runtsa ba sai tsawon da taga daren yayi mata ma, anan kiran assalatu ta fito tayi alwala ta koma tayi Raka'atanul Fajr, tana zaune tana Addua tana jiran a kira Sallah Aysha ta tashi, alwalar tayi itama tazo sukayi sallar. Basu suka tashi daga wajen sallar ba sai da gari yayi sha. Shiryawa ta soma yi a gaggauce saboda yana yin gidan nasu da yadda layin bandaki yake, sannan ta saka Aysha ma ta shirya suka sha Koko suka fita. Napep suka hau har unguwar, a daidai kofar wani tangameman gida suka tsaya Aysha ta daga kai tana karewa gidan kallo, katon gaske ne iya ganin mutum, a hankali gate din gidan ya shiga budewa, wata bakar mota kirar Hyundai ta fito da mugun guda har ta kusa bige Aysha, da sauri Ammi tasa hannu ta finciko ta, tabi motar da kallo tana kisissima abu a ranta, girgiza kai tayi bayan kurar da ya bad'e su da ita ta lafa ta ja hannun Ayshan suka nufi gate din, suka kwakwasa a hankali, ta jikin har yar bular dake jikin gate din me gadin ya leko. "Wa kuke nema?" Yace yana musu kallon tsaf "Maigidan muka zo gani." "Maigidan fa? Kun sanshi ne? Kuma yasan da zuwan ku ko Yaya?" "Be san da zuwan mu ba, kace masa Safiyya ce kawai." Shiru yayi yana tunanin yaje ko kar yaje, dan yasan halin Alhaji sarai a irin wannan abun sai ya jawo ya kore shi ma daga aikin, sake kallon su yayi yaaga dai basuyi kama da almajirai ba sai dai talakawa ne kana kallon su, sai ya saki kofar ya tafi cikin gidan yana addu'ar Allah yasa kar a samu matsala.   Tsawon mintuna goma sai gashi ya dawo, hannun sa da d'an karamin complementary card ya mika mata "Yace ki sameshi a nan." Ya juya ciki Juya katin Ammi tayi, ba haka taso ba dan tana bukatar ganin sa yanzu yanzu, kafin lokaci ya kure mata, kafin abinda take tsoro ya faru, hannun Ayshan ta sake ja da sauri suka bar kofar gidan, zuciyar ta fal zulumin abinda zai je yazo.  *_Abinda Ke Cikin Zuciya_* *_Hafsat Rano_* Page 19 www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac. _*ASSALAMU ALAIKUM SISTERS..!_* _*INA MASU NEMAN INDA ZASU SAMU INGANTATTUN: _* _*HERBALS APHRODISIACS MA’ANA NA GARGAJIYA BANA HADIN BATURE BA MAI SIDE EFFECT..?_* _*TO KU MATSO, DOMIN NESA TAZO KUSA.._* _*ZEE HERBALS APHRODISIAC_* _*ZEE HERBALS APHRODISIAC_* _*ZEE HERBALS APHRODISIAC_* _*MUNZO MUKU DA INGATTTUN KAYAYYAKI WANDA ZASU GYARA KI CIKI DA WAJE_* _*MUNADA SUPPLEMENT MASU GYARAN JIKI DANA FATA, WANDA ZASA SAKI KIYI SHEKI FATAR KI TAYI LAUSHI. TAYI LUWAI LUWAI TAMKAR TA JARIRAI_* _*AKWAI SUPPLEMENT NA KAYAN MATA WANDA ZASU GYARA KI, KIJI KI TAMKAR BUDURWA, SUPPLEMENTS DINMU BASU DA SIDE EFFECT, DOMIN AN HADO SU NE DAGA INGATTATTUN ITATUWA, WATO NATURAL PRODUCTS NE ACIKI._* _*KAI BA ANAN KADAI MUKA TSAYA BA, MUNA DA INGATTUN KAYAYYAKIN MATA WANDA KESA KISHIYA KWAFA, WANDA DUK INDA SARAUNIYA TAKAI KIN WUCE, WANDA ZASU TSATSO MIKI MARTABAR KI DA KIMAR KI_* _*AKWAI INGATTATTUN MAGUNGUNA, NA CUTUTTUKAN DA SUKA SHAFI DAN ADAM DAMA JINNU.. KAI DAMA WANDA BAMU AMBATA BA.. ZEE HERBALS APHRODISIAC (MASARAUTAR INGATTATTUN MAGUNGUNA KENAN)_* _*KYAU, ARHA, INGANCI, RAHUSA... SAI ZEE HERBALS APHRODISIAC_* _*MANHAJOJIN MU NA SOCIAL MEDIA: KAMAR INSTAGRAM DA WHATSAPP DAMA NAMBAR TARHON MU: DOMIN SHIIGA KUGA IRIN KAYAYYAKIN MU TUNTUBE MU TA_* _INSTAGRAM LINK DIN MU:_ www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac _WHATSAPP LINK DIN MU:_ https://Zeeherbalsaphrodisiac.whats.bz _NAMBAR TARHON MU_ 08169380189 _*DA A BAKA LABARI GWARA KA BAYAR.. KIZO A DAMA DAKE YAR UWA, KI ZAMO DAYA DAGA CIKIN KASAITATTUN MATA MASU AJI.. MUNA GARIN KATSINA, SANNAN KAYAN MU MUNA BADA SU AKAN FARASHIN SAYA ‘DAI DAI KO SARI.. MUNA TURA KAYAN MU A KO’INA A FADIN NAJERIYA._* _*BE YOUR OWN BOSS, BUILD YOUR OWN EMPIRE, BE THE WHOLE WORLD OF HIS MAJESTY( YOUR HUBBY) BE THE ONLY CENTER OF ATTRACTION WITH ZEE HERBALS APHRODISIAC. OUR PRODUCTS LASTS LONGER AND VERY EFFECTIVE. NO SIDE EFFECTS. AVAILABLE N WHOLESALE/ RETAILS.. DELIVERY IS NATIONWIDE. 100% TESTED AND TRUSTED_* **** Tun da ya tashi yau yake jin sa babu dadi, kamar zai samu attack musamman yadda garin yake da alamun hadari, mafiya yawan lokuta a irin wannan yanayin asthma tafi tasar masa shiyasa ma daya ga yanayin garin na yau kamar akwai kura kura ma sai yayi zaman sa a daki, be san me yake faruwa ba har zuwa sanda hadarin ya taso, ya tashi da sauri ya rurrufe windows ya sassauke labulayen ya koma ya zauna still yana jin sa kamar mara lafiya. Yana zaune yaji an saka hannu an taba kofar, ya kalli kofar kadan sannan ya tashi yaje ya bud'e, tana tsaye idonta na fitar da hawaye me zafi, zafin maganganun da Mah-Mah ta gama fad'a ma Sultan ba tare da tayi la'akari da ita dake tsaye a wajen ba, ta gama tayi shigewar ta ciki lokacin har yayyafi ya dan fara kad'an kad'an.  Da sauri cikin tashin yace "Subhanallahi,Me yake faruwa? Wani ne bashi da lafiya?" Girgiza mas kai tayi, karo na farko da taji ya bata tausaya saboda yadda ya rikice har yana hada kalmomin wajen fad'a, gefe ya matsa mata ta shiga cikin dakin, sannan ta zame a hankali ta tsuguna a k'asa tana cigaba da kukan, "Dan Allah, na roke ka da Allah free me, ka taimake ni dan Allah karka bari ayi auren nan, wallahi bana son ka da sigar soyayya, ban taba son ka ba kuma bazan taba son ka ba, idan ma na aure ka toh wallahi zuciya ta ba zata taba kasancewa da kai ba, ta yaya kake tunanin zan iya yi maka biyayyar aure bayan bana son ka ko da kadan ne?" "Shi aure ana gina shi ne bisa so da kaunar juna, yarda da juna akan abu guda sai komai ya fi tafiya daidai, idan aka ce ko yaushe bangare daya ne zai yi ta kidan sa yayi rawar sa, rayuwar ba zatayi dadi ba, dole sai an samu commitment from both sides sannan ne za'a samu abinda ake so, zaman aure zama ne ba na dan lokaci, zama ne wanda ba'a san ranar kareshi ba, wala'alah sai daya ya mutu ko kuma shi auren ya mutu sannan ne za'a rabu, me yasa kowa ba zai gane hakan ba? Me yasa idon kowa ya rufe ya kasa gane hakan?" "Ki bani dama dan Allah Amrah, ki bani damar da zaki san ni waye, nayi miki alkawari idan har still baki ji kina so na ba zan barki kamar yadda kika bukata." "Me yasa sai na baka dama sannan zaka katse wannan one sided alakar tamu, duk damar da zan baka ba zaka taba samun waje a zuciya ta ba, na fad'a, zan kuma fad'a yanzu, Safwan bana son kaa." Idan har akwai wani tashin hankali toh ya biyo bayan mutum ya kalli tsabar idon ka ya ce baya son ka, musamman mutumin da kake ganin shi kad'ai ne zaka iya bawa zuciyar ka, kalaman ta sun yi ma zuciyar sa nauyi, nauyin da tasa hannayen sa suka shiga kakkarwa, idanun sa suka shiga juyawa a hankali kamar na wanda ya sha wani abun maye, bata kula da halin da ya shiga ba, ta mik'e jin ruwan na kara karfi, tayi nufin barin dakin, sai dai kafin ta kai ga kofar taji karar faduwar abu, ta juyo da sauri, hannayen sa na cigaba da kakkarwar idanun sa sun k'afe suna neman rufewa, da gudu tayi kansa jin yadda yaja sunan ta da karfi kafin komai na jikin sa ya cika ya daina aiki. **Daya bayan daya kalmomin suka shiga amsa kuwwa a kunnen sa, ya dinga jin suna shiga suna fita da sauri da sauri, jujjuyawa yaji kansa nayi, zuciyar sa tayi zafi ainun, ya shiga yin fashin baki a duk kalmomin yana so ya ware su ya ajiye kowacce a mazaunin daya dace, ciki babu maganar data fi daga masa hankali kamar wadda Mah-Mah da kanta ta kirashi maci Amana sannan ta jefi iyayen da suka kawo shi duniya da kalmomin da yake jin kamar ta dauki fetur ne ta zuba ta kawo ashana ta kyesta masa, zafin da yake ji ba kadan bane, sai yaji yana bukatar yayi abinda ya dace tun kafin komai ya kwabe, idan har mutanen da suka zauna dashi tun yana karamin sa har ya kawo yanzu zasu iya yi masa shaidar wani mugun abu, bayan shi din tarbiyyar su ne, su suka rene shi suka nuna masa yadda zai iya banbance what's wrong and right, toh be san kalar kallon da mutane zasuyi masa ba, Idan har abinda ke cikin zuciya ya bayyana, ya zama dole ya san abinda ya kamata yayi. Juyawa yayi da nufin ficewa daga gidan duk kuwa da yayyafin dake kara karfi sai yaji kamar faduwar abu, sai kuma yaji kamar muryar Safwan cikin mawuyacin hali, a take ya tuno, ya ga sanda Amrah ta nufi bangaran bayan da Mah-Mah ta bar wajen, tashin hankalin da yake ciki be barshi ya gane abinda take son yi ba, da sauri ya nufi dakin hankalin da a matukar tashe, ya bud'e kofar,be san sanda ya kai kansa tsakiyar dakin ba, ya hau jijjigashi da karfi yana kiran sunan sa, babu alamun motsi a tattare dashi, daga shi yayi ya dora shi saman gadon, yayi saurin jawo first-aid kit din sa ya shiga fito da komai na ciki yana hada abinda zai bukata waje daya.   A hankali numfashin sa ya soma daidai ta amma be farfado ba, sai ya daura masa drip ya juya da sauri zai fita domin samo wata allura da be san ya akayi bashi da ita ba, sai kuma ya tsaya ya kalle ta, kuka take sosai kamar ranta zai fita, tausayin su dukka ya sake kamashi, suna cikin tsaka me wuya. "Ki kula dashi zanje na samo allura." Gid'a masa kai tayi ya fita da sauri ita kuma ta matsa gaban gadon tana kare masa kallo. ****Da karfi sosai ruwan yake sauka babu alamun tsayawar sa nan kusa, iska ce me karfi hade da walkiya me tsananin haske ke kara yanayi da karar saukar ruwan, karfe biyar da yan mintuna agogon dakin ya nuna sai dai yadda garin yayi duhu sosai zaka dauka dare ne, tsaye take tsam a gaban gadon tana dubansa cikin zubar hawaye, bata damu da ta share su ba ko tayi yinkurin tsaida zubowar tasu dan hakan ne kadai saukin da take samu a radadin da zuciyar ta ke mata. Turo kofar akayi ta dago da sauri tana sauke idonta akansa, kayan jikinsa sun jike jagaf, idanunsa sun kada sun yi ja jajur ya iso gaban gadon da sassarfa, allura ce a hannun sa, yayi saurin hada ta a jikin sirinji ya dure ta cikin drip din dake sauka a mugun hankali wanda sai ka lura sosai sannan zaka iya gane fitar sa. "Ya sultan..." Ta kira sunan sa cikin dashewar murya, rinannun idanun sa ya dago ya sauke akanta yace "Tun bayan fitar da nayi be motsa ba?" Girgiza masa kai tayi tana matsawa baya, ajiyar zuciya ya sauke da d'an karfi sannan ya gyara masa zaman kansa sosai yana duban sa, duba na tsanaki me cike da tarin manufofi, gefe ya kauda kan sa yana kara karfafawa kansa guiwar abinda yake shirin aikatawa shine daidai. "Zuwa safiya idan Allah ya kaimu zai tashi kamar babu abinda ya faru." Yace yana motsa jikin ledar drip din kadan. Shiru sukayi na wani lokaci kafin yace "Amrah... Zan tafi, zan tafi nesa da kowa badon inaso ba, badon hakan shine farin cikin zuciya ta ba, sai dai hakan shine abinda ya dace, abinda ya zama tilas da nayi shi domin shine kadai kwanciyar hankalin mutanen da suka cire rayuwata daga kangin wahala suka lullubeta da tarin alkhairan su wanda ba zasu kirgu ba, suka yanta ni na zama kamar kowanne d'a dake gaban iyayensa. Sunyi min dukkan gatan har na zama abinda na zama a yanzu." "Magana d'aya kake..." Ta katse shi da sauri "Me yasa ni ba zaka duba ni ba? Tabbas rama alkhairi da alkhairi shine, amma ka fad'amin, me kayi da ya zama butulci ga alkhairi da suka yi maka? Ka yarda ka kuntatawa rayuwa da ruhin mu akan farinciki su? Wacce irin zuciya ce wannan? Wacce irin zuciya ce...?" Ta karashe tana rufe bakin ta kar kukan da take ta rikewa ya fito. Jijiyar kansa tayi rud'u rud'u tana harbawa da sauri da sauri, hannu yasa ya dafe kan nasa da yake jin kamar zai guntule daga gangar jikinsa. Takowa ya shiga yi a nutse har ya isa gaban ta inda ta durkushe tana kuka a hankali, kafafuwan sa ya dire a gabanta yana jin tashin hankalin sa na karuwa saboda yadda take fitar da kukan daga chan cikin zuciyar ta, sai dai ya zai yi? Mutumin daya kare rayuwar sa wajen ganin ya samu waraka daga mummunan ciwon zuciyar dake damun sa tun yana zanin goyo, ace kuma sai da komai yazo karshe ya sake maidashi farko, idan yayi haka sam beyi adalci ba,babu abinda ba zai iya sadaukarwa Safwan ba, idan ma rayuwar sa yake so zai iya bashi dan yafi karfin komai a gareshi ciki kuwa harda soyayyarshi. Sai dai hakan na nufin cutar da tasa zuciyar da yake jin tana masa wani masifaffen ciwo da zugi, ya sota tun ranar data fara isowa duniya, tana cilla kafafuwanta tana kuka da d'an karamin bakin ta, a rana Allah yasa masa kaunar ta a zuciyar sa, ya kuma cigaba da dakon sonta har zuwa lokacin daya bayyana mata, ta karbe shi hannu biyu suka raini soyayyar su har zuwa lokacin da komai ya kwabe, lokacin daya tabbatar da ta tsere masa har abada,lokacin daya tabbatar da itace zabin mutum na farko a duniya da yake so da ganin kimar sa, wanda alheransa basa yankewa a gareshi, ya masa dukkan gata ya daga darajar sa a duniya. Dolen sa ne yayi duk yadda zaiyi wajen ganin ya boye *Abinda Ke Cikin Zuciyar sa* har zuwa iya wa'adin kwanakin da Allah ya dibar masa zai yi a doron k'asa.   Lungu da sako kukan ta ke bin ilahirin jikinsa yana zagaye kowanne sako, da ace yana da damar bude mata zuciyar sa daya bude mata taga yadda take, amma ya suka iya? "Ki daina kukan nan haka dan Allah." Ya fad'a kamar zaiyi kukan shima, bata daina ba sai ma kara karfin kukan tayi yayi saurin kallon gadon da Safwan yake kai, ganin be motsa ba yasa ya maida duban sa kanta cikin kasa da murya yace "Ina sonki, son da ban taba yi wa wani mahaluki irin sa, ina miki so kwatankwacin yadda uwa ke son d'an ta,zan tafi, zanyi nisa dake da d'an-uwa na domin hakan shine kwanciyar hankalin mu. Mubi zabin iyayenmu muyi musu biyayya hakan shine dacewarmu, sai watarana!" Sai ya mike kamar wanda aka tsikara yayi hanyar barin dakin. Mikewa tayi ta kira sunan sa da sauri tana jan kuka kamar zata shid'e, taku biyu ya kara ya dangana da kofar, sai daya kama handle din sannan ya daga mata hannun sa daya alamun bye-bye ya fita da mugun sauri hannun sa dayan dafe da kirjinsa. Sai ta durkushe a wajen tana sakin kuka ta furta "Nooo...." Kukan yake shima wiwi, duk yadda yaso kar su bayyana sai da ya kasa rike su, girgiza kai kawai yake bayan ya gama jin komai, wacce irin soyayya Sultan yake masa har haka? Da ya zabi ya sadaukar masa da abinda yasan da zaman sa a zuciyar sa tun basu mallaki hankalin kansu ba. Dan yana tuna wani lokaci da ake hira da abokai kowa yana maganar budurwar sa, suka matsa masa akan sai ya fadi tasa, lokacin basu fi aji uku a sakandire ba, ya tuna amsa da ya basu _"Ni bani da budurwa sai mata, na riga na zabi matata tun tana yar jinjirar ta, ku ne a ruwa."_ Tun daga lokacin suke tsokanar sa na aljana dan basu yarda da wata soyayya da yar karamar yarinya ba. Lallai soyayya bata yi musu rana ba, data hada su wajen son abu guda, son kuma me tsanani da wahalar da ruhi. "Kai ka chanchanci ka sameta dan uwa na, zanyi dukkan kokari na wajen ganin na samar maka da farin ciki ko da hakan na nufin...." Rufe kofar da yaji anyi ne alamun Amrah ta fita shi ya bashi damar yin kukan da yake rikewa, ina Sultan zai tafi a wannan ruwan? Wa yake dashi kaf duniyar nan kamar shi, bayan haka ma ta yaya zai iya cigaba da rayuwa me dadi ba tare dashi ba? Lallai yana daukar kaunar da yake masa a matsayin wasa, dole ya nuna masa ba shi kadai yake da ikon rama alkhairi ba, shi ma dan halak ne wanda yasan halacci. A hankali ruwan ya fara tsayawa saboda gabatowar magriba, hayaniyar jama'ar dake cikin gidan nasu ta cigaba da karuwa wadda dama karfin ruwan ne ya hana aji ta, tun da har babu wanda yasan da halin da ya shiga dazu dole ne ya tashi ya karfafa jikinsa domin samun karfin aiwatar da kudurinsa. **** Tafiya yake ba tare da yasan ina yake sakawa da cire kafarsa ba, duhun magribar ya kara disashe kaso hamsin na ganin sa, ganin yana neman samun matsala yasa ya daidaita kansa ganin ya kawo titi ya tsaida abin hawa ya fad'a masa inda zai kaishi. Suna isa ya cire kudin sa ya bashi sannan yasa hannu a aljihun sa domin daukar key ya tuna komai na motar sa da ya bari a gidan Mubarak, katangar ya kalla ganin zai iya hawa ta jikin gate din sai kawai ya kama ya dira domin bazai iya jira ko ya koma ba. Yana shiga ya cire kayan jikinsa da suka soma bushewa da kansu ya watsa a laundry yayin saurin shiga ganin magriba na neman tseremasa. Wanka yayi a gurguje ya saka kaya ya kabbara sallar a cikin dakin, bayan ya idar ya jima yana musu Addua, a hankali yaji zuciyar sa ta soma sanyi, tunanin abinda zai yi ya shiga dawo masa daki daki. Da farko dai dole ya waiwayi rayuwarsa ta baya domin yin duba cikin abinda ya rufe ya hanawa kansa tunanin sa ganin cewa ya riga ya gama tabbatar wa kansa su din babu alkhairi a tarayyar su shiyasa ma har sukayi wasarairai da rayuwar sa har ta shiga tangal-tangal wanda ba dan Safwan ba, da tuni yasan komai ya kare watakil ma an shafe babin wani me irin sunan sa a doran kasar, dan dole ne cikin biyu ayi daya. Saboda yadda rayuwar yaran da suka taso cikin gidan marayu ke karewa da zarar sun kai wani mataki da babu me iya taiamaka musu ko ya dauki nauyin su. Amma ta ina zai fara? Mutum daya ce zata taimaka masa sai dai be san ta inda zai fara neman ta ba, tsakanin sa da gidan sakon Daddy ne shima adah,kafin ya fara samun na kansa ya zama shine meyi, shima sai ya zama aike kawai yake musu ta hannun Mubarak tun da baya kasar.   Ya zama dole ya waiwayi rayuwarsa ta baya ko dan sanin abinda ke boye, ko dan maganganun da dokin zuciya ta dibi mummy ta gaggaya masa su wanda sukayi nasarar dawo dashi bayan.   Sai ya tuna sanda yaje kai sakon karshe gidan marayun, ta kirashi daki tace "Sultan har yanzu baka ji kana bukatar jin wani abu daga cikin rayuwar ka ba?" Girgiza mata kai yayi "Duk abinda kika ga Allah ya rufe toh baya bukatar a budeshi, bana jin dana sanin rayuwa ta, saboda haka bana bukata gaskiya." Yake tayi masa Wanda aka ce yafi kuka ciwo, sannan tace "Kayi tunani, idan ka yanke shawara kazo ka same ni,saboda halin rayuwa, karka dau dogon lokaci." A lokacin be dau maganar ta da wani muhimmanci ba shiyasa ma be sake waiwayen maganar ba, a yau sai gashi yana bukatar sanin abinda ke boye, yana fatan hakan ya zamar masa mabudin kofar alkhairi.Hafsat Rano Page 20 www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac. _*ASSALAMU ALAIKUM SISTERS..!_* _*INA MASU NEMAN INDA ZASU SAMU INGANTATTUN: _* _*HERBALS APHRODISIAC MA’ANA NA GARGAJIYA BANA HADIN BATURE BA MAI SIDE EFFECT..?_* _*TO KU MATSO, DOMIN NESA TAZO KUSA.._* _*ZEE HERBALS APHRODISIAC_* _*ZEE HERBALS APHRODISIAC_* _*ZEE HERBALS APHRODISIAC_* _*MUNZO MUKU DA INGATTTUN KAYAYYAKI WANDA ZASU GYARA KI CIKI DA WAJE_* _*MUNADA SUPPLEMENT MASU GYARAN JIKI DANA FATA, WANDA ZASA SAKI KIYI SHEKI FATAR KI TAYI LAUSHI. TAYI LUWAI LUWAI TAMKAR TA JARIRAI_* _*AKWAI SUPPLEMENT NA KAYAN MATA WANDA ZASU GYARA KI, KIJI KI TAMKAR BUDURWA, SUPPLEMENTS DINMU BASU DA SIDE EFFECT, DOMIN AN HADO SU NE DAGA INGATTATTUN ITATUWA, WATO NATURAL PRODUCTS NE ACIKI._* _*KAI BA ANAN KADAI MUKA TSAYA BA, MUNA DA INGATTUN KAYAYYAKIN MATA WANDA KESA KISHIYA KWAFA, WANDA DUK INDA SARAUNIYA TAKAI KIN WUCE, WANDA ZASU TSATSO MIKI MARTABAR KI DA KIMAR KI_* _*AKWAI INGATTATTUN MAGUNGUNA, NA CUTUTTUKAN DA SUKA SHAFI DAN ADAM DAMA JINNU.. KAI DAMA WANDA BAMU AMBATA BA.. ZEE HERBALS APHRODISIAC (MASARAUTAR INGATTATTUN MAGUNGUNA KENAN)_* _*KYAU, ARHA, INGANCI, RAHUSA... SAI ZEE HERBALS APHRODISIAC_* _*MANHAJOJIN MU NA SOCIAL MEDIA: KAMAR INSTAGRAM DA WHATSAPP DAMA NAMBAR TARHON MU: DOMIN SHIIGA KUGA IRIN KAYAYYAKIN MU TUNTUBE MU TA_* _INSTAGRAM LINK DIN MU:_ www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac _WHATSAPP LINK DIN MU:_ https://Zeeherbalsaphrodisiac.whats.bz _NAMBAR TARHON MU_ 08169380189 _*DA A BAKA LABARI GWARA KA BAYAR.. KIZO A DAMA DAKE YAR UWA, KI ZAMO DAYA DAGA CIKIN KASAITATTUN MATA MASU AJI.. MUNA GARIN KATSINA, SANNAN KAYAN MU MUNA BADA SU AKAN FARASHIN SAYA ‘DAI DAI KO SARI.. MUNA TURA KAYAN MU A KO’INA A FADIN NAJERIYA._* ***A saman abin sallah ya kusa kwana yana addu'ar Allah ya kawo masa hasken abinda yake shirin tunkara, abubuwa biyu masu muhimmanci da zai yi, na farko sanin shi kansa, sai na biyu masarautar saji, alkawari yayi ma kansa sai ya taimaka wa bayin Allah nan, duk da be sanar dasu abinda ya shirya yi ba har suka rabu, sai dai ya tabbata ya samu duk wasu bayanai da zasu taimaka masa.   Karar wayar sa ta farkar dashi baccin daya dauke shi a wajen da yayi sallar bayan yayi asubah, a dan firgice ya tashi dan yadda baccin ya hau kansa sosai yasa hannu ya dauki wayar lokacin har kiran ya tsinke, sai tarin misscalls da ko ba'a fad'a masa ba yasan na waye, kiran ne ya sake shigowa, ya goge fuskar sa da bayan hannun sa sannan ya daga, kafin ya gama daidaita wayar a kunnensa ya jiyo masifar sa "Me kake tunanin ka aikata?" "Ka saurare ni..." Yace muryar sa a hankali "Babu abinda zaka ce malam kawai ka dawo kasan dai ba zan iya cigaba da shirye shiryen nan babu kai ba, na kira Mubarak shine yake fad'a min wai zaka je ina ne ma? Ni banma tsaya naji ba." Ya fad'a kai tsaye pretending kamar ba san komai ba "Toh.." yace yana runtse idon sa had'e da sauki ajiyar zuciya jin Safwan din be san komai ba à "Zan dawo amma ka bani time, wani abu ya taso min urgent zan zama busy Amma zan dawo." "Ka dau daga nan har zuwa two weeks din, kawai dai karka yarda kayi missing ranar, it's my day kuma ba zan iya komai idan baka nan ba." "I promise you zan dawo ayi komai dani. "Shikenan." Yace sannan ya kashe    Number Mubarak ya nemo ya kirashi sukayi magana sannan ya kashe, ya koma ya zauna yana kulle idon sa kamar me bacci. Yana zaune yaji ana knocking, sai kuma yaji an saka key an bud'e, be motsa ba har ya shigo hannun sa dauke da jaka da sauran abubuwan ya zube su a gefen sa, bud'e idonsa yayi yana kallon sa har yayi ma kansa wajen zama "Are you ok?" Yace yana dubansa ganin yadda duk ya fita hayyacin sa daga rabuwar su zuwa yanzu. "Gani nan ne dai, ka dauko min komai da komai da nace?" "A tunani na, amma ka duba ka gani dai idan akwai wani abu, ga breakfast nan na tawo maka dashi dan nasan babu abinda ka sawa cikin ka." "Nagode sosai Mubarak." Yace a hankali Mikewa yayi ya dauko d'an basket din daya zo dashi da yake dauke da abincin ya bud'e musu ya zuba komai suka hau ci babu me magana a ciki har suka gama, wanka Sultan ya shiga yayi, ya fito ya dauki kayan da Mubarak din ya kawo masa ya saka daya sannan suka fita tare a motar Mubarak din bayan ya shigo da tasa cikin gate din.    Kai tsaye orphanage din suka nufa, bakin sa dauke da Adduar Allah yasa abinda zai ji ya zama me dadin sauraro ba abinda zai sake dagula masa lissafi ba.      Sun isa gidan lokacin da yaran ke cike a harabar suna wasannin su, a take tunanin sa ya dauke shi zuwa chan baya, lokacin da shi ma yake a cikin su,without any hope ko future dan duk yaron dake cikin gidan nan bashi da wani future idan ba Allah ya taimake shi ya fita daga gidan ba, ba zai ce ba'a kula dasu ba, daidai gwargwado ana yi fiye ma da tunanin wasu dake waje, amma maganar gaskiya itace rayuwar su bata da wani muhimmanci a society tun da babu abinda zasu iya taimakawa dashi in any way,an kashe musu rayuwa tun kafin su san mecece ita kanta rayuwar balle su iya tsayawa da kafafuwansu su taimaki kansu da Al'umma baki d'aya.     Ta cikin su ya dinga ratsawa yana jin kamar a lokacin ne komai yake faruwa, duk wajen da yaxo sai ya kalla ya tuno wani memory nasa a wajen har ya dangana da babban ofishin, amma sai ya tsaya yana jin tsoron abinda zai tarar, a hankali ya dan buga kofar kad'an, yana fatan ta jiyo shi ba tare da ya sake bugawar ba, kafin ya gama tattaunawa da zuciyar shi aka bud'e kofar, ya daga kansa yana kallon wanda ke tsaye a gaban sa, Malam Bahaushe kamar yadda suke kiran sa, tsaye ya na kallon sa, kallon son tuno inda yasan fuskar Sultan din, zai yi magana kenan yaji ance "Sultan..." Waigawa yayi ya kalli me maganar, Malam Bako ne, sai ya fad'ad'a fara'ar fuskar sa ya juya wajensa "Malam." Ya kira sunan sa sannan ya dora "Barka da warhaka Malam." "Barka dai Sultan, ina ciki aka zo aka cemin kazo, ashe dai kai din ne kuwa da gaske." "Nine Malam." Yace yana murmushi "Toh muje ko? Naji kana nema na." Yace yana kallon Malam bahaushe da yadda yake dubansu su dukka, sai yace "Oga Sir wannan tsohon member ne na gidan nan kila ka manta shi kasan yaran da yawa." "Ina wuni?" Sultan ya gaishe shi a gajarce ganin yadda yake kallon sa, be ji ya amsa ba har suka bar wajen suka nufi wata bishiya a chan k'asan gidan shi da Malam Bako. "Karka ji nace kana nema na bayan nasan ba neman nawa kake ba, Aziza kake nema ko? Ita kake zo gani?" "Aziza?" Ya ambata da sigar tambaya "Maman Yara toh, da haka ka santa ko?" "Eh malam, sai dai alamu sun nuna bata gidan kamar, yadda naga abubuwa da yawa." "Ai ta dade da barin nan din, kuma dama tace min zaka zo nemanta wataran, ta kuma ce na baka wannan." Sai ya ciro wata envelope a rufe ya mika masa yasa hannu ya karba yana jujjuyata a hannun sa. "Amma mesa tabar gidan nan?" "Toh ba zan ce kai tsaye ga dalilin barin nata ba, abun dai da alama daga sama ne, haka mu ma kawai muka tashi da maganar tafiyar ta, kuma bamu san ainihin abinda yasa tafiyar ba, sai dai mun san tafiyar ba ta dad'i bace duba da yadda tazo katsaham, a ranar kuma aka maye gurbi da Malam Bahaushe kamar yadda ka gani, amma ko shi baban naku (Daddy) ya san dalilin hakan, duk kuwa da har yanzu komai na gidan yana hannun sa ne." "Toh nagode Malam, bari na tafi." Ya mike yana saka hannu a aljihu, ya ciro kud'i masu dan kauri ya mika masa, gashi Malam ko akwai abinda zaà yi wa yaran dasu." "A yayi Albarka." Yace yana saka hannu ya karba, sannan sukayi sallama ya tafi. Mubarak na ganin shi ya taso daga chan inda ya samu ya zauna yana jiran sa "An dace?" Girgixa masa kai yayi suna nufar motar "Bata gidan, sai dai ta bar min sako." "Ok." Yace sannan yayi ma motar key suka bar wajen.     A asibiti ya ajiye shi ya shiga ciki shi kuma ya wuce domin shiryawa ya tafi wajen aiki. Takawa ya shiga yi har ya dangana da babban office din MD, yana zuwa shima yana isa kusan a tare ma suka je, hannun sa ya kama suka shiga office din yana amsa gaisuwar sa. Ya jima sosai a cikin office din sannan ya fito ya tafi. State Library ya wuce daga nan, still takardar sa na makale a hannun sa, sai daya shiga ciki, chan inda babu hayaniyar komai ya zauna sannan ya soma bud'e takardar a hankali har ya gama warwareta baki d'aya. _"A lokacin da zaka riski sakon nan nawa, na tabbata da nai maka nisa, bana so ka nemi ne dan ba zaka same ni ba,ban sani ba ko watarana, idan da rabon mu gana,akwai abubuwa da yawan gaske da nake son sanar dakai amma babu hali, sai dai sunayen mutanen nan zai taimaka maka k'warai wajen samun haske a abinda ka saka a gaba, inayi maka fatan alkhairi a koda yaushe."_ Sunaye ne a rubuce da babban baki, kowanne yana nuna arrow zuwa na gaba, sai dai dukkansu akwai tazara me yawa a tsakanin kowannen su. Sunan d'aya ne ya dauki hankalin sa sosai ganin shi har da address a rubuce a jiki. *_Safiyanu Madaki_* yayi maimaita sunan ya sake maimaitawa kamar me son tuno wani abu, biro yasa ya zagaye sunan sannan ya nannade takardar ya tura ta a aljihun sa ya fito daga wajen. *** Kallan jikin card din take tana kallon hanya, suna zuwa address din ta biya me adaidaita sahun kudin sa suka nufi building din, kan Aysha a daure yake da al'amarin Ammi ta kasa gane abinda suke nema wajen mutumin da kallo d'aya zaka yi ma gidan sa ka san ba karamin mutum bane, yau rana ta uku kenan suna sintirin zuwa amma yaki ganin su, amma basu daina zuwa ba, gashi gaba daya Ammi ko sana'ar ta ta, ta daina a kwana ukun nan haka suke fama da kansu sai dai ko k'ad'an bata nuna damuwar hakan ba, damuwar ta, tafi ga yadda zasu yi suga mutumin nan wanda yau kafin su fito Aysha ta sanar ma Muhammad abinda ke faruwa dan shi be san komai ba kuma Ammin taki sanar dashi. Da kallo me gadin ya bisu dan ya gane su sarai a kwana biyun da suka zo, sai dai yau ba kamar wadanchan ranakun biyu bane, yau suna zuwa ya taso ya bude musu kofa sannan ya basu wajen zama, ya shiga ciki. Jim kad'an sai gashi ya fito ya koma wajen zaman sa yana kad'a kafarsa, suna zaune basu ce masa komai ba har zuwa sanda wayar sa tayi k'ara, ya d'aga da sauri sannan ya taho wajen su. "Ku taho." Yace Da sauri suka bi bayan sa, har zuwa wani katafaren fargajiya wadda ke cike da shuke shuke, ba zaka taba zata akwai mutum a wajen ba, yana zaune bayan sa na fuskantar su, suka zagaya suka zauna a wasu kujeru guda biyu da aka ajiye a gabansa. Waya yake k'asa k'asa be dago ba balle ya amsa sallamar da Ammin sukayi masa, sai da ya kashe mintuna masu yawa yana wayar sannan ya dago yana duban ta, duba irin na tsanaki me tattare da ma'anoni masu yawa. "Safiya?" Yace yana kad'a kansa. "Kina da naci da yawa, kwana uku kina sintirin zuwa, na dauka da kika zo sau biyu zaki hakura, ashe zaki dawo, kina nan da halin ki na juriya da naci a komai." "Naga Mahdi, na ganshi a kasuwa kuma ya ganni, kuma kasan hakan me yake nufi ko?" Sai ya kafe ta da ido kamar me nazari, sai kuma ya mike da sauri ya na danna wayar sa "Da yaushe kika ganshi, a wanne irin yanayi da kuma lokaci, sannan kin tabbata be bi ki yaga inda kike ba?" "Wacce tambaya zan amsa a ciki, bayan tsawon lokacin nan rashin amsa daga gareka ya hanani cika burin Maimartaba." "Hello Musa." Yace yana fita daga wajen da sauri. Ajiyar zuciya Ammi ta sauke taki yarda su hada ido da Aysha. "Ammi... Wai me yake faruwa?" "Yanzu ba muhallin tambaya bane Aysha, ki nutsu." Shiru sukayi dukka, sai gashi ya dawo ya zauna yana ajiye wayar "Karki damu komai zan san yadda zan yi." "Ina yake?" Tace masa kai tsaye "Baki yarda da cewa zan yi abinda ya dace ba? Baki yarda dani ba?" "Na yadda da kai a dah amma banda yanzu, na yarda da kai har na baka amanar abinda yafi komai muhimmanci a gare mu baki daya, amma me kayi? Ka ha'ince ni ka kuma barni da kaina bayan kasan bani da kowa." "Safiya!?" Yace yana kallon Aysha "Safiyanu Madaki!" Ta ambata muryar ta ras, da wani irin mamaki yake duban ta, kai tsaye babu ko sakayawa? Lallai Safiyya ta shirya tunkarar sa. "Me kike so nace miki? Baki yarda da abinda nace miki shekarun baya ba? Da kafafuwansa zai kai kansa, ranar da dukkan abinda ke lullube a cikin zuciya zai bayyana, ranar na zuwa, nan kusa." Mikewa tayi tana girgixa kanta "Ka bamu sabon wajen zama, sannan ga yarka nan na kawo maka." Ta nuna masa Aysha tana kauda kanta. Da sauri ya mike har yana ture kujerar da yake kai. "Kina nufin?" "Yarka ce, cikin da ka barni dashi kenan, ban sanar dakai ba sai dan sanar dakai din bashi da Amfani, sai dan sanin kai din waye da yadda ka dauke ni." Sai ta juya wajen Aysha da ta sandare tana duban wanda aka kira da mahaifin ta "Kiyi hakuri Aysha, wannan shine mahaifin ki da kike son gani, bayan auren mu da watanni uku ya sakeni." Duban sa tayi, babban mutum me ji da kudi da aji, sai ta kalli Ammin, bata sani ba ko wahala ce ta maida ta haka, amma sai taga sam babu gamin hadi ita da mutumin da ta kira da mahaifin ta,ya ninka ta a komai nesa ba kusa ba, toh kenan idan har sunyi aure akwai dalilin da yasa sukayi auren kenan? Har da zai sake ta a wata uku kachal?" "Aysha...?" Ya kirata da muryar sa da ta ji tana mata amsa kuwwa a kunnen ta. "Aysha... Kiyi hakuri ki yafe min " Yace yana matsawa daf da ita, "Mahaifiyar ki ita ta hana ni sanin ki balle har nayi miki abinda uba ya kamata yayi, saboda wani laifi da take ganin nayi mata wanda sai nan gaba kad'an zata gane." Shiru tayi tana sauraron sa har ya gama maganganun sa da bata gane komai a ciki ba, ita Ammi na gefe bata tanka musu ba har ya gama sannan ya dauki waya yayi magana, yana gamawa yace "Ku je ku shirya dan Allah Safiyya, sabon gida zaku koma." Bata ce komai ba taja hannun Aysha dake ta faman waigen mutumin da aka kira da mahaifin ta, har suka gama ficewa daga wajen sannan suka fito bakin titi suka hau abin hawa. "Ammi dan Allah?" Tace tana marairace murya ganin sun kusa zuwa gida "Ki bari muje gida." "Tohm." Tace taja bakin ta tayi shiru. Suna zuwa suka hau had'a kayansu waje d'aya, duk abinda Ammi take sauri sauri take yi,suna cikin hadawa Muhammad ya dawo, ya tsaya yana kallon su. "Ammi?" "Muhammad babu lokacin doguwar magana, barin gidan nan zamuyi idan muka koma inda zamu koma zan fad'a muku komai, har ma da abinda nake boye muku, kafin lokaci ya kure min." Bece komai ba, shima sai yasa hannu ya taya suka karasa hadawa, sannan suka zauna zaman jiran wanda zai zo su tafin kamar yadda Safiyanu Madaki yace. Sauran yan gidan Ammi tasa suka je sukayi wa sallama, sai duk suka nuna rashin jin dadin tafiyar da zasuyi haka da wuri haka. Bayan sun dawo daki suna zaune akayi sallama a waje, Muhammad ya tashi zai je, Ammi ta tsaida shi tace "Ina zuwa." Mayafinta ta yafa ta fita, wajen mintuna biyar suna zaune shiru bata dawo ba, Muhammad ya tashi ya fita dan yaga abinda ya tsaida ta, sai dai abin mamaki babu ko me kama da ita a layin, da sauri Muhammad ya dawo ciki yana kwala kiran Aysha, ta fito tana tambayar sa lafiya. Waje suka sake komawa suka hau duddubawa sai dai babu Ammi sama ko k'asa. *** Karar ganguna da kalangu ne ke tashi a kowanne lungu na Masarautar, duk inda ka kalla zaka ga mutane na kaiwa da komowa, hakan ya nuna ana wani gagarumin taro ne ko kuma wani shagalin biki a Masarautar, sai dai a irin wannan ranar, a irin kwanan watan Sarkin na shirya musu wani shagali na musamman da babu wanda yasan dalilin shirya shi, kowa ya kan samu abinci me rai da lafiya yaci har ma yayi guzarin sa zuwa gida.    A wani babban Fili dake cikin masarautar anan ne ake gudanar da bikin. Daga chan saman wani tudu an shirya kujeru na alfarma, manyan yan fad'ar sarki ne a zazzaune kowannen su yasha nadi irin na sarakai, sarki be fito ba tukunna, mafiya yawan lokuta baya fitowaa ya kan dai dawo fad'ar sa dake kusa da filin ya zauna yana jin duk abinda ke faruwa. Yau ma hakan ne ya faru, yana zaune akan karagar sa, mutane uku da ya aminta dasu kaf Masarautar, Magatakarda, Waziri da Madaki na zaune a k'asa suna tattaunawa, sakon ya iske su. Me sakon ne ya fadi k'asa yayi gaisuwa, suka amsa masa da sarki ya gaishe shi, sannan ya mika wata takarda, ya koma gefe ya durkusa, magatakarda ne ya karba ya warware ta sannan ya soma karantawa a fili bayan sarki ya bashi umarni. Da wani irin yanayi dukka suke kallon shi har ya gama karantawa ya nannade ta ya mika ta ga Waziri, dubawa ya sake ki sannan ya kalli Sarki yana rissinawam "Allah ya baka yawan rai." Da hannu sarkin yayi masa alamar da tasa shi duban d'an aiken sannan yace "Mahdi ya tabbatar da abinda yake fad'a? Ya sani babu Wasa tsakanin sa da Masarautar, idan har abinda ya rubuta a jikin wasikar nan gaskiya ne, muna bukatar ya bayyana a gaban fad'a gobe warhaka tare da ita." "An gama ranka ya dad'e."Hafsat Rano Page 21 www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac. _*ASSALAMU ALAIKUM SISTERS..!_* _*INA MASU NEMAN INDA ZASU SAMU INGANTATTUN: _* _*HERBALS APHRODISIAC MA’ANA NA GARGAJIYA BANA HADIN BATURE BA MAI SIDE EFFECT..?_* _*TO KU MATSO, DOMIN NESA TAZO KUSA.._* _*ZEE HERBALS APHRODISIAC_* _*ZEE HERBALS APHRODISIAC_* _*ZEE HERBALS APHRODISIAC_* _*MUNZO MUKU DA INGATTTUN KAYAYYAKI WANDA ZASU GYARA KI CIKI DA WAJE_* _*MUNADA SUPPLEMENT MASU GYARAN JIKI DANA FATA, WANDA ZASA SAKI KIYI SHEKI FATAR KI TAYI LAUSHI. TAYI LUWAI LUWAI TAMKAR TA JARIRAI_* _*AKWAI SUPPLEMENT NA KAYAN MATA WANDA ZASU GYARA KI, KIJI KI TAMKAR BUDURWA, SUPPLEMENTS DINMU BASU DA SIDE EFFECT, DOMIN AN HADO SU NE DAGA INGATTATTUN ITATUWA, WATO NATURAL PRODUCTS NE ACIKI._* _*KAI BA ANAN KADAI MUKA TSAYA BA, MUNA DA INGATTUN KAYAYYAKIN MATA WANDA KESA KISHIYA KWAFA, WANDA DUK INDA SARAUNIYA TAKAI KIN WUCE, WANDA ZASU TSATSO MIKI MARTABAR KI DA KIMAR KI_* _*AKWAI INGATTATTUN MAGUNGUNA, NA CUTUTTUKAN DA SUKA SHAFI DAN ADAM DAMA JINNU.. KAI DAMA WANDA BAMU AMBATA BA.. ZEE HERBALS APHRODISIAC (MASARAUTAR INGATTATTUN MAGUNGUNA KENAN)_* _*KYAU, ARHA, INGANCI, RAHUSA... SAI ZEE HERBALS APHRODISIAC_* _*MANHAJOJIN MU NA SOCIAL MEDIA: KAMAR INSTAGRAM DA WHATSAPP DAMA NAMBAR TARHON MU: DOMIN SHIIGA KUGA IRIN KAYAYYAKIN MU TUNTUBE MU TA_* _INSTAGRAM LINK DIN MU:_ www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac _WHATSAPP LINK DIN MU:_ https://Zeeherbalsaphrodisiac.whats.bz _NAMBAR TARHON MU_ 08169380189 _*DA A BAKA LABARI GWARA KA BAYAR.. KIZO A DAMA DAKE YAR UWA, KI ZAMO DAYA DAGA CIKIN KASAITATTUN MATA MASU AJI.. MUNA GARIN KATSINA, SANNAN KAYAN MU MUNA BADA SU AKAN FARASHIN SAYA ‘DAI DAI KO SARI.. MUNA TURA KAYAN MU A KO’INA A FADIN NAJERIYA._* ***** ***Duk inda suke tunanin zasu duba sun duba amma babu ko me kama da Ammi balle ita kanta, zuwa lokacin sun fara tsorata da lamarin, Aysha kuka take sosai, tausayin su ya darsu a zuciyar yan gidan, suka fito aka cigaba da neman Ammin tare dasu. Ana haka ne wata mota ta tsaya a daidai kofar gidan, suka tafi da sauri suna zuwa yana fitowa, driver Alhaji Safiyanu Madaki ne dan Aysha ta gane shi sanda suka je wajen. Da sauri suka isa wajen sa, har suna hada bakin tambayar ina Ammi? Kai tsaye yace musu be ganta ba, zuwan sa kenan Alhaji ya aiko ya tafi dasu. Hankalin su ya kara tashi akan na da, dan da sunyi tunanin ko chan wajen nasa ta koma ko kuma dai shine ya aiko a dauke ta. Gefe Muhammad yaja hannun ta, suka matsa yana kafe ta da idon sa da yayi mugun kad'awa. "Me ya faru da kuka je wajen sa?" "Da muka je..." Ta soma bashi labarin abinda ya faru har karshen maganar da sukayi yace zai turo a dauke su,da wayar da ya fita yayi da kuma sunan da Ammi ta ambata (Mahdi) wanda yasa Alhajin fita yayi wayar, komai ta fad'a masa, yayi shiru yana son gane me hakan ke nufi, sai dai duk iya kokarin sa na son dora abinda ya faru a ma'aunin da zai gane komai ya k'asa, idan ya kamo nan sai ya kwance ta chan, it doesn't make sense to him gaba daya. Ammi taje wajen sa, tace taga wani, ya fita yayi waya, ya dawo sunyi magana again sannan yace zai turo a dauke su, daga nan kuma aka zo aka ce ana sallama, Ammin ta fita, shiru shi kuma yanzu ya aiko din a dauke sun, dukkan wannan abin be bashi ma'ana guda d'aya da zai nuna abinda yake faruwa ba. Ya tabbata dai tafiya akayi da Ammin tasu, wadda tun bayan tasowar su bata taba nuna musu wani ko wata a matsayin wanda ta sani ba, sai yau katsaham tazo wa da kanwar tasa da yake gani a matsayin kanwar sa uwa d'aya uba daya sabon labarin da ya sashi a shakkun, shi waye kenan idan har mutumin da suka je suka gani shine mahaifin Aysha, toh shi waye nasa mahaifin? Me ya faru ko kuma me yake shirin faruwa.?    Wajen driver suka koma, yace Aisha ta shiga motar shi kuma ya koma ya fiffito da kayan su, ya tayashi suka saka a cikin motar, ya nemi alfarma wajen Malam Tsalha makocin su akan idan Ammi ta dawo kafin shi ya dawo ya fad'a mata sun je wajen Alhaji Madaki, amsa masa yayi da toh sannan suka tafi. *Sultan* ***Gida ya koma ya dauki motar sa, ya sake duba address din gidan sannan ya dauki hanya. Yadda unguwar take Babbar unguwa dake dauke da gidaje a tsare, kowanne gida na dauke da number a jiki ya taimaka masa k'warai wajen saurin gane gidan, daga gefe chan yayi parking, ya tsaya yana kallon gidan. Menene hadin sa da maigidan da har ya fito a cikin sunayen mutanen da zai nema. Bud'e murfin motar yayi ya sauko, ya nufi gidan kai tsaye, a tsaye ya tsaya ya kwankwasa gate d'in, maigadi ya leko ta yar kofar, sai kuma ya zare sakatar ya fito gaba daya, hannu Sultan ya bashi suka gaisa sannan ya tambaye shi ko Alhaji Safiyanu Madaki yana nan, d'an jim yayi yana nazari, kwana biyun nan ana yawan zuwa neman uban gidan nasa, ya kuma jaddada masa kar ya kuskura ya sake barin ko waye yazo in dai ba har shine ya fad'a masa ba. Amma sai kuma ya dubi Sultan, be yi kama da irin mutanen da Alhajin yake nufi da kar ya barsu ba, shi gaba daya ma kwarjini Sultan din ya cika masa ido da ma filin wajen gaba daya. "Yana nan kuwa?" Sai yayi firgigit ya k'asa duban sa yace "Alhaji baya nan yayi wata yar tafiya, amma me zai hana ka nemi shi a waya ko kuma dai ka fad'a min abinda idan ya dawo zan fad'a masa, kaga zai fi sauki idan ka dawo kawai ganin sa zakayi." "Ko zaka taimaka ka bani number ka, idan yazo sai ka fada masa Azizah ce ta turo wani bawan Allah, idan ya yarda zai ganni sai kayi min ko da flashing ne idan yaso sai na dawo." "Toh hakan ma yayi yallabai." Ya fada yana washe baki, ciki ya shiga da niyyar dauko wayar sa ya bawa Sulthan din ya saka tasa number a ciki yayi flashing sai yaga tasan dan ba wai sanin ta yayi da kah ba, yana dauko wayar yaji mahaukacin horn din da ko ba'a fada masa ba yasan waye, da gudu ya kwasa yayi gate din, ya hau kokarin budewa a rikice, ji yayi gate din ya yi saukin turawa, sai da ya kai karshe ya juyo yaga Sultan tsaye hannun sa a jikin gate din alamar tare suka bude. Maimakon wanda aka bude kofar domin shi ya shiga, sai ya tsaya idon sa akan Sultan fuskar sa dauke da mamakin waye shi?    Karbar wayar Sultan yayi ya saka number shi, sannan ya kira ya ga number yayi saving, ya mika masa yayi masa godiya ya juya da nufin barin wajen. Da sauri Ameer ya balle murfin motar ya fito "Minti daya Dan Allah." Yace yana tsayawa a gabansa, hannu Sultan ya bashi sukayi musabiha. "Sunana AmeeR." "SULTAN." Yace yana murmushi "Kazo wajen Daddy ne?" "Eh wallahi, nazo ganin sa amma ban same shi ba, amma zan dawo." "Ok..." Sai yayi shiru. "Sai anjima?" Sultan yace Dafa kansa wanda ya kira kansa da Ameer yayi, yace "Kamar na san fuskar ka waallahi, a zahiri ko a mafarki? Ban sani ba, kawai inaji kamar ace na hadu da wani celebrity da na dade ina fatan haduwa dashi, something like that, wani irin strange feeling na kamar kasan wani kuma ka manta aina." Murmushi Sultan ya sake yi "Kasan hakan na faruwa, may be mun taba haduwa din kuma, ko kuma me kama dani ka sani." "Umm... Probably, toh amma dan Allah ka bani number ka, idan na tuna inda na sanka, I ll give you a call." "Ok ba damuwa." Yace sannan ya karanto masa numbers din ya saka a wayar sa, ya kira back shima ya gani yayi saving da Ameer Madaki, shi kuma ya tambaye shi da me zai saving yace masa Sultan. Da haka suka rabu sai da Ameer ya ga fitar motar sa daga layin su sannan ya ja tasa ya shiga gida. For the first time a rayuwar sa yau ya hadu da wanda yaji yana so ya zama role model dinsa, tun be kai ga sanin sa ba amma yaji yayi masa, shigar sa, nutsuwar sa, gayun sa, kai hatta tafiyar sa akwai wani strange abu a cikin ta ,uwa UBA maganar sa da tafiyi masa kama da ta sarakuna ko wasu manya manyan masu kud'i dai, shi dama a rayuwar sa yana son gayu da fame, yaso fara waka Daddy ya hanashi amma da tuni shima wani big time celebrity ne yanzu.    *** *Amrah* ***Babu abinda aka fasa na shirye shirye, musamman bangaren Mah-Mah da tafi kowa murnar auren, sosai take shiryawa ranar tana kuma gayyatar duk wani na kusa da ita har ma dana nesa. Kwana biyu da bata ga Sultan ba sai ta d'anji babu dad'i, kenan fushi yayi dan ta masa fad'a, ita a ganin ta ai ba laifi bane dan uwa ta nuna wa d'anta kuskuren sa, abinda tasan kawai taji babu dad'i da fad'an nata ya chanja salon da ba wai ta shirya da zuciyar ta akanta fadi hakan ba, sai dai bacin rai ne tasan ya kwashe ta, ta farfada masa abinda ta fad'a din duk da a ganin ta shine yayi abinda ya tunzura ta.     Har daki ta samu Safwan da tambayar ko ina Sultan din, yace mata yana asibiti ne, hankalin ta ya kwanta suka cigaba da shirye shirye hankali kwance.    A bangaren Amarya Amrah ma shirye-shiryen na tafiya daidai a wajen kowa amma banda ita da umma, har ga Allah umma bata son auren sai dai Abba yaki bata hadin kan da zai taimaka wajen ganin an fasa, maganar sa daya ce Hajiya tafi komai da kowa a wajen sa, dole taja bakin ta tayi shiru kuma ta cigaba da kokarin kwantar wa da Amrah din hankali tana nusar da ita muhimmancin biyayya ga iyaye.    A haka aka shiga satin biki, idan kaga Amrah zaka dauka ciwo ta kwanta ta tashi saboda yadda ta lalace, duk da gyaran jikin da take samu amma be boye damuwar da take ciki ba, auren wanda baka so masifa ne sai wanda ya taba shiga irin yanayin sannan ne zai fad'a maka yadda yake. Sukuku takeyi komai, yawancin abubuwan ma sai dai tabi Afrah da kallo idan tana yi, dama ita ba kawa ce da ita ba, sai cousins su ne akan komai.     Tun ranar da abin ya faru bata sake saka both Sultan da Safwan din a idon ta ba, babu wanda itama kuma tayi yunkurin nema, ta kan ji wani lokacin suna magana da Afrah ko a waya akan abinda zasu bukata.     Ranar laraba me kunshi tazo tayi musu rantsattsen hadadden kunshi, sosai kunshi yayi kyau a hannun Amrah, sai dai ita ko k'ad'an bata ga hakan ba, da an bi ta ta ma babu wani kunshi da zatayi, dan dai anfi karfin ta ne kuma Umma tace ta bar komai a hannun Allah ta cigaba da addu'a zai kawo mata mafita, idan Safwan mijinta ne dole ne ayi auren idan ko ba mijin ta bane ko da duk duniya sun taru akan son suyi aure ba zai aureta ba. Hakan yasa ta dan kwantar da hankalin ta amma ba wai dan ta hakura ko tana son shi ba.   Kamu kawai sukayi washegari dan yadda ta kafe babu abinda zaà yi, yan uwan umma suka ce dole ne ayi kamu al'adace dangin ango zasu zo. Amma kuwa har aka gama kowa ya watse bata bar kukan da take ba wanda mutane da yawa sun zata ire iren kukan da Amare sukeyi ne, akayi ta bata baki, wanda kuma suka san dalilin kukan nata basu ce komai ba har aka gama.    Daki ta shiga ta kulle ta hau cire komai tana wurgi dasu, kafin ta dire akan guiwar ta tana jin wani irin zafi,shikenan daga gobe komai ya kare, tasan ita da rayuwar farin ciki har abadah. Babu abinda zuciyar ta bata sak'a mata ba, har sai da taji kamar ta had'a kayan ta, ta gudu ta shiga duniya amma ba zata iya ba, she's still young and naive bata san takamaimai ma me zatayi ba, haka ta zauna tayi ta kuka har sai data ji idonta na mata yaji yaji, sannan ta shiga toilet tayi alwala taxo tayi sallolin da suka tsere mata dan lokacin wajen karfe sha biyun dare, ta kwanta lamo tana tausayin kanta. ***Matsanancin ciwon kai ke damun sa har baya gani sosai, ya matsa ma kansa sosai da tunanin abubuwa da yawa, gashi ya kasa samun ganin Safiyanu Madaki har yanzu idan ya kira maigadi sai yace be dawo ba, dole ya hakura ya jira dan be san ta inda zai fara ba bayan shi. Yana kwance yaji alarm din da yasa ya kad'a, ya tuna da wayar da sukayi da Daddy jiya akan lallai ya ganshi a wajen daurin auren,ko dai Daddy be fad'a ba ai ya zama dole ya je ko da baya cikin garin ne balle, dan ma Allah ya taimake shi Safwan ya rufa mishi asiri yace ma Daddy din abu ne ya rike shi a asibiti da sai ya kawo wani abu wanda baya fatan hakan.    Da k'yar yasa hannun sa ya dafa ya tashi, ya shiga toilet yayi wanka ya fito ya shirya cikin normal kayan sa ya nufi gida.    Wajen dukka abokan su sun hallara, har da ma wanda suka zo tun jiya aka sauke su a wani gidan Daddy, anan angwayen suke saboda haka kai tsaye chan ya nufa, suna ganin sa sukayi masa cha kowa na fad'an abinda yake son fad'a. Wani ya kalle shi yace "Amma wallahi ban taba ganin d'an rainin wayo irin ka ba, auren ma sai ka yi masa yanga?" Karaf Safwan yace "Babu ruwanku da shi,daga zuwan sa kun sashi a gaba, haba dan Allah." "Muje ciki kaga kayan da na zaba mana." Yace yana jan sa suka shiga ciki suka bar sauran kowa na fad'ar albarkacin bakin sa.   Kaya ne iri daya, farar shadda da akayi ma dan ubansun aiki a jiki da wani bakin zare me kauri, sai takalma sau ciki bakake masu kyau da suka haska fatar su dukka, dinkin manyan riguna ne, kuma dama tun da dadewa sukayi wa kansu alkawarin duk ranar auren su idan ya zama ba tare za'a yi ba toh kaya iri daya zasu sa. "Sunyi kyau sosai." Yace yana dagawa. "Yauwa ka shirya bari naje waje, kayi sauri amma kaga lokaci." Daga masa kai Sultan yayi yana jin dadin yadda yaga Safwan din, da alama yana murna da wannan ranar, kuma alamu sun nuna ya samu sauki sosai bayan da ya tafi. Kayan ya dauka ya hau sawa yana kokarin kore tunanin dake neman kutso masa a daidai lokacin wanda sam be kamata yayi ba. Ita din yanzu ta zama matar dan uwa kuma amininsa, babu wani abu da ya rage tsakanin su sai matsayin ta na matar Safwan dinsa. Yaso ya kara ganin ta bayan ranar ko sau daya ne suyi magana ya yi kokarin sake fahimtar da ita, amma yadda abin ya kasance ne ya hanashi dan baya son Safwan yayi tunani irin wanda Mah-Mah tayi, ko kuma mutane suyi masa wani kallo na daban ko maci Amana ko wanda be san alkhairi ba. "Ina miki fatan alkhairi da zaman lafiya me dorewa." Ya furta a hankali sannan ya fito suka dunguma zuwa masallacin dake kusa da farkon shigowa layin nasu.    *** Yadda wajen ya cika sosai zaka tabbatar da ba karamiin tara mutane daurin auren yayi ba, waje waje suka dinga bi suna gaisawa da mutane, suna ji aka fara gabatar da abinda ya tara mutane.    Gefe Sultan ya koma da sauri ya ciro wayar sa dake ta faman ringing be ji ba, Madaki's Gateman ya gani a rubuce, da sauri yabi kiran yana dagawa yace "Lafiya Babah? Ya dawo?" "Ya dawo jiya da daddare, kuma yau ina ganin ya sauko na isar da sakon ka, sai naga har ya fika son haduwa da kai dan cewa ma yayi na kiraka a lokacin ka fadi inda kake shi zaizo sai kuma aka yi rashin sa'a kiran be shigo ba, sai yanzu ya saka na sake kira da baka daga bane ya bar wajen nan ya koma ciki." "Alhamdulillah, bari na tawo yanzu." Yace yana jin wani irin karfi, karfin tunkarar komai da zaizo masa. Kallon wajen yayi yaga hankalin Safwan na chan, yayi saurin fita daga wajen da sauri ya fad'a motar sa yayi reverse ya bar wajen.    A daidai lokacin,limamin masallacin ya sanar da dauruwar auren Muhammad Sultan Da amaryar sa Amrah. _ZAFAFA BIYAR 2021_*🔥 _*SUKAR BAYA*_💚 _BILLYN ABDUL_ ( _kwai cikin qaya_ ) ( _raina kama_) ( _wutsiyar raqumi_ ) *_SIRADIN RAYUWA_*💛 _SAFIYYA HUGUMA_ ( _alqawarin Allah_ ) ( _daurin boye_ ) ( _Dangantakar zuci_ ) 💙 _*KIBIYAR AJALI..*_💜 _MISS XOXO_ (Sulke baya tsare ta sai ta wuce) ( _Igiyar zato_) ( _Kaimin halacci_ ) ( _Naufal_ ) *_ABIN DAKE CIKIN ZICIYA_*🧡 _HAFSAT RANO_ ( _ruhi daya_ ) ( _Sauyin qaddara_ ) ( _Daurin goro_ ) *_MIN QALB_*❤️ _MAMUHGEE_ ( _buri daya_ ) ( _tarayya_ ) ( _eznah_ ) Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 0903 234 5899 IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 09033181070 Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥[4/7, 6:44 AM] Maman Maryam: www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac. _*ASSALAMU ALAIKUM SISTERS..!_* _*INA MASU NEMAN INDA ZASU SAMU INGANTATTUN: _* _*HERBALS APHRODISIAC MA’ANA NA GARGAJIYA BANA HADIN BATURE BA MAI SIDE EFFECT..?_* _*TO KU MATSO, DOMIN NESA TAZO KUSA.._* _*ZEE HERBALS APHRODISIAC_* _*ZEE HERBALS APHRODISIAC_* _*ZEE HERBALS APHRODISIAC_* _*MUNZO MUKU DA INGATTTUN KAYAYYAKI WANDA ZASU GYARA KI CIKI DA WAJE_* _*MUNADA SUPPLEMENT MASU GYARAN JIKI DANA FATA, WANDA ZASA SAKI KIYI SHEKI FATAR KI TAYI LAUSHI. TAYI LUWAI LUWAI TAMKAR TA JARIRAI_* _*AKWAI SUPPLEMENT NA KAYAN MATA WANDA ZASU GYARA KI, KIJI KI TAMKAR BUDURWA, SUPPLEMENTS DINMU BASU DA SIDE EFFECT, DOMIN AN HADO SU NE DAGA INGATTATTUN ITATUWA, WATO NATURAL PRODUCTS NE ACIKI._* _*KAI BA ANAN KADAI MUKA TSAYA BA, MUNA DA INGATTUN KAYAYYAKIN MATA WANDA KESA KISHIYA KWAFA, WANDA DUK INDA SARAUNIYA TAKAI KIN WUCE, WANDA ZASU TSATSO MIKI MARTABAR KI DA KIMAR KI_* _*AKWAI INGATTATTUN MAGUNGUNA, NA CUTUTTUKAN DA SUKA SHAFI DAN ADAM DAMA JINNU.. KAI DAMA WANDA BAMU AMBATA BA.. ZEE HERBALS APHRODISIAC (MASARAUTAR INGATTATTUN MAGUNGUNA KENAN)_* _*KYAU, ARHA, INGANCI, RAHUSA... SAI ZEE HERBALS APHRODISIAC_* _*MANHAJOJIN MU NA SOCIAL MEDIA: KAMAR INSTAGRAM DA WHATSAPP DAMA NAMBAR TARHON MU: DOMIN SHIIGA KUGA IRIN KAYAYYAKIN MU TUNTUBE MU TA_* _INSTAGRAM LINK DIN MU:_ www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac _WHATSAPP LINK DIN MU:_ https://Zeeherbalsaphrodisiac.whats.bz _NAMBAR TARHON MU_ 08169380189 _*DA A BAKA LABARI GWARA KA BAYAR.. KIZO A DAMA DAKE YAR UWA, KI ZAMO DAYA DAGA CIKIN KASAITATTUN MATA MASU AJI.. MUNA GARIN KATSINA, SANNAN KAYAN MU MUNA BADA SU AKAN FARASHIN SAYA ‘DAI DAI KO SARI.. MUNA TURA KAYAN MU A KO’INA A FADIN NAJERIYA._* _*BE YOUR OWN BOSS, BUILD YOUR OWN EMPIRE, BE THE WHOLE WORLD OF HIS MAJESTY( YOUR HUBBY) BE THE ONLY CENTER OF ATTRACTION WITH ZEE HERBALS APHRODISIAC. OUR PRODUCTS LASTS LONGER AND VERY EFFECTIVE. NO SIDE EFFECTS. AVAILABLE N WHOLESALE/ RETAILS.. DELIVERY IS NATIONWIDE. 100% TESTED AND TRUSTED_* *2__0* Sallah ce kawai take ta dani, bayan ita kam babu abinda nake yi banda kukan zuci. Duk tunani na yana kan wanda ake shirin aura min, ban san shi ba, idan ma na san shi to ya boye min tunda ni har yanzu ba wanda ya taba tunkarata fa maganar aure. Mas'oud shine wanda rai da zuciya ta suka amincewa, shi kuma gashi ya yi sanya har an bawa wani ba shi ba. Wayyo Allah na ina cikin kaddarorin rayuwa mabanbanta, marasa kamaceceniya ta ko wace fuska. Su Mami kuwa babu wanda ya zo yaji kukan da nake yi, sai dai na jiyo dariyar su wacce bana raba d'ayan biyu magana ta suke yi. Har dare ban kuma saka wani abu cikin baki na ba, sam na dena jin yinwa saboda rashin nutsuwar zuciya. Ina idar da sallah isha'i nabi lafiyar gado ina share hawaye. Da kyar na dakko waya ta na kunna tare da jonawa jikin charge, nan naga messages d'in Mas'oud yana ta tambayar lafiya naki dauka, ko bani da lafiya, dan Allah in yi masa reply ko zai ji dadi. Duk na karanta amman naki masa reply d'in sanda bashi da wani amfani, ya riga ya gama da rayuwar mu gabaki d'aya tunda shine ya yi ta jan lokaci, da yazo ya fada ai da duk an san tsakanin mu, amman ya dinga cewa zai zo, zai aiko, gashi nan lokaci ya k'ure mana a sanda mukafi buk'atar kadancewa da juna. Ina ji kirji na yana zafi nasan na yunwa ne amman naki zuwa naci abinci saboda har lokacin bana sha'awar cin komai. Gashi babu mai lallashi na bare a tilasta min ko ruwan shayi nasha, haka na kwanta har gari ya waye banci ba. Koda na tashi da asuba da kyar nayi sallah, jiki na naji yana ta min wani irin ciwo kamar an sassara ni haka na dinga ji. Da yake weekend ne sunday sai na koma kan gado na kwanta, zazzabi ya rufe ni. Allah ya taimake ni da aka fito breakfast kawu daddy yaga bana gurin sai be yi magana ba ya tashi tsam ya nufi dakin da nake. Yana shiga ya tarar da ni cikin blanket, ya dinga kiran suna na amman na kasa Kwakwkwaran motsi, sai yasa hannunsa a goshi na yaji zau kamar garwashi, cikin tashin hankali yake magana. “Innalillahi wa'ina ilaihir rajiun, Khadija baki da lafiya haka? Me yake damunki?” Jin da ya yi bana iya cewa komai yasa shi kiran su Mami da karfi, sai gasu kuwa da gudu suna tambaya daddy lafiya? “Bata da lafiya naji jikinta akwai zafi. Abin da yasa na kira ku ke Hameedah kizo ki bata taimakon farko da ya dace.” “Okay daddy.” Tayi maganar tana taba jikina, tace za'a yi min allura sai ta saka min drip yadda zan ji dad'in jikina. Haka kuwa aka yi ta min allurar ta kuma sanya min drip a daidai wannan lokacin ne Mas'oud ya kira waya ta, Shukrah ta dauka, ganin sunan Mas'oud yasa ta tashi ta fita. Duk da ina cikin wani yanayi hakan da ta yi sai da ya sanya ni cikin faduwar gaba dan ban san abin da zata gaya masa ba. A can parlor kuma Shukrah guri ta samu ta zauna tare da kara wayar a kunne kai kace ita aka kira. Cikin kashe murya da kisisina ta shiga yi masa magana. “Assalamu alaikum.” “Amin wa'alaikis salam, dan Allah bata kusa ne.?” “Eh... A'a.” “Ban fahimta ba.” Mas'oud ya tambaya cikin rashin fahimtar abin da take nufi.” “Wai kana nufin bata sanar da kai abin da yake faruwa ba? Idan kuwa haka ne Dije taci amanarka, har kai zata boyewa.” “Innalillahi wa'ina ilaihir rajiun. Idan har na fahimce ki dai dai, kina son gaya min cewa akwai abinda ya kamata na sani a gurin ta amman taki gaya min ko?” Sai da ta yi farrrr da kwayar idanunta sannan ta gyara zama tace. “Kwarai ma kuwa, ba abin wasa bane dan yana da kyau ka sani tunda naga kamar kun zama aminai.” “Toh dan Allah ki had'a ni da ita muyi magana please sister Shukrah.” Tayi mamakin yadda ya gane cewa itace, sai dai ranta ya d'an so su da taji ya damu da jin Dije, amman ba bu yadda ta iya dole da d'an daure da kishi tace. “Yanzu kam ba zata iya daga waya ba, sai dai idan anjima kila idan taga dama.” “Shikenan Shukrah na gode sai anjima.” Be kuma jiran cewar ta ba kawai ya katse zuciyar shi ta shiga cikin tunanin abin da yake faruwa. Shi sai yasan babu abin da ya had'a shi da Khadija na rashin jituwa. Amman wane irin abu ne Shukrah tace ana boye masa? Dole yana son jin koma menene, kuma daga bakin Dije dan ita zata warware masa kullewar da kansa ya yi. A ranar shi kansa da kyar ya gudanar da wasu al'amura sa, still kuma ya ci gaba da kiran ta amman a kashe, hakan ya sake tayar masa da hankali har ya fara shirin zuwa gidan na su. Tsab Mas'oud ya shirya cikin manyan kaya shadda ruwan kasa wacce aka yi masa gajeren d'inki, sunyi masa kyau ya dora hula wacce ta dace da kayan jikin nasa ya dauki turare ya dora tare da jan mukullin motar sa ya fito. Addu'a kawai yake yi Allah yasa yaje yaji alkairi daga bakin Khadija, yana jin zuciyar shi tana karfafa masa gwiwa wajan samun nasara akan duk abin da zai zo bakin ta, bai taba kawowa rabuwa zasu yi ba dan yana da yakinin aure a tsakanin su. Ya yi horn mai gadi ya leko, ganin shi yasa ya bude ba tare da wani shakku ba. Wajan motar da ake kai ta gurin aiki ya aje tashi, tare da dakko wayarsa ya kuma kiran ta, cikin sa'a kuwa tana zaune kan sallaya taga sunan shi ta dauka ba tare da tace komai ba. “Ki daure ki fito ina compound d'in ku.” Duk da irin dauriyar da take janyowa hakan be haka muryar ta yin rawa ba, taja majina waje silar kukan da tayi ne ya sakar mata da tsinkakkiyar majina marar kauri tace. “Me zan fito nayi maka bayan ka riga ka tarwatsa mana duk wata dama da muke da ita?” “Bana gane abin da kike nufi shi yasa nazo kafa da kafa dan na ganki. Dan Allah ki daure kizo muyi magana ta fahimta.” Kamar karna je haka nake ji, amman kuma zuciya ta tana son ganin shi a zahiri dan na kalli yadda zai dauki maganar. Katsewa nayi dama da hijab a jikina na tashi da kyar na fito, babu kowa a parlorn sai na fita kai na tsaye ba tare da na sanar da Mami ba. Tsaye na ganshi gurin motar shi yana latsa waya, yadda naga ya kuma yin kyau ne ya sake ruda ni, kamar nayi shekara ban ganshi ba haka naji. Na daure na karasa har wajan sannan na tsaya ban kula shi ba saboda haushin sa da nake ji. “Da alamu nayi babban laifi da har na cancanci irin wannan horan ko Oum Waleed? Kin san yadda rashin daga wayar ki yasa hankali na ta shi? Wallahi tun jiya na kasa cin abin cin arziki saboda tunanin abinda ya hanaki daukar wayata. Shin me nayi miki sweetheart?” Naja wani gauran numfashi mai radadi a zuciya, hawaye suka zubo min nasa hannu da sauri na share dan bana son dogon zancen da zai min, nace dashi. “Yaushe ne zaka zo gidan nan kace kai ne wanda zaka aure ni?” Ya kalle ni tare da cewa, “Na yi miki alkawari nan da karshen wata uncle's dina zasu zo gidan nan nemar min aurenki harda saka rana.” Wata kwallar bakin ciki ta sake sakkowa kan kumatu na, naja kukan da yake tahowa na hadiya ina kallon kasa nace. “Nayi zaton zaka ce gobe da sassafe, ashe har yanzu jinkirin a gurin ka yake. Ban san me zan ce maka ba, sai dai kawai nasan kai ne ka janyo muka rasa junan mu Mas'oud.” “Ban fahimta ba Oum Waleedah, ta ya muka rasa juna bayan duk gamu a raye muna numfashi.?” Na yi saurin cewa. “Numfashi marar amfani ba, ta iya yiwuwa kai a gurin ka kana yin mai amfani, sabanin ni da zan shiga gidan mutumin da ban san ko waye ba, ta ya za kai kace ni ina numfashi? Ka wahalar dani Mas'oud, ka koyar dani darasi mai matukar wahalar da zuciya. Bana tunanin zan san meye jin dadi da yanci a cikin rayuwa ta, zanje na rayu da wani ba kai ba Mas'oud, kana ji kana gani za'a kai ni inda bana so. Dan Allah Mas'oud ka rufa min asiri kar na rasaka please ka ceci rayuwa ta saboda da kai ta fara soyayya....” Cak numfashin sa ya tsaya na dan wani lokaci, baki bude yake kallo na cikin zare ido da alama yaji maganar ne cikin tsakiyar kansa. Ya matso dap dani har ina iya jiyo bugun da zuciyar shi take yi da karfi sannan kuma cikin sauri. Kamar zai rike ni haka ya soma yi yana magana a daddaburce hankali a tashe. “Dan Allah idan mafarki nake yi wanda yake kusa dani ta yi gaggawar tayar dani. Wallahi tunda nake ban taba yin mummunan mafarki ba irin wannan.” Cikin kuka murya a dashe nace dashi. “Ba mafarki kake yi ba da gaske ne wannan maganar da nake maka. Sai dai nima ina fatan kawu daddy ya dawo yace min da wasa yake yi a yau din nan.” “Innalillahi wa'ina ilaihir rajiun na shiga uku ni Mas'oud wannan wace irin mummunar kaddara ce? Oum Waleed dan Allah karki bari a rabu mu, wallahi ina sonki. Gobe zan turo uncle's d'ina ayi maganar koda basu taho da kudin ba, su san da zaman mu ni dake kar su rabu mu dan girman Allah.” Yadda yake magana a gigice shine ya sake tayar min da hankali na tabbatar da idan bamu yi da gaske ba komai zai iya faruwa. Kamar na juya na tafi saboda naga shima ya fara zubar da hawaye, sai dai na juyo ba tare da na bari mun had'a ido ba nace masa. “A wannan gabar bani da ta cewa Mas'oud, sai dai ina fatan zaka yi duk yadda zakai wajan karkato da zuciyar kawu daddy har ya amince da auran mu. A shirye nake tsab da idan ya kuma tuntuba ta da maganar ka zan amsa dan kar na cuci kai na, amman fa ni bazan iya zuwa yanzu nace dashi ba zan auri wanda ya bani ba, saboda yadda baka cancanci wulakanci a guri na ba, haka ma kawu daddy be cancanci tozarci daga gare ni ba. Dama tuntuni damar tana hannunka, yanzu ma tana hannunka sai ka nema mana mafita.” Ina gama magana na ruga gida da gudu ina wani sabon kukan wanda yafi na farko zafi da radadi. Ban san yadda ya kare ba a compound, sai dai wajan karfe goma naji kawu daddy ya shigo yana yiwa Mami magana. “Ikon Allah, yaran zamani sai addu'a kawai.” “Alhaji me kuma aka yi maka? Ko samari ne ka hadu da su akan titi marasa kunya.” Yana kokarin zana ne yake cewa. “A a babu ko d'aya daga ciki. Yaron nan ne Mas'oud abokin aikin Khadija. Ina jin ko labarin auran ta yaji yanzu shine ya kawo kanshi wai shi da ita sun dade suna soyayya tare da burin yin aure, wai yana ta shirin turo manyan sa sai yaki ance an bayar da ita. Shine nace da me ya hana shi bayyanawa tuntuni sai yanzu?” Jin maganar aure na ne yasa Mami sauya fuska, can kuma sai ta ce tana zuba mishi juice a glass cup. “Kaima Alhaji har yanzu ka ki gaya mana waye wanda zaka aura mata. Ni ban taba ganin inda aka yi wannan abin ba, ko dan bani na haifi Dijen ba shi yasa ake ta boye min shi?” “Ko daya wallahi Hajiya, abin da yasa ban fada ba shi angon ne ya roki arzikin dan Allah karna fada sai ranar auran. Kinji dalilin da yasa ko ita Khadijan ban gaya mata waye ba.” “Ai shikenan, idan ta fashe ma gani ai.” “Zaku gani kam insha Allahu. Yaron ma na bashi hakuri nace ya yi hakuri aure nan da rana ita yau za'a daura shi da ikon Allah.” “Uhmm Alhaji kenan, kana bani mamaki tun zuwan yarinyar nan gidan nan, komai na ta baka nuna min shi kai tsaye sai ka yi kwana kwana. Amman ba komai lokaci ne tunda gashi ta kusa tafiya nata gidan.” “Ki dena yi min fassara akan komai Hajiya. Yarinyar nan marainiya ce kin kuma san yadda Allah ya bayar da amanar rikon maraya. Dan Allah ki tayani faranta mata har zuwa ranar da ya rage mata a cikin gidan nan.” Tamkar ya yi da gunki ta yi masa banza hakan ya kara tabbatar masa da cewa idan ya gaya mata wanda Dije zata aura akwai rashin hankali. Sai ya kuma jan bakinsa ya yi shiru be sake cewa komai ba har lokacin kwanciya ya yi ya tafi daki. Ni kuwa tunda naji yace ya bawa Mas'oud hakuri na koma gefe naci gaba da kuka na wanda babu mai lallashi. *MASARAUTAR BASANNABAS* (Sarki Salman Aliyu Salman SAS) Kafin kace wani abu tuni sarki Salman ya kuma susucewa akan son auran Dije, sarautar ta kuma fita daga cikin zuciyar shi ta yadda ko sunan sarki baya son yaji an ambata masa. Duk da ya rage sauran sati daya a daura auran sa, ga kuma ta fiyar da aka ce zai yi zuwa Cyprus, kuma babu wanda za a fasa indai yana da rai da kuma lafiya a jikin shi. Komai dama da ya dace ango ya yiwa amarya, Sarki Salman ya bawa Alhaji Isma'il kudadenda za'a siya. Shi kuma ya kai wa wata mata kwangilar hadowa ba tare da ya sanar da ita ko na meye ba, daman ita aikin ta kenan, duk abinda mutum yake bukata a had'a masa na aure ko na gida tana yi a biya ta. Yana zaune a cikin fada yama rasa abin yi saboda Sam baya cikin hayyacin shi, ya jiyo muryar Ciroma yana gyaran murya yana cewa. “Allah ya taimake, rana ita yau shine ranar da zaka je taron nan, an shirya maka komai sai fatan zuwa da dawowarka kawai, Allah ya kara maka lafiya.” .._Afuwan! Kunji shiru ko? Wallahi kwana biyu inata fama da chronic ulcer. Har takai na kwanta a asibiti na yan wasu kwanaki shysa kukaji shiru, Shekaran jia akai discharging. Ina fatan na same ku lpy? Nagode k’warai da addu’oin ku. KIBIYAR ajali zai cigaba da samuwa Insha Allah da zarar naji karfin jiki na sosai.. Na gaishe ku, Gaisuwa mai kima.._ ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥 [4/7, 6:44 AM] Maman Maryam: www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac. _*ASSALAMU ALAIKUM SISTERS..!_* _*INA MASU NEMAN INDA ZASU SAMU INGANTATTUN: _* _*HERBALS APHRODISIAC MA’ANA NA GARGAJIYA BANA HADIN BATURE BA MAI SIDE EFFECT..?_* _*TO KU MATSO, DOMIN NESA TAZO KUSA.._* _*ZEE HERBALS APHRODISIAC_* _*ZEE HERBALS APHRODISIAC_* _*ZEE HERBALS APHRODISIAC_* _*MUNZO MUKU DA INGATTTUN KAYAYYAKI WANDA ZASU GYARA KI CIKI DA WAJE_* _*MUNADA SUPPLEMENT MASU GYARAN JIKI DANA FATA, WANDA ZASA SAKI KIYI SHEKI FATAR KI TAYI LAUSHI. TAYI LUWAI LUWAI TAMKAR TA JARIRAI_* _*AKWAI SUPPLEMENT NA KAYAN MATA WANDA ZASU GYARA KI, KIJI KI TAMKAR BUDURWA, SUPPLEMENTS DINMU BASU DA SIDE EFFECT, DOMIN AN HADO SU NE DAGA INGATTATTUN ITATUWA, WATO NATURAL PRODUCTS NE ACIKI._* _*KAI BA ANAN KADAI MUKA TSAYA BA, MUNA DA INGATTUN KAYAYYAKIN MATA WANDA KESA KISHIYA KWAFA, WANDA DUK INDA SARAUNIYA TAKAI KIN WUCE, WANDA ZASU TSATSO MIKI MARTABAR KI DA KIMAR KI_* _*AKWAI INGATTATTUN MAGUNGUNA, NA CUTUTTUKAN DA SUKA SHAFI DAN ADAM DAMA JINNU.. KAI DAMA WANDA BAMU AMBATA BA.. ZEE HERBALS APHRODISIAC (MASARAUTAR INGATTATTUN MAGUNGUNA KENAN)_* _*KYAU, ARHA, INGANCI, RAHUSA... SAI ZEE HERBALS APHRODISIAC_* _*MANHAJOJIN MU NA SOCIAL MEDIA: KAMAR INSTAGRAM DA WHATSAPP DAMA NAMBAR TARHON MU: DOMIN SHIIGA KUGA IRIN KAYAYYAKIN MU TUNTUBE MU TA_* _INSTAGRAM LINK DIN MU:_ www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac _WHATSAPP LINK DIN MU:_ https://Zeeherbalsaphrodisiac.whats.bz _NAMBAR TARHON MU_ 08169380189 _*DA A BAKA LABARI GWARA KA BAYAR.. KIZO A DAMA DAKE YAR UWA, KI ZAMO DAYA DAGA CIKIN KASAITATTUN MATA MASU AJI.. MUNA GARIN KATSINA, SANNAN KAYAN MU MUNA BADA SU AKAN FARASHIN SAYA ‘DAI DAI KO SARI.. MUNA TURA KAYAN MU A KO’INA A FADIN NAJERIYA._* _*BE YOUR OWN BOSS, BUILD YOUR OWN EMPIRE, BE THE WHOLE WORLD OF HIS MAJESTY( YOUR HUBBY) BE THE ONLY CENTER OF ATTRACTION WITH ZEE HERBALS APHRODISIAC. OUR PRODUCTS LASTS LONGER AND VERY EFFECTIVE. NO SIDE EFFECTS. AVAILABLE N WHOLESALE/ RETAILS.. DELIVERY IS NATIONWIDE. 100% TESTED AND TRUSTED_* *2___1* Samun kansa ya yi da jinjina kai alamar yaji sai dai tunanin sa yana ga yadda za'a daura aure baya garin sai kace na asiri. Amman kwarin gwiwar da jarumar zuciyar shi take bashi shine ya sanya shi jingine fargabar tashi da take neman ruguza masa lissafi. *KHADIJA (DIJE)....* Tun daga ranar da kawu daddy ya sanar dani ranar aure na ban sake fita ko nan da compound ba, ma'ana tun ranar da Mas'oud yazo naje gurin shi. Shi kuwa tun yana kira na ina kin dagawa har ya hakura sai dai ya kira Shukrah da ya karbi lambar ta dan ya dinga jin bayani game da ni. Hankali na be sake tashi ba sai ana sauran kwanaki uku kawu daddy ya kira ni wai za a kawo kayan lefe, a gabansa nace to, amman a raina fata nake Allah yasa motar masu kawowar tayi hatsari duk su mutu kowa ma ya huta. Mami kiri kiri tace ba za a soya komai ba dan tasan suma masu kawo kayan zasu kwallafa rai da cin kaji, dan haka tace yadda suka zo da tuwo a cikin su, nan d'in ma tuwon za a yi musu dan shi suka saba ci, harda cewa su kila na dawa da masara suke ci nan kuma na shinkafa za'a yi musu miyar taushe tasan sai sunyi murna a yau. Ni dai ban yi magana ba saboda ko a jikina idan ma tace tuwon karfe za ai musu bana jin zai dameni saboda nima ba san ganin su nake yi ba. Shiryawa nayi tsab na bar gidan saboda nasan ko sun zo sai Mami ta wulakantani a gaban su, nasa Tukur ya kai ni gidan su Aisha, ina shiga ta fara murnar gani na muka shiga dakin ta, kamar jira ni kuma nake yi kawai na kwanta kan gadon ta na fara kuka mai taba zuciya. “Ahh kawata menene haka da girmanki? Haba kuka sai kace wata yar karamar yarinya.” Still na sake fashewa da kukan ta dinga shafa baya na cikin nuna kulawa. Tunda aka fara wannan maganar auran ban samu wannan gatan ba na lallashi sai yau kuma a yanzu da Aisha take ta tausar min da zuciya tun kafin ma taji abinda nake yiwa kukan. Sai da nayi mai isa ta sannan na sanar da ita abinda duk ya ke faruwa, ta tausaya min kwarai da gaske sannan ta bani shawara akan na daure na karbi zabin daddy koda kuwa ace mijin gurgu ne ko makaho na daure na zauna dashi kodan farin cikin kawu daddy. Ya zan yi? Innalillahi wa'ina ilaihir rajiun dole na karbi wannan auran ko ta halin ya ya ne, gaskiyar Aisha ne ya yi min abinda ko iyayen da suka kawo ni duniya basu min ba. Ashe kuwa idan hakane ya cancanci fiye da wannan sadaukarwarma a gareni, dan idan nace zan bijire ni kaina bazan taɓa yafema kaina ba har randa numfashina zaibar gangar jikina. Haka na zauna a gidan su Aisha tana ta lallashi da ban hakuri tare da bani labarai makamanta irin wannan auran da za ai min, da kuma shawarwari masu ƙyau da amfani.          Jinai zuciyata ta rage nauyin datai min sosai, na kuma samu y'ar nutsuwa duk da banajin son auren har yanzu. Haka na shiga sauke ajiyar zuciya ina sake godema Allah akan k'addarorina da suke zuwa gareni daki-daki. Ina fata da addu'ar zama cikin mutane masu hak'uri da cin ribar hak'urin koda ba'anan gidan duniya ba. *DR ISMA’ELA RESIDENCE....* Saboda tsabar wulakanci irin na su Mami ko malmala bata sa an yiwa tuwon ba, haka tace su juye a kula wai sa dinga zabtara. Wajan ƙarfe hudu kuwa akai horn mai gadi ya bude motoci tsala-tsala suka shigo harabar gidan. Tasama su Ya Shukrah suke leken su, hakan yayi da-dai da fara fitowar mutanan motocin.      Abin daure kan ashe su uncle Hashim ne da iyalansa sai uncle Kabiru shima da nasa family d'in duk sun zo biki, nan da nan su Ya Waleedah suka sakko da gudu suna musu oyoyo cike da murnar ganinsu. “Ya akai babu labari Meenal?” “Eh cewa akai karmu fada idan muka gaya muku ba za a zo da mu ba.” “Ina amaryar take?” “Ku shiga ciki mana kun tsaya anan zai zance kuke yi." Cewar Uncle Kabiru yana rufe mota. Duk sai suka runtuma ciki suna murnar ganin junan su. A parlorn kasa iyayen suka zauna inda Mami ta fito gurin su. Suna ta hira sai ga Alhaji Isma'il ya sanar dasu cewa an fasa kawo kayan lefe sai ranar daurin aure za a hado da su, Mami ranta ya baci dan taso wulakanta duk wanda ya yi kuskuren biyo masu kawowa sai aka samu aka si. Baki kuwa sai sabon abin ci aka yi musu dan duk cewa suka yi ba zasu ci tuwo ba, kawu Hashim ne kawai yaci saboda shi yana son tuwo sosai. Ni kuwa ban koma ba sai da aka yi isha'i sannan Aisha ta rako ni har mota Tukur ya dawo dani gidan gabana yana faduwa wani dum... Dum... Dum.. Na shiga cikin parlorn jiki na a sanyaye kamar wace ba ta da laka.. “Oyo yo ga amarya ta dawo.” Naji sautin muryoyi daban daban, duk a zato na fa yan kawo lefe ne basu zo da wuri ba har suka kai wannan lokacin. Sai da na dago kai na sosai na kallesu sannan na fahimci ko su waye, cikin farin ciki nima na rungume su tare da sakin kuka dan na tabbatar suma daurin aure na suka zo. Na gaida su suna ta lallashi na sun dauka na dadewa ban gansu bane dan kawu Hashim har da cewa. “Last month wallahi naso zuwa na dauke ki, muje kiyi mana ku sati daya ne Allah be yi ba sai yanzu. Kiyi hakuri Khadija ki bar kuka Allah ya ji kan iyayen ki da rahama.” A hankali na ce. “Amin.” Daga nan suka bani kayan da aka dinko min daga can Lagos wanda zan yi fitar biki dasu, kawu daddy ya sanar min cewa an fasa kawo min lefe sai ranar daurin aure. Naji dadi sosai saboda har lokacin banji cewar zan auri wani ba Mas'oud ba, abin da kamar wahala duk da cewa bana daukar kiran da yake yi min dan gujewa fadawa fushin ubangiji. Zuwan su Meenal dasu Badiyya yaran uncle Kabiru da na uncle Hashim yasa na dan rage zaman yin kuka, dole suka sani a gaba da hira da kuma tursasani wajan cin abinci, wai kar naje gidan miji ina da ulcer a yi tunanin ba'a bani abinci a gidan mu. A ranar kam alhamdulillahi na d'an yi bacci, sai dai duk na riga su farkawa, nayi sallah na zauna ina nemarwa kai na sauki a gurin Allah madaukakin sarki. Bani da buri yanzu irin naga wannan zakwakurin da yazo ya rushe min duk wani farin ciki na, yasa na tsani komai na rayuwa a lokaci daya. Su kuwa sun dade basu farka ba dan babu irin tashin da ban yi musu ba amman basu tashi ba sai da suka tashi da kan su. Wajan karfe takwas matar uncle Kabiru ta kira ni, naje take tambaya ta anyi min gyaran jiki kuwa? Na yi kasa da kai waye zai yi min bayan bani da uwa a duniya? Kawu daddy dai ya yana yi min iya abinda zai iya, Mami ita ya kamata ta yi min wannan amman ko a jikin ta, bata ki ma a kai ni ina cikin yanayin kazanta ba babu ruwan ta ita tunda basu Shukrah bane. “Amman garin ya hakan ta faru?” “Babu komai Aunty, kawai ni ce nace bana so.” “Shine suka kaleki saboda kince bakya so? Toh maza ki tashi ki shirya yanzu kizo ni zan miki, Allah yaso nazo da komai na yi da kenan haka za a nannade ki a kai ki gidan mijin. Ai Khadija ko kana da kyau cewa akai ka kara yin wanka sai kafi haka kyau, musamman ke da zaki doshi gidan girma mai daraja kamar yanda muke fata.” Na yi shiru zuciya ta kamar zata kone jin maganar gyaran jikin nan, sam bana so dan nasan zan gaya yin kyau kuma hakan zai sanyayawa mijin rai abinda ni kuma bana so wallahi. Na tashi kamar zan fadi sabo da sauri na bar gurin, ina ta kufce-kufce ta yadda na gujewa gyaran jikin amman sai da tasa aka nemo ni muka shiga dakin da ba za a dame mu ba ta yi min. Mami kam ko a jikin ta bama taso taji ance za a min wani abun na kulawa wanda ita ya dace tayi min amman ta shafawa idanunta kwallin rashin mutunci saboda hassada da bakin kyashi. Subahanallahi ni kai na sai da naji canji a jiki na lokacin da aka gama yi min dilka da halawa na musamman, da yake yar asalin yerwa ce tasan ta kan kamshi mai zama a jikin ɗan adam. Naji wani dadi fiye da yadda nake tsammani, sai dai bana jin zan iya bari wanda ba Mas'oud ba ya kwashe wannan ni'imar. Koda aka gama cewa tayi na tafi daki karna sake na fito waje, komai nake bukata nasa a kawo min nace mata to. Abin da ya bani mamaki duk sunyi anko wai na bikin ne, lallai sun shiryawa auran nan mu duk bamu sani ba. Ganin kowa ya yi ne yasa Ya Waleedah da Ya Shukrah suka je kasuwa suma suka siyo irin material d'in sannan suka kai aka dinka musu saboda kar a yi musu surutu. Sai da naga abin da gaske ne sannan na tashi na dauki wayata na shiga toilet tare da kunna famfo yadda ko nayi wayar babu wanda zai iya jiyo ni. Bugu daya tamkar daman ni yake jira kawai naji ya daga murya shi a can kasa kasa. “Yanzu ba zaka tsamo ni daga fadawa wannan auran ba daddyn Waleed? Kar kai min haka dan Allah. Da nace ba zan kuma kula ka ba sai randa ka samo mana mafita, amman na kasa gashi na kirawo ka da kai na.” A hankali naji yana magana dan sai na kasa kunne sosai nake iya jiyo abinda yake fada. “Ban san me zan iya ce miki ba Oum waleedah, yanzu haka ina kwance a asibiti tun shekaran jiya. Bana jin zan iya kuma numfashi daga lokacin da aka ce kin zama mallakin wani ba ni ba.” “Ya Subahanallahi na shiga uku, Mas'oud yanzu kana asibiti? Da gaske ba kai zan aura ba? Wallahi nasan ina cikin tashin hankali, dan Allah karka guje min bazan iya rayuwa ba bu kai, ka tallafawa zuciya ta Mas'oud, idan ba hakaba wallahi nima gawata za'a kai gidan koma wanene.” Kasa cewa komai ya yi, sai muryar wata mata da naji tana min magana cikin lallashi, da alama mahaifiyarsa ce. Cikin sanyin murya take min magana itama kamar zata yi kukan saboda naji yadda take rawar murya. “Ina son ku dauki kaddara Khadija, aure dama mukaddari ne, ki godewa Allah ya baki lafiya damar raya sunnar ma'aikin mu annabi Muhammad S.A.W. Wannan itace jarabawar ku, ya kamata ace kunyi tawakkali wajan karbar ta yadda Allah zai ji tausayin ku a wani barin na rayuwar ku ta nan gaba. Muna muki fatan alkairi cikin auran da zaki yi, daman Allah ya riga ya rubuta ba zaku auri junan ku keda Mas'oud ba, ki yiwa iyayen ki biyayya mun san tabbas bake kika guje shi ba daga Allah ne. Sai anjima Khadija Allah ya yi miki albarka kinji, Allah ya kare rayuwarki kuma a duk inda zaki tsinci kanki.” Tana kaiwa nan ta katse. Ni kam me zanyi ban da sulalewa kasa na rushe da kuka, na dinga yi ina yin cilli da duk abin da na gani kusa dani. Su Zarah suka zo suna bugun kofar saboda sun ji abin nawa ya yi yawa, naki budewa shine suka je suka kirawo su Mami sannan na bude tare da fadawa jikin matar kawu Hashimu. “Ya isa Dije wannan kukan na meye kuma?” Na samu kai na da cewa. “Baffa na da Ummata duk basu cikin duniyar nan.” “Lahhh haba Dije baga mu ba, ko mu baki yi farin ciki da ganin mu ba sai mu koma inda muka fito dan farin cikin ki.” “A a Aunty wallahi ba haka nake nufi ba, kawai tuno dasu nayi.” “Allah sarki, daman haka ne wata rana zaka ji ina ma kana tare da su. Amman kiyi hakuri ki dena kuka kinga gidan aure zaki je kar kije kiyi rama dama gata nan duk kin fada.” Haka suka dinga lallashi na damin nasiha har sai da nayi shiru sannan suka rabu dani. Ban kuma yin kuka ba saboda bana so a zauna ayi ta min magana kar naje na bata musu rai su ji haushi na bayan bani da kamar su a duniyar nan. *RANA BATA KARYA...