*ABIN DA CIWO* Na © Rahma Kabir MrsMG. Wattpad @rahmakabir Page 1. *Gargad'i* _Ban yarda a juya mini labari ba ko ayi afmani da wani ɓangare na labarin ko kuma satar fasaha, ko a ɗaura min shi a wata kafa na media ba tare da izini na ba, dan Allah a kiyaye_ BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM. Sameeha tana cikin wani irin farin ciki mai matukar girma gaya, kullun cikin ɗoki da kosawa take yi akan komawa mahaifatarsu da zasu yi gabaɗaya ita da iyalinta, tunda Abban Amrah ya sanar da ita ya samu transfer na aikinsa zuwa Abuja kuma an kammala ginin gidansu da yake kaduna an saka komai sai tarewa, hakan yasa ta fara shiri tana haɗa kaya tun kafin ya saka ranar da zasu bar garin lagos, tayi alkawari ba zata sake zama a wani gari ba sai kaduna kusa da 'yan uwanta, kasantuwar Abuja ne ya koma yasa ta samu natsuwar ruhi ganin in mutum yaso a ranar zai iya zuwa kaduna daga abuja ya koma, ta san ganin Abban Amrah ba zai yi mata wahala ba shiyasa ta sanar da shi kaduna zata zauna in yaso duk karshen mako yazo ya gansu, kuma ya amince da haka saboda yana matukar son farin cikinta tunda itama tana iya kokarin ta wajen faranta masa. Dole ma Sameeha tayi doki domin sun shafe shekara biyu da watanni rabonsu da kaduna tana cikin tsantsar kewar ahalinta, kuma tsawon shekara goma kenan da suka yi a lagos sakamakon aiki da ya kai Aminu mijinta tare da kasuwanci da yake taɓawa, amma duk da daɗewarsu a nan bai sa ta saba da zaman garin ba kuma a nan duk ta haifi yaranta, ɗanta na farko Adamu ya ci sunan mahaifin babansa suna kiransa da Abi, shekarunsa tara sai Amratu da take da shekara shida bata sake samun wani haihuwar ba, suna dai fatan samun kari nan gaba duk da tsawon shekaru shida da suka ɗauka rabonsu da samun wani karuwa. Kullun burin Sameeha bai wuce ta wayi gari ace sun bar lagos sun koma kaduna ba, saboda kowa nata yana can haka shima mijinta Aminu duk danginsa suna can, banda aure wajibine wani sa'ilin ji take kamar ta barshi ta dawo kusa da ahalinta, musamman in aka ce ana taron biki bata samu zuwa ba ji take kamar tayi tsuntsuwa ta buɗe ido ta ganta a kaduna, ita dai macece mai mugun son 'yan uwanta daga dangin uwa har na uba, tana kokarin bautawa zumunci sosai dan in akace abu ya taso ko bata zo ba zata yi aiken kuɗi. Mijinta Aminu yana iya kokarinsa gurin kyautata mata bata rasa komai ba na jin daɗi ba domin za a iya cewa tana ɗaya daga cikin mata masu gata a gidan aurensu, dan kuwa tayi dace da miji nagari na nunawa sa'a, rayuwarsu tamkar su suka samu takarsa da biro suka tsara yadda suke so ta kasance, duk da mutum tara yake bai cika goma ba kuma duk faɗin jin dad6in akwai kaddara da ka iya faɗawa bawa ko ya zama silar samuwar aljanna ko kuma mutum ya faɗa tarkon dana sani. A lissafin Sameeha kwanaki sun shuɗe har lokacin barinsu Lagos yayi saboda gobe In Sha Allah zasu hau jirgin rana ya sauke su a garin Kaduna garin gomna, kira ne ya shigo wayarta ta ɗauka da sauri ganin mahaifatarta ce ke kirata. Assalamu Alaikim Ummaaa. Ta faɗa cikin fara'a da farin ciki, sai da umma ta saki murmushi kafin tace. Na'am ɗiyar umma ya shirye shirye dan na san ba zaki bar kanki ba sai kin ganki a kaduna. Hmmm umma ɗoki nake duk na ƙosa na ganku, da fatan su Yaya Zaidu dasu Anwar sun je sun kakkaɓe mana kurar gidanmu. Ai ko sunje sai dai sun tadda Hauwa da matar wan mijinki Laure a gidan, suka ce su dawo sun gama gyaran ko ina. Amma ya aka yi key yaje hannunsu ni Abban Amra bai faɗa mini zasu je yin wani gyaran gida ba, ni bana son irin wannan shisshigin. Haba Sameeha ina laifin anyi miki hidima, to karki yarda ki fara halin da zasu tsaneki, ina ruwanki in sunje ina ce 'yan uwan mijinki ne, idan ma sunyi abinda ba haka ba sun fi kusa da shi, ni bana son ki fara korafi da su. Amma umma wlh gulma ce yasa suka je gidan na tabbatar Hauwa ta kitsa komai ta amsa key gidan a hannun Yaya Alhasan. Koma dai miyi bana son ki jawa kanki damuwar dangin Aminu ki zauna da kowa lafiya dan yanzu ne ya kamata ki kwantar da kai ki gane halinsu dan ki san yadda zaki zauna da su. Hakane Allah yasa mu dace. Idan mun shigo In Sha Allah zan zo dan a nan gunki zan kwana muyi hirar yaushe gamo. To ɗiyar umma Allah ya kaimu goben ya kawoku lafiya. Ta amsa da Amin kana suka yi sallama Sameeha ta aje wayar tana mamakin wai Hauwa da Laure sun je gidansu sun yi musu gyara, mutanen da sam basa kaunar cigabanta ƙiri ƙiri Laure take nuna mata tsana saboda taki yarda taja ragamar gidanta, dan a yadda ta lissafa taso ace Sameeha ta mayar da ita abokiyar shawararta, domin ta rika sanin duk abinda ke wakana a tsakaninta da mijinta da kuma irin rufin asirin da suke ciki, amma Sameeha ta nuna mata kar take kallonta ta ki bada kofa balle fuskar da zata yi mata kutse a zaman gidan mijinta, wannan yasa ta tsaneta ta kasa danne hassadarta akan rayuwar walwala da suke ciki domin kaf danginsu Aminu yafi rufin asiri yana da kadarori da kuma aikin da yake yana samu kudi sosai, dan duk wani hidima in ya taso shine mutum na farko da ake fara faɗawa ansan zai yi da karfin guiminsa ba tare da ƙorafi ko gori ba, in ya bayar to baya so ma a ambaci sunansa, yana matukar kaunar 'yan uwansa da son hidimta musu, itama Sameeha tana kara masa kwarin guiwa sosai akan abinda yake yi bata taɓa hanashi yin alkhairi ba tunda itama yana yiwa yan uwanta hidima, bata san wahalar sana'a ba domin duk abinda ya taso nata yana yi mata, duk wannan yana ɗaya daga cikin abinda ya kawo mata bakin jini a gurin Laure da kuma 'yar korarta Hauwa ganin Aminu ya tare akanta da 'ya'yanta, banda surutu da suke yi akanta wai ba ta son shiga cikinsu ta ware kanta, tare da kai sukarta da gulmarta a gurin Aminu, har cewa suke in ta koma Kaduna Allah yasa ta riƙa bari ana zuwa mata gida dan sam bata son shiga cikinsu, Aminu sai dai ya toshe kunnensa tare da basu hakuri dan yasan matarsa tana da kirki ba tada wani abun da za a kushe tana da son mutane dan tasha bashi sako in zai je kaduna akan ya kai musu, amma basa gani kullun sai binta da sharri suke yi, wani labarin ma a bakin Sa'a matar yaya Kamalu take ji saboda ita bakin ganga gareta, tana tare da su kuma tana tare da Sameeha, abinda ta guntsa na gulma a gunsu sai ta kira Sameeha ta fesa masa, haka kuma in ta bigi ruwan cikinta ta kwashe ta faɗa musu, a hankali sai magana ya rika dawo mata tasan kuma da Sa'a kaɗai tayi zancen, tunda Sameeha ta farga ta ganeta sai ta iya takunta da ita dan ta kame bakinta duk labarin da ta ɗauko nasu ta faɗa mata to bata faɗar wata magana da zai zame mata kilu ta ja bau, sannan bata yarda ta bata nata labarin sai um da um um hakan yasa itama Sa'a ta rage shige mata. Ta tabbatar da komawarta kaduna sune mutane na farko data san zasu kawo mata tasgaro da farin cikinta, dan sosai Laure ta mayar da ita kishin saure kuma ance yafi asalin zama da kishiya zafi, ga kuma Hauwa da take yayar Aminu dan ita ce ke binsa ta fiye nuna mata isa da son girman tsiya, dole ita sai ta nuna gadara da iko akan Aminu sai dai yadda ta gode Allah Aminun shima ba baya ba, sam baya yarda da duk abinda tazo masa da shi matawar zata yi kutse a cikin rayuwarsa ta takura masa, ta tabbatar da zuwa gidan da suka yi a matsayin gyaran gida ba alkhairi ya kaisu ba, wani munafurcin ya kaisu wanda Allah kaɗai ya sanshi, amma tunawa da tayi anyi musu saukar Alqur'ani da sadakar abinci a satin daya gabata wanda ɗan uwanta Zaidu ne ya jagoranci komai, saboda shima akwai key da ya amsa na gidan a hannun yaya Alhasan, sai ta sauke ajiyar zuciya tana cewa a fili. Allah ya sa alkhairi a komawarmu Kaduna, ka kauda idon munafukai da makiya akanmu. Amin Mamanmu. Amra tace tana karasa shigowa ɗakin ta zauna kusa da ita tana cigaba da cewa. Mama ai babanmu zai sauya mana makaranta mai kyau a can ko, kuma wanda anty ba zata riƙa dukanmu ba ko. Sosai kuwa har ya sama muku ma da mun koma zai je yayi muku register, makaranta ce mai haɗe da boko da islamiya. Sannan batun anty in baki yi laifi ba taya zata riƙa dukanki haka kurum, ni dai ina so ki zama daliba mai ilimi da kwazo da kuma jin magana. Allah dai ya kaimu gobe lafiya dan iyanzu haka muna cikin gidan Umma In Sha Allah. Amra gyaɗa mata kai take yi tana murmushi dan itama ta na son su koma can. Duk zuwansu a family hau ɗinsu Aminu suke sauka dan babban gidane da akewa laƙabi da gidan Alhaji Ado Meyare. Sai dai Allah yayi masa rasuwa tare da matarsa Amina shekara ɗaya ke tsakanin rasuwarsu, su asalinsu 'yan garin meyare ne daga Alhaji har Umma 'yan can ne aikin gomnati ne ya kawo Abba cikin garin kaduna da yake ɗan boko ne sosai. Yanzu shekara shida kenan da rasuwar Umma Amine, wanda yayi dai dai da shekarun Amrah an haifeta da sati biyu Umma ta rasu sanadin ciwon sugar, sun bar yara biyar. Alhasan shine babba kuma ya manyanta sosai dan yaransa shida ya aurar da mata biyu da babban ɗansa Namiji, saura su uku da suke gabansu duk kamaranta suke yi, matarsa ce Lauratu a nan gidan suke zaune amma a wani part duk nan ta haifi yaranta tun tana amarya take a gidan, shiyasa komai da zai shiga ya fita tana da masaniya, kamar yadda mijinta yake babba itama haka take nuna isarta, sai Kamalu da yake bin Alhasan shima abnan gidan yake zaune da matarsa Sa'adatu, yaransu huɗu ya aurar da babbar 'yarsa sai namiji daya ke karatu a jami'a me bi masa kuma tana kokarin kammala secondary sai autarsu da take da shekara bakwai. Sai Hauwa take bin Kamalu tana da yara biyar ta aurar da biyu mace dana miji saura uku da suke gabanta, ita tana zaune a gidan gadonsu tare da mijinta, gidan yana nan kusa da family hause ɗinsu saboda mijinta bayi da karfi Abbansu ya basu gidan akan su zauna har sai yayi nashi, sai kuma Aminu da yake bi mata shekara goma kenan da aurensu da Sameeha yaransu Adam ɗan shekara Tara sai Amratu da take shekara shida. Sai kuma autarsu Ummu Salma ta kamma digree ɗinta tana koyarwa a secondary wanda a yanzu haka ana shirin yin aurenta da wani Junaid ɗan kasuwa ne. * Lokacin da Abban Amra ya dawo bayan yayi wanka yaci abinci yara duk sunyi barci, ita da shi suna zaune a falo ta yi filo da cinyarsa suna kallo, Sameeha ta ɗago kanta tana dubansa. Abban Amra ashe su Yaya hauwa ce suka je yi mana gyaran gidanmu. Kamar ya? ni ban san sun je ba, amma naga kin ce su Zaidu zasu je kuma haka na faɗawa yaya Alhasan. Aiko tare taje da yaya Laure su suka cewa su Zaidu su tafi har sun gama gyaran gidan. Ikon Allah, wannan aikin ai ba nasu bane, da alama sun ƙosa mu koma. Murmshi tayi mai sauti dan tasan Aminu ba zai faɗi wani abu mara daɗi akansu ba, dan ba lallai ya hango abinda take hange ba duk da bata yi musu zargin saka musu mugun abu a cikin gidan ba, dan tana yi musu kyakkyawan zato na basa bin malamai, amma munafurci da gulma da mayar da karamar magana a zama babba to sun shahara a wannan fannin, haka ta sauya musu hira da wani zancen, daga bisani suka tashi suka isa bedroom ɗinsa suka kwanta. Washe gari. Da wuri suka gama shiryawa dama tuni sun sayar da kayan dake gidan na katako dama gidan gabaɗaya, kayan sakawansu da ɗan abin amfani kamar su kayan kitchen duk sun loda a buhuna da komai, tuni mota tazo suka kwashe su suka kama hanyar kaduna ya rage sune da 'yan jakan hannu. Sha biyu a airport tayi musu bayan mintuna aka fara kiransu, nan suka je suka yi duk abinda ya dace kana suka wuce filin jirgi suka shiga, minti goma da shigarsu jirhinsu ya ɗaga zuwa garin Kaduna, wanda suke cike da farin ciki mara misaltuwa a dalilin komawarsu kusa da dangi. Bayan sun iso Kaduna suka fito suka tadda motar yaya Alhasan dana yaya Kamalu suna jiransu, cike da murna suka isa garesu suka shiga gaisawa daga bisani Aminu ya shiga motar yaya Alhasan tare da Abi, ita kuma Sameeha ta shiga motar Kamalu ita da Amrah, suka wuce zuwa gidansu dake nan Unguwar dosa 'yan majalisu, yaya Alhadlsan sunata hira da Aminu akan sauyin gurin aikin daya samu, ita dai Sameeha ba um ba um um dan bata wani yi sabo da Yayyinsa maza ba, tana matukar basu girma tamkar iyayen Aminu ne, shiyasa tayi gum har suka isa gidansu wanda ya buga hon mai gadi ya wangale gate, nan ta hango mata cike a gidan suna ta hada hada tamkar ana biki, gabanta ne yayi mugun faɗi da tunanin meyasa zasu taru a gidan dan zasu dawo kawai, bayan sun saka sati mai zuwa ne ranar da kowa zai zo suyi walima murnar dawowarsu da tarewa a sabon gida. Ummu Sultan da Samha ce. [7/7, 13:04] Buhainat😁: *ABIN DA CIWO* Na © Rahma Kabir MrsMG. Wattpad @rahmakabir Page 2. Bayan yaya Kamalu yayi parking sai ga matan dake gidan da yara sun zo sun zagaye motarsu suna faɗin oyoyo tare da yin guda, Sameeha dai fitowa tayi tana kallon ikon Allah wanda a yadda suka tsara ba zasu sanar da sauran dangi yau ne dawowarsu ba har sai an kwana biyu kafin za a faɗa tare da gayyatar su walima da suka shirya yi, yadda taga suna ta yi mata sannu yasa ta saki fuska tana amsawa, bayan sun shiga cikin falon ne suka ganshi kaca kaca anci abinci da ruwan gora da lemukan gora an zubar wani gurin an zubar da ruwa yayi dama dama falo dai ya fita hayyacinsa, ga cushing da suke sababbi anci abinci akai duk an zubar, cabar mamaki da haushi yasa Aminu bai tsaya a falon ba ya wuce zuwa falonsa ya buɗe ya shiga ciki ya zauna a cushing, kana ya cire hular kansa ya tallabo fuskarsa da hannu bibbiyu, sai ga su Yaya Alhasan sun biyo bayansa suna balbale faɗa, Sameeha itama ta shigo ciki da yara sannan su Hauwa suka biyo su suka tsaya cirko cirko suna sauraren faɗan da Alhasan ya ke yi musu akan yadda suka mayar da gida kamar ana hidimar biki ko suna, har murhu suka dasa a tsakar gida suka yi girki, Yaya Alhasan ya dubesu yana cewa. Da izinin waye kuka zo gidan nan kuka dasa shagali kamar za a tarbi amarya, wannan ai hauka ne da rashin hankali, fisabilillahi ya dace ace Aminu ya dawo yaga gidansa haka. Ina ce mun tsara sai bayan kwana biyu za a faɗawa dangi lokacin walimar da za a yi na dawowarsu. Yaya mu wlh munyi ne dan suga tsantsar murna da farin cikin dawowarsu da muka yi, ba da wani nufu muka yi haka ba, kuma In Sha Allah yanzu zamu gyara ko ina.. Cewar Hauwa, Kamalu ya daka mata tsawa. Ai na tabbatar ke ce kika yi shelar sun dawo saboda bakinki ba farsa kamar radion daya samu matsala, rarara haka kike, shiyasa ni inyi sirri da ke Allah ya kyauta, ke kuma wa kika tambaya da kika kwaso jiki kika zo. Ya kare maganar akan matarsa Sa'a da sai raba ido take dan tabbas su suka shirya abinsu ba tare da mazan sun sani ba, Hauwa itace shugaba sai Laure data karfafa lamarin, Laure ce ta yi magana cikin jin haushi. Haba daga taya murna sai cibi ya zama ƙari, mu munyi abinmu domin Allah ne da kuma zumunci amma baku yaba ba sai kushewa. Hauwa kun ga ku zo mu tattara mu tafi tunda suma wanda muke damonsu basu ji daɗin ganinmu ba, hmmmm ba shakka Aiziki kashi tun kafin abu yayi nisa an fara nuna mana wariyar launin fata, to Allah ya horewa kowa. Dama ai ke girman jiki gareki amma da kina da hankali ke ce zaki hana wannan haukar da kuka shirya, amma kika biye su kuka aiwatar da abin takaici. Cewar Alhasan cikin zafi, ƙanwarsu Salma ce tace cikin fuskar tausayi. Dan Allah yaya kuyi hakuri yanzu zamu gyaran gidan. Anty Sameeha fatan kun dawo lafiya. Lafiya lau Alhamdulillah, da fatan mun same ku lafiya, yaya Laure yaya Hauwa anty Sa'a dan Allah ku yi hakuri ni sam banga laifin da kuka yi ba, ku rabu dasu yaya, kuma nayi murnar wannan tarba da kuka yi mana dan soyayya ce ta kawo haka, Allah ya saka da alkhairi ya bar zumunci. Dalla rufe mana baki munafurcin banza. Cewar Hauwa data katseta ta wuce fuuu kamar guguwa, suma sauran suka bi bayanta bayan Laure ta sakar mata wata uwar harara suka fice. Sameeha sauke ajiyar zuciya tayi ta koma ta zauna tana bawa su Yaya hakuri akan subar maganar haka komai ya wuce, ita sam bata ga laifin su ba tunda mai kaunarka shine zai tarbeka da farin cikinsa, duk da a cikin ranta ba haka bane amma dole ta nuna kawaici dan tasan faɗan suna yi ne saboda ba zata ji dadin faruwar abinda suka yi ba, Aminu ma nuna musu yayi komai ya wuce, nan suka yi salama da su suka wuce, suna fita Aminu ya rufe kofar falonsa da key dan sam baya son hayaniya ya shige bedroom ɗinsa ya bar Sameeha da yara a falo itama tana mamakin wannan rashin lissafi da suka aikata mata sai dai ta san da biyu suka yi, kuma taji daɗin yadda su Yaya Alhasan suka kwarkwance musu ko banza ba zasu kara yi mata wannan shisshigin ba. *** Laure da Hauwa. Suna fita tsakar gida suka sanar da 'yan uwa cewar zasu tattara su koma family house ɗinsu dake unguwar dosa, sai su cigaba da hidimarsu saboda dama jiran dawowarsu suke yi su koma can, suka saka aka yi shara ciki da waje aka yi mofin kitchen da falo gida ya dawo hayyacinsa duk da ba wani gyara ya samu mai kyau ba, suka kwashe murhu da tukunya suka saka a baron da aka ɗauko shi dan daga can babban gida suka ɗauko, saboda Umma ta siya musu tukwane da kuloli saboda sha'ani, Laure takan ba da hayarsu a bata kudi, kuma ba wanda ya hanata dan saboda gadara da take a gidan kuma ba umma balle Abba a raye, haka suka tattara da yara suka wuce ba tare da sun yi musu sallama ba, da yake ba wani nisa sosai a tsakaninsu wasu a kafa suka tafi babban gida, wasu kuma suka tari napep ya karasa da su, Laure da Hauwa sune karshen tafiya suka jera a kasa suna yi suna surutu cike da takaicin abinda su Alhasan suka yi musu, Hauwa ta mele baki tana cewa. Ni Sameeha tafi bani haushi, ai da taso karemu lokacin da yaya Alhasan ya fara magana sai tayi kokari ta tare shi, amma sai da suka kare mata cin mutunci kafin ta iya saka baki. Ni kin san miye ma? na kula da shi tunda suka shigo wani gani gani take mana da kallon raini ita matar Alhaji, wlh yarinyar nan nan gaba Allah kaɗai yasan iskanci da wulakancin da zata yi mana, dan haka ni zan kama kaina dan bazan bari raini ya shiga tsakaninmu ba. Haba Yaya Laure wane ita? ai uban kuturu yai kaɗan, kuma bata isa ta hana mu zuwa gidan ɗan uwanmu ba dan a sama ta same shi wlh, in kuma ta kawo mana wargi sai nayi sanadin da tabar gidan mu aura masa wacce muke so. Allah yasa Aminu kar ya baku kunya dan naga yana mutuwar son Sameeha kamar ta gama da shi. To na nawa kuma, ko kin mance mahaifin mamanta malami ne ai tuni aka kafe sunan Aminullahi a allon ƙarfe, sai yadda tayi da shi dan an wanke an bashi ya sha. To Allah ya kyauta amma in tasan wata ai bata san wata ba mu zuba mu da ita. Yauwa yanzu naji batu ai sai dai muga bayanta ba dai mu taga karshenmu ba, wlh yadda na tsani mutuwata haka na tsani ganin Sameeha a gidan Aminu tunda ta nuna mu bamu isa da ita ba. Amma gobe In Sha Allah zan dawo gidan na ja mata layi dan nan ba Lagos bane, mun dawo kusa da juna komai da zata yi yana kan idonmu. Hmmm har kin tuna mini da batun yar aikin da kika ce na samo, jiya agent ɗin ta kira ni ta sanar dani an samu. Yauwa yaya Laure zamu je kuwa tare, dan mu ga yarinyar kuma mu ɗaurata a hanyar yadda muke so,  kinga kenan zamu rika jin labarin duk abinda ke faruwa a gidan. Cewar Hauwa tana wani sha'umin murmushi, sosai suka cigaba da fito da hassadarsu akan Sameeha, bayan in an tsaresu ba su da wani hujja da zasu faɗa laifin da Sameeha ta yi musu, kawai daibbakin ciki daular da take ciki suke yi kuma sun kasa juyata kamar yadda suka so. *** Sameeha. Sai da ta tabbatar da sun fita kafin ta fito falon ita da yara, sai ta fita tsakar gida taga sun gyara gidan amma akwai sauran inda ya dace a share sannan akwai inda ya kamata a saka ruwa a wanke, ba zata iya wannan aikin a ranar ba sai dai ta bari zuwa gobe in Allah ya kaimu tayi. Babban gida ne da aka zuba masa kudi aka kerashi yadda ake son ya kasance, falo biyu ne a gidan falon farko shine na Sameeha da ɗakuna guda gudu, ɗaya na ta ɗaya na Abi ɗaya kuma na Amrah, sai guda ɗaya extra saboda baƙi, sai katon kitchen da store a ciki an zuba komai na buƙata sannan akwai bayi ɗaya a falon duk da a ko wani ɗaki da bayin, sai falon Aminu da yake madaidaici da ɗakuna biyu, ɗaya bedroom ɗinsa ɗaya kuma ya aje muhimman takardunsa wato study room da kuma kayan motsa jikinsa, an zuba komai dai na buƙata. Sannan can bayan gida akwai BQ guda biyu da bayi da kitchen sannan akwai bishiyoyin mangoro da gwaiba har da gwanda da lemu, yar karamar garden dai da rumfar shan iska da kujeru, sai parking space a nan farfajiya an ajera mota uku a ciki, ɗaya na Aminu ɗaya na Sameeha hotuwar nashi da yake hawa ya bar mata sai ya saya sabo, sai na ɗaya na kai yara makaranta, ga kuma ɗakin me gadi a bakin gate komai dai gwanin sha'awa. Sameeha da ta koma falo sai ta aika Abi ya amso key ɗin ɗakunansu dan duk suna rufe, kuma key yana hannun yaya Alhasan sai da suka zo ne ya bawa Aminu su, da ace su Hauwa sun samu key ɗin da fa sun gama ganin sirrin gidan da komai yadda zasu ji daɗin karaswa, tana tsaye sai ga Aminu ya fito daga falonsa tare da Abi, da murmushi ta kalle shi tana cewa. Allah yasa bamu tasheka a barci ba. A'a idona biyu tunda na shiga nake amsa waya kin san harkan aikinmu ba hutu, amma gaskiya gidan nan sai kin kira su Ikram sun zo sun tayaki gyara dan sam bai gyaru yadda ya kamata ba. Eh dama na bari gobe In Allah ya kaimu sai nayi aikin yanzu me zan ɗaura maka kaci, dan mu muna da abincin tarba da ummanmu ta yi mana, kasan can zamu kwana. Eh da yake ni ba ɗan umma bane dole a ware ni, to nima dani zaku tafi in cika cikina a can in yaso sai na wuce can babban gida in kara gaisawa dasu Yaya, ƙila ma na kwana can. Abban Amrah na isa nace kai ba ɗan umma bane, kawai banyi maka tayin zuwa ba ne dan baka ce zaka ba. To yanzu nace zani Madam Meeha matar Aminun Alhaji Ado. Sai ta kwashe da dariya yaran suna taya ta shima dariya yayi sai ya wuce ya buɗe ɗakinta suka shiga suna wow wow kamar motar asibiti, an zuba funitures masu tsanani kyau da burgewa wanda suka yi oder daga company MG Furnitures wanda show room ɗinsu yake Freetime house kusa da asibitin giwa kan titin Ali Akilu. Zaku iya tuntuɓarmu a nan 09034940106 domin karin bayani akan ko wani irin kaya da kuke muradi. Bayan sun gama ganin ɗakin Sameeha haka suka fito suka shiga ganin ɗakunan dake falon har zuwa kitchen komai yaji an zuba kuɗi kuma buƙata ta biya, bayan sun shiga store ne suka tadda an buɗe buhun shinkafa ɗaya an ɗiba, ga kuma mai dake galam da aka diba shima, Aminu ya buɗe freeza da aka zuba musu kaji ɗanye gyararru da ganda da kifi. Ya ƙirga kajin yaga guda takwas madadin guda goma sha biyar da yaya Kamali ya faɗa masa an zuba a ciki, ya juyo fuskarsa cike da ɓacin rai. Amma wlh Hauwa da Laure sun wuce gona da iri, na tabbatar sune suka yi wannan aikin, ashe abincin da suka dafa namu suka ɗiba, na ɗauka taya murnan nasu da gaske ne da suka cika mana gida suka ɓata, gaskiya dole na taka musu burki dan bazan jure wannan cin kashin ba. Haba Aminu in rai ya ɓaci hankali ke nimoshi, 'yan uwanka ne fa suka ci abincin nan, arziki ne ma ayi maka irin haka, idan ba suna ganin kai nasu ba ne taya zasu yi haka, ni dan Allah karka yi musu magana faɗar da su Yaya Kamalu suka yi musu ya isa kar kazo kayi magana su mayar da abin wani iri. To amma fisabilillahi ba zasu iya faɗa mini za suyi abu ba sai dai kawai mu dqywo mu tadda gida kaca kaca, ashe ma abincin gidan suka ɗiba suka yi wannan wandaƙar, duk lemuka da ruwan dana siya mana wanda zamu jima muna amfani dasu shi suka kwashe suka shanye, wannan ai haukane da mugunta.. Kayi hakuri dan Allah kuma kayi musu uzuri na tabbatar ba zasu sake yin haka, Abi da Amrah kuje ku ɗauko hula da hijab da jakata mu wuce gidan umma. Ta kare maganar akan yaransu, sai suka fice da sauri ita kuma ta mayar da kallonta gurin mijinta. Dan Allah Abba Amra komai ya wuce kuma bai dace kana irin wannan maganar a gaban yaran nan ba hakan ba tarbiyyarmu bace. Wlh raina ne ya ɓaci amma zan kiyaye, mu je gidan Umma dan naga la'asar ta kawo jiki. To tace masa sai suka fito, yaje inda motarsa take ya cire mata riga ya budte ya shiga ciki ya kunna ya kawota tsakar gidan, suka shiga gabaɗaya mai gadi ya buɗe musu gate suka fice. Ummu Sultan da Samha ce. [7/7, 13:04] Buhainat😁: *ABIN DA CIWO* Na © Rahma Kabir MrsMG. Wattpad @rahmakabir Page 3. Gidan Umma. Suna isa rafin guza Aminu yayi parking a ƙofar gidansu Umma suka fito ya rufe mota suka ɗunguma cikin gidan da sallama, da gudu kanwarta Ikram ta fito ta zo ta rungumeta tana murna sosai da ganin yar uwarta, Anwar ma ya fito yana dariya ya gaishe da Aminu, Aminu ya amsa yana kama hannunsa tarw'e da tambayarsa makaranta, Umma da yaya Zaidu suka fito suna yi musu maraba, sai suka yada zango a barandar gidan kan shinfiɗar babban tabarma, nan suka shiga gaisawa daga bisabi suka shiga hirar yaushe gamo, sai umma ce ta katse hirar tana cewa. Sameeha maza tashi ku shiga ciki abinci yana nan a falo ki zuba muku dan na san da wuya in kunci wani abu. Wlh kamar kin san muna jin yunwa kuwa, Abban Amrah, Abi da Amrah mu shiga ciki kun ji mu fara cika k'kundunmu kafin mu cigaba da hira, dan yau nasan sai dare ya raba muna aikin abu guda, duk sai an bani labaran abubuwan da faru da bamu nan. Eh lallai akwai babban aiki a gurin Zaidu da su Ikram dan ba dani za ayi wannan hirar ba. Cewar Umma tana 'yar dariya, suma dariya suka yi suka shiga ɗakin umma wanda yake madaidaicin falo ne da kuma uwar ɗaka a ciki, akwai kujerun zamani da kuma kayan kallo a ciki, Sameeha sosai take fito da ummanta dan tana kashe musu kuɗi sosai sam basa cikin matsin rayuwa duk da Mahaifinsu ya rasu, umma ita ce kaɗai matar Malam Aliyu, asalinsa shi ɗan Maiduguri ne zama ne ya kawo iyayen iyayensu Kaduna har suka yaɗu, umma kuma 'yar nan kaduna ce fulanin Zaria, a nan suma iyayenta suke a unguwar kawo har Allah ya haɗa ta da Aliyu ya ganta suka yi soyayya har ya aureta ya ajeta a nan gidan gadansu dake nan kawo, yana aikin sayar da kayan mashin a nan kasuwar kawo har Allah ya hore masa ya gida masu wannan gidan da suke ciki a rafin guza, Zaidu shine ɗansu na farko sai Sameeha da kuma Ikram sannan Usman da suke kira da Anwar dan ya ci sunan mahaifin babansu. Anwar yana ƙarami Baba ya rasu wanda mota ce ta bigeshi a babban titi kawo nan take yace ga garinku, kaf danginsu ba wani mai ƙarfi umma ce ta tsaya akan ƴaƴanta tana sana'ar sayar da waina a cikin gida tana biya musu kuɗin makaranta har suka kawo girma, Zaidu shine ya samu yin digree wanda Saneeha a iya secondary ta tsaya. A taron walimar saukarta na Al-qur'ani ne da ya zo ɗaya da walimar 'yar gidan yaya Kamalu dan ajinsu ɗaya a islamiyarsu dake a sabon kawo, shi ne Aminu yaga Sameeha a wannan taron ya kamu da sonta, har ya bi ta hannu  Laila 'yar Kamalu ya kafa soyayyarsa a gurin Sameeha. A haka dai soyayya tayi ƙarfi har ya kaisu ga yin aure wanda ana ɗaurawa washe gari aka wuce da Sameeha Lagos in da yake aikinsa. Tun da Sameeha tayi aure umma ta dena wahalar aikin waina dan duk wata take yi musu aike da kuɗin da zai wadace su, har sunan Zinariyar dangi ake kiranta saboda ta fita zakka dan ta auri mai rufin asiri sosai, dangin umma gidansu gidan yawa ne amma a ɗakinsu su biyu ne rak umma Halima itace babba sai kanwarta Rukayya, ita tana aure a can Zaria da zuri'arta. Dangin Baba kuwa akwai wansu Baffa Talle da suke uwa ɗaya uba ɗaya dan du uku ne a ɗakinsu, yana zaune a cikin gidan family hause ɗinsu, sai kuma ƙanwarsu Gaggo Zulaihatu tana aure a badarawa, sannan sauran waɗanda suke 'yan uba maza uku mata biyu, dan mamansu ita ce amayar kuma duk sun rasu har da kishiyarta da mahaifinsu, ya rage yaran ne kuma sun rike zumuncinsu sosai. Goggo Zulai tana da yara huɗu, Junaid da Abdullahi sai Sadiq da autarta Najwa, baba Talle kuwa Allah bai bashi haihuwa ba da yake baida cikakken lafiya, sai dai yaran 'yan uwansa yake riƙewa a matsayin nashi. .. Suna gama cin abinci waina ce da miya yaji tantakwashi sai jelof ɗin shinkafa wanda umma ta dafawa su Abi kila ba zasu so waina ba, dan duk yara akwai ƙauna mai ƙarfi a tsakaninsu da shinkafa, wainar kuma sunyi ne saboda Sameeha dan tana mugun sonsa, sai kunun Aya mai daɗi da soyyyar kaza. Sameeha ta samu takeawy na roba ta zubawa Aminu soyayyar kazan ta kulle a leda kana ta ɗaukar masa kunun aya da aka zuba a medium ɗin gorar swan suka fito yayi sallama dasu Umma, sai ta rakoshi har mota ta saka masa kaza da kunun a mota suka yi sallama tana kara bashi haƙuri akan kar ya yiwa su Hauwa magana yavbar komai ya wuce, gyaɗa mata kai yayi yana murmushi ya tada mota ya wuce yana yaba kyawun halin Sameeha, mace ce mai rufin asiri da sanin yakamata, shiyasa har abada ba zai gushe ba gurin kyautata mata, haka ya tafi yana tunaninta da shiga kewar yau ba zasu kwana a tare ba. Sameeha tana shiga gida suka gabatar da sallah kafin suka fito tsakar gida gabaɗaya suka zauna a tabarma, nan ta shiga bawa umma labarin abinda ya faru ɗazun, umma tace cikin kulawa. Ai ni banga abin ƙorafi ba a nan tunda mai sonka shike ɗokin ganinka, su Alhasan da basu yi musu magana ba, dan gyaran gida ko a nan zaki samu masu tayaki ku gyara. Umma kenan na kula sam bakya so na faɗi ƙorafin su Hauwa, amma wlh gumunta ce kawai suka yi. Wlh kuwa Anty mugunta ce taya zasu ɓata gida har kujeru sannan su kwashe muku ruwa da lemuka. Cewar ƙanwarta Ikram data saka baki a hirarsu, umma ta nunata da yatsa. Ba ruwanki a wannan maganar karna sake jin bakinki, ke kuma wlh ki shiga hankalinki dan banga amfanin wannan ƙananun ƙorafin ba, in ma da biyu suka yi muku haka kansu suka yiwa ai. Murmushi Sameeha tayi dan ta san umma ba zata taɓa bin bayanta ba, tunda ta auri Aminu in dai ta kawo mata maganar anyi mata abu wlh umma bata bin bayanta sai dai wani abin ma ta bata laifi, shigowar Yaya Zaidu daya dawo daga masallaci ne ya katse muna hira ya samu karamar kujerar mata ya zauna yana cewa. Mutanen Lagos ansha jirgi dan bazan ce hanya ba. Ya rayuwa da kuma halin da kasarmu take ciki. Alhamdulillahi ai kasarmu sai addu'a, shuwagabanni ne gasu nan kowa ya samu dama sai dai yayi shanya, Allah yasa mu dace. Ya batun aiki har yanzu baka samu ba? Ameen dai, aiki ya samu tunda na buɗe shagon aikin printing karashe ne ya rage na fara aiki, kinsan harkan ne yanzu komai sai da kuɗi. To Allah ya taimaka, amma zan kara yiwa Abban Amrah magana in ya samu dama sai ya baka. Ai nasan da ya samu zai nime ni kawai dai lokaci ne bai yi ba Allah yasa muna da rabo a gomnatin. Suka amsa mishi da amin kana umma tace. To kin ganshi nan aure yake nima a haka shi ba aiki amma yana nimarwa kanshi nauyi. To umma ai ya kai ya aje iyali kuma In Sha Allah in ya ɗauko mu zamu haɗu mu dafa masa, kuma muna da Allah. Au haka zaki ce? Cewar umma, sai Sameeha tasa dariya Zaidu yana taya ta yace. Yauwa 'yar gari na san dama ko kowa ya juya mini baya ke kina tare dani. Kin san ma wacece? Sai ka faɗa yayanmu. Najwa ce 'yar gidan Goggo Zulai kinga abu ne na gida tuwona maina ba za a cika buri ba. Kai amma naji daɗin wannan magana kunga zumunci zai ƙara karfi. Amma da fatan Najwan ta amince dan kar a tilastata. Ta amince amma kinsanta da rawar kai, mu uku take tare damu wai saboda tsaro, tasan kuma cewa ni bana cikin mayaudara tunda ni na gidana. A hankali zata rabu dasu kasan ba zai yuwu lokaci guda ba, har yanzu tana zuwa haddar ko ta haɗa? Ta hadddace izu ashirin da biyar, kafin Aurenmu In Sha Allah zata haɗa. Sameeha tace Allah ya kaimu, sai suka cigaba da hira, nan take Sameeha ta turawa Zaidu dubu ɗari a account ɗinsa dan tana da shi, yana gani ya kalleta yana murmushi. Kuɗin gyaran shagonka ne ka ƙarasa Allah yayi jagora. Cewar Sameeha, Zaidu yama kasa magana dan wlh gani yayi kuɗin sunyi yawa bai taɓa zato ba, ya kalli umma yana cewa. Dubu ɗari fa ta tura mini umma. Rabonka ne ya rantse, sai ka amsa kayi mata fatan alkhairi. Cewar umma cike da jin daɗi, nan Zaidu ya dinga kwararo mata addu'a suna amsawa da amin, gabaɗaya fuskarsu cike da farin ciki da annashuwa duk da mahaifinsu baya raye amma suna cikin rufin asirin Allah babu wanda yake cikin damuwa, duk da Zaidu ne kaɗai yayi karatu mai zurfi ya karanta computer seiance digree, ita kuma Sameeha iyakarta secondary duk ta taso ta cigaba amma Allah bai mufa ba tayi aure, Ikram data gama secondary ta cigaba da Islamiya sanawiyya yanzu aji biyar take itama ana jiran saurayinta ya fito ne ayi maganar aure, Anwar kuma yana aji shida a secondary yana shirin fita, suna da ilimin addini daidai gwargwado kuma sun samu ingantacciyar tarbiyya. Sai gabda magrib Zaidu ya fita su kuma suka yi alwala suka shige ɗaki. *** Najwa. Bayan sallar isha'i Zaidu yaje zance, suna zaune a ƙofar gidansu kan dalaki ga hasken tantarki ya haska gurin, a cikin hirarsu ne yake faɗa mata Sameeha ta dawo, Najwa ta soma murna tana cewa. Alhamdulillah naji daɗin dawowarsu kuwa da fatan suna lafiya. Lafiya lau sunan a gidanmu zasu kwana gobe In Sha Allah zata koma gidanta da wuri saboda suyi gyare gyare. Aiko zan zo nima a yi dani dan na ƙosa naga yadda gidanta ya tsaru, kasan ni a rayuwata ina mugun son harka ta masu kuɗi, balle kuma abu namu maganin a kwaɓemu na samu gidan yin walima in na tashi aure. Hajiya Najwa sarkin son kuɗi, to kiyi fatan nima na samu kuɗi na gida miki gida na alfarma. To Allah ya baka, wlh kasan ni abinda ke burgeni da masu kuɗi yadda suke rayuwa cikin sauƙi da jin daɗi, gida mai kyau motoci na alfarma ga kuma sutura mai kyau, kai komai masu mai kyau ne, mafarkina shine na ganni a irin wannan rayuwar. Kiyi fatan Allah ya baki arziki mai albarka ba wanda zai zame miki damuwa ba, da yawan masu kuɗin da kike gani wlh damuwar da suke ciki na jarabawar da Allah yayi musu yafi ƙarfin tunaninki. Kai yaya amma dai suna cikin kuɗi, ai da wani talaucin gwara kayi kuɗin Allah ya jarabceka ko ba komai mutum baya cikin wahala. Allah ya kyauta to dan naga kinyi nisa, ni anya ma nan gaba in wani mai falleliyar mota ya zo gunki ba zaki rabu dani ba kuwa? Kai yaya duk son kuɗi na bai kai haka ba, kuma ai mun gama magana lokaci muke jira, tunda ko wani bawa Arzikinsa yana goshinsa. To yanzu naji kin yi magana mai kyau, ni bari na tafi sai zuwa jibi ko gata In Allah ya kaimu zaki ganni. To yaya dama um.. Ta faɗa tare da yin shuru tana susa kai, Zaidu ya kura mata ido yana 'yar murmushi dan ya san wani abin zata tambaye shi, yace cikin kulawa. Faɗi kanki tsaye karki yi shakka ni ɗan uwanki ne mai yi miki duk kan hidimarki. Dama yau inna tuwo ta mana kuma wlh kasan ni da tuwo bama shiri, shine nake so ka siya mini indomie. Ai yau kin wuce cin indomie dan ajihuna yana da nauyi, yanzu ki shiga gida zan je na siyo miki abu inna dawo zan kira ki fito ki amsa. To tace masa tana yi masa godiya, haka ya kunna mashin ɗinsa roba roba ya wuce ita kuma ta shiga gida tana kwalawa inna kira har sai da ta dangana da ɗakin inna ta buɗe labule ta ganta zaune a dadduma tana jan carbi, shiga tayi ta zauna har sai da inna ta idar kafin ta kalleta tana cewa. Wai ke Najwa yaushe zaki yi hankali? Randa kika aurar dani Inna. Ta bata amsa tana 'yar dariya, daƙuwa inna tayi mata tana cewa. Allah ya shiryaki auta, to lafiya kike mini ɗan kira kamar kin haɗiyi ƙarfe. Inna anty Sameeha ta dawo yau yanzu Yaya Zaidu ke faɗa mini. To ai ke ce baki sani ba amma ni tun ɗazun nayi waya da ummansu ta faɗa mini. Laaa shine baki faɗa mini ba. To da ban faɗa ba ai gashi kin sani yanzu, kuma ɗazun kina islamiyya koda kika dawo na manta To inna zani gobe In Allah ya kaimu naga gida dan wlh ina son naga daular da Anty Sameeha ke ciki. Idan kin ga daular me zai kareki dashi? kinga Najwa! kinga ki cire rayuwarki da shegen son kuɗi. Inna kuɗi shine rayuwa ki barni na so su, kuma so kike nayi rayuwa a gida irin wannan, wlh ina fatan na yi auren jin daɗi ba ƙarma ƙarma ba, wani sa'ilin ji nake dama ba a gidan nan aka haifeni ba da a gidan wani hamshaƙi ana halittoni, wlh da duk ba ruwana da cin miyar kuka balle wani koko. Auzubillahi! Najwa kina da hankali kuwa? da iliminki kike wannan zancen, to ki tuba wa Allah dan maganarki ta kauce hanya. Ni da baki samu ilimin addini ba Allah kaɗai yasan irin rayuwar da zaki taso a ciki. Sannan da kike maganar baki son ƙarma ƙarma ashe yaudarar Zaidu kike yi da kika ce shi zaki aure shi. Kai inna nifa da wasa duk nake maganata, kina ta yi mini dogon sharhi sannan... Bata ƙarasa maganarta ba kira ya shigo taga Zaidu ne da sauri ta miƙe tana amsa kiran ta fice, da kallo inna ta bita tana yi mata addu'ar shiriya dan lamarin Najwa yana bata mamaki akan dogon buri da son kuɗi, gata da ilimin addini sosai amma akwai shagala. Ummu Sultan da Samha ce. [7/7, 13:04] Buhainat😁: *ABIN DA CIWO* Na ©Rahma Kabir MrsMG. Wattpad @rahmakabir Page 4. Najwa tana fita Zaidu ya mika mata fararen leda guda biyu ta amsa tana washe baki da godiya, suka yi sallama ta shiga gida ta zube ledan gaban inna ta zauna tana dubawa, ledar farko kayan tea ne a ciki sai leda na biyu kuma gasasshiyar kaza ce dankwaleliya da kuma cips da kwai da miyar albarka a cikin wani foil paper daban, Najwa taja numfashi tana sauke shi a hanlaki tare da haɗiye miyau. Allah ya shiryeki Najwa ya rabaki da cutar kwaɗayi, dan na kula shine kawai yake damunki, na tabbatar ke ce kika saka shi wannan siyyar da ba shiri saboda nayi tuwo maƙiyinki. Kai innata koda na roƙeshi ɗan uwana ne fa, kuma matsayin wa yake a guna ko ba soyayya akwai ƙauna ta jini. Hmmm ni kwashe kayanki ki tafi da shi ɗakinki kafin babanku ya shigo, kin san dai baya son irin wannan abin. Ai da sauri ta miƙe ta kwashe ledanta ta fice dan ta san babansu bayi da wasa, inna ta bita da cewa. Saura ki cinye baki aje min ba. Dariya Najwa tayi ta shiga ɗakinta tana gyara zama ta soma cin kazar nan kamar mayunwaciyar zaki. Najwa kenan ga sani ga shagala take ta kenan, yarinya ce mai natsuwa da iya shiga ta mutunci, dan bata saka gyale hijab ne har kasa da safa, nikaf ne sai in zata islamiya take sakawa, shekarar da ta wuce ta kammala secondry bata cigaba ba dan babansu bayi da ƙarfi kuma ma irin mutanen nan ne masu ra'ayi bai yarda tayi boko da ta wuce secondary ba, mazan ne dai suke da garantin cigaba sai dai gabaɗayansu ma sunƙi mayar da hankali ga karatun boko, babbansu Junaid bakaniken mota ne sai mai bi masa Abdullahi ustaz ne yana koyarwa a islmaiya, sai kuma na uku Sadiq tela ne sannan Najwa da yanzu take makarantar haddar alqur'ani tun bayan yin saukarta da shekara biyu da ya wuce, ta haɗa izi ashirin da biyar. Ance mutum tara yake mai cika goma ba to gaskiya itama ta samu naƙasu a fannin yawan buri, tana mugun son rayuwar masu kuɗi da wayewarsu, duk da tana da tarbiyya sosai amma bai hana ta nuna maitar son kuɗinta a fili ba, idan aka ce hidima ta masu kuɗi ne aka gayyaceta to ba karamin bashi muhimmamci take yi ba, shiyasa ko a makaranta kawayenta yaran masu kuɗi ne, sai ta tabbatar da akwai kumbar susa kafin take bada kofar ayi abota da ita, kuma tun tana karama da wannan aƙidar ta taso wataƙila dan ko su talakawa ne yasa take kwaɗayin haka, saboda duk danginsu babu masu kuɗi sai dai masu ɗan rufin asirin Allah, yanzu ne dai da Sameeha ta fita zakka a cikinsu ta zama musu zakaran gwajin dafi, shiyasa Najwa take mugun sonta har hakan yasa ta yanke amincewa da auren Zaidu saboda hakan ne kaɗai zai ƙara mata kusanci da ita kuma ta riƙa shiga cikin masu kuɗi, dan a ganinta Sameeha tana da kawaye masu kuɗi sosai, sannan ta samu gidan kashe kwaɗayinta tunda ta san basa rabo da kaji da kayan daɗi, addu'arta Allah yasa Sameeha tana da sakin fuska da son mutane duk da tasan halinta a da ba tada matsala, amma kila yanzu kuɗi ya sauyata dan wasu in sun samu rana basu iya shanya ba. *** Washe gari da wuri Najwa ta shirya ta tafi gidansu Zaidu, ta samu har sun gama shiri zasu tafi Zaidu ne ma ya tsayar dasu akan su jirata ta ƙaraso, Najwa ta gaishe su cikin girmanawa kana Sameeha ta ce su wuce dan akwai aiki a gabansu, suka fito Zaidu ya tare sumu napep biyu, Sameeha da yaranta sai Najwa da Ikram a dayan napep ɗin tare