_*ABUNDA KA SHUKA*......... _*(shizaka girba)*_ *MALLAKIN* 👇 *ZAINAB USMAN KUMURYA* *FARIN JINI WRITERS ASSO.....*📚 ~*Free novel*~ *Bismillahirrahmanirrahim* 0️⃣1️⃣ "Darmanawa,kumbotso local government,kano Nigeria." ...........kiran sallar farko na asuba,a kunnena.ahankali na tashi zaune ina salati tare da karanto addu'ar tashi Daga bacci.yunkurawa nayi na mike,na lalulubi makunni kwan dakin danake,saboda da akwai wutar nefa.tabarmar Dana tashi Daga kai na nannade bayan na kunnan kwan,haske ya gauraye dakin.jingine tabarmar nayi agefe,na ninke zanin dana lulluba dashi,akan jakar kayada na ajiyeshi.tatsatstsen filon danake kwanciya akai na matsar gefe.dakin fess yake bawani datti,kafin na kwanta seda na share simintin tass.fitowa nayi madaidaicin tsakar gidannamu,iskace take kadawa,kadan_kadan dama lokacin sanyine.kitchen dinmu na nufa, Wanda yake cike da uban shirgi. Kayan hadin fanke na dakko na kwaba,ajiyeshi nayi agefe kafin gari ya waye ya kumburo. Dankalin Hausa dake cikin bugu na fara kwasowa,ina zubawa a wani faranti,Medan girma.seda na cika faranti sannan na fito,tsakar gida.ruwa na jawo arijiya a cikin bokiti tare da dakko wuka na fera ferayewa.seda na ferayeshi duka sannan na fara masa yankan biyar_biyar kamar yadda muke siyarwa. Kafin nagama feraye dankalin,har masallatai sun shiga sallah.wasuma sun idar.bandaki na shiga nayi tsarki tare da dauro alwala,na koma dakina natada na shimfida kodaddiyar dardumata na tada sallah.ina idarwa na mike da sauri,saboda kar gari yayi haske bangama ayyukanaba.lazimun sallarma sena aikin inayi haka nakeyi kullum.awarar dana dafa tun Daren jiya na dakko nafara yankawa.ina gama yanka awarar,na dakko barzazzen waken kosai na wanke shi,tattasai da attaruhu da albasa na zuba akan waken na nufi kai markade.ba kowa alayin,amma ba'abun danaji saboda na saba fita a irin wannan lokacin. Kofar gidan abude take sedai karota da'akayi. Dasallama na shiga cikin gidan,matar gidan tana bakin rijiya tana Jan ruwa.bokitin hannuna na'ajiye,na tsugunna har kasa ina gaisheta.da fara'arta ta amsamun tare da fadin. " *Maryama* ta babangida,har kin fito kenan,sannunki Allah ya miki albarka. "Ameen mama nagode,bari naje idan aka markada nadawo nadauka. " A'a maryam nasan akwai ayyuka da yawa agabanki,kibari zan turo salihu ya kawo miki,idanna markada. "To mama nagode,idan yazo seya karbi kudin." Toh badamuwa maryama.sallama na mata,na koma gida.sauri_sauri na fito da kaskon suyata,da murhu tsakar gida,inda nake suyata kulkum,itace na hada na saka Leda na kunna. Kafin ya kama na tattare bawon dankalin dana bare.komai danake bukata na aikina na kawoshi gaban murhu.mai na zuba akasko nasa masa albasa,yana soyuwa na fara saka fanke.gari harya fara haske.amma har lokacin matar gidan bata tashiba,tana daki tana bacci,dama kullum sekunsan karfe tare take tashi daga baccin asara.har fanken ya soyu,na kwasheshi,na zuba dankali.salihu ne yashigo gidan da bokitin markade akansa,dasauri na tashi na sauke masa.ina masa godiya,daki na shiga na dakko kudin markaden na bashi,fanke na zuba masa atakarda,ya karba ya juya.gishiri da maggi na zuba a kullin kosan,dankalin yana soyuwa,nafara sakin kosai,saboda anfi siyansa shiyasama munfi yinshi da yawa........ *************** Yana tsaye gaban mudubin dakinsa,bayan ya gama shirinsa,tsadadden agogo,me matukar kyau da daukai ido, yake daurawa a tsintsiyar hannunsa. da alama,office zeje.wata kyakkyawar budurwace ta turo kofar dakin tashigo,fara Tass da ita,doguwa Medan madaidaicin jiki,doguwar fuska gareta,medauke da dogon hanci har baka dara_daran idanuwanta farare tass, bakinta dankarami,abun sha'awa.taci kwalliya cikin wani tsadadden yadi,maroon colour ya kara haskaka,farar fatarta.takafa daurin dankwali na zamani akanta tashin kamshi takeyi,me dadin gaske.fadada fara'arta tayi,ganin masoyinta muradin zuciyarta.fadawa kirjinsa tayi tana fadin "morning my baby" lumshe idonsa yayi,ya bude,alamun ya amsa.batare da yace komaiba.murmushi tayi domin tasaba da miskilancinsa. Pink Lips dinsa dayake matukar burgeta ta sumbata,tare dan shashshafa wuyansa,zuwa bayansa.behanataba kuma betayataba,ita kadi tayi abunta ta gama.kuma dama ta saba da hakan.hannunsa ta kama tare da fadin"our breakfast is ready,kowa ya hallara kaikadai ake jira shine mommy tace inzo inkiraka.ko kallonta beyiba balle tasa ran ze amsa mata.binta kawai yayi suka fice daga dakin.part din gaba daya suka bari,suka nufi wani shashen daban agidan.samarine guda hudu a zaune akan dinning din.sewata 'yar dattijuwa,wadda saboda gayu da kudi idan kaganta zata zakayi 'yar 40 years ce.kallonsu takeyi cike da sha'awa aranta tana addu'ar Allah yanuna mata ranar auransu.kallon matashin tayi fuskarta dauke da fara'a tace"my son sannu da fitowa.kai kawai yadaga mata batare da yace komaiba.kujerar gefenta yaja ya zauna,gaggaishesa matasan dake kan dinning din suka shigayi,hakan yana nuni da duk kannensane.hannu kawai yake daga musu. Matarce ta dubi,budurwar tare da fadin " *suhailat*, serve us pls. Bata fuska tayi alamun bataso hakanba,nandai babu yanda zatayine.serving din kowa tayi sannan ta koma ta zauna.cike da nutsuwa kowa yaken cin abincinsa. Kadan yaci kayan breakfast din,sedan tea dayasha ya mike alamun ya gama.kallonsa mommy tayi tace"son" badai katashiba,me kaci anan. Yamutsa fuska yayi,kamar anmasa dole yace" am ohk mom" ya fada kasa_kasa.bejira mezataceba yayi hanyar barin falon. Suhailat ta bishi da kallo,yanda yake tafiya cikin takunsa na cikakkun maza.hakan bakaramin kara burgeta yakeba. Haidar ne yakalli dan'uwansa dake gefensa,zannurain harnaji sa'ida amma da ambarmu da ciwon baki,baka isa kayi maganaba,sannan seyace zaka saka masa ciwon kai.dariya zannurain yayi,ai yaya *musty* akwai takura turo baki suhailat tayi tace"ai hakan shine daidai dama Ku takuratace da Ku,surutunku yayi yawa."sadiq ne yace"kadai kina kare masoyinkine amma ai gaskiya suka fada. Mommy ce ta dubeta,kyalesu daughter kici gaba da break dinki,karsu makarar dake keda zaki school, sukuma suna gida. Itama Kadan ta karaci ta mike.sallama ta musu.sama ta haura,ta dakko hangbag dinta me matukar kyau wadda tashiga da kayan jikinta.ko mayafi bata yafaba tayi waje. Direban yana ganinta ya taso da sauri,"hajiya sannu da fitowa dafatan kin tashi lafiya. Wani banzan kallo ta wurga masa tana yamutsa fuska tamkar taga kashi. "Malam kayi sauri nika saukeni,ka tsaya kanamun surutun banza daban tashiba zaka ganni. " tuba nake hajiya yafadi hakan yana bude mata bayan motar.tsaki taja,tana harararsa ta shige motar.jiki a sanyaye ya shige gaban motar,yabata wuta megadi ya wangale musu makeken gate din gidan suka fice......... ************** Saleemat ce tayi sallama,amsa mata nayi ina mikawa yaron dake tsaye kosan daya siya.ta shirya abunta cikin uniform dinta,zata tafi school.a kullum naga saleemah,se inji dama nice.inason makaranta inason karatu.amma inaji ina gani anhanani. Kujera ta dakko ta zauna akusa dani kallona takeyi cike da tausayawa. "Saleemat yanaga kin zauna kina kallona lafiya? Girgiza kai tayi tace" babu komai maryam,yanzu ke ahaka zakici gaba da zama,daga bauta se bauta,ba boko ba islamiyya,da kuruciyarki gaskiya ni nagaji da ganin ahaka.murmushi nayi me ciwo,wata kwalla ta tararmun a ido,nace" toya zanyi saleemah,fadan dayafi karfinka seka maidashi wasa,akullum.cikin kaiwa Allah kukana nake,ya kawomun sassauci acikin rayuwata. Saleemah batace komaiba ta mikomun naira darin hannunta gashi ki zubamun kosai da dankali,kuma ni bance ki kyautamunba,kinsan halin *gwaggo ladi* murmushi kawai na mata bance komaiba na zuba na bata. Karfe Tara na safe,gwaggo ladi ta fito daga dakinta.maganarta azafafece tatabbatarmun data fito.seda gabana yayanke ya fadi,domin kuwa yanzu inta faramun bala'i harse ta kwanta bacci take sararamun.wata tsawa ta dakamun. "Ke maryam! Dan matsiyacin ubanki bakya ganin mutanene kika tsaya kike Abu ahankali,bazakiyi Abu da jikiba.nandanan jikina ya kama rawa,saboda masifar tsoron gwaggo ladi danakeyi. To nikadaice abun yamun yawa ga suya ga sallamar mutane.gashi kuma Allah yasanyawa sana'artamu albarka muna samun ciniki sosai.hakan yasa nake dan Tara layi,amma dazarar gwaggo ladi ta fito zata fara zagina tana tsinemun akan bakin ciki,nake mata shiyasa bana saurin sallamar mutane ita kuma tana daki akwance, koda sallamar mutane bata tayani,kuma innagama ta 'amshe kudinta cas tana zagina.ko biyar bazata barmunba. Cikin rawar murya nace "kiyi hakuri gwaggo yanzu zankwashe wannan na sallamesu. " da hakurin ta mutu sadakar nawa kika bayar,shagiya munafukar yarinya,kina Abu sum_sum kamar ta Allah.shiru nayi ina cigaba da aikina,idan da sabo,nariga dana saba da halin gwaggo.da masifarta.buta ta dauka ta shige bandaki tana mitarta. Karfe goma da 'yan mintuna,kamar yadda nasaba kullum,yauma komai ya kare.Alhamdulillah.har nemama akeyi babu.duk wani Abu danasan zan wanke na tattara nakai gurin wanke_wanke.dakin gwaggo,na nufa da sallama.seda taga shan kamshinta sannan ta bani izinin shigowa. Tana kwance akan gadonta.durkusawa nayi abakin gadon na mika mata jakar danake zuba kudi acikinta.rankwashin kaina tayi Wanda bansan lefin menamata tamun hakanba.hararata takeyi tamkar idonta ze zazzago."munafukar yarinya,me suffar 'yan wuta,kidinga wa mutane wani sum_sum kamar ta Allah,mudai ba'agurinmu kika gado wannan bakin halinba,sedai can agurin dangin ubanki.dauki indomien can guda biyu da akwai biyu kidafomun kikawomun.inda tanunamun na nufa na dauka na fice da saurina dankar nakarayin wani lefin.to yanzu kuma menai mata,ita matarnan komai na mata banmata daidaiba,komai nayi lefine.kullum cikin zagina da aibatani take.hawayen da suka tararmun a idona suka fara zubowa.yaushe zan huta da kuncin rayuwa ni maryam.a hankali nake Jan kafata har bakin murhun,bayana kamar ya balle saboda gajiya.guntun garwashin danayi suya akai na Dora mata indomien. Sharar gidan na kama duk da bawi datti se 'dan kura dayayi. Seda na share gidan Tass,sannan na kwashe indomien a faranti nakai mata daki.tanata faman irga kudin cinikin da mukayi,hakan yasa yanzu bansamu rabon fadaba.saboda gwaggo ladi,idan ta harkar kudi ko magana batayi,shegen San kudi gareta.guntun tuwon danaci jiya da dadaddare shina Dora akan wuta na dumama.bayan ya dumamu na sauke na faraci,saboda matsananciyar yunwar datake addabata.kullum.dama tuwon nishine abincina da safe da daddare.ina cikin ci gwaggo ladi ta kwallamun wani kira, "ke! Ke maryam.dasauri na tashi zuciyata na bugawa jikina ya kama rawa dannasan wannan kiran bana alkhairi bane. Zubewa nayi a gabanta jikina,na rawa cikin rawar murya yace" gwa..g..go..ga..ni,wani wawan mari ta daukeni dashi,dan uban ubanki,ina kudina da kika boyemun,domin nasan cinikuna yafi haka. "Wlh gwaggo ban boye miki,ko ficikaba wannan shine kadai cinikin da'akayi.nafada mata haka hawaye na zuba daga idona. " to ubanwa kika bawa wani Abu acikin kayana. Babu kowa gwaggo sedan gidan me markade daya kawomun markade na bashi fanke guda biy.....aiban karasaba naji ta rufeni da duka ta ko'ina akan fanken naira 20 bacin cinikin dubunnan dana mata.inda sabo yaci ace nasaba da dukan gwaggo,domin kullum seta jibgeni babu gaira babu dalili.seda ta gaji dankanta ta kyaleni,tana tsinemun tare da aibatani. Jan jiki nayi nadawo tsakar gida,hawayene masu zafi kawai suke fita daga idona.bansan menayiwa gwaggo ladiba,ta tsaneni,kullum cikin azabtar dani takeyi.abincin daban karasa Ciba kenan,na tattara kayan na fara wanke_wanke.inayi ina sharar hawaye. Seda nagama na maida komai muhallinsa. Girkin abincin rana na Dora,shinkafa da miya gwaggo tace na dafa.dorawa nayi.bandaki na wanke kafin shinkafar ta tafasa na tace. Seda naga girkin sannan na faki idon gwaggo,na Dora ruwan wanka,saboda banda kauri babu abunda nakeyi.daki na kaimata abincin duka.wanka nayi,na wanke hakorana Tass da gawayi,domin duk kudinnan da gwaggo take samu,amma bani da MacLean da burush.alwalar sallar azhar na dauro.saboda har anfara kiran sallar.bayan nagama shiryawa nayi sallah.waken suya na auno,na jika zankai markaden awarar yamma...... *************** Karfe daya suhailat ta fito daga lecture,kuma daga ita tatashi kenan.amma tayiwa mommy karya tace mata se 6:00 pm zata tashi.kamar yadda ta saba kullum seta kara lokaci.wayarta ta dakko kirar iPhone 12,takira wani saurayinta akan tafito yazo ya dauketa. Wata farar motace ta tsaya a gabanta,wani matashi ya fito yana fadada fara'arsa, babbar yarinya dama jiranki nake tayi,kinji dadin danaji kuwa dana ganki.murmushi ta masa tare da fadin,"nima naji dadin ganinka saboda inada bukatar adan yamutsani.dariya ya saki."kinkuwa samu tawan,gaban motar yabude mata ta shiga.domin suhailat macece me izza,daji da kai.zagayawa yayi yashige shima bayan ya rufe mata kofar.wani matsakaicin gida ya kaita,ba kowa agidan,hakan yasa da kanshi ya fito ya bude get din gidan.sannan suka shiga.karamin gida amma yayi matuakar kyau da tsaruwa.suna shiga bedroom din gidan ta fara cire kayan jikinta,.janta yayi suka fada kan gado............✍️ *BY* *zeey kumurya* https://chat.whatsapp.com/LvF2kmkAjrZ2UUUZ2ZzvaN *ABUNDA KA SHUKA*......... _*(shizaka girba)*_ *MALLAKIN* 👇 *ZAINAB USMAN KUMURYA* *FARIN JINI WRITERS ASSO.....*📚 ~*Free novel*~ *Bismillahirrahmanirrahim* 02 Bayan ya danyi mintuna,da jikawa na tace ruwan na kara daurayewa,nanufi gidan markaden.ina zuwa bansamu layiba,tsayawa nayi aka markadamun sannan na dawo gida.har lokacin gwaggo tana daki,yau gantalallun kawayennata basu zoba.seda na fara tace awarar sannan na kara hura wuta na daura.salimata ce ta shigo gidannamu da sallamarta.fadada fara'ata nayi ina mata sannu da zuwa.kujerar tsugunno ta dakko,ta zauna.nima wata na dakko na zauna a kusa da ita. "Saleemat harkin dawo Daga school, din." na dawo maryam ya gida ya aiki. "Lafiya kalau,saleemat.ya umma. "Umma tananan kalau,dama zuwa nayi nadan tayaki aiki kafin lokacin islamiyya yayi. Dasauri nace" haba saleemat,aina kusa gama aikin,awarafa kawai zan dafa,se dakan yaji.dakinyi zamanki agida kin taya umma aiki.hararata tayi,tace."umma ta gama aikinta,ki dakko yajin nadaka miki lokaci yana tafiya.sanin danayi kona roki saleemat babari zatayiba,yasana mike na nufi kitchen. Barkono na dakko da su maggi da gishiri.gabanta na kawo na ajiye mata.da kanta tatashi da dakko turmi,ta fara dakan. Nima cabejin awara na dakko na dawo kusa da ita na zauna na fara yankawa.dubana saleemat tayi tace."yau gwaggo batananne. "tananan, na bata amsa atakaice. "Najita shiru ne,kuma banga kawayenta da suka saba zuwa sun zoba. "nima nayi mamaki saleemat da basu zoba,kila anjima ki gansu. Saleemat tace. "Gwarama da basu zoba,saboda zuwannasu ba alkhairi bane,duk du suke kara zuga gwaggo take miki abunda taga dama. "hmmm kawai nace. "Umma tace kwana 2 baki lekotaba. "dan Allah saleemat kibata hakuri insha Allah anjima idanna gama aikina da wuri,kafin nafara awarar magriba,zan lekota. "Allah yasa domin ke kullum haka kike baki da lokacin kanki,gaskiya gwaggo ladi muguwa ce,tana azatar dake sekace kedin ba jinintabace.tana zalintarki da yawa,ta hanaki samun ishashshen ilimi sannan kuma ta zaunar dake agida se bautar dake takeyi. Aiko abaiwa ta siyeki se haka,wannan......da sauri na rufe mata bakinta,ina waro idona waje, kofar dakin gwaggo na kalla,cike da tsananin tsoro. "Kiyi a hankali mana saleemat karta jiyoki. Ture hannuna tayi Daga bakinta,tana hararata,tace." Dalla can,dama ke shegen tsoronkine yake jamiki komai,da tun farko kinnuna mata baza ki juraba,ai bazata dinga tula miki wannan uban aikinba kamar jakaba. Wukar hannuna na'ajiye ina duban saleemat,nace."haba saleemat,mahaifiyatafa ta rasu mahaifina kuma kamar yadda gwaggo ta fada,guduwa yayi yabar mahaifiyata tunda cikina,kuma ba'asan kowa nasaba.gwaggo itace ta rikeni bayan rasuwar inna,nake zaune a gidanta,ta ciyar dani da abincinta kome namata banfadiba,tunda ta rikeni bata barni ina garari a titiba,shiyasa duk aikin danake mata banajin komai,domin ta cancanki haka. "Hmmm,maryam kenan,dududu shekarar gwaggo nawa tana rikeki,kumama dan tana rikonki seta miki wannan izayar. Numfashi naja,nace" saleemat ki godewa Allah daya barki da iyayenki,rashin iyaye bakaramin masifa da bala'i bane,burina arayuwa inyi ilimi me zurfi,amma hakan besamuba,nasan da mahaifiyata tananan da rai dako me zatayi setayi wajen ganin nasamu ilimi.na karshe zancen idona yana ciccikowa da hawaye.dafa kafadata saleemat tayi tace."Kiyi hakuri Maryam,kowa dakika gani a duniyarnan datasa kaddarar,ke taki jarrabawar kenan,kuma kidena yarda da maganar gwaggo datake cewa,babanki ya gudu, be zama lallai gaskiya bane,kila kawai tana fadane danta bataki.kiyi hakuri wata rana se labari,kedai kawai kici gaba da'addu'a,zakiga komai yazo miki cikin sauki.hawayen daya zubomun na share nace shikenan saleemat nagode,insha Allah zan cigaba da addu'a. "Yawwa kawata share hawayen inbaki wani labari me dadi. Murmushin karfin hali nayi ina goge hawayena." Inajinki to bani labarin. Labarinta da saurayinta tashiga bani.saleemat tana sona sosai,tana kokarin ganin nayi farin ciki akodayaushe,shiyasa na bata wani babban matsayi araina.tana bani labarin har muka gama abunda mukeyi.se wajen karfe uku da rabi tatafi saboda lokacin islamiyya ya yayi.kamar karta tafi haka naji,amma babu yanda zanyi.sallar la'asar nayi.bayan na idar gwaggo ta kirani ta bani abincin rana,ina gamaci na hau yanka awarar Dana dafa.......... Sai da 5:00pm ta wuce kamal ya sauke suhailat a department dinsu.sallama sukayi ya tafi.kiran mommy tayi taturo mata da driver domin ita tafi karfin waya da driver. mintuna goma shabiyar,se gashi ya karaso school din.tana hangosa ta nufo inda yake,fuskarta a hade,se wani ciccin magani take,tana yatsina fuska sekace wata basarakiya.saboda jijji da kanta da uban girman kanta ko kawar arziki bata da ita.gani takeyi tafi karfin kula kowacce yarinya a school din. Dasauri driver ya fito daga motar yana bude mata bayan motar.wani kallon banza tabishi dashi. "Seyanzu kaga damar zuwa seda gama shanyani,tun yaushe nake jiranka,ta fadi hakan tana jifansa da wani mugun kallo. " yanzu duk saurin danayi,da gudun dana dinga kwararawa yarinyarnan bata ganiba,ya fadi hakan aransa.amma a fili seyace"kiyi hakuri hajiya insha Allah hakan bazata kara faruwaba,kinsan hanyar da akwai gosl....."Dalla malam ni shiga kajani,banason wani bayaninka na banza da wofi.ta katsesa cikin tsawa. Dasauri ya shiga gaban motar bayan ta shiga itama,suka dauki hanya. Ba kowa a falon kasa,sama ta haura nanma ba kowa,dakinta ta nufa.kamar yadda ta fita ta barshi kaca_kaca haka ta dawo tatarar dashi,wani dogon tsaki taja,jakar hannunta kawai ta ajiye ta nufi dakin mommy. Mommy! Mommy! Ta shiga kwala mata kira. "Na'am daughter nah,harkin dawo.yamutsa fuska tayi tana zama a gefen mommy. "nadawo mommy amma nayi matukar gajiya." Ai dole my daughter throughout fa yau kina school ai dole ki gaji. "Niba wannanbama mommy, wai har yanzu ba'a samo me aikiba,dakinafa yanda nafita na barshi haka nadawo na samesa.kaca_kaca bakiji yanda raina ya baciba.dafa kafadarta mommy tayi,am sorry daughter ananan ana binkitawa,amma bari zansa su talatu ki gyara miki dakin yanzu.bata fuska tayi nifa tsofaffinan bawani iya gyara sukayiba. " kidaiyi hakuri daughter kiyi maleji,kafin asamo yarinya. "Shikenan mommy bari naje na dubo yaya,yau gabadaya nayi missing dinsa. Tafadi hakan tana mikewa tare da ficewa daga dakin.murmushi kawai mommy tayi. Yana zaune a falonsa,akan 3 star wayarsa yake lallatsawa,suhailat ta shigo dakin,fuskarta dauke da murmushi kamar ba itace,wannan Mara fara'arba,me kallon kowa a wulakance,kodagowa beyiba balle ya kalli inda take.zama tayi agefensa,tare da kwantawa ajikinsa tana shakar daddadan kamshinsa. "Babynah I missed you,ta rada masa hakan a kunnensa.ahankali ya dago da kansa,yana jifanta da wani rikirkitaccen kallo,batare da yace mata komaiba.hannunta ta fara jawo dashi ajikinsa,tana shashshafa bayansa, harshenta tafito dashi tana lasar wuyansa zuwa habarsa. Ahankali ta hade bakinsu guri daya tafa sucking tattausan lips dinsa.lumshe idonsa yayi badan yanajin komaiba,shi kansa yana mamakin yanda duk wani Abu da suhailat take masa bayajin komai na feeling ajikinsa,ko wani canjin yanayi. Ba ita kadaibama,harta da turawan dayayi rayuwa acikinsu matan koda sunyi hugging dinsa bayajin komai. Shikansa yana tambayar kansa anya kuwa yanada lafiya.jiyayi suhailat tana Neman wuce gona da iri,hakan yasashi dawowa daga duniyar daya tafi. Tureta yayi daga jikinsa,baya tayi tana fitar da numfashi dai_dai idonta harya canza kala tsabar jaraba,lips dinta na kasa ta taune,kara matsawa jikinsa tayi,a shagwabe tace"pls my baby,kabarni na kara sucking lips dinka,inajin dadi sosai,gakuma soft skin dinka bana gajiya da......wani mugun kallo daya wurga mata yasata saurin hadiye maganarta,kofa ya nuna mata da hannunsa cikin kakkausar murya yace"get out!! Sum_sum ta mike ta fice jikinta asanyaye,saboda tasan halinsa baya son musu,duk da tsananin sonda yake mata hakan bayahanashi cin ubanta,idan ta masa ba daidaiba.dafe kansa yayi tare da runtse idonsa.bayan ta fice daga dakin, aransa yake cewa,jarabar suhailat tayi yawa,dan bayason ta damune shiyasa yake kyaleta take masa abunda taso,amma ya lura kullum.iskancinnata kara yawa yakeyi,amma zeyi maganinta.kiran sallar magriba da'aka kirane yasashi mikewa,dakinsa ya koma yayi alwala a toilet dinsa,ya nufi masallacin dake manne ajikin gidansu. Kafin magriba na kafa kaskon a warata saboda har anfara zuwa nema.ina tsaka da suyar awarar bayan sallar magriba, abun mamaki,gwaggo ta fito daga daki da saurinta. Maryam zo kije gidan lantana yanzunannan zaki karbomin wani sako,kiyi sauri sakonna saurine,kuma kinga da sauran awara karki zauna. "Toh gwaggo insha Allahu bazan zaunaba,dakina nanufa da niyyar in shiga na dakko hijabi,saboda na jikina yana dan kauri kaurin hayaki,amma gwaggo ta dakamun wata irin tsawa," gidan uwarwa zaki kuma bayan na fada miki sauri nakeyi. Da sauri nayi hanyar fita,jikina na rawa.lantana tana gandun sarki ne,da dan nisa tsakaninmu hakan yasa nake tafiya da dan sauri sauri..... Text yayiwa mommy zeje gurin abokinsa,lukman saboda damunsa dayakeyi akan bayason zuwa wajensa sedaishi yayita zuwa.mommy tana ganin text dinsa tayi murmushi, domin dama sometimes yasaba mata hakan,idan zefada mata Abu befiya kirantaba,sedai ya mata text.reply ta masa akan Allah ya kiyaye hanya.shikadai yaja motarsa,yatafi batare da koda drivernsaba....... Kusan minti goma sha biyar nayi ahanya,kafin nakarasa gidan lantana.amma nadaje lantana ta barni a tsakar gida ta shige daki,fiye da minti talatin sannan ta fito ta bani sakon.a lokacin raina yakai kololuwa wajen baci,domin nasan tana sane tamun haka,ga tsoro da fargabar abunda gwaggo zatamun yamun rufdugu akaina. Ashe sakon kudine shiyasa naga gwaggo tana rawar jiki.karba nayi na nufi gida.wajen ba mutane sosai,hasalima tunda na taho banhadu da kowaba,gudu na farayi zuciyata na bugawa,tsorone me tsanani ya kamani Wanda bansan kona meneba....... Cikin takunsa na cikakken namiji,jarumi, yake tafiya,shida lukmanne daya rakoshi ze tafi gida,tafiya sukeyi zasu karasa gurin motarsa,dayay parking a gefen titi.kamar an cillota daga sama kawai jiyayi ta bugi kirjinsa,da sauri nayi baya jinnayi karo da mutum,banzataba banyi tsammaniba,saboda hankalina gaba daya baya jikina,yayi gida.wani daddadan kamshine yaziyarci hancina,wanda tunda uwata ta haifeni bantabajin irinsaba.wata irin bugawa kirjina yayi da karfi,jikina ya fara rawa,kaina naji ya mugun saramun, jinayi kawai nayi luuuu zanfadi,taroni yayi da tattausan hannunsa,ya hadeni da jikinsa.wani irin yammm yaji ajikinsa,tsigar jikinsa ta tashi ta mimmike,lokaci daya yanayinsa ya sauya,lumshe idonsa yayi cikin amsar bakon yanayin daya riskeshi,zuciyarsa na bugawa dasauri da sauri,kafarsace ta gagara daukarsa,kasa mukayi gabadayanmu dani dashi,shi yafarayin kasa ni kuma na fada kan faffadan kirjinsa,wani mahaukacin feeling ne yaji ya bujuro masa,jinta a kwance a kirjinsa, Wanda betaba jin irinsaba tunda yake arayuwarsa.✍️ *BY* *zeey kumurya* *AUNDA KA SHUKA*......... _*(shizaka girba)*_ *MALLAKIN* 👇 *ZAINAB USMAN KUMURYA* *FARIN JINI WRITERS ASSO.....*📚 ~*Free novel*~ *Bismillahirrahmanirrahim* 0️⃣3️⃣ ...........Bansan ya'akaiba kawai gani nayi na mike tsaye,jikina ya kama kyarma tamkar anjonamun schocking, wannan shine karon farko arayuwata dana taba hada jiki da wani da namijin,dayan da suke tarene ya rike hannuna,ganin bana cikin nutsuwata yace. "sannu 'yanmata,ba bakin magana se rawa kawai na jikina yakeyi,tamkar mazari. Tattaro duk wata juriyarsa yayi,ya mike tsaye,har yanzu yanajin bakon yanayin ajikinsa. Dakyar na tattara nutsuwata na sunkuya nadauki sakon gwaggo daya fadi kasa,Allah yasama kudin a cikin Leda ta sakamun.ban kara kallon Wanda muka fadi tareba,saboda kunya da tsananin tsoron daya rufeni. Kai na akasa,cikin rawar murya nace" ka..yi..ha..kuri...dan.. Alllah,shiru yayi kawai batare da yacemun komaiba. wani tsorone ya kara mamayeni karnaje kobe hakuraba. Dayan ne kawai yamun magana. "Karki damu 'yan mata,amma dai kidinga kula gashi dare yayi,muje mu rage miki hanya ko? A'a nagode,ina gama fadar hakan na kama hanya na fara tafiya,zuciyata cike da zullumin,kodai Wanda na buge kurmane,amma banda haka mezesa mutum yaki magana.gashi gaba daya kamshin turarensa ya gamemin jikina,Jinakeyi tamkar yana gurin har yanzu.saitin zuciyata na dafa,saboda har lokacin tana bugawa da sauri da sauri.numfashi na sauke,wani bakon yanayi dabansan na meneba yana ziyartata. Dubansa lukman yayi ganin yanda gaba daya yanayinsa ya sauya,shi duk a tunaninsa ransane ya matukar baci akan abunda ya faru,hakuri ya hau bashi,amma seyaga ya daga masa hannu kawai,gurin motarsa ya nufa ya bata wuta. Ikon Allah ne kawai yakaishi gida,saboda har lokacin jiyakeyi tamkar tana kwance a kirjinnnashi,wani irin yanayi yake ciki me wuyar fassarawa. Bedroom dinsa ya nufa tare da fadawa kan gadonsa,ina ze ganta,a ina zekara ganinta,ya kara rungumeta kozeji irin yanayin dayaji sanda tana kwance a kirjinsa,gashi ko fuskarta beganiba,saboda gurin ba wadataccen haske,kansa ya dafe,tare da runtse idonsa,zuciyarsa na bugawa da sauri da sauri.... Kusan minti talatin nayi ahanya,saboda tunanin mutumin da na buge,se lumshe ido nakeyi saboda dadin kamshinsa,dayaki barin jikina,seda nazo kwanar gidanmu sannan na tuna da Abunda na bari,ga tuyar awara gashi gwaggo tace inyi sauri.addu'ar Neman tsari na fara karantowa a zuciyata.cike da tsananin tsoro na shiga gidan da sallama ta.gurin suyar awarar na kalla,kaskon na gani da guntun mai akasa, alamun an gama suyar awarar. Dakin gwaggo na nufa zuciyata na tsananta bugu,babu wutar nepa,amma dakin gwaggo da akwai sola. Tana zaune akan doguwar kujerar dake dakinnata,ta Dora kafa daya kan daya. Tsugunnawa nayi agabanta, "gwaggo ga sakonnaki" na furta cikin sanyin murya. Wani mugun kallo ta jefeni dashi,tace."gidan ubanwa kika tsaya kusan awa biyu,kuma nakira lantana tacemun tun dazu ta baki sakon. Baya na farayi ina bawa gwaggo hakuri,domin bansan mezance mataba,nasan yau me kwatata a hannun gwaggo se Allah.wata wayar wuta ta janyo agefenta me matukar kauri ta zubamun agadon bayana,da gudu na tashi nayi tsakar gida ina kokarin fita waje,amma seda gwaggo ta cimmun.dukana ta hauyi kota ina,sekace jaka,ihu nakeyi da dukkan karfina ina Neman taimako,ina bata hakuri,amma tamkar kara zugata nakeyi. Umman su saleemat wadda katangar gidansu take jikin namun gidan,itace ta shigo da saurinta.tsakiyarmu ta shiga ta rike wayar hannun gwaggo.da sauri na tashi na buya abayanta ina sakin ajiyar zuciya,akai akai. "Ke suwaiba,ki matsamun ki bani guri kuma ki cikamun bulala,gwaggo ce take fadar haka cikin daga murya,se zaro ido takeyi ta fiffika tamkar wata sabuwar kamu. "Bazan cikaba,gwaggo.yaza'ayi ki samu yarinya marainiyar Allah ki maidata sekace jaka,kullum sekin jibgeta haka akeyi. Tafa hannuwa gwaggo ta farayi tana salati,"ni zakiyiwa rashin kunya suwaiba,har cikin gidana.lallai wuyanki yayi kauri,kifita daga safgata suwaiba,banason shishshigin da kikemun akan maryam. "Ba shishshigi bane gaskiyace gwaggo kuma dole a fada miki,amma ni ba rashin kunya zan mikiba.Abunda kikeyi ba kya kyautawa... " yaza'ayi in kyauta in aiki yarinyar tun dazu taje ta zauna,amma se yanzu zata dawomun gida,dama nasan tun ba yauba,ai bin maza takeyi idan kuma sharri na mata kamshin turaren ubanwa takeyi,gatanan ai ki shanshanata kiji.saboda yadda gwaggo take magana cikin kakkausar murya tare da daga murya mutane 'yan gulma harsun fara shigowa gidannamu. Juyowa umma tayi tana kallona,hawayene kawai yake kwaranya daga idona har lokacin. Tabbas taji wani kamshi a jikina,amma hakan bazesa ta gasgata maganar gwaggoba,domin tasan maryam tasan halinta ciki da waje tasan abunda zatayi da Wanda bazatayiba. "Maryam kifada mana gaskiyar abunda ya faru.labarin komai na kwashe na fadawa umma, amma kawai senaji nauyin dace mata na fadi ajikinsa,kawai sena cemata bugeshi nayi. Karyata maganata gwaggo tayi,tana cewa "wanne irin kamshine wannan daga ka buge mutum seya zauna ajikinka,inma zanfadi gaskiya infada,ai dama bayau na fara zuwa yawon karuwancinaba.hakuri umma ta kama bata,wasu matama da suka shigo hakuri suka hau bata. Dakyar gwaggo ta hakura amma da cewa tayi seta karyamun kafa taga da wadda zanna zuwa iskancinnawa. Dukan da gwaggo tamun bedameniba kamar yadda take ta faman aibatani,tana dangantani da Kalmar karuwa,durkusawa nayi agurin ina sakin kuka me tsuma zuciya.lallashina umma ta hauyi da banbaki amma Sam bana cinta bana fahimtar metake cewa, wani zafi zuciyata takemun, ahankali na mike na shige dakina bayan kowa ya watse daga gidannamu..... 9:00 pm,suke hallara akan dinning gaba dayan gidan domin yin break fast,kuku kamar yadda yasaba ya gama komai,ya jera akan dinning. Kowa ya hallara amma banda mustapha. Kiransa mommy tayi har 3 missed call amma bedagaba. Kallon suhaita tayi tace" daughter jeki duba ki gani ko lafiya yau son befitoba. Haidarne yace"haba mommy muci abincinmu kawai kinsanfa shi big bro,bawani damuwa yayi da cin abinci ba.harararsa mommy tayi,idan shi bedamuba nina damu,daughter kiyi sauri kikirawoshi. Suhailat abunnema ya samu tashi tayi tana yiwa haidar gwalo,ta nufi part dinnasa.Baya falo hakan yasata nufar bedroom dinnasa,yana kwance idanunsa,a lumshe tamkar me bacci.tama manta da wani sakon kiranshi da'akace tayi,shaukinsa da wata muguwar sha'awarsace take fizgarta.fadawa tayi jikinsa,tana shigewa jikinsa,yayi nisa a tunanin yarinyar dabe saniba yaji mutum ajikinsa,abunda suhailat bata zato ba,kuma betaba mataba.jitayi yazagaye bayanta da hannayensa yana shafa bayan ta,yana kara matseta ajikinsa.cikin tsananin jin dadi Mara misaltuwa.suhaital ta fara kokarin kissing dinsa,soyake yaji irin yanayin dayaji dazu amma bejiba,ahankali ya bude dara_daran idansa,akan fuskar suhailat ya sauke su,da sauri ya tureta daga jikinsa, tare da mikewa zaune. ransa a matukar bace. Itama suhailat din tashi tayi ganin yanda lokaci daya ya sauya,zatayi magana yanuna mata hanyar kofa,tashi tayi tana turo baki gaba ta fice daga dakin. Tunda mommy taganta tasha jinin jikinta,ganin yanda take babbata rai,dariya haidar da zannuraini suka kwashe da ita. Haidar yace"dama seda na fada miki karkije kokinjema baze zebo. Harararsa tayi tamkar zatayi kuka tace"mommy kinga su yaa haidar ko? Mikewa mommy tayi tace"kyaleni dasu daughter.Ku zauna,kuci abincinku bari naje na sameshi. Yana zaune kamar yanda suhailat ta barshi,mommy tashigo bedroom dinnasa.zama tayi agefensa,tare da jawoshi jikinta.cikin rarrashi tafara magana "haba my son,meyasa bakason cin abinci,baka tsoron wani ciwon yakama munkai,please kazo muje muyi dinner.shagwabe fuska yayi sekace yaro yace." Mommy a koshe nakefa, ni tea kawai zansha. Shafa kansa mommy tayi cikin tsananin kaunarsa, "shikenan my son bari naje ha hado maka. Dakanta ta dafa masa a kitchen din part dinsa,seda yasha sosai tana lallabashi kamar karamin yaro,sannan ta kyaleshi.tana fita ya nufi toilet yasakarwa kansa ruwa koyaji sanyi aransa.domin gaba daya yarasa meke damunsa...... Tunda nashiga daki nake kukan tausayin rayuwata,kusan minti goma gwaggo ta shigo dakin. "Dan ubanki bazaki tashi kikarasa sauran ayyikankiba,maganarta cikin tsawa ta sani dagowa da sauri,mikewa nayi na nufi hanyar fita.jikina a sanyaye nake aikin yau,tunanin dan gayun dana gani yamun tsaye acikin zuciyata. Seda sha biyun dare ta wuce na samu kaina,domin har girki seda nayi. Bayan na karayin wanka nayi sallar isha'i na kwanta akan tabarmata.saboda tarin gajiya da ciwon kan dake damuna saboda kukan danayi tuni bacci ya kwasheni,cikin mintuna kalilan. ************* Karfe 7:30am,ya gama shirinsa tsaf na zuwa office. Ko break beyiba saboda batashi yakeba,mommy ma awaya ya sanar mata ya tafi.ma'aikatan gidanne suketa gaishesa,hannu kawai yake daga musu. Drivernsa,yana hangosa ya fito da sauri tare da bude masa gaban motar yana gaisheshi. Shima hannu kawai yadaga masa. Ya shige motar. 7:45 sun isa ma'aikatar tasu,kullum haka yake zuwa baya latti,saboda shi bayason karya ka'ida.driver na rike da briefcase dinsa har office dinsa.ma'aikata se kwasar gaisuwa sukeyi a gurinsa. Zama yayi akan kujerarsa.sakatariyarsa ce ta shigo office dinnasa,gaishesa tayi tare da dakko masa wasu takardu ta 'ajiye masa a gabansa,cikin girmamawa.sannan ta juya ta koma wajen zamanta. Wata budurwace ta shigo ma'aikatar cikin wata rantsatstsiyar mota. Faka motar tata tayi agurin da'aka tanada domin ajiye motoci.tana sanye da wani Riga da siket na atamfa,dinkin Yakama jikinta sosai,ana ganin shatin komai na jikinta.taci daurinta ture kaga tsiya,ta cokaloshi.gashin dokin data kara ya sakko har gadon bayanta. Fuskarta dauke da bakin glass,takalmin dake kafarta me shegen tsinine.hannunta dauke da wayarta,da wata hadaddiyar handbag.wadda tashiga da kayan jikinta.babu mayafi a jikinta.tafiya ta farayi cikin takunta na Jan hankali.duk inda ta ratsa se'an kalleta.office dinsa ta nufa direct. Sakatariya tana zaune taga mata tashigo ta wuceta,magana ta fara mata tana kokarin dakatar da ita,amma ko juyowa batayi ta kalletaba.batare da Neman iziniba ta murda handle din kofar office din tashige. Yana cikin danne_danne a laptop,kawai yaga mace ta shigo masa,ba sallama. Dagowa yayi cike da tsantsar mamaki yana kallonta. Karasowa tayi gaban table dinnasa, Jakarta ta ajiye akai,tare da zare glass din dake sanye a idanunta,shima ta ajiyeshi. Zama tayi akan daya daga kujerun dake gaban table dinnasa,tare da Dora kafa daya kan daya.kallonta kawai ya tsaya yakeyi yanda ta dage tana abubuwa sekace office din ubanta. Murmushi tayi akaron farko tana wani fari da idonta tace" *mustapha sulaiman me nasara* kallon mamaki kakemun ko? Aidama na fada maka bazan barkaba,kuma bazan dena bibiyarkaba harse ka soni, kota tsiya kota arziki.........✍️ *BY* *zeey kumurya* *ABUNDA KA SHUKA*......... _*(shizaka girba)*_ *MALLAKIN* 👇 *ZAINAB USMAN KUMURYA* *FARIN JINI WRITERS ASSO.....*📚 ~*Free novel*~ *Bismillahirrahmanirrahim* 0️⃣4️⃣ ..........mtssss yaja wani dogon tsaki,ya maida hankalinsa akan abunda yakeyi batare da yace mata kalaba,domin shi bashi da lokacinta.kara gyara zama tayi tana kallonsa tamkar zata lashesa.wayar dake gefensa ya latsa tare da karawa a kunne. "Kizo yanzu" kawai ya furta tare da kashe wayar.ya hade girar sama data kasa.sakatariyarsace ta shigo office din da sallama. Cikin girmamawa tace. "Sir gani" dagowa yayi yana dubanta,budurwar data shigo ya nuna mata da hannu batare da yace komaiba. Ta gane meyake nufi,maida dubanta tayi ga budurwar wadda take ta taunar cingum dinta hankali kwance,tana girgirza kafafuwanta.bayani ta fara masa cikin girmamawa. "Yallabai kawai gani nayi tataho zata shigo office dinka,ina mata magana kuma,ko saurarena batayiba,nayi kokarin hanata amma....Daga mata hannu yayi tare da nuna mata kofa.da hannunsa.ficewa tayi Daga office din,budurwar ta bita da harara.tana jifanta da wani mugun kallo. Wani mugun kallo ya wurga mata tare da fadin"get out from my office.murmushi tayi tare da fadin," aidama bakai kace inzoba,Nina gama nazo da kaina,dan haka bangama kallonka ka bari idannaga zantafi da...."I said get out" cikin tsawa ya fada mata hakan tare da mikewa tsaye yana nuna mata kofa. Idanuwansa har kada sunyi ja saboda bacin rai.jijuyoyin kansa gaba daya sun fito rudu_rudu.tashi tayi tamaida glass dinta tare da daukar Jakarta,tace. "Zantafi mustapha amma kasani,sekayi nadama da danasanin korata da kayi da kuma wulakantani,ni nafi karfin wulakanci, saboda ina sonka,kulkum nazo seka koreni,yauce rana ta karshe dazan kara zuwa office dinka,amma kajira matakin da zan dauka,zakasan kayi da *laila*,saboda ina sonka mustapha, wulakancin yau daban,na Gobe daban.kusan 2 years ina binka ina rokanka kasoni amma kaki,amma bakomai kajira abunda ze biyo baya.tana gama fadar hakan tafice fuu,tamkar zata tashi sama.ganin yanda ta fito ya bawa sakatariyarsa dariya,kyalkyalewa tayi da dariya,daman tasan karshen zancen kenan,domin bayau laila tasaba zuwaba,yana mata wulakanci.amma kota kanta batabiba tayi tafiyarta,saboda bata ita takeba. Komawa yayi ya zauna tare da dafe kansa,jingina jikinsa yayi ajikin kujerar,tare da lumshe idonsa.yarinyarnan jarababbiyace,Daga zuwanta tasa masa ciwon kai.wayarsace ta fara ringing cikin amo, me dadin sauti.hartayi ringing ta katse be dagaba.kara kira akayi still beyi picking ba.ankira yakai sau biyar,amma yaki picking.amma anki hakura dadena kiran. Tsaki yaja,ahankali ya bude tsumammun idanuwansa,wayartasa dake gefensa,ya dakko ya duba. *love one* yagani yana yawo akan screen din wayar,suhailat ce.katse kiran yayi ya tura mata text. _*I will call you later*_ Suhailat data shirya cikin wani rantatstsen less dinkin Riga da skirt,ya matukar kamata,tayi kyau sosai.se tashin kamshi takeyi.murmushi tayi bayan taga text dinsa,kokadan bata fushi dashi,duk kuwa wulakancin daze mata,baya damunta. dama ta shiryane ta kirasa taji muryarsa.yau ma kamar jiya,ko mayafi bata daukaba.jaka kawai ta dauka ta nufi dakin mommy.mommy tana zaune akan makeken royal bed dinta, waya takeyi da daddy,suhailat ta shigo dakin. Murmushi mommy tayi tare da fadin "gatananma ta shigo bari na bata wayar.mika mata wayar mommy tayi tace" ga daddy nan zakuyi magana.karba tayi ta cikin shagwaba tace"morning my dad,"morning my daughter. "daddy,yaushe zaka dawone munyi missing dinka dayawa fa. "Inanan dawowa my daughter ayyukane sukai mini yawa.ya karatun dafatan dai ananan anayi ko? " eh daddy"yawwa daughter kikara dagewa. "Insha Allah daddynah,bye. " yawwa 'yar albarka bawa mamanki wayar. Sallama mommy sukayi da daddy bayan ta karbi wayar. "Daughter har kin fito. " eh mommy na fito, mom nifa nagaji da rashin 'yar aikinnan,tsofaffinnan bawani Abu suka iyaba,dafa kafadarta mommy tayi tace"jiyama munyi waya da lami tacemun insha Allah yau zata binkito me aiki. "Yadaifi gaskiya mom,bari na karasa school sena dawo. "Adawo lafiaya my daughter,Allah ya kiyaye ya bada sa'a. "Ameen ta amsa tana fita daga dakin....... Gudu takeyi sosai a mota ranta a matukar bace yake,daidai wani madaidaiçin gida ta tsaya ta fara danna horn ba kakkautawa,da sauri gate man ya taso ya wangale mata gate din gidan. Tura hancin motartata tayi da gudunta,dasauri megadi yayi gefe domin ta kusa bita kansa.parking motar tayi tare da fitowa,ko murfin motar bata rufeba ta nufi cikin gidan. Suna zaune suna hira suka ganta ta fado dakin tamkar anjefota,jakar hannunta ta cillar tare da fadawa kan gado tana sauke numfashi,dan kwalin kanta ta cire tayi wulli dashi akan gadon.galala kawai suka saki baki suna kallonta. "Laila,lafiya kuwa meyafaru kika shigo mana a hargitse haka,ko wani abun mustapha ya miki. Tashi tayi zaune tana sauke doguwar ajiyar zuciya. Dayar da batayi maganaba ta tabe baki tare da fadin,dama nasan za'ayi haka, seda nace mata kartaje kotajema mustapha wulakantata zeyi,amma ta nace seda taje. "Haba Sakina kada kiga lefin laila,soyayyace taja mata haka.itama ba lefinta bane. Mikewa tsaye laila tayi ta fara zarya adakin, kafin ta dubesu,cikin tsananin bacin rai tace." Sakina! Habiba!, Yau itace rana ta karshe dazan kara zuwa wajen mustapha,amma wlh wlh wlh zesan ya wulakantani,seya gane ni laila nafi karfin wulakancinsa.sena masa tabo a rayuwarsa Wanda baze taba mantawa daniba,sena illata masa rayuwa.tana gama fadin hakan ta fice Daga dakin. Binbayanta sukayi da kallo dukansu.habiba tace"hmm kamar zata iya,kullum tadinga tabar mustapha amma nasan baza ta iyaba,narasa wani irin so laila takewa mustapha."hmmm, kyaleta kawai, batace zata dau matakiba,muzuba ido muga matakin dazata dauka........ ********** Yau tunda na tashi da ciwon jiki na tashi,amma haka na daure naketa ayyukana,domin nasan ban isa nace bazanyiba.karfe goma da rabi,na tashi Daga tuyar su kosai.kayan wanke _wanke na hada na koma bakin rariya na farayi.ina cikin yin wanke_wanken wata kawar gwaggo me suna lami tayi sallama,dam naji gabana ya fadi,Wanda bansan dalilin hakanba.addu'a na hauyi a cikin zuciyata. Amsa mata sallamar nayi ina mata sannu da zuwa.wani kallo naga tana bina dashi Wanda bansan kona meneneba. Nidai na gaisheta naci gaba da aikina. Yau kam naci sa'a data shigo bata zageniba,amma tabbas nasan kafin tatafi seta kullamun wani sharrin. Gwaggo tana dakinta a kwance tayi shurum sekace kayan wanki,ta kure radio tana jin waka.lami tashigo dakinnata. "Hajiya lami manya manyan kasa yau kece a gidannawa,nasan ganinki alkhairine. Gwaggo ta fadi haka tana tashi zaune,tare da rage sautin radionnata.zama hajiya lami tayi agefenta ta bata hannu suka kashe,tace wlh kam ladi,yau kinganni wata samuwace tasa nazo gurinki,arziki ne na kawo miki idan kinaso. Gyara zama gwaggo tayi ta fuskanci lami tace" dagaske lami, fadamun menene? "To,dafarko dai kinsan alhaji sulaiman menasara. "Haba lami nasanshi mana,mutumin dayayi fice a garin kano dama kasar baki daya,saboda tarin dukiyarsa da ma'aikatunsa. "Yawwa 'yar gari Ashe kingane,to nima wata hajiyace take zuwa gidansa,gurin matarsa.jiya jiyannan ta kirani tace mun nasamo,'yar aiki,gidan suna bukatar 'yar aiki kuma yarinya sukeso me jini ajika shine nace bari nazo gurinki nasan zaki bada marya......me kike nufi lami duk 'yan kauye da masu Neman aikatau kirasa wazaki ce zaki kai aiki sai maryam,gwaggo takatseta da saurinta. Dafa kafadarta lami tayi,kwantar da hankalinki kawata abun bana zafi bane,da arziki agidan wasu ai gwara agidanku,ki bar maryam din mana taje tayi aikin. " Sam_Sam lami,bazata sabuba,yanzu idanna bada maryam aikatau Waze dinga kula da sana'ata,Waze dingamun aikin gida,kuma sannan 'yan uwanmu na kauye,se sun tambayeni ina nakai maryam. "Wannan duk ba matsala bane ladi, nasan kudin da kike samu a sana'arki a wata bekai 200,000 to ita duk wata zata dinga biyanki 200,000.kinga ya isheki kinemo 'yar aiki kema idan kinaso ta dinga miki,ko 30,000 kika bata zata miki,kinga kinci riba biyu gata Sana'a gata aikin maryam. Jinjina kai gwaggo takeyi cike da mamaki tace " yanzu lami dan aikin gidan da maryam zata musu shine zasu ringa bata 200,000 anya kuwa lami gaskiyane. "To mene 200,000 a gidan alh,sulaiman menasara,kinga idan baza ki iyaba innemi wata.lami ta yunkura zata yashi. Dasauri gwaggo ta dakatar da ita,Haba lami karki tafi mana,200,000 aiba wasa bace,shikenan na amince,idanma yanzu kikeson tafiya da maryam din gatanan kutafi. Dariya lami tayi tace" shegiya kawata taji nera,daman nasan zaki yarda,kokefa yanzu zakiga kin canza kin fito gari. "Allah ko kawata gwaggo ta bata hannu suka tafa,wayaki kudi,ai kudi sine jin dadin rayuwa,barima na kirata ta hada kayanta seku wuce,aiba jira babu jinkiri. " gaskiya kam,domin suna bukatar me aiki da gaggawa,ayanda hajiyar tacemun. "maryam,maryam maryam, gwaggo ta hau kwalomun kira rass!!! Gabana ya yankeya fadi domin nasan kiran gwaggo ba alkhairi bane,dama nasan za'a rina,da sauri na amsa tare da tashi na nufi dakinnata. Durkusawa nayi agabanta, "gani gwaggo. "Yawwa maryam koma dakinki ki hado kayanki zaku tafi da lami zata kaiki wani gida aikatau,gwaggo ta fadi haka cikin halin ko'in kula. ..Zaro idanuwana nayi waje cikin kidima nace"gwaggo wanne aikin kuma. Wata muguwar harara ta cillomun tace"aikin uwarki,gidan alh.Suleiman menasara zakije ki musu aikatau. Dasauri na dafe kirjina,saboda wata irin bugawa da zuciyata tayi."nashiga uku gwaggo,rarrafawa nayi na karasa gareta,kafafuwanta na kama idona na zubda hawaye,nace"gwaggo dan girman Allah,Dan darajar annabi muhammadu S.A.W. gwaggo,karki kaini aikatau,kiduba maraicina gwaggo,kada ki kaini inda ba'asan mutuncinaba,zanzauna dake,zan miki duk abunda kikeso,idan wani lefin na miki kikace haka,kiyi hakuri dan Allah,bazan kuma mikiba wlh, kirufamun asiri kamar yadda Allah yarufa miki,kici gaba da rikeni gwaggo....wata hambara ta kaimu da kafarta,baya nayi ina sakin kuka me tsuma zuciya,tausayin kaina da rayuwata nakeyi. Lami data saki baki tana kallona tace"ladi! Kai amma yarinya akwai bakin ciki,wannan ba 'yar halak bace,ba 'yar daza'ayi arziki da ita bace.banda haka keda zakije gidan Hutu gidan dadi,mene abun damuwa.aikin dazakiyi bawani meyawa bane,gidan burjik yake da ma'aikata.kawaidai sunasan yarinyane..."bar bata bakinki wajen yimata bayani lami,dolenema taje aikinnan dan ubanta,ko yanka naman jikinta zasu dingayi,zaki tashi kije ki shirya kose nazo na tattakaki.da gudu na tashi memakon na nufi dakina kamar yadda gwaggo tace sena fice na nufi gidan su saleemat. Umma tana tsakar gida akan kujera tana tsintar shinkafa,nafada kanta ina sakin wani marayan kuka. Dasauri ta dagoni tana tambayata "lafiya maryam,meyafaru me gwaggon ta miki? Cikin shashshekar kuka nace" umma kitaimakeni wai gwaggo aiki zata kaini gidan alh.sulaiman menasara,wlh umma banason zuwa masu kudinnan basanin darajar mutum sukayiba,umma burina Inyi ilimi me zurfi arayuwata amma gwaggo ta hanani,kuma hakanma be ishetaba seta kaini aika....kuka ne yaci karfina.rungumeni umma tayi a jikinta cikin sanyin murya ta fara mun magana"kiyi hakuri maryam,kowanne bawa da irin tasa kaddarar,haka taki kaddarar tazo miki,kiyi hakuri kije kiyi aikin zakiga ribar abun agaba.kedai kawai duk inda kika tsinci kanki ki rike mutunci,da gaskiya, kiji tsoron Allah akan duk abunda zakiyi,zaki samu nasara. "Haba umma,menayiwa gwaggo dazata kaini aikatau,aikatau dinma gidan babban mekudi. Dagoni umma tayi Daga jikinta ta fara sharemun hawayena"kiyi hakuri maryam,ni kaina na girgiza nayi mamaki dajin gidan daza kije aiki,amma ita gwaggon ta inama tasan gidan mesanaran,harda zata kaiki aiki can. "Wlh nima umma bansaniba,kawartace lami tazo shine tace inbita muje ta kaini. Jinjina kai umma tayi tace."nasan son kudin gwaggo ne zesa ta amince,batare da tunanin irin rayuwar dazakiyi agidanba,kokuma halin dazaki shigaba,ita dai kawai taturaki kiyi aiki duk wata abata kudinta,amma abun da mamaki ace yanzu kamar wannan gidan basu da me aiki,anya kuwa babu wani lauje cikin nadi. " umma nima abun da nake tunani kenan,ina tunanin zuwana gidan ba alkhairi bane,dan yau gaba daya jikina asanyaye yake,tunda na tashi gabana yake ta faduwa,Ashe ga abunda zesameni. "Kidena cewa haka maryam kitashi kije kar tayi ta jiranki,Allah yana tare da me gaskiya, zamuyi ta tayaki da addu'a kema kuma kidage,domin babu abunda ya gagari ubangiji. Hawayen fuskata na share,nace. "Yanzu umma shikenan tafiya zanyi,in fuskanci wata sabuwar rayuwar,tafiya zanyi inbarku,kukadaine mutanen danake gani nakejin dadi,inajinki umma tamkar uwata dana rasa,a kullum kina nunamun rayuwa kina fadamun abunda yake na dai_dai,ga 'yar uwata kuma saleemah me kaunata dason ganin farin cikina,yanzu idannatafi na barku,Waze dinga mun abunda kukemun gaskiya umma bazan iyaba" zaki iya umma ta katseni da sauri,kada ki damu maryam ai bamu rabuba,nahar abada,duk sanda kika samu lokaci sekidinga kawo mana ziyara.jin muryar gwaggo nayi har gidan su saleemat tana kwalamun kira.zanyi magana umma ta hanani."tashi kije maryam Allah ya bada sa'a.kisa aranki Allah yana tare dake akoda yaushe.cikin sanyin jiki na mike,inajan kafafuwana dasukamun nauyi. Gaskiya na yadda gwaggo bata kaunata,bata daukeni a matsayin komaiba.anya kuwa zan iya zuwa aikatau dinnan,zuciyatace ta fara bani shawara in gudu kauye kawai wajen 'yan uwan innata........✍️ *By* *zeey kumurya* *ABUNDA KA SHUKA*......... _*(shizaka girba)*_ *MALLAKIN* 👇 *ZAINAB USMAN KUMURYA* *FARIN JINI WRITERS ASSO.....*📚 ~*Free novel*~ *Bismillahirrahmanirrahim* 0️⃣5️⃣ ...........Saboda naji hankalina be kwanta da aikatau dinnan dazaniba,haka dai na daure nafice Daga gidansu saleemat. A soron gidanmu naci karo da gwaggo ina kokarin shiga tana kokarin fita.wani gigitaccen mari ta wankeni dashi. "Dan ubanki kinaji nace miki sauri akeyi shine kika fice kin tafi sanarwa kanwar ubannakiko,to dakika fada mata ta hanaki tafiya mana,zaki wuce ki tafi kose naci ubanki,gwaggo ta karashe zancen tana rankwashina.hannuna dafe da kuncina,idanuna na zubar da hawaye nake duban gwaggo. Tsugunnawa nayi akan gwiwoyina na kama kafarta ina rokonta a karo na biyu." Gwaggo kimun rai,karki kaini aikatau dinnan naji hankalina be kwanta dashiba inajin tamkar zuwana ba alkhairi ba.....hanbari gwaggo tayi yasani kasa karasa zancena,baya nayi ina kara volume din kukana,matsowa gwaggo tayi da nufin yimun shegen duka.lami ce tataho daga cikin gidan jin kukana ta rike gwaggo. "Haba ladi,kin manta inda zamujene da ita,sokike suki daukarta kinsan halin maryam yanzu kina dukanta seta langwabe.sakin gwaggo tayi ta kamoni,tashi kije ki shirya mu wuce,kema kece da taurin kan tsiya,banda haka ni banga abunga damuwa ananba,gidan hutufa zaki cigabane yasameki.tafiya na farayi tamkar kazar da kwai ya fashewa aciki,na nufi cikin gidanmu.gwaggo tana bina da wata uwar harara. bani yanda zanyi bani da zabi,bani da mafita banda nabi lami.jikina a sanyaye,haka na hada 'yan tsummokarana acikin bakko.hawayene kawai yake malala a idanuwana.harna gama hada kayana.ko wanka da cin abinci gwaggo bata barni nayiba,haka nabi lami ina kuka kasharban,mutuwar innata tadawomun sabuwa tamkar yau ta mutu,nasan datananan dahaka bata faru daniba.amma gwaggo ko tausayina batajiba.sema jaddadamun takeyi nayi aiki da kyau,nayi duk abunda aka sani na bisu sauda kafa....... Files ne da yawa agabansa yana signing ajiki,wayarsa dake gefe ta fara ruri alamar tana bukatar agaji.a hankali ya mika hannunsa ya dakko,mahaifinsane yake kiransa.Daga wayar yayi ya kara a kunnensa. " Assalamu alaikum" ya furta cikin daddadarr muryarsa. Cikin tsananin farin cikin jin muryar dannasa,daddy ya amsa masa sallamarsa,gaisawa sukayi ya tambayesa ayyuka da komai da komai.sanar masa daddy yayi ya shirya yau da yamma,yaje a abuja zasuyi meeting da wasu abokanan kasuwancinsa,saboda shi abubuwa sun rikesa baze samu damar dawowa kasa yanzuba.fuskarsa ba yabo ba fallasa ya amsa masa da insha Allah.ajiye wayar yayi bayan sunyi sallama. Shikam Sam zuwa abujannan bemasa dadiba,saboda bayason yayi nisa da 'yan uwansa da mahaifiyarsa,amma babu yanda zeyi dole yaje,saboda babu jayayya tsakaninsa da mahaifansa.yarasa meyasa mahaifinsa,komai na harkar kasuwancinsa yake dorashi,duk da yanada manyan yara amintattu,amma komai shiyake sawa akan gaba,gashi shi kuma bayason Hulda da mutane.bayason hayaniya kokadan.ganin zaman zebata masa time,yasashi mikewa ya dakko white paper yayi rubutu akan tafiyar dazeyi na tsawon sati biyu.sakatariyarsa ya kira ya bata takarda dayayi rubutu takaiwa manager na company........ Adaidata sahu mukahau nida lami har lokacin hawaye kawai nake fitarwa Daga idanuwana,munyi tafiya me nisa sannan muka iso wata unguwa,wadda bansantaba,lokacinma dazamu hau adaidaita sahun banji inda lami tace masaba,saboda hankalina baya jikina.sallamarsa tayi muka nufi wani madaidaicin gida me kyau.matane dayawa a falon da muka shiga kala_kala.sannu lami ta musu muka nufi wani daki dake cikin falon.nidai binta kawai nakeyi tamkar rakumi da akala.wata matace kwance akan gadon dakin da muka shiga,farace sosai amma kana ganinta kasan ta kara Dana kanti,tana dan kiba.tana ganinmu ta tatashi zaune da fara'arta tana mana sannu da zuwa."kai gaskiya lami naji dadin ganinki,dama hajiya tanata kirana.tsugunnawa lami tayi agabanta tana kwasar gaisuwa,nima tsugunnawa nayi kamar yadda lami tayi cikin ladabi na gaisheta.wani kallo naga tana bina dashi Wanda nakasa gane ma'anarsa.murmushi tayi tare da kamo hannuna. "Matsonan 'yata kinji.shiru nayi tare da sunkuyar da kaina kasa.ina wasa da yatsun hannuna.kallon lami tayi tace"lami ina kika samo wannan kyakkyawar yarinyar haka.inafatadai kamar irin wadda nace miki anaso kika samo wato Mara gata.wani irin harbawa zuciyata tayi,araina nace.Mara gata kuma,to ina matarnan zata kaini,mezasuyimun da suke bukatar mata gata,Irina. innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,ya Allah kakawomun dauki a duk....maganar lamice ta katsemun zancen zucin danakeyi. "eh hajiya kamar irin wadda kikace kinaso nasamo,insha Allah baki da matsalar komai.dasauri na dago ina duban. Lami.idanuwana gaba daya sunyo waje,zuciyata na bugawa da sauri _dasauri.alamun tsoro da razani sun bayyana karara akan fuskata. Dafa kafadata matar tayi "kada kidamu 'yata ba wani Abu bane,gidan Hutu zakije dan aikin dazakiyi kadanne.ga fuskarkinanma kinci kuka kin koshi,nasan kewar gidane,amma candinma a hankali zaki saba dashi.maida kallonta tayi ga lami. "lami nagode sosaifa,barina kawo miki sakonki.itama zatayi wankane taci abinci sannnan na kaita gidan hajiya. Kudi me yawa ta bawa,lami Wanda bansan konawa bane,tatafi.kamar yanda ta fada haka tasa aka kawomun abinci me rai da lafiya,da farko kinci nayi amma matarnan tatakuramun dole naci.sejana takeyi ajikinta.bata nunamun kyamar komaiba,abun har mamaki ya bani.wanka tasa nayi ta kawo wata doguwar Riga me kyau,me adon duwatsu.rigar tamun kyau sosai,hijabin danazo dashi na Dora ajikina.umartata tayi na kwanta akan gadonta na dan runtsa,domin taga da alamun gajiya a tattare dani.kwanciya nayi tare da lumshe idona na fada duniyar tunani.saboda halin danake ciki bazan iya wani bacciba. Kafin la'asar ya gama bucking komai na tafiyarsa,karfe biyar jirginsu ze tashi.misalin karfe hudu ya fito cikin shirinsa tsaf,fuskarnan kamar kodayaushe babu walwala,a tsuke take.musammanma yauda yake jimamun barin gida.gaba daya kannensa da mahaifiyarsa ne za su yasan makarantarma seta baro gaba data tazo tayi ta masa kukan shagwaba,shikuma babu abunda ya tsana sama da kukan mace arayuwarsa.haka suka rankaya suka rakashi,seda jirginsu ya tashi sannan suka nufo gida cike da tsananin kewarsa......... Nikadai kwance a daki matar gidan ta fita gurin bakinta,har akayi sallar azhar na kasa bacci,sakawa da kuncewa kawai nakeyi,ina tunanin rayuwata.tashi nayi nayi sallar azhar bayan na idar na jero nafiloli tare da mikawa me duka kukana,akan yakareni aduk inda nake.nadade a zaune akan sallaya harsaida naji zuciyata tayi sanyi,kafin na mike nakoma kan gadon na kwanta.mintuna kadan bacci ya daukeni,abunka da babu a house,najini akan lallausar katifa.cikin baccina naji ana bubbugamun bayana ahankali.bude idanuwana nayi,ina karewa inda nake kallo.da sauri na tashi zaune saboda tunowa da inda nake.matar nance tsaye akaina tanamun murmushi. Shafa kumatuna tayi tace,am sorry natasheki Daga baccin ko,lokacine yana kurewa kitashi kiyi sallah semu wuce.kaina kawai na Daga mata,ina bin bayanta da kallo.mamakinta gaba daya ya cikani yanda kokadan bata kyamata.sauka nayi daka kan gadon na nufi toilet na dauro alwala.kafin na idar da sallah Ankara kawomun wani abincin.shima cewa nayi bazanciba,saboda akoshe nake.amma matarnan tatakuramun na tsakuri kadan naci.inagama ci muka dauki hanya,saboda kar dare yayi. wata mota me kyan gaske,muka shiga,abaya muka zauna nida ita se direbanta agaba.yana tukamu. Tafiya mukayi me dan nisa,sannan muka shigo wata unguwa,me matukar kyau da tsari.yanayin layikan unguwarma kadai abun burgewane.kowanne layi da get dinsa,gashi kowanne gida andankarashi wannan yana wane wannan, wannan yana wane wannan. Araina nake cewa dama da irin wannan unguwannin a garin kano,wani layi naga mun karya kwana munshiga get dinsa.wani makeken gida nagani a hannun damana,Wanda tunda nashigo unguwar banga me kyau da girmansa da tsaruwarsaba.sakar baki nayi ina kallonsa,ko wanene me wannan dankareren gidan oho,kai wannan sedai gidan wani babban dan siyasane.wannan gida haka sekace akasar turai.get din farko na gidan muka wuce,tafiya kadan na kara ganin wani get din agaba.Wanda anan drivan hajiya ya fara horn.rasss,gabana yayanke ya fadi,badai wannan gidan za'akaini aikatauba,shikenan lami ta saidani,gidan 'yan yankankai akakawoni.tunanina ya tsayane daidai lokacin daka wangalemana kofar get din gidan,me matukar girma.harabar gidan kanta katuwace ta isa a gina kamar gidanmu uku acikinta,wannan ma hasashenane kawai amma banga karshentaba.parking space muka nufa,Wanda aka lullubeshi da wata runfa,motocine dayawa a gurin.nidai sakar baki nayi ina kallon ikon Allah.ga wasu mutane datunda muka shigo gidan nake ganinsu,masu korayen kaya,suna shawagi kamar dai security ne.kama hannuna matar tayi tana murmushi. "Maryam mun iso gidanfa,seki fito mu nufi ciki.wani gwauron numfashi na sauke,ina dubanta.bude murfin motar tayi bayan ta sakarmin hannuna,bin bayanta nayi nima na fice Daga motar.ina rungume da 'yan kayana. Bansan tayaya zan misalta kyawu da tsaruwar gidanba,tare kuma da girmansa.part,part ne da yawa agidan,tsakanin kowanne da dan'uwansa akwai tafiya.mun wuce na1,na 2.na uku naga ta nufa,Wanda yafi duka wadanda muka wuce kyau da tsaruwa. Matattakala muka fara takawa,wadda take abakin part din,hawa hudu muka iso bakin kofar part din,wani Abu naga hajiya ta danna Wanda bansan komeneneba.mintuna kadan wata mata da bazata wuce shekara talatinba tazo ta bude mana kofar.aljannar duniya na fada lokacin Dana ganni acikin wani hadadden falo,Wanda ko'a mafarki bantaba tunanin shigarsaba a rayuwata.lallai kudi yana gurin masu kudi.ga wani kamshi da sanyin a.c daya ziyarceni a lokaci guda.ban boye kauyancinaba na fara bin ko'ina na falon da kallo.sannu da zuwa matar tayiwa hajiya.jagorarmu ta farayi da'alama ita zata kaimu wajen matar gidan.wata kofa muka kara shiga,nanma wani falonne Wanda yafi na farko haduwa.gaba daya na manta da abunda ya kawoni gidan,na manta da wata fargaba.abinci kawai nake bawa idanuwana. Matattakalar bene,naga matar ta nufa damu.nidai kawai binsu nakeyi abaya zugwi_zugwi.se tuntube nake tayi.hannuna hajiya ta kama ganin yanda nakeyi.ita a tunaninta tsoro ne ya kamani. "Kikwantar da hankalinki kinji 'yata,babu abunda zefaru dake,tunda naganki naga kin shiga raina,dabadan hajiya ta tsanantaba dani zan rikeki a wajena.saboda kin burgeni gaki da nutsuwa.babu abunda zefaru dake agidannan,kisaki jikinki kinji.gyada mata kai kawai nayi,amma zuciyata na bugawa.wani matsanancin tsorone naji ya lullubeni.addu'a nafara karantowa acikin zuciyata ta Neman taimakon Allah,da tsarinsa. Kafin mu shiga kofar falon seda muka jira aka bude mana,wowww na furta acikin zuciyata saboda girma da tsaruwar falon,babu wani tarkace acikinsa,amma falon ya matukar haduwa fiye da wadanda muka wuce na baya.kalle kallena nakeyi bansan mun iso gaban mutanen gidanba,seda hajiya ta taboni sannan na dawo hankalina,zubewa hajiya tayi akasan carpet, din dake malale a falon.nima tsugunnawa nayi kaina a kasa,araina nace lallai gaba da gabanta.Hajiyace ta fara magana cikin girmamawa,"Hajiya barka da hutawa,dafatan kina cikin koshin lafiya,dafatan na sameku lafiya.wata murya me cike da aji da izza naji tace"lafiya kalau lami,kin cika alkawari dafatan yarinyar ta cika duka sharadan Dana lissafo miki."eh hajiya gaba daya ta cika,babu matsalar komai.maida dubanta matar gidan tayi kaina tacemun "yan mata yaya sunanki.se alokacin na dago na dubeta kai masha Allah,ta dace da gidannan gaskiya,kyakkyawace sekace India,tayi ado cikin wani rantsatstsen less,koda bansaniba amma babu shakka kunnanta da hannuwanta da wuyanta daham,saboda yanda suke daukar ido. "maryam" na furta a hankali, saboda tsareni da tayi da ido tana kallona.kawar da kaina nayi gefe,kyawawan samari guda hudu idanuwana sukayi tozali dasu,tamkar babu su a falon kowannensu yanata latsa wayarsa.kamarsu daya gaba dayansu dayane kawai ya banbanta dasu.sunkuyar da kaina nayi saboda wani mugun kallo da daya Daga cikinsu ya wurgomun. Muryar hajiyar gidan naji tana cewa"shikenan lami,zaki iya wucewa zan miki transfer zuwa anjima,sauran abubuwan kuma zamu tattauna awaya. "To hajjaju makkatu,nagode Allah ya kara girma da daukaka da arziki Mara yankewa,na barki lafiya. Da ameen kawai ta amsa mata.mikewa hajiya,danaji itama ankirata da lami tayi,tayi mata sallama.dafa kaina tayi "to maryam Nina wuce,semun sake haduwa. Kawai senaji kwalla tacikomun idanuwana,senaji banaso tatafi ta barni domin bansan taya zanfara rayuwa awannan gidanba.gyada mata kai kawai nayi,har lokacin kaina yana kasa.ina wasa da yatsun hannuna. Bayan tafice daga falon hajiyar gidan,ta umarci wadda ta mana jagora datakaini dakin dazan zauna.tashi nayi nabi bayanta.Acikin falon ta nunamun dakin dazan zauna.abude yake hakan yasa tura kofar dakin nayi kawai na shige.katon dakine me dauke da saitin kayan gado masu tsananin kyau da daukar ido.tsayawa nayi ina karewa dakin kallo,ko ina tsaf dashi tamkar da mutum aciki."Yanzu ni zan kwana a wannan dakin nikadai,a wannan dakin zanci gaba da rayuwata,dakin da ko rabinsa a kyau bantaba tunanin shigarsaba,Jan kafata nayi na karasa bakin gadon,na zauna.katifar dake kan gadonma ita kanta ta dabance.ajiye kayana nayi.ina cigaba da karewa dakin kallo tare da sake_sake iri iri araina,da sabuwar rayuwar dazan fara. Kiran sallar magriba ne ya tasheni daga karanta wasikar jakin danakeyi.wata kofa Dana gani acikin dakin na nufa wadda nake kyautata zaton ta bayice.ina budewa kuwa naga toilet ne.shima toilet seda nayi kauyanci araina nace sekace daki shima.wasu abubuwan dabantaba ganinsuba nagani,banyi karambanin taba komaiba,famfo kawai na kunna nayi alwala nafito.na idar da sallah,kenan ina addu'oina matar data kawoni dakin ta shigo da sallamarta.amsa mata nayi se alokacin nasamu damar gaisheta amsamun tayi fuskarta dauke da murmushi. Tace"Kizo inji hajiya tanason ganinki. " Mikewa nayi nayi bayanta muka fice daga dakin.kamar dazu yanzumma ita da yarantane,sedai yanzu naga wata mace,tana kwance akan cinyar hajiyan ita kuma tana shafa kanta,tana mata magana.agabansu naje na durkusa kaina a kasa nace "hajiya gani. Dasauri naga budurwar dake kwance akan cinyarta ta mike zaune.........✍️ *By* *zeey kumurya* *ABUNDA KA SHUKA*......... _*(shizaka girba)*_ *MALLAKIN* 👇 *ZAINAB USMAN KUMURYA* *FARIN JINI WRITERS ASSO.....*📚 ~*Free novel*~ *Bismillahirrahmanirrahim* 0️⃣6️⃣ ............Nunani ta farayi da hannunta tana jifana da wani mugun kallo"mommy wannance me aikin. shafa kumatunta hajiyan tayi "eh,itace daughter."Ammafa mommy senaga kamar bazata iya aikinba,kalletafa sanyinta yayi yawa.jifa yanda take tafiya kamar bata da laka. " hmmm,daughter kenan rabu da 'yayan talakawannan idan sunason kudi zagewa sukeyi,suyi aiki.tabe baki tayi bata kara cewa komaiba,amma se kallona takeyi.nidai ina durkushe ina dubansu. Maido da dubanta hajiya tayi gareni ta faramun magana. "Maryam kikacemun sunanki ko? "eh hajiya. "ohk, Aikin dazakiyi agidannan iya part dinnanne,kawai.anjima za'azo a miki bayanin aikin daza kidingayi.ina fata bazan samu matsala dakeba,kinga wadannan,ta nunamun duka matasan dake dakin.ahankali na dago ina dubansu.taci gaba da magana.dukansu 'yayanane,idan sukaje aiki suka dawo anan suke zama,saboda haka kome suka saki kiyi,banason bacin ransu kokadan dan haka kibisu sau da kafa. "Insha Allah hajiya zankiyaye. nafada cikin sanyin murya ta."zaki iya komawa,dakinki.harna mike sekuma naga dacewar naje nagaida 'yayannata. Gabansu naje na durkusa nace. "ina wuninku."Daga Wanda yadago ya wurgamun kallon banza,seme bina da harara,da kallon tsana.guda dayane Wanda kamarsa ta bambamta danasu.ya ajiye wayar hannunsa,fuskarsa dauke da fara'a ya amsamun gaisuwata.harda 'yan tambayoyi yamun.tare damun fatan nasara arayuwata.naji dadi sosai yanda be kyamaceniba kamar sauran 'yan uwansa.mikewa nayi jikina a matukar sanyaye na fara tafiya.karaf idona ya hadu Dana wannan budurwar.wani kallon tsana naga tana jifana dashi se wani yamutsa fuska takeyi tamkar taga kashi. "Jibeta yanda take tafiya tamkar kazar da kwai ya fashewa a ciki.muryar budurwar na tsinkayo tana fadar haka.kwashewa da dariya naji sunyi,"to kekuwa suhailat bataci ta koshiba ai dole kiganta haka.da sauri na karasa dakin danasauka,dan bazance nawaba.idona ya cicciko da kwalla.saboda na fuskanci mutanennan basusan darajar dan Adam.yanzu haka zanyi rayuwa acikinsu.tsanata da kyamata kawai nake hangowa a atattare dasu,nabar kyarar gwaggo Ashe nanma zan tadda wata.hawayene yafara zubowa Daga idanuwana,na tausayin rayuwata. Turo kofar dakin akayi,da sauri na dago ina kallo bakin kofar.wata 'yar tsohuwace domin ko tantama banayi tayi jika dani.sallama tayi na'amsa mata,ina goge hawayen fuskata.tsugunnawa nayi cikin girmamawa na gaisheta.murmushi tamun,tana amsamun gaisuwata.kamo hannuna tayi muka zauna a bakin gado."yarinya yaya sunanki. "Sunana maryam. "Allah sarki,maryama ta baban gida,.ni kuma sunana talatu nice babba a masu aikin gidannan,nice wadda hajiya ta turo in miki bayanin aikin dazakiyi amma kafin sannan,idan bazaki damuba inason jin labarinki,wato tarihin rayuwarki. Dasauri na dago ina mata kallon mamaki. "mamaki kikeyi ko 'yannan,na shigo na tarar dake kina kuka,Daga gani dole akayi miki a aikinnan,inason jin labarin kine domin insan ta inda zan iya taimakonki. shiru nayi ina juya maganganunta araina,banason tuno abubuwan da suka faru a baya arayuwata,amma kuma a kallo daya danayiwa matar ta shiga raina,kuma bazan iya mata musuba,kodan kasancewarta babbace. " Baaba,labarina yanada yawa amma zan takaita inbakishi. "Yawwa yarinya,dafatan bantakuramikiba,inason sanin wani abune Daga gareki,domin nima inason sanar dake wani Abu game da gidannan.numfashi naja tare da gyara zama na farabawa baaba talatu tabarina. *************** "Sunana maryam,na tashi na ganni a hannun kakata,wadda ake kira inna.a unguwar darmanawa dake nan kano.innata itace ta haifi mahaifiyata.ita kuma mahaifiyata ta rasune a wajen haihuwata hakan yasa bansantaba.innata kawai nasani.mahaifina kuma tunda cikina,inna tacemun aka nemeshi aka rasa.dama badan kasarnan bane dan Niger ne.bashi da kowa yazo kasarnan neman kudi.anan cikin garin kano yake sana'arsa.innata tacemun,itadai batasan sanda suka fara soyayya da mahaifiyata ba,kawaidai da mahaifinta yace ta fito da miji tace shitakeso,duk da tarin masoyan datake dasu,domin mahaifiyata kyakkyawace.kyawun asalin Fulani. Nanfa inna tace bata isa ta auri,Wanda ba'ason asalinsaba,ita kuma mahaifiyata ta dage dole seshi takeso.inna kuma ta kafe tace sedai ta zaba,ko shi ita.amma mahaifiyata taki hakura dashi,har ciwo ne ya kwantar da ita.ganin tana kokarin mutuwa mahaifinta yace yabata shi.ita kuma inna tace be isaba.sedai idan mahaifiyata ta mutu.shikuma mahaifinta yace shiya haifi maryam,dan haka Wanda takeso ze bata baze mata auran doleba,kokuma yanaji yana gani ita kadai din dayake da ita yarasata.dama ita kadaice 'yarsu.inna tanaji tana gani aka daura auran mahaifiyata da mahaifina.inna tacemun,kwata kwata batason auran tayi iya yinta kar ayi auran,amma Allah yayi dole se'anyi.haka inna ta hakura,amma tace babu ita babu mahaifiyata. Bayan bikin befi da wata dayaba,Allah yayiwa kakana rasuwa.halin dasu inna suka shiga baze misaltuba.a lokacin mahaifiyata tayi Dana sanin bijirewa inna,tazo tana kukanta ta nemi yafiyarta domin ta gane duniyar ba gidan zama bace.itama inna a lokacin jikinta yayi sanyi,hakan yasa ta sassauta mata,amma bata sakko dukaba.a lokacinma tanata fama da laulayin dan karamin ciki. Haka sukaciga da rayuwa,tsawon shekara uku.inna tacemun mahaifiyata bata taba zuwa ta kawo mata karar mahaifinaba,akan ya mata wani Abu ba daidai ba koya muzguna mata.kana ganin yanda suke rayuwama,kasan cikin kwanciyar hankali da jin dadi sukeyinta.duk da mahaifiyata Daga ta samu ciki baya wuce wata uku ya bare.amma kokadan mahaifina be nuna damuwarsaba,ko kuma ya canzawa mahaifiyata.ita cema take damuwa akan haka, shikuma yana kwantar mata da hankali. Tayi barin ciki,yakai biyar Allah yayi dai zanzo duniya. Mahaifiyata tasha wuya akan cikina tamkar zata mutu haka take shan wahala.hakan yasa inna ta dakkota ta dawo da ita gidanta.duk shima suna tunanin ze bare kamar sauran.amma abun mamaki ana wuce wata uku,hudu se ciwo ya dauke,ta komar sumul da ita.ta koma gidanta suka cigaba da rainon cikina ita da mahaifina.soyayya sosai mahaifina yake nunawa cikin,tun lokacin yaketa siyan kayan haihuwa. Saboda murnar wannan cikin ya tsaya tunda haryakai wata shida.mahaifina dama akusuwar kantin kwari yake a shagon wani uban gidansa.inna tace mun,yana samu sosai.yanada rufin asirinsa.wata rana yaje kasuwa mahaifiyata taga har dare bedawoba.shida yake dawowa kafin magriba.hankalinta ya tashi,ta kira duk Wanda take tunanin suna tare an tabbatar mata daya taho gida lafiya kalau.shiru_shiru tana jiransa,amma har wajen goman dare shiru,bedawoba.zarar hijabinta tayi ta nufi gidan inna tana kuka ta sanar mata.itama inna ta girgiza sosai,amma ta daure ta kwantar wada mahaifiyata hankali.shiru_shiru har cikin dare bedawoba.abun kamar wasa har washegari.duk inda ake tunanin za'a sameshi anje bayanan.hanakalin mahaifiyatafa ya tashi bataci batasha se aikin kuka.tun ana saran ganinsa har kwanaki suka shude babu shi,babu labarinsa.nan maganganu suka dinga yawo akan ya gudu yabar mahaifiyata,dama abunda yasa yake zaune da ita danbata haihu bane,yanzu kuma tunda yaga zata haihu shine ya gudu ya barta.bayason wahalar 'yaya.tundaga ranar mahaifiyata ta koma,bata da aiki se kuka,tun inna tana rarrshinta harta zuba mata ido.haka tacigaba da rainon cikina cikin bakin ciki.ranar wata juma'a da yamma ta haifeni.a gida ta haihu.bayan an gama gyarata aka miko mata ni.inna tacemun kamarmu daya,hakan yasa ta kuramun ido tana kallonna.idanuwanta cike da hawaye.lafiya kalau ta haihu,amma bayan befi awa biyuba, wani ciwon cikina me tsanani ya kamata.ana kokarin kaita asibiti,tace kada su wahalar da Kansu ita mutuwa zatayi,amma tabar wasiyya,idan Allah yarayani a bani wata takarda data rubuta tana cikin kayanta.kuma asamun sunanta wato maryama,saboda shine sunan da mahaifina yace mata zesaka idan ya haifi diya mace.su inna basu kulataba da ita da maganganunta,suka dauketa zasu kaita asibiti domin sunyi tunanin zafin ciwone yasata fadar haka.amma kafin sukaiga asibitin Allah ya mata rasuwa. Inna tayi kuka,tamkar ranta ze fita.mutuwar tilon yartata bakaramin dukan ta tayiba.ta gane rabonane yasa mahaifiyata ta dage seta auri mahaifina. Hakan yasa tayafe mata duniya da lahira.ita kanta shedace akan mahaifiya mutumin kirkine,kawai dai matsalarsa rashin sanin asalinsa.inna ta rungume ni,tacigaba da rainona cikin so da tsantsar kauna,tana jina tamkar maryam dinta data rasa.inna bata boyemun sunaba maryam take kirana dashi. Nataso cikin gata da kulawa a wajen innata.innata bata rageni da komaiba.abincin siyarwa,dasu sobo da kunun aya, shine sana'ar da inna takeyi take rufa mana asiri.duk da girma yafara kamata.komai nakeso innata tanamun,tasani a private school. Tare da islamiyya.Burina arayuwata,inyi karatu me zurfi Insamu aikinyi,in hutar da inna Daga wannan wahalar datakeyi,kullum tana bakin wuta.inna bata da 'yan uwa a garinnan,yan uwanta duk suna can kauye a garinsu.iyayenta kuma Allah ya musu rasuwa. 'Yar uwarta guda dayace,da suke uwa daya,uba daya wato gwaggo. Amma nidai tunda naso so daya nataba ganin gwaggo a gidan innata.innata batamun irin rikonnan da'ake cewa rikon kakaba,ta shagwabaniba kota sangartani.ta bani tarbiyya ingantacciya.tun ina karama take nunamun rayuwa,takemun nasiha,akan narike mutuncina.nakasance me hakuri a duk halin Dana shiga.bansan kowaba,se innata.itace uwata itace ubana,itace dangina.itace gatana.shakuwa me karfi,tare da tsantsar kaunace a tsakanina da innata.dominni a lokacinma saboda yarintata,bansan ba itace ta haifeniba.innata macece,ta mutane saboda kirkinta da mutunta dan'adam. Dogon Numfashi,naja ina duban baaba talatu,nace "zan takaita miki labarinane,saboda yanayin lokaci.domin idannace zan fayyace miki komai,semu kwana anan bangama mikiba. "Tom shikenan maryam,kici gaba domin inason jin karshen labarinnannaki. "Wata rana,nadawo Daga school, da misalin karfe biyu na rana.a lokacin shekarata goma shabiyu. Ina J.S.S 1. Da sallamata na shigo gidan da murnarta ina kwalawa inna kira,kamar kodayaushe,idanna dawo.turus na tsaya ganin banga innata a kitchen ba,agurin saida abincin ta.babu alamun ma tayi girkin yau.dasauri na nufi dakin da muke kwana ina kwala mata kira.Kudundune na hangota akan gado ta lulluba da abun rufarmu.jakar makarantata na cillar na nufi kan gadon.ina cigaba da kiranta.yaye bargon data lullaba nayi,jikinta se rawar Dari yake.wuyanta na taba naji zafi zau. "Innata baki da lafiya meyasameki meke damunki.na tambayeta kwalla na taruwa a idona.Bakinta ta fara motsawa alamun tanason tace wani Abu,amma maganar taki fita.jikinta serawa yake hakoranta na hadewa kamar me jijjiga.bantaba ganinta cikin ciwo irin hakaba.kuka na farayi ina girgizata.tare da tambayarta abunda yake damunta,amma inna ta kasa magana.abunda yafi tsoratani yanda naga idanuwanta sun juye.gashi gida ba kowa dagani se ita. Wani tunanine yazomun cikin zuciyata.dasauri na tashi nanufi gidan su umman saleemat,dake jikin gidanmu. Umma! Umma! Nashiga kwala mata kira. "Na'am maryam wannan kiran hakafa,lafiya? "Umma innace bata da lafiya,tana kwance jikinta se rawa yakeyi. "subhanallah, shiyasa yau banji hayaniyar masu siyayyar abinciba,muje inga jikinnata.bari in dakko hijabina........✍️ ```sannu bata hana zuwa,sedai adade ba'ajeba.kada kudamu da sannu zamuzo inda kukeso.```🥰😘 *By* *zeey kumurya* *ABUNDA KA SHUKA*......... _*(shizaka girba)*_ *MALLAKIN* 👇 *ZAINAB USMAN KUMURYA* *FARIN JINI WRITERS ASSO.....*📚 ~*Free novel*~ *Bismillahirrahmanirrahim* 0️⃣7️⃣ ..............Muna shiga dakin nida umma,mukatarar inna har lokacin jikinta se rawa yakeyi.dasauri umma ta karasa kanta dagota tayi taji jikinnata yayi zafi sosai,"maryam debomun ruwa abaho,kitaho da towel. "To umma" har lokacin kuka kawai nakeyi.da sauri na debo ruwan nakawo mata.harta fara cirewa inna rigarta,kara umartata tayi naje nakirawo wani isa me chemist dake bakin layinmu. Cikin yan mintuna muka iso gidan nida Dr isah,a lokacin har umma ta gama gasawa inna jikinta.dubata yayi ya mata allura tare da sanya mata Karin ruwa.se alokacin nasaki wata ajiyar zuciya.saboda ganin jikin innata ya dena rawa,numfashinta yana fita dai_dai alamun ta samu bacci.magunguna ya rubuta ya bani yace kafin tatashi naje na siyo,kuma atabbatar tasha koda ruwan tea ne idan ta tashi.ranar ninayi duka aikin gida.saboda inna babu abun data iyayi.abinci kuma ummace ta kawo mana.washegari, jikin inna tatashi dashi da sauki.amma bata warke duka ba. Inna tayi_tayi inje school,amma nace mata nibazanjeba.seta kara samun sauki.haka ta hakura ta kyaleni.bayan nagama share_share da wanke_wanke.muna zaune adaki da inna,ta dubeni tace. "Maryam,ina horanki daki kasance me juriya,akan duk halin dakika tsinci kanki aciki.komai runtsi komai wahala kada ki zubar da mutuncinki,domin mutuncinki shine kadararki.koda na mutu,kada ki koma kauye wajen 'yan uwana,kici gaba da zama anan saboda kisamu ingantaccen ilimi,saboda iliminkine kadai ze taimakeki a rayuwarki.nasiha sosai inna tamun me ratsa zuciya me kama da wasiyya.rungumeta nayi ina kuka nace."inna kidena fadar haka bazaki mutuba,insha Allah harse kinga yayana,kinci gajiyar ilimin da kika dorani akai.lallashina kawai inna tafarayi.itama tana zubar da hawaye. Bayan kwana 2 inna ta warke rass,tamkar ba itaba.hakan yasa na koma makarantata.naci gaba da karatuna.sekuma wata sabuwa,bayan befi wata biyuba inna ta fara wani irin ciwo,cuta me tsanani.ko hannunta bata iya dagawa.sedai akwantar atayar.gashi babu me jinyarta ni kuma alokacin nayi kankanta.ummace take dawainiya damu da sauran makotan arziki.'yan uwan innata na kauye sunzo amma basu wani jimaba,suka koma.ciwofa yakici yaki cinyewa.babansu saleemat ne yakai inna asibiti.aiko ana zuwa suka bata gado.babu me jinyar inna,umma kuma ga 'yayanta ga aikin gida,baze yiyu tazo asibiti jinyaba.hakan yasa akace dole wani Dan uwan inna seyazo jinyarta. Dakyar wani kanin babansu inna,yasamu gwaggo a yawon gagarinta.da farkoma datazo cewa tayi baza ta iya jinyaba,amma kuma kome tatuna Daga baya kuma seta amince.nidai banda insaka inna agaba ina kuka babu abunda nakeyi.makarantama dakyar umma ta lallabani na koma.inna tayi watanni a asibiti,a canza mata wannan a maidata wannan.gaba daya dan kudin data mallaka duk ya kare a yawon asibiti.amma cuta dai tananan a jikinta.ahaka har na shiga J.S.S 2,nida saleemat.bayan dogon lokaci da inna ta dauka tana jinya.cikin ikon Allah se sauki yafara samuwa har aka sallamota muka dawo gida.murna a gurina kamar me innata ta warke. A lokacin gwaggo ta nuna tanason tafiya amma inna ta hanata.taitai mata fada akan rayuwar datakeyi da girmanta bane dorewa bace.gwaggo tayi aure_aure,amma bata taba haihuwaba.kuma duk auran datayi bata jimawa take fitowa,saboda masifarta da rashin mutuncinta ba kowa ze iya zama da itaba.gashi taita Tarawa mutum kawayenta 'yan duniya a gida.ta yarda ta zauna damu da kyar,duk da badadin zama mukeji da itaba. amma,kullum.seta fice yawonta.inna sedai kawai ta bita da addu'ar shiriya. Watarana,danar dabazan taba mantawa da itaba arayuwata, na dawo daga school da murnata,saboda a makaranta anzabemu nida saleemat acikin wadanda zasuyi J.S.S.C.E EXAM. Saboda kokarinmu.base munyi j ss3,ba kawai zamu tafi senior class.kamar kodayaushe idannadawo daga makaranta gwaggo batanan,yauma haka,dakinmu na nufa,inna tana kan sallaya azaune tana lazimi. "Innata! Innata! na shiga kwada mata kira tare da fadawa jikinta. "Oh ni,fateemah maryam koyaushe zaki girma.dariya nayi nace "kai inna na girma mana,amma agurinkine bana girma,tunda ni kadaice bani da kani.murmushi inna tayi ta shafa kaina tace. " idan baki da kani maryam,ai wataran uwa zaki zama,dan ko yanzu akai miki aure zama zakiyi. Rufe fuskata nayi da hannuna,cikin jin kunya. "Kai inna aure kuma,nidai ban girmaba.sonake nayi karatu me zurfi,na zama likita idan baki da lafiya base munje asibitiba,nizan baki magani da kaina,in miki allura. Murmushi inna ta karayi tace."Allah yasa maryam dita,Allah ya cika miki burinki,nima burina naga kinyi karatunnan maryam. " Ameen innata,yawwa inna,nazo miki da wani daddadan albishir. A makaranta yau aka kawo mana form din makarantar science ta kano,shine aka zabemu hardani da saleemat,nanda watanni kadan zamu zana. "Wacce makarantar science din kuma maryam?. "makarantar da usainan bayan gida tayi me fararen uniform da ratsin Kore. " to aike,maryam naga yanzu aji biyu kike,shine kuma za'akaiki babbar sakandire,ai bakiyi aji uku ba. "Principal din makarantarmuce,ta kirawo mu harda 'yan aji 3,shine aka mana wata 'yar jarabawa kuma naci,makina haryafi na 'yan aji ukun. "Toh shikenan maryam,Allah yabada sa'a ya taimaka. "Ameen inna,nafadi hakan ina mikewa zuciyata cike da murna.na fara cire uniform dina.wani kallo naga inna tana bina dashi Wanda nakasa gane kona mene. " inna lafiya naga kinamun wannan kallon. "Babu komai maryam.mikewa tayi taci gaba da jero nafilfilolinta.lafiya kalau muka wuni da inna,munata hirarmu cikin nishadi. Amma anayin magriba,tacemun kanta yana mata ciwo.ta kwanta,dakyar ta samu tayi sallar isha'i. Ta kara kwanciya. Cikin dare naji inna tana wani irin nishi,sama_sama nakeji cikin baccina,tun tanayi a hankali harnaji ya hanani bacci.tashi nayi na lalubi makunnin kwan dakin na kunna. Inna nagani,hannunta dafe da kirjinta,numfashinta na fita dakyar."inna meyafaru,meyasameki.innalillahi.......kanta kawai take girgizamun tanamun nuni da hannunta,tana kokarin yimun magana amma ta kasa.dakyar nagane ruwa take bukata.da sauri na fita na dakko mata me sanyi na kawo mata. Seda tashanye Tass,natambayeta na karo mata tacemun A'a. Gyara mata kwanciyarta nayi,saboda ganin numfashinta ya fara daidaita.ina jera mata sannu.hannunna ta kama cikin muryar marasa lafiya tafaramun magana."maryam! Kidauki duk kaddarar datazo miki arayuwa,kada ki butulcewa Allah.jikina yana bani bazan kara wasu kwanaki masu yawaba.ki riki gaskiya aduk inda kike,sannan kuma jigon zaman duniya,hakuri. Kiduba kasan gadona,akwai wata akwatin karfe.cikin wata jaka,zakiga wata takarda da wasu hotuna.hotunan mahaifinkine Dana mahaifiyarki,takardar kuma mahaifiyar kice ta rubuta tace abaki.kirjina yanamun ciwo sosai maryam,tamkar andoramun dutse haka nake jinsa inaji ajikina ajalin......da sauri na rufewa inna bakinta ina sakin kuka,"inna kidena cewa haka,bazaki mutu yanzu ba insha Allah,kinyi cutama datafi wannan kuma gashi kin warke,wannanma insha Allah nasan zaki warke. Inna ta bude baki zatamun magana wani tarine ya sarketa,ta fara yinsa ba kakkautawa.tamkar numfashinta ze fita.da gudu na fice daga dakin na nufi dakin da gwaggo take kwana,na fara bubbuga mata kofa da karfi. Dakyar gwaggo ta tashi,cikin masifa take tambayata menene.cikin kuka na mata bayani tataimakeni mukai inna asibiti.amma gwaggo seta rufeni da masifa tana zagina,rokonta nakamayi amma Sam gwaggo taki yarda tace bacci takeji da safe, akaita asibitin babu abunda zefitar da ita cikin darennan.jikina a sanyaye na koma dakinmu.shiru na tarar da inna idonta,a rufe.abunka da yarinta,sena sauke ajiyar zuciya ina cewa,tama samu bacci ya dauketa. Bargo na lulluba mata,nima na kwanta,amma Sam nakasa bacci juyi kawai nakeyi.har asuba. Amma abun mamaki senaga inna bata tashi sallahba,kyaleta nayi saboda naga bata da lafiya.har gari yafara haske inna bata tashiba.kuma abunda yaban mamaki yanda ta kwanta haka take ko juyi batayiba. Tashinta na farayi ina bubbuga jikinta,amma shiru inna ko motsi.hannunta na daga naji yakara nauyi,ina sakinshi naji ya koma sharaf.wata irin bugawa zuciyata tayi,wani gumi yafara tsatstsafomun.kiran sunanta na farayi da karfi ina jijjigata da dukkan karfina,amma shiru.ihu na kurma,na nufin dakin gwaggo ina bugawa inacemata tazo inna ta suma,mukaita asibiti.amma gwaggo tana fitowa ta tsinkamun mari, wai tun cikin dare na hanata bacci.idan ban tafi na bata guriba seta babballani. Ina gunjin kuka,na zare sakatar gidanmu,na nufi gidansu saleemat.gidan abude yake,idan babansu yaje masallaci baya kara rufewa.ko sallama banyiba saboda rudewa kafata ko takalmi babu,umma tana kokarin hura gawayi saboda yan makaranta ta hangoni nashigo a hargitse. "Maryam lafiya dasassafennan? "Umma kitaimakamun mukai inna asibiti ta suma,kuma babu inda yake motsi ajikint...ai umma bata bari na karasaba tayi hanyar fita,dama da hijabinta ajikinta.bin bayanta nayi.muna zuwa naga ta kara kunnanta akan hancin inna, duddubata naga tanayi.batacemun komaiba,kawai gani nayi taja bargo ta lullube inna har fuskarta. Janyoni tayi jikinta idanuwanta na zubar da hawaye,sonake nayi magana amma na kasa,saboda nidai nasan Wanda ya mutu kadai ake lullubewa.dakyar na iya tambayar umma cikin rawar murya."umma,bangane me hakan yake nufiba,umma dan Allah kada kicemun innata ta mutu,wlh nima mutuwa zanyi.cikin San kwantarmun da hankali,umma tace"innarki bata mutuba,bari na fadawa baban salermah,yasamo mota mukaita asibiti. Ajiyar zuciya na sauke.umma ta rabani da jikinta ta fice daga dakin.intakaice miki zance,baban saleemah yazo,da wani likita har dakin inna,karshe dai likitan ya tabbarmana,Allah ya karbi baiwarsa inna,ya mata rasuwa. Cakumar likinta nayi,ina kuka nace."karyane innta bata mutuba,innata bazata taba mutuwa tabarniba.janyeni umma tayi daga jikinsa,itama tana kuka tace."haba maryam, kefa musulmace,kuma kinsan dukkan merai mamacine,ki yarda da kaddara,yanzu inna bata bukatar kukanki addu'arki kawai take bukata. "Yanzu umma kema kinyarda inna ta mutu,wlh bata mutuba suma tayi,damafa bata da lafiya mukaita asibiti,wancan karanma haka tayi,umma kitaimakeni mukaita asibiti,nasan zata tashi,inna bazata mutu ta barniba.kuka kawai nakeyi na fitar hankali,ina maganganu marasa kan gado.hannuna umma ta kama muka fice daga dakin. Duk wannan abun da akeyi gwaggo tana daki tana barci,har lokacin bata fitoba. Kafin karfe 7 na safe,gidanmu ya cika da mutane anata koke koke,makuta da abokanan arziki domin inna ta kowace,kowa seyabonta yakeyi.se'alokacin gwaggo ta fito ta kama kukan munafurcinta,babu Wanda yabi ta kanta. Nidai ina zaune nayi jigum,kukanma babu ya dauke,zuciyata ta kekeshe.duk da ni yarinyace a lokacin amma nasan dacin mutuwa.bin kowa nake da kallo,domin ni banyarda inna ta rasuba,nasan suma tayi kuma zata farfado. Seda 'yan kauyenmu suka karaso sannan,aka mata sutura.nidai ina daki umma ta rikeni gam taki sakina.wata 'yar uwarsu innace,dasukazo daga kauye tazo ta kama hannuna,ta kaini dakin inna.wata irin harbawa zuciyata tayi saboda ganin inna,kwance a cikin makara,kwace hannuna nayi na fada kan makarar ina sakin kuka."wayyo innata,dan Allah kitashi,karki tafi ki barni,kitashi kice musu baki mutuba,inna bani da kowa seke,meyasa zaki tafi kibarni,kece uwata,kece ubana,kekadai nake gani inji dadi araina,innaaaa!!!..... Kuka yaci karfina. Janyeni akayi,su baban saleemah da wasu 'yan uwan inna,suka kinkimi makarar. Wani karfine yazomun na tashi da sauri, na kankame makarar,ina ihu ina fadin baza'a fitarmun da innataba,amma inaji ina gani aka janyeni aka ficemun,da sanyin idaniyata,me tallafar rayuwata. Bankara sanin meyafaruba,se farkawa nayi na ganni akan cinyar umma,tanamun firfita,idanta yayi luhu_luhu alamun taci kuka ta koshi.yunkurawa nayi dakyar,na tashi zaune.sannu mutanen dake dakin suka kama yimun,kaina kawai na iya daga musu.saboda wata muguwar sarawa da kaina yakemun.dole na hakura nadau dangana,akan tabbas inna ta rasu.amma tashin hankalin da rudanin da zuciyata ta shiga baze misaltuba.kowa yazo ya ganni seya zubarmun da hawaye.nasiha sosai umma tamun.akan yadda da kaddara.nayi kukan fili Dana zuciya.Mara adadi akan rashin inna.haka akayi sadakar uku aka watse,a lokacin mutuwar inna tadawomun sabuwa.bana ci bana sha,se aikin kuka.dakyar umma take sani nakecin kwayoyin abinci,suma jinsu nakeyi tamkar madaci.komai ya tsayamun cak.kunci da damuwa sun taru sun mun yawa.hakan ya haifarmun da matsanancin ciwon kai,Wanda ko idona dakyar nake motsawa.karshedai har kwanciya nayi a gadon asibiti saboda ciwo,mutuwar gwaggo ta dakeni sosai,kuma har yau bata bar dukanaba,idannatunota inajin tamkar yau abunyafaru. Ahankali ahankali komai yake wucewa na duniya,haka innata ta shude ta zama sedai tarihinta,ahankali rashinta yafara bin jikina,nabawa zuciyata hakuri da dangana akan rashin innata.addu'a kawai nake mata nasan shine abunda tafi bukata.'yan uwan inna,sunso tafiya dani kauye amma gwaggo tace"zata rikeni anan,saboda makaranta ta,badan sunsoba,suka hakura suka barni,awajenta. Gwaggo ta gaje,gidan innata,tagaje komai nata.ta koma dakinta ma da zama ni kuma ta koroni dayan dakin.gwaggo bata bani abinci,babu ruwanta da cina balle shana.shargoriyarta kawai takeyi.tatara kawayenta su cika gidan,su kunna kida suyita rawa wataranma har maza take kawowa.mutuwar inna ko'ajikinta.umma ce,take bani abinci da duk wani Abu danake bukata.kudin makaranta kuma babansu saleemat ne yake bamu tare.ahaka rayuwa taita tafiyarmun babu dadi kokadan.cikin ikon Allah muka zana jarrabawa,kuma duk munci nida saleemat.nayi farin ciki sosai,danaci, kuma naji dadi.shine Abu na farko daya sanyayamun rai bayan mutuwar inna.amma naso inna tananan tatayani murna. Babansu salermat ne yamana,komai tun daga uniform,littattafai da duk abubuwan da'ake bukata.duk da shima bawani karfine dashiba,sedai rufin asirin Allah. Nafara makaranta,kuma inajin dadinta sosai,tana debemun kewa.amma term 2 kawai naje,gwaggo ta hana.tacemun tagaji da zama ba Sana'a dole inzauna,indinga mata Sana'a agida.nayi kuka,na roki gwaggo,amma gwaggo taki hakura.akan haka har fada sukayi da umma.baban saleemat yace"umma ta kyaleta saboda shi bayason fitina.tun daga lokacin gwaggo ta maidani tamkar jaka,ko wata baiwa.nice,wankinta,shara,wanke_wanke,girkin gida dana kayan sana'arta.baruwanta da kankantar shekaruna haka take tulamun uban aiki.bani da Hutu kwata_kwata se cikin dare.Tun inayi ina kuka saboda rashin sabo da gajiya,harna saba.mugunta kala_kala nashata a wajen gwaggo,ta rabani da kowa,har umma ta hanani zuwa wajen ta,sedai na saci hanya naje,bata saniba.naci wahala bakadanba,awajen gwaggo.duk abunda zan mata,bata gani sedai ta sakamun,da duka koda zagi,ko mugun alkaba'i.gwaggo bata da imani,kokadan muguwace ta karshe,kanta kawai tasani arayuwarta.indai zata samu kudi ko menene zatayi,makota kowa kuka yakeyi da ita.saboda munanan dabi'unta. Ajiyar zuciya,nasauke ina duban baaba talatu,data kuramun ido kawai tana saurarona,idanuwanta na zubar da hawaye.nima hawayen fuskata na share,nace"wannan shine takaitaccen labarina.naso fayyace miki komai,amma lokaci baze barmuba,kuma banason tuno wasu abubuwan da suka faru dani. "Gaskiya,maryam kinga rayuwa tunkina yar karamarki,labarinki akwai abun tausayi,Allah yajikan innarki da mahaifiyarki.mahaifinki kuma idan har yana raye Allah ya bayyana miki shi,da gaggawa. "Ameen baaba,nagode. "to,amma maryam wayakawoki gidannan aikatau?. "Wata kawar gwaggoce lami,ta dakkoni daga gida,amma ba ita ta kawoniba wata hajiya lamice daban. Jinjina kai talatu tayi,tabbas nasan hajiya lamin,mutuniyar hajiyace sosai.Mikewa baaba,talatu tayi tana fadin,"muje muyi sallah kinga har anyi isha'i.sena fada miki aikinki a gidannan,da kuma takaitaccen tarihin gidan,kafin masu gidan su fito cin abincin dare. Bayan mun idar da sallah,talatu ta gyara zamanta ta fara bani labarin gidan."kamar yadda kika sani,sunan me gidannan alh.sulaiman menasara.fitaccen dan kasuwane,Wanda yake da shaguna a kasuwannin garinnan da kuma kamfanoni da dama.alh.mutumin kirkine,gashi da kyauta kuma shi baya wulakanta talaka.sedai kuma gaskiya bashida iko da gidansa,domin matarsa tafi karfinsa juyasa takeyi, abunda tace shiza'ayi a gidannan.ita kuma hajiya,gaskiya batasan talaka,ya rabeta.idan kazo da Neman taimako zata taimaka maka,amma fa ita Sam bata Hulda da talaka.macece ita meson a girmamata,ana nuna mata kuma ita tafi kowa.gata da bala'in son 'ya'ya,kamar me.idan kinaso Ku shirya da ita to kiso 'ya'yanta.wadannan samarin dakika gani duka 'ya'yantane.kome zasuyi mara kyau bata kwabarsu,akwaima daya babbansu me suna mustapha,Wanda hajiya duka tafi sonsa agidannan,tamkarma tsoransa takeji.tana masifar sonsa,bata boye soyayyar datake masa. Duka 'yayan,gidannan basu da mutunci,nidinnan dakika ganni da girmana,dakamun tsawa sukeyi.guda dayane acikinsu me suna sadiq,shine na 2,shikadaine yayo halin babansa,yanda kamarsa take daban haka halinsa,yake daban.domin shi kowa nasane,kuma baya wulakanta mutane,kamar sauran 'yan uwansa. Se kuma uwar gayya,wato suhailat,taci uwar kowa a rashin kunya da wulakanta mutane a gidannan. Bata tsoron kowa,duk girmanka idan ka mata badaidaiba setace zata tsinka maka mari.mustapha ne kadai,take tsoro kuma take shayi agidanna.shine Wanda zata aura kuma.ita 'yar kanwar hajiyace,mahaifinta kuma kanin alhajine.ita kadai suka haifa,ankawota yaye gidannan,iyayenta sunyi tafiya sukayi hadari Allah ya musu rasuwa.hakan yasa zamanta yadawo gidannan gaba daya.hajiya da alh,da sauran yayyenta suka dauki son duniya suka Dora mata.kasancewarta ita kadaice mace. Ki lura,kisan irin zaman dazakiyi da kowa,domin yaran gidannan basu da mutunci ko kadan,wulakanta mutum ba komai bane agurinsu.dayannan Dana gaya miki shikadaine me hali na gari.sekuma babbansu,Wanda shi tsabar miskilancinsama ba'a gane halinsa.kinganninan nafi shekara 20 ina aiki agidannan, amma bazance miki ga abunda yafiso da Wanda bayasoba.wannan shine halayensu atakaice. Ajiyar zuciya na sauke,nace." Toh baaba,nagode sosai kuma insha Allah zan zauna da kowa daidai da halinsa. "Yawwa yarinya,sekuma maganar aikin daza kidingayi.zaki dinga gyara dakin hajiya Dana suhailat.da kuma duka falukan dake part din nan.se wanke_wanke.amma banda girki kuku ne, yake girki,kekuma idan suka hallara zasu ci abinci zaki dinga saving dinsu.sekuma wani aikin idan wani yagadama yasakaki dankaran Kansa. "shikenan baba talatu nagode sosai.Allah yasaka da alkhairi. Mikewa talatu tayi,har ta kai bakin kofa bankuma San meta tunaba, naga ta juyo ta dawo ta zauna. "maryam! Takirawoni,cikin wata irin murya bata jira na'amsaba taci gaba da magana,tunda naganki naji kin shiga raina,kuma naga bakiyi kama da irin 'yan kauyen da'ake kawosu aikatauba,dakika bani labarinki naji wani matsanancin tausayinki ya kamani,hakan yasa na kudiri niyyar taimakonki,kin rabu da masifar gwaggo,to nanma akwai wata babbar masifar.zanfada miki wani sirri na gidannan Wanda ba kowane yasanshiba,ko wasu masu aikin gidannan basu saniba,balle wani na waje.amma sekinmun alkawarin idanna fada miki bazakiyi yunkurin barin gidannanba.rasssss!!! Gabana yayanke ya fadi,duk da bansan meneneba,amma daga ji nasan ba'abun dadibane. "Insha Allah baaba,bazanyi yunkurin guduwaba, na miki alkawari."kinsandai nauyin alkawari,kada kikarya. "Insha Allah,baaba.nafadi haka cikin zakuwar jin mezata cemun. Dogon numfashi baaba talatu taja,tace. "Hajiya bata taba daukar babbar mace a matsayin me aikin part dinnanba,tafison yarinya karama kamarkinnan.kuma duk yarinyar da'aka kawota.aikatau gidanna,sedai a wayi gari aga anmata fyade,anyiwa 'yan mata masu aiki sama da 10,haka agidannan, kuma duk wadda aka mata fyaden bata jimawa take mutuwa.......✍️ *BY* *zeey kumurya* *ABUNDA KA SHUKA*......... _*(shizaka girba)*_ *MALLAKIN* 👇 *ZAINAB USMAN KUMURYA* *FARIN JINI WRITERS ASSO.....*📚 ~*Free novel*~ *Bismillahirrahmanirrahim* 0️⃣8️⃣ .............mikewa tsaye nayi cikin tsananin kaduwa da razana."innalillahi,wa'inna'ilaihirraji'un.naita maimaitawa saboda bugawar da zuciya takemun,tamkar zata Faso kirjina ta fito,haka nake jinta.mikewa talatu tayi ta kama,hannuna ta kara zaunar dani. "Maryam,ki kwantar da hankalinki,insha Allahu hakan baze faru akankiba.dasauri na dago ina dubanta.gyadamun kai tayi alamun tabbatarwa.taci gaba da bayaninta."ba'ayiwa kowacce yarinya fyade setayi watanni,kuma abunda ze baki mamaki,ba'asan Wanda yakeyin fyadenba.duk da yaran gidannan basaji,rayuwarsu gaba daya a turai sukayita.a can suke karatunsu gaba daya,sesun gama karatu uban yake dawo dasu nan,suyi aiki.duk da basasan zaman kasarnan kokadan,amma kasancewar alh. Me kishin kasarsane,yasa baya barinsu acan yake dawowa dasu,nan.suhailat ce kadai,basu kaita karatu wajeba,duk da burinta kenan,amma hajiya Sam taki,saboda kaunar datake mata, bazata iya bari tayi nesa da itaba,sedai idan tayi hutun makaranta se taje duk kasar datakeso tayi Hutu acan. Dafarko bangane fyade akewa yan aikin gidanba,sedai kawai na wayi gari naga basanan,seda akayiwa jikata sannan nagane,itace yarinya ta Biyar a wadanda akayiwa,na tambayeta wane tacemun bata saniba,bama ta hayyacinta aka mata kawai farkawa tayi ta ganta cikin mawuyacin hali. Kudi kawai hajiya tabamu metarin yawa tare da kaita asibiti,harta warke amma kuma bayan wasu kwanaki ta fara wani irin ciwo tamkar ana tsotse ta kafin kuma ta mutu. Gaba daya bayanin da baaba,talatu takeyi bana fahimta,kokadan.saboda hankalina baya jikina.hannunta na kama cikin kuka nace."nashiga uku ni maryam,baaba wannan kuma wanne irin bala'ine Allah yakawoni,dama shiyasa hajiya lami ta tambaya, *bani da gata* Ashe da wani Abu a kasa, akwai wani kulli da suke kullaw.....kukane yaci karfina na kwantar da kaina,akafadar talatu ina cigaba da fashewa da kuka.bubbuga bayana ta farayi alamun rarrashi. "Kiyi shiru maryam,na miki alkawari zan taimakeki,yanzu dai lokaci ya kure mana,idan hajiya ta fito taga har yanzu,inanan zata gane na fada miki wani Abu,zantafi da safe zanzo nanuna miki yanda zakiyi amfani da komai na gidannan ,alokacin idan kin samu nutsuwarki zankarasa miki bayani. Sannan kuma ina gargadinki da kada kinuna wata alama,da hajiya zata gane,wani Abu ya faru,domin idan ta gane Daga ni harke munacikin matsala.janyeni tayi Daga jikinta ta mike ta fice Daga dakin.gaba daya kwakwalwata ta kulle,tunanina ya tsaya narasa tunaninma mezanyi,mutuwar innatace ta dawomun sabuwa,nasan datananan da duk banshiga wannan bala'inba.knocking kofar dakin aka farayi da sauri na tashi na nufi toilet na wanke fuskata,sannan na fito,na bude kofar. Matarnan nagani,hannunta dauke da faranti,da sauri nakakaro murmushin yake,ina mika hannu na karbi farantin hannunta,sannu na mata.tacemun bakomai ta juya ta fice.wasu hadaddun food flaks ne,masu matukar kyau akan faratin.murdawa na hauyi dakyar na samu na iya budewa,wani kamshine ya daki hancina,na abincin dake ciki.babu tantama Daga ganin abincin ze hadu,amm Sam naji bana sha'awarci ko yunwama banaji saboda zullumin dake addabar zuciyata.maida murfin nayi na rufe.na zabga tagumi...... Fitowarta kenan Daga toilet,ta hango wayarta tana ringing.batabi ta kantaba,kararasawa gaban mudubi tayi ta fara mulke jikinta da tsadaddun lotions dinta,tafi 20 minutes agaban mudubin,kafin,ta koma ta bude ward rope din kayanta dake cike makil da kaya,ta dakko wata red gawn me adon black,pant kawai tasaka da bra,ta zirata ta matukar kamata,kasancewar rigar robace.gashin kanta wanda bashi da cika da tsayi sosai ta kamashi da wani red ribbon.gaban mudubi ta koma tana karewa kanta kallo,ita kanta tasan tayi kyau,duk da ba wata kwalliya tayiba.perfumes dinta ta fesa sannan ta koma ta dakko,wayarta.missed call din kamal, ta gani.murmushin tayi,tare da bin bayan kirannashi. "Hello kamal!" ta furta, bayan ya ɗaga wayar. cikin wata wahalalliyar murya yace."aini fushi nakeyi baby,yau kwata-kwata koki nemeni,kuma kinsan banajin dadi idan banjiki ajikina ina kuguigwitakiba".ya karashe zancen tare da busa mata wani numfashi cikin son yarikitata. Wani dogon numfashi taja saboda sakonsa ya isa inda yakeso."am sorry my kamal,nima nayi missing dinka,but don't worry,gobe bani da lecture throughout muna tare.wani ihun murna kamal yasaka wanda yasa da sauri suhailat ta kashe wayarta.karya kashe mata dodon kunne. Number,habibinta tayi dialing tayi ringing harta gama be daukaba.tana shirin tashi kuma yakirata,da sauri ta picking cikin,zumuɗinta.shagwaɓarta kawai taita zuba masa,tana faɗa masa yanda tayi missing ɗinsa.Da kuma,korafin,ya tafi basuyi sallama.samu yayi,ya lallabata.kusan 20 minutes suna wanda,wanda gaba daya suhailat ce take ta surutunta. Cike da murna ta fito,daga dakinta zuwa falo domin yin dinner...... Dare ya tsala, amma babu digon bacci a idona.ina zaune na zabga uban tagumi,se kuncewa da sakawa nakeyi amma babu mafita,gashi nayiwa baaba,talatu alƙawarin,bazan gudu daga wannan *baƙin gidanba* shawarar zuciyata nabi nafada toilet na watsa ruwa,tare da dauro alwala,na fara jero nafilfili ina kaiwa Allah kukana.bansan adadin raka'ar danayiba nasan dai na dade ina sallar.Ina zaune akan daddumar ina lazimi hannuna naɗaga nafara rokon Allah. _ya Allah ina roƙonka da tsarkakan sunayenka,kakareni da karewarka,ka tallafi rayuwata,ya Allah kaine gatana bani da wani gata senaka.Allah kakawomun ɗauki arayuwata,ka nisantani da duk wani abunda ze cutar dani,ka bayyanamun mahaifina da gaggawa idan har yana Raye, alfarmar darajar annabinka._ shafa addu'ar nayi,inajin wata nutsuwa tana zagaye dukkan jikina,kunci da damuwar danake ciki gaba daya,ya fara yayewa.mikawa Allah komai nayi,tare da kudirin fuskantar kowacce irin kaddara ta rayuwa ta.nasan Allah baya bacci kuma yanaji yana gani. Da wannan tunanin na mike na ninke sallàyar da nayi sallah,abincin da'aka kawomun na tsakura naci kadan,bayan nagama na hau kan gado na kwanta,na lulluba da bargon Dana gani a ninke a gefen gadon.zuciyata cike da kewar umma,da saleemat harma da gwaggo,cikin mintuna kadan wani bacci me nauyi yadaukeni....... Kiran assalatune ya tasheni daga baccina,dakyar na yunkura na tashi nayi sallah,saboda wani bacci danakeji,ina idarwa kuwa nakara Jan bargo na koma baccina. Ina cikin daddadan baccina, Wanda na manta rabon danayishi naji ana tashina.ahankali na bude shanyayyun idanuwana, baaba talatu nagani tsaye akaina.yunkurawa nayi na tashi zaune,gaisheta nayi.amsamun tayi tare da zama agefena. "Da'alamudai maryam jiya baki samu kinyi bacciba,tunda gashi har rana tafito baki saniba.murje idona nayi nace. "Eh baaba,bansamu nayi bacci da wuriba. Amma duk da haka nayi mamakin dadewar da nayi ina bacci." "Kitashi ki watsa ruwa,kishirya nafara nuna miki abubuwan,saboda yau zaki fara aikinki". " tom baaba,na amsa mata ina sauka Daga kan gadon. "Akwai komai na amfani dazaki bukata adakinnan,harda kayan sawa idan kin shirya kisameni a falo. Dakai na amsa mata na nufi toilet. Sabon burush din danagani da MacLean nayi amfani dasu,wajen wanke bakina.kamar yadda baaba talatu,ta fada akwai komai na amfani adakin, kayan shafene kawai babu sosai,kayan sawama gasunan burjik a wardrobe din dakin,abunda ya matukar dauremun kai kenan.banyi gigin saka kowanne kayaba,kayana na saka.na nufi falo gurin baaba talatu. Tundaga kan toilet ta fara koyamun yadda zanyi amfani da komai,se kuma kitchen shima ta nunamun komai yadda zanyi amfani dashi,Alhamdulillah kuma na gane sosai,sedai dan abunda baza'arasaba Wanda se ahankali,tana nunamun take fadamun sunan kowa nagidan,da kuma yadda zan tafiyar da aikina. Dakina muka koma bayan ta debo mana kayan breakfast,tare mukaci abinci da baaba,tanata bani labaran ban dariya, duk akokarinta nasan ganin ta kwantar mun da hankali. Bayan mungama na tambayeta nace."waini baaba,wannan kayan Dana gani nasawa na waye"?. Murmushi baaba talatu tayi tace"nakine maryama.cike da mamaki nadago na kalleta "nawa kuma baba"? "Eh maryam,kidauki dukkayan dakika gani adakinnan kisaka mallakinkine,kafin kizo nawatane amma yanzu ya zama naki,idan za'akawo me aiki gidannan kafin tazo komai dazatayi amfani dashi se'an tanadar mata.yanzu ni zanje nafara aikina,naga goma ta kusa idan nagama komai anjima zanzo nakarasa miki bayanin gidannan.kekuma Daga yanzu zaki fara aikinki. Kayan da mukaci abinci,na tattara na kai kitchen seda na fara gyara dakina na wanke toilet sannan na gyara falon gidan, nayi mopping dinsa,amma abunda ya bani mamaki har lokacin babu Wanda yafito na gidan.araina nace wannan wanne irin baccine.kukune ya fito Daga kitchen yafara jera abinci akan dinning,gaisawa mukayi cikin rubabbiyar hausarsa,sejana yakeyi da surutu.ni kuwa dariya hausarsama take bani.hakan yasa nabiye masa,tamkar munsaba da juna munata hira.fitowar hajiya ya katse mana hirarmu,ta fito cikin takunta na ishashshiyar mace,taci kwalliya kuma tayi kyau sosai.fuskarta ba yabo ba fallasa.tsugunnawa nayi har kasa ina gaisheta amsawa tayi tana bina da wani irin kallo.nidai ina tsugunne kaina akasa,ina jiran umarni.kusan mintuna 10 muna haka,yayantane suka shigo gaba dayansu falon. Daya bayan daya naga suna hugging dinta,ita kuma sefara'a take saki.babu Wanda ya kulani acikinsu da gaisuwar danake musu. Se guda dayannan.gaba dayansu suka nufi dinning har hajiya.gajiya nayi da tsugunno na koma gefe na rakube,ina kallonsu kawai. "Haidar yakaji yau,munsha baccinmu mun more, saboda big bro bayanan dayanan da tuni muntashi tun dazu" dariya haydar din yayi "kaidai bari ai big bro akwai takura" harararsu mommy,tayi batace komaiba.kamshinta yarigata karasowa falon,rasss gabana yayanke ya fadi,haka kawai Allah yadoramun wani matsanancin tsoronta a kallo daya Dana mata,arayuwata.tana sanye cikin wani Riga da wandon jeans,rigar iya gwaiwace,kanta sanye da wata hula me matukar kyau. Dagudu ta karasa ga yan uwanta tayi hugging kowanne,sakin baki nayi ina kallonsu araina nace sukuma haka al'adarsu take,sekace ba musulmaiba,domin ni aganina,wannan badaidai bane, mu'aro al'adar daba tamuba........maganar suhailat ce ta dawo dani hankalina cikin tsawa takemun magana. "Dalla malama me kike jira,ko zuwa kikayi kisamu agaba kina kallonmu da kwalakwalan idanuwanki,kamar mujiya" dasauri na mike jikina har rawa yakeyi na karasa dinning din,batare da nace komaiba.kamar yadda baaba talatu tacemun sena tambayi kowa abunda yakeso,takan Wanda naji ankira da haydar na fara. "Yaya haidar me kake bukata?" Na tambayesa kaina akasa. Wani banzan kallo ya watsomun yana karemun kallo tundaga sama har kasa. Dagowa nayi ina kallonsa jin yayi shiru,kamar yadda kowa na falon yayi,wata uwar harara ya wurgomun,yace "dawannan dattin hannunaki zaki zubamun abinci." da sauri na kalli hannuna fess yake babu dattin komai,kawai tsabar son ya bakantamun raine,kuma yayi nasara. Seda yagama mun shakiyancinsa,sannan ya fadamun abunda yakeso. Tsabar kasaitama da hannu yanunamun abunda yakeso din.zuba masa nayi nacigaba da tambayarsu ina zubawa kowa. Suhailat ce ta karshe,tambayarta nayi amma memakon ta bani amsa senaji ta tsinkamun mari. "Ke wacce irin dabbace,mahaukaciya jahila" dafe kuncina nayi idona ya fara kawo ruwa. "Kiyi hakuri aunty suhailat",duk da bansan mena mataba,amma na bata hakuri. Tsaki taja tare da tabe baki,ta fadamun abunda takeso na zuba mata.babu Wanda yayi magana akan abunda tamun,cin abincin su kawai suke hankali kwance. Dakin hajiya na nufa,domin gyarawa,bayan nagama shan kukana adaki,na yadda mutanen gidan suke nunamun kyama a fili.duk yanda nake ganin kyan dakin Dana sauka,amma kokama kafar wannan beyiba,bansan yazan fasalta kyau da tsaruwar dakinba. "Aljannar duniya na furta afili,wannan daki haka sekace baza'a mutuba.babu wani datti adaakin sosai,gadon nafara gyarawa....seda nagama gyaran dakin duka sannan koma toilet.bayan nagama da dakin hajiya na koma dakin suhailat,alokacin duk sun fashe Daga falon se hajiya kadai tana kallo. Itama dakin suhailat din tamkar na hajiya,kalar kayan dakinne kawai kowa danasa,seda nagama kare masa kallo sannan na fara gyarawa,amma ita suhailat,dakinta da datti sosai,tamkar ba maceba, duk yayi kaca kaca kayan data cirema gasunan akasa,dakin gaba daya ba kintsi komai a hargitse.toilet dintama duk datti............ ******************** Kwance yake akan makeken royar bed dinsa,se juyi yakeyi yakasa tashi.hannunsa dafe da mararsa,saboda wani ciwo datake masa,ga muguwar sha'awar data addabesa,lumshe idonsa yayi cikin jin azabar ciwo,tare da taune lips dinsa na kasa..........✍️ *Kuyi hakuri da wannan,zanje dubiyane amma insha Allah gobema zakujini da daddadan page😍😘🥰* *BY* *Zeey kumurya* *ABUNDA KA SHUKA*......... _*(shizaka girba)*_ *MALLAKIN* 👇 *ZAINAB USMAN KUMURYA* *FARIN JINI WRITERS ASSO.....*📚 ~*Free novel*~ *Bismillahirrahmanirrahim* 0️⃣9️⃣ ............sosai yakejin azabar ciwon marar,Addu'a yafara karantowa yana neman taimakon ubangiji,cikin ikon Allah yasamu ciwon yafara lafa masa.daurewa yayi ya yunƙura, ya tashi zaune,agogon bangon dake ɗakin ya kalla, "yasalam" ya furta tare da dafe kansa,saboda ganin lokaci yana Neman ƙure masa,ga wadanda zasu kawo kaya suna jiransa.miƙewa tsaye yayi ya nufi toilet ya sakarwa kansa ruwa,kozeji sanyi ajikinsa.yakai 20 minutes yana wankan,kafin yafito daure da towel a ƙugunsa,sedan karami dayake goge jikinsa dashi.cikin mintuna ƙalilan ya shirya,cikin wasu tsadaddun ƙananan kaya,Wanda suka ƙarbi jikinsa.fuskarsa tayi fayau alamun ba ƙlu yakeba.batare da yayi tunanin cin abinciba ya kwashi wayoyinsa ya zira a pocket dinsa,ya fice daga ɗakin......... *********** Seda na gyara mata ɗakin tsaf,gwanin sha'awa.se'alokacin kyawu da tsaruwar dakin ya ƙara fitowa,tsayawa nayi ina ƙara kallon ɗakin,araina nace dakin suhailat haryaso yafi na hajiya haɗuwa.ga kamshin room freshener, Dana turaren wuta dake tashi adakin.seda nagaji dan kaina da kallon,sannan na fito naja mata kofar.babu kowa yanzu a falon, se TV daketa aikinta ita kaɗai,har nazo zanshiga ɗakina naji wata sassanyar murya ta kira sunana."maryam!" Juyowa nayi ina kallon me kirannawa cikin mamaki,batare Dana amsaba. Fuskarsa ɗauke da murmushi yazauna,akan kujera. Me kirkin gidanne,kamar yadda nasa masa suna. "Kiƙaraso mana maryam,ya faɗi haka yana dakko wayarsa yafara latsawa,ƙarasa nayi gabansa cikin sanyin jiki na durƙusa aƙasa. ɗagowa yayi yana kallona,sunkuyar dakaina nayi kasa saboda kallon danaga yana bina dashi. " haba maryam,kisaki jikinki dani mana,ki zauna akan kujera ki tashi daga kasannan. "A'a nanma ya isa na furta masa hakan saboda bugun da zuciyata takemun.duk yadda yaso na zauna akan kujera amma naƙi,dole ya haƙura yace."kinsan meyasa na kiraki,girgiza kaina nayi alamun a'a.cigaba yayi da magana. " inason na baki haƙuri,akan abunda aka miki a gidannan,banji dadiba,amma babu yanda zanyi, haka halin ƴan'uwana yake se..katsesa nayi dacewa "babu komai,yaya kokaɗan banji haushiba kokuma na damu."murmushi yayi cikin jin daɗin kiransa da yaya datayi yace."shikenan ƙanwata ga wannan ya miko mun ledar dake hannunsa,ɗagowa nayi ina kallonsa cike dason ƙarin bayani. "Kayan kwalliyane nasiyo miki,nasan Ku mata dason kayan ƙyale_ƙyale. Murmushi nayi cikin jin daɗin nuna kulawarsa agareni "nagode sosai,Allah yasaka da alkhairi Allah yakara buɗi. "Ameen,amma babu godiya atsakaninmu maryam,tunda naganki naga kin burgeni saboda nutsuwarki,da kamalarki,daga ganinki daga gidan tarbiyya kika fito.inason kuma kimun wata alfarma guda ɗaya.! "Ni kuma,har inada wata alfarma dazan iya maka.na tambayeshi cikin Saudi ina nuna kaina da hannuna. Murmushi yayi me sauti yace. "Ke mana,maryam ai kowanne dan'adam yanada alfarmar dazeyiwa wani arayuwarsa,komai kudinsa kuwa, kuma komai talaucinsa.nasan kina tunanin matsayina da naki kamar baza ki iyamun alfarmaba,to ni agurina da talaka da me kudi duk ɗayane,tunda duk Allah ne ya halicci kowa kuma ya'ajiyesa a inda yaso.jinjina kaina nayi cikin gamsuwa da bayanansa. Alfarma danakeso kimun maryam itace,inaso kiɗaukeni tamkar yayanki dakuke ciki ɗaya,Wanda zaki iya fadamun kowacce irin matsalarki,da damuwarki.dasauri na kallesa jin furucinsa,amma bance komaiba. "Shiyasa nace miki kimun alfarma,yanzudai kifaɗamun me kike da buƙata da baki tararba agidannan. Numfashi naja,nace."babu komai danake da buƙata,akwai komai na amfani agidannan. "Um,um maryam kidaiyi tunani,kada kiji kunya ko nauyin sanar dani.shiru nayi nayan sakanni,sannan nace hijabaine,kawai abunda zance ina bukata.murmushi yayi, "Ashe ƙanwar tawa malamace,tom shikenan insha Allah zansiyo miki. Inashirin yin magana hajiya ta shigo falon.gabanane yayanke ya fadi,tsoro me tsanani ya kamani,ina tunanin kozatamun fada akan ganina tare da ɗanta.Amma ko kallona batayiba, sema fara'a data fara yiwa ɗanta. "A'a my son,bakatafi aikiba har yanzu. Shafa kansa yayi yace. "mommy yanzu nake shirin ƙarasawa." ya faɗi hakan yana mikewa. "Sekadawo ɗan Albarka,adawo lafiya, Allah ya bada sa'a." "Ameen" ya'amsa yana fice daga falon.kamar batasan dani agurinba ko kallon inda nake batayiba,ta maida hankalinta akan kallon television. Gajiya dayi da zaman na mike dankaina,cikin sanyin jiki na nufi ɗakina.ledar daya bani,na ajiye a kan mudubi,na fito nafara kwashe kayan kan dinning ɗin da sukaci abinci,na kai kitchen nafara wanke_wanke. Zuciyata cike da tunanin maganarmu da *me kirkin gidannan*.......... A department dinsu,driver yayi parking motar.da sauri ya fito ya buɗe mata bayan motar. Cikin izzarta ta fito daga motar, tana yamutsa fuska,tana kallon kowa ɗai_ɗai,wani kallon banza tayiwa drivern,tace"saura kuma idannatashi nayita jiranka. Rankwafar da kansa yayi,insha Allah hajiya baza'ayi hakaba.wata uwar harara ta wurga masa,tana Jan dogon tsaki.tayi wucewarta.duk inda ta gifta se'ankalleta.masu Neman suna se magana suke mata.Wanda ya mata tadaga masa hannu,Wanda be mataba kuma ko kallonsa batayi. Wani guri ta ɗan samu ta tsaya ta dakko wayarta ta danna kiran kamal. "Hello kamal ina school fa.kamal daya gama shirinsa tsaf,ita kawai yake jira yace. "ohk babbar yarinya ganinan just 5 minutes. Abokinsa dake gefensa yadubesa yace. "Kamal kardai kacemun haryanzu kuna tare da babbar yarinya ƴar gidan alh.menasara. dariya kamal yayi irinta yan duniya yace,muna tare abokina, yarinyar taki barina,sedaifa shegen wayone da ita,har yanzu taki bari inshiga gidan dadinta.sedai kawai mu taɓe juna tatashi tayi gaba. "Kai abokina amma karako iskanci duniya,yanzu kai duk duniyancinka amma kakasa yimata dabara,dalla malam ko reaping dintane kayi. Waro ido kamal yayi, "kai sokake a daureni kenan,kamanta waye ubanta akasarnar,kabarni da ita,nikadai nasan gadar zaren danake hada mata da kanta zata bukaci inyi sex da ita. Dariya abokinsa yayi yabasa hannu suka tafa. "Kaimafa kamal baka da dama, nasan dama bazaka ƙyaleta haka kawaiba. "kaidai bari kawai abokina,bari naje karta gaji da jirana,kasanta yar rainin hankalice. Suhailat ko zama batayiba saboda,zaƙuwa.ta matsu tajita kamal yana yamutsata.Allah ya halicceta da muguwar sha'awa.amma duk da haka batataba yin sex ba,tafiso ta fara akan habibinta muradin ranta. Yana shigowa department din ya hangota,gabanta yaje yayi parking motarsa. Harararsa tayi bayan ya fito daga motar. Hannayensa ya hade guri daya alamar roƙo," sorry babbar yarinya,sarauniyar mata.kaf school dinnan babu kamarki akyawu da kudi da wanka,da gayu da....ɗaga masa hannu tayi cikin jin dadin kalamansa,domin ita mutum ce me matukar son ayabeta. "Muje kawai,ka wanke kanka,amma da nayi niyyar baka punishment,saboda nadaɗe a tsaye gashi kowa se kallona yakeyi da wasu kazaman idanuwansu. Dariya yayi yana bude mata gaban motar,shi kuma yazagaya ya shige suka dauki hanya..... Akan stool ta ajiye Jakarta, wayarta kuma akan mudubi ta'ajiyeta,bayan ta shigo dakin da suka saba masha'arsu. Zama tayi a gefen gado tanayin wata mika tare da gantsarewa,idanunta harsun fara canza kala saboda fitina.kamal kuwa yana falo,yana sane yau ja mata aji zeyi,seyaga ƙarshen jijji da kanta. Kayan jikinta ta fara cirewa domin ita indai ta wannan fanninne bata da wani Jan aji,towel ta dauka ta daura ajikinta bayan tayi tunbur,ta nufi falo duba kamal domin tajishi shiru_shiru. Yana kwance dagashi sedan boxer,yana kallo. Fadawa tayi jikinsa,tana binsa da wani mayen kallo.rungumota yayi jikinsa,yana shafe ta.lumshe idonta tayi tana busa masa numfashinta a fuska. Ahankali ta fito da harshenta ta fara lasar lips dinsa,cikin ƙwarewa.hannunta tasa tana shafa sumar kansa,tare da gefen kunnansa.lumshe idonsa yayi yana kara mannata da jikinsa zuciyarsa na bugawa da sauri_sauri. Bakinta ya buɗe ya zira harshensa ya fara mata wasa dashi cikin ƙwarewa,wani zazzafan kiss yafara sakar mata,cikin ƙwarewa.nandanan suhailat ta ruɗe,abunka dame jira dama.ta fara mayar masa da martani. Cak ya dauketa yayi daki da ita,bayan ya rabata da towel ɗin jikinta.akan bed ya kwantar da ita.domin se sunfi walawa anan....... ************ Drivensa yana bakin mota yana jiransa,yana ganin fitowarsa ya karaso garesa yana kwasar gaisuwa.kamar kodayaushe hannu kawai yadaga masa.dasauri ya bude masa front seat,cikin girmamawa.shiga yayi motar suka nufi babbar ma'aikatar mahaifinsa dake garin abuja.cikin mintuna kalilan suka karasa,tsadadden agogon hannunsa ya duba.yana da sauran 20 minutes kafin su shiga meeting din.wayarsa me tsananin tsada ya dakko.missed call din suhailat ya gani.murmushi yayi tare bin bayan kiran. Suhailat ana kwasar daɗi,wayarta ta fara ringing. Dukda tsananin daɗin datakeji da sauri ta kwace jikinta,daga sucking dinta da kamal yake mata.tamkar yar maye ta miƙe ta fara tafiya,cikin tsananin ɗokin jin kiran masoyinta,domin ringing tune ɗinsa daban tasa masa,batare da tunanin komaiba ta daga wayar. "Hello my life" ta furta cikin wata wahalalliyar murya,saboda tsabar jaraba. Wata uwar tsawa ya buga mata, "suhailat where are you by now?" Cikin firgita ta tattaro nutsuwarta tace" sc..school." Muryarta na rawa. Ajiyar zuciya ya sauke,yace. "Ohk zankiraki idan kin koma gida,bejira mezata ceba,yakashe wayar. Yanayin dayaji muryar ta, tamkar tana cikin feeling,amma yanzu ya danganta hakan dako tana class ne,tayi picking call din,shiyasa muryar ta tayi kasa sosai,dankar ajita.itama anata ɓangaren ajiyar zuciyar ta sauke,tasan halin kayanta da saurin fahimtar mutum,yanzu seya gane halin datake ciki,Allah ma ya taimaketa yayarda da ƙaryar data masa,data yabawa aya zakinta. Ajiye wayar tayi ta nufi kan gado inda kamal yake kallonta tamkar wawa,cigaba sukayi da masha'arsu.( ya Allah ka shirya mana zuri'a.Ameen🙏🙏)......... **************** Yau kwanana3,agidan aikina.amma tamkar nayi wata uku,haka nakeji.saboda kwata_kwata banajin daɗin zaman gidan.gashi bansan meyafaruba, tundaga ranar da muka rabu da baaba,talatu banƙara ganintaba.gashi ni kuma,ko ƙasa bana sauka sosai, ballema harna samu na fita daga part din.to inma nafita ina nasan inda take,awannan makeken gida,unguwa guda.a zaman danayi nagane halin kowa na gidan. Ita hajiya bazata sakar maka fuskaba,kuma bazata kulaka da hiraba,sedai kawai tasaka Abu kayimata.kuma duk abunda ƴaƴanta zasumun babu ruwanta,ko kala bazataceba.amma na fuskanci tana tsananin son suhailat sosai,fiye da sauran ƴaƴanta. Sadiq shine babba a waɗanda nasani a gidan,kuma shine me kirkin gidan.kullum yadawo daga aiki idan yashigo part din hajiya, zamuyi hira sosai,yajani ajikinsa,tun ina ɗari_ɗari dashi harnazo nasaki jiki dashi. Hajiya koda taganmu tare bata nuna wani Abu na bacin rai.se mabiyinsa,faruq.shikam baya shiga sabgar kowa,ko'atsakaninsu baya musu magana sosai,sabgar gabansa kawai yakeyi,baya kyarata kuma baya sakarmun fuska. Se ƙananun wadanda sukuma twins ne,zannurain da haydar.su kam sosai suke nunamun tsana,musammanma haidar.banda tsawa da hantara babu abunda yake haɗani dashi.duk kuwa da takatsantsan din danakeyi wajen ganin banyi abunda zasu cimun fuskaba. Se'uwar gayya suhailat,wadda tafi kowa nunamun tsana,ni kuma Allah yadoramun bala'in tsoronta,Wanda bansan daliliba.gata da shegen zagi tamkar ƴar maguzawa.dabi'unta Sam babu tarbiyya acikinsu,intayi wata shigar tamkar ba ƴar musulmaba,ga shegen son jiki da kazanta. halayensu kenan Dana fuskanta,hakan yasa naci maganin zama da kowa. Yau da tsananin kewar gida na tashi,kewar umma da saleemat ta cikamun zuciya,har gwaggoma inaso naganta.cikin sanyin jiki nayi aikina,nagama.a kullum idannayi aikina nagama,sedai in zauna inyi kallo ko kuma inyi karatun alqur'ani me girma.inason fita inɗan zaga gidan,amma shegen tsorona ya hanani.babu kowa duk sun fice aiki,suhailat kuma antafi school dagani se hajiya. Ina zaune a falo ina kallo,domin idan basanan a falo nake zama nakeyin kallona.amma dazarar sun dawo zankoma ɗakina. Hajiyace ta fito daga ɗakinta cikin shigarta ta alfarma,wayarta kare a kunnanta tana waya.zama tayi akan kujera cikin lallami take magana. "Bezeyiyuba my son,zankira dad dinnaku na masa magana,dole kadawo gida yau,tunda baka da lafiya,canɗin waye ze kula dakai,dama munyi kewarka sosai,nafison kadawo kusa dani inkula dakai dakaina.banji me'aka ceba aɗaya ɓangaren,kawai gani nayi hajiya ta washe bakinta. "Yawwa my son,kokaifa seka ƙaraso bari na fara shirin tarɓarka......✍️ *(sorry baku jini da wuriba,akasi akasamu 🙏🙏😘🥰)* *BY* *zeey kumurya* *ABUNDA KA SHUKA*......... _*(shizaka girba)*_ *MALLAKIN* 👇 *ZAINAB USMAN KUMURYA* *FARIN JINI WRITERS ASSO.....*📚 ~*Free novel*~ *Bismillahirrahmanirrahim* 1️⃣0️⃣ ............Ajiye wayar tayi jikinta har rawa yakeyi tsabar murna,araina nace gaskiya hajiya Tana ji da wannan baƙonnata dazezo,tunda nazo,gidannan bantaɓa ganinta cikin farin ciki makamancin wannan.....katsemun tunani tayi ta hanyar kiran sunana.da sauri na'amsa mata tare da bata dukkan hankalina. "Zo ki ɗan tayani wani aiki a kitchen, ta faɗi hakan tare da miƙewa.nima miƙewar nayi nabi bayanta.... _____________________________ Hajiya gwaggo,tunda maryam tatafi taketa murna ta kusa zama hajiya, ko,kewartama batayiba.200,000 duk wata banda kuɗin da zata ɗinga sakata tana sato mata.ai ita kam taji daɗin wannan abu. Tunɗaga soron gidan zaka tabbatar gidan yayi babban rashin me kula dashi,saboda yanda zakaci karo da datti da uban tilin wanke_wanke a tsakar gida.gwaggo bata komai tunda maryam tatafi,tasa ayi mata cikiyar me aiki har yanzu shiru. Yauma kamar kullum,se wajen goma na safe tatashi daga bacci,ba sallah balle salati,bakinta kawai ta kuskure.ta dawo ta haɗa shayinta,dama tana da ruwan zafi a flaks, da bredi ta fara ƙasuma,Tana cikin ci taji ana sallama. Da sauri ta mikƙ ta boye biredin harda lullubewa Tana goge bakinta dan kar agane tanacin wani Abu.Amsa sallamar tayi Tana fitowa tsakar gidan,wata ƙawartace ta suka Daɗe basu haɗuba.waro micimicin idanta gwaggo tayi waje,cikin mamaki tace. "Amina yau kece agidannawa. Amina data tsaya kawai Tana ƙarewa gidan kallo tace. "Nice ladi. "maraba,marabanki shigo mana kika tsaya daga waje kamar wata baƙuwa. Bayan sun gaisa Amina ta dubi gwaggo tace, "ladi,naga gidannaki kamar bashiba,nasaba idannashigo gida inganshi fess,gwanin sha'awa, har sha'awar gidannan nakeyi, idannazo.amma yau naganshi kaca_kaca nayi zatonma kin tashine,wasune a gidan.dariya gwaggo tayi tace. "Ai bake kaɗai bama duk Wanda ya shigo gidannan,haka yake cewa. Memun aikince batanan. "Allah sarki,ni ina shirin tambayarkima ina maryam ɗin,Dana shigo bangantaba.nan gwaggo ta kwashe labarin komai tabawa Amina. Baki buɗe take kallon gwaggo,yanda taga ko'ajikinta. "Ke yanzu ladi,maryam ɗin kika bayar aikatau,Bakya tunanin abunda zeje ya dawo,bakisan inda aka kaitaba,kedai kawai kinbayar da ita.ta mutu ko tayi rai badamuwarki bace.dariya gwaggo ta ƙarayi, "ke Amina,sana'afa takemun ai ni banki maryam tayi shekara 20 Tana wannan aikinba,har addu'a nakeyi Allah yasa karta samu miji nan kusa,ballema tayi aure,tabar aikinnan..... *********** "Saleemat,wai bazakici abincinnanba seyayi sanyi,numfashi saleemat ta sauke tace. "Umma banajin wata yunwa a halin yanzu,kewar maryam ta cikamun zuciya,hankalina yakasa kwanciya da tafiyarta aikinnan. Kujerar tsugunno,umma ta dakko ta dawo gaban saleemat ta zauna. "Haba saleemat tunda maryam tatafi kin kasa kwantar da hankalinki,addu'a yakamata kiyi mata bawai kiyita damuwaba. "umma ai dolene indamu,kinsanfa maryam da zurfin ciki,gata da haƙuri kodama Tana fuskantar wata matsala bazata faɗa manaba,ni kuma jikina yana bani bata jin daɗi aduk inda take. "A'a saleemat,banason kina cewa haka insha Allah maryam Tana cikin kwanciyar hankali.daƙyar umma ta samo kan saleemat taci abinci,domin tun ranar data dawo tatarar da mummunan labarin,tafiyar maryam shikenan taketa damuwa. Itama umman daurewa kawai takeyi amma zuciyarta cike take da zullumi...... ************** Aiki sosai mommy tasakamu,domin kuwa bani kadai bace ta karo wasu mata guda 2 Wanda bansan subama a gidan.Amma karfin aikin ita takeyin kayanta.Abinciccikane kala_kala,da kuma kayan snacks. Duk akan mutum ɗaya.sekace Wanda mutum 20 zasuzo. Hajiya ta fita naji masu aikin suna gulma. ɗayace ta dubi daya tace."Al_mustapha ikon Allah,ai ina ganin yanda hajiya taketa hidimarnan nasan shine zedawo domin ko alh.ze dawo bata masa irin wannan hidimar. "Hmmm,kedai bari salame hajiya Tana matukar ji da wannan ɗannata,tamkar shikadai ta haifa. "Ai ni naji daɗin dawowarsa,yanzu zakiga yaran gidannan sun nutsu,mundena kwana da kidaden banzan da suke samana. Nidai kawai spring ross ɗin,da hajiya ta barmun naci gaba soyawa,gaba ɗaya maganganunsu baganewa nakeba. Tun wajen 11,muke aiki se daf da la'asar muka gama.sosai nagaji tubus.sonake kawai na watsa ruwa na kwanta na huta.duk da inajin yunwa amma nayi matukar gajiya. Ina fitowa ɗaga kitchen suhailat na shigowa falon, seda zuciyata ta buga saboda tsoronta,amma ko kallona batayiba ta nufin gurin mommy ta rungumeta Tana tsallen murnar dawowar yayanta.ƙara rungumeta itama mommy tayi Tana dariya.ɗakina na wuce ina mamakin wannan murna da mommy da suhailat sukeyi akan dawowar wannan bawan Allah,kai zanso naganshi.hijab din jikina na cire,na fara zuge zip din rigata.daƙarfi aka buɗe kofar ɗakina.Dasauri na kalli bakin ƙofar suhailat ce ta shigo,babu sallama. Atare zuciyoyinsu suka buga.saboda nidai nasan ba alkhairi ne ya kawotaba. Ita kuma suhailat saboda tsananin mamakin ganin dirin jikin da Allah yayiwa maryam. "Kutmar haka yarinyarnan take da surar jiki me kyau.suhailat ta faɗi hakan aranta.wani baƙin ciki,da hassadane ya mamaye zuciyarta.yanzu duk yadda takeji da kanta,amma wannan ƴar matsiyatan ta fita kyan ƙira.jibi wani uban shap tamkar ita tayiwa kanta,ga manya_manyan nonuwa tsayayyu.munafuka shiyasa kullum take fama da hijabi,wata tsanar maryam ce ta ƙara lulluɓeta.ni kuwa rigata na fara kokarin mayarwa cikin sauri saboda har takai ƙasa,dan ma da under wear da vest ajikina,amma duk da haka banjo daɗiba data ganni ahaka.wani mugun kallo ta wurgomun Tana hararata. "Ke dabba! Kije ga kayana can ki wankemun.cikin ladami na'amsa mata da "toh".duk da Kalmar dabba,data kirani dashi ya matukar bakantamun rai,nakasa sabawa da muzantanin datakeyi.idanuwanane ya cicciko da kwalla,kokarin mayar da ita nayi,na juya na nufi toilet,bayan ta fice ɗaga ɗakin. Cikin 10 minutes nayi wankan, shiryayawa nayi,sallar la'asar na tayar.seda na idar na nufi ɗakin suhailat. Itama time din fitowarta kenan ɗaga toilet Tana daure da towel iya Rabin cinyarta ya tsaya,da'alama wanka tayo. kunyar ganinta nayi ahaka,duk kasancewarta mace ƴar uwata,amma aganina hakan bedaceba.juyawa nayi zan fice naji muryarta ta dakamun tsawa."gidan uwar waz aki? Juyowa nayi kaina akasa ina wasa da yatsun hannuna. Cigaba tayi da maganarta cikin faɗa. "Tun yaushe naje na kiraki amma se yanzu zaki zomun,saboda tsabar iskanci kema kin waye kinzo kinfara cin daula,dama shi talaka be iya samun guriba. "Kiyi hakuri aunty suhailat,wanka nayine.nafaɗi hakan cikin sanyin murya. Dariya naga takamayi tamkar wata sabon kamu,da mamaki nake kallonta. Karasowa gabana tayi tanamun wani kallon wulakanci. "Wanka,wankafa kikace,ahakan kikai wanka kina fama da tsami da warin dauda,ke dama dena wankan kikayi dan ba fita kikeba."Dall,ni wuce kimun abunda nasaki wawiya kawai nonsense. Jikina a matukar sanyaye na wuce zuwa toilet dinnata,zuciyata cunkushe da baƙin cikin kalamanta. Aƙasa na hango pants dinta da bra dinta,girgiza kaina nayi cikin takaici, ga gurin saƙale kaya amma bazata saƙaleba,sedai ta zubar a ƙasa tsabar sakarci,daga yanayin suhailat irin matannanne da babu abunda suka iya. Kwashe kayan na farayi ina zubawa a bucket. Saboda nafi ganewa wankin bucket akan na washing machine. Ina ɗaga wai pant dinta naga jini,da sauri na yardashi cikin ƙyanƙyami,araina nace kobatasan ta hadamun dashiba,domin wannan abun ai sirrin mutum ne,ina ƙara daga wani shima naga jinin harma ya fara bushewa. Matsar dasu nayi gefe zuciyata harta fara tashi,na wanke mata bra din na shanya,na fito.har lokacin Tana gaban mudubi,tanata shafe_shafe towel din jikinta ya kunce ya kusa faɗuwa,amma ko'ajikinta. "Aunty suhailat nagama" batare data kalleniba tace. "Barina na duba nagani koya fita,dan idan befitaba sekin sake.tsayawa nayi kawai bance komaiba. Kusan 5 minutes sannan tatashi ta nufi toilet ɗin. dasauri naga ta fito ta ƙaraso gabana"Kan ubannan,kagamun matsiyaciyar yarinya ahakan kikecemun Kingama,shikuma wancan dakika warefa uwarkice zata wankemun.runtse idona nayi,wlh harga Allah nagaji da zagin da takemun. "kiyi haƙuri aunty naga da najasa ajikinsu ne,kuma...wani wawan mari ta tsinkamun. "Lallaima yarinyarnan harni kike faɗawa da najasa,nufinki dai bazaki wankemunba.to meye marabarki da najasar,to bari kiji shi abunda kike cewa nasaja yafimun ke daraja agurina domin shi daga jikina yafito.dan haka kiyi sauri ki shiga ki wankemun,kafin na saɓa miki kamanni. Hawayene kawai yake bin kuncina,duk kuwa da yanda naso mayar dasu amma seda suka zubo.Marin datamun bemun zafiba kamar yadda ta dangantani da najasa.inaji ina gani haka nakoma nafara wanke mata,gani Allah yayini da ƙyanƙyamin wannan abun.nawama ƙyanƙyaminsa nakeyi balle na wani.ina wankewa ina kuka,kukan abubuwa da yawa.ga wani mahaukacin tashi da zuciyata takemun.Allah,Allah nakeyi nagama karnayi mata amai a toilet. nakara jawa kaina wata masifar. Ina gamawa na fito ko kallon inda take banyiba,saboda raina yayi matukar baci,muzantar tayi yawa. Dan kawai ubangiji ya halittoka a talaka,seka zama wulakattacce da kai da banza duk ɗayane a wurin mutane. Da gudu nakarasa ɗakina saboda aman dayaketa tasomun,Allah ma yaso babu kowa a falon.sosai nayi aman,duk da bawani abun kirki acikina,tunda rabona da abinci tun breakfast.kuskure bakina nayi,na fito na kwanta.ina maida numfashin wahala.tare da takaicin wannan wahalalliyar rayuwar danakeyi ta ƙasƙanci,bansan sanda wani baccin wahala ya kwasheniba dama da tarin gajiya ajikina....... Karfe 5 saura gaba ɗaya ƴan gidan sun hallara domin zuwa taro babban yaya,suhailat anci kwalliya kamar ba gobe,cikin wata red gawn me adon black,wadda ta matuƙar kamata jikinta se rawa yakeyi acikinta,tayane kanta da wani Dan karamin veil black,tayi kyau sosai tamkar ka saceta.farin ciki da murnar datakeyi yau baze misaltuba,kwana 4 dinnan dabayanan jitake tamkar sati 4. Tayi matuƙar kewarsa. Haidar da zannurain kuwa bawani farin ciki sukeyi da dawowarsaba,saboda ze katse musu jin daɗi.dan fitar nan dasukeyi ta ɗare ze katse musu ita.mota biyu sukayi,ɗaya mommy da suhailat ne abaya,se kuma driver a gaba.ɗayar kuma,haydar ne yake driving se zannurain a front seat,baya kuma faruq da sadiq. 4:55 pm,a filin saukar jirgi na malam aminu kano,ta musu. Dafe zuciyarsa yayi saboda tsananta bugu datake masa,Wanda besan daliliba, ahankali yake sakkowa daga matattakalar jirgin janye fa trolly ɗinsa,idanuwansa ya lumshe saboda shakar iskar garin mahaifarsa da yayi,yana jin farin ciki sosai aransa,na dawowarsa gida *kano ta dabo tumbin gwiwa* tafiya ya farayi cikin gentle dinsa,fuskarsa babu fara'a kamar koda yaushe.su mommy suna tsaye suna baza ido ganin anata fitowa.suhailat ce ta fara hangoshi. Taɓo mommy tayi,"laaa mommy kinganshi ya fito." Kamar yaji metace shima ya kalli inda suke,bazasu iya jira yaƙarasoba,hakan yasasu nufar inda yake.tunda yafito yan matan dake gurin suke binsa da kallo,cike da burgewa kowacce tanaji aranta dama wannan hadaddan guy din yazama mallakinta.murmushi yasaki kadan,saboda hango yan'uwansa kuma guɗan jininsa sun nufo garesa.da gudu suhailat ta karasa garesa ta fada ƙirjinsa,cikin tsananin murna da doki.shima beyi ƙasa a gwiwaba,ya mata masauki a faffadan kirjinsa,tare dasa tausasan hannayesan yazagane bayanta. Wata nannauyar ajiyar zuciya suhailat ta sauke,lumshe idanuwanta tayi Tana shakar daddadan kamshinsa. Saboda tsabar jaraba,har yanayinta ya fara sauyawa,shafa bayansa tafarayi tama manta a inda suke. Daidai lokacin su mommy suka karaso,raba suhailat yayi daga jikinsa wadda ta kasa magana, da hannu yake amsawa yan uwansa,welcoming din dasuke masa,hugging dinsa sukayi one,by one. Mommy kamar ta maidashi ciki,haka takeji. Duk da baifaɗaba,amma fuskarsa ta bayyana yana cikin farin ciki,sadiq ne ya karbi trolly dinsa suka nufi mota.hannun suhailat ya kama,wadda taketa kallonsa tamkar zata cinyesa,ya matukar yi mata kyau,ya kara wani fresh. duk da fuskarsa tayi fayau alamun ya ɗan ji jiki.Hannunta ya murza,tare da ɗage mata gira,yayi mata alama da hannunsa alamun yadai yaga tayi shiru. Lumshe idanta taƙari tare da lasar lips dinta. Kwantar da kanta tayi ajikinsa,batare da tayi maganaba.saboda itakaɗai tasan metakeji jinta datayi,ajikinsa.ahaka suka ƙarasa motar, front seat yashiga sukuma suna baya kamar yadda sukazo.mommy se tambayoyi take masa,akan ciwonsa,da'abunda yake damunsa. Atakaice yace mata zazzabine.... Direct part ɗinsa ya nufa,duk da mommy taso yaje part ɗinta amma yace mata seya huta zezo.dole haka tasa ƴan aiki suka kwashi kayan data shirya masa zuwa part ɗinsa. Mommy dakanta ta haɗa masa ruwan wanka yashiga.kafin ya fito duk sun fice daga part ɗin,domin sunsan halinsa bayason hayaniya,musammanma daya kasance yau ya dawo.bayan ya ɗauki wasu mintuna ya fito,shiryawa yayi cikin ƙananan kaya,wayarsa ya dauka ya fito falonsa. dinning ya nufa koze samu abunda yake buƙata,amma beganshiba.tsaki yaja,kobi takan liyafar da aka shiryamasa beyiba,ya koma ɗakinsa,text yayiwa mommy akan yana bukatar coffee.... Wata mahaukaciyar yunwace tatasheni ɗaga bacci,toilet na shiga na wanke bakina sannan na fito zuwa kitchen, ina addu'ar Allah yasa babu kowa a falo. Amma kash!,addu'ata bata karɓuba dukansu suna falon amma banda mommy. Suhailat tana ta tsokanar su yahaydar akan yayanta ya dawo, su kuma sunata kukkumbura. Kamar na juya na koma,sekuma naga rashin dacewar hakan tunda sun Riga dasun ganni. Kaina akasa na fara tafiya cikina na kiran chiroma.sannu na musu,amma ko kallo ban ishesuba,yayasadiq ne kawai ya amsamun. Ina shiga kitchen mommy tana fitowa hannunta ɗauke da wani basket me matuƙar kyau,ban kalli mene acikiba,saboda hankalina yanaga aɗɗa'ami. Kafin nayi magana,mommy tarigani. "Yawwa maryam dan kaiwa my son wannan,part dinshi yana gaban namu daga right side dinki,idan kin fita.kiyi sauri dan Allah Dan bayason jira, dama tunanin me kaimasa nakeyi su salame duk sunyi part ɗinsu, su suhailat kuma duk sun gaji......✍️ *BY* *zeey kumurya* *ABUNDA KA SHUKA*......... _*(shizaka girba)*_ *MALLAKIN* 👇 *ZAINAB USMAN KUMURYA* *FARIN JINI WRITERS ASSO.....*📚 ~*Free novel*~ *Bismillahirrahmanirrahim* 1️⃣1️⃣ .............Wani magidancine Wanda zekai kimanin shekara 40. zaune a wani hadaddan restaurent,waya yakeyi.daga bisani kuma yasauke wayar yana wani munafukin murmushi.wata matashiyar budurwace ta shigo restaurant din tana sanye da wani red din Less,da adon baki ajikinsa.ta yafa mayafi black,hang bag din hannuntama black ce.black beauty ce tana dan kiba.gurin magidancinnan ta nufa,sallama ta masa tare da zama akujerar dake fuskantarsa.murmushi dauke a fuskarta. "Barka da zuwa *P.A* "barkanka da warhaka me girma *MD* dadina dake P.A bakya jinkiri idan ankiraki shiyasa nakeson aiki dake.dariya P.A tayi,ai dole kaganni da hanzari me girma,MD. Kasan ance idan kaji kira samune. mikewa tsaye yayi tare da zura hannunsa duka acikin aljihunsa. Maimunatu! Yakira ainihin sunanta. "Na'am MD" kinsan meyasa na kiraki wajannan,girgiza masa kai tayi alamun a'a. Murmushi yakarayi yace" ayanzu kiran gaggawa ya riskeni oga mustapha yadawo garinnan,ayau sabanin da dayace zeyi sati biyu.bamusan dalilin dawowarsaba amma munsa a bincika mana.matsowa yayi daf da ita,wani aiki mukeso ki mana akan oga mustapha,maimuna karki sake wannan damar ta wuceki idan kika yarda zaki yimana wannan aikin,kinada babban rabo na makudan muliyoyin kudi,idan kuwa akayi nasara a aikin,zaki samu ninkin abunda muka baki a farko. Cikin Neman Karin bayani tace"wanne irin aikine wannan me girma MD. dariya yayi yace. "P.A kenan bazan fada miki aikinba sekin yarjemun zakiyi. Shiru P.A tayi na wasu mintuna kafin ta numfasa ta fara magana. "Me girma MD,bazan ki tatakaba,amma a gaskiya banason nayi abunda ze cutar da oga mustapha, saboda tsananin son da nake masa,da kuma halaccinsa agareni. Kafin yazo wannan ma'aikatar lokacin mu yarane na can kasa,kuma shuwagabannin wannan kamfanin alokacin azzalumaine,mun azabtu a wajensu. Amma zuwan oga mustapha, yacanza mana matuka,mutum ne shi me adalci,dakuma tsaiwa akan aikinsa.tasanadinsa yanzu gani a matsayin P.A dinsa. Dariya MD,ya kyalkyale da ita. "Haba P.A, kada garin Neman gira kirasa ido,kada kizo daga baya kiyi bawan ba kanin. Sanin kankine oga mustapha yana da mata agida,yar uwarsace kuma kowa yasan ita ze aura.sannan kuma duk bayanin da kikeyi na oga,ya miki halacci karki manta duk tare yamana,amma ki sani a rayuwar nan ta yanzu kowa kansa yasani,dan haka kibar batun wani oga,kawai ki kama aiki,Wanda ta sanadinsa zakiyi arziki Mara yankewa. Aikinnan ba nawa bane shima nasakani akai. Kallonsa takeyi tamkar meson karanto wani Abu a fuskarsa. "Nima MD banason tufkar dana dade inayi shekara da shekaru nayi kuskuren dazata warware gaba daya. Gashi kuma naji na kwadaitu da son wadannan makudan kudi daka ambata. Zama yayi ya tsiyaya lemon dake kan table din gabansa. Kurba yayi yace. "Ina mai tabbatar miki bazakitaba dana saniba a wanna aikin,aikine daya kunshi manyan kasarnan,dayan kasuw.,kekuma naga ke amintacciyar oga ce shiyasa nasakoki aciki.kedaice zaki mana abunda muke bukata. Kada kiyiwa kanki azanci,idan kingama shawara ki sameni gobe a office idan antashi,sena jiki. Yana gama fadar haka ya mike ya dauki mukullin motarsa da wayarsa yayi gaba.binsa kawai P.A tayi da kallo harya bacewa ganinta....... ************* Ai Jinayi tamkar nadora hannu aka na kurma ihu,saboda yunwar danakeji harwani jiri_jiri nake gani.gashi kuma mommy ta hadani da aiki,kuma bani da damar bijirewa.cikin sanyin jiki na karba basket din,na juya nayi waje.suhailat na ganina ta mike,"mommy yazakibawa wannan abar ta kaiwa yaya coffee,kinsanfa yaya da kyankyami,idan takai masa dakyar idan zesha.kuma kinsanshi befiyason karikican kowanne irin mutaneba,balle ita dabata san tsarinsaba.bari na kaimasa da kaina.mommy dake bina abaya tace. "Kiyi zamanki my daughter nasan ze karba,banason kina wahala da yawa yanzufa kika gama korafin kingaji.badan tasoba ta koma ta zauna.tana zabgamun uwar harara. Cigaba nayi da tafiya zuciyata na kuna,kafata har hardewa takeyi,se hada hanya nakeyi.tunda nazo gidan yaune nafara fitowa farfajiyar gidan.tsayawa nayi ina bawa idanuwa abinci,nama manta da wani sauri da'akace inyi.wasu shuke_shuke da fulawoyi da suka zagane gidan sunfi komai burgeni.ahankali nake tafiya ina kallon ko'ina,nayi tafiyar 5 minutes na iso wani part kamar yadda hajiya tace daga part dinta seshi. "Ya Allahu" na furta a fili saboda tunkafin na shiga part din nasan ankashe masa dukiya,yaci uwar na hajiya a kyau da tsaruwa. Tamkar da zinare aka ginasa,saboda wani sheki da gininsa yakeyi. Kamar part din hajiya,shima seda nahau step me matattakala 4. Nanfa ake yinta,wata irin koface wadda bantaba ganin irintaba,banmasan ta ina zan budeba.in komane in sanar da hajiya kokuma inyi yaya? Na tambayi kaina.kusan 2 minutes,ina tsaye ina sakawa da kwancewa. se Allah yajehomun da wani bawan Allah,danaga ya tunkaro inda nake.dama tunda nazo gurin naganshi zaune akan kujerar roba daga gefen part din. Murmushi yamun nima na mayar masa. "Yan mata da alama gurin oga kikazo ko? "Ehhh na amsa masa. "Ohk,nine babba acikin yaransa na gidannan,bejira mezanceba kawai naga yatsaya agaban kofar,kawai gani nayi kofar ta bude da kanta,bin bayansa nayi da sauri nima nashige,muna shiga falon naga ta rufe kanta. "Yawwa yanmata,nasan abunda ya tsayar dake kenan daga yanzu idan kikazo haka zaki dingayi zakiga ta bude,ki hau kan steps dinnan zakiga falo yana ciki,idan kuma bayanan kiyi knocking dakin dakika gani na farko a falon.godiya na masa sosai yasakai ya fice. Suman tsaye nayi saboda se lokacin nagama karewa falon kallo. Banyasan yazan misalta muku tsaruwa da kyawun falonba,kokuma kayan ciki,kawai Ku kissima da kanku.wannan wane irin mutum ne da komai nasa na dabanne a gidannan, wani kugi da cikina yayi yasani yin azamar hawa benen domin nayi sauri na kaimasa sakon nakoma naci abinci,ga lokacin sallar magriba ya gabato. Tasbihi kawai nafarayi araina lokacin dana shiga falon saman,ga wani sassanyan kamshi dayake tashi,Wanda ya mun kamar nasanshi,ko kuma na taba jinsa. Aradu aka barni a falonnan akace in zauna,ko abinci bazan nema,kallonsa zantayi yana debemun kewa,saboda tsaruwarsa. Wani lumtsumeman center carpet na taka,Wanda ya mamaye tsakiyar falon.baya cikin falon hakan yasa nanufi dakin da Adam yace na kwankwasa.tunda natashi daga bacci naji zuciyata tana dan harbawa,amma ina kusantar dakinnasa senaji bugun ya tsananta. Tunda yayiwa mommy text ya koma bakin gado ya zauna,zaman jira. 5 minutes yajira yaji shiru, dafe mararsa yayi datake dan masa ciwo kadan_kadan.shiru shiru bega ankawo masa coffee dinma,gashi yariga ya saba idan beshaba bayajinsa daidai.har mintuna ashirin suka shude baga ankawo masa.shi mutum ne dabaya maimaita Abu idan yafada yafada kenan,hakan yasa be kira mommy ma, yaji dalilin dayasa ba'akawo masaba. Ammafa ransa harya fara baci.lumshe idonsa yayi tare da cize lips dinsa na kasa. Ahankali nafara knocking kofar dakin. Tsaki yaji jin ana knocking, abunda abude yabar kofar,kuma kofar idan tana key mutum yana ganewa.(😂😂😂sorry guy,ta babangidan batasan wannan tsarinba,tukunna dai senan gaba) ko motsawa beyiba balle yayi tunanin tashi,saitin zuciyarsa datake ta bugawa kawai ya dafe. Tun inayi kadan_kadan harna farayi da karfi,saboda nafara gajiya ga yunwa na kwakular cikina.ga wannan bugun da zuciyata takemun, Wanda na alakantashi da na tsorone kawai,domin ni kaina nasanni da shegen tsoro tamkar farar kura,ga kuma abunda akacemun akansa.dafe kansa yayi cikin tsananin bacin ran,wanne shashashanne yake buga masa kofa haka,tamkar ze ballata,ko kuma yasa masa ciwon kai. Cikin zafin rai ya mike ya nufi kofar,jin anki dena bugun,zuciyarsa na bugawa tamkar zata fasa kirjinsa ta fito. Bude kofar yayi. _"Hasbunallu wanimal wakil, ya hayyu ya kayyumu._ t nafara karantowa a fili saboda arba danayi da wani kyakkyawan halitta,bugun zuciyatane ya tsananta,runtse idanuwana nayi atunanina gamo nayi,amma ina kara budewa nakara ganinshi,ya kuramun wasu fitinannun idanuwansa wadanda sukasa jinin jikina tsinkewa.kasa nayi da idona,ina tasbihi ga ubangijin dayayi wannan kyakkyawar halitta. Nandanan jikina yafara rawa,basket din dake hannunane ya subuce ya fadi kasa,jikake tasss! flaks din ya fashe ruwan coffee din ya fara malala akasa,se turiri yakeyi,da sauri yayi baya saboda jin ruwan coffee din akafarsa.........