* (Sai dai uwar diya taji kunya.) Tun da ya tashi yake jin wata ni'imatacciyar iska tana ratsa sassan jikin sa, a cikin ransa yasan hakan baya rasa nasaba da auran Khadija yar jarida da zai yi, yarinyar da ta tafi da rabin imanin sa. Yaji a duniya yana son kasan cewa tare da ita a cikin gidan shi, komai sabo haka ya tana da, koda yake an tanade su ne dan yau ce ranar da zai yi tafiyar nan zuwa Cyprus. Amman shi a nashi bangaren zasu kasan ce ne matsayin na daurin aure. Daure da towel ya fito ya tsaya wajan dressing mirror yana karewa kanshi kallo. Matashin sarki kenan mai ciki ta nagartacciyar haiba da cikar zati. Mijin Shaheedah angon Khadija a yau da ikon Allah. Lotion d'in sa ya dauka tare da bin sassan jikin sa yana shafawa. Bayan ya gama tsab ya kuma bin jikin da oil perfume da kuma body spray masu azababban kamshi. Shiga ya yi wacce take bayyana cewa shi din sarkin ne ba wai carki ba. Ya Subahanallahi tsarki ya tabbata ga wanda ya halicci wannan bawan nasa, ya kawata shi da gabobi managarta masu cikakkiyar haiba. Lallai ba karamin kariya rawanin da yake sawa yake bashi ba, dan irin su sarki Salman ne suke sawa yan mata suna mafarkin mallaka a matsayin mazajen aure, abokan rayuwa na har a mutu. Kamshinsa kawai ya isa rikita zuciyar mai shaka. Ya riga yayi sallama da kowa tun a daren jiya, shiyyasa yana kammala shirinsa kai tsaye ya fito falon farko na sashen nasa. Cikin hanzari Jakadiya ta zube tana mika gaisuwarta. Kafin ta mike ta fita da hanzari ta sanar da fitowarsa. Taku yake tamkar wani hawainiya, ga kuruciya ga jinin mulki na kai kawo a kowacce jijiya da gabban jikinsa. Tun kafin bayyanarsa garesu hadiman sashen nasa duk suka zube domin mika gaisuwarsu gareshi. Tafiya yake kawai batare da amsama kowa ba. Kamar kullum idanunsa na sake cikin gilashinsa na ka'ida. Sai da ya wucesu gaba daya kafin wasu suyi saurin mikewa su dafa masa baya. Sun iske fadawa suma tsaitsaye a kofar fada suna jiran fitowar mai martaban. A take suma dai zubewar duk sukayi suna mika gaisuwa. Suma dai basu samun amsar ba, sai cikin fadawanne ke ansawa da fadin, "Sarki yaji ku, shima ya gaisheku". Lumshe idanu sarki Salman yayi daga cikin gilashinsa yana sauke wata ajiyar zuya a hankali, wani irin yanayine ke sauka masa a gabban jiki da baisan na minene ba. Haka dai akai masa rakkiya har gaban jerin motocin dake a jere zuka-zuka suna jiransa. Ruf dogarai sukai masa da rigunansu har ya shige daya daga cikin motocin data fi kowacce koshi da daukar hankali, sai da aka rufe kofar sannan suka marmatsa suma suka nufi motocin da zasu shiga. Kamar yanda ya saba sai da ya karanto addu'ar fita a gida a cikin ransa, kafin motocin su fice daga masarautar zuwa airport. *_GIDAN BIKI KHADIJAA(DIJE)_* ———- _Afuwan! Kunji shiru ko? Wallahi kwana biyu inata fama da chronic ulcer. Har takai na kwanta a asibiti na yan wasu kwanaki shysa kukaji shiru, Ina fatan na same ku lpy? Nagode k’warai da addu’oin ku. KIBIYAR ajali zai cigaba da samuwa Insha Allah da zarar naji karfin jiki na sosai.. Na gaishe ku, Gaisuwa mai kima.._ ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥Wannan littafin na kudi ne, AMANA CE, duk wanda yayi mana sharing dinsa shi ALLAH! Idan kina/Kana so ki/ka karanta ki/ka tuntubi numbobin nan* *0903 234 5899* Or *09033181070* Page 22 Hansatu Rano *** Hannu tasa ta toshe kunnuwan ta saboda hana su jin yadda ake gudanar da daurin auren wanda kamar a tsakiyar dakin da take ake daurawar, daidai saitin gidan nasu akwai loudspeaker din masallacin a jikin wata pole shiyasa duk abinda ke faruwa a masallacin kowa na jinsa. Rawa taji jikin ta ya fara, alamun zazzabi na neman rafketa daidai lokacin da mutumin dake fad'an duk abinda ke faruwa a cikin masallacin saboda wadanda ke waje suji, ya ce "An daura auren S..." Bata iya bari taji karashen ba ta kwalla k'ara da karfi tana sake matse kunnenta. Da sauri Umma ta shigo d'akin a rikice,jin karar ta, wanda yayi daidai ta sanarwar daurin auren da kuma yadda abin ya sauya salo, babu wanda mamaki be kamashi ba, amma kafin su kai ga neman karin bayani suka ji ihun ta. A kwance take a k'asa tana kuka sosai,har tana kokarin shid'ewa, da sauri Umma ta riko ta "Baki da hankali? Ko kuwa baki da tawakkali ne? Bance miki kiyi hakuri ba komai yayi zafi maganin sa Allah ba? Why? Wannan sam ba halin k'warai bane, rashin yarda da kaddara ne, Allah na jarraba bawan sa ta fuskoki daban daban, domin yaga karfin imanin sa. Kika san dalilin da Allah ya zaba miki shi a matsayin miji? Ko kinsan cewa sau da dama muna son abu amma ba alkhairi bane a garemu, sai Allah ya barmu da zabin mu yaga yadda zamuyi. A komai zabin Allah shine gaba, dan haka ki tashi kafin mutane su gama gane halin da kike ciki a samu abin magana daman ana ta kus-kus, ki karfafa jikin ki, ki karbi zabin da Allah yayi miki." "Umma an daura fa." Tace tana jan kuka "Eh an daura, kuma aure ya dauro ba." "Shikenan." Tace sai kuma ta sake saka kuka "Wallahi Umma mutuwa zanyi." "Amrah?" Umma ta kirata tana bata rai "Kar na kuma ji kin fad'i haka." Sai ta mik'e "Ki karfafa jikin ki, uwani zata shigo ta taimaka miki ki shirya." Da kai ta amsa ta koma ta kwanta, da gaske kenan har Umman ma ta daina sauraron ta, ta daina tsaya mata kenan?"    Toh idan ta tsaya mata ma me zata iya yi tunda an riga an daura? Ta zama matar shi sai abinda yaga dama yayi, shikenan ita rayuwar ta, ta kare babu sauran abinda zai kuma birgeta. Tana jin sanda Uwanin ta shigo, ta shiga ta had'a mata ruwan wanka sannan ta fito, da k'yar ta tashi ta shiga, ta taba ruwan jin da d'an sanyi sai ta kara na zafin yayi zafi sosai saboda yadda take jin sanyi na hudata, ta dade a ciki tana fatan ace ba gaske bane duk abinda ke faruwa, komai ma be faru ba tana chan tana rayuwar ta hankali kwance. Jin an taba kofar ne yasa tayi saurin karasawa ta fito, ta zauna bayan ta saka kayan da aka ajiye mata na wani rantsattsen lace fari tas da Afrah tasa aka dinka mata shi, ba yadda batayi da ita akan bata so ba amma ta share ta suka je da wasu cousins dinsu suka rakata wajen wani tela. Kayan sun yi kyau kuma sun zauna a jikinta sosai, tana zaune saitin mirror tana kallon kanta da fuskarta da tayi fayau babu ko mai balle ta sami arzikin powder aka turo dakin. Afrah ce da mukarraben ta, sai wata matashiyar budurwa a bayan su dauke da jaka. "Ga Amaryar nan Feedo, dan Allah ki fito da ita sosai saboda angonta ya kasa gane ta, ya kara akan sadakin da ya bayar." "In sha Allah." Wadda aka kira da Feedo din tace tana ajiye kayan hannun ta. Ita dai Amrah bata tanka musu ba, kallon su kawai take dan ba wani gane musu take ba yadda take jin zafin zazzabin na sake karuwa. Kwalliya ta hau yi mata cikin son nuna kwarewar ta, tana jin yadda Amrah ke fitar da hucin zafi, sai ta rage kwalliyar tayi mata simple sannan ta bata ruwa da paracetamol da Amrah ta nuna mata inda yake ta ballo mata tasha, tayi mata sallama ta tafi. Tana fita Amrah tayi saurin cire daurin kan, ta kwanta bayan ta rufe kofar dakin da key ta lullube jikin ta gaba daya tana jin sanyi sosai kamar an jefe ta a k'ankara. ***Waige-waige Safwan yake yana neman Sultan, duk wanda ya tambaya sai yace be ganshi ba, haushi ya kamashi ya ciro waya ya kirashi, amma har ta gama ringing be daga ba, maida wayar aljihu yayi da nufin komawa ciki, wani dake tsaye a hanyar fita yace "Wai sultan kake nema?" "Eh wallahi, yanzu yanzu fa muna tare." "Ya tafi ai, shigowa ta kenan naga fitar sa a mota amma be ganni ba kamar ma sauri yake." "Ok Nagode." Yace yayi ciki yana jin haushin Sultan din sosai, kenan idan da gaske shi din aka daura wa auren haka zai tafi ya barshi shi kad'ai kenan. Ciki ya koma suka cigaba da karbar mutane shi dah Mubarak da Adnan. Bayan kowa ya tafi, suka nufi wajen da suka shirya yin reception, sosai Safwan ya gaji, gashi yana jin wani nauyi a chan kasan zuciyar sa amma ya daure, da yaso yaki zuwa wajen reception din amma yasan hakan zai zama magana a wajen abokan su ace babu shi babu sultan din, dole ya bisu suka je akayi komai aka gama sannan suka nufi gida. Mah-Mah na zaune cikin yan uwanta tasha gayu sosai ana karbar baki, gefe daya kuma hankalin ta na kan daurin auren, suna jin komai suma daga nan, su Hajiya Umma kuma na ta shiga da fita ana rabon abinci. Ta shigo da manyan coolers din waina da sinasir zata ajiye kenan kunnen su ya jiyo musu abinda mutumin ke cewa. Da sauri duk yan gurin suka kalli juna, sannan suka maida kallon su kan Mah-Mah da ta kusan yin mutuwar zaune. "Kamar Sultan naji an ce ba Safwan ba fa." Wata mata tace tana kallon Mah-Mah. "Haka kuwa nima naji." Wata ma ta fad'a duk suna kallon fuskar Mah-Mah da ta kasa cewa komai sai son tabbatar da abinda kunnen ta ya jiyo mata. A hankali ta tashi, tayi part din Daddy tana laluben number sa a wayar ta, tana shiga ta rufe kofar ta kirashi, zagaye falon take tana addu'ar Allah sa ya daga dan tasan yana cikin mutane. Ringing din tai tayi amma be daga ba, be masan tana kiran ba dan yadda ya shiga busy ga mutanen da ya tara yana ta kokarin attending ma kowa. Chanja akalar kiran nata tayi zuwa number Safwan, no answer, Sultan no answer, haka tayi ta kiran duk wanda tasan zata kira amma kamar hadin baki babu wanda ya daga. Burin ta kawai taji halin da Safwan yake ciki, ta kuma ji yadda akayi hakan ta kasance. Toh kodai Sultan ne yayi wani abun da yasa aka maida auren kansa? Tunani tai tayi akan dalilin da zai sa ayi hakan amma ta kasa samo amsa daya. Tashi tayi ta fito, a hanya suka ci karo da Umaima dake ta faman rusa kuka kamar an mata mutuwa, kamar ta make ta haka taji, zata kara mata damuwa akan wadda take ciki da wani banzan kukan ta da ita sam bata ga amfanin sa ba tunda wanda take domin shi be masan tana yi ba. Zatayi magana ta daga mata hannu da sauri "Umaimai dan Allah!" "Bansan me yake faruwa ba ni kaina." Sai ta wuce ta da sauri tayi gate, har ta kai sai kuma ta fasa, idan ta shiga gidan tace musu me? Komawa tayi ciki tana jiran dawowar su suyi mata bayanin yadda akayi hakan ta kasance. Rabin hankalin ta ya tafi tunani,bayan Hajiya Umma ta faffada mata magana sai taji da gasken tayi sakaci da yawa, da har bata hana sultan dawowa gidan ba har bayan a daura auren, sai gashi ma da kanta ta neme shi bayan abinda ya aikata a tunanin ta duk kuskure ne, yanzu kuwa da haka ta faru sai taji babu wanda ta tsana kamar Sultan din,musamman yadda aka juya zancen ya koma wani iri daban. Tana nan zaune taji ana ga su Safwan sun dawo, da sauri ta fito, yana tsaye suna magana da wasu yan uwan Daddy, kallo daya tayi masa tasan ba kalou yake ba, yadda yake ta yamutse fuska da yadda ta ga yana fitar da numfashi da d'an sauri yasa tayi saurin isa wajen, ba tare da tace komai ba ta shiga jan hannun sa,bangaren Daddy ta wuce dashi suna shiga ta tura shi sannan ta rufo kofar. Yi yayi kamar zai fadi tayi saurin riko shi tana kiran sunan sa "Mah-Mah kai na, kai na kamar zai cire, zuciya ta ciwo Mah-Mah, ki taimaka min mutuwa zan, ina jin zafi, ina jin wani iri Mah-Mah." Kuka ta saka tana jijjigashi "Me kayi wa kanka Safwan, me kayi, Innalillahi wa Inna ilaihi, nayi da na sanin shigowar ka rayuwar mu Sultan, wannan wacce irin masifa ce. Me kayi Safwan" "Abinda ya dace shi nayi, shi yafi chanchanta da ya same ta, kuma Shikenan sai a hana shi? Sam hakan ba daidai bane Mah-Mah, me yasa baki fad'a min shi yake son ta ba, saboda karki rasani ko? Saboda ni danki ne ko? Shi kuma bashi da kowa, idan ma ya mutu shikenan ko? Wannan ba Mah-Mah ta bace, Mah-Mah ta ba zata taba haka ba." "Safwan!" Ta kira sunan sa tana rufe bakin ta "Karki ce komai, kiyi min Addua Mah-Mah, inajin zafi a zuciya ta, kiyi min Addua ki roka min Allah,ki daina kuka da an kwana biyu shikenan zan manta." "Kayi shiru, maganar tana kara maka ciwo ne Safwan, ina zuwa, bari na kira Daddy, za'a kaika asibiti zaka samu sauki." Rike hannun ta yayi da sauri yana lumshe idon sa. "Karki kira kowa Mah-Mah, ki zauna dani kawai,ki zauna a kusa dani dan Allah." "Amma kana bukatar likita Safwan,ya za'a yi na barka da ciwo?" "Toh ki kira min SULTAN." Yace yana kulle idon sa. ***A kofar gidan yayi parking ya dauko waya da niyyar kiran Maigadin, yaaga misscalls rututu, ganin hadda Mah-Mah ya dan saka shi tunanin dalilin kiran. Be bi kiran ba ya kira Maigadin, yana waje kawai yace masa sannan ya kashe, ya kuma kashe wayar tasa dan baya son kowa ya kirashi yanzu. Karar bude kofar yaji ya dago da sauri, babban mutum ne wanda a kalla zai yi shekaru 50 haka, yana sanye da doguwar riga irin wadda mafiya yawan maza ke sawa yayin zaman gidan, hannun sa rike da wayoyin sa, fuskar sa na nuna tsantsar farin cikin sa. Da sauri Sultan ya balle murfin motar ya fito, suka hadu tun kafin ya karaso wajen motar. "SULTAN!?" "Barka da rana." Yace yana dan rissinawa. "Barka dai." Sai kuma yace "Bismillah, nan d'in gidan ku ne ai kai ba bako bane." Ajiyar zuciya Sultan ya sauke dan yana ta tunanin irin karbar da zai masa, sai yaga akasin abinda ya zata, kai tsaye yabi bayan sa, suka shiga gidan yana gaba yana binsa a baya, har suka dangana da main parlour din gidan ba inda yake sauke bakin sa ba, parlour da yake ajiye duk wani bako nasa me muhimmanci. "Bismillah." Ya nuna masa wajen zama. Zama Sultan yayi yana dan satar kallon parlour yadda ya tsaru, komai na parlour abin kallo ne. "Ina xuwa." Yace ya fita, chan ya dawo dauke da robar ruwa da cup akan tray ya ajiye a gaban sa. "Ina cikin tsananin farin ciki yau, Allah ya cika min burin da na dade ina fatan cikar sa, yau gani ga ka Sultan." "Mun same ku lafiya?" "Alhamdulillah wallahi, ina Aziza?" "Ban same ta ba ko da naje gidan, sako ta barmin akan lallai na neme ka, bayan kai akwai wasu mutanen da bansan su waye ba, dalilin da yasa nazo gareka kenan, idan ka san wani abu da ya shafi neman iyaye na, ka fad'a min dan Allah." Mikewa yayi ya shiga zagaye dakin, Sultan ya bishi da kallo har ya zagayo ya tsaya a gaban sa sannan yace "Na sani Sultan, nasan kai waye, nasan iyayenka farin sani, sanin da zai yi wuya a samu wanda yayi musu irin wannan sanin." Da sauri ya mike tsaye, "Su waye? Aina suke?" Matsowa yayi ya dafa shi, yayi wani shu'umin murmushi yace "Relax, kwantar da hankalin ka." Yace yana wuce shi, ya koma wajen da ya tashi sannan ya nuna masa in da shima ya tashi yace "Sit." Zama yayi a gefe, duk ya kasa kwantar da hankalin nasa, yana so yaji wani abu akan su, amma alamu sun nuna ba zai zama abu me sauki ba. "Sultan." Ya kira sunan sa "Nasan iyayenka kamar yadda na fad'a maka, kuma nasan inda suke,kuma su ma basu da abun da suka fi burin gani fiye da kai, sai dai hakan ba zata samu ba har sai ka yi wani aiki, aiki me matukar had'ari, idan har ka samu nasara nayi maka alkawarin kaika har gaban su." "Menene aiki?" Yayi maganar muryar sa ta fito tar dan ya gane wani abu guda daya, akwai abubuwa masu yawan gaske da suke a rufe, da yake bukatar ya bud'e su daya bayan d'aya, zai bi duk umarnin sa domin cimma burin sa. "Madallah da kai." Yace sannan ya cigaba "Zagaye take da masu tsaron ta a kalla su goma talatin wanda suka zagaye katangar baki dayan ta, haka daga gate din farko zuwa na biyu akwai masu tsaron wajen su bakwai, daga na biyu zuwa na uku su biyar, kofar da zata sadaka da bangaren akwai masu tsaro su goma.." Sai ya sake mikewa "Idan har ka iya shiga Masarautar Saji, ka wuce wadannna masu tsaron kofofin, ka dangana da turakar Maimartaba Sarki Bello Moddibo Saji, a cikin wata katuwar akwatin karfe akwai barin zobe guda biyu a rarrabe da juna, su nake so ka dauko min, ka kawo min bakin gari ni kuma a lokacin zan sadaka da iyayen ka." "Masarautar Saji!?." Ya fad'a yana mikewa da sauri "Eh ita, kasan wani abu akanta ne?." Girgiza masa kai yayi "Ko kad'an, ina dai son sanin menene alakar neman iyayena da masarautar?" "Zaka sani gaba kad'an." "Shikenan." Yace yana murmush wanda yasa Madaki kallon sa da mamaki, "Me ya sani?" Ya tambayi zuciyar sa "Ko yasan?" Da sauri ya girgixa kansa "Be sani ba gaskiya, da bazai zo tambaya ba." Ya bawa kansa amsa cike da gamsarwa. "Idan har wannan shine zai sada ni da iyayena, zanyi, sai dai ka sani, ka cika alkawari kamar yadda kace zakayi, idan har na same ka da cin amana, zan yi maka abinda bakaa taba tunani ba." "Nayi alkawari." Yace Tashi Sultan yayi ya d'an rissina kad'an yace "Zan tafi." Sai yayi hanyar fita, bayan ya kai kofa ya juyo yace "Rana ita yau, a daidai wannan lokacin mu hadu a chan, na barka lafiya." Ya karasa ficewa, cikin takun sa da ya darsar da tsoro a zuciyar Madakin "Anya abinda yake shirin yi daidai ne?" Ya tambayi kansa "Toh amma ai abinda yayi shekara da shekaru yana jira kenan, ba zai kasa a guiwa ba har sai ya ga yayi nasara, kuma nasarar tana tare da Sultan! Kira ya shigo wayar sa,ya daga yana cigaba da kallon hanyar da Sultan din yabi ya fice "Hello Musa? Babu labari ko? Eh suna hannu na yaran,toh shikenan ka cigaba da bincikawa idan bamu sameta ba toh lallai sun same ta su, ba damuwa sai ka jini." Ya ajiye wayar ya tashi ya shiga ciki. ***Yana fita ya samu wani waje yayi parking ya dora kansa a saman sitiyari, tunanin abinda ya kamata yayi kawai yake, tun bayan da sunan Masarautar Saji ya fito a abinda zai yi domin samun iyayensa, yaji wani irin karfi yazo masa, karfin da be san yana dashi ba, karfi ba na jiki ba, karfin tunkarar duk wani abu da zai zo masa. Dago kansa yayi da sauri ya dauko takardar nan ya sake binta, sai kuma ya dauki biro da wata takardar ya shiga rubuta duk sunayen da zai iya tunawa a labarin da Babah ya bashi (mutanen da suka hadu a Canada) kansa yayi matukar daure wa ganin yadda duk sunayen da suke jikin takardar da ya karbo a gidan marayu sun fito a dayar da ya rubuta. Me hakan ke nufi? Ya ambata a dan tsorace Karar wayar sa ta dawo dashi tunanin da ya tafi da yayi matukar daure masa kai, sunan Mah-Mah ne hakan yasa yayi saurin dagawa "Sultan kana Ina? Kayi sauri dan Allah kazo jikin Safwan ya matsa." "Gani nan yanzu yanzu." Yace da sauri, ya kunna motar ya bata wuta w ransa yana mamakin abinda zai tada ciwon Safwan din a irin wannan rana. Ya yasan an riga an daura auren toh me kuma ya faru? Tunawa da yayi da an daura auren yasa yaji wani iri. "Ya rasata har abadah." Rano Forgive the typos KUNA BUƘATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA'ARKU A PAGES ƊIN BOOKS ƊIN ZAFAFA BIYAR 2021?. To kuzo ga dama ta samu💃🏻💃🏻.         Ina ma'abota son a tallata musu hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?. Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon haziƙan marubanku ƴan biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da saƙo ta dalilin shafukan littatafai. Ga duk mai buƙatar a saka masa tallan kayan sana'arsa a shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntuɓar waɗan nan Numbers 0903 234 5899 or 09033181070 ta WhatsApp, idan har agama buks ɗin kana buƙata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauƙi. Idan kuma wasu adadin pages kake buƙata koda ɗaya ne duk zamu saka maka akan farashi mai sauƙin gaske🤓. Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike neman sauƙi😻😻😄🤗. ______________________ _ZAFAFA BIYAR 2021_*🔥 _*SUKAR BAYA*_💚 _BILLYN ABDUL_ ( _kwai cikin qaya_ ) ( _raina kama_) ( _wutsiyar raqumi_ ) *_SIRADIN RAYUWA_*💛 _SAFIYYA HUGUMA_ ( _alqawarin Allah_ ) ( _daurin boye_ ) ( _Dangantakar zuci_ ) 💙 _*KIBIYAR AJALI..*_💜 _MISS XOXO_ (Sulke baya tsare ta sai ta wuce) ( _Igiyar zato_) ( _Kaimin halacci_ ) ( _Naufal_ ) *_ABIN DAKE CIKIN ZICIYA_*🧡 _HAFSAT RANO_ ( _ruhi daya_ ) ( _Sauyin qaddara_ ) ( _Daurin goro_ ) *_MIN QALB_*❤️ _MAMUHGEE_ ( _buri daya_ ) ( _tarayya_ ) ( _eznah_ ) Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 0903 234 5899 IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 09033181070 Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥Wannan littafin na kudi ne, AMANA CE, duk wanda yayi mana sharing dinsa shi ALLAH! Idan kina/Kana so ki/ka karanta ki/ka tuntubi numbobin nan* *0903 234 5899* Or *09033181070* Page 23 Hansatu Rano *** A high speed yake tafiya yana fatan ya isa akan lokaci dan yadda Mah-Mah ta kirashi kad'ai da kuma yadda yaji muryar ta ya gane akwai matsala. Yana isa ya kashe motar ya fito, mutanen da ke waje suka bishi da kallo, ya wuce su da sauri ya shige ba tare da ya kawo komai ba, yana shiga yayi saurin wucewa part din Daddy yana dan jin wani iri ganin yadda kowa ke masa wani kallo da be san na menene ba. Tura kofar dakin yayi, Mah-Mah zaune gaban Safwan da kai tsaye ba zaka gane bacci yake ko ido biyu ba, idon sa yayi k'asa sosai dan sai da yaji Mah-Mah tà ambaci sunan Sultan sannan ya dago, fuskar sa dauke da murmushin karfin hali. "Karka tashi." Sultan yace ganin yana kokarin mikewa. "Mah-Mah me ya faru dashi?" Ya tambaya sanda ya isa gaban sa,ya ciro stethoscope yana son jin heart beat dinsa. "Gashi nan kamar ciwon nasa ne ke neman kwantar dashi." Tace still tana cigaba da kuka "Zai samu lafiya,kiyi hakuri Mah-Mah." "Inyi hakuri... Dama idan kaji ana bawa mutum hakuri toh an cuceshi ne, bayan duk rokon da nayi maka Sultan, bayan duk maganar da nayi maka akan kayi hakuri, amma ka toshe kunnuwan ka bayan kafi kowa sanin halin da zai shiga, me Safwan yayi maka me zafi haka da ya chanchanci wannan hukuncin naka?" "Mah-Mah dan Allah ki bari." Safwan yace yana jin ciwon nasa na karuwa. "Ba zan bari ba, ban san alkhairi yana juyewa ya zama sharri ba sai yanzu, gashi nan kana kallon halin da ya shiga duk akan abinda yafi karfin sa a wajenka, amma saboda ka kuntata mana ka zabi yin biris da abinda nace maka ka zabi ka cutar da shi, nayi dana sanin shigowar ka cikin family dina, nayi dana sani wallahi..." "Mah-Mah dan Allah ki tsaya ki saurare ni, babu laifin Sultan ko daya akan abinda kike tunani..." "Babu laifin sa? Babu laifin sa kake ce min?" "Eh...Babu laifin Sultan a wannan abun. ." Daddy ya fad'a yana shigowa ciki. "K'warai Sultan bashi da laifi, be masan abinda yake faruwa ba ko nace ya faru, wanda ni da Safwan da mahaifin Amrah mu muka zauna muka yi abinda ya dace, Sultan be san an daura auren sa da Amrah ba, baya wajen kuma kawo yanzu da kike tuhumar sa be san akan me kike magana ba..." Sai ya matso ciki sannan yace "Safwan da kansa yazo ya sameni,ya fad'a min duk abinda ke faruwa wanda kin sani amma kika boye min, ya kuma fadi abinda yake ganin shine daidai, muka je muka samu Prof akan maganar ya kuma nuna mana yasan da maganar Sultan din kuma itama yarinyar shi take so..." "Kina tunanin auran ne zai bawa Safwan lafiyar ciwon da yake fama dashi tun shekaru masu tsawo? Ko kina tunanin aura masa yarinyar da ko k'ad'an bata son shi taimakon lafiyar sa mukayi? Ko daya. Kinsan menene aure, Kinsan wanne irin zama ne, anyi ma ana son juna both side ya aka kare? Babu abinda zai faru sai kara lalata abin da zamu yi..." Baya jin duk abinda Daddy yake cewa tun bayan da kunnensa ya jiyo masa Daddy yana maganar an daura auren sa da Amrah, a take jin sa ya dauke dif ya kuma daina fuskantar komai, har zuwa sanda Daddy ya dafa shi, yayi firgigit kamar wanda ya farka daga mafarki, ya kalle shi da idon sa da suka chanja launi. "Karka damu da abinda mutane zasu ce Sultan, da kai da Safwan duk yayanmu ne, ka yi hakuri da abinda mahaifiyar ku ta farfada maka a baya da yanxu, ajizanci ne irin na d'an Adam. Ka sani babu wanda yake auren matar wani, kuma babu Wanda ke ketare kaddarar sa, saboda ita kaddara rubutaccen al'amari ne tun bayan da aka busawa bawa rai, sai dai addu'a ta kan rage karfin kaddara ko ta chanja ta zuwa wani abu daban." "Haka ne, nagode Allah ya kara girma." Yace yana yin k'asa da kansa. "Sai ka shirya zuwa anjima sun ce za'a kai amarya, inda aka tsara nan za'a kaitan,idan yaso shi Safwan duk sanda Allah ya kawo tasa matar sai yayi amfani da d'ayan." "Daddy dan Allah ayi min alfarma, zuwa sati daya kafin a kaitan." Yace a hankali "Kana da wani abu ne?" "Eh." Ya daga kansa. "Shikenan zan samu Prof da maganar, sati daya dai kayi duk abinda zakayi idan yaso sai a kaita." "Allah ya kara girma." Fita Daddy yayi sai a sannan sultan ya lura da Mah-Mah bata dakin, be ji fitar ta ba, dawo da kallon sa yayi kan Safwan da shima yake kallon sa. Cije baki Sultan yayi, da ace Safwan din Kalou yake da babu abinda zai hanashi bugunsa wallahi, amma duk da haka sai ta kama hannun sa ya murde sosai har sai da yayi kara. "Karasa ni zakayi?" "Baka kyauta min ba Wallahi ,baka kyauta ba ban kuma yi murna da abinda kayi ba Wallahi ko k'ad'an." (karyar banza😂ana so ana kaiwa market) "Naji, ni bance baka kyauta min ba sai kai, wallahi da ace zan iya da sai na maka abinda zaka yi mamaki, me kaso kayi kenan? Shikenan ni kowa gani yake rayuwa ta limited ce shisa kowa sai ya hakura da abu ya barmin, sau nawa kana kwana da yunwa saboda ni? Sau nawa kana karbar duka na a makaranta, shine yanzu ma zaka sadaukar da abinda kake so saboda ni, nine abin tausayi ko? Kuma kaine kadai kasan abinda ya dace kenan." "Safwan..." "Barni kawai na gama fad'an abinda ke raina." Ya fad'a a hasale "Banji dadin abinda kayi min ba, kuma da ace sai da akayi auren na gano wallahi ba zan taba yafe maka ba, ta yaya ma kake tunanin zan iya rayuwa me dadi bayan na gano abinda kayi?" "Duk baka fuskance ni ba Safwan, banyi dan wai kaine me rauni ni kuma zan iya jurewa ba, nayi ne saboda kai kafi komai muhimmanci a waje na, babu abinda zaka nuna kana so ina da iko dashi na hanaka,babu shi wallahi." "Na yarda na yarda, amma ai baka da ikon chanja Abinda ke cikin zuciyar Amrah idan kana da ikon chanja taka ko?" Shiru yayi be ce komai ba. "Baka da amsa ai, malam karka sake irin wannan ganganci ne." "Ba zan sake ba." Yace dan ya gane Jan maganar ma wani pain take karama Safwan din. "Me yake maka ciwo yanzu?" Yace yana taba chest dinsa. "Babu komai na dawo daidai bayan allurar, I'm just weak ne so zan kwanta nayi bacci zuwa anjima." "Ok." Yace yana mikewa "Zan dawo anjima na sake duba ka, if you need anything call me." "Yes sir." Yace yana masa murmushi. Fita yayi ya ja masa kofar, da sauri Safwan ya tashi ya zauna yana saka hannun sa a saman kirjin sa, babu abinda yayi sauki na daga abinda yake ji sai ma karuwa da yayi, da gaske cire soyayya a zuciya ba karamin abu bane. "Allah ka sassauta min." Yace a hankali hawaye masu zafi suka sauko daga idon sa zuwa saman fuskar sa. ***Tana tsaye gaf da kofar, fuskar ta da ta dame sakamakon kukan da take wanda ya hadu da uban powder da ta gambaza ya sa ta sake chanja kama sosai, saura kad'an ya bigeta yayi saurin matsawa yana mamakin abinda take a wajen. "Magana nake so muyi." Tace kai tsaye, tana saka bayan hannun ta, ta goge fuskar ta. "Ok ina jinki." Yace yana tsayawa sosai "Wai da gaske kayi aure?" Maimakon ya amsa mata sai yace "Akwai matsala ne?" "Eh akwai, Mah-Mah bata fad'a maka komai ba?" "Me fa?" "Sakon da Mummy ta bata tun kana Canada." "Sako, sako? Ban gane me kike nufi ba." "Ya Sultan." Afrah ta kirashi tun kafin ta karaso wajen ganin shi tsaye da wadda ta tsana, Umaimah. Juyowa sukayi su dukka, ta karaso da dan saurin ta fuskar ta a sake tace "Ango kasha kamshi." "Ke ko?" Yace yana murmushi "Naji dadin yadda komai ya kasance wallahi,nayi muku murna." "Thank you sis." Yace "Dama Ya Adnan ne yace nayi maka magana kazo ka duba Amrah, tana kwance bata da lafiya, ya kira wayar ka baka daga ba." "Me sameta?" "Ciwon so mana." Tace tana dariya. "Allah ya shirye ki, nasan ba zai wuce ciwon kai ba, bari na shiga ciki na dauko miki magana ki kai mata." Kallon Umaimah tayi taga reaction din fuskarta, kamar hakan yayi mata dadi dan da tayi mugun hade fuska amma sai taga ta dan saki fuskar, da sauri kuwa tace "Allah gwara dai kazo muje ka duba ta da kanka, kasan ta fa bata shan magani gwanda kawai ayi mata allura." "Idan ma mutane kake tunani, toh tana dakin ya Adnan, mutane sun yi yawa a ciki shine Umma tasa muka rakata dakin Adnan ta kwanta a chan." "Ok sai kiyi min jagoranci." Yace sannan yayi hanyar fita. Kallon Umaimah tayi ta sakar mata murmushi sannan ta wuce. Wani irin kunci ne ya ziyarci zuciyar ta, wannan wanne irin wulakanci ne, magana fa take masa amma kamar ma ya manta da ita a wajen, ba ma kamar bane ya manta da babinta yayi tafiyar ta ya barta tsaye. Kukan da ta yi kokarin tsaidawa ne ya dawo mata saboda tsabar takaici. (iska na wahalar da me kayan k'ara) ***Itace a gaba yana biye da ita, da yake bangaren Adnan din a farkon shiga gidan yake shi yasa babu wanda ya ga shigar su sai yan tsirarin mutane. Kofar ta tura, sai ta tsaya bata shiga ba ta bashi hanya "Iya nan zan tsaya." "Ok." Yace yana cire takalmin kafar sa sau ciki, kayan da yasa ne na dazun farare sai dai ya ajiye babbar rigar a mota lokacin da yaje ganin madaki. Dan karamin madaidaicin daki ne da yasha carpet gaba daya me taushi, takawa ya shiga yi kafar sa sanye da ankle sock baka, tun da suka dawo be shigo dakin ba sai yau. Daga chan saman gadon ya hange ta, ta cure waje daya kamar sardine ta lulluba da mayafin ta daya sauko ya rufe kafarta ruf ya kwanta a k'asa. Ja yayi ya tsaya yana lissafi da kidddigar abubuwan da suka faru dashi a cikin awoyin da basu gaza biyar ba. Haduwar sa da Madaki da yadda ya haska masa wani haske na daga abinda yake son sani, sannan sai kuma aure, auren da ya cire daga tsarin sa a yanzu sai gashi Allah ya chanja komai ba tare da yayi komai ba. Idan yace ya taba tunanin komai zai chanja a dan karamin lokaci irin haka yayi karya, Lallai idan ka dogara da Allah komai zai zo maka da sauki. Motsawa tayi, kamar zata juyo sai kuma ta fasa,ta cigaba da baccin ta, duk d ba jin dadin baccin take ba amma zai rage mata mugun tunanin dake damun ta, tunanin ta a gidan Safwan suna rayuwa a inuwa daya. Ta gaban ta ya tsaya, ya tsura mata ido yana kallon doguwar fuskar ta tun daga saman girar ta, zuwa habar ta,dan madaidaicin hancin ta da ya dace da yanayi da tsarin halitar ta,zuwa d'an karamin bakin ta. Abu yaji ya tafi masa daga makoshin sa ya fad'a cikin sa, kamar ace ka tara abu a bakin ka sannan ka hadiye shi a lokaci guda, sai dai nasa be san menene ba. Durkusawa yayi akan guiwowin sa, a gabanta yasa hannun sa daidai hancin ta, yadda yaji tana fitar da hucin zafi yasa yayi saurin kai hannun sa saman kanta, yaji wani irin zafi, da sauri ya sa hannu ya yaye mayafin da ta rufa dashi, hakan yasa ta farka da sauri. Da wani irin yanayi take kallon sa, me yake yi anan? Ta tambayi kanta, tunowa da tayi yasa tayi saurin tashi. "Jikin ki yayi zafi sosai." Yace ba tare da ya kalle ta ba, yana kallon wayar sa. A kunne yasa wayar "Kizo please ki tawo da bowl da abu haka me tsafta kamar towel ko pieces na wani abu, me kyau dai." "Yawwa, da ruwa da cup." Yace bayan ya sake kira. Ajiye wayar yayi a gefen gadon, ya kalleta, ta tatttare kafafuwan ta, ta dora su a saman gadon ta cusa kanta tsakanin kafafun nata tana jin wani irin faduwar gaba. "Sannu." Yace mata sannan ya fita, da sauri ta dago kanta tabi bayan sa da kallo, me yake haka? Tana nan taji an taba kofar, da sauri ta maida kanta ta rufe idon ta kam, kamshin turaren sa da ya karu akan wanda ya fita ya bari yasa ta gane shine ya dawo, tana jin sa ya ajiye abu a kusa da ita, sai kuma taji an shigo, sai taji maganar Afrah. "Gashi Dr." Tace tana ajiye kayan hannun ta. "Yawwa kanwata." "Zan iya tafiya?" Tace "A ah taimaka mata, tasha maganin nan, sai ki taimaka mata ta goge jikin nata, inda hannun ta ba zai kai ba ki tayata." "Tabdin, wallahi Allah aiki umma ta sani, wasu baki tayi tace na kaisu ciki nà basu abinci." "Toh... Yanzu ya za'a yi?" Ya tambaya yana kallon bangaren Amrah yaga reaction dinta "Ka taimaka dan Allah, kafin nan na gama idan yaso abinda zan karasa sai na karasa." Da sauri Amrah ta dago ta kalli Afrah, bata san Afrah cikakkiyar mahaukaciya bace sai yau, tasan me kuwa me take fad'a? Kallon da Afrah taga Amrah nayi mata ne yasa tace "Please Ya Doc, kaga kai doctor ne ita kuma patients dinka ce, ai ba wani abu bane ko?" Ta karashe tana kunshe dariyar ta ganin yadda daga Sultan din har Amrah suke kallon ta kamar wadda tayi wani sabo. "Bari naje." Kawai tace ta fice da sauri, tana fita ta saka dariya sannan tasa key ta rufe kofar ta waje tayi tafiyar ta. "Nan da la'asar sai na dawo na bud'e su, kafin nan ita ta gama ciwon soyayyar tata." Tace tana tura key din a aljihun da akayi mata a jikin gown din ta. Ba ruwana yasin, Mom Sultan kina Ji dai ko?😁😁😁 KUNA BUƘATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA'ARKU A PAGES ƊIN BOOKS ƊIN ZAFAFA BIYAR 2021?. To kuzo ga dama ta samu💃🏻💃🏻.         Ina ma'abota son a tallata musu hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?. Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon haziƙan marubanku ƴan biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da saƙo ta dalilin shafukan littatafai. Ga duk mai buƙatar a saka masa tallan kayan sana'arsa a shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntuɓar waɗan nan Numbers 0903 234 5899 or 09033181070 ta WhatsApp, idan har agama buks ɗin kana buƙata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauƙi. Idan kuma wasu adadin pages kake buƙata koda ɗaya ne duk zamu saka maka akan farashi mai sauƙin gaske🤓. Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike neman sauƙi😻😻😄🤗. ______________________ _ZAFAFA BIYAR 2021_*🔥 _*SUKAR BAYA*_💚 _BILLYN ABDUL_ ( _kwai cikin qaya_ ) ( _raina kama_) ( _wutsiyar raqumi_ ) *_SIRADIN RAYUWA_*💛 _SAFIYYA HUGUMA_ ( _alqawarin Allah_ ) ( _daurin boye_ ) ( _Dangantakar zuci_ ) 💙 _*KIBIYAR AJALI..*_💜 _MISS XOXO_ (Sulke baya tsare ta sai ta wuce) ( _Igiyar zato_) ( _Kaimin halacci_ ) ( _Naufal_ ) *_ABIN DAKE CIKIN ZICIYA_*🧡 _HAFSAT RANO_ ( _ruhi daya_ ) ( _Sauyin qaddara_ ) ( _Daurin goro_ ) *_MIN QALB_*❤️ _MAMUHGEE_ ( _buri daya_ ) ( _tarayya_ ) ( _eznah_ ) Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 0903 234 5899 IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 09033181070 Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥Page 24 Hafsat Rano ***Ta k'asan idon sa yake kallon ta, yadda ta takure a waje daya ta kasa daga Ido ta kalle shi ma, yadda ya cika wajen da kwarjinin sa yasa tayi lakwam ta dinga jin sanyin da take ji na karuwa sosai.    Nazarin ta yayi sosai, sai yayi murmushi ya taso daga inda yake zaune ya dawo gaban gadon, ya dan tsaya kad'an sai kuma ya zauna a gefen gadon. "Me kike ji apart from zazzabin?" Muryar sa ta ratsa ta, ta sake dunkulewa waje d'aya tana jin yadda kamshin turaren sa ya sake cika wajen. "Babu komai." Tace a gajarce. Hannun rigar sa ya nannade zuwa saman damtsen sa wanda hakan ya zama kamar wata al'adar shi, sannan ya jawo bowl din da Afrah ta shigo dashi da dan karamin towel ya dora saman bedside drawer. "Lay down." Yace a hankali, da sauri ta kalle shi, kallon da yasa shi jin kamar zai yi melting a wajen, kallon da yayi nasarar dawo da wata irin zazzafar kaunar da yake mata wadda ya dauke ta ya kaita chan bayan zuciyar sa ya rufe ta ruf, amma da kallo d'aya tak, sai gata ta dawo inda take a da wanda dama dole akayi mata babu yadda ta iya. "Taimaka miki zan, jikinki yayi zafi sosai." Yace yana matse towel din,girgiza kanta tayi da sauri sannan cikin murya kamar zatayi kuka tace "Wallahi zan iya." "Lay down." Ya sake cewa yana saka idon sa cikin nasa. "Please..." Taja kalmar tana sake matse wa "Please." Shima yace, ba tare da wani dogon tunani ba ya saka hannun sa ya kama nata, wani irin shock suka ji a tare da sauri duk suka janye hannun su, ya mike tsaye yana maida towel din cikin ruwan ya juya zuwa wajen da ta ajiye magungunan ya ballo ya dawo ya mika mata. Karba tayi ya mika mata ruwan tasha tana yamutse fuska dan ta sani magani. Ajiye cup din yayi wanda wajen karba sai da hannun sa ya sake haduwa da nata,inda ya sake jin yadda zafin zazzabin ya karu. Be yi shawara da itaba kawai yasa hannu ya mikar da ita a saman gadon, tayi yinkurin tashi yasa hannu a saman bakin sa "Stay still Malama, babu abinda zan miki just wannan help." Runtse idon ta tayi lokacin da taji saukar towel din a saman goshin ta, a hankali ya dinga goge mata har zuwa saman wuyanta, sannan ya kama hannayen ta ya goge mata, sai kuma ya tafi zuwa kafarta, wadda tasha jan lalle da yayi masifar karbar fatar ta, tsayawa yayi yana bin zara-zaran yan yatsun kafarta ta da kallo. Dan bud'e idon ta tayi kad'an sannan ta mayar ta kulle da sauri sanda taji ya sake dawowa sàman kan nata. "Zaki iya juyawa." "Naam?" Tace da sauri. "Bayan wai dama..." "Dan Allah ya isa haka." Tace still idanun ta a rufe, murmushi yayi kad'an sannan ya ajiye towel din "Shikenan na bari." Ajiyar zuciya ta sauke da karfi wadda tasa shi kallon ta. Girgiza kansa yayi yana kallon kofa, kafin ya dawo da kallon sa kanta yace "Kinci abinci?" "Um um." "Why? Tun yauhe?" "Jiya." "What? Are you serious? Kina so ulcer ta kama ki ko?" Bata ce komai ba, sai ya ciro waya ya kira Afrah "Ki kawo mata abinci, idan tea zai samu ki hado dashi." Ya ajiye wayar "Bansan baki ci komai ba, nazo na baki magani kuma." "Umm." Tace a zuciyar ta mamakin abinda ke faruwa take, Safwan take expecting gani a wajen nan ba Sultan ba, amma mesa Sultan ne, kuma kai tsaye yake komai kamar ya manta da wacece ita a  wajen shi yanzu, matar Safwan dinsa, bata gane komai ba gashi bata san wa zata tambaya ba. Bude kofar da akayi ne ya sa ta kalli kofar, ajiye kayan hannun ta tayi tana dariya k'asa-k'asa. "Ya Sultan gashi, akwai wani abun?" "Babu for now, idan ta ci abincin nasan zata samu bacci idan yaso sai ki dinga zuwa kina dubata." "Toh, toh ai hakan ma yayi." Tace tana murmushi "Bari na tafi toh." Tayi gaba abinta, tana musu dariyar mugunta. Tana fita ta maida kofar ta rufe ta yadda take, tayi tafiyarta, sai dai wannan karon mammakon ta koma cikin gidan waje tayi abinta bata kuma san yaushe zata dawo gidan ba. "Sit up." Yace mata bayan ya zuba mata abincin a plate, ya had'a mata tea me kauri a cup. Zama tayi ta jingina da fuskar gadon ya mika mata tea din ta karba ta fara sha a hankali. "Wai duk zazzabin nan nawa ne?" Da sauri ta zare cup din daga bakin ta aamma bata yi magana ba, wani irin murmushin gefen baki yayi ya cigaba "Dan Allah ya Sultan, ka taimaka ka aure ni, dan Allah zan mutu wallah,ah ooo wash my heart zata narke."  Yace yana dafe daidai saitin zuciyar sa yana dariya sosai "Me?" Tace tana bata fuskar ta "Kin manta yadda kika dinga bi na kina roko na, kinga handsome dan saurayi ko? Toh shikenan ki gode Allah application dinki da kika yi ta turowa an karba, Allah ya mallaka miki ni, I'm all yours now and forever." Ya karashe fuskar sa na nuna yadda yake ji, kusan mutuwar zaune tayi da jin abinda yace, sai taji kamar a mafarki, kenan Sultan Allah ya bata ba Safwan ba? Amma take ta fama da wahala kowa yaki fad'a màta, "Alhamdulillah." Tace a hankali ashe ya ga sanda bakin ta ya motsa da abinda tace, tasowa yayi ya zauna sosai kusa da ita wannan karon har kafad'ar sa na gugar ta ta. "Alhamdulillah ya Allah. Shine abin godiya dan Allah ne kad'ai yasan dalilin da yasa hakan ta faru." Sai ya juyo yana fuskantar ta sosai, fuskar sa na nuna seriousness dinsa "Ga Sultan a gabanki Amrah, maraya wanda bashi da uwa ba uba, abubuwa da yawa sun faru a dan lokacin nan da baki ba zai iya fad'an su ba a yanzu,akwai gagarumin abinda yake gabana Amrah, wanda nake jin kamar wani rami ne me zurfi, sai dai ina bukatar taimakon ki, komin runtsi karki cire tsammani, komai zai faru ki sani Sultan dinki zai dawo gareki,safe and sound, ki yi ta min addu'a dan yanzu ke kika fi kowa kusanci dani,haka kuma Allah na karbar addu'ar mata akan mijin ta. Zaki yi min ko wifey?" "Zan yi in Sha Allah." "Nagode sosai, for now zaki zauna a gida zuwa sati daya kamar yadda mukayi magana da Daddy yace zai sanar ma Abba. Wait for me kinji, ki shirya sosai, dan Sultan dinki ba na wasa bane." Ya karashe yana kashe mata Ido daya. Kunya ta kamata sosai ta cusa kanta cikin kafarta tana yin dariya k'asa k'asa . Kafadarta ya kama ya mikar da ita tsaye, ya tsaya a gaban ta sosai har tana jin hucin numfashin sa a saman kanta dan sosai ya fita tsawo duk da ba za'a sata a layin gajeru ba amma idan ta tsaya a gaban irin su Sultan toh dole za'a ga gajartar ta. "Will you wait for me? Zaki jirani?" "I will wait for an eternity." Tace a hankali "Masha Allah, bani da abinda zai bani tsoro yanzu, knowing I have you zan yi komai na dawo a karamin lokaci." "Allah ya taimaka ya bada sa'a." "Amin ya Allah." "Amin ya Allah." Ya sake maimaitawa. Shiru sukayi dukkan su, kowa da abinda yake tunani,  a hankali taji zazzabin na barin ta, taji wani irin mixed feeling na shigar ta, irin kamar ace ka gama sanin cewa ka rasa abu me muhimmanci a gareka har abada, sai kuma ya dawo gareka a lokacin da ka cire tsammani. Knocking akayi a kofar, sai kuma suka ji an saka hannu an murda kofar, "Ba dai yarinyar nan tafiya tayi min da key din ba." Suka ji yace. Dan karamin tsaki Adnan yaje sannan ya sake cewa "Toh Ina ma ta tafi ne? Wannna yarinyar." Suna ji ya bar wajen, sai ta kalli sultan taga shima ita yake kallo "Rufe mu tayi?" Daga kafad'ar sa yayi irin I don't care din nan sannan yace "Na sani." "Yanzu ya zamuyi?" "Kwana zamuyi kawai." "What!? "Kwana... Ko haramun ne?" "Amma fa..." "Me?" Yace getting more closer than before, sai ta hau stammaring. Hannu yasa ya sakalo waist dinta ya yi hugging dinta firmly. Mutsu-mutsu ta fara ya sake riketa kam yana manna hancin sa akan fuskar ta. Runtse idon ta tayi sanda taji saukar bakin sa a saman kanta, sannan yayi kissing saman idon ta, da both side na cheeks dinta. "Matsoraciya." Yace yana sakin ta, kamar zata fadi sai kuma ta tsaya tana jin kamar ta nutse saboda kunya. ***Da wani irin yanayi ta shiga bud'e idonta, a hankali har idon nata ya gama budewa tas ta kuma fuskanci a inda take duk da duhun da ya mamaye dakin, ta san wajen tun tsawon lokaci kuma babu abinda ya chanja sai ma kara tsufa da wajen yayi. Dakin horo kamar yadda mutanen Masarautar ke kiran sa dashi, dakuna ne na kara kananan gaske, sai dan karamin makewayi a cikin kowanne, shekarun baya ta taba kasancewa a cikin wajen sai gashi yau ma ta sake dawowa ciki. Sai dai wannan zaman yasha banban da wanchan.    Bata san tsawon kwanakin data dauka a wajen ba, daga ruwa babu wani abu da ta saka a cikin ta, ba wai dan ba'a batan ba, sai dan bata jin akwai sauran kalar makircin da bata sani ba.      Ta galabaita sosai tana kwance lamo a k'asa taji takun tafiyar mutane da maganganu k'asa k'asa, kafin ta gama tantance muryoyin nasu aka budo kofar aka shigo, da k'yar ta cire kanta ta kalle su, ta maida kanta k'asan tana jin wani irin tsanar su na sake karuwa a zuciyar ta. "Kin dauka zaki iya tsere mana?" Daya ya tambaya yana fashewa da dariya. "Idan har kin yi tunanin bamu san inda kike ba tsawon lokacin nan yasa bamu neme ki ba toh kinyi karya, mun barki ne zuwa lokacin da ya dace." Bata ce kala ba, tayi shiru tana jin su har suka gama suka fita. "Allah kana kallo, karka bawa wandannan azzaluman nasara." ***A matukar firgice ya tashi, yana lalubar glasses din idon sa, hannun sa ya sauka akan wani abu kamar kwalba, yayi yar kara kad'an ya tashi sosai sannan ya kunna bed side lamp. Babu komai a dakin da zai nuna wani abu ya faru kamar yadda ya gani a mafarkin sa. Kasa komawa baccin yayi har gari ya waye sosai, hadiman sa ne suka shiga kaiwa da komowa a bangaren har komai ya daidaita kamar yadda aka saba kullum. Suna zama a fad'a mutumin ranar ya sake dawowa, wannan karon a dan rikice yake fiye da ranar. Umarni aka bawa kowa ya fice ya rage daga shi sai Maimartaba Sarki Bello Moddibo Saji, faduwa yayi k'asa jikin sa na rawa yace "Allah ya baka yawan rai ranka ya dad'e, abinda yake tunkaro mu babba ne wannan karon. Shukar da sukayi tayi yad'o har ta fitar da amfani, amfanin dake neman zamar mana matsala a yanzu." Sai ya sauke kayan hannun sa, ya fito da mudubin ranar, wannan karon danjoji guda uku ne masu matukar haske suke tunkaro su sannan sun fitar da shape kamar triangle daya a sama, sai da Sarkin ya d'an zabura har ya kusa direwa daga kujerar sa sai kuma ya daidaita yana duban sa. "Ya akayi haka ta faru? Bayan mun samu TABBACIN hakan ba zata faru ba, bayan babu sauran abinda muka bari da bamu rufe ba, toh ina matsalar take? Waye ya ha'ince mu? Waye yaci amanar mu da muka kasa sani sai yanzu da komai yake shirin karewa? Waye wannan!" "Ranka ya dad'e!" "Kafin faduwar rana, ina so kazo min da bayanin wanda yaci amanar mu, ka nemo shi ko waye." "An gama ranka ya dad'e." Yace da sauri yana tattare komai. Yana fita Sarki ya bada umarnin yau babu zaman fada. Kowa yayi mamaki dan hakan bata taba faruwa ba. Manage please©® Hafsat Rano Page 25 Wannan littafin na kudi ne, AMANA CE, duk wanda yayi mana sharing dinsa shi da ALLAH! Idan kina/Kana so ki/ka karanta ki/ka tuntubi numbobin nan* *0903 234 5899* Or *09033181070 * Kafin faduwar ranar kamar yadda ya bashi umarni, ya dawo da labarin da ya firgitashi ainun. Faduwa yayi kamar ko yaushe yayi gaisuwa, sannan cikin tsantsar biyyyar ya soma bayani. "Akwai gagarumar matsala ranka ya dad'e, akwai shiri me girma akan zoben nan, wanda idan aka yi wasa zai koma hannun da ya fito ba tare da shi hannun yasan da hakan ba." "Kamar ya?" "Zai shigo masarautar nan bisa umarnin Madaki, zai kuma dauki zoben nan, sannan zai damka shi a hannun Madakim, wanda idan har hakan ta kasance, komai ya lalace,komai ya baci." "Babu wanda yake da ikon kai hannu akan zoben nan face shi d'in tsatso ne daga tsatson wannan ahalin, waye wannan da zai shigo Masarautar nan har ya iya daukar zoben?" "Allah ya baka yawan rai, shine abu na karshe da muka kasa gani, muka kasa samun amsar sa, abu daya muka sani shine ranar jummah me zuwa hakan zata kasance." "Idan har mun fuskanci abinda kake so ka fad'a, kenan Madaki...? "Be hakura ba tsawon wannan lokacin yana bibiyar duk ayyakun mu." Gid'e kai Sarkin yayi cikin gamsuwa sannan yace "Waye yake mana zagon k'asa?" "Ayi min aikin Gafara ranka ya dad'e, ba kowa bane sai Yarima me jiran gado." Tsaye ya mike, da sauri kamar idon sa zai fado k'asa, sai kuma yayi k'asa da kansa cikin tsananin mamaki, mamakin abinda yake shirin faruwa dashi, d'an cikin? Ko dai be gani daidai bane? Amma kuma babu yadda za'a yi yayi wasa da aikin nan ko dan muhimmanci sa ga mutane masu dama. "A kira sarkin kofa!" Da gudu wani bafade ya fita, cikin kankanin lokaci ya dawo tare da wanda aka kira da Sarkin Kofa "A tsaurara tsaro a kara matakan tsaro a kowacce kofar shigowa da fita daga Masarautar nan, sannan ya atabbatar babu wasu bakin fuska da zasu shigo ba tare da an tantance su ba, duk wanda yayi gardama ko ya nuna wani abu da baku yarda dashi ba, a aika shi garin da ba'a dawowa!" Takawa ya shiga yi cikin tsananin bacin rai, ya juya ya shige ciki ya bar mutane da yawa da tunanin abinda ke faruwa ko yake shirin faruwa, babu wanda ya taba ganin sarkin a irin wannan yanayin. **Tun da ya koma ciki sai ya k'asa zama, ya jawo akwatin karfen dake k'asan gadon sa ya bude ta, kayayyaki ne a ciki birjik masu muhimmanci a wajen sa, sai dai kaf ciki babu kamar barin zoben nan wanda zai iya cewa shine duk matakin nasarar sa. Yana nan a inda ya ajiye shi, ajiyar zuciya ya sauke da karfi ganin babu abinda ya sameshi, maidawa yayi ya rufe ruf ya tura ta ciki.     Kamar yadda ya tabbatar da shud'ewar mutane masu yawa a baya, haka zai tabbatar da shud'ewar duk wani abu da zai kawo masa cikas a cikin mulkin sa. Ko da kuwa kusancin sa ya kai kusanci dake tsakanin d'a da mahaifi ne.     A lokaci me tsawo, bayan shud'ewar wasu al'amura da suka zama wani sirri nasa, sirrin da duk amintar dake tsakanin su bata sa ya sanar dashi ba, sirrin da ya zama wani tsani na duk nasarar da ya samu. Sirrin Kasancewar sa Sarki a Babbar Masarautar irin Masarautar Saji. Sai dai yasan yayi abubuwa da yawan gaske kafin hakan ta kasance, wanda ya tabbata Idan har za'a koma baya, idan har za'a tariyo masa abubuwan da suka farun ba lallai ne ya iya yarda da gaske sai da ya yi irin wannan gwagwarmayar ba sannan komai ya kasance ba.    Ya tuna wani lokaci, suna zaune da shi, suna hira irin ta makusanta aminan juna, ya dauko masa zancen da yayi amfani wajen samun nasarar sa, yayi amfani da damar ya jefi tsuntsu biyu da dotse guda daya.    Dunkule hannun sa yayi ya daki iska dashi, ya ja iska zuwa hunhun sa, sannan ya fito da ita. _"Bello... Ina so kasan ba ko yaushe ne rayuwa take tafiyar wa mutum a yadda yaso ba, sau da dama abubuwa na chanja salo da alkibla daga inda bakayi zato ko tsammani ba..."_ Kalaman da dan uwan sa ke yawan maimaita masa a wanchan lokacin, sai dai be taba daukar su da muhimmancin da har zai zauna yayi bitar su ba, amma a yanzu sai yaji yana bukatar sanin ma'anar su, musamman da yake hango wani gagarumin abu na tunkaro su. Ta Ina zai fara? Safiyya da aka tabbatar masa da wanzuwar ta a cikin Masarautar sa duk da har yanzu be je ya ganta ba, ko kuma Safiyanu Madaki dake shirin kawo masa cikas ta inda be yi zato ba. Idan kuma ya gangara kan matan nan guda biyu, da taurin kai ya hanasu amsa abinda yake nema a wajen su tsawon lokacin nan. Ta Ina zai fara ne? Yarima Bilal na masa zagon k'asa, d'an da ya haifa da cikin sa, yake ma so mara iyaka. A bangare daya kuma, hasken da ke tunkaro Masarautar tasa da ya gani da idon sa, wanda adah yake ganin su dishi dishi amma yau sai ya gansu da matukar haske, suna kuma da kusanci da shi a duk inda suke.    Gabatowar magriba yasa shi katse tunanin sa, ya fita zuwa masallacin dake cikin Masarautar suka gabatar da sallah.. Zaman sa yayi a cikin masallacin har sai da akayi Isha'i sannan ya koma shashen sa da rakiyar manyan makusanta sa. Sun yi tunanin zai zauna dasu akan abinda ke faruwa sai suka ga yayi shigewar sa ciki ya barsu da hangamemen baki cike da mamakin Sarkin. A lokacin da kowanne bawa ke samu ya kwanta ya hutar da zuciya da gangar jikin sa, a lokacin ne su kuma suke cikin tsananin azabtuwa da kalolin azabobin da ake musu, duk da haka basu taba jin a ransu zasu mika wuya ba, basu taba jin zasu taba sanar dashi abinda yake son sanin ba.    Da sauri duk suka zube a k'asa, cikin kankan da kai suka shiga yi masa kirari, takawa yake yana wuce dukkannin kofofin har ya dangana da inda yake son isa, da sauri wanda yake tsaron wajen ya bud'e masa kofar yana ja baya "Allah ya baka yawan rai." "Sun shirya fad'ar abinda muke so muji?" "Basu shirya ba ranka ya dad'e, ko dazu mun yi musu abinda muke tunanin zasu karaya su mika wuya, sai dai duk yadda suka jigatan be sa sun karaya ba, daya daga ciki ma tana cikin ciwo, Kamar ba zata kai ba." "A basu magani, a dakatar da duk abinda ake musu, a basu abinci me kyau, nafi son rayuwar su fiye da komai, dole ne su rayu, domin rayuwar tasu da kasancewar su a hannun mu zai zama wata tawaya ga abokan gaba!" "An gama ranka ya dad'e." Juyawa yayi ya bar wajen zuciyar sa cike da kudurin abinda zai aiwatar. Yana kuma jiran ranar da ko ma waye zai saka kafa a cikin Masarautar. A ranar ne zai tabbatar da abinda ya dade yana zargi! **** ***Zamewa tayi ta zauna a tsakar dakin kunya na sake kamata, maza sai dai a barsu, sam basu da ta ido wallahi, tana jin shi yana tsokanar ta, tayi masa banza. Kira taji yana yi da wayar sa, kafin chan a daga. "Wai kana ina dan Allah?" "Ina dakin ka ina jinyar matata." "Wait what? Wai kana cikin gidan? Toh ai nazo dakin a rufe ko? Kai tsaya ai kuwa kamar naga takalmi a wajen amma hankali na yayi gaba ban lura ba. Wai da gaske kana ciki?" "Muna ciki wallahi." Ya fad'a yana kashe mata ido daya, dauke kanta tayi da sauri tana murmushi "Eh wallahi Afrah ce ta rufe mu, ah tana sane ta rufe, kuma dole na bata tukwuici ba." "Toh shikenan ina jiran ka." Yace sannan ya ajiye wayar, yazo ya zauna a gefen ta ya tankwashe kafarsa kamar yadda tayi har kafar tasa na gogar tata. Babu wanda yayi magana kowa da abinda yake tunani a ransa, har zuwa sanda aka bud'e kofar, Afrah a gaba tana raba idanu Adnan na bayan ta suka shigo. Hararar ta Amrah tayi bayan tayi saurin jan jikin ta ta matsa gefe sannan ta kad'a hannun ta alamun zaki sani. "Me tayi miki?" Yayi maganar yana tashi tsaye "Babu komai." "Kike hararar ta kuma?" "Yawwa dai Ya Sultan, ai idan ba'a gode min ba ai ba za'a zageni ba ko?" "Saboda kinyi abin arziki ko?"  Adnan riga amsawa yana hararar ta  "Kinyi abinda ya dace kanwata,kuma nagode sosai." "Toh kindai ji." Tace tana wa dariya "Muje dan Allah, ba kai ba Safwan babu dad'i ai kuma kasan dole mutane zasu neme ku." Kiran sunan Safwan da Adnan yayi yasa Sultan saurin tashi, ya akayi ya shagala haka har ya manta da halin da ya barshi, duk da alkawarin da yayi na komawa ya duba shi, hanyar fita yayi Adnan din ya bishi suka tafi yana mishi bayanin yadda abubuwan suke. "How far?" Afrah tace tana dariyar shakiyanci "Afrah wallahi ki kiyaye ni!" "Me nayi? Daga taimako? Ki rantse da Allah ban taimaka miki ba, bari naji." Ta kai hannu saman kanta "Ehen, ina fever din?" Hannu Amrah ta saka ta taba kan nata itama, da gaske babu zazzabi, bata ma san sanda akayi ya tafi ba, murmushi kawai tayi bata amsawa Afrah ba, dan bata masan me zata ce mata ba, dan wani karatun duk yadda aka karanta maka shi ba zaka taba gane shi ba sai yazo kanka.    Ciki gidan suka koma, Amrah ta sake wanka ta chanja kaya, mutanen dake ta tambayar ina Amarya ta dinga bi daya bayan daya tana gaishe su, su kuma suna mata fatan alkhairi a sabuwar rayuwar da zata shiga. Sosai take jin dadin addu'ar, a k'asan mokoshin ta, take amsa musu da Amin,ita kuma Afrah sai ta amsa a fili. ***Ran Hajiya ya baci sosai, fad'a take ta inda take shiga bata nan take fita ba, shi dai Abba be ce komai ba har ta yi ta gama,dan ya riga yasan Allah ne yayi Sultan din ne mijin shisa ma hakan ta faru,amma bashi da bakin da zai yi convincing hajiyar shiyasa ya bita da ban hakuri kawai ya ja bakin sa yayi shiru. Fad'an ta akan abu biyu ne, akan me za'a dauki Amrah a bawa wanda bashi da asalin, kuma ma a boye komai sai bayan an daura sannan kowa zai sani, idan wani abu ya faru fa? Idan labari ya chanja daga abinda suka sani fa? "Hajiya dan Allah kiyi hakuri, ina ganin kamar Sultan ba shine ya zaba ma kansa hakan ba, jarrabawa ce da zata iya samun kowa, kuma kinga Sultan duk a gaban idonmu ya tashi, tare ma da namu yayan,tarbiyyar su daya ce da Adnan da Safwan din, dan Allah Hajiya ki manta da komai kiyi musu Addua." "Bance ai ba hakan bane ba, kawai dai kasan za'a iya samun wani hali daban da mu bamu san dashi ba, kuma ko ma ba haka ba, kuka san ta hanyar da akayi aka same shi? Wacce uwa ce zata bar danta idan har ba wani abun kunyar tayi ba?" "Hajiya!?" "Nayi karya ne? Yawancin yara irin haka abinda ya faru kenan, kalilan dinsu ne ba hakan ba." "Toh dan Allah Hajiya mu kyautata ma Sultan zato,ko ba dan komai ba, ko dan Kasancewar sa yanzu a matsayin mijin yarmu." "Toh me zance? Bayan sai da ka gaba yin abinda ka ga dama sannan ka sanar dani, Allah ya basu zaman lafiya." "Amin ya Allah, kiyi hakuri Dan Allah." "Nayi!" Tace a gajarce Sake bata hakurin yayi, ganin da gaske ba zata taba yarda da  dalilin nasa ba yasa ya bita a haka kawai. Saboda haka ne ma ya fasa fad'a mata akan tariyar Amrah wani sati me zuwa,yasan yadda zata kara hawa akan maganar, sai kawai ya sake bata hakuri yayi sallama ya tafi yana fatan Amrah ta samu rayuwa me inganci da Sultan, yana ji a ransa Sultan ba zai bashi kunya ba kamar yadda mutane da yawa suke tunani. Tun da maganar iyayen sultan ta fito wadda Abban ya rasa ta ina maganar ta fara shikenan mutane da yawa suka chanja yadda suke ganin Sultan din a dah, akwai wadanda ma suka fita harkar sa kamar dai yayi wani abu ne mara kyau ko kuwa shi ya zabi rayuwar sa ta zama a hakan. Har yaje gida yana tunane tunanen abinda ya sa mutanen duniya suke irin haka. ***Yana kwance kansa na masifar sara masa, idon sa daya ya kanne shi ta side din da yake masa ciwon ya dora hannu a saman kan ya dafe, tun bayan fitar SULTAN din be iya aikata komai ba, sai faman tunane tunane. Ya riga ya san abinda yayi shine daidai amma kuma ya kasa karbar hakan, zuciyar sa ta gaza daukar komai har yake jin tayi matukar yin weak din da bai taba jin irin sa ba. Iska ya fezar me zafi ya sake maida idon sa ya kulle jin an budo kofar. Mah-Mah ce dauke da tray ta shigo ta tura kofar sannan ta ajiye tray din ganin kamar bacci yake ta juya bayan ta kalle shi ta fita.   Kara bude kofar akayi, Sultan ne da Adnan suka shigo, yayi sauri isa wajen sa. "Safwan, are you alright!?" Yace yana taba fuskar sa, dan bud'e idon sa yayi ya kalli Sultan din sai kuma ya mayar ya rufe. "Abinda nake tsoro kenan,you ruined everything Safwan, da bakayi abinda kayi ba yanzu kalli yadda kake ji, why? Me yasa ka zabi haka? Is this what you call sacrifice? Um?." Yayi maganar da sauri da sauri yana firfiro da kayan cikin first aid kit dinsa "Sultan please..." "Shishh, karka ce komai, maganar zata iya lalata abubuwa da yawa, just stay still." Ya matso kusa dashi yana dora masa dan karamin pillow a saman kansa yadda zai samu support. "Kana jina?" "Eh..." "Yawwa." Yace yana kafa masa inhaler a baki A hankali ya shiga jan numfashin nasa da yake jin yana kokawar dauke masa.  sauka a hankali ya daidaita. "Alhamdulillah." Sultan da duk ya jike da zufa yace yana kama hannun sa daidai wajen pulse din sa "Kana tunani da yawa ne, ka daina tuna komai ka cire komai a zuciyar ka, zan maka allurar bacci for you to be safe, idan ka tashi, komai zai wuce, komai zai zama kamar ba'a yi ba." "Sannu Safwan." Adnan da duk tausayin su ya kama shi yace daga chan gefen inda yake tsaye,be iya amsa masa ba saboda yadda allurar taa fara daukar sa. Drip Sultan ya ciro ya daura masa ganin kwanukan da aka ajiye na abinci be taba komai ba, ya kuma san dama ba ci din zai ba saboda halin da yake ciki. Fita Adnan yayi ya barshi a ciki ya zauna yana kallon sa lokaci zuwa lokaci.     Ganin zaman ba na yanzu bane yasa ya shiga tunanin abinda zai fara. Da farko dai ya na son duk information akan Masarautar Saji, yana son ya san yadda suke gudanar da koman su, tun daga safiya zuwa dare, yaña so yasan iya adadin mutanen dake cikin Masarautar da kuma wadanda suke da kusanci da Sarkin na sosai. Ta Ina zai fara? Me yasa a duk sanda ya tuna abinda ke gaban sa sai yaji kamar idan ya tafi tafiyar kenan,amma kuma ya rasa dalilin da yasa yake jin ba zai taba iya fasa zuwan ba duk kuwa da abinda yake ji din.    Yayi nisa a tunanin sa har be ji sanda Mah-Mah ta shigo ba, tsayawa tayi ta na duban sa, sai kuma ta kalli Safwan dinta dake kwance yana karbar drip, a haka rayuwar sa zata kare Kenan shi? A haka zai ta fama da  lalurar ne wai? Ji tayi zuciyar ta, ta tsinke sosai, tausayin danta take ji, irin tausayin da uwa zata ji akan d'anta, abinda take guje masa kenan, abinda take ji masa tsoro kenan, shi tasa zuciyar bata da karfin da zata yi irin wannan sadaukarwar. Tasowa yayi ya tsuguna a gaban ta, "Tabbas duk wata uwa da d'an ta yake a irin halin da Safwan yake ciki dole ne ta shiga damuwa, amma wallahi tallahi Mah-Mah, ban yi abinda nasan zai cutar da Safwan ba, bansan ya akayi yasan komai ba, bansan wanda ya fad'a masa ba, kuma wallahi da nasan abinda zai faru kenan da na hana faruwar sa." "Na sani Sultan, nasan abinda zaka iya da wanda ba zaka iya ba, sai dai na kasa daina ganin laifin ka,kasan saboda me? Saboda ni uwa ce, da bata san komai ba sai son samun lafiyar d'anta." "Me zanyi ki daina ganin laifi na dan Allah Mah-Mah? Ke uwa ce a gareni, babu kuma wanda zai so fushin mahaifiyar sa." "Kana so kasan abinda zaka yi na daina ganin laifin ka anan Sultan??" "Eh..." "Ka tabbata zaka iya?" "In Sha Allah zanyi duk abinda kike ce." Taku tayi kad'an zuwa gaban gadon da Safwan din yake kai, ta taba saman goshin sa tana tuna abinda suka tattauna da yan uwanta, shawarar da suka bata tayi matukar tasiri a zuciyar ta. Juyowa tayi tana fuskantar sultan din sosai. "Inaso ka fita daga rayuwar mu, kayi nesa da mu ta inda zamu manta da wanzuwar ka a cikin gidan nan, sannan kafin ka tafi, inaso ka sakar ma Safwan Amrah ya aura! _ZAFAFA BIYAR 2021_*🔥 _*SUKAR BAYA*_💚 _BILLYN ABDUL_ ( _kwai cikin qaya_ ) ( _raina kama_) ( _wutsiyar raqumi_ ) *_SIRADIN RAYUWA_*💛 _SAFIYYA HUGUMA_ ( _alqawarin Allah_ ) ( _daurin boye_ ) ( _Dangantakar zuci_ ) 💙 _*KIBIYAR AJALI..*_💜 _MISS XOXO_ (Sulke baya tsare ta sai ta wuce) ( _Igiyar zato_) ( _Kaimin halacci_ ) ( _Naufal_ ) *_ABIN DAKE CIKIN ZICIYA_*🧡 _HAFSAT RANO_ ( _ruhi daya_ ) ( _Sauyin qaddara_ ) ( _Daurin goro_ ) *_MIN QALB_*❤️ _MAMUHGEE_ ( _buri daya_ ) ( _tarayya_ ) ( _eznah_ ) Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 0903 234 5899 IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 09033181070 Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥[4/12, 11:04 PM] Maman Maryam: ©® Hafsat Rano Page 26 Wannan littafin na kudi ne, AMANA CE, duk wanda yayi mana sharing dinsa shi da ALLAH! Idan kina/Kana so ki/ka karanta ki/ka tuntubi numbobin nan* *0903 234 5899* Or *09033181070 ***Da sauri ya dago, yana son ganin ainihin gaskiyar abinda tace din,be yi tunanin abinda zata ce kenan ba. Sosai ya shiga shock har ya rasa me ma zai ce "Mah-Mah?" "Abinda nake so kayi kenan, a matsayin rama alkhairi da alkhairi, a matsayin tukwuicin abinda mukayi maka, idan kayi wannan bani da sauran komai a kanka." Juyawa tayi da nufin barin dakin, sai kuma ta tsaya ta juyo "Karka manta, kayi alkawarin zaka yi ko menene." Ta karashe sannan ta fice daga dakin. Bin inda tabi ta fita yayi yana ganin kamar be ji daidai ba, kamar ba abinda Mah-Mah take son fad'a ba kenan, kamar ma ba ainihin Mah-Mah da ya sani bace ba, an chanja ta ne da wata daban ko kuma anyi brainwashing dinta ne.    "Zan iya? Zan iya?" Ya shiga tambayar kansa, sai kuma ya girgixa kai "No...Ba zan iya ba, aure ba wasan yara bane, aure abu ne me girma da be kamata ayi irin wannan wasan dashi ba." Ya bawa kansa amsa a fili yana girgiza kansa. "Amma Safwan fa? Be chanchanci komai ba a wajenka? Ko da hakan shine abu na karshe da zaka aikta?" Wata zuciyar daga chan bayan kansa ta tunasar dashi "Toh ita kuma Amrah fa? Baku tunanin rayuwar ta sai Taku? Me take so menene zabin ta? Babu wanda ya damu sai kanku kuka sani?" Wata zuciyar ta sake haska mishi. Damke hannayen sa yayi a kirjinsa yana jin zafi Sosai, zafin yadda abubuwan suke kasancewa, me yasa abubuwan ke masa kwan gaba kwan baya ne? Ya riga ya gama gane wani abu guda daya, Mah-Mah ta zama selfish woman, babu abinda ta sani take tunani sai Safwan, ba kuma wai Kawai saboda Safwan din ne take masa abubuwa ba, ya lura kamar harda tsanar sa da tayi a yanzu da kuma rashin son ganin sa da bata yi kusa da ita ko Safwan, tana ganin kamar shine ke kara saka Safwan din a halin da yake ciki.    Sultan mutum ne me matukar zuciya Amma zai wuya kai tsaye ka gane hakan, ya iya danne zuciyar yabi ka a yadda kake so, musamman idan yana mugun ganin mutuncin ka. Dukkanin su basu taba ganin dayan side din sa ba wanda yayi matukar kokari wajen daidaita kansa , saboda inda ya samu kansa da kuma yadda suka karbe shi, shiyasa yayi ma kansa alkawarin zama a karkashin su da bin dukkanin umarnin su, indai be saba wa Mahaliccin sa ba. Sai dai anzo gabar da ya kamata shima a rayuwar sa ya nuna yasa me yake, ya kuma nuna yana da zuciya a kirjin sa. Kuma shima tsayayyen namiji ne. Allah da kansa ya halarta saki amma baya so. Saboda haka, da ba'a daura ba toh tabbas yayi niyyar barma Safwan, amma tunda haka ta faru ba zai zama me butulce ma Allah ba.   Taku daya yayi ya isa gaban gadon, kallon sa yayi kad'an sannan a hankali yace "I'm sorry Safwan, I'm so Sorry." Sai ya juya cikin wani irin taku da be san yana dashi ba, ya fice daga dakin, ya kuma bi ta hanyar da yasan akwai karancin mutane ya bi fice gaba d'aya daga gidan. ***A hankali ta d'aga idon ta, ta kalli matar da suke tare tsawon lokacin nan, ta kuma kalli kofar taga masu tsaron nasu sun dan matsa daga wajen saboda rana. Sai ta dan matsa k'adan jikin ta, ta tallafi kanta ta dora a saman kafarta, sosai take cikin wahala bata komai sai fitar da numfarfashi. "Zaki iya sanar dani dalilin da yasa kike cikin wajen nan?" Cikin muryar da kana ji kasan tana jin jiki tace "Zan iya, ko da hakan na nufin katsewar numfashi na." "Ina sauraron ki..." "Sunana Aminatu, ina daya daga cikin hadiman gidan nan a tun zamanin adalin sarki, Sarki Usman Muhammad Moddibo Saji." "Aminatu, Kece dama? Duk zaman nan da mukayi tare amma ban taba gane ki ba? Dama tsawon wannan lokacin kina cikin wajen nan, amma babu wanda ya sani?" "Ina nan tun ranar da abin nan ya faru, tun ranar ko hasken rana basu barni na sake gani ba, me yasa hakan ta faru dani? Me yasa suka kashe min rayuwa tah?" "Zaki iya bani labarin abinda ya faru?" "Eh zan iya." "Madallah." Tace tana gyara mata zaman kan nata. "Watanni goma sha takwas na dauka ina goyon ciki, cikin da aka saka min shi ba tare da izini na ba, saboda bani da galihu,bani da wanda zai ce dan me, nasha bakar wuya matuka, wanda sai da aka saka min sau uku yana zubewa sannan aka samu ya zauna. Tun ranar da na bar Masarautar ban kuma shigo ta ba, ina chan garin na Lagos inda muke zaune a wani babban gida ni da Yabi da masu yi mana aiki, sai masu duba lafiya ta mutum biyu nurses sai likitan da yake zuwa ko yaushe ya duba ni." "Cikin hukuncin Allah, na haihu lafiyw, na haifi yara maza biyu tagwaye, girma da lafiyar su ya bawa duk mutanen da muke tare dasu mamaki, sai dai bayan zuwan su duniya da mintunan da basu gaza talatin ba, suka dira a garin bisa umarnin maidakin sarki, su biyu ne, sai dai mutum daya na gane, Babbar amintacciyar baiwar Gimbiya, suna zuwa suka ce an umarce su ne da tafiya da yaran. Hankali na ya tashi,na hau kuka sosai ina rokon su da su bar min yaran duk kuwa da nasan dama za'a yi haka, tun kafin suzo duniya Gimbiya ta fad'a min abinda zai faru duk ranar da suka zo duniya. Sai dai ba abu bane me sauki raba ni da yaran, wanda ban taba sanin ina son su ba sai bayan da suka iso duniya, naji zan iya yin komai akan a bar min su. Na dinga rokon su akan dan Allah karsu tafi dasu, suka nuna min dole ne su tafi dasu saboda umarni ne da basu isa su ketare ba. Ina ji Ina gani suka tafi da yaran. Nayi kuka sosai har sai da naji kamar ido na zai fita daga gurbin sa. A k'asa na durkusa ina kuka sosai, sai na lura da alamun takalma a tsaye a gabana, na daga ido na da sauri. Yana tsaye a gabana, banji shigowar sa ba, ko dan halin da nake ciki ne? Ya karasa matsowa ya tsuguna a gabana yana bina da kallo "Kina kukan rabuwa da yaran ne?" Yace yana kallon cikin ido na, da sauri na daga masa kai ina jan numfashi "Tashi tsaye." Yace min yana matsawa baya. Tashi nayi ya mika min wani k'yalli "Share hawayen ki." Karba nayi na share sai dai basu daina zuba ba hawayen. Da hannu yayi wata alama sai gasu sun shigo, Maza ne manya majiya karfi, suka rissina a gaban sa. "Ku wuce da ita da kakarta, zan biyo bayanku." "Toh." Suka had'a baki sannan suka umarce ni akan na wuce muje, nabi su ina tunanin inda zasu kai ni, ciki muka fara komawa suka tisa mu a gaba ni da Yabi sai filin jirgi, karo na biyu da na sake dawowa tun bayan zuwa na garin. Bayan kamar awa d'aya jirgin mu ya d'aga.    Tun daga farkon hanyar da zata kaika Masarautar zuwa karshen ta, mutane ne suke ta tururuwar isa Masarautar wadda alamu suka nuna gagarumin abu ne yake faruwa a Masarautar. Hannun Yabi na kama da naji itama ashe rawa duk kuwa da mu a mota muke mutanen kuwa a k'asa suke. Muna zuwa kofar Masarautar muka ganta a rufe sai dai akwai tsaro sosai dan yadda wajen ya cika mutane na ta hayaniya. Lekawa wanda ke gaban motar mu yayi, suna ganin shi suka yi saurin bud'e kofar, motar ta kutsa kai cikin Masarautar. Bamu tsaya ko ina ba sai gaban fad'ar, fad'ar Maimartaba Sarki Usman Muhammad Moddibo Saji, sai muka ga ashe cikar da akayi a wajen ma kad'an ce akan ta ciki. "Ku fito." Yace mana bayan ya daidaita motar a waje daya, na sake kankame hannun Yabi dan yadda nake jin kamar zan fadi saboda jiri muka fito, duk sai hankalin mutane suka koma kanmu, kamar sun ga wani abun mamaki. Kai tsaye cikin fad'ar aka umarce mu da shiga. Daga nesa na hango wani kamar Maimartaba a k'asa kansa a duk'e,sai wadda ko tantama banayi Gimbiya ce a gefen sa, tana kuka sosai sai dai babu wanda ke kallon ma inda take. Kaina ya sake kwancewa ganin wani daban akan gararar Sarkin, wanin da ba kowa bane sai dan uwan Sarkin da duk wanda ya kwana ya tashi yasan yadda shakuwa me karfi ke tsakanin sa da Sarkin, dan babu yadda za'a yi Sarki yayi wani abu ba tare da sanin sa ba. Gefe muka samu muka rakube, karo na farko da muka samu kanmu a irin wannan wajen da ke ciki da manyan mutanen Masarautar wanda da tsakanin mu dasu sai dai hange daga nesa. "Masha Allah, gasu ma sun karaso." Wani da yake tsaye ta gefen Sabon sarkin yace, duk suka maida kallon su kanmu. "Taso." Wani ya bani umarni, ban iya tashi ba sai jan kafa da nayi na isa gaban su, na dukar na kai na saboda yadda kwarjinin su ya cika wajen. "Wannan itace yarinyar da sukayi amfani wajen cimma burin su,kuma itace ta haifi yaran nan guda biyu da suka dauko suka nuna wa kowa a matsayin yaran da gimbiya ta haifa, gata nan sai kuji daga bakin ta." Wani da ya kasance babba a cikin yan majalisar Sarki yace "Baiwar Allah muna son jin me ya faru." "Karki ji tsoron komai, kiyi bayani babu wanda zai miki komai anan." Wani ya dora akan abinda dayan yace. Ba tare da dogon tunani ba na shiga basu labarin komai, wanda sai bayan na sanar musu da komai sannan na fuskanci duk abinda yake faruwa, sannan na fuskanci gadar zare aka shirya ma Sarki da gimbiya. Bayan jin bayani na, mutane suka yi ta girgiza kai wanda ina kallon lokacin da Sarkin ya girgixa kansa yana jin kamar k'asa ta zage ya shige.    Sai dai ashe duk abin nan ba wai ainihin abinda ya faru bane, ba wai ainihin maganar da aka fara ba kenan, kawai sunyi amfani da magana ta ne wajen sake tabbatar da abinda suke son tabbatarwa dumbin al'ummar Masarautar Saji.    Mutane ne wanda a kalla zasu kai su goma aka bawa umarnin shigowa cikin fad'ar, dukkanin su kallo daya zakayi musu kasan suna cikin tashin hankali, na farko ne ya fara magana. "Tsawon shekara guda kenan da kashe min dan uwana, kuma ba kowa bane sai Maimartaba Sarki Usman." Da sauri Sarki Usman ya dago kansa, mamakin maganar mutumin da be taba gani ba ya shige shi, shi da tun da ya fara mulki be taba salwantar da ran ko da kiyashi bane, balle mutum sukutun da guda? Amma ba wannan ba ne zai baki mamaki, sai yadda dukkan mutanen nan suka kawo kwakkwarar hujjar da har yanzu ni kaina na k'asa gane yadda akayi hakan ta faru, idan dai zaka duba karfin hujjar da suka kawo ne to tabbas babu wanda ba zai bawa Maimartaba laifin ba, amma kuma anya zai aikata haka? Anya zai iya kashe mutum akan haihuwa? Ko da sun aikata min zalunci mafi muni duk akan haihuwar amma ban yarda da Maimartaba zai iya aikata hakan ba." "Menene Hujjar da suka yi Amfani da ita akan Maimartaba?" "Na farko an samu shaidar mutane kusan arba'in wanda daga ciki har da makusanta Maimartaba, sannan dukkanin gawarwakin mutanen an same su ne a wani dakin sirri na Maimartaba din, wanda babu wanda yake shiga wajen sai shi Sarkin shi kad'ai." "Hmm..."  