da kayanta dan zata kwana biyu a can har sai sun gama kimtsa gidan. Suna isa bakin gate suka sauka dama Zaidu ya sallami masu napep tun kan su taho, Abi ya buga gate mai gadi ya buɗe yana ganinsu ya shiga yiwa Sameeha sannu da zuwa ya buɗe musu ƙofa suka shiga, tun daga farfajiyar gidan Najwa take karewa gidan kallo tana faɗin masha Allah tana maimaitawa, har suka isa ƙofar shiga falo Sameeha tayi amfani da key ta buɗe musu ganin ba motar Aminu tasan baya nan, suna shiga Najwa ta zube a cushing tana sauke numfashi da wani irin tsantsar murna wanda ya bayyana a fuskarta, saboda yadda falon ya tsaru yayi matular burgeta da hango kanta dama itace ce mamallakin gidan, sam ta kasa danne farin cikin tana cewa. Alhamdulillah Masha Allah La Kuwwata Illah Billah, Anty Sameeha kin dace da gidan duniya saura na lahira, wlh gidanki tamkar irin gidajen da muke gani a cikin fina-finai, ya tafi da imanina Allah ya sakamu a danshinki, ni kam kamar in dawo nan gabaɗaya da zama dan wlh ba karamin kankaro mini mutunci zai yi in kawayena suka ganni a nan. To Najwa ai ga ɗaki nan sai ki kwaso kaya ki dawo mu cigaba da zama. Ai wlh Baba bazai barni bane kawai amma da sai na dawo, ko da yake ko hutu na riƙa zuwa ina buga hotunan da zan riƙa posting a status, ko ba komai muma muna da gida mai kyau. Allah ya kyauta miki Najwa ke dai har yanzu ba zaki bar wannan shegen ƙarya da buri ba. Cewar Ikram tana balla mata hararar wasa, Najwa ta miƙe ta yi tattaki ta isa inda Ikram ke tsaye ta dafa kafaɗarta tana cewa. Ke me za a fasa ai ina nan akan bakana, dole in yi kwaɗayin kuɗi domin cikin talauci na taso, da ace na gaji arziki ba zanta magana irin haka ba, ki barni na faɗa koda a iya baki ne na dai furta, kuma kuɗi abin so ne ba wanda baya son jin daɗi. Naki dai yayi yawa wlh, yanzu na tabbatar da kin ci sunanki wato ga sani ga shagala. Faɗi ki kara 'yar uwa. Kun ga, ku bar wannan taƙaddamar ku zo ku fara aiki bana son Abban Amra ya dawo bamu ci karfinsa ba, Ikram ina ga ke zaki shiga kitchen ne ki ɗaura mana shinkafa da miya ki gyara kaza biyu kiyi mana peper chicken. Cewar Sameeha tana fitowa daga ɗakinta data shiga aje jaka, Najwa tayi wani shewa tana rawa da wakar. Ewe gidan masu kuɗi gidan daɗi, za muci kaza zamu kaza. Allahu yahadiki Najwa. Cewar Ikram, Najwa tace Ameen wa iyyaki tana kalkale dariya, motsa kofa da suka ji ne yasa suka mayar da hankalinsu ganin waye zai shigo, sai ga Aminu ya bayyana cikin tsadadden shadda da hula akansa yayi matukar kyau, wani irin sumar wucin gadi Najwa tayi numfashinta har ɗaukewa yayi ya dawo, nan take taji kirjinta yana wani bugawa da sauri da sauri ga kanta daya yi mata wani girr, tunda take bata taɓa ganin Namiji daya tafi da imaninta lokaci ɗaya ba kamar wannan da ya shigo, ana cewa so farad ɗaya a ganin farko to tabbas ta tabbatar da hakan yana faruwa dan kuwa nan da nan ta faɗa cikin wani kogon bege da mafarkin samunsa a matsayin miji, sai dai kalmar data ji yaran suna Abba oyoyo yasa ta farka daga kogon tunanin data faɗa ta tsaya sororo tana kallon ikon Allah jiki a matuƙar sanyaye. Abban Amrah ashe baka yi nisa ba na ɗauka ba yanzu zan ganka ba. In koma kenan bakya buƙatar ganina a yanzu. Ni ɗin banza na nace ka koma. Cewar Sameeha tana dungurin kanta, suka saka dariya ya karaso falon ya zauna a cushing yana cewa. Kewarku yasa na taho yanzu dan wlh jiya nayi kwanan kaɗaici, gashi gobe da sassafe zan wuce Abuja ana nima na. Wayyo daga dawowarmu ko hutawa baka yi ba, ni dai ina burin naga ranar da zaka aje aikin nan ka dawo ka zauna guri guda. To ya za ayi Meeha ai duk wanda ya tara iyali dole ne ya fita nima. Ina kwana yaya. Lafiya lau Alhamdulillahi Ikram ya karatu ana ta taɓawa. Ikram ta amsa da lafiya lau kama ta wuce kitchen dan ɗaura girkin da Sameeha ta sakata, sai a lokacin ne Najwa ta sauke raunannen ajiyar zujiya ta ce. Ina kwana. Lafiya lau ya amsa sai ya miƙe yana duban Sameeha. Baƙuwa muka yi ne? Eh ɗiyar Gaggo Zulai ce wanda nake faɗa maka ita kenan mata 'ya mace. Ai in gaya maka ma haɗin gida za muyi musu Zaidunmu ne zai aureta. Kai masha Allah Allah ya sanya alkhairi yasa ayi damu, idan kin gama basu aikin ki zo ki tayani shirya kaya dan ina ganin sati biyu zuwa uku zanyi a Abujan nan dan wlh akwai ayyyuka rututu da suke niman shan kaina. Wayyo ni Sameeha har sati Uku, ina tunanin sati guda zakai ka dawo gaskiya bazan yarda ba. Ta faɗa tana fuskar shagwaba, Aminu yayi dariya ya wuce zuwa falonsa Sameeha ta bi shi tana yi mishi mitar kwanakin sunyi yawa, Najwa da kamar an daskarata a gurin ta bisu da ido tana jin wani irin damuwa da kuma haushin Sameeha daya ɗarsu mata a zuciya nan take, sosai taji haushin faɗa masa da tayi wai zata auri Zaidu, sai ta koma cushing ta zauna tana sauke ajiyar zuciya dan har ga Allah tunda take bata taɓa jin yanayi irin wannan ba akan wani ɗa namiji ba sai akan Aminu, wanda har numfashinta da zafi yake fita, jikinta ya ɗauki ɗumi da shiga tashin gankali, ga koshi ga kwanan yunwa ita taga samu taga rashi, dan tasan ko mutuwa zata yi Mijin Sameeha ya haramta a gareta dan tasan babu ta yadda zata yi ta mallakeshi a matsayin miji, dole ne ta lallashi zuciyarta ta samawa kanta lafiya, sai ta miƙe tana kokarin yaƙi da shaiɗan ta wuce kitchen wajen Ikram. Sallamar Hauwa yasa Sameeha fitowa daga falon Aminu, cikin sakin fuska ta ƙarasa falon tana yi mata sannu da zuwa ta nuna mata gurin zama, Hauwa ta zauna suka shiga gaisawa sai bayan sun nisa ne Hauwa tace. Ina Aminu ko yana babban gida ne? Yana ciki yana haɗa kaya gobe zai tafi Abuja. Ohh aikin kenan ba zama, dama nazo gurinki ne mu tattauna. Ina jinki yaya Hauwa amma kafin nan bari na kawo miki abin motsa baki. A'a yi zamanki ba na bukatar komai dan a koshe nake. Sameeha ta koma ta zauna dan harta miƙe, Hauwa ta cigaba da cewa. Dama na zo ina yi miki tunin abinda kika sani ne, akan sanin Aminu ɗan dangi ne, kuma rashin zamanku a nan kaduna yasa duk ba ayi saboda dake ba, dan haka ina so ki saki jikinki da mutane, ki shiga cikinmu a dama zumunci dake dan in kika ce zaki ware kanki wlh ba zaki ji daɗin mu'amala damu ba, dan na kula baki son mutane bakya so a raɓeki. Hmmm yanzu Yaya Hauwa maganar kenan da ya kawo ki. Eh itace ta kawo ni sannan in sanar dake gobe zan aiko miki da 'yar aiki wacce Laure ta samo miki, dan wannan gidan naki saida me tayaki aiki in ba haka ba kar ki zo ki fara tara datti gida ya lalace. To ni nace muku ina buƙatar 'yar aiki ce? Sannan ma in zan nima 'yar aiki dole sai ku ne zaku kawo mini? wannan wani irin son kai ne da shiga hurumin da ba naku ba, to ki koma ki faɗawa Lauren bana son 'yar aikin dan baku isa ku ce zaku yi iko da abinda yake matsayin ikona ba. Rashin kunya zaki mini Sameeha. Hauwa ta faɗa da ƙarfi tana dukan kirjinta, Sameeha ta kalleta da kyau. Idan haka kika ɗauka to shi na miki, wlh baku isa ku juyani ni da gidana ba ko wacce taje taji da matsalar gabanta, haba ni kaɗai ce wacce take auren ɗan uwanku da zaku sakani a gaba, tun ina Lagos baku barni da ƙananun munfurcinku ba gashi na dawo nan zaku dasa miki iko to wlh uban kuturu yayi kaɗan. Ke Sameeha yaya Hauwan kike faɗawa haka? Cewar Aminu daya fito falon wanda yayi daidai da lokacin da Sameeha take faɗa mata magana, sai Yaya Hauwa ta fashe da kukan munafurci tana faɗin. Ni zaki zaga kici mituncina daga gyara ka yanka to ai bazai zama sauke mu raba ba. Ta miƙe a fusace tana goge hawaye zata wuce Aminu ya dakatar da ita. Dan Allah yaya Hauwa ki tsaya. Ke Sameeha ki bata hakuri ko na sassaɓa miki, baki isa ki wulaƙanta mini 'yar uwa ba kinyi kadan wlh, nace ki bata haƙuri! Ya faɗa a tsawace, Sameeha da hawaye ya cika mata ido dan wlh Abin da ciwo matuƙa azo har gidanka anima takaka sannan ace ka bayar da haƙuri, tace cikin damuwa. Kiyi haƙuri hakan ba zai sake faruwa ba In Sha Allah. Ba shakka Sameeha daga abin arziki kin mayar da shi abin tsiya, ai wlh kinyi da 'yar halak dan zan baki mamaki, ba zan sake kawo miki magana irin wannan ba kuma zanje in isar da sakonki ga Laure cewar kince baki son 'yar aikin da ta samo miki. A'a yaya Hauwa dan Allah kiyi haƙuri kuma na amince a kawo mana 'yar aikin, Sameeha ki kaɓeta tunda sunyi ne dan su kyautata miki, kuma dama dole zaki samu mai taya ki aiki ga kuma zaman gidan zai miki ba daɗi ke kaɗai in yasa sun tafi makaranta. To Abban Amrah Allah ya kawota da alkhairi. Daga haka ta juya tana share hawayen daya zubo mata a kuncinta ta shige ɗaki, Su Najwa kuwa da suka fito suka tsaya a kofar kitchen komai ya faru akan idonsu, dan haka suna ganin Sameeha ta shige ɗaki sai suka koma ciki, Ikram tana ƙananun surutai akan abinda Hauwa ta yiwa 'yar uwarta, Najwa dai tsaki take ta ja dan damuwarta daban ba wannan ne a gabanta ba, dan yadda ta ƙara tozali da Aminu wutar soyayyarsa ƙara ruruwa ta yi a zuciyarta. Cakwakiya! To muje zuwa... Ummu Sultan da Samha ce [7/7, 13:04] Buhainat😁: *ABIN DA CIWO* Na ©Rahma Kabir MrsMG. Wattpad @rahmakabir Page 5. Aminu har gate ya raka Hauwa kafin ya dawo ya shiga ɗakin Sameeha ya sameta a kwance tana kuka ya isa da sauri ya ɗagota ya rungume yana cewa. Dan Allah kiyi haƙuri Meeha wlh nasan ba kida laifi saboda nasan halin Hauwa, kawai bana so na goyi bayanki ne ta ce mun yi mata rashin mutunci taje tana yaɗawa 'yan uwa, sannan a kullun ina baki shawara ki daina biye musu duk abinda zasu yi miki, nasan wlh haushi kawai suke yi da ni'imar da kike ciki dan banga abinda kika taɓa yi musu ba. Amma kasan abin da ciwo su tasani a gaba ni banyi musu komai ba, ƙiri ƙiri ni da gidana sai wasu ne zasu yi iko da shi ni ban isa inyi abinda nake so ba. Ni dai ina ƙara baki haƙuri ki dai na wannan kukan komai zai wuce da yardan Allah, kuma in zamanki a nan zai zama damuwa ina ga zan sama mana wurin zama mai kyau a Abuja mu koma can gabaɗaya kinga ba mai saka miki ido ko takura. Ni dai nafi son nan, sai dai mu riƙa zuwa maka hutu. To ai shikenan kukan ya isa haka, tashi muje mu karasa haɗa kayan kin san da wuri zan fita, ina son komai ya kasance a haɗe guri guda kar sai na tafi na tuna da ban saka wani abu a jaka ba. To tace masa ya kama mata hannu suka fito zuwa ɗakinsa. Sai yamma lis Najwa ta wuce gida bayan Sameeha ta cikata da kayan arziki ta kaiwa inna sannan da sakon gaisuwa kuma ta bata kuɗin mota ta tafi, Ikram har titi ta rakata ta samu abin hawa suka wuce. Ita dai Najwa duk wannan mutunci da suka yi mata bai burgeta ba dan sosai zuciyarta take hasko mata dama ita ce ta dace da wannan gidan, gani take yi a komai tafi Sameeha wato kyau, fari da yarinta, duk da Sameeha itama ba baya ba wajen kyau ga diri da cikar zati, fara ce amma ba can ba kuma tana da idanu dan kallo ɗaya za ayi mata a gane anyi mace a gurin, itace ta biyo Umma sak haske kawai Umma ta fita, Ikram tafi kama da su Anwar saboda babansu suka biyo, ana ganinsu anga kanuri ga hanci zar har baka duk da suna da duhu amma suma suna da nasu kyan, Ita Sameeha haɗa kyau biyu tayi saboda wushiryar baba ta gada da kuma dimple. Najwa da tunani barkatai ta isa gida wanda gabaɗaya tunanin yadda zata zama matar Aminu take yi, sai dai har ta cimma gida bata samu matsayar shawara ba, dan ta hango babu wata hanya da zata samu haka sai dai ta lallashi kanta ta yakiceshi a rai. Yadda inna ta ganta sukuku yasa tace. Lafiya na ganni sai kace wacce akayi wa duka ko duk gajiyar aikin ne.? Inna kaina ke min ciwo kuma ba wani aikin wahala nayi ba kawai dai zuciyata take raya mini wani abun da ko mutuwa zanyi ba zan sameshi ba. Uuu hum cutar kuɗin ne ya kamaki ko me? Inna wlh gidan anty Sameeha shine mafarkina, shine burin dana daɗe ina saƙawa, wlh hango kaina kawai nake ace nine mamallakin wannan gidan, kuma Inna ashe haka mijinta ya haɗu kin san dama ban taɓa ganinsa ba, wlh yayi matuƙar kwanta mini a rai, zuciyata idan ba karya take yi mini ba na kamu da son sa. Tas taji inna ta ɗauke ta da kyakkyawar mari tana waro ido waje cike da takaicin abinda Najwan take faɗa. Dan ubanki kin fara hauka ne, kina da hanki kuwa Najwa? kin san me kike faɗa?. Wlh inna ina cikin hankalina kawai dai zuciyata ta kamu da son abinda ta san ba zata samu ba. Inna ina jin wani irin sabon yanayi a ƙirjina wanda ban taɓa jin irinsa ba akan wani namiji ba, ki taɓa zuciyata kiji yadda take buga mini wlh bani da lafiya. Najwa tayi maganar tana kuka da taɓa gefen zuciyarta, inna sakin baki tayi tana kallonta cike da tsantsar mamakinta. Gaskiya ne Najwa wlh ba ki da lafiya dan da alama kwakwalwarki ta taɓu. To wlh ki sakawa ranki har gaban abada ba zaki taɓa samunsa ba dan ya haramta a gareki, ko kin mance Babansu Sameeha shine ya saki nono na kama uwa ɗaya uba ɗaya nake da shi, dan haka kar naji kin bawa wani labarin wannan shashancin naki. Nima inna nasan dole ana barin halak dan kunya, In Sha Allah ba zaki sake jin wannan maganar ba. Tana gama faɗar haka ta miƙe ta shige ɗakinta ba dan ta hakura ba sai dan rashin samun goyon bayan inna yasa ta faɗa mata haka, sai dai wani ɓangare na zuciyata yana sanar da ita ta haƙura shine mafita amma wani sashi kuma yana ƙara hasko mata daular gidan Sameeha da kuma kyawun Aminu daya firgita zuciyarta lokaci guda ya sakata cikin wani yanayin da ba zata iya misaltashi ba. A wannan ranar barci ɓarawo ne ya sace Najwa dan harga Allah tunani yaƙi barin zuciyarta, ɗan barcin da ta samu ma cike yake da hargitsin mafarkin gidan Sameeha da kuma Aminu. Gari da ya waye Najwa ta tashi wasai tamkar wani abu bai damunta, ta koma walwalarta dan sosai take son nunawa Inna tabar maganar Aminu, amma kuma ta gama yanke shawarar zuwa gidan ƙawarta Nafeesa ta bata shawara akan ƙudurinta. Abokiyar cin mushenta ce duk wani abu na sirri wa junansu suke tattaunawa, Nafeesa wayayyar 'yar boko ce dan ta samu yin Diploma a masscom, da ta gama ne ta shiga makarantar hadda suka haɗu da Najwa wanda tasu ta zo ɗaya kuma iyayenta suna da rufin asiri, a sanadin haɗuwarsu ne Najwa take ɗan sanin abubuwan more rayuwa har take kokarin kwaikwayanta, yanayin shiga ne kaɗai bata yarda ta sauya ba, dan Nafeesa tayi tayi ta koya mata saka gyale amma Najwa bata yarda ba, sai dai a fagen burin auren mai kuɗi halinsu guda amma ita Nafeeaa ba tada kwaɗayi tunda ta taso cikin jin daɗi. Najwa da ta gama aikinta ta shiga ɗakin inna ta gaida baba ta tambaye shi zata gidan ƙawarta Nafeesa amso assignment da aka bayar jiya Lahadi da bata samu zuwa Hadda ba, Baba yace to kana ya bata ɗari biyu na mota ta amsa tana godiya sai ta fito, sai inna ta biyo bayanta tana cewa. Da fatan maganar da kika yi mini jiya kin barta har abada dan bana so ki sanar da wani. Haba inna ai tuni na ƙaryata zuciyata na mance komai, kuma In Sha Allah ba zaki sake jin magana irin wannan ba. Yauwa Auta Allah ya miki albarka, ina ganin zan yiwa Babanku magana akan Zaidu ya turo a yi maganar aurenku kawai a huta. Inna ai na taɓa yin magana da Zaidu yace a bashi lokaci, kin san yanzu ne yake kan buɗe shagonsa. Hakane fa to Allah yasa jinkirin ya zama alkhairi, ki dawo da wuri karki daɗe dan zan je barka a can unguwarmu kawo anjima. To ta ce mata ta wuce zuwa gidan su Nafeesa dake malali. Wajen ƙarfe goma ta isa ta buga gate aka buɗe mata ta shiga, a farfajiyar gidan ta samu Nafeesa tana buga kwallo, tana ganin Najwa ta taho gareta da sauri tana yi mata oyoyo, Najwa tayi dariya tana cewa. Yaushe zaki girma ne Nafeesa da kike buga kallo sai kace wata yarinya. Wlh exercise nake yi kin san sai ana yi ana motsa jiki, ya jiya ban ganki ba a makaranta kuma na kira wayarki bata shiga. A gida na barta saboda naje gidan cursin sister ɗita da suka dawo gada Lagos. Ayya ko wannan antynki da kike faɗa mini ƙanwar Zaidu. Eh ita fa yanzu ma akanta na zo ki ba ni shawara. Nafeesa ta ce to kana ta kama hannun Najwa suka shiga cikin gida har zuwa falonsu, basu samu kowa a ciki ba dan haka ta jata zuwa ɗakinta, bayan sun zauna a kan gado Nafeesa tace. Kawata naga damuwa a fuskarki, ki bani labari ko wulaƙanci tayi miki ne dan naji kin ce suna da kuɗi ko. Eh, ai da wulaƙanci kaɗai tayi mini wlh dana ji daɗi, na faɗa so ne, ina nufin soyayyar mijinta. Nan Najwa ta kwashe labarin komai ta faɗa mata har da yadda suka yi da inna. Kut amma wlh kin ɗibo da zafi, zuciyarki bata faɗa miki gaskiya ba Najwa. Mijin ƙanwar Zaidunki fa kike so. Nafisa ta faɗa tana riƙe haɓa, Idon Najwa yayi rau-rau kamar zata yi kuka. Ya zanyi Feena a ganin farko na kamu da sonsa, ya haɗa duk wani abu da nake mafarkin samu a gurin namijin da nake so, ga kyau ka kuɗi ga asali komai ya haɗa, irin dai mazan nan da ake kira first class wanda ake kwatance a cikin labaren littafan hausa. Ke ki faɗa mini a takaice mijin novel. Cewar Nafeesa tana 'yar dariya. Najwa ta dafa hannunta tana cewa. Yauwa shi fa. Ki gaya min yadda zanyi dan na faɗawa inna na bar maganar, amma har ga Allah ban haƙura ba ina son samunta ko ta halin ƙaƙa tunda ba haramci in ya aureni. To ke meya kai ki faɗawa inna, kin san ko mutuwa zaki yi ba zata taɓa yarda ba saboda kar zumuncinsu ya lalace, amma ni tambaya ɗaya zan miki, dagaske kina son aurensa ko so kike kawai ki dan taɓa soyayya da shi kici kuɗinsa.? Soyayyar aure nake masa, gidan da Anty Sameeha take ciki irinsa nake son gani kaina a ciki, dan gaskiya burina kenan. To ki saka aranki kamar kin samu, amma dole sai mun kauce hanya fa. A'a Feena wlh ba zan bi malamai akan wannan ba, idana imani da kuma tsoron Allah, duk da ina da shagala amma ba zan yi shirka ba. Nafeesa ta kwashe da dariya tana tafa hannu sai da tayi mai isarta kafin tace. Na manta fa ashe da mahaddaciya nake magana, to nima ba wannan nake nufi ba, tunanina in har kina so ki zama matarsa to dole sai Anty Sameeha ta bar gidan. To ta ya hakan zai faru? Ba kin ce basa shiri da 'yan uwansa ba, to ta hannunsu zaki fara bi wato ki haɗa kai ya yayarsa Hauwa kika ce ma sunanta ko? Eh. To hakan shine zai fara baki Ƙofar fara samun shiga gidan Aminu. Najwa tayi shuru tana tunani, can ta nisa tana cewa. To ta ya zan haɗa kai dasu? Shiga cikinsu za kiyi ki tayasu kushe Sameeha da nuna kyamar abinda take yi musu, da karin sharri ke duk ki haɗa ki faɗa in dai zai sa ki samu shiga a gunsu. Anya zan iya kuwa? Anty Sameeha bata taɓa yi mini wani abu ba wlh. To zauna karki yi sai ki fasa cikar burin naki. Kije kiyi tunani sauran plan ɗinmu zan kara nazari akansa. Haka Nafeesa ta dinga iza Najwa tare da hasko mata in har tana son samun cikar burinta to sai tabi shawarar da ta bata. *** Sameeha. Aminu da wuri ya tafi dan jirgin ƙasa ma yabi, kafin ya tafi saida ya gabatarwa Sameeha da sabon driver Mai suna Hamza da zai riƙa kaisu anguwa ko kai yara makaranta da aike kasuwa, duk da yace sai in ya dawo zai yiwa su Abi register makaranta, wajen ƙarfe tara da rabi na safe sai ga Hauwa ta zo da mai aiki suka gaisa kamar komai bai faru jiya ba sai ta ɗaura da cewa. Sameeha ga mai aikin nan sunanta Jamila, sai ki bata ɗakin da zata zauna dan na kwana ne saboda daga ƙauye aka ɗaukota. To shikenan an gode, Abin da Sameeha tace kenan dan bata so tayi magana mai tsayi ya jawo rikici, sai Hauwa tace. Ya batun walimar da zaku yi? Ko kun fasa saboda Aminu baya nan. Bamu fasa ba za ayi asabar mai zuwa In Sha Allah dan mun gama tsara komai. To madallah, in akwai taimakon da kike buƙata sai kiyi magana tunda taro ne na mutane da yawa yana buƙatar shawara. Idan da yuwuwar hakan zan kiraki In Sha Allah. Daga haka Hauwa ta miƙe tayi mata sallama ta wuce, Sameeha sai da ta tabbatar da ta tafi kafin ta ƙarewa mai aikin kallo, yarinya ce da ba zata wuce shekara sha biyar ba zuwa sha shida, duk da ƙauyenci ya nuna a tare da ita amma a feƙe take, Sameeha ta gyara zama tana cewa. Ina so na sanar dake bana son ƙazanta ki riƙa wanka, kuma duk lokacin da mijina yake gari kar ki sake na ganki kin fito falo, aikinki daga shara sai mofin shima iya falo da ɗakin yara, ɗakina da ɓangaren babansu ni zan gyara, sai wanke wanke, sannan ko bana nan ban yarda kiyi girki ba, kar in ganki a gurin injin wankinmu ki wanke kayanki a waje ba ruwanki da namu wankin. Idan na kamaki da munafurci ko rashin gaskiya wlh zan koreki dan bazan ɗauki rashin arziki ba. To anty In Sha Allah zanyi duk yadda kika ce. Yauwa kuma zan riƙa baki dubu goma duk wata. Su kuma cewa suka yi dubu sha biyar zaki biyani. To su daban ni daban, sai yadda naga kamun ludayin aikinki tukuna ki samu haka. To jamila tace tana cuno baki dan gaskiya ba haka suka yi dasu ba, sai da ta tabbatar da za a biyata sha biyar kafin ma ta yarda da zata yi musu aikin da suka saka ta, saboda sun gama jera mata duk rahoton da suke so ta kawo musu akan Sameeha da duk abinda ke wakana a gidan. Sameeha ta miƙe ta ce ta bita a baya, suka isa wani ɗaki dake kusa da kitchen ta buɗe, akwai gado a ciki da komai dan ɗakin an yi shi ne saboda baƙi, tace nan ne ɗakinta kuma ta kula da tsaftarsa dan bata yarda da ƙazanta ba, Jamila gyaɗa kai tayi ta shiga ta zauna a gefen gado, Sameeha ta fita zuwa ɗakinta da su Abi suke ciki tare da Ikram suna kallo dan akwai tv a ciki. Jamila da harara ta bita tana yatsine fuska taja tsaki ta ɗauko wayarta a jaka ta danna number ɗin Hauwa, bugu ɗaya ta ɗauka ta ce cikin make murya. Wlh Hajiya matar nan ba tada kirki sai ɗaure fuska take kamar dai bata son ganina a gidan, kuma wai dubu goma zata biya ni bayan ba haka muka yi da ku ba, gaskiya ni dai ku cikasa mini dan wlh aikin da kuka sakani yana da wahala fa. Karki damu Jamila ni zan cikasa miki ai ke tamu ce duk abinda kike so shi za a yi, kin ga dai yadda take ko, to ina so ki riƙa bani labarin duk abinda ke faruwa a gidan. Karki ji komai ai ni nayi miki alƙawari. Daga haka suka yi sallama Jamila ta ajye wayar ta kwanta rigingine cike da nutsuwa tana sauke ajiyar zuciya tare da latsa laushin katifar kamar gidan ubanta. [7/7, 13:04] Buhainat😁: *ABIN DA CIWO* Na ©Rahma Kabir MrsMG. Wattpad @rahmakabir Page 6. Sameeha tana shiga ɗakinta ta zauna a gefen gado tana cewa. Ikram ku tashi ku koma falo da kallonku ina so na ɗan samu barci. To anty amma har Yaya Hauwa ta tafi ne? Eh 'yar aiki ta kawo mini gata can na bata ɗakin kusa da kitchen sam hankalina bai kwanta da yarinyar ba, gata dai 'yar kauye ce a yanayin shigarta amma alamu ya nuna idonta a buɗe yake. Ai Wlh anty ke kika kyalesu amma da nice banga 'yar iskan da ta isa tayi mini haka ba, kuma umma sam bata bin bayanki ɗazun ina ji da kuna waya sai faɗa take yi miki. Allah shawarar da zan baki tana yin wata guda ki sallameta, in sunyi magana kice bata yi miki aiki mai kyau, kinga sai ki sa umma ta nima miki wata. Hmmm umma cewa tayi wai ko marina Hauwa tayi karna rama na rabu da ita saboda sharri suke kokarin bina dashi, ni kam bazan ɗauka ba wlh, shiyasa ma ba zan sake faɗawa umma matsalata da su ba tunda ba bin bayana take yi ba. Ni ina ganin ɗiyar Inna Rukayya zan ɗauko kawai in sakata a makaranta tunda kinga su can ba wani karatu suke samu ba. Shikenan ma ba ruwanki da wata 'yar aiki tunda aikin gidan ba wahala, na tsakar gida kyasa mai gadi da driver suna gyara miki. Allah dai yasa mu dace. Cewar Sameeha, Ikram ta amsa da amin kana ta tasa ƙeyar yaran suka fice daga ɗakin. **** Najwa. Har ta isa gida tana tunanin shawarar da Nafeesa ta bata akan ta haɗa kai da su Hauwa, sai dai ita tana ganin kamar ba zasu karɓeta ba ƙila suyi zargin ko Sameeha ce ta sakata, amma zata yi iya kokarinta ganin ta tusa kanta in dai zata samu cikar burinta, dan sai da Nafeesa ta ƙara hasko mata auren Aminu kafin ta ƙara jin kwarin guiwa, a yadda take jin zuciyarta tana bugawa so take ta ƙara tozali da shi taji muryansa ko hakan zai saka ta samu sukuni, sai dai ko taje gidan ba zata ganshi ba dan ta san zai yi tafiya kuma sai ya jima bai dawo ba kamar yadda Ikram ke fadya mata, koda ta isa gida ta samu inna ta tafi barkan da ta ce mata, dan haka ta kwanta a ɗaki tare da danna wayarta da take rakani kashi, taja guntun tsaki tana cewa. 'Yar wayar zamanin nan ma ta gaga in riƙe saboda duk samarin nawa talauci yayi musu kanta, haba wlh dole in sauya sheƙa nima in faso gari a dama dani, dan na gaji da wannan rayuwar maneji, yanzu da ace ina da babban waya ƙila in lalubashi a facebook in ga hotonsa ko ɗan chart in fara da shi. Ta ƙare maganar tana jan guntun tsaki, sai ga kiran Zaidu ya shigo kamar ba zata ɗauka ba ta ɗaga kiran ta saka a kunne tana sallama, Zaidu ya amsa mata yana cewa. Amaryata ya gajiyarki na jiya da fatan Sameeha bata gajiyar min dake sosai ba. Hmmm ai gajiya tabi lafiya, kyawun gidanta ma ba zai sa naji na gaji ba dan Wlh Anty Sameeha ta dace da gidan duniya. Gaskiya kam gidanta yayi kyau Allah ya bamu kuɗi masu albarka na gina miki kamar sa ko wanda ya fishi. Ameen ya rabbi, dama ina shirin kiranka sai naka ya shigo. Ok ina jinki me ya faru.? Waya nake so Android wacce ake yayi na gaji da riƙe rakani kashin nan. Kaga ko da baka samu zuwa ba sai mu riƙa yin charting ko. Hakane amma yanzu ina cikin uzuri sai in na gama da shagona In Sha Allah zan siya miki mai kyau, dama tuntuni nake tunanin yin haka. Ai dama na san ba zaka siya mini ba sai dai kayita mini hanya hanya, in ba ta ƙuƙe mini ba ai da bazan tambayeka ba. Sai kit ta kashe wayarta dan ta nuna masa taji haushi kuma da gaske haushin ta ji dan gabaɗaya ji tayi ta tsaneshi bata son ganinsa, Zaidu ya ƙara kiranta amma taƙi ɗauka har sai da yayi mata kira sama da uku tayi banza da shi, ya tura mata da sakon. _Kiyi haƙuri zan shiga kasuwa yanzu in siyo miki koda second hand ne sai ki fara amfani da shi kan na samu kuɗi na siya miki sabuwa._ Data karanta ta ɗan saki murmushi sai ta ki bashi amsa akan bata sauko ba dan ta ƙara tunzurashi ya siyo mata ɗin, ta yatwine fuska. Dama tuntuni haka nake maka da yanzu na dan samu abinda na sama a jikinka, Nafeesa tasha bani shawarar haka sai naƙi yarda ganin kar in fito da kwaɗayi ga samarina su raina mini wayo kuma suna yi mini kallon ustaziya mai hankali kar na zubar da kimata, amma yanzu ma duk zan yi maganinku na zubar daku gabaɗaya a kwandon shara, Saboda nayi mijin da ya kere sa'a zai fito mini da ajina sosai. Tana gama faɗar haka ta miƙe ta fito dan ɗaura abincin rana tunda Inna tabar mata sallahu a gurin Yaya Sadik da ta samu a gidan. *** Zaidu. Yana zaune a ɗakin umma suka yi waya da Najwa, bayan ya gama tura mata sako ya duba umma yana cewa. Wani lokacin yarinyar nan ina rasa inda tunaninta yake zuwa, gata da ilimi amma wani lokacin bata aiki da shi. Meya faru kuma? Ummu tace tana dubansa, sai ya bata labarin yadda suka yi yanzu, umma ta ce cikin faɗa. Haba Zaidu ai tayi maka kawaici tunda sai yanzu take nuna maka tana son babbar waya, kuma ai ya kamata ka siya mata tunda ita ce ake yayi, ko Ikram baka ga wacce Saurayinta ya siya mata bane, in har kana so ka samu zuciyar Najwa dole sai kana kyautata mata, tunda 'yar uwarka ce ko ba soyayya kayi mata dan zumunci. Amma umma nace mata ta bari na samu kuɗi yanzu ina fama da shagona ne. Ka ɗauka cikin kuɗin ka siya mata mai saukin kuɗi itama ta shiga zamani a dama da ita, na tabbatar in kai ka fara siya mata waya a samarinta ka ciri tuta kuma zaka samu matsayi mai kyau, sannnan gidansu ma ba zasu hana ta riƙe wayar ba tunda kai na gidane ka bata wayar. To shikenan umma zan duba na gani, amma naga tun yanzu kina goyon bayanta kar nan gaba tayi mini laifi na kawo kararta ki shigar mata. Aiko kasan ko kaine da gaskiya ba zanbi bayanka ba dan yana da kyau in nuna kawaici, ba zan soka ba in ƙita dan na haifeka. Amma ai wasu iyayen ko nasu keda laifi goyon bayansa suke yi. To ni ba irin wannan iyayen bane ai kaso naka duniya ta ƙishi, kaƙi naka duniya ta soshi. Wannan zancen haka yake ummanmu bari na fita na fara niman mata wayar kafin ta fashe dan fushi. Ya faɗa yana 'yar dariya, umma dariyar tqyi tana a dawo lafiya Allah ya tsare ya amsa da amin ya wuce kasuwa. Kamar yadda yayi mata alƙawari da yamma bayan sallar la'asar ya isa ƙofar gidansu ya aika mata yaro da wayar a cikin leda da karamar takada a ciki ya wuce. Najwa ce a tsakar gida yaron ya samu ya bata sakon yace inji Zaidu, ta amsa da sauri sai yaron ya fita, inna ta fito daga bayi tana cewa. Me Zaidun ya aiko miki da shi? Yanzu zan duba in gani. Ta bata amsa tana zama a karamar kujera, ta buɗe ledan taga kwalin waya wato sabuwa ya siya mata kimanin na dubu hamsin da biyar, wani tsalle ta daka tana murna tare da cewa. Inna waya toch ya siya mini wlh kin ganta sabuwa dal a kwali. Allah yasa ba matsa masa kika yi ya siya miki ba dan nasan halinki. Kai innata! wlh hakanan yaji ra'ayin kawo mini wata kila ya samu Kuɗi ne ko kin mance siyayyar daya yi mini shekaran jiya. To Allah ya sanya alkhairi ya yi masa albarka. Amma ni nafi son ya turo ayi maganar auren nan zanfi samin natsuwa. Inna tunda shi yace a bashi lokaci a jirashi, in kuma rabon wani ya ratsa ya yiwa kansa. Me kike nufu da wannan maganar? Najwa ko dai yaudarar yaron nan kike ba sonsa kike yi ba kisa muji kunya? Da bana sonsa inna ai bazan bari soyayyarmu tayi tsawo haka ba, kusan shekara guda fa muna tare. Hmmm inna tace tayi bismillah ta fara alwalar sallar la'asar, Najwa kuwa ta miƙe ta shiga ɗaki ta saka wayar a caji cikin tsananin murna, ta duba takardan dake cikin ledan ta karanta sakon bada haƙuri ne, murmushi tayi tana mele baki, duk da wannan hidimar da yayi mata baisa ta sauko daga ƙudurinta ba dan gani take yi ma ta samu abinda zai sa ta samu kusanci da Aminu. ... Ana gobe walima. Najwa ta shirya tsaf ta tafi gidan Sameeha da nufin kwana zata yi, sai dai zuwanta da dalili saboda tana son ta samu number ɗin Aminu a wayar Sameeha, dan ta buɗe facebook tayi searching sunansa amma bata samu ba, ta san koda baya facebook to yana WhatsApp dan haka ta ke buƙatar number, saboda shawarar da suka yi kenan da Nafeesa a chat, dan tuni suka cigaba da tsare tsarensu ta online, sosai Nafeesa taji daɗin Wayar da Najwa ta samu dan ya ƙara musu kusanci da juna kuma zasu riƙa yin komai a waya ba lallai dole sai sun haɗu ba. Tana isa ta samu ana ta shirya kujeru a kasan kanofi da aka kafe su guda huɗu a tsakar gidan, tuni Sameeha ta saka aka samo mata hayarsu zuwa gobe zasu zo su kwashe, dan so take komai a yi shi cikin tsari, maganar abinci ma bayarwa tayi a yi musu bata so ta bawa Kowa aiki, tasa ayi waina da sinasir da miya, jelop din shinkafa da alale sai kaji guda talatin da aka gyaresu suna aikin suyansu ita da Ikram sai Mai aikinta, akwai rago da yaya Kamalu yace za a gasa shi a kawo musu goben, sai drinks kuma da ruwa gasu nan katam katam da yaya Kamalu ya kawo dan shine Aminu ya bawa kuɗin siyayya. Najwa tana shiga falon da sallama bata samu kowa ba dan duk suna kitchen, sai ta sauke idonta a kan katon hoton Aminu dake manne a bango ga kuma wanda suka ɗauka tare da Sameeha da kuma wanda suka ɗauka da yaran, sai ta sauke ajiyar zuciya a hankali tana cewa a zuciyarta. 'In Sha Allah saika zama mallakina sai na yi mulki a cikin zuciyarka.' Sai ta wuce zuwa kitchen ta samesu sunata aikin suyan kaji, suka shiga murnan ganinta Ikram tana cewa. Oyoyo matar babban yaya, ashe zaki zo? Haba zan zo mana tunda ni nace zan zo ai. Ina yini anty Sameeha ya shirye shirye? Lafiya lau Alhamdulillahi Najwa, yasu inna fatan kowa lafiya. Lafiya lau sun ce a gaisheki. Inna tace ba zata samu zuwa ba saboda akwai suna a nan gida kawo. Allah sarki nima badan taron nan ba da dani za ayi sunan, amma In Sha Allah zan je inyi musu barka. Allah ya yarda, yanzu me zan tayaku dashi? Zo ki karɓi suyarnan in je in watsa ruwa dan zafi nake ji. Cewar Sameeha, Najwa tace to amma zata aje jaka ta dawo, sai ta fita ta shiga ɗakin Amrah ta aje jakarta ta cire hijab ta dawo ta amsa aikin, Sameeha ta tafi ɗaki ta barsu, Najwa ta kalli Ikram tana murmushi. Bakuwa Anty tayi ne? A'a Jamila ai 'yar aiki ce da su yaya Hauwa suka kawota. Ashe har ta zo, 'yan mata sannunki. Yauwa Jamila ta bata amsa a takaice, kiran daya shigo wayar Ikram ce yasa ta miƙe ta fita daga kitchen ɗin, a lokacin dabara ta faɗowa Najwa tace cikin jan Jamila da hira. Sun barki kin ɗanɗana kazar kuwa? Sun bani amma kin san kaza bata isata tunda gida babu maƙota sai ɗai ɗai. Ɗauko ledan can ki ɗiba iya yadda kike so kije ɗakinki ki ɓoye kici abinki hankali kwance, nima kinga zan ɗiba kasona kafin su zo dan nasan halin Anty akwai rowar tsiya. Jikin jamila yana rawa ta ɗauki baƙar leda ta ɗiba kazar iya son ranta ta fita da sauri ta shiga ɗakinta ta ɓoye kana ta dawo tana washe baki cike da mugun farin ciki. Amma ke 'yar uwar mai gidan ce ko? Dan na kula danginsa basa shiri da anty. Hmmm ni ƙanwarta ce amma babanta shine yayan mamana, sai dai ni ina zuwa ne saboda takurani da inna tayi, dan sam Anty Sameeha ba tada kirki. Ai naga alama dan tunda na zo gidan nan take zuba mini dokoki ga shegen saka mini ido, abu kaɗan nayi suke kyarata ita da ƙanwarta, gaskiya naga ke kina da kirki ba halinku ɗaya ba. Hmmm sai ma gobe zaki ga yadda zata yiwa 'yan uwan mijinta, sam basa jin daɗinta ni har tausayinsu nake. Cewar Najwa tana taɓe baki, a zuciyarta kuma tana jin wani daɗi da farin ciki dan ta samu Jamila zata fara aika sakonta gurin su Hauwa, saboda ta san sun turota ne wu riƙa samun labarai a gurinta, kuma ga dukkan Alamu Jamila zata yi mata matuƙar amfani a cikin rawar da zata taka a gidan, muryar Jamila taji tana cewa a hankali dan kar ajita. Kin san Allah na tsani matar nan addu'a nake Allah yasa Alhaji ya saketa ya auro mai mutunci. Hmmm da nine 'yan uwansa sai na saka sun yi mata kishiya. Cewar Najwa itama a hankali, Jamila ta saka dariya tana cewa. Wlh kuwa da nayi murna naga ƙarshen ɗaga kai. Jamila sunanki ko? Eh. Ina so za ki yi mini wani abu wanda zan biyaki da kuɗi mai tsoka amma ina so ya zama sirri a tsakaninmu, idan kika faɗawa wani wlh sai na saka an ɓatar dake dan mijin da zan aura soja ne kina yi mini ba daidai ba zan saka ya harbeki da bindigarsa. Wlh zanyi miki kome kika so in dai zaki biya ni, amma dan Allah karki saka a harbeni. Jamila ta faɗa tana zare ido, Najwa ta saka dariya tana cewa. Ke wasa nake miki naga duk kin firgita ne, kawai dai zolayarki nayi, amma naga tamu ta zo ɗaya bani number ɗinki ko gaisawa mu riƙa yi. Sai a lokacin Jamila ta samu kwanciyar hankali ta saki murmushi tana ce mata wayarta tana ɗaki anjima zata bata, Najwa tace to suka cigaba da aiki, sai dai ita Najwa da abinda take saƙawa a cikin zuciyarta, haka nan taji ta gwada Jamila dan ta hasko ƙila nan gaba tayi mata amfani, kuma ta kula yarinyar akwai wayo da son kuɗi, ta tabbatar da hakane su Hauwa suka yi amfani suka ja ra'ayinta ta zo aiki gidan, itama zata yi amfani da wannan damar wajen samun cikar burinta. [7/7, 13:04] Buhainat😁: *ABIN DA CIWO* Na ©Rahma Kabir MrsMG. Wattpad @rahmakabir Page 7. Ikram da ta dawo kitchen ɗin ta cewa Jamila taje ta gyara falo inji Anty Sameeha saboda gobe ba za shi sharaba sai zuwa yamma in baƙi sun tafi, Jamila ta miƙe ta fita Ikram ta zauna suka cigaba da aikin suna hira da Najwa, har suka gama suka a dana komai kafin suka fito Jamila ta soma gyaransa. Suna zaune a falo sai ga Anty Sameeha ta fito cikin doguwar rigar material da hula akanta, ta zauna a cushing tana cewa. Ikram yanzu na gama waya da Aminu yace in kulle ɗakina dana rana kar na bari a shiga ayi mana barna, dama bana gaya miki haka zanyi ba to shima yanzu ya gama faɗa mini, dan haka ku shirya da wuri ku ɗauki duk abinda kuke buƙata ku kai shi ɗakin Jamila dan a can zamu tare, shima key ɗinsa yana hannunna koda zaku ɗauki abu sai ku faɗa mini. Gaskiya gwara ayi haka dan bamu san mutanen da zamu zo ba Anty, tunda wannan ne karo na farkon taro da za kiyi a gidan, sannan ma a farfajiya za ayi walimar. Cewar Ikram Sameeha tace. Sosai ma ni da ban san ya halinsu yake ba gwara in yi wa abin tufkar hanci a rabu lafiya da kowa, ni wlh na ƙosa ma ayi a gama na huta. Ai Anty kunyi ƙoƙari a wannan marra da muke ciki zaku yi shagali ba biki ba suna ba, kawai dan kun dawo kaduna ne fa. To Najwa Aminu yace za a yi haka shiyasa nima na mara masa baya, gwara ayi ɗin a sada zumunci dan da yawan 'yan uwansu ma ban sansu ba. Cewar Sameeha sai ta cigaba da yi musu bayanin yadda take so su saka mata ido a gidan dan ita ba lallai ta samu damar yin haka ba saboda tarban mutane. Sai da aka kira sallamar magrib kafin suka miƙe kowa wanne ya nufi ɗaki domin yin salla. Jamila tana ɗakinta zaune tana huta gajiyar aiki data kwasa, sai kira ya shigo wayarta ta duba taga Hauwa ce sai ta mike ta zo ta rufe ƙofarta da key ta ciki ta koma ta zauna a bakin gado ta ɗauki wayar da sauri dan ta kusa tsinkewa. Jamila meke wakana a gidan? Jamila ta shiga karanto mata shirye shiryensu tana cewa. Hajiya ai wlh na ci nama sosai wata 'yar uwar Anty Sameeha ta ce na ɗiba na ɓoye saboda tasan anty da baƙar rowa, itama sai zaginta take da alama 'yan uwanta suma basa jin daɗinta. Hmmm ba mamaki suma ba mutunta su take yi ba, In Sha Allah da wuri ma zan zo gidan. Daga haka suka yi sallama, a lokacin ne aka shiga buga ƙofar Jamila, a zabure ta miƙe tana dafe kirji da fargaban Allah yasa ba a ji wayarta ba, ta isa ƙofar ta buɗe sai taga Najwa ce ta saki dariyar yake tana cewa. Amty ashe kece? Sunana Najwa dan ban kai matsayin anty ba. Amma ai Ikram cewa ta yi itama anty ce karna ƙara kiran sunanta, kedai kina da mutunci sam ba ruwanki da girman kai. Halinsu guda da Sameeha ai, ga kayana zan ɓoye anan saboda gobe rufa ɗakuna zadu yi wai kar ayi musu sata. Innalillahi... yanzu zargin mutane take yi da zasu yi musu sata, to in hakane sai ta fasa yin taron. Ke ni bar wannan zancen dan ƙona mini rai yake, bani wayarki na saka miki number ta. Jikin Jamila na rawa da zumuɗi ta miƙa mata wayar, Najwa ta amsa ta saka number ɗinta ta yi filashin sai ta yi mata saving da Anty N ta nuna mata. Kinga sunan dana aje a wayarki sai ki riƙe da kin ga haka inna kira to ni ce. To nagode, kuma ina jin daɗin yadda kike kulani, wlh tunda na zo gidan nan rayuwa nake kamar marainiya, Allah yasa zaki jima baki tafi ba. Wa! Taf a gobe In Sha Allah zan tafi ba zan zauna ba ana yi mini wani gani gani ba da kafa mini dokar da ba zan iya bi ba. Tana gama faɗar haka ta juya ta fice bayan ta adana kayanta a ɗakin, da kallo Jamila ta fita tana mamakin halin Najwa yadda take da kirki da sauƙin kai, nan take ta yiwa Hauwa flashing ba jimawa ta kirata sai take shaida mata Sameeha zata rufe ɗakunanta dan kai'r su zo suyi mata sata har da karin gishirinta, Hauwa kuwa ta mulmulo wani ashar ta kashe wayar cike da takaici da irin matakin da zata ɗauka in sun zo ta hanasu shiga ɗakunan, dan dama da burin haka a zuciyarsu saboda basu san kalar ɗakunan ba. Najwa kuwa da ta fita falo ta amsa wayar Ikram da sunan zata tura app saboda ba tada abubuwa a wayarta, data gama ta mika mata tana duban anty Sameeha tace cikin karya wuya da marairaicewa. Anty dan Allah ki bani wayarki na tura abubuwa kinga wayar tawa ba wasu abu saboda sabowa ce sai nayi mata lodi. Najwa nifa wayata bata zuwa hannun kowa saboda ban gama sanin kanta ba tunda Abban Amrah ya siya mini, ko su Abi sai dai su ɗauki tsohuwar tawa. Kai anty xender kawai zan shiga na tura app. Sameeha bata kuma magana ba ta cire mata key ta miƙa mata, Najwa ta amsa ta shiga xender ta duba inda hotuna suke, sai taci karo da hotunan Aminu dama wanda suka ɗauka tare da Sameeha, wasu cikin kayan barci wasu kuma cikin shiga mai kyau, nan ta shiga turawa iya son ranta, kana ta koma app ta tura sai ta shiga In da ta yiwa kanta sending ta goge hutunan data tura dan kar Sameeha ta ganota, sai ta fita a xender ta shiga contact sai dai duk dubawan data yi bata ga sunan Aminu ba sai ta shiga wajen dailing call nan taga ansa Hasken Meeha, tana ƙoƙarin duba number ɗin ta ɗauka sai kira ya shigo wayar, da sauri ta fita daga gurin da ta shiga ta miƙa mata wayar, Sameeha ta amsa taga umma ce sai ta miƙe ta wuce ɗakinta tana amsa kiran, Najwa ba ƙaramin