✍️ *kuyi manage da wannan, na shiga shagalin bukukuwa ne,wannanma dakyar nasamu na muku,ko editing banyiba.kuyi hakuri please.🤤🙏🙏* *BY* *Zeey kumurya* *ABUNDA KA SHUKA*......... _*(shizaka girba)*_ *MALLAKIN* 👇 *ZAINAB USMAN KUMURYA* *FARIN JINI WRITERS ASSO.....*📚 ~*Free novel*~ *Bismillahirrahmanirrahim* 1️⃣2️⃣ ..............Tashin hankali da rudani da matsanancin tsorone suka ziyarceni a lokaci guda. "Nashiga uku, na furta a fili saboda ganin ya kone bayan zubar masa da coofee harda konasa nayi,nasan yau mommy idan ta kamani sedai wata baniba.ganin yanda ya zauna abakin gado,amma kunar tamkar ba'ajikinsaba kawai dai ya lumshe idansa.tunanin inda zan samu ruwa na farayi.dan karamin fridge me kyau na hango a dakin,da sauri na nufeshi na dakko ruwan roba me sanyi a ciki. Kafin na karasa garesa kawai naga cikin azama ya janyoni na fado saman gadon,duk da kan gado na fada amma naji jiki.saboda yanda ya warbar dani.wani matsanancin tsorene ya kara rufeni,nandanan jikina ya kama rawa.da sauri na mike daga kwancen danake,saboda tunawa da inda nake.kokarin sakkowa nayi,senaga Ashe kwalbar flaks dince data tarwatse a gabana na kusa takawa shiyasa ya janyoni. Ajiyar zuciya na sauke nadan saci kallonsa.kokarin zuba masa ruwan nayi a kafarsa,amma wata uwar harara ya jefomun. Dasauri nayi kasa da idona,cikin rauni na fara magana,kwalla harta taru a idona. "Dan Allah,kayi hakuri wlh bansan haka zata faruba kayi hakuri dan Allah.nakarasa maganar da fashewa da wani matsanancin kuka,saboda na rasa mafita,bansan hukuncin daze dauka akainaba. Dafe kansa yayi cikin tsananin takaicin wannan yar kauyen yarinyar.tazo ta dameshi,sannan kuma ta zubar masa da cofee harda konasa.yanzu kuma tazo ta dameshi da wani banzan kukanta.ita kuwa mommy ina ta samu wannan *yar shilar yarinyar.* duk maganar dana masa kodagowa beyi ya kalleniba,balle nasakaran zemun magana,araina nace kodai kurmane,babu shakka ma kurmane, afili nace," Allah sarki ga kyau ga kudi amma Allah ya tauyeshi ta wani fannin.cikin sanyin jiki na tashi,na dakko abun share daki,domin su bada tsintsiya suke amfaniba nikuma bansan sunan abunba. Flaks din daya tarwatse na fara sharewa,a wani Dan basket me kyau na zuba,Wanda nake kyautata zaton shine na zuba sharar dakin,saboda kowanne daki na gidan da akwaisa. Hadadden toilet dinsa na nufa Wanda kyawunsa da tsaruwarsa ya zarce duk wani toilet dana gani agidan. moffer na dakko na goge coffee din daya zube Tass,na kara yayyafa ruwa na goge. Ajiyar zuciya na sauke bayan naga dakin ya koma need kamar da.satar kallonsa nayi,naga shima niyake kallo,Wanda na kasa fassara kallon kona menene. Kiran sallar magriba da ladanin masallacin gidan ya kwalla ne yasani nufar kofa daniyyar fita,amma kamar saukar aradu naji wata daddadar murya,amma a dan kaurare take. "Ki hadomun wani" tsayawa nayi cak nibanyi gababa ni banyi bayaba,saboda matukar firgita "Ashe dama yana magana na tambayi kaina,ga zahiri nan kuma,wata zuciyar ta bani amsa. too!, shiko wannan wanne irin mutum ne,daga ganinsa zeyi murdadden hali,da muskilanci bana wasaba. Motsin bude kofar toilet yasani juyowa da sauri,harya shige toilet dinsa.da sauri nima na juya na fice daga dakin.cikin sauri_sauri, gudu_gudu na fice daga part dinnasa gaba daya. Ina kokarin shiga part din mommy yaya sadiq yana fitowa da alama masallaci zashi. "Maryam.lafiya naganki a firgice kuma kin Dade,tundazu naketa zaman jiranki zamuyi wata magana.tattaro nutsuwata nayi ina murmushin yake nace babu komai yasadiq kawaidai ina saurine zanyi sallah. "Anya kuwa maryam? Yakara tambayata yana tsareni da idanuwansa. "Dagaske yaasadiq babu komai. "Toh shikenan ni zan tafi masallaci idannadawo zamuyi magana.kai kawai na gyada masa na wuce ciki. Babu kowa a falon duk sun fice.ajiyar zuciya na sauke ina godiya ga Allah. Cikin mintuna kalilan na tafasa masa coffee din,Allah yasoma bansha wahalar ganinsaba. A wani flaks din na zuba masa. Acikin hijabina na zura,ina addu'ar kar Allah ya hadani da kowa harnaje na dawo. Cikin ikon Allah kuwa bangamu da kowaba,se tsirarrun masu aiki.wlh na matukar gajiya,zaryarnan danayi ga yunwa jinake tamkar zanci babu,ga nauyin sallah akaina dan har an idar. Baya dakin,alamun bedawo daga masallaciba. Ajiyar zuciya na sauke,ajiye masa flkas din nayi. Se'a lokacin na samu nutsuwar karewa dakin kallo. Bansan yazan misalta muku kyawu da tsaruwar dakinba,amma fa ya bala'in haduwa. Juyawa nayi dan karyazo ya sameni,na fice daga dakin. Ina sauka falon kasa naci karo dashi wani na biye dashi abaya,nandanan zuciyata ta hau luguden bugu,tafiya nafara yi tamkar kazar da kwai ya fashewa aciki,cikin matsanancin tsoronsa. Ko kallon inda nakema beyiba yayi hayewarsa sama. Na bayannasane kawai yamun magana.gaishesa nayi muryarsa namun kamar na Santa,ko kuma nataba jin irinta,amma nakasa tuno inda nasantan. Kawar da tunanin nayi daga raina na koma part dinmu. Seda nafara cin abinci sannan nayi sallah,abincinma kadan naci saboda yunwar taci ta cinyeni.falo na dawo na tarar da yaa sadiq,shikadai a zaune. Yana latsa wayarsa. Zama nayi a kusa dashi akan kujera,saboda yanzu nariga na saba dashi. ina maida numfashi. Kallona yayi, "anya kuwa lafiya kike maryam naga gaba daya dukkin canza. "Bakomai fa yaasadiq da gaske,gajiyace kawai Kasan yau munsha aiki. Gyada kai yayi yace. "Hakane dama maganar danakeso muyi akan karatunkine,a ina kika tsaya,akaratunki kinga zaman gidan haka babu dadi sekicigaba ko? Dasauri na dago ina kallonsa saboda jin yasosomun inda yakemun kaikayi. Cikin matukar murna nace,"yaya! Makaranta kuma,kana tunanin hajiya zata bari. Murmushi yayi yace "indai mommy ce bata da matsala,zata bari. Dafe kirjina nayi cikin matukar murna,Ashe inada rabon cigaba da karatu a duniya,Ashe idan Allah yaso zan iya cika burina na duniy...katsemun tunani sadiq yayi, "ki shirya zuwa Monday zamuje school din se'asan yanda za'ayi. ina shirin magana mommy ta fito daga dakin ta. Sallama tayi mana ta zauna akan kujera. Dubanta yaasadiq yayi. "Mommy ina mata maganane akan zanmaidata school zaman haka babu dadi. Kamar daga sama naji muryarta tana tambayata. "A wanne class ta tsaya,akaratun?. Satar kallonta nayi nace "ss 1,amma yanzu yan mate dinmu this year zasuyi candy.gyada kai kawai tayi batacemun komaiba.tana bina da kallon data saba bina dashi,Wanda bansan kona meneneba. Yaasadiq ne yace. "Babu matsala idan mukaje za'asan yanda za'ayi. Godiya na masa,hajiyama na mata na tashi na koma daki.kamar na taka rawa dan murna. "Gaskiya yaasadiq yamun komai arayuwa,idan yamaidani makaranta,yataka babbar gudunmawa arayuwata.bazan taba mantawa dashiba,na bashi babban matsayi a zuciyata.gashi dadin abun hajiya bata hanaba. Wazanwa wannan daddadan albishirdin. Saleemat ce ta fadomun arai. Allah sarki yar'uwata me kaunata,gaskiya gobe zangwada tambayar hajiya kozata barni naje unguwarmu.ko minti talatinne nayi na dawo,Allah yasa ta barni......... Dauriya kawai yakeyi amma kafarsa tana masa zafi kadan_kadan. A falo suka yada zango shida lukman.dubansa lukman yayi yace. "Abokina wai meyake damun Kane naga gabadaya ka canza. Lumshe idansa kawai yayi bece komaiba, wani Abu yake tunani aransa,game da yarinyar dazu. Mikewa yayi ya shiga dakinsa ya dakko flaks din data kawo masa. Dakansa ya dakko musu cup,ya tsiyaya musu.shi mutum ne me tsantsani,da kyankyami.amma kwata_kwata seyaji baya kyankyamin yarinyar. Kodan bega wata kazanta a tattare da ita bane. yafison shan coffee da zafinsa,kurba daya ya masa. yaji kamar ba kalar Wanda yasabasha kullum ba, ya masa dadi sosai.haka yaita kurba yana lumshe ido se cup din kawai ya dire.hira sukayi sosai da amininsa,amma karfin hirar lukman ne yakeyi...... Danazo serving dinsu banganshiba, hamdala nayi araina danbansan da idon dazan kallesaba.gani daya dana masa wani mugun tsoronsa yakamani.ga wasu idanuwansa dayake tsare mutum dashi,duk subi su rikirkitaka.inajin suhailat tana tambayar mommy shi,mommy tace,yace zeyi dinner sa a part dinsa.nidai ina gama abunda zanyi na wuce dakina.yau kam bansamu rabon zagi daga kowaba kuma bansan daliliba...... Suhailat, suna gama dinner ta nufi part dinsa.yana zaune a bakin gado ya tasa laptop agaba,yanata latsawa. Da sallama ta shiga bedroom dinnasa,dan tasan halinsa idan batayi sallama cin ubanta zeyi.a saman lebbansa kawai ya amsa batare da dago ya kalletaba.zama tayi agefensa tana masa wani shu'umin kallo tamkar zata cinyesa. Tana matukar son mustapha arayuwarta,ta matsu ta karasa karatu asha bikinsu,yazama mallakinta ita kadai.bata fuska tayi cikin shagwaba tace."yaya baka ganni bane.dagowa yayi ya kalleta yana sakar mata tsadadden murmushinsa me zautar da ita.ido daya yakashe mata bece mata komaiba.ya maida hankalinsa kan aikinsa.kwantar da kanta tayi a kafadarsa tana shakar daddadan kamshinsa. Ya dauki tsawon 15 minutes sannan yakashe laptop din.hira sukayi sama_sama.tana fada masa yanda tayi missing dinsa,murmushi kawai yake mata.ita kadai taketa masa surutu. Seda yace mata yau agajiye yake,yanason yayi bacci. sannan ta barshi badon tasoba ta tafi. Missed call din kamal ta gani har 5,bin bayan kirannasa tayi amma shima bedaukaba. ajiye wayar tayi ta shige toilet tayi wanka.kayan bacci tasa,ta haye luntsumeman gadonta. tafara sana'artata wato chatting. Kullum seta raba dare sannan take bacci,banda chat da samari babu abunda takeyi, suyi ta hirar batsa.kokuma video call da kamal.kiranta kamal yayi sukasha hira,akarshe yasanar mata da zezo gobe ya gaida mum dinta.batare da tunanin komaiba ta amince masa yazo gidannasu...... Washegari,ta kama juma'atu babbar rana. tunda na tashi sallar asuba bankomaba,sonake nayi aikina da wuri naje gida.karfe 8 nagama shara da moping gyaran dakinsune kawai banyiba da wanke_wanke. Kukune ya fito daga kitchen yana jera kulolin abinci akan dinning.gaisawa mukayi dashi,hira yafaramun cikin gurbatacciyar hausarsa. Na lura shi mutum ne me shegen surutu ni kuma bana shiri dame surutu. Amma shi yana bani nishadi saboda hausarsa dariya take bani. Wajen 8:30,samarin gidan suka shigo falon,mikewa tsaye nayi na gaishesu,kamar kodayaushe babu Wanda ya amsamun se yaya sadiq. direct kan dinning suka nufa suka zauna,nima kasa na samu na rakube. Cikin wata uwar tsawa haydar yacemun, "ke mahaukaciyar inace kina ganinmu, mun zauna amma bazaki taso kiyi serving dinmuba. Dasauri na mike ina basa hakuri,saboda naga mommy da suhailat nasu fitoba shiyasa banyi yunkurin zuba musuba. Ina cikin zuba musu mommy ta fito daga dakin ta.gaisheta nayi,kamar kodayaushe ta amsamun babu yabo babu fallasa. Itama zuba mata nayi na koma gefe ina jiran hamshakiya. Mintuna kadan ta fito itama,cikin shrinta. Bakar abayace ajikinta wadda ta matukar haska farar fatarta.tayi kyau sosai. "Ina kwana,aunty suhailat" wani mugun kallo ta watsomun "daban kwanaba,zaki ganni" kasa nayi da kaina,meye lefina a ciki kuma danna gaisheta ita komai Lefine agurinta. Tana zama itama naje na zuba mata break dinta. Harna nufi dakin hajiya zan gyara naji muryar suhailat. "Ke!" Tsayawa nayi amma banjuyoba. "Kutmar, lallaima yarinyarnan wuyanki yayi kauri. ina miki magana kinki juyowa saboda tsabar raini ko? Juyowa nayi ina bata hakuri saboda banason tashin hankali. "Dalla ni,rufemun wani rubabben bakinki,nonsense kawai.zanyi bako anjima,kafin na dawo daga school ki hada masa drinks,sannan kuma zakuyi aikin delicious dinsa tare dasu salame.amsa mata nayi cikin girmamawa nashige dakin Hajiya. Seda nagama aikina tsaf,nima na karya. sannan na koma nayi wanka. Shiryawa nayi cikin wata atamfa dinkin doguwar Riga.yay mun dass ajikina.turaruka masu sanyin kamshi na fesa wadanda yaasadiq ya kawomun.hijabina iya gwiwa nasaka Wanda ya shiga da kalar kayan. Tsayawa nayi agaban mudubi ina karewa kaina kallo. Nikaina nasan na canza,a yan kwanakin danayi a gidannan. To zanci me kyau,insha mekyau, sabulun wanka me kyau,man shafawa me kyau.makwanci me kyau gashi tunda nazo banga ranaba. Falo na fito da niyyar tambayar mommy, zan fita. a kitchen na tarar da ita tana shirya kaya a wani katon kwando. (Da'alama dai na dan lelentane.)"Sannu da aiki mommy" "yawwa,am maryam dan kaiwa son breakfast dinsa,idan kika dawo sekiyi aikin da daughter tasakaki. atunaninta aikin suhailat na taho yi. dammmm!! Zuciyata ta buga,yaseen ni nama manta dashi kwata_kwata agidan,dazu da safe agurin break bangansaba shiyasa bantuna dashiba. Karba nayi ina amsa mata. "Kiyi sauri maryam,yana saurine ze fita. Akwai plates a kitchen dinsa,ki duba ki dakko seki zuba masa. "Toh mommy na'amsa cikin ladabi. Tunda na nufi part dinnasa zuciyata take luguden bugu, tundaga falon kasa sihirtaccen kamshinsa ya ziyarci hancina lumshe idanuwanayi saboda dadinsa.sama nahau,shima dai kamshinnasane yamun sannu da zuwa.kan dinning na ajiye kwandon. Kofar dake kusa dakinshi na bude cikin sa'a kuwa nanne kitchen. Tsayawa nayi ina kallon kitchen din,Wanda ko wata amaryar albarka.sekace mace komai kwai a kitchen din. Ba karya ya hadu shima.Plates din na dakko seda nadaurayesu sannan na dawo falo.rasss,gabana yayanke ya fadi ganinshi zaune akan dinning yana latsa wayarsa. Karasawa nayi cikin matukar tsoronsa na ajiye plates din,gaishesa nayi amma ko kallona beyiba.tambayarsa nayi mezan saka masa nanma shiru kamar besan ina gurinba.tsayawa nayi ina kare masa kallo.kananun kayane ajikinsa,rigar farace Tass, se bakin wando.kayan sun masa kyau sosai,se yanzu naga tsananin kamarsa da mommy.gajiya nayi da tsaiwa nafara serving dinshi,ina kunkuni kasa_kasa. Komai zuba masa nake acikin plate ina tura masa gabansa. Na dakko farfesu zan zuba masa,nadan saci kallonsa. Idanuwansa tsam akaina yana jifana da wani irin kallo.nandanan jikina yafara rawa. Allah yagani tsoron idanuwansa nakeyi,saboda suna saukarmun da wani yanayi ajikina.ban Ankara kawai gani nayi spoon din yafadi daga hannuna,ferfesunne ya zube akan table din.cikin matukar tsoro na dago ina kallon gefen dayake. Gaba daya roman farfesun ya tsatstsallu a gaban farar rigarsa........✍️ *yauma ba editing,am sorry*🙏🙏 *By* *zeey kumurya* *ABUNDA KA SHUKA*......... _*(shizaka girba)*_ *MALLAKIN* 👇 *ZAINAB USMAN KUMURYA* *FARIN JINI WRITERS ASSO.....*📚 ~*Free novel*~ *Bismillahirrahmanirrahim* 1️⃣3️⃣ ...............Kallonta kawai ya tsaya yanayi cike da takaici da bakin ciki,bayan ta shigo ta samesa bata masa sallamaba, sannan tana ta masa surutun banza,yanzu kuma yana sauri zeje office tazo ta bata masa Riga,dolene ya hukunta yarinyarnan yau. Nikuwa jikina rawa yakamayi saboda matsanancin tsoro da razana,wlh bansan ya'akayi ludayin ya subce daga hannunaba.batare dana bari na kallesaba,na tsugunna akasa akan gwiwata idona tab da kwalla na fara magna. "Dan Allah Dan annabi,kayi hakuri wlh bansanib".... "Shut up!" Yadakamun wata uwar tsawa,wadda najita har tsakiyar kaina,hawayen dake makale a idonane yafara zuba,akan fuskata jikina yacigaba da rawa tamkar mazari. Kallonta kawai yakeyi,gata yarinya karama amma se shegen rashin jin tsiya,ga dan banzan tsoro. Inajin yanda idanuwamsa suke yawo ajikina,amma nakasa dago kaina na kallesa. Mikewa yayi bekaracemun komaiba,ajiyar zuciya na sauke,ina bin bayansa da kallo. Tashi nayi, nafara goge inda na zubar da romon,amma fa bandena kukaba. Yayi kusan 5 minutes sannan ya fito sanye da wasu kayan ajikinsa,hannunsa dauke da rigar dana bata masa.dafe kansa yayi aransa yace. "Ko a ina mommy ta samo wannan yarinyar, ita kam Sam kuka baya mata wahala,yanzu meyamata datake ta kuka,yana zaman zamansa zatasa masa ciwon kai. Ina rakubu tamkar almajira naji ya cillomun rigartasa a jikina, yayi hanyar fita batare dayace mun komaiba. Fahimtar danayi fita zeyi kuma ko break din beyiba, senaji ba dadi saboda nice sanadiyyar hakan. Cikin marairaicewa nace masa. "Dan Allah karka fita bakaci abincinnanba,idan ka tafi haka bazanji dadiba wlh." ni kaina seda na furta hakan naji wani iri. Kamar daga sama yaji muryarta tana rokonsa,tsayawa yayi cak, zuciyarsa na masa kuna shifa bayason mutum me yawan takura, dolene yasanar da mommy karta kara aiko masa yarinyarnan. Juyowa yayi karaf muka hada ido,da sauri nayi kasa da nawa idon saboda wata uwar harara daya wurgomun. Ahankali ya fara takowa zuwa dinning din,da hannu ya nunamun kofa alamun na fice masa. Sum_sum nafara tafiya rungume da rigarsa,duk da befadamunba amma nagane nufinsa na wanke masa. A falon kasa na tsaya ina maida numfashi,tare da daidaita nutsuwata. Saboda ina fita a haka kallo daya mutum zemun yagano zallar firgici da tsoro a tattare dani. Ninke rigarsa nayi wadda sassanyan kamshinta ya mamaye ni,a hijab dina na boyeta na nufi hanyar fita daga part dinnasa........ Kamar amafarki na hangi baaba talatu da'alamun fita zatayi saboda naga ta nufi get din tsakiya.wani sanyi naji araina, tafiya na farayi cikin sauri_sauri saboda na cimmata. "Baaba talatu" nakira sunanta bayan na matso kusa da ita. Juyowa tayi itama cikin mamaki tace, "maryam!" "Na'am baaba talatu ina kwana, kamo hannuna tayi batare data amsamun gaisuwataba,fara'a fal fuskarta. Tace, "maryam dake nake kwana nake tashi araina,kullum,inaso naganki amma badama." "Baaba to meyasa yanzu kikadena zuwa part din hajiya,nima inason ganinki amma bansan inda zansamekiba. "Hmmm,maryam,kenan ai se hajiya ta kiramu muke da damar shiga part dinta,amma ke kina da ikon dazaki iya fitowa kije ko'ina agidannan, kinga wancan dan karamin part din idan kika wuce na hajiya,to nanne part dinmu na yan'aiki idan kikazo zaki ganni." "Kai amma naji dadin ganinki baaba,insha Allah idannagama aikina zanzo anjima,nifa nayi tunanin ma bakya gidannan." Murmushi baaba talatu tayi tace, "banda abunki maryam,ina zani ai nanne gurin Neman abincina,yanzudai sauri nakeyi zanje dubiya, wata yar garinmuce datayi aure anan jiya tayi bari,shine zanje na dubota banason a shiga masallaci bandawoba. "Toh,shikenan baaba,sekin dawo,ki mata sannu,Allah yakiyaye." "Ameen maryam sena dawo" part dinmu nanufa zuciyata cike da murnar ganin baaba talatu dama akwai tambayoyin danakeson nayi mata. Mommy bata falo,may be tana dakin ta. abunda yake kara dauremun kai da gidannan tunda nazo banga bako ko daya yazoba,kodayake bandade da zuwaba kila shiyasaka. Dakina nashiga na'ajiye masa rigarsa acikin cover da nufin idannaga aikin dazanyi sena wanke masa. Kitchen na shiga, kuku na tarar yana kokarin Dora lunch tun yanzu,dariya nayi masa nace, "kai emeka tun yanzu zaka Dora girki?" Cikin hausarsa yacemun madam karamace tasakashi aiki kafin ta fita. Jinjina kaina nayi,dannagane aunty suhailat yake nufi. Tsayawa nayi ina karewa kitchen din kallo narasama wanne kalan drinks zan hada, na iya drinks kala_kala,tunda shine sana'ar innata. amma bansaniba koze musu dadi. Yanke shawara nayi bari kawai na mata zobo,da kunun aya da lemon kwakwa. tunda na kware wajen yinsu,dan da azumi munayi a gidan umma nida saleemat. Cikin freezer na duba,naga akwai duk abunda zan bukata. Sedai banga aya da zobo ba a kitchen din,amma naga kwakwa da dabino da madara da sugar, dasu flavour. Tambayar emeka nayi amma yakasa gane me nake nufi, dole se dakin hajiya na shiga na tambayeta. Tacemun inje kitchen injirata zata saka akawomun,godiya na mata na koma kitchen na fara gogo kwakwar da zanyi lemo da ita. Mintuna kadan wata mata ta kawomun aya da zobon dayawa, wanke ayar nayi na jikata...... ( typing da wahala danayi muku yanda tayi lemon,da kunun ayar.) Ina cikin aikina naji fitinannen kamshinsa ya mamayemun hancina, nandanan naji zuciyata ta hau luguden bugu Wanda narasa na menene aduk lokacin damukayi kusanci dashi senaji hakan a tattare dani,lekawa nayi ta window ina kallonsa,yana sanye cikin manyan kaya yanzu sabanin sanda na baroshi kananane,kayan sun matukar yimasa kyau,amma ba hula akansa, dakin mahaifiyarsa ya shiga. Ajiyar zuciya na sauke na dawo na cigaba da aikina,araina ina tunanin tome yahanasa zuwa gurin aiki,kodai haryaje ya dawone? Babu amsa,wata zuciyar ta fadamun hakan. Se kusan karfe 2,nagama aikin drinks din saboda nayishi da yawa ko wanima zesha. A fridge nasakasu duka. Bayan na zubawa emeka nasa, ai kuwa nasha santi a gurinsa. Nidai dariya kawai natayi masa. Daki na koma saboda inatajiran wadanda aunty suhailat tace,zamuyi aiki tare amma shiru_shiru basu zoba,ashe ni bansaniba a part dinsu sukayi aikin,dama kayan snacks ne,sukayi mata. Wanka nayi tare da dauro alwala nayi sallah. kwanciya nayi da nufin nadan huta. banmasan sanda bacci ya daukeniba..... Tunda ta fice daga falon ya bita da kallo ta gefen ido,besan sanda murmushi ya subce masaba saboda yanda takeyin komai nata a tsorace,kuma da yarinta. Kadan ya taba breakfast din ya mike ya koma dakinsa,fasa zuwa office dinma yayi gaba daya saboda lokaci ya kure,gashi yau Friday, 12 yake baro office saboda masallacin juma'a. Aiki yayi a laptop dinsa,sannan ya mike yayi wanka yayi shirin zuwa masallaci. Seya fara zuwa ya gaida mommy sannan zewuce masallacin. Lokacin dayashiga part din mommy,yana kallonta ta gefen ido tana lekensa ta window, wani murmushi yayi Wanda shikadai yasan ma'anarsa,ya shige dakin mahaifiyarsa....... Suhailat se da 2 ta wuce,ta dawo gida. A matukar gajiye ta dawo dama ita langwaice batason aikin wahala,zaman lectures ma wahala ne agurinta. wanka tayi ta shirya cikin wani hadadden Dubai less.dinkin Riga da skirt ne,yamata dass a jikinta. Ta kafa daurinta tayi kyau sosai,tamkar ka saceta. Suhailat irin matannanne dakana ganinsu zakaga tsantsar kyawunsu. Taci turaruka kala_kala setashin kamshi takeyi. Waya sukayi da kamal yasanar mata yana kan hanya. Abinci taci kadan kafin yakaraso. Amma zuciyartarfa cike take da tsoron yayanta. A kan zuwan kamal Tasan dai idan tace masa abokin karatuntane,ze yarda. Dakin mommy ta nufa tasanar mata kamal yanakan hanya. Mommy macece me son ra'ayin yayanta dabin abunda sukeso. Hakan yasa batayi yunkurin hana kamal zuwaba, koda yakema hakan bakomai bane agurinsu,dan abokin yarka yakawo mata ziyara gida.kuma tayarda da abunda suhailat tace mata akan,kamal abokin karatuntane..... Kamal shikadai yazo gidan su suhailat,kuma wannan shine zuwansa na farko gidan. Bin gidan yakeyi da kallo yana jinjina yanda aka kashewa gidan kudi, tabbas dolene, yabi shawarar abokinsa, yasan yanda yayi ya auri suhailat kodan yaci kudin babanta. Sema yanzu dayazo gidannasu,yakara jin kwadayin aurannata. Murmushi yayi yana kissima abubuwa da yawa aransa,kafin yafara Neman auran suhailat dolene yafara kawar da *almustapha sulaiman menasara* daga doron duniya,domin idan har yana raye suhailat baza tataba auransaba. Yadade da sanin tarihin soyayyar mustapha azuciyar suhailat, wani murmushin yakara saki,akaro na biyu........ Tarba sosai kamal yasamu daga gurin suhailat,babban falon bakin daddy suhailat ta kaishi bayan ta taryoshi da kanta. Ina cikin baccina naji andakamun duka abaya,da sauri na bude idona saboda dukan ya shigeni. Tozali nayi da aunty suhailat dataketa zabgamun uwar harara. "Sannu hamshakiya kinzo kin kwanta kina bacci,ina abunda nace miki kihadamun?." "Kiyi hakuri aunty suhailat banmasan baccin yadaukeniba,nahada miki drinks din yana fridge." Wani banzan kallo ta jefeni dashi,tace, "to kina nufin dakaina zan dakko drinks din nakaimasa koyaya?." Sakkowa nayi daga kan gadon ina girgizamata kai,hijabina na dauka nasaka nabi bayanta zuwa kitchen. Acikin wasu hadaddun jug na zuzzuba masa drinks din. Bayan su salame tace nabi zuwa inda ta saukeshi,sukuma suna dauke da kayan abincine zasu kaimasa,suna gaba ina binsu abaya. Da nisa gaskiya daga part dinmu zuwa part din da'aka saukeshi. Nidai har yanzu mamakin girman gidannan nake, gida kamar unguwa,gashi part part din gidan yayi yawa. Kamal yana zaune yana latsa wayarsa suka shiga suka ajiye masa kayan abincin,nice ta karshen shiga. araina nace,ji uban kayan da'aka shiryamasa shikadai, kuma idan yatashidai kadan zeci iya cikinsa. wani talakan kuwa yanacan abunda zecima bashi dashi.Tunda na shiga naga yadago ya kuramun ido, yana kallona. Tsaki naja kasa_kasa domin ni natsani kallo arayuwata. Gaishesa nayi ina ajiye masa kayan akan center table din gabansa, amsawa yayi yana bina da wani mayen kallo. Harna juya zanfita yatsayar dani da fadin, "Yan mata baki karasa ladankiba,baki zubamun drinks dinba." Dawowa nayi zan zuba masa, amma bance komaiba, Karamin Kofi nadauka nafara tsiyaya masa,raina yafara baci da kallon dayake bina dashi,duk nabi na tsargu. Shiko kamal se lasar lips dinsa yake tundaga ta shigo falon yaganta yajita masa,aransa yanacewa ina suhailat ta samo wannan yarinyar kyakkyawa, danya shakaf da ita,duk da acikin hijabi take amma daga gani tana da manyan kayan aiki. Yanzu kuwa data tsugunna seya kurawa fuskarta ido,yana ganin yanda taturo dan karamin pink lips dinta gaba, aijiyayi tamkar ya janyota jikinsa ya tsotseshi,daga gani zeyi taushi da dadi. Tundazu nake mika masa cup din,bayan na tsiyaya masa lemon kwakwar amma naji yaki karba,dago kaina nayi dannaga meyahanashi karba,senaga kallona kawai yakeyi sekace ze cinyeni. Kara bata rai nayi nace, "Karbi" adakile nayi maganar. Kamar Wanda ya firgita ya miko hannu da niyyar karba, kawai jinayi ya hada da hannuna ya damke da cup din. Kokarin kwace hannuna nayi amma yaki sakarmun se wani murmushi yake jifana dashi. Kawai jinayi kwalla ta cikamun idona,saboda bakin ciki da takaici,na bude baki zanyi magana aunty suhailat ta shigo falon..............✍️ ```Kuyi hakurifa 2 days kunjini shiru,nayi busy ne.amma yanzu komai ya daidaita zaku dinga jina yanda yakamata insha Allah ``` *BY* *zeey kumurya* https://chat.whatsapp.com/Fjc94fL7wBLAM29Wl7L1FB *Masu bina p.c, in'sasu a group din abunda kashuka....yacikane. Amma ga sabonan na bude sekuyi joining. Amma dan Allah,dan girmansa badanniba banda maza mata zallah, kuma idan kinsan ba comment zakiyiba karkishigomun,idan kina group din REAL ZEEY KUMURYA KO ABUNDA KASHUKA..1 shima karki shiga pls and pls.🙏🙏* *ABUNDA KA SHUKA*......... _*(shizaka girba)*_ *MALLAKIN* 👇 *ZAINAB USMAN KUMURYA* *FARIN JINI WRITERS ASSO.....*📚 ~*Free novel*~ ```BANI DA BAKIN GODIYA, A GAREKU MASOYANA,SABODA YANDA KUKA NUNAMUN KAUNAR BOOK DINNAN,ALLAH YABAR KAUNA A TSAKANINMU ME DOREWA,ALKHAIRIN ALLAH YAKAIMUKU A DUK INDA KUKE,A FADIN DUNIYA🥰😘.KAMAR YADDA NA MUKU ALKAWARI FARKON WATANNAN ZANCIGABA,GASHINAN NA CIKA ALKAWARINA, SEDAIFA BA KULLUM ZAKU DINGA JINABA.🤗``` *TUKWICI AGAREKI AUNTY ZAINAB ALIYU JIGAWA, NAGODE DA KAUNARKI DA KULAWARKI AGARENI,ALLAH YA BARMU TARE HAR'ABADA😘* _*THIS PAGE IS FOR YOU,UMMUL AMINA,KIYI YANDA KIKESO DASHI🥰*_ *Bismillahirrahmanirrahim* 1️⃣4️⃣ ...........Da sauri na saki cup din dake hannuna bayan yacikamun hannun, cup din ya fadi kasa ya tarwatse cikin tsananin tsorata na mike tsaye, shima mikewar yayi da sauri saboda kar lemon yabatasa. Wani mugun kallo aunty suhailat take bina dashi, cikin tsana dajin haushi. Tana karasowa gabanmu ta daga hannu da nufin ta kwadamun mari, runtse idona nayi cikin tsammanin jin saukar mari, amma har wasu sakanni suka wuce banjiba. Ahankali na bude idona, senaga Ashe bakonnatane ya rike hannunnata yana girgiza mata, kai.cikin tsananin bacin rai ta fara magana. "Haba kamal yazaka hanani hukunta wannan matsiyaciyar yarinyar, baka ganin abunda tayine, sekace mahaukaciya zata wani sakar maka cup, idan da yabata maka jikinkafa" ta karasa maganar cikin karaji da daga murya. "look baby, ai itama tsautasayine batasan hakan zata faruba, haba bakiga yarinya bace kidena mata magana haka mana" wani kallo ta watsama masa batace komaiba, Nidai ajiyar zuciya kawai nake saukewa, cikin hanzari na nufi kofar fita, saboda ganin yana kokarin janyota jikinsa. Zama kamal yayi yadora suhailat akan cinyarsa, yace. "Haba baby bagirmanki bane kidinga daga murya akan abunda bekaiyakawoba." "Hmm, bazakaganebane kamal natsani yarinyarnan over, haushinta nakeji" murmushi kamal yayi aransa yace, "dole kitsaneta mata tunda tafiki komai da komai." Amma a fili seyashiga lallashinta yana tattabeta....... Da sauri nake tafiya tamkar zantashi sama, tsayawa nayi abakin kofar falo ina daidaita nutsuwata. Ahankali na bude kofar falon na shiga, mommy ce kadai zaune a falon. Sallama na mata kawai na shige dakina. kan gado na fada ina maida numfashi tunanika kala_kala araina, ga haushin wannan dan akuyar yacikamun zuciya,haka kawai ze rikemun hannu wlh, Allah ya isana. Arayuwata na tsani namiji dan iska. Agefe guda kuma ina mamakin aunty suhailat,yanda take mu'amala da dan iska, haryana tabata. Mtss naja tsaki a fili cikin takaici,nakawar da tunaninsu daga araina. Mikewa nayi na dakko rigar *oga* dankarna manta,nakara wani lefin dannaga ya kulu akan rigarnan. Tasss na wanke masa ita a toilet dina, natisa wankinta yakai sau biyar, sedanaga tayi kal sannan na barta. A toilet din nashanya masa.Alwalar sallar la'asar na dauro na fito, dan anyi sallar tun dazu. Bayan na idar da sallar nafito domin zuwa part din su baaba talatu. Mommy nagani zaune afalo, da suhailat da bakonta. Bata fuska nayi sosai sabida kallon gefen idon dayake bina dashi. Aunty suhailat kuwa se uwar harara take zabgamun, kusa da mommy na durkusa nace, "mommy zanje gurin baaba talatu" kallona tayi na wasu sakanni, batacemun komaiba,harnayi tunanin bazata barniba senaji tace, "ki dauki lemon kwakwa a kitchen zaki ganshi na zuba a jug,kikaiwa my son,seki wuce daganan" "toh mommy nagode." Na'amsa mata cikin ladabi. Kitchen din nashige na dauka, zuciyata nadan bugawa nanufi part dinnasa, harga Allah tsoron bawan Allah nan nake,tsoroma kuwa bana wasaba. A falon kasa na tarar dashi yanada aiki a system dinsa,yacanza kaya zuwa kanana. Sannu namasa, batare daya dagoba ya amsamun dakai, harzankai lemon kan dinning, sekuma naga dacewar na ajiye masa agabansa, akan center table din gabansa na ajiye masa, ina satar kallonsa. Harna juya zantafi yatsaidani da fadin, "exucuse me pls" juyowa nayi ina kallonsa, da hannunsa yanunamun wata kofa a falon yana fadin, "help me with cup" "ohk sir" na'amsa masa cikin ladabi. Kofar dayanunamun na nufa na bude, kitchen din hadadden shima, bantsaya wani kare masa kalloba na nufi inda naga kofinan, seda na daurayesu sannan na kawomasa na fice daga part din. Ajiyar zuciya nasauke ganin yanzu mun rabu lafiya, part din da baaba talatu ta kwatantamun naje, karamin part ne, yana dauke da babban falo da se dakuna. Gasu salame nan zaune da sauran 'yan aiki, kowa yana sabgar gabansa gaishesu nayi na tambayesu baaba talatu,wani daki suka nunamun godiya na musu nashiga da sallama. Baaba talatu zaune take akan dadduma tana lazimi, zama nayi agefen katifar dake dakin ina jiran ta karasa. "Maryama, ashedai zakizo Aida nayi tunanin bazakizoba" baaba talatu tafada bayan kammala laziminta. "tun dazu nakeson zuwa baaba sekuma nayi wani aiki danagama kuma bacci yadaukeni" "ayya sannunki, aikina da kokari ya aikin,kinadai jin dadinsa" "eh baaba, ai aikinma babu yawa nariga nasaba fiye da haka agida." Gyara zama nayi sosai nace "baaba talatu, dan Allah kikaramun Karin haske akan abunda kikafadamun wlh kullum cikin zullumi nake, da tsoro acikin gidannan" "maryama ki kwantar da hankalinki insha Allah, babu abunda ze faru dake, kedai kawai kidage da addu'a kuma kiyi takatsantsan da kowa na gidannan." Numfashi nasauke nace, "to baaba talatu kincemun lokacin da'akeyin wannan mummunan abun duka yaran gidan basanan towa kike zargi kenan?" "Bawai ina nufin dukansu basananbane kawata_kwata, a'a,lokacin daza'ayi idan wannan yananan to wannan bayanan, zakiga wani lokacin da'akayi mutum ukun sunanan kokuma hudu kokuma biyu,inafatan kingane." Jinjina kai nayi nace, "eh nagane baaba amma ni abunda yafi tsoratar dani dakikace duk wadda akayiwa fyaden mutuwa takeyi" "Eh to gaskiya kuskuren danayi kenan dana fada miki haka, saboda bansan na sauranba,ammadai tabbas na jikata hakance ta kasance." "To shi megidan baaba meyasa bazedau matakiba, kodan gudan bacin sunansa a idon jama'a, musamman dayakasance ana fadar alkhairinsa sosai agarinnan" "bansaniba gaskiya maryam, domin tabbas alh mutumin kirkine" ajiyar zuciya nasauke, nidai har ga Allah zaman gidannan a tsorace nakeyinsa. "Amma baaba da lefin hajiyama, kuma ni tana aikena part din danta ko tunanin wani Abu yafaru batayi. Murmusawa tayi tace, " Aishi wannan gaskiya bana zarginsa saboda kafinma kiganshi a part din hajiya ana jimawa, kuma wannan abunda akeyi adakin masu aikin akeyi harnan akebinsu, shikuwa daga gurin aiki se part dinsa,befiya zuwa nanba gaskiya,amma ai bata aikenkipart din sauran yarannata?" "Ehh,baaba bata aikena." "Yawwa" Munsha hira da baaba talatu sosai, takuma kwantarmun da hankali, Allah yanaji yana gani, kuma baya barci shize kareni,babu wayo ko dabarata. Seda nayi sallar magriba nabar part dinnasu, har kofar part din hajiya ta rakoni. Tambayarta nayi akan zan iya tambayar hajiya zuwa ganin gida, tatabbatarmun dazan iya kuma hajiya zata barni. Babu kowa a falo yanzu, dakina nashige, rigar yaya dana wanke nadakko harta bushe, dama bata dawani nauyi. Tunda nazo gidan naga iron sabo adakina, bantaba guga dashiba seyau nace bara nagoge masa rigar. Jonawa nayi nafara gogewa, ina gugar ina tunanin maganarmu da baaba talatu, ban'ankaraba tsautsayi ya afkamun iron din yakwashe wani guri agaban rigar kuma dayawa ya kwashe. Wani gumine yafara tsatstsafomun duk da a.c da fankar dake dakin, "nashiga uku ni maryam, meyakaini goge rigarnan, tsautsayi ko karambani yanzu gashi na kona masa, nasan idan yaji lefin dana aikata masa sedai wata baniba" wata hautsinawa cikina yayi, matsanancin tsorone ya lullubeni. Ninke rigar nayi cikin rashin sanin mafita, addu'a nakeyi araina Allah yasaukakamun duk hukuncin dazemun. Adaren yau kam abincima kadan natsakura naci, saboda zullumi. Inayin serving dinsu na kwanta dama nayi sallah ta, addu'a nashigayi araina ga tsoron zaman gidannan ga tsoron gamuwata da oga kwata_kwata,baccinakam adaren ragaggene, dandaima baccin barawone,bansan sanda yasaceniba. washegari, inayin sallar asuba nafara gyaran dakina,yau sonake nagama aikina da wuri domin inason zuwa unguwarmu. Harna gyara falo na koma dakina na kwanta, babu Wanda yafito,har kuku kuwa. Tunawa nayi yau Saturday, may be weekend basa tashi da wuri. Se wurin karfe goma da wasu mintuna suka fito,nima fitowa nayi danyin aikina. Serving dinsu nayi ina gaishesu,wasu suna amsawa wasu kuwa ko kallo ban ishesuba, ninama Riga nasaba da hakan,kamar kullum yauma duk sun hallara amma babu oga. Harna juya zantafi mommy ta tsaidani da fadin na shiga kitchen madauki breakfast dinsa nakai masa. Seda zuciyata ta buga sosai, saboda tsoro. Amsa mata nayi nakoma dakina nadakko rigartasa na boyota acikin hijabi. Basket din kayan Karin kumallonnasa na dauka, zuciyata na dukan tara_tara, ina tafe Inayin addu'a. Da sallama nashiga falon kasa, babu kowa se mayen kamshin turarensa,sama na haura, yana zaune akan kujera 2siter yanata fama aiki a computer. Dukda bugun da zuciyata takemun haka nadaure nashiga da sallama, labbensane kawai ya motsa alamar ya amsa. Tsugunnawa nayi cikin girmamawa nace, "ina kwana" batare daya dagoba yadagamun hannunsa, karasa wa nayi najere kayan akan dinning, gabansa na dawo na durkusa akaro na biyu, cikin matukar tsoro na mika masa rigarsa. Dagowa yayi yakalleni na wasu y'an sakanni sannan yadauke kansa karbar rigar yayi ya budata. Kallona yakeyi yana kallon rigar, nandanan jikina yafara rawa, saboda babu wasa kokadan a fuskarsa. "Dan Allah kayi hakuri, wlh bada sanina na konaba,tsautsayine" nafadi haka cikin rawar murya inashirin fashewa da kuka. "Meyasa kika konamun Riga?" Yajehomun wannan tambayar cikin tsawa,fuskarsa a hade. Cikin in'ina nace, "ba....ba.ko..mai." Daradaran idanunsa yazubamun, kasa nayi dakaina hawaye yafara zuba a idona,saboda tsoro. Cillomun rigar yayi becemun komaiba,yamaida hankalinsa akan abunda yakeyi. Ahankali nadago kaina na kura masa ido, duk yanda naso dauke idona daga kallonsa amma nakasa, yana sanyene cikin farar jallabiya. Gaskiya ada gaba daya kallon tsoro nake masa, seyanzu nakara ganin tsantsar kyawunsa, ada inaganin kamarsa da mommy, amma yaunagane yafita kyau nesa bakusaba, babuma hadi, kuma ba mommy kadaiba dukama mutanen gidan duk ya fisu kyau,farar fatarsuce kawai daya. Mintuna goma, suka shude, amma beko kara kallonaba, nikuma aikin kallonsa kawai nakeyi ina tasbihi ga ubangijin dayayishi,wani Abu naji yana shigata akansa, Wanda bansan yazan fasalta mukuba, domin bantaba Jinhakan akan waniba. Kafata ta sagemun saboda tsugunnon danayi, gyarata nayi ina sauke doguwar ajiyar zuciya. Kallona yayi ya nunamun hanyar kofa, tare da fadin, "kisan yanda zakiyi kikawomun wata rigar,bakonanniyaba, tunda ke bakyajin magana,kokuma na babballaki agidannan" waro idona nayi waje cikin tsorata nace, "dan All....." "Go out!" Yakatseni cikin tsawa. mikewa nayi ina kara sauke nannauyar ajiyar zuciya, ajiye rigartasa nayi ina satar kallonsa, wata uwar harara ya wurgamun dasauri na dauki rigar nafara tafiya, Ina tafe ina waiwayensa harna fice. Tsaki yaja bayan ta fice, yalura yarinyar akwai yarinta sosai atattare da ita, ga kuma abunda yatsana wato saurin kuka,ga kuma rashin ji. Yarasa meyasa mommy takeson irin wadannan yaran a matsayin y'an aiki,wadanda babu abunda suka iya banda shirme, dasawa mutum ciwon kai. tabe bakinsa yayi yacigaba da aikinsa..... (Kaikadai dai🤤) Ina tafe ina gulmarsa araina, hoton fuskarsa yaki bacememun daga idona,gadai tsoronsa daya cikamun zuciya,amma jinakeyi dama bekoreniba inzauna inta kallon fuskarsa me kyau,niyau fadannasama burgeni yayi. Seda nafara ajiye rigar adakina, sannan nafara gyaran dakunan su mommy. Abun mamaki mommy bata tambayeni mena tsaya yiba harna dade. Se suhailat cema naji tana magana tana hararata, nibanmaji metaceba, hankalina yana wani gurin daban. Bayan nagamane na tambayeni mommy, inason zuwa gida, tace nabari senakara kwanaki yanzu yayi kusa, dududu satina dayafa. Haka na hakura na koma dakina, bayan na dibi abincin Karin kumallona, inagama ci na kwanta, Inata tunanin yanda zan iya biyansa rigarsa, niba kudiba idanma inada kudin inazansamu rigar insai masa, Allah ka sassauta zuciyar bawannanka ya hakura, dan tun jiya danakaimasa lemo na fuskanci ransa abace yake. bansan sanda bacci yayi awongaba daniba Inata tunane_tunanena.......... Suhailat ce tashiga falon mustapha da sallama, duk da sallama ba dabi'arta bace, amma shi tana masa dantasan idan batayiba casata zeyi. Bedago ya kalletaba ya'amsa mata akan labbansa. Zama tayi agefensa tana fadin, "yayana ina kwana?" Dagowa yayi yajefeta da wani kallo be amsa mataba,yamaida kansa, yacigaba aikinsa. Marairaicewa suhailat tayi ta fara magana cikin shagwaba. "Haba yaya ina maka magana kaki kulani, meyafarune jiyama da daddare nakiraka da yawa amma bakayi picking ba, pls yaya I'm sorry idan na maka lefi" Wata uwar harara yadago ya zabga mata, wadda tasa yayan cikinta hautsinawa. "Waye Wanda yazo gurinki jiya?" Yajefo mata wannan tambayar cikin kakkausar murya. Rasss! Gabanta yayanke yafadi, dama yasan kamal yazo, nashiga uku ni suhailat, Ashe duk boyon danakeyi yasan da zuwannansa. Cikin alamun rashin gaskiya tace, "am... Cla..ss ma..te dinane" "kifadamun gaskiya, kinsan banason karya ko?" Yafadi haka yana tsareta da idanunsa, kasa tayi da kanta cikin matukar tsoro, batason fushinsa ko bacin ransa, saboda be iya fushiba. "Dagaske nake yaya" bekara cemata komaiba yacigaba da aikinsa. Gajiya tayi da zama ta mike jiki asabule ta fice, dankarta kara wani lefin. mommy ce kawai zata iya shawo mata kansa, yanda taga tsananin bacin rai atattare dashi....... Seda akayi sallar azhar na tashi wanka nayi tare da dauro alwala. Ina idar da sallah nafita falo domin yin kallo, dannagaji da zaman da kwanciya kuma nasan yanzu babu kowa a falon. Ina shiga falon naga yaya sadiq, shikadai azaune. Da mamaki nake kallonsa. "Yaya sadiq, ina wuni?" Nagaisheshi bayan nazauna. "Lafiya kalau, maryama ya gidan?" "Alhamdulillah yau lafiya naga baka fita aikiba?" Murmushi yayi yace, "kinmanta yau weekend ne" "eh hakanefa bamanta" tasowa yayi yadawo kusa dani yazauna. "Meke damunkine maryam, naga kamar da damuwa akan fuskarki?" "Bakomai yaya, amma meyasa kullum.kake tambayata haka." Murmusawa yayi yace, "saboda inaganin hakan atattare dakene, amma senaji kinje bakomai, ko bakyajin dadin zaman gidannamune?" "A'a kokadan bahaka bane kawaidai kai kake ganin haka" bebani amsaba yazira hannunsa acikin aljihun wandonsa, wani zobe na azurfa me kyau ya mikomun yana fadin, "saka wannan ahannunki, naga hannunki ko ring daya babu" cike da mamaki nake kallonsa, "kaii yaya sadiq, amma yayi kyau sosai, nagode Allah yasaka da alkhairi." "Babu komai kanwata ni dake da suhailat duk daya nadaukeku agurina,duk abunda zangani insai mata kema zansiya miki" murmushi nayi inasaka azurfan a danyatsana na tsakiya,naji dadin kalamansa sosai, kaf gidannan bayan baaba talatu babu Wanda nakejin dadin kasancewa dashi tamkar yaya sadiq, yanada kirki sosai bakamar yan'uwansaba,shiyasa nasaki jikina dashi. Azurfar tamun kyau ahannuna kuma tamun dadidai tamkara angwadani. Godiya namasa sosai, harseda yacemun godiyar ta isa haka. labari ya shiga bani na'abun bandariya, daga baya muka koma hira. gaskiya yadebemun kewa sosai, wadda harta mantar dani rikicinmu da oga. Muna cikin hirarne mommy tashigo falon. Tunda tashigo namata sannu, naja bakina nayi gum. Hira suka farayi da danta, nikuma na maida hankalina akan kallo. Zannurainne yashigo falon, zama yayi agefen mahaifiyarsa, gaishesa nayi, bayare daya kalleniba ya'amsamun, yau kam naci sa'a ya'amsamun amma duk da haka gwarashi akan haidar. "Mommy yaufa ba'a gyaramun dakiba, yanacan yayi kaca_kaca." "Meyasa my son, su salame basuzobane?" "Sunzo ina bacci, that is the why" "ohk bari nakirasu yanzu su gyara maka" "no, mommy leave them, wannan yarinyar taje ta gyaramun kawai". Bansan meyasaba naji gabana yayanke yafadi, duka maganar dasukeyi inajinsu, Allah yasa kar mommy ta yarda naje na gyara masa, nifa harga Allah bansan zuwa dakin maza, sukuma naga hakan bakomai bane agurins......."maryam kije kigyarawa zannurain dakinshi yanzu" muryar mommy takatsemun tunani. Cikin ladabi na'amsa mata. "Toh mommy, amma bansan inane dakinba" kwatantamun part dinnasu mommy tayi, mikewa nayi zuciyata babu dadi, nafice. Ina kallon fuskar yaya sadiq nagane Sam beji dadin hakanba. Da tafiya daga part din mommy zuwa nasu, suma part dinnasu babbane kuma shima yayi kyau. Sama nahau kamar yadda mommy tacemun, dakin dake left side, nashiga. Banwani tsaya karewa dakin kalloba, saboda burina inyi ingama gyaran. Filallika nasauke kasa nafara karkade zanin gadon, wani abune karami naga yafado daga kan gadon, dauka nayi ina dubawa. Zaro idonayi nayi waje, domin bazantaba mantawa da abunnanba, saboda asanadinsa aka taba zanemu lokacin muna j.s 3, wata kawarmu aka kamashi, ni'a time dinma bansan ko meneba, sedaga baya salimat takemun bayani wai sunansa *condom*, da kuma dalilin dayasa ake amfani dashi. Ajiyewa nayi zuciyata cike da mamaki, tome zannurain yakeyi dashi shida ba mataba. Ajiyewa nayi tare da Tabe baki, nacigaba da gyaran dakin, nagama gyaran gado ina kokarin share dakin, naji anturo kofar dakin. Dasauri nadago dan ganin meshigowa, zannurain dinne, yana kokarin maida kofar yarufe........✍️ _*idan banga ruwan comments ba zamu koma gidan jiya, kuma bansan guntun comment dogon sharhi nakeso*_ *BY* *Zeey kumurya* *ABUNDA KA SHUKA*......... _*(shizaka girba)*_ *MALLAKIN* 👇 *ZAINAB USMAN KUMURYA* *FARIN JINI WRITERS ASSO.....*📚 ~*Free novel*~ *Bismillahirrahmanirrahim* 1️⃣5️⃣ ..........maida kofar yayi ya rufe,hakan yayi daidai da buguwar da zuciyata tayi, cak na tsaya rike da tsintsiyar ahannuna,ina kallonsa, hade fuskarsa yayi yana bina da wani mugun kallo tamkar yaga kashi, wayar hannunsa ya ajiye akan mudubi,toilet naga ya nufa,becemun komaiba. Wata sassanyar ajiyar zuciya nasauke,bayan ya shiga toilet din. Sunkuyawa nayi nafara sharar,cikin sauri,sonake kafin ya fito nakarasa saboda kasancewarmu a daki daya bedaceba. Ko Rabin dakin banyiba,naji ana knocking kofar dakin,ajiye tsintsiyar hannuna nayi naje na bude,zuciyata nadan bugawa. Yaya sadiq nagani tsaye fuskarsa ahade, kallona yayi na wasu sakanni,sannan yace, "wuce mu tafi" da mamaki nake kallonsa,zanyi magana yadagamun hannu,jiki asanyaye nabiyo bayanshi muka fice. Tafiya mukeyi amma babu Wanda yayiwa dan'uwansa magana,nalura ransa abace yake sosai,danni tunda nazo gidanma bantaba ganinsa cikin irin wannan bacin ranba,domin shi mutum ne ma'abocin fara'a da raha. Har kofar part dinmu yarakani, satar kallonsa nayi naga shima ni yake kallo,duk senaji na tsargu, ahankali na juya na fara tafiya, na shige part dinnamu. Wata sassanyar ajiyar zuciya sadiq yasauke bayan tashige,shima juyawa yayi ya koma part dinnasu.......... Turus zannurain ya tsaya bayan yafito daga toilet din,ganin babu maryam adakin, ga shara ta fara kuma bata karasaba. Cikin dacin rai ya fita domin ganin iskancin daya hanata karasa masa gyaran dakin,ga toilet dinma bata wankeshiba. A falon kasa yaci karo da yaya sadiq,daya shigo part din,zagaye shi yayi yana kokarin fita sadiq ya rukosa. Tsayawa yayi batare daya juyoba, "kama dena wani sauri,kana tafiya fuuu kamar zaka tashi sama,nasan mekake shirinyi,toni nace ta koma,ka gyara dakin da kanka,kokuma Wanda suka saba gyara maka su gyarama,aidama ita banda gyaran dakinku aka dauketa aiki a gidannan,danhaka daga yau karka kara sata gyaran daki,nafada maka,kuma karka kuskura kace zaka mata wani abun!" Yakarasa zancen dadan daga murya, zannurain bashi dadamar musawa sadiq abunda yace,domin duk fitsararsu basayiwa yayyensu,dan daddy bebasu wannan tarbiyyarba,ga kuma oga kwata_kwata mustapha yanajin labarin kayiwa nagaba dakai rashin kunya seya sabarmaka. Juyawa yayi,yakoma sama yana kunkuni aransa amma bece komaiba........ Seda gabana yafadi danashiga falo,ganin suhailat kwance akan cinyar mommy ita kuma mommy tana waya,ni indai ba tsautsayiba bana kaunar abunda zehadani da suhailat. Sallama nayi batako kalkeniba balle ta amsamun,mommy cema kawai tadagamun hannu tana bina da kallon dabana ganemasa, narasa meyasa indai muna guri daya duk dagowar dazanyi senaga mommy tana bina da wani irin kallo,araina nakance ko dabi'arta kenan kalllon mutane oho,danni kallonnata yafara isata. Dakina nashige. Mommy bayan tagama wayar datakeyi ta shafa kan suhailat Wanda ko dankwali babu,tana fadin, "yadai daughter naga kamar ranki abace,meke damarmunkene.?" Cikin tabara tace, "mum, yayanefa daga naje part dinsa dazu yayitamun fada yanamun tsawa,karshema koroni yayi wai duk akan kamal yazo gidannan,kuma nafada masa abokin karatunane" murmushi mommy tayi tace, "aidama nasani,toki kwantar da hankalinki kidena damuwa bari nakirasa awaya nabashi hakuri" "yawwa mommy ta thanks" pick mommy tamata agoshi. ta dakko wayarta ta yi diarling number shi, har 2 missed call tamasa amma bedagaba. "Kinga daughter, beyi picking call dinba,amma mubari zuwa later idanma bekiraniba senaje har part dinnasa,natausheshi" "tom shikenan mum,bari naje na kwanta bacci nakeji" suhailat ta fadi haka tana tashi daga jikin mommy. "Ohk daughter sekin tashi"...... Bayan sallar sala'ar ina toilet ina wanke kayan dana cire naji,ana knocking kofar dakina,tsane hannuna nayi na dauraye na fito na bude. Daya daga cikin masu aikin gidan ce, gaisawa mukayi tacemun infito falo hajiya tana nemana. Amsa mata nayi nakoma na dakko hijabina nasaka,ina mamakin mommy,yanda idan tana nemana bazata iya zuwa takiraniba da kanta, dukda muna part daya,sedai ta turo wasu dasukecan da nisa,aganina ai wannan wahalace. Da sallama abakina na karasa falon,ina bin bakin masu kamala dake falon da kallo. Wata dattijuwace,sekuma wata yar budurwa dako zata girmemun kadanne. Tsugunnawa nayi na gaishe da dattijuwar cikin ladabi, ta amsamun fuskarta dauke da fara'a,ita kuwa matashiyar se kallona takeyi. Sannu namata,amsawa tayi ta kara da fadin, "aunty,kinga nasaki baki se kallonta nakeyi,naganta kyakkyawa masha Allah,mommy ina kika samu wannan me aikin kyakkyawa da ita,gata kuma......"kai aliya badai danbanzan surutuba,daga ganin yarmutane zaki fara cikata da surutu." Wadda sukazo taren ta fadi haka,da alama kuma mahaifiyartace saboda tsananin kamar dasukeyi. Nidai murmushi kawai nayi,mommy ma murmushin tayi tana kallona. "Maryam baki mukayi,kije kihado musu abinci" cewar mommy tana mikewa. Cikin ladabi na amsa mata ina tashi. "Bari inzo intayaki" cewar budurwar itama tana mikewa,Murmushi nakara mata akaro na biyu. Tare muka Shiga kitchen din, muka hado kayan muka jera akan dinning, mamakinta ya cikani,daga ganinta itama daga gidan kudi ta fito,amma jibi yanda takemun babu kyama kokuma nuna banbanci,ashe dai masu kudin akwai masu kirki. dakina na koma,bayan mun kammala. "Gaskiya aunty me aikin gidan daddy menasara,ta burgeni zanso ta zama frnd dita,bari nagama cin abincin nan naje musha hira." cewar aliya tana kokarin kai abinci baki. Harararta aunty tayi tace, "zadai kije cikata da shegen surutunnan naki, Mara kan gado,to itadai kinga yanda take, daga ganinta bameson hayaniya bace,karkije ki takura mata." Tura baki gaba,Aliya tayi tafara cin abinta. (Hajiya saudart kanwar alh menarasace,uwarsu daya ubansu daya,dama su uku iyayensu suka haifa,daga alh menasara,se baban suhailat sekuma auta hajiya saudart,wadda suke kiranta da aunty. ) ita kanta aunty,maryam ta burgeta, gani daya data mata tagane yarinyar tana da nutsuwa, da hankali. ina cikin shanya kayana najitashigo dakin da sallama,dama abude nabar kofar. Har bakin toilet din takaraso rike haba tayi tace, "sannunki da aiki, dakanki kike wankin,bada masu wanki agidanba kidinga basu mana" "ai wankin babu yawa,kayan dana cirenefa" "lallai agaisheki,nikuwa kinganninan na tsani wanki da wanke wanke arayuwata." Murmurshi na mata kawai,ina mopping toilet din bayan nagama shanyar. Aliya bata damu da shirun da maryam tamataba, tace. "Nikuma. Maryam aunty suhailat tananan tunda mukazo banji duriyartaba" "tananandai dazuma kafin kuzo tana falo,ammadai yanzu bansaniba kota fita" nabata amsa ina fitowa daga toilet din. Zama mukayi abakin gado,tabe baki aliya tayi tace, "hmmm,kilanma tana jinmu taki fitowa,shiyasafa dakyar na biyo aunty gidannan, saboda kwata_kwata bama shiri da ita, kingadai babanta da auntynmu uwarsu daya ubansu daya,amma seta dinga daddaga mun kai,gata da masifa,amma ina zuwa naganki senaji dadi dannasamu abokiyar hira." Dariya nayi danyadda take magana ta matukar bani dariya,"wow kinga yadda kika kara kyau kuwa,dakikayi dariyar nan,ga dimples dinki sunkara lotsawa,dama nice ke." Murmushi kawai namata, nace. "Kemafa kyakkyawace amma.kindage seyabon kyauna kikeyi" "hmm,mekyau inda babu kyawawa irinkuba." nanma murmusawa kawai nayi.Hira tashiga yimun tana bani labarai, harta fadamun daga kaduna suke,tanata bani labarin kawayenta dana school, lokaci daya naji tashiga raina, baburuwanta gaskiya, tamkar wadda muka Dade da sanin juna, nalura daga ganinta bazatayi wulakanciba,bata duba matsayina agidanba,tasaki jikinta dani tanatamun hira,nima naji dadin haka,kobakomai zata debemun kewa kafin suntafi....... *___________________* *MUSTAPHA* *___________________* Har sallar azhar yanata faman aiki, sallah ce tasheshi dama kuma ya kammala, abunda yakeyi. Yunwace yaji tana nukurkusarsa,dinning ya nufa inda maryam tajere masa abinci, yahada tea yasha sannan yatsakuri sauran kayan break din,dahar time din dazafinsu basuyi sanyiba,saboda flaks din dasuke ciki masu rikon zafine sosai, yaci. Sedayaje sallah yadawo sannan yayi wanka ya shirya cikin kananun kaya, Wanda suka matukar yimasa kyau. Direbansa yakira,yazo ya daukesa zuwa kamfanin dayake aiki,domin yanason yaduba wasu ayyukane. Time din da mommy takirashima yanacan,shiyasa beyi picking call dintaba, sedaga baya yaga missed call dinta,text ya turamata,akan yaje office ne,yana sauri shiyasa beshigo yamata sallamaba sedai idan yadawo. Dama ka'idane kullum idan yadawo daga sallar asuba,baya komawa part dinsa seya fara zuwa yagaida mommy,yaga kuma yatatashi,sannan yakoma part dinsa. Yanaganin text din da suhailat ta masa kala_kala naban hakuri,karantawa kawai yayi amma bemata reply ba. Shifa Sam bayajin son suhailat aransa,bayan na yan'uwantaka, saboda shi sam bakalar macen dayakeso bace suhailat. Suhailat tanada rawar kai,da hayaniya. Shikuma yafison mace silent Mara hayaniya. Kawai yana tausayin suhailat ne yanda take tsananin sonsa, shiya shima yake nunamata yana sonta, kuma sannan iyayensuma suna farin ciki da soyayyartasu. A'da Sometimes yana tunanin anya kuwa yanada lafiya,kamar kowanne namiji, saboda bayajin wani feeling kokadan ajikinsa, amma kuma segashi yanzu harciwo feeling yake samasa,tundaga ranar da accident yahadasu da yarinyar dabesan ina zegantaba, gashi asanadiyyarta komai nasa yana kokarin canzawa,danma yadage da shan magunguna yanzu, dabesan halin dazeshigaba. Watsar da tunanin komai yayi daga ransa yacigaba da abunda yakawosa. Se kusan magriba yabaro office din,sanda ya shigo gida ana kiraye_kirayen sallar magriba, beko shiga cikin gidanba,ya nufi masallaci. Part din mommy yanufa bayan an idar da sallah,shida sauran yan'uwansa dasuka hadu a masallaci. Babu kowa a falon duk suna daki, aunty ce tafito daga dakin dake jikin na mommy,Wanda ana take sauka idan tazo gidan. Da mamaki mustapha yake kallonta,danbesan tazoba. Shikuma su sadiq sunsan tazo harsun gaisama. Fadada fara'a aunty tayi tace, "sannunka boy seyanzu kadawo kenan agogo sarkin aiki,tunda nazo nake cikiyarka aunty atika tacemun katafi office, kai weekend dinma bazaka hutaba" shagawabe fuska yayi yace, "wai auntynah haryanzu boy dinnan baze fita daga bakinkiba, nifa bansan sunan" karasawa aunty tayi kusa dashi ta kamo hannunsa tana fadin, "sorry my son,nariga nasabane,zomuje kazauna kahuta dannasan ka kwaso gajiya" su haidar kuwa dasuke kallonsu se guntse dariya sukeyi, indai aunty tazo gidan seta tsokanesa tace masa boy, saboda dayana yaro haka akecemasa,daya girmane yayi cancel din sunan. Zama sukayi akan kujera,yana gaisheta. Aunty macece,me kirki da saukin hali,gashi tana jansu ajiki,musammanma mustapha, haka kawai takejin wani Abu agame dashi me kamar tausayi,Wanda batasan dalilin hakanba. Mommy ce tadawo falon itama. Daga baya kuma suhailat tashigo, se satar kallon mustapha takeyi, shikuma daga gaisuwar daya amsa mata,bekara mata maganaba, cigaba da hirarsu sukayi da aunty. Adakina mukayi sallah,da muka idarma hira Aliya tacigaba damun, araina mamakinta kawai nakeyi yanda bata gajiya da magana,gaskiya Allah yahore mata baiwar surutu. Aunty ce dakanta tashigo dakin da sallama, amsa mata mukayi ta Dora da fadin, "sannu Aliya,kinzo kincikata da surutu, narasa irinki aliya kogajiya da magana bakyayi" murmushi nayi nace, "babu komai aunty hirafa mukeyi" "kai aunty, nifa bani da surutu,kawaidai banaso inga nazauna shirune" "naji nidai,kitaso kigaisa da yan'uwanki kowa ya hallara afalo." Zunbur aliya ta mike tayi bakin kofa, nikuma ina zaune ko motsawa banyiba. Juyowa aliya tayi tana kallona, "kitaso muje mana tare maryam" "A'a aliya kije kawai zanfito anjima" takuramun aliya tayi,dole na mike muka fita tare. dashi nafarayin tozali,hakan yahaddasamun wata faduwar gaba,bantaba ganinshi yana murmushi ba seyau naga yanayiwa aunty,dimples dinsa duka kumatu biyu sun lotsa abun sha'awa,akodayaushe idan na kallesa karamun kyau yakeyi,yanzumma hakance ta kasance. "Oyoyo yaya.....muryar aliya ta katsemun tunani, sekuma naji itama tayi shiru,kallonta nayi naga ta wani nutsu harta da tafiyartama ta canza. Dariya naga su yaya sadiq sunsaka mata,ashesu sunsan dawar garin, ganin mustapha ne yasata nutsuwa ba jiri,ta wani koma salihar gaske,dantasan halinsa farinsani. Shikuwa ya wani tsare gida, yana latsa waya. Akasa muka zauna,kusa da aunty muka gaishesu. Daga gaisuwar bankara cewa komaiba,na sunkuyar da kaina kasa, zuciyata na luguden bugu kamar kodayaushe idan mukayi close dashi,ga daddadan mayen kamshinsa gaba daya ya mamaye falon,se lumshe ido nakeyi ina sauke ajiyar zuciya akai_akai saboda dadin kamshinnasa .itama Aliya duk shegen surutunta shiru tayi,su yaya sadiq ne suketa hirarsu shidasu aunty,shima ogan shiru yayi yacigaba da latsa waya. Suhailat se kallonsa takeyi tamkar zata hadiyesa. Kiran sallar isha'ine ya tarwatsa taron,dama a takure nake da zaman,nina fara mikewa nashige daki,ina kallon suhailat tana bina da wani mugun kallo. Aliyama biyo bayana tayi tana fadin, "nida dodo" dariya na tsuntsire mata saboda yanda tayi maganar tamkar taga dodon gaske. "Allah kuwa maryam,bakiga nayi tsitba aitun watarana a gidannan Inata zuba,shikuma yana zaune kawai yana kallona, sedaga bayane yakirani gabansa ya murdemun baki,harkuka nayi saboda azaba,tundaga ranar idan yana guri kodogon numfashi banasonyi" murmushi nayi ina nufar toilet nace, "maganinki yayi ai" "hmmm,danshirunnan danayi bakina haryafaramun tsami yasin" "kai aliya banda sharri" "bawani sharri gaskiyace, ai gaskiya aunty suhailat zatayi kokari, danzama da yaya musty se hakuri, kodayake shine maganinta ai,tunda itama bata da kirki" alwalata nafara ina fadin,"kekadai dai". Koda muka idar da sallah bamukoma faloba, aliya tamakure akarshen gado sekashe murya take tana waya da saurinta,kamar ba itace me karadinnanba. Nidai kayana nahau kwasowa daga toilet na dinke nasasu a cikin cover. Ganin har 9 tayi nafita domin musu serving abinci,dannaga wayar aliya bata kare bace. Aikuwa Ina fita kuku,nata jera abincin akan dinning,sukuma dukansu kamar dazu suna zaune a falon. Yana gamawa mommy ta umarci kowa dayataso suci abincin. Dukansu suka hallara amma banda oga dayaketa aikin latsa waya, aunty ce ta dubeshi tace, "Muhammad yanaga baka tasoba" satar kallonsa nayi,tasowa yayi kawai becemata komaiba. Ajiyar zuciya nasauke,nafara serving dinsu,dauriya kawai nakeyi amma nikadai nasan halin da zuciyata take ciki, gawani mahaukacin bugu da takemun. Aliyace tafito daga daki, tayani serving din tayi mukarasa,aunty da yaya sadiq ne kawai suke mana sannu. Juyawa nayi zantafi,aliya dake kokarin zama tace,"A'a maryam ina zakije kuma?" "daki zankoma" "wanne irin daki kuma maryam,kizo kici abinci" cewar aunty data karbe zancen. Babu Wanda yayi ko tari acikinsu,harnadawo na zauna,se suhailat daketa kallonmu tana tabe baki nida aliya. zuba abincinnayi,jujjayashi kawai nakeyi amma nakasa ci, saboda bansababa duk senaji natakura,gashi duk dagowar dazanyi idon yaya sadiq nakaina. Aunty ce tamun magana akan naci abincin mana,dole nadaure nafara tura abincin tamkar inacin magani. Mustapha ne yafara tashi aunty namasa tsiyar haryanzu yananandai da rashin son cin abincinsa. Murmushi kawai yamata yafice,daga falon gabadaya. Daya bayan daya suka dinga tashi,nikuma atare muka tashi nida aliya. Dakina nakoma toilet nashiga nayi fitsari nadawo na kwanta,dan yanayin danakejin kaina baze misaltuba,inajin aliya ta shigo tanamun magana,wai ita anan zata kwana,shiru na mata dan ina fama da zuciyatane, har gwanin iya sata yasaceni bansan sanda ta kwantaba........ Washegari gari lahadi,yau ma basu tashi da wuriba,nima danayi sallah komawa bacci nayi,se wajen 10 natashi,aikina nayi kamar kullum danasaba tare da taimakon aliya. Yanayin dana kwana dashi yabarni,sedaifa duk abunda nakeyi tunanin mustapha ne,manne acikin raina. Yauma acikinsu nayi Karin kumallo,bisa umarnin aunty kamar jiya,amma yau naga ogan bezoba. Abunda yake bani mamaki,duk abunda aunty tace,mommy bata musu kota hana,balle sauran yayangidan. Suhailat kam na lura tafi kowa jin haushin hakan,danbanda harara babu abunda take aikamun dashi harmuka tashi. Namaci sa'a banmaci zagiba,itama naga kwana 2 duk tayi wani sukuku da ita. Munagamawa na tattara kayan,nakai kitchen mukayi wanke_wanke sannan mukayi wanka. Bayan munshirya aliya tatakuramun wai dole senazo munje garden din gidan,hijabina na zunbula muka fito. Mommy ce zaune afalo tayi bakuwa,bakuwar irin manyan matannanne, masu ji da gayu kamar mommy, taci kwalliya da gwalagwalai se tashin kamshi takeyi. tunda muka fito takafeni da ido,gaisuwar damuke matama seda mommy ta tabota sannan ta amsa,mudai ficewarmu mukayi. Maida kallonta bakuwar tayi akan mommy tana zauke ajiyar zuciya bayan su maryam su fita, gyara zama tayi tace. "Kekuwa atika ina kika samo wannan dankwaleliyar yarinya haka,gaskiya yarinyarnan tamun wlh, nidazakimun wani taimakoma dakin bani ita natafi da ita,tamun koda 2 weeks ne namaida maitata........✍️ ````kuyi hakuri da dogon jira, amma yanzu insha Allah zakudinga jina yanda ya kamata```` *BY* *zeey kumurya* *ABUNDA KA SHUKA*......... _*(shizaka girba)*_ *MALLAKIN* 👇 *ZAINAB USMAN KUMURYA* *FARIN JINI WRITERS ASSO.....*📚 ~*Free novel*~ *Bismillahirrahmanirrahim* 1️⃣6️⃣ ...........Bata fuska mommy tayi tace,"haba baraka wannan yar yarinyar nawa take, kedai wlh maitarki tacika yawa." Murmushi bakuwar da mommy takira da baraka tayi tace, "hmmm,ninasan menagani atika,irin wadannan yaran,sunfi dadin harka" tabe baki mommy tayi ta kawar da kanta gefe batace komaiba. Ganin haka yasa baraka sako wata hirar daban, amma ta kudirce aranta kotayayane seta lashi zumar maryama,dan yarinyar ta mata, daga ganin farko data mata.... Garden din gidan da tafiya, danni gurin dayakema bantaba zuwaba,banmasan dashi agidanma. Gurin ya matukar yimun kyau, da burgeni. Ga wata ni'imar iska dake kadawa ahankali,me kwantar da zuciya. Kujerun roba, aliya ta kwaso mana, domin mu zauna. Amma kafin na zaune seda nadan zagaya naga gurin, gaskiya masu kudi sun huta,iya kanshi gurinma ya isa yadaukewa mutum kewa. Zama nayi ina sauke ajiyar zuciya. "Kyan zaman gurinnan ace mutum yana tare da masoyinsa, susha soyayyarsu seyafi dadi." Cewar aliya. Murmushi namata,kawai na lumshe idona, narasa meyasa fuskar mustapha takemun gizo a acikin idona,hotonta kuma yayi tsaye kyam acikin zuciyata. Cikin dariyar keta aliya tace, "um'um,kaga su maryam manya kintafi tunanin naki masoyinkenan" numfashi na sauke tare da bude idona,ahankali ina hararar aliya nace, "banson iskanci,ni ina naga wani masoyi" dariya takara kwashewa da ita tace, "fadanma ko kyau bemikiba, gwaramadai hararar" banza na mata. Ita kuma tashiga bani labarin saurayinta, korar duk wani tunani nayi daga zuciyata mukasha hirarmu da aliya. Kiran sallar azharne yatadamu muka koma cikin gida... Suhailat ce, zaune a falon sama na part din mustapha, shima yana zaune, se latse_latsen waya yakeyi. yauda kanta ta kaimasa breakfast dinsa. tazone ta kara bashi hakuri, dan har yanzu be sakko mataba.yanuna mata dai ya hakura,amma yaki sakar mata fuska. Se satar kallonsa takeyi tana hadiyar yawu, sotake tajita kwance akan faffadan kirjinnasa tana shafa lallausar fatarsa amma ba dama, danbataga fuskar hakanba. Kwana biyunnan duk atakure take, sotakema ta fita anjima gurin kamal amma kuma tana tsoron wani sabon fushinnasa. "Pls my love am sorry again" ta fadi haka cikin marairaicewa, tamkar zata fashe da kuka. kallonta yayi, sekuma ta bashi tausayi. Sakin fuskarsa yayi daga dauren datake. Amma bece mata komaiba. Ajiyar zuciya suhailat ta sauke, ganin ya hakura duk da bece mata komaiba amma tasan ya hakura. Hira tashiga yimasa, irinta masoya tare da kalailameshi da kalaman soyayya,hardai tasamu suka shirya suka koma kamar da..... Aunty kuwa bayan sungama breakfast part din masu aiki ta wuce gurin talatu,domin itace abokiyar hirarta idan tazo gidan, amma basa wata doguwar hira da mommy. Bayan sungaisa aunty ta dubi talatu tace, "talatu,naga wata sabuwar yarinya a gidannan ita kuma daga ina, aka samota,naga batayi kala da sauran masu aikin gidannanba?" gyara zama talatu tayi,tabawa aunty labarin maryam atakaice. Cike da tausayawa aunty tace, "kai wasu mutanen son zuciyarsu yayi yawa, bandahaka aikamata yayi ace kamar wannan yarinyar tana makaranta tana karatu yanzu,amma shine aka turota aikatau,gata yarinya me hankali da nutsuwa, itama aunty atika narasa meyasa take kaunar yara kananu a aikatau, dan wani abu yataba faruwa dakai can abaya, shikenan kuma yanzuma seyakara faruwa, gata da yara samari bafata dai akeba amma bata tunanin wani Abu ya faru, musamman yanzu da zamani ya lalace ga kuma sharrin shedan" "Allah dai ya kyauta" kawai baba talatu tace, Aranta kuma cewa tayi, "danma bakisan meyake faruwa agidan bane" wata hirar suka kama daban... Lokacin damuka koma part din duka yaran gidan,suna zaune a falo,bakuwar mommynma ta tatafi,yaya musty ne kawai babu a falon se suhailat da aunty. Aliyama zama tayi sukasha hira, dan jiya bata samu damar hira dasuba,nidai daki na wuce nayi sallah ta, sedaga baya aliya tashigo itama tayi. Haka muka karasa wunin yau cikin farin ciki nida aliya. nidai zuwansu aliya gidan yamun dadi,aunty ma data dawo part dinmu, ta kirani tamun tambayoyi akan rayuwata, tare da mun nasiha. Godiya na mata sosai,seta tunamun da ummansu salima. Dan itama kullum cikin yimun nasiha takeyi. Yau kam kwata_kwata banga ogaba, kuma kosaudaya mommy bata aikeni part dinsaba,senaji dadin hakan saboda maganar rigarsa tananan daram araina. Amma kuma a wani bangaren na zuciyata,senaji ina kwadayin ganinsa.😳🤤 Washegari tun asuba dana tashi,bankoma bacciba nayi ayyukana,saboda yaya sadiq yacemun kafin yawuce office zamuje school, kamar yadda yamun alkawarin. murna da farincikin danake ciki yau baze misaltuba, waiyau nice zankoma makaranta da sunan cigaba da karatu, gaskiya yaya sadiq yataimakeni, Allah ya biyasa kawai. Kafin 8 munje makarantar office din principal mukaje, akamun tambayoyi akan karatuna. Alhamdulillah na amsa yanda yakamata, Matsalata kawai rashin iya turanci,hakan yasa yaya sadiq yace zedaukar mini me lesson yadingamun da yamma. Kudin duk da aka bukata yaya sadiq, yabiya. Atake aka bani, uniform da littafan karatu. Ss2, aka kaini, amma bazan fara zuwa yauba, se gobe idan Allah yakaimu, nace zanfara zuwa. Da murnata nashigo daki, bayan yaya sadiq ya saukeni agida ya wuce aiki, aikuwa yau yasha addu'a da godiya me tarin yawa agurina. Rukunkume, aliya nayi saboda murna. Itama tayani tayi mukayi tayin murnar tare. Seda muka gama murna sannan na dubeta nace, "Aliya gaskiya yau ina cikin farin ciki sosai, gashi makarantar ta burgeni da'alama kuma ana karatu sosai" "ai gaskiya makaranta da dadi maryam, zaman gidan haka badadi, seki dage kiyi karatu karkibawa yaya sadiq kunya" murmushi nayi cikin jindadi nace, "insha Allah aliya zanyi karatu sosai" "haka akeso Allah yataimaka." "Ameen" auntyma tatayani murna sosai, takuma mun addu'ar nasara. Hakama baaba talatu danaje nasanar mata. Mommy kam, danaje nanunamata karba tayi itama tasamun albarka, dana mata maganar aikin gidan, seta kafin natafi nayi abunda zan iya kawai, idannadawo na karasa, godiya na mata, nakoma naciga da shirye_shiryen fara zuwa school gobe........ *______________* *MUSTAPHA* *______________* Tunda yadawo daga sallar asuba shima be koma bacciba,abubuwansa ya karasa ya shirya cikin kananun kaya,wadanda suka matukar amsarsa. Yayi kyau sosai,kamalarsa da cikar zatinsa sunkara fitowa. Karfe 7/15 kamar kodayaushe yagama shirinsa tsaf, ko breakfast beyiba, yadau briefcase dinsa, seda yabiya part din mommy yaymata sallama ita da aunty, sanna yafito. Direbensa yana tsaye abakin mota yana jiransa, yana hangoshi ya taho cikin girmamawa yana gaisheshi tare da amsar briefcase din hannunsa, ya bude masa mota yashiga,shima yazagaya ya shige, yatada motar suka fice, bayan ya gaisa damasu gadin gidan. Yau kam ma'akaitar duk ma'aikatan sunzo da wuri,sabanin sati dayan dabayanan kowa kashin kansa yakeci. Cikin takunsa nakasaita ya fito daga motar,direbansa na biye dashi abaya rike da briefcase dinsa. Ma'aikatan dake kaikawo,aharabar ma'aikatar se kwasar gaisuwa sukeyi. Mikewa sakatariyarsa tayi cikin girmamawa tana kwasar gaisuwa,tare da amsar briefcase dinsa daga hannu direba takai masa cikin office dinsa. Bayan yazauna akan kujerane yatura sakatariyarsa ta kira masa P.A. tare suka dawo office din. P.A sewata karairaya takeyi da yauki, amma kobitakanta beyiba,bayan sallamar daya amsa mata. hankalinsa yana kan duba wani files dayakeyi. Tari P.A takamayi ba kakkautawa, dagowa yayi yana kallonta, tare da yimata sannu. Kanta kawai ta iya daga masa, har tarin ya lafa, sekuma yakara turniketa ba kakkautawa. Hankali atashe mustapha ya mike zaune, atunaninsa asmartace tatashi, nuni take masa da hannu ga fridge din dake office din, alamun yabata ruwa. Dasauri cikin tausayawa ya nufi fridge din, ya dakko mata ruwan yabude yakawo mata ya kafa mata abaki. Seda tasha kusan Rabin, robar sannan ta janye bakinta tana sauke ajiyar zuciya, tare da maida numfashi. Yunkurin tashi tayi, sekuma tayi luuu zata fadi kasa, dasauri mustapha yatarota jikinsa, cikin azama,yana jera mata sannu. wal_wal haske ya bayyana a office din, nadaukar hoto......✍️ _*wlh banajin dadi sosai, mura na damuna,kuyi hakuri da wannan guntun page din, gashi ina fama da matsalar ido, amma zakujini gobe insha Allah. Your du'a is needed😢🙏*_ *BY* *Zeey kumurya* *ABUNDA KA SHUKA*......... _*(shizaka girba)*_ *MALLAKIN* 👇 *ZAINAB USMAN KUMURYA* *FARIN JINI WRITERS ASSO.....*📚 ~*Free novel*~ *Bismillahirrahmanirrahim* 1️⃣7️⃣ ...........Hankalin mustapha gaba daya yana kan P.A, hakan yasa be lura da abunda ke faruwaba. bubbuga bayanta yahauyi ahankali,saboda tarin daya kara sarketa harta samu ta dawo nutsuwarta,tarin ya tsaya. Taimaka mata yayi takoma kan kujera, se lumshe ido takeyi, tanajin dama su dawwama tana kwance a kirjinsa, tana shakar daddadan kamshinsa. wani sonsa da kaunarsane yakara ninkuwa aranta, harzuciyarta ta fara kokwanto akan anya kuwa ta kyauta masa, mutumin daya tsamota daga duhun talauci, daga rana zuwa inuwa, amma yau da ita aka haka baki domin cutar dashi, anya kuwa tayi wa kanta adalci....daddadar muryarsa me cike da kasaita takatse mata tunaninta. "Dama kinsan bakida lafiya kika fito aiki,?" Ya fadi haka yana kallonta. Cikin muryarta data dan dashe tace, "lafiya kalau natashi, yanzune kawai naji tarin" "ohk, bari nakira doctor yadubaki" "no, sir, base kakira doctor ba, yamatsayamun tarin" ta fadi haka cikin sauri. Kallonta yayi nawasu sakanni, yadan tabe baki yace, "Alright, Allah yakara sauki" "Ameen, thank u so much sir" be'amsa mataba sewata takarda daya mika mata, karba tayi taduba, sannan ta mike ta masa sallama ta fice, tana tafe tana waigensa......... Kafin yamma nagama shirina tsaf na zuwan school gobe, nagoge uniform dina, najera books dina a school bag dita. Jinake kamar na zuko gobe tadawo yau saboda zumudi, aliya se dariya takemun tana tsokanata. Tunda nazo gidannan babu abunda yasani farin ciki kamar wannan, yanzu saurana islamiyya, itama inason komawa. Allah sarki, yar'uwata salima,nasan itama idan taji wannan labarin zatayi farin ciki sosai, umma ma haka. Kewarsu naji tacikamun zuciya, masoyan kwarai kenan. Kaina dake tsefe, aliya tasani wankewa, aunty ta rangadamin kitso, dama nayi kwanaki dakan atsefe. Godiya nayiwa aunty sosai bayan tagamamun. "Wow mairo, kinga yanda kitsonnan yayi kyau, gaskiya kina da kyan kitso gaki da gashi, ga tsawo da cika,gashi baki sidik, kedai kinji dadinki komai naki mekyaune." Cewar aliya tana shafa kitson. Murmushi nayi kawai mekama dana yake, kamar yadda aliya take yabona haka kullum salima ma takemun. Tabbas nikaina nasan Allah yayimun baiwa ta kyawu, amma idannatuna bani da kyawun nasaba, senaji wani kunci da daci yaziyarci zuciyata. kyau ko dukiya bashine cikar kamalar mutumba, *ASALI* shine abun tunkaho da alfahari ga kowanne dan Adam, amma ni bansan nawa asalinba, banmasan ina zannemesuba. Kwalla ce ta jikamun ido, kasa nayi da kaina ina kokarin mayar da ita dan karsu aunty sugani, Amma hakan beyiyuba seda wani hawaye ne dumi ya ziraromun. arikice aliya ta hau tambayata "lafiya maryam, meyafaru meya saki kuka, ko baki da lafiya ne?" shiru namata ina share hawayen fuskata, nikadai nasan halin danake shiga idannatuna wacece ni. Cike da tausayawa aunty take kallon maryam, daga ganin yarinyar akwai abunda ke damunta acikin zuciyarta. Ganin aliya ta matsamata da tambaya, ita kuma tayi shiru se aunty ta dubi aliya tace, "Aliya kowanne dan'adam yanada sirri nasa nakansa arayuwa, sanin abunda kedamunta ayanzu bashine abun bukataba, addu'a kawai zaki tayata da ita, akan Allah yayaye mata koma menene" gyadawa aunty kai, aliya tayi cikin gamsuwa. dafa kafadar maryam aunty tayi tace, "kiyi hakuri maryam da rayuwa, a duk yadda tazo miki, kikuma godewa Allah. kowadakika ganshi datasa irin kaddarar, kuma komai me wuce wane arayuwa, na dadine kona wuya." Nasiha sosai, aunty tayiwa maryam me kwantar da hankali dasanya nutsuwa. sosai naji dadin tunasarwar da aunty tamun, har radadin da zuciyata kemun naji ya ragu,sakar jikina nayi muka koma kamar da, muka cigaba da nishadinmu nida aliya........ *_________________* *HAJ.GWAGGO* *_________________* Tun tafiyar maryam, haryau datafi sati ba'asamomata me aikinba, ansamo mata wata yarinya dai, tana zuwa taji lissafin ayyukan gwaggo tace bazata iya jaki work ba, aiki babu hutu. gwaggo taita mata masifa tace karta iya din, aikin da'ake nemansa ido rufe danma ita tasamu za'a dauketa, taje dubunta zasuzo. Kamar kodayaushe yauma se rana tatashi daga asararren barcinta, bakinta kawai ta kuskuro ta dawo ta hada tea tahau sha, tana Karin kumallon tana mitar maryam taki zuwa, balle ta kawo mata abun duniya, dan bakin hali irinnata. Sallama taji ana kwadawa abakin kofar gidanta, banza tayi tacigaba da cin abincin ta, cigaba akayi da kwada sallamar, hakura tayi ta mike ta zari mayafinta,ta nufi kofar gidan tana fadin, "jaraba da masifar duniya, ko ubanwaye zezo mata gida wannan farar safiyar ya takura mata oho, itadai tasan ba bashin uban wanda take ci..... Tsayawa tayi cak, bayan ta karaso kofar gidannata cike da mamakin ganin Wanda batayi zaton ganinsaba. "Malam audu!" Gwaggo ta ambata cikin mamaki. "Na'am ladi, kinyi mamakin ganina ko?" "Sosaima malam audu, Ashe rai kanga rai, shigo_shigo maraba lale marhabun" gwaggo tayi gaba yana binta abaya, se kallon gidan yake, yana mamakin yanda gidan duk yabi ya mutu, ga tarin ledodi da abubuwa na rashin shara. Rabonsa da gidan tun mutuwar inna. (Malam audu, dan'uwan mijin innane, wato kakan maryam, kani yake agurinsa, inafatan kun gane) atsakar gida cikin datti gwaggo ta masa shimfidar tabarma, zama yayi adarare. Gwaggo ta dakko kujerar tsuguno ta zauna,ko tunanin kawo masa ruwa batayiba. Suka gaisa, gwaggo se washe masa baki takeyi, saboda tasan malam audu, shime alkhairi ne, ko lokacin da inna take raye shikadai yake waiwayarta ayan uwan mijinta. Gyara zama malam audu yayi yace, "ladi ina jikartawane, banga gilmawartaba kotana makarantane." Cikin kaudi inna tace, "eh, tana makaranta aidayake bata wasa da karatu akwaita da himma" "ai hakan yanada kyau, Dama zuwa nayi ince tashirya ta hada kayanta, idan zan koma gobe Lagos dim, mutafi tare ta koma hannuna da zama, tunda kinga ke macece, ita kuma yarinyarnan........ "Malam Audu, mekake nufi maryam din zaka rabani da ita?" Gwaggo ta katsesa cikin karaji, fara'ar dake fuskata gaba daya ta dauke. Batajira amsarsaba, cikin makirci ta fashe da kukan munafurci, tana fadin. "Yanzu maryam din danake gani inji dadima, ita kake kokarin rabani da ita, ko tausayina bakaji, tunda ni Allah bebani haihuwaba, ita kadai nake kalla inji dadi,shine kake kokarin rabani da ita" Tausasa murya malam audu yayi yace, "bahaka bane ladi, rayuwafa yanzu ta sauya, rikon maryam da namiji yadace ba maceba, yarinyarnan yanzu koda aurantane ya tashi a misali, bata da kowa wani namiji tsayayye daze tsaya mata, nikuma kinga kafinnazo garinnanma senadauki shekaru,shiyasa naga gwara ace tana hannuna" kafewa gwaggo tayi ita bazata bada maryamba, shikuma malam audu yasan halin gwaggo sarai, babu Allah aranta, shiyasa yakeson yadauke maryam daga hannunta, dan yarinyar tana matukar bashi tausayi. Ganin inna ta kafe se malam audu yace, "shikenan ladi tunda kinkafe bazakibada maryam ba, insha Allah zandinga kokarin wajen ganin ina ziyartarku akai_akai, yanzu bari najira tadawo daga makarantar naganta sena wuce." Cike da rashin gaskiya, inna tace, "ai ba makarantar jeka kadawo takeba, makarantar kwana takeyi" "haba ladi, kanki daya kuwa zakidau yarinya marainiyar Allah, kikaita wata makarantar kwana?" Malam audu yafadi haka cikin dan fada. "To, malam audu itafa yarinyarnan ita tace tanason makarantarnan" "to kuma dantace tanaso seki biye mata kikaita, ai ita yarinyace kuriciya nadamunta, ke kuma......"Haba malam audu, kazo se masifa kakemun, nimafa maryam dinnan jininace bazan cutar da itaba, kuma makarantar ba ita kadai tatafiba, harda kawarta tanan gidan saleemat, kuma shi alh. Adon shiya kaisu da kansa" ajiyar zuciya malam audu, yasauke domin yasan mahaifin saleemat, mutumin kirkine. "Shikenan ladi, wacce makarantarce sena biya naga maryam din" sosa kai gwaggo tahauyi cikin in'ina tace, "um..um, kajima sunan makarantar ya kwantamun, kasanni dake ba bokonnayiba barikewa nakeba" cikin takaici malam audu, yafarawa gwaggo fada, danta fara kaishi bango, ganin sakacinnata yayi yawa, banda haka kadauki yarinya kakaita makaranta,amma kace kamanta sunan makarantar. Gwaggo datasan bata da gaskiya anan, kuma tana tsoron yaganota setahau bashi hakuri, tace masa bari taje gidansu saleeman tatambayo..... Saleemat yau bataje school ba saboda ciwon marar daya addaba mata tun cikin dare, seyanzu datasha magani tasamu ya sarara mata. Fitowa tsakar gida tayi, ta kama shara, umma nahanata, amma tace ta barshi zata iya taji sauki. "Suwaiba, suwaiba!" Abunda gwaggo tashigo gidan tana fada kenan ko sallama babu. Umma dake hura wuta tafito daga kitchen din tana fadin. "Na'am gwaggo lafiya?" "Inafa lafiya suwaiba, wannan jarababben dan ka'idar yazomun,zedaga mun hankali" "wakenan gwaggo?" "Malam audu na Lagos mana...labarin abunda yafaru tsakaninsu gwaggo ta bata atakaice, ta kara da fadin, "suwaiba kitaimakeni kifadamun sunan wata makarantar kwana ta gwamnati da kika sani, infada masa. Idanyaje yagama bulayinsa ba'asametaba,aiya hakura." Cike da mamakin halin gwaggo umma take kallonta, cikin sauke numfashi tace mata, "kice masa nannan shekara take" "yawwa suwaiba nagode" gwaggo ta fadi haka, tare da juyawa ta fice." Saleemat dake tsaye rike da tsintsiya tace, "haba umma, yazaki fada mata, kenan kina goyon bayan karyar datayi?" "Bagoyon bayan karyar gwaggo nakeba, saleemat, kinsan halin gwaggo yanzu idan banfada mataba, seta hauni da tsinuwa ta tataramun jama'a, kibarta kawai kome tayi ita da Allah, insha Allahu aikatau din data tura maryam, seya zamo mata alkhairi." "Shikenan umma, Allah yasa" cike da kewa da begen kawar kirki, kuma yar'uwa, saleemat tacigaba da shararta. Itama umma, komawa kitchen tayi tacigaba da aikinta. Malam audu, bejira komaiba yashuri takalminsa bayan gwaggo ta fada masa sunan makarantar, yafice domin zuwa dubata,gwaggo tana ala raka taki a zuciyarta......... *___________________________* *ALH. MENASARA HOUSE* *____________________________* Bayan sallar magriba mommy ta aiko kirana, danaje setacemun induba kitchen ta hadawa son dinta abinci, inkaimasa,amsa mata nayi nafito. Dakina nadawo,domin neman rakiyar aliya zuciyata cike da tsoro. Amma senaga bata dakin, dakin aunty na nufa, tanacan kuwa. Dubanta nayi bayan nayi sallama sun amsa nace, "Aliya dan Allah zokirakani nakaiwa yaya mustapha abinci part dinsa" zaro ido waje aliya tayi tace, "cabdijan, rufamun asiri, inkin ganni a lahira kaini akai, aini nan dakika ganni bana kaunar abunda zehadani da yaya, kinga dadin danakeji kuwa,dabaya zama a part dinnan sosai" "haba aliyata dan Allah kizo kirakani kinga darene tsoron hanya nakeji" "mene hakane aliya, kitashi ki rakata mana" cewar aunty. "Nifa yanzu ina zuwa, zefara hararata yanacemun parrot ko turkartive." "To karya yayi, bahaka kikeba, kitashi kuje,aidama ba tsari tatafi ita kadai,part dinnasa." gwalo nayiwa aliya, ina kunshe dariya nafice, tashi tayi tana babbata rai ta biyoni abaya. Dundu tadakamun abaya, bayan munfito. Dariya na mata nashige kitchen nadakko basket din da'aka hada masa abincin. Tunkafin musauka kasama muka shirya da aliya, tafaramun surutu. Tunda muka tunkaro part din gabana yake dukan tara_tara, nikam narasa wannan bawan Allah, meyaymun nake tsoronsa haka. Aliyama tsit tayi daga hirar datakemun, dataga munhau falon sama. Ahankali na murda handle din kofar falon, dama nice agaba, dan aliyama dacewa tayi bazata shigaba a waje zata tsaya,seda naroketa sannan ta yarda zata bini har ciki. Mustapha yau bedawo dawuriba daga office, saboda meeting din dasukayi bayan antashi daga aiki. A matukar gajiye, yadawo ga kuma yunwa datake nukurkusarsa, dan yau dabinone kawai acikinsa dayaci a office, sekuma coffee dayasha. Yana dawowa wanka kawai yayi, yaje yayi sallar magriba, seyanzu kuma daya dawo, shine yakira mommy tasa akawo masa abinci. Yana zaune a kujerar dake pacing kofar shigowa falon, suhailat tana gefensa, wai tazo ganinsa yau gaba daya bata ganshiba, tayi kewarsa. Da sallama dauke a bakina nashiga, ina sauke wata boyayyiyar ajiyar zuciyata, saboda daddadan kamshinsa daya ziyarci hancina. wata irin bugawa zuciyata tayi saboda ganin suhailat a falon, tawani kura masa ido se kallonsa take. Sekace ta samu TV, shikuma yanata sana'ar tasa latsa waya. Tunda nazo gidan nasan da labarin auransu, amma bantaba ganinsu tare irin hakaba, wani Abu naji yaziyarci zuciyata. Karasawa nayi cikin falon, gaishesu nayi, shidai naga sanda ya amsamun, ta hanyar motsin da kyawawan labbansa sukai, lokacin dana saci kallonsa. ita kuwa suhailat wani banzan kallo ta bini dashi. Ajiye kayan nayi, akan dinning da Sauri, na juyo da niyyar fita, haka kawai naji banji dadin ganinsu tareba, komeyasa oho?, kumama banmanta da rikicinmu na riga dashiba.. Se'a lokacin na lura Ashe aliya bata shigo falonba, makalewa tayi a corridor. "Ke!" Naji muryar aunty suhailat, nasan dani take dan haka natsaya cak. "Ke wacce irin mahaukaciyace, kuma dabba, jaka Mara lissafi." Cikin jin zafin kalamanta na juyo ina kallonta amma bance mata komaiba. Kawai jinayi ta tsinkamun mari, batare dana mata lefin komaiba, dafe kuncina nayi, idona na cikowa da kwalla dama kwana 2, bansha wulakancintaba. Cigaba da magana tayi cikin karaji, "matsiyacin ubanki ne zezo yazuba masa abincin, dazaki fice baki zuba masaba, banza me kamada alade, har ina miki magana kinamun shiru, kinwani tsareni da wadannan idanunnaki tamkar na mujiya" muryana na rawa ina shirin fashewa da kuka, nace, "kiyi hakuri aunty suhailat, bansan yanzu zeci abincinbane, shiyasa banzuba masaba" "aidama tunda ke jakace baki da kwakwalwa, kwakwalwarki ta kifice,bazaki saniba, stupid kawai idiot,m"........Marin da mustapha yasakarmata a kuncine, yasata hadiye maganarta, batare data shiryaba ba.........✍️ _*jiya nace zanmuku posting,bansamu dama bane, mura ta addabamun sosai, seyau nasamu na muku. Nagode da addu'oinku. JUMA'AT MUBARAK*_ *BY* *zeey kumurya* *ABUNDA KA SHUKA*......... _*(shizaka girba)*_ *MALLAKIN* 👇 *ZAINAB USMAN KUMURYA* *FARIN JINI WRITERS ASSO.....*📚 ~*Free novel*~ *Bismillahirrahmanirrahim* 1️⃣8️⃣ .........Ba suhailat kadaiba, nikaina na matukar firgita da Marin daya mata. Cike da tsantsar mamaki tare da al'ajabi suhailat ta dafe kuncinta, tare da dago kanta ta zuba masa idanuwanta cikin son tabbatar da shidinne take gani agabanta, kuma haryadaga hannu ya mareta, abunda koda tana karama betaba mataba, anya kuwa ba mafarki takeba. Mustapha dake tsaye yana jifanta da wani kallo shima cikin tsantasar bacin rai, jikinsa har tsuma yakeyi, idanunnan sunkada sunyi jajur. Yariga yasan halin suhailat na rashin da'a da mutunci, amma betaba tunanin abunnata yakai hakaba. cikin tsananin bakin da takaici suhailat tace, "yanzu yaya akan wannan...... "shut up!, stupid. Get out"!!!!!! Yafadi haka cikin tsawa da karaji, tare da nuna mata kofa da hannunsa. baya naja dasauri saboda matukar tsorata jikina harya fara tsuma,tsawar tasa har cikin tsakiyar kaina najita. Juyawa tayi tafara tafiya fuuuu tamkar zata tashi sama har bangaje maryam tayi, ta fice daga falon,hawayen bakin ciki nazirara daga idonta,tasan halinsa idan taki fita,seyayimata abunda yafi mari agaban wannan banzar yarinyar. Maida kallonsa yayi ga maryam, ya galla mata wata uwar harara. Cikin kakkausar murya yacemata. "what are you waiting for?" Aikafinma yakarasa najuya nafice dagudu, zuciyata na luguden bugu. Komawa kan kujera yayi yazauna, yana maida numfashi. Kansa dake saramasa, saboda yar hayaniyarnan yadafe, zuciyarsa na masa zafi. Kokadan bayason yaga anacin zarafin dan'adam da Allah yabasa daraja, da kima,irin haka. Lumshe kyawawan idanunsa yayi tare da kwantar da kansa ajikin kujera,cikin kunar zuci...... A corridor mukayi kicibus da aliya,kankameta nayi inasakin kuka me tsuma zuciya,Wanda bansan dalilinsaba,kalaman suhailat dai,nasaba dajinsu,marinma bayau tafara munba,kawaidai hoton yanda nashigo nagansu yaki bacemun daga idona. Rungumeta aliya tayi tsam ajikinta tana dan bubbuga bayanta, cikin tsananin tausayawa, duk da batasan meyafaruba, amma tasan halin suhailat, gashi kuma taga itama ta fito a fusace tana hawaye. Kusan 2 minutes sannan tazareta daga jikinta, tare da kama hannunta suka fara tafiya batare datacemata komaiba. Mommy da aunty dasu haidar ne zaune a falo, amma banda yaya sadiq. Tamkar ancillota sukaga tafado falon dagudu tana kuka. Dasauri mommy ta mike tatareta cikin rudewa take tambayar, "lafiya,meyafaru?" Kowa na falon zuba mata ido yayi yana kallonta. Bata bata amsaba, se kankameta datayi tana sakin kukan banza. Girgizata mommy tahauyi, cikin dimuwa tana fadin, "daughter wai menene, kinsa hankalina yatashi kowani abunne yasamu my son,pls tell me what happen?" Cikin kuka suhailat tace, "mommy wlh yau sewaccan bakar yarinyar yar matsiyata tabar gidannan,tunda bagidan ubanta bane." "Wacce yarinyar kenan daughter?" Mommy tatambayi suhailat tana dagota daga jikinta. Gabadaya hankalin mommy idan yayi dubu yatashi, saboda ganin yartata na kuka, Wanda tamanta rabon dataga tana kuka irin haka, ba mommy kadaiba sukansu su haidar hankalinsu atashe yake, duk sunyo kanta suna mata tambayoyi,cikin rudewa. Aunty dai kawai tsayawa tayi tana kallon ikon Allah,duk da itama hankalinnata yadan tashi,danda farko da suhailat tashigo tadauka wani mummunan abunne yafaru. tsagaita kukan suhailat tayi cikin shan majina tace, "mommy yaya nefa yamareni akan na mari waccan banzar me aikin" zaro ido waje mommy tayi tace, "shi son dinne ya mareki dakansa, akanme to, akan wanne dalili?" hada karya da gaskiya suhailat tayi tafadawa mommy, wai maryam dince tamata rashin kunya,kuma tahada mata makirci har yayan ya mareta. Jinjina kai mommy tahauyi cikin bacin rai, tace. "Aidama talaka be iya samun guriba, tana gidan ubanki tanacin arziki shine zata miki haka, lallai kan mage yawaye." Haidar ne ya amshe zancen dacewa, "kyaleta mommy, zata shigo tasameni, zatasan akanta aka mari suhailat, sena rama mata Marin akanta" zama mommy tayi tare da dora suhailat akan cinyarta, tafara rarrashinta tare da share mata hawaye. Adaidai lokacin mukashigo falon, wata mahaukaciyar faduwar gabace ta ziyarceni, ganinsu duka a falon, zannurain da haidar sunyi tsaye cirko_cirko, fuskarsu na nuna tsantsar bacin rai. yaya faruq kuma yana zaune, yana latsa wayar sa, tamkarma besan abunda ke faruwaba. Idonane yasauka akan mommy, tsantsar bacin rai da fushi na hango afuskarta, Wanda tunda nazo gidan bantaba ganiba, wani mugun kallo take jehomun. Kasa nayi dakaina dasauri zuciyata na bugawa da sauri_sauri dama nasan alhakalin marinnan akaina ze kare. Aunty kuwa kallonsu kawai takeyi baki bude, yanda duk suka wani rude, suna tada jijiyoyin wuya akan anmari suhailat. Tasan mustapha, tasan halinsa akan dan karamin Abu baze mari suhailat ba. Cikin sanyin jiki nake taka kafata har tsakiyar falon a matukar tsorace. aliya dake gaba tsayawa tayi ganinsu ahaka, tamkar Wanda aka aiko musu sakon mutuwa. Cikin zafin rai haidar yayi kan maryam danufin yarufeta da duka. fahimtar hakan yasa aunty mikewa da sauri, ta kare maryam, tare da tsaida haidar da fadin, "haba haidar mekake shirinyine dukanta zakayi kome, aiba itace da lefiba tunda ba ita ta mari suhailat dinba" tsayawa haidar yayi, jikinsa na tsuma se huci yakeyi, yana jifan maryam da wani mugun kallo,amma bece komaiba. "Haba aunty,kibarshi mana ya hukuntata,bakiji me suhailat tace bane, aikome meyafaru itace sila" cewar zannurain. Hararsa aunty tayi tace, "kai kazo kahukuntata dinmana" nidai ina bayan aunty na boye, ina zubar da hawayen bakin ciki. Cikin fusata mommy tasauke suhailat daka kan cinyarta ta mike tsaye tana duban aunty tace, "menene hakane saudart, yazakihana yara su hukuntata, wato kinzabi bare akan yar,dan'uwanki kenanan, gaskiya ni kidenamun irin wannan,tunda kikazo gidannan sewani jajjan yarinyarnan kikeyi ajiki, sekace kekika kawota, ina ni nakawota gidannan,dan haka dani da yayana, muna dadamar yimata duk abunda mukaga dama." Masifa sosai mommy tahauyi, mamakintane yacikamun zuciya dama masifaffiyace haka, wani matsanancin tsoronta ne yashigeni, danni arayuwata banason masifa da fada. Girgiza kai kawai aunty tayi, amma batace mata komaiba, hartakai aya. Yanda ta wani hakikance tana bala'i, duk maganganu na rashin tarbiyya da da'a, dayarta ta fada,tare da muggan kalamai akan yarwani bata kwabetaba, sema goyon bayanta datayi. "Allah yabaki hakuri, aunty atika, nibanyi haka da wata manufaba,banyi kuma danna bata miki raiba" aunty tafadi haka, tare da kama hannuna, tajani zuwa dakinta. Aliya dakebin kowa da kallo, tamkar TV tasauke numfashi tare da juyawa tabi bayan uwarta. Da harara suhailat ta bisu duka, cikin jin takaicin hana dukan maryam da aunty tayi tace, "yanzu mommy kina kallo ta janyeta,amma bazaki hanaba, nidai gaskiya mommy yarinyarnan tabar gidannan kawai, hakanne zesa hankalina ya kwanta,danni gaskiya nafara tunanin mayyace" cikin rarrashi mommy tace, "kiyi hakuri daughter, nikadai nasan matakin dazan dauka akanta, ai saudat din zata bar gidan ba dawwama zatayiba, seta gwammace kida da karatu," lallaba yayanta mommy tahauyi, musammanma suhailat da haydar, harta samu suka sakko, takuma cewa suhailat ta kwantar da hankalinta zataje ta samu mustapha har part dinnasa da kanta,ta masa magana,takuma basa hakurin fushin dayayi da ita. Adakin aunty kuwa, maryam sekuka takeyi ita setabar gidan, saboda ta matukar tsorata dasu mommy, tasan daba aunty yau, kashinta ya gama bushewa, gashi shima yaya sadiq bayanan, dama shikadaine me kaunarta agidan. Aunty ce, tahau lallacinta tare da lallabata akan ta kwantar da hankalinta babu abunda zasu mata, masifar iya yauce kawai daga yanzu angama. Aliya tambayar aunty tahauyi wai meyafaru?" Dubanta aunty tayi tace, "bansaniba sarkin son zance, naga ai tare kuka je, komai agabanki yafaru" shiru aliya tayi, dantasan idan tacewa aunty batashiga ba fada zata mata. Ajiyar zuciya kawai nake saukewa, saboda kukan danaci. Kaina nakan cinyar aunty, itakuma tana shafa kaina cikin tausayawa. Kiran sallar, isha'i ne yatadamu, aunty tashige toilet din dake dakinta, nikuma nida aliya muka fice zuwa dakina. Suna zaune a falon dukansu har yanzu, sunkuyar da kaina kasa nayi banyarda nahada ido da kowannensuba. Suhailat kuwa bin maryam take da wani mugun kallo, cikin tsana, tanajin wata matsananciyar tsanar maryam nakara mamaye zuciyarta. Nidai banmasan tanayiba, daki muka shige. Muna alwala ina bawa aliya labarin abunda yafaru apart din yaya, saboda addabamun din datayi da tambaya, tun shigowarmu dakin...... Tunda yazauna bayan fitarsu ko motsawa beyiba, ko abincinma be kallaba, duk da yunwar dake nukurkusarsa. kiran sallar isha'inne shima ya mikar dashi, dakinshi ya shiga yadauro alwala yafito yanufi masallacin dake manne da gidannasu. Ana idar da sallah, yataso ko gaisawar dayasabayi da mutane yau betsayaba, saboda ciwon dakansa kemasa,burinsa kawai yaje ya kwanta ya huta. A palonsa na sama yatarar da mommy, hakimce akan kujera, cikin mamaki yake kallonta. Fadada fara'a mommy tayi akan fuskarta, cikin tausasa lafazi,da nuna tsantsar kulawa tace, "welcome my son" tamkar ba itace, tagama zuba masifa dazuba. sakin fuskarsa yayi daga tsuken datake, yazauna agefen mommy yana sauke numfashi tare da daga mata kai alamar amsawa. Shafa fuskarsa mommy tayi cikin tsantsar kulawa tace, "meyafarune son naganka cikin damuwa" kallon mommy yayi bece mata komaiba, yasan suhailat tasanar da ita komai,shiyasama tazo part dinnasa. "Nothing mom" yafada cikin sanyin murya, yana lumshe idonsa. Matsawa jikinsa mommy tayi, ta kwanto dashi jikinta,cikin so da kauna. Ahankali takai hannunta tana shafa bayansa,tasan halinsa idan ransa yabaci befiyason doguwar maganaba. Ajiyar zuciya yahau saukewa,yayi luf ajikin mommy,yanajin kaunar mahaifiyarsa harcikin ransa. Yanason mommy fiye da kowa a duniyarnan. "Son meyasa ka mari daughter akan waccan yarinyar kuma agabanta.?" Mommy tajeho masa wannan tambayar. Taune lips dinsa nakasa yayi, sannan yace, "mom, suhailat bataji, yarinyarnan babu abunda tamata amma tahau zaginta,da marinta. tare da siffantata da dabbobi, dan'adam da Allah yayishi da daraja,da kima, amma tadinga kamantata da dabbobi,shine abunda yafi komai konamun rai mom, banmasan sanda natashi na maretanba." cikin bacin rai yayi maganar. Shafa kwantacciyar sumar kansa mommy tahauyi tace, "kasan suhailat fa yarinyace, sekana hakuri da ita, kuma zanjamata kunne akan takiyayi hakan anan gaba, naga ranka ya baci, kasan banason abunda zebata maka rai kokadan, ayi mana hakuri nasan munyi lefi." Mommy ta karasa zancen tana sakin murmushi. Kaikawai yagyada mata, ya lumshe idonsa tare da gyara kwanciyarsa ajikin mommy. Kallon dinning mommy tayi, taga babu alamun antaba abincin dake kan dinning din. cikin dan kaduwa tace, "yasalam, my son, haryanzu bakaci abincinnanba, haba son dan Allah kadena zama da yunwarnan seta maka illa,pls son kadinga kokarin cin abinci akan lokaci" kama hannayenta yayi cikin tsananin kaunarta, yana murmushi yace, "insha Allah mom" murmushi itama mom tamasa, tare masa kiss agoshinsa. Rabashi tayi daga jikinta, ta mike. Dakanta ta shiga kitchen dinsa ta dakko plate da serving spoon, ta zuba masa abincin ta kawo masa hargabansa takuma bashi abaki. Mommy na matukar sonsa fiye da tunanin me tunani, Wanda shikansa yana mamakin hakan, musamman dayakasance bashi kadai tahaifaba, bata boye sonsa ko'agaban kowaye. shikadaine yake taba mata suhailat dinta yazauna lafiya, amma da wanine ya mari suhailat yau, dabataza kyaleshiba koda kuwa acikin sauran yayantane. Seda tatabbatar dayaci yakoshi sannan tabarsa, ta masa sallama tatafi. Dakinsa yashige ya kwanta akan makeken royal bed dinsa, haryanzu yanajin zafi da haushin abunda suhailat tayi, amma taci darajar mom dinsa, daseya kara hukuntata. Yanajin karar shigowar sakonni, amma yayi banza da wayar yasan baze wuce suhailat dinbace....... Tunda muka idar da sallah aliya taketa mita da masifa,akan abunda yafaru, nidai shiru namata na kwanta, saboda matsanancin ciwon dakaina yakemun. Seda aka kirata awayane nasamu sa'idar mitartata. Dukda matsanancin ciwon dakaina yakemun haka na yunkura, nafito falo saboda ganin 9 harta gota, nasan ni suke jira inyi serving nasu. Ilai kuwa, dukansu suna zaune a kan dinning din harda yaya sadiq. Kuramun ido yayi yana kallona, amma becemun komaiba,harna karasa garesu, inadan jin tsoro ganin babu aunty a falon, karnaje sumin wani abun dadintama da yaya sadiq. Amma senaga babu yakoda kalleni, ajiyar zuciya nasauke. Cikin sanyin jiki nafara serving dinnasu, inayi ina taune lips dina saboda azabar ciwon kai. Takan yaya faruq nafara, inakan yaya sadiq,aunty tafito. Kallon maryam kawai aunty tayi, tagane batajin dadi, dama tasan kukan datasha seya samata ciwon kai. "Maryam, kibarshi kikoma daki kikwanta, aliya tazo ta karasa,tunda naga bakyajin dadi." cewar aunty, bayan taja kujera tazauna agefen mommy. Dama hutunnakeda bukata, dan harwani jiri_jiri nakeji. Kai nagyadawa aunty kawai najuya, aliyanma harta fito, sannu tamun takarasa dinning din,nikuma nashige daki. Ajiyar zuciya sadiq yasauke, bayan maryam tabar falon yadubi aunty yace, "aunty meke damuntane wai, nagama idanunta kamar kuka tayi" "ciwon kai" aunty tabashi amsa atakaice. Aliya ta bude baki zatayi magana aunty ta harareta, dauke kanta tayi tafara rattabowa yaya sadiq bayanin abunda yafaru, duk hararar da aunty take aika mata kuwa, seda takai aya, ta tsaya. Suhailat ma cike da jin haushinta take harararta, itafa shiyasa batason yarinyarnan shegen surutu gareta da shishshigi. Jinjina kai kawai sadiq yake cikin takaicin halin mahaifiyarsa da yan'uwansa. Shiyasa tunda yashigo yaga fuskokinsu babu walwala, kamar ko yaushe. Hakadai sukayi dinner yau kowa zuciyarsa babudadi. Ina kwance bacci yaki daukata,aunty tashigo dakin hannunta dauke da plate da ruwa. Ajiyewa tayi tahau tashina atunaninta bacci nakeyi. Tashi zaune nayi, tace nasakko naci abinci nasha magani, senafi jin dadin baccin. Banmata musuba na sakkowa naci abincin kadan, aunty taitai nakara nace mata nakoshi, maganin tabani nasha nakoma na kwanta, itakuma tafice tanamun addu'ar samun sauki. Har bacci yafara daukata Aliya tashigo dakin, wayarta tasamu a kunnena wai yaya sadiq zemun magana. Karba nayi na rike, sallamar dayamun na amsa. Cikin murayata dako fita batayi saboda baccin danakeji. Sannu yamun, yakuma bani hakuri akan abunda yafaru, nuna masa nayi babu komai, mukayi sallama nabawa aliya wayarta, nagyara kwanciyata,nakoma baccina.........✍️ *BY* *zeey kumurya* *ABUNDA KA SHUKA*......... _*(shizaka girba)*_ *MALLAKIN* 👇 *ZAINAB USMAN KUMURYA* *FARIN JINI WRITERS ASSO.....*📚 ~*Free novel*~ *Bismillahirrahmanirrahim* 1️⃣9️⃣ ..........Da matukar bakin ciki suhailat tayi daren yau, gashi ita babbar damuwarta fushin mustapha, idanunta kawai hasko mata sanda abunda yafaru sukeyi,yanda taga ransa ya matukar baci, ita bataga wani abun bacin rai acikin abunda tayiwa maryam ba, kuma koma metayi mata aiduk akansane. Juyi tayi akan makeken gadonta datake kwance, kusan 12 nadare Amma babu bacci Sam a idonta, tun dazu take kiran wayarasa taki shiga,gashi texts take tura masa naban hakuri tare da kalaman soyayya, amma shiru babu reply. Tafin hannunta takai ta shafi kuncinta, haryanxu tanajin wani dimmm akunnenta na Marin datasha. Mikewa zaune tayi saboda wani kunci dayaziyarci zuciyarta. "Wai yanzu akan wannan kucakar yarinyar ya mareni" ta fadi haka a fili cikin tsananin takaici, kwafa tayi aranta tana kissima irin muguntar dazatayiwa maryam kala kala a gidannan. Kiran wayarta da'akayine ya katse mata tunanin ta, koda bata dubaba tasan kowaye, kamal ne. Banza tayi da wayar, shikuma yayi ta nacin kira, tsaki taja a fili. Sannan ta tashi ta dakko wayar, tayi picking, suka fara hirarsu wadda rabi duk batsace,wayartasu da kamal dinnema tadan rage mata damuwa...... Abangaren mustapha kuwa besan sanda bacci yayi awongaba dashiba. Wajen 1 na dare, yafarka a matukar firgice bakinsa dauke da addu'a saboda wani mugun mafarki dayayi,wanda yakasa fahimtar me mafarkin yake nufi. Gaba daya yahada wata uwar zufa, duk da fankar dake kadawa a dakin, danya kashe a.c tun kafin yakwanta. Sosai mafarkin ya firgitashi amma yakasa tuno komai acikin mafarkin. Ajiyar zuciya yake saukewa akai_akai, abunda kwakwalwarsa ta iya tuno masa shine yaga wata yarinya a mafarkin, da wasu mata da wani namiji, kuma duk kamar yasansu a mafarkin,amma yakasa tunosu azahiri. Korar tunanin mafarkin yayi daga ransa, dan mafarki ba gaskiya bane. Mikewa yayi cikin sanyin jiki ya nufi toilet yadauro alwala,yadawo yafara jero nafilfili kamar yadda yasaba a kowanne daren Allah........ Abangaren sadiq kuwa, tausayin maryam gabadaya yacika masa zuciya, baya kaunar halin mahaifiyarsa dana yan'uwansa kokadan,dandai babu yanda zeyine. Da tunanin maryam ya kwana aransa cikin wani irin bakon yanayi me wuyar fassaruwa agareshi........ *WASHEGARI* Mustapha kamar yadda yasaba, kullum bayan yafito daga masallaci ya nufi part din mommy, dakin mommy yafara shiga suka gaisa sannan ya nufi dakin aunty. Aunty na zaune akan darduma tana lazimi yashigo dakin, zama yayi agefenta. Yana fadin, "asamu a addu'a aunty" murmushi aunty tayi tace, "insha Allah, addu'a ai kullum cikin ymuku ita mukeyi." Cike da kaunar kanwar mahaifinnasa yagaisheta. Amsawa aunty tayi tare da gyara zama tace, "dama tun jiya inason magana dakai, sekuma bamu haduba" maida hankalinsa yayi duka ga auntyn amma bece komaiba. Cigaba da magana aunty tayi. "Mustapha meyasa jiya ka mari suhailat, nayi mamaki gaskiya dan nasan hakan ba halinka bane?" "Aunty nikaina bansan sanda na maretanba,Abunda tayine ya matukar konamun rai shiyasa" yafadi ahaka muryasa adakile. "Shikenan mustapha amma adai, kiyaye gaba, dan wataran ma'aurata zaku zama kaida ita, jirama nake yaya yadawo kasarnan, ayi maganar aurenku, shekarunku sunja,karatun ta karasa adakinta. Danyanzu ko su haidar da zannurain sun isa aure, balle kuma kai." Kwantar da kansa yayi ajikin aunty yace, "duk yanda kikace haka za'ayi little mom, Allah yatabbatar mana da alkhairinsa." Shafa kansa aunty tayi, tace "ameen" cike da tsananin kaunarsa da tausayinsa, tarasa meyasa takejin tausayinsa aranta, kuma tun yana karami takejin hakan akansa, alhalin babu abunda yanema yarasa arayuwarsa. shiyasa duk miskilancinsa seda tajawoshi jikinta sosai, haryayi matukar sabo da ita, yake kuma sanar mata da duk wata matsalarsa. Hira suka dan taba akan kasuwanci da kuma halin rayuwa, duk da karfin hirar aunty cekeyi. Sannan yatafi.... Duk murna da dokin danakeyi na zuwa school, duk babu dana tashi saboda da bacin rai na kwanta. Ciwon kan dake damuna yasauka sosai, yanayin danake jima kafin na kwanta duk babu, amma zuciyata ce sam babu dadi. Ina idar da sallar asuba, nafara ayyukana, sharar falo nayi da mopping sekuma wanke_wanken kayan da'aci abinci dadaddare. Inagama wanke_wanken nashirya komai tsaf, tare da shareshi shima nayi mopping. Ina kokarin fita daga kitchen din, kuku yashigo, sama_sama muka gaisa dashi bakamar kullumba dayake tsayar dani da surutunsa, duk da hausarsa ko fita batayi,amma munashan hira dashi. harna koma dakina aliya baccintatake, dama tana idar da sallah ta koma. Toilet na nufa na wanke, sannan nayi wanka. Uniform din makarantar na dakko da nufin shiryawa, riga da wadone rigar har gwiwa, se wani karamin hijabi iya kafada. Tsayawa kawai nayi ina kallon kayan, ina tunanin tayanda zansakasu, harna iya fita dasu ahaka. Ganin lokaci yana kuremunne yasa kawai na daure nasaka, sunkoyi dass ajikina, tsayawa nayi agaban mudubi ina karewa kaina kallo, kayan sunyimun kyau sosai,sedai rigarce ta kamani daga kirjina. Dankwali na daura,nadakko hijabin danayi sallah nafito falo. Kuku begama breakfast ba, gashi har 7/30 tayi. Babuma Wanda yafito acikin gidan. Dakin aunty nanufa, knocking nayi tabani izinin shiga. Da sallama nashiga. Zama nayi akan carpet din dake gaban gadon, ita kuma aunty tana kan dadduma da'alama karatun alkur'ani takeyi, saboda kur'anin dana gani agabanta. Gaisheta nayi ta amsamun cikin fara'arta. Bayan mungama gaisawarne, cikin ladabi nadubeta nace, "Aunty dama nashiryane zamu tafi makarantar, kuma naga haryanzu ko abincin kuku begama hadawa balle nayi serving dinku, kuma yaya sadiq 7/40 yacemun zamu tafi." "Badamuwa maryam, kije kutafi schl din, tunda kinga yau zaki fara zuwa karki fara da latti, aliya tayi serving dinnamu, amma kafin ki tafi kishiga kisanar da aunty atika" "tom aunty nagode senadawo" "yawwa maryam, Allah yakiyaye yabada sa'a, kikula sosai kinji, banda kawaye barkatai,kiyi karatunki kawai" "insha Allah aunty zankiyaye" nafadi haka ina mikewa, tsaidani aunty tayi, hang bag dinta naga ta dakko, kudi ta dakko naira 500 ta mikomun. Girgiza kainayi nace, "kibarshi kawai aunty" batarai aunty tayi tace, "bansan musu maryam, bakici komaiba zaki tafi sannan kuma kiki karbar kudi, kiduba inda ake ajiye kayan snacks a kitchen kidauka kihada da yoghurt wannan kudin kuma kyayi break dashi" amsa nayi namata godiya nafice, cike da kaunarta dakuma yabon halinta. Cikin tsoro nanufi dakin mommy danbansan da fuskar dazata tarbeniba, amma abun mamaki senaganta kamar babu abunda yafaru, takarbeni kamar kullum fuskarta babu yabo ba fallasa, dana fada mata abunda kefaruwama tace muje bakomai, Allah yabada sa'a. Kitchen nashiga na dakko cake da yoghurt kamar yadda aunty ta umarceni, dakina na koma domin dakko school bag dina. Aliya natar tana waya. Murmushi kawai na mata, cike da mamakinta ko gajiya batayi da waya. cire hijabin jikina nayi, na dakko karamun na makarantar nasaka. "Wow maryam, wlh bakiga yadda uniform dinnan ya miki kyauaba" "aike dama komai kyau yake mun" nabata amsa ina rataya jakata. "Allah dagaske nake maryam, yamiki bala'in kyau, karkijefa ki tadawa malaman makarantar hankali" hararta nayi na dauki hijab din dana cire nakara mayarwa, dangaskiya bazan iya fita hakaba, inajin kunya. Idannaje bakin get nacire naninke nasa ajaka. "Yaya sadiq nefa yakirani yanzu shinema yatasheni daga bacci, yace yana waje yana kiranki,tun dazu." "Ohk,bari nakarasa, sena dawo, bye" "Allah yakiyaye I will miss u wlh" cewar aliya tana marairaicewa. murmushi namata nace, "nima zanyi kewarki sosai da surutunki" dariya mukasa dukanmu namata sallama, na tafi. A bakin part dinmu, naci karo da yaya sadiq, yana kokarin shiga. Cikin mutuntawa mukagaisa, yana sanarmun dama yanzu yake shirin shiga yakirani yaji shiru. Duk da hijabin dake jikina,amma seda yaya sadiq yace kayan sunmun kyau sosai. Godiya na masa cikin jin kunya. Muna tafe muna hirarmu akan makarantar, harmuka karasa parking space. Damuka shiga motane yake kara bani hakuri, akan abunda yafaru jiya, nuna masa nayi bakomai ninama manta. Duk da abun yana raina, musammanma yanayin dana baro yaya mustapha, haka kawai tun jiyan naji badadi saboda fushin dayayi, yauma da kwadayin son ganinsa natashi, inason naganshi naga halin dayake ciki. Harmukaje makarantar tunaninshi kawai nakeyi. Seda muka fara zuwa office din principle sannan akasa wata tarakani class dinmu. Yaya sadiq ma yabani kudi,tun a mota. Duk dagewar danayi bazan karbaba, nakuma sanar masa aunty tabani, amma yabata rai yace dole sena karba. Ganin ransa ya baci sena karba namasa godiya. Bansan yazan misaltamuku yanda nakejin zuciyataba ahalin yanzu, wani irin yanayi take ciki kamar nadamuwa. Amma hakan behanani yin farin cikiba, saboda ganina a makaranta a kuma aji. Ajin yankadan natarar time din dana shiga, kuma mata da mazane a ajin, duk senaji kunya ta lullubeni danni nasaba makarantarmu matane zalla,gashi nacire hijab dina, sekarami na makarantar kawai. Sallama naiwa matan dana tarar a ajin, se bina sukeyi da kallo, duk senaji na tsargu. Watace tamun magana da fara'arta ta kuma nunamun kusa da ita, tace nazo na zauna. Godiya na mata nazauna, tambayata tayi sunana nafada mata. *MARYAM AHMAD* ita kuma tacemun sunanta, *ZAINAB ILYAS MIJINYAWA* banfi 5 minutes dazamaba, malami yashigo ajin.......... Gaskiya makarantar ana karatu sosai, gashi ajin babu yawa. Wani abunnagane wani kuma banganeba, saboda matsalar turanci daba komai nake jiba. Zee mijinyawa tana da kirki sosai, da'aka fito break duk abunda banganeba ita takaramun bayaninsa da hausa,nakuwa gane sosai. Ban fita ko'inaba cake dindanazo dashi naci, itadai zee tafita. Naji dadin makarantar sosai gaskiya, banfuskanci wata matsalaba kodaga gurin sauran yan aji. Malamaima kowa yashigo seya tambayeni sunana, tare damun welcoming. Karfe 2/15 ake tashi daga makarantar. Da'aka tashi tare muka fito da zee da wasu kawayenta, bayan tabani aron books dinta nayi copy note a gida. Kamar yadda yaya sadiq yacemun direba zezo yadaukeni, hakance ta kasance kuwa. Ta gurin number motar nagane shi, saboda duka motocin gidan anrubuta *MENASARA* .yana bakin gate yana jirana kuwa, sallama naiwa su zee nashige muka tafi gida, zuciyata cike da farincikin yau gani na koma karatu,da yardar Allah zancika burina,dana innata. Mintuna kalililan muka karasa gidan,dama makarantar babu nisa,koda kafama zan iya dawowa. A parking space nakara maida hijabina, danga masu aikin gidan sunata kaikawo, a makarantar ma dan babu yanda zanyine. Aunty da mommy da aliyane, zaune a falon sama. Da sallama nashiga. Atare duk suka amsamun suna kallona, dagudu aliya tataho ta rungume ni, aunty na mata fadan kardai ta kadani. Nima rungumeta nayi cikin murnar ganinta. Jakata ta karba, sannu da gida naiwa su aunty, aunty tamun sannu da zuwa da tambayata ya karatun, mommy kuwa sedai kallonnanta muka shige daki. Aliya kamar ta lasheni, dan murnar dawowata waidama tagaji da zaman kadaici. Kozama banba nashige toilet na watsa ruwa tare da dauro alwala nafito nayi sallah. Kafin na idar aliya harta kawomun abinci,da ruwa. Allah sarki aliya masoyiyar asali, komai nata idan tayi tana tunamun da salimat ne, itama haka take nunamun irin wannan kaunar. Ina cin abinci ina bata labarin school din. Bayan nagama cin abincin na dakko jakata, kudin da aunty da yaya sadiq suka bani nanunawa aliya, cewa tayi na ajiye watara zasumun amfani. Rabawa nayi nabata rabi, amma tacemun wlh bazata karbaba. Cikin jin haushinta na'ajiye kudin, na dakko littafaina na fara kwafar note, itama aliya wani ta dakko tana tayani. Rubutun dayawa, dan anyi nisa a term din. Har bayan magriba muna note din, sallah ce kawai ketadamu. Badon mungamaba,sedon hannunmu dasuka gaji muka bar note din haka gobe nakarasa. Tun dayamma yaya sadiq yakira aliya, wai yaji kona dawo gida. Banima wayartayi mukayi magana, ya tambayeni ya school din da kuma karatu. Nace masa komai lpy klu,sai godiyar Allah..... Suhailat yau bata dawo gidaba se daf da magriba, kuma tun 9 ta fice. Saboda tabiya ta gurin kamal sunyi badakalarsu, ahakanma daurewa tayi tadawo badon sungaji,dajunaba. Tanata yamutsa fuska tashigo gidan ita adole ta gaji. Mommy sewani lallabata takeyi ita kuma tana wani narkewa. Aunty datun yamma tafara mitar dadewar suhailat din, batayi shiruba data dawo seda tatambayeta dalilin dadewarta. Cemata tayi practical suka tsayayi. Seda tayi wanka ta shirya, da nufin zuwa part din mustapha, amma aunty tahanata zuwa. Aganin aunty hakan bedaceba,yarinya budurwa taringa zuwa part din namiji, aiko uwa daya uba daya kuke bedaceba, balle su da'akwai soyayya atsakaninsu. Ran,suhailat a matukar bace ta koma dakinta, ita tamatsu aunty ta tafi saboda tagaji da takurarta, dama ita takurane da ita, a cewar suhailat fa......✍️ _*kuyi hakuri da jina shiru, school ce ta boyeni, se'adarennan nasamu na muku, gashinan bayawa kuma ba editing🥰*_ *BY* *zeey kumurya* *ABUNDA KA SHUKA*......... _*(shizaka girba)*_ *MALLAKIN* 👇 *ZAINAB USMAN KUMURYA* *FARIN JINI WRITERS ASSO.....*📚 ~*Free novel*~ *Bismillahirrahmanirrahim* 2️⃣0️⃣ ............Zama tayi abakin gadonta cike da takaicin hanata zuwa ganin masoyinta da aunty tayi, gashi tun tana school takirashi bedagaba kuma bebiyo bayan kirannataba, datace bazata kara kiransaba itama zatayi zuciya dashi, amma takasa zuciyarta bazata iyaba. Wayarta dake hannunta ta kunna ta kara dialing number sa akaro naba adadi,daga jiya zuwa yau. Mustapha yana zaune a falonsa yana kallon news a TV, kiran waya yashigo wayarsa, dakko wayar yayi yaga suhailat ce, dafe kansa yayi, yaga missed calls dinta dayawa kuma yace zekirata amma shaf yamanta. Rejecting yayi ya kirata. Cikin zumudi suhailat tadaga wayar danda tayi tunanin rejecting yayi badon yakirataba. Wata doguwar ajiyar zuciya ta sauke jin daddadar muryarsa ta doki kunnenta da sallama. Maimakon ta amsa sallamartasa seta samasa kukan shagwaba, lumshe idonsa yayi tare da taune lips dinsa, bayason kuka kokadan arayuwarsa kona yara bayasonji balle na mace, kukan mace yana taba masa zuciya. Fesar da iska yayi daga bakinsa yace, "autar mommyyyy"! Yanda yaja sunannata seda taji wani yarrrr ajikinta, itafa ko muryarsa taji tada mata da sha'awa take, balle kuma taganta agabansa,ita kadai tasan metakeji. Cikin kukan tace, "na'am" "menene?" Yatambayeta cikin sigar rarrashi,tausayinta gabadaya yacika masa zuciya, shima ba'asonranta yake mata abubuwa kodan tsananin sonda take masa, amma suhailat dince idan baya mata haka bazatana shiga taitayintaba. Cikin shagwaba ta fara masa korafin kira da texts datayita masa,ganin ya sakko,haryana mata magana cikin sanyin rai. Rarrashinta yafarayi, tare da mata nasiha akan abunda tayi. Hakuri tabashi tace masa tadena. Cigaba ta masa da surutu cikin jin dadi, da farincikin sun shirya, shikuma sedai kawai yabita da um, ko um'um. Hakan baya damun suhailat danta riga tasaba da wannan halinnasa. Itadai burinta yacika tundadai yasakko daga fushin dayake da ita. Damashi haka yake, wani lokacin yanada saurin sauka, wani lokacin kuma seda kyar....... Falo muka fito nida aliya, yau kam tanacemun mu fita muyi hira bamusu nafito. dukansu samarin gidan da aunty da mommy suna zaune a falon, amma banda oga da suhailat,da yaya sadiq. Wani tunanine ya darsu a zuciyata, na maybe suna tare a part dinsa, wani iri naji, zuciyata babu dadi, Tambayar kaina nayi araina. "Wai ma mene ruwana acikin rayuwarsu danake damunkaina?" Musammanma shi mustapha danake yawan tunaninshi, kuma aduk lokacin dana tunashi se gaba ya fadi. Nakan alakanta hakan da matsanancin tsoronsa danakeji, danshi mutum ne me kwarjini, kuma ni a sanin dana masa masifaffene, gashi ya iya daka tsawa,me hautsina yayan cikin mutum. Lumshe idona nayi ina fasalto kyakkyawar fuskarshi acikin zuciyata, Wanda bansan yazan fasalta muku shiba azahiri. Narasa ina yagado wannan kyawun nasa, dan mommy dai da sauran yan gidan duka basu kaishi kyauba, amma nafi inatunanin a wurin mahaifinsa yagada, tunda shikadaine bantaba ganiba agidan. Wata doguwar ajiyar zuciya nasauke, aliya dake gefena suna hirarsu ta juyo ta kalleni da Sauri, ahankali naji tace, "lafiyarki kuwa maryam?" Bude idona nayi nakalleta nace, "lafiya ta kalau,me kika gani" girgizamun kai tayi alamun ba komai, ta juya sukacigaba da hirarsu. Hira sukeyi amma hankalina gabadaya baya kan hirar tasu, addu'a kawai nakeyi araina. Allah yakawo abunda zesa mommy ta aikeni part din yaya mustapha, dalilin fitowatama daga daki kenan,amma naji shiru yau bata aikeniba. Har ka kira sallar isha'i muna falon, ayanda nakeji araina jinake kamar nacewa mommy bata da aikene yau gurin yaya mustapha, wani irin azalzala zuciyata takemun nason ganinsa. Cikin sanyin jiki natashi nanufi dakina donyin sallah, adakinma seda aliya tatambayeni wai meke damuna,nace mata babu komai domin ni kaina bansan mezance mataba, banmasan abunda ke damuna dinba. Haka nakarasa daren yau jikina duk asanyaye, gashi bansamu damar ganinnasaba. Abincima kadan natsakura naci, yaya sadiq ma harkiran aliya yakarayi awaya ta bani, yahau tambayata wai meke damuna yaganni kamar mara lafiya, amasar dai dayace bakomai, gajiyar school ce kawai, nace masa. yanzu yaya sadiq yaragemun magana acikin yan'uwansa,tsakanina dashi gaisuwace kawai, tunda aliya tazo gidan sedai yakirata awaya Muyi magana. Bayan mungama dinner na kwashi kayan da'aka bata na wanke. Aliya yau bata tayaniba tana dakin aunty time din danayima. Ina gamawa nadawo dakina nashiga toilet fitsari nayi tare da dauro alwala nadawo nahaye gadona nakwanta, bajimawa bacci yadaukeni dan gaskiya banajin dadin jikina, kuma jikinnawa da yar gajiya. Wajen 11 saura aliya tadawo dakin, kallon maryam tayi cikin jimami da tausayinta, danyanda ta lura da maryam irin mutanennanne da damuwa take wahalar dasu sosai. Gobe zasu koma k.d shine dalilinma dayasa ta dade adakin aunty har wannan lokacin suna hada kayansu, dukda kayannasu bawani yawane dasuba, tsabaracema meyawa saboda kowa nagidan yakawowa aunty tasa shine suka tsaya shirya kayan,dama da niyyar kwana uku sukazo, aunty tazone kawai taga yanda suke. Aliya jitayi kamar tafasa bin aunty gobe, setaji batason barin maryam ita kadai,jikinta gabadaya yayi la'asar. Cikin sanyin jiki ta tattara duk wani nata dake dakin maryam ta hade guri guda, a hang bag dinta. Dama su agogontane da abun hannunta. Kashemusu light din dakin tayi ta kwanta agefen maryam,zuciyarta babu dadi....... Washegari tare mukayi aiki da aliya yau itama bata koma bacciba. Dayake mu biyune kafin 7 mungama komai, wanka nayi nashirya cikin uniform dina sabo, dan set biyu aka bani a makarantar. Kamar jiya yauma hijabi nadora akai nanufi dakin aunty,danna gaisheta. Bayan mungaisa aunty tace, "toh maryam sedai ince Allah yakaddara saduwarmu,dan yau zamu tafi, kafin kidawo daga school ma muntafi" cikin matsananciyar faduwar gaba nake kallon aunty, zuciyata na bugawa, yanxu su auntyn danake kallo nakejin dadi agidannan suma tafiya zasuyi. Cikin rawar murya nace, "aunty tun yau zaku tafi naga baku dade da zuwaba?" Murmushi aunty tayi tace, "Abbansu aliya yanata kirana indawo, ga kuma makarantar aliya,nima banso tafiyarba naso jiran dawowar yaya, danyacemun yakusa dawowa amma tafiyar tazamarmun dolene" shiru nayi bance komaiba. Janyoni aunty tayi ta kwantar da kaina akan kafadarta, cikin lallami ta fara mun magana. "Karki damu kanki maryam, nanbada jimawaba zakiga nadawo, bana jimawa nake dawowa, kinji maryam tah" gyada mata kai nayi ina kokarin maida kwallar data cikamun idona nace, "shikenan aunty kugaida gida, Allah yakiyaye hanya, amma zanyi kewarku sosai" shafa fuskata aunty tayi tace, "ameen maryama muma zamuyi kewarki, kedai kawai abunda nakeso dake kidage da karatunki kikuma kula da kanki, kikara hakuri akan Wanda kikeyi agidannan, duk abunda kike bukata kuma kitambayi sadiq kinji" "tom aunty nagode sosai da kulawarki agareni." Bakomai maryam, Allah yamiki albarka, kije kikarasa shirinki karkiyi latti, kafin kitafi kibiyo tanan zan baki sako, karki bari aliya ta tsaidaki da surutunta dannasan halinta,sarai.,seta makarantar dake" Murmushi nayi na mike nafice, zuciyata babu dadi kokadan. Aliya nazaune a bakin hado ta rafka tagumi nashigo dakin da sallama ciki_ciki, tsayawa nayi kawai ina kallonta daga ganinta itama jikinta yayi week. Ahankali tadago da kanta ta zubamun ido, karasawa nayi bakin gadon nazauna agefenta dafa kafardarta nayi nace, "aliya Ashe yau zakutafi shine baki sanarmunba, seyanzu aunty take sanarmun" numfashi aliya tasauke tace, "kiyi hakuri maryam,aunty ce tace karna fada miki seyau,dantasan seki tashi hankalinki kikasa bacci." "Yanxu idan kuka tafi seyaushe?" Natambayeta idona nacikowa da kwalla, kwanaki ukunnan damukayi tare dasu jinta nake tamkar mundau wasu shekaru tare, yanzu idan suka tafi shikenan rayuwar kuncin danake agidannan zata dawo,tunda sukazo ko kallon banza babu Wanda yamun agidan se ranar da abunnan yafaru saboda ganin idon aunty. Na lura duka yaran gidan suna Shakkar aunty. Banmasan hawaye yafara zuba daga idonaba seda naji hannun aliya tana sharemun, itama idonta duk yayi kwal_kwal kamar zatayi kukan. gabadaya tausayin maryam yacika mata zuciya,tasan halin yan'uwanta sarai ba kirkine dasuba,tasan maryam zaman hakuri kawai takeyi agidannan. Rungumeta tayi tsam ajikinta ganin taki dena kukan, cikin rarrashi take bubbuga bayanta. Magana tafara mata cikin rarrashi da lallami akan tayi hakuri, insha Allahu dazarar anmusu hutun school zatazonan tayi hutunnata gabadaya tare da ita. Dakyar aliya tasamu maryam ta hakura tadena kukan. Toilet nashiga nakara wanke fuskata,sannan nadawo nakarasa shirina, aliya nata bani labaran bandariya duk dan nasaki jikina. Nikuma se nuku_nuku nakeyi naki tafiya, harseda yaya sadiq yakira wayar aliya akan yana waje yana jirana. Dakin mommy naje, namata sallama,yau dakantama tace intafi karnayi latti base nayi serving dinsu ba. Kuku harya gama hada breakfast yau da wuri, diddibarmun aliya tayi na tafi dashi, dakin aunty na koma kamar yadda tace. Wani littafin addu'oi ta dakko ta bani har guda biyu, tace nadaure nadinga karantawa arana koda saudayane. Godiya na kara mata sosai, itakuma tanata kwararamun addu'oi. Har bakin motar da yaya sadiq yake ciki aliya ta rakani. Abincin dake hannunta ta mikomun tare da fadin, "to maryam segani nabiyu" karba nayi cikin sanyin jiki nace, "nagode aliya,kugaida gida Allah yakiyaye hanya" "ameen" cewar aliya tana maida hankalinta akan yaya sadiq dake zaune acikin mota amma ya bude murfin, kafafunsama suna waje. yatsaya kawai yana kallonmu da sauraronmu. "Yaya sadiq ga maryam nan, dan Allah kakularmun da ita amana karka bari ko kuda yatabata, balle kuma wani Abu yabata mata rai." Murmushi mukayi nidashi saboda yanda aliya take maganar, yace, "baki da damuwa yarkanwata indai maryam ce zankula miki da ita fiye da yanda kike tunani." "Yawwa yayana, maryam bye bye, semunyi waya, insha Allah zandinga kiran wayar yaya sadiq muna gaisawa, I will miss u over" da kai kawai nabata amsa, saboda ina bude baki tsaf zan iya saka kuka, daurewa kawai nakeyi. Zagayawa nayi na shige cikin motar, daga mun hannu aliya tayi ta juya tatafi,ina binta da kallo. Tada motar danaji yaya sadiq yayi yasani dauke ido daga kanta,ina sauke ajiyar zuciya. Kallona yayi dasauri sekuma yadauke kansa yayi yaja motar muka tafi. Hawayen dake makale a idonane yasamu damar zirarowa, nikuma haka kaddarata take arayuwa, duk Wanda nakejin dadin zama dashi, sena rabu dashi..... "Yasalam, maryam! Kuka kuma, kiyi hakuri pls nasan kunyi sabo da aliya Wanda dole zakiji zafin rabuwarku, amma kukan bashine mafitaba, kidena kinji" murya yaya sadiq ta katsemun tunani. Daga masa kainayi ina share hawayena. "Yawwa kokefa, duk sanda kikeson ganin aliya na miki alkawari zankaiki, ammafa idan kindena kuka" dasauri nace, "nadena yaya sadiq Allah" murmushi yayi yace toh shikenan kyakkyawa" shiru nayi bance masa komaiba, shima yaya sadiq shirun yayi har muka karasa school din. Yau kam sukuku nayi a makarantar har zee seda tatambayeni ko bani da lafiya, nace mata lpy ta klu. Koda aka tashi nadawo gida, duk senaji gidan babu dadi, saboda su aliya suntafi kamar yadda aunty tace, zama nayi bayan nayi sallah na rafka tagumi ina tunanin rayuwata, ganin tunanin babu abunda ze karamun se damuna sena tashi na dakko littafin addu'ar da aunty ta bani, na karanta, cikin ikon Allah se zuciyata tayi sanyi,damuwata duk ta ragu. Haka rayuwa take Allah baya barin wani Dan wani yaji dadi. Bayan na gama karantawa na tashi naci gaba da ayyukana......... *BAYAN KWANA UKU* Rayuwata ta koma kamar tada agidan alh. Menasara,rayuwar kadaici da kunci da tsangwama agurin yaran gidan, a gurin yaya sadiq kawai nake samun sauki, bayan tafiyar su aliya munyi waya da ita har sau biyu, a wayar yaya sadiq, aunty ma haka. Harda yayantama mungaisa, yacemun aliya tanata damunsa da zancena. Dadin abunma ina zuwa makaranta, tanadaukemun kewa sosai, nasaba da zee sosai da sauran kawayenta, su salma da humaira. Kullum yaya sadiq ne yake kaini, driver kuma ya dakkoni. Yanzuma bana gamuwa da yaran gidan sosai, dan dasafe kafinma su fito natafi makaranta da rana idannadawo basanan sai dare muke haduwa. Abangaren suhailat kuma, cin karanta take babu babbaka tunda aunty tatafi, kullum setaje gurin kamal sun sheke ayarsu, kuma ta dawo zuwa part din mustapha, danma yanzu kotaje bawani kulata yakeyi sosaiba sedai tagaji da zama da tatafi, babban abun dayake kara tada hankalinta yanzu ko hannunsa baya bari tataba. Ko zuwa tayi da niyyar tabashi kamar da, bata iyawa saboda babu fuska. Shikuma mustapha ayan kwanakinnan aiki yakeyi tukuru, gashi a week dinnan zeyi promotion na ma'aikata a companynsu dole ne ya nutsu yamaida hankali danganin yayi adalci ya'ajiye kowa a inda yadace dashi. Yanzu kam yagane babban kuskuren daya tafka arayuwarsa na barin suhailat tana hugging dinshi da abubuwan dabasu daceba,ada baya daukar hakan amatsayin lefi saboda ganin suhailat cousin dinsace. Zuwannan da aunty tayi shiya kara tunatar dashi abunda yamanta, nasiha aunty tamasa sosai akan illar hakan,yasan aunty bata taba ganinsu a hakanba, kawaidai ta masa wa'azinne akan tunatarwa irinta da da uwa. shine dalilin dayasa yayiwa kansa alkawari idan ba aure sukayiba insha Allahu hakan bazata kara faruwa atsakaninsuba,sedai bisa kuskure. Mommy amatsayinta na uwarsu yakamata ace ita tafara nuna musu illar hakan, tunda sometimes agabanta suhailat din take hugging dinsa. Amma sedai tanuna jindadin hakan. Yana matukar son mommynsa amma bayason wasu halayennata, da first halinta dabayaso shine kyamar talaka, tana nuna musu takala bakowa bane, tana nuna musu talaka tamkar ba cikakken mutum bane. Alhalin Allah dakansa yafada shiyake bada wadata da arziki ga wanda yaso. Kuma badon yafisansa yabasaba, sedon ganin damarsa. kuma aduk sanda yaso ze iya kwacewa. To meyasa ita mommy bata tunanin wata rana suma zasu iya rasa tasu dukiyar, kokuma talakan datake rainawa yamusu ranar wani abun, domin kowa da irin baiwar da Allah yamasa. Sekuma hali na biyu na mahaifiyarsa dabayaso,macece ita me mugun son kanta da yayanta, kome yayanta zasuyi badaidaiba bazata musu maganaba, balle ta kwabesu. Komai sukayi nuna musu take daidaine, gashu kuma batadamu da musu wata kyakyakkyawar tarbiyyaba, ilimin addini kuwa duk basu dashi yanda yakamata, shima dan ya taba zama agurin auntyne lokacin su mommy dukansu suna america, shikadaine a naija, shiyasa yasamu ilimin addine sosai. Sekuma abu na uku, yanda mommy take juya mahaifinsu sekace wani danta, se'abunda tace yayi sannan zeyi, bayajin maganar kowa setata. Wadannan halaye na mahaifiyarsa bayasonsu kokadan, dandai babu yanda zeyine uwa, uwace tafi karfin wasa, sedai addu'a dabaya gajiyawa dayi mata akodayaushe akan Allah yaganar da ita gaskiya.....✍️ ```BA EDITING YAU🤤😔``` *By* *zeey kumurya* *ABUNDA KA SHUKA*......... _*(shizaka girba)*_ *MALLAKIN* 👇 *ZAINAB USMAN KUMURYA* *FARIN JINI WRITERS ASSO.....*📚 ~*Free novel*~ *Bismillahirrahmanirrahim* 2️⃣1️⃣ *BA EDITING YAU🤤😎* ........Yau asabar babu school hakan yasa bantashi da wuriba se wajen goma na tashi, ayyukana nayi duka, saboda yau ina gida. Amma kwanakin da suka shude bakomai nakeba nake tafiya school cikin abunda banayi harda gyaran dakin suhailat da mommy, senadawo nakeyi. Yau time din dana shiga dakinta bacci takeyi bata tashiba, ko agurin break ma banga tafitoba. Se bayan la'asar nagama aikina, saboda har wanki nayi. Ina gamawa nayi wanka nashirya cikin wata doguwar riga mara nauyi da hijabi karami irinna makannan, acikin siyayyar kayan da yaya sadiq yasiyomun jiyane. Duk wani Abu na amfanin mata seda yasiyomun jiya har kayan unders yasiyomun dasu pad, siyayya yamun sosai ta bajinta, duk a kokarinsa na ganin narage damuwa, ga wani tattali da kulawa dayake bani na musamman. nikam nikadai nasan halin danake ciki saboda rashin ganin mustapha, zuwa yanzukam nafara tunanin akwai wani Abu dayake faruka dani akansa, tunaninsa da wani abu dabansa komeneba ya yawaita araina, kullum bana iya bacci sena dauko rigarsa dake gurina nashaki kamshinsa sannan nake samun nutsuwa. Yau kwanana biyar banganshiba tun ranar da abunnan yafaru, wata mahaukaciyar kewarsa naji tacikamun zuciya. Duk wannan abun dake damun maryam akan mustapha kokadan batayi tunanin so bane, dan ita bama tasan menesodinba, anata shirmen kawai burgeta yakeyi. Bayan na idar da sallane, nadakko addu'ar da aunty tabani nakaranta. Wajen 2/30 mommy ta aiko wata me aiki kirana, a kitchen naje nasameta tanata hada kayan snacks tana package dinsu, sannu da aiki namata,amsawa tayi takara da fadin, "maryam Ku kwashi kayannan dakeda jummai kukai part din my son yanada bakine.'' Cikin faduwar gaba na'amsa da to. Ambatarsa da mommy tayi kawai yajefani cikin wani irin yanayi na doki da zumudin ganinsa, a wasu kwanduna masu kyau madaidaita guda biyu mommy tajera kayan, daya na dauka itama jumman tadauki daya, mukanufi part dinnasa zuciyata na bugawa kadan_kadan. Sama_sama muke dan hira da jummai, har muka karasa part dinnasa. Wata bugawa zuciyata tayi lokacin damukasha part dinnasa, dan banyi zaton ganinsa a falon kasaba, amma muna shiga dashi nafara cin karo, se sauran abokannasa da sunkai su six, wata boyayyiyar ajiyar zuciya nasauke, daddadan kamshinsa gabadaya ya mamayemun hancina. Gaishesu muka hauyi daya bayan daya, suna amsawa cikin sakin fuska, shine na karshen gaisuwar saboda yanacan gefene yanata faman latsa waya, tun shigowarmu ko motsawa beyiba balle yadago ya kallemu, gaisuwarma da muka masa hannu kawai yadaga mana, batare daya dagoba. Kananun kayane ajikinsa, Wanda suka matukar yimasa kyau, idanunsa sanye da wani siririn glass baki, tsintsiyar hannunsa nadauke da wata azurfa, tunda nazo gidan duk sanda zangansa da ita nake ganinsa, se kuma wani zobe na azurfa me kyau shima, yasa adanyatsansa na tsakiya,dayan hannunnasa kuma agogene shima me kyau. Acikin yan sakanni nakaremasa kallo, jinakeyi dama karna dena kallonnasa, sefaman sauke ajiyar zuciya nakeyi ahankali. Cikin tsananin farin cikin ganinsa na karasa dinning na ajiye kayan hannuna, senajini nadawo daidai dana gansa. "Oh Allah ni maryam me nakeji haka akan wannan bawan Allan ne?" Nafadi haka araina cikin mamakin wannan bakon al'amari agareni. Daya daga cikin abokan musty mesuna fahad se kallon maryam yakeyi tunda tashigo yarinyar ta masa kyau matuka, nakusa dashine yazunguresa tare da fadin, "fahad kaga wata yar baby, mekyau ko?" Sauke numfashi fahad yayi yace, "hmmm kaidai bari faruq bakaga nasaki baki ina kallontaba" "wlh aboki babyn tayifa" cewar faruq dayakebin maryam da kallo dasuke kokarin fita. Dakatar da ita fahad yayi da fadin, "yan mata yazaki tafi baki gama aikinkiba?" jin maganar mutum kamar dani yake sena juyo ina kallonsa amma bance komai ba, dagemun gira yayi tare da fadin, "eh mana baki zuba mana abunda kika kawo manaba, gashi naga kina kokarin fita, danni nan dakika ganni bakaramar yunwa nakejiba, dan zuwa gurin dinning dinma wahala ze bani" lukman dasuke hira da sauran abokannasu yayi murmushi me sauti danya gano inda fahad yadosa akan maryam. Shikam tunranda yafara ganin yarinyar yaji ta burgeshi amma bawai sonta yakeba, dan yana da budurwarsa bikinsama saura 2 weeks dalilin bikinnema yahadasu anan dansu tattauna. Nima murmushi nayi ganin yanda yayi maganar na juya da nufin zubo musu. Mustapha dake zaune yana saurarensu yadago yace, "ke!" Cak na tsaya cikin matukar tsorata saboda cikin kakkausar murya yayi maganar, bejira amsataba yanunamun kofa alamun na fice. Sum_sum naja kafata nafice dama jummai tayi gaba abinta. Galala su lukman suka tsaya suna kallonsa, shikuwa yawani maze tamkar bashi yayi maganarba yacigaba da latsawayarsa hankalinsa kwance. "Haba musty bayan muguntar daka mana, kaki fadamana kanada kanwa kamar wannan,sannan yanzu kuma naganta dakaina shine zaka korarmun ita, bamugama magana da itaba" cewar fahad yana hararar mustapha, a tunaninsa maryam cousin din mustapha ce, danbata masa kala da me aikiba,kuma harwata kama yaga sunayi. Banza mustapha yamasa danyasan halin fahad dama, shiyasa ya kora maryam, danyanzu seyace yana sonta. "To namamajo, aidama tunda naga kallonta nagane inda kadosa" cewar lukman yana dariya, suma sauran dariya sukasa ganin yanda fahad ya wani kebe fuska. "Ah, karna kalleta tamunne ai, idan kasamu wannan amata ai kagama dacewa, ga kyau ga nutsuwa da kamala ga hankali, nidai gaskiya tamun zanje nasamu mommy mugana,aknta" "irinkune maso jawa mutum raini, yanzu wannan yarinyar karama zakace kanaso, to tun wurima kacireta daga ranka dan ammata miji" mustapha yafadi haka batare daya dagoba. Kallonsa suke gabadayansu yanda ya wani maze tamkar bashi yayi maganarba. Faruq ne ya amshe zancen dacewa, "mene abun raini aciki, ai irin wadannan matan inkasamesu kagama morewa" "bari kaidai abokina, katayani da addu'a kawai Allah yasa nadace agurinta, koma wane mijin da'aka mata kwaf daya zanmasa na kwacemasa ita, yan bakin ciki kuma sedai suga anayi ehe!" cewar fahad yana mikewa zuwa dinning danya debo kayan da kansa. Banza musty yamasa bece kalaba, shifa dagaske yake har cikin zuciyarsa gani yake rainine kace kanason mata kananu kamar maryam, mema zasu iya yimaka, sedai suta maka shirme,da shiririta.🤤🥺 Ina tafe ina gulmarsa acikin zuciyata, haushi duk ya isheni nikadai nasan dadin danaji sanda abokinshi yakirani, ko banza zanta kallonsa amma yanzu yamun bukulu ya koroni. A kofar part dinmu naga yaya sadiq tsaye yazubamun ido kawai yana kallona harna karaso kusa dashi. "Yaya sadiq barka da warhaka" muryar maryam ta katse masa tunanin daya tafi akanta, firgigit yadawo daga duniyar daya lula yace, "yawwa maryam ya gida ya weekend?" "Lafiya kalau yaya" "to masha Allah, anjimafa bayan la'asar me lesson dinnaki zefara zuwa" "eh yaya banmantaba aina zamuyine?" Juyawa yaya sadiq yayi yanunamun wata yar rumfa dake dan nesa damu, yace, "acan zakuyi" "toh yaya nagode sosai da dawainiyar da kakemun, Allah yakara budi yabiyaka da aljannah" "ameen, maryam,kinyi kyaufa" rufe fuskata nayi cikin jin kunya nace, "nagode" murmusawa yayi yana binta da kallo. Maryam tana matukar burgesa komai tayi kyau take masa, gawani bakon al'amari dayakeji akanta. sallama namasa na wuce ciki,bin bayanta da kallo sadiq yayi harta shige, ajiyar zuciya yasauke ya juya yatafi. A falo natarar da mommy da suhailat, araina nace, "seyanzu tatashi kenan" gaisheta nayi bata amsamunba sedai uwar harara tare da mugun kallo data bini dashi, dama jiya kafin natafi school bamu rabu ta dadiba, masifa tayitayi akan ina tafiya ina barin aiki, wai dole sedai idannagama aikin natafi makarantar ko karfe nawane, mommy ce ta tausheta shine ta hakura da kyar. Ko dakina banshigaba nanufi dakinta, na gyara mata. Gyaran dakinta yana daukarmun lokaci saboda kodayaushe kaca_kaca yake, kamar me yara kanana dabata gyara dakin. Bata kintsa komai, komai taci kota cire atsakar dakin zata barbarzar, kuma haryanzu ninake wanke mata kayan unders dinta. Bayan nagama na koma dakina nayi sallar la'asar sannan na tattara duk abunda zan bukata nanufi gurin lesson dinmu. Me lesson din haryazo, gaisawa mukayi babu bata lokaci, yafaramun. Me lesson din yana da kirki sosai, gashi da faran faran, kuma alhamdulillah nagane sosai, da kananun sentence na turanci yafaramun, yakuma rubutamun sunan wasu littattafai yace nabawa yaya sadiq yasiyomun, se wajen magriba muka gama yatafi. Danayi sallahma nayita bitar abunda yakoyamun harya zauna daram akaina. Washegari, tun kiran farko mommy tazo tatasheni da kanta, dayake yau natashi nayi sallar dare, ina kan dadduma naji ana knocking kofata, cike da mamaki da tsoro nace, "waye?" Sai naji muryar mommy ce ta amsa, shine hankalina ya kwanta naje na bude. Sanarmun tayi na fito aikine damu yau megidan ze dawo, babu bata lokaci nabita zuwa kitchen. Aiki muka kama bakama kafar yaro, nifa har yanzu nadena mamaki, wai duk wannan kayan ciye_ciyen duk akan mutum daya akeyi, sukuma haka masu kudi suke, ina mutum zekai wannan abincin. Har gyaran gida ranar na musamman akayi, komai ankara tsaftaceshi na wanki an wanke, na gogewa an goge, gabadaya part din mommy ya kaure da kamshi, saboda turarukan da'aketa sanyawa, duk da ba'a part din ze saukaba, dannaji sanda mommy tatura aje agyara masa part dinsa. Gabadaya yan gidan kowa kaga fuskarsa cike da annuri da farin ciki take, hatta masu aiki kuwa, saboda dawowar megidan. Fara'ar dabantaba ganiba yau naganta a fuskar mommy da suhailat, se buge_bugen waya sukeyi suna fada alh. zedawo. Gaskiya mahaifi akwai dadi, yanda suke murna da rawar jiki,banga lefinsuba akan dawowarsa, inama nima zanga mahaifina, inama nima nawa mahaifin zedawo gareni, da kuwa duk wani bakin cikin dake zuciyata nasan seya yaye. Gaskiya masu iyaye araye kuma atare dasu sunji dadinsu.(Allah kabarmu da iyayenmu, kakuma rabamu dasu lafiya, Wanda suka rigamu gidan gaskiya kuma, Allah yagafarta musu. Ameen). Se bayan azhar nasamu kaina, jikina duk yayi tubus da gajiya, ko karyawa banyiba yau,yunwa se nukurkusata takeyi, abinci nadiba naci, kadannema yasamu yashiga cikinnawa, kamshi duk yagama cikamun ciki, ruwa na watsa nafito nayi sallah, lafiyar gado nabi domin rama bashin baccin dake kaina........ Gabadaya ahalin gidan alh.menasara yau suna cike da murna da farincikin dawowarsa gida, dan gaskiya ya jima a tafiyar dayayi. Ma'aikatan gidanma ba'abarsu abayaba wajen taya murna, domin sunsan idanyadawo kakarsu ta yanke saka. Mutum ne shi me kirki, baya kyamar talaka ko kadan, gashi da kyauta sabanin mommy dabata kyauta kokadan, shiyasa yayanta duk ita suka gado, mustapha ne kadai me wannan kyautar irintashi, se sadiq dake bimasa baya. Karfe uku jirginsu ze sauka, tun karfe 2 kowa nagidan ya shirya dan tarboshi, harda mustapha dake cike da farinciki shima, sekuma abokan alh. Menasaran dasuma zasuje tarbar tasa. 2/40 a filin airport din ta musu suna jiran saukarsa...... Cikin farin ciki yake sakkowa daga matattakalar jirgin fuskarsa dauke da annuri, lumshe idonsa yayi cikin Jin dadin shakar iskar kasarsa me albarka dayayi. Alh. Menasara kenan, mutum me cikar zati da kamala hadi da kwarjini, kamarsa daya sak da sadiq kamartasu harta baci, hatta duhun fatarsu dayane. Masha Allah kyakkyawane shima, dan har yafi mommy kyau sedai kawai ta nuna masa hasken fata. Fuskarsa dauke da fara'a yake tafiya cikin nutsuwa,iyalansa da abokanansa suna ganinsa suka karaso garesa, da gudu haidar da zannurain suka fada jikinsa cikin tsananin murna. Rungumesu yayi tsam ajikinsa shima yana shafa kawunansu. "Welcome dad" suka fada atare. "Thank u dears" yabasu amsa, daidai nan su mommy suka karaso garesa, kowa narige_rigen hugging daddy. Daya bayan daya yake rungumesu suna gaisawa, mustapha ne na karshe daya tsaya kawai yana kallonsu cike da sha'awa, fuskarsa cike da annuri. Takawa daddy yayi har daf dashi yayi hugging dinsa yana fadin, "Muhammad dina, I really missed u'' lumshe idonsa yayi cikin kaunar mahaifinnasa yace, "missed u too dad'' shafa kansa daddy yayi cike da matsananciyar kaunarsa. Sannan yasakesa suka shiga gaisawa da abokanansa kuma amininansa. Dunguma sukayi duka zuwa mota....... Gaba daya ma'aikatan gidan sun hadu a harabar gidan suna jiran karasowarsa, suna shigowa kuwa suka nufo motar tasa da musty yake driving domin yimasa sannu da zuwa. Yanadaga cikin motar yake miko hannu suna gaisawa cikin fara'arsa dabata yankewa afuskarsa. Domin shi mutum ne me yalwar fara'a. Har kofar part dinsa musty ya kaisa, sannan yafito dasauri ya bude masa kofa yafito. Daddy kuwa sesamasa albarka yakeyi. Dukansu suka dunguma zuwa part dinnasa dayasha gyara se tashin kamshi yakeyi. Mommy tana gefenshi tanata zuba masa kissa, domin mommy macece me kissa kisisina, duk da tagama mallake daddy se'abunda tace yakeyi, Amma duk da haka yanashan kulawa da tarairaya agurinta. Dakanta ta hada masa ruwan wanka yayi, sannan yadawo falon. Ko zama mommy bata bari yayiba ta kama hannunsa zuwa dinning, zama yayi yana fadin, "kai atika ko yar hirarnan ta yaushe gamo bazaki bari muyiba zaki zarto dani cin abinci, Allah yadawo dani yanzu zakita dirkamun abinci duk nabi na kara kiba.'' Dariya mommy tayi tace, "naji din ai gwara kayi kibar, kokafiso inta barinka da yunwa,kanabin restaurant cin abinci'' murmushi yayi kawai bece komaiba, kamshin abinciccikan gabadaya yagama badade hancinsa. Mommy dakanta tayi serving dinsa, sauran abokanansama dinning din suka dawo, mommy tasa suhailat tayi serving dinsu. Hira sosai sukesha da iyalansa, musamman suhailat auta, databi ta manne masa se shagwaba take zuba masa, shikuma yana biye mata. Sallar la'asarce tatadasu suka nufi masallaci..........✍️ *BY* *Zeey kumurya* *ABUNDA KA SHUKA*......... _*(shizaka girba)*_ *MALLAKIN* 👇 *ZAINAB USMAN KUMURYA* *FARIN JINI WRITERS ASSO.....