Wadda ake bawa labarin taja doguwar ajiyar zuciya "Bayan nan me ya faru?" "Bayan nan komai ya kare, mutanen wannan Masarautar da kansu suka yi wa Sarki da Gimbiya korar kare, korar da ba'a taba yiwa ko da bawa bane irin sa balle Sarki, sai dai babu al'ummar da zasu kama Sarkin da ya kasance shugaba a gare su da wannan laifin su kyale ba." "Kina nufin tun ranar babu wanda ya sake jin labarin Sarkin da gimbiyar?" "Babu wanda ya sake ji?" "Toh amma ya akayi kika samu kanki anan? Ina jariran ya akayi dasu?" Kuka ta saka sosai ta kasa magana, tana tuna yadda komai ya kasance bayan ta basu yardar ta, ashe Amfani Kawai sukayi da ita don cimma manufar su. "Da kansa Sarki Usman ya dauki yaran ya damka su a hannu na, ya kuma umarce ni da na tafi, nayi nisa da kowa na fara sabuwar rayuwa. Ya kuma gargade ni da kar na kuskura na dawo komai runtsi. Nayi abinda yace na dauki yaran da Yabi da nufin barin Masarautar. A hanyar mu ta tafiya ne muka hadu da wani me suna Mahdi, ya tsaidamu sannan ya umarce mu da mu zo ya kaimu inda zamu zauna xuwa gobe saboda kar mu tafi yanzu dare yayi mana, muka yarda dashi ya kaimu wani gida. Cikin dare muna kwance naji kamar kakarin mutum, na tashi da sauri na haska yar karamar fitilar, Yabi na gani a kwance tana kakarin mutuwa, da sauri na yi kanta ina kiran sunanta, bata iya amsawa ba sai dai ta dauki hannu na ta saka wani abu a ciki, ta dan hasken na kalla sai naga zobe me me tsananin haske, muryar ta na fita da k'yar tace "Ki dauki yaran ku gudu, zasu kashe su." "Su waye zasu kashe su? Me mukayi musu?" Na hau tambayar ta ina kuka sosai ganin yadda cikin ta ke fidda jini. "Karki bata lokaci Aminatu, kiyi hakuri ba zan rayu ba, amma duk yadda zakiyi ki tabbatar yaran sun rayu, ki tabbatar sun kai lokacin da ya kamata su kai." Tashi nayi da sauri jin motsin an taba kofa, nayi kan yaran na dauke su na yi saurin neman hanyar da zan gudu, window na kalla naga tsawon ba zai yiwu na iya hawa ba, na dawo ciki ina kuka Ina tunanin yadda zanyi na tseratar da yaran ko da ni bazan rayu ba. Da sauri na shinfida mayafi na wanda ya kasance babba kuma me kauri na daure su a ciki na bar musu yar hanyar da zasu sha iska. Daga chan gefe na hangi wata igiya, ba tare da dogon nazari ba na jawo igiyar na daura ta a jikin mayafin nawa,sannan nayi wajen window na leka naga iya zurfin wajen, nayi addu'a sannan na zura su ta window Ina jan igiyar hankali na a tashe duk yadda ake buga kofar wadda sai a sannan na gane Yabi rufe kofar tayi. Kamar an rik'e igiyar haka naji, na kama tagar na leka,sai naga inuwar mutum a tsaye a wajen, ban iya tantance mace ko namiji ba a lokacin sai da ta juya don barin wajen da mugun sauri, ina kallo ta kwance igiyar daka jiki ta rungume su tsam a jikinta, sannan cikin dakikun da basu wuce uku ba ta bace wa gani na, a daidai lokacin suka balla kofar suka shigo, a kuma lokacin ne zoben dake hannu na ya subuce ya fad'i, naji karar faduwar sa nayi saurin durkushewa a wajen na hau lalubawa, 'bari daya hannu na ya samu nasarar dauka, na dunkule shi ina mamakin yadda akayi zoben ya rabe." "Tun daga ranar, na cinci kaina a cikin wannan wajen da ban taba saka ran fita ba, na rasa kakata a ranar, na rasa yarana." "Lallai kin fuskanci abubuwa masu yawan gaske, sai dai Ina miki albishir da kwanakin da suka rage miki anan kad'an ne." "Ta yaya zan fita daga gidan nan?" "Allah ne zai yi ikon sa akan Azzalumai." Rano [4/12, 11:04 PM] Maman Maryam: Hafsat Rano Page 27 ***Kasancewar Gate din a bud'e yake ya basu damar ganin duk shige da fitan dake faruwa tsakanin gidajen biyu, Afrah ce ta matsa mata akan lallai sai sun fito compound din sunyi hoto, suna tsaye suna hotunan ta hangi fitowar sa daga gidan nasu, hankalin ta, ta tattara gaba daya tana kallon sanda yayi wajen motar sa. Tana tsaye jikin kofar da zai shiga motar, ta zubo da attachment din dake kanta yazo fiye da rabin bayan ta, sai kuma ta daura dan siririn dankwali a saman gashin, riga da skirt ne a jikin ta sai dai zaka rantse da Allah fitted gown ce yadda suka bi suka tafi da tsarin jikinta, kamar dama chan tare da jikin nata a ka yi su. "Who's she?" Ta zunguri Afrah tana nuna mata Umaimah dake tsaye suna magana da Sultan din ta, duk da bata ji me suke cewa ba amma sai taji ranta ya sosu, ko dan ganin yanayin yarinyar, duk kuwa da zaman ta a k'asar turai amma zata iya banbance tsakanin me tarbiyya da mara shi. "Wace ita?" Ta sake tambayar Afrah "Wata lowclass girl ce, sanda muka zo da Abba itama tazo hutu gidan Mah-Mah, kamar ko niece din Mah-Mah ce a yadda naji, ta fiya jin kanta shiyasa ni sam bata min ba, sannan naga alamu da take taken ta, ya sultan take so." "Ok yayi." Ta amsa a dakile, gaba d'aya sai taji hoton ya fita kanta, ta kasa dauke ido daga kansu har sai da ta ga SULTAN din ya shiga mota ya tafi, ita kuma ta juya zuwa cikin gidan, fuskar ta dauke da murmushin da ta barwa Amrah tunanin murmushiin menene? "Karma ki bata lokacin ki akan irin wannan tsohuwar." "Ba zaki gane ba Afrah, irin su zasu iya yin komai domin samun abinda suke so." "Ya Sultan baya son ta, ba kuma zai taba son ta ba nasan, kalle ta fa kamar wata masara babu kyawun gani." "Ke kike ganin haka." "Comman, karki bata ranar ki da kanki da tunanin abinda ba me yiwu wa bane." "Naji...Mu koma ciki Toh." Ciki suka shiga still Afrah na cigaba da son ganin tayi convincing dinta ta kuma nuna mata dole sai ta yi shining idon ta, idan ta tsaya sanyi da salo salo sai dai taji anayi ba ita, dan yanzu mata akan namiji babu abinda ba zasu iya ba to win him over. ***Hannun sa daya na saman steering, daya kuma yana rik'e da wayar sa wadda yake kokarin kiran numbers din da yazo ya tarar da misscalls bayan barin wayar ta da yayi a mota ta kwana, jiya da ya dawo gidan be shiga da komai ba, abincin da ya tsaya yayi order ya dauka kawai shima kuma chacchakala kawai yayi ya rufe shi yayi kwanciyar sa. Bin kiran ya fara yi daya bayan daya wanda yawanci na abokan su ne sai yan asibiti. Yana gamawa dasu ya nemo number Amrah zai kira ta kiran mai gadin gidan Alhaji Safiyanu Madaki ya shigo, be daga ba sai da ta gama ringing sanñan yabi kiran. "Hello..." "Nine Sultan, na kikkiraka da layi na baka daga ba, idan ka samu lokaci kazo gida akwai maganar da nake so na fad'a maka." "Ina wani abu me muhimmanci ne, maganar ba zata yiwu a waya ba?" "Eh gaskiya." "Shikenan zanzo." Ya katse kiran be jira amsar sa ba, ya rasa me yasa kawai yake jin haushin Alhaji Safiyanu, ko dan tunanin da yake akansa na son Amfani dashi domin cimma manufar sa ne yasa hakan? Ko kuma dai akwai dalili? Ba zai dai taba bari yayi amfani dashi ba for his selfish interest.   Jujjuya wayar take a hannun ta, zuciyar ta duk babu dadi, a zaton ta zai dawo bayan tafiyar tasa jiya, ko da bazata tare ba ya kamata ya dawo ya ganta kafin ya kwanta, kuma ta kirashi sau biyu be daga ba be kuma biyo kiran ba, duk sai taji ta damu da hakan, har sai da damuwar ta nuna a cikin yanayin ta.     Wayar ce tayi kara, har ta dan tsorata dan bata yi zato ba, ta kalli sunan me kiran tana sake bata fuskar ta alamun tayi fushi kamar yana gabanta. Sai da ta kusa tsinkewa sannan ta d'aga muryar ta a chunkushe tace "Hello?" "Assalamu alaikum." "Wa alaikasalam, goodmorning." "Morning my wife, kin tashi lafiya?" "Lafiya Lou." "Ya naji ki haka haka? Are you ok?" "Umm." "Toh waye ya taba min ke? Umm? Tell me, adunanu ne ko afiruwa?" "You, you, you." "Ni kuma? Me nayi ni kuma? Bawan Allah." "Baka dawo jiya ba, na kira no answer, kuma baka kira back ba sai yanzu." "God! I'm so sorry kinji,wallahi jiyan nan ba zaki gane ba, anyway gani a kofar gida, kizo dakin Adnan sai muyi magana." "Ok." Tace tayi hanging kiran ta tashi da sauri, sabuwar atamfar dake jikin ta wadda akayi ma dinkin simple gown ta sake dubawa, tayi mata kyau sosai ta karbi kalar fatar ta, dan lip balm ta shafa ta sake fesa turare ta fito,a falo ta ga Amrah da sauran bakin da basu tafi ba taja hannun ta suka fito. "Rakani dan Allah." "Ina kuma?" "Ya Sultan ne yake dakin ya Adnan." Da sauri Afrah ta kwace hannun ta tana ja baya. "Wallahi ba zan je ba, an gaya miki wai ana raka mata ne wajen mijin ta, kiji ki da wani zance." "Haba Afrah, dan Allah ki rakani." "Kai you most be kidding me, yasin ban zuwa, zan iya kaiki bakin boarder dai, daga nan sai na yo kwana na barki ki karasa." "Bakin boarder kuma?" "Eh mana, iya kata bakin dakin." "Muje naji." Tace tana sake jan hannun ta. Suna zuwa kofar dakin Afrah ta warce hannun ta, ta yi tafiyar ta tana mata dariyar mugunta. A hankali ta tura kofar ta shiga kamar barauniya, ya na zauna a k'asan carpet ya kalmashe kafar sa dake sanye cikin bakar safa, hannun sa rik'e da cup yana shan tea suna magana da Adnan. "Bafa za'a maida min daki dandalin masoya ba ehe." Saurin sauke kanta k'asa tayi kunyar ya Adnan na sake kamata "Idan mutum yaji haushi yayi zuciya shima." "Haka kace? Karka manta yanzu matsayin yayanka nake." "Au auw, haka ne fa, sorry babban yaya, na tuba." "Yafi dai." Yace yana karasa sanya takalmin sa, yazo yayi hanyar fita yana cigaba da mita. Ajiye cup din yayi ya mike tsaye sannan ya bud'e hannayen sa. "Come please." Noke kafad'a tayi, ya sake cewa "Pleaseeeeee...." "Ba kai ne ba." "Are you still angry?" Yace yana matsawa inda take. "Ok I'm sorry, bazan kara ba, wani abu ne ya faru which bana son ma tunashi, ba wai na manta dake bane, kina makale a nan." Ya nuna saitin heart din sa. "Kin yafe min?" "Umm." "Oya give me a hug." Ya sake bud'e hannayen sa wider than before. Kunya take ji, ta k'asa motsawa tayi abinda yake so, ganin da gaske ba zata yi ba yasa kawai ya saka hannu ya jawo ta, yayi hugging nata kam kam yana shakar daddadan kamshin turaren ta da ya kusa tafiya dashi zuwa wani bigire na daban. "Knock knock..." Akayi knocking, janye wa tayi kad'an shi kuma ya amsa sallamar da Adnan yayi "Sorry to interrupt, Safwan ne yake neman ka,it seems like yana ta kiranka baka daga ba, ya damu sosai yanzu ma ya shiga gida, rashin ganin motar ka da beyi ba yasa be kawo kana nan ba, ni kuma ban fad'a masa kana nan din ba tunda bansan dalilin ka ba." "Nasan zai neme ni dama, shiyasa ma na ajiye motar a chan bayan layin." "Ok idan ka samu time ka kirashi." Ya juya ya fita. "Wani abu ne ya faru?" Ta tambaye shi tana kallon sa. Daga kafadar sa yayi "Babu komai fa." "Amma yake neman ka?" "Eh tun jiya bamu hadu ba, kinsan dole ya neme ni." "Owk." Tace tana jan bakin ta, tayi shiru dan taga alamar ba zai ce komai akai ba.    Mood din sa ne taga ya chanja, yayi shiru alamar tunani yake yi. Tunanin kuwa yake yadda zai yi avoiding Safwan idan har zai zo wajen Amrah kafin ya tafi, baya so su hadu yafi so ya fita daga rayuwar tasu kamar yadda Mah-Mah tayi masa umarni, amma besan ta ina zai fara ba. Mikewa yayi ya kama hannun ta ya rike cikin nasa. "Zan dawo da daddare, take care of your self, for me." Sai yayi kissing bayan hannun nata yayi murmushi "Wannan abun yayi miki kyau a hannu." Kallon hannun nata tayi, tayi murmushi kad'an, dayan hannun sa ya zura a aljihu ya ciro kud'i ya saka mata acikin tafin hannun ta "Ki yi amfani dashi idan kina bukata,you are now my responsibility bana so ki tambayi su Umma komai kinji?" "Nagode Allah ya kara budi." "Amin ya Allah, amin." [4/12, 11:04 PM] Maman Maryam: Hafsat Rano 28 ***Ciro wayar sa yayi ya kira, ganin an bud'e kofar gate din yasa ya fito ya rufe kofar ya nufi cikin gidan, gaisawa sukayi da Baba Maigadi ya wuce kai tsaye inda suka hadu ranar, kafin ya karasa isa sukayi kichibis dashi, "Laaa." "Kana lafiya Ameer?" "Lafiya Lou Wallahi." "Masha Allah, Alhaji na ciki?" "Eh bismillah." Yayi gaba ya bishi a baya. Su biyu ne a falon suna magana k'asa kasa, suna ganin shi suka mike tsaye, wanda suke taren ya kafe shi da ido babu ko kiftawa "Shigo mana Sultan." "Barka da rana." "Barka dai, kana lafiya?" "Lafiya Lou." Sai suka zauna a kusan tare "Me za'a kawo maka?" "Babu komai." "Ok, abinda yasa na kiraka,akan tafiyar nan ce, sun riga sun san da zuwan ka, saboda haka zamu chanja rana, ko alamis ko asabar, sannan tafiyar ka kai kad'ai ba zata yiwu ba, duba da baka da sani akan hanyoyin shiga Masarautar, saboda haka ga Musa, shine wanda zai jagorance ka a tafiyar." "Akwai wani abu bayan nan?" "Akwai, kurkuku me lamba 108 akwai mutane biyu masu matukar muhimmanci a tafiyar nan taka, ka tabbata ka samu ganin su,kayi magana dasu ko da na wssu mintuna ne." "Sai me?" "Shikenan ina tunanin, sauran abubuwan idan kaje chan zaka gane." "Alhamis zamu tafi, ka zama cikin shiri." "Na barku lafiya." Yana fita suna shigowa, mace ne da namiji, kallon su yayi çikin wani yanayi, sai kuma ya wuce su da sauri ya fice ganin yadda suma suke kallon sa. ***Mah-Mah bata taba tunanin Sultan zai yi kunnen uwar shegu da maganar ta ba, sai da taji shiru be ce komai ba, be kuma dawo gidan ba balle ta turke shi da maganar, duk da jikin Safwan din da sauki sai dai tasan dauriya kawai yake yana son nuna babu komai bayan ita kuma tasan ba haka bane.    Shiryawa tayi ta shiga gidan su Amrah ranar ta samu Umma ita kad'ai, Amrah na daki Afrah kuma taje gidan Hajiya. Bayan sun gaisa sukayi ma juna Allah sanya alkhairi da yadda al'umaran suka chanja lokaci daya. Bata nuna ma Umman komai ba, abinda taso taji akan Sultan ne amma sai taji Umman bata ce mata komai ba. Suna zaune sai ga Hajiya ta shigo, ranta a bace Afrah na biye da ita tana mata magana. Tashi Umma tayi da sauri tana mata sannu da zuwa ta amsa sannan ta amsawa Mah-Mah gaisuwar da take. "Kira min Amrah maza." Tace wa Afrah tana samun wajen zama. Tare suka dawo sai a lokacin Amrah ta gaida Mah-Mahn ta zauna a gefen Hajiyar tana tsokanar ta, sai dai ganin kamar ba a mood din wasan take yau ba yasa tasha jinin jikinta. "Maza kira Mijin ki yanzu yanzu, kice nace yazo ya dauke ki ku tafi, ba zai yiwu ba, a daura miki aure ki cigaba da zama a gida ba, ban yarda da wannan iskancin ba kuma ba za'a yi shi dani ba, kirashi maza." Sai ta juya wajen Ummah "Duk laifin ku ne da har kuka yarda,yaran yanzu masu shegen wayon tsiya, sai su auri yarinya su barta a gida sai sun samu abinda suke so sai suce sun saketa, anyi ba daya ba ba biyu ba, nan nan nan wata yarinyar makocin mu akayi mata wannan rashin albarkar, yanzu tana nan ya maida ita karamar bazawara yayi tafiyar sa k'asar waje." "Gaskiya be kyauta ba." "Amma Hajiya nace tunda ga ita Maman sultan din, sai kawai ta kirashi idan ya dawo gida ta fad'a masa yazo su tafi, ba wai a kirashi yanzu haka katsaham ba ko?" "Tace miki itace babar tashi, ko tace miki ta isa dashi ne? Nasan da ita a wajen ai, na ganta kuma amma ba haka nake so ayi ba, ke Amrah, kira shi maza ki bani wayar nan." "Na tura masa text message zai gani." Tace tana kumbura baki "Ba zaki kira shi ba kenan?" "Gashi ma yana kira." "Bani shi nan." "Haba Hajiya, haba Hajiya." "Rufe min baki ba dake ake magana ba uwar iya, ki tsaya auren naki yazo tukunna." "Salamu alaikum, kana ji, kazo yau ba sai gobe ba, ka tattara matar ka, ka tafi da ita, ba haka ake mu a garin mu ba., Yawwa toh." Ta sa hannu ta kashe kiran sannan ta ajiye wayar ta tashi. "Shi kuma idan ya dawo sai ki turo min shi." Tayi gaba suna mata Allah ya kiyaye bata bi ta kai ba tayi tafiyar ta tana sababi. "Sai ki tayata ku hada kayan." Umma tace tana sauke ajiyar zuciya "Amma da an bari Abban nasu ya dawo ko?" Mah-Mah tayi saurin fad'a "Babu abinda zai ce akan maganar mahaifiyar sa." "Toh ajira Sultan din, yazo tukunna, kila ma akwai abinda zai ce." "Gwara dai su shirya komai bana son abin magana." "Bari toh na koma, Allah ya sanya alkhairi ya basu zaman lafiya." "Amin ya Allah, angode sosai." Afrah ce ta taimaka ta had'a duk abinda tasan zata bukata waje d'aya, saman gado tayi hayewar ta, ta kwanta tana jin wani yanayi me kama da tsoro tsoro tun bayan da Hajiya ta kirashi, ya kuma yi mata text zai xo idan anyi sallar isha'i. Har akayi magriba ta kasa katubus, ba abu ne me sauki ba barin gida, ka bar iyayenka da yan uwanka ka tafi ka fara sabuwar rayuwa , rayuwar da baka san yadda zata zo maka ba sai ka shigeta, duk kuwa da yadda kaso ka hasaso ta ta wuce nan.    Kamar yadda yace ana idar ta sallar sai gashi, lokacin Abba ya dawo. Kai tsaye falon Abban ya wuce. Tare suka shigo da Umma ta samu gefe ta makale tana jin kamar ace mata k'et ta zura da gudu.    Nasiha me ratsa jiki Abba yayi musu, ya kuma tunasar dasu akan hakkokin kowannen su akan dayan su, ya kuma jaddada musu kalmar nan ta hakuri a zaman aure wanda Idan babu ita, da yawa yawan mutane da basu zauna lafiya ba, daga karshe ya karkare da yi musu addu'a da fatan samun kwanciyar hankali da zaman lafiya a gidan aurensu. Umma ma tayi nata fad'an daidai gwargwado. Kuka sosai Amrah take, kukan rabuwa da iyayenta, fita sultan yayi ya basu waje don su samu damar magana da ita sosai.    Yana tsaye a jikin mota ya jingina bayan sa yana kallon layin nasu da yayi tsit saboda tasowar hadari kasancewar lokaci ne na damuna. Jin an bud'e kofar yasa ya waiga, yana kallon yadda take tahowa hannun ta a cikin na Afrah kanta a lullube da mayafi.   Da sauri ya bud'e mata gidan gaba, ta saka kafarta bakin ta dauke da addu'a, "Sai da safe Ya Sulthan." "Sai da safe Afrah." Sai ta sunkuya daidai kunnen Amrah "Sai da safe." Bata sa ran xata amsa ba dama. Tana tsaye har suka fita daga layin, taji wasu hawaye sun biyo kunci ta,zata yi missing Amrah sosai. A hankali yake tukin, zuwa lokacin har an fara yayyafi kad'an kad'an, sanyin AC da sanyin garin suka hadu  suka cika ko ina, kankame jikinta tayi, ta lafe a jikin kofar motar. Hannun sa ya zuro cikin mayafin ta data dunkunkune kanta dashi ya kama hannayen ta yasa a cikin nasa ya cigaba da tukin sa hankalin na rarrabuwa. Parking yayi a gefen hanya ya fita da dan gudu ya shiga wani shop, be dad'e a ciki ba ya fito ya zo ya bude baya ya zuba kayan ya ja motar suka tafi.    Suna isa gida ya kashe motar, yana kallon ta, ta dan hasken da ya hasko cikin motar. "We are home." Yace yana smilling. Kama murfin motar tayi ta fito, ya zagayo da sauri ya rike hannun ta. "Kar ruwa ya jik'a min ke." "Bismillah." Suka nufi kofar shiga main gidan. Mukulli ya ciro ya bud'e sannan ya ja baya ya bata hanya. Da bismillah ta shiga ya biyo bayan ta bayan ya koma ya debo ledojin da yazo dasu. A takure ya sameta a kan kujera, ya ajiye kayan ya zauna a kusa da ita. "Kinga yadda abubuwan suka kasance ko? Ba da wani dalili nace ki zauna a gidan ba, sai dan abinda zan fuskanta bana son ina chan kuma ina tunanin halin da kike ciki, atlease idan kina gida zan samu peace of mind, Amma bansan hakan zai bata ran Hajiya ba." "Hajiya abu kad'an ke bata mata rai ai." "Tana da gaskia, kuma banga laifin ta akan abinda tayi ba, sai ma murna da nayi dan dama ina ta dana sanin zaman da nace ki yi, God I need my wife a kusa dani." "Umm." "Tàshi mu je muyi alwala, mu yi wa Allah godiya." Tashi tayi suka shiga bedroom, ita ta fara shiga tayi alwalar zuciyar ta na dukan uku uku ta fito, shima ya shiga yayi ya fito ya shinfida musu abin sallah, sukayi raka'a biyu sukayi addu'a sannan ya dafa kanta ya karanto addu'ar da tazo mana. Tashi yayi ya fita, sai gashi ya dawo da kayan da ya siyo. Ya ajiye sannan yazo ya kamata ya mikar da ita, ya janye mayafin da ta rufe jikinta dashi, ya ajiye a saman gadon. Ya jawo ta zuwa wajen da ya ajiye komai. Kasancewar dare ne gashi kuma lokaci yaja yasa suka dan ci komai kad'an, ta shiga tayi brush a lokacin ruwan da ake ya kara karfi sosai. Sanda ta fito baya dakin, kashe wutar tayi ta kwanta tana rufe idon ta. Shigowa yayi bayan ya sauya kayan sa zuwa kanana masu dan nauyi kad'an, ya hawo kadon yana kiran sunan ta. Shiru tayi masa sai yayi murmushi kawai dan yasan ba wai tayi bacci bane. Gefen ta ya samu ya kwanta yana sauke ajiyar zuciya da karfin. Matsawo yayi ya dawo daidai kusa da ita, yasa hannu ya juyota suna fuskantar juna, idon ta a rufe kam sai dai eyelashes dinta na ta rawa. "Wannan idanun sun karyata ki, bud'e kiga." A hankali ta dan bud'e idon kad'an, sai kuma tayi saurin rufe su ganin yadda ya matso so so so close to her. Kissing saman kanta yayi in a passionate way, ya daga kanta dake saman pillow ya dora shi akan damtsen hannun sa, Sannan ya ture dankwallin kanta, gashin ta me matukar sulbi ya bayyana, hannun sa ya tura ciki ya shiga zagayawa dashi yana sakar kamshin hadaddun shampoo da conditioner din da tayi amfani dasu. A hankali yayi mata magana a kunne ,maganar da ta saka ta dunkulewa waje d'aya ta shiga kankame jikin ta.    "Please say yes." Ya sake rada mata yana cigaba da zagaya hannun sa a saman soft skin dinta. "Please..." Ya sake k'asa sosai da voice dinsa. A hankali ta daga masa kanta hawaye na bin fuskar ta. "I love you so much." Sai ya kankame ta sosai yana jin kowanne lungu da sako na zuciyar sa na cikewa da tsantsar kaunar da yake mata. It's time da zai nuna mata yadda take a zuciyar sa. Goodnight 😗😴😴 ***Hasken wayar sa ne ya farkar dashi daga baccin da ya sake dauke su bayan sunyi sallar asubah, gefen sa ya kalla, ta makalkaleshi ta chusa kanta cikin jikin sa tana fitar da numfashi. Murmushi ne ya subce masa tuno abinda ya faru some hours da suka wuce. This is the best night ever a wajen sa. Alhamdulillah ya shiga jerawa dan shi ne kad'ai abi godia. ***Shiryawa yake tayi da sauri da sauri yana dubanta, cup din dake hannun ta take ta faman jujjuyawa ta kasa sha tun da ya fad'a mata tafiyar da zai yi bayan kawo ta da kwana daya tal, yasan dole zata damu, amma ba zai iya bari wannan damar ta wuce shi ba, yaji dadi da ya kira Abba yayi masa iya bayanin da zai fuskanta ya kuma amince xai turo mata Afrah, Hakan ya dan kwantar mishi da hankali.    Yana kama saka kayan yazo ya zauna yana jawo ta jikin shi, ya karbi cup din ya saka mata a baki. "Kiyi hakuri, kiyi min addu'a kinji, in Sha Allah babu abinda zai faru, ki kula da kanki idan kuna bukatar wani abu ki fad'a ma Adnan." "Kwana nawa zaka yi?" "Bansani ba Amrah, bansani ba,Amma zan yi kokari naga na dawo da wuri, for you." "Shikensn Allah ya bada sa'a ya dawo da kai lafiya." "Amin matata." Da hak ya samu ta dan saki jikin ta, ya sake taimaka mata ta sake gasa jikinta sosai ya bata pain reliever sannan yace ta kwanta kafin Afrah tazo. Sai da ta rakashi har gate, yana daga mata hannu tana daga masa ya fice daga gidan. Ciki ta koma tayi kuka sosai har sai da kanta ya soma ciwo. *** Alhamdulillah, ina yiwa kowa fatan shiga Watan Ramadan lafiya, Allah ya sadamu da duk Alkhairan dake ciki, ya bamu ikon sauke nauyin ibadar yasa muga Daren lailatul Khadr yasa muna cikin bayin da za'a yanta. Sai Allah ya kaimu Bayan Sallah da rai da lafiya. Ayi ibadah lafiya[5/20, 9:05 AM] Maman Maryam: Hafsat Rano 28 ***Ciro wayar sa yayi ya kira, ganin an bud'e kofar gate din yasa ya fito ya rufe kofar ya nufi cikin gidan, gaisawa sukayi da Baba Maigadi ya wuce kai tsaye inda suka hadu ranar, kafin ya karasa isa sukayi kichibis dashi, "Laaa." "Kana lafiya Ameer?" "Lafiya Lou Wallahi." "Masha Allah, Alhaji na ciki?" "Eh bismillah." Yayi gaba ya bishi a baya. Su biyu ne a falon suna magana k'asa kasa, suna ganin shi suka mike tsaye, wanda suke taren ya kafe shi da ido babu ko kiftawa "Shigo mana Sultan." "Barka da rana." "Barka dai, kana lafiya?" "Lafiya Lou." Sai suka zauna a kusan tare "Me za'a kawo maka?" "Babu komai." "Ok, abinda yasa na kiraka,akan tafiyar nan ce, sun riga sun san da zuwan ka, saboda haka zamu chanja rana, ko alamis ko asabar, sannan tafiyar ka kai kad'ai ba zata yiwu ba, duba da baka da sani akan hanyoyin shiga Masarautar, saboda haka ga Musa, shine wanda zai jagorance ka a tafiyar." "Akwai wani abu bayan nan?" "Akwai, kurkuku me lamba 108 akwai mutane biyu masu matukar muhimmanci a tafiyar nan taka, ka tabbata ka samu ganin su,kayi magana dasu ko da na wssu mintuna ne." "Sai me?" "Shikenan ina tunanin, sauran abubuwan idan kaje chan zaka gane." "Alhamis zamu tafi, ka zama cikin shiri." "Na barku lafiya." Yana fita suna shigowa, mace ne da namiji, kallon su yayi çikin wani yanayi, sai kuma ya wuce su da sauri ya fice ganin yadda suma suke kallon sa. ***Mah-Mah bata taba tunanin Sultan zai yi kunnen uwar shegu da maganar ta ba, sai da taji shiru be ce komai ba, be kuma dawo gidan ba balle ta turke shi da maganar, duk da jikin Safwan din da sauki sai dai tasan dauriya kawai yake yana son nuna babu komai bayan ita kuma tasan ba haka bane.    Shiryawa tayi ta shiga gidan su Amrah ranar ta samu Umma ita kad'ai, Amrah na daki Afrah kuma taje gidan Hajiya. Bayan sun gaisa sukayi ma juna Allah sanya alkhairi da yadda al'umaran suka chanja lokaci daya. Bata nuna ma Umman komai ba, abinda taso taji akan Sultan ne amma sai taji Umman bata ce mata komai ba. Suna zaune sai ga Hajiya ta shigo, ranta a bace Afrah na biye da ita tana mata magana. Tashi Umma tayi da sauri tana mata sannu da zuwa ta amsa sannan ta amsawa Mah-Mah gaisuwar da take. "Kira min Amrah maza." Tace wa Afrah tana samun wajen zama. Tare suka dawo sai a lokacin Amrah ta gaida Mah-Mahn ta zauna a gefen Hajiyar tana tsokanar ta, sai dai ganin kamar ba a mood din wasan take yau ba yasa tasha jinin jikinta. "Maza kira Mijin ki yanzu yanzu, kice nace yazo ya dauke ki ku tafi, ba zai yiwu ba, a daura miki aure ki cigaba da zama a gida ba, ban yarda da wannan iskancin ba kuma ba za'a yi shi dani ba, kirashi maza." Sai ta juya wajen Ummah "Duk laifin ku ne da har kuka yarda,yaran yanzu masu shegen wayon tsiya, sai su auri yarinya su barta a gida sai sun samu abinda suke so sai suce sun saketa, anyi ba daya ba ba biyu ba, nan nan nan wata yarinyar makocin mu akayi mata wannan rashin albarkar, yanzu tana nan ya maida ita karamar bazawara yayi tafiyar sa k'asar waje." "Gaskiya be kyauta ba." "Amma Hajiya nace tunda ga ita Maman sultan din, sai kawai ta kirashi idan ya dawo gida ta fad'a masa yazo su tafi, ba wai a kirashi yanzu haka katsaham ba ko?" "Tace miki itace babar tashi, ko tace miki ta isa dashi ne? Nasan da ita a wajen ai, na ganta kuma amma ba haka nake so ayi ba, ke Amrah, kira shi maza ki bani wayar nan." "Na tura masa text message zai gani." Tace tana kumbura baki "Ba zaki kira shi ba kenan?" "Gashi ma yana kira." "Bani shi nan." "Haba Hajiya, haba Hajiya." "Rufe min baki ba dake ake magana ba uwar iya, ki tsaya auren naki yazo tukunna." "Salamu alaikum, kana ji, kazo yau ba sai gobe ba, ka tattara matar ka, ka tafi da ita, ba haka ake mu a garin mu ba., Yawwa toh." Ta sa hannu ta kashe kiran sannan ta ajiye wayar ta tashi. "Shi kuma idan ya dawo sai ki turo min shi." Tayi gaba suna mata Allah ya kiyaye bata bi ta kai ba tayi tafiyar ta tana sababi. "Sai ki tayata ku hada kayan." Umma tace tana sauke ajiyar zuciya "Amma da an bari Abban nasu ya dawo ko?" Mah-Mah tayi saurin fad'a "Babu abinda zai ce akan maganar mahaifiyar sa." "Toh ajira Sultan din, yazo tukunna, kila ma akwai abinda zai ce." "Gwara dai su shirya komai bana son abin magana." "Bari toh na koma, Allah ya sanya alkhairi ya basu zaman lafiya." "Amin ya Allah, angode sosai." Afrah ce ta taimaka ta had'a duk abinda tasan zata bukata waje d'aya, saman gado tayi hayewar ta, ta kwanta tana jin wani yanayi me kama da tsoro tsoro tun bayan da Hajiya ta kirashi, ya kuma yi mata text zai xo idan anyi sallar isha'i. Har akayi magriba ta kasa katubus, ba abu ne me sauki ba barin gida, ka bar iyayenka da yan uwanka ka tafi ka fara sabuwar rayuwa , rayuwar da baka san yadda zata zo maka ba sai ka shigeta, duk kuwa da yadda kaso ka hasaso ta ta wuce nan.    Kamar yadda yace ana idar ta sallar sai gashi, lokacin Abba ya dawo. Kai tsaye falon Abban ya wuce. Tare suka shigo da Umma ta samu gefe ta makale tana jin kamar ace mata k'et ta zura da gudu.    Nasiha me ratsa jiki Abba yayi musu, ya kuma tunasar dasu akan hakkokin kowannen su akan dayan su, ya kuma jaddada musu kalmar nan ta hakuri a zaman aure wanda Idan babu ita, da yawa yawan mutane da basu zauna lafiya ba, daga karshe ya karkare da yi musu addu'a da fatan samun kwanciyar hankali da zaman lafiya a gidan aurensu. Umma ma tayi nata fad'an daidai gwargwado. Kuka sosai Amrah take, kukan rabuwa da iyayenta, fita sultan yayi ya basu waje don su samu damar magana da ita sosai.    Yana tsaye a jikin mota ya jingina bayan sa yana kallon layin nasu da yayi tsit saboda tasowar hadari kasancewar lokaci ne na damuna. Jin an bud'e kofar yasa ya waiga, yana kallon yadda take tahowa hannun ta a cikin na Afrah kanta a lullube da mayafi.   Da sauri ya bud'e mata gidan gaba, ta saka kafarta bakin ta dauke da addu'a, "Sai da safe Ya Sulthan." "Sai da safe Afrah." Sai ta sunkuya daidai kunnen Amrah "Sai da safe." Bata sa ran xata amsa ba dama. Tana tsaye har suka fita daga layin, taji wasu hawaye sun biyo kunci ta,zata yi missing Amrah sosai. A hankali yake tukin, zuwa lokacin har an fara yayyafi kad'an kad'an, sanyin AC da sanyin garin suka hadu  suka cika ko ina, kankame jikinta tayi, ta lafe a jikin kofar motar. Hannun sa ya zuro cikin mayafin ta data dunkunkune kanta dashi ya kama hannayen ta yasa a cikin nasa ya cigaba da tukin sa hankalin na rarrabuwa. Parking yayi a gefen hanya ya fita da dan gudu ya shiga wani shop, be dad'e a ciki ba ya fito ya zo ya bude baya ya zuba kayan ya ja motar suka tafi.    Suna isa gida ya kashe motar, yana kallon ta, ta dan hasken da ya hasko cikin motar. "We are home." Yace yana smilling. Kama murfin motar tayi ta fito, ya zagayo da sauri ya rike hannun ta. "Kar ruwa ya jik'a min ke." "Bismillah." Suka nufi kofar shiga main gidan. Mukulli ya ciro ya bud'e sannan ya ja baya ya bata hanya. Da bismillah ta shiga ya biyo bayan ta bayan ya koma ya debo ledojin da yazo dasu. A takure ya sameta a kan kujera, ya ajiye kayan ya zauna a kusa da ita. "Kinga yadda abubuwan suka kasance ko? Ba da wani dalili nace ki zauna a gidan ba, sai dan abinda zan fuskanta bana son ina chan kuma ina tunanin halin da kike ciki, atlease idan kina gida zan samu peace of mind, Amma bansan hakan zai bata ran Hajiya ba." "Hajiya abu kad'an ke bata mata rai ai." "Tana da gaskia, kuma banga laifin ta akan abinda tayi ba, sai ma murna da nayi dan dama ina ta dana sanin zaman da nace ki yi, God I need my wife a kusa dani." "Umm." "Tàshi mu je muyi alwala, mu yi wa Allah godiya." Tashi tayi suka shiga bedroom, ita ta fara shiga tayi alwalar zuciyar ta na dukan uku uku ta fito, shima ya shiga yayi ya fito ya shinfida musu abin sallah, sukayi raka'a biyu sukayi addu'a sannan ya dafa kanta ya karanto addu'ar da tazo mana. Tashi yayi ya fita, sai gashi ya dawo da kayan da ya siyo. Ya ajiye sannan yazo ya kamata ya mikar da ita, ya janye mayafin da ta rufe jikinta dashi, ya ajiye a saman gadon. Ya jawo ta zuwa wajen da ya ajiye komai. Kasancewar dare ne gashi kuma lokaci yaja yasa suka dan ci komai kad'an, ta shiga tayi brush a lokacin ruwan da ake ya kara karfi sosai. Sanda ta fito baya dakin, kashe wutar tayi ta kwanta tana rufe idon ta. Shigowa yayi bayan ya sauya kayan sa zuwa kanana masu dan nauyi kad'an, ya hawo kadon yana kiran sunan ta. Shiru tayi masa sai yayi murmushi kawai dan yasan ba wai tayi bacci bane. Gefen ta ya samu ya kwanta yana sauke ajiyar zuciya da karfin. Matsawo yayi ya dawo daidai kusa da ita, yasa hannu ya juyota suna fuskantar juna, idon ta a rufe kam sai dai eyelashes dinta na ta rawa. "Wannan idanun sun karyata ki, bud'e kiga." A hankali ta dan bud'e idon kad'an, sai kuma tayi saurin rufe su ganin yadda ya matso so so so close to her. Kissing saman kanta yayi in a passionate way, ya daga kanta dake saman pillow ya dora shi akan damtsen hannun sa, Sannan ya ture dankwallin kanta, gashin ta me matukar sulbi ya bayyana, hannun sa ya tura ciki ya shiga zagayawa dashi yana sakar kamshin hadaddun shampoo da conditioner din da tayi amfani dasu. A hankali yayi mata magana a kunne ,maganar da ta saka ta dunkulewa waje d'aya ta shiga kankame jikin ta.    "Please say yes." Ya sake rada mata yana cigaba da zagaya hannun sa a saman soft skin dinta. "Please..." Ya sake k'asa sosai da voice dinsa. A hankali ta daga masa kanta hawaye na bin fuskar ta. "I love you so much." Sai ya kankame ta sosai yana jin kowanne lungu da sako na zuciyar sa na cikewa da tsantsar kaunar da yake mata. It's time da zai nuna mata yadda take a zuciyar sa. Goodnight 😗😴😴 ***Hasken wayar sa ne ya farkar dashi daga baccin da ya sake dauke su bayan sunyi sallar asubah, gefen sa ya kalla, ta makalkaleshi ta chusa kanta cikin jikin sa tana fitar da numfashi. Murmushi ne ya subce masa tuno abinda ya faru some hours da suka wuce. This is the best night ever a wajen sa. Alhamdulillah ya shiga jerawa dan shi ne kad'ai abi godia. ***Shiryawa yake tayi da sauri da sauri yana dubanta, cup din dake hannun ta take ta faman jujjuyawa ta kasa sha tun da ya fad'a mata tafiyar da zai yi bayan kawo ta da kwana daya tal, yasan dole zata damu, amma ba zai iya bari wannan damar ta wuce shi ba, yaji dadi da ya kira Abba yayi masa iya bayanin da zai fuskanta ya kuma amince xai turo mata Afrah, Hakan ya dan kwantar mishi da hankali.    Yana kama saka kayan yazo ya zauna yana jawo ta jikin shi, ya karbi cup din ya saka mata a baki. "Kiyi hakuri, kiyi min addu'a kinji, in Sha Allah babu abinda zai faru, ki kula da kanki idan kuna bukatar wani abu ki fad'a ma Adnan." "Kwana nawa zaka yi?" "Bansani ba Amrah, bansani ba,Amma zan yi kokari naga na dawo da wuri, for you." "Shikensn Allah ya bada sa'a ya dawo da kai lafiya." "Amin matata." Da hak ya samu ta dan saki jikin ta, ya sake taimaka mata ta sake gasa jikinta sosai ya bata pain reliever sannan yace ta kwanta kafin Afrah tazo. Sai da ta rakashi har gate, yana daga mata hannu tana daga masa ya fice daga gidan. Ciki ta koma tayi kuka sosai har sai da kanta ya soma ciwo. *** Alhamdulillah, ina yiwa kowa fatan shiga Watan Ramadan lafiya, Allah ya sadamu da duk Alkhairan dake ciki, ya bamu ikon sauke nauyin ibadar yasa muga Daren lailatul Khadr yasa muna cikin bayin da za'a yanta. Sai Allah ya kaimu Bayan Sallah da rai da lafiya. Ayi ibadah lafiya [5/20, 9:05 AM] Maman Maryam: Abinda Ke Cikin Zuciya Page 29 *Barka da sallah* ***Knocking ake sosai ta mike da k'yar cikin yanayin bacci me karfi ta nufi kofar, tun bayan tafiyar sa baccin ya dauke ta anan saman kujera, gajiya ce sosai a tattare da ita ga wani azababben ciwon kai dake damun ta plus gajiyar da oga kwata kwatan ya had'a mata jiya. Da k'yar ta isa gate din cikin dashashiyar murya tace "Waye?" "Ai nazata ko bin sa kikayi,wannan bugun da nayi tayi..." Da sauri ta zare lock din tana jin dadi, tayi saurin rungume ta kankam. "Bacci ya dauke ni wallahi." "Baccin gajiya ko?" Afrah tace tana kashe mata ido daya, duka ta kai mata sannan ta mika hannu "Kinji da gulmar ki, bani jakar kayan naki dallah." "Yawwa kamar kin san na gaji." Ta fad'a tana sakar mata jakar, ciki suka juya da nufin shiga suna cigaba da hirar su kamar ba jiya jiya suka rabo ba, suna haura balcony din aka buga kofar gidan da karfin gaske, kallon juna sukayi a tare "Kina da baki ne?" "A'ah..." Sake bugawa akayi, ta ajiye jakar ta nufin kofar tana tambayar waye, ba'a yi magana ba sai cigaba da bugun da akayi, tayi saurin isa ta sake cire lock din, ta dan bud'e kofar kad'an ta yadda ba za'a ganta daga waje ba tace "Waye?" "Bako ne, maigidan yananan?" "Baya nan." "Toh... Ko dai ba address din bane, ko ba gidan Dr Sultan bane?" Yace cike da tantama "Nan ne, amma baya nan." "Toh Toh... Madallah, idan ya dawo kyace masa nazo." "Toh wa za'a ce masa?" Shiru be amsa ba, ta sake tambaya shiru, sai ta dan leka kanta wajen kad'an sai taga ashe ma ya tafi, rufe kofar tayi tana komawa ciki dan tuni Afrah ta shige. "Wai waye naji kin dad'e." "Wani ne, bansan waye ba wai Sultan yazo nema." "Ko sune na gansu a kofar gida suka bini da kallo, har ma na dan ji na tsargu domin yanayin su be min ba, kamar marasa gaskia wallahi." "Toh..." "Idan kunyi waya ki tambaye shi ko akwai bakon da yake expecting, dan yadda k'asar nan tamu ta lalace, gashi kiwon mutum ake ba dabba ba." "Malama karki tsorata ni,babu abinda zai faru, tsarguwa kawai kikayi dallah." "Toh Allah yasa." Tace tana dariya ganin yadda Amrah ta nuna alamun tsoro, sai ta kauda maganar suka shiga wata amma k'asan zuciyar ta sai taji ta kasa aminta da mutanen da ta gani dazun, addu'a tayi kawai ba tare da ta sake daga maganar ba dan yadda Amrah ta nuna ta tsorata karta kara tsoratata. Ganin azahar ta tawo yasa suka shiga kitchen a tare, suka girka noodles suka ci a kitchen din sannan suka dawo falon suka cigaba da kallo suna hira, lokaci lokaci Amrah na kiran wayar Sultan amma switch off, da ta ga haka sai ta dinga tura masa message duk sanda ta kira tasan idan ya kunna dole zai gane. Addu'a ta bishi da shi suka cigaba da hira da Afrah Amma k'asan zuciyar ta babu dadi tana tunani da fatan Allah ya tsare shi ya kaishi lafiya ya kuma bashi nasara a abinda ya saka a gaba. ***Daga nesa ya hange shi tsaye ya na d'an dube dube, ya tsaida me napep din ya biya shi sannan ya fito yana gyara zaman jakar dake rataye a kafadar sa ya nufi inda yake. Tun kafin ya karasa ya ganshi yayi saurin tawowa suka hadu a hanya. Kallon tsanaki Sultan yayi masa kad'an sannan ya mika masa hannu suka gaisa yana karantar yanayin sa cike da nazarin abubuwa da dama a tattare dashi, na farko yanayin shigar sa sai kuma yanayin da fuskar sa take ciki wadda ta sake saka sultan din cikin wani yanayi na tunani. "Muje ko?" Yace bayan ya dan kalli agogo samfurin apple dake hannun sa.  Har ya fara tafiya sai ya tsaya "Musa ko? "Eh Musa ranka ya dad'e." Jinjina kansa yayi kad'an "Kai ne jagoran tafiyar bani ba, kai ya kamata ka shiga gaba." "Haka ne, bismillah." Yace yana nufar wata bakar mota, dakatawa Sultan yayi da bin sa yace "Bana tunanin zuwan mu a motar gida zai taimakawa abinda zamu je yi." "Tabbas ba zai taimaka ba, dama iya kar mararrabar zamu idan yaso sai mu karasa daga chan." Jinjina kai yayi kad'an sannan ya bi shi ya shiga motar,shi kuma yaja suka tafi. Tafiya ce me matukar nisa wanda tun sultan na duba dukkannin bayanan daya tatatara har ya hakura ya dangana da kallon hanyar yana sake lafewa a jikin motar da babu abinda yake tashi a cikin ta sai karar na'urar sanyaya waje. La'asar sakaliya suka isa inda musan yace, ya gangara gefen wata yar karamar hanya zuwa wani madaidaicin gida wanda ya zama kamar shi kad'ai ne a wajen. Shi dai Sultan be ce komai ba yana bin komai da ido. "Yallaabai ina dan zuwa dan Allah." Da ka ya amsa masa ya fita da sauri ya shiga gidan, jim kad'an suka fito da wasu mutane su uku, suna magana har suka karaso wajen motar, ganin haka yasa SULTAN bude kofar ya fito. "Barka da zuwa." Suka fad'a a tare har suna dan russunawa. "Ranka ya dad'e wannan shine zamu bashi ajiyar motar, wadannan kuma su zasu dauke mu har Masarautar Saji Idan Allah ya yarda." "Allah ya kaimu lafiya." Kawai yace Babura ne guda biyu, Sultan ya hau daya Musa ma ya hau daya suka dauki hanyar Masarautar Saji. Gabannin magriba suka isa, sai dai yadda harabar Babbar Masarautar ke cike da wasu irin manyan fitulu masu hasken gaske yasa wajen ya zama kamar rana, daga chan gefe suka sauke su, sannan suka nufi wata hanya daban suka bar Sultan da Musa a tsaye. Da ido Sultan ya shiga bin Babbar Masarautar wadda take da fadin kasa sosai ga wasu manya manyan bishiyu masu kyau da suka kara kawata wajen, girman ta ya kai girman wani garin, gidaje ne daga kowanne bangare nata wanda ya kasance an musu ado da irin adon da ake ma gidan sarauta. Tun kafin su karaso Masarautar ya lura da yadda tsari da kyau da Allah ya bawa garin na Saji,babban birni ne cikin manyan birane wanda kai tsaye zaka kirashi da lamba daya indai akan kyau da tsari ne. Hankalin sa ne ya dawo kan masu tsaron Masarautar wanda a kalla sun ta samma su talatin kowannen su babu annuri a fuskar sa, zagaye suke kawai kamar mayunwatan zaki masu farautar neman abinda zasu ce, amma idan akayi la'akari da dalilin da yasa aka sake bazasu a wajen zaka san cewa dole ne su jajirce dan kuskure daya zasuyi komai ya lalace. "Karka yi magana duk abinda zasu ce kayi shiru, mun riga mun tsara komai." Musa ya rada masa a kunne sannan yayi gaba shi kuma Sultan ya bishi suka nufi Babbar kofar da zata sada ka da cikin Masarautar. Kamar mutum mutumi haka Sultan ya shiga binsa yana jin kamar jinin jikinsa na tsittsinkewa yana bin hanyar da ba ita aka tanada masa domin bi ba, wani irin sakayau yake jin sa, irin abinda be taba ji ba sai sau biyu, na farko a asibiti watarana da MD ya kirashi, sai kuma a Canada. Sai kuma yau da yake jin kamar ma har wani sanyi sanyi yake ji na ratsa shi, ko kuma ace a dauko kankara a dora masa a jiki a kuma zo a rufe ta da babban mayafi. Har suka karasa inda zasu din be iya sake fahimtar komai ba, yana jin sanda Musa yake magana da wani dake chan gefe shi kad'ai, sai kuma yaga ya taso sun sake bin sa har zuwa wajen wasu su uku suma, sannan suka je wajen wasu, anan suka dan bata lokaci sai kawai yaga an bud'e musu kofar ance su shiga, kallon Musa yayi yaga baya kallon sa sai ma saka kansa da yayi suka shiga takawa cikin Masarautar wanda yake jin duk wani takun da zai yana amsawa a dukkan gabobin sa. Tafiya suka shiga yi da dan sauri duk da haka be bari abu daya na daga Masarautar ya tsere masa ba, ya bi komai yadda ya kamata ya kuma karance wani abu kad'an daga cikin yadda mutanen Masarautar suke al'amuran su, wanda kallo daya zakayi musu ka gane basu da maraba da bayi, wanda tsantsar wahala da rashin walwala yayi ma katutu. A wata kofar katako suka tsaya, wani da Sultan ya lura da yanayin yadda yake abubuwan da sauri sauri yayi saurin bud'e musu, suka kutsa kai ciki sannan yaja kofar ya rufe yana sauke nauyayyar ajiyar zuciya kana ya bar wajen bayan ya tabbatar da babu wanda ya gansu. ***Hannun sa a goye a bayan sa yana kaiwa da komowa tsakanin dakin, daga chan gefe wasu ne a durkushe kansu a k'asa , dakin yayi shiru dukkanin su suna jiran suji abinda Sarkin zai ce, tsawon lokaci be ce komai ba sai dan siririn tsaki da yake ta ja a hankali a hankali. Sun cire rai da zai ce wani abu sai kuma ya koma da baya ya hau kan karagar sa, sannan yace cikin kaushin murya. "Idan har abinda muke tunani zai shigo cikin Masarautar nan a gobe, ya zama dole mu tabbatar da zuwan sa hannu, duk da bamu da Ikon ganin ko menene ko waye, sai dai jikina na bani wani gagarumin abu ne ke tunkaro mu, dan haka ba zamuyi kasa a guiwa ba wajen ganin mun kare martabar abinda muka dad'e kafin mu same shi, ya zama dole ne, kowa a cikin ku ya zama a shirye shiri bana wasa ba, dan bamu san wanne shiri sukayi a kanmu ba." "An gama ranka ya dad'e." Suka had'a baki wajen fad'a, wani daga ciki ya duka kad'an sannan yace "A duban da nayi dazu, sai naga abun na kusa damu sosai, kusan da nake jin tsoron kar mu sakankance su shammace mu, ina ganin ya kamata a sake dubawa." Babban yayi karaf da sauri yace "Kana nufin abinda na gani akan zuwan nasu gobe ba daidai bane? Ko kana nufin bansan aikin da nake ba ne?" Ya karashe a dan hasale. "Ba ina nufin hakan bane, sai dai..." "Ya isa!" Sarki ya dakatar dasu "Yanzu ba lokacin musu bane ko nuna wani yafi wani, lokaci ne na aiki babba, aikin da yafi wanda kukayi a baya, ruwan kune ku bar komai ya lalace." "Tuba muke ranka ya dad'e." Fuu ya tashi ya shige ciki ya barsu zaune, a hankali duk suka fice daya bayan daya cikin shigar su ta kowanne lokaci idan zasu zo ziyarar sarkin. ***Karewa dakin kallo Sulthan yayi, babu komai sai wata tabarma daga gefe, sai tarin wasu kaya daga dayan bangaren dakin, sai dai akwai bandaki karami a manne a ciki, da sauri ya sauke jakar sa, ya nufi kofar bayan ya tabbatar da hasashen shi, alwala ya dauro saboda ya samu yayi sallar data tsere masa, yana fitowa musa ma ya a shiga yayi alwalar shima, sultan ya jasu suka rama sallolin da suka tsere musu sannan suka yi Isha'i wadda ake yi a daidai lokacin. Pad din sa ya ciro ya bud'e yana duba sakonnin da Amrah ta turo masa akan ta kira shi a kashe dan kashe ta yayi gaaba daya, murmushi yayi me kyau sannan ya tura mata reply,few lines masu ma'ana, kafin tayi reply ya maida wayar flight mood saboda baya son ta kira shi ta masa tambayar da bashi da amsar ta shima. Suna nan zaune wanda ya rako su ya sake shigowa, ya ajiye musu kwanon abinci guda biyu kowa a gaban sa,ya rissina sosai wajen bawa Sultan wanda har yaso ya bawa Sultan din mamakin yadda suke girmamashi duk da be san dalili ba, be ma kuma san me Madaki da wannan amintaccen yaron nasa Musa suke shirya wa akansa ba, ya riga dai ya gama shirin sa shima lokaci yake jira ya aiwatar da komai amma kafin nan zai cigaba da bin su a yadda suka yi nasu tsarin. ****** Assalamu alaikum Barkanmu da Sallah ya iyali? Masu complain na ki dawowa kuyi hakuri, abubuwa ne suka sha min kai plus bana gari. Hankali na gaba daya yana kan rubutun nan tunda duk abinda ka fara burin ka kawai ka gama shi ka sauke nauyi. Nayi typing da yawa yana Wattpad sai dai ntwrk sam ya hanani logging, complain din da naji ne ciki hadda maganganu marasa dad'i yasa na rubuta wannan din yanzu. Nagode [5/20, 9:05 AM] Maman Maryam: ©️®️ Hafsat Rano Page 26 Wannan littafin na kudi ne, AMANA CE, duk wanda yayi mana sharing dinsa shi da ALLAH! Idan kina/Kana so ki/ka karanta ki/ka tuntubi numbobin nan* *0903 234 5899* Or *09033181070 ***Da sauri ya dago, yana son ganin ainihin gaskiyar abinda tace din,be yi tunanin abinda zata ce kenan ba. Sosai ya shiga shock har ya rasa me ma zai ce "Mah-Mah?" "Abinda nake so kayi kenan, a matsayin rama alkhairi da alkhairi, a matsayin tukwuicin abinda mukayi maka, idan kayi wannan bani da sauran komai a kanka." Juyawa tayi da nufin barin dakin, sai kuma ta tsaya ta juyo "Karka manta, kayi alkawarin zaka yi ko menene." Ta karashe sannan ta fice daga dakin. Bin inda tabi ta fita yayi yana ganin kamar be ji daidai ba, kamar ba abinda Mah-Mah take son fad'a ba kenan, kamar ma ba ainihin Mah-Mah da ya sani bace ba, an chanja ta ne da wata daban ko kuma anyi brainwashing dinta ne.    "Zan iya? Zan iya?" Ya shiga tambayar kansa, sai kuma ya girgixa kai "No...Ba zan iya ba, aure ba wasan yara bane, aure abu ne me girma da be kamata ayi irin wannan wasan dashi ba." Ya bawa kansa amsa a fili yana girgiza kansa. "Amma Safwan fa? Be chanchanci komai ba a wajenka? Ko da hakan shine abu na karshe da zaka aikta?" Wata zuciyar daga chan bayan kansa ta tunasar dashi "Toh ita kuma Amrah fa? Baku tunanin rayuwar ta sai Taku? Me take so menene zabin ta? Babu wanda ya damu sai kanku kuka sani?" Wata zuciyar ta sake haska mishi. Damke hannayen sa yayi a kirjinsa yana jin zafi Sosai, zafin yadda abubuwan suke kasancewa, me yasa abubuwan ke masa kwan gaba kwan baya ne? Ya riga ya gama gane wani abu guda daya, Mah-Mah ta zama selfish woman, babu abinda ta sani take tunani sai Safwan, ba kuma wai Kawai saboda Safwan din ne take masa abubuwa ba, ya lura kamar harda tsanar sa da tayi a yanzu da kuma rashin son ganin sa da bata yi kusa da ita ko Safwan, tana ganin kamar shine ke kara saka Safwan din a halin da yake ciki.    Sultan mutum ne me matukar zuciya Amma zai wuya kai tsaye ka gane hakan, ya iya danne zuciyar yabi ka a yadda kake so, musamman idan yana mugun ganin mutuncin ka. Dukkanin su basu taba ganin dayan side din sa ba wanda yayi matukar kokari wajen daidaita kansa , saboda inda ya samu kansa da kuma yadda suka karbe shi, shiyasa yayi ma kansa alkawarin zama a karkashin su da bin dukkanin umarnin su, indai be saba wa Mahaliccin sa ba. Sai dai anzo gabar da ya kamata shima a rayuwar sa ya nuna yasa me yake, ya kuma nuna yana da zuciya a kirjin sa. Kuma shima tsayayyen namiji ne. Allah da kansa ya halarta saki amma baya so. Saboda haka, da ba'a daura ba toh tabbas yayi niyyar barma Safwan, amma tunda haka ta faru ba zai zama me butulce ma Allah ba.   Taku daya yayi ya isa gaban gadon, kallon sa yayi kad'an sannan a hankali yace "I'm sorry Safwan, I'm so Sorry." Sai ya juya cikin wani irin taku da be san yana dashi ba, ya fice daga dakin, ya kuma bi ta hanyar da yasan akwai karancin mutane ya bi fice gaba d'aya daga gidan. ***A hankali ta d'aga idon ta, ta kalli matar da suke tare tsawon lokacin nan, ta kuma kalli kofar taga masu tsaron nasu sun dan matsa daga wajen saboda rana. Sai ta dan matsa k'adan jikin ta, ta tallafi kanta ta dora a saman kafarta, sosai take cikin wahala bata komai sai fitar da numfarfashi. "Zaki iya sanar dani dalilin da yasa kike cikin wajen nan?" Cikin muryar da kana ji kasan tana jin jiki tace "Zan iya, ko da hakan na nufin katsewar numfashi na." "Ina sauraron ki..." "Sunana Aminatu, ina daya daga cikin hadiman gidan nan a tun zamanin adalin sarki, Sarki Usman Muhammad Moddibo Saji." "Aminatu, Kece dama? Duk zaman nan da mukayi tare amma ban taba gane ki ba? Dama tsawon wannan lokacin kina cikin wajen nan, amma babu wanda ya sani?" "Ina nan tun ranar da abin nan ya faru, tun ranar ko hasken rana basu barni na sake gani ba, me yasa hakan ta faru dani? Me yasa suka kashe min rayuwa tah?" "Zaki iya bani labarin abinda ya faru?" "Eh zan iya." "Madallah." Tace tana gyara mata zaman kan nata. "Watanni goma sha takwas na dauka ina goyon ciki, cikin da aka saka min shi ba tare da izini na ba, saboda bani da galihu,bani da wanda zai ce dan me, nasha bakar wuya matuka, wanda sai da aka saka min sau uku yana zubewa sannan aka samu ya zauna. Tun ranar da na bar Masarautar ban kuma shigo ta ba, ina chan garin na Lagos inda muke zaune a wani babban gida ni da Yabi da masu yi mana aiki, sai masu duba lafiya ta mutum biyu nurses sai likitan da yake zuwa ko yaushe ya duba ni." "Cikin hukuncin Allah, na haihu lafiyw, na haifi yara maza biyu tagwaye, girma da lafiyar su ya bawa duk mutanen da muke tare dasu mamaki, sai dai bayan zuwan su duniya da mintunan da basu gaza talatin ba, suka dira a garin bisa umarnin maidakin sarki, su biyu ne, sai dai mutum daya na gane, Babbar amintacciyar baiwar Gimbiya, suna zuwa suka ce an umarce su ne da tafiya da yaran. Hankali na ya tashi,na hau kuka sosai ina rokon su da su bar min yaran duk kuwa da nasan dama za'a yi haka, tun kafin suzo duniya Gimbiya ta fad'a min abinda zai faru duk ranar da suka zo duniya. Sai dai ba abu bane me sauki raba ni da yaran, wanda ban taba sanin ina son su ba sai bayan da suka iso duniya, naji zan iya yin komai akan a bar min su. Na dinga rokon su akan dan Allah karsu tafi dasu, suka nuna min dole ne su tafi dasu saboda umarni ne da basu isa su ketare ba. Ina ji Ina gani suka tafi da yaran. Nayi kuka sosai har sai da naji kamar ido na zai fita daga gurbin sa. A k'asa na durkusa ina kuka sosai, sai na lura da alamun takalma a tsaye a gabana, na daga ido na da sauri. Yana tsaye a gabana, banji shigowar sa ba, ko dan halin da nake ciki ne? Ya karasa matsowa ya tsuguna a gabana yana bina da kallo "Kina kukan rabuwa da yaran ne?" Yace yana kallon cikin ido na, da sauri na daga masa kai ina jan numfashi "Tashi tsaye." Yace min yana matsawa baya. Tashi nayi ya mika min wani k'yalli "Share hawayen ki." Karba nayi na share sai dai basu daina zuba ba hawayen. Da hannu yayi wata alama sai gasu sun shigo, Maza ne manya majiya karfi, suka rissina a gaban sa. "Ku wuce da ita da kakarta, zan biyo bayanku." "Toh." Suka had'a baki sannan suka umarce ni akan na wuce muje, nabi su ina tunanin inda zasu kai ni, ciki muka fara komawa suka tisa mu a gaba ni da Yabi sai filin jirgi, karo na biyu da na sake dawowa tun bayan zuwa na garin. Bayan kamar awa d'aya jirgin mu ya d'aga.    Tun daga farkon hanyar da zata kaika Masarautar zuwa karshen ta, mutane ne suke ta tururuwar isa Masarautar wadda alamu suka nuna gagarumin abu ne yake faruwa a Masarautar. Hannun Yabi na kama da naji itama ashe rawa duk kuwa da mu a mota muke mutanen kuwa a k'asa suke. Muna zuwa kofar Masarautar muka ganta a rufe sai dai akwai tsaro sosai dan yadda wajen ya cika mutane na ta hayaniya. Lekawa wanda ke gaban motar mu yayi, suna ganin shi suka yi saurin bud'e kofar, motar ta kutsa kai cikin Masarautar. Bamu tsaya ko ina ba sai gaban fad'ar, fad'ar Maimartaba Sarki Usman Muhammad Moddibo Saji, sai muka ga ashe cikar da akayi a wajen ma kad'an ce akan ta ciki. "Ku fito." Yace mana bayan ya daidaita motar a waje daya, na sake kankame hannun Yabi dan yadda nake jin kamar zan fadi saboda jiri muka fito, duk sai hankalin mutane suka koma kanmu, kamar sun ga wani abun mamaki. Kai tsaye cikin fad'ar aka umarce mu da shiga. Daga nesa na hango wani kamar Maimartaba a k'asa kansa a duk'e,sai wadda ko tantama banayi Gimbiya ce a gefen sa, tana kuka sosai sai dai babu wanda ke kallon ma inda take. Kaina ya sake kwancewa ganin wani daban akan gararar Sarkin, wanin da ba kowa bane sai dan uwan Sarkin da duk wanda ya kwana ya tashi yasan yadda shakuwa me karfi ke tsakanin sa da Sarkin, dan babu yadda za'a yi Sarki yayi wani abu ba tare da sanin sa ba. Gefe muka samu muka rakube, karo na farko da muka samu kanmu a irin wannan wajen da ke ciki da manyan mutanen Masarautar wanda da tsakanin mu dasu sai dai hange daga nesa. "Masha Allah, gasu ma sun karaso." Wani da yake tsaye ta gefen Sabon sarkin yace, duk suka maida kallon su kanmu. "Taso." Wani ya bani umarni, ban iya tashi ba sai jan kafa da nayi na isa gaban su, na dukar na kai na saboda yadda kwarjinin su ya cika wajen. "Wannan itace yarinyar da sukayi amfani wajen cimma burin su,kuma itace ta haifi yaran nan guda biyu da suka dauko suka nuna wa kowa a matsayin yaran da gimbiya ta haifa, gata nan sai kuji daga bakin ta." Wani da ya kasance babba a cikin yan majalisar Sarki yace "Baiwar Allah muna son jin me ya faru." "Karki ji tsoron komai, kiyi bayani babu wanda zai miki komai anan." Wani ya dora akan abinda dayan yace. Ba tare da dogon tunani ba na shiga basu labarin komai, wanda sai bayan na sanar musu da komai sannan na fuskanci duk abinda yake faruwa, sannan na fuskanci gadar zare aka shirya ma Sarki da gimbiya. Bayan jin bayani na, mutane suka yi ta girgiza kai wanda ina kallon lokacin da Sarkin ya girgixa kansa yana jin kamar k'asa ta zage ya shige.    Sai dai ashe duk abin nan ba wai ainihin abinda ya faru bane, ba wai ainihin maganar da aka fara ba kenan, kawai sunyi amfani da magana ta ne wajen sake tabbatar da abinda suke son tabbatarwa dumbin al'ummar Masarautar Saji.    Mutane ne wanda a kalla zasu kai su goma aka bawa umarnin shigowa cikin fad'ar, dukkanin su kallo daya zakayi musu kasan suna cikin tashin hankali, na farko ne ya fara magana. "Tsawon shekara guda kenan da kashe min dan uwana, kuma ba kowa bane sai Maimartaba Sarki Usman." Da sauri Sarki Usman ya dago kansa, mamakin maganar mutumin da be taba gani ba ya shige shi, shi da tun da ya fara mulki be taba salwantar da ran ko da kiyashi bane, balle mutum sukutun da guda? Amma ba wannan ba ne zai baki mamaki, sai yadda dukkan mutanen nan suka kawo kwakkwarar hujjar da har yanzu ni kaina na k'asa gane yadda akayi hakan ta faru, idan dai zaka duba karfin hujjar da suka kawo ne to tabbas babu wanda ba zai bawa Maimartaba laifin ba, amma kuma anya zai aikata haka? Anya zai iya kashe mutum akan haihuwa? Ko da sun aikata min zalunci mafi muni duk akan haihuwar amma ban yarda da Maimartaba zai iya aikata hakan ba." "Menene Hujjar da suka yi Amfani da ita akan Maimartaba?" "Na farko an samu shaidar mutane kusan arba'in wanda daga ciki har da makusanta Maimartaba, sannan dukkanin gawarwakin mutanen an same su ne a wani dakin sirri na Maimartaba din, wanda babu wanda yake shiga wajen sai shi Sarkin shi kad'ai." "Hmm..."  Wadda ake bawa labarin taja doguwar ajiyar zuciya "Bayan nan me ya faru?" "Bayan nan komai ya kare, mutanen wannan Masarautar da kansu suka yi wa Sarki da Gimbiya korar kare, korar da ba'a taba yiwa ko da bawa bane irin sa balle Sarki, sai dai babu al'ummar da zasu kama Sarkin da ya kasance shugaba a gare su da wannan laifin su kyale ba." "Kina nufin tun ranar babu wanda ya sake jin labarin Sarkin da gimbiyar?" "Babu wanda ya sake ji?" "Toh amma ya akayi kika samu kanki anan? Ina jariran ya akayi dasu?" Kuka ta saka sosai ta kasa magana, tana tuna yadda komai ya kasance bayan ta basu yardar ta, ashe Amfani Kawai sukayi da ita don cimma manufar su. "Da kansa Sarki Usman ya dauki yaran ya damka su a hannu na, ya kuma umarce ni da na tafi, nayi nisa da kowa na fara sabuwar rayuwa. Ya kuma gargade ni da kar na kuskura na dawo komai runtsi. Nayi abinda yace na dauki yaran da Yabi da nufin barin Masarautar. A hanyar mu ta tafiya ne muka hadu da wani me suna Mahdi, ya tsaidamu sannan ya umarce mu da mu zo ya kaimu inda zamu zauna xuwa gobe saboda kar mu tafi yanzu dare yayi mana, muka yarda dashi ya kaimu wani gida. Cikin dare muna kwance naji kamar kakarin mutum, na tashi da sauri na haska yar karamar fitilar, Yabi na gani a kwance tana kakarin mutuwa, da sauri na yi kanta ina kiran sunanta, bata iya amsawa ba sai dai ta dauki hannu na ta saka wani abu a ciki, ta dan hasken na kalla sai naga zobe me me tsananin haske, muryar ta na fita da k'yar tace "Ki dauki yaran ku gudu, zasu kashe su." "Su waye zasu kashe su? Me mukayi musu?" Na hau tambayar ta ina kuka sosai ganin yadda cikin ta ke fidda jini. "Karki bata lokaci Aminatu, kiyi hakuri ba zan rayu ba, amma duk yadda zakiyi ki tabbatar yaran sun rayu, ki tabbatar sun kai lokacin da ya kamata su kai." Tashi nayi da sauri jin motsin an taba kofa, nayi kan yaran na dauke su na yi saurin neman hanyar da zan gudu, window na kalla naga tsawon ba zai yiwu na iya hawa ba, na dawo ciki ina kuka Ina tunanin yadda zanyi na tseratar da yaran ko da ni bazan rayu ba. Da sauri na shinfida mayafi na wanda ya kasance babba kuma me kauri na daure su a ciki na bar musu yar hanyar da zasu sha iska. Daga chan gefe na hangi wata igiya, ba tare da dogon nazari ba na jawo igiyar na daura ta a jikin mayafin nawa,sannan nayi wajen window na leka naga iya zurfin wajen, nayi addu'a sannan na zura su ta window Ina jan igiyar hankali na a tashe duk yadda ake buga kofar wadda sai a sannan na gane Yabi rufe kofar tayi. Kamar an rik'e igiyar haka naji, na kama tagar na leka,sai naga inuwar mutum a tsaye a wajen, ban iya tantance mace ko namiji ba a lokacin sai da ta juya don barin wajen da mugun sauri, ina kallo ta kwance igiyar daka jiki ta rungume su tsam a jikinta, sannan cikin dakikun da basu wuce uku ba ta bace wa gani na, a daidai lokacin suka balla kofar suka shigo, a kuma lokacin ne zoben dake hannu na ya subuce ya fad'i, naji karar faduwar sa nayi saurin durkushewa a wajen na hau lalubawa, 'bari daya hannu na ya samu nasarar dauka, na dunkule shi ina mamakin yadda akayi zoben ya rabe." "Tun daga ranar, na cinci kaina a cikin wannan wajen da ban taba saka ran fita ba, na rasa kakata a ranar, na rasa yarana." "Lallai kin fuskanci abubuwa masu yawan gaske, sai dai Ina miki albishir da kwanakin da suka rage miki anan kad'an ne." "Ta yaya zan fita daga gidan nan?" "Allah ne zai yi ikon sa akan Azzalumai." Rano [5/20, 9:05 AM] Maman Maryam: Hafsat Rano Page 27 ***Kasancewar Gate din a bud'e yake ya basu damar ganin duk shige da fitan dake faruwa tsakanin gidajen biyu, Afrah ce ta matsa mata akan lallai sai sun fito compound din sunyi hoto, suna tsaye suna hotunan ta hangi fitowar sa daga gidan nasu, hankalin ta, ta tattara gaba daya tana kallon sanda yayi wajen motar sa. Tana tsaye jikin kofar da zai shiga motar, ta zubo da attachment din dake kanta yazo fiye da rabin bayan ta, sai kuma ta daura dan siririn dankwali a saman gashin, riga da skirt ne a jikin ta sai dai zaka rantse da Allah fitted gown ce yadda suka bi suka tafi da tsarin jikinta, kamar dama chan tare da jikin nata a ka yi su. "Who's she?" Ta zunguri Afrah tana nuna mata Umaimah dake tsaye suna magana da Sultan din ta, duk da bata ji me suke cewa ba amma sai taji ranta ya sosu, ko dan ganin yanayin yarinyar, duk kuwa da zaman ta a k'asar turai amma zata iya banbance tsakanin me tarbiyya da mara shi. "Wace ita?" Ta sake tambayar Afrah "Wata lowclass girl ce, sanda muka zo da Abba itama tazo hutu gidan Mah-Mah, kamar ko niece din Mah-Mah ce a yadda naji, ta fiya jin kanta shiyasa ni sam bata min ba, sannan naga alamu da take taken ta, ya sultan take so." "Ok yayi." Ta amsa a dakile, gaba d'aya sai taji hoton ya fita kanta, ta kasa dauke ido daga kansu har sai da ta ga SULTAN din ya shiga mota ya tafi, ita kuma ta juya zuwa cikin gidan, fuskar ta dauke da murmushin da ta barwa Amrah tunanin murmushiin menene? "Karma ki bata lokacin ki akan irin wannan tsohuwar." "Ba zaki gane ba Afrah, irin su zasu iya yin komai domin samun abinda suke so." "Ya Sultan baya son ta, ba kuma zai taba son ta ba nasan, kalle ta fa kamar wata masara babu kyawun gani." "Ke kike ganin haka." "Comman, karki bata ranar ki da kanki da tunanin abinda ba me yiwu wa bane." "Naji...Mu koma ciki Toh." Ciki suka shiga still Afrah na cigaba da son ganin tayi convincing dinta ta kuma nuna mata dole sai ta yi shining idon ta, idan ta tsaya sanyi da salo salo sai dai taji anayi ba ita, dan yanzu mata akan namiji babu abinda ba zasu iya ba to win him over. ***Hannun sa daya na saman steering, daya kuma yana rik'e da wayar sa wadda yake kokarin kiran numbers din da yazo ya tarar da misscalls bayan barin wayar ta da yayi a mota ta kwana, jiya da ya dawo gidan be shiga da komai ba, abincin da ya tsaya yayi order ya dauka kawai shima kuma chacchakala kawai yayi ya rufe shi yayi kwanciyar sa. Bin kiran ya fara yi daya bayan daya wanda yawanci na abokan su ne sai yan asibiti. Yana gamawa dasu ya nemo number Amrah zai kira ta kiran mai gadin gidan Alhaji Safiyanu Madaki ya shigo, be daga ba sai da ta gama ringing sanñan yabi kiran. "Hello..." "Nine Sultan, na kikkiraka da layi na baka daga ba, idan ka samu lokaci kazo gida akwai maganar da nake so na fad'a maka." "Ina wani abu me muhimmanci ne, maganar ba zata yiwu a waya ba?" "Eh gaskiya." "Shikenan zanzo." Ya katse kiran be jira amsar sa ba, ya rasa me yasa kawai yake jin haushin Alhaji Safiyanu, ko dan tunanin da yake akansa na son Amfani dashi domin cimma manufar sa ne yasa hakan? Ko kuma dai akwai dalili? Ba zai dai taba bari yayi amfani dashi ba for his selfish interest.   Jujjuya wayar take a hannun ta, zuciyar ta duk babu dadi, a zaton ta zai dawo bayan tafiyar tasa jiya, ko da bazata tare ba ya kamata ya dawo ya ganta kafin ya kwanta, kuma ta kirashi sau biyu be daga ba be kuma biyo kiran ba, duk sai taji ta damu da hakan, har sai da damuwar ta nuna a cikin yanayin ta.     Wayar ce tayi kara, har ta dan tsorata dan bata yi zato ba, ta kalli sunan me kiran tana sake bata fuskar ta alamun tayi fushi kamar yana gabanta. Sai da ta kusa tsinkewa sannan ta d'aga muryar ta a chunkushe tace "Hello?" "Assalamu alaikum." "Wa alaikasalam, goodmorning." "Morning my wife, kin tashi lafiya?" "Lafiya Lou." "Ya naji ki haka haka? Are you ok?" "Umm." "Toh waye ya taba min ke? Umm? Tell me, adunanu ne ko afiruwa?" "You, you, you." "Ni kuma? Me nayi ni kuma? Bawan Allah." "Baka dawo jiya ba, na kira no answer, kuma baka kira back ba sai yanzu." "God! I'm so sorry kinji,wallahi jiyan nan ba zaki gane ba, anyway gani a kofar gida, kizo dakin Adnan sai muyi magana." "Ok." Tace tayi hanging kiran ta tashi da sauri, sabuwar atamfar dake jikin ta wadda akayi ma dinkin simple gown ta sake dubawa, tayi mata kyau sosai ta karbi kalar fatar ta, dan lip balm ta shafa ta sake fesa turare ta fito,a falo ta ga Amrah da sauran bakin da basu tafi ba taja hannun ta suka fito. "Rakani dan Allah." "Ina kuma?" "Ya Sultan ne yake dakin ya Adnan." Da sauri Afrah ta kwace hannun ta tana ja baya. "Wallahi ba zan je ba, an gaya miki wai ana raka mata ne wajen mijin ta, kiji ki da wani zance." "Haba Afrah, dan Allah ki rakani." "Kai you most be kidding me, yasin ban zuwa, zan iya kaiki bakin boarder dai, daga nan sai na yo kwana na barki ki karasa." "Bakin boarder kuma?" "Eh mana, iya kata bakin dakin." "Muje naji." Tace tana sake jan hannun ta. Suna zuwa kofar dakin Afrah ta warce hannun ta, ta yi tafiyar ta tana mata dariyar mugunta. A hankali ta tura kofar ta shiga kamar barauniya, ya na zauna a k'asan carpet ya kalmashe kafar sa dake sanye cikin bakar safa, hannun sa rik'e da cup yana shan tea suna magana da Adnan. "Bafa za'a maida min daki dandalin masoya ba ehe." Saurin sauke kanta k'asa tayi kunyar ya Adnan na sake kamata "Idan mutum yaji haushi yayi zuciya shima." "Haka kace? Karka manta yanzu matsayin yayanka nake." "Au auw, haka ne fa, sorry babban yaya, na tuba." "Yafi dai." Yace yana karasa sanya takalmin sa, yazo yayi hanyar fita yana cigaba da mita. Ajiye cup din yayi ya mike tsaye sannan ya bud'e hannayen sa. "Come please." Noke kafad'a tayi, ya sake cewa "Pleaseeeeee...." "Ba kai ne ba." "Are you still angry?" Yace yana matsawa inda take. "Ok I'm sorry, bazan kara ba, wani abu ne ya faru which bana son ma tunashi, ba wai na manta dake bane, kina makale a nan." Ya nuna saitin heart din sa. "Kin yafe min?" "Umm." "Oya give me a hug." Ya sake bud'e hannayen sa wider than before. Kunya take ji, ta k'asa motsawa tayi abinda yake so, ganin da gaske ba zata yi ba yasa kawai ya saka hannu ya jawo ta, yayi hugging nata kam kam yana shakar daddadan kamshin turaren ta da ya kusa tafiya dashi zuwa wani bigire na daban. "Knock knock..." Akayi knocking, janye wa tayi kad'an shi kuma ya amsa sallamar da Adnan yayi "Sorry to interrupt, Safwan ne yake neman ka,it seems like yana ta kiranka baka daga ba, ya damu sosai yanzu ma ya shiga gida, rashin ganin motar ka da beyi ba yasa be kawo kana nan ba, ni kuma ban fad'a masa kana nan din ba tunda bansan dalilin ka ba." "Nasan zai neme ni dama, shiyasa ma na ajiye motar a chan bayan layin." "Ok idan ka samu time ka kirashi." Ya juya ya fita. "Wani abu ne ya faru?" Ta tambaye shi tana kallon sa. Daga kafadar sa yayi "Babu komai fa." "Amma yake neman ka?" "Eh tun jiya bamu hadu ba, kinsan dole ya neme ni." "Owk." Tace tana jan bakin ta, tayi shiru dan taga alamar ba zai ce komai akai ba.    Mood din sa ne taga ya chanja, yayi shiru alamar tunani yake yi. Tunanin kuwa yake yadda zai yi avoiding Safwan idan har zai zo wajen Amrah kafin ya tafi, baya so su hadu yafi so ya fita daga rayuwar tasu kamar yadda Mah-Mah tayi masa umarni, amma besan ta ina zai fara ba. Mikewa yayi ya kama hannun ta ya rike cikin nasa. "Zan dawo da daddare, take care of your self, for me." Sai yayi kissing bayan hannun nata yayi murmushi "Wannan abun yayi miki kyau a hannu." Kallon hannun nata tayi, tayi murmushi kad'an, dayan hannun sa ya zura a aljihu ya ciro kud'i ya saka mata acikin tafin hannun ta "Ki yi amfani dashi idan kina bukata,you are now my responsibility bana so ki tambayi su Umma komai kinji?" "Nagode Allah ya kara budi." "Amin ya Allah, amin."Abinda Ke Cikin Zuciya Page 29 *Barka da sallah* ***Knocking ake sosai ta mike da k'yar cikin yanayin bacci me karfi ta nufi kofar, tun bayan tafiyar sa baccin ya dauke ta anan saman kujera, gajiya ce sosai a tattare da ita ga wani azababben ciwon kai dake damun ta plus gajiyar da oga kwata kwatan ya had'a mata jiya. Da k'yar ta isa gate din cikin dashashiyar murya tace "Waye?" "Ai nazata ko bin sa kikayi,wannan bugun da nayi tayi..." Da sauri ta zare lock din tana jin dadi, tayi saurin rungume ta kankam. "Bacci ya dauke ni wallahi." "Baccin gajiya ko?" Afrah tace tana kashe mata ido daya, duka ta kai mata sannan ta mika hannu "Kinji da gulmar ki, bani jakar kayan naki dallah." "Yawwa kamar kin san na gaji." Ta fad'a tana sakar mata jakar, ciki suka juya da nufin shiga suna cigaba da hirar su kamar ba jiya jiya suka rabo ba, suna haura balcony din aka buga kofar gidan da karfin gaske, kallon juna sukayi a tare "Kina da baki ne?" "A'ah..." Sake bugawa akayi, ta ajiye jakar ta nufin kofar tana tambayar waye, ba'a yi magana ba sai cigaba da bugun da akayi, tayi saurin isa ta sake cire lock din, ta dan bud'e kofar kad'an ta yadda ba za'a ganta daga waje ba tace "Waye?" "Bako ne, maigidan yananan?" "Baya nan." "Toh... Ko dai ba address din bane, ko ba gidan Dr Sultan bane?" Yace cike da tantama "Nan ne, amma baya nan." "Toh Toh... Madallah, idan ya dawo kyace masa nazo." "Toh wa za'a ce masa?" Shiru be amsa ba, ta sake tambaya shiru, sai ta dan leka kanta wajen kad'an sai taga ashe ma ya tafi, rufe kofar tayi tana komawa ciki dan tuni Afrah ta shige. "Wai waye naji kin dad'e." "Wani ne, bansan waye ba wai Sultan yazo nema." "Ko sune na gansu a kofar gida suka bini da kallo, har ma na dan ji na tsargu domin yanayin su be min ba, kamar marasa gaskia wallahi." "Toh..." "Idan kunyi waya ki tambaye shi ko akwai bakon da yake expecting, dan yadda k'asar nan tamu ta lalace, gashi kiwon mutum ake ba dabba ba." "Malama karki tsorata ni,babu abinda zai faru, tsarguwa kawai kikayi dallah." "Toh Allah yasa." Tace tana dariya ganin yadda Amrah ta nuna alamun tsoro, sai ta kauda maganar suka shiga wata amma k'asan zuciyar ta sai taji ta kasa aminta da mutanen da ta gani dazun, addu'a tayi kawai ba tare da ta sake daga maganar ba dan yadda Amrah ta nuna ta tsorata karta kara tsoratata. Ganin azahar ta tawo yasa suka shiga kitchen a tare, suka girka noodles suka ci a kitchen din sannan suka dawo falon suka cigaba da kallo suna hira, lokaci lokaci Amrah na kiran wayar Sultan amma switch off, da ta ga haka sai ta dinga tura masa message duk sanda ta kira tasan idan ya kunna dole zai gane. Addu'a ta bishi da shi suka cigaba da hira da Afrah Amma k'asan zuciyar ta babu dadi tana tunani da fatan Allah ya tsare shi ya kaishi lafiya ya kuma bashi nasara a abinda ya saka a gaba. ***Daga nesa ya hange shi tsaye ya na d'an dube dube, ya tsaida me napep din ya biya shi sannan ya fito yana gyara zaman jakar dake rataye a kafadar sa ya nufi inda yake. Tun kafin ya karasa ya ganshi yayi saurin tawowa suka hadu a hanya. Kallon tsanaki Sultan yayi masa kad'an sannan ya mika masa hannu suka gaisa yana karantar yanayin sa cike da nazarin abubuwa da dama a tattare dashi, na farko yanayin shigar sa sai kuma yanayin da fuskar sa take ciki wadda ta sake saka sultan din cikin wani yanayi na tunani. "Muje ko?" Yace bayan ya dan kalli agogo samfurin apple dake hannun sa.  Har ya fara tafiya sai ya tsaya "Musa ko? "Eh Musa ranka ya dad'e." Jinjina kansa yayi kad'an "Kai ne jagoran tafiyar bani ba, kai ya kamata ka shiga gaba." "Haka ne, bismillah." Yace yana nufar wata bakar mota, dakatawa Sultan yayi da bin sa yace "Bana tunanin zuwan mu a motar gida zai taimakawa abinda zamu je yi." "Tabbas ba zai taimaka ba, dama iya kar mararrabar zamu idan yaso sai mu karasa daga chan." Jinjina kai yayi kad'an sannan ya bi shi ya shiga motar,shi kuma yaja suka tafi. Tafiya ce me matukar nisa wanda tun sultan na duba dukkannin bayanan daya tatatara har ya hakura ya dangana da kallon hanyar yana sake lafewa a jikin motar da babu abinda yake tashi a cikin ta sai karar na'urar sanyaya waje. La'asar sakaliya suka isa inda musan yace, ya gangara gefen wata yar karamar hanya zuwa wani madaidaicin gida wanda ya zama kamar shi kad'ai ne a wajen. Shi dai Sultan be ce komai ba yana bin komai da ido. "Yallaabai ina dan zuwa dan Allah." Da ka ya amsa masa ya fita da sauri ya shiga gidan, jim kad'an suka fito da wasu mutane su uku, suna magana har suka karaso wajen motar, ganin haka yasa SULTAN bude kofar ya fito. "Barka da zuwa." Suka fad'a a tare har suna dan russunawa. "Ranka ya dad'e wannan shine zamu bashi ajiyar motar, wadannan kuma su zasu dauke mu har Masarautar Saji Idan Allah ya yarda." "Allah ya kaimu lafiya." Kawai yace Babura ne guda biyu, Sultan ya hau daya Musa ma ya hau daya suka dauki hanyar Masarautar Saji. Gabannin magriba suka isa, sai dai yadda harabar Babbar Masarautar ke cike da wasu irin manyan fitulu masu hasken gaske yasa wajen ya zama kamar rana, daga chan gefe suka sauke su, sannan suka nufi wata hanya daban suka bar Sultan da Musa a tsaye. Da ido Sultan ya shiga bin Babbar Masarautar wadda take da fadin kasa sosai ga wasu manya manyan bishiyu masu kyau da suka kara kawata wajen, girman ta ya kai girman wani garin, gidaje ne daga kowanne bangare nata wanda ya kasance an musu ado da irin adon da ake ma gidan sarauta. Tun kafin su karaso Masarautar ya lura da yadda tsari da kyau da Allah ya bawa garin na Saji,babban birni ne cikin manyan birane wanda kai tsaye zaka kirashi da lamba daya indai akan kyau da tsari ne. Hankalin sa ne ya dawo kan masu tsaron Masarautar wanda a kalla sun ta samma su talatin kowannen su babu annuri a fuskar sa, zagaye suke kawai kamar mayunwatan zaki masu farautar neman abinda zasu ce, amma idan akayi la'akari da dalilin da yasa aka sake bazasu a wajen zaka san cewa dole ne su jajirce dan kuskure daya zasuyi komai ya lalace. "Karka yi magana duk abinda zasu ce kayi shiru, mun riga mun tsara komai." Musa ya rada masa a kunne sannan yayi gaba shi kuma Sultan ya bishi suka nufi Babbar kofar da zata sada ka da cikin Masarautar. Kamar mutum mutumi haka Sultan ya shiga binsa yana jin kamar jinin jikinsa na tsittsinkewa yana bin hanyar da ba ita aka tanada masa domin bi ba, wani irin sakayau yake jin sa, irin abinda be taba ji ba sai sau biyu, na farko a asibiti watarana da MD ya kirashi, sai kuma a Canada. Sai kuma yau da yake jin kamar ma har wani sanyi sanyi yake ji na ratsa shi, ko kuma ace a dauko kankara a dora masa a jiki a kuma zo a rufe ta da babban mayafi. Har suka karasa inda zasu din be iya sake fahimtar komai ba, yana jin sanda Musa yake magana da wani dake chan gefe shi kad'ai, sai kuma yaga ya taso sun sake bin sa har zuwa wajen wasu su uku suma, sannan suka je wajen wasu, anan suka dan bata lokaci sai kawai yaga an bud'e musu kofar ance su shiga, kallon Musa yayi yaga baya kallon sa sai ma saka kansa da yayi suka shiga takawa cikin Masarautar wanda yake jin duk wani takun da zai yana amsawa a dukkan gabobin sa. Tafiya suka shiga yi da dan sauri duk da haka be bari abu daya na daga Masarautar ya tsere masa ba, ya bi komai yadda ya kamata ya kuma karance wani abu kad'an daga cikin yadda mutanen Masarautar suke al'amuran su, wanda kallo daya zakayi musu ka gane basu da maraba da bayi, wanda tsantsar wahala da rashin walwala yayi ma katutu. A wata kofar katako suka tsaya, wani da Sultan ya lura da yanayin yadda yake abubuwan da sauri sauri yayi saurin bud'e musu, suka kutsa kai ciki sannan yaja kofar ya rufe yana sauke nauyayyar ajiyar zuciya kana ya bar wajen bayan ya tabbatar da babu wanda ya gansu. ***Hannun sa a goye a bayan sa yana kaiwa da komowa tsakanin dakin, daga chan gefe wasu ne a durkushe kansu a k'asa , dakin yayi shiru dukkanin su suna jiran suji abinda Sarkin zai ce, tsawon lokaci be ce komai ba sai dan siririn tsaki da yake ta ja a hankali a hankali. Sun cire rai da zai ce wani abu sai kuma ya koma da baya ya hau kan karagar sa, sannan yace cikin kaushin murya. "Idan har abinda muke tunani zai shigo cikin Masarautar nan a gobe, ya zama dole mu tabbatar da zuwan sa hannu, duk da bamu da Ikon ganin ko menene ko waye, sai dai jikina na bani wani gagarumin abu ne ke tunkaro mu, dan haka ba zamuyi kasa a guiwa ba wajen ganin mun kare martabar abinda muka dad'e kafin mu same shi, ya zama dole ne, kowa a cikin ku ya zama a shirye shiri bana wasa ba, dan bamu san wanne shiri sukayi a kanmu ba." "An gama ranka ya dad'e." Suka had'a baki wajen fad'a, wani daga ciki ya duka kad'an sannan yace "A duban da nayi dazu, sai naga abun na kusa damu sosai, kusan da nake jin tsoron kar mu sakankance su shammace mu, ina ganin ya kamata a sake dubawa." Babban yayi karaf da sauri yace "Kana nufin abinda na gani akan zuwan nasu gobe ba daidai bane? Ko kana nufin bansan aikin da nake ba ne?" Ya karashe a dan hasale. "Ba ina nufin hakan bane, sai dai..." "Ya isa!" Sarki ya dakatar dasu "Yanzu ba lokacin musu bane ko nuna wani yafi wani, lokaci ne na aiki babba, aikin da yafi wanda kukayi a baya, ruwan kune ku bar komai ya lalace." "Tuba muke ranka ya dad'e." Fuu ya tashi ya shige ciki ya barsu zaune, a hankali duk suka fice daya bayan daya cikin shigar su ta kowanne lokaci idan zasu zo ziyarar sarkin. ***Karewa dakin kallo Sulthan yayi, babu komai sai wata tabarma daga gefe, sai tarin wasu kaya daga dayan bangaren dakin, sai dai akwai bandaki karami a manne a ciki, da sauri ya sauke jakar sa, ya nufi kofar bayan ya tabbatar da hasashen shi, alwala ya dauro saboda ya samu yayi sallar data tsere masa, yana fitowa musa ma ya a shiga yayi alwalar shima, sultan ya jasu suka rama sallolin da suka tsere musu sannan suka yi Isha'i wadda ake yi a daidai lokacin. Pad din sa ya ciro ya bud'e yana duba sakonnin da Amrah ta turo masa akan ta kira shi a kashe dan kashe ta yayi gaaba daya, murmushi yayi me kyau sannan ya tura mata reply,few lines masu ma'ana, kafin tayi reply ya maida wayar flight mood saboda baya son ta kira shi ta masa tambayar da bashi da amsar ta shima. Suna nan zaune wanda ya rako su ya sake shigowa, ya ajiye musu kwanon abinci guda biyu kowa a gaban sa,ya rissina sosai wajen bawa Sultan wanda har yaso ya bawa Sultan din mamakin yadda suke girmamashi duk da be san dalili ba, be ma kuma san me Madaki da wannan amintaccen yaron nasa Musa suke shirya wa akansa ba, ya riga dai ya gama shirin sa shima lokaci yake jira ya aiwatar da komai amma kafin nan zai cigaba da bin su a yadda suka yi nasu tsarin. ****** Assalamu alaikum Barkanmu da Sallah ya iyali? Masu complain na ki dawowa kuyi hakuri, abubuwa ne suka sha min kai plus bana gari. Hankali na gaba daya yana kan rubutun nan tunda duk abinda ka fara burin ka kawai ka gama shi ka sauke nauyi. Nayi typing da yawa yana Wattpad sai dai ntwrk sam ya hanani logging, complain din da naji ne ciki hadda maganganu marasa dad'i yasa na rubuta wannan din yanzu. NagodeAbinda ke cikin zuciya Hafsat Rano Page 30 **** Tashi yayi maimakon ya ci abincin da aka ajiye masa sai ya bud'e jakar sa ya dauko cake da fresh milk yasha kad'an. Abincin Musa ya dauka yaci sosai yana kallon sa, da yaga ya cinye tas sai ya tura masa nasan gaban sa yace "Ba ci zanyi ba." Murmushi Musa yayi ya ja kwanon gabansa kara cin kusan rabi sannan ya kora da ruwa, sannan yayi hamdala. Duk Sultan na hankalce dashi sai da ya ga ya gama ya maida komai gefe ya gyara zama yace "Musa, inaso zan tambaya kà." "Allah yasa na sani." Ya amsa da sauri yana tattara hankalin sa gaba daya wajen sa. "Wanne shiri kukayi kai da Madaki? Me kuka tsara akan abinda ya kawo mu.?" "Allah ya taimake ka, da farko dai zamu cigaba da zama anan ne kwana uku zuwa sati, zuwa dai sanda Maimartaba zai yi wata tafiya da aka tabbatar mana da cikin satin nan ce, idan yaso daga nan sai muyi abinda ya kawo mu, mu fice." "Idan har haka ne, me yasa kai ba zaka iya dauko masa abinda yake so din ba? Sai ni dole." "Saboda kai kad'ai ne zaka iya." Musa ya amsa masa kai tsaye. Shiru Sultan yayi yana tattare maganar waje d'aya, sai kawai ya tashi ya shiga zagaye dakin yana jin lallai akwai wani kulli da Madaki ya shirya masa, amfani zai yi dashi ya cimma wani burin sa, ba zai taba bari suyi wasa da rayuwar sa ba, zai kuma nuna masu shi ma namijin duniya ne, zai basu mamaki idan har ya gama binciken da yake akan komai ya gano akasanin yadda suka zo masa.    