haushi taji ba wato rijiya ta bada ruwa amma guga ta hana, sai dai kuma hotunan Aminu data tura a wayarta zai rage mata damuwar da take ciki na rashin ganinsa a nan kusa, ta sauke ajiyar zuciya ta miƙe tana cewa Ikram ita zata kwanta sai da safe, Ikram ta yi mata addu'ar a tashi lafiya sai ta wuce ɗakin Amrah ta shiga ta kwanta a gefe dan Amrah tuni tayi barci. Rigingine ta kwanta ta shiga inda hotuna suke ta soma kallon hotunan data tura, wanda yake tare da Sameeha sai taji wani ƙululun baƙin ciki ya tokareta kamar ta mayar da gurbin Sameeha da nata hoton, ji take kamar ta samu wuƙa ta sokawa hoton Sameeha ko zata samu sassaucin kishin da take ji a zuciyarta, ganin ba zara daure ba yasa ta goge hotunan da yake tare da Sameeha ta bar nashi shi kaɗai da wanda ya ɗauka da yara, ta ɓata lokaci mai tsayi tana ƙarewa Hotunan Amimu kallo wanda hakan ƙara tunzura soyayyarsa take yi a zuciyarta tana jin idan bata sameshi ba mutuwa kawai zata yi, zata yi duk abinda ya dace dan ta mallakeshi a matsayin mijinta, sosai shaiɗan ya cigaba da ƙawata mata shi a zuciya wanda take ganin itace ma kaɗai ta dace da shi da gidan gabaɗaya ba Saneeha ba, text ɗin Nafeesa ya shigo wayar akan ta hau online, da sauri ta kunna datarta ta duba Nafeesa sai taga tana kai, dan haka ta tura mata hoton Aminu guda ɗaya wanda yake sanye da ƙananun kaya, Nafeesa tana buɗewa sai ta turo da imoji mai zare ido tana cewa. Ba dai wannan bane Aminun. Wlh ƙawata shine, yanzu na turasu a wayar Sameeha. Amma gayen nan ya yi fitinannen Haɗuwa ƙawata, dole ki rikice domin ni kaina ya burgeni, dan haka wlh ki riƙe wuta ki sameshi dan kunyi matuƙar dacewa da shi. Hmmm ina nan zuciyata kamar ta faso ƙirjina saboda sonshi dake bugawa, wutar sonshi ruruwa yake kamar zai tarwatsa zuciyata, Nafeesa numfashina har waji ɗaukewa yake ya dawo in na tuna shi, ki gaya min ya zanyi na aure shi a yanzu ina jin zan iya yin komai, ina nufin mai zan aikata in dai zai zama nawa, ban damu da duk wani abu da zai biyo baya ba, ni dai na same shi kawai. Ki kwantar da hankalinki ki saka a ranki kin same shi kin gama, kedai ki kama kafa da 'yar uwarsa Hauwa, na tabbatar zaki samu saukakkiyar hanyar samunsa, kuma ki dage da addua sosai nima zan taya ki, kuma ranar lahadi kiyi ƙoƙari ki zo makaranta akwai maganar da zamu yi. Najwa tace mata to kana suka cigaba da hirarsu, tana kallon maganar Zaidu amma taƙi kulashi dan yanzu bata shi take ba, gani take koda a ƙafa aka ɗaura mata shi ba zata iya ja ba dan tafi ƙarfin ajinsa, yanzu ne take ƙara kallon kanta a matar babban mutum ita ba matar yara bane ko talakan da bai iya ciyar da kansa ba balle yace zai kula sa ita. **** Washe gari. Da wuri suka gama shiryawa suka tanadi komai da suke buƙata suka saka a ɗakin da Jamila ke ciki, Sameeha ta kulle ko ina ta saka key ɗin a ƙaramar fos ɗinta sai ta bawa Ikram ta saka a ƙaramar jakarta ta rataya a kafaɗa, wurin takwas da wani abu mutane suka fara zuwa dan duk danginsu Aminu ne ciki har da Hauwa ta zube akan carpet ɗin falo tana matsa ƙafarta dan a ƙafa ta tako wai ta motsa jiki, Sameeha ta zauna tana yi mata sannu suka gaisa kana Hauwa tace Me da me kuka tsara ne.? Sameeha ta sanar da ita abincin da ta bayar ayi da bayanin komai daya dace ta faɗa mata, sai ta ɗaura da cewa. In kin huta sai muje kitchen na nuna miki naman kajin da muka soya ki cire naku dan kar azo ayi ta rabowa mutane ya ƙare. Aiko kinyi kyan kai mu je na gani dan ba wani hutu zanyi ba yau ba zama an saci ɗan barawo, ta miƙe suka wuce kitchen, Sameeha ta nuna mata ta samu guri ta raba kajin biyu sai ta juye a leda mai zane zane tana cewa. Wannan yayi mana, sauren kya bawa baƙi. To Sameeha tace mata amma har zuciyarta bata ji daɗi ba tunda anyi abu dan mutane ne amma ta kwashe rabi, sai ta adana sauran, Yaya Hauwa ta ce. Buɗe mini ɗakinki na ɓoye shi sai zamu tafi na amsa. Yaya na ɗauka na ɓangaren mutane ku ne kike ɗiba ko da sun zo ki saka musu a abincin. A'a wannan namu ne na gida in mun je babban gida zamu raba. To shikenan kawo in aje miki a ɗakin Jamila dan key ɗin ɗakina baya hannuna. Ina kika kai keyy ɗin? ki amso mana ki buɗe ki saka mini a ciki. Key ɗin yayi nisa gaskiya. Sameeha kina nufin ba zaki nuna mana ɗakin muga yadda yake bane ko me? Ba haka nake nufi ba, na dai rufe su ne saboda kar a samu matsala. Saboda kun tara ɓarayi ba a gidan dole zaki ce haka, Allah dai ya kyauta miki, da kin san hakane da baku shirya walimar ba kowa ta zauna a gidansa tunda baki yarda da mutane ba. Hauwa ta faɗa cikin ɗaure fuska, Sameeha bata ce mata komai ba tayi waje cike da damuwa dan bata so suyi abinda bai dace ba yasa ta fita bata bata amsa ba, A lokacin Najwa ta shigo tana kallon yaya Hauwa da fuskarta a ɗaure, Najwa ta matsa gabda ita tana cewa a hankali. Yaya iya abinda tabaku kenan? Wlh ta ɓoye wani ba iyakar yawan kazar ba kenan. Hmmm anty Sameeha ta bani da rowa. In dai ita ce zata aika, tunda ba ƙaunarmu take ba. To wai ma kinji me tace, rufe ɗakinta zata yi kar ayi mata sata, hatta ni da nake 'yar uwarta wlh fitar mini da kayana tayi daga ɗakin ta kaishi ɗakin 'yar aiki, sam bata so a raɓeta kamar ita kaɗai ce mai arzikin duniya, ni badan innata ta takura mini ba wlh da ban zo ba. Lallai ta cika butulu tunda har ta iya yiwa 'yan uwanta, mu ma ba zamu sha ba. Ya sunanki 'yan mata.? Najwa sunana, jiya na zo amma sai wani shan ƙamshi take yi kamar bata so zuwana ba, 'yan uwanmu da yawa sunce ba abinda zasu zo suyi a gidan dan karta wulaƙanta su saboda in tazo garin nan bata zuwa gidan kowa sai ɗakin umma take maƙalewa. Ashe haka take? Innalillahi wa inna ilaihir rajiun gaskiya Allah ya wadaran halinta wannan ba matar aure ba. Allah yaya Hauwa ku saka shi ya ƙara aure kawai domin kuma a dama daku a gidan ɗan uwanku in kun zo ba ruwanku da ita. Jiya ina ji tana magana da Ikram akan irin tanadin rashin mutunci data yi muku idan kuka nima shigo gonarta. Hmmmmm Hauwa tace tana cije gefen lebenta tare da ƙanƙance ido ɗaya tana girgiza kai. *Zaku jini shuru a kwana biyu saboda muna da biki sai mun kammala da yardan Allah zaku jini. Ina godiya da addu'arku da kuma soyayyar ku gareni Allah ya saka da alkhairi ya bar kauna. Rahmarku ce* [7/7, 13:04] Buhainat😁: *ABIN DA CIWO* Na ©Rahma Kabir MrsMG. Wattpad @rahmakabir Page 8. Hauwa tsabar bacin rai ji tayi kamar taje ta rufe Sameeha da duka amma dole ta bawa zuciyarta hakuri sai ta ce. Jeki abinki Allah yayi miki albarka ya baki miji nagari, dan da baki faɗa mini ba to ba zamu san meke faruwa ba. Ameen yaya kuma idan na samo wani labarin zan zo in faɗa miki. Hauwa jin Najwa ta faɗi haka ta ɗan washe baki dan dama burinta ta riƙa jin komai dake faruwa a gidan shiyasa ma ta kawo mai aikin da suka nimo da kansu, gashi lokaci guda Najwa ta faɗa mata labari sama da na Jamila, dan haka ta rage murna tana cewa. Yauwa 'yar gari ai dama irin haka nake buƙata, dan haka ga wayata saka mini number ɗinki domin abubuwan dake wakana a gidan nan nake so a riƙa faɗa mini yadda zan ji daɗin ɗaukar mataki akan Sameeha. Tayi maganar tana miƙawa Najwa wayarta, Najwa ta amsa da sauri ta saka mata number wayarta ta danna kira ya shiga ta kashe tana cewa. Wani suna zan saka miki? Saka mini sunanki tunda na riƙe kuma zan riƙa ganewa tunda 'yar bokon nan munyi na san hausa. Ta faɗa tana ɗan murmushi, Najwa tayi mata saving sunanta kana ta miƙa mata wayar tace. Har gida zaki riƙa jin labarin komai dan babban burina Anty Sameeha ta girbi duk abinda takewa mutane. Hauwa gyaɗa kai tayi tana murmushi dan sosai Najwa ta faranta mata rai ta gusar mata da ɓacin ran da Sameeha ta kunsa mata, sai Najwa ta wuce tana 'yar dariyar samun nasara cikin ƙanƙanin lokaci, sosai take jin farin ciki da hango haƙƙarta tana gab da cimma ruwa, ashe shawarar da Nafeesa ta bata ba ƙaramin aiki zai yi mata ba gashi ba aje ko ina ba ta samu shiga a gurin Hauwa, abinda bata sani ba itama Hauwa abinda take so kenan shiyasa tafiyarsu ta zo ɗaya, ko wannan da mugun nufin dake cikin zuciyarsa akan Sameeha da bata yi musu laifin komai ba sai tsabar son zuciya da hassada da yake damunsu. Hauwa da ta fito daga kitchen ɗiyarta Adama mai aure ta ƙaraso da sauri tana cewa. Mama muna ta nimanki ashe kina kitchen gasu yaya Laure can a farfajiya sun zo. Mu je na samesu, ungo riyke mini wannan ledar ki saka a cikin buhun dana baki a jiya, kuma wlh ki adana min shi kar a sace. To Adama tace ta amsa ledar ta saka a cikin hijab dan dama ta san da shirin Hauwa da ta zo taron, tace zata samar musu abincin da zasu ci a gida da dare ba sai sunyi girki ba, itama saboda ɗaurawa ƙarya cewa mijinta tayi biki suke da shi a family house ɗinsu dan haka kwana zata yi, da ya barta sai ta je gidansu da shirin kwana. Hauwa tana fita ta isa wajen 'yan uwa da suke a cikin rumfar, nan suka gaisa kana ta kama hannun Laure ta jata suka koma can gefe ta shiga labarta mata abinda Sameeha tayi mata akan rufe ɗakuna da tayi dan kar ayi mata sata da labarin da Najwa ta bata kaf babu abinda ta rage, Laure ta riƙe haɓa tana cewa. Amma anyi mara mutunci mu zata wulaƙanta to wlh ko taƙi ko taso sai ta buɗe ɗakunan mun bawa idonmu abinci. Kuma kika ce yarinyar data baki labari 'yar uwarta ce? karfa ace Sameeha ce ta saka ta dan tayi mana zagon ƙasa fa, ta riƙa sanin duk shirinmu akanta. Haba Laure wlh ba dai ni Hauwa za ayi wa haka ba, kuma ƙiri ƙiri na hango tsanar Sameeha a cikin idon Najwa a takure take da zaman gidan, ke koma aikota tayi ta bugi ruwan cikina ne ina daidai da ita kuma kifi na ganinka mai jar ƙoma, bata isa ta yi mini wani abu ba dan na gaba yayi gaba wlh shekaru ba ɗaya ba akwai tazara. Haka suka cigaba da tattaunawa, a hankali kuma gida yana ta cika da 'yan uwa. Sameeha tana can tana hidima da amsar baƙi da gaisuwarsu. Wajen sha ɗaya da rabi masu abinci suka kawo su Hauwa suka zo gurin suka tsaya suna cewa a d'ɗibar musu nasu, masu abinci basu kula su ba suka shiga jera kayan aikinsu dan sune zasu yi savin mutane ka faɗi abinda kake so a zuba maka, Sameeha ta buƙaci haka dan bata so ayi rigima ko ace ta nuna wariya ba a bawa wasu abinci ba, masu rabon abincin suka aika Sameeha ta zo suka nuna mata su Hauwa da maganar da suka yi musu, Sameeha ta kalli Hauwa da Laure tana cewa. Yaya wannan masu rabon abincin ne duk abinda mutum ke so shi za a bashi, nayi hakane domin a hutar da kowa. Hmmm amma ɗazun dana zo baki yi mini bayanin haka ba, yanzu kinsa zasu yi mana kallon mayunwata, sannan wannan duk salon ɓata kuɗi ne meye na wani kiran masu rabon abinci gamu, mu miye amfaninmu matsayinmu na manya. Ba haka nake mufi ba Yaya, naga walima muka yi gayya shiyasa bana so na wahalar da kowa. Iyaka mu haɗu muyi zumunci na murna da ganin juna. Allah ya kyauta, Hauwa muje mu zauna kafin anjima mu kuma jin wani salon wulaƙancin. Cewar Laure da ta yi gaba Hauwa tayi ƙofa tabi bayanta, Sameeha ta girgiza kai ta juya gurin masu abincin tana yi musu bayanin duk wanda za a zubawa abinci a saka masa naman kaza sannan a yankawa mutum naman rago da aka gasashi, suka ce mata to kana ta wuce cikin falo ranta a ɓace, Ikram tana ganinta tace. Su Hauwa ne ko? Wlh Anty da kinji shawarata da baku haɗa walimar nan ba, da kin bi kowa zuwa gidansa ki gaisa dasu ki yi musu alkhairi, amma na kula sam mutanen nan basa sonki. Allah yasa mu dace, nasan ko meye zan musu bazan fita ba tunda basu na bawa ragamar komai ba suyi yadda suke so ba. Su damuwarsu dani kome zanyi na faɗa musu na wakiltasu suyi mini jagora a cikin lamarin gidana, ni kam wlh uban kuturu yayi kaɗan banga wacce zan yiwa wannan biyayyar ba tunda ba haifata suka yi ba, ko mahaifiyar Aminu da tana raye bata yi mini irin wannan ikon ba. Kin ga mu je can waje gabaɗaya. Cewar Sameeha sai ta miƙe suka fita tare da Ikram dama Najwa tana wajen. Dangin Umma sosai suka zo musu amma dangin babansu basu zo ba saboda sunan da ake yi a family house ɗinsu na matar ƙanin su Gaggo Zulai wanda suke 'yan uba, ɓangaren dangin Aminu sune suka cika gida dan sosai suka zo wannan walima. Zuwa ƙarfe uku gida ya tunbatsa DJ yanata sakar musu sauti masu rawa nayi abu dai gwanin sha'awa, kuma har lokacin abinci bai ƙare ba duk wanda ya zo sai an zuba masa, su Hauwa kuwa sai aika yara suke yi suna karɓo musu suna juyewa a kular data ɗauko tana tarawa, Sameeha har cikinsu taje ta zauna aka yi hira da ita ana raha, abin dai gwanin ban sha'awa da burgewa kamar ba wani abu a cikin ransu. Ana kiran sallar la'asar DJ ya kashe kayan kiɗansa sameeha ta sallame shi dan a lokacin suka yi zai tafi. Aka fara shiga cikin falo dan yin sallah, waɗanda suka fara shiga suka fito da gudu suna faɗin wuta wuta a kitchen dan sosai kitchen ɗin ya turniƙe da hayaki, ƙirjin Sameeha yayi wani irin mugun bugawa har yasa ta kasa tsayuwa ta samu kujera ta zauna tana fidda numfashi da kyar tare da faɗin Innalillahi... A zuciyarta, su Hauwa sune kan gaba gurin shiga suna rafka salati nan fa k'ƙauri ya fara fitowa waje, mai gadi ya zo da sauri tare da driver da suke bakin gate suka shiga cikin falon, duk matan suka fito ko wanne cike da tashin hankali, Driver shine yayi jarumta ya faɗa kitchen ɗin yana toshe hanci saboda ƙauri da hayakin dake tashi, ya hango electric gas ne ke ci da wuta sai ya juya yana dube dube sai ya hango abin kashe gobara dake manne a bango ya je ya sauri ya ɗauka ya shiga fesawa a inda wutar ke ci, cikin ikon Allah wutar ta mutu sai hayaki daya ke fita, dama tuni mai gadi yaje ya cire wutar daga nepa, ya shigo yana yiwa driver magana. Wutar ta mutu kuwa? daga ina ne ma wutar ta kama.? Daga wannan electric gas ɗin ne ya kama, ƙila an kunna an mance ba a kashe ba. Driver ya bashi amsa, sai suka fito gabaɗaya, matan dake ƙofar falo ɗin suka tare su da tambayar wutar ta mutu? suka sanar dasu ta mutu sai mai gadi ya wuce ƙofar gate driver kuma ya ƙarasa inda Sameeha ke zaune ta dafe kanta da hannu biyu yace. Hajiya munyi sa'a wutar ta mutu, daga electric gas ne ya tashi amma a iya shi ya tsaya, ƙila anyi mantuwa an barshi a kunne. Da sauri Sameeha ta dago lokacin daya fara magana da ya kai aya ta sauke numfashi tayi masa godiya kana ya wuce, Sameeha ta kai kallonta ga Ikram da Najwa tana cewa. Dama an bar kitchen a buɗe? Ya aka yi aka bar gas a kunne. Gaskiya anty a kashe yake dan last shigata ba komai akansa kuma bangon ma a kashe yake, sai dai in wani mugun ne ya shiga ya kunna dan ya tada gobara saboda ƙeta da hassada, Allah ki sallami koma tunda la'asar tayi in ba haka ba kar a zo a tayar miki da wani tashin hankali dan na kula dangin mijinki baƙin ciki suke yi da ganinki a wannan gidan. Cewar Ikram ranta a ɓace, Najwa ta mele baki tana cewa. Ɗazun naga wata yarinya ta shiga sai dai bazan iya gane fuskarta ba kuma babbace, wlh yanzu haka ita suka aika ta kunna dan su tayar da gobara In Sha Allah ta Allah ba tasu ba, gwara ki sallame su kawai, tunda mu namu dangin kaɗan ne duk sun tafi. Sameeha bata ce komai ba ta miƙe ta isa inda masu abinci suke ta saka su tattara kayansu su bar mata sauran abincin, kana ta juya ta mufi inda 'yan uwan umma suke tace musu ta gode da zumunci su gaida gida taron ya ƙare dama la'asar suka yi da Aminu a watse, suka yi mata fatan alkhairi dan sun fahimci bata cikin natsuwarta shiyasa basu ja ba suka yi mata uzuri tunda abu yana niman zama da tashin gobara, ta ƙirga dubu goma ta basu na kuɗin mota cikin kuɗin da Aminu yace ta sallami mutane, suka amsa suna ƙara yi mata godiya da nuna jinn daɗinsu da kuɗin, ta koma gurin masu abinci ta saka suka yanka mata wani part na rago suka saka a leda suka bata taje ta basu, da farin ciki suka bar gidan sai da suka tafi ta koma wajen su Hauwa dan tayi haka ne kar suga abinda zai wakana a tsakaninta dasu, saboda tasan ba zasu kwashe ta daɗi ba, Sameeha tace musu. Dama ƙarfe huɗu Aminu yace a tashi a wannan taron shiyasa nazo na faɗa muku, ga dubu goma sha biyar daya bayar kuyi kuɗin mota in kun tashi tafiya, nagode da zumunci Allah ya saka da alkhairi sai mun sake haɗuwa, In Sha Allah zan zo yi muku ban gajiya. Wlh baki isa mu tafi yanzu ba dan sai bayan sallar magrib zamu tafi, haba ai da sauran lokaci mu mun saba sha'ani sai dare muke tafiya, ki kira Aminu ki faɗa masa in kowa ya tafi to mu sai dare. Kuma nawa kika bawa 'yan uwanki suka tafi da zaki bamu dubu sha biyar na tabbatar ba haka Aminu yace ki bamu ba. Cewar yaya Hauwa a cikin faɗa kamar tana jiranta, Laure ta saki shewa ta tafa hannu tana cewa. Su Sameeha masu gida, ai ba sai kinyi mana kora da hali ba zamu tafi, ke Hauwa tunda bata buƙatar mu kai dare tashi mu tattara yanamu yanamu mu kama gabanmu. Wlh yaya Laure ba inda zamu, haka kurum da sauran lokaci mu tafi z in ta sallami wasu to mu ne zamu sallami kanmu, nan fa gidan ɗan uwanmu ne ko kwana muka ce za muyi banga abin damuwa ba. Eh nasan da gidan ɗan uwanku ne yasa nake baku haƙuri tare da isar da umarninsa tunda kuna kallo gobara ta nima tashi a gidan, ni kuma bani da natsuwar da za a cigaba da wani hidima, abu ne da aka fara tun safe ina ganin dan an tafi yanzu ba matsala bace. Kuma da kike maganar kuɗin dana bawa 'yan uwana ina ruwanki idan nayi adalci wannan kai nayi wa, in kun raina kuɗin ne sai ki kira ɗan uwanki ki faɗa masa kuɗin daya bayar yayi kaɗan. Ta juya zata wuce, Adama ɗiyar Hauwa ta jawo gyalen Sameeha da ƙarfi har yana sauka a kafaɗarta ta shiga nunata da yatsa. Wlh baki isa ki faɗawa mamana magana a gabana ba ina kallonki, taya zaki wulaƙanta ta a bainan nasi saboda mun zo gidanki, to wlh ahir ɗinki in ba haka ba zan keta miki rigar mutunci kuma babu abinda kika isa kiyi, dama ance ɗan talaka bai iya samun guri ba, baki gaji arziki ba shiyasa kike niman yiwa mutane rashin mutunci to bari kiji... Bata ƙarasa ba Sameeha ta wanka mata kyakkyawan mari, Adama ta kama kuncinta tana waro ido waje, nan fa duk matan dake gurin suka miƙe, waɗanda suke can nesa ma suka matso, su Ikram ma suka ƙaraso gurin inda Hauwa ta shiga surfa masifa Laure tana tayata, sai kumfar baki suke sauran mata suma suna tayasu, Ikram tazo ta shiga tana rama zagin da suke yiwa Sameeha, wanda ita tama kasa magana sai kallonsu take suna dungure mata kai, abinda yasa bata yi magana ba saboda tasan duk abinda zai fito daga bakinta ba mai daɗi ba ne, kuma hakan zai ƙara wutar faɗan har yakai ƙila su bigeta tunda sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi, Ikram da ta shigar mata sai faɗan ya koma gunta suka shiga zaginta, sai Adama ta tsakumota suka fara dambe, wuri ya kaure da hayaniya wanda Najwa komawa gefe tayi ta shiga ɗaukar su video a wayarta, tana jin daɗin ɗaukar yadda zata ji daɗin nunawa Nafeesa da bata labarin abinda ya wakana, da yake gabaɗaya hankalinsu yana gurin faɗan babu wanda ya kula da Najwa tana ɗauka, da kyar Sameeha ta kwace Ikram a hannun Adama dan tafi ƙarfinta Ikram ba tada jiki siririya ce, Ikram da aka kwaceta da kyar ta shiga yi mata Allah ya isa tana zaginta tana cewa dangin mayu saboda ta ji mata ciwo a fuska da yaƙushi, Sameeha janta tayi sai da suka isa ƙofar shiga falo ta buɗe ƙofar ta turata ciki tana gargaɗinta akan karta sake ta fito, sai ta dawo ta tasa ƙeyar yaranta tace suje falo, a lokacin ne Najwa ta fito daga maɓoyarta na ɗaukar video da take yi, Sameeha ta ce ta wuce falo tace to, sai ta koma ta sallami masu abinci ta saka suka shigar mata da sauran tace gobe In sha Allah zata kawo musu kulolinsu, sai da suka shigar mata da komai kana ta wuce falon ta shiga ta kulle ta ciki ta barsu Hauwa a tsakar gidan sunata surfa zagi da masifa. [7/7, 13:04] Buhainat😁: *ABIN DA CIWO* Na ©Rahma Kabir MrsMG. Wattpad @rahmakabir Page 9. Sameeha zama tayi a cushing ta shiga zubda hawaye saboda ɓacin rai da kuma damuwar da suka jefata ciki, abin da ciwo yadda suke niman ɗaura mata laifin da bata san tayi musu ba, tasan ko ranta zata basu ba zasu taɓa sonta ba muddun bata yi musu abin da suke so ba, wato ta riƙa binsu tana yi misu biyayya sauda ƙafa tare da bin duk wani umarninsu da suka sharɗanta mata, gabaɗayansu jugum jugum suka yi ko wanne da damuwar da yake damunsa, tunda har lokacin su Hauwa masifa suke yi da zage zage har da buga musu ƙofar falo suna cewa su buɗe musu su shigo su ga yadda ake koyar da biyayya, Sameeha ta goge kwalla ta ɗauki wayarta ta kira Aminu bugu biyu ya ɗaga yana cewa. 'Yan walima har an watse kenan? Ko da yake dama la'asar muka yi ki sallami kowa kema ki samu ki huta.. Sasshekar kukanta yasa shi gimtse maganarsa ya ƙara gyara zama cike da mamaki ya cigaba da cewa. Sameeha meya faru naji kamar kuka kike yi, su Hauwa ne ko? Dan nasan halinsu basa ƙaunar a zauna lafiya. Sameeha sai ta fashe masa da kuka ta shiga bashi labarim duk abinda ya faru cikin kukan bata rage masa komai ba, salati ya shiga jerawa sai ya kashe wayar da sauri ya duba number ɗin Yaya Alhasan ya kira shi, yana ɗauka ya shiga zayyano masa komai shima Alhasan salati yayi yace zai je gidan yanzu ya kwantar da hankalinsa In Sha Allah zai tsawatar musu, sai suka kashe wayar Aminu ya kuma kiran Sameeha ya shiga lallashinta yana bata haƙuri yana cewa. Naga alama su Hauwa ba zasu barki ki zauna cikin kwanciyar hankali ba dan haka zan nima mana gida anan Abuja idan na dawo sai mu ɗiba kayanmu na sawa mu koma can in yazo ma riƙa zuwa hutu a nan gidanmu. Yanzu saboda su sai muƙi zama cikin ahalinmu, bayan burina na kasance cikin dangi nima a dama dani kuma mu kara sanin juna da fahimtar juna a tsakaninmu, wlh dalilin su Hauwa ba zai sa na bar kaduna ba dan na dawo kenan ba wani garin da zan ƙara zama. Kawai dai kuyi wa abin tufka dan wlh ina musu kawaici duk ran da suka ƙureni za a yi ɓatacciya. Shiyasa nace kafin akai ga haka dole kiyi hakuri kibar kaduna dan bazan iya da wannan rikicin ba, da aiki na zanji ko da tashin hankali da suke jawo mini, ki ƙara bawa Ikram hakuri In Sha Allah hakan bazai sake faruwa ba, kuma ki fara haɗa kayanku dan baza mu cigaba da zaman kaduna ba na gama maganata. Yana kaiwa nan a maganarsa ya kashe wayar Sameeha ta bi wayar da kallo tana jin zuciyarta na zafi, Ikram tace. Ai dama nasan ƙarshe dole ki bar garin nan ki bishi Abuja, dan haka shine kawai mafita. Wlh Ikram ba inda zani basu isa su saka nabar kaduna ba dan nan nake son zama, idan har muka koma Abuja hakan ya nuna sun ci galaba akai na, so nake na zame musu ciwon ido mai wuyar warkewa kuma sai gani sai hange, dole na fito musu da asalin halina tunda rashin mutunci ba a gadonsa kowa ara yake ya yaɓa. Wlh da gaskiyarki anty karki yarda ki koma Abuja, taya zasu raba mana zumunci muna jin daɗin kin dawo nan zamu riƙa zuwa muna cin kayan daɗi. Cewar Najwa cikin zuga Sameeha dan sosai zuciyarta ta tsinke data ji hukuncin da Aminu ya yanke, idan har suka koma Abuja ta san ta shiga uku Aminu ya ƙara yi mata nisan da ba zata taɓa samunsa ba, karshe ta kamu na ciwon so da zai yi ajalinta, dan haka dole ne tayi iya ƙoƙarinta ganin basu bar kaduna ba, jin maganar Sameeha da tayi yasa taji kwarin guiwar zugata akan karta yarda su koma can, Ikram ta galla mata harara. Ai dama ke badan Allah zaki so su zauna anan ba sai dan kwaɗayi da kika sabarwa kanki, wlh Najwa in baki wasa ba bakinki sai ya ci abinda zai kashe ki. Ikram bana son sakarci ko kin mance matsayin Najwa a gunmu da zaki riƙa faɗa mata duk abinda yazo bakinki, ki na sane da jininmu ce ita kuma itace matar Yaya Zaidu da zai aura ko da kin girmeta dole ki bata wannan girman, kuma abinda ta faɗa gaskiya ne babu abinda zai sa na bar kaduna wallahi. Cewar Sameeha tana gargaɗin Ikram, Ikram bata ƙara magana ba Najwa kuwa ta sakar mata murmushi tana yi mata gwalo, Ikram harara ta balla mata tana ƙofa sai ta miƙe ta wice ɗakin Sameeha dan ta yi wanka saboda su Adama sun camama mata jiki duk ciwo yake mata. Tana shiga ɗakin ta kira umma ta zayyana mata komai, umma a wannan karan itama ranta ya ɓaci ta aje kara ta dinga faɗa tana cewa yanzun nan Zaidu zai kawota, abin nasu yayi yawa itama Sameeha 'yar dangi ce kuma tanada gata ba zai yuwu su riƙa yi mata cin kashi ba dan ita ba shara bace da za a zubar da ita a duk inda aka ga dama, dan in bata nuna ɓacin ranta ba to gama ba sakewa zasu yi, Ikram taji daɗin bayanin Umma wanda ta ce sai sun zo ta kashe wayarta. Bayan kusan minti talatin sai ga Yaya Alhasan da yaya Kamalu zun so gidan, su Hauwa suna ganin shigowarsu suka sha jinin jikinsu ko wanne ya shiga hankinsa, suka ƙaraso gabansu suka tsaya suna kallonsu ɗaya bayan ɗaya kafin Alhasan yace. Kun kyauta abinda kuka yi, kuma wlh duk sai naci mutuncinku, marasa lissafi da tunani, daga zuwa cin arziki sai abu ya zama rashin hankali da hauka, dole dai sai kun saka kanku a cikin irin dangin mijin nan da basu da kirki ake faɗarsu a duniya, to ina dai dai da iskancinku kuma daga yau duk shegiyar data kuma tako ƙafa tazo gidan nan naji labari abinda zanyi mata Allah kaɗai ya sanshi, dan har gida zanbi mace naci ubanta kuma.. Bai ƙarasa maganarsa ba su Umma suka shigo ita da Zaidu, suka jira har suka ƙaraso gurin da suke Alhasan da Kamalu suka gaisheta kana Zaidu shima ya gaishesu, a lokacin su Sameeha suka fito daga ɗaki suka ƙaraso dan Zaidu ya kira Sameeha yace mata suna gate tace su buga mai gadi zai buɗe musu, Umma ta ce cikin damuwa. Dan Allah Hauwa ina so ku faɗa mini meye Sameeha tayi muku da kuka saka mata wannan karan tsanan haka, tunda ta Aure Aminu kuke yi mata abubuwa tana kawo min magana amma ban taɓa bin bayanta ba, dalilin zuwana yanzu so nake naji me take yi muku sai na sakata ta baku haƙuri komai ya wuce, dan gaskiya lamarin bai mini daɗi ba tunda har ya kai ga fara duka, ina son Sameeha dan haifarta nayi ba daga sama ta faɗo ba, ba zai yuwu daga dawowarsu a hana mata kwanciyar hankali a gidanta ba. To ai itace ta kawo rikicin ta fara marina saboda ta zagi mamana na saka baki. Cewar Adama data tari numfashin Umma, Kamalu cikin daka tsawa yace. Zo nan dan ubanki, uban waye yace ki saka baki? Adama ta matso nesa da shi ta tsaya tana turo baki, aiko daya yi wani tsalle ya kifa mata mari mai kyau ya rankwatseta akai yana zaginta, Hauwa ta ce cikin faɗa. Haba taya za a dakeni a hanani kuka, ya zaka huce haushinka akanta, dan me daga mayar da magana sai duka. Idan baki mini shuru ba Hauwa wlh zan ci kaza kazan ubanki 'yar banza kawai mara mutunci ba duk kece kika kawo wannan hargitsin ba. Dan Allah Hajiya kuyi haƙuri In Sha Allah hakan ba zata sake faruwa ba kuma zan ɗauki tsattsauran mataki akan haka. Cewar yaya Alhasan kamar zai rufe Hauwa da duka, nan suka cigaba da yi musu masifa suka ce su tattara su bar gidan kuma idan suka ƙara zuwa gidan Sameeha ta faɗa musu zasu ɗauki mataki, kana fa su Hauwa suka wuce soƙai soƙai ko wacce cike da ɓacin rai, Laure dai ta kasa magana dan tasan halin mijinta da ɗaukar zafi idan bata yi wasa ba sai aurenta ya samu gargada, shiyasa ta sakawa bakinta kwaɗo da linzami tabi sahun sauran matan ba tare da yin ko tari ba, haka itama Sa'a bata iya cewa komai ba dan tasan halin Kamalu bai da wasa, sai da suka bar gidan umma ta sake jajjada musu su ɗauki mataki dan ba zata yarda da zancen duka ba, suka tabbatar mata da hakan bazai sake faruwa ba kana suka bata haƙuri, Sameeha tayi musu godiya ta ɗaura da cewa. Aminu yace wai zan bar kaduna mu koma Abuja dan Allah kuyi masa magana ya barni a nan na zauna cikin 'yan uwa ni banga abinda zaisa ya yanke wannan hukuncin ba dan su Hauwa sun saba yi mini bita da ƙulli duk in da naje ma ba fasawa zasu yi sai dai in Allah yasa su gane gaskiya. Dama wannan ba dalili bane da zai sa ku sake barin Kaduna, In Sha Allah za muyi masa magana ba in da zaku koma. Cewar Kamalu, nan ta sake yi musu godiya suka yi mata sallama suka wuce, su Umma suka wuce zuwa falo, sai da suka zauna kafin Umma tace. Sameeha da za kiji ta tawa da kin bi mijinki kin huta da fitinarsu. Tsoransu taje ji kenan? aiko wlh ni banga dalilin da zai sa ta bar kaduna ba muna jin dadin ta dawo kusa damu. Cewar Zaidu, nan dai suka dinga tattaunawa, Najwa ta buɗe kunne tana ta ɗaukar magana, sai daga baya ta ce ita zata tafi, Sameeha taje kitchen ta ɗibar mata sauran abinci a babbar kula da naman ragon da kaji tace ta kaiwa inna, ta bata dubu uku Najwa ta amsa tana godiya, Zaidu ne ya ɗauketa a mashin ɗinsa yace in ya sauketa zai dawo ya mayar da umma gida. A hanya da suke tafiya Zaidu ke cewa Najwa. 'Yan matana wai laifin me nayi ne kwanakin nan kike ta shareni? Tunda na siya miki waya ya kamata ace kin sauko daga fushinki ko. Hmmm ni ba wani abu kawai dai karatu ne ke hanani yin magana da kai. Amma ina ganinki a online ina miki magana sai dai baki kulani, ko shima karatu kike a gurin.. Hira nake da ƙawayena bana ganin maganarka sai in na fita daga group. Kuma lokacin sai naga ka sauka. Najwa ko dai kin samu wani ne kina son kiyi mini halinku na mata. Ai kasan dama ni a kasuwa nake mai rabo ka ɗauka, duk yadda ka ɗauka to hakan ne dan na kula ka fiye zargi da mita, idan dan wayan da ka siya mini ne sai na mayar maka da abinka, nasan ina da wanda sai kawo mini sabuwar waya wacce tafi wanda ka bani. Haka ma zaki ce? Eh! Ta faɗa cike da tsiwa tana murguɗa masa baki kamar yana kallonta, girgiza kai yayi yana Allah ya kyauta ya cigaba da tuki bai sake magana ba har ya sauketa ta shiga gida ba tare da ko godiya ba sai cin magani take tana ɓata fuska, Zaidu ya sauke ajiyar zuciya yaja mashin ɗinsa ya wuce, tunaninsa ya gama bashi Najwa tayi sabon saurayi kuma da alama mai kuɗi ne tunda yasan halinta tana da son abin duniya, sai dai bai taɓa kawowa lokaci guda zata sauya masa ba, ashe ba sonsa take ba yaudararsa kawai take yi, idan hakan zai kawo saɓani da zumuncinsu zai haƙura da ita kawai ya nima wata, amma zai cigaba da binta a haka ya ga iya gudun ruwanta. Zaidu bayan ya koma gidan Sameeha yadda suka ganshi ba annuri yasa Umma ta tambaye shi ko lafiya, ya zauna ya zayyano musu duk abinda Najwa take masa dama abinda tayi masa yanzu da ya kaita gida, Sameeha tace masa. Ko dai dama bata sonka tuntuni kawaicin zumunci yasa take saurarenka, to gwara tun wuri kasan matsayin data ajeka dan kar azo a samu matsala, idan ba zai yuwu ba ka nima wata dan bana son zumuncinsu ya samu matsala. Gaya masa dai tun farko daya zo mini da maganar sai da na jinjina amma daya dage nabi sa da addu'a, dan haka kasan me kake ciki da ita, idan bata yinka ka kama kanka cikin salama. Tashi ka mayar dani gida, Ikram sai yaushe zan ganki? Cewar umma, Ikram tace. Tsakanin Alhamis ko juma'a bayan mun seta gidan In Sha Allah zan dawo. Ta faɗa tana miƙewa tare da ɗaukar musu kular da suka zuba musu abinci da ledar da suka saka musu kayan lemu da ruwa, dama mazubin da suka saka musu nama. Har gate suka rakasu suka hau mashin tare da aje musu kayan a gaban mashin ɗin, Zaidu ya jasu suna daga musu hannu, sai suka dawo cikin gida Sameeha ta sanar da mai gadi ya samo masu aiki su gyara mata farfajiyar gidan, sannan in masu ɗibar kanofi da kujeru sun zo ya buɗe musu su shigo su kwashe dan ta sallamesu, sai ta wuce cikin gida. Ta samu Ikram tana waya ta zauna tana kwalawa jamila kira ta fito da sauri daga ɗakinta dan dama tun ɗazun da su Hauwa suka tafi ta shigo ciki ta shige ɗakinta, sai da ta tsuguna a gaban Sameeha kana ta ce gani. Yauwa gobe In Allah ya kaimu da sassafe nake so ki gyara mana gida bana so na tashi naga baki yi komai ba. Zaki iya tafiya. Cewar Sameeha, sai Jamila ta ce mata to kana ta miƙe ta wuce tana ƙunƙuni da zancen zuci. Dama ɗazun sunyi miki dukan tsiya sun kumbura miki baki muga ta yadda zaki yi magana, shegiyar mata ko tausayi na bata ji, ko da yake kuɗi zata biyani dole ta bautar dani. Ta ƙare zancen tana turo baki ta buɗe ƙofar ɗakinta ta shige. *** Najwa. Da daddare tana kwance a ɗakinta tana chart da Nafeesa tare da bata labarin abubuwan daya wakana a gidan Sameeha ta voicing, bata rage mata komai ba dan har video data ɗaukar mata ta tura mata, Nafeesa ta buɗe tana kallo, sai da ta gama ta tura mata voicing da cewa. Shegiya ƙawata amma kwakwalwarki tana bala'in ja, lokaci guda kin yi abubuwa da yawa masu muhimmanci, to ina mai tabbatar miki da in kika ɗaure a haka zaki cimma nasara wlh, kuma kinga video nan da kika turo mini bani kaɗai zan gani ba sai duk duniya sun gani, dan yaɗa shi za muyi a social media mu rubuta cewa matar ɗan uwansu ce tayi musu wulaƙanci dan sun zo gidanta saboda su talaka ne, bata ƙaunar kowa ya raɓeta tare da Allah ya wadaren masu hali irin nata. Najwa data gama saurare ta saki wani shewa tana dariyar mugunta na jin daɗi, sam wannan tunanin bai zo mata ba ga shi Nafeesa ta ƙara hasko mata matsalar da zata ƙara saka Sameeha a ciki sai tace. Wlh nayi matuƙar murna da kika tunatar dani wannan labari dan haka na bar miki wuka da nama ki bayar a yaɗa yadda ko bincike ya zo ba za a gane waye ya ɗauka ba, kuma ina kyautata zaton wannan videon zai ƙara wutar ƙiyayya a tsakaninta da su Hauwa, zata ƙara tsanarsu da tunanin sune suka yi mata haka da gangan dan zu tozarta ta a idon duniya. Nafeesa ta turo mata sticker na rawa tana cewa. Akwai wani ɗan makarantarmu da muka yi poly tare, yasan kan media sosai shi zan turawa ya yaɗa. Najwa ta yi mata godiya sai suka cigaba da hira inda Najwa ke bata labarin yadda suka yi da Zaidu ɗazun, Nafeesa tace gwara ta yi masa haka ta fara zame masa dan ya cire rai da tunanin samun aurenta. [7/7, 13:04] Buhainat😁: *ABIN DA CIWO* Na ©Rahma Kabir MrsMG. Wattpad @rahmakabir Page 10. Hauwa. Da tsananin ɓacin rai suka bar gidan suka kama tafiya a ƙafa ba mai cewa wani a tsakanin Hauwa, Laure da Sa'a da yake su uku suka jera, sauran sunyi gaba da yara wasu kuma sun tari abin hawa sun wuce, suna cikin tafiya har su Alhasan suka wuce su a motar Kamalu, Sa'a ce tayi ƙofa tana cewa. Allah ya wadaran naka ya lalace, ina takaicin yadda su Kamali suke bin Aminu sai kace shine babbansu, komai ya tsara musu shi suke yi basa iya yin ra'ayinsu, ko da yake mai kuɗi sarki ne dole ya amshe girman su sun zama fadawa, basa ganin laifinsa da matarsa komai suka yi daidai ne. To Aminu ya gama kashe musu zuciya basa iya ƙoƙarin nima ya gama ɗaure musu gindi komai yana yi musu, ina ce motocin da suke hawa duk shi ya siya musu, idin hidima ya taso musu shi suke faɗawa yayi musu kunga kuwa har abada Sameeha ba zata taɓa yin laifi ba a gunsu, dan haka sai dai mu zuba ido muga abinda zai turewa busu naɗi, dan kuwa wulaƙanci yanzu muka fara gani a gunta tunda ta samu masu tsaya mata kuma bamu isa mu ja dasu ba dole ta taka mu son ranta. Cewar Laure rai a ɓace, Hauwa kuma ta kasa magana sai taunar leɓenta na ƙasa take yi saboda tsabar baƙin ciki da ke nuƙurƙusanta. Hauwa baki ce komai ba kinyi shuru. Cewar Sa'a, Hauwa ta taɓe baki tana cewa. To ni me zan ce bayan sun gama yanke hukunci, kamar yadda suka faɗa nima bazan sake zuwa gidan Aminu ba in dai Sameeha tana ciki, tasha zamanta nima na zauna a inda Allah ya aje ni, ta dai gama lalata mana zumunci. Ta ƙare maganar tana jan tsaki, wayar Sa'a data yi ƙara yasa basu yi magana ba, tana ɗaukota a jaka taga Kamalu ne tace cikin damuwa. Kunga Kamalu ne yake kira har sun kai gida, bari na tari napep na ƙarasa dan bana son rikicinsa, in ba haka ba yau sai ya hana mini barcin kwanciyar hankali wlh. To mu dai sai mun zo, dan babansu ma baya nan daga ni sai yara shiyasa na ce sai dare zan tafi, to uwar iya ta koremu sai kace wasu tumaki. Cewar Hauwa, nan Sa'a ta tari napep tayi gaba sai da ta wuce kafin Laure tace. Wani mataki zamu ɗauka dan Wlh ni bashi ta ci, yadda ta saka su Alhasan suka dizgamu gaban sirikanmu da 'ya'ya. Banyi maganar bane saboda kin san Sa'ade uwar surutu ce ina buƙatar sirri. Nima ganin ta yasa banyi magana mai zafi ba, amma wlh Sameeha sai ta bar gidan nan kamar yadda ta saka aka koremu itama sai Aminu yayi mata korar kare, ai ta jawa kanta dan wlh watan barin ta gidan ya kama, sai ta yi dana sanin abinda tayi mana, dan sam ba matar aure bace ita tunda tana niman haɗa mu da 'yan uwanmu, In Sha Allah ni da kaina saina sama masa mata ta mutunci wacce zata yi mana biyayya taso mu tamkar nata 'yan uwan. To Hauwa kina ganin ta wace hanya zamu ɓullo wa lamarin dan lokaci yayi da zamu nunawa Sameeha ita ƙaramar 'yar iska ce, kuma mu nuna mata muma muna da rana. Ki bar komai a hannuna, aure zan fara niman masa mu gani in zai yarda, in yaƙi kuma sai mu bi masa ta bayan gida na shiga malamai ayi musu farraƙu shi da Sameeha, dan sai ta bar gidan nan wallahi da ni take zancen. Cewar Hauwa tana tafa hannunta cike da masifa, haka suka cigaba da ƙulle ƙullensu suna ta kwashewa Sameeha albarka wanda kuma kansu suke zagi kuma fata nagari aka ce lamiri. Sai da Laure ta shiga gidan Hauwa ta ɗibar mata naman kaza kafin ta wuce gida tana cewa zata ɓoye abinta taci a hankali. Adama data shigo bedroom ɗin mamanta tana cewa. Allah mama ki bani dama na koma naci uwar miki Sameeha, dan ji nake in ba dukan kawo wuƙa nayi mata ba ba zan huce takaicina ba. Sha kuruminki akwai abinda zanyi mata wanda yafi duka ciwo, daga ni har ku ba mai sake zuwa gidan idan Aminu ya dawo mayi zumunci dashi a babban gida sai naje mu gaisa. Ai mama baiyi dacen mata ba, ƙiri ƙiri take nuna bata son hurɗa damu, Allah yasa ya ƙara aure muga ta iskanci. Adama ta faɗa tana zama a gefen gadon Hauwa tare da buɗe ledan naman kaza ta ɗauki cinya, tana ci tana cigaba da zagin Sameeha, Hauwa dai ranta a dagule yake dan sai mugun alwashi take ɗauka a zuciyarta dan in har bata ga Sameeha ta wulaƙanta ba to hankalinta ba zai kwanta ba. ... Da safe suna karyawa wayar Hauwa ta hau ƙara, yaron Adama Sadiq yaje ya ɗauko mata a tv stand ya kawo, ta duba sai taga Najwa ce sai ta ɗauka da sauri suka gaisa kana Najwa ta ɗaura da cewa. Yaya dama na kira ne nayi muku ban gajiya jiya da kuma jimamin abin da ya faru, Allah ya ƙara muku haƙuri dan wlh Abin da ciwo, ko ni korata tayi tace na tafi ta sallame ni bata son damuwa, haka na tafi komai bata bani ba, kuɗin napep ma sai da na isa gida na shiga na amso a hannu Inna kafin na sallame shi. Allah ya kyauta, ai dama in bata yi haka ba to bata ci sunanta ba, gajiya tabi lafiya Najwa, 'yar uwarku dai ba tada mutunci tasa an wulaƙantamu a bainan nasi. Ai wlh naso ace kunyi musu dukan ciya kun fasa musu jiki dan har Ikram ba mutunci ne da ita ba, jiya kun sha zagi da tsinuwa, cewa take taji daɗin hukuncin da yayyinku suka yanke, kuma duk wacce ta zo gidanta sai ta kira ta faɗa masa, Ikram tace ai kawai ta saka a kawo mata karnuka duk wacce ta zo tasa a sakar mata kare su korata, Sameeha tace ita bin Aminu ma zata yi subar garin dan ba zata iya da jaraba da kwaɗayinku ba, dan ta lura talauci ke damunku, wai ko wacce ta kwaso yunwa kun zo kun saki ciki sai ɗirkan abinci kuke yi kamar mayu. Inalillahi wa inna ilaihir raji'un! mu suka yiwa wannan zagi, amma Allah ya ɗebe musu albarka, In Sha Allah yadda ta wulaƙanta mu itama sai ta wulaƙanta a duniya. Cewar Hauwa cikin baƙin ciki kamar zara rushe da kuka dan sosai maganganun da Najwa ta faɗa mata sun daki zuciyarta, tsanar da takewa Sameeha ya ƙara ninkuwa, ji take da za a bata damar kashe mutum guda to Sameeha ce zata kashe dan duk duniya ba tada maƙiyiyar data wuce ta, nan ta baza kunne Najwa tana ta faɗa mata maganganu na ƙarya tana hawa ta zauna, daga Ƙarshe Najwa fashewa tayi da kukan ƙarya tana cewa. Wlh yaya abin da ciwo sosai jiya da kyar nayi barci akan abinda ya faru, wlh ba dan Sameeha 'yar uwata bace da sai nayi hanyar da sai na auri mijinta naga iya ƙarshen wulaƙanci da iskanci. Wani 'yar uwa? abin da babu haramci, ai wlh da ba ƙaramin baƙin ciki zata shiga ba ace 'yar uwarta ce ta aure mata miji, amma wlh da hakan zai faru dana fi kowa farin ciki, ke ni sai yanzu naji ɗan farin ciki da wannan maganar taki, saboda barinta gidan bashi ne mafita ba ayi mata kishiya da kuma wacce ta sani shine zai fi girgizata ta shiga tashin hankali, kinga mu farin ciki goma da