*📚 ~*Free novel*~ *Bismillahirrahmanirrahim* 2️⃣2️⃣ ........Nima kiran sallar da'aka kwallane yatadani daga barcina badon bacci ya isheniba, ina lumlumshe ido saboda bacci nanufi toilet na kuskure bakina tare da dauro alwala nadawo nayi sallah, addu'ata na dakko nakaranta cikin sauri bayan na idar da sallah. Inagamawa na dauki kayan lesson dina nafita. Babu kowa a falon yayi shiru tsit, a falon kasa nema naga wata me aiki guda daya tana kallo, gaisawa mukayi nafice. Yauma kamar jiya me lesson din haryazo, gaisheshi nayi mukafara abunda ya kawomu. Alh menasara basu koma cikin gida da wuriba daga masallaci saboda gaisawa da jama'a, ya kara fiye da minti talatin sannan suka koma gida. Aka baje afalonsa anata shan hira, alh, menasara mutum ne mejan yayansa ajikiajiki Da nuna musu kauna tsababa,amma shi gaskiya bakamar mommy ba yana tsawatar musu idan sukayi badaidaiba. Masu aikin gidan mata sunata zuwa gaishesa. Sadiq ganin bega maryam tazoba ya mike yafita domin kiranta itama tayiwa daddy sannu da zuwa. Muna cikin yin lesson dinne yaya sadiq yazo gurin da muke, sallama yayi mana muka amsa, yakara da fadin, "maryam daddyfa yadawo tun dazu, anata zuwa yimasa sannu da zuwa amma bangankiba. Dafe kaina nayi nace, "oh am sorry yaya sadiq nayi zaton koyana hutawane yanzu, kar'aje adamesa.'' " A'a babu wani damu kije kawai yanzu anata zuwa yimasa sannu da zuwa'' "gaskiyadai maryam yakamata kije kugaisheshi yanzu" cewar memun lesson daya karbe zancen. "Ohk to malam nagode, bari naje se wani satin kenan ko?" "Ehh maryama Allah yakaimu darai da lafiya." "Ameen" nafurta haka ina mikewa da littafafai ahannuna. Musabaha yaya sadiq sukayi da malam tare dayin sallama muka tafi. Seda nakoma na'ajiye kayan hannuna sannan nafito muka tafi. Muna tafe yaya sadiq namun hira nikuma zuciyata se bugawa takeyi kadan_kadan. Suna cigaba da kwasar hirarsu cikin jindadi muka shigo falon da sallama. Yaya sadiq nagaba ina binsa abaya. Gabadayansu shiru sukayi suna kallonsu maryam sundai amsa musu sallamar dasuka musu. siririn tsaki suhailat taja aranta tace, "narasa meyasa yaya sadiq yake shishshigewa wannan figaggiyar yarinyar, waishi sarkin tausayi." Mommy kuwa kallon data sababin maryam dashi tabita dashi. Su haidar da zannurain kuma da kallon tsana, faruq shidama bedamu da al'amarin kowaba sabgar gabansa yakeyi. Mustapha kuwa kallonsu kawai yakeyi, yana karewa maryam kallo, soyake yagano me fahad yagani ajikin wannan kwailar yarinyar dayabi yarude jiya ya addabeshi da zancenta. Daddyma kallonta yakeyi cikin rashin sani, dan kwata_kwata beyi tunanin me aiki bace. Wani ido naji yana yawo ajikina Wanda yasanyamun wata kasala da mutuwar jiki, bugun zuciyatane yakaro, kasa dago kaina nayi na kalli kowa duk senaji na tsargu. Har gaban daddy yaya sadiq yajani, tsugunnawa nayi agabansa cikin sanyin murya nace, "Ina wuni?" Cikin fara'a daddy ya amsa da lafiya kalau yan'mata ya mutunen gida da karatu?" "Alhamdulillah" daga haka nayi shiru danbansan mezance masaba. Abokanansa danagani na gaisar suma nayiwa mommy sannu da gida. Daddy daketabin maryam da kallo cikin sha'awa, daga gani yarinyar tana da hankali. Maida kallonsa yayi ga sadiq yana murmushi yace, "Abubakar yasunan surukartawane?" Danshi daddy yadauka maryam budurwar yaya sadiq ce. Wata zabura suhailat dake gefen daddy tayi tace, "haba daddy, Allah yasawwake wannan kucakar tazama surukarka,Allah yakiyaye jibetafa daddy wata kazama da ita" "idan tazama kuma sekiyi yaya?" Cewar mustapha yana jifan suhailat da wani irin kallo. Gabadayansu juyawa sukayi suna kallonsa,nima dagowa nayi cikin matukar mamaki na kallesa, ko a mafarki naji muryar datayi maganar sena gane, saboda tana saukarmun da wani yanayi najin dadi ajikina. Tsit suhailat tayi bata kara cewa komaiba, sedai bakin ciki da tsanar maryam daya cika mata zuciya. Mommy kuwa galala tayi kawai tana kallonsa amma takasa magana, se tambayar kanta datakeyi aranta me kalamansa suke nufi akan maryam. Shiko sadiq yaji dadin amsar da yayannasa yabawa suhailat, dan kaf falon babu Wanda ya isa ya tsawatarwa da suhailat mommy ta barshi, harshi kanshi daddy kuwa, mustaphannede kawai. Shiko gogan badawani Abu yafadi hakaba kawai amsa yabawa suhailat danta bashi haushi,bayason adinga muzanta dan'adam. tabe baki yayi yadauke kansa daga kan kowa ganin yanda suka zuba masa ido,sekace Wanda yaci musu bashi. "yaya sunanki yanmata?" Cewar daddy yana tsare maryam da ido, yanda ta dago tayi da idanunta, seyaga tamkar yasan fuskarta kokuma wata mekama da ita,kokuma wani me irin kallonta. "Sunana maryam, kuma nice me'aikin part din hajiya a gidannan" nabashi amsa a kagauce saboda na matsu nabar falon. "Maryam!" Mustapha ya maimaita sunan aransa, betabajin sunantaba seyau inma ankirata agabansa bejiba, shikam tunda yatashi arayuwarsa yakeson sunan maryam, haka kawai kuma yaji yanason sunan, shiyasa da maryam ta fada ya maimaita sunan aransa. "Masha Allah maryama, Allah yayi albarka yataimaka." "Ameen nagode, se'anjima a huta lafiya" nafadi haka ina mikewa gyadamun kai yayi nikuma nafice daga falon. Daga ganin farko nafuskanci alh.menasara yanada kirki bakamar mommy ba, kamar yadda ake fadar halayensa agari, na taimako da yawan sadaka ga marasa karfi. Shiyasa yaya sadiq yake da kirki Ashe halin mahaifinsa garesa kamar yadda kamanninsuma yazama daya. Maganar mustapha tamun tsaye azuciyata tamkar yanzu yafada se kuwwa takemun akunne, "muryarshi akwai dadi, nafadi haka araina ina lumshe ido. Harna karasa part dinmu,tunaninshi manne a zuciya ta. Dakina nashige na dakko littafina na lesson nashiga dubawa. Acan falon daddy kuwa cigaba sukayi da hirarsu suka manta da wani batun maryam, amma banda sadiq da tunaninta ke tsaye kyam acikin zuciyarsa, da kuma suhailat da haushinta ya cika mata zuciya,gashi akanta mustapha yaji haushinta, tasan setaci kwa_kwa kafin ya hakura. Har dare basu dawo part dinba seyaya sadiq ne kadai yazo yakawomun waya wai aliya takira tace yabani mugaisa. Daganan kuma yazauna muka dan taba hira akan makaranta, naji dadin zamanshi kuwa dan dama atsorace nake da zaman nikadai, dandaima falon kasa da masu aiki, asamane nikadai. Se wajen karfe 9 yatafi yace naci abincina na kwanta su a part din daddy zasuyi dinner. Abincin na debo naci, nakoma daki nayi kwanciyata bacci bayan na bame kofata....... **************************** Kwanaki nata tafiya rayuwa tana shudewa dadadi babu dadi ga kowanne dan Adam,hakance ta kasance ga maryam. Yau gashi har alh, menasara yayi sati biyu da dawowa. Rayuwata natafiya acikin gidansa, cikin rashin jin dadi, saboda kyara da kyamar danake fuskanta ga suhailat yafi nada. Dadina daya yanzu kawai ina zuwa makaranta ko zama bana samu sosai, danyanzu nafara zuwa islamiyya ta safe 9_11, asabar da lahadi. Yaya sadiq ne yakaini, anan bayan layinmu take babu nisa da kafatama nake zuwa. Kulawa da kaunar da yaya sadiq yake nunamun bazata misaltuba, harna rasa dame zansaka masa arayuwa. Yayimun abunda bazantaba mantawa dashiba akullum cikin yimasa addu'a nakeyi Allah yabiya masa bukatunsa na duniya da lahira. Bani da matsala da megidan kokadan, danshima tamkar aunty yake, gashi da barkwanci da ban dariya, tamkar bame kudiba. Duk da ba kullum nake ganinsaba amma na fuskanci hakan daga gareshi, danseyayi kwana 3 kafin yazo part din mommy,sedai kullum su sunacan. A kowanni sakanni dayake wucewa tunanin mustapha na karuwa a zuciyar maryam, yanzu kam abunna bani tsoro matuka,gashi duk ranar daban ganshiba hankalina atashe yake, nayitabin duk wata hanya kenan danasan zangansa konaji dadi araina. Gashi banasamun ganinnasa kullum senayi kwana 3 ko 4 bamu haduba, sedai idan Allah yataimakeni mommy ta aikeni wani lokacin. Alhamdulillah ina maida hankalina sosai akan karatu danyanzu muna gabda fara jarrabawa. Wani satin zamu fara da yardar Allah. Abangaren sadiq kuwa, yagama tabbatarwa da kansa da zuciyarsa son maryam yashigesa,amma yakasa tunkararta yasanar mata seyayi niyyar fada mata sekuma yakasa, saboda besan yazata dauki al'amarinba, kuma yana ganin kamar tayi kankanta amata zancen soyayya yanzu. Aunty tayiwa daddy zancen yin auransu suhailat da mustapha, amma koda yatuntubi mommy da maganar, setace Sam bata lamuntaba se yarta takarasa karatu tunda saura shekara daya da watanni sugama. Hakuri daddy yabawa aunty akan tabari suhailat din takarasa karatunnata, badon aunty tasoba ta hakura tabisu addu'a kawai. Su mustapha kuwa kai yayi caji sunata shirye_shiryen bikin lukman, ga aikin office gashi kuma komai na bikin dashi akeyi, dukda yaso turjewa akan hidimar bikin amma abokansa sukace be'isaba yana aminin ango dole ayi komai tare dashi. Cike da tsananin murna natashi yau saboda zanje unguwarmu ganin gida, tun jiya na tambayi mommy kuma tabarni bata hananiba. Dama biki sukeyi tun ran laraba suka fara haryau lahadi, kullum da yamma sesun fita se dare suke dawowa, kuma dukansu har samarin gidan. Sedai naje part din su baaba talatu musha hira kafin su dawo. Yaya sadiq jiya yace nashirya muje bikin, nace masa a'a yayiyayi amma naki zuwa anannema naji labarin Ashe bikin abokin yaya mustapha akeyi shiyasa kwana biyu bangansaba,kewar ganinsa duk tacikamun zuciya. Da wuri nagama duka ayyukana kafin 12 nashirya tsaf cikin wani less dinkin riga da zanine, yamun dass ajikina. Tunda nazo gidan bantaba saka mayafiba seyaudai nace bara nasaka. Banyi wata kwalliyaba powder kawai na mutstsika nasa lipstick fari a lebena se kwalli. Simple dauri nayi nadora mayafina kalar kayan. Tsayawa nayi ina kallon kaina a madubi senaga nayi kyau hasken fatata yafara dawowa zamana a gidannan na wata daya da kwanaki. Duk Wanda yasanni ada kafin nazo gidan yaganni yanzu zega tabbas nacanza. Takalmi da jaka nasa kalar kayan na fesa sassanyan turaren danake sawa, Wanda duk acikin siyayyar yaya sadiq suke,ledar dana kwasarwa saleemat,da gwaggo turaruka da mayuka nashafawa nadauka nafito. Seda nafara zuwa dakin mommy namata sallama tukun, itama shiryawa natarar tanayi zata gidan biki. Ina kokarin fita daga falon suhailat tafito daga dakinta, cikin shirinta tayi kyau sosai itama. Cike da mamaki suhailat take satar kallon maryam, setaga yarinyar ta wani kara kyau da haske, ga wani sassayan kamshin dake tashi ajikinta. "Sannu da fitowa aunty suhailat" maryam ta katse mata tunani da fadar haka. Bata amsaba sema yatsina fuska datayi tace, "kekuma inazaki?" cike da doki da zumudi nace, "zanje ganin gida ne" tabe baki suhailat tayi batace komaiba tayi gaba. Nidai bandamuba saboda farincikin danakeji danyau zanga umma da saleemat dita da gwaggo. Seda nafara zuwa nayiwa baaba talatu sallama sannan na nufi parking space inda yaya sadiq yake jirana, danyace shize kaini tin jiya dana fada masa zani gida. Yana bakin gurin kuwa yana jirana, har mamakin yaya sadiq nakeyi kullum bana jiranshi sedai shi yajirani ko makaranta zamu. Tunda sadiq yahango maryam yakura mata ido, tayi matukar yimasa kyau yau, duk da mayafi tasaka amma yarufe mata ko'ina na jikinta, tayi shigarta ta mutunci, harta karaso garesa amma yakasa dauke idonsa daga kanta. Wani kallo naga yaya sadiq yana bina dashi, dukse naji na tsargu, daurewa nayi nagaisheshi cikin sanyin murya naji ya amsamun. Babu bata lokaci muka shige mota yaja muka tafi dama tun jiya nafada masa sunan unguwarmu. Yau tafiyar tamu babu hira, waka kawai yake samana a motar ta soyayya. Cikin abunda befi 20 minutes ba muka isa ungurmu ta *darmanawa* wata boyayyiyar ajiyar zuciya nasauke murna tacikamun ruhina, jinake tamkar nayi shekaru rabona da unguwar,Muna tafe ina nuna masa hanya har kofar gidan gwaggo, Allah yasoma mota tana shiga har layinnamu. Cikin zumudi na bude kofa da nufin fita. Tsayar dani yaya sadiq yayi da fadin, "to sarkin hanzari zaki tafi ko sallama bamuyiba, idan kinshiga kimun iso zanshigo mugaisa da mutanen gidan. Cikin jin kunya nayi murmushi nace, "to yayana" sannan na fice daga motar. Binta yayi da kallo harta shige, Kalmar *yayana* data kirashi da ita tamasa dashi. Lumshe idonsa yayi tare da kwantar da kansa ajikin kujera. Da gudu nashiga gidan ina kwalawa gwaggo kira, "gwaggo! Gwaggo!'' Hajiya gwaggo tana daki tana lissafin kudi taji ana kwala mata kira. Ajiye kudin tayi da sauri tana fadin, "wanakeji haka kamar muryar maryam" "nice gwaggo" nafadi haka ina shiga dakinnata. "Oh ni ladi, yanzu yannan seyau kika tuna dani, wato kinsamu daula kinmanta da niko" "kai gwaggo bazata sauya halintaba" nafadi haka araiana, a fili kuwa senace, "haba gwaggota karkice haka mana, kullum da tunaninki nake kwana nake tashi" Hararata gwaggo tayi tare da fadin, "kinganki kuwa maryam, sekace matar gwamna fatarki kamar jikin kifi dan kyau, amma da kina bazaki aikatau dinnanba,gashinan yanzu kinje kinajin dadinki kinyi limun buki dake." Dariya nayi bayan nazauna agefenta nace, "ai gwaggo bawananne abun murnaba harfa makaranta aka sani agidan boko da islamiyya" memakon naga gwaggo tayi murna senaga ta kebe baki tace, "wannan yarinyar jarabbaki tasan karatu yawa gareta, keda aka turaki aiki meyakaiki kuma yarda asaki a makaranta, dayaushe kikesamun lokacin aikin kenan?" "Gwaggo ai aikin bawani meyawa bane, idannadawo nakeyi" batakara bi takan zancenba.ledar hannuna ta kalla tace, "mene wannan aleda badai shine iya dan abun dakika kawomunba, yanzu maryam saboda bakin hali irinnaki kina irin wannan katon gidan amma zakizo gurina da dan abunda zaki kawomun kena....sallamar dawani yaro ya kwadane yakatsewa gwaggo zancenta, mikewa tayi tafice tana amsawa. Da kallon takaici nabita,ita ko murnar ganinama batayiba ta abunda nakawo mata kawai takeyi, ko tambayata wanne hali nake ciki agidan batayiba, babu ruwanta ko yankan naman jikina akeyi, itadai na kawo mata kudi da kaya. kai nayarda da'ake cewa me hali baya taba canza halinsa. Dakinnata nabi da kallo gaba daya yayi kaca_kaca wani bashi_bashine yake tashima adakin, itama tayi wani dukun_dukun da ita, idonta harda kwansar bacci. Wata guda naji gwaggo ta rangada tana fadin, "kai haihuwa me dadi, yanzu duk wannan kayan Wanda sukazo da maryam dinne yakawo,wayyo dadi." Dasauri nafito daga dakin har inayin tuntube, jin abunda gwaggo tace. Turus na tsaya ina kallon kayan da yara suketa shigowa dashi, kayan abincine, shinkafa taliya macaroni, indomie magi hardasu gwangwanin madara, da born vita,milo katun_katun din gwangwanaye da crase din kwai guda biyu. Daya daga cikin yaran na kalla nace, "kai dan malam wayabako kayannan yace kukawo?" "Wanine a waje acikin wata katuwar mota mekyau'' kama haba nayi cike da mamaki, yaya sadiq kenan shine da wannan hidimar, dannasandai shine awaje acikin mota, dan layinmu mota biyu bazata zaunaba,kuma nasan yana waje yana jirana, to inama kayannan suke danni bangansuba a motar. "A boot mana" nabawa kaina amsa. Gwaggo dake tsaye tanata zuba sunbatu da santi, tazari wani mayafinta a igiya tana fadin, "bari naje mugaisa, kai abu yayi kyaufa" tsayar da gwaggo nayi amma taki tsayawa nasan yanzu setace ta bani kunya agurin mutumin danake ganin girmansa, jikina asanyaye nabi bayanta cike da takaicin halayenta. Sadiq yana tsaye ajikin motarsa yana sallamar yaran dasuka kai kaya gidansu maryam, gwaggo tafito tana washe hakora tace, "sannu dan arziki irin albarka, yaron kirki, aiba akasa kadibaba gada kayi, haka halin mahaifinka yake kyauta gareshi" karasowa sadiq yayi har gaban gwaggo ya tsugunna yana gaidata, amsawa gwaggo tayi cikin jindadi tana dariya. Daidai nan nakaraso zauren gidanmu, wani bakin cikine yakamani jin kalaman da gwaggo take sakarwa yaya sadiq, na roko. Waidama bata da abinci bata dame kawo mata, segashi Allah yajeho matashi, dabezoba dabatasan yanda zatayi da kantaba,ga bata kudi duk bashikan mutanene akanta. Kalamaidai na zubar da mutunci da aji gwaggo take masa harda kukan munafurci, ga wani Karin abun takaicinma tundaga soro gidan duk bola da yaana. Bangamajin surukatannataba nakoma ciki, tunda abunda nake gudu ya auku. Sauri nayi kafin tadawo na kwaso turaruka da mai acikin Wanda nazo dashi nakai dakina na gidan na boye, dan idan tagani bazata bari nabawa saleemat dinba. Shima dakin gabadaya yayi kura, da yaanar ga wani uban shirgi Mara kan gado aciki. Seda tagama babatunta da zubar da mutuncin sannan tadawo, da kudi ahannunta me yawa da sadiq yabata. Rawa tahauyi da juyi atsakar gida duk dan murna. Mutum angirma ba'asan angirmaba. Fita nayi don muyi sallama da yaya sadiq. kunyarsa duk ta lullubeni nama kasa hada ido dashi, hakadai mukayi sallamar yace bayan magriba zezo yadaukeni. Ina dawowa gidan nacire kayan jikina, nadauki wani zanin gwaggo Medan hankali nadaura nahau gyaran gidan gwaggo. Tsakar gidan nafara sharewa zuwa soro, bola himuli natara. Sannan na dawo wankin bandaki, duk yabi yadafe se uban zarni da wari, haka na wanke matashi tass ina tsartar da yawu. Kayan wanke_wanke nahada shima himili guda, wasu kwanukan duka anbar guntun abinci aciki haryayi funfuna. Bazan iya wankewaba gaskiya tattarasu nayi nakai bola na wanke sauran dazan iya. Tass nagyarawa gwaggo gidanta cikin abunda befi awa biyuba, har tsintsiya nasa na rage yanar gidan. Seda nayi wanka dan kyankyamin jikina nake sannan nasa kayana nayi sallar azhar.gyaran dakintane seda na idar da sallah kawai namata. Amma gwaggo ko sannu batamunma, nidama dan Allah nayi badon itaba. Lissafe lissafen kudinta kawai takeyi. Wankine kawai banyiwa gwaggoba, shima dan ina saurine inje inga masoyiyata saleemat. Maryam na kallon gwaggo tanacin bredinta da miya, amma kotayi batamataba dukkuwa da uwar bautarnan data mata. Jakata nadauka nace mata zanje gidansu saleemat. Ledar danazo da ita dama tuni ta janyeta, seda tacaje jakata tass harda jikina taga babu komai sannan ta barni na tafi, wai duk dan karna kaiwa su saleemat komai, gwaggo, gwaggo hmmmm🤔🤔...........✍️ _*shima wannan ba editing,🤤 nagode da addu'oinku, Allah yajikan musulman dasuka rigamu gidan gaskiya baki daya*_🙏😭 *BY* *zeey kumurya* *ABUNDA KA SHUKA*......... _*(shizaka girba)*_ *MALLAKIN* 👇 *ZAINAB USMAN KUMURYA* *FARIN JINI WRITERS ASSO.....*📚 ~*Free novel*~ *Bismillahirrahmanirrahim* 2️⃣3️⃣ ..........Salimat yau wanki sukesha ita da umma, tana sabawa umma na tishi da dauraya. dan'autansu me suna hanifne ya shigo da gudu yana kwalawa saleemat kira,tun daga soro. "Yaya saleema,yaya saleema!" "Na'am, autan umma ya'akayine irin wannan kira haka" "yanzu naga yamaryam ansauketa a wata mota me kyau" saleemat dabatayi tunanin ganin maryam yanzuba tace, "autan umma banason karya, ina kaga yamaryam din, sedai idan wata kagani." "Allah yasaleemat yamaryam nagani itafa da wani mutum me mota" murmushi umma tayi tace, "mutanen dake zuwa gidan gwaggo ai yawa garesu, yadaiga wata yake tunanin maryam dince, danyaga kullum cikin zancenta muke" "gaskiya dai, amma banda haka maryam meze hadata da wani harda za'akawota a mota, bama na tunanin zuwan maryam unguwarnan yanzu" cewar saleemat tana mikewa domin shanya kayan da umma ta dauraye. Turo baki hanif yayi ganin sun karyatashi ya juya ze fita. Hanashi fita saleemat tayi dan yanzu idan yafita se lokacin islamiyya yayi bedawoba. Harsuka gama wankin hirar maryam sukeyi, abunda ya kara tabbatar musu ba maryam ce tazoba,jin gudar gwaggo dansunsa gwaggo bazatayiwa zuwan maryam wannan murnarba. wanka saleemat tayiwa kannenta biyu ta shiryasu suka tafi islamiyya. Cike da murna da doki nanufi gidansu saleemat bayan nadau kayan dana boye adakina. Saleemat na bakin rijiya tanajan ruwan wanka bayan tayi sallah taci abinci na shigo gidan da sallama. Da matukar mamaki saleemat ta juyo tana kallon bakin kofa tare da sakin gugan hannunta a lokaci guda tana waro idanunta waje. Fuskata dauke da murmushi nacigaba da tunkararta mamakin ganin maryam yahana saleemat ko motsi balle ta amsa sallamar data mata. Cikin ihun murna kuma, ta kwasa da gudu ta rukunkume maryam, nima rungumeta nayi ajikina cikin jindadin ganinta,atare muka sauke ajiyar zuciya ni da ita. Umma ce tafito daga daki tana fadin lafiyarki kuwa salima kikasaki guda haka, wannan aise kifadarwada mutum gaba ga Ku.....maganar umma ce ta tsaya ganin salimat rungume da wata. Sakin maryam salimat tayi cikin tsananin murna da farincikinganin maryam mara misaltuwa tace, "umma she dagaske hanif yake maryam tazo" kafin umma tayi magana nanufeta da gudu na rungumeta itama ina fadin, "ummata nayi kewarki sosai" umma dake cike da dinbun mamaki da farincikin ganin maryam tace, "maryama dagaske kece agidannamu yau" "nice umma" nafadi haka ina sakinta. "Maraba lale marhabun diyata, kai amma naji dadin ganinki,shigo, shigo, shigo" umma ta kama hannuna muka shiga daki. saleemat dake tabun maryam da kallo ganin cikin kwanaki kadan ta sauya tabi bayansu zuwa dakin. Farin cikin datake ciki yau baze misaltuba naganin kawa,aminiya,kuma yar'uwarta da kulkum take kwana take tashi da ita aranta. Gaishe da umma maryam tayi tare da dan taba hirar yaushe gamo, salimat dai tatasa maryam agaba kawai tana kallonta. Fita umma tayi da kanta domin takawowa maryam abinci da ruwa. Hararar salimat nayi bayan umma tafita nace, "wannan kallonfa, kintasani agaba ko kewatama bakiyiba ko" matsowa kusa da maryam suhailat tayi ta rungumuta a jikinta tace, "haba tawan, aike ko fada miki akayi banyi kewarkiba nasan zaki karyata, naga kinkaramun wani kyaune da fresh ga wani daddadan kamshi dake tashi ajikinki, kuma ta ummanki kike bataniba,shiyasa namiki shiru" "hmmm,ainazo zaki fara, ya kwana 2 ya makaranta?" "Alhamdulillah muna shirin farama waec" "masha Allah,Allah ya taimaka yabada sa'a, kinsan nima nakoma school da islamiyya" cikin mamaki salimat take duban maryam,amma batace komaiba. "Dagaske kawata,nakoma makaranta,nima" nafadi haka ina murmushi. rukunkumeni salimat tayi cikin tsananin murna tana murmushi tace, "wayyo dadi, amma gaskiya maryam naji dadin wannan labarin, amma gaskiya mutanen gidan suna da kirki dasuka saki a school" daidainan umma ta dawo da ruwa da abinci ahannunta harda lemo, dasauri muka tashi muka karbeta ina mata sannu tare da godiya. Cikin tsananin farin ciki salimat ta mata bayanin na koma makaranta, tayani murna umma tayi sosai tare damun addu'ar samun nasara. Abinci umma tace na sakko naci, jallop din taliyace da zafinta taji kayan hadi daidai misali, wanka salimat ta shiga kafin nagama cin abincin, umma kuwa tarasa inda zatasaka maryam don farincikin ganinta fess,batayi zaton zasu ganta hakaba, ga kuma daddadan labarin ta koma karatu, umma setaji wata nutsuwa hankalinta ya kwanta akan aikatau din maryam. Bayan nagama cin abincine umma ta dubeni tace, "maryama ya gidan aikinnaki babu dai wata matsala ko?" Ajiyar zuciya nasauke nace. "Gashinandai umma kinsan masu kudi, inadai dan fuskantar matsala daga wasu yayan gidan,amma matar gidankam babu wata matsala, bata shiga sabgata idan ba aiki zanmataba. Sauran ma'aikatan gidanma muna zaune lafiya, kuma kome zasuci agidan nima zan iyaci, ba'amun iyaka da abinci ko sha kowanne irine,megidan dabayananma danaje gidan yayi tafiya, sati biyu dasuka wuce yadawo kuma shima gaskiyadai bashi da matsala................ Labarin komai na gidan maryam tabawa umma, harda kirkin da sadiq da baaba talatu suke mata da zuwan su aunty, labarin fyaden da'akewa yan aikin gidan kawai bata fadawa ummaba dan kar hankalinta yatashi,tadaice tatayata da addu'a akan Allah yakareta daga duk wani sharri nagidan. Numfashi umma tasauke tace, "Dama ba duka hali yazama dayaba, " Allah yasakawa wannan yaro dayake dawainiya dake da alkhairi, Allah yabiyasa da aljannah, sukuma sauran yaran gidan sekiyi takatsantsan da bacin ransu, kikuma kama kanki tunda kince yaran gidan duk samarine. kikara hakuri maryam komai lokacine, kuma komai me wucewane kinji" "insha Allah umma nagode sosai" salimat ce ta dawo dakin umma kuma tafita domin karasa aikin gida. Labarin gidan alh. Menasara nabawa maryam atakaice itama, addu'a taitaiwa yaya sadiq itama dakuma kara bani baki. Sallar la'asar mukayi sannan mukacigaba da hirarmu cikin jindadin ganin juna dakuma kewa. Farincikin kasancewa da salimat ayau yaragemun tunanin mustapha araina, amma duk da haka yana fadomun arai lokaci zuwa lokaci. Muna cikin hira naga salimat tayi shiru tana kallona. cikin mamakinta nace, "Menene naga kintsaya kina kallona?" Numfashi salimat ta sauke tace, kamar akwai abunda kedamunki Wanda kike kokarin boyemun amma fuskarki tagaza boyewa seda ta nuna" nuna kaina nayi da hannu nace, "nikuma gaskiya babu abunda yake damuna" kama hannun maryam salimat tayi tace, "bekamata ayanda Muke dake kiboyemun wani abu dake damunkiba, muna zaunannen senaga kinyi shiru harda lumshe ido, kina sauke numfashi, tabbas hakan alamace ta akwai abunda yake damunki acikin ranki" "gaskiya babu komai, sedai ko tunanin exam dazamu fara next week" "hmmm, maryam kenan maganar dakikeyi yanzu tana kara fallasa abunda ke ranki,kinsan maryam nasanki nasan duk wani moment dinki, kifadamun abunda ke damunki kona samu kwanciyar hankali, domin kuwa tabbas idan kika tafi ahaka, zaki barni cikin damuwane, kifadamun koda wata matsala dakike fuskanta agidan aikin,nikuma zanbaki shawarar dazata amfaneki tare da tayaki da addu'a da yardar Allah" shiru nayi ina sauke numfashi, tabbas salimat tayi gaskiya, aduk lokacin da mustapha yafadomun araine nake shiga yanayin data fada, kuma salimat bata cancanci na boye mata komai na rayuwataba,kuma dama ina son tambaya akan abunda nakeji akan mustapha. Wata doguwar ajiyar zuciya nasauke ina duban salimat nace, "nima bansan meke damunaba kawata, amma na tsinci kaina acikin wani irin yanayi a kwanakin dasuka shude, zuciyata ta kasance kullum cikin tunanin wani bawan Allah take, dakuma kwadayin ganinsa akodayaushe, aduk lokacin dana gansa inajin zuciyata na wata irin bugawa tare da samun nutsuwa araina, inajin dazan wuni ina kallonsa bazan gajiba, bansan yanda zan kwatanta miki yanda nake jinsa arainaba, ada nayi tunanin tsoronsa danakeji seda daga baya kuma naga abun yawuce akirashi da tsoro" "waye shi?" Salimat ta jehomun wannan tambayar. Labarin musty na bata atakaice. Shiru salimat tayi, domin tagane maryam ta kamo da son mustapha ne, batare data saniba, amma bazata fada mataba dankar tatada mata da hankali, zata tayata dai da addu'a Allah yayaye mata, domin abunda baze yiyubane wannan, soyayyar maryam da danmekudi irin alh. menasara, bata mata fatan hakan koda nangaba, domin ayanda maryam tabata labarin yaran gidan zasu zangwametane kawai su kyareta, koda ta auresa bazataji dadin danginsaba. to idanma bahakaba shi Wanda takeso din yamasan tanayi, inma yasan tanayi zesotane,mutumin da tasan ko kallo maryam bata ishesaba. Addu'a salimat tacewa maryam tadage da ita, tare kuma da nisanta kanta da haduwarsu da mustapha zataji saukin abun aranta,kuma dantariga tasawa ranta tsoronsane yiyasa takejin hakan akansa. Godiya na mata,cikin yarda da abunda tacemun batare da tunanin komaiba. Hirarmu muka cigaba dayi...... Se wajen magriba nabar gidansu salimat,bayan nabata kayan dana kawo mata taitamun godiya kuwa ita da umma, har gidan gwaggo salimat ta rakani,bayan umma ta karamun nasiha akan na tsare mutuncina. Koda na koma gida, gwaggo batanan ta fita, dama nayi mamakin yanda akayi har nayi wannan dadewar gwaggo bataje ta kiraniba, ashe batananne,amma da alamun ba nisa tayiba dannaga janyo kofar gidan kawai tayi bata rufe da kwadoba. Hajiya gwaggo anatafi kai kudi gidan adashi. Nanma seda muka kara wata sabuwar hirar sannan tatafi. se ana sallar magriba gwaggo ta dawo, time din data shigoma ni sallah nakeyi. "Sannu da zuwa gwaggo" nafada bayan na idar da sallah. "Uhm, aikece za'aiwa sannu kinje gidan uwartaki kinyi zamanki tana doraki akan hudubar banza ko" zanyi magana gwaggo ta hanani. "Rufemun baki ni, bansan jin komai daga gareki, gobe inkika zo base nakara barinki zuwaba, sannan abu nagaba danakeson fada miki, karki kara zuwamun batare da kudi masu yawa ko kayan masarufiba" "to ni inna ina zansamu kudi balle harna siyo miki wani abu, kudin aikatau dinma ko ganinsa banba, kawaidai matar gidan tacemun tabada ankawo miki lokacin danayi wata guda agidan" cikin fada gwaggo tace, "kajimun sakarar yarinya se'anbaki zaki kawomun, fakar idonta zakiyi ki dakko, kayanma kidinga sata da kadan_kadan kina boyewa idan yataru seki sato hanya kikawomun" dasauri na kalli gwaggo cikin matukar mamakinta ina maimaita Kalmar _Hasbunallahuwani'imalwakil_ araina, narasa hali nasan abun duniya irin na gwaggo,yanzu ita danake kallo amatsayin uwa ita take umartata danayi sata. Cikin takaici nace, "gwaggo satafa kikace, idan wataran aka kamanifa,koba hakabama gaskiya bazan iya sataba, sedai na dinga tara miki kudin makarantata" "to yar bakin ciki, me shegen bakin hali, kar Allah yasa ki iya din" bala'i gwaggo tashigamun tana zagida da tsinemun, nidai shiru na mata bakin ciki cunkushe azuciyata, har hawayen bakin ciki seda nayi. Sallamar wani yaroce tasa nasamu salamar bala'innata. Yaya sadiq ne yazo zamu wuce gida, kafin nayi wani yunkuri gwaggo harta fice gurinsa. Jakata nadauka nafito nima. Gwaggo nata masa banbadancinta a son zuciya irinnata yakara bata kudi, sadiq ganin maryam tafito yayiwa gwaggo sallama ya nufi mota. Tsayawa nayi inayiwa gwaggo sallama, akokarina nasan takoma gida, dan idan tana tsaye agurin bazata barni nakoma nayiwa su umma sallamaba, kuma nasan baba yadawo yanzu inason shima nagaisheshi. Gwaggo kuwa tasan nufin maryam shiyasa taki komawa gida, wai ita kar sadiq yace zegaida umma balle yabata wani abun. Seda taga nashiga mota haryakunnan munfara tafiya sannan ta koma ciki,tana cewa sadiq setazo gidan. Nikuma ina ganin haka nace masa nayi mantuwa banwa umma sallamaba, kashe motar yayi yace muje shima seya gaidata. Abakin kofar gidan ya tsaya nikuma nashiga, gaisawa mukayi da baba nayiwa umma da salimat sallama nakuma sanar mata da sakon sadiq, hijabi umma tasaka ta leko soro suka gaisa cikin girmamawa, godiya sosai umma ta masa akan dawainiyar dayakeyi akan maryam. Kudi sadiq yadakko yabawa umma, amma umma Sam taki karba karshema tashi tayi ta koma ciki. Saleemat data rakoni yabawa kudin, itama kin karba tayi, dakyardai ta karba ahakanma seda nasaka baki, sallama mukayi cike da kewa da begen juna muka rabu. Muna cikin tafiyane, yaya sadiq yadubeni yace, "wato zuwa kikayi kinata yayatani na miki abu ko?" Murmushi nayi nace, "a'a yaya kawaifa cemata nayi kamaidani makaranta,shine ta maka godiya" "Shikenan" yace atakaice.dubansa nayi dakyau nace, "yaya sadiq naga kamar wani abu nadamunka tundazu dazamu tafi, da'alamunma bakaje bikinba?" Numfashi sadiq yasauke yace, "banajin dadi ne maryam kuma gobe zanyi tafiya, daddy ya aikeni Abuja." "ayya yayana sannu mekedamunka" nafadi haka cikin tausayawa. _"cutar sonki"_ yafadi hakan aransa,amma a fili seyace, "ciwon Kaine da kuma gajiya" "sannu, Allah yakara sauki, kuma ahaka zakayi tafiyar,kadaga mana zuwa wani lolacin" girgiza kai yayi alamar a'a yace, "baze yiyuba abunda zanyi yana da mahimmanci." "Tom shikenan yaya, Allah yakiyaye hanya yakuma kara sauki" "ameen" yafada cikin sanyin murna. Shiru sukayi na wasu mintuna kowa da tunanin dayakeyi aransa, ni ina tunanin halin dazan shiga idan baya gidan, domin shine garkuwata,acikin gidan. Shikuma sadiq yana tunanin tayanda zefadawa maryam yana sonta. Candai na katse shirunnamu dacewa, "kuma kwana nawa zakayi a abujan?" "Zakiyi kewatane idannatafi" sadiq yatambayeta yana kallonta. Batare da tunanin komaiba, nace, "sosaima yaya" wani murmushi yayi yace, "kozaki binine mu tafi tare" "ai mommy bazata bariba" "Injiwa zata bari mana" "tom shikenan zanbika" nafadi haka ina murmushi. Daidai nan muka karaso gida. Seda yayi parking sannan yadubeni yace, "tun yamma aliya take kirana nabaki waya zaku gaisa, kishiga ciki kihuta kiyi sallah kici abinci, zanzo muyi magana,sekuma nakira miki aliyan" "tom yaya nagode sosai, se'anjiman" nafadi haka ina bude motar na fice. Dai dai lokacin da maryam tafito haidar yakaraso parking space din, zedau mota ze fita. Tsayawa yayi yana kallon maryam cike da mamaki, shida farkoma beganetaba sedaga baya,takara masa kyau. "dama haka yarinyarnan take da kyawun sura, shiyasa kullum cikin zunbula hijabi take, gatadai yar karama amma akwai kayan aiki, lalle zeso ya more wannan kyakkyawan jikinnata" yafadi haka aransa yana lasar lips dinsa..........✍️ *BY* *zeey kumurya* *ABUNDA KA SHUKA*......... _*(shizaka girba)*_ *MALLAKIN* 👇 *ZAINAB USMAN KUMURYA* *FARIN JINI WRITERS ASSO.....*📚 ~*Free novel*~ *Bismillahirrahmanirrahim* 2️⃣4️⃣ .........Tunda nafito daga motar na hango haidar,sanin danayi bawani shiri mukeba sena dauke kaina ina kokarin wucewa batare dana masa maganaba, kamar daga sama naji muryarsa cikin tattausan lafazi yana cewa. "Yanmata babu magana" cak na tsaya cike da mamakinsa da wanine yacemun koda a mafarki haidar zemun magana irin haka zan karyatashi domin tsakanina dashi magana cikin tsawa da masiface take hadamu. Murmushi na kirkiro nace, "ayya yahaidar bangankaba ina wuni" "lafiya kalau" ya amsa yana bina da wani shu'umin kallo, nidai daga haka bankara maganaba nayi gaba danse naji abun wani banbarakwai. Shiko haidar binta yayi da kallo yana ayyana mummunan kudirinsa akanta harta kulewa ganinsa. Ahankali nake tafiya ina zancen zuci harna karasa part dinmu, su mommy basu dawoba, me'aikin danake gani kullum tana zaune a falo tana kallo, gaisawa mukayi na wuce sama. Jakata na ajiye a daki nashiga kitchen nadibo abinci domin wata yunwa nakeji, a falo na zauna naci bayan na kunna kallo. Inagama cin abincin na shige daki, domin yin sallar isha'i. Bansan sanda su mommy suka dawoba, seda nagama duk abunda zanyi adaki na fito falo naga mommy ta fito daga kitchen. "Sannu da dawowa mommy" "yawwa maryam yakika baro mutan gidan" "lafiya kalu sunata agaisheku" "toh muna amsawa, yawwa maryam shiga kitchen zakiga nahada wa alh, abinci bari na dakko mayafi kibini part dinshi, dashi" cikin ladabi na amsa mata sannan na shige kitchen din na dakko, seda nadan jira sannan mommy tafito muka tafi. Daddy yana zaune a falonsa na tsakiya,yana karatun jarida yana kurbar ruwan shayi muka shigo falon. Wani sassanyan kamshine yadaki hancina, seyau nasamu damar bawa idona abinci a part din daddy. Gaskiya part din yahadu iya haduwa, danhar yafi na mommy kyau, amma nakasa gane wanne yafi kyau shida na mustapha, kawaidai abunda nagane yafi na mustapha girma. Masha Allah gaskiya kudi yana inda yake, komai najin dadin rayuwa akwai a part din daddy, duk da iya faluka biyu nagani a part din. Har kan hadadden dinning dinsa naje na'ajiye abincin, sannan na dawo gabansa na durkusa na gaishe sa. Amsamun yayi kamar kodayaushe cikin fara'arsa. Mikewa nayi namusu sallama nafice. Ina fita na hango yaya mustapha yana tahowa,ya kara waya a kunnensa,alamun waya yakeyi. Nandanan zuciyata tahau aikinta a duk lokacin data gansa, wata boyayyiyar ajiyar zuciya nasauke ina satar kallonsa ta gefen ido. Yayi kyau sosai yau shigar manyan kaya yayi, kansa harda hula. fitinanne kamshinsa yacikamun hanci,tun kafin yakaraso. Cikin takunsa nakasaita da daukar hankali yake tafiya. Wata nutsuwace naji ta lullubeni, dana gansa se ajiyar zuciya nake saukewa akai akai. Ahankali nake tafiya har mukayi clash, dakyar na harhado kalmomi abakina nace, "ina yini" ina dan rissinawa batare daya kalleniba yadagamun hannu ya wuce abinsa, yabarni da mayen kamshinsa. Lumshe idona nayi wani murmushin daban shirya masaba ya subcemun. Yanayin dana tsinci kaina na farin ciki baze misaltuba a wannan lokacin. Tunaninsa manne acikin zuciyata nakoma part dinmu, a falo na tarar da yaya sadiq yana kallon news shikadai azaune. Sallama namasa batare daya juyoba ya amsamun zama nayi a kujerar dake pacing dinsa nace, "yaya ya kannaka" "yayisauki sosai maryamaaaa" yaja karshen sunan yana kallonta. Nima shiru nayi ina kallonsa gabadaya duk ya canza yayi wani iri,kamar baya cikin nutsuwarsa, inajindai ko tafiyar dazeyice bayaso dole aka masa.ajiyar zuciya sadiq yasauke tare da dauke kansa daga kallon maryam, wayarsa yazaro daga aljihu ya lalubu number aliya ya danna mata kira. Alama yayimun da hannu alamun nazo na karba, tasowa nayi ahankali na karba na koma mazaunina tare da kara wayar akunnena. "Hello, yasadiq tadawo?" Murmushi nayi me sauti nace, "ehh nadawo" daga daya bangaren aliya cikin farin ciki tace, "mairota, ykk ya gida ya school ya samari?" "Komai da kowa lafiya kalau, samari kuma seku manya ai" nabata amsa fuskata dauke da murmushi har lokacin. "Hmmm zama kifadi gaskiya, nasan yanzu kinyi baby's irin ten dinnan a school idannazo zaki bani labarine" "nikuma sekace wata ke,dazanyi samari har 10, ya aunty?" Nakawar da wancan zancen da tambayar aunty. Aunty tananan klu, dafazamuzo muyiwa daddy sannu da zuwa to kuma munfara exam ne, sedai wani lokacin" "ohk, Allah ya kaimu, nifa ince nayi mamaki dabaku zoba naga anata zuwa gaishesa" "zamuzo nan kusa insha Allah" "Allah yakawoku lafiya" "ameen maryam, se anjima, zanyi karatune dama kira nayi naji ykk" "toh aliya nagode sosai kigaidamun da aunty pls" "zataji insha Allah, nima kigaidamun da nakarfen kafin nazo mugaisa" "Allah yashiryeki" nafadi haka ina dariya tare da kashe wayar. Mikawa yaya sadiq wayar nayi, daya tsaya kawai yana kallon maryam, ita batamasan yanayiba. Shiko ya kura mata ido yanda take magana cikin siririyar muryarta bakaramin kyau take kara masaba. Hira mukadanyi da yaya sadiq kadan akan makaranta, sannan mukayi sallama ya tafi, bayan yayi_yayi nafada masa menakeso yakawomun a tsaraba naki. Yauma a part din daddy zasuyi dinner, secan anjima zasu dawo. dakina nakoma nacigaba da al'amurana. A part din daddy kuwa, bayan maryam ta fita daddy ya juyo yana kallon mommy yace, "wai ko atika a ina kika samo wannan yarinyar?" "Meyafaru dear kake tambaya?" "Naganta batayi kalar yaran da'ake kawowa aikatau bane, kuma ni yanayin kallonta yanamun kamar nasan me irin kallon, kuma namijine" shiru mommy tayi cikin faduwar gaba, tabbas itama tadade tana kallon hakan agurin maryam din tun randa tafara ganinta, kuma ita tagane me irin kallon maryam din,amma bazata tunawa daddy ba danbataso ya tuna, yanzu seya ballo mata wani ruwan. Kuma abunda yake bawa mommy mamaki, kwata_kwata maryam bata kama da Wanda kallonnasu yake daya, amma yanda take dago idonta tana dan lumsheshi shima haka yake, musammanma dayana yaro, idan maryam tayi kallon se mommy taga tamkar shine dayana yaro. Numfashi ta sauke tace, "haba dear har akwai wani kallo nadaban da wani yakeyi,kallodai ai duk kallone, kawai kaikake ganin haka" kafin daddy yabawa mommy amsar maganarta mustapha ya shigo falon da sallama. Cikin tsantsar kulawa da kauna. suka amsa masa, zama yayi atsakiyarsu yana musu sannu da gida. Hular kansa yacire ya ajiye, dukta takura masa ga gajiya sosai ajikinsa. Tsokanarsa daddy yahauyi ganin yanda yaketa faman yamutsa fuska. Mommy kuwa kwantar dakansa tayi akan kafadarta tare da shafa lallausar sumar kansa. Cikin tattausan lafazi tace, "son ya taro da gajiyar biki" lumshe idonsa kawai yayi tare da daga mata kai alamar amsawa. Wayarsa dake hannunsa aketa kira, kindagawa yayi danyasan abokansane suke Neman caza masa kai, sunga basu gansaba. dan yanzuma sulalowa yayi ya gudo, da'ana zancen kai amarya, shikam baze iya wani kai amaryaba, sabgar mata ai ciwon kai zasu kara masa akan Wanda yake damunsa. Fahimtar da mommy tayi da gajiya atattareshi seta mike ta dakko masa ruwa da lemo me sanyi ta bashi yasha. Yakwaji sanyi aransa dandama da kishirwar atattare dashi. Mommy dakanta tayi masa tausa, tanayi tana jera masa sannu. Daddy kuwa nagefe yana kallonsu cike da ban sha'awa da burgewa, yanajin dadin yanda mommy take kula da mustapha yanda yakamata.......... washegari yaya sadiq asubanci yayi yatafi,hakan yasa bamu haduba. Drivern dayake dakkoni shine yakaini school yau. Duk senaji kewar yaya sadiq ta lullubeni, dama shi sabo haka yake. Yau laraba kwanan yaya sadiq biyu da tafiya, gaskiya nayi kewarshi sosai gidan duk badadi. A kwana biyunnan haidar yasakarmun fuska sosai, wani lokacinma idan muna zaune yayita jana da hira. Abunna matukar bani mamaki,haidar daya tsaneni sosai yanzu kuma shikemun haka. Bankawo komai arainaba na canzamun din dayayi. Suhailat ce dai jiya i yau, tamkarma kara mata tsanata akeyi. Yanzu kullum bayan magriba senaje gaida daddy har part dinsa bisa umarnin mommy, anannema nake ganin mustapha nake samun nutsuwa. Nadage ina karatu sosai saboda banaso nabawa yaya sadiq kunya. Yau tunda nadawo daga school naketa faman solving di maths da zee ta kara koyamun, danyanzu yafi bani wahala akan duka sauran subjects din da mukeyi. Alhamdulillah yanzu ina fuskantar turanci ba lefi, dan malamin lesson dina yadagemun sosai, kuma a school kwata_kwata ba'a Hausa se turanci shiyasa. Satina na uku kenan a school din, amma munyi text yakai 7. Gobe zamuyi ta maths din shiyasa na dukufa akanshi. Bayan magriba ina zaune a falo ina kallo nikadaice duk suna part din daddy, tunda yadawo ba kullum suke zaman part dinba. Nima banjima da dawowa daga gaisheshiba. Jinayi kawai ansa hannu an rufemun ido, a matukar tsorace nafara kokarin banbare hannun, amma na kasa. Sedayaga dama dankansa sannan ya sakarmun idon yana dariya. Dasauri na juyo ina kallonsa, haidar ne. Ajiyar zuciya nasauke na juyar dakaina bance masa komaiba. Zagayowa yayi yazauna akusa dani yana fadin, "matsoraciya jibi yadda duk kikabi kika wani firgice se sauke numfashi kike" nibesanma haushi najiba, dominni tsoratanin dayayi bedameniba kamar tabamun fuska dayayi, duk senaji raina ya baci. Danne bacin raina nayi nace. "Ai dole In tsorata yaya haidar, bansan da shigowarkabafa kawai jinka nayi." "Tom shikenan Allah yabaki hakuri yar kanwata" yafadi haka yana hade hannunsa guri daya alamar roko.🙏gyada masa kai kawai nayi, namaida hankalina akan kallon danakeyi. Jana ya shigayi da hira, nikuma ina kakkaucewa danse naji zuciyata bataso kasancewa dashiba. Ko fahimtar hakan yayi daga baya daya gaji dan kansa yatashi ya tafi. Nina matsuma gobe tayi yaya sadiq yadawo. Yau a part dinmu sukayi dinner, amma banda daddy da mustapha. A gurin serving dinnasuma haidar se magana yakemun ina basarwa,harda cewa nima nazauna naci abincin tare dasu mana nace masa aini nakoshi. Dasuka gamama ina wanke_wanke a kitchen seda yakara shigowa ya takuramun. Besan banason wannan kusancinnamu dashiba, dan haka kawai naji zuciyata bata yarda da wannan canjinnasaba. Misalin karfe biyu na dare na tashi domin yin sallar nafila, ina toilet ina alwala naji kamar motsi adakina, dif nayi domin natabbatarwa. amma se naji shiru,cikin tsananin tsorata naja kafata ina sanda nafito zuciyata na dukan uku_uku. Dama kofar toilet din abude nabarta saboda bankunnan hasken dakinba, na toilet dinne kawai a kunne. Cikin dan hasken dake dakin, naga kamar gilmawar mutum yafita tare da jan kofa. Jikina har rawa yakeyi saboda tsoro, dama gani sarkin tsoron. hannuna na karkarwa na kunnan light din dakin haske ya gauraye. Bin dakin nahauyi da kallo cikin faduwar gaba, tabbas anshigomun daki, saboda wani irin kamshin turare Mara dadi danaji yana tashi adakin,bugun zuciyatane ya karu,saboda razani. _la'ilaha'illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin_ nashiga maimaitawa araina ina tunkarar kofar dakin, inajan kofar kuwa ta bude, alamun babu key ajikinta,kuma ni nasan akulle nabarta. Wani matsanancin tsorone ya kara lullubeni addu'a nashiga karantowa a fili, jinake kamar na leka falon naga kowaye amma kuma tsananin tsoro yahanani lekawar..ahankali namaida kofar na rufe tare dasanya mata key. Zama nayi abakin gado hawaye na zuba daga idona, abun yazo kaina kenan. afili na fara magana. *ya Allah kakareni daga dukkan me nufina da sharri , ya Allah kada kabawa koma waye damar ketamun haddi, Allah narokeka, Allah kakawomun dauki, acikin wannan al'amari* kuka nafashe dashi meban tausayi, bantaba tsorata da abunda baaba talatu tacemun irinna yauba, takurewa nayi akan gado, tsoro da razani duk sun baibayeni, gani nakeyi tamkar mutumin zedawo. gashi bani dame taimakona a wannan Daren, idan mutumin dayawo, mommy yanzu a part din daddy take kwana daga ni se suhailat asaman yanzu. Kalaman innata data taba fadamun sune suka dawomun arai. _*maryam, wani baya karewa wani abunda Allah yakaddara seya samesa, duk abunda yasameki na kunci kona damuwa, kada kinemi taimakon kowa se Allah, shikadaine ze iya kareki daga sharrin me sharri, kisawa ranki Allah yana tare dake aduk inda kike, kuma shine zekareki akan komai, kikasance memikawa ALLAH kukanki daneman taimakonsa akodayaushe.*_ wasu hawaye masu dumine suka shiga kwaranyomun saboda tunawa da innata. nadade a dunkule nikadai ina faman rera kuka da addu'a araina. Dakyardai na rarrashi zuciyata na mike nakoma toilet nasake dauro alwala nafito nasaka hijabina na tada sallah domin kaiwa Allah kukana. har ketowar alfijir ina gaban ubangiji,seda aka kira sallah natsagaita. zama nayi tare da rafka uban tagumi ina tunane_tunane, tunanin hanyar kawai dazanbar gidannan nakeyi,tunda ankawomun hari nafarko gobema za'a iya kawomun na biyu gwara kawai nabar gidan na huta. sallar da'aka tayarne yasani mikewa nabi limamamin nima. Bayan an idar na dakko alkur'ani me girma nashiga karantawa, izu biyu nayi nadakko addu'ar da aunty tabani itama na karanta. Seda gari yayi haske tangararau sannan na mike daga kan dadduma nafita nafara ayyukana. Jikina asanyaye yau nakeyin komai tamkar wacca kwai yafashewa aciki, kuku naganina yafara tambayata meke damuna ko banda lafiyane, babu komai kawai nace masa,danni yau maganaba banaso nikadai nasan halin da zuciyata take ciki nafargabar zaman gidannan. Ina gama ayyukana nakoma daki nayi wanka nashirya cikin uniform dina. Kotunanin abinci banba nazumbula hijabina nafito domin tafiya school. Mommy nagani a falo taci kwalliya da'alama turakar miji zata koma. Gaisheta nayi ta'amsa tana bina da kallonta, yaukam ta kuramun ido sosai. Harna fara tafiya ta tsaidani da fadin. "Maryam lafiya kike kuwa,naganki haka?" "Lafiya kalau mommy, kainane kedanmun ciwo" nabata amsa kwalla nataruwa a idona ta tausayin kaina. "Ayya sannu, Allah yasawwake dafatandai kinsha magani ko?" Kaina gyada mata alamar eh. Sannu ta karamun nikuma nafice. Kodanaje makarantarma su zee da salma setambayata suke lafiya nake, nace musu marata kemun ciwo kawai dansu barni. Sannu sukamun dafatan samun sauki. Dakyar na iya zana text din damukayi, danni yau komai ya kuncemun tsoro da fargabane kawai acikin raina. Gashi yau bamu tafi gida da wuriba saboda munyi practical din biology. Seda 4 tawucema nadawo gida. Abun mamaki ina shiga falo naga yaya sadiq zaune, dama ina school Inata addu'ar Allah yasa yadawo. Jinayi gabadaya Rabin damuwata tatafi, wani farincikine ya lullubeni kamar naje narungumesa haka naji. Murnar danakeyi taganinsa kasa boyuwa tayi, zama nayi ina jera masa sannu da zuwa da tambayarsa ya hanya. Shikuwa sadiq ganin yanda maryam tayi murnar ganinsa alamun tayi kewarsa seyaji tamkar anmasa albishir da aljannah, domin hakan nanuni da cewa itama tafara damuwa dashi. hira muka dan taba yana tambayata ya karatu da komai da komai nace masa komai lafiya. daga karshe yacewa maryam taje ta kimtsa tafito tasamesa afalo. saboda sadiq yakudiri niyyar yau zesanar da maryam abunda ke ransa,koyahuta. Wanka nayi tare dayin sallah sannan naci abinci, dan yunwa tafara nukurkusata. Kamar yadda yaya sadiq yace nasamesa afalo anan naje nasamesa. Shikadaine a falon ya kwantar da jikinsa ajikin kujera idanunsa a lumshe. Zama nayi agefensa inafadin "sannu yaya sadiq ya gajiyar" bude idonsa yayi yasaukesu akan maryam sannan yace, "yawwa maryama be babban suna, kema sannunki, yakaratunne" "alhamdulillah yaya" gyadamun kai yayi tare da janyo ledar dake gefensa ya mikomun yana fadin ga tsarabarki tunda kinki fadamun abunda kikeso" cikin jin kunya nace, "yaya sadiq mekuma kasiyomun kaibaka gajiya dan Allah dayimun hidima, abun yayi yawa wl.... "Shiiiiii" yaya sadiq yakatseni yana Dora danyatsansa abaki yace, "babu wata hidima maryam anan, kuma banason wata doguwar godiya rike kawai" karbar ledar nayi tare da fadin ''nagode" hararata yayi saboda godiyar dana masa, murmusawa nayi ina kallonsa. Gabadaya yarame yayi wani iri, kamar bashiba. Kasa daurewa nayi nace, "yaya lafiya kuwa naganka wani iri kokayi cutane a tafiyar dakayi" girgizamun kai yayi alamun a'a tare da fadin, "wani abu ke damuna maryam, gabadaya yahanani sukuni dajin dadin rayuwa" "subhanallah wanne irin abune wannan yaya sadiq?" natambayeshi cikin yanayin damuwa. "Idan kinjima bazaki iya magancemunba kitayi da addu'a kawai" marairaicewa nayi nace, "karkace haka yaya, kafadamun mana koda da shawarace se'inbaka da kuma addu'ar" harga Allah nadamu da damuwar yaya sadiq,senaji duk babu dadi dayace wani abu nadamunsa. Sadiq kuwa juya abunda zecewa maryam yakeyi aransa, besan yazataji abunba kokuma ta daukesa. Ganin yayi shiru yana tunani sena cemasa. "Shikenan yaya, Allah yayayemaka koma meke damunka tunda bazaka fadamunba." Kallona yajuyo yayi nawasu sakanni,kamar yadda nima nake kallonsa, zuciyata nadan harbawa. wani gwauran numfashi yasauke. Ya dauke kansa daga kallona yace, *MARYAM! CIWON SONKI KEDAMUNA!!*..........✍️ *BY* *zeey kumurya* *ABUNDA KA SHUKA*......... _*(shizaka girba)*_ *MALLAKIN* 👇 *ZAINAB USMAN KUMURYA* *FARIN JINI WRITERS ASSO.....*📚 ~*Free novel*~ *Bismillahirrahmanirrahim* 2️⃣5️⃣ *DEDICATED TO👇* *MEERAH* *NANA* *Xeey* *abjamila824* *Jidderh m Ahmad* *Maman jani* *pheenar_Abdallah* *Aseeyah* *Comments dunku nasani nishadi masoyan asali,nagode sosai Allah yabar kauna*❤️🥰 ...........Cikin tsananin dimuwa dajin kalaman yaya sadiq nake kallonsa baki bude cikin rashin abunyi, tabbas ayanda yayi maganar babu alamar wasa acikinta,balle ince wasa yakemun. Wani yawu na hadiye cikin rawar murya nace, "yaya sadiq kasan me kake fada kuwa, kokamanta maryam ce agabanka yar aikin gidanku?" Juyowa yayi yana kallona da idanunsa da suka sauya launi,cikin wata kasalalliyar murya yace, "nasani maryam, nasan kece agabana,kuma gaskiyar abunda ke zuciyata nake fadamiki *INA TSANANIN SONKI DA KAUNARKI MARYAM*" yakarasa zancen yana taune lips dinsa gami da runtse idonsa. Tashin hankali Wanda ba'asamasa rana, wacce irin fitina yaya sadiq yakeson kunnomun agidansu dazece yana sona. Wani gwauron numfashi nasauke zuciyata na dokawa nace, "yaya sadiq!" bude idonsa yayi yazubamun amma bece komaiba. Kasa nayi dakaina narasama mezance masa, ganin abunnake tamkar mafarki nakeyi yauni yaya sadiq yace yana sona, *"SO FA!"* girgiza kaina nahauyi ahankali nafara magana batare dana dago kainaba. "Yaya sadiq wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa babu........ "Look maryam banason jin wadannan kalamanki, please and please maryam, ki amincewa soyayyata, zuciyata nagab da bugawa. idan har kikaki amsar soyyata zanshiga mummunan hali. Maryam na miki alkawarin bazaki kuka daniba insha Allah, zanzame miki bangon rayuwa, zanshayar dake zallar kauna da tsantasar soyayya azamanmu" dagowa nayi na kallesa da sauri yanda yaketa rokona,gabadaya ya marairaice duk yabi yabani tausayi. Kaina gabadaya ya kulle narasa abunyi, wannan shine karon farko arayuwata da wani danamiji yace yana sona, kuma mutum me kima da daraja a idanuna. Kawar dakaina nayi daga kallonsa nace, "dole nafadi abunda bakasan ji yaya sadiq, nifa mutum ce talaka ba yarkowaba, kaikuma fa,da akwai bambamci sosai atsakanina dakai kuma ni gaskiya ayanzu babu soyayya atsarina domin banshirya mataba, kayi hakuri idan kalamaina sun bata maka rai." Runtse idonsa yayi cikin takaicin kalamanta zuciyarsa na masa zafi yace, "maryam bakisan soba, bakisan zafinsa da radadinsaba. So baya duba cancanta ko kamata balle kuma matsayi. So baya shawara a lokacin daze shige zuciyar mutum. kisani inasonki a duk yanda kike koda kece karshen talauci a duniya, da talaka dame kudi duk dayane agurin Allah, nima haka yake agurina, dan haka kicire batun matsayi a soyayyata dake. Bazan miki doleba kokuma na tursasaki akan dole sekin soniba, kuma dan Allah banason kiduba abubuwan dana miki kice zaki soni dan haka, nafison kisoni dan karan kanki. amma zanbaki nanda kwana 3 kije kiyi shawara,akan haka, kuma kada ki cuci kanki,wajen bani amsa. nabarki lafiya" yakarasa zancen yana Mikewa tsaye. Bejira amsar da maryam zata bashiba yafara tafiya, cikin daci da kunar zuciya,kallona daya mutum zewa sadiq yagane yana cikin tsananin damuwa. Daskarewa nayi a zaune tamkar mutum mutumi ina binsa da kallo amma nakasa magana, harya fice daga falon. Lumshe idona nayi ina sauke dogon numfashi. "Anya kuwa nayiwa kaina adalci, yaya sadiq be cancanci nakishiba, yamun halacci arayuwa, amma inda matsalar take mahaifiyarsa, koda na amince masa munfara soyyya ba yarda zatayi da auranmu, musamman da abun yahadarmun biyu ga rashin asali ga kuma talauci." Nafadi hakan araina. Nakasa tabuka komai, kwakwalwata ta tsaya tunaninma nakasa, inadai zaune ni kadai afalon. Addu'a nakeyi Allah yasa mafarki nakeyi bagaskiya bane wannan al'amari. Kiran sallar magriba ne yasani motsawa na mike tare da daukar ledar da yaya sadiq ya bani nayi dakina, zuciyata cike fal da damuwar bakon al'amarin daya tunkaro rayuwata Wanda bantaba tunaninshiba koda nan gaba.cikin sanyin jiki nayi alawala nayi sallah, nadade ina addu'a acikin sujjadata akan Allah ya warwaremun duk wata matsala ta rayuwata yakuma tabbatarmun da abunda yake na alkahairi agareni. Ga matsalar jiya bangama fita daga cikiba yau ga yaya sadiq ya kara shigomun da wata. Koda na idar da sallarma zama nayi Inata tunane_tunane. Da kyar na iya yunkurawa domin zuwa nagaida daddy. Ledar da yaya sadiq yabanima ko budeta banma na'ajiye acikin loka. Mommy da daddy da suhailat sukadai na tarar a falonnasa. Tunda maryam tashigo daddy ya kura mata ido yana kallonta, yarinyar tana matukar bashi sha'awa hankali da nutsuwarta, yanaso yamata tambayoyi akan rayuwarta, musamman yanzu daya gano da Wanda kallonnasu yake iri daya ga kuma muryarta datake masa........."ina wuni daddy" muryar maryam ta katse masa tunani, da gaisuwarta. Cikin fara'a yace, "lafiya kalau maryama, ya karatunnaki" "Alhamdulillah" "to masha Allah, Allah yataimaka yayi albarka" "ameen daddy nagode" nafadi haka cikin jindadi ina mikewa domin komawa. Inajin dadin addu'ar daddy akodayaushe kullum nazo seya samun albarka. Sallama nayi musu na fice... Daren yau gabadaya a wani irin yanayi nayishi, tunanin abunda yaya sadiq yafadamun yamun tsaye a zuciya. Ga kuma tsananin tsoro na abunda yafaru jiya, I najin tsoron karyauma a kara shigomun. Addu'a makamin mumini ita nakama inatayi afili da cikin zuciyata. Abunda yakara tadamun da hankali danazo serving dinsu na dinner babu yaya sadiq, da mommy ta tambayi su haidar sesukace yace bayajin dadine. Shiru naga mommy tayi bata kara cewa komaiba. Senaji duk babu dadi, yanzu akaina yaya sadiq ko abinci yakici, akaina ze shiga damuwa irin haka, gaskiya yakamata nayi tunani kada nazama me saka alkhairi da sharri. Nima kasa cin abincinnayi se sakawa da kwancewa nakeyi, idannayi tunanin amincewa yaya sadiq se kuma intuno badakalar daza'asha alokacin dazancen yafito. Karshedai na yanke shawarar zanyi shawara da zee gobe idan Allah yakaimu naje school. Baccina nayau rabi da rabine ga tsoro ga damuwa, danaga abun bana kare bane sena tashi na nahauyin sallar nafila........... Washegari, kamar kodayaushe 7/30 nagama shirina, nasaba yaya sadiq kafin wannan time din yazo falo yana jirana, amma yau dana fito senaga wayam babushi. fita nayi koyana mota yana jirana amma nanma se driver nagani, yacemun tundazu yake jirana oga yace shize kaini. Hankalinafa idan yayi dubu yakara tashi, me yaya sadiq yake nufi, jikinnasane kokuma me? bani dame bani wadannan amsoshin seshi. Da'aka fita break yau banfitaba, dama ni ba kullum nake fitaba, balle yau danake cikin damuwa. Su zee dai sun fita. bata jimaba ta dawo ita kadai. Zama tayi agefena tace, "maryam Ahmad lafiya, yau naganki sukuku dake, kodai jikinnakine.?" Girgiza mata kai nayi alamun a'a sannan nace, "zee yau wata matsalace dani nake Neman shawararki amma dan Allah inaso abun yazama sirri tsakanina dake." Cikin mamaki zee take duban maryam, tace. "Matsala kuma maryam wacce iri" numfashi nasauke. "nabawa zee labarin abunda yake faruwa atakaice." Cike da tsantsar mamaki zee take kallon maryam, domin bata taba tunanin maryam aiki takeyi agidan alh menasaraba. dan batayi kala da masu aikiba. Gyara zama zee tayi tare da dafa kafadar maryam tace, "kamar yadda kikafadamun sadiq ya miki abubuwa arayuwa na alkhairi yakamata kema kisaka masa da alkhairi. Kicire tunanin wai mahaifiayarsa ko yan'uwansa baza susokiba, wannan duk ba matsala bace, domin badasu zaki zaunaba, kuma babu wanda ya isa yahana abunda Allah yarubuta faruwa, duk bala'i da masifar mutum kuwa,idan Allah yayi ke matarsace babu Wanda ya isa ya hana. Maryam zanbaki shawara wadda nasan zakiji dadinta, bazan taba fada miki abunda ze cutar dakeba, danko nice bakebama haka zanyi. Ki amshi soyayyar yaya sadiq hannu, bibbiyu natabbata bazakiyi danasaniba nangaba. Yaya sadiq yakai asoshi, gashi kyakkyawa, ga kirki ga saukin hali, gadai abubuwa na qualities dayawa yana dashi wanda kowacce mace zataso mijinta yakasance haka. Kuma koda yanzu bakyajin sonsa azuciyarki nangaba zaki sosa. Yarinya kisaki jiki kawai Ku kwashi romon soyayya, gashi kun bala'in dacewa dashi kuwa" takarashe zancen da murmushi a fuskarta. Shiru nayi ina juya maganganunta araina, tabbas duk abunda zee tafada gaskiyane, kuma insha Allah zanyi amfani da shawararta duk da haryanzu wani bari na zuciyata cike yake da tsoron yau nice da soyayya, nida banmasan menene sonba, balle harna iya wata soyayya. Ajiyar zuciya nasauke nace, "nagode sosai kawata, Allah yabarmu tare insha Allahu zanyi amfani da shawararki." "Yawwa tawan kokefa, Allah ya kade muku fitina da sharrin shedan atsakaninku yakuma tabbatar mana da alkhairi musha biki" ta fadi haka tana rungumoni ajikinta. "Ameen" nafada cikin jin kunya. "Inyeee, yanmata masoya harna hangoki kinawa yaya sadiq kallon luv, dan wannan idanunnaki masu kyau nasan zasu bada wuta wajen kara hargitsashi." Zee tafadi haka cikin shakiyanci. Dariya namata kawai cikin jin dadi, senaji tamkar ansauken wani katon dutse daga kirjina, duk senaji na matsu a tashi injewa yaya sadiq dina da daddadan albishir. Amma duk wannan abun dake faruwa daga jiya zuwa yau, tunanin yaya mustapha nanan daram araina kamar kodayaushe, amaimakon idanuna su dinga haskomun hoton yaya sadiq senashi kawai nake gani. "Wannan bawan Allah, bansan sanda zandena tunaninshiba, tare dajin faduwar gaba idan na tunoshi" nafadi haka araina ina lumshe ido😳🤐.......... Yau din senajita wata tadaban arayuwata inajin tamkar ancanzani. Ina dawowa gida natarar da yaya sadiq shikadai a falon mommy, da alama beje office ba. Wata sassanyar ajiyar zuciya nasauke na shiga falon da sallama. Sadiq dake kwance akan kujera 3 star tunanin maryam yahanashi sukuni, daga yammacin jiya zuwa yanzu dabe gantaba gaba daya yakasa samun nutsuwa. Amsa mata yayi yana binta da kallo, duk yanda yaso dauke idonsa daga ganta amma yakasa,wani garin ciki yaji sanda yaganta ajiyar zuciyarsa yahausaukewa akai akai dama dawowar tata yake jira. Nikuwa ganin yaya sadiq yana kallonta senayi kasa da kaina cikin jin kunya, zuciyata na bugawa. Ahankali nakarasa garesa naxauna aka can carpet nace, "yaya sadiq sannu da gida yajikinnaka" "dasauki maryam ya makarantar?" Yafadi haka yana tashi zaune, cikin sanyin murya me tattare da damuwa. "Alhamdulillah" daganan nayi shiru ina wasa da yanyatsun hannuna, nama rasa ta ina zanfara masa maganar, kalmomun bakina duk sun gudu. Fahimtar hakan sadiq yayi yace, "maryam kamar da magana abakinki ina fatandai lafiya ko" tattaro duk wata nutsuwata da juriyata nayi na daure nace, "yaya sadiq na'amince da soyayyarka." Nafadi haka cikin rawar murya. farincikin da sadiq yaji alokacin da maryam tafadi haka baze misaltuba, hannu yadaga sama yace, "Alhamdulillah" har sau uku. Fuskarsa dauke da fara'a bakinsa yaki rufuwa,betaba tunanin zata amince masa haka da wuriba,tsareta yayi da idanunsa cikin tsananin farin ciki,yakasa dauke idonsa daga ganta. Mikewa nayi da sauri nafara tafiya cikin sassarfa saboda matsananciyar kunyarsa data lullubeni. "Kije ki shirya, kifito zamuyi magana" natsinkayi muryar yayasadiq yana fadar haka, banjuyoba nidai nashige daki. Tsayawa nayi ajikin kofa ina sauke numfashi tamkar wadda tayi tseren gudu, gani nakeyi kamar nayi gaggawar amincewa yaya sadiq, amma idannatuna kalaman zee se inji hankalina ya kwanta.nadade atsaye ina jimantawa kaina, dakyar naja jiki nashiga toilet na watsa ruwa tare da dauro alwala nafito natada sallah. Ina sallah tunanin tsarabar yaya sadiq ta fadomum arai, aiko ina idarwa na dakko ledar na bude danganin menene aciki. Waro idona nayi waje duka saboda abunda nafara tozali dashi, wayar hannuce kirar android yar madaidaiciya. Bansan takan wayaba balle nasan matsayinta kawaidai tun a jikin kwalin naga anrubuta _Samsung_ ajikin wayarma haka. Ajiyeta nayi agefe, domin gaskiya mayar masa da wayar zanyi, abun yayi yawa dawainiyar tayi yawa gaskiya. Se abu nabiyu dana gani agoguna guda 6 na karfe masu matukar kyau da daukar ido. Gaskiya na jinjinawa yaya sadiq a wajen kyauta, shiko gajiya bayayi nihar kunyar amsar abu nakeyi ahannunsa. Wata takardace ta karshe anannade, se tashin kamshi takeyi. warwarewa nayi naga rubutune amma typed akayi. Gyara zama nayi nafara karantawa kamar haka: *________________________________________* ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️ _*SAKON ZUCIYATA ZUWA GAREKI MARYAMA SARAUNIYAR MATA, TAURARUWATA SANYIN IDANIYATA*_❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️ _*maryam, kisani sonki yamun babbar illa acikin zuciyata nagane hakanne ta hanyoyi kamar haka, akowanne second dayake shudewa tunaninki na manne acikin zuciyata, aduk lokacin dana dau wasu awanni bangankiba senaji gabadaya nutsuwata tatafi, harse naganki nake samun nutsuwa. Idanuwana basa gajiya da kallon kyakkyawar fuskarki, aduk.lokacin dana ganki inajin farin ciki Mara misaltuwa acikin zuciyata, inajin wata nutsuwa me tattare da nishadi tana bin gabban jikina, ianjin dama in dawwama ina kallonki,zuciyata na bugawa aduk lokacin dana tunaki. Komai naki na burgeni, maganarki, nutsuwarki, tafiyarki,tattausan murmushinki. Akodayaushe hoton kyakkyawar fuskarki na manne acikin idona da zuciyata, mar.........*_ Wani yawu me daci na hadiye makut, zuciyata na mahaukacin bugu, jikina gabadaya yakama rawa takardar ta fadi kasa batare dana karasa karantawaba, wani uban gumine yahau tsatstsafomun ta ko ina ajikina. dakyar na'iya furta Kalmar "innalillahi,wa'inna ilaihirraji'un." Meyake shirin faruwa da rayuwatane, duka abunda yaya sadiq yarubuta amatsayin soyyayya agareni, sunakeji akan yaya mustapha, kenan hakan yana nufin nima nakamu da son yayamustapha, *sonsa nakeyi.* Tashin hankali!.............✍️ _kuyi manage da wannan pls,tun shekaran jiya naso Baku sekuma nafita,jiya kuma naje school bansamu kainaba se dare,nafara typing bacci yadaukeni seyanzu nasamu na muku. kuyi hakuri da typing error banyi editing ba ina saurine zani school_ *BY* *zeey kumurya* *ABUNDA KA SHUKA*......... _*(shizaka girba)*_ *MALLAKIN* 👇 *ZAINAB USMAN KUMURYA* *FARIN JINI WRITERS ASSO.....*📚 ~*Free novel*~ *Bismillahirrahmanirrahim* 2️⃣6️⃣ ..........."innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un, allahummma ajirni fil masibati, wa'aklifni khairan minha" naita maimaitawa a fili, cikin dimuwa da razanin kwakwalwa, zuciyata na tsananta bugu. Tabbas babu tantama son mustapha nakeyi, nashiga uku ni maryam wacce kaddarace ta kawoni gidannan ta wahala kota azabar rayuwa zankirata. Mikewa tsaye nayi ina goge gumin dake tsatstsafowa asaman goshina. zarya nafarayi ina kaiwa da komowa,cikin mawuyacin halin dabansan yazan misalta muku shiba. Sonake hawaye yasilalomun ko zanji dadin abunda nakeji acikin zuciyata na damuwa. "Yazama dole nacire soyayyar mustapha daga cikin zuciyata, to tayaya? Natambayi kaina, tunanin maganar damukayi da saleemat na tuno. Babu shakka saleemat tagane son yamustapha nakeyi shiyasa tace nayi nesa dashi. Tahakane kawai sonsa zebar cikin zuciyata, kuma sannan zanyi kokarin ganin na cusa son yayasadiq acikin zuciyata tare kuma dadagewa da addu'a, ta hakanne kawai wannan *kaddararren son* zefita daga zuciyata, wannan wanne irin jarabtace, son Wanda besan kanayiba, bemasan dazamanaba, banda haukan so ta bakin yaya sadiq inani inason yayamustapha. mutumin dabe Masan inayiba, besan daniba. zama nayi ina sauke ajiyar zuciya, aganina nasamu mafitar cire son yaya mustapha acikin zuciyata. tunane tunane nayi tayi har akayi sallar isha'i amma nakasa mikewa nayi, yau tsabar firgici kogaida da daddy banjeba, nama manta. dakyar na lallaba naje nayi alwala nadawo nayi sallar. Acikin sallahta addu'a natayi akan Allah yaciremun son yaya mustapha acikin raina,nama godewa Allah dasonnasa beyi mugun tasiri azuciyata. Ina zaune na rafka uban tagumi, naji ana knocking kofata. Ahankali na mike naje nabude, yaya sadiq nagani tsaye,nishaf namamanta yace zamuyi magana. Kasa nayi dakaina saboda kallon daya tastareni dashi, banason yagano wani abu nadamuwa kokadan. Juyawa yayi yana cewa, "kikaraso muyi magana" cikin sanyin jiki nabi bayanshi batare dana amsaba, na zauna agefensa. Yau samannamu shiru, duk basanan, tunda nadawoma ko mommy banganiba nasan suna part din daddy. Satar kallon yaya sadiq yayi, shima duk ya rame kamar baya cikin nutsuwarsa, duk yayi wani iri. Ko duk sonnawane yamaidashi...... "Maryam naji dadin amincewa soyayyata dakikayi, nayi farin ciki Mara misaltuwa, harna rasa bakin miki godiya. Amma dan Allah inason kifadamun gaskiya, har zuciyarki abunda kike fadamun gaskiyane, kokuma kin amincewa soyayyata dan wani abu, kokuma dan kina ganin idan kikaki amincemun kamar bakiyi halarciba. nibanason natursasaki balle namiki dole akan soyyata, kuma banaso ki cutu, inafatan kingane menake nufi. Gyada masa kai nayi cikin danne damuwata nace. "duk abunda nafada maka yaya, har cikin zuciyata yake, cancantarka da kamatarkace yasa na amince maka. Kowacce mace datasan kanta, zatayi alfahari dakai idan ta sameka amatsayin mijinta, shiyasa nima bazanso damarnan ta subcemunba." Daga haka nayi shiru danbansan mekuma zankara cewa, wadannan dinma dakyar na iya furtasu burina a yanzu kawai insamu kadaici. Cikin jin dadin maganganun maryam sadiq yace, "gaskiya bazance nataba jin kalamai masu dadin wannan arayuwataba,idanma naji toh gaskiya namanta, yau kam maryam kinwarkamun da ciwon dake damuna acikin zuciyata, yau zanyi kwanan farinciki dana dade banyi irinsaba, nagode,nagode, nagode sosai, maryam da amsar tayin soyayyata dakikayi, ubangiji yamiki sakayya da gidan aljanna" "amin" na'amsa ina sauke numfashi nakara da fadin, "ammafa yaya sadiq akwai matsala a soyayyarmu" dasauri yajuyo cikin mamaki yana kallona, yace. "Matsala kuma wacce iri kenan" gyara zama nayi cikin jin dacin abunda zanfada nace,"Yaya sadiq koda ahalinka basu hana soyyarmu saboda talaucinaba zasu hana saboda rashin asalina, ninan dakake ganina bansan mahaifinaba kuma bansan kowa nasaba, dangin mahaifiya kawai gare..." Nakasa karasa zancena saboda kukan dayake kokarin kufcemun. Cikin tsananin tausayawa yaya sadiq yace, "kada kidamu maryam dan wannan, ni sadiq ina sonki ahaka kuma zan iya rayuwa dake ahaka, insha Allahu kuma zantayaki da addu'ar Allah ya bayyana miki dangin mahaifinki. Kuma indai maganar iyayenane, daddy bashi da matsala, shi mutum ne me fuskantar abu da kuma masa duba na fahimta, nasan insha Allahu ze fahimcemu. Ita kuma mommy nasan ta yanda zan shawo kanta,harta amince, kikwantar da hankalinki banason ganin kina damuwa." Ajiyar zuciya nakara saukewa akaro na babu adadi, nace. "Shikenan insha Allah zandena damuwar, sannan kuma yaya ina neman wata alfarma dakai guda daya a soyayyarmu dan Allah kamun ita" "uhm, inajinki fadamun wacce irin alfarmace." Cewar sadiq yana maida hankalinsa duka akan maryam. "Yaya sonake ka boye soyayyata dakai,tayanda babu Wanda ze fuskanta" cikin sauri sadiq yace, "banganeba mekike nufiba?" "Ina nufin midunga soyayyarmu aboye kada kowa nagidannan yasani ko kuma wani awaje har zuwa wani lokaci nan gaba." "To maryam mene fa'idar hakan, akwai wani abu aibune a soyayyar tamu, nikam nafison nanuna miki soyayya agaban kowa ta yanda zaki tabbatar da har zuciyata ina sonki" "kayi hakuri yaya, dan Allah kamun wannan alfarma, ina da dalilin haka, idan lokaci yayi zanfada maka dalili. Shiru yaya sadiq yayi na wasu sakanni, sannan yace. "Shikenan maryam namiki wannan alfarmar, inafatan lokacin bame tsaho bane." "Bawani me tsaho bane insha Allah" "tom shikenan kikoma ciki ki huta naga kamar duk agajiye kike, da safe zamu karasa magana" kai kawai na gyada masa na mike na koma daki, dama nagaji da zaman. Shiko sadiq binta yayi da kallo, cikin so da kaunarta gami da tausayinta, ya lura tabbas akwai abunda yake damunta, a yanzu amma ze tambayeta da safe yaji. Ina shiga daki na kwanta saboda nemawa kaina nutsuwa dan har wani jiri_jiri nakeji yana dibata. ********** Apart din daddy kuwa, yau yaran gidan duk basu je canba, mustapha yana part dinsa suhailat kuma taje gurinsa,dama sune suka fiya zama a part dinnasa. Mommy ce kawai tare da daddy suke hira. Daddy yana lura da lokacin da maryam take zuwa gaishesa, yauseyaga har lokacin ya wuce bata zoba, har an fara kiran sallar isha'i a wasu masallatan. Duban mommy yayi danyakasa hakuri, domin aduk lokacin dayaga maryam zuciyarsa na kokarin tuno masa wani abu daya manta. Yace, "hajiya yau kinga yarinyarnan shiru batazo gaidaniba ko lafiya" takaicine yaturnike mommy, bedamu da yayansa nacikinsa dabasu zoba sewatacan daban, danne rashin jindadin hakan tayi tace, "kasan jiki da jini, kilan tadawo daga makaranta ta gajine, amma innakoma part din zantambayeta dalili." "Hakane, ai yarinyarma tana da kokari gata da hankali da nutsuwa daga ganinta daga gidan tarbiyya tafito" daddy yafadi haka yana mikewa domin zuwa yayi alwala yatafi masallaci. Wani kallo mommy tabishi dashi batace komaiba, se abubuwan datake kissimawa aranta. Shidai daddy toilet yanufa yayi alwalarsa yafice. *_________________________________________* *MUSTAPHA* *_________________________________________* Komai na tafiyar masa yanda yakamata, musamman agurin aiki, dasukayi promotion din dazasuyi, amma duk da haka yanzu basosai yake samun kansaba, tunda daddy yana gari. Kullum bayan magriba seyaje sun tattaunawa akan harkar kasuwancinnasu, se can dare yake samun kansa. Yau kam daya dawo akwai aikin dazeyi shiyasa beje part din daddyba sedai waya da sukayi, yana dawowa daga masallaci yadukufa akan system. Suhailat bayan ta dawo daga school da yamma likis kamar kodayaushe. Wanka tayi ta shirya cikin wasu hadaddun kaya riga da skirt yan kanti. Tayi kyau sosai, ta bulbule jikinta da turaruka se tashin kamshi takeyi. Yau sotakeyi ta gigita yayannata, tayanda zata samo yayarda ta tabashi, tayi matukar kewar lallausar fatarsa. Cikin takunta na kasaita da isa ta fito tanufi part dinnasa. Kamar kodayaushe kofarsa abude take, shi mutumne ba'abocin yawan rufe kofaba, saboda yatsani ayi knocking yataso yabude, shiyasa yake barinsu a bude, se can dare yake rufewa. bedroom dinsane kawai idan yana ciki yake kullewa. Afalonsa na kasa tatarar dashi, wata dagowar ajiyar zuciya ta sauke tafara binsa da kallo tamkar zata lashesa. Singlet ce ajikinsa da wando three quarter, kasancewar lokacin zafi yashigo yanzu, danshi Allah yahalicceshi mutum ne mejin zafi ajikinsa, shiyasa baya kaunar zafi kokakan. Sallama ta masa,dagowa yayi da sauri yana kallonta dan besan da shigowartaba, kallonta yayi na wasu sakanni, sannan yamaida kansa kan abunda yakeyi bayan ya amsa mata sallamar. Zama suhailat tayi a gefensa cikin faduwar gaba, domin taga daya ganta maimakon yayi murna sema bata rai dayayi. Kurawa damtsensa da kirjinsa ido tayi, tana hadiyar yawu. Sotake takai hannu tatabasa kotaji dadi amma babu fuska, tarasa meyasa yake mata haka yanzu, baya bata duk wata kulawa data dace ta soyayya. Magana tayi masa amma yashareta, batasan haushinta yake jiba saboda shigar datayi, duk da ita suhailat aganinta tayi shigar mutunci,dan tasan halinsa. Cikin raunin murya suhailat ta kara masa magana da fadin, "haba yaya meyasa kakemun hakane yanzu, baka nemana karage duk wata kulawa da kake bani, idannazo gurinkama kokuma inmun hadu, sedai kaita batamun rai, baka sakarmun fuska, pls yaya idan wani abunnamaka kayi hakuri mu koma kamar da, zuciyata baza ta iya jurar wannan yanayinba, kasan ina tsananin sonka da kaunarka." Takarashe maganar da sakin kuka, domin harga ALLAH soyayyarsa na azabatar da ita. Runtse idanunsa yayi, cikin tausayinta. Shikansa bazece ga dalilin dayasa yake mata hakaba. Suhailat tana bukatar kulawarshi, tunda tana tsananin sonsa kuma itace matar daze aura, shi halayentane bayaso amma idan yatuna ba itace babbar me lefiba, lefin mommy ne, tunda itace bata tsawatarmata seyaji haushinta dayakeji yaragu. Ahankali yakai hannu, ya kwantar da kanta akan kafadarsa batare dayace mata komaiba, yaci gaba da aikinsa. Wasu ajiyar zuciya suhailat tahau saukewa, dama abunda takeso kenan, tasan hakan daya mata alamun rarrashine. Lumshe idonta tayi cikin jin dadi tana shakar kamshinsa. Can kuma ta bude idonta ta kurawa kyakkyawar fuskarsa ido, gaskiya tayi dace da masoyi, abunda yake kara rikitata kenan akansa kyawunsa, tarasa ina yasamo wannan kyannasa, tunda mommy da daddy basu kaisa kyauba, a familynsuma kaf tana tunanin babu me kyawunsa. Badon yagama aikinba ya ture system din yace ta bashi labari,bayan yarabata da jikinsa. Aiko suhailat ansamu abunyi nantaita masa zuba, cikin jin dadi, danma yarage mata jin dadin, daya rabata da jikinsa. seda aka kira sallar isha'i tatafi, shima badon tasoba danma dai yace ze kirata anjimane. ********** Yau a part dinmu sukayi dinner,danaje serving dinsu mommy tatambayeni meyasa banje nagaida daddy ba nace mata baccine yadaukeni. bansaniba. Yaya sadiq kam yaubezo gurin dinner dinba, bankuma San daliliba. Haidar nata kwasata da hira, suhailat kuwa sedai harare harare dataketa wullomun, batasan bata ita nakeba abunda ke kainama yafi karfina,dakyar ma na iya serving dinnasu na koma daki. Saboda bana hayyacina ko yunwa banaji, kokari kawai nakeyi nacire tunanin yaya mustapha daga zuciyata, amma abun yaci tura, fuskarsa kawai nake gani a idona, ga wata jarababbebiyar kewarsa data addabeni amma na kudurcewa raina kozan mutu bazanbari mukara haduwa dashiba saidai bisa tsautsayi. Dama tunda daddy yadawo mommy ba sosai take aikena part dinsaba kamarda. Haka naita juye, juye akan gado ina tunane_tunane, gashi cikina ciwo yakemun nasan lokacin yin al'adatane yayi, namamanta banyiwa yaya sadiq zancen wayar daya baniba, seda nadawo naganta natuna,killaceta nayi dasafe inzan wuce school nabasa. Ana wata ga wata, gadamuwa nacimun rai, gakuma azababben ciwon ciki, daya addabamun kamar kodayaushe idan zanyi period. Ko motsawa nakasayi balle nayi yunkurin fita karbo magani agurin mommy, gashi dare yana karayi. Dafe cikin kawai nayi ina salati, gabadaya nahada uban gumi, se murkukusu nakeyi. Secan zuwa dare nasamu yalafamun bayan nafarajin alamun digar jinin daga jikina, bankaiga yunkurin mikewaba wani wahalallen bacci yadaukeni. Ban farkaba se cikin dare, jikina duk yamun tsami, kirjina har wani nauyi yakemun saboda damuwa, ga wani azababben ciwon kai. haka na daure nashiga toilet na tsafatace jikina nadawo na kwanta jikina sam babu kwari kasala duk ta lullubeni ga wani sanyi danake ji yana ratsa jikina, kuma nakasa tashi inkashe koda fankane, se lulluba nayi da bargo. a wahalcedai nakarasa daren yau. Washegari, da zazzabi natashi mezafi ajikina, hakan yasa nakasa koda tashi daga kwancen danake. Mommy dakanta taje har dakin maryam danganin shiru bata fitoba, ganin halin datake ciki mommy ta kira family doctor dinsu yazo ya duba maryam. Dan taga maryam din najin jiki se rawar dari takeyi. Allura doctor din yamun tare da bani magunguna. Baba talatu mommy takira tazo ta kula dani, baccine yakara daukeni. Baba talatu ita ta fanshi maryam tayi ayyukan part din. Se wajen 1 na farka, alhamdulillah naji dadin jikina sedai kasalar jiki. Yau kam ba batun zuwa school dama Friday ce. Tea me kauri baba talatu ta hadamun nasha tanata jeramun sannu, anan take sanarmun sadiq yazo har sau biyu bantashiba. Danasha tea din kuma senaji dadi sosai, wanka nayi nadawo nakara kwanciya. Alhamdulillah,kafin yamma na wartsake zazzabin yasauka,kodan nasha maganine. yaya sadiq yakara dawowa yamun sannu. Amma suhailat mun hadu kotamun sannu, kuma nasan tasan bani da lafiya. Hakan bedameniba tunda gashi Allah ya bani lafiya. Littafin literature nadauka, naduba saboda ta kansa zamu fara exam ran Monday. Da daddare danaje gaida daddy, yayitamun sannu haryana cewa dahar part dinma zezo yadubani da kansa sekuma gani nazo. Bayan nadawo muka hadu sa yaya sadiq,namasa zancen maido masa da waya, seya nunamun bacin ransa akan hakan, yakuma ce inada bukatar rike waya nima kodan karatu da sauran abubuwa, nakuma dinga gaisawa da kawaye da yan'uwana,nace masa mommy bazatayi fadaba, yacemun ba'abun da zatace, dan yasaimun waya. Dakko wayar nayi ya kunnata, dama acike take yacazamun ita, nunamun duk yanda zanyi amfani da ita yayi, yakuma bude mun abubuwa. Godiya na masa sosai, muka cigaba da hirarmu cikin nishadi, ammafa duk abunda ke faruwa ayinin yau tunanin yaya mustapha nanan daram araina kamar kodayaushe, babu abunda yaragu daurewa kawai nakeyi a kokarina nason cireshi daga raina,dan ma naganshi dazu a part din daddy kewarsa ta ragu daga raina...........✍️ *Ku dakaceni zuwa dare, zankara Baku wani da yardar Allah, inason nakarashe book din kafin azumine,idan Allah yabani iko. naso muku typing fiye da wannan, amma gaba daya zafi ya hargitsani😔* *BY* *zeey kumurya* *ABUNDA KA SHUKA*......... _*(shizaka girba)*_ *MALLAKIN* 👇 *ZAINAB USMAN KUMURYA* *FARIN JINI WRITERS ASSO.....*📚 ~*Free novel*~ *Bismillahirrahmanirrahim* 2️⃣7️⃣ _*DEDICATED TO FAUZIYA S MADAKI (MY AUTA) much love dear💔💘🥰🥰😘*_ *_________________________________________* *AFTER SIX MONTHS* *_________________________________________* ..........Rayuwa nata tafiya tamkar gudun ruwa, (Allah yasa mudace) yau gashi harnayi kusan wata takwas agidan alh, menasara. Nasamu cigaba agidan sosai ta fannin ilimi, dan yanzu gashi harmun shiga ss3. Azaman danayi na watanninan agidan bakaramin canzawa nayiba, nakara kyau da fari, dama bakin na wahalane da hayaki. Canzawar danayi bata wasa bace, naxama kalar yayan masu kudinnan, fatata tacanza tayi kyau tayi sumul_sumul,hatta gashin kaina yacanza yakara baki da tsawo saboda gyara. Komai na gayu da amfanin ya mace yayasadiq yana saimun, har yawa sukemun nake bayarwa,kuma ba'amun iyaka da duk wani abunci kosha agidan,yanda yayan gidan zasuci nima haka zanci komene son raina . Zuwa yanzun kaina ya waye sosai, amma ba irin wayewa wacca ba'asoba wayewa tasanin rayuwa. Zuwa yanzu turanci yazauna sosai abakina, littattafan addinima nasansu sosai, kur'ani me girmama nakusa saukeshi. Gaskiya babu abunda zancewa yaya sadiq domin shine silar zamana komai arayuwa. Zuwa yanzun shakuwa me karfi tashiga tsakanina da yaya sadiq,duk wata damuwata yasani nima nasan tasa, shine abokin shawarata. sedaifa har yanzu babu digon sonsa acikin zuciyata, son mustapha ne zaune daram araina, nayi ina yina da kokarin ganin nacire sonnasa amma nakasa, amma duk da haka ina iyakar kokarina wajen ganin nabawa yaya sadiq kulawa yanda kamata, kamar yadda yake bani. Soyayya mukeyi me tsafta da tsari, koda hannuna yaya sadiq betaba rikewaba. Kuma har wannan lokacin aboye mukeyin soyayyartamu,babu Wanda yasani sedai zee dana fada mata tun farko. danko saleemah banfadawaba haryanzu. Aliya tadawo har sau biyu, amma aunty sau daya takara dawowa,nima naje har kadunan na musu wuni guda, tarema mukaje da yaya sadiq. Naje unguwarmu wajen gwaggo dasu saleemat sosai, dan yanzu duk sanda nakeson fita yaya sadiq yana kaini, har gidan kawayena. Saleemat tataba zuwa gurina sau daya, shima dakyar umma tabarta. Gwaggo kuwa tasha cemun zatabiyoni idannaje sena mata wayo nagud,do,dannasan idan tazo kunyatani zatayi. Zaman danayi ayanzu nagane halin kowa nagidan dakuma yanayin gidan. Shidai megidan yana da kirki sosai, gashi bashida fariya ko karya, Allah yabashi kudin daze iyayin abubuwa na jindadin rayuwa, amma kuma yanayin komai nasa daidai misali baya zafafawa. Yanada gidajen mai, da makarantu na boko dana islamiyya, da kamfanunnuka na sarrafa abubuwa, sannan gashi mutum ne meyawan sadaka da kyauta. sabanin mommy datake komai nata cikin fariya da nuna isa gami da gadara, amma haryau nakasa gane halinta,wani lokacin tamaka kirki, wani lokacin kuma rashin kirki. gidan alh, menasara basayin baki kwata_kwata, kawayen mommy ne kadai suke zuwa se su aunty. Amma ko yan'uwan ta bantaba ganiba agidan tunda nazo. Suhailat halin mommy ne da ita Sak, babu ta Inda tabarta, kamar yadda suke tsananin kama. Har yanzu tsakanina da ita kyara da hantara,narasa meyasa ta tsaneni haka. Su zannurain da haidar kuwa, yanzu nasamu lafiya musammanma haidar shiri muke dashi sosai har karatun boko yana koyamun abunda banganeba. Sai *heartbeat* (mustapha) sunan danasa masa kenan. Shima na fuskanci wasu daga cikin halayennasa.Shi mutum ne miskili,irin miskilancinnan me cin rai nashariya. amma gaskiya yanada kirki sosai, kuma sam baya shiga sabgar mutane, kuma bayason raini akwai tsare gida, shiyasa kannensa suke masifar tsoronsa, last kuma shi masifaffene,nakarshe idan aka tabosa. Daddy mutum ne metafiye_tafiye, amma idan yaxo gida yana jimawa kafin yakoma. Yaya sadiq ma yanzu baya wata agida seyayi tafiya,harkar kasuwancinsu. Yau laraba, sakaliyar yammace, zaune nake nikadai a garden ina tunanin rayuwa. Yaya sadiq bayanan yayi tafiya tun shekaran jiya. Kewarsa gaba daya tacikamun zuciya, shiyasama nazo garden din na zauna, kullum anan muke tadinmu nudashi. Nikam haryanzu hankalina yakasa kwanciya akan soyayyarmu dashi nasan zeyi wahala su mommy su amince masa ya aureni, dandai yadagene. aduk lokacin dana fada masa haka, seyayta lallabani yana bani baki akan zasu amince. Tunani nakeyi akan maganarmu dashi last kafin yatafi, yacemun dazarar yadawo zefadawa daddy abunda ke tsakaninmu shiyagaji da wannan boye_boyen damukeyi. inda naji dadima daddyn bayanan kuma bedade dayin tafiyarba. Ganin magriba tagabato sena nabar garden din. Ina cikin tafiya kafinnakarasa part dinmu, nahango motar tashigo. Haka kawai naji gabada yafadi bankuma san daliliba. tsayawa nayi danganin waze fito daga motar. Wata sassanyar ajiyar zuciya na sauke ganin Wanda yafito bayan drivernsa yabude masa murfin motar, yaya mustapha ne ashe shiyasa zuciya ta tahau luguden bugun data saba aduk sanda naganshi, lumshe ido nayi cikin wani irin yanayi. "Oh ni maryam, bansan sanda zandena son wannan bawan Allahn ba." Nafadi haka afili cikin tsananin damuwa. Nayi iyakar yina wajen ganin nacire sonsa daga zuciyata amma abu yafaskara, narasa wannan wacce irin kaddara ce. Gashi wani irin zazzafan so nake masa, wanda idan nawuni bangansaba gabadaya fita nake daga hayyacina,narasa mekemun dadi aduniya,harse nagansa nake samun nutsuwa. Yanzunma dana gansa bakaramin dadi najiba, gaskiya so bemun adalciba nikadai nasan irin wahalar da zuciyata takesha akan bawan Allah nan, mutumin da nasan yamun nisa nahar abada, bazantaba samunsaba, domin nikaina nasan niba kalarsa bace, yawuce ajina. idanma na samesa ina zan iya kishi da suhailat? Yanda take tsananin sonsa, bata iya boye soyyayar datake masa agaban kowa manuna masa kauna takeyi,tsaf zata iya wa mutum illa akansa. Anma fara zancen bikinsu tunda suhailat din tana level 4 ne yanzu, tana kammalawa kuma za'asha bikinsu. Cikin sanyin jiki naja kafata datamun sanyi nacigaba da tafiya. Mommy natarar zaune afalo ita kadai, sannu namata ina kokarin shiga dakina ta kirani. Dawowa nayi na tsugunna agabanta. "Yawwa maryam, tundazu nake nemanki,binta tacemun kinfita garden, kinsan saura kwana 3 Christmas gobe su kuku zasu tafi garinsu se bayan 2 week zasu dawo, yanzu aikinki yadadu a gidannan harda girki kezaki fanshesa, inafatan kin iya girkin ai" dagamata kai nayi alamar eh. "Ohk, sannan kuma se gyaran part din son shima duk masu masa aikin dasuke masa zasu tafi tarene, zaki dinga zuwa kina masa tun sassafe kafin kitafi school danshi yafison kafin yafito yaga angama masa komai,." Damma kirjina ya buga, gabana yayanke yafadi, yanzu part dinsa zandinga zuwa gyarawa, meyasa mommy bazata tura waniba seni, nifa adole nake barin muna haduwa dashi, danba yanda zanyine,amma gashi mommy takara kusantamu, dan babu tayanda za'ayi nagama gyara part dinsa duka ace bamu hadu b..."maryam!" Mommy takatsemun tunani da kiran sunana. "Na'am" na'amsa ina sauke numfashi. "Dafatan kinji duka abunda nace miki kuma zaki kiyaye." "Insha Allah mommy" "yawwa daga gobe zaki fara, zaki iya tashi ki tafi" ahankali na mike nafara tafiya tamkar wadda kwai yafashewa aciki. bani da zabi banda bin umarnin mommy tunda aikinta nakeyi agidan. Da wuri nayanke shawarar zan kwanta yau, saboda karnayi latti gurin tashi da wuri gobe,tunda aikina ya ninku akannada. bayan nayi serving dinsu nima naci abincin na kwanta. Ina kwanciya naji wayata na vibrate nasan yaya sadiq ne. Janyota nayi nadaga tare yin sallama,cikin danne abunda kedamuna. Daga daya bangaren yaya sadiq yace, "Wa'alaikissalam tauraruwar zuciyata, harnaji dadi danaji wannan daddadar muryartaki, wata nutsuwace ta lullubeni, dako gaba daya nakasa aiwatar da komai" Murmushi nayi nace, "Nima inanan kewarka ta hanani sukuni,yayana" "Uhm, shine kokikirani balle kimun dan text ko?" "Sorry yayana, nasan kana aikine shiyasa amma ai namaka sakon zuciya da zuciya, shi'ai nasan ya'iso gareka" Murmushi yayi me sauti cikin jin dadin kalamanta yace, "Naganshi indai wannanne, dafatan nima kibiyar dana harbo miki ta reply ta karaso gareki" "Ehhh, mana tunyaushe shiyasama kaga ai nakai haryanzu kalau, dabata karasoba datuni katawo jinya ai,danda bazankai yanzu lafiya kalauba".... Hira muka cigaba dayi irinta ta masoya, duk da ni karfin hali kawai nakeyi, dakyar yaya sadiq yabarni shima danyaji nafara masa shiru alamun bacci yafara Cina. Munagama wayar kuwa bacci yadaukeni bajimawa. Cikin baccina naji ana tabani, dafarko nayi tunanin a baccine sedaga baya naji abun ya girmama,kuma kamar azahiri. Bude idona nayi ahankali, tacikin duhu naga kamar inuwar mutum akaina, wata mahaukaciyar bugu zuciyata tayi tamkar zata faso kirjina tafito, cikin tsananin firgici da tsorata nayi yunkurin mikewa zaune, amma aka mayar dani kwancen danake aka danneni da karfi tamkar za'a ballani,numfashinama dakyar yake fita. Wani irin kamshi me kamar kaurine yake tashi daga jikin mutumin, irin wanda naji randa aka taba shigomun daki. runtse idona nayi jikina gaba daya yahau kyarma, addu'ar neman tsari daga Allah nafara karantowa araina, domin shikadai gareni ahalin yanzu kuma shine kadai ze iya kubutar dani. Cikin wata irin dashashshiyar murya mutumin yafara magana. "Yarinya yau babu me kwatarki ahannuna, yau sena cika burina na karshe arayuwa akanki, yau mafarkin dana dade Inayi ze tabbata agaskiya, kece cikar burina na karshe arayuwa,dan haka dole nacikawa kaina burinaaaa!!!!..........✍️ *kyan alkawari cikawa, kutaba wannan,ko editing banyiba. zamu hadu gobe, insha Allah* *By* *zeey kumurya* *ABUNDA KA SHUKA*......... _*(shizaka girba)*_ *MALLAKIN* 👇 *ZAINAB USMAN KUMURYA* *FARIN JINI WRITERS ASSO.....*📚 ~*Free novel*~ *Bismillahirrahmanirrahim* 2️⃣8️⃣ .............Cikin wani irin karfi danaji yaziyarceni na hankade mutumin daga kaina tare da mikewa zaune da Sauri ina maida numfashi,da sauri da sauri. jabaya nafarayi cikin tsananin tsorata gami da razani, bakina nacigaba da karanto addu'ar neman tsarin daga ubangiji ,kafin na kara wani yunkuri mutumin yakara yowa kaina, cikin azama naja baya sosai harnakai karshen gado, sonake na kurma ihu,kozan samu dauki amma nakasa tamkar ansa super glue anrufemun baki,nakasa koda motsashi,ga wani kauri_kauri dake tashi daga jikin mutumin dayake kokarin tarwatsamun kaina. saboda tsabar tsorata cikina se har wani kugi yakemun. Hannunsa yakuma sawa yadamki gashin kaina da karfi yana kokarin maidani kasa, saboda tsananin azabar data ziyarceni, bansan sanda nadankara masa cizo a gefen wuyansaba. Wata yar siririyar kara yasaki tare da sakina yasauka daga kan gadon da sauri,ya fice daga dakin da gudu. Nima cikin fitar hayyaci nasakko,nabi bayansa numfashina nafita dakyar, banmasan inda nake jefa kafataba,hannuna dafe da kaina dayake mugun saramun gami da juyamun, ina fita falo naga wayam babu kowa harya fece, kuma falon akawai haske balle ince buya yayi, daidai lokacin mommy tafito daga dakinta cikin firgici ta fara fadin, "maryam lafiya meke faruwa, naji anbuga kofar falo da karfi" ban iya bata amsaba saboda wani jiri daya kwasheni nayi kasa luuuu zanfadi, dasauri mommy tataho tatarota jikinta, girgiza maryam tahauyi tana tambayarta lafiya,maryam batamasan tana yiba tatafi duniyar suma. Daukar maryam mommy tayi takaita dakinta ta kwantar da ita akan gado. Ruwa me sanyi ta debo tahau shafawa maryam a fuskarta zuwa wuyanta,kusan 12 minutes tana mata haka, kafin maryam taja wani dogon numfashi, ajiyar zuciya mommy tasauke ganin maryam ta farfado, hartaji sanyi aranta kar yar mutane, ta mace mata. "Maryam,maryam,maryam!" Naji muryar mommy asama tana kiran sunana, ahankali na bude idona dayaymun nauyi ina kallonta dishi_dishi, sonake namata magana amma nakasa harshena yamun nauyi, tunanin abunda yafaru nake kokarin yi, amma nakasa,ga wata sarawa da kaina yakemun tamkar ze rabe biyu. Duk da bana cikin nutsuwata amma yanayin mommy dana fuskanta, gaba daya arude take, har wani gumi naga tana hadawa. Mayar da idona nayi na lumshe,cikin karfin hali nafara karanto addu'a acikin raina, cikin ikon Allah bansan sanda bacci ya daukeniba.... Ahankali na bude idona Wanda hakan yayi daidai da kiran sallar asuba da'ake kwadawa. Ahankali na yunkura na tashi zaune ina karewa dakin mommy kallo, jikina rass najishi babu ciwon komai kamar jiya. tunanin abunda yafaru har ganni adakin mommy nake kokarin yi amma nakasa, hakura nayi da tunanin na sakko daga kan gadon nanufi toilet domin yin alwala, abunda ya bani mamaki mommy bata dakin. Koda nafito daga toilet din sena ga mommy zaune akan dadduma da hijabi ajikinta. Kallon maryam mommy tahauyi cikin kura mata ido, nidai kasa nayi da kaina ina kokarin gaisheta naji tace, "maryam harkin tashi, yakikejin kannaki yanzu?" cikin sanyin murya nace mata, "dasauki mommy,yama tafi duka" "masha Allah haka akeso, ga dardumacan dakko sekiyi sallar" dakai na amsa mata na dakko dardumar na shimfida, kaina gaba daya ya kulle narasa tuno mekefaruwa. Jam'i mukabi dukanmu nida mommy, ana idarwa nayi lazimina na mike naiwa mommy sallama nakoma dakina. Dakin na tsaya ina karewa kallo, babu wata alama data nunamun wani abu yafaru, dakin fess dashi setashin kamshin room freshener yakeyi da turaren wuta. Toilet nafada nayo wanka nadawo shap_shap nasaka uniform dina na zunbula hijabi,dakina na tattare kafin gari yayi haske intafi gyaran part din *heartbeart.* 6:18,am. Nafito daga part dinmu nanufi nashi, ma'aikatan gidan burjik kowa nata aikinshi a farfajiyar gidan, masu shara nayi masu bawa flower ruwa nayi gasunandai sunata fama. Ahankali nabude kofar part dinnasa bakina dauke da sallama, tsayawa nayi ina karewa falon kasan kallo, namanta rabona dana shigo part dinnan, ancanza komai na falon,tundaga kan kujeru labulaye center carpet komaidai ancanza daga Wanda nasani. Falon fess naganshi babu datti, ga wani daddadan kamshi dayake tashi, toni banmaga abun datti daza'a gyaraba ananba. Ganin zanbatawa kaina lokaci, sena shiga inda mommy tacemun nadakko abun shara, nashare falon, bayan na kwashe yar kurar dana tara nayi mopping din falon, da goge_gogen su TV da dinning. Kafin nagama duk senaji nagaji dan falon yafi na mommy girma. Kitchen din kasan nashiga shima na gyara cikin Sauri danna kusa latti, dama kasannasa babu bedrooms, daga falo se toilet se kitchen, shima toilet din, wankeshi nayi tass,tsaf dai nagyara kasan nanufi sama ganin har 7 ta wuce. Sauri_sauri na fara gyara falon saman,ina cikin goge kan dinning naji wani irin yanayi ajikina, zuciyata ta fara bugawa, da sauri na juyo bayana. Ido hudu mukayi dashi yana tsaye yana kallona, daddadan kamshinsa gaba daya ya mamaye falon, cikin shirinsa na zuwa office yake tsaf harda briefcase dinsa a hannunsa. Shi mustapha mamakin ganin maryam yayi, duk da mommy tafada masa zata turo masu aiki su gyara masa part dinsa beyi tunanin wannan yarinyar zata turo masaba, gashi kuwa abunda bayaso harya fito bata gama aikinba,dama banda abun mommy wannan yar mutsilar yarinyar ina zata iya wani aiki. "Ina kwana" nagaisheshi cikin faduwar gaban kallon danaga yana mini fuskarsa a tsuke, gyadamun kai yayi har lokacin bedena kallonaba, nidai tsaye nayi kaina a kasa nakasa cigaba da aikin, sedanaga yajuya ya fara tafiya sannan na dago ina kallon bayansa harya fice. Ajiyar zuciya nasauke, nahau gulmarsa araina. Yarame, amma bakaramin kyau yakaramunba, nadade banganshi close to close hakaba, sedai gani daga nesa. Wani irin nishadi naji acikin zuciyata dana gansa, gaskiya so bala'ine,senaji dama ya zauna inta kallonsa. Cikin jindadi nakarasa aikin part din nasa. makullin daya ajiye akan kujera nadauka narufe duka kofofi biyun nasama dana kasan part din, sannan na koma part dinmu.mommy dasu binta masu aiki sunata kokarin hada breakfast a kitchen,mukullin part dinnasa nabawa mommy,namusu sannu da aiki na wuce dakina. Karasa shiryawa nayi. Nadakko wayata zan kashe naga missed call din yaya sadiq, dama munsaba kullum kafin natafi school semunyi waya. Banbi bayan kiranba saboda nayi latti, text kawai namasa nakashe wayar, cikin kudin da yaya sadiq yake bani, nadauki 500 nafito natafi. Koda nadawo daga school nasha aiki sosai, har dare ina fama, ga girkin rana gana dare. Aiko jikina yayi tubus da gajiya....... *********************** Yau kwana 8 dafara aikin gyara part din yaya mustapha,da duka aikin gidan. Yaya sadiq kuma kwanansa biyu da dawowa daga tafiyar da yayi. karfe 6,nagama shirina na nufi part dinshi. cikin tsananin farinciki, inajin dadin wannan aikin,saboda kullum ina ganin *heartbeat* yanda yakamata,koda naje da wuri nagama aikin, idan befitoba se inta lakai_lakai harse yafito nagansa. Aiko yanzu kullum da murmushi dauke a fuskata nake wuni,yaya sadiq har yakasa hakuri yatambayeni meyake sani farin ciki haka, nace masa duk murnar dawowarsace. Kafin 30 minutes nagama gyaran kasansa, nanufi sama. Inayi ina waigen koze fito amma harna gama ko motsinsa babu, kin tafiya nayi koze fito amma naji shiru mintuna fiye da 15 sun shude befitoba, haka na taso jiki a sabule cikin takaicin rashin ganinsa na fito daga part din,jinake kamar na koma kozan tarar yafito. Abakin part dinmu nayi kicibus da yaya sadiq, cike da mamaki ya tsaya yana kallona. ''Maryam, daga ina haka tundazu Inata jiranki kizo mu wuce na saukeki harna gaji dajira na biyo bayanki." "Yihakuri yayana, mommy ce ta aikeni nakaiwa yaya mustapha abu" "what!,me kuma mommy ta aikeki kai masa da sassafennan" yafadi haka cikin karaji haryaso ya bani tsoro. Dama banfada masa ina zuwa part din mustapha yimasa aikiba,dannasan seya hanani,nikuma bazanzo hakaba kodan karna dena ganin kyakkyawar fuskar *heart beat* ina jindadi. "tea nefa tabani nakaimasa" nabashi amsa ina dan bata fuska. Ajiyar zuciya sadiq yasauke yace, "shikenan nizan wuce naga 8 ta kusa, karnayi latti a office driver ya kaiki" yakarashe zancen yana duba agogon hannunsa. "Tom,Adawo lafiya, Allah yakiyaye" "ameen, matar sena dawo kikulamun dakanki. "Insha Allah byeee" nakarashe zancen ina daga masa hannu alamar bye_bye fuskata dauke da murmushi. Adaidai lokacin aunty suhailat tafito daga part dinmu, dasauri kuma naga tajuya takoma ciki. Nima juyawa nayi nashige domin naje nakarasa shirina. "Mom,mom,mom" suhailat take ta kwalawa mommy kira tundaga falo harta shiga dakinta. "Na'am, my daughter irin wannan kira haka" zama suhailat tayi agefen mommy tana fadin, "mom, nifa wani abu nake zargi a gidannan mara yiyuwa" cike da mamaki mommy tace, "banganeba suhailat wanne abune haka" tabe baki suhailat tayi tace, "mom nifa ina zargin waccan kujakar yarinyar yaya sadiq yake soyayya da ita" "wacce yarinya kenan daughter" "hmm,mom kenan. Wacce yarinya garemu banda house girl din gidannan, maryam take kowa,ohi mata" murmushi mommy tayi tace, "haba suhailat,tayaya za'ayi sadiq yayi soyyaya da maryam, kawaidai kinsanshi shina kowane." "Kai,mom banda irin wannan, tunda ake kawo yara gidannan aikatau wakika taba ganin yayima haka, yanafa kula da yarinyar sosai, yana kashe mata kudi mom kamar bakya ganine" "Ina gani daughter kuma ina sane dashi,amma bandauki hakan da wata manufaba gaskiya,dankinsan sadiq dina damacan shi mutum ne me kyauta da tausayawa mutane." "Mommy kenan, amma yanda yakeyiwa maryam din hidimane yayi yawa, kulawar dayake bata ta wuce ace iya tausayawace kawai." Dafa kafadar suhailat mommy tayi tace, "karki damu kanki akan haka daughter zan bincika nagani koma menene zansan tayanda zan bullo masa" "yadai kamata mom,dankaryaje yadakko mana abun kunya,da Allah wadai a idanun jama'a" suhailat ta fadi haka tana mikewa, sallama tayiwa mom ta fice, dama school zata tsegumi yadawo da ita. Zuciyata cike da tunanin yaya mustapha gami da kewarsa, nakarasa shirina nafito nayiwa mommy sallama nafice. Harna nufi gurin danasan driver yana jirana senaji ina, bazan iya barin gidaba batare dana ganshiba nariga dana sabarwa idona da zuciyata da ganinsa kullum, ahankali na juya nanufi part dinnashi,haka kawai naji zuciyata na bugawa, gashi kuma ina danjin tsoron bansan mezance masaba,idannakoma. Ahankali na tura kofar falon kasa senajita abude, ajiyar zuciya nasauke cikin farin ciki ganin yananan befitaba. Sama na haye cikin sauri, shima ina tura kofar najita abude. Anan na tsaya kuma ina sake_sake araina,wata zuciyar tanacemun nashiga bedroom dinsa wata zuciyar tana gargadina ga aikata hakan, domin aka'idama hakan bekamataba, kuma shima idan yakamanifa nasan sena yabawa aya zakinta. harjuya kuma senaga ina bazan iya komawa batare dana ganshiba tunda nazo kuma sedai komai zefaru yafaru ta fanjama fanjam,so ya rufemun ido,burina kawai ingansa. Cikin kwarin zuciya na juyo na dawo, duk da bugun da zuciyata takemun haka na runtse ido na bude dakin danasan yana ciki, cikin ikon Allah kuwa kofar dakin abude take, ahankali na tura zuciyata na tsananta bugu, tsayawa nayi ina kallonsa yanda yake kwance akan makeken gadonsa,tamkar gawa. Jikinsa gabadaya alullube yake da bargo, fuskarsa ce kawai a bude, idanunsa a lumshe da'alama bacci yakeyi. Cikin sanda nafara taku, harnaje gaban gadon natsaya ina kallonsa, ina sauke ajiyar zuciya akai_akai. Ina tunanin intasheshi amma kuma inajin tsoro, atunanina baccine yadaukesa batare dayasan lokaci yayi hakaba. "Maryam,karkiyi kuskuren haka,tunda dai kinganshi hankakinki ya kwanta kitafi kawai,kar tsautsayi yasashi farkawa yaganki tsaye akansa,mezakice masa yakawoki dakinsa" wata zuciyar ta gargadeni da aikata haka. Badon nasoba sedan tsorandanakeji najuya nafara tafiya,ina tafe ina waigensa harna fice daga dakin. Senajini duk wani iri,zuciyata sam babu dadi,kamar wani abu mara dadi nashirin faruwa dani. Haka kawai naji hankalina sam yakasa kwanciya bankuma san daliliba. Inda driver yake jirana naje nasamesa, nasanma harya gaji da jirana.......... Mommy ganin har wajen 10 son dinta bezo yagaishetaba setaji hankalinta yakasa kwanciya, shida yake zuwa gaisheta tun bayan sallar asuba amma yau haryanxu shiru, gashi tanata kiran wayarsa no respond,gashi maryam yau bata kawo mata key din part dinshiba,ita kuma tamanta bata tambayetaba. Yanke shawara kawai tayi gwara taje taduba taga ko lafiya yake. wayarta kawai ta dauka ta nufi part dinnashi,tanata addu'ar Allah yasa lafiya yake, dantasan bakaramin abune zehanashi fitaba. Kamar yadda maryam tabarshi haka mommy taje tasamesa, a kwance tamkar gawa. Cikin sauri mommy takarasa kan gadon dayake, tana kiran sunansa,cikin dan daga murya. "Son,son,son" amma taji shiru,zare bargon daya lulluba dashi tayi, ganin yanda yake hada uban gumi, wani irin huci mom taji yana tashi saga jikinsa, numfashinsa na fita da sauri da sauri. Cikin tsananin firgita da yanayin data ganshi takai hannu, tataba goshinsa. Dasauri tajanye hannunta saboda zafin dataji kannasa yayi, tamkar anzuba masa garwashi,gashi babu inda yake motsi ajikinsa, numfashin dayake fitarwane kawai zesa kagane yanada rai,abunda ya kara firgita Mommy kenan. Cikin tsananin gigita dayanayin da mommy taganshi, ta kwalla kara tahau jijjigashi tana kiran sunansa da karfi,tana fadin. "My son, meke damunka haka, pls d katashi dan Allah! Son,son!" dasauri kuma ta mike tamkar wadda aka tsiraka tafice da gudu daga part din cikin tsananin tashin hankali, farfajiyar gidan tanufa tana kiran ma'aikatan gidan akan suzo dasauri su taimakamata takai mustapha asibiti. Wani daga cikin ma'aikatan gidan me suna Adam, shiyafara zuwa. "Hajiya lafiya kuwa, meke faruwa?" Yatambayi mommy cikin mamaki saboda betaba ganinta a irin wannan yanayinaba. "Inafa lafiya Adam, nazo nasami son dina cikin mawuyacin hali na rashin lafiya,kutaimakamun nakaishi asibiti karya mutu narasashi" mom takarasa zancen cikin tsananin damuwa tamkar zata fashe da kuka. "subhanallah muje hajiya,muje, muje" juyawa mommy tayi cikin sauri da tsananin tashin hankali cikin part dinnasa,Adam na biye da ita abaya. wasu ma'aikatan dasuka karaso gurin yanzu suma suka rufa musu baya cikin sauri,ganin alamun babu lafiya..........✍️ _*kutayani da addu'a,Allah yasa nasamu nasara akan abunda nasa gaba pls🙏😢*_ *BY* *zeey kumurya* *ABUNDA KA SHUKA*......... _*(shizaka girba)*_ *MALLAKIN* 👇 *ZAINAB USMAN KUMURYA* *FARIN JINI WRITERS ASSO.....*📚 ~*Free novel*~ *Bismillahirrahmanirrahim* 2️⃣9️⃣ .........Hankali atashe mommy take nunamusu mustapha,dake kwance yanda ta barshi bayan sun isa har cikin dakinsa, babu bata lokaci suka nufeshi suka cuccuboshi kamar yadda mommy tace, suka fito dashi zuwa mota. Mommy da jikinta keta rawa saboda tsabar firgici, ta dauki wayarta data ajiye agefen gadon tun shigowarta dakin, tafara Neman number daddy domin kiransa tasanar masa halin da'ake ciki,sannan itama tabi bayansu adam da sauri. Tana tafe tana kiransa amma bedagaba harta katse, cigaba tayi da kiransa amma harta shiga mota bedagaba,driver nagaba, mommy kuma tana zaune akan kujerar mezaman banza, se mustapha da'aka kwantar abayan kujera. Cikin sauri driver yafigi motar, mommy kam gabadaya baya tajuya tana kallon mustapha,gani takeyi tamkar kafin wani lokaci kankani ze iya mutuwa, basuyi nisa da tafiyarba wayarta ta fara kara. Jikinta narawa ta dakko tadaga da sauri ganin daddy ne, sallama daddy yayiwa mommy, batare data amsa masaba, cikin tsananin rudu tace, "alhaji, my son naje natarar kwance a part dinsa babu lafiya, kuma babu Inda yake motsi ajikinsa senumfashinsa dake fita kadan_kadan,yanzuma munakan hanya zamu kaisa asibiti." Takarashe zancen da fashewa da kuka. Abangaren daddy cikin kidima yace, "Subhanallah, dama bashi da lafiyane" cikin shashsheka mommy tace, "lafiyarsa kalau muka rabu jiya" numfashi daddy yasauke yace, "ohk, kukarasa general hospital dashi bari nakirasu nasanar musu zuwanku, kujirayi zuwana nanda dare, ganinan zantaho nima insha Allah" da "to" kawai mommy ta amsa masa ta kashe wayar, number yan'uwansa tafara laluba tana kiransu daya bayan daya tana sanarmusu,suhailat ce kawai bata kiraba. Hankalinsu gabadaya yayi matukar tashi, kowa barin inda yake yayi cikin gaggawa yanufi asibitin. Driver shima kara gudu ganin yadda mommy ta gigice tanata kuka tamkar ance mata mustaphan ya mutune. Cikin 18 minutes suka karasa asibitin, ma'aikatan asibitin harsun fito da gadon tura mara lafiya suna jiransu. Acan mommy tatarar da sadiq shi haryaje yana jiransu. Cikin sauri ma'aikatan suka karasa gaban motar su mommy da gadon daukar marasa lafiya suka kama mustapha suka dorashi akai suka fara turashi da gudu zuwa cikin asibitin. Mommy ma rufa musu baya tayi,tana tafe tana saba mayafi, ita da yaya sadiq, datashin hankalinsa ya ninku fiye dana da, dayaga halin da dan'uwansa yake ciki, beyi tunanin ciwon yayi tsanani hakaba. Emergency aka nufa da mustapha, cikin wani daki likitotin suka shiga dashi, suka dukufa dubashi domin ceto numfashinsa dake barazaranar karewa. Mommy se kaiwa da komowa take aharabar gurin,yayin da sadiq yatsaya jingine da bango dafe da kansa, cikin tsananin tashin hankali, kafin 20 minutes su haidar duk sun halla a asibitin, cikin damuwa suka hau tambayar mommy meyafaru amma mommy takasa basu amsa, ita burinta likitocin su fito suce mata danta yafarfado. Abangaren daddy kuwa suna gama waya da mommy yakira aunty yasanar mata. Nandanan aunty ta rude tafara shirin tahowa kano babu bata lokaci..... ************** Ina school ne,amma gabadaya hankalina yana gida. Zuciyata takasa samun nutsuwa. Karatunma yau ba fuskantarshi nakeba. zee dake hankalce da maryam tundazu ta zungureta,cikin rada_rada tace, "mairota lafiyarki kuwa,naga gaba daya bakya cikin nutsuwarki,se tagumi kikeyi" ajiyar zuciya nasauke nace, "babu komai kawata" "hmmm,kifadamun gaskiya kokunsamu matsalane da yaya sadiq" girgiza mata kai nayi alamun a'a. Shiru zee tayi batakara cewa komaiba, tamaida hankalinta ga karatun da'ake musu. nikam na matsu atashi hankalina gaba daya yayi gida...... ************** Gwaggo ce, tsaye a gidansu su saleemat rike da kugu tazone akan dole se saleemat ta rakata gidan alh,menasara tunda tataba zuwa, ita tasan unguwar gidanne bata saniba. saleemat dai nazaune tana danna wayarta hankali kwance, dama umma batanan tafita taje asibiti ganin likita tun safe, kannenta kuma sun tafi school se ita kadai agida. Kara cokalo harbatsatstsen daurinta gwaggo tayi gaba,cikin masifa tace, "kefa dama yarinyarnan bakida kirki da mutunci kokadan, banda haka nazo tundazu ina miki magana amma kinmaidani yar iska kinki kulani, da suwaibace zaki mata haka." Kallon gwaggo saleemat tayi tace, "amma gwaggo kina kallo dai umma batanan, nikadaice kuma maryam koda munjema batanan tana school" "Toni dama nace miki gurin wata maryam zani meruwana da wata maryam,gurin mutanen gidan zani ingaishesu" kafin saleemat tabawa gwaggo amsa wani almajiri yashigo yacewa gwaggo tazo tayi bakuwa tana kofar gida atsaye. Wani dogon tsaki gwaggo taja tana fadin, "wacce gantalalliyarce kuma tazomun ina shirin fita, amma mujedai ingani" takarashe zancen dabin bayan yaron. Itadai saleemat hamdala tayiwa Allah tasamu salama. Gwaggo nafita taga wata tsohuwar kawarta dasuka fi shekara basu haduba. irin matannanne masu zaman saudiya, gatanan fess da ita taci gayunta. wangale baki gwaggo tayi cikin mamaki tace, "hajja gana,dama rai kanga rai" murmushi matar tayi tace, "gashi kuwa ladi mun hadu" makullin dake hannun gwaggo tasa tabude gidan tana zubawa hajja gana maraba cikin muryar ganinta. Bayan sun shiga gidan, hajja gana tazauna agefen gadon gwaggo adarare saboda kyankyami tace, "wato haryanzu Ladi halinkidai besauyaba na kazanta" bata fuska gwaggo tayi tace, "nifa matsalata dake kenan hajja,shegen tsantsaini iyayin tsiya,kinsaba da saudiya ko'ina fess,aibaza kihada nan da canba,kuma ni gaskiya aiki wahalar dani yakeyi,bazan iya wani bautar gidaba,barinshi nake yaci dattinshi yagama" "Gyada kai hajja, tayi tace. "Amma kin iya fita tun farar safiya gidan makota,ana jiyo muryarki har kwararo kinata kwakwazo" "badole kijini har kwararoba hajja,yarinyace naje nace tarakani gidan da maryam take aikatau amma taki,saboda tsabar bakin hali" "ladi!, wacce maryam din ce take aikatau kuma, badai takiba.?" "Ita mana, ai aikatau nakaita" cike da takaici hajja tace, "amma wlh ladi, Allah wadaran halinki yanzu duk abunda maryam take miki a gidannan shine kika dauketa kikakaita aikatau,saboda zalinci" cikin rashin damuwa gwaggo tace, "yoo duk abunda takemun yafi kudin dazansamune" "hmmm, ladi tsinannen son kudinkine ze kasheki, banda haka dudu nawane kudin aikin da ake biyan masu aiki,nasan bekai ribarki ta sana'ar da yarinyarnan take mikiba" dariya gwaggo tayi tace, "wannan dayawa ne hajja, gidan alh. Menasaranefa take aikin, 200,000 duk wata haka nake jinsu dumus yanzu takai kusan wata tara tana aikin, kudina sunanan a ninke ina tarawa" galala hajja tayi tana kallon gwaggo, tsabar takaicima takasa magana. Secan ta numfasa tace, "ladi, wlh wlh wlh idan bakiyi wasaba son kudinkine ze kasheki. Tsabar masifa kidauki yarinya kikaita aikatau,ke bakirasa ciba baki rasa shaba, yarinyarnan duk irin bautar datake miki amma be ishekiba sekin cutar da ita h...... "dakata hajja, wai meyasa kowa yazo seya dinga bankyautaba,bankyataba, danna kai maryam aikatau. Yarinyarnan fa tawace, duk wanda zesota abayana yake, kuma aikinnan data tafi, hutantane dacigabanta itama. Bakiga yanda ta canzaba tayi bul_bul abunta tayi fari kal kamar kya tsaga jini yafito ajikinta, kuma sunsata a makaranta to kuma mene faduwa anan,aganinama aise riba data samu" gwaggo takatse hajja dafadin haka cikin masifa. "Ladi,yakamata kidinga tunani akan abubuwan dazaki aikata kafin ki aikata, 200,000 yayi yawa a kudin aiki, ko aikin gwamanati sekana babban aiki zaka samu 200,000" dariya gwaggo tayi tace, "kinmanta kudin mutuminne hajja, kuma gashi da kyauta ance,koda maryam bata masu aiki ayanda ake fadar halinsu ze iya bamu kyauta"Hararar gwaggo hajja tayi tace, "gaskiya ladi haryanzu bakisan duniyaba, to bari kiji infada miki,masu kudi sunfiki son kudinsu, idanma zaki dawo cikin hankalinki kidawo kinsan inda yake miki ciwo. Haka kawai baza'adinga daukar makudan kudi ana baki amatsayin iya na aikin maryam, ninasan halin masu kudi,nazauna da manyan masu kudi, dan haka ina baki shawara kije kidakko maryam tunkafin kiyi danasani, kada kiyi sanadin abunda za'a cutar da marainiyar Allah. Ladi, kinsan illar cutar da maraya kuwa, kiji tsoron Allah mana ladi, duk abunda kikayiwa yarinyarnan abaya be isaba kiba sekin kaita inda........... "kinga dan Allah hajja, dakata. Niba wa'azai nace kizo kimunba, ku mutane bakwason fadar alkhairi sedai kuyita munana zato, maryam dai bazan dakkota daga gidan aikatauba, sena tara kudin zuwa saudiya da siyen makeken gida, dan haka ki sauraramun. Dan'uwan mijin innama yazo yayi nasa nagaji, dan haka kema kisauraramun,kibarni inyi abunda naso,daga zuwanki karki batan rai." Kallon gwaggo kawai hajja takeyi cike da mamakin shegen son kudi irinnata, gashi kuma kudinnata baya ciyuwa, tana dai danci acikinta, amma ko suturar arziki bata iya daurawa, kullum ita kenan bin gidajen masu adashi tana zubi. Sanin halin gwaggo na kafiya da naci akan abunda tasa agaba yasa hajja, ta kyaleta da maganar maryama,amma ta kudircewa ranta insha Allah setaje ta dakko maryam dakanta, danyanda duniyarnan ta lalace, ta safarar yara kanana yan mata zuwa kasar waje. itama sam hankalinta beyarda da wannan aikinba,ga uban kudin da'akace ana bayarwa,akan dan aikin gida. abunda mamaki sosai,dama can ita rayuwar yarinyar nabata tausayi. (Gwaggo, yakamata kiyi hankali mana, ayanda kawayenki da suke zugaki akan abunda kikeyiwa maryam ada, amma yanzu duk abunsu su suke kara tunatar dake,abunda kikayi badai_dai bane,amma kinkasa ganewa.).......... ******************** Awanni biyu sun shude,amma har lokacin su mommy basusan halinda mustapha yake cikiba,likitocin dai suna kansa har wannan lokacin. Haidar dakanshi yaje makaranta yadakko suhailat, aiko tana zuwa taji abunda yafaru ta haukata gurin da kuka, tana kiran abarta taje taga mustapha. Wata nurse ce ta tausheta tare da bata baki, aka samu tayi shiru da gunjin datakeyi, mommy kam zuwa yanzu ko magana bata iyayi. Daddyma yakirasu yakai sau biyar domin yaji yanayin jikinnasa, shima yanacan yanata cuku_cukun tahowa naija. Se wajen daya saura likitocin suka fito gabadaya su mommy sukayi kansu da tambayar yaya jikinnasa. Dr, musaddiq wanda shine babba acikin likitocin ya dubi su mommy yace. "Hajiya ku kwantar da hankalinku munsamu numfashinnasa yadaidaita munma daura masa drip, tare dayimasa allurori,yasamu bacci yanzu" "to yanzu doctor zamu iya shiga muganshi" mommy ta fadi haka da saurinta. "Ehh, zaku iya shiga ku ganshi" ai ko gama rufe bakinsa Dr, beyiba suka nufi dakin dukansu. Duban yaya sadiq Dr, yayi ganin duk yafisu tawakkali yace, "abokina idan badamuwa kasameni a office mana, muyi magana" "ohk badamuwa" yaya sadiq yabashi amsa, tare da bin bayansa zuwa office dinnasa. Mustapha na kwance, akan gadon asibitin dakin dayake, shikadaine adakin se wani gado dake gefennasa. Kusa dashi su mommy suka kasara suka kura masa ido cike da jimami. Gaba daya jikinsu haidar yayi sanyi da ganin halin da yayannasu yake ciki. Duk'abun mutum idan yaga mustapha ahalin dayake ciki seya tausaya masa, lokaci daya ya zabge yayi wata uwar rama, ga numfashinsa dake fita a wahalce, bawan Allah shikadai yasan azabar dayake ji ajikinsa. Kuka suhailat ta fashe dashi tana fadin, "mommy yanzu yayane kwance ahaka kamar gawa, mom dubeshifa yanda yakoma,sekuma karasa gaban gadonnasa tana fashewa da kuka. "mommy kam takasa magana se girgiza kai kawai takeyi hawaye na malala a fuskarta. Acan office din Dr, kuwa bayan sun shiga sun zauna. Dr yadubi sadiq yace, "sadiq! Agaskiya dan'uwanku yana cikin wani yanayi na mawuyacin hali, numfashinsa gaba daya yayi sama, dakyar muka samu muka shawo kan matsalar, saidaifa wata matsalar daban, duk binkicenmun munkasa gano meke damunshi takamaimai daya yashi a wannan halin,naso ace mahaifiyarku nayiwa wannan bayanin amma naga gaba daya naga a rude take, bazama ta fuskanci me nake cewaba, shiyasa nakiraka kai kazo domin na maka bayani." Numfasawa yaya sadiq yayi, cikin tsananin damuwa data kasa boyuwa har a fuskarsa yace, "doctor kaina gabadaya ya kulle narasama mezance akan wannan al'amarin,saboda jiya lafiya kalau muka rabu dashi, yau fa kawai akaga yatashi da wannan ciwon metayar da hankali,da sanya rudu a zuciya." "Haka dama ikon Allah yake yawuce gaban komai, wannan kadanne daga cikin ikonnasa. Fatanmu kawai Allah yabashi lafiya, yanzudai mun dibi jininshi zamu auna, insha Allah zamu gano inda matsalar take semusan abunyi" "tom shikenan Dr, mungode sosai bari naje naga jikinnashi." Musabaha sukayi sadiq yafice daga office din zuciyarsa Sam babu dadi......... ****************** Kasancewar yau Friday, 12:30 ake tashinmu, kuma duk ran Friday yaya sadiq ne yake zuwa daukata idan yana gari. Idan yadawo daga gurin aiki seya biyo mutafi kafin ya wuce masallacin juma'a. Jiransa natsayi a bakin gate din makaranta, amma shiru_shiru bezoba, babu shi babu driver,nasan wani babban uzurine yatsaidashi. Ganin nayi kusan mintuna 20 atsaye dalibai duk sun tafi, su zeema sunjima da tafiya,ga lokacin masallaci yakusato, nasan yanzu ankusa kashe hanya. Adaidaita sahu na yanke shawarar hawa kawai yakaini gida. dama makarantar tamu akan titi take. Guda daya na tare yace nakawo 100 babu bata lokaci na haye muka nufi gida. Har kofar gida yakaini na ya saukeni nabiyashi hakkinshi. Gaba daya jikina babu dadi kokadan, knocking nayi megadi yazo ya budemun, gaishesa nayi nawuce ciki. Maimakon nayi hanyar part dinmu, sena nufi part din yaya mustapha sonake kawai naganshi, naji dadi azuciyata. Harna kusa zuwa wata zuciyar ta tunatar dani yanzu hakafa yana masallaci saboda lokacin sallah yayi,tokodama bahakaba idannaje mezance masa? Juyawa nayi cikin sanyin jiki nakoma nanufi part dinmu. banci karo da kowaba a part din kasa hakama nasama. gaba daya part dinma tsit najishi. Dakina na wuce nayi wanka tare da dauro alwala, nayi sallah. Ina idarwa bayan nayi lazimi nakaranta khahfi. Kwanciya nayi saboda wani bacci dayake cina, inason naje nacewa mommy nadawo nakuma kunna wayata nakira yaya sadiq nasan yanzu shima yakirani yaji kona dawo gida,amma wani irin bacci nakeji, bari nayi nadan runtsa idan natahi nayi duk abunda zanyi............. Karfe biyu na rana,a garin kano tayiwa aunty, danma a motor driver dinta yakawota, taso biyo jirgi sekuma taga ze bata mata lokacine kawai. Itakadaima tataho aliya tana school batamasan tatahoba se sallahu tabar mata gurin masu aikinta. Wayar sadiq takira yasanar mata asibitin dasuke suka nufi can. Su mommy ansha kuka ita da suhailat sun hakura sunyi shiru. Se tasashi dasukayi agama suna kallonshi. Su haidar kuwa dakyar sadiq ya taushesu suka nufi masallaci. Daddy ma yakirasu yace jirgin karfe uku zebiyo. Su aunty nashigowa asibitin suka hadu dasu yaya sadiq sundawo daga masallaci. Tunda aunty tagansu taji gabanta yafadi yanda taga fuskokinsu babu walwala kokadan kamar mustaphan mutuwa yayi, tatabbatar bakaramin jiki yake jiba. Ahanzarce ta fito bayan driver yayi parking, tabi bayansu yaya sadiq dasukayi gaba dansu basu gantaba. "Sadiq, sadiq" aunty ta kwalla masa kira lokacin data kusa cimmusu. Gabadaya suka juyo suna kallonta. "Aunty harkin karaso, sannu da zuwa" cewar sadiq. "Nakaraso sadiq yajikinnasa,ina fatan da sauki dai ko" "jiki alhamdulillah za'ace,sauki kam sena Allah." shiru aunty tayi jin abunda sadiq yace, hankalinta ya kara tashi,dama kwana 2 se mafarkinsa takeyi cikin mawuyacin hali. Gaisheta su zannurain sukayi asanyaye, itama ahakan ta amsa musu suka dunguma zuwa dakin dayake. Mommy nazaune ta rafka uban tagumi,kana ganinta kasan hankalinta sam ba'a kwance yakeba duk ta wani burkice. Doctor ne tsaye akan mustapha yana dubasa, bisa takurawar mommy,ganin mustapha yaki farkawa har yanzu. Da sallama dauke abakunansu duka suka dakin. Doctor ne kawai ya amsa musu amma mommy kodagowa ta kasayi, suhailat kam tatasashi agaba takasa motsawa daga inda ta zauna,se sauke ajiyar zuciya take saukewa akai_akai............✍️ *BY* *Zeey kumurya* *ABUNDA KA SHUKA*......... _*(shizaka girba)*_ *MALLAKIN* 👇 *ZAINAB USMAN KUMURYA* *FARIN JINI WRITERS ASSO.....*📚 ~*Free novel*~ *Bismillahirrahmanirrahim* 3️⃣0️⃣ .........Karasawa kusa da mommy aunty tayi tagaisheta tare da tambayarta me jiki, cikin dashashshiya gami da sanyin murya mommy ta amsa mata. Tausayin mommy gaba daya yacika aunty, lokaci daya harta rame tayi zuru_zuru,kamar me jinyar itama. Gaisawa aunty sukayi da doctor dayake kokarin fita. "Doctor me'ake ciki ne, dan Allah kafadamun halin da dana yake ciki tun safe amma haryanzu kunkasa gano meke damunshi" mommy ta tsaida Dr, dake kokarin fita da fadin haka idonta na zubar hawaye. Asanyaye Dr yajuyo,shikansa jikinsa yayi sanyi da lamarin, sunyi kwajin jininma amma benuna musu akwai wani abu dake damunsaba, cikin son kwantarwada mommy hankali yace, "hajiya kikara hakuri munakan aikine, insha Allahu kafin dare zamu gano abunda kedamunsa" "to yaushe ze farfado" "shima nanbada jimawaba insha Allah,ciki gaba da masa addu'a kawai." shiru mommy tayi tana ayyana matukar mustapha be farfado ayauba sesuncanza asibiti, ita barima daddy yazo, kasar gaba daya za'a bari dashi. Gwara suje wata kasar aduba mata lafiyar danta. Cike da tausayawa aunty takebin mustapha da kallo, ita kanta bakaramin tsorata tayiba daganin yanda mustaphan yakomab lokaci daya, ahankali ta karasa daf da dashi takai hannu tataba goshinsa, zafin datajine yasata sauke hannunta dasauri, wannan wanne irin ciwone yake damun sa, zafin jikinsa ba irinna zafin ciwo bane data sani, nasa tamkar ana rura garwashin wuta, ga kuma bayanin dataji Dr,yanayiwa mommy na ba'asanma meke damunsaba. bin jikinsa tacigaba dayi da kallo,gaba daya jikinnasa ya shika ga numfashinsa dake fita dakyar. wani wahalallen numfashi aunty ta sauke afili ta furta. "Ya Allah,kabawa wannan yaro lafiya, kakawo masa sassauci da rangwame acikin wannan ciwon" gaba daya suka hada baki gurin cewa "ameen" jikin aunty gabadaya yayi sanyi, itakam wannan ciwo na mustapha ya firgitata ba kadanba, bata tunanin wannan ciwon na tashine. Kafadar suhailat dake gefenta ta dafa cikin rarrashi tafara mata magana. "Kiyi hakuri suhailat ba kukane mafitaba ahalin yanzu, addu'arki kawai yake bukata" aunty ta karashe zancen da share mata hawaye, ganin tunda tashigo dakin suhailat kuka kawai takeyi. Duk sesukabawa aunty tausayi, tabbas dole duka hankulansu ya tashi domin mustapha tamkar uba yake agurinsu duka, da daddy yana gari dabaya gari, shine ke musu komai, kuma duk da baya sakar musu fuska amma yajasu ajiki sosai, koyaya yaga wani sauyi atattare dasu ze tambayesu menene matsalarsu kuma ya magance musu ita,gwargwadon iyawarsa. mazauni aunty tayiwa kanta, sadiq yana bata bayanin ciwon mustaphan dakuma bayanin da likita ya masa....... Seda uku na rana ta wuce natashi daga bacci, nayi mamakin dadewar danayi ina baccin, duk da sam baccin bayamun dadi kawaidai yinshi nayi. cikin sauri na sakko daga kangadona nashiga toilet na kuskure baki, dannasan yanzu haka mommy tanacan tana jirana, ga girki zanyi. Nayi zaton ganin yaran gidan a falo kasancewar yau Friday,amma senaga babu kowa. Kofar dakin mommy naje nayi knocking naji shiru, komawa kan kujera nayi nazauna, atunanina tana wani uzurinne,mintuna biyar suka shude naji shiru. Yanke shawara nayi kawai bari naje naduba may be bacci takeyi. Koda nashiga dakin senaga batanan, mamakine yakamani dan gaskiya da wuya kaga mommy batanan a irin wannan lokacin, kuma babu alamun tana toilet,amma nasan banisa tayiba tunda har tabar dakinta abude. Fitowa nayi nanufi kitchen nafara wanke_wanken dabanyiba. Harna gama nakoma dakina nayi sallar la'asar ko motsin bera banjiba a part dinba balle na mutum. Se a lokacin nadakko wayata na kunna, ina kunnawa sakon yaya sadiq na shigowa,karantawa nafarayi acikin zuciyata kamar haka. _*my love,am sorry yau banzo na dakkokiba wani babban uzurine yatsaidani, dafatan kina lafiya,tun dazu naketa kiran wayarki akashe. need your du'a sweet*_ murmushi nayi tare da lumshe idona, aduk lokacin danaga wani sako na yaya sadiq koyamun kalamai na soyayya se'inji dama daga gurin yaya mustapha nake jinsu, tausayin yaya sadiq ne yakamani, ganinshi kullum cikin yin abunda zesani farinciki yakeyi amma ni kuma zuciyata naga wani can daban dabemasan ina yiba, aduk lokacin dana tuna haka se inji wani kunci yaziyarci zuciyata, da ina da yanda zanyi dana sauya sonda nakewa yaya mustapha zuwa ga yaya sadiq domin shiya cancanta zuciyata taso, amma kash nayi iya yina amma nakasa yin hakan, kullum son mustapha kara ta'azzara yakeyi acikin zuciyata. bude idona nayi ina sauke numfashi, nanemo number yaya sadiq na danna masa kira. Sadiq dawowarsa kenan daga restaurant yaje yasiyo musu abinci bisa takurawar aunty, dataga alamar babu me niyyar cin abinci, shine tace yaje yayo musu take away, ba'azauna haka ba'aciba. fita yayi daga dakin rejecting yayi sannan yakara kiranta. dama nasan baze dagaba sedai ya katse, kullum yaya sadiq cikin sakamun kati yakeyi amma baya taba daga kirana, sedai nakira aliya ko salimat musha hirarmu. dagawa nayi tare dayin sallama, amsamun yayi. Senaji muryarsa kamar bashi da lafiya. "Yayana lafiya kuwa, naji muryarkar haka?" Natambayeshi cikin kulawa. Numfasawa sadiq yayi yace, "lafiya kalau maryam, ina kikashiga naita kiran wayarki akashe?" Batare dana yarda da amsar daya baniba, nace. "Agajiye nadawo daga school ne, kuma ina dawowa bacci yadaukeni bandade datashiba" "ohk" kawai yace yayi shiru. nima shirunnayi na wasu sakanni kafin na katse shirunnamu dacewa, "anya kuwa yaya lafiya kake, naji muryarkafa akwai damuwa acikinta,pls dan Allah kafadamun meke damunka" wani zazzafan huci ya fesar yace, "maryam gaskiya da akwai matsala,yaya ne yau aka wayi gari bashi da lafiya,cuta me tsanani yanzuma muna asibi.....wata muguwar faduwar gabace ta ziyarceni, cikin gigita na katse yaya sadiq da fadin" wanne yayan kuma?" "yaya mustapha mana" shima yabani amsa. cikin sauri nace, "meke damunshi" bayanin halin da mustapha yake ciki sadiq yayiwa maryam atakaice. Kasa magana nayi saboda tsabar tashin hankalin jin *heartbeat* bashida lafiya. wani uban gumine yahau karyomun ta ko'ina ajikina, dukda banganshiba amma gabadaya tausayinsa yagama cikamun zuciya, naji babu abunda nake da bukata duk duniyarnan sama danaje nagansa naga halin dayake ciki. "Hello,maryam" muryar yaya sadiq tadawo dani cikin nutsuwata. wani yawu me daci na hadiye dakyar cikin tattaro nutsuwata, da sanyin murya nace, "na'am yaya, yanzu yajikinnasa" "dasauki za'ace maryam" "Allah yakara sauki,yabashi lafiya" "Ameen maryam,bari nakoma ciki." Sallama mukayi yadatse wayar. Tagumi na rafka cikin matukar damuwa, Ashe dama bashi da lafiya shiyasa yau befitoba har rana. Wayatace tahau vibrate alamun kira. Ahankali nakai hannu nadakko, ganin aliyace nadauka dasauri. "Hello maryam Ashe yayan kano bashi da lafiya" "wlh aliya nima yanzu yaya sadiq yake sanarmun" "nima naje school ne nadawo natarar aunty batanan shine masu aikinmu suke sanarmun tataho kanone yaya bashi da lafiya,inata kiran wayarta taki shiga,shine nace bari nakiraki" hankali nane yakara tashi jin abunda,aliya tace. Kenan ciwonnashi ya tsananta matuka tunda har aunty dake wani garin tazo. bamuyi wata hirar kirkiba mukayi sallama, dukanmu zuciyoyinmu babu dadi,tadaicemun gobe zasuzo ita da abbansu. Zarya nafarayi adaki ina tunanin hanyar dazanbi inje asibiti ayau ingano yaya mustapha, dan inbanganshiba akwai matsala. yunwar danake jima tuni nanemeta narasa,hankalina gaba daya yanaga inje inga jikin *heartbeat* ......... Acan asibiti kuwa jikin mustapha ne yakara rikicewa numfashin nasa dayake fita dakyar dinma yadauke dif, hankalinfa su mommy gabadaya inyayi dubu yatashi, mommy ma faduwa tayi sedaukarta akayi itama aka bata gado, aka mata allura tasamu bacci. Suhailat kam kuka takeyi sosai iya karfinta, tana sumbatu tana fadin, "dan Allah yaya katashi karka mutu katafi kabarni" ire_iren wadannan kalamai kawai takeyi. Aunty kuwa babu kuka na ido sena zuci. Fitowa sukayi gabadayansu daga dakin dayake, sukuma likitocin suka dukufa akansa domin ceto numfashinsa. su aunty suna bakin gurin atsaitsaye cikin karayar zuci, su haidarma se kuka suke, ga yaya ba lafiya ga mommy ma ta fadi,abun gwanin ban tausayi. Fiye da awa daya likitoci suna kan mustapha, har wani babban likitane yazo daban mesuna Dr, jibril. Karshema su aunty gani sukayi anfito dashi akan gadon tura marasa lafiya an nufi wani dakin daban dashi. Cikin tashin hankali su aunty sukabi bayansu dukansu, amma kafin su karasa har sun shige dashi dakin sun rufo. Hankalinsufa ya kara tashi, suka kara gigicewa. Se bayan magriba likitocin suka fito suna share gumi, dakyar suka samu numfashin mustapha yadawo ahakanma seda suka samasa oxygen, su Kansu likitocin ciwon mustapha ya tsoratar dasu yakeyi, gashi sunkasa gano takameman meke damunshi, sun masa gwajin jini, sundau hoton zuciyarsa, har gwajin kwakwalwa sun masa amma babu abunda suke gani na sakamakon wani ciwo nadamunsa. Abunda yake kara tsoratar dasu zafin da jikinsa yakeyi. Gabadaya su aunty sukayi kansu da tambayarsu ya jikinnasa, Dr, jibril ne yace musu subari suje suyi sallah su dawo, sesu musu bayani. Suma su sadiq din aunty cewa tayi suje suyi sallar, itama tatada tata agurin dama da alwalarta ta sallar la'asar. Suhailat kuwa tana zaune fuskarnan tayi jajur saboda kuka, wai ita batayin sallar. koda su yaya sadiq suka idar da sallah suka fito daga masallacin dake asibitin daddy yakirasa yasanarmasa yakaraso yana airport yazo ya daukesa. Shida zannurain suka tafi dakkonsa haidar da faruq kuma suka koma ciki. Aunty da suhailat na dakin mommy daketa bacci azaune, sunyi jigum_jigum. ahaka su haidar suka shigo suka samesu. Ahankali mommy ta bude idonta tana karewa dakin kallo, zumbur kuma ta mike zaune tana kokarin sakkowa,dasauri aunty da suhailat sukayi kanta suka riketa. Rungumeta suhailat tayi ajikinta tana fashewa da kuka. "Saudart, ina my son, yamutu ko, dan Allah karkicemun ya mutu" mommy ta fadi haka tana haki. Aunty bata,bata amsaba seda tajinginata da filon dake kan gadon sannan tace, "be mutuba aunty atika,amma suncanza masa daki kuma sunki barinmu shiga,amma babban likitan yace zasuje suyi sallah seyazo ya mana bayanin abunda kedamunsa" lumshe ido kawai mommy tayi batace komaiba. Mikewa aunty tayi domin sanarwada Dr,mommy ta farfado. a tare sukadawo dakin dawata nurse mace, sannu tayiwa mommy tare da tambayarta jikinta, dakai kawai mommy ta amsa mata. Duddubata takarayi ta fice. Su haidarma sannu sukayiwa mommy suka sanarmata isowar daddy. Agigice daddy yakaraso cikin asibitin, su sadiq na biye dashi abaya. dakin da sadiq yanuna masa mustapha yana ciki yanufa direct da nufin shiga,amma Dr jibril yatsaidashi. Tsayawa daddy yayi yana kallon Dr. Hannu Dr, yamikawa daddy sukayi musabaha yakara da fadin. "Ranka yadade, barka da wannan lokacin dafatan ka sauka lafiya" "lafiya kalau" daddy ya bashi amsa akagauce.danya matsu yaji meke damun dannasa. Fahimtar hakan da Dr, yayi seyace. "Idan babu damuwa,mu shiga nan dakin namuku bayanin gabadaya dan bayanin bazeyiyu atsayeba" yakarashe zancen da nuna dakin da mommy take ciki. dakin suka nufa gabadayansu. Mommy tana ganin daddy, takara rikecewa,itadai abarta taje taga danta. Karasawa kusa da ita daddy yayi cikin rarrashi yace, "kikara hakuri, atika insha Allahu zaki gansa anjima." Cikin kuka mommy tace, "daddy danbaka halinda my son yake cibane, bafaya numfashi...." lallaba mommy daddy yahauyi, dukda shima dauriya kawai yakeyi, amma zuciyarsa kwadayin ganin dansa kawai takeyi. bayan mommy tayi shiru, suka maida hankalinsu duka akan Dr dominjin mezece. Gyara murya Dr,yayi yafara magana yana duban daddy. "Ranka yadade, azahirin gaskiya munkasa gano takamaimen ciwon dake damun yaronka, munyi iya gwaje_gwajenmu akan duk abunda muke zargin ze iya haifar masa da wannan ciwon, amma result din dai baya bamu da wani ciwo ajikinsa. " haba doctor duk halin da dana yake ciki, amma kace kunkasa gano ciwon dake damunsa gaskiya Dr, nalura kamar bakusan aikinkuba, nidai Ku sallamemu kawai mucanza wani asibitin, kokuma mu fita dashi waje." Cewar mommy cikin zafin zuciya. Duban mommy Dr, yayi yace. "Hajiya bahaka bane, tun safe likitocinnan suke kansafa, ganin sun kasa gano mekedamunsa suka kirani. Ni'inama tsaka da aiki suka kirani, dabama zanzoba seda suka sanarmun yaronkune dakuma halin dayake ciki, haka na katse komai danakeyi nataho. ina zuwa ko zama banyiba nadukufa akan dubasa,amma haryanzu danake muku bayaninnan bamu gano meke damunsaba. amma ina ganin ta bakin naki zamubi, afitar dashi wajen kawai,su zasufimu gano mekedamunsa. Numfasawa aunty tayi tace, "bantari numfashinkaba doctor amma ni ayanda naga jikin mustapha dakuma bayananku kamar ba ciwon asibitine kedamunsaba, ina ganin kawai mukoma gida ayi masa na hausa." "Wanne irin na hausa kuma, mekike nufin yana damun yarona, nidai babu maganin hausan daza'ayiwa dana, kawai a fitarmun dashi waje aduba lafiyarsa." Mommy tafadi haka cikin hayayyakowa. Gyada kai doctor yayi yana kallon aunty yace, "tabbas abunda kika fada hajiya gaskiyane. Don muna samun irin wannan case din, na irin wadannan ciwukan da'ake rasa kansu dadama. Amma daga ankoma gida anyi nahausa sekaga andace idan Allah yaso. Ni likitane danasan aikina,amma idan zakuyi amfani da shawarata, ku koma dashi gida Ku nemar masa maganin hausa, idanma fitar dashidin zakuyi to kukaishi kasa me tsarki. (saudiya) domin gaskiya bana tantama ciwon dake damun mustapha bana asibiti bane, kodan wani irin zafi da jikinsa yakeyi........✍️ *AYI HAKURI DA TYPING ERROW BA EDITING NE* *By* *zeey kumurya* *ABUNDA KA SHUKA*......... _*(shizaka girba)*_ *MALLAKIN* 👇 *ZAINAB USMAN KUMURYA* *FARIN JINI WRITERS ASSO.....*📚 ~*Free novel*~ *Bismillahirrahmanirrahim* *3️⃣1️⃣* ...........Nidai gaskiya doctor dana bazan masa maganin hausaba,kawai Ku sallamemu yanzu mucanza asibiti kafin safiya muyi shirin fita dashi waje,tunda Ku kunkasa gano abunda kedamunsa." Mommy ta fadi haka tana batarai. Kallonta aunty tayi yanda take hakikancewa tana magana tamkar ba ita tagama lagwai_lagwai dazuba. Daddy da tunda aka fara maganar bece komaiba seyanzu ya numfasa yana duban doctor yace, "amma doctor mekake tunanin yana damunshi,kokuma yake kawo irin wannan ciwon haka." "Agaskiya alh,a yanzu dai bazance gashiba amma su masu maganin idan kukaje gurinsu zasu sanar muku da yardar Allah,yanzudai Ku barshi anan zuwa safiya mukara ganin abunda Allah zeyi akansa, semusan abunyi." "Toh shikenan doctor mungode yanzu zamu iya zuwa muganshi" "ehh,zaku iya zuwa ba matsala,amma se'akiyaye,danma naga kundamune shiyasa nabarku kuje kuganshi,amma aka'ida babu meshiga gurinsa,ayanzu. "ohk,insha Allah zamu kiyaye Dr." musabaha daddy sukayi da doctor yamusu sallama ya fice. Babu bata lokaci suma su daddy suka mike dukansu suka nufi dakin da mustapha yake. Yanayin dasuka ganshi bakaramin kara firgita daddy yayiba,gashinandai akwance shiba rayuwaba shiba mutuwaba, tambayoyi daddy yafara yiwa mommy akan ko abu yasamesa jiya kafin ya kwanta,kokuma yace mata wani guri najikinsa na masa ciwo, mommy tace babu komai lafiya kalau suka rabu. jikin daddy gabadaya yayi sanyi da ciwon mustapha, harya fara tunanin ko ciwon ajali ne yakama mustaphan dan haka yake shima arasa meke damun mutum. Addu'a kawai daddy yashiga yimasa acikin ransa akan Allah yabashi lafiya.... Yinin yau gabadaya cikin rashin nutsuwa nakarasashi, nayi tunanin duk hanyar dazanbi dazan iya zuwa naga yaya mustapha a yau amma bansamuba. Gashi banason na kira yaya sadiq akan inason zuwa, yayi tunanin wani abu daban,zama nayi naita tunane_tunane har akayi sallar magriba. Dakyar na iya tashi nayi sallah, sannan na dafa indomie guda daya,na watsawa cikina dan kar yunwa tamun illa. Ganin duhun dare yayi se tsoro yakamani ni kadai a part din. kamar daga sama naji tunanin abunda yafaru dani ranarnan yadawo cikin kwanyata, tiryen tiryen kamar yanzu abun yake faruwa. wani matsanancin tsorone yakamani, cikin sauri na mike na dauki wayata nafice daga part din gabadaya bayan na janyo duka kofofin part din na rufe. Part din su baba talatu nanufa,ina tafe ina tunanin abunda yafarun a kokarina nasan tuno wanene yazo da niyyar ketamun haddi, duka dai yayan gidan nasan muryoyinsu harma da megidan, kuma Wanda yazomun dindai yayi magana, "tokodai yaya faruq ne?" natambayi kaina, domin shine tunda nazo gidannan, jin muryarsa danayi befi a kirgaba. zato zunubi hakan yasani yin istigfari tare dayin addu'ar koma waye Allah yakareni daga mugun nufinsa. koda naje part din su baba talatu naji sunata zancen ciwon mustaphan, dayake drivern dayakai su mommy asibiti akwai matarsa acikin ma'aikatan gidan agurinsa ta jiyo musu. Nidai dakin baaba talatu nashige na kwanta bayan mungaisa dasu. zuciyata sam babu dadi, namarasa meyake damuna ahalin yanzu. Karatun kur'ani me girma na kunna awayata inaji ko zuciyata zata samu sukuni....... Acan asibiti kuwa tuburewa mommy tayi ita se'ancanzawa mustapha asibiti tunda nandin sunkasa aiwatar da komai. Hakuri daddy da aunty suka shiga bata tare da nuna mata, itafa lafiya ba likitoci ke bada itaba, Allah ne yake badawa a lokacin dayaso. Dakyar mommy ta hakura akan su kwana a asibitin zuwa safiya se'asan abunyi kamar yadda doctor yafada. Bayan sallar isha'i daddy yacewa dasu sadiq sukoma gida hakannan dasafe sazo, mommy kam dama anan zata kwana, suhailat ma daddy yace tabiyo su yaya sadiq amma tace, Sam itama a asibitin zata kwana, haka daddy yace abarta ta kwanan. Aunty kuwa harta mike zata tafi, daddy yace ta zauna itama ta Kwana,tace masa ai anyi yawa amma yace ta kwanandai danyaga tafi mommy hayyaci. shima zuwa anjima ze koma gida idan sungama tattaunawa da doctor. Adakin baba talatu nayi sallar isha'i, abinci ta zubo ta kawomun nace mata nakoshi naci abinci kafin na fito. Takuramun tayi naci kadan danma naji dadin zuciyata danaji karatun. Harna kwanta yaya sadiq yakirani, yacemun ina ina, nacemasa ina part din su baaba talatu, yacemun meyasa bazan kwana a part dinmuba, nace masa tsoro nakeji nikadai. Wai ni raguwace banda haka mene abun tsoro nadawo nan na kwanta, nace masa wlh bazan iyaba. Badan yasoba ayanda na fuskanta ya hakura ya barni na kwanan anan. sanarmun yayi yadawo gida zedebarwa su mommy kayane yakaimusu seya dawo, kamar nace masa zan bisa sekuma naji becemunba nima senayi shiru, amma yasha tambaya aguna akan yajikin yaya mustapha. nikadai adaki su baaba talatu suna falo suna hira, se juye_juye nakeyi akan katifa amma nakasa bacci. Mikewa nayi dama da alwalata nashiga jero nafilfili akan Allah yabawa *heartbeat* lafiya.......... Washegari,tunda sassafe daddy da sadiq suka koma asibiti, inda suka tarar da wani mummunan tashin hankalin,domin jikin mustapha yafi yanda suka barshi jiya rikicewa, dansu mommy kam yanda sukaga rana haka sukaga dare, dakyar likitocin suka samu suka shawo kan matsalar numfashinsa ya daidaita. Babban tashin hankalin su mommy rashin farfadowarsa. ganin haka yasa daddy babu bata lokaci yafara kiciniyar fitar dashi kasa me tsarki domin aduba lafiyarsa. Kafin karfe goma nasafe yan dubiya sunfara zarya a asibitin, danma ba'abari ashiga aganshi sedai ayiwa su mommy yame jiki. Abokanan daddy da iyalansu gamida makota da mutanen da'ake mutunci se tittidowa suke ta ko'ina. rashin lafiyarsa ta barbazune a daren jiya da yan'uwansa suka dora a social media. Yan'uwansu daddyma sunzo ba lefi,hakama na mommy......... Baccin dana samu yau bawani ishashshe bane, danbefi na awa biyu da rabiba, nadade ina sallar tawa duk dan akan Allah yabawa *heartbeat* lafiya, dannalura addu'a kawai yake bukata ahalin yanzu. Tunda duku_duku nakoma part dinmu saboda zanwa su mommy breakfast tun da aka idar da sallar asuba yaya sadiq yakirani yasanarmun. Tare muka koma da baaba talatu danta tayani aikin, munayi muna hira akan ciwon mustapha, duk ni hankalina gabadaya yana gurinsa jinakeyi kamar nayi tsuntsuwa naje nagansa. wajen 8:20 mungama komai munshirya tsaf yaya sadiq yazo yadauka, yauma senaji kamar ince zanbisa amma senakasa fada masa. dole haka nahakura nakoma nayi wanka nashirya na tafi islamiyya batare danaci koda abinciba. Su aliyama kafin 11 sunzo kano itada abbansu da yayanta, direct asibitin suka wuce. Koda akatashi daga islamiyya nadawo gida, senatarar gidan da baki yan dubiya. uniform kawai nacire mukahau aikin abinci dasu baaba talatu, nikam dauriya kawai nakeyi dan har wani jiri_jiri nakeji da zazzabi, kuma nasan yunwace da damuwa, dan tun jiya babu wani abincin kirki acikina. Tea nahada me kauri nasha sannan nafarajin yar nutsuwa. Muna cikin aikin, su aliya da aunty suka dawo gidan, yau aliya babu bakin surutu idanuntama sunyi luhu_luhu alamun taci kuka ta koshi, aunty cema yau me dauriyar yiwa mutane magana. Duk wanda yazo daga asibiti jiki asanyaye yake dawowa dan jikin mustapha kam sedai addu'a. Hankalina bakaramin kara tashi yakeba idan akayi zancen jikinnasa da yanda yake. kasa karasa aikinma nayi sebarmusu nayi nakoma daki nasha maganin ciwon kai saboda saramundin dayakeyi, kwanciya nayi wani wahalallen bacci yadaukeni. Acan asibiti kuwa mommy tatadawa daddy hankali akan ita sedai akai danta India ba saudiyaba,saboda tasan ciwonsa bana Islamic bane na asibitine. dole daddy badan yasoba yacanza akalar shirin tafiyar daga saudiya zuwa India. nadade ina baccin se bayan la'asar na tashi, bayan nayi sallah nakira yaya sadiq dan yau gabadaya bamuyi wayaba, yanzu kam banyi kasa a gwiwaba nasanar masa inason naje nadubu yaya mustapha yacemun idan yadawo da wuri semuje tare........ Ba'asamu damar fita da mustapha India ba ayau se washegari da karfe 10 nasafe jirginsu ze tashi, da mommy za'aje da daddy da kuma yaya sadiq, suhailat ma taso zuwa amma daddy yahana saboda makarantarta. Inatajiran yaya sadiq yazo muje asibiti amma har dare bezoba, se wajen 11 yakirani wai abubuwane suka shamasa kai nayi hakuri. bakin cikin danaji baze misaltuba, haka na hakura, yauma banyi kasa a gwiwaba natashi cikin dare nakai kukana gurin me duka, akan yatashi kafadun *heartbeat.* washegari tun sassafe aunty ta koma asibitin. Nikuma time din inata aikina dannayi sauri muje asibitin da aliya kafin natafi islamiyya. mungama shirinmu aunty takira tace muzauna dan harma sunwuce airport zasu tafi India, aijinayi tamkar anwatsamun garwashin wuta acikin raina, har toilet nashiga na buya nayi kuka saboda takaici, yanzu shikenan ban ganshiba harsun tafi ina ganin yaya sadiq nakirana amma naki dagawa, danshi nadorawa alhakin rashin zuwana asibiti daya kaini tun shekaran jiyan aida haka bata faruba. Su aunty ma bayan sallar azhar suka shirya suka tafi gida, sauran bakinma haka dama wasu tun jiya suka tafi. Suhailat ta dawo se kuka takeyi,mommy kam rabonda nasata a idona tun shekaran jiya da safe......... *AFTER 3 DAYS* Alhamdulillah su mommy sunje India lafiya, kuma jikin mustapha yayi kyau bakamar suna gidaba, danyanzu zafin jikinsa ya ragu kuma numfashinsa yadaidaita ya koma normal, sedaifa haryanzu besan wayake kansaba, ko idanunsa bebudeba har yanzu,kuma suma dai basu gano ciwon dake damunnasaba,suna dai ta gwaje_gwaje.......anan gida kuwa, suhailat ta damu kanta sosai, gashi ita ba gwanar addu'aba balle tadinga samun sauki, hakadai ta daure ta koma makaranta bisa umarnin daddy, kullum cikin waya da video call suke ita dasu mommy. Nikam gidan gabadaya yamun wani irin girma da fadi saboda rashin mustapha, ga yaya sadiq da mommy duk basanan,gaba daya yanzu nakoma wata sukuku dani. Yaya sadiq yaturomun hoton yaya mustapha ta WhatsApp naganshi, dukda a hoto naganshi amma yanajin jiki sosai,badare ba rana kodayaushe cikin yimasa addu'a nake. Tsakanina da suhailat yanzu gaisuwace kawai take hadamu,sekuma idan zata sakani aiki. Suhailat ce zaune acikin wata rumfa a school da'aka tanada dan zaman dalibai ita kadaice zaune a inda take tana jiran driver yazo yadauketa. Kirane yashigo wayarta dake hannunta tana latsawa, kamal ne yake kiranta dagawa tayi ta kara akunnenta. "Hello, babbar yarinya" murmushi suhailat tayi tace, "kamal nawa ykk" "lpy klu, ya garinne" "gari babu dadi kamal, kadawo kenan" "nadawo baby luv, yau da safennan, wanka kawai nayi nadan huta nace bari nakiraki domin nayi matukar kewarki" dariya suhailat tayi saboda yanda yadaddage yana magana, tace. "Nima nayi kewarka sosai my kamal, wai mekazaunayi a can kayi wannan dadewar?" "Bari kawai kedai babbar yarinya wani mahimmin aikine yatsaidani amma yanzu nagama, anci nasarama komai normal, kina inane haka" "ina school ina jiran driver zezo mutafi" "ah haba dawuri haka, bari nazo naganki kijirani nanda 15 minutes ganinan zuwa" bejira amsar suhailat ba ya katse wayar. Bin wayar tayi da kallo tana murmushi, itama tayi kewar kamal sosai, dansunfi wata basu haduba yayi tafiya kuma inda yaje wani kauyene ko waya basayi gurin babu network. kamar yadda yace kafinma 15 minutes din yakaraso, kiranta yayi ta fada masa inda take yazo yasameta. ahankali ta mike cikin takunta na kasaita na isa gurin motar tasa, wani fitinannen kallo kamal yake binta dashi me cike da jaraba yana lashe lebe. dakanta ta bude murfin motar tashiga fuskarta dauke da murmushi. tana zama kamal yasa hannu yamata wata muguwar runguma harseda ta tsorata. "wayyo kamal kasheni zakayine, kk mun irin wannan cabka haka." bebata amsaba se lumshe idonsa dayayi yana wani shinshina wuyanta yana kara manneta da jikinsa tare da busa mata numfashinsa. lumshe idonta tayi itama tsigar jikinta na tashi harta farajin sauyin yanayi ajikinta, daurewa tayi ta kwace jikinta daga garesa tana sauke numfashi. cikin wata irin murya kamal yace mata, "haba sweet, kwana nawa banji duminkiba amma shine yanzu munhadu zakimun rowar kanki pls ina cikin wani hali kibarni na samu nutsuwa dake" yakarashe zancen yana kara janyota jikinsa. itama tana bukatar wasannin dasuka saba ahalin yanzu, to amma damuwar rashin lafiyar mustapha bazata barta taji wani dadiba yanzu. Cikin sanyin murya tace masa, "kamal nima ina cikin bukata amma zuciyata cike take da damuwa shiyasa kaganni haka,am sorry" cikin nuna damuwa kamal yatambayeta meke damunta, atakaice ta masa bayanin abunda kefaruwa. damuwarsa sosai yanuna tare da yiwa mustapha addu'ar samun lafiya, suhailat taji dadin hakan kuwa danbatayi zaton haka daga gareshiba tunda mustapha yakasance abokin takararsane. Daga rarrashi kuma yazarce da lalabuta, ganin yana neman wuce gona da iri acikin makaranta, tace masa suje gidansa dan itama ta fara hawa network. abun nema yasamu ga kamal dama haka yakeso danyagama shirinsa tsaf yau akan suhailat, motar ya kunna ya bata wuta sukabar makarantar. Koda sukace gidansa abinci ya kawo yace suci, suhailat tace masa ta koshi ita kawai ya latseta take da bukata, lemo ya matsa mata setasha dole badan tasoba tadauka tasha. daki yajata suka fara masha'arsu, saidai yaufa abun yafi na kullum dan suhailat tafishi zakewa, wata mahaukaciyar sha'awace take cinta, duk abunda kamal yake mata danta samu gamsuwa yamata, amma bata gamsuba. sunfi awa biyu yana tabeta amma taki hakura, koya barta seta kara janyoshi sunkoma, karshema datagaji seta samasa kuka akan yana sane yaki gamsar da ita, rarrashinta yahauyi amma taki hakura domin gabadaya bata cikin hayyacinta. ganin tasa kuka kamal yarungumeta ajikinsa tare da fadin, "am sorry, sweet wlh namiki duk abunda nasan zegamsar dake,bansan kuma me kikesoba saidai in sex kike bukata." Da sauri tadago daga jikinsa cikin wahalalliyar murya tace, "pls kamal inason sex din indai ze gamsar dani." waro ido kamal yayi cikin pretending yace, "sweet kinsan me kike cewa kuwa, sex fa! keda bakyason sex, gaskiya bazan iya sex dakeba kar'azo samu matsala" cikin kuka tace, "babu wata matsala kamal, yau inaso kamal pls sex to me, I'm in needed,Inajin kamar zan mutune marata, pls kamal help me" takarashe zancen tana goggamasa nonuwanta akirjinsa. wani munafukin murmushi kamal yayi hakansa yakusa cimma ruwa, cikin zafi_zafi yafara aika mata da hot romance wanda suka kara haukatata, kafin daga baya ya shigeta da karfinsa........