Zai fara da kurkukun nan da daga nan kuma zai dauko abinda yace masan ya dauko sai dai ba zai bashi kai tsaye ba, shima zai buga nasa wasan ne daidai da yadda ya dace.    Daren ranar be wani yi baccin kirki ba, a kusan zaune ya karasa kwanan ya saka wannan ya kwance wannan, ganin lokacin yaja sosai yasa kawai ya karasa raya daren yana addu'ar Allah ya yanke masa wahalar neman iyayensa da yake ya kawo masa komai a cikin sauki. ***Dakin Mah-Mah ta kwankwasa, yana kwance da wani littafi a hannun sa, jikin sa ya dan yi karfi sai abinda ba za'a rasa ba, tashi yayi ya dora jallabiya akan gajeran wandon sa sannan ya bud'e.    Tray ne a hannun ta, da sauri ya mika hannu zai karba "Mah-Mah bakya gajiya." "Ya jikin naka?" Tace bayan ta ratsa ta gefen sa ta wuce ciki, bin bayan ta yayi ya zauna a gefen ta. "Na samu sauki ai." "Masha Allah, Allah ya karo saukin." "Amin Mah-Mahn mu." "Kai da wa?" "Nida Sultan." "Karbi, maza cinye." Ta mika masa plate din tana share zancen.  Hannu yasa ya karba ya ajiye a gefe yace "Mah-Mah..." "Na'am." "Dan Allah ki daina ganin laifin Sultan akan abinda ya faru, Sultan yayi iya kokarin sa wajen boye min halin da suke ciki, da yake Allah ya kaddaro ita din matar sa ce, sai yasa naji komai da kunne na, kuma nayi alkawarin cika masa burin sa kamar yadda yayi kokarin cika min nawa." "Toh baban yan tsari, ni bana son maganar nan ma, kaci abincin kar yayi sanyi." Sai ta tashi tayi hanyar fita tana sababi "Ka bi ka damu kanka akan wanda be damu da kai ba,kana ganin tun da yasa kafa ya fice daga gidan nan ranar da aka daura auren ka sake ganin sa? Ko ya kiraka yaji halin da kake ciki?" "Mah-Mah...!" "Please Safwan, bana son zancen nan." "Shikenan Mah-Mah, Allah ya baki hakuri." "Yafi, kaci abincin ka gyara jikinka, Mubarak ma yazo neman ka dazu kana bacci." "Zan fito idan na gama." "Yawwa." Tace sannan ya ja masa kofar. Girgiza kansa yayi ya soma cin abincin a hankali ***Su wajen uku ne a zaune a gaban sa,kansa a k'asa yana duba wata takarda, murmushi yayi bayan ya gama ya dago yana mikawa daya daga cikin su. "Yaro be san wuta ba sai ya taka." Yace yana tuntsurewa da dariya. "Karku damu da komai, ban fito ba sai da na shirya, ba kuma zan yi wasa da damar da na samu ba, zamuyi amfani da abinda muka san zai yi saurin mika wuya, saboda haka yanzu aikin ya rage naku, komai yana cikin bayanan da na tura muku kwanan baya, har da address da komai, kamar yadda yake bincike da zakulo komai akammu, haka muma zamuyi nasa, duk da munsan kusan komai a kansa sai dan abinda ba za'a rasa ba." "Ya za'a yi da yaron nan Muhammad? Tunda har yanxu babu labarin mahaifiyar su." "Zuwa yanzu banyi tunani akan sa ba, Amma shima zai mana amfani sosai wajen kama Sultan a hannu,saboda haka yanzu mu bar komai a yadda yake, ku fara aikin da yake gabanmu yanzu." "Shikenan, angama." "Ku tabbata ba'a samu wata matsala ba." "Ba za'a samu ba." "Shikenan duk yadda akayi, sai muyi waya." ***Suna kwance wajen karfe daya na dare, Amrah ta dad'e da bacci ita kuma Afrah na kwance tana danna wayar ta, shiru babu sound din komai sai ta fara jin kamar motsi kad'an kad'an, daina abinda take tayi ta sake kasa kunnen ta, da gaske motsin ne amma ta wajen bayan d'akin, matsawa tayi kad'an ta makale jikin Amrah tsoro na cikata, an dade tana jin motsin kafin ta daina ji, da k'yar ta samu ranar tayi bacci saboda tsoro.    Da safe suka tashi normal, bata cewa Amrah komai ba, sukayi breakfast suka zauna zaman kallon wani series film wanda ya dauke hankalin su sosai.    Suna zaune Ya Adnan yazo, ya kira Afrah ta bud'e masa kofar, zuwan sa ya sa suka sake shagala da hira, suka dafa abinci suka ci tare har wajen tara na dare yana gidan sannan yayi musu sallama ya tafi. Yana tafiya tunanin motsin da Afrah taji jiya ya dawo mata, sai a lokacin taji haushin mantawar da tayi bata gaya ma Ya Adnan din ba. Har sukayi shirin kwanciya hankalin Afrah ba a kwance yake ba. Hira Amrah take mata amma taki sakewa suyi hirar sosai musamman da aka dauke wuta wajen goma da rabi duk sai garin yayi tsit, ganin haka yasa Amrah ta kyale ta, ta kwanta bayan sunyi addu'ar kwanciya bacci sun kuma rufe ko ina. Kamar yadda Afrah tayi tunanin zata sake jin motsin ranar ma sai bata ji ba, har bacci barawo ya kwashe ta wanda bata sake farkawa ba sai da aka fara kiraye kirayen sallar asubah. ***Yana zaune har garin yayi haske sosai, yana jin yadda hayaniya ke tashi alamun mutanen Masarautar sun firfito kowa zai yi uzurin sa, sake kishingid'a yayi yana jin yadda komai yake wakana. Sosai lokaci yaja suna nan zaune, Musa ya sake komawa bacci ya tashi, ya shiga ya gyara bandaki ya fito. "Ko zaka watsa ruwa?" Ya tsaya a gaban sultan yana rik'e da sabon soso "Ok." Ya mike ya shiga ya yi wankan a gurguje ya fito babu Musa a dakin ya chanja kaya zuwa kanana marasa nauyi ya zauna, yana zama Musa ya dawo ciki ya samu waje ya zauna shima.   ***Tawaga guda ce ta sarki da mukarraban sa suka nufi kofar Masarautar, kowa yayi mamakin fitowar sarki a lokacin, da kuma zuwan sa kofar, sai dai babu wanda yasan dalilin sai makusantan Sarkin. Sun dade a wajen suna lura da duk wani shige da fice na Masarautar ba tare da sun san cewa abinda suke kokarin hanawa shigowa ciki shi tuni ya tsufa a cikin Masarautar.     Har magriba babu wani bako da ya zo da nufin shigowa Masarautar, haka suka tattara suka koma da tunanin yadda akayi bayanin da suka samu akan cewa yau za'a shigo Masarautar tasu.     Suna komawa duk suka zube a gaban Sarkin bayan yasa an kira masa manyan yan duban Masarautar tasa. "Ya akayi haka?" "Ina matsalar take?" Babu wanda ya motsa a cikin su, duk kansu na k'asa, dalilin babu wanda xai iya kushe ko kalubalantan abinda Babban su ya duba, tabbas duk sunyi nasu binciken a bayan nasa kuma sunga akasin abinda shi din ya dubo amma basu da ikon cewa ba haka bane, ko sun fad'a din ma Sarki ba yarda zai ba, saboda yafi yarda da gamsuwa da abinda Babba ya fad'a masa.   Ganin ba zasu ce komai ba yasa Sarki bello komawa ya zauna sannan ya umarce su da su fito da kayan aikinsu, suka dukufa, tsawon lokaci babu wani haske da suke gani a aikin nasu sai ma duhu da ya mamaye babu wani alamun akwai nasara, duk sun tsorata da abinda suka gani, sai dai babu wanda yake da k'warin guiwar sanar da Maimartaba abinda suka gani din. Hakan ya saka jan lokaci me tsawo kowa yana jiran wani ya fara magana, shirun nasu ya kara tunzura Sarki Bello Moddibo Saji ya daka musu tsawa me karfi yana nuna su. "Zan saka a sauke min kawunan ku dukka Idan har zakuyi min wasa." Da sauri Babba ya yaye nad'in kansa, ya kuma duka sosai cikin k'asa da murya yace "Allah ya huci zuciyar ka shugaban sarakuna, gaba salaman baya salaman, tuba muke bamu da nufin bata wa sarki rai, sai dai abinda muka gani ne ya saka mu a cikin dimuwar da har muka gaza cewa komai." Yana daya daga cikin abinda yasa Sarki Bello Moddibo Saji ke ji dashi kenan, yasan yadda zai bullo masa idan ma ransa ya baci, a hankali yaji ransa na sauka kad'an kad'an, idanun sa da suka soma chanjawa suka dan washe ya muskuta kad'an. "Ina matsalar take?" "Abinda muka gani Allah ya baka yawan rai shine, tabbas akwai masu yi wa aikin mu zagon k'asa, kuma suna aiki ne bayan sun samu labarin abinda muke kokarin yi, tabbas wanda muke zaman jira yazo har kusa da Masarautar nan, sai dai tun daga nan komai yayi baki bama iya ganin komai akai, mun duba babu wani kuskure,abu daya da muka tabbatar dashi shine ya dauko hanyar zuwa, amma bamu tabbatar da yadda ta kasance ba bayan zuwan nasa." Zufa me yawan gaske Sarki ya share, ya had'e hannun sa waje daya yana ayyana abinda ya kamata yayi, ga dukkan alamu komai na neman kwabe masa, a tunanin sa tunda yana da wannan bataliyar na gaban sa babu wanda zai iya aikata komai ba tare da sanin sa ba, sai gashi duk da yasan da komai amma ya kasa aiwatar da wani abu akai. Duk da haka ba zai k'asa a guiwa ba,ba kuma zai bawa abokan gaba damar da zasu samu galaba akan sa ba, zai iyakar kokarin sa. A take ya tattara su, yasa aka bud'e musu wani babban daki anan cikin fad'ar tasa, suka dukufa aiki. Ciki ya koma ya fiddo da akwatin karfen nan, ya sake tabbatar da abinda yake ciki yana nan a inda yake, sannan ya mayar ya ajiye. ***Saida yaji kafa ta dauke gaba daya, ya tashi ya shirya, yayi nad'in kamar yadda ya tsara, ya fita bayan ya rufo wa Musa dakin wanda yayi nisa a baccin sa. Tafiya ya shiga yi a hankali yana kallon ko'ina, yadda ya samu zanen Masarautar haka komai yake, ya haddace kowanne lungu da sako na Masarautar shiyasa kansa tsaye yake tafiya yana kaucewa duk wani waje da yasan zai tarar da masu tsaron wajen. Tazarar da ke tsakanin inda aka ajiye su zuwa kurkukun yasa yayi doguwar tafiya kafin ya isa. Sanda ya isa, ya samu wani corridor ya tsaya saboda yadda wajen ya cika da tsaro. Yana nan tsaye wani daga ciki yayo wajen yana juya wata zabgegiyar dorina a hannun sa. Nannade hannun rigar sa Sultan yayi yana zuwa daidai wajen da yake ya sa hannu daya ya toshe masa baki, kokarin kwacewa yake ya daga masa kudade masu yawan gaske, zaro ido yayi ganin kud'i sai ya daina kokarin kwacewa ya saki jikinsa, sai da Sultan ya tabbatar da gane abinda yake nufi sai ya sake shi, suka sake matsawa chan inda babu kowa. "Me kake so?" Ya tambaye shi yana dube duben hanya alamar a tsorace yake. "Ka nutsu, inason ganin mutanen dake cikin kurkuku me lamba 108 ne, idan har ka taimaka na samu ganin su, zan baka ninkin wadannan kudaden nayi alkawari." "Amma Sarki ya hana kowa ganin su, ya saka tsaro sosai akai, ina jin tsoro." "Babu abinda zai faru, idan ma wani abu ya faru, ba zan taba ambatar ka a matsayin wanda ya taimaka min ba, zan dauki laifin dukka nayi wannan alkawarin." "Ka tabbata zaka bani ninkin wadannan kudaden?" "Zan baka, ka rike wadannan yanzu, zan kara maka kafin na bar nan." "Shikenan ka tsaya anan." Yace sannan ya karbi kudin ya juya da sauri. Tsawon lokaci ya dauka dan har sultan ya fara tunanin ko yaudarar sa yayi sai gashi ya dawo. "Tawo." Kawai yace masa da sauri yana juya, da saurin shima Sultan din ya bishi yana fatan ya samu abinda yake nema kafin yakai ga daukar wa Madaki abinda yake so. Babu kowa a wajen kamar dazu, kai tsaye kurkukun suka nufa ya daga kansa ya na kallon inda aka rubuta number, babu kowanne daki a kusa da nasu shi kad'ai ne a wajen daga chan karshe. Matsa masa yayi ya bashii hanya. "Kayi sauri dan Allah, kar na shiga matsala." Kafad'ar sa Sultan ya dafa "Karka damu." A hankali ya tura kansa ciki, da farko baya ganin komai sai duhu sosai da ya mamaye dakin, sai da ya shiga ciki sosai sannan ya hange mutane biyu a zaune, daya ta jingina da kafad'ar daya, wani irin tsoro ne ya kamasa ganin mutanen da ke ciki matana, mata a irin wannan yanayi, mata da suke da daraja da kima su aka wulakantar saboda neman duniya, duk da besan wanne irin abu suka aikata aka kawo su wajen ba, amma yasan komene basu chanchanci wannna hukuncin ba, be taba sanin abinda ake fad'a a gidan sarauta haka yake ba sai da ya shigo Masarautar Saji, tsantsar zalinci da mulkin mallaka ake ma al'umar musulmi. Hawaye yaji na neman zubo masa, yasa hannu ya share yana jin zuciyar sa na zafi, yana jin da ace zai samu dama,da ace zai iya wani abu, da ace shi din wani ne me karfin iko a Masarautar da ya chanja komai, amma waye shi? Shi da bashi da uwa balle uba, baya raba daya biyu a cikin matan nan ko daya itace mahaifiyar sa, ko kuma wata makusanciyar sa tunda har Madaki yace ya neme su lallai kafin ya bar Masarautar. A sanyaye ya karasa ya durkusa a gaban su yana kallon yadda daya daga ciki ke fitar da numfashi a wahale, kamar ma bata da lafiya. "Kuyi hakuri." Ya samu kansa ta furtawa bayan yayi kokarin tattaro abinda ya kamata ya fad'a musu da zai rage musu rad'adin abinda suke ji ya kasa, da sauri ta bud'e idonta, ta sauke su akan sa, a lokaci daya ta mik'e tsaye tana sake fitar da tsantsar mamakin ta. "SULTAN!" Ta furta da sauri tana nuna shi da hannu. ***Kai tsaye kurkukun ya nufa, daga shi sai amintaccen bawan sa guda daya, tun kafin ya karasa aka bada sanarwar isowar Sarki, cikin wani irin tashin hankali bafaden nan ya shiga, yasan babu wata hanya da Mutumin da ya bari ya shiga wajen zai bi ya fice ba tare da sun hadu da sarkin ba, ba kuma zai iya fitowa kafin sarkin ya karaso ciki ba. Be gama fita daga cikin tashin hankalin da yake ba, Sarkin ya karaso fuskar sa a matukar bace, kallo daya zakayi masa kasan akwai babban al'amarin da ya kawo shi wajen. Fitsari ne kawai yaji ya fara bin kafar sa da yaji muryar bawan nan na isar da sakon sarki akan a bud'e masa kurkukun me lamba 108. ***I'm very sorry please🙏🙏🙏🙏🙏_Abinda ke cikin zuciya_ _Hafsat Rano_ _Page 31_ ***Mike kafarsa yayi yana kallon yadda ta dan daga ta kumbura, kwana biyu baya jin dadin jikinsa, sosai kafar ke matsa masa har wani lokacin sai yaji kamar ba zai iya takata ba. Yana zaune ta turo kofar ta shigo, ya bita da kallo har ta zauna a gaban sa, zaman dirshan, irin zaman da be taba gani tayi a gaban sa ba tun zuwan su k'asar. Sosai ya maida hankalin sa akanta dan yasan ba karamin abu bane ya kawo ta. "Ya akayi gimbiya?" Yace ganin taki cewa komai. Shiru tayi tana kallon k'asa, hannun ta daya tana murza shi jikin zoben dake dayan hannu. Dabi'ar ta kenan tun lokacin baya idan har tana son yin magana dashi kuma maganar ta kasance mai muhimmanci ce a wajenta, murmushi yayi me kyau, hakan da tayi ya tuna masa da lokacin chan baya,sanda suke cikin kwanciyar hankali kafin komai ya lalace ya zama tarihi, sai dai be fitar da rai ba, yana ji a ransa kukan su ya kusa karewa, komai zai dawo musu ko da ba a yadda yake a baya ba saboda shekarun da suka ja, amma yana fatan wani yanki na farin cikin su ya dawo suyi rayuwa irin wadda ya dad'e yana musu mafarki. "Ina sauraron ki, kinsan babu abinda yafi muhimmanci a wajena fiye da damuwar ki,dan Allah ki sanar dani ko da ba zan iya yi miki wani abu akai ba, amma ina so mu raba damuwar tare." Matsawa tayi kad'an ta sake kusantar sa, fuskarta na sakewa ba kamar farkon zuwan ta falon ba, tace "Na damu da yaron nan Muhammad, na kasa samun nutsuwa tun ranar da ya barmu, me yasa nake jin sa haka a raina?" "Be ke kad'ai ba, ni kaina hakan ce a wajena, sai dai nafi alakanta haka a matsayin rasa wanda zamu iya tattaunawa dashi akan rayuwarmu da mukayi tsawon lokaci sai bayan haduwar mu dashi, watàkila hakan ne dalilin da yasa muke jin sa har cikin ranmu." "Haka ne." Tace tana jan ajiyar zuciya. "Zan kokarin had'a ki dashi gobe a waya kinji? Idan kukayi magana hankalin ki zaifi kwanciya nasa." Da sauri tace "Yauwa dan Allah." "In Sha Allah." Yace yana murmushi. "Nagode." "Anything for my queen." Sai kawai tayi murmushi. *** "Sultan kaine anan?!" Ta matso sosai, dan hasken da ya ratso ta cikin dakin ya bashi damar ganin ta sosai, da sauri yasa hannu ya rufe bakin sa, fuskar sa na dauke da mamaki, tun lokacin da ya shigo dakin nad'in da yayi wa kansa ya cire hakan ya bata damar ganin fuskar sa, ba wata bace face Maman Yara, matar da dalilin neman ta ne ya kawo shi wajen nan, amma me take anan? Menene alakar ta da wannan rikirkitarciyar Masarautar me cike da mugayen mutane, menene alakar ta da Madaki da kuma dalilin da yasa tace ya neme shi wajen neman iyayen sa? Bashi da amsar ko daya a ciki, sai dai ganin ta yanzu ya sa shi jin wani sakayau a ransa, yana da yakinin abubuwan zasu zo masa da sauki tunda ya tabbatar da tasan wani abu game dashi ko ba dukka ba. Amma abinda be sani ba shine, suna da lokaci kuwa? Me zai faru idan komai ya lalace aka gano ya shigo wajen, za'a iya chanja musu wani wajen da har abadah ba zai sake ganin ta ba. "Maman Yara!" "Alhamdulillah, Allah kaine abin godiya, sultan ya akayi ka shigo nan, yaushe ka shigo Masarautar? Ka hadu da Malam Bako? Ka hadu da Madaki ?" Da ka ya amsa mata sannan yace "Madaki ne ya turo ni akan wani zobe, ya kuma ce lallai na nemi kurkukun nan kafin na fita, hakan da zanyi shine zai sa ya had'a ni da iyayena." "Karka taba yarda ka bashi abinda yake nema, nima kaina na yarda dashi har na bar komai a hannun sa ba tare da nasan mugun nufin sa ba, zoben nan shine duk wani matakin nasarar Sarki Bello, kuma shine yake dauke da duk wani kulli da akayi maka kai da yan uwanka da iyayen ka, kaine magajin Masarautar Saji Sultan, kaine kad'ai zaka gyara komai ka dawo dashi yadda yake, sai dai ba abu bane me sauki, sai ka kula, sai ka kula!" "Magajin Masarautar Saji?" Ya tambaya muryar sa dauke da wani irin Amo, cikin rashin fahimtar abinda take nufi." Daga masa kai tayi da sauri sannan tace "Kai din dana ga Adalin Sarki, Sarki Usman Muhammad Moddibo Saji!" Sai ta dora "Akwai abubuwa da yawa da dole sai ka samu zoben nan, wanda barin yake tare da Aminatu gata nan, anan ne komai zai dinga warware kansa a hankali a hankali." Sai ta bud'e hannun sa ta saka masa shi ta rufe sannan tace, "Karka bata lokaci dan mutanen nan basu da kirki, kayi sauri ka aiwatar da abinda ya kamata kafin su farga da kai, ka dage da addu'a dan itace take rik'e da kai har zuwa wannan lokacin Sultan." "Wacece wannan matar?" Ya nuna Aminatu dake kwance tana bin sa da kallo sosai, idanun ta na fitar da hawaye masu zafin gaske. Girgiza masa kai Maman Yara tayi "Abubuwa da yawa ba zaka sansu yanxu ba, babu lokaci Sultan, Idan har kayi nasarar daukar zoben nan, zaka samu dukka amsoshin da kake nema, amma a yanzu mu bar komai a yadda yake." "Amma..." "Shissshi..." Tayi saurin saka hannun ta tayi masa alamar yayi shiru, k'asa kunne tayi taji da gaske sanarwa ake na isowar sarki,sai a lokacin shima Sultan din yaji abinda yasa ta dakatar dashi, a birkice ya maida kallon sa kanta da sauri yace "Zan dawo, zan fitar daku daga nan ba za'a dau lokaci ba." Daga masa kai tayi tana jin yadda takun tafiyar Maimartaba na kara kusanto su, hannu ya sa ya maida nadin kansa ya rufe har fuskar sa sai kwayar idon sa da take a bud'e, yaji an turo kofar an shigo, bawan ne a gaba yana shigowa ya durkusa daga gefe da sauri Sultan yayi yadda yayi shima ya durkusa a gefen sa. Cikin takun sa me cike da Izza ya shigo ciki, ya sauke idon sa akan Sultan da wani irin yanayi. "Waye kai!" Ya daka masa tsawa, tsawar data firgita hatta masu tsaron kofar wajen amma ko gezau Sultan be yi ba, a yadda yake jin zuciyar sa na tafarfasa zai iya tashi yayi kukan kura ya damki wuyansa har sai ya daina numfashi, amma da ya tuna matan nan biyu da bawan nan da ya taimaka masa wanda yasan idan har ya bari aka gane yadda ya shigo wajen toh yasan karshen ta kashe Sarkin zai yi, shi kuma ba zai samu damar yin abinda ya kamata ba. Wadannan dalilan su ne suka sashi kasa komai, ya cigaba da karanto Addua a zuciyar sa, ya dogara da Allah yasan kuma shi kad'ai ne zai iya fitar dashi daga halin da yake ciki. Mikewa bawan nan yayi ya fita, sai gashi sun dawo tare da wani faffafan mutum me wani irin yanayin halitta, kallo daya zaka masa kasan babu d'igon Rahma a fuskar sa, takobi ne irin Wanda ake kira da gayawa jini na wuce tsirara rike a hannun sa, ya fad'i yayi gaisuwa sannan yayi wajen Sultan ya dora takobin a saman wuyan sa ta bayansa. "Waye kai? Ta yaya ka shigo Masarautar nan? Waya baka izinin shigowa nan?* "Nine na bashi izini." Ya fad'a yana tsayawa a kofar, dukka suka juyo, Maimartaba Sarki Bello Moddibo yace "Yarima!?" "Tuba nake ranka ya dad'e, waje na yazo abokin karatu na ne, sai muka fito zagaye dazun daga nan muka shigo nan muna duddubawa,wani uzuri yasa na koma na barshi anan." Babu wanda ya tanka, sai ma ficewa da duk sukayi suka bar su su uku, sanin su ne Sarkin baya had'a soyayyar kowa data tilon dansa yarima, shiyasa ma be iya cewa komai akan abinda yace din ba, sai ya maida hankalin sa wani wajen daban. "Ahmad muje ko?" Yarima yace yana matsa masa hanyar, cike da mamaki Sultan ya mike tsaye kansa a k'asa ya dan duka kad'an alamar girmamawa ga Sarkin sannan ya raba shi suka fice tare da wanda be san waye ba, be kuma san dalilin da yasa shi kareshi a lokacin da ya tabbatar idan ma ba'a sauke wannan takobin a kansa ba toh za'a rufe shi har sai bincike ya tabbatar da waye shi. Tafiya suke babu wanda ya tanka wa wani, har suka isa wani katafaren gini me kyau da tsari, masu tsaron wajen ne birjik a wajen da masu kula da shashen, wata kofa ce ta bud'e suka shiga ciki sannan ta rufe. A jikin kofar Sultan yaja ya tsaya, ya harde hannun sa yana duban mutumin da aka kira da yarima, juyowa yayi bayan ya rage kayan jikin sa, ya nuna wa Sultan wajen zama. "Bismillah." Yace yana zama shima "Me kake nema a wajena?" Kai tsaye Sultan ya tambaye shi ba tare da ya zauna din ba. Watsa hannu yarima yayi zuwa saman kujerar yayi murmushi "Ni dana taimaka maka, maimakon kayi min godiya sai kuma tambaya haka?" "Daga sanda na shigo Masarautar nan, na lura da abu guda daya, duk masu fad'a aji na Masarautar nan kowa cike yake da son kansa, kowa yana kokarin kare martabar sa ne, me yasa bazan yi tunani akan ka ba? Bayan baka sanni ba baka taba gani na ba?" "Niko na sanka, sanin da kai kanka bakayi wa kanka ba, ni na baka damar shigowa cikin Masarautar ba tare da kasha wahala ba, haka kuma idan ka yarda dani zan taimaka maka wajen samun abinda kazo nema." "Idan har ina bukatar taimakon naka ko?" "Dole ne zaka bukata, saboda ire iren rana irin ta yau Wanda baka san sau nawa zasu zo ba nan gaba." "Zan koma masaukina." Yace ba tare da ya bashi amsar abinda yace ba. Dage kafad'a Yarima yayi cikin rashin damuwa yace "Duk sanda kaji kana bukatar taimako na, ka zo kanka tsaye nan ne bangare na." Yana gama fad'an haka ya tashi ya bar falon baki d'aya. Fita sultan yayi ya koma dakin da suke, yana tura kofar ya tarar da Musa a tsaye hankalin sa a tashi, kin bari yayi su had'a ido ya kwanta tare da juya bayan sa sannan ya rufe idon sa ruf. Yana bukatar yayi tunani sbaoda haka baya son doguwar magana balle ta hanashi tuna komai. _Kaine Magajin Masarautar Saji."_ muryar Maman Yara ta shiga amsa kuwwa a kunnen sa. _Kai din dana ga Adalin Sarki Maimartaba Usman Muhammad Moddibo Saji!" Da sauri ya mike zaune, ya dauko wani littafin sa a cikin jakar kayan sa, ya bud'e inda ya rubuta muhimman abubuwa akan labarin bayin Allah nan, a hankali ya sauka zuwa inda sunan yake rubuce baro-baro yana tuna sanda ya rubuta shi bayan ya dawo daga gidan watarana. _Usman Muhammad Moddibo Saji._ Ji yayi kansa na juyawa, yayi saurin saka hannu ya dafe yana tariyo labarin da ta bashi. _"An zalunce ni Muhammad, an raba ni da abun da ko dabba aka raba ta dashi takan shiga tashin hankali..."_ Hawaye yaji sun fara gudu a saman fuskar sa, hannayensa suka shiga karkarwa cikin wani irin yanayi da be taba sanin yana dashi ba, ya cigaba da tattara bayanan yana hadawa da wanda ya samu yanzu. Zuciyar sa ce yaji ta bushe,yaji wani irin abu me kamar karfi ya shige shi, tun kafin yasa yana da alaka dasu yaji cewa damuwar su tasa ce kuma zai iya komai akan su, amma yanzu da ya san akwai wani abu babba tsakanin sa dasu, yaji yadda yake ji a kansu ya ninku ninkin baninkin, yaji zai iya taka kowaye ya shigo hanyar sa ko yayi yinkurin tsadashi. Zai yi amfani da kwakwalwar da Allah ya bashi wajen yin wasa da tasu dakikiyar kwakwalwar wajen kaisu k'asa. Duk da besa shi din waye a cikin yayan da Maimartaba Usman Muhammad Moddibo Saji, amma zai yi komai dan ganin komai ya dawo kamar yadda yake. Da farko zai yi amfani da yarima wajen cin galaba akàn azzalumin ubansa, sannan yayi amfani da Ameer wajen kai Madaki k'asa, sai kuma sauran da be sani ba zai sansu yanzu. Had'a komansa yayi waje d'aya, ya kalli Musa dake zaune daga gefen chan, yana kallon bayan sa yace "Ka koma inda ka fito gobe kace wa ubangidan ka aikin ka ya cika, ku jirani kamar yadda mukayi alkawari a bakin garin zan kawo muku abinda kuke bukata, sannan ka fad'a masa idan ya kuskure aka samu akasi zan nuna masa na fishi sanin duniya." Da sauri Musa ya kalle shi zai yi magana yaga ya fice daga dakin. Tashi yayi da sauri ya leka, duhu ne ta wajen dakin nasu dan haka be ga inda yayi ba. Hannu ya dunkule ya bigi bango dan be san yadda haduwar su zatayi da Madaki ba idan ya koma masa a gobe. ***Kai tsaye bangaren Yariman ya koma, babu wanda yayi masa magana ya tura kai ciki, baya falon alamar ya kwanta, dakin da yake kallon sa ya bude ya shiga ya ajiye kayan sa ya kwanta bayan ya rufe kofar. ***Kamar yadda suka shigo Masarautar haka ya barta da asubar fari. Kai tsaye ya wuce inda yasan zai samu Madakin, suna zaune a lokacin da wasu abokan sana'ar sa suna tattaunawa akan wasu kaya Musan ya shigo, yanayin da Madaki ya ganshi yasa ya sallami mutanen suka zauna Musan ya fad'a masa abinda ya faru daga zuwan su har jiya da daddare. Murmushi Madaki yayi me kyau ya dauki waya ya danna kira yasa ta a handsfree sannan yace "Dama nasan zamuyi haka dashi, shiyasa nima nayi nawa shirin da zan kamasa da hannu na." "Hello... Kana ji? Yau daddare kuje ku aiwatar da aikin nan dana saka ku." "Yawwa shikenan." Ya kashe yana cigaba da magana "Kayi aiki me kyau, abinda za'a yi yanzu kaje gida karka damu zan karasa komai." "Toh shikenan." Yayi masa sallama ya tafi. "Sultan baka san waye Madaki ba, yaro be san wuta ba sai ya taka, zan bika a yadda kake muga iya inda zaka tsaya, sai dai dole zaka dawo kabi abinda nake so a lokacin da zaka samu labarin da zai bugar maka da zuciya ya kuma saka cikin tashin hankalin da baka sani ba, zanyi amfani da wannan lokacin wajen cimma buri na!" ***Amrah na tsaye a harabar gidan tunanin ta ya tafi wajen Sultan da tun ranar farko bata kuma samun sa ba, ko da tayi masa message din ma babu reply, ta damu sosai amma take kokarin boye wa saboda Afrah amma sam hankalin ta ba a kwance yake ba, gashi takamaimai bata san inda yaje ba balle ta samu relief, haka take buya tayi kuka sosai ta share amma sosai take jin rashin dadi akan tafiyar da yayi. Yau ma tunanin ne ya dame ta yasa ta fito compound din karta damu Afrah,tana tsaye jikin wata shuka yar karama da bata yi wani girma ma, tana kallon wani waje kamar me son ganin wani abu a wajen taji anyi knocking a kofar gidan, da sauri ta kalli wajen, sai kuma tayi saurin yin wajen gate din da zuciyar ta, tace masa ko Sultan ne ya dawo, tana zuwa bata tambayi waye ba ta zare lock din.. Rano na kara baku hakuri dan Allah ku yafe min 😴😴😴🙏🙏🙏😭😭😭😭😭😭😭😭 _©Hafsat Rano_ *Page 32* _ASSALAMU ALAIKUM BEAUTIFUL PEOPLE.. INA KUKE YAN UWA NA MATA? TO KU MATSO KUSA DOMIN GA DAMA TA SAMU.. KAI BAMA MATA KADAI BA, HAR IYAYEN MU MAZA, ZAKU IYA KAWO SISTERS DINKU, DAUGHTERS DA MA WIVES DINKU. KAI HARDA BAE DA KE SHIRIN ZAMA MRS🤩😉...!_ _UMMU AYMAAN’S KITCHEN, UMMU AYMAANS’S KITCHEN, UMMU AYMAAN’S KITCHEN..._ _INA YAN UWANA MASU SON SU KOYI BAKING DA DECORATIONS? TO NESA TAZO KUSA.. UMMU AYMAAN’S KITCHEN ZATA KOYAR DA MATA MASU SON SU KUYI BAKING DA DECORATIONS NA KWANAKI BIYU. AKAN FARASHI ME RAHUSA, NAIRA DUBU 6 KACAL, (6k)._ _ZATA KOYAR NE A UNGUWA UKU LAYIN MAIFATA, ZARIA ROAD KANO.. PRACTICAL CLASS NE, SANNAN AKWAI GARABASA DA NA NESA DAKE SON SU KOYA SUMA ZASU IYA KOYA TA ONLINE DUK AKAN NERA DUBU SHIDA KACAL, DUK ABUNDA YA KUNSHI BAKING ZATA KOYAR KAI HAR MADA BONUS NA DECORATIONS._   _*CLASSES DIN KWANA BIYU NE, AKWAI PRACTICAL DA ONLINE, CLASSES DIN ZA’A YISU NE RANAR 5 DA 6 GA WATAN YUNI WATO 5&6 OF JUNE (NEXT MONTH)RANAR WEEKENDS ASABAR DA LAHADI*_ _* 2 DAYS DEMO CLASS ON BIRTHDAY CAKE.. (BAKING AND DECORATIONS)* YAR UWA HANZARTA KI BIYA KI KOYA KEMA KIN HUTA DA BIYAN BAKERS, DA KANKI ZAKI IYA YIN NAKI, DA DUBU 6 ZAKI IYA BIRTHDAY CAKES KALA KALA, WANDA BA KARAMAR SANA’A BACE, IDAN YARAN KI KO KANNENKI ZASUYI BIRTHDAY KIN HUTA SIYA SE KEYI DA KANKI, KIYI KI BIRGE MAI GIDA AS SUPRISED GIFT.. INA YAMMATA? IRIN CAKE DINNAN ME HEART KI KOYA KIYI KI BAWA BABYN BABY🥰 LOVE IS LIFE, CAKE IS LOVE🙃._ _BA ANAN KADAI TA TSAYA BA, TANAYIN DUK WASU MOUTHWATERING SNACKS AND CONTINENTAL DISHES😋, AKWAI NA YAN GAYU IRIN SU CAKE PARFAIT, CUPCAKES, SAMOSA, SPRING ROLLS, MEAT-PIE, DOUGHNUTs, DUKA WADANNAN TANAYIN SU NE NA BUKUKUWA, SUNA, SHAGULGULAN TARO, KAI DAMA NA CI HAKA KAWAI😋_ _BA ANAN KADAI TA TSAYA BA, TANA CLASSES NA GIRKIN ZAMANI DANA GARGAJIYA, MOUTHWATERING DISHES NA YAN GAYU, MESA KISHIYA KWAFA, WANDA FACCALA ZATA DINGA CIZON YATSA, IRIN HADADDEN GIRKUNA MAI SA KUNNUWAN MAIGIDA SU MOTSA. KAI HARDA NA BUKUKUWA KUNA IYA ORDER TA MUKU SHI_ _INSTAGRAM HANDLE DINMU:_ Ummu_aymaan_kitchen _DOMIN KIRAN NAMBAR TARHON MU DAN KARIN BAYANI DA BIYAN KUDIN SHIGA SAI A TUNTUBEMU TA: 08032964266_ _MUNA TURA KAYAN SNACKS DINMU A KOINA A FADIN NIGERIA, 100% TESTED AND TRUSTED.._ _UMMU AYMAAN’S KITCHEN IS YOUR NO 1 STOP KITCHEN FOR MOUTHWATERING DISHES, BAKES AND SNACKS_ *** "Sannu." Tace tana kallon fuskar ta, bayan ta bud'e kofar "Sannu, Amarya?" Murmushi Amrah tayi bata ce komai ba "Makociyarki ce anan baya, shine nace bari na shigo mu gaisa kafin ki shisshigo mana." "Oh Allah sarki, bismillah toh." Ta wuce gaba ita kuma tabi bayan ta, tana satar kallon gidan. Suna shigowa Afrah ta tashi daga kwanciyar da tayi tace "Bakuwa akayi ne?" "Eh anan baya take shine ta shigo a gaisa." "Sannu da zuwa." "Yawwa sannu, wacece Amaryar ne?" Karaf Afrah tace "Nice." "Toh bakya bace, ai amarya bata nuna kanta." Dariya suka saka gaba daya, tashi Amrah tayi ta kawo mata ruwa da lemo, ta dawo ta zauna, suka dan cigaba da magana duk da ba sosai Amran ke saka bakin ta ba sai dai tayi dariya kamar kowanne lokaci, Afrah ce ta zage kamar sun saba da matar wadda da alama itama Eh ce indai a magana ce. Ta dad'e sosai dan har aka kusa kiran sallar magriba sannan tayi musu sallama ta tafi. ***Kwance take a saman cinyar ta, kanta da ya sha attachment sosai ya bazo ya rufe saman fuskar ta, ranta a bace yake tun lokacin data samu labarin banzan yarinyar nan ta tare a gidan Sultan, sai da tayi kuka sosai da k'yar Anty Amina ta kwantar mata da hankali amma a k'asan ranta bata jin zata iya hakura da Sulthan, son da take masa bana wasa bane, shine k'adai guy din da komai nasa yayi mata, kuma ita a iyakar rayuwar ta kaf bata san wani abu wai shi babu ba, komai ta nema tana samu har ma da wanda bata nema ba, a haka ta taso babu kuma abinda ya chanja sai ma gaba da yayi dan tayi girman da ko ba'a samar mata abinda take so ba zata samar ma kanta.    Ringing din wayar Anty Amina ya dan dawo da ita daga tunanin da ta tafi, ta cire kanta kad'an tana duban Anty Aminar da ta kara wayar a kunnenta tana magana. "Kai har kun gama? Amma dai ba wucewa zakiyi ba ko? toh shikenan sai kin shigo." "Waye zai zo?" Ta tambaya tana tashi zaune "Wai Yaya Umma (Hajiya Umma) ce tazo wata seminar, na manta shaf munyi magana tace idan ta gama zata shigo sai ta kwana, sai dana ga kiranta wallahi na tuna." "Wow amma naji dadin zuwan ta... Kwana nawa zatayi.?" "Basa wuce kwana uku ai suke gamawa, ban dai sani ba amma." "Ko kwana nawa ne ma dai naji dadin zuwan ta." Tayi tsalle cike da farin ciki, Hajiya Umma was her favourite, tasan abinda zatayi ta samar mata abinda take so no matter how cost, brain dinta was sharp wajen figuring abinda ya kamata shiyasa tasu tazo daya sosai. Irin mutanen nan ce ita no nonsense saboda haka bata ragawa kowa, and she's filthy rich, komai da aji da kud'i take yin sa, kuma bata tsoron spending ko nawa ne ma evil plan dinta. Tana sauya kayan jikin ta, suka turo dakin tare, da wani irin mugun tsalle ta d'ane ta, suka saka dariya. "Umaimah bakya girma sam." Tace bayan ta sake ta sun zauna a gefen gadon "Allah ba zaki gane yadda nayi missing dinki ba, gashi yaushe ma muka rabu, amma dai i need you now more than ever ma, shisa na matsu kuma nakasa boye farinciki na." "Toh gani,me kika ajiye min?" Sai ta kalli Anty Amina ta turo baki "Auw ba za'a yi a gaba na ba kenan?" Tace tana tafa hannu "Toh dai kinji, magana ce tsakanin uwa da yarta." "Ai shikenan, idan tayi wari maji." "Aiko ba tayi warin da zaku ji." "Shikenan, muje kici abinci idan kika huta sai ki saurari yar taki." "Idan har zan iya cin wani abu ma kenan, ai sai naji uzurinta tukun." "Lallai toh sai kun fito." Ja musu kofar tayi, Umaimah ta kalli Hajiya Umma ta narke sosai, hawayen da take makalewa suka shiga saukowa a saman fuskar ta. "Ashssha, kuka umaimai? Kuka fa? Lallai ko menene babba ne, waye ya taba min ke?" "Sultannnnn..." Taja sunan tana sake matsar kwalla. "Sultan? Wanne Sultan waye shi waye uban sa a garin nan?" "Sultan fa,na gidan Mah-Mah." "Mtsw..." Taja dogon tsaki "Me yayi miki? Ni wallahi wannan yaron sam be min ba, kwata kwata yaron be min ba,da kika ce Sultan ni sam ma na manta da shi da rayuwar sa shiyasa ko kawo shi banyi ba wallah..." "Wani abun yayi miki hala? An kwaso mana dai jaraba wallahi..." "Kai Aunt, son sa fa nakeyi ni babu abinda yayi min." Ta tura baki cike da jin haushin abinda tace akan Sultan din. Tafa hannu Hajiya umma ta hau yi tana jera salati "Mun shiga uku, yanzu kema yaron nan sai da ya lashe mana kurwar ki, Innalillahi amma wannan yaro, chan ana fama da Safwan yaron nan har yanzu be dawo daidai ba, kema kuma yanzu ki bullo da wannan babban zancen bayan na zata zancen wasa ne sanda naji k'ishin-k'ishin da biki." "Toh wai ma ba yayi aure bane, me zaki ci dashi duk yaran dake kano da Lagos shi kad'ai kika gani kaf?" "Ni dai wallahi shi kad'ai nake so, kuma na zata zaki taimaka min shiyasa ma na sanar dake, shikenan zan nema wa kaina mafita tunda babu wanda zai fuskance ni, ai nima yanzu nayi girman da zan iya maganin matsalata." Sai ta tashi da sauri zata bar dakin, hannun ta Hajiya Umma ta riko ta dawo da ita ta zaunar tana kokarin saita kanta "Ba haka bane shalele, ki gane shi fa yaron nan babu wanda yasan asalin sa, ba'a ma san daga wacce nahiya ya taho ba, da zaki duba dai ko a cikin family ne, sai na shige miki gaba ayi komai..." "Allah ni shi kad'ai nake so, bana son kowa kuma ban damu ba ko daga sama ya fado, tunda mutum ne ba aljani ba ina sonshi a haka." "Trkashi..." Tace tana rike habar ta "Amma Umaimah...." "Shikenan,tunda babu wanda zai taimaka min, shikenan, amma duk abinda nayi kar azo daga baya ace min dan me." Ta juya mata baya tana harare harare, Tashi tayi ta dawo bangaren data juya ta kama hannun ta ta rike a cikin nata fuskar ta dauke da murmushi tace "Zan taimaka miki,if that's what you want, duk da bana son yaron nan sam,amma zanyi kokarin ganin na soshi saboda ke, zai zo da kansa neman aurenki, I promise you that." "Da gaske kike? Dan Allah da gaske?" "Na taba miki wasa ko na miki alkawari ban cika ba? Wait and see, sai dai bana so kiyi komai, ko kiyi taking wani foolish decision, ki jira ki gani kawai." "I love you, I love you so much, you are the best." Ta rukunkumeta tana kyalkyala dariya. ***Bayan su kawai yake iya gani, suna zaune suna magana daga gani kuma maganar da sukeyi me muhimmanci ce, amma shi maganar su ba damuwar sa bace, yazo ne akan maganar Ammin su, Alhajin yayi shiru be ce komai ba, ya ajiye su kawai ba wani bayani gashi ganin sa akwai wahala, anan ne kad'ai kake samun ganin sa freely shiyasa kawai yazo dan sun fara gajiya da ajiye sun da yayi. Ya kusa kaiwa inda suke yaji suna maganar da ta firgita shi, ya tsaya tsak yana jin duk abinda suke cewa, tsoron sa ya karu lokacin da mutanen da suke tare da Alhaji Safiyanu Madaki suka mike domin tafiya, wasu irin mutane ne marasa kyaun gani, kana ganin su kaga rashin imani a tattare dasu, da sauri Muhammad yayi k'asa da kansa yadda ba zasu iya ganin sa ba har suka wuce. Maimakon yayi abinda ya kawo shi sai ya samu kansa da bin bayan su da sauri har yana kokarin faduwa. ***Shafa'i da wutri tayi, ta kwanta a saman abun sallar wayar ta na gefen ta, tunanin shi take tana ayyana kalar girman abinda zai sashi irin wannan tafiyar rana daya tak da tarewar ta, tasan yadda Sultan yake son ta sosai, tasan kuma bashi da wani wajen da zai je bayan gidan su. Lallai akwai wani babban al'amari da ya saka shi yin komai, zata cigaba da tayashi addu'a Allah ya taimaka masa ya bashi nasarar komene yaje nema. Har wajen sha biyu tana kwance akan sallayar da yake akwai wuta, jin tana jin bacci ya saka ta tashi tayi nafila raka'ah biyu, ta dad'e a sujjada tana rokan Allah akan auren su da kuma ahinda ya sako mijin nata a gaba, sai da taji da gaske har cikin zuciyar ta tayi addu'a sosai sannan ta hakura, ta ninke sallayar ta dora ta saman bedside drawer ta cire hijab din ta ajiye, kallon Afrah da tayi d'aid'ai a saman gadon iska na hurata tayi, ta dan yi dariyar kwanciyar ta ta, ta cinye fiye da rabin gadon ko da kwanciya zatayi sai dai ta rabe ta gefen ta. Dakin ta fita ta rufo mata kofa kai tsaye ta wuce dayan d'akin. Tana shiga ta kunna hasken dakin, kamshin turaren sa tun ranar da ya tafi yaki barin dakin, gadon ta kalla da ido tana tuna komai, ta taka a hankali ta isa gaban gadon, ta tsuguna akan guiwar ta tana dora kanta a saman gadon. She's badly missing him, fiye da tunanin me tunani. Kamar da wasa taji wayar ta na vibration, ta cire kanta ta duba, sunan wanda bata yi zato ko tsammani bane,duk da tunanin sa da take a lokacin amma bata yi tunanin ganin kiran sa ba, a irin wannan lokacin kuma. Da sauri ta d'aga zuciyar ta na harbawa da sauri da sauri. Shiru tayi tana jin yadda ya ke sauke ajiyar zuciya da karfi. "My wife..." Ya kirata yana jin wani bangare na damuwar sa na melting, "Please talk to me, ko fushi kike dani?" "Um um..." Tace "I'm very sorry, very sorry." "Kana ina?" Tace sounding so worried "Gani nan ne Amrah, bansan inda nake ba, ban masan me yake shirin faruwa dani ba, kawai addu'a nake bukata,I'm very weak, abinda nake nema da na rasa tsawon lokaci na sameshi yanzu amma cike yake da sark'akiya, da zubar jinin bayin Allah. Kiyi min addu'a kinji, adduar ki kad'ai ce yanzu domin ke kad'ai nake da." "In Sha Allah babu abinda zai faru." "Amin..." "Me kike har yanzu bakiyi bacci ba? Are you thinking about me?" "A ah ni sallah nayi." "Sai kika kwanta kina tunani na ko? Gani na dawo kin bani warm hug irin na ranar nan ko?" "Laaa Allah ba haka bane.." "Toh yaya ne? Uhm?" "Kawai nazo nan ne Afrah ta tsare wajen kwanciyar, shine na dawo nan dakin, zan kwanta ma kenan ka kira." "Wow, magana ta, ta fito dai kina missing dina shine kika zo nan, Kinsan akwai unforgettable memories a dakin..." "La'ilah..." Tace tana danne fuskar ta. Dariya ya saka da dan karfi sai kuma ya rage murya "That night was one of the best night in my life baby." Da sauri ta toshe kunnenta, ta kifa wayar tana dariya k'asa k'asa. Sultan zai kashe ta da kunya. Tana jin sa yayi ta kiran sunan ta,taki magana har sai da ya gaji ya kashe wayar bayan yayi mata sai da safe. Tashi tayi tana dan zagaya dakin wani shauki ma kamata,hannun ta, ta harde waje daya tana rufe idon ta na ganin komai, duk da ba zata dorar da komai ba a ranar,amma itama tasan shine best night dinta.    Jona wayar ta, tayi jikin socket bayan ta gama zagayen ta kwanta tana kankame pillow sosai a jikinta. Wani irin bacci me dadin gaske ya dauke ta ba tare da ta shirya masa ba. ***Da yawan su suka zagaye katangar gidan, babban cikin su da wasu su biyu sai matar nan ta dazu data shigo gidan suka saka kai a cikin gidan suna yi suna bud'e kowacce kofa suka tarar har suka dangana da falon gidan. Afrah ce ta tashi firgigit ta waiwaya gefen ta, babu Amrah sai wajen ta, da sauri ta diro daga saman gadon tayi hanyar toilet, ta bud'e da sauri jin motsin na karuwa, bata ciki, da sauri tayi wajen kofa ta saka key sanda taji ana kokarin taba kofar dakin. Kafarta karkarwa kawai take jikinta na wani irin kad'awa da matukar tsoro sanda taji muryar mutane radau a falon suna magana k'asa k'asa. Kuka ne yazo mata tayi saurin saka hannu ta toshe bakin ta tana tunanin ina Amrah taje bayan a dakin ta barta har tayi bacci.    Jin maganganun na cigaba da tashi ta lallaba da sauri ta dauko wayar ta dake k'asan pillow ta shiga kiran Abba,no answer ta koma Kiran Ya Adnan, haka ta dinga bin numbobin kowa tana kira amma babu wanda ya daga. Toilet tayi saurin shigewa ta saka key ta tsugunna a wajen tana kuka da sauri da sauri tana sake kiran numbers din, tun tana kiran number close family har ta koma Kiran na nesa amma babu wanda ya daga. Ita ko Amrah tayi nisa sosai a baccin ta, baccin da take jin dadin sa sosai suka bud'e dakin, suka shiga, matar nan ta dazu ta matsa gaban gadon bayan daya daga ciki ya haske fuskar amrahn da touchlight me haske sosai. "Itace?" Ogan ya tambaya "Eh itace." Ta amsa, gefen gadon ya buga da kafa, hakan ya farkar da Amrah a firgice ta tashi, sai dai hasken da ya haske mata ido yasa ta koma da sauri tana saka hannun ta tana kare wa. "Who are you?" Tace da karfi tsoro na shigar ta "Tashi..." Taki tashi "Tashi!!!" Ya daka mata tsawa,da sauri ta tashi tana saka kuka. Hannu yasa ya finciko ta da karfi, kanta ya bugu da saman gadon ta kwalla wata irin kara saboda zafin da taji. "Oga maigida fa yace karmu dora mata yatsa fa." Wani daga bayan sa ya tuna masa deal din. "Na sani, bana son taurin kai ne." Ya amsa a dakile,kafin yace "Wuce muje." Da sauri ta tashi tana matse jikin ta,tana kuka, har sun fara tafiya ya juyo da sauri "Hadiye kukan nan stupid!" Tsit tayi tana jan numfashi, kofar dakin da Afrah take ce ta bud'e ta fito da sauri, tayi wajen Amrah tana kuka sosai, rike junan su sukayi suna kuka Afrah ta shiga basu hakuri "Dan Allah karku tafi da ita, dan Allah kuyi hakuri." "Shissh!" Ya dora hannun sa a saman lips din sa. "Shegiya idan kema baki mana shiru ba sai mun had'a dake, kuma wallahi muka tafi dake sai na yi tasting wallahi." "Dan Allah ku taimaka mana." Amrah ta fad'a tana jan numfashi, wani kallon banza ya bita dashi sannan suka kwashe da wata mahaukaciyar dariya. "Ku ma daina bata bakin ku, kuna hada mu da Allah dan wallahi babu abinda zamu fasa, tafiya zamuyi dake idan kinga kin dawo sai wannan mijin naki yayi mana abinda muke so." "Wuce muje dallah kuna bata mana lokaci." Rike ta Afrah tayi, yasa hannu ya fincike ta, ya shiga jan hannun Amrah tana turjewa har harabar gidan inda suka ajiye motar su, yawan su da Afrah ta gani ya kara tsorata kowanne su dauke da zungureriyar AK 47. Tana kallo suka saka Amrah a motar suka tafi da ita. Kamar zata zare haka ta dinga gudu a harabar gidan tana ihu, wanda ya jawo hankalin makota kowa da yayi luf sai da aka tabbatar sun tafi sannan aka shisshigo, wasu mata suka taimaka suka rike Afrah dan ko aina na jikin ta rawa yake kamar mazari.   Da asubah bayan sun tashi sallah Abba ya dawo ya dan kishingid'a a falo yana jin BBC hausa, ya jawo wayar sa zai duba date kawai yaga misscalls din Afrah da mugun yawa, tashi yayi zaune yana ji a ransa ba lafiya ba, yabi kiran zuciyar sa na karyewa. A lokacin Afrah na kwance a gidan makotansu na baya, wayar ta na kan ruwan cikin ta, tana ta kuka kiran ya shigo, ta tashi a zabure ta dauka tana fashewa da kuka. "Lafiya Afrah?" "Amma barayi sun shigo sun tafi da Amrah cikin dare." "Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun." Ya mike tsaye jiri na daukar sa. Umma da ta fito da waya a hannun ta tana kallon kiran da Afrah tayi mata, tayi saurin karasowa jin Abba ya rafka Innalillahi. "Yanzu ke kina Ina?" "Toh gamu nan." Yace yana ajiye wayar da sauri "Prof Lafiya kuwa?" "Babu lafiya Aisha, Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun, barayi sun shiga sun tafi da uwata Aisha." "Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun." Umman ta fashe da kuka, "Na shiga uku, wannan wanne irin tashin hankali ne..." "Karmu bata lokaci, muje dan Allah." Da sauri suka fita, lokacin Adnan sun gama waya da Afrah shima ya tawo da sauri suka hadu a hanya, suka dunguma suka tafi unguwar umma na kuka sosai. ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥©Hafsat Rano _Page 33_ ***Fitowa yayi jin kamar motsi a falon,hannu yasa da sauri ya toshe hancin sa ganin kwalaben giya baja-baja a tsakiyar falon, idon sa ya sauke akan doguwar kujerar da yake kwance, a matukar buge yake yana magana ciki-ciki alamun baccin ya soma daukar sa. K'asa karasawa Sulthan yayi yadda mamaki ya kamashi, dama dai tun ganin da yayi ma Yariman yasan ba kansa kalou ba yadda yake magana ma, amma beyi tunanin haukar tasa ta kai haka ba. Komawa yayi ya rufe kofar ya kwanta. Be wani yi baccin sosai ma yaji ana kira a masallacin cikin Masarautar, toilet ya shiga yayi alwala ya fara yin Raka'atanul Fajr, ya zauna yana karatun alkurani a hankali, har sai da yaji ana kokarin tada ikama sannan ya tashi yayi Fajr. Turo kofar akayi, ya tsaya a kofar yana rik'e da kugun sa yana kallon Sultan dake daure igiyar takalmin sa, murmushi ne dauke a fuskar sa yana kallon Sultan din da irin karfin halin sa na shigowa har shashen sa yayi wa kansa masauki. Ya yarda da gayen ba da wasa ya zo ba Amma zai nuna masa ya fishi sanin sarauta da ma bariki gaba daya. "Ka sauya shawara kenan?" Yace yana sauke hannayen nasa. D'aga kafad'a Sultan yayi sannan yace "As you can see..." "Madallah kayi kyaun kai." "Me kake bukata a wajena?" Sultan yace yana masa kallon cikin ido sosai. "Bana bukatar komai kamar yadda kai kake bukata a wajena." "Kamar me kenan?" "Kana tunanin shiga turakar Maimartaba abu ne me sauki ko?" "A tunani ba." "Toh Ba Abu bane me sauki kamar yadda kake tunani, amma zan iya taimaka maka, ka dauki abinda zaka dauka ka bar Masarautar nan idan ka yarda." Shiru Sultan yayi kamar ba zai ce komai ba, sai kuma ya dubi Yariman yana takowa zuwa gaban sa, "Inaso na shiga yau da daddare, idan ka shirya sai ka taimaka, ni kuma zan fita kamar yadda ka nema." "Shikenan, za'a shigo da kayan karin kumallo, sai kaci ya huta zuwa daren, na barka lafiya." Be jira ta cewar Sultan ba ya ja masa kofar yana wata irin tafiya cike da kasaita. Hannu Sultan ya saka a cikin gashin kansa da ya soma taruwa ya birgita shi yana jin kamar yayi ihu, baya jin dadin jikinsa tun da ya tashi amma zai kokarin karfafa kansa, yaki ne babba a gaban sa da dole sai ya jajirce ya tsaya a kan digadigansa sannan zai yi nasarar sauke mulkin zaluncin da ake a wannan Masarautar. ***Gaba d'aya hankalin su ya tashi, duk wanda Afrah ta kira a daren nan sun samu labarin sace Amrah, hankalin Safwan yayi mugun tashi dashi da Adnan da Abba suke yawon zuwa police station da wasu wuraren da ya kamata, idan ka gansu zaka dauka basu da lafiya ne gaba dayan su yadda duk suka chanja halitta suka koma wata kala ga wahala ga rana ga yunwa sosai. Babu wani da yake da sukunin saka wani abu a cikin su babu ma me tunanin nan, su umma da sauran yan uwa na gidan ana jimama, Afrah kuwa zazzabi ne ya rufe ta sosai sai da aka yi mata allura sannan aka samu tayi bacci. Har la'asar ana jiran kiran wayar su kamar yadda akayi tunani amma babu wanda ya kira, hakan ya sake daga hankalin kowa musamman Ummah da Afrah dan lokacin ta farka. Zuwan Hajiya ya sake hargitsa wajen, kuka take tana kiran sunan Sultan tana cewa ya cuce su, duk hankalin mutane ya koma kanta wadanda ma basu san komai akai ba suka bada hankalin su akanta, sosai take kukan tana cigaba da cewa "Ni dama chan ban yarda da yaron nan ba, Yaron da aka ce ba'a san asalin sa ba, babu abinda ba zai iya aikatawa ba, ban yarda wasu ne suka dauke Amrah ba, sai dai shi da kansa ya sace ta." "Haba Hajiya, haba Hajiya ya za'a yi mutum ya sace matar sa, dan Allah ki daina fad'a." Wata Kanwar Abba tace tana kokarin saka Hajiyar tayi shiru, amma maimakon haka sai ta sake tunzura ta "Idan bashi ya sace ta ba yana Ina? Wanne irin abu ne zai taso masa haka ya tafi ya bar yarinya da kai ta kwana daya, kuma duk kiran duniya an kira wayar sa a kashe, sai ki gayan gidan uban da yaje ko shima sace shin akayi?" "Kiyi hakuri dan Allah, ko ma menenn Allah zai bayyanata cikin koshin lafiya, zargi yanzu duk bashi gane Addua ce kawai mafita." Wata yar uwar Umma da takaici ya kama tayi maganar tana jin kamar ta tashi ta bar wajen. Ganin babbace yasa Hajiya yin shiru bata sake cewa komai ba. Mutanen da suka shisshigo jaje da yan uwa suka shiga tattaunawa akan abinda hajiyar tace kowa na tofa albarkacin bakin sa. ***Shiru dare ya tsala sosai baka jin karar komai sai daga chan nesa,idon Sultan biyu yana jiran shigowar Yarima kamar yadda yace masa dazu, yana yi yana duba time din wayar sa da ya saka ta a flight mood, yana so ya kira Amrah amma baya so ya tashe ta daga bacci, ba kuma yaso su fara waya Yarima ya shigo. Jin an taba kofar yasa ya daga kansa, kananan kaya ne a jikin sa da pcap daya sauko da ita zuwa saman fuskar sa. Girgixa kai Sultan yayi da Allah ya shirya a ransa da tabbas Yarima ba mutumin arziki bane yadda yake abubuwan sa. Ba zai so wani abu ya hado su dashi ba dan yasan mutane irin su nada hatsari musamman mutum da yake mu'amula da kayan maye. Be jira abinda Yariman zai ce ba ya mike "Ka shirya ko?" "Eh." "Ok muje." Yace yayi gaba, Sultan yabi bayan sa, suka fito a tare, da sauri bayin dake kofar wajen suka taso, yarima ya daga musu hannu duk suka koma da sauri. Tafiya kad'an sukayi suka isa, kamar yadda yake a jikin zanen Masarautar da yake tare dashi haka yake a zahiri, da ido ya Kalli tsari da kyaun wajen kamar a wata k'asa, katon gini ne na gaske wanda ya kasance bangaren Maimartaban, shuke shuke ne masu matukar kyau da suka sake kawata wajen sai wasu fitulu masu haske mara karfi kala kala suka sake kawata wajen sosai. Wajen yafi kowanne bangare yawan masu tsaro dan ciki suke dam suna kaiwa da komowa, yana cikin tsarin Maimartaba Sarki Bello Moddibo Saji, yawan masu tsaron sa Wanda yake jin kamar yawan nasu shine garkuwar da, kamar babu abinda zai same shi tunda suna zagaye dashi, sai dai be sani ba, babu abinda suka isa suyi masa akan abinda ya Allah ya kaddaro masa zai faru dashi. Basu yi mamakin ganin Yarima a wannan lokacin ba, bayan tafiyar sa kenan daga wajen mahaifin nasa, amma babu wanda yake da Ikon hanashi ko tambayar shi abinda ya sake dawo dashi din, hakan kamar ganganci ne wanda zai iya jawo ma mutum rasa ransa ma baki d'aya. Be amsa gaisuwar da suke ta faman jera masa ba, wadda take shiga ta fita ta dayan kunnen sa saboda rashin muhimmanci ta gareshi har suka dangana da babban falon Sarki Bello Moddibo Saji. Tsayawa yayi ba tare da ya shiga ba, ya kalli Sultan dake bayan sa yayi wani kayataccen murmushi, wanda ya bar Sultan a tunani kala kala, be yi magana ba ya kutsa kai cikin falon Sultan na biye dashi. Babu ko d'igon haske a ciki, sai da ya nemi ma kunnin hasken dakin ya kunna haske ya mamaye ko ina. Babu kowa a falon sai karar na'urar sanyaya daki da ta cika wajen sosai wani irin sanyi me ratsa bargo na huda su. Tsum Sultan ya tsaya yana sake karewa falon kallo yana son ganin wani abu da zai sake bashi haske akan abinda yake shirin yi. Sai dai babu komai kasancewar babu wasu shirgi ko tarkace a falon komai neat a muhallin sa. Da hannu Yarima ya nuna masa wata kofa bayan ya matso kusa dashi sosai, "Wannan itace kofar da zata kaika turakar Maimartaba, kuma anan zaka samu abinda kake nema, kayi sauri bamu da lokacin batawa zan jira ka anan." Daga masa kai Sultan yayi yana sake damke barin zoben dake hannun sa sosai ya nufi kofar bakin sa dauke da addu'a. ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥 ©Hafsat Rano Page 34 ***Duhu ne sosai a dakin wanda yasa har baya ganin gaban sa, dawowa yayi da baya ya bud'e kofar hasken falon na ratso wa ciki kad'an, tunawa yayi da wayar dake aljihun sa, ya ciro ta yana rufe kofar sannan ya kunna dim light na wayar ya shiga haskawa.  A saman wata doguwar couch ya hangi mutum a kwance sambal, hannayen sa sun kusa sauka k'asa, da dan sauri ya karasa wajen ya haske shi, yayi saurin ja da baya ganin Sarki ne a wani irin yanayi kamar me rai kamar mara rai, tsoro ne yaji ya shige shi, idan har Yarima Bilal zai iya yiwa mahaifin sa haka, waye zai bari kaf duniyar nan? Amma kuma sai wani tunani ya darsu a zuciyar sa, anya kuwa dan sa ne na gaskiya? Domin dai a yadda mutane suka lalace da son duniya da son mulki babu abinda ba za zasu iya aikatawa ba. Idan har d'a zai iya aikata wata cutarwa  ga iyayen sa, toh kuwa wacce irin duniya ce muke ciki haka. Amma kuma sai yayi tunanin ai dama shi fa sharri dan aike ne, duk inda yaje zai dawo, kuma shiyasa ake so mutum ya aikata alkhairi a ko yaushe, idan aka bi kidddigar mutanen da Sarkin ya zalunta, toh tabbas ba zai tsira ba, ba zai tsira a wajen kowa ba kuwa ciki hadda iyalansa da yayi komai saboda farin cikin su.   Girgiza kai yayi ya wuce zuwa abinda ya kawo shi, akan guiwar sa ya durkusa bayan ya tattare hannun rigar sa zuwa damtsen hannun sa. Bismillah yayi ya shiga jawo akwatin da yaji ta da wani irin nauyi, beyi garaje ba ya cigaba da jawo ta a hankali har ya gama fito da ita gaba d'aya, dan matsawa yayi baya da sauri ganin wani haske me karfi ya fito daga ciki, yayi sama. Sauke ajiyar zuciya yayi yana addu'a a fili a hankali, ya riga ya san ba karamin abu ne a cikin akwatin ba. Komawa yayi ya sunkuya ya d'aga murfin da yake a bud'e babu padlock a ciki sai dai alamar shi a jiki. Tarkace ne sosai a ciki tun daga kan takardu, wukake da wasu kayan a nannade,sai wasu irin abubuwa kamar layu a nannade suma da yawan gaske, daga gefe wani mukulli ne na karfe an masa ajiya ta musamman,kusa dashi wata yar karamar akwati ce, karama sosai an nannade ta da wani bakin kyalle me sulbi.   Ada kafin ya iso wajen tunanin sa zoben nan ne kad'ai a ciki, sai dai ganin abubuwa da yawa yasa shi son sanin dukka, sai dai yasan bashi da ishashen lokacin yin komai amma still yana da bukatar dubawa, layoyin nan ya kwashe tas ya zuba cikin aljihun sa. Sannan ya maida hankalin da yafi karkata akan karamar akwatin nan, yayi saurin ciro ta sannan na warware nad'in da akayi mata, a rufe take da mukulli, ya sake ciro mukullin da ya gani a kusa da ita ya saka a jiki ya bud'e. Kamar yadda yayi tunani hakan ce ta kasance,zoben ne a ciki, an dora shi akan wani jan kyalle me kyau da sulbi shigen wanda aka nannade akwatin dashi, sai dai kamar yadda ya sani babu wani bangare na jikin zoben ya saka shi ciro wanda yake tare dashi, yayi kokarin had'e su, kamar yadda zaka hada karfe da mayen karfe haka barin ya hade da jikin dayan barin ya bada zobe cikakke, a daidai lokacin yaga Maimartaba ya motsa k'ad'an fuskar sa na daurewa sosai bakin sa na yin motsi alamar yana son fad'ar wani abu. Kallon zoben Sultan yayi ya runtse idon sa ganin wani irin haske da zoben ki fitar wa, be taba hasashen shi a cikin irin wannan badakalar ba sai gashi ya samu kansa dumu-dumu a ciki, bismillah yayi ya zura zoben a babban dan yatsan hannun sa, wani abu ya shiga ji na yawo a saman kansa,  zuciyar sa na sake karfi sosai yana jin kamar tana ingiza shi zuwa wani abu mai girma. Jingina yayi da bangon dakin saboda yadda yaji dakin na juya masa kamar zai fado akan sa ya dafe kan sa da hannun sa dayan yana karanto duk addu'ar da tazo bakin sa, a hankali ya sulale a wajen yana jin idonsa na nauyi sosai, kad'an kad'an ya dinga rufewa har ya rufe gaba daya. Shigowa Yarima Bilal yayi tare da wata mata, ya kunna hasken dakin yana murmushi zuciyar sa fes, bai taba tunanin zai samu cikar burin sa da sauki haka ba, sai gashi komai ya zo masa da mugun sauki, gefen da SULTAN ke yashe ya kalla yayi dariya sosai sannan ya kalli akwatin da ya jima yana kulafucin ta, kasancewar bashi da wata nasaba da Masarautar yasa ya kasa samun yadda zai kai hannun sa kanta, sai gashi a daidai lokacin da yafi bukatar ta, Musa amintaccen Yaron Safiyanu Madaki ya kirashi ya guntsa masa kyakkyawan labarin da ya sanya shi cikin matukar farin ciki shi da mahaifiyar sa, ya kuma yi amfani da damar wajen amfani shima da Sultan din kamar yadda Madakin ke kokarin yi, sai dai shi yayi sanya a aikin nasa don kuwa sai dai ya sake wata dabarar, kujerar Masarautar Saji yanzu ta Bilal ce, Muhammad Bilal Bello Moddibo Saji a zahiri, a bad'ini kuma*Muhammad Bilal Surajo*  Dukawa yayi ya fiddo takardun kamar yadda suke, ya dauke su ya mika wa ma mahaifiyar tasa sannan ya karbi na hannun ta wanda suka kasance iri daya sak ya nufi inda Maimartaba ke kwance ya farfado amma kamar be san me yake wakana ba, kama hannun sa yayi da karfin gaske ya saka masa biro, sannan ya dora a daidai wajen da zai saka hannu, da sauri Maimartaba ya dora hannun sa akai sannan ya saka hannu kamar yadda Yariman ya bukata. Wani irin farin ciki ne ya ziyarci zuciyar sa, ya mika mata da sauri yana cewa "Kalli kiga, ta saka hannu, ya saka hannu wallahi, shikenan an gama, Kurunkus." Yace yana zare ido kamar sabon mahaukaci. Karba tayi ta duba ta saka dariya itama "Lallai sai yanzu nasan na haifi d'a, sai yanzu nasan da cewa kai jini na ne da gaske." Durkusawa yayi ya dauko wata wuka, masu, da wani sanda, sai doguwar takarda dake a nannade ya warwareta, yana karanta dokokin Masarautar Saji yana dariya. "Wannan dokar tasa ce, daga yau tawa zan shinfida yadda naso." "Kayi min daidai." Tace tana duba kayan, komai yacika, wadannan sune shaidar da take nuna sarautar Masarautar, kuma ana bawa duk sarkin dake kan mulki, kamar wani sign ne na Masarautar tun fil'azal "Ina kayan karka manta dasu fa." "Af kinga na manta shaf." Yace yana ciro kayan ya warware su. Kayan sarauta ne tun daga kan babbar riga da rawani da sauran su, kayan akan bawa duk sarkin da zai hau mulkin ya saka su a ranar da za'a yi nadi.    Hasaso kansa ya shiga yi a cikin kayan gobe, yasan zai fi kowanne Sarki haskawa a cikin kayan kuwa saboda shi suka dace, ganin ya samu dukkan abinda yake bukata yasa ya saka kafa ya tura akwatin karkashin gadon, bashi da bukatar zoben duk da shine abu mafi girma a cikin sarautar Masarautar,amma kasancewar babu barin ya saka har ya bar Sultan din ya dauka domin babu amfanin da zai yi idan babu cikon sa.    Fita sukayi suka bar Sultan a dakin, daga bisani wasu fadawa suka zo suka ciccibe shi bisa umarnin Yariman suka maidashi shashen sa suka saka shi cikin dakin da ya tare suka rufe. ***Da sanyin safiya aka shiga gyara Babbar Fadar Masarautar wadda sarki be fiya zama a cikin ta ba idan ba wani abu me muhimmanci za'a yi ba ko nadin sarauta. Duk manyan Masarautar suna kan hanyar zuwa fadar bisa ga umarnin Sarki kamar yadda dan aiken ya sanar dasu, babu wanda be yi mamaki a cikin su ba,dan ba haka Sarkin ya saba yi musu ba.     Kafin kace me ciki da wajen fadar ya cika taf, dan layi layi yarima ya saka me shela sanar da baban taro wanda ake bukatar kowa ya hallara. Duk manyan yan fada sun gama isowa sun zazzauna suna jira fitowar Sarki suji dalilin taron gaggawa haka da kuma ya had'a da mutanen gari ma. Sun dan dau lokaci a zaune kowa na tattaunawa da na kusa dashi kofar da aka san Sarkin na shigowa ta cikin ta, sai dai a maimakon aga Sarkin sai suka ga Yarima ya fito cikin shigar da ta saka da yawan su tsorata, kai tsaye kan karagar Maimartaba ya nufa ya haye fuskar sa daure tamau ya saka wani bakin glass a saman rawanin da ya kusan cinye kafatanin fuskar sa. "Lafiya Yarima?" Waziri ya tambaya yana mikewa tsaye. Da hannu Yarima ya bada umarni wasu fadawa suka shigo da sauri suka zube bayan sun ajiye kayan dake hannun su wanda Yariman ya dauko su a cikin akwatin nan. Da mugun mamaki duk suka kalli Yariman, sanin muhimmanci kayan d kuma abinda hakan ke nufi. Tsam suka yi kowa ya kasa furta komai har sai da Yariman da kansa ya taso sannan ya dauki takardar da Sarki ya saka hannu ya mika musu yana murmushi. "Ina so ayi sauri a aiwatar da abinda yake cikin takardar nan, bana so a bata lokaci." Daya bayan daya suka dinga karbar takardar suna dubawa, gashi nan bayanin komai a rubuce ga kuma saka hannun Maimartaba da kansa. Sosai kansu ya daure suka cika da mamakin abinda zai saka Maimartaba murabus ya dora Yarima bayan kowa yasan sarautar itace rayuwar sa.   Babu lokacin bincike ko bin kwakkwafi domin komai da ake bukata Yariman ya gabatar dashi, babu bata lokaci aka shiga bikin nadin sarauta, aka nada Yarima Bilal a matsayin sabon sarkin Masarautar Saji. Mutane da yawa ransu be so ba, musamman da kowa yasan waye Yariman da mugun halin sa, amma basu da bakin magana tunda suka kori Sarki Usman Muhammad Moddibo, shikenan komai ya lalace musu,Komai baya tafiyar musu yadda ya dace, sun dauki hakan a matsayin hakkin da suka dauka na adalin Sarki me son talakawan sa, me dora duk wata bukatar su a saman tasa. Sun jima suna saka ran dawowar shi, har suka hakura suka fitar da rai. Sai gashi yanzu a maimakon su samu chanji me kyau daga mulkin Sarki Bello, sai gashi sun kuma samun wanda yafi shi muni ta kowacce fuska, domin duk mutumin da aka ce mashayin giya ne, toh babu kuma sauran wanda za'a hada shi dashi indai a kima da mutunci ne, domin mashayi babu abinda ba zai iya aikatawa ba.    Bayan an gama nadin ne wasu daga ciki suka bukaci ganin tsohon Sarkin, amma sai Yarima ya nuna musu baya nan wata tafiya me muhimmanci ta taso masa a daren jiya ya tafi, duk da basu yarda da hakan ba, amma babu wanda ya isa ya musa,haka duk suka ja bakin su sukayi shiru dan abinda zai biyo baya ba zai kyau ba.   *** Da k'yar ya tashi yana jin kansa yayi wani irin mugun nauyi, leben sa ya bushe jikin sa yayi wani mugun sakayau kamar wanda aka kwashe masa kayan cikin sa, yunkurawa yayi ya tashi yana tuno abinda ya faru da shi last kafin ya daina gane komai, da sauri ya kalli hannun sa, ya kurawa zoben ido yana kallon yadda yake walwali sosai. Komai da ya faru dashi ya faru ne akan zoben nan, saka shi da yayi a hannun sa shine dalilin da ya sume har ma ya dau tsahon lokaci kafin ya farfado. Be san wanne irin zobe bane haka, amma yana da yakinin akwai wani abu babba game da zoben, wanda yafi tunanin zai iya rusa dukkan Masarautar idan ya fad'a hannun da bai dace ba, tsawon lokacin nan karfin zoben ya ragu ne saboda kasancewar sa a rarrabe, amma yanzu da ya zama a waje daya, be san me zai faru ba kuma, be kuma san wanda zai tambaya ba kuma.   Zagaye dakin ya shiga yi yana tunani abubuwa da yawa, gefe daya kuma zuciyar sa na azalzalarsa da son wani abun da be san menene ba. Jikin window ya matsa ya yaye laluben yana kallon waje, takun tafiyar da yaji yasa shi waigo wa da sauri. Shigar sa ta jiya ta banbanta da ta yanzu, inda yake cikin shigar Saraki, fuskar sa a rufe da rawani, sosai shigar ta burge Sultan a karo na farko a rayuwarsa har yaji yayi sha'awar hakan, kauda tunanin yayi ya fuskance shi ganin yazo daf dashi. "Idan ka shirya akwai wanda zai maka jagora zuwa hanya, ina fatan zaka cika alkawarin ka na barin Masarautar." "Ban taba yin alkawari na saba ba, saboda haka bazan fara a yanzu ba." "Madallah." Yace yana matsawa "Ba lallai mu sake haduwa ba, saboda sake shigowar ka nan din abu ne me matukar wuya kasancewar yanzu nayi maka nisan da sai dai hange daga nesa, amma ka sani, idan har kayi kokarin yin wani abu, ka tabbata zan maka abinda baka taba zato ba." "Wannan din gargadi ne ko shawara?" Sultan yayi masa tambayar yana d'age gira. "Gargadi ne kuma umarni ne daga Maimartaba Sarki Muhammad Bilal Bello Moddibo Saji." "Maimairta?" "K'warai, kamar yadda kaji." Juya maganar Sultan ya soma yi da sauri da sauri a cikin zuciyar sa, kenan Bilal yayi amfani dashi ne wajen samun sarauta, kenan dama shi abinda yake bukata kenan, toh amma mesa be damu da zoben ba shi kamar yadda Madaki ya damu dashi fiye da sarautar?   Zagaye shi yayi ransa na baci ganin yadda yayi wasa dashi "Kayi amfani dani ka samu sarauta,kana tunanin ka fini wayo kenan? Ko kana tunanin bansan abinda nake ba?" "Kusan haka ne, duk yadda ka dauke shi toh haka din ne, tunda na har ka yarda nayi Amfani da kai toh kuwa duk ta sigar da ka kira hakan daidai ne." "Lallai ka tafka babban kuskure." Sultan yace muryar sa na sake fito da bacin ran da yake ciki sosai. "Dakata!" Ya daka masa tsawa "Karka manta da wanda yake gaban ka, bare kace zaka fadi duk maganar da tazo bakin ka, zan iya sa a rufe min ka kare rayuwar ka a kurkuku, dan haka ka iya bakin ka." Yana kaiwa nan ya fice daga dakin, dafe kai Sultan yayi yana jin kamar ya kurma ihu, anyi amfani dashi wajen sake tura bayin Allah a cikin halin tashin hankali, "Ya Allah!" Ya furta da karfi yana zubewa a wajen. "Sarki ya bada umarnin muyi maka rakiya zuwa mararraba." Daya daga ciki yayi maganar, be ce musu komai ba, ya tashi ya tattare komai dinsa ya tura a cikin jakar sa, ya rataya ta suka fito bayan sun rufe shashin gaba daya.   Kai tsaye kofar Masarautar suka nufa, ba tare da ya sake waiwayen komai ba ya fice daga ciki yana ji a ransa zai dawo nan kusa, zai dawo idan ya gama tabbatar wa kansa da shi din waye a Masarautar!   A chan k'asan wata bishiya suka tsaya dashi sannan suka koma, matsawa yayi da sauri jikin bishiyar ganin mutane a zaune. "Maman Yara?" Ya kira sunan ta, da sauri ta waigo, fuskarta ta fad'ad'a da farin cikin ganin sa. "Sultan!?". "Ya akayi kuka zo nan?" Yace yana kallon matar dake kwance akan kafar maman yaran idon ta a rufe tayi masifar ramewa ta d'ashe kamar ma bata da jini. "Muna kwance cikin dare wasu su biyu suka zo, suka fito damu suka kawo mu nan suka tsaya suna gadin mu har gari ya waye, daf da zaka iso wajen nan suka bar nan." Shiru Sultan yayi, kenan da gaske Yarima Bilal yake da yace baya bukatar ya sake dawowa, yasan kuma tabbas zai dawo saboda su shiyasa ya fito masa dasu. "Taimaka mata ku dan matsa bari na samo mota." Yace kawai ba tare da yace komai akan maganar ba, wayar sa ya ciro ya kunna ta, messages suka fara rige-rigen shigowa, na Madaki da ya shigo karshe ya fara budewa "Idan ka shirya bani abinda nake so, ni kuma zan baka matar ka, idan kuma ka shirya hanani, ka sani matar ka na hannu na." "Innalillahi, Amrah!" Ya furta da sauri, ya fita daga kan message din Madakin ya shiga sauran. *Afrah* _"Ya Sultan wasu sunzo sun dauke Amrah#Sobs"_ *Safwan* _"Where are you, wayar ka off, call back ASAP."_ _"Are you ok? Kana ina please ka kunna wayar ka."_ Kasa cigaba da karanta messages din yayi, kafar sa har rawa take ya tafi da sauri ya tsallaka titi, ya tawo da wani me mota, Maman yara ta taimaka aka saka Aminatu a motar, suka dauki hanya yana ta faman kira duk taki shiga. Hankalin sa ya kai kololuwa a tashi, be so Madaki ya saka wani nasa a cikin harkar su ba, ba zai barshi ba wallahi idan har yayi wani foolish abun. Sake ciro wayar yayi ya tura masa message _"Karka kuskura kayi wani abu, idan har wani abu ya samu iyali na, ba zan barka ba Wallahi."_ Ya tura masa sannan ya sake gwada kiran wayar Safwan, yayi sa'a kuwa ta shiga. "Hello Sultan, kana ji?" "Ina ji Safwan, yanzu na ga message dinka..." "Kana Ina? Wayar ka a kashe." "Na dan shiga matsala ne,kayi kokarin kwantar wa su Umma hankali, zan dawo da Amrah safe and sound, nayi wannan alkawari, Amma pls ka ji dasu, nasan suna cikin tashin hankali." "Shikenan, please come back soon, abubuwan sun fara baci, Hajiya ta dora laifin a kanka,Infact ka shiga cikin suspects bayan bayanin da Hajiya ta bayar a station." "Ya Salam, shikenan Safwan, ka kula da komai, ina hanya da na shigo zan maka waya ka fito mu hadu." "Owk Allah ya kiyaye." Ajiyar wayar yayi, ya kwantar da kujerar da yake kai yana kulle idon sa. ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥  ©®Hafsat Rano Page 35 Zafafa Biyar na kud'i ne! ***Kai tsaye asibiti ya wuce dasu, be shiga ba ya kira wani colleague din sa ya had'a shi dasu sannan ya roke shi da aka basu muhimmiyar kulawa musamman dayar matar dan ba karamar jigatuwa tayi ba.    