ashirin, kuma nasan ke ba zaki yi irin halinta ba tunda tarbiyya ba ɗaya ba. Yaya nifa ba zan iya ba dan wannan yadda bata so a raɓeta sai ta kashe mutum akan ayi mata kishiya, tsoroma take bani, dan sosai nasan ƙulle ƙullen asirin da take ƙullawa mijinta, shiyasa ta mallake shi. Au na shiga uku nayi suɓul da baka ashe da yaya nake maganar, dan Allah karki faɗawa kowa wannan maganar dan Ikram ke faɗa mini a matsayin sirri. Wani sirri kuma ai wlh naji daɗi da kika faɗa mini, ko baki faɗa bama mun san ba haka ta barshi ba amma zamu ɗauki mataki, nagode Najwa Allah yayi miki albarka yasa ki gama da duniya lafiya. To yaya In Sha Allah na samu lokaci har gida zan zo, amma kafin nazo sai na sake komawa gidan Sameeha na samo miki labari, duk da nace bazan sake zuwa ba, amma kodan ku riƙa sanin meke faruwa a gidan dole na je dan nima babu abinda nake so sama da naga Anty Sameeha ta wulaƙanta kamar yadda take wulaƙanta mutane dan har Innata bata bari ba, shiyasa ai jiya bata je ba tace ni ce zan je dole ba dan halinta ba sai dan kirkin iyayenta. Aiko nagode kin ga kina samo mana labari muna ƙara shirya wa matakin da zamu ɗauka, tunda ni ba zan sake zuwa gidan ba yazo ya zama abin magana. Cewar Hauwa, a haka suka yi sallama ta kashe wayar tana duban Adama fuskarta cike da murmushi dan gabaɗaya tun jiya rabon fuskarta da annuri sai yanzu da Najwa ta gama labarta mata magananganu, Adama tace. Hala wannan 'yar uwarta ce ta kira dan naga yarinyar tana da hankali ba irinsu ba. Itace ta kira Adama, ai kina jin zagin da su Sameeha suka yi mana, yanzu zama bai ganni ba bari naje babban gida nayi magana da Laure, dan zuciyata ta fara kwanciya da yarinyar nan, itace dai dai wacce ta dace Aminu ya aura, kinga su can mun haɗa musu rikicin dangi kamar yadda taso ta raba kawunanmu, sannan Najwa tamu ce sai abinda muke so zata yi a gidan, duk da abin zai yi wuya amma sai nasa anyi mana aiki akan Aminu kai waye. Amma mama anya hakan zai yuwu? kin fa ce da Baban Sameeha da maman Najwa uwa ɗaya uba ɗaya. Adama zai yuwu mana ai babu haramci. Amma ana barin halak dan kunya. Ba a wannan zamanin ba, nasan ba zamu sha wuta gurin shawo kan Najwa ba, tunda Aminu yanada nagartan da za a so shi, ga kyau ga kuɗi ga nasaba komai ya haɗa, in yaso sai ya raba musu gida, ni dai in hakan ya faru wallahi baƙin ciki na ya yaye banda saurin ɓacin ran Sameeha, dan mun gama ƙunsa mata baƙin ciki, kuma kiri kiri zan nuna mana mune muka haɗa auren dan tasan mun isa da Aminu. To Allah ya tabbatar, in dai hakan zai faru to ƙarshen Sameeha yazo. Ke bari na tashi naje gida, wlh ji nayi ma na ƙoshi. Cewar Hauwa data miƙe cikin sauri ta wuce ɗaki, ba jimawa ta fito sanye da hijab ta fice tana cewa sai ta dawo. Gida uku ke tsananinta da gidansu dan haka tana shiga bata tsaya ɓata lokaci ba ta wuce sashin Laure, tayi sa'a Alhasan ya fita yaran ma duk sun tafi makaranta, ta zauna dirshen akan kafet kamar yadda Laure take zaune a gurin ta baje ƙafa daga ita sai ɗaurin kirji, tana cin taliyar Hausa da ta dafa ta zuba naman kaza a ciki, ta kalli Hauwa tana cewa. Idan na ganki a irin wannan lokacin to nasan akwai labari Allah yasa dai mai daɗi ne. Hmmm maganganu kam nazo dashi duk da dai na ɓacin rai ne, sannan kuma akwai shawarar dana yanke wanda nake so mu tattauna. Yanzun nan Najwa ta kirani ta gama faɗa mini ɗibar albarkan da Sameeha tayi mana. Nan fa Hauwa ta shiga zayyano mata maganganu tana yi tana tafa hannu da riƙe haɓa tare da ƙanƙance idonta, Laure salati kawai take tana kwashewa Sameeha albarka, da Hauwa ta gama ne tace. Kin san shawarar dana yanke domin mu huce takaicinmu, to na samarwa Aminu mata cikin sauƙi ba sai na sha wuya ba. Wacece kika samo? Ni dai da kin bari mun bincika da kyau mun samo wacce ba zata watsa mana ƙasa a ido ba. To Najwa na yanke shawarar zai aura, dan itama cewa tayi da ba dan Sameeha 'yar uwarta bace da sai ta auri Aminu taga karshen wulaƙanci, kin ga kuwa wlh yarinyar nan zata share mana hawaye, kuma mun jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya, na farko Sameeha zata shiga cikin kunci akan zata yi kishi da 'yar uwarta, na biyu kuma Najwa tamu ce sai abinda muke so zata yi mana, kinga a hankali zamu saka tayi waje da Sameeha ba sauran labarinta a gidan Aminu, can kuma zasu ƙarata da rikicin dangi, mu kuma cikin ruwan sanyi buƙatarmu zata biya. Wayyo Allah daɗi, Ayyiririri, amma wannan shawara tayi Hauwa. Sai dai akwai sauran rina a kaba, ya za muyi da uban gayya Aminu dan kin san abu ne mai wuya ya yarda da aurenta cikin ruwan sanyi. Haba Laure sai kace mu ba 'yan cikin garin Kaduna ba, wajen malam mai allon ƙarfe zan kai sunan sa ya cika masa aiki, sannan ma ai ba zamu bayyana Najwa bace kai tsaye, hatta Sameeha ba zamu bari tasan ita zai aura ba har sai anyi ta ganta, dan Najwa zamu gargaɗeta ko a gidansu karta bari asan Aminu mijin Sameeha ne zata aura, dan ba lallai iyayenta su bamu haɗin kai ba. Gaskiya naji daɗin wannan magana yanzu mu bari komai ya lafa tukuna kafin mu taso da wannan maganar, mu dai mu cigaba da shirinmu, ki ƙara jan yarinyar a jikinki har ki sanar da ita buƙatar mu, in ta amince sauran masu sauƙi ne. Cewar Laure, Hauwa ta bata hannu suka tafa tana jin farin ciki kamar ma aniyarsu ta biya, haka suka cigaba da ƙulle kullensu sai wajen sha ɗaya da rabi kafin Hauwa ta bar gidan. **** Sameeha. Tana zaune a falo tana hutawa dan basu daɗe da karyawa ba, ta kunna tv tana kallo gasu Abi suna wasa a carpet da yake duk sunyi wanka kuma Jamila ta gama gyaran falon, farfajiyar gidan ma mai gadi ya kira wasu sun zo sun tattara gidan sun kwashe bola an biyasu sun tafi. Ikram kuma tana kwance a gado tana kallon abubuwa a facebook, nan taci karo da videon faɗansu na jiya sai ta karanta bayanin da aka yi a ƙasansa, tsabar mamaki da fargaba yasa ta tashi zaune tana rafka salati, nan ta shiga comments section ta samu sai zagin Sameeha ake yi, cike da tashin hankali jiki yana rawa ta sauko a gado ta nufi falo. _Abin da ciwo ace naka shike bada kai, ana zaton wuta a maƙera sai a tsinceshi a masaƙa, kuma wani lokacin makashinka yana nan tare da kai_ Mu je zuwa. [7/7, 13:04] Buhainat😁: *ABIN DA CIWO* Na ©Rahma Kabir MrsMG. Wattpad @rahmakabir Page 11. Ikram tana isa falon ta miƙawa Sameeha wayarta tace cikin rawar murya. Anty kinga an samu wanda ya ɗauki video ɗinmu na rikicin jiya sun yaɗa a social media har da tagging fuskarki da aro ana cewa ke ce matar da kike yiwa dangin mijinki wulaƙanci dan sun zo gidanki walima. Kalla dai ki gani. Hannun Sameeha yana rawa ta amsa ta shiga kallo zuciyarta ta gama tsinkewa sai hawaye ya soma zarya a kuncinta, har ta gama kallo ta miƙawa Ikram wayar tana share hawaye tana cewa. Sharrin su Hauwa ne dan a cikinsu aka samu shaiɗanin daya ɗauka ya yaɗa domin su zubar mini da mutunci a idon duniya, kuma duk wanda ya zageni Allah ya isa dan bazan yafe ba. Amma wlh mutanen nan basu da kirki rashin imaninsu har ya kai su yaɗa video irin wannan dan suci mutuncinki, sauƙin abin hoton fuskarmu bai fito sosai ba saboda daga nesa aka ɗauka. Koma waye yayi mana haka to yama kansa kuma... Bata gama magana ba wayarta ta shiga ƙara taga Zaidu ne, tana ɗauka shima maganar video yayi mata, nan ta fashe masa da kuka ya dinga bata haƙuri yace tabarwa Allah duk wanda yayi mata haka sai Allah ya saka mata, haka suka aje wayar, a takaice haka ta dinga amsa wayar mutane wanda suka gani duk dai haƙuri suka bata, dan har Yaya Kamalu ya kirata yace zasu ɗauki mataki. Cikin damuwa ta kira Aminu yana ɗauka ta bashi labari yace cikin fada. Na gaji da abinda su Hauwa suke yi mini yanzu, su rasa abinda zasu saka mini da shi sai suci mutuncinki, ai bake suka tozarta ba ni suka tozarta, kiyi haƙuri zan ɗauki mataki. Yana kaiwa nan a maganarsa sai ya kashe wayarsa, ya duba agogo yaga ƙarfe sha biyu saura sai ya kira wani da yake aiki a gurin jirgin ƙasa yace zai tura masa kuɗi ya siya masa ticket na ƙarfe biyu zai je Kaduna da yake yanzu sau biyu jirgin ke zuwa Kaduna daga takwsa na safe sai kuma biyun rana, yana gama wayar sai ya shiga toilet dan ya watsa ruwa ya fito ya shirya. Sameeha kuwa saboda damunta da aka yi da kira dan duk wanda yaga videon sai ya kirata, ya sata kashe wayarta gabaɗaya, tayi kuka harta gode Allah Ikram sai bata haƙuri take yi, umma ma ta kira a wayar Ikram ta bata haƙuri tace dama dole rayuwa tana tafiya da ƙalubale dan haka jarabawa ce sai ta ɗaure zata ci, kuma matakin nasara yana tare da yin haƙuri, maganganu ta gaya mata masu daɗi da ya sakata samun natsuwa. Da aka kira sallar azahar ne suka shiga ɗaki dan gabatar da sallah. **** Najwa. Lokacin data kira Hauwa tana tare da Nafeesa dan rubuta mata maganganun tayi a takarda wanda zara faɗawa Hauwa kuma itama ta ƙara da nata, sun haɗu a islamiyya ne wanda dama tun jiya suka shirya zata kira Hauwa ta shinfiɗa mata karyan maganganu da zai sa ta samu shiga a gurinta, wani aji suka shiga da ba a amfani da shi wanda empty yake ko kujeru babu, a nan ta saka katin data siya ta kira Hauwa kuma tayi sa a ta ɗauka, shine ta samu damar faɗa mata maganganun da suka ƙara hautsina Hauwa ta dinga sakin magana, lokacin da ta gama wayar ta saki shewa cike da tsantsar farin ciki Nafeesa ma tana dariya ta miƙa mata hannu suka tafa tace. Ƙawata saura kiris ki samu Aminu a hannunki domin kayanki ya tsinke a gidin gaba, dan naga kin zurata ta hau ta zauna har da cewa ai babu haramci dan kin auresa, ga dukkan alamu ta yaba da ke Najwa kinga sauran aiki ita zata ƙarasa miki, yanzu abu na gaba shine ki riƙa kai mata ziyara akai akai kina riƙe ɗan tsaraba, ke ko omo ne ki kai mata, wlh zaki ƙara shiga zuciyarta sosai taji duk duniya babu wacce ta dace da kaninta sai ke. Bari kawai Feena har wani gumi nake ji saboda tsabar farin ciki da nake ciki, kuma wlh ban taɓa tunanin maganar dana faɗa zai yi tasiri a zuciyarta ba, ko da yake me niman kuka ne aka jifeshi da kashi. Ai in zani gidan sai kin ƙara bani haske akan maganganun da zan je mata dashi, sannan san siya wani abu na kai mata, amma kawata ya zanyi da Zaidu.? Cewar Najwa tana riƙe haɓa, Nafeesa ta kalleta tayi 'yar dariya. Malama ta inda aka hau tanan ake sauka, ki cika masa iska ya ƙara gaba dan kuwa bakin rijiya ba gurin wasan yaro bane, a yanzu akwai tazara a tsakaninku ke ba matar yaro ba ce. Kuma ni kin san tunanina nafi son 'yar uwarsa ta fita daga gidan kafin ki shiga ta yadda zaki sakata ki wala ba ruwanki da matsalar kishiya, dan kin san fa zaku buga da ita tunda aure ne na cin amana za kiyi, to gwara ayi mata me gabaɗaya ta ƙara gaba kema ki zuba naki 'ya'yan ki cike gida Hajiyata. Itama Hauwa baki ji abinda tace bane, so suke ta bar gidan fa, dan haka dole ne zan ƙara iza wutar ƙiyayyarsu akanta yadda zasu haɗo mata bama-bamai tayi checking out wlh ta bani guri. Sai suka tafa suna dariya daga haka suka fito daga ajin suka wuce asalin ajinsu suka shiga, a yanzu tunda ta sakawa kanta masifar soyaygar cin amana ko haddar bata iya haɗawa ta kai, ta shiriri ce ko da tazo sai dai taga ana kaiwa, amma ita tunanin Aminu data kwallafawa ranta ya hanata ta yi bitar karatun balle ta yi yunkurin kai haddar, Nafeesa dai tana kai nata tunda ita ba tada wata damuwa dan kuwa tana da wanda zata aura, jira ake ya fito daga short service daya shiga na NDA ayi bikinsu. Bayan an tashi daga makaranta ne, Najwa tana cikin napep zata gida sai wayar Ikram ta shigo tana kiranta, ta ɗauka da sauri dan tasan wani labarin zata samu, nan Ikram take faɗa mata an samu shaiɗanin daya ɗauki videon faɗarsu ta jiya an yaɗa a special media wanda har hakan yasa Aminu zai zo kaduna saboda zai yi magana da 'yan uwansa, ya jawa su Hauwa layi da iyalinsa dan yasan duk sharrinsu ne suka yi haka. Najwa jin Aminu zai shigo gari yasa ta ji wani farin cikin ya lulluɓe bargon zuciyarta tana sakin murmushin ba zata, tace cikin zaƙuwa. Aiko gani nan zuwa yanzun muka tashi a makaranta, ashe sharrin da suka kuma jifanta da shi kenan, amma naji daɗi da Aminu zai zo ya ci musu, ai gwara ya nuna musu yana son matarsa. Ke dai bari wlh abin da ciwo, mutane sai kiranta suke yi suna jajantawa, in dai haka ake dangin miji to Allah ya wadaransu ya rabamu da sharrinsu muma ba muyi aure ba. Ameen 'yar uwa ina tafe In Sha Allah yanzu. Yauwa gwara ki zo dama zan miki maganar yaya Zaidu, haba Najwa ya kike so ki watsa mana ƙasa a ido, karki yi mana haka mana, muna farin ciki zumunci zai tkara ƙarfi. Ke ni rabani da wani maganar yaya Zaidu wlh ni tuni na canja sheƙa bana yayinta dan wuciyar rakumi yayi nesa da ƙasa, na samu wanda zai saka ni a farin ciki kamar yadda Anty Sameeha take cikin daula dumu dumu har kuma ku zo kuci arziki. Ahaf ai dama na faɗa, wahalar da kansa yake dan nasan halinki da shegen kwaɗayi da buri, to wlh ɓata masa lokaci da kika yi Allah ya isansa shegiya mayyar kuɗi. Cewar Ikram tana kaiwa nan ta kashe wayarta cike da takaicin Najwa tare da ƙudurta zagin da zata yi mata in ta ƙaraso, dan sai ta yi mata wankin babbar bargo, Ita kuma Najwa dariya ta saki tana jin daɗin ta samu hanyar da zata aika sakonta ga Zaidu cikin sauki, dan dama tun da ta rabu da Nafeesa take tunanin yadda zata yarda kwallon mangoro ta huta da ƙuda, sai gashi Allah ya kawo mata hanya mafi sauƙi da zata isar da saƙonta. Ba ƙaramin alfahari da Nafeesa take yi ba tare da farin cikin zamowarta aminiyarta, ashe can da kanta a murfi yafe sai yanzu da Nafeesa ta wayar mata da kai ta gane da ta tafkawa kanta babban kuskure ta cucu kanta abanza, dan bata ganin zata tsinci wani abin arziki a aurenta da Zaidu, dan shima cima zaune ne bai koshi ba balle ya kosar da ita. Ta sauke ajiyar zuciya ta cewa mai napep ya wuce da ita unguwar dosa 'yan majalisu zata ƙara masa kuɗinsa, mai napep yace to kana suka cigaba da tafiya ita kuma ta kira wayar Hauwa, bata ɗauka ba sai ta tura mata da saƙo kamar haka. _Yaya Hauwa an samu wani ya ɗauki video ɗin faɗarku na jiya ya saka a social media ana ta zagin Sameeha, yanzu haka Aminu yana hanyar zuwa Kaduna da yace kune kuka yiwa matarsa haka kuma zai ja muku layi a tsakaninku, dan haka sai ki shirya maganar da zaki yi dasu, yanzu Ikram ta kira ni take faɗa mini shiyasa na Kira in sanar dake._ Sai ta tura mata, tana sakin wani shu'umin murmushi dan bata taɓa zaton videon zai yi mata aiki ba har haka, sai gashi ya jawo mata masoyinta zata samu damar yin rozali da shi, ita kuwa babu abinda zata sakawa Nafeesa dashi face Addu'ar gamawa lafiya dan gabaɗaya duk wannan shirinta ne, kai ilimi akwai daɗi dole ne itama in tayi aure ta koma makarantar boko ta ƙara wayewa dan akwai bambanci sosai da wayewar boko da ta islamiya, gashi dai in ilimin addini ne tafi Nafeesa amma kuma ita ta fita wayewa saboda tayi boko sama da secondary. Da tunani barkatai suka isa gidan Sameeha lokacin karfe biyu saura. Lokacin da Hauwa ta idar da sallah ta ɗauki wayarta taga miscall din Najwa sai ta duba sakon data tura mata, tana gama karantawa ta miƙe a zabure tana salati, tare da sanyawa Najwa albarka dan tasan in ba ita ba babu yadda zata san da wannan ƙulli da aka shirya musu, ga babu kowa a godan balle ta tambaya ko sunga videon ko tasa su bincika mata a facebook, kiran Laure tayi a waya bugu ɗaya ta ɗauka ta shelenta mata sakon Najwa, Laure ta saki murmushin takaici. Yo ke ce baki sani ba amma tun ɗazu Sa'a ta nuna mini a wayarta, yanzun nan Alhasan ya gama balbalin bala'i a gidanmu ya fita, yace kuma Aminu yana hanya in ya ƙaraso zasu kira ki kizo ayi wacce za a yi. Wlh ya zo ɗin gabaɗayansu ina dai-dai dasu, akan Sameeha babu wanda ya isa ya faɗa mini magana inyi shuru in kyalesu, idan ta gama dasu to ni bata gama dani ba kuma wlh zanyi maganin Aminu na yiwa rufkar hanci. Hmmm dama ina shirin in kiraki in faɗa miki sai ga kiranki, amma wannan yarinya ta zame mana babban CID, ke ni banga amfanin wannan 'yar aiki Jamila ba wlh, tunda har yau ba wani labari data kawo mana mai daɗi irin wannan. Saki layinta Laure, ni dai wannan yarinya zan tsaya tsayin daka sai ta auri Aminu dan wlh itace ta dace da shi, ba ƙaramin biyayya zata yi mana ba, zan shiga in fita har sai hakkarmu ta cimm ruwa koda kuwa kuɗina zai ƙare. Jamila kuma akwai lokacin da zata yi mana amfani. Hmmm Allah ya kaimu anjima muga wainar da za a kashe. Ameen, a tsakanin ni dasu shege ka fasa, ke ni duk wanda ya ɗauki video nan Allah yayi masa abarka, ai ba sharri aka mata ba halinta ne aka bayyanawa duniya, kuma kaɗan ma ta gani, In Sha Allah sai Aminu yayi mata saki uku ta fita daga gidan cikin damuwa da dana sani. Allah ya amsa bakinki Hauwa. Hauwa tace Amin ta kashe wayar da har mtn sunyi mata warning kuɗinta saura minti ɗaya ya ƙare, Hauwa ta cigaba da zagaye ɗakinta tana cizon yatsa da gyada kai, tare da ayyana irin bala'in da zata sauke sumu in dai suka kawo mata wargi, dan wlh ba zata taɓa yarda a yi mata cin kashi ba a dalilin Sameeha, ƙaramar hauka zata yi musu ayi uwar watsi. *Afwan biki muke ta fama da shi.* [7/7, 13:04] Buhainat😁: *ABIN DA CIWO* Na ©Rahma Kabir MrsMG. Wattpad @rahmakabir Page 12. Ikram. Ta zauna a cushing tana cika tana bacewa dan sosai Najwa ta ɓata mata rai da maganar banzan da tayi mata aka Zaidu, Sameeba ta fito daga kitchen da plate a hannuta na abinci ta zauna tana kallon Ikram. Lafiya na ganki a fusace kamar kububuwa, da waye kika yi waya yanzu? Da Najwa ce, tana niman raina wa mutane hankali. Nan ta kwashe komai ta faɗa mata, Sameeha tayi murmushi tana cewa. To meye abin ɗaga hankali, ai gwara da ta nuna halinta tun yanzu akan sai nan gaba bayan an saka biki ko anyi auren tace bata yi zumunci ya samu matsala. Amm anty ɓata masa lokacin da tayi fa, da irin hidimar da yake ta yi mata ya tashi a banza. Bai tashi a banza ba in dai domin Allah ya yi mata to yana da ladansa. Kuma dan Allah ko tazo karki mata maganar, ki bari muji da abinda ke gabanmu. To ni sai yanzu nake tunanin zuwan me zata yi ma? Ta nuna bata yi da ɗan uwanmu wani cigaba zata yi da hurɗa damu, shegiya sai baƙar kwaɗayi, gwara tun wuri ki taka mata burki dan bana son wannan zaryar da take yi miki a gida. A'a Ikram bana son irin wannan maganar ko ba soyayya a tsakaninta da Zaidu, ita 'yar uwarmu ce da bamu isa mu yakiceta ba, sannan ni ba zata taɓa gundurata ba tunda abinci kashi ne, tazo ta ci ta tafi ina ce shine dai damuwarki?. Ikram kwafa tayi ta miƙe tana magana ƙasa ƙasa dan gabaɗaya takaici ya cika mata zuciya, gana su Hauwa ga kuma Najwa da ta kara mata, Sameeha da guntun murmushi ta bita, sam Ikram ba tada haƙuri ana mata abu take nunawa har ma tayi faɗa akai, saɓanin ita da take danne damuwa a zuciyarta sai dai yayi ta cinta bata iya ramawa, sai dai zuwa yanzu dole zata koyi fitar da damuwa dan taga in tana yiwa su Hauwa shuru shuru to zasu kaita su baro ne, ta san su ba irin wanda za ana yiwa kawaici bane. Tana cikin cin taliyar data dafa musu jelof ɗin man gyaɗa da kifi, Najwa ta shigo da sallama fuska sake Sameeha ta tarbeta har ta ƙaraso ciki ta zauna suka gaisa, Sameeha tace. Tashi ki shiga kitchen ki ɗibo abinci dan naga daga makaranta kike, hala ko gida baki isa ba.? Hmmm maganar da Ikram ta faɗa mini yasa na fasa zuwa gida na tawo nan, amma na sanar da inna a waya na wuto gidanki. Anty Allah ya shiga tsakaninki da mutanen nan amma sam basa sonki da alkhairi. Aniyar kowa zata bishi. Amm yaya Aminu bai ƙaraso ba? Tukuna dan sai ya kai la'asar tunda jirgin ƙarfe biyu ne kuma atleast sai sunyi awa biyu da mintuna a hanya. Najwa tace Allah ya kawo shi lafiya sai ta miƙe ta wuce kitchen dan ta ɗiba abinci, Sameeha tace amin ta cigaba da cin abincinta dan bata yarda damuwa yana hanata cin abinci ba. Najwa ta zuba abinci mai mata ta fito ta zauna tana ci ba jimawa sai ga tikram ta fito daga ɗaki tare da su Abi tana kallon Najwa ta kawar da kai taƙi yi mata magana, Najwa kuwa ta taɓe baki taki kulata haka suka cigaba da zaman falon ko wanne da abin da yake saƙawa har suka kammala cin abincin suka cigaba da kallo. Wajen ƙarfe uku saura sai ga Zaidu ya zo gidan saboda Ikram ta kirashi ta faɗa masa sakon Najwa ta kuma sanar da shi ta zo gidan, shiyasa yace bari yazo suyi magana ta faɗa masa baki da baki ba zata aure shi ba. Najwa tana ganinsa tasha jinin jikinta domin har ga Allah bata shiryawa haɗuwa da shi ba sai komai ya koranye, amma ta san duk shirin Ikram ne ta kirashi yazo, haka ta haɗe fuska kamar an kashe mata wani dan dole zata kwaci kanta ba zata yarda su liƙa mata shi dole ba dan an wuce auren tilas yanzu, sai da ya gama gaisawa da Sameeha yayi mata jajen abin da ya faru kana ya kalli inda Najwa take zaune tana cika tana batsewa, yace cikin danne zuciyarsa. Hajiya Najwa ba magana ne ko dai sakon da kika bawa Ikram da gaske ne, dan ban gamsu ba shiyasa na zo da kaina naji laifin me nayi dana cancanci haka. Ai ba se kayi laifi ba zan ce bana yin auren, kawai dai na hanga na duba naga baka cika sharuɗɗan mijin daya dace na aura bane, tunda har yanzu baka shiryawa aurena ba, ni kuma aure nake son yi kuma da wanda ya dace. Yanzu nine ban shirya aure ba haka muka yi dake? Meye aibi na kuma? Ina ce ke kika tsaidani kan batun turowa. Eh saboda baka samu aiki ba kuma bana tunanin shagon daka buɗe zai riƙe mu. Najwa duk me ya kawo wannan maganar? kin mance komai yin Allah ne, tunda ni naji nace zan iya sai ki zuba ido kiga na kasa ɗin kafin ki yanke mini hukunci. Hmmmm ai wlh yaya Zaidu dama Najwa can ba sonka take yi ba yaudararka take yi tunda ba tun yanzu ba nasanta da shegen buri, ka rabu da ita kawai ga matanan da yawa a gari masu tarbiyya sai ka zaɓa zaka aura. Cewar Ikram data ƙara kuluwa da maganganun Najwa, Sameeha ce ta nuna ta da yatse ta ce ta wuce su tafi cikin bedroom karta sake jin bakinta, itama ta miƙe ta tasa keyar su Abi dan ba zata saka baki ba tunda ta kula Najwan ba mutunci ne da ita ba kar tace ma sunyi mata taron dangi, ba su kai ga shiga ciki ba suka tsinkayi maganar ta tana cewa da ƙarfi. Ai da kin rabu da ita ina daidai da zamaninta, kuma aurensa ɗin ne bazan yi ba dan ba aji na bane idan kinji haushi ki rufe ido ki aureshi, 'yar rainin wayo kawai, ina da dalilin da zan rabu dashi tunda bai cika sharuɗɗan mijin daya dace na aura ba, shiyasa tun wuri na fito na faɗa dan kar abu yayi nisa ace nayi yaudara. Tana gama faɗar haka ta wuce fuuu kamar guguwa cike da borin kunya dan dama da hauka ake nadeta. Zaidu da ido ya bita dan ya kasa magana haka suma su Sameeha da ido suka rakata har ta fice daga falon, sai duka dawo suka zauna Ikram sai zuba masifa take yi Sameeba tace. Dan Allah ya isa haka tunda wacce kike yi dominta ta tafi, kai kuma yaya Zaidu dan Allah ka rabu da ita a cigaba da mutunci, nasan dai abin da ciwo amma haka zaka danne dan tazo da yaudara amma kanta ta cuta. Ai Sameeha kamar yadda ɗa yake barin cikin uwarsa to na rabu da ita har abada, ban taɓa tunanin Najwa zata yi mini haka ba ashe ba tada mutunci a gabanku take faɗa mini magana ko kimata bata gani ba, da in aure ta ina dana sani gwara na haƙura kuma zata haɗu da daidai ita duniya ce. Kayi hakuri yaya kuma Allah ya baka ta gari. Cewar Sameeha. Ameen amma bani ba ƙara niman 'yar danginmu, ke na aje niman aure har zuwa nan gaba na nima kuɗi dan 'yan matan yanzu ido a kuɗi ne in ba kada Naira ba a yi da kai. Ba duka aka zama ɗaya ba wlh yaya akwai nagari suna nan suna jiran mazan aure, dan nima kaga ba ruwana da buri da son duniya ko anty Sameeha Allah ne ya kawo mata Aminu ta aureshi kuma suna tare ne har dukiyarsa ta bunƙasa. Cewar Ikram, nan suka cigaba da tattaunawa har aka kira sallar la'asar Zaidu yayi musu sallama ya wuce gida zuciyarsa a jagule saboda ya rasa Najwa duk da yana yiwa Allah godiya data bayyana masa zahirin yadda ta ɗauke shi. Koda ya isa gida ya faɗawa Umma komai, cewa tayi Alkhairi ne rabuwarsu kuma Allah ya zaɓa masa nagari dama tana ta addu'a akai to rabuwan shine mafita dan itama tayi mamakin kalaman Najwa zata yi kokari tayi magana da inna su tsawatar mata inda miji ma ta fito dashi su aurar da ita dan alamunta ya nuna ta fara sauka daga tarbiyyar da suka bata, wataƙila ta samu sabbin kawaye masu hure mata kunne ko kuma saurayin da yake kokarin sauya mara tarbiyyarta. Wajen biyar saura Aminu ya shigo gidan, ruwa kawai yasha yace Sameeha ta miƙe ta ɗauko mayafi su tafi babban gida dan sun gama haɗuwa su suke jira, Sameeha hijab ta ɗauko ta zumbula ta fito suka wuce a motarta dan nashi motar ya saka driver ya wanke masa ita, suka bar yaran a gida tare da Ikram. *Yau gidan biki har biyu naje ban samu zama ba kuyi hakuri da wannan In Sha Allah zaku samu mai yawa gobe In Allah ya kai mu* [7/7, 13:04] Buhainat😁: *ABIN DA CIWO* Na ©Rahma Kabir MrsMG. Wattpad @rahmakabir Page 13. Babban Gida. Su Aminu suna isa suka tadda mutanen gidan a asalin part ɗin iyayensu, wanda suke rufe shi sai in wani abu muhimmi ko kuma sha'ani suke buɗewa, bayan sun zauna a katon kafet daya malale ɗakin dan babu kujeru, suka gaggaisa tare da ɗan taɓa hira kafin Alhasan ya koro bayanin musabbabin haɗuwarsu, yayi dogon sharhi tare da jan kunne da kuma nasiha akan muhimmancin zumunci da kuma haɗin kan junansu, daya ja fasali sai Kamalu shima ya ɗauka yayi nashi bayanin daga bisani suka bawa Laure damar magana buɗar bakinta sai cewa tayi. Duk wannan dogon bayanin banji kun yiwa Sameeha faɗa ba, domin duk ita ce musabbabin faruwan waɗannan abubuwan, kuma naji kuna ta zancen mune muka saka aka ɗauki video dan mu tozarta ta, haba haba ai da hankakinmu zamu yi mata haka ba, sai kace dama muna shirye da faɗan data kawo da kanta, gaskiya ba kuyi mana adalci ba dan bamu san komai akan maganar video ba. Laure ba mun taru bane dan mayar da magana, ko ku amsa laifinku ko karku amsa kune ba kuda gaskiya, kuma mun taru ne a nan domin mu kawo sulhu a tsakaninku, ku yafi juna komai ya wuce. Cewar Alhasan, a lokacin Aminu yayi gyaran murya ya soma magana. Ba tun yau ba suka ɗauki karan tsana suka ɗaurawa Sameeha ina sane da haka amma nake kawar da kai, sai dai gaskiya haƙuri na ya fara ƙarewa, ace duk rikicinku bai tsaya a nan har sai kunyi shela da matata a duniya tare da zagi da Kasafi, wannan dalilin yasa na baro duk abinda nake yi nazo gareku domin a kawo karshen rikicin nan, gaku ga Sameeha ku faɗi abinda take yi muku da kuka sakata a gaba. To ance maka wani abu tayi mana, me ko zata mana tunda ka zama sallamamme a gunta, sai abinda ta kitsama zaka zo kana yiwa mutane ɓaɓatu, iye Aminu gaka mai mata, da fatan ka tambayeta rashi mutuncin data yi mana a gidanku, har da cewa ba zata buɗe mana ɗakuna mu gani ba saboda gamu ɓarayi kar muyi muku sata, to kusha kuruminku ni dai in taka ƙafata inje gidanka sai in Sameeha bata nan dan kar in je tace nayi mata wani abin. Amma yaya Hauwa wannan ba magana bace, karki wasa da damarki dan Wlh in kika bari girmanki ya zube a idona ba zamu kwashe ta daɗi ba, tunda ba haifata kika yi ba da zaki rika iko dani dududu shekara biyu kika girme mini, ina kokarin baki girmanki kuma.... Kai Aminu ka daina wannan maganar bana son haka, anzo nan a sulhunta ne ba a yi rikici ba. Cewar Kamalu, Hauwa ta ce cikin faɗa. Ka barshi ya nuna min ni banda mutunci a idon matarsa taji daɗin raina ni, ko da yake ma ta gama raina ni ɗin tunda bata ɗauke ni a bakin komai ba, to wlh in ita ta shanyeka ni bata isa ba kuma mun barka da ita. Hauwa bana son sakarci ba hayaniya na kira muyi ba, yanzu dai ko wanne yayi hakuri ya mayar da fushinsa, ke Sameeha kiyi hakuri kuma ina so ki basu haƙuri idan da da akwai abinda kika yi wanda baki sani ba, in dai hakan zai kawo maslaha tunda ke ce ƙarama. Haba yaya ita da aka muzgunawa itace kuma zata basu haƙuri, ku duba wannan lamarin fa, a gaskiya ni ban kawota dan ku danne mata hakki ba, sune ya dace su bata haƙuri domin kowa ya san gaskiya a bayyane take, yaya Hauwa itace shugabar kawo rikici kuma saboda sun rainata har Adama ta iya saka baki tana gayawa Sameeha magana bata iya tsawatar mata ba, to ni ina son matata kuma nasan halinta ba mai son rikici bace tsawon shekara goma da nayi na ita nasan wacece ita, dan haka Sameeha tashi mu wuce kuma In Sha Allah gobe zamu bar garin nan gabaɗaya sai in sun ganta su nemi ci mata mutunci. Yana kaiwa nan a maganarsa ya miƙe a fusace dan sosai ransa ya ƙara ɓaci, Kamalu yace cikin faɗa. Ya zaka ce haka, kana so ka nuna mana mu bamu isa da kai ba ko, to tunda mu ba muda muntunci sai ka tafi ɗin. Gwara dai ya nuna muku Sameeha ta gama da shi, in ba haka ba yana cikin hayyacinsa ne zai gaɗi maganganu son ransa saboda mace. Cewar Hauwa, Aminu yanuna ta da yatsa. Idan kika kuma faɗin magana mara daɗi akan matata wlh saina ɗauki mataki, domin na kula kin yarda girmanki kare yaci. Ni zaka faɗawa haka? dan ubanka kama isa ka riƙa fada mini magana haka, mace tana son raba mana zumunci kace kar ayi magana, ni kake dagawa yatsa saboda tsinanniyar matarka... Ni ba tsinanniya bace wlh, Abban Amrah mu tafi kawai dan banga alamar za a yi sulhu a nan ba. Cewar Sameeha a fusace data miƙe ta kama hannun Aminu ta soma janshi, su Alhasan suna cewa su tsaya amma ina sunyi gaba, Hauwa tace cikin ɗaga murya. Taya zai tsaya ya zama jani talau, uwarsa ta bashi umarni ya kama kai ya tafi, Allah ya waranki Sameeha, yadda kike niman bata mana zumunci Allah ya mayar miki da aniyarki, matsiyaciya har gidan ƙananan mutane... A fusace suka ga Aminu ya dawo ya isa kan Hauwa ya daga hannu zai kifa mata mari, Yaya Kamalu yayi saurin tare shi ya fizgo hannunshi ya sauke masa mari a kuncinsa, Aminu ya dafe kunne yana dubansu. Alhasan yace cikin ɓacin rai. Allah ya kyauta, Aminu kayi matuƙar bani mamaki ba haka su Abba da umma suka tarbiyyantar damu ba, ke kuma Hauwa kece musabbabin komai saboda kin mayar damu 'yan iska bamu isa dake ba, shiyasa gashi ba aje ko ina ba Aminu yana niman raina ki, kuma da gaskiyarsa dan babu wanda za aci zarafin iyalinsa bai ji haushi ba, dan haka ki fita idanuna kafin in yi miki wulaƙanci. Shikenan yaya ba za a fadi gaskiya ba zaku yi mini taron dangi, yau ni har Aminu yake niman marina saboda mace.. Hauwa ta ƙare maganar tana fashewa da kuka, Aminu bai iya cewa komai ba face hakuri daya basu ya juya ya fice daga falon idonsa yayi jajir saboda ɓacin rai, shi mutum ne mai zuciya amma kafin yayi shi sai an kai goro an kai bari. Su Alhasan gabaɗaya suka mayar da fushinsu akan Hauwa, suka yi mata tas tare da tunatar da ita gabaɗayansu arzikin Aminu suke ci, banda Allah yasa shi mai tausayine da dukkansu suna cikin halin rayuwa, koda yaushe cikin yi musu hidima yake bai taɓa gazawaba, dan haka bai cancanci haka daga gunta ba dole ta sauke girmanta suje har gida su bashi hakuri domin shi aka yiwa laifi kuma akan gaskiya yake saboda ita Hauwa ta kasa riƙe girmanta, sannan tayi amfani da kausasan maganar da ya ƙara fusata Aminun har ya nima marinta, suka koma kan matansu suma suka yi musu kaca kaca sai da suka basu haƙuri, kafin suka sauko kana suka ce bayan sallar magrib zasu je gidan Aminu domin ayi sulhu, Hauwa dai dole suka yi mata amma ason ranta ba inda zata, tsana da kuma kiyayyar Sameeha ya ninku a zuciyarsu ita da Laure dan sosai suke jin zasu iya komai dan su fitar da ita a gidan Aminu. **** Sameeha. Koda suka fita Sameeha ce taja motar suka koma gida. Suna isa ya wuce falonsa ta bishi a baya tana lallashinsa, hawayen da yake dannewa ne ya sauka akuncinsa yayi saurin shafewa yana yawq cikin dakiya. Ina so ki haɗa kayanku na sawa da komai na amfaninku gobe In Sha Allah zamu bar Kaduna. To tace masa ta miƙe ta fita dan itama ta gama yankewa gwara ta bishi saboda hakan ne kaɗai zai kawo karshen rikicinta dasu, tana son mijinta tana kuma son farin cikinsa ba zata cigaba da biyewa 'yan uwansa ba su kawo musu tasgaro a cikin zamansu ba. Ta samu Ikram a ɗakinta ta bata labarin abin da ya faru, jikin Ikram a sanyaye tace. Gwara ki bishi kawai komai ya zo karshe, dan babu amfanin baɗi ba rai, tunda su Hauwa ba zasu fasa ba sun riga sun tsaneki, Allah ya shiga tsakaninki dasu, sai ki dage da addu'a, bari na tayaki baɗa kayan su Abi. Tana gama faɗar haka ta fice ta wuce ɗakin Amrah ta fara haɗa mata kaya. Sameeha zama tayi a bakin gado ta rafka tagumi, itama ranta a ɓace yake, ta shiga tunanin me ta yiwa Hauwa da zafi haka data cancanci wannan natsar, wayarta ce ta yi ƙara ta duba taga Umma ce ta kirata, ta ɗauka cikin sanyin murya, kamar tana jira umma ta tambaya lafiya? Sai ta fashe mata da kuka tana bata labarin abinda ya faru, Umma tace cikin lallashi. Kiyi hakuri ki barwa Allah, ke dai dangin Aminu sune jarabawarki, kuma ma dole su tsaneki tunda kina cikin wadatar da suka kasa danne hassadarsu, dan haka ki tattara kibi mijinki kamar yadda ya faɗa, ai da nan da Abuja baki da hanci ne ko a rana guda zaki zo ki koma, Allah ya shiga tsakaninki da sharrinsu, kuma ki dage da addu'a kina yawan sadaka dan wallahi ki guji mutumin daya nuna miki ƙiyayya kiri kiri, dan bai ki ace kin mutu ba. Nan dai ta dinga bata baki har ta samu natsuwa tace mata anjima bayan Sallar isha'i zasu kawo Ikram gida daga nan suyi sallama tunda yace jirgin kasa na safe zasu bi, daga haka suka yi sallama. Sai ta miƙe ta soma haɗa kayanta tana jin wani sanyi a ranta akan maganganun da umma tayi mata, itama sai yanzu daga dacewar ta matsa kusa da mijinta su cigaba da rayuwa, dan ta san in tana nan ba zasu taɓa barinta ta samu sukuni ba. Ana yin sallar magrib su Kamalu suka haɗu suka tawo gidan Aminu, da suka iso kofar gate suka yi parking Sai duk suka fito, Sa'a ta buga gate mai gadi ya buɗe musu sai suka shiga ciki. Koda suka isa falon sun murɗa handle suka ji a rufe sai suka buga Ikram da take falon taje ta buɗe, tana ganin sune ta juya ta koma ciki ta shiga falon Aminu ta sanar dasu zuwansu sai ta fito ta gaishesu ta koma ɗakin Abi da shi ya rage ta gama haɗawa kaya, su Aminu suka fito suka ƙara gaisawa kamar ba komai, nan dai Alhasan ya shiga basu haƙuri kana ya cigaba da yi musu nasiha wanda yasa duk jikinsu yayi sanyi, dan shi kam Allah ya bashi baiwar iya magana gashi da ilimi Masha Allah, nan suka haɗu suka yafi juna Hauwa har da kukan munafurci tana niman gafarar Sameeha tare da basu hakuri, Aminu yace komai ya wuce haka itama Sameeha tace ta yafe, sai kuma suka ɓuge da hira, kiran Sallar Isha'i ne yasa mazan suka fita masallacin kusa da gidan dan suyi sallah, su kuma su Hauwa Sameeha tayi musu jagora zuwa ɗakinta dan suyi nasu sallar a nan, sai ta fito ta basu guri, nan fa suka shiga kashe kwarkwatan ido suna magana ƙasa ƙasa tare da zungura baki akan maƙudan kuɗin da aka kashe a ɗakin, dan hatta bayinta abin kallo ne dan duk sai da suka leka ko ina, da suka idar ne suka dawo falo dama Sameeha tasa Ikram ta dafa jelof ɗin kuskus da soyayyar kaza tsaf tsaf dan zu ci, da su Aminu suka dawo ne suka gabatar musu da abinci dinning su mazan suka ci akai, matan suka ci a nan carpet ɗin falon, bayan sun kammala ne suka yi bankwana dan Aminu ya tabbatar musu da tafiyarsu ba fashi gobe In Allah ga kaimu, basu ja ba dan basa so su tauye shi. Har gate suka yi musu rakiya suka wuce kana suka jero Aminu na cewa. Ko dai zaki zauna ɗin tunda naga komai ya daidaita kuma dama ba son zaman Abuja kike yi ba. Ƙafata ƙafarka dan gwara na bika nima hankalina zai fi kwanciya. Su Meehan Aminu masu miji, ko dai ko dai kinyi tunanin kar na samu wata a can ta ɗauke mini hankali. Haba dai Mijin Meeha dan ita kaɗai aka yi shi ehe... Sameeha ta faɗa cikin walwala da farin ciki haka suka shiga falon, sai da suka natsa kafin suka kai Ikram gida suka gaisa da Umma kana suka yi musu sallama umma tasa musu albarka tare da basu shawarwari wanda zai inganta rayuwarsu, da suka tashi tafiya umma sai da ta keɓe da Sameeha ta ƙara yi mata magana musu daɗi da kuma tunatar da ita wasu abubuwa, kafin suka fito Aminu ya aje musu bandir ɗin 'yan dubu ɗai ɗai wanda ya kama dubu ɗari, kafin suka fito suka shiga mota suka dawo gida, a ranar dai sunyi kwanan farin ciki da jin tamkar duk matsalarsu ta yaye an samu kyakkyawar maslaha da fahimta. *** Hauwa. Koda suka sauketa a kofar gida tsayawa tayi a zaure bata shiga ciki ba, sai ta riƙa lekensu har suka shigar da motarsu cikin gidansu kafin ta fito ta tari napep ta wuce unguwar kanawa gidan malam mai allon ƙarfe, dan ba zata iya hakurcewa safiya ba yadda zuciyarta ke azalzala mata, tsantsar baƙin cikin barinsu Aminu Kaduna ya kainainaye zuciyarta, har wani ɗaci ɗaci take ji in ta haɗiye miyau. Da suka isa sai ta sallami mai nalep dan har kofar gidan ya kaita tunda malamin ba ɓoyayye bane, ta aika wani yaro data gani ƙofar gidan ya sallamo mata malam, ba jimawa yaron ya fito yace Malam yace ta shiga ɗakinsa na zaure gashinan zuwa, Hauwa ta miƙawa yaron naira goma ta shiga zauren zuwa ɗakin, ta tura ta shiga ba kowa sai tarkacen kayan aikin malinta, ba jimawa sai ga Malam ya shigo da sallama ya isa mazauninsa ya zauna yana ƙare mata kallo da idanunsa daya sha baƙin kwalli, Hauwa ta gaishe shi ya amsa fuska sake dan ya wayi fuskarta tunda ba yanzu ne farkon zuwanta gunsa ba. In ban mance sunan ba Hauwa ko? Eh ita ce, ashe ba zaka manta dani ba. Ina zan manta dake, ko ba kece kika zo amsar mallakar miji ba da kuma 'yarki da ta samu matsala da miji aka yi miki maganinsa. Kwarai nice. Hauwa ta fada tana murmushi tare da gyara zamanta dan ta ji daɗin koro masa bayani. [7/7, 13:04] Buhainat😁: *ABIN DA CIWO* Na ©Rahma Kabir MrsMG. Wattpad @rahmakabir Page 14. Malam mai allon ƙarfe ya kalli Hauwa da kyau yana cewa. Yau ma na san wani dalilin ya kawo ki dan haka ina saurarenki ko zan iya yi miki maganin damuwar ki. Yauwa Malam wlh wani babban abune ya kawo ni gunka wanda zan iya kashe ko nawa ne domin buƙata ta biya. Matar ƙanina ne ta sakomu a gaba shi ne nake so a datse igiyar aurenta yayi mata saki uku a wulaƙance. Ya sunanta kuma shima ƙanin naki ya sunanshi? Sunanta Sameeha shi kuma Aminu. Bari na kafe sunansu a allon ƙarfe muga amsar da zai bamu, sai dai kinsan ni bana ƙarya, duk abinda sakamako ya bani to shi nake faɗawa mutum ko yayi masa daɗi ko kar tayi. Nasani malam ban mance komai ba. Cewar Hauwa tana jinjina kanta, Malam yace yauwa kana ya ɗauki allon karfensa ya soma jawo wasu kalamai tare ɗaura yatsarsa manuniya a kan Allon ya shiga yin rubutu wanda nan take zane ya soma fitowa a jikin allon, sai da ya gama kafin ya ƙurawa Allon ido tamkar yana kallon wani abu a jiki, ya ɗauki minti goma a haka kafin ya yi ajiyar zuciya ya shafe allon da tafin hannunsa ya ajiye shi a gefe, ya dawo da kallonsa gareta ya soma da cewa. A gaskiya matarsa ta Allah ce kuma akwai kyakkyawar tsari a jikinta saboda bata wasa da ibada, dan haka babu wani asiri da zai kamata, sai dai ɗan uwanki zamu iya yin wani abu akansa tunda ba ya tare da tsari, sannan ban hango rabuwa a aurensu ba a yanzu sai dai na hango akwai gargada anan gaba wanda wani duhu ya rufeshi bazan iya sanin ko miye ba. Innalillahi wa inna ilaihit raji'un. To malam ba yadda za ayi a sashi ya ƙara aure. Zan iya amma sai in ya rabu da matarsa. Yanzu babu abinda za a iya yi akai dan a shiga tsakaninsu. Babu gaskiya a nan. Amma zasu yi tafiya gobe ina so a dakatar da tafiyar tasu. Wannan zan iya yi miki aikinsa amma kan ɗan uwanki zai faɗa, shi ne zai dakatar da tafiyar da kansa. Dama shi yace zasu tafi dan ita Sameeha ba so ma take ba, to ba damuwa ayi mini wannan aikin ko tanan na samu nasara kuma ba zan fasa haifar da matsalar da sai ya rabu da ita ba. Dama sai dai in ku zaku yi amfani da wata hanyar da zaku haɗasu har hakan yayi tasirin da zaku raba su, kuma duk inda zaki in dai malamin gaskiya ne to wannan sakamakon zai sanar dake sai dai in yana so yaci kuɗinki ne zai ce ba haka ba. Hauwa tayi jimm tana sauraren zuciyarta, can ta nisa tayi masa godiya tace yayi aikin da zai hana tafiyar, ta kirga dubu takwas daga posa ɗinta ta ajiye masa a gabansa tana cewa. Ga dubu