✍️🙄 *By* *zeey kumurya* *ABUNDA KA SHUKA*......... _*(shizaka girba)*_ *MALLAKIN* 👇 *ZAINAB USMAN KUMURYA* *FARIN JINI WRITERS ASSO.....*📚 ~*Free novel*~ *Bismillahirrahmanirrahim* 3️⃣2️⃣ .............Sosai suhailat taji zafi kasancewar shine karonta na farko data taba yin sex arayuwarta,amma duk da haka batasha wata wahala sosaiba. Kamal yau farincikin daya tsinci kansa aciki baze misaltuba abunda yadade yana nema Allah yabashi yau yayi nasarar amshe budurcin suhailat, aiko yadade yana abudaya da suhailat. seda komai ya lafa kuma sannan tarin nadama da tsoro suka zowa suhailat, tambayar kanta tafarayi anya kuwa tayiwa kanta adalaci, mezatacewa yaya mustapha idan sunyi aure. hawayen nadama tafara zubarwa cikin tsananin nadama, janyota kamal yayi jikinsa yahau rarrashinta da yaudararrun kalamansa harya yasamu tayi shiru karshema bacci yadauketa... Dana dawo daga school yau senaga aunty suhailat bata dawoba, kuma yanzu da wuri take dawowa bata kaiwa yammannan kamar da, abun mamaki harnayi aikina nagama suhailat bata dawoba, nikuma gani nikadai a part gashi duhu yafarayi tsoroma nakeji, haka nazauna nikadai tsuru a falo, se kunna kallo nayi danya debemun kewa. Suhailat tasha bacci sosai se dafda magriba ta farka, mamakin dadewar datayi tana bacci tayi. Dasauri ta mike tashiga toilet jikinta duk ya mata tsami se zugi datakeji kadan_kadan akasanta, wanka takarayi tare da gasa jikinta tafito tashirya ta dauki jakarta tafito falo inda kamal yake. cikin yaudararsa yatareta,ya kama tarairayarta yana lallabata,itadai kawai cemasa tayi yakaita gida,cikin tsananin farin ciki kamal yadauketa cak a hannu har bakin mota yakaita yadireta,sannan ya bude mata motar tashiga shima yazagaya yashiga driver seat yajasu zuwa gida. shiru suhailat tayi a motar ko uffan bataceba,duk kuwa da kokarin janta hira da kamal yakeyi, wani iri takejinta kamar ba itaba, duniyar gabadaya ta sauya mata,gashi tasan su mommy sunata nemanta basu sameta a wayaba danta kashe wayar gabadaya. har cikin gida kamal yakai suhailat ya'ajeta,yayi kokarin kara rarrashinta amma tafito dasauri tashige gida. Ina zaune a falo nikadai tsuru naga taga shigo tamkar ancillota ko sallama babu, gabanane yayanke yafadi ganin yanayinta kamar Mara lafiya duktayi wani iri, senayi tunanin ko wani abune yasamu yaya mustapha. Kasa hakuri nayi nace mata, "aunty suhailat lafiya kuwa naga yau kindade baki dawoba ko baki da lafiyane?" Cak suhailat ta tsaya daga kokarin shiga dakin datakeyi, juyowa tayi ta gallawa maryam harara tayi wucewarta,daki. bandamu da abunda tamunba,hasalima ni wani matsanancin tausayintane naji yakamani,batare danasan daliliba,cigaba nayi da kallona har akayi sallar isha'i sannan na tashi nakoma dakina. Suhailat kuwa tana shiga daki ta zube akan gado tana maida numfashi, wayarta ta zaro acikin Jakarta ta kunnata,bayan ta kunnu ta kunna data tahau online. tana hawa taga mommy online dasauri ta danna mata voice call,danbataso takirata video call taga halin datake ciki. Mommy tana kwance a masaukinsu tana hutawa tana chatting dinta,bama ta asibin a wannan lokacin, kiran suhailat yashigo wayar ta, dasauri ta daga dama tanata nemanta tundazu bata shigaba. "Hello mom'nah" "na'am, daughter ina kika boyene yau tun dazu nake nemanki a waya bansamekiba" cikin son boye damuwarta tace, "mom yau bandawo da wuriba kuma dana dawo bacci yadaukeni seyanzu natashi nayi wanka na kunna wayar" "ayya,daughter sannu,inafatandai bakyashan wahala a school din" "um,banasha mom, kewarkuce dai kawai tadameni data yayana" murmushi mommy tayi tace, "muma munyi kewarki sosai,kodayaushe daddy cikin zancenki yake." "Yawwa mom,kirokarmunshima dan Allah inason zuwa a week dinnan." "kibari next weekend su haidar zasuzo sekibiyosu kuzo tare" wani irin dadine ya lullube suhailat zataje taga life dinta nankusa, hira sukacigaba dayi da mommy tanata tambayarta abubuwan gida dayanda abubuwa suke tafiya,kafin daga bisani sukayi sallama. kwanciya suhailat tayi bayan sungama waya da mom tana tunani akan abunda yafaru da ita yau ita da kamal, tana ganin yanata kiranta amma taki dagawa, ko abinci bata nemaba balle tayi tunanin yin sallah tacigaba da kwanciyarta.............. Kwanci tashi babu wuya agurin Allah, yausu mustapha sunfi wata daya a India,amma dai jikinnasa gashinan gashinanne,har wanna lokacin besan wake kansaba bashi da aiki se bacci kuma komai sedai a masa,sedai a kwantar a tayar gashi memakon yarame sewata irin kumbura yakeyi. Yaya sadiq yazo gida sau biyu, daddyma yazazzo gida su suhailatma sunje can Indian saudaya sunduba jikinnasa. Aunty tazo kano itama taga yanda muke nida suhailat, mommy ce dai bata taba zuwa tunda suka tafi. Suhailat daa abunda yafaru tsakaninta da kamal yadameta, amma daga baya kuwa seta ware tamaida komai bakomaiba,kuma sukacigaba da mu'amalarsu da kamal. Munyi hutu a school na jaranawar second term da mukayi, yanzu saurana term daya nayi candy, a islamiyyaba munsauke alkur'ani amma a biye, bikin sauka kawai yarage mana shima ankusa samana rana. Acan India kuwa daddy ganin jikin mustapha yakiyin yanda akeso yace gaskiya gida za'adawo amma mommy taki yarda, seda aunty taje taga jikindai basauki sannan ta matsawa daddy dole badon mommy tasoba ta bari adawo gidan. yau talata yaune kuma su mommy zasu dawo, farin cikin danake ciki baze misaltuba yau zanga *heartbeat* tun safe muka gyare masa a part dinsa saboda acan zeyi jinyartasa. Aunty ma tazo kanon amma banda aliya. wani malami a Zaria,daya shahara a karya sihiri da cire jinnu daga jikin mutum,da maganin mayu dadai sauran lalurori, aunty tayi tattaki dakanta harzuwa kauyen dayake ta masa bayani akan ciwon mustapha, domin taji ana fadar kyan maganinsa sosai. dafarko cewa yayi akawo masa mustaphan har inda yake, sekuma aunty ta rokesa akan idan babu damuwa sutafi kano tare dashi, saboda yanayin da mustapha yake ciki, idan akace za'azo dashi garin wahala kawai za'asha saboda kauyen dayake basuda titi me kyau hanyoyin duk a rube suke. beyi wata doguwar gardama ya amince yabiyo aunty kano, amma da sharadin baze kwanaba aranar zejuyo gida saboda masu zuwa karbar magani, aunty tace babu komai ahakanma sungode. Karfe biyu na yamma a naija taiwa su mommy, haidar ne yaje ya dakkosu a airport zuwa gida. ina zaune ina karatun alkur'ani aunty tashigo dakin danake da sallama,amsa mata nayi bayan na kai aya narufe alkur'anin. "Maryam karatu akene" murmushi nayi nace "eh aunty" "masha Allah, yagajiyar aikin da kukasha" "babu gajiya aunty" gyara zama aunty tayi tace, "dama zuwa nayi nace miki,kije part din baki kitahoda malaminnan damuka zo tare,kirakashi part din Muhammad,nizan karasa kisameni acan" amsa mata nayi ta mike tafice, nima ajiye kur'anin nayi a ma'ajiyarsa nafito, na nufi part din bakin. Malamine me cike da kamala da nutsuwa,yanata lazimunsa naje nasameta. gaishesa nayi cikin mutuntuwa, sannan na isar masa da sakon aunty. biyoni yayi a bayana har zuwa part din *heartbeat* gabana sefaduwa yakeyi, ga farincikin zanganshi gakuma fargabar halin dazanje in riskeshi aciki. A falon sama na tarar da mommy, da aunty da daddy harda yaya mustapha. kallon mommy nakeyi kamar yadda itama take kallona irin kallon data sabamun, nikuma ina mata kallon mamakin yanda naganta,tamkar bame cinyaba, babu wata alamar damuwa a tattare da ita,amma fa aganina. cikin fara'a nakarasa gareta ina gaisheta dan itace acikinsu nadade bangantaba,amsamun tayi itama da fara'ar dauke a fuskarta takara da fadin, "maryama, ya gidan ya karatu?" "Alhamdulillah mommy, yame jiki" "jiki sai godiyar Allah" "Allah, yakara sauki yasa kaffarace" "ameen, duka dakin suka hada baki gurin amsawa" gaishe da daddy nayi dasuke magana da malam,shima ya amsamun da fara'arsa. Daddy nema kanaganinsa kasan yana cikin damuwa,dan har yar rama yayi. inason na tambaya ina mara lafiyar amma na kasa, haka na mike nafice nabasu guri. jagora daddy da yaya sadiq suka yiwa malam har dakin mustapha inda yake a kwance akan gado yana bacci. itadai mommy ba'ason rantaba aka dauko malaminnanba shiyasama bata wani bashi mahimmanciba. sadiq ne yakara yiwa malam bayanin abunda yake damun mustapha dalla_dalla, duddubashi malam yayi da baiwar da Allah yabasa. Shikansa malam yayi mamakin ciwon mustapha amma ko tantama bayayi aikin sihirine ko jinnu a ciwon mustapha. jakar magungunansa ya dakko yabawa daddy wani kullin magani, na karya sihiri. Za'a kwabashi da man habbatussauda se'adinga shafe masa jiki dashi safe da dare, se kuma ruwan jarka dayace abashi yayi tofi aciki shima yace kullum adinga diga masa abaki, atabbatar yana shiga cikinsa,insha Allahu ko wanne irin sihirine ajikinsa seya karye. godiya sosai daddy da aunty suka masa, kudi masu kauri daddy yabashi a matsayin sadaka danyaki fadar abunda za'a bashin. Bayan anyi sallar la'asar daddy yasa driver ya maidashi gida........ Mommy ce zaune a dakinta ita da daddy da aunty suna tattunawa akan abunda malam yace. "Nifa gaskiya sam banyarda da abunda malaminnan yaceba, kawaidai yazo yafadi abunda yagadamane, amma acikin awanni biyu harya gane sihiri akawa son" cewar mommy tana tabe baki. "Aunty atika kenan, aisu irin wadannan malaman baiwace Allah yabasu, kuma ni nayarda da abunda yace, saboda wlh ciwon Muhammad yayi kama da sihiri, idan kikayi la'akari yanayin ciwonnasa. Duk ciwon dakikaga anrasa gane kansa balle gindinsa, kuma ankasa gano meke damun mutum, tobaya wuce jinnu, kokuma asiri ko mayu" cewar aunty. kara tabe baki mommy tayi tace, "to saudart shiko mustapha, waye zemasa wani asiri, me yaywa wani, shida ko harkar mutane baya shiga" "hmmmm,aunty atika kenan, bar mutum kawai yanda kika gansa,zakiga kina rayuwarki baruwanki da mutum amma shi akwai mugun nufinsa akanki, mudai kawai muyi addu'a Allah yarabamu da sharrin makiya da mahassada" "amin, amma ni banso akayiwa mustapha wani maganin hausaba, dandai kundagene shiyasa na bari, danni gaskiya banyarda da wani ingancinsaba" daddy dayake saurarensu yace, "yanzu duk wannan zancen bashi bane, addu'a kawai itace mafita,kuma mu jarraba amfani da maganin malam din muga abunda Allah zeyi. Ita ko,aunty shiru tayi kawai tana kallon mommy, yanda taga yanzu hankalinta ya kwanta ba kamar farko da mustapha yafara cutaba, duk wannan muguwar damuwar datakeyi akan ciwonnasa yanzu tadena....... Kamar yadda malam yace adingawa mustapha amfani da magani haka ake masa, kullum babu fashi, yan dubiya kuwa kullum cikin zuwa sukeyi kota ina, duk da ba'a bari aganshi saboda bakin mutane, kowa da abunda zece. yau tsawon sati guda kenan anayiwa mustapha amfani da maganin, yaya sadiq ne yake jigilar shafa masa maganin da diga masa ruwan kodayaushe, amma jikin mustapha tamkar ba'a magani babu abunda yakaru nasauki sema karin ciwo, zuwa yanzu daddy yafara sarewa da ciwon mustapha ganin yakijin magani, mommy kuwa se masifa take tana cewa dama seda tace kar'ayi wani maganin hausa gashi babu abunda yayi sema karin ciwo. Aunty ce take kara tausarsu akan akara gwadawa zuwa nanda sati daya idan beyiba se'acanza wani malamin kokuma a fitar dashi kasar saudiyan kawai. *MARYAM* Har yau bansamu naga mustapha ba duk kuwa da matukar gwadayin ganinsa danake sonyi, yaudai nakasa hakuri seda nacewa yaya sadiq inason ganinsa dan tunda yafara ciwo banganshiba, shine yace dasafe nazo shine agurinsa sena shiga naganshi. da misalin karfe goma na safe bayan nagama aikina nanufi part dinnasa, babu kowa kuwa kamar yadda yaya sadiq yace seshi dayake kula dashi, seda najirashi a falo yagama kimtsashi sannan yafito yace nashiga naganshi. da mamaki na kalli yaya sadiq nace, "yaya nikadai zanshiga bandakai" "haba maryam,kemafa yar gidace kishiga kawai babu matsala zanyi wayane tun dazu ake kirana da ina ciki" gyada masa kai nayi. Ahankali na mike nafara tafiya zuciyata na luguden bugun datasaba aduk lokacin danayi kusanshi dashi. ahankali na murda handle din kofar dakin nashiga da sallama, dukda nasan babu me amsamun. Faduwar gaba da karuwar bugun zuciyatane suka dirarmu alokaci daya sanda nayi arba dashi kwance idanunsa a lumshe. jankafata nayi data faramun nauyi nakarasa gaban gadon ina mai kura masa ido. Jallabiyace ajikinsa wadda babu alamar datti a tattare da ita. "Ya Allah muntuba,Allah ka iya mana" nafada acikin zuciyata ina kara girmama ikon Allah, mutum me kwazo da kasaita,shine acikin wannan yanayin kwance komai sedai a masa,lallai muji tsoron Allah domin duniya abar banzace. Lumshe idona nayi ina tuno yanda yake abaya da lafayarsa amma yanzu gashi a kwance ko hannunsa baze iya dagawaba. ahankali nabude idona nasauke akan kyakkyawar fuskarsa da ita kadaice bata kumburaba ajikinsa. Hawaye ya shiga kwaranyomun a fuskata na tsananin tausayinsa, ga wani gumi dayaketa tsatstsafo masa na azabar ciwo, kawai jinayi nakai hannuna kan goshinsa ina ina share masa gumin kansa batare dana shirya yin hakanba, dukda wani zafi da huci danakeji a tafin hannunnawa amma nakasa cirewa daga goshinsa, sema kara kamasa kandanayi da danyatsuna biyu kamar yadda akeyi idan za'a kamawa me ciwon kai, kai. nafara karanto abunda ake karantawa nakamun kai acikin zuciyata, jikinane kawai yabani yanda kannannasa yake zuba uban gumi yana masa ciwo, seda na kammala karanta duk abunda ake karantawa sannan nasakar masa kannasa. Rankwafowa nayi daidai fuskarsa har ina jiyo hucin numfashinsa a fuskata,lumshe idona nayi,bugun zuciyata kuma ya karu, hannuna na rawa nakaishi daidai bakinsa naraba kananun lips dinsa nasama dana kasa, nafara karanto ayoyin rokiyya a fili yana shigarsa tacikin kunnensa kuma ina tofawa acikin bakinsa, dan idannatsaya debo ruwa nace zantofa aciki zanbatawa kaina lokacine, kuma yaya sadiq yana falo yana jirana. naji abakin aunty ciwon dake damunsa ana tunanin jinnune, duk da tsananin tsoron danakeji akan abunda nake aikatawa,amma haka na daure zuciyata, nacigaba da karanto masa domin wannan shine kadai taimakon dazan iya masa,kuma nasan bazan kara samun wata damar dazan masa irin wannanba.........✍️ *kuyi manage da wannan* *By* *zeey kumurya* *ABUNDA KA SHUKA*......... _*(shizaka girba)*_ *MALLAKIN* 👇 *ZAINAB USMAN KUMURYA* *FARIN JINI WRITERS ASSO.....*📚 ~*Free novel*~ *Bismillahirrahmanirrahim* 3️⃣3️⃣ ..........cikin ikon Allah harna gama karanta masa yaya sadiq bezo kiranaba kuma babu wanda yashigo,abunda ya bani mamaki kenan. Ammafa naji ajikina, dan naji jikina yayi mun wani iri kuma se rawa yakeyi, gabadaya na hada gumi ga wani mahaukacin bugu da zuciyata takemun. ahankali nakai hannuna dake karkarwa na taba goshinsa,senaji zafin jikinnasa ya ragu, se ajiyoyin zuciya naji yana saukewa akai_akai cikin baccinnasa, dauke hannuna nayi daga kannasa nima ina sauke ajiyar zuciyar. badon nasoba bakuma danna gaji da kallonsa naja jiki nafito zuwa falo, abun mamaki babu yaya sadiq babu dalilinsa, zama nayi akan kujera ina maida numfashi hannuna dafe dakaina dayake mugun saramun,wani irin shauki da kaunar yaya mustapha ne, yake kara ninkuwa araina gami da tsananin tausayinsa,daga gani base anfadaba kasan yana jin jiki,dakuma azabar ciwo, dama dazan iya dana maido da ciwonnasa jikina, wasu guntayen hawayene suka silalomun wanda bansan dalilinsuba,tabbas idan Allah yabaka lafiya yagama maka komai najin dadin rayuwa. nakai ten minutes azaune ina jiran yaya sadiq amma naji shiru bedawoba, mikewa nayi zanje naduba falon kasa koyacan, a kan steps mukacikaro da mommy,datake hawowa benen cikin sauri har bangazata tayi, bayanayi dasauri harna kusa faduwa dama jikina babu kwari sekuma narike karfen benen. "Maryam!" naji mommy takira sunana da alamun mamaki. Gabanane yayanke yafadi danbansan me mommy zatamunba intaga nikadaice agurin danta. "Na'am" na'amsa mata cikin rawar murya. "Mekike anan" cikin dauriyar abunda nakeji ajikina nace mata, "mommy nazo duba yayane, shine yaya sadiq yace injirashi zeje yadawo, kuma haryanzu bedawoba" mommy batakaramun magana sebina datayi da kallo, kasa nayi da kaina cikin faduwar gaba. "Yanzu sadiq son din yabarmun shikadai shikuma yakama gabansa" mommy ta fadi haka cike da bacin rai" batajira mezanceba ta raba tagefena tahaye saman. wata nannauyar ajiyar zuciya nasauke ina bin bayanta da kallo, "yanzu da'ace ina dakin mommy tazo tasameni mezance inayiwa danta,nagodewa Allah daseda nafito ita kuma tazo. Karasa sauka nayi nafice daga part din,banga yaya sadiq ba harna karasa part dinmu. Dakina nashige na kwanta akan gado,kaina na juyamun,addu'a nashiga karantowa acikin zuciyata har baccin wahala yadaukeni. Cikin baccina naji ana kiran sunana tare da tabani, ahankali na bude idona dasuka sauya kala saboda bacci, nace. "Uhm" muryar aunty naji tana fadin, "maryam, kitashi kiyi sallah baccin ya isa haka, har 2 tawuce fa" mikewa nayi zaune cike da mamakin dadewar danayi ina baccin ina yar mika nace, "aunty har 2 fa tawuce kikace banmasan nadade hakaba" "aitun dazu nashigo naga kina tashan bacci,nima baccinnayi banjima da tashiba" "bari naje nayi sallah aunty" nafadi haka ina sauka daga kangadon har yanzu idona begama budewaba kamarma inkoma baccin haka nakeji" bakina na wanke na dauro alwala nafito nayi sallah, har lokacin aunty tana kishingide akan gadona tana danna waya. bayan na idar aunty tadubeni tana murmushi tace, "kinjini da mutuniyar taki, wai yaushe zandawo kokuma ita tabiyoni" murmushin nayi nima nace, "gaskiya dai aunty dakin taho da ita, yanzu se ita kadai agidan ko?" "Maryam makaranta shiyasa bantaho da itaba,amma jibi Friday zance yayanta yakawota seta koma ran sunday, kuma bata gidama tana gidan kanwar abbansu dayake bamu da nisa" "yawwa aunty, harnaji dadi dakikce zatazo Allah yakaimu jibin" "ameen" gyara zama nayi natambayi aunty abunda yake damuna arai dafadin"aunty yame jikin kuwa" "jiki da sauki maryam, daga gurinshi nakema nabiyo tanan,yau jikinnashi yayi kyau sosai" gyada kai nayi nace, "Allah ubangiji yakaro sauki,amma aunty meyasa ba'abashi rubutu kokuma adinga masa tofi aruwa ana shafa masa ajiki" "nima dafarko nayi wannan tunanin maryam,amma ganin malam yabashi na shafawa ajikin yasa banmaida hankali akan adinga masa hakaba, kuma shima yabada tofin ana diga masa abaki" "hakane aunty, amma ni aganina addu'a bata yawa, malaminmu na islamiyya ya turamun ayayoyin da ake karantawa na rokiyya a wayata wanda SUDAIS ne yake karantawa,kullum kafin nayi bacci sena kunna naji harna haddacema yanzu, meze hana adinga kunnamasa shima yanaji, nikuma zantofa aruwa se'abashi yasha kokuma ashafa masa ajiki." Cikin gamsuwa da bayanan maryam aunty tace,gaskiya maryam kinkawo abu me kyau,aidamu bamuyi tunanin koda karatunne adinga kunnamasaba, wannan shawarartaki tayi sosai maryam, mungode Allah yasaka da alkhairi, anjima bayan la'asar idan zani semuje tare a fara masa." "Bakomai aunty fatanmu kawai,Allah yabashi lafiya" hira mukacigaba dayi da aunty, zuciyata fess da farinciki zandinga ganin *heartbeat* kullum, kuma da izinin Allah seya samu rangawame aciwon dake damunsa dan ayar Allah bakarya bace,kuma alkur'ani warakace ga dukkan kowanne ciwo. Kamar yadda aunty tace, dayamma mukaje na kunnamasa karatun adakinsa ita kuma takawomun ruwa a cup na tofa aka shafe masa jikinsa dashi. mommy da aunty tafada mata abunda za'adinga yiwa mustapha batace komaiba, daddy kam yayi farinciki sosai yayta sawa maryam albarka. Tundaga ranar kullum senaje namasa safe da dare,wataranma aunty tana falo nikadai take bari adakin inyi ta kallonsa. Kuma alhamdulillah jikinnasa yanasamun sassauci, dan wannan kumburin jikinnan nasa duka babu yanzu, saidaifa wani abun mamaki, duk sanda nazo nakunna masa karatun kuma akashafa masa ruwan tofin ajikinsa sejikinsa yayi sanyi kamar nakowa, amma washegari, ina kara zuwa za'a masa se'aji zafin jikinnasa yadawo zafi zau se ankuma masa yake tafiya. Su aliya sunzu sunyi kwana biyu ita da yan'uwan abbansu da yayanta,umma da saleemat ma sunzu harda gwaggo, duk sunzo dubiya, muna waya da saleemat ne nakefada mata ciwon yaya mustaphan, shine tafadawa umma, umman tace kodan kirkin sadiq zasuzo suduba yayansa,shine tayiwa gwaggo magana sukazo tare. Gwaggo anzo gidan alh.menasara hankali ya kwanta, mommy kam bata wani kulasuba daga gaisuwa shikenan, danma aunty tananan itakam ta karbesu hannu bibbiyu faran_faran. Yau asabar wanda yakama daidai da saura kwana 2 mukoma school, bayan nadawo daga islamiyya karfe 11/30 muka nufi part dinnasa nida aunty, dama a irin wannan lokacin kullum muke zuwa, kafin muje yaya sadiq yagama masa na malamin da'ake masa. A bakin kofa muka tarar da yaya sadiq ze fita, gaisawa mukayi aunty tayi gaba tabarni dashi. "Malamata" yaya sadiq yafada cikin sigar tsokana, batarai nayi nace, "kaganga ko, zaka kafara kenan" murmushi yayi yace, "to ba malamar bace, karya nayi" "a'a niba malama bace dalibace me koyo" "toh shikenan na yarda, gobefa zanwuce me'aza bani dazan dinga tunawa dake kullum da kullum inji kamar muna tare." "Mekakeso kafada mana se'inbaka" "kinyarda infadi koma mene zakiban" "insha Allah indai ina dashi zanbaka" "tom shikenan kibari segoben idan zamuyi sallama zanfada miki, danse yamma zan tafi," "Allah yakaimu goben lafiya" "ameen, malama sekin fito" yafadi haka yana dariya. kin kulasa nayi nayi tafiyata, inajinsa yana cigaba da dariyarsa. A falon saman na tarar da mommy, hakimce akan kujera tanata latsa waya hankalinta kwance, gaishenayi tare da mata yame jiki nashige daki. Aunty tana gaban gadon ta rafka tagumi tana kallonsa nashiga dakin da sallama,amsamun tayi batare data dauke idonta daga kallonsaba. wayata dake hannuna na kunna, nasaka karatun, dai_dai saitin kunnensa anan ake ajiyemasa nannaje nasamasa, nadawo nabude fridge din dake dakinsa na dakko ruwa nazuba a cup, nazauna inabin karatun azuciyata ina tofawa acikin ruwan, aunty ma bin karatun takeyi, karatun yanada dan yawa, munfi rabi munma kusa gamawa aunty tafita zata amsa waya, harna gama tofawa karatun yakare aunty bata dawoba, karambani nayi nadau cup din zanshafa masa ruwan ajiki, dama aunty ce take shafa masa kullum. ahankali nazauna abakin gadon bayan na ajiye cup din agabana akasa, kura masa ido nayi cikin tsananin kaunarsa, wani shaukin sansa da tausayinsa na mamaye dukkan jini da tsoka najikina, ahankali natsiyayo ruwan ahannuna nafara shafa masa a fuskarsa, zuciyata na luguden bugu tamkar zata faso kirjina tafito, wani irin bakon yanayi naji ya bakunci dukkan gabban jikina wanda bansan yazan misalta muku shiba, lumshe idona nayi lokacin danake shafa masa ruwan a wuyansa zuwa saman kirjinsa, wani irin laushine da fatarshi gata da santsi, hannayensa duka biyun nashafa masa tare da kafafunsa, dama iya inda ake shafa masa kenan. wayata dake gefensa na dauka na tsaya kawai ina kallonsa, zancen zuci nakeyi nikadai akan koyaushe bawan Allah zetashi yacigaba da rayuwa kamar kowa se Allah. hannun haguna dake rike da wayata nadafa fuskar gado dashi, hannun damana kuma nasashi asaman goshinsa ina shafe masa ruwan dayake gurin, ban'auneba kawai naji wayata tafada ta bayan fuskar gadon. da sauri na dago cikin takaicin fadawar wayar, "yanzu ni tayaya zan iya dakko wayata ana gurin." nafadi haka a fili cikin rashin sanin abunyi, niba'abun infadawa aunty wayata tafadaba tacemun meyakaini gurin, balle kuma mommy. shiru nayi inatunanin mafita, can wata dabara ta fadomun nakoma karshen fuskar gadon na leka sena hango dan kyalli kwabar wayata amma tayimun nesa bazan iya dakkowa tananba, dawowa nayi nahau kan gadon ina kallon fuskar yaya mustapha, ahankali nakai hannuna duka biyu na matsar dakansa gefe yakoma karshen filon dayake inda nacire kannasa nanna dora gwiwata na leka fuskar gadon, adaidai nan kuwa na hango kyallin wayartawa amma bazan iya daukowaba, hakura nayi nabar leken, nazo zandaga gwiwata kawai naji wani abu metudu acikin filonnasa, cike da mamaki nazare kafata duka nasaka hannuna atsakiyar filon ina ta bawa, wani abu naji nariko ahannuna ta cikin rigar filon kamar dutse. mamakine yakamani na mene kuma zekawo dutse cikin filo, Allah sarki bawan Allah yana kwance abu yanata damunsa aka amma saboda babu bakin magana baze iya fadaba. ahankali cikin lallabawa nakara saukar dakansa kasa daga kan filon gabadaya, na juya filon tabaya nazuge zip din rigar filon nazira hannu na dakko abun. ajiye abunnayi akan gadon nazuge zip din namaida filon daidai nakara kamo kannasa nadora akai ahankali. Abunda nadakko nakurawa ido, abun kamar kaskon turaren wuta yanayin shape dinshi,amma karamine sosai harda murfinsa kamar tukunyar dandankuwa da yara sukeyi da kasa. sakkowa nayi daga kan gadon nadauki abun ahannuna, wani dogon numfashi naji yaya mustapha yasauke harya kusa tsoratar dani, dasauri na kallesa naji yanata sauke ajiyar zuciya tare da numfarfashi. ahankali kuma naga fatar saman idonsa tana motsi kamar ze bude ido, dasauri nafita da gudu zuwa falo ina kwalawa aunty kira, aunty dake waya da abbansu aliya takatse wayar dasauri jin kiran da maryam take kwala mata, "lafiya maryam" aunty tatambayi maryam tana mikewa tsaye gabanta yana faduwa. cikin haki nace, "aunty zokigani naga idonsa yana motsi" ai aunty bata jira maryam takarasa abunda zatajeba tanufi dakin dasaurinta, ilaikuwa seta tararda abunda maryam tafada mata, cikin tsananin jin dadi aunty tace, "Alhamdulillah maryam, sauki yafara samuwa da yardar Allah, tunda har wani abu najikinsa yafara motsi" nima cikin tsananin farin ciki nace, "insha Allah, aunty dama naji yanata sauke ajiyar zuciya" shafa kansa aunty tayi tace, "Allah yakara baka lafiya Muhammad, Allah yasa warakarkace tazo,dakuma karshen ciwonka" "ameen aunty" "kinshafa masa tofinne" aunty tafadi haka bayan tadago tana dubana. "Eh aunty" "yawwa dama Inata addu'ar, Allah yasa kinshafa masa abban aliyane yatsaidani awaya shiyasa." "Tom aunty bakomai bari nakoma" "ohk, maryam,mungode sosai Allah yayi albarka" "ameen" nafadi haka ina juyawa nafita, haryanzu abunnan yana hannuna na damkeshi, tare da boye hannunnawa acikin hijabi. bayan fitar maryam aunty ta dauki guntun ruwan tofin tasa acikin fridge, tazauna agefen gadon tabi bayan kiranda abbansu aliya yaketa mata bayan katse kiran datayi. Cikin sauri nake tafiya saboda Allah,Allah nake nakarasa part dinmu nabude abun hannuna naga menene, Allah yasoni babu kowa a falo nayi sauri nashige dakina. ajiye abunnayi akan madubi, nafara kokarin budewa amma abun yaki buduwa tamkar ansaka gam amanne, hakura nayi ganin nayi_nayi yaki buduwa nabarshi a gurin nakama sabgar gabana,danbanyi tunanin wani abune me mahimmanciba. Se bayan sallar azahar aunty tadawo daga part din mustapha, ta baro mommy da haidar agurinsa. Bayan sallar lasa'ar nafito falo nahadu da yaya sadiq yana kokarin fita da sauri yatsaya yace, "maryam, ina kika ajiye wayarki inata kiranki akashe" "yayana ta mutune ba caji" "haba maryam duk wutarnan amma kika bari wayarki ta mutu kuma tundazu bakisa cajiba" "baccine yadaukeni kuma namanta bansaka cajinba seyanzu dana tashi" "ohk,tafiyar danace miki zanyi gobe tadawo yau" da mamaki nake kallon sa nace, "yaya yau kuma ai yamma tayi kabaridai goben" "wlh maryam, kiran gaggawane yasameni daga kamfanin daddy na abuja" cikin sanyin jiki nace, "shikenan yayana Allah yakiyaye hanya" "to mene kuma, ko bakyason natafi naga dukkinyi wani iri" kaina nagyada masa alamun eh, haka kawai naji banason yatafi jikina duk yayi sanyi. "Kiyi hakuri kinji maryam dita, aiba dadewa zanyiba zandawo befi nayi sati dayaba ki saki jikinki kinji, karki karyamun gwiwa" danne damuwata nayi ina murmushi nace, "shikenan yayana, Adawo lafiya Allah yakiyaye, ya kare hanya kakuma kulamun da kanka" murmushi sadiq yayi cikin jin kalaman maryam yace, "kokefa yar matata, nagode sosai, kikulamun dakanki kema sosai I will miss u" "miss u too dear" nafadi haka kaina akasa, cikin fadada fara'a sadiq yace. "Byeeer I love you" hannu nadaga masa alamar bye_bye nace, "love u too" sekuma najuya da sauri nakoma dakina. Murmushi sadiq yayi yanabin maryam da kallo cike bansha'awa da tsananin kaunarta, harta shige daki sannan ya juya yatafi. Wuraren karfe 5:30 muna zaune nida aunty a falo aunty suhailat tashigo falon, da alama daga unguwa take, dan taci kwalliyarta hannunta kuma nadauke da jaka. seda tazo tsakiyar falon tayi sallama shima dantaga aunty ne dabaza tayiba. "Suhailat daga ina haka dannasan yau ba school" aunty tafadi haka bayan mun amsa mata sallamar tata. "Naje gidan wata friend ditane" itama suhailat din ta bata amsa da haka. Kallon suhailat aunty takeyi cike da tuhuma ganin yanda taga gabadaya ta canza sannan tace, "wakika tambaya" cike da kosawa suhailat tace, "mom" atakaice. aunty bata kara cewa komaiba, ita kuma suhailat tashige daki tana tutturo baki gami da kunkuni. Daga gurin kamal take, yanzu kullum ta Allah sesun hadu sun sheke ayarsu, ko duba mustapha ma saudaya take zuwa a rana, yanzu tazama yar hannu, idan bataje tayi sex da kamal ba kullum bata samun nutsuwa. Aunty takanas taje har dakin mommy bayan sallar magriba tayi mata magana akan fitar suhailat, se mommy tace ita batason haka mene nadamuwa akan yawan fitar suhailat din, yar marainiyar Allah ma se'ansa mata ido,adai dinga kyautata zato. Ran aunty yayi matukar baci dajin kalaman aunty, amma ta daure batace mata komaiba tatashi tafito ta bata guri,ita bada wata manufa tafada mataba,tafada matane kawai akan amata fada ganin yawonnata yayi yawa, alhalin kuma ga wanda ake saran yazama mijinta kwance babu lafiya. kewar wayata duk ta isheni yau, gashi nakasa fadawa kowa tafada bayan gado, seda daddare daza'asawa yaya mustapha karatu nake fadawa aunty, fada tamun akan meyasa banfadaba tundazuba har gashi dare yayi, dole yanzu sedai abari da safe adakkomun. guntun ruwan safe kawai aunty ta shafa masa, tunda babu wayar saka karatun. Yau zannurain da faruq ne zasu kwana dashi tunda sadiq bayanan. Kafin 10 nadare nayi bacci tunda babu waya ahannuna, dama ita takesa nakai 11 a online muna chat da kawayena a group dinmu na school. cikin baccina yauma naji ana lalubata gami da yamutsani da karfin gaske, a matukar firgice na farka ina kokarin kwarara ihu, naji anrufemun baki, irin kaurin danaji wancan karon yauma shinaji, "ya Allah wannan wacce irin masiface da jaraba gami da bala'i waye wannan memugun nufinne?" nafadi haka araina cikin tsananin firgici gami da razani. banyi kasa a gwiwaba gurin karanto addu'a da kokarin kwatar kaina iya iyawata, gabadaya jikina rawa yakeyi zuciyata na harbawa da sauri_da sauri, ga wani jiri_jiri danakeji yana kwasata amma haka nadaure nacigaba da kokarin kwatar kaina, harna samu na kwaci kaina natashi da mike da sauri na sauka daga kan gadon ina kokarin guduwa, dasauri mutumin yabiyo bayana yadamki gashin kaina da karfi, kara na kwalla da iyakacin karfina saboda matsananciyar azabar data ziyarceni, juyo dani mutumin yayi yafara kokarin maidani kan gadon, turjewa nayi naki tafiya, tamkar masu dambe haka mukahau kokawa ninaki yarda yakaini kasa shima yaki hakura, seja baya nakeyi duk da dakin duhune dinkim amma haka nafara laluban kan mudubin dakina kozan samu makami, cikin ikon Allah naji nataba gaban madubin, hannuna nasa nadaki ruwan madubin da karfi, jikake bassss! Yayi kara ya karye, ko zafin yankar da madubin yamun atafin hannuna banjiba na kara karyo wani, hannunsa daya da mutumin yarike hannuna yana kokarin jana nakartawa mudubin da sauri yasakarmun hannunnawa, rike katakon madubin nayi gam nakara daga madubin dayake hannuna na yankesa goshi cikin duhu batare dana masan inda na yankaba, cikin tsananin jin azaba mutumin ya janyo maryam da dukkan karfinsa, da nufin ya tumurmusata cikin tsananin zafin rai,ganin tana bata masa lokaci. gabadaya muka taho nida madubin, mutumin ya cillani akan gadon, shikuma madubin yafadi kasa, wani abune me kyalli,naga yayi tsalle daga kan madubin yafadi a acan gefe akasa jikake toshhhhhhh!! yafashe wani bakin hayaki yafara fita daga cikinsa tare da wata muguwar kara data karade part din gabadaya me barazanar toshe kunnen mutum yakoma kurma. fashewar abun yayi daidai da tashin mustapha zaune daga kwancen dayake tamkar gawa cikin wani irin yanayi yana kiran sunan ALLAH da dukkan karfin muryarsa da Allah yayi masa............✍️ *By* *zeey kumurya* *ABUNDA KA SHUKA*......... _*(shizaka girba)*_ *MALLAKIN* 👇 *ZAINAB USMAN KUMURYA* *FARIN JINI WRITERS ASSO.....*📚 ~*Free novel*~ *Bismillahirrahmanirrahim* 3️⃣4️⃣ ...........A matukar firgice zannurain dake gefensa a kwance ya farka daga bacci, saboda karar abunnan harnan suka jiyota, ga kuma sunan Allah da mustapha yakira tamkar acikin kunnensa, ahankali yakai hannu yana shafa inda ya'ajiye wayarsa jikinsa gabadaya na kyarma saboda tsorata, dakyar yasamu ya lalubota ya kunna fitila inda mustapha yake yahaska yaganshi a zaune, bayansa jingine da fuskar gadon amma idanunsa a rufe. Se numfarfashi dayake saukewa akai_akai. abunda ya matukar bawa zannurain mamaki kenan tamkar bashi yaji yana kiran sunan Allah yanzu ba, amma cikin abunda befi sakan gomaba har yayi shiru yakoma gidan jiya,haska kasan dakin zannurain yayi yaga babu faruq babu alamarsa kuma alhalin harya kwanta faruq yana cikin dakin. Number daddy yafara dialing domin yasanarmasa abunda yake faruwa....... A,part din mommy kuwa, dasauri na toshe kunnuwana da duka hannayena biyu saboda muguwar karar dake tashi adakina, wani mahaukaciyar juyawa naji kaina namun tamkar numfashina zebar gangar jikina, daga nan bankara sanin inda kaina yakeba. cikin zafinnama mutumin yasaki maryam yasakko daga kan gadon yafice da gudu kamar wancan lokacin, aunty tana kan sallaya taji wannan muguwar karar itama, dasauri ta mike tana karanto sunan Allah, dakuma addu'ar neman tsari daga abunki, cikin abunda befi sakan 5 ba, taji karar ta dauke dif, ajiyar zuciya ta sauke cikin dakakkiyar zuciya ta fito falo, karaf a idanunta taga mutum yabude kofar falon yafice da sauri, kasancewar falon akwai wadatuwar haske, cike da tsananin mamaki tayi yunkurin nufar kofar dantaga waye wannan, amma fitowar suhailat a firgice da gudu ya katse mata hanzari, rukunkume aunty suhailat tayi saboda tsananin tsorata da karar dataji, jikinta se rawa yakeyi tamkar mazari tama kasa magana tsabar firgici. ganin yanda take a matukar tsorace aunty ta rungumeta ajikinta tahau tofa mata addu'a akai. Hankalin mommy a matukar tashe tafito daga dakinta, kosu aunty dake tsaye bata kalli inda sukeba tanufi dakin maryam cikin sauri tamkar zata tashi zama, janye suhailat aunty tayi daga jikinta tabi bayan mommy dasauri danse yanzu talura da wani hakayi dayake fita ta wajen key din kofar dakin maryam, suhailat ma cikin sauri tabi bayansu. azafafe mommy ta tatura kofar ta shiga dakin tana kiran sunan maryam da karfi. aunty dake bimata baya tana shiga dakin wani wari gami da kauri mara dadi yaziyarci hancinta, toshe hancinta tayi dasauri cikin tsananin dauriya takarasa shiga dakin, suhailat kuwa dasauri tayi baya tarin dabata shirya masaba ya turniketa, laluban makunnin dakin mommy tayi ta kunna light haske ya gauraye dakin. cike da mamaki gami da tsoro aunty take kallon abunda yafashe din, yanda wani bakin hayaki yake tashi daga cikinsa. Mommy kuwa cike da tsananin tashin hankali take kallon abun, nandanan jikinta yadauki kyarma idanunta sukayi jajur alamar tsananin tashin hankali. Aunty bata lura da halin da mommy take cikiba, tanufi kan gado inda maryam take kwance itama tana kiran sunan ta, amma taji shiru. Batare dawani bata lokaciba aunty ta dakko maryam tafito da ita daga dakin da saurinta cikin tsananin rudewa ganin maryam babu alamar numfashi ajikinta ga wannan hayakin ze iya cutar da ita idan akabarta acikinsa, gakuma jinin dake zuba ahannunta, direct dakinta ta nufa da ita ta shimfideta akan gado,suhailat nabiye da ita abaya a tsorace................ Daddy cikin baccinsa shima yaji wannan karar kamar a zahiri kamar a mafarki, bejima da kwanciya ba bacci nacin sa hakan yasa betashiba, amma kiran wayarsa da'ake tayine yasashi dole yatashi ya dakko wayar yaga zannurain ne, gabansane yayanke yafadi danyasan ba lafiyaba, daga wayar yayi da sauri yakara akunnensa kafin yayi magana zannurain yarigashi dafadin "daddy pls kazo part din yaya yanzu" aiko bari daddy beyi yakarasa zancenba, ya mike da sauri yafice daga part dinnasa, danyanda yaji muryar zannurain yasan bakalauba. zannurain kuwa yanata faman jijjiga mustapha gami da kiran sunansa, ahaka daddy yakaraso yazo yasamesu. "Usman lafiya meyafaru dashi" daddy yashigo dakin yana tambayar zannurain cikin tashin hankali. "Dad, inacikin bacci naji muryarsa yana kiran sunan Allah, amma kafin nayi yunkurin tashi harya koma haka, ahaka na tashi nagansa a zaune." Cikin tsananin farin ciki daddy yace, "usman! Dagaske mustapha dakansa yatashi zaunennan kuma harda magana" "eh daddy dagaske wlh, nima nayi matukar mamaki" wata nannauyar ajiyar zuciya daddy yasauke, tare da fadin. "Alhamdulillah" harsau uku, sannan yakai hannu ya kunna light din dakin. zama yayi a gefen gadon tare da janyo mustapha jikinsa, sakayau daddy yajishi babu wannan mugun nauyi dayayi sanda yana ciwo, gajikinshi normal babu zafinnan kokadan, hannunsa yakai yataba goshinsa yaji shima babu wannan zafin, umarta zannurain daddy yayi yadakko masa ruwa me sanyi a fridge, dasauri zannurain ya mike, ya dakko ruwan ya mika masa, zuba ruwan daddy yayi ahannunasa yahau shafawa mustapha afuskarsa zuwa wuyansa, wani dogon numfashi mustapha yaja, ahankali yafara bude idonsa yana sauke ajiyar zuciya. cikin tsananin farin ciki mara misaltuba daddy yakira sunansa, be amsa masaba se kallo daya bishi dashi. Zannurain dayakasa magana saboda tsananin murna yace, "yaya!" maida kallonsa mustapha yayi akan zannurain ya kura masa ido, cikin tsananin doki zannurain yafara neman layin mommy danya mata wannan daddadan albishir din danyasan setafi kowa murna da farfadowar mustapha, kiran ya shiga amma mommy bata dagaba, behakuraba yakuma kirannata. Daddy dake ta kallon mustapha cike da tsananin tausayawa ganin yanda yaketa sauke ajiyar zuciya ya dubi zannurain yace, "nasan mominku kake kira, idan bata dagaba ka kyaleta zuwa safiya, kakara kiranta" ajiye wayar zannurain yayi yadawo kusa dasu daddy yakama hannun dan'uwansa fuskarsa dauke da fara'a menuni da zallar farin cikin dayake ciki. ganin yanda mustapha yakurawa robar ruwan da haidar ya dakko se daddy ya fuskanci kamar yanason ruwanne, dakkowa yayi yakafa masa abakinsa, aiko tamakar jaririn daya dade besha nonon uwarsaba haka yakama kukkutar ruwan, sedayashanye tasss. sannu daddy yamasa, lumshe idonsa kawai yayi yana cigaba da sauke ajiyoyin zuciya. Kwantar dashi daddy yayi akan gadon, yanufi toilet din dake dakin yadauro alwala yafito yafara sallah dannuna godiyarsa ga ubangiji maji rokon bayinsa dayabawa mustapha lafiya a lokacin dabasuyi zatoba ko tsammaniba, zannurain kuwa yakasa barin kusa da yayansa se kallonsa yakeyi cike da farin cikin tashinnasa............ Mommy bayan fitar aunty da maryam takai hannu da nufin daukar abunda yafashedin sekuma tayi wani tunani tafasa ta fice daga dakin dasauri cikin wani irin yanayi mewuyar fassaruwa. hankalin aunty a matukar tashe take shafawa maryam ruwa ajikinta, suhailat kuma namata firfita bisa umarnin aunty. gashi hankalin aunty ya rabu biyu, sotake taje taga menene adakin maryam dayake hayaki, tabbas kotantama batayi akwai wata kulallaliya akarkashin kasa da kuma kitimurmura dake faruwa,sannan kuma ga tunanin wanda tagani yafice daga falon. hannun maryam aunty ta wanke mata jinin tare da daure matashi da kyalle. Kusan 20 minutes sannan maryam taja dogon numfashi gami da mikewa zaune a firgice tana kokarin guduwa tare da fadin, "waye kai, meyasa kakeson cutar dani kayi hakuri dan Allah karka rabani da martabata, aunty, mommy kutaimakeni,karku bari yabatamun rayuwa!" Kalaman da maryam takeyi kenan cikin kuka. Fahimtar da aunty tayi bata cikin hayyacinta seta riketa gam ajikinta tahau shafa bayanta.tare da karanto addu'a tana tofa mata. Luf maryam tayi ajikin aunty, tana sauke ajiyar zuciya. Can kuma cikin wahalalliyar murya tace, "ruwa,ruwa" suhailat ce tatashi tadakko takawo mata, domin ita kanta jikinta yayi sanyi da yanda abubuwan suke faruwa ta kuma fahimci wanine yazo domin ya cutar da maryam din a kalamanata. Ruwan aunty tabawa maryam tasha sannan ta kwantar da ita akan gado tana cigaba da tofa mata addu'a, bajimawa bacci menauyi yayi awon gaba da ita. ganin maryam tasamu bacci aunty tadubi suhailat tace, "kikwanta kema kinga tsakiyar darene zanje naduba dakin maryam din" gyada mata kai suhailat tayi, sotake tatambayi aunty meke faruwa amma takasa magana. ficewa aunty tayi ta nufi dakin maryam zuciyarta namata sake_sake, kalaman maryam sunkara sata acikin duhu,kenan wanda tagani ya fita farmaki yakaiwa maryam. "tabbas akwai abunda ake kullawa maryam, tunda naga wani yafita da gudu daga falonnan sannan kuma ga abunda nagani adakinta, ga kuma kalaman datakeyi. amma insha Allahu koma waye sedai mugun nufinsa yakoma kansa" aunty ta fadi haka afili, sanda tashiga dakin maryam din, bin dakin tahauyi da kallo daga gani ansha artabo tsakanin koma waye da maryam, ganin yanda dakin yake duk a hargitse. Tsugunnawa tayi agaban abunnan tana karanto ayatul kursiyyu a fili sannan tasa hannu tadauki abun, dasauri aunty tasakeshi saboda zafin dataji ahannunta yana shirin konata. Kurawa abun ido tayi danganin menene aciki, abunda kawai ta fahimta wata yarkaramar layace sekuma gashi dake saman layar, har lokacin kuma hayaki nafita daga cikin abun kadan_kadan. aunty macece dabata tsoro kokadan akan irin wadannan abubuwan, tunani barkataine sukazo mata cikin kwanyarta akan abunda yafaru. Daddy seda ya idar da sallah yake tambayar zannurain ina faruq, yace masa shima tashi yayi yaga begansaba. duddubawa daddy yace yayi ko yana wani dakin, amma zannurain yaduba ko'ina a part din begansaba har kasa begansaba. Daddy beyi tunanin komaiba danyasan halin faruq, may be abunnasane ya motsa ya koma part dinsu...... Mommy tana komawa dakinta cikin tsananin tashin hankali ta daukko wayarta missed call din zannurain tagani, dama tasan za'ayi haka dantasan zuwa yanzu mustapha ya mike. wata Number ta lalulubo takira takara wayar a kunnenta, ringing biyu aka daga cikin kunar zuciya gami da tsananin bakin ciki mommy tafara magana. "Dan' albarkana, ya'akayi haka ta faru meyasa al'amuran suka lalace yauma bakayi nasara akannata bane?" Daga daya bangaren akace, "hmmmm, mommy yarinyar tana wahalar damu gashi gabadaya ta dagula mana lissafi tadawo mana da hannun agogo baya, muna gabda cimma nasara akan abunda mukayi shekaru muna nema, amma rana daya tazo ta ruguza mana komai. waiyama akayi wannan kaskon yazo dakinta?" "bansaniba nima wlh, shine abunda yafi komai dagamun hankali dasani dimuwa" cewar mommy cikin tsananin bacin rai. "Mommy, akwai matsalafa domin *boka tsidau* yacemun aikinmu yana gab da lalacewa,matukar bamu dageba" wata mahaukaciyar dariya mommy takece da ita, kafin daga baya ta hade rai tace, "karyane dana, aikina baze taba lalacewaba nicefa atika, kaidai kazuba ido kaga abunda zanyi, itama yarinyar datake batamun shirina sena kasheta da hannuna,.!,domin tunda tazo gidannan komai nawa yakeyin baya" mommy takarasa zancen cikin Karaji,zuciyarta na tafarfasa. "Amma mo.... " karkace komai dana, kaidai kawai katabbatar kabar gidannan adarennan kafin wani yaganka" mommy tana gama fadar haka ta katse kiran tare da bin bayan kiran zannurain,amma harta katse shima bedagaba, time din yaje duban faruq wayartasa kuma tana silent shiyasa daddy beji kiranba. Aunty ta jima durkushe agaban abunnan tana karanto addu'a tana tofawa acikinsa, sannan tasamu hayakin dake fita daga cikinsa yadena fita. ahankali takai hannu akaro na biyu ta dauki abun setaji babu zafinnan, dakinta ta nufa dashi dauke ahannunta...... *AFTER SOME HOURS* Har safiya su aunty basusan halin da'ake cikiba game da farfadowar mustapha, kuma haryanzu maryam bata tashiba aunty ma bata tashetaba,duk da zuciyarta a kwadaice take dajin ina maryam ta samo abunnan. zannurain bega missed call din mommy ba sebayan daya dawo daga masallacin sallar asuba,yabi bayan kirannata kuma bata dagaba. A masallaci daddy haidar kawai yagani bega faruq ba, ya tambayi haidar koya baroshi a part dinsune yace masa besaniba koyana cikin dakinshi. tare da haidar suka dunguma duka zuwa part din mustapha, dan tun kafin a tada sallah zannurain ya guntsa masa yaya ya mike. Aunty takira daddy danta sanar masa abunda yake faruwa yace mata tazo part din mustapha shima akwai abunda yakeson sanar mata, takuma biya tataho da mommy dansuna ta sabanin kira da ita. Koda aunty tazo dakin mommy, seta tarar mommy tana cikin toilet hakan yasata ficewa tafadawa suhailat idan mommy tafito tasamesu a part din mustaphan. Mustapha yana kwance akan gado, idanunsa a lumshe amma ba bacci yakeba, su haidar suna zagaye dashi, sun rasa inda zasu tsoma kansu dan farinciki, ahaka aunty tashigo ta samesu bakinta dauke da sallama, amsa mata sukayi atare fuskokinsu dauke da murmushi. da mamaki aunty take kallonsu kafin tace wani abu haidar yay caraf yace, "auntynmu kibani goron albishir dan albishir din dazan miki yacancanta kibani goro me daraja, yayanmu ya warke harya mike zaune dakans......"dagaske kake haidar" aunty tafadi haka cikin tsananin farin ciki tana nufar inda mustapha yake. "Dagaske yake saudart" cewar daddy yana murmushi. "Godiya ta tabbata ga Allah, me rahama dajin kai ga bayinsa,Allah kakara sassauta mana, ka kara mana lafiya, Allah duk wanda yake cikin hali na jinya Allah shima kabashi lafiya" aunty tafadi haka tana shafa fuskar mustapha, gabadaya suka amsa mata da "ameen", banda mustapha dako bude idonsa beyiba. "Yaya yaushe ya farfado dinne?" aunty tatambayi daddy. "Tun jiya cikin dare zannurain yakirani yasanarmun wai ya tashi a firgice,amma yanzu komai yayi daidai danhar wanka usman yataimaka masa yayi gami da sallah, amma maganacefa haryanzu beyiba" "kai, masha Allah, jiki yayi kyau, ai maganar se'ahankali zeyine da yardar Allah,ahakanma angodewa Allah, sannu kaji Muhammad Allah yakara sauki" "ameen,ameen" duban zannurain aunty tayi tace, "amma zannurain a wani irin firgici ya farka?" Numfashi zannurain yasauke yace, "aunty nidai ina bacci naji wata irin kara daganan kuma senaji muryarsa yatashi yana kiran sunan Allah" "kara kuma harnan kunjiyo wannan karar?" Aunty tatambayeshi cike da mamaki, "aunty nima ai naji" cewar haidar, daddy ma cike da mamaki yace, "aiko nima naso naji wata kara cikin baccina, karar mene" shiru aunty tayi batace komaiba, se gyada kai kawai takeyi,cikin ranta tace. "Tabbas babu tantama abunda tadakko daga dakin maryam shine abunda yafashe kuma yayi wannan karar, kuma yanada nasaba da ciwon mustapha, to amma meyakaishi dakin maryam, ko wanda tagani yafita daga dakin shine ajiye abun" bata dame bata wannan amsar se maryam, itace zata fayyacemata zare da abawa tunda adakinta abun yafaru, daddy yabude baki danufin yakara tambayar aunty akan wai meke faruwane ganin tayi shiru, amma shigowar mommy da suhailat ta hanashi maganar. Su haidar naganin mommy suka ruga gareta suna rige_rigen sanar mata yaya yatashi, dansunsa setafi kowa farin ciki da tashin mustapha, atare suka sanar mata, pretending na murnar da mommy tayi akan tashin mustapha baze misaltuba, harda kukanta na murna, suhailat ma tayi murna sosai, kokunyar su aunty batajiba taje ta rungumeshi tana shashshafashi. mommy cikin tsananin murnar datake nunawa ta karasa gabanshi, ta kama hannunsa ta rike tana fadin, "my son, tashi kaga mommynka, bude idonka naganka naji dadi araina, yau ranar farin cikin muce son, tunda Allah yabaka lafiya" a matukar firgice mustapha ya bude idonsa gami da tashi zaune yafara ja baya daga kusa da mommy,jin muryarta yana fadin, "pls mommy kiyi hakuri idan wani lefinna miki kidenamun abunda kikemun kullum pls mom,inajin azaba sosai ajikina..!" cikin raunananniyar yayi maganar yana sakin numfarfashi,alamun dakyarma ya iya yin maganar. dafe kirji mommy tayi tace, "son kasan mekake cewa kuwa, nicefa mommynka koka manta nine" girgiza kai mustapha yahauyi yana kara jabaya, rikeshi haidar yayi ganin kamar baya cikin hayyacinsa. cikin tashin hankali mommy ta juyo tana kallon daddy, idanunta na zubar da hawayen munafurci tace, "daddy kaji me son dina yake cewa, yau nice son bayason narabeshi, wai ina masa wani abu, wlh anshiga tsakanina da dana, anmasa mugun asirin daya manta kansa pls daddy kayi wani abu akai,wlh angamamun da dana" ta karasa zancen tana fashewa da kuka. wani irin kallo aunty takebin mommy dashi na tuhuma, kafin daddy yayi magana, sukaji daga bakin kofar dakin anacewa, "babu wanda yayi masa asiri danya rabaku, face ke dakikayi masa asirin dakanki akokarinki na ganin ya mutu, danki cika wani banzan burinki,saboda bake kika haifesaba. sekuma Allah bebaki nasaraba gashi ya warke a lokacin dabakiyi tsammaniba...........✍️ *BY* *zeey kumurya* *ABUNDA KA SHUKA*......... _*(shizaka girba)*_ *MALLAKIN* 👇 *ZAINAB USMAN KUMURYA* *FARIN JINI WRITERS ASSO.....*📚 ~*Free novel*~ *Bismillahirrahmanirrahim* 3️⃣5️⃣ ...........Gaba daya suka juya atare cikin tsananin mamakin jin muryar me maganar gami da abunda yafada, mutumin dasuka manta rabon dasuji yayi doguwar magana irin haka. "Faruq! ni mahaifiyarka kake jifa da wadannan muggan kalaman, nikake cewa nayiwa dana nacikina asiri kuma bani na haifesaba,kana cikin hayyacinka kuwa faruq!?" mommy tafadi haka cikin tsawa da matsanancin tashin hankali. murmushi faruq yayi, gami da yin taku yakaraso har gaban mommy yace, "ina cikin hayyacina mommy nake fada miki wadannan maganganun,kidena wani borin kunya,kina nuna kamar bakisan abunda kinfi kowa sanin saba,yau ranar tonan asirinki ce tazo keda wanda kuke shirya komai tare, kisani asirin dakikamun na shekara da shekaru ya karye hakama wanda kikayiwa daddy ya karye" kafin mommy tayi magana aunty tatari numfashin faruq tana duban daddy tace, "yaya kanajin me faruq yake cewa akan mahaifiyarsa amma kayi shiru kana kallonsa, menene gaskiyar al'amarin yaya?" Shiru daddy yayi bece komaiba amma fuskarsa tana nuni da tsantsar damuwa, da tashin hankali,kusan 50 second sannan ya numfasa yace, "tabbas atika ba'ita ta haifi mustapha b..." wata hantsilowa mustapha yayi daga kan gado jikinsa gabadaya yadauki wata irin kyarma hannunsa narawa yahau nuna mommy yana kallon daddy, magana yakeson yayi amma yakasa se bakinsa dake motsi alamar yanason yace wani abu. aunty, haidar,zannurain atare suka mike tsaye cikin tsananin dimuwa jin abunda daddy yace,aunty hartana yarda wayarta kasa batare data saniba, baya mustapha yayi luuu,ze fadi kasa,dasauri daddy yataro jikinsa,suka zauna abakin gado, dama jikinnashi babu kwari gakuwa wani bakin zance dayakeji wanda yake kokarin saka zuciyarsa ta buga, wanda yajishi tamkar saukar ruwan narkakkiyar dalma atsakiyar kansa. kallon mommy aunty takeyi amma itama takasa magana se girgiza kai kawai takeyi, aranta tana cewa, "wanne irin burine wannan da mommy takeson cikawa wanda har tayiwa danta na cikinta da kuma mijinta asiri,kuma take kokarin kashe mustapha" mommy kuwa jitayi gabadaya yawun bakinta ya kafe kaf, zuciyarta tahau harbawa dasauri cikin tsananin tashin hankali bata taba tunanin abun zezo mata ahakaba, "nashiga uku ni atika,yanzu kenan sulaiman ze iya tuno komai daya faru ada" mommy ta fadi haka atunaninta azuci tayi maganar, amma seta tsinkayi muryar daddy yana fadin, "tabbas tunanina yadawo akan abunda kika gusarmun da hankali akansa, kuma ranar wanka ba'aboyen cibi yau zansanar da mustapha abunda nake da burin sanar masa shekara da shekaru,amma kika rufe mun baki ruf namanta nakasa sanar masa." wani irin murmushi mommy tayi me ciwo cikin karfin hali tace, "to seme, sulaiman idan kafada masa, kadade baka sanar da mustapha gaskiyaba, to bari kaji insanar maka fadar abunda kake kokarin yi, daidai yake da tonawa mustapha asirin dani dakai muka rufa masa arayuwarsa" shima daddy murmushin yayi yace, "insha Allahu, fadata saidai tazamo masa alkhairi arayuwarsa" mommy tana kokarin sake magana sadiq dake falo tundazu yashigo dakin asukwane fuskarsa murtuk babu alamun fara'a yana bin kowa da kallo dai_dai, zaro ido aunty tayi cikin tsananin razani ganin rigar dataga mutumin jiya datagani yafita da ita ajikin sadiq,ga kuma kansa yane da hirami, hannunsa duka biyun da safunan hannu, alhalin ba lokacin sanyi bane. dafe kanta tayi tana furta Kalmar hazbunallau wa'inimal wakil afili. tana addu'a aranta,Allah yasa abunda take zargi karya tabbata kokuma fatan idonta beganin mata daidaiba,kai bamata tunanin haka sediq ze aikata abunda take tunani,kilan jiyanne idonta beganinmata daidaiba. "Sadiq meyadawo dakai yau kuma?" Mommy tatambayeshi cikin tsananin firgici tana kallonsa. be'iya bata amsaba se faruq daya nuna mata da hannunsa. zama aunty tayi dabas akasa tamarasa mezata kira wannan bakon al'amarin me cike da rudu da tashin hankali acikinsa. Mommy ma zama tayi a gefen gado gumi na tsatstsafoma mata ako'ina najikinta, domin bata taba tunanin abun zejuye mata hakaba, bata taba tunanin wannan ranar tonan asirin zata zomataba arayuwarta, tarasa wanne sakaci tayi dakomai nata ya lalace, amma duk da haka zuciyarta bata sadudaba, takudircewa ranta agama wannan rikicin dakanta zata koma gurin boka tsidau,yasake mata sabon aiki. Faruq ma zama yayi akasa agefen aunty, haidar da zannurain kuwa basa gane komai akan abunda yake faruwa,kwakwalensu gabadaya sun toshe tsabar tararrabi sunma kasa magana, yanzu dama ba mommynsuce ta haifi mustapha ba, "to wacece ta haifesa?" tambayar da suhailat data daskare a tsugunne itama takeyiwa kanta kenan, shiru dakin yadauka kowa da tunanin dayakeyi acikin ransa,babu wanda yadamu da yanda sukaga sadiq,dominsu basusan komaiba akan fyaden da akeyi agidanba,hatta da daddy kuwa, mommy ce kadai tasani seshi meyin da faruq. aunty ce tanisa cikin tsananin damuwa ta katse shirun tana duban daddy tace, "yaya kafada mana abunda yake faruwa kunsamu acikin duhu kaida faruq da aunty atika,kasanarma menene kuke boyewa da kuma gaskiyar al'amari akan abunda mu bamu saniba,sannan kuma tayaya Muhammad yazama badan aunty atikaba, wacece mahaifiyarsa to?." numfasawa daddy yayi yakalli su haidar da sadiq yace su zauna labarine me tsaho, babu musu dukansu suka yiwa kansu mazauni cikin son jin yanda daddy ze warwaremusu yanda abun yake, daddy ma raba mustapha yayi da jikinsa ya zaunar dashi akan gadon bayan yasamasa filo abayansa,cikin tsananin tausayawa ganin yanda numfashinsa yake fita dakyar tsabar tashin hankali. gyara zama daddy yayi yafara magana kamar haka: Kamar yadda kuka sani, sunana sulaiman Abdullahi, iyayenmu mu uku kacal suka haifa, nine babba se mebimun isma'il se auta saudart. Mu cikakkun yan kanone muna zaune a unguwar gwammaja. Mahaifinmu tun muna yara Allah yayi masa rasuwa, lokacin banfi shekara 12 ba,shikuma isma'il shekara 8,yayinda saudart take karama sosai danko yayeta ba'ayiba. Mutuwar mahaifinmu bakaramin girgizamu tayiba nida innarmu,tashin hankalin da muka shiga baze faduba, haka mahaifiyarmu ta rungumemo ta cigaba da rainonmu ta kuma tashi tsaye da neman kudi domin ta rufa mana asiri. Nima tun lokacin banzaunaba nafara yan bugegene domin na dinga taimakawa mahaifiyata, dan babu metaimakonta se Allah, kunsan yanda zumuncin yanzu ya lalace, babu mekulaka sekana dashi, yan'uwan mahaifinmu ba wani kula sukeyi damuba,amma duk da haka bamu yada suba muna zuwa mugaishesu nida isma'il. haka muka cigaba da rayuwarmu cikin rufin asirin Allah, harnakai munzalin zama saurayi, lokacin nagama degree na farko,saboda halin rayuwa sena tsaya da karatun haka nacigaba da yan buge_bugena,dan mahaifiyarmu girma yakamata wasu sana'oin duk bata iyasu. Ina da shekara ashirin da hudu, itama mahaifiyarmu Allah yamata rasuwa bayan gajeriyar jinya datayi, A wannan lokacin munshiga tashin hankali fiye da mutuwar mahaifinmu, danni kusan zaucewa nayi seda aka hadamun da rokon Allah sannan nadawo nutsuwata,haka mukacigaba da rayuwa cikin maraici da kuncin rayuwa, wata cousin din innarmu itace tadauki saudart, domin innarmu bata da yan'uwa dasuke uwa daya ko uba daya. Gidanmu yazama daga ni se isma'il muke rayuwa aciki, bani da wasu abokanai hakama isma'il, mune abokan junanmu komai tare mukeyi mu nemi shawarar juna, muhaka mu binne tare. bayan rasuwar innata da watanni nafara zuwa kasuwa da taimakon wani Dan ajinmu damukai makaranta tare me suna sa'idu. wani alh, yahadani dashi nake masa jiran shago anan kasuwar wanbai,Wanda da shi sa'idunne yake masa,sekuma yanzu yasamu wani kasuwancin shine yakaini na maye gurbinsa. cikin ikon Allah tunda nakoma shagon se cinikin shagon ya ninku fiye dana baya, kullum idan aka tashi daga kasuwa sena biya gidan alhajin munyi lissafe lissafenmu sannan nake komawa gida, to a wannan zuwa gidan alhajin danakeyi anan nahadu da atika (mommy) gidansu makotane da gidan alhajin, kullum naje da yamma zanganta ita kuma tadawo daga islamiyya ita da kawayenta, amma fa kullum cikin yin fada take, wataranma harda dambe, danni kaina nasha rabasu. Kuma a lokacin ba yarinya bace, da girmanta danta zama cikakkiyar budurwa zama tayi shekara 19,sedai tana da karamin jiki. Kullum idan ta ganni setayi ta kallona, nikuma bansan meyasaba dariya take bani saboda tsiwarta,se'inta tsokanarta. Watarana bayan nazo mungama abunda zamuyi da alh, nafito zantafi gida segata da gudunta tatareni tabani wata takarda,nace mata ta mecece, tacemun idannaje gida nakaranta nagani. Banyi tunanin komaiba nakarba nazira a aljihu na wuce gida. Ninama manta da wani batun takardar data bani, seda nazo bacci zancire riga najita acikin aljihuna, dakkowa nayi ina mamakin menene, seda naganta kuma sena tuna, warwarewa nayi nakaranta, gabadaya abunda takardar ta kunsa wai atika tana sonane, dariyama ni abun yabani nazauna nayita kyakyatawa danni a lokacin ko tunanin wata soyayya banayi, tunanin yanda zansamu rufin asirin kaina na tallafi rayuwar yan'uwana kawai nakeyi. Isma'il ne yatambayeni mene yasani dariya haka, takardar hannuna nabasa ina basa labarin atika, tsaki yayi bayan yagama karantawa yakada baki yace, "yaya niko zakayi soyayyama bana fatan kayi da irin wadannan marasa kunyar, dandaga ganinta bata da tarbiyya tunda har tana mace ta iya furta maka kalmarso" bance masa komaiba,saboda bandauki zancen gabadaya da wani mahimmanciba nayi kwanciyata bacci. washegari kamar kodayaushe bayan nabaro kasuwa nazo unguwar su atika, ina fitowa kamar kullum muka kara haduwa da ita, ba kunya tatambayeni kona karanta takardar data bani, nace mata eh, seta tambayeni kona amince da soyayyarta, dariya kawai namata nawuce dan a tunanina wasa kawai takeyi itama. Intakaice muku zance,kullum se atika tatareni ta jaddadamun itafa sona takeyi dagaske, tun ina daukar abun wasa harnima naji nafara tausayinta dan wataran har kuka take sanyamun akan insota, batare danayi shawara da kowaba na amincewa soyayyar atika muka fara soyayya, dukda ni jikina yana bani bazamuyi aureba, danni talakane sukuma su atika suna da kudinsu, seda soyayyarmu tayi nisa nakejin labarin ashe atika itama marainiyace babu uwa ba uba, agurin kanin mahaifinta take, kuma anrigaya da anmata miji, yana kasar waje yana karatune shiyasa ba'ayi aurannasuba. banyi kasa a gwiwaba nasanarwada atika akan muhakura da juna tunda anrigaya anmata miji, amma atika tace sam ita batasan wannan zanceba ni takeso kuma ni zata aura. kanin mahaifinta yafatattakeni yace karna kara zuwa gurin yarsa, idanba hakaba seyasa andaureni, tundaga ranar dayamun hakan koda nazo unguwar bana sauraren atika, amma atika taki hakura dani har kasuwa take biyoni shagona, nayi mata rarrashin duniya akan muhakura da juna,amma atika takiji. Atika irin matannanne masu kafiya da taurinkai, rikicin da'aki da atika agidansu akan tahakura dani baze misaltuba,karshema kanin mahaifinta cewa yayi ta zaba koni koshi tace tazabeni, haka yatattaro mata kayanta yakoreta, tana kuka kanwarta na kuka, dayake su biyu iyayensu suka haifa, kafin su rasu, yan'uwa da abokan arziki suka dinga rokon marikin atika akan yayi hakuri tacigaba da zama agurinsa, amma yace yarantse matukar bata canza ra'ayintaba shima bazata cigaba da zaunar masa agidaba, tunda tace be'isa da itaba. itama atika ta kafe akan bakanta. cikin masu bawa kawun atika baki harda wannan alhajin danake zuwa gurinsa, toni kuma ganin atika ta guji kowa nata saboda ni, senayanke shawarar auranta a wannan lokacin, duk da nasan bawani karfi gareniba amma auranta shine kadai halarcin dazanmata akan abunda tamun. bansamu matsalaba agurin magabatanaba danaje musu da zancen zanyi aure, sudai tunda ficikarsu bazatayi ciwoba basu da damuwa, isma'il nema yanunamun kin amincewarsa danshifa atika bata masaba, dakyar nasamu na rarrasheshi ya amince. Ubangidana shine yatsayamana nida atika a aurenmu, ita yay mata kayan daki da kayan amfanin gida, nikuma yahadamun lefe. Gidanmu damuke ciki dama daki ukune kuma bawasu masu girmaba, guda biyu nagyarawa atika dayan kuma na hanyar kofar gida isma'il yacigaba da zama aciki, ubangidana shine yazama waliyyin atika aka daura mana aure atika tatare agidana, gaskiya babu karya atika tanunamun soyayya, tasoni kamarme azamanmu, dafarko bamu samu wata matsala da itaba,seda Allah yayiwa megidana rasuwa magada suka amshe shagonsu. Nashiga tashin hankali bakaramiba, domin bansan wacce Sana'a zankamaba wadda zan rufawa kaina asiriba. Isma'il shima alokacin baya sana'ar komai, hasalima karatu yakeyi ninake daukar nauyinsa, rayuwafa ta sauyamana gabadaya ga atika nadauke da dankaramin ciki a lokacin, abincin dazamucima wataran gagararmu yakeyi, ga atika bata hakuri kokadan akan rashi, kullum cikin mita da masifa takemun akan nafita nasamota abunda zataci, haka nake fita nayi yan buge_bugena daga bayama senakoma yin dako akasuwa, duk dan asamu abun kaiwa bakin salati. Watarana ina zaune a kasuwa bayan anyi sallar la'asar naji ankira sunana,cike da mamaki najuya jin muryar abokina sa'idu,cikin mamaki nace, "sa'idu dama rai kanga rai" danrabona dashi tunda yasamarmun aiki agurin megidana. "Gashi kuwa munhadu sulaiman, tun dazu nashigo kasuwar inata nemanka se nura yace inzonan zansameka" gaisawa mukayi cikin farincikin ganin juna, se kallon sa'idu nakeyi yanda yacanza daga gani kudi sunzauna masa, tambayata yayi menakeyi yanzu nace masa buga_buga ce kawai tunda alh, yarasu har yau bansamu wata kwakkwarar sana'aba. jimantamun sa'idu yayi sosai, yace idan zan iya zuwa *NIJER* indinga saida takalma zebani jari narasa nadinga kaiwa can, danshima sana'ar dayakeyi kenan acan shiyasama yabarnan, kuma harkar akwai samu sosai acikinta. shiru nayi ina nazari dagacan kuma nace masa, "toyazanyi da iyalina tunda idannace zantafi dasu candinma bani da masauki kuma bani da kudi balle inkama mana haya" murmushi sa'idu yayi yace, "wannan duk ba matsala bace, zakabar iyalinnaka anan gidane, kafara zuwa kaikadai kafin muga abunda Allah zeyi, zuwa lokacin dazaka samu abunda ake fata seka dauketa kukoma can gabadaya, idankatashi sarar kaya sekazo kaikadai kakoma." godiya nayiwa sa'idu sosai nace masa zanje gida nayi shawara tukunna, yacemun ba matsala idannayi shawarar abunda nayanke zezo gobe mu hadu, seyaji. Koda nakoma gida sena nemi shawarar isma'il akan abunda sa'idu yazomun dashi,aiko isma'il yayi murna sosai, kuma yacemun na amince damace Allah yabani,nanemi albarka abun kawai natafi nafara. banfadawa atikaba seda mukagama magana da sa'idu muka shirya komai yanda abun zekasance, har Lagos mukaje muka saro takalman, nanfa atika tatubure sedai mutafi tare dakyar nasamu na lallabata bayan na cikata da kudi, dannasan mutuniyar tawa akwai son kudi, nakuma ajiye musu komai dazasu bukata itada isma'il ishashshe, alokacin nayi niyyar dakko saudart domin tataya atika zama, amma marikiyartata taki bada ita, dansunsan halin atika ba mutunci garetaba. Cikin ikon Allah,mukaje nijer lafiya nida sa'idu nakuma fara sana'ata itama da taimakon sa'idu. Naji dadin zama akasar nijer sosai, inda cikin dan kankanin lokaci nasaba da mutane, nakai kusan wata biyu sannan nazo ganin gida, anan na tarar da wani mummunan labari na barewar cikin danabar atika dashi, gashi atika tazama jarababbiya kullum se fada da makota da yawon gantali, isma'il yacemun yana iyakacin yinsa wajen ganin yahanata amma taki hanuwa, banyi kasa a gwiwaba nazaunar da ita namata nasiha takuma nunamun tadauka. Tundaga wannan lokacin nakoma safarar takalma daganan gida Nigeria zuwa kasar nijer, kuma alhamdulillah Allah yadafamun ina samun alkhairi sosai acikin sana'ata. Banfi shekara da fara zuwaba nadauke atika muka komacan Inda nakama mana haya a can din mukacigaba da rayuwarmu, tunda zamana acan yafi yawa gwara ace matata tana kusa dani, yan'uwana kuwa ina musu aiken kudi yanda yakamata. tundaga wannan barin cikin da atika tayi bata kara koda batan wataba, gashi ni kuma Allah ya halicceni mutum ne meson yara, kullum cikin addu'a nake, Allah ya'azurtamu da samun yaya. Atika taso dakko kanwarta jamila tadawo hannunta da zama lokacin dazamu koma nijer,amma kanin mahaifinta yace baze bataba. Rayuwa tasauyamun sosai nasamu budi da nasara aharkar kasuwancina sosai, nasamu rufin asirina daidai gwargwado. abokina sa'idu shine yasamun sunan *menasara* daganan sunan yabini wasuma idan kace musu sulaiman bazasu sugane nikake nufiba sekace musu *menasara* watanmu shida dakomawa nijer dazama nida atika, Allah ya'aiko mana da wani iftila'i, kayana na shago sunkare kaf, natattara kudadena a buhu, zanzo gida nayi siyayya, lokacin account beyi yawaba, dama tafiyar dare mukayi yan fashi da makami suka tare motarmu akan hanya,suka kwace komai namu dagamu se tufafin jikinmu sukabarmu, se juyo damu driven yayi domin dama yawancinmu sare_sare zamu kuma gashi ankwace kudin sarin, dayawa daga cikin wadanda muke a motar kusan zaucewa sukayi,manyan maza magidanta segamu da kuka shabe_shabe da hawaye. wannan fashin da'aka mana bakaramin talautamu akayiba, danseda takai ta kawo naira biyarma gagararmu takeyi, dan abincin da sauran kudin da'akabarwa mata agida duk ancinyesu. Nashiga cikin tsananin tashin hankali bakanba a wannan lokacin narasa ina zantsoma kaina, gashi ko kudin motarma dazan mana mudawo gida Nigeria nida atika kozan samu abunyi anan babu. Alokacinne kuma atika ta fitomun da ainihin halinta na rashin imani da tausayi, kullum cikin yimun tijara da rashin mutunci take, akan rashin da Allah yadoramun, bata ganin nima bayin kaina bane. Kaddarace Allah yadoramun dakuma jarrabawar rayuwa. Watarana da daddare ina zaune a tsakar gidanmu ranar munwuni bamuciba nayi tagumi ina tunanin yanda rayuwa tazomun atika tafito daga daki ta tsayamun aka cikin masifa tafaramun magana, "sulaiman yanaganka anan kazauna, wato bazakaje kasamomun abunda zanciba, mekake nufine, sedai inyi tazama da yunwa ta takasheni" janye tagumin danayi, nayi cikin rarrashi nafara mata magana da fadin, "dan Allah atika kiyi hakuri, kinga yanzu dare yayi bansan inda zannufa insamo miki abunda zakiciba,amma kibari zuwa safiya insha Allahu zannemi koda wankaune domin inbaki abunda zakici" rike kugu atika tayi tace, "wlh baka isaba sulaiman yau bazaka kwana agidannanba seka nemomun abunda zanci, danbazan zauna yunwa tamun lahani abanzaba" cikin takaicin halin atika na rashin tausayi nace, "haba atika amma kinsan nima babuce Allah yadoromun lokacin da ina dashi aina baki abincin" "kaga sulaiman nifa babu ruwana da wani babunka nidai kawai kanemomun abunda zanci, tunda kai kakawoni nan ka'ajiyeni danhaka dole kasamarmin abunda zanci, dankasan shi ciki besan wani babuba ehe" bancemata komaiba namike nafice daga gidan, lokacin goman darema ta kusa. Duk inda nasan zanje insamo wa atika koda biscuit ne amma naje bansamoba, haka nadawo gida jikina asabule lokacin dare yafarayi dan 12 saura, atika harta rufe gida, kwankwasamata nayi ta bude, koda taga hannuna babu komai seta maida kofar gidan tarufe tana fadin wlh bazan shigoba matukar bansamo mata abunda zataciba. wani bakin cikine yaziyarceni nida gidana amma ahanani shiga, meyasa atika bata tausayinane nimafa yunwarnan nakeji amma tunsafe nake yawon nema mata abunda zataji amma bata gani. Wata shawara zuciyata tabani akan naje unguwar masu kudi mana, inrokesu su sanmun koda danyen abincine inkawowa atika tadafa, ko tunanin dare banyiba nakama hanya natafi dukda nisan dake tsakaninmu dasu. ina tafe nakadai tunkis tunkis harna shigo wata unguwa dako sunanta bansaniba amma dai ta masu kudice, kowanne layima da gate dinsa kuma duk an rurrufesu,tsayawa nayi ajikin wata bishiya ina maida numfashin wahala, tunaninma tayanda zan iya komawa gida nakeyi dannagaji likis ga kishirwa dake damuna. ahankali nafarajin taku daga bayana alamar ana gudu, cikin tsoro najuya ina karanta addu'a acikin raina, mutum na hanyo yana gudu da dukkan karfinsa, seda ya matso kusa naga Ashe macece goye da yaro hannunta kuma dauke da wata jaka. Cike da mamaki da tsoro nake kallonta kamar yadda itama ta tsaya cak tana kallona. Cikin karfi hali nace, "baiwar Allah mutum ko aljan?" Cikin hausarta dabata fita sosai tana haki tacemun. "bawan Allah mutum ce ni kamarka" bata jira mezancemataba ta hau kici_kicin kunce dan bayanta bayan ta ajiye jakar hannunta akasa. niko tsayawa nayi kawai ina kallonta cike da mamakin meya fito da ita daga gida cikin darennan, gata yarinya karama danko atika batayiba gata fara jajur kyakkyawa da ita kana ganinta kaga cikakkiyar buzuw..... Katsemun tunani tayi ta hanyar mikomun jaririn hannunta tana kuka tana fadin, "bawan Allah, dan Allah kataimakeni kagudarmun da jaririnnannawa,wlh kashemunshi zasuyi,kuma yanzu suna dubawa basu ganniba zasu biyo bayanane, nikuma dasu kashemun dana gwara ni sukasheni shiya rayu, kataimakeni kagudarmun dashi shikadai Allah yabani, banaso narasashi,wlh dana dan halak ne da ubansa, shima babannasa sun kasheshi shine shima yanzu sukeson kasheshi" takarasa zancen tana fashewa da kuka, tsayawa nayi kawai ina kallonta zuciyata namun wasi_wasi akan abunda tace. "Kataimakeni, sunkusa karasowa, karikemun dana da amana dan Allah,kagudarmun dashi karsu karaso su kashemunshiiiiiiii!..............✍️ *By* *zeey kumurya* *ABUNDA KA SHUKA.........* _*(shizaka girba)*_ *3️⃣6️⃣* ...........Tsayawa nayi kawai ina kallonta cikin kura ido, domin tabbatar da abunda take fada har cikin zuciyarta gaskiyane. Kasancewar gurin da wadatar hasken kwayayan gidan mutane ina ganin yanda hawaye yake zuba daga idanunta tamkar ankunna fanfo se shatata yakeyi. Cikin tsananin tausayawa nakai hannu nakarbi yaron daketa bacci abunsa, duk wannan uban gudun da mahaifiyarsa tasha amma be farkaba. "Suwaye zasu kashe miki danki, kuma akanme?" Na tambayeta ina kallonta bayan na karbi yaron. girgizamun kai tahauyi cikin kuka tace, "babu ishashshen lokaci dazan makama bayanin kosu suwaye,amma dai su mugayene azzalumai wadanda san duniyarsu yamantar dasu Allah, sun kashemun mijina, nima basu kyaleniba Neman rayuwata sukeyi data dana,duk akan abun duniya." wani numfashi taja tare da runtse idanunta tace, "kagudu karsu karaso,domin ni nasan duk inda nashigama agarinnan,sesun nemoni sunkasheni,kadauki wannan jakar zata taimakeka arayuwa" batajira amsataba ta bude idonta takurawa danta idanunta dasuke zubar hawaye, sumbatar goshinsa tayi gami dayin magana da yarensu cikin kuka me karya zuciyar mesaurare. Har cikin zuciyata nakejin kukan matarnan, tsabar tausayinta ita da danta nama kasa magana, se kwalla data cikamun idona. Ina shirin kara mata magana najiyo taku alamun ana tahowa inda muke, dasauri muka juya dukanmu nida matar daga inda ta bullo daganan takun yake tahowa, nikaina ba itaba bakaramin tsorata nayiba domin ga dukkan alamu wadanda take fadane suka biyo bayanta bisa ga yadda naga duk ta firgice. Rungume yaron nayi a kirjina da hannun haguna, hannun damana kuma na rarrafa nahaye kan bishiyar damuke tsaye akasanta, domin nanne kadai gurin dazan iya buya bazasu ganniba. cikin ikon Allah kuwa nahaye bishiyar tamkar dan biri ina maida numfashi, ninama manta da jakar datacemun indauka seda naga tadauketa ta ziramun acikin wani kurmin bishiyar. Sannan ta ruga da gudu ta miki wata hanya, ko minti 4 bata cika da tafiyaba wasu mutane guda hudu suka karaso gurin, hannayensu dauke da fitilu hanyar da matar tabi nan suka mika suma da gudu, naji sunyi magana cikin yarensu na buzaye amma banfahimci mesukaceba ga dukkan alamudai hango matar sukayi. wata nannauyar ajiyar zuciya nasauke bayan sunbar gurin,wani matsanancin tausayin matarne yakamani,lallai mahaifiya, mahaifiyace tazabi danta yarayu ahannun wanda bata saniba,batasan daga inda yakeba akan akashemata shi, tazabi ita tarasa rayuwarta danta yarayu. wasu zafafan hawayene suka shiga kwaranyomun inajin dama zan iya danaje nataimaki matarnan daga hannun azzaluman mutanen data ambata. rokon Allah nashigayi akan Allah ya kubutar da ita, insha Allahu bazasu samu nasara akantaba. Nakai kusan minti talatin akan bishiyarnan ina sakawa da kwancewa sannan nadiro jikina asanyaye. Jakar data ajiyemun nadauka senaji jakar da nauyi,mamakine yakamani ganin yanda matarnan ta iya gudu da ita ga kuma goyon yaro abayanta, kodayake gudun ceton rai bazataji nauyin komaiba. Goyo yaron nayi abayana nadauki jakar naruga da gudu zuwa gida, domin nima a matukar tsorace nake, gani nake kamar mutanennan zasu iya dawowa su riskeni. yunwa da gajiyar danakeji ada gabadaya yanzu sunbar jikina,burina kawai inganni acikin gidana na tseratarwa da matarnan da danta. Cikin ikon Allah, nakarasa gida lafiya alokacin tsakiyar darene gari yayi shiru, se haushin karnuka da kukan tsuntsaye. Nadade ina kwankwasa kofa kafin atika tazo tabudemun kofar. nasan bacci tafara, aiko ko tsayawa batayiba ta juya takoma dakinta, ni dadin hakanma naji,danbansan yanda zamu kareba idan taga yaron bayana. Dakina nashiga na kunce yaron nashimfideshi akan tabarmar dake dakin bayan na kunna light haske ya gauraye dakin. kurawa yaron ido nayi cikin tsananin tausayinsa, gashi kyakkyawa dashi fari kal harwani pink_pink yake tsabar fari. hannuna nakai nashafa kwantacciyar sumar kansa baka sidik, so da kaunar yaron nashiga cikin raina afili na furta. "Ya Allah, karaya wannan bawannaka, kabani abunda zan iya rikeshi,kakuma bani ikon rikeshi bisa amana batare dana cutar dashiba" badon nagaji da kallonsaba na mike nabude wata tsohuwar jakata danake ajiye abubuwa nasaka jakar da matarnan tabani aciki na mayar na zuge na ajiye. kamar ance injuyo naga yaronnan ya bude idonsa yana wawure_wawure da hannunsa yana kaiwa baki dasauri nanufeshi nadaukeshi, aikuwa yabude baki yacanyara kuka, jijjigashi nahauyi cikin son yayi shiru amma ina tamkar kara zugashi nayi se ihu yake da dukkan karfinsa abun tausayi. Se'alokacin nayi tunanin watakila yunwace take damunsa,nanfa hankalina idan yayi dubu yatashi domin banda abunda zanbashi acikin gidannan. Yana hannuna nafita dashi domin nabashi ruwa ko Allah zesa yayi shiru kafin safiya nanemo abunda zanbasa. Atsakar gidan nayi kicibus da atika tafito a hargitse. Gabanane yayanke yafadi danbansan yanda atika zata dauki maganar yaronnanba, tsayawa tayi cak tana kallona cike da tsananin mamaki kafin naji ta lailayo wani uban ashar gami dacewa, "sulaiman mezan gani haka, jariri ahannunaka ina kasamoshi, ina cikin baccina naji kukan yaro yacikamun kunne kamar amafarki, shine nafito inleka waje inga tsinannen yaro daya hanani bacci, kuma se'inganshi acikin gidana" bance mata komaiba harna debo ruwan akofi nazauna nakafawa yaron abaki, nandanan kuwa yakama wawurar kofin da baki abun tausayi yahau kukkutar ruwan, sedayasha kusan rabin kofin sannan nacire kofin daga bakinsa kuka yasaka alamun ruwan be'isheshiba. kara mayarmasa nayi yakarasha, atikadai tana tsaye tana kallon ikon Allah. seda yakarashan ruwan sosai sannan na'ajiye guntun ruwan. bekarayin kukanba hakanyasa na kwantar dashi akan kafadata ina shafa bayansa, abunda yakara burgeni da yaron yanda yake tsaf sewani daddadan kamshi dake tashi ajikinsa. Kallon atika nayi nace tabiyoni dakinta muyi magana, masifa tahauyi wai maganar mezamuyi ita kawai nafada mata inda nasamo yaro, maimakon nakawo mata abinci sedai kawai taga nashigo mata gida da yaro. Juyin duniya atika tashiga daki muyi magana amma taki, dole haka namata bayani atsakar gida. Bala'i da masifar da atika tamun adarennan baze misaltuba tijira kala_kala akan sena fita da yaron daga gidan,kilama wata naje nayiwa cikin shege ta haifamun dan shine zanzo inhada karyata gata wacca batasan metakeba akawomata rainon shege gida. maganganunta sunbatan rai amma dai haka nadaure naki kulata nashige dakina nabarta atsakar gida tanata hayagaga makota najinta. dakinma bantsiraba haka tabiyoni taitamun tijara. Halaccin da atika tamunne kawai yasa adarennan bantsige igiyar aurena akantaba,amma raina yabaci matuka danne zuciyata kawai nayi bankulataba. Ranar yanda naga dare haka naga rana,ga kukan dayaron yashigayi shima tamkar ana zarar numfashinsa nasan yunwace take damunsa. Seda asuba nasamu yayi bacci, harnaje masallaci nadawo betashiba. Alokacin banhakuraba nakara zuwa dakin atika nabata hakuri dannasan kowacce macece rana tsaka mijinta yakawo mata jariri gida da tunanin dazatayi, da kyar nashawo kan atika tahakura zamu rike yaronnan,amma seda namata uwar magiya daban baki gami da rantse_rantse akan abunda nafada mata shine gaskiyar al'amari. Aranar da duku_duku nafita Neman abunda zamuci, cikin kudurar Allah wani makocinmu yakaini wani guri nayi aikin safiya nasamo dan abunda ba'asaraba. Cikin tsananin farinciki na auno abunda zamuci da kayan hadi na kawo gida, shikuma yaron na auno masa madara gwangwani daya. Koda nakoma gida yanda nabar yaron adakina haka nashigo nasamesa yanata tsala kuka, atika ko kallon inda yake batayiba, cikin sauri nanufeshi nadaukeshi nahau jijjigashi dama ina wajene amma gabadaya hankalina yana kansa. danayiwa atika maganar tanajinsa yana kuka amma ko daukarsane aitayi. Seta kada baki tacemun ita bata haifi daba bazatayiwa wata bautaba, itakuma tanacan tana hutawa. bankulataba nadama madarar danashigowa da yaron da ita nabasa yasha, dannasan yunwace ke dawainiya dashi. bansaniba ko yunwar dake damunsace kokuma danda ruwan sanyi nadama masa yana gamasha se amai. hankalinafa yatashi danbansan mezan kuma bashiba. Ruwa nabashi yasha sannan na masa wanka nagoyeshi abayana bajimawa bacci yadaukeshi. Atikadai sedai ta kalleni tatabe baki. Intakaice muku zance, nikadai nayita wahala da yaronnan inda nasa masa suna *Muhammad mustapha* nayita wahala sosai dashi, dan dafarkoma har rashin lafiya yayi kamar baze rayuba, sedaga baya yasamu lafiya. banfi wata dafara rikonshiba nasamu aiki a wani guri, shinema hankalina yadan kwanta dannasamu sana'ar dazamu dinga kaiwa bakin salati. atika tsana kururu take nunawa mustapha, tun yana yaro haka zatayi ta daka masa tsawa shiko bemasan metakeba. nine wankansa, inbashi abinci, tsarkin kashi da fitsari duk nine tare muke kwana tashi. Sedai innafita atika taga yadameta da kuka sannan zata bashi abinci, tana bashi tana zaginshi wataranma hardasu dungure masa kai. Nikuma Allah yadoramun matsanancin so da kaunar mustapha, bana gajiya da daukarsa inta masa wasa, wannan abun yana kara bakanta ran atika gami da kara mata tsanar mustapha aranta. Watarana ina daki inayin karatun alkur'ani da sassafene, lokacin mustapha yayi kusan wata takwas ahannunmu, yanata rarrafensa atsakar gida yana wasansa. Atika kuma tanata kokarin hada mana abunkari domin fitar wuri nakeyi zuwa gurin aiki, shayi ta sauke atukunya kafin tajuye a flaks, abunka da yaro yana ganin ta ajiye tukunyar ya rarrafa gurin da gudunsa, ina daga daki ina hangoshi banyi tunanin komaiba dannaga atika tana gurin nasan bazata barshi yataba tukunyarba, sunkuyar dakaina nayi nacigaba da karatuna. Ihun da mustapha ya kwallane yasani dagowa dasauri, hangoshi nayi yabude murfin tukunyar yatsoma hannunshi acikin ruwan shayin atika na kallonshi tacigaba da aikinta. dasauri nafito daga daki nadaukeshi cike da tsananin tausayawa, gabadaya ya gigice se kuka yakeyi da dukkan karfinsa. ruwa nadebo nashiga kwara masa ahannunnasa seda nazuba masa ruwan sosai, sannan nadakko gishiri na barbada masa natottofamasa addu'oi. dakyar nasamu bacci yadaukeshi bayan yaci kuka yagode Allah, muryarshi hardashewa tayi, se faman ajiyar zuciya yake saukewa. Har hawaye seda namasa alokacin tsabar tausayawa. bayan naje na kwantar dashi adaki nafito nasamu atika datake ta aikinta hankali kwance nace mata. "Kin kyauta atika, yau nakara tabbatar da imaninki ragaggene kina kallon yaron harya bude tukunya da ruwan zafi aciki amma kigagara daukeshi. Toya kone hankalinki ya kwanta, zanfita idan kintashi duk abunda kikaga dama kimasa kokasheshinema kiyi,amma kisani Allah baze barkiba, *Abunda kikashuka shizaki girba* kema bakisan ahannun wanda danki ze rayuba nangaba, zaki iya haihuwa kimutu kibar dan, domin babu wanda yasan zeyaru da dansa har abada, itama uwarsa batasan wannan kaddarar zata sametaba aduniya, kuma ki sani zalintar marayan Allah kikeyi,kikiyayi gamuwarki da ubangiji" inagama fada mata haka najuya nafice daga gidan raina a tsananin bace. Hakadai mukacigaba da rayuwa a garin nijer ina rainon mustapha, yaro me tsananin hakuri idan kaji kukansa tobakaramin abubane, atika tamasa mugunta kala_kala duk abunda zecutar dashi koda tana gani bazata hanaba, yasha zuba yaji a idonsa kokuma yaji ciwo da wani abun. Amma duk da haka yaron Kallon mahaifiya yakewa atika, danyana ganinta sefara wangale mata baki yana mikamata hannu alamun tadaukeshi. Ko yarane suka shigo namakota idan kiwarsa tatashi seyaki zuwa gurinsu yayita binta,ita kuma intaga dama ta daukeshi tana dungure masa kai, idanbatagadamaba kuwa ko kallonsa batayi sedai yayi abinsa shikadai yagama. Mustapha befi shekara dayaba ahannunmu atika tafara laulayin ciki, murna da farincikin danaji bazata misaltuba, duk da ina kallon mustapha amatsayin dana amma nima inason naga dana nacikina, atika tayi murna sosai taita yada habaici ga yaron dabemasan me duniya take Cikiba, dan ita a ganinta danbani da dane yasa nakeson mustapha yanzu kuwa tunda zansamu nakaina sena rage sonsa. batasan abunbahaka bane soyayyar mustapha acikin jinina take, ina kaunarsa sosai gami da matsanancin tausayinsa. Alhamdulillah zuwa wannan lokacin nasamu rufin asirin kaina, natara kudadena. Harna fara tunanin dawowa kasata dazama gabadaya kodan yawan Aiken danakesha daga gurin yan'uwana musammanma Isma'il kanina. Wataranar juma'a dabazan taba mantawa da itaba arayuwata, bayan ansakko daga masallaci dama ranar juma'a bama fita aiki. Lokacin cikin jikin atika yayi wata hudu, ina zaune adakina ina ware kayana masu amfani damarasa amfani danbanajin zankara sati biyu a nijer. Jakar danake ajiye abubuwa nasauko senajita da nauyi sosai, mamakine yakamani domin ni namamanta da batun jakar da babar mustapha ta bani, tun ranar kuma bankara dakko jakarba. cike da mamaki na ajiye jakar na budeta, tozali nayi da jakar se'alokacin natunata,to jarabar atika kadaima ta isa tasa tamanta da ita. Banyi kasa agwiwaba na dakkota, yarkaramar jakace me gurare ajikinta. Kananun zip din nafara budewa, a wani naga azurfa babba bata danyatasaba ta tsintsiyar hannu, sekuma wani abu kaman tambarin gidan sarauta kona wani abu dai, anyi rubutu da yaren French ajiki, ajiyesu nayi agefe na bude babban zip din jakar, abunda nayi tozali dashi acikin jakarne yakusa zautar dani............✍️ *Ba editing🥺😋* *TO MASOYA WANNAN SHINE LAST PAGE DINMU KAFIN AZUMI, SEKUMA IDAN ALLAH YAKAIMU BAYAN SALLAH,ZAMU DORA A PAGE 37 INSHA ALLAH, NAGODE MASOYAN ABUNDA KASHUKA ALKHAIRIN ALLAH YAKAI MUKU ADUK INDA KUKE AFADIN DUNIYA* *By* *zeey kumurya* *ABUNDA KASHUKA....* _*(shizaka girba)*_ *3️⃣7️⃣* *INAWA DAUKACIN AL'UMMAR MUSULMI BARKA DA SALLAH, DAFATAN ANYI SALLAH LAFIYA. ALLAH YA MAIMAITA MANA YA AMSHI IBADUNMU,AMEEN*🙏🥰 *Bismillahirrahmanirrahim* ..........Gwalagwalaine a duddunk'ule tamkar duwatsu se daukar ido da kyalli gami da walwali sukeyi. jikina na rawa nasaka hannu nadakko curi daya ina dubawa dannakara tabbatarwa. dan gani nake tamkar idonane kemun gizo,babu tantama gwalagwalaine acikin jakarnan. ahankali nadago ina kallon mustapha dake kwance yana bacci, ina tunanin wanne irin kudine da mahaifiyarsa haka dahar tabani wannan irin kayan dukiya haka, kamar kuma antsikareni sena mike dasauri nafice ina kwadawa atika kira domin tazo tatayani ganin abunda nagani ko idonane yake mun gizo. "Lafiya sulaiman kake kwadamun irin wannan kira haka sekace sabon makaho?" cewar atika tana yamutsa fuska. cikin rudu nace mata, "atika abun mamaki nagani, kema zokiga abunda nagani" banjira amsartaba najuya nakoma dakina tana biye dani abaya, da hannu nanuna mata jakar batare danace mata komaiba. tsugunnawa tayi tadakko *gold* din daya ahannunta tana dubawa. Zaro ido atika tayi waje cikin gigita tace, "sulaiman wannan ai gold ne ina kasamo su,waya baka,ko satowa kayi?" banbata amsaba se zama danayi agefenta ina kara fito da sauran ina dubawa. kara tambayata atika tayi akaro nabiyu da fadin"sulaiman tambayarkafa nake kamun shuru,kuma kana jina". Cikin daukewar tunani daga kwanyata nace mata. "Ranar da mahaifiyar mustapha ta bani shi aranar tabani acikin wannan jakar, ninama manta da ita seyau ina duba kaya naganta shine na dakko naga menene aciki senaga wannan abun nida farkoma nadauka nine bangani daidaiba,shiyasa nakiraki kitayani gan...." gani kawai nayi atika ta washe baki tatashi ta rangada guda gami da juyi tana rawa tana waka cikin tsananin farin ciki,batare data bari nakarasa zancenaba. sakin baki nayi kawai ina kallon ikon Allah. Surar mustapha tayi daketa baccinsa tahau yimasa rawa tana fadin. "Yaro ashe da arzikinka kake tafe, Ashe ta sanadinka mafarkina zecika inzama matar attajiri,kai amma Allah yayiwa mahaifiyarka albarka, nikam tagamamun komai arayuwata databawa sulaiman wannan irin dukiya metarin yawa" cikin tsananin mamaki nake dubanta baki bude, dakyar nayi dauriyar cemata, "atika mekikeyi hakane?" Bata kulaniba secigaba da juyi da mustapha datayi, aiko mustapha yace besan zanceba, yaji ana wujijjigashi tuni yafarka da kukansa. zama tayi tana lallashinsa abunda atika bata taba yimasaba tunda nakawoshi gidan. seda yayi shiru ta dubeni tace, "yanzu sulaiman semu dawo da tafiyarmu gida nankusa muje musaida wadannanan gwalagwalan muwataya mu fancakala muyi wadaka da dukiyar datazo mana, tsuntsu daga sama gashashshe" kallon mahaukaciya nayiwa atika sannan nace mata, "haba atika yadaga ganin dukiya hankalinki yabar jikinki gabadaya duk kinbi kin burkice, wannan dukiyar dakike gani bazan taba komai daga cikintaba, dukiyar marayan Allah ce, zan ajiye masa harzuwa sanda ze girma ya juya abarsa,kuma ni bana cire ran bazankara ganin mahaifiyar mustapha ba, ko wani nata, lokaci kawai nake jira dazannemomasa danginsa insha Allahu, kinga kuwa dazarar munhadu dole nabasu dansu da dukiyarsa" gabadaya fara'ar dake fuskar atika daukewa tayi hartana kokarin yarda mustapha dake kan cinyarta. Cikin takaici tace, "lallaikuwa sulaiman daka cika me bakin hali, mu raini yaron sannan kuma kace bazamuci dukiyarsaba salon inya girman yajuya mana baya, bayan mungama cin wahalarsa,wlh baka isaba abunda bazeyiyuba kenan,aka'idama wannan dukiyar tazama tamu tunda yanzu mune uwarsa mune ubansa,mune shansa da suturarsa" Bankulataba saboda na fuskanci ganin dukiyarnan yana kokarin sakata maida haram halak agaremu. maganganu atika tayita fadamun akan dama bangaji arzikiba dole ince haka, tayi hakuri dani alokacin da babu yanzu kuma Allah yakawo mana hanyar arziki bazan toshetaba, dan haka dole muci dukiyarnan . nidai bankulataba namayardasu cikin jakar narufe na ajiye. tundaga wannan lokaci atika takoma nunawa mustapha kauna da kulawa da tarairaya fiye da tunanin me tunani, abunnata seya dinga bani mamaki, dama shi abun duniya yafi komai saukin canza halin mutum. Kwana biyu daganin wannan gwalagwalai mukayi sallama da mutanen garin niger muka dawo kasarmu me tarin albarka Nigeria tare da wannan dumbin kayan dukiyar. Munsauka lafiya agarinmu kano,agidanmu da muke kafin mutafi anan muka sauka, isma'il yakara gyara gidan saboda alokacin yasamu sana'a yanayi anan gando suke aikin kafintanci, anan muka tarar da saudart (aunty) tazo itama domin tarbarmu. Mustapha fa yasha dauka ranar agurin mutane, dama tun lokacin da mahaifiyar mustapha tabanishi bajimawa na musu aiken cewa atika tahaihu, shiyasa duk daukarsu mustapha dan cikinmune. Kowa se yaba kyawun da Allah yayiwa mustapha yakeyi, itadai atika sedai kawai ta kalli mutum amma badamar magana, dan tun lokacin danaga tana bobbotsarewa akan rikon mustapha nace mata duk ranar data sanar da wani mustapha badanmu bane a bakin aurenta, wannan daliline yasa taboye sirrin har kawo yau danake baku labarinnan bata taba fadawa waniba, domin babu karya atika tana tsananin sona batason rabuwarmu. anan gidan muka cigaba da zama, kullum atika tadinga damuna kenan da maganar dukiyarnan, nikuma gaskiya ina tsoron tabata danbansan ya matsayin hakan yake a musulunciba. danaga ta isheni sena nemi shawarar dan'uwana rabin jiki isma'eel nakuma fada masa yanda muka samu mustapha, isma'il yasha mamaki sosai yakuma tausayawa mustapha tare da yiwa mahaifiyarsa addu'ar Allah ya kubutar da ita yakuma kaddara saduwarta da danta. Shawara yabani akan muje gurin wani malamin addini kawai mutambayesa. Haka kuwa akayi mukashirya mukaje gurin wani babban malami namasa bayanin abunda yake faruwa,seyacemun. Zan iya juya dukiyar mustapha tunda mahaifiyarsa Lokacin data bayar cewa tayi nadauka zata taimakamun amma fa da sharadi tunda wata kila gadon mustaphanne idan yagirma zanbashi ragamar dukiyarsa gaba daya. Godiya nayiwa malam nace za'akiyaye insha Allah. Kodanadawo gida nafadawa atika abunda malam yace, seta tubure tace ita sam batayarda idan mustapha ya girmaba ace masa dukiya tasaceba, kawai nabarta amatsayin tawa. nikuma nacewa atika bata isaba maganar Allah zanbi batataba, akan hakan harfada mukayi da atika. Isma'eel ne yahadani da wani baban abokinsa dayake sana'ar saida gwalagwalai, acikin gold din ko rabi bandibaba amma danaji kudinsu seda na girgiza domin milliyoyi aka siya tun a wancan zamaninma. danaga harkar gold din ana samu sosai senace bari kawai nima nakoma harkar saida gold din. Sauran na dakko aka narkamun zuwa sarka da dankunnaye gami da zobuna,wannan shine farkon silar arzikina a duniya. cikin watanni kadan cinikifa yabude kudi se zuwa sukemun kota ina, nikaina har tsorata nayi kar'a zargeni domin gwalagwalannan kudi suke kawowa bana wasaba. nanfa yan'uwa sukamun caa da tambaya ina nasamu wannan uban jarin haka dare daya, nanna sanar musu, ubangidane dani agarin Niger shiya dorani akan dukiyarsa, dayake bawani damuwa sukayi da lamarinmuba sebasu wani tsananta binkiceba. Ganin arziki yasamu atika tatada balli akan ita bazata haihu agidan damukeba sena sake mana gida mekyau na yangayu. Naso ki,amma isma'eel yace namata babu komai ai. Anan unguwar tarauni nasai wani katon fili natamfatsa ginina me matukar kyau nazamani muka koma. Burin atika yacika tafara shiga sahun matan attajirai. Ko kwana goma bamuyi da komawaba atika tahaifi danta namiji nasa masa suna *abubakar sadiq.* bayan haihuwar abubakar bajimawa Allah yayiwa marikin atika rasuwa, bayan yasha doguwar jinya. kafin yarasu seda atika tanemi gafararsa bisa takurawata akan abunda tamasa a lokacin auranmu. Munji mutuwar tasa sosai,bayan sadakar bakwai atika ta dakko kanwarta jamila tadawo hannunta da zama. Arzikina kara habaka yakeyi abun har mamaki yake bani. hakan yasa nafara saro kaya daga kasashen waje ina saidawa. kafin wani lokaci arzikina yahabaka sunana yafara kewaya sassa na garin kano a jerun masu kudi, nakasarwa atika bakin aljihu tana wadaka da kudi son ranta. tasa abunda takeso taci abunda takeso. Cikin ikon Allah kuma se atika take ta haihuwa akufai_akufai, dan sadiq beyi shekara biyuba tahaifi faruq, shima befi shekara biyuba ta haifi yan biyu haidar da zannurain daganan kuma haihuwar ta tsaya mata. atika macece me matukar son yayanta bata kaunar lefinsu kokadan, amma soyayyar datake nunawa mustapha daban take, nikuma banyi tunanin komaiba dadin hakanma nakeji dannayi tunanin sauyin rayuwar da muka samune yasata sassauta masa. soyayya ce ta kullu tsakanin isma'eel da jamila kanwar atika, munji dadin hakan sosai dan gaskiya atika ba halinsu daya da jamilaba, jamila yarinyace me hakuri da hankali babu ruwanta. tana gama makaranta akayi bikinsu tare aka hada dana saudart. ansha shagali sosai,lokacin su zannurain basufi shekara ukuba a duniya. Zuwa lokacin nashahara akudi sosai nashiga sahun attajiran kasarnan sunana ya yado a birni da kauyuka. Samun kudina besani girmankai ko kyamatar talakaba. har lokacin kowa nawane kuma abun hannuna berufemun idoba base nafadaba kunsan kyautata ba yabon kaiba. Sabanin atika data dauki girmankai da izza gamida kasaita ta dorawa kanta, matan yan siyasa da manyan masu kudi sune abokan huldarta, yan'uwanta kuwa danawa ko kallo basu ishetaba. ta raina arzikinsu tafi karfin ta kulasu. Nagina masallatai da makarantu da kamfanunnuka nadora abokanaina akai da yan'uwa. na hakawa iyayena dasuka rigamu gidan gaskiya rijiyoyi da fanfuna akauyuka da gurararen da suke bukatar ruwa. har saudart tayi haihuwar fari jamila bata haihuba, nanfa tatada hankalinta harda koke_koke domin ita macece meson yaya, nida kaina nabata hakuri da banbaki nace bataga yanda atika tayibane yanzu kuma da Allah yabata haihuwar gashi hartayi yaya biyar. takara hakuri komai lokacine. cikin ikon Allah ba'afi shekara biyu da zancen haihuwarba itama Allah yabata haihuwar diya mace. Zokuga murna gurin ahalinmu domin dukkanmu bamu da diya mace, saudart ma namiji ta Haifa. Ranar suna yarinya taci sunan mahaifiyarmu Ummukulsum amma ana kiranta da *suhailat* suhailat tataso cikin soyayyar yan'uwa da iyaye kasancewarta ita kadaice mace, kowa sonta da riritata yakeyi amma babu kamar atika. Mustapha nema baya nuna mata wata kauna, domin shi damacan tun yana yaro miskiline nakarshe kuma bayason hayaniya ita kuma suhailat akwai kuka da tabara shiyasa sam basa shiri. Bayan arba'in dintane muka dawo wannan gidan dana tamfatsashi, part din da mustapha yake yanzu anan isma'eel yazauna shida medakinsa jamila. hakan yasa kullum suhailat tana gurinmu shan nonone kawai ke maidata gurin mahaifiyarta. Arziki nadada bunkasa yayin da burukan atika nadada yawaita, munjejje saudiya munsauke farali gami da umra akaro dayawa. Akullum cikin fadawa atika da isma'eel nake kobayan raina idan mustapha ya mallaki hankalin kansa su damkamasa dukiyarsa gabadaya a hannunsa. domin ko mutuwa nayi yayana basu da gado acikinta. Wannan magana tawa bakaramin bakanta ran atika takeba a duk sanda nafada mata haka. Haka rayuwa tayita tafiya kullum samuna kara gaba yakeyi kamar yadda nima kullum cikin sadaka da bada kyauta nake, domin banmanta halin danashigaba lokacin ina halin talauci. Mustapha primary school kawai yayi anan kasar atika ta matsa sedai afita dashi waje yakarasa karatunnasa, kin amuncewa nayi amma nacin atika yasa nabarsa yaje yayi,shima ba'ason ransaba umarnin mahaifiyarsa kawai yabi yatafi. Ranar bakin ciki arayuwata ranar dabazan taba mantawa da itaba itace ranar da isma'eel yayi hatsari ya mutu shida medakinsa ahanyarsu ta zuwa abuja, fadar irin tashin hankalin damuka shiga a lokacin rasuwar su isma'eel baze faduba. mutuwar ta shigeni sosai nayi rashin dan'uwa Rabin jiki abokin shawara gakuma tsananin tausayin suhailat da maraici yasameta tuntana yar karamarta. danma karfin rikonta ahannunmu yake dantamafi shakuwa da atika fiye da mahaifiyarta. daga gaisuwar isma'il da mustapha yazo yace baze koma karatu wajeba, alokacin saboda atika bata son bacin ransa tahakura badon tasoba yadawo gida dazama. Bayan mutuwar su isma'il atika suka tafi kasar turkey ita da yara duka mustapha ne kadai bandashi yace baze busuba, se yakoma gurin saudart da zama. anan yakarasa Senior class dinsa, saboda su atika sundade a turkey dansunyi kusan shekara 4 sannan suka dawo, nima se zamana yafi karfi a can tunda iyalina sunacan,nan kuma da masu kularmun da dukiyata. bayan sun dawo mustapha yakoma america domin cigaba da karatunsa anan yayi degree dinsa nafarko dana biyu har *PHD* dinsa. Tundaga lokacin da isma'il yarasu abubuwa suka fara tabarbarewa, nazama tamkar uwargijiya da baiwarta tsakanina da atika se'abunda tace nayi shinakeyi, kuma duk abunda zatayi nabadaidaiba ban isa na tsawatarmataba. Tarabani da yan'uwana dama ita nata bawani damunta sukayiba. yarama kowa abunda yakeso shiyakeyi babu me kwabarsu,bankuma isa natsawatar musuba. Alokacin ne kuma namanta da batun dukiyar mustapha cefa a hannuna ina juyata, senaji kawai tamkar damacan dukiyar tawace. Burin danake dashi na insanar da mustapha dukiyarsace da kuma burin komawa garin Niger domin nemomasa danginsa duk yakau daga kwakwalwata nama manta dashi gabadaya, sabanin da da kullum da tunanin hakan nake kwana nake tashi araina. kawaidai abunda nasan nayi duk wani harka ta kasuwancina ina saka mustapha akan gaba, sauran yayanama kowa yagama karatu zandorashi akan harkar kasuwancina. Wannan shine takaitaccen labarin dazan Baku, dakuma yanda muka samu mustapha." shiru dakin yadauka bakajin motsin komai se karar fanka da sassauke numfarfashi da kowa yakeyi. Gabadaya bakunansu sun musu nauyi sunkasa sarrafa harshensu balle susamu damar koda furta harafi dayane, saboda tsabar mamaki gami da al'ajabi da jimami. Mustapha kawai kallon daddy yakeyi tunda yafara bada labarin, wani irin yanayi yakeji ajikinsa me wuyar fassaruwa,yanda yakejin zuciyarsa tamkar ana rura masa wutar garwashi acikinta, gani yakeyi tamkar daddy kirkirar labarin yayi kawai ya basu. tayaya ze iya daukar wannan bakon al'amarin ace mominshi me kaunarsa meson ganin farincikinsa akodayaushe ba'ita ta haifesaba. ahankali ya yunkura idanunsa a lumshe tsabar damuwa ko gani bayayi ya mike yana layi ya karasa gaban mommy yadurkusa yakama hannunta, cikin wahalalliyar murya menuni da me ita shikadai yasan azabar dayakeji yace, "mommynah, nike nasani amatsayin mahaifiya kuma kenaso nacigaba da kallo amatsayin uwata dan Allah kimusantamun abunda daddy yafada konaji sanyin tafarfasar da zuciyata takemun,wlh kwakwalwata bazata iya daukar wannan lamarinba" wani irin kallo mommy tamasa me wuyar fassaruwa tana murmushin mugunta tace, "mustapha kada ka bata bakinka gami da wahalar dakanka akan abunda yake na gaskiya zuwa wanda bashi bane. ninan atika dakaganni banasonka bana kaunarka mesonkama bana sonshi imfact madai duk duniyarnan babu wanda na tsana sama dakai mustapha, saboda haryau zuciyata bata yarda da zancen sulaimanba, nafi yarda da ciki yayiwa wata a waje ta haifeka" mommy tafadi haka babu alamar nadama a tatattare da ita. Gabadaya yarannata ido suka zuba mata suna kallonta yanda take magana babu alamun rahama akan fuskarta. Aunty kuwa kanta nakasa tana karanto addu'ar samun nutsuwa domin kuwa yanda taji al'amarin a baibai waiba mommy ce tahaifi mustapha ba, kuma duk irin tarin soyyayar datake nuna masa ashe duk na muguntane,lallai mommy ta iya zagon kasa,kuma ta cika cikakkiyar makira. mustapha cikin fitar hayyaci yakara damke hannun mommy idanunsa nazubar da hawaye yace, "mommy meyasa bakya sona wanne lefi namiki arayuwa, please and please mommy kisoni sona gaskiya nike kadai nasani amatsayin uwata kome zakimun kuwa bazantaba canza matsayinkiba,domin banida kamarki" dagowa aunty tayi tana kallonsa cike da tausayawa idanunta nazubar da hawaye, yanda yake kuka yana rokon mommy, abunda ta manta rabon dataga kukansa, domin shi mutum ne mejuriya akan komai. tabbas akwai tashin hankalin da idan yazowa mutum duk jarumtarsa be isa ya jure masaba. daddy ma cike da tausayawa yake kallon dannasa abun kaunarsa, duk da daddy yasamu wasu yayan amma bayajin kaunarsu kamar yadda yakejin ta mustapha,kaunar mustapha daban take acikin zuciyarsa. Faruqne ya matso yakama mustapha yarungumeshi ajikinsa. shima idanunsa nazubar da hawaye yace, "yaya mustapha dama nine kai, domin kai kayi sa'ar mahaifiya sabaninmu dabayi sa'artaba, mahaifiyarka tazabi mutuwa kaikuma karayu saboda tsananin kaunar datake maka,amma mu mommy da kanta take cutar damu duk dan akan duniya tabbas nasan idan kaji irin abubuwan da mommy tamaka na cutarwa zaka tsaneta, kuma bakaikadai ta cutarba harda wasu bayin Allah dabasujiba basu ganiba duk domin dukiyarka ta zamo mallakinta ita yayanta,inama ana canza uwa dase nazanca mommy wlh, domin bata da imani kokadan" yakarashe zancen yana fashewa da kuka meban tausayi. mommy ce ta amshe zancennasa da fadin, "bana nadama kodanasani arayuwata tunda nafarata, kuma ayanzuma banyiba kuma bana fiddaran zanci nasara akan abunda nasa gaba,domin duk abunda na kudura arayuwata sena cimma nasara akansa komeneshi kuma komun wuyarsa ko....." "ba'aiwa Allah izgili kada kiga kinsamu nasara abaya kiyi zaton zaki kara samu nangaba, insha Allahu alkadarinki ya karye daga yanzu, kuma da sannu zaki girbi *abunda kika shuka* da hannunki" daddy yakatse mommy da fadin haka cikin tsananin bacin rai gamida takaicinta tare da danasanin kasancewarta matarsa. Mommy batabi takan maganar daddyba. tadubesu duka tace, "bari na baku kadan daga cikin labarin irin abubuwan dana aikata duk domin nasamu biyan bukatar raina" gabadaya ido suka zuba mata akaro nababu adadi amma banda sadiq dakansa yake a sunkuye tunsanda daddy yafara bada labari. Mikewa mommy tayi tai taku uku sannan ta fara magana kamar haka:..........✍️ *BY* *zeey kumurya* *ABUNDA KASHUKA* _*(shizaka girba)*_ *3️⃣8️⃣* *Bismillahirrahmanirrahim* ............Nakasance ni macece me hassada gami da kyashi akan duk wanda naga wani yafini samun wani abu na rayuwa tun ina yar karamata,tun ina budurwa na baci da bin bokaye da malaman tsibbu". duban daddy mommy tayi tacigaba da magana. "Sulaiman yakamata ace kayi tunani akan yanda na dage kai nakeso da aure alhalin nakasance mace me shegen son kudi kai kuma baka da kudi a lokacin kuma Wanda kawuna yakeso yabani yafika kudi,amma na nadage kai nakeso. To kasani auranka danayima ina da dalilin yinsa kuma ban aureka da niyyar zama dakai na dindinba,na aurekane amatsayin garkuwa wanda dazaran nagama cimma burina zan tilasta maka ka sakeni" dasauri daddy yadago da niyyar yiwa mommy magana amma tadaga masa hannu alamar yadakata sannan taci gaba da magana. "Na aurekane bisa umarnin wani boka danaje gurinsa akan wata bukatata yakuma tabbatarmun da bukatata bazata biyaba harse na auri miji irinka kamar yadda ya siffantamun, kuma gashi nayi nasara na aureka nacika burin dayasa na aureka tun aurenmu bajimawa, amma bazan fada muku ko wanne buri bane saboda ba huruminku bane. lokacin da burinnawa yagama cika ina kokarin cewa kasakeni wannan arzikin yazomana shiyasa nafasa rabuwa dakai. Idan baka mantaba afarkon aurenmu nayi barin ciki toba barewa yayiba nina zubar dashi da kaina domin banason haihuwa dakai, daganan kuma nafarashan magungunan hana daukar ciki, daga baya kuma Allah yanunamun ikonsa duk da inashan maganin amma sega cikin sadiq, a lokacin naso zubar dashi kawai kuma sena hakura. Tun lokacin daka kawo mustapha haka kawai naji tsanar yaron ta cikamun zuciya sannan kuma zuciyata ta kasa aminta da labarin daka bani akan yanda kasamesa. hakan yasa tun yana dan jariri nayita gasa masa azaba iri_iri wanda kai sulaiman baka saniba kana gurin aiki, Allah ne kawai yayi mustapha yanada rabon shan ruwa a duniya datuni yadade da mutuwa domin na dade ina yunkurin kasheshi. bayyanar dukiyar mustapha shine abu nafarko mafi rinjaye acikin duk wani abu nafarinciki daya sameni arayuwata,bansan yazan misalta muku farin cikin danayiba a wannan lokacin, domin dama nican burina sonake inzama matar hamshakin me kudi wanda duniya tasanshi sekuma gashi Allah yakawowa sulaiman kudin a lokacin da banyi zatoba. Sedai kuma wata matsala daya da sulaiman yacemun dazarar mustapha ya girma ze damka masa dukiyarsa gaba daya a hannunsa. Alokacin daya fadamun natada hankalina naita fadace_fadace domin dai sulaiman yacemun yajanye ra'ayinsa amma yaki. Nanfa nafara tunanin hanyar dazanbi dan ganin nahana wannan kudiri nashi cika. haka muka cigaba da rayuwa ina nunawa mustapha kauna fiye da kowa a duniyarnan kuma koda wasa bantaba fadawa wani bani nahaifi mustapha ba domin ina da muradin nakasheshi dazarar yakai wasu shekaru kuma banason agane nina kasheshidin. sulaiman yasakarmun bakin aljihu inayin yanda naso da kudi hakan yasa nabazama gurin bokaye Neman maganin dazan hallaka mustapha cikin sauki nakuma mallake sulaiman akan se abunda nace yayi shizeyi. wata kawata hannatu ita tahadani da wani boka wanda shiyakemun aiki har yanzu wato *boka tsidau* ta kuma tabbatarmun da aikinshi tamkar yanka wuka yake duk abunda nakeso yamun zemun amma fa yana bada aiki masu wahala gami da cazar kudi. nace mata nidai indai bukatata zata biya koma menene zanyi kuma ko nawane zan kashe ba matsala bane. can wani kursungumin kauye a garin katsina hindatu ta kaini inda anan bokan yake da zama, muna zuwa tunkafin nafada masa bukatata yasanarmun hakan yasa nakara gasgasta zancen hindatu na aikinsa nada kyau, domin alamar karfi tanaga me kiba. abu nafarko dayasanarnun zanyi shine nafara kawar da duk wani wanda yasan mustapha badanmu bane, ma'ana nakasheshi. Godiya namasa nadawo gida.Tun daga ranar nafara bin duk hanyar dazanbi danganin na kashe isma'il domin a iya sanina shikadaine yasan wannan maganar, dama kuma inajin haushin yanda sulaiman yake sakasa a komai na harkar kasuwancinsa kuma damacan bama wani shiri dashi duk da yakasance mijin kanwata. Isma'il gabadaya a kowanne sati yana abuja yana kula da kamfanin dake can na sulaiman, se weekend yake dawowa nan kano, ko tausayin suhailat banjiba a lokacin nasa aka cire burkin motar sulaiman wata ranar Monday da safe ranar ze koma abuja, Ashe ni bansaniba jamila ta tatakura masa a daren da ana gobe zasuyi tafiyar akan tanaso tabishi abujan itama shine suka shirya suka tafi tare. dama suhailat a gurina ta kwana aranar. Tafiyar sassafe zasuyi shiyasa jamila batazo mana sallamaba, kuma tasan idan tazo bazan barta su tafi tareba saboda banason tayi nisa dani, shiyasa idan tace zata bishi nake hanawa. seda suka fice daga gidan sannan tamun text a wayata nibanmaga text dinba seda aka kira sulaiman akace sunyi hatsari duk sun rasu, hankalina bakaramin tashi yayiba danaji harda yar'uwata tuggun dana hada yakama nayi kuka kuma nayi takaici amma duk da haka bansadudaba bayan rasuwar tasu komai yalafa nakoma gurin boka, yacemun aikina akan mustapha baze tafi yadda akesoba harse na hada da namiji saurayi wanda betaba aureba kuma yakasance jinin sulaimanne,amma a lokacin yabani maganin dazanyi amfani dashi domin na mallake sulaiman din, kuma maganin yamun aiki yanda nakeso. Nikuma a lokacin na fito da kissa da kisisina tare da biyayya akan sulaiman tamkar wata ta Allah, duk dan na kawar da tunaninsa akan zargina da wani abu agaba. Haka nacigaba da rainon suhailat cikin tsananin so da kaunarta domin ita nake gani ta debemun kewar yar'uwata rabin jikina. Naso mustapha ya lalace yanda sulaiman zeji ya tsaneshi shiyasa na turashi karatu kasar waje amma abun Allah seshi be lalaceba yayana nacikina su suka lalace. Nayi nasarar mantar da sulaiman komai akan mustapha saboda yanda kullum cikin zancen dukiya batasa bace ta mustapha ce. Ni kuma da raina da lafiyata bazan bari wannan dinbin dukiyar ta tserewa yayanaba inaji ina gani. Lokacin da yarana sadiq da faruq suka tasa suka zama samari senajewa da boka tsidau da maganar ga samarin ansamu,yayan sulaiman nema nacikinsa kuma bani da matsala dasu zasumun komai danakeso,tunda yayanane. boka yacemun akwai maganin daze bani inawa mustapha amfani dashi ze mutu cikin sauki, amma wannan azurfar dake tsintsiyar hannunsa wadda da ita mahaifiyarsa tabawa sulaiman acikin jakarnan tana bashi kariya ga sihiri kuma mustapha mutum ne meriko da addini gami da addu'a dan haka sedai muyi wani aikin daban. Aikin da boka ya bani shine yanason daya daga cikin yayana yayiwa yanmata guda goma shabiyar fyade sannan kuma daga baya aljanunsa zasu shanye jinin jikinsu su mutu,bayan ya shanye wanda yazuba na budurcinsu. daga zarar nayi haka to burina guda biyu ze cika aduniya na mutuwar mustapha da mutuwar sulaiman aranar da akayiwa yarinya ta goma shabiyar din fyaden koda bata mutuba. Gaskiya wannan aikin da boka yabani ya girgizani bakadanba domin bansan ina zansamu yanmataba wadanda zanyi aiki dasuba a lokacin. Alokacin inada wata me aiki dake kula da part dina wadda bazatafi shekara 40 ba, se sulaiman ya nuna yana sonta ze aureta. aiko nan nayita bala'i na kuma koreta, sulaiman yata bani hakuri domin Alokacin aikin boka nacinsa se'abunda nace yayi shiyakeyi. Da wannan abun na fake aka dinga kawomun yara yanmata aikatau sadiq na musu Fyade sena maidasu gurin iyayensu su karasa mutuwa acan. Da farko faruq nafarawa maganar bukatata domin naga duk cikin yayana yafi kowa zuciya gami da kwazontaka amma faruq yaki bani hadin kai se wasu wa'azizzika daya shiga yimun danaga yana kokarin tonamun adiri sena bada sunansa gurin boka ya rufe masa baki tundaga lokacin faruq ya koma tamkar kurma seya wuni yakwana beyi maganaba. kuma kome akayi baze iya magana akaiba sedai yabi mutum da ido kawai. Lokacin dana tunkari sadiq da maganar nayi mamaki daya amincemun da gaggawa domin banyi zaton haka daga gareshiba kasancewarsa mutumin kirki azahiri, daga lokacinma senadena zuwa gurin boka da kaina sedai natura sadiq yajemun. yanmata uku aka farayiwa fyaden wanda duk wata tsohuwace take kawomun su daga kauyensu daga baya mutanen garin suka ganeta se sukasa aka kamata har gidan yari aka akaita nikuma namata gargadi da cewa matukar tabari sunana yafito acikin abun senasa ankarar da duka danginta hakan yasa ta tsorata taki fadin sunana bansan kuma yasuka karkeba ita da mahukunta. talatu itace farkon me aikina kuma ita kadaice tasan sirrina saboda abun yafaru akan jikarta da wasu yan garin su guda biyu data kawomun. sena koma bin kauyuka daban_daban inda ba'asanniba inasa ana dakkomun yara aikatau ahaka har'akayiwa yara 14 fyaden saura daya kenan. Boka yatabbatarmun dacewa aranar da akayiwa ta cikon 15 din mustapha da sulaiman bazasu kwana arayeba. Maryam itace yarinyar danasa wata kawata lami ta nemomin tun ranar da aka kawo maryam gidannan a kallon farko dana mata naji gabana yayanke yafadi, wanda kuma bansan daliliba. hakan yasa nake yawan kallonta dan ganinakeyi kamar zangano wani abu atattare da ita. Maryam itace ta zamo silar lalacewar kowanne shirina." Numfashi mommy taja ta kalli mustapha fuskarta cike da tsantsar mugunta tace, "bayan duk wannan abubuwan namaka asirin da bazaka taba iya wata mu'amalar aure da wata diya maceba, hakan yasa ko tunanin aure bakayi. Boka tsidaune yacemun matukar nabari kayi aure kowanne shirina ze lalace. Lokacin da suhailat tazomun dabatun kai takeso hankalina bakaramin tashi yayiba, saboda nasan sulaiman yanajin zancen zece ayi auranku, amma ganin yanda suhailat din duk tabi tadamu sena maka zancen kuma nace kasota,amma seta gama karatu zakuyi aure,duk dan hankalinta ya kwanta amma banada niyyar kuyi aureba. Nabi hanyoyi dadama domin ganin na muzantaka gami da bataka a idon jama'a amma banyi nasaraba, har yan kamfaninku nahada baki dasu duk dan abata maka suna. idan zaka tuna wata rana da P.A tazo office dinka tayi tari amatsayin asmarta tatashi hartazo zata fadi ka tallafota jikinka, alokacin manager ya daddaukeku photo a wayarsa da niyyar ya watsashi aduniya amatsayin kuna lalata amma ita P.A din ta gogeshi saboda tace tana sonka bazata iya ahada baki da ita a cutar dakaiba. Na kyaletane kawai saboda nasamu hanyar dazan kasheka cikin sauki wato wannan cutar dakayi ta watanni. wani maganin boka yabani yace inmaka turare dashi cikin dare, zanga abun mamaki. Cikin Daren ranar da sadiq yakawomun maganin nazo namaka turaren a lokacin ma idanunka biyu nace maganin tsarin jiki zanmaka. Shine da safe katashi da wannan ciwon, dalilin dayasa kenan nakafe baza'a maka maganin hausaba, amma saboda takurawar saudart seda takira malaminnan, maganin malaminnan yana aiki sosai hakan yasa namisanya makashi da wani maganin daban dayake kara ta'azzara ciwonnaka harta ruwan tofin daya baka seda nasauyashi. Kullum cikin dare zanzo inwatsa wani magani koni ko sadiq acikin wannan yarkaramar tukunyar kasar da maryam ta dauka wadda ni dakaina nasanya maka ita acikin filonka,kuma acikintane sihirin dana maka yake wanda nahada harda gashin kanka. Addu'ar da maryam take maka shiyake sanyaya tukunyar daga mugun zafin datake dashi tana zafafa maka jikinka, nikuma dazarar tsakiyar dare tayi zanzo inkara barbada magani acikinta wanda zata koma ainihin zafinta. bansan ya'akayi tukunyarnan taje hannun maryamba, tabbas maryam tazamemun ciwon idanu, ta rushemun ginin dana debi shekaru masu yawa ina ginasu acikin yan mintuna. kasani mustapha maryam ta batamun duk wani shirina akanka amma banhakuraba danni mutumce bame raguwar zuciyaba zankoma incigaba indora daga inda natsaya senaga bayanka dakai da maryam da sulaiman d....." "karya kikeyi mushirika da yardar Allah karshenki yazo kuma zakiga sakayya tun anan gidan duniya kikiyayi ranar da *zaki girbi abunda kikashuka* na sharri da hannunki" cewar aunty cikin kuka data katse mommy da wannan maganar. Gabadaya dakin kuka sukeyi banda daddy daya daure yakeyin na zuci,amma idanunsa sunyi jajur saboda tsananin bacin rai da bakin ciki da damuwa gami da dumbun takaicin halin mommy. da kuma mustapha dayaji jikinsa yayi masa wani irin sanyi duk ya shika, tsanar mommy gabadaya ta gama baibaye zuciyarsa ta maye gurbin tarin kaunar dayake mata. bayason mugunta kuma bayason mugun mutum, yanxo mommy akan dukiya tayi sanadiyyar rasa rayukan mutane da yawa, ko tunanin itama wataran zataje inda sukaje din batayi, lallai wanda yayi nisa bayajin kira,yaji yatsani kansa da duniyarma gabadaya,yanayin dayakejin kansa baze misaltuba. Cikin kuka haidar yadubi mommy dake tsaye har lokacin yace, "mommy amma baki kyautamanaba mu yayanki mukika cuta kika bata mana suna, wlh nayi danasanin kasancewarki mahaifiya a gareni, kin cutar damu gashi baki bamu tarbiyyaba w....." Kuka yaci karfinsa meban tausayi wanda yasashi kasa karasa abunda yakeson cewa. Suhailat ma kuka takeyi tamkar ana zare mata numfashi dataji mommynta mafi soyuwa agareta ita tayi sanadiyyar barin mahaifanta duniya. Daddy ne yadubi sadiq Cikin kunar zuciya yafara magana. "Amma sadiq kabani mamaki kaida nake ganin ko mutuwa nayi zaka gajeni segashi dakai aka hada baki gurin yin wannan mummunan danyan aikin, yanzu mezakacewa da ubangijinka idan ka mutu akan cutar da bayinsa da basujiba basu ganiba dakayi" cikin shashsheka sadiq yadago yana duban daddy yace, "daddy kagafarceni wlh sharrin shedanne da kuma sharrin zuciya, gami da hudubar mommy. Tabbas yau naji wata nadama ta lulllubeni gamida kunyar ubangijina akan abunda nadade ina aikatawa tsawon wasu shekaru". maida dubansa yayi akan mommy yacigaba da magana. Kin cutar dani mommy kindorani akan zunubin da ubangiji baze taba yafemunba, mafi girman zunubi kuma agurin Allah ga kuma hakkin wadanda nazalunta,wanda ahalin yanzu basa doran duniya bare nanemi yafiyars..." kukane yaci karfinsa. faruq ne yashare hawayen dake malala akan fuskarsa yadubi daddy yace, "babu shakka zuwan maryam alkhairi ne agidannnan domin kuwa ta sanadinta duk wani shirin mommy ya lalace wanda harnima nadawo cikin hayyacina daga mugun asirin da mommy tamun. Duk abunda mommy da sadiq suke kullawa ina sani amma harshena baze iya sarrafuwaba balle harna fadawa wani. A duk lokacin da sadiq yakaiwa wata yarinya hari a gidannan ina hankalce dashi sedai bani da ikon hanashi kokuma natona masa asiri. Wannan ruwan addu'ar da maryam takeyiwa mustapha kullum idan yayi guntu shinake zuwa nasha batare da kowa yasaniba, da haka harna farajin nima nafara dawowa daidai. A Daren jiyane da zannurain yayi bacci nadauka ruwan nasha a lokacinne kuma naji dukkan nutsuwata ta dawo, kaina yamun wasai tamkar ansaukemun wani abu me mugun nauyi acikinsa. Dama tunda naji sadiq yace yayi tafiya nasan batafiya yayiba domin haka yakeyi duk sanda zeyi mummunan aikinshi seyace tafiya zeyi. barin part dinnan nayi gabadaya nakoma part din mommy na buya a inda babu me ganina, kuma inada yakinin dama da yardar Allah sadiq baze samu nasara akan maryam ba, harya shiga dakin yafito banbar part dinba, ina tsaye a inda nabuya naga yafito da gudu dafe da goshinsa nima binbayansa nayi dasauri harya buya ajikin fulawoyi sukayi waya da mommy duk ina biye dashi besaniba ya tashi da niyyar guduwa shine narikeshi kokuwa muka shiga yi dashi hardai nayi nasara akansa saboda yafara galabaita ga jinin dake zuba ajikinsa. Kamasa nayi nakaishi can bayan gida na daureshi dankarya gudu, seda azubane nadaukeshi nakaishi asibiti aka masa treatment a hannunsa da goshinsa shinema kuka ganmu munshigo tare dashi. dama nataho da niyyar nazo na fayyace muku komai sekuma natarar da yaya mustapha yatashi haryana'iya magana da kansa" Shiru dakin yayi bayan faruq yagama magana, babu abunda kakeji se tashin kukan suhailat dana sadiq,aunty kam girgiza kai kawai takeyi tana mamakin rashin imani irinna mommy sekace ba musulmaba,akan duniyar dakowa zebarta. Mustapha kuwa jikinsa yayi tubus tamkar andafa dankali ko danyatsansa daya ya kasa motsawa soyayyar mahaifiyarsa gami da muradin ganinta susuka cika masa zuciya,yanajin tamakar yabude idonsa yaganshi agabanta. kudiri yadaukarwa kansa ayau ba gobeba zefara nemanta a duk inda take acikin duniyarnan matukar tana numfashi . Zannurain datun dazu shine bece komaiba ya katse shirun nasu yana duban mommy da fadin. "Mommy dan Allah kihakura haka, duk abunda kikayi abaya be ishekiba sekinyi yunkurin karayin wani mugun abun, memakon kikoma ga Allah kinemi yafiyarsa da wadanda kika zalinta amma sema kara wani kudirin kikeyi babu alamar nadama atattare dake, bayan kuma Allah yanuna miki ishara a lokaci daya ya karya dukkan wani shiri naki da kikayi shekaru masu yawa kina kullawa." Wata dariya Mommy takece da ita irinta marasa imani sannan tace, "yaro man kaza, ai rago shiyake ja baya a fada. Karfa kamanta akan wannan cikar burinnawa yar'uwata guda daya tal tarasa rayuwarta kuma nice sanadi, sannan kuma kawata hindatu data rakani gurin boka, naga irin mutuwar wulakancin datayi a sanadiyyar bin bokaye, duk besa nasadudaba se dan wannan abun. To kusani ba gudu baja da baya yanzu aka fara wasan,idan kaga banga bayan mustaphaba da sulaiman to katabbatar bana numfashi a doron duniya.............✍️ _*Ba editing🙄🥺*_ *BY* *zeey kumurya* *ABUNDA KASHUKA* _*(shizaka girba)*_ 3️⃣9️⃣ *Bismillah irrahmanirrahim* ..............Mommy tana gama fadar haka tajuya tafice daga dakin gabadaya tana kissima irin muguntar dazata kara shiryawa mustapha harma da maryam da daddy nangaba. har aunty ta mike zata bita daddy ya katseta da sauri ta hanyar fadin, "ina zaki kuma saudaurt?" batare da aunty ta juyo ta kalleshiba tace "zanje naduba jikin maryam ne, nasan zuwa yanzu tatashi" daddy yasan halin aunty sarai idan aka bata mata rai idan bataje ta mayar da martaniba batajin dadi yasan gurin mommy zata suyita cacar baki. Hakan yasa yace mata tadawo ta zauna zasuyi magana. batare da aunty tasoba tadawo ta zauna tana sassauke numfashi gami da huci cikin tsanananin takaicu. duban aunty daddy yayi da kyau sannan yace, "a matsayinki na mace wadda yakamata ace kin fini saka ido akan al'amuran cikin gida ina son kifadamun gaskiya akan duk wannan mummunan aikin da'ake aikatawa acikin gidana baki saniba.?" wani gwauron numfashi aunty ta sauke tace, "wlh yaya koda wasa bantaba jin wannan zancenba kokuma naga wani abu makamancin haka, duk da ina yawan zuwa gidannan amma ai kasan nimaba mazauniyar garinnan baceba tayaya zansani" shiru daddy yayi cikin tsananin takaici gami da kunar zuci, jin abun yake tamkar almara wai a cikin gidansa, dan cikinsa yakewa yara mata fyade. "Wa'iyazubillah" yafaurta a fili idanunsa na taruwa da kwallar bakin ciki, yarasa wacce irin mace Allah yabasa, yarasa wanne irin son duniyane da mommy. Yanzu duk daular datake ciki ita da yayanta amma be ishetaba to wanne irin kudi takeso ita kuwa tayi arayuwarta. Faruq ne yakatse daddy daga tunanin dayake ta hanyar fadin, "yanzu daddy kana kallo mommy tatafi batare dakadau wani kwakkwaran mataki akantaba ai kamata yayima kamikata ga hukuma su hukuntata akan lefin datayi" wani yawu me daci daddy ya hadiye dakyar kafin ya numfasa yace. "Babu matakin dazan dauka akan atika umar, kuma bazan mikata ga hukumaba kodan darajarku ku yayanta, amma maganar aure tsakanina da ita ta kare bazan iya kuma cigaba da zama da ita ba" "haba daddy wanne bashine iya hukuncin dayakamata kamataba kawai, kamar yadda yafaruq yafada yakamata kamikata ga hukuma su hukuntata" cewar haidar dayakatse daddy cikin tsananin takaici gami da bakin cikin abunda mahaifiyarsu ta aikata. "Hakan yakamata nayi nima Aliyu, amma kasani Allah ba azzalumun bawansabane da sannu tun anan gidan duniya zenunawa atika ishara akan abunda ta aikata, domin " duk *ABUNDA KASHUKA SHIZAKA GIRBA*" shiru sukayi kowa da abunda yake sakawa acikin zuciyarsa. suhailat ce tatashi tafice daga dakin tana kuka wiwi meban tausayi, haidar ne yabi mata baya cikin tsananin tashin hankali. aunty ma batare data kalli kowaba tamike tafice domin tadubo maryam dan zuciyarta na ayyana mata tamkar mommy tanacan tana mata wani mugun abun. Zannurain da faruq ne suka bi bayanta, sadiq kam kunya tahanashi koda dagowa ne, shikansa betaba tunanin wannna ranar tonan asirin zata zo masaba arayuwarsa, dakyar ya iya mikewa shima yafice.binsa da kallo daddy yayi cikin tsananin mamakin sadiq din daya kasa barinsa har yanzu, sadiq din dayake ganinsa me hankalin dababu kamarsa kaf cikin yayansa amma shine yake aikata wannan danyen aiki. gaskiya yayi Allah wadai da auren mommy dayayi, ta cucesa ta cutar masa da yayansa tabata musu tarbiyya, yana tunanin ze sake shawarane ya mika mommy da sadiq hannun hukuma ta bakin su faruq din, domin yazama izna agaresu anan gaba. Mustapha dake zaune tamkar mutum mutumi, domin bazece ga a duniyar dayake cikiba. Saitin zuciyarsa yadafe da hannunsa saboda harbawar datakeyi gamida zafi tamkar ana watsa masa garwashi, gabadaya yadena fahimtar komai, duniya juya masa kawai takeyi. cikin tsananin dauriya idanunsa a lumshe ya sakko daga kan gadonnasa yafara takawa zuwa gurin da daddy yake a zaune. Kafafunsa tamkar ba'ajikinsaba saboda taruwar jinin da sukayi nazama guri daya, ga nauyin dasuka masa ga wani jiri dayake jibanshi abu goma da ishirin duk shi kadai. daddy dake binshi da kallo cike da tausayawa ya lumshe idonsa saboda wata kwalla data cika masa ido na tsananin tausayin mustaphan, yasan dole yafi kowa shiga tashin hankali agame da wannan al'amari domin rashin asali bakaramin tawaya bane ga rayuwar dan'adam. Ahankali ya tsugunna agaban daddy akan gwiwowinsa ya dora hannunsa akan cinyar daddy, ilahirin jikinsa rawa yakeyi saboda tashin hankali.bCikin tsananin dauriya yafara magana dakyar da muryarsa dake nuni da tsantsar damuwa yace. "Daddy bani da baki kokuma wasu kalmomi dazanyi amfani dashi gurin gode maka arayuwata, domin Kaine jigo kuma bango na rayuwartawa. tabbas kacika mutum me tsananin kirki da hali nagari da samun kamarka zeyi wuya a zamanin yanzu. Daddy alfarma daya zakamun ayanzu shine kafadamun inda mahaifiyata tabakani, nikuma ayau ba gobeba zantafi nemanta kuma da izinin Allah indai tana raye bazan dawoba harse nagamu da ita." Yakasarashe zancen yana sassauke numfashin wahala tare da zubar hawaye masu dumi akan kuncinsa. Ahankali daddy yabude idanunshi dasuka rine zuwa ja yasaukesu akan fuskar mustapha. Hannunsa yakai yafara goge masa hawayen fuskarsa cikin tsanani so da kaunarsa kafin yafara magana kamar haka. "Insha Allahu, mustapha bama fada makaba kawai zanyiba, dakaina zankaika har garin kuma natayaka Neman mahaifiyarka da danginka, dama burinane hakan tun kafin yau. mustapha be iya cewa komaiba, saboda yanayin dayakejin kansa, mikewa yayi juwa nadibansa yanufi toilet domin yasakarwa kansa ruwa kozeji dadin jikinsa. binsa da kallo daddy yayi cike da tausayawa harya shige toilet din. cikin sanyin jiki shima ya mike ya fice daga part din.... Apart din mommy kuwa, mommy cikin sauri takarasa part dinnata direct dakinta ta nufa tafara hada abubuwan datasan zasuyi mata amfani domin tasan koda daddy befurta mataba tasan zamanta agidansa yakare daga yau, kodama bekareba yau dole ta bazama Neman mafita akan wannan kuncewar al'amarinnata dayazo mata alokacin dabatayi zatoba. cikin sauri take diban abubuwanta masu amfani tana zubawa acikin wata handbag dinta. Tana cikin hada kayan suhailat ta shigo dakin da gudu da kukanta. Sororo mommy tayi tana kallonta kafin ta tabe baki tacigaba da diban kayanta. ganin kukan suhailat din yaki karewa mommy ta dubeta a kufule tace, "daughter wai lafiya kikazo kika sani agaba da kokekoke?" cikin shan majina suhailat tace, "mommy dan Allah meyasa kikayi haka, meyasa kika cutar da yaya irin haka, me yayi miki da kika masa irin wannan tsanar?" Wani murmushi mommy tayi kafin tadubi suhailat tace, "daughter haryanzu ke yarinyace bakisan me duniya take cikiba,kuma duk bayanin dazan miki bazaki gane menake nufiba, amma komai danakeyi danku nake" mommy ta karashe zancen da daukar mayafinta ta yafawa. "wai mommy mekike shirinyi, ina kuma zaki?" suhailat tatambayi mommy cikin tsananin mamakin ganin yanda take ta sauri zata fita. "Zankoma gidanane dake lamido kafin gobe kuma nabar garin gabadaya" baki sake suhailat take kallon mommy ta bude baki zatayi magana mommy takatseta ta hanyar fadin. "Banson kikara cemun komai daughter, abunda nakeso dake kawai shine ki kwantar da hankalinki zandawo nanbada jimawaba,acan dinne senafi jin dadin yin aikin dazanyi batare da wata matsalaba." Mommy tana gama fadar haka ta fice daga bedroom dinnata cikin sauri batare data jiraa msar suhailat ba. wani kuka suhailat tafashe dashi cikin tsananin jin takaicin halin mommy, duk abunta da mugun halinta bazata iya abunda mommy tayiba gaskiya mommy tabata mamaki bakadanba. A falo mommy sukayi kicibus da aunty data shigo. Aunty danne bacin ranta tayi taki koda kallon inda mommy take tayi shigewarta dakinta inda maryam take. Mommy kuwa bin aunty tayi da kallo kafin tayi wani murmushi da ita kadai tasan ma'anarsa sannan tafice tanufi parking space, yau ko direbanta bata nemaba dakanta zatayi driving din. Har lokacin maryam tana kwance tana baccinta, sedai daga gani baccinnata bana jin dadi bane, a wahalce take yinsa. Ahankali aunty takarasa gareta tasa hannunta tana shafa fuskarta, tausayin maryam ne yakara mamaye mata zuciya yanda take fitar da numfashi kana gani kasan na wahalane. toilet aunty ta nufa ta watso ruwa ajikinta domin taji dadi, dan yanda takejin kanta a wannan lokacin baze misaltuba, jinta take a wata duniyar databan tsabar damuwa. Tana fitowa daga toilet din taga maryam na mutsu_mutsu alamar tatashi. Da sauri aunty ta karasa gareta ta tallafota jikinta tana kiran sunan sunanta. Memakon maryam tabata amsa se kuka data saka cikin wata wahalallaiyar murya tafara fadin, "dan Allah kumaidani gida gurin gwaggo ta, gwara na zauna agurinta akan zaman gidannan da'ake son cutar da rayuwata d...... Rufe mata baki aunty tayi, ganin haryanzu bata gama dawowa cikin nutsuwartaba, daidai lokacin daddy ya murda handle din kofar dakin bakinsa dauke da sallama, yazone domin yaduba jikin maryam din, kuma yanata knocking aunty bata jiba, kalaman maryam gabadaya akunnensa tayisu, runtse idonsa yayi cikin tsananin takaicin wai yau gidansa ake neman tsarin zama acikinsa, gaskiya atika ta gama dashi. Muryar maryam da yanda tayi maganar cikin kuka yatuno masa da muryar matar dabaze taba mantawa da itaba arayuwarsa, tamkar itace ta dawo take masa magana a yanzu. cikin sanyin jiki yakarasa cikin dakin inda sautin kukan maryam ne kawai yake tashi, aunty kuma na aikin rarrashinta. "saudart jikinnatane haryanzu" aunty dabatasan da shigowarsaba ta juyo tana kallonsa idanunta cike da kwalla tace, "inajin fa yaya haryanzu bata dawo hayyacintaba,yanzu ta farka sekuma ta fara surutai" daddy bece komaiba ya mike yanufi karamin fridge din dake dakin ya dakko ruwa a roba medan sanyi, ya tsiyaya a cup sannan yatofa addu'a yamikawa aunty yace tabawa maryam din tasha. Tallafota aunty tayi takafa mata cup din a baki, aiko Tass maryam ta shanye ruwan. "Akaro miki ruwan?" Aunty ta tambayeta. Girgiza kai tayi alamar a'a tana sauke ajiyar zuciya, taimaka mata aunty tayi ta koma ta kwanta saboda jikinta sam babu kwari. "ya Jikinnaki, yanzu inane kuma yake miki ciwo?" Aunty ta jero mata wannan tambayar. kanta dake mugun sara mata ta nunawa aunty da hannunta idanunta a lumshe, se kuma hannunta inda ta yanke da madubi. "sannu Allah yakara sauki, hannunnaki kuma bari nakira doctor yazo yaduba mikishi" gyada mata kai kawai ta iyayi. tanaso tatambayeta yajikin mustapha amma maganama wahala take mata. "Maryama, sannu kinji,Allah yakara sauki" muryar daddy ta doki kunnena, bude idona nayi da sauri najuya inda najiyo sautin muryartasa. Daga masa kai nayi shima alamun da sauki. fita daddy yayi ya zauna a falo, ya rafka tagumi yanata tunane_tunane. Aunty ce ta mike ta hadowa maryam tea mekauri, taimaka mata tayi,cikin ikon Allah kuma tasha sosai. Se'alokacin naji wata nutsuwa tafara lullubeni har gumi yana tsatstsafomun ajikina. aunty ce tataimakamun takaini toilet domin nayi wanka ko zankara jin dadin jikina. Jikina Sam babu kwari haka nadaure na watsa ruwan. ga zuciyata dakemun wani irin bugu tamkar wani abu yana shirin faruwa dani. Falo aunty tadawo gurin daddy bayan maryam tashiga wanka, zama tayi agefensa tana kallonsa yanda ya rafka uban tagumi da hannu bibbiyu. danne duk wata damuwarta tayi domin ta taushi dan'uwanta danta fuskanci yana cikin tsananin damuwa. Cikin tausasa lafazi tafara masa magana. "Yaya dan Allah kayi hakuri akan abunda yafaru mudauki komai amatsayin kaddara wadda tariga fata. kuma rubutacciya haka Allah ya kadarto mana babu yanda zamuyi." wani gwauron numfashi daddy yasauke sannan yadubi aunty Cikin raunin murya yace, "saudat zuciyata cike take da tsananin bakin cikin abunda atika tayi,yanzu ace a gidana akeyin wannan danyen aikin, amma bansaniba yanzu idan duniya taji kotasan halin da'ake ciki wanne kallo za'amun, dayawan mutanema cewa zasuyi ninakeyi dan wata bukatar kaina" "kayi hakuri dai yaya, mugodewa Allah dayasa maganar bata yaduba ita kuma aunty atika kabarta ita da Allah,shikadai yasan meze mata" "hmmm, nacanza tunani saudart zankai karar atika da sadiq ga hukuma da kaina, domin a yanke musu hukunci daidai da abunda suka aikata" da sauri aunty tadago ta dubi daddy cikin mamakinsa, shida dazu_dazu yagama cewa yabarsu da halinsu amma kuma yanzu yacanza ra'ayi. kara gyara zama aunty tayi ta fuskanceshi sosai, sannan tace. "Haba yaya yakuma zakace haka, hannunka baya taba rubewa kayanke kayar, sadiq naga nadama tsantsa a idonsa, nasan yanzu yanacan yarasa ina zesaka kansa. Kuma yanzu idan kayi kararsu katonawa mustapha asirinsa dake rufe, duniya zatasan kowaye shi. kaga mukuma bazamuso hakaba, dan Allah yaya kamar yadda kace da farko kabarsu da halinsu yanzunma kajanye batun mikasu ga hukumar." "Saudat abunda atika tayifa bakadanbane ta cutar da bayin Allah dabasujiba basu ganiba, kina ganin idan muka barsu bamuso kanmu dayaba" "yaya babu batun sankai, ayanzu koda kayi karar anti atika tanada kudin dazata iya kwatar kanta, tunda kasan shari'ar yanzu bata Allah baceba, karar anti atika da sadiq daidai yake da muntonawa kanmu asiri" shiru daddy yayi bekara cewa komaiba. Ganin haka aunty tashiga rokonsa gami da bashi baki, dan ita bazataso ayi karar su mommy, batason kowa yasan mustapha badan daddy bane. badon daddy yasoba yahakura yakuma tabbatarwa da aunty ta shirya idan anyi sallar la'asar zasu tafi Niger domin nemo dangin mustapha, kuma da maryam daza'atafi. Aunty taso fahimtar dashi hakan bamafita bane, domin idanma sunje Niger din gurinwa zasu nufa ta ina zasu fara Neman wani dangin mustapha, kuma kodama sunsan inda zasu nufa yau yayi wuri su tafin, tunda mustaphan ba ishashshiyar lafiya gareshiba. Amma daddy yace mata hakan kawai shine mafita dan mustapha yatada hankalinsa sosai. Badon tasoba ta amince. batayi kuma tunanin komaiba da daddy yace, zasu tafine tare da maryam, danko befadaba bazatabar maryam dinba dankar mommy ta cutar da ita. Daddy bayan sungama magana da aunty direct masallacin dake manne ajikin gidansa yanufa domin ya kaddamar da abunda ya kudurcewa ransa tun a lokacin dayayi arba da maryam, yadade da kudirin aransa amma yau yayi alkawarin kafin subar kasarnan seya idda nufinsa. Kamar yadda yazata kuwa liman na zaune a masallacin shida wasu tsirarun mutane. Gaisawa sukayi da kowa cikin mutunci da sakin fuska tamkar babu abunda yake damunsa,duk da karfin haline kawai yakeyi. Gefe suka koma shida malam liman yamasa bayanin bukatarsa, yakuma tabbatarmasa da a yanzu yakeson ayi. Sauran mutanen dake masallacin malam liman yahado kansu atake agurin aka daura auren da daddy yabukata akan sadaki naira dubu hamsin wanda daddynne yabada. Malam liman ne yayi waliccin amarya daddy kuma na ango.(To Allah yasanya albarka a auran, yabada zaman lafiya me dorewa, tunda daddy bebari naji daurin auren konasu wayeba😜).... Ina fitowa daga toilet natarar aunty ta kwasomun kayan dazansa daga dakina. Amma ita bata dakin. murmushi nayi nadauki kayan nafara sawa, zuciyata cike da kaunar aunty, yanda take nunamun kulawa ko yar cikinta sehaka. Tunanin yaya sadiq ne yafadomun acikin raina, haka kawai naji gabana yayanke yafadi dana tunasan. nasan yanzu yanata nemana a waya besameniba, amma idan aunty tashigo zance ta aramun wayarta na kirasa. kayan kawai nasaka nafito falo domin naje nagaishe da mommy, aunty nagani tafito daga kitchen hannunta dauke da plate da cokali. "Sannu aunty" "yawwa maryam, yajikinnaki?" "Dasauki aunty" "Allah yakara sauki, kizo kici indomie dinnan kenadafawa sekisha magani, zamuyi wata tafiyane yanzu, nakira doctorn ma yacemun gashinan zuwa" da mamaki nake kallon aunty cikin sanyin murya nace mata. "Aunty tafiya kuma, ina zamu?" "nima dai bansaniba maryam haka dai yaya yacemun, sekiyi sauri kici abincin munayin sallah zamu tafi" cewar aunty tana ajiye mun plate din akasa. "To aunty bari naje nagaida mommy, yau antofawa yaya addu'ar kuwa?" kallona aunty tayi sannan tace, "kici abincinki kawai anti atika batanan, shikuma mustapha jikinsa yayi sauki sosai, alhamdulillah" ajiyar zuciya nasauke aboye tajin dadin aunty tace, jikin heartbeat dina yayi sauki. Zama nayi akan carpet na bude plate din da aunty takawomun nafara cusa indomien badon inajin dadintaba, saboda yanda zuciyata take bugawa inajin tamkar wani bakon al'amari nashirin faruwa dani ayau...........✍️ *kuyi hakuri da typing error, yauma babu editing* *By* *zeey kumurya* *ABUNDA KASHUKA....* _*(shizaka girba)*_ *4️⃣0️⃣* *Bismillahirrahmanirrahim* ..........Abangaren su faruq kuwa, gabadaya part dinsu suka nufa zuciyoyinsu babu dadi, kowa dakinsa yashige ya kullo kofa domin samun kadaita. sadiq da nadama gami da kunya suka masa katutu yakasa zaune yakasa tsaye zarya kawai yakeyi a dakinsa abubuwa biyu ne suke damunsa a wannan lokacin. Na farko wata zazzafar kaunar maryam ce ta mamaye masa zuciya. na biyu kuma boka tsidau yatabbatar masa da cewa matukar aiki ya lalace to ciwon da mustapha yakeyi ze dawo kansa ne. a yau kam yayi nadamar kasancewar mommy mahaifiyarsa, ta cusa masa abunda baze taba amfanesaba arayuwarsa. Fiye da shekaru goma ta cusa masa kiyayyar mustapha me tsanani acikin ransa, ta nuna masa mustapha babban makiyinsune, alhalin bahaka abun yakeba. wani zazzafan huci ya fuzgar, hannunsa yakai ya ware hiramun dake kansa gami da cire safar hannunsa, dinkin da'aka masa yabayyana na ciwon da maryam taji masa. fadawa kan gado yayi sharab, zuciyarsa na masa kuna jiyakeyi tamkar ya kashe kansa dan bakin ciki, ga wata kewar maryam data cika masa zuciya. Da farko da yaudara yafara son maryam, amma zuwa yanzu son yarikide masa yakoma nagaske wanda yake barazanar tarwatsa masa zuciyarsa. kansa yafara bubbugawa akan gadon a fili yafara magana. "Mommy, why,..! why, dakika zabarmun wannan rayuwar, meyasa nabiye miki nakai kaina ga halaka,yanzu da wanne ido zankalli maryam wadda tabani dukkan yarda da amanarta, ta dauki a amatsayin bango na rayuwarta, koyaya zataji idan taji labarin ninake kokarin rabata da mutuncinta. Tabbas ubangiji baze barniba akan cutar da bayinsa wanda basujiba basu ganiba danayi. kansa yarike dayake kokarin tarwatsewa saboda damuwa, wannan ranar besan dame zekirataba arayuwarsa.......... naci indomie fiye da rabi, sannna na rufe plate din saboda aman dana faraji yana tasomun, ahankali na mike nanufi dakin aunty domin nace ta bani aron wayarta nakira yaya sadiq dina. Da sallama nashiga dakin, aunty dake hada kaya acikin wata yar karamar jaka ta amsamun sallamar batare data dago ta kalleniba. zama nayi akasan gado cikin sanyin murya nace, "aunty dan Allah kibani aron wayarki zankira yaya sadiq nasan yanzu yanata kirana besameniba" dagowa aunty tayi tazubawa maryam ido, cikin tausayinta domin ta dade da fuskantar soyayya sukeyi, gashi harta kasa hakuri tatambayeta Aron waya takirashi, batasan shine me kokarin bata mata rayuwaba, koda daddy befadaba dama aunty ta dukurcewa ranta bazata bar takara kwana acikin wannan gidan da'ake burin cutar da itaba. kasa nayi dakaina ganin aunty tana kallona, wata kunyartace ta lullubenu wata zuciyar tawace tacemun kodai aunty tasan muna soyayya da yaya sadiq dinne. "Maryam, nakirashi ai tundazu amma wayartasa bata shiga, akashe ake cewa" aunty tafadawa maryam haka, domin batason tasan komai tunyanzu tafison sekomai ya lafa tukunna. "Shikenan aunty" nabata amsa cikin sanyin jiki. domin bugun zuciyatane yakaro akannada... Mustapha yadau tsahon mintuna 20 a toilet kafin yaja kafa yafito saboda matsanancin jirin dake kwasarsa amma bawai dan ruwan ya isheshiba. kan gadonsa yafada Cikin mawuyacin hali, jikinsa na wata irin kyarma, dakyar ya iya jan bargo ya lullube jikinsa saboda wani sanyi sayaji yana shigar jikinsa. tunanin abubunwa dasuka faru abayane suke dawo masa kwanyarsa, tabbas biri yayi kama da mutum, mommy tasha siyo masa kayan maye domin yadingasha, wai rayuwarce seda haka. Agaban mommy suhailat take hugged dinsa kota dane kan cinyarsa amma mommy bazata kwabetaba sema ta nuna jindadinta. Mommy bata bashi tarbiyyya tagariba kokadan tayi masa abubuwa dadama domin ya lalace amatsayin soyayyar datake masane haka, Allah ne kawai yakareshi dakuma tsaiwar dakan da daddy yayi wajen ganin rayuwarsa ta inganta. wasu hawayene masu matukar dumi suka digo masa, wanda dakyar yasamu suka zubo. har yanzu yana mamakin wai mominsa datafi kaunarsa fiye da komai da kowa a duniya ita ce take furta Kalmar tsana agaresa saboda abunda duniya. har yanzu yanajin guntun kaunar mommy acikin zuciyarsa, kobabu komai ta raineshi kuma ita yataso yake kallo amatsayin uwa. zurfaffen tunani yashiga sosai akan rayuwarsa wanda hakan yakara haddasamasa matsanancin ciwon kai dana zuciya, tun yana gane meyakeyi haryafice daga hayyacinsa,komai yadauke masa dif....... Daddy akokarinsa nason tafiyarsu takance da wuri, yadauki mota yafita dakansa domin yimusu cuku_cukun tafiyar, ga wayarsa dake Cikin aljihunsa sekiransa akeyi ga tarin damuwar dake addabar ransa. tukin kawai yakeyi amma hankalinsa baya jikinsa yanacan duniyar tunane_tunane. be'ankaraba sekawai jiyayi ya gwabzi wata mota adaidai dangi. Cikin tsananin firgici daddy yafara ambaton "subhanallah" a fili, dasauri yayi parking motar tasa yafito ko rufewa kofar beyiba. mutane harsun fara taruwa saboda motar ta jirkicene anata kokarin dago da ita. shima daddy karasawa yayi akafara kiciniyar daga motor dashi. direban dake tuka motar yafito babu wani rauni ajikinsa sedai juya dake dibansa sakamakon jirkicewar da motar tayi, dan motar ta barin dama ta jirkita. Anyi nasarar juyar da motar har'aka fito da matar da direban yake tukawa, sedai matar babu alamar numfashi atattare da ita. tashin hankali wanda ba'asamasa rana. "Ana wata ga wata" daddy yafurta hakan azuciyarsa. "Ya Allah kasa ba kisan kai nayiba" yakara furta haka lokacin da'aka dakko matar a hannu rai ahannun Allah,babu inda yake motsi ajikinta. hankalin direban idan yayi dubu yatashi. Se kiran "innalillahi'wa'inna'ilahirraji'un" yakeyi kamar yadda daukacin mutanen wajen keyi. Cikin sauri daddy yayi gaba zuwa wajen motarsa aka Sanya matar abayan motar. Kasancewar daddy ba boyayyen mutum bane, mutane se fadin. "Yallabai Allah yakiyaye gaba sukeyi" driver seat daddy yashiga direban motar kuma yashiga front seat daddy yaja motar yanufi asibitin aminu kano. wayarsa yazaro yakira bakanikensa yasanarmasa yazo ya dauki motar dayabugedin yatafi da ita, tare da kiran asibitin yasanar musu da zuwansu. Cikin mintuna kalilan suka karasa asibitin abakin emergency yayi parking motar yafito dasauri yabude bayan, ma'akaitan asibin suka kama matad suka sanyata akan abun tura marasa lafiya suka nufi ciki da ita dasaurinsu, suma su daddy rufa musu baya sukayi......... Doctor yazo yaduba hannun maryam yasa mata maganin,yakuma bata wasu dazata dinga sha. har Aunty tagama hada yan abubuwan datasan zasu bukata atafiyarsu sukayi sallar azhar amma daddy shiru_shiru bedawoba bekuma kirataba. part din mustapha takoma domin tagano halin dayake ciki, tana zuwa tatarar dashi cikin mummunan yanayi. cikin kidima mommy takira daddy danta sanar masa. "Hello, yaya ina katsayane?" numfashi daddy yasauke yace, "saudart ina hanyata tatafiya na bugi wata motane, yanzu haka muna asibiti" "innalillahi'wa'inna'ilaihirraji'un, subhanallah Allah yasadai babu wanda yayi mummunan rauni" "to, su biyune dai acikin motar, da driver da wata mata, direban yar buguwa yayi, sunma samasa ruwa, matar cedai kwance haryanzu likitoci nakanta" "ya Allah, Allah katakaitamana" "ameen" "yanzu kuna wanne asibitinne" "Aminu kano" "OK, bari muzo nida su faruq, Allah yakiyaye gaba" bayan sunyi sallama mommy takira faruq tace yadakko mota yazo bakin part din mustapha. taboyewa daddy halin da mustapha yake cikine saboda kar abun yamasa yawa,wannan tashin hankali har ina, dama haka rayuwatake,watarana dole se Allah ya jarrabeka. koda faruq yazo yaga halin da mustapha yake ciki hankalinshi yatashi sosai shima, batare da bata lokaciba yakira su haidar suka kamashi sukasashi a mota suka nufi asibiti dashi. aunty ce, tafadawa asabe me aiki sunfita, idan maryam tatashi tasanar mata, dantunda tasha maganin da doctor yabata sekuma bacci yadauketa. Asibiti mafi kusa dasu suka kaishi wanda yakasance private ne, suna zuwa aka karbeshi likitoci suka rufa akansa,domin ceto rayuwarsa........ mommy cikin mintuna kalilan takarasa gidanta dake lamido, wanda babu kowa aciki se megadi. horn tahau dannawa ba kakkautawa megadi dake kwance adakinsa yana bacci yaji horn din tamkar a mafarki. ahankali yabude idonsa yajidai azahiri yakejin horn din, dasauri yatashi yasuri rigarsa yasaka yafito danyaga waye a wannan lokacin yakatse masa baccinsa. karamar kofar gidan yabude ya leka, ganin motar mommy ce yasashi komawa da sauri ya bude mata get din, zuciyarsa cike da mamakin ganinnata domin tunda yazo gadi gidan bata taba zuwa a irin wannan lokacin ba, tafi zuwa da yamma koda daddare. A fili ya furta "banda abuna,ita da gidanta mene nawa aciki." gudu_gudu, sauri_sauri, yakarasa inda mommy take bayan yarufe gida. "Hajiya sannu da zuwa dafatan kin iso lafiya" yafadi haka yana kokarin karbar jakar hannunta kamar yadda yasaba a kodayaushe idan tazo yakai mata har cikin falo. Amma yau ga mamakinsa seyaga tadaga masa hannu bata bashi jakarba, bakuma ta amsa masa sannun dayake mataba tayi wucewarta ciki. kallonta kawai yatsaya yanayi harta bacewa ganinsa, zuciyarsa cike da mamakin ta, dan duk da bata da sakin fuska amma yau yaga abun yafi na kullum, yana tunanindai akwai matsala tunda gashima ita kadai tazo, sabanin da datake zuwa da driver wani lokacin ma, harda danta. komawa dakinsa yayi domin cigaba da baccinsa. Momy tana shiga falo ta ajiye jakarta gami da mayafinta akan kujera, zuciyarta sam babu dadi, zarya tafarayi afalon cike da tsananin damuwa, se'alokacin wani gumi yafara keto mata. tanunawa su daddy warkewar mustapha bedaga mata hankalibane dankarsuga gazawarta da wuri. Amma bakaramin dimuwa gami da tashin hankali tashigaba, musamman datasan boka yace, idan aiki ya lalace komai zekoma kan sadiq ne. Tarasa meyasa tun mustapha yana karami kome tamasa na sharri sedai taganshi akan yayanta, taso mustapha ya lalace yazama mebin mata kuma takadirin dan shaye_shaye amma kuma sebezamaba, seyayantane sukeyi. lokacin da mustapha suka fara soyayya da suhailat agabanta suhailat zata dane kan cinyarsa kotayi huging dinsa amma bata hanata, duk dan mustaphan yalalace amma kuma belalace dinba. "tabbas! yazama dole natafi Neman mafita ayau ba gobeba, yanzu_yanzu ma kuwa!" mommy ta fadi haka a fili,tana cizon yatsa. (Hmmm, momy kenan, aishi sharri dan aikene.) wayarta dake cikin jaka ta dakko ta lalubo number wata kawarta takirata. tayi sa'a wayar tashiga amma harta katse bata dagaba,kara kira tayi nanma bata dagaba. Tsaki mommy taja afili ta furta. "ko'ina binta tashiga tabar wayartata oho,Inata kiranta amma taki dagawa" kara kiranta tayi akaro na uku, harta kusa katsewa sekuma ta daga. "Hello kawata, uwargida agidan alh mai nas".......... "kinga dalla ni badogon zance nanemaba, ina kika shiga inata kiranki baki dagaba" mommy ta katseta da fadin haka. "ina falone ina hutawa wayar kuma na daki" "ohk, idan babu damuwa inason ganinki yanzu domin akwai wata matsala babba" "matsala kuma atika, tame?" binta tatambayeta cikin kidima. "Kedai kawai idan da hali kizo, maganar bazata yiyu a wayaba, amma bana gida zanturo miki address din inda nake sekizo kisameni." "Tom, shikenan ba matsala ganinan zuwa yanzunnan" "yawwa binta sekin karaso" mommy nagama fadar haka ta katse wayar, address din inda take ta turawa binta kawarta. jefar da wayar tayi akan kujera bayan text din yaje, zama tayi itama akan kujerar ta rafka uban tagumi da hannu biyu tana tunane_tunane. Bayan 40 minutes binta ta karaso gidan da mommy take, bayan tafito daga motarta sungaisa da megadi take tambayarsa ina mommy, dantaga gidan part 2 ne. jagora megadi yamata har bakin part din da mommy take, godiya ta masa ta karasa bakin falon tayi knocking. Ajiyar zuciya mommy ta sauke jin ana knocking, dantasan bintace ta karaso. "A shigo" tafada atakaice domin kofar abude take. turowa binta tayi tashigo taname bin falon da kallo, kafin tace, "atika wannan gidanfa,gidan waye?" mikewa tsaye mommy tayi tace, "bashine abun damuwaba binta ahalin yanzu. Ina cikin matsala kikaraso muyi magana ina bukatar shawararki." binta batayi musuba ta karasa cikin falon tazauna akan kujera ta fuskanci mommy tace, "Atika inajinki wacce irin matsalace gareki, kinsa hankalina gabadaya ya tashi" shiru mommy tayi nakusan mintuna uku kafin tafara magana kamar haka."binta inason ganin bayan mustaphanah, da sulaiman mijina, inason ayau ba gobebe nashafe labarinsu a doron duniya, ke atakaicedai inason nakashesune.!" cikin tsananin mamaki binta take duban mommy baki bude, kafin tayi karfin halin fadin, "atika! Kinsan mekike fada kuwa, kokinfara haukane, danki da mijinki kikeson ganin bayansu,kikeson kashesu kuma akanme to?" "Akan kudi" mommy tabata amsa agadarance. "Kudi kuma atika, kudinme to?" gyara zama mommy tayi tace, "labarine me tsaho amma zantakaita miki shi nabaki" ........... Labari mommy tabawa binta tundaga ranar dasuka samu mustapha har kawo yau. baki hangame binta take kallon mommy, tama kasa magana saboda dinbun mamaki, gani takeyi tamkar mommy kirkirar labarin tayi kawai tabata, yaron datake matukar sonsa fiye da komai a duniya amma ita take fadin ta masa mugayen abubuwa irinka,gaskiya ta jinjinawa hali irinna mommy, domin duk shedanancinta bazata iya abunda mommy tayiba. Jikinta a sanyaye tace, "Atika!, dagaske kike wannan labarinnaki,nifa kwanyata ta kasa dauka,amma tayaya kika gudanar da duk wadannan ayyuka batare da sanin kowaba tsahon shekaru?" taune lips mommy tayi tace, "kinga alamar wasa akan fuskata dazan miki karya. dagaske nake mustapha badana bane nacikina, kuma ina gudanar da aikinane cikin sirri a wannan gidan nida sadiq, abunda yasa babu wanda ya'ankare tsawon lokacin dana dauka inayi, saboda sadiq nake aikawa gurin boka tsidau, ninayi shekaru banje gurinsaba sedai idan sadiq yaje ya hadamu a waya. ko zuwa gidannan damukeyi babu wanda yasani, danse yamma lis nake zuwa kuma ta get din baya muke fita. Abundai da kawai yarana da megidana suka sani inada wannan gidan kuma ina zuwa lokaci zuwa lokaci ina dubashi." wani dogon numfashi binta taja sannan tace, "yanzu ke Atika duk daular dakike ciki, gamida kudaden da kike juyawa wanda har karshen rayuwarki zasu isheki, amma shine kika aikata haka, gashi yanzu asirinki yatonu, batare da kincinma kudirinkiba. mene amfanin hakan, gaskiya Atika duk tsagerancina gamida son duniyata da shu'umancina amma nasara miki gami da jinjina miki" wani murmushi mommy tayi tace. "Lallai binta haryanzu bakigama sanin Atikaba, tokisani nawuce duk yanda kike tunani indai akan cikar burinane babu abunda bazanyiba arayuwarnan. Dakike maganar kuma duk dukiyar danake ciki, amma senayi hankorin wata. Namiki uzuri, bakisan tarin dukiyar da golds din mustapha sukayibane shiyasa zakice haka"...... "Amm"....."dakata binta" mommy ta katse binta ta hanyar daga mata hannu kamar yadda itama ta katseta. "Bana kirakibane muyita ja'inja kokuma jan maganaba, nakirakine kawai kibani shawara domin kaina gabadaya ya kulle, narasa mafita. gashi kuma boka yamana gargadin dazarar aiki ya lalace karmu koma gurinsa" Ajiyar zuciya binta tasauke tace, "yanzu yakikeso ayi?" mikewa mommy tayi tsaye tadanyi taku sannan ta tsaya tace, "sonake mustapha, menasara da wannan tsinanniyar yarinyar maryam su mutu ayau. Shiru binta tayi kafin yadago kai ta dubi mommy dake kallonta tace. "Kidawo kizauna sena fada miki yanda za'ayi" babu musu mommy tadawo tazauna suka fuskanci juna binta tafara bata shawara..... suhailat bayan taci kukanta ta koshi bacci yadauketa adakin mommy batare data shirya masaba. se wajen 2 tafarka. tashi tayi dasauri tafito falo,tana mamakin baccin datayi. tsit taji falon babu alamar mutum acikin part din. Dakin aunty ta nufa tana kwala mata kira, amma taji shiru. handle din dakin ta murda tajishi a rufe, tayi knocking ma taji shiru. maryam dake ciki tana bacci batamasan metakeba. duddubawata tayi har kitchen batagantaba, har dakin maryam ta leka. "To ina aunty tatafi, ko itama tatafi tabartane?" tatambayi kanta. kasa ta sauko inda tatarar da daya daga cikin masu aikin gidan a falo. Tambayarta tayi ina aunty, tace mata sunfita ita da su faruq. mamakine yakama suhailat akan ina kuma suka tafi suka barta ita daya agida.sama takoma dasauri ta shiga dakinta tadakko wayarta, number mommy tayi dialing. mommy suna zaune ita da binta sunata sakawa da kwancewa har lokacin kiran suhailat yashigo wayarta. dakkowa tayi taduba ganin sunan Sweet daughter nayawo akan screen din wayar yasata dagawa dasauri. cikin kuka suhailat tace, "mommy, kintafi kinbarni suma gashi suma sunfita dukansu seni kadai agidan" mikewa tsaye mommy tayi tace, "what? daughter banganeba suwaye suka tafi?" "Daddy, da aunty da yaya, dasu yafaruq da wannan yarinyar" muryar mommy narawa tace, "ina suka tafi?" "Bansaniba mom, danbasu fadaminba, nima asabe ce takefadamun" yawun bakin mommy ne ya kafe kaf, murnarta ta koma ciki, dafe kanta tayi, dakyar ta iya kokarin cewa. "Kihada kayanki yanzu zansa adakkoki akawoki inda nake" "to mommy" jefar da wayar mommy tayi, batare data katse kiranba, kotaba suhailat amsaba. "Lafiya Atika mekefaruwa kuma?" binta tatambayi mommy cikin mamakin ganin yanda yanayinta yasauya lokaci daya, harta fara zufa. wani numfashi mommy taja mehade da huci tace, "wai su sulaimanne sukayi tafiya yanzu basa gidan, se suhailat kadai,kenan hakan nanufin zasubar garinne kokuma yaya?" "tafiya kuma, zuwa ina?" binta ta tambayi mommy. "Oho, inazansani inanan" mommy tafadi haka akufule tana share zufar data tsatstsafo mata a goshinta. shiru binta tayi ganin mommy a kidime take. ita kuwa mommy zarya tahauyi a falon tsahon wasu mintuna, kafin ta dauki wayarta dasauri. number sadiq ta lalubo takira, tayi sa'a kuwa tashiga sedai bedagaba harta katse. tamai missed call yakai 5,amma yakidagawa. dole ta hakura takira driver dinta, akan yadakko suhailat yakawota gidan da take.........✍️ *BY* *zeey kumurya* *ABUNDA KASHUKA* _*(shizaka girba)*_ *4️⃣1️⃣* *Bismillahirrahmanirrahim* .........Daddy ne zaune a office din wani doctor yana masa bayanin abunda kedamun matar dayaka buge. "Yallabai ka kwantar da hankalinka ba wata matsala bace babba, buguwa kawai tayi a kanta, kuma alhamdulillah munshawo kan matsalar,fatanmu kawai Allah yasa ta farka cikin hayyacinta. sekuma dogon suma datayi. yanzu zaka iya shiga kaganta, da yardar Allah zata farka zuwa nanda awanni biyu munmata allaurar baccine" wata doguwar ajiyar zuciya daddy yasauke bayan doctor yagama masa bayani. se'alokacin hankalinsa yafara kwanciya yawu ya hadiya dakyar yace. "Shikenan doctor nagode sosai" "babu komai, yallabai. fatanmu kawai Allah yabata lafiya yakuma kiyaye gaba" "ameen,ameen" daddy ya amsa. Paper doctor yamikawa daddy ta magungunan daza'asiyane. sallama daddy yamasa yafita bayan ya karbi paper. dakin da'aka kwantar da direban nan daddy yanufa, yayi sa'a kuwa ya farka har nurses sun cire masa karin ruwan da'aka masa. da sallama daddy yashiga dakin, amsa masa direban yayi yana kokarin mikewa zaune. taimaka masa daddy yayi yazauna yana jera masa sannu. shidai direban mamakin daddy kawai yakeyi yanda yake nuna damuwa da kulawa agaresu tamkar ba shahararren me kudiba,da wanine sedai yabiya kudi yace amsusu dukkan abunda yadace tunda yana da halin yin hakan, shikuma yakama gabansa. Kuma ga dukkan alamu shima yana saurine ze gudanar da wani uzurinnasa. daga ganinsa rayuwarsa bashida damuwa,ko girman kai irinna wasu masu kudin. lallai samun kamar alh, mai nasara se"..... "Sannu, yajikinnaka" daddy yakatse masa tunaninsa da tambayarsa. ajiyar zuciya yasauke yace "dasauki Alhaji" zama daddy yayi akan kujerar dake fuskantarsa yace, "Allah yakaro sauki, yasa kaffarane" "Ameen Alhaji" "yawwa, zuwa yanzu yakamata ace kakira gida kasanar dasu halin da'ake ciki" "nayi yunkurin yin hakan tun dazu, amma Inata kiran number maigidanta ita hajiyar bata shigaba" "Allah, sarki, tokuma babu wani dazaka kira seshi, kota yayantafa" dan jimmm, direban yayi kafin yace. "Ai bata da yaya ranka yadade, sedai yayan yayanta dasuke zaune gida daya, sukuma gaskiya bani da number dinsu" jinjina kai daddy yayi yace. "To ita ina wayarta semunemi number mukira, kaga ai baze yiyu ace haryanzu wani nata besaniba" "hakane, Alhaji, wayartata tana cikin Jakarta, kuma ina tunanin mun barota a cikin motar mu" daddy bekara cewa komaiba se wayarsa daya dakko daga aljihun gaban rigarsa yakira bakaniken daya tura yadauki motartasu, yace masa yaduba motar idan yaga jaka aciki yadakkota yabada akawo masa asibitin aminu kano yanzu. Amsa masa bakaniken yayi cikin girmamawa sannan yaduba, yana dubawa kuwa yaga jakar, a take yabada aka kawowa daddy. Number da matar tayi waya da ita last, ita daddy yakira. wata kawartace dazatayi bikin yarta, bikinma matar tataho, kuma wannan shine karonta na farko zuwa kano daga garin *jos*. kawartata ta rude sosai, dama tanata kiran wayarta taji kota karaso bata shiga, cikin hanzari suka kimtsa ita da wasu yayanta suka nufo asibitin. ansamu number maigidannata ta shiga shima ansanar masa. masallaci daddy yanufa domin yin sallah, bayan yagama kiraye_kirayen wayar zuciyarsa cike da mamakin abunda yatsaida su aunty karasowa asibitin haryanzu.......... Abangaren su aunty ma, ansamu anshawo kan ciwon mustapha, dama damuwace kawai ta masa yawa, wanda hakan yasa jininsa yahau sosai. dukansu sunsashi agaba sunyi tagumi jigum_jigum, su haidar harda kuka dasukaji daddy sunyi accident. wannan wacce irin jarrabawace daga wannan se wannan, to Allah yatsayar haka,shine addu'ar dasukayi kawai. Numfashi aunty ta sauke cikin karayar zuci, na wannan bakon al'amari daya samesu. wayartace tayi kara. Ahankali tasa hannu ta daukkota, Abban aliyane ke kiranta dagawa tayi dayin sallama cikin sanyin murya. "Wa'alaikumussalam, hajiya sauda yajikin mustaphan?" (Dayake takirasa tafada masa) "dasauki Abbansu, gashinanma yanata bacci" cikin tausayawa abbansu aliya yace, "Allah yakara sauki, Allah yayankewa yaronnan wannan wahala haka" "Ameen, abbansu, kuntahone?" "A'a, yanzudai zamu taho, dan auta bata jima da dawowa daga islamiyyaba" "shikenan, Abbansu sekun karaso" sukayi sallama aunty ta kashe wayar. number daddy takira, har 3 missed call tamasa bedagaba, time din yana sallah ne, seda ya idar yabiyo bayan kiran. bayan tadaga yace, "hello saudart" "na'am, yaya yamasu jikin" "dasauki Alhamdulillah, danshi direbanma ya warware matarcedai haryanzu tana kwance tana bacci" "Allah yakara sauki yakiyaye gaba" "Ameen, sauda. Najiku shiru kuma baku zoba haryanzu, gashi su ashema ba'a garinnan sukeba, daga jos sukataho biki, babu wanda yazo haryanzu danbanma jima dasanar musuba, sedai gidan dasukazo bikin sunce gasunan zuwa." shiru aunty tayi gabanta nadan faduwa, tana tsoron ta fada masa mustapha babu lafiya yakara shiga wani tashin hankalin. "Hello, sauda naji kinyi shiru, ina mustapha fa?" wata boyayyiyar ajiyar zuciya aunty ta sauke tace, "yaya mustapha, gashi kwance babu lafiya muna asibitima yanzu haka, shine dalilinma dayasa kajimu shiru" "innalillahi, meke damunsa kuma?" "damuwace kawai yaya, hartasa jininsa yahau, naki fada makane saboda kar hankalinka yatashi, ga wancan ga wannan" "ya salaammm, ya subhanallah" daddya yafadi haka cikin tsananin damuwa yana fesar da numfashi. "hakuri zamuyi yaya, haka Allah yakaddaro mana babu yanda zamuyi, amma insha Allahu, komai zedaidaita, banason katada hankalinka yaya, kacigaba da juriya da addu'a, da yardar Allah komai zezama tarihi kamar ba'ayiba" jinjina kai daddy yayi yace, "hakane sauda, yanzu kuna wanne asibitin?" Asibitin aunty tafada masa, yace gashinan zuwa. Daddy bebar asibitinba seda kawar matarnan tazo, yakuma siyo dukkan magungun da'aka bukata gami da duk wani dayasan zasu bukata, se wajen karfe biyar yabar asibitin.... Direban mommy yakai mata suhailat kamar yadda ta bukata, suhailat tana shiga falon gidan taga mommy zaune ta rafka uban tagumi. dagudu tatafi tafada jikinta ta rungumeta tana kuka. "Cikin takaicin dake nukurkusar mommy tace, "Meyafaru daughter?" "Mom, meyasa kikayi haka, gashi yanzu duk suntafi sunbar gidan, mom dan Allah kiyi hakuri kijanye kudirinki kibawa daddy hakuri kidawo gida, mucigaba da rayuwarmu medadi kamar da." janye suhailat mommy tayi daga jikinta tana fadin. "Yaro man kaza!". daga haka bata kara cewa komaiba ta mike tanufi daya daga cikin dakunan dake falon. suhailat kuwa kuka tacigaba tayi, domin ita damuwarta daya a yanzu maganar auranta da mustapha batasan ina maganar ta kwanaba, tana matukar kaunarsa bazataso ta rasashiba. wayarta dake cikin jaka ta dakko saboda kiran da'ake tamata tuntana mota. kamal ne yake kirannata, cillar da wayar tayi akan kujera danbatashi takeba a yanzu. Binta kuwa dama tunda taga mommy ahaka, tamata sallama tayi tafiyarta. Abun duniyafa yataro yayiwa mommy yawa, takasa zaune takasa tsaye, ita burinta a yanzu kawai tasan ina su daddy suke, idan tasan haka to komai zezo mata da sauki aganinta........... Maryam, tadade tana bacci sosai dantayi fiye da awa uku, sebayan la'asar tatashi. Ahankali ta sakko daga kan gadon aunty ta nufi toilet, alwala ta dauro tadawo tatada sallah ganin har lokacin ta yana kokarin kurewa. bayan ta idar tazauna tana addu'a, Alhamdulillah taji saukin jikinta sosai, zugi da radadin da hannunta shima se kadan yanzu. tunani nashigayi akan abunda yafaru dani jiya, amma nakasa tunawa, gaba daya kaina ya kulle. kawar da tunanin hakan nayi nashiga wanda yazamarmun jiki wato tunanin mahaifina, koyana raye koya mace se Allah. A fili na furta "ya Allah kabayyamun mahaifina,kowani dan'uwansa kafin na mutu." nima naga dangina kamar kowa. hawayen daban shirya musubane naji sunabin kuncina, koyaushe zandena kukan rashin mahaifi da danginsa se Allah. mikewa nayi naninke dardumar danai sallah akai na ajiye. bakin kofa nanufa na bude nafita. Falon babu kowa bakamar yadda nazataba, kitchen nanufa nanma babu kowa, dakin mommy naje nayi knocking nanma shiru. gabanane naji yafadi kawai senaji ina tsoron zaman kadaicin, danna fuskanci babu kowa asaman. harna nufi dakina sekuma nafasa nasauka kasa. Ajiyar zuciya nasauke saboda ganin asabe me aiki. Cikin jindadi nace. "Aunty asabe, sannu da gida" "yawwa maryama kintashi" "eh" "yajikinnaki" "dasauki, inasu mommy ne da aunty naji gidan tsit" "wlh duk basanan maryam, dan hajiya babbama yaubansata a idonaba, se hajiya karamace tacemun idan kintashi nafada miki sun fita" jikina asanyaye nace, "to aunty asabe nagode, bari nakoma sama" ina tafe ina tunanin ina su aunty da mommy suka tafi, kodai jikin yaya mustapha ne yayi tsamari suka tafi gurin magani.?" bani dame bani amsa, hakan yasa nace. "Allah yasa alkhairi ne fitar tasu" kitchen na shiga nahada tea, nasha sannan nasha maganina da doctor yabani. zama nayi afalo cikin rashin sanin abunyi nahau karanta wasikar jaki........ Daddy ne zaune agaban gadon da mustapha yake kwance yakura masa ido cikin tausayawa, yaro mejuriya da dauriya akan dukkan abunda yasamesa amma wannan yakasa jure masa, se faman shan wahalar ciwo yakeyi. gaskiya atika ta cutar dashi, amma sakamakonta yanaga ubangiji shiyasan meze mata. Ahankali yabude lumsheshshun idanunsa yana bin saman dakin dayake da kallo. beyi yunkurin koda motsiba face silik din dakin daya kurawa ido kawai yana kallo, daddy yanacan duniyar tunani bemasan yatashiba. aunty dake zaune akan darduma tana lazimi kamar ance tadago takalleshi taga yafarka. mikewa tayi tana fadin, "yaya kaga yatashi" maganar aunty tadawo da daddy daga duniyar tunanin daya tafi. "Masha Allah" daddy yafadi haka cikin farin ciki yana kallon mustapha daya juyo yakura musu ido baya ko kiftawa. "Sannu, son yajikinnaka bari nakira doctor" cewar aunty tana kokarin juyawa tafita. da hannu yamata alama alamun karta fita tazo garesa. aunty bata musaba takarasa gareshi. kama hannunta yayi, cikin tsananin kaunarta dabayajin yanawa kowacce diya mace aduniya bayan mahaifiyarsa se ita. girgiza mata kai yahauyi kafin yayi karfin hali fara mata magana da muryarsa dabata fita sosai saboda ciwo da fadin. "Kada kiwahalar da kanki aunty wajen kiran doctor,domin nasan wannan ciwonnawa bana tashi bane inaji ajikina shine zezama ajalina" yakarashe zancen yana taune lips dinsa,saboda azaba da zugi da zuciyarsa kemasa. kwallace tatararwa aunty a idonta, kokarin maidata tayi tace. "haba Muhammad, kadena irin wannan zancen ba lokacin yinsu bane,insha Allahu zaka samu lafiya kawarke kakoma kamar da" kara damke hannun aunty yayi tare da runtse idanunsa, dago hannun aunty yayi yadora adaidai saitin zuciyarsa yafara magana a wahalce. "Aunty kinjifa yanda zuciyata take bugawa, inajin wani irin radadi acikinta dama dukkan jikina, aunty inaji tamkar ana zarar numfashi nane" bude idonsa yayi yadorashi akan na aunty wadda hawaye keta kwarara akan kuncinta yacigaba da magana. "Aunty nikam gwara mutuwa da wannan"....... hannu aunty tasa tatoshe masa bakinsa da sauri ta hau girgiza masa kai, Cikin kuka tafara magana. "Haba Muhammad, kaifa musulmine kazama me yarda da kaddara aduk yadda tazo maka. kada kazama me butulcewa Allah, duk abunda hakuri bebakaba rashinsama baze bakaba, kayi hakuri insha Allahu duk wannan abunda ze faruwa wataran seya zama tarihi, kaji tamkar ba'ayiba. Very soon zaka koma rayuwar farinciki da jindadi fiye da da." lumshe idonsa yayi yanajin ninkin kaunar aunty nakara ratsa zuciyarsa. ahankali yakai hannu yana share mata hawayen dake fuskarta batare daya bude idontasaba,dan har cikin ransa yakejin kukannata. murmushi aunty tayi Cikin tsananin kaunarsa ta rike hannunnasa ta sumbata. Ahankali tace, "bakaso kaganni ina kukane son?" daga mata kai yayi alamun eh. "To idan kanaso indena se kamun alkawarin zaka dena damuwa, zaka mikawa Allah dukkan lamuranka, kuma zaka dena tunane_tunane. domin shine yajanyo maka wannan ciwon dakakeyi." bude idonsa yayi yana murmushi yace, "nadena uwa tagari, kuma alkawari namiki insha Allah zandena tunanin komai, indai zakiji dadi" murmushi aunty tayi Cikin jindadi tace. "Nagode sosai, son,Allah yabaka lafiya." takarashe zancen dakai hannu tana shafa lallausar sumar kansa. Daddy dake tsaye yana kallonsu cike da bansha'awa da tausayawa, duk dauriyarsa amma seda kwalla tacika masa ido, amma bebarta tazuboba yamaidata. Yana mamakin yanda sauda take kaunar mustapha, fiye da yayan cikinta a yanda take nunawa. itama ayanxu tausayi take bashi, duk hankalinta ba'a kwanceba, tabaro yayanta da mijinta duk dan akan takula da mustapha, gaskiya ya jinjina kaunar datake masa. cike da kauna mustapha ke binta da kallo harta fice domin kiran doctor. sannu daddy yakarayiwa mustapha cike da tsananin kulawa. Aunty tare suka dawo da doctor ya duddubashi bayan yamasa sannu da addu'ar samun sauki. bayan fitar doctor bajimawa su faruq suka dawo dakin, alokacin mustapha yana zaune yajingina bayansa da filo, aunty tana bashi tea a baki. Sunyi matukar farincikin ganinsa ahaka, cike da dunbin farinciki suka karasa garesa suna jera masa sannu. dakai kawai yake amsa musu, yanamejin tarin kaunarsu acikin zuciyarsa. mustapha yatabbatarwa kansa duk duniya bashida kamar daddy da ahalinsa, yanajin koda yayi katarin ganin mahaifiyarsa ko wani nashi, baze iya barin su daddy ba, sedai sucigaba da kasancewa tare. yanda yaga kowa yana nuna jindadinsa da farincikinsa akan yanda sukaga yasamu lafiya, seyaji wani dadi da sanyi yana ratsa zuciyarsa, ahankali damuwar dake cunkushe acikin ruhinsa tafara gushewa, Cikin ransa amabaton sunan Allah kawai yakeyi. Aunty ce, ta umarci faruq idan yayi sallah yaje yadakko maryam, yakawota asibitin tasan yanzu tamacan tanata zullumi dama ita ba cikakkiyar lafiyaba, gashi tabarta ita kadai a gida. ina zaune a falo bayan na idar da sallar magariba naji ana kokarin bude kofar falon. Ajiyar zuciya nasauke domin duk a tunanina aunty ce tadawo, amma senaga ya faruq. da sallama yashigo falon, amsa masa nayi Cikin girmamawa tare da gaisheshi. bayabo babu fallasa ya amsamun, yakara da fadin. "Ki shirya, aunty tace nazo nadaukeki nakaiki gurinta" aida sauri namike domin zaman kadaicin ya isheni, dama yanzu nake tunanin zuwa part din su baaba talatu idan su aunty basu dawoba. dadduma kawai nakai daki nakulle dakin sannan nafito muka tafi, bayan na kulle kofar falon gabadaya. Bamuyi wata tafiya menisaba naga munkaraso wani guri, nibanma gane ina bane seda muka fara tafiya na fahimci asibitine. gabanane yayanke yafadi dannasan baze wuce yaya mustaphane, bashida lafiyaba. yana tafe ina binshi abaya, zuciyata na luguden bugu har muka karasa bakin kofar dakin, inda bugun zuciyata yakaro fiye dana da. jikina asanyaye nashiga dakin da sallama, cike da fargabar halin dazan riskeshi aciki na rashin lafiya. Ina dago kaina karaf muka hada ido dashi bayan nashiga dakin, dan gadon dayake kai yana fuskantar kofar ne. wata mummunar faduwar gabace ta ziyarceni bugun zuciyata ya karo, tamkar wadda akayiwa dole nakasa dauke idona daga cikin nasa, duk da tsananin kwarjinin dayamun, dauriya kawai nakeyi. yanda maryam taji faduwar gaba dasuka hada ido da mustapha haka shima yaji, haka kawai kuma yaji yakasa dauke idonsa daga kanta. kallon maryam Aunty tayi, ta kalli mustapha, da sauri tajuyo takara kallon maryam Cikin tsananin mamakin abunda tagani, kara maida kallonta tayi akan mustapha, abunda tagani dai shita kara gani babu canji, bakamar yadda tazataba ko idontane kemata gizo............✍️ _*sorry, zakuga typing error, inajin baccine🥱* *BY* *zeey kumurya* *4️⃣2️⃣* *Bismillahirrahmanirrahim* .........Sosai abunda aunty tagani ya matukar bata mamaki ba kadanba, kuma wani Ikon Allah bata taba luraba seyau kodan yau tataba ganinsu suna kallonne alokaci guda? kasa nayi da nawa idon saboda juriyar tawa ta kare, ahakanma nikadai nasan yanda nakejin zuciya na kallon kwayar idonsa danayi akaron farko arayuwata, jikina gabadaya jinsa nake a matukar sanyaye. "Maryam kikaraso mana" muryar aunty ta katsemun tunanin danake. Ajiyar zuciya nasauke cikin dauriya nakarasa ciki, daddy nafara gaisawar wanda yaketa murmushi a boye wanda shikadai yasan ma'anarsa. cikin fara'a da kulawa ya amsamun ya tambayeni Jikina nace masa da Sauki. jikin aunty na matsa nace, "aunty nah, ina wuni?" "Lafiya kalau, diyata ya Jikinnaki?" Aunty ta amsamun da murmushi dauke akan fuskarta. "Naji sauki aunty, dan yanzuma babu abunda nakeji na ciwo ajikina" "Masha Allah, haka mukeson ji, Allah yakaro sauki" "Ameen, yajikin yaya" "Alhamdulillah" aunty ta fada tana maida dubanta garesa. ya lumshe idonsa kawai yanajinsu. shiru dakin yy kowa da abunda yake tunani acikin zuciyarsa,inaso namasa ya jiki, amma kuma nakasa kwarjininsa dayakemun duk ya cikani. nayi tunanin ina zuwa zanga mommy da suhalat amma kuma sebangansuba, kamar na tambayi aunty sekuma na kyale tunda ba hurumina bane. Daddy ne yakatse shirunnamu da fadin, "saudart, bari naleka candin nakara dubasu." aunty tagane asibitin da mara lafiyarsa take yake nufi. "Tom, yaya kagaishesu kafin muzo" "zasuji insha Allah, yanzuma ai dasu Aliyu zamu koma, kekuma ko gobe da safene sekuje" "toh, sekun dawo" Maryam da mustapha dai basu gane inda maganarsu daddy da aunty ta dosaba, dan mustapha besan daddy sunyi accident ba, aunty tace kar afada masa seya kara samun sauki. faruq dake zauna yana danna waya yabi bayan daddy suka fita tare, kujerar da daddy ya tashi nan Maryam ta koma ta zauna. tunanin yaya Sadiq ne yafadomun arai, bansan nadamu dashi hakaba seyau dabanji duriyarsaba gaba daya, duk senaji kewarsa ta cikamun zuciya. tunanika kala_kala nahauyi akansa, nasan duk inda yake ba kalau yakeba, tunda har wuni guda benemeniba, amma bansaniba ko wani aikinne yadauke masa hankali. kasa daurewa nayi nadubi aunty nace, ''Aunty yau kuwa kunyi waya da yaya Sadiq?" cikin son basar da zancen aunty tace, "ehh, yacema yana gaisheki" ajiyar zuciya nasauke cikin jindadi tunda sunyi waya da aunty nasan yana lafiya kenan. "Ina amsawa" nafadi haka ina maida kallona kan tv dake dakin. har gurin mota faruq yaraka daddy inda su haidar suke jiransa sannan yakoma ciki. Wannan ciwon na mustapha babu wanda yasani dan aunty tace kar'asanar da kowa saboda kar sirrin boye yafito fili....... Bayan tafiyar daddy bajimawa matar ta farfado, Alhamdulillah ta farko cikin hayyacinta sedai babu bakin magana se ido datakebin kowa dashi. "Sannu Aisha" cewar kawarta tana kara matsawa jikin gadon. ido kawai ta bita dashi dankokanta bazata iya motsawa, saboda wani dimmm dataji yamata. yamata wani irin nauyi kamar andora mata dutse. Duban daya daga cikin yayannata matar tayi tace. "Rasheedah, jeki kirawo doctor kice masa ta farka" "toh, umma" wadda aka kira da rasheedah ta amsa tare da fita daga dakin. cike da jimantawa kawartata take kallonta, kana taka Allah na tashi, lafiya lafiya fa sukayi waya tace mata sunshigo Kano, amma ba'afi minti talatinba segashi ta riski wannan mummunan labari. yanda Aisha taci burin zuwa Kano da bikinnan amma gashi zuwan bezo mata da dadiba,Allah karabamu da mummunar kaddara, Allah ma yatakaita batayi wani rauni meyawa...dawowar doctor da rasheedah yakatse mata tunaninta. gaisawa sukayi da doctor yamusu yame jiki, sannan yaduba matar. Tambayar matar yayi inane yake mata ciwo bayan yatambayeta jikinnata. Kanta ta nuna masa da hannunta sekuma kafadarta ta barin dama. mammatsa mata kafadar yayi, ita kuwa se runtse ido takeyi, sannu yake mata, dama yasan dole zataji ciwo agurin tunda tanan ta fadi, danma Allah yatakaita amma dazata iya samun karaya akafadar. gefen fuskartama duk ta kukkurje. Seda yamata duk abinda yadace sannan yafita. kawartatama sallama tamata tatafi akan zata dawo Anjima, danse kiranta akeyi a waya. babbar yarta rasheedah ta bari, sekuma direban matar. harsu daddy suka karaso yan'uwan matar basuzoba, dama se cikin dare daddy yayi tsammanin zuwansu dan hanyar bata da kyau. sun mata sannu, kuma sundan jima sebayan isha'i suka bar asibitin........ Wajen 8:30 su aliya sukazo asibitin, zuwansu kenan ko gida basu jeba. naji dadin ganin aliya sosai itama haka. basu wani jimaba, aunty tatasamu agaba muka koma gida, harda ita. daddy da faruq aka bari agurin mustapha, Maryam jitayi tamkar karsu tafi don bata gaji da kallon heartbeat dintaba. hankalin ahalin alhaji mainasara yafara dawowa jikinsu, tunda Jikin mustapha Alhamdulillah, yayi kyau, dasu Maryam ma suka tafi sunbarshi yana ta baccine....... *BAYAN SATI DAYA* jikin mustapha yayi kyau sosai yanda akeso, jininnasa yadaidaita. Yacire komai na damuwa daga cikin ransa, dan kullum daddy da aunty cikin yimasa nasiha sukeyi. Maryam ma taji sauki sosai, yankewar datayi ahannu ya warke dama bawani yanka sosai mudubin yamataba. Zuwa wannan lokacin Maryam tagane, gidan babu lafiya, tunda gashi sati guda cur batasaka yaya Sadiq da mommy da suhalat a idontaba. kuma batakara tambayar aunty komai game dasuba, tunda ta lura bataso tasani. Ammafa abun yana matukar daure mata kai, ace kamar mustapha babu lafiya, amma mommy tatafi tabarshi, tunda ita haryau batasan meyake faruwaba. Aunty tanaso ta tambayi Maryam taji tayaya wannan tukunyar sirihin da mommy tayiwa mustapha asiri tazo dakinta amma basu samu sun kebeba, saboda zirga_zirgar asibiti, gana mustapha gana matar da daddy yabuge. Mommy tasamu information din su daddy suna gari, harma da accident da ciwon mustapha, duk taji labari. sungama shirinsu da kawarta binta zata rakata gurin wani hamshakin boka a garin Niger acan wani kauye. Nanda kwana 3 masu zuwa zasuyi tafiyar, danma binta ta tsaya yin wani uzurinta datuni suntafi. Suhalat kam,gabadaya kwanakinnan tayisune cikin tsananin damuwa na rashin kasancewa da mustapha dakuma rashin sanin matsayinta agurinsa,taso zuwa gida amma mommy tahanata. Abangaren Sadiq kuwa gabadaya ya boye kansa daga idon mutane, kodayaushe yana dakinsa a kulle, yarame yayi baki, ga kewar Maryam data addabeshi, mommy kullum seta kirashi a waya, amma baya picking. kullum cikin zullumi da tsammanin kamuwa da ciwo yake kamar yadda boka yafada. ko abinci baya iyaci, seyaji tamkar ze mutu yake iya jefa wani abu acikinsa. daddy kam yana sane, amma yayi banza da lamarinsa. Aunty cema takewa daddy zancensa akan yakamata su jawoshi ajiki tunda yayi nadama, amma daddy yayi biris yace tabarshi nadamama aitana gaba bega komaiba har yanzu,tunda shi yasiya da kudinsa...... Yau zamuje dubo matar da daddy yabuge nida aliya da aunty, dan tun washegarin ranar bamu kara komawaba, ranar damukajema bacci takeyi. misalin karfe hudu na yamma muka fito cikin shirunmu, bansan daliliba bankuma san meyasaba gabana yaketa faduwa tunda akayi zancen zuwanmu dubiyar, yanzumma da muka fito hakance ta kasance. muna cikin tafiya aliya tadubi aunty tace, "aunty pls kibani key nayi driving dinnan" harararta aunty tayi tace. "Aizaki iya zuwa ki kwata, uwar rawar kai kawai" duk da yanayin danakejin kaina seda na murmusa, aliya kuwa tsit tayi bata kara maganaba,se baki data turo gaba. Aunty da aliya suna matukar burgeni, suna kuma bani nishadi, har inji dama nice da mahaifiyata. "Allah kajikan mahaifiyata da innata, dama dukkan musulmi baki daya. Ameen" nafadi haka araina Aunty ce tayi driving dinmu har asibitin.........✍️ *By* *Zeey kumurya* *4️⃣3️⃣* *Bismillahirrahmanirrahim* ..........Da bismillah na fito daga motar saboda gani nake tamkar wani abu ne zesameni saboda yanda nakejin zuciyata. Aunty nagaba aliya nabinta abaya seni kuma ta karshe har muka karasa dakin da matar take. matar tana zaune akan gadonta, mahaifiyarta da kanwarta sune ke kwana tare da ita, suna zaune suma akan wani gado dake dakin, se megidanta shima dayazo yana zaune akan wata kujera dake fuskantar matar. da sallama aunty ta yaye labulen dakin ta shiga. a tare suka amsa mata gaba-dayansu harda marar lafiya. dasauri kanwar matar ta mike tanawa aunty sannu da zuwa tare da nuna mata gurin zama. Kafin aunty tagai ga zama muma munshigo dakin, bakunanmu dauke da sallama. kaina na kasa na shiga dakin, gefen aunty muka karasa muka zauna. Duban mahaifiyar matar wadda ta manyata sosai aunty tayi tace, "ina wuni baaba" "lafiya kalau, yarnan ya hidima damu?" Murmushi aunty tayi tace, "haba baaba aiba wata hidima, Yamejikin?" "Jiki da sauki, Alhamdulillah" "Masha Allah, Allah yakara sauki" kanwar matar ce tagaida aunty, muma muka gaishesu duka mukayiwa mejiki sannu. har lokacin kaina na kasa. Muryar dattijuwar naji tana fadin, "ai likitanma yace insha Allahu, gobe ko jibi za'a iya sallamarta, tunda jikinnata ya warware. Tun shekaran jiyama take cewa a sallameta ita ta koma gida, likitanne yace ta dad'a hakuri zuwa gobe." "Allah Sarki, ai zamanne guri daya babu dadi, duk se mutum yaji yatakura" cewar aunty. "Hakane kuma da wannan dan wannan, to ita kaddarace bawa be'isa ya kauce mataba, yanda Aisha taci burin zuwa bikinnan tanata murna zatazo Kano taga ya Kano take, ashe rabon wahala ne ke kiranta" "To Allah ya takaita yakiye gaba, Allah yasa kaffarane" wayar kanwar matar ce tayi kara alamun shigowar kira. kafin wani a dakin yakara magana. dakkowa tayi taduba tace, "Mama kinga, aunty Maryam ce take kira, kuma naga da number dinta ta naija ce, ko sun saukane?" "watakil Asiya daga kiji dai" wayar harta katse se Asiyan ce tabi bayan kiran. dadokinta ta amsa sallama kafin tace, "Aunty Maryam, saukar yaushe?" daga daya bangaren matar tace, "saukar yanzunnan Asiya, ko gida bamu karasaba muna hanya nadora sim dina nace bari nasanar muku ya jikin A'ishan?" "Dasauki bari na bata wayar" ta karashe zancen tana mikawa mara lafiyar wayar. basu wani jima suna wayarba ta mikawa mahaifiyartasu, ita sundan jima suna magana sannan ta mikawa mijin matar shima sukayi magana. daga gani wadda sukeyin wayar da ita suna ji da ita, yanda kowannensu yake farinciki da hakan, su Aunty sungane hakane ta fuskokinsu data bayyana tsantsar farincikin da suke ciki. mundan jima sannan muka musu sallama muka tafi. Kafin mutafi seda Aunty taje office din doctor suka kara tattaunawa akan ciwon matar sannan muka nufo gida. hamdala nayi ga Ubangiji da muka dawo gida lafiya babu abunda yafaro, dan yanda zuciyata taitamun rawa nayi tunanin wani abunne ze faru dani. Adaren yau aka sallamo yaya Mustapha daga asibiti, itama matar da daddy yaje da daddare likita yatabbatar masa gobe insha Allahu zasu sallameta... Tunanin yaya Sadiq ya yawaita acikin zuciyata a daren yau, jikina duk ya sanyaya komai cikin rashin kuzari nayisa, har Aunty take tambayata koda matsalane nace mata babu komai. Bayan mungama komai munzo kwanciya nakasa daurewa nadubi aliya nace. "Aliya niko dan Allah Intambayeki mana" inajinki matar yayana?" harararta nayi nace, "banson iskanci se'inma fasa tambayartaki" "yihakuri tawan ta abubakari kwandon sukari" ta fadi haka tana dariya. numfashi nasauke nace, "kamar kuwa kinsan akanshi zantambayeki, aliya yau kimanin fiye da sati guda kenan bansashi a idonaba, nasan dai yacemun zeyi tafiya amma baze jimaba zedawo, gashi wayata batanan bare nakirashi naji ko lafiya, nikuma ina kunyar na tambayi aunty" "hmm,wlh bake kadaiba nima nayi mamaki dabanga yaya Sadiq ba har tsawon sati guda,shida su mommyba. Dana tambayi aunty nace mata suna ina, setacemun bata sani ba. amma nifa nafi kyautata zaton bakalauba,akwai abunda ke faruwa agidannan" shiru nayi, domin nima nadade ina tunanin da akwai wani abu dake faruwa a gidan, banda haka ace duk ciwon da Mustapha yayi babu mommy ba yaya Sadiq ba suhalat, kuma ko zancensu banji Aunty tanayiba ko waya banga sunayiba gas... "Kinyi shiru Maryam" aliya ta katsemun tunanin danakeyi. Ajiyar zuciya nasauke nadago nadubeta nace, "narasa abun cewane Aliya, amma inason sanin halin dayake ciki, zuciyata cike take da kewarsa, dan Allah kitambayarmun Aunty halin dayake ciki" "shikenan kawata karki damu, kikwanta kiyi baccinki, zan tambayarmiki ita insha Allahu, dasafe" kwanciya nayi ina fadin, "nagode" atakaice, dan yanda nakejina doguwar maganama bazan iya taba. inajin Aliya na tsokanata wai soyayya dadi, nidai namata banza, harta gaji ta kwanta itama. Abangaren Sadik ma, yau tunanin Maryam ya yawaita aransa fiye da kullum, kewarta ta masa katutu a zuciya, jiyakeyi tamkar zerasata ne. Idanuwansa ita kadai suke da muradin gani. kaunar Maryam na azabtar da dukkan jiki da zuciyarsa. betaba tunanin abun zejuye masa hakaba, daga soyayyar wasa da yaudara ta juye zuwa ta gaske, soyayyar Maryam tamasa bazata tamasa mugun kamun dake barazanar tarwatsa kwakwalwarsa. yazama dole gobe yafita danya ganta koyaji sauƙin abunda yake ji acikin zuciyarsa........ washegari Mustapha yatashi garau tamkar bashine yayi wannan doguwar jinyarba,dama haka Allah ke ikonsa. babu wani guri ajikinsa dayake masa ciwo. Yariga ya fawwalawa Allah al'amarinsa kuma ya amshi kaddarar datazo masa cikin rayuwarsa da hannu bibbiyu, addu'a kawai yake yi Allah yabashi juriya akan abinda ya jarrabesa dashi. babban abunda yafi komai dugunzuma hankalinsa idan yatuna shifa yanzu besan asalinsaba, besan wani jininsa. wannan abu idanyatunashi seyaji yatsani duniyarma gabadayanta. gashi yau tunda yatashi yakejin wani iri ajikinsa, haka dai yadaure yayi wanka yashirya cikin wani yadi mekyau da tsada milk colour. part din daddy yanufa jikinsa a matukar sanyaye tamkar anmasa duka. daddy nashirin fita shikuma yana shigowa, a falo sukayi kicibus. cike da tsananin farinciki daddy yake dubanshi wanda har yakasa boyuwa a fuskarsa, saboda ganin Mustapha fess dashi yana takawa da kafafunshi. fuskarsa ce, kawai tayi fayau da ita sekuma haske daya kara. "Good morning Dad" mustapha yafadi haka, cikin danne damuwar dake nukurkusar ransa. "Morning too, son. Dafatan katashi lafiya" "lafiya kalau daddy" yabashi amsa bayan ya zauna a daya daga cikin hadaddun Royal chair din dake falan. "Masha Allah, son daga gani babu tambayata jiki yayi kyau, dama yanzu nake shirin zuwa part dinnaka nadubaka, kafin na wuce asibiti, doctor yakirani tundazu zebasu sallama." "Alright, sekadawo" daddy kamar yace masa su tafi tare, sekuma dai kawai yafasa yasa kansa ya tafi. Lumshe idanunsa yayi bayan daddy yafice, mommy ce tafado masa a rai. haryau yakasa mantawa da ita, acikin ransa. Mamakintama yaki barinshi ace duk tarin kaunar data nuna masa duk ba gaskiyabane, ita kuwa mommy wacce irin mutum ce...... ahaka Aunty da daddy yaturota takawo masa abinci tazo ta samesa yanata tunane_tunane. nasiha taita masa cikin hikima kamar kodayaushe, dakanta ta bashi abincin abaki, duk dan yadena damuwa. danta hango damuwa karara acikin idanunsa. shima boye duk wata damuwarsa yayi yazage yayi break fast din, sosai yaci abincin duk dan Aunty taji dadi. Aikuwa Aunty taji dadin sosai, tata jero masa addu'oi..... Daddy yaje asibiti yatarar harsun gama shirinsu, ciwon matar begama warkewaba bandejin kawai aka cire mata,dandai ta matsane kawai aka sallamesu. kanwartata tun sassafe suka wuce ita da driver da mamanta. megidantane kawai yazauna su tafi tare. Da niyyarsu daga asibiti su wuce Jos,amma daddy yace dole sesun biya ta gidansa. wajen 12 na rana suka karaso gidan alhaji menasara. Part din mommy daddy yakaisu, sun samu tarba sosai a gurin su Aunty. Daddy ne yacewa Aunty su shirya tare zasu tafi Jos din, suraka matar. Aikuwa Maryam da aliya se murna za'a tafi dasu. dan Aunty tace bazata tafi tabarsuba kafarta ƙafarsu. Mustapha yana kwance a falon daddy, daddy yakirasa a waya yace yazo part din mommy yagaisa dasu matar kafin su wuce, tunda basu taba haduwaba. Amsa masa yayi cikin ladabi sannan ya mike yafito yanufi part din mommy.........✍️ *kuyi manage da wannan pls* *By* *Zeey kumurya* *4️⃣4️⃣* *Bismillahirrahmanirrahim* ...........Cikin takunsa me cike da nutsuwa da kasaita gami da daukar hankali ya shigo falon mommy bakinsa dauke da sallama, daddadan kamshinsa mesanya nutsuwa ya mamaye falon gaba-daya. wata ajiyar zuciya daban shiryamataba nasauke, tare da maida kallona bakin kofa dasauri ina satar kallonsa. gaba-daya mutanen dake falon suka amsa masa sallamartasa a lokaci guda. akan carpet ya zauna ya fuskanci matar da megidanta ya gaishesu. matar datunda Mustapha yashigo ta kura masa ido tana kallonsa. numfashi ta sauke ta amsa masa gaisuwar batare data dauke idonta daga kallonsaba. shikuwa Mustapha kansa yana kasa bemasan tanayiba. Daddy yace, "wannan shine babban dana, sunanshi Mustapha, shine kuma mara lafiyar danace muku" mijin matarne ya amshe zancen da fadin "Allah Sarki, sannu kaji dan samari ya jikinnaka" "dasauki" ya amsa atakaice, saboda yanayin dayakejinsa yafara yawaita. "Allah yakara sauki" matar tafada still dai idanta nakan Mustapha bata dena kallonsaba saboda ita kadai tasan metagani a tattare da Mustapha'n. Aliyace ta gaisheshi cikin girmamawa, nima cikin dauriyar abunda nakeji agame dashi nagaisheshi. Daddy ne yadubemu yace, "Maryama kuje kukarasa shiryawa yanzu zamu wucefa munayin sallah,kuma a yau zamu dawo insha Allah" "to daddy" muka amsamasa cikin ladabi, tare da mikewa muka nufi dakin Aunty. duban daddy matar tayi tace, "Alhaji hardasu a yan rakiyar ne?" murmushi daddy yayi yace. "Ehhh, mamansu tace bazata tafi ta barsu sukadaiba" mijin matarne ya amshe zancen dacewa. "Amma Alhaji dasunyi zamansu har ita Hajiyan, aganina wannan ai wahalar daku zamuyi, bayan dawainiyar dakukasha damu yanzukuma harda rakiya." dubansa daddy yayi cikin tsanaki yace, "haba, wannan ba wahalar dakai bane, muda mukeso akulla zumunta, wadda zata dore har'aba. Aiko bakomai maje muga muhallinku" "Amma dai da wannan dannaka zamu tafi ko?" matar ta fadi haka tana kallon Mustapha. shima daddy kallonsa yayi yace, "A'a bandashi" "to nidai gaskiya inason yarakamu sa....." "Saboda kinga kyakkyawan saurayi ko?" mijinnata ya katse ta dafadar haka. murmusawa tayi tace. "Ehhh, najidin" "uhmm, kodai kinaso kihadashi da mummunar yarki *umaimah* ne?" dariya suka saka har daddy, amma banda Mustapha dabemasan mesukeba, yatafi can wata duniyar daban. "Nidai kawai inaso yakaramu babu ruwanka dameyasa" matar ta fadi haka tana dariya. daddy batare da tunanin komaiba yace, "to shikenan tunda kince haka, semu tafi dashi din, da dakaninsa zamu tafi, amma tunda kince haka semu tafi dashidin ba wani abu" "yawwa Alhaji godiya nake"..... Bayan anyi sallar azahar kamar yadda daddy yafada muka fito gabadayanmu domin tafiya. Ni, Aunty, Aliya, daddy sekuma matar da mijinta. bamusan da yaya Mustapha za'a tafiba seda mugaka yafito cikin shirinsa, yacanza kaya banadazu bane. yanzu wata dakakkiyar shaddace ajikinsa kalar light blue, yayi matukar kyau,amma fuskarnan tasa a tsuke take daga gani ba'ason ransa za'ayi wannan tafiyar dashi ba. Matar da daddy yabuge ita bada wata manufa tace atafi da Mustapha ba, sedan wata yar yayanta dasuke gida ɗaya ta ganshi. yarinyar sunanta umaimah, budurwace amma zatayi shekara 27. Ita umaimah ta kasance tana bala'in son kyakkyawan namiji gentle duk wanda yazo yace yana sonta setace ita bemataba, haryanzu bataga kamar namijin datakeso ta auraba, kullum cikin siffanta yanda takeso mijinta yakasance take. A lokacin da matarnan tayi arba da Mustapha, setaga babu abunda yayi saura daga yanda umaimah take siffanta yanda takeso mijinta yakasance a tattare da Mustapha. shine abun yamatukar bawa matar mamaki, dansu gani sukeyi kamar baza'a iya samuba gashi kuma kamar yadda take so dan hamshakin mekudi, harta matsu sukoma gida taga yanda umaimah zatayi idan taga Mustapha'n. Mota muka shiga nida Aunty da Aliya da matar, yaya faruq ne zeyi driving dinmu. suma su daddy wata sukahau sukuma driver ne zeyi driving dinsu, nayi zaton a mota zamu Jos din, amma senaga muntsaya a wani guri,gurin katon filine. Fitowa daddy yace muyi. babu bata lokaci muka fita dukanmu mukabi bayan daddy zuwa cikin gurin. ashe airport ne mukazo, seda muka dan jira daddy yayi magana da wasu mutane sannan muka kara yin gaba. wajen wani abu muka tsaya, mekamar jirgin sojoji *(JET)* (kasancewar garin Jos basuda filin saukar jirage, shi yasa daddy yayanke shawarar su tafi a jet din) Gani nayi kowa a cikinmu yana shiga cikin shi babu fargabar komai, nikam senaji wani iri tunda bantaba hawaba, banma taba tunanin zanganni a airport ba balle harta kaini ga shiga jirgi. senaji kamar mafarki nake, wai yau nice zanhau jirgi har yayi shawagi dani a sama. danne duk wani kauyancina da fargabata nayi, nayi bismillah nima na hau. Bayan anyi duk abunda yakmata muka lula sama, banda ya faruq da driver su gida suka koma. Ajiyar zuciya nasauke nadubi aliya dake kusa dani kasa_kasa nace mata. "Ke kinji yanda nakejina kuwa gaba daya atsorace nake" dariya aliya tayi ahankali yanda babu mejinta seni tace, "aina lura dake tun ashigowa tamkar mekoyon tafiya" "kedai bari abunda baka saba" "kenima wannan ne hawana na uku, dama indai zakuyi tafiya da daddy, indai irin state ne haka ba wata kasarba a Jet yake zuwa" "auww, dama wannan ne jet din a wani American firlm nataba ganinsa" "ehhh, shine na dady ne yanama da wani bayan wannan" kawar da zancen jet dinnayi da fadin "kinwa Aunty zancen yaya Sadiq kuwa?" "Ehhh, na mata tacemun zamuyi maganar idan mundawo daga tafiyar yan" "Tom shikenan,Allah yadawo damu lafiya" "Ameen"..... Munsauka a garin Jos lafiya a unguwar *Rikkos.* Garin lumlumlum dashi babu zafi, bakamar kanoba da muke da tsananin rana, garin ya burgeni gasu da duwatsu. Hamdala matarnan tayi ganin sun sauka a gida lafiya, ita kam zuwa Kano bemata dadiba amma bawa baya kaucewa kaddararsa koda a gidama take idan Allah yayi setayi accident din. Gidannasu babbane me kyau daga gani suma masu haline. Amma irin family house dinnanne. wani part dake hannun dama muka nufa,muka yada zango a falo. wata mata ce tatarbemu wadda bazata haura shekara 32 ba. da fara'arta se sannu da zuwa take mana. dukkanmu muna zaune a falon harda yaya Mustapha da daddy. duban matashiyar matar A'isha tayi tace. "Zuhura ina Aunty Maryam, dasu mama?" "Mama tana part dinta, ammi kuma tana ciki, may be bataji zuwanku bane" mikewa A'isha tayi ta shiga wani daki dake falon bayan tace mana zuwa, itama matar damuka tarar mikewa tayi ta shige kitchen. Shiru falon yayi, nikam tunda muka shigo gidannan gabana yake faduwa bana wasaba, abun harya bani tsoro sosai, akwanakinnan inajin haka sosai atattare dani amma na yanzu yafi na kullum, addu'a kawai nashiga karantawa a cikin zuciyata. satar kallon yaya Mustapha nayi naganshi yajingina bayanshi da jikin kujera idanunsa a lumshe tamkar kowanne mafiya yawan lokuta danake ganinsa. maida kallona nayi ga Aliya datake danne danne waya. maman matar damuka kadece ta shigo falon da sallama ita da kanwar matar fuskokinsu dauke da fara'a. "Sannunku da zuwa" tsohuwar ta fada bayan ta zauna. daddy ne ya amsa mata da fadin. "Yawwa sannu baaba, dafatan kunzo gida lafiya, ya hanya?" "Lafiya kalau Alhaji, sannunkufa angode, Allah yasaka da alkhairi" "Ameen, ameen" gaisheta mukayi gabadayanmu amma banda yaya Mustapha dako motsawa beyiba, itama kanwar matar gaisawa mukayi ta nufi kitchen gurin zuhura. "Mustapha!" Daddy yakira sunansa ganin yanayin dayake ciki. Mustapha dayakejinshi a wata duniyar daban, saboda wani matsananci bugu da zuciyarsa take masa,kansama jinsa yakeyi tamkar ze rabe biyu. idanuwansa da suka masa nauyi yabude a hankali ya kalli daddy. amma bece komaiba. kallo daya daddy yamasa yasan da akwai matsala saboda yanayinsa gaba-daya ya sauya.ya hango tsantsar damuwa a idanun dannasa. cikin tausayawa daddy yace masa. "Ga mahaifiyarsunan kugaisa" maida dubansa yayi ga matar, zuciyarsa na kara tsananta bugu, cikin matukar dauriya yace mata. "Ina wuni?" asanyaye. matar wadda ta zuba masa ido kawai tana kallonsa tace. "Lafiya kalau, ya jikinnaka" (dayake duk sunsan bashi da lafiya) dauriyarsa ta kare hakan yasa ko harafi daya baze iya kara furtawa dan yanayin dayakejin kansa ya yawaita, dakai kawai yabata amsa. gaba-daya falon yabasu tausayi musamman Aunty da daddy dasukan damuwarsa, kawar dakai Aunty tayi daga kallonsa cike da tsananin tausayinsa. Maryam kuwa batasan daliliba kawai taji kwalla tacika mata ido. maman azatonta jikinnasane dan haka tace, "Allah yakaro sauki, aidama yayi zamansa tunda bashi da lafiya, tafiyarma seta karawa mutum ciw..." Fitowar matar da daddy ya kade ita ta katsewa mama maganar datakeyi. wata kyakkyawar macece tamkar balarabiya biye abayanta, tana sanye da abaya me matukar kyau, wadda taji adon dutsuna, ta yane kanta da mayafin abayar. tana sako kafarta cikin falon wayarta dake hannunta tayi kara alamun kira, dakatawa tayi ta daga wayar cikin wani irin bakon yanayi mewuyar fassaruwa daya risketa a lokaci daya. kafin tagama wayar su zuhura sun fito daga kitchen hannayensu dauke da farantai dake dauke da ruwa da lemuka,suka dire agabanmu. da sallama kyakkyawar matar ta karaso falon, gabadayanmu muka daga kai muka kalleta saboda dadin muryarta duk da ta manyanta. siririn farin glass din dake idonta ta zare ta rike a hannunta, kyawawan idanunta farare tass suka bayyana wanda ta saukesu akan fuskar Maryam.............✍️ _*masu complain na rage yawan typing, kuma kun rage yawan comment ne, idan kun gyara nima zan gyara*_ *By* *zeey kumurya* *4️⃣5️⃣* *Bismillahirrahmanirrahim* ...........A tare zuciyoyinsu suka buga da karfin gaske, kallon cikin ido matar take yiwa Maryam. Ita kuwa Maryam dasauri tayi kasa da idonta bugun zuciyarta na tsananta. a ranta tana fadin, "tsarki ya tabbata ga Ubangijin da yayi wannan kyakkyawar halitta." ita kuwa matar kara kafe Maryam tayi da ido, zuciyarta nacigaba da bugawa saboda mamakin abunda tagani a tare da Maryam. mama dabata lura da halin da Maryam da matar suke cikiba ta fadada fara'a tana duban matar tace. "Wannan matar yayansu ce daya rasu, shine babban dana, lokacin da akayi hatsarin tana Saudiya ne ta kaiwa mahaifiyarta da kaninta ziyara se jiya ta dawo" kallon matar daddy yayi a karo na biyu zuciyarsa na kissima masa wani abu akanta, muryarta ta masa dadi bakadanba, yayi mamaki daya kalli fuskarta yaga ta manyanta dan muryartata tamkar ta wata matashiyar saboda dadinta da sanyinta. ga muryartata ta sanya masa wani abu a cikin zuciyarsa wanda yakasa gane ko menene, hakan yasa yaji yanakuma son yakarajin muryartata. numfashi matar ta sauke, tana kokarin daidaita nutsuwarta. maida kallonta tayi ga Aunty datake gaisheta. Amsa mata tayi cikin sakin fuska. tana kokarin zama akan hannun kujerar da mama take, tamkar ance ta dago kanta idanunta yasauka akan Mustapha,daya kafeta da ido yana kallonta. wata mahaukaciyar bugawa zuciyarta tayi cikin tsananin razani tafasa zaman datake kokarinyi, ilahirin jikinta ne yadauki rawa tamkar mazari, hannunta na rawa take nuna Mustapha tanason tayi magana amma takasa, wani dimmm taji kanta yayi juwace ta kwasheta kawai segani akayi tayi kasa zata fadi. Dasauri matar da daddy yakade da mama sukayi kanta saboda sunfi kusa da ita, gaba-daya mutanen falon sukayi kanta, banda Mustapha dayakasa koda motsi, da Maryam. "Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un" abun bakunansu kawai suke iya furtawa kenan. "Zuhura kikira Saddam, maza yazo mukaita asibiti jibifa jikinta yashika ko numfashi batayi" cewar matar da dady kayade cikin tsananin tashin hankali. "Nashiga uku, ni salamatu, dan Allah kutaimakamun mukaita mota, base munjira wani Saddam ba, semunje ta mace mana" mama tafadi haka tana hawaye. Aunty ce tace, "dama tanayin haka, kotana da wani ciwonne" "wlh bata da ciwon komai yarnan, bamu taɓa ganin tayi haka ba, seyau" mama tabawa Aunty amsa da fadin haka. "Ina ganinfa kamar suma tayi, a kawo ruwa mugwada watsa mata,zata farfaɗo insha Allah" daddy yafadi haka cikin son ya kwantar musu da hankali, ganin yadda gaba-daya hankulansu yatashi, zuhura da kanwar matar da daddy yakade harsun fara kuka. zuhurance tayi sauri taje ta dakko ruwa a fridge ta kawo, zuba mata ruwan aka shigayi a fuskarta zuwa kirjinta. kusan mintuna biyu ana zuba mata ruwan kafin taja wata doguwar ajiyar zuciya. Numfargashi tafara saukewa akai,akai. ganin ta farfaɗo sukayo kanta da mata sannu zukatansu cike da Murna. "Babu shakka familinnan suna matukar son matarnan" Aunty ta fadi haka a cikin ranta. A hankali ta bude idanunta tana kallon mutanen dake zagaye da ita, hannun matar da daddy yakade ta kama, cikin sanyin murya me cike da rudani tace mata. "A'isha bani ruwa insha, guntun ruwan da'aka tsiyaya mata, A'ishan ta taimaka mata ta bata tasha. Ajiyar zuciya ta sauke tana kallon mama tace, "mama wani mafarki nayi me rikitarwa" "wanne irin mafarki kuma diyar kirki" maman tatambayeta cike da mamaki. "Mama tunda natashi yau, nakejin wata irin faduwar gaba, jikina duk babu dadi kamar wadda wani mugun abun zesama, sekuma yanzu nayi mafarki A'isha tashigo dakina tasameni wai inzo mugaisa da mutanen dasuka bugeta, shine naga wani a zaune a falonnan, wlh yanda kikasan mijina na farko daya rasu babu abun daya banbantasu nakamanni, shine abun ya matukar firgitani" dammmm! Zuciyar daddy ta buga, jin muryar matar, a yanayin datayi magana yanzu babu banbanci da muryar matar data bashi Mustapha, shikanshi yana mamakin yanda amon muryar matar yakasa bacewa daga kwanyarsa duk kuwa da tsayin shekarunnan da aka dauka, a lokuta da dama idan yana zaune shikadai kalaman matar suna masa amsa kuwwa a cikin kwakwalwarsa. gabadaya falon tsit yayi dama Mustapha da Maryam basusan me'akeba. Sukuwa su mama, basu wani dauki zancen matar da mahimmanciba sun dauka zafin ciwon daya sametane lokaci daya ya firgitata. Aunty kuwa kallon matar kawai takeyi, ta kalli Mustapha ta kalli maryam. nuna Mustapha tayi tana kallon matar tace, "ko wancanne wanda kika gani ɗin?" dasauri matar ta kalli inda Aunty ta nuna mata, tozali idanunta suka mata da Mustapha wanda idanunsa suke a lumshe yanzu saɓanin dazu dayakafeta da tsumammun idanunsa shiyasama ta tsorata sosai harta sume. gani kawai sukayi ta mike tsaye zumbur, kura masa ido tayi na wasu sakanni kafin ta fara murza idonta dan tabbatar da ba gizo yake mataba. cikin karaji da matsananciyar rudewa muryarta na rawa tace, "sh...sh..shi..ne wlh, shineeeee!." takarashe zancen da jan maganar. "shine wa Aunty Maryam" Aisha tatambayeta tana riketa ganin yadda duk ta burkice lokaci daya, mama baki sake take kallonta, danko sanda mijinta dan maman yarasu batayi irin wannan birkicewarba da gigicewa. "Dan Allah A'isha wanene shi wannan din danake ganinsa, koku bakwa ganinshine, kikalleshi zakiga kamarshi da miji na *MODIBBO*" "Danane" muryar daddy ta doki dodon kunnenta, dasauri ta kwace daga rikon da A'isha ta mata, taje gaban daddy cikin kuka tafara masa magana da fadin. "Danka, kuma?" To meyasa yake kama da mijina, hatta azurfar hannunsa irintace a hannun mijina harya mutu" "wai MARYAM, meke damunki ne, wanne mijinnaki kike magana akai, mufa bamugane mekike nufiba,gabadaya duk kinbi kin firgitamu" mama tatambayeta cikin dunbin al'ajabi, dan ita abun matar yafara bata tsoro harta fara tunanin ko matar tayi gamone. hannunta Aunty takama ganin duk falon sunkasa aiwatar da komai, hatta daddy kuwa daya tsaya kawai yana kallon matar. cikin lallami Aunty tafara mata magana. "Baiwar Allah, nasan ke musulmace kuma kinsan babu ta yadda za'ayi wanda yamutu yadawo, a kalamanki kuma naji kina fadin mijinnaki yarasu, kuma wannan danmune dashi mukazo garinnan, kinga babu tayanda za'ayi yazama mijin ki" "tabbas mijinannawa yarasu tun shekara fiye da talatin dasuka wuce, Amma kuma yau gashi naga wani me matukar kama dashi ai dole na shiga rudu" "baku da dane tare da mijinnaki?" Aunty tatambayeta cikin son tabbatar da abunda take zargi. kasa matar tayi dakanta idanunta na shatatatar da hawaye, tausayintane yacika su mama da iyalanta. cikin matsanancin kuka tace, "bani da ɗa ko ɗaya a duniyar nan" hawayene yaciko idanun Aunty, wani matsanancin tausayinta ne taji yashigeta lokaci ɗaya. shikanshi daddy seda kwallar tacika masa ido saboda yanda matar take kuka tamkar ranta zefita, ga dukkan alamu an sosa mata wani mikine a cikin ranta. Lokaci daya Mustapha daya kurawa matar ido kawai yana kallonta tun sanda tafara magana, yaji wani matsananci tausayinta gami da zazzafar kaunarta ta cika masa zuciya. rungume matar Aunty tayi tsam ajikinta, sedai batayi yunkurin rarrashintaba dan ta hanata kukan datakeyiba. tasan kukanne kadai ze rage mata radadin datakeji a cikin zuciyarta dan rashin haihuwa ba karamin abu tawaya bane ga dan adam. Maryam da aliyama hawayene kawai yake zuba a fuskarsa na tausayin matar, dan duk wani me imani idan yaga yadda matar take kuka seya zubar mata da hawaye. su mama kuwa mamakine yakamasu na matar, dan bata taɓa shiga irin wannan yanayinba akan rashin haihuwartata, saboda macece ita me tsananin tawakkali akan duk yadda rayuwa tazo mata,lokuta da damama mijinta yafita nuna damuwa akan rashin haihuwar tata. Daddy dayakejinsa tamkar mafarki yake, saboda duk wata alama dazata nuna masa matarnan mahaifiyar Mustapha ce ta bayyana agareshi. Saboda hujjojin dayake dasu kwarara guda biyu. Nafarko zancen azurfar dake hannun Mustapha datayi, na biyu kuma kukanta datakeyi yanzu yayi iri daya sak da wanda tayi lokacin data bashi Mustapha. sunayen Allah kawai yake kira danshima nutsuwarsa kokarin barinshi takeyi, haryanzu yakasa tabbatarwa da kansa ba mafarki yakeba, matar data bashi Mustapha itace tsaye agabansa. tattaro duk wata dauriyarsa yayi ya sarrafa harshensa dakyar yace, "kin taɓa haihuwa ne?" barin jikin Aunty tayi da sauri saboda yanda tambayar ta daki zuciyarta batare data dena kukan datakeba tace. "Ehhh!" tamkar mekoyan magana. mamakine yakama su mama domin su bata taɓa ce musu tataba haihuwaba, sun sandai tataba aure kafin ta auri baban Saddam. dauke kukan datakeyi tayi dif tamkar ba itaba, taci gaba da magana. "Nataba haihuwa na haifi yaro namiji amma yanzu bansaniba koyana raye koya mutu dan......" "Yazakiji idan nace miki wannan shine dannaki dakika taɓa haifa?" Daddy yakatseta da fadin haka cikin karfin zuciya yana nuna mata Mustapha. Ba ita kadaiba babu wanda kalaman daddy basu daki zuciyarsaba a falon, hatta Aunty kuwa da take da haske akan hakan. Maryam da aliya sunfi kowa shiga rudu, dama aliya itacan arude take banda zare idanu tana kallon mutane babu abunda takeyi. Maryam kuwa bata fahimtar komai, cikin duhu kawai kalaman daddy suke kara sanyata. Shikuwa gogan wato Mustapha wata muguwar faduwar gabace ta riskeshi shifa gani yakeyi abubuwan dasuke faruwa duka mafarki yakeyi ze iya farkawa wani lokacin. batasan sanda ta kama hannun daddy ba duka biyu tana maimaita kalmar. "daaanaaa...daaanaaa..." Tamkar wata mara fahimta. Abin gwanin ban tausayi. daddy danne wani abu daya darsu a zuciyarsa yayi yace, "ehh, dankine, duk da banji wani bayani akan kiba amma wasu hujjojina masu karfi sun tabbatar mun da kece matar dakika bani jariri, a wani dare akasar *Niger* a garin *Niamey*?" ilahirin jikintane yaɗauki kyarma gami da ɗauke war numfashinta na wasu sakanni a lokaci guda. Tabbas bazata taba manta wannan ranar data bayar da danta gudan jinintaba harta koma ga mahaliccinta. "Kidena mamaki, akan ikon Allah, domin buwayarsa ta wuce tunanin me tunani, shine me sauya al'amari a duk sanda yaso kuma a lokacin dayaso,kije ga danki da Ubangiji ya hadaku a lokacin da bakuyi tsammaniba dukanku." murmusawa daddy yayi yamaida kallo nsa ga Mustapha daya zama tamkar mutun mutumi yace. *"Son, come to your real mom"* A matukar firgici ta juya ta kalli su mama, da mamaki yahanasu koda kwakkwaran motsi idanuwansu kawai suke bawa abinci suna ganin abun tamkar wasan kwaikwayo, banda haka daga mutane sun rakosu sekuma dansu yazama na wata. cikin sauri ta juya ta nufi inda Mustapha yake wanda ko motsawa beyiba daga zaunen dayake, zuciyarta na tsananin bugawa tasa hannunta dake rawa tafara balle botiran gaban rigar Mustapha, lumshe idansa yayi shima tasa zuciyar natsananta bugu tamkar zata faso kirjinsa ta fito, wanda har mahaifiyartasa tanajin bugun zuciyar tasa. singlet fara kar itace ta bayyana bayan ta gama balle botiran gaban rigar tasa, cikin zafinnama da karfin dabatasan tana dashiba ta yaga singlet din gida biyu, faffadan kirjinsa fari tass dashi me dauke da kwantaccen bakin gashi yabayyana. a kirjinsa daga ɓangaren dama ta kurawa ido, wani abune asaman nononsa baki. (rowa) abunka da farin mutum tafito tayi dodar. cikin fitar hayyaci saboda tsabar farinciki tarungume Mustapha ajikinta tana me fashewa da kukan murna. "babu shakka, kai danane nacikina, dukda nasan mafarki nakeyi,zan iya farkawa a kowanne lokaci amma hakan baze hanani nuna farincikinaba akan ganinka......." Zantuka tayi ta saki na farinciki cikin matsanancin kuka tamkar zata shide tana shafa sumar kansa. shikuwa Mustapha lokacin data rungumeshi wata doguwar ajiyar zuciya yasauke, yanajin wani shauki nabin dukkan jiki da ruhinsa, wata nutsuwa saya rasa a rayuwarsace yaji ta lullubeshi lokaci guda, ga tsananin kaunar matar data cika dukkan zuciyarsa. wasu sanyayan hawayene suka fara zuba akan kuncinsa..........✍️ *By* *Zeey kumurya* *4️⃣6️⃣* *Bismillahirrahmanirrahim* .............Yarasa a wacce duniya yake saboda, dadi,al'ajabi da mamaki. Tamkar ansauke masa wani abu mai nauyi a cikin zuciyarsa haka yaji. farinciki mara misaltuwa ne yamamaye dukkan baƙin cikin dake cikin zuciyarsa. jikinsane yayi wani irin sanyi tubus hakan yasa yakasa tabuka komai, koda danyatsa daya yakasa motsawa. falon yayi tsit bakajin komai se sheshshekar kukan *ammi* wadda take kara manne Mustapha akirjinta, tanajin tamkar ta maidashi ciki saboda tsabar kauna. lumshe idonsa yayi yakara kwantar da kansa ajikinta yana shaƙar sassanyan kamshinta,wani dumi yaji yana shiga jikinsa, ajiyar zuciya yake sassaukewa akai_akai. Aliya da tsaiwa ta gagareta ta zube akan kujera cikin rawar murya ta dubi daddy dayaketa murmushi me nuni da yana cikin tsananin farin ciki tace. "Da..daddy.. tayaya tazama mom dinsa?..mommy fa?.." taku daddy yayi yazauna a kusa da ita har lokacin fuskarsa nadauke da murmushi, gefen kuncinta yashafa yace, "bazaki fuskanci komaiba, autar Aunty amma very soon nasan zakigane yanda abun yake nanbada jimawaba" yanda aliya ta kurawa daddy ido tana kallonshine yagane bata fuskantar meyake nufi. Aunty ma zama tayi a kusa da Maryam wadda ta kurawa su Mustapha ido, ko kiftawa batayi. share hawayen fuskarta Aunty tayi tare da kauda kanta daga kallon su Mustapha. Sosai tausayinsu yake ratsa zukatan kowa dake falon musamman ma ammi. A hankali mama tafara jan kafarta data mata nauyi tazo gaban daddy, cikin daukewar tunani tace masa. "Alhaji, dan Allah, kafitar damu daga cikin duhun dakuka samu, gabadaya kunsa zuciyoyinmu cikin tararrabi, tayaya danku dakukazo dashi zezama dan Maryama.?" "Labarine metsaho mama, dole semun zauna mun nutsu sanna zamu warware muku zare da abawa" "daddy yabata amsa cikin girmamawa. numfashi kawai ta fesar taja kafarta, ta karasa inda su Mustapha suke, tafarawa ammi magana cikin lallami danta fuskanci tahakane kawai zata iya barin wannan kukannata. "Haba, Maryam kukan na menene haka,kiyi hakuri kiyi shiru kibar kukan haka, kizo ki fitar damu daga cikin duhun dakika sanyamu" a hankali taraba jikinta dana Mustapha wanda ya wani manne mata, sekace karamin yaro. Kukan datakeyi ta dena se ajiyar zuciya take saukewa. Mustapha kuwa kasa yayi dakansa idanunsa a lumshe, beso tsohuwar ta katse masa samun nutsuwa da jindadin dayakeji dalilin jinsa a jikin mahaifiyarsaba sedai tsananin miskilancinsa baze bari kagane yanayin dayake cikiba. kama hannun ammi, mama tayi tazaunar da ita akan kujera ta fara share mata hawayen fuskarta cikin tsananin so da kaunarta. Tun ba yauba, ta fuskanci akwai wani abu dake damun zuciyar ammin, tana dannewane kawai, domin lokuta da dama tana taddata cikin zurfaffen tunani ko kuma cikin yanayi nadamuwa. kallon Mustapha kawai ammai takeyi takasa dauke idonta daga kansa, wani sanyi takeji yana ratsa zuciyarta. maida kallonta tayi ga mama tare da kama hannunta cikin sanyin murya tace, "mama dan Allah abunda yake faruwa gaske ne ba mafarki nake ba, wlh nakasa tabbatarwa da kaina." cikin tausayawa mama tace. "Gaske ne Maryama ba mafarki kikeba, azahiri komai dakika gani yake faruw...." Ai ammi bata bari mama takarashe zancen taba ta zube a kasa tana sujjada domin nuna godiyarta ga Ubangiji. "Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah" daddy, aunty, mustapha, ammi suke furtawa a cikin zukatansu tamkar hadin baki cike da tsananin farin ciki. A'isha da kanwarta mesuna Halima tare da surukarsu wato zuhura, mazauni sukayiwa kansu dan sunga abun bana ƙarau bane, ga ƙafafuwansu duk sun sage saboda tsaiwa............. farincikin da dady da Mustapha da ammi suka nuna akan haɗuwar Mustapha da mahaifiyarsa a wannan lokacin baze misaltuba, duk miskilancin Mustapha kasa jurewa yayi yaje ya rungume mahaifiyarsa cikin tsananin shaukinta da kaunarta mara misaltuwa a cikin ransa, tabbas ya yarda mahaifiya daban take, dan yanayin dayake jin kansa akan bayyanarta baze misaltuba. ita kuwa ammi se shafa kansa takeyi tana sumbatarsa, takasa dauke ido daga kallonsa ko kunyar surukartata yau bataji. babu abunda yaraba Mustapha da mahaifinsa hatta tafiyarsu kuwa, har miskilanci data fahimci Mustapha'n dashi duk na mahaifinsa ne, yanayin yanda yake kallon abu dakuma lumshe ido shine kawai irinnata, amma komai na mahaifinsa ne. mama ganin kamar sun manta dasu agurin ta junansu kawai sukeyi tace sudai, ammi tazo ta fitar dasu daga cikin duhun dasuke. badan ammi tasoba taraba jikinta dana danta, abin kaunarta tace kowa yaje yayi Sallah don har anyi la'asar sannan ta basu labarin. Bayan kowa ya idar da sallar suka kara hallara a falon dukansu kowa yazaku yaji yanda abun yakasance, dan abun yarikitar dasu bakadanba musamman Maryam da aliya dasukasan mommy ce ta haifi Mustapha. Gyara zama ammi tayi tafara bada labarinta kamar haka... "Sunana MARYAM IBRAHIM, mu yan ƙasar NIGER ne, anhaifeni a garin NIAMEY. Anan natashi anan na girma anan nayi makarantata anan nayi aure. mahaifina ba wani mekudi bane saidai yanada rufun asiri daidai gwargwado. mahaifiyarmuce kaɗai matarsa kuma mu biyu ta haifa, nice babba se kanina MUHAMMAD. muntaso cikin son junanmu, iyayenmu sunbamu tarbiyya wadda kowa yake yabanmu. inada shekara goma sha biyu kanina kuma tara, Allah yayiwa mahaifinmu rasuwa. Tun daga wannan lokacin rayuwa ta fara sauya mana,muka fara rayuwar maraici. Muhammad yakasance yaro me kwazo da zuciya. Tun baifi shekara goma sha biyuba, yake ƙoƙarin neman nakansa. Akwai wata makociyarmu matar tana da kirki sosai, kuma tsohuwace ta manyanta. mijinta itama yarasu yabarta da yaya maza guda biyar, tasake aure ta haifi yaro ɗaya shima mijinnata yarasu, se yan'uwan baban yaronnata suka daukeshi. Saboda masu kuɗi ne sosai, mahaifin yaron yamutu yabar masa dukiya me tarin yawa. Duk kafin a haifeni akayi haka, tsohuwar dakanta take bani labari. saboda Allah yahada jinina da ita. nibanmasan tana da wani ɗa ba, bayan biyar ɗin data haifa da mijinta na farko, dan da mijinta na biyun yarasu seta dawo gurin ƴaƴanta suka cigaba da zama tare. Tumunin takabar da'aka bata na gadon mijinta shitake juyawa take saide_saide. matar tana sona sosai kasancewar bata ƴa mace, haka zata saimun kayan kwalliya na mata da abubuwan buƙata. Seda dannata ya girma yazama saurayi sannan yadawo gurin ta, a lokacinma duka yayannata biyar ɗin sunyi aure. Sanda yadawo gurinta inada shekara 16. Kyakkyawane shi, dominshi ruwa biyu ne, mamansa buzuwace kamar mu, mahaifinsa kuma bafulatanine. Haka kawai Allah yadoramun tsoronsa dan gaskiya yana da kwarjini, gashi miskili, kuma baya sakarmun fuska, amma fa akwai shi da kyauta. Abun hannunsa betsone masa idoba. amma suna shiri sosai da kanina Muhammad saɓanin Ni, hakama mahaifiyarmu kullum seya shiga yagaisheta yamata abun arziki. sana'ar saida gwala-gwalai yakeyi yana zuwa Dubai da Saudiya yana sarowa, Allah kuma yabuda masa sosai. sauran yan'uwansa sesuka hade kansu suke nuna basa kaunarsa, afili karara suke nunu masa kiyayya. Amma shi babu ruwan shi haka yake girmamasu kuma komai suka ce yamusu yana musu, yasai musu gidaje yabasu jari, kuma idan suka zo da bukata haka zemusu. mahaifiyarsu da kanta take masa faɗa, akan yadena yawan basu kudi tunda suma barasawa sukayiba. Aduk lokacin da tamasa zancen haka, sedai yayi murmushi yace mata "idan be musuba wazewa bashifa da wasu yan'uwa sesu, tunda mahaifinsa shikadai yahaifa shima. ai bashida kamarsu. Watarana dabazan taɓa mantawa da itaba a rayuwata. Ranar juma'a da safe. Nashiga gidansu domin duba mahaifiyarsa a lokacin bata da lafiya tana zazzaɓi, ina shiga gidan naci karo dashi a harabar gidan yana tsaye. seda gabana yafadi dana gansa bansan kuma meyasa ba, kuma seyamun kyau sosai tamkar wani Balarabe, satar kallonsa naitayi harnazo giftawa tagabansa seda na lumshe idona saboda kamshinsa dana shaka me dadin gaske. kaina na kasa nagaisheshi. me mamakon ya amsamun seyace mene ne kallonsa. dasauri na dago nasaci kallonsa senaga yahade rai, tsorone yakamani nafara bashi hakuri, ganin duk na firgice seyayi murmushi kawai ya wuce abinsa, nima jikina ba kwari nakarasa ciki. Ranar agidan na wuni inata aikece aikece, shikuma yazo yazauna yasamun ido yana kallona, duk motsin danayi idansa na kaina. duk se naji na takura. In takaicemuku zancedai a daren ranar yacemun yana sona. nayi matukar mamakinsa danni banyardabama,tun daga ranar nafara wasan buya dashi duk hanyar danasan zata hadamu seda na kauce mata, har gidansuma nadena zuwa. har gida mamansu tazo ta sameni tace kotamun wani lefinne nadauke mata kafa, nace mata wlh babu komai. babu yadda na iya haka naci gaba da zuwa gidansu dankar mahaifiyar sa tayi tunanin wani abu. Aiko watarana yaritsani yace sena fada masa, shi dodo ne danake gudunsa, nace masa a'a. yace to idannakara gudunsa seya fadawa mahaifiyarsa yana sona. dasauri nace masa a'a karya fada mata nadena insha Allah. Tun daga ranar kullum semunyi tadi, dannima gaskiya inason sa. Dan duk inda ake neman namijin da mace zatayi alfahari dashi MODIBBOnah yakai. tun inajin kunyarsa harna rage. munsaba dashi sosai mun kuma shaku iya shakuwa. Tun munayin soyayyar a boye harta fito fili kowa yasani. mahaifiyarsa tafi kowa murna dajin labarin soyayyar mu, saɓanin mahaifiyarmu dabatayi murnaba, bansan kuma meyasa ba dan alokacin bata fadamunba. munkai kusan shekara muna soyayya dashi sannan akayi zancen aurenmu, aka saka ranar aurentamu. ba'awani saka lokaci me tsahoba na bikin. Tun daga lokacin yan'uwansa suka dora mana karon tsana nida mahaifiyata da kanina, wai kwadayine zesa na auresa badon Allah ba. nikuma ina matukar sonsa shiyasa tsanar dasuke mana ko'ajikina mahaifiyarmucema take damuwa. Rana bata karya, segashi lokacin da'aka saka na bikinmu yazo. Ansha shagali sosai anyi taro lafiya angama lafiya, muka tare a gidanmu dake cikin unguwartamu dai, amma da ɗan tafiya daga gidanmu. munyi rayuwarmu ta farinciki da jindadi da kwanciyar hankali, soyayyar damukasha da megidana *ALHASSAN MODIBBO* bazata faduba, yasoni ya tattalani kamar kwai, nima kuma ina matukar sonsa. yabani farinciki arayuwata duk abunda nakeso shiyakemun. Nandanan na murje nakara fari nayi haske, ana ganina anga ina cikin kwanciyar hankali Alhamdulillah. Nanfa tsanar da yan'uwansa sukemun ta karo, waina mallake musu dan'uwa se'abunda nace yayi shiyake. Shifa sesuka fara masa zagon kasa, suna masa wayo suna cin dukiyarsa a boye batare da saninsa ba. Aurenmu befi da wata biyar ba, Allah yayiwa mahaifiyarsa rasuwa, alokacin ina dauke da karamin ciki. Munji mutuwarnan sosai, mutuwar tadakeni nayi kuka tamkar raina ze fita, daga karshema shiya komo yana rarrashina. A hankali mutuwar tabi jikinmu muka hakura muka koma yimata addu'a. Tundaga lokacin yan'uwansa suka fara nuna masa wayonsu a fili, suka dinga binsa suna yabasu kadarorinsa. Shima dake yaganesu seya k',i basu. Mubamu saniba ashe sunacan suna haɗa masa gadar zare. watarana muna zaune a falo da daddare, ranar yadawo daga Dubai yayi sarin gwalagwalai masu yawa, ko inda ake narka masa su a maidasu dankunnaye da sarka bekaiba, ya a jiyesu a gida, yace dasafe zekai dan lokacin yagaji. a lokacin cikina yakai wata 7. Muna zaune naga yakuramun ido yana kallona, tafin hannuna nasa narufe masa idon nace. "Wannan kallonfa" hannuna yacire daga fuskarsa yana bina da wani kallo dayasa jikina duk yayi sanyi yace. "Nasone!" murmusawa nayi cikin jindadi duk da faduwar gaban danakeji amma haka nadaure nace. "Mijina, ina sonka sosai,ina addu'ar Allah yabarmu tare harkarshen rayuwarmu..." kalamai masu dad'i da sanyaya zuciya mukaita fadawa junanmu a wannan daren, a ranar MODIBBO yanunamun soyayyar dabetaba nunamun irintaba, soyayya me tsayawa arai dasanya nishadi a duk sanda aka tunata" shiru ammi tayi tana sauke numfashi, lokaci daya yanayinta yasauya idanunta yakawo ruwa. wani yawu medaci tahadiye sannan ta cigaba da magana. "Amma duk da haka jikina a sanyaye yake kamar wata mara lafiya, shima kuma haka na lura danashi'karfin hali kawai yakeyi. kaina na bisa cinyarsa bacci yasaceni, a falon ya kwantar dani ya tada sallar nafila kamar yadda yakeyi kowanne dare. Bansan mekefaruwaba se farkawa kawai nayi naji suna magana da wasu mutane a falon. bude idona nayi da sauri kokarin mikewa zaune nayi najini rungume ajikinsa. Abunda naji yana fadane ya matukar dagamun hankali. "Kome zakumin kumun,amma karku taɓamun lafiyar matata da abunda ke cikinta" ai bansan sanda na kwace daga rikon dayamunba, ina kallon mutane. Fuskokinsu duk a rufe da wani bakin kyalle. cikin tsorata nace musu. "Suwaye ku,? mekukazoyi gidanmu? mekuke bukata?" Wani me ƙatuwar muryane a cikinsu naji yace. "Ran mijin ki mukazo dauka" cikin zafin rai nace masa, "ƙarya kakeyi, baka isa ka kashe shiba matukar kwanansa bekareba. Ai rannasa ba'a hannunka yake......" kafin na karasa maganata naji daya a cikinsu yadagi yacillar gefe, cikin zafin naka da karfin zuciya namike zankoma gun mijina, suka karayin gefe dani. Intakaice muke zance, ina kallo a gabana, mutanennan marasa imani da tausayi masu zuciyar kafirai suka yankamun mijina, duk da uwar magiyar daya musu akan su kyaleshi karsu maida masa da ɗa/ya Maraya tun kafin suzo duniya, su fadi ko nawa sukeso,kome sukeso zebasu,amma sukace su sam basa bukatar komai. ransa kawai suke da bukata. Inaji ina gani suka masa yankan rago" kuka me karya zuciyar me saurarensa ammi tafashe dashi tamkar a lokacin abun yafaru.......✍️ *BY* *zeey kumurya* *4️⃣7️⃣* *Bismillahirrahmanirrahim* ...........Babu wanda bezubar da hawayeba a falon se dady da Mustapha. shikam Mustapha zuciyarsace take tafarfasa tsabar bakin ciki da tausayin mahaifansa, jiyayi dama shima kukan zesamu yazo masa, koyaji sauƙin radadin dake damunsa a zuci. Farararen idanunnan nasa sun kada sunyi jajur, jijiyoyin kansa gaba daya sun mike sunyi rudu_rudu. kasa kawai yayi dakansa yana fesar da zazzzafan huci daga cikin bakinsa. daddy ma dauriyace kawai domin karya kara karyarmusu da zuciya, lallaminsu yafarayi duka da fadin. "Kuka bashine maganiba, duk da nasan tausayine yasaku kukan, amma yakamata kuyi hakuri kuyi shiru, kar kukan yajanyo muku wata matsalar, musammanma ke dakike kukan tun dazu" yakarashe zancen yana kallon ammi. shiru suka masa babu wanda yace masa kala, dakyar dai dady yashawo kan ammi tayi shiru tacigaba da bada labarin cikin raunin murya. "kafin su kasheshin sunsha dambe dashi a kokarin shi na kwatar ransa, dan har wasu yajiwa ciwo da naushin daya dinga kai musu, to Sarkin yawa yafi Sarkin Karfi. susu biyarne shikuma shi ɗaya, kuma su da makamai a hannunsu. ni kuwa banda ihu babu abunda nakeyi ina neman taimako, ɗaya daga cikinsune yatoshemun baki, da gwabjejen hannunsa. maimaita kalmar shahada yayitayi harsuka yankashi sekace wani dabba. kansa nayi da gudu bayan sun fice ina jijjigashi ina kururuwa ina fadin yatashi karya tafi yabarni. gaba-daya nima nayi dama_dama a cikin jinin dake fita daga jikinsa, tun ina fahimtar menakeyi harna dena. farkawa kawai nayi naga gidan a cike da mutane, ga jami'an tsaro suna jiran na farfaɗo suji karin bayanin abunda yafaru. mahaifiyatace a kaina da kanina Muhammad, gaba-daya ido yadawo kaina, masumun sannu nayi masu kallon tsegumi namun. nidai dakyar na yunkura na tashi zaune saboda nauyin da kaina yamun, ashe nadade a sume dan har anyi masa sutura. Dakin dayake mahaifiyata ta kama hannuna ta kaini, muna shiga na hangoshi a makara da gudu na kwace hannuna daga nata nanufi gurin da makarar take na kwanta akan gawartasa na fashe da kuka, surutai naitayi irin na fitar hayyaci, dakyar aka banbareni daga jikinsa, ina kallo aka fitar dashi zuwa gidansa na gaskiya. Tundaga wannan lokacin nazama ba uhmm ba um'um, saidai naitabin mutane da kallo, banaci banasha kuma bana kukan fili sena zuci, a haka har akayi sadakar uku. Nidai bazance ina cikin hayyacinaba a wannan lokacin, suma kam nayita ba adadi, ga tsohon ciki. Seda na kwanta jinya a asibiti, dannamafi wata a kwance, mahaifiyata kullum cikin kuka take, dan duk sun fitar da rai dani. Kanina Muhammad koyaushe cikin kwantarmun da hankali yake, tare da alƙawarin seya daukarmun fansar mijina akan wadanda suka kasheshi ko su waye. Mahukunta nata aikinsu na binkice akan kisan. kwana biyu da sallamoni daga asibiti yan'uwan MODIBBO sukazo akan rabon gado, nace musu suje surike komai ni banaso. banason komai na dukiyar na bar musu. Muhammad ne, yace hakan bazeyiyuba ai rabon gado Allah ne yace ayi, kuma ko badonniba, abunda ke cikinafa ai dole a fitar masa da hakkinsa. Sukuwa yan'uwansa ba hankali harsun fara hada kan kadarorinnasa suna mallakesu. Muhammad ne yaje yasamu wani yayan abokinsa lauya yafada masa, shikuma yashigar da maganar kotu. segamu har gaban alkali. Alkali yace, ai babu zancen rabon gado yanzu harse na haihu anga menahaifa. dan haka a tattaro duka abunda ya mallaka a damka masa har zuwa lokacin dazan haihu, budar bakinsu secewa sukayi ai anyi scanning anga mace ce, a cikina dan haka ayi raba kawai. mamakinsu bakadanbane ya kamani, dan duk jinyar danasha ko duniya basuzoba, amma wai anmun scanning anga macece. Alkali kuwa fatattakarsu yayi yace dole sena haihu, kar wanda yakara zuwa masa da batun harse na haihu. Ba'afi wata dayin hakaba, na haihu a asibiti bayan uwar wahalar danaci. Nahaifi yaro kyakkyawa me kama da ubansa, lafiya kalau dashi. Nakai kwana 3 bansan waye akainaba, bayan na haihu. saboda damuwa tamun yawa,jinina yahau sosai. Nafi sati a asibiti sannan aka sallamoni. yaro yaci sunan *Muhammad* nayiwa kanina takwara, saboda soyayyar dake tsakanina dashi, dakuma yanda yake son Muhammad, kodayaushe yana hannunsa, har wanka yake masa sekace mace. kullum cikin fadamun yake, idan yayi aure nabar bishi Muhammad, yarikesa. Haihuwar yaron ita taragemun kaso 50 nadamuwar danake ciki akan mutuwar adalin mijina. soyayyar uwa da danta, daga Allah ne, bansan yazan fasalta muku yanda nakejin kaunar danakewa Muhammad karami ba. Munje kotu alkali yamana rabon gado, tunda namiji aka haifa yan'uwan modibbo basu da komai a cikin gadonsa, komai nasa na yaronsane seni da'aka bawa tumunin takaba. tundaga wannan rana damukaje kotu yan'uwan modibbo suka sakomu a gaba, nida mahaifiyata da kanina. suka takura mana suka tsangwamemu. watarana bayan munyi arba'in, sukazo mun da wata fitinar akan dole sena basu dukiyar Muhammad, tunda sune danginsa na uba, zasu rike masa su juya masa kafin ya girma. harna mike zan tattaro musu kanina Muhammad yashigo gidan, dayaji abunda ke faruwa abakin mahaifiyarmu yace basu isaba baza'abasu komai na dukiyar Muhammad. fada sosai abun yazamarmusu da Muhammad duk da befi ɗan cikinsu ba, daga karshe dai dole suka hakura suka tafi. Yan'uwan mahaifin modibbo danaje musu yawon arba'in sena fada musu abunda yake faruwa, shine sukace natattaro komai nakawo musu aisu basu isa sun kwata ahannunsuba. haka kuwa akayi natattara komai nakai musu. Gwalagwalan da modibbo yasiyo a ranar daya rasu sukadaine ban bayarba. dama a cikin wata jaka yake, sena boye jakar a dakina. Akwai wata a zurfa a hannun modibbo, tunda nasanshi da ita nasanshi da ita, seda ya mutu aka cireta. itama sena jefata a cikin jakarnan dakuma tambarin gidansu modibbo, duk na hada na ajiye. Watarana da daddare muna cikin bacci, wasu mutane suka hauro mana gidanmu. basu tunkari dakin kowaba senawa. Ina rungume da Muhammad a kirjina naji ana ƙoƙarin rabani dashi ta ƙarfi. da sauri na farka, shima Muhammad din farkawa yayi yana tsandara kuka. cikin matukar tsorata naja baya, ina kara kankameshi a kirji na. tare da fadin, "suwaye ku?" wata dariyar rashin imani wani acikin su yakece da ita, sannan yace. "Wadanda suka kashe megidanki ne, yanzu kuma munzo mukashe wannan dannakine, daya hana ruwa gudu." tsoro metsanani ne yakamani, zanin goyonsa dake kan gadon, na yayiba na mike tsaye na goyeshi, suna tsaye suna kallona basucemun kalaba. cikin kuka nace musu, "wai kudin suwaye, me mijina da yarona suka muku? Kunkashe mun mijinma bazaku barmuba, sekun biyo dannawa guda daya tilo shima kunkasheshi, kuwanne irin marasa imani ne? Wlh Allah bazai barkuba ku....." Wata uwar tsawa wani a cikin su yadakamun. wadda tasani hadiye maganata, batare dana shiryaba. maganganu yashiga yimun wanda bana fuskantar komai saboda dimuwa da razani, tunanin hanyar dazanbi inkubutar da dana kawai nakeyi. A kalamannasa dai na fahimci yace, turosu akeyi kuma saboda dukiyar modibbo ne. jin haka sena fara neman inda jakarnan take domin na basu, dansu kyalemun dana. seda nagama shan wahala nanemo jakar, nace musu ga dukiya nan, indai dukiyace. Nidai dan Allah subarmun yarona karsu rabani dashi, kokuma ni su kasheni akan sukasheshi. A lokacin senaji gwara ni namutu shiya rayu. wata irin kaunarsa nakeji, tana kara mamaye zuciyata. mutanennan sukace susam Muhammad akace sukashe kuma sesun kasheshi, sannan su tafi da dukiyar. daukar jakar nayi kamar mika musu zanyi, nafaki idonsu nafada toilet na kulle, bubbuga kofar suka hauyi da nufin su ballata. ganin danayi tsaf zasu iya balla kofar su shigo su riskeni sena fara tunanin mafita. shawara zuciyata tabani akan nayi nesa da garin kawai, inda halima nabar kasar gaba daya,ta hakane kawai zan tsira daga sharrin muggan mutanennan. batare da tunanin komaiba na amince da shawarar zuciyata, window din toilet dinmu na kalla naga zan iya fita ta cikinsa, harna bar jakarnan sekumadai nadawo nadauka dannasan zatamun amfani nan gaba, na ratayata, a kafadata, na gyara goyon Muhammad tamau, na fice ta window. da wani irin gudu dabansan ina dashiba nafice daga gidanmu naita falfalashi. Banmasan inda nake jefa kafataba kawai shiga duk layin dana gani yakeyi. nasan balla kofar toilet din sukayi sukaga bananan shine suka biyo bayana, ina cikin guduna kamar ance in juya na hango kyalli fitilarsu daga can nesa. Abunda yasa nagane sune, kuma ni sukebi, duk layin dana shiga nan hasken fitilar yakebi shima. hankalinafa ya kara tashi gashi harna fara gajiya da gudun, ina shan kwanar wani layi nayi kacibus da wani mutum...........(labarin abunda yafaru tsakanin ta da dady ta basu sanna ta cigaba) bayan na bashi yaron senaji hankalina ya kwanta, koda sun cimmun bani da damuwa tunda ɗana ya tsira da yardar Allah, kuma dukiyar da'ake fadan akanta bazasu sametaba. wata mota nagani tazo ta wuce ta gabana ina cikin gudu, can kuma naga motar ta dawo ta tsaya a gabana, kokarin canza hanya nayi cikin tsananin tsorata. mai motar ne yafito da sauri cikin harshen Hausa yacemun. "Baiwar Allah, zoki shiga mota narage miki hanya, naga wasu mutane sunata gudu da muggan makamai karsu suganki suyi miki wata illar, gashi yanzu dare ya tsala" jin kalamansa yasa da sauri na bude bayan motar na shige batare da tunanin komaiba, shima ya koma cikin motar. kafin yakai ga jan motar mutafi azzaluman mutanennan sun karaso layin.........✍️ _*kuyi hakuri da wannan, banjin dadine, dakyar nasamu na muku wannan ɗinma. ABUNDA KASHUKA FAN'S GROUP, nagode sosai da addu'oinku, Allah yabar zumunci mai ɗorewa Ameen🥰🙏*_ *By* *zeey kumurya* *4️⃣8️⃣* *Bismillahirrahmanirrahim* ............Fitilar dake hannunsu na hango ta cikin glass din motar,suna tafe suna dube_dube. wata boyayyiyar ajiyar zuciya nasauke lokacin danaji me motar yaja motar mun fara tafiya. Se'alokacin naji wani gumi yana ketomun duk da motar akwai sanyin a.c amma tamkar heater haka tazamarmun. tunanin mahaifiyata da kanina ne yafadomun a cikin zuciya, "yaya zasuji idan suka wayi gari sukaga babu ni a cikin gidanmu?" natambayi kaina, wasu zafafan hawayene naji sun zubomun a kuncina. Ga wata masifaffiyar kewar ɗana data cikamun zuciya, danasan zan hado da wannan bawan Allah, da bazan bada yarona ga wani wanda bansaniba, bansaniba shima koba mutumin kirki bane, idona yarufe a lokacin dana bada ɗana ko tunanin me mutumin yakeyi cikin dare a waje banyiba na bashi dana, kuka me karfine yatahomun, da sauri na cusa kasan dankwalina na toshe bakina dan kar kukan yafito. "Kiyi hakuri, ki fawwalawa Allah dukkan lamuranki, kuma dukkan tsanani yana tare da sauki" mai motar yafadamun haka cikin sanyin murya. Ajiyar zuciya nasauke ina kokarin hadiye kukana nace masa. "Nagode" "ina kika nufa ne, acikin wannan daren" ya tambaye ni. shiru na masa dan bansan mezan kumace masa ba, danni kaɗai nasan irin azabtuwar da zuciyata takemun. kuncin danake ciki a wannan lokacin baze misaltuba, rasama tunanin dazanyi nayi, tun ina gane wasu abubuwan harna fice daga hayyaci na, saboda damuwa. farkawa kawai nayi naganni a cikin gidannan, kwance akan gado, ansanyamun drip a hannuna. mama da mutumin daya daukoni a mota tare da matarsa na gani adakin, sannu suka shiga yimun tare damun ya jiki, nidai da ido kawai nake binsu,ba bakin magana. Bayan ruwan yakare anciremun, mama tataimakamun nayi wanka, tabani tea nasha bisa dole sannan nasha magani narama sallolin da'ake bina azaune. bansan yazan fada muku halacci da karramawa irin ta mutanen gidannanba, sun rike tamkar jininsu, mama tasoni sosai, dan bata banbantani da ƴaƴanta. Alokacin su A'isha suna yanmata tare take hadamu take yimana komai. A duk lokacin da mama da *Alhaji Bashir* (wanda yaɗauki ammi a mota) suka tambayeni tarihina bana ce musu komai sedai naita kuka, hakan yasa suka kyaleni suka dena tambayata. matar alhaji Nasir, zakiyya macece me kirki tajani a jikinta sosai bata nunamun wani abu na kyara ko tsangwama. A lokacin danazo gidan Saddam yana karami danko yayeshi batayiba. seyazama kullum nice mai rainonsa yana hannuna kokuma in goyeshi, shiyake debemun kewar Muhammad dina, wanda kullum sena kulle kaina adaki nayi kukan rashinsa dana adalin mijina. Ga kewar mahaifiyata data kanina tana damina a rai. haka rayuwa taita tafiya. wasa_wasa segashi har nayi shekara biyu a NIGERIA a garin JOS. Alhaji Nasir, dan kasuwane yana sarar kaya yana kaiwa gariri, ranar daya dakkonima yakai wa wani abokin kasuwancinsa kayane, kuma dare yamasa a hanya, gashi yana da uzurin dazeyi a safiyar ranar shiyasa bebari ya kwanaba a nijer ɗin. Lokacin da alhaji Nasir yanuna yana son aurena, kin amincewa nayi saboda yadda muke da matarsa. mama tayita bani baki akan na amince da auren, indai zakiyyace bata da matsala. Itama zakiyyan a lokacin dakanta ta dinga nunamun bakomai tana bani baki. Ganin haka sena amince, dama kuma bakinshi nakeba. suda basusan asalinabama suka nemi na shiga cikin zuri'arsu seni zankisu. munyi aure da alhaji Nasir muka cigaba da rayuwarmu cikin farin ciki. Alhaji Nasir yana kwatantata adalci atsakaninmu, muma kuma muna mutunta juna nida zakiyya, hakan yasa zamanmu lafiya lau. Saddam yana shekara 6, zakiyya takuma samun ciki. ta haifi yarta mace, aka samata sunan mama ummussalma, amma umaimah ake cemata. Umaimah batafi shekara 1 ba, akayi bikin A'isha da wani abokin alhaji Nasir. umaimah nada shekara uku Allah yayiwa mahaifiyarta zakiyya rasuwa. Se rikonsu yadawo hannuna gaba-daya ita da Saddam, nikuma har zuwa wannan lokacin ko batan wata bantaba yiba. Alhaji Nasir yama fini damuwa da rashin haihuwata shida su mama. wani lokacin ma ninake bashi baki, duk da nima abun nadamuwana amma haka nake danne zuciyata bana nunawa. Kullum da tunanin Muhammad ɗana, da mahaifiyata nake kwana nake tashi. A haka rayuwa tayita tafiya, ahalin gidannan suna sona sosai, tunda nake agidannan bantaba fuskantar wata matsala ta kyara ko cin mutunciba, girmamawa da mutuntawa itace tsakanina da kowa. Bayan wasu shekaru masu yawa munje kasa me tsarki sauke farali, Allah yahadani da kanina da mahaifiyata, munyi murna mara misaltuwa sosai a lokacinnan. mahaifiyata ta sanarmun da sun shiga tashin hankali bakadanba dasuka wayi gari babu ni a cikin gidanmu. kanina yashigar da yan'uwan modibbo kara akan sufito dani da ɗana, danyasan babu me zaceni sesu. Kuma yanada kwakkwaran hujja akan hakan, ganin dasukayi zetona musu asiri, sesuka masa asiri yabar kasar gaba-daya aka nemeshi aka rasa. Se bayan wasu shekaru yakoma, ya dauke mahaifiyarmu suka koma Saudiyya da zama anan yayi aure yanzu yana da yara guda biyu, mace da namiji. Se'alokacin su mama sukasan tarihina, dama tun lokacin da alhaji Nasir ze aureni, nasanar masa na taba aure mijinnawa yarasu. Amma banfada musu inada yaroba. mahaifiyata tamun fada sosai akan meyasa nabawa wani dabansanshiba yarona. daga karshe kuma takoma addu'a akan Allah yasa yana hannu nagari, idan yana raye Allah yahadamu, idan kuma ya mutu Allah yaji kansa. Alhaji Nasir a hanyarsa ta dawowa daga Niger wata ranar Litinin yakai kaya, Allah yamasa rasuwa. Naji mutuwarsa sosai shima kamar modibbo, nayi kukan rashinsa. Gashi shikadaine dan mama namiji se kannensa gasunan mata ne guda biyu, A'isha da nafisa. yanzu shekara biyu kenan da rasuwar tasa. Kanina yaso nakoma Saudiyya da zama, amma naki amincewa saidai nadinga kaimusu ziyara. dannasan idan natafi su mama bazasuji dadiba, gakuma umaimah datake kallona a matsayin mahaifiya, bazan iya tafiya inbartaba. Zuwa yanzu nariga na fidda rai, daganin Muhammad ɗana, dan shekara 33, ba wasabace. saidai kullum cikin yimasa addu'ar alkhairi nake, a duk inda yake." numfasawa ammi tayi tace, "inafata yanzu dukkanninku kun fita daga cikin duhun da kuke" Maryam data kurawa matar ido kawai tana kallonta, kasa tayi dakanta tana hawayen dabatasan dalilinsuba. Mama ce, tace. "Gaskiya Maryama kinsha gwabarmaya, kai mutane babu Allah a ransu yanzu duk wannan abun dayafaru akan dukiyane fa, dukiyar daza'amutu abarta." Aunty ce ta amshe zancen da fadin. "Hmmm, wlh mama abun ba daɗin ji, mutane gabadaya kudi yasa sun manta da Allah, kaga mutum yayi shirka, yayi kisa duk akan kuɗi, kuma karshedai dole mutuwa mutum zeyi ya barshi, Allah yasa mudace kawai." "Ameen, suka amsa gaba-daya banda maryam da Mustapha daya amsa aransa. Kallon ammi daddy yayi yace, "angano wadanda suka kashe modibbonnaki?" kallon daddy ammi tayi itama, dasauri kuma ta dauke kanta daga kallonnasa sannan tace. "Ehhh, anganosu yan'uwansane suka sanya a kashe shi, yanzu haka suna gidan yari anmusu daurin rai da rai, dasu da wadanda sukayi kisan, amma mutumin biyu a cikinsu sun rasu, da babban su, da kuma na tsakiya yanzu saura su uku." cikin gyada kai mama tace, "kinjifa, yanzu mene ribarsu akan abinda suka aikata?.. gashi yanzu karshe sedai sukare rayuwarsu a gidan yari, gashima wasu daga cikinsu harsun je inda shi modibbon yaje" "to ai dama mama duk *ABINDA KASHUKA, SHIZAKA GIRBA* arayuwarnan" cewar Aunty. Aliya kam mamakine yakara kasheta dataji wai mommy ba ita tahaifi yaya Mustapha ba, duk tarin kaunar datake nuna masa. gyaran murya daddy yayi yace. "Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah. dukkan godiya da yabo sun tabbata ga Allah madaukakin sarki, daya nuna mana wannan ranar gabadayanmu, Allah yajikan wadanda suka rigamu gidan gaskiya mukuma intamu tazo yasa mucika da imani, Allah yarabamu dayin abin da zamuzo muna danasani akansa a rayuwarmu, Allah yaraya mana zuri'a, yashiryar dasu bisa tafarkin addinin Islama" "Ameen, ameen" suka amsa gaba-daya. duban ammi daddy yayi yace. "Nasan yanzu zuciyarki babu abunda takeson ji, sama dana baki labarin abunda yafaru bayan kinbada danki ko?" Murmushi ammi tayi tace, "kamar kashiga zuciyata kuwa, inason sanin kaina bawa ɗana, kokuma wanine yabaka riƙonsa kuma ina son sanin wacece ta raini ɗana, domin nagode mata." shiru daddy yayi na wasu sakanni, yayinda ammi taketa kallonsa. "Nifa senaga tamkar nasankama amma narasa ina nasankan" A'isha ce tatari zancen ammi da faɗin, "zakisanshi mana, ko da agidan TV ko jaridu ne, shine fa alhaji mainasara" waro ido ammi tayi waje irin na mamakinnan tace. "Alhaji mainasara, shahararren dan kasuwar nan danakeji ana fadarsa" "ehh, shifa" gyada kai ammi tayi cikin mamaki. mamace tace, "kinyi mamaki ko Maryama, kinganshidai mutumin damukejin labarinshi a duniya, yau gashi zaune tare damu. Ai mainasara mutumin kirki ne, bakigaba yanda yamana da muna asibitinnan, karramawa babu irin wadda bamuganiba hakama ahalinsa suma masu mutunta dan'adam, basu dauki rayuwar su da zafiba,sundauki duniyarsu da sauki, shiya kullum yake ganin cigaba a al'amuransa." murmushi daddy yayi ya kalli agogon hannunsa yaga har lokacin magriba yakusa, kuma yau yakeso su koma Kano, gashi yabar matukin jet dinsa a waje yana jiransu. gyara zama yayi yabasu labarin, daga lokacin da ammi tabashi Mustapha, har kawo yau atakaice. be boye musu komai ba, nadaga abunda mommy ta aikatawa Mustapha, dakuma taimakon da Maryam tayi agidansa. amma bece Sadik ne yakeyin fyaden ba. Tafa hannuwa mama takeyi tana sallallami tace, "yanzu Alhaji macece ta aikata wannan abubuwan itama akan dukiyar, kai duniya ina zaki damune?.. wannan wanne irin masiface da bala'i, kadaukarwa kanka hakkin mutane saboda wani banzan burinka na duniya" "Gaskiya matarnan tacika shu'uma, kuma makira, Allah wadaran halinta" cewar nafisa. Maryam da aliya kuwa suman zaune sukayi dajin abunda mommy ta aikata, yanzu sungano dalilin dayasa mommy bata gida. Rungume Aunty ammi tayi ajikinta tana hawaye tace, "nagode sosai da yanda kika kula da ɗana, kika tsaya tsayin daka wajen ganin rayuwarsa ta inganta, Allah yasaka da alkhairi." kara rungume ta, Aunty tayi itama ajikinta tace. "Babu komai ai yiwa kaine, kuma Ni haryanzu Muhammad, kallon ɗana nake masa, babu abunda yacanza." sakin Aunty ammi tayi tana murmushi tace, "bazan gaji da miki godiyaba, Allah yaraya miki zuri'a ya kare gabanki da bayanki" "ameen" kallon Maryam ammi tayi, tundaga kallon farko data mata, taji kaunar yarinyar tashiga ranta. yarinyar ta burgeta ga nutsuwa a tattare da ita. yanzu kuma dataji abunda tayiwa ɗanta setaji kaunar tata ta karu aranta. "Zonan diyata yar albarka" ammi tacewa Maryam. A hankali ta mike cikin matukar sanyin jiki, ta nufi gurin ammi. rungumeta ammin tayi ajikinta, tana saka mata albarka, lokaci daya Maryam taji kaunar matar ta shiga ranta. Duban Zuhura mama tayi tace. "Zuhura, kije kidakko Abul mana magriba ta gabato." "Toh, mama" zuhura ta amsa mata cikin girmamawa sannan ta mike tashiga wani daki ta dakko ɗanta, mesuna Nasir amma ana masa lakabi da Abul. Jaririne dan befi wata uku ba. Sosai su mama suka jimanta halin mommy, dana yayyin baban Mustapha, ga kuma mamakin yanda Allah, yasakawa dukiyar Mustapha albarka. Ammi ma tayi mamaki sosai, dataji wai dukiyar Mustapha ce, tazama haka, gashi Allah yasa mata albarka, mutane da dama sun amfana da ita. duban daddy tayi tace. "Yanzu ina matar taka, inason ganinta itama namata godiya, ko bakomai ta rikemun yarona, bazan gazaba zanta mata addu'ar shiriya, Allah yasa tatuba takoma ga Allah" kasa kawai daddy yayi da kansa yana jinjina kyawun hali irinna ammi, duk abunda akace mommy tayiwa yaronta amma bata zagetaba, kota aibatataba se fatan shiriyama data mata. kallon Mustapha wanda yayi shiru tamkar baya falon daddy yayi yakira sunansa. "Son!" A hankali ya juyo lumsheshshun idanunsa ya kalli daddy, tare da motsa labbansa ya amsa masa. "Ina son sanar dakai wani abune, duk da nasan namaka karfa_karfa a cikin rayuwarka, amma inafatan zaka yafeni kakuma fahimci manufata" kallon daddy kawai Mustapha yakeyi amma be fuskanci meyake nufiba. fahimtar hakan daddy yayi. a gogon hannunsa ya kalla a karo na biyu. dagowa yayi yadubi kowa sannan yace. "Lokaci na kurewa, gashi a yau nakeson mukoma Kano, amma akwai abu guda daya danakeson sanar daku. A ranar da Mustapha ya warke daga ciwon dayayi, naje masallaci bayan an idar da Sallah nasamu liman mukayi magana akan wata bukatata,liman ya amincemun. batare da wani bata lokaciba nasa aka daura auren *MUSTAPHA da MARYAM* ni nayi waliccin mustapha,liman yayi na Maryam, tsirarun mutanen dasuka rage a masallaci suka zamto shaida"...........✍️ *By* *zeey kumurya* *4️⃣9️⃣* *Bismillahirrahmanirrahim* ..........A razane Maryam ta dago ta kalli daddy zuciyarta na tsananta bugu tamkar zata faso kirjinta ta fito. gabadaya yawun bakinta kafewa yayi,kallon daddy take a matukar razane, kana ganinta kasan a matukar rude take dajin al'amarin. shiko mustapha lumshe idonsa yayi cikin yanayin da baze misaltuba. cikin tsananin farin ciki ammi tace. "Kaii, Masha Allah Alhaji, Allah yasanya albarka Allah yasa hadinnan yazame mana alkhairi, kai Masha Allah, amma naji dadi sosai Ubangiji ya tabbatar da alkhairi yabasu zaman lafiya da zuri'a dayyiba" "Ameen" Aunty ma kallon daddy kawai takeyi cike da dunbin mamakinsa bata taɓa tunanin abunda ze fadaba, kenan. amma kuma taji dadin wannan hadin da yayi sosai, dama kalar matar data dace da Mustapha'n kenan ba kalar su suhalat ba. tasan Maryam bazata taɓa bawa daddy kunyaba da yardar Allah. Aliya kam se murmushi take saki, najin dadi dakuma na shakiyanci ganin yanda Maryam duk tabi ta firgice. gashi kuma sun bala'in dacewa seyanzuma take ganin haka. sotake su hada ido da Maryam,amma ta sunkuyar dakanta. Maryam Sarkin kuka, se hawaye takeyi tarasa na farinciki ne, kona me?... gashi dai zuciyarta ta jima da kamuwa da kaunarsa, amma kuma hada aurensu da dady yayi yazo mata a wani irin yanayi na fargaba da tsoro. Daddy kam, nazarin Maryam kawai yakeyi yasan ya mata katsalandan acikin rayuwarta, shikansa yasan be kyauta mataba. besaniba kotana da wanda takeso. Amma shi yanada dalilin dayasa ya aura mata Mustapha'n, kuma yana fatan aurennasu yazamo musu alkhairi gabadayansu. cikin sanyin murya me nuni da rarrashin wanda akewa maganar daddy yafara mata magana. "Maryam! Bansan da kalmomin dazanyi amfani dasu gurin baki hakuriba akan wannan auren dana miki batare da yardarkiba, a matsayina na wanda bakomai bane a gurinki, amma duk da haka lokaci bekure mikiba, idan har kinga zaki cutu, kokuma kina ganin natauye miki wani hakki na rayuwar ki, karkiji komai ko wani nauyi ko kunya, tunda rayuwarkice. kifadamun idan bakyason aurennan, kamar yadda nasa aka daura yanzu senasa a warwaresa." Ajiyar zuciya nasauke, kaina na kasa bandagoba. kukan dake kokarin kufcemun na danne nace. "Babu komai daddy, aikaima ka isa dani, insha Allahu zanmaka biyayya gwargwadon iyawata bazan baka kunyaba" daga haka nayi shiru a raina ina fadin, "tayaya zan yarda a warware wannan auren da....." "Masha Allah, haka nakeson ji Allah yamiki albarka, yabaki yaya masu biyayya kamar yanda kikamun" daddy yakatsemun tunani da fadin haka. Addu'a sosai daddy yaita kwararawa mustapha da Maryam. kowa nagurin sesawa auren albarka yakeyi. nikuwa nayi shiru ina saurarensu jinakeyi tamkar mafarki nake zan farka wani lokaci. sonake na kalli fuskar gogannawa naga a wanne yanayi yake ciki amma nakasa. Ammi ko se kara rungumeni take ajikinta. Mustapha kuwa ko kwakkwaran motsi beyiba, miskilancinsa kuwa baze bari kagane yanayin dayake cikiba game da maganar aurannashi..... Sallar da aka shiga a masallaci ta tarwatsa zaman, dady da Mustapha suka nufi masallaci. Aunty tana da alwalarta,dadduma kawai zuhura ta kawo mata tatada sallah a falon. Maryam da aliya ne suka shiga daki domin yin Sallah. zaune suke akan darduma bayan sun idar da Sallah. "Mairota how market?" Aliya tafadi haka tana kwashewa da Maryam da dariya, ganin yadda take komai jikinta asanyaye. banza Maryam tamata bata kulataba, dan ita haryanzu zuciyarta takasa yarda wai yanzu aure yashiga yatsakaninta da *heart beat* dinta. matsowa jikinta Aliya tayi ta fara mata magana seriously. "Wlh Maryam, kinyi dace da miji bakadanba domin yaya Mustapha irin mijin dakowacce mace zataso ta mallakeshine, amma ke nasan mene damuwarki akan wanan aurennaku. abu na farko dake damunki saboda kina da wanda kikeso wato yaya Sadiq, na biyu kuma kina tunanin yanda zakiyi rayuwa da wanda baya sonki" da mamaki Maryam ta kalli aliya, tamkar ta shiga zuciyarta dan abunda aliyan tace shine abinda take ta tunani tun dazu. daga mata gira aliya tayi tace, "koba haka bane" numfashi na sauke nace. "Hakane aliya, ni namafi tunanin yaya Sadik, dan yana matukar sona nasan bakaramin tashin hankali ze shigaba idan yaji wannan abun" "gaskiya abun babu daɗi rana daya arabaka da masoyinka dake da yaya Sadik dole zaku shiga damuwa, daman, amma kuma hakuri zakuyi dan bamusan alkhairin dake cikin wannan aurennakuba. shikuma yaya Mustapha kisha kuruminki, dan idan ana kuka akan soyayya seya miki shaɓe_shaɓe har da gunji, nina fada miki kuma." "Hmmm, aliya kenan bana tunanin haka agurinsa tunda shima kinsan yana da wadda yakeso,kawai babu yanda zeyine" tabe baki aliya tayi tace. "Wai ant suhalat kike nufi, tabb aiba wani sonta yakeba,kawai biyayya yayiwa mommy yake kulata, banda haka mezeyi da wata suhalat mace ba kamun kai" shiru namata domin nikadai nasan halin da zuciyata take ciki. baki aliya taita bani akan aurennan da dady yamun tana tausata. batasan nafi kowa murna da aurannanba kawai dai fargabata daya yanda zamuyi tarayya matsayin miji da mata dashi,nasan akwai ja. daga karshe kuma seta koma tsokatana wai zanyi fama da miskilancinsa. Ammi ce dakanta tazo takiramu domin Muci abinci. Da kyar daddy yayarda su tsaya suci abincin dan da cewa yayi tafiya zasuyi, mama ta masa magiyar yabari su kwana da safe sesu wuce, amma yace mata hakan baze yiyuba. Domin bakaramin ayyuka ne agabansaba, dan missed called din dake wayarsama kadai ya ishe sa, ga harkar kasuwancinsa yanaso gobe yakoma acigaba da daga inda aka tsaya. kadan sukaci abincin kowa yace yakoshi, Maryam kam batafi lauma biyuba tace takoshi. Mustapha kam beciba, Aunty ce tacewa ammi haka yake, bedamu dacin abinciba sedai coffee ko tea. ammi bata bata lokaciba ta shiga kitchen ta dafa masa hadadden shayi dayaji kayan hadi, ta kawo masa. tamkar zata bashi a baki saboda kauna. kafin isha'i su dady sungama shirinsu na tafiya. ammi tacikasu da kayan su bagaruwa da dabino datazo dasu daga Saudiyya, suna kewar juna sukayi sallama,bayan sunyi musayar numbobin juna. Maryam se kwakube Aunty take, batasan anan za'a bartaba tunda mijinta bandashi za'a tafi ze zauna gurin mahaifiyarsane. Afarfajiyar gidan Aunty ta tsaidata da fadin. "To, Maryam saduwar alkhairi, insha Allahu gobe kafin na koma kd, zanje gidan gwaggonki na mata bayani, inda halima har kauyennaku semuje da yaya suma mumusu bayani" Maryam bata amsawa Aunty ba, se kuka data fashe dashi tare da riketa. tausayintane yacika Aunty, aliyama se hawaye na tausayin maironta. rungumeta Aunty tayi tana bubbuga bayanta alamun lallashi. cikin kuka tace. "Aunty dan Allah nidai zan biki mutafi" duk dauriyar Aunty seda kwalla ta cika mata ido, domin itama bakaramin missing Maryam zatayiba. maida kwallar data cika mata idon tayi tadago da Maryam daga jikinta. cikin lallami tace mata. "Kiyi hakuri diyata, ai zandawo nanbada jimawaba, kuma aikinyi sabuwar mommy, gaki ga amminki zata miki fiyema da abunda zanmiki, kikwantar da hankalinki kidena damuwa, idan kuma mukayi waya da ammi tacemun kina damuwa tobazanzo intafi dakeba." Aunty ta karashe zancen tana sharemun hawayen fuskata. gyada mata kai nayi alamun gamsuwa. Addu'ar fatan nasara ta mun. rungume juna mukayi da aliya cikin shaukin juna muna kuka, da kyar Aunty ta rarrashemu muka yi shiru. harta juya zata tafi nace mata. "Aunty yaya Sadik fa, inajin tausayinsa." maganar Maryam karaf a kunnen Mustapha daya baro gurin daddy, yazo sukara yin sallama da Aunty. "Karki damu Maryam, nasan mezance masa dabaze damuba" Aunty tafadamun haka tana kallon Mustapha. cikin karayar zuci najuya nakoma cikin gidan dazan fara sabuwar rayuwa a cikinsa,jikina a matukar sanyaye. a zaune nataddasu dukansu a falon sunata maida zance. kaina na kasa na musu sallama, gefen Aunty zuhura datake bawa yaronta nono na zauna. jana ammi da mama suka shigayi da hira duk dan insaki jiki dasu musammanma ammi. seda kusan mintuna 20, suka shude sannan ya shigo falon, bakinsa dauke da sallama. amsa masa mukayi gaba-daya, ammi fuskarta dauke da fara'a ta nunawa mustapha gefenta yaje ya zauna. kallo daya zakayiwa ammi katabbarta da tana cikin tsananin farin ciki. fuskarta cike take da annuri, tarasa ina zata tsoma kanta saboda jindadi da murna. harta kira mahaifiyarta da kaninta tasanar musu. kaninta yace ze kirata anjima ta video call suga mustapha. muna zaune a falon Saddam da mijin A'isha suka shigo. suna zama mama tafara rattaba musu bayanin abunda yafaru........... *KANO* Yau suhailat da wani matsananci ciwon kai da zazzaɓi tatashi. jikinta gaba-daya rawar dari kawai yakeyi. misalin ƙarfe 11 na safe mommy tashigo dakin datake tana fadin. "kinanan kina wannan shegen baccinnaki na jaraba ko? kinsandai nan bagida bane babu masu aiki, kitashi kifito kimun shara." Wasu hawayene masu zafi suka zubowa suhailat, ita kadai tasan azabar datakeji ajikinta amma mommy tashigo tana mata masifa, duk mommy tabi ta canza mata yanzu kullum se fada da masifa, kamar ita tadora mata damuwar dake damunta. kan gadon datake mommy ta karasa da nufin tatasheta. tana dora hannu ajikinta taji zafi zau. "suhailat bakida da lafiya ne?" suhailat bata bata amsaba, hawa gadon mommy tayi ta janyota jikinta. da sauri suhailat ta janye jikinta daga na mommy, saboda kamshin turarenta data shaka bemata dadiba. kafin tayi wani yunkuri tuni wani amai yataho mata, kokarin sakkowa tayi daga kan gadon kafafuwanta kawai ta zuru aman ya kufce mata, ta fara kelayashi a nan bakin gadon, tamkar zata amayar da kayan cikinta saboda azabar aman, se haki takeyi tana kelayashi. kallonta mommy tayi cikin wani irin yanayi na alamar tambaya. gaba-daya suhailat din ta canza mata, jikinta har wani yalo yakeyi tsabar fari, ga cika data kara sekace wata matar aure, seyanzu ta lura da hakan. jan jiki tayi takoma kan gadon ta kwanta tana sauke numfashi,bayan aman ya tsaya mata. "Sannu" mommy tace mata adakile. dole ta mike tahau gyara gurin tanayi tana tsaki, bayan tagama gyara dakin ta gogeshi tass. ta dakko room freshener ta hau fesawa. suhailat na shaka wani aman yakara taso mata, da gudu tatashi tanufi toilet ta fara kakari. tsayawa mommy tayi cak tana kallonta zuciyarta cike da fargaba gami da wasiwasin meke damun suhailat din take ta kwara amai haka. wani tunani tayi dasauri tafice daga dakin taje dakin datake taɗauki wayarta takira likitanta ta mata bayani atakaice. Address din gidannata ta tura mata. da rarrafe suhailat ta fito daga toilet din, jikinta gabadaya ya mutu babu kwari kokadan a bakin toilet din ta kwanta, domin ko kan gadon bazata iya karasawaba. mommy data shigo taganka a haka tana numfarfashi se tausayinta ya tsirga mata. dagata tayi ta kaita kan gado ta kwantar, suhailat kam se toshe hanci take dan batason turaren mommy kokadan daga mata hankali yakeyi bakadanba. yanda jikinta yayi zafi zau se mommy ta rage mata kayan jikinta, towel ta dakko da ruwa ta daddanna mata ajikinta, se zafin jikinnata yaragu,amma se rawar sanyi take. lulluba mata blanket mommy tayi bajimawa bacci yadauketa. fita mommy tayi tafara rage ayyukan gidan. wajen 12/30 doctor din tazo. Bayan sungaisa mommy tamata jagora zuwa dakin, har lokacin suhailat baccinta takesha. duddubata ta shigayi, tanayi tana tambayar mommy yanayin yanda taga jikinnata. jininta ta diba tace, zataje asibiti ta auna seta dawowa da mommy da result din. godiya mommy ta mata, sukayi sallama ta tafi...........✍️ *By* *zeey kumurya* *ABINDA KASHUKA....* *5️⃣0️⃣* *Bismillahirrahmanirrahim* .........A ɓangaren Sadik kuwa yau da wani matsanancin ciwon kai yatashi wanda ko idansa yakasa budewa saboda azabar ciwon kan, hakanne yasa besamu yafito ganin Maryam ba, kamar yadda yaci alwashi jiya. daga ciwon kai jikinshi gaba-daya yaɗauki wani irin zafi, da kyarma. tun yana iya sanin duniyar dayake ciki harya fice daga hayyacinsa........ ******************** *DARMANAWA* Saleemat ce zaune adakinta da waya a hannunta yau wurin sati guda kenan tana trying number'n Maryam amma a kashe. cikin takaici tafito daga dakinnata ta nufi dakin umma. ''umma wlh haryanzu wayartata a kashe, kuma su ba matsalar NEPA ba, bare nace caji ne babu a wayartata." saleemat ta fadi haka bayan ta daga labulen dakin. umma tana dubanta tace, "toko matsalar network ne, saleema?" "gaskiya umma bana jin network ne, wayarce dai a kashe" "to Allah yasa dai lafiya" "lafiya kalauma insha Allah, nafi tunanin wayarce ta samu matsala" "to Allah yasa muji Alkhairi" "Ameen, umma bari nakarasa ninkin danakeyi naje gidan gwaggo nasanar mata dakaina" murmushi umma tayi tace, "saleemat ba kunya, kawo kayan lefennaki zaki fada mata da kanki" dariya saleemat tayi tace, "Aiso nake na kunnota kwana biyu shiruma banjitaba" umma tace, "nimun hadu da ita jiya, dana fita, naga tanata sauri ne, shiyasa banfada mata kawo kayan ba.".... Gwaggo tana zaune adakinta tanata lissafe kudinta na adashi dana aikatau din Maryam. tanayi tana mitar sabon wata yashiga amma shiru bataji alert na aikatau din Maryam ba, gashi tanata kiran number'n lami bata shiga. sabuwar me aikin datayi me suna laure ce tashigo dakin ko sallama babu. zabura gwaggo tayi tashiga boye kudin akasanta. tana fadin, "ubanme yashigo dake dakina babu sallama, kinga laure kikiyayeni" tabe baki lauren tayi tana jijjiga kafa tana jifan gwaggo da kallon raini tace. "Kekika sani dai, uwar mako da rowa, wannan uban tumulin kudin ina kikasamoshi gwaggo?" cikin harzuka gwaggo tace, "bansaniba uwata, nace bansaniba, kujimun yarinya da fitsara haifata kikayi dazakizo ki titsiyeni da tambaya, to a gidan uwarki nasamo" "badai uwataba gaskiya" laure ta fada tana kauda kai gefe. "bazan kulakiba dannasan uwarki bata baki cikakkiyar tarbiyyaba, ina fatan kingamamun ayyukana. "Cabb, wannan uban ayyukan sekace wata jaka, nayidai iya abinda zan iya" rike haba gwaggo tayi tace, "aa..lallai laure rashin kunyartaki kullum kara gaba take to wlh baki isaba sekinmun duka ayyukan gidannan, zandinga biyanki kudin aikine a banza bakyamun aiki yanda Yakamata. wani kallon banza laure tayiwa gwaggo sannan tace. "Nawane kudinnaki da har kikemun iko akansa, akan 20,000 din dako kayan kwalliya bata isata na siya" "kinsan da haka meyasa kikazo mun aikin, Ai da sekiyi zamanki uwarki ta dinga baki" laure zatayi magana wayarta dake kan cinyarta tayi kara, fita tayi domin ta daga wayar. gwaggo ta bita da harara. kullum sesunyi sa'insa da laure, yarinyar da inda ta haihu setayi jika da ita. amma ta rainata laure bata da tarbiyya kokadan, duk fadan gwaggo da masifarta laure tafi karfinta, duk iskancin dataga dama shitakeyi kuma gwaggo bata isa ta hanataba sedai kallo da ido. kullum se gwaggo tashiwa Maryam albarka tana cewa, "yarinya me biyayya da hakuri bakamarkiba laure" a duk sanda gwaggo ta fadi haka se laure tatabe baki tace da gwaggo. "To kinsan da itan kika daukeni, kije ki dawo da ita mana" a kauye lami tasamowa gwaggo laure, dududu batafi wata da zuwaba amma ta gallabi gwaggo, ga yawon bin samari. gwaggo tanata cigaba da lissafinta na kudadenta, zuciyarta fari kal kamar takadda tatara kudin komawa Saudiyya. Ashe fitar da laure tayi tana waya, wani saurayinta ɗan daba ne yakirata wanda sukayi magana tun jiya zasuzo da abokansa suyiwa gwaggo fashi. tunda ta kyallara ido taga kudin gwaggon takirasa ta fada masa, amma da sharadin bayan sun kwaci kudin itama zebata nata kason. Bayan befi 40 minutes ba, suka karaso unguwar. Laure ce tafita dakanta ta tarosu ta musu jagora har kofar dakin gwaggo.(fashi da ranar Allah🤔) Gwaggo kawai jitayi an banko mata daki anfado babu ko neman izni, susu biyarne. suka tsaya mata cirko_cirko ai. zabura tayi, ta mike tsaye tare fadin. "Subhanallahi suwaye ku, wadannan samudawa daku zaku shigomun gida har daki. lafiya?" daya daga cikinsune yace, "lafiyar ce takawo haka" wuka da yafito da ita daga aljihunsa tare da karbar wani mulmulallen karfe a hannu wani yana muzurai yacewa gwaggo. "Ki bamu kudin dake cikin gidannan ta lallami kokuma na fardeki na kwata" "wanne kudi kuma, uwarku ta bani ajiyan...." "Ke!" wani daga cikinsu yadaka mata da tsawa yana zaro wuka shima daga aljihunsa yana nuna gwaggo da ita. duk da gwaggo ta tsorata amma bakinta be mutu ba, kuma tace kome zesu mata bazata basu dukinba. ganin tana bata musu lokaci, wanda ya mata magana da farko ya kwada mata ƙarfen hannunsa akafa sau biyu, gwaggo ta hau ihu tana neman taimako. Toshe mata baki sukayi sannan suka datsa mata wuka agefen kafadarta, ga azabar yanka gata rufe mata baki da hanci da sukaimata, nanfa numfashinta yafara sarkewa daga karshema se numfashin ya dauke dif. Kasan gadonta kawai suka daga sukaga kuɗin acikin leda babba sekuma wani a cikin tarkacen kwanukanta, seda suka kwace kuɗin gwaggo kaf, ko sisi basu barmataba sannan suka tsallaketa suka fice. suna fita laure tabi bayansu da kunshin kayanta dama tagama hada komai nata. Saleemat bayan tagama abunda take tayi wanka ta nufi gidan gwaggo. tundaga soro take zuba sallama amma taji shiru, tsayawa tayi a tsakar gida dan basa shiga dakin gwaggo. sallamar tacigaba dayi amma taji shiru. kofar banɗaki ta kalla taganta abude babu kowa a ciki. "Ko gwaggo batananne?" Saleemat ta tambayi kanta. amma kuma ai ko fita zatayi tana rufe dakinta koda tabar gidan abude. dakinnata ta shiga da sallama dauke abakinta, atunaninta ko gwaggo bacci take. yanayin dataga gwaggo bakaramin firgitata yayiba, kwance taganta baki a daure cikin jini, ga dakinta duk a birkice. cikin kidima ta fice da sauri taje ta sanar da umma, tare suka dawo gidan da umma. bakaramin gigita ummantayiba itama, fita tayi tasamu wani makocinsu ta masa bayani, saboda suna ganin girman umma mazan unguwar shiyasa ya yarda ya shiga gidan gwaggo amma badan itaba. hankalinsu umma a tashe ta kira baban saleema ta fada masa halin da'ake ciki. Napep aka samu akasaka gwaggo aka nufi asibin AMINU KANO da ita............. Likitar mommy bata dawo kawo mata result dinba seda yamma bayan ta tashi daga aiki, kafin tazo suhailat tayi amai yakai sau hudu, kuma taki cin komai, amma zazzaɓin jikinnata yasauka, se Rashin kwarin jiki kawai kedamunta, har wanka ta iya yi da kanta. likitan ta girgiza dataga abun dake damun suhailat din. Jiki a sanyaye ta nufo gidan mommy, gaisawa sukayi da mommy dake zaune a falo tana waya, sannan tatambayeta ina suhailat ta nuna mata dakin datake da hannu. suhailat na kwance, Dr ta shigo dakin da sallama. Amsa mata tayi tare da yunkurin tashi zaune. "Sannu patient ya jikinnaki? cewar Dr, bayan ta zauna akan stool din mudubi. tace "Da sauki Dr," "Masha Allah, yanzu i nane yake miki ciwo?" Dr, tatambayeta tana tsareta da ido. Tana yamutsa fuska tace, "kaina sekuma jikina da babu kwari inajin kasala sosai, sekuma jiri da tashin zuciya" Dr, tace. "Sannu, yaushe rabon dakiga period ɗinki?" dan jimm suhailat tayi tace. "Gaskiya namanta" "ohk, bari nasa Miki drip dinnan" Dr, ta fadi haka tana janyo jakar kayan aikin datazo dasu. Allurai taiwa suhailat na tsaida aman, sannan tasa mata karin ruwa. magunguna ta rubuta tabawa suhailat. addu'ar Neman sauki tamata sannan ta fice daga dakin cewa zuciyarta cike da tausayinta. Har lokacin mommy bata gama wayar datakeba. zama tayi taɗan jira mommy'n. katse wayar mommy tayi badan ta gamaba sedan ganin Dr ta fito. tace "Sannu Dr, harkun gama?" Dr, tace "Ehh, Hajiya namata allurar tsaida aman nakuma samata ruwa" "ok, babu magungunan daza'a siya?" "Akwai na rubuta nabata" "yawwa Dr, Nagode, amma babu kuɗi cash a hannuna, amma insha Allah anjima zanmiki transfer" "babu komai Hajiya, nizan wuce, ga result ɗin abunda ke damunnata" Dr, ta fadi haka tana mikewa. karba mommy tayi ta'ajiye akan kujera batare data dubaba, kokuma tatambayi Dr, abunda ke damun suhailat dinba, hankalinta nakan wayar dasukeyi ita da Binta akan zuwansu gurin boka gobe. sallama sukayi da Dr, tafice. daukar wayarta mommy tayi takira Binta suka cigaba da maganarsu........ Su dadddy sun sauka a garin Kano lafiya. daddy zuciyarsa fess yakejinta yau yasauke dakon dake kansa na shekaru masu dama. Aunty a part din su baaba talatu ta sauka, anan sukayi sallah itada Aliya,baaba talatu ta kawo musu abinci sukaci sannan Aunty tatara ma'aikatan gidan mata tace musu za'a sallamesu gobe, badon sunyi lefin komaiba. amma za'acigaba da biyansu albashinsu, godiya sukayiwa Aunty duk da basusan dalilin hakan ba. abunda yasa Aunty tayi haka, a ganinta bedace suci gaba da zama agidanba tunda babu mata a gidan, bazeyiyu su zauna daga su se ya'yan gida da megidaba. seda suka kebe a daki sannan Aunty tayiwa baaba talatu bayanin abunda yake faruwa atakaice kamar yadda ta bukata. sosai baaba talatu tacika da rudu, da al'ajabin wannan abu. Amma batayi mamakiba dantasan halin mommy ciki dabai. amma bata taɓa zaton ba ita tahaifi Mustapha ba. Aunty tana fitowa daga part din su baaba talatu ta nufi part din su Sadik, dan yau ta kudurcewa ranta seta ganshi taga halin dayake ciki, ai hannunka baya taba rubewa ka yanke kayar. su faruq duk suna part din daddy. knocking din dakinnasa ta shigayi, data murda handle din tajita a rufe. bubbuga dakin taitayi amma bebudeba, dole ta hakura ta kyaleshi. part din daddy ta zarce, nan suka hadu sukaita hira dasu faruq cikin nishadi, daddy da Aunty nabasu labarin abunda yafaru a jos. sunyi farin ciki sosai dajin yayansu yahadu da mahaifiyarsa. Amma fa zasuyi missing yayansu sosai............✍️ *Kuyi manage da wannan, muhadu gobe idan meduka yakaimu* *By* *zeey kumurya* *ABINDA KASHUKA....* *5️⃣1️⃣* *Bismillahirrahmanirrahim* ...........Mommy bata tashi duba result din da Dr, ta kawo mataba se bayan magriba. wani irin zabura tayi ta mike tsaye daga zaunen datake lokacin da taga abunda ke rubuce a jikin takardar. gani tayi kamar idontane benuna mata daidaiba, dakinta ta nufa da sauri ta dauki glass dinta ta saka sannan ta kara duba takardar abunda tagani da farko dai shita kara gani, da sauri ta fito falo hartana tuntube ta dauki wayarta tayi Dialing number doctor, ringing uku Dr, ta daga da sallamarta. batare da mommy ta amsa mataba tace: "Dr, Rahila yanaga wani result daban gane masaba, kodai bana suhailat din bane?" Cikin girmamawa Dr, tace. "Hajiya shine mana, natane" mommy na haki tace, "to ai bangane meke damunnatabane kimun bayani yanda zangane" numfashi Dr, taja tace: "Hajiya am sorry to say suhailat na dauke da ciki na tsawon sati shid......" "What" mommy ta katseta cikin karaji tare da yarda takardar hannunta. "Dr, kinsan mekike fadamun kuwa, suhailat din tawace take da ciki?" "Yes mah" abinda Rahila kawai tace mata kenan dan ta san duk bayanin dazatayiwa mommy a yanzu baza ta taɓa fuskantartaba. batare da mommy ta kashe wayarba ta cillar da ita akan kujera tanufi dakin suhailat da saurinta. suhailat tana kwance tana tunanin Mustapha wanda kewarsa ta cika mata zuciya ta hanata sukuni. turo kofar dakin da mommy tayi da karfi yasata tashi zaune a firgice, gabantane yayanke yafadi ganin yanayin mommy'n. cikin tsananin bacin rai mommy tafara magana, "suhailat! nizaki kunyata, ki tozartani a idon duniya, ubanwa ya miki ciki?" Rasssss gaban suhailat yayanke yafadi cikin rawar murya tace. "Mo..mo..mmy cik..ciki kuma?" wani mugun kallo mommy'n ta watsa mata sannan tace. "Rahila zata miki karya ne, kuma yanayin ciwonkima kadai ya isa ya zama shaidar kina da shigar ciki, kifadamun ubanda ya miki ciki kafin na illataki yanzunnan" runtse ido suhailat tayi cikin tsananin tashin hankali, wata mahaukaciyar bugawa kirjinta yashiga yi. "Nashiga uku, yanzu idan yaya naji labarin cewa nayi ciki ze aureni kuwa?" ta fadi haka hawaye na zubo mata. cikin tsawa mommy tace. "Ina tambayarki uban da ya miki ciki, keta wani banzama can kike ko?" cikin kuka suhailat tace. "Kamal ne" "kamal" mommy ta maimaita cikin tsananin mamaki. jijjiga kai kawai mommy takeyi kafin tayi kwafa ta fice daga dakin. kuka sosai suhailat ta fashe dashi, ita zancen ciki betada mata hankaliba kamar yadda take tunanin rasa Mustapha, domin idan har yaji wannan labarin tasan maganar auransu ta rushe, danyasha fada mata yatsani zina kuma yatsani mazinaci!.......... mommy tana zaune a falo ta rafka tagumi abun duniya duk ya isheta, kullum seta Kira layin Sadik amma bata samunsa. gashi gobe da sassafe zasu tafi Niger ita da Binta, tana son neman shawarar Binta akan cikin dake jikin suhailat amma kuma batason tonawa kanta asiri dantasan binta bata da sirri, zuwa zatayi tayita yamadidi da ita a cikin kawayensu. shawara ta yanke kawai suna dawowa daga Nijar din zata kai suhailat a zubar mata da cikin, tunda Binta tace baza su wuce sati daya ba zasu dawo. da wannan tunanin taji zuciyarta ta dan mata sanyi akan damuwar datake ciki.......... kusan raba dare su Aunty sukayi suna shan hirarsu cikin nishadi, kokadan su haidar basuyi zancen mommy ba. se Aunty cema tace musu yakamata zuwa yanzu ace sunnemeta sunji halin datake ciki, dan kome mommy ta aikata mahaifiyarsuce matsayinta baze taba canzuwa a gurinsuba. sukace mata da safe insha Allah, zasu kirata........ *JOS* Sallar isha'i ce ta ta tashemu, bayan an idar muka dawo aka cigaba da hira. se kusan karfe biyu na dare sannan kowa ya nufi part dinsa, ashe part din da muke zaune na ammi ne. falo ne da dakuna uku, kowanne da toilet a ciki. Dakinta ammi tace naje na kwanta a kan gado. shikuma Mustapha ta bude masa wani dakin, da kanta ta share masa ta gogeshi tass, sannan ta sakamasa turaren wuta me dadin kamshi, a darennan seda ta wanke masa har toilet, duk da yana cewa tabarshi dare yayi da safe a gyara amma ammi tace a'a baze kwana A cikin dattiba. wanka nayi a toilet din ammi, kafin na fito ammi ta'ajiyemun wata rigar bacci sabuwa mara nauyi. rigar kawai nasaka kawai na kwanta saboda ciwon kan dake damuna, ga wani irin bacci danakeji. Mustapha yau yana cikin tsananin farin ciki, mara misaltuwa yanda ammi takeyin nan_nan dashi yafi komai yimasa dadi. dakin ya shiga da sallama bayan ammi tagama gyareshi, tsaf dashi dakin setashin kamshi kawai yakeyi. kayan jikinsa ya fara ragewa sannan ya shige toilet yayi wanka tare da dauro alwala. idanuwansa yau a bushe suke ko baccinma bayaji saboda farinciki, a gefe guda kuma zuciyarsa cike take da kewar yan'uwansa. dan yasan ammi bazata barshi yakoma Kano nan kusaba. tsayawa yayi a gaban madubin dakin yana tsane sumar kansa, tunanin abunda zesa a jikinsa yayi, dan gaskiya baze iya maida kayan daya cireba. Kwankwasa kofar dakin da'akayi ya katse masa tunaninsa. batare da yayi maganaba yaje ya bude kofar, ammi ce tsaye hannunta dauke da wata leda, dama yasan itace, murmushi yamata kamar yadda itama shine dauke akan fuskarta. "Sannu ammi, yakamata kije ki huta haka dare fa ya raba" yafada mata cikin sanyin murya. murmushi ta masa tace, "to shikenan Muhammad, baka bukatar wani abu?" Yace, "saidai abun sallah" mika masa ledar hannunta tayi tana fadin, "bari na dakko maka" karba yayi yajuya ya koma ciki. ledar ya bude ya duba, jallabiyace guda uku masu kyau, se tashin kamshi suke ammi ta feshesu da turare. murmushi yayi cikin tsananin jin kaunar ammi a ransa ya dauka guda daya ash colour yazira a jikinsa. ammi ce tashigo dakin da sallama ta ajiye masa daddumar a gefen gado. "Thank you real mom" murmushi ammi tayi me sauti dajin abunda yace. tana murmushin tace, "kana da fake mom ne?" murmushi yayi shima amma bebata amsaba, ya zauna a gefen ta tare da kwantar da kansa akan kafadarta. shikadai yasan irin dadin dayakeji idan ya rabi jikin ammi, yanajin dama karta tafi ta zauna su kwana tare, itama ammin hakanne anata bangaren bataso tabar gudan jininnata a halin yanzu shiyasa tun dazu takasa zuwa ta kwanta. tana shafa lallausar sumar kansa tana masa tambayoyi akan wasu abubuwa na rayuwarsa da suka shude, tun yana bata amsa har bacci ya daukeshi ajikinta, bacci me cike da nutsuwa daya manta rabon dayayi kamarsa. a hankali kamar wani jariri ammi ta lallaba ta kwantar dashi tare gyara masa kwanciya. kana kallon yanda yake baccin kasan cikin kwanciyar hankali da jindadi yake yinsa. Addu'a ta tofa masa, sannan tayi kissing goshinsa da kumatunta. seda ta rage masa hasken dakin sannan ta fice cikin shaukin dannata. sanda ta koma dakinta Maryam ta jima dayin bacci, wanka tayi itama sannan tafito tafara jero sallah domin nuna godiyarta ga Allah...... Har aka fara kiraye_kirayen sallah ammi bata runtsaba tana kan sallaya tana rokarwa danta addu'oin samun dacewa duniya da lahira. seda akayi kiran assalatu sannan ta mike. kan gado ta nufa inda Maryam take a kwance tanata sharar baccinta tafara tashinta a hankal tana kiran sunanta. A hankali Maryam ta bude idanta dake cike da bacci. "Diyata ki tashi lokacin sallah yayi" daga mata kai Maryam tayi tana kara lumshe ido kamar zata koma baccin. falo ammi tafita domin tatashi Mustapha shima, tana tura kofar dakin taga bayanan se motsin ruwa dataji a toilet, juyowa tayi takoma daki tunda yatashi. da kyar na iya tashi zaune, saboda baccin be isheniba. nina manta a inda nake, seda na watstsake na tuna, hakan yatabbatarmun da abunda yafaru jiya ba mafarki bane gaske ne, dan da kokwanto a raina na kwanta bacci musammanma aurenmu da *heartbeat* nafijin abun tamkar almara. toilet na shiga nadauro alwala, hijabi ammi tabani na zira na tada sallar. Bayan mun idar nadanyi lazimina nadubi ammi nace, "ina kwana ammi" da fara'a tace. "Lafiya kalau, ya kwanan bakunta?" "Lafiya kalau" na'amsa cikin jin kunyarta. hira ammi tashigamun tare mun tambayoyi akan rayuwata cikin hikima nikuma ina bata amsa. seda gari yafara haske sannan ta tashi ta fita. Tana fita nima na mike nashiga gyaran dakin, duk da babu wani datti a cikinsa se tashin kamshi dayake, bayan nagama na wanke toilet tass sannan nafita falo. Ammi bata falon kuma bata kitchen tanacan sunashan hira da danta. (Allah Sarki uwa mai dadi, Allah kajikan iyayenmu😥🙏.) nariga nasaba da aiki idan na tashi da safe shiyasa duk randa banyiba se injini wani iri. kitchen din na shiga, dan babbane komai tsaf an killakeshi a mahallinsa, kayan da akaci abinci jiya da daddare su nahada na shiga wankewa, dan jiya hira bata bari anyi wanke_wankenba. Ina cikin yi ammi ta shigo ta sameni, kama baki tayi tare da fadin. "Diyata wayasaki aiki, na shiga dakima naga kin gyara shi fess, yanzu kuma shine kikazo kika kama wanke_wanke, aida kinbarshi nima zanyine kokuma zuhura idan tashigo setayi, dan ma umaimah batananne amma ita takeyi base kin wahalar da kanki ba." murmushi nayi amma bance mata komaiba, danni banga abun wahalarwaba. da kyar ta barni na karasa amma da cewa tayi sedai na barshi ta karasa. Wajen karfe tara Aunty zuhura ta kawo mana lafiyayyen abinci na breakfast ammi da kanta ta zubamun ta dibarwa danta nasa takai masa daki, nidai har lokacin bamu hadu dashiba, inason inje ingaisheshi amma kuma nakasa. Ammi abayoyi da jallabiyoyi take saidawa, kaninta yana turo mata daga Makkah kokuma intaje ta taho da wasu. Dilar datazo da ita a wannan zuwan datayi ita ta kunce, ta dibarwa Maryam abayoyi da yawa kafin a aiko mata da kayanta. shima Mustapha ta dibar masa jallabiyoyi. bayan nagama cin abinci nayi wanka na shirya cikin wata abaya me kyau a cikin wanda ammi ta kawomun, na yane kaina da mayafinta. ammi tace in fito muje mugaida mutanen gidan. se'alokacin muka hadu dashi, kaina a kasa nagaisheshi bayabo bafallasa ya amsamun. Part din mama muka fara zuwa mukagaisheta sannan part dinsu aunty zuhura, nasu matar da daddy yakadene na karshe. Bayan mundawo part din ammi, mukayi waya da Aunty tatambayeni babu matsalar komai nace mata babu, ta kara jaddadamun anjima zataje gidan gwaggo ta fada mata, nace dan Allah idan taje ta hadani da ita a waya. daga baya Aunty tabawa Aliya wayar mukasha hira tanatamun shakiyancinta da barkwancinta.......... *KANO* Mommy tun sassafe suka doka sammako suka wuce nijer, bayan ta dokawa suhailat uban warning akan ko kofar gida kartayi gigin lekawa, kuma karta fadawa kowa tana ciki koda wasa, tasa asamo mata wadda zata dinga kula da ita, anjima zatazo. mommy ta a jiyewa suhailat ishashshen kudi da kayan abinci daze isheta kafin ta dawo. Likitoci basu karbi gwaggo ba, seda aka kira dan sanda sannan suka karbeta. inda suka kwada mata karfe a kafa ta samu karaya a gurin, sun mata dori sannan kuma suka mata ɗinki a kafadarta inda suka yanketa da wuka, anmata karin jini kuma saboda jinin data zubar. Duk abinda aka bukata na kuɗi kona wani abun, baban saleemat da umma ne sukeyi. Allah yatakaita barayin basu tafi da wayar gwaggo ba, da ita aka kira yan'uwanta na kauye aka sanar musu.... Bayan Aunty sungama waya dasu Maryam dan har Mustapha ma takira sungaisa. wayar faruq takira tace yazo ya sameta a falon mommy. Da sallama ya shiga yazauna a gefen Aunty Bayan ta amsa masa. Aunty ce kadai a falon Aliya tana daki tana hada musu kayansu. "Ina kwana Aunty" "lafiya kalau faruq, yau baka fita aikin bane?" "Ehh, Aunty yanzu nake shirin fita, dan tun safe daddy yamun magana to nadanyi wani aikine a system" "ok, Allah yataimaka" "ameen" "dama maganar Sadiq zan maka, yakamata zuwa yanzu mudubashi musan halin dayake ciki, danbazeyiyu a barshi hakaba, ace mutum ya kulle kansa a daki babu ci da sha na kirki, jiya damuka dawo naje nadubashi naji kofarshi a rufe, idan kana da extra key na dakinsa ka bude muga halin dayake ciki, hankalina ya kasa kwanciya. Ai hannunka baya rubewa kayanke kayar. Dazu danayiwa yaya maganar seyace in kyaleshi, amma yanzu tunda yafito kaje kadubomunshi." numfashi faruq yasauke yace, "shikenan Aunty, Bari naje naduboshi" "yawwa faruq ina jiranka." Mikewa yayi yakoma part dinsu, dakinshi ya shiga ya binkico key din dakin Sadiq dayake dashi. A mawuyacin hali yasamu Sadiq jikinshi ya wani sandare kamar gawa, gashi ko numfashi bayayi. Hankalin faruq a tashe yasanar da yan'uwansa da Aunty, babu bata lokaci suka daukeshi zuwa asibiti.......... *Bayan sati daya* Har yau mommy bata dawoba kamar yadda tacewa suhailat, suhailat ta kira wayarta amma bata sametaba. Su faruq ma sunkikkira mommy dansu sanar mata ciwon Sadiq suma basu sametaba, suhailat kuma idan suka kirata bata dagawa. Su Hajiya gwaggo an farfaɗo amma batasan wake kantaba, sesunbatu take tana kiran "kudadenta,kudadenta." An kawo lefen saleemat Masha Allah kaya sunyi kyau sosai, ansaka bikinta bayan karamar sallah da sati hudu. Abangaren su Maryam kuwa komai natafiya yadda yakamata, gidan kowa haba_haba yakeyi dasu. Ammi tayiwa Maryam da Mustapha siyayya ta kaya sosai. Mustapha tun kwanansu uku a Jos din, yakebin Saddam kasuwa domin yacewa Ammi baze iya zaman gidaba kamar wata mace. Motarta ammi tabasa yake zirga_zirga da ita. Tsakaninsa da Maryam gaisuwace kawai take hadasu. Part din mijin ammi, nan ammin tasa aka gyara musu aka yimasa fenti da dan gyare_gyare. Falone da 2 bedrooms a part din se kitchen da ɗan karamin store. komai sabo dal ammi tasa aka samusu, amma Mustapha ne yabiya kudin. danda tace ita zata biya yahanata. Kullum suna waya dasu Aunty, mustapha yaso zuwa yaduba jikin Sadiq, amma daddy yahana. Danyace idan yataho Maryam bazataji dadiba, idan ya barta ita kadai. Yau juma'a, kuma yaune ango da amarya zasu koma part dinsu subar na ammi, yau kuma *umaimah* zata dawo daga hutun dataje gidan kakanninta na wajen uwa...........✍️ *By* *Zeey kumurya* *5️⃣2️⃣* *Bismillahirrahmanirrahim* ..........Da misalin ƙarfe 11 na safe muna zaune a falon ammi nida Aunty zuhura, yaronta yana hannuna ina masa wasa muna hira jefi_jefi. kamar a mafarki naji kamshin turarensa, nidai nasan yana kasuwa kuma baya dawowa a irin wannan lokacin. dago kaina nayi da sauri yayi daidai da shigowarsa falon bakinsa dauke da sallama. maida kaina kasa nayi zuciyata na ɗan bugawa, a hankali na amsa masa sallamar dan dakyarma inyaji, saɓanin Aunty zuhura da har gaisawa sukayi ta masa sannu da zuwa, nidai daga amsa masa sallamar bankara koda kallon inda yakeba nacigaba da yiwa Abul wasa. yanda Maryam bata kalli Mustaphaba, haka shima ko kallon inda take beba yashige dakin ammi bayan sungama gaisawa da zuhura. kallon Maryam zuhura tayi tana sakin murmushi, miskilancinsu na bata dariya, yanda idan suka haɗu suke wani basarwa tamkar ba ma'aurataba, zataso taga wanda zefara aje miskilancinsa tsakanin Maryam da Mustapha. Nikam banmasan tana kallonnawaba natafi duniyar tunanin yanda zamanmu ze kasance ni da shi a mahalli ɗaya. Ammi na zaune a bakin gado tana waya da wata cousin dinta datake Niger mustapha ya shigo dakin da sallama, zama yayi a gefenta yana jiran ta gama wayar, befi 1 minute da zamaba sukayi sallama ammi ta aje wayar. tana dubanshi tace."NOOR, yanaga kadawo daga kasuwar dafatan dai lafiya?" lips dinshi na kasa yaɗan lasa sannan yace. "Lafiya kalau Amminah, daddy ne yakirani akan karatun waccan" tsareshi ammi tayi da ido tace wace waccan kuma batasa suna ne?" shafa kansa yayi tare da lumshe idonsa a hankali kamar bayasonyin magana yace, "me sunanki" ita ammi ma dariya yaso ya bata, yanda ya wani basarwa, tace. "Uhm, inajinka meyafaru da karatunnata?" yana latsa wayarsa yace. "Daddy yace, anemi PRIVATE SCHOOL abiya mata tayi NECO, tunda WAEC lokaci ya kure, ran monday zasu fara. Idan Allah yakaimu November_december setayi PRIVATE WAEC" ammi tace. "Hakanma yayi Allah yataimaka yabada sa'a, kayiwa Saddam magana seya samo mata makarantar dazatayi" amsa mata yayi cikin girmamawa sannan ya mike yayiwa ammi sallama ya fice. daya dawo ze fitama bandago na kalleshiba, inaji dai Aunty zuhura ta masa Allah yakiyaye hanya. Lekowa ammi tayi takirani, da Abul a hannuna na mike nanufi dakinnata. Bayan na zauna ta bani abu a kofi kamar magani, tun washegari garin ranar danazo kullum seta bani nasha sau uku a rana. da daddare kuma kafin na kwanta tasani inci fruits. karbar abul tayi daga hannuna dayaketa bingira mata dariya. Seda na shanye tass sannan na ajiye cup din ina yamutsa fuska saboda rashin dadi. wani abu ta mikomun daban tace in lasa, maganine na gari aka kwabashi da zuma, shikam nasha sosai ta dadin rai saboda zaki_zakin zuma, a kunyace nakesha duk da ammi hankalinta nakan Abul. da farko data fara bani bansan amfaninsaba, seda ta hanani tsarki da ruwan sanyi saidai na dumi sannan na gane. kuma kullum kafin nayi bacci setasa na shiga ruwan zafi wanda ta tafasashi da lalle da wasu ganyayyaki masu amfani. da safe kuma ina tashi zata samun turaren tsugunno a kasko. inna gama dashi tasamun na turare jiki. banshanyeba na ajiye saboda cikar danaji cikina yamun, akan mudubi na ajiye robar bayan na rufe da murfinta. Ammi tace, "yawwa ɗiyata kinsha sosai ko?" A mutukar kunyace na dagawa ammi kai, kaina na kasa. kwantar da Abul tayi a kan gado sannan ta dakko wayarta tana fadin, "bari nakira antinku takirani tun dazu tace na baki wayar kina wanka, nace idan kinfito zankirata kuma na sha'afa" komawa bakin gado nayi nazauna ammi ta mikomun wayar bayan ta shiga, daukar Abul tayi suka fita parlour. "Assalamu alaikum" Aunty ta fada bayan ta daga wayar. amsa mata nayi na kara da faɗin, "ina kwana Aunty" tace. "Lafiya kalau, ya Jos din, ina fatan komaidai lafiya" nace, "lafiya kalau Aunty, yajikin yaya Sadik" tace, "jiki Alhamdulillah za'ace Maryam, dan yanzuma haka suna hanyar zuwa saudiyya shida yaya da zannurain, tunda nandin kullum ciwon kara gaba yake." cike da tausayawa gami da jimantawa nace. "Allah ya bashi lafiya, yasa karshen wahalar kenan" Aunty tace, "Ameen Maryam, yau insha Allah zanje gidan gwaggonki saboda zirga_zirgar asibiti yasa bansamu najeba" "bakomai Aunty aikina kokarima sosai wlh" "to yaza'ayi Maryam girman kenan" "hakane ina aliya fa?" "Tanacan tana ta shiri kinsan yau zamu wuce kd" "kigaidamun da ita Aunty" "zataji insha Allah, ya angonki?" Murmushi nayi cikin jin kunya nace, "yananan kalau aunty" "amminku tacemun yau zaku koma bangarenku ko" "ehh Aunty" fada Aunty tashiga yiwa Maryam sosai, akan aure da yanda zata kula da mijinta da hikimomi da dabaru da kissa na zaman aure. mun dade muna waya da Aunty, dan munfi awa ɗaya, har aliya tafito itama Aunty tabata wayar muka gaisa sannan mukayi sallama, na koma falo. A kitchen na tarar da ammi da Aunty zuhura sunata aiki, nima tayasu nayi duk da ammi taso hanani amma nadage senayu........ *KANO* Aunty bayan sungama waya da Maryam ta kira layin suhailat, suhailat tana zaune abun duniya duk ya isheta, ga zaman kadaici dan har yanzu tananan da bakin girman kanta tafi ƙarfin tayi hira da matar da tazo tana yi mata aiki. gashi mommy ta hanata fita, ta hanata hawa online tana ganin kiransu faruq amma bazata iya dagawaba saboda tsoron masifar mommy. seyanzu kuma cikin yake damunta, ta matsu mommy ta dawo aje a zubar dashi gashi kullum cikin ciwo take babu lafiya. tanasoma ta sanar da kamal maganar cikin. a hankali ta kai hannu ta dakko wayarta jin tana vibrate alamar shigowar kira, ajiyar zuciya ta sauke me karfi ganin sunan Aunty yana yawo akan screen ɗin wayar, hannunta har rawa yakeyi wajen picking dantasan zata samu information akan Mustapha. jinta daga Aunty tace, "suhailat!" cikin mamaki. "Na'am Aunty" "meyake faruwa ne, in'ankiraki bakya dagawa, wayar Aunty Atika kuma bata shiga" rasa abun cewa suhailat tayi,tayiwa Aunty shiru kawai. "Bakya jinane suhailat" "inajinki Aunty, mommy'n batananne tayi tafiya Niger" "Niger kuma? To ke kina ina?" "Ina gidanta" "kekadai?" "Eh, sekuma mai aiki da maigadi" shiru Aunty tayi tana girmama rashin hankali irinna mommy, banda haka yazakayi tafiya me nisa irin haka, kabar yarinya budurwa ita kadai a gida" numfasawa Aunty tayi tace, "kituromun address din gidan zanzo nadaukeki anjima" "toh Aunty" suhailat ta amsa cikin jindadi zata koma gida kusa da masoyinta. kafin tatambayi Aunty ina mustapha Aunty ta kashe wayarta. Duban aliya dake danna waya Aunty tayi cikin bacin rai tace, "taso muje" kallon Aunty aliya tayi ganin yanda ta sauya lokacin ɗaya tace. "Lafiya Aunty? Meyafaru?" "Bansaniba kinsan bansan yawan tambaya ko?" shiru aliya tayi ta dakko hijabinta suka fita. batasha wahalaba wajen gane gidan gwaggo da kwatancen da Maryam ta mata, suna ɗan tattambaya har sukazo gidan. A kofar gidan gwaggo Aunty tayi parking, bayan sun fito daga motar taga gidan a kulle, Aunty bataji dadiba ganin gidan a rufe. Aranta tace, "sun rafka sabani kenan da gwaggo" har zata cewa aliya su koma gida kawai, se kuma tayi shawarar shiga makota kobatayi nisaba, dan ita yanzu idan tabar Kaduna batasan ranar dawowartaba. Gidan umma suka shiga. Umma tana daki tayi baki yan ganin lefe, saleemat kuma tana kitchen tana girki. Da sallama suka shiga, saleemat dake kitchen ta amsa musu, tsayawa sukayi a tsakar gida bayan kamar 2 minutes saleemat ta fito. Da fara'a dauke akan fuskarta tace, "sannunku da zuwa" duk da bata wayesuba. "Ku shigo tana ciki" Aunty tace, " barshi nanma yayi muna sauri ne" "to bari namata magana" saleemat ta fadi haka tana nufar dakin umma, sanar mata tayi tayi baƙi kuma sunce suna saurine. Biyo bayan saleemat umma tayi, da fara'a itama tayiwa su aunty sannu da zuwa, tare da kaisu falo. Bayan sun zauna sun gaisa umma tace. "Saidai banganekuba" murmushi Aunty tayi tace, "dama bakisanmu, nazo nanne makotanku naga gidan a kulle, shine nace bari nazo natambaya ko kwatancenne banganeba" umma tace, "gidanwa kuke nema" "gidan wata gwaggo wadda take rikon yarinya Maryam" umma na mamakin abunda yakawo wadannan kyawawan mutane, masu tattare da kamala gidan gwaggo, duk da sunsha hijabansu amma kallo ɗaya zakasamu kasan a daga gidan hutu suke, tace. "Eh, nanne kuwa bakuyi batan kaiba, saidai yanzu haka tana asibiti batada lafiya" "subhanallahi meyasameta" Aunty tatambaya cikin razani. atakaice umma ta musu bayani. Cikin jimantawa Aunty tace, "Allah Sarki, Allah yabata lafiya, yakiyaye gaba, sukuma wadanda sukayi Allah yatoni asirinsu" "Ameen" umma da aliya suka amsa a tare. "Tana wanne asibitin yanzu" Aunty ta tambaya. "Aminu Kano" daidai lokacin saleemat ta shigo dakin hannunta dauke da ruwa, godiya su Aunty suka mata, sannan suka kara gaisawa. Aunty ce tayiwa umma bayanin abunda ke tafe dasu atakaice. kafin umma tayi magana, saleemat cike da mamaki tace. "Maryam ditace take da aure yanzu?" "Ehh ita, kinsan iko na Ubangiji babu yadda baya canza al'amari, mu mutane muna namune Allah natasa, rabon aurennasune yakai Maryam aikatau gidan yaya" ganin yanda suka cika da mamaki, umma takara musu bayani sosai yanda zasu fuskanta karsu dauki abun da wata manufa. sun dan jima a gidan suna tattaunawa akan al'amarin seda sukayi sallar azahar sannan aunty suka tafi da saleemat asibiti dubo gwaggo. Lokacin dasukaje gwaggo tana duniyar bacci. wadda ke zaune a gurinta Aunty tayiwa bayaninsu kansu takuma tabbatar mata zasu dawo nan bada jimawaba harda Maryam din, seda Aunty ta cikasu da Alkhairi sannan suka musu sallama suka tafi. seda ta biya ta dauko suhailat bayan ta sallami matar dake zaune da ita, se bayan la'asar dai ta komo gidan daddy........ *JOS* Girke_girke mukayi, munsha aiki gaskiya. duk wannan hidimar akan yarinyar gidan dazata dawone wadda kullum senaji ammi da Aunty zuhura, da mama sunyi zancenta wai ita umaimah. daga jin yadda suke zancenta suna matukar ji da ita. Bayan mungama aikin nayi wanka na shirya cikin wata doguwar riga kalar dark pink, anmata adon baki da wasu fulawoyi a gaban rigar. faka gashin kaina dayasha gyara nayi ya sauka har gadon bayana, tattareshi nayi na cusa a cikin ribbom sannan na dakko wata bakar hula nasaka. dankunne fashion masu kyau nasaka tare da agogo da zobe. kwalli kawai nasaka a idona se white lipstick danasawa lips dina. humra me dadin kamshi na shafa a jikina, se wani turare na fesawa me sanyi da dadin kamshi. seya hadu yabada wani kamshi me dadin gaske. Kallon kaina nayi a mudubin dakin ammi, nikaina nasan nayi kyau, fatata tayi haske sosai jikina kuma ya murmure, tona samu kwanciyar hankalin zuciya tunda na mallaki *heartbeat* dina. Maryam tana daki tana shiryawa umaimah ta dawo gidan, cike da farin ciki ahalin gidan suka tarbeta kowa na murna da farincikin dawowarta musamman ammi. Itama anata bangaren umaimah cike take da murnar dawowarta gida tayi missing dinsu sosai musammanma amminta, harsuka gama tarbe_tarbenta Maryam tana daki batamasan sunayiba. lokacin da Maryam ta gama shirinta ta shigo umaimah tana daki tana wanka. kusa da ammi naje na zauna bayan na musu sannu da gida. wayar Aunty na dauka nafarayin game, ita kuma suna hira da Aunty zuhura da mama. Bayan kamar 20 minutes umaimah ta fito daga dakinta karaf idonta yasauka akan Maryam, da dunbin mamaki take kallonta, danbatasan da zaman Maryam a gidanba. Aranta tace, "to wannan yarinyarfa, kodai daga Saudiyyan da Ammi taje tataho da ita?" a wani bangaren na zuciyarta kuwa kishi ne da kyashi ya turniketa na ganin kyawun Maryam, ita macece dabatasan taga anfita kyau, sekuma gashi yau taga wadda tafita komai da komai a cikin gidansu. hade rai tayi cike da hassada ta dauke kallonta daga kan maryam, kusa da mama taje ta zauna tana wani narke mata ajiki tana zuba mata shagwaba. se'alokacin Maryam tasan da zuwanta falon, dago kai tayi ta kalleta, mamakine yacikata ganinta katuwace amma take wannan sangartar, kallo daya Maryam ta mata ta dauke kanta tacigaba da game dinta. Ammi ce ta dubi Maryam tace, "ɗiyata ga autatah fa, danace miki tayi tafiya Abuja. kakaro fara'a Maryam tayi cikin sanyin muryarta tace, "sannu yakike" fuskarta babu fara'a tace. "Lafiya kalau" bankara cemata komaiba itama haka, a gani ɗaya dana mata naji ni sam batamunba, ita kam umaimah bakin ciki ne yakara turniketa dataji Muryar Maryam me sanyi da zaki, "yarinyar komai ta hada ga kyau ga zakin murya, salon yanda take maganama kawai abun burgewane" umaimah ta fadi haka a ranta cikin kyashi. Daidai lokacin Saddam da Mustapha suka shigo falon bayan sunyi sallama, kasancewar yau juma'a da wuri suke dawowa daga kasuwa. kamar ance ta kalli kofa idanunta ya sauka akan Mustapha. wani mayen kallo tabi mustapha'n dashi without control her self, kallonsa take tamkar zata lashesa............✍️ *By* *zeey kumurya* *5️⃣3️⃣* *Bismillahirrahmanirrahim* ............. Umaimah har wani zunkuɗowa take daga kan kujera tana sakin baki da hanci tana binshi da mayen kallo, Saddam da zuhura tare da Maryam ne suka lura da kallon da take masan, ammi kuwa hankalinta yana kan ɗanta bata luraba. wani kishine yazo ya turnikemun zuciya irin me dacinnan, nibanmasan haka kishin yakeba dan bantaba jin na Aunty suhailat irin hakaba, yanda take kallonsa kamar idonta ze cire, tabe Bakina nayi nadauke kaina daga kallonta zuciyata namun kuna. Ita kuwa zuhura murmushi tayi dantasan za'ayi haka. Saddam ma murmushin yayi yakau da kansa daga kallon Umaimah. Mustapha seda yagaida amminsa da mama sannan ya zauna a kusa da Maryam, dan babu wani gurin zama da yay saura a falon senan, kuma shima ya lura da kallon da umaimah take masa. Lumshe idonsa yayi saboda kamshin Maryam daya shaka kamshin ya masa daɗi sosai. Ita kuwa Maryam bata rai tayi hartana turo dan karamin bakinta gaba batasaniba saboda zafin kishi. A hankali ya bude idanunnasa ya kalli Maryam ta gefen ido. Umaimah wadda takasa dauke idonta daga kansa sekara sakar baki da hanci take tana kallonsa, a ranta tace. "Wowww, wowww amma guy dinnan ya haɗu iya haɗuwa, yatafi da imanina, amma daga gani brother din yarinyarnanne" dan ita kama taga Maryam da Mustapha sun mata. danna wayar ammi kawai nake amma bansan menake dannawaba tunda yazauna a kusa dani nanemi nutsuwata na rasa, kawai daurewa nake ga kamshinsa gaba-daya ya cikani. kara kallonta nayi naga har lokacin bata dauke idonta daga kansaba, sonake na kalleshi naga ko shima ita yake kallo amma nakasa. Mamace tatabo umaimah tana cemata. "Ke! Mekike kallo hakane?" Ajiyar zuciya umaimah ta saki ta juyo ta kalli mama a hankali tace, "mama suwaye wadannan wai? daga ina suke?" mama tace. "Bakin amminki ne" umaimah na far da ido tace, "amma suna da kyau sosai kamar ammin, musammanma namijin yafi kyau ga muryarsa me dadi" cikin tsokana mama tace, "yau wacce rana umaimah ta yabi wani ɗa namiji arayuwarta" tana satar kallon Mustapha tace, "mama ai yakai a yabeshinne, wlh bantaba ganin namijin daya mun kyau kamarshifa, guy ɗinfa yayi mama" murmushi kawai mama tayi batace komaiba. Maida kallonta tayi ga yayanta tace. "Yaya Saddam ina yini" "lafiya kalau sisina, aitunda nashigo nakeson na miki magana naga kunata sirri da mama senace bari najira ku gama." Dariya tayi tace, "kasan tsakanina da tsohuwarnan da amana" "hakane yar lelen mama, kindawo lafiya" "lafiya kalau yayana" maida kallonta tayi ga Mustapha tana wani fari a kokarinta nata dauki hankalinsa tace, "ina yini" sarai yasan dashi take amma ya mata banza tamkar bejiba. Ammice tace dashi, "NOOR ana gaisheka" batare daya kalletaba yace. "Lafiya" atakaice. hira suka shiga yi dukansu amma banda Maryam da Mustapha dasukayi dif tamkar basa falon, umaimah se wani iyayi take idan zatayi magana tana wani fari da ido, wanda takeyi danshi bemasan tana yiba. Bayan sunyi sallar la'asar ammi zata kaiwa Mustapha abinci, umaimah ta karba ta kai masa har daki tana wani yaya NOOR, gabadaya tabi ta susuce dataga mustapha. Shiko mustapha haka kawai yaji yarinyar bata masaba dan daga ganinta zatayi rawar kai, data kawo masa abincinma hade ransa yayi, a niyyar umaimah ta zauna suyi hira dashi amma ganin ba fuska seta fice badan tasoba. Yana gama cin abincin ya fice daga gidan. Misalin ƙarfe biyar da yan'mintuna bayan nagama haɗa komai nawa kamar yadda ammi tace, ina zaune adakinta akan gado nikadai, ammi da Aunty zuhura suna part dinmu suna kara gyarawa. Ammi tace ta shigo dakin da sallama, amsa mata nayi cikin girmamawa. Ammi tana kallona tace, "yawwa Maryam kingama haɗa komai, har su turarukan da mayukan?" cikin sanyin murya kamar yadda jikinama yake a sanyaye nace, "ehh ammi nagama" wayarta ta mikomun tana fadin, "yanzu aka kirani da wata number wai ana nemanki" nace "ba Aunty bace kuma" ammi tace, "ehh ba ita bace wannan ma kamar yarinya" cikin mamaki na karbi wayar na duba number senaga kamar nasan number'n. danna kira nayi nakara a kunnena. Ammi ta dauki jakar da Maryam tahada kaya tafice. seda wayar takusa katsewa sannan aka daga da sallama. wayyo daɗi, wani farinciki naji ya lullubeni danaji Muryar sahibata kawar asali, kawar rufin asiri saleemat. cikin ɗoki nace, "saleemat!" itama tana dariyar jindadi tace, "na'am kawata nayi kewarki sosai wlh" "hmmm, kedai bari saleemat dazunnan nagama zancenki acikin raina, ya gida yasu umma da baba da kowa da kowa" "duk lafiya kalau Maryam" "Masha Allah, ina Habibi Adam?" "Habibi yananan kalau, ke ankawo lefenafa tun waccen satin" "kai haba, shine ba labari" "wlh Maryam nakai wata ina neman wayarki bata shiga" "wayar ta fadine, wai dagaske kike ankawo lefennaki saleemat" "dagaske mana, zan miki wasane dakina chat ma dana turo miki kingani" "kaii, amma naji dadi kawata Allah yasanya Alkhairi, Allah yasa damu za'ayi." "Ameen" hira muka shigayi irinta amininan juna, harna tambayeta inata samu numbar ammi tacemun aunty ce ta bata. muna cikin hirarne nace mata, "ina gwaggo kuwa saleemat? Aunty tacemun idan tazo zata hadani da ita inata jiranta naji shiru" saleemat tace, "gwaggo tananan lafiya kalau" (dayake Aunty tarokesu karsu sanar da Maryam ciwon gwaggon dantasan halinta tada hankalinta zatayi tayita koke_koke, tafison idan tazo kafin azumi seta taho da ita ta duba gwaggon.) nace, "kigaidamun da ita sosai, kikarbomun number'n tama kituromun nakirata" "toh" kawai saleemat tace, ta kawar da zancen da fadin. "Yanaji wai muryarki kasa_kasa, kodai angonnaki ya tumurmushekine a gado" ta karasa zancen tana dariya. Cikin jin haushi nace. "Bansaniba yar iska, ni kaiwa umma wayar mugaisa" dariya tacigaba dayi harta kaiwa umma wayar, mungaisa sosai da umma na mata Allah yasanya Alkhairin lefen saleemat. Umma tamun yar nasiha akan aure na mata godiya mukayi sallama. banbari saleemat ta karbi wayarba na kashe dannasan tsokanata zata cigaba dayi. Haka kawai naji ina hawaye, dama jikina duk a sanyaye yake yau. goge hawayena nayi da sauri jin tafiya a falo, dan kofar dakin abude take. Ammi ce kuwa ta shigo dakin, bata lura da halin da Maryam take cikiba dan tayi kokarin boye damuwarta. Ammi tace, "Maryam kungama wayar" nace "ehh, wata kawatacema ashe Aunty ce ta bata number'n ki" tace. "ayya, kema Yakamata ace kina da waya a hannunki, bari NOOR yashigo sena masa zancen yasiyo miki" ban iya cewa mata komaiba dan kuka ze iya kufcemun" zama ammi tayi akan gado tana fadin "washh" araina nace. "Ai dole kigaji" saboda ammi kwata_kwata bata zama, koyaushe cikin dawainiya take damu nida yaya Mustapha, har tausayi take bani. "Sannu ammi" na furta a hankali. "Yawwa Maryam" mikewa nayi nace "ko in miki tausane" muryar ammi na nuni da gajiya tace, "dakuwa kin kyauta ɗiyata" kwanciya tayi akan gado nikuma nashiga yimata tausar............ *KANO* Suhailat tunda suka dawo gida taketa baza ido taga ta inda zata ga Mustapha, amma ko alamarsa bata ganiba. kasa hakura tayi taje har part dinsa, amma setaga a kulle. Da hanzarinta ta dawo bako kunya tatambayi aunty. Aunty kawai tace mata yayi tafiya ne. bataji dadiba kuma bataso hakaba, ta koma daki ta ɗauki wayarta taita kiransa amma wayar bata shiga, haka ta hakura zuciyarta babu daɗi kokaɗan. Aunty sunyi waya dasu daddy sun isa lafiya. wajen karfe biyar tasa suhailat ta hada kayanta danda ita zata wuce Kaduna, suhailat bata iya hada kayanba saboda batajin dadin jikinta. Se aliyace tana kunkuni ta hada mata, bisa tursasawar Aunty. Aunty kallon suhailat kawai take tunda ta dakkota yanda gabadaya ta zabge ta rame, se uban fari kamar zabiya. gashi sebin tiles take tana kwanciya, Aunty dai takasa hakuri tatambayeta meke damunta. setace mata wai malaria ce. Aunty baiwar Allah babu tunanin komai aranta seta yarda ta mata fatan samun sauƙi....... *JOS* Duk da part din dazamu zauna yana jikin na ammine,dan amminma tacemun anan ta zauna kafin mamansu Saddam ta rasu, seda ta rasu ta dawo inda take yanzu. Amma wlh jinake kamar wani garin za'akaini me nisa gashi zuciyata cike take da fargabar yadda zamannamu ze kasance, nasan dai ni ina matukar sonsa amma shi nasan baya sona. Idannatuna hakan se inji duk zuciyata ta karaya jikina yayi zanyi, musamman ma yanda yake nuna halin ko'in kula akaina. dauriya kawai nakeyi ina boye damuwata. Zuwa yanzu umaimah tasan waye mustapha a gurin ammi, kuma tasan Maryam matarsa ce, dan part din mama taje ta matsa mata da tambaya akan waye mustapha, seda mama tabata labari ta samu sa'ida. Tsana da haushin Maryam ne suka cika mata zuciya ganin ta rigata mallakar irin mijin datake mafarkin samu, amma dadinta daya dayakasance gida ɗaya zasu zauna, ita kuwa zatasan yanda zatayi tajanyo hankalinshi yadawo kanta, zatayi duk yanda zatayi ganin ta kwaceshi daga hannun wannan karamar yarinyar wato Maryam. Bayan sallar magriba ammi tasani nayi wanka na shirya cikin wata hadaddiyar doguwar riga me kamar alkyabba yanayin jikinta. nayi kyau sosai acikinta, nafeshe jikina da daɗaɗan turaruka masu sanyi kamshi. Bayan nagama shiryawa ammi tamun faɗa akan zamantakewar aure, mama ma, tamun. nidai hawaye kawai nakeyi ina saurarensu. Bayan sallar isha'i ammi ta kama hannuna ita da mama suka rakani har inda yake a matsayin dakina ta zaunar dani akan gado. nasha kuka sosai bayan sun tafi. Daga baya kuma na rarrashi kaina nadena kukan. A hankali na tashi nakarewa dakin kallo yayimun kyau sosai sai kamshin turaren wuta da sabon fenti yakeyi. kayana su ammi sun jeremun su a cikin cover, su turaruka da mayuka duk anjeremun akan mudubi, komaidai need abun gwanin ban sha'awa. Falo na fito shima yayi kyau sosai babu wani tarkace, yasha labulaye masu kyau. daga falo kitchen nanufa, shima yaji kaya komai na amfani akwaishi. dakina na koma bayan nagama kalle_kallennawa, dakinsane kawai banyi gigin shigaba. ina mamakin wai wannan gidanane da kayan cikinsa komai nawane, nida bantaba zaton zansami koda rabin wannan ba. Zama nayi a bakin gado nashiga sake_sake. Ƙarfe goma da yan mintuna ya shigo part dinnasu, hannunsa dauke da ledoji manya. Kitchen ya nufa ya ajiye kajin daya shigo dasu kamar yadda ammi tace yasiyo. Shima seda yagama karewa gidan kallo, shima gidan yamasa kyau sosai, kafin yashiga daki seda ya saita kayan kallo danshi mutum ne meson kallon news da kallon ball. Ina zaune tsuru naji shigowarshi ajiyar zuciya nasauke cikin jindadi,dandama a tsororace nake da zaman nikadai, nandaima da wutar NEPA ne. Dakinshi ya shiga ya ajiye sauran kayan dayashigo dasu, sabulayene da mayuka da turaruka. Nashi ya kwasa ya jera a gaban madubin dakin. sannan dauki sabulu da saban towel din daya shigo dasu ya nufi toilet. bayan kusan 30 minutes yafito yazira jallabiya yafashe jikinshi da turaruka ya kwanta. Lumshe idansa yayi yana tunanin wannan aure da daddy yamasa. shiyanzu besan yazeyi da yarinyar mutaneba, tunda bashi da lafiyar daze bata hakkinta na aure akansa, kodama yanada lafiyar baya tunanin waccan karamar yarinyar zata iya dashi, shifa yaraina Maryam a matsayin matarsa ganinta yake yar karamar yarinya, dandai baze iya bijirewa daddy bane da....... wayarsace ta katse masa tunaninsa ta hanyar yin vibrate. Ahankali ya bude idansa ya tashi ya dakkota daga kan madubi. MY UNCLE yagani yana yawo akan screen ɗin wayar. kanin ammi ne dayake saudiyya kullum sesunyi waya dashi, dagawa yayi sukasha hira har yaransa yabawa suka gaisa sannan sukayi sallama. Nasihar da daddy yamasa ranar da zasu koma kano itace ta dawo masa kwanyarsa tamkar yanzu yake masa ita. "Mustapha, karike yarinyarnan amana kaga marainiyace kuma bata da wani gata sena Allah, idan ka cutar da ita Allah baze barkaba. Kuma yazama dole kakula da cinta da shanta da kuma lafiyarta." Mikewa yayi yaɗauki ledar daya shigo da ita, bisa umarnin da zuciyarsa ta basa akan yakamata yaje yaga lafiyarta kafin ya kwanta, tunda yanzu amanace ita a hannunsa, da wannan tunanin ya nufi dakinta. Maryam dataga zaman ya isheta gashi ko digon bacci a idonta, seta tashi dama da alwalarta ta shimfida sabuwar daddumarta ta tada sallah.............✍️ *By* *Zeey kumurya* *5️⃣4️⃣* *Bismillahirrahmanirrahim* ............ Ahankali ya tura kofar dakin yajita a bude, bakinsa dauke da sallama ya shiga dakin. wata irin faduwar gabace ta ziyarceni duk da Sallah nake jin shigowartasa. kamshinsane yatabbatarmun da shine, gaba-daya jinayi na diririce, narasama menake karantowa a cikin sallar saboda tsabar fargaba. shiko mustapha ganin sallah Maryam take, seya ajiye ledar hannunsa ya juya ya fice. Ajiyar zuciya nasauke jin yafita na sallame sallar amma banko motsaba daga inda nake, duk da yafitan amma bandawo cikin nutsuwa taba.gani nake kamar ina juyawa zanganshi yadawo cikin dakin, kusan 16 minutes sannan na daure na tashi daga kan dardumar har lokacin daddadan kamshinsa bebar dakinba. hijabin jikina na cire na ajiye, leda nagani dabansan da itaba a dakin. cikin mamaki na dakkota nafara fito da kayan dake ciki, sabulayen wanka ne dana wanki,se MacLean da sabbin burush guda biyu da mayukan shafawa harda sosan wanka me kyau acikin ledarsa araina nace, "gaskiya wannan ya iya siyayya, komai dayasan zan bukata seda yasiyo." mayar da kayan nayi cikin ledar bayan na dauki abunda zan bukata a yanzu na ajiye a gefen gado. Toilet na fada nayi wanka, ina fitowa na zira rigar bacci nafada kan gado dan wani irin bacci naji inaji lokaci daya...... Washegari, bayan nayi sallar asuba ban koma bacciba, Alqur'ani me girma na dakko na karanta izifi uku nayi narufe na ajiye. Addu'a nayi sosai akan rayuwata, nayi mana addu'a sosai akan aurennan namu da hearbeat senaji duk wani tsoro da fargaba ya kaumun daga zuciya. Ƙarfe bakwai da yan mintuna nafito daga dakina domin na gyara gidan. babu wani datti yananan fess dinsa. kujerun na karkade nashare dan dattin dabaza'arasaba a falon, nagoge dining da tv. Kitchen na shiga shima babu wani abun datti a cikinsa, leda na hango akan karamar freezer dake kitchen din, da dan mamaki nakarasa nahau dubawa, dan jiya dana shigo babu da ita. kaza nagani a ciki har uku, se zuba kamshi takeyi. shiru nayi cikin karayar zuci, araina nace. "Kazar amarci dakowanne ango yake siyowa matarsa ya lallabata yabata taci, amma ni nawa angon saboda baya sona seyazo yadireta a kitchen" kwallace ta cikamun idona, maida ita nayi yanda naganta nafito daga kitchen din zuciyata namun kuna. "Yaushe bawan Allah'n nan zesoni? kamar yadda aliya tace, anya kuwa zanga wannan ranar ba yaudarar kaina nakeba kuwa? abun da kamar wuya" natambayi kaina hawaye na zubomun daga idona. Knocking din kofar falon akayi yasani saurin goge hawayennawa, kofar na nufa na bude batare da tambayar wayeba. Umaimah ce tsaye hannunta dauke da basket da kayan breakfast a ciki, ammi ce dazata kawo da kanta umaimah tace tabata takai musu, dan a zatonta mustapha ne ze bude kofar amma setaga Maryam. bata rai tayi sosai ta wani hade fuska, ko sannun da Maryam ta mata bata amsaba. matsa mata nayi ta wuce ciki nima nakoma na zauna akan kujera bankara kallon koda inda takeba harta fice danna lura yar rainin hankalice. tana fita na tashi na kulle kofar, inajin yunwa gaskiya dan tun jiya da rana rabona da abinci. Flates na dakko da cups nadibi abinda zanci nanufi dakina, Allah sarki ammi nasan wannan duk aikintane. koda nagamaci banfitoba wanka nayi na kwanta ina tunanin yanda zamanmu zecigaba dashi. seda goma ta wuce nafito Falour'n dauke da kwanukan danayi amfani dasu, nasan zuwa yanzu kam yafita. kan dinning na kalla naga shima kwanukan dayayi amfani dasu a gurin, da alamama bejima da fitaba danga kamshin turarensanan a falon. Tattara kwanukan nayi duka nakai kitchen na wanke na kara kimtsa wasu abubuwan. sannan naje na gaida ammi cike da jin kunyarta, a tunaninta mustapha yananan befitaba, muna gama gaisawa tace inkoma gurin mijina. Ƙarfe 12 na rana aka kawo mana wuta, dama nagaji da zama ba abunyi sena kunna kallo..... Yaran makota sun shigomun yau sosai harda yanmata kamar ni, dan su mama duk sun sanar amarya tatare. naji dadi kuwa sosai dama kewa ta isheni har bayan la'asar sannan suka tafi. kara gyara gidan nayi naturareshi da turaren wuta me dadi, Aunty zuhurace ta aikomun dashi da yawa a cikin bokiti. se kusan magriba mustapha yadawo gidan, ina zaune a falo ya shigo. Lumshe idonsa yayi saboda wani ni'imtaccen kamshi dayaji falon yanayi. shikam yanason kamshi a rayuwarsa yana kuma san tsafta. A hankali ya kalli inda yaji muryatarta data amsa masa sallamar dayayi, danbe zaci tana falonba. becemun komaiba yawuce dakinshi, ni kuma na bishi da kallo zuciyata cike da shaukinsa. Lumshe idona nayi nafada duniyar tunani, har aka kira sallar magriba inanan zaune inda yabarni. da kyar na yunkura na shiga daki nayi alwala danyin sallah. Da daddare yaya sadam yazo har part dinmu yace inshirya da safe zamuje amun passport za'akai makarantar dazanyi NECO. Wayyo daɗi kamar ze kasheni dan Murna dan da har na fiddarai da karatun...... *2 weeks later* Munje school din dazanyi exam nida yaya Saddam angamamun komai na exam din. goma ga azumi zamu fara exam din insha Allah. Zamanmu da *heartbeat* jiya ie yau babu abunda yasauya, tsakanina dashi gaisuwa ce, ko abinci bana zuba masa da kansa yake zubawa yaci. Amma yanzu kullum kafin yafita seya duba yanda natashi kafin yayi baccima seyazo ya Dubani. bantaba shiga dakinsaba, koda da sunan gyara danbanga wannan fuskarba. Kullum yana fita ina gama ayyukana zantafi part din ammi muyita hira da Aunty zuhura. Umaimah kuwa bama magana kwata_,kwata, da ina gaisheta naga bata amsawa nadena. Inta ganni setayi ta hararata tana bata rai, niko da ita da banza duk ɗaya na daukesu gurina. duk abunda ke faruwa tsakanin Maryam da umaimah zuhura tana hankalce dasu kuma tasan Umaimah son mustapha takeyi. shima Mustapha'n zuwa yanzu yagane inda umaimah ta dosa akansa. yana zuwa part din ammi zata fara shishshige masa ta kawo masa ruwa da lemo, tana iyayi tana fadin. "Yaya NOOR inkawo maka abinci, kokuma yaya NOOR mezakaci indafa maka" haka zataita masa iyayi da neman suna, shiko yamata banza abunka da miskilin mutum, gashi yarinyar bata burgeshi kokadan. Muna waya da Aunty da saleemat akai akai a wayar ammi, dan har yau besaimun wayarba, yace sena gama exam da ammi ta kuma masa maganar. Yau ma kamar kullum Muna zaune a falon ammi, yau nida itane kadai Aunty zuhura taje gidansu ita da umaimah ta rakata, munata hira da ammi akan azumi daya rage saura kwana uku. wayar ammi ce ta kawo haske alamar kira, dauka tayi taduba. mikomun tayi tana fadin, "gashi ke ake nema ɗiyata" tasowa nayi na karba nadaga. Saleemat ce, tace. "hello mairota" ina murmushi nace, "na'am kawata yakike" "lafiya kalau, naje asibitine gurin gwaggo tace nakira mata ke" cikin tsananin mamaki nace, "gwaggo kuma bakincemun tayi tafiyaba?" "a'a batafiya tayiba Maryam"..... Nan saleemat tabawa Maryam labarin abunda yafaru da gwaggo. Hawaye shabe_shabe a fuskata nace, "yanzu saleemat kin kyautamun kenan, ace kamar gwaggo bata da lafiya amma kiƙi fadamun seyanzu, idan da mutuwa tayifa?" cikin kwantar da murya saleemat takeson ta fahimtar da Maryam dalilinsu nayin hakan, amma Maryam taki saurararta se kuka take. Ammi dake ta tambayar Maryam a rude ganin kukan datake ta kwace wayar tunda Maryam din taki mata bayani se kuka. Tambayar saleemat tayi, saleemat tayiwa ammi bayanin komai harda boyewar da Aunty tace suyiwa Maryam. Ammi tace. "Ayya Allah yabata lafiya, amma meyasa Hajiya sauda tayi haka, aida tabari anfada semuje harmuma mudubota, amma yanzu bari na lallami Maryam ɗin, zankiraki anjima seki kaiwa gwaggonnata wayar" salimat ta amsa mata cikin girmamawa sannan ta kashe wayar. da kyar ammi ta shawo kan Maryam tayi shiru ta dena kukan. Kiran saleemat ammi tayi ita kuma ta kaiwa gwaggo. gwaggo jiki yayi sauki sosai tunda yanzu har zama tanayi da kanta, sedaifa bata magana ta zama shiru_shiru, dantafara saduda da duniyar, tasan alhakalin Maryam ne yafara kamata. jiya da Aunty takara dawowa dubata take fada mata Maryam tayi aure, da kuma yanda auren yakasance. Gwaggo seta sawa abun albarka, da dane kuwa da tuni tahau tijara tana masifar ita bazata yardaba sai'andawo mata da jikarta. Ta waya Aunty ta hada daddy da gwaggo, ya mata yajiki yakuma bata hakuri akan auran daya yiwa Maryam batare da saninsu su dangintaba. Gwaggo tace bakomai ahakanma sun gode, daddy besan dadine yacikataba na wayar datayi dashiba. se washe haƙora take kamar ba mara lafiyaba ita tayi waya da alhaji *mai nasara* Aunty ta cika gwaggo da kudi da kayan masarufi masu yawa kafin su tafi, ita da megidanta sukazo. Seda ammi suka gaisa da gwaggo sannan tabawa Maryam wayar. "Gwaggo!" Maryam ta fada cikin zumudi. cikin karaya da nadama gwaggo tace, "na'am Maryama" "gwaggo yajikinnaki?" "Dasauki Maryam" "sauki sosai, wlh gwaggo bansan baki da lafiyaba" Maryam ta fadi haka tana hawaye. "Nasani Maryam, nasan dakin sani datuni kinzo dubani, aike yarinyar arziki ce yar albarka" tsananin mamaki ne yacika Maryam dajin abunda gwaggo tace, kodai mafarki take kokuma tsananin ciwo ne yasa gwaggo saduda, har take kiranta da yar albarka, abunda bata taɓa ji gwaggon ta faɗa mataba tunda suke. Numfashi Maryam tasauke tace, "gwaggo zanzo kafin azumi insha Allah, nadubaki." "A'a Maryama kizauna tunda kinga ba gari ɗaya mukeba, bayan sallah in Allah yakaimu sekizo, tunda naji sauki yanzu" dagewa Maryam tayi setazo amma gwaggo tahanata, tace ta bari ko cikin azumi ne tazo. Ammi ma ta roki gwaggo suzo koda a gobene, amma gwaggo tace suyi zamansu. Suna gama wayar ammi ta dubi Maryam tace, "ki kwantar da hankalinki gobe insha Allahu zamu sedai kawai su ganmu kwatsam." Daɗine yacika Maryam gobe zata je taga gwaggon ta da saleemat dinta,kuma hankalinta ya kwanta dasukayi waya da gwaggo taji jikinnata da sauki, dan da saleemat ta fada mata ta dauka gwaggo magashiyyan take a kwance. domin Maryam bazataso gwaggo tamutuba, dan ita kadai gareta yar uwa ta jini sosai, shinema abunda yasata kuka dan idan gwaggo ta mutu bata da wani sauran dangi najiki dazata bugi kirji ta nuna. Da yamma bayan nagama aikina nadawo part din ammi. Kitso zatamun danbansan zuwa Kano kaina babu kitso, namanta rabon danayi kitso ma. Manya_manya nace ammi tamun dan tundaga tazar gashin nafara jin zafi. Aiko gaba-daya kannawa yaɗaure se zafi yakemun saboda nadade ba kitso. se tauna lips nake ina runtse ido. kafin magriba muka gama na mata godiya sosai nakoma part dinmu. Ina zuwa dakina na lambace mai akan kozanji sauƙin radadin dakan yakemun amma a banza. falo na dawo na zauna a kasa, ko dankwali bandauraba balle nasa ribbom nasaki jelar kitson har gadon bayana, dama shukune kitson. dafe kan nayi saboda ciwon dayakemun, nayi dana sanin yin kitsonnan ni banma taɓa yin kitso yamun zafi kamar hakaba. Da sallama dauke a bakinshi ya shigo falon, tsayawa yayi cak yana kallon gashin kan Maryam cikin mamaki. jin kamshin turarensa yasani dago da kaina dasauri dan bansan yashigoba, Banji sallamarsaba. kasa nayi da kaina gabana na faduwa ganin ya nufo inda nake. Fuskarsa a daure yace, "waya miki kitsonnan?" Kaina nakasa bandagoba nace, "ammi ce" "ammi?" Ya maimaita da alamun mamaki. gyada masa kai nayi. Yana kallon gashin yace, "ammin ce ta miki kitso da attachment?" dasauri nadago na kallesa. "Attachment kuma?" Namaimaita araina. A hankali nace, "A'a ba attachment bane" harararta yayi ganin ta raina masa hankali duk wannan tulin gashin tana nufin tace masa gashintane. zama yayi akan kujerar dake fuskantar ta, yadora kafa ɗaya kan ɗaya. Babu wasa a fuskarsa yace. "Dakkomun abun da ake kitso dashi" kallonsa nayi nace, "wanne abun kitson?" Banza yamata bekuma mata maganaba, shi bayason ayita jan magana shiyasa bekuma tambayarta me aka kara mata a kitsonba, amma yasan mezeyi yagane da kansa, kuma idan har karya ta masa seyayi maganinta, danshi baya kaunar musu. toni bangane meyake nufiba, "abun da ake kitso? Kibiya kenan yake nufi watakila" nafadi haka araina. batare da tunanin komaiba na mike nashiga daki nadakko masa kibiyar bayan nasaka dankwalina na rufe kaina. tsugunnawa nayi sannan na mika masa kibiyar, ina kokarin tashi kawai naji yasa hannunshi ya mikar dani tare da jawoni nafada jikinsa.........✍️ ```Nace zanmuku update around 9,Allah beyiba wani uzurin yakara tsaidani. Am sorry again se yanzu nasamu dama na muku, amma ko editing babu``` *By* *zeey kumurya* *5️⃣5️⃣* *Bismillahirrahmanirrahim* ...........Wata irin bugawa zuciyata tayi da ƙarfi lokacin dana jini ajikinsa batare da zato ko tsammaninaba. shiko mustapha lumshe idonsa yayi cikin wani irin yanayi dabeyi zatoba, zuciyarsace ta hau bugawa da sauri_sauri. kara firgicewa nayi ganin yana gyaramun kwanciyata akirjinshi, gaba-daya na tsorata jikina ya kama rawa saboda bansan mezemunba. runtse idona nayi kawai ina kara shigewa jikinsa batare danasaniba, ajiyar zuciya nahau saukewa ahankali cikin wani irin yanayi, luf nayi ajikinsa ina shaƙar daddaɗan kamshinsa me saukarmun da nutsuwa,wani dumin ni'ima naji yana ratsa jikina, har wani bacci_ bacci me daɗi naji yana fizgata. shiko mustapha kasa aiwatar da komai yayi, wata irin kasalace take baibaye dukkan gaban jikinsa. A hankali ya buɗe lumshashshun idanunsa, cikin matukar dauriya da yanayin daya tsinci kanshi yakai hannunsa dake ɗan rawa yacire ɗankwalin kan Maryam, jedar kitson data tusa a cikin ɗankwalin ta zubo a gadon bayanta. kansa yadora akannata yana shaƙar kamshin kanta daya matuƙar yimasa daɗi, batare dayasan yayi hakanba. A haka yakama jelar kitson ƙeya guda ɗaya yafara warwareshi da kibiya, be iya tsifarba hakan yasa se cisgar mata gashi yake, amma Maryam ko zafi daya batajiba batamasan meyakeba tatafi duniyar shauki, sekara manne masa take tamkar wata mage, da alama ta manta ajikin wanda take. Yayi 12 minutes kafin yagama tsefe kitson guda ɗaya jal, amma dakyar yakarasa saboda baƙon yanayin dayake kara dabaibayeshi mara misaltuwa. A hankali ya ajiye kibiyar akan kujera Zuciyarshi cike da tsananin mamakin ganin tabbas gashintane bata masa karyaba. Yaga mata masu gashi da yawa amma be taɓa ganin kamar na Maryam akan Hausa Fulaninmuba, yasan aunty da mommy da suhailat suna da gashi sosai amma be kama kafar na Maryam ba, kallon kannata kawai yake cike da shauki, shi mutum ne meson yaga gashi akan mace, yana kaunar yaga yana shafashi. A hankali yakai hannunsa yana shafa kitsonnata tamkar me mata tafiyar tsutsa. Wata nannauyar ajiyar zuciya Maryam ta sauke tana kara gyara kwanciyarta ajikinsa. Da sauri ya dago da fuskarta daga kirjinsa yabi fuskarta kallo. Bacci takeyi hankalinta kwance, numfashin datake saukewa a hankali ne, yasa yagane bacci takeyi. Kurawa kyakkyawar fuskarta ido yayi zuciyarsa na bugawa. Cikakkiyar girarta da kwantaccen gashin dake goshinta zuwa gefen kunnenta gami da zara_zaran eyelashes dinta, yasa isa shaida idan ka kalleta kasan zatayi gashi. Kara maida kanta tayi cikin jikinshi tana kara kankameshi. Wata irin kasalace take kara baibayeshi, tsigar jikinsa gaba-daya tatashi. Lumshe idonsa yayi cikin rashin sanin abunyi, yanaji ana kwada kiran Sallah amma yakasa motsa koda danyatsansane. "To meyake shirin faruwa dashi haka ne?" Yatambayi kansa, betaba tsintar kansa a irin wannan yanayinba seyau, yanayine me wuyar fassaruwa ga zuciyarsa dake ta aikin bugawa, kansane yaji yasara masa. tsawon 5 minutes suna zaune a haka, ita Maryam baccinta takeyi cikin kwanciyar hankali, baccin da bata masan sanda yadauketaba. Dakyar ya iya bude idanunsa dasuka masa matukar nauyi, tattaro duk wata dauriyarsa yayi yafara ƙoƙarin rabata da jikinsa a hankali dankarta tashi. Daukarta yayi cak kamar wata baby ya kwantar da ita akan doguwar kujera. A hankali yake kokarin zare hannunsa daga jikinta cikin lallabawa dan karta farka. Mikewa yayi ya kalleta na wasu sakanni, sannan ya fara tafiya yanufi dakinshi jikinshi a matukar sanyaye. kafin yayi alwala har an tada sallah anyi raka'a ɗaya. dakyar yake iya ɗaga kafafunshi yake tafiya. duk da yayi alwala amma yanayin dayakeji bebarshiba, bayan kasala har wani yammmm...yakeji ajikinsa,Tsigar jikinsa har lokacin batabar tashi ba. a haka dai yadaure yaje masallacin yayi Sallah. koda yadawo gidan part din ammi yawuce kamar yadda yasaba kullum, babu kowa a parlon dakinta yashiga bakinsa dauke da sallama. Ammi tana zaune akan darduma tana lazimi ya shigo. zama yayi a gefen gado tare da dafe kansa dayake cigaba da sara masa. seda ammi ta shafa sannan ta juyo ta dubesa tare da fadin, "NOOR an dawo?" Dago kansa yayi cikin dauriya da abunda yakeji yace. "Ehh ammi ya gida" bata amsa masaba se kafeshi datayi da ido kafin tace. "NOOR lafiya kake kuwa naganka wani iri?" "Lafiya kalau ammi" yabata amsa yana zaro wayarsa daga aljihunsa dan karta kuma masa wata tambayar. kallonsa ammi take sosai kamar meson tagano wani abu a tattare dashi, taga kamar wani abu nadamunsa amma tasan halinsa tunda yace mata babu komai koma da akwai ɗin ba fada mata zeyiba. Nisawa tayi tace, "Maryam ta faɗa maka gobe zamu kano ko?" Da sauri yadago yadubi ammi so surprise yace, "Kano kuma?'' ammi tace "ehh, zamuje dubo gwaggon tane bata da lafiya"...ammi tabashi labarin abunda yasamu gwaggo. Cikin tausayawa yace, "Ayya, Allah yabata lafiya" "Ameen" "amma a goben zaku dawo ko?" "A'a sedai jibi" "ok, Allah yakaimu lafiya." wata hirar suka cigaba duk da shi daurewa kawai yake dan kar ammi tagane wani abu, amma shikadai yasan meyakeji ajikinsa da zuciyarsa...... Maryam bayan fitarsa ba jimawa ta fara mutsu_mutsu tana rarumar jikin kujera kozataji shi, gaba-daya baccin yadena mata daɗi se juyi take. A hankali ta buɗe idanta tunda baccin yagagara daɗi. da sauri ta tashi zaune kamar wadda aka tsikara. sosai mamaki yakamata "bacci da magarubarnan?" Tatambayi kanta, tana dafe kanta. tunaninma ya akai tayi baccin tahauyi. "Ajikinshi bacci yadaukeni kenan kokuma ya?" Maryam ta fadi haka a fili tana waro duka idonta waje. shafa kanta tayi taji babu dan kwali. mikewa tsaye tayi ta dauki dankwalinta da kibiyar dake kan kujera ta nufi dakinta zuciyarta cike da tunanika kala_kala, abunda yafi daure mata kai baccin datayi batasan sanda yadauketaba.... Bayan ta idar da sallar magriba ta fara haɗa kayan dazasuyi tafiya gobe, ita da ammi zata bartama kwana biyu zatayi a Kano, tanason ganin Aunty ma, amma Aunty tace mata bazata samu zuwaba kafin azumi kamar yadda tace, abubuwa sun mata yawa sedai cikin sallah insha Allahu zatazo..... Maryam anayin sallar isha'i tadebi abincinta tayi daki bayan ta jera masa nasa akan dinning, da wuri takeso tayi bacci danta matsu gobe tayi, kuma batason ta kara hada ido dashi danwata irin kunyarsace taji ta lullubeta. Mustapha kam daren yau gaba-daya bayajin daɗin jikinshi, kamshin jikin Maryam dana kantane kawai yake masa gizo a hanci, koda ya kwanta bacci daya rufe idansa kyakkyawar fuskarta kawai yake hangowa lokacin datana bacci ajikinshi, da kyar yasamu bacci yadaukeshi........ *KADUNA* Aunty tun ranar data dakko suhailat ta fuskanci wani abu a game da yanayin ciwon suhailat ɗin domin bata iyacin komai, sedai taitashan drinks da kayan zaki su take wuni tana sha, idan kuwa Aunty ta matsa mata taci wani abun, to seta amayar dashi, gashi Aunty tayi_tayi suje asibiti a dubata taki yarda ita wai lafiyarta kalau ta warke. Aunty ta rabu da ita ta kyaleta, saidai duk abunda take Aunty na hanhalce da ita ta saka mata ido ne, kawai tana kallon gudun ruwanta....... _*Agurguje*_ Su Maryam sunje Kano lafiya sundawo lafiya, gwaggo ta tarbesu faran_faran, ammi ta hadata da Mustapha a waya shima yamata yajiki, Maryam hankali ya kwanta taga jikin gwaggo da sauki sosai kuma ta hadu da aminiyarta saleemat da Ummanta... Anshiga wataran Ramadan lafiya, wata me dunbin albarka da sanya farinciki a zukatan kowanne Musulmin kwarai. komai natafiyarwa Maryam yadda yakamata a cikin wannan wata me albarka, saidaifa tsakanin ta da maigidanta babu wani sauyi na mu'amalar auratayya. kwanci tashi babu wuya a gurin Allah yau gashi har ankai azumi 10, yau ne kuma su Maryam zasu fara zana jarrabawar NECO. Tun ƙarfe 8 tagama shirinta cikin uniform dinta. yayi das ajikinta ya mata kyau sosai. jakarta ta dakko ta dawo falo ta zauna tana jiran mustapha yafito dan shi zekaita da kansa. TV na kunna ina kallon wa'azi kafin yafito. se 8:30 yafito, nikuwa duk na zaku kafin yafito seduba time nake karna makara saboda ƙarfe 9 muke da paper. ina ganin yafito na mike nadauki jakata na rataya, sannan na dubeshi nace. "Ina kwana" be amsamunba sebina dayayi kallo, kasa nayi da kaina ina wasa da zoben azurfan hannuna da yaya Sadiq yabani. Tsawon 2 minutes yana kallonta sannan yace. "Ahala zaki makarantar?" da sauri na dago na kalleshi sannan na fara duban kaina, inason ganin menene beyi daidaiba ajikina ganin babu komai cike da confidence dina nace masa. "Ehh" fuskarsa a hade seriously yace. "Bazaki fita da wadannan kayanba" yana gama fadar haka ya juya ya fice, ya barmun kamshinsa a parlon. binsa nayi da kallo baki buɗe harya fice daga falon. dakina na koma dasauri na tsaya gaban mudumi ina karewa kaina kallo. "To me kayan jikina yayi?" nafurta haka a fili cikin raunin murya. riga da wando ne, uniform din. Rigar har kasan gwiwata kuma bata kamaniba sosai, se hijabi nasu karamine na makarantar, amma ni seda yaya sadam ya kara dinkomun wani medan girma danya rufemun duwawu ta bayana. ganin lokaci naneman kuremun sena fice nabi bayanshi nasan baze wuce part din ammiba. umaimah tana tsaye a bakin kofar falon ammi tana waya da wata kawarta tana bata labarin mustapha da irin sonda take masa. kawartata tace mata. "Kai kawata amma natayaki murna da samun masoyi zabin ranki, amma najifa kincemun shu bemasan kina yiba kuma yanada mata." Murmushi umaimah tayi tace, "wannan ba matsalata bane kawata, tunda muna gida ɗaya, zanyi ƙoƙarin naga yajanyo hankalinshi gareni, kuma indai dan ta matarshine ai basonta yakeba itama, dan daga dukkan alamu *matar cushe* cefa, tunda na fuskanci Baya sonta dan baya nuna mata wata kulawa" karaf wannan maganganun da umaimah tayi a kunnen Mustapha dake ƙoƙarin shigowa falon, kofar falon a buɗe take shiyasa yaji. duk dashi bame fuskantar abubuwan mutane bane idan badashi aka kasaba, amma wannan maganar ta umaimah kam yagane dashi da Maryam take, wani muskilin murmushi yasaki yana ayyana wani abu aransa. Ko kallon inda take beyiba daya shiga falon, Umaimah kuwa ganinsa yasa ta katse wayar da sauri tare da faɗin, "yaya NOOR ina kwana" benuna yajitaba balle yajuyo harta saran ze amsa mata. binsa tayi da kallo kamar wata mayya harya shige dakin ammi. Ajiyar zuciya ta sauke wani masifaffen sonsa na kara fisgarta, ta saba dama idan ta masa magana baya kulata indai ba'agaban ammi bane, amma ita hakan baya damunta kokaɗan, dan jikinta yana bata wataran mustapha ze kaunaceta. dakinta ta shige domin tacigaba da wayarta. Ammi ta dubeshi bayan sungama gaisawa tace, "harka kaita makarantar?" Kafin yabata amsa Maryam tashigo da ɗakin da sallamarta cikin ɗari_dari. "Ina kwana ammi" ta fadi haka kanta na ƙasa. Ammi na murmushi tace, "Lafiya kalau ɗiyata ya ibadah" kamar wata munafuka na saci kallonsa sannan nace, "Alhamdulillah" maida kallonta ammi tayi garesa tace, "katashi ku tafi dan takusa latti taran ta kusa" yana wani tsare gida yace, "wai ahaka zata makarantar?" Ammi tace, "kamarya a haka zata?.. meyafaru?" shiru yayi kamar bazeyi maganaba sekuma can yace, "kayan jikinta mana" ammi tace, "A'a mesukayi to? makarantafa zata ba wani gurin ba, uniform ne ai, dole dasu zata ai" bekara cewa komaiba ya mike yayi gaba. daɗine ya lullubeni danda harna tsorata karyace a fasa zuwan. cikin girmamawa nacewa ammi. "Sena dawo" tamun fatan nasara nabi bayanshi da sauri. murmushi ammi tayi, dantagane tsantsar kishine kawai kedamun mustapha. yana gaba ina binshi a baya, seda yarufe part dinmu da key sannan muka tafi. satar kallonsa nayi damuka shiga mota naga ransa abace yake sosai senaji duk babu daɗi. A hankali nace "kayi hakuri dan Allah" banza yamun tamkar bejiba. Arayuwata banason shariya kawai senaji hawaye yacikamun ido, ina ƙoƙarin maidashi amma seda yazubo. kallonta yayi ya tabe baki yacigaba da tukinsa. Har cikin makarantar muka shiga, parking yayi yadubeni bece komaiba, niba bance masa komaiba na bude motar nafita. Binta yayi da kallo harta shige compound din makarantar, lumshe idonsa yayi yatada motar yatafi. Ina shiga natambayi wata daliba inda ake exam din, Tacemun ita canzata inzo muje. se wajen ƙarfe goma aka kawo mana paper'n jarrabawar, bamu fara da wuriba dan haka seda 12 ta wuce muka fito. Tafiya kawai nakeyi ɗan zaman da mukayi harna fara gajiya, gashi bansan a me zankoma gidaba danbecemun zezo yadaukeniba, kuma babu ko sisi a hannuna gashi rana ta kwalle. Ina cikin tafiya kamar a mafarki na hango motarsa fake a bakin gate, wani irin farinciki naji dama rana se dukana take da sauri na karasa wajen motar na bude na shiga, sallama na masa ya amsa ciki_ciki. kwantar da kaina nayi ajikin kujera ina lumshe idona tare da sakin ajiyar zuciya saboda sanyin ac dayafara ratsani gami da shaƙar daddaɗan kamshinsa. seda naji yayi parking alamun munzo gida sannan na bude idona. A hankali nace, "Nagode" be amsamunba se kallona dayayi, kallonsa nayi nima karaf muka haɗa ido, dasauri najanye nawa zuciyata na ɗan bugawa. juyawa nayi na bude murfin motar nafita. shima budewa yayi yafito bayan ya kashe motar. daidai lokacin umaimah tafito zata fita, taci uwar kwalliya a tsakar ranarnan dayake bata azumi yau shine ammi ta aikata. Kawar da kaina nayi daga tana inda take, danzuwa yanzu nagane dalilin dayasa bata kaunata saboda tanason *hearbeat* ɗina. shiko mustapha ganin umaimah yasashi karasawa kusa da Maryam da sauri ya kama hannunta, yana wani dubanta ƙasa_kasa, duba menuni da zallar kauna ga wanda akewa, yafara magana yanda umaimah zataji cikin taushin murya menuni da zallar kaunah. "Haba hubbynah wayace kiyi tafiya aranarnan sekin wahalarmun da kanki, ga azumi gashi kinsha wuyar school, kijira Ni mana nazo nayi aikina" yakarashe zancen yana wani kannemun ido. Niko mamakinsane ya kasheni,nama kasa motsi se kallonsa kawai nake. kamar bashine yaketa haɗe rai ɗazunba. kafin nayi wani yunkuri naji yadaukeni cak..........✍️ *By* *zeey kumurya* *ABINDA KASHUKA...* _*BY*_ _*ZEEY KUMURYA*_ *5️⃣6️⃣* *Bismillahirrahmanirrahim* ........Taga_taga umaimah tayi kamar zata fadi saboda tsabar firgici. da kyar ta iya daidaita nutsuwarta ta tsaya da kafafunta, saboda tsabar razani da abunda tagani, wani tukuku taji ya turnike mata zuciya, bayan daukar Maryam da Mustapha yayi harda wani bin fuskarta da kisses, wannan wanne irin mugan gani tayi yau da ranar Allah. wani abu taji yatokare mata a kirji, binsu tayi da kallo kawai harsuga shige cikin gidan kamar wata sakarya. wata tsanar Maryam taji takara cika mata kowanne sashe na zuciya, takasa koda motsi mustapha da Maryam kawai take hangowa a idonta manne da jikin juna. "ita kuma shegiyar yarinyar harda kara wani kwanciya ajikinsa kamar jikin ubanta" umaimah ta fadi haka afili hawaye masu zafi nazubo mata. ita tananan tana haukanta mustapha bason Maryam yakeba, bazatasha wuyar janyo hankalinsa garetaba, ashe ita bata sanina yana son maryam irin haka. kallon da Mustapha yayiwa Maryam shi kadai ma ya isa yatada mata hankali, balle kuma ganinta rungume a jikinsa. Umaimah tayi nadamar fitowar ta a wannan lokacin babu adadi, datasani tun dazu da ammi taketa cemata tatafi aiken tatafi, dabataga wannan abun dayake kokarin tarwatsa mata zuciyaba. son mustapha kullum karuwa yake acikin zuciyarta, mijin datake mafarkin ta aura taki sauraren kowa saboda shi, yau gashi ta haɗu da wanda yafi wanda take tunanin samun ma, amma wata banzar yarinya tana kokarin kawo mata cikas, ta dade a tsaye a gurin tana sake_sake da kyar ta iya jan kafarta tatafi, da ji tayima kamar ta koma ta fasa fitar........ Idona a runtse harya saukeni, sosai kirjina ke dukan uku_uku cikin wani irin yanayi. gabadaya salon nasa yadauremun jijiyoyin jiki tamau, jinin jikina kuwa babu tantama ya daskare. Kaina naƙasa nakasa kallon koda inuwarsace har ya buɗe Kofar part dinnamu ya shige abunsa beko ƙara kallon inda nakeba. jan kafata dakyar nima nayi nabi bayansa. harnayi wanka nayi Sallah bandawo daidaiba, kwanciya nayi akan gado na lumshe idona ina tuno ni a jikinsa, wani murmushi ne na farinciki ya subcemun, kankame filo nayi a kirjina inajin dama shine.(🙄azumi ne dai mero) bansan sanda bacci me daɗi yadaukeniba......... Ammi tana kwance akan gadonta tana bacci, sama_sama takejin wayarta na ringing. A hankali tatashi zaune, bacci fal idonta ta janyo wayar ta daga ta kara a kunnenta. "Assalamu alaikum" daga ɗaya ɓangaren aka faɗa. 'wa'alaikassalam" ammi ta amsa sallamar tana tunanin kamar tasan Muryar me maganar. gaisawa sukayi duk da ammi bata gane shiba. Daddy ganin bata gane shiba yace, "kina magana da yaronki mainasara" murmushi ammi tayi tace, "yaro kodai ubangida" cikin zolaya daddy yace, "yaro dai, tunda ke baki nemeniba nina nemeki, kodan yanzu ɗanki yazo hannunkine shiyasa kika dena neman mu" murmushi me sauti ammi tayi tace, "to ayi hakuri na tuba kaina bisa wuyana zandinga nemanka akai_akai daga yanzu insha Allah" "dakuwa kin kyauta, dan zanso hakan sosai" batare da tunanin wani abu akan maganar daddy ba ammi tace. "yame jiki kuwa" "jiki da sauki Alhamdulillah, tunda yanzu yadawo hayyacinsa yana gane abubuwa." "Masha Allah, Allah Ubangiji ya ƙara sauki yasa kaffarane" "ameen ya Allah" daddy yatambayi lafiyar su Maryam da kowa da kowa, ammi tace duk suna lafiya. Numfasawa daddy yayi yace. "Hajiya Maryam nakirakine muyi magana akan dukiyar Mustapha dake hannuna, tun kwanaki nakeson muyi maganar ciwon Sadiq yatsaidani amma yanzu tunda komai yadaidaita semusan yanda za'ayi." ammi tace. "Yallabai, aini bani da hurumi akan wannan maganar, Muhammad ai ɗankane kuma dukiyarsa takace, a ganina babu wani bukatar yaza'ayi da dukiya, kacigaba da juyata kawai agurinka, amma ni bazan karbi komaiba, kuma Muhammad haka" cike da mamakin ammi daddy yace. "Hakane Hajiya, mustapha ɗanane amma yazama dole nabashi hakkinsa dake wajena, tunda yanzu shima yakai munzalin daze iya juya ta" "to shikenan kazamu lokaci kazo semu tattauna akan hakan." godiya daddy yamata sukayi sallama. Se kusan la'asar natashi daga bacci. Fuskata na wanke na kuskure bakina sannan na nufi part din ammi, dan anan muke aikin azumi na duka gidan. A baranda natarar da ammi da mama A'isha suna ferayar dankali. Mama kuma tana gefe tana wankin waken kosai. Bayan mun gaisa ammi ta dubeni tace, "ɗiyata har kin tashin kenan, dazu NOOR yashigo ai, yacemun harkun dawo amma kin kwanta, ya exam din.?" Kaina na ƙasa nace, "Alhamdulillah" "Masha Allah, Allah yabada sa'a" gabadaya muka amsa da "ameen" ciki na shige na nufi kitchen. Aunty zuhura ce, kadai a kitchen din tana girki. "Aunty zuhura sannu da aiki" nafada bayan na shiga kitchen din. "Yawwa Mamana, kindawo kenan" "nadawo Aunty zuhura tun kafin 1." "Sannunki ya jarrabawar?" "Lafiya kalau, Aunty zuhura. Bari nazo natayaki aikin" Aunty zuhura na murmushi tace, "dakinyi zamankima danna kusa karasawa miyace kawai tayi saura, kar a wahalar da babynmu" murmushi kawai nayi bance komaiba, nafara tayata aikin. Zuhura dama tana sane tayiwa Maryam wannan zancen, danta fuskanci har yanzu babu abunda yashiga tsakaninsu da mustapha, danta fuskanci yanada shegen miskilanci, amma zata taimakawa Maryam da dabaru ta yanda zataja hankalin mustapha zuwa gareta, Wannan miskilancinnasa duk se tayi maganinsa. fita tayi tacewa Maryam tana zuwa, bayan kamar minti goma ta dawo da waya kare a kunnenta tana faɗin. "Bangane tunda kukayi aure haryanzu babu wani abu daya tsakaninkuba." shiru tayi alamar tana sauraren wanda suke maganar na tsawon 50 seconds sannan tace. "Haba salma kekamar ba wayayyiyaba ace haryanzu kinkasa ɗaukar hankalin Tahir zuwa gareki yana mijinki kuma kuna gida ɗaya, haba salma karki bani kunya mana." Shiru ta karayi na wasu sakanni kafin tace, "wannan duk ba matsala bane, salma dan hadaku aure akayi, ai baza'ace shikenan bazakuyi soyayya kuyi rayuwar aure kamar kowaba, kuma koda baya sonki tunda ke kina sonshi sekiyi kokari kibi duk hanyoyin dazaki jawo hankalinsa zuwa gareki, kefa macece" Takarayin shiru sannan tacigaba da fadin. "Akwai hanyoyi da dama salma dazakibi kijawo hankalin mijinki zuwa gareki, batare daya gane danshi kikeba kokuma kina son shine, shifa namiji tamkar jaririne agurin matarsa duk ta yadda kikabi dashi haka ze tashi yana miki, yanzu idan kika zauna kuncigaba da rayuwa a haka kefa zaki cutu, danshi idan yana da bukatar mace aurensa ze kara, kuma yadinga bawa matarsa kulawa kekuma kina gefe ko oho, gwarama tun wuri kifarka daga nannauyar baccin dakike kibawa makiya kunya, kijawo hankalin mijinki zuwa gareki tun kafin dare ya miki kizo kina cizon yatsa" ta karayin shiru tana saurare sannan tace, "yawwa kawata yanzu naji batu, bari na baki wasu shawarwari danasan insha Allahu zasu taimaka miki. idan yana zaune a falo irin da daddarennan yana kallo, kekuma ki tsalo wankanki cikin kananun kaya, ki baza kamshi a kowanne lungu da sako na jikinki me daɗin gaske, wanda dole idan ya shaka seya dago ya kalleki, karkiji kunya ko tsoron komai, kifito falon abinki kina tafiya ta daukar hankali, kiyi kamar baki ganshiba kishige kitchen kamar zaki dauko abune, in kinfito zaki koma kice masa sannu, kiyi kamar se lokacin kika ganshi kikoma daki abinki, kiyi kamar kwana uku kinayin haka, seki dena fitowar. Nina faɗa miki da gayyama zena zaman falon danyaga fitowarki, duk randa baki fitoba kuwa ki leko ta window zaki gansa yana kallon kofar dakin ki hankalinsama gabadaya baya kan kallon, to yanaso kifito ya shaki kamshi yaga kuma abubuwan harka na juyawa. Sannan kuma kisan dabarun dazaki na yi jikinki na haɗuwa da nashi" Shiru ta ƙara yi, sannan tace. "Kai salma na rasa irinki, yanzu bakisan yanda zakiyi jikinku ya haɗu ba, to bari na baki misali ɗaya. Bayan kinyi abinda nace miki kamar na sati ɗaya ko biyu. wataran bayan kinfito falon, sekinzo kusa dashi, seki fadi da gangan ki zube a kasa, zaki ga yataso da saurinsa yana tambayarki meyafaru duk yabi ya rude, to yana tsoron kar ko kinji ciwo sosai yadena ganin gilmawarki. kekuma seki langwabe harda hawayenki ki rirrikeshi kina nuna masa kin firgitane tare da zuba masa shagwaba, duk miskilancinsa ranar zakisha mamaki nina faɗa miki, kamshin dakike zubawa kadai ya isa ya hautsina masa lissafi." Shiru ta kumayi daga can tayi dariya tace, "yawwa kawata kinfara hawa layi haka nakeso, ki dauke masa hankalin daga kan yanmata masu farautar mazajen wasu, dama gaki da kyanki da jiki na daukar hankali....." Shawarwari da dabaru masu yawa zuhura ta lissafo sannan tayi sallama ta aje wayar. kallon Maryam tayi wadda tayi tsit tana sauraren zuhura da dukkan hankalinta tace. "Sannu mamana, na barki kinata aiki ke kadai ko, wlh wata kawatace ta kirani akan matsalar ta ita da mijinta" murmushin ƙarfin hali na kakaro nace, "bakomai Aunty zuhura ai babu ma wani aikin" murmushi kawai Aunty zuhura tayi. suna aikin tana satar kallon Maryam, yanda tayi tsumu alamun tana tunanin wani abu, tasan abubuwan data faɗane Maryam take tunani akai, dama kuma duk wayar datayi pretending ne kawai, dan Maryam din taji tayi, ai kuwa tayi nasara danta saka Maryam a zullumi da tunani... Har aka sharuwa bansakashi a idonaba, jikina yau duk a sanyaye. Maganganun Aunty zuhura se yawo suke a kwanyata. "Tabbas duk abubuwan data faɗa hakane, karnaje natsaya kallon ruwa kwado yamun kafa, yazama dole nima nadage dan ganin na jawo hankalinsa gareni, tunda ina tsananin sonsa, ga kuma masu kawo masa farmaki daga waje, amma matsalar bansan ta ina zan faraba, ko shawarar Aunty zuhura zannema, takaramun haske da dabarun yanda zanjawo hankalinnasa.".... Haka dai naita tunane_tunane nikadai. Be shigo gidanba seda aka idar da da sallar asham, ina jinshi ya kunna kallo a falo amma nakasa fita falon, duk da zuciyata na azalzalata naje nafara aiwatar da abunda naji aunty zuhura nafadawa kawarta amma nakasa, hakura nayi na kwanta bacci saboda tashin dare..... Washegari bantashi daga barci da wuriba saboda yau se 11 mukeda exam, kafinma na tashi daga barci ya fita. seda na gyara gidan tsaf nayi wanka na shirya cikin Uniform dina sannan na nufi part din ammi domin na gaisheta. Suna zaune a falon ita da umaimah nayi sallama na shiga, ammi ta amsamun amma umaimah se bina datayi da kallon banza. muka gaisa da ammi cikin fara'a. duban umaimah nayi dan kar ammi ta zargi wani abu nace mata "Aunty umaimah ina kwana?" Umaimah da tunda Maryam ta shigo taji wani baƙin ciki ya turniketa, saboda ganin Maryam yanzu ya kara tuno mata da abunda yafaru jiya. maimakon ta amsawa Maryam gaisuwarta seta faki idon Aunty ta galla mata harara tare binta da wani wulakantaccen kallo, ran Maryam ya ɓaci taji babu daɗi sosai, amma ta daure ta dubi ammi tace. "Ammi zan wuce naga 10:20 tay..." Bangama rufe bakina sassanyan kamshinsa ya ziyarci hancina. Lumshe idona nayi cikin jin daɗi ina sauraren daddadar muryarsa yana sallama. Rabona dana ganshi tun jiya daya dakkoni daga school, da asubama daya tasheni sahur ban wani ganshiba ina buɗe kofa ya juya ya tafi.. muryarsa naji yana faɗin, "taso mu wuce" mikewa nayi cikin jin daɗi dannasan dani yake. Ammi tana murmushi tace, "har ina zanyiwa yiwa Ali driver magana yakaita, ashema kana tafe" kallon Umaimah data kura masa ido da mayen kallonta yayi, sannan ya maida kallonsa kan Maryam, yana wani kankanne ido irin kallon luv dinnan yace. "Nafison na kaita da kaina ammi, karnaje amun gudu da ita a mota a wahalarmun da ƴar matata." yana gama faɗin haka ya juya ya fice abunsa. Naji daɗin abinda yafada sosai ko ba komai ya wankemun bacin ran da umaimah ta samun, duk da nasan ba har zuciyarsa haka bane, dan umaiman yayi, kamar jiya daya ɗaukeni amma farincikin danaji baze misaltuba, dandai ammi tana gurinne dase na faɗa masa magana nima wanda zata kara kular da umaimah'n. Cikin jin kunya nayiwa ammi sallama nabi bayanshi. Aiko Umaimah ta shaka ba kadanba. Amma duk da haka ba gudu ba ja da baya a son mustapha yanzuma ta fara, wannan soyyayar dayake nunawa Maryam setayi duk yadda tayi ta dawo kanta seta jawo hankalinsa gareta kota yayane.......✍️ *Kuyi hakuri da wannan na koma school ne.* *By* *zeey kumurya* *5️⃣7️⃣* *Bismillahirrahmanirrahim* ..........Ammi ta rakasu da murmushin jin daɗi, dama ita burinta kenan taga sun haɗa kansu kuma Alhamdulillah ta lura babu wata matsala a zamannasu.... Yana gaba ina binsa abaya har muka karasa gurin motar, na zagaya na shige bayan shima ya shiga. kafin ya kai ga kunna motar wayarsa ta hau ruri cikin amo me daɗin sauti. dagawa yayi ya kara a kunne tare da yin sallama. Amsa masa akayi sannan yace, "Aunty ina kwana, ya ibadah?" Da sauri na kallesa jin ya ambaci sunan Aunty. daga can ɓangaren bayan Aunty amsa masa gaisuwar ta ƙara da faɗin, "Muhammad suhailat ce keson magana dakai, ta dameni inkira mata kai, wai ita idan takiraka baka samun wayarka." Cikin matukar mamaki yace, "suhailat kuma?" Gabanane yayanke ya fadi jin sunan Aunty suhailat daya ambata. Aunty tace, "ehh" bekara cewa komaiba duk da zuciyarsa cike take da mamakin meyakai suhailat gidan Aunty, tunda yasan ba zuwa takeba. nikuwa tsumu nayi ina saurarensu. Suhailat bayan Aunty ta mika mata wayar cikin azabarbi tace, "yayana! I missed you, dan Allah yaushe zaka dawo, wlh gaba-daya duk nabi nadamu, ganinka kawai nakesonyi" lumshe idonsa kawai yayi bece mata komaiba. suhailat taita masa magana amma kememe yaki cemata ko "kala" harda kukanta amma yayi biris abunsa karshema kashe wayar yayi dan kar Aunty ta karba ta masa faɗa akan kin kula suhailat ɗin da yayi. kallon Maryam yayi ta kasan ido, ta haɗe rai sosai an tsuke bakinnan. tabe bakinsa yayi ya tada motarsa suka wuce....yauma damuka tashi shiyazo ya ɗaukeni, Ni mamakinshi nake yanda yake barin kasuwa yadawo ya dakkoni sannan ya koma. Bayan ansha ruwa kafin sallar isha'i, su Maryam suna zaune a falon ammi dukansu suna hira. Ammi ta dubemu nida umaimah tace, "ɗiyata ku tashi kuje gurin Musa tailer, seki zabi ɗinkin da kikeso ya miki ya kuma gwadaki" a hankali nace "to ammi, da nisane gurin?" Aunty zuhurace tace, "da ɗan nisa kadan gaskiya" umaimah kuwa kallon su kawai take tana tabe baki, dan zuhuranma ba wani shiri suke da itaba. Ammi ta dubeta tace, "Autatah ki tashi kuje tare, bari nakira NOOR yakaiku idan babu abunda yake idan kuma yana wani uzurin sena kaiku da kaina." Da umaimah harzatace kanta na ciwo bazata raka maryamba, amma jin ance mustapha ne ze kaisu seta fasa. Ammi ta dakko waya takirasa ta sanar masa, yace mata su jirasa gashinan zuwa. ammi na sanar musu Umaimah ta tashi da sauri ta shige daki, turare ta bulbula har yayi yawa. Tana fitowa Aunty zuhura tace, "kai umaimah wannan turaren dakika saka yayi yawa har yana hawa kai fa" murguda baki tayi ta zauna batace komaiba. Ammi ce tace, "gaskiya autah yayi yawa" cikin sangarta tace, "ammi feshi biyu nayifa haka turaren yake" ammi zata kuma Magana wayarta tayi ƙara, dagawa tayi mustapha yace mata yana jiransu a mota. Bayan ta kashe wayar ta dubemu tace, "ku tashi kuje kunsan bayason jira" Zuhura na dariya tace, "ai da gimbiyarsa dole yajirasu" murmushi nayi kawai, na musu sallama muka tafi. A gajiye nake tafiya yau nagaji sosai kuma azumin yaɗan kolani. ina gaba tana bina a bayana danna rigata fitowa daga falon. yana zaune acikin motar ya buɗe murfin ƙafarsa ɗaya na waje yana latsa wayarsa. zagayawa nayi na buɗe front seat na shiga da sallama ɗauke abakina. batare ɗaya dagoba ya amsamun acan ƙasan makoshi. Yana ganin umaimah tataho ya maido ƙafarsa ya rufe Kofar, kunna motar yayi, ya kuma kunna light din motar. kallon fuskar Maryam yayi yaga itama shi take kallo karaf suka haɗa ido. Hararata yayi nayi sauri na ɗauke idona daga kansa ina kebe fuska. umaimah ta buɗe bayan motar ta shiga sannan tace, "yaya NOOR ina wuni, dafatan kasha ruwa lafiya" "lafiya" yabata amsa atakaice yana tada motar. reverse yayi megadi ya buɗe mana get muka fice daga gidan. umaimah na masa hanya har muka karasa. A kofar wani shago mukayi parking, umaimah ta fito ta dubi Maryam daketa lumshe ido bacci fal cikinsu tace, "ki fito" mustapha na kallon Maryam yace, "ina zata?" Umaimah tace, "ciki zamu shiga ze aunatane ta kuma zaɓi ɗinkin datakeso" fuskarsa a tsuke yace, "bazata ta shiga cikin wannan mazanba" galala umaimah tayi tana kallonsa baƙin ciki fal ranta yanda mustapha yake nuna kishin Maryam akan komai. Maryam kam sama_sama take jinsu amma bata fahimtar mesuke cewa bacci yafara fuzgarta. umaimah batace masa komaiba ta juya ta nufi cikin shagon, bayan kamar 10 minutes suka fito tare da toilor ɗin. gaishe da mustapha yayi, Maryam kuma data wartsake dakyar ta gaisheshi. Ya dubeni yace, "Hajiya wanne irin ɗinki za'a miki?" Nace masa "style me kyau kawai" yace, "doguwar riga ko riga da skirt koda zani?" "Kamata doguwar riga" mustapha dake latsa wayarsa tamkar baya saurarensu ya fadi hakan. na kallesa kawai bance komaiba. Toilor'n yace, "angama ranka ya dade" umaimah ma ta faɗa masa irin ɗinkin takeso. Toilor'n yace to nafito ya gwadani, amma Mustapha ya hana. Toilor'n yace masa, to umaimah seta gwadani amma kememe bawan Allah nan yahana waishi baza'a gwada masa mata a titiba. Dariya kawai toilor'n yayi yacemun muje to zezo har gida ya karbi measurement ɗina. muna cikin tafiya a mota naji mutum ya janyoni jikinsa. lumshe idona nayi ina sauke ajiyar zuciya. daidai kunnena yakai bakinsa cikin wata sanyin murya yacemun "kin sakarmun nauyi fa" aiko kamar ya tunzurani nakara manne masa a jiki. umaimah dake baya ta hadiye wani yawu me daci a ranta tana faɗin. "Tsabar jaraba yana tukinma amma seya wani rungumeta, gashi se wani rada_rada yake mata, kamar sun manta da ni a motar" mtss taja siririn tsaki tana hararar bayan Maryam. Mustapha sarai yaji tsakin da umaimah tayi kawai sharewa yayi. kafin suje gida Maryam tayi bacci ajikinsa. yanayin parking umaimah ta buɗe kofa ta fice. Kallon Maryam yayi yaga baccinta take hankali kwance, se numfashi take saukewa a hankali. Kurawa fuskarta ido yayi a karo na biyu a rayuwarsa bekuma san dalilin kallonnata dayakeba. tabe bakinsa yayi bayan yagama ƙare mata kallon, a hankali yafara ƙoƙarin rabata da jikinsa. Maryam kuma ta ƙara kankameshi. Lumshe idonsa yayi ya ƙara rabata da jikinnasa. Maryam ta buɗe idonta a hankali tana jingina jikinta da kujera, buɗe murfin motar yayi ya fice abinsa, bekara koda kallon inda nakeba . da kyar nima na daure na fito, wani irin bacci nakeji. Kulle motarsa yayi yanufi masallaci dan har anyi isha'i anfara asham. Ban koma part din ammi ba, na koma namu...... Kwanci tashi asarar mai rai. Yau 23 ga watan Ramadan yau kuma muka gama exam dinmu ta NECO, dayake babu wani interval sosai. A 'yan kwanakinnan wata shakuwace ta shiga tsakanin Maryam da Mustapha, wanda su kansu basu gane hakanba. Mustapha matukar da umaimah a guri ze nunawa Maryam kulawa da tattali koda a gaban ammi ne kuwa. Hakan kuwa bakaramin kona ran umaimah yakeba. gashi kullum son mustapha karuwa yake a ranta tarasa yadda zatayi, zuciyarta nabata shawarar ta sanar masa kawai koze amshi tayinta, amma kawarta ta hanata tace ta bari a gama azumi tasan mezasuyi dole mustapha yasota. Maryam kam ta fara gwada abubuwan da taji zuhura na fadawa kawarta a waya, ta kuma dage da addu'a akan Allah ya waiwayo mata da hankalin mustapha gareta. Mustapha kuwa yanzun baya gane kansa dan kwata_kwata bayajin daɗin jikinsa, yakuma rasa meke damunsa. Gashi yanzu babu abunda yaji yanaso sama daya dinga jin Maryam ajikinsa yana shaƙar daddaɗan kamshinta, yanason kamshin jikinta sosai. kullum seya ayyana ya rungumeta ba'adadi amma seya kasa. saboda yana ganin Maryam zata rainashi gata yarinya ƙarama ai girmansa seya zube. Ya lura kuma yarinyar itama miskikar kantace. Yau exam din rana sukayi 2_4 daya dakkota be koma kasuwaba ya kwanta a dakinsa. ita kuma Maryam tana part din ammi sunata aikin girki. tunani yakeyi kawai ta yanda za'ayi su kwana tare, badan ya mata komaiba sedan kawai soyake yajita a jikinsa suna bacci tare. mikewa yayi ya fice bayan yasamo mafita. yau nasha wahalar azumi sosai, dama gashi har yau bansha a zumiba. kafin asha ruwa kamar kullum zandebo abincinsa in ajiye masa akan dinning, mukuma dama a part din ammi muke shanruwa. Bayan na jera masa komai akan dinning na koma part din ammi na sheme akan carpet kafin akira sallah. Aunty zuhura se tsokanata take. Ammi kuwa se sannu takemun tana faɗin, "wannan megidannawa yana wahalarmun dake ɗiyata" duk a zaton ammi karamin ciki ne dani, kullum seta dinga cemun Yakamata insha azumi in dan huta saboda lafiyarmu. Idan ta fadi haka senaita mamaki araina ince. "Dududu yaushe muka tare da har suke tunanin inada ciki, inma ha hakaba nida ko wata mu'amalar aure bata taɓa shiga tsakaninmuba ta ina za'a samu cikin." Da'aka sha ruwa kunun aya kawai nasha yacikamun ciki. Aiko jikina ya mutu murus kamar anmun shegen duka, dakyar na lallaba na koma part dinmu nayi Sallah, ina idarwa na baje akan gado se bacci. Ban tashi farkawaba se wajen 9:30. sallar isha'i nayi na fito falo domin na samarwa kaina abunda zanci. yana zaune a falo yana kallon labarai. "Sannu da zuwa" na masa ya amsamun dakai. kan dinning na nufa na dibi sauran abincin daya rage naci na koshi sannan na koma daki. Mustapha daketa satar kallon Maryam harta gama ta koma daki. Bayan kamar 10 minutes da shigarta dakin, ya dauki wata leda dake gefenshi yabi bayanta. A hankali ya taɓa handle din dakin yaji kofar a buɗe take, ajiyar zuciya yasauke ya tura kofar a hankali. kamar yadda yazata Maryam tana toilet tana wanka, murmushin mugunta yayi ya aiwatar da abunda zeyi ya fice. Yana fita ba jimawa Maryam ta fito daga toilet tana daure da towel. gaban mudubi na nufa na zauna akan stool nafara shafa tsadaddadun lotions masu kamshi ajikina. seda na mulke jikina tass dasu sannan nabi kowanne lungu da sako na jikina na shafeshi da daddaɗar humrar da Aunty zuhura ta bani gami da body spray me sanyin kamshi. lokar mudubi na janyo na dakko alawata da kullum senasha kafin na kwanta, itama Aunty zuhura ce ta bani tace nadinga sha kafin na kwanta bacci. kokaɗan banajin bacci a idona tunda banjima da tashiba. Addu'a nafarayi Allah yasa kafin nagama shiryawa yabar falon, intafi part ɗin ammi musha hira, dan wataran hanani zuwa yake yace dare yayi, shiyasa kafin yadawo nake guduwa harse yagaji da kansa yazo yakirani. white lipstick na shafa kawai a lips ɗina na Mike da nufin na dakko kaya. Abunda nagani a kan gadone yasani kwalla wata gigiciyar ƙara a matuƙar firgice nayi baya na manne da bango ina runtse ido tare da karanto duk addu'ar datazo bakina. A hankali na buɗe idona kaɗan cikin tsoro na ƙara kallon kan gadon. abunda nagani dai shi nakara gani, kadangarene jangwala gwada katoto kamar ma yana motsi yanzu. da gudu na nufi kofa na buɗe nafice daga dakin nama manta babu kaya a jikina se ɗan guntun towel........✍️ *By* *zeey kumurya* *ABINDA KASHUKA...* _*BY*_ _*ZEEY KUMURYA*_ *5️⃣8️⃣* *Bismillahirrahmanirrahim* ........... Mustapha dake zauna a falo yana kallonsa hankali kwance tamkar beji ƙarar da Maryam ta kwallaba. A matukar tsorace na fito falon jikina na wata irin kyarma karasawa nayi na faɗa jikinshi cikin fitar hayyaci sosai na tsorata saboda arayuwata ina bala'in tsoron kadangare. lumshe idonsa yayi jinta ajikinshi yana sakin boyayyiyar ajiyar zuciya, Maryam kam ta kankameshi rawa kawai jikinta yakeyi idanunta a runtse. A hankali yasa hannunsa yana ƙoƙarin rabata da jikinsa, cikin basarwa yace, "mene haka?" hannunta na rawa ta nuna masa Kofar dakinta. Lips dinshi na kasa ya lasa wannan yace, "what happened?" Maryam da idanunta babu abunda yake hangomata se kadangarennan ta kasa masa bayani, tsigar jikinta se tashi take tanajin tamkar kadangarenne a jikinta. rikeshi tayi sosai tana sakin kuka tama kasa masa bayani. Lumshe idonsa ya kumayi cikin jin bakon yanayi na ziyartarsa saboda yanda sulbin fatar jikinta yake goguwa ajikinsa. yanajin kukan datake har cikin ransa bakuma ya tunanin ze iya jurar cigaba dajin kukannata. Tausayintane ya tsirga masa ganin yadda duk tabi ta tsorata jikinta se ɓari yake, beyi tunanin zata tsorata hakaba. a hankali ya ƙara saka hannunsa ya dago fuskarta daga jikinshi zuciyarsa na ɗan bugawa ya kura mata tsumammun idanunsa. Maryam da har yanzu ta kasa buɗe idonta se ƙara runtse idanta take, ta kudundune jikinta tanajin yanda idanuwansa ke yawo ajikinta. cikin kasalalliyar murya ya ƙara tambayarta. "Meyafaru a dakinnaki" "lizard🦎" ta bashi amsa hawaye na zubo mata. Yana nuna so surprise yace, "lizard?" Gyada masa kai tayi har lokacin idonta a rufe yake. ƙoƙarin sauke yayi daga jikinsa yana faɗin, "bari na duba dakin" kuka Maryam ta saka tana ƙara kankameshi gani takeyi yana barinta kadangaren ze kara biyota. lips dinsa ya lasa tare da fesar da numfashi yace, "zan cire miki ne daga dakin" girgiza kai Maryam ta hauyi cikin kuka tace "Ni kar katafi ka barni tsoro nakeji" cikin sanyin murya yace, "to muje tare, seki nunamun inda yake" nanma Maryam kin yarda tayi domin kome za'a mata bazata ƙara komawa dakinta a yauba. Be kuma cewa komaiba, jikinta yabi da kallo, musamman ma gashin kanta daya bazu a gadon bayanta. a hankali yakai hannunsa yana tattare mata gashin ya haɗe shi guri guda shafashi ya shiga a hankali yana lumshe ido. ƙara cusa kanta tayi cikin kirjinsa tana shaƙar daddaɗan kamshinsa gami da sassauke ajiyar zuciya, ta rike shi gam ga dukkan alamu har lokacin a matukar tsorace take. A hankali yayi ƙasa da hannunsa yafara shafa wuyanta zuwa bayanta cikin wani sabon yanayi dayake fizgarsa. wani abu naji ya tsirgamun a gabadayan jikina lokacin danaji lallausan tafin hannunsa akan fatar bayana, wani irin tsorone ya ƙara dirarmun, zuciyata ta fara bugawa. mutsu_mutsu na farayi ajikinsa hawaye na zubomun wanda bansan dalilinsuba. jin tana mutsu_mutsu mustapha ya fara bubbuga bayanta a hankali irin yanda akewa yara, bakinsa yakai saitin kunnenta yafara hura mata iskar bakinsa. tsit nayi nadena mutsu_mutsun cikin jin daɗin abinda yakemun, a hankali wani bacci me daɗi yafara fizgata bansan sanda baccin ya ɗaukeni ba gaba-daya. Jikintane yaji ya saki rigon data masama ta cika, hakan ya tabbatar masa da bacci ne ya ɗauketa, ya fuskanci tana da saurin bacci. a hankali ya dago da fuskarta daga jikinsa ya kura mata ido, a duk lokacin daya kalleta yana ganin wani abu dayake daure masa kai a tattare da ita. ɗan karamin bakinta ya kalla data ɗan turoshi gaba, pink lips dinnan nata se kyalli suke, ajiyar zuciya ya sauke yayi ƙasa da idonsa, towel jin jikinta ya kunce yanda ta kudundune jikinta ne yasa be zameba daga jikinnata, amma gaba-daya rabin kirjinta a waje yake. "jikinta me kyau ko ina bul_bul" ya furta hakan a ransa batare daya saniba. sosai jikinsa ya sauya masa ganin maryam a haka, kasalace take ƙara lullubeshi,wani irin sanyi jikinsa yayi. duk yanda zuciyarsa ke tunzurashi yayiwa Maryam wani abu amma yakasa, lips dinta yabashi burgeshi yanaso yamata koda kiss ne amma yakasa aiwatar da komai, daya daga hannunsa da nufin ya shafa kirjinta seyaji jikinsa ya kama rawa, kansa na sara masa. Rungumeta kawai yayi tsam ajikinsa cikin wani irin yanayi yana shaƙar kamshinta dayake ƙara saukar masa da kasala. kusan 30 minutes suna haka, Maryam tanata baccinta cikin kwanciyar hankali, saɓanin mustapha dayake cikin wani irin yanayi na rashin jin dadi me wuyar fassaruwa, duk da yanajin wata nutsuwa nabin jikinshi amma yarasa meyake masa daɗi ga mararsa data daure masa. da kyar ya iya ƙoƙartawa ya kashe TV ya dauki maryam sukayi dakinsa, dakyar yake iya taka kafarshi danma maryam ɗin bata da wani nauyi. a hankali yake ƙoƙarin shinfideta akan makeken gadonsa, kamar wata jaririya haka ya lallaba ya a jiyeta yana cize lips dinsa. yana ƙoƙarin zame hannunsa daga jikinta ta zabura a tsorace ta kankameshi ajiyar zuciya ta sauke tana ƙara lafewa ajikinsa. runtse idonsa yayi tsigar jikinsa na tashi, wani yarrrr yakeji ajikinsa. idanunsa a lumshe batare daya buɗe ba, yakai hannunsa ya fara gyara mata towel ɗin jikinta dake ƙoƙarin barin jikinnata gaba-daya, idanuwansa bazasu iya jurar kallon jikintaba a yanayin dayakejinsa a yanzu. Seda ya tabbatar yarufe duk wani abu daze iya tayar masa da hankali a jikinta, sannan ya buɗe idanunsa da suka kada sukayi jajur ya sauke akanta. Cinyoyinta ya kurawa ido, yanajin tamkar yakai hannu ya shafasu amma yakasa koda daga danyatsansa ɗaya da niyyar hakan, blanket ya jawo ya lullubeta. zare hannun damansa yayi daga jikinta ya dafe kansa dake sara masa. "Me yake shirin faruwa dashine?" ya tambayi kansa cikin dacin zuciya. shi mutum ne meson yaga ya haifi ya'ya a rayuwarsa amma baya tunanin zega wannan ranar, tunda gashi ya ƙara tabbatarwa da kansa bashi da lafiya kamar kowanne ɗanamiji. ada canbaya abun baya damunsa kokaɗan, amma yau yaji yana bukatar shima yazama mutum kamar kowa, yana bukatar samun nutsuwa ajikinsa, yanajin feeling sosai a yanzu, amma baze iya tabuka komaiba. numfashi ya fesar daga bakinsa yafara kiran sunayen Allah aransa koyaji sauƙin abunda yake damunsa. A hankali nutsuwa ta fara zuwar masa, zuciyarsa ta fara sanyi daga kunar datake masa. cikin kwarin zuciya ya lallaba ya zame maryam daga jikinsa domin yaje ya watsa ruwa ko yaji sanyi ajikinsa. A hankali ya mike ya nufi toilet amma kafin yakai ga shiga yaji muryar Maryam a firgice tana kiran "yaya,Yaya, lizard!" Tsayawa yayi cak tare da juyowa ya kalleta, idanunta a rufe amma se shafa gadon take tana kiran sunansa, be ankaraba yaga tazo bakin gado garin lalubenta zata fadi, kafin yayi wani yunkuri harta fado kasan gadon. da sauri ya karasa ya tallafota jikinsa a hankali yace, "sorry" yana gyara mata gashin kanta dayake ƙoƙarin rufe mata ido. buɗe idonta tayi a hankali cikin shagwaba tace, "shine zaka tafi ka barni nikadai seya ƙara biyoni" cize lips dinsa yayi, cikin gajiyawa yace. "Babu wani lizard fa" tana matso hawaye tace, "Allah akwai nafa ganshi da idona" bece mata komaiba ya maidata kan gadon ya direta ya juya. kudundunewa nayi acikin blanket, har yanzu a tsorace nake da ganin kadangaren danayi. seyanzu na tuna babu komai a jikina se towel, gabanane yafadi dana tuna shifa ya daukoni ya kawoni dakinsa tunda bada kafata nazoba. "Yanzu haka ya ganni babu kaya fa" na fadi haka a raina. ganin ze shige toilet din nayi sauri nace, "nifa Allah tsoro nakeji bazan iya zama ni kaɗaiba" akufule yajuyo yace, "toilet din zan shiga dake?" ganin yanda yayi maganar fuskarsa a hade senayi ƙasa da kaina na fara hawaye. siririn tsaki yaja sannan ya shige toilet din. yayi danasanin sakawa Maryam lizard dinnan, gashinan yanzu bayajin daɗin jikinsa kokaɗan. ya dade yana a toilet din kafin ya fito, niko na makure a karshen gado cikin blanket, duk da da haske a dakin amma a matukar tsorace nake. kuka na fara ganin yaƙi fitowa da wuri. ɗaure da towel iya kugunsa ya fito, da wani ƙarami kuma yana goge sumar kansa. Tunda yafito yajita sarai tana shashsheka amma yaki kallon inda takema. karasawa gaban mudubi yayi ya farawa shafe_shafe. Ina ganin ya fito na sauke ajiyar zuciya amma bandena kukanba, ganinshi a haka yasa na runtse idona da sauri kirjina na dukan uku_uku, bantaba ganin namiji babba haka ba rigaba. juya masa baya nayi na kwanta badon babu kaya ajikinaba tashi zanyi infice inbar masa dakin. Duk abunda takeyi yana kallonta ta cikin madubi, tabe bakinsa yayi yacigaba da shirinshi. har ya gama shiryawa cikin wata jallabiya milk colour me kyau, maryam batayi shiru da kukan tabarar datakeba. dafe kansa yayi dayake matukar sara masa, yarasa dame zeji da kukannata dayake taɓa masa zuciya kokuma da abunda ke damunsa. ganin bata da niyyar yin shiru cikin tsawa yace mata. "Ki rufemun baki ko kuma na zaneki yanzunnan" hadiye kukan nawa nayi da sauri cikin tsoronsa. Ajiyar zuciya yasauke jin tayi shiru, ya lura shagwaba ce kawai ke damunta, seya mata da zafi_zafi sannan zasu shirya. zama yayi a bakin gadon, kallonta yayi yace, "tashi ki barmun ɗaki" a hankali nace "ni tsoro nakeji" "to tashi muje na cire miki lizard din" "um'um, nidai kakaini gurin ammi" na faɗi haka kamar zan fashe da kuka. shiru ya mata be ƙara ce mata komaiba. ƙasa ya sauka ya zauna kawai ya lumshe idonsa. har kusan ƙarfe ɗaya be ƙara koda kallon inda takeba yananan a zaune cikin yanayin damuwa. Maryam kuwa tuni bacci ya ƙara daukarta bayan tagama cin kukanta. har lokacin bayajin daɗin jikinshi, a hankali ya mike ya fice dankar ta farka. dakinta ya shiga ya dauke lizard din robar daya ajiye, har ya juya ze fita sekuma ya dawo ya buɗe wardrobe dinta, dogowar riga kawai ya ɗaukar mata da hijabi saboda sallah, kashe light din dakin yayi sannan ya fice. seda ya kashe na faloma sannan ya koma dakinsa. tananan yanda yabarta, kayan ya ajiye mata a gefen gadon, ya boye lizard din sannan ya shiga toilet ya dauro alwala, cikin dauriya yakeyin komai. be kashe mata light din dakinba, dan yanda take zabuwannan idan tatashi taga duhu seta cika gidan da ihu. fita yayi zuwa Masallaci. Ƙarfe biyu da 'yan mintuna, na dare Maryam ta farka. A hankali ta buɗe idonta tana miƙa da salati dauke abakinta. yunkurawa tayi ta tashi zaune, domin tayi sallah kamar kullum tunda goman ƙarshe ta shiga. mararta taji ta daure tamau. yatsina fuska tayi ta janye blanket din data lullube jikinta. sakkowa tayi daga kan gadon tana daura towel ɗin jikinta. ware ido ta hauyi kozata ganshi a dakin ganin bayanan ta sauke ajiyar zuciya me ƙarfi, tama manta ba dakintabane seyanzu data mike ta ƙara wartsakewa. abunda ya faru kafin baccinta ne ya dawo mata kwanyarta. dakin na fara bi da kallo, domin yau shine shigowata ta farko tun tarewarmu. komai tsaf a kintse fes_fes, mayen kamshinsane kawai yake tashi a dakin. A fili nace "ashe ya iya gyaran dakin, amma da a gida ake masa." kayana na gani akan gadon, cike da mamaki na karasa ina dubawa. daukar rigar nayi nazira na daura towel a samanta, tunda babu komai a jikina kuma rigar shara_shara ce. toilet na shiga nayo alwala, masallaci har sun kusa idarwa, ƙarfe uku suke tashi dama. tunda zanyi fitsari nasan da matsala, dan inayin fitsarin marata na ƙara daurewa. ina tada sallah naji tsaiwar ta gagareni saboda juyamun da cikina ya farayi daurewa nayi, nayi raka'a biyu. ina sallamewa na durkushe a gurin hannuna dafe da cikina ina taune lips ɗina. "Ya Allah" na furta saboda wani murdawa da cikin yamun. kwanciya nayi akan dardumar ina juyi na rasa inda zan tsoma kaina, ciwon karuwa yake. ina nan kwance ina kuka da murkususu ya shigo dakin. ganinta a haka yasan ba kalauba. karasawa yayi kusa da ita ya tsugunna batare daya taɓataba yace, "menene?" jin muryarsa yasa natashi zaune da sauri, cikin azabar ciwo nace masa. "Ci..cik...cikina" muryarta na rawa saboda kukan danakeyi. wata murdawa da cikin yamun bansan sanda na faɗa jikinshi ba, hakan yayi dai_dai da fara zubowar jini daga ƙasana..........✍️ *BY* *Zeey kumurya* *ABINDA KASHUKA....* _*BY*_ _*ZEEY KUMURYA*_ *5️⃣9️⃣* *Bismillahirrahmanirrahim* ..........Inajin dumin jinin nabin jikina amma nakasa motsawa balle nayi yunkurin tashi domin na tsafta kaina dan gudun kar jinin ya ɓata ni. Taune lips ɗina kawai nayi saboda azabar murdawar cikin, hawaye na zuba daga idona. sannu kawai Mustapha yakewa Maryam amma bata masan yanayiba. Dagata yayi da niyyar ya dakko wayarsa ya kira likitan ammi ganin ciwon bana ƙarau bane, da sauri ya saketa ta koma kijinnasa yana yamutsa fuska ganin jini ajikin rigarta kasancewar rigar tana da haske kuma babu komai acikinta. maida kaina nayi na kwantar a kan kirjinsa ina sauke ajiyar zuciya, idona na lumshe saboda fara sararamun da cikin da yayi, runtse idonsa yayi zuciyarsa babu daɗi, hakan yasashi kasa aiwatar da komai. A hankali na buɗe idona tare da yunkurawa na sauka daga jikinsa cikin tsananin jin kunya da takaici. cize lips ɗina nayi na daure na mike na fara jan kafata cikin dauriya na fice daga dakin zuciyata cike da tsananin kunyarsa, banajin ko ido zan iya ƙara haɗawa dashi a yau, gaskiya abunnan bemun adalci ba, yarasa a inda zezomun se'agabansa. ina shiga daki na cire hijabin jikina na wuce toilet. wanka nayi da ruwa me dumi na tsaftace jikina. Bayan na fito na dauko magani nasha sannan na kwanta, nama manta da wani batun lizard din jiya, ta kaina kawai nakeyi..... Cike da kyankyami ya buɗe idonsa jin tafice daga ɗakin, waro idonsa yayi waje yana bata fuska saboda ganin jinin har jikin jallabiyarsa ya ɓata. tsaki yaja ya mike da sauri ya shige toilet ya cire jallabiyar zuciyarsa harta fara tashi. dana sani kawai yakeyi akan sakawa Maryam lizard din da yayi a daki, da duk haka bata faruba, yana zaman_zamansa yajawa kansa ganin kazanta. yana jan tsaki ya wanke jallabiyar. cike da kyankyami ya goge dakinsa duk da jinin be diga a ƙasaba, tare da saka Room freshener. koda lokacin sahur yayi beci komaiba, ko ruwan tea beshaba, saboda tashin zuciyar dake damunsa, ze iya yin aman abu idan yaci shiyasa yakicin komai. Bayan ya dawo daga masallaci ya nufi dakinta domin yaga jikinnata. A Hankali ya tura kofar dakin ya shiga, tana kwance can ƙarshen gado ta takure jikinta kamar me jin bacci. karasawa kan gadon yayi yana kallonta, bacci take hannunta dafe da mararta. "Sleeping sickness" ya furta hakan a fili. juyawa yayi ya fita bayan ya duba maganin datasha ta ajiye sauran akan madubi. Bantashiba se wajen ƙarfe 11:00 am, Alhamdulillah cikin yasararamun sedan abunda baza'arasaba. Ayyukana nayi kamar kullum dana saba. Tea kawai nasha na nufi part din ammi...... Azumi uku kawai nasha nadora aka cigaba dani. cikin kwanakin da suke shude gaba-daya wasan buya nake dashi saboda kunyarsa danake ji. bana fitowa falo sena tabbatar ya fita, kafin ya dawo kuma zan gama komai na gudu part din ammi, idan yazo kiranane kawai muke haɗuwa. yau idan munkai azumi 29 ana saka ran gobe sallah, tun safe masu kitso da jan kunshi suka zo har gida suka mana. Kananun kitso nace amun, aiko nasha zama dan munfi awa biyu a zaune. gashi andauramun lalle a ƙafata. Umaimah se hararar Maryam take cikin hassada da kyashin ganin yawan gashin maryam ɗin, ita tana fama da kanta kamar me, dan bata da gashi kokaɗan, kitsonma dana na ƙari tace ayi mata ammi ta hana. har bayan azhar ina zaune, seda aka cire lallen na samu sa'ida. Zanen lallen yayi kyau sosai a farar ƙafata, gashi lallen ya kama sosai. Bayan ansha ruwa ina kwance a falonmu a ƙasa kan carpet, jikina duk a gajiye saboda aikin da mukasha yau, sanin danayi baya dawowa se bayan sallar isha'i shiyasama nazo falon na kwanta. labarai nake kallo, saboda inji koza'ace anga wata. banji buɗewar kofarsaba, balle shigowarsa se kamshin turarensa kawai naji. kallo bakin ƙofar nayi, da sauri na tashi zaune ganinshi ina amsa sallamar yayi gabana na faɗuwa, binsa nayi da kallo ta ƙasan ido, maimakon naga ya nufi dakinshi senaga ya karaso cikin falon ya nemi guri ya zauna akan 2 seater batare daya kalli inda nakeba. "Sannu da zuwa" na furta haka cikin sanyin murya kaina na ƙasa. kamar bejiba ko motsawa beyiba da sunan amsamun sema cigaba da danna wayarsa dayayi. kusan 3 minutes sannan naji yace, "yawwa" a can ƙasan makoshi kamar wanda akawa dole, batare daya dagoba. kamar na shareshi nima amma dai na daure na ƙara ce masa, "ga abincinka can akan dinning" girgiza kai yayi srioustly yace, "banacin abincin kazamai" waro idona nayi duka waje ina kallonsa, araina nace. "Kazama kuma? nice kazamar kenan yake nufi, to menayi na kazantar?" bakina na turo gaba tare bata fuskata kamar zanyi kuka nace. " Aini ba kazamabace?" banza yamun kamar bejiba. idona nane ya duri ruwa, naji babu daɗi sosai dayacemun kazama, gashi ina masa magana yana shareni. bansan sanda hawaye ya zubomun ba, duk da kokarin da nayi dan kar hakan ya faru. A hankali ya dago kansa ya kalleta. mamakine ya cika masa zuciya ganin tana hawaye. "To me aka mata?" Ya tambayi kansa. kallonta kawai ya tsaya yanayi yanda hawaye yaketa zuba daga idonta, kamar wadda aka daka. lumshe idonsa yayi yana fesar da numfashi. A hankali ya mike ya sauka ƙasan kujera, daf da ita ya zauna yana jifanta da wani kallo dashi kansha besan yanayiba. tafin hannunta yakama a hankali, wanda hakan yasasu jin sauyi gaba-daya ajikinsu. lallen da aka mata yakurawa ldo, kunshin ya burgeshi sosai. zamansa akusa dani yasa bugun zuciyata sauyawa, wani yarrrr naji a jikina lokacin daya kama hannuna. daurewa kawai nayi na lumshe ido. a hankali ya kai hannunsa ya fara share mata hawayen fuskarta dan yanzu yagane meyasa ta kukan. bakinsa yakai saitin kunnena cikin wani irin amon murya me narkar da zuciya yace, "what are you crying?" Batare dana buɗe idonaba na nuna shi da hannuna tsigar jikina na tashi. murmushi yayi ya kwantar da kanta akan kafadarshi. ajiyar zuciya na sauke me ƙarfi, ina ƙara lafewa ajikinsa. sosai nake tsintar kaina a wani irin yanayi a duk lokacin dana jini ajikinsa, yanayine me wuyar fassaruwa amma yanamun daɗi sosai, ina jin tamkar na dawwama ajikinnasa. kitson da aka mata ya shafa yace, "shine baki nunamun kitson sallar da lallenba ko?" cikin shagwaba nace, "bakaine kacemun kazama ba" bakinta data turo gaba ya shafa da finger dinsa yace, "bakazamar bace" kamar zan fashe da kuka nace, "Allah Ni ba kazama bace" wannan karon murde bakin yayi ganin ta ƙara turoshi gaba yace, "wacce kikamun ajikinafa" shiru nayi ina ƙara runtse idona cikin jin kunya. se yanzu nagane meyasa yacemun kazama. hannunsa yakai ya fara shafa cikina slowly, yace. "Ya jikinnaki" "na warke" na faɗa a wani irin baƙon yanayi saboda shafa cikina dayake. lips dinsa ya lasa tare da sauke numfashi ya cire hannunsa daga jikinta. raba kanta yayi da kafadarsa yana faɗin, "dagani Ni karkimun bacci a jiki" badan nasoba na bar jikinnasa. wayarsa dake gefensa ya dakko ya fara latsawa, mikomun yayi yana faɗin. "Take it" karbar nayi cikin rashin fahimta. Ganin bata ganeba yace, "Antinki keson magana dake" fadada fara'a ta nayi akan fuskata cikin jin daɗi na ƙara wayar a kunnena ina faɗin "Salamu alaikum" jin antin ta ɗaga. "Wa'alaikumussalam, Maryam ya gida." nace "lafiya kalau, Aunty nah, ya kowa da kowa" "lafiya kalau suke, ya ibadah" "Alhamdulillah Aunty, yaushe zakizo nayi missing dinki sosai" "munanan tafe tafe cikin sallah insha Allah" murmushi nayi nace, "Allah ya kaimu lafiya, ina aliya" Aliya dake gefen Aunty tana jiran ta bata wayar tace, "ganinan matar yaya, tun dazu nake mata alama ta bani wayar taƙi bani" dungura mata wayar Aunty tayi. Dariya nayi nace, "Aliya kina jin azuminnan kuwa, naji muryarki radau da karadinta" aliya tace, "hmmm idan ana sallah ba'a magana mairo, wlh azuminnan ya garani, Allah ya karba kawai. "Ameen ya Allah, ya skull?" "Skul Alhamdulillah munma yi hutu" hira muka shigayi da Aliya, aiko Aliya ta dage tanata zuba. Mustapha daya kurawa Maryam ido yana kallonta yanda take motsa ɗan karamin lips dinta bakaramin daukar hankalinsa yayiba. kawai jinayi ya kwace wayar. kallonsa nayi cikin mamaki, a hankali nace. "Meyasa ka kwace? bamu gama hirarmubafa" yana danna wayarsa yace, "kunsamu kati ne?" girgiza kai nayi alamar A'a. ina dubansa kamar zanyi kuka. dagowa yayi yamun kallon cikin ido, da sauri na lumshe idona dan bazan juri kallon kwayar idonshiba. numfashi ya sauke a hankali ya mike tsaye. bude idona nayi na sauke akansa a hankali ganin ya nufi kofa nace. "Fita zakayi?" juyowa yayi ya kalleni ya gyadamun kai. "Zan bika" na faɗa cikin sanyin murya, batare danasan sanda maganar ta fitoba. "Masallaci zani" ya fadi haka yana ficewa daga falon. murmushi nayi bayan ya fita, zuciyata cike da tsananin farinciki ganin ya fara sakemun yanzu, ba kamar farkon aurenmu ba. Mikewa nayi nima na shiga daki jin anfara kiran sallah, zuciyata cike da nishadi. ina idar da Sallah na yafa mayafin abayar dake jikina nanufi part din ammi. Suna zaune Dukansu matan gidan kowacce tana duba ɗinkin da tela yakawo ɗazu. da sallama nashiga. suka amsamun dukansu cikin fara'a, amma banda umaimah data haɗe rai tacigaba da duba kayanta. guri na samu na zauna ina gaishesu. Ammi ta dubeni tace, "Maryam kayanki suna dakina ki shiga dauko" cikin girmamawa nace "toh ammi, idan zan wuce zan dauka. Angode Allah yasaka da Alkhairi, yajikan mahaifa. murmusawa Ammi tayi cikin jin daɗin addu'ar Maryam tace, "Ameen ɗiyata, ina NOOR ne tun safe ban ƙara ganinshiba" ina ɗaukar Abul dake kwance a ƙasa ganin ya fara kuka nace, "dazu kuma ya fita Masallaci" tabe baki umaimah tayi cikin jin haushin Maryam, kayanta ta kwasa bayan taja tsaki ƙasa_kasa tayi dakinta. Mama da mama A'isha ma, nasu suka dauka suka fita. Aunty zuhura ta karbi Abul ta bashi nono. Bayan yagama sha na ƙara karbarsa ina masa wasa yanata bingiramun dariya. yaya sadam da mustapha ne suka shigo falon. Umaimah da fitowarta kenan daga ɗaki tace, "yaya NOOR sannu da zuwa" tana karashe maganar tana wani fari da ido. beko kalletaba ya zauna a gefen Maryam bayan sun gaisa dasu ammi, kamarma bejitaba. kallonsa nayi ya harareni ɗauke kaina nayi daga kansa nacigaba dayiwa Abul daketa bingiramun dariya wasa. kaina babu ɗankwali bansan jelar kitsona tafito ta gefen wuyanaba seda naji Abul ya riƙe mun. A Hankali nake ƙoƙarin kwacewa daga hannunsa dan kar yayi kuka, shikuma ya rikte gam yaƙi saki. Mustapha dake kallon Maryam ta gefen ido yana ganin abunda ke faruwa, murmushi yayi ganin Maryam se yatsina fuska takeyi. hannunsa ya zira ta bayanta ya zagayo dashi ya cire gashin maryam daga hannun Abul cikin dabara. Ɗaukar Abul ɗin yayi yana faɗin. "Seka cire mana gashin saboda mamanka umaimah bata dashi ko?"...✍️ _*BY*_ _*ZEEY KUMURYA*_ *ABINDA KASHUKA...* _*BY*_ _*ZEEY KUMURYA*_ *6️⃣0️⃣* *Bismillahirrahmanirrahim* ..........Ya ƙarashe zancen da lakucewa Abul kumatu, shiko se bingira masa dariya yake abunsa. murmushi Aunty zuhura da YaSaddam sukayi me sauti. Umaimah kuwa sakin baki da hanci tayi tana kallonsa cikin tsananin baƙin ciki da takaicin yanda ya dizgata a gaban matarsa. ita mamakima take ko a ina yasan gashinnata oho?. kallonsa nake nima cikin mamakinsa, kamar bashi yayi maganar ba ya wani waske yanawa Abul wasa. A hankali ya juyo ya kalleni ya kannemun ido ɗaya tare da dagemun gira, lumshe idona nayi a hankali saboda salonnasa ya tafi dani. Mayafin Maryam daya ɗan zame yasaka hannunsa ya janyo tare da maida mata gashin daya fito ciki. numfashi na sauke a hankali still idona na lumshe saboda tattausan hannunsa daya taɓa gefen fuskata. umaimah ta hadiye wani yawu me daci da kyar, duk abunda mustapha yayiwa maryam akan idonta. mikewa tayi fuu cikin bacin rai ta shige dakinta. Dan idan tacigaba da zama a falonnan se zuciyarta ta buga. suna haɗa ido da ammi ta hararareshi tace, "ka kyauta ka batamun ran autah" murmushi ya mata kawai bece komaiba. numfashi na jawo na fesar da kyar na buɗe idona. batare dana kalli kowaba ba mike na shiga dakin Ammi na dakko kayana. Kafin na fito har yabawa yaya sadam Abul ya fice, sallama na musu nima nabi bayansa. yana zaune a falo idanunsa a lumshe na shigo falon bakina dauke da sallama ƙasa_ƙasa. A zuciyarsa ya amsa mata. Bedroom ɗina na wuce ganin be kulaniba, da niyyata inje innuna masa kayan sallar da ammi tamun. Bayan fitar su Maryam Ammi ta shiga bedroom din Umaimah ta rarrasheta, umaimah harda kuka dan bakin ciki. misalin ƙarfe 11 na dare ina kwance akan gadon idona a lumshe amma ba bacci nakeba, tunanin *heartbeat* kawai nakeyi, tunda nashigo dakin na kwanta amma nakasa bacci se juyi nake, har light din dakin na kashe. a hankali naji turowar kofar dakin gami da shaƙar kamshinsa. buɗe idona nayi amma ban motsaba zuciyata na ɗan bugawa. Kunna touchlight ɗin wayarsa yayi ya haska kan gadon, yasan dama zuwa yanzu tayi bacci. Ledar daya shigo da ita ya ajiye a gaban madubi. Seda ya ɗanyi jimmm, kamar me nazarin wani abu sannan ya fice. Ajiyar zuciya nasauke, na ƙara maida idona na rufe. Inajin kamar na tashi na bishi mu kwana tare amma bazan iyaba, duk yanda nakeson hakan dole na jure na hakura..... Washegari ranar idin sallah ƙarama, ranar da kowanne musulmi yake farinciki da fatan zuwanta, hakance ta kasance nima a gurina. Tunda asuba na tashi nayi ayyukana saboda nasamu damar zuwa sallar idi. kafin karfe bakwai nagama shirina cikin wata dakakkiyar shadda milk colour, tasha ɗinki me matuƙar kyau. feshe jikina nayi da turaruka masu sanyin kamshi. ledar dana gani tunda na tashi najanyo na shiga dubawa. Takalmane masu kyau kala biyu da jaka, da mayafai da sarka da ɗan kunne harda agogo duk a cikin ledar. murmushi nayi cikin jin daɗi. ƙarfe bakwai da rabi nanufi part din ammi cikin shirina tsaf na zuwa Masallaci. Acan na tarar da yaya sadam da Aunty zuhura suma cikin shirinsu. Gaisawa mukayi cikin fara'a. Ammi bata falon hakan yasa na wuce dakinta. bansan yana cikiba seda nashiga na ganshi zaune gefen gadon ammi da waya kare a kunnensa alamun waya yake. zama nayi akan carpet din dake gaban gado bayan mungaisa da Ammi, ina satar kallonsa ta gefen ido. yayimun kyau sosai fiye tunanin me karatu, shadda ce fara ƙal ajikinsa, kansa dauke da hula wadda ta masa kyau bakadanba. ƙasa dauke idona nayi daga kansa. Maganar ammi naji tana cewa, "NOOR kabata wayar su gaisa da UNCLE dinnaka, kullum yana tambayata ita amma basu taba gaisawaba. gyada mata kai mustapha yayi sannan ya mikawa Maryam wayar. tashi nayi a hankali naje na karbi wayar ina kallonsa shima kallonnawa yakeyi se idanunmu suka sarke cikin na juna. Runtse nawa idon nayi da sauri saboda yanda naji bugun zuciyata ya sauya. kara wayar nayi a kunnena tare da faɗin "Assalamu alaikum" cikin murya me cike da nutsuwa naji ance, "wa'alaikimussalam" "ina kwana" na furta hakan bugun zuciyata na karuwa. "Lafiya kalau, *Maryama*" yanda na faɗi sunannawa senaji wani iri a zuciyata dana kasa tantance menene, numfashi na jawo na fesar da kyar nace. "Dafatan anyi sallah lafiya".... Mungaisa dashi sosai, yamun addu'oi dafatan nasara arayuwata. godiya na masa na mikawa yaya wayar. Bayan sun gama wayar mustapha ya dubi ammi yace, "yace zezo cikin watannan insha Allah" da'alamun mamaki akan fuskar ammi tace, "dakuma yacemun baze samu zuwaba, saboda ayyuka sunsha masa kai sedai wani watan." "Hakadai yacemun yanzu" mustapha ya fadi haka yana mikewa da niyyar fita. "To Allah yakaimu lafiya." Gaba dayanmu gidan muka dunguma zuwa masallaci. Nida ammi da umaimah muka hau motar yaya. Aunty zuhura, da mama da mama A'isha da mijinta suka hau motar yaya sadam. Anyi sallar idi lafiya antashi lafiya sedai fatan Allah ya maimaita mana. bayan antashi Aunty zuhura tayiyyi mana pictures a wayarta sannan muka dawo gida, aka cigaba da hidimar Sallah...... *KADUNA* Aunty ce tafito cikin shirinta na zuwa Masallaci dakin da suhailat da aliya suke ta nufa domin takirasu ganin sunki fitowa. da sallama ta shiga amma saboda cacar bakin dasukeyi basujiba. tsayawa kawai Aunty tayi tana kallon aliya dake magana cikin tsiwa. "Wlh nidai nagaji da kazantarnan taki gaskiya, amma kome zaki faɗa sedai ki faɗa Ni... Tsawa Aunty ta daka mata da faɗin. "Aliya mene haka? wanne shashancine wannan?" Cikin bacin rai aliya tace, "Aunty kullum fa bata ɗauke ko tsinke a dakinnanan amma bana magana haka zangyara, amma baya jimawa ta ƙara batawa, yauma ina tashi na gyara shi amma daga fitowarta daga wanka harta fara batawa, danna mata magana ta fara zagina wai zan mata rashin kunya, ko dan naga gidanmu tazo." Rai a haɗe Aunty tace mata. "Shine dan baki da kunya zaki faɗa mata haka, sa'arkice. Kuma dan bata gyara dakiba seya zama abun magana bakya ganin bata da lafiyane." Aliya zatayi magana Aunty ta katseta da sauri. "Banason na ƙara jin bakinki anan, zoki fice kikirawomun abbanku mu wuce, karmu makara." Aliya kamar zatayi kuka dan takaici ta fice ɗaga ɗakin. Fuska babu walwala Aunty ta dubi suhailat dake cika tana batsewa ganin bata da alamun shiryawa tace, "ke bazaki masallacin bane?" Suhailat na yamutsa fuska tace. "Banajin daɗin jikina bazan iya zuwaba." wani kallo Aunty ta mata me kama dana tuhuma harseda suhailat ɗin ta tsargu sannan ta fita batare datace mata komaiba. Suna tafiya a mota ammi ta dubi aliya cikin ƙasa_ƙasa da murya dan kar abbanta dake gaba yaji tace mata. "Kidena kula suhailat kuna hayaniya, yar uwarkicefa Aliya, kuma gaba take dake." aliya kamar zatayi kuka tace, "Aunty itacefa..." Cikin lallami Aunty ta katseta da faɗin, "kiyi hakuri da duk abunda zata miki, kidena kulata kinji 'yar albarkata" gyada kai aliya tayi tana turo baki gaba. Bayan sun dawo daga masallacin sunci abinci ammi ta nufi ɗakin da suhailat take. suhailat tana kwance tana aikin kallon hoton mustapha daya zame mata jiki Aunty ta shigo dakin. zama Aunty tayi akan gado tana duban suhailat dabatasanma ta shigoba tanacan tana tunanin Mustapha tace. "Suhailat!" Firgigit suhailat ta dago ta kalli Aunty, amma tagaza cewa komai. Aunty bata damu da yanayin datake cikiba tace, "meyake damunkine wai naga bakida walwala.?" Idantane ya kawo ruwa cikin raunin murya tace. "Inason ganin yaya, nayi kewarsa" Aunty na tsareta da ido tace. "Bayan wannan fa?" tana kauda kai daga kallon Aunty tace. "Nothing" fuska babu walwala aunty tace. "Suhailat kina boyemun kina da ciki ko?" Rassss gaban suhailat ya yanke ya fadi duk tsagerancinta seda ta girgiza dajin Aunty ta gane tana ciki. Tashi zaune tayi cikin rudu tace, "Aunty ciki kuma?" Harararta Aunty tayi tana ƙara haɗe rai tace. "Karki ƙara yunkurin boyemun, tun kafin kizo duniya nake ganin mata masu ciki, kuma nake ganesu. Tun kafin azumi nagane ciki gareki ta alamomi masu yawa da suka nuna musamman yanzu da cikinnaki ya fara fitowa." Aunty ta ƙarashe zancen tana kallon cikin suhailat daya fara dagowa dan wata huɗu da kwanaki. suhailat kasa magana tayi se kuka data fashe dashi. Tausayintane ya kama Aunty, duk da abu yana tadda hali amma suhailat mommy ce ta cuceta dabata tarbiyya tagariba. Lokacin da Aunty ta gane suhailat tanada ciki bakaramin dimuwa da damuwa tashigaba. ƴar ɗan'uwanta guda ɗaya jal daya mutu ya bari itace da wannan abun kunyar, tasan baƙaramin tashin hankali daddy ze shigaba idan yaji wannan zancen, shiyasa har yau ta kasa sanar masa......Muncigaba da shagulgulan sallah cikin kwanciyar hankali, munjejje unguwa da ammi munje gidan su Aunty zuhura har danginsu mama duk mun zazzaga. Yau Biyar ga sallah tun asubar fari mommy ta sauka a garin Kano. Tun kafin azumi suka baro garin NIGER, Binta ta dawo Nigeria yayin da mommy ta wuce ƙasar da suka zauna acan baya tayi azuminta acan, a cewarta bazata iya azumi a naija ba rana tayi yawa. se washegarin sallah ta dawo Nigeria ta sauka a garin Abuja gidan wata kawarta matar wani ɗan majalisa, seyau kuma tayi asubanci ta biyo jirgin ƙarfe 6 na safe zuwa Kano, batason asan da dawowarta harta se ta gama gudanar da kudirinta akan daddy da mustapha harma da maryam. shiyasa ta dako sammako dan karma wani daya santa ya ganta. Tana sauka a filin jirgi ta saki wani murmushin da ita kaɗai tasan ma'anarsa, zuciyarta fari ƙal tanajin kamar burinta ya gama cika. Driver'n ta data kira tun daren jiya ta sanar mata zuwannata yana gurin yana jiranta. Jan trolly dinta tayi ta nufi inda ta hango motarsa. dasauri ya fito daga mota shima ya karbi trolly'n hannunta yana jera mata sannu da zuwa cikin girmamawa. a ƙasaice ta amsa masa. Buɗe mata gidan baya yayi ta shiga, shima yazagaya ya shiga driver seat bayan yasaka trolly'n nata a But. gidanta dake lamido cresent tace yakaita. Cikin mintuna 20 suka karasa gidan kasancewar hanyar babu go slow tunda safiyace. Har cikin falo driver'n yakaimata kayanta. mommy dake tsaye tana karewa falon kallon cikin tsananin mamaki, ko sauraren sallamar dayake mata batayiba, ganin falon duk yayi kura. dakin da suhailat ta zauna ta nufa tana kwada mata kira, amma taji shiru. mamakine ya ƙara kamata ta shiga dube gidan tana kwala kiran sunan suhailat ɗin amma taji tsit. hankalintane ya fara tashi, cikin sauri ta fito ta nufi dakin megadi ta kwala masa kira. megadi dake ƙoƙarin komawa baccin da zuwan mommy ya katse masa ya fito da sauri daga dakinsa. A rude mommy tace, "inuwa ina yarinyar dana bari a gidannan?" Megadi na kallon mummy da mamaki yace, "wacce fa?" "Yarinyata dai dana bari budurwa, kafin na tafi nace maka karka barta ta fita ko da leke" megadi yace. "To to, nagane. Ai wata matace tazo suka tatafi da ita." Agigice mummy tace, "what? wacce matar?" Megadi daya fara ɗan firgita yace. "Bansantaba Hajiya" cikin tsawa mommy tace, "bakasantaba shine kabari tafitarmun da yarinya, saboda bakasan me kakeba, bakasan aikinkaba." Masifa mommy ta masa sosai kamar zata cinyeshi ɗanye. shikuma yanata aikin bata hakuri, bata saurareshiba ta wuce ciki fuuu, bayan ta tabbatar masa da duk abunda yasamu yarinyarta seta hukuntashi. tana shiga falon ta buɗe handbag dinta ta dakko wayarta jikinta na tsuma tayi dialing number suhailat. Suhailat na kwance tana baccinta wayarta ta fara vibrate, har Kiran ya katse bata dagaba. seda mommy ta mata 3 missed call sannan tatashi dakyar ta janyo wayar tana jan tsakin katse mata baccinta da akayi. batare data duba wake kirannataba ta ɗaga wayar tare da karawa a kunnenta. "Suhailat!" Mommy ta faɗa da ƙarfi. Zunbur suhailat ta tashi zaune tare da cire wayar daga kunnenta ta duba wanda yakirata. *Sweet mom* ta gani. "Suhailat bakya jinane" mommy ta ƙara faɗa. Cikin damuwa suhailat tace. "Mom, se yau kika tuna dani?" Cikin faɗa mommy tace, "niba wannanba suhailat, wacce matar ce tazo ta daukeki har gidana?" "Aunty ce" ta bata amsa. "What!? Aunty, wacce Aunty'n?" Mommy ta tambayeta cikin karaji. "Aunty'n Kaduna mana" "kina nufin saudart" "eh ita" mommy tana kankance ido cikin bala'i kamar suhailat na ganinta tace. "Waya faɗa mata inda kike?" Suhailat data fara gajiyawa da faɗan mommy tace. "Nina faɗa mata" mommy tace, "akan me to, banayi warning dinkiba kafin na tafi, kuma ina matar dana barku tare a gidan?" Suhailat tace, "kirana tayi a waya shine na faɗa mata, ita kuma matar aranar da muka taho ta sallameta tatafi." masifa mommy ta shiga yiwa suhailat kamar taɓabbiya akan bin Aunty datayi, a karshe tace mata kuma ta shirya kayanta zata turo a ɗauketa a yau dinnan, suhailat ta amsa mata sannan mommy ta kashe wayar. Babu ɓata lokaci suhailat tatashi ta hau haɗa kayanta, dama zaman gidan auntinnan duk a takure take jinta. Aliya bata dakin tana kitchen suna haɗa breakfast dan yau zasuje Jos sukaiwa su maryam ziyara. Aunty ce tashigo ɗakin ɗan ganin ko suhailat tatashi. ganin yanda suhailat ɗin take haɗa kayan se Aunty ta tsaya turus tana kallonta kawai. can ta nisa tace, "kayan me kike haɗawa haka suhailat, bafa dadewa zamuyi a Jos dinba, jibi insha Allahu zamu dawo" suhailat tana haɗa kayan yari dinta tace, "Aunty nifa Kano zankoma" aunty na mata wani kallo tace. "Akanme?" Shiru suhailat tayi dan batasan me zata cewa Aunty ba. Babu wasa a fuskar Aunty kokaɗan tace, "ki hada kayan da zaki bukata na 2 days kamar yadda nace miki jiya, ki kuma shirya, karki bata mana lokacin" tana gama fadar haka ta juya ta fice. suhailat tabi bayanta da kallo ranta babu daɗi. ta rasa wazatabi maganarsa mommy ko Aunty? zama tayi kawai a bakin gado ta rafka tagumi. Tasan halin Aunty sarai, tun tana yarinya. Aunty nada hakuri amma bata daukar raini ko wani mis_behav. Mommy kuma yanzu ta koyi yimata masifa amma duk da haka tafi tsoron Aunty akan mommy, kuma bazata bijirewa Auntyba dan tasan ita kaɗaice zata sa mustapha ya yayarda ya aureta, dan haka dole tadinga bin umarnin ta. badan tasoba ta tashi ta ƙara haɗa kaya kamar yadda Aunty tace mata. Ƙarfe tara suka fito cikin shirinsu tsaf suka yiwa masu aiki sallama da abbansu aliya driver'n Aunty ya daukesu zuwa Jos. Suna fara tafiya mommy ta Kira suhailat, seda ta saci kallin aunty sannan ta ɗaga, amma ta kasa magana. Mommy tace, "daughter ga shinan naturo za'azo a daukeki" kasa_kasa suhailat tace, "mommy bama kaduna fa" a harzuke mommy tace "kuma ina?" "Munje wani gida da su Aunty a Jos, amma yanzu muna hanyar dawowa, idan muka dawo sena kiraki" tsaki mommy taja tace, "to sekun dawo ɗin, karfa kifada mata na dawo garinnan, dan banaso kowa yasani." "Toh mommy bazan faɗaba" har mommy zata katse wayar tatuna tace, "dafatan dai baki faɗa mata maganar cikinnanba" satar kallon Aunty suhailat tayi tace. "Ehh" daga haka sukayi sallama. Yau ina cikin farinciki, wanda kallo ɗaya zakamun kagano hakan saboda zuwansu Aunty. Tun jiya muka fara haɗa musu delicious, yauma munayin sallar asuba muka fara. Se wajen 12 muka gama komai. Part dinmu na koma naɗan kwanta akan gado da nufin na ɗan huta bansan sanda bacci ya ɗaukeni. Su Aunty sun iso lafiya inda aka musu masauki a part din ammi. Su mama dasu ammi se maraba da zuwa suke musu. Aliya kam baza ido takeyi taga ta inda zataga Maryam ɗinta ta bullo. Suhailat kam kallon su kawai take da mamaki, tasandai wadannan ba yan'uwan daddy bane sedai ko yan'uwan babansu aliyane. Amma duk inda ammi tayi se binta take da ido. Bayan sungama gaisawa ankawo musu ruwa sunsha Aunty tace, "ina Maryam ne da Muhammad?" Ammi tace, "bari nakirasa naji" ta ƙarashe zancen tana latsa wayarta tayi dialing number mustapha. Mustapha yana kwance a dakinsa akan gado kiran ammi yashigo wayartasa, dauka yayi ya daga ammi ta sanar masa su Aunty sun iso suzo shida Maryam. Mikewa yayi da hanzari ya fito ya nufi dakin maryam. Fitowata daga wanka kenan ina shiryawa naji ana knocking, sauri nayi na karasa shirinnawa sannan na buɗe Kofar. kallo ɗaya yayi mata ya dauke kansa, kamar bayason yin magana yace. "Su Aunty sun karaso" bandamu da yanda yamun maganaba dan naga kwana biyu miskilancinnasa ya motsa. faɗaɗa fara'ata nayi cikin jin daɗi na dakko mayafina nabi bayansa. Sunata shan hirarsu yayi sallama ya shiga falon. da sauri suhailat ta mike tsaye jin muryarsa da kuma ganinsa da tayi un_expected da ƙarfi tace, "yaya!" cikin tsananin mamaki da farinciki tana waro idonta waje, domin bata taɓa tsammanin ganinsa a wannan lokacinba a kuma nan garinba. kallo ɗaya ya mata yaɗauke kansa batare dayace mata ƙala ba. suhailat babu jira ko tunanin komai ta taho da gudu ta faɗa jikinsa ta rungumeshi tana murmushi cikin tsananin murnar ganinsa. daidai lokacin Maryam ta ƙaraso falon. Tsayawa nayi cak cikin matsananciyar faduwar gaba, Muryar Aunty suhailat ce ta tabbatarmun da itace inda take cewa. "Yaya i missed you so much" kallonsa kawai nakeyi naga yanayin re_action ɗin dazeyi ina ƙoƙarin fizgo numfashina ganin yana ƙoƙarin daukemun. Wani irin kishi naji acikin raina ganin wata mace kwance a kirjin mijina, bansan ya a kayiba kawai gani nayi najuya na fice daga falon ina haɗe hanya. Cire suhailat yayi daga jikinsa batare yace mata komaiba yana yamutsa fuskarsa kamar yaga kashi shima ya juya yabi bayan Maryam. suhailat dabatama lura da zuwan Maryam ba, balle tasan ita tabi ta taho itama zata bishi. Tsawar da Aunty ta matace yasa ta tsayawa zatayi magana ammi ta ɗaga mata hannu, fuskarta a haɗe tace. "dawo ki zauna" suhailat kamar zatayi kuka ta dawo ta zauna tana leken kofa. Umaimah kallon suhailat take cikin kishi, yanda tayi ya tabbatar mata da itama son mustapha'n take. Part dinmu na nufa na faɗa kan kujera ina sakin kuka, wani irin zafi da daci nakeji a cikin zuciyata, duk murna da farincikin zuwansu Aunty danake ya gushe. Banmasan haka nake da kishiba seyau, idona yarufe gani nake yayan shima ya rungume suhailat ɗin, kifa kaina nayi a hannun kujera ina sakin kuka mara sauti dana tuno yanda suhailat ta kwanta a kirjinsa. Yayi 3 minutes tsaye yana kallon Maryam da batasan yana tsayenba, a hankali ya tsugunna zuciyarsa babu daɗi ganin tana kuka ya dagota tare da janyota a hankali ta faɗa jikinsa. Rikesa nayi sosai ina ƙara volume din kukana, tare da sakin ajiyar zuciya. Lumshe idonsa yayi zuciyarsa na bugawa jinta ajikinsa. A hankali yasa tattausan hannunsa ya dago fuskarta. Narkarkkun idanunsa ya zuba acikinnata idon dake cike da hawaye. dif na hadiye kukannawa ina kallonsa nima, duk yanda naso nadauke idona daga cikinnasa amma nakasa. Kallon cikin ido mukewa juna, sosai bugun zuciyata yake ƙara ninkuwa, ganin bashi da niyyar dena kallona na runtse idona, wani abu naji yana yawo ajikina a sanadiyyar wannan kallonnasa dana kasa gane masa. Mustapha kallon Maryam yake with out control, batare daya saniba. Komai ya kwance masa daga kwanyarsa fuskarta ya matso daf da tasa har sunajin hucin numfashin juna, tare da bugun zuciyoyinsu. hawayene suka cigaba da shatata daga idona, ga tsoro da fargaba danaji sun lullubeni saboda betamun irin hakaba tunda muke, bamu taɓa kusanci me taɓa zuciya irin wannan ba, duk da idona a rufe yake amma nasan be dauke idonsa daga kainaba, saboda yanda nakejin wani abu kamar tsinkewar jini ajikina. Lumshe idonsa yayi tare da fesar da numfashi cikin wani irin yanayi mara misaltuwa. A hankali yake ƙara kusanto da fuskokinsu, bakinsa ya dora akan lips din Maryam batare daya shiryawa hakanba. zabura nayi cikin tsananin tsorata na fara kokawa da numfashina dake ƙoƙarin daukemun saboda dimuwa, kuka na saki ina ƙoƙarin raba jikina da nasa. Ajiyar zuciya ya sauke me ƙarfi yana ƙara manneta da jikinsa karon farko a rayuwarsa ya fara sucking lips ɗinta cikin tsananin zaƙuwa........✍️ *BARKANMU DA JUMA'ATU BABBAN RANA🕋* *By* *Zeey kumurya* *ABINDA KASHUKA....* _*BY*_ _*ZEEY KUMURYA*_ *6️⃣1️⃣* *Bismillahirrahmanirrahim* ...........Jikinane ya kama kyarma jin yanda yake tsotsar lips ɗina kamar ze ciremun. yanda jikin Maryam yake rawa haka shima Mustapha jikinsa yakeyi, se numfashi yake fitarwa da sauri da sauri yana ƙara manneta da jikinsa kamar ze maidata ciki. Yakai 7 minutes yana kissing ɗinta cikin nutsuwa da salo me wuyar mantawa da tsayawa arai. a hankali ya zare bakinsa daga nata yana maida numfashi badon ya gaji da kissing ɗinnataba sedan kawai ya barta ta sarara. lumshe idonsa yayi cikin mawuyacin hali na bukatuwa da ita. Ni kuwa boye kaina nayi a kirjinsa ina maida numfashi kamar wacce nayi tseren gudu, har yanzun hawaye be bar zuba daga idonaba. A hankali cikin dauriya ya dagota daga jikinsa domin zamanta ajikinsa yana ƙara masa feeling. fuskarta ya dago da tafin hannunsa a karo na biyu ya zuba mata tsumammun idanunsa da suka rine sukayi ja, wanda suke ƙara rikitata. Idanunsa cikinnata yasa tafin hannun damunsa a hankali ya fara share mata hawayen fuskarta. rufe idona nayi ina turo baki gaba nace, "kadena kallo na haka" murmushi ne ya subuce masa dabe shirya masaba. cikin wata irin murya kamar me rada yace, "why?" a shawabe nace, "ina jin wani iri a jikina" be ƙara cewa komaiba ya sakeni. A hankali na mike da kyar jikina kamar anmun duka saboda kasala, ban ƙara dubansaba na nufi ɗakina na nashige domin na wanke fuskata. Binta yayi da kallo har ta shige, ajiyar zuciya ya sauke yana maida numfashi, harna fito yana zaune a falon yanda na barsa, sena ganshi kamar mara lafiya kokuma wanda wani abu ke damunsa, senaji duk babu daɗi ganinsa a haka, kamar na tambayesa abunda ke damunsa,tunawa da nayi su Aunty sun jima da zuwa, sena ja ƙafata na fice daga falon cikin sanyin jiki. seda nazo zan shiga falon kuma naji wani iri na abunda danayi sanda naga suhailat a jikin yaya, wata kunyar su naji ta lullubeni, musammanma ammi. Daurewa nayi na shiga falon da sallama. suna falon gaba-ɗaya sunata shan hirarsu, su ammi sun cikawa su Aunty gabansu da kayan ciye_ciye da drinks. suka amsamun sallamata atare amma banda umaimah da suhailat data dago da sauri jin Muryar Maryam. Da gudu Aliya tataso ta rungume maryam cikin tsananin murna. Nima rungumeta nayi ajikina cikin farin ciki. Suhailat kallon Maryam kawai take da matuƙar mamaki. " _kamar maryam me aikin mommy ?_" suhailat ta furta hakan aranta cikin tantama, tana tunanin ba Maryam din bace, kamace kawai, dan wannan tafi Maryam ɗin data sani fari da kyau gami da wayewa. sakin juna mukayi da aliya cikin murmushi, ƙasa_ƙasa tayi da murya yanda ni kaɗai zanji tace, "matar yaya, mene sirrinne? Irin wannan kyau haka, ga abubuwa se juyawa suke duk kiwon yayannawane haka?" Harararta nayi nace, "daga zuwanki zaki fara, Ni matsamun inje gurin auntynah" dariya aliya tayi, Ni kuma na wuce gurin Aunty daketa sakin murmushi tun shigowar Maryam, daga yanda taga Maryam ɗin tasan tana cikin kwanciyar hankali. Suhailat Binta tayi da ido kamar wata doluwa. Rungume Aunty nayi ina faɗin "oyoyo Aunty nah, dafatan kunzo lafiya" aunty na ƙara faɗaɗa fara'arta tace. "Lafiya kalau Maryam dita, dafatan kina lafiya?" "Lafiya lau Aunty" na faɗi haka ina sakinta da murmushi dauke a fuskata. Suhailat ta haɗiye wani yawu tana duban Aunty tace. "Aunty wai wannan Maryam ɗin dana sanice house girl dinmu?" cikin rashin jin dadin house girl da suhailat ta kira Maryam Aunty tace, "ehh" maida kallonta tayi ga Maryam cikin tsananin mamakin yanda taga yarinyar ta sauya mata. Ba yabo ba fallasa nace, "ina wuni Aunty suhailat" tana ɗauke idonta daga kallon Maryam ɗin tace. "Fine" zuciyarta cike da mamakin wai gidan waye sukazo? da taga Maryam da yayanta. Tasan dai Aunty tace mata yaya yayi tafiya ne, to kenan nan garin shine inda yazo, to ita kuma Maryam ɗin metake a gidan? "May be nan ɗin ma aikatau tazoyi" suhailat tabawa kanta a cikin zuciyarta. (Ke kaɗai dai🤕) ƙara kallon kofar falon tayi a karo na ba adadi sannan ta juyo ta dubi Aunty tace, "wai ina yayanne Aunty, naga haryanzu be ƙara shigowa ba?" Harararta kawai Aunty tayi, bata bata amsaba cikin takaicin yanda take nuna rashin kunyarta a fili a gaban kowa, tun daya fita take ta maganarsa ita tayi missing ɗinsa kaza_kaza. Aliya ta dubi Maryam tace, kawata zo innuna miki wani abu" ta faɗi haka tana latsa wayarta. tashi nayi fuskata dauke da murmushi na koma kusa da aliya. tana cigaba da latsa wayartata tace, "Ina yayan wai?" "yana part dinmu" na bata amsa. wayartata ta mikomun tana faɗin "kalli hotunan kayan nan" karba nayi nafara kalla, waro idona nayi waje saboda ganin hotunan wasu ƴan'iskan kaya wanda idan mutum yasasu basu da maraba da tsirara. kallonta nayi so surprise nace, "wannan kayanfa ina kika samosu aliya?" wani murmushin tayi tace, "kike wani zaro mun ido dankinga wannan kayan, to sune tsarabar dana kawo miki" ƙara waro idona nayi waje nace, "inye me dasu Aliya?" Hararata tayi tace, "bangane kiyi me dasu ba, kiyiwa yayana kwalliya mana" nima harartata nayi nace, "kwalliyo mata, to ba daniba wannan tambaɗar, a inama kika samo kayanma tukunna?" "Bansabiba ke, tunda na miki gwanintama ban burgekiba kinsan wahalar danasha kafin nasamosu?" ganin yanda tayi da fuska senayi murmushi nace, "haba kawas, kema kinsan ba haka bane, kinsan babu ta yanda za'ayi in iyasa wadannan kayan ajikina" "to cewa nayi kisa kifita dasu, mijinki kawai zakisawa ya gani ai" kallon aliya nayi baki buɗe, araina ina faɗin. "Abunda baze taɓa yiyubama kenan" kafin wani acikinmu ya ƙara magana, Ammi ta katse mana muhawarar tamu da faɗin, "yata kizo kuci abinmana karyayi sanyi, tun dazu ankawo muku amma kunki ci kamar wasu baƙi" tana kallon Aliya tayi maganar. cikin girmamawa aliya amsa mata da "to" sannan tatashi ta nufi gun dinning, ta barni da wayarta a hannu. Suhailat ma seda ammi ta mata magana sannan ta mike itama. Umaimah ta rakata da harara, tunda suka zo ƙala bata haɗasu da suhailat ɗin ba, ta lura yarinyar nada jin kai da dagawa ga kuma fuskanta datayi itama tanason abunda takeso wato Mustapha.... Mustapha yayi fiye da 20 minutes a zaune a inda Maryam ta barshi, koda ƙwaƙwkwaran motsi beyiba, saboda yanda yakejin wani feeling na bijiro masa, se sassauke numfarfashi kawai yake a wahalarce. ganin zaman baze ƙaresaba ya mike da kyar, yana taune lips dinsa ya wuce bedroom ɗinsa. Rage kayan jikinsa yayi ya shige toilet yasakarwa kansa ruwa, kozeji sauƙin abunda yakeji ajikinsa. Suna cikin cin abincin suhailat ta dubi Aunty tace, "Aunty wai nan gidan wa mukazo" batare da Aunty ta kalletaba tace, "gidan freind ɗina ne" da mamaki suhailat tace, "Amma me ya kawo yaya gidan?" Kafin Aunty ta bata amsa mustapha yashigo falon da sallama. a tare suhailat, umaimah da Maryam suka kallesa zuciyar kowaccensu cike da kaunarsa. Maryam ce ta fara janye idonta daga kansa ta maida kan wayar dake hannunta tana amsa masa sallamar da yayi. mikewa suhailat tayi da sauri, cikin daka tsawa Aunty tace mata. "Dawo ki zauna ki ƙarasa cin abincin ki" cikin sangarta suhailat tace, "Aunty nina koshi da abincin kibarni naje naga yaya, nayi kewarsafa over wlh" tabe baki aliya tayi tacigaba da cin abinta. Aunty na ƙara haɗe rai tace, "nace ki dawo ki zauna ko?" Suhailat kamar zatayi kuka, ta koma ta zauna tana kunkuni aranta. becewa kowa ƙala ba, se Maryam dayabi da kallon ƙasan ido ya nufi gurinsu Aunty. Aunty na kallonsa da fara'a tace, "son manya, nayi zaton zakuzo mana yawan sallah ai" murmushi yayi ya kawar da zancen da faɗin. "Kun zo lafiya" "lafiya ƙalau son, ya al'amura dafatan anyi sallah lafiya?" Shafa kansa yayi yace, "lafiya" atakaice yana kallon suhailat data kura masa ido kamar zata cinyeshi ɗanye. Aliya cikin nutsuwa tace, "yaya ina wuni" batare daya kalletaba ya amsa mata, yana jan kujerar kusa da Aunty ya zauna. Mikewa suhailat tayi tsama ta nufo gurinsa da niyyar hugging ɗinsa, wani mugun kallo ya watsa mata saboda gane nufinta da yayi. sanin halinsa da tayi yasata tsaya kamar zatayi kuka tace, "yaya baka kulaniba" kallonta yayi yana ɗan sakin fuskarsa yace, "how are you" "fyn and you" ta bashi amsa da haka cikin farin cikin ganinsa, banza ya mata bebata amsaba. Komawa tayi ta zauna cikin karayar zuciya, fargaba da tsorone suka cika mata zuciya, dan batasan matsayin soyayyartaba yanzu a gurinshi, amma dayake tasan halinsa na miskilanci ko a da canma haka yake mata, seta dauka yanzumma hakane........ Bayan sungama cin abincin suka koma cikin falon, hira suka shigayi da Aunty, gabadaya akan kasuwan daddy ne da kuma ciwon Sadiq, har mustapha yacewa aunty yaso zuwa dubashi amma daddy ya hana, Aunty tace masa. "Ai jikin Sadiq ɗinma yayi sauƙi, a satinnan zasu dawo seyaje ya dubashi a gida." suna cikin hirarne aunty ta dubeshi tace, "karka nunawa suhailat Maryam matarkace a yanzu, kayi duk yanda zakayi karta gane, na gargadi Aliyama tun daga gida akan haka." da mamaki yake kallon Aunty amma bece komaiba. Aunty ta cigaba da magana da faɗin, "saboda banaso Aunty Atika ta sani yanzu, kuma idan suhailat ta sani kamar ta sanine, Allah shine abin tsoro, amma kaji tsoron sharrin mutum ma, kuma ko badan Aunty atikaba, suhailat ɗinma idan tasani hauka zata mana a gidan mutane kasan halinta dai sarai." gyadawa Aunty kai yayi amma yasan dole se suhailat ɗin ta sani ko a bakin su ammi ne. suka cigaba da hirarsu cikin kaunar juna. Niko part ɗina naja Aliya muketa hirarmu cikin nishadi, aliya dabata gajiya se zuzuta kyan dana ƙara takeyi. Suhailat kam tana dakin da suka sauka tana shan baccinta. Da daddare muna daki nida aliya a part din ammi, wani littafi nake karantawa me daɗi a wayarta, dazu take bani labarin book ɗin, shine nace tabani nakaranta. tanatamun hira Bama saurarta nakeba. Aunty ce tashigo ɗakin, bayan tayi sallama mun amsa mata tace. "Maryam ki tashi ki koma part dinku dare yayifa har goma saura." Batare da tunanin komaiba nace, "Aunty anan zan kwana yau" "nan ina?" Aunty ta tambayeta haka. "Aunty anan tare daku" wani kallo Aunty ta mata fuskarta babu wasa tace, "tashi ki wuce ni, banason shiririta" tashi nayi daga kwancen danake badon nasoba, sedan bazan iya musu da Aunty ba na dubi aliya nace, "taso muje mu kwana tare" kallon Aunty aliya tayi taga ta harareta. girgizamun kai aliya tayi alamun a'a. Nace "dan Allah kizo muje kinji kawata" "Aunty ce tace. "Akanme zata biki, kizo ki wuce ki tafi ke kaɗai" mikewa tsaye nayi da wayar aliya a hannuna. Aliya tace, "ke karki tafarmun da waya mana" ina cigaba da tafiyata nace, "ki bari da safe na baki, na matsu na ƙarasa labarinnan" mikewa tsaye Aliya tayi zatabi Maryam ta kwato wayarta. Dakatar da ita Aunty tayi da faɗin, "bar mata mana, idan dan wayane ga wayatanan kikira, keda baza ki iya hakuraba na dare ɗaya" komawa aliya tayi ta zauna tana faɗin, "to bani wayar taki" mika mata Aunty tayi. Maryam kuwa harta fice daga ɗakin. A falo na tarar da ammi na mata sallama na fice, suhailat ma tana falon tana bacci akan kujera. Tun dazu Aunty tace taje daki ta kwanta, taƙi ita setaga shigowar yayanta sannan zata koma daki, be shigoba kuma bacci ya ɗauketa. A falo natarar dashi a zaune akan kujera yana kallo kamar kullum, da sallama na shiga, banji ya amsamun ba amma dai na masa sannu da hutawa na shige ɗakina. ajiye wayar aliya nayi akan gado na rage kayan jikina na shige toilet..... Binta kawai Mustapha yayi da kallo harta shige dakin. Ajiyar zuciya ya sauke me ƙarfi, dama zaman jiran dawowarta yake. Hankalinsa gabadaya baya kan kallon dayakeyi, idan da za'a titsiyeshi bezece ga abunda ake acikin TV'n ba. zuciyarsa gaba-daya tana gurin Maryam yarasa meyasa tunaninta ya yawaita acikin zuciyarsa a kwanakinnan. wani numfashi me ƙarfi yaja ya fesar yana runtse idonsa, wani irin sanyi yakeji ajikinsa, dumin jikinta kawai yakesonji a halin yanzu yasan shikadaine ze masa maganin abunda yakeji, amma kuma idan matsalar take besan ta yaya hakan zata faruba, tun yayi sallar isha'i yadawo gidan tunanin ta yanda zasu kwana tare yau kawai yakeyi amma haryanzu ya kasa samun hanyar, miskilancinsa kuma baze barshi ya tunkareta da bukatarsaba. Ɗan ƙaramin tsaki yaja, ya buɗe idonsa dasuke wani lumshewa ya mike batare daya kashe kayan kallonba ya nufi bedroom ɗinsa, toilet ya shige domin yin wanka zuciyarsa babu daɗi......tunda na fito daga wanka ake kiran wayar Aliya banbi ta kantaba na ƙarasa gaban mudubi na fara shafe jikina da lotion, harna gama shafe_shafe na ba'adena kiran wayar aliya ba. Rigar bacci kawai na zira na ɗauki hijabina kato har ƙasa shima na zira. wayar na ɗauka har lokacin kira ake ba kakkautawa. Sweet dita danake sha kullum na ɗauko na jefa a bakina sannan na fita falo da wayar a hannuna, banganshi a falo. Hakan yasa nayi sauri nanufi kofa domin na kaiwa Aliya wayarta, dan bazan iya da wannan addabar kiranba. Mustapha yana hango Maryam ta cikin window'n dakinshi, tunda ya fito daga wanka ya kasa komai, zarya kawai yakeyi a dakinshi yana sake_sake. Ajiyar zuciya ya sauke bayan ta fice daga falon, yasan part din ammi zataje, kuma yasan kome zatayi Aunty bazata barta ta kwanaba seta korota. Jallabiya ya ɗauka ya zira ya fesa turare kaɗan, ya fito ya nufi kitchen domin ya haɗa coffee ya sha, dan jiyake kamar hancin cikinsa ze tsinke. Babu kowa a falon ammi se suhailat dake barci haryanzu, dakin dasu Aunty suke na shiga sallama. Fitowar Aunty kenan saga wanka taga Maryam kamar daga sama. Da mamaki tace, "Maryam yanaga kin dawo" ina mikawa Aliya dake kwance tana kallona da alamun mamaki nace, "wlh aunty tun ina wanka ake kiran wayar Aliya, harna gama shiryawa ba'adena kiranba shiyasa nace bari nakawo mata" numfashi Aunty ta sauke tace, "hmmmm" kawai. ƙara kiran wayar akayi, Aliya ta ɗaga da sauri ta tashi ta raba ta gefena ta fice tana satar kallon Aunty. tabe baki kawai Aunty tayi tacigaba da shirin kwanciyarta, seda safe nayiwa Aunty na fito. Aliya ganin Maryam ta fito ta katse wayar datake tana dubanta tace, "matar yaya, irin wannan zuba kamshi haka kamar anyi barin turare ajikinki ko duk na zuwa office din oga ne" murmushi nayi bance komaiba na fice, dan idan na tanka mata shakiyancinta zata cigaba damun. Bansan daliliba ina fitowa naji wata irin faduwar gaba ta riskeni, bugun zuciyata kuma ya sauya ta fara bugawa da sauri da sauri. dafe kirjina nayi ina kiran sunan Allah araina. jikina a sanyaye na koma part dinmu, still yanzuma banganshi a falon ba, ɗakina nayi ƙoƙarin wucewa, fitowarsa daga kitchen hannunsa ɗauke da cup yasani tsayawa. Kallonsa nake ina ƙoƙarin daidaita nutsuwata har ya zauna akan kujera yana kurbar Black tea din a hankali. damuwa na hango ƙarara akan fuskarsa kuma yanayinsa kamar bashida lafiya ma. A hankali na fara taku still idona na kansa, kusa dashi naje na zauna cikin tausayawa nace. "Yaya baka da lafiya ne?" Lumshe idonsa yayi yanajin kamar ya yanyota ya rungumeta ajikinsa, daga mata kai kawai yayi alamar eh. kamar zanyi kuka nace, "Ayya sannu meke damunka?" " _Kece!_ ya faɗa acikin zuciyarsa amma a zahiri seya nuna mata kansa kawai da hannu batare daya buɗe idonsaba. Sannu na masa tare da fatan samun sauƙi na wuce dakina ganin kamar bayason magana. buɗe gajiyayyun idanunsa yayi yana fesar da wani zazzzafan numfashi daga bakinsa, kamar ya bita yace karta tafi amma baze iyaba yana kallo ta shige dakinta. Ajiye cup din hannunsa yayi ya mike yana taune lips ɗinsa, hannunsa dafe da mararsa ya shige bedroom ɗinsa. Kan gado yana faɗa cikin rashin kuzari zuciyarsa babu daɗi sosai mararsa ke murda masa kamar yayi hauka haka yakejin kansa, be taɓa jin kansa a irin wannan yanayinba se sau ɗaya a rayuwarsa, lokacin da accident ya haɗashi da wata yarinya yaje gidan su abokinsa. gumi ne yake tsatstsafo masa a jiki ta ko'ina.... Tunda na koma daki sena kasa sukuni, zuciyata ta kasa nutsuwa, yanayin dana ganshi nasan yana jin jiki bakadanba musamman yanda idanunshi sukayi ja, nasanma da kyar ma idan yasha magani. Tuna lokacin da nayi ciwon ciki nayi da azumi, haka ya dinga zarya a dakina yana duba jikina, nima Yakamata ace naje na bashi kulawa,dan yana buƙatar kulawar tawa a halin yanzu a matsayina na matarsa. Kamar antsikareni na mike, inda nake ajiye magungunana naje na buɗe na dakko Panadol na fice daga ɗakin, seda na ɗauki robar ruwa mara sanyi sannan na nufi dakinnashi zuciyata na ƙara tsananta bugu.....✍️ _*Thank you so much my FAN'S for your wishes and du'a. Allah yabar kauna da zumunci me ɗorewa.❤️🥰*_ *By* *Zeey kumurya* *ABINDA KASHUKA.....* _*BY*_ _*ZEEY KUMURYA*_ *6️⃣2️⃣* *Bismillahirrahmanirrahim* ........... Har na ƙaraso bakin kofar dakinnasa sena tuna ban dauko cup ba, juyawa nayi na koma kitchen na dakko na dawo. A hankali kamar mara gaskiya na murda handle din dakin tare da turawa. kwance na hangoshi yayi ruf da ciki idanunshi a lumshe, hannunsa ɗaya dafe da kansa. Tausayinsane ya ƙara lullubeni, a hankali nake takawa har na ƙarasa gaban gadon idanuna akansa. Tunda ta shigo dakin yaji alamun anshigo, amma ya kasa buɗe idonsa yaga ko waye, seda ta ƙaraso ya gane itace ta hanyar sassanyan kamshinta daya ziyarci hancinsa. Farin ciki mara misaltuwa ne ya lullube zuciyarsa gami da mamakin abunda yakawota dakinsa adaidai wannan lokacin, dan be taɓa zatoba, ko motsawa beyiba duk da yanda zuciyarsa take azalzalarsa akan ya buɗe ido koda kallontane yayi koyaji sauƙi aransa. Ajiyar zuciya na sauke ina tunanin ta ina zanfara, dan atunanina bacci yake. A jiye ruwan da cup din gami da maganin nayi akan bedside, a hankali na hau kan gado na zauna daf dashi zuciyata na ƙara tsananta bugu, tafin hannuna na dora akan forehead dinsa, bayan na zame hannunsa a hankali daga kannasa, zafi naji akannasa ga jijiyoyin kansa duk sun fito rada_rada se gumine dake ɗan tsatstsafowa kadan_kadan a goshinsa, daga gani kan bakaramin ciwo yake masaba. Ƙasan hijabina nasa na fara goge masa gumin. Ajiyar zuciya ya sauke sassanya yana ƙara lumshe ido lokacin dayaji tattausan tafin hannunta akan goshinsa. seda na goge masa gumin tass sannan a hankali na fara kiran sunansa domin na tasheshi na bashi maganin yasha, dan banga alamun yasha maganinba. "Yaya..yaya!" Buɗe idansa yayi a hankali ya saukesu akan kyakkyawar fuskarta. cikin tausayawa nace, "sannu ya jikinnaka?" Daga mata kai kawai yayi still idanunsa na kan fuskarta. "Allah ya ƙara sauƙi" na faɗa a hankali ina tashi na sauka daga kan gadon. Robar ruwan na ɗauka na tsiyaya a cup na ballo maganin guda biyu, kan gadon na dawo na taimaka masa ya tashi zaune, filo nasa masa ya jingina bayansa, sannan na dakko maganin na bashi, karba yayi ya sha ya kora da ruwan, sannan ya mikomun sauran maganin yana sauke ajiyar zuciya, Ni Ko se jera masa sannu nake cikin tausayawa. Zamewa yayi ya koma ya kwanta tare da lumshe idanunsa. kamar kar na tafi na barshi haka nakeji, zuciyata ta cika da tausayinsa yanda yake taune lips dinsa nasan ba ƙaramin jin jiki yakeba. jiki a sanyaye na tashi na fice bayan na kashe masa light din dakin, ina masa addu'ar samun sauƙi a cikin raina. Yana jinta harta fice amma yakasa tabuka komai, murnarsa duk ta koma ciki na zuwanta, ya rasa meyasa daya ganta yakasa aiwatar da komai akanta, duk da yanda yake cikin tsananin bukatarta a yanzu. hangota yakeyi a idanuwansa yanda takeyin komai cikin nutsuwa da sanyinta lokacin datake bashi magani, yaga tsananin tausayasinsa a cikin idanunta. ciza lips ɗinsa yayi cikin takaici. besamu bacci ya daukeshiba se can dare........ Washegari kamar kullum danayi sallar asuba ban koma bacciba, karatun Alkur'ani mai girma nayi, seda gari ya fara haske sannan na tashi na fara gyara gidan. Har yau bana girki a part ɗina, sedai mu haɗu muyi a part ɗin ammi, na safe Kuma kafinma nagama aikina ammi ta aiko ankawo mana..... suhailat tunda Aunty ta tasheta tayi sallah da ƙyar take ta tambayar "ina yaya, ko ba'agidan yake kwana bane.?" Aunty da aliya banza suka mata suka cigaba da sabgarsu ko tanka mata basuyiba. Kafin su fito, ammi ta shigo dakin da kanta sun gaisa, bayan sungama gaisawa ta dubi suhailat dake ta kallonta tace. "Wannan ƴar gidan Alhaji mainasara ce?" Aunty tace, "A'a mahaifinta kanine a gurinsa Ni kuma yayanane, amma Allah ya masa rasuwa tun tana yarinya shida mahaifiyarta, se rukunta ya koma hannunsa." cikin tausayawa ammi tace, "Allah sarki, Allah yajikansu ya gafarta musu" suka amsa baki ɗaya da "Ammeen" ammi ta ƙara cewa, "yaranshi nawa ne? har yau be kawo mana suba" murmushi Aunty tayi tace, "su huɗu ne, kuma duk mazane. Abunda yasa basu zoba saboda harkar kasuwancinsa duk sune akai, babban kuma kinsan suna saudiyya mabiyanshi kuma tare suke jinyarsa da yayah, suma su haidar ɗin kullum mukayi waya zancensu yaushe yayansu ze dawo Kano sunyi missing ɗinsa." Ammi na murmushi itama tace, "su a tsammaninsu Muhammad ze koma Kano da zamane?" Aunty tace, "ehhh mana ko kinfiso ya zauna anan?" Ammi tace, "ehhh gaskiya inda so samune nafiso ya zauna anan, amma shima naga yafison ya koma Kanon" Aunty tace, "to ai kinga can ya taso, a can komai nasa yake, kuma harkar kasuwancinsama duk yana can, zeyi wuya mutum yayi rayuwar Kano yazonan yaji daɗin rayuwa, kinsan nan da can da banbanci." Ammi tace "hakane kam to idan Allah yakaimu bayan babbar Sallah sesu koma Kanon da gabaɗaya" suhailat dake sauraren hirar tasu ta dubi Aunty tayi farat tace, "Aunty nima Dan Allah kibarni anan, idan yayan ze koma semu koma tare" wani kallo Aunty ta wurga mata sannan tace, "A'a, gobe zamu tafi tare" suhailat ta marairaice tace, "Please Aunty I want....." Aunty ta katseta cikin faɗa, "nace fa bazaki zaunaba gobe zamu tafi" ammi ta tari Aunty da faɗin, "haba Hajiya sauda kibarta mana ta ɗan kwana 2 tunda tanaso" Aunty tace, "Tana zuwa makaranta shiyasa" ammi na duban suhailat tace, "To kinji ɗiyata ashe da makarantarki, kiyi hakuri ki bitan ku tafi, idan kukayi hutu sekizo mana" suhailat batace komaiba, amma bataso hakaba, taso Aunty ta barta ta zauna anan ɗin kusa da yayanta, duk da batasan alaƙarsu da mutanen gidanba, amma ita wannan ba damuwarta bace, Ita dai tunda zata dinga ganin yayanta kullum zata zauna. Tun jiya da yamma ta kashe wayarta saboda kar mommy ta addabeta da kira, dan tunda taga Mustapha a gidannan tasa aranta ta samu gidan zama. (Suhailat badai hankaliba 🤣) hirar duniya ammi da Aunty suka shigayi. Aliya kuwa dama tana kitchen aunty ta turata suna aiki ita da umaimah da Aunty zuhura.... Se kusan ƙarfe goma nagama aikina, duk da ba wani aiki bane a gidan amma kullum haka nake, sena wanke komai nayi goge_goge, har kayan dana cire duk se na wankesu shiyasa bana kammala aikina da wuri. ina toilet ina wanka Aliya ta shigo part ɗin, fitowa kawai nayi daga wanka naganta zaune a bakin gado tana danna waya. Da mamaki nace mata, "ke yaushe kika shigo ko motsinki Banji ba" Aliya ta ajiye wayar hannunta tace, "yanzu na shigo na kawo muku kayan break, se yanzuma kika tashi kenan?" Ina karasawa gaban mudubi nace, "sekace wata ke, zanta bacci har safiya haka" cike da shaƙiyanci Aliya tace "nasani ko yanzu kin koya, tunda yanzu kina lole mana jikin yaya" ban kulataba nacigaba da shafa maina. Bayan mun shirya muka fito falo na haɗa tea nasha da soyayyiyar wainar kwai da dankali, ina ci ina yamutsa fuska ina babu daɗi tunda aliya tacemun ita tayi. Itama da bakinta baya shiru ba kyaleni tayiba, mayarmun take. Cin abincin nake amma hankalina yana kan kofar dakin yaya, so nake na ƙarasa cin abincin naje na dubo jikinnasa. ina gama karyawa na nufi dakinnashi, Aliya kuma na kitchen tana wanke kwanukan danayi amfani dasu. Amma abun mamaki Koda na buɗe Kofar dakinnasa senaga wayam bayananan, amma dakinnasa fess dashi se tashin kamshinsa yake dana room freshener. A part din ammi na tarar dashi suna hira da Aunty, cikin shirinsa da alamama fita zeyi. Naji daɗin yanda nagansa da alamun yaji sauƙi kenan. ban wani jima da zuwaba ya fita. Suhailat yauma taso ta shishshige masa amma be bata fuskar hakanba, daga gaisuwarta daya amsa be ƙara kallon koda inda takeba. Ita batason bayason ganintaba, saboda indai ya kalleta seya tuno da mommy, shikuma bayason ya dinga tuna mommy so yake yayi deleting ɗinta gabadaya daga cikin rayuwarsa ko tunata bayason ya dingayi. Yauma haka na wuni a part din ammi, munashan hira cikin nishadi, sosai zuwansu Aunty yaymun dadi. Aunty ta kirani daki ta tambayeni, ko akwai wata matsala a zamanmu da yaya, nace mata babu matsalar komai. nasiha ta ƙaramun akan zamantakewar aure, ta kuma bani wasu turaruka masu kamshi tace kullum kafin na kwanta na dinga tsugunno dashi, wani kuma na turara jikine dana shafawa harda na turare kaya duk ta bani. Cike da kunya na karba na mata Godiya. Yauma se dare na koma part dinmu, tun safe dana ganshi a part din ammi ban ƙara sakashi a idonaba dana dawo kuma banganshi a falo ba kamar yadda na zataba, haka na wuce ɗakina zuciyata babu daɗi, kewarsa duk ta cika mun zuciya kamar naje naganshi haka nakeji, amma bazan iyaba, tunda innaje bansan mezan ce masa yakawoniba.... Abangaren mustapha ma, zuciyarsa cike ta wuni da tunanin maryam har mamakin kansa yake akan yanda tunaninta ya yawaita acikin zuciyarsa. duk abunda zeyi tunaninta na makale a cikin zuciyarsa. yau kam yaji sauƙin jikinsa sosai, dan tunda ya tashi ciwon kan da ciwon marar yasarara masa, yayi zaton yauma zatazo ta ƙara dubasa amma yaji tsit, ya gama budget dinshi akanta yau idan tazo, amma ta bata masa shiri. zuciyarsa babu daɗi shima ya kwanta cike da takaici. (🙄 kai kaje mana, wannan miskilancin naka ya ishemu fa🤕🥺)..... Washegari su Aunty suka tafi tun safe, kamar na bisu haka naji. su ammi ma sunso su Aunty su ƙara kwanaki amma Aunty tace tafiya zasuyi saboda makarantar Aliya, wani satin zasu koma kuma zataje dangin babanta kafin su koma. Suhailat ma kamar tayi kuka, se botsare_botsare take tana bata rai, Aunty dai ko kulata batayiba tafiyace dai dole seta yita. Direban ammi ne ze kaisu gida, dan direban su Aunty tun a ranar daya kawosu ya juya ya koma. Wunin yau gabaɗaya cikin rashin walwala nayishi saboda tafiyar su Aunty. Danma munyi waya dasu saleemat ne da gwaggo, shiya ragemun kewar su antin..... Har bayan sallar magriba ina part din ammi, bayan na idar da Sallah naji babu abunda nakeson ci se wainar fulawa. kitchen din ammi na shiga na hado kayan hadi na fara kwabawa, Aunty zuhura tazo diban abinci ta tarar ina kwabawa, tsokanata ta shigayi wai yau kuma babynnasu waina zeci, dariya nayi kawai bance mata komaiba. Na fara soyawa ammi ta shigo kitchen din tana faɗin, "Maryam dakanki kikeyi, kinsan ita waina idan mutum ne ya soya da kansa baya iyaci, dakin fadamun dana soya Miki da kaina ai, kokuma nasa umaimah ta soya Miki" cikin ladabi nace mata, "Ammi ai zan iyaci, agidama idan inaso ni nake soyawa da kaina" murmushi ammi tayi tace, "To ai yanzu da da ba ɗaya bane Maryam, sekiga yanzu kin soya kuma kinkasa ci." nace, "ammi fa zan iya da gaske" ammi tace, "toh shikenan ɗiyata sekin gama." Se bayan isha'i nagama soya wainar. Yawuna har tsinkewa yake tun kafin nagama, dibar tawa nayi acikin flaks sauran kuma na barwa su ammi. Part dinmu na wuce, akan dinning na aje flaks din sannan na nufi ɗakina, toilet na faɗa cikin sauri nayi wanka tare da dauro alwala. Shap_shap na shirya cikin wata doguwar rigar mara nauyi Black colour, wadda na turarata da turaren da Aunty ta bani, tun bayan sallar azhar nayi kabbasunta amma haryanzu kamshin yananan ajikin rigar. wanda ta bani na shafawa a jiki na shafe jikina dashi lungo da sako, turaren yanada daɗin kamshi sosai shiyasa naita mulkashi ajikina. Hijabi na zira na tada sallah, bayan na idar na fito falo batare dana cire hijabin jikinaba, flate na dakko a kitchen da robar yaji na dawo kan dinning na zuba wainata na faraci, ina tunanin har yanzu yaya bedawo ba... Tare suka shigo gidan shida yaya Saddam, bayan sunyi sallah ne suka tsaya tattaunawa akan kasuwancinsu. sallama sukayi kowa ya nufi part ɗinsa. Key din hannunsa yayi amfani dashi ya buɗe Kofar palon domin beyi zaton ta dawo daga part ɗin ammi ba. A hankali ya tura Kofar ya shiga bakinsa dauke da sallama. na gutsuro wainata zankai baki na ganshi kamar daga sama ya shigo, kasa kai wainar nayi cikin bakina na maidata cikin plate, na tsaya ina kallonsa, bugun zuciyata na sauyawa. shima tsayawa yayi yana kallonta, kurawa juna ido sukayi daga ɗan nesa batare da sun shirya hakanba, kowa zuciyarsa cike da kewar ɗan'uwansa. Tun safe a gurin rakiyar su Aunty basu ƙara haɗuwa ba se yanzu. Nina fara janye ido daga kansa ina sauke ajiyar zuciya. A hankali na amsa masa sallamar da yayi. a hankali yafara takowa har gurin dinning din, kujerar dake fuskantar tawa yaja ya zauna. kaina na ƙasa nace, "sannu da zuwa" gyada mata kai yayi idanunsa na kan guntuwar wainar dake cikin plate din. kasa cigaba da cin wainar nayi se jujjuya hannuna kawai nake a ciki saboda zamansa a gurin, ga idanunsa danakeji suna yawo a jikina. Wani tunani ne yazomun cikin zuciyata, mikewa nayi na nufi kitchen, binta yayi da kallo harta shige, Ajiyar zuciya ya sauke ya maida kallonsa kan wayarsa dake hannunsa. plate na dakko na dawo, ragowar wainar dake cikin flaks na zuba na tura masa gabansa. kallon wainar yayi ya kalleta da alamun tambaya akan fuskarsa. yaji na miko masa nace, "yaya ga waina" kallonta yayi da murmushi dauke akan fuskarsa yace, "ai wannan abincin matane bana maza ba" ina zama a kujerar dana tashi nace, "maza ma sunaci sosaima" yana kallonta yace, "to nidai bazan ciba, Nagode" shiru nayi ban ƙara cewa komaiba. Ganin yanda fuskarta tayi kamar bataji daɗi ba dan yace baze ciba seya mike yana faɗin, "ki kawo mun coffe ɗakina" amsa masa nayi da "toh" dakinsa ya nufa zuciyarsa na basa kwarin gwiwa akan kudirinsa akan Maryam, domin yagaji da yanda yake abzatuwa akan abunda yake halalinsane, yau kam ya shirya tsaf domin angoncewa. (🤔musty an ajiye miskilancin kenan, to mairon mudai yarinyace.🥺)......✍️ *By* *zeey kumurya* *ABINDA KASHUKA....!