Kiran Safwan yayi, ya fad'a masa inda yake so yazo, cikin kankanin lokaci ya iso tunda dama shi yake jira tun dazun. Da yake a mota yake sai kawai Sultan din ya shiga ba tare da Safwan din ya fito ba, yana shiga ya kwantar da kujerar motar ya jingina da kansa da yake masa masifaffen ciwo ga wani abu me nauyi daya tokare masa makoshi ya hanashi hadiyar yawu. "Ina ka shiga duk kwanakin nan?" Dagowa yayi ya kalli Safwan din, wanda shi ma ya zubawa Sultan din ido ganin masifaffiyar ramar da yayi cikin yan kwanakin da yayi be ganshi ba, sosai ya kadu da ramar Sultan din tun da yasan ba karamin abu bane zai sashi irin wannan ramar farat daya bayan kuma shi yayi tunanin tunda ya samu Amrah komai zai tafi daidai. "Ina cikin matsala Safwan, ina kuma bukatar taimakon ka a matsayin ka na dan uwana kuma cikakken lawyer,ko da abun zai kaimu ga kotu nasan zaka tsaya min." "Wanne irin abu ne haka dan uwana ya shiga bayan nasan shi din ba me yawan hayaniya bane balle fad'a,menene yake faruwa ne wai dan Allah!" "Nasan inda Amrah take..." "What? Toh me muke bata lokaci kuma?" "Dole sai mun bi komai a sannu idan muna so mu karbo ta daga hannun shi." "Waye shi?" Safwan ya tambaya mamakin Sultan din na cikashi "Safiyanu Madaki." "Safiyanu Madaki? Ina kuwa na taba jin sunan nan?" Da sauri Sultan ya mike ya zauna "Ka taba jin sunan? Aina? Zaka iya tunawa?" "Umm..." Yayi shiru yana tunani "Yes! A cikin wasu takardun Daddy ne, ban dai ga ainihin abinda takardun suka kunsa ba, amma tabbas naga sunan wajen saka hannu, amma zai iya yiwuwa bashi din bane sunane yazo daya." "Ok ok, Allah sa hakan ne, dan bana jin akwai wani abu da zai hada Daddy da wannan da na sani." "Wai menene ya had'a ka dashi, kuma ma yaushe kayi masa wannan sanin?" "Safwan, Ina tunanin na kusa sanin ainihin waye ni..." Yace yana lumshe rinannun idonsa da suka turu da ja sosai "Kamar ya? Ban gane ba dan Allah ka ganar dani, me kake boye min ne? Na chanchanci haka kuwa Sultan." "Zan fad'a maka, dama dole zaka sani ko ba yau ba, yanzu dai bamu da ishashen lokacin labari, yadda Amrah zata fita daga matsalar nan ce kawai yanxu abin tunani, it's my battle, ni kad'ai bana so ya shafi duk wani na kusa dani." "And she's your wife, ni kuma I'm your brother, kaga kuwa duk abinda ya shafe ka ya shafe mu." Yace yana kallon sa straight in the eyes dan ya gane haushin da yaji da yace battle dinsa ne shi kad'ai. "I'm sorry, ba wai wani abu nake nufi ba..." "Yanzu menene abin yi." Yace yana ignoring maganar. "Wannan yake so!" Sultan ya mika masa hannun sa da zoben yake jiki "Zoben nan yake so, sannan ne zai kyale ta." "Menene special akan zoben haka?" Daga kafad'a Sultan yayi "Ban sani ba, kawai nasan dai daga jiya zuwa yau ina jin wani strong bound Tsakani na da zoben, ina jin kamar dama chan it belongs to me, kamar dama ya bata ne yanzu na dawo dashi. Yanzu dai nasan Madaki yana jiran zuwa na, ko kira na, nasan ya shirya wa hakan, dole ni kuma nayi playing nasa at his own game, kamar yadda ya chanja tsarin shiga Masarautar saboda wasa da tunanin sarkin, haka nima zan masa." "Kana ganin barin ta a wajen ba zai zama matsala ba toh? Ba zai mata komai ba?" "Babu abinda zai mata, trust me nasan abinda yake so, so ba zai taba yin abinda zai saka ya rasa damar sa a yanzu ba." "Shikenan, amma yanzu kana cikin wanda ake nema, so be kamata kazo gida ba, ya za'a yi?" "Mu hadu same time same place gobe, karka bari ko Adnan yasan dawowa ta, sai dai kawai na kawo musu ita." "Ok tam." "Ina zan kaika yanzu?" "Maidani asibiti ina da patients." "Ok. Yace ya juya motar zuwa hanyar asibitin. Har gaban wajen ya kaishi, sai da yaga shigar sa sannan ya juya ya fita daga asibitin yana jin duk babu dad'i. Ya san abinda ya faru na daya daga cikin abinda yasa Sultan din shiga wannan matsalar, da Mah-Mah bata matsa masa ba da babu abinda zai sakashi tunanin sanin abinda yake rufe tunda iya tsawon zaman sa dashi be taba nuna hakan ba. ***Tura wa yayi ya shiga bakin sa dauke da sallama bayan ya shiga wajen colleague din nasa ya ji progress din, ya kuma bashi room number da suke da sauran abubuwan da za'a bukata, takardar biyan kudin ce a hannun sa da sauran abubuwan bukata ciki hadda jini da za'a kara mata. A saman dankwallin ta tana Sallah ya samu Maman Yara, ya tsaya ya jingina da bangon dakin har ta idar, juyowa tayi ta fad'ad'a fara'ar fuskar ta. "Sultan sannu kaji?" Murmushi yayi ya matsa ya zauna akan kujerar dake ajiye a gefe kasancewar dakin su kad'ai ne private room, "Ya jikin nata?" Yace yana kallon kan gadon "Da sauki wahala ce kawai." "Allah ya kara sauki, ga magangunan da ake bukata zan je a siyo sai kuma jinin da za'a kara mata gobe shima." "Allah yayi Albarka, sannu kaima, wannan rayuwar cike take da mutane marasa tsoron Allah." "Haka ne." Shiru sukayi kowa da abinda yake tunawa a ransa "Sultan." Ta kira sunan sa "Ka samu sakona wajen Malam Bako ko?" "Na samu, sai dai ban fahimci komai ba a ciki, illa mutum daya da sanadiyar sa ne na shigo Masarautar..." "Safiyanu Madaki." Ta fad'a tana girgiza kanta "Abinda yasa na saka neman sa, saboda shine ummul aba'isin kusan komai da ya faru." "Menene alakata da shi da Kuma Masarautar? Ina jin kamar akwai wani abu me girma tsakani na da Masarautar." Murmushi Maman yara tayi cike da jin dadi, dadin zuwan lokacin da tayi ta jira tsawon wannan shekarun, dama ta fad'a musu, watarana na zuwa, da komai zai bayyana, a ranar ne zasu gane cewa sun bar baya da kura, a ranar ne mutane da yawa zasu ji kunya, kunya irin ta duniya,kafin akai ga zuwa lahira. "Alhamdulillah Sultan, Allah shine abin godiya, kuma shine madogara idan ka dogara dashi ya isar maka, a lokacin da suka yi tunanin sun rufe babin rayuwar ka, a lokacin ne Allah ya turo, ya kuma saka ka zama nagartacce wanda dukkan iyaye zasuyi alfahari da kai. Duk da ban san inda Maimartaba da Gimbiya suke ba a halin yanzu, amma nasan duk sanda suka ganka zasu fi kowa farin cikin kasancewar ka dan su." "Sun cire wa mahaifiyar ka abu mafi soyuwa a ranta, suka dasa mata bakin ciki a zuciyar ta, sannan daga karshe suka yi makircin da ya saka su barin tushen su, asalin su. Duk dan saboda mulki, mulkin da za'a yi shi a duniya a barshi a duniya, mulkin da idan bakayi wasa ba zai kaika wuta. Sultan idan ba Allah ba, waye zai raya d'a ba tare da mahaifiyar sa ba?ya kuma shiryar dashi zuwa tafarkin daidai? Mahaifin ka Sultan shine Sarki Usman Muhammad Moddibo Saji, kuma shi ya damka amanar ka a hannu na, shine kuma mamallakin *SMM Orphanage* wanda ya gina shi da sunan ka (Sultan Muhammad Modibbo Saji*), ba tare da ya san kai din zaka yi rayuwa a ciki ba, tsawon wannan lokacin ina neman yadda zan yi na sadu da Maimartaba, sai dai garin neman yadda zanyi, Madaki yayi amfani da hakan wajen chanja komai, wanda yayi sanadiyar kasancewa ta a inda ka ganni." Juyi sosai kan Sultan ya shiga yi har sai dai ya rike karfen gadon, sai yanzu ya gane dalilin da ya saka yake jin su a ransa sosai, ya damu da damuwar su har yake jin zai iya komai. Wani karfi ne yaji ya zo masa na gaske, ya mike ya tsaya akan digadigansa ba tare da ya jingina da komai ba. Lokaci yayi da zai dawo wa da iyayensa martabar su, lokaci yayi da zai nunawa Madaki zan iya dashi, lokaci ne da ya kamata ya kalubalanci Bilal da kuma mahaifin sa, da sauran kuma wanda ma be gama sani ba. Wani irin haske zoben hannun sa yayi, Maman Yara ta kalli hannun nasa da sauri, sannan tayi murmushi. Jini ba karya bane, kamar yadda yake babu wanda zai iya Amfani da zoben nan face shi din ya kasance jinin Maimartaba, haka ce yanzu ta kasance, kasantuwar zoben a hannun sa kad'ai ya isa ya warware komai, amma duk da haka ba zata sanar dashi komai ba, zata fi su shi yayi komai da kan sa. "Wacece ita?" Ya nuna matar da ke kwance wanda a dah ya saddakar da ita ce mahaifiyar sa. "Aminatu, labarin ta daban yake." "Itace aka yiwa dashe?" " Ya akayi ka sani?" "Bincike nayi akai." Yace yana boye mata gaskiyar inda ya samu labarin. "Lallai Sultan dina ya girma, girman da nake buri da fata, itace kuwa Sultan, itace." "Ina yaran?" "Akwai wata mata Safiyya, wadda muke tunanin ita ce ta karbi yaran, sai dai rashin sanin inda take shine, amma tabbas Madaki yasan inda take, ya kuma san wani abu game da yaran tunda na taba jin shi yana maganar be san ina wajen ba." "Shikenan, bari na siyo magungunan na dawo." Sai kuma ya tsaya yana saka hannun sa a aljihu, ya fito da layoyin nan ya zube su a gaban ta "Bansan na menene ba, amma ina ganin kone su za'a yi kawai." "Tare da zoben suke?" "Eh a dakin sarkin na debo su." "Ikon Allah, shikenan zan san abinda ya kamata a yi dasu." "Madaki yana son zoben!" Yace yana kallon ta "Karka kuskura ka bashi, idan har yaje hannun sa komai ya lalace,wahalar da mukayi shekaru munayi ta zama a banza." "Shikenan." Ya juya da sauri ya bar dakin, kai tsaye office dinsa ya nufa bayan ya bawa wani masinja ya bawa takardar magungunan. Yana shiga ya durkusa a k'asa, ya rasa me zai yi,kuka ko dariya, kasancewar sa da na halak da ga iyaye masu matukar daraja. Be san a wanne gurbi zai ajiya yadda yake ji a zuciyar sa ba, ya san dai kawai he's beyond happy.    Wayar sa da ya manta ya saka ta a flight mood yaji tana kara, ya dauka ganin Umaimah yasa shi ajiye wayar, kiran na katsewa ya kashe wayar gaba daya, bashi da lokacin ta yanzu dan haka ma ba zai bata lokaci wajen magana da ita ba, maganar ta ta da yasan ba me ma'ana bace. ***Tana zaune ta hada kanta da guiwa, tayi kuka har ta gaji, gashi babu wanda ya zo inda take tunda suka kawo ta suka ajiye ta, a tunanin ta irin kidnappers din nan ne, tunda yanzu k'asar gaba d'aya ta zama haka, amma rashin zuwan su da kuma yanayin yadda suka dauko tan yasa ta tsorata da su din su waye?    Kallon kafarta tayi da suka saka wata igiya suka daure mata, bayan ta gwada guduwa tayi, ta cigaba da kukan da take rerawa, a rayuwar ta bata san wata wahala ba, bata da hayaniya ko yawan magana shiyasa yanzu duk ta shiga wani irin yanayi. Batayi zato ba ko tsammani taji an turo kofar dakin, ta dago idon ta ya sauka akan sa, babban mutum ne cikin shigar manyan kaya, ya tsaya daga kofa yana kare mata kallo "Yarinya ce ma ai karama." Yace yana kallon na bayan sa "Eh oga." "Owk a cire mata igiyar nan, na fad'a muku karku mata komai fa, amma me yasa?" "Guduwa taso yi ne oga." "Kuna me zata gudu? Idan ma ta gudu ai kuna nan a kofar ba matsawa zakuyi ba ko? Sai ku hanata." "Toh oga." "Akwai abinci na tawo mata dashi a mota, a turo wani ya dauka, kici abinci kinji? Babu abinda zamuyi miki mijinki kawai muke bukata anan, ya kawo min kayana na bashi ke, Idan kika ga be zo ba toh tabbas baki da muhimmanci a wajenshi." *** ***A wani irin yanayi yake zagayawa ransa a matukar baci tunda ya samu labarin zaman Yarima Bilal sarki, tabbas wani yana masa zagon k'asa,kuma tabbas a cikin yaran sa ne da ido ya shiga binsu dukkan su sun sunkuyar da kan nasu k'asa, "Waye munafukin dake fitar da maganganun mu?" Duk sukayi tsuru tsuru, babu wanda yayi magana, "Babu Wanda zai magana ko?" Shiru "Ku tashi ku bani waje, zan yi bincike duk wanda na gano sai na masa wulakancin da bai yi zato ba." Sum sum sum duk suka mike suka fita. Lallai Yarima ya shammace shi, be taba kawo shi a rai ba balle yayi tunanin zai kawo masa matsala, amma tunda be samu zoben nan ba, mulkin nasa na dan lokaci ne kawai, shi zai yi kokarin samun sa sannan yayi amfani da karfin sa wajen samun cikar burin sa. ***Tsayawa yayi a harabar wajen yana waige-waigen neman abinda yake son ganin, kasancewar unguwar babu mutane ya saka wajen ya zama tsit babu haske ko kadan, ledojin da ya zo dasu ya daga ya kalla sannan ya nufi gidan yana fatan samun Ammi a ciki dan shi sam be yarda da Mutumin nan ba, kawai yasan boye ta yayi yana wasa da hankalin su, bayan kuma yaji maganar da suke ranar da wadannan mutanen ya sake tabbatar da hakan, shiyasa yayi ta bibiyar su har ya gane inda suke,ya kuma ga zuwan Madakin yau shiyasa yayi alkawarin shiga gidan yau ko ta halin kaka. Kansa tsaye ya nufi cikin gidan, ya sa hannu ya kwankwasa kofar yana matsawa baya. Wata murya kakkaura tace "Waye?" Shiru yaki magana yana ji yana kokarin zare sakatar, "Waye kai?" "Alhaji ne ya aiko ni." Ya d'aga masa ledojin hannun sa. "Meye wannan din?" "Abinci ne." "Alhajin yace ka kawo mana?" Ya karba ya bud'e daya, shinkafa ce da kaza, ya hadiyi yawu ya shiga kwalawa wanda suke tare kira. "Mudi, mudi! Zo kaga abin arziki." "Menene?” "Duba, Alhaji yace akawo mana." "Kai kai, kutrun ubanchan, yo kodai Ya hajj ya samu abinda yake so ne? Wannan dabge haka." "Toh waya sani, muje ciki a ga yadda za'a kasafta ta." Sukayi ciki sun ma manta da shi da yake tsaye, da sauri yabi bayan su, ya makale jikin wani gini, su kuma suka shiga ciki suka dira akan abincin kamar tsofaffin mayunwata. Sai da suka gama cinye abincin tas suka tsotse kashin sannan maganin ya soma aiki a kansu, a hankali suka dinga bajewa suna kwanciya bacci me nauyi na dauke kowannen su.   Da sauri ya fito, ya bud'e dakin ya tsaya yana kallon yarinyar dake zaune ta dora kanta a saman guiwar ta, "Ke kad'ai ce anan?" Da sauri ta dago "Kwantar da hankalin ki, babu me zuwa yanzu, ke kad'ai ce anan?" Daga mishi kai tayi tana hawaye "Babu kuma wata matar da kika tarar anan?" "Babu." Dafa kansa yayi kamar zai ihu, ina Ammi take toh? "Shikenan, muje." Yayi gaba d sauri, ta biyo bayan sa sukayi hanyar fita da mugun sauri. Wata mota ce ta shigo layin suka yi saurin makalewa a jikin wani kango, ya dube ta cikin tashin hankali yace "Number wa kika sani a yan gidanku?." ***A daidai wajen da suka hadu jiya yau ma suka hadu, Sultan na shiga motar ya kwanta dan zai iya cewa jiya sam be runtsa ba, yana tunani, ga wani irin son ganin Amrah dake nukurkusar zuciyar sa, yasan ta da saurin kuka, yasan kuma tayi babu iyaka watàkila ma hawayen nata ya kafe. Gefe daya kuma zuciyar sa na muradin sake ganin su, yayi musu albishir ya kuma cika musu alkawarin da yayi musu, amma baya so su dawo kasar har sai komai ya kammala zai je da kansa ya dauko su, ya dawowa da Masarautar da mutanen ta abinda suka rasa tsawon lokaci.   Kai tsaye gidan Madaki ya kwatantawa Safwan suka dau hanya, kafin su karasa aka kira sallar magriba, suka tsaya a masallaci suka fara yin sallar sannan suka karasa. Fitowa sukayi a tare, Safwan ya rufe motar suka nufi gidan suna tafiya a jere. Kwankwasa gate din Sultan yayi Maigadin ya leko, yana ganin shine yayi saurin bud'e kofar yana washe baki. "Yallaabai barka da zuwa." "Barka dai Baba." "Alhaji na ciki?" "Yana nan, magana za'a yi masa? Dan nasa kamar ransa a bace yake." "A ah ai yasan ma da zuwan mu, kawai ka jagorance mu zuwa wajen sa." "Ah toh ai shikenan ma, bismillah." Suka bi bayan sa, sun kusa isa Safwan yaja hannun sultan ya tsaida shi "Hold your temper man, ka bar komai a hannu na." "Zan iya gaggaya masa magana ne a yadda nake jin raina." "Yaushe sultan ya zama me zafin zuciya?" "Ba zaka gane ba, wannan mutumin devil ne." "Duk da haka, Amrah na tare dashi so sai mun bi komai a sannu." "Shikenan, I ll adjust." "Better." "Bismillah, Alhaji kayi baki." "Su waye?" Yace ransa a bace "Mune." Sultan ya amsa suna kutsa kai cikin falon. Tashi yayi tsaye "Dama nasan zaka zo, nasan zaka zo ai mace ba wasa bace,ina aike na?" Daga masa hannu Sultan yayi, ya kalli zoben da sauri, ya shiga matsawo yana son gasgata idon sa, da gaske complete zoben ne ko kuwa dai wani zoben ne daban? Yasan tun a wanchan lokacin aka rasa barin zoben amma aina sultan ya samu har ya hade shi sannan har ya saka shi a hannun sa. "Ba sai ka matso ba, kamar yadda ka gani, zoben ne cikakke, sai dai yanzu abu biyu ne zasu saka ni baka zoben nan, na farko alkawarin da kayi min na had'a ni da iyayena idan na dauko maka zoben, sai na biyu matata, ba muyi haka da kai ba, mesa zaka daukar min mata?" "Saboda ka turo yaron da na aike ku tare, wanda ya tabbatar min ba zaka bani zoben nan ba tunda ba haka muka tsara ba, shiyasa ni kuma nayi maka abinda nasan zaka kawo min zoben cikin ruwan sanyi,amma ya akayi haka? Ya akayi ka samu zoben dukkan sa?" "Wannan ba damuwar ka bace, ina so ka cika alkawarin ka na farko, maganar iyaye na, sai kuma matata da nake son gani yanzu, idan har ka cika wadannan sharudan zan cire maka zoben na baka." "Kana so ka kure ni ne Sultan?" Shiru yayi yana kauda kansa gefe, "Ina zuwa." Yace ya tashi ya shiga wata kofa, be dad'e ba ya dawo sai dai tare yake da wani tsohon mutum da kuma wata dattijuwar mata, kallo daya zakayi musu ka tabbatar da yadda talauci yayi musu katutu, wahala sosai ta nuna a jikin su barin ma tsohon da har wani malkwadewa yake saboda rama. "Gasu nan, wadannan din sune iyayenka, kar kuma ka tambaye ni ta yaya, zaka samu amsar komai a bakin su." "Yaro Sultan ashe kana raye?" Suka had'a baki wajen fad'a, ba wai yanayin su ne ya hana Sultan din magana ba, sai yadda Madaki yake so ya raina masa yawo, be san yasan abubuwan da ba lallai shi din ya sani ba,Amma duk da haka ba zai yi saurin mika wuya ba, zai bishi a yadda yaso din. Tashi yayi yana masa kallon cikin ido, kallon da ya dan firgita Madakin amma ya dake, idanun Maimartaba sak yake gani a cikin kwayar idon Sultan din, amma sai ya dake ya jira yaji me zai ce "Ka cika alkawari daya, saura daya." "Ka fara bani zoben ni kuma zan baka matar ka..." "Ai ba haka mukayi ba..." Karar wayar sa ta katse shi, ya ciro ta yana kallon number, kafin ya daga ya saka ta a kunnensa "Na turo maka da address yanzu yanzu kazo ina tare da matar ka, kazo kafin su farga saboda haka kayi sauri dan Allah." Da sauri yace "Gani nan." Sai ya juya wajen Madaki "Zan dawo, abu ya taso min urgent amma zan dawo." Ya juya da sauri Safwan yana take masa baya. Waya Madaki ya dauka yana jan gashin gefen bakin sa yace "Yaro be san wuta ba..." "Hello! Gashi nan ya fito,ku bishi ku kawo min zoben hannun sa, idan yayi gardama ku harbe shi!" **Assalamu alaikum Lovelies 😂 ina neman ahuwa bisa rashin jina a yadda ya kamata, hakan ya samo asali ne sakamakon wani baban uzuri daya rike ni, amma in Sha Allah na dawo. Masu cewa sunyi fushi akan littafin nan kuyi hakuri, kurciya Billy da Xoxo sukayi min na bace bàt a yanar gizo😂😂😂 Da na dawo kuma sai ya zama duk sanda na dauki wayar zan yi typing sai bacci ya kwamushe ni. Ahuwa bayin kaina bane😂😂😂 Lolz😎😎😎😎😎😂 Gashi nan readmore 10ne cif na biya Bashi😂⛹️⛹️⛹️⛹️⛹️⛹️ ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥© Hafsat Rano Page 36 Zafafa biyar na kud'i ne!!! *** Shi yake driving din yana duba address din, tafiyar da nisa sosai shiyasa suka dan dauki lokaci kafin su isa, ya sauka daga kan kwaltar ya shiga gangarawa ta wata hanya da bata da kyau sosai.     Yanayin yadda suke binsan be sa ya gane suna bin nasa ba, ganin hanyar ta kare daga inda suke ya saka su fitowa suka kashe motar, Safwan ya karbi key din shi kuma ya saka waya a kunne yana dialing number da aka kira shi da itan, tana ta ringing ba'a daga ba, har ta katse yayi saurin sake dialing looking very stressed out. Still wayar tana ringing amma no answer, kansa ya dora a saman motar yana jin kamar yayi failing, dafa shi Safwan yayi, yana kokarin calming nasa, ya karbi wayar yana sake gwada kiran shima, yana kira aka daga sai dai muryar sa tayi chan ciki "Muna ta bayan wata bishiyar mangoro, akwai wanda suke neman mu ne and suna kusa sosai, please kuyi sauri, amma kuzo da yan sanda dan akwai bindiga a hannun su." "Kana ji, karku fita daga wajen,muna kusa daku muma sannan..." Daukewa wayar tayi, ya kalla da sauri sai ya ga kiran yayi disconnecting "Me yace?" "Neman su suke amma sun buya, kana ganin ya kamata muzo nan mu kad'ai? Akwai bindiga a hannun su, kar muyi risking life din Amrah." "Ya zamuyi Safwan? Babu wani tunani a kai na, komai ya zama blank I'm not thinking straight,me ya kamata muyi yanzu?" "Mun riga munzo, dole ba zamu fita daga wajen ba, ina ji a raina we are surrounded." "Then ka tura wa Adnan da location din da muke, ka fad'a masa briefly yadda zai gane." "Good idea." Yace da sauri yayi abinda Sultan din yace tare da bayanin yadda Adnan din zai gane sannan ya kirashi, yana dagawa yace ya duba whatsp dinsa yayi saurin kashe kiran.     Duddubawa suka shiga yi har suka hango bishiyar mangoron,babu tazara a tsakanin su saboda haka kai tsaye suka nufi wajen. Wani iri Sultan ya shiga ji a jikin sa kamar bashi da lafiya, wani irin weakness ne yake sauko masa, ya kalli zoben hannun sa da yayi duhu sosai, sannan suka cigaba da tafiya a hankali har suka isa daf da bishiyar, kafin su karasa suka hangi wasu mutane su biyu suna shawagi a wajen, alamar sune ke neman su Amrah. Makalewa su Sultan sukayi yadda ba zasu gansu ba, aamma su suna kallon su daga inda suke, sun dan jima a tsaye a wajen sai kuma suka juyo suka bar wajen, da sauri Sultan fa Safwan suka karasa bayan bishiyar, Amrah na durkushe a k'asa idonta na zubda hawaye babu ko takalmi a kafarta, da wani irin sauri Sultan ya durkusa a gabanta, ya saka hannu ya jawo ta jikin sa gaba d'aya yana jin kamar kirjin nasa ya bud'e ya saka ta ciki. "Ya Sultan..." "Shissh...I'm here." Yace yana sake rik'e ta sosai, yana shafa bayanta a hankali "Sultan, yakamata mu fita daga wajen nan." Mikewa Sultan yayi tare da ita, ya kalli Muhammad dake tsaye shima yana kallon sa, yaji wani abu ya fizgeshi da karfi, da sauri duk suka kalle shi har Amrah ganin wani haske fari sosai na fita daga jikin zoben hannun sa. Ba karamin mamaki Sultan yayi ba ganin yadda zoben yayi haske sosai hasken da tun da ya saka shi be taba ganin yayi shi ba, sai kuma yaji wani sakayau kamar an cire wani abu me nauyi a jikin zoben.    A daidai lokacin Sarki Bello ya farka da ihu, ihun da ya jawo hankalin mutanen da yawa dake kusa da wajen,da sauri Yarima Bilal ya kutsa kai dakin da Sarkin yake tun ranar, waige waige ya tarar dashi yanayi bayan ya jawo akwatin ya duba babu komai yana ganin Yarima Bilal din yayi wajen sa da sauri "Yarima, ya shigo gidan nan, ya dau zoben nan, wallahi ya dauka, shikenan komai ya kare, komai yazo karshe." "Wanne zoben?" Yarima yace dan shi har ga Allah ya manta da wani batun zobe. "Amm baka sani ba ko? Na tuna baka san amfani shi ba, me ya faru dani? Ya akayi na ganni a haka." Sai kuma ya kurawa Yariman ido sosai, ya kalli kayan jikin sa da rawanin dake kansa, sai kuma ya tuna abinda ya faru ranar, bayan sun jima suna hira shi da Yariman, dan tare suka ci abinci ma, daga nan kuma be iya tuna abinda ya faru ba. "Yarima?" Yace yana nuna shi da hannu bayan ya tabbatar da abinda yake tunani. Kicin-kicin yayi da fuska yana kallon Sarki Bellon "Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun, shikenan ka gama dani, ka kashe ni, dama chan sarautar kake wa, shine ka taimaka masa ya shigo har nan ya dauki abinda kai kanka baka Isa kayi mulkin nan ba idan yana tare dashi, wanne irin mahaukaci ne kai, wanne irin d'a ne kai, Idan kayi hakuri dukkan fafutukar da nake akan wa nake yi? Nace akan wa nake yi idan ba kai ba." "Menene wai amfani shi wannan zoben da kake magana." "Zoben nan, shine garkuwata, garkuwar ka, kai dama duk wanda yake da alaka damu, gaba ki daya tsatson mu, barin zoben nan shine dalilin zama ta akan kujerar da har ta baka sha'awar da ka iya yaudarar ni mahaifin ta akanka,ko kasan kasantuwar zoben a hannun sa, wanda na gani yanzu a mafarki, komai ya lalace, ina kyautata zaton ya had'a daya barin domin karfin sa ya kai duk inda ake so ya kai.." Shiru Yarima Bilal yayi yana jin gefe daya na zuciyar sa na dana sanin abinda ya aikata, me yasa ma be yi kakkwaran bincike akan zoben ba shima. Wani bafade ne ya tsaya dgaa kofa, yace "Allah ya baka yawan rai, buzu da jama'ar sa na son ganin ka." Kallon juna Yariman sukayi da sarki Bello, wanda gaba daya yanayin sa ya chanja wani abu me kamar tsoro ya bayyana a fuskar sa, yasan dalilin zuwan su, ya kuma san ba abu bane me sauki dawo da zoben nan. "Muje." Yace mishi suka fito zuwa fadar, babu kowa kamar dai yadda yake duk sanda suka zo ganin Sarkin, dukkanin su sun bayyana tashin hankalin su karara, duk a tsaye suke sai buzu ne da ya ajiye wannan mudubin a k'asa be riga ya mike ba, kan Yarima tsaye ya wuce zuwa karagar mulkin ya haye, suka kalle shi dukka amma sai sarki ya basar ya matsa yana kallon mudubin, sai dai abinda ya gani wanda be yi zato ba shine ya sakashi ja baya da sauri "Ya akayi haka? Ta yaya suka hadu da juna "Kasantuwar zoben a hannun su ya saka hakan Allah ya baka yawan rai." Sake matsawa yayi ya durkusa yana kallon danjojin, shiru yayi yana nazarin abinda yake faruwa. Mikewa yayi daga durkusan ya koma ya zauna sannan yace "A kawo baiwar nan." Duk sunyi shiru aka shigo da ita, aka gurfanar da ita a gaban su. Kowa ya zuba ido yana kallon abinda Sarkin zai yi, da kansa ya taso ya tsaya sannan yace "Ina yaran da kika tafi dasu? Suna raye dukkan su ko daya ne yake raye ko duk sun mutu? Idan kika yi min karya..." Sai ya saka hannu ya zare takobin dake makale a jikin Buzu yace "Sai na sare kanki a yanzu yanzu." "Kayi min rai, tabbas yaran suna raye tunda ni da hannu na na raini daya, sai dai dayan ne bansan inda yake ba, tun bayan da na bar nan dasu, Madaki yà karbar min daya ya rik'e, tun daga ranar bansan ina ya kaishi ba, nasan dai tabbas yana raye, tunda ko da muka hadu be cemin ya mutu ba." "Ina wanda kika raina din?" "Yana nan, kafin a tawo dani nan na barsu a gida." "Ku maida ita ku rufe ta!" Yace yana jefar da takobin, Fita sukayi da ita, ***Yana zaune ya mike kafar sa da take masa masifaffen ciwo, Al'qur'ani me girma ne a hannun sa yana tilawa sai yaji wani abu kamar cirar k'aya ya fita tun daga tsakar kansa ya sauka zuwa tafin kafar sa, a hankali ya nemi ciwon kafar ya rasa, ya mike da sauri domin son tabbatarwa, da gaske babu ciwon babu alamar sa, sai wani irin sakayau da ya ji jikin sa yayi har yaji kamar zai fadi, dafa wa yayi ya zauna ya dauki landline ya kira dakin ta, tasowa tayi ta sameshi a zaune ya kalmashe kafar tasa wadda rabon da yayi irin zaman ya manta, zama tayi a gefen sa tana karantar sa. "Ina ciwon kafar?" "Babu." Yace yana jujjuya kafar "Ikon Allah." "Aifa sai ikon Allah, amma sai nake jin kamar zanyi zazzabi, kinga kuma na kinga ma kiran da nayi miki na manta abinda zan ce miki, kaina yayi wani dum babu dad'i." "Toh, sannu Allah ya sa ba zazzabin bane, dan zazzabi baya maka da sauki." "Ga girma ba." "Allah ya sauwake, bari na samo maka magani." "Yawwa Gimbiya, taimaka min da black tea dan Allah." "Da me kuma?" "Sai karamar wayata zan kira Sultan." Shigewa tayi shi kuma ya zauna yana kisissima abinda ke shirin faruwa dashi yanzu kuma. ***Duk suka tsaya suna kallon hasken wanda yayi matukar daure musu kai, hasken yayi nasarar ankarar da mutanen nan suka juyo da sauri zuwa inda suka ji kamar motsi a wajen, hannun Amrah Sultan ya kama, suka soma tafiya da sauri Safwan da Muhammad na bayan su. Daga chan hanyar shigowa wanda Madaki ya bawa aikin bin Sultan din ne tsaye suna jiran fitowar sa, suna tsaye suka ji jiniyar yan sanda, "Babah me nake ji kamar sheggun mutanen chan." "Sune mana, amma kamar basu kusa karasowa ba ai." "Kawai mu kutsa kai muyi abinda ya kawo mu, mu fece kafin su karaso." "Kawai ba, hakan zamuyi." Ciki suka shiga a kafa, lokacin jiniyar na kara matsowa sosai. Daga nesa suka hango mutane biyun nan dake bin su Sultan a bayan su, wanda su basu masan suna binsu ba, sauri kawai suke su isa wajen motar su. "Ka gansu chan Baba, su biyu ne dama yace ko? Kawai mu bud'e musu wuta, mu koma muce yayi gardama mun sheke shi, sai mu cire zoben kawai kamar zai fi." "Abinda kawai zamuyi kenan, karya bata mana lokaci har sheggun chan su karaso." "Ah toh mu saita ta kawai." Saitawa sukayi daidai lokacin su Sultan sun iso wajen mota, babu zato babu tsammani sai jin harbi sukayi wanda ya tafi direct ya sauka a akan Safwan da yake kokarin bude motar, ya kwalla k'ara da karfi ya zube a wajen, da gudu sukayi kansa Sultan na kwala kiran sunan sa a gigice, "Safwan! Safwan." Rike shi Muhammad yayi yana kokarin saka hannun sa a daidai inda jini ke fitowa ta wajen da bullet din ya shiga. Jin harbin ya saka suma masu bin nasu suka shiga maida wuta a tunanin su yan sanda ne, sosai Amrah ta gigice ta fara neman hanyar guduwa wanda bata yi aune ba ta bugu da wata katuwar bishiya dake gabanta, zubewa tayi a take ta kwalla k'ara itama, karar da ta sake ruda Sultan yayi kanta da gudu yana kiranta. Kuka Sultan yake wiwi, kukan da be taba yin irinsa a rayuwar sa ba, mutane biyun da suka fi kowa kusanci dashi, a sanadiyar sa yau gasu a cikin mawuyacin halin mutuwa ko rayuwa, yes shi likita ne kuma yadda yaga Safwan na fidda jini da yadda Amrah ma kanta ya bugu har ta sume yasan tabbas za'a iya rasa su, ko kuma ita ta samu wani internal ingury, amma for Safwan, bashi da tabbas.    Zuwan su Adnan da yansanda wajen ya saka suka arce amma sunyi nasarar kama mutum daya acikin wandanda suka fara harbin da har ya samu Safwan.     Daukar Safwan din sukayi aka sashi a mota wanda gaba daya hankalin su ya tashi ganin halin da yake ciki, karma Daddy da yayi matukar kaduwa da ganin d'an sa a halin rai ko mutuwa. Tun dazu yake neman wayar sa bata shiga ashe nan suka tawo shi da Sultan din, wanne irin so yake wa Amrah haka ne da har zai iya risking life dinsa, sannan sultan, yana masa son da ya zama wani abin dubawa, wanda baya iya ganin shi a damuwa ba tare da ya taimaka masa ba.   Duk tsawon shekarun nan Safwan has been very good to Sultan, yana kin duk abinda Sultan din yaki ko da kuwa shi yana son abun,yana kuma zama cikin damuwa duk sanda Sulthan din ya shiga damuwa. Duk da shi ma Sultan din hakan ce a wajen sa, amma shi nasa da banbanci da na Safwan, shi yana yin komai ne domin rama halacci kamar yadda yake ganin anyi masa, ba kamar soyayyar da shi Safwan din yake masa ba wadda ta kasance daga Allah.    Har suka karaso cikin gari suka kuma nufi asibiti Daddy be samu hanyar da zai sanar wa Mah-Mah abinda ya faru ba, be masan ta yadda zai fara ba, yace mata wajen cetar Amrah ne ko kuma yace mata wajen rakiyar SULTAN ne? Yasan ba zata saurari kowanne a ciki ba, saboda dukkan su biyun sune mutanen da Safwan yake so, kuma sune soyayyar su ke bashi wahalar da har take kaishi gadon asibiti, yanzu gashi nan ta kawo shi inda ko su kansu Sultan da Amrah basu da TABBACIN abinda zai faru. Duk da itama unconscious aka dauko ta amma ba kamar Safwan ba, da bullet ya ratsa ta jikin sa ya huda. Yadda yake zubar da jini kad'ai abin tsoro ne.    Da gudu ma'aikatan suka iso suka karbe shi, aka nufi ICU dashi, wasu kuma suka karbi Amrah aka wuce da ita emergency room. Makalewa sultan yayi a jikin wani gini ya durkusa a wajen, zafin da yake ji yana fitowa daga chan k'asan zuciyar sa zuwa saman fatar shi ba abu bane me sauki. Me yasa duk be yi tunanin abinda zai faru ba yayi risking rayuwar Safwan wanda be san komai ba sai farin cikin sa, Safwan deserve something very very good tunda yana da heart me kyau, yana son kowa da zuciya tsarkakakkiya.    Da sauri ya tashi kamar wanda aka tasa, ya girgiza kansa yana kara karfafa kansa "Babu abinda zai same su, babu abinda zai same su." Ya cigaba da fad'a yana tafiya, a tsaye ya tarar da Abba, Adnan da Daddy hankalin su a tashe, duk suka bishi da kallon tausayi. Durkusawa yayi a gaban Daddy yana sauke kansa kasa ya kasa cewa komai "Sultan, tashi kaji? Addu'a kawai suke bukata a yanzu, muyi musu addu'a." Gid'a kansa yayi da sauri yana tunawa da addu'a. Tabbas addu'a suka fi bukata fiye da komai yanxu, zaije yayi musu addu'a yanzu. Masallacin cikin asibitin ya nufa, yana jan kafar sa har ya isa, ya daura alwala a gaban fanfon wajen ya shiga ciki ya dukufa kai kukan sa wajen ALLAH. Be san iya kar adadin da ya dauka a wajen ba, sai da yaji an dafa kafad'ar sa, ya juyo sukayi ido da Adnan da idon sa ya chanja sosai kamar gauta, ya tashi da sauri "Adnan ya ake ciki?" Ya rik'e shi "Amrah ta farka, tana son ganin ka." "Safwan fa? Karka cemin he's still unconscious dan Allah, ba zan iya dauka ba." "Mu cigaba da addu'a." "Ya Allah!" Ya kama kansa dasauri, yayi baya kamar zai fad'i, Adnan ya rike shi da sauri. "Zai samu sauki in Sha Allah, mu cigaba da addu'a." ***Daga kai yayi ya kalli abinda aka rubuta a saman dakin kafin ya tura ya shiga, a kwance take an nannade mata kanta da farin bandeji inda ta bugu, drip ne a daure a hannun ta wanda yake shiga a hankali. Babu kowa a dakin, kasa karasawa yayi yana jin kamar ba zai iya karasawa ba, kamar ma ba zai iya takawa ba yake ji, ganin ta motsa yasa shi ya isa wajen ya tsaya a gaban gadon, fuskar ta tayi fari sosai ta fad'a, hannu ya kai ya shafi gefen fuskar ta, ya kama hannun ta guda d'aya ya rik'e a cikin nasa, yana jin zafin jikinta da nashi na haduwa waje d'aya. Kansa ya dora a saman gadon daidai inda kanta yake yana jin kamar ya cire ciwon ta dana Safwan ya dora akan sa, basu chanchanci kasancewa a wannan state din ba saboda shi. "Sultan..." Ta kira sunan sa a hankali, dagowa yayi idon sa ya sauka a cikin nata, yayi mata murmushi da sauri, ta mayar masa tana daga hannun ta dayan. "Karki motsa,I'm here, me kike so? Kina son wani abu?" Girgiza kanta tayi hawaye na gangarowa daga idon ta "Karka sake tafiya ka barni." "Ba zan sake ba, I promise you, duk inda zanje tare zamuje." Murmushi tayi, shi kuma yayi kissing din saman idon ta tayi saurin runtse idonta tana jin wani irin feeling. ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥© Hafsat Rano Page 37 Zafafa biyar na kud'i ne!!! _*INA MASU NEMAN MAGANIN INFECTION SADIDAN? MAGANIN NI’IMAH, MAGANIN GYARAN HIPS AND BOOBS? MAGANIN BASIR....NA HAUSA BANA BATURE ME KWANTAR DA CIWO BA? TO KU MARMATSO KUSA, DOMIN YAU MUNA TAFE DA ALBISHIR WANDA ZAI FADADA MURMISHIN FUSKOKIN KU.. YA KUMA KAWATA ZUKATAN KU. MUN GWADA MUN GANI, MAGUNGUNANTA SUNADA KYAU KUMA SUNA DA AIKI.. BABU SIDE EFFECT, ANYI SU NE DAGA TSAFTATTUN KAYAN ITATUWA, DA SIRRIN CHADIAN HERBALS.. KARNA CIKAKU DA SURUTU;_ _*AISHA S BAYERO TRADITIONAL MEDICINE AND HERBAL RESEARCH CENTER..._* _KUNJI SUNAN KO? CENTER CE TA MAGUNGUNAN GARGAJIA, WANDA DUK WANI DAMUWA DAKE DAMUNKA IDAN HAR KAZO WAJEN S BAYERO TA KARE DA YARDAR ALLAH.._ _KADAN DAGA MAGUNGUNANTA SUN KUNSHI:_ _MAGANIN SANYI _ _MAGANIN NIIMA SET_ _MAGANIN NANKARWA _ _MAGANIN KIBA BABBA DA _KARAMI _ _MAGANIN HIPS _ _MAGANIN GYARAN NONO _ _MAGANIN RAGE KIBA _ _MAGANIN SAKA FEELING _ _MAGANIN CIDA KWAI _ _ZUMA YAR ASALI_ _MAGANIN BASIR KOWANNE IRI _ _HODAR NI’IMA _ _MAGANIN MALLAKA _ _GUMBAR NONON RAK’UMI _ _GUMBAR MADARA _ _TURAREN FARIN JINI _ _KAZA MARA KWAI _ _TURAREN MALLAKA 3 STEP _ _HAD’IN MATAR MINISTER 1_ _KAZA ME KWAI_ _STEP 2:_ _TURAREN MALLAKA ME KWALBA _ _ME KUNAMA DAN MATSI _ _TURAREN GOSHI _ _TURAREN QIRJI _ _TAUWADAR MATA _ _MEMORY _ _KAHON MALLAKA_ _YAJIN MAZA_ _TEA DIN MAZA _ _DAMBUN MATSI_ _MAN AYU_ _MAN DAMO PURE _ _KWALLIN IDONKA IDONA _ _GARIN SHA DAKA ME KYAU _ _KUBEWAR MATA_ _DUKA WADANNAN INGATTUN MAGUNGUNA NA GARGAJIYA HAJ AISHA NA DASU GANGARIYA.. HERBAL MAGUNGUNA NE MASU KYAU DA INGANCI.. TAFIYAYYU NA KASAR CHAD. CHADIAN HERBAL MEDICINE AND RESEARCH CENTER.. KYAU, INGANCI.. RAHUSA... SAI MAGUNGUNAN *AISHA S BAYERO TRADITIONAL MED AND HERBAL RESEARCH CENTER...._ _NUMBER WAYAR WHATSAPP: 08121491609 KO KIRA TA NUMBER 08145873617._ _ADIRESHI: KUNTAU KARSHEN KWALTA KAN A KARASA YAN TIFA, DAIDAI GADON KAYA CEMENT.._ *** "Me ya same ki a kafa?" Ya fad'a yana taba kafar daidai wajen da suka daure , wajen yayi shati yayi ja abinka da farar fata "Wai dan karna gudu." Tayi maganar a hankali tana tuno abinda ya faru Shiru yayi ya kalli k'asa bece komai ba, be san kalar rashin mutuncin da zai wa Madaki ba idan suka hadu, haduwar su ba zatayi kyau ba, zai nuna masa ya taba masa abinda ba zai iya kyale shi ba. Tunowa da yayi da mutanen da ya gabatar masa a matsayin iyayen sa ya tabbatar da Madaki ya gama raina shi, raini irin na karamin yaron da be san komai ba. Ko ina ya samo su ma oho, daga gani yayi amfani da talaucin su ne ya saka su aikin. Shigowar Dr Labaran da Dr Fiddausi ya saka Sultan mikewa yana matsawa baya "Dr. Ashe kana nan." Mika masa hannu Sultan yayi suka yi musabah sannan yace "Ina nan." "Ok amarya ya jikin naki?" "Da sauki." "Akwai abinda ke miki ciwo?" "Kaina." "Owk zai daina a hankali." Kallon ta Sultan yayi yaga tana ya mutsa fuska tana cije baki, sai ya maida duban sa wajen Dr Fiddausi yace "Dr tana bukatar bacci kamar." "Owk dama za'a mata allurar da zata huta sosai, nurse fati zata shigo dasu yanzu." "Owk thank you Dr." Fita tayi bayan ta duba abinda zata duba tayi wa Amrah bf da sauran abinda ya dace. Kamar wanda maganar ta fizgo daga bakin shi haka yayi maganar da tun dazu yake son tambaya amma yana tsoron abinda Dr Labaran din zai ce "Dr Safwan fa?" "Alhamdulillah, zamu ce tunda an samu nasarar tsaida jinin kuma an cire bullet din, abu daya yanzu ake bukata shine jini, saboda yayi loosing jini da yawa,and he's still unconscious zamu dai ga abinda Allah zai." "Dama ba'a saka jinin ba!?" Ya fad'a yana kallon Dr din hankalin sa a tashe "No, an dauki sample na jinin nashi an kai lab za'a yi test, sannan na fad'a wa su Baba su tsaya da an yi test din su karba a samo jinin da sauri, ba'a san blood group dinsa ba kasan." "Wannan ai emergency transfusion ne, ya za'a tsaya wasa Dr?" "Kasan sabon tsarin asibitin tun bayan wanchan case da aka samu na yaron nan da aka sa ma wrong jini da akayi amfani da I'd card din sa wajen ganin blood group din nasa, ashe ba daidai bane a karshe  ya rasa ransa." "Oh Allah." Ya juya da sauri ya fita, ya nufi blood bank din, yana tafiya kamar zai hard'e saboda sauri, ya rasa abinda yasa ake samun irin wannan negligence wasu lokutan a asibitocinmu. Yana isa ya karbi blood bag yayi sauri ya kai lab din, AB+ ne shi haka ma Safwan, blood group dinsu daya dan be manta sanda suka yi ba lokacin zasu shiga school, ya tuna a lokacin bayan sun karbo result din suna dubawa Safwan yace _"Kaga ashe ma har blood group dinmu dayà ne."_ _"What a coincidence." Sultan yayi maganar yana kallon result din_ _"Ikon Allah kenan, kaga duk wanda yake neman jini a cikin mu sai daya ya bashi."_    Daga idon sa yayi yana kallon yadda jinin ke taruwa a bag din, yana kuma hasaso halin da Safwan din yake ciki, halin rai ko mutuwa. Gaba daya ji yake kamar be taba shiga aji da sunan koyon karatun likitan ci ba, kamar ma babu komai ma akan nasa sai tarin tashin hankali da tunanin halin da Safwan din yake ciki. Baya jin ko allura aka bashi a yanzu zai iya yiwa mutum balle su bada magani ko aiki.     Yana kwance bayan sun gama daukar jinin sun fita yana hutawa kafin ya tashi Adnan yazo kansa ya tsaya, gaba daya shi kansa Adnan din a hargitse yake balle shi, yana tsaye har ya gama hutawa sannan ya tashi Adnan din ya taimaka masa suka fito daga ciki suka jera a tare zuwa main building din sannan suka karasa inda su Abba suke, lokacin har an fara kiraye kirayen sallar asubah, masallaci suka wuce kai tsaye bayan Adnan ya leka Amrah yaga tana bacci.    Bayan sun yi sallar sun dawo, Daddy ya ciro wayar sa da yaji tana da vib a aljihun sa, yasan Mah-Mah ce kuma tun dare take kira anma sai ya kasa gaya mata komai ya tura mata da sakon zai iya kai wa dare be dawo ba. Abun yayi matukar daure mata kai,haka ta cigaba da kiran Safwan shima amma shi gaba daya wayar tasa ma switch off, abinda ya karaa tasar mata da hankali kenan har ta kasa runtsawa tana tunanin abinda zai sa Daddy kwana a wani waje kuma yaki daga wayar ta ma balle suyi magana, dole jikin ta ya bata akwai matsala. Shiyasa tana yin Sallah ta sake kiran sa dan zuciyar ta, ta gaza daukar abinda shaidan ke ta raya mata.   Matsawa kad'an Daddy yayi ya daga wayar gami da sallama "Dan Allah me yake faruwa ne? Hankali na ya kasa kwanciya Ina jin kamar babu lafiya, wani abun ya samu Safwan ne? Dan Allah karka boye min." "Kina jina? Ki kwantar da hankalin ki, muna asibiti ne Safwan ya dan gamu da tausayi,Amma.... "Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun, na shiga uku, me ya sami Safwan din?" Ta fashe da kuka tana mikewa tsaye, "Ki kwantar da hankalin ki, in Sha Allah zai samu lafiya." "Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun, Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun." Kashe wayar yayi ya girgiza kansa, yasan dama dole ne ta shiga tashin hankali, shiyasa ma kawai yace mata ta tawo din dan yasan ba ma yarda xatayi ta zauna a gidan ba, sai dai be san zuwan nata abinda zai haifar ba, be san ta yadda zata kalli abun ba baya so tazo ta sake saka sultan a cikin wani tashin hankalin, wannan na yanzu ma kad'ai ya ishe shi.    Kusan a tare Mah-Mah suka iso da su Afrah, har lokacin babu wanda yasan halin da Safwan din yake ciki. Sun shiga sun duba Amrah dake ta bacci suka fito suka rufe mata kofar saboda Dr tace tana bukatar hutu saboda kanta.    Kasancewar Amrah a asibitin ya saka Mah-Mah ta gane me ya faru da Safwan. Sosai ta shiga yin kuka tana fad'ar maganganu, maganganun da suka sake saka Sultan a cikin matukar damuwa, da k'yar Daddy ya samu tayi shiru sai kuka da take k'asa k'asa su Umma na bata baki.     Ana cikin haka Anty Amina ta kirata, kamar ba zata duba ba, ganin Amina ce yasa ta tashi ta daga kiran tana kuka. "Lafiya Yaya?" "Amina, Safwan ne kidnappers suka harbe shi, yanxu haka bamu san halin da yake ciki ba." "Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun, yaushe?" "Jiya." "Wayyo, Allah ya bashi lafiya, bari zan kiraki yanzu, bari na duba ko za'a samu flight sai mu tawo da Umaimah Ya Ummah, ki kwantar da hankalin ki Allah zai bashi lafiya." "Amin." Katse kiran tayi, ta koma wajen da ta taso ta zauna. Fitowar Dr's din daga dakin ya saka duk suka mike, Su kayi wajen sa "Dr ya jikin nasa? Ya farfado?" "Ku cigaba da yi masa addu'a, duk da akwai numfashi a tare dashi amma yana cikin critical condition, addu'ar ku kawai yake bukata a halin yanzu." "Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun." Suka had'a baki, matan suka cigaba da kuka mazan kuma suka matsa baya suka jingina da bango suna addu'a. Sultan da yaji wani dum a tsakiyar kansa yayi saurin bin Dr din, "Dr, dr..." "Na'am, Dr ya masu jikin?" "Alhamdulillah." "Allah ya basu lafiya." "Amin ya Allah, Dr me kuke gani game Safwan?" "Eh toh, kasan dai ba zamu fito fili muce wa iyalen mara lafiya ba zai rayu ba, ko mu fad'a musu abinda zai tada musu hankali, amma maganar gaskiya Safwan baya responding, kasan da matsalar heart din nan tashi, dole abin zai sake zama complicated, ga jinin da ya rasa, I can't say enough, amma kaima Dr ne, a very good one ma, ka shiga ka ganshi, ka duba report din da dr Labaran ya rubuta." "Shikenan Dr, thanks you." "Allah ya bashi lafiya." Ya wuce shi, kasa motsawa daga inda Sulthan yake yayi, yaji kamar an sare masa gabobin sa, da k'yar ya ja kafafuwan sa a hankali ya kaisu dakin, ya tura kofar kamar me jin tsoro, tsoron abinda zai tarar.   Da wani irin yanayi yake kallon wanda yake kwance a gadon asibitin, wanda yake amsa sunan Safwan dinsa, yayi wata iriyar rama ta ban mamaki, ga wani mugun fari da yayi wanda kallo daya zaka masa kasan babu wadataccen jini a jikin sa. Numfashin sa dake sama sosai ya kalla ta jikin oxygen din dake makale a hancin sa, fuskar sa ta sirance sosai leben bakin sa ya bushe yayi fari fat.    Rike gefen gadon sultan yayi, ya durkushe a wajen kuka na tawo masa, kukan halin da Safwan yake ciki, kuma duk a dalilin sa, a dalilin son faran tawa birnin zuciyar sa, yes yasan yana da bukatar iyayen sa a kusa dashi musamman da ya tabbatar da wanzuwar su a doran k'asa ba wai mutuwa sukayi ba, amma da ace an bashi zabi tun farko, an bashi zabin haduwa dasu ko shigar Safwan din wannan halin toh tabbas zai zabi ya hakura da su din saboda Safwan din.    Babban dalilin da ya saka shi k'in fad'a wa har Amrah abinda ya shirya da tafiyar sa duk dan kar su shiga ciki,duk dan kar wani abu ya same su ne, sai gashi komai ya juya masa, a lokacin da yake farin cikin samun asalin sa, a wannan lokacin ne kuma yake bakin cikin halin da Safwan da Amrah suka shiga saboda shi.   Gani yayi ya motsa, ya tashi da sauri yana son gasgata abinda idon sa ya ke gani, da gaske motsin yayi, yana kuma cigaba da kokarin motsa jikin nasa duk kuwa da ciwon da yake jiki. "Safwan!" Ya kira sunan shi ganin yana kokarin bude idonsa,daina motsawa yayi ya tsaya chak, sai kuma yayi wani nishi me karfi sannan ya bud'e idon ya dora su akan Sultan dake tsaye a gaban sa a rikice ya shiga kokarin had'a magana, maganar da ke fitowa daga chan k'asan mokoshin sa, "Karka yi magana, karka ce komai." Ya rik'e hannun sa kakam ya shiga duba shi yana son tabbatar da komai daidai. "Sultan, Nagode, Nagode sosai da duk kulawar ka gareni, kayi dawainiya dani tun muna yara har yanzu baka daina ba..." "Shissh, ka daina magana kana hurting kanka, baka bukatar yin magana kayi shiru dan Allah." "Dan Allah ka barni na ce wani abu." "Ba zaka sake magana ba, sai na baka dama." Yace yana cigaba da duba shi Shigowa duk sukayi, Mah-Mah ta karaso da sauri tana kuka "Safwan, sannu kaji, sannu." Ta rike hannun sa tana kuka sosai, kukan yadda ya zama a cikin kwana daya kachal "Mah-Mah...." Yayi mata murmushi kad'an wanda ya tsaya iya kan lips din sa kawai "Na'am, nice Safwan, sannu Allah ya baka lafiya." Matsawa baya sultan yayi, ya saka bayan hannun sa ya goge fuskar sa. Dr ne suka shigo da sauri, Dr Labaran ya fara fad'an shigowar da sukayi dukkan su, babu kuma wanda yaje ya kirasu da ya farfado, fita duk sukayi aka bar Sultan da ya rike hannun Safwan din. Duddubawa suka sakeyi Sultan na kallon su, sun dad'e suna tsaye a kansa suna bincike,kafin Dr Labaran ya fita ya bar Dr Osas da wani Dr Bashir suna cigaba da duba shi. Dr Labaran na fita Safwan din ya fara tari sosai, tarin da ya saka Sultan mikewa tsaye yana mamaki da tsoron abinda ya kawo tarin, sosai tarin ya cigaba da karuwa wanda ya saka su Dr Osas a cikin tashin hankali suka rufa akansa, aman jini ya fara sosai kamar zai amayar da kayan cikin sa, rik'e shi sultan yayi tsoro na shigar sa, idon sa yayi masifar kad'awa yayi wani irin ja, jijiyoyin kansa duk sun fito radau suna harba jini da sauri sauri, kokarin tsaidawa Safwan tarin suke sai dai abin nasa kamar ma gaba gaba yake yi.    Kamar wasa sai ga wasu manyan Dr hadda su Dr Ahmad duk sun zo, su wajen bakwai akan sa hadda Sulthan duk da shi babu abinda yake yi babu kuma abinda yake aikatawa sai bin su da ido kawai yake kamar ma be san abinda yake faruwa ba, ko kuma shima ya samu wata babbar matsalar a kansa dan ko juya kan baya iyayi saboda yadda yake masa ciwo.    Sun yi iyakar kokarin su da zasu iya, sun yi duk yadda suke tunani da hasashe,amma babu wanda ya iya da abinda Allah ya hukunta. A hankali gabobin jikin sa suka dinga saki har suka saki gaba daya suka tsaya chak suka daina aiki gaba d'aya. Sai a lokacin Sultan ya samu wani karfi, ya ture Dr Ibrahim yayi kan Safwan din "Safwan! Safwan! Ka tashi dan Allah, karka yi min haka, ba zan iya dauka ba ,zuciya ta ba zata iya dauka ba, dan Allah kar muyi haka da kai ka tashi." Rike shi dr Labaran yayi yana kokarin kwacewa ya saka karfi sosai ya matse shi yana son fad'a masa magana amma yaki sauraran sa, kokari suke dukkan su ya sauraresu amma gaba daya jin sa da ganin sa sun dauke, sai gashi zai zube sukayi saurin tallafar sa aka dora shi a dayan gadon suka shiga bashi taimakon gaggawa. ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥©Hafsat Rano 38-40 ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE!!! _INA MA’ABOTA KARATUN LITTATTAFAN HAUSA? WANDA ZAI NISHADANTAR DAKU, YA FADAKAR, YA KUMA TSUNDUMA KU A KOGIN LOBAYYAR KAUNA? TO KU MATSO KUSA... DOMIN MUNZO MUKU DA ALBISHIR DIN WANI GANGARIYAR LITTAFI.. DAYA NE TAMKAR DA DUBU.. YAZO DA WANI SALO NA DABAN WANDA ZAI SANYAYA ZUKATAH.._ _LITTAFIN *UNCLE NE...* LITTAFI NE FIRST OF ITS KIND, DA YAZO A WANNAN SHEKARA TA 2021. AN BAJE KOLIN BASIRA A BOOK DIN UNCLE NE.._ _”Wait... Dakata hafsat Rano, Kina nufin NIMCYLUV, dai shararriyar murubuciyar nan itace tazo da wani salon rubutun..?..”_ _”Kede bari Billyn Abdul.. Tsaya kiji kanun labarin a tak’aice..*NIMCYLUV* Tace book din a ta’kaice labarin *UNCLE NE* ne yana tafe:_ _Da farko yana mata kallon uwa wacce ta haife shi kuma jigon rayuwarsa, ashe itace silar rushewar rayuwarsa😢yarinyar da yakewa kallon ƙanwa uwa ɗaya Uba ɗaya ita aka wayi gari ta zama MATAR SA🙆🏻‍♀️ ƙaddara ta haɗashi da (Ahlil kitab) kiristan ya bata farin ciki, kulawa, soyayya, harya samu ta musulunta, Dalilinta sbd al'ƙawarin aure da yyi mata,ashe ba sonta yake ba🤔yaje birnin NUFAR domin kai masu tayin Muslunci, sun amince da hakan amma sharaɗin dole ya kwanta da ƴarsu,🤦🏼‍♀️gashi bashi da cikakkiyar lfy mazantakarsa bata aiki😫 ashe mahaukaciya ce ta haife shi.._ “_Kai lalle akwai runguntsumi acikin wannan littafi..  Ba za’ayi babu ni ba, Domin Za’a sha lagwadar romon dadi. shin tayaya ake biya Hansatu?_” _”Ai ta Abdul..LITTAFIN *UNCLE NE* Naira 300 ne, Idan kuma kana son vip inda za'a ake posting sau biyu a rana kuma za'a baku littafan data rubuta na kuɗi sai ka bada 600 mai ma kon 1k.. number asusu wato bank account details: 0116886423 : account name sulaiman Na’ima S. Bank name: unioun bank: Sai a tura shedar biya ta 08119237616... A nuna mata ƙauna ta hanyar turowa ta account🤲🏻kamar yadda Za’a  faranta maku a littafin UNCLE NE_ _(Best romantic love story of the year//Had’adden labarin kauna na shekarar 2021)_ ***Mikewa Mah-Mah tayi zumbur, tayi hanyar dakin, Daddy ne yayi saurin rike ta, ya girgiza mata kai cike da tausayin halin da take ciki, yasan tana son Safwan son da bata taba yiwa wani irin sa ba, ya kuma san yadda take fama duk lokacin da wani abu ya samu Safwan din, shiyasa ma yanxu da Safwan din yake a halin da babu wanda zai iya fad'an me zai faru, ya ke tausayin ta sosai, irin tausayin da yaji a wasu lokuta da suka sude a lokacin da basu samu haihuwa ba. "Dan Allah ki kwantar da hankalin ki, ki barsu suyi aikin su, mu cigaba da addu'a in Sha Allah zai samu sauki, kinga fa wajen su nawa ne a ciki, muyi addu'a kawai." Komawa tayi ta zauna amma ta kasa tsaida kukan da take, kukan da duk wata uwa da danta ya samu kansa a irin wannan tashin hankalin zatayi. Farkawar Amrah ya saka duk suka tafi dakin, taimaka mata Umma tayi ta zauna ta jingina da pillow. Kowa yayi mata sannu, Mah-Mah tana dubata da koma chan dakin da Safwan yake ta zauna ta barsu, tana zama yan uwanta mata suka zo suma suka zauna tare duk akayi jigum ana jiran tsammani.    Dadewar likitocin a ciki ya kara tashar da hankulan su, kowa ka gani addu'a ce a dauke a bakin sa. Da gudu Dr Bash ya fito, suka tashi gaba daya sukayi wajen sa "Dr ya Ake ciki dan Allah?" "Sai dai kuyi hakuri." Yace musu ya wuce da sauri, ya dauka wa Dr Ahmad abu ya dawo ya wuce su ya shiga ciki. Rik'e Mah-Mah akayi da wani mugun jiri ya kwashe ta, saura kadan ta fadi a wajen Allah ya taimaka suka rik'e ta, "Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun, Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun,kulli nafsin za'ikatil ma'aut!" Sai tayi shiru bata sake cewa komai ba, kawai ta shiga bin yan uwan nata da ido da suke kuka amma ta kasa magana, "Kiyi kuka Dan Allah, kiyi kuka ko zaki samu sauki, karki ce zaki kume dan Allah kiyi kuka." "Anya da gaske suke?" Tace tana kallon ta Sai kuma ta dafe kanta "Sai dai kuyi hakuri, kenan ya mutu, haka likitan nan yake nufi ko?" Ta sake tambaya tana kallon su, tausayinta ya saka kowa har wadanda suke kusa da wurin zubda hawaye, sai kawai ta dinga juya kanta da sauri da sauri tana girgiza shi "Be kamata ya mutu ba, Safwan ya sha wahala, gaba daya rayuwar sa a jinya ya yi ta, tun haihuwar sa kawo yanzu be ji wani dadi ba, kullum a wahala yake, ya kamata ace shima yayi rayuwa irin ta kowa.... Be kamata ya mutu ba..." Da sauri Anty Farida ta rufe mata Baki "Dan Allah kiyi shiru, karki yi sabo, zafin mutuwa ba zai saka kiyi Sabo ba, Allah ne ya halicci Safwan, ya dora masa jinya ba wai don Baya son sa ba, a ah sai dan Ya gwada karfin imanin sa da namu, yanzu kuma da ya karbi abin sa, bamu da hurumin tambayar dan me? Domin Shi yafi mu sansa." "Nayi shiru, nayi shiru." Ta Shiga fad'a tana girgiza kanta "Astg...." Ta dinga maimaita Sai a sannan kuka ya zo mata, ta durkusa a wajen ta shiga yin sa a hankali ba tare da daga murya ko ihu ba. ***Duk sun dukufa akan Sultan da ya ke kokarin shiga mugun hali, suna bashi tallafin da zasu iya. Dr Ahmad ne kad'ai akan Safwan wanda yake kokarin ganin ya tabbatar da zargin sa. Da sauri ya matso da ventilator machine ya had'a ya saka masa yana kokarin ganin ya daidai ta respiratory failure da ya samu dazun, kamar an fisgo numfashin haka ya dawo da karfi har sai da ya fitar da kara, sai kuma ya shiga fitar dashi da dan sauri da taimakon Allah da taimakon Machine din. A hankali ya fara daidaita har ya dawo daidai, sai dai har lokacin babu wani abu a jikin Safwan din daya motsa sai wannan numfashin da ya samu nasarar dawowa. "Alhamdulillah!" Suka had'a baki wajen fad'a, Dr Labaran ya mika ma Dr Ahmad din hannu sannan yace "Kaga ikon Allah ko Dr?" "Wallahi, alhamdulillah." Dr Osas da yake ta wajen Sultan ya juyo "Dr Sultan ma ya samu kansa, but nayi masa allurar bacci saboda yadda jinin sa yayi mugun hawa, tunanin mun rasa dan uwan nasa da gaske yasa na masa allurar kar muje sad news din yayi breaking dinsa, sai gashi kuma ya samu numfashin ya dawo." "Hakan da kayi daidai ne Dr." Dr Labaran yayi saluting dinsa yana murmushi. "Thanks Sir." Fitowa sukayi suka bar Dr Bash a ciki da yake sake examining Safwan din, abu daya zasu jira yanzu shine farkowar which basu san yaushe ba, zai iya daukar lokaci sosai, amma suna fatan ya tashi din. Wucewa Dr Ahmad sukayi Dr Labaran kuma ya tsaya a inda su Daddy suke, Abba yayi karfin halin cewa "Dr yaushe za'a bamu shi mu tafi dashi?" "Ina za'a tafi dashi? Ko zaku chanja masa asibtii ne?" Kallon juna sukayi, Daddy ya matso da sauri "Dama wai gawar tasa..." Katse su Dr Labaran yayi da sauri "Ai be mutu ba, da ransa dogon suma yayi kuma yanzu an samu ma numfashin sa ya dawo daidai, duk da he's still unconscious amma ana saka ran farkawar sa ko zuwa nan da 3days ne." Da sauri Mah-Mah ta taso, ta rufe bakin ta da mayafin ta tana dariya hade da kuka "Da gaske kake Dr? Da gaske?" "Baa wasa da mutuwa ai Hajiya." "Alhamdulillah ya Allah." "Sai dai an kara samun sabon patient, Dr Sultan ma an bashi gwada, tunanin ko Safwan din ya rasa ransa ya saka Sultan din faduwar data saka shi suma a take, gaskiya soyayyar da yake ma dan uwansa ba karama bace, ki gode wa Allah Hajiya, Allah ya had'a miki kan su, kuma tabbas kin yi kokarin basu tarbiyya me kyau." Sai ya juya ya tafi, shiru Mah-Mah tayi, karo na farko tun Bayan abubuwan da suka faru taji abinda tayi wa Sultan bata kyauta ba, bata kyauta ba yadda akayi idon ta ya rufe ta manta waye ma Sultan din, yaron da ta raina da hannun ta, shi din kamar Safwan ne, tarbiyyar ta ce, ita ya sani a matsayin uwa har kuma gobe yana mata kallon uwa, soyayyar da yake wa Safwan din zata iya cewa tafi wanda shi safwan din yake masa, shi yake kula da dukkan al'amarin Safwan din tun suna kanana, har suka girma be taba gajiya ba, ya kan hakura da komai na jin dadi in dai Safwan zai samu farin ciki, ya akayi ta manta wannan? Har tayi masa abinda har ta mutu ba zata daina jin kunya ba, d'a na kowa ne, kuma baka san wanda zai taimake ka ba, baka san waye Alkhairin ka ke tare dashi ba, ya akayi ta biye wA sharrin zuciya har ta kasa ganin daidai da aikata daidai? Ta manta da cewa da haihuwa da mutuwa da aure duk lokaci ne,idan lokacin yayi dole ayi, ta manta da fad'ar nan ta hausawa dake cewa Matar mutum kabarin sa, babu kuma wanda zai auri matar wani. Duk ina ilimin ta yake? Ina sanin ya kamatan ta ya tafi da har ta yarda da rudin zuciya.    Ko da ta shiga dakin da suke a kwance, sai ta tsaya chak ta rasa wajen wanda zata je, ta cigaba da kallon su cike da tausayawa, dukkan su a dalilin dayan su suka shiga halin da suke ciki a yanzu.    Matsawa tayi gaban gadon Sultan din, ta dafa kansa ta yi masa addu'a, har lokacin idon ta na zubda hawaye, tana jin dana sani da tausayin Sultan din. Sai data tsaya a wajen sosai tana tuna abubuwa da yawa sannan ta nufi gadon Safwan din, shima tayi masa addu'a kamar yadda tayi wa Sultan sannan ta fita. Ita kad'ai ta shiga ta gansu shima saboda tausayin ta da Dr Labaran yaji yasa yace ta shiga din dan shi duk a tunanin sa duk su biyun yayan ta ne, yasan dole ta damu ta shiga tashin hankali saboda yasan yadda uwa take son yayanta. ***Tun da suka isa asibitin sai Muhammad ya tsaya wajen yan sandan nan ya basu dukkan bayanan da suke bukata sannan suka rakashi har gida, yana zaune yana tunanin ya kamata ya koma asibitin ya duba jikin su Aysha ta leko tana kiran sa. "Ya Muhammad!" "Ya akayi?" "Yanzu Baba Altine ta zo take cewa wai yan sanda sunje gidan Alhaji zasu tafi dashi amma wai baya kasar, kowa yayi mamakin zuwan yan sandan amma babu wanda yasan dalili." "Owk." Yace yana juyawa, yasan dalilin zuwan nasu ya kuma san Madakin ba zai zauna ba, tunda aka kama yaron sa daya ya tabbatar da zai shiga hannu shima, ga bayanan da ya bayar da kuma abinda suma su Sultan din zasu bayar a had'a, shi be damu ba, burin sa kawai Ammi ta dawo, tunda yasan idan aka kama Madakin zai fad'a musu inda ya kai musu mahaifiya. "Baka ce komai ba yaya?" "Me zance Aysha? Kawai aiki ne ya biyo ta kansa." "Idan suka tafi dashi Ammi fa? Yaushe zata dawo ita?" Idon ta yayi raurau zatayi kuka. "Addu'a!" Juyawa tayi ta fita, tasan halin Muhammad din sarai, sai tace ma bata taba ganin miskili irin sa ba, idan baya jin magana toh sai ya wuni ko k'ala be ce ba, duk kuwa da ita yana ma sakar mata suyi hira amma idan yan abun suka motsa sai yayi mata mirsisi, sanin cewa ba zai ce komai din ba yanzu yasa ta hakura ta barshi.    ***Sun cika dakin sosai yan uwa da abokan arziki, Amrah na zaune tana kallon kowa, hankalin ta rabi ya tafi kan halin da Sultan take tun bayan da labarin abinda ya faru ya bazu, so take ta tambaya ko akwai wanda ya san ya ake ciki amma ta rasa wanda zata tambaya, musamman tun zuwan hajiya da maganganun da ta farfada tun bata ma san dalilin da ya saka akayi kidnapping Amrah din ba, sai kawai taja bakin ta, ta tsuke tayi masa adduar samun sauki da shi da Safwan din dukka. Tun bayan azahar Sultan ya tashi, kafin ya gama bud'e idon sa ma Dr Osas ya sanar dashi condition din Safwan din da abinda ya zata da kuma abinda ya faru, hakan yasa ya mike da kwarin sa,duk da kansa na masa ciwo har lokacin amma labarin da ya samu ya saka shi raguwa zuwa kaso mafi yawa. Shi kad'ai ne a dakin Safwan na dakin sa daban, tashi yayi da k'yar Adnan ya taimaka masa ya shiga yayi alwala yazo ya rama sallolin dake kansa, sannan ya bukaci ganin Safwan din, babu wanda ya hanashi, haka suka fito shi da Adnan da zai raka shi, a hankali yake tafiyar saboda yadda yake jin iska na kad'a shi kamar zai fad'i, ya iske su Mah-Mah a waje suna zaune da wasu mata da be tsaya tantance su waye ba, ya wuce su kawai ya tura kofar dakin, a yadda ya ke tun bayan zuwan su asibitin haka yake still sai dai yanzu da banbanci da dazu, yanzu akwai alamun nutsuwa a baccin da yake yi, ya dade a tsaye, yana duba file din da bayanan dake jiki kafin ya ajiye, ya gyara masa kwanciyar sa ya fito. "Sultan be ganmu bane?" Ya Umma tayi maganar tana kallon Mah-Mah "Ba lallai idan ya lura damu ba, shima yana bukatar hutu don shima ba lafiyar ce dashi ba." "Toh me kuma ya sameshi? Bayan shine ya jawo komai." "Dan Allah Ya Umma mu bar maganar nan, yanzu ba lokacin ta bane wani lokacin." Da mamaki Ya Umman ta kalle ta, ganin ta dauke kai yasa ta tabe baki tayi shiru tana tunanin abinda ya hau kan Mah-Mahn.     A kofar dakin ya tsaya yana jin hayaniya na tashi, fasa shiga yayi ya koma dakin sa ya bari idan suka ragu sai ya je ya ganta, duk da ta matsu ya ganta din amma haka zai hakura xuwa anjima din.    Rufe idon sa yayi kamar me bacci a zahiri sai dai a bad'ini tunanin abinda ya kamata yayi kenan, dole zai koma Canada, kuma dole zai tawo dasu domin dawowar su shine zai kawo kusan karshen komai, amma dole sai ya jira Safwan ya samu sauki, Maman Yara da wannan Matar sun dawo daidai, Amrah ma ta samu sauki tunda da ita zai yi tafiyar ba zai sake barin ta ba ko nan da chan zaije. Sai yaji chan kasan zuciyar sa, zuciyar sa dake son sauya halin da take ciki na bacin rai ta maye gurbin sa da farin ciki ta rada masa wata magana, maganar da ta saka shi yin murmushi duk da ba har chan ciki murmushin yake ba.    Mike kafarsa ya sake yi yana son kore tunanin zuciyar tasa musamman a wannan halin da yake ciki na ganin lafiyar Safwan.    Sai kuma saurayin nan ya fado masa, saurayin da ya taimaka ma Amrah, menene hadin sa da Madaki, me ya kai shi wajen me kuma yake nema? Be sake ganin sa ba tun bayan sun dawo,be ma kuma tuna dashi ba sai yanzu. Tashi yayi da sauri ya zauna yana tuna sanda ya ganshi a gidan Madaki sun shigo a lokacin shi kuma zai fita, idan har yana da alaka da Madakin me zai saka ya taimaka wa Amrah? Ba shi da amsar,sai dai yana jin son sake haduwa dashi, akwai tambayoyi masu yawa da zai masa, yana jin sa sosai kamar ba ranar ya fara sanin sa ba, kamar sun dade da haduwa a wani waje daban wanda ba zai tuna ba.   Haka ya cinye lokacin wajen tunanin abubuwan da ya kamata yayi, shigowa Adnan yasa ya tashi suka je sukayi Sallah, maimakon ya dawo sai yayi zaman sa a masallacin har akayi isha'i, yayi shafa'i da wutri ya dan zauna kafin ya fito. Kai tsaye dakin da Amrah take ya nufa, ya tsaya a kofar ya kwankwasa, Umma ce sai Hajiya da wata kanwar Abba kawai sauran sun tafi, plate ne a hannun Hajiyan tana ta sababin kin cin da Amrah tayi tana mitar inda za'a samu lafiya idan ba'a ci abinci ba ya kwankwasa. Umma ce tace a shigo amma sai ya tsaya ya kasa shigo. "Ya Sultan ya ka tsaya anan?" Afrah da dawowar ta daga gida kenan ta dauko wa Amrah wasu kayan da brush da toothpaste ta fad'a daga bayan sa. "Afrah..." "Bari nayi musu magana." Tace tana shigewa ciki Komawa yayi daga gefe ya tsaya, yana tsaye suka fito, ya durkusa kansa a k'asa ya gaida su, Hajiya da tayi gaba kawai bata tsaya ba ya dan kalla sai kuma ya kalli Afrah dake masa maganar ya shigo ciki. Kamshin turaren sa ne ya fara yi mata maraba, ta bud'e idon ta, ta rufe a hankali ta sake budewa tana jin wata nutsuwa na shigar ta "Gata nan ya Sultan, taki cin abincin kuma Dr tace taci abinci sannan ayi mata allurar ta, sai fama ake da ita kila idan kasa baki taci." Sai kuma tace "Auw ya jikin? Ashe wai kaima baka ji dad'i ba, dazu naji ana fad'a." "Da sauki." "Allah ya kara sauki." "Amin ya Allah, Nagode!" "Bari naje wajen su Umma." Tayi gaba ta rufe kofar. Ledar da Afrah ta ajiye ya dauka ya fito da kayan ciki, bra ce da pant sai doguwar riga da toothpaste, da sauri Amrah ta rufe idon ta ganin ya daga bra din yana kallo, sai kuma ya ajiye su a gefe ya matso. "Ya jikin naki?" Kin bud'e idon ta tayi, tayi shiru dan sosai taji kunyar ganin kayan da yayi, har da dagawa yayi ya kalla sosai tana kallon sa ta gefen ido. Kafin ya shigo ta riga ta gama tsara yadda zata yi masa idan ya shigo, zata tambaye shi ya jikin sa, ta kalle shi sosai saboda she's missing him, amma daga shigowar sa sai taji gaba daya tayi losing confidence, ta kasa daga ido ta kalle shi musamman ganin yana kallon underwears dinta, a take abinda ya faru ana gobe ranar da zai tafi ya faru, hakan ya kara saka ta cikin matsananciyar kunyar sa taki bud'e idon ta. Tana jin idon sa akanta yana bin kowanne lungu da sako na jikin nata da kallo, idon sa yayi mata karfin da ta shiga jin sanyi sosai kamar wadda zazzabi zai rafke. "Zaki chanja kaya ko?" Yayi maganar yana dago kayan. Tashi yayi ya shiga toilet din dakin, ya tara mata ruwa sannan ya fito, yazo ya kama hannun ta "Tashi ki watsa ruwan sai kici abincin." "Na'am..." "Lemme help you." Ya rik'e ta, ya taimaka mata ta sakko, ta tsaya a gaban sa so close har tana jin hucin numfashin sa da yake da zafi. "Ya jikin?" Ta tambaye shi "Alhamdulillah." Juyawa tayi zata tafi taji ya rike mata riga ta baya "Bari na taimaka maki, naga kamar har yanzu akwai weakness." Zip din ya kama ya shiga zuge mata, sai da yazo tsakiyar bayan sannan ya saka hannu ya balle mata bra din, da sauri ta juyo tana kallon sa, hankalin ta a tashe. "Comman, taimaka miki zan,idan kika shiga sai kawai ki cire gaba daya." "O... Ok." Tace tayi saurin juyawa tayi hanyar toilet din, "Amrah..." Ya kira sunan ta, tsayawa tayi amma bata juyo ba, ya tako ya tsaya a bayan nata, yasa hannu ya juyo da ita, yayi kokarin shigar da idon shi cikin nata amma ta ki, matso da ita yayi sosai har jikin ta na taba nasa, yasa hannu ya taba bandage din dake saman kan nata ya girgixa kansa "I'm sorry, so sorry." Bata bud'e idon ta ba, ya shafa fuskar ta da cikin hannun sa, a hankali ya kai bakin sa saman nata ya bata light kiss, wanda ya saka ta jin wata irin juya, tayi saurin dafa bangon wajen. Cikin tashin hankali ta saki kofar, zuwan su kenan ta tambayi Sultan, taje dakin da yake baya nan shine ta biyo shi nan, hankalin ta ya tashi da aka ce mata baya jin dadi Shima, shine duk ta rikice ta biyo shi nan din, sai dai abinda ta gani ya saka ta kusan shid'ewa, mutumin da aka ce shima sai da aka bashi taimakon gaggawa shine a tsaye yana kissing mace. Yadda ta saki kofar ne ya saka Sultan juyowa, Amrah tayi saurin shigewa toilet shi kuma ya koma wajen kayan abincin ya shiga zuba musu. **Ayi mun afuwa rashin jina, yara suka lalata min charging point n wayar©®Hafsat Rano Page 41 Ina ma’abotan son ingataccen yaji, Different Flavors that complements each other, Yajin da ke daidaituwa da duk sinadaran abinci na al’adance da zamanance, Muna muka albishir da sanardaku cewa nesa tazo kusa domin @the_flavorland by Aceey yakawomuku duk nau’ukan yajinda kuke iya buqata Saboda yajin ya hada da: Daddawa Yaji, Waton yajin daudawa Garlic Yaji, waton yajin tafarnuwa da kuma Beef Yaji, wato yajin Nama kuma me hade da nama Domin ayukkanku da yau da kullum wanda ya hada da: Dahuwar abinci/nau’uka na miyoyi DA Gashe gashe da soye soye kamar su Kaza Kifi Nama Doya Dankalin turawa/hausa Awara Danwake Gurasa Kwado da dai sauransu.... Ba Mu tsaya anan ba—— The_flavorland ya hada da kayan tande tande da lashe lashe da suka hada da Hoppers wato Fara Milky candies wato alawar madara da kuma Milky balls wato Gullisuwa da de sauran abunda rai ke buqata... Zaku iya tuntubar mu a kafofin sada zumunta kamar haka IG: @the_flavorland Whatsapp:08104673847 Sending Some treats your way.... l Let us satisfy your cravings: We Deliver anywhere and everywhere. ***Gama zuba abincin yayi, sannan ya ciro magungunan ya ajiye a gefe ya zauna yana cigaba da duba file din, shiru bata fito ba, ganin ta dade yasa ya tuna kayan da zata saka na ajiye a gefe, ya san kuma ba zata maida na jikin ta ba, dauka yayi ya tsaya a kofar ya kwankwasa "Ga kayan ki saka." Zuro hannu tayi xata karba ya rik'e,ta ja ya sake rikewa yana kokarin bud'e kofar, da sauri ta danno kofar, yayi dariya kad'an, dama tsokanar ta yake yi, bata yayi ya koma wajen da ya taso, sai gata ta fito tana taba saman kanta tana yatsine ido. Da sauri ya tashi ya riko ta, sannan ya taimaka mata ta zauna sosai. "Zanyi sallah." "Ok." Yace ya ciro hijab a kayan ya saka mata, ya taiamaka mata ta zauna tayi sallolin a zaune, tana gamawa ya dauko abincin ya ajiye ya matso da ruwa da magungunan, "Oya." Ya debo abincin ya nufi bakin ta, a kunyace ta bud'e bakin ya saka mata, ta marairace fuska kamar zata yi kuka, babu taste a bakin ta ko k'ad'an, "Ba zan iya ci ba." Ta juyar da bakin ta gefe ganin ya sake debowa, ajiye yayi ya had'a mata tea, sai ta karba tasha sosai, sannan ya bata fruit taci kad'an tasha magani da k'yar saboda yadda ta tsane shi. Sannu yake ta faman jera mata cike da kulawa da tausayawa. "Zan kwanta." Tace masa jin kan nata na mata ciwo. Sake taimaka mata yayi ta kwanta sannan ya karasa cin abincin da taki ci duk da shima dan wanda yacin kad'an ne, saboda rashin appetite da rashin karfin jiki. Yana gamawa suka shigo tare da Nurse Falmata da zata yi mata allurar, yan sanda ne su biyu,hannu ya basu suka gaisa sannan suka bukaci magana da Amrah suna son daukar statement din ta, shi ya sake taimaka mata ta tashi zaune, ta amsa musu duk tambayoyin su, sannan suka bukaci sultan ma ya bada nasa bayanin. Fita sukayi ya juya zai bi bayan su Nurse Falmata ta tsaidashi "Dr sai fa ka taimaka, dan dazu ma da k'yar aka yi mata." Kallon Amrah yayi da idanun ta suka fito sosai alamar tsoro, yayi murmushi ya matso. "Kin cika tsoro, allurar ma?" Yace yana zama kusa da ita, sannan ya jawo ta jikin sa, ya dora mata fuskar ta a saman fad'ar sa, kamar yadda ake rike kananan yara haka ya rike ta, ya rada mata wani abu a kunnen ta wanda ya saka ta mantawa da allurar da za'a yi mata, da hannu yayi ma Nurse Falmata da tayi mata,fuskar ta cike da murmushi ta matso tayi mata allurar, sai bayan da ta cire sannan ta motsa tana son tashi, ya sake matse ta sosai. "Malama don't pretend sai bayan an gama zaki wani tashi, kin san sanda akayi miki?" Ya tsare ta da ido bayan ta dago kanta. "Bata sani ba kam Dr, Allah ya bada zaman lafiya." Nurse Falmata tace tana juyawa ta bar dakin tana murmushin abinda ya faru. Turo baki Amrah tayi tana son tashi, hana ta yayi, ya zagayo da hannun sa ta bayan ta, "Police din nan suna jiran ka fa." Cikata yayi dan har ga Allah ya manta dasu, ya juya ya bar dakin. Kasa controlling farin cikin da take ciki tayi, ta dinga blushing, kumatun ta har wani lotsawa yake saboda farin ciki, babu abinda yafi soyayya dadi idan kayi dace, musamman da mutum irin sultan wanda yasan yadda zai ya faranta maka. Hajiya da kanwar Abba basu dawo dakin ba sai Umma da zata kwana ita da Afrah suka shigo suka zauna, basu dad'e da zama ba ta koma baccin cike da mafarkin Sultan ***Ko gaban ta bata gani, haka ta karasa wajen da suke zaune, kad'an ya rage ta taka kafar Mah-Mah Allah ya kiyaye. "Ke Umaimah, me kike yi haka?" Anty Farida ta yi maganar ganin yadda take kamar zata fad'i, rik'e ta Ya Umma tayi, ta jata gefe. "Menene?" "Bakin gani nayi, Sultan tare da banzar yarinyar chan, wayyo zuciya ta zata fashe wallahi." Da sauri Ya Umma ta rufe mata baki "Karki tara mana mutane anan kike daga murya haka, Matar sa ce fa." "Allah Anty Ummah ba zan iya dauka ba, zuciya ta na mun zafi noo I can't take it." Ta girgiza kai tana buga kafa da karfi "Nace ki bar komai a hannu na ko? Kinga ban yi wani abu bane ko Yaya? Ki bar komai hannu na." "Lokaci tafiya yake ai." "Karki damu, ki barmun komai kawai kinji yar albarka?" "Shikenan." Ta barta a wajen tayi hanyar da ba wajen da su Mah-Mah ke zaune ba. "Allah ya kiyaye wallahi,yadda na tsani yaron nan ficika ba zan kashe ba, haka zaki hakura ki samu wani me arziki da tushe ki aura." Tayi maganar tana komawa wajen su Mah-Mah. ***Abubuwa sun kara baci a Masarautar Saji,gaba daya komai ya tabarbare, sosai Yarima Bilal da Sarki Bello ke haurawa sama, shi Sarki Bello damuwar sa yadda za'a yi komai ya daidaita, wanda shi kuma Yarima ta mulkin kawai yake wanda shi a haukan sa tunda ya samu shikenan,be san abinda zai biyo baya ba. Duk wadanda ke da ruwa da tsaki a cikin maganar sun shiga damuwa, gashi aikin suke babu dare babu rana amma shiru kake ji kamar an shuka dusa, ko isasshen bacci basa yi suna kulla yadda komai zai kasance, ya kuma cigaba da tafiyar musu kamar yadda yake, sai dai abinda basu sani ba shine... Allah zai ta arawa mutum dama ne, har zuwa wani lokaci, lokacin tonan asiri, lokacin jin kunya da dana sani mara amfani. Madaki tun da ya samu labarin kama yaron sa daya da akayi, ya tsallake ya bar kasar, dama akwai tafiyar da zai yi washegarn ranar Kawai sai yayi amfani da wannan ya cikawa wandon sa iska, duk da ba wai ya hakura bane amma kuma yana bukatar lokacin tunani. ***A hanya suka hadu da Umaimah, tayi kamar zata fad'a kansa da ta ganshi, yayi baya kadan "Are you ok?" Tace tana kallon jikin sa, tayi kokarin kai hannu saman kansa fuskar ta na nuna tsantsar tausayin sa "Ya jikin? Me yake maka ciwo yanzu?" "Babu komai, na samu sauki." "Amma ka rame sosai." "Yaushe kuka zo?" "Dazu, nazo zan dubaka dazu sai..." "Ohh kece kika shigo dazu dama?" "Amma mesa baki shigo ba kika koma?" "Naga kamar u guys are busy ne, bana so na dame ku." Tayi maganar tana son karanta expression din fuskar sa. "Ok. Yayi." Ya juya ya cigaba da tafiya, jerawa tayi suka cigaba da tafiyar tare tana cigaba da yi masa hira, da k'yar yake hada kalma uku zuwa hudu wajen amsa mata, dan bata san yadda ya gaji bane shiyasa, gashi sai son sako maganar Amrah take a fakaice tana son ganin yadda zai yi, ya jima da sanin take taken ta, ya kuma san dalilin da yasa take hakan. Shi ba wannan ne a gaban sa ba, da tasan abubuwan ma da suke kansa da ta shafa masa lafiya ta barshi da wannan uban zancen nata. Suna kawowa dakin da Safwan yake ya ja ya tsaya sannan yace "Ba'a shiga wajen sa." Yayi gaba kawai ya barta a tsaye, yasan bin sa zatayi da be mata haka ba, shiyasa ya dakatar da ita dan ba'a bukatar hayaniya ko surutu a dakin shiyasa babu wanda yake shiga daga Mah-Mah sai Daddy sai kuma Sultan din. Dakin Safwan din Sultan ya koma ya zauna yana lura da duk motsin sa, har wajen uku na dare be runtsa ba, baya jin baccin gaba d'aya,sai wajen asubah ya kwanta ana kiran sallar ya tashi,yayi sallah ya zauna ya bud'e wayar sa ya bud'e wani app din Al'qur'ani ya shiga karantawa a nutse. ***Leka wa Maman Yara ta sake yi tayi, tana mamakin abinda ya hana Sultan zuwa ya gansu tun bayan ya fita, duk sai taji babu dadi tana kuma tunanin Allah yasa lafiya dan tasan babu abinda zai hana shi zuwa garesu sai dai idan wani abu ya rike shi. "Me yasa har yanxu Sultan be dawo ba?" Aminatu tayi maganar tana kallon Maman Yara "Yanzu ma maganar sa nake a raina, Allah dai yasa lafiya." "Amin." Sai sukayi shiru gaba daya. Kowannen su na fatan ba wani mugun abu bane ya tsaida shi ya hana shi zuwa. Babu wanda Maman Yara take tunawa irin Madaki,tana tsoron abinda zai iya akan Sultan din tana kuma addu'ar Allah kar ya sake bashi dama akan kowa ma. ***Shiryawa yayi, ya dan ci abincin da Baba Altine ta dafa musu ya fito, so yake ya fara zuwa ya duba su a asibitin sai ya wuce wani waje. Keke napep ya hau ta kaishi har kofar asibitin ya sauka a gate ya shiga a kafa, duk da besa dakin da zai same su ba amma yasan ba zai sha wahalar nema ba, ya rik'e sunan Sultan da Safwan din ma saboda haka kai tsaye reception ya nufa, ya tambaye su, kwatanta masa sukayi yayi godiya ya tafi. Sai dai maimakon yayi bangaren maza sai ya nufi bangaren mata, ya duba number dakin itace wadda aka fad'a masa, ya tura ya shiga bakin sa dauke da sallama, direct kofar shigowa take kallo saboda haka yana shiga da ita ya fara cin karo. Wani irin shock yayi, yayi saurin cewa "Kuyi hakuri ba dakin da nake nema bane." Ya juya da sauri, "Bawan Allah!" Ta dakatar dashi, ta taso har da saurin ta "Yaya sunan ka?" Ta tambaye shi tana kallon fuskar sa "Muhammad." Sai ta girgiza kai, "Shikenan." "Sai anjima." Ciki ta dawo ta zauna, fuskar ta dauke da damuwa "Lafiya Aminatu?" "Ko kin sanshi ne?" "A ah, bansan shi ba, kawai dai..." "Kuskuren lamba ya samu da alama." "Eh daga gani." Tayi maganar tana sauke ajiyar zuciya. *** Sau wajen biyar kenan Daddy na katse kiran sa tun bayan da ya karanta sakon sa, be san dalilin kiran ba amma sai yake jin ba alkhairi bane kiran nasa, mamakin sa yadda akayi ya samu number sa, bayan dogon lokacin da aka dauka be sake jin duriyar sa ba. Ganin da gaske kiran ne ke sake shigowa yasa ya kashe wayar tasa ma baki d'aya, yayi abinda zai ya dauki abinda zai dauka ya koma asibitin. *** Manage pls!!!!!!!!!!!!!    © Hafsat Rano Page 42 ****Ina ma’abotan son ingataccen *yaji* Different Flavors that complements each other, Yajin da ke daidaituwa da duk abinci na al’ada by da zamani, Muna muka albishir da sanardaku cewa nesa tazo kusa domin *@the_flavorland by Aceey* Sun kawomuku duk nau’ukan yajinda kuke iya buqata Saboda yajin ya hada da: *Yajin daddawa* *Garlic Yaji* waton yajin tafarnuwa da kuma *Beef Yaji*  wato yajin nama kuma me hade da nama Domin ayukkanku da yau da kullum wanda ya hada da: Dahuwar abinci/nau’uka na miyoyi da Gashe gashe da soye soye kamar su Kaza Kifi Nama Doya Dankalin turawa/hausa Awara Danwake Gurasa Kwado da dai sauransu.... Ba Mu tsaya anan ba—— *The_flavorland* ya hada da kayan tande-tande da lashe lashe da suka hada da _Hoppers_ wato *Fara*😛 _Milky candies_ wato *Alawar madara* da kuma _Milky balls_ wato *Gullisuwa* Da de sauran abunda rai ke buqata... Zaku iya tuntubar mu a kafofin sada zumunta kamar haka *IG:* *@the_flavorland* *Whatsapp:* *08104673847* *Sending Some treats your way....* *Let us satisfy your cravings:*       We Deliver anywhere and everywhere. ***Sau wajen biyar kenan Daddy na katse kiran sa tun bayan da ya karanta sakon sa, be san dalilin kiran ba amma sai yake jin ba alkhairi bane kiran nasa, mamakin sa yadda akayi ya samu number sa, bayan dogon lokacin da aka dauka be sake jin duriyar sa ba. Ganin da gaske kiran ne ke sake shigowa yasa ya kashe wayar tasa ma baki d'aya, yayi abinda zai ya dauki abinda zai dauka ya koma asibitin.   Yana zuwa ya tarar da Safwan ya farka, duk da babu wanda ya shiga dakin sai drs din sai Sultan da dama yake ciki, amma su Mah-Mah sun ce masa wai Sultan din ne yaga yana motsi, shine ya dubashi yaga ya dawo hayyacin sa. Kowa ka kàlla a wajen a cikin farin ciki yake, suna tsatsaye ana jiran fitowar Dr's din suji idan komai lafiya. Mah-Mah bakin ta ya gaza rufuwa gashi ta kasa zama waje daya sai zagaye take.    ***Sai da suka tabbatar da babu wani abu apart from ciwon jikin sa wajen da bullet din ya shiga, heartbeat din sa ta dawo daidai he's stable, dan har ya bud'e idon sa ya kuma yi magana da SULTAN duk da ba me tsaye bace. Murnar da Sultan yake ciki fad'a ma bata baki ne, har tsokanar sa su Dr Labaran sukayi, yayi dariya kawai dan yasan duk bayanin da zai musu akan waye Safwan a wajen sa ma bata baki ne, shiyasa kawai yayi dariyar ya cigaba da mika godiyar sa ga Allah da be dauke Safwan a lokacin da yafi ko yaushe bukatar sa ba, lokacin da shima zai ji dadin Sultan din fiye da kowanne lokaci.    Sallama sukayi masa suka bashi sauran abubuwan da Safwan din zai bukata, ya matsa ta side din kansa murmushi kwance a fuskar sa, duk a lokacin ya koma bacci amma bacci ne wannan normal kamar wanda kowa ma yake yi, ba kamar wanchan da ba zaka tantance wanne hali mutum yake ciki ba.    Fitowa yayi su Mah-Mah da sauran yan uwa suka dunguma suka shiga,bai koma ba sai kawai ya nufi gate din asibitin a kafa, ya tsallaka titi kai tsaye wajen wasu mutane masu neman taimako yaje, ya rarraba musu kud'i sukayi ta murna suna sa masa albarka, sannan ya koma ciki ma yabi wasu dakunan ya basu kud'in. Yana cikin wannan zagayen ne ya tuna da su Maman Yara duk da ba wai ya manta dasu bane, amma ya kamata ace ya koma ya gansu. Abubuwan ne da yawa sosai, shiyasa shaf ya manta sai yanzu. Da sauri ya nufi bangaren nasu, sai dai kafin ya karasa suka hadu da Muhammad a hanya. "Muhammad?" Ya tambaya yana son tabbatar wa "Eh nine." Ya amsa yana daga kai Hannu ya bashi suka gaisa sannan yace "Ina ka shiga tun ranar ban sake ganin ka ba?" "Gida na wuce bayan sun dauki statement dina, shine yau na dawo na sake duba jikin nasu, ina fatan da sauki?" "Alhamdulillah wallahi, da sauki." "Allah ya kara sauki. " "Muje daga chan muyi magana please idan babu damuwa." Sultan yace yana nuna masa wasu kujeru daga gefe, "Ok." Suka nufi wajen, suka zauna sannan Sultan yace "Dan Allah Muhammad tambayar ka zan, ina fatan zaka fad'a min gaskiyar komai, da farko na taba ganin ka a gidan Safiyanu Madaki, duk da ba wai munyi magana bane na zo fita kai kuma kun shigo, ba lallai ma idan kun lura dani ba, amma ni na ganku,sai kuma abinda ya kai ka wajen nan har ka taimakawa Amrah, menene hadin ka da mutum irin Madaki?" Shiru Muhammad yayi, ya shiga tunanin ya fad'a masa ko kuma kar ya fad'a masa? Ya kamata kuwa ya yarda dashi haduwa daya? Idan kuma shi dinma yana da alaka da Madakin ko kuma shi din ba abin yarda bane? Toh amma kuma be yi kama da mutum mugu ko macuci ba, bisa abinda ya faru ma kamar dai shi din ma wani abu Madakin ya yi masa, ko kuma wani abu ya nema a wajen sa. Sake kallon Sultan din yayi, kaso mafi rinjaye na zuciyar shi na yarda dashi, yarda irin wadda zaka bawa mutumin da ka gama sanin halin sa, girma da kimar Sultan din cike da wani irin kwarjini da haiba ya saka babu wani bata lokaci ya budewa Sultan din komai, har zuwa lokacin da aka tafi da Ammi da abubuwan da suka faru bayan nan. Zumbur Sultan ya mike, ya kama hannun Muhammad din ya mika dashi yace "Yanzu baka san inda ita Ammin take ba?" Girgiza masa kai yayi "Abinda naje nema kenan, sai kuma nayi rashin sa'a, ba ita bace a wajen matar ka ce." "Ya sunan Ammin na gaskiya?" "Safiyya!" "Kai kad'ai ne ko kuma ku biyu ne?" "Ni da kanwata ne Aysha." "Aysha? Mace kenan? Kanwar ka? Ko kuma..." "Kanwata ce." "Ok Ammi bata taba ce maka kai din yan..." "Ta fad'a min, ranar da wasu yan biyu masu kama daya suka zo wajen matar da muke gida daya dasu, shine Ammi take cewa ai ni ma yan biyu ne, amma bama kama mu." "Ina dayan?" "Bata ban amsa ta ba a lokacin dana tambaye ta, sai kawai tace min ba yanzu ba." Shiru Sultan yayi yana tattara bayanan yana kuma jin tabbas matar nan da Maman Yara ta fad'a masa da k'yar idan ma ba ita ce ba, "In Sha Allah Ammi zata dawo cikin koshin lafiya, karka damu zan taimaka maka." Ya dafa kafad'ar sa cikin son kara masa k'warin guiwa. "Nagode sosai." "Karka damu, samin number wayar ka in case ko zan neme ka" Ya mika masa wayar sa, ya saka masa ya kirashi shina ya ga tasa yayi saving sannan suka yi sallama ya tafi shi kuma ya karasa dakin da su Maman Yara suke. "SULTAN!" Ta taso da sauri ta rik'e masa hannu, durkusawa yayi ya gaishe ta, bata amsa ba ta zura masa ido ganin muguwar ramar da yayi "Me yake damun ka?" Tace tana taba saman kansa "Zazzabi na danyi ne kwana biyu, shiyasa ma ban shigo ba, ya jikin naki?" "Ayya sannu Allah ya kara sauki, gashi nan duk ka rame wallahi, ni kalau nake Aminatu ce dama itama gashi nan ta dàwo hayyacin ta, dama wahala ce da rashin kula.". "Sannu kaji? Allah ya kara sauki." "Ina wuni?" Ya dan rissina ya gaishe ta, bata iya amsawa a haka ba, ta sauko kanta na k'asa sosai ta gaishe shi cike da mutuntawa, sosai hakan yasa shi jin babu dadi ganin Babbar mace na durkusa masa, "Kice dan Allah ta daina durkusa min, ina jin kunya Wallahi?" Ya fadawa Maman Yara yana chanja fuskar sa zuwa kalar rashin jin dad'i "Tana da dalilin ta babba nayin haka, hakan kuma shine ka'idar gidan sarauta, dole ta girmama ka a matsayin ka na Yarima, kuma sarkin gobe da yardar Allah." Wani irin banbarakwai SULTAN yaji, ya kasa cewa komai kawai ya shiga hasaso kansa a matsayin jinin sarauta, wadda be taba tunani ko hasashen zama cikin ta ba, ta ina ma zai fara idan har abinda Maman Yara ta fad'a ya tabbata? Kamar tasan zancen da yake kenan a zuciyar shi sai ji yayi tace "Idan har lokacin da duk muke jira yayi, zaka gane abinda nake fad'a maka, gado ba karambani bane Sultan, dole ne zaka iya, domin ko a yanzu ka tabbata jinin sarauta, tun yanayin tafiyar ka da yanayin komai naka cike da nutsuwa babu baragada, lallai za'a yi gagarumin Sarki wanda baa taba yin irin sa ba a kaf tarihin Masarautar Saji." Murmushi kawai Sulthan yayi, bashi da abin fad'a, idan ma akwai toh be san me zai ce ba, sai kawai ya matsa gaban inda Aminatu take, yace "Ya sunan matar da ake tunanin itace ta karbi yaran?" "Safiyya." Maman Yara ta amsa duk da ba da ita yake ba, juyowa yayi yace "Ina *** Kusan kwana uku kenan yana neman number Sultan din amma bata shiga,duk sun damu saboda sun jima rabon da suyi magana dashi, ranar bayan ya gama duk abubuwan da ya saba, ya sake gwada kiran, sai gashi ta shiga, yayi saurin saka ta a kunnen sa, yana addu'ar Allah yasa ya d'aga, kafin ya gama addu'ar yaji an daga, cikin nutsuwar sa yayi sallama "Babah." Ya kira sunan shi kamar kowanne lokaci, daya daga cikin abinda yake kara masa jin Sulthan din a cikin ransa shine kiran sa da lakanin Baba, ya kan ji dad'i mara misaltuwa "Muhammad! Ina ka shiga kai kuwa, ka bar Babanka cikin tunani." Sauke ajiyar zuciya Sultan din yayi yana jin wani irin peace of mind, yana jin cewa wannan din da yake magana dashi shine mahaifin sa, ya kuwa zai ji idan ya samu labarin? Yasan zasuyi farin ciki mara misaltuwa, kamar yadda shi ma yayi,Allah ne ya had'a su ba tare da sun san alakar su ba, ya kuma jefa kaunar junan su a tsakanin su, tabbas babu tantama su din iyayen sa ne, saboda yadda yake ji game dasu be taba jin irin sa akan wasu ba, ko da kuwa Daddy ne da Mah-Mah. "Ina neman afuwa Baba, ban yi hakan da gangan ba, sai don wata matsala da ta taso min." "Matsala Muhammad? Wacce irin matsala ce?" "Ba wata Babba bace, amma zanzo kwanan nan, zanzo na ganku." "Zaka zo da gaske, kai Masha Allah,wannan labarin nasan zai faranta ran gimbiya,nasan zata yi matukar farin ciki." "Tana kusa?" "A ah amma bari na kai mata." "A ah Baba, da kanka? Zan sake kira anjima dai." "Toh shikenan." "Ya kafar? Tayi sauki?" "Kafa tayi sauki sosai sai godiyar Allah, ciwo kamar cirar k'aya wallahi, Allah dai ya kara mana lafiya." "Amin Baba." "Karka manta ka kira fa, karka manta." "Ba zan manta ba in Sha Allah." "Allah yayi maka albarka, sai ka kira." "Amin ya Allah." Cire wayar yayi,yana jin farin ciki na lullube shi, "Alhamdulillah ya Allah." Ya furta a hankali sannan kai tsaye ya wuce dakin da Safwan yake yana fatan ya farka daga baccin da yake. Sai dai be same shi ido biyu ba, sai Mah-Mah kawai a dakin da Anty Amina Maman Umaimah, gaishe su yayi ya juya ya rufo musu kofar. Yana so yaje ya duba Amrah amma kuma yasan dakin da mutane, tunda dazu ya wuce yaga alamun akwai mutane. Amma kuma ya kamata yaje ya duba tan, haka zai daure yaje din baya son yadda kowa ke ficewa Idan yaje din ne shiyasa baya sakewa yayi ta xuwa din amma tana makale da tunanin sa ko yaushe. Yau be tsaya ba kamar wanchan lokacin, yayi sallama aka amsa sai kawai ya shiga, duk suka yi saurin tashi, Umma ma ta tashi da sauri yace "Dan Allah umma ba sai kun fita ba." Duk da haka babu wanda ya tsaya din, suka gaisa da Umma da sauran duk suka fice yaji duk kunya ta kamashi musamman saboda abinda Hajiya tace da tazo fita "Munafurci wai kar a fita, mu babu kalar munafurcin mata da miji da bamu sani ba ehe." Da sauri Umma ta karasa ficewa kunya na kamata saboda itace a gaban Hajiyan kuma ta tabbata Sultan din ma yaji me Hajiyan tace. Girgixa kai kawai yayi yana kunshe dariyar sa. Murmushi suka samar ma juna a tare, ya dora hannun sa a saman kanta daidai wajen bandage din, ta matse fuska kad'an "Yana miki ciwo ne?" "Ba sosai ba." "Ok bari suzo sai su sake dubawa, yaushe akayi dressing wajen?" "Dazu nurse din tazo tayi." "Ok ya jikin naki?" "Da sauki." "Sosai?" "Sosai." "Sannu kinji?" "Uhum." "Shine kika koreni jiya ko? Wa na kama?" Yayi maganar yana matsawa kusa da ita sosai "Ni? yaushe? Ni Allah ban kore ka ba." "Kin manta?" "Uhum... Ni.. Ni ban kore ka ba Allah." "Uhum... Kinsan me? Nayi missing naki sosai, sosai, sosai, kuma nayi dana sanin tafiya na barki, bansan zan yi missing naki me yawan haka ba sai bayan da naje, naji me ma yasa na tafi." "Uhum..." Tace tana juua idon ta, "Kamar da gaske." Ta dora "Allah da gaske nake." Ya rik'e hannun ta ya dora a saman chest din sa "My heart beats for you 💜💚💘" kinji? Zame hannun ta tayi, tace "Banji komai ba." "Shikenan, ni bari naji naki, zan gane how much kikayi missing dina." Da sauri ta ja baya ganin yana kokarin dora hannun sa a saman chest dinta "Umm..mmm... Ba sai kaji ba dan Allah." "Mesa? Ki tsaya naji mana idan ba tsoro ba." "Dan Allah ,kaga fa bani da lafiya." Ta karashe tana karyar da muryar ta "Matsoraci dai baya zama gwani." "Ummm, kaci abinci?" Ta chanja maganar Kallon ta yayi sosai, kallon cikin ido har sai da ta rufe idon nata saboda yadda kwarjinin sa ya cika wajen, daf da ita ya sake matsawa, ya rada mata wata magana a cikin kunnenta, maganar da ta saka ta kusan bude kasar wajen ta rufe kanta saboda kunyar sa, bata san Sultan ya kai haka ba, ita duk kallon da take masa dah na mara magana da son hayaniya bata taba tunanin zai iya irin wannan zantuttukan ba, kasa dagowa tayi tayi dana sanin yi masa tambayar, bata yi tunanin zai chanja maganar zuwa wani abu daban ba,tana jin sa yana mata dariya taki kulashi. Sai kuma taji ya daina dariyar lokacin da aka budo kofar "Ya Sultan." Taji muryar mace na masa magana, dagowa tayi, ganin wadda bata zata ba a dakin yasa ta yin kicin kicin da fuska, "Bansan kana nan ba, Mah-Mah ce tace nazo na duba ta." Tayi maganar tana kallon fuskar amrahn "Ok gata nan, babyy za'a dubaki." "Ya jikin?" "Alhamdulillah." Ta amsa a kajarce "Allah ya kara sauki." Sai ta juya kan Sultan "Ya Sultan kamar fa ya Safwan ya tashi, naji ma ance kai yake nema." Da sauri ya mike yayi fice ba tare da yace komai ba. Murmushin mugunta Umaimah tayi, dama chan tayi niyyar korar sa shiyasa tayi masa haka, tun da taga bata ganshi ba a chan tasan yana nan. Wajen da Sulthan din ya tashi ta koma ta zauna tana karewa amrahn kallo, kallo irin na raini. "Sorry na raba masoya ko? Opss I'm so sorry." Yadda tayi maganar kawai ya isa ka gane inda ta dosa, shiru Amrah tayi zuciyar ta na mata zafi, tasan Umaiman da gayya tayi abinda tayi saboda tasan waye Safwan a wajenshi. Shigowar Afrah ya saka Umaiman mikewa tana cigaba da taunar chewing gum tace "Allah ya kara sauki Amarya, bari naje wajen angon naki akwai muhimmiyar maganar da yace zamuyi." Wani irin tukuki ne ya dinga tasowa Amrah,tana kallo ta juya ta fice fuskar ta cike da farin ciki,wani kuka Amrah taji ya taho mata, da sauri Afrah ta dakatar da ita "Wallahi idan kika ce Zakiyi mata kuka zaki sha wuya, irin wadanda yan iskan sai ka nuna musu kai ma dan kanka ne wallahi sannan zaku daidai ta,tazo har inda kike, ta saka ki kuka bayan shi Wanda take magana akai ba wai saurayinki bane, mijin ki for that matter, lallai." "Tama raina ki ne, da tun farko ma zata shigo miki haka kai tsaye bayan taga kowa a waje, ni wallahi dan bana wajen ta shigo ne da sai na hanata wallahi." Cigaba da sababi Afrah tayi bata tanka mata ba, sai kawai ta kwanta tana jin zafin abinda Umaiman tayi mata. ***Sultan na zuwa ya tarar har lokacin Safwan na baccin sa, be farka ba kuma, sai a sannan ya gane dalilin da yasa Umaiman tayi masa haka, so take ya bar dakin dan tasan ba zai iya kuma sake tsattsallake su Umma ya sake komawa ba. Dole ya hakura zuwa lokacin da kafa zata dauke a barta ita da Afrah kawai shine zai sake. Tunawa da yayi da yace zai sake kiran Babah yasa ya kira a lokacin, Gimbiyar ce da kanta ma ta daga,suka gaisa suka dan yi magana ta nuna farin cikin ta akan zuwan da ya ce zai yi, sannan ta bawa Babah yace ya turo da ACC details dinsa sune zasu dauki nauyin zuwan nasa, da yaso yayi musu ganin ran baban ya baci ya saka ya sauko ya hakura yace zai turo. Da haka ya samu ya lallaba su sukayi sallama. Yana kashe kiran wani kiran ya shigo, ya daga "Ka shigar da Hukuma cikin abinda ya had'a mu, toh ka sani idan bincike yayi bincike zai nuna kowa ,ciki harda wadanda baka taba tunani ba." "Me yasa ka kirani?." "So nake mu hadu, zaka ga abinda zai baka matukar mamaki, idan har ka yarda zaka zo,kai ka dai kuma, zan turo address din in da zaka sameni, karka sha wahalar kiran Yan sanda domin ni Alhaji Safiyanu Madaki ba zan kamu ba." "Ni kad'ai nake da matsala da kai,saboda haka karka sake saka wani nawa a ciki, zanzo ka turo da address din." "Ok karfe uku na yamma daidai." Bin wayar Sultan yayi bayan ya katse, kenan Madaki yana kasar ko dawowa yayi? Ko kuma kuskure aka samu yan sandan suka ce ya bar kasar ko kuma ya saye yan sandan, cikin biyu dole ayi daya, yafi zargin saye sun yayi, wannan kasar tamu shiyasa ba zamu cigaba ba ko k'ad'an. "Zanzo na sameka Madaki, ni kad'ai kamar yadda ka bukata.!" **Not Edited©® Hafsat Rano Page 43 *MIMICOS COLLECTION* Gidan kayan kawa da kayan alatun kece raini, ina masu neman inda zasu gwangwaje su gyagije da jakunkunan yan gayu, laces, atamfa takalma, kayan yara, jewelries designer perfumes masu dan karen kamshi da sauran su?, kuyi maza ku karzayo *MIMICOS COLLECTION* Muna nan a Naibawa titin danhassan ,layin sp baba muhd ko a neme mu a number wayar mu 07035209753. Muna maraba da masu siyan daidai ko sari. Kuma muna aikawa a kunne lungu da sako na fadin kasar nan. Karku bari a baku labari. MIMICOS COLLECTION gidan yan gayu, kayan yan gayu masu tafiya daidai da zamani. ***Murmushi kawai Sulthan yayi, bashi da abin fad'a, idan ma akwai toh be san me zai ce ba, sai kawai ya matsa gaban inda Aminatu take, yace "Ya sunan matar da ake tunanin itace ta karbi yaran?" "Safiyya." Maman Yara ta amsa duk da ba da ita yake ba, juyowa yayi yace "Ina tunanin itace." Yace yana zama "Ka samu labarin ta ne?" "Eh...." Zumbur Aminatu ta tashi "Aina? Tana ina dan Allah?" Sosai ta bashi tausayi "Bansan takamaimai inda take ba, amma na hadu da Muhammad." "Muhammad?" "Eh yace min sunan Ammin su Safiya, sannan kuma tana hannun Madaki, sannan kuma yace min shi din yan biyu ne amma shi kad'ai ne a wajen Ammin, bata kuma fad'a masa ina dayan yake ba." "Dan Allah ina yake? Ina so na ganshi dan Allah!" "Kiyi hakuri, zaki ganshi, ki kwantar da hankalin ki." Komawa tayi ta zauna, suka cigaba da magana da Maman Yara yana kara samun information din da duk yake bukata. Sai da ya tabbatar ya kwantar mata da hankali sannan yayi musu sallama ya tafi. ***Duk da be san abinda zai tarar ba idan ya je amma ya saka a ransa zai je din, shi kad'ai kuma dan baya son sake saka kowa a cikin matsalar sa. Sai da kusan ukun tayi sannan ya samu sakon sa da address din, yayi murmushi me kyau "Lokaci yayi." Ya furta yana mikewa daga inda yake zaune, ya riga ya shirye komai, ya kuma tabbatar da ba za'a samu matsala ba. Gida ya fara zuwa, yayi wanka ya gyara fuskar sa da sajen sa, yayi fes dashi kamar wanda zai je zance, ya saka manya kaya farar shadda da Babbar Riga da akayi wa aikin bakin zare, ya saka hula da takalmin sa sau ciki tare da bakar safa, sosai ya fito kallo daya zaka yi masa kaji ya burgeka. Motar sa ya dauka yayi mata key kai tsaye ya nufi address din. A waje ya tsaya, ya tura masa da sakon ya iso, ya ciro wani farin glass ya saka a fuskarsa, ya bud'e kofar ya zuro kafafuwan sa yana jiran sa. Yana zaune wani matashin yaro yazo yayi masa magana. Kashe motar yayi, ya kulle ya bi shi suka nufi wani katon gida. Bangarori ne da yawa a gidan, sannan akwai mutane masu yawa a ciki, wanda da yawan su hadiman gidan ne sai kuma wasu maza manya da su kuma suke gadin ciki da wajen gidan. Wuce su sukayi, suka dangana da wata babbar kofa, inda yaron ya saka hannu ya bud'e sannan ya ja baya kad'an "Yana ciki." "Ok." Yace ya kutsa kansa ciki, Madaki da yake tsaye yana jiran isowarshi ya sha jinin jikin sa, ganin irin shigar da Sulthan din yayi wadda ta fito da shi sosai ya cika, kwarjinin sa da yake hana Madakin masa wasu abubuwan ya sake bayyana, be taba ganin shi da manyan kaya haka ba, shiyasa ya ji wani abu ya taba shi, wanda ke zaune tare da Madakin ne ya amsa sallamar Sultan din, be jira an bashi wajen zama ba yayi wa kansa wajen zaman, ya hard'e kafarsa ya shiga girgiza ta tana lilo. "Gani? Me yasa kake nema na?" "Saboda kazo mu karasa abinda muka fara, ban dauka zaka saba alkawari ba tun farko, idan ba haka ba, me yasa ka chanja shawara akan bani zoben?" Kure shi da ido Sultan yayi, sai kuma yayi murmushi ya murza zoben sannan yace "Na zata mun wuce wannan wajen, idan ma maganar saba alkawari ne toh kaine ka fara, saboda me yasa zaka saka iyali na a ciki?" "Saboda alamun da ka nuna ba zaka bayar da zoben ba, tun bayan da ka dawo da Musa gida na tabbatar da haka." "Menene amfanin zoben ne wai har haka?" "Kana nufin baka sani ba?" Dayan yayi maganar "Um um, ban sani ba, na dai ga kawai zobe ne kamar kowanne zobe ma, me yasa kuka damu dashi har haka? Ko ance musu shine tikitin shiga aljanna ne?" Kallon juna sukayi, suka yi magana da juna ta yadda Sulthan din ba zai gane ba. "Ka gane? Shi wannan zoben kamar wani sign ne na family din mu, tun farko a gidanmu ya kamata ya zama, toh sai akayi mana fin karfi har ya bar hannun mu, shine muke so ya dawo wajenmu, babu wani amfani da yake dashi bayan shaidar nan kawai." "Madallah, kace idan nazo zaka fad'a min abinda zai bani mamaki, duk da dama kai din baka rabo da bada mamaki, tun da har ka iya gabatar min da bayin Allah nan a matsayin iyaye na, ina fatan ka sallame su ka biya su kudin aikin su har da kari, domin aikin su yayi kyau sosai, zasu mafi kyau da wasan hausa." "Ba wannan maganar bace yanzu Sulthan, magana daya ce, akwai muhimman abubuwa da na sani game da kai, kuma nayi alkawarin ko da ban hada ka da su ba,zan fad'a maka inda zaka neme su, na farko iyayenka, na biyu kannenka da suka taso tare damu, na uku...." "Ina ka kai ta?" Ya katse shi "Wa?" "Safiya!" "Ina kyautata zaton tana cikin Masarautar, sai dai bani da tabbacin hakan saboda har yanzu ban tabbatar din ba." "Ina jinka..." "Idan har ka yarda zaka bani zoben nan, nayi maka alkawarin fad'a maka komai." Zare zoben Sultan yayi, hasken ya kara tashi me karfi, duk suka zuba ido cike da mamaki, karfin zoben yayi yawan da zai dauki hannun Madaki ko mukarraban sa, dama a lokacin da yake ba a hade bane,duk da haka Madakin me karaya ba, ya matso ya mika hannu Sultan ya dora masa zoben a saman tafin hannun sa. "Ina sauraren ka!" Cikin tsantsar farin cikin da Madaki be taba samun kansa a ciki ba, yake kallon zoben yana kallon mutumin, tsawon lokaci abinda ya hana masa cikar burin sa kenan, "Ina sauraren ka!" Sultan ya kara magana yana hard'e hannayen sa "Kamar yadda nayi alkawari, yadda ka cika min buri na kaima zan cika maka, zan fara da baka tarihin zoben nan da abinda zai iya yi." "Kasantuwar Zoben nan ya samo asali ne a wani lokaci, lokacin da Sarautar Saji ta samu matsala, alokacin da aka rasa sarkin da za'a nad'a a cikin yayan Sarki Abubakar Muhammad Moddibo Saji, Wanda ya kasance kaka a wajen Sarki Bello da Sarkin Usman wanda ya kasance mahaifin ka, a lokacin ne Sarki Abubakar ya hadu da wani mutum ya fita ran gadi, ya bashi wannan zoben ya kuma tabbatar masa da duk wanda zoben nan ya zaba shine zai yi Sarautar Saji, haka yazo gida ya kira dukka yaran sa, kowanne aka bawa zoben sai zoben ya fad'i daga hannun sa, har aka zo kan Sarki Muhammad Moddibo Saji wanda shine kakan ka, sai zoben nan ya zabe shi, tun daga lokacin hakan ya zama al'adar Masarautar Saji, babu me Mulkarta sai wanda ya mallaki zoben nan. Bayan kakanka Sarki Muhammad Moddibo Saji, sai mahaifin ka shima ya hau, ya kuma cigaba da kasancewa da zoben nan duk kuwa da shi be wani yarda da zoben ba kasancewar sa dan boko. Sai dai be sani ba,Sarki Bello yayi amfani da karfin Malaman tsubbun sa, ya chanja komai akan zoben, inda ya zama duk wanda ya mallaki zoben toh tabbas shi ne zai karbi mulkin, saboda haka yasa nayi ta kokarin samun zoben, saboda daukar fansar abinda Sarki Bello yayi wa ahalin mu baki daya bayan hawan sa kan karagar mulkin, ya kore mu daga Masarautar kora irin ta wulakanci. Sai dai ban samu damar daukar zoben ba duk kuwa da na samu damar hakan ba adadi, babu wanda zai iya kai hannu akan zoben sai kai kad'ai sultan, saboda karfin zoben duk wanda ya dauka kafin ka dauke shi zai iya rasa ransa ma baki d'aya." "Me yasa sai ni kad'ai zan iya?" "Saboda kai ne wanda zoben ya zaba tun kana cikin mahaifiyar ka, shiyasa suka salwantar da cikin tun kafin ka zo duniya, sai kuma Allah ya kaddara sai ka taka." "Me yasa zoben ya zabe ni? Bayan komai da kaga ya faru da bawa mukaddari ne daga Allah, dama chan an rubuta zai zama abun ko zai samu abun." "Sultan baka san sha'anin Sarauta ba." "Muhammad shine yaron da Safiya ta raina? Ina wanda kai ka tafi dashi? Yana raye ko ya Mutu?" "Shine, kuma shima dayan yana raye, wanda akayi nufin kashe su ni kuma na taiamaka wajen tseratar dasu." "Yana Ina?" "Sultan..." "Yana Ina?" Kallon zoben Madaki yayi, sai kuma ya kalli Sultan yayi murmushi ya matso daf dashi yace "A duk labarin nan, wannan zaifi maka dadin sauraro, ina fatan ka bani tukwaici me girma." "Ina jinka." Wayar sa ya ciro ya nuna masa wani hoto "Kasan wañnan?" Shiru Sultan yayi ya kurawa hoton ido, babu ko kiftawa amma ya kasa magana, ya rasa me zai ce sai kawai ya daga kansa a hankali zuciyar sa na bugawa da sauri da sauri yace "Na sanshi." "Good. " Ya sakar ma Sultan din wani shu'umin murmushi, girgiza kai Sultan yayi yace "Kana nufin...?" Kafin ya karasa Madakin yace "K'warai da gaske, kana mamaki ne? idan kana mamaki kayi bincike shi, zaka samu sauran bayanan a wajen sa." Da sauri ya mike ya nuna shi da hannu "Ban yarda ba, ba zan yarda ba kuma saboda kai din ba abin yarda bane, babu karyar da ba zakayi ba domin cikar burin ka." "Zaka iya bincike idan har baka yarda ba, bani da amsar da zan baka domin har yanzu ban samu bayanin komai daga gareshi ba." Komawa Sulthan din yayi ya zauna, ya taba Bluetooth din dake makale a kunnen sa, wanda sai a lokacin Madaki ya lura dashi, yayi saurin tashi cikin tsananin tashin hankali "Kar muyi haka da kai Sultan!" "Arrest him!" Yace a lokacin da kofar falon ta bud'e, suka shigo a guje su wajen goma suka zagaye Madakin. "DSS!" Ya furta yana zaro idon sa Sara masa Sultan yayi, ya matso gaban sa, yasa hannu ya bud'e tafin hannun sa da ya dunkule zoben, ya zare yana cigaba da murmushi "This belong to me, greediness din ka, ya kaika inda kake a yanzu, idan baka yi bayanin inda ka kai min dan uwa ba zakayi bayani a office din su, kasan kuma su ba kamar roundom police bane da zaka yi bribing da banzan kud'in ka ba." "Amma kasan ba haka mukayi da kai ba?" "Kai ne ka koya min, kuma dan ka, dan cikin ka shine ya taiamaka har hakan ta kasance!" "Ameer!" Ya furta da karfi yana zaro ido "Kuje dashi Sir! Thank you so much." "Karka damu Dr, zamuyi abinda ya kamata." Tusa keyar Madakin sukayi suka fito dashi, sai a sannan ya ga yadda akayi wa cikin gidan, an tattara dukka ma'aikatan an zuba su daki Daya. A Mota suka sashi suka tafi dashi tare d wannan wanda suke taren. Wajen motar sa Sulthan ya nufa yana jin wani karfi na saukar masa,yana jin sai yanxu yayi abinda ya dace. Shafa fuskar sa yayi ya saki murmushi "Canada!" Ya furta a hankali yana lumshe Ido "He can't wait ya isa garesu." tare da amrahn sa, tare da yan uwan sa da yake fatan samun su, sai kuma abinda Madakin ya nuna masa ya dawo masa, tsoro ya shige shi, me yasa Madakin zai kawo masa shi a matsayin wanda zai nema, me yasa be gaya masa komai kai tsaye ba kamar yadda ya bàshi labarin zoben, ko dai da gaske yake? Nooo ba zai yiwu ba! ***Chan bayan asibitin Maman Yara ta nufa, ta samu wani waje da babu komai ta ciro layoyin nan, ta saka ashana ta kyesta musu wuta, tana kallon yadda wutar ta tashi sama sosai dan har sai da ta ji tsoro, kafin kuma wani bakin abu baki kirin ya fito daga ciki yayi sama shima.... Yau dai ga guntun page, bani da enough charge. Muje zuwa Canada, it's gonna be fun!!!!!! ©® Hafsat Rano Page 44-45 ***Tana kallo har wutar ta gama ci, ta watsa ruwa ta karasa kashe ta, zuciyar ta babu dadi ga wani irin kanta da ya hau sarawa kamar zai cire. Dafa wa tayi da k'yar ta karasa dakin nasu ta kwanta zazzabi na rafke ta. ***Gidan sa ya sake komawa, ya duba abubuwan da za'a bukata a gidan, ya duba dakin da yake son ajiye su Maman Yara, ya sake fita ya siyo duk abinda za'a bukata saboda yana so a sallame su har da Amrah ma, Safwan kad'ai za'a bari shima saboda wasu abubuwan da dole a asibitin ne za'a same su. Sai da ya tabbatar da ya gama hada komai na bukata a gidan, sannan ya koma asibitin, lokacin daf da magriba ne, Sallah ya tsaya ya fa rayi sannan ya shiga cikin asibitin. Da mayyar sa ya fara cin karo, dauke da basket da Mah-Mah ta bata ta kai dakin da Amrah take, yayi saurin dauke kai amma ta ganshi, dole ya tsaya suka gaisa ta nuna masa kayan hannun ta, jinjina kai kawai yayi be ce komai ba, yana tunanin ko Mah-Mah ta chanja ne? Dan ya ga chanji sosai a tare da ita, rashin maida hankali akai ya saka be gane hakan ba sai yanzu. Wucewa yayi dan so yake a sallame su a ranar duk da ka'idar asibitin ne ba'a sallama da irin lokacin amma tunda su ne masu sallamar zasu iya yi a duk sanda suka so. Dr Osas ya samu sukayi magana, yace ba komai tunda shi ma doc ne sai ya karasa kula dasu. Tare suka fito suka je su duba su Maman Yara, ganin ta a kwance rigis ya saka Sultan din cikin damuwa,Amma da ta ce masa babu komai sai ya kyale ta, suka sake yiwa Aminatu binciken da ya kamata sannan aka sallame ta. Gidan ya wuce kai tsaye, ya kaisu ya nuna musu daki da komai da zasu nema sannan ya sake komawa asibitin. Sosai jikin Safwan yayi kyau dan har yana iya zama yayi wasu mintunan, har ma yayi hira duk da ba doguwar hira yake ba amma alhamdulillah, yanzu ma yana zaune amma a kishingid'e, Mah-Mah ce kawai dashi a dakin kowa ya tafi sai Umaima da ta aika ta kaiwa Amrah abinci wanda kullum take aika musu. Shigowar sultan ya saka Safwan din yin murmushi, ya tsuguna ya gaida Mah-Mah kamar yadda ya saba, ta amsa a sake ba tare da wani abu a cikin muryar ta ta ba, wajen Safwan ya nuna, ya bashi hannu yana me jin dadin yadda ya samu sauki sosai "Yau ina ka shiga ne naji ka shiru?" "Na shigo kana bacci, ya jikin naka?" "Alhamdulillah! Sai godiyar Allah." "Alhamdulillah, toh Allah ya kara sauki, akwai wajen ke maka ciwo ko babu dad'i haka?" "Babu gaskia, alhamdulillah sai dan abinda ba zaa rasa ba." "Toh ko..." "Sultan." Mah-Mah ta kira sunan sa, ya fasa maganar da yake "Na'am Mah-Mah?" "Kayi hakuri dan Allah, duk abubuwan da nayi maka a baya wallahi sharrin zuciya da shaid'an ne, kayi hakuri." "Iyaye basa taba dukan dansu dan basa sonshi, sai don su gyara shi, haka uwa babu abinda tafi so sama da yayanta, amma hakan me hana ta hukunta su ba idan sukayi ba daidai ba, wannan shine soyayyar gaskiya, idan kayi abu mara kyau a nuna maka laifin ka. Ni baki mun komai ba Mah-Mah, domin ke din uwa ce har gobe, bana kallon ki da wata siga ta daban bayan wadda nake kallon ki tun farko." "Nagode Sultan, wallahi nima haka ne a wajena, bansan me ya hau kaina ba, dan Allah kayi hakuri ka kuma daina fushi akan maganar da nayi maka ta karshe, ka dawo gida mu cigaba da rayuwar mu kamar da." "Subhanallahi...Idan har zan iya fushi dake Mah-Mah, toh tabbas banyi amfani da kyakkyawar tarbiyyar da kika bamu ba." "Sultan... Nagode." Tace tana sauke kanta k'asa, saboda yadda kunya ta hana ta dagawa ma ta kalle shi, toh ai bata da ma idon da zata iya kallon nasa "Allah yayi maka albarka, ya albarkaci auren nan, ya baku zaman lafiya da zuri'ah dayyiba." "Amin." Ya amsa a chan k'asan makoshin shi, Safwan da yayi shiru tun da suka fara maganar sai murmushi kawai yake ya amsa da "Amin ya Allah." Hararar sa Sultan yayi sukayi dariya a tare "Yaushe zaka sallame ni ne dactora?" "Sai ka kara sati uku haka naga yanayin naka." "Rufa min asiri wallahi bazan iya ba tab!" "Haka ko zaka hakura, tunda nine me cewa." "Aikuwa dai, idan yayi biyayya toh." Mah-Mah ta shiga zancen tana jin wani irin farin ciki, kwatankwacin wanda take ji idan suna irin wannan rahar tasu kafin ta dauki hudubar shaid'an. "Nabi wallahi, nayi biyayya Ranka ya dade, Allah yaja da kwanan ka." Yayi maganar yana dungule hannu, kallon sa Sultan yayi tunanin sa na turawa zuwa Masarautar Saji, ko yaya suke ciki tsakanin UBA da DAN da yake shirin waiwaya dan da lokaci kadaan? Yanzu ba tasu yake ba shiyasa ma ya share ko ta kansu be sake bibiya ba. Yanzu tunanin yadda zai isa ga iyayen sa kawai yake, ba kuma zai je shi kad'ai ba sai tare da yan uwan sa in Sha Allah. Tunanin yan uwan sa da ya shigo ne ya saka ya tuna hoton da Madaki ya nuna masa, yayi saurin girgixa kansa, "Ba zai yiwu ba kawai so yake yayi wasa da tunanina." Yayi maganar a zuciyar sa. Sallamar da Daddy yayi a kofar ya saka shi kallon kofar da sauri, ya kafe shi da ido yana son alakanta abinda Madakin yake nufi da kuma fuskar Daddy da babu komai sai kamala da dattako data nuna. Ya sake girgiza kansa ya karo na biyu, sai kuma ya tuna da maganar Safwan _"Na taba ganin sunan a jikin wasu takardun Daddy."_ "Ya Allah." Ya furta a hankali ya shafi kansa "Sultan." Ya tsinkayi muryar Daddy akan sa, da sauri yace "Barka da shigowa Daddy." "Tunanin me kake haka kai kuwa, akwai matsala ne?" "A ah babu komai." Yace yana kokarin tura maganar Madakin zuwa chan bayan kansa, dan ko kusa be hango yiwuwar hakan ba, akwai ta inda aka samu matsala dai dole, ko dai Madaki yana so ya bata masa tunani ne, ko kuma an samu misunderstanding. Cigaba sukayi da tattaunawa da Daddy har lokaci yaja sosai, sai ya tuna da sallamar Amrah da yake so yayi, amma yana son ya fara yi mata bayanin su Maman Yara ba sai taje gidan kawai ta gansu ba. Duba agogon hannun sa yayi, ya ga har lokaci yaja sosai, yasan zuwa lokacin Umma ta koma gida tunda Afrah ce take kwana yanzu. Kai tsaye ya wuce chan din. Tun da ta kai abincin me makon ta tafi sai ta samu kujera ta hakimce, ta ciro wayar ta tana daddanawa kamar me yin chat, lokaci zuwa lokaci tana sakin yar karamar dariya alamar chatting yayi dadi, babu wanda ya tanka mata a cikin su. Sai dai Amrah ta kasa dauke tunanin ta daga kanta, sai ta fara tunanin toh ko da SULTAN suke chatting din? Duk sai taji babu dad'i taji tana jin haushi sosai. Ko da ya shigo dakin, sai ta daure fuskar ta, ya kalle ta da sauri yaga ta dauke kai, ya juya ya kalli Umaima da shigowar shi ya sakata daina abinda take ta washe bakin ta. "Ya Sultan..." "Ya Sultan sannu da zuwa." Afrah ta fad'a tana aika mata da kallon banza, maimakon ya amsa na Afrah sai ya fara amsa kiran Umaiman "Ashe kina nan?" "Ina nan wallahi." Tace tana kankance idanun ta "Afrah ya garin? Ya me jiki?" "Da sauki." Ta amsa a chunkushe tana jin haushin yadda ya bawa Umaiman attention, tashi tayi zata fita tace "Malama ki basu waje." "A ah ta zauna..." "Umaimah dan jira ni pls na gaisa da Madam two mint." Far tayi da idonta, ta sake gyara zaman ta tana kallon fuskar Afrah da ta ji wani abu ya soke ta, tayi saurin ficewa tana bugo kofar. Takawa yayi ya isa gaban gadon, ta ji kwalla na taho mata tayi saurin maida ta, ya lura da sanda ta maida kwallar, yayi wani kasaitaccen murmushi, ya rankwafo kanta, karfen dake jikin zip din gaban rigar ta ya makale a jikin tasa rigar, hakan ya kara basu kusanci, kokarin yadda zata cire karfen ta hau yi yayi saurin rike hannun ta, a hankali ya rada mata "Stay still... Wani abu nake son koya miki." "Ya jikin naki?" Ya tambaya yana dora saman goshin sa akan nata,daga idon ta tayi sama, tana kallon sa tana son gane abinda yasa yace ta tsaya. "Idonki fari tas,I like it,nooo I love it zance." Murmushi tayi ta rufe idon, ya kalli saman idon nata da suke rufe ya bata light kiss a wajen... "Ina son mace me kunya, me aji me class..." Ya dora "Ba ballaga ba, wadda bata san me yake mata ciwo ba, komai classy yafi, just like you Amrahhh..." Yaja sunan yana fitar da siririn murmushi "Garam...." Aka buga kofar, garin dagowa suka buge da kai kowa ya dafe nasa "Ouch..." Suka fad'a a tare "Ka fasa min ciwo na." "Kin fasa min kaina dai, wayyo Allah." "Akan ciwo na fa ka fasa min." Tace tana kokarin yin kuka. "Kadanba ni kika kusa fasawa ba, karki yiwa bayin Allah asara wallahi." Hawayen da tun dazu take rikewa suka zuba, yasa hannu ya goge mata yana girgiza mata kai "Kina yin kuka shikenan taga lagon ki, kinyi na farko Afrah ta fada min, wannan ya zama last, shiyasa na hana ta fita saboda na nuna miki abinda ya kamata kiyi,I'm all yours, karki yarda ta saka miki wani tunani a ranki, babu komai tsakani na da ita, bayan alakar dake tsakanin Mah-Mah da Anty Amina, so please karki damu kanki kinga ba dad'i kike ji ba." Wata matsananciyar kunyar ce ta kama ta,tasa tafin hannun ta, ta rufe fuskar ta da sauri. Dariya ya shiga yi mata yana tsokanar ta mai kishi, mai kishi. Kin kulashi tayi, taki kuma dago kan tana jin kamar k'asa ta tsage ta shige, wato Afrah munafuka shine ta fad'a masa tayi kuka, zata kama ta ne wallahi. Wayar ta dake kusa dashi tayi haske, ya saka hannu ya dauka ya shiga karantawa a fili _"Ni dai na wuce gida zan dawo gobe, kice wa Ya Sultan ya karasa jinyar ki yau, saura kuma kiyi wannan sanyin jikin naki... Ki"_ da sauri ta wafce wayar wata kunyar na sake kamata, "Bani dan Allah na karasa..." Kashe wayar tayi baki daya, yayi dariya yana cigaba da tsokanar ta. "Allah dai ya shiwa Afrah albarka ta san abinda ya dace wallahi, haba mutum da matar sa sai yayi raragefe sannan zai zo ya ganta, shiyasa fa na dage ayi sallama yau, sai gashi Afrah ta biyani." Yayi maganar yana fadawa saman gadon. "Karka karya musu gado." "Sai a siyo sabo." Tashi tayi ta sauko, ta wuce toilet shi kuma ya je ya saka key a kofar, ya dawo ya shinfida babbar dardumar dake cikin kayan su, ya zauna ya fito da warmers din abinci, yana zubawa ta fito, ta wuce shi ta dau hijab ta hau Sallah, tana idar ya, ya matso da abincin gabanta. "Ko tanbayar ina nake samun abinci naci bakya yi, Allah sarki ni." Tasan neman magana yake, ita kuma bata shirya hakan ba, sai ta share shi ta dau spoon din da ya saka a gabanta ta shiga cin abincin, nan ma sai da yayi ta tsokanar ta, karshe ta tashi ta koma saman gadon tayi kwanciyar ta. Toilet din shima ya shiga, yayo alwalar yazo yayi shafa'i da wutri ya jima yana addu'a sosai, tana kallon sa har ya gama, sannan ya taso ya zauna a gefen gadon, sai kuma ya tashi ya bud'e jakar da aka saka blanket din gidan su da ya tawo mata dashi bata ma yi amfani dashi ba saboda Umma ma sunzo da wani, ya shinfida a saman dardumar, ya dawo yace ta sakko, ta kalle shi sai kuma ta sakko din, ya dauki pillown da dayan bargon ya saka pillow ya kwanta, a gefe ta zauna ya mika mata hannu, "Zo muyi magana." Kama hannun nasa tayi, ya jawo ta zuwa saman chest din sa, tayi shiru tana jin fitar heartbeat dinsa. "Da farko dai zan fara da..." Ya fara bata labarin komai tun daga farko har karshe zuwa sanda aka kama Madaki, da kuma su Maman Yara da ya kai su gida sannan da zancen tafiyar su Canada, ya karkare da "Kinji duk abinda ya faru, sai dai duk ciki babu wanda ya fi daga min hankali irin karshen,hoton da Madaki ya nuna min, ya zanyi?" Sosai tayi mamakin yadda abubuwan suka kasance kamar a film musamman zuwan sa Masarautar,a nutse cikin hikima babu baragada ta bi dukkannin maganar tasa kowacce gaba ta yi magana akai, yayi shiru yana sauraren ta, hannun sa na zagayawa a cikin gashin kanta, yana kuma daukar duk abinda take fada masa, cikin hikima ta nuna masa abubuwan da yayi na kuskure sannan ta yaba wasu abubuwan da yayi suma, batun hoton nan kuma ta bashi shawara, shawarar da ta saka shi kankame ta yana jin dad'i da relief, lallai mace ta gari rahma ce, tun yaushe yake ta tunanin yadda zai yi amma ita cikin abinda be fi yan mintuna ba ta warware masa komai. Tabbas mace abokiyar shawara ce, maza da yawa basa bawa mata wannan damar wadda suke rasa shawara me matukar muhimmanci a cikin duk abinda suka saka a gaba. Sun dade suna hira har ma basu san iya kar dadewar da sukayi ba, hira ce me dad'i da saka annashuwa, basu san lokacin da bacci barawo ya sace su ba. ***Da sauri ta karasa shiga dakin ganin shi a kwance ko motsawa bayayi "Maimartaba, Maimartaba!" Ta shiga kiran sunan sa tana jijjigashi, kuka ta saka ta fito da sauri, ta dauki wayar sa ta kira emergency number, cikin abinda be kaza yan mintuna ba sai ga mota daga nearest asibiti, suka dauke shi suka saka shi a mota aka wuce dashi asibiti. Number Sultan tayi ta gwadawa amma taki shiiga, duk ta rikice ta rasa me zatayi, kuka kawai take tana jin ta tsani komai da kowa da irin rayuwar da sukeyi su kad'ai babu dangi babu yaya. Ba dan Allah yasa ta shigo dakin nasa a lokacin ba, da bata san me zai faru ba, sosai tausayin sa ya kamata ganin da gaske a wannan lokacin babu abinda yafi bukata sama da yaran sa, su tallafe shi su tsaya akansa, hakan ya kara saka ta a matukar damuwa, gashi babu wanda zata kira balle ta samu sassaucin abinda take ji idan sukayi magana da wani. ***Ita ta fara tashi, ta yunkura zata mike ya maida ita yana lumshe Ido "Asubah tayi fa." Tace tana kallon fuskar sa ta dan hasken da ya shigo ta saman kofar dakin. *Um um.." ya sake kankame ta, yana makale ta sosai "Ka tashi please". "Bafa muyi bacci sosai ba." Yayi maganar yana kin bud'e idon. Daddagewa tayi ta mintsine shi, yayi saurin ware idanun, ya sake da sauri ya hau sosai wajen "Maimartaba kike yiwa haka? Lallai yarinyar nan." Lokacin har ta kai kofar toilet, tayi masa gwalo ta shige da sauri ta saka key, ko da ta fito yana zaune ya kunna wutar dakin,ya harare ta irin hararar wasa. "Allah sai na rama, zaki gane baki da wayo." Dariya tayi, yayi kamar zai rik'e ta sanda zai shiga toilet din, ta zille da sauri tana dariya. Sallah sukayi, ya dauke kayan shinfidar, ya ce ta koma kan gadon ta kwanta tunda ba wani bacci sukayi sosai ba, kwanciya tayi ya gyara mata komai sannan ya zauna zuwa sanda garin yayi haske, sannan ya koma gida. Yana zuwa ya shiga daki ya rage kayan jikin sa ya kwanta, nan da nan bacci ya dauke shi me karfin gaske. Sai wajejen sha daya ya tashi, yayi wanka ya fito, ya shiga ya gaida su Maman Yara ya same su suna zaune suna hira, yayi mata ya jikin sannan yace zai tawo musu da kaya saboda su chanja dan tun wanda suka tawo dashi ne. Mota ya hau, ya tunkari inda yake saka ran samun Daddy, yana tafe yana tunanin yadda komai ya tafi kamar yadda suka tsara. Lokacin da Madaki yayi masa kiran nan, yayi recording komai, yana katse kiran ya nemo number wani abokin sa babba a DSS, ya bashi bayanin komai, number wayar sa ya bukata, a take suka yi tracking number suka gano location din da yake, da kuma komai akan gidan wanda ya kasance gidan wanda aka kama sun tare ne, hatta abinda sukeyi a gidan sai da suka gano suka kuma tashi mutum biyu cikin farin kaya suka isa gidan suka sake samun information akan komai. Ko da Madaki ya turo address din already su sun isa wajen wasu ma suna cikin gidan cikin badda kama. Babu abinda ba za'a iya yi ba idan ana son a dakile abubuwan da ake yi a k'asar nan tamu akan harkar rashin tsaro amma babu me yi. Allah ya kyauta. Sanda ya shiga layin nasu,zuciyar sa sai da ta buga saboda tsoron abinda zai tarar, amma idan ya tuna hakan ce hanya kad'ai da zai iya cire wasiwasin da Madakin ya saka masa. Bama wannan ba kad'ai, atleast zai taiamaka masa wajen karasa sauran abubuwan da yake son karasawa da yake ta fadi tashi shi kad'ai, yasan zai bashi shawara a matsayin sa na mahaifi shawarar da zata taimaka masa. Yana yin parking Afrah suka fito ita da Adnan, daga gani asibitin zasu,yayi saurin rufe baki yana girgiza kai "Wai sai yanzu zaki koma?" "Na zata wallahi kana chan." Tace tana rufe baki. "Aiko sai anci ki tara, kika barta ita kad'ai." "Ayi hakuri." Dariya yayi suka gaisa da Adnan,ya shiga ciki su kuma suka wuce. Kai tsaye falon ya wuce, ya tura kofar cikin rashin kuzari, gami da sallama. Yana tsaye da remote control a hannun sa, ya juya da sauri. "Sultan." "Barka da gida Daddy." **** Banyi editing ba, I'm very very busy ne Wallahi. Afwan. Wadanda sukayi min magana ta PC banyi reply ba, kuyi hakuri ba a nutse nake ba ban zauna ba. " ©hansatu rano Page 46 Zafafa biyar na kud'i ne!!! *** Yana tsaye da remote control a hannun sa, ya juya da sauri. "Sultan." Ya kira sunan shi yana takowa zuwa tsakiyar falon "Barka da gida Daddy." Yayi maganar yana russunawa "Ina kwana Daddy?" "Lafiya lou Sultan, ya gajiya da dawainiya? Allah dai yayi muku albarka." "Amin Daddy." Dan jim yayi, har Daddy ya gama dube duben tashar sa, ya zauna yana dora hannun a saman kujerar da yake kai "Akwai labari ne sultan?" Yayi maganar rabin hankalin sa na kan talabijin din. "Dama wata magana nazo muyi Daddy, ina ban takura ba." Juyowa yayi gaba d'aya ya kalle shi "Ina sauraron ka, menene ya faru?" Gyara zama Sultan din yayi, ya kalmashe kafar sa yadda zai ji dadin zaman sannan yace "Dama Daddy akwai abubuwan da suka faru..." Ya shiga bashi labarin komai cikin hikima ba tare da Daddy ya fuskanci takurawar Mah-Mah ce ta saka shi tunanin neman sanin waye shi din, tiryan tiryan yake bin komai har ya kai gabar da ya samu address din Madaki, sai a lokacin yaga Daddyn yayi sak kamar zai yi magana sai kuma ya cigaba da sauraren sa. Be rage komai ba, ya kwashe komai da ya faru, ya sanar dashi har zuwa haduwar su ta karshe da Madakin da kamashin da yasa akayi, sai dai be kai ga fad'awa Daddy abinda Madakin yace masa ba ya dakatar dashi bayan yayi kamar zai kware har sultan din yayi saurin tashi ya dauko masa ruwa ya bashi, be iya sha ba ya ajiye a gefe sannan yace "Yanzu Sultan ace duk ka shiga irin wannan matsalolin amma sai yanzu zamuji, me yasa baka sanar dani ba tun farko, baka tsoron abinda zai je ya dawo? Kasan waye Madaki kuwa Sultan?... Mutumin da babu Imani a ransa babu..." Sai kuma yayi saurin yin kwana yace "Mutumin da daga yadda ka bani labarin sa babu abinda ba zai iya ba domin ya cutar da kai, ko nace ma ya cutar da kai tunda ga dan uwan ka nan da matar ka badan Allah ya kiyaye ba waya san abinda zai faru!?" "Dama Daddy..." "Dama me sultan? Sai bayan da komai ya lalace? Banji dad'i ba gaskia, kuma baka kyauta ba." "Ayi hakuri Daddy in Sha Allah hakan ba zata sake faruwa." "Allah yasa..." "Yanzu ina shi Madakin yake?" "Yana DSS office." "Owk." Yayi shiru Tunanin ta yadda zai masa magana ya shiga yi, shiru kake ji a falon sai karar talabijin din kawai da har sun gama program din da Daddyn yaso kalla. Daurewa Sultan yayi ya kira sunan shi "Daddy dama akwai wani abun." "Ina jinka." "Ranar da naje wajen Madakin nayi masa maganar dan uwan nawa da yake tare dashi wanda binciken da nayi ne ya sa na gane hakan..." "Ya fad'a maka inda yake.?" "A ah..." "Ehen...Nasan ba zai yi saurin fad'a maka ba dama ai." "Be fad'a min ba, amma sai ya nuna min hoton Ka yace kai ne zaka fad'a min inda yake..." Da sauri Daddy ya mike "Hotona... Ni kuma Sultan?" "Abinda ya saka ni a matukar damuwa kenan, nasan Madaki so yake yayi wasa da hankali na, ban yarda ba ko da ya fad'a ba Wallahi, ban kuma yi maganar ba wai don na tuhume ka, a ah... Ina so na kawai na samu nutsuwar zuciya, nasan idan nazo wajen ka mukayi magana zan ce da gaske Madaki karya yake min, zan kuma san yadda zanyi na cigaba da neman sa." "Sultan?!" Ya kira sunan sa da karfi "Kayi hakuri Daddy idan magana ta, ta bata maka rai." "Ko daya Sultan, ko daya wallahi..." Ya dora "Be fad'a maka komai akai ba?" "A ah..." "Shikenan, ka kaini in da yake na ganshi." "Ok yanzu ko sai anjima?" "Yanzu Sultan." Wayar sa ya ciro yayi dialing number Farouk D abokin nasa da case din ke hannun sa, ya fad'a masa zasu zo tare da Daddy idan zai yiwu su ga Madaki, yace zasu iya zuwa babu matsala. Tashi Daddyn yayi ya shiga ciki ya shirya ya fito suka tafi. Har suka isa babu wanda yayi magana, shi Sultan tunanin abinda zai faru idan sunje din wanda tun daga response din Daddyn ya gane da gaske ya san Madakin, tsoron kar abinda yake tunani ya zama gaske yasa ya kasa yin magana har suka isa. Suka fito suka shiga ciki ta wata kofar baya bayan Farouk D din da kansa ya fito yayi musu jagoranci zuwa ciki. A saman wani benci suka taddashi yana zaune ya juya bayan sa, karasawa Daddy yayi Sultan kuma ya koma da baya ya fita saboda ya basu damar yin magana. "Madaki." Daddy ya kira sunan shi, da sauri ya waiwayo, ganin wanda be yi zato ba ya saka shi mikewa fuskarsa dauke da mamaki "Nasan dama zaka zo!" Yayi maganar yana takowa zuwa wajen sa. "Menene hadin ka da Sultan?" "Menene hadin mu dashi dai zaka ce." "Na zata mun dade da rufe wannan maganar, mesa ka dago ta har kace ya same ni, bayan kasan ba haka mukayi ba, kasan dai akwai sharadin da muka gindaya kafin hakan ta kasance." "Amma kasan da haka, ka daina daga wayata, ka chanja layi domin kar na neme ka,sannan na kira ka bayan na tura maka message kaki dagawa?" "Saboda babu abinda yayi saura tsakanin mu." Daddy ya fad'a kai tsaye "Ina yaron yake?" "Allah yayi masa rasuwa tun da dadewa." "What! Haba Sulaiman, kar ka maida ni karamin mutum mana, ya zaka zo min da maganar da hankali ba zai dauka ba." "Baka yarda da mutuwa ba kenan." "Ban yarda da wannan din ba dai." Mikewa Daddy yayi yace "Ka gaya wa Sultan dan uwan sa Allah yayi masa rasuwa, sannan ka tabbata da ka wanke ni, zanyi kokarin ganin ka bar nan." Ya juya ya fice yana jin kamar be kyauta ba,amma idan be yi haka ba ya zai yi? Ta ina zai fara ma? Sultan na ganin shi ya taso da sauri. "Kaje kuyi magana dashi." Wucewa Sultan yayi shi kuma ya zauna a inda Sulthan din ya tashi. Yana shiga ya tarar da Madakin ya kifa kansa a kan tafin hannun sa,daga nesa dashi ya tsaya,jin motsin mutum ya saka Madakin dagowa "Yaushe zaka saka su sallame ni daga nan?" "Sanda ka shirya fito min da d'an uwana, sanda ka shirya karbar hukuncin mugayen laifukan daka dade kana aikatawa, da kai da duk wani wanda yake da hannu a ciki,kasan kuma su DSS ba kamar sauran police bane balle ka basu cin hanci su sake ka, idan har kaga ka fita daga nan, toh sunyi bincike sun tabbatar da kai din ba mai laifi bane, saboda haka ya rage naka." "Idan na fad'a maka gaskiya akan maganar dan uwanka zaka saka su barni na tafi?" "Ina jinka." _"Bayan Mun baro Masarautar, ina rik'e da yaro daya, safiya tana rike da daya har muka kai gidan dana shirya zata zauna ita da yaran. Na bud'e muka shiga, na nuna mata duk abinda ya kamata ta sani sannan na fita na siyo wa yaran madarar da za'a basu wanda tuni sun fara kuka. Na dawo aka shiga basu Madara, kwana biyu tsakani daya daga cikin yaran ya fara wani irin rashin lafiya,dama chan mun lura da rashin kuzarin sa akan dan uwansa, haka muka tafi muka kaishi asibiti, bayan anyi masa abinda ya kamata likitan hankalin sa ya tashi ganin yaron na dauke da mugun ciwo, ciwon zuciya."_ Wani irin bugawa zuciyar Sultan tayi, irin bugawar da bata taba yi ba, wani irin tsoro ya shige shi, yaji kamar kafar sa zata zame shi ya fad'i a wajen _Mu kanmu hankalin mu ya tashi, musamman Safiya tunda ita mace ce, kuma gata da tausayi sosai kuma ta kwallafa rai akan yaran. Muka fito bayan likita ya bamu shawarwarin da zai bamu akai, da abinda ya kamata muyi da kuma wani babban likitan zuciya da zai had'a mu dashi. Tafiya muke kowa da abinda yake tunani a tsakanin mu, a lokacin bani da komai sai yan kudaden da basu da yawa, gashi irin wannna ciwon akwai cin kud'i sosai. Wajen zama na nunawa safiya nace ta zauna ta jirani, sannan na koma cikin asibitin ina son nayi wa likitan wata tambaya, ban karasa ba, na hadu da wani mutum a zaune, ya had'a kansa da guiwar sa, daga gani yana cikin tashin hankali mara misaltuwa, dafa shi nayi ya dago da sauri, sai dai yadda idanun sa suka yi masifar ja yasa nayi baya cikin mamakin abinda zai saka shi a wannan halin. _"Bawan Allah me yake damun ka?" Nayi masa tambayar ina kallon sa, girgixa kai yayi hawayen dake kwance a cikin idanun sa suka gangaro. "Subhanallahi." Nace _"Dan Allah ka fad'a min abinda yake damun ka." Domin ni a tunani na ko kudi aka yanka masa da zai biya a asibitin bashi dasu kuma bashi da hanyar samun su, duk da yanayin shigar sa bata nuna hakan ba. Abinda ya fito daga bakin sa ya bani mamaki matuka _"Bawan Allah ina cikin gagarumar matsala, bana jin akwai wanda ya kai ni shiga cikin tashin hankali, na kashe d'a na da kaina, d'an da muka dad'e muna addu'ar Allah ya bamu,d'an da muka sameshi bayan tsawon lokaci da muka dauka muna nema, bansani ba, bansan yana ajiye a wajen ba wallahi, na zauna akan jinjirin d'ana da aka haifa yau kwana uku, wanda uwar sa ke cikin halin rai ko mutuwa, duk saboda wahalar haihuwar sa, ya zanyi da raina?"_ "Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun, garin yaya bawan Allah?" "Kaddara! Tsautsayi, bayan yazo duniya ne aka dauke shi aka kaishi nursery inda ake ajiye yara saboda lura da sukayi yasha ruwa wanda ya faru saboda doguwar nakudar da mahaifiyar tayi kafin daga karshe ayi mata aiki a ciro d'an. Ina zaune dazu na dawo daga dubo yaron wanda har ma sun ce gobe zasu bamu yaron saboda ya samu sauki, sai ga kira daga chan nursery din, suna nema na, nayi sauri naje suka bani takarda suka ce naje na siyo wata allura, na tafi naje na siyo na dawo, sai ban ga kowa a cikin wajen ba, sai na shiga kai tsaye da niyyar na jira su, tsautsayi ashe sun ciro shi daga cikin kwalbar da yake sun saka masa kaya, da niyyar su bani shi idan akayi masa allurar sun sallame shi daga nursery din, fita me kula da wajen tayi ta dauko wani abu, ganin ba dadewa zatyi ba yasa ta ajiye shi a kan doguwar kujerar dake ajiye a gefen dakin, ta nannade shi a cikin shawl dinsa, ban sani ba, wallahi ban lura ba ban kuma yi tunanin yana wajen ba, na zauna akan sa." "Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun, Allahu Akbar, gaskiya bawan Allah na tausaya maka, Allah ya jikansa yasa masu ceton mu ne." "Amin." Ya amsa min cikin yanayi, na danyi jim kad'an sai kuma nayi gaba, har na wuce shi sai na dawo bayan wani tunani ya darsu a raina "Idan na baka yaro jinjiri haihuwar kwana uku zaka karba?" A zabure ya dago, ya tashi tsaye da sauri "Wallahi tallahi zan karba, zan kuma kula dashi tamkar dan cikina, zan bashi ingantacciyar rayuwa nayi maka wannan alkawarin, dan Allah ka taimaka min." "Yan biyu ne, sai dai an haife shi da ciwon zuciya gashi bani da kud'in da zan iya daukar nauyin ciwon sa, Idan ka yarda zaka kula dashi, za kuma ka bani wasu kudade masu yawa da zan kula da d'an uwansa, nayi maka alkawarin bar maka shi har abadah, na fita daga rayuwar sa ba zaka sake gani na ba kuma." Da sauri yace _"Na amince wallahi, ko nawa kake so zan baka."_ "Shikenan ina zuwa." Nayi gaba na koma wajen da na bar safiya na karbi jinjirin guda daya nace mata ina zuwa, na juyo na kawo masa, ya tashi da sauri ya miko hannu, ban bashi ba nace ya fara cika alkawari, motar sa muka nufa ya ciro cheque ya rubuta min kudade masu yawan gaske, ya bani, sannan yace yana bukatar muyi yarjejeniya a rubuce akan ba zan dawo daga baya nace ya bani yaron ba domin yana so idan matar sa ta farka ya bata shi a matsayin wanda suka haifa,na yarda mukayi ya saka hannu nima na saka sannan ya karbi yaron ni kuma na karbi cheque din na juya na tafi."_ Dafa bangon wajen Sultan yayi jin zai fad'i da gaske _"Safiyanu Madaki! Na taba ganin sunan a wasu takardun Daddy."_ Sultan yaji maganar Safwan na amsa kuwwa a kunnensa _"Yanà da ciwon zuciya_" zuciyar sa ta sake fad'a masa, runtse idon sa yayi yana hango kalar tashin hankalin da mutane da yawa zasu shiga idan har wannan labarin ya fito, me zaiyi? Farin cikin samun Safwan a matsayin dan uwan sa na jini ko kuma tunanin yadda Safwan, Mah-Mah da sauran mutane zasu ji idan har maganar ta fita, tabbas dole ne komai ya bayyana, idan ya rufa ya bar maganar yana ganin kamar be wa mutane hudu adalci ba, Maimartaba, Gimbiya, Aminatu da kuma Safiya. Gefe daya kuma idan ya tuna kalar tashin hankalin da Mah-Mah zata shiga sai yaji wani irin weakness, me ya kamata yayi? "Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun." Kawai yayi ta maimaita dan beyi tunanin labarin zai juye ya zama haka ba.© Hafsat Rano Page 47 ***"Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun." Kawai yayi ta maimaita dan beyi tunanin labarin zai juye ya zama haka ba.   Juyawa yayi ya fice da sauri be jira Madakin ya gama ba, ya iske Daddy a tsaye yana jiran fitowar sa, daga ganin yanayin fuskar sa akwai firgici musamman ganin Sultan din ya dad'e a ciki. "Me yace maka?" Daddy ya tambaya da sauri, girgiza kai kawai Sultan yayi zai yi magana Farouk D ya fito. "Dr akwai wasu bincike da mukayi inda muka gano wasu harkoki da yake yi wanda basu dace ba, toh dai muna cigaba da bincike duk abinda muka samu zamuyi aiki akai. "Nagode sosai oga, kuyi aikinku babu matsala." Sai ya mika masa hannu "Bari mu wuce, thank you very much." "Babu damuwa." "Baba agaida gida." Ya dan rissina yana kallon Daddy. Har suka isa mota suka shiga Sultan yaki yarda su had'a ido da Daddy da ya gama karantar sa tsaf yasan kuma ya samu wani information akan labarin. Sai da ya bari ya tada motar suka hau titi sosai sannan yace "Sultan bani da zabi ne a lokacin, ka saka kanka a matsayin halin da nake ciki a lokacin, ina tunanin ba kowa ne zai ketare ba, bayan haka ban san dalilin da Allah ya kawo Safwan cikin rayuwar mu ba, may be kaddarar shigowar sa ita tasa yaron mu ya rasu, idan naki karba kamar nayi butulce ne." Sai ya dora "Sannan Sultan kai kanka ka sani, zaman Safwan a wajen mutum irin Madaki,da tuni rayuwar sa ta lalace, ina ganin hakan da nayi shine kawai mafita garemu dukka. Duk da babu ranar da zata fito ta fadi banji a raina cewa irin wannan ranar na zuwa ba, sai dai tsoro na daya ne, halin da mamanku zata shiga da kuma halin da Safwan zai shiga, ga lalurar sa, idan na tuna wannan sai naji duk na rasa inda zan saka raina naji dad'i, ya zanyi idan na zama sanadiyar tarwatsewar rayuwar mutanen da nayi iyakar kokari wajen kare wa, ta yaya zan fara sanar da su wannan labarin? Ta yaya Sultan?" Shiru Sultan din yayi be tanka ba, kansa yana kallon titi yana jin sanda kwalla ta taru a idon sa, me zai ce ne wai?kamar Daddy ya san me yake tunani a ransa sai ji yayi yace "Kace wani abu dan Allah sultan,kace banyi son zuciya ba wajen abinda na aikata sai son kare rayuwar su, idan kace nayi ha'inci ko zalunci hakika ba zan taba yafewa kai na ba." "Bakayi ba Daddy, bakiyi ba, kai uba ne irin wanda kowanne d'a zai yi farin cikin samu, kuma tabbas kaddara ce me karfin gaske ta shigo da mu cikin rayuwar ku, kuka kuma karbe mu hannu biyu ba tare da kun gaza ba... Sai dai." Sai yayi shiru, yana tunanin ta yaya ma zai iya cewa Daddy kuskuren sa daya rashin sanar da Mah-Mah da Safwan din,bai san da wanne kalar magana zai yi amfani ba,duk wadda ya kamo sai ta goce ko kuma yaga bata yi daidai da abinda d'a ya kamata ya fad'a wa wanda yake ma kallon mahaifi ba a matsayin gyara, yanayin yadda yake ta kokawa da zuciyar sa wajen hado kalmomin ya saka daddy cewa "Sai dai nayi kuskuren rashin sanar dasu Sultan, nayi kuskure sosai, idan babu komai ai akwai halin mutuwa ko?" "Tsoron abinda zai faru ya saka na bar Abin a cikin zuciya ta, na binne shi nayi kokarin karbar kaddara ta da hannu bibiyu, idan na kalli tsantsar kaunar da ke tsakanin Safwan da Maman ku sai naji bani da sauran damuwa, nasan babu wanda yasan abinda ya faru saboda haka bani da fargabar wataran wannan farin cikin da nake gani a tare dasu zai kau, sai gashi cikin rashin sani, Allah Hakeem ya sake kawo ka cikin rayuwar mu, ba tare da sanin alakar dake tsakani ba, lallai wannan shine kaddarar da ake cewa bawa baya ketare mata,yanzu ya mahaifanku suke ji rashin ku tsawon wannan lokacin, 'yaya uku ba daya ba, wannan wane irin zalunci ne,tabbas mutane basa tsoron Allah basa tunanin mutuwa da hisabi, da ana tuna za'a mutu da abubuwa da yawa ba'a aikata ba Sultan." "Idan na hanaka sada Safwan da iyayenku ban musu adalci ba, na kuma so kaina ainun, saboda haka na baka dama Sultan, na baka dama kayi duk abinda ya dace, ina rokon Allah ya duba niyyata da zuciya ta ya kawo min komai cikin sauki." "Amin Daddy, in Sha Allah komai zai warware cikin sauki, da nayi niyyar had'a tafiyar tare da su dukka kafin komai ya chanja, amma yanzu zanje ni kad'ai, idan yaso a wannan lokacin kayi kokarin fahimtar da Mah-Mah, yadda zata fuskanta duk da ba wai abu ne me sauki ba, ina fatan komai yazo da sauki." "In Sha Allah, Sultan amma dan Allah kar a sanar da Safwan har sai ya samu lafiya sosai, bana son abinda zai taba lafiyar sa dan Allah." "Nayi maka alkawari Daddy, har sai ku da kanku kunji ya kamata ya sani kun sanar dashi sannan zan gabatar masa dasu, kun fi kowa sanin sa, saboda haka ku ya kamata ku fad'a masa." "Nagode Sultan." Gida ya maida Daddy, ya dauki wayar sa ya kira number Muhammad, be daga ba har ta gama ringing, kawai sai ya wuce asibiti, ya fara zuwa aka sallami Amrah ya kaisu gida ita da Afrah sannan ya dawo ya koma wajen Safwan.   Yau ranar daban ce da sauran ranaku, haka ma matsayin Safwan din ya banbanta da na baya duk kuwa da ada din ma yana jin sa ne sosai kamar d'an uwa na jini, ko da ya shiga sai ya tsaya ya hard'e hannun sa ya jingina da kofar "Kana sauri ne?" Safwan yayi maganar yana dubansa "A ah, akwai matsala ne?" Ya tako zuwa tsakiyar dakin "Ko daya, kawai na gaji da asibitin nan ne, inaso a sallame ni, tunda gaka pls ka saka su sallame ni." "Sai ka kara sati daya, sai ka koma gida Dr Labaran ya tunda zuwa yana dubaka." "Har sati?be yawa ba." "Be yi ba, kamar yau ne ka kwantar da hankalin ka." "Tunda kace, shikenan amma sati daya kawai wallahi." "In Sha Allah." "Ka zauna mana, kwana biyu baka zama balle muyi magana, naga kamar akwai abinda yake damun ka, idan akan abinda ya faru ne pls karka saka a ranka, haka Allah ya tsara." "Babu abinda ke damuna, zan koma Canada!" "Wait what!" "In sha Allah." "Why so soon? Wani abun aka turaka?" "No wannan personal tafiya ce, ba zan dad'e ba kuma in Sha Allah." "Personal? Zan iya sanin me? Cause jikina na bani something is not right." "Karka daga hankalin ka, tafiyar alkhairi ce in Sha Allah, kayi min addu'a." "Baka da doubt akan wannan, zan maka as always,just make sure you stay safe." "I ll, kaima make sure you stay healthy, kasha magani banda korafi, kar ka ce kuma su sallame ka lallai idan sunce ka zauna kuma." "Sallamar dai? Toh shikenan ba zan ce ba." "Yawwa good b..." Ya rufe baki da sauri yana dariya "Boy ko? Dan kayi aure ka barni, zan yi rama ne bari na tashi daga gadon nan." "Zaka rame yaro, Allah kuwa." Dariya suka saka a tare, suka cigaba da hira har zuwa sanda Mah-Mah suk shigo da wasu kawayenta da suka zo duba Safwan din, yadda take ta nan nan da Safwan din ya sake saka Sultan a tsananin tausayin ta, yasan idan komai ya bayyana ita zata fi kowa zama a bar tausayi, tashi yayi ya fita ya shiga cikin asibitin,suka hadu dasu Dr Ahmad dasu Dr Osas suka yi hira sosai, anan ya sako wa Dr Ahmad maganar ajiye aiki da yake son yi, sosai ran Dr Ahmad ya baci ganin cewa bangaren Sultan din basu da yawa ana bukatar sa sosai, yanzu ma saboda abubuwan da yadda suka kasance ya saka yayi shiru akan Sultan din, sosai yayi kokarin fahimtar dashi duk da be fito kai tsaye ya sanar dashi dalilin sa ba, amma sai yayi funfurus yace ba zai saurare shi ba, idan ma so yake dai a kara masa lokaci ya bashi enough ya gama sorting out duk matsala da yace ta taso masa. Haka ya hakura yayi musu sallama ya tafi. Ya koma ya sake duba Safwan sannan ya fito ya wuce gida. ***Bayan sultan ya ajiye su a gida ya tafi, suka shiga tare wajen su Maman Yara suka gaishe su, suka amsa cikin girmamawa, Maman Yara ta tambayi wace Amaryar, karaf Afrah tace itace,Amrah tayi kasa da kanta tana murmushi. Ganin haka yasa Maman Yara gane Amrah ce, sukayi ta tsokanar Afrah tana dariya, sai kuma hira ta barke tsakanin Maman Yara da Afrah inda farat daya taji matar tayi mata ita ma kuma taji Afrah ta burgeta babu girman kai ga faran faran da kirki. Amrah ba gwanar magana bace shiyasa idan aka yi abu sai kawai tayi murmushi karshe sai tayi musu sallama ta nufi dakin ta. Kan gado ta fad'a, tayi ruf da ciki tana tunanin me ya kamata tayi, tana kwance Afrah ta shiga ta hawo gadon ta shiga jan hannun ta. "Tashi zakiyi malaama ki gyara jikin ki." "Wai Afrah me yasa kin raina ni ne haka dan Allah?" "Allah ba raini bane, kece kin fiya sanyin jiki, kika zauna kina wannan nuku-nuku din naki sai dai kiga anayi wallahi." "Naji, toh me zanyi?" "Tashi zakiyi muje na wanke miki kan nan naki kafin na wuce gida, kiyi wanka ki shirya fes." "Bani fa da lafiya!" Ta marairace "Sai kiyi, Allah tashi zakiyi kin ga." Ta hau nade hannu, tashi Amrah tayi dan dama itama tunanin da take kenan, taimaka mata Afrah tayi ta wanke kanta tas ta busar mata dashi da hand dryer sannan ta gyara mata shi yayi kyau sosai. Kitchen Afran ta sauka ta dora simple dish ta bar Amrah ta shiga wanka. Shiryawa tayi sosai ta gyara jikin ta, tabi ko wanne lungu musamman bayan guiwar kafarta, da wuyanta da hannayen ta da turarurruka masu sanyin kamshi. Simple kaya ta saka wanda suka dace da yanayin lokacin ta iske Afrah a kitchen din suka karasa aikin tare, suka jera komai a saman dinning. "Bari na wuce gida." Rik'e ta Amrah tayi "Dan Allah karki tafi, ki bari gobe dan Allah." "Mesa? Baki ji me umma tace ba?" "Ai na kira Abba nayi masa maganar yace Allah ya kaimu goben, yau fa aka sallamoni sai kuma a barni ni kad'ai?" "Auw wai har Abba kika kira? Tabdin." "Please please please..." "Shikenan, Allah ya kaimu goben." "Yeee thanks swthrt." Tayi hugging dinta suka saka dariya. Zama sukayi, suka kunna kallo kafin a kira sallah, shiru Amrah tayi tana tunanin maganar da sukayi da Sultan jiya, wunin yau gaba daya tunanin maganar take, matsawa tayi kusa da Afrah ta kira sunan ta "Abokin kuka shi ake fadawa mutuwa ance." Tayi maganar tana dora kanta akan saman kafar Afrah "Lallai kinji hausa, aina kika ji wannan karin maganar?" Dariya Amrah ta saka "Ya Sultan ne jiya ya fad'a min." "Yawwa ko da naji." "Afrah magana zamuyi, amma tsakanin mu,mu biyu dan Allah karki fad'a ma ko umma ce, sai lokaci yayi, yanzu ma abinda yasa zan fad'a miki saboda na rasa wanda zai fadawa gashi maganar na ci na, kinsan dai irin yadda abun yake." "Nayi alkawari ba zan fad'a ma kowa ba." "Ya Sultan ya gano family sa!" Tayi maganar cike da farin ciki. "What!" Afrah ta zame kanta daga kafarta ta dafe chest din ta "Allah da gaske." "Ohh My God! Masha Allah, Alhamdulillah, kai amma naji dad'i kuma nayi masa murna, ya akayi haka? Dama irin haka na faruwa bayan lokaci me tsawo?" "Al'amarin Allah Afrah, babu yadda baya kasancewa, na tuna umma ta taba cemin tana ji a ranta Sultan zai hadu da yan uwansa sooner or later, har ta bani labarin wata da ta bata a hatsarin mota, aka dauka mamanta ta mutu a hatsarin ashe da ranta, aka kaita wani gari far from inda akayi hatsarin wata mata ta dauke ta, ta kula da ita har ta girma, tayi aure ta haifi yaya da yawa, kwatsam wata mata me tallan mai da kuli-kuli dake kawo talla gidan tace mata akwai wata mata a gari kaza, suna bala'in kama, haka dai a karshe sanadiyar me tallan man nan aka gano ashe uwa da 'ya ne shiyasa take ganin kamar su sosai." "Ikon Allah!" "Yafi gaban komai, kuma kinga shi case din ya Sultan daban..." Sai ta bata labarin a takaice amma banda maganar karshe ta Daddy tunda bata san yadda sukayi ba, ita dai Afrah tsabar mamaki ta gaza cewa komai, mamakin ta be karu ba sai da taji cewa ashe Sultan din d'an sarki ne, anan tayi tsalle ta dire akan Amrah tana ihun murna "Wallahi ba karamin kyau zakuyi ba a fad'a wai wai, akwai ruguntsumi wallahi, zan so naga idon Shegiyar Umaiman nan lokacin kinyi mata nisa." "Ni kuma expression din Hajiya kawai nake so na gani wallahi." "Kinsan ta kuma da son abin duniya, balle ace Sarauta kai, ai dole kowa ya kiyaya har Mah-Mah wallahi Allah." "Hmm." "Ranki ya dade kina bukatar wani abu ne?" Afrah data zame k'asa tayi maganar cike da girmamawa, tuntsurewa Amrah tayi da dariya, haka sukayi ta hira cike da farin cikin abinda yake tunkaro su wanda har Afrah ta fi ma Amrah nuna zakewarta, hango kanta kawai take a Masarautar irin Masarautar Saji. Kira salla ne ya tashe su daga zaman da sukayi, sukayi alwala sukayi sallah bayan sun idar sukayi waya da Umma ta sake duba jikin Amrah sannan tace lallai lallai Afrah ta dawo gobe. ***Kamar yadda yake kaidar sa ko yaushe, baya shigowa gida tun dama chan idan yaga magriba ta gabato, sai ya jira anyi sallar sannan ya wuto gidan wani lokacin ma sai ya jira anyi isha'i sannan yake dawowa. Yau ma haka ce ta kasance, ya tsaya a wani masallacin hanya yayi sallah ya dad'e yana addu'ar Allah ya saukaka komai sannan ya fito, kiran layin Muhamad ya sake yi a karo na biyu, yayi sa'a tana shiga ya daga, suka gaisa ya ce yazo gobe ya same shi ya bashi address din inda zaizo ya kuma ce masa idan zai yiwu su tawo shi da kanwar sa. Ya amsa masa sannan sukayi sallama. A aljihu ya jefa wayar, ya ja iska zuwa hunhun sa ya fezar ya ji hucin ta taba saman kuncin sa. "Alhamdulillah ya Allah." Ya furta dan yasan babu abin yarda da godiya sai Allah, yadda ya warware masa kusan komai a cikin sauki fiye da yadda shi yayi tunani. Ya kuma juya abubuwan suka zama a yadda shi zai fi kowa farin ciki da hakan, idan ba Allah ba yasan babu wanda zai masa wannan shiyasa baya gajiyawa wajen nuna godiyar sa cikin kankan da kai. Mota ya koma ya shiga, har ya dau hanyar gida sai ya tuna be siya komai ba, ya juya ya samu wani supermarket ya shiga ya sai abinda yasan zasu bukata sannan ya nufi gida. Suna zaune suka ji ana bud'e gate din, da sauri Afrah ta mik'e tsaye "Ango is back, bari kiga na gudu wajen su Maman Yara tun kafin ya tarar dani anan." "Pls ki tsaya, Afrah!." "Sai kiyi kuma, tashi zakiyi kije ki tarbe shi." "Kai ni da ban da lafiya?" "Goodnight." Ta daga mata hannayenta alamar bye-bye ta yi ficewar ta. Kamar wadda kwai ya fashewa a jiki haka ta ja kafafuwan ta, ta bud'e kofar falon ta tsaya ta kasa karasa fita, tana jin sanda ya rufe kofar motar ta ji takun tafiyar sa zuwa inda take tsaye, motsawa tayi da nufin komawa ya karaso hannun sa dauke da ledoji. "Sannu da zuwa..." Tayi maganar tana mika hannu zata karbi kayan hannun sa, kin bata yi, ya had'e su a hannu daya, yasa dayan hannun ya riko ta "Ke da baki da lafiya, ai sun miki nauyi." "Basu min ba." Tace tana sake mika hannu "Noo barshi." Ciki suka shiga ya ajiye kayan da sauri ya saka dayan hannun ya had'e ta da jikin sa "Irin wannan tarbar nake so." "Ok sir." "Kamar gaske, ya jikin naki? Akwai abinda ke damun ki?" "Babu komai, kawai weakness." "Zai tafi a hankali, I promise." Ya d'age mata gira yana murmushi. Kallon dining tayi, ya kalli wajen yaga warmers a jere, ya mike ya nufi wajen yana kallon ta "Don't tell me girki kikayi?" "Afrah ce ta yi ni kad'an na tayata." "Da baku wahalar da kanku ba, yaushe kuka dawo ma har kuka huta balle azo maganar girki." Jan kujerar yayi ya zauna ya ja mata ta kusa dashi ita ma ta zauna sannan yace "Thank you so much, kunyi kokari Allah yayi muku Albarka." "Amin." Ta amsa tana daukar plate domin zuba masa, karba yayi ya zuba musu a tare "Bismillah." Tare suka ci abincin suka gama, ya tayata suka kwashe kayan sannan yace ta karashi wajen su Maman Yara, suka kwashi ledojin abinda ya siyo musu suka kai musu,suka tarar da Afrah ana ta shan hira ana dariya, Aminatu na bata labarin gidan sarauta da yadda bayi suke a gidaje irin wadannan. Sosai hirar tayi mata dadi ta samu chance ta dinga shigar da tambayoyin ta kad'an kad'an. Shigowar su Amrah ya katse labarin, Sultan da Maman Yara suka fito harabar wajen sukayi magana ya fad'a mata komai da komai, da kuma niyyar sa ta tafiya, tayi masa addu'a da fatan alkhairi sannan ya fad'a mata Muhammad zasu zo gidan nan su zauna tare da kanwar sa, kar su yi saurin sanar dashi komai har sai gasu ga Safiya da Madaki da su Maimartaba da kowa da kowa dai. Tayi alkawarin kiyaye wa sannan sukayi sallama. ***Kayan jikin sa ya rage bayan sun dawo ya shiga wanka, ita kuma Amrah ta nufi dakin ta, ta dauki magungunan ta tasha ta kwanta a gefen gado ta ciro wayarta tana dannawa. Bayan kamar mintuna talatin ta tashi ta kashe wayar ta saka a charge ta shiga tayi wankan ta fito ta saka kaya kenan ya turo kofar ya shigo, laptop ce a hannun sa da charger ta, ya jona ya jawo ta zuwa saman gadon, ya hau ya zauna ya mike kafar sa ya dora ta a saman kafar tasa sannan ya bud'e "Kinsha maganin ki?" Yayi maganar yana kallon ta "Eh nasha." Tace "Good zo ki tayani aiki." Zuwa tayi ta zauna a gefen sa, ya jawo ta sosai ya dora kanta a saman kafad'ar sa, ya shiga sarrafa na'ura me kwakwalwar tana kallo, "In sha Allah na gama mana arranging komai, har flight ticket na siya, tafiya zamuyi." "Da wuri haka?" "Toh me za'a jira umm? Hankali na bazai kwanta ba idan banje ba, ba na kuma so na tafi na barki again, kinga dai abinda ya faru da irin maganganun da mutane sukayi tayi akai, Allah yaso Umma da Abba sun sanni sun san halina da wasu bare bansan abinda xai biyo baya ba." "Allah ya kaimu." "Amin ya Allah." Yace yana rufe laptop din, ya dora ta saman bedside drawer, ya jawo ta jikin sa ya tallafi fuskar ta da hannun sa "Did you missed me?" Girgiza kai tayi alamar a'ah, da sauri yace "Da gaske kike?" "Da gaske." Tayi maganar tana dariya ganin yadda ya zaro ido. "Ohh na gane, na gane, wayo zaki min ko? toh naji idan ma ke bakiyi missing dina ba nikam nayi, sosai sosai sosai sosososooi...." Zatayi magana ringing din wayar sa ta katse ta, kamar ya share sai kuma ya dauka, ganin number kasar waje yasa ya mike sosai ya daga da sauri, "Muhammad!" "Na'am, barka da dare Hajiya." "Muhammad ina ka shiga kwana biyu number ka bata shiga, Maimartaba yana cikin wani hali." "Subhanallahi, me ya samu baban "Muna asibiti ko motsi bayayi sai numfashi kawai. Suna ta binciken su amma har yanzu basu gano matsalar ba, na rasa yadda zan Muhammad gashi bamu da kowa." "Ki kwantar da hankalin ki, in Sha Allah zai samu lafiya, nima ina hanya in Sha Allah, ki kwantar da hankalin ki Dan Allah." "Shikenan Muhammad, Allah ya kawo ka." "Amin ya Allah." Zagaye ya shiga yi a dakin cikin tsananin tashin hankali, baya son wani abu ya samu maimairta har sai ya wanke shi, gaskiya tayi halin ta, gefe daya kuma yana so ya rayu da iyayen sa, da yan uwansa zuwa wani lokaci. Rik'e shi Amrah tayi, yayi saurin rungume ta chest dinsa na bugawa "Babu abinda zai sameshi ko? Zanje na same shi muyi magana ko? Kice min zai samu sauki." Kuka ta saka ta dinga shafa Bayan sa tausayin sa na ratsata "Babu abinda zai sameshi in Sha Allah." Tace muryar ta na rawa. "In sha Allah." Shima yabi bakin ta ya fad'a yana daga kansa. Alwala sukayi, sukazo sukayi nafila suka roka masa lafiya, sun dad'e kafin su kwanta duk kuwa da Sulthan baya jin zai iya runtsawa sai dai bacci barawo ya sace shi. © Hafsat Rano Page 48 *** Alwala sukayi, sukazo sukayi nafila suka roka masa lafiya, sun dad'e kafin su kwanta duk kuwa da Sultan baya jin zai iya runtsawa sai dai bacci barawo ya sace shi.   Kiran farko a kunnen sa, ya mike ya fara yin wanka sannan yayi alwala, yazo yayi nafila ya zauna yana karatun Al'Qur'ani har aka kira na biyu, ya rufe ya maida shi ma'ajiyar sa sannan ya matsa gaban gadon ya saka hannu ya shafa gefen fuskar ta, bud'e ido tayi a hankali, yayi mata murmushi. "Lokacin sallah yayi." Yunkurawa tayi zata tashi ta maida ita. "Ba'a mikewa haka kai tsaye daga tashi daga bacci." Komawa tayi, yayi mata murmushi kad'an ya wuce ya sake daura wata alwalar domin ita alwala tana kankare zunubi ne shiyasa baya gajiya da sabun ta ta a ko yaushe, wasu mintuna ta dauka jin ta dawo fully yasa ta mik'e itama, ta mitsitsike idonta sannan ta sauko ta saka bed side slippers din ta nufi wajen wardrobe din ta, hijab ta ciro da doguwar riga ta ajiye a gefen gadon ta shiga tayi alwalar sannan ta fito sukayi jam'i a cikin dakin. Bayan sun idar sukayi azkar sannan ya koma saman gadon ita kuma ta dauki Al'qur'anin ta shiga karantawa a hankali.    Yana kwance yana tunani bacci ya dauke shi me karfin gaske, ajiye karatun tayi ta cire hijab din ta samu gefen gadon ta kwanta dan idonta a cike yake da baccin itama dan ba wani yin sa tayi sosai ba aka kira sallah.     