takwas in da ciko sai ka sanar dani in ƙara. Wannan ma yayi tunda ba aiki ne me wuya ba, sai dai zaki ƙara dubu biyu saboda zan yanka kaza na yi hadaya da jininsa. Tace to kana ta ƙara masa dubu biyar tace sauran ya ƙara cefane, malam ya washe baki yana dariya ta mike tana yi masa godiya ta fito guiwa a sanyaye dan ba haka taso ba, kuma kamar yadda ya faɗa mata koda taje gurin wani sai dai yaci kuɗinta tunda tasan aikinsa kamar yankan wuƙa ne. Haka ta dawo gida ta zuba kunne dan jin ta inda labarin fasa tafiyarsu Aminu zai zo mata. *** Aminu. Cikin dare ya farka a barci a gigice yana zufa hankalinsa a matuƙar tashe sai salati yake yi jikinsa yana kakkarwa, cikin barci Sameeha ta ji motsinsa ta farka ta juyo tana dubansa, yadda ta ganshi yasa tayi saurin miƙewa zaune tana dafa kafaɗarsa da cewa. Lafiya meke faruwa? Wani irin mugun mafarki nayi wlh wai kidnapers sun sakawa jirginmu bomb, kuma wai da suka samu nasarar tsaida jirgin duk sun tafi damu zuwa cikin daji, inda suka kashe Abi suka yiwa Amrah Fyaɗe... Da sauri Sameeha ta rufe masa baki tana salati tare da cewa. Kayi shuru haka babu kyau faɗar mugun mafarki, hala kayi mantuwa baka yi addu'a ba ka kwanta. Wlh kuwa ina danna waya barci ya sace ni banyi ba. To sai ka kori shaiɗan ka koma barcinka Allah ya kyauta In Sha Allah ba abinda zai faru sai alkhairi, mugun mafarki daga shaiɗan ne kuma ba gaskiya ba ne. Humm yace mata ya sauya kwanciyarsa zuwa ɓarin dama yayi addu'a ya tofa ya rufe ido, sai dai barci ya ki ɗaukarsa sai tunani da tsoro daya kewaye illahirin zuciyarsa, Sameeha kuwa ta samu barci mai kyau dan sai da aka yi asubahi Aminu ya tasheta akan ta tashi tayi sallah, dan shi kam idonsa biyu aka kira, ya sauka yayi alwala ya wuce masallaci. Wajen ƙarfe bakwai Sameeha tana ta hada hadan fito musu da kaya dan tasan lokacin tafiyarsu yayi, kafin takwas ya kamata su isa wajen shiga jirgin ƙasa, tun da ta tashi tayi sallah ta soma shiri duk suka yi wanka, ta shiga kitchen ta haɗa musu breakfast kafin ta tasa yaran suka karya ita kuma ta nufi ɗakin Aminu, ta sane shi a kwance yana duban sama ta zauna gefen ƙafarsa tana jan yatsunsa, ya sauke ajiyar zuciya ya mayar da kallonsa gareta Sameeha tace. Alhaji naga ko shiryawa baka yi ba kuma kasan ƙarfe takwas da kwata jirgin ke wucewa, gashi har bakwai da minti goma. Madam Meeha tafiyar nan sai nan da wani lokaci gaskiya dan hankalina ya kasa kwanciya da mafarkin da nayi, ni kaɗai zan koma Abuja na soke tafiyar daku sai nan gaba, kuma nima a mota zan koma driver zai jani mu tafi zuwa anjima. Da wani irin kallo Sameeha ta dubeshi fuska a dagule kamar zata fashe da kuka. Haba Abban Amrah sai da muka gama saka rai zamu tafi, duk nabi nayi sallama da mutane meyasa zaka yi mini haka. Kuma fa mafarki ba gaskiya bane, sannan duk wanda ya dogara ga Allah ya isar masa. Na san da haka amma ni dai abinda naga ya dace nayi kenan, kiyi haƙuri nan gaba zan shiryawa zuwanku dama tafiyar ba shiri saboda rikicinku da su Hauwa ne, kuma yanzu naga komai ya daidaita, zan bawa Kamalu kuɗin da zaije ya yiwa su Abi register makaranta In Sha Allah next week nake so su fara zuwa. Yanzu tashi za kiyi ki haɗa mini ruwan wanka me zafi ki zo ki kamani ki kaini bayi kiyi mini wanka na more miki ki samu lada. Ya kare maganar yana 'yar dariya tare da jan hancinta, murmushi tayi masa tana jin idanunta suna cikowa da hawaye tunawa da wani moment da tayi a rayuwarsu, Aminu da yaga yanayinta sai ya tashi zaune yana cewa. Ehen Hajiyar kuka me kuma kika tuna dan nasanki da mugun son soyayya, sai kace daga ƙasar indiya aka kyankyaso ki. Kai fa hala daga turai aka turoka ka faɗo Nigeria baban love. Ta faɗa tana dariya, miƙewa yayi ya yi kamar zai kamota zai ta zille masa suka shiga zagaye falon suna kwasan dariya kamar wasu kananun yara, Aminu yaƙi barin Sameeha har sai da ya kamata ya rungume ta ta baya yana cewa. Har gaban Abada ina kaunarki Meeha ke ce haskena kuma farin cikin rayuwata, da babu ke a duniyata tabbas da babu ni. Allah ya barmu tare mijina ya kuma karemu daga dukkan abin ƙi ya tsole idon makiya, amma kasan ina sonka kuma son da babu gargada ko wasa a ciki, akanka nasan so kuma nasan yadda ake gudanar da tubalin kauna, domin na samu damar yi maka gini a zuciyata wanda duk wuya babu abinda zai sa ya rushe. Na yarda dake matar Aminun Alhaji Ado meyere. Sameeha ta saka dariya shima yasa dariya sai ta zame jikinta ta wuce bedroom ɗinsa dan ta haɗa masa ruwan wanka, cike da tsantsar tausayinta ya bita da kallo har yana jin hawaye suna cika masa ido, yasan Sameeha macece mai matuƙar kirki, hakuri, kawaici da juriya shiyasa ko kaɗan baya son matsawa nesa da ita yana son su kasance a tare har abada mutuwa ce kaɗai yake fatan ya rabasu. Sai ya koma ya zauna ya ɗauki wayarsa ya kira Alhasan ya sanar dashi ya fasa tafiya da Sameeha zasu cigaba da zama dasu, Alhasan yaji daɗin haka domin ya tabbatar da Ƙaninsa ya sauko, haka ma daya kira Kamalu ya ji daɗi bayan sunyi sallama ya kira Hauwa ita jimantawa tayi, dan nunawa tayi da dai ya tafi dasu ko hankula zasu kwanta, yace tunda komai ya wuce zasu cigaba da zama anan kaduna yana son zumunci ya gyaru ya kuma ƙara karfi a tsakaninsu, Hauwa tace Allah yasa hakan shine Alkhairi, yace Amin kana suka yi sallama. Hauwa tunda ta wayi gari take cikin zullumi ta tunanin waye zai sanar da ita fasa tafiyar nasu, haka ta danne ta cigaba da hidimar gidanta sai dai abin yana cinta a zuciya, kuma bata so ta kira kowa dan kar asan da saka hannunta a fasa tafiyar saboda ko Laure ba zata faɗawa ba, zata bar abin a zuciyarta, kiran Aminu yana ɗaya daga cikin abinda ya faranta mata rai a wannan ranar tayi murna tayi shewa ta yi rawa tare da alƙawarin zata je har gidan malam ta yi masa godiya ta ƙara masa wani hasafi dan bukata ta biya, sai dai kuma yanzu ne ya dace ta tashi da yaƙi, dole ne zata nuna komai ya wuce ta fara ɗaura ɗamarar lalata zaman nasu, dan in har Sameeha bata bar gidan Aminu ba to fa ba tada kwanciyar hankali tunda ga malam yace Aminu ba zai taɓa ƙara aure ba sai in Sameeha ta bar gidan, haka ta dinga saƙa da warwara tare da hangen ina mafita. Wajen ƙarfe sha biyu Aminu ya tafi Abuja tare da driver, sun rabu cikin kewa sosai, a lokacin ne Sameeha ta kira Umma ta faɗa mata itama bata so basu tafi tare ba, amma sai tayi musu addu'ar Allah yasa hakan shine alkhairi, umma tace sai ta fara tunanin sana'ar da zata yi dan hakan ne kaɗai zai rage mata damuwa tare da zama busy a hidimar gabanta, sannan ta kara ja mata kunne kar ta riƙa shiga harkan su Hauwa koda kuwa zaginta suka yi kar ta biye musu, tace. Umma ai ni na kara daukar darasi akan su dan haka nayi hankali, kuma ina so na fara kiwon kifi dan ance akwai albarka a ciki kuma akwai lada sosai. Masha Allah hakan kuwa yayi sai kiyi shawara da Aminu duk abinda ya yanke shikenan. Sameeha tace to kana suka dan taɓa hira daga bisani suka yi sallama. *** Najwa. Tunda ta bar gidan Sameeha ta wuce gida rai a ɓace, ta zauna a gefen inna data yi shinfiɗar tabarma a tsakar gida tana zuge zogale ɗanye da baba ya siyo ɗazun a kasuwar sati. Auta naga kin dawo da wuri. Wlh kuwa ai lamarin nasu ne ba daɗi Inna, sam basa kaunar Anty Sameeha. Ni da zata ji shawara da tabi mijinta ta huta da fitinarsu. Haba inna mu kuma da muke zuwa cin arziki aja mana kenan, a'a wlh tayi zamanta tare da yin maganinsu dan ko ta bar garin ba zasu fasa binta da sharri ba. Ke dai kin bani da kwadiya Najwa ashe da biyu kike ma zuwa gidan, to zanja miki layi da zuwa kuwa dan kin san dai Zaidu zaki aura ba zan bari ki gama zubar da mutuncinki ba wlh, dan na kula ke sam ba ki da hankali sai ana yi miki seti kamar tinkiya uwar tambele kike jin kanki. Innaaa! nifa Allah bana jin na dace da auren Zaidu, dan haka zan cigaba da jira har Allah ya fito mimi da miji mai kuɗi, tunda masu hannu da shuni suna son farar mace kuma kinga nima ina da nawa kyan ga fari ga hanci. Baki inna ta saki tana dubanta. Allah inna ni matar manya ce ba ƙanana irin Yaya zaidu ba, ni sai yanzu ma nake ganin wautata dana amsa masa zan aureshi. Aiko wlh baki isa ba, ba zaki sanya naji kunya ba, ɗan yayana zaki ce baki so shifa ya saki nono na kama, haba Najwa ki sake tunani. Aiko in kika matsa mini wlh sai na shiga duniya dan bazan taɓa aurensa ba, hmmm nifa nama fada masa kuma yace ya haƙura. Innalillahi wa inna ilaihir raji'un wannan yarinya kin tona mana asiri, yanzu Zaidun kika cewa kin fasa, shikenan kin ɓata zumunci. Ni ban ɓata zumunci ba inna, ai gwara da tun yanzu ne na faɗa ba sai da aka saka rana ba ko aka ɗaura. Wlh in kika takura mini sai dai ki nime ni ki rasa. Cewar Najwa da ta miƙe tana zumɓuro baki ta shige ɗakinta tana ƙananun magana, inna baki sake ta bita da kallo cike da mamaki da kuma tsoron sauyawarta lokaci guda, dan ba haka halin Najwa yake ba ta rasa me ya sauyata haka, dole ne ta hanata zuwa gidan Sameeha dan zarginta yana bata ganin kayan alatun da take ne yasa ta soma sauyawa da tunanin auren mai kuɗi, damuwarta da wani ido zata kalli Umma Halima akan abinda Najwa tace ta faɗawa Zaidu ta fasa, girgiza kai tayi tana nimawa 'yarta tilo daya shiriya. Da daddafe baba daya dawo, bayan naci abinci ya natsa sai Inna ta koro maza zancen Najwa akan tace ba zata auri Zaidu ba, baba yace ta kirata Inna ta miƙe ta fito ta shiga ɗakinta ta sameta tana amfani da waya wato charting. Ki zo Babanku yana kira. Au inna ƙarata kika kaiwa baba, to wlh duk abinda za kuyi mini sai dai kuyi amma bazan auri Zaidu ba. Inna kasa magana tayi ta fice, Najwa ta miƙe ta fito ta shiga ɗakin baban ta zauna, bana ya dubeta da kyau. Najwa me Zaidu yayi miki da kika fasa aurensa ko so kike muji kunya. Baba dama fa ni ban yi masa alkawarin aure ba, kuma na faɗa masa ya shiga cikin manema ne in da rabonsa shikenan sai ayi dashi, kuma ni wlh bai kwanta mini ba tunda, kawai dai ina yi masa kawaicin ɗan uwa ne, kuma ina ganin ƙila a gaba in yana zuwa zance zan ji ina sonsa, to kuma har yanzu banji komai ba shiyasa na bashi hakuri kawai mu rabu lafiya dan kar gaba na zo na fito da wani yace na yaudareshi. To shikenan ba zan miki dole ba, amma ina so nan da wani lokaci ki cewa wanda kike so ya turo dan bana son tara samarin nan, gwara ki fito da miji ayi auren kowa ya huta. Yanzu malam abinda zaka ce mata kenan? Cewar inna data yi kasake da kai, baba yayi 'yar murmushi. To ya zamu yi Zulai, so kike muyi mata dole rai ya ɓaci, ai tunda ta riga ta sanar da Zaidu magana ta ƙare, kuma In Sha Allah ba abinda zai taɓa zumunci, dan nasan Halima tana da kirki da sanin yakamata. Hakane, Allah yasa mu dace, Najwa hankinki ya kwanta ko. Sosai ma Innataaa. Ta faɗa tana dariya, Inna ta yi kamar zata kai mata hannu Najwa ta miƙe ta fice tana dariya, tare da jin farin cikin ta gama da matsala guda ɗaya, yanzu saura na gaba wato yadda zata auri Aminu. **** BAYAN WATA BIYU. A bubuwa da yawa sun faru ciki harda fara zuwan su Amrah makaranta, kuma zuwa lokacin Sameeha taga sauyi sosai daga dangin mijinta, yanzu basa nuna mata wata tsana ko kyara, tana zuwa gurinsu suma suna zuwa gidanta susha hirar zumunci, musamman yadda bikin Salma ƙanwarsu Aminu ya taso wanda suke saka ran nan da wata guda za ayi shi, hakan yasa duk wani tsare tsaren bikin da Sameeha suke yi dan har kiranta suke taje ayi shawara da ita, sosai hakan yake faranta ran Aminu dan yana da labarin komai saboda Sameeha tana bashi labari, shiyasa shima ya sakar mata bakin aljihunsa sosai dan duk abinda aka nima na maganar kuɗi nan take take badawa, idan kuma fita zasu yi ita ke ɗibarsu a motarta su tafi, haka suke binta kamar raƙumi da akala zuna zuba mata ido, a bayan idonta kuwa su tsine mata dan kuwa ba ƙaramin ƙara mata bakin jini yayi ba, a cewarsu duk son iyawa ne yasa take yi musu haka, ita kuma domin Allah take yi badan komai ba, Hauwa kuwa a ganinta ita ya dace Aminu ya riƙa bawa kuɗi tana aiwatar da komai tunda itace shirin komai ke hannunta. _Zaku iya fara biyan kuɗinku domin muna gab da gama season 1 mu tsunduma a season 2 wanda sai kun biya kuɗinsa kafin zaku cigaba da samun cigaban wannan labarin ɗoɗar har zuwa ƙarshensa. Bononza na kwana biyar akan N300 idan kwanaki biyar ya ƙare In Sha Allah zai koma asalin kuɗinsa N400, dan Allah ku mara mini baya._ Pay N300 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a tura MTN card N300 a 09034940106, masu so ta pc su tura N600. Sai a tura shaidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu. [7/7, 13:04] Buhainat😁: *ABIN DA CIWO* Na ©Rahma Kabir MrsMG. Wattpad @rahmakabir Page 15. Hauwa. Tana zaune a falonta ta miƙe ƙafa tana duba kayan fitan biki data siyo a kasuwa, Adama ta ɗaga leshi tana cewa. Wlh mamanmu zaki cizo da bikin nan dan ko matar kawu Aminu sai dai ku goga. Ai shiyasa nayi ta shiri a hakali dan kinga daga kan Salma mun gama aurarwa sai na 'ya'ya. Wai mama ya batun Sameeha ne naga komai ya daidaita kin saki makamanki. Adama ta faɗa tana duban Mamanta, Najwa da ta ke cikin ɗakin Hauwa data idar da sallah ta miƙe da nufi fitowa falon ta tsinkayi maganar Adama, sai ta ja tunga ta tsaya taji me hauwan zata ce, saboda dama yawan zuwa gidan da take yi tana so taji a ina aka kwana, dan wata biyu kenan taga komai ya lafa babu wani rikici, gashi kuma ta daina zuwa gidan Sameeha tun lokacin data ce ba zata auri Zaidu ba, da kunya ma taje gidan tunda tasan bata shuka abin arziki ba shiyasa ta maƙale a jikin Hauwa, kamar yadda Nafeesa take bata shawara akan ta dage da zuwa gidan dan ta riƙa sanin meke faruwa, sai dai duk zuwan da take yi ba wani labari dan Hauwa sosai ta sake mata suke abin arziki, ban da 'yan siyayya da take wa Hauwa ta kawo mata tare da zagewa tayi mata aikin gida, wannan yasa Najwa ta ƙara shiga zuciyar Hauwa take jin dole ma tayi yadda zata yi ta auri Aminu dan tasan ta dalilin Najwa zata samu abubuwa sosai jikin ɗan uwanta, kuma zata yi mata biyayya sai abinda suke so zai wakana a gidan. Najwa ta maƙale kunenta sosai a jikin ƙofa tana jin Hauwa na cewa. Adama ban faɗawa kowa bane amma naje gurin malam mai allon ƙarfe fa, shi ne yayi mini aikin da Aminu bai ɗauke Sameeha daga garin nan ba, babban damuwata da kuma abinda ya kashe mini guiwata malam yace Aminu ba zai taɓa ƙafa aure ba har sai in ya saki Sameeha, dalilin da yasa kenan guiwata tayi sanyi amma na bari sai mun gama bikin Salma kafin zan fara shiri akanta dan wlh ban haƙura ba, Sameeha dole sai ta bar gidan nan ta bawa Najwa ta shiga dan yarinya itace daidai da Aminu tana yi mini biyayya tamkar ni na haife ta, na gama magana da ita tace zata aure shi amma ba zata iya kishi da Saneeha ba dan hakan da kunya, to kinga itama ba zata yarda ayi auren ba sai in Sameeha bata gidan. Mama amma hakan naga da kamar wuya gurguwa da auren nesa, yadda kawu Aminu ke son matarsa bana jin akwai abinda zai rabasu. Kisha kuruminki zasu rabu cikin sauki In Sha Allah, yanzu tashi za kiyi ki tafi gurin Laure ki amso ankonku mu zo mu kai ɗinki da wuri kan biki ya zo tunda saura sati huɗu. Kuma wannan maganar da muka yi kar inji kinyi magana da wani. To tace mata ta miƙe ta fita zuwa babban gida, Najwa kuwa komawa tayi ta zauna a gefen gadon Hauwa tana jin damuwa a ranta, dan sosai maganar ta tsaya mata a zuciya akan ba zata samu auren Aminu ba sai in ya saki Sameeha, wanda abu ne mai kamar wuya gurguwa da auren nesa, kuma a kullun sonsa ƙaruwa yake yi ta gama kwaɗaitawa zuciyarsa aurensa domin a kullun kallon kanta take yi a matsayin Sameeha, jiki a sanyaye ta fito daga ɗakin sai dai ta danne damuwarta dan kar Hauwa ta gane, ta zauna a cushing Hauwa tana cewa. Har kin fito? Eh, bari na wuce dama nace bari mu gaisa ne amma kasuwar sati zani na yi siyayya. Aiko na gode Najwa Allah yayi miki Albarka, ya cika mini burina naga kin auri ɗan uwana. Murmushi Najwa tayi tana sunne kai ƙasa ba tare da ta amsa ba cike dajin kunya, sai ta miƙe tayi mata sallama ta wuce Hauwa tana shi mata da albarka tare da binta da kallo har ta fita cike da jinta a zuciyata, sosai take burgeta da natsuwarta da kunya da tarbiyyanta da yake ƙara sakawa ta samu gurbin a cikin ranta. Najwa tana fita ta kira Nafeesa a waya ta tambaye ta tana ina? Nafeesa tace tana unguwar rimi gidansu cousin ɗinta Binafa, Najwa tace tayi mata kwatance dan ba zata iya jira ba dole tazo su haɗu akwai magana mai muhimmanci da zasu tattauna, Nafeesa ta faɗa mata sunan layi kana tace in tazo ta kirata zata fito ta ɗauke ta, a haka suka rabu Najwa ta tari napep ta sanar dashi unguwar da zai kai yace dubu ɗaya, bata wani damu ba ta hau dan kuwa abinda ke gabanta ya wuce tsayawa tayi latsin kuɗin napep ɗin, tunda ma tanada yan kuɗinta, saboda bata wasa gurin wanke samarinta da suka nace suna son aurenta. Koda ta isa sai ta kira Nafeesa ba jimawa ta fito tare da wata 'yar budurwa da bata wuce sa'anninsu ba, Najwa ta hango su sai ta soma tafiya har ta isa suka haɗu suka juya cikin gida, Binafa da ta ga Kyawun Najwa ta haɗiye miyau ta kasa shuru tace. Beb ina kika samo mai kyau haka? Dan ubanki wannan sai dai ki ganta ki kyale dan ba 'yar hannu bace ki mai da baƙin miyau dan tafi karfinki. Ta bata amsa cikin gatsali, Najwa dai tana jinsu dan bata gane ina zancen su ya dosa ba, sai da suka shiga cikin gidan Najwa ta gane cewar Nafeesa fa danginsu masu kuɗi ne dan gidan har yafi nasu Nafeesa kyau, gashi gidan sama ne hawa ɗaya kato, sai dai koda suka shiga ta ƙara raina kanta amma duk tsaruwar falon bai kai kyan na Sameeha ba, ita kam har yau bata ga gidan daya kai na Sameeha tsaruwa ba, sama suka haura zuwa ɗakin Binafa suka shiga ciki tare da sakawa ɗakin key dan kar azo a katse musu hirarsu, Nafeesa taja hannun Najwa suka zauna a kan gado tana cewa. Kawata meke faruwa ne na ganki duk a cikin damuwa. Najwa ta ja fasali ta soma bata labarin duk abinda taji Hauwa na faɗawa 'yarta, ta ƙara da cewa. Kenan ni sai dai nayi ta dakon sonsa amma bazan same shi ba, duk daular da nake hangen kaina a ciki ya tabbata mafarki, Nafeesa yaushe burina zai cika ko haka dai zan ƙare da auren talaka. Ta ƙare maganar idonta yana cika da kwalla, Binafa ta saki shewa tana tafa hannu tana cewa. Yanzu ke akan namiji kike niman asarar hawayenki, wai ko wannan waye haka daya firgita tunaninki? wacece kuma take niman hanashi samunsa? Ku fayyace mini labari yanzun nan ku samu mafita. Nafeesa ta soma bata labari a takaice Binafa tace. Kice mini auren cin amana zaki kiyi, sannu da kokari Najwa da kike niman raba mata da mijinta, amma kuma karfin halinki ya burgeni haka nake son mace ta jajircewa akan duk abinda take so, kin ganni wlh duk yarinyar dana kyalla ido na ganta naji ta yi mini har naji sha'awarta tofa sai na lashi zumarta, danni zan iya komai domin cikar muradina. Ai ke dabance Binafa tunda ke mata kike bi ba maza ba, Allah dai ya shiryeki ya rabaki da wannan mugun halin. Hakan yafi mini wlh akan namiji ya saka mini ciwon zuciya, kema kinsan bana son wargi. Dan dai kinki yarda ki shigo cikinmu ne amma da kin gane namiji abin banza ne. Najwa ta kalli Nafeesa ta koma ta kalli Binafa sai yanzu ne hankalinta ya tattara maganarsu ta gane cewar Binafa 'yar lesbian ce, zata buɗe baki tayi magana Binafa ta rigata. Karki damu dani yan mata ni babu abinda zan miki tunda banji sha'awarki ba, amma kuma ni zan baki mafitar da zaki samu Aminu. Ku bani balarin ya tsarin gidan yake da ita kanta matar gidan. Najwa jin zata samu mafita yasa ta shiga bata labarin Sameeha da komai data sani, Binafa tace. Ai yazo gidan sauƙi tunda ba mai zama bane Aminun, dan haka ni da ƙawata Hanan zamu je mu farmaketa, tunda mace da mijinta ba a rabata da sha'awa, gashi Aminu ba mazauni ba kullun sai dai ta yi ta fama da ciwon mara, ga wannan maganin ki san yadda zaki bayar a saka mata a cikin abinci ko abin sha yana mugun tada sha'awa. Sauran aiki ki bar shi a hannuna, amma fa sai kun tabbatar mini da yaushe mijin zai dawo kafin komai zai wakana. Kina nufin zaku je gidan kuyi kwartanci da ita ko me? Kusan hakan ne amma sai mun tabbatar da mijin zai dawo ya ganmu dumu dumu kamar yadda dai miji ke maka kwarto a gidansa, wannan karan abin ya sauya salo mata zai kama da matarsa. Wow wow wow amma wannan abin yayi sai dai ina tunanin anya zai yi aiki kuwa? namiji yafi jin kishin matarsa sosai in ya ganta da namiji. Cewar Nafeesa, Binafa ta saki murmushi. To yanzu mata sun karɓe kambun, in mace tana da aure basu cika yarda subi maza ba sai ɗai ɗai ke haka, amma da yawa sun bi bin mata 'yan uwansu, dan haka wnnan zai yi aiki fiye da lissafinku. Wannan maganin taya zai isa gidanta? Binafa ta faɗa tana daga musu kwalin maganin, Najwa ta saki murmushi tana cewa. Ina da wacce zata yi mini wannan aiki, saboda ina shiri da mai aikinta sosai dan haka bani kawai nasan yadda komai zai tafi cikin tsari, kuma itace zata riƙa bamu update ɗin dawowarsa, dan nasan zata yi mini komai musamman ma in na bata kuɗi. To aiki ya kammalu sai ranar ƙaddamarwa. Ki fara ƙirga ranar fitar Sameeha daga gidanki. Cewar Binafa tana 'yar dariya, suma dariyar suke yi cike da jin daɗin samuwar mafitarsu. Sai gabda magrib Nafeesa da Najwa suka bar gidansu Binafa dama aikota ummansu tayi ta samu guri ta rashe, da yake baban Binafa shine yayan maman Nafeesa. Binafa irin sagartattun yaran nan ne da uwa ba kwaɓa kaka ba tsanani, ita ce kaɗai mace a gidan shiyasa kowa ya ke bata kulawa daga iyayenta har yayyinta, wannan kulawar ya jawo ta faɗa mummunar rayuwar lesbian, hakan ya faro ne tun daga makarantar secondary ita da ƙawarta Hanan da sauren kawayensu, har suka shiga jami'a suna tare bawai dan maza basa kulasu ba sai dan su sun keɓe kansu da mu'amala da su a cewar su namiji bai kai ya wulaƙanta su ba, kuma yadda suka riƙa a harkar basa jin sha'awar namiji kwata kwata shiyasa taƙi aure duk da iyayen suna so tayi, sai cewa tayi a ƙara mata lokaci, Hanan dai tayi aure bai daɗe ba ya mutu ta cigaba da harkanta da matan data saba, shiyasa sun gagari iyayensu sai abinda suke so suke yi sai dai har gobe babu wanda yasan ga abinda suke aikatawa, sai Nafeesa da itama nuna mata suka yi ta haɗe dasu tace ba zata yi ba tana tsoron Allah hakan yasa ta shiga musu wa'azi sai dai bai yi tasiri ba, Binafa ta roki Nafeesa data rufa mata asiri zata bari da zarar tayi aure, ta sakar mata kuɗi mai yawa wanda yasa Nafeeaa taja bakinta tayi shuru shiyasa bata cika zuwa gidan ba sai an aikota suke haɗuwa, sai gashi yau Binafan zata yi mata rana tunda zata kawo musu ƙarshen matsalar Najwa. Sai da mai napep ya fara sauke Nafeesa kafin ya juya ya sauke Najwa a gida wanda a lokacin ana gabda kiran sallar isha'i. Tana isa ta samu yayanta Junaid yana zaune a tsakar gidan suna zancenta da Inna, koda ta ganshi gabanta sai da ya faɗi ta ƙarasa ciki jikinta a sanyaye, da harara ya bita yana cewa. Wai gidan uban waye kike zuwa ne yanzu, kin fara sabon yawo har kikai dare a waje. Ko kin mance da dokar gidan nan ne akan kar ki riƙa bari magriba tana yi miki a waje. Yaya bikin ƙawata za ayi to munata shirye shirye ne fa. Ni baki faɗa mini biki za kuyi ba Najwa, cewa kika yi zaki je gidan su Nafisa ki dawo akwai maganar da zaku yi na gasar karatu da aka shirya a makarantarku. Ina mamakin yadda halinki ya sauya lokaci guda Najwa ki zauna kina shinfiɗawa mutane karya. Allah inna biki muke yi ban dai faɗa miki bane kuma dagaske za muyi musabaƙar Al-Qur'ani a makaranta. Kuyi hakuri ba zan sake ba. Ai kin saba kiyi laifi ki bada haƙuri, to wlh daga yau in na ƙara ganin haka sai na kusa karyaki. Cewar Junaid a fusace, Najwa ta buro baki ta wuce ɗaki tana cewa a zuciyata. Na kusa dai hutawa da wannan masifar naka, zan yi aurena na bar muku gidan gabaɗaya sai wanda naga dama yaje mini gidana. Ta zauna a gefen gado tana cire safar ƙafarta dan bata yawo ba safa, tunawa da tayi da plan ɗinsu da suka shirya yasa ta saki murmushi ta ciro wayarta a jaka ta dubo number ɗin Jamila ta kirata, kiran ya kusa tsinkewa ta ɗauka tana sallama, Najwa ta amsa tana sakin murmushi. Hajiya Jamila kwana da yawa ko ɗan flashing zamani ba kya yiwa mutane. Anty kin san ni ba wani kuɗi nake sawa a wayar ba sai in an kirani dan ba fita nake sosai ba, ya kwana biyu? Kin dai na zuwa gidanmu bama ganinki. Makaranta ya ɓoye ni yanzu ma wani dalili yasa na kiraki ina so gobe mu haɗu, amma a layin dake bayanku, wani aiki zaki mini na dubu ashirin, idan kinyi aiki da kyau zan caske miki kuɗinki. Wlh zanyi aikin dan babu abin da ba zan iya yi ba akan wannan kuɗin, ace lokaci guda na samu dubu ashirin kamar mafarki, nan fa da dubu goma ake biyana duk wata aiko nagode sosai. Yauwa zan fito ƙarfe goma na safe kuma zan kiraki kafin na ƙaraso sai ki fito mu haɗu. To Jamila tace mata cike da tsantsan murnan kuɗin data ambata, ɗan sosai ta kwaɗaitu da su, Najwa ta koma ta kwanta tana tunanin yanzun wa zata daki hancinsa ta samu dubu ashirin, sai ta tuna da Zaidu da suna tare ta san wlh zai bata, taja guntun tsaki tace bari ta latsa wani saurayinta Shamsu, shima ba laifi yana da sakin hannu kawai bai yi mata bane saboda baƙine sosai kamar shuni, gashi yana mugun sonta, nan take ta tura masa da sakon tana buƙatar kuɗi dubu goma kuma cikin sauri, dan wani abu muhimmi ne ya taso mata, ta tura tare da account number ɗinta. Shamsu daya ga sakonta ya saki murmushi yana cewa. Uwar son kuɗi zanyi maganinki. Yana gama faɗar haka ya tura mata dubu ashirin tare da sakon. _Sauran kuɗin kisa kati a waya, amma ki tabbatar da in na zo hira maganar aure za muyi dan wlh na gaji da jan ran da kike yi mini._ Ya tura mata, Najwa tana ganin alert ta saki ihu cike da murna, data karanta sakonsa ta saki wani uban murmushi ta mele baki. Aiko zaka ji a salansa wlh, dan blocking layinka da komai zanyi yanzu, ka gama yi mini amfani. Ta ƙare maganar tana ɗage gira ta zauna da kyau ta shiga blocking ɗinsa. _Zaku iya fara biyan kuɗinku domin muna gab da gama season 1 mu tsunduma a season 2 wanda sai kun biya kuɗinsa kafin zaku cigaba da samun cigaban wannan labarin ɗoɗar har zuwa ƙarshensa. Bononza na kwana Huɗu akan N300 idan kwanaki biyar ya ƙare In Sha Allah zai koma asalin kuɗinsa N400, dan Allah ku mara mini baya._ Pay N300 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a tura MTN card N300 a 09034940106, masu so ta pc su tura N600. Sai a tura shaidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu. [7/7, 13:04] Buhainat😁: *ABIN DA CIWO* Na ©Rahma Kabir MrsMG. Wattpad @rahmakabir Page 16. Najwa wani tunani ta sake yi bayan ta zauna tayi shuru da mintuna, a daren ta ƙara kiran Jamila tace mata ta bata kwana biyu zata sake kiranta su haɗu saboda wani uzuri ya taso mata, Jamila tace mata to sai ta kashe wayar tana gyara kwanciya. Najwa sai da ta ɗauki kwana biyu bata fita ba saboda kar Inna ta saka mata ido, ta natsu sosai tana nazarin yadda zata ɓillowa Jamila ta amince da bukatarta, duk da ta san zata iya yin komai akan kuɗi amma dole in ta ciza ta huta dan kar kwaɓarta tayi ruwa, hakan yasa ta samu damar haɗa wata dabara da kuma wani makirci dan ta gogawa Hauwa nata kashin kajin, hakan yasa ta kuma shafe kwana biyar tana lissafi. A ranar da ta cika kwana bakwai cif da haɗa plan ɗinsu dasu Binafa wato ya kama yau juma'a to daren ranar Najwa ta ɗauki kwalin maganin da Binafa ta bata, ta tsaya tana wani nazari sai da ta kai mintuna tana yi kafin ta sauke numfashi tana sakin murmushi, gabaɗaya magani guda takwas ta ɓallesu ta tashi ta ɗauko wata santana leda dake cikin ɗakinta wanda inna ta adana na saka tuwo, ta kulle ta fita tsakar gida ta samu ba kowa sai ta shiga kitchen ta ɗauki taɓarya ta daddaka maganin ya koma gari ta dawo ɗaki ta sauya masa leda saboda wannan ya faffashe, ta mayar ta saka a jakar islamiyyanta, ta duba agogon wayanta taga ƙarfe tara da minti uku, lokacin ne ta ƙara kira Jamila tace mata ta fito da ƙarfe goma na safe su haɗu, tace mata to sai ta kashe wayar ta gyara kwanciyarta. ****** Sameeha. Tana zaune a falo tana lissafin biki saura kwana 21 wato saura sati uku, kayan da zata yi fitan biki dasu ta tuna bata amso daga ɗinki ba, dan haka yasa tace zata je gurin telanta ta duba ko ya gama dan so take kan lokacin komai ya kasance a hannunta, shiyasa gari yana wayewa ta shirya yara da kayansu zata kaisu gidansu suyi hutu saboda sun samu hutun makaranta wanda tace sai biki ya rage saura kwana ɗaya zata ɗauko su saboda ta samu damar yin zirga zirga, sai ta soma ninke kayan Amrah tana sakawa a trolly wanda zasu tafi dashi gidan umma, sai kuma ta buɗe murya ta kwalawa Jamila kira sai gata ta fito ta tsaya tana cewa gata. Yauwa jeki ki kwaso mini takalmar Abi ki zo da tsumma ki goge min su. To tace mata sai ta wuce taje ta dawo ta soma aikin gogesu, wayar Sameeha tayi ƙara ta ɗauka ganin Aminu ne, bayan sun gaisa take ce masa. Maganar kuɗin da kace zaka turo na kama hol ɗin taron sisters eve da zamu yi, in kuma ka yarda sai muyi a gidan nan tunda wlh komai ya wuce ba wata matsala. Sameeha maganin kada a kuma to kar a fara, zan turo da kuɗin kawai dan bana son damuwa, ya batun su Abi sun kammala exam ko? Eh gasu nan ina haɗa musu kaya zasu gidan umma sai biki saura kwana ɗaya kan su dawo saboda na samu lokaci sosai na huta da kuma zirga zirgan bikin. Hakan yayi ki gaida umman, ina ganin nan da sati biyu zan dawo. Allah ya kaimu ya dawo da kai lafiya. Ya naji kamar ba kya missing ɗina, har kin fara sabawa kenan da rashin ganina. Haba my Man, missing ai ya zama jinin jikina kawai dai juriya ce yasa kaji na dake kamar ba komai. Murmushi yayi yace sai zuwa anjima, haka suka yi sallama ta aje wayar, ta cigaba da haɗa kayan, a lokacin Jamila take cewa. Anty na gama, kuma ina so in faɗa miki zan fita anjima zan je duba wata yayata da take mando ta kirani bata da lafiya. Amma baki taba faɗa miki kina da 'yan uwa anan ba. To da ya yake ba muyi hirar ba kuma nima bason fita nake ba shiyasa baki sani ba. Ok Allah ya kiyaye hanya sai dai ki dawo da wuri dan nima fita zanyi wata ƙila sai yamma. To tace mata kafin ta miƙe ta wuce zuwa ɗakinta. Sameeha wajen ƙarfe tara da rabi ta bar gidan ta rufe duk ɗakunansu ta bar kitchen a buɗe saboda tace Jamila in ta dawo ta gyara mata kayan miya ta niƙa ta dafa shi saboda ya soma lalacewa kar suyi asara, kafin ta wuce gidansu a motarta ta kwashi yara da kayansu daga nan zata biya gurin telanta, Tana fita ba daɗewa Jamila ta bugawa Najwa flashing sai gashi ta kirata nan take. Kin fito ne Jamila? A'a ki zo gida anty Sameeha ta fita kuma sai yamma zata dawo. Ok tace tana kashe waya, Jamila ta koma ta kwanta dan dama ta faɗawa Sameeha zata fita ne saboda haɗuwa da Najwa amma data ji itama fita zata yi sai ta fasa, karin takaicin ta tace zata fita amma ko na mota bata ce mata gashi ba, tunda tazo gidan wani kuɗi bai taɓa haɗasu ba a matsayin kyauta sai dai albashinta kawai take bata, sosai take ganin rowar Sameeha dan a ganinta yaci ace zuwa yanzu ma ta ƙara mata albashi, ga yadda take bautar da ita da aiki kamar jaka, sauƙin ta ma abinci tana ci tana koshi sai kuma in bata nan ta zabgi nama taci mai mata, kuma bata taɓa yi mata magana ba ƙila bata ganewa ana ɗiba naman ne. Bayan kamar minti talatin da shida sai ga Najwa tazo gidan, ta yi nocking da sauri Jamila ta fito ta buɗe mata ƙofa dan ta rufe ta ciki, suka ƙarasa suka zauna tare da gaisawa, Najwa ta dafa kafaɗar Jamila da yake kujera ɗaya suka zauna tace. Jamila wani aiki ne Yaya Hauwa ta sakani sai dai ni zaiyi wuya na iya aikata shi saboda ni ba a gidan nan nake zama ba, kuma ita ta saka nayi ne ganin Sameeha yar uwata ce nafi kusa da ita, amma kuma dawowata gidan nan zai mini wahala saboda ina zuwa makaranta can malali, to ganin tace biyana zata yi nace mata zanyi mata aikin, amma sai daga baya na yanke shawarar bari na baki aikin kema ki samu naki rabon, sai dai ina so ya zama sirri a tsakaninmu domin maganar nan daga ni sai yaya Hauwa muka yita, sai ke yanzu da zan faɗa miki kar ki sake ki bari tasan ke na bawa aikin, dan Wlh zaki jawa aikinki nima ki ja mini. Anty Najwa wannan wani irin aikine haka? Ba mai wuya bane amma ana buƙatar kiyi takatsantsan kuma ki riƙe sirri. Wannan magani ne da Anty Hauwa ta karɓo gurin wani malaminta akan a riƙa zubawa Sameeha a abinci domin ya fara aiki a jikinta kafin Aminu ya dawo dan ayi farraku a tsakaninsu. Saboda babban burinta ta bar gidan ni in maye gurbin Sameeha, kinga kema inna samu damar auren mai gidan aikinki ya tabbata a gidan nan kuma albashinki dubu ashirin duk wata. Tana kaiwa nan taja fasali, Jamila ta saki wani murmushin jin daɗi taji batun kuɗi, tace cikin zaƙuwa. Wlh da ba ƙaramin murna zanyi ba in kika zamo matar gidan nan, kuma gwara a setawa Anty hanya dan ba tada kirki ko kaɗan, hakuri kawai nake yi da ita, ashe kema Hajiya Hauwa ta sanar dake yadda take son raba aurensu, nima dalilin daya saka kenan ta ɗaukeni aiki, sai dai kuma bana samun labaran da zan faɗa mata wlh, saboda anty bata yin komai a gabana. Ta ƙare maganar tana taɓe baki, Najwa tayi murmushi. Yaushe munafukar zata bari kiji bayan tana zarginki akan zaki kwashe ki faɗa musu tunda su suka kawo ki aiki, yanzu dai ga maganin nan ki ɓoye ki riƙa saka mata a cikin juice zaifi aiki da kyau. Kuma wlh in kika bari na kamaki karki ambaci sunana ko Hauwa dan wlh saurayina soja yana nan, kina kuskure zan aiko a kamaki ya kashe ki a banza. Jamila ta zaro ido waje cike da tsoro. Haba Wlh bazan taɓa bari ta kamani ba, ai tana yawan sakani na miƙa mata kankana ko abarba su tafi so, kinga zan riƙa saka mata in ban samu dama ba, to ko a cikin abinci na barbaɗa. Yauwa haka za kiyi, ga dubu goma idan kin gama aiki da kyau zan cikasa miki dubu gomanki. Jiki yana rawa Jamila ta amsa kuɗin ta shiga ƙirgawa ta samu ya cika cif. Nagode Anty Allah ya ƙara arziki yasa ki auri Alhaji. Ameen. Yanzu zan riƙa kiranki a waya kina faɗa mini abinda ke faruwa da kuma faɗa mini tabbacin ranar da Alhajin zai dawo. Eh ɗazun naji suna waya yace nan da sati biyu zai dawo. Yauwa ki riƙa saka kunne musan yaushe ne ranar da zai dawo, amma da yaushe yafi dawowa? Da safe yafi shigowa. To shikenan zan tafi sai munyi waya. Najwa tace tana miƙewa, Jamila ma ta miƙe tana koro mata godiya dan ba ƙaramin daɗin kuɗin taji ba saboda tana hada so ta fara kuɗin ne in ta tashi aure ta siya kayan 'yan birni masu kyau, Najwa ta tafi Jamila ta juyo ta koma ɗakinta tana hango yadda zata fara saka mata maganin, dan kuwa tana ɗan sakata aikin kitchen ɓangaren abinci haka, da farko ne taki yarda da ita amma daga baya ta saki komai, ko dan taga bata kamata da wani a bun munafurci bane shiyasa ta saki, kuma gashi ta koma tana shiri da su Hauwa. Najwa tana cikin napep ta kira Binafa ta faɗa mata yadda tayi da Jamila, da yake sunyi musayar numbern waya, Binafa tace ba damuwa ta saka kunne sosai susan ranar dawowar Aminu, sannan ta tura mata addreshin gidan zasu fara kai ziyara amma sai in Sameeha bata nan, ta yadda mai gadi zai shaida fuskarsu itama Jamila yar aiki ta gane suna zuwan gidan a wannan lokacin akai akai, amma sai in tana binciko musu Sameehar bata nan kafin suje, yin hakan duk taku ne da kwantan ɓauna. Najwa ta yi dariya tana ƙara yi mata godiya a haka suka rabu, nan take ta tura mata adireshin gidan da bayanin komai yadda zasu gane. Sameeha bata dawo ba sai bayan sallar magrib, ta zauna a cushing tana kiran jamila, data fito tayi mata sannu da zuwa tace ciki gajiya. Jeki markaɗa mini sauran gwandan nan ki zuba madara ki niƙa karki saka min ruwa, sai ki kawomin shi da kauri shi nake jin sha, sannan ki kawo plate guda biyu zan zuba miki abinci na tawo dashi daga gidanmu. To tace mata sai ta wuce zuwa kitchen, dama a kitchen ɗin ta adana maganin inda tasan babu wanda ya isa ya gani, ta ɗauko shi ta maƙale a cikin rigarta ta soma aikin data sakata, a cikin nikan ta barbaɗa maganin ta mayar da shi ma'ajiyarsa tazo ta haɗa komai, data gama ta kawo mata tare da plate data ce ta kawo, Sameeha ta saka mata tuwon shinkafa miyar zogale da nama ta bata ta wuce tana godiya, itama ta saka nata amma sai da ta shanye smoothy ɗin kafin ta fara cin abinci, data gama ta shiga ɗaki ta yi wanka tayi shirin barci ta kwanta dan tana fashin sallah kuma akwai gajiya a tare da ita saboda aiki sosai ta yiwa Umma dan tayi mata kwalemar dakinta. Da safe data tashi jin kanta tayi cikin wani irin yanayi na feeling, abin har mamaki yake bata dan rabon da ta ji haka ta manta tunda ta dena shan maganin mata saboda miji baya kusa saboda ta samawa kanta lafiya, rabon ma data sha wani magani ta mance lokacin dan an jima, kayan fruit kawai take sha suma badan su ƙara mata komai ba sai dan jikinta ya yi kyau, kuma sosai suke nunawa a jikinta dan tayi fresh sosai gwanin burgewa, sai ta bayar ƙila smoothy ɗin gwanda data Sha jiya shine ya taso mata da sha'awa tunda akwai madara a ciki, wankan tsarki tayi dan ranar ne ta gama al'ada sai ta shirya tayi salla kana ta fito ta haɗa masu abin kayi, tana gama karyawa ta fice saboda sunyi da telanta zata je da wuri ta amso kayanta, daga can kuma zata je babban gida kan batun cincin ɗin amarya da za ayi, saboda Hauwa ta kirata akan tazo ayi shawarar yadda zata kasance. *** Binafa. A safiyar Binafa ta kira Najwa akan zasu je gidan Sameeha amma ta kira ta tambaya ko tana nan, suna gama waya nan take ta kira Jamila ta tambayeta sai take faɗa mata bata nan sai ta kashe waya, Najwa ta sake kiran Binafa ta faɗa mata, tace yanzu zasu je gidan da ƙawarta Hanan dan su fara aikinsu. Binafa a motarta ta fita ta biya gidansu Hanan ta ɗauke ta suka wuce, basu sha wuyar gane gidan ba, suka yi parking mota daga nesa da gidan suka tako da ƙafa har kofar gate sai suka buga, mai gadi ya buɗe yana ganin baƙin fuska ya tsaya tana tambayarsu. Wa kuke nima?. Baƙin Sameeha ne. To ai bata nan yanzu ta fita. Zamu jirata. Binafa ta faɗa a takaice, sai da mai gadi ya ƙare musu kallo yaga ba wani mummunar abu a tare dasu dan hijab suka sha har ƙasa, sai ya buɗe musu suka shiga zuwa falo da yake Kofar a buɗe yake sallama suka yi suka samawa kansu gurin zama, Jamila ta fito daga kitchen da take yin wanke wanke ta ƙaraso tana yi musu sannu da zuwa. Sameeha fa? Cewar Hanan. Bata nan bata daɗe da fita ba amma ko a kirata? A'a bari kawai, amma kawo mana ruwa mu sha. Tace to ta koma kitchen ta kawo musu ruwan gora da kofi biyu, suka amsa suka sha kana suka ce mata zasu tafi. Su waye zance mata? Karki damu zamu dawo anjima ko gobe. Cewar Binafa, to tace musu kafin suka fita ta rufe kofar falon ta koma ta cigaba da aikinta. Su Binafa suna fita suka shiga mota Hanan tana cewa. Dole yarinyar nan ta rikice akan mai gidan, kinga hoton masu gidan kuwa mijin ya haɗu kam. Ni matar naketa kallo domin wlh har cikin zuciyata tayi mini, dan har tafi Najwa kyau, gata 'yar bulbul jikinta komai yaji. Wato dai zamu kwashi dami a kala. Cewar hanan tana 'yar dariya, Binafa dake tuƙi ta ɗage gira tana dukan sitiyarin mota cike da murmushi a fuskarta. _Zaku iya fara biyan kuɗinku domin muna gab da gama season 1 mu tsunduma a season 2 wanda sai kun biya kuɗinsa kafin zaku cigaba da samun cigaban wannan labarin ɗoɗar har zuwa ƙarshensa. Bononza na kwana biyar akan N300 idan kwanaki biyar ya ƙare In Sha Allah zai koma asalin kuɗinsa N400, yau saura kwana uku bononza ya ƙare._ Pay N300 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a tura MTN card N300 a 09034940106, masu so ta pc su tura N600. Sai a tura shaidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu. [7/7, 13:04] Buhainat😁: *ABIN DA CIWO* Na ©Rahma Kabir MrsMG. Wattpad @rahmakabir Page 17.             