* _*BY*_ _*ZEEY KUMURYA*_ *6️⃣3️⃣* *Bismillahirrahmanirrahim* .........Binsa nayi da kallo harya shige dakinsa, ajiyar zuciya na sauke me ƙarfi ina lumshe idona, sonsa da shaukinsa na ƙara yawaita a cikin zuciyata. Yaya Sadiq ne ya fadomun arai, gabana ne ya yanke ya faɗi, da sauri na buɗe idona na kalli yatsun hannuna, azurfar da ya bani har yanzu tana hannuna. A fili na furta "ko wanne hali yake ciki yanzu? ko yaji sauƙi daga cutar dayake? Ko yaya yaji da yaji labarin na auri ɗan'uwansa? Se Allah." mikewa nayi jikina a sanyaye na shige dakina, toilet na shiga nayi brush saboda manjan danaci a waina dayake mun makaki a makogoro, duk da nayi brush ɗinma amma banji daidaiba, alawar danake sha kullum na dakko na saka abakina sannan na fito daga ɗakin na nufi kitchen din. Jikina a sanyaye na haɗa masa coffee din, sosai nakejin ba daɗi ajikina saboda tuno yaya sadiq danayi, bawai dan soyayyar da muka yiba, se dan tsananin tausayinsa. juye masa coffe ɗin nayi a cikin tea flaks ƙarami na ɗauki cup na nufi dakinnashi bugun zuciyata na sauyawa. Knocking nayi a hankali, nayi 3 minutes a tsaye sannan yazo ya buɗe mun, a niyyata in mika masa kawai in juyo amma senaga ya juya ya koma ciki batare daya karbaba, binsa nayi badan nasoba na ajiye masa akan bedside locker, rigar wanka ce ajikinsa ga kuma jikinnasa da ruwa alamun daga wanka ya fito. bance masa komaiba ina ajiyewa na juyo na nufi kofa da niyyar fita se naji yace, "ki dafomun indomie guda ɗaya" juyowa nayi na kallesa yana tsaye a gaban madubi yana shafa mai, kamar zanyi kuka na amsa masa sannan na fita. wani munafukin Murmushi mustapha yayi yacigaba da shafe_shafensa. Cikin mintuna ƙalilan na dafa masa indomie'n guda biyu dan a ganina ɗaya bazata ishesaba. Juye masa nayi a cikin plate na ɗauki fork guda ɗaya na nufi dakinnashi. Harya gama shiryawa,yana zaune akan carpet a kasa yana operating system, a hankali lokaci zuwa lokaci yana kurbar coffee din dana kawo masa. Da sallama na shiga ɗakin, batare daya dagoba ya amsamun, a gabansa na ajiye masa plate ɗin, na mike da niyyar fita. Alama yamun hannunsa alamun najirashi. Komawa nayi na zauna a ɗan nesa dashi akan carpet din, lumshe idona nayi ina shaƙar kamshinsa daya ƙara yawaita a ɗakin fiye da dazu dana shigo. wani iri nakejin jikina kamar wata mara lafiya. Ko minti biyar banyi da zamaba naji yana faɗin, "wakika dafawa wannan indomie'n?" buɗe idona nayi da sauri na sauke su akan fuskarsa, haɗa ido mukayi na ɗauke idona da sauri nace masa. "Kai mana" still idanunsa na kanta yace, "da yawa haka nace miki?" Yamutsa fuska nayi kaɗan nace, "wannan ɗin ce me yawa, guda biyu cefa kawai" "amma ai ɗaya nace miki" ya faɗi haka cikin wata irin murya kamar me rada. Ya tsareni da tsumammun idanunsa. "To ainaga ɗayar bazata ishekaba shiyasa" na faɗi haka cikin shagwaba. be ƙara cemun komaiba, ya sa cokali ya fara cin indomie'n sa hankali kwance cikin nutsuwa. kaɗan yaci ya tashi yana faɗin, "ki cinye kafin na fito" waro ido na nayi waje nace, "nifa na koshi cikina kamar ze fashe" becemun komai ba, se toilet daya shiga abunsa. Rufe flate ɗin indomie'n nayi na matsar gefe, ban kawo komaiba akan zaunar dani ɗin da yayiba, tunanina wani aikin ze sakani. jingina bayana nayi ajikin gado, sosai bugun zuciyata yake karuwa. Na rasa meyasa a ƴan kwanakinnan nakejin hakan a tattare dani. fitowa yayi daga toilet din yana faɗin, "kije kiyi alwala" "alwala kuma?" na tambayeshi da mamaki ɗauke akan fuskata" yana dakko dadduma yace mun, "ehhh karatu zamuyi." "Karatu kuma?" na maimaita a zuciyata, amma a zahiri mikewa nayi na nufi toilet din, sanin danayi baya son musu ko jayayya. Toilet din nashi, fess dashi babu ko digon ruwa a ƙasa, kamshi sabulu me daɗi ne yake tashi a toilet din. Sink na nufa nayi alwalar na fito. Yana zaune akan dadduma ya fuskanci alkibla, yana ganin na fito ya mike yana faɗin, "zo mu fara sallah tukunna" a hankali nace "nayi Sallah tafa" "eh nasani" ya faɗi haka yana bina da wani kallo. ban ƙara cewa komaiba, na ƙarasa na tsaya a bayansa. Tada sallar yayi nima nabi bayansa, raka'a biyu mukayi. Muka sallame, tambayoyin yafaramun akan addini, tsabar rashin wayona har yanzu na kasa harbo jirginsa, Ni harga Allah na ɗauka karatun zamuyi da gaske. duk da yadda yake tsareni da ido da kuma baccin da nakeji haka na daure nake bashi amsar duk abunda ya tambayeni daidai gwargwado, nayi mamakin iliminsa a kan fannin addinin musulunci, dan tambayoyinma se mutum nada ilimin ze iya yinsu. Tun ina bashi amsa har na dena se lum_lumshe idona nake bacci na cina, ganin tana gyangyadi seya janyota jikinsa a hankali, kwantar da kanta yayi akan kirjinsa a tare suka saki wasu boyayyun ajiyar zuciya, lumshe idonsa yayi saboda yanda sassanyan kamshin turaren datasa ya bugi hancinsa, tunda ta shigo dakinsa yake jin kamshi, amma yanzu da kusancinsu ya Karu se tasirin kamshi ya sauya a gareshi. A hankali batare daya buɗe idonsaba ya dafa kanta ya karanto addu'ar da Annabi (S.A.W) ya koyar game da sabbin ma'aurata a fili. zarcewa yayi da shafa gefen fuskarta bayan yagama karanto addu'ar. bacci me daɗi ne yayi awon gaba da Maryam, se ƙara manne masa take a jiki kamar mage. jin saukar numfashinta a hankali yasan baccin ya ɗauketa, ajiyar zuciya ya sauke tare da jan numfashi ya buɗe idonsa da suka fara canza kala, kurawa kyakkyawar fuskarta ido yayi yana kallonta, a duk lokacin da yayi mata kallo irin haka se yaji gabansa ya faɗi, hannunsa yasa a hankali yana zagaye kananun pink lips ɗinta data dan turo gaba, masu taushi. Yayi 10 minutes a haka yanata aikin kallonta da shafa fuskarta cikin tsananin shauki. Tallafota yayi gabadaya a jikinsa ya yunkura ya mike ya kwantar da ita akan gado. Lallabawa yayi ya rabata da jikinsa. Daddumar da sukayi sallah ya nade ya ninke ya ajiye, tea flaks da cup din dayasha coffee ya ɗauka ya fita dasu yakai kitchen ya dawo. Hangota yayi tanata mutsu_mutsu akan gadon, plate din indomie'n ya ɗauka, jinsa da nauyi yasashi buɗewa, mamakine ya kamasa ganin yanda yabar indomie'n haka take, "kenan bata ciba?" Ya tambayi kansa. Shi duk daukarsa taci. girgiza kai kawai yayi itama yakaita kitchen din. Kafin yadawo Maryam harta farka, amma bata buɗe idontaba, saboda baccin besaketaba kawai dai yadena mata daɗine. laptop din da yayi amfani da ita ya ɗauka ya kaita ma'ajiyarta. Sannan ya cire jallabiyar jikinsa ya ajiye, besan meyasaba yakejin wani iri a zuciyarsa akan abinda yake son aikatawaba, tun kafinma ya tunkari Maryam ɗin kasala ta fara lullubeshi. ƙwarara zuciyarsa yayi ya nufi kan gadon. (Bawai ragontakace take hana mustapha kusantar Maryam ba, idan baku mantaba a bayanan mommy na abubuwan data aikata harda asirin hana mustapha iya mu'amala ta sex da kowacce mace, sha'awarsama aka ɗauke masa gabaɗaya, shiyasa ko feeling be taɓa jiba a rayuwarsa se lokacin da suka fara haɗuwa da maryam kafin ta fara aiki agidansu. Amma boka yatabbatarwa da mommy cewa, mustapha ze iya yin sex da mace amma se wadda ta kasance jininsace. Ma'ana yar'uwarsa ta jini, kuma daga ranar da hakan ta faru asirin da'aka masa ze karye ya koma kamar kowanne lafiyayyen namiji kuma ze iya yin sex da kowacce mace koda ba jininsa bace. Mommy bata taɓa zaton mustapha ze haɗu da wani jininsaba a lokacin shiyasa ta amince da sharaɗin boka akayiwa mustapha asirin, shiyasa yake shiga wani yanayi a duk lokacin da yayi niyyar yin wani abu da Maryam. dafatan kun gane🤝.) seda ya kashe light din ɗakin sannan ya hau kan gadon ya kwanta a hankali cikin dauriya da abunda yakeji ajikinsa. Janyota yayi jikinsa yasa hannunsa ya zagaye bayanta. Ajiyar zuciya ta sauke tana ƙara gyara kwanciyarta a kirjinsa wani bacci me daɗi na fizgarta. A hankali yake ƙoƙarin cire mata hijabin jikinta, cikin muryarta me cike da bacci tace, "yayaaaaa..." taja sunannasa. "Uhm" ya amsa mata batare daya dena ƙoƙarin cire mata hijabinba, tsigar jikinsa na tashi yarrrrr. tana jinshi amma baccin dake cinta yasa batayi yunkurin hanashiba. A hankali yake shafa bayanta tare hura mata iskar bakinsa a fuskarta. Ƙara cusa kanta tayi cikin kirjinsa tana sauke ajiyar zuciya, kwantaccen gashin kanta baƙi sidik ya fara shafawa a hankali yana lumshe ido tare da fitar da numfashi zuciyarsa na bugawa da sauri_sauri. Yanayi biyune, ya riskesa a lokaci ɗaya. yanayin dayakeji a koyaushe idan yana tare da Maryam, da kuma wani irin feeling dayake bijiro masa, ga kamshin jikinta dayake ƙara masa tasiri gurin jin wani fitinannen feeling akanta. A hankali ya buɗe idonsa ya ɗan rabata da jikinsa, habarta ya dago ya dora bakinsa akan lips ɗinta ya fara bata wani hot kiss yana lum_lumshe ido. wata irin sarawa kansa yake masa kamar ze tsage amma duk da haka baze iya fasa aiwatar da kudirinsa ba yau kome zeji. tsotsar lips dinnata yake kamar ze cire mata yana ƙara manneta ajikinsa tare da shashshafa jikinta zuciyarsa na tsananta bugu. Maryam tun tanajin abun kamar a mafarki harta farka a tsorace ƙoƙarin kwace jikinta tayi saboda rashin sabo da abunda yake mata amma hakan ya gagara.....wasu sakonni masu wuyar faɗa Mustapha yake aikawa maryam cikin wani irin salo me tsayawa arai da wuyar mantawa. hawayene kawai yake shatata a idon Maryam wanda batasan dalilinsuba. Jikinsu gabaɗayansu kyarma yakeyi. zuciyar Maryam banda dokawa a miliyan ba abunda take saboda tsabar firgicin yanda mustapha yake yamutsa mata jiki a zafafe amma kuma yanayin komai cikin nutsuwa. mustapha baya hayyacinsa kwata_kwata sarrafa maryam kawai yakeyi a matuƙar buƙace, duk da yanda yakejin jikinsa tamkar ana yayyanka naman jikinsane saboda azaba, ga kuma wani bakon yanayi mara misaltuwa daya tsinci kansa a ciki. Maryam bata ƙara firgicewa seda taji yana karanto addu'ar saduwa iyali cikin wata iri murya dabata fita sosai.(Battery low....🤐)....... Adaidai wannan lokacin mommy dake zaune akan gadonta tanata trying number'n suhailat taƙi shiga Tun shekaran jiya, taji gabanta yayi wani irin yankewa ya faɗi, tamkar wadda akayiwa wani abun sega gumi yana tsatstsafowa daga jikinta kuma fanka da ac'n ɗakinta duka a kunne suke, ajiye wayarta tayi a gefe cikin wani irin tashin hankali datake cikinsa tun kwana 2 dasuka wuce, sakamakon jin labarin ciwon Sadiq datayi da kuma labarin cewa mustapha baya Kano shida maryam, tun jiya tasa a binciko mata inda Mustapha'n yake amma har yau shiru babu wani labarin samun inda yake. Maryam kuwa bata jin ta ita, domin duk a tunaninta tana gurin Aunty ne. sauka tayi daga kan gadon ta fara kaiwa da komowa tana zancen zuci. taso ta fara gudanar da aikinta akan su Mustapha tun jiya, amma se gashi sunzo sun ɓata mata shiri. wayarta dake kan gadoce ta fara ringing, da sauri ta nufi kan gadon domin ta dauka, dan ita yanzu cikin maraba da kowanne kira take. Haidar ne yake kiranta wanda taita kiransa tun yamma amma be ɗagaba. Da sauri ta ɗaga tare da kara wayar a kunnenta tace "se yanzu kaga damar kirana kenan?" Cikin kakkausar murya tayi maganar. Haidar dake kwance akan gadonsa idanunshi a lumshe, cikin murya me cike da gajiya yace, "ba haka bane mommy, wlh yanzu ko Lokacin kanmu bamu dashi saboda yawan sabgogi, mu biyunefa yanzu akan komai na daddy muyinan muyi can shiyasa." Tabe baki mommy tayi tace, "hmmm wai ace ina matsayin mahaifiyarku amma babu me nemana a cikinku tsawon kwanakin da muka ɗauka Bama tare, saboda angama hure muku kunne ko?" Haidar yace, "wlh mommy munnemeki amman bamu samekiba yaza'ayi ac....." Katseshi mommy tayi da faɗin "naji Ni duk ba wannanba, inashi mustapha'n yake?" Haidar yayi ɗan jimmm, sanin halin mahaifiyarsa yasan zata kuma iya yin wani mugun abun seya mata ƙarya yace, "yana London mommy" "London?" Mommy ta maimaita a matukar razane. "Ehh" haidar yabata amsa a takaice. wani gumi daya yanko mata a goshi ta goge da tafin hannunta sannan tace, "me ya jeyi a London ɗin?" Yace, "bansaniba mommy" "ƙarya kake haidar kasani" srioustly yace, "mom da gaske bansaniba dana sani mezesa bazan faɗa mikiba." shiru mommy tayi cikin rashin sanin abunyi. Jin shirun yasa haidar yace, "mommy yau nagaji dayawa ina bukatar hutawa yanzu da safe zankiraki" mommy saboda tsabar takaici kasa bashi amsa tayi. cillar da wayar kawai tayi akan gado ta rafka tagumi hannu biyu ta fara tunanin mafita, dan ita wlh kome ze faru bazata fasa aiwatar da kudirintaba, idan ba gani tayi mustapha da daddy sun bar duniyarnanba bazata taɓa samun nutsuwaba. dan haka dole tayi shirin zuwa London a satinnan domin binciko Mustapha a duk inda yake.......... Ƙarshe azaba da wahala Maryam yau tashata, tayi kuka iyakacin ƙarfinta harseda muryarta ta dashe, duk wanda ta sani kuwa yau seda takira sunansa da neman agaji da taimakonsa har inna dake ƙasa yau tasha kira gurin Maryam. Mustapha kam bemasan tanayiba, yau Maryam ta kaishi duniyar dabe taɓa tunanin zuwantaba ko a mafarki, ta kaishi duniyar dabesan yaze misalta daɗin taba da sanya nutsuwa a zuciya da gangar jiki ga duk wanda yajeta. Rungumeta yayi tsam a kirjinsa bayan komai ya lafa, yanajin wani farinciki, nishadi, annashuwa, daɗi, nutsuwa dabe taɓa jin irinsuba a rayuwarsa. sauke numfarfashi kawai yake tare da ajiyar zuciya yana shafa kan Maryam, wadda tuni baccin wahala ya kwasheta. Addu'a kam yau Maryam tashata a wajen mustapha kamar ba gobe, sunfi 30 minutes a haka sannan da kyar mustapha ya iya rabata da jikinsa. A hankali ya yunkura ya tashi zaune, ciwon kan da yanayin dayake ciki da kasala, gabaɗaya sun barshi. sauka yayi daga kan gadon yana jinsa tamkar bashiba tsabar shauki, murmushi ne kawai yake subce masa batare daya san yanayiba. wani wasai yaji kansa tamkar ansauke masa wani abu me nauyi daga kannasa, duk wani kunci da damuwa dayakeji acikin zuciyarsa a yau duk ya kau, tarin farin ciki ne kawai acikin zuciyartasa yau. Toilet ya shiga ya sakarwa kansa shower, seda ya tsarkake jikinsa sannan ya fito daga toilet din daure da towel a kirjinsa. Light din ɗakin ya kunna haske ya gauraye ɗakin agogon dake manne a bangon ɗakin ya kalla, yaga har uku na dare ta wuce. Aransa yace, "lallai ya dade yana abu ɗaya" wardrobe ɗinsa ya nufa ya dauko boxer da wata jallabiyar yasaka a jikinsa. Dadduma ya dauko ya shimfida ya fuskanci alkibla yatada sallah. Raka'a biyu yayi, amma ya dade yana addu'a a cikin sujjadarsa akan Allah yabasu zaman lafiya da zuri'a dayyiba, ya kawar musu da duk wata fitina a zaman auransu. Bayan ya sallame ya koma kan gadon, zama yayi ya tasa Maryam a gaba yana kallonta, yana jin wani baƙon abu yana ratsa zuciyarsa akan Maryam ɗin, a hankali yake shafa fuskarta datayi jage_jage da hawaye cikin tsananin tausayinta, yasan wahala iya wahala ya wahalar da ita. Mikewa yayi da sauri tunawa da yayi tana buƙatar taimako a halin yanzu, be kamata ya barta hakaba. Toilet ya shiga ya tara mata ruwan ɗumi acikin bahon wanka, komawa dakin yayi ya dakkota cancaskat yasata a cikin ruwan hakan yasata farkawa daga baccin datake ba shiri, zabura tayi jin wata irin azaba na ratsata tare da fashe da kuka. Kwantar da kanta yayi akan kirjinsa ganin tana ƙoƙarin tashi, a hankali yake shafa kanta cikin tausayawa. Kuka sosai Maryam takeyi saboda wata azaba dake ratsata ta ƙasan ta kamar an jajjaga mata attaruhu a gurin haka takeji. idanunta a rufe suke gam duk da tafarka daga baccin datake, wata irin matsananciyar kunyarsa takeji. Seda ruwan yayi sanyi sannan ya ɗauketa daga ciki, barin ruwan yayi ya tsiyaye sannan ya ƙara tara mata wani. Seda ya canza mata ruwan sau uku sannan ya barta a ciki yace idan yayi sanyi tayi wankan tsarki ta fito. Banza ta masa bata amsa masaba. Murmushi yayi kawai ya fice. Ajiyar zuciya nasauke me ƙarfi, zuwa yanzu Ni kaina daɗin ruwan nakeji. radadin danake ji ya fara sassauta mun, seda ruwan yayi sanyi kamar yadda yace, sannan na barshi ya tsiyaye, wankan tsarkin nayi na lallaba a hankali na fito daga bahon wankan, taku ɗaya nayi na kwalla ƙara na tsugunna a gurin ina sakin kuka. Mustapha dake saka rigar filon zanin gadon daya sake ya barshi ya nufi toilet din da sauri. Ƙarasawa inda take yayi ya rungumota ajikinsa a rude yace, "meyafaru?" cinyata na nuna masa da hannu ina dungulewa guri ɗaya saboda babu komai a jikina. "Sorry" ya faɗi haka yana bubbuga bayana alamar rarrashi. ƙoƙarin daukata yayi naƙi, ganin yanda take dunkule jikinta ya gane metake nufi, murmushi yayi kawai ya mike ya dakko towel ɗinsa babba ya kawo mata. karba nayi har yanzu na kasa buɗe idona cikin shagwaba nace, "ka dena kallona to" juya mata baya yayi yana murmushi yace "to nadena" buɗe idona nayi a hankali kamar me tsoron kar naga wani abu, ganin ya juyamun baya nayi sauri na daura towel ɗin. juyowa yayi da sauri na maida idona na rufe ina turo bakina gaba. ɗaukarta ya ƙarayi still fuskarsa ɗauke da murmushi. A kan gadon ya kwantar da ita, shima kwanciyar yayi ya rungumeta a jikinsa yana shafa bayanta a hankali, ba jimawa wani baccin ya ƙara ɗauke ta.......✍️ *By* *Zeey kumurya* *ABINDA KASHUKA....* _*BY*_ _*ZEEY KUMURYA*_ *6️⃣4️⃣* *Bismillahirrahmanirrahim* .........A hankali ya lallaɓa ya rabata da jikinsa ƙoƙarin tashi yayi Maryam ta ƙara matsowa jikinsa ta kankameshi tana ƙara turo bakinta gaba, cikin lallabawa da dabara ya ƙara zareta daga jikinsa, filo yasa ya maye mata gurbinshi da shi. Kissing goshinta yayi sannan ya sauka daga kan gadon. AC'n ɗakin ya kashe saboda sanyin asuba daya fara busowa. zanin gadon da ya cire ya ɗauka ya shiga toilet dashi ya wanke. Da ƙaramin towel dauke a hannunsa ya fito, gashin kanta data jika gurin wanka ya tsane mata, sannan yaje ɗakinta ya dakko mata wata doguwar riga me ɗan kauri ya saka mata, bacci takeyi amma daga gani kasan na wahala take, yanda take dunkule jikinta yasan sanyi takeji. Fankar dakin ya kashe gaba-ɗaya ya ƙara lullubeta da bargo. Daze tafi masallacin sallar asuba yaso ya tasheta tayi sallah, amma yasan yana tashinta rigima kawai zataita masa ta hanashi zuwa masallacin shi kansa shiyasa ya fasa tashinnata. light ɗin dakin ya rage mata sannan ya tafi zuwa masallaci. Har ya dawo tananan yanda ya barta a ƙudundune, lallaɓawa yayi ya tasheta domin tayi Sallah, da kyar ta iya tashi tana zuba masa taɓara, ɗaukar ta yayi ya kaita toilet din ya taimaka mata tayi alwala, wani tausayintane yake ƙara lullubeshi ga jikinta yayi zafi zau alamar da Zazzaɓi ajikinnata, a zaune tayi sallar danko tsaiwa bazata iya yiba. Bayan ta idar da sallar ya ƙara lallabata ta koma bacci. Ajiyar zuciya ya sauke bayan tayi baccin, tana kwance akan faffaɗan kirjinsa ta kankameshi gam kamar zata koma cikinsa, bayanta yake shafawa a hankali cikin tsananin shauki. Farincikin dayake ciki yau baze misaltuba, tabbas a yau ya ƙara tabbatar da aure ni'ima ne. A hankali ya zare Maryam daga jikinsa, tausayinta yakeji sosai har can ƙasan ransa, dare ɗaya amma fuskarta hartayi fayau ta faɗa. Sauka yayi daga kan gadon ya ɗauki wayarsa dake kan bedside, duba time yayi yaga 6:32 am. Contact ya shiga ya lalubo number'n famili doctor din su ammi da ammi ta taba tura masa saboda tsaro kokuma idan irin haka ta faru yayi dialing, kira ɗaya yayi sa'a kuwa ta shiga, amma harta katse ba'a ɗagaba, ajiye wayar yayi ransa babu daɗi, yana ganin idan har bakwai tayi doctor'n bata biyo bayan kiranba ɗaukar Maryam kawai zeyi ya kaita asibiti a dubata, dan yanda ta kasa tafiyarnan ba ƙaramin tayar masa da hankali yayiba, yana tsoron kar yaje koya jimata ciwo ne. yana ƙoƙarin tashi wayarsa ta fara yin vibrate, dauka yayi ya duba, DR.husna ya gani yana yawo akan screen ɗin, da sauri ya daga bakinsa ɗauke da sallama. Amsa masa sallamar tayi suka gaisa duk da bata ganeshiba, a takaice ya mata bayani daga gidan dayake kiranta yace mata yanada patient ne. Doctor tace, "ok gidan marigayi Alh Nasir kenan?" Yace "eh" tace "Ayya Allah ya ƙara afuwa, yanzu ina shiryawa ne zani asibiti amma kajirani nanda 40 minutes insha Allah zan biyo ta gidan kafin na wuce hospital" godiya mustapha ya mata sukayi sallama ya kashe wayar. kan gadon ya koma, hannunsa ya dora akan wuyanta yaji har yanzu jikinta da zafi, gyara mata kwanciya yayi, sannan yayi kissing pink lips ɗinta da suke matuƙar burgeshi. Falo ya fito ɗauke da Alkur'ani mai girma. Akan Centre carpet ya zauna ya buɗe Alkur'anin ya fara karantawa cikin kira'arsa me daɗin sauraro..... 7:28 kamar yadda Dr.Husnah tace ta ƙaraso gidan, wayar mustapha ta kira ta sanar masa zuwanta, fita mustapha yayi domin ya taho da ita. tunda ya taho Dr, take kallonsa da alamun mamaki domin batasanshi a gidanba, ita a zatonta duk Saddam ne ya kirata har ya ƙaraso bata ɗauke idonta daga kansaba. Sallama ya mata ta amsa ta ƙara da faɗin, "kaine wanda mukayi waya?" daga mata kai mustapha yayi alamun eh. Kallonsa ta kuma yi tace, "ok muje naga mara lafiyar" gaba yayi ta bishi a baya. A falo ta zauna shikuma ya shiga domin ya tada Maryam. yana shiga ɗakin ya ganta zaune akan gado harta tashi. karasawa yayi gareta da sauri, Maryam kuwa tana ganin ya shigo ta fara matso hawaye. Rungumota yayi ajikinsa yana faɗin, "am sorry, na barki ke kaɗai ga doctor nan tazo zata dubaki" gyada masa kai Maryam tayi cikin dauriya tana cize lips ɗinta, ta dan jima da tashi daga baccin amma ta kasa koda sakkowane daga kan gadon saboda yanda takejin kafarta tamkar ba'ajikintaba, ga ƙasanta dake mata radadi har yanzu. rabata yayi da jikinsa sannan ya fita suka shigo tare da doctor. Dr,husnah ta ƙarasa gaban gadon, duk da yanda Maryam takejin jikinta haka ta daure ta gaisheta. Amsa mata tayi ta tambayeta jiki kuma. dakai maryam ta amsa mata. Tambayar Maryam tayi meke damunta, shiru Maryam tayi ta kasa bata amsa se satar kallon Mustapha datayi. Murmushi doctor tayi ta kalli Mustapha tace ya ɗan basu guri, be musaba ya fita falo. ƙara kallon Maryam dr tayi ta tambayeta meke damunta, batare da maryam tayi maganaba ta nuna mata kanta da kafarta, cikin hikima doctor take tambayarta ina da inane yake mata ciwo ita kuma tana bata amsa, murmushi doctor tayi lokacin data gano bakin zaren. Duba Maryam tayi sosai duk da dakyar Maryam ɗin ta bari ta duba kasannata, mustapha beji mata rauniba kamar yadda doctor tayi zato ruwan zafi kawai jikin Maryam ɗin yake buƙata. kama Maryam tayi ta kaita toilet ta gasa mata jiki tayi sosai da ruwan zafi, musamman ƙasanta da cinyarta da taketa complain akan tana mata ciwo. Ai kuwa Maryam taji daɗin gashin jikin da Dr, ta mata duk tsamin da jikinta yake mata yanzu babu, zugin datake ji a ƙasantama ya ragu sedai kaɗan_kaɗan da kantama ta lallabo ta dawo daki daga toilet din, kan gadon ta ƙara hayewa ta kwanta tana sassauke ajiyar zuciya. dubanta doctor tayi tace, "yanzu ya kika jin jikinnaki?" cikin sanyin murya Maryam tace, "naji daɗin shi sosai, kainane kawai har yanzu yakemun ciwo" doctor tace, "shima ze dena insha Allah, nizan wuce Allah ƙara sauƙi" a hankali Maryam tace, "ameen nagode" sallama doctor ta mata ta fice. yana zaune akan kujera idanunsa a lumshe, jin fitowar Dr, yasashi buɗe idon a hankali. doctor na murmushi tace, "to ango nizan wuce, Allah ya ƙara sauƙi ya kawo mana twins nanda 9 months" murmushin gefen baki yayi yace, "Amin nagode sosai" "babu komai ai, na mata duk abunda ya kamata, yanzu a samu a bata ko da tea ne ta ɗan sha, da kuma maganin ciwon kai, dan tanata complain kannata na mata ciwo." Amsa mata mustapha yayi sukayi sallama tatafi, bayan yace tatura masa account number ɗinta. Doctor taso shiga su gaisa da ammi amma ganin har 8 ta wuce, kawai seta tafi, se yanzu data ƙara kallon Mustapha taga kamarsa da ammi, hakan yasa ta tabbatar ɗan tane. duk da bata da tabbas a hakan hakan, dan ta kwana biyu batazo gidanba, tun lokacin haihuwar Abul datazo Barka bata ƙara zuwaba sedai waya kawai sukeyi da mutanen gidan lokaci zuwa lokaci..... Kitchen ya shiga ya tafasa mata ruwan zafi da kansa, a kitchen din ya haɗa mata tea me kauri a cikin wani madaidaicin cup din roba me murfi. Da sallama ɗauke a bakinsa ya shiga ɗakin. ina jinshi amma ko matsawa banyiba sema ƙara rufe idona danayi gam gabana na faduwa. A jiye cup din yayi ya ƙarasa kan gadon, hannunsa yasa a wuyanta yaji zafin jikinnata ya ragu, ajiyar zuciya ya sauke Sannan ya fara ƙoƙarin dagota a hankali duk da yasan ba bacci takeba, yanda take ta kifkifta idantane yasa ya gane hakan. cire hannunshi nayi daga jikina hawaye ya fara zuba daga idona. Dafe kansa yayi a fili ya furta "ya Salam" ganin yanda take hawaye hannunsa yasa ya juyo da ita suka fuskanci juna, tattausan tafin hannunsa yasa ya fara share mata hawayen, kamar ƙara zugata yayi ta fashe da kuka, janyota yayi ya rungumeta tsam a jikinsa yana sauke numfashi, a hankali yasa hannunsa yana ɗan bubbuga bayanta amma bece mata komaiba, shi kanshi har kansa ya fara masa ciwo. daidai kunnenta yakai bakinsa murya ƙasa_ƙasa yace, "what happened? Ko jikinne? girgiza masa kai nayi alamun a'a ina ƙoƙarin sauka daga jikinsa. Riketa yayi gam da hannu ɗaya, ɗayan hannun kuma ya dago fuskarta a hankali ya matso tasa daf da ita, a hankali yasa harshensa ya lashe hawayen nata dasuke cigaba da zuba. dif na ɗauke kukan se jan numfashi kawai nake. seda ya shanye hawayennata tass sannan yayi kissing saman idonta duka biyun, wanda hakan yasa naji tsigar jikina na tashi yarrr.... finger ɗinsa yasa yana shafa cikakkiyar girarta da murmushi ɗauke a fuskarsa, yanda take ta kifkifta ido ne yake bashi dariya, tanaso ta buɗe idonta amma ta kasa. a hankali yace, "ki buɗe idonki karyaje ya manne yaƙi buduwa" make kafadata nayi na turo bakina gaba. yana dariya ƙasa_ƙasa yace, "shikenan tunda kinki buɗewa nidai babu ruwana idan idanki ya manne, bakisan mutum idan yayi kuka ya rufe idansaba kuma idan ya dade arufe mannewa yakeba." Kafinma ya ƙarasa na buɗe idannawa da sauri, murmushi yayi cikin jin daɗi dama soyake kawai ya kalli cikin idonnata. ƙoƙarin sauka nayi duk da yadda nakejin daɗin zama ajikinnasa amma zuciyata cike take da tsoronsa kar naje ya ƙara tumurmusheni, kin bata damar hakan yayi. Kyabe baki tayi kamar zatayi kuka Ɗan sassauta riƙon da yayi mata yayi yace, "sorry pls karkiyi kuka" cikin shagwaba nace, "to ba kai bane" waro fararan idanunsa yayi waje yace, "me nayi kuma?" bata bashi amsaba se ƙoƙarin saka masa kuka datayi. Kwantar da kanta yayi akan kirjinsa yana danne dariyar dake cinsa, dan yasan yanda take kan darunnannata idan yayi dariya kuka zata sa masa. Luf nayi a kirjinsa ina shaƙar daddaɗan kamshinsa. tunawa yayi da tea din daya shigo dashi, dagota yayi daga kirjinsa yana faɗin. "Muje kiyi brush kizo kisha tea" maida kaina nayi cikin kirjinsa nace, "um'um bazanshaba" "why?" Yatambaya yana ƙara dago dani. Cikin shagwaba nace, "Ni bazanshaba kawai, kamaidani gurin ammi kuma bazan ƙara kwana a part dinnanba" murmushi yayi me sauti yace, "to se kinsha tea din sannan zan kaiki gurin ammin" tashi nayi daga jikinshi kamar zanyi kuka nace, "to zan sha" barinta yayi ta sauka daga kan gadon da kanta, so yake yaga kozata iya tafiya yanzu da kanta. A hankali kamar yar kaciya take tafiyar, tashi yayi da sauri ya kama hannunta suka ƙarasa toilet din, sabon brush ya dakko ya matsa mata MacLean ya bata. da kanta tayi brush ɗin dan da cewa yayi ze mata taƙi yarda, ƙara kama hannunta yayi suka fito, duk da yanzu ta ɗan kwarara tafiyartata ba kamar dazu dasuka shigoba. Akan cinyarsa ya ɗora ta, yana bata tea din a baki kamar wata yar baby cikin lallabawa. seda tasha sosai sannan ya kyaleta. kulawar da mustapha yake bawa Maryam ba ƙaramin daɗi takeji arantaba, duk da tasan bawai soyayyace tasa yake mata hakaba, saboda abunda ya matane, a nata tunaninfa. duk da tagama shan tea ɗin besauketa daga jikinsaba, a ganinsa idan ya kwantar da ita akan gadonma jikinta ciwo zeyi, yanda yakejin kansa a wani irin yanayi na shauki dazata yarda goyatama zeyi. knocking kofar falo dayaji anayine yasa ya sauketa daga jikinsa badan yasoba. Fita falon yayi ya buɗe Kofar bayan ya tambayi waye, umaimah dake ɗauke da basket na abincin breakfast dinsu ta amsa masa da cewa itace. Taci uwar kwalliya kamar aljana da safiyarnan, cikin rangwada da iyayi tana wani far da ido kamar wata sabuwar makauniya tace, "yaya NOOR ina kwana, dafatan ka tashi lafiya" "lafiya" ya bata amsa a takaice yana komawa cikin falon. Dinning ta nufa ta ajiye basket din, tana tafe tana satar kallonsa harta kusa tuntube. Mustapha dake tsaye yana kallonta yace, "ki zuba komai kaɗan_kaɗan ki kawomun ɗaki" bejira amsartaba ya juya ya koma daki. Cikin tsananin farin ciki umaimah ta shiga kitchen din Maryam ta dakko tire da ƙananun plates ta zuzzuba masa komai kaɗan kaɗan kamar yadda yace, jikinta har rawa takeyi tsabar zumuɗin zata kaiwa Mustapha abinci har ɗaki, domin damar data ɗade tana jirane yau Allah yabata. Zuciyarta cike fal da murna ta ɗauki tire din ta nufi dakinnashi tana wani karkada jiki yanda zata ƙara rikita mustapha ya faɗa tarkonta.(🤣🤣🤣🤣 _Ni ba zance komaiba, Team ɗin umaimah da Maryam 👉gareku_).....✍️ _*By*_ _*Zeey kumurya*_ *ABINDA KASHUKA....!* _*BY*_ _*ZEEY KUMURYA*_ *6️⃣5️⃣* *Bismillahirrahmanirrahim* ..........Batare datayi knocking ba ta murda handle din ɗakin ta shiga babu ko sallama. Maryam tana kwance akan gado tayi rigingine idanunta a lumshe, mustapha kuma ya zaune ta wajen kafafunta ya ɗora su akan cinyarsa yana mammatsa mata a hankali, daya shigo ne take masa complain din har yanzu bata jin daɗin kafartata shine yace bari ya mata tausa. Umaimah da bata taɓa tunanin ganin Maryam a ɗakin ba ba ƙaramin shock ta shigaba data ganta harta kusa yarda tire ɗin hannunta, Allah dai ya taimaka be faɗin ba ta ajiyeshi. Ita duk a tunaninta Maryam tanacan ɗakinta tana bacci shiyasa ma Mustapha'n yace ta kawo masa daki. "ashe tananan kwance ita hamshakiya yana mata tausa kamar wani bawa da uwargijiyarsa" umaimah ta faɗi haka aranta ranta na ɓaci. Wani irin ɗaci ne ya ziyarci zuciyarta ƙasa kawai tayi kanta zuciyarta na wani irin bugu saboda kunci batare datace ƙalaba ta mike da niyyar tafiya. Mustapha dake kallonta yace, "jirani" buɗe idona nayi a hankali mukayi ido huɗu da umaimah, kallonta nake cike da mamaki dan banmasan sanda ta shigo ba, maida kallona nayi garesa da'alamun tambaya, dagemun gira yayi tare da mun wani lallausan murmushi, nima martanin murmushin na maida masa. A hankali mustapha ya sauke kafar Maryam daga jikinsa yana faɗin "my one kinji daɗin kafar yanzu ko?" Gyada masa kai nayi ina yunkurin tashi zaune. ƙara kallon Umaimah nayi nace mata. "Sannu fa" umaimah dake tsaye kamar dogari ta haɗiye wani yawu me ɗaci makut tace, "yawwa" kamar an mata dole tana kau da kai gefe. Sakkowa mustapha yayi daga kan gadon yana duban umaimah ya mata nuni da hannu alamar ta kawo masa kayan abincin kusa dashi, ɗauka tayi cikin sauri ta kai masa tana tunanin zece ta tafi karta ƙara ganin abunda ze ɓata mata rai, amma setaga ya ƙara tsaida ita, badan tasoba ta tsugunna ɗan nesa dashi kaɗan tana hararar Maryam ta gefen ido. Juyawa yayi ya kalli Maryam cikin wata irin murya me daɗin saurare da tsumar da zuciya yace, "luv sakko kiyi break" dan ɓata rai nayi na girgiza kaina tare da faɗin, "na koshi fa" wani kallo yamun wanda na kasa gane masa sannan ya lumshe idonsa ya buɗe cikin wani irin salo me narkar da zuciya. hannunsa ya mikomun yace, "to zo kiji" batare dana kama hannunnasaba na sakko daga kan gadon ina ƙoƙarin zama a gefensa bazantaba kawai naji na janyoni na faɗa kan cinyarshi. Cikin shagwaba nace, "washhh....ka kusa ballanibafa" gefen fuskata ya shafa yana murmushi cikin rada yace mun, "idan na karyaki dawa zan dinga....." (🥺 nidai zeey musty be barni naji ƙarshen zancennashiba) Fuskata na rufe cikin jin kunyar abunda ya faɗa ina murmushi. Kissing gefen wuyana yayi ya ƙara gyaramun zamana ajikinshi, tire din ya ƙara janyowa gabanmu ya shiga bubbɗewa. kamshin stew ne ya daki hancina lumshe idona nayi yawuna na tsinkewa. Soyayyayiyar doya da kwai ya dakko yanka ɗaya ya kai bakina yana faɗin "haa" make kafada nayi ina turo baki gaba nace, "nace maka na koshifa" marairaice fuska yayi cikin lallashi yace, "haba tawan ki daure kici ko kaɗan ne, banason yunwa ta illatamun ke" ƙara shagwabewa nayi na kwantar da kaina a kirjinsa nace, "nifa bakina babu daɗi, kabarni kawai kaikaci" hannunsa yasa yazagaye jikina yace, "ki daure kici ko kaɗanne Please, kinsan idan bakiciba bazan iya ciba nima, Please dear eat" ya ƙarashe zancen yana kuma marairaicewa. a hankali nace, "to bani zanci" kiss ya sakamur a gefen kuncina yace, "yawwa matar Aljannah ta." murmushi nayi cikin jin daɗin yanda yakemun. Doyar ya ƙara mikomun bakina a hankali na buɗe bakinnawa ina jiran ya samun kawai se kai bakinsa yana dariya ƙasa_ƙasa wadda ta ƙara fito da tsananin kyawunsa dimples ɗinsa na kunci biyu suka ƙara lomawa abun sha'awa. bata rai nayi na turo bakina gaba kamar zanyi kuka. a hankali cikin nutsuwa ya fara taunawa yana jifana da wani irin kallo ƙasa_ƙasa yana wani munafukin Murmushi. seda ya cinye sannan yaja karan hancina yace, "yadai Madam" cire hannunshi nayi daga fuskata na yunkura da nufin na tashi ina faɗin, "kuma ba ruwana dakai" maidani yayi jikinshi yace, "am sorry zo in baki" kawar da kaina nayi nace, "bazanciba kuma" batare da yayi maganaba ya ƙara dakko yankan doyar guda ɗaya ya saka a bakinsa amma ba dukaba dan gefe kaɗan, Juyo da fuskata yayi daf da tasa har muna jiyo hucin numfashin juna, 'yan yatsunsa guda biyu yasa ya buɗe bakina banzataba kawai naji ya haɗe bakina da nashi ya sakamun doyar bakinshi acikin bakina. umaimah dake tsugunne a gefe tamkar almajira tana kallonsu tamkar ta samu TV, wani irin zafi zuciyarta take mata, takaici da baƙinciki duk sun lullubeta abunda yafi kona mata rai yanda mustapha ya tsayar da ita, kuma tamkar ya manta da ita se sha'aninsu sukesha wanda ke ƙoƙarin tarwatsa mata zuciya, gashi bazata iya tafiyaba batare da mustapha ya bata umarniba dan gudun karta saɓa masa. Lumshe idona nayi ganin yadda yake kallona kuma yaƙi sakin bakinnawa, wani irin yammm..nakeji ajikina saboda lips dinsa dake gogar nawa, a hankali nake taune doyar harna cinye, ƙoƙarin janye bakina nayi daga nasa amma yaƙi bani damar hakan sema ƙara mamular lips ɗina da yake yana tsotsa, seda ya tsotsa san ransa sannan ya sakarmun bakin yana sauke numfashi, nima sauke numfashin nake cikin wani irin baƙon yanayi daya riskeni. Harga Allah na manta da wata umaimah a ɗakin, seda naji yana mata magana da faɗin. "Sorry na barki kina jirana ko? dama gyaran falo zaki ɗan gyara mana idan babu damuwa" yanda yayi maganar zaka gane da tsantsar rainin hankali yayita. Umaimah datake jin kamar ta fasa ihu, ta tattaro duk wata dauriyarta tace. "Ok babu damuwa" buɗe idona nayi da sauri na kallesa nace, "data barshi nima zan iya fa" lakacemun kumatu yayi yace, "no kibarta tayi kawai keda baki da lafiya ina ke ina wani aiki" zanyi magana ya ɗora finger dinsa aka lips ɗina yace "shiiiiii, kinsan banaso kina wahala ki barta tayi kawai" maida kallonsa yayi ga umaimah yace, "you can go" mikewa umaimah tayi cikin wani irin mummunan yanayi, har wani jiri_jiri takeji tsabar baƙin_ciki, tana fita falo ta saki kukan datake ta dannewa, durkushewa tayi a ƙasa, mustapha da Maryam kawai take hangowa a idonta manne da juna suna zuba love. datasan wannan baƙincikin zatazo tatarar da wlh bazata kawo musu breakfast dinba, gashi abunda yafi bata mata rai wai ta gyara musu falo, wato bayason matarsa ta wahala itace baiwa kenan ita zata wahala. Kwafa taja ta share hawayenta ta mike ta fice batare data gyara falonba. Ni kuwa bayan fitar umaimah na dubeshi srioustly nace, "Allah yaya daka barta tatafi zan iya gyara gidan da kaina" hararata yayi yace, "baki da lafiyar zan barki kiyi wani gyaran gida." ina tashi daga jikinshi nace, "nafa warke Ni, dama kuma ba cuta nakeba." Be ƙara mun magana se abincin daya cigaba da ci hankali kwance cikin nutsuwa. Seda ya gama ya dubeni fuska babu wasa yace, "zo" ganin yanda yayi yasa na matso kusa dashi, abincin ya dinga ɗiba yana bani a baki fuskarsa babu walwala kamar bashi yagama yintaba ɗazu. seda ya tabbatar data koshi sannan ya rufe sauran. Tashi yayi ya dakko magani da ruwa yazo ya ɓalle ya mikomun, nida banason shan magani harda zanyi musu naga yamun wani kallo, ba shiri na karba na sha ina yatsina fuska. ganin yanda ta tsorata dashi seya ɗan saki fuskarshi, ɗaukarta yayi cak suka kwanta akan gado, bargo yaja ya lullubesu cikin tsokana yace, "tunda kin warke bari na ƙara" "Ni ban warkeba" na fadi haka kamar zan fashe da kuka danna ɗauka dagaske yake ze ƙara yi ɗin. daga kafadarsa yayi yana tabe baki yace, "ke kika faɗa da bakinki, Ni baruwana ƙarawa zanyi" kuka tasa wanda kana gani kasan na taɓara ne tace, "nidai A'a kuma sena faɗawa Aunty idan ka ƙara" murmushi yayi yasa hannunsa yana ƙara rungumeta ajikinsa ganin tana ƙoƙarin tashi. Kuka Maryam take bilhakki, shafa kanta ya hauyi cikin lallashi tare da hura mata iska daga bakinsa a cikin kunnenta. amma bece mata komaiba, ganin kukannata bana ƙare bane, seya dago fuskarta, idanunta a rufe suke baccima ya fara ɗaukarta amma tsabar rigima batabar kukanba, a hankali ya zira mata lips dinsa na ƙasa acikin bakinta, dif ta dauke kukan ta fara mamular lips dinnasa kamar jaririn daya kama nonon uwarsa tana sakin ajiyar zuciya. seda ya tabbatar bacci ya ɗauketa sosai sannan ya zare lips dinnasa a hankali daga cikin bakinta. Kwabe fuska tayi ta turo baki gaba alamun bataso hakanba. lips dinta ya shafa a fili yace, "rigima girl" yana aikin kallonta besan sanda shima bacci me daɗi ya ɗaukeshiba..... Su ammi suna falo sukaga umaimah ta shigo kamar anjehota, ammi ta dubeta da mamaki tace "lafiya kuwa auta?" girgiza kai kawai umaimah tayi alamun a'a batace komaiba. Mama dake cin abinci tace, "yazakice a'a bayan gakinan kin shigo kamar wata mara lafiya, kuma daga kai wa mutane abinci kinje kin zauna tun dazu, yanzu amminki tagama zancenki tana ko abinci baki ciba zataje ta kirani." Mikewa umaimah tayi tana faɗin "batajin daɗi ne shine yaya NOOR yasa na gyara musu gidan" zuhura dake bawa Abul tea tace, "gyaran gidan da'aka sakine shine kike bata rai haka?" Umaimah bata bata amsaba ta shige ɗakinta. Ammi kuwa tuni hankalinta yayi kan ƴar surukartata dataji ance bata da lafiya, wayarta ta ɗauka ta lalubo number'n Mustapha tayi dialing dantaji meke damun maryam din. Har Kira uku ta masa amma bedagaba. Fuskarta da alamun damuwa take duban su mama tace, "Allah yasa dai jikinnata ba tsanani yayiba, gashi kuma na kira NOOR ɗinma bedagaba. Cikin son kwantar da hankali mama tace, "karki wani tada hankali 'yata, kinsan mace me ƙaramin ciki ba'a rabata da dan laulayiba, insha Allahu ciwon ba wani me tsanani bane" cikin sanyin murya ammi tace, "Allah yasa, amma da zuwa zanyi na dubota, dan idan banga yanda jikinnata yakeba hankalina baze kwantaba." mama tace, "to kije kawai ki dubotan, kice muna mata sannu, idan mungama muma zamu shigo." mikewa ammi tayi tana amsawa ta fice ta nufi part ɗin su Maryam. Knocking tayi taji shiru hakan yasata tura Kofar ta shiga bakinta ɗauke da sallama, tayi sallama takai uku amma taji shiru. Ɗakin maryam ta shiga taga wayam ba kowa. fitowa tayi ta nufi ɗakin mustapha, duk da zuciyarta na mata tuni da hakan kamar bedaceba, amma hankalinta baze taɓa kwanciyaba idan bataga yanda jikin Maryam ɗin yakeba. Seda tayi knocking nanma taji shiru sannan ta tura kofar ɗakin a hankali ta shiga bakinta dauke da sallama. Ajiyar zuciya ta sauke ganin su kwance suna bacci, se yanzu hankalinta ya kwanta tasan tunda Maryam ɗin ta samu bacci jikin da sauƙi kenan. fita tayi taja musu ƙofar a hankali, seda ta rufe musu ta falonma yanda sena cikine kawai ze iya buɗewa sannan ta koma part ɗinta...... A hankali na buɗe idona tare da zare jikina daga nasa na tashi zaune ina salati acikin zuciyata, fuskarsa na kalla inajin wani sonsa na ƙara ratsa zuciyata, kusancin damuka samu daga jiya zuwa yau, da kuma kulawar daya bani ba ƙaramin tasiri yayi acikin zuciyataba. Hannuna nakai a hankali na shafi kwantaccen sajensa wanda yake ƙara fito da kyawunsa cikin raina ina faɗin, _"Ya Allah kanunamun ranar da wannan bawannaka ze soni, kamar yadda nake tsananin sonsa."_ ɗauke hannuna nayi daga kan fuskarsa ina sauke ajiyar zuciya, a hankali cikin lallabawa na zare hannunsa daga jikina dan kar ya farka, sauka nayi daga kan gadon na ɗauki tire ɗin damukaci abinci na fice daga ɗakin. seda na fita falo na duba time naga har 12 na rana ta wuce, lallai mun dade mune shan bacci, amma naji daɗin jikina sosai danayi baccin. Dan ciwon da kaina yakemun ya dena, kawai dai ina jin jikina fayau babu kwari ne. ko ɗakina ban shigaba na fara gyaran gidan, falo na fara sharewa nayi mopping na saka turaren wuta, sannan na nufi kitchen na gyarashi nayi wanke_wanke, sannan na shiga ɗakina shima na gyarashi tass. Bayan na gama na faɗa toilet nayi wanka na ƙara gasa jikina, tare da dauro alwalar sallah azahar. Cikin wata doguwar rigar atamfa na shirya, banyi wata kwalliyaba amma na budade jikina da turaruka masu daɗin kamshi. ganin har 1 ta wuce, sena tada sallah ta......✍️ *By* *zeey kumurya* *ABINDA KASHUKA....!* _*BY*_ _*ZEEY KUMURYA*_ *6️⃣6️⃣* *Bismillahirrahmanirrahim* ..........Bayan na idar da sallar na fito da nufin naje na tashi yaya yayi Sallah, knocking din ƙofar falon da'ake shiya tsaidani. Kofar na nufa na buɗe bayan na tambayi waye? Aunty zuhura ce, faɗaɗa fara'a nayi nace, "Aunty zuhura sannu da zuwa" "yawwa Mamana" ta faɗa tana shigowa falon tare yin sallama, amsa mata nayi ina gaba tana bina a baya. Kallon yanda Maryam take tafiya yasa Aunty zuhura ta gane abunda ya faru, duk da maryam ɗin tayi iyakar ƙoƙarinta wajen ganin ta daidaita tafiyar tata yanda baza'a ganeba, amma seda zuhura ta harbo jingin. zama sukayi akan kujera suka ƙara gaisawa, Aunty zuhura ta mata ya jiki. Maryam ta amsa da faɗin "da sauki dannama warke" Aunty zuhura na murmushi tace, Allah ya ƙara sauki" Maryam tatambayeta ina Abul, tace yanacan gurin mama. Aunty zuhura bata wani jimaba tatafi tacewa maryam zataje ta dawo anjima... mustapha yana cikin baccinshi cike da jin daɗi da nishadi, amma tashin Maryam datayi ta barshi duk se yadena jin daɗin baccin. lalube_labule kawai yakeyi da hannunsa a gefensa koze jiyota amma sedai yaji filo, haka dai yacigaba da baccin babu daɗi. A hankali na tura Kofar dakin na shiga, kan gadon na nufa na hau na zauna ina tunanin ta ina zan fara tashinnashi. kyakkyawar fuskarsa me cike da kwarjini na kurawa ido da murmushi ɗauke a fuskata. wani irin farin ciki nakeji mara misaltuwa a cikin zuciyata, jina nake a wata duniya me nishadi da annashuwa, gani nake yau a duniya babu wanda yakaini farin ciki, saboda kasancewata da mutumin da bantaba zaton ze zamto miji a gareniba, amma ikon Allah gashi mun kasance matsayin ma'aurata har mun haɗa shimfida. Lumshe idona nayi saboda kwallar dabansan kota meceba data cikamun ido, tafin hannuna na kai kan cikakkiyar sumar kansa baka sidik me laushi da daɗin shafawa a hannu, na fara shafa masa idona a lumshe cikin tsananin shauki ina sauke ajiyar zuciya. nayi 6 minutes ina shafa kannasa zuwa zajen fuskarsa da bayan kunnensa. Mustapha kuwa duk da bacci yake amma ba ƙaramin jin daɗin abinda take masa yakeba, har wata ajiyar zuciya yake sassaukewa. baccin daya dena masa daɗi ya fara masa yanzu. ƙasa nayi da hannuna ina shafa wuyansa zuwa saman kirjinsa, tunawa danayi lokacin sallah na kurewa yasa nayi ƙoƙarin ɗauke hannuna daga jikinsa domin na tasheshi yayi Sallah, amma naji zaraf ya rikemun hannunnawa, a hankali nake ƙoƙarin zarewa amma ya rike gam da hannunsa. kyale masa nayi senaga ya maida hannun kan kirjinshi ya ɗora nashi akai ya manne. murmushi nayi kawai cikin jin daɗi da farin ciki. A hankali nasa ɗayan hannuna na ɗauke nashi sannan na zare nawa daga kirjinnasa, hakan danayi kuwa kamar tashinshi nayi daga baccin. a hankali ya buɗe lumshashshun idanunsa da suka sirka saboda baccin yayi, ya saukesu akan fuskarta, nima kallon fuskartasa nake hakan yasa idanunmu suka sarke cikin na juna, kasa janye idona nayi daga nasa kamar koyaushe idan ya kalleni, kallon cikin kwayar idonnasa nake zuciyata na tsananta bugu, banfi 30 seconds ina kallonsaba na lumshe idona saboda wata kasala datake lullubeni a sanadiyyar kallon kwayar idansa da nayi, batare dana buɗe idonaba a hankali nace, "ka tashi kayi sallah, kar lokaci ya kure" lumshe ido mustapha yayi cikin rashin jin daɗin rufe idonta datayi ta katse masa wani abu dake bin ilahirin jikinsa a sanadiyyar kallon kwayar idonta dayakeyi gashi ta masa kyau sosai. Tafin hannunsa yasa ya kamo nata a hankali ya haɗesu guri guda yana murzawa, a tare sukaji wani irin shock a jikinsu. batare daya saki hannunnataba ya buɗe idonsa tare da tashi zaune jin abinda tace. zama yayi a daf da ita har jikinsu na gogar na juna, bakinsa yakai daidai kunnenta cikin cool voice dinsa data ƙara sanyi saboda daga bacci ya tashi yace, "haka ake tashin miji a gurinku?" ya ƙarashe zancen yana ɗan matse hannunta dake haɗe da nasa. wayyo Allah, bansan ya misalta muku yanda naji ba a jikina sanadiyyar wannan maganar dayamun, turo bakina nayi gaba bance komaiba. kissing kuncinta yayi sannan yasa ɗayan hannunsa ya kama lips ɗinta da finger dinsa guga biyu ya matse yace, "wannan lips ɗin, nasan mezan masa a dena turomunshi gaba" da sauri na gimtse su, dan ban manta tsotsar dasukasha jiya agurinsaba ta fitar hayyaci har zafi seda sukamun. Tattausan murmushinsa yayi ya cire hannunsa daga bakinta, tare da zare ɗayan daga nata ya sakko daga kan gadon bakinsa ɗauke da salati. ban iya wani yunkuriba duk da yadda naso hakan har ya shige toilet din, duk da ya saki hannuna amma bandenajin wani yarrrr...... ajikinaba gami da kasala. Ajiyar zuciya na sauke na tashi na fara gyara gadon daya yamutse. kafin ya fito harna gyara ɗakin shap_shap na fice falo, zama nayi akan kujera ina sauke numfashi ɗankwalin kaina na cire saboda kan ya ɗan sha iska dan har yanzu da lema a jikin gashin duk da uban man kitson dana shafa kuwa, danma kitsone akan amma datuni na busar da gashin............. *KADUNA* Su Aunty sun sauka lafiya, tun a daren jiyan sukayi waya da ammi data kirasu dantaji ko sun sauka lafiya. Tun da suka taho suhailat take damun Aunty da tambaya akan gidanwa sukaje, da kuma tambayar me Maryam take a gidan dan daga baya ta fuskanci maryam ba aiki take a gidanba, itama tana rayuwar yanci ne kamar kowa na gidan. se kuma ammi dataga tana mata kama da mustapha musamman ta idanunsu da yanayin yanda suke kallon mutum, dansu ba normal kamar kowa kallonsu yakeba kuma Maryam ma taga irin kallon take. shine abunda ya ƙara bata mamaki ya kuma ɗaure mata kai, Aunty dai bata kulataba da tambayoyinta balle ta bata amsa, hakama Aliya dataketa karatun Novel ɗinta a wayarta. Yau da safe bayan suhailat tagama shan baccin asararta ta tashi tayi wanka ta fito falon Aunty. Babu kowa a falon, fridge ta nufa ta buɗe ta dakko hollandia me sanyi ta nemi guri ta zauna ta fara sha a yangance. tana cikin sha Aunty ta shigo falon ta dawo daga part din abbansu aliya ne. sallama tayi suhailat ta amsa mata ciki_ciki, dan har yanzu haushin Aunty taƙi barinta a jos take. batare da Aunty ta zaunaba tace, "suhailat wai banace kidena shan abu me sanyi bane, bakisan illa bane a gareki da abunda ke cikin ba." Zunburo baki tayi gaba tace, "To Ni fa Aunty banajin daɗin komai se abu me ɗan sanyin." Harararta Aunty tayi bata ƙara cewa komaiba, se kwace sauran hollandia'n datayi ta shige bedroom ɗinta bayan tacewa suhailat ta shirya zasuje asibiti anjima. suhailat ta amsa mata kamar zatayi kuka saboda kwace mata hollandia'n datayi. Itafa ta gaji da wannan wahalallen cikin, ace kullum cikin shan wahala take, tun daga ranar da Dr. Ta tabbatar tana da ciki, har yau bata ƙara samun ishashshiyar lafiya ajikintaba, inda Allah ma yataimakama bata kwadayi_kwadayi, gashi cikin yayi sanadiyyar katsewar karatunta, kuma a tunaninta shiya hana Aunty tada maganar auransu da mustapha, shiyasa take ƙara tsanar cikin. Kamal ne ya faɗo mata a rai, tanason kiranshi kodan ta sanar masa tana ɗauke da cikinshi amma kuma tana tuna gargardin mommy data mata akan karta sanar masa, kuma ko yanzu ta kunna wayarta seya kirata kokuma ya mata text. kawar da tunanin kamal tayi ta faɗa na masoyinta mustapha, ita yanzu kawai neman hanyar dazata koma Jos take batare da Aunty ta saniba, dan yanda takeson kasancewa da yayannata ko'a motar haya zata iya zuwa Jos ɗin, Ita dai burinta kawai taganta kusa da masoyinta kota halin ƙaƙa..... Aunty zuciyarta babu daɗi ta ajiye guntun hollandia'n akan bedside locker. Tanajin ciwo sosai a cikin zuciyarta akan cikin dake jikin suhailat, kawai tana dannewane, ita fargabartama ta yanda zata iya sanar da daddy maganar cikin dake jikin suhailat ɗin, ita kanta suhailat ɗin tanason ta zaunar da ita ta mata tambayoyi akan cikin da kuma wanda ya mata cikin, amma taga suhailat ɗin kwata_kwata babu nutsuwa a tattare da ita, gashi wani abu dayake ƙara bawa Aunty takaici, suhailat bata da tarbiyya ko ladabi ko kaɗan. duk kwanakin datayi agidannan har yau bata san gari ya waye taje ta gaishedda Abbansu Aliya ba, kullum se Aunty ta turata take zuwa, masu aikin gidanma ta lura hakuri kawai suke da halinta, amma basajin daɗin zama da ita. shiyasa yayan Aliya kwata_kwata baya shiga sabgarta tunda canma bare kuma yanzu, duk da shi mutum ne me fara'a da barkwanci kamar Aliya, Aunty har faɗa take masa akan yanda yakewa suhailat ɗin. Ajiyar zuciya Aunty ta sauke ta bar tunanin danba mafita bane a gareta, addu'a itace kawai mafita. wayarta ta dakko ta kira likitan su ta sanar masa zasuzo asibiti anjima......... ************ Ya ɗan jima a toilet din sannan ya fito, dakinnasa ya shiga bi da kallo ganin yanda Maryam ta gyareshi, yanda ta ɗame gadon ta jera filollika yafi komai burgeshi, gadon tamkar ba'a taɓa hawa ankwanta a kanshiba. Ashe shi da duk jagwalgwala abunsa kawai yake be iyaba, kuma shi idan zeyi gyaran dakin seya ɗauki lokaci da me tsayi kafin yagama amma ita gashi acikin lokaci kaɗan harta gyara ta fice. Karasawa yayi gaban madubi ya ɗauki lotion ɗinsa ya fara shafawa a lallausar farar fatarsa wadda ta jiku da hutu. Cikin some minutes ya gama shirinsa cikin ƙananun kaya wanda suka amshi jikinsa da matuƙar yi masa kyau sannan ya tada sallah.... Falo ya fito hannunsa riƙe da wayarsa yana latsawa, maryam da hankalinta yake kan kallon datakeyi batamasan ya shigo falonba. A bayan kujerar datake ya tsaya, sunkuyo da fuskarsa yayi daidai da tata ya hura mata iska daga bakinsa a fuskarta, lumshe idona nayi da sauri a ɗan tsorace saboda bansan da zuwansa falonba, yanzu daddaɗan kamshinsane ya tabbatarmun da shine. batare daya janye fuskarsa daga kusa da tataba yace, "ya jikinnaki?" numfashi na sauke me ƙarfi saboda yanda yake gogamun sajen fuskarsa a kumatuna nace, "da sauƙi" cikin matuƙar raunin murya. kafin ya kuma magana aka fara knocking kofar falon, wayarsa ya ajiye a gefena sannan ya zagayo ya nufi kofar, da ido nabi bayanshi da kallo cikin wani irin baƙon yanayi ina sauke numfashi. Ammi ce hannunta ɗauke da basket data haɗo musu launching aciki. Murmushi suka saki a tare ita Mustapha lokacin da sukayi 4 eyes. cikin murmushin yace, "sannu da zuwa AMMINAH" itama da murmushin a fuskarta tace, "yawwa MY NOOR" tare da yin hugging ɗinshi lumshe idonsa yayi yana ƙara hugging ɗinta shima cikin tsananin so da kaunar dake tsakanin ɗa da mahaifiya. sakinsa ammi tayi ta shafa kansa tace, "ya jikin takwarata?" Da mamaki ya kalleta dan be san ta saniba. shanye mamakinsa yayi yace, "da sauƙi" ya ƙarashe zancen da karɓar basket din hannunta. Ammi tace, "Allah ya ƙara sauƙi yasa kaffarane" "Ameen" ya amsa yana kama hannunta suka shiga cikin falon. kallonsu nake cike da ban sha'awa da burgewa, sunmun matuƙar kyau, kana ganinsu kaga uwa da ɗanta. sakin hannunsa ammi tayi ta ƙaraso gurin Maryam tana faɗin, "ɗiyata sannu ya jikinnaki?" da sauri na zamo daga kan kujerar danake ina daura ɗankwalina cikin girmamawa nace, "da sauƙi ammi, ina wuni" ammi cikin jin daɗin yanda taga jikin maryam tace, "lafiya kalau ɗiyata, Masha Allah haka akeso, naga jikinnakima da sauƙi bayanda nayi zaton ganinkiba, Allah ya ƙara sauƙi, ya inganta" "ameen" na'amsa ina ƙara yin ƙasa da kaina cikin jin kunya, gani nake kamar tasan meyafaru. zama ammi tayi akan kujerar danake, Ni kuma na zauna a ƙasan kujerar. Shima Mustapha zama yayi a gefen ammi ya kwantar da kanshi akan kafadarta. Kallon fuskarsa ammi tayi tace, "meke damunta ne?" yace, "zazzaɓi" atakaice. Ammi tace, "amma kuma shine bakuje asibiti anduba taba NOOR?" Yace "na kira family doctor ɗinku tazo ta dubata" da mamaki ammi tace, "Dr husnah?" Yace "ehh" ammi tace, shine bata shigo part ɗina mungaisaba" yace, "may be, tana sauri ne, danda early morning tazo, kuma daganan zata wuce aiki" ammi tace, "ehh hakane ai nasan Dr husnah akwai kirki, amma duk da haka Yakamata ku fara zuwa asibiti dan adinga duba lafiyarta dana abunda ke cikinnata" dagowa nayi da sauri na saci kallonsa, shima kallon maryam ɗin yayi sannan yayi murmushi yace "to ammi zamuje insha Allah" shafa kuncinsa ammi tayi tace, "yawwa, Allah ya ƙara lafiya, ya muku albarka ya baku ƴaƴa na gari masu albarka" "Ameen summa ameen" muka amsa a tare. tashi nayi na ɗauki basket ɗin da ammi ta shigo dashi na abinci na nufi kan dinning dashi na ajiye sannan na shiga kitchen.......✍️ *Kuyi manage da wannan Please, gobe insha Allahu zan baku new update, Ku ƙara hakuri dani dai.🥺🙏* *By* *Zeey kumurya* *ABINDA KASHUKA....!* _*BY*_ _*ZEEY KUMURYA*_ *6️⃣7️⃣* *Bismillahirrahmanirrahim* ...........Binta da kallo Mustapha yayi harta shige kitchen din cike da tausayawa yasan dauriya kawai amma bata jin daɗin jikinta. cire kansa yayi daga kafadar ammi batare dayace mata komaiba ya mike yabi bayan maryam. Itama ammin tausayin maryam takeji matsananci, tarasa meyasa kuma, tun ranar data fara ganinta taji tausayinta me tsanani ya zirga mata, kuma a duk lokacin data ganta setaji wani abu acikin zuciyarta dabatasan meneneba, tanason ta tambayeta ina mamanta da babanta suke? Suna raye ko sun mutu? Tunda ita dai bata taɓa jin tayi zancensuba ko wani ɗan'uwanta bata taɓa ji tayi zancensaba, sedai gwaggonta kawai. kuma ammi ta fuskanci tamkar maryam ɗin tana da wata damuwa a tattare da ita. Numfashi ammi ta sauke a ranta tana faɗin, "yau kam insha Allahu bazatayi ƙasa a gwiwaba zata tambayi Maryam tarihin rayuwarta"......Maryam tana cikin dauraye flate ɗin dazata zuba masa abinci ya shigo kitchen din, tsayawa yayi daga bakin kofa yana kallonta, bansan ya shigoba se kamshin turarensa kawai naji gami da jin wani abu na yawo ajikina kuma bugun zuciyata ya sauya, juyowa nayi naganshi tsaye ya harde hannunsa a kirji, kasa ɗauke idona nayi daga kallonsa amma ba directly ido da ido ba, saboda tsananin kyawun daya ƙaramun, kayan jikinnasa sun masa matuƙar kyau sosai, fuskarsa se annuri take, kamar na dawwama ina kallonsa haka naji. Takowa yayi a hankali ya ƙarasa inda take ya tsaya daf da ita yana kallon fuskarta, shafa saman idonta yayi cikin wani salo yace, "wannan kallon fa, kamar yau kika fara gani na?" Lumshe idona nayi ina sauke numfashi bance komaiba. Rungumeta yayi ta baya a jikinsa tare kai hannunsa ya shafa cikinta yana murmushi yace, "bari inji lafiyar baby nah" buɗe idona nayi da sauri na ɗan waro shi waje cikin mamakin Abunda yace, amma bance komaiba. Seda yagama shafemun cikin son ransa yana shishshina wuyana sannan ya sakeni ya fita, ina sassauke numfashi na ɗauki plate din da cokali da saving spoon na fice daga kitchen din. Kan dinning na koma na zuba masa abincin a cikin plate danni bana tunanin zan iya cin wani abu a yanda nake jin jikina. Rufewa nayi da wani plate din na dora spoon akai na nufi cikin falon, akan Centre table na ajiye. Ammi ta dubeni tana murmushi tace, "sannu ɗiyata" murmushi nayi nace, "yawwa" sannan na koma na dakko masa ruwa da cup na kawo na ajiye. Ammi se sannu takemun kamar wadda nayi wani babban aikin, ga wani kallo datake bina dashi dana kasa gane masa. zama nayi a ƙasan kujerar da suke na dubi yaya dake latsa wayarsa nace, "yaya ga abincin" gyada mun kai kawai yayi. Ammi da kanta ta sakko ƙasa ta zauna kusa dani, nuni tamun da hannu na miko mata abincin, tashi nayi na dakko mata na ajiye mata a gabanta. kallon Mustapha tayi tace, "NOOR sakko kaci abincin mana kar yayi sanyi" batare daya dagoba daga latsar wayar da yakeyiba yace, "ammi taci kawai, Ni naci later" ammi tace, "A'a, nasan halinka anjiman baci zaka yiba ka sakko kawai" ajiye wayar tasa yayi yana murmushi ya sakko ya zauna a ɗayan gefen ammin, muka sata a tsakiya kenan. Buɗe plate ɗin saman tayi ta saka spoon a cikin hadaddiyar pride rice din dataji kayan hadi se tashin kamshi take, ta debo abincin ta kai bakin mustapha, buɗe bakinsa yayi a hankali ta zuba masa. ƙara debowa tayi ta kai bakin Maryam, duk da banajin cin abincin amma haka na buɗe bakina a kunyace nima ta zubamun.....haka ammi taita bamu abincin a baki cike da kulawa da kauna gami da tattali, harseda muka cinye duka na cikin plate din, ruwa ma da kanta ta tsiyaya a cup ta bamu, duk ni naso karba nasha da kaina amma tace ita zata bani ta cikashe ladanta. Plates din da mukaci abincin na ɗauka na kai kitchen na tsaya dauresu. Mustapha bayan yagoge bakinsa da tissue ya kama hannun ammi ya haɗe da nasa yana murmushin yace, "nagode Ammi nah, Allah yasaka Miki da gidan Aljannah" murmushi ammi tayi ta tsare shi da ido tace, "Ameen, amma NOOR, meyafaru ne yau, naga kana cikin farinciki wanda yakasa boyuwa a fuskarka" murmushi yayi a karo na ba'a daɗi daga daren jiya zuwa yau yace, "babu komai ammi nah" ammi ta masa wani kallo tace, "akwai mana NOOR duk wannan murmushin dakake fa nasan bana kawai bane" murmushin ya kumayi me sauti sannan yace, "au da bana murmushin?" Ammi ta hararesa tace, "kafi kowa sani ai, bama murmushi kawai ba, komai naka ya canza a yau har maganarka ta yawaita akan da, yau ko ɗan miskilancinnan babu" wannan karon dariya yayi saboda yanda ammin tayi maganar, shi kanshi yasan yau ɗin rana ce ta dabance a cikin rayuwarsa kuma kamar yadda ammi ta faɗa yana cikin tsananin farin cikin, a yanda yake jin kansa ma yanaji tamkar babu wanda ya kaishi farin ciki a yau. Itama ammi murmushi tayi bata ƙara cewa komaiba. A haka Maryam ta fito ta samesu, itama Maryam ɗin ammi ta lura tana cikin farin cikin, hakan yasa ta fasa yiwa Maryam tambayar data kudiri niyyar yimata akan rayuwarta dan karta yi sanadin tadawa Maryam ɗin da damuwarta. Ammi ta daɗe a part ɗinmu muna hira cikin nishadi, tanata bamu labarin yan'uwanta da dangin mahaifin yaya, senaji dama nice nake da dangin mahaifin kamar haka. Takuma ce bayan sallah insha Allahu zamuje Niger ɗin mu zazzaga yan'uwa, dan har yau bata sanar musu da bayyanar mustapha'n ba, tafiso ta kaishi su ganshi da idanunsu. Mustapha dama yana da kudirin ya tambayi ammi yanason ta kaishi yaga danginsa se gashi tamasa zancen da kanta. Bayan sallar magriba muna zaune a falon ammi, dazata dawo daga part dinmu na biyota muka taho tare. Umaimah datake kwance a ɗaki tun safe tana kunci ta fito falon cikin shirinta da alama fita zatayi. Ina kwance akan doguwar kujera, ina yin game a wayar ammi, banko motsaba balle na dago na kalleta. umaimah ta harari maryam taja wani uban tsaki ta shige ɗakin ammi ganin bata falon, ina jinta amma duk da haka nayi kamar bansan da halittarta a cikin falonba. Ammi na ninke wasu abayoyi dazata bawa direbanta ya kaiwa wata mata da zata siya umaimah ta shigo dakin, ammi ya dubeta tace, "ke kuma lafiya kike kuwa yau" tana zama a gefen ammi tace, "lafiya kalau nake" ammi tace, "to mene kuma kike ta ɓata rai, tun safe kin kule a ɗaki ko abincima bance kinciba" umaimah ta zunburo baki gaba tace, "babu komai fa ammi dagaske, kainane ke mun ciwo amma yanzu ya dena nasha magani" ammi ta mata wani kallo tace, "Allah ya ƙara sauƙi" taci gaba da ninkinta. Umaimah tace, "Ammi zani gidansu Farda ne, na shigo na faɗa miki" ammi tace, "gidansu Farida kuma a darennan? mezakiyo?" Umaimah tace, "ammi abu kawai zangani, yanzu zan dawo" "mene abun da zaki gani, baza ki bari se Allah yakaimu safiyaba kije" umaimah ta marairaice tace "Please ammi nah, dan Allah kedai ki barni yanzu zandawo wlh ba jimawa zanyi ba" ammi ta mata wani kallo kamar tanason ta gano wani abu tace, "shikenan yanzu dama zan aiki driver gidan Hajiya zulai, seki bisa ya saukeki, idan ya kaimata seya dawo ya ɗauke ki" umaimah tana murmushin jin daɗi tace. "Yawwa amminah nagode" "saura kuma ki daɗe" ammi ta fadi haka tana saka abayoyin a cikin wata jaka. "Insha Allahu Ammi bazan dadeba" ammi ta bata jakar kayan ta fice. ko da ta fito ma seda ta ƙara hararata da tsakin sannan ta fice, ni batasan ba ta ita nakeba dan bana jin daɗin jikina. Umaimah ce zaune a kan gadon ɗakin kawarta kuma aminiyarta farida ta rafka tagumi da hannu biyu. Faridance ta shigo ɗakin hannunta ɗauke da plate data kawo mata ruwa. ajiye plate din tayi akan locker sannan ta hau kan gadon ta zauna itama tana duban umaimah tace, "kawata lafiya naganki wani iri kamar mara lafiya ko kuma me wata damuwar? Umaimah ta sauke numfashi tace, "inafa lafiya kawata, aini da abunda yake damuna gara ace cuta nake wlh" farida tace, "me ya faru tawan?" Umaimah ta ƙara sauke wani nannauyar numfashi tace, "ina cikin babbar matsala kawata" wai matsalar me? Ki faɗa mun abu, kinzo se kwana_kwana kikemun ki tafi kanki tsaye mana kinsan banason hakafa" farida ta fadi haka a ɗan hasale. Umaimah kamar zatayi kuka tace, "akan yaya NOOR ne" farida taja tsaki tace, "dama nasan tatsuniyar bata wuce ta koki, meyafaru to?" Umaimah tace, "ina ganin kamar fa ya gane ina sonsa" "meyasa kika ce haka" "saboda kulawar dayake nunawa matarsa a gabana kamar da gayya yakeyi" farida tace, "to so what, idan ya gane dama ai haka mukeso mu" umaimah tace, "inafa akeson haka, mutumin da yau yayi abunda ya kusa tarwatsa zuciyata, har kuka da seda nayi, Allah yasoma kukan be kufcemun a gabansu ba, shida shegiyar matartasa me kama da aljanu" farida tace, "me ya miki yau ɗin?" Cikin ɗacin rai umaimah taba farida labarin abunda ya faru yau, ta ƙara da faɗin, "wlh farida a lokacin nemar yawu nayi na rasa daga bakina, jikina kamar an zukemun jini haka naji saboda tsabar baƙin ciki, kuma duk abubuwannan dayake mun me makon sonnasa ya ragu daga cikin zuciyata sema karuwa yake, dan Allah kawata ki bani shawarar abunda zanyi na janyo hankalinshi gareni, yasoni nima, ya bani kulawa kamar yadda yake bawa matarsa" farida tace, "to waike kina nufin har yanzu baki fara aiwatar da abunda na baki shawara kiyiba" gyada mata kai umaimah tayi alamar alamar eh. "To me kike jira da baki faraba?" Umaimah tace, "bakisan yaya NOOR bane, yana da kwarjinin da bazan iya tunkararsa da abunda da kike cewa nayiba banmaga fuskar hakanba, ina tsoron kuma kar naje garin neman gira na rasa ido" farida tayi wani tsaki tace, "Ni dan Allah ki nunamun pics din Noor dinnan dakika dameni da zancenshi" Batare da tunanin komaiba umaimah ta dakko ƴar ƙaramar handbag dinta ta zaro wayarta ta shiga gallery, hoton mustapha data tura a wayar ammi wanda yayi ranar idi cikin manya kayan ta lalubo. Miƙawa farida wayar tayi tace, "kingan shifa" hannun farida har rawa yake ta karbi wayar. _"wow handsome guy, kutmar... Aini duk yanda nake tunanin yanda guy dinnan yake da yanda umaimah take fasaltamunshi ya wuce nan, jibeshifa sekace shi yayi kansa gaskiya dole umaimah ta ruɗe amma wannan guy din dani ya dace bada umaimah ba_" farida ta fadi haka a cikin zuciyarta lokacin da idanunta sukayi arba da hoton mustapha. kallon Umaimah tayi tana shanye abunda takeji a cikin zuciyarta game da mustapha a kallo ɗaya data masa a rayuwarta tace, "gaskiya umaimah banga lefinkiba da kika ruɗe akan guy ɗinnan dan ya haɗu" umaimah tace, "hmmm, danma baki ganshi a fili ba, sema kinga yanda yake tafiya gently da yanda yake magana a yangance, ke a taƙaice dai komai nashi abun burgewa ne da ban sha'awa. musammanma, yanda yake nunawa matarsa soyayya yafi komai ƙara tsundumani a kogin sonsa, har hangoni nake kwance a kan faffaɗan kirjinnannsa nima yana bani kulawa, wayyo ranar senayi kuka dan murna" wani banzan kallo farida tayiwa umaimah a fakaice kallon baki da hankali sannan tace. "Shawarar dai danake baki a kullum ita zan ƙara baki idan zaki ɗauka to" umaimah kamar zatayi kuka tace, "inason gwada abunda kike faɗamun amma kuma ina tsoron kar kwabata tayi ruwa" farida ta tabe baki tace, "babu wani ruwa da kwabarki zatayi, wannan abun danake faɗa miki shine kawai mafita a gareki. Domin idan baki saniba ki sani, mazan yanzu yan iskane idan bada hakanba ba'asamun zuciyarsu bare ma ke kinga ke kike sonsa shi baya sonki....." Mahaifiyar farida ce ta shigo ɗakin tana duban umaimah tace, "umaimah anzo ɗaukarki fa" umaimah tace, "to mama bari na fito" jakarta ta ɗauka ta yafa mayafinta ta sauka daga kan gadon tace "to kawata nizan wuce, ammi tace karna jima semunyi waya" Farida itama ta mike tana faɗin, "muje intaka miki" har gurin motar farida ta raka umaimah sukayi sallama umaimah ta shige motar suka tafi. Wani murmushin mugunta farida tayi bayan wucewar su umaimah, tana sane ta bata guguwar shawarar datasan bazata fishshetaba, tun kafin taga hoton mustapha taji kawai tana ƙyashin umaimah ta mallakesa, yanzu kuma data ga hotonshi setaji bata da wani buri a duniya daya wuce itama ta mallakesa a matsayin mijinta, domin babu ƙarya guy ɗin ya haɗu ƙarshen haɗuwa......✍️ *By* *Zeey kumurya* *ABINDA KASHUKA....!* _*BY*_ _*ZEEY KUMURYA*_ *6️⃣8️⃣* *Bismillahirrahmanirrahim* .......... Umaimah suna tafiya a mota tana tunanin maganganunsu da farida, da kuma shawarar datake bata a kodayaushe akan Mustapha, duk da tsananin so da kaunar datakewa mustapha bazata iya tunkararsa da wata mu'amala ta banza ba, saboda hakan ba dabi'arta bane kuma ko ba don haka ba, bataga fuskar dazata iya tunkarar mustapha da wani zance na banza ba, mutumin da ko gaisuwarta seyaga dama yake amsawa ta ina zata iya tunkurarsa da wannan abun...... Bayan fitar umaimah ba jimawa Aunty zuhura ta shigo falon, bayan tayi sallama na amsa mata ta dubeni tace, "mamana ya jikinnaki?" A hankali nace, "da sauƙi" tace, "Allah ya ƙara sauƙi, dazu kuma nace miki zan dawo ban dawoba, aiki ne yamun yawa kinsa yau ni kaɗai ce" nace, "babu komai Aunty zuhura ainama warke" tace, "dama abu zan baki, amma idan babu damuwa yanzu kibini part ɗina sena baki" tashi zaune nayi ina ɗan yamutsa fuska nace, "ok muje to, amma bari na miƙawa ammi wayarta" tace, "to" ammi tana haɗa kaya na shiga ɗakin, bayan nayi sallama nace, "ammi sannu da aiki" tana dubana tace, "yawwa ɗiyata, ya jikinnaki dai" nace "naji sauƙi sosai ammi" ammi tace, "to Allah ya ƙara sauƙi, kindaici abincin ko?" "A'a banciba amma zanci kafin na kwanta." Na fadi haka ina miƙa mata wayarta. Karba tayi tana faɗin, "har kin gama wayar?" Nace, "A'a taƙi shiga may be network ne" ammi tace, "ai haka yake dama wani lokacin, kema yakamata noor ya sai miki waya, na rasa meyake jira har yanzu yaƙi sai miki" murmushi nayi kawai na juya fita. Magungunan mata Aunty zuhura ta bani, dana sha, dana tafasawa a shiga ciki, dana tsugunno" na karba a kunyace na mata Godiya na koma part ɗina. Adanasu nayi a kitchen, inayin sallar isha'i na tsakuri abinci naci kaɗan nasha maganin ciwon kai, dan har lokacin kan na ɗan saramun. da kyar na iya watsa ruwa saboda yanda nake jin jikina, ina fitowa na shafa mai da turare sama_sama, na zira wata rigar bacci na haye gado na kwanta, ba jimawa bacci ya ɗauke ni..... Mustapha tun yamma da Maryam ta tafi part din ammi yake aiki a system ɗinsa, jibi su daddy zasu dawo daga Saudiyya shine daddy'n ya bashi wani aiki yanaso ya kammala masa kafin su dawo, seda aka kira sallar magriba ya ajiye ya tafi masallaci, be ƙara dawowa gidan ba seda tara na dare ta wuce. Time ɗin daya dawo maryam tana ɗakinta tana wanka, be mayi zaton ta dawo ba, saboda sanda zata tafi part din ammi ce masa tayi acan zata kwana. ɗakinsa ya shige shima a ɗan gajiye yake hakan yasa ya rage kayan jikinsa ya faɗa toilet. Bayan ya fito ya shirya cikin wata jallabiya brown colour, wadda ta masa kyau sosai se tashin daddaɗan kamshinsa yake. wayoyinsa ya kwasa guda biyu a hannu ya fito ya fice daga part din gabadaya ya nufi na ammi domin yakirawo maryam. Umaimah ce kaɗai zaune a falo tana cin abinci, yau da yunwa ta wuni saboda ɓacin rai seyanzu da taji yunwa ta kusa kasheta shine tana dawowa ta sauka akan abincin. Yana turo ƙofar tun kafin ya shigo daddaɗan kamshinsa ya fara kai wa hancinta ziyara, lumshe madaidaitan idanta tayi tana ƙara bubbuɗe kofofin hancinta yanda zata shaki kamshin yanda yakamata. sallama yayi babu yabo ba fallasa. Umaimah ta gyara zama tana tattaro nutsuwarta ta buɗe idonta ta sauke akansa cikin iyayi da neman suna ta amsa masa sallamar ta ƙara da faɗin, "yaya NOOR sannu da zuwa, ina yini" beko kalli inda take balle ma ya nuna yasan da zamanta a falon ya nufi ɗakin ammi ganin bata falon ita da wadda yazo nema. Ita kuma sakarya ta bishi da kallo baki buɗe. kamar koyaushe baya shiga ɗakin ammi se yayi knocking, yanzunma knocking din yayi. Ammi dake tsaye a gaban madubi tana fesa turare ta ajiye turaren ta nufi kofar ta buɗe. Sallama yayi cikin sanyin murya, ammi amsa masa tare da bashi hanya ya shigo cikin ɗakin. Ammi tana k gyara kayan kan mudubinta tace, "inata jiranka tun dazu ka shigo najika shiru har ina shirin kwanciya" yace, "kwanciya kuma da wuri haka ammi?" Ammi tace, "ehh na gajine yau baccin wuri zanyi" yace, "ayya sannu" ammi ta amsa da "yawwa, ta ƙara da faɗin. "Yaushe daddynka ze dawo ne, dazu munyi waya da uncle ɗinka yacemun yau yaje sun haɗu, harma daddy'n yace masa a cikin week ɗinnan zasu dawo." Mustapha yace, "jibi yace mun zasu dawo" ammi tace, "Allah yakaimu lafiya, kukuma se yaushe zakuje?" Yace, "Ran laraba insha Allah, amma ni kaɗai zani" ammi ta juyo ta dubeshi tace, "kai kaɗai kuma banda Maryam?" yace, "ehh" atakaice. Ammi tace, "shikenan, dama naji tana za'ayi bikin kawarta a cikin watannan seta biya ta dubashi idan taje" bece komai ba, saboda shi sam bayason wata alaƙa dazata ƙara haɗa Maryam da Sadik. ammi ta nufi kofa ta fita batare ta ƙara ce masa komaiba. wayarsa dake hannunsa ya shiga latsawa yana jin zuciyarsa babu daɗi. Ammi da plate ɗin abinci ɗauke a hannunta ta dawo ɗakin, agabansa ta ajiye tana faɗin "NOOR sakko kayi dinner" yamutsa fuska yayi bece komaiba ya sakko ya zauna a saman carpet din bakin gado, yasan ko yace baze ciba, ammi seta tursasashi. Ammi taga yanda yayi da fuska tayi kamar bata ganiba, tasan yanda taga ransa a bacennan ba ƙaramin aikinshi bane ya kwanta beci abincinba, shiyasa bazata barshi ya tafi ba seya ci abincin ko kaɗanne. dawowa ɗakin ta ƙara yi dauke da ruwa da ƙaramin cup ta ajiye a gabanshi tana kallon fuskarsa, shima kallonta yake cike da tsananin kaunarta. Hannunta ya kama ya sumbaci tafin hannunta, a hankali yace, "thanks UMMUNAH" murmushi kawai ammi tayi batace komaiba, zama tayi a kusa dashi tana kallonshi cike da so da kauna. A hankali ya fara cin abincin cikin nutsuwa kamar bayason ci bayan yayi bismillah. kaɗan yaci ya ajiye spoon din ya rufe abincin ya dakko ruwa ya tsiyaya ya sha. A fili ya furta "Alhamdulillah" mikewa yayi ya ɗauki wayoyinsa yayiwa ammi sallama ya tafi. ammi tayi murmushi bayan ya fita, komai idan mustapha yana yi se taga kamar midibbontane, komai nasu iri ɗaya ne sak babu ta inda Mustapha ya bar mahaifinsa seta yanda yake kallon abu da yanayin idanuwansa shine kawai ya dakko na ammi. abincin ta ɗauka ta fice dan ta kai kitchen tana jin zuciyarta babu daɗi itama, saboda tuno tsohon mijinta datayi......... Mustapha yana shiga part ɗinsu ɗakin Maryam ya nufa direct, tunda beganta a part din ammi ba yasan tana ɗakin. ɗakin dulum babu haske ko kaɗan, yana mamakin yanda take bacci a haka bata barin hasken ko kaɗan. Torch light din wayarsa ya kunna ya haska kan gadon. tana ƙudundune kamar koyaushe kamar wadda take kwanciya a tsorace ta dunkule guri ɗaya. A hankali ya ƙarasa kan gadon ya haye yana ƙara haskata. Blanket din data rufa ya janyeshi daga jikinta a hankali juyi tayi ta matso daf dashi hannunta ɗaya ta ɗora akan cinyarsa tana sauke numfashi taci gaba da baccinta hankali kwance, fuskarta ya haska sosai kifkifta ido ta fara yi saboda haske mata idon da yayi. Ajiyar zuciya ya sauke, ya ɗauke idonsa daga kallon fuskarta. Blanket din ya janye gaba-daya daga jikinta, ya gyara mata kwanciya, yana yin komai cikin dauriya ne, amma tuni ya fara neman nutsuwarsa ya rasa saboda rigar jikinta shara_shara take, kuma duk ta dage sama santala_santalan cinyoyinta duk suna waje. ga kamshin jikinta dake ƙoƙarin hargitsa masa lissafi. kwanciya yayi a gefenta ya janyota jikinsa yana sakin ajiyar zuciya tare da lumshe idonsa, blanket yajanyo ya lullube musu rabin jikinsu. Maryam se ƙara manne masa jiki take, kanta ya ɗora akan hannunsa guda ɗaya, ɗayan kuma ya fara yawo dashi a jikinta yana shafa lallausar fatarta me sulbi yana sakin numfashi a hankali a hankali cikin jin daɗi, Maryam kuwa jitayi tamkar susa yake mata baccinma se ya ƙara mata daɗi. seda ya shafeta san ransa amma a hankali yadda bazata tashiba sannan ya kyaleta badon yasoba, se dan karya wuce gona da iri ya kai matakin dabaze iya hakura da itaba. rungumeta yayi tsam ajikinsa kamar ze maidata ciki, addu'a ya tofa musu bajimawa bacci ya ɗaukeshi..... *MOMMY* Yau da wani a zababben ciwon kai tatashi ko idonta dakyar take iya buɗewa, shine dalilin dayasa ba fita dan fara shirin tafiyarta Landon ba, a daren jiya bata samu ishashshen bacciba saboda tunane_tunane data dingayi. Haka ta wuni kwance akan gado tana juyi saboda kannata kamar ze tsage gida biyu haka take jinsa. Se bayan la'asar ta samu ya ɗan sassauta mata harta kira likitanta ta zo ta dubata. Magunguna ta rubuta mata, ta kuma ce mata ta rage yawan damuwa domin a halin yanzu jininta ya hau sosai. Megadinta ta bawa takardar da Dr. Ta rubuta mata magungunan ya siyo mata a wani pharmacy, shine da tasha ta samu bacci ya ɗauketa..... _*BAYAN KWANA UKU*_ Tattali sosai mustapha yake nunawa Maryam, kodayaushe yana gida manne da ita yana bata kulawa, sallah ce kawai take fitar dashi. maryam kuwa se taɓararta take zuba masa son ranta kusancinsu na ƴan kwanakinnan ba ƙaramar shakuwa ya haifar a tsakaninsu ba, wanda su kansu basu gane hakanba. Kullum tare suke kwana manne da juna, amma Mustapha be ƙara yiwa Maryam komaiba saboda yadda take a tsorace da shi, kullum idan zasu kwanta a ɗari_ɗari take, duk abunda take yana sane da ita, kyaleta kawai yayi tagama abunta. Maryam tama manta da magungunan da zuhura ta bata, bata amfani dasu. lalle kawai take tafasawa tana tsarki dashi safe da dare, se ruwan ɗumi da datake tsarki dashi parmanantly. Taji sauƙin jikinta sosai, yanzu batajin komai na ciwo a jikinta ta koma normal kamar da. Yau talata gobene kuma mustapha ze tafi Kano dubo Sadik jiya monday suka dawo, maryam batamasan da tafiyar tasaba har yau dan be faɗa mata ba. Yau mustapha ya fita kasuwa tun safe, Maryam setaji gabadaya yau bata jin daɗi a cikin zuciyarta, gashi kuma se dare suke dawowa. Bayan sallar la'asar ina zaune a falo na ina karatun Al_Kur'ani megirma. kamar a mafarki naji kamshin turarensa ya cika falon, dago da kaina nayi da sauri na kalli bakin kofa, shine ya shigo bakinsa ɗauke sallama. cikin tsananin farin cikin ganinsa na amsa masa, sannu da zuwa na masa ya amsa ya wuce ɗakinsa. rufe Alkur'anin nayi na ajiyeshi a gefen darduma sannan na mike na nufi kitchen na dakko robar ruwa guda ɗaya tare da ƙaramin cup na nufi ɗakinnashi, yana zaune a bakin gado ya cire takalmin kafarshi, yana cire rigar jikinshi na shiga ɗakin. "Slm alkm" na faɗa cikin sanyin ina satar kallonshi. batare daya kalleniba ya amsa. Ajiye ruwan nayi na gabansa na koma gefensa na zauna, kallon ruwan yayi ya kalleni. ɗan zamowa nayi daga kan gadon danake na buɗe robar na tsiyaya masa ruwan na miƙa masa. karba yayi tare da furta "thanks" a hankali. tass ya shanye ruwan, ya tambayeshi a karo masa ya girgizamun kai alamar a'a. bance komaiba na ɗauki ruwan da cup din na fito falo bin bayanta yayi da kallo harta fice, ajiyar zuciya ya sauke ya ƙarasa cire kayan jikinsa ya faɗa toilet. ban koma dakinnashiba bayan na ajiye ruwan zama nayi a falo ina tunanin rayuwa. Se wajen ƙarfe 6 ya fito daga ɗakin cikin shirinsa na ƙananun kaya, kallonsa nake ta ƙasan ido yamun kyau sosai, kowanne kaya yasa amsar jikinsa suke kamar danshi aka yosu dama can, gashin kannannasa yasha taza ya kwanta abun sha'awa, dama shi bama'abocin saka hula bane koda yasa manyan kaya. kasarowa cikin falon yayi ya zauna a kusa dani, lumshe idona nayi saboda daddaɗan kamshinsa daya cikamun hanci. A hankali batare dana buɗe idonaba nace, "in kawo maka abinci?" "Later" ya faɗa yana ɗaukar remote ya kunna TV ya fara kallon Labaran yamma. yanayi yana kallon fuskar maryam data ɗauke masa kai tana kwabe fuska, yasan ko meyasa take hakan murmushi yayi kawai ya shafi gefen fuskarta yace, "yadai? ƴan mata" shagwabe fuska nayi sosai nace, "ina alawata?" ɗan buɗe bakinsa yayi kaɗan yana fito da kyawawan idanunsa waye alamun shock dinnan yace, "oh, sorry namanta ne" kallonsa nayi na ɗauke kai ina turo baki gaba, tun jiya alawar da Aunty zuhura ta bani ta kare, yau tun safe dana tashi naketa bashi sallahun ya siyomun na maimaita masa sau da yawa saboda karya manta,amma seda ya manta. murmushi mustapha yayi ganin yanda tayi da fuska. Janyota yayi jikinsa ya kwantar da kanta akan kafadarshi tare dasa hannunshi ya zagaye bayanta, Ajiyar zuciya na sauke na ƙara lafewa ajikinnasa. A haka muka kasance harya gama kallon. Tashi yayi yacemun zashi gurin ammi daganan ze wuce masallaci, Allah ya kiyaye na masa tare da fatan dawowa lafiya. Tunda ya fito daga part ɗinsu ta hangoshi ta fito ne itama zata fita, ajiyar zuciya ta sauke cikin jin daɗin ganinsa, rabon data ganshi tun jiya da safe, tsayawa tayi cak tana kallonsa. Wani tunani ne ya darsu a cikin zuciyarta akan shawarar da fareeda ta bata, duk tana jin tsananin tsoro amma haka ta ƙarfafa zuciyarta akan ta jarraba kawai kozatayi nasara, tunda tabi duk hanyar da zatabi dan ganin yasan da ita amma duk a banza, ita kuma a yanda takejin sonsa acikin zuciyarta da burin datake dashi na auren mijin kece sa'a bazata iya hakura dashiba, dole tayi duk yadda zatayi wajen ganin ta samu gurbi acikin zuciyarsa, ga kuma dama ta samu bazata bari ta kufce mataba. tana ganin ya ƙara kusantota ta tafi da gudu tana faɗin "yaya NOOR oyoyo" tare faɗawa kirjinsa.😳........✍️ *By* *Zeey kumurya* *ABINDA KASHUKA....!* _*BY*_ _*ZEEY KUMURYA*_ *6️⃣9️⃣* *Bismillahirrahmanirrahim* ..........Kamar ta watsa masa garwashin wuta a jiki haka yaji saboda tsabar takaici, da ƙarfin gaske kamar ze ballata ya rabata da jikinsa wani wawan mari ya wanketa da shi, seda jinta ya ɗauke na wucen gadi saboda ƙarfin marin. kamar wata kara ya cillar da ita ta fadi ta baya yayi gaba abinsa yana jin wani irin zafi a cikin ransa. _"wanne irin sakaci yayi da har yarinyar ta rainashi haka_" ya faɗi haka a ranshi danshi a ganinshi wannan ba ƙaramin raini bane. kwafa yayi kawai ya danne ɓacin ransa ya shiga part din ammi. Umaimah da kyar ta yunkura ta iya tashi hannunta dafe da kuncinta cikin tsananin baƙin ciki da kunar zuci, part din mama ta nufa tana hawaye dan fitarma da zatayi gabadaya taji ta fitar mata a rai, kuma bazata iya komawa part din ammi ba dan batasan da idon zata kalleshiba. mama na ɗakinta Umaimah ta shiga falo ta zauna akan kujera tana rusa kuka, haushin fareedah gabadaya ya cika mata zuciya, tunda gashi ta aiwatar da abunda tace ɗin tayi kuma ba'aci nasaraba, yanzu batasan wanne mataki ze ɗauka akantaba akan abunda ta masa....Mustapha sama_sama suka gaisa da ammi, duk da yadda yaso boye ɓacin ransa amma seda ammi ta gane. harta tambayeshi da faɗin "NOOR kana lafiya kuwa?" daga mata kai kawai yayi alamar eh. Ammi bata kuma ce masa komaiba se ido data tsareshi dashi, dan tasan ba haka bane faɗa kawai yayi. seda aka kira sallar magriba ya mata sallama ya nufi masallaci. Bayan anyi sallah mama tataso umaimah a gaba suka zo part ɗin ammi, ammi na kitchen tana ƙarasa girki ita da zuhura taji mama na kwada mata kira. Fitowa tayi tana faɗin "lafiya mama?" Mama ta dubi umaimah dataci kukanta ta koshi tace, "yarki ce na fito na sameta tanata kuka kamar wadda aka ce mata kin mutu, kuma na mata tambayar duniyarnan meyafaru taƙi bani amsa, shine nace bari inzo ko ke kinsan meyafaru" ammi ta dubi umaimah da kyau tace, "Auta meyafaru?" Umaimah ta girgiza mata kai alamar a'a. Ammi tace, "baki da bakine ina tambayarki kina gyada mun kai kamar kadangaruwa" umaimah cikin muryar data ci kuka ta koshi tace,"ba komai" ammi tace, "kukan daɗi kike kenan?" umaimah data fara tsorata da yanda ammi take mata magana tace, "A'a" ammi ta tabe baki tai komawarta kitchen. umaimah ta shige ɗakinta cikin mamakin yanda ammi ta mata, tasan halin ammi zata yi ta tattalinka tana rarrashinta akan abu, amma idan ka isheta seta kyaleka tayi banza dakai. mama tabi ammi kitchen tana faɗin, "dama wai ba daga nan take bane?" Ammi tace, "nifa lafiya kalau muka rabu da ita, zataje gidan zulfa (kanwar mamanta) data kirata tace taje, toni banmasan bata tafiba ashe part ɗinki tayi tana kukan banza." Mama tace, "to me akai mata?" Ammi tace, "wlh mama bansaniba, kwana biyunnan na lura akwai abunda ke damunta bata da aiki sedai ta zauna taita kunci ita kaɗai, na tambayeta, na tambayeta meyake damunta amma yarinyarnan kullum setacemun ba komai shiyasa na watsar da ita kawai" zuhura dake jinsu tayi murmushi kawai dan tasan meke damun umaiman. Mama tace, "ikon Allah, to ko dai rashin auren dabatayi bane ya fara damunta yanzu?" Ammi tace, "Rashin aure kuma?" mama tace, "eh mana, kila yanzu abun ya fara damunta" ammi ta tabe baki tace, "tasan ze dametan take korar duk wanda yazo da sunan aurannata" mama tace, "ai kinsan yarinta, yanzu kuma ta fara hankali shine abun ze dameta." Ammi tace, "to ai ba damuwa ya kamata ta zauna tayi tayiba, setayi addu'a Allah yakawo mata mijin nagari tayi auran" mama tace, "hakane, Allah ya kyauta" A bakin part ɗin ammi muka haɗu da mama zan fito ita kuma zata fita, gaisawa mukayi cikin fara'a na wuce ciki. har bayan sallah isha'i ina part ɗin ammi, tare muka ƙarasa girki da muka gama muka zauna nida aunty zuhura muna hira. umaimah ce ta fito daga ɗakinta bata kalli kowa a cikinmu ba ta wuce ɗakin ammi. Ammi na toilet tana wankewa umaimah ta shiga, har toilet din umaimah ta bita, tsayawa tayi a bakin kofa tace, "Amminah sannu da aiki" fuska babu walwala ammi tace, "yawwa" umaimah ta ƙarasa cikin toilet din tana faɗin "ammi kawo na tayaki" ammi tace, "barshi" a taƙaice. umaimah jiki a sanyaye ta koma ɗaki ta zauna a ƙasa ta dafe kuncinta da har yanzu take jinsa wani dimmm saboda marin datasha. 5 minutes later ammi ta fito, bata ko kalli inda umaimah takeba ta nemi guri ta zauna a bakin gado ta mike kafarta cikin gajiya. umaimah tatashi ta hau kan gadon, kwantar da kanta tayi a jikin ammi cikin shagwaba tace, "Amminah dan Allah kiyi hakuri kidena fushi dani, wlh bana iya jurar fishinki ko kaɗan" ammi ta harareta tace, "me kikamun dazanyi fushi dake" umaimah tace, "kiyi hakuri dai amminah Please" ammi ta sauke numfashi tace, "to naji, meke damunkine kwana biyunnan? kinsan dai bazan juri ganin ki a haka ba cikin damuwa" umaimah ta kama kame_kame ta rasa me zata cewa ammi. Ammi ta mata wani kallo tace, "Aure kike so ko umaimah?" gaban umaimah ne ya yanke ya faɗi ganin ammi ta ramkota, tabbas a yanzu babu abinda takeso sama da taga tayi aure. ƙasa tayi da kanta batace komaiba kwalla na cika mata ido. Ammi ta ɗan sassauta murya tace, "ki faɗamun mana daughter idan baniba waza ki faɗawa" umaimah ta ƙara rungume ammi tace, "Eh" tana sakin kuka ammi ta dubeta cike da tausayawa tace, "to ai ba kuka yakamata kiyiba, ko kuma kiyita kunci ba addu'a zakiyi Allah ya kawo miki mujin kiyi auren..." faɗa ammi tashiga yiwa umaimah sosai akan korar samari data dingayi a baya, ta faɗa mata. "Itafa rayuwa komai yazo maka a matsayin kaddararka karba kakeyi hannu bibbiyu, idan kace dole bazakayi aure ba, seka samu irin mijin da zuciyarka takeso zaka mutu bakayi aureba ballema ita umaimah data tsawwala akan yanda takeso mijin dazata aura ya kasance zeyi wuya ta samu, yanzu gashi ta doshi kusan shekara 30 a gida babu auren babu manemi, tunda manemanma yanzu babu, dama ita mace ai lokaci gareta, idan ta kai wani munzalin samarin ma ɗauke ƙafa suke" nasiha dai sosai ammi ta mata, umaimah harda kuka, ammi ta rarrasheta tace ta dage da addu'a kawai. umaimah kamar ta faɗawa ammi son mustapha ne ke damunta, amma dai ta daure bata faɗa matanba. Se wajen ƙarfe tara na bar part din ammi da abincinmu. Key ɗin hannuna nayi amfani dashi na buɗe part din. A kan dinning na ajiye abincin na wuce ɗakina nayi wanka nayi shirin bacci, abinci kawai yaragemun naci. falo na dawo na duba agogo naga har 9:32 pm. nayi mamaki sosai danaga har yanzu yaya be dawo ba, dan yanzu anayin sallar isha'i yake dawowa. ina ƙoƙarin komawa ɗakina ya shigo falon, ajiyar zuciya na sauke cikin jin daɗi. da fara'a na juyo na kallesa, yanda yayi sallama acici fuskarsa babu walwala se jikina yayi sanyi. Mustapha ɓacin ran umaimah be bar zuciyarsa ba har yanzu, amma ganin maryam da yayi se yaji zuciyarsa ta ɗan sanyaya. zama yayi akan kujera yana fesar da numfashi tare da lumshe idanunsa. "Sannu da zuwa" na faɗa cikin sanyin murya ina takowa zuwa inda yake. beko motsaba balle ya amsa. sosai naji babu daɗi a cikin zuciyata, nima ban ƙara cewa komaiba na nufi kitchen na ɗauko mana plate da spoon, abincin na zuba mana mu biyu saboda a kwanakinnan tare muke cin abinci shiyasama tun dazu banciba na tsaya jiranshi. A gabanshi na ajiye na dakko mana ruwa da juice da glass cups duk na ajiye. zama nayi a ƙasan na dubeshi nace, "yaya ka sakko muci abinci" Buɗe idonshi ya yayi ya kalli abincin a hankali yace, "kici kawai" kallonsa kawai na tsaya inayi cike da mamakinsa yanda yake mun yau, na lura amma ransa a bace yake. Cikin lallami nace, "dan Allah kayi hakuri ka sakko muci, Ni bazan iya ci ni kaɗai ba" shiru yamun kamar bejini ba. tashi nayi da nufin naje na kwanta dannima banajin zan iya cin abinci yanda nake jin zuciyata babu daɗi a sanadiyyar halin dana ganshi a ciki. Caraf naji ya riƙo hannuna ya maidani na zauna. A hankali ya zamo ya sakko shima daga kan kujerar ya zauna daf dani, batare daya kalleniba ya janyo kwanon abincin gabansa ya buɗe yasa spoon ya ɗiba ya kai bakina. kauda kaina nayi hawaye na zubomun da bansan dalilinsuba. Runtse idansa yayi zuciyarsa na masa ɗaci ganin hawayenta. maida abincin daya debo yayi cikin plate ya ja numfashi ya fesar, buɗe idonsa yayi ya kalleta hawayen take ba kakkautawa. "Ya Salam" ya furta a fili yana janyota jikinsa. Aransa yana mamakin saurin kukanta, kukanta har yayi yawa. Dan yatsansa yasa yana share mata hawayen fuskarta, shiru nayi na bar kukan ina sauke ajiyar zuciya dama abunda nakeso kenan najini a jikinshi. bece komaiba ya gyara mata zamanta akan cinyarsa, abincin ya debo ya ƙara kaiwa bakinta. buɗe bakina nayi a hankali ya zubamun. seda na cinye ya ƙara debo wani ze samun a baki nace masa, "kaima kaci" girgizamun kai yayi yace, "am ok" gimtse bakina nayi na turoshi gaba. bakina ya ƙara kai spoon ɗin yana tsuke fuska tare da mun wani kallo, ba shiri na buɗe bakin ya zubamun, da kanshi ya ciyar da ita, seda ya tabbatar ta koshi sannan ya kyaleta bayan ya bata ruwa da lemon juice tasha. Tashi nayi daga jikinshi na ɗauke sauran abincin na kai kitchen, kafinna fito harya wuce dakinshi. Ɗakina na wuce nima nashiga toilet nayi brush. Harna kwanta na tuna da wani sako da ammi ta bani nabashi dazu, banmasan meneba, abu nedai a cikin leda. ɗauka nayi na nufi dakinnashi. yana zaune yana operating system akan gado ta shigo ɗakin da sallama. batare daya dago ba ya amsa mata. ajiye ledar nayi akan locker nace, "ga saƙo, ammi tace na baka" dagowa yayi ya zuba mata lumshashshun idanunshi bece komaiba se ya kutota da yayi da hannunsa alamun ta ƙaraso. A hankali na taka na hau kan gadon na zauna a gefensa. har lokacin kallonta yake yana jin wani abu na yawo acikin zuciyarsa game da ita. kuncinta ya shafa yace, "Sarkin rigima, waya taɓoki?" kirjinshi na nuna da hannuna ina kwabe fuska. waro ido yayi yanajin wani nishadi a cikin ranshi kasancewarsu tare wanda harya mantar dashi ɓacin ran da umaimah ta sakashi. yace, "Ni kuma?" gyada masa kai nayi alamar Eh. fuskarsa ya matso da ita daf da tawa yace, "me nayi kuma?" lumshe idona nayi nace, "baka siyomun alawataba kuma kakicin abinci, kuma se ɓata ranka kake kana...." haɗe fuskokinmu dayayi guri ɗaya yasa na haɗiye zancena batare dana shiryaba bugun zuciyata na sauyawa. karan hancinsa yake gogawa akannata a hankali, kusan 40 seconds suna haka, kafin janye fuskarsa daga tawa yana sauke numfashi a hankali yace, "zan siyo miki sweet ɗinki insha Allah gobe idan naje Kano" "Kano kuma?" Na faɗa cikin mamaki ina buɗe idona. dagamun girarsa yayi alamar eh. marairaicewa nayi nace, "amma tare zamu tafi ko?" "Why" ya tambayana yana kallon cikin idona nace, "Ina son ganin gwaggo" ɗauke idonsa yayi daga kanta ya maida kan system ɗin sa, ba haka yaso ji daga garetaba. girgiza kai yayi alamar a'a. kalar tausayi nayi sosai domin harga Allah inason zuwan nace, "Please yaya kaje dani" yace, "zakije amma ba gobe ba" kamar zanyi kuka nace, "nidai gobe dan Allah" shiru ya mata, dama yasan indai yace mata zashi kano setace zata bisa. kashe laptop din yayi ya tureta gefe. kawar da zancen tafiyar yayi da faɗin "daddy yana gaisheki" nace, "ina amsawa, waya kukayi?" dagamun kai alamar eh. "Kakiramunshi nima mugaisa tunda nazo garinnan bamu taɓa wayaba" "dare yayi yanzu, ki bari idan naje gobe zan haɗaku a waya" shawabe fuska nayi sosai nace, "dan Allah katafi dani yaya, nayi missing Kano sosai Allah" kwanciya yayi ya janyoni jikinsa yana shafa bayana yace, "ammi tacemun za'ayi bikin freind ɗinki a mont dinnan ki bari time ɗin sekije." cikin shagwaba nace, "Ni dai zan bika goben" yace, "sedai ki zaba ɗaya, idan kika bini gobe bazaki bikin ba kinyarda?" shiru nayi na fara ƙoƙarin tashi daga jikinshi, maidani yayi yasa hannunshi duka biyu ya zagaye bayana. Mutsu_mutsu tafarayi a jikinshi ta saki kukan zallar taɓara kukan da babu ko digon hawaye. bakinsa ya kai saitin kunnenta ya fara hura mata iska yana shafa ƙananun kitson kanta. Lumshe idona nayi ina ƙara cusa kaina cikin kirjinsa ina shaƙar daddaɗan kamshinsa........✍️ *By* *Zeey kumurya* *ABINDA KASHUKA....!* _*BY*_ _*ZEEY KUMURYA*_ *7️⃣0️⃣* *SUBSCRIBE* _DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV_ https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ *MARUBUTA DA MASU SON ZAMA MARUBUTA DA WANDA SUKE BUƘATAR MENTOR😍📚✍🏻* _ASSALAMU ALAIKUM_ _AMINCIN ALLAH DA RAHAMAR SA SU ƘARA TABBATA GA ANNABI MUHAMMAD (S.A.W)_ 1. MARUBUCIYA CE KE, BAKI SAN YAYA ZAKI FIDDA LABARIN DUGU KO GAJERE BA..? 2. SHIN KINA SON KIYI LITTAFIN SIYARWA KINA TSORO ZA'A SIYA KO A KA SIN HAKA...? 3 MARUBUCIYA CE KE,AMMA HAƊA LABARI YANA BAKI WAHALA,SANNANA IDAN KIN FARA LABARIN NA SAURIN YAKE MAKI...? 4. KIN DAƊE KINA RUBUTU NE AMMA HAR YANZU LITTAFANKI BASA KARƁUWA WAJAN MAKARANTA...? 5. MARUBUCIYA CE KE? AMMA KINA DA MATSALA WAJAN RUBUTUNKI,KINA BUƘATAR WACCE ZA TANA GUIDE NAKI WAJAN RUBUTU, MA'ANA KINA BUƘATAR MENTOR...? 6. A MATSAYIN KI MARUBUCIYA KINA DA MATSALA NE? AMMA KINA TSORAN FAƊAR MATSALAR KI SABIDA GUDUN WULAƘANCI...? 7.MARUBUIYA CE KE, AMMA BAKI SAN YADDA ZA KINA AMFANI DA, WATTPAD, TELEGRAM, FACEBOOK,OKADA BOOKS BA...? 8. MENE MATSALAR KI A RUBUTU? TSARA LABARI? ƘA'IDOJIN RUBUTU,SANIN AL'ADUN YARUKA DABAN DABAN? 9. KINA SHA'AWAR RUBUTA LABARIN FILM MA'ANA YADDA AKE RUBUTA SCRIPT? KO KUMA KINA SHA'AWAR RUBUTA DRAMA? 10. AT THE END KINA SHA'AWAR RUBUTA LITTAFIN YA ƘI NE AMMA BA KISAN YAYA AKE BA..? *GABA ƊAYA MARUBUTAN MU WANNNAN DAMA CE A GAREKU GA DUKKAN WANDA YA KESON SHIGA WANNAN ƘUNGIYA KO NACE GROUP ,BAWAI ƘUNGIYA CE WACCE AKE RUBUTU A ƘARƘASHIN TA BA, A'A WANNAN HAƊAKA NE, MAGANA DAI GROUP NE NA TAIMAKON JUNA DA BAWA JUNA SHAWARA,KO DA KINA DA ƘUNGIYA ZAKI IYA SHIGA WANNAN GROUP ƊIN MAI TAKEN* _*ELEGANT ONLINE WRITER'S*_ *GROUP NE DAYA SHIRYA TSAF DOMIN TAIMAKON ƳAN'UWA MARUBUTA DA KUMA MASU SHA'AWAR ZAMA MARUBUTA* _GA DUKKAN WANDA YAKE SHA'AWA MUNA DA TSARE TSARE DABAN DABAN SANNAN KUMA AƘWAI FORM DA ZA'A BAKA KA CIKE,BAWAI HAKA KAWAI ZA'A SAKA MUTUM BA MAI SON SHIGA WANNAN GROUP ZAI IYA TUN TU ƁAR WA ƊAN NAN NUMBOBIN KAMAR HAKA. 1. 08069224458 2. 09066710753 3.08167120325 SANAWAR DAGA SHUGABANNIN GROUP ƊIN NA EXCO *ELEGANT ONLINE WRITERS.* *Bismillahirrahmanirrahim* ........Bacci me daɗi ne yayi awun gaba da maryam cikin kankanin lokaci. A jiyar zuciya ya sauke jin saukar numfashinta alamun bacci take. a hankali ya lallaba ya janyeta daga jikinsa ya kwantar da ita a gefensa. filo yasa mata tare da gyara mata kwanciya ya tofeta da addu'a. tashi yayi zaune yana jin kamar kar ya matsa daga kusa da ita. Fuskarta ya kurawa ido cikin wani irin yanayi kamar me son gano wani abu a fuskar. a wani ɓangaren kuma sosai ta masa kyau yanda take yin baccin, zara_zaran gashin idonta sun kwanta har ƙasan idonta abun sha'awa, bakinta ya kalla yayi murmushi ta ɗan turoshi gaba kamar kodayaushe idan tana bacci. ɗan yatsansa yasa a hankali ya shafi pink lips ɗinta cikin sauƙi, kamar ya zugata ta ƙara turo lips ɗin gaba, hakan da tayi ba ƙaramin kyau ta ƙara masaba yana son yaganta cikin yanayin shagawa shiyasa some times yana sane yake tabota, amma bayason kukanta ko kaɗan. wayarsa dake gefensa yasa hannu ya dakko, kunnawa yayi ya shiga Camera ya fara ɗaukar face ɗinta a hoto, kala uku ya mata pics din, kuma tayi kyau sosai a hoton murmushi yayi ya ajiye wayar, blanket yasa ya lullubeta sannan ya sauka daga kan gadon. Toilet ya fara shiga yayi wanka, bayan ya shirya cikin fararen kayan bacci masu taushi ya fita zuwa falo. kitchen ya shiga ya haɗa cofee ya yasha. Light din falon da ɗakin maryam dana kitchen din ya kashe ya koma ɗakinsa. seda ya ƙara duba wani abu a laptop dinsa sannan ya kashe musu light din ɗakin ya hau gadon ya kwanta shima. janyota yayi jikinsa yana sakin ajiyar zuciya, sosai yake cikin buƙatuwa da ita, amma wani tausayinta yakeji danshi kallon yarinya ƙarama yakewa maryam, a ganinsa idan ya fiya takura mata kamar da matsala, lumshe idonsa yayi kawai ya ƙara mannata a kirjinshi kamar ze maidata ciki, mutsu_mutsu Maryam ta farayi hakan yasa ya sassauta mata riƙon daya mata ya shiga shafa bayanta, shiru tayi taci gaba da baccinta, shikam ya ɗan jima kafin bacci ya daukesa..... Washegari, Bayan anyi sallar asuba Maryam ta shiga gyaran gida mustapha kuma ya koma baccinsa. Bayan na gama gyaran gidan na koma ɗakina nayi wanka na shirya cikin wata doguwar rigar a baya dark blue, an mata ado da Stones masu sheki da walwali a gaban rigar da kasan hannunta. Ribbom nasa na daure gashin kaina, wata hula nasaka me kyau Black colour gaban hular me V ne, hakan yasa gaban kitsona ya fito se yayi kyau sosai, kwalli kawai nasa da white lipstick me ɗan ɗanƙo, se barima da na sa a kunnena. amma ni kaina nasan nayi kyau. Agogo na kalla naga goma na safe saura 2O minutes, falo na fito da nufin naje ɗakin yaya, kafin na ƙarasa se gashi ya fito cikin shirinsa shima, sanye yake cikin wani milk ɗin yadi me matuƙar kyau da tsada. Kallonsa Maryam take kamar yadda shima ya kura mata ido yana kallonta, tayi masa kyau sosai ze iya cewa ma tunda suke take be bata ganin ta masa kyau irin na yauba, kallon idanunta yayi yanda take kallonsa se yaji gabansa ya faɗi saboda abunda ya gani, sosai ya cika da mamaki mara misaltuwa zuciyarsa na ɗan bugawa ya ƙarasa takowa gareta, daf da ita ya tsaya harsuna jiyo hucin numfashin juna. Ƙasa nayi da idona da sauri murya ƙasa_ƙasa nace. "Ina kwana" be amsamunba se haɓata daya kama ya dago fuskata, lumshe idona nayi da sauri ganin yasaka idonsa cikin nawa bugun zuciyata na sauyawa, numfashi ya furzar a hankali kamar me rada yace, "Please ki buɗe idonki I want see something" bude idonnayi a hankali amma ba'akan fuskarsaba dan bazan iya haɗa ido dashiba. kallon idonta yake sosai da yanda take kallon gefe zuciyarsa nacigaba da bugawa, ya kai mintuna uku yana kallon idonnata, a hankali ya saki haɓartata yana sauke numfashi. shafa gefen kuncinta yayi yana murmushin gefen baki yace, "kinyi kyau" kallonsa nayi da sauri dan be taɓa faɗamun hakaba tunda muke, gira ya dagemun yace, "sosai fa" ƙasa nayi da kaina a hankali nace, "Nagode" cikin tsananin jin daɗi, murmushi yayi ya kama hannuna muka ƙarasa muka zauna akan kujera. Kwantar da kaina yayi akan kafadarsa yace, "me kikeso in siyo miki tsaraba" ya ƙarashe zancen yana haɗe hannuna da dashi. girgiza kai nayi alamar A'a, yana kallon fuskata yace, "why?" nace, "banason komai nidai kawai ka tafi dani dan Allah" wayarsa dake gaban rigarsa ce ta fara vibrate, hakan yasa be bani amsaba ya zarota ya daga ya kara a kunnensa, 3 seconds yace "Wa'alaikumussalam" ya ƙara ɗan jim kafin yace, "ohk ganinan" katse wayar yayi yana duban fuskar Maryam yace, "ki faɗamun me kikeso zan wuce ne yanzu" dago kaina nayi daga jikinsa da mamaki nace, "yanzu zaka tafi?" gyadamun kai alamun eh. Nace, "baka cifa abinci ba" yana bina da wani irin kallo yace, "ehh zanci acan" zan ƙara magana ya tashi tsaye tare kamo hannuna nima ya tadani. Tafiya ya farayi still hannunsa riƙe da nawa, hakan yasa nima na fara binsa kamar raƙumi da alaƙa, a zuciyata ban yarda ko kaɗan tafiyar zeyiba da gaske, saboda babu wata alama data nuna haka , tunda bacin wayarsa banga komai a hannunsaba. a bakin kofa ya tsaya yana kallona ƙasa nayi da kaina cikin wani irin sanyin jiki, ɗayan hannuna ya kama ya haɗe a hannunsa fuskarsa ya matso da ita daf da tawa yace, "zan wuce kimun addu'a" dago da kaina nayi na kallesa kwalla na taruwa a idona cikin sanyin murya nace, "wai dagaske kake tafiya zakayi yanzu?" daga mata kai yayi cikin matuƙar tausayinta, jiyake kamar ya canza ra'ayinsa ya tafi da ita amma akwai dalilin dayasa baze tafi da itanba. hawaye sosai Maryam take yi, rungumeta yayi tsam a jikinsa yana ɗan bubbuga bayanta, riƙe shi Maryam tayi sosai itama kamar me tsoron kar a rabata dashi. sosai yakejin ba daɗi a cikin zuciyars, ga kukanta dake taɓa masa zuciya yanajin kamar tana watsa masa garwashi a cikin zuciyarsa. Sun kai 6 minutes a haka kafin a hankali ya rabata da jikinshi jin tayi shiru se ajiyar zuciya datake saukewa. Hannunsa yasa ya share mata hawayen fuskarta. Idanunta ya kalla yace, "menene?" Girgiza masa kai nayi alamar A'a sannan nace, "Allah ya kiyaye hanya ya kaiku lafiya" "ameen" ya faɗa cikin wata irin murya, yanajin wani abu na yawo acikin zuciyarsa akanta. ƙasa na ƙara yi da kaina, inajin zuciya ba daɗi kamar na fashe da kuka haka nakeji. Kallonta yakeyi tamkar yau ya fara ganinta, kamar ya fasa tafiyar haka yakeji shima, danne duk abunda yakeji a zuciyarsa yayi ya kalli tsadadden agogon hannunsa yaga lokaci, sakin hannunta yayi yace, "bye, kikula da kanki" dago kaina nayi hawayen danaketa ƙoƙarin maidawa suka zubo. Lumshe idonsa yayi ya buɗe, ƙara janyota yayi jikinsa ya share mata hawayen fuskarta yana jifanta da wani kallo, amma bece komaiba. Cikin sanyin murya nace, "yaushe zaka dawo?" "Gobe" ya faɗa cikin wata irin siririyar murya. Ajiyar zuciya na sauke nace, "Allah ya kaimu, ka gaishesu sosai" yace, "zasuji insha Allah" ya ƙarasa zancen tare da kissing forehead ɗina, murmushi nayi na lumshe ido ina ƙara lafewa a jikinsa ina jin tamkar mu dawwama a haka. Shima Mustapha a nasa bangaren haka ne, ga kamshin jikinta daya masa daɗi sosai harya sanya ya fara jin wani irin baƙon yanayi ajikinsa, daurewa yayi ya rabata da jikinsa, gefen fuskarta ya shafa ya fice batare daya yarda ya ƙara kallon idontaba, saboda karta karya masa zuciya. binsa nayi da kallo harya fice daga falon gabadaya, sosai nakejin wata irin kewarsa tun yanzu ta lullubeni, jan ƙafata nayi na faɗa kan kujera na zauna ina sauke numfashi. Mustapha shima jikinsa duk a sanyaye ya nufi part din ammi. A falo ya tarar da umaimah tana mopping tana ganinshi kamar wadda taga dodo ta zura da gudu tayi ɗakinta, tabe bakinsa yayi dan ba ita yakeba ya shiga ɗakin ammi. Ammi na dubansa bayan sun gaisa tace, "bangane tafiya zakayiba yanzu bakaci komaiba, yau bamu tashi da wuri bane shiyasa mukayi late gurin aiki" mustapha ya ɗan ja numfashi yace, "karki damu ammi zanci abinci idannaje can" ammi ta masa wani kallo, batace komaiba ta mike ta fice daga ɗakin. binta yayi da kallo cikin kaunar ta, shi kanshi yana jin yunwar amma yanda zuciyarsa take cike da ɗokin ganin daddy dasu haidar yasa baya ta abincin. Bayan wasu mintuna ammi ta dawo ɗakin hannunta ɗauke da cup data haɗa masa tea me kauri, batace komaiba ta mika masa. ba musu shima ya karba ya fara sha, a hankali yake kurba har yasha sosai, ya ajiye sauran, ammi bata kyaleshi haka ba seda ta bashi dabino me ɗan yawa tace yaci, be cinye dukaba a leda tasa masa sauran tace yaci a hanya. Sallama ya mata ya tafi, bayan ta kwarara masa ruwan addu'a tare da jaddada masa karya manta ya tahowa da Maryam da wayar hannu. daze tafi yana kallon part ɗinsu kamar ya shiga ya ƙara ganin yar matartasa, amma dai ya hakura be shigaba ya nufi inda driver'n ammi yake jiransa tun dazu..... Tunda na zauna nayi jugum ni kaɗai, ƙwaƙwkwaran motsi banyiba, na kusa awa a haka da ƙyar na yunkura na tashi na shiga ɗakina na dakko hijabi na saka na fito zuwa part ɗin ammi. Suna falon duka matan gidan har mama nafisa datayi tafiya dangin mijinta se jiya da daddare ta dawo. danne damuwata nayi muka gaisa da kowa faran_faran nayiwa mama nafisa sannu da zuwa. umaimah se jifan maryam take da wani mugun kallo, ita dai maryam tunda ta gaisheta kota kanta bata ƙara biba. ɗaki ammi ta kaimun abinci tace inje inci, yanda nake jina wani iri abincinma bana son ci, haka dai na daure na cuccusa, duk da hakanma kaɗan naci na barshi.....✍️ _Zaku iya ƙara jina da daddare insha Allah_ *By* *Zeey kumurya* *ABINDA KASHUKA....!* _*BY*_ _*ZEEY KUMURYA*_ *7️⃣1️⃣* *SUBSCRIBE* _DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV_ https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ *Bismillahirrahmanirrahim* ..........Wunin yau gabadaya a ɗakin ammi na yishi, ina ta juyi akan gado ko aiki banyiba. Sosai kewar yaya ta cikamun zuciya, gashi Ni ba wayaba balle na kirashi koshi ya kirani. Bayan sallar la'asar ina zaune akan dadduma a ɗakin ammi, idar da Sallah ta kenan ammi tashigo ɗakin, zama tayi a gefen gado tana dubana tace, "ɗiyata ya kannaki?" _Dayake dazu data tambayeni meke damuna nace mata kaina ke ciwo_ nace "da sauƙi" tace, "to Allah ya ƙara sauƙi, bari na kawo miki abinci kici kisha magani, gobe da safe idan Allah yakaimu da kaina zan kaiki asibiti, wannan ƙananun ciwukan su suke zama babba Allah ya kiyaye dai" nace "ameen" ammi ta ɗauki wayarta tayi dialing number'n mustapha, amma be ɗagaba mikomun wayar tayi tace, "gashi idan yakira ki ɗaga bari na kawo miki abincin. Karbar wayar nayi ita kuma ammi ta fice, number salimat na lalubo nayi dialing, karawa nayi a kunnena jin tana ringing, ringing uku ta ɗaga da sallama. Amsa mata nayi na ƙara da faɗin "Amaryarnan baki da kirki ko kaɗan" dariya tayi tace, "rashin kirkin menayi kuma kawata?" nace, "ko nemana bakyayi, rabon da muyi waya dake tun sallah" saleemat tace, "wlh bahaka bane, kinsan ba wayarki bace banason na kira bansamekiba" nace, "idan kika kira kodayaushe zaki sameni, sedai da daddare ne baza ki sameniba" saleemat tace, "to dama ina Ni ina kiranki da daddare ai nasan lokacin kina...." Katseta nayi da fadin, "naji karkimun iskanci da kika saba, ina ummata?" Umma tananan kalau wlh, ya Jos ɗin?" Nace, "Masha Allah kigaidamun da umma sosai dan Allah, Jos lafiya kalau" saleemat tace, "zataji insha Allah" nace, "saura kwana nawa ne bikin?" Tace, "saura sati huɗu duk da satin bikin" nace, "Allah yakaimu, baki turomun ankon ba to, kar lokaci ya kure na rasa ɗinki" saleemat tace, "ke umma ta sai miki ankon duka, dama guda biyu ne, harta bada a miki ɗinki." Cikin jin daɗi nace, "Allah sarki ummata, ita datake da hidima amma shine harda saimun anko, Nagode sosai Allah yasaka da Alkhairi, ki bata wayar na mata Godiya. Saleemat tace, "ameen, amma ta fita yanzun taje kasuwa, anjima idan ta dawo zankiraki na haɗaku" nace, "to Allah yakaimu, ina gwaggotah" tace, "gwaggo tananan kalau, dazu ma ta shigo da rana" nace, "inason kiranta a waya ko har yanzu bata da wayane?" Saleemat tace, "akwai waya a hannunta bari yanzu zan fita sena karbo miki number ta, naturo Miki" nace, "to Nagode" mukayi sallama na kashe wayar. Ammi ta shigo ta kawo mun abinci da ruwa da maganin ciwon kai, ta tambayi har yanzu be kiraba, nace mata eh. Ina cikin cin abinci wayar ammi ta fara ringing, ni kaɗai ce a ɗakin ammi ta ƙara fita. Ɗauka nayi na duba gabana na faduwa, na ɗauka yaya ne senaga bakuwar number, kamar kar na daga se kuma dai na daga tana daf da tsinkewa. Muryar wadda naji tayi sallama yasani saurin cewa, "gwaggo!" Cikin doki, gwaggo ma a ɗaya ɓangaren cikin fara'a tace, "na'am Maryama" nace, "gwaggo nayi kewarki da yawa" tace "nima haka Maryama, ai bansan ana samunki a wayaba da tuni na karbi lambar na kiraki" nace, "nima gwaggo bansan kinyi wayaba ai, ya jikinnaki?" gwaggo tace, "jiki da sauƙi, amma har yanzu da sanda nake dogarawa nake tafiya" cikin tausayawa nace, "ayya Allah ya ƙara sauƙi, yaushe zakizo gwaggo?" gwaggo tace, "ina son zuwa naganki Maryama ko dan na nemi yafiyarki akan irin cutarwar dana miki, amma ƙafata bazata juri zaman mota ba" nace, "gwaggo dan Allah ki bar wannan zancen, Ni babu abunda kikamun idanma da akwai na yafe miki tuntuni" gwaggo cikin kuka tace, "kayya Maryam da akwai abunda na miki mana, gashinan yanzu tun ba'aje ko'inaba na fara ganin sakayya nasanma kaɗan nagani dan...." "Dan Allah gwaggo kidena faɗin haka karki sani kuka nima, Ni bakimun komaiba" gwaggo tace, "shikenan yar albarka nadena, Allah ya miki albarka, ya baki ƴaƴa nagari kamar ke masu hankali da biyayya, Allah yajikan mahaifiyarki Maryama da yaya Fatima(inna), ya kuma bayyana miki mahaifinki idan yana raye da danginsa" nace, "ameen gwaggo ina su baba Ilya da sauran mutan ƙauyen?" Gwaggo tace, "sunanan kalau, suna yawan zuwa suna dubanima ba subi ta halinaba" nace, "to duk a gaidasu" tace, "zasuji ya maigidannaki?" Nace, "yananan kalau, yau yama taho Kanon" gwaggo tace, "Allah yakawoshi lafiya, dafatan dai komai lafiya" nace "lafiya kalau gwaggo" mun ɗan jima muna hira da gwaggo sannan mukayi sallama, wayar da mukayi da gwaggo ta ragemun damuwar kewar yaya danake ciki, cin abincina nacigaba dayi..... *KANO* Tunda suka shigo Kano yake bin garin da kallo yanajin farinciki na ratsa zuciyarsa, ji yake kamar yayi wasu shekaru rabonshi da Kanon, wata sassanyar ajiyar zuciya ya sauke lokacin da suka shigo katon layinsu ya hango gidansu. Sedai kuma lokaci ɗaya ya tuna wani abu daya dishashe masa farincikin da yake ciki, ba komai ya tuna face mommy. Lumshe idonsa yayi ya jinginar da kansa a jikin kujera yana ɗan jan numfashi. A ƙaton gate din gidan na tsakiya driver'n ya tsaya ya fara danna horn, bajimawa wasu daga cikin masu gadin gidan suka taso suka wangale musu gate din, dama already sun san da batun zuwansa. Buɗe idonsa yayi a hankali jin sun shigo gidan, glass din barin dayake ya zuge ƙasa a hankali, ma'aikatan gidan ya shiga ɗagawa hannu kamar yadda suma suke masa, kasancewar driver'n slowly yake tafiya da motar har sannu da zuwan da suke masa yana ji, parking space suka nufa yana cigaba da bin gidan da kallo, babu abunda ya sauya a gidan tun bayar tafiyarsa har zuwa yau. Zannurain, haidar da faruq da tundazu suke dakon zuwansa a harabar gidan suka nufo gurin motar tasu da sauri zuciyoyinsu cike da ɗoki da son ganin ɗan'uwansu. A hankali ya buɗe murfin motar ya ziro ƙafarsa guda ɗaya, seda ya ɗanyi wasu sakanni sannan ya ziro ɗayar itama, kafin ya fito dukansa daga cikin motar, dai_dai nan su haidar suka ƙaraso gurin, haidar ne yayi sauri ya rigasu ƙasarawa garesa yana dariyar farinciki ya rungumeshi yana faɗin, "welcome big bro" rungumeshi shima Mustapha yayi cikin tsananin farinciki yace, "Thank you dear" suma su faruq rungumeshi sukayi gaba-ɗayansu suna welcoming dinshi, abun gwanin ban burgewa. duka ya haɗa su shima ya rungume cikin jin daɗi da farin ciki mara misaltuwa, da kyar suka sakeshi kowa yana faɗa masa yanda yayi missing ɗinsa, shidai murmushi kawai yake saki yana binsu da kallo, haidar riƙe da hannun damansa zannurain kuma na hagu, faruq kuma yana gabansu suka nufi cikin gidan, bayan sun haɗa driver'n da wani ma'aikacin gidan domin ya kaishi masauki, part ɗin daddy yaga sun nufa dashi. A main parlour suka tarar da daddy zaune shida wasu yan'uwansa har da wata mace cousin din su daddy ce, tun randa su daddy suka dawo tazo gidan, a gidan da aka riƙe Aunty take sunanta Hajiya zuwaira yara kuma na kiranta da mami. Daddy na hango mustapha ya mike ya taryoshi cikin farincikin ganinsa fuskarsa ɗauke da murmushi, Shima Mustapha sakin su haidar yayi, yayi hugging daddy cikin tsananin kewarsa. Daddy yace, "welcome son, dafatan kun ƙaraso lafiya" mustapha na sakin daddy yace, "thank you Dad, mun ƙaraso lafiya kalau" daddy ya shafa kansa cikin tsananin farin cikin ganinsa, yayi matuƙar kewar ɗannasa ba kaɗan ba. daddy riƙe da hannunsa suka ƙarasa cikin falon, gaishe da mutanen falon Mustapha yayi cikin girmamawa, suka amsa masa suma cikin fara'a. daddy se nan_nan yake da mustapha yarasa inda ze sakashi dan farincikin ganinshi. Bayan sun gama gaisawa daddy ya tambayeshi ya su Maryam da ammi, yace masa duk sunan kalau. daddy da kanshi ya masa jagora zuwa bedroom ɗinsa kamar wani bako, mustapha murmushi kawai yake ciki jin daɗin yanda daddy yake masa, a toilet din daddy yayi wanka, kafin ya fito faruq ya kawo masa wasu sabbin ƙananun kaya. Bayan yagama shiryawa yayi sallar la'asar dabe samu yayita akan lokaci ba, ya fito falo inda yatarar an shirya masa lifaya ta abubuwan ciye_ciye dana sha. Mami da kanta ta kama hannunsa ta kaishi har dinning, zama yayi yadubeta yace, "Nagode mami" mami na serving dinshi cikin tausayinshi akan abunda mommy ta aikata masa tace, "bakomai ɗana, ashe haka al'amura suka faru" gyada mata kai kawai yayi alamar eh, danshi bayason ana tuno masa da abunda ya faru abaya. mami tace, "Allah ya kiyaye gaba,ya rabu da mutane masu irin halin Atika, Allah ya rabamu da sharrin makiya" cikin sanyin murya yace "ameen" mami ta tura masa abincin data zuba gabansa tana faɗin, "ya iyalinnaka, Alhaji yace kayi aure" yace "sunanan kalau" mami tace, "Masha Allah, Allah yabaku zaman lafiya da zuri'a dayyiba ya haɗa kanku" yace, "ameen" yana cin abincin mami tana masa hira, harta masa murnar gamuwa da mahaifiyarsa. Bayan ya gama cin abincin daddy ya masa jagora zuwa ɗakin da Sadiq yake. Yana kwance akan gado yana bacci kamar gawa, ya rame yayi baƙi bakadanba. Mustapha tsayawa yayi yana kallonsa cike da tausayawa, kallon daddy yayi yace, "dad wai meke damunsa ne?" Daddy ya sauke dogon numfashi yace, "gashinan dai Son, ciwonnasane dai ankasa gane kansa, a Saudiyyan dai suna masa maganin Islamic, shine jikinnasa yayi kyau haka" jinjina kai mustapha yayi cikin jimantawa aransa yana mamakin abunda daddy yace, akan jikin Sadik duk yanda yaganshi ɗinnan ace wai ahakanma jikin yayi kyau. Kiran sallar magriba ne yafitar dasu daga ɗakin. Bayan sun dawo daga masallaci su haidar suka zagayeshi suna masa hira, shima sakin jikinsa yayi ya biye musu suka sha hira, hakan ya ɗauke hankalinsa be kira ammi ba, ya sanar mata sun sauka lafiya, saidai duk abunda yake tunanin Maryam na nan manne a cikin ransa....... Bayan na gama cin abincin na fita falo muka ɗan taɓa hira dasu Aunty zuhura, har akayi sallar magriba wayar ammi na hannuna ina dakon kiransa amma naji shiru, ammi ma ta tambayeni ya kira nace mata A'a, har akayi sallar isha'i be kiraba. Ajiye wayar nayi zuciyata babu daɗi na kwanta akan gadon ammi, dan anan zan kwana, bacci ne ya ɗaukeni batare dana shirya masaba......... Mustapha be samu kansaba se kusan ƙarfe goma na dare, part ɗinsa na gidan anan ze kwana, daddy yayi zaton tare zasuzo da Maryam shiyasa yasa aka gyarashi tsaf idan sunzo su sauka. yana shiga ɗakin shi ya zaro wayarsa daga aljihunsa, missed call ya gani har 5, na ammi 2 sena Aunty 1 se kuma wata bakuwar number 2. Layin ammi ya kira dan cike yake da kewarsu musammanma yar meronsa. Ammi ta ɗaga wayar da sauri dama tana hannunta, mustapha ya mata sallama ta amsa ta ƙara da faɗin, "NOOR ina shiga ne inata jiranka baka ɗagaba?" Mustapha yace, "babu inda na shiga ammi, muna tare dasu daddy ne banma dakko wayarba se yanzu" ammi tace, "amma kasan ai zan nemeka inji ya kukaje kanon, yanzu hankalina harya fara tashi danaji shiru ina shirin kiran dad dinnakama tunda kai na kiraka baka ɗaga ba, kiranka ya shigo" mustapha yayi murmushi yace, "ayi hakuri Amminah kinsan mun daɗe bamu haɗu ba muna ta hirar yaushe gamo" ammi tace, "shikenan kunje lafiya?" Yace, "lafiya kalau" ammi tace, "Masha Allah" shiru yayi yanaso ya tambayi Maryam amma miskilancinsa ya hanasa, ammi jin yayi shiru tace, "kaje ka kwanta ka huta to, da safe mayi waya" yace, "Allah yakaimu" ammi tace, "Ameen, karka manta fa, idan Allah yakaimu goben kaje kagaida gwaggonta" yace "insha Allahu" ammi ta katse kiran. ajiyar wayar yayi ya rage kayan jikinsa ya shiga toilet ya watsa ruwa, be tsaya yin komai ba ya kwanta saboda gajiyar dake damunsa, lumshe idonsa kawai yayi amma sam bacci yaƙi zuwa, sosai kewar Maryam take damunsa, yanzu daya kwanta kamar an ƙara masa kewartata, ya saba kwanakinnan manne da ita yake bacci yana shaƙar kamshinta dayake matuƙar yi masa daɗi, yana shafa lallausar fatarta, secan dare ya samu bacci ya ɗauke sa bayan yagama juye_juye da rungumar filo.....✍️ *By* *Zeey kumurya* *ABIN DA KA SHUKA....!* _*BY*_ _*ZEEY KUMURYA*_ *7️⃣2️⃣* *SUBSCRIBE* _DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV_ https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ *Bismillahirrahmanirrahim* ..........Washegari haka na tashi sukuku dani kamar mara lafiya, baccinma gabadaya be mun daɗi ba, a daren jiya na farka ya kai sau uku, zuciyata babu daɗi ko kaɗan, kallo ɗaya mutum ze mun ya gane hakan. Gari na fara haske muka shiga kitchen nida ammi, duk dauriyar danake na boye abunda yake raina seda ammi ta gane. Ina cikin ferayar dankali ta dubeni tace, "ɗiyata jikinne dai?" A hankali nace "A'a, aina warke" ammi tace, "ki koma ɗaki ki kwanta, yanzu zuhura zatazo semu ƙarasa aikin tare, idan mun gama sena kaiki asibin" nace, "Toh ammi" na ajiye wukar hannuna na fice, ɗakin ammi na koma na kwanta akan gado. Lumshe idona nayi ina hango yaya a idona cikin matuƙar kewarsa, yanda nakeji a raina kamar bana tare da wani sashi na jikina, Har ƙarfe tara na safe inanan kwance, da naga kwanciyar bazata munba, sena tashi na hau gyaran ɗakin ammi, bayan na gama na fito falo da nufin na gyarashi shima sena tarar da umaimah tana mopping, bance mata komaiba kamar yadda itama naga babu alamar hakan a tattare da ita, ficewa nayi daga falon gaba-daya, umaimah ta raka Maryam da harara tana tabe baki. part ɗinmu na koma dannayi wanka, kafin nayi wankan seda na gyara gidan duk da babu wani datti a cikinsa, na daɗe a ɗakin yaya ina shaƙar kamshinsa dake manne a ɗakin kamar yananan, kamar kar na bar ɗakin haka nakeji, ba dannasoba na fito ɗaga ɗakin na koma ɗakina bayan na gama gyarashi, wanka nayi na shirya cikin sauri saboda nasan ammi tanacan tana jirana zamu asibiti. ina komawa part din ammi na tarar har sungama aikin sun karya, itama ta shirya jirana kawai take. Abinci na debo na faraci a ɗakinta, kafin na gama cin abincin ammi tayi baƙi, Bayan na gama cin abincin na fito falo muka gaisa dasu, mata ne guda uku se kallona sukeyi, ammi ta dubeni tace, "Maryam kinga nayi baƙi, ki bari gobe idan Allah ya kaimu sai muje" nace "Allah yakaimu lafiya" ɗaki na koma na ɗauka comp da kibiya na fara tsifar kaina..... Da ƙyar ya iya tashi yaje masallaci yayi Sallah saboda baccin dake cinsa tunda besamu wani ishashshen bacciba a daren jiya, yana dawowa daga sallah ya ƙara bin lafiyar gado, wayarsa dake gefen kansa ta fara ringing wanda shine yayi sanadiyyar farkawarsa daga baccin. yana yatsina fuska na dakko wayar ya duba, Aunty ce take kiransa kafin ya kai ga ɗagawa har kiran ya katse, bin bayan kiran yayi, ringing ɗaya ta ɗauka tare yin sallama, cikin murya me cike da bacci ya amsa mata yana tashi zaune, ya ƙara da faɗin "ina kwana Aunty" aunty tace, "lafiya kalau Muhammad, bacci kake ne naji Muryar haka?" ɗan gyaran murya yayi yace, "ehh yanzu na tashi" Aunty tace, "Toh ko inbari later mayi maganar?" yace "A'a dama ina son kiranki naga missed call ɗinki jiya" aunty tace "ehh dama inason kamun transfer din kudi ne" yace "ok kamar nawa?" Aunty tace "1.5 ma is ok" aransa yana mamakin me Aunty zatayi da Kudi haka, amma ya danne mamakinsa yace, "ok zantura Miki anjima" Aunty tace "thank you, kana kanonne?" Yace "ehhh nazo tun jiya" Aunty tace "nima a satinnan zan shigo insha Allah" yace "Allah yakawoki lafiya" daga haka sukayi sallama ya katse kiran. jingina bayansa yayi da jikin gado yana lumshe idonsa, Maryam kawai yake hangowa a idonsa, tafiyarta, maganarta da yadda takeyin komai cikin sanyi duk yake tunawa, buɗe lumshashshun idanunsa yayi, wayarsa dake hannunsa ya latsa, pics ɗin daya mata tana bacci ya lalubo ya fara kalla, wani murmushi ne ya subuce masa, yayi missing shagwabarta sosai, yayi 10 minutes yana kallon hotonnata cike da shauki, zooming pic din yayi dai_dai pink lips ɗinta daketa kyalli kamar a zahiri yake ganinsu, wayar ya kai bakinsa yayi kissing pic ɗin, a fili ya furta "I MISSED YOU" badan yagaji da kallon pic dinba ya a jiye wayar ya mike a hankali ya nufi toilet. Ya ɗauki lokaci kafin ya gama shiryawa ya fito falo, a falon ya tarar da haidar zaune yana latsa waya. haidar yana ganinshi ya ajiye wayar hannunsa cikin murmushi yace, "ina kwana yaya" mustapha ma dan murmusawa yayi yace, "lafiya kalau" haidar ya nuna masa dinning yace, "your breakfast is ready, tun dazu Mami ta shirya maka" murmushi yayi ya juya ya nufi gun dinning din, da kanshi ya tsakuri ɗan abin da ze iya ci, yaci ya barshi, goge bakinsa yayi da tissue ya mike yana hamdala ga Allah. tsadadden agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa ya duba yaga har 11am, ta wuce, wayarsa ya zaro daga aljihun gaban rigarsa yayi dialing number ammi, lokacin ammi tana falo tare da baƙin ta,Maryam kuma tatafi part ɗin Aunty zuhura domin tayata tsifa, ammi ta ɗaga bayan sun gaisa tace masa. "Ya me jikin kuma?" yace, "da sauƙi" ammi tace "Allah ya ƙara sauƙi" yace "ameen" haidar daya fahimci dawa mustapha yake wayar yace "yaya bani mugaisa da ita" mustapha bece komaiba ya miƙa masa wayar, tasowa haidar yayi ya karba, suka gaisa da ammi sosai cikin mutunta juna, ammi ta masa yame jiki tace kuma ya gaida daddy, miƙawa mustapha wayar yayi sukayi sallama da ammi ya kashe wayar, yanzuma miskilancinsa ya hanashi tambayar Maryam duk da yanda zuciyarsa take cike da tsananin kewarta, gashi ammi itama taƙi masa zancenta bare yasan halin datake ciki, sosai yake bukatar jin koda muryar tane ko yaji sauƙin a bunda yake a cikin ransa, kamar ya kuma kiran Ammi yace ta bata wayar haka yakeji, amma baze iyaba. siririn tsaki yaja ya fesar da huci, a ransa yace _"da tana da wayarta da duk haka bata faruba"_ mikewa yayi yana duban haidar yace, "muje na gaida daddy da mami ka rakani wani guri" haidar ya amsa masa suka fito suka nufi part ɗin daddy, bayan sun gama gaisawa da daddy ya ƙara duba jikin Sadik dake ta bacci still, yacewa daddy zeje wani guri ya dawo, kasuwar sai da wayoyi yacewa haidar ya kaishi, waya me kyau da tsada ƙirar kamfanin samsun ya siyawa Maryam, suna komawa gida yayiwa Aunty transfer din kudin da tace ya mata. Da yamma bayan sallar la'asar mustapha da daddy ne suka fito cikin shirinsu zasu gidan gwaggo domin gaisheta, da mustapha yacewa daddy ze jene, shine daddy'n yace suje tare shima ya gaishenta ya kuma duba jikinta, seda suka kira Aunty tayiwa driver'n Daddy kwatance gidan sannan suka tafi. basusha wahalar gane kwatancen layinba tunda babu nisa da titi kuma wajen firamare ne, direban yasan gurin, gidannedai seda suka tambaya aka nuna musu. A Kofar gidan gwaggo direban ya faka motar kasancewar motar tana shiga har layin. fitowa sukayi daga motar mustapha ya shiga bin layin da kallo, dan wannan shine karo na farko daya zuwa irin wannan unguwar a rayuwarsa, abokinsa lukmanne ya fado masa rai, ya manta rabon da suyi waya dashi gashi yanzu yayi aure baya unguwar gandun sarki, daya biya ta gidansu sun gaisa. yaro Daddy ya samu ya turashi gidan gwaggo dan a sanarmata da zuwansu, gwaggo na zaune a tsakar gida akan tabarma ita da asabe wadda take zaune a gurinta yaron ya shigo yayi sallama, su gwaggo suka amsa masa. Yaron yace "wai ana sallama da gwaggo" gwaggo tace, "Ni kuma dannan suwaye?" Yace "wasu ne a mota me kyau su biyu suma masu kyau" gwaggo tace, "jeka tambayo kace suwaye" yaron ya fita bajimawa yadawo yace, "wai yace Alhaji mainasara ne da.." gwaggo ta kwalalo ido waje ta katse yaron da sauri tace, "wakace yaro?" Yaron ya kuma cewa "Alhaji mainasa" gwaggo ta dubi asabe da dunbin mamaki a fuskarta tace "asabe! Kinji wa akace yana sallama, wai Alhaji mainasara ko kunnenane beji daidaiba?" Asabe tace, "a'a gwaggo shi akace" gwaggo ta dubi yaro tace, "jeka maza kace ya shigo" ta juyo ga asabe tace, "dakko musu wannan ƙatuwar daddumarnan sabuwa ki shimfida musu" asabe ta mike da sauri ta dakko dardumar ta shinfida, daidai lokacin su Daddy sukayi sallama. gwaggo ta amsa musu tana washe gajiyayyun haƙoranta tana binsu da kallo cikin tsananin farin ciki tace "sannunku da zuwa Alhaji, dafatan kunzo lafiya?" Daddy ya zauna da fara'a yace "lafiya kalau baaba ina wuni" gwaggo kamar zata ɗauki Daddy ta ɗora a cinya yanda take acting tace "lafiya kalau Alhaji, ya iyali?" Mustapha dai kawai kallonta yake ta ƙasan ido, a ganin farko daya mata a rayuwarsa yaji sam matar bata masaba" bayan sun gama gaisawa da daddy kamar wanday akaiwa dole yace "ina yini" gwaggo ta kalleshi da Fara'a tace "lafiya kalau dannan" daga haka be ƙara cewa komaiba, asabe ta gaishe da daddy da mustapha suka amsa mata. gwaggo ta dubeta tana kunce hannun zaninta tace "ungo ɗari biyu nan kisiyo musu lemo da ruwa, bari in kawo muku abinci" Daddy ya dakatar da ita da faɗin, "A'a baaba ki barshi, a koshe muke mukam" gwaggo tace "to ai ko ruwa kwasha Alhaji" Daddy yace "ki barshi baaba mungode, ya jikinnaki kuwa" gwaggo tana maida 200 ɗinta cikin zani tace, "jiki ai yayi sauƙi Alhamdulillah" Daddy yace "Masha Allah, Allah yakara lafiya, ai naso zuwa tun wancan lokacin to sai kuma wani uzuri ya tsaidani" gwaggo tace "bakomai ai Alhaji, a hakanma Nagode ai naga saƙo gurin Hajiya(Aunty) nagode" Daddy yace "babu komai, sai kuma maganar yarinya Maryam dana aurar da ita batare da neman izni ko yardarku ba, da....." Gwaggo ta katseshi da sauri da faɗin "haba alhaji, babu komai ai, kaima uban Maryam ne kana da iko akanta, ka kai da zartar da duk wani hukunci dakaso, mune da godiya ai dabaka kyamacemuba ha haɗa zuri'a damu" Daddy yayi murmushi ya mata Godiya, shidai mustapha yayi tsit kamar babu shi a gurin. Gwaggo se sakarwa daddy zantuka takeyi, shi kuma kawai sedai ya bita da murmushi da eh'ko A'a, ganin ƙarfe shida ta gabato Daddy yacewa gwaggo su zasu wuce, nuna mata Mustapha yayi yace "ga sirikinnakifa, shine mijin Maryam ɗin" gwaggo ta gwalalo ido waje tana kallon Mustapha, aranta tace _"yanzu wannan mutumin me kama da Balarabe shine mijin maryam"_ jinjina kai tayi tace, "Masha Allah, ɗana ashema kaine sirikinnawa to Allah ya baku zaman lafiya, dafatan dai baka fuskantar wata matsala daga gurinta?" Mustapha ya gyada mata kai kawai. Tace "aidama nasan Maryama yarinyar kirki ce gata da biyayya da hankali, bata da wata matsala ko...." maganar gwaggo ta makale lokacin dataga uban kuɗin da Daddy ya fito dasu daga alhajinsa ya ajiye a gabanta.Gwaggo ta wangale bakinta tana duban Daddy dake cewa, "bamu samu mun taho da komai ba ga wannan a sai goro" gwaggo ta haɗiye wani yawu tace, "Alhaji angode Allah yasaka da Alkhairi, ya raya zuri'a yajikan mahaifa, Allah ya ƙara buɗi" Daddy ya amsa da "Amin" yana bin bayan mustapha wanda tuni yayi gaba, gwaggo har ƙofar gida ta bisu babu ko lullubin kai se ɗan kwali tana zuba musu Godiya, mustapha yana jingine jikin motar yana latsa wayarsa, saleemat ce ta fito daga gidansu hannunta riƙe da leda zata kaiwa wata kawarta a tamfar anko, kallon su Daddy take cike da mamaki ganinsu a ƙofar gidansu, gasu ƴan gayu dasu wanda kallo ɗaya zaka musu kasan Naira ta zauna a gurin su, bata lura da gwaggo sai daga baya anan ta gane ashe gurinta sukazo, gaishe da Daddy tayi cikin girmamawa duk da batasanshiba, amma tana ganin kamar tasan fuskarsa, amma ta kasa tuno inda tasan sa, Daddy ya amsa mata da fara'a, shima Mustapha gaisheshi tayi a ranta tana yaba kyawun da Allah yayi masa kamar ba ɗan ƙasar nan ba, ya amsa ba yabo ba fallasa, ta gaida gwaggo ma ta wuce, seda gwaggo taga barin motar su daddy layin, Sannan ta dogara sandarta ta koma cikin gida da ƙyar kamar wadda zata bisu. Zama tayi akan dardumar dasu daddy suka tashi ta ɗauki kuɗin tana jujjuyashi a hannunta kafin ta dubi asabe tace "Asabe kinga ikon Allah ko, nida na ɗauki Maryam na kaita aikatau danta wulakanta se gashi ita aikatau ɗin ma ya zamar mata Alkhairi, jibi fa wanda akace shine mijinnata kamar shi yayi kansa dan kyau, anya kuwa wannan ma bahaushe ne kuwa?" Asabe tace "ikon Allah kenan gwaggo yafi gaban komai, amma dai Maryam tayi sa'ar miji" gwaggo tace "Ni duk ba ma wannan ba, wai yau Ni Ladi nice Alhaji mainasara yazo har cikin gidana da sunan ya gaisheni, wayyo daɗi kasheni wlh jinake kamar mafarki nake asabe..." Haka gwaggo taita zubarta cikin tsananin farin cikin yau Alhaji Mainasara ya zo gidanta, asabe dai se dariya take mata, Maryam kam tasha addu'oi kala_kala, kamar ba ita ce da gwaggo take tsine mata ba gami da aiba tataba........✍️ *Na so page ɗin ya fi haka amma abubuwa sun shamun kai yau ɗinnan, mu haɗu bayan sallah idan Allah yakaimu inda za mu ƙare book ɗin gaba-daya cikin kwanaki ƙalilan da yardar Allah, AYI SALLAH LAFIYA MASOYA.* *By* *Zeey kumurya* *ABIN DA KA SHUKA....!* _*BY*_ _*ZEEY KUMURYA*_ *Bismillahirrahmanirrahim* *7️⃣3️⃣* ...........Se azhar na baro part din aunty zuhura, acan na wanke kannawa, na busar dashi Bayan mun gama tsifar, part din ammi na koma nayi Sallah sannan na shiga kitchen muka ƙarasa girki Ni da umaimah, har lokacin baƙin ammi sunanan, muna gama girkin ko tsayawa cin abincin banba na koma part ɗinmu, sosai kewar yaya ta cikamun zuciya kamar mara lafiya haka nake jina, komai ina yinsane cikin dauriya da ƙarfin hali, amma idan na tuna yau ze dawo se inji farin ciki ya lullubeni, gyaran part ɗinmu na shiga yi bakama ƙafar yaro cikin zumuɗi, ko ina na shareshi nayi mopping na sauya zanin gadon ɗakina dana ɗakinshi bayan na feshesu da turare, gidanma gaba-daya na buɗade shi da turaren wuta me daɗin gaske, se wajen ƙarfe shida na gama gyaran gidan, wanka na faɗa toilet na tsalo na shirya cikin wata atamfa super ɗinkin riga da zani, ɗinkin rigar yayi matuƙar kyau yamun dass a jikina, gashin kaina na faka a ƙeya, ya sauka har gadon bayana, nannade gashin nayi a jikin ribbom ɗin kaina na kafa daurin ture kaga arziki(ba ture kaga tsiyaba🙁), dankunne da sarka masu kyau na saka, harda agogo da abun hannu duk na saka, ba wata kwalliya nayiba amma Ni kaina nasan ba ƙaramin kyau nayiba, powder kawai nasawa fuskata kalar fatata, se kuma kwalli da white lipstick me ɗan ɗanko se cikakkiyar girata dana taje da brush ɗin tajeta, humra na me sanyi da daɗin kamshi na buɗaɗe jikina da ita, tare da turaren fesawa shima me sanyin kamshi da daɗi, se kamshin ya haɗu ya bada wani kamshi me daɗin gaske, kallon kaina nayi a madubi na ƙara kallo a fili nace, "ALHAMDULILLAHILLAZI, AHSANIL KALK'I WA KALK'IHI" jin cikina ya fara kiran ciroma saboda yunwa, na dakko mayafina daya shiga da a tamfar na yafa a saman kaina, na fito na nufi part din ammi danna ci abinci. Fitowar Maryam daga part ɗinta yayi dai_dai da zuwan fareedah gidan, tazo ne dantaga Mustapha ta fara nuna masa kudirinta a kansa, amma ita da kissa zata masa bada hauka irin na umaimah, tana sanye da zunbulelen hijab har ƙasa, a matsayin ita mutuniyar kirki ce. Maryam na gaba batama lura da itaba ita kuma tana binta a baya, ƙurawa bayan Maryam ido tayi tana kallon yanda jikinta yake juyawa duk da mayafi, zanin data daura ya fito mata da shap ɗin jikinta sosai, ta taka step ɗin bakin part din ammi mayafinta ya zame daga kanta, bata tsaya gyarashi ba tunda tana ganin ta ƙaraso part ɗin, kallon gashin Maryam daya fito ta ƙasan daurinta kawai fareedah takeyi, ƙara sauri tayi domin zuciyarta cike take da son ganin fuskar me wannan dirarren jikin da kuma uban gashi haka baƙi sidik se sheki yakeyi yaji man kitso. da sallama na shiga falon, suna zaune dukansu da ammi da Aunty zuhura da umaimah, suka amsamun a tare har umaiman tunda taga ammi tana falon, amma batare data ɗagoba, zuhura data saki baki tana kallon Maryam tace, "wow Masha Allah, gaskiya Mamana kinyi kyau sosai, kin fito zam a amaryarki, sedai kash ɗan'uwana bayanan" murmushi kawai nayi na zauna a gefenta, araina nace _ai danshi nayi kwalliyar_ umaimah ta dago da kanta da sauri, jin bayanin zuhura ta kalli Maryam, sosai itama Maryam ɗin ta mata kyau, cikin kyashi da hassada tace, aranta, " _shegiyar yarinya se kyan tsiya kamar aljana_" ta tabe ta maida kanta kan wayarta, ammi na murmushi tace "ai dama ɗiyata akwai kyau Masha Alla.." shigowar fareeda ta katse mata zancenta, gaba-daya muka kalleta muna amsa mata sallamar datayi. idon fareedah na kan Maryam ta tsugunna ta gaida ammi da zuhura. suka amsa mata cikin fara'a, gaisheta nayi nima tunda daga gani ta girmeni, ta amsamun tana ƙara ƙuramun ido, umaimah ta tabe baki ganin kallon da fareedah takewa Maryam ta mike tana faɗin shigo mana kika zauna a nan, fareedah tana tafe tana satar kallon Maryam ta bi bayan umaimah zuwa ɗakinta, Aunty zuhura ta ajiye Abul dake hannunta ta tashi ta ɗauki wayar ammi tace, "na baro wayata a wajena, bari na miki hoto a wayar ammi" ammi ta mike ta shiga kitchen tana murmushi, gyara mayafina nayi Aunty zuhura ta fara mun hoton, tayi kusan kala biyar nace, "Aunty zuhura a barshi haka" zuhura tace, "Tom shikenan, amma bakiga yadda kikayi kyau ba, tasowa nayi na karba wayar na duba, hotunan na duba sunyi kyau sosai, bata wayar nayi nace, "yayi kyau gaskiya sosai" zuhura tace, "hmmmm, ainaso kanina yananan yaga wankannan, amma duk da haka bazan bari yayi missing ba seya gani a hoto" dariya kawai nayi na nufi kitchen dannaci abinci. ammi na ƙoƙarin fita da plate a hannunta na shiga kitchen din, nace "sannu ammi" tace "yawwa ya jikinnaki" nace "na warware" ammi tace, "Masha Allah, aina gani gakinan kinyi shar dake" murmushi nayi cikin jin kunya. ammi ta ƙara cewa, "jiya da daddare NOOR yakira kinyi bacci, dazuma ya kira kina part din zuhura" lumshe idona nayi bugun zuciyata na sauyawa jin ambaton farin cikinta da ammi tayi, ammi bata jira amsataba tace "idan kin gama cin abincin seki kirashi" nace "Toh" a hankali ina ƙarasawa cikin kitchen din, ammi kuma ta fice. A ɗakin umaimah kuwa bayan sun shiga, umaimah ta zauna a bakin gado tana bata rai batare da tacewa fareedah komai ba, Fareedah bata damu da yanda ta mata ba ta zauna a gefen ta tace, "kawata wace waccan dana ganta a falo kyakkyawa da ita, amma dai yar'uwar ammi ce ko?" Umaimah ta kebe baki tace "to uwar gane_gane, aidama naga tunda kika shigo kallonta kawai kikeyi" fareedah tace "ba dole na kalleta ba, naga mace ga kyau ga diri ga gashi ga daɗin murya, ga iya tafiya, ga wani kamshi datake zubawa me daɗi da sanyi ga...." Umaimah ta katseta cikin tsananin baƙin ciki, da fareeda tasan yanda yabon Maryam yake tafarfasa mata zuciya da bata yi a gabanta, tana hararar fareedan tace "to itace matar yaya NOOR ɗin" fareedah ta gwalalo idonta waje tace, "wanne yaya NOOR ɗin? ba dai wanda kike so ba?" Umaimah ta gyada mata kai tana haɗiyar wani yawu me ɗaci. Fareedah taja wani uban numfashi tace "wannan ƴar yarinya ɗanya shagab itace matar tasa?" Umaimah tace ",se kuma kiyi" fareedah ta jinjina kai a ranta tace _"dama yana da wannan tsaleliyar yarinyar me zeyi dake?"_ amma a fili se tace "ya maganar abunda nace miki kiyi dafatan dai kinyin?" Kafin umaimah ta bata amsa ammi ta shigo ɗakin da sallama, plate din hannunta ta ajiye a ƙasan gadon tana faɗin "fareedah ga abinci" bata jira amsartaba ta dubi umaimah tace, "ki kawo mata ruwa auta" umaimah tace "toh" fareedah na murmushi tace "Nagode ammi" bayan umaimah ta kawo mata ruwan ta ƙara dubanta tace "baki bani amsar tambayar dana miki ba" Umaimah ta kalleta cike da tsananin takaici tace "babu amsarne shiyasa banbakiba" "kamar ya? Ko baki gane akan me nake magana ba" cewar fareedah tana cire hijabin jikinta danya fara takura mata, umaimah tace "nagane mana, akan gurguwar shawarar dakika bani mana" fareedah ta haɗe rai ganin yanda umaimah take mata tunda tazo tace "wai mene hakane ina miki magana kina wani amsamun kamar ana miki dole, se wani babbata rai kike, idan dannazo gidankune sena tashi na tafi" ganin yanda fareedah tayi se umaimah ta ɗan saki fuska tace "ina cikin haushin abunda shawarar da kika bani ta haifarmunne, kin takuramun nayi harda kirana a waya kina ƙara jaddadamun, duk da banaso amma haka na daure na aikata ƙarshe ba'ayi nasaraba se uban mari dana sha" fareedah tayi ƙoƙari ta danne dariyar dake neman kufce mata tace "bangane me kike nufi ba? Shi yaya NOOR ɗinne ya mareki?" umaimah ta sauke wani numfashi tabawa fareedah labarin abunda ya faru, ta ƙara da faɗin, "tun daga ranar ban ƙara bari mun haɗu da shi ba, saboda bansan matakin daze dauka a kainaba, ga wata irin kunyarsa danake ji" fareedah zuciyarta fari ƙal kamar takarda, a ranta tace _"wawiya, haka zanta sakaki kina yin abunda ze kara tsanarki"_ afili kuwa setace "to mene danya miki haka, ai wannan shine alamun nasara" umaimah ta mata wani kallo na baki da hankali amma batace komaiba, fareedah ta ƙara gyara zama tace "mantawa nayi ban faɗa miki ba, ai dama su maza haka suke, dazarar ke kika fara nuna musu kuyi irin wannan harkar sai sun miki haka, karki wani damu danya miki haka, burga ce kawai ya miki da kuma ya nunu miki irin shidin na Allah ne, amma idan kika cigaba da masa zakiga ya dawo shima yana biye miki, wataranma shi ze nemeki da kanshi" umaimah jitayi kamar ta rufe fareedan da duka saboda haushin maganganunta, amma ta danne bacin ranta tace "kinga kibar fa wani dagon jawabi, aini anyi na farko anyi ƙarshe bazan kuma ƙara masa irin abinda na masa ba" fareedan ta kebe baki tace, "kin haƙura dashi kenan, duk da irin tarin soyayyar da kike masa?" umaimah tace "ban haƙura ba, amma na yanke shawarar danake ganin ita kaɗai zata fishsheni" fareedan tace "wacce shawara kika yanke?" Tace "na yanke shawarar zan faɗa wa ammi kawai ina sonsa, nasan...." Fareedah dataji tamkar ta caka mata mashi a kahon zuciya takatseta da faɗin, "lallaima umaimah, aiko wannan shine babban kuskuren dazaki tafka a arayuwarki, ki faɗawa ammi ta tursasashi ya aureki, kije a matsayin matar tushe mara daraja a idon namiji, ya samu damar wulakantaki kenan son ransa" umaimah da jikinta ya fara ɗan yin sanyi jin abunda fareedah ta faɗa tace, "kuma fa hakane fareedah nima da nace bazan faɗa mataba, amma nayi tunanin,nayi tunanin naga bani da wata mafita se hakan" fareedah tace "to karma ki soma faɗa mata wlh, indai zaki ɗauki shawarata, amma kiyi tunani sosai akan hakan" shiru umaimah tayi, ta rafka tagumi, fareedah kuwa se harararta take a fakaice, aranta tana cewa _"senayi duk yanda zanyi banbarki ki faɗawa ammi wannan maganar ba, dannasan dazarar kin faɗa mata magana ta ƙare, yanda ammi ta matsu kiyi aurennan zashi zatayi ya aureki, Ni kuma bazan taɓa bari kiyi aure kibarniba, balle kuma har ki auri wanda zuciyata takeso..."_ umaimah ta katse mata tunaninta da faɗin "ki sakko kici abincin karyayi sanyi" fareedah bata musa ba ta sakko daga kan gadon ta fara cin abinci.... Bayan na gama cin abincin na zauna a falo muka cigaba da hira da Aunty zuhura, wayar ammi na hannuna na ajiye ta a gefe ban kira yayanba shima kuma be kira ba, Ni duk a tunanina yau ze dawo, shiyasa rashin kirannasa be dameniba. Se bayan sallar magriba fareedah ta tafi, bayan ta gama ƙara dora Umaimah akan gurbatacciyar hanya da munanan shawawarinta, ita kuma dayake bata da wayo ta yarda da shawarwarinnata, fareedah dazata tafi haka taita kallon Maryam harseda Maryam ɗin ta tsargu. har bayan sallar isha'i wayar ammi na hannuna ina dakon kiransa, Ni kaɗai ce zaune a falon yanzu, Aunty zuhura ta koma part dinta ammi kuma na ɗakin ta umaimah ma haka, tunanin yaya kawai nake da kewarsa ta cikamun zuciya, ammi ce ta shigo falon, zama tayi a kujerar dake fuskantata tace "kin kirashi kuwa?" Buɗe idona nayi a hankali nace "nakirashi ammi, amma wayar taƙi shiga" ammi tace "sharrin network ne, nasan ze kira anjima, may be shi idan yakira ta shigo" mikewa nayi na miƙa mata wayar nace "ammi gashi zan koma part dinmu na fara jin bacci" ammi tace "yau ba'anan zaki kwanaba, ko kinbar jin tsoron yanzu?" Nayi murmushi kawai, ammi tace "kiyi kwanciyarki anan, gobe idan yadawo seki koma" _"gobe kuma_?" na maimaita haka a raina, komawa nayi kan kujera na zauna saboda wani irin zafi danaji ya ziyarci raina, daure abinda naji araina nayi a hankali nace "Toh ammi Allah yakaimu" ammi tace "ameen" kwanciya nayi akan kujera zuciyata na mun suya, Ni inanan kewarsa ta hanani sukuni, inata shirye-shiryen tarbarsa, shi kuma yanacan yana sha'aninsa hankali kwance, yacemun yau ze dawo ashe se gobe, nasan tunda ammi ta faɗa haka ne, kuma gashi har dare ma yayi bedawo ɗinba, ta tabbata se goben, tashi nayi na koma ɗakin ammi na rage kayan jikina na kwanta ko wanka banyiba saboda yanda nake jin zuciyata babu daɗi, na daɗe da kwanciya inata juyi bansan sanda bacci ya kwasheniba, yau ma seda maryam tayi bacci mustapha ya samu kansa ya kira ammi, yau kam beyi nauyin bakinba, ya tambayi ammi Maryam, ammi ta shaida masa tayi bacci. Washegari tunda asuba da mukayi sallah muka fara aikin snacks na tarbar yaya bisa umarnin ammi, danni duk shirin danake na dawowarsa na manta da batun yi masa abun tarba, bayan mungama aikin, na koma part dinmu, yauma banyi sanyaba na ƙara gyara part dinnamu fiye da jiya, bayan nayi sallar la'asar naci abinci na kwanta bacci saboda gajiyar dake addabar jikina..... Mustapha yau tun safe ya gama shirinsa na komawa Jos, amma Daddy ya hanashi tafiya, su haidar ma se roƙonsa suke ya ƙara kwanaki kar ya tafi yau, shidai murmushi kawai yake musu, shikanshi bayason ya tafiyar ya barsu, amma dole ya tafi a yau, dan wata irin kewar Maryam ce take addabarsa wanda idan begantaba a yau akwai matsala, kwana biyun da yayi be gantaba beji muryartaba jinsu yake kamar wata biyu sukayi rabonsu da juna, wajen 12 na rana,faruq ya kaishi super market ya lodowa Maryam kayan zaki, su sweets da choculates da popcorn, su kuma su ammi turaruka yasai musu kala_kala, se can yamma Daddy ya barshi ya tafi da ƙyar, su haidar kamar zasuyi kuka, shima cike da kewarsu ya barosu, a Jet din daddy za'a maidashi, dama driver'n ammi already ya koma Jos tun jiya da safe... Maryam bata jima tana baccinba ta tashi, ƙara gyara gadon tayi sannan ta shige wanka, cikin wani haddadden less black colour an masa zanen fulawa me kyau da orange colour ta shirya, ɗinkin riga da skirt, ɗinkin ya zauna dass a jikinta yayi matuƙar yi mata kyau, hips ɗinta ya fito sosai ajikin skirt, daurinta ta kafa irin na zamani wanda ya ƙara kawata kyawun kwalliyar tata, ɗan kunne da sarka da zobuna da abun hannu haɗi da agogo masu kyau tasaka, ta bulbule jikinta da turaruka masu sanyin kamshi da daɗi, sosai yau tayi kyau fiye da jiya kamar ka saceta, har aka kira sallar magriba tana gaban madubi tana shiryawa, duk da fushi take da yayannata amma so take ta burgeshi sosai, seda aka shiga sallah ta bar gaban madubin ta shimfida darduma ta zira hijabi ta tada sallah dama da alwalarta tayi tun da ta shiga wanka. Mustapha se daf da magriba suka ƙaraso gida, hakan yasa be shiga gidanba ya bawa megadi ajiyar kayan tsarabarsa ya nufi masallaci...........✍️ *BARKANMU da sallah, da fatan anyi sallah lafiya,ALLAH ya maimaita mana, ameen.* _*JUMA'AT MUBARAK🕌🕋*_ *By* *Zeey kumurya* *ABIN DA KA SHUKA....!* *BY* *ZEEY KUMURYA* *7️⃣4️⃣* *Bismillahirrahmanirrahim* ..........Ana idar da Sallah ya nufo gida, wani irin farin ciki yakeji a cikin zuciyarsa zaiga meronsa da amminsa, ƙara gaisawa sukayi da maigadi ya ƙara masa sannu da zuwa Sannan ya karbi kayansa ya wuce cikin gidan, garin yayi lum_lum alamun haɗari, part ɗinsu ya nufa direct zuciyarsa cike da muradi gami da ɗokin ganin Maryam, a hankali ya tura ƙofar falon ya buɗe, wata sassanyar ajiyar zuciya ya sauke tare da lumshe idonsa yana shaƙar daddaɗan kamshin turaren huta dana room freshener dake tashi a falon, ga sanyin AC daya ratsashi, a hankali ya buɗe idonsa yana bin falon da kallo, kamar yau ya fara shigowa cikinshi yayi 3 minutes yana kallon falon sannan ya fara taku ya nufi ɗakinshi, da sallama ya shiga duk yasan babu kowa, ledodin hannunsa ya ajiye a gaban mudubi yana bin dakinnashi da kallo cike da burgewa, ganinshi fess dashi se tashin kamshi yake, murmushi yayi cikin jin daɗi ya juya ya fice daga ɗakin ya nufi dakin Maryam, Maryam na ajiye darduma a cikin cover ya shigo ɗakin da sallama cikin daddaɗar muryarsa, Jin muryarsa a dodon kunnena yayi dai_dai da wata irin bugawa da zuciyata tayi, lumshe idona nayi inajin wani sanyi na ratsa zuciyata tun kafin na kaiga kallonshi, a hankali na juyo bisa umarnin zuciyata data azabtu da kewarsa, mustapha kuwa tsayawa yayi a jikin kofa yana kallonta ya harde hannayensa a kirjinsa, yana sakin tattausan murmushi akan fuskarsa, wani nauyi da kirjinsa ya masa yaji yana raguwa a hankali, sanyi da farin ciki na maye gurbinshi a zuciyarsa, kamshin jikinta dana ɗakin ya haɗu ya bada wani kamshi me daɗin gaske wanda ya saukar masa da nutsuwa, ɗago da idanta tayi a hankali ta kalli fuskarsa shima kallonnata yake hakan yasa idanunsu ya harɗe guri guda, ƙara buɗe lumshashshun fararen idanunsa yayi ganin wani irin kyau data masa yana bin surar jikinta da kallo, wani yawu ya haɗiye yana jin wani abu na bin dukkan ilahirin jikinsa a kanta, be san yayi kewarta dayawa ba seyanzu daya ganta a gabansa, ita kuwa Maryam suna haɗa ido tayi ƙasa da kanta tana ɗan turo bakinta gaba, kasa jurewa yayi ya ƙarasa inda take, daf da ita ya tsaya yanajin bugun zuciyarsa na sauyawa, wani dogon numfashi yaja saboda kamshin jikinta daya shaƙa, nima lumshe idona nayi saboda daddaɗan kamshinsa daya cika hancina ina sauke ajiyar zuciya, a hankali yasa tattausan tafin hannunsa na dama ya shafi kuncina, cikin wata irin siririyar murya yace, "Ummuuuuu....!" yaja sunan wanda hakan yasa naji tsigar jikina tayi wani irin tashi yarrrr, ƙara ƙasa nayi da kaina bandagoba kuma ban motsaba, balle na amsa masa, hannunsa yasa ya ɗago haɓar ta, idanuwansa yasanya cikin nawa yana jifana da wani fitinanne kallo ƙoƙarin kauna nawa idon nayi daga nasa amma yaƙi bani damar yin hakan, runtse idona nayi da sauri saboda bazan iya jurar kallon kwayar idonsa ba, kwallar da bansan kota menene ba ta cikamun ido, ɗan yatsansa yasa yana shafa saman idona cikin wani irin salo, murya ƙasa_ƙasa yace "kinyi kyau sosai" ya ƙarashe zancen tare da busa mun iska daga cikin bakinsa a fuskata, wani gwauron numfashi na sauke hawayen daya cikamun ido na kwaranyowa ta gefen idona, runtse idonsa yayi yanajin zafi na ratsa zuciyarsa sanadiyyar ganin hawayenta, a ɗan rude yace "me nene?" Ko bakiyi farin ciki da dawowataba?" girgiza kai nayi alamun a'a, ina ƙoƙarin haɗiye kukan dake neman kufcemun, rungumeta yayi tsam ajikinsa, a tare suka saki ajiyar zuciya me ƙarfi, shafa bayanta yake a hankali, lumshe idonsa yayi yana shaƙar kamshin jikinta daya saukar masa da kasala gami da tada masa feeling a kanta, nima luf nayi a jikinshi ina ƙara kwantar kaina a kirjinsa cikin tsananin farin ciki, ajiyar zuciya kawai nake saukewa ina shaƙar daddaɗan kamshinsa me saukar mun da nutsuwa, sunyi kusan 5 minutes a haka kafin ya rabata da jikinsa a hankali, bece komaiba yaja hannunta suka ƙarasa bakin gado, zama yayi ya zaunar da ita akan cinyarsa, bakinsa yakai saitin kunnenta cikin wata irin murya me narkar da zuciya yace "I MISSED YOU" lumshe idona nayi ina saukar numfashi amma bance komaiba, be damu da yanda take masa shiru da, dan yau wani abu yakeji a zuciyarsa game da ita dabe taɓa jin irinsaba, juyo da fuskarta yayi yace "yan mata ba magana ne, ko in koma inda na fito?" girgiza kai nayi alamun a'a ina turo baki gaba, shafa lips dinta daketa zuba kyalli yayi yana murmushi yace "toh meyafaru?" a hankali nace "kai ne" kwantar da kanta yayi a kirjinshi yana shafa gefen fuskarta yace "me nayi?" Idona a lumshe nace "katafi ka barni, kuma jiya naita jiranka baka dawo ba" karan hancinta yaja yace "am sorry" dago kaina daga kirjinshi nace "sannu da zuwa, dafatan ka dawo lafiya?" hararar wasa yamun yace "seyanzu?" Murmushi nayi cikin jin daɗi nace "A'a, yasu Daddy?" Yace "sunanan kalau" nace "Masha Allah, ya jikin yaya Sadiq?" wani kallo naga yamun bece komaiba, ya saukeni daga jikinsa, mikewa yayi ya kama hannuna yana faɗin, "muje ki rakani gurin ammi" sakin hannunnasa nayi na tafi na dakko mayafina, ƙura mata ido yayi sosai ganin yanda take tafiya mazaunanta na juyawa, ina jin yanda idanunsa ke yawo a jikina, harna dakko mayafin na yafa na juyo be bar kallona, seda na matso kusa da shi nace "muje" Ajiyar zuciya ya sauke ya ƙara kama hannunta suka fice daga ɗakin, tafiya muke amma ni yake kallo kawai baya ganin gabansa, muna haɗa ido ya sakarmun murmushi yace "kinyi kyau sosai" murmushi nayi cikin daɗi nace "Nagode" zukatansu cike da tsananin farinciki kasancewa tare suka nufi part ɗin ammi, sosai mustapha yake kallon Maryam kamar yau ya fara ganinta, a kwana biyun dayayi basa tare ta sauya masa ba kaɗan ba, ta ƙara kyau da haske da cika, sunzo steps din dazasu shiga part ɗin ammi yayi tuntube, saboda kallon Maryam daya ke, kallonsa nayi ina dariya, ganin yanda yayi da fuska kamar wani yaro nace "sannu" keɓe fuska yayi ya matse hannuna dake cikinnasa, yana kallon fuskarta, sosai dariyar datakeyi ta ƙara mata kyau, munzo shiga part ɗin ammi nayi ƙoƙarin kwace hannuna amma yaƙi sakarmun sema ƙara matseshi da yayi, da sallama muka shiga falon, umaimah ce kaɗai a zaune a falon, ɗago kanta tayi da sauri ta kallesu, bugun zuciyarta na sauyawa, wani bala'in kyau da dacewa Maryam da mustapha suka mata, kasa dauke idonta tayi daga kansu, sukuwa daga sallama basu ko kalli inda takeba suka shige ɗakin ammi, umaimah ta sauke wani dogon numfashi bayan sun shige ɗakin, tanaji aranta dama ita ce suka jero da mustapha haka ya riƙe mata hannu, gaskiya dole ta dage dan ganin ta mallaki mustapha a matsayin miji itama, ammi tana murmushin farin cikin dawowar ɗannata ta amsa musu sallamar da sukayi, sakin hannun Maryam mustapha yayi ya ƙarasa gareta yayi hugging dinta, ammi ta shafa sumar kansa still fuskarta ɗauke da murmushi tace, "welcome Noor" sakinta yayi ya zauna a gefenta sannan yace "thanks You ammi" ammi tace, "dafatan ka dawo lafiya, ya hanya?" Yace "lafiya kalau" ammi tace "yame jikin fa, dasu daddy'nnaka?" Yace "da sauƙi, su dad sunanan lafiya" ammi tace "Masha Allah" kwantar da kansa yayi akan kafadarta a hankali yace "I missed you ammi nah" ammi tayi murmushi kawai ta shafi kansa batace komai ba, amma zuciyarta cike fal take da farin cikin dawowar ɗannata, Maryam tana zaune a kan carpet din gaban gado, tana kallonsu cike da ban sha'awa da burgewa, sun ɗan taɓa hira da ammi sannan ammi tace ya tashi yaje yaci abinci, duba time yayi ya ga lokacin sallar isha'i ya kusa, mikewa yayi yace "bari yaje masallaci ya dawo" ammi tace "toh sekadawo" hannunta ya sumbata sannan ya fice bayan ya kashewa Maryam ido. Ammi ta bisa da kallo cike da tsananin kauna, kwana 2 da yayi a Kano ba ƙaramin kewarshi tayi ba, batasan kuma yazatajiba randa akace ya koma Kano da zama gaba-daya, maida kallonta tayi ga Maryam tana murmushi, ta mata kyau sosai ba kaɗan ba, aranta "Tubarakalla Masha Allah" ba jimawa da fitarsa aka kira sallah, da alwala hijabin ammi kawai na zira na tada sallah, ana idar da Sallah a masallaci kowa ya fara watsewa saboda haɗarin daya ƙara hadowa ga iska dake kadawa me daɗi, tare suka dawo gida shida yaya Saddam, babu kowa a falon Ammi daya shigo yana ƙoƙarin shiga ɗakinta ammi ta fito da hijabin da tayi Sallah a jikinta, murmushi ammi tayi tace "yanzu nake shirin kiranka a waya naga garin kamar da haɗari" yace "ehh, haɗarinnema a garin sosai" ammi tace "Allah ya kawo mana ruwa yau, kwanakinnan seya hado kamar za'ayi ruwan seya baje" yace "ameen" ammi ta nufi dinning yabi bayanta, kujera taja masa tace "zauna kaci abincin kar ruwa ya sauko kunanan" zama yayi ammi ta fara saving dinshi, kallon abubuwan datake zuba masa kawai yake, bayan ta gama ya dubeta yace "wai ammi duk wannan abubuwan cikina zasu shiga?" ammi tace "eh mana, kuma seka cinye duka" murmushi yayi kawai ya ɗauki glass cup ya tsiyaya ruwa yayi bismillah ya fara sha, ammi ta wuce ɗakinta, tacewa Maryam taje gurin mijinta, cike da kunya Maryam ta fito falon, tunda ta fito yake kallonta yana taunar ferfesun kayan cikin rago a hankali, kaina a ƙasa na ƙarasa gurin dinning din, saboda kallon kurillan dayake mun, harna zauna a kujerar gefensa be dena kallona ba, kallonshi nayi ina na turo baki gaba amma bance komaiba, ferfesun ya debo a cokali ya kai bakina yana tsareni da ido, buɗe bakinnawa nayi a hankali ina kallon ƙofar dakin ammi ya zubamun, ajiye spoon din yayi yace "nima bani" waro idona nayi waje na nuna masa dakin ammi da hannuna, dage kafaɗarsa yayi alamun ko ajikinsa, murmushi nayi na debo ferfesun a cokali nakai bakinsa, buɗe bakin yayi yana jiran na samansa, sai na ɗauke cokalin na kai bakina na zuba ina murmushi, kallona yayi sai kuma yayi murmushin shima, bece komaiba ya karbi spoon din ya cigaba da cin abincinsa, kaɗan_kaɗan ya taɓa komai da ammi ta zuba masa yasha drinks yace intashi mu tafi, tashi nayi ina faɗin "ina zamu, Ni anan nake kwana ai" be ko kalleniba balle ya tankamun, sallama muka yiwa ammi muka fice, garin da haɗari sosai ga iska me ƙarfi tana kadawa, riƙe hannuna yayi muka ƙarasa part dinmu da ɗan sauri saboda ɗan yayyafin da aka fara, ɗakin shi ya nufa damu, satar kallonsa nayi amma bance komaiba, seda muka shiga ya saki hannuna, bakin gado naje na zauna, shikuma ya ƙarasa gaban mudubi ya cire agogon hannunsa ya ajiye, wayoyinsa ya zaro daga aljihu ya ajiye su suma akan mudubin, ɗaya daga cikin ledodin daya shigo dasu ya dauko ya ajiye a gaban Maryam yace, "ga sweet dinki nan shazumama, na cika alkawari ko?" Murmushi nayi nace "eh mana, Nagode sosai" maballin rigar jikinsa ya fara cewa yana faɗin, "kijirani na watsa ruwa, idan na fito akwai maganar da zamuyi" nace "Toh"ina dudduba ledar daya bani, wata ƙatuwar choculate na ɗakko na buɗe na fara sha cikin jin daɗi, ya ɗan daɗe a toilet din kafin ya fito sanye da bathrobe a jikinsa da ƙaramin towel yana goge sumar kansa, kallonta yayi yaga ledodin data faka a gefenta duk ta shanye abubuwan ciki, alawarta take sha hankali kwance ko kallonsa batayi ba, girgiza kai kawai yayi yawuce gaban mudubi, ina ganin ya matsa na ɗauki ledodin dana zubar na miƙe na fice daga ɗakin, ban dawo ba seda na tabbatar da zuwa lokacin yagama kimtsawa, zaune na sameshi akan gado yana waya, zama nayi agefensa, be wani jimaba sukayi sallama ya kashe wayar kallona yayi yace "Daddy na gaisheki" ɗan ɓata fuska nayi nace "meyasa baka bani shi mun gaisaba? kace ma idan kaje zaka haɗa mu muyi waya" yace "meyasa duk sanda nakira ammi kinyi bacci, ko kuma bakya part ɗin ta? dazuma kafin na taho nakirata bakyanan" nace "bakomai" yace "baccinki kike ko kewatama bakyayi?" na ɗan turo baki gaba nace "to ai kaine baka kira da wuri" yace "ƙarfe goma aiba dare bane sosai, kuma ke Meyasa baza ki karbi wayar ammin kikirani ba ke, kafin kiyi baccin?" Ta kallesa tana fito da manyan idonta waje alamun mamaki. be ƙara ce mata komaiba akan batun, juyowa yayi ya fuskanceta sosai yace "ina son na Miki wata tambaya" nace "Toh" shiru ya danyi na wasu sakanni yana kallonta kamar me nazarin wani abu sannan yace "ya kuke da gwaggo?" kallonsa nayi da sauri dan ban taɓa zaton tambayar daze munba kenan, kauda kaina nayi nace "kakata ce" yace "sure?" Nace masa "eh" gyada kai yayi ya ƙara cewa "ta wajen baba ko mama?" wani abu naji ya tsargamun mara daɗi a cikin zuciyata daya ambaci baba, cikin sanyin murya sosai nace "mama ta" ganin yanda yanayinta ya sauya lokaci se yace "am sorry idan tambaya ta ɓata miki rai" girgiza kai nayi ina maida kwallar da cikamun ido nace "A'a" numfashi ya sauke ya kama hannayena suka biyu ya riƙe cikin nasa yace "zaki iya bani tarihin rayuwarki a yanzu?" sosai tambayar tasa ta daki zuciyata, ban taɓa tunanin ze taɓa mun irin wannan tambayar ba a zamanma auranmu, kallonsa nayi cikin sanyin murya nace "Meyasa ka tambayeni?" "Saboda mun zama abu ɗaya" ya bani amsa cikin tarar numfashina, wata ajiyar zuciya na sauke nace "ehh, zan baka" ya ɗan murza hannuna yace "ki faɗamun komai da komai, kada ki rage ko ki boyemun wani abu daga cikin tarihinki Please" cikin raunin murya nace "insha Allah" be ƙara cewa komai se ido daya zubamun alamun Ni yake sauraro kawai, gyara zama nayi tare sauke wani gwauron numfashi, na bashi tarihin rayuwata tun daga farko har ƙarshe, kallonta yake cike da tsanananin so da kaunarta gami da wani tausayinta me tsanani daya cika masa zuciya, kuka takeyi tamkar ranta zai fita domin an famo mata ciwon dake damunta a cikin zuciya shekara da shekaru, kwantar da kanta yayi akan kafadarsa batare da yayi yunƙurin hanata kukan datake ba, runtse idonsa yayi tare da taune lips ɗinsa, yasan zafin mutum ya taso ace basan danginsaba musammanma dangin mahaifi, domin tunda yake a rayuwarsa be taɓa jin irin zafi da kunar zucin dayajiba lokacin da yaji labarin basu Daddy ne suka haifeshi ba, yasan ɗacin datakeji ranta ya ninka wanda yaji a lokacin, danshi ya taso cikin soyayyar marikansa saɓanin ita data taso cikin kunci da matsin rayuwa gami da maraici, wani irin haushin da zafin gwaggo yake ji a cikin ransa, musamman idan ya tuna mugunta da azabtar da Maryam datayi, da Kuma kai Maryam aikatau datayi wanda badan Allah ya kare taba da tuni bata numfashi a doron duniya, ko kuma kodama tana rayen cikin mawuyacin hali da kuncin rayuwa sanadiyyar aikatau ɗin, a hankali ya buɗe lumshashshun idanunsa da suka kaɗa sukayi jajur ya saukesu a fuskar Maryam da har lokacin kuka take me ban tausayi, tattausan tafin hannunsa yasa ya fara share mata hawayen fuskarta ciki tausayawa, ji yake shima tamkar ya zubar mata da hawayen, kamar ƙara zugata yayi share mata hawayen da yake maimakon ta dena kukan sema wasu sabbin hawaye ne masu ɗumi suke ƙara kwaranyowa daga idanunta, kamar zeyi kuka yace "Please ki dena kukannan yana taɓa mun zuciya sosai, Please I beg you!" Maryam cikin sheshsheƙa tace "dole nayi kuka, domin kukanne kawai ze ragamun radadin da nake ji acikin zuciyata" shiru tayi tana cigaba da kukan kafin ta shiga girgiza kai tace, "bansan mahaifina ba, bansan kowa nashiba, ban kuma san randa zan sani...." kuka ne yaci ƙarfinta ta kasa ƙarasa abunda take son faɗa, ɗago fuskarta yayi daga jikinsa ya matso da ita daf da tasa, cikin wata irin cool sexy voice yace, "ki dena kuka, na miki alƙawari zan maye miki gurbin baƙin cikin da ke cikin zuciyarki da farin ciki a sauran rayuwarki tanan gaba insha Allah, i promised this" buɗe idona nayi na kalleshi zuciyata na tsananta bugu, idanunshi ya sanya cikin nawa yana mun kallon ido cikin ido kamar ze haɗe idanunnamu guri guda, murya can ƙasan makoshi cikin wani irin salon karya harshe me narkar da zuciya yace *"I LOVE YOU"* kamar wadda aka tsikara haka nayi wata irin zabura domin ban taɓa tunanin jin wannan kalmar daga gareshi ba a yanzu, wata irin harbawa zuciyata tayi, bin fuskarsa na hauyi da kallo cike da tsananin mamaki, jinjinamun kansa yayi alamun tabbatarwa sannan ya ƙara cewa *"I LOVE YOU SO MUCH MARYAMMMMMM.....!"*........✍️ *By* *Zeey kumurya* *7️⃣5️⃣* ...........Lumshe idona nayi wani sanyin daɗi na ratsa zuciyata, a rayuwata bazan iya tuna wasu kalamai da naji suka mun daɗi kamar yadda kalma I love You ɗin yaya ta munba, ko haɗa aurenmu da Daddy yayi bekai wannan kalmar yimun daɗi a cikin zuciyata ba, gabadaya damuwar danake ciki na nemeta na rasa, wasu hawaye masu sanyi dana tabbatar na farin ciki ne suka zubo daga idanununa, a hankali shima ya lumshe idonsa yana jin wani matsananci feeling akanta, fuskarta ya hade da tata har suna jiyo hucin numfashin juna, a hankali yake goga karan hancinsa akannata numfashinsa na fita da sauri da sauri, buɗe lumshashshun idanunsa yayi da suka ka sukayi ja saboda fitina, harshensa ya fito fashi ya fara lashe mata hawayen fuskarta cikin matsanancin sonta dake ƙoƙarin tarwatsa masa zuciya, wani dogon numfashi ta sauke tana jinta a wata duniyar daban ta nishaɗi, kasa yayi da harshensa ya dora shi akan kyawawan laɓɓanta ya fara zagaye su cikin wani irin salo daya kusa zautar da Maryam, ƙanƙarmeshi tayi sosai wani baƙon yanayi me wuyar fassaruwa na riskar ta, sunyi 3 minutes a haka kafin a hankali ya raba fuskokinsu yana sauke numfashi kamar wanda yayi tseren gudu, kwantar da kanta yayi a kirjinshi ya shiga shafa bayanta ganin yanda jikinta yake rawa, numfarfashi na shiga saukewa nayi luf a jikinshi ina shaƙar daddaɗan kamshinsa, ganin ta dena rawar jikin ya ɗago ta daga jikinsa yana bin fuskarta da kallo, buɗe idona nayi na sauka daga jikinsa na koma na jingina da fuskar gado ina maida numfashi, bece komaiba ya sauka daga kan gadon a hankali fita yayi daga ɗakin gaba-daya, bin bayansa nayi da ido har ya fice, ajiyar zuciya na sauke farin ciki mara misaltuwa na ƙara mamaye dukkan zuciyata, _"i love You maryam"_ na maimaita kalmar sa ta ƙarshe a gare Ni, wani murmushi na saki me sauti tare da kai hannu na shafa lips ɗina ina jin tamkar a yanzu yake lasarmun shi, inanan zaune cikin tsananin sauƙin sa, ya dawo ɗakin da sallama ɗauke a bakinsa, lumshe idona nayi da sauri domin wata irin kunyarsa nake ji, can ƙasan makoshi na amsa masa sallamar, kayan bacci ya ɗaukowa Maryam a ɗakinta a fitar da yayi, ajiye mata su yayi akan cinyarta ya ɗan rankwafar da kansa dai_dai fuskarta yace "ki tashi kiyi wanka mu kwanta inajin bacci" batare dana buɗe idonaba na gyada masa kai alamar Toh be ƙara cewa komaiba shima ya ƙarasa gaban mudubi ya ɗauki wayoyinsa, zama yayi akan stool ya shiga latsa wayarsa, a hankali na miƙe na sakko daga kan gadon ina satar kallon inda yake, kayan baccin daya ajiyemun na ɗauka na shige toilet dinsa, murmushi yayi bayan ta shige toilet din, singlet din jikinsa da wando three-quarter ya cire ya miƙe ya ajiye su, ya rage daga shi se boxer, kashe light din ɗakin yayi ya haye kan gado ya kwanta ya lulluba da blanket, ban wani jima a toilet din ba na fito, ajiyar zuciya na sauke me ƙarfi ganin ɗakin da duhu, dama inata tunanin yanda zan bari ya ganni da ƴar guntuwar rigar baccin dake jikina, a hankali nake taku na ƙarasa gaban madubi, ribbom ɗin kaina na cire na ajiye, wayarshi dake kan mudubi na ɗauka na haska na ɗauka lotion na shafa a jikina, sannan na ɗauki daya daga cikin turarukansa dake kan mudubin na fesa a jikina, switched din wayar nayi na ajiye, a hankali kamar me sanda nake taku wai ni karna tashesa na ƙarasa na hau kan gadon, ta bayanshi na kwanta ina fuskantarsa, kamar na matsa jikinshi na rungumeshi haka nakeji amma bazan iyaba dan karna ballowa kaina ruwa, kusan 5 minutes da kwanciyarta ya juyo a hankali yana kallonta, Maryam da idanunta suke a rufe amma ba bacci take ba, ta ɗan buɗe idonta kaɗan tana kallonsa itama, hannunsa yasa yajawota jikinsa, a tare suka saki wata sassanyar ajiyar zuciya, cikin rada yace "Ummu" nace "uhm" yana ƙara shigar da ita jikinsa yace "bakici abinci ba zaki kwanta?" nace "naci fa" yace "yaushe?" nace "kafin ka dawo" yace "wannan daban, dinner nake nufi" a shagwabe nace "to ai da yamma naci, kuma yanzu nasha choculate naci popcorn ya cikamun ciki" be ƙara cewa komai ba, se gashin kanta daya shiga shafawa, hannuna na ɗora akan kirjinsa kwantaccen gashin kirjinsa naja nace "mene wannan yaya?" yace "aush da zafi fa" ƙara ja nayi nace "hakanne da zafi" runtse idonsa yayi ya cire hannuna daga jikinsa, turo bakina nayi gaba nima na cire hannunshi daga kaina, murmushi yayi bece komaiba se ƙara rungumeta da yayi a kirjinsa yana shaƙar kamshin gashinta, a hankali ya ɗora hannunsa akan kafadarta cikin dabara yake ƙoƙarin sauke hannun rigar jikinta ƙasa, ɓata fuska nayi nace "yaya" zuciyata cike da tsoro domin ban manta azabar danaciba wancan karon, shiru ya mata be amsaba sedai yabar ƙoƙarin sauke mata hannun rigar ya koma shafa damtsen hannunta, a shagwabe na ƙara cewa, "yaya kamun shiru" yace "mene ne?" kamar zanyi kuka nace "bakomai tunda kaki kulani da farko" lips ɗinsa na ƙasa ya lasa bece komaiba, dan ya gane rigimar dabe sha kwana 2 biyu bace za'a masa yanzu, dama kullum se sun kwanta bacci take masa duk dan kar ya mata wani abun, yana sane kawai kyaleta yake, jin yamun shiru na fara mutsu_mutsu a jikinsa ina ƙoƙarin tashi daga jikinnasa, ƙara lumshe idonsa yayi yana sakin wani numfashi saboda yadda yakejin breast ɗinta na goguwa a kirjinsa kasancewar babu bra a jikinta, Bakinsa ya ɗora akan kunnenta yace, "me yafaru wai?" nace "ba kaki kulani ba" cikin sexy voice yace "am sorry my angel bari na miki hira me daɗi kina so ko?" nace "ehh, kamun da yawa har nayi barci" dannasan idan nayi bacci bazai tasheni ba, balle ya mun abunda nake tsoro ba, wani munafukin Murmushi yayi ya fara mata kalaman soyayya masu daɗin saurare, da sanya mutum cikin nishaɗi, lumshe idona nayi ina ƙara mannewa ajikinsa cikin tsananin jin daɗin kalamansa, kamar a mafarki haka nakejin abun, wai yau nice kwance a kirjin *hearbeat* ɗina yana rattabomun kalaman soyayya haka, wani irin farin ciki da sanyin daɗi ne ke ratsa zuciyata, jina nake kamar a ƙololuwar sama saboda nishaɗi, a hankali yake yin ƙasa da rigar jikinta still bakinsa na cikin kunnenta yana jero mata tsadaddun kalam kauna, ina jinshi amma banyi yunkurin hana shiba, saboda daɗin kalamansa da nakeji, ciremun rigar yayi gabadaya daga jikina ya fara yawo da hannunshi a sassan jikina cikin tsananin zaƙuwa, luf nayi ina karɓar sakonsa duk da a matuƙar tsorace nake, a hankali ya ɗago da fuskarta ya haɗe bakinsu guri ɗaya ya fara kissing ɗinta a zafafe, while yana cigaba da sarrafata cikin wani salo me tsayawa arai da wuyar fassaruwa.(duk wayon amarya.....🤣🤣). Rungume take a jikinsa yana lallabata bayan sun fito daga wanka, har lokacin kuka take ƙasa_ƙasa, bayanta yake bubbugawa a hankali yana hura mata iskar bakinsa a cikin kunnenta da haka ya samu bacci me nauyi ya ɗauke ta, ajiyar zuciya ya sauke ya gyara mata kwanciya a jikinshi, ba jimawa shima baccin ya ɗaukeshi. washegari, a hankali na buɗe idona, akan kyakkyawar fuskarsa, lumshe idona nayi na ƙara budewa ina sauke numfashi, hannuna na kai a hankali na shafi kwantaccen sajen gefen fuskarshi, ɗan motsawa yayi kaɗan nayi sauri na ɗauke hannuna daga fuskarshi dan kar naje ya farka, zare jikina nayi daga jikinsa a hankali na tashi zaune, addu'ar tashi daga bacci na karanto a raina, kallon fuskarshi nayi, nayi murmushi cikin jin daɗi da farin cikin kasancewarmu tare, hannunshi dake jikina na zare a hankali, ƙara maido hannunshi yayi yana matsowa jikina sosai, lallausar kwantacciyar sumar kansa na shafa cikin kaunarsa, ina kallon fuskarsa, ɗauke hannuna nayi daga kansa na janyo filo nasa masa a kirjinsa, rungume filon yayi, ajiyar zuciya na sauke na sakko daga kan gadon, falo na fita, kamar dare haka falon yake saboda duhu, kunna light din falon nayi haske ya gauraye, agogon bango na kalla naga har 8 ta wuce, window naje na yaye labule na leka, garin yayi duhu dindum, haɗari ya hado bana wasa ba, iska me ƙarfi ce take kadawa, jiya da daddare ba'ayi ruwan sosai ba yayyafi akayi kaɗan,sakin labulen nayi na nufi ɗakina, ina jin jikina babu daɗi dan jiyama naci kwakwa a hannun yaya sedai ba kamar wancan karon ba,yau Jikinane kawai yake mun ciwo, gashin kaina na fara busawar sannan na shiga toilet na tara ruwan zafi na shiga ciki, naji daɗin jikina kuwa sosai da nayi haka, kaya na canza na koma ɗakinshi, yana kwance yana baccinshi yanda na barshi, toilet na shiga na kwaso kayanmu da muka cire jiya dana bacci na dawo ɗakina na wanke, kafin na gama wankin ruwa ya sakko me ƙarfin gaske kamar ba farkon damuna ba, bayan nagama wankin na share ɗakina da falo, dan bazan iya mopping ba, wankin danayi naji duk nagaji. ɗakinshi na ƙara komawa, har lokacin be tashi ba, zama nayi akan locker na janyo ledar daya kawo mun jiya na dakko choculate guda ɗaya na fara sha, yana jin shigowarta yayi shiru kamar bacci yake tashinsa kenan daga baccin, a hankali ya buɗe lumshashshun idanunsa ya zuba mata, yanda takeshan choculate ɗin kamar wata yar baby, yarintarta ta fito sosai ga wani kyau data masa, a jikina naji ana kallona juyowa nayi na kalli gadon muka haɗa ido, waro idona nayi da alamun mamakin ganin ya tashi, wani kayataccen murmushi ya sakarmun, da hannu yamun alama naje gurinshi, a hankali na tashi na hau kan gadon na zauna a gabansa, kaina a ƙasa nace "ina kwana" lumshe idonsa yayi ya buɗe a hankali batare daya amsa mata ba, se ido daya kafeta dashi, turo bakina nayi gaba nacigaba da shan choculate ɗina, yunkurawa yayi ya tashi zaunen shima yana salati a hankali, kwantar da kanshi akan kafadarta yana leken fuskarta a ƙoƙarin sa na san su haɗa ido yace "kin tashi lafiya" na gyada masa kai alamun eh, yace "yanzu ba ciwon jikin?" ƙara gyada masa kai nayi, yace "dama jiyanma duk raki ne" kawar da zancen nayi da faɗin, "yaya ruwa akeyi sosai" window ya kalla yace "ai shine ya tashe ni" nace "amma dai yau bazaka fita ba?" yace "why?" nace "ruwa mana" yace "idan ya tsaya zan fita ai" na ɗan ɓata fuska nace "ka bari gobe ka fita, kaga jiya ka dawo baka gama hutawa ba" yana gogamun sajen fuskarsa a kuncina yace "gobenma haka zaki ce karna fitan" nace "Allah bazanceba, ka huta yau kaji, kaga ruwa ma ake" yace "to dama nace miki zan fita ne" nace "ai nasan zaka ce zaka fitanne" murmushi yayi yace "bakyaso in fita" na gyada masa kai alamar eh, ɗayan hannunshi yasa ya kwantar da ita a jikinshi yace "nima banason na fita, na fiso in zauna inta kallonki ina jin daɗi" lumshe idona ina shaƙar kamshinsa bance komaiba, ragowar choculate ɗin hannuna ya karba yace "daga tashi se shan zaƙi? shan zaƙin ki yayi yawa Ummu, shiyasa kike ciwon ciki, zan kwashe sauran na ledan ce na bayar kin gama shan rabonki" ɗago kaina nayi daga jikinshi cikin shagwaba nace "to bakai ka siyomun ba?" yace "ai ba siyo miki nayi ki shanye a lokaci ɗaya ba, kaɗan_kaɗan zaki dinga sha, kuma shima ba kullum ba, amma ke jiya kinsha da yawa, yauma daga tashi tun dira akansu" cikin marairaicewa nace "to kayi hakuri karka kwashe sauran zan dinga sha kaɗan_kaɗan ɗin" yace "to na barmiki, amma idan kika shanye kafin 1 month bazan ƙara siyo miki ba" nace "to na yarda, yanzu bani wannan na ƙarasa shanyewa" yace "A'a kingama shan na yau" nace "Please daga wannan fa shikenan se gobe zan ƙara" yace "to anjima sai kisha" badon naso ba na haƙura, amma na ɓata fuska sosai, murmushi yayi yace "muje muyi wanka" nace "ni nayi ai" yace "sai kimun ni" waro manyan idanunta tayi waje sosai tana kallonshi, daga mata gira yayi yana jifanta da wani irin da kallo daya kashe mata jiki, barin jikinshi nayi na koma gefe na kwanta nace "bacci nakeji" bace mata komaiba ya miƙe ya sauka kan gadon ya shige toilet, ajiyar zuciya ta sauke tare da lumshe ido cikin jin daɗin ya shige wankansa shi kaɗai, dan batasan zatayiba daya takura se sun shiga tare, jiyama da sukayi taren kuka ta dinga masa, kuma har sukayi suka fito idanunta a rufe suke, batasan ya dawo ɗakin ba, sai ji kawai tayi an ɗauketa, be direta a ko inaba se a cikin ruwa tajita, yanzunma idanunta a rufe sukayi wankan tana ta aikin turo baki gaba, shikuma yanata tsokanarta.. Tsaye yake a gaban madubi yana shafa mai da towel daure a ƙugunsa, Maryam kuma tana kan kado ta ƙudundune jikinta tunda suka fito daga wankan ta kasa kwakkwaran motsi, kunyarsa take ji sosai kamar ƙasa ta zage ta shige cikinta haka take ji, juyowa yayi a hankali ya dubeta, da sauri ta juya masa baya, murmushi yayi ya ƙasara bakin gadon ya tsugunna a gabanta, ƙara yunkurin juya masa baya tayi towel din jikinta ya kunce ya ɗanyi ƙasa, rabin Brest ɗinta ya fito waje, "saurin riƙe towel din tayi tana hawaye tace "kadena kallo na" idanunsa akan kirjinta yace "dama Ni ba kallon ki nake ba, ko kinga mun haɗa ido?" tana ƙara volume ɗin kukanta tace "gashinan kana kallar mun...." se kuma tayi shiru ta fashe da kuka, dama kaɗan take jira akan tsokarta da yay tayi da suna wanka, tashi yayi ya zauna a gefenta ya janyota jikinsa ya rungume yana murmushi yace "nifa ban kallar miki komai ba" cikin kuka tace "amma ai kagani a toilet" yace "shima ban kalla ba fa" ya ƙarashe zancen yana share mata hawayen fuskarta, shiru tayi jinta ajikinsa tana sauke ajiyar zuciya, gashin kanta ya shafa yace "to tashi muje in shiryaki, kinga time yana tafiya ba muyi break ba" barin jikinshi nayi nace "zan shirya da kaina" yace "shikenan jeki ki shirya" nace "toh rufe idanka, karka kalleni" ya rufe idon yace "na rufe" kallon fuskarshi nayi naga idanunshi a rufe, ta bayanshi na sauka daga kan gadon ina faɗin "karka juyo sai nace nagama" ya gyadamun kai, na ƙarasa gaban mudubi na fara shafa mai, inayi ina kallonshi ta cikin mudubi, harna gama shafe_shafe na be jiyoba, sai dai kuma ba kayan da zansa a jikina, tunda nawan ya jiƙasu suna toilet a shanye.........✍️ *By* *Zeey kumurya* *ABIN DA KA SHUKA...!* *7️⃣6️⃣* ........... Zama nayi a kan gado na dunk'ule guri ɗaya bance masa komaiba, jin shirun yayi yawa Mustapha ya juyo ya kalleta, keɓe fuska tayi tana turo baki gaba kanta a ƙasa, bece mata komai ba shima ya tashi ya ƙarasa gurin wardrobe ya buɗe ya dakko kayansa ya shirya, ƙofa ya nufa ganin haka Maryam tace, "yaya mezan saka?" batare daya juyoba yace "ki tashi ki dakko mana" bejira amsar taba ya fice, ɗakinta yaje ya dakko mata kaya da duk wani abu zata buƙata, inanan inda ya barni ina tunanin yanda zan iya fita a haka ya dawo, a ƙasan mak'oshi yayi mun sallama, nima na amsa masa a zuciya. Ƙarasawa yayi kan gadon ya ajiye kayan a gabanta, kallon kayan nayi na kalleshi nace "Nagode" ya gyada mun kai kawai, kasa shiryawa nayi duk da ga kayan a gabana, gashi ya ƙuramun ido kuma ya haɗe rai kamar ba shiba. Ganin tana ɓata masa lokaci yace "ke nake jirafa" nace "to ka fita inshirya Please" be tankamun ba, be kuma ɗauke idonshi daga kaina ba, turo bakina nayi hawaye na zubomun na fara shiryawa, tabe baki yayi ya tashi ya ɗauki wayoyinsa ya shiga latsawa, bayan tagama shiryawa tana d'aura ɗankwali ya dubeta yana murmushi yace "kinyi kyau sosai" nima kin kulasa nayi, murmushi yayi me sauti ya ƙaraso inda nake ya kama ɗankwalin yace "kawo in daura miki me kyau" sakar masa nayi, kasancewar kayan nata yadi ne me ɗan santsi saiya kasa daurawa, riƙeshi kawai yayi batare dayasan yanda ze fasaltashiba, cukurkuda mata yayi ya daura mata yace "nagama, kuma bakiga yanda ya miki kyauba sosai" nayi murmushi nace "Nagode bari na gani" na tashi na kalli madubi, dariya ce ta kusan kufcemun saboda wata inyamura dana koma, na danne dariyartawa nayi murmushi nace "kayi ƙoƙari amma bari na gyara maka" yace "ki mace banyiba" murmushi nayi na kunce daurin na sake wani. kama hannuna yayi muka fito falo, wayarsa ce ta fara ringing cikin sound me dadi, bebi takantaba ya zauna akan kujera tare da zaunar dani akan cinyarsa, wayar ya duba yabi bayan kiran ya kara a kunnensa. Ammi tayi masa sallama ɗaga ɗaya ɓangaren, ya amsa mata ya ƙara da faɗin "ina kwana ammi" ammi tace "lafiya kalau, NOOR naga har 10 ta wuce, ga breakfast ɗinkunan nagama tun dazu kazo ka daukar muku, danni bana iya fita idan ana ruwa, umaimah kuma bacci tace" yace "toh ammi ganinan" tace "toh" tare da kashe wayar, ya shafi fuskar Maryam datake kallonsa, a hankali nace "zan bika" yana saukeni daga jikinsa yace "part din ammi zani, na karbo mana break" nace "muje tare kaji" yace "ana ruwan zaki fita" ya ƙarasa zancen yana nufar ɗakinsa, Umbrella ya ɗakko ya fito ya tafi, be wani jimaba ya dawo, da kansa yayi sarving ɗinmu, ya ciyar dani, yace yau bazanyi komai ba shizemun. Soyayya,kulawa, da tarairaiya Maryam tasha su yau a gurin mustapha fiye da koyaushe tun auransu, ita kuwa se shagwab'a da taɓara take zuba masa, ya dakko wayar daya siyo mata ya bata, Maryam murna kamar ta kasheta...... *Bayan sati uku* Mustapha ne zaune yana kallon labarai a TV, lolaci zuwa lokaci yana kallon kofar ɗakin Maryam, tunda ya dawo daga sallar magriba bai sata a idonsaba, tana ɗaki wai fushi take akan yaƙi siyo mata sweet, sosai shan zakinta ya karu yanzu fiye da da, wanda ya kawo mata daga Kano basu fi sati ɗaya ba ta shanye, ya ƙara siyo mata wasu harta ƙara shanyewa, gashi batason cin abinci yanzu sai yayi mata dagaske yake ta samu taci. wayarsa ce tayi ƙara, ya ɗakko ya duba, Aunty ce take kiranshi ɗagawa yayi da sallama, bayan sun gaisa Aunty tace, "Muhammad, dan Allah inason na haɗa ka da suhailat kuyi magana, kwana biyunnan ta dameni bata da zance sai naka, ko abinci bata ci wlh, sai aikin kuka, damuwarta kuma matsala ce a halin yanzu, because of another reason." Mustapha yayi shiru na wasu sakanni kafin yace, "Aunty me zance mata kuma?" Aunty tace "just took to her koma mene Please!" yace "shikenan amma sai dai muyi chat" Aunty tace "why?" ya mata shiru, dan shi bayajin ze iya ƙara yin magana da suhailat a rayuwarsa, gwaradai chat ɗin, Aunty jin yayi shiru tace "ohk, kuyi chat ɗin" yace "Tom" sukayi sallama ya kashe wayar. Maryam ce ta fito daga ɗakinta, ajiyar zuciya ya sauke cikin jin daɗin ganinta, kallonta yake ta ƙasan ido tayi masa kyau sosai, tana sanye cikin wani riga da wando ƴan Pakistan Red colour, ta ƙara kyau da cika, hasken fatarta ya ƙara fitowa. bata kalleshi ba, itama kamar Yadda shima ya ɗauke kai kamar bai san da fitowartaba, kitchen ta nufa duk da bata da abunyi a kitchen din, ta fito ne dan taganshi kawai taji daɗi, ita kanta ta gaji da fushin datake dashi shi kuma yaƙi lallashinta, takai 10 minutes a kitchen din sannan ta fito, wayam taga falon bayanan, zama nayi akan kujera na sauya tasha na fara kallo, sai da aka kira sallar isha'i naga ya fito ɗaga ɗakinsa, ƙara ɓata rai nayi sosai na turo bakina gaba, murmushi yayi kawai ya kalleta ya fice zuwa masallaci, ganin ya fita na tashi na koma ɗaki nima danyin Sallah. Bayan ya dawo Aunty ta ƙara kiransa, ɗagawa yayi Aunty tace "nasata ta kunna wayarta ka mata magana, dan ita tanata maka magana tun kafin yau amma baka gani, yana nuna kamar kayi blocked ɗinta" yayi ɗanjim kafin yace "bani da Number ta" Aunty tace "Bari na tura maka" shiru yayi bayan sun gama waya Aunty yana tunanin me suhailat zatace masa, danshi ya riga da yayi deleting ɗinta gabadaya a cikin rayuwarsa, amma zai saurareta yanzu saboda Aunty. miƙewa yayi ya nufi gurin ƴar rigimarsa. ina zaune akan darduma idanuna a lumshe, so nake kawai najini a jikinshi dan baƙaramin missing ɗinsa nayi ba, yariga ya sabarmun koyaushe idan yana gida muna manne da juna. da sallama ya shigo ɗakin, buɗe idona nayi da sauri na juyo na kalli k'ofa tare da amsa masa sallamar, ba yabo ba fallasa yace "ki fito kici abinci" tashi nayi nabi bayanshi, a tare mukaci abincin kamar kullum, kuma a baki ya bani amma fuskarsa a haɗe sosai, ɗakinsa ya koma bayan mungama, bin bayansa nayi bayan na kawashe kayan da mukaci abincin na d'auraye, yana kwance akan gado yana latsa wayarsa bayan ya rage kayan jikinsa, tunda ta shigo ya k'ura mata ido, sosai shima yayi kewarta yayi kewar ɗumin jikinta dake saukar masa da nutsuwa, a ƙasan gadon na zauna ina turo baki gaba bance komaiba, murmushi yayi kawai aransa yana mamakinta, gaba-daya yanzu ta sauya abu kaɗan sai ta hau fushi, gashi indai be lallashetaba bazata kulashi ba, idan ya shareta kuka taita kuka tana damuwa. Tashi zaune yayi yana kallonta ganin yanda ta keɓe fuska zatayi kuka yace "zo" tare da ware mata hannunsa, da sauri na tashi dama abunda nakeso kenan na faɗa jikinshi ina sakin ajiyar zuciya, rungumeta yayi tsam a jikinsa shima yana sakin ajiyar zuciyar, a hankali yace "am sorry tawan, mun shirya ko?" girgiza kai nayi alamun a'a, yace "why?" A shagwabe nace "ba kaine kak'i kulani ba tun dazu" yayi murmushi yace "yanzu aina kula ki ko? kuma ai duk kece rigimar ki tayi yawa yanzu" na turo bakina gaba bance komai ba, na dora hannuna akan kirjinshi ina wasa da kwantaccen gashin kirjinsa, kissing lips ɗinta data turo gaba yayi yace "i missed you so much" nace "nima haka" gashin kanta ya shiga shafawa yana shishshina wuyanta, lumshe idona nayi cikin sanyin murya nace "yaya" yace "uhm" nace "zansha sweet da choculate" yace "babu" gashin kirjinsa naja tare da mintsinar breast ɗinsa, runtse idonsa yayi dan yaji zafi amma bece komai ba, bubbuga kirjinsa na shiga yi ina ƙananun kukan da babu hawaye, ɗagota yayi daga kirjinsa cikin lallami yace "mene ne?" nace "Sweet" ajiyar zuciya ya sauke yace "da safe zamuje ki zaba wadda kike so da kanki kinji" nayi murmushi cikin jin daɗin zan fita nace "dagaske yaya" ya gyadamun kai yace "promise" nace "thank you" ya lakacemun hanci yace "murna kike zaki fita ko?" nayi dariya nace "eh mana" yace "ina wayarki?" nace "tana ɗaki" yace "when last da kuyi waya da Aunty?" nace "3 days ago" yace "to albishirin ki" nace "goro" yace "a'a Ni banason goro" nace "me kake so?" yace "two things, saboda albishir ɗin dazan miki biyu ne" nace "me kake so toh?" yayi kasa da murya yace "kiss" na ɗan waro ido nace "da me kuma?" yace "something special for your own choice" na ɗanyi jimm nace "na yarda faɗamun albishir ɗin, na matsu inji" Yace "result ɗinku na NECO ya fito, gobe idan mun fita zamu biya capay mu duba" cikin farincikin nace "Alhamdulillah, naji daɗi sosai yaya, mafarkina ya kusa tabbata" yace "wanne mafarkin?" nace "na karatu" yace "kinason karatu ne?" nace "sosai ma yaya, burin innatama kenan taga nayi na karatu" yace "me kikeson karanta?" Nace "inason na zamu likitar mata" ya shafi kuncina yace "gud girl, insha Allah Zaki cika burinki very soon, amma sai kin haifamun kids" ya ƙarashe zancen yana shafa shafaffen cikinta, na shagwabe fuska nace "sai na tsufe kenan" yayi murmushi yace "A'a, a shekara nawa ne, kin haifamun, ni ko 3 kika haifa sun isa seki tafi karatunki" nace "idan ina karatunma ai zan iya hai....." sai kuma nayi shiru, yace "wahala zakisha, ga karatu ga rainon ciki ko baby, ki bari ki haifamun ko 2 ne, nayi miki alkawarin karatu har sai kince kingaji" na kwantar da kaina a ƙirjinshi, nace "Allah yakaimu lokacin" cikin jin daɗi yace "Amin" abunda yake ƙara burgeshi da ita kenan, kome yace mata tayi bata musa masa, koda bataso kuwa. nace "saura ɗayan albishir ɗin" yace "sai kin fara bani gorona" na dago da kaina nace to rufe idonka na maka, ya ɗan murmusa tare da lumshe idonsa, kallon small pink lips d'insa tayi na watsu sakanni, a hankali ta ɗora nata lips ɗin akan nasa ta fara tsotsa, hannunsa yasa abayanta ya ƙara mannata da jikinsa cikin jin daɗin yanda take tsotsar lips dinnasa kamar ta samu sweet, a hankali da dabara ya zira harshensa cikin bakinta ya fara bata wani hot kiss.... ya daɗe yana kissing ɗinta, da kyar ta samu ya barta, shima dan anata kiran wayarsa ne, kwantar da kanta yayi a kirjinshi yana shafa gashinta tare da sauke numfashi, luf nayi ajikinshi nima ina maida numfashi, a hankali ya ɗauko wayarsa, Aunty ce ta kirashi dataga be ɗagaba ta turo masa message na tura masa number'n suhailat ta whatsApp, baibi bayan kiran ba sai reply ya mata. cikin muryarshi datayi ƙasa sosai yace "Ummu" nace "uhm" yace "bacci" nace "um, um" yace "tashi inabaki ɗayan albishir ɗin" na tashi zaune yace "jibi Monday insha Allah Aunty tace zata zo ta ganki" na rungumeshi nace "Allah yakaimu, dama nayi missing ɗinta ita da Aliyata" yace "meyasa bakije kin gansu ba" nace "ai bazaka barni ba, kuma inaso inje sau ɗaya na taɓa zuwa fa" yace "ki bari zansa mana sai muje, bayan ta tazo" nace "toh" yace "to abani ragowar goro na" nace "kanason in maka waƙa?" yayi murmushi me sauti yace "banajin waka, amma indai ke zaki mun inaso, dannasan zatayi daɗi a wannan daddaɗar muryar taki" nayi murmushi na gyara zamana akan cinyarshi na fara rera masa wakar kamar haka: _labarii a zuciya kaine, soyayya ce taka tayi tasiri ɗan gataa._ _Ehh....burinaa, ko dare ranaa, roƙo Allah nai gamo da Alkhairii, cikin rainaa, tunaninaa, lissafi nake nai gamo mainurii, kaine nawa wanda naggani rannan, kana taffiya sawaye akan tsarii, kaine dai, muradindai, na kamu, da sanka da nadamu ɗan gataaah._ _Ehh...abin sonaa, kazamo nawaa, shi ranar farin ciki ba'a boyewaa, misali kaika kasance na nunawaa, koma meza'ayi kai bani canzawaa, ka'entani nadena rud'ewaa, babbar magana k'aunarka tai yalwaa, dakai zanii, taho janii, kalami naso daure kayi minni ɗan gata..... ɗan gataaah.......ɗan gataaah_. lips ɗinta kawai ya ƙurawa ido, yanda take motsasu abin sha'awa, ga muryarta datayi daɗi gurin karya wak'ar gwanin daɗi, kamar karta dena haka yaji. Ya sauke ajiyar zuciya yace "Wow tayi daɗi sosai wakar a bakinki, amma kuma naji kinyi shiru kici gaba mana" nace "aina gama, shikenan ita" yace "to ki ƙaramun wata" nace "ita kaɗai fa na iya, kabari sai na ƙara koyar wata zan maka" yace "a ina kike ji?" nace "a wayar Aunty zuhura na tura" yace "ok, muje muyi wanka, bacci nakeji" da mamaki na kalleshi nace "tun yanzu" yace "uhm" yana saukeni daga jikinsa, tare mukayi wankan kamar kullum, duk da har yanzu bandena jin kunyarsa ba, kamar yadda na kasa sabawa dashi a tarayyar auratayya, ko kayan bacci be bari sunsaba suka kwanta rungume da juna, bayan wasu mintuna yaji saukar numfashinta alamun tayi bacci, ajiyar zuciya ya sauke ya lallaɓa ya zareta daga jikinsa, turo baki tayi ta ɓata fuska sosai, tashi zaune yayi ya maye mata gurbinsa da filo, gyara mata kwanciya yayi ya lullubeta da blanket iya wuya, sauka yayi daga kan gadon ya kunna light ya ɗakko wayarsa, gefen gadon ya dawo ya zauna yana kallon Maryam ganin bata motsa ba, ya maida hankalinshi kan wayarsa, data ya kunna ya shiga whatsApp, Number'n suhailat da Aunty ta turo masa, yayi add to contact sannan ya shiga yayi unblock ɗinta ya mata "slm" suhailat dama tana online ɗin tana ganin ya mata magana ta shiga yi masa reply da sauri, daganan kuma ta shiga zuba masa maganganu, duk dai akan tayi missing ɗinsa ne, tanason ganinsa, sai turo masa emogi na kuka take wai ya dena sonta, shi dai kawai gani yake ba reply, a hankali ta buɗe idonta dan baccin yadena mata daɗi gabadaya, yanzu bata iya bacci kwata_kwata idan ba ajikinsa, ita kanta abun yana bata mamaki, ko sallar dare zai yi sai ta tashi itama, tashi zaune nayi a hankali ina kallon bayanshi da mamakin abunda ya tayar dashi, shida yace yanajin bacci, matsowa nayi kusa dashi cikin Muryar bacci nace "yaya" juyowa yayi da mamakin jinta a kusa da shi, yace "uhm, ina baccin?" na turo baki nace "ba ka tashi ka barni ba" na karashe zancen ina kwantar da kaina a kafaɗarsa, daidai nan wayarsa tayi ɗan vibrate alamar shigowar sako, kallon wayar nayi ba da niyyar komai ba, idona ya sauka akan sunan wanda suke chat naga ansa *baby suhailat*..........✍️ *By* *Zeey kumurya* *7️⃣7️⃣* ..........Kallonsa nayi da sauri ina tashi daga jikinsa zuciyata na wani irin bugu, _"baby suhailat"_ na maimaita sunan a raina, kallonta yake shima ganin yadda take binsa da wani kallo kamar na tuhuma, yanda ta kura masa ido ko kiftawa babu ya gane da akwai wani abu, ƙoƙarin janyota jikinsa yayi taƙi yarda, cikin mamaki yace "mene ne wai kike kallona haka?" banza na masa na runtse idona, ina jin wani irin tuk'ik'i a cikin raina, na manta da suhailat kwata_kwata a rayuwata, kenan ashe har yanzu suna tare basu rabu ba suna soyayya, wasu hawaye masu dumi ne suka zubomun daga ido na, mustapha dake kallonta tamkar ya samu TV yaji wani irin zafi a ransa, bayason zubar hawayenta ko kaɗan, datasan yanda yakeji a ransa data dena kuka kwata_kwata a gabansa, janyota jikinsa yayi da ƙarfi yace "meyafaru ne?" janye jikina nayi daga nasa nace "ka kyaleni kaje kacigaba da chat da baby'nka" sai kuma na fashe da kuka, sosai kalamanta suka taɓa zuciya tare da bata masa rai, sai yanzu ya gane akan me take masa haka, latsa wayarsa yayi dan ya duba yaga ko akwai inda ya cewa suhailat wani abu na soyayya ko baby, numfashi ya sauke da yaga sunan da yayi sarved number'n suhailat da shi, a haka Aunty ta turo masa da number'n, shikuma dayazo sarving a wayarsa be canza ba shima yayi sarving a haka, ajiye wayar yayi ya matsa kusa da ita, rungumeta yayi ya fara mata cikin taushin murya yana bata hakuri, amma Maryam taƙi saurarensa kukanta kawai takeyi, rarrashin duniya ba wanda mustapha bewa Maryam ba amma taki ji, yasan dama dole sai yayi fama, amma beyi zaton zata tirje haka ba, ƙarshe ma sai ta bar jikinsa ta koma can ƙarshen gado ta cigaba da kukanta, kyaleta yayi yana jin zuciyarsa babu daɗi ko kaɗan, kansa harya fara sara masa, wayarsa ya ƙara ɗauka, missed voice calls din suhailat ya tarar rututu da taita zuba masa ganin yayi offline, kashe datarshi yayi ya kashe wayar gaba-daya, a hankali na ƙara dawowa kusa dashi, kaina na dora akan kafadarshi ina cigaba da kukana, yana jinta ya mata shiru duk sautin kukan ta na ƙara bata masa rai, yasan shiya mata lefi domin koma ba ita ba, ko wacce mace ce taga haka zata nuna kishin ta, amma shi bega abun ta zauna taita masa kuka ba, bayason kukanta ko kaɗan, amma ita kamar an mata jajjagen albasa a ido, abu kaɗan sai kuka. juyowa yayi a hankali ganin bata niyyar dena kukan cikin tsawa yace "kimun shiru haka" dif ta ɗauke kukannata tana ƙara kankameshi, sosai ta tsorata dashi daya mata tsawar, ajiyar zuciya ya sauke me ƙarfi, a hankali ya janyota ta fado kan cinyarsa, rungumeta yayi tsam a kirjinsa yana sauke numfashi, cizon shi tayi akan brest d'insa, murmushi yayi kawai duk da yaji zafin cizon, dago ta yayi daga kirjinsa yana shafa Brest dinta yace "in rama?" lumshe ido tayi tana turo baki gaba, ya ɗan muntsineta kaɗan, ta kebe fuska kamar zatayi kuka, kissing lips dinta yayi yana murmushi ya jata suka koma kan gadon suka kwanta tana manne a jikinsa, juya masa baya tayi ta matsa daga kusa dashi, janyota yayi tare da juyo da ita cikin lallami yace "am sorry, kinsan bazan iya bacci bakya jikina ba" cikin shagwaba tace "bakai ka mintsineni ba" yana shafa kanta yace "to rama" gashin kirjinshi ta shiga ja tana muntsinin shi akan Brest d'insa, ita a dole ramawa take, cire hannunta yayi da zafi ya isheshi yace "ai kin rama" tace "nidai ban...." bakinsa daya dora akannata yasata yin shiru, ta shiga sauke numfashi, saida yayi kissing dinta sosai sannan ya kwantar da kanta a kirjinshi, ƙara kankameshi tayi tare da dora bakinta akan nipples d'insa tana tsotsa, numfashi yaja sosai saboda baƙon yanayin da yaji a jikinsa, bajimawa bacci ya ɗauketa. Ajiyar zuciya ya sauke ya lullubesu tare tofa musu addu'a. Washegari, kamar yadda ya faɗa suka fita da Maryam ta jido kayan zakinta, sannan suka biya ta capay aka duba mata result ɗinta, yayi kyau Alhamdulillah an samu abunda ake fata. Yau Monday, misalin ƙarfe 6 na safe Aunty ce zaune a dakinta tana shiryawa domin tafiya Jos, suhailat na zaune a gefen gado tana kallonta, tun da Aunty ta ce mata zatayi tafiya jikinta ya bata Jos zata duk da bata faɗa mata, a karo na babu a daɗi tace "Aunty dan Allah wai ina zaki?" Aunty a kufule tace "inda kika aike ni" suhailat tace "Please Aunty zan biki" Aunty tace "a hakan zaki bini gidan mutane?" suhailat tayi shiru batace komai ba, Aunty tacigaba da shirinta, can suhailat ta ƙara cewa "toh Aunty zani Kano Please" Aunty tayi shiru tana tunanin yakamata kuma suhailat ɗin taje Kano, ko dan damunta da Daddy da su haidar suke da tambayarta ita, amma kuma dole saidai suje tare dan tayiwa Daddy bayanin cikin dake jikin suhailat ɗin, Aunty ta dubeta tace "ki bari idannawo sai na kaiki, tunda ba jimawa zanba a inda zani, gobe zan dawo" suhailat cikin jin daɗin Aunty ta amince zata je Kano, tace "toh" kafin ƙarfe 7, Aunty ta gama shirinta tsaf ita da mamy zasu tafi, amma mamin bata ƙaraso gidantaba, a hanya zasu haɗu, saida tajawa Aliya kunne akan kome suhailat zata mata karta kulata, dan ma yanzu Aunty taga suhailat ɗin kamar tayi hankali. Saukar rana su Aunty sukayi, Maryam tana part ɗin ammi lokacin dan mustapha tun safe ya fice, muna zaune a falo naji sallamar Aunty, da gudu na tashi naje na rungumeta, itama rungumenin tayi cikin murnar gani na, sakinta nayi ina faɗin "Aunty sannu da zuwa" Aunty dake bin Maryam da kallo cikin jin daɗin ganin yanda ta ƙara kyau ba kaɗan ba, tace "yawwa Maryam ɗita" na bata guri ta shige na gaida matar da suka zo tare, ta amsamun cikin fara'a. ammi ta taresu da fara'a itama, bayan angama gaisawa nace "Aunty ina aliya?" Aunty tace "tana gida na baro ta" nace "meyasa baki taho da ita ba?" Aunty tace "saboda school, amma itama taso zuwa" nace "wannan satin zani biki Kano, idan angama bikin insha Allah zan biyo Kadunan" Aunty tace "Allah ya kaimu lafiya" muka amsa da "Ameen" Aunty ta dubi ammi tace "akwai kaya a mota, kuma suna da yawa, akwai wanda ze iya shigo dasu?" Ammi tace "ehh, bari nayiwa mai gadi da mu'azu magana" Aunty tace "toh, direbobin da suka kawo mu suna gurin sai su buɗe musu motocin" ammi ta amsa mata tare da fita waje, tashi nayi na kawo musu ruwa da juice, aunty bin maryam da kallo kawai take, ganin irin canzawar datayi bata wasaba, jikinta ya ciko sosai musamman kirjinta, ga farin data ƙara, kwanciya nayi bayan na kawo musu ruwan domin yanzu nafi jin dadinta fiye da komai, dakin ammi su Aunty suka shiga danyin sallah, ammi ta dawo su mu'azu na biye da ita a baya da manyan jakunkuna a hannunsu masu matuƙar kyau pink colour waɗanda ake zuba kayan lefe a cikin su, suka ajiye suka ƙara juyawa suka kwaso wasu, ɗai_ɗai,ɗai sai da suka shigo da guda goma sha biyu da wasu k'atun_k'atun ɗin leda guda biyu, da mamaki muke kallon kayan nida ammi, amma dai bamuce komai ba, sai da su Aunty suka idar da Sallah sannan take mana bayanin wai kayan lefe nane, mu buɗe mugani. sosai na cika da mamaki domin ban taɓa zaton haka ba, ammi kuwa farin ciki ne ya cikata ba kaɗan ba, domin dama tana da niyyar haɗawa Maryam lefen tunda ba'a mata ba, kaya na alfarma masu kyau da tsada Aunty ta haɗa, dan fiye da rabin kayan order'nsu aka mata ɗaga Dubai, kuma itama tasa kuɗinta a lefen, sosai lefen yayi kyau komai yaji enough, kayan sawa, takalma, mayafai hijabai, kayan bacci, unders, ƙananun kaya, abayoyi, kayan shafe_shafe dana kwalliya, turaruka jakunkuna ɗankunnaye da sarkokinsu, duk dai gasunan, sarkar gold har biyu ta sako ta zobe ɗaya, kallon kayan nake cikin tsananin farincikin wai duka nawa ne, abunda ban taɓa tsammanin zan samu koda kwatan_kwatansu ba, ammi ta rungume Aunty cikin farin ciki tana zuba mata Godiya, kimarta da kaunarta na karuwa a cikin ranta, domin duk wanda zai so ɗanka irin haka babban masoyinka ne. Aunty tace "kidenamun godiya haka ammi, domin nima mustapha ɗanane, duk abunda zanwa su aliya zan masa shima" ammi tace "hakane, Allah yabar zumunci mai ɗorewa a tsakaninmu, ya raya miki zuri'a" Aunty tace "ameen" matsawa nayi jikin Aunty a hankali nace "Aunty nah, nagode sosai Allah yasaka Alkhairi" Aunty ta shafi kuncin maryam tace "mijinki zaki yiwa godiya, dan kuɗin sane" nayi murmushi cikin jin kunya. kafin yamma kowa na gidan yaga lefen banda umaimah saboda batanan, har makota da ake mutunci duk sun shigo sun gani, kowa sai sam Barka da Masha Allah yake. Da yamma ina kwance a falonmu akan doguwar kujera, daga zuwa ajiye tsarabar da Aunty tamun na ɓige da kwanciya, da sallama ya shigo falon duk da beyi tunanin ze sameta ba, tashi zaune nayi da sauri ina amsa masa, tattausan murmushi ya sakarmun tare da ware mun hannayenshi, tashi nayi nima ina murmushi duk da banason tashin na ƙarasa gurinshi na faɗa jikinshi, hannunsa yasa ya zagaye bayanta suka saki ajiyar zuciya a tare, lumshe idona nayi ina shaƙar daddaɗan kamshinsa da nake jin daɗin sa fiye da koyaushe a yanzu, a hankali nace "sannu da zuwa" sai da ya rabani da jikinsa tare mun kiss a goshi sannan yace, "yawwa, yana ganki anan, nayi zaton kina can wurin Aunty" nace "yanzu na dawo, na ajiye abu ne, kuma na kwanta na kasa tashi." bece komai ba ya kama hannuna muka shiga ɗakinshi, muna shiga na hau kan gado na kwanta shikuma ya shiga cire takalmanshi, bayan ya gama ya cire har kayan jikinsa ze shiga toilet ya dube ni, yace "ba tayi" lumshe idonana nayi kawai na girgiza masa kai alamun a'a, bece komai ba ya shige toilet din, harya fito ina nan yanda ya barni ko kwakkwaran motsi banyi ba, ya gama shirinsa tsaf cikin ƙananun kaya da suka matukar yi masa kyau, sai tashin daddaɗan kamshinsa yake. kan gadon ya hau ya janyota ya ɗora kanta akan cinyarsa wuyanta ya taɓa yace "anya Ummu lafiyar ki kalau kuwa?" nace "meka gani?" yace "nidai kawai kalar me cuta kika mun" nace "toni babu inda yake mun ciwo a jikina, lafiya kalau nake" yace "zan kaiki dai hospital gobe, a dubaki" nace "ba sai mun jeba, Allah ni lafiya kalau nake" shiru yayi kawai yana kallonta, nace "kayi kyau" yayi murmushi yace "amma bankai kiba ai" nace "kama fini, wama ze haɗa" yace "ba kya kallon kanki a mudubi amma, kin ƙara kyau sosai, jikinki kamar madara" nayi dariya nace "kai kuma naka kamar nono" yayi dariya kawai tare da tashina zaune yace "muje ingaida Aunty" tashi nayi badannaso ba, muka fita, yana kulle Kofar part ɗinmu yace, "yawwa naga anmun wani text me daɗi ana zubamun godiya" nace "ohhh sorry, yanzuma na manta daka dawo ban maka ba, thank you so much, kuma akwai tukuici me tsada" yace "thank for what?" nace "komai ma" ba ƙara cewa komai ba ya kama hannuna muka nufi part ɗin ammi. Mustapha yayi farin ciki da mamaki sosai dayaga kayan da Aunty ta haɗo, shiya ma manta ana wani lefe a aure, wato shine dalilin kuɗin da Aunty ta karba a hannunsa, yana duba kayan kamar yadda Aunty ta umarceshi yace "amma Aunty, wannan kayan ai sun fi ƙarfin kuɗin da kika karɓa" Aunty tayi murmushi kawai, dan ita da ita zatayi lefen duka, wani dalili ne kawai ya sata karɓar kuɗinnasa, tace "to ai shikenan tunda dai an haɗa" yace "a'a Aunty ki...." Aunty ta katseshi da faɗin "ka kalli kaya kawai, amma baruwanka da nawa aka kashe" godiya sosai shima Mustapha yayiwa Aunty, shiyasa a kodayaushe yake ƙara kaunarta da ganin girmanta, domin Aunty mutum ce. washegari tun safe su Aunty suka koma, ammi tayi_tayi su ƙara kwana suka ce a'a, dama kawo kayan kawai suka zo. Yau Laraba, ana ie gobe zan tafi Kano bikin saleemat, tun safe ammi ta kira aka zo har gida aka mun kunshi da kitso me kyau, zaman kitson da lallen da nayi duk sai naji jikina babu daɗi, dama ta bakin yayan kwana 2 banajin daɗin jikina, kawai naki faɗa masa ne, dan nasan tsaf sai ya hanani zuwa bikin, jiyama yayi_yayi muje asibiti nak'i yarda, gashi yau ko abinci na kasa ci. Da daddare ina kwance akan gado a ɗakina, shikuma yaya yana haɗamun kayan da zan tafi da su, a cikin ɗinkakkun kayan lefena na ɗauka wanda zanyi fitar biki dasu, ya ɗauko wani less zai sa a cikin jakar dayake haɗa kayan nace, "karka sakashi, na fasa zuwa dashi" bai kulata ba, ya cigaba da haɗa kayan, ya lura rigimartata yau tafi ta kullum, tun jiya da daddare ya haɗa mata kayan tafiyar, amma yau da safe sai tace ta fasa zuwa dasu, ta sake zab'ar wasu ya haɗa mata, yanzu ma a darennan tace sai ya sake haɗa mata suma ba zata da su ba, gashi yau yana dawowa ta tareshi da rigimar an mata kitso mai zafi harda masa kuka kamar shi ya aiketa, ya rarrashe ta, anzo cin abinci kuma taƙi ci, tabarshi yaji da kewarta ta 1 week da zeyi mana. na bata fuska kamar zanyi kuka nace "yaya meyasa kasamun shi? ka cire Please nifa na fasa zuwa dashi, banason kalarshi" bai ko kalletaba balle tasa ran ze amsa mata, yana gama haɗa kayan ya fice daga ɗakin abinsa.......✍️ _*saura ƙiris mu huta gabadaya🥺*_ *By* *zeey kumurya* *7️⃣8️⃣* .........Tashi zaune nayi inajin ba daɗi a zuciya ganin yanda ya fita kamar ransa a b'ace, ni kaina banajin daɗi akan abin da nake masa, amma haka kawai nake tsintar kaina indai ina tare da shi, sai inta neman fitina,a kasalance na tashi na bi bayanshi, baya falo hakan yasa na nufi ɗakin shi, yana kwance akan gado yana latsa wayarsa, sallama nayi cikin sanyin murya, ajiyar zuciya ya sauke, a can ƙasan makoshi ya amsa mun, ban damu ba na haye kan gadon na kwanta a jikinsa ta baya, cikin shagwab'a nace "yaya" yay mun banza, na ƙara cewa "yaya" ya ƙara mun banza, sai na saka masa kukan shagwaba, lumshe idonsa yayi cikin rashin sanin abunyi, ganin yaƙi kulani sai na ƙara volume din kukan, juyowa yayi cikin faɗa yace "idan na ƙara jin uhm ɗinki, kin fasa zuwa bikin, idan kuma ba kijiba, ki cigaba" tsit nayi na kwantar da kaina a ƙirjinshi ina turo baki, yace "ɗaga mun jikina" ƙara riƙe shi nayi nace "kayi hakuri na dena" yace "ko d'igon hawaye karki bari ya ƙara fitowa daga idonki, idan kina so na haƙura" nace "bazan ƙara ba" ya shafa kitson kanta, yace "ki dena kuka baby tah, banajin daɗi idan kinayi" nace "to ba kai bane kake mun abunda nake kukan ba" yace "yanzu mena miki, kika zo kika cikamun kunne" nace "ba kace ƙunshi na yayi kyau ba, kuma nazo ina maka magana kak'i kulani" ya kamo hannuna yana shafa gurin ƙunshin yace "yayi kyau sosai" nace "bakaga na ƙafar ba" ya tashi zaune ya matsa gurin ƙafata ya duba lallen, yayi kissing ƙafar yace "shima yayi kyau sosai" nace "bakamun a hannun ba" murmushi yayi ya kama hannunnawa yayi kissing ɗinshi shima, nace "thanks" ina murmushi, yace "kitson ya dena zafin?" na ɗan shagwabe fuska nace "yanayi kaɗan_kaɗan" yace "sorry, zai dena duka insha Allah" nace "Allah yasa, kazo muyi bacci, bacci nakeji" yace "wanka fa" tashi nayi zaune nace "muje muyi to" Washegari tun safe Maryam aka gama shiri, sai murna take zataje Kano, mustapha kallonta kawai yake yana jin kamar yace ta fasa tafiyar, dan ma tare zasu tafi, amma tun yanzu ya fara kewarta. Sai kusan 11 suka yiwa su  ammi sallama suka tafi, dayake a Jet din Daddy zasu tafi, mustapha yayi waya anzo a ɗaukesu, dan baya son dogowar tafiya a mota, kuma  maryam ɗinsa ma bayason ta wahala a zaman Mota, cikin wasu mintuna suka sauka a Kano, Daddy ya turo direba ya ɗaukosu zuwa gidansa, muna shigowa layin su Daddy, na tuna rayuwata gidan, gabana ne ya faɗi dana tuno yaya Sadiq da mommy, lumshe idona nayi kaina kwance akan kafadar yaya ina tuna rayuwar gidan, kamar banyiba yanzu gashi komai ya wuce, shafa gefen fuskata da yaya yayi shiya dawo dani daga duniyar tunanin dana lula, d'ago kaina nayi ina bin gidan kallo dan har mun ƙaraso ciki, becemata komai ba dan bayajin daɗin zucuyarshi ko kaɗan, buɗe murfin motar yayi ya fita, ajiyar zuciya na sauke nima nabiyo bayansa, kama hannunta yayi suka nufi cikin gidan, a part din Daddy suka yada zango, dan daddy'n yana gida bai fita ba, Daddy kallon Maryam da mustapha kawai yakeyi cikin tsananin farincikin ganinsu, canzawar da Maryam tayi da ƙara gogewar datayi ya ƙara fito da kamar da mustapha da Maryam suke masa. Maryam tasha kararramawa da girmamawa a gidan Daddy, kamar ba ita ce da abar wulakantawa ba a da, su haidar suma sai nan_nan suke da ita, sai bayan magriba suka nufi gidan gwaggo, Maryam bata ga Sadiq ba, kamar zata tambayeshi kawai sai ta fasa, amma tayiwa Daddy da su haidar yame jiki. Mustapha da kansa yake driving ɗin su zuwa gidan gwaggo, Maryam na nuna masa hanya dan ba wani gane gidan yayi ba, yana yin parking baikai ga kashe motar ba, Maryam ta buɗe ta fita da gudunta ko handbag ɗinta bata ɗauka ba, ta shige gidan gwaggo tana kwala mata kira, gwaggo tana banɗaki taji muryar Maryam ta dogaro ƴar sandarta ta fito da sauri tana faɗin, "Muryar wa na keji haka kamar ta mutanen Jos" Maryam ta ƙarasa gareta ta rungumeta tare da faɗin "nice gwaggo, oyoyo gwaggo ta" gwaggo tace "oh ni ladi, zaki kadani" na saketa ina turo baki nace "gwaggo duk murnar ganin ki cefa" gwaggo tayi dariya tace"to ai kinsan ƙafartawa lallaɓawa nake" na  marairaice fuska nace "gwaggo wai har yanzu ƙafar batayi sauƙi ba?" gwaggo tace "sauƙi sai na Allah Maryama, inanan ina amsar magani dai" na kama hannunta muka fara tafiya nace "Allah ya karo sauƙi gwaggo,  sannu" gwaggo tace "Ameen, sannunki sannunki da zuwa, ya hanya, kunsha hanya" nace "Alhamdulillah" gwaggo ta miko mun dadduma na shimfida a ƙasan ɗakinta, muka zauna muka ƙara gaisawa, yaro ne ya shigo ɗauke da kayana, nace "Laa gwaggo tare fa muke dashi" gwaggo tace "mai gidannaki?" nace "Ehh" tace "kuma shine kika barshi a waje?" bata jira amsataba ta kalli yaron daya shigo da kayan tace "maza kacewa wanda ya baka kayan ya shigo" yaron ya amsa mata ya fice, nace "gwaggo ke kaɗai ce agidanne?" tace "asabe ta fita, na aiketa nan bayan layi yanzu zaki ganta ta dawo" miƙewa nayi na matsar da kayannawa na gyarawa yaya shimfudar daddumar, Ni kuma na koma bakin gado  kusa da gwaggo na zauna. Bayan 5 minutes yaya ya shigo bakinsa ɗauke da sallama, muka amsa masa, gwaggo ta tashi ta leka tace "shigo ciki mana, kamar wani bak'o" baice komai ba yashigo ya zauna, cikin miskilancinsa ya gaida gwaggo, gwaggo ta amsa masa da fara'a, daga gaisuwar bai ƙara cewa komai ba ya mike yayiwa gwaggo sallama ya fice, gwaggo ta dube ni tace "to kije kuyi sallama mana" na tashi nabi bayanshi, har ya shige motar dana fita kofar gidan, buɗewa murfin nayi na shiga nima da sallama, ya amsa mata cikin sanyin murya nace "yaya" yace "uhm" tare kallonta yana ƙoƙarin boye damuwarsa, na matsa kusa dashi ina shafa sajen fuskarshi nace "meke damunka?" numfashi yaja ya fesar ya juyo ya fuskanceta yana k'ak'alo murmushi yace "nothing" na kwantar da kaina a kirjinshi ina kallon fuskarsa, handbag ɗita ya mikomun yana faɗin "Take your bag, saboda zumuɗi kin manta da ita" ban karb'a ba, sai ƙara lafewa danayi a jikinsa, kwalla na zubomun, wata irin kewarsa na fara ji tun kafin mu rabu, haska fuskarta yayi da wayar hannunsa jin tayi shiru, abun da yayi tunani kuwa shi takeyi, taune lips d'insa yayi bece komai ba, dan shima ji yake kamar yayi kukan saboda yanda yakeji a ransa, murya ƙasa ƙasa yace "kukan na mene?" na turo baki gaba nace "yaya tafiya zakayi ka barni ko?" yace "Ehh, amma ai zan dawo na ɗauke ki mu koma gida" nace "yaushe?" Yace "idan kun gama biki mana" nace "a'a nidai kazo gobe?" ya shafi gefen fuskarta yace "gobe ba time, Daddy yace zani Abuja in the early morning" nasa kuka nace "to ni zan bika Abujan" runtse idonsa yayi kukanta na taɓa masa zuciya, ita kuwa kukanta take bil haqqi, bubbuga bayanta ya shiga yi cikin rarrashi yana hura mata iska a cikin kunnenta, shiru nayi ina sauke numfashi tare da ƙara kankameshi kamar zan koma cikinsa, nace "kaji yaya zan bika, ni banason kayi nesa dani" yace "Ummu bikinnaku fa?" cikin shagwaba nace "na fasa, binka zanyi" yayi murmushi yace "um'um, in tafi dake kitamun kukannannaki, kice sai na dawo dake" nace "Allah bazan maka ba" yace "baza fa ki bini ba, ba kincemun best freind ɗinki bace amaryar?" nace "eh" yace "to ai ba za taji daɗi ba, idan bakiyi attending bikin ba" nayi shiru bance komai ba, yayi murmushi jin yadda take ta kankameshi, dagota yayi daga jikinsa ya ɗora mata jakarta akan cinyarta, kuɗaɗe ya ɗauko bandir ɗin 1k, ya buɗe jakar ya saka a ciki yace "gashi ki bawa gwaggo" ya ƙara ɗauko wani yasa yace "wannan kuma ki bawa amarya" ya ɗakko bandir ɗin #200 guda biyu yasa yace "wannan kuma kiyi lik'i" kallonsa kawai na tsaya ina yi, ya ƙara ɗakko wani kuɗin yasa yace "wannan kuma na sweet ɗinki ne" cikin sanyin murya nace "yaya kuɗin sunyi yaw...." ya ɗora ɗan yatsanshi akan lips ɗina yana faɗin "shiiiiii" nayi murmushi ganin yanda yayi da fuska nace "Nagode sosai yaya, Allah yasaka da Alkhairi ya ƙara buɗi" yace "ameen" yana zugemun jakar, ya dago ya kalleni yace "sai yaushe?" ɓata fuska nayi sosai tare da turo baki gaba nace "yaushe zaka dawo daga Abujan?" yace "may be next tomorrow or Sunday" na waro ido waje nace "har Sunday, nidai ban yarda ba, yamun nisa" ya janyoni jikinsa yace "to yaushe kike so?" nace "jibi" yayi shiru na wasu sakanni, yasan aikin da zai yi a Abuja baze yiyu yayi shi a 1 day ba, amma saboda ya kwantar mata da hankali yace "Allah yakaimu" nace "ameen" yana dagoni daga jikinsa yace "kije gida, gwaggo na jiranki kuyi hira" na kwabe fuska nace "kora tama kake" yace "Ni na isa" na koma jikinsa na kwanta ina shaƙar kamshinsa nace "kasamun turarennaka a cikin kayana?" yace "ehh, nasa miki duka wanda nake amfani dasu" ya ƙarashe zancen yana kunna light din motar, wayarsa ya zaro daga aljihunsa gaban rigarsa ya latsa ya ɗauke mu a hoto, nayi dariya ya ƙara mana wani, ya mana da yawa sannan ya mun ni kaɗai, na karbi wayar ina dubawa nace "kaima bari na maka" yace "ai bazanyi kyauba" nace "nidai sai na maka" yayi murmushi har dimples ɗinsa suka loma sosai na masa hoton, na nuna masa nace "ka gani kayi kyau sosai, katuramun duka, ya turamun ta whatsApp, na ɗauko wayata na kunna data suka shigo, duba tsadadden agogon hannunsa yayi yace "zan wuce, Daddy na jirana" nayi shiru ina kebe fuska, fuskarsa ya matsar daf da tata a hankali yace "Please don't cry, ko bananan karkiyi kuka kinji" nace "bazan ba" yace "promise" nace "i promised" ya haɗe bakinsu guri guda ya fara kissing ɗinta, yayi 4 minutes yana kissing ɗinta, kafin ya zare bakinsa a hankali yana sauke numfashi ya kalli cikin idonta yace "i love You so much Habibty, and am gonna miss you" lumshe idona nayi cikin jin daɗin kalamansa bance komai ba, yayi kissing saman idona yace "ba reply" na turo masa kawai, yayi murmushi tare kissing lips ɗinta, ya kama hannunta yana messaging yace "byee" na buɗe idona na saukesu akan fuskarsa, tattausan  murmushi yamun na mayar masa tare da zare hannuna daga nasa, cikin sanyin murya nace "bye bye" jikina a matuƙar sanyaye na buɗe murfin motar na fita ina jin kamar na fashe da kuka, ya bita da kallo kawai kamar yace ta dawo, hannu na d'aga masa bayan na rufe motar, shima ya dagomun hannu, nayi murmushin ƙarfin hali na juya na tafi, gidansu saleemat na nufa, sai da yaga shigewarta sannan yaja ajiyar zuciya ya kunna motar yayi reverse ya tafi zuciyarsa cike da shauk'in ta da kewarta. ina shiga gidan su saleemat ana fara kiran sallar isha'i, da umma na fara cin karo tana jan ruwa a Rijiya, umma ta amsa sallamar da nayi ta ƙara da faɗin "Maryam!" Ina murmushi nace "na'am umma" umma tace "maraba  lale, sannunki da zuwa, saukar yaushe?" nace "yau ɗinnan nazo umma" saleemat dake banɗaki ta fito da sauri tazo ta rungumeni, nace "amarya bakya lefi" ta sakeni tana haskani da fitilar hannunta tace "ai kece amaryar, irin wannan kyau haka, ni ai badaban naji muryarki ba, bazance ke bace, zata zan wata balarabiyar ce" nayi murmushi kawai, tajani muka nufi ɗakinta, bayan na zauna ta ƙara haskani, nace "ke mene haka ne?" tace "wlh Maryam bakiga yanda kika canza ba, aurennan ya karbe ki" ina cire mayafin abayar danayi rolling nace "ya ranki" tace "fari tass" nace "ina angonki?" tace "hubbynah yananan kalau" muka shiga hira akan sha'anin bikinta, umma ta shigo ta kawomun ruwa muka ƙara gaisawa, anan nayi Sallah isha'i, ina cikin cin tuwon da umma data kawomun na dubi saleemat nace "ina autan umma ne, banji shiba" saleemat tace "bai shigo ba" nace "inason ya siyomun IBON ne, kar dare yayi" saleemat tace "alawa a darennan, ke kuma cikin da shan Zaki yazo miki?" nace "bani da wani ciki ni, sadaka zanyi da alawar" tace "ok, gogemun hadda, ai ana ganinki anga me ciki" nace "sai kuma kiyi" banbar gidansu saleemat ba, sai tara da rabi shima sai da gwaggo ta turo Asabe kirana, Sani k'anin saleemat ya siyomun IBON ɗita da yawa na juyeta a jaka bayan na basu tasu, kuɗin da yaya ya bani da 20k ɗin da ammi tabani na bawa saleemat na bata, sukai taimun godiya ita da umma, gwaggo ma ina zuwa na bata nata, asabe ma, na bata a cikin kuɗi na, tun kafin nayi wanka na kira yaya be d'aga ba, har nayi wanka na kwanta bai kira ba, na ƙara kiransa bai d'aga ba. har dare yayi sosai be kirani ba, Ni kuma na kasa bacci sai juyi nake akan gadon gwaggo, har gwaggo ta gaji tamun magana da faɗin "Maryam ko sauro ne, ya dameki?"  nace "um,um" da ƙyar na samu bacci ya ɗaukeni, dan sosai nayi kewar yaya. Mustapha kuwa yana can suna tattaunawa da Daddy akan harkar kasuwanci, sai da yazo bacci yaga missed call ɗin Maryam, yasan zuwa lokacin kuma tayi bacci, shiyasa bai kirata ba, ya bari sai da safe........ Anyi bikin saleemat Lafiya, angama lafiya, kwana uku akayi ana bikin, ran Friday akayi bridal shower, asabar kamu, Lahadi aka daura aure aka miƙa amarya gidanta, amarya da ango sun sha kyau ranar bukukuwa, kuma ango yayi ƙoƙarin kama guraren biki masu kyau daidai ƙarfinsa, kullum sai munyi waya da yaya, amma har yau Monday bai dawo ba, ayyuka sun sha masa kai, kullum saidai ya lallaɓani. ina zaune bayan sallar azhar ina cin dubulan da alkaki na garar saleemat wayata ta fara ringing, na dakko na duba ganin suna ammi yasani dagawa da sauri tare da yin sallama, ammi ta amsamun nace "ina wuni ammi" tace "lafiya kalau ɗiyata, ya taro?" nace "Alhamdulillah, yasu Aunty zuhura da mama?" tace duk sunanan kalau, yaushe zaku dawo ne?" nace "ammi har yanzu bai dawo daga Abujan ba" ammi tace "haka yacemun da mukayi waya, yace ayyukan da yawa" nace "haka yacemun nima, amma insha Allah wani satin zamu dawo" ammi tace "Allah yakaimu, ki gaida gwaggon naki da maman amarya" nace "zasuji insha Allah" mukayi sallama ta kashe wayar. kiran wayar yaya nayi bai dauka ba, na ajiye wayar cike da takaici, tashi nayi na dakko turarukansa daya bani, kullum sai na fesa su duka a jikina amma basa mun irin kamshin jikin yaya, kuma na masa complain yacemun da iya su kaɗai yake amfani, kwanciya nayi akan gado ina tunanin yaya, nayi missed komai nasa over, muryarshi, maganarshi, murmushin sa, kamshinsa, lallausar fatar jikinsa da nake lolewa kullum. na daɗe a kwance har saida gwaggo ta shigo tana faɗin, "Maryam kina d'aki a kwance, bazaki gidan amaryar bane? gashi can za'a tafi" na ɓata fuska nace "ehh" gwaggo tace "saboda me?" na mata shiru dan bazan iya ce mata kewar yaya ce take damuna ba, gwaggo  tace "ai shikenan, ki tashi kici abinci to" nace "naci dubulan na koshi" gwaggo tace "ke, Maryam ki raba kanki da shegen cin zakinnan, sai kinje kin haifi ɗa mara cikakkiyar lafiya ko?" nace "gwaggo nifa banda komai, tun da nazo kike fadar haka" gwaggo tace "to ai duk wanda ya san ciki, yana kallonki ya ga mai ciki" nayi shiru amma ban ɗauki zancen gwaggo da mahimmanci ba, tunda nasan nidai bani da komai, har dare yaya bai kirani ba, ni kuma ban ƙara kiranshi ba, ga kewarshi na daɗa addabata, har kuka nayi. Har washegari bai kiraniba, kuma banga ya hau online ba, hankali na ya fara tashi, yau babu walwala kokaɗan na tashi, jikina ma kamar mai cuta, ko abinci ban ciba, dama kwana biyu bana iya cin abincin. Wajen sha biyu na rana umma ta aiko in shirya zamuje gidan saleemat nida kanwarta, banso zuwaba amma haka na shirya muka tafi, mun jima a gidan kuwa muna shan hira, dan sai bayan la'asar muka dawo. Mustapha sai yau ya samu kansa ya baro Abuja, ayyuka sun sha masa kai ba kaɗan ba, yana abujanne amma hankalinshi gaba-d'aya yana gurin Maryam, yayi matuƙar kewarta, ji yake kamar baya tare da wani ɓangare na jikinsa, bai taɓa tunanin a rayuwarsa zai so mace irin haka ba, sati ɗaya da yayi basa tare, jinsa yake kamar wani mara lafiya, baccima dan dai ya iya sata ne, yake sake ci, gashi bazai iya barin aikin Daddy ya taho ba, amma da tuni ya dawo yaga ƴar matar tasa, jiya da yau baisamu kansa ba sai cikin dare, saboda yanda ya matse aikin yanaso yayi ya dawo, shiyasama bai samu ya kira Maryam ba, Bayan la'asar jirginsu ya sauka a Kano, yana zuwa gidan Daddy wanka kawai yayi,  yayi Sallah, ko abinci bai tsaya ciba ya nufi gidan gwaggo. ina kwance akan gadon gwaggo ina kallon pics ɗinmu da mukayi ranar a mota,  fitowata daga wanka kenan ko kaya bansaka ba. Mustapha ya turo yaro gidan gwaggo ya sanar da zuwansa, gwaggo tana zaune a tsakar gida tace aje ace ya shigo, ya shigo suka gaisa da gwaggo, gwaggo ta shiga masa godiyar kuɗin daya bata, shidai ya mata shiru, ta kwalawa Maryam kira, maryam bata jiba tana can duniyar begen *hearbeat* ɗinta, gwaggo tace masa ya shiga ɗakin, ya mike ya shiga. tsayawa yayi a bakin kofa yana kallonta, saboda ta juyawa ƙofar baya batasan da shigowarshi ba, Lumshe idona nayi jin kamshinsa da nayi missing na mun gizo a hanci, yanda kamshin yake ƙara ziyartar hancina yasa na buɗe idona tare da juyowa da sauri, gabana nane ya yanke ya faɗi, lokacin da nayi arba dashi tsaye a bakin k'ofa ya harɗe hannayensa a kirji, na rufe idona na ƙara buɗewa dan gani nake kamar gizo yakemun, wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyata dana tabbatar da shidinne, yayi mun murmushi tare da waremun hannayen sa, na tashi da sauri na ƙarasa na faɗa jikinsa, ya rungumeni tsam ajikinsa tare da sakin ajiyar zuciya yana faɗin "i missed you" na ɓata fuska sosai zanyi kuka nace "Ni ban yarda ba" yace "really" nace "bacin kaje ka daɗe, kuma jiya baka kirani ba, yauma haka" yace "kar kice haka, kinsan bazan taɓa kin kirankiba, duk a ƙoƙarin son nazo na ganki ne nayi busy" nace "to amma..." Ya katseni da faɗin "Am sorry, yanzu gani ai na dawo, mai kika ajiyemun?" na bar jikinshi ina murmushi nace "me kake so?" be amsa mata ba, sai bin jikinta da yayi kallo, kasancewar daurin kirji ne kawai a a jikinta, yana jin wani feeling ɗinta na bijiro masa, ya sauke numfashi ya shafi fuskarta yace "kinsan ke kaɗai nake so ai" na kwanta a jikinshi ina boye fuskata a kirjinshi, a hankali ya zare ta daga jikinshi yana fesar da numfashi yace "ki shirya, ina jiranki a mota zamu wuce gidan Daddy" nace "toh" ya juya ya fice dan idan yana kallonta zai iya yin abin kunya a gidan surukai. Cikin mintuna ƙalilan na shirya cikin wata doguwar riga mara nauyi irin me bin jikinnan, na ɗora hijabi akai, wayata kawai na ɗauka na fita tsakar gida nacewa gwaggo "gwaggo zamu gidan Daddy tare da yaya" gwaggo tace "to sai kun dawo, Allah ya kiyaye" nace "ameen" a cikin motar na samesa, yana latsa waya, ganin ta shigo ya ajiye wayar ya bita da kallo, na ɗan ɓata fuska nace "wannan kallon fa?" yace "naga kin ƙara kyau abinki" nace "hmmmm, nayi muni dai" zai yi Magana wayarsa tayi ƙara, dubawa yayi tare ɗagawa, bayan yayi sallama, an amsa yace "na ɗan fita ne, amma yanzu zan dawo" ya katse wayar, ya janyoni jikinsa, na lumshe idona nace "turarunka daka bani, basa mun irin kamshin jikinka" yace "kuma duka wanda nake amfani dasu na baki" nayi shiru kawai ina shaƙar kamshinsa da yake saukarmun da nutsuwa, ya kunna motar muka tafi. Bayan fitar Mustapha zuwa gidan gwaggo ba jimawa sukayi sabani da su Aunty sukuma sun zo, a part ɗin mommy suka sauka, babu kowa a gidan sai masu aiki da faruq dake kula Sadiq, Daddy da su Haidar duk suna gurin aiki basu dawo ba. Ko zama basuyiba Aunty taja suhailat  part ɗin Daddy suka duba jikin Sadik, suna zaune a falon Daddy, Aunty tacewa Faruq "Muhammad bai dawo daga Abujan bane? Munyi waya ɗazu yacemun before 5 jirginsu zai sauka, yanzu kuma naga 6 saura. Faruq yace "yadawo tun ɗazu, may be yana part ɗin shi yana hutawa" suhailat na jin haka ta miƙe ta fita ta nufi part dinnashi, Aunty batayi tunanin komai akan fitar suhailat ɗin ba, ta ɗauka part din Mommy zata koma, wayarta ta ɗakko ta kirashi, yace mata yafita amma gashinan zuwa. Muna tafe ina bawa yaya labarin bikin saleemat, har muka ƙaraso gida, beyi parking a parking space ba, har ƙofar part ɗinsa ya ƙarasa damu, suhailat dake tsaye a bakin k'ofar ɗinnasa tana jiransa, tana ganin mota anyi parking tasan shine, nufo gurin motar tayi da sauri, Mustapha ya buɗe murfin motar ya fito ya zagaya ya buɗewa Maryam ta fito itama, dai_dai lokacin suhailat ta ƙaraso gurin motar..........✍️ *By* *Zeey kumurya* *7️⃣9️⃣* ...........Wani wawan burki suhailat taja tare da waro idanuwanta duka waje, Mustapha yaga Suhailat sarai amma yayi kamar bai san da wanzuwar halittarta a gurin ba, ya kama hannun Maryam ɗinsa, tare rufe murfin motar. Suhailat ta haɗiye wani yawu mai ɗaci, ilahirin jikinta rawa yakeyi hannunta ta ɗaga da ƙyar ta nuna Mustapha cikin ƙara da rawar murya tace "yaya! wacece wannan?" gabanane ya yanke ya faɗi da naji muryar suhailat, domin bansan da ita a garin bama balle nayi tunanin ganin ta a gidan, riƙe hannun yaya nayi gam, ina kallonsa. Ya shafi gefen fuskata yana murmushi ba tare da yace komai ba, ya jani muka fara tafiya, Suhailat data sandare a gurin ta bisu da kallo, cikin tsananin tashin hankali mara misaltuwa, wani irin juyawa kanta yayi, lokacin da tayi katarin ganin Mustapha ya ɗauki Maryam cak a hannunsa kamar wata y'ar baby, lokacin da zasu haura kan step ɗin bakin part ɗinsa, dafe kanta tayi kirjinta na wani irin bugu, _"mafarki nakeyi ko gaske my life ne tare da wata mace, macen ma house girl ɗinmu, to me hakan yake nufi?"_ ta faɗi haka a fili cikin ƙaraji tana yarfe hannu, juyawa tayi tamkar mahaukaciya ta nufi part ɗinnasa, amma kafin ta kai har sun shige ya rufe kofarsa. bubbuga ƙofar ta hauyi tana faɗin "wlh bazan yadda ba, bazai yiyu ba, ina duniyar inganka da wata mace ba niba, wlh sai na kasheta!" ihu take tayi tana zuba surutanta, data gaji kuma sai ta bar bakin k'ofar ta kwasa da gudu ko nauyin cikin jikinta bata jiba ta nufi part din Daddy, a hanya suka ci karo da Aunty zata koma part din mommy, cikin tsawa Aunty tace "ke, baki da hankali kike gudu haka? kina lafiyar ki kuwa?" Suhailat ta tsaya tana zuba uban haki tare da fashewa da kuka tace "Yaya ne" Aunty tace "Muhammad?" Suhailat tace "Eh shine" Aunty bata ƙara cewa komai ba tayi gaba abinta, Suhailat ta bita a baya tana cigaba da kukanta, a falon Mommy aunty ta zauna tana faɗin "ke banason shirme, uban me Muhammad ɗin ya miki kika sani a gaba kina mun ihu haka, kuma me ya kaiki gurinsa ma?" Suhailat taja majina tace "Aunty tare fa naganshi da waccan kujakar yarinyar sun sauka a mota, kuma harda kama mata hannun" Aunty tace "ke mene naki a ciki to?" Suhailat da bata taɓa tunanin aure ne tsakanin Maryam da Mustapha cikin kuka tace "Aunty dole na damu mana, yaya fa shine wanda zan aura, kuma naganshi tare da wata, nasan duk dan ya k'untatamun yayi haka, Aunty dan Allah ki bashi haƙuri, nasan duk akan cikinnan yake mun haka" Aunty ta kalleta ta tabe baki kawai, Suhailat taci gaba da kukanta zuciyar na mata zafi da kuna, musamman idan ta tuna yanda mustapha ya ɗauki Maryam, a haukanta ita ta ɗauka duk abunda Mustapha yayi dan ya k'untata mata yayi dan tasan babu abunda zai haɗa Mustapha da Maryam wanda ya wuce aikatau, tasan abunda yayiwa Maryam ɗinma dan taji haushi yayi. A kan gadon ɗakinsa ya dire Maryam, lumshe idona nayi inajin ba daɗi sosai a cikin raina ganin Suhailat da nayi, takalmin kafarshi ya cire tare da zare mata na ƙafar ta itama, hawa kan gadon yayi ya zauna tare da ɗora kanta akan cinyarshi, a hankali ya zare mata hijabin jikinta gami da hular kanta ya shiga shafa kitson kanta yana sakin ajiyar zuciya. Buɗe idona nayi a hankali cikin jin daɗin yanda yake shafamun kan nace "yaya" ya ɗan fesar da numfashi yana bin jikinta da kallo yace "uhm" shiru nayi bance komai ba, yace "menene?" na ɗan turo baki gaba nace "ba komai" tattaremun rigata ya farayi ta ƙasa, na riƙe hannunsa zuciyata na ɗan bugawa, cikin cool voice yace "ciremun zanyi, kisha iska naga ana zafi" na tashi zaune da sauri nace "banajin zafi ni" ya janyoni jikinsa ya rungumeni a kirjinshi, a jiyar zuciya na sauke me ƙarfi tare da kwantar da kaina a ƙirjinshi, hannunsa yasa ya zagaye bayanta yana sakin ajiyar zuciya, yana jin yanda ɗumin jikinta yake ratsashi ga wani ni'imtaccen ƙamshi da take mai daɗi da kwantar da zuciya, bai yi yunƙurin yi mata komai ba, duk da yanda yake cikin tsananin buk'atuwa da ita. kiran sallar magriba ya sashi zare ta daga jikinsa a hankali yana sauke numfashi, komawa jikinsa nayi dan bangajiba, yayi murmushi tare da ƙara zareta daga jikinsa, na kwabe fuska tare da turo baki gaba, kissing lips ɗinta yayi yace "sorry, muje muyi sallah" ya ƙarashe zancen tare da sauka daga kan gadon, na bishi da kallo kawai har ya shige toilet, alawala ya dauro ya fito, na sauko daga kan nima ina kallonshi nace "ka tahomun da alawa Please bakina ɗaci" ya dagamun kai kawai ya fice. Bayan an idar da Sallah ina kwance akan gado ina game a wayata ya shigo ɗakin, bakinsa ɗauke da sallama, na amsa masa ina dubansa, tun da muka shigo na fuskanci yanayinsa gaba-d'aya ya sauya kamar na me ɓacin rai, tashi zaune nayi nace "sannu da zuwa" yace "yawwa" tare da mikomun hannu, sakkowa nayi na kama hannunnasa, gyara mata hijabin jikinta yayi ya jata suka fice, part ɗin Mommy ya nufa dasu domin su gaida Aunty, na ɗan shagwabe fuska nace "yaya ina alawata?" yay mun banza, shikam tunda yaga suhailat yaji ransa yayi wani mugun ɓaci, yaso yayi control ɗin kanshi gurin boye ɓacin rannasa dan kar Maryam ɗin ta gane, amma ya kasa boyewa, ga abunda ya gani a jikin suhailat ɗin ya dugunzuma masa hankali, yana fatan Allah yasa idonshi gizo ya masa, dan har yanzu yana kallon suhailat a matsayin ƴar uwarsa ta jini, a sanin da yayiwa suhailat ko tumbi bata dashi cikinta a shafe yake, amma yau duk da hijabi a jikinta ya ga cikinta ya ɗan turo irin na masu ciki, runste idonsa yayi tare da matse hannun Maryam yana jin wani irin ɗaci a ransa, ƴar ƙara na saki ya buɗe idonsa da suka fara kadawa sukayi ja tare da sassautawa mata riƙon hannun. Aunty na zaune a falo ita kaɗai, Suhailat kuma tana ɗaki ta kulle kanta tana kuka da bori kamar sabuwar kamu, sai yanzu take takaici da bata damk'o Maryam ta mata dukan mutuwa ba, amma ta kudirce a ranta indai suka ƙara haɗuwa sai ta yabawa aya zak'inta. Inayin sallama na hango Aunty kwace hannuna nayi na ruga da gudu na rungume Aunty cikin murnar ganin ta ina gaisheta, Aunty na murmushi tace "Lafiya kalau Maryam, ya biki" nace "Alhamdulillah" Aunty tace "Allah ya sanya Alkhairi" na amsa da "ameen" Aunty ta dubi Mustapha suka gaisa, bayan sun gama gaisawar ya tashi ya fice, binshi nayi da kallo harya fice, sosai na hango damuwa a tattare dashi, sai naji zuciyata duk babu daɗi, na sauke numfashi kaɗan na dubi Aunty nace "Aunty baki zo da Aliya ba?" Aunty tace "Ehh, basuyi hutun school ba" nace "shiyasa da mukayi waya batacemun zaku zo ba" Aunty tace "ai bazata faɗa miki ba, tanata fushin nace bazan zo da ita ba" nayi murmushi kawai, muka ɗanyi shiru na wasu mintuna, ni inata baza su ido inga ta inda suhailat zata bullo, can dai na dubi Aunty nace "Aunty ina baaba Talatu kuwa?" Aunty tace "tana garinsu, kinsan masu aikin gidannan duk sun tafi, sai masu mazaje masu aiki a gidanne kawai suka rage, tun da babu mace a gidan" nayi shiru ina tuna Mommy da yanda ta zuba iko a gidannan, amma yanzu kamar ba'ayi ba, "ko tana inama oho?" Sai bayan sallar isha'i yaya yazo muka koma part d'insa, har na taho banga ko da gifatawar Suhailat ba, shikuma har lokacin fuskarsa babu walwala, a falo ya zauna nima na zauna a kusa dashi, cikin lallami da karyar murya nace "yaya nah" ya juyo ya kalleta yana jin ɓacin ransa na raguwa, nace "meke damunka?" ya girgizamun kai alamar ba komai, na marairaice sosai nace "dan Allah kayi haƙuri ka faɗamun, ko ni na maka wani laifin?" na ƙarashe zancen idona na kawo ruwa, janyota jikinsa yayi yace "karki kuka Please" na turo baki nace "to ka faɗamun meke damunka, tun ɗazu sai bata rai kake kuma kaki kulani" yayi murmushi yana kallon fuskarta yace "dagaske babu komai, ina tare da ke mai zai dameni" ganin ya saki fuskarsa sai naji daɗi sosai a raina ina kallon cikin idonshi nace "banason naga kana damuwa ko kaɗan" ya lumshe idonsa cikin jin daɗin maganarta yace "dagaske" nace "dagaske mana yaya" ya ƙara rungumeni a jikinsa, knocking din da akeyi yasashi sauketa ya tashi yaje ya buɗe Kofar, faruq ne hannunsa ɗauke da leda da yayi musu take a way na abinci da drinks, Mustapha ya karba ya dawo ciki, yunwa nakeji sosai dan rabona da abinci tun safe shima kaɗan naci, shiyasa yana kawo wa ba musu na zuba mana muka fara ci, da kanshi yake bani a baki, kuma duk lauma ɗaya idan naci sai yamun kiss a saman lips ɗina, wai dan nafi cin abincin da yawa, aiko naci sosai dan abincin yamun daɗi. Bayan mungama mukaje part din Daddy muka gaisheshi, Daddy ya dubi Mustapha yace "yaushe zaku koma gida?" Yace "Gobe insha Allah" Daddy yace "yaushe zaku dawo Kanon gaba-daya da zama?" yace "Bayan sallah kamar da sati biyu haka" Daddy yace "Allah ya kaimu, itama ammin taku zata dawo Kanon da zama insha Allah" Mustapha ya murmusa kawai baice komai ba, bamu jima sosai ba muka dawo part ɗinsa, wanka kawai mukayi muka kwanta. Aunty ce zaune a falon Daddy ita da Suhailat data taso ta da ƙyar, Daddy kawai ido ya zubawa Suhailat gumi na yanko masa ta ko'ina a jikinsa, idanunshi sun kada sunyi jajur saboda tsananin ɓacin rai da kunar zuciya bayan Aunty ta gama rattabo masa jawabi akan cikin dake jikin Suhailat, Aunty ta kwantar da murya ganin yanayinsa tace "kayi haƙuri yaya, kada ka sanya damuwa a ranka har wani ciwon ya kamaka, bawa baya taɓa kaucewa ƙaddararsa, wlh nima ba ƙaramin tashin hankali na shiga ba a lokacin dana gane tana da cikin, na kulle kaina a daki ni kaɗai naci kuka na, daga baya kuma na fawwala wa Allah komai." Daddy ya sauke numfashi kawai baice komai ba, tsana da danasanin auran Mommy suka ƙara cika masa zuciya, domin duk lalacewar da suhailat tayi ita ta ɗora ta akan hanya, itace silar lalacewar tata, ya dubi Aunty yace "nama rasa me zance sauda, jin abunnake kamar almara ƴar ɗan'uwa guda ɗaya jal da ya barmun amanar ta itace take ɗauke da cikin shege" sai kuma yayi shiru yana maida numfashi, itadai Suhailat tana durk'ushe tana kuka, Aunty ta danne tata damuwar cikin kwantar da murya ta shiga bawa Daddy baki, ganin yanda ya damu matuƙa fiye da yanda tayi tunani, da ƙyar ta samu Daddy'n ya sassauta damuwarsa yace "shikenan Sauda, babu yadda zanyi nasan wannan wata jarrabawar ce daban, kuma zanyi ƙoƙari wajen ganin na cinyeta, Allah ya bata lafiya ita da abunda ke cikinnata ya kuma raba lafiya" Aunty tace "ameen" Daddy ya dubi Suhailat yace "kafin ku koma kadunan, ki turomun wanda ya miki cikin zamuyi magana" yana gama faɗar haka ya tashi ya shige ɗakinsa, dan Kaɗaici kawai yake buƙata a halin yanzu, Aunty taja Suhailat suka koma part ɗin Mommy, Suhailat ta tambayi Aunty ina Mustapha ya kai sau biyar amma Aunty ko sau ɗaya bata ganka mata ba, ta mata banza. Washegari misalin ƙarfe goma da ƴan mintuna na safe, mustapha ne kwance akan doguwar kujera yana kallon Maryam data ke ta ɓata rai tana turo baki, tun bayan da suka karya tace ya kaita gurin Aunty shikuma yaki, saboda yasan bacci takeji dan jiya be barta tayi wani baccin kirki ba, ya rarrasheta akan tayi baccin yanzu kona 1 hour ne amma taki, shikuma yaƙi barinta taje gurin Aunty'n, shine ta kwace wayarsa ta matsa daga kusa dashi ta koma wata kujerar ta zauna, shikuma ya tasata a gaba da kallo yana murmushi, dan kallonta kaɗai ma ya isa sanyaya masa zuciya, wayarsa dake hannuna nace ta fara ƙara, dubawa nayi naga number ce babu suna, k'in bashi nayi harta katse aka sake kira, ya tashi zaune tare da faɗin "a bani wayata mana, tunda ana kira na ko" na turo baki gaba na tashi na kai masa, ya karbi wayar tare da janyota ta faɗa jikinsa ya matse gam yanda baza ta iya tashi ba, nima banyi yunƙurin tashin ba nayi luf a jikinsa, d'aga wayar yayi ya kara a kunne, Muryar mace yaji kuma kamar yasan muryar, daga ɗaya ɓangaren aka ce "Ranka ya daɗe, dafatan ka tashi lafiya" yace "lafiya" a taƙaice, ta ƙara cewa "nasan har yanzu baka gane da wa kake magana ba, kana magana da P.A dinka ce" yayi shiru kamar yadda nayi shiru ina sauraren sautin muryar mace da naji, can yace "Ok nagane" P.A tayi murmushi cikin jin daɗi tace "na kira in gaishe kane, in maka ya jiki da kuma jajen abubuwan da suka faru" cikin mamakin yanda akai P.A tasan abubuwan yace "Ok thank" tare da kashe wayarshi. na d'ago kaina nace "dawa kayi waya?" yayi wani munafukin murmushi yana kashemun ido yace "budurwatace" nace "wacece ita?" yace "nace miki budurwa tace, kuma kinsan me?" nayi shiru ina ɓata fuska sosai, ya ƙara kashemun ido yace "tana sona sosai, kullum tana cemun I LOVE YOU" na fashe da kuka ganin da gaske yake, har wani nishaɗi yake yi yana faɗamun wai tana sonshi" yace "menene kuma na kuka, tambayata fa kikai na faɗa miki" cikin kuka nace "to sai ka faɗamun kuma, ba sai kacemun watace da banba amma ba budurwa kaba harda wai...." na kasa ƙarasawa naci gaba da kuka na yace "sai nai ƙarya kuma, a'a gwara dana faɗa miki gaskiya, budurwace tana sona sosai kamar ranta, ko da yaushe tana cemin I LOVE YOU" ya ƙarashe zancen da kissing lips ɗinta yana murmushi, kuka nasa sosai na shiga dukan kirjinsa ina kukan nace "ai nima ina faɗa maka" yace "baki taɓa faɗa mun ba ni" na masa banza na cigaba da kukana, ganin yanda take kukan bil haqqi ya shiga rarrashin ta, taƙi saurarensa, bakinta ya buɗe a hankali ya zira mata lips ɗinsa, da sauri na cafka na fara tsotsa kamar jariri na shan nonon uwarsa ina sauke ajiyar zuciya, inajin daɗin sucking lips ɗinsa sosai yanzu, sai inji kamar na samu sweet, ya sauke ajiyar zuciya jin tayi shiru ya shiga shafa bayanta a hankali, sai da na tsotse masa lips ɗin son raina sannan na cizeshi kaɗan, ya zare bakinsa da sauri daga nata yana sauke numfashi, na kwantar da kaina a ƙirjinshi ina turo baki gaba, ya leko da kansa wajen fuskata yace "sweetheart harda cizo kuma" nace "um" yace "da zafi fa" nakai finger na kan lips ɗinnasa nace "sannu" yace "yawwa" tare da sharemun hawayen fuskata, ya dagoni daga jikinsa yace "muje mu gaida Daddy da Aunty, tunda kinki yin baccin" na tashi na shiga ɗaki na dakkona hijabina na fito, ya mikomun hannunsa na mak'e kafada naƙi riƙe masa, ya matso kusa dani yace "to zo in ɗaukeki" na ƙara maƙe kafad'a, yace "goyo fa" da sauri na d'aga masa kai, yayi murmushi ya tsugunna yace "hau" na haye bayansa ina dariya yace "shikenan" nace "Ehh" ya tashi tsaye yana faɗin "wash kina da nauyi fa" na masa gwalo ina dariya, a bakin k'ofar part d'in ya sauke ni yana maida numfashi, yace "kin sagarmun da baya" nace "sannu, amma goyon da daɗi zaka kuma mun?" ya murmusa yace "zan dinga miki kullum ma" cikin jin daɗi nace "Nagode" ya kama hannuna muka fice, part ɗin Mommy muka fara zuwa muka gaida Aunty, aunty kallon Maryam kawai take yanda taga ta ƙara dashewa tayi fari ga nishi da takeyi kaɗan_kaɗan irin na masu ciki. Bayan sun gaida Daddy ya ɗauketa suka nufi gidan gwaggo. Mommy Tasha cinya sosai, daga ciwon kannan ya koma mata cuta mai tsanani, Binta kawartace ta samo mata mai kula da ita tana biyanta, Mommy kamar bazata rayu ba, sai a satinnan ta fara samun sauƙi, ta rame sosai tayi baƙi ga wasu kurashe manya duk sun fito mata a jikinta, yau ta tashi da jikinnata da kwari babu laifi, tun safe ta shirya zasu fita ita da Binta, duk da har yanzu ba wai lafiyar ta isheta bane amma tsabar masifa zata fita, tana ciwonne amma hankalinta gaba-d'aya yana kan Daddy da Mustapha akan mummunan kudirinta akansu, yanzu fitar daza tayima zataje tayi visa ne na zuwanta London neman Mustapha, tana ta jiran Binta zata rakata amma shiru_shiru bata zoba, gashi tana ta kiran wayarta bata shiga, ganin har 12 ta wuce ta ɗauki mukullin motarta tayiwa mai jinyarta sallama ta fice dan zuwa gidan Binta. Mustapha suna zuwa gidan gwaggo basu wani jimaba Maryam ta kwaso kayan ta ta musu sallama, Mustaphama ya shiga yayi wa gwaggo sallama shima, har gidan umman saleemat ma ya shiga ya mata Allah ya sanya Alkhairi, sannan suka tafi. A titin commissioner road Mommy tazo zata karya kwana, su sukuma su Mustapha suna ɗayan hannun an tsaidasu, kamar ance Mommy ta juya, tana juyawa tayi katarin ganin Mustapha kasancewar glass din motar tasu a zuge yake........✍️ *By* *zeey kumurya* *ABIN DA KA SHUKA....!* *8️⃣0️⃣* *Bismillahirrahmanirrahim* .........Cikin tsananin kad'uwa Mommy ta bisu da kallo kirjinta na mahaukacin bugu, gaba-d'aya ma ta manta tuk'i take a tsakiyar babban titi, gani take tamkar mafarki take zata farka ba Mustapha'n ta gani ba, mutumin da take nemansa ruwa a jallo, horn d'in da ake ta danna mata ya dawo da ita cikin nutsuwarta, tuk'i tacigaba dayi slowly tana waigen su Mustapha, ganin anbasu hannu sunyi gaba yasata juya motarta da sauri a ƙoƙarin ta na zagayowa ta bi bayansu, wata Babbar Mota ce ta danno kai, tunda titin yana tafiya ne a hannu ɗaya, Motar baisan da motar Mommy ba, tunda yasan yuturn akeyi idan mutum zai zagayo, a guje ya taho hakan yasashi yin ciki da motar Mommy tayi tsalle ta jirkice a tsakiyar titi. Mai motar bai tsayaba yayi gaba abinsa da mugun gudu, tsayawa mutane suka fara yi na cikin Mota suka fara fiffitowa da tsirarun masu tafiya a ƙafa, aka fara ƙoƙarin ceto ran Mommy, sai da aka ɗaga motar sannan aka samu aka zaro ta cikin mawuyacin hali, jini na zuba a jikinta, wani bawan Allah ne yayi shahada yace a sata a motarsa, aka nufi Asibin Nasarawa da ita. Sai da suka biya ta super market suka yiwa su ammi tsara ba sannan suka koma gidan Daddy, anayin sallah azhar Mustapha yace su tafi, Maryam bata soba tayiwa Aunty sallama suka tafi, Daddy kuwa sai da ya rakasu har airport. Suhailat bata samu bacci ba a daren jiya, sai da garin Allah ya waye baccin yayi gaba da ita, har su Maryam suka tafi bata tashi ba, Aunty tanata buga mata kofa tun safe ko dan ta tashi ta karya amma taƙi tashi, sai bayan tafiyarsu Mustapha ba jimawa tatashi, Aunty tana daki tana waya da Abban su Aliya, Suhailat ta shiga ta sameta, zama tayi ta jira Aunty'n ta gama wayar, Aunty ta dubeta fuskarta babu walwala sam tace "Sai yanzu kika ga damar tashi?" Suhailat tace "Banyi bacci bane jiya, sai da safe na samu ya ɗaukeni" Aunty tace "meya hanaki baccin?" Suhailat tayi shiru, Aunty ta tab'e baki tace "kije kiyi ta sa damuwa aranki, tun kina yar ƙaramarki kijawa kanki wani ciwon" Suhailat tana hawaye tace "Aunty wlh inason yaya sosai, kuma kun sani, amma shi naga yanzu ya dena sona baya tani, ko nemanama bayayi" Aunty tace "amma tun kwanaki da kika damu danki kika ƙi ci kika ƙi sha nace miki kibar wata maganar yaya sai Allah ya saukeki lafiya ko?" Suhailat tace "Aunty wlh bazan iya ba, ni kaɗai nasan yanda nake ji a raina, dan Allah ki rokeshi ya dawo mu cigaba da rayuwar mu kamar da" ta ƙarashe zancen tana fashewa da kuka. Aunty tayi shiru cikin jin tausayinta, tana ji a ranta da zata iya da tasa Mustapha ya aure ta, amma tasan idan tayi haka tayi rashin adalci, dan Suhailat sam bata dace da kamilin namiji irin Mustapha ba, sai dai idan shi ya furta yana sonta da kansa. Aunty ta dubeta da kyau tace "Suhailat Muhammad ɗin da kika sani yanzu ba na da bane, yanzu rayuwarsa ta canza zaiyi wuya ya iya auranki, musamman idan yasan abinda kika aikata" Suhailat ta d'ago da sauri tana kallon Aunty tace "Aunty bangane rayuwarsa ta sauya ba, kuma dama baisan ina da ciki ba? to Meyasa yakemun haka? Ko akan abunda Mommy ta masa ne?" Aunty tace "ko ɗaya ba akan abinda Aunty Atika ta masa bane, Mustapha yanzu yana rayuwa ne cikin nutsuwar da kwanciyar hankalin da ya rasa a da, Muhammad yayi gamo da mahaifiyarsa, kuma da ita yake rayuwa a Jos sannan kuma a halin yanzu yana da mata wato Maryama dan haka....." mikewa tsaye Suhailat tayi Zuciyarta na wani irin bugu, ilahirin jikinta ya ɗauki rawa kamar an jona mata shocking, so take tayi magana amma ta kasa, wata ƙara ta kwalla tare da zubewa ƙasa a suma, Aunty dake kallonta tayi kanta cikin tashin hankali tana kiran sunanta tare da jijjigata, Fahimtar da tayi suma tayi yasata tashi ta ɗauko ruwa mai sanyi a cikin fridge ta shiga shafa mata a fuska zuwa wuyanta, Suhailat taja wani dogon numfashi tare da buɗe idonta da suka matuƙar yi mata nauyi a hankali ta saukesu akan Aunty, Aunty cike da tsananin tausayawa tace "sannu Suhailat" Suhailat ta fashe da wani irin kuka hawaye masu ɗumi suna kwaranyo mata, cikin kukan tace "Aunty dan Allah dagaske kike yaya yayi aure da waccan yarinyar?" Aunty tace "Ehh, Suhailat idan zan baki shawara ki ɗauka ki cire Muhammad daga ranki tun wuri, dan yanzu ba take yake ba" Suhailat ta yunkura ta tashi zaune numfashinta na fita da kyar tace "Aunty bazan iyaba, wlh bazan iya jurar rashinsa ba a rayuwata, komai zai faru sai dai ya faru amma wlh sai na aureshi, aida yana sona sai dai in shiga tsakaninmu a kai, a yau ba a gobe ba sai na bishi har Jos ɗin" Aunty data saki baki tana kallonta tace "Tun farko Suhailat ke kika cushi kanki, da'ace baki ɓata rayuwarki da yawon banza ba, dana san tabbas Mustapha ke ze aura" Suhailat bata bi takan maganganun Aunty ba ta cigaba da maganganunta na hauka cikin ihu kamar zautacciya, Aunty ta shi zata fita ganin abunnata harda iskanci, kafin ta kai ga fita faruq ya shigo a gigice yana faɗin "Aunty! Aunty!' a dan ruɗe Aunty tace "lafiya faruq kake mun wannan kiran, ko wani abu ne ya samu Sadiq ɗin?" Faruq cikin tashin hankali yace "yanzu wani freind ɗina likita a Nasarawa hospital ya kirani, wai an kawo Mommy sunyi accident kuma tana cikin mummunan hali" Aunty tace "Subhanallah dama Aunty Atikan tana ƙasar nanne?" Yace "ban sani ba Aunty, dannima tunda tabar gidannan rabona da ita" Aunty ta dafe kanta tana kiran "innalillahi..." Suhailat ma shiru tayi tana sauraren faruq, Aunty ta dubeshi tace "kaje asibitin yanzu da sauri, ni zan zauna gurin Sadiq kafin yaya ya dawo, sai mu taho asibitin muma, ka kira su Haidar ka sanar musu" ya amsa da toh sannan ya fice, Aunty tabi bayanshi zuwa part din Daddy domin kula da Sadiq zuciyarta cike da jimanta accident din Mommy, suka bar Suhailat nan zaune zuciyarta na mata wani irin zafi da k'una, yanda takeji a ranta a yanzu idan tayi arba da Maryam zata iya kasheta, ko kaɗan labarin accident d'in Mommy bai wani daga mata hankali ba, ita damuwarta kawai akan Mustapha ne. Aunty tana zaune a falon Daddy cikin damuwa Daddy'n ya dawo, miƙewa Aunty tayi fuskarta na nuna tsantsar damuwa tace "yaya kaji wai Aunty Atika tayi accident" Daddy cikin rashin damuwa yace "when" Aunty tace "yanzu faruq ke faɗamun yama tafi asibitin" Daddy yace "Allah ya sawwake ya kiyaye gaba" yana ƙoƙarin hayewa sama Aunty ta tsaidashi da faɗin "haba yaya, yanaga kana ƙoƙarin shigewa, kamata yayi ai ka tafi asibitin kaima, amma naga ko damuwarka baka nuna ba" Daddy yace "damuwar me kuma zan nuna akan macen data zama silar sanyani cikin tashin hankali, macen da babu Alkhairi kwata_kwata a tattare da ita sai sharri, macen da..." "Haba yaya, abinda ya faru ya riga daya wuce, kome tayi dan kanta, aiko ƴaƴanta da suka gujeta ya isheta ishara, kai kuma ko dan darajar ƴaƴan dake tsakanin ku kaje ka dubata, dan faruq bakaga yanda hankalinshi ya tashi ba, kuma kasan da yafi kowa jin takaicin abinda ta aikata yafi kowa yin burus da ita, amma dake uwa uwa ce yanajin tayi hatsari hankalinshi ya tashi bakaga ba, a gigice yazo ya faɗamun" Daddy ya sauke nannauyen numfashi yace "shikenan bari naje driver ya kaini" Aunty tace "ko kaifa, Allah ya kiyaye sai munyi waya naji jikinnata, nima inna gama abunda nake zanzo asibitin" Daddy ya amsa mata tare da ficewa daga ɗakin, Aunty kuma ta shiga kitchen ta fara kiciniyar dafa abinci. Mun sauka lafiya a garin Jos, Part ɗinmu muka wuce direct muka ajiye kayanmu, kwanciya nayi akan gadon ɗakinsa ina maida numfashi, ya dubeni yace "taso muje part ɗin Ammi" na daure na tashi ba dan nasoba saboda naji daɗin kwanciyar, ya kama hannuna muka fita, muna tafiya nace masa "kuma yaya bamu biya ta kadunan ba" yace "to ba Aunty'n tana Kano ba" nace "hakane fa" ammi ta tarbemu cikin tsananin murna da farin ciki, muna munyi murnar ganinta dan munyi kewarta ba kaɗan ba, abinci kala_kala ta mana na tarbarmu, bayan mun gama cin abincin yaya ya fita ni kuma na zauna muna shan hira dasu ammi da Aunty zuhura, sai dare na koma part ɗinmu. *BAYAN SATI D'AYA* Duk wata alama da zata nuna Maryam tana da shigar ciki ta bayyana, amma ita da Mustapha basu gane ba, kasancewar basu san takan abun ba, bata da aiki yanzu sai kwanciya dan ko a zaune take sai ta dinga jin jiri, ga kwadayin dare data fara, rigima da shagwaba kuwa harda na siyarwa dan yanzu har ammi yi mata take. Mustapha sun koma Kano shida ammi sun dubo jikin Mommy, wadda ke kwance rai a hannun Allah bata masan inda kanta yake ba, ta samu karaya a hannu da kafa duka na dama, sai kuma buguwa da tayi akai da ƙananun ciwuka abun dai babu kyan gani, jikin Sadik ya fara sauƙi tunda yanzu har yana gane inda kansa yake, amma dai duk da haka sai dai a kwantar a tayar. Suhailat sosai ta tada hankalinta a cikin satinnan, bata da aiki sai kuka ko abinci bata iya ci sai Aunty ta tilasta mata take dan watsawa kaɗan, tayi baƙi ta rame duk ta fice daga hayyacinta, kamar ba ita ce wannan uwar gayun ba, to ga ciki gashi tasawa kanta damuwar abunda bazata samu ba, hakan ya haifar mata da zazzaɓi mai zafi da ciwon kai, Aunty tayi lallamin tayi faɗan amma duk a banza, ƙarshe ta zuba mata ido tace taje ta kashe kanta ita bazata iya ba, tunda ita bata da tawakkali. Misalin ƙarfe goma da ƴan mintuna na dare, ina kwance akan gadon yaya inacin dabino, shi kuma yana ƙasa yana operating system, isata dabinon yayi na tashi na ajiyeshi akan bedside, sakkowa nayi na zauna a kusa da yaya ina kallon fuskarshi, a hankali ya dago ya zuba mata narkukkun idanunshi, na matsa jikinsa sosai na kwantar da kaina a kafaɗarsa, ya shafi fuskata yace "har kin gama cin dabinon?" Nace "ehh, ya isheni" wuyanta ya taɓa yace "jikinki da zafi fa jewel" na lumshe ido bance komai ba sai ƙara manne masa jiki da nayi, a hankali nace "yaya zanci kaza gashashshiya" yace "kaza kuma a darennan" na ɗan turo baki nace "uhm" ya shafa ɗamamman cikinta yace "baby kin koyi ci da yawa, yanzu duk abubuwan da kika ci baki k'oshi ba?" cikin shagwaba nace "nidai dan Allah yaya kasiyomun" yace "ki bari gobe idan Allah ya kaimu, yanzu kinga aiki nake kuma dare yayi" nace "a'a nidai yaya ina son ci sosai, idan banci ba bazan iya bacci ba" ya sauke numfashi yace "shikenan ɗauko hijabinki muje" na tashi da murnata na saka hijabi muka tafi, da ƙyar muka samu gurin sai da kazar tunda har yau shima ba gama sanin garin yayi ba, guda uku ya siyo mun yace inta ci, tun a Mota na fara ci dan ina ganin kazar yawuna yayi wani irin tsinkewa, baifi rabin ɗaya ba naci naji na k'oshi, adana abata nayi nace da safe zanci, ina gama ci nasha ruwa na kwanta bacci a jikin yaya, cikin dare cikina yace baisan zance ba ya dinga murdamun, tun inajin abun kaɗan_kaɗan har ya farkar dani daga bacci, juyi na shigayi akan gado ina addu'a, wani irin amai naji yana tasomun da gudu na tashi nayi toilet hakan ya farkar da yaya, amai na shiga kelawa, sai da na amayar da kazarnan tass yaya na zuba mun sannu, ya taimakamun na wanke bakina da fuskata ya dawo dani d'aki, shi kuma ya gyara toilet d'in, da nayi aman naji daɗin murdawar cikin harna samu bacci ya kuma ɗaukeni. Sai dai me kafin asuba na tashi aman ya kai sau huɗu, sai da na amayar da duk wani abu da naci kafin na kwanta, duk jikina yayi laushi ga wata kasala gami da jiri da suka lullubeni, Mustapha hankalinsa idan yayi dubu ya tashi, tausayinta gaba-d'aya ya gama cikashi, gashi sai kuka take masa sannu kawai yake zuba mata kamar shima zai mata kukan, yana jin tamkar ya dawo da ciwon jikinsa, ruwa ya samu ya tofa mata addu'a ya bata tasha, Allah ya taimaka aman ya tsaya ta samu bacci ya ɗauketa da asuba. Kafin ƙarfe takwas sun gama shirinsu na zuwa asibiti, asibitin su Dr husnah zai kaita yama kirata tace yazo asibitin ya sameta, yau banyi musun zuwa asibitin ba, danni kaɗai nasan me nake ji a jikina, yau ko aikin gida ban iya yi ba, shi yayi komai, ya sakamun hijabina ya kama hannuna muka tafi, part ɗin Ammi muka nufa, tana kitchen suna aiki, zama nayi akan kujera dan bazan juri tsaiwaba, Ammi ta fito jin sallamar su, kallo ɗaya tayiwa Maryam tasan ba lafiya ba, Mustapha ya gaisheta nima na zamo daga kan kujerar na gaisheta, ammi ta amsamun ta ƙara da faɗin "ɗiyata lafiya kike kuwa?" Mustapha ne ya bata amsa da faɗin "bata jin daɗi ne, yanzuma asibiti zamu na shigo na faɗa miki" Ammi cikin tausayawa tace "Ayya, Allah ya ƙara sauƙi, wanne asibitin zaku kuma?" yace "Asibitin su Dr, husnah dannama kirata tace insame ta ƙarfe 8" Ammi tace "kasan asibitinne?" Yace "A'a driver'n kune ze kaimu, aishi ya sani ko?" Ammi tace "ehh yasani sosaima" Mustapha ya duba tsadadden agogon hannunsa yace "zamu wuce 8 ɗin ta kusa" Ammi tace "saikun dawo, Allah yakiyaye" muka amsa da Ameen, na tashi ina taune lips ɗina, Ammi tace "sannu kinji ɗiyata, Allah ya baki lafiya" na amsa cikin sanyin murya tare da ficewa, yaya ya biyo bayana. ya kama hannuna cikin tausayawa yace "sannu baby" na gyada masa kai kawai yace "har yanzu cikin na murda miki?" nace "a'a bakina ne kawai kemun ɗaci, sai jikina da babu kwari" yace "sorry zai dena insha Allah, ko in d'aukeki nace "a'a, zan iya tafiya" muka ƙarasa parking space yana zubamun sannu, bayan ya kira direban ammi muka shiga motar, muka shiga baya nida yaya ina kwance a jikinsa. Ba nisa asibitin sosai cikin wasu yan mintuna muka ƙarasa, kiran Dr husnah Mustapha yayi ta masa kwatancen office dinta, da tambaya suka gane gurin, sai da muka ɗan jirata ta ƙaraso, dan sanda mukaje bata zoba, bayanta muka bi kamar yadda tace har cikin office dinta muka zauna a kujerun gaban table ɗinta. Dr husnah na duban Maryam tace "amarya ya jikinnaki?" kaina a ƙasa na amsa mata, suka gaisa da Mustapha nima na gaisheta, ta dube ni da kyau tace "me yake damun kine ko kuma ince ya kike jin jikinki?" a hankali nace mata "ina jin jikina babu kwari ga jiri dake damuna, sai kuma zazzaɓi kaɗan_kaɗan, jiya kuma harda amai. Mustapha kallon Maryam kawai yake, yadda take faɗar abunda ke damunta amma shi ko sau ɗaya be taɓa sani ba, kullum sai ta dinga lafiyar ƙalau take. Dr husnah yace "yaushe rabon da kiyi period ɗinki" nayi shiru dannama manta da wani abu period, batare da tunanin komai ba nace "tun azumi" Dr husnah tayi murmushi tana duban Mustapha tace "zamu ɗauki jininta da kuma sauran gwaje_gwaje sai mu gano abinda ke damunta." yace "ok badamuwa." Anyiwa Maryam duk abunda ya dace, inda sakamako ya bayyana tana da shigar ciki na sati 8, Mustapha jin abun yayi tamkar a mafarki ya rungume Maryam ɗinsa cikin tsananin farin ciki da murna, yayiwa Allah godiya babu a daɗi, alheri mai yawa ya cika Dr husnah dashi sannan suka dawo gida, suna dawowa gida ya bata abinci taci tana gama ci sai bacci, su ammi duk sun shigo sun dubata. Tattalin Maryam sosai Mustapha yakeyi baya barinta tayi komai na aiki, shi yakeyin komai duk da ita batasan hakan tafiso tayi aikinta amma yaƙi barinta, ko Part ɗin Ammi baya barinta zuwa saboda wai idan taje zata iya yin aiki a can, sai dai inya fita ta samu taje. Yau juma'a wanda ya kama babbar Sallah saura sati ɗaya, yau kuma k'anin Ammi da iyalansa da mahaifiyarsu zasu zo, dama suna Dubai yana harkar kasuwancinsa kusan watansu guda kenan a can, yau kuma zasu iso naija da yardar Allah........✍️ *Allah kanunamun ranar da zan gama book ɗinnan🥺.* *By* *zeey kumurya* *ABIN DA KA SHUKA....!* *8️⃣1️⃣* .........Kwance nake a k'irjin yaya nayi shiru ina jin yanda bugun zuciyata yake k'aruwa, tun jiya da daddare gabana yake ta fad'uwa wanda bansan dalilin hakan ba. Shafa kanta Mustapha yayi cikin tsananin tausayinta, jikinta yayi zafi zau alamar zazzaɓi, cikin tsantsar kulawa yace "princess d'ita" na dan d'ago na kalleshi amma bance komai ba, fuskarta tayi fayau ga damuwa ƙarara akan fuskartata, yace "Please tell me, what happened to you?" cikin sanyin murya ina ƙoƙarin b'oye damuwata nace "babu komai yaya, ka yarda dani" yayi shiru kawai yana kallonta, tun jiya yaga yanayinta gabad'aya ya sauya, ga damuwa a tattare da ita, ƴar girimar da take masa ma jiyan batayiba, tambayar duniya ya mata meke damunta ko inane yake mata ciwo amma tace babu, yayi fushi ya kyaleta tasa masa kuka tace ita dai kawai ya tofa mata addu'a, batajin daɗi ne, yau kuma tunda safe data tashi yaji jikinta da zazzaɓi, yace suje asibiti a dubata taƙi, wai ita kar a mata allura. Na shafi gefen fuskarshi ganin yanda yake kallona, ajiyar zuciya ya sauke ya kai hannunsa ya shafi cikina yace "baby'nmu na wahalar dake ko, sorry" nayi murmushi ganin yanda yayi maganar nace "um, um yaya baya wahalar dani" yace "Allah yasa" na marairaice nace "yaya dan Allah ka barni naje na taya su ammi aiki, ko zanji k'warin jikina" yace "A'a, ki barsu suyi ai suna da yawa, yanzuma kuma sun kusa gamawa, koma ba hakaba keba cikakkiyar lafiya ba inake ina aiki" na turo baki gaba nace "wai yaya ni haka zanta zama bazan dinga aiki ba" yace "a'a amma dai sai baby'nmu yayi k'wari zaki cigaba" nace "haka akeyi dama?" Yace "mu haka zamuyi" nayi shiru ina tunanin wai nice yau da ciki, nice zan haihu nanda wasu watanni, zan zama uwa nima, wata irin soyayyar cikin da kaunarsa ce take ƙara cikamun zuciya. Bayan sallar azhar Dr husnah ta ƙaraso gidan, tun safe mustapha ya kirata akan rashin lafiyar Maryam, tace idan ta taso daga aiki zata biyo ta dubata. Ina d'akin yaya a kwance shi kuma yana falo, ya shigo yana dubana yace "bacci kike ne?" na girgiza masa kai alamar a'a, ya ƙaraso kan gadon ya zauna a baki yana faɗin "ga Doctor nan tazo zata dubaki" na tashi zaune ina kwabe fuska nace "yaya dan Allah kace mata karta mun allura, wlh tanada zafin hannu" ya shafa fuskarta yana murmushi yana tuno darun da'aka sha da ita a asibiti time ɗin da za'a dibi jininta da yi mata allura, cikin kwantar da murya yace "dubaki kawai zatayi ta baki magani" na turo baki gaba nace "nifa lafiyata k'alau" becemun komai ba ya tashi ya fita, two minutes suka dawo ɗakin tare da Dr husnah da sallamarsu, bayan na amsa musu ta dubeni tana murmushi tace "maman biyu, me raki" nayi murmushi kaina a ƙasa nace "ina yini" tace "lafiya ƙalau, ya jiki_jiki?" cike da kunya nace "da sauƙi" ta ƙaraso kan gadon ta buɗe jakar ta ta fara dubani, bayan ta gama ta dubi Mustapha tace "zazzaɓi ke damunta, amma bayan shi babu matsalar komai, yanzu zan rubuta mata magani sai ka siyo mata tasha, tunda batason allura" Mustapha yace "ai gwara ayi mata allurar, dan maganin ma basha zatayiba" na marairaice nace "nidai nafison maganin kuma zansha" yace "shima basha zakiyiba na sani" ya maida dubansa ga Dr husnah yace "kimata allurar kawai" Dr tayi murmushi ta shiga haɗa allurar, na kalli yaya kamar zanyi kuka, ya ɗauke kanshi, bayan tagama haɗa allurar tace "saifa ka riketa" ya tako ya hawo kan gadon ya janyoni jikinsa, na riƙe shi gam dan har na fara jin kamar antsikaramun allurar ajikina, jin hannun Doctor a jikina tana ɗan yin ƙasa da skirt d'in jikina na runtse idona ina ƙara ruk'unk'ume yaya, tana tsikaramun nayi wani zillo hawaye na kwaranyomun, sosai naji zafin allurar gashi dama duk a tsorace nake, yaya ya shiga mulmulamun gurin yana hura mun iska a cikin kunnena, na cizeshi a gefen wuyansa, ya shafa gashin kanta a hankali yace "sorry baby nah" nayi masa shiru ina sauke numfashi tare da ƙara lumshe idona, wani irin bacci na fizgata, cikin abun da baifi 5 minutes ba bacci ya ɗaukeni, Mustapha ya kwantar da ita a hankali jin tayi bacci ya fita falo inda Doctor take jiransa, suka ɗan ƙara tattaunawa akan jikin Maryam ɗin, tace masa babu matsalar komai sannan sukayi sallama ta tafi. Misalin ƙarfe uku da 'yan mintuna uncle ɗin Mustapha suka ƙaraso gidan su Ammi cikin k'oshin lafiya. Ammi tana harabar gidan tana jiransu, ganinsu yasa ta nufesu da sauri tana ƙara faɗaɗa fara'a akan fuskarta, mahaifiyarta ta fara rungumewa tana mata sannu da zuwa, sannan k'aninta MUHAMMAD mai tsananin kama da ita, sai matarsa kyakkyawa da ita da yaranta twins mace da namiji. Aunty ta jasu zuwa part d'in baƙi na gidan, wanda yasha gyara saboda zuwansu, bayan sun zauna aka ƙara gaggaisawa, Mama, Zuhura, mama Nafisa da Umaimah suma sun ƙaraso falon dan tarbarsu, UNCLE MUHAMMAD wanda yaranshi suke kiranshi da ABBU, sai baza ido yake yana son ganin ta inda d'anshi Mustapha zai ɓullo, mahaifiyarsu su ammi wadda suke kira da HAJJA itama haka dan dama ganin ɗan jikallennata ne ya kawo ta Nigeria. Da sallama ya shigo falon gabad'aya suka zubo masa ido zuciyoyinsu cike da d'okin ganinsa, shi kanshi a nashi a ɓangaren haka ne, fuskarsa ɗauke da murmushi ya ƙarasa ya rungume UNCLE d'insa, wanda ya k'ura masa Ido, cikin Muryar mai cike da zallar farin ciki yace, "welcome my dearest uncle" Abbu ya shafa kansa fuskarsa ɗauke da yalwataccen murmushi yace "welcome Son like no other, nice to meet you" cikin tsananin kaunar uncle d'innasa yace "me too" tare da sakinshi ya nufi gurin wadda yake da tabbacing itace grandmother d'insa saboda yadda take kama da Amminsa duk da ta manyanta, Hajja wadda ta saki baki da hanci tana kallonsa cike da tsananin mamaki ta fashe da kuka cikin hausarta da bata fita sosai "Allah k'adiran, mai girma da juya al'amari a duk yadda yaso, tabbas wannan babu tantama jininmune kuma jinin modibbo, lallai ikon Allah ya wuce gaban komai, yaro mai tsananin kama da ubansa, yanda kasan modibbo haka nake ganinsa" mustapha ya ƙarasa gareta ya rungumeta, ta rungumeshi itama tana cigaba da kuka tana faɗin "ashe da rabon zaka dawo garemu, Allah ya jikan mahaifinka adalin mutum mai farar zuciya wadda ke cike da alheri" Mustapha ya amsa da "ameen" tare da sakinta ya shiga share mata hawaye, yanajin wata irin kaunarta na ratsa masa zuciya, Ammi tayi ƙasa da kanta tana ƙoƙarin maida kwallar data taron mata a ido saboda tuno mata da mutumin da bata da kamarsa a duniya, Hajja ta ƙara ruk'unk'ume Mustapha a jikinta tana kuka, ya samu ya lallasheta tayi shiru, amma fa duk inda yayi idanta na kansa, gurin matar UNCLE d'insa wadda yaranta suke kiranta da Ummee yaje ya gaisheta, twins suka taho jikinsa gabad'aya suna gaisheshi, yara kyawawa 'yan kimanin shekara 7, sai larabci suke zuba masa, Mustapha ya ƙurawa macen ido saboda yadda take acting ɗinta sai yaga kamar Maryam ɗinsa, musamman idan ta waro manyan fararen idanunta ko kuma ta turo ɗan ƙaramin bakinta gaba idan, ya rungume yaran a jikinsa cikin kaunarsu. Su ammi suka cikawa su Hajja gabansu da lemuka nasha kala_kala da ruwa, Abbu kuma sanin da Ammi ta masa baya shan abu mai sanyi, sai ta kawo masa had'add'en shayin data masa na musamman. Ammi ta dubi Mustapha tace "ina ɗiyata kuwa, ko batasan sun ƙaraso bane" Mustapha ya ɗan shafi kansa yace "tana bacci ne, amma bari na taso ta" Hajja ta amshe zancen da faɗin "a'a, karka tasota barta tayi baccinta, abunda muna gidan ba yau zamu tafi ba, idan ta tashi ma gaisa" Mustapha yace "ai lokacin Sallah ma yayi kuma ta jima tana baccin" Ammi tace "katasota toh tunda ko abincin rana bata ciba" ya amsa tare da miƙewa, Umaimah ta bishi da kallo cike da kaunarsa, twins suka ce zasu bisa, umminsu ta hanasu. Na farka daga baccin tun ɗazu amma ban tashi ba, ina kwance akan gadon jikina yayi wani irin sanyi sai faduwar gaba da nake tayi, addu'a na shiga yi a cikin raina kona samu sauƙin abunda yake damuna, idona a lumshe yaya ya shigo ɗakin, gadon ya hawo ya janye blanket d'in dana lullube jikina, ya shafa fuskata tare da faɗin "princess har kin tashi?" na buɗe idona a hankali na sauke su akan kyakkyawar fuskarsa, kai na gyada masa alamar eh. Ya janyoni jikinsa yana faɗin "time ɗin Sallah yayi, muje muyi alwala" bance komai ba, ban kuma yi yunkurin motsawa da niyyar tashi ba, sai kwanciya da nayi a jikinsa nayi lamo, ya d'ago fuskata fuskarsa na nuna damuwa yace "Princess me yake damunkine wai, ko jikinne?" na girgiza masa kai alamar a'a, ya taɓa wuyana yaji zafin jikina ya ragu sai gumi dake tsatstsafomun alamun zazzaɓin ya tafi. Bai ƙara cemun komai ba, ya ɗauke ni ya kaini toilet, shap_shap yamun wanka nayi brush, muka dauro alwala sannan muka fito. Yana ƙoƙarin fita yace "kiyi sauri ki shirya kije part d'in baƙi su uncle sun ƙaraso tun ɗazu, bai jira amsataba ya fice jin antada sallah a masallaci. Shiryawar na shiga yi cikin sauri kamar yadda yace, sai dai bansan Meyasa ba nakejin zuciyata na wani irin bugu tun ɗazu, yanzu kuma daya sanarmun da zuwansu uncle sai bugun zuciyar ya k'aru. Bayan na idar da Sallah na nufi part d'in baƙin, da sallama na shiga falon kyakkyawar matar dake zaune wadda bazata wuce shekara 38 ta amsamun tare da bina da kallo, na ƙarasa gabanta na durkusa har ƙasa na gaisheta domin nafahimci itace matar uncle, ta amsamun da fara'a a fuskarta ta ƙara da faɗin "kece sirikartamu kenan" nayi murmushi tare dayin ƙasa da kaina cikin jin kunya, Hajja ta fito daga d'akin da tayi Sallah Hanifa na biye da ita a baya, haka kawai Hajja taji gabanta yayanke ya fad'i, ummee ta dubeta tace "Hajja ga kishiyar taki fa, kyakkyawa da ita kamar mijinta" Hajja ta zauna akan kujera tana bin Maryam da kanta ke ƙasa da kallo tace "to sannunta, amma dai nasan duk kyanta na fita shiyasa ta kasa d'ago kai ta kalleni" nayi murmushi tare da tashi na nufi gurinta muna haɗa ido gabana ya faɗi sosai, _hasbunallu....._ na shiga karantawa a raina saboda faduwar gaban ta isheni, itama Hajja anata ɓangaren haka, kafe Maryam da ido tayi ko kiftawa babu, na daure duk da abunda nakeji a raina na gaisheta cikin girmamawa, tsohuwar mata ce amma hutu da jin daɗi ya boye tsufanta, tana kama da Ammi sosai, ta amsamun gaisuwata tare da cigaba da tsokanata. Haneefah ta matso jikina tana mun murmushi tare da mun magana cikin harshen larabci, na shafa kanta inajin wata kaunar yarinyar lokaci ɗaya ta shigemun zuciya, itama kuma lokacin dana kalleta sai da gabana ya faɗi, surutu take tamun, cikin abunda na fuskanta ta faɗamun sunanta Haneefah, tana da ɗan'uwa Haneef yabi Abbunsu masallaci, ummee tacemun nayiwa Haneefah turanci tana ji. Muna zaune muna shan hirarmu da Haneefah ammi ta dawo ɗakin, Hajja da Ummee kuwa kallonmu kawai suke kamar sun samu TV, Ammi ma data shigo sai da ta kalli Maryam ta kalli Haneefah, ta ƙara kallousu, tayi haka ya kai sau uku, sannan ta sauke numfashi ta amsa sannu da zuwan da Maryam ta mata, tare da tambayarta ya jiki, dan Dr husnah, ta biya sun gaisa ɗazu tace Maryam tazo dubawa. Haneef na gaba Abbu na binshi a baya suka shigo falon, Hannef ganin yar'uwarsa gurin Maryam shima ya nufi gurinta ya zauna a jikinta yana gaisheta, amsawar da Maryam tayi yasa Abbu wata irin juyowa yana kallon Maryam a wani irin yanayi na rud'ewa, dan jin Muryar da tayi kama data wadda bazai taɓa iya mantawa da ita ba a rayuwarsa, a hankali na d'ago kaina jin wanin yanayi na baƙuntar zuciya da gangar jikina, na kalli mutumin da Haneefah take nunanmu tana faɗin "ga Abbunta ya dawo" cikin harshen turanci, wani abu da bansan ya zan misalta muku shiba ya ziyarci zuciya, kasa gaisheshi nayi Saboda wani nauyi da harshe na yamun, Abbu dayake ganin tamkar Maryam ɗin shi daya bari tsawon shekaru masu yawa yace "Maryam!" cikin ƙaraji, Ammi ta dubeshi da tsantsar mamaki tace "kasanta ne ɗan'uwa?" Bai iya bata amsa ba sai jikinshi daya ɗauki wani irin rawa nuna Maryam yake da hannunshi amma ya kasa magana, ƙasa yayi luuu zai fadi Mustapha da shigowarsa kenan ya tafi da sauri ya riƙeshi, zaunar dashi yayi akan kujera gabad'aya su Ammi suka yo kansa suna masa sannu cikin tsananin al'ajabin abinda yasashi a cikin wannan hali lokaci ɗaya. Hajja ta dafa kafadarsa cikin yarensu na buzaye a ɗan ruɗe take faɗin "Muhammad meyafaru?" Abbu ya sauke wani gwauron Numfashi yana fitar da numfashi da k'yar yace "Hajja gamo nayi, naga wata kamar matata Maryam danake baku labarinta kuma tayi magana har muryarsu iri ɗaya" Ammi ta juya da sauri jin abinda yace ta kalli Maryam data kasa koda motsi, idanunta a lumshe hannunta dafe da kanta, Ummee ta mik'o masa ruwa mai sanyi wanda ta tsiyayo masa a cikin wanda ammi ta kawo musu, ya karba yayi bismillah ya fara sha, ajiyar zuciya ya sauke bayan ya gama shan ruwan ya dafe kansa daya fara sara masa. Mustapha kallonsa kawai yake bece komai ba zuciyarsa na bugawa shima, Ammi ta tattaro dauriyarta dan itama a ruɗe take tace "Muhammad ba gamo kayi ba, wadda kagani akwaita a zahiri kuma itace matar NOOR kuma itama sunanta Maryam, amma nasan ba ita bace wadda kake nufiba" Abbu ya mike da sauri yana faɗin "ina take?" Ammi ta nuna masa Maryam dake zaune kamar mutum mutumi, ƙarasawa yayi gurin Maryam da sauri ya rungumeta a jikinsa cikin tsananin zak'uwa yace "dan Allah wacece ke? ya akai kike tsananin kama da Maryam d'ita? dan Allah ki faɗamun ko kin santa ki kaini inda take dan Allah" Maryam tayi tsit tana jin wani irin abu na ratsa jikinta a sanadiyyar jinta a jikin Abbu, Abbu ya saki Maryam ya dubi Ammi a ruɗe yace "ƴar'uwa ki mata magana ta faɗamun dan Allah, inason ganin Maryam d'ita kullum da tunaninta nake kwana nake tashi a raina ita da cikina dana tafi na barshi a jikinta" Ammi ta kama hannunsa ta zaunar dashi cikin kwantar da murya tace "ka nutsu Muhammad ka mana bayanin waccen Maryam kake nufi" yace "Matata! Matatace, itace matata ta farko wadda mak'iya suka shiga tsakaninmu suka rabani da ita da garin Kanon gabad'aya shekara kusan 20 kenan yanzu" Ammi ta zauna dab'as a kusa dashi dan ita bata taɓa sanin da batun wata matarsa Maryam ba, Hajja ta zauna a ɗaya gefennashi tana faɗin "wai kana nufin matar Muhammad itace kagani kamar Maryam ɗin da kake bamu labarinta?" Ya gyad'awa Hajja kai idanunsa a kan Maryam, da kanta ke ƙasa har lokacin, Mustapha ma kallonta kawai yake. Ummee ta ƙarasa ta zauna a kusa da Maryam ta rungumeta a jikinta tana addu'ar fatanta ya zama gaskiya akan Maryam, ko dan ta samu nutsuwar mijinta da kwanciyar hankalinsa gami da farincikinsa ya dawo, dan yasha faɗa mata bazai taɓa samun hakan ba, harsai yaga Maryam d'insa ya nemi yafiyarta akan tafiya da yayi ya barta. Ammi ta dubi Hajja so surprise tace "kema kinsan Maryam ɗin dayake magana akanta ne?" Hajja tace "eh matarsa ce daya aura a Kano tun bayan barowarsa daga nijer" ammi tace "to me ya rabasu, kuma a yanda na fuskanta tunda ya barta bai waiwayetaba" Hajja tace "shi zaki yiwa wannan tambayar" Ammi ta maida dubanta ga Abbu tace "Please Muhammad ka fitar dani daga cikin duhu, I want know alot about what you said" Abbu yaja wani gwauran numfashi yace "labari ne mai tsayi ya Maryam, amma zanyi ƙoƙari na tak'aita miki, amma kafinnan inason nasan wacece ita wannan Maryam ɗin" Ammi tace "forget about this bro, ka fara bamu labarin taka Maryam ɗin, zakasan ko ita wace daga baya" ganin yanda Ammi ta damu Abbu basan ransa ya fara basu labarin kamar haka. "Ranar dana tsinci kaina bana k'aunar ƙara zama a ƙasar nijer, na tattara yan kuɗaɗen hannuna na biyo motar haya zuwa ƙasar Nijeriya, a garin Kano muka sauka, bansan kowa ba, ban kuma san inda zan nufa ba, tunda ban taɓa zuwa garin ba, wata makarantar Allo naje na zauna cikin almajirai, malamin Allon ya kirani yamun tambayoyi akan rayuwata, nace masa ni Maraya ne bani da kowa daga garin nijer nake, malamin ya tausayamun sosai yace in zauna tare dashi a cikin almajiran, haka nacigaba da zama anan a matsayin almajiri, tun ina jin ba daɗin zaman garin harna ware na saba da mutane. Anan nayi shekaru tare da malamin, inayin yan ƙananun sana'oina irin su wankau da aikin gidan masu kuɗi, nasha wahala ba kaɗan ba a zaman danayi a Kano, amma ko kaɗan bana tunanin gida da ƴan gida rayuwata kawai nakeyi. Allah ya haɗani da wani Alhaji mai kuɗi dayake da shaguna a kasuwar kantin kwari, yana zuwa gurin malaminmu sosai yana kawo sadaka ana masa addu'a, Allah ya haɗa jinina dashi yana sona sosai harya ɗaukeni nake masa yaron shago, lokaci ɗaya na fara samun 'yan kuɗaɗena, sai na bar cikin almajirai na dawo unguwar darmanawa na kama shago haya nake kwana a ciki, anan Allah ya haɗani da Maryam, yarinya mai kyau kirki da ladabi ga kunya, munyi soyayya sosai da Maryam duk da nasan be zama lalli na auretaba tunda ni ba ɗan gari bane, mahaifiyarta taso hana aurenmu Lokacin da Maryam ta fitar dani a matsayin miji amma mahaifinta yace tunda taji ta gani tana so yabani ita, munyi farin ciki sosai da hukuncin da mahaifinta ya yanke akanmu, akayi auranm muka tare anan unguwar ta darmanawa na kama haya, matsala ta farko dana fara fuskanta tunda nazo garin Kano itace ta mahassada a gurin sauran ma'aikatan da muke aiki a ƙarƙashin maigidana, saboda yanda yake fifitani akansu yajani a jiki kamar ɗansa ya aminta dani, komai ni yake ɗorawa akan gaba a harkar kasuwancinsa duk da akwai yaransa da suka fini dad'ewa a gurin, ranar da Alhaji ya yayeni ya buɗe mun shago na karan kaina ranar na bar Nigeria bisa layar zanar da akamun, ban tsinci kaina a ko'inaba sai a ƙasar Sudan, wata irin tsanar garin Kano aka sanyamun araina wanda ko tunawa da ita nayi sai inji wani irin zafi a raina, duk da na baro matata mafi soyuwa a gareni da bani da kamarta a wannan lokacin, gashi tana ɗauke da juna biyun dana kwallafa rai a kansa amma sai naji duk sun fitarmun daga rai, nasha wuya ba kaɗan ba a garin Sudan, wanda idan na tsaya fayyace muku ita zan ɗauki lokaci mai tsawo, Amma dayake Allah mai jinkan bayinsa ne a kodayaushe sai ya haɗani da wani Balarabe ɗan ƙasar Saudiyya, ta sanadiyyar uban gidan wani abokina da suke harkar kasuwanci na haɗu dashi, shima ya haɗamu. Mutumin ya ɗaukeni har ƙasa mai tsarki inda muke zaune a Jidda, ya ɗorani akan harkar kasuwanci, anan nayi arzik'i ba kaɗan ba, da addu'a da taimakon Ubangiji hankalina ya fara karkata ga gida na fara tuna ƴar'uwata da mahaifiyata, watarana na katse komai na shirya na tafi ƙasa ta haihuwa, nayi sa'ar tarar da mahaifiyarmu da rai saidai cikin mummunan hali na ciwo, a sanadiyyar rashina dana yayata. Hakan yasa na ɗaukota na dawo ita garin Saudiyya na mata magani ta warke rass sai damuwar rashin ƴar'uwata kawai dake damunta, kullum cikin addu'ar Allah ya bayyana mana ita muke. Na haɗu da khadija (Ummee) anan Saudiyya dan itama mazauniyar cance ita yan'uwanta sunayin aikatau, amma asalinta haifaffiyar garin Katsina ce, anan Nigeria. A wani aikin hajji da mukaje kamar a mafarki Allah ya haɗamu da Yar'uwata, a 'yan shekarunnan tunanin Maryam ya yawaita a cikin raina musamman dana fara zuwa Nigeria gidan Yar'uwata, amma da zarar nayi yunƙurin zuwa Kano sai inji wani k'unci ya cikamun zuciya, akwai randa na daure nazo garinnan na shirya babu wanda ya sani na tunk'ari hanyar Kano da nufin naje na dubo matata, jin da nayi kamar ana zaremun numfashi yasa na juyo ba shiri na fasa zuwa, na kwatanta hakan sau da yawa amma azabar da nakeji a jikina yasa na kasa zuwa Kanon har yau danake baku labrinnan." Abbu ya sauke numfashi yana kallon Maryam da take ta kuka a jikin Ummee tamkar ranta zai fita, ita kanta batasan dalilin kukannata ba, addu'a takeyi a ranta Allah yasa ta farka daga baccin datake yi, dan tasan mafarki take ba gaske bane ta gamu da Mahaifinta, abunda ta daɗe da fitar da rai da ganinshi a rayuwarta, Mustapha ya lumshe idonsa yana jin kukannata har cikin ransa, Ammi da jikinta yayi sanyi ba kaɗan ba ta miƙe ta nufi inda Maryam take, janyota jikinta tayi ta shiga rarrashin ta, da ƙyar ta samu Maryam ɗin tayi shiru, ta rok'eta ta basu tarihin rayuwarta, Maryam tana kuka ta basu labarinta kaf, Mustapha kuwa tuni ya fice dan baze juri sauraren kukannataba, Abbu na kuka ya taso ya rungume Maryam tsam a jikinsa yana faɗin "ashe da rabon zanga jinina na jikin Maryam kafin na mutu, ki yafemun ɗiyata na rashin waiwayarki da banyi ba tsawon rayuwrki har ake miki kallon mara uba da asali, Allah yajikan Maryam ɗita da inna" Maryam tayi luf a jikinsa tana sauke ajiyar zuciya, amma duk da haka ta kasa yarda ba mafarki takeba wai k'anin ammi shine mahaifinta, mijinta mafi soyuwa a gareta ɗan'uwantane na jini, amminta yar mahaifintace, tanajin abun kamar almara wai yau itace a jikin mahaifinta, Hajja na hawaye itama ta taso ta rungumesu duka a jikinta, ammi ma hawaye take ummi ma haka abun gwanin ban tausayi, su Haneefa sunyi tsuru kawai suna kallon ikon Allah. Bayan angama koke_koken da al'ajabi Ammi ta kira su Mama ta sanar musu da abun farinciki da tsantsar ikon Ubangiji, sunyi mamaki suma sosai, amma ikon Allah yafi gaban komai. Maryam tayi lamo a jikin mahaifinta daya yaƙi yarda tabar jikinsa, kallonta yake kawai cike da tsantsar kaunarta da mamaki, shiyasa tun sanda suka taɓa yin waya da Maryam yaji muryarta zuciyarsa ta d'okantu da son ganinta ashe yarsace ta cikinsa. Yau kam farinciki da yana kisa daya kashe Maryam, harta kira gwaggo da Aunty da saleemat ta sanar musu, gwaggo kusan zaucewa tayi dan mamaki, taji kamar tayi tsuntsunwa tazo taga Ahmad ɗin, danta tabbatar da shi ɗinne. Ammi sosai tayi farinciki da wannan al'amari, shiyasa ashe tun randa ta fara ganin Maryam taji ta shiga ranta sosai, kuma ta daɗe tana mamakin yanda idanun Maryam yake irinnasu ashe itama jininsuce. Har dare Maryam tana cikin danginta anata hira, abincima da ƙyar ammi ta tilasta musu sukaci, ganin dare yayi Ammi tace Maryam ta tashi ta koma part d'insu, ta kwabe fuska sosai tace a anan zata kwana, Hajja tace Ammi ta k'yaleta su kwana tare, babu alamun bacci a idanun su Maryam hirarsu kawai sukesha Hajja na basu labarin yan'uwa, sai can dare Maryam taga message ɗin Mustapha buɗewa tayi sauri ta karanta _"I MISSED YOU SO MUCH MY PRINCESS"_ Maryam tayi murmushi ta tura masa reply da _"MISSED YOU TOO YAYANA"_ yayi murmushi lokacin dayaga reply ɗin, dama yasan yau tare da Abbunta zata kwana, shiyasama bai koma part d'in ba, danyasan indai yaje zatace zata biyoshi, shikuma yau ya mata uzurin ta kasance da mahaifinta a wannan daren, dan yasan yanda suke d'okin ganin juna darenma bazai ishesuba, ya ƙara tura mata wani text ɗin da _Ina tayaki murnar haɗuwa da mahaifinki, nayi farin ciki sosai da hakan matata."_ na tura masa reply da _"Thank you"_ sannan na kashe wayata, muka cigaba da shan hirarmu. Da safe na koma part d'inmu, gyaran gado na tarar da yaya yana yi, na tsaya a jikin kofa ina kallonsa ina murmushi, sai yanzu dana gansa nasan nayi missing d'insa, ya juyo ya kalleni, waro idonsa waje yayi sosai yace "yaushe kika shigo?" nace "tun ɗazu, har nayi sallama bakajiba" yace "tunaninki nakeyi" na ƙarasa kusa dashi cikin girmamawa nace "Gud Morning" ya rungumeni a jikinsa tare da faɗin "morning princess, how was your night" nace "Alhamdulillah and very very sweet" yayi murmushi tare da jan karan hancina yace "sure?" na gyada masa kai ina kallonshi cike da k'auna nace "I'm sorry na barka jiya kai kaɗai" yace "babu komai ai dear, kuma ko kaɗan ban damu ba ko kuma nayi fushi, farinciki kawai nayi tare da raya daren ta hanyar yin Sallah, dannuna godiyata ga Allah na ganin mahaifinki da kikayi tare kuma da murnar matata ƴar'uwatace ta jini" na lumshe ido ina ƙara kwanciya ajikinshi hawayen farin ciki na taruwa a idona, har yanzu mamaki da al'ajabin abun be barniba, amma idan na tuna ikon Allah ya wuce gaban komai sai nayi godiya ga Allah kawai. Cikin sanyin murna nace *I LOVE YOU MY HEARTBEAT* k'ura mata ido Mustapha yayi cikin tsananin jin daɗin kalamanta, cikin tsananin shauki yace "repeat it again please" nayi murmushi hawayen idona na zuba aka fuskata nace *"I love You so much, I love you more and more, my hero, my husband, my besty, my everything, I love you for today, for tomorrow and for ever"* Rungumeta ya ƙara yi a jikinsa sosai kamar zai maidata ciki, so da k'aunarta na ƙara ninkuwa a cikin ransa, kalamanta sun sanyaya masa zuciya ba kaɗan ba, murya ƙasa ƙasa yace "thank you so much, and I love you too" nayi luf a jikinshi ina shaƙar daddaɗan kamshinsa, ya shafa cikina yace "nayi missed baby'nmu" na d'ago da kaina nace "shima yayi missing ɗinka sosai" ya ƙara shafa cikin yana kallon cikin idona yace "dagaske" na daga masa kai tare da lumshe idona dan bazan juri kallon ƙwayar idonsa ba" yasa tattausan tafin hannunsa ya sharemun hawayen fuskata tare da jerumun wasu tsadaddun kalaman soyayya wanda suka sa najini a duniyar sama, saboda shauk'i, daga ƙarshe kuma ya zarce da romancing ɗina...... Sasai Abbu yake nunamun k'auna da tarairaya gami da kulawa, haka ma Ummee da Hajja da Ammi wadda take bani wata sabuwar kulawa fiye da ta da, ga ƙannena da kodayaushe suna manne dani, sosai nake son yaran, tabbas jini da mahaifa ba ƙarya bane soyayyarsuma daban take. Bayan babbar Sallah da sati ɗaya mukaje Kano, Hajja da Abbu suka yiwa Daddy godiya akan riƙon Mustapha, sannan mukaje gidan gwaggo, Abbu yayi mata ta'aziyyar inna da mahaifiyata, gwaggo ta dinga kuka cikin nadamar abubuwan data aikata a rayuwarta, musamman zalintar Maryam da tayi, gashi duk mugunta da cutar da ita datayi Allah ya kareta, ta kaita aikatau da niyyar ta wulak'anta mata rayuwa, sai gashi sanadin aikatau ɗin ta haɗu da mahaifinta tare da auran miji na kere Sa'a, kuma ta zamo yanzu itace gatanta. Lokacin da muka biya ta asibiti duba Mommy sai da nayi kuka, Saboda mawuyacin halin da take ciki, kafarta data karye ta rub'e sai d'oyi da wani ruwa mai wari take fitarwa, ashe tana da sugar a jikinta hakan yasa ƙafar ta rub'e, waje za'a fita da ita a yanke ƙafar. Suhailat kam zuwa yanzu ta gane Mustapha ya riga da yayi mata nisa, Saboda yadda yake bawa Maryam kulawa da nuna mata soyayya a gaban kowa tamkar ita kaɗaice mace a duniyar. Tayi kuka kamar ranta zai fita, taji duk duniyar babu wanda ta tsana sama da Mommy, domin itace tun farko bata ba ta tarbiyyar ingatacciyaba, gashi yanzu tana ji tana gani ta rabu da Mustapha wanda take masa masifar so, ƴar aikin datake gani a wulak'ance ita ta sameshi. Da mukaje duba yaya Sadiq ya dinga roƙona gafara yana kuka, ni bansan abunda yamun ba amma duk da haka nace masa na yafe masa, sai da mukaje Kaduna nake faɗawa Aunty, tacemun ai shine wanda yaita ƙoƙarin ketamun haddi, baƙaramin ɗimuwa nayi ba dajin wannan mummunan labarin, nayi mamaki kwarai da jin yaya Sadiq ne yakeyin fyad'en, nayi kuka kuma saboda tuna yanda ya nunamun k'auna, ashe duk ta yaudarace, ni ina ganin duk gidan babu wanda ya kaishi hankali ashe fuska biyu gareshi, na masa addu'ar shiriya da kuma roƙon Allah ya ƙara karemu daga mutane irinsu da duk wani mai nufinmu da sharri. Daga Kaduna muka dawo Jos mukayi shiri muka ɗara zuwa ƙasar *NIJER* dukanmu, mun zaga 'yan'uwa da dangi namu dana mahaifin yaya, har kukan daɗi sai da nayi ganin jinina da yanda suke rububinmu da nuna mana k'auna nida yaya, watanmu guda acan muka dawo gida Nigeria cike da kewar asalinmu, kamar karmu taho suma can da ƙyar suka bari muka taho. Bayan mun dawo da sati biyu muka dawo Kano da zama gaba-d'aya, inda muka tare a k'aton gida mai kyau da Daddy ya bawa Yaya, Walima Ammi ta shirya mana bayan muntare saboda farinciki da faruwar abubuwa, aka tara yan'uwa da abokan arzik'i akaci akasha, kowa ya tafi, gida ya rage daga ni sai Yaya sai baaba Talatu da yaya yasa Aunty ta ɗakkota dan tadinga ɗebemun kewa idan bayanan, ta kuma tayani aikace_aikace. Mustapha na zaune a ɗakinsa yana operating system, Maryam ta turo ƙofar ɗakin ta shigo a hankali, tana sanye cikin bubu da'aka ɗinka mata ita da wani yadi mai kyau red colour, cikinta ya fito ɗan wata shida kuma ta ƙara k'iba da murjewa, sai tashin k'amshi take me daɗin gaske, sallama ta masa cikin zazzak'ar muryarta. Mustapha ya lumshe idonsa cikin jin daɗin ƙamshinta daya kaiwa hancinsa ziyara, ya amsa mata sallamar tare da buɗe lumshashshun idanunsa ya zuba mata yana jifanta da wani fitinannen kallo, Maryam ta ajiye teaflaks d'in hannunta a kan bedside, zama tayi a kusa dashi tana murmushi ta hura masa iska a ido, Ajiyar zuciya ya sauke ya kwantar da kanta a kafaɗarsa, sumar kansa ta shafa tace "sannu da aiki hubby" ya shawabe fuska yace "yawwa" Maryam tana murmushi tace "ka gaji ko?" ya gyada mata kai, kuncinsa ta shafa tace "sorry ka kusa gamawa ai" ya ƙara gyaɗa mata kai tare da shigewa jikinta, hannunsa yasa ya shiga shafa cikinta, Maryam tace "ga cofee ɗin na kawo maka, kasha sai kacigaba da aikin" ya bar jikinta yana faɗin "Toh Princess" zuba masa coffe ɗin tayi a cup ta miƙa masa, ya karb'a yayi bismillah ya fara kurb'a idanunsa k'ur akanta, tayi masa kyau ba kaɗan ba. Bayan ya gama shan cofee ɗin na kwantar da murna cikin ladabi nace "yaya yaushe zamuje dubo Mommy" yamun shiru ya janyo laptop ɗinsa yacigaba da aikinsa, na matsa jikinshi na kwantar da kaina a kafaɗarshi cikin shagwab'a nace "yaya kamun shiru" batare daya kalleniba yace "ba zamu bane" nace "why?" yace "kawai" shiru nayi kawai ina kallonsa, tun shekaran jiya Mommy'n suka dawo, amma nayi_nayi muje mu dubota yaƙi. ya d'ago ya kalleta jin tayi shiru, na ɓata fuska tare da turo baki gaba, numfashi ya sauke yace "bari na ƙarasa aikinnan, idan anyi sallah sai muje" nayi murmushi nace "thanks" yaja karan hancina yace "shikenan anbar ɓata rai" nayi dariya ina ƙara lafewa a jikinsa. Bayan sallar isha'i mukaje gida gidan Daddy muka dubo Mommy, mummunan halin da Mommy take ciki bazai misaltuba, ta rame tayi baƙi ga babu kafa ɗaya, ga kuraje sun ƙara feso mata ta ko'ina a jikinta, ɗakin da take gabad'aya wani irin ƙarni da wari yake, Mommy tana ganin su Maryam ta fashe da kuka, kasa haɗa ido tayi da Mustapha saboda tsabar kunya da nadama, su da take nufa da sharri gashinan suna rayuwarsu hankali kwance cikin jin daɗi, ita kuwa gatanan kwance da rayuwar wahalar da take ta gwammace gwara mutuwa, ɗayar ƙafar ta tama taji ciwo annannad'eta da bandeji, itama likitoci sunce idan ciwon bai warkeba sai dai a yanke ta itama. Maryama kuka ta saka dataga halin da Mommy take ciki, Mustapha ya rungumeta ya rarrasheta. Sosai na tsorata da duniya ganin halin da Mommy ta tsinci kanta, lallai rayuwa kayi da kyau sai kaga da kyau, amma Mommy *ABIN DA TA SHUKA SHI TA FARA GIRBA* Suhailat tana Kaduna gidan Aunty ta haihu sati biyu da suka wuce ta haifi yarta mace, Sunan Mommy Aunty tasawa yarinyar, Lokacin da sukazo dubata Mommy taga yarinyar ta dinga kuka da ihu abun duniya duk ya isheta ta zama kamar mahaukaciya, sai surutai da faɗar abubuwan data aikata takeyi. *BAYAN WATA UKU* Rayuwa mai cike da jin daɗi, farin ciki da kwanciyar hankali Maryam da Mustapha suke gudanarwa cikin tarairaya gami da tsantsar kaunar juna, burin kowannensu yaga ya faranta ran ɗan'uwansa. Anyi Engagement ɗin Aliya da saurayinta da suke shan soyayya, bikinta kafin azumi ita dasu haidar da zannurain harma da faruq, duka za'a haɗa a sha Shagali, Mommy ta haukace hauka tuburan, hakan yasa aka maidata gidan mahaukata ake kula da ita acan, Suhailat kuwa Daddy yace tana yaye yarta zai d'aura mata aure da Kamal, Kamal beyi musu ba lokacin da Daddy yace ya auri Suhailat, dan har yanzu bai dena santaba kuma ko ba komai ze auri 'yar shahararren mai kuɗi, Suhailat cedai batayi farin ciki da auran kamal ɗin ba, dan son Mustapha nanan daram a ranta, kullum cikin kuka take da damuwa taƙi haƙura, Aunty kuwa bata kulata sai kallo da ido, abu ɗaya take maimaita mata shine "Mustapha ya riga daya mata nisa, nisa na har abada" Sadiq ya koma abun tausayi, ko cikin mutane baya iya shiga saboda kunya da nadamar abunda ya aikata, sai dai ya kulle kansa a daki yayi ta kuka yana neman gafarar Allah akan abunda ya aikata, ga ciwo yaƙi barinsa ya tafi ya dawo yake masa. Daddy ya bayyanawa Ammi abunda yake ransa game da ita, da farko ta bujire dan bata da niyyar ƙara aure a arayuwarta, amma da Daddy ya haɗa ta da Hajja, Hajjan ta mata nasiha sai ta amince zata auri Daddy'n, amma tace sai bayan ta aurar da Umaimah, tunda Umaimah'n ta samu wani mutum mai mata biyu zai aureta, itama ta haƙura da Mustapha tunda baya sonta, dan bayan dawowarsu Kano ta ƙirashi a wata ta sanar masa tana sonsa, shikuma ya mata wankin babban bargo, hakan yasa ta haƙura ta karb'i ƙaddararta. Yau Litinin yau Maryam an ɗanɗana yaƙin mata wato haihuwa, tun cikin dare ta fara nak'udar sai kusan azahar Allah ya sauketa lafiya ta sunkuto 'yarta mace kyakkyawa mai kama da Mustapha, da yamma aka sallamota suka dawo gida. Aunty da gwaggo da baaba Talatu ne tare da ita, Ammi kuma tana hanya bata ƙarasoba, Hajja da ummee ma sai gobe zasu zo insha Allah. Zaune nake akan gado jaririyar tana kan cinyata, Aunty tana gefe na, Aliya kuma tana ƙasan gado, gwaggo kuma tana falo tare da umman saleemat da saleemat, Kallon yarinyar nake inajin wata irin zazzafar k'aunar ta na ƙara ratsa zuciya, Aunty ta dubeni tace "Maryam ki bawa yarinyarnan nono tasha, tun ɗazu yarinya sai neman abinci take" na ɓata fuska bance komai ba kuma banyi yunk'urin ciro nononba, Aliya cikin shaƙiyanci tace "Nonanne ba'ason mugani kuma dole sai an fito dashi muganiba" na harareta, Aunty ta haɗe rai ta dubi Aliya tace "to baza ki ganiba tashi ki fita" Aliya ta tashi tana dariya ƙasa_ƙasa kafin ta kai ga fita Mustapha ya shigo ɗakin bakinsa ɗauke da sallama, muka amsa masa a tare, Aliya ta fice Aunty ta masa sannu da zuwa sannan ta mik'e itama tana faɗin "ki tabbatar kafin na dawo kin bata nonon tasha" nace "toh" Mustapha ya zauna a kusa da Maryam yana kallonsu ita da babyn cike da k'aunarsu da ban sha'awa, yarinyar ta fara mutsu_mutsu tana ƙoƙarin saka kuka, Mustapha ya dubi Maryam yace "yunwa fa takeji, ki bata abincinta mana" na turo baki nace "Ni bansan yadda zan ba taba ai" ya waro idonsa waje yace "You mean tun ɗazu baki bata tasha ba" nace "ehh" yace "meyasa?" nace "toh mutane sunyi yawa a ɗakin kowa saiya gama kalleni" baice komai ba ya zuge zip d'in rigata yayi ƙasa da rigar ya ciro nonon daga cikin bra, wanda ya ƙara cika da ruwan nono, ba tallafo yarinyar yasa mata a baki, aiko tayiwa nonon wata irin cabka, na runtse idona tare da janye nonon da sauri, yarinya kuwa tasa kuka ya kalleni da alamun tambaya nace masa "da zafi fa" cikin rarrashi yace "sorry ze dena ai, ki bata tasha kinga kuka take" na ƙara sa mata ta fara tsotsa tare yin shiru, ina kallonsa nace "wannan baby'ntaka daga gani zatayi ci, ba kaji yanda take zuk'eniba" yayi murmushi saboda yanda tayi maganar yace "ai ba'a ƙasa ta ɗaukoba kema waya sani ko haka kikayi" na turo baki nace "to ni banma shaba, sai dai inkai ta gado" ya kwantar da kanshi akan kafadata yace "nima bansha da yawa ba ai" na shafa fuskarsa ina murmushi bance komai ba. Bayan tasha ta k'oshi bacci ya ɗauke ta, na cire nonon daga bakinta ina yamutsa fuska na maidashi cikin bra, Yaya ya ɗauketa yana kallona yace "zafinne dai" nace "eh, gashi duk yamun nauyi" yace "sorry idan muka shanye nida baby ze dena miki" nayi shiru ina kallonshi shikuma ya k'urawa babynshi ido, na kwanta a jikinshi nace "ya kake jinka yanzu, kazama Daddy" yayi murmushi tare da kissing goshin yarinyar yace "farin ciki mara misaltuwa Princess, Nagode miki sosai da..." na rufe mishi baki da hannuna nace "ka godewa Allah, domin shi ya bamu" yayi murmushi yace "Alhamdulillah, Allah ka ƙara bamu wasu masu albarka, ka shiryar mana dasu bisa tafarkin addinin Muslunci" nace "ameen, ya maganar karatuna tunda na haifa maka baby'n" yace "sai kin ƙaran uku, munyiwa Abbu da Aunty da Daddy takwarori" na waro ido nace "sai na tsufa kenan" yace "a'a bazaki tsufa ba tawan" cikin shagwaba nace "nidai yaya Please ka barni nayi yanzu" yayi kissed lips ɗina yace "kin zama mama yanzu ya kamata ki dena rigima" nayi murmushi nace "bazan iya denawaba, indai ina tare dakai kuma zaka rarrasheni" yace "i like it kuma bazan gaji da rarrashinkiba, maganar karatunki kuma idan *little Maryam* tayi wayo sai ki zaɓi duk ƙasar da kikeso a faɗin duniya muje kiyita karatunki harsai kin gaji" cikin farinciki nace "dagaske yayana?" yace "gasken gaskema, tunda kika haifamun baby kingamun komai a rayuwarnan, naduba_naduba naga babu abunda ya dace na saka mishi dashi face hakan, tunda shine babban burinki a rayuwa, nayi miki alƙawari insha Allah kina gama karatun zamu dawo nan gida Nigeria nagina miki k'aton hospital naki na kanki" na rungumeshi sosai cikin tsananin farin ciki nace "thank you so much hubby, Allah yakaimu time d'in da rai da Lafiya" ya musu kyakkyawar runguma ita da baby'n yace "babu godiya a tsakaninmu my love, kin cancanta na miki komai a duniyarnan my princess" nayi luf a jikinsa inajin k'aunarsa na ƙara ninkuwa a rai, tabbas nikam nayi dacen miji mai tsananin k'aunata da bani dukkan wata kulawa danake buƙata, a hankali nace "I LOVE YOU SO MUCH MY WORLD BEST" yace "love You too princess" na lumshe idona ina ƙara mannemasa inajin wata nutsuwa na ratsa zuciyata, a yanzu bani da wata sauran damuwa ko matsala a rayuwata, Mustapha ma a nasa ɓangaren ji yake duk duniya babu wanda ya kaishi dace da mace tagari mai haƙuri, tsafta, kyawawan d'abi'u da uwa uba tarbiyya da biyayya ga addini. Zuciyarsa fess yakejinta bashi da wata sauran damuwa tunda yayi dace da mace tagari, dama Manzon Allah (S.A.W) yace "mace tagari itace jin daɗin rayuwar duniya" (Allah ka haɗamu da abokan zama nagari, ameen.) _ALHAMDULILLAH, ALHAMDULILLAH, ALHAMDULILLAH. BAYAN DOGON ZANGO DANA ƊAUKA INA RUBUTA LITTAFINNAN YAU ALLAH YA NUFA NA KAMMALASA, ABUNDA NA RUBUTA DAI_DAI ALLAH YA HAƊAMU A LADAN, WANDA NAYI KUSKURE ALLAH YA YAFE MINI, MASOYAN *ABIN DA KA SHUKA* BANI DA BAKIN GODIYA A GAREKU SAI DAI KAWAI INCE, ALLAH YA BAR ZUMUNCI DA K'AUNA, ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MUKU A DUK INDA KUKE A FAƊIN DUNIYA, SAI MUN HAƊU A SABON BOOK ƊINA WANDA ZAI ZO MUKU NAN BADA JIMAWABA INSHA ALLAH._ *😥😥😥😥😥😥Wlh zanyi missing ɗinku sosai MASOYA, harnama fara tun yanzu.🥰😭*