Ita ta fara tashi, tayi saurin saukowa daga gadon tana kallon d'an karamin agogon dake gefe. "Ya Salam!" Ta furta tana mikewa da sauri, goma ce zatayi. A hankali ba tare da tayi wani motsi sosai da zai tashe shi ba ta bar dakin. Kitchen ta nufa duk da har yanzu bata wani jin karfin jikin ta amma zata iya yi musu simple breakfast, ko fried yam and egg sauce ko tea da toasted bread ko dai wani abun. Duddubawa tayi taga abinda ya kamata tayi tayi saurin had'a komai ta gama ta ajiye anan tsakiyar falon ta koma ta dauki hijabin ta, ta saka ta nufi wajen su Maman Yara, a zaune ta tadda su da alama sun jima da tashi, ta russuna ta gaishe su suka amsa cikin girmamawa kamar ko yaushe, ta ajiye kayan a gefe "Ba dai girki kikayi ba?" Maman Yara tayi maganar tana zaro ido "Uhum..." Tayi murmushi bata ce komai ba "Kayya, ke da ba lafiya ce dake ba, ai da bakiyi wahala ba, mu nan kingan mu Yarima ya kawo mana kayan shayi ga flask dinmu da biredi tuni mun sha ma." "Babu komai." Tace tana mikewa "Akwai abinda za'a yi miki ne?" Aminatu tayi maganar tana tashi, girgiza kai amrahn tayi da sauri tana tuno abinda Sultan ya fad'a mata akan matar da matsayin ta a wajen Safwan, "Babu abinda za'a yi Umma, nagode." "A'ah ko shara ce, ga kwanukan da aka bata jiya da yau duk sai na wanke ai." "Allah da kin barshi sai na wanke." "Ko alama, ba zaki wanke ba, akan wanne dalili? Menene amfanin mu toh mu?" Tayi maganar tana kallon Maman Yara "Gaskiya." Tace "Karki damu kuje kinji 'yata?" "Toh." Tace ta fita aminatun tabi bayan ta, tare suka shiga falon ta shiga gyarawa duk da babu komai na datti, ta gama duk da kusan tare ma sukayi da amrahn duk da hanatan da take dan ita nauyin matar take ji sosai, kitchen ta shiga ta wanke kayan tas ta gyara kitchen din komai ya fito neat, sannan ta koma wajen su. Dakin ta, ta koma ta tura a hankali, a zaune ta same shi yayi wanka ya saka kaya yana kokarin saka links a hannun sa. "My wife." "Har ka tashi?" "Shine kika k'i tashi na ko? Kika saka na makara." "Na zata ba da wuri zaka fita ba ai." "Kin ga fa a yadda naso tara na bar gidan nan, amma ji har sha daya d wani abu, Allah Allah ni bazan yarda ba." Dariya ta saka ganin yadda yakeyi, shima yayi dariyar ya taso ya riko ta. "Dariya ko?" "A ah da gaske ba dariya nake ba." "Toh mene? Umm?" "Kawai kawai, umm umm bari nayi wanka." Da sauri ya sake ta ya matsa baya "What! Yan yan yan yan, wannan amaryar tawa wace kala ce?" Kunya taji tayi saurin cewa "Ai dazu fa nayi shine yanzu zan sakeyi." "Kai anya? Wannan Amaryar tawa kuwa anya? Anya?" Kin magana tayi ta wuce toilet din da sauri ta manta ko towel bata dauka ba. Gefen gadon ya koma ya zauna yana kunshe dariyar sa, he can't wait ayi diramar da za'a yi idan ta tashi fitowa. Yana nan zaune, wayar sa a hannun sa yana faman dannawa lokaci lokaci yana kallon kofar toilet din, knocking tayi ya tashi tana ajiye wayar sannan ya nannade hannun rigar sa, ya tsaya a kofar yana rike kugunsa. "Ya akayi?" "Please towel zaka bani da hijab dina." "A nawa?" "Na'am?" "Nace a nawa? Kinsan ba'a aikin banza haka nan." "Pleaseeeee." "Pleaseeeee nima..." Ya kwaikwayi muryar ta "Please, please please." Dauko mata towel din yayi, ya tsaya a kofar yace "Gashi." Hannu ta zuro zata karba ya dauke, ya sake cewa "Gashi." Ta kuma miko hannu ya sake daukewa yana dariya "Bari na shigo na baki." Da sauri ta rufe kofar ta murza key, ya kwashe da dariya sosai "Allah ke matsoraciya ce ta gaske, bud'e ki karba kiyi sauri I'm hungry." Budewa tayi ya mika mata, yayi kamar ya bar wajen, maimakon ya bar wajen sai ya hard'e hannayen sa a kirji ya jingina da jikin mirron dakin saitin toilet din, da karfin ta, ta fito a tunanin ta baya dakin, turus tayi ganin mutum a tsaye, tayi kamar ta koma gashi babu damar komawar, kamar munafuka haka ta wuce shi sum sum ta bud'e wardrobe ta dauko kayan da zata saka, ta sake zuwa zata wuce shi ta koma toilet ya sha gaban ta, "Lemme help you." Ya mika hannu ya karbi kayan, da sauri tasa hannu zata karba ya daga sama "Don't be stubborn, taimakawa kawai zan." Kafadarta ya kama ya zaunar da ita a gaban mirron, ya bud'e mata man ya ajiye mata a gabanta, yana kallon yanayin fuskarta ta cikin mudubin kamar kace k'yet ta fita da gudu, murmushi yayi a ransa ya raya _"Akwai lokaci."_ Rankwafowa yayi saitin kunnen ta, "Mrs Muhammad Sultan ba dai tsoro ba, anyways za'a yi wani akai, yanzu dai ki shirya a nutse ina jiran ki a falo, kafin ki gama bari naje mu gaisa da su Maman Yara." Juyawa yayi ya fita, ta sauke ajiyar zuciya tana kankame jikin ta, abubuwa da yawa suka saka take son Sultan, ciki har da wannan bangaren nasa, he's so caring, idan ka ganshi a haka kamar bashi ba, amma idan yana wani abun hmm. Sai kuma wani gefen na zuciyar ta ya tunasar da ita _"Kiyi addu'a Allah yasa ya dore a haka."_ "In sha Allah." Ta furta a fili sannan ta shiga shiryawar a nutse kamar yadda yace din tana yi tana blushing ita kad'ai. Ko da ta fito har ya bud'e breakfast din,ya had'a musu tea tana zama sukayi bismillah suka soma ci, har suka gama babu wanda yayi magana sai kallon ta kawai da Sultan din yake ta faman yi yana murmushi. Mikewa yayi, yayi hamdala yace "Zan fita, take care of yourself, zan iya dawowa late, idan akwai wani abu just give me a call." "Ok a dawo lafiya." "Allah yasa." Zata mike yace ta zauna ta karasa breakfast din, hannu ta daga masa alamar bye bye ya fice ita kuma ta karasa cin abincin ta tattare wajen ta gyara ta zauna ta kunna tv.    ***Yinin ranar be zauna ba sam ya kira Gimbiya sun yi magana ya kara kwantar mata da hankali sosai, tace masa Maimartaba ma ya motsa har yayi magana duk da ba'a ji me yace ba Daga nan yayi asibiti daga asibiti ya wuce wajen da Madaki yake tsare inda yake samun labarin ashe Madakin bayan abubuwan da yayi,yana cikin manyan masu supplying bullets da ake amfani dasu wajen kai hare-haren dake damun kasar nan, yayi mamaki sosai yadda wai ace musulmi akan abun duniya xai iya salwantar da rayuwar wasu mutane da basu ji ba,basu gani ba. Dole case din ya sake zafi sosai sai ya zama kamar ma sun ajiye case din kidnapping Amrah da yayi an shiga wannan babban case din. La'asar likis ya gama ya nufi gidan su, ya samu Daddy a harabar gidan yana zaune yayi nisa a tunani, wanda sam be ji sallamar Sultan din ba sai da ya zauna a gefen sa. "Sultan kaine." "Nine Daddy, barka da gida ina wuni?" "Lafiya lou Sultan." "Kuna lafiya? Ya jikin Amrah?" "Da sauki Alhamdulillah." "Masha Allah, Allah ya kara sauki." "Amin ya Allah." "Safwan ma jiki yayi kyau, sai karashe kawai nace dai kar su sallame shi saboda ciwon nan." "Ah jiki yayi kyau, wa ya dauka ma zai rayu?" "Haka ne, Allah ya kara sauki." "Amin ya Allah, Allah yayi muku albarka." "Naje wajen Madaki dazu, abubuwan dai babu dad'i, suna kan bincike dai har yanzu." "Allah ya rufa asiri, ya bada sa'a." Kawai Daddy yace yana girgiza kansa.  Maganar tafiyar su yayi ma Daddy yayi musu addu'a sannan yayi sallama ya tafi. Maimakon ya wuce gida sai ya tsaya wajen Mubarak sukayi magana sosai sannan ya tafi. Tun da ya tafi babu abinda tayi sai kallo da danna waya, sai bayan da tayi sallar la'asar ne ta tashi ta dora girki, hadadden girki irin wanda tasan Sultan din naso, dama ita a wannan bangaren ba baya bace. Cikin kwarewa tayi komai ta kammala a daidai lokacin da ya dace,ita din mutum ce me kazar kazar musamman a wajen girki da aikin gida saboda sune abubuwan da tafi so fiye da komai   Hannun ta ta wanke a gaban sink ta sa dan karamin towel ta tsane su tana sake duba komai, mutum ce ita me matukar tsafta da kyankyami, hakan yasa take aiwatar da komai cikin tsantsani da takantsantsan had'e da zallar kwarewa. A tsakiyar falon yanzu ma ta jera komai dan ta lura kamar yafi sakewa a kasan fiye da saman dining din. Sai data sake kallon komai ta tabbatar yayi, tayi murmushi ta yi saurin fad'awa tayi wanka a gurguje ganin lokacin ya ja. Light make-up tayi mara hayaniya ta saka wasu kayanta na cikin lefe riga da skirt ne masu kama da yan kanti, ta gyara kanta ta saka turaren gashi me dadin kamshi, sannan tabi ko ina da khumra da turarurruka masu sanyin kamshi. Sai data gama komai ta zauna sannan taji shigowar sa, yau babu wani tunani ta fita da sauri ta bud'e kofar, ta gama jira ya shigo da motar ya rufe gidan sannan ta fita ta karasa kafin ya karaso suka hadu a hanya, "Tubrakallah!" Yace yana murmushi "Welcome home." "Thanks dear." Hugging dinta yayi suka dunguma suka shiga ciki, duk yadda take sunnewa sai da ya saka ta saki jikinta dashi fiye da dazu, suka ci abincin yana ta santi sannan yace zai wanka, tashi tayi ta shiga ciki domin hada masa ruwan wankan sai gashi ya shigo daure da towel a kugun sa, ya saka kafa ya tura kofar toilet din ta rufe ya murda key yana kashe mata ido "Let's bath." Yace yana matsawa kusa da ita, a matukar tsorace take tayi saurin cewa "Wallahi nayi, ban ma dade dayi ba." "Na sani, na gani ma ai, kawai karawa zakiyi." "Wayyo Allah, ni wallahi nayi wanka." "Bari muga." Ya matso ta sosai, ya saka hannun sa ya zagaye waist dinta, ya dora fuskar sa a saman kafadarta "You look cute idan kina jin tsoro, ba wani abu fa nace ba, just wanka, ke kamar wata yar garin chan." Shiru tayi bata tanka ba, dan tasan tunda yayi niyyar sai yayi, sai kawai ta rufe idon ta, tana jin shi yana kidan sa da rawarsa shi kad'ai. Daren ranar ya sake zama memorable a wajen sa, kusan ma fiye da na farkon amma banda wajen Amrah, ga yadda garin ya saki babu zafi sai iska dake kad'awa me dadin gaske. Jawo tayi gaba daya jikin sa yayi hugging nata so tight kamar wani zai kwace ta. Da haka barci me karfi ya kwashe su *** Ana gobe zasu tafi, ya kaita gida tun safe, ya wuce asibiti, yaji dadin ganin jikin Safwan ya sake yi, suka dade suna hira dan a chan ya cinye fiye da rabin lokacin, daga nan suka fita tare da Adnan suka siyo abubuwa sannan suka wuce gida. Tare suka shiga gidan da Adnan, suna zaune da umma suna hira suka yi sallama suka shiga, sai ga Sultan ya k'asa daga kai ya kalli Umma, yayi ta sunne kai Afrah da Adnan na tsokanar sa, be kula su ba, sai umma ce ta hanasu sannan ta tashi ta basu waje, abinci aka kawo musu suka ci, sannan suka tafi inda suka wuce gidan Hajiya bayan sun jira Abba yazo sun masa sallama. Babu wani karba da Hajiyan tayi wa Sultan din, dan har yanzu ba wai ta huce bane, ba kuma ta gamsu da Sultan din ba kamar wanda shine ya zaba wa kansa rayuwar a haka. Basu wani dad'e ba sukayi mata sallama suka tafi, suna zuwa karasa hada abinda zasu hada kawai sukayi suka kwanta saboda su tashi da wuri. ***Jirgin karfe sha daya na safe zasu hau, saboda haka kafin lokacin sun gama shirya komai, Adnan da zai kaisu airport shida Afrah tuni sunzo, har da Umaimah da Mah-Mah da tun jiya dama ita a asibiti yayi mata sallamar sa, sai gata tare dasu Adnan din babu wanda yayi tunani a cikin su. Basu wani bata lokaci ba suka wuce airport din, suna zuwa basu dade sosai ba aka kirasu, sukayi sallama da kowa idon umàima akan Sultan yana sallama da mutane, kuka ne taji yazo mata tayi saurin maida su tana karfafa kanta, tafi karfin haka tunda ta riga ta gama shirya abinda kawai zatayi dan ba zata zauna son sa ya kashe ta a banza ba, shi yana chan yana watayawar sa, taso da ita akayi tafiyar nan Amma babu komai rai dai. ***Manage manage. Yan tafiya Canada su o'o da o'o ina fatan kun gama had'a jaka ko?😂😭😭🔆🔆Abinda Ke Cikin Zuciya Page 49 ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE!!! ***Hannun ta ya kama ganin yadda idon ta ya cicciko, ya mintsine ta kad'an tayi saurin kallon sa, ya girgiza mata kai yana murmushi.   Har suka gama duk abinda ya kamata su yi hannun sa na sarke a cikin nata, ta rasa dalilin da yasa yake son rike hannun ta ko da yaushe, ko hakan na cikin abinda yake so ne? Bata sani ba. Sai da suka dangana da wajen zaman su a cikin jirgin sannan ya sake ta, ta zauna shima ya zauna kusa da ita, ya cije bakin sa kad'an a lokacin da yayi tunanin halin da Maimartaba yake ciki, idan ya tuna sai yaji kaso me yawa na murnar da yake ta ragu, musamman da yake jin kamar wannan din shine ganin sa dasu na farko. Tana lura dashi yadda yanayin sa ya chanja, duk sai taji babu dad'i, tasan kuma abinda yake damun sa duk kuwa da yadda yake kokarin daurewa, fuskarsa kad'ai ta isa ta fallasa asirin zuciyar sa, amma karfin zuciya irin tasa, ta gaza nuna gajiyawa ko kuma sarewa akan abubuwan da suka faru dashi a dan kankanin lokaci, sai ma kokari da yake wajen ganin ya faranta wa duk wanda yake tare dashi. Tasan da gaske yana cike da damuwa, amma bata san ta yadda zata fara taimaka masan ba, rufe idon ta tayi, ta jingina da saman kujerar tana sauke ajiyar zuciya.    Tayi nisa a tunani har bata san sanda akayi sanarwar jirgi zai tashi ba, jin sa kawai tayi daf da ita, yana kokarin daura mata belt din, bata yi motsi ba har ya gama, ta bud'e idon ta daidai lokacin da yake kokarin daga kansa, idonta ya hadu cikin nasa, wanda taga ya sake chanja kala sosai. "Ya Sultan...!!" "In Sha Allah komai zai dawo daidai." "In sha Allah." Ya amsa a hankali yana hasaso yadda koman zai dawo daidai, yadda rayuwar sa da ta Safwan zata yi juyi zuwa wani bigire na daban, bigiren da basu taba tunani ko hasashen kasancewa a ciki ba, a yanzu yafi tausayin Safwan a kansa, yafi tausayin Muhammad a kansu baki daya, dan kusan shi akafi cuta duk ciki, babu wani isheshen ilimi sai wahalar rayuwa, ta wannan bangaren zai iya cewa su ba karamin gata Allah yayi musu ba, dan da sun taso cikin Masarautar ba lallai su samu ilimin kamar haka ba gaba daya zasu kudundune kansu ne a sha'anin sarauta.     Tafiyar 12hours da yan mintuna ta kai su, kasancewar dukkan su ba bakin k'asar bane yasa kai tsaye suka san abinda ya kamata su yi. Hotel din da Sultan yayi musu booking tun a gida suka wuce kai tsaye, nan yake so su fara sauka kafin su nufi asibitin duk da be riga ya kira Gimbiya ya sanar mata da zuwan nasu ba.    Sai da suka fara wanka suka gabatar da sallolin da suka tsere musu sannan yayi musu ordering abincin cikin hotel din suka ci. Suna gama ci ya mik'e, yace mata zai je ya dawo, kamar tace zata bishi sai kuma ta fasa, ta kwanta tana jin babu dad'i.    Yana fita ya kira wayar gimbiya, bata daga ba da farko, ya riga yasan asibitin da Maimartaban yake zuwa sai kawai ya nufi chan din. Kafin ya karasa ta kira shi back, ya daga yace mata ya kusa karasowa asibitin, murna ta hau yi ta fad'a masa inda suke idan ya shigo sannan ta kashe. Matsawa tayi gaban gadon Maimartaban daya farka tun dazu har ma sukayi magana inda yayi mata maganar da ta yi matukar bata mamaki, maganar da ta dau lokaci me tsawo tana bukatar ji daga bakin shi amma bata taba ji ba, tun zuwan su k'asar. _"Gida zamu koma gimbiya, zaman mu ya kare anan."_ murmushi tayi data tuna maganar da ya gama yi mata daxu dazun nan, maganar da ta saka ta cikin matukar farin ciki mara misaltuwa, murnar ta, ta kasa boyuwa, ta kuma yi mamakin chanjawar Maimartaban bayan farkawarsa. Abinda ya kara bata mamaki dashi shine yadda gaba daya ya chanja, ya dawo ainihin Maimartabar sa, wanda ta sani a shekarun baya a cikin Masarautar Saji, ba Maimartaban da ta sani a Canada bane, kwayar idon sa kawai ta kalla ta yarda da cewa mulki ba karya gane. Tun bayan yayi mata maganar be sake cewa komai ba, yayi shiru kamar bashi ba. "Sultan yana hanya." Tace tana tsayawa ta wajen kafarsa, be dago ba kwata-kwata kamar yadda tayi tunani, sai kallon ta da yayi, ya daga mata kai alamar toh, jiki a sanyaye ta koma ta zauna tana mamakin abinda zai sauya mijin nata haka farar daya.    Tsayawa yayi a kofar dakin, ya kurawa dakin ido, kamar an sassara kafarsa haka yaji, ya kasa daga ta, ya ja ta zuwa idan zuciyar sa ke tura shi, ya jima a hakan be san yaya zasu karbe shi ba, be kuma san takamaimai me zai ce musu ba kai tsaye. _"Nine danku Sultan? Ko me?"_ Girgiza kai yayi, yayi sallama a hankali ya tura kofar, tun kafin kofar ta gama budewa gimbiya taga Maimartaba ya yinkura zai tashi, fuskar sa dauke da wani yanayi me wuyar fassarawa, da sauri ta karasa tayi kokarin taimaka masa amma sai ya dakatar da ita, ya zauna sosai ta saka masa pillow ta saman kansa. "Sultan!" Ta kira sunan sa ganin ya kasa karasa shigowa "Shigo ciki mana, kamar bako?" Da hannu Maimartaba ya yafito shi, ya tafi kamar wanda ake ingizawa, ya isa gabansa, ya kasa daga kai ya kalle shi, yadda kwarjinin sa ya cika wajen ya kara taimakawa sosai wajen yadda Sultan din ya kasa sakewa.    "Babah...!" "Zo Muhammad." Matsawa yayi sosai, Maimartaba ya kamo hannun sa zai rik'e, yayi saurin sakin hannun ya kurawa hannun ido "Muhammad ina ka samu zoben nan?" Kasa Sultan yayi da kansa, yaji kwalla na sake cikowa a idon sa, me zai ce masa? "Dan Allah ka amsa min Muhammad, ina ka samu zoben nan, har ya kasance a hannun ka?" Daga masa kai Sultan yayi ya kasa magana, hawayen da yake rikewa,hawayen farin ciki suka shiga gangaro masa. "Bayan na koma Nigeria, na tafi da alkawarin yin abu biyu, dawo muku da farin cikin ku da kuka rasa wanda nake jin kamar wani hakki ne akai na wanda ya zama dole na cika shi, sai kuma neman iyayena, Wanda wani dalili me karfi ya saka ni bibiyar waye ni? Bansan cewa zaren zai jani ya had'e ni a waje daya bane... " Abinda ya faru tun tafiyar sa har haduwar su da Maman Yara ya sanar masa, ya dora "Tace nace maka Azizah ce" Karkarwa jikin Maimartaba yake, gimbiya kuma da ta dago abubuwa da yawa a zancen ta durkushe a wajen kukan ta na fita a hankali "Aziza tace maka Sultan? Itace ta kula da kai tun kana karami, har zuwa lokacin da gidan daka taso suka dauke ka? Sunan ta Aziza Sultan?" "Sunan ta kenan, tace ina fad'a maka zaka gane." "Alhamdulillah ya Allah, alhamdulillah ya Allah." Ya ringa maimaitawa ba kakkautawa, hannun sa dake matukar rawa yasa a saman kan Sultan din yace "Jini ba karya bane Muhammad ,tun da na ganka naji ina sonka, ashe kai din jinina ce, jini na da gimbiya, kai din gudan jinin mu ne da muka fi so fiye da komai a duniya." "Taimaka min na sakko Sultan, ko yanzu Allah ya dau raina Alhamdulillah, zan wanke kaina a wajen mahaifiyar ka, duk da nasan hakan be isa wanke kan nawa ba, amma zan kwatanta Muhammad." Taimaka masa Sulthan yayi ya sakko, ya matso gaban ta, ya daga ta tsaye ya kama hannun Sultan ya saka cikin nata _"Ina cikin jiki na?"_ NoWannan tambayar ita ce tambayar da kika fi yi min fiye da kowacce irin magana ma, yau zan amsa miki Maryama "Ga d'anmu nan, wanda zalunci ya saka aka so salwantar mana da rayuwar sa, da yake Allah yayi zai taka k'asa, sanadiyar rayuwar sa  mutane da yawa zasu amfana dashi yasa Allah ya raya mana shi,ni da kaina na dauke shi na bawa Azizah shi, na kuma umarce ta da tayi nisa da mu, nayi imani idan Allah yayi akwai sauran rayuwar sa a gaba zai dawo da kafarsa, a lokacin da duk wani me sharri ba zai iya aikata masa komai ba." Bata iya magana ba, tayi saurin rungume shi kukan ta na karuwa sosai, ita kad'ai tasan me take ji a yau, wanne irin hali take ciki, ashe dama zata ga wannan ranar? Amma me yasa Maimartaba be taba fada mata cewa yana raye ba, ba da shi yayi, yayi mata shiru ya bar ta, tana shan wahala tsawon lokaci. "Kar kiyi tunanin da gayya na raba ki da danki Maryama, banyi hakan dan na kuntata miki ba, sai dan na kare rayuwar mutane da yawa da hakan zata shafa." "Da ka fad'a min, da komai be baci haka ba, da ka fad'a min da mun yi tunanin abinda ya kamata muyi tare." "Idan har muna da lokacin hakan kenan? Idan har wanda suke nufin mu da sharrin zasu bamu wannan damar ko?" "Su waye? Sun isa suyi mana abinda Allah be mana ba?" Shiru yayi, yanzu ba wannan lokacin bane, da sauran lokaci, da saura. Jin yaki cewa komai ya saka Gimbiya jan hannun Sultan, suka fita daga dakin, girgiza kai Maimartaba yayi wani irin dadi na ratsa shi, yasan idan har ba jin komai tayi ba, ba zata taba fuskantar shi ba, shiyasa ba zai ce mata komai ba, sai ranar da komai zai bayyana, ba tare da wani tunanin ko hakan ne ko ba haka bane, a ranar yasan zuciyar ta zata sake karyewa, amma abun zai zo da sauki. Baya jin wani sauran ciwo, sai wani karfi ma da yaji ya sake zuwar masa, karfin tunkarar azzaluman mutane, maha'inta masu fuska biyu. Chan wajen wasu kujeru ta ja shi, suka zauna fuskarta ta gaza boye farincikin da take ciki, sunan sa kawai take kira sai kuma tayi shiru ta kasa cewa komai, shi kansa jin sa yake wani daban kamar bashi ba, kamar an chanja shi ne da wani na daban, be taba hasaso wadannan mutanen a matsayin iyayen sa ba. Rayuwar sa ta fara ne daga gidan marayun nan, zuwa tafiya da Daddy yayi dashi inda hakan ya zama sanadin budewar rayuwar sa, har ya zama abinda ya zama har suka ganshi cikin kyakkyawar kama da kyakkyawar tarbiyyar, bashi da kamar Daddy da Mah-Mah dan su din iyaye na nagartattu. Musamman Daddy duk da yasan ko daya cikin shi da Safwan basu da wata alaka dashi amma ya kula da rayuwar su ya inganta musu ita ta yadda kowa zai yi sha'awar su.    Tambayoyi masu yawa gimbiya tayi masa, ya amsa mata yadda yasan zata fahimci komai, yanayin yadda fuskarta ke fad'ad'a da tsantsar farin ciki kad'ai ya ishe shi. Basu san dare yayi sosai ba, har sai da suka ji kiran Maimartaba ta wajen wani ma'aikaci, tashi sukayi suka koma ciki, ya zuba musu Ido da suka shigo yana jin dad'i mara misaltuwa. A tsakiya suka saka Sultan din, suka hana shi yin komai, suka dinga tattalin sa, har yaso mantawa da baiwar Allah dake chan tana jiran dawowar sa. Ko da yace musu zai tafi masauki kin yarda sukayi, Gimbiya ta rikice tana ganin kamar shikenan ya tafi, yayi kokarin fahimtar da ita amma taki sauraren sa, sai ya matsa waje Maimartaba yayi masa magana k'asa k'asa. Shi yayi wa Gimbiya bayani aikuwa ta sake rikicewa tace dole ya je ya tawo mata da Amrah ta ganta, tana so taga matar dan ta. Hakuri ya bata akan gobe da sassafe zasu zo, da k'yar ta yarda duk da haka sai da ta rakashi har waje, ta kuma ta jaddada masa lallai suna sallah su tawo nan, su kuma tattaro kayan su, dan ba zata sake barin su suyi mata nisa ba ***Ruf da ciki tayi bayan ta sha kukan ta, ta koshi, ta rasa dalilin da ya saka ta kukan duk da tasan ya kamata yayi wannan dadewar ba kuma wai tana jin haushin yaje ya dad'e din bane ba, ta rasa kawai dalilin da ya saka taji babu dad'i, ko dan tayi tunanin tare zasu ya kuma yi tafiyar sa ya barta? Tana jin sanda ya saka key ya bud'e kofar, ya shigo da karsasshin sa ya kira sunan ta, rufe idon ta, tayi kamar me bacci, ya hawo gadon da sauri ya juyo ta, ta runtse idonta. Chakulkuli ya shiga yi mata,tayi kokarin shanye wa amma ta kasa resisting, ta bud'e idon ta da sauri tana rik'e hannun sa "Please bana son wannan abun wallahi." "Mesa kikayi kamar kina bacci bayan nasan idon ki biyu?" "Toh ba kaine ba!" "Allah sarki ni bawan Allah, me nayi kuma?" "Ba komai." Tace tana tashi zaune,ta sauka daga gadon, biyo ta yayi, ya riko ta "Tell me, me nayi? Are you angry with me?" "Uhum." "Comman,me nayi?" "Na zata dani zaka je, nasa rai shine kayi tafiyar ka, bayan nima na matsu ya gansu." "Ohh ya Allah, wallahi gani nayi munyi long journey kinga kina bukatar hutu, gashi ba wai wani gama samun sauki kikayi gaba daya ba, shiyasa kawai nace bari naje na barki ki huta, ashe bansan nayi laifi ba." Shiru tayi zuciyar ta na sauka, ta turo baki ta kasa cewa komai sai kunya ma data ji, idon ta ya taba "Ba dai kuka kika zauna kikayi tayi tun tafiya ta ba?" "Ni ban... Ban yi kuka ba." "Idon ki ya fad'a min, kuka kika yi tayi, ya Allah, sai kinje kanki yayi ciwo ko? Ba sai ki fad'a min kice zaki ba, ai bazan ce a ah ba, amma kika zauna kikayi ta kuka? Kuka fa." "I'm Sorry." "Ba zan karba, nayi fushi ma." Ya koma ya zauna, kusa da shi ta zauna tace "Kayi hakuri." "Um um ni bazan ba." "Dan Allah!" "Toh naji, amma karki sake irin haka, ko abu nayi be miki ba, kiyi magana, communication is the key to successful marriage, idan akwai communication gap a tsakanin mu ba zamu ji dadin zaman ba." "Ba zan kara ba." "Good girl, yanzu muje na baki labarin yadda komai ya kasance,I'm super excited, Alhamdulillah ya Allah." Zama sukayi cikin cushion din dake dakin, ya dora kansa a saman cinyar ta, ya fara bata labarin, taji dadin yadda komai ya kasance, ta kuma taya shi murna sosai, shi kansa ya rasa kalar farin cikin da yake ciki, kamar yana yawo a saman gajimare haka yake jin sa. Hannun ta dake yawo a cikin kansa ya saukar masa da kasala, ya rik'e hannun yana tashi "Bacci kike son sani a wayo a wayo." "Auw, bansani ba ai." " Ba wani kina sani,so kike nayi bacci ko? Toh Allah kuwa ba zan ba, yadda garin nan yayi dad'i." "Toh ni bacci zan, bari na kwanta." Ta tashi ta nufi kan gadon, riko ta yayi ta dawo baya, ta kusa fado masa akai, yayi k'asa da idon sa yana mata kallo me cike da ma'anoni. "Biyani labari na." "Labari? Yaushe nace zan biya ka?" "Baki ce ba, amma ai kinsan ba'a aikin banza ko?" "Toh ai ni bani na nema ba, kai ne kace zaka bani." "Still dai zaki biya." "Hum um, wannan ai wayo ne." "Whatever yarinya, sai kin biya." "Bacci ma nake ji, goodnight." "Nima baccin nake ji, let's cuddle." Ya sake jan hannun nata, kansa ta fado wannan karon baki daya, ya zagaye ta da hannayen sa ya rada mata wata magana a kunnenta. Ta rasa yadda akayi Sultan ya fitsare kafarsa, idan suna tare koma mata yake kamar bashi ne wannan abokin su ya Adnan din ba mara magana, duk da itama yace mata miskila amma sai take ganin kamar ya fita, sai yanzu take ganin ashe ba haka yake ba, idan ya zakulo wani zancen rasa ina zata saka kanta take. Yadda baccin yayi masifar dad'i ya saka suka makara, ita ta fara tashi, tayi saurin janye jikinta daga nasa, ta zubawa fuskarsa ido, yadda yake baccin kad'ai ya isa ya tabbatar maka da ya samu peace of mind, a nutse yake fitar da numfashin sa fuskar sa kwance da murmushi, kamar ba me bacci ba, hannu ta kai saman sajen sa ta shafa a hankali. Tashi tayi ta shiga toilet ta had'a ruwa me dumi da wasu kayan wanka hadin su masu kamshi, ta wanke jikinta tas ta fito, har lokacin baccin sa yake peacefully, sai taga kamar ma yafi ko yaushe yi mata kyau, shiryawa tayi tana yi tana kallon sa,har ta gama sannan ta koma ta had'a masa ruwan shima ta fito. Rasa yadda zata tashe shi tayi, da sauri ta tashi wani tunani ya fado, last a gida bayan tayi wankan ta, tayi alwala tazo tashin sa kawai ya jawota jikin sa karshe sai da ya saka ta sake wankan. Fasa tashin sa tayi, ta fara yin sallah sannan taje ta tashe shi, tana ganin yayi yinkurin bude Ido tayi saurin tashi tana dariya. Tashi yayi yana cije baki, yayi mata alamar zai kamata next time ya wuce toilet din dan har lokaci ya fara ja. Breakfast sukayi, suna yi suna hira da juna cikin farin ciki, suka shirya a tare suka saka kayan da suka san ba zasu takura ba, musamman ma ita da wannan ne karo na farko da zasu hadu da surukar ta ta, dole tayi abinda zata so da dan tasan yanzu Sultan bashi da wadda yake so sama da ita. A shirye suka fito gwanin sha'awa, idan ka kalle su sai ka sake kallon su, suka nufi asibitin a ran Sultan yana tunanin yadda zai shigo da maganar Safwan da Muhammad, yana kuma tunanin ya bari idan suka koma tunda yasan ba wani dadewa zasuyi ba, zasu tattara su koma anan ne kuma komai zai bayyana. *** *Masarautar Saji* Komai ya sake lalacewa, irin lalacewar da mutanen Masarautar basu taba gani ko hasashe ba, Yarima Bilal ne yake yadda ya ga dama, babu kuma me tsawatar masa ko ya hana shi, su buzu da mukarraban su sun dukufa aiki amma sun rasa dalilin da yasa komai yake juye musu, duk abinda suka shirya sai sun gama hada komai sai su ga ashe babu abinda yake yi,kamar zasu haukace haka suke, Sarki Bello yafi kowa firgicewa, musamman ranar da ya samu bakuncin wanda be yi tunani ba, zuwan sa da labarin da yazo dashi ya sake saka su dukka a rudani, ya zama kullum basu da aiki sai ganin sun samu wani abu komai kankantar sa, da zai bud'e musu hanya komai kankantar ta, amma kuma babu. Haka suke ta fama basu hakura ba, gashi shi kansa Sarki Bello ba ishashiyar lafiya ya cika ba tun bayan abinda Yariman yayi masa ranar da ya taimakawa SULTAN ya dauki zoben, amma ba ta lafiyar sa yake ba, ta yadda komai zai daidaita ne ya tafi kamar yadda yake shekarun baya. ***Ciwon Ido ne ya matsa ni gaba wallahi, da k'yar nake iya kallon screen din shiyasa kwana biyu abubuwan sai a hankali.Abinda Ke Cikin Zuciya Page 50 ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE!!! *Sunana Nafisa k Abdullahi am a singer, actress.. wakokina are based on siyasa da kuma na sarakuna * https://youtu.be/1VyZ6f1GTWg *(YouTube link)👆🏾* *This is my YouTube channel IN SHAA ALLH! I will be bringing to you my latest films, And musical videos* *NafisaKabdullahi* *Sabuwar ficacciyar jaruma ce data shahara wajen fina finai da kuma wakoki na siyasa, Masarautu da sauran su* *Ina masoya makaranta littafan zafafa? Ku fito ga dama ta samu, Munason a nuna mana k’auna ta hanyar subscribing a sabuwar channel dinnan ta Nafisa mai suna a sama. 👆🏾A kalla a kuma danna kararrawa domin sauraron shirye shiryen ta a duk sanda ta dora..* *Danna kararrawa domin kasancewa da ita da zarar ta dora sabbin shirye shrye.* *DAN ALLAH! Ayi subscribing, Akuma dinga viewing, Inda hali ma ayi comment da sharing zuwa ga wanda basu sani ba...* *Akwai Facebook page dinta mai suna: https://www.facebook.com/preetyfeenat.abdullahi* *Domin karin bayani sai a tuntub’i Nafisa kai tsaye ta number ta: * *08071172003* *kada ku mance ko minene daya danganci wakokin al’adun hausa, Da ire-iren fina-finan mu na hausa, Nafisa zata dinga kawo muku shi a wannan sabuwar channel din nata, Saboda haka MASOYA a temaka aje ayi mata subscribing a kuma dinga kallan abubuwan data dora.*. *** *** *Masarautar Saji* Komai ya sake lalacewa, irin lalacewar da mutanen Masarautar basu taba gani ko hasashe ba, Yarima Bilal ne yake yadda ya ga dama, babu kuma me tsawatar masa ko ya hana shi, su buzu da mukarraban su sun dukufa aiki amma sun rasa dalilin da yasa komai yake juye musu, duk abinda suka shirya sai sun gama hada komai sai su ga ashe babu abinda yake yi,kamar zasu haukace haka suke, Sarki Bello yafi kowa firgicewa, musamman ranar da ya samu bakuncin wanda be yi tunani ba, zuwan sa da labarin da yazo dashi ya sake saka su dukka a rudani, ya zama kullum basu da aiki sai ganin sun samu wani abu komai kankantar sa, da zai bud'e musu hanya komai kankantar ta, amma kuma babu. Haka suke ta fama basu hakura ba, gashi shi kansa Sarki Bello ba ishashiyar laiya ya cika ba tun bayan abinda Yariman yayi masa ranar da ya taimakawa SULTAN ya dauki zoben, amma ba ta lafiyar sa yake ba, ta yadda komai zai daidaita ne ya tafi kamar yadda yake shekarun baya.    Shigowa suke tayi Masarautar da zarar labari ya kai musu, suna da yawan gaske, wasu ma zakayi mamaki idan ka gansu saboda rabon su da Masarautar an dau lokaci me tsawo, sai gasu suna ta shigowa wanda abun yaso bawa mutane mamaki, har suka fara zargin babu lafiya, sannan kuma suka hau kananan zantuttuka musamman wadanda suka san abinda ya faru shekarun baya. Rana guda suka ware a cikin ranakun da suke da muhimmanci a wajen su,aka aikawa duk wanda yake da ruwa da tsaki a harkar, da su hallara a ranar dole. ***Ta kasa zama tana ta zagaye a dakin, motsi kad'an sai ta leka ko zata gano su, yana kallon ta be ce mata komai ba, yasan dama zatayi abinda ma yafi haka, shi kansa misalta irin farin cikin da yake ciki ya isa, ko da likita ma yazo duba shi da safe cewa yayi he's good for discharge saboda yadda ya ganshi akan kafafunsa ba wani alamun ma ya kwanta. Ganin taki nutsuwa ne ya saka shi saka baki ya kirata, ta amsa hankalin ta still yana kofar, "Gimbiya zasu zo fa, kila sun makara ne wajen tashi kinsan sun yi tafiya." "Amma ya kamata ace sunzo tuni, I'm damn worried." "Don't be, zasu zo in Sha Allah." "In shaAllah..." "Assalamu alaikum." Sultan yayi sallama yana turo kofar dakin, yadda fuskar su ta fad'ad'a zuwa tsananin farin ciki zaka gane yadda jin maganar sa kad'ai ta saka su, ya shigo bayan sun amsa Amrah na biye dashi, fuskar ta fayau tana ta kokarin riga shi shiga domin ganin su waye wadannan lucky parents din da suka samu yaya kamar Sultan da Safwan? Ta san dole su din sun yi ta kowanne bangare, bata gama ayyanawa a ranta ba fuskarta ta hasko mata Gimbiya, Babbar mace yar gayu ta karshe, yadda tayi tunanin ta, ta wuce haka nesa ba kusa ba, a dah tana ganin Mah-Mah a jerin hadaddun mata yan kwalisa, amma ganin Gimbiya sai ta shafe Mah-Mah a idonta, hatta skin colour dinta abun kallo ne, koman ta kamar na Sultan sai dai basa kama, yafi dauko kalar fatarta da wasu abubuwan nata. Rik'e ta, tayi ta rungume ta a jikinta tana jin wani irin yanayi na wai itace yau da d'an cikin ta a gaban ta, tare da matar sa kila ma har da rabon baby girl ko boy, bakin ta ya gaza rufuwa ta kuma kasa daina mika godiya ga Allah azza wa zalla,domin shi ne ya amsa mata addu'ar ta a lokacin da ba tayi zato ko tsammani ba. Yadda suka sake da Amrah daga Maimartaban har Gimbiyar ya saka Amrah sakin jikinta dan ta lura su mutane ne masu sanin yakamata , masu matukar kirki da faran faran, yadda Maimartaba yayi ta jan ta da hira yana mata tambayoyi ya saka ta kaunar mutumin ganin babu girman kai ko izza irin ta wasu masu Sarautar, musamman ma shi da yake matsayin Sarki. Babu kalar soyayyar da mutane biyun nan basu nunawa Amrah ba, dan hatta abinci Gimbiya ce tace su zauna ita da SULTAN ta basu, sukayi ta mata dariya Maimartaba yana tsokanar ta, ita dai bata damu ba, so take abinda ta dade tana hasashe ne, bata damu da girman da sukayi ba, ita kallon yara kanana take musu musamman Sultan da take ganin kamar dan babyn ta ne aka dawo mata dashi, so take ta nuna masa soyayyar da tasan yayi lacking duk kuwa da girman sa, shi dai duk ya rasa ina zai saka kansa saboda murna, wai shine yau yake gaban iyayensa suna treating dinsa kamar karamin yaro, iyakar rayuwar sa be taba jin sa haka ba, shi a kullum kallon babba yake baya taba tunanin kansa a irin matsayin, shiyasa yake wa Sultan acting din babban wa saboda baya daukar kansa kamar yadda shi Safwan din yake abubuwa musamman a gaban Mah-Mah, yayi ta sha'awar hakan idan yaga yanayi amma baya taba hasaso kansa irin wannan yanayi, sai gashi yau ya samu kansa a irin yanayi ya kuma ji yadda Safwan din yake ji musamman idan yaga yana wa Mah-Mah shagwaba duk kuwa da girman sa, ashe dai komai girman ka a gaban iyayenka kai din yaro ne karami, suna kuma kallon ka a yaro ne duk sanda kake gaban su. Zaman asibitin dai sai ya zama kamar ba asibiti ba, gashi su akwai tsari ba haka kawai zasu sallami mutum ba, sai da lokacin da suka diba ya cika sannan suka zo suka sake duba shi sosai, suka tabbatar da jinin nasa ya dawo normal da kuwa yayi mugun hawa har sunji tsoron kar ya samu matsala, sai da suka tabbatar da komai normal sannan suka yi discharging dinsu, suka tattara sukayi gida inda Sultan ya wuce domin dauko musu kayan su daga hotel din. Wani irin shiri Gimbiya ta saka hadimanta suka hau yi, daki guda aka ware aka gyara shi gyara na gaske, aka kawata shi da kayan kawa. Anan aka sauke Amrah a ciki, kafin ma Sultan ya dawo ta tare a ciki, yana zuwa Gimbiya ta saka masa full stop tun a kofa, tasa aka karbi kayan aka shiga dasu sannan tace ya wuce bangaren Maimartaba a chan ne masaukin sa yake, ya hangame baki zai yi magana ta tura shi ta jawo kofar tana dariya "Yata tana bukatar hutu." "Ni kuma fa?" Yayi managar yana langabe mata kai, dungure masa kai tayi, ya taba gurin yana sosawa. "Wash kaina." "Wuce muje." Ta tusa shi gaba har wajen Maimartaba, yana kishingid'e fruits a gaban sa sai dai ko kallon su be ba, ya yi zurfi a tunani, yana ganin su ya tashi zaune da sauri yana fad'ad'a fara'ar fuskar sa. "Allah Nagode maka da ka dawo min da farin cikin gimbiya ta." Dariya suka saka a tare, "Ga danka nan na kawo maka,a barni na 'yata." "Auw yar haka ce?" "Eh." "Shikenan zo Muhammad, rabu dasu idan tayi wari ma zamuji ai ko me Ake kullawa." "Ba zatayi ba kuwa." Juyawa tayi ta koma, Sultan ya zauna daga gefen Maimartaba, ya shiga matsa masa kafa a hankali. "Muhammad ya rayuwa?" "Alhamdulillah Baba." "Kaga yadda Allah yake al'amuran sa ko?" "Wallahi Babah, abubuwan sun zo a wani yanayi." "Tsarin Allah kenan, wanda yafi na mutum, shekara nawa muna faman jiran wannan ranar, kuma kazo ba tare da sanin mu ba, ka tafi duk bamu san alakar da Ke tsakanin mu ba, idan ba Allah ba,waye ya isa? Shine yake fitar da rayayye daga cikin matacce, ya kuma fitar da matacce daga cikin rayayye, yanzu buri na daya ya rage Muhammad, shine ganin Aminatu." "Idan na ganta bani da sauran damuwa Muhammad, an cutar da baiwar Allah an chanja mata rayuwa da komai, bamu kyauta ba sam Muhammad, bamu kyauta ba, shiyasa Allah ya saka kayi nisa damu nisan da har muka cire rai da kai." "Na san inda take Babah." Da sauri yace "Ka san inda Aminatu Muhammad?" "Na sani, suna tare da Maman Yara a gidana." "Maman Yara?" "Atika." "Ta yaya suka hadu da Atika?" "A Masarauta." Sai ya bashi labarin komai da yadda sukayi da Madaki da zuwan sa kurkukun da komai da ya samu ta hannun Maman Yara, "Sai yan biyu da suma suna nan a raye, Safiyya da ta tafi dasu ana tunanin tana Masarautar." "Da gaske kake Muhammad? Da gaske suna da rai?" "Suna raye..." "Tafiya Nigeria ta zama dole a garemu Muhammad, dole mu koma inda muka fito,nasan mutane da yawa zasu ji mamakin dawowar mu, musamman idan muka dirar musu ta inda basuyi zato ba." Sai ya daga hannun sa Sama "Ya Allah ina kara Godiya a bisa ni'imomin da kayi min, Alhamdulillah ya Allah." "Wannan labarin sai mun koma, yadda Gimbiya zata sake shiga farin ciki sosai, yanzu idan aka sanar mata zata daga hankalin ta ne akan tafiyar, ni kuma nafi son muyi komai a tsakane." "Hakan ma yayi." "Allah yayi maka albarka Muhammad, hakika Masarautar Saji tayi sarki irin wanda bata taba yi ba, dama Alhaji yana da rai yaga yadda burin sa zai cika." "Sarki Babah?" "Tabbas Muhammad, in Sha Allah da hannu na zan nada maka rawanin ka, kai ne ka chanchanta ka dace, ni yanzu nayi girma bana bukatar hayaniyar sarauta, zan huta a gida kai kuma ka kula da komai." Shiru Sultan yayi yana jin yadda maganar tayi masa nauyi, Sarki fa? Sultan na gidan marayu, wanda su Mah-Mah da Daddy suka tausaya wa rayuwar sa suka tsamo shi suka chanja masa rayuwa, shine yau ake masa albishir da zai zama sarki, me zai ce ne wai? Yana da bakin magana ma kuwa? Duk maganar da suka cigaba da yi akan sarauta ne, da yadda abubuwan suke wanda be taba tunanin hakan suke ba, sun dau lokaci suna hirar dan har abinci tare suka ci, Safwan ya kirashi, ya daga suka dade suna magana daga karshe sukayi sallama. Sultan cike yake da zulumin yadda Daddy zasu kwashe da Mah-Mah, sannan yana tsoron har Safwan ya shiga tashin hankali, abubuwan suka hadu sukayi masa yawa shi yasa ma kai tsaye be gaya ma Maimartaba su waye Yan biyun ba ya bari sai sun koma tunda har ma an fara shirye shiryen tafiyar. Tana kwance a dakin da yafi mata kama da aljannar duniya, ta kudundune a cikin bargo saboda sanyin da take ji, tafiyar Gimbiya kenan daga wajen ta sun dade suna hira itace ma gyara mata kai da kanta suka kuma ci abinci tare. Ita ta kwanta ita kuma ta fita domin kawo mata wata madara daga dakin ta. Kansa ya fara lekowa ya tabbatar bata ciki, dan idan yazo kora shi Gimbiyar keyi wadda a yanzu Amrah ta saka mata suna Ummi. Da karfin sa ya shigo ganin bata nan, ya lallaba ya shiga bargon, da sauri ta zabura zata mike, ya saka dukkan hannun sa ya danne ta, "Wa na kama?" Yayi maganar yana bata fuska. "Ka daga ni." "Anki, wai ni kike ma wannan shan kamshin don kinzo wajen Ummi ko?" "Ni fa ba shan kamshi nake ma ba." "Menene Toh? Kinsan yadda na shirya ma zuwa kasar nan kuwa?" "Please ka daga ni wallahi kayi nauyi." "Anki din, sai Ummi tazo." "Ummin?" Ta rufe baki cike da mamaki "Eh ai ba kunyar ta nake ji ba." "Tab lallai, babu ruwana wallahi." "Ni da ruwana, an maida mutum marayan karfi da yaji." "La'ila!" Tayi maganar tana kunshe dariyar ta, kicin-kicin yayi da fuska, zai yi magana yaji tahowar Ummin tana maganar da wata mai aikinta. A zabure ya mike, ya sakko ya tsaya daga chan gefe kamar munafiki, turo kofar tayi hannun ta dauke da madara me zafi, kallon sa tayi, yadda yayi firit da fuska , dariya ya bata ta shiga yi tana matsawa wajen Amrah da take tayata a hankali tana satar kallon me bakin maganar kamar an saka abu an rufe bakin kuma, har wata nutsuwa ya kara a gaban Ummin yana sunne kai. "Zo Sultan." Ta yafito shi bayan ta zauna a gefen gadon, yazo ya zauna ta dora kansa a saman kafadarta, ta rufe idon ta kwalla na taruwa sosai a idon ta. Sun dade a haka, sannan ta fita ta barsu a dakin tana jin wani iri, tunanin yan uwanta da garin su da komai nata ya dawo mata sabo fil. Ummi na fita ya janye bargon, ta shiga ja yana ja "Yarinya kin zata ke kad'ai take so?" Bata ce komai ba don taga take taken sa.. . ***Pls wadda tasan ingantaccen maganin ciwon ido irin wanda mura ke sawa, da mura irin me kama makogaro da saka kaikayin makogoron pls tayi min magana pc. Note banda maganin asibiti pls 😭😭😭 irin remedies haka na gida pls nagodeAbinda Ke Cikin Zuciya Page 51 ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE!!! Tana kwance a dakin da yafi mata kama da aljannar duniya, ta kudundune a cikin bargo saboda sanyin da take ji, tafiyar Gimbiya kenan daga wajen ta sun dade suna hira itace ma gyara mata kai da kanta suka kuma ci abinci tare. Ita ta kwanta ita kuma ta fita domin kawo mata wata madara daga dakin ta.    Kansa ya fara lekowa ya tabbatar bata ciki, dan idan yazo kora shi Gimbiyar keyi wadda a yanzu Amrah ta saka mata suna Ummi.   Da karfin sa ya shigo ganin bata nan, ya lallaba ya shiga bargon, da sauri ta zabura zata mike, ya saka dukkan hannun sa ya danne ta, "Wa na kama?" Yayi maganar yana bata fuska. "Ka daga ni." "Anki, wai ni kike ma wannan shan kamshin don kinzo wajen Ummi ko?" "Ni fa ba shan kamshi nake ma ba." "Menene Toh? Kinsan yadda na shirya ma zuwa kasar nan kuwa?" "Please ka daga ni wallahi kayi nauyi." "Anki din, sai Ummi tazo." "Ummin?" Ta rufe baki cike da mamaki "Eh ai ba kunyar ta nake ji ba." "Tab lallai, babu ruwana wallahi." "Ni da ruwana, an maida mutum marayan karfi da yaji." "La'ila!" Tayi maganar tana kunshe dariyar ta, kicin-kicin yayi da fuska, zai yi magana yaji tahowar Ummin tana maganar da wata mai aikinta. A zabure ya mike, ya sakko ya tsaya daga chan gefe kamar munafiki, turo kofar tayi hannun ta dauke da madara me zafi, kallon sa tayi, yadda yayi firit da fuska , dariya ya bata ta shiga yi tana matsawa wajen Amrah da take tayata a hankali tana satar kallon me bakin maganar kamar an saka abu an rufe bakin kuma, har wata nutsuwa ya kara a gaban Ummin yana sunne kai. "Zo Sultan." Ta yafito shi bayan ta zauna a gefen gadon, yazo ya zauna ta dora kansa a saman kafadarta, ta rufe idon ta kwalla na taruwa sosai a idon ta.   Sun dade a haka, sannan ta fita ta barsu a dakin tana jin wani iri, tunanin yan uwanta da garin su da komai nata ya dawo mata sabo fil. Ummi na fita ya janye bargon, ta shiga ja yana ja "Yarinya kin zata ke kad'ai take so?" Bata ce komai ba don taga take taken sa, ta mike zata bar dakin ya saka mata kafa ta fado kansa, "Ouch." Tace tana mulmula goshin ta "Raguwa, kin gama shan kamshin?" "Um um." "Oya fad'a min, me Ummi take baki? Mene wannan?" Ya nuna cup din madarar "Madara ce." "And?" "Ba komai, just milk." "Ban yarda ba, lemme check." Zaunar da ita yayi, ya dauki cup din ya kai bakin sa ya sha, ya lumshe idon sa gardin madarar na ratsa shi. "No wonder kika makale anan, ashe kayan dadi kike kwasa kika bar ni ina chan ina chan ina shan wuya." "Wuya?" "Eh mana, can't you see how badly I'm missing you? Ban taba ganin ango iri na ba, Allah sarki ni." Dariya tayi, ta karbe madarar ganin sai sha yake, ta sha dan ba karamin dadi madarar tayi mata ba. Tallafe kansa yayi da hannun sa, ya lula a duniyar tunanin maganganun da Maimartaba yayi masa dazu, har ta gama ta tashi ta wanko bakin ta, ta dawo be sani ba, sai da ta zauna sosai ajikin sa sannan ya dube ta, yayi mata murmushi me kyau, ya kwanta akan bayan sa, ta dora kanta a saman chest dinsa. "Na damu sosai, ina tsoron yadda Safwan zai karbi maganar nan Amrah." "In sha Allah abinda kake tunani ba zai faru ba, in Sha Allah." "I hope so, amma gaba daya hankali na a tashe yake, ko Daddy ya sanar wa Mah-Mah?" "Komai zai zo da sauki, in Sha Allah." "In sha Allah." A tare suka fito, bayan Ummi ta aiko an kirasu, tare suka ci abincin daren, duk yadda Amrah take cike da matsananciyar kunya amma haka ta daure suka yi suka gama sannan suka zauna akayi hira wadda bata iya saka baki sai murmushi kawai. Maimartaba ne ya fara yi musu sallama ya tafi ya kwanta saboda yana bukatar hutu,chan Amrah ma tayi musu sallama saboda taga hirar akan rayuwar Sultan din ce da Ummin ke ta yi masa tambayoyi yana bata amsa, tasan suna bukatar kasancewa su biyu shiyasa kawai ta tafi, ta dauki wayar ta tayi logging whatsapp suka shiga hira da Afrah tana bata labarin abubuwan da suka faru. Jin an taba kofar ne ya saka ta saurin kifa wayar ta rufe idonta pretending kamar bacci take, tana jin sa ya shigo, ya wuce kai tsaye toilet ya watso ruwa ya fito, ta bud'e idon ta kad'an ta kalle shi, yana tsaye daure da towel iya kugu, yana goge kansa, da sauri ta maida idon ta rufe zuciyar ta na bugawa da sauri. Tana jin sa ya hawo gadon, tayi tunanin sai matso kusa da ita ya kwanta sai taji ya kwanta a gefe ya dora kansa a saman sangalalin hannun sa, ya kurawa saman dakin ido, ji tayi babu dad'i, tasan tunani yake tayi bacci shiyasa, bata so taga yana tunani haka, duk sai taji babu dadi da gaske. Suna kwance a haka kowannensu ba bacci yake ba sai dai shi Sultan be san idon ta biyu ba. Motsi tayi kad'an ya kalli wajen da take, idon ta a bud'e take kallon sa ta dan hasken da yake shigowa dakin.Kafin yayi magana ta mirgino ta dora kanta a saman hannun nasa itama, yayi mata murmushi ta mayar masa. "Na zata bacci kike ai." "Um um, ido na biyu." "Me kike? Tunani?" "A ah, chatting muke da Afrah." "Don't tell me idon ki biyu sanda na shigo, you pretend kamar kina bacci amma?" "Na zata ka gane ni ai." "Um um, da gaske na dauka bacci kike, ashe wayo kikayi min." "Toh ba kaine ba." "Ni kuma? Ya Allahu, me nayi dis time Kuma?" "Ba komai." "Sai kin fad'a min, or else?" Yayi maganar yana juyowa suna facing juna "Me?" Ta tambaya tana dan matsawa "I'll hug you, I'll kiss you and..." "I'm sorry." Tayi saurin cewa tana kokarin tashi. Dariya yayi sosai yana maida ita "Allah kin cika tsoro." "Na daina." "Toh naji, muyi bacci, let pray sai kowa ya rufe idonsa and we sleep, shikenan?" Daga kanta tayi, suka karanto addu'ar kwanciya bacci a tare, suka tofa a ko ina sannan suka kwanta. Da safe suka tashi suka shirya sannan tace ya fara fita dan ita bazata iya jerawa tare dashi ba, dariya yayi mata ya fita, sai da ya dade da fita sannan tayi shahada ta fita, babu kowa a falon alamun ma masu gidan basu tashi ba, shi kad'ai ne a falon yana waya, bata zauna ba sai kawai ta koma daki ta zauna, chan ta sake dawowa ta tambaye shi Kitchen lokacin ya gama waya, ya nuna mata ta tarar da masu aiki ne a ciki suna ta kokarin had'a breakfast, ita ta karba ta tsaya akai suka had'a hadadden breakfast wanda tasan zai farantawa in-laws din nata rai. Sai chan Ummin ta fito, Sultan lokacin yana dakin Baban, tayi ta shiwa Amrah albarka bayan masu aikin sun fad'a mata abinda tayi, amma tace karta sake ta bar su suyi aikin su ne, bayan haka ma idan suka koma Masarautar dole ta hakura da komai. Ita dai Amrah taji ne kawai, girki passion dinta ne saboda haka ko ina ta samu kanta zatayi shi da farin ciki dan yana cikin abinda yake sata nishadi. Tare suka fito Baban ya shirya tsaf, yayi shigar manyan kaya, sosai ya fito a ainihin waye shi, duk suka tashi sai da ya zauna sannan suka zauna. Yanzu ma kamar jiya tare sukayi breakfast din, bayan sun gama Sulthan suka fita tare da Baban, su kuma suka zauna a wajen suna hira. A daidai lokacin Daddy ya gama shiryawa, Mah-Mah ta gabatar masa da abincin sa, sai dai bashi da appetite din da zai iya ma cin abincin, yasan sultan ba wani dadewa zai ba, ya kuma san idan suka dira a k'asar nan komai zai bud'e, baya so ta fara ji a wajen wani shiyasa ya yanke hukuncin fad'a mata kawai, idan yaso sai ya nemi alfarmar Maimartaban akan su bar masa Safwan din dan shi dai za iya cewa ba Mah-Mah kad'ai ba, hatta shi baya iya jin zai dau rashin Safwan din. A shirye take taci kwalliya sosai, kasancewar ta mace yar kwalisa gashi tana cike da farin cikin samuwar lafiyar Safwan, saurin zuwa asibitin take dan yace mata yana so yaci tuwo shiyasa ta dawo gida tayi masa lafiyayye ta sake shiryawa zata tafi wajen nasa. "Daddy ga abincin fa, mutumin ka ne tuwo miyar ganye." "Zanci, amma nafi so muyi magana." "Magana? Allah yasa lafiya." "Alhamdulillah, ko da yake kar Safwan yayi ta jiran abincin, muje akai masa idan yaso da daddare sai muyi maganar." "Owk tam shikenan." Asibitin suka nufa, suka tarar da Safwan din a zaune ma suna hira da wani abokin karatun sa, ya gaida su yayi musu sallama ya tafi, tare suka zauna suka ci abincin a kwano daya, duk da Daddy be wani ci sosai ba amma still yaci don kar ya saka Mah-Mah a tunani tunda ta riga ta sanshi tasan abinda yake hanashi sukuni har yaki cin abinci ba karami bane. Har dare suna nan, sai da wanda zai kwana a asibitin wani dan sister din Mah-Mah yazo sannan suka tafi gida. A gajiya Mah-Mah take, tayi saurin wucewa dakin ta, ta kwanta saboda yadda take jin ta babu dad'i, tana kwance bacci ya soma daukar ta, Daddy ya turo dakin ya shigo, ya kalle ta cike da tausayawa, ya matsa gaban gadon ya zauna ya bata baya. Motsin sa yasa ta tashi ta zauna. "Bansan me yasa ba nake jin duk babu dad'i, baccin ma sama sama yake daukata ko me yasa?" "Zamu iya yin maganar yanzu?" "Ya Salam, kaga har na manta zamuyi magana,Allah ya yaye min mantuwar nan tawa." Shiru yayi yana harhada maganar, ya hada ta yafi sau goma tana kwacewa, har ta kosa tayi tunanin ba zai ce komai ba, sai kuma yace "Da farko ina so na fara da baki hakuri, tabbas nayi miki laifi me girma, amma dan Allah ina rokon da ki yafe min." "Iya zama na da kai ban taba samun ka da wani abu ba, kullum burin ka shine ka faranta min, ni kuwa me zakayi min har haka da zaka nemi yafiya ta?" "Tabbas nayi amfani da kokari na faranta miki,wajen bata komai, amma sai dai banyi dan nasan gaba zai zama abinda zai goge duk farin cikin da na samar miki ba, idona ya rufe a lokacin buri na, na samu yadda zan faranta mikin, bansan cewa akwai gaba ba, dole komai daren dadewa gaskiya zatayi halin ta." "Dan Allah Daddy ka fad'a min me ya faru? Aure kayi baka fad'a min ba? Kana da wata matar saboda ta haifa ma yara ko?" Girgiza kai yayi da sauri "Idan wannan ne zai fi min sauki ai." "Toh menene, dan Allah ka fad'a min." Juyowa yayi gaba daya, ya kama hannun ta ya rik'e sannan ya saukar da kansa k'asa sosai "Kiyi hakuri,kiyi hakuri,Safwan ba dan mu bane!" _"Safwan ba d'anmu bane!"_ _"Safwan ba dan mu bane!"_ _"Safwan ba dan mu bane!"_ Haka ta shiga jin kalmomin na amsa kuwwa a kunnen ta, kanta yayi wani irin sarawar da be taba yi ba, bakin ta ya gagara furta kalma daya sai ma rawa da jikin ta ya hau yi, da k'yar ta iya daidaita bakin bayan ta fisge hannun da ya rike ta mike tsaye tace "Safwan ba d'anmu bane?" "Tabbas... mune iyayen Safwan amma ba mune mahaifansa ba, bamu muka haife shi ba." "Ta ya haka ta faru?" Tayi maganar cikin kuka sosai "Kaddara ce wallahi" "Ina d'ana? Ina yake toh?" "A ranar da yazo duniya a ranar ya koma." "Innalillahi wa inna ilaihi rajiun." Ta shiga furtawa da sauri da sauri, ta kasa gasgata abinda taji, wane irin al'amari ne wannan? Shekaru masu yawa kana tare da d'an ka, rana daya sai azo ace ba dan ka bane, tabbas dole ka rude,kokari take ta ajiya komai a ma'aunin tunanin ta amma ta kasa, kokari take ta tabbatar da shin gaske ne ko mafarki take irin mugayen mafarkan nan wanda idan kana yinsu zaka yi ta Allah Allah ya farka ka tabbatar da ba gaskiya bane, sai dai wannan al'amarin yasha banban da mafarki, wanda duk duniya shine mutum na farko da yafi kowa kusanci da ita, ya kuma fi kowa sanin yadda take son Safwan, shine a tsaye a gabanta yake jaddada mata cewa Safwan ba danta bane, toh idan ba danta bane dan waye? Ya akayi haka ta faru? Waye yayi musu wannan aika aikar, wanne irin abu ne haka? Ta kasa gane komai sai jijiiga kanta kawai take tana kuka sosai, kokari yake ya rik'e ta yayi mata bayani amma taki sauraren sa, ja kawai take da baya har ta kai jikin mirror dake dakin,jin taje karshe ne ya saka ta durkushewa a wajen tana jan kukan da take, tana cigaba da maimaita kalmar Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun. ***Nagode sosai Wallahi,naga remedies kala kala har ma nayi trying wasu. Alhamdulillah Nagode ma kowa©® Hafsat Rano *Page 52* RanoNet www.ranonet.com.ng Register for your amazing data at a very cheap price. Mtn 1gb @300 naira only *** Idan tace kukan da take zai rage kaso mafi yawa na abinda take ji a zuciyar ta tayi karya, tun bayan da Daddy ya gama yi mata bayanin komai, ta kuma fuskanci komai taji komai ya dawo mata sabo fil,taji dama ace gaskiya ya fad'a mata tun a lokacin, da bata ji irin abinda take ji yanzu ba, da tun a lokacin ta sawa zuciyar ta salama ta hakura, amma sai yanzu da ta riga ta gama sakankancewa, sannan rana daya yazo mata da irin wannan mummunan labarin. A wanne bangare zata ajiye wannan mummunar ranar?    Da k'yar ta karfafa kanta, ta shirya ta nufi asibitin da safe saboda ranar za'a sallame Safwan din, ba zata ce ta runtsa ba gaba d'aya ranar, yanayin fuskarta kad'ai zaka kalla ka gane cewa ba daidai take ba. Ko da ta isa asibitin sai data fara tsayawa ta kalli kanta sosai a jikin mirror, sannan ta sake gyara fuskarta ta sosai sannan ta nufi cikin asibitin. Duk yadda ma'aikatan wajen ke gaisheta ta kasa sakin fuskarta yadda ta saba musu, duk sun tabbatar babu lafiya amma kuma sunyi mamaki saboda yau za'a sallami Safwan sun zata sai tafi kowa murna.    Da taje kofar shigar ma sai ta kasa shiga, taji kamar an bige kafafuwan ta, taji kwalla na taruwa a idonta, tayi saurin maida ita, tayi sallama ta shiga tana rufe gefen fuskar ta da mayafin ta. A tsaye ta tarar da Safwan din gaban yar durowar, da sauri ya juyo da fara'ar sa, sai yayi turus ganin yanayin ta "Mah-Mah..." "Na'am Safwan, ya jikin naka?" "Alhamdulillah, are you sick?" "A ah Safwan." "Mah-Mah kuka kikayi?" Ya matso da sauri, bata sanda hawayen da take rikewa ba suka shiga sauka akan kuncin ta, tayi saurin saka mayafi ta rufe fuskar ta, ta shiga yin kukan a hankali. Sosai ya rikice yana tambayar ta me akayi mata? Waye bashi da lafiya amma ta kasa amsa masa, kokarin tsaida kukan take amma yaki tsayawa, a haka Daddy ya shigo ya tsaya ya kasa karasowa, da dauri Safwan yayi wajen sa "Daddy me akayi ma Mah-Mah? Me akayi mata dan Allah." "Bata jin dad'i ne Son, karka damu idan muka je gida zamuyi magana." Cikin yanayi mara dad'i Safwan din ya koma gaban Mah-Mah, ya durkusa yana jin kamar ya maida abinda take ji har ya sata kuka kansa, duk tsawon rayuwar sa, ta kula dashi, tayi masa dukkan gata , ta dauki lalurar sa akanta bata iya runtsawa duk sanda yake cikin ciwo,ya kanyi tunanin anya akwai wanda ya kaishi sa'ar uwa kuwa?    Soyayyar da take masa ba kad'an bace, duk da kowacce uwa dama tana son yayanta, amma shi tashi soyayyar da take masa was beyond... Yana lura da ita har aka gama cike cike aka sallame shi ta kasa had'a ido dashi, ya lura kamar ma kallon sa ne yake saka ta kuka, ya rasa dalili duk ya damu, me zai saka Mah-Mah a cikin irin wannan halin haka?    Ana discharging dinsa ya kira Sultan a waya, ya fad'a masa sukàyi magana sannan ya kashe, suka dunguma suka wuce gida. Ko da suka isa gidan ma sai da mamaki ya sake kama shi, yasan babu yadda za'a yi Mah-Mah ta kyale shi musamman daga fitowar sa daga asibiti, amma sai yaga abun mamaki, suna zuwa tayi saurin shigewa daki ta bar shi da Daddy a falo, da k'yar ya isa dakin sa, ya kwanta a saman gado yana tunanin sabon al'amarin da ya shigo gidan nasu, wanda ya lura daga Mah-Mah har Daddy kamar wani babban al'amari ne yake damun su, kawai shi Daddy dan namiji ne shiyasa ya daure yake kokarin nuna babu komai, amma fuskarsa ta nuna akwai damuwa babba, ta yaya zai bullowa al'amarin? Gashi Sultan dinsa baya nan balle ya taimaka masa as always. Yana kwance ya k'asa katabus har aka turo kofar, Mah-Mah ce dauke da tray kamar ko yaushe mafiya yawan lukuta idan bashi da lafiya, ta chanja shigar ta zuwa wasu kayan na daban kamar fita zatayi, ta ajiye kayan a gefe ta matso, lokacin ya mike zaune yana kallon ta cikin kalar tausayi "Kayi wanka kuwa?" "Ban ba, tun da na shigo kwanciya kawai nayi." "Ai da kayi wanka zaka fi jin dadin jikinka, oya tashi." Tayi maganar still bata kallon sa, kin tashi yayi, a raunane ya kira sunan ta, "Mah-Mah." "Na'am Safwan?" "Mah-Mah dan Allah me yake faruwa? Na kasa samun sukuni, Mah-Mah ko nayi muku wani laifin ne ban sani ba, dan Allah ki fad'a min ko yafiyar ku ce sai na nema." Dafa kansa tayi kwalla na taruwa a idonta, ta k'asa magana dan idan tayi zata iya fallasa asirin zuciyar ta, kokari tayi ta karfafa kanta, ta kakalo murmushin da ita kanta tasan ba wai na gaske bane tace "Bana jin dad'i ne Safwan, yanzu ma asibtii nake son zuwa naga doctor." "Subhanallahi, are you dat sick?Bari nayi wanka sai muje toh,ko kuma muje haka kawai idan na dawo nayi." "Calm down, ba wani abu bane da zaka tada hankalin ka, kawai dai zanje su dan duba ni, ba dadewa zan ba, kayi wanka kaci abincin kafin na dawo." "Please muje Mah-Mah, hankali na ba zai kwanta ba kika tafi ke kad'ai." "Please Safwan, kar muyi haka da kai, get some rest ba zan dad'e ba in Sha Allah." "Shikenan, Allah ya dawo dake lafiya." "Amin ya Allah." Zama tayi ya juya, har ta kai kofa ya kira sunan ta "Mah-Mah..." Juyowa tayi bata amsa ba, murmushi yayi mata sannan yace "You are the best mother in the whole world." "And You are the best son any one can have." Sai ta juya da sauri ta bar dakin, ya koma da baya ya zauna dabas a saman kujerar dakin yana tunanin abinda ke shirin faruwa, tabbas akwai abu a zuciyar Mah-Mah da bata so ya sani, ko menene sai ya binciko shi dan hankalin sa ba zai taba kwanciya ba. Gidansu Mah-Mah ta wuce dan tana bukatar space, space daga wajen Daddy, tana bukatar ta zama ita kad'ai tayi tunanin yadda abubuwan suka zama, ta kuma yi tunanin yadda maganar zata buya ba tare da wasu sun sani ba, son samun ta ba tare da Safwan din ma ya sani ba, duk da a maganar Daddy da yayi mata ya nuna lallai Safwan dole ya sani, amma sam bata yarda ba, bata amince ba domin ko babu komai ita din itace uwar Safwan, dan ta shayar dashi dan haka take jin babu Wanda zai raba ta dashi bayan ta gama wahalarsa. ****Shirye shiryen tafiyar ya kankama, Maimartaba ya riga ya gama shiryawa ranar, ya kuma kudire a ransa ba zai raga ma kowa ba, shiyasa ma yayi komai akan lokaci, ya kuma kira mutumin da yafi yarda dashi akan kowa yanzu, wanda ya hadu dashi lokacin da yake cikin tsananin bukatar wani ya taimaka masa, ba kuma wai da kudi ko wani abu ba, dan zai iya cewa baya jin har ya kare rayuwar sa zai bukaci kudi, domin Allah ya bashi ba kad'an ba, kamfanonin da yake dasu da gidajen mai ba zasu lissafu ba, shi yake kular masa dasu,bai kuma taba samun wani abu a tare dashi ba, tun bayan barin sa k'asar sau biyu suka taba haduwa wanda shi ne yazo wajensa, amma duk da haka suna waya kusan kullum saboda yaji progress din yadda abubuwan suke tafiya, akwai wani kuduri a ransa na mika dukiyar sa zuwa gidajen marayu da masallatai da dai abubuwan da zasu kara nauyin mizanin sa kasancewar bashi da kowa banda gimbiya, sai ga Sultan a lokacin da suka cire rai, wannan ya saka ya chanja shawarar komai ya kuma tsara abinda ya kamata yayi idan sun koma.     Be taba kiran sa be daga ba sai yau, yayi mamaki k'warai da har yayi masa kira uku babu ansa, sai yaji kamar akwai abinda yake faruwa dashi, har la'asar yana jiran kiran sa amma be kira din ba, ya sake gwadawa amma yanzu sai akace masa switch off, yayi mamaki sosai amma sai ya bar hakan a matsayin wani abu ne ya samu wayar tasa.     Yana kishingid'e suka fito zasu fita, Sultan ne a gaba Amrah na binsa a baya, kafin su karaso wajen sai da suka tsaya a dan corridor din ya taimaka mata ta gyara zip dinta wanda bata san be kai chan sama ba, ya mintsine ta bayan ya gyara matan tayi yar kara ta kai hannu yayi saurin gocewa ya shigo falon yana kunshe dariyar sa.    A kusa da Maimartaba ya zauna, ya dora hannun sa a saman kansa yayi addu'a, hakan cikin al'adar Maimartaba ce wanda yake saka Sultan a cikin matukar farin ciki. "Sannu da hutawa Babah." "Yawwa Muhammad, fita zakuyi ne?". "Eh wai chan gidan zamu je akwai mutanen da zata wajen su." "Ya kamata, yaki 'yata." Matsawa Amrah tayi gabansa suka sashi a gaba ita da Sultan din, ya dora hannun sa a saman kanta itama yayi mata addu'ar sannan ya saka musu albarka baki daya, sallama sukayi masa suka fita, ya bisu da kallo yana sauke ajiyar zuciya. A baya suka zauna, ya cire pad dinsa ya shiga dannawa,lokaci zuwa lokaci yana kallon titi, har suka iso inda zasu, be dago ba yace mata zai danje wani waje ya dawo,fita tayi tana gyara zaman rolling din kanta, suka ja motar suka tafi, a hankali ta taka zuwa gidan, ta danna door bell ta tsaya tana kallon hanyar da motar tabi, me yasa yake acting haka? Yanzu zai yi wasa yanzu zai yi kamar baya wajen. "Sarauta" zuciyar ta, ta tunasar da ita, jijjiga kai tayi kawai ita sam bata son wannan side din nashi, tafi son yayi ta tsokanar ta, tana jin dadin haka, bud'e kofar da akayi ne yasa ta maida hankalin ta kài, malamar su ce da ta koya musu karatu, wadda zata iya cewa tafi kowa kusanci dasu a k'asar tunda ba wani harka sukayi sosai da mutanen ba, ganin Amrah yasa ta saurin rungume ta, "La'ila, da gaske wai ko da wasa?" "Anty..." "Shigo ciki." Ta matsa mata tana fad'ad'a fuskar ta, gefe Amrah tabi ta shiga falon,  "Bismillah." Ta nuna mata wajen zama,zama tayi ita kuma ta nufi kitchen, ta hado mata ruwa da lemo da snacks akan tray ta kawo mata, sannan ta zauna suka gaisa "Yaushe kuka zo?" Ta tambaye ta "Ranar Wednesday." "Yasu Umma da kowa da kowa? Ke kad'ai kika zo Ina Afrah da Abba?" "Suna Nigeria." "Ke kad'ai kika zo kenan?" "Ni da shi muka zo, tare ma muka zo har kofar gidan nan ya wuce wani wajen." "Adnan?" "A ah, Ya Sultan." "Dan Allah, amma shine be shigo ba. Wani abun kuka zo kenan." "Umm..." Amrah tace ganin yadda Aunty Muhsinan ke mata tambayar kwakwa alamun tana son taji wani abu, ba zata iya ce mata ai tayi aure ba, sai kawai ta share suka cigaba da hirar abubuwan da suka faru bayan barin su garin. Har azahar suna tare, yau kasancewar babu karatu yasa gidan babu kowa yaranta ma suna chan gidan In-laws dinta, duk motsin ta Amrah na lura da komai, yadda take gudanar da gidan ta cikin kwarewa da iyawa. Har la'asar tana gidan be dawo ba be kuma kirata yace gashi nan ba, ita kuma maimakon ta kirashi sai ta share duk kuwa lokaci zuwa lokaci sai ta duba wayar taga ko ya kira, Anty Muhsina na lura da ita, bayan sun yi sallah ne sai ta karbi wayar Amrah tace zata ga hoton su Ummah a Nigeria, bude mata Amrah tayi ta bata ta shiga kalla har tazo inda take zargi, hotunan bikin Amrah din, tayi saurin cewa "Tunani na dai ya zama gaskiya, ashe Amrah anyi biki, shine ko ki fad'a min tun dazu da kika zo nayi noticing naki." Da sauri Amrah ta rufe fuskarta ta saka dariya, ajiye wayar tayi ta dawo kusa da ita, "Bude fuskarki, ba wai iya kar karatu kawai nake koyawa ba, har da yadda zaki zauna lafiya da mijinki, feel free with me karki ji nauyin komai, wannan rayuwar idan kika tsaya kunya za'a yi babu ke, so ki ajiye wannan kunyar a side, duk kuwa da kunya adon mace ce, amma akwai limit." Shiru Amrah tayi amma dai ta bud'e fuskar tata, tayi zuguri tana sauraron ta. "Da farko sai kin zama me tsafta, Idan nace tsafta ina nufin tsafta ba wai kawai shara ba, you have to be neat in and out, jikin ki, gidan ki have to be very tidy shine first step, sai kamshi, kamshi rahma me, kamshi yayi Amrah, ke kanki idan kina kamshi zaki dinga jin ki different balle kuma wanda kike tare dashi, gidan ki ya zama yana kamshi always, safe rana turaren nan babu kiwa, dama bangaren kirki na baki lambar yabo har ma da gyaran amma dole ki kara himma kinji? Karki yi wasa yawwa." "Know what your husband wants, like and dislike, akwai banbancin tsanaki abinda yake so da kuma abinda yake bukata kin gane? Ki san kuma kowanne da lokacin da yake bukatar tasa, sai ki san abinda ya dace kiyi, kisan damuwar mijinki, ki san yadda zaki magance masa ita, ki zama abokiyar shawarar sa, ki dinga bashi shawarwari idan abu ya taso, ki zama me gyara shinfida ki kin gane me nake nufi, ki zama available duk sanda mijinki ya zo da bukatar sa ." "Kisan lokacin da yake in the mood, da lokacin da yake bukatar zama shi kad'ai, karki ce dole dole sai ko yaushe ya zama yadda yake, akwai damuwa akwai gajiya akwai matsalolin yau da kullum." "Ki zama me iya magana, ba kowanne magana zaki iya budar baki ki fadawa mijinki ba, daga lokacin da kike fad'a masa kowacce magana shima ba zai ji kunyar Yaba miki duk wadda tazo bakin sa ba duk kuwa da munin ta, ko matsala kuka samu yayi miki laifi talk to him politely, shine zai fi fuskantar ki har ma kuyi solving matsalar ku ba tare da 3rd party ko hayaniya ba,amma idan kikace zakiyi masa gyara da tashin hankali toh ba zai dauki gyaran naki ba, kuma ba zai tsaya ya saurare ki bama." "Mata muna da mood swings na yarda da wannan, saboda haka kiyi iyakar kokarin ki wajen daidaita fushin ki ko bacin ranki, saboda mata da yawa mood swing din da muke samu na taka muhimmiyar rawa wajen wasu manyan matsalolin da aure ke fuskanta a yanzu." "Ki zama me godia, mijinki ko kayan abincin gida ya siyo learn to appreciate him, kiyi masa addu'ar karuwar samu suna jin dad'i sosai da sosai." "Ki iya hira, ba wadda zata dinga gundurar sa ba, ba kuma gulma ba, yau kice wannan gobe kice wance, zaki ga ba zai wani dinga baki attention ba idan kinayi, kisan me zaki fad'a game da yan uwanki da iyayenki dan wasu mazan will use that against you musamman idan Abu ya taso ko kuka samu matsala." "Ki koyi sana'ah idan mijinki zai kyale ki, yanzu ba'a zama saboda yawancin maza basa son bani,bayan haka kuma abubuwan na yi musu yawa dan haka idan kina sana'a zaki taimaka ta wanne bangaren." "Amrah wasu Mazan na da rauni wajen ibadah, sai kun hada karfi wajen gyara gidan ku, kin taiamaka masa wajen tsaida ibadun sa, sannan zaku samu nagartaccen gida. Kiyi addu'a sosai ki kuma lura da komai, karki zama ballazar mace, ki zama mace me aji me class, al-mar'atu saliha." "Inaga with this little advise, da kula da dangin sa da iyayensa da ban saka ba, da wasu abubuwan da na manta ina fatan zaki yi amfani dasu, ina yi miki fatan alkhairi a sabuwar rayuwarki, ina rokon Allah ya baku zaman lafiya da zuri'ah dayyiba, ya albarkaci auren ku." A hankali ta amsa da Ameen, abubuwan da Aunty Muhsina ta fad'a mata sunyi matukar tasiri a ranta, taji atleast tana so ta gwada dukka shawarwarin. Mikewa Aunty Muhsina tayi, ta wuce ciki sai gata ta dawo dauke da wasu robobi da wani littafi, ta bud'e jakar Amran ta zura littafin "Idan kika samu lokaci ki karanta,akwai tips da yawa tun daga farkon auren har zuwa tarbiyyar yara." "Nagode sosai Allah ya saka da alkhairi." "Amin ya Allah." "Ungo wannan, fara dashi." Da ido ta kalli robar kamar zatayi magana sai kuma ta karba ta kafa kai, madara ce ashe, amma irin wadda babu mix din komai, madarar ce zallarta, sai data shanye tas sannan ta ajiye, ta sake mika mata wani cup da ta tsiyaya mata a ciki, rabi tasha ta ajiye, ba wai don babu dad'i ba sai don cikin ta ya cika kuma. "Bari nayi miki parkaging ragowar zaki ji dadin amfani dashi." "Nagode." Ta fad'a a kunyace "Baki tambayi mene ne ba, komai tambaya ake baki ji ance matambayi baya Bata ba?" "Kinsan baure?" Girgiza kai tayi "Toh idan kin koma ki saka a nemar miki *Sassaken Baure *Kanumfari *Citta *Minannas *Mazarkwaila Ki dinga dafa su kina sha koyaushe, zaki iya yi da yawa ma ki saka a fridge yafi duk kayan tarkacen nan, sannan ki dimanci shan madara fresh one, sai su dabino kunan Aya, cucumber da zogale kiyi blending kisa madara,farfesu kisha romonki. Sai kuma bangaren gyara ta waje, seatbath da ganyen magarya sannan amfani da misk bayan al'adah kamar yadda yazo a hadith Nana Aysha tana amfani da misk bayan ta gama al'adah tasa a auduga tayi cleansing wajen. Idan kika yi haka sai ki tafasa ganyen magaryar ki kiyi seat bath kamar na minti goma sha biyar shikenan." "Akwai abubuwa da yawa Amrah, naso tun zuwan ki muka fara, amma yanzu ma Alhamdulillah." "Nagode sosai Allah ya saka da alkhairi." "Amin amin, naji kamar kiran sallah, muyi sallah sai mu dora ko?" Murmushi tayi, zuciyar ta fes dan komai ta ajiye a kwanyar ta, tana jin dadin sabon karatun da bata sani ba, bata san ma yana existing ba sai yanzu. Suna idar da sallar kiran Sultan ya shigo,yace mata suna waje kawai ya ajiye wayar, ta tashi Anty Muhsina ta rike ta, ta ja hannun ta zuwa wani daki a gidan, "Gyara fuskarki, ki saka turarurruka gasu nan, bari na saka ya shigo kafin ki gama." "Toh." Tace ta fita ta barta, ta zauna tana kallon kan mirror dake cike da kaya da kayan kamshi kamar za'a bud'e shago, ta shiga daukar su daya bayan daya tana amfani dasu, sanyin kamshi ne dasu ba mai hayaniya ba, nan da nan dakin ya sake daukar kamshi, ta gyara fuskar ta ta mutsuka powder ta saka lipstick kad'an sannan ta fesa wasu turarurrukan, tana ajiye na karshen Anty Muhsina ta shigo, ta kalle ta tayi murmushi "Akwai saura amma dai kinyi kokari." Tissue ta ciro ta bata, tace ta goge lipstick din data saka, sannan ta dauko mata wani romantic jambaki red ta bata, ta saka abinka da fara sai gata tayi wani irin kyau, "Perfect." Tace sannan tace su je, Yana zaune rike da cup a hannun sa, kansa da yake sara masa sosai ya dafe da hannu daya, rabin hankalin sa ya tafi akan wayar da sukayi da Daddy dazu, tausayin Mah-Mah da kuma tunanin yadda za'a sanar da Safwan su suka hadu suka tarar masa, gashi yau gaba daya be zauna ba, abubuwan Maimartaba yake ta yi har magriba, so yake su gama komai kafin su bar k'asar, baya jin ya saka wani abu a cikin sa tun safe, sai wannan ruwan bunun da Aunty Muhsina ta bashi da yayi masa dad'i sosai, yaji gaba daya system din cikin sa ya karba, da yana jin wani kabaibai a cikin amma da yasha sai yaji kamar hanjin sa ma ya warware daga dunkulewar da sukayi waje daya. Labaran da ake nunawa a talabijin ya dan dauki hankalin sa, har be ji fitowar su ba, sai kamshin da yayi ma kofofin hancin sa lale marhaban, da sauri ya waigo, idon sa ya sauka akan fuskar ta, be san sànda ya sakar mata murmushi ba, ta mayar masa tana zama a kujerar dake gefen inda ya zauna. "Sannu da zuwa." Tace k'asa-kasa tana karantar yanayin sa da ya nuna gajiya sosai. Da ka ya amsa mata,sannan ya ajiye cup din yana mikewa "Zamu wuce aunty, angode allah saka da alkhairi." "Amin Sultan, ka kyauta daka kawo ta,dan kaf kasar nan babu wanda muka shaku kamar maman su, munyi zaman mutunci shiyasa nake jin su kaman yayan ciki na." "Allah sarki." "Allah ya baku zaman lafiya, ayi ta hakuri da juna don shine kinshikin zaman lafiya, sannan communication is the key to every successful marriage, ku tattauna matsalar ku, shine zaku samu saukin komai, ayi ta hakuri da kau da kai da addu'a." "In sha Allah,mun gode k'warai." "Nice da godia." Sallama sukayi mata, suka jera har wajen motar inda driver ke jiran su, shi ya bud'e mata ta shiga sannan ya zagaya ya shiga suka tafi. Babu wanda yayi magana a motar, kamar yadda suka tawo dazu haka ma yanzu, ya maida hankalin sa sosai akan wayar hannun sa. Tunanin ta yaya zata fara aiwatar da abubuwan da ta koya yau ta shiga yi, kunya take ji sosai musamman da yanzu ne zata fara ire-iren wadannan abubuwan, amma kuma dole ne ta koya din saboda hakan shine ya dace. Shahada tayi ta matsa zuwa tsakiyar kujerar, ya dago daga kallon wayar tasa, yayi mata murmushin ya maida kansa ya cigaba da abinda ya keyi, shiru tayi tana jin nauyi amma haka ta daure, ta matsa sosai jikin sa, yana jin ta yayi kamar be san ta matso ba, ta dora kanta a saman kafadarsa. Kashe hasken wayar taga yayi, ya zura ta cikin aljihu sannan ya saka hannu ya dago kanta, ya juyo baki d'aya yana kurawa fuskarta ido. "Gani, what did you have for me?" Shiru tayi kuma, hannun sa ya saka ya dangwali saman lips dinta "Wannan jambakin yayi kyau, yayi miki kyau." "Thanks." Tace a gajarce "Ya yau din? Nayi ta jiran call dinka." "And baki kirani ba, da sai ki kirani kiji ina wannan bawan Allah ya makale, kila ina chan anyi cefanan kaina ma." Rufe bakin ta, tayi da sauri "Allah ma ya rufa asiri." "Amin ya Allah, misali ne kawai, next time irin haka kikaji shiru call me kinji, ina chan ne wasu harkoki sun rik'e ni, ban ci komai ba Allah sarki ni." "Ayya Allah sarki, sannu." "Shikenan?" "Me?" "Sannu kawai, nothing for me?" "Babu komai." Tace tana yarfe hannu " Ni kamshin nan ne ma, kaman zan zauce, ina kika samo shi?" "Ba ko ina." Hancin sa ya dora a saman kanta, ya shaki kamshin sannan ya sauko da fuskar sa zuwa saman wuyan ta, idon sa a rufe ya bata light kiss a wajen, ta ja numfashin ta da sauri jin yadda numfashin sa ke sauka akan wuyanta. "Ina son kamshi." Yayi maganar yana matso da face dinshi ta wajen bakin ta, kafin tayi magana ya dora lips dinsa a saman nata a nutse. **©®Hafsat Rano 53 & 54 **** *_kunsan me ake kira da ƘURE ADAKA?_* _To ba kowa bane illa MAAB LUXURY HOME_ *_Wadanda suke a shirye kuma kullum a tafe wajen kawo muku ingantattun kayan qawata gida masu inganci da kuma kyan gaske_* *idan matsalarki inda zaki samu kaya 'yan yayi masu inganci to kakarki ta yanke saqa,koda kuwa saqar qarfe ce,saboda zuwan MAAB LUXURY HOME* _SUN TANADAR MUKU KAYA KAMAR HAKA_ _dinner set_ _serving trays_ _cutlery set_ _jugs_ _foodflask_ _thermoflask_ *kai dama dukkan wani nau'in kaya na qawata gida da maidashi aljannar duniya* *_hausawa sukace gani ya kori ji,maza garzaya wadan nan shafukan namu don ganewa idanunku irin kayayyakinmu_* *instagram* https://instagram.com/maabluxuryhome?utm_medium=copy_link *facebook*:maab luxury home *website* http://maabluxury.com _Ko ka tuntubesu ta lambar waya kamar haka_ +491521 4642007 *suna nan a garin kano,maza taho ayi daku*🏃🏾‍♀️🏃🏾‍♀️🏃🏾‍♀️🏃🏾‍♀️🏃🏾‍♀️ ***Kai tsaye dakin mahaifiyar ta wadda ta jima da rasuwa ta nufa,ta bud'e dakin ta shiga bata ko bi takan matan gidan ba, burin ta kawai ta kadaita bata kuma son a bata wata shawara ko umarni akan abinda take jin babu me raba ta dashi sai Allah wanda dama shine ya hada su din. Kwanciyar ta kenan taji an turo kofar data dan rufe ta an shigo, tayi tunanin daya daga cikin matan baban nata ne amma sai taji muryar  Hajiya Umma, ta tashi daka kwanciyar ta zauna ita kuma ta karaso ciki. "Da gaske dai yara suke da suka ce sun ga shigowar ki, na dauka ma wasa ne wallahi dan dana tambayi su Hajja ma cewa sukayi anya?" "Ina wuni Ya Umma?" "Lafiya lou, ya jikin Safwan?" "Da sauki Alhamdulillah." "Lafiya kuwa? Akwai matsala dan jiki na ya bani ba kalaou ba." Kuka ta saka kawai, dama abu da zuciya a kusa, abin na cin ta yana nukurkusar zuciyar ta, shiyasa daga tambaya sai kuka dan tana jin kukan ne kad'ai zai rage mata rad'ad'in da take ji, "Subhanallahi, lafiya? Me ya faru?" "Bana jin dad'i ne kawai ya Umma." "Wannan ba zancen kamawa bane sam sam,ta ya zaki shigo gida ki tawo nan ba tare da kin nemi kowa ba, kuma na tambaye ki matsala ki fashe da kuka, dole dole akwai abinda ya faru, dole ne." Shiru Mah-Mah tayi, ta yaya ma zata fara furta cewa Safwan ba dan ta bane, ta yaya? Waye ma zai tsaya ya saurareta? Zancen ma gaba daya ba wai wanda zai samu karbuwa bane, musamman kuma tana so ta rufa asirin mijin ta, bata so ta fad'awa duniya abinda ya faru, har su zama labarin da za'a dinga kwatance dashi ba. Ba ma wannan ba, sam yanzu ta dawo daga rakiyar Ya Umman saboda abinda ya faru a baya shiyasa yanzu ma taji tsoron sanar mata kar ta ingizata tayi abinda zai fi nada muni wanda zai jawo ta rasa Safwan din ma baki d'aya.      Tashi tayi kawai ta wanko fuskarta a bayi, ta fito ta goge ta, ta dauki jakarta tayi hanyar fita daga dakin dan tana ganin zuwan nata gidan ma kamar wani tonan asiri ne gareta. "Ya Ummah bari na wuce, kiyi hakuri ba wai bana son sanar dake bane,sai dan cewa ciki ba dan abinci kawai akayi shi ba, wannan maganar sirri nace, ina kuma fatan ba zaki ji komai ba akan hakan." Rik'e baki Hajiya Umma tayi, sosai maganar ta daketa, me Mah-Mah take nufi kenan? Har ta fice daga dakin, ta kuma fice gaba daya daga gidan bayan ta gaida su Hajja Hajiya Ummah bata fito daga mamakin da ta shiga ba, jikinta yayi sanyi k'warai, ta k'asa barin wajen sai da k'yar ta ja kafafunta guiwa a sake ta bar gidan tana jin bacin ran wulakanci da Mah-Mah tayi mata, ko da yake bata ga laifin ta ba, ita da ta damu da ita ta cusa kanta a harkar da babu ruwanta ita ta jawo ma kanta wulakanci.    Ko da ta dawo gida ma sai ta shige gidan su Amrah wajen Umma tayi zamanta dan tasan nan ne kad'ai wajen da zata samu nutsuwa, daga baya ma sai tayi kwanciyar ta a falon Umman ba kuma tare da Umman ta nemi tasan dalilin hakan ba duk kuwa da taga alamun babu lafiya amma bata tambaya ba saboda bata so ta shiga hurumin da ba nata ba.    Har la'asar Mah-Mah na gidan bata tafi gida ba babu kuma wanda yazo neman ta anan taci abincinta dama gashi tana son girkin Umman, , tun da Daddy ya dawo yaga motar ta a waje ya kuma duba gidan yaga bata nan yasan tana gidan su Amran,be matsa mata akan lallai ta dawo ba, saboda yasan tana bukatar zuciyar ta, ta huta da abinda ya tunkaro su shi dinma dauriya kawai yake a matsayin sa na namiji amma har zubda hawaye sai da yayi. Ko da Safwan ma ya tambaye shi sai yace babu komai ya kwantar da hankalin sa ya maida jikin sa zasuyi magana idan Sultan ya dawo. Hakan ya saka ya kwantar da rabin hankalin sa yana jiran dawowar Sultan din. **** Har suka isa gida hannun sa na cikin nata, kanta a saman kafad'ar sa, tun bayan da ya gama amsa wayar da ta gane daga Safwan ne taga ya sake yin shiru ya shiiga tunani, bata tambaye shi ba har suka karasa gidan. Da suka fito daga motar ma sai kowa yayi nasa waje ta nufi wajen Ummi shi kuma ya wuce wajen Babah. Bata san dadewar da sukayi tare da Baban ba dan har kusan goman dare Sultan din be neme ta ba. Tana shiiga daki ta tsaya a gaban mirror tana kallon kanta, ta kara haske tayi wani irin fresh banda yar ramar da tayi ta chanja sosai. Sai ta tuna abinda Aunty Muhsina tace mata akan aure, murmushi tayi ta shafi fuskarta, tana tuno wasu abubuwa. Ta cikin mirror ta hangi shigowar shi, kafin ta juyo ya karaso, ya saka hannunsa ya zagayo dashi ta cikin ta, ta sakar masa murmushi suna kallon juna ta cikin mirror. "My wife." "Umm..." "Me kike kallo?" "Ba komai." "Fad'i gaskiya, kina kallon beautiful fuskarki kina admiring ko, kina kuma godiya Allah." "Um um, kawai gani nayi kamar nayi fari sosai." Tayi maganar tana kallon fuskar shi ta cikin mirror din, juyo ta yayi ta zama shi take kallo, ya kare mata kallo sosai sannan yayi murmushi "Sai glowing kike kamar wata a dare sha biyar, menene sirrin?" "Nothing, kawai dai..." "Kawai dai kawai dai, ok ni ai na san sirrin." "Menene sirrin?" "Zan fad'a miki anjima." "Um um please ka fad'a min yanzu, ni yanzu nake so na sani." "Really? Yaushe kika yi baki haka?" Ya matso da fuskar sa kusa da tata sosai "Jiya, yau, dazu, dama ina da baki kawai dai..." "Kawai dai jan class." Ya karasa ya kai hannu ya lakace mata hanci "Afrah ta koya miki magana wife." "Dama ina yi fa." "Um na yarda, baki tambaye ni komai ba, har nayi fushi na,na huce." "Laaa, kayi hakuri Allah abun na raina, kawai naga kamar kana busy ne shiyasa." "Toh naji, yanzu dai damuwa ta Safwan ce, tunda Abba yace min ya fad'a ma Mah-Mahn duk da dai abun ba sauki amma still yazo da sauki fiye da yadda mukayi tunani, yanzu damuwar mu Safwan ne, yadda zai dauki zancen shi da ba cikakkiyar lafiya ba." "Ya Sultan..." "Umm..?" "Ya Safwan mutumin kirki ne, kuma ya riga yasan kaddara, kuma ya yarda da kai fiye da kowa da komai, kaine zaka fad'a masa saboda kai kad'ai ne zaka iya fad'a masan,nasan da farko zaiji babu dadi, amma kuma babu wanda zai samu iyaye kamar su Ummi yace zai ma Allah butulci, ko ta wanne bangare gata ne Allah yayi ma mutum." "Tabbas Safwan bashi da matsala, matsalar daya yanayin da aka bi aka haife su, Kinsan wannan abun shi zai fi tsaya musu a zuciya daga shi har Muhammad din, wanda zan iya cewa tsawon rayuwar sa be san akwai wani abu wai surrogacy ba,be taba tunani ko hasashe ba, bayan haka karki manta Aminatu na raye ba mutuwa tayi ba, ga Ummi a gefe daya, kinga abun is somehow complicated." "In sha Allah komai zai tafi daidai, ka daina damuwa abin da ya riga ya faru ya faru sai dai a kori gaba, Allah ya yafe mana." "Haka ne, Amin ya Allah, I'm now relief, thank you so much wife." "It's my pleasure dear." "Umm, guess what?" "What!?" "Gobe fita zamuyi, zamu je wurare da yawa, inda ma baki taba sanin yana existing ba, and I'll make sure you have the best time of your life,." "Umm really!?" "Yess yess, zaki gani, just make your self ready." Ya kashe mata ido daya "In sha Allah, I can't wait." "I can't wait too." Yayi curving fuskarta da tafin hannun sa, with out another word ya had'e bakin su waje daya. Early morning Amrah tashi, saboda zumudi ta hau shiryawa, dama tun a daren bayan Sultan yayi bacci ta fidda kayan da zasu saka ta ajiye musu a gefe, hatta shoe and bag sai data ajiye, tana tashi kuwa ta hau shiryawa, tayi light make-up ta saka wasu riga da skirt yellow and Red rigar zuwa wajen guiwar ta sai skirt din da ya kasance straight skirt, ta yane kanta da veil tayi kyau sosai, tana kokarin saka rolling pin ya fito daga wanka, ya tsaya daure da bathrobe yana kallon ta, tayi kyau sosai kamar ka sace ta. Lokaci daya abu yazo masa akan sa, ya juya ya koma toilet din, jim kadan ya dawo ya wuce wajen kayan da ta ajiye masa ya zauna ya dauki mai zai fara shafawa, "Kamar karar ruwa nake ji, ko ban kashe ba?" Yayi maganar yana kasa kunne, "Aikam naji nima." Tace tana mikewa, ta nufi toilet din ba tare da tunanin komai ba, tana shiga yayi wata dariya ya tashi yabi bayan ta har da dan gudun sa, a lokacin ta kashe fanfon ta juyo sukayi kicibis a dan corridor da ya raba toilet din da dakin ya saka hannu ya tokare kofar yana mata dariyar k'asa k'asa. "Ya Sultan... Please please kar muyi haka da kai." Tace da sauri bayan tayi figuring abinda yake shirin yi, shiyasa ma ya kunna fanfon ashe duk trap ne. "Duk wayon amarya..." Yayi maganar yana matsowa ciki, "Na shiga uku..." "Na shiga uku..." Ya kwaikwayi maganar ta, kafin ta sake cewa komai ya riko ta, ya maida ta cikin toilet din tana mata dariyar mugunta. Duk magiyar da ta dinga yi masa be jita ba, sai da suka sake wani wankan tare suka bata lokaci sosai sannan suka fito, tana ta sunne kai tana ciccijewa ya dinga mata dariya, dole ta sake sabon shiri ta chanja wasu kayan. Ranar Amrah zata iya cewa was one of the best days of her life, sun yi having fun sosai, taga soyayya iya kar soyayya, sun ajiye komai sunyi enjoying ranakun ba kad'an ba, su ne Niagara falls, Quebec City, Lake Ontario,Cape Breton Island , Montreal da sauran wuraren shakatawa a k'asar ta Columbia. Daga nan suka zarce Ice Hotel suka ci abinci a chan suka wuce resort dinsu, lokacin dare yayi sosai saboda haka kwanciya kawai sukayi. Haka suka yi kwanakin suna shakatawa karshe suka yada zango a Manitoba in da anan ne Amrah taga gata, sai da tayi kwallar farin ciki yadda Sultan yake tarairayar ta, tayi addu'ar Allah ya dawwamar da kauna a tsakanin su Allah ya kauda duk wani abu da zai shiga cikin rayuwar auren su da nufin ruguza su. Anan take jin ashe Ummi ce ta shirya musu tafiyar da kanta, kunya ta kamata da ya gaya mata, taji tana jin kunya idan suka koma. Ranar da zasu dawo Ummi da kanta ta tare su, Amrah na sussunewa amma sai taga kamar ma Ummin bata fuskanta ba, kawai sai ta fuske aka shiga hira da labari gwanin sha'awa. Sulalewa tayi ana cikin hirar ta gudu daki, ta kunna wayar ta wadda ta barta a gida tun ranar, ta turawa Afrah message ta kwanta rigingine tana tuna komai tana murmushi.     Sati guda suka kara a k'asar suka shirya tahowa inda suka yanke shawarar fara ziyartar dakin Allah su yi addu'a sannan su tafi., daga Gimbiyar har Maimartaban wani irin yanayi suke jin su, zasu tafi k'asar su abinda suka riga suka cire rai ma akai.    A chaan Masarauta kam suna cikin farin ciki, saboda labarin da Buzu yazo musu dashi na cewa lallai Ahalin Usman basu isa su tako kafarsu su shigo ba, ya kuma basu tabbacin anyi aiki sosai akan hakan,wannan ya kwantar da hankalin su ainun, suka shiga farin ciki da murna, har da had'a wata gagarumar walima akaci aka sha akayi hani'an sannan kowa ya kama gabansa a matsayar ranar da suka zaba zasu hadu dukkan su.     Yarima Bilal ko nace Sarki Bilal dai yadda zaku fi ganewa na kurbar tagomashin mulki,mulkin da zuba masa ido kawai sukayi zuwa lokacin da komai zai daidaita,shi a haukan ma gani yake kamar wai tsoron sa ne ya hana su tankawar, be san duk cikin su babu me raga masa, don ma ana ganin idon mahaifin sa shiyasa har suka kyaleshi ya kai wannan lokacin. ***Tun da suka ha wo jirgi sai jikin su ya kara sanyi, da wani irin tsoro tsoron abinda zasu je su tarar, amma sai zuwan su saudiyya ya rage musu kaso mafi rinjaye na cikin zulumin da suke ciki.   A wani babban hotel suka sauka nan kusa da harami, suka dukufa ibadah babu dare babu rana, aikuwa sunji dadin kwanakin nan fiye da tunani har suka dinga jin kamar babu wani abu a gaban su da suke shirin tunkara.    A dan zaman da su kayi a kasar sukayi sabo da wata mata yar k'asar Sudan da take zaune a k'asar me suna Hafsah, anan ta basu sirrukan turare da gyaran jiki, babu kunya Ummi ta saka Amrah a gaba sai da ta koyi komai a cewar ta wai su sun tsufa Amrah kuwa yarinya ce, chan k'asan zuciyar ta kuma ta nayi ne domin farin cikin Sultan. Ko da suka zo tafiya sai da sukayi kuka, musamman Amrah da suka yi masifaffen sabo da Hafsah tare suke zuwa duk inda zasu tsawon kwanakin nan, tayi musu hidima sosai shiyasa da suka zo tafiya suka ji duk babu dad'i, amma a haka suka hakura dan tafiyar su ta zama dole. Ta kuwa had'a musu sha tara ta arziki musamman kayan gyara da hadaddun turarurruka na jiki da na gida.    ***Kana ganin shirin da Daddy yayi kasan ko ba'a fad'a maka ba, mutanen da zai hadu dasu yau masu matukar muhimmanci ne a wajen sa, duk da tun ranar da sukayi maganar nan da Mah-Mah bata sake ko da kallon sa bane balle tayi masa magana, musamman da ta nuna masa zasu iya cigaba da boyewa ba sai Safwan din ya sani ba ko dangi, amma yaki yace ko da hakan shine last abu da zai yi dole ne, ba wai don baya son Safwan ba, sai dan sanin su waye tsatson Safwan din.    Da zai fita kamar ko yaushe sai da yayi mata sallama, ta amsa a ciki, ya girgiza kai kawai har yaje kofa sai kuma yace "Yau muna da manyan baki, bawan ALLAH da nake kulawar wa da dukiya da gidan marayun sa yana hanyar sauka a k'asar sa, sannan kinga su Sultan ma suna hanya, sai ayi abinda ya dace." Bata ce komai ba har ya fita, haka kawai sai taji duk wani iri, taji kamar zuwan nasu zai taso wani abu ne musamman da yace mata Sultan ma suna hanya tasan kuma dole ne idan tare suke cikin jirgi daya da bawan Allahn nan toh kuwa tabbas tare zasu sauka, kuma dai tare zasu iso gida tunda dole ne Sultan ya biyo Daddy su tawo. Daga nan kuma tasan da SULTAN din ya dawo za'a tada zancen Safwan dinta, shiyasa labarin zuwan nasu be mata dad'i ba, amma kuma tuna girma da martabar da bawan Allah nan yake dashi a wajen su, dole ne tayi wani abu, ko dan halacci da yayi musu da karamci.    Kamar ba zata tashi ba sai kuma ta mik'e tana kwala kiran mai aikinta Fati, da sauri ta shigo ta kofar kitchen hannun ta rike da duster, "Gani Hajiya." Ta dire akan kafarta "Akwai baki, muna da snacks din nan da yawa ko?" "Eh akwai jiya ma bayan kin shiga daki Maman su Afrah ta aiko da wasu." "Ok Allah sarki bata gajiya, toh ayi warming din su sai a dora abinci, zanzo na saka hannu amma ki dora ruwan abincin." Juyawa tayi bayan ta amsa ta wuce ciki, kaya Mah-Mah taje ta chanja ta dawo kitchen din tana tunanin abinda ya kamata a tanadar musu.    Har suka kammala komai wajen karfe ukun rana basu karaso ba, duk da dama Mah-Mah ba wai tasan lokacin saukar tasu bane amma kuma bata dauka zasu dauki lokaci haka ba, dakin Safwan ta nufa ta tarar a rufe, tasan shima inda yayi baya wuce airport din duk da be taba fita ba tun da aka sallame shi sai yau din, ta kuma san da k'yar idan bashi da Adnan bane kila har da Afrah ma suka tafi, komawa tayi ciki tayi kwanciyar ta bayan ta saka an kunna turaren wuta a babban falon da Daddy ke ajiye manyan bakin sa. A chan airport abun da ya faru yayi matukar daurewa Daddy, da Maimartaba rai, har da Sultan ma da be yi tunanin akwai wata alaka tsakanin su ba amma kuma sai yaga akasin abinda yayi tunani, tabbas Daddy tarar su Babah yazo airport din tunda shi dai basuyi magana ba bayan wadda sukayi ya fad'a masa ranar da zasu iso k'asar. Shi kansa Daddy ya shiga mamakin ganin Sultan din da kuma Maimartaba a tare, ga dukkan alamu ma tare suke, duk da iya kar dadewar da sukayi suna mu'amula da Maimartaban daidai da rana daya be taba sanin shi waye ba, be taba tambayar sa akam rayuwar sa ba, amma kuma a yadda ya gansu da Sultan da yadda yaga koman su tare sai yaji ya sake sinkewa da lamari, kenan bawan Allah nan da bashi da kamar sa a kaf Duniya shine mahaifin yaran sa Sultan da Safwan? Ko kuwa Yaya?    Isowar su Safwan wajen ya saka SULTAN jin wani iri, ya kama hannun Safwan ya jawo shi har gaban Maimartaba, yayi k'asa da kansa, da sauri Safwan ya durkusa har k'asa ya gaida mutumin da yaji wani irin kwarjinin sa ya kamashi, hakan da Sultan yayi yasa Maimartaba gane waye Safwan, ya kafe shi da ido kwalla na taruwa a kurmin idon sa, Allah hakim, shine yake tsara komai a yadda yaso, a kuma san da yaso, hannun Safwan din ya kama ya mikar dashi,ba tare da yace komai ba ya jawo shi jikin shi ya rungume yana jin kaunar shi na kama shi, kauna irin ta d'a da mahaifi wadda bab irin ta a kaf duniyar nan. Wani irin abu ne ya daki Daddy, da ya gama fahimtar komai cikin dan kankanin lokaci, wannan bawan Allah, shine mahaifin Sultan da Safwan, kuma shine wanda ya jima be ga mutum me karamci da dattakon sa ba,kuma shine tsohon Sarkin Masarautar Saji wanda a lokacin labarin abinda ya faru dashi ya zagaye ko ina a fadin k'asar. Sai yaji ya sake masa girma a ido, ya cika wajen gaba d'aya, cikar kamalar sa abun kallo ce, sai abu daya da ya lura dashi ta farat daya, komai nasa irin na Sultan ne hatta da yanayin tsaiwar da yayi, yadda yake magana a nutse da kuma yadda yake murmushin sa, duk na Sultan ne, hankalin sa ya maida wajen gimbiya, wadda ya tuna ta, itace dai wadda suke tare a wanchan lokacin, sai girma da ya sake nunawa a tare da ita akan wanchan lokacin, sai yaji wani irin tausayin ta,shigen wanda yaji a lokacin da basu da d'a, ita kuma da aka raba ta da nata fa? Ya taji kenan? Lallai tayi tawakkali fiye da shi wanda yayi a lokacin da ya tabbatar da ya rasa nasa, ya k'asa hakuri ya godewa Allah wanda dama shine ya bashi ya kuma karbe, amma sai yabi son zuciyar sa yayi abinda ayanzu zai zamar masa abinda zai dame shi ya hana shi sukuni. Duk da yasan be cuci daya daga cikin su ba, daga Sultan din da suka same shi daga sama har Safwan din da suka same shi tun yana summa, yasan yayi musu rikon da duk wani uba zai wa dan sa, ya kuma san sun chanchanci zama iyayen Safwan na gaskiya ko da basu haife shi ba, ko dan shayar dashi da Mah-Mah tayi. Amma kuma ba zai taba hana iyayen sa na asali suma su ji dadin dansu ba, dan su suka ma fisu bukatar shi. Har aka shiga motar, aka kuma dauki hanyar gida Daddy be dawo daga tunanin da ya tafi ba, wanda a daidai lokacin shima Sultan ya shiga tunanin alakar Daddyn da Maimartaba, sai da suka kusa isa gida Sultan da yake zaune a gefen Safwan da yake tuka motar, inda Ummi da Amrah da Afrah suke a a baya, ya ciro wayar sa ya kira Adnan, sukayi magana sannan ya kashe ya jingina kansa da jikin kujerar ya fad'a tunani. Yana so ayi komai a gama dan haka ne ma ya saka Adnan yaje ya dauko Maman Yara da Aminatu ya kuma tawo da Muhammad da Aysha zuwa gobe idan Allah ya kaimu ayi komai saboda yafi so su isa Masarautar Saji da karfin su. ***Nagode sosai da sakonnin ku, naji dad'i Allah saka da alkhairi, na samu sauki sai abinda ba za'a rasa ba. Masu korafi ban yi niyyar magana ba, amma duk wanda kaj ance bashi da lafiya toh fa bashi da lafiyar ne domin ba'a karya da ciwo, kwanana hudu kenan ana min karin ruwa (drip)har leda goma. Dole mutum ba zai samu lokacin kansa ba ballantana rubutu, shi rubutu dan nutsuwa ne, idan baka da nutsuwa ba zaka iya ba. Ina neman alfarmar zan dinga fashin kwana daya daya har muka abinda Allah zai yi. Nagode sosai Allah ya bamu lafiya baki d'aya.[7/6, 10:00 PM] Maman Maryam: ©® Hafsat Rano *Page 55* RanoNet www.ranonet.com.ng Register for your amazing data at a very cheap price. Mtn 1gb @300 naira only *** Isowar su yayi daidai da faduwar gaban Mah-Mah, taji kamar an dauke wani abu me matukar muhimmanci a rayuwar ta, ta mike da k'yar, lokacin da taji an bud'e kofar an shishigo, ta dauki hijab dinta da k'yar ta saka ta fito, suna zazzaune a falon, daya bayan daya ta bisu da ido kafin ta karaso ta zauna tana musu sannu da zuwa, idon ta ya tsaya akan Gimbiya dake zaune kusa da wani dattijon mutum wanda bata raba daya biyu shine uban gidan mijin nata, sai dai yadda ta tsammani ba haka ta gani ba, ta zata zata ga wasu iyayen kuma daban wanda suka iso tare da Sultan, amma kuma ganin yadda Sultan din ya zama free da mutanen da tayi wa kallon bakin Daddy sai taji tunanin ta ya kwance.    Gaisuwar da aka shiga yi tsakani ma duk hankalin ta baya kai, ta tafi tunani da addu'ar Allah yasa Sultan din shi kad'ai yazo, muryar Daddy ta tsinkaya a kanta yana maimaita "Hajiya ko zasu shiga ciki?" Da sauri tace "Bismillah Hajiya ,muje ciki." Murmushi Gimbiya tayi mata, ta maida mata itama sannan ta mik'e suka nufi ciki suka bar su a falon.    Tashi Sultan yayi, Safwan ma ya mike suka fita, Maimartaba ya bisu da kallo Daddy na lura dashi, yayi murmushi me kyau sannan ya maida hankalin sa akan sa "Nagode Nagode Nagode Alhaji Sulaiman, baki na ba zai iya kwatanta girman da kake dashi a waje na ba, nayi matukar farin ciki da na same ka a matsayin wanda sultan yake hannun sa, duk da dama na san cewa ko waye ya rike shi haka ba karamin mutum bane me girma da karamci, amma kuma ganin ka ya saka na kara tabbatar da cewa kaidin managarci ne, mutumin kirki ne wanda yasan ya kamata, kayi kokari wajen tarbiyyar su kuma har gobe kai ne uban su, basu da wani uba sama da kai, ina fatan amincin mu ya dore har zuwa zannatul Firdaus." "Amin Maimartaba, Amin ya Allah, ni kaina nayi farin ciki da yadda al'amarin ya juye, haka dama Allah yake al'amarin sa, wannan din tsarin Sa ne, shi ya ga dama hakan ta kasance bamu kuma isa muce don me?" "Haka ne, haka ne." Maimartaba yayi maganar yana girgiza kansa, yana jin farin cikin kasancewar mutumin da yake jin sa tamkar danuwansa a matsayin wanda ya rik'e mishi yara, riko irin na uba nagartacce. Sai kuma tunanin Muhammad ya fado masa, shi babu ilimin haka Allah ya kaddaro masa, amma babu komai hakan ma alhamdulillah. "Ina fatan Sultan ya sanar dakai komai game da labarin Safwan da yadda ya kasance a hannun mu." "Ya sanar dani, hakan ya kara girman ka a waje na, ka sani ba kuma zan dauke maka shi bane, har gobe daga Safwan har sultan duk ikon ka ne, ina so dai muyi zama na musamman saboda halin rayuwa, daga nan sai mu dunguma mu tafi Masarauta, idan komai ya daidaita shikenan." "Allah ya bamu sa'a, Nagode Nagode da dukkan abubuwan da kayi min a rayuwa, Allah ya saka maka da alkhairi." "Kayya, nine zan maka wannan godiyar domin samun mutum kamar ka ba karamin abu bane, gaskiya yanzu tayi karanci a cikin al'umma, abu ne da yafi komai sauki dan uwan ka yaci amanar ka, ya ha'ince ka idan ka amince masa, ni kaina na hadu da sharrin dan uwa na, yayi komai dan kawai ya samu abinda idan ma ya samu anan duniya zai yi shi kuma ya bar shi, kafin shi wasu sunyi sun shude haka za'a yi wasu ma bayan shi su shude, haka rayuwar take baki daya, yau kai ne gobe ba kai bane." "Tabbas haka ne, mutane ne basa ganewa, shiyasa ake yin abubuwa kawai ba tare da tunin gaba ba, son zuciya ya rufe wa mutane da yawa ido sun manta da ko babu tsufa akwai mutuwa, dole ne kuma ka girbi abinda ka shuka alkhairi ko sharri ***Tuni Gimbiya ta saki jikin ta da Mah-Mah, itama Mah-Mah da farko ta kasa sakewa amma ganin yadda matar ta sake da ita sosai yasa itama ta saki jikin ta, tare suka ci abinci tayi ta santin girkin da kayan snacks din, murmushi kawai Mah-Mah tayi tana jinjina wayewar matar, ruwan wanka ta had'a mata ta shiga wankan ita kuma ta fito ta saka fati ta tattare kayan da suka ci abincin ta gyara wajen.    Zama Mah-Mah tayi a falo ta jira ta fito, chan sai gata ta fito ta shirya ta zauna tana kallon tv fuskarta fayau cike da farin ciki wanda kallo daya Mah-Mah tayi mata ta gane yanayin da take ciki da zuwan ta k'asar. "Tunda muka zo banga Amrah ba?" Daya maganar tana kallon Mah-Mah "Auw nan kusa damu ne gidan su ai, ta chan ta fara zata shigo anjima k'adan nasan." "Ok Allah sarki, nayi kewar ta ne, Allah ya kawo ta." "Amin." Mah-Mah tace maganar na tsaya mata a makwallato, tayi kewar ta? Yaushe sukayi sabo haka har da zata ce tayi kewar ta?" "Allah sarki ai tana da shiga rai duk da rashin son maganar ta" Mah-Mah tace tana son maganar tayi tsawo ko ta dauki haske "Tana da shiga rai kam, jinta nake kamar yar dana haifa, naso 'ya mace sosai Allah be bani ba, shiyasa zuwan da sukayin nan yasa muka shaku sosai, gata da hankali da nutsuwa." "Haka mahaifiyar su take ai,mace me kirki." "Allah sarki.. "Sun samu tarbiyya sosai ai." "Ai daga gani, naji dad'i da ta kasance sirikar mu, sannan ta dace da Sultan, shi dinma ya samu tarbiyya nagartacciya, Shigowa Sultan da Safwan sukayi hannun su sarke da juna, hakan ya saka suka maida hankalin su wajen su, fara'ar da Mah-Mah ta gani shinfide akan fuskar Ummi ya saka ta karkare abinda take tunani. "Kuzo yaran albarka." Ummin tace tana mikewa, a Zbayyane take koman ta babu kunya, suka zube a gaban ta, ta kama hannun su dukka tana jin da ace yan biyun ta sun rayu da yanxu sun zama kamar Safwan, ina Aminatu ta shiga?  Tunanin ya gifta mata, tayi saurin girgixa kanta bata so tunanin ya bata mood dinta. "Wai ko a gidan ku Sultan ya sauka ne?" Mah-Mah da mamaki ya kasa barin ta, tayi maganar kirjin ta na bugawa "Achan suka zauna gaba daya, ai cewa nayi babu inda zasu sauka da ya wuce wajenmu, dole suka tattaro kayan su suka dawo." "Angode da dawainiya." Mah-Mah tace tana jin relief,katse mata hanzari Sultan yayi da maganar sa da bata zata ba. "Mah-Mah..." "Na'am Sultan?" "Sune iyayena..." "Na'a..aam!??" "Anjima in sha Allah za'a zauna sai ayi duk maganar da za'a yi, akwai bakin da zasu zo anjima k'adan in Sha Allah, ina fatan dukkanmu mu amfana da zaman, ina kuma fatan a samu fahimtar juna a zaman da za'a yi." Sultan yayi maganar kansa na k'asa.     Jikin Mah-Mah ne yayi sanyi, ta juya da sauri ta kalli Safwan da suke magana da Ummi cikin farin ciki, bata jin me suke cewa saboda yadda gaba daya jinta ya dauki a lokacin, kwalla ta taru a idon ta, Sultan da yaga komai yayi sauri mikewa "Mah-Mah ina magana." Ya juya yayi hanyar corridor da zata kaika bayan gidan, tashi tayi da k'yar tabi bayan sa,ta same shi a tsaye ya hard'e hannuwan sa, yana ganin ta ya dire akan kafafuwansa, ya hade hannayen sa waje daya yace "Mah-Mah dan Allah kiyi hakuri, nasan ba abu bane me sauki a wajen mu baki daya musamman Safwan, dan Allah kiyi hakuri." "Sultan me yasa baka son farin ciki na? Ashe banyi maka abinda na chanchanci farin ciki ba? Ashe baka dauke ni a matsayin uwa ba Sultan? Kasan yadda nake ji? A duk ta dalilin ka? Kaine ka dage da bincike har ka gano wannan abun, duk da kuma kasan yadda abun zai taba ni amma ka share, burin ka kawai yadda zaka kuntata min ka hanani farin ciki, saboda kuskure daya da nayi kuma na baka hakuri akai, me yasa Sultan? Me yasa?" "Wallahi Allah shine shaidata, banyi hakan domin nasan abinda zai faru ba kenan, ban taba tunani ko hasashen hakan ne zai kasance ba, ta yaya zan so tashin hankalin ki bayan ke din kece kikayi min dukkan gata, kike rik'e ni tamkar dan cikin ki, me yasa zan so ki shiga damuwa?" "Saboda taurin zuciya irin taka Sultan, saboda nayi maka laifi shine nima kake so ka kuntata min, idan har gaskiya kake fad'a me yasa ba za'a bar maganar Safwan ba? Me yasa ka dage lallai-lallai sai ka musguna min ka raba ni da abinda ka san bana had'a soyayyar sa da kowa?" "Saboda hakan shine daidai, saboda dole ne Safwan yasan iyayen sa, yasan ba mune muka haife shi ba, yasan wadannan bayin Allah masu karamci sune iyayensa, sannan suma su san dan su." Daddy yayi maganar fuskar sa a had'e tamau, juyowa sukayi da sauri ta kalle shi, ya karaso yana sake tamke fuskar sa dan har ga Allah Mah-Mahn ta soma fusata shi. Dora yayi ya cigaba bayan ya tsaya a gaban ta "Idan har kince ba'a miki adalci ba, su kuma iyayensu suce me? Mahaifiyar su tace me? Rasa yara har uku tsawon shekaru ba abu bane me sauki, bata taba sanin ya kake ji ba akan yayanka, gwara ke kinyi experiencing motherhood amma ita fa? Kinsan irin bakin cikin da ta kunsa? Kinsan me tayi going through all this year's? Baki sani ba, kawai farin cikin ki kike Kira, karki zama mace me son kanta, me butulcewa rahmar ubangiji." "Dan haka dole Safwan shima ya san iyayen sa, su sanshi, ya rage nasu suce ya zauna damu,ko kuma su bukaci dan su kusa da su, duk hurumin su ne, ikon su ne ba namu." "Iyayena Daddy? Ba kune iyaye na ba dama!!!?" Yayi maganar hawaye na zuba a idon sa sosai, da sauri Sultan yayi wajen sa, ya rik'e shi a jikin sa yana jin hawayen na neman zubo masa shima amma yayi ta maza ya tare su, dan baya bukatar su yanzu "Tabbas abinda kaji shine gaskiya Safwan, mutanen da suka zo tare da Sultan a matsayin iyayen sa kai ma sune iyayenka, dole ne ka sani dan ranar wanka ba'a boyon cibi, duk da haka ku dukka yayanmu ne, ba wai hakan na nufin babu ku babu mu ba, amma suma suna bukatar sanin ku." "Daddy...!?" "Karka ce komai, idan kaji wani iri a zuciyar ka kayi addu'a, ka kuma godewa Allah da baiwar da yayi maka, su din iyaye ne da kowanne d'a zai yi burin kasancewa dasu." "Alhamdulillah ya Allah." Kawai ya furta, ya runtse idon sa da karfi hawaye na cigaba da sauka a idon sa, hannun sa Sultan yaja suka fice ta kofar bayan sannan suka dangana da dakin su. A durkushe suka tarar da ita tana kuka sosai, kamar zata shid'e, duk da kukan itama Mah-Mah take yi amma sai tayi saurin yin wajenta, ta rik'e ta ta tada ita tana kyautata zaton taji komai, kai tsaye daki suka nufa ta zauna da ita a gefen gadon dakin ita ma ta zauna dukkan su babu wanda yayi yinkurin tsaida hawayen da yake zubarwa babu kuma wanda ya tanka a cikin su.    Zuwa wani lokaci zuciyar su ta fara sauka a hankali, Ummi ce ta zame ta sauka k'asa, "Tabbas dani dake muna kan abu daya ne, sai dai ni nawa farin ciki ne, inda naki ya zama bakin ciki, nasan yadda kike ji saboda na shiga irinsa tsawon lokaci, sai yanzu Allah ya kawo karshen damuwa ta, ashe akwai ranar da zanyi farin ciki nima? Karki ga kamar bana tausaya miki halin da kike ciki, ina tausayin mu dukka amma kuma ina bukatar yaya na, ina bukatar su kwatankwacin yadda kike bukatar su, amma duk da haka bana nufin dauke miki su, har abada ke din kece uwar su, basu da kuma wata uku a bayan ke." "Nagode Allah ya saka da alkhairi, ba abu bane me sauki rana daya kana tare da danka ace ba danka bane, kowacce uwa ce dole zata shiga tashin hankali balle ni da dukkan komai nawa ya tattara ne akan Safwan, ina yi masa son da ban san adadin sa ba, ina kuma tunanin dalilin shayarwa ita ta kara shakuwar mu, amma babu komai haka Allah ya kaddara min,nayi imani da kaddara mai kyau ko mara kyau." "Na sani, nasan yadda kike ji... Kiyi hakuri Safwan dan ki ne,ke ya sani jiya, ke ya sani yau ke kuma zai cigaba da sani har gobe, ke din kece mahaifiyar sa." "Nagode, nagode Nagode Allah ya saka da alkhairi." "Amin ya Allah." ***Suna zaune suna hira Adnan ya shigo, dama tun tafiyar Sultan shine yake kula dasu yake musu komai bisa umarnin Sultan din, yanzu ma kiran da yayi masa yasa shi wutowa nan din kai tsaye bayan sun tashi daga wajen aiki. Gaisawa sukayi ya fad'a musu Sultan ne yace yazo ya tafi dasu, a shirye suke dama sai kawai suka rufe kawunan su suka bishi, daga nan suka wuce inda zasu dauki Muhammad da Aysha wanda dama tuni ya kira Muhammad din a waya tunda shi din ma da Sultan din zai yi tafiya ya had'a shi dashi sai ya zama komai zasuyi sai sun sanar da Adnan din. Haka ma case din Madaki Adnan din ne akai shi yake yin komai.    Isar su kofar gida yayi daidai da fitowar Amrah da Afrah zasu shiga gidan Mah-Mah, ganin motar Adnan din ya saka suka fasa shiga suka tsaya suna kallon motar da mutanen dake cikin motar. Ganin su Maman Yara ne ya saka su saurin matsawa, suka gaisa sannan sukayi wa Amrah sannu da zuwa sannan suka dunguma suka shiga gidan inda Adnan ya wuce zuwa nasu gidan dan a gajiye yake tikis yana bukatar hutu.    Kai tsaye falon Mah-Mah suka zarce, Muhammad ya tsaya daga harabar gidan be bisu ba. Lokacin Sultan suna zaune da Safwan yana warware masa yadda abubuwan suke, yayi shiru yana sauraron san yana kuma mamakin yadda akayi abubuwan suka zama haka.    Kuka ba shine zai chanja komai ba, sbaoda haka ya tsaya kawai yana sauraren sa, tausayin Ummi da na Aminatu ya kamashi, yasan duk cikin su babu wanda be shiga damuwa ba ta dalilin su amma kuma sai yaji yafi tausayin matar da aka ce ta dauki cikin su tsawon watanni goma sha, ba mutum daya ba kuma har biyu, duk da cewa anyi amfani da komai daga wajen Maimartaba da Gimbiya akayi mata dashen dashi amma kuma dole ne a kirata da mahaifiyar su, ita tayi komai na dawainiya dasu a ciki ta kuma haife su duk kuwa da C's akayi mata aka cire yaran.    Tunanin yadda zai gansu ya hau yi, yana tuna lokacin da suka hadu da Muhammad a wajen da suka je tafiya da Amrah, da yadda yaji wani abu game dashi a lokacin Amma sai ya bar hakan ba matsayin tausayin sa da kuma sadaukarwar da yayi ba tare da yasan wace Amrah ba.    Zabura Ummi tayi ganin wadanda bata taba saka ran gani ba, "Azizah, Aminatu?" Ta kira sunan su tana mikewa da sauri, jikin ta na wani irin rawa kamar mazari, durkusawa sukayi a gabanta, lokacin har Aminatu ta fara kuka, kukan da ya tuna mata da abun da ya faru. A gefen su Ummin itama ta durkusa, tana jin burin ta da addu'ar ta, ta gama cika a yanzu, duk addu'ar ta da ta dad'e tanayi akan wannan ranar ce, akan wadannan mutanenn sai gashi Allah ya had'e mata su a lokaci daya.     Babu wanda ya yi yinkurin bawa wani hakuri, suka sha kukan su suka more, sannan ne suka dawo hayyacin su, aka shiga tambayar bayan rabuwa, da kalar rayuwar da suka fuskanta.    Daddy ne yayi kiran Mah-Mah a waya yace duk suzo falon sa gaba d'aya, tashi sukayi suka dunguma chan kowa ya zauna aka sake sabuwar gaisuwa sannan Sultan da ya zama kamar shine mahadar kowa ya fara magana a nutse.    A wannan zaman, kowa ya fahimci yadda abubuwan suke, labarin Aminatu ya taba kowa dan kusan kowa sai da ya zubar da kwalla da tana fad'an kalar azabar da tasha a hannun azzaluman mutenan.    Anan aka gabatar da Safwan da Muhammad a matsayin yan biyun da akayi mata dashen su, inda Muhammad ya rayu tare da Safiyya shi kuma Safwan Madaki ya bada shi a wajen su Daddy. Sosai maganar ta daki Muhammad, dan har yaso yafi Safwan shiga cikin yanayi akan maganar ko kuma dan shi ba a lokacin yaji maganar ba?    Kallon su Aminatu ke yi hawaye masu zafi na fita daga idon ta, su dinma ita suke kallo, kowa da abinda yake tunani akan Al'amarin. Ummi kam ba'a cewa komai, fasalta yanayin da take ciki na farin ciki ma bata baki ne, sai ta kalli wannan ta kalli wannan ta rasa ina zata saka kanta don murna, samari ne dukkansu masu jini a jiki, masu kyawu da cikar kamala,duk kuwa da nakasun ilimin dake tare da Muhammad amma shi din ma bashi da aibu, ya kuma samu ilimin sa na addini daidai da yanayin sa da yanayin rayuwar da suka taso a ciki.    Sai bayan komai ya lafa ne, Maimartaba yayi gyaran murya, sannan yayi bayani cikin jawabin sa wanda ya saka kowa a cikin farin ciki. Suka kuma daura aniyar yin komai domin kaman ya kasance kamar yadda yake a tsare.    Da haka taron ya kare bayan dogon lokacin da suka dauka ana yin sa. *Two weeks later*     [7/6, 10:02 PM] Maman Maryam: ©®Hafsat Rano Page 56 RanoNet www.ranonet.com.ng Register for your amazing data at a very cheap price. Mtn 1gb @300 naira only **** Motocine guda Biyar dukkansu rufe suke ruf da bakin glass, motar farko Muhammad  ne yake tuka ta, Sultan a gefen sa sai Daddy da Maimartaba a baya, ta biyu kuwa Ummi ce a ciki da Amrah da Maman Yara, Safwan ne yake jan motar, sai ta uku Mah-Mah ce da Aminatu, sai Aysha Adnan na tukawa,in da motocin karshe guda biyu suka kasance kaya ne cike a ciki sai driver kawai. A kofar Masarautar suka ja suka tsaya, masu tsaron kofar duk suka zuba musu ido, cike da mamakin zuwan nasu duk kuwa da gagarumin taron da ke gudana acikin Masarautar, babban cikin su ne ya taso ya iso wajen motar ya kwankwasa glass din, Sultan ya juya baya ya kalli Maimartaba, yayi masa izini ya bud'e, ya bud'e a hankali, da sauri me tsaron kofar ya daga hannun sa sama ganin Sultan din cikin shigar kayan sarauta hadda rawani irin na manyan Masarautu dauke da kunnuwa biyu. "Allah ya baku yawan rai, Barkan ku da zuwa Babbar Masarautar irin Masarautar Saji." Babu wanda ya tanka sai lumshe Ido kawai da Sultan yayi masa kad'an ya bud'e su, da gudu ya koma wajen kofar ya saka aka wangale kofofin suka tura motocin su ciki, masu tsaron kofar suka bi bayan motocin da akayi wa lamba da SMMS 1 har zuwa 4 da kallo suna tunanin wadanne Masarautar ne suka zo haka, daga gani Babbar Masarautar ce.    Kai tsaye gaban Babbar Fadar suka nufa, dama Sultan yasan wajen, da ido kawai Maimartaba yake bin komai zuciyar sa babu dadi, yana tuna abinda ya faru a shekarun baya, har suka samu waje sukayi parking idanun mutane basu bar kansu ba, gaban fad'ar a cike take taf, babu abinda kake ji sai kid'ekid'e da bushe bushe.    Daga ciki manyan Masarautar ne suna cike da farin ciki, Sarki Bello Moddibo Saji be fito ba, suna ciki suna magana da Bilal wanda ya tubure lallai ba zai bada Sarauta ba, wanda suke so a yau ayi komai ya maida wa mahaifin nasa sarauta, tun suna lallaba shi har suka fara yi masa wuta wuta amma be sa ya saduda ba, sai ma maganganu da yake fad'a har yana ikirarin zai saka a rufe duk wanda yace zai kawo masa cikas ciki kuwa har da mahaifin nasa, abun yayi matukar basu mamaki basu kuma yi tunanin iskancin nasa ya kai haka ba, gashi dole dai suna bukatar abubuwan da suka zama jigon Sarautar daga wajen sa kafin su gudanar da komai.   Karar jiniya ce ta cika Masarautar wadda ya saka su maida hankalin su gaba daya, suka fito da sauri da mamakin zuwan Maigirma gwamna wanda daga jin jiniyar kasan shine, babu sanarwa zuwan ba zata hakan ya nuna lallai akwai wani babban al'amari, a gefen da su Sultan sukayi parking motocin su a gefen nan ne motocin mai girma gwamna suka tsaya suma. Ganin haka ya saka Maimartaba Sarki Usman Muhammad Moddibo ya balle murfin motar ya fito, Sultan, Safwan da Muhammad suma suka fito a kusan lokaci daya, suka tsaya daga bayan sa Sultan a tsakiyar su kowannen su sanye yake da shigar Sarauta, idanun Sultan makale da glass dan siriri fari wanda ya sake fito dashi sosai, zoben hannun sa ya shafa kad'an lokacin da suka karasa wajen Maigirma gwamna da ya taho suka hadu.   A daidai lokacin Sarki Bello da mukarraban sa suka fito da sauri. Wata irin zabura sukayi dan ganin wanda basu taba tunani ko hasashen gani ba, hasali ma makasudin wannan taron nasu akan nasarar da suka samu akansa ne, a firgice suka bi yara matasan dake bayan sa, idon Sarkin ya sauka akan hannun Sultan da yake murza zoben yana kallon cikin idon sa wanda kana gani kasan da biyu yayi hakan, daga nan inda suke aka rasa wanda zai karaso ya tarbi Maigirma gwamna. Kallon Maimartaba Gwamna yayi sukayi murmushi sannan suka haura zuwa inda suke tsaye zufa na karyo musu. Take musu baya su Sultan sukayi kowannensu fuskar sa dauke da farin ciki mara misaltuwa.   Fuskar Sarki Bello kad'ai zaka kalla ka tabbatar da irin tashin hankalin da ya shiga, ya kasa furta kalma daya har suka cimmasa, sai a lokacin yayi ta maza ya shiga yiwa Maigirma gwamna sannu da zuwa, amma kuma idon sa yana kan Sarki Usman da yake masa murmushi me cike da ma'anoni ta cikin nadin sa. Kamar wanda aka bige wa kafa haka ya jasu zuwa cikin fad'ar inda a lokacin kowa ya tsure, duk suna tsattsaye kamar wadanda aka dasa, kansu duk a k'asa musamman wadanda suka zama masu fuska biyu a wajen Sarki Usman din.    Kai tsaye kujerar da aka tanada domin gwamna nan ya zauna, Yarima Bilal ya yi saurin danewa kujerar Sarkin, kunya ta kama Sarki Bello amma ya kanne ya samu gefe ya zauna, daf da shi Sarki Usman ya zauna shima yayi saurin kallon sa, gefe Maimartaba ya kalla kamar be san me kallon nasa yake nufi ba. Daga wajen fad'ar tuni wajen ya kaure da ife-ife da sowa, babu abinda kake ji sai murnar mutane kowa na kokarin tofa albarkacin bakin sa, manyan da suka san waye Sarki Usman suka shiga bawa yaran da suka taso bayan tafiyar sa labarin irin halayen sa, wanda dama sun jijji wasu a wajen iyayen su, abin ka da matasa masu jini a jiki, tuni suka dauki hayaniyar suka shiga buga abubuwa suna kiran sunan Sarki Usman, hakan ya sake saka Sarki Bello da mukarraban sa a matukar tashin hankali, gashi har lokaci Maigirma gwamna be ce komai ba akan zuwa bazatan da yayi, sai amsa gaisuwa kawai yake yana murmushi.    Kokarin daidaita wajen akeyi dan tuni wajen ya dinke taf da mutane, wane gaya wa wane har mata ma dake cikin Masarautar duk sun fito, wasu na kuka, kukan farin ciki wasu na dariya.    Ummi da hawayen ta ya cigaba da sauka ta dinga binsu daya bayan daya daga cikin motar kukan ta na karuwa, tana jin wani abu yana zagaye kowanne lungu da sako na jikin ta, niyyar bud'e kofar tayi Amrah ta riko hannun ta da sauri. "Ummi karsu yi miki wani abu, kiyi hakuri wajen ya lafa." Komawa tayi ta zauna tana girgiza kanta, sai kuma tasa tafin hannun ta, ta toshe bakin ta gudun kar kukan ya fito sosai.   Duk yadda jami'an tsaro da fadawa sukayi kokari tsaida mutanen nan amma abin ya fassaka, ihu kawai suke suna Kiran sunan Sarki Usman. Duk abin nan da ake a kunnen Sarki Bello da jama'ar sa, gashi kunya duk ta kamashi abinda Yarima Bilal yayi masa balle yayi wani abu akai, yana nan zaune kamar kowa Gwamna ya tashi ya soma magana, "Assalamu alaikum warahmatullah wabarkatuh..." Yayi sallama "Wa alaikumussalam warahmatullah wabarkatuh." Jawabi ya shiiga yi akan makasudin zuwan sa Masarautar, da labarin da ya samu na saukar Sarki Bello ya dora dansa akai, yaron da duniya ta tabbatar da rashin chanchantar sa da zama shugaban al'umma, dan haka ne gwamnati ta shigo ciki, ta kuma bada umarni bisa ga sharadin da yake a shashi na 104 na dokar k'asa, ta sauke Sarki Bilal daga kujerar mulki ta nad'a Yarima Muhammad Sultan Usman Moddibo Saji a matsayin sabon sarkin Masarautar Saji, bisa ga dalilai masu karfi da duk wanda yake cikin nan wajen yasan su, ya kuma san zabin da gwamnati tayi ba zabi ne irin na tumun dare ba, zabi tayi bisa chanchanta da dacewa, ta kuma yi amfani da koke da korafin al'umma domin ita gwamnati dama ta mutane ce." K'asa k'asa maganganu suka dinga tashi a cikin fad'ar, wani daga cikin dan majalisar sarki ya mik'e yace "Bama goyon bayan wannan sabon tsarin, bamu yarda da shigo mana da bare cikin mu ba, bamu da masaniya akan waye Muhammad Sultan da har za'a bashi damar mulkarmu,saboda haka muna so gwamnati tayi mana bayani yadda zamu gane." Murmushi kawai Maimartaba yayi, ya sake gyara zama yana kallon yadda wasan yake tafiya, Sultan da yaji kamar an dora masa wani abu a take, yaji baya shakka ko tunanin wani a wajen ya tashi, ya daga hannun sa duk suka zuba masa na mujiya, "Sultan Usman Moddibo Saji, babban d'a ga Sarki Usmwn Moddibo Saji, wanda aka raba shi da mahaifiyar sa tun yana ciki, aka so salwantar da rayuwarsa, cikin jahilci da rashin sanin cewa duk wanda Allah ya kaddara masa rayuwa babu wanda ya isa ya hana shi, shine yau a gaban ku, dauke da abinda kuka rasa, wanda ya zama kamar wata shaida ce ta zama cikakken Sarki me iko, ina fatan wannan..." Ya nuna zoben hannun sa "Ya ishe ku hujja... Saboda haka idan akwai me yin magana sai yayi." Tashi gwamna yayi, "Za'a aiko wakili da rubutacciyar takarda akan sabuwar dokar da gwamnati ta saka, sannan gwamnati ta shirya yin nadin sabon sarki nan da kwana uku idan Allah ya kaimu, saboda haka kuna da nan da kwana ukun ku karkare komai." Da haka ya juya, masu tsaron lafiyar sa da mukarraban sa na gwamnati suka take masa baya, babu wanda ya iya tashi ya rakashi, yana fita wani tsoho cikin bacin rai yace "Gimbiya bata da d'a, bata taba haihuwa ba, ta ya akayi aka haife ka, kuma ta yaya ka mallaki zoben hannun ka?" "Ni da kai da kowa anan da duk wanda yake da hannu yasan cewa Gimbiya na da 'yaya ba d'a ba, ya kuma san yadda akayi gimbiya ta rasa d'anta na farko." "Karya kake yi yaro, karka zo mana da sabon abu nan kaji." "Ka iya bakin ka, ka kuma rik'e girma da tsufan ka, kafin kayi nadama." Shiru yayi ganin yadda Sultan din yayi magana fuskarsa a had'e, sosai ya fito a jinin sarautar sa, tamkar mahaifin sa lokacin da yake kamar sa, komawa yayi lakwas be sake magana ba, ran Sultan da ya baci ya kalli fadawan da suke kofa a zafafe yace "Akwai baki a mota a shigo dasu." Rige rigen fita suka yi, aka je aka shigo dasu Amrah, babu wanda be yi shock ba ganin Gimbiya, Maman Yara da Aminatu a tare.    Sarki Bello ya tashi da sauri yana nuna Maman Yara da hannu "Atika! Atika!" "Allah ya taimake ka,Nice nan maafarki kake ba." "Ina kika shiga, tsawon wannan lokacin." "Ina nan ina ruwa kamar yadda Allah ya hukunta sai nayi." "Inaaaa... Inaaa jinjirin da... daa.. kike tafi tashi." Ya karashe kamar an fizgo maganar. "Gashi nan a gaban ka, Allah yayi hukuncin Sa akan shi, ya raya shi rayuwa me inganci." "Daa..maaa...ha'iin..ta ta ki.. kayi??" "Idan hakan na nufin ha'inci ba? Toh hakan ne." "Ke! Ki kula da wanda kike magana dashi." Wani bafade yayi maganar yana daka mata tsawa. Wani kallo Sultan yayi masa, ya dauke kansa yana cije bakin sa. Tasowa wasu dattijai su biyu masu farin gemu sukayi, suka matso suka kama hannun Sultan, yayi musu murmushi kad'an ba tare da ya saki fuskarsa ba, cikashi sukayi suka isa gaban Sarki Usman suka zube kowannen su kansa a k'asa "Barka da zuwa Sarkin sarakuna, hakika mun yi matukar farin ciki da dawowar ku, Allah ya tsare ku ya kare ku a duk inda kuke, Alhamdulillah." "Barka dai Wambai, barka dai Waziri." Ya amsa musu a ciki fuskar sa dauke da fara'a. Masu Nad'in Masarautar ne suka matso kusa, aka umarci Yarima Bilal da ya sauka, aka ce wargi ma wuri yake samu, yadda yaga Sultan, Safwan da Muhammad, da kuma yadda yake jin ihun mutanen ciki da wajen Masarautar yasan bashi da damar musu domin idan yace zai ja komai zai iya faruwa, ya lura da yadda jikin su Sarki Bello ma yayi tubus balle shi karamin kwaro, ko babu komai ai ya d'ana, shiyasa ma ana cewa ya saukan ya sauko babu musu, Sultan ya dare kujerar aka shiga nada masa rawani sannan aka bashi abubuwan da suka zama cikin dokoki da sharudan zaman mutum Sarki a Masarautar ta saji, cikin kankanin lokaci akayi komai aka gama, aka tabbatar da Sultan a matsayin sabon sarki, labarin da ya shiga kowanne lungu da sako na k'asar ma baki daya, hakan ya kara saka mutanen gari a cikin farin ciki, baka jin komai sai murna da sambarka. Kafin kace kwabo wajen Masarautar ta dinke tsaf da mutane ta kowanne lungu tuttulowa suke domin nuna farin cikin su bisa nadin sabon sarkin da ya kasance da ga adalin Sarki, Sarki Usman Muhammad Moddibo Saji wanda mutane suke kauna.    Dole aka raka su Ummi cikin Masarautar saboda maza manya da masu kudi da yan siyasa dake ta shigowa kowa yaji dawowar Sarkin sai ya taho. Daya bayan daya Sarki Bello da mukarraban sa suka dinga ficewa har suka gama ficewa tas ya zama babu sauran kowa sai Sabon Sarki SULTAN da yan uwansa a gefen sa da Maimartaba da jama'ar sa.     ****Bayan abubuwan sun fara lafawa ne Sarki Muhammadu Sultan ya saka aka kirawo tsohon Sarki Bello da jama'ar sa, suka dawo cikin fad'ar, daga nan ya saka aka je kurkuku aka fito da kowa ya saka aka taho da Safiyya nan, aka kuma kirawo su Maman Yara duk suka hallara, kan Sarki Bello a k'asa yana tunanin abinda Sultan din zai ce. Maimartaba ne yayi gyaran murya bayan kowa da ake bukata ya iso, ya soma jawabi a nutse "Ina yiwa kowa fatan alkhairi ina kuma fatan na samu kowa lafiya bayan dogon lokacin da na dauka bana nan ni da mai daki ne,wanda da yawan ku anan kunsan makasudin da hakan ta faru, wanda zan iya cewa rami ne ka hak'a mun Bello ka tura ni ciki duk kuwa da yardar da nayi da kai, sai dai duk da haka babu abinda zan maka ko nace maka, sai dai fa ka sani dole ne zaka girbi abinda ka shuka tun a duniya..." "Kai ne ka bani shawarar yiwa baiwar Allah Aminatu dashe, ashe ba da zuwa daya ka bani shawarar ba, sai dan na fad'a ramin da ka hak'a min me matukar zurfi." "Sannan kuma da kai ne aka had'a baki wajen rama ni da d'a na, duk kuwa da lokacin ban san har da kai ba sai daga baya, nayi mamaki k'warai da na same ka kai da Buzu a cikin irin wannan abun,bayan kaf Duniya babu wanda nafi yarda dashi kamar kai, haka babu wanda gimbiya ta yarda dashi kamar dan uwanta buzu, sai kuma ya zama na ashe ku din da muka aminta daku kuñe kuka lalata mana farin ciki... Ku da kuka fi kowa kusanci damu..." "Kiyi hakuri Gimbiya da abinda zaki jii..."  Ya kalli bangaren da Ummi take yayi maganar sannan ya cigaba "Mahaifin ki da dan uwanki Buzu su suka taimaka wajen shigar ki kunci da bakin ciki tsawon wannan lokacin, da taimakon su Bello ya zama duk abinda ya zama haka da taimakon su aka raba ki da gudan jinin ki, bani da gamsasshiyar hujja a lokacin shiyasa ban iya yi miki bayani ba. A lokacin da abun ya faru, nayi amfani da damar wajen sanya Aziza ta fita da jaririin daga Masarautar ,a tunanin su baya numfashi, wanda nasan idan suka san haka zasu halaka shi ne ko ta halin kaka, shiyasa na nuna miki bansan abinda ma kike magana akai ba, nayi kamar bansan kullin da akayi ba duk kuwa da bansan su waye kai tsaye ba amma nasan abinda suka shirya. Abinda yasa tsawon wannan lokacin ban sanar miki da abinda ya faru ba, saboda bani da masaniyar inda Aziza take, bansan inda zan neme ta balle naji halin da jaririn yake ciki, a tunani na ma ko bashi da rai ko kuma sun kama su sun yi musu wani abun. Dalilin haka yasa na kamu da ciwon hawan jini me karfi...Page 57 RanoNet www.ranonet.com.ng Register for your amazing data at a very cheap price. Mtn 1gb @300 naira only Mahaifin ki da dan uwanki Buzu su suka taimaka wajen shigar ki kunci da bakin ciki tsawon wannan lokacin, da taimakon su Bello ya zama duk abinda ya zama haka da taimakon su aka raba ki da gudan jinin ki, bani da gamsasshiyar hujja a lokacin shiyasa ban iya yi miki bayani ba. A lokacin da abun ya faru, nayi amfani da damar wajen sanya Aziza ta fita da jaririin daga Masarautar ,a tunanin su baya numfashi, wanda nasan idan suka san haka zasu halaka shi ne ko ta halin kaka, shiyasa na nuna miki bansan abinda ma kike magana akai ba, nayi kamar bansan kullin da akayi ba duk kuwa da bansan su waye kai tsaye ba amma nasan abinda suka shirya. Abinda yasa tsawon wannan lokacin ban sanar miki da abinda ya faru ba, saboda bani da masaniyar inda Aziza take, bansan inda zan neme ta balle naji halin da jaririn yake ciki, a tunani na ma ko bashi da rai ko kuma sun kama su sun yi musu wani abun. Dalilin haka yasa na kamu da ciwon hawan jini me karfi wanda nasan zai bini har karshen rayuwa ta. Tabbas shi zalunci dan aike ne, koman daren dadewa zai dawo wa me shi, sai gashi a lokacin da bakayi zato ba, na dawo tare da kuma abin mamaki da al'ajabi, albarkar yara uku riris masu daraja da cikakkiyar tarbiyya, kaga ko anan ya kamata ka gane duk abinda Allah ya kaddara zai faru toh babu makawa sai ya kasance." "Haka yake Sarkin sarakuna." "Saboda haka zan bar komai a hannun Sarki Muhammad Sultan, duk hukuncin da ya dace daku zai muku shi tunda yanzu ni ba hurumi na bane." "Kasan dalilin da ya saka nayi maka haka? Sau daya ka taba zama kayi tunanin halin da nake ciki bayan mahaifin mu ya fifitaka akai na? Komai nasa kaine, magana daya biyu sunan ka zai kira, be taba tunawa dani ba ko kuma yayi magana ta ba, kai ne kawai a gaban sa, duk abinda ya faru shine ya jawo, shine ya assasa tsanar ka a zuciya ta, ya saka naji babu abinda ba zan iya ba akan ka." "Wannan ba hujja bace, wannan ba uzuri bane Bello, saboda son faran tawa kanka sai ka cutar dani cuta mafi muni da girma? Akan me? Me nayi maka tsawon rayuwar mu da na chanchanci wannan toxarcin daga gareka? Ban taba zartar da abu ba tun da na hau mulkin nan sai da yardar ka, na yarda da kai saboda kai din dan uwa na ne, jini na, amma me kayi? Kayi amfani da hakan ka cutar dani da iyali na da basu ji ba basu gani ba, Bello shi mulki da kake gani na Allah ne, wanda yaso yake bawa, ba wai zabin mutum bane, saboda haka hujjarka bata isa hujjar da zaka aikata min wannan danyen aikin ba, bayan korar da kuka saka akayi min irin korar kare, kuka samin ciwo me nauyi Wanda zan ji bana sha'awar komai da ya shafi k'asar ma baki d'aya." Dukkan gurin kowa yayi tsit ana sauraron Maimartaba, yayi magana me tsawo da ma'ana. Shigowar da akayi da Madaki ne ya katse maganar Maimartaba, aka kuma juya maganar zuwa abubuwan da suka faru da yadda suka faru suka kasance din, Maman Yara ta basu labarin yadda tayi bayan ta tafi da Sultan da irin wahalar da ta sha sosai kafin Allah yasa ta samu aikin nan a gidan marayun, kowa sai da ya jinjina mata yadda ta sadaukar da rayuwar ta domin cika alkawarin da ta dauka wa maimartaba a lokacin da zata bar Masarautar.    Safiya ma da tun shigowar da akayi da ita Aysha ta koma jikin ta, ta makale ta bada labarin yadda sukayi da yan biyu, da yadda sukayi rayuwa bayan ta rabu da Madaki, da yadda ta raini Muhammad din da yar da ta haifa Aysha ita da Madaki. Ta karkare da "Ban san inda ya kai jariri dayan ba, babu kuma tambayar da banyi masa ba akan hakan, amma be sanar dani ba, sai ma chanja min da yayi cikin lokaci kad'an yayi kud'i ya gina gida yayi aure ni kuma ya rufe babi ba, duk da haka nasan inda yake ina bibiyar koman sa har zuwa lokacin da na same shi, sai kuma dauke ni da aka zo har gida akayi, aka kawo ni nan aka shiga azabtar dani duk dan na sanar musu da inda yan biyun suke dan sun gani a tsafin su yaran suna raye dukkan su, sannan sun ga cewa biyu suna tare da da juna daya kuma daban amma kuma sun kasa ganin komai bayan wannan, bazan iya fad'a musu ba, dan yadda nake son Aysha haka nake son Muhammad, shiyasa na gwammace su kashe ni akan na fad'a musu wani abu." Gaba daya dakin ya sake yin shiru, Jijiyoyin kan Sultan suka sake fitowa sosai suka yi manya manya dasu, yadda yake ji a ransa zai iya yin komai ga duk wanda yake da hannu a ciki, duk kuwa da har da kakan su da wan mahaifiyar su amma be damu ba, dole ne su fuskanci hukuncin abinda sukayi.    Duk wani wanda yake da abin fad'a ya fad'a, tun daga kan Maimartaba, Ummi, Sarki Bello, Maman Yara, Madaki, Safiya da kuma sauran manyan Masarautar, masu jin kunya, sun ji duk kuwa da ance kunyar mara kunya asàara. Amma basu nuna nadamar su sosai akan abinda sukayi ba. Sultan da tunda aka fara magana be tanka ba, yana bin komai a nutse duk kuwa da zuciyar shi ba a nutsen take ba, a chunkushe take da abubuwan da suka dinga fitowa daga bakunan mutanen, da kuma yadda yasa aka fito da mutane daga kurkukun wasu tun farkon hawa mulkin Sarki Bello suke ciki, duk sun chanja kamanni saboda azabtarwa, a take ya ce duk ya yafe musu ko menene sukayi ya kuma umarci a fitar da wasu kudade mas yawan gaske a basu.     Daga nan ya bada umarni aka tattare su Buzu da jama'ar sa da duk wani me hannu a ciki, aka zuba su a kurkukun zuwa ranar da za'a yi nadin  na sosai daga nan sai asan abinda ya kamata ayi dasu,da haka ne aka karkare zaman.     A sabon bangaren da sarki Bello ya gina kwanan na da nufin komawar sa idan ya karbi mulkinsa a hannu Yarima Bilal Sultan da Amrah suka tare, katon waje ne gini irin na zamani wanda akayi shi a cikin kwanaki kad'an, aka kuma kawata shi da duk sani abun more rayuwa, su Safwan da Muhammad kuwa da su Maimartaba suma shashe guda aka ware musu, kowa da part din sa, aka kuma nemar wa Maman Yara, Safiyya da Aminatu suma nasu part din.     Yar shara ce a jikin Sultan sai dogon wando,ya cire manyan kayan wanda ya gama korafin zafi su Gimbiya suna masa dariya, Safwan ne ya taso ya dawo kusa dashi ya riko hannun sa sukayi wa juna murmushi,sai kuma ya daki damtsen hannun sa bayan ya dunkule nasa hannun, rike masa hannun Sultan yayi da karfi yace "Sarkin kake rik'ewa haka?" "Matsoracin sarkin?" Maimartaba ya fad'a cike da tsokana. "Yarona ba matsoraci bane, maganar sa kad'ai ta isa ka gane za'a yi gagarumin Sarki." "Kai dai kina tare masa ne, tsoron rawani fa yake yi." "Zai daina ne, ko son?" "Nama daina Ummi nah." "That's my boy." Sai ta juya wajen Muhammad da yake murmushi kawai tace "Baka ce komai ba Son." "Shi ai baya son magana Ummi, shi har yafi Maimartaba Sultan rashin son magana." A cewar Safwan yana rik'e still da hannun Sultan din shima kuma yana rik'e da nashin, yadda ya fad'i Maimartaba Sultan din ya saka su darawa baki daya, wai Sultan ne Maimartaba, gimtse fuska yayi ya kaiwa Safwan din duka da dayan hannun "Ka raina sarki, zansa a baka horo me tsananin." "Tuba nake Ranka Ya Dade." Ya makale hannun sa irin yadda ake wa sarakuna. Murd'e shi Sultan ya shiga ihu, da sauri Ummi ta taso ta rik'e shi, duk suka saka dariya "Wai Ummi wa kika fi so ne?" Sultan yayi maganar yana zama a gefen Amrah da take murmushi, "Dukkan ku ina so." "Naga kamar kinfi son yan dunkurman nan." "Suwa?" "Gasu nan, basa magana sai murmushi kawai." Ya nuna Muhammad da Amrah "Kar a damar mun my little Son, shi da yarinya ta babu ruwan su da hayaniya, ko dai da kuka saba sai kuyi tayi." "Shiyasa nace kin fi son su Allah." "Bar rantsuwaa, tafi son sun." "Sharri dai kawai za'a min kawai." "Ni kuma waye me sona? Babu farin jini wayyo ni Safwan." "Kaine na gaban goshin ai." Ummi ta yi maganar cike da nishadi, haka sukayi ta hira suna tsokanar juna har sai da suka saka Muhammad da Amrah maganar da gaske. ***Suna zaune a masaukin da aka sauke su, hawayen ta yaki tsayawa babu irin bakin da Daddy be yi amfani dashi ba wajen lallashin ta amma taki , tashi yayi bayan ya bata hakuri ya fito ya bar mata dakin. Yana zama Safwan ya shigo, ya zauna a gefen sa yana kallon kofar dakin "Daddy kuka take har yanzu?" "Eh wallahi." "Bari naje." Ya tashi ya shiga ciki, ta juyo ta kalle shi ya karaso ciki, "Safwan?" "Mah-Mah dan Allah ki daina kukan nan, kar ya jawo miki wata matsala." "Dole ne nayi kuka Safwan, amma ba wai kukan wani abu nake ba, kukan rabuwa da kai ne, yadda naga Masarautar da yadda naga Maimartaba yana magana na tabbata suna bukatar ku dukka a kusa dasu, saboda ku karbi komai na sha'anin mulkin, zuciya ta, ta gaza daukar hakan, gani nake kamar mafarki nake Safwan, gashi naki na farka balle na gane mafarkin ne ko kuwa gaskiya?" "Gaskiya ne Mah-Mah, haka Allah ya tsara ya kaddara, amma kuma ba hakan na nufin kin rasa ni ba, ina tare daku a koda yaushe, babu inda zai je na barki." "Kayi alk'awari?". "Nayi alk'awari, zan kasance da kowannen ku a duk lokacin da kuka bukace ni." "Nagode Safwan, nagode." Goge mata hawayen yayi, yayi mata murmushi tausayin kansu shi da ita na kamashi, yasan ba abu ne me sauki ba shi kansa a wajen sa balle ita.   A dakin ya zauna suka cigaba da hira dan duk son ta kwantar da hankalin ta, ya samu kuma ta kwantar din har ma ta sake kamar babu abinda ya faru. ***Ranar da aka shirya domin yin nadi na musamman wanda ya kasance gagarumin taro ne Maimartaba ya shirya Masarautar ta dinke taf, babu masaka tsinke, tambura ne da ganguna ke tashi ta ko ina. Manya manyan baki ne daga kowanne lungu ke ta shigowa duk dan taya Maimartaba din murna, zuwan Maigirma gwamna ya saka aka shiga taron kai tsaye, akayi komai a tsari aka nada Muhammad SULTAN a matsayin sabon sarki officially, aka bashi kyaututtuka masu yawan gaske, akayi hotuna, abun gwanin ban sha'awa.     Babu abinda ya kara kayatar da mutane kamar jawabin da Sultan din yayi me cike da ma'ana. Hajiya kakar su Amrah da yan uwansu duk sun zo tunda labarin ya bazu ko Ina, jikin Hajiya har rawa yake saboda tsabar murna bakin ta ya gaza rufuwa duk wanda ta gani sai tace masa ai Sulthan din mijin jikar ta ne, Afrah tayi ta mata dariya tana fad'a mata maganganu amma tayi mirsisi ta shafe idon ta da toka tace bata san tayi duk abinda Amrah take cewa ba, soke-soken ta ne kawai amma kam ita ta samu wajen zama dan dole Sultan ya nema mata wajen zama a Masarautar dan ba ta ba komawa gida tazo kenan. Kiri kiri ta nuna son zuciyar ta a fili, girgiza kai kawai umma tayi tana mamakin halin mutane wato dai wanda yake dashi yanzu shine mutum, mulki, kudi sune komai idan ka same su ka gama.    Labarin da ya iske su Umaimah ya saka ta shiga tashin hankali, Hajiya Umma da kanta ta kira Anty amina ta sanar mata komai,jikin ta sai rawa yake wai Sultan din da ta raina ta tsana shine yanzu ta zama Sarki, Sarki me mai daraja ba wai kowanne irin Sarki ba. Suna gama wayar Umaimah ta kirata ta saka mata kuka, ita ce ta hanata aiwatar da abinda tayi niyya tace zata yi wani abu, gashi nan tana ji tana gani Sultan din yayi mata nisa, nisa irin na tsakanin sama da k'asa, tasan yanzu ko ganin sa bata isa tayi haka kawai ba. Sosai itama Hajiya Umman tayi dana sanin rashin yin abinda ya dace din, ta bari kiyayyar da take masa tayi tasiri a kanta, da tuni Umaiman ce zata shiga gidan Sarautar yanzu, ko babu komai zata ce yarsu na auren Sarki, darajar su zata dagu sosai. Da k'yar ta tattaushe ta, ta bata hakuri tace zata san me zatayi, ta samu ta ajiye wayar ta ma kashe ta baki daya dan tasan Umaiman zata iya sake kira ta tayar mata da hankali bayan ita kanta dana sanin abinda tayi ma SULTAN din kawai take yi, tana jin da za'a koma baya da babu abinda zai hana ta jashi jiki ta nuna masa kulawa. Cizon yatsan ta, ta dinga yi tana dana sani wadda aka ce k'eya ce, wanda yayi gaba yayi gaba ita da Sultan sai dai hange daga nesa ko kuma ta ganshi a telbijin idan ana wani taron. ***Bayan taron ya watse, kowa ya kama kansa, anan ne Sultan ya shigo shashen Ummin inda dukka bakin suke ciki harda yan uwan Ummin da be sansu ba, dasu Umma da Hajiya da dai duk jama'ar su na bangaren Gimbiya Amrah da wasu kuma matan abokan Maimartaban ne da yayan su. Tare yake da fadawa suna kare shi, ya gaggaisa dasu fuskar sa kusan rabi a lullube da rawani, kasa hakuri Hajiya tayi ta taso tayi wajen sa fadawa suka dakatar da ita bayan wani ciki ya daka mata tsawar da ta kusan zata sakin kashi a wando. Da hannu Sultan ya dakatar dashi, ya janye abinda ya rufe masa fuskar ya dan duka kad'an fuskar sa babu yabo babu fallasa yace "Sannu da zuwa Hajiya." "Sannu Sultan, yaron kirki, Allah ya sanya alkhairi Allah ya tayaka riko, Allah ya sa ka gama lafiya Allah ya..." Dakatar da ita suka sake yi, tayi saurin yin shiru kamar ruwa ya cinye ta, murmushi Sultan yayi ya juya suka take masa baya suka fice daga shashen.    Kai tsaye shashen sa ya nufa, ya shiga ya umarce su su barshi shi kad'ai, suka dawo bakin wajen suka tsaya kamar masifa, yana shiga ya fad'a saman gado. "Wash Allah nah." Sai kuma ya tashi da sauri "Yanzu shikenan duk abinda zai shi sai dai ayi masa? Yanzu yana bukatar Amrah a kusa dashi amma kuma baya son ace sai ya saka wani wai yayi mata iso ko wani abu. Wayoyin sa ya tashi ya dauko da ya zube su a kan gadon yayi dialing din number ta, sai dai har ta gama ringing bata daga ba, yayi jifa da wayar yana jin shi gaba daya a takure.    Yana nan a kwance yaji anzo kofar dakin, sai kuma yaji magana kamar daga sama "Ranka ya dad'e gimbiya tazo tana son ganin ka." Da sauri ya mike yayi hanyar fita, sai kuma ya tuna wai fa shi Sarki ne, dunkule hannun sa yayi ya cije baki sa cikin jin haushi yace "A shigo da ita." Komawa yayi ya zauna, sai gata ta shigo sanye da alkyabba an mata kwalliya me sanyi da kyau, kallon ta yake har ta karaso, yanayin tafiyar ta ya nuna masa rashin kuzarin da take dashi, zaunar da ita yayi a gefen sa, ta sakar masa murmushi tace "Congratulations,Allah ya sanya alkhairi,ya taya mu riko." Sai hawaye shar-shar, da sauri ya sa hannu ya goge mata su yana girgiza mata kai "Don't cry, idan kika yi kuka ni kuma me zanyi?" "Bansan kukan yazo bane." "Menene ya saki kuka? Kin takura ko?" "Ni kawai yadda ake ta jaddada min nauyi ya hau kaina, nauyin mutane masu yawa, sai nake jin kamar ba zan iya ba, kamar I'm too small for that,kamar Ummi ce ya kamata ta karbi wannan wajen,duk na zama confused bansan me zanyi ba." Juyo da ita yayi suna kallon juna... "Trust me kinji? Zaki iya ba wani big deal bane, ita ma Ummin da haka ta fara, karki tashi hankalin ki zakiyi komai perfectly fine, I trust you nasan zaki iya, kawai nutsuwa zakiyi ki fuskanci komai, karki yi saurin yarda da kowa har sai kin tabbatar da mutum kin gamsu da halayyar sa, be very vigilant, gidan sarauta da mutanen cikin sarauta are very cunning, za'a iya shiga jikinki ayi abinda za'a cutar damu baki daya, sanin ABINDA KE CIKIN ZUCIYAR Mutum sai Allah, wani zai nuna maka soyayya a fili amma a cikin zuciyar sa ba hakan bane, baya kaunar ka baya son ci gaban ka, ki nutsu ki koyi komai, ki zama fearless karki yarda a taka ki, ki kuma zama me nutsuwa da sauraro wajen zartar da hukunci karki yi abu a cikin fushi you might end up regretting." "Zanyi duk abinda kace in Sha Allah." "Yawwa, that's my wife, ki taimaka min nima wajen nawa aikin dan mace tana taka rawa sosai mijin ta ya zama na gari ko akasin haka, ki zama me bani shawara idan kinga zanyi ba daidai ba, karki ji cewa ai ni Sarki ne ina da right nayi komai, a'ah duk abinda mukayi sai Allah ya tanbaye mu." "In sha Allah." "Allah ya taimaka mana ya bamu sa'a ya kare mu daga sharrin masu sharri " "Amin ya Allah." *** Yadda rayuwa ta juya wa bayin Allah da yawa zaka yi mamaki, Maman Yara ta samu wani dattijon mutum ta aura inda Maimartaba ya zamar mata uba Ummi kuma uwa sukayi mata komai, duk da ta girma amma hakan ba hana su yi mata duk abinda suka san zai faranta mata ba.    Haka ma Safiya, itama ta samu miji amma ita a wajen Masarautar ne, tayi auren ta ta tare a gidan sa, bata tafi da Aysha ba dan dama tana hannun Ummi tun dawowar su Masarautar, sai ya zama na sai Aminatu kawai. Watarana Sultan ya fita ya dawo bayan an gama case din Madaki inda aka sameshi da wasu mugayen halayen aka mika shi kotu ta yanke masa wasu shekaru a gidan kaso, hakan yasa Sultan ya kara tattare hankalin sa waje daya, yake gudanar da mulkin nasa cikin kwarewa da takatsantsan.    A wajen da Maimartaban yake shakatawa ya tadda shi, ya sallami kowa suka zauna, bayan sun gaisa ne ya kawo masa bukatar ya auri Aminatu ko dan saboda su Safwan da Muhammad, shiru Maimartaba yayi dan har ga Allah bashi da bukatar aure a wannan lokacin amma kuma tabbas ya kamata a san me yakamata ayi mata tunda tun farko sune suka bata mata rayuwa, gashi babu Maman Yara babu safiya zaman zai ishe ta.ce mishi yayi zai yi tunani zai shawara duk abinda ya yanke zai fad'a masa, haka kuwa akayi ranar gaba daya tunanin abin ya wuni, daga karshe dai ya tunkari Ummi da maganar duk kuwa da a tsorace yake da yadda zata dauki abun amma sai yayi mamakin data amsa kai tsaye ta kuma bashi goyon baya dari bisa dari. Ganin haka sai kawai ya kirawo Sultan yace masa ya amince, yaji dad'i sosai yayi ta godiya, babu bata lokaci aka daura auren na Maimartaba da Amaryar sa Aminatu.     Rayuwa ta cigaba da gangarawa, har Adnan yayi aure ya samu mata a nan cikin family su. Bayan bikin sa ba'a dad'e ba ita ma Afrah ta fitar da miji aka sha biki. Sultan ko nace Sarki Sultan yaso da Safwan akayi amma shi Safwan din be nuna interest dinsa akan abun ba shiyasa be masa maganar ba yayi shiru kar a zo a bata zumunci.    Bayan bikin Amrah ne kuma akayi bikin Aysha itama, Muhammad da Safwan kuma babu wanda yake ko maganar budurwa, musamman ma Safwan gwara shi Muhammad yana kokarin ganin ya samu wani abu a karatun da yake yi, tun dawowar su dama ya koma makaranta toh gaba daya hankalin sa ya karkata achan. **** A tsaye take jikin window dakin ta dora hannayen ta a jiki ta bawa kofar dakin baya, a zahiri kallon yadda tsarin wajen yake take, amma kuma a bad'ini tunanin yadda al'amarun suka kasance take yi.   Yadda rayuwar ta chanja baki daya daga bigiren da suke zuwa wani bigire na daban, ta dauko su ta kawo su wata duniya daban ta wadda suka saba suka santa.  Juyowa tayi gaba daya ta zurawa dakin ido tun daga kan makekeken gadon dakin xuwa kayan furniture's din dake dakin zuwa suturar ta dake damke a cikin wardrobe. Sauke nannauyar ajiyar zuciya ta da ta tuna abinda Maimartaba yace mata da yana yi musu nasiha. Girma ne ya hau kansu tabbas, girma irin na shugabantar al'umma masu yawa da mabanbantan halaye da d'abi'a. Dole ne komai ya chanja irin chanjawar da zaiyi daidaito da yanayin da suka samu kansu a ciki.    Da baya ta dawo tsakiyar dakin ta zauna, sai kuma ta mik'e ta sake komawa zuwa windown, ta daga gaba daya curtains din ta leka sosai, motoci ne manya suke shigowa cikin shashen nasu, da sauri ta saki labulayen, tayi saurin isa gaban mirror ta dauki turarurruka masu kamshi ta feshe jikin ta dashi, sannan ta bare wani chewing gum me sanyin kamshi ta jefa a bakin ta, ya tsiyayi humra ta shafe hannuwan ta da kasan wuyanta, ta koma ta zauna a gefen gadon tana jiran shigowar shi. Sallama Jakadiya tayi a kofar, ta bata izinin shigowa, zubewa tayi a k'asa kanta a duke tace "Ranki ya dad'e, Maimartaba yana hanyar shi ta shigowa." Daga mata hannu tayi, ta juya da sauri ta fice,tana fita kamshin turaren sa ya iso cikin dakin, had'e da takun tafiyar sa wadda ke cike da salo me matukar kayatarwa. Idon ta k'yer akan kofar har ya shigo gaba daya ciki. Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke a fili, ta tashi da dan sassarfa ta isa gareshi. Hannun sa ya saka ya rungume ta a kirjin sa, ya sauke ajiyar zuciyar shima. "Sannu da zuwa hayatee." "Yawwa honey,Ashe haka nayi missing dinki? God kwanakin nan suna cikin boring kwanaki na." "Nima haka, nayi missing dinka kamar Kamar me, gaskia ni mulkin nan ya fara isata, babu damar zama da mijin ka a duk lokacin da kaso, wani lokacin ma sai an baka izini haba." Ta tura bakin ta gaba cikin takaicin abin "Ni kaina ba dad'i nake ji ba wallahi." "Toh ya zamuyi? Haka zamu hakura." Tace lokacin da suke zama a kujerar dakin, damke hannun ta yayi, ya matso da ita jikin sa sosai, ya matsa da bakin sa yayi mata peck a kunci itama tayi masa, yace "Guess what?" "What!?" "Umrah zamu tafi next week, daga nan sai mu wuce mu huta sosai, tunda abubuwan nan suka kasance bamuyi having time of our lifes ba, tun barin mu Toronto." "Da gaske!?" "Da gaske!" "Wow, amma naji dad'i, ina zamu je? I'm stucked here wallahi, koman motsi idan nayi sai ace ranki dade me kike so? Na gaji." Dariya ya kyalkyale da ita sosai, dan yadda tayi maganar da gasken ta gaji, daga ita har shi basu da interest a mulkin, shima dai kawai saboda ba yadda zai yi ne, Safwan ba wani lafiya ce ta ishe shi ba, Muhammad kuma karatu ma yake yanxu akwai long way a gaban sa, gashi Baba yace sam ba zai kara mulki ba ya gama a rayuwar sa, shiyasa bashi da option shima amma har ga Allah yana cutuwa da hakan. "Nasan yadda kike ji, and I'm very sorry for that, mu kuma tamu kaddarar kenan." "Haka ne, toh Alhamdulillah ya Allah." "Yawwa that's my wifey, yanzu me kika tanadar min? Kinsan dai nayi kewar ki." "Kawo kunnen ka." Matso dashi yayi, ta rada masa magana a kunne, yayi dariya yana rik'e ta ganin zata gudu, dariyar take itama, da k'yar ya kyaleta ta tashi ta taimaka masa yayi wanka, sannan suka fita main falon wajen da zai zauna yaci abinci. Suna fitowa duk masu kula daga wajen suka watse sai kukun da yayi girkin kawai, da hannu Amrah ta nuna masa ya matso, ya matso da sauri tunda dama yasan me kiran ke nufi, abincin duk yabi ya dandana bayan wasu mintuna sannan ta sallame shi, ta shiga zuba musu a plate, shi kuma yana danna waya kansa a k'asa. Sai da ta gama zuba abincin sannan tayi masa magana ya ajiye     Bayan sun gama ne suka zauna duba inda ya kamata suje suyi ko two weeks ne, tare suke dubawa duk inda yayi musu sai a cire a ajiye, a haka har suka gama tara wuraren, sannan suka fi su daya bayan daya suna son tantancewa. Daga karshe suka karkare akan Maldives. Wayar sa ya jawo ya kira Safwan, yace yayi musu booking komai da komai daga Umrah da za'a su zasu wuce wani wajen.   Haka kuwa akayi, suka dunguma har su Maman Yara suka tafi, aka bar Safwan da Muhammad akan sha'anin mulkin. Kamar an zare ma Sultan wani nauyi haka yaji shi sakayau, sukayi Umrah suka gama lafiya sannan sukayi musu sallama suka nufi Maldives. ***Tafiya ce me matukar muhimmanci da tsayawa a zuciya, sun yi komai cikin farin ciki irin wanda basu taba samun kansu a ciki ba, ana gobe zasu tawo Amrah ta fara zazzabi me zafi, duk da haka ta daure suka fita karasa siyayyar da zasuyi, kasancewar hotel din da suka sauka a wajen ruwa yake, sai ya zama na sun tsaya a wajen kafin su koma ciki, suna tsaye hannun sa a cikin nata suna kallon yadda ruwan ke hawa da sauka gwanin sha'awa, kamar wasa sai taji tana jin jiri, ta jingina da jikin sa sosai yadda zata fi jin dadi amma sai taji kamar na mintsine ta a mara, cikin kankanin lokaci sai ciwon mara, ta shiiga ya tsine fuska hankalin Sultan din na kan ruwa yana kallon wasu tsuntsaye masu kyau sai yaji ta damke hannun sa da ta rike da karfi, ya waiwayo ya kalle ta sai yaga hawaye na sauka a idon ta "Lafiya?" Ya taro ta da sauri ganin zata fad'i, kuka ta shiga yi tana rik'e marar ta, da sauri ya sunkuce ta sukayi cikin hotel din. Akwai karamin clinic a ciki yana zuwa suka karbe ta lokacin har ta fara bleeding so badly, duk Sultan ya rikice ya riga ya gane miscarriage zatayi, amma ya akayi be gane tana da ciki ba a matsayin sa na likita? Haushin kansa yaji kwalla na taruwa a idon sa, yana son yara sosai sosai, da yasan tana dauke da cikin nan da babu abinda zai saka suzo nan. A ranar tayi barin cikin, tasha wahala sosai kamar ba zatayi rai ba, dole suka fasa tafiya a washegarin amma suka baro resort din da suke. Sai da ta warke sosai sannan suka dawo. Tun daga lokacin ya zama yana observing komai sai dai shiru kake ji wai malam yaci shirwa. Rayuwa ta cigaba da garawa cikin hukuncin Allah, Matar Adnan ta haihu, haka ma Afrah, Safwan ya samu wata yarinya itama sun daidaita har ma an saka musu rana, lokacin bikin ne Amrah ta sake samun ciki Sultan ya hanata yin komai, amma shima cikin be zauna ba ya fice,sosai suka damu suka kuma shiga binciken abinda yasa cikin ke zubewa, wata babbar likitan mata Sultan din ya saka aka nemo ta zama ita ke kula da Amrah, ta duba ta sosai tace babu abinda yake damun ta kawai lokaci ne be yi ba. Dole suka hakura suka barwa Allah zuwa lokacin da Allah zai kawo. Shakuwa tsakanin Sultan, Muhammad da Safwan ba'a magana, komai daya zai sai da sanin daya, kansu a had'e yake babu wanda yake jin cikin su. Safwan kamar yadda yayi na Mah-Mah alkawari, zaman sa da rayuwar sa tafi yawa a wajen Masarautar, baya kwana biyu be je ya ganta ba, gidan sa a nan kusa da su Maman ya zauna duk son ya faranta mata, har kuma gobe ita din yake ji a matsayin mahaifiyar sa, shiyasa ma Muhammad da Sultan suka fishi shakuwa da Ummi da Maimartaba, hakan kuma baya rasa nasaba da dama su chan suna lacking iyayen shi sultan dukka shi kuma Muhammad mahaifi, shiyasa zasu fi sabawa dasu ba kamar shi ba. ***Mah-Mah ce ta kira Amrah a waya tace mata umaimai tana so tazo Masarautar. Tace mata sai tazo, da tazo Amrah tasa aka shigo da ita, ta bata hakuri ta kuma bata katin bikin ta da wani bayerabe da suka hadu da wani bikin kawarta a Lagos din, sosai Amrah tayi mata murna, ta kuma taimaka mata taga Sultan din shima ta bashi hakuri, sannan ta taf tana musu fatan alkhairi dan tasan sun mata nisa sai dai kallo ***Alhamdulillah ya Allah, anan na kawo karshen littafin nan nawa me suna Abinda Ke Cikin Zuciya, ina godia sosai da hakurin da kukayi wajen bibiyar littafin nan, ina kuma baku hakuri akan rashin jina yadda ya kamata. Ina ma kowa fatan alkhairi ina kuma rokon Allah ya yafe mana kurakuren da mukayi. Ina rokon Allah ya bawa duk wata mace da take neman haihuwa yaya masu albarka, masu jin kai. Na sadaukar da littafin nan nawa zuwa ga duk wata TTC MOTHER (trying to conceive) Allah ya azurta kowa da yaya masu albarka. Zafafa biyar na godia da kaunar da kuke nuna musu, Allah ya bar zumunci har zuwa aljanna. Zaku iya zuwa website dinmu me suna Ranonet.com.ng domin yin register,ku siya data Mtn a farashi me sauki. Sannan yar uwa zaki iya zama reseller inda zaki dinga siyar da datar kema ki samu naki, yafi zaman banza kina kwance a gida. Domin karin bayani sai ku yi min magana pc. Nagode #Son so😘😘😘😘     Rano