Last freepage season 1. * Binafa. Bayan zuwan farko da suka yi sai da suka sake zuwa kusan sau biyu kuma duk basa samun Sameeha a gida, sannan duk in sun tashi tafiya sai sun tabbatar mai gadi baya gurin, yana ganin shigarsu amma baya sanin fitansu, shima sosai yake mamakin zaryan da suke yi dan in Sameeha ta dawo baya sanin lokacin da baƙin suka tafi, zuwa na ƙarshe da suka yi ranar monday wanda ya kama zuwa na huɗu kenan, kuma a cikin satin da Aminu yace zai dawo ne, sun samu Sameeha tana gida dan plan ɗinsu kenan da suka tsara, dan mai gadi yau ya tabbatar da zuwansu sun sameta a gida, suna zaune a falo sun sha dogon hijab suna jiran Sameeha ta fito wanda Jamila ta shiga ɗakinta ta sanar da ita, lokacin wanka ta fito shiyasa tace su jirata ta kimtsa, shadda ta saka doguwar riga bubu tasha aiki, sai ta saka hula akanta dan bata so ta ɓatawa wanda suka zo gidan duk da bata san ko su waye ba, a haka ta fito har ta ƙaraso gunsu tana yi musu kallon rashin sani, sai suka gaisheta ta amsa fuska sake. Amma ban waye ku ba daga ina? Muma munyi mamakin ganin ke ce matar gidan saboda kwatance aka yi mana da nan gidan, cousin ɗinmu ce aka yi bikinta to lokacin bama gari shine tayi mana kwatance domin muzo muga ɗaki, amma kuma sai muka ga ashe ba gidan muka je ba. Allah sarki, gaskiya ba nan bane ƙila baku gane kwatancen bq amma da kun kirata a waya kunji. Sai dai na sake gwadawa dan tun ɗazun muke kira baya shiga. Allah yasa ya shiga to. Sameeha ta faɗa tana mikewa dan ta kosa su tafi saboda so take ta fita lanbun gidan ta sha iska tare da jin kamshin furanni, saboda ita kanta gidan yayi mata ba daɗi ita kaɗai ta saba da kwaramniyar su Amrah, su Binafa suka miƙe suna yi mata godiya sai kallonta suke suna hararo garar da zasu kwasa, ji suke dama ta zama 'yar hannu su morewa rayuwa, ita dai sai anjima tayi musu sai da suka fita kafin ta kwalawa Jamila kira ta fito ta rusuna a gabanta. Daga yau kar ki ƙara barin mini ƙofar falo a buɗe duk wanda ya buga sai kin tabbatar da gurina yazo kafin ki buɗe masa, waɗannen matan ba saninsu nayi ba kin barsu su kaɗai a falo sunyi kane kane, idan masu cutarwa ne shikenan anyi an gama, to ki kula da kyau. Kiyi haƙuri zan kiyaye. Yauwa gwara dai ki kula saboda duniya ba gaskiya kowa ya zama mugu dan dama mugu bai da kama, haka kurum ki barsu su shigo ashe bani suke nima ba, kuma kin tafi ɗaki kin barsu su kaɗai, ai da sai ki zauna inna fito sai ki tafi. Wayarta da ta yi ƙara yasa ta ɗaga ta koma ta zauna bayan ta gaisa da Aminu sai suka shiga hirar biki daga bisani tace masa. Noor yaushe zaka dawo ne gaskiya gidanmu yana buƙatar Haskenka. In Sha Allah ranar asabar zan shigo da Safe saboda zanje kano wani meeting, kuma tunda su Abi basa nan ki shirya mu tafi tare sai ranar monday mu dawo. Allah ya kaimu amma me kake so in shirya maka ranar asabar ɗin in kazo sai ka ci mu tafi. Karki wahalar da kanki, kuma ai da sauran lokaci tunda yau monday idan Allah ya kaimu friday in ina son wani abu sai na sanar dake. Haka suka ƙara taɓa hira akan bikin Salma domin a satin bikin zai dawo, da suka yi sallama Jamila ta ƙara bata hakuri Saneeha ta sallameta ta wuce, a zuciyarta kuma tana mamakin cewa da tayi bata sansu ba, sosai kanta ya ɗaure tunawa da zarya da suke yi a gidan, koda yake duk zuwansu basa samunta wataƙila kuskuren kwatance aka yi musu suke ta zuwa, amsar da wani ɓangare na zuciyarta ta bata kenan sai ta miƙe ta wuce dan tuni Sameeha ta wuce ɗakinta dan ta ɗauki ƙaramarta waya ta tafi lanmu. Jamila tana shiga ɗaki ta tadda wayarta ta ƙara koda ta duba Najwa ce, ta ɗauka da sauri tana shigewa bayi ta kulle, tambayar data yi mata ya girgiza lissafinta da tace. Me Sameeha tace batan baƙin mata biyu da duka zo sun tafi? Dama kin san da zuwansu? tace to bata sansu ba karna sake barin Kofar falo a buɗe. Nan ta kwashe komai ta faɗa mata, Najwa ta sauke numfashi tana cewa. To bakin Yaya Hauwa ne domin suma ta ɗauke su aiki ne akan Sameeha, shiyasa bata sansu ba kuma Hauwa ita ta turosu akan yau su zo su sameta a gida, dan haka idan sun ƙara zuwa ki buɗe musu ƙofa ki barsu su shiga ɗakinki su ɓoye a nan, koda kwana ya kama zasu yi to a ɗakinki zasu zauna, karki bari Sameeha tasan suna cikin gidan. Yaushe Aminu zai dawo ko har yanzu baki sani ba.? Ɗazun nan tayi waya dashi a gabana wai ranar Asabar da safe zai dawo. To ranar Juma'a baƙin zasu zo domin suna so su haɗu da Aminu ne. Ki dai kula dan karki ɓata mana aiki. Cewar Najwa cike da gargadi, To Jamila tace kana ta yanke wayar, Jamila dai duk sun gama ɗaure mata kai dan ta kasa gane wani abu suke son shiryawa Sameeha, tsoronta da fargaba ace asirinsu ya toni, addu'a ta shiga yi Allah yasa su gama komai cikin nasara ba tare da ɓarkewar wata matsala ba. . Najwa. Shigowar inna ɗakinta yasa ta yanke kiran da sauru, inna ta bita da kallo tana cewa. Ina sallah naji kina ambatan sunan Sameeha shine na zo naji me ya faru? Au! kai inna wato kunnenki ya nan ke da kike sallah, to maganar bikin ƙanwar mijinta nake da wata 'yar islamiyarmu tada ce tasan Salma shine na ce mata nima 'yar uwata Sameeha tana auren yayanta. Ohoo na ɗauka ko kin je gidan ne dana hanaki zuwa. Haba inna ai nayi Hankali me zai kaini gidan kuma bayan naga sai shamin ƙamshi suke dan na rabu da yayansu, ko da yake ita Anty Sameeha ba ruwanta Ikram ce dai uwar kanzagi. To ai da gaskiyarta tunda ɗan uwanta kika wulaƙanta, koni nan haushinki naji da kika watsa mini ƙasa a ido. Ni dai Inna ki mini addu'a Allah ya cika mini burina. Idan na Alkhairi ne ya cika miki, dan nasan bai wuce na shegen burin auren me kuɗi ba. Kwana biyu ma naga kin rage yawo kin natsu Allah yasa ki ɗaure. To inna bani da wani sabga shiyasa na natsu tunda muna muraja'an musabaƙar da za muyi na makaranta, kuma fitana ai sai da dalili nake yinsa. Hmmm Allah ya nuna mini aurenki dai na huta. Ta faɗa tana harararta, Najwa dariya tayi tabi bayan inna da kallo data fice daga ɗakin, ta gyara kwanciya tana jin wani farin ciki na kusantowar cikar burinta daya kusa cika. ***** Ranar Juma'a. Sameeha. A ranar gidan kakanninta dake kawo ta kai ziyara, wato gidan iyayen ummansu, a can ma ta samu su umma dan sunyi dama zasu haɗu domin su sada zumunci. Ɓangaren su Binafa kuwa bayan sallar la'asar sun zo gidan Sameeha da shirinsu dan ƙaddamar da aikinsu da suka gama shirya masa, ko da suka zo mai gadi ya buɗe musu suka shiga ya saba da ganin sun zo ko da mai gidan bata nan hakan yasa bai damu ba, dan ya hango akwai alaƙa mai ƙarfi a tsakannsu da Sameeha ta 'yan uwanta taka. Jamila ta san da zuwansu dan komai Najwa ke faɗa mata, hakan yasa suna buga ƙofa ta zo ta buɗe musu suka wuce ɗakinta Jamila suka zauna a gefen gado bisa umarnin Najwa data ce ta basu damu su zauna a ɗakinta kuma zasu jira Saneeha ta dawo amma kar ta sanar da ita akwai baƙi, hakan yasa tayi gum da bakinta domin cike aikin sauran dubu goma daya rage zata bata, saboda tun ranar farko data samu sa'ar sakawa Sameeha maganin nan to Sameehan bata sake shan wani fruit ba sai juice ɗin roba take sha, kuma abinci da kanta take dafawa ta ɗiba nata kafin take kiran Jamila ta ɗauka nata, kamar tasan ana shirya mata wani abu kuma ita a bangaren ta gani tayi smoothy ɗin data sha rannan shine ya sakata sha'awa, shiyasa ta hakura da shan duk wani fruit dan kar ya tada mata zaune tsaye tunda ba miji a kusa, sai ta koma shan lemun gora kuma tunda ta daina shan fruit ɗin bata sake jin wani matsala irin da wancen ranar ba, shiyasa ta samu nutsuwa saboda tayi maganin matsalarta. Jamila kuwa sanar da Najwa tayi komai hakan yasa Najwan ta sanar da Binafa, sai Binafa tace kar ta damu akwai wani hanyar da zasu bi koda basu yi nasarar tada mata sha'awa ba, to akwai maganin da zasu bawa Jamila ta tabbatar ana gobe mijin zai dawo ta saka mata a abinci ko abin sha, abin maye ne mai zautar da mutum kuma baya saka barci sai dai mutum ya jishi a rikice kuma ba cikakken ƙarfi saboda yana kashe jiki, hakan yasa Najwa ta samu natsuwa tace zata haɗasu da Jamila wanda hakan ne ya faru a zuwan su yau gidan, kuma Jamila ta tabbatar musu da Aminu gobe Asabar zai dawo, saboda a gabanta Sameeha tayi waya dashi har tana tambayarsa abin da yake so a dafa masa saboda yace da sassafe zai fito dan zai je Kano akwai wani meeting da zasuyi mai muhimmanci, to zai biyo ta gida kafin ya wuce ta shirya tare zasu je, Jamila sai ta tsinci kanta cikin zullumi wanda yasa ta kasa zama a ɗakinta ta dawo falo ta zauna cike da tunani barkatai, wanda maganin da suka bata akan lallai ta saka wa Sameeha a abinci ko abin sha ya tsaya mata a zuciya, haka dai ta danne komai dan dole ta ƙarasa aikin da ta yi alkawari akai, kuma hange dubu goman yasa ta ƙara aro jarumta. Sameeha sai bayan sallar magrib suka baro gidan kakanninsu a motarta ta kwaso su, sai da ta wuce gidan umma ta sauke su har da yaranta kafin ta juya akalar motarta ta dawo gida, bayan ta shiga falo ta samu Jamila a nan falo da ta samu a buɗe, da yake in tasan ta kusa dawowa takan buɗe ƙofar, ta kalleta da kyau. Yau kuma me kike yi a falon ke kadai? kuma baki saka kayan kallo ba. Zaman ɗakin ne ya isheni shiyasa na dawo nan, kuma ina tsoron na kunna kayan kallo ki gani kiyi faɗa. Babu faɗan da zan yi miki in dai ba zaki yi mini ɓarna ba, tashi kije ki yanka mini tattasai da albasa, ki ɗauki kaza ɗaya dake fridge ki tafasa mini, gani nan zan zo na dafa mana taliya shap shap. To tace mata kana ta miƙe ta wuce kitchen Sameeha kuwa ɗaki ta shiga ta rage kayan jikinta ta fara gabatar da sallar magrib kafin ta fito daga ita sai vest da siket ta shiga kitchen ta samu ta yi mata duk abinda tace, sai da naman ya tafasa kafin ta daura mai ta soya su kafin ruwan tafashen ta ɗaura musu sanwar taliyar, bayan ta gama tace wa Jamila ta kula da girkin zata je tayi sallar isha'i da aka kira dan har an shiga masallaci an tayar da sallar, Jamila ta ce to, kamar tana jira ta fito ta ciro kwalbar maganin da suka bata ta zuba shi duka a cikin sanwar taliyar ta saka dulayi ta motsa kana ta rufe ta ɗaure kwalbar a cikin baƙar leda ta fito ta shiga ɗakinta da sauri, ta samesu a zaune ko wacce da waya tana charting, ta miƙa musu ledan data ɗaure kwalbar tana cewa. Na zuba shi duka a cikin sanwar Taliyar data ɗaura yanzu. Aikinki na kyau 'yan mata, dan har na ƙara miki dubu biyar akan cikon dubu gomanki. Cewar Binafa da take magana a hankali tana yi mata jinjina da babban yatsa, Jamila murmushi tayi ta juya da sauri ta fita zuwa kitchen. . Aminu. Wajen ƙarfe shida kira na gaggawa ya shigo wayarsa akan meeting ɗinsu da za ayi a gobe asabar ƙarfe biyun rana an dawo da shi ƙarfe tara na safe bisa wani babban dalili, hakan yasa ba shiri ya taso driver sun wajen aikinsu ya bashi motarsa yace su kamo hanyar kaduna, daga shi sai briefcase ɗinsa sai wayoyinsa guda biyu, bai sanar da kowa zai zo ba hatta Sameeha bai faɗa mata ba, dan ya san in ta sani zata hana shi zuwa saboda halin da ƙasar yake ciki na rashin tsaro musamman a arewacin Nigeria, sannan kidnapers sun yi wa hanyar Abuja baƙin fanti wanda kowa yasan ba ƙaramin ta'asa suke yiba sai dai Allah yayi mana maganinsu, hakan yasa bai faɗa mata ba dan ya zame mata zuwan ba zata. Sameeha da ta idar da sallah sai ta ce bari ta kira Aminu taji muryansa, koda ta kira ya ɗauka amma bata jinsa saboda rashin network hakan yasa ta kashe kiran sai ga text ɗinsa ya shigo. _Meehata karki damu zan kira ki anjima kaɗan._ Murmushi tayi ta aje wayar ta fito zuwa kitchen lokacin har ta sauya kayan barci dan so take tana cin abinci ta yi barci, dan gobe In Allah ya kaimu ta tashi da ƙarfinta saboda zuwa kano da za suyi, ɗoki take sosai dan rabonta da kano ta manta akwai ƙawayenta na WhatsApp group Sirrin 'ya mace da yawa a can da suka yi mugun sabo, ana zumunci da kuma abubuwan ƙaruwa da ake gudanarwa, sosai take ƙara samun ilimin rayuwa a wannan group ɗin, komai a tsari suke yinsa kamar yadda musulunci ya tanadar, sun zama tamkar 'yan uwa, hakan yasa ta fara lissafin inda zata je kai ziyara dan har ta yi magana da mata kusan uku ta pc akan in ta shigo zasu ganta. Ta samu Jamila a kitchen tana zaune. Kin duba taliyar tayi kuwa.? Ruwa ya rage ya tsotse. Sameeha tace ok sai ta isa tukunyar ta buɗe taga tayi tace. Ai ni haka nake sonta nasha da romo romo tafi mini daɗi, ɗauko plate na saka miki nima ma saka nawa. To Jamila tace ta dauko plate biyu ta bata, Sameeha ta amsa ta kashe gas ta soma zubawa Jamila ta saka mata yankan naman kaza ɗaya tace ta sallameta, kana ta zuba nata, saboda ta ƙosa ta ci a kitchen ɗin ta zauna tayi masa cin tsaf, sai da ta cika cikinta sosai kafin ta gama ta aje plate ɗin ta sha fanta da ruwa ta fito tana jin jikinta ya fara yi mata nauyi, zarginta barcin da take ji ne ya fara kawo jiki, taso ta zauna a falo abincin data ci tabi jikinta kafin ta kwanta, amma ina idanunta sunƙi bata haɗin kai sai ta wuce ta shiga ɗaki ta kwanta, dan har ji tayi ɗakin yana juya mata, sosai ta shiga mamakin yadda jikinta yayi sanyi kalau kamar dai ana jira taci abinci ne ganiyar data kwaso ya rufeta. Nan muka kawo ƙarshen season 1 wato ƙarshen freepages.. Ko me zai faru? Ga Aminu yana hanyar dawo wa dan yana gabda shigowa gida... Sameeha taci magani a cikin abincinta bata sani ba ta soma shiga wani yanayi na maye... Binafa da Hanan suna cikin gidan wanda gabaɗaya shirinsu na safiyar asabar ne, sai kuma ga kuma Aminu yana hanyar dawowa. Me zai faru? Shin burin Najwa yana cika? Ya ƙarshen ta zai zama? Su Binafa suna cin sanara akan Sameeha kuwa? Ya bikin Salma sai kazance da Su Hauwa suka ci burinsa.? Burin Hauwa yana cika kuwa akan aurawa Aminu Najwa da kuma sakin Sameeha da take so yayi.? Ya ko wanne yake karɓan sakamakon karshensa.? Sai mu tara a cigaban wannan labarin don samunsa kai tsaye har zuwa ƙarshe In Sha Allah. _Bononza na kwana biyar akan N300 idan kwanaki biyar ya ƙare In Sha Allah zai koma asalin kuɗinsa N400, yau saura kwana biyu bononza ya ƙare._ Pay N300 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a tura MTN card N300 a 09034940106, masu so ta pc su tura N600. Sai a tura shaidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu. [7/7, 13:04] Buhainat😁: *ABIN DA CIWO* na Rahma Kabir MrsMG. Season 2 loading... 18. Arewabooks @rahmakabir13 zaku samu cigaban labarin kai tsaye domin sai ya fara sauka a can kafin WhatsApp. Bononza N300 saura yau da gobe In Sha Allah, zuwa monday zai koma asalin kudinsa N400. Labarin Sameeha ce wacce yarinyar kanwan babanta take son aure mata miji ta karfin cin tuwo, sai dai Sameeha ba tada masaniyar haka domin Najwa ta wasa wukarta wajen yi mata bita da kulli, cin dunduniya, makirci da zagon kasa dan ta samu damar fitar da Sameeha cikin sauki ba tare da an zargeta ba ta kuma aure mijinta cikin sauki. ABIN DA CIWO. Idan baki karanta freepages season 1 ba ki tuntubeni a number ta pc 09034940106. Duk wanda yasa kudinsa ya siya ba zai taba nadama ba domin zaki karu da ilimin zamantakewar rayuwa, babban tunatarwa ce sosai dan wani lokacin muna zaton wuta a makera ne sai mu tsinceshi a masaka. Ko me zai faru? Ga Aminu yana hanyar dawo wa dan yana gabda shigowa gida... Sameeha taci magani a cikin abincinta bata sani ba ta soma shiga wani yanayi na maye... Binafa da Hanan suna cikin gidan wanda gabaɗaya shirinsu na safiyar asabar ne, sai kuma ga kuma Aminu yana hanyar dawowa. Me zai faru? Shin burin Najwa yana cika? Ya ƙarshen ta zai zama? Su Binafa suna cin sanara akan Sameeha kuwa? Ya bikin Salma sai kazance da Su Hauwa suka ci burinsa.? Burin Hauwa yana cika kuwa akan aurawa Aminu Najwa da kuma sakin Sameeha da take so yayi.? Ya ko wanne yake karɓan sakamakon karshensa.? Sai mu tara a cigaban wannan labarin don samunsa kai tsaye har zuwa ƙarshe In Sha Allah. Pay N300 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a tura MTN card N300 a 09034940106, masu so ta pc su tura N600. Sai a tura shaidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu. [7/7, 13:04] Buhainat😁: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shaidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.* 18. Jamila. Data shiga ɗakinta da plate ɗin abincin da Sameeha ta zuba mata sai ta cewa su Binafa. Kunga ta zuba mini abincin kuma da maganin da na zuba mata a ciki. Ki samu leda baƙa ki saka a bola, idan maganin ya fara aiki a jikinta ko ɗaga ƙafa ba zata iya ba dan haka ki shiga kitchen ɗin ki dafa mana indomie muma za muci. Cewar Hanan data bata amsa, Binafa ta jefa mata baƙar leda data ciro a jakarta sai Jamila ta ɗauka ta juye taliyar a cikita ɗauke naman ta goge inda ya shafi abincin jikin zaninta ta fara ci dan in ta hakura da taliya wlh ba zata iya haƙura da naman ba, zancen data yi kenan a zuciya ta samu guri ta zauna tana yagar naman, Binafa ta kalleta tana cewa. Naman ma ba zaki iya haƙura da shi ba? Barni naci wlh gida babu makota sai ɗai-ɗai tun tana suyarsa nake haɗiye yawu, kuma na goge inda ya taɓa abincin kafin na soma ci. Ƙuda dai gurin kwaɗayi yake mutuwa, watarana sai in kashe kanki abanza saboda kwaɗayi. Sai wani cakal cakal kike yi gwanin ƙazanta. Cewar Hanan tana balla mata harara, Jamila ta haɗiye wanda ta tauna ta tsaya galala tana kallonsu tare da runanin ko dai maganin mutuwa suka sakawa Sameeha a abinci, nan take cikinta ya karta ta ce cikin tsoro. Ko guba kuka sa na saka mata a cikin abincin? In shine ma ai kin riga kinci sai dai muce Allah ya jikanki. Cewar Binafa data ɗaure fuska, a zabure Jamila ta miƙe tana salati babu inda jikinta baya rawa, ga sauran naman a hannunta ta kasa ci balle ta yar. Ke karki ɓata mana aiki ki yi mana shuru da wasa muke yi, taya zamu baki guba ki saka mata kuma mu zauna zaman jiranta ai tuni zamu cikawa bujenmu iska. Cewar Hanan, Jamila ta haɗiye miyau kwad tana sauke ajiyar zuciya sai kuma duk taji naman ya fice mata a rai, haka ta haƙura ta saka shi cikin ledan data zuba taliya ta ɗaure, ta shiga bayinta ta wanke hannu, sosai ta basu dariya haka suka shigayn dariyar ciki ciki dan kar a jisu. Lokacin da suka ji motsin Sameeha ta fito daga kitchen sai suka zabura suka miƙe tare da shigewa bayi dan kar ta leƙo ta gansu, sai da suka tabbatar ta shiga ɗaki kafin sula fito lokacin sun samu Jamila ta fita da plate da kuma ledan abincin, suka zauna a gado suna kallon juna. Hanan anya zan iya jurewa sai asuba zamu far mata, gaskiya a matse nake. A'a Binafa mu dai bari zuwa lokacin dan kar mu ɓata shirinmu dan kinsan barci mai nauyi zai iya ɗaukemu bayan kura ta lafa, gwara mu yi barci yanzu sai mu saka alerm da zai tashe mu da asubahi. Bazan iya ba Hanan, ko kaɗan zanje na ragewa kaina zafi in yaso sai na ƙara tara na asubahin. Hmmmm Hana tace sai ga Jamila ta dawo cikin ɗakin tana cewa. Na fita ta ƙofar kitchen naje babban bolan gidan na saka abincin dan kar ta gani a boln kitchen da safe ta tuhumeni. Kinyi kyan kai 'yan mata, ki bari zuwa anjima saiki dafa mana indomie. Ina tsoron karta gane na ɗiba kinsanta akwai bin diddigi. Idan kinga ta damu da hakan ba, dan matsalar dake gabanta yafi indomie. In kuma zaki kwana da yunwa ba damuwa mu zamu iya fita mu samu abinda zamu ci. Cewar Binafa, Jamila bata ce komai ba ta koma ta zauna duk abin duniya ya isheta, duk a takure take da zaman ɗakin saboda su, sannan cikin tsananin fargaba take akan kar Allah yasa asirinsu ya tonu, duk ta ƙosa su gama su tafi duk da bata san asalin me zasu aikata ba a gidan. Wajen ƙarfe goma saura, Binafa ta fara hamma sai ta miƙe tana cewa. Nasan zuwa yanzu maganinmu ya fara aikinsa bari in dubata in dawo, zuwa anjima sai mu shiga kitchen ɗin muga me zamu dafa dan na kula wannan baƙin tsoro ne da ita gwara ta kwana da yunwa akan ta dafa mana indomie. Muje tare dan ban yarda da wasa tare ci bambam ba. Nasan ki sarai wlh kamar yunwan cikina. Hanan tace haka sai suka fito falo shuru ba kowa ga hasken fitilan ba a rage ba balle a kashe, suka dunfari ɗakin Sameeha babu fargaba ko tsoro dan sun san hakkarsu ta cimma ruwa tunda taci maganin. *** Sameeha. Lokacin data hau kan gado sosai take jin barci har ya fara kamata, amma bayan mintuna sai ta farka firgigit kamar an tsikareta data, buɗe ido sai taga ɗakin na juya mata, tayi yunƙuri zata tashi amma ta kasa saboda wani nauyi taji jikinta yayi mata, ga kuma kanta da take ji yana juyawa tamkar an sauya ta, dan gani take kamar lilo ake da ita, haka ta dinga juyi a gado shima sai da tayi da gaske take iya mirginawa. A cikin wannan yanayin su Binafa suka shigo ɗakin, Sameeha tana ganinsu taji ƙirjinta ya buga tare da tunanin meya kawo su gidanta a wannan lokacin, sai ta soma nazari ko mafarki take yi dan sosai ta gane fuskarsu tunda ɗakin da haske sosai. Ganin sun dunfaro ta yasa ta ware idonta don ta tabbatar da ba mafarki bane. Su waye kuuu? Me ya kawo ku? Ta faɗa cikin muryan maye, ganin sun hau kan gadon yasa tayi saurin yunƙurawa amma ta kasa tashi, hakan yayi matuƙar bata mamaki ganin duk jikinta ya saki lokaci guda, nan take ta fara zargin akwai abinda taci ko tasha wanda ya haifar mata da haka, tunawa da ta barwa Jamila girki yasa zarginta ya faɗa akan ta saka mata wani abu a abinci wanda hakan ya hasko mata an shirya mata gadar zare, kaico ta fara yi da dana sanin sakaci da tayi na sakewa da Jamila lokaci guda, tunda tasan su Hauwa ba son zamanta a gidan suke yi ba. Binafa ce ta fara cire hijab ɗinta ta yasar a ƙasa, itama Hanan haka tayi jikin Sameeha ya fara rawa domin ta gane inda suka dosa, idan sun kai hannu jikinta sai ta ɗago hannu ta ture tana ƙoƙarin kai musu duka sosai suka yi mamakin jarumtarta sai dai sun bayar jininta yana da ƙarfi, Hanan ta kaiwa hannunta duka. Wlh ko kinƙi ko kinso sai mun huta dake. Shegiya sai shegen kyan jiki. Binafa ko kinji yadda fatarta ke da silɓi. Hmmm cikin hutu take ba dole komai yaji ba. Ta bata amsa hakan yasa suka fara kokarin cire mata rigar barcin amma Sameeha ta hana su ta shiga kokawa da su duk da tana a kwance. Aminu. Motarsu ta tsaya a bakin gate ya sauko tare da briefcase ɗinsa ya juya yana cewa driver. Ka tafi da motar ka nimo mana mai cikin daren nan koda na black market ne, dole ya kasance mun samu full tank nasan kuɗin dana baka zai isheka, saboda da ƙarfe bakwai nake so mubar garin nan. Da anyi asuba ka zo. To yace masa sai ya wuce shi kuma Aminu ya buga gate mai gadi da ya fara gyangyaɗi a benci ya tashi firgigit ya zo jikin gate ɗin bai buɗe ba ya shiga tambayar waye, Aminu yace. Ka buɗe mai gidan ne. Nan take mai gani ya gane muryansa cikin sauri ya buɗe ƙaramin ƙofa ya shiga, yana kokarin jan gate yace ya barshi ba da mota yake ba, Mai gadi ya kwaso kaisuwa Aminu ya amsa kana ya wuce, daya ƙarasa falo kamar zai yi nocking dan yasan lokacin sun rufe kofa amma sai ya fasa ya kama handle ya murɗa sai ya samu a buɗe yake, cikin mamaki ya shiga ganin falon ma da haske basu kashe wutan ba, sai ya wuce center table ya aje jaka da wayoyinsa ya nufi ɗakin Sameeha direct dan yasan yanzu haka barci ne ya kwasheta duk bata yi aikin rufe ƙofa da kashe wutan data saba yi ba. Yana murɗa handle ya faɗa ɗakin, ganin mata akanta ɗaya tana ƙoƙarin cire mata rigar barci ɗayan kuma tana yi mata kiss a fuska, sai yaji gabansa yayi mummunar faɗuwa ya saki salati da ƙarfi tare da. Innalillahi wa inna ilaihir raji'un. Ya cigaba da maimaitawa sai ya juya da sauri ya bar ɗakin, zaman dirshen yayi a tiles daga gefen kofan ya shiga rusa kuka kamar an yi masa mutuwa, daga bisani ya miƙe da kyar ya koma cushing ya zauna kansa sai sara masa yake yi ga numfashinsa da yake yin wani irin fita cikin huci. Su Binafa duk da kusan tarkonsu ya kama kurciya sai da suka tsorata dan sun gane mai gidan ne, kuma basu ji daɗin dawowarsa yanzu ba dan sun so sai sun samu biyan buƙatar su akan ta. Beb plan ɗinmu ya faɗa amma bamu samu biyan buƙata ba, gashi ko kaya bamu cire ba balle ya yi zargin ta sosai. Cewar Binafa kamar zata fasa ihu, Hanan bata ce komai ba ta sauko jikinta yana rawa ta ɗauki hijab ɗinta ta saka, Binafa itama ta saka Hibab suka fito falo nan suka ganshi zaune ya dafe kuncinsa da hannu biyu yana hawaye. Koda yaji fitowarsu bai ce musu komai ba sumsum suka wuce dakin Jamila suka ɗauki tarkacensu suka fito, Jamila tana biyosu a baya, ganin Aminu yasa taja wani mugun burki ta koma da baya ta shige ɗaki ta saka key ta rufe ta shiga tsananin tashin hankali da tsoro ganin asirinsu ya tonu tunda ya dawo ya gansu, bata san cewar su a cikin tsarinsu hakan dama suke so ba, ta zauna a tile dirshen ta soma kuka tana ta shiga uku asirin ta ya tonu. Su Binafa har sai da suka kawo ƙofar fita suna tunanin zai dakatar dasu amma sai suka ga bai ce musu komai ba sai suka fice. Suna fita cikin zafin nama ya miƙe ya banko ƙofar ɗakin Sameeha ya sameta shurum a kwance kamar yadda suka barta, duk da rigar barcinta yana jikinta babu wani alamun sun taɓata, hawaye kawai take zubawa domin ta gama sanin makirci aka haɗa mata, damuwarta me ya dawo da Aminu a yanzu? Sannan duk abinda zata faɗa masa ba zai taɓa yarda ba. Aminu zaman dirshen yayi a ƙasa jikin ƙofa dan yadda ya ganta ya ƙara kashe masa jiki, sai ya soma cewa cikin kuka. Sameeha sai da nace miki ki bari na sauwaƙe miki kije ki yi aurenki dan nasan ba lallai ki jure ba, kika ce zaki jure gashi yanzu na zo na kamaku kuna kokarin aikata mummunar ɓarna, nasan nima ina da laifi da tun farko na haƙura da ke da hakan ba zai same ki ba. Kin yi mini halacci kin jure na tsawon shekara shida ban kusance ki ba. Yanzu ne na tabbatar da dalilinki na ƙin bina Abuja, zan shedeki cewar da muna Lagos ba kya aikata komai nan ɗin ma baki daɗe da faɗawa wannan halakar ba ƙila, tun kafin lamarin yayi nisa ki kasa auren namiji gwara na sake ki akan ki faɗa tarko lesbian, dan mugun abune mai wuyar wahalar warkewa, mummunan fasadi ne da Allah ya halakar da mutanen Annabi Luɗ a.s. Batun yara Allah zai raya mana su zan kula da tarbiyyansu, dan ya zama dole mu rabu domin matsalata ba tada magani kullun cikin nima nake amma har yau ban dace ba. Da matsanancin kuka ya ƙare maganar yana shassheƙa, itama Sameeha kukan take mai tsanani dan baƙin ciki, tama kasa magana gashi jikinta yayi nauyi ba zata iya tasowa ta matso kusa da shi ba, Aminu ya cigaba da cewa. Rabuwarmu shine kawai mafitarki Sameeha, bana fatan ranar tashin ƙiyama ki tashi cikin mutanen da Allah zai hukunta, ina fatan duk mu kasance a aljanna, a dalilina bazan bari rayuwarki ta salwanta ba bazan bari ki wulaƙanta ba, zan sadaukar da soyayyarki domin kuɓutar da ke daga halaka, ina sonki Sameeha amma dole zan haƙura domin na fitar dake daga cikin gargada da zullumi. Wannan maganar ta zama sirri bazan taɓa faɗawa wani wai akan dalilin na kamaki kina lesbian ba, domin ni nasan ba halinki bane, zan sake ki ne akan dalilin kuɓutar dake daga faɗawa halaka tunda har kin fara kawo mata gidan nan, nan gaba ina tsoron ki faɗa zina duk da ina da kyakkyawar yaƙini akanki. Dan Allah! dan Allah Aminu karka sake ni wlh ba abinda kake zargi bane shirya mini aka yi. Ta faɗa cikin matsanancin kuma muryanta cikin sanyi da kuma sautin maye. Sameeha har abin maye kike sha? Waye ya sauya min ke kika zama haka, ashe In bana nan ɓarna kike yi ban sani ba.? Innalillahi wa inna ilaihir raji'un. Ya ƙara fashewa da kuka, wannan karan jikinsa har rawa yake yi duk ya fita hayyacinta, ya cigaba da magana cikin matsanancin kuka. Abin da ciwo Sameeha, na sakeki Sameeha, na datse igiyar aurenmu guda uku wannan shine kawai adalcin da zan iya yi miki, idan ba haka ba nan gaba za a samu matsalar daga ni har ke mu shiga wuta, zanyi nesa dake ta yadda ba zaki sake ganina ba nima bazan ƙara ganinki ba. Nasan muna yiwa juna wani irin so, amma lokaci yayi da dole haƙuri shine zai zame mana magani. Rabuwar mu da ciwo amma a hankali zamu saba. Sameeha wani ƙara ta saki da bata san sanda ta ari jarumta ba ta mulmulo ta faɗo ƙasa tim tana kokarin jan jikinta zuwa gare shi, amma Aminu ya miƙe da sauri yana wani irin kuka mai gunji, jijiyoyin kansa har sai da suka bayyana ɓaro ɓaro, jikinsa kuwa rawa yake yi ga wani sanyi daya ji yana shigarsa, nan take zazzaɓi ya kama shi ya wuce ɗakinsa da sauri ya rufe ƙofa ya faɗa doguwar kujera ya kankame jikinsa yana ci gaba da kuka. Sameeha ihu ta shiga yi tana faɗin ta shiga uku tare da cewa. Innalillahi wa inna ilaihir raji'un. Shikenan sunyi nasarar rabani da kai Aminu, Wlh ba abinda kake zargi bane ban taɓa aika mummunar abu ba ina kokarin riƙe maka mutunci na, na yarda da cewar ko wace cuta da maganinta, wanda hakan yasa na keɓe sha'awa ga komai, domin nasan watarana zaka warke. Hauwa me nayi muku haka da zafi? dama kince ba zaki taɓa sona ba kin tsaneni. Na shiga uku naaaa. Ta ƙare maganar tana cigaba da kuka sannan tana kwance a ƙasa, wanda a lokacin ma ta saki fitsari dan ba zata iya kai kanta bayi ba, jikinta rawa yake sosai ga wani zazzafan zazzaɓi ɗaya rufeta, kuka take mai gunji da ihu tana kwalawa Aminu kira. _Masoyana... Masu maganar dan Allah kar auren Sameeha ya mutu, kar ku manta ko wani aure rai ne da shi idan har hakan yana cikin ƙaddarar mace duk yadda takai ga takacancan sai ya rabu ko kuma mutuwa ta raba. Sannan Sameeha tayi sakaci da abu uku na farko Addu'a, na biyu tayi saurin sakewa da su Hauwa ga yadda suka nuna mata kiyayya ƙiri ƙiri, duk wanda yace baya sonka to wlh in ya dawo yana sonka akwai dalili, maƙiyinki duk yadda kaso burgeshi wlh in dai yace saiya ga bayanta to ba zai taɓa kyaleka ba koda kullun zai faɗi ba zai fasa ba. Sannan abu na uku ta yi saurin yarda da Jamila har take bata aikin girki ta saka mata hannu, wanda tana da tabbacin agent ɗin su Hauwa ce. So tari makashinka yana tare da kai. Kuyi haƙuri haka labarin yazo na tabbatar muku akwai happy ending In Sha Allah._ [7/7, 13:04] Buhainat😁: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shaidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.* 19. Sameeha ganin ba sarki sai Allah yasa ta fara ambaton istigafari da salatin Annabi s.a.w hawaye yana bin kuncinta, ta ɗauki kusan minti talatin a haka kafin ta iya ƙarfin hali taja jikinta zuwa bayi sai ta buɗe ta rarrafa ta isa ciki ta haɗawa kanta ruwan wanka ta shiga cikin baho, a hankali ta zame rigar jikinta ta gyara zama tare da yin lamo a cikin ruwan, sai barci ya fara fusgarta tare da jin zafin ruwan yana ratsata, ta ɗauki kusan minti ashirin a cikin ruwan dan har saida ya fara rage zafi, tana ƙoƙarin fitowa taji sallamar Hauwa ta shigo ɗakinta, dam dam taji ƙirjinta ya buga tana jan salati a zuciyarta, sai ta koma cikin ruwan tayi lamo dan bata san me zata yi ba a wannan lokacin ga jikinta sam ba ƙarfi. Su Binafa suna fita suka kira Najwa suka sanar da ita komai, cikin tsananin farin ciki ta shiga zuba musu godiya tace zata zo gobe su haɗu dan suyi murna a tare, bayan sunyi sallama sai ta kira Jamila har wayan ta tsinke bata ɗauka ba a kira na biyu ne Jamila ta rarrafa ta ɗauki wayar dake kan gado ta ɗauka tana sasshekar kuka tare da cewa. Alhaji ya dawo asirinmu ya toni shikenan kin ja mini matsala na shiga uku. Dalla kiyi mini shuri, waye yace miki asirinmu ya tonu? to haka tsarin aikin yake domin burinmu Aminu ya dawo ya kama Sameeha da waɗannan matan, kuma buƙata ta biya dan da safe zamu ji labarin ya saketa. Yanzu ina so ki kira wayan Yaya Hauwa ki shaida mata gidanku ba lafiya Aminu ya dawo kinji sunata rikici. Idan kin yi haka to aikinki ya kammala, kuma da wuri zan kawo miki cikon dubu sha biyar ɗinki, dan Binafa tace ta ƙara miki dubu biyar. To to Jamila tace cikin tsantsar farin ciki dan sai yanzu ta gane sharri suka ƙullawa Sameeha, duk da bata ji daɗin haka ba amma ya zata yi tunda kuɗi ta fito nima kuma ta same su. Wayarta ta shiga dubawa ta danna number ɗinta Hauwa tayi mata flashing, ta riƙe wayar tana jiran ta kirata, bayan kamar minti goma sai gashi ta kirata ta daga da sauri, Hauwa tace cikin ƙasa da murya kamar ma ta fara barci. Lafiya kike kirana cikin daren nan? Hajiya ku zo gidanmu wlh ba lafiya Alhaji ya dawo sunata rikici da anty Sameeha. Hauwa bata iya cewa komai ba ta kashe wayar tana dirowa daga kan gado, ai zama bai ganta ba dan har wani farin ciki ta fara ji tana addu'ar Allah yasa ma ya saketa su huta, agogon wayarta ta duba sai taga ƙarfe goma da minti asirin, farin cikinta mijinta baya nan dan tasan da yana gari bata isa ta fita ba a wannan daren, hijab ta zura ta fito falo tana yiwa Jamilu magana me bima Adama, akan zata je babban gida ta dawo yanzu, to yace mata dan hankalinsa yana kan kallon tv da yake yi. Hauwa tana isa gida sashin Kamalu ta fara isa ta buga masa kofa Sa'a ta buɗe sai Hauwa tace ta kira masa Kamalu, da yake yana falon sai ya miƙe ya zo ƙofar, ssi tace tazo ne zasu yi magana sai ya fito suka matsa can gefe, Sa'a ta koma ɗaki, nan Hauwa ta karanta masa abinda 'yar aikinsu Sameeha ta faɗa mata, cike da mamaki yace. Anya kuwa? Ya ce mana gobe ne zai dawo, amma bari na kira yaya Alhasan muji. Sai ya ciro wayarsa da ya ke aljun jallabiyarsa ya dannan number din Alhasan, yana ɗauka yace ya fito tsakar gida za suyi magana yanzu. To yace ya kashe wayar Laure tana lafiya yake nimansa cikin dare, yace shima bai sani ba sai ya fita zai ji. Da ya fito ya yi mamakin ganin Hauwa a lokacin nan ya tambayesu lafiya? Hauwa ta koro masa bayani, sai ya ɗaga wayarsa ya kira Aminu sai dai duk kiran da yayi masa baya shiga, sai yace Kamalu ya fitar da motarsa suje gidan su gani, dan sosai suma hankalinsu ya tashi. Wajen sha ɗaya da minti biyar suka iso ƙofar gidan a waje Kamalu yayi parking suka fito Hauwa ta buga gate mai gadi ya tambaya su waye sai Alhasan yace sune, ganin ya gane muryansu ya buɗe musu suka shiga, shima yayi mamakin ganin su sai ya bisu da Allah yasa lafiya a zuciyarsa, da sallama suka shiga falon amma ba kowa ga wayoyin Aminu da jakarsa, hakan ya basu tabbacin ya dawo, sai Kamali ya wuce falon Aminu yana buga ƙofa, itama Hauwa ta wuce ɗakin Sameeha ta tura kofa tana sallama, jin ba a amsa ba kuma ba kowa data gani a ciki ta fito falon tana cewa bata ga kowa a ɗakin Sameeha ba, Aminu dake kwance yaji buga gate sai dai bai tsammaci 'yan uwansa bane a wannan lokacin, jin muryansu da yayi a falo yayi matuƙar ɗaga masa hankali amma sai ya yi sauri ya miƙe ya shige bedroom ɗinsa ya cire kayansa ya zura jallabiya ya wanke fuskarsa a bayi, ya fito falonsa kenan sai ga Kamalu ya shigo suka yi kiciɓis suna kallon juna, yanayinsa kawai da Kamalu ya gani ya tabbatar da ba lafiya ba, sai ya juya Aminu yabi bayansa zuwa falo ya tsaya kamar yadda ya gansu a tsaitsaye sunyi cirko cirko suna zuba masa ido, Alhasan yace cikin damuwa. Aminu meke faruwa ne? Ina Sameeha? Hauwa ta leƙa ɗakinta bata ganta ba, ita take sanar damu wai mai aikinku ce ta kira ta ta sanar da ita gidan ba lafiya. Saɓani na samu da Sameeha kuma na saketa ta wuce gidansu. Ya samu basu wannan amsar jin basu ga Sameeha a ɗakin ta ba, yasan tana cikin gidan bata fita ba ƙila tana bayi ne, addu'arsa Allah yasa har su tafi ba zata fito ba dan baya so su ganta cikin maye, salati duk suka haɗa baki suna ambata, Alhasan yace cikin faɗa. Kana da hankali kuwa Aminu me Sameeha zata yi maka yarinyar da take da mutunci da hankali har ta cancanci Saki? wlh ka bani mamaki, anya kana cikin hayyacinka? Yaya ina da dalili kuma itama sakin ta ga ya fi mata, dan haka dan Allah ku fita daga cikin maganar nan. Wlh ba kai bane Aminu an sauyaka domin Aminunmu da na sani yana matuƙar son Matarsa wanda zai ita aikata komai akan farin cikinta, kodai ka fara haɗuwa da matan banza sun fara hure maka kunne ne. Cewar Kamalu kamar zai rufe shi da duka. Aminu ya cije yace cikin dakiya. To ban isa na kula matan bane? kawai dai na gaji da ita ina buƙatar hutu taje gidansu ta huta nima na huta tunda saki ɗaya nayi mata ai ba yawa. Alhasan ne ya sauke mata kyakkyawar mari yana cewa. Dan ubanka mu zaka faɗawa haka ashe ka fara shaye shaye bamu sani ba, to wlh baka isa ka jawo mana abin kunya ba dole goben nan In Sha Allah zamu je ka dawo da matarka, kuma idan na bincika ka fara bin matan banza sai nayi matuƙar saɓa maka sha sha sha, ina yi maka kallon mai hankali ashe mutumin banza ne kai. Ko me zaku ce kuce kuma ko me zaku mini ku mini amma wlh bazan dawo da Sameeha ba na gama yayinta, ku barni na wataya naji daɗin duniyata, shiyasa na sauwaƙe mata dan na rage nauyinta akaina yadda zan more rayuwata. Kuma nan gaba kadan aurena zan yi da wacce ta dace dani. Innalillahi wa inna ilaihir raji'un. Alhasan da Kamalu suketa ambata jikinsu sosai yayi sanyi da furucinsa dan gabaɗaya sun bayar ko asiri aka yi masa dan sam ba Aminunsu bane, shi kuma Aminu da gangan yayi haka domin ya bada laifin sakin akansa dan ya rufawa matarsa asiri ya dauki laifin gabaɗaya, Hauwa kuwa wani mugun farin ciki take ji dan gani take yi kamar asiri wata budurwarsa tayi masa suka samu galabar rabashi da Sameeha, sai ta nisa tace. Yaya da alama anyi masa asiri ne dan baya cikin hayyacinsa, ni wlh duk wacce tayi wannan aiki ta yi matuƙar burgeni domin ta yi nasarar karya kadarin Sameeha, dan wlh itama ba ƙaramin asirin mallaka take yi masa ba, ku kuke ganinta mutumiyar kirki amma tuni ta gama da Aminu shiyasa bayi da zance sai nata, dan haka godiya za muyi ga Alkah daya kuttoshi daga hannun Sameeha, itama wacce ta asirce shi Allah bazai bata nasara ba dan nima masa magani za muyi har Allah yasa ya dawo hayyacinsa ya samu matar kirki ya aura, dan tuntuni nake masa hangen wata yarinya ɗiyar mutunci, amma saboda nasan halinsa zai bani kunya shiyasa nayi shuru ban faɗa ba, kuma Sameeha ba zata taɓa barinsa ya ƙara aure ba. Idan baki yi mini shuru ba sai na ci mutuncinki Hauwa, ai dama nasan soyayyar da kika dawo kina yiwa Sameeha na dole ne dan munfi karfinki, kuma ki kuka da kanki. Cewar Kamalu, Aminu mamakim furucin Hauwa kawai yake yi amma lokaci yayi da shima zai yi maganinta cikin ruwan sanyi, sai yace. Yaya dama kin san Sameeha asiri take yi mini kika yi shuru? amma kin cuceni zumunci bai ce haka ba, aikuwa tunda naji haka na ƙarasa saki biyun ya koma saki uku wlh na saki Sameeha saki uku ko duniya zata haɗu akaina ta saku, kuma ina maraba da duk wacce zaki kawo mini domin nasan ba zaki taɓa yi mini zaɓin banza ba. Kaci ubanka Aminu lallai na yadda ba kada hankali, to bata saku ba tunda ba a hayyacinka kake ba. Alhasan ya faɗa kamar zai ƙara marinsa, Aminu yayi murmushin daya fi kuka ciwo. Wlh Tallahi Billahi ina cikin hankalina kuma na saki Saneeha saki uku ko kuso ko kar kuso na gama yankewa kaina hukunci tunda ba kune zaku zauna min da ita ba, rayuwata ce hakan shine yafi mini. Yana gama faɗar haka ya juya ɗakinsa ya shige yana mai rufe Kofar da key ya zauna dirshen jikin ƙofa yana yin wqni marayan kuka mara sauti, shi kanshi yasan yayi jarumtar yi musu rashin ɗa'a da bai taɓa yi musu irinsa ba, hakan shine kaɗai mafitarsa domin ya ɗaurawa kansa laifi kowa yaga baƙinsa akan asirin Sameeha ya tonu. Hauwa kuwa kamar ta fasa guɗa dan mugun farin ciki domin hakan ma ya bayyana karara a fusarta, a fusace Alhasan ya bar gidan Kamalu ma yabi bayansa Hauwa kuwa sai da tayi wani rawa da duwawu kafin tabi bayansu tana shanye farin cikinta dan kar faɗan ya dawo kanta tasan halinsu sosai. Sameeha duk taji taƙaddamar da ya faru dan lokacin data ji Hauwa ta fita daga ɗakin ta yi saurin fitowa da bin bango ta zura jallabiya, sai dai lokacin data ji suna magana ta tsaya jikin ƙofa ta gama saurarensu, kuka kawai take yi yadda taji Aminu ya ɗaurawa kansa laifi kacokan, tasan tayi rashin miji mai matuƙar sonta da son farin cikinta, Allah ya isa ta shiga ja ga duk wanda nayi nasarar rabata da shi, sai da suka tafi kafin ta buɗe ƙofar ta isa ɗakin Aminu tana bugawa, miƙewa yayi ya buɗe, yana ganinta yayi saurin bata hanya ta shigo sai ya rufe Kofar yana cewa. Su Hauwa basu ganki ba ko? nace musu kin je gida. Ban fito ba sai da suka tafi. Ta faɗa cikin sanyin murya, sai ta tsuguna akan ƙafarta ta fara kuka tana cewa. Wallahi Tallahi Billahi Amimu bansan waɗan nan matan na, bani ce na gayyato su suka zo ba, ban san waye ya shirya mani wannan gadar zaren ba, ban taɓa aikata wani masha'a ba saboda kore sha'awa ta ba, a karan kaina ban taɓa biyawa kaina buƙata ba. Dan Allah ka yarda dani ka janye sakin daka yi mini. Aminu shima durƙusawa yayi a gabanta yana kuka yace. Sameeha na riga na gama yanke mana hukunci wanda nasan hakan shine dai dai, kuma na yarda dake baki aikata komai ba domin maganganun Hauwa ya saka mini shakku da zargin wani abu, mu barwa Allah In Sha Allah Allah sai ya bayyana gaskiya. Idan kinje gida ki sanar dasu nine na sauya na fara shaye shaye dabin matan banza, to da kika mini magana shine na fusata na sakeki bana son kowa yasan asalin matsalarmu Sameeha. Idan na ɓoye wa kowa to wlh bazan ɓoyewa umma ba, kuma bazan taɓa iya yi maka wannan sharrin ba, Allah yasa hakan ya zama mana alkahiri amma wlh Abin da ciwo a zuciyata wanda babu ranar warkewa. Nima Sameeha ciwon da kike ji nawa yafi naku, wannan ita ce ƙaddararmu Allah ya bamu juriya yasa munci jarabawarmu. Tashi ki koma ɗakinki dan yanzu babu igiyar aurena akanki, kuma ki kwashe kayan ɗakinki da kayan kitchen gaba ɗaya da kujerun falo, hatta abinci da komai na store na bar miki karki bar komai, yara kuma In an kwana biyu zan zo na ɗauke su. Yana gama faɗar haka ya miƙe ya wuce ɗakinsa, ya barta a tsugune tana rusa kuka, ta jima a gurin kafin ta rarrafa ta miƙe ta wuce ɗaki ta kwanta a gado, akan idonta aka kira sallar asuba, zuwa lokacin maganin ya fara sakinta sai dai jiri da bugun zuciya ke damunta, hakan yasa har taji fitar Aminu daga gidan ya kuma dawo bata iya tashi tayi sallah ba, sai wajen shida na safe ta tashi da kyar ta shiga bayi dan ji take kamar iska na ɗibarta saboda ramar data yi a dare ɗaya, wanka ta sake yi da ruwa mai zafi sai ta ɗauro alwala ta fito ta gabatar da sallar asubahi a zaune, data idar ta cigaba da jan istigfari a zuciyarta ta ɗaura kanta a gefen gadon, a lokacin wajen bakwai saura matsin fitowar Aminu taji ta ɗauka ko zai leƙota amma shuru. Aminu ya fito cikin shirin tafiya yasha manyan kaya, shima har rama yayi dan idanunsa zun zurma, fuskarsa a ɗaure ya isa ƙofar ɗakin Jamila ya buga, Jamila da tun asubahi ta farka ta kasa fitowa dan duk taji abinda ya faru a tsakaninsa da 'yan uwansa, tayi mamaki sosai daya ɓoye ganin 'yan matan nan a gidansa, kanta ya ɗaure sosai ga yadda abubuwa suka faru sannan suka cukuikuiye mata kai, da kyar ta samu barci ya ɗauketa a dare, kiran sallar asubahi ya tashe ta dan ta saka alarm da ringing ɗin kiran sallah, ta kasa fitowa ne dan bata san da wani ido zata kalli mutanan gidan ba, buga ƙofar ta yayi matuƙar ɗaga mata hankali dan a zabure ta sauko daga kan gadon tazo ta buɗe, tana ganin Aminu ne taja da baya zata koma ciki ya daka mata wata uwar tsawa. Ina zaki koma munafuka, wato har kin iya haɗa munafurci ki kira Hauwa ki faɗa mata gidana ba lafiya ko, shiyasa ashe Sameeha tun farko taki yarda ki mata aiki ashe da gaskiyarta munafurci zaki haɗa mata, to maza ki haɗo kayanki yanzun nan na baki minti biyar ki bar mini gidana, in ba haka ba sai na saka 'yan sanda sun kamaki sun ɗaure ki har sai igiya tayi rara. Na shiga uku dan Allah Alhaji kayi hakuri yanzu zan tafi. Ta faɗa cikin rawar murya, ta koma ciki ta ɗauki jakar gana mazgo ɗinta da tarkacenta dake waldrob ta zuba a jaka ta ɗauki wayarta ta zura hijab ta fito, haka Aminu ya tasa ƙeyar ta har gate yace idan ta bari ya ƙara ganin fuskarta ko a hanya ne sai ya karya ta, kuma munafurcin da tayi tayi a kuɗin aikinta na watan dan bazai bada ba, Haka ta wuce tana kukan baƙin ciki dan sosai ta gama lissafin kuɗin da zata haɗa a watan in an biyata, ta shiga jan ƙafa da gana mazgo a kanta tama rasa ina zata mufa, amma ya zama dole ta nima Najwa dan ita kaɗai ce zata taimaketa, kuma a yanzu ba zata iya zuwa gun Hauwa ba dan gani take kila ba zata amsheta ba kuma tana tsoron ta haɗu da Amimu a can. [7/7, 13:04] Buhainat😁: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shaidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.* 20. Aminu ya koma cikin gida ya zaun falonsa ya rubutawa Sameeha takardan saki ukunta kana ya ɗauki abinda zai ɗauka ya fito falo ya aje mata takardan akan center table yasan zata gani ta ɗauka, sai ya fita zuwa ƙofar gate dan tuni mai motarsa yazo, ya buɗe mazaunin baya ya shiga ya zauna da bisimillah, nan take yaji hawaye ya cika masa ido tunawa da tare da Sameeha zasu tafi, sai ya shiga ambaton innalillahi... A zuciyarsa ya yi saurin share hawayen daya zubo masa tare da jin raɗaɗin rabuwa da matarsa wacce yake da yaƙinin ba zai taɓa samun kamar ta ba, a ganinsa sakin shine kawai mafita duk da ya yarda da rantsuwar da tayi masa akan bata aikata lesbian ba amma idan ya tuna yadda yaga 'yan matan a kanta sai zuciyarsa ta shiga gargada da shakku akan haka, shiyasa yaga rabuwarsu shine kawai mafi alheri. Ya gama yankewa ba zai ƙara aure ba tunda ba lafiya ce da shiba zai cigaba da rayuwa a haka har zuwa ranar da zai bar duniya, sosai zai inganta rayuwar yaranta domin su samu tagomashin duniya da lahira dan shi ne kaɗai gatan da zai nuna musu a yanzu, shiyasa ya yanke shawarar zai riƙe 'ya'yansa a hannunsa dan zai iya kulawa da su. Amma wani ɓangare na zuciyarsa kuma yana so ya kure tunanin Hauwa bisa takurawa rayuwarsa da tayi wanda yake ganin abinda take yi masa sam ba so bane face muzgunawa, shiyasa ya ce zai auri wacce tace ta samo masa, dan ya sakata cikin uku masifa kamar yadda ta addabi rayuwarsa data iyalinsa, lokaci yayi da zai nuna mata kurenta sannan ya samu damar haɗawa kwakwalwarta zafi dan sai ya gunnusa mata ya sakata a matsala, idan bai yi haka ba to bazai taɓa jin ya huce daka haushinta da yake ji ba. Wannan tunanin yasa shi tuna shekara shida baya daya wuce, saboda Hauwa itace ta zamo masa silar matsalar da yake ciki, duk da ƙaddararsa ce yazo a haka amma Hauwa ce sila. Shekara shida daya wuce... Lokacin Sameeha ta haifi Amrah da kusan mako guda dan sunyi taron sunansu a iya mutanen arzikin da suke hulɗa dasu a nan Lagos, ba wanda yazo daga kaduna saboda nisa da kuma yanayin tsadar rayuwa da mutane suka fara fuskanta a mulkin daya shuɗe, shiyasa kowa sai dai ya kirasu yayi musu barka, babu wanda ya aika musu da wani abin alheri sai umma itama kayan gyaran jiki ne da kuma kayan kuka daddawar miya da yaji, banda ita babu wanda yayi musu abu dan Aminu yace su barshi, Hauwa dama tace ita ba abinda zata bayar dan ƙarawa mai ƙarfi ƙarfi ne. Bayan kwana biyu da suna jikin mahaifiyarsu ya tashi sosai dan har an kwantar da ita a asibiti Aminu yaso zuwa amma suka ce ya barshi ta samu lafiya har an sallame su, to sai dai waya yake yi dasu akai akai yana jim jikinta dan har ita kanta umman tasu suna waya tana kwantar masa da hankali, hakan yasa Aminu ya saki ransa ya daina damuwa game da rashin lafiyar nata ya cigaba da harkan gabansa. Bayan kwana biyar da sallamo Umma a ranar ta rasu bayan sallar la'asar wanda ciwon dai ya kuma tashi kirji da haki da yake damunta, kafin sukai ga asibiti tace ga garinku nan, kuma hakan yayi daidai da sati biyu da haihuwar Sameeha. Aminu yana cikin mota zai je gida saboda ya baro office ɗinsu, ganin gosilo zai ɓata masa lokaci yasa shi sauya hanya yabi ta baya inda mutane basu cika bi ba saboda rashin kyawun hanyar, yana tsaka da tuƙi Hauwa ta kirashi kamar bazai tdauka ba sai kuma ya fasa dan ɗazun yaga miscall ɗin yaya Kamalu, bai samu kiransa ba ya bari inya je gida ya kirashi, kuma dama ya kirashi ne ya faɗa masa jikin umma ya tashi sai bai ɗauka ba, hakan yasa ya riƙe kan mota da hannu ɗaya ya ɗauki wayar da hannun dama, kururuwar kukan Hauwa yaji tana magana da ƙarfi. Aminu umma ta rasu yanzu nan, shikenan mun zama marayu ba Abba ga umma ta tafi ta barmu. Innalillahi wa inna ilaihir raji'un, kayi kokari kazo yau ku gana dan sunce kafin magrib za a kaita. Aminu wani abu yaji ya sara masa a kai ga wani bugu da zuciyarsa tayi wanda nan take ta tsaya cak ta daina aiki, wayar ma faɗuwa tayi Hauwa tanata helo helo ganin bai amsa ba ta kashe wayar, shi kuma Aminu motar tasa tafiya ta cigaba da yi wanda bai san halin da yake ciki ba, nan motar ta sauka a hanya taje ta daki falwaya daya kusa karyewa, yana dakansa fol ɗin ya faɗo kan motarsa hayaki ya fara fita daga injin motar, mutane sai ihu suke suna salati da kiran jesus, domin wani irin mugun hatsari ne ya auku wanda kowa ya sadakar wanda yake cikin motar ya mutu. An fitar da Aminu da kyar a cikin motar dan saida akayi kokarin daga falwayar kafin aka fito da shi jina jina baya ko motsi, haka aka kai shi asibiti cikin mutuwa ko rai. A takaice Aminu sai da ya ɗauki sati baya cikin hayyacinsa, saboda ya samu internal injury saboda jini ta hanci ta baki ya riƙa fitarwa. Ga karaya a ƙafarsa ta hagu sannan ga wani ƙarfe daya cakan masa mararsa wanda sai da aka yi masa ɗinki a gun, abubuwa dai masara daɗi ya wakana a wannan hatsarin. Sameeha a lokacin da labari ya isheta kamar zata yi hauka dan saida tayi kwana biyu bata san inda mijinta yake ba, office ɗinsu Aminu ta je a nan ne suma suka san ba a ganshi ba, dan suma sunta ƙoƙarin kiransa bai shiga ba. 'Yan office ɗin sune suka tsananta bincike har aka gano inda yayi hatsari tare da sanin asibitin da aka kai shi. Sameeha ta kira gida ta faɗa musu suma sun yi matuƙar shiga tashin hankali sosai ga mutuwar Umma ga kuma Aminu da ake cikin zullumin rasa shi, dan gaskiya Allah ya mufeshi da tsawon rai bisa tarin raunukan daya samu. Sai da yayi jinyar kusan wata biyu a asibiti wanda Kamalu shine ya kula da shi har aka sallamoshi suka koma gida, 'yan uwansa sun so su bar garin ya koma gida ya cigaba da jinya amma yace kar su damu zai yi a nan gidansa, haka suka tattara suka tafi Sameeha ta cigaba da kulawa da shi har tsawon wata shida a lokacin ƙafa ta warke sarai ya dawo lafiya sai tabo ne ya rage. Sai dai kuma baya tantance wari da ƙamshi saboda buguwar da yayi akansa sannan kuma ko kaɗan baya jin sha'awa, hakan yasa yaje asibiti ya ga likita inda likita ya tabbatar masa da buguwar da yayi a kai ne yasa baya jin ƙamshi da wari amma a hankali zai dawo, sannan ɓangaren sha'awarsa kuma ya tabbatar masa da akwai wata jijiya data samu matsala daga mararsa, domin tun lokacin da yayi accident suka bincika suka san haka sai dai sun ɗaurashi akan magunguna wanda suka yi zaton ya samu lafiya sai kuma gashi ya dawo musu, anan likita ya turashi scanning koda ya dawo da result sakamakon ya nuna ba wata matsala a jikinsa hakan yasa likita ya ƙara bashi antibiotics ya tafi. Aminu tun yana ganin lamarin da wasa har sai da ya tabbatar da babban matsala ce tunda ya kasa sauke hakkin Sameeha, rabonsu da ita tun kafin ta haifi Amrah, tausayi take bashi sosai dan tana yawan fama da ciwon mara, hakan yasa dole yake mata wasu 'yan dabaru ta dan samu natsuwa, Aminu ya shiga niman magani bana hausa bana turawa ba, duk maganin daya ji ya shafi matsalarsa zuwa yake ya amsa, sai da aka shafe shekara biyu a haka ba wani sauyi, dalilin daya saka kenan ya nima shawarar Sameeha akan su haƙurcewa juna ya saketa taje ta auri wani dan zamansu haka ba zai yuwu ba tunda ita ke cutuwa, Sameeha tace ita bata yarda ba tunda yana mata 'yan dabaru hakan yayi mata, sannan tana ƙoƙarin kiyaye shan duk wani abu da zai riƙa taso mata da sha'awa, shiyasa ta yakicewa kanta shan wani maganin mata ko ƙarin ni'ima, ganin ta dage masa yasa ya barta suka cigaba da zamansu tunda shima yaga babu wani damuwa a tare da ita kuma yana son matarsa. Sai dai lokaci zuwa lokaci sai yaji kamar babu adalci a cikin zamansu, ko ya yi mata magana rubutawa take yi akan ita zata ita rayuwa da shi a haka kuma ko wani cuta da maganinsa, in sunyi hakuri watarana zasu dace. Hakan yasa suka haka rami suka binne wannan matsalar ba tare da sun faɗawa wani ba balle ya kawo musu shakku ko miskilar fahimta ga zamansu ba, dan ko wani mutum da irin tunaninsa, Sameeha ko mahaifiyarta bata taɓa kuskuren faɗa mata ba balle 'yar uwa o ƙawa, har suka shafe shekara shida a haka sai a wanda a lokacin ne Aminu ya samu transfer zuwa Abuja, shine suka dawo kaduna suka tadda taraliyar data kawo sanadin rabuwarsu. Aminu daya kawo karshen tunaninsa sai ya kasa danne hawayensa dan yana matuƙar son Sameeha, ga tuna iyayensu da yayi, haka ya share hawayensa ya jingina bayansa ga mota ya rufe ido yana jin, duk abinda Hauwa tayi masa bai ga guda ɗaya daya nuna soyayya ce ba, tsabar son zuciya ce da ƙeta wanda yayi alwashin sai ya gwada mata shima, uwa ɗaya uba ɗaya suke amma sam kowa da irin halinsa. ***** Sameeha. Sai da ta tabbatar daya fita kafin ta miƙe da kyar ta fito falon dan duk taji yadda suka ƙare da Jamila, taso ta samu damar yiwa Jamila wasu tambayoyi dan sosai ta zargeta da saka mata wani abu a cikin abinci, sai dai bata samu dama ba tunda ya koreta, data fito falon kamar an ce ta kalla center table nan ta hango farar takarda, gabanta ya yanke ya faɗi dan tasan saki dai ya tabbata yanzu ta haramta ga Aminu, abu kamar wasa amma ta zama babba, ta isa gurin ta duka ta ɗauka sai ta samu kanta da zama a center table ɗin kafin ta buɗe ta karanta cewar ya saketa saki uku badan baya sonta ba sai dai hakan shine kaɗai mafita a garesu. Kuka ta fashe dashi mai sauti tana ambaton sunan Allah, sai taji Aminun ya yi matuƙar bata haushi dan duk halaccin data yi masa take hange, bai dace ya yanke mata hukunci irin wannan ba, gani take yi kamar har lokacin bai yarsa bata aikata lesbian ɗin ba, ya kamata ace shine mutum na farko da zai shaideta tunda tsawon shekara shida suna cikin wannan matsalar bai taɓa ganin haka daga gareta ba, sannan wayarta yasha amsa yayi amfani da ita bai taɓa ganin wani abu mara daɗi a ciki ba, dan ko film ɗin batsa bata taɓa kallo ba balle tace zata iya biyawa kanta buƙata, sai duk taji ta tsane shi da komai na gidan, kamar an tsikareta ta miƙe ta koma ɗaki ta zauna bisa daddumarta sai ta cigaba da istigfari, wajen takwas saura ta ɗauki wayarta data ɗaura bisa gado ta lalubo number ɗin Zaidu ta danna kira, yana gani ya ɗaga dan yana shirin yin wanka ne ya fita. Hallo hajiyar ƙanwata zinariyar danginmu, ya akayi kira da sassafe. Guntun murmushi tayi daya fi kuka ciwo tace cikin dakiya murya a sanyaye. Yaya Zaidu ina so ka zo gidana kaida Ikram yanzu, amma dan Allah karku faɗawa umma nan zaku zo, kayi kamar aikenta zaka yi. Me ya faru kuma? Ko su Hauwan sun sake yi miki wani abu ne? Yaya ba lokacin bayani a waya, sai dai in kun zo. Ok yace mata kana ya kashe wayan yana tunanin to meke faruwa, Allah yasa lafiya yace kana ya cire jallabiyarsa ya saka rigar wandon daya ke jikinsa ya fito daga ɗakinsa yana kwalawa Ikram kira, da sauri ta buɗe labulen ɗakin umma ta leƙo. Yaya Zaidu shirin makaranta nake yi fa, na kusa yin latti. Aiko yau ba zaki islamiyar nan ba saboda aikenki zanyi, wani saƙo zaki amso mini yanzu a can kawo cikin sauri. Yaya muna shirin jarabawa ne fa. Tunda ba jarabawar bace ai da sauƙi jeki sauya kaya ki fito yanzu, in kuma da uniform ɗin zaki je to sai ki saka hijab ina jiranki a waje. Zaidu bana son irin wannan fin ƙarfin fa, saboda me zaka hata zuwa islamiya iye? kai me zai hanaka kaje ka amso saƙon. Cewar umma data fito daga wanka, Zaidu ya shafa kai yana 'yar dariya. Umma wlh uzurine mai ƙarfi zanje yi shiyasa zan aiketa idan ta dawo da wuri sai taje makarantan tunda nan tashar kawo zata ba nisa. Dalla malama kije ki saka hijab kina ɓata lokaci. Ya ƙare maganar akan Ikram data tsaya tana sauraren maganarsu da Umma, da sauri ta koma ciki ko uniform ɗin bata cire ba ta ɗauki hijab ɗin makaranta tana gungunai dan sam bata ƙaunar fashin islamiya, ta fito tana cewa umma ba zata zauna ba yanzu zata dawo ta wuce makaranta, Umma tace sai da dawo tana kwalawa Abi kira akan yazo yayi wanka ta fito daga bayi. Ikram ta samu Zaidu ya tare musu napep yace ta shiga, sosai ta sha mamaki ganin tare zasu, sai da suka fara tafiya a hanya yake ce mata Sameeha ce ta kirashi akan suje gidanta kuma bata so umma ta sani tukuna, jikin Ikram yayi sanyi tace . Allah yasa dai Lafiya. Zaidu yace Amin sai duk suka yi shuru ko wanne da irin sakon da yake karɓa a zuciyarsa. Suna isa gidan Zaidu ya tsaya biyan mai napep ɗin Ikram ta rigashi zuwa gate ta buga, mai gadi ya buɗe musu sai suka shiga tare da gaishe shi, ya amsa fuska sake dan sosai suke burgeshi da irin gaisuwar mutunci da suke yi masa saɓanin dangin Aminu da suke yi masa kallon uku saura kwata, ya shaida tarbiyyansu sosai kamar yadda Sameeha ta tarbiyyantar da yaranta dan suma akwai gaisuwa da girmama na gaba. Da suka shiga falo ba kowa sai Zaidu ya zauna a cushing Ikram ta wuce ɗakin Sameeha tana buɗe ƙofar ta ganta zaune a dadduma ta ɗaura kanta a gefen gado, da sassarfa Ikram ta ƙarasa gabanta ta tsuguna tana cewa. Anty ba ki da lafiya ne? Sameeha ta kalleta cikin murmushi a fuskarta ga idonta yana ciko da kwalla. Ina yaya Zaidu? Ta tambayeta ba tare da ta amsa mata nata tambayar ba. Yana falo in kira shi ne.? Eh Sameeha tace a takaice, sai ikram ta miƙe da sauri ta fita ba jimawa suka shigo tare da Zaidu wanda shima cikin mamakin kiransa cikin ɗakinta yake yi, tunda matsayinsa na yayanta baida hurumin zuwa ɗakin kwananta in ba babbar lalura ba kamar yadda yake hasashe ba tada lafiya ne, suna shiga ciki Zaidu ya tsaya a kanta yana cewa. Sameeha me yake damunki kika zabge da rama haka lokaci guda? Ko gudawa da Amai kika yi jiya? Aminu bai dawo bane? Ya dawo jiya da dare ga sakon daya bar mini da zai fita. Ta miƙa masa farar takardan hannun ta, Zaidu da Ikram suka kalli juna ko wanne zuciyarsa cike da zullumin abinda ke takardan, Zaidu ya sa hannu ya amsa ya buɗe takardan ya soma karantawa, wani irin bugawa zuciyarsa tayi tare da sakin salati yana tasbihi ga Allah, Ikram data ruɗe ta shiga tambayarsa meke faruwa? ganin bai bata amsa ba sai salati yake yasa ta fisge takardan ta soma karantawa, wani irin jiri taji ya kamata wanda yasa dole ta zaune a gefen gadon tana jin tsigar jikinta yana tashi alamun aljanun jikinta sun motsa dan tana da su, kuka ta fashe da shi tana ambaton sunan Allah. [7/7, 13:04] Buhainat😁: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shaidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.* 21. Sameeha ta kallesu tana jin wani kukan baƙin ciki yana turnuƙota amma haka ta shanye tace cikin dakiya. Ƙaddarata ce da jarabawa, addu'a zaku taya ni da shi akan Allah yasa naci. Yanzu taimaka mini za kuyi na haɗa kayana na kwashe su kafin ya dawo gidan nan. Ko da yace ya bar mini kayan funitures ɗin ɗakin nan da kuma kayan kitchen da komai na falo, to Amma ni dai ba zan ɗauki komai ba face kayan sakawana da sauran abubuwan da suke muhimmi nawa. Meya faru Sameeha? ki faɗa mini laifin me kika yi masa daga dawowarsa ya sake ki. Kamani yayi da 'yan mata guda biyu muna masha'a shiyasa ya sakeni. Wani mugun zabura Zaidu yayi ya ƙara ja da baya yana nunata da yatsa. Ko duk duniya zasu taru akan wannan maganar wlh bazan taɓa yarda ba, na san wacece ƙanwata ba zata taɓa aikata barna irin wannan ba. Ki faɗa mini gaskiya kafin hannuna ya sauka a jikinki. Ya ƙare maganar a tsawace kamar zai daketa, a lokacin ne ta fashe da mugun kuka ta fara basu labarin tun dawowarta daga gidan kakansu da komai daya faru, dama zuwan da su Binafa suka yi ranar monday, nan take Ikram ta miƙe ta tsandara uban ƙara sai ta zube a ƙasa Aljanu sun tashi ta fara surutai akan makirci aka ƙulla mata, kuma na kusa da ita ne suka shirya mata haka kuma ba zasu yarsa ba sai sun ɗauki fansa, nan ta zabura ta miƙe zata fita da sauri Zaidu ya kamata ƙam ya kwantar da ita kan gado ya danne mata hannu da ƙafa ya soma tofa mata addu'a, faɗe suke. Kabarmu mu ɗauki mataki, ku barni nayi magana, ku bari na faɗa muku waɗanda suka aikata wannan aikin. Amma ina Zaidu yaƙi basu dama ya cigaba da addu'a, har sai da ya samu nasarar korasu kafin ta saki atishawa sai ya saketa ta tashi ta zauna duk jikinta yana yi mata tsami. Zata yi magana Zaidu ya hanata ya mayar da dubansa kan Sameeha. Kenan bai tsaya yaji daga bakinka ba ya yanke miki hukunci? kuma bai yi bincike ba kawai ya sakeki. Gaskiya Aminu bai kyauta mana ba yaci amanar yardan da muka yi masa. Ba wannan ne yasa ya sakeni ba. To akan menene yayi sakin? Akan tsawon shekara shida baya iya sauke hakkin aurensa akaina, saboda accident ɗin da yayi ya samu matsala wanda yanata niman magani har yau ba a dace ba, to shine ya sakeni akan wannan dalilin, saboda wai adalcin da zai yi mini kenan dan kar na faɗa aikata zina da ɓarna. Wani irin kallo Zaidu yake jifanta da shi wanda yasa ta sunne kai ƙasa tare da tsoron abinda zai ce. Dan ubanki kina cikin irin wannan matsalar baki taɓa faɗawa wani ba, ko umma data haifemu ai yaci ace tasan da maganar dan a tayaku niman magani, bansan meyasa kike da mugun zurfin ciki ba Sameeha, to ga abinda shurunki ya jawo miki, dan haka Aminu ba zai taɓa yarda ba amanarsa kike ci ba tunda yana da hujja, haka kurum ki kashe kanki abanza saboda namiji, gashi ai bai tsaya duba halaccin shekara shida da kika yi masa ba ya lafta miki saki uku lokaci guda bai tsaya bincike ba, kuma yasan tarin laifin nasa ne koda kuwa kin aikata haka. Kinga rashin wayonki ko, komai ki mayar dashi ba komai ba sai kace 'yar fari, sai ki tashi mu wuce gida dan wlh koda saki ɗaya yayi miki kin bar aurensa tunda shi bai da mutunci. Wlh yanzu haka rabon wasu yaran ne Allah ya kawo rabuwarku tunda kuwa inda lafiya lau ne da yanzu Amrah tayi ƙanne biyu, Allah yasa hakan shine mafi alkhairi. Ikram tace Amin wanda itama haushin zurfin cikin Sameeha take ji, haka suka miƙe suka fara haɗa kayanta, Zaidu yace tunda har shine yace ta kwashe kayan gidan, to wlh ba zasu bar masa ba sai sun ɗiba idan ta tashi wani auren tayi amfani dasu, Sameeha dai jinsu take yi duk jikinta a sanyaye itama yanzu take ganin laifinta na ƙin faɗar matsalar Aminu ga su Umma, wata ƙila da an tayasu niman magani, ta tabbatar da ta tafka wauta da kuskure,wanda hakan yanzu ya zame mata izina. Zaidu ya fita daga ɗakin yaje falo ya duba number ɗin wani abokinsa Sani, yana ɗaukan kiran ya tambayeshi ina zai samu motar kwashe kaya babba, Sani ya sanar dashi akwai wani a unguwarsu bari ya kira ya tambaya yaji ko yana gari. A haka suka rabu ya kashe waya ya koma ciki yana cewa. Ikram idan kin dawo dai dai ki tashi ki fara haɗa kayanta ki zuba su a kwati, ni bari naje naga kitchen ɗin na fara fitar da kaya dan a yau nake so mu kwashe kayan In Sha Allah ba zai dawo ya samu komai ba, dan magana ta ƙare da ba sauran igiya balle a tsammaci jiran ya mayar da ita. Kema Sameeha dauriya zaki yi ki tashi ki kama mata haɗa kayan dan hannu daya baya ɗaukar jinka, dole sai mun yi da jiki zamu kammala komai akan lokaci. Ikram ta miƙe tana cewa to Sameeha kuwa gyada kai tayi dan zama bai ganta ba tunda saki ya tabbata, Zaidu ya fice zuwa kitchen ya soma haɗa kaya yana sauke su daga kanta dan cewa yayi tas zai kwashe su tunda shi yace ya bar mata. Ba daɗewa sai ga kiran Sani sai ya ɗauka Sanin ke ce masa mutumin yana gari, sai Zaidu yace ya tura masa number ɗinsa suyi magana, Sani yace to sai ya kashe kiran bayan mintuna sai ga number ɗin mutumin ya turo masa, Zaidu ya yi copying number mutumin ya kirashi nan suka yi ciniki akan dubu goma zai kwashe kayan, sai Zaidu yayi masa kwatance yace in ya ƙaraso zai kirashi. Sun kai kusan ƙarfe ɗaya na rana suna aikin haɗa kaya, dan har mai motan daya zo shima ya saka musu hannu, sannan drivernsu shima ya taya su da mai gadi, nan suka tattara komai suka yiwa mai mota lodin farko sai suka tafi tare da Zaidu suka isa gida, da yake a gidansu akwai wani empty ɗaki da kuma garejin mota da umma ki zuba itace a da data yi yayin sayarwa, nan suka juye kaya tas umma tana tambayar lafiya? Zaidu yace sai in sun dawo tukuna, haka suka bar umma cikin tunani da zullumin meke faruwa tunda ta gane kayan daga gidan Sameeha ne, Haka suka ƙarasa kwashe kayan dakin Sameeha, har kayan store sun kwashe tas basu bar komai ba, dan a takaice sai da mai motan yayi sahu uku kafin Zaidu ya sallame shi, Ya amsa key ɗin motar Sameeha yace su fito su shiga su wuce, a lokacin ne Sameeha ta fashe da sabon kuka tana ƙarewa falonta kallon ƙarshe sai da Ikram ya kama hannunta ta jata kafin suka fice daga falon. Ta tsaya tana kallon mai gadi da driver. Nagode bisa ɗawainiyar da kuka yi Allah ya saka musu a mizani , ni zan tafi dan zamana ya ƙare a gidan nan yau, Allah ya sada fuskarmu da alkhairi. Sai ta cigaba da share hawayen dake gangaro mata, suma suka shiga yi mata fatan alkairi tare da yi mata jaje dan sosai lamarin ya taɓasu, basu ji daɗin abinda ya faru ba dan Sameeha tana matuƙar yi musu alkhairi, haka ta shiga mota Zaidu ya jasu suka wuce ko wanne ransa a jagule suka nufi gida, umma kuma tana can cike da damuwa da ƙosawar su dawo su amsa mata tambayoyin da suka cika mata zuciya, dan kwashe kayan Sameeha yayi matuƙar girgizata da tunanin ba lafiya ba, hakan yasa ko abincin rana ta kasa ci. ****** Najwa. Da tsananin farin ciki ta wayi gari kamar anyi mata babban kyauta, tana zaune a tsakar gida tana son yin wanke wanke data haɗa, dan so take tayi saurin gama aiki ta fita zuwa gidansu Nafeesa ta ɗauketa su je gidansu Binafa, sai ga kira ya shigo wayarta ta miƙe ta isa bambun ruwa data ɗaura wayar akai, ta ɗauka sai taga Jamila ce sai da ta ɗan yamutse fuska kafin ta ɗauki kiran, sai dai kuma ta yanke kiran nan ta tuna bata kira sai dai a kirata, Najwa ta shiga ɗakinta ta zauna a gefen gado kafin ta kira Jamila, tana ɗauka Jamila ta fashe da kuma. Anty Najwa Alhaji yau da sassafe ya koreni, tun ɗazun nake niman number ki yaƙi shiga zai yanzu. To ni da kika kirani yanzu me zan yi miki? Kuɗina zaki cikasa mini, sannan ba kince zaki cigaba da aiki dani ba in kin auri Alhaji. Hahaha ashe ke wawuya ce ban sani ba, kina tsammanin zan yarda dake ne Jamila? Bayan dake aka haɗawa 'yar uwata tuggu, na sani nan gaba ki haɗa baki da wasu a cuceni, ai sai dai kije ki nima wani aikin amma ba Najwa ba tunda ko auren ma ba a yi ba. Batun kuɗinki ki faɗa mini inda kike a yanzun nan zan zo na kawo miki sai ki wuce garinku. Yanzu abinda zaki ce dani kenan Anty? bayan nayi miki aiki domin cikar burinki. To ai biyanki nayi ko kuma Hauwa ce ta saka ayi aikin ba ni ba. Zaki faɗa mini inda kike ko sai na kashe wayata kiji a salansa. Najwa ta faɗa a ɗan tsawace, jikin Jamila da yayi sanyi da mamakin Najwa, sai ta faɗa mata inda take sai Najwa tace ta jirata a gun gata nan zuwa sai ta kashe waya, Jamila da mamaki yasa ƙafarta ta kasa ɗaukarta sai ta nima guri ta zauna tana jin ciwon abinda Najwa tace mata, wato kenan taci moriyar ganga ta yada korenta, haka ta rafka tagumi duk abin duniya ya isheta. Najwa kuwa aje wayar tayi ta fita ta fara wanke wanke dan ba zata fita yanzu ba dole sai tayi aikin gida da ta saba yi dan kar inna ta fara yi mata mita da faɗa, sai da ta gama aikinta tsaf ta shiga wanka ta fito ta shirya cikin doguwar rigar atamfa ta zuba hijab har ƙasa ta nima nikaf ta ɗaurawa fuskarta ta saka safa, cikin ƙanƙanin lokaci ta gama komai ta fito zuwa ɗakin inna ta ɗage labule tana cewa. Inna na wuce makarantar sai in na dawo. Najwa ba kince yau ba makaranta ba saboda musabakar da kuka fara, sai monday in an cigaba da yi. Inna kirana aka yi akan ana nimanmu a makarantar shiyasa zanje. To a dawo lafiya amma karki daɗe dan nima zan fita zuwa anjima. To tace mata kana ta saki labulen ta fita, sai da tayi tafiya mai ɗan nisa a ƙafa ta iske wasu 'yan shaye shaye dake a can sama layinsu, sai ta tsaya a gabansu tana cewa. Yane Lawali, ina so ka haɗani da yaranka guda uku zasu yi mini wani aiki yanzu. Najwan Inna ke ce kika wani ɓoye a cikin niƙabi, wani aiki za ayi miki? ai ko mi zai naje da kaina kin san ke tamu ce ta mutunci, tunda kina bani hamsin ɗari ina kashe yunwar cikina ba wani eh yane. Dariya Najwa tayi tace. To kwata kwata sau nawa na taɓa baka kuɗi? bai wuce sau biyu ba. To ai ni zuciyata bata mance alheri kuma duk mai bani ina yi dashi. Hakane to mu je in ka shirya sai ka ɗiba yara biyu, akwai wata yarinya da nake so ku bata tsoro ta yadda ba zata sake marmarin zuwa Kaduna ba. Angama ranki ya daɗe, amma fa zaki bamu na makari dan yasin yunwa nake ji banci komai ba tun safe. In dai wannan ne karka damu ina da nauyi. Ta faɗa tana yin gaba, sai Lawali ya nuna mutum biyu daga cikin waɗanda suke tare yace su tafi, sai ya yiwa sauran sallama akan sai sun dawo. Haka Najwa tayi gaba suna binta a baya kamar dai ba tare suke ba, Napep ta tare musu da suka iso titi ta zauna a gaba gefen mai Napap su kuma jeru su uku a baya sai suka wuce. Dai dai inda Jamila ta faɗa mata suka sauka sai tace mai napep ya jirasu tana zuwa sai ta juya tana dube dube, can ta hango Jamila tana zaune jikin wani gida, ta yi gaba su Lawali suna binta har suka isa gaban Jamila suka tsaya, Najwa ta ɗaga niƙaf, Jamila da sauri ta miƙe dan sai a lokacin ta gane ta. Anty Najwa ashe ke ce, tun ɗazu nake zuba idon ganinki. Eh wani uzuri ya riƙeni, muga wayarki. Najwa tace tana miƙa mata hannu, Jamila da bata kawo komai ba ta miƙawa Najwa wayar ta amsa ta buɗe bayan wayar ta ciro sim ɗinta, sai ta balla shi gida biyu ta jefar a kwata, kana ta goge duka number ɗin da yayi saving akan wayar kuma ta goge dialing call, Jamila data gama shan gubar mamaki sai ta buɗe baki tana kallonta ta nisa tace. Ya zaki karya mini sim? hakan me yake nufi? Saboda bana so ki ƙara yin waya da duk wanda kika san ya sanni. Sannan ma ina so ki sani yanzun nan zaki bar garin nan in ba haka ba zan saka a ɓatar dake saboda asirinmu ya rufu. Lawali ina so ku gargaɗeta akan karta sake zuwa garin nan, in ba haka ba kuka ganta kasheta zaku yi har lahira. Nan fa cikin Jamila ya ɗuru ruwa ta soma cewa cikin tashi hankali. Anty Najwa ya zaki yi mini haka, ban taɓa zaton haka daga gareki ba, ni ki bani cikon kuɗina in tafi ba sai kin saka sun tsorata ni ba. Kuɗinki ai kin gama amsa, dan dubu goman nan shine rabonki. Wlh baki isa ba ai ba haka muka yi dake ba, haka kurum kin saka nayi miki aiki kin sakani a shiga uku gashi an koreni, kin samu biyan buƙata an saki matar gidan, ai bai dace ki saka mini da butulci ba kuma Wlh... Bata ƙarasa maganarta ba taji saukar mari Lawali ya yi mata, kafin tayi aune sun rufeta da duka suna cewa ta isa ta ɗaga muryanta akan Najwa, sai da suka yi mata lilis tana ihu gashi babu masu ceto, dan unguwar shuru ba kowa sai tsilli tsillin mutane ke wucewa, Najwa ne ta dakatar dasu tana cewa. Lawali dukan ya isa haka, ina so ku saka mini ita a wancen napep ɗin ku rakata tashar mota ta shiga motar garinsu, kar ku baro gurin har sai motarsu ta bar tasha. Nawa zan biyaku. Haba ai ke ta gida ne ki bada ko nawa ne Hajjaju Najwa. Najwa ta saki murmushi ta buɗe jakarta ta dauko kuɗi ta basu dubu uku uku, sai ta basu dubu biyu su sallami mai napep, haka suka amsa suna godiya tare da washe baki dan rabonsu da su samu kuɗi irin haka sun mance, Jamila sai kuka take tsabar sun tsoratata ta kasa magana balle ta jerewa Najwa Allah ya isa da take ta yi a zuciyarta, Najwa ta kalleta tana murmushi. Duk randa naji labari kin zo garin nan saina saka an kashe ki, kin san dai zan iya saboda ni fuska biyu ce kuma ga shi kinga ɗayan fuskar da baki sani ba, nice nan Najwa ga sani ga Shagala ina iya komai akan duk abinda zai shiga hanyata ya hana mini farin ciki, dan haka ki shiga hankalinki. Tana gama faɗar haka ta mayar da niƙaf ɗinta ta wuce abinta, su kuma Lawali suka tasa ƙeyarta suka sakata a napep dan a tsakiyarsu ta zauna a baya, ɗayan ya zauna a gaba suka wuce tasha zuciyarta kamar ta faso ƙirjinta dan baƙin ciki, Najwa ta tsayar da ita gubar mamaki tayi mata lumbu lumbu ɗaukar mara sani, ashe ita kara da kiyashi ne, yanzu ta tabbatar da ta aikatawa kanta babban kuskure wanda ya sauketa a tashar dana sani, ga koshi ga kwanar yunwa, abubuwan data aikatawa Sameeha ne kawai ke yawo a zuciyarta gashi tun ba aje ko ina ba ta soma ganin sakamako, Allah baya barci kuma Alhaki kuikuiyo ne, ga mari ga tsinka jaka, sannan ga babu albashin watan ga babu cikon kuɗinta ga kuma kari da duka, ga kuma alhakin Sameeha data ɗauka duk ita kaɗai, da ace zata samu dama tabbas da kafin ta bar garin nan sai ta towana Najwa da Hauwa asiri ko wanne zakararsa tayi cara kwaɓarsu tayi ruwa, ta fasa kwan da duk zai bure kowa da wari tunda abin na cin amana ne da yaudara. Haka ta dinga saƙe saƙe har suka isa tasha suka sakata a motar garinsu Lere, basu bar tashar ba sai da motarsu ta tafi, Jamila ɗimbin dana zani da cizon yasha ya gama kashe zuciyarta, sai matsar kwalla take yi cike da tarin baƙin cikin abinda Najwa ta aikata mata. [7/7, 13:04] Buhainat😁: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shaidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.* 22. Najwa tana isa gidansu Nafeesa sai ta samu Binafa a gidan a she nan taje ta kwana saboda jiya dare yayi kuma bata son faɗan yayanta Bello shiyasa ta nufi gidansu Nafeesa dan ta saba yin haka, da farin ciki Najwa ta ƙarasa gefen gadon dakin ta zauna tana dariya. Gaskiya nayi farin cikin ganin ki Binafa anan, dama na zo ne domin naja Nafisa mu je gidanku. Ai a nan na kwana ma ban je gida ba. Ya kin samu labarin an saki Sameeha.? Cewar Binafa tana dafa kafaɗar Najwa cike da son jin ƙarin bayani. Jamila ta faɗa mini ya saketa amma har yanzu ban ji labari daga family ba tunda da ace inna taji zata faɗa mini. To yanzu meye abu na gaba tunda burinki ya cika Sameeha ta fita. Cewar Nafeesa cike da farin ciki itama a fuskarta, Najwa taja fasali kana ta miƙe tayi tafiya taku biyu ta ƙara juyowa ta tako ta tsaya tana riƙe kugu. Yanzu auren Aminu ne kawai ya rage mini inga ina kan matsayin Sameeha wannan shine cikar burina, mun riga mun takaitawa Hauwa hanya yanzu itace zata ƙarasa sauran aiki. Da kyau ta wajena mata a gidan Aminu ko ba fosta, kuma ko anki ko anso kin zama ne. Cewar Binafa ta ƙare maganar tana rafka guda. Ai babu abinda zance miki sai Allah ya saka miki da alkhairi ya biya miki duk kan buƙatunki. In Sha Allah idan na auri Amimu kuɗi suka zo hannuna sai nayi muku kyautar bazata, dan wannan aikin da kuka yi mini dole ne na biyaku da abu mai tsoka, yadda ba zaku manta dani ba kamar yadda nima bazan manta daku ba bisa wannan gagarumin aiki da kuka yi mini. Kar ki wani ji kin damu fatana ki shiga gidan ki samu kansa, idan kin samu natsuwa a lokacin sai ki sallame mu. Cewar Binafa, nan dai suka ci-gaba da hira wanda duk rabi akan shagalin bikin da zasu yi ne idan aurenta da Aminu ya tabbata. Kiran daya shigo wayar Najwa shine ya katsesu ta buɗe jaka ta ɗauko sai ta waro idonta waje tana ce musu. Wallahi Hauwa ce ta kira ni fa. Ɗauka! ɗauka muji me zata ce. Cewar Nafeesa cike da zaƙuwa, Najwa tayi gyaran murya kana ta zauna gefen gado kafin ta ɗauki kiran da sallama wanda har ya kusa katse wa, Hauwa ta amsa sai suka gaisa kana tace. Najwa na kiraki ne inyi miki albishir cewar Aminu ya amince da zai aureki, kuma nasan kin samu labarin ya saki Sameeha ko? Innalillahi wa inna ilaihir raji'un, yaushe? Me ya faru ya saketa? Wlh kadarinta ne ya karye duk asirin da take masa munyi nasarar ya bar jikinsa, shi da kansa yace ya gaji da ita har saki uku yayi mata abu kamar almara. Taf amma wannan abu da ban mamaki yadda yake mugun son Anty Sameeha ace lokaci guda ya saketa, anya ba wani laifin dai tayi masa ba ya saketa kuwa? Ya tabbatar mana da ba laifin da tayi masa shine dai ya gaji da ita ya saketa, alamu sun nuna kamar ya haɗu da wata mace ne ta nima rikita masa kwakwalwa da har ya saki Sameeha. Wayyo Allah banji mata daɗi ba wlh. Najwa tace cikin marairaice murya. Hauwa da ta ji haushin maganarta. Amma ban san ke sakarya bace sai yanzu, ke da zaki yi murna da rabuwarsu zaki aure shi, dan haka ki ma fara shiri Aminu baida wata mata sai ke dan ke tamu ce. To Yaya ina godiya Allah ya bar ƙauna ya saka miki da Alkairi, ina jin daɗin yadda kike mini kuma In Sha Allah zan miki biyayya bazan taɓa baki kunya ba. Amma naji daɗin furucinki Allah ya yi miki albarka idan komai ya daidaita zaki jini. Najwa ta yi mata godiya sai suka yi sallama suka kashe wayar, Najwa ta kwashe da dariya tana cewa. Da sannu kowai zai zama nawa, ai kunji hirarmu da ita, dan volume din wayata yanada ƙarfi ana ji. Munji komai sai dai basu san ke ce shegiyar da kika haɗa komai ba, amma nayi mamakin yadda ya ɓoye maganar ya kamamu da ita, mai yasa ya rufa mata asiri? wlh naso kowa yaji yadda zata sha wuya kafin ta auru, daga nan sai ta faɗa irin harkanmu gadan gadan. Cewar Binafa, sai a lokacin Najwa ta tuna da ya rufa mata asiri sai tace. Wlh nima banji daɗi daya rufe maganar ba, naso ace kowa yaji yadda 'yan uwansa zasu ƙara tsanarta. Amma kuma kun san dole yaso rufe maganar ko dan kare mutuncin 'ya'yansa. Cewar Nafisa, nan suka gasgata zancenta akan ya rufe maganar ne saboda yaransa, Najwa tace. Yo ni ko a haka kasuwa ta tashi ai ɗan koli yaci riba, koda bai fallasa ba buƙata ta biya, saura ƙiris dai na ganni a wannan tamfacecen gidan na zuba mulki na yadda nake zo. Kina wuta ƙawata ina binki da fetur. Cewar Nafisa sai ta bata hannu suka tafa, Binafa ta miƙe tana cewa zata yi wanka ta shirya ta wuce gida, sai ta shige bayi, Nafisa da Najwa suka cigaba da hirarsu cike da farin ciki. ***** Hauwa. Lokacin da suka baro gidan Aminu a hanya su Alhasan sai ɓaɓatu suke yi, rabin zancensu dai akan dole zasu nimawa Aminu maganin sammu domin sun gama yarda asiri aka yi masa, har suka isa ƙofar gidan Hauwa suka sauketa sai suka wuce gida. Hauwa da wani irin farin ciki ta shiga kamar an yi mata kyauta kujerar hajji, ta kasa rufe farin cikinta har sai da ta faɗawa yaronta maganar, yace Allah ya kyauta yanzu sai su aura masa wacce tasan darajan mutane, Hauwa tace. Ai tuni ma na samo masa dan da zafi zafi ake dukan ƙarfe, ba zama an saci ɗan ɓarawo. Wlh yadda nake ji kamar na zuba ruwa a ƙasa nasha, kadarin Sameeha dai ya karye munga ƙarshen rashin mutunci da fitsara. Ta ƙare maganar tana tafa hannu tare da 'yar dariya sai ta wuce ɗakinta ta zauna bakin gado ta lalubo number ɗin Adama, ta danna kira bata yi tunanin dare yayi ba haka, cikin barci Adama taji wayarta na ƙara a falonta, dan ta saka a chaji ta kwanta saboda basu ciki samun wuta ba a unguwarsu shiyasa bata wasa da saka chergy in sun kawo, kamar ba zata tashi ba mijinta Kamis ya juyo yana cewa. Ke Adama tashi kamar wayarki naji tana ƙara a falo. Wlh naji duk wanda ya damu da kiran ya ƙara kira da safe, yanzu kusan sha buyun dare fa. Kika san kiran mai muhimmanci ne gwara kije kiji. Ba dan ranta yaso ba ta fita falo wanda har kiran ya tsinke wani ya sake shigowa, a fusace taje ta ɗauki wayar sai dai sunan wacce ta gani yasa ta ɗan saki ranta tare da mamakin meyasa Mama zata kirata a wannan daren, kiran na gab da katse wa ta ɗaga tana cewa. Mama Allah yasa lafiya irin wannan kiran cikin dare, walh ina barci naji ƙara kamar bazan taso ba ashe ke ce. Adama albishir na kira nayi miki akan Aminu dai ya saki Sameeha saki uku. Kai dan Allah mama, me tayi masa haka? amma wannan labari ya min sugar. Nan Hauwa ta kwashe komai daya faru a gidan Aminu ta faɗa mata a takaice, Adama cikin tsantsar farin ciki tace. Ai dama ance ƙarshen alewa ƙasa wlh, aniyarta dai ta bita kuma Allah ya rabashi da auren wata mai kalar halinta dan bana fata a ƙara, ace mace sai baƙin hali da raina mutane tare da ɗagawa kamar wata ɗiyar gomna. Kuma 'yar gidan malam Shehu ce ba, ai ɗan talaka wani bai iya samun guri ba Adama, Allah dai ya kyauta sai da safe in kin samu shigowa to sai ki zo mu kyarasa maganar dan yanzu zamu fara fafutukar aura masa wacce muka zaɓa masa kafin ya tubure. Idan Kamis ya barni zan zo mama sai da safe. Cewar Adama tana kashe wayar sai ta saka a silent ta mayar chergy ta koma ciki, Kamis duk yaji hirarsu, data koma ciki yake cewa. Yanzu auren wata dan ya mutu ake kiranki a faɗa miki har kina murna, to naji kina inna barki zaki je? to ba inda zaki wlh. Haba Kamis mama ce tace naje fa, kuma matar kawuna ɗin nan da nasha baka labarinta ba tada mutunci itace aka saka. To Allah ya kyauta ya tsayar akanta, amma fa ba inda zaki bana son yawan fitar nan. Adama ta turo baki dan sosai take jin haushin wannan mulkin da yake zuba wa, dole zata nima maganin mallaka ta yi maganinsa. ayi namiki sai kafiya da gadara kamar mutanen farko, aiko zan yi maganinka. Tace a ranta tana gyara zama kwanciya. Hauwa kuwa a wannan dare barci ɓarawo ya kwasheta dan tsabar murna ta kasa sukuni sai tunanin yadda zata haɗa auren Najwa da Aminu kawai take yi. Koda gari ya waye taso taje babban gida da sassafe amma sanin 'yan uwanta basu fita aiki yasa ta haƙura har sai kusan goma na safe kafin ta isa gidan, a tsakar gida ta soma kwalawa Sa'a da Laure kira dan hirar bana cikin ɗaki ba ne, tasan sun jita yasa ta koma ƙasan bishiyar mangoro ta zauna a kan wata ƙaramar kujera data gani, ba jimawa Sa'a ta fito can sai ga Laure itama ta fito nan fa suka shiga gaisawa Laure tana cewa. 'Yar halak kinƙi ambato yo shiri nake na garzaya gidanki kika rigani, ashe dai anyiwa shafaffiya da mai checking out jiya. Wlh haka nima Kamalu yake faɗa mini duk hankalinsa a tashe da kyar yayi barci, ni ko barcina nasha cike da farin cikin an yi waje da ita munga ƙarshen wulaƙanci. Cewar Sa'a tana dariya, Hauwa tayi shewa tana tafa hannu. Daɗina da gobe saurin zuwa yau dai ƙaryar Sameeha ta ƙare, amma fa naso ace tana nan akayi bikin Salma dan taga yadda zamu tsaɓa ado ta gane ba ita kaɗai bace take shigar manyan atamfofi da leshi. Ke gwara da akayi haka kinga zamu yi shagalinmu a gidan ba tare da ta saka mana ido ba muyi yadda muka ga dama. Cewar Laure, Sa'a ta mele baki. Allah yasa ya bari muyi taron a can dan kun san dai halin Aminu murɗaɗɗen mutum ne. Yama isa ya hanamu shagalinmu a gidan, yo duk da gidansa ne ai muma muna da iko akansa dole ma ya barmu musha bidiri. Yanzu kunsan me nazo muku da shi so nake mu fara maganar bikin wannan yarinya Najwa da Aminu domin mu ƙara gunnusawa Sameeha ta haɗiye rai ta mutu dan ubanta. Kuma anjima nan zamu dira a gidansu su bamu yara dan bata isa tace zata riƙe su ba, koni zan riƙe 'ya'yan Aminu na basu tarbiyyar da ya dace. Ina bayanki wlh dan ƙafata kafarki tare zamu je mu yaga biradi mu yarda leda son ranmu, yo ai yanzu ne lokacin da zamu rama duk wani cin mutunci da tayi mana wlh. Cewar Laure tana tafa hannu, Sa'a ta riƙe haɓa tana cewa. Ni dai ba zani ba dan nasan Halin Kamalu sai ya huce haushinsa a kaina, amma badan shi ba wlh sai na je na bawa ido abinci naga idon mara kunya. Ai wlh ke ce kike bawa Kamalu dama yake yi miki mulkin mallaka, ki daina tsoronsa yadda zaki ji dadin rayuwarki, dan ni Wlh Alhasan bai isa ba ni da shi kar ta san kar ne, sai dai ya gama bambamin faɗarsa ya rabu dani. Gaya mata dai Laure dan na kula kan Sa'a har yanzu yana a murfi bata san kan dawon garin ba, kinga dai su 'yan uwana ne ko amma wlh ban goyi bayan ku riƙa jin tsoronsu ba ai maza ba a yi musu haka tunda ba bayi suka aura ba, dole sai kin tsaya tsayin daka kin karɓawa kanki 'yan ci. Ni yanzu Sa'a ɗauko tabarma ku zauna mu tattauna batun auren Aminu da yarinyar nan tun kafin yazo yace ya fasa. Ta kare maganar tana kallon Sa'a sai ta juya ta wuce ɗaki tana tunanin maganar da Kamalu yayi mata jiya da daddare akan ta kiyayi su Hauwa duk da yasan 'yar uwarsa ce amma yace ta fita harkansu ita da Laure, in ba haka ba sai sun sabauta mata aure tunda yasan ba alkairi suke shukawa ba. Taje dawo daga ɗauko tabarma ta shimfida suka zauna, a nan suka cigaba da hira har Hauwa ta yanke shawarar kiran Najwa akan tayi mata albishir, duk a kunnensu tayi maganar daga bisani ta yi sallama da Najwa suka ɗaura hira, sai wajen ɗaya suka tsaida hirar akan zasu yi sallah su tafi rafin guza gidansu Sameeha amso yara. Hauwa a ɓangaren Laure tayi sallah da suka idar sai da Laure ta dafa musu taliya dafadukan man ja suka ci wajen biyu da kwata suka fito suka tsaya Kofar ɗakin Sa'a suna kwala mata kira, tana jinsu ta shige bayi dan ba zata je ba ta jawa kanta matsala tunda tasan halin Kamalu da ɗaukar zafi, Hauwa tace su tafi tasan Sa'a ba zuwa zata yi ba saboda shegen tsoron Kamalu da take yi, haka suka kama hanya suna fita titi suka samu napep ya wuce dasu. **** Sameeha. Suna shiga gida umma dake zaune kan ƙaramar kujera a tsakar gida ta miƙe tana binsu da kallo har suka ƙaraso in da take suka tsaya cirko cirko umma ta rigasu da cewa. Meke faruwa ne? Kar dai zargin da nake yi shine ya tabbata. Sameeha me kika aikatawa Aminu da zafi haka har kika ƙure haƙurinsa? Umma da kin bari mun natsa sai ayi maganar. Rufe mini baki Zaidu kafin in saɓa maka, wato kai ubanta ba da ka tasa su kuka yi gaban kanku ni kun aje ni a gefe, saboda baku san darajata ba da baza ku nima shawarata ba ko. Umma ba haka bane dan Allah kiyi haƙuri muna gudun sakaki tashi hankali ne shi yasa muka yi komai bamu sanar dake ba amma tunda mun sawo zaki ji komai. Cewar Ikram da idonta ke kawo kallo dan a cikin sanyin murya tayi maganar, yadda umma taga yanayinta yasa ta yi shuru Sameeha kuma ta sunne kai kasa tana danne kukan daya ke zuwa mata. Zuwan Amrah da Abi suna yi mata oyoyo yasa ta fashe da kuka ta tsuguna a gabansu tana kallonsu tare da yin kuka mara sauti sai hawaye ke ambaliya da nishin kukan, suma yaran sai suka saka kuka suna tayata, umma kasa tsayuwa tayi ta koma kujerar da take zaune tana kallonsu duk jikinta a sanyaye, su Zaidu suna bawa Sameeha haƙuri tare da tunatar da ita akan tayi haƙuri ta karɓi ƙaddararta hannu biyu. Dan Allah ku fitar dani haske duk kun ɗaureni da jijiyoyina, ko dai Aminun ya rasu ne? Umma da rasuwa yayi ai sai dai mu tafi tare dake gidanta. Kuma da ma rauwar ne daya fi sauƙi. Cewar Zaidu daya samu guri ya zauna dan ya gaji da tsayuwa, Sameeha ta jaye yaran daga jikinta ta rarrafa zuwa gaban umma ta kama hannunta tana cewa. Umma ki yafe mini bisa rashin cika miki alƙawarin dana yi miki akan zama da Aminu duk wuya duk runtsi, wlh ba yin kaina bane mummunar ƙaddara ce ta faɗa mini wanda banda cumi banda dabara. Umma Aminu ya sakeni saki uku, haka ya rabu dani akan ya kamani da laifin da ban aikata ba, umma wai kamani yayi da 'yan mata muna masha'a shine yasakeniiiii. Ta ƙare tana maganar da matsanancin kuka kamar zata shiɗe, umma ta damƙi hannunta da ƙarfi jikinta yana rawa. Wlh ba zan taɓa yarda da wannan maganar ba domin nasan tarbiyya da nayi miki, ki yi mini bayani dalla dalla yadda zaki fiddani daga ruɗani Sameeha, Innalillahi wa inna ilaihir rajiun, saki har uku lokaci guda wannan wani irin ƙaddara ce. Umma nifa gwara da auren nan ya mutu dan in har bai mutu ba gaba zata iya aikata abinda ya kashe mata auren. Cewar Zaidu sai ya cigaba da faɗawa umma duk abinda Sameeha ta faɗa musu, itama Sameeha cikin kuka ta bawa umma labarin komai, umma ta share hawayen daya gangaro kuncinta ta kama hannun Sameeha tana cewa. Inna fahimce ki gadar zare aka ƙulla miki ya rufta dake, to ai shikenan sunyi nasara akanki amma kuma Allah yaga komai kuma shine zai wanke ki Sameeha, In Sha Allah rayuwarki sai tayi albarka, sai maƙiya sunji kunya matuƙa, Allah ya shiga lamarinki ya rabaki da baƙin ciki da ƙuncin duniya. Ki daina kuka domin Allah bai manta dake ba kuma akwai ranar sakamako, Allah yasa hakan shine mafi Alkairi. Bari na ɗaura muku ruwan wanka kuyi dan nasan kun ɗebo gajiya, Allah ya yi muku albarka gabaɗaya, kuma sai mu taru mu amsa wannan jarabawar duka ko. Amsa mata suka yi da Amin kana ta miƙe cike da dakiya dan ta ƙara musu ƙarfin guiwa, sai ta wuce kitchen dan ɗaura musu ruwan wanka kamar yadda ta faɗa, shigowar su Hauwa da sallamarsu yasa ta fito da sauri, suma su Sameeha suka kafesu da ido har suka ƙaraso cikin gidan suka tsaya. [7/7, 13:04] Buhainat😁: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shaidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.* 23. Hauwa sai da tayi musu kallon tsaf kafin ta taɓe baki tana cewa. Ina yini umma, ashe abin da ya faru da Sameeha kenan to Allah ya kyauta ya tsayar a kanta, kuma In Sha Allah nan ba da jimawa ba Aminu zai gwaggoje da Amaryarsa sabuwa fil a leda. Dan Allah idan ba Alkhairi y kawo ku ba ku fice mana daga gida. Cewar Zaidu cikin daga murya, Laure tace tana nuna shi da yatsa. Kai kuma a suwa kare da gudun layya, ba gunka muka zo ba sai ka ja Please ka rungumi sorry ɗan saurayi. Hauwa da Laure dan Allah ban son tashin hankali, tunda mai haɗawa ya raba banga amfanin ɗaukar baɗi ba rai ba. Cewar Umma, Hauwa tace tana kallon Sameeha. Muma ba tashin ha kali ya kawo mu ba mun zo gurin Sameeha ce gata nan zaune, yara zata bamu dan ba zamu yarda su cigaba da zama a gunta ba. To ba zan bada ba idan Aminu ya aiko ku kuce yazo da kansa ya karɓesu, kuma ku sani ƙaddara tana kan kowa. Eh mun san da ƙaddara tana kan kowa, amma mu muna murna da rabuwarku domin kadarinki ne ya karye, duk asirin da kike yi masa yazo ƙarshe, to Alhamdulillahi zamu ce kuma aniyar kowa zata bishi. Dan Allah ku bar gidan nan ni bana son fitina, nan ba gidan Sameeha bane da kuka saba yin duk abinda kuka ga dama, wlh bazan ɗauka ba, zoku fice tun kan raina ya ɓaci. Wlh ba zamu bar gidan nan ba sai Sameeha ta bamu yara, idan ba haka ba zaku ga tashin hankalin da baku taɓa gani ba, yara dai ba mai shan nono duk da wayonsu balle kuce ba zamu riƙe su ba. Cewar Laure a fusace, Hauwa tana cewa Faɗa musu dai, sai karkaɗa jiki take yi cike da masifa, yaya Zaidu ya miƙe ya fara zuba musu masifa dan duk abinda yazo bakinsa taɓa musu suke yi, Ikram ma ta miƙe tana mayar musu da martani, nan fa musayar magana ta cigaba, umma tana cewa su Zaidu suyi shuru amma ina ransu ya ɓaci, Sameeha dai da yara suna zaune a kasa sai rusa kuka suke yi, cikin ƙanƙanin lokaci maƙota suka fara shigowa ga kuma yara da suka yi cincirindo a Kofar gidan, saboda Tsananin zuciya Sameeha ta fusata ta wuce dakin umma ta jawo jakunan yaran, kayan data gani a kasa ta buɗe ta riƙa sakawa tana kuka kamar ranta zai fita, sai ta jawo akwatinan yaran guda biyu sai jakan takalma guda ɗaya ta zo har gabansu Hauwa da suke masifa baki har kumfa yake, ta dire jakunan ta juya ta damƙo hannun yaran duka biyu suka sakata a tsakiya tazo gaban su Hauwa ta ce cikin tsawa da kuka. Hauwa Laure, Gasu nan ku tafi dasu bada su dama naje gidan Aminu ba kuma zan iya rayuwa ko babu su, ku fice mana daga gida tun kafin na kira hukuma, kuma daga yau duk shegiyar data kuma tako ƙafarta gidan nan kotu ce zata raba mu, 'ya'yan iska marasa imani da mutunci, ku fita nace. Sameeha ta ƙare maganar da tsawa da matsanancin kuka sai ta yi baya ta durƙushe akan guiwarta tana wani irin kuka da jijjiga, umma ta matsa kusa da su Abi. Kuyi haƙuri kunji mamanku zata riƙa zuwa tana dubaku Allah yayi muku albarka. Wlh ni ba zan bisu ba da mamana zan zauna. Cewar Abi yana kuka, Amrah ma tace. Nima ba zanje ba ga mamana a nan. Haƙuri za kuyi domin tafiyarku shine zai kawo karshen rikicin nan. Idan Abbanku ya dawo zai kawo ku. Cewar Umma cikin lallashi ta fadi haka ne domin su yarda su bisu, Abi ya kalli Umma da kyau dan ya gasgata abinda tace, Umma ta gyada masa kai na tabbatarwa, sai ya kama hannun Amrah ya ɗauki jakar takalminsu suka yi hanyar waje, Hauwa ta ɗauki akwati ɗaya Laure ma haka sai suka wuce Hauwa tana cwaa. Allah mun gode maka daka rabumu da alaƙaƙai, wannan jaraba har ina. Suka fice suna hirar abinda ya faru, Umma ta ce mutane da suka shigo su fice tunda an gama abin kallo, suna fita ta rufe ƙofar gidan ta dawo ciki ta wuce kitchen ta shiga haɗa wutar gawayi dan ɗaura musu ruwan wanka, su Zaidu zama suka cigaba da yi sunyi jugum jugum kamar waɗanda aka yiwa shegen duka, kowanne fuskar a dame tare da baƙin cikin abinda ya faru, Sameeha kam lokaci zuwa lokaci take share hawayen da suka gangaro mata, ba ƙaramin jarumta tayi ba data basu yaran, tasan sune sanyin idaniyarta in tana ganinsu zasu ɗebe mata kewa da kuma damuwar da take ciki, amma tasan halin su Hauwa idan bata bada yaran ba sun dinga jelar zuwa kenan aita ɗauki ba daɗi, shiyasa ta kawo karshen rikicin ta miƙa su tasan da wuya Aminu ya barsu a hannun Hauwa, ƙila ya dawo mata da su kafin ya shirya karɓansu a hannunta, wannan tunanin yasa ta ɗan ji sanyi a ranta da fatan Allah yasa ya dawo dasu. *** Su Hauwa suna isa babban gida suka tadda Sa'a tana daka yaji tana gqninsu ta saki daka tana guda da murna akan sun yi nasarar kwato yaran, Hauwa tace. Dalla matsa ki bawa mutane guri mai shegen tsoron tsiya, ai kam anyi bake dan sai da muka kwashi 'yan kallo kafin suka bamu yaran. Ai shiyasa naga kun daɗe ashe anyi taraliya, to madalla tunda kunyi nasara. Laure Alhasan ya dawo fa ya tambaye ni ina kike nace kin leƙa gidan Hauwa, bai daɗe da fita sallar la'asar ba. To sannunshi da dawowa, ina daidai da rigimarsa dan nasan sai yayi faɗa. Cewar Laure tana taɓe baki tare da zama a ƙaramar kujera saboda gajiya da tsayuwar da suka yi a gidan su Sameeha. Laure zama bai gambu ma mu tashi muyu sallah kafin mu zauna zaman labari, dan sai na huta sosai kafin zan wuce gida da yaran, idan ma Alhasan ya shigo ma faɗa masa, dan Wlh dole yara su dawo hannunsu tunda muke da alhakin riƙonsu. Ke barni na huta wlh ƙafata minjirya take yi mini tsabar na daɗe a tsaye, ga nan muƙamuƙi na har riƙe mini yake saboda wage bakin da nayi ina masifa. Hauwa taja wata kujera ta zauna, Sa'a ta koma gurin dakanta tana jefo musu tambayar ya suka kwashe dasu Sameeha, Hauwa ta shiga rattafo mata zance Laure na tayata, suna tsaka da hirar Alhasan ya dawo ya shigo gidan, ganin yaran Aminu da kaya sun rakuɓe a guri guda yasa shi kallon su Hauwa ya ƙarasa nesa dasu kaɗan ya tsaya. Kar dai zuwa kuka yi ku ka ɗauko yaran nan? Wlh yaya zuma muka yi ni da Laure muka amso su, saboda ya dace yara su dawo dangin ubansu tunda muna a raye zamu iya riƙe su, saki uku yayi mata balle mu barsu a hannunta mu saka ran zai maidata. Kafin su bada yaran ma sai da muka yi bata kashi tukuna. Innalillahi wa inna ilaihir raji'un, Aminu shine yace ku ɗauko masa yaran ko gaban kanku kuka yi.? Haba Alhasan sai yace aje a ɗauko su? ai ya dace dama su dawo nan mana tunda dai yara da wayonsu babu mai shan nono, kuma ai da uba ake ado, shi kanshi Aminu zai ji daɗin mun sauƙaƙa masa ɗauko su da zai yi. Cewar Laure cike da ƙarfin guiwa, Alhasan ya kawo wuya sosai dan ransa yayi matuƙar baci. Da izinin waye kika bi Hauwa ɗauko su? ko nayi dake zaki je? Abu na zumunci har sai na nima izini Alhasan, ai wlh Aminu tamkar ɗan uwana yake shiyasa nima na tafi, an zam ɗaya. Lauratu ki tashi ki tafi gidanku na sakeki saki ɗaya kuma wlh idan kika ƙara wata magana sai na datse duka igiyar aurenmu dan na gaji da halinki, da ba haka kike ba amma yanzu da girma ya kamaki madadin ki ƙara hankali amma sai kike ƙara zama yarinya, to na gaji. Ke kuma Hauwa ki tashi ki mayar da yaran nan tun kafin na kai hannuna jikinki Wlh dan baki fi ƙarfin duka ba a guna, shegiya mai mugun hali, na rasa ina kika samo wannan halin naki na rashin hankali da son zuciya, kina yin abu sai kace jahila, zaki tashi ki mayar dasu ko sai na ɓallaki a gidan nan. Ya kare maganar a fusace, Hauwa ta miƙe ranta a ɓace tana jin kamar ta ɗuɗɗura masa zagi sai dai ba hali, ta wuce inda yaran suke ta daka musu tsawa akan su tashi su wuce. In kika kuskura kika huce akansu sai na baki Mamaki Hauwa kuma zan kira na tambaya naji ko kin mayar dasu shashasha. Cewar Alhasan daya wuce zuwa part ɗinsu, Laure ta bi bayansa tana yi masa magiya. Dan Allah Alhasan kayi haƙuri ba zan sake ba sharrin shaiɗan ne, yanzu ace sai da muka doshi hanyar tsufa zaka sakeni ga yara duk sun girma harda surukai, dan Allah ka rufa mini asiri kamar dani, dan wlh da kunya naje gida nace ka sakeni. Na dai gaya miki ki tafi gidanku, da can baki san kin girma ba kike abu sai kace kina cin ƙasa, ashe kin san kina da surukai kike aikata duk iskancin da kika ga dama, to na gaji wlh. Har suka shiga ɗakinsu tana bashi baki shi kuma yana yaɓa mata magana, Sa'a sai da suka kulewa ganinta kafin ta saki wani uban shewa. Allah na gode maka daban bisu ba dani ma yau tawa ta sameni, yau dai Laure kina ruwa kusa da kada, ashe duk cika bakine akan baki tsoronsu gashi a gabana ya danƙara miki saki, da sannu kowa zai girbi abinda ya shuka, shiyasa tun wuri na samawa kaina lafiya na kama aurena In Saha Allah bazan sake biye ta taku ba ku kaini ku baro. Sai ta cigaba da daka tana daga taɓarya tana wakar Marigayi Mamman Shata. _Ku gargaɗi mai gina ramin mugunta..._ Tana yi tana murmushi. Hauwa kuwa tana fita gidanta ta wuce da yaran ta saka kayansu a ɗakinta tace su zauna a falo suyi kallo, sai ta shiga kitchen ta ɗaura girki tana yi yana sakin maganganu duk kuwa akan Alhasan, ba ƙaramin haushi taji ba akan sakin da ya yiwa Laure amma tasan dole zai mayar da ita tunda da igiya biyu, in ba haka ba ai zasu ja musu magana Aminu ya saki mata shima ya saki Laure abu kamar shirin film, ga bikin Salma saura kwana shida, tunawa da tayi da wani kawunsu ƙanin Umma yasa ta fito daga kitchen ta ɗauki kawayarta ta kirashi, bayan sun gaisa ta koro masa bayanin abinda ke faruwa, nan yayi ta salati ya shiga yin faɗa akan ya Alhasan da girmansa zai saketa wannan shirme ne yace, tabar maganar a hannunsa zai shigo da dare gidan, Hauwa ta roƙeshi akan karya faɗa musu ita ce ta kira shi, yace karta damu sai suka yi sallama. Salma data dawo daga wajen gyaran jiki ta yada Zango a sashin Sa'a, nan take bata labarin abinda ya faru cikin faɗa Salma tace. Allah ya ƙara, gwara da ya saketa suna abu sai kace basu girma ba, wannan ai jakanci ne da rashin hankali su jawa mutane zagi, aiko yanzu zan faɗawa yaya Aminu yazo ya ɗauke yaransa dan Hauwa ba tunani ke gareta ba. Tana kaiwa nan a maganarta ta danna number ɗin Aminu ta kira shi, yana ɗauka suka gaisa kana ta shiga bashi labarin abinda su Hauwa suka yi, Baiyi mamaki ba dan yasan zasu aikata abinda yafi haka. Allah ya kyauta yanzu haka muna hanya zan dawo Kaduna daga Kano zan zo gidan na ɗauke su ki rabu da ita, sai dai ta ganni naje kawai. Yafi, dan Wlh ni bana son abinda suke yi, ga Laure nan itama Yaya ya saketa, ayi mata sai kace tinkiyoyi basu san ciwon kansu. Allah ya kyauta Aminu ya kuma cewa sai ya kashe waya yana jin wani baƙin ciki yana daɗuwa a zuciyarsa, shi kam bai san me zai yi ba ya rama abinda Hauwa take masa ba, hanya ɗaya ne ya yarda da aure data ce masa shine zai yi maganinta wlh, ya faɗa a ransa yana cije leɓensa. Sai bayan sallar Magriba Aminu ya shigi kaduna, yasa driver ya wuce dashi gidan Hauwa, da suka isa ƙofar ya fito daga mota ya shiga gidan kai tsaye har zuwa falo ya yi sallama, yaransa suna jin muryarsa suka tashi daga abincin da suke ci faten doya, dan tusawa kawai suke yi badan suna jin daɗinsa ba sai dai Hauwa data matsa sai sun ci, Aminu yana shigowa Amrah ta ruga da gudu taje ta rungumeshi shima ya kamata, Abi shima yazo ya rungumeshi ta gefe, a lokacin Hauwa ta fito daga daki. Aminu har ka dawo nayi zaton ai zaka kwana can. Wlh ganin mun gama meeting ɗin yasa nace bari na dawo, to da yake an sanar dani kin ɗauko yara shiyasa na zo nan. Halan su Sameeha ce suka faɗa maka, ai ɗazun sai da muka yi tsiya kafin suka bayar da yaran. Kin kyauta kuwa danni ma ina da niyyar amso su, amma yanzu zan tafi dasu gida mu kwana dan nayi kewarsu, jibi monday In Allah ya kaimu zan dawo dasu nan tunda a ranar zan koma Abuja. To ba damuwa, kai Abi jeka ɗauko jakar kayanku ku cire wanda zaku amfani dasu. Yace to ya wuce da sauri ya kwaso akwatunan, Aminu yace. Bari muje da kayan kawai in yaso sa kwaso na gida gabaɗaya su zo. Hauwa bata kawo komai a ranta ba ta ce to dan sosai take jin farin cikin yadda ɗan uwanta yake binta sau da ƙafa saɓanin yana tare da Sameeha, shiyasa ta ƙara tabbatar da asiri tayi masa ta raba tsakaninsu wanda a da har rashin kunya yayi mata akan Sameeha. Har mota ta rakasu suka wuce kana ta dawo gida. Aminu bayan sun isa gida yace Driver ya zo da wuri zai tafi da kaya Abuja da safe, yace to kana ya tafi da motar dan ya ƙara shan mai da ita. Aminu suka shiga ciki, yace su jirashi a falonsa ya shiga ɗaki ya watsa ruwa ba jimawa ya fito sanye da jallabiya, ya buɗe ɗakin Sameeha yaga wayam sai da yaji ciwo a ransa bai yi zaton zata yi saurin kwashe kaya ba, damuwa ya kewaye illahirin zuciyarsa ya jawo Kofar ya wuce kitshen nan ma ya tadda ba komai falon ba komai dama a falonsa yaran suka zauna. Sai ya ɗibesu a motar da ake kaisu makaranta suka fita suka ci abinci a wanu restaurant, basu suka dawo ba sai bayan ƙarfe goma Amrah ma har tayi barci, ya kaita ɗakinta ta kwanta kana ya soma haɗa musu kaya Abi yana taya shi dan yaƙi barci saboda Aminu yace masa zasu haɗa kayansu gobe In Sha Allah da wuri zasu tafi Abuja dan ba zai barsu a nan kaduna ba. Sune har ƙarfe sha ɗaya suna abu ɗaya, Aminu yace Abi ya kwanta da safe zasu cigaba, haka ya lallaɓa yaron ya kwanta a ɗakinsa kafin ya fito ya cigaba da haɗa musu kaya dan ko barci baya ji duk da akwai gajiya a jikinsa, amma damuwar da yake ciki yasan ba zai barshi yayi barci ba, sosai yake ji dama bai saki Sameeha ba amma kuma in ya tuna a yadda ya gansu sai yaji sakin shine mafi alkhairi, trolley huɗu ya cika na kayansu, sai gana mazgo na littafai da takalma, bashi ya kwanta ba sai gurin ƙarfe biyu shima sai da yasha wani kwayar magani mai saukar da gajiya da kuma saka barci, ba jimawa barci ya ɗauke shi. [7/7, 13:04] Buhainat😁: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shaidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.* 24. Gari yana waye wa driver yazo ya loda kayansu Aminu a mota dan ba ƙaramin kaya ya ɗibar musu ba, da nufin sun bar Kaduna kenan sai dai su riƙa zuwa suna sada zumunci. Driver ya tafi da kayan dan su jirgin kasa zasu bi, Aminu ya saka suka yi wanka dan har Amrah ta iya sai dai ya tayata shiryawa suka fito gabaɗaya da nufin a hanya zai siya musu abinda zasu karya da shi, Aminu sai da ya sauke wutar sashinsu gaba ɗaya ya kashe komai ya dawo ya rufe ɗakuna kana ya rufe ƙofar falo. driver mai kai su Abi makaranta dama yazo tun ɗazu akan kiran da Aminu yayi masa sai suka shiga mota ya kai su bakin gate, Aminu yace ya tsaya ya fito mai gadi ya risina yana kwasar gaisuwa Aminu ya miƙa masa dubu biyar yana cewa. Wannan kuɗin kaje a buɗe maka account da komai, domin ta nan zan dinga tura maka albashinka duk wata, sannan idan kana da iyali zaka iya ɗauko su ka saukesu a ɗakunan dake can baya ku zauna a nan kafin Allah yasa in dawo. Wannan kuma dubu arba'in ne gasu. Alhaji kuɗin na menene? Albashinka ne na ƙara maka na wannan watan domin ka ƙara siyan abinci da komai tunda dama a cikin gidan ake baka na rana da na dare. Nagode Alhaji Allah ya saka da alkhairi ya ƙara arziki, In Sha Allah yau zanje in bayar a buɗe mini asusun banki sai na saka a tura maka numbobin. Aminu yace Masha Allah kana ya wuce ya shiga mota suka wuce, mai gadi sai juya kuɗin yake cike da tsantsar murna da tunanin yadda sai fara kashe su, har motarsu ta kusa fita Aminu ya kwala masa kira, sai ya isa da sauri ya risina. Gani yallaɓai. Yauwa ina so naja kunnenka ka kula da gidan nan da zarar ciyayi sun fara fitowa ka faɗa mini sai na tura maka kuɗi ka samu masu gyara suyi, karka riƙa barin gidan yana datti. Kuma daga 'yan uwana duk wanda yazo karka barshi ya shiga mini gida, nasan dai su yaya Kamalu ba zasu zo ba, amma su Hauwa ban yarda ka buɗe musu gida ba tunda kasan dai ba kowa a gidan. In Sha Allah zanyi yadda kace Allah ya saukeku lafiya sai kun dawo. Sai Aminu ya ɗage gilas ɗin motar na baya driver ya jasu suka wuce. Mai gadi ya ja gate ya rufe da kwaɗo ya koma ya zauna a benci yana lissafin yadda zai je kauyensu ya ɗauko matarsa ko kuma ya kirasu su kamo hanya, amma sai ya nima 'yar katifa wacce tafi na ɗakinsa ya saya da ɗan kayan amfani. **** Babban Gida Da safe Alhasan ya fito zai je wajen Kamalu suyi magana, Laure ta fito daga ɗaki fa biyoshi tana ƙara bashi haƙuri akan abinda ya faru jiya, dan ta samu da kyar ya mayar da ita aka Kawu Lawal da ya zo ya saka baki dole ya mai da ta. A fusace ya juya yana cewa. Wai da banyi haƙuri ba zan mayar dake ne, karki dameni, idan kin so ki cigaba da yi mini iskanci dan Wlh aure ma zan ƙara na huta da damuwar da kike ƙunsa mini. Aure fa kace Alhasan.? Laure ta faɗa tana dukan ƙirjinta, Alhasan ya gyara tsayuwa yana cewa. Kuma budurwa zan nima yadda zan yi kara'i da kyau. Yana gama faɗar haka ya wuce ta yana 'yar dariya a ransa dan yasan ya kaɗa mata 'yan hanji dole zata shiga hankalinta, tunda mace komin tsufarta bata ƙaunar kishiya, ita kuwa daskarewa tayi a tsaye ta kasa kwakkwaran motsi dan sosai maganar nashi ya kashe mata jiki, daga bisani taja kafa zuwa ɗaki tana jin babu daɗi a ranta, ta san dai tabbas ta kai Alhasan bango tunda tana sane da bata kyautata masa, lokaci yayi da zata gyara tun kafin ya aiwatar da zancen kishiyar da yace zai yi mata. Alhasan kuwa magana suka yi da Kamalu akan ɗauko yaran da Hauwa tayi, yace zasu je gidan Hauwa su kwashi yaran su mayar dasu gidansu Sameeha, dan ya samu labari bata mayar da yaran ba, suna cikin maganar Aminu ya kira Alhasan a waya, ya ɗauka suka gaisa kana Aminu yace. Dama na kira ne na sanar daku na dawo daga kano jiya to yau kuma na wuce Abuja, sannan na karɓi yara a hannu Hauwa yanzu haka dasu zan tafi. Amma Aminu bai dace lokaci guda ka raba yaran nan da mahaifiyarsu ba, da ka basu lokaci itama ta samu natsuwa sosai, yanzu haka maganar nake da Kamalu kenan akan zan kwashe yaran a gidan Hauwa na mayar dasu. Ai yaya zan buƙaci yaran su kasance tare dani, dan har mun kama hanya ma yanzu sai dai zamu riƙa zuwa hutu. To waye zai kula dasu kai kana fama da aiki, ga kuma makarantarsu da suka fara anan Yaya zan sauya musu makaranta kuma zan samu mai kula dasu, In Sha Allah ba zasu yi maraicin uwa ba. Kenan babu zancen yin aure kuma ko? Aminu dan Allah kar ka fara rayuwar da zai lalata rayuwar ka. In Sha Allah zan kula, kuma ba Hauwa tace ta sama mini mata ba, ita nake saurare naga irin zaɓin nata. Kai ka yarda da zancen wannan mahaukaciyar ne, aini sam ban saka Hauwa cikin masu hankali, ayi mace sai kace tinkiya uwar tamɓele. Aminu sai da ya murmusa yace cikin dakiya. Yaya ina ganin tunda har ta faɗa a bata dama wata ƙila a dace. To Allah ya kyauta ya tsare hanya. Aminu yace Amin kana yace ya sanar da Kamalu yadda suka yi, Alhasan yace ba damuwa sai suka yi sallama ya kashe wayar. Nan Alhasan ya faɗawa Kamalu yadda suka yi Kamalu yace. Tunda haka ya zaɓa ai shikenan kiga ma baya nan za ayi bikin Salma, Aminu fa ta sauya sai dai mu bishi da addu'a. Allah ya kyauta Alhasan yace kana suka cigaba da tattauna bikin Salma da za ayi ranar juma'a. ... Ranar laraba aka fara shagalin bikin Salma wanda ranar Alhamis zasu yi sister eve, Hauwa tace ya kamata suje gidan Aminu suga yadda gidan yake kafin su aika masu kanofi su jera kujeru, ita da Laure suka je dan tuni ta sake suka cigaba da sabgar biki, ko da Hauwa ta kawo mata zancen Sameeha cewa take ai ba ruwanta tunda sanadin Sameeha aka saketa ko sunanta bata son ji, Hauwa dariya tayi tace ta dai tsorata ne kuma ma tunda bata gidan Aminu yara basa hannunta ai zancenta ya shafe kuma sun rufe babinta. Koda suka isa gidan sun samu a rufe suka buga mai gadi yace waye ba tare daya buɗe ba. Dalla malam buɗe mana ko baka gane Hauwa bace yayar mai gidan. To wlh yallabai yace karna bar kowa ya shiga masa gida, dan haka ku koma inda kuka fito. Kan kaza kazanka ko baka gane da waye kake magana ba. Hauwa tayi magana tana ƙunduma zagi, Mai gadi bai kuma magana ba ya koma ya zauna, suka cigaba da buga ƙofa suna zage zage yana jinsu yaƙi tanka musu. Haka suka gaji dan kansu suka tafi, tun a hanya Hauwa take kiran Aminu yana gani amma yayi banza da ita dan yasan dalilin kiran, ba zai taɓa yarda suyi Wani biki ba su ɓata masa gida dan yasan halinsu. Zage zage Hauwa da dinga yi har suka isa gida wanda Salma da ta ji abinda ya faru tace. Ni Ban ga abin ɗaukar zafi ba tunda nan gidan ma yana da fadin, sai muyi abinmu a nan gida ba karya ba karairayi, kuma yana da gaskiga tunda yasan irin ɓarnata masa gida da akayi lokacin dawowarsu, dan haka banji haushi dan ya hana muyi taro ba. Ai dama ke baki da zuciya tunda har kin samu damar kare shi, muna nima muki mutunci amma kina iskanci, yanzu baƙin naki a nan zaki sauke su. Meye aibin gidan mahaifina? wlh a nan za a yi bazan taɓa gujewa gidanmu ba, tunda shima da kyanta ba ruwana da wani ƙarya. Hauwa ta matso kamar zata buge mata baki ta matsa da sauri. Wato aure zaki yi amma bakinki bai mutu ba ko Ummu Salma, zaki ci ubanki ne namiji sai ya koya miki hankali, Laure muje mu zauna mu sake shawara. Salma dariya tayi mata dan halin Hauwa sai ita, suka wuce zuwa sashin Laure suka ɗaura zancensu daga inda suka tsaya. ... Haka aka ɗaura auren Salama aka kai ta Hayin Banki, gidanta mai kyau two bedroom filat da bayi da komai a ciki dan haya mijinta ya kama. Anyi biki yayi daɗi amma a gurin su Hauwa ba haka suka so ba, dan duk burin da suka ci bai auku ba, haka dai aka gama lafiya kowa ya watse daga 'yan cikin gari har 'yan ƙauyensu da suka zo kowa ya tafi. ***** Sameeha. Zazzaɓi sosai tayi dan har sai da aka kwantar da ita a asibitin dake nan kusa dasu tayi jinyar kwana biyu dan ko abinci bata iya ci, sai yawan kuka da rashin samun barci, ba komai yake damunta ba sai rabata da yaranta da suka yi, tayi tunanin Aminu zai dawo dasu amma koda tayi waya da Salma tayi mata Allah ya sanya alkhairi take faɗa mata ma ya tafi dasu Abuja, tun umma tana rarrashinta har sai da ta rufeta da faɗa tana cewa. Maza ki kashe kanki abanza gashi can shi Aminu ya cigaba da rayuwarsa, da yaran sun dameshi da yanzu ya dawo miki dasu, idan ma zaki cire ranki dasu gwara ki cire ki samawa kanki lafiya. Amma umma sai kace zaman ƙiyayya nake da Aminu da zai yanke mini irin wannan hukuncin. Sameeha ta faɗa idonta na ciko da kwalla ta tashi zaune daga kwanciyar da tayi akan doguwar kujerar ɗakin umma, Ikram zata yi magana sai ga sallamar Inna da Najwa sun zo gidan, suka shigo suka zauna Umma tana yi musu lale, nan suka gaisa sai inna ta ɗaura da cewa. Na dawo in duba jikin Sameeha ne, wannan yarinya Allah yasa kin ci jarabawarki, ina mamakin sakin da Aminu yayi miki hakanan ba da wani laifin azo a gani ba. Da yake su Umma sunki faɗar komai game da sakin Sameeha saboda gudun surutu, umma ta ɗaura da cewa. Ai ta samu lafiya, amma ta dai kasa sakawa kanta haƙuri ne akan yaranta. Dole ta ji ciwon rabuwa dasu Halima, uwa da 'ya'yanta ai sai Allah, yayi saurin rabata dasu wlh ,madadin ya barsu in ta samu miji sai a mayar masa dasu. Allah ya saka miki ya zaɓa miki miji nagari Sameeha sannu ko. Cewar Inna da matuƙar tausayawa, Najwa tace cikin damuwa. Anty Sameeha Allah ya baki lafiya ya baki wanda ya fishi dan Aminu bai kyauta ba, yadda naji ma su Hauwa sai murna suke yi har da cewa zasu aura masa wacce ta fiki. Wani murmushi Sameeha tayi wanda ya kuɓuce mata dan rabon da tayi shi ma ta jima. Wlh zanyi murna su samo wacce ta mini din, dan dama Aminu ai sai wacce ta fini ya dace ya aura, dan haka bana baƙin ciki wlh, Allah ya nuna mana rai da lafiya. Ta ƙare tana wani murmushi, umma da Ikram sun fahimci inda maganarta ta dosa suma murmushin suka yi, wanda Najwa bata so haka ba taso ace sunji haushi musamman Sameeha ta ƙara shiga damuwa. Sai taga akasin haka, nan suka cigaba da hira har kusan sallar Magriba kafin suka bar gidan. A daren Ranar kuwa Sameeha ta samu barci dan sosai ta yi ƙoƙarin ya kice damuwa ganin shima Aminun da yayi sakin ya cigaba da lamarinsa ya mance da ita, karin abinda yasa ta saki yadda taji wai aure zasu yiwa Aminu, tasan ko ya amince to lalai saiya ƙunsa musu baƙin ciki tunda yasan bai da lafiya, tayi ma mamaki da bai sanar da 'yan uwansa rashin lafiyarsa ba, hakan yana nufin ya cigaba da ɓoye maganar kenan. ... Haka rayuwa ta cigaba da tafiya tun ana kwanaki aka zo mako aka dawo wata, Sameeha tana ta warwarewa bisa maganganun da Umma suke yi mata na kwantar da hankali da kuma ƙarfin addu'a. Wajen La'asar suna zaune a tsakar gida bisa tabarma umma ta kalli Sameeha tana cewa. Ohh yanzu fa har kinyi wata uku da kwanaki Sameeha, rayuwa kenan kamar komai ba zai wuce ba ga dai shi mutuwar aure ya tabba har kin fita idda. Allah ya kawo miji nagari sai na haɗa ki da Ikram idan saurayinta ya fito. Aure kuma Umma? ai bana tunaninsa a nan kusa, ni wlh zan iya zana a haka ba aure kuma ba abinda zai dame ni. Makaranta ma nake sha'awar komawa. Aiko baki isa ba dan ba a gidan nan zaki zauna mini ba, da rai na da lafiya bazan zuba miki ido ki kashe kuruciyarki ba a banza. Makaranta kuma sai dai islamiya ba dai boko ba dan ba zan amince ba. Cewar Umma, Sameeha tana dariya zata yi magana sai ga Zaidu ya shigo da sallama yana cewa. Maganar me ake yi ba za a jira na dawo ba ayi dani. Dan na han go farin ciki duk a fuskarku. Maganar aurenka da Najwa muke yi shiyasa ka ganmu muna ta dariya. Cewar Ikram cike da zolaya, Zaidu yasha kunu yana danƙara mata harara. To bari kawai na koma dan bani da hurumi a cikin zancenku, saboda ko a ƙafa aka ɗaura mini Najwa wlh saina kwanceta. Ya ƙare magana yana zama kusa da Sameeha a kan tabarma da yake babba ce, duk dariya suka saka masa Umma tana cewa. Rabu da Ikram kasan halinta da tsokana, ni gwara ma daka shigo ina so dama muyi maganar sana'ar da Sameeha zata fara dan zamanta hakanan ba daɗi, kuma sana'ar zai riƙa ɗebe mata damuwa. Wannan gaskiya ne, to ke Ƙanwata zinariyar gidanmu me zaki fara sayarwa. Ai yaya ni ina mata sha'awar ta buɗe Saloon dan kun ga ta iya kitso sosai hakan zai sa ta warware saboda hulɗa da mutantr, in yaso sai ta samu wacce ta iya Saloon ta riƙa yiwa mutane tana biyanta, idan ma ta koya ta iya shikenan ko ni zan riƙa kama mata. Cewar Ikram, sosai suka yaba da shawarar Ikram ɗin Zaidu yace. Me zai hana ɗakina dake kusa da gate a rufe shi ta ciki sai a fasa ta waje amayar da shi shago, in yaso sai na koma wancen ɗakin na kusa da kitchen a kwashe kayan ciki. Amma umma me kika ce. Babana hakan yayi dan dama kama shagon shine babban damuwar, tunda ɗakinka in aka fasa ta waje yana kallon hanya to ya dace ayi yadda kace, in yaso sai ta fara siyan kayan Saloon ɗin a hankali. Umma maganar Saloon fa yana buƙatar kuɗi sosai, ga gyaran shagon shima kashe kuɗi ne, kuma kinga muna lallaɓa kuɗin hannuna muna rufawa kanmu asiri. Sai dai ko na sayar da motata. Allah ya kyauta, haba Sameeha sai kace bana raye, ba sai kin sayar da motarki ba ni na ɗauki nauyin gyara miki shagon in yaso kayan Saloon ɗin ki riƙa saya a hankali har ki tara, kuma inna samu kuɗi nima zan riƙa baki kina sayansu a hankali. Cewar Zaidu, Ikram tace. Aiko shawara tayi dan haka gobe in Allah ya kaimu Anty zan raka ki kasuwar gari mu fara tambayo kayan, ko kuɗi kaɗan ki riƙe mu fara tsintowa. Hakan za a yi sai kuje kawai, kinga kya ga gari tunda ba fita kike yi ba. Waya sani ko ta samo mana bazawari kiji an koma zancen aure. Cewar Zaidu cike da zolaya, Sameeha tace cikin murmushi. Haba yaya sai kace kun gaji da ganina a gidan. Ba zancen mun gaji bane, da sauran ƙuruciyarki wlh ba zamu zuba ido mu riƙa kallonki ba. Ikram tashi ki saka mini abinci, wai me kuka dafa ne yau. Tuwon shinkafa miyar shuwaka, Allah yasa zaka iya ci. Cewar umma dan tasan baya son miyar a cewarsa ɗaci yake yi masa. Ya zanyi dole haka zan tusa tunda na koma agola ɗan kishiya, Allah yasa kun wanke da kyau bata wannan ɗacin. Aure kawai zaka yi ka huta muma mu huta da ƙorafinka. Ana zancen Najwa kana cewa baka so. Cewar umma, sai duk suka saka dariya suka cigaba da hira cike da raha babu wata damuwa a tare da su, dan Sameeha tuni ta dangana ta barwa Allah lamarinta. [7/7, 13:04] Buhainat😁: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shaidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.* 25. Da safe Ikram zata tafi makaranta tace wa Sameeha ta jirata ta dawo sai su tafi kasuwar, Sameeha tace ba zata jirata ba dan bata son shiga kasuwa da rana, umma tace gaskiya gwara taje da wuri ta dawo, Ikram bata so ba taso ace tare suka fita dan wannan fitan shine na biyu da Sameeha zata tayi tun dawowarta gida, na farkon gidan kakaninta taje ita da Ikram da Anwar, Ikram ta tafi da zummar zata dawo da wuri harta roƙi Sameeha akan ta jirata. Sameeha ta shirya cikin baƙar jallabiya ta sanya marron ɗin hijab ta sauki ATM ɗinta ta saka a fos sai ta yiwa umma sallama wajen goman safe ta fito daga gida, sai taji kamar iska zai ɗauketa dan rabon data fito waje ta manta dan koda zasu gidan kakansu a motarta suka tafi, ta isa titi ta tari napep drop dan bata son ɓata lokaci, yace dubu ɗaya da ɗari biyar ta ciro kuɗinsa ta bashi ta shiga suka wuce, sai kallon gari take tana ganin sauye sauyen unguwanni dan bata fahimci ma haka wurare suka sauya haka ba saboda a da fitarta a motanta ne, hanya kawai take kallo, sosai taji iskar dake dukan fuskarta yana mata daɗi ashe zama a gida tamkar preson ne wani lokacin dan sam baka sanin ya iska me daɗi yake saika fito. Har suka ƙarasa cikin gari mai napep yace ya jirata ne ta dawo ya mayar da ita ganin ya samu ta biyashi da kyau, tace masa ya tafi zata daɗe a kasuwar karta ɓata masa lokaci, sai ta wuce shima ya wuce. A hankali take tafiya tana ganin yadda kasuwar gabaɗaya ta sauya dan sabuwar kasuwa ta shiga, tana tafiya sai shagunan kayan yara take gani abin yana bata sha'awa da tuna nata yaran, nan take kewarsu ya dawo mata sabo har taji idanunta suna ciko da kwalla, ace da ranta da lafiya ƙiri ƙiri 'ya'yanta sunyi mata wuyar gani, wani mutum ne ya tare ta yana cewa me take son siya? tace shagon sayar da kayan saloon, sai ya jata can ciki suka isa wani shagon kayan Saloon, nan fa ta zauna suka fara ciniki tana faɗan abinda take so ana faɗa mata kuɗin su, ganin abubuwan sun tsefe da tsada yasa tace zata dawo dan gaskiya in ta biye zata kwashe kuɗin daya rage mata na bankin kaf, ta amsa card ɗin me shagon akan in ta dawo zata kira dan da wuya ta gane shagon saboda can cikin kasuwa ne. Ta fito bakin hanyar kasuwa ta gaban wasu manyan plaza, daga kasan wani gidan sama ta karanta sunan wani ƙaton shago an rubuta Khairy boutique, Sameeha har ta gota sai ta tsinci kanta da komawa ta shiga shagon, kayan yarane English wears dana manya, harma da gefen atamfofi kusan komai da akwai har da takalma da jakuna, Sameeha tana shiga wani saurayi ya yi mata sannu da zuwa sai kuma wasu 'yan mata biyu suka tare da suma da nasu welcome ɗin tare da nuna mata gurin zama duk sanye suke da t-shirt da sunan boutique ɗin, suka tambayeta me take so Sameeha ta tsinci kanta da cewa kayan yara take so ɗan shekara goma dana mace 'yar shekara takwas, nan fa suka fara ɗibowa suna nuna mata, ta shiga zaɓa har sai da ta cire musu bibbiyu, suka ce bari su kira ogansu tana nan suyi maganar kuɗi, ɗaya daga cikin 'yan matan ta isa wani ƙofa da yake nuna alamar ƙaramin office ne sai ta shiga, ba jimawa sai ga wata mace kyakkwawa black beauty ta fito tare da wancen yarinyar data je kiranta, ta samu guri ta zauna a wata farar kujera, suka gaisa da Sameeha kana suka fara cinikin kaya sai kuɗin ya tashi akan dubu talatin da biyu, Sameeha tana ƙoƙarin ciro ATM ɗinta ta basu su cire a pos, sai kira ya shigo wayarta sai ta fasa ɗauko ATM ɗinta ta ciro waya, sai taga Ikram ce ta ɗauka tana cewa. Ikee ya har kin dawo makarantar ne?" Na dawo Anty saboda mu tafi kasuwar, sai na tadda har kin wuce umma tace ki tafi kar ki jirani, shine nace ki faɗa mini ina zamu haɗu yanzu na hawo mota na zo. Sannu Hand back ɗin Sameehan Umma, wato dole dai sai kin biyo ni, to nima yanzu zan dawo dan gaskiya kayan saloon ɗin nan sunyi wuta sai na sake nazari da lissafi kan na siya, yanzu haka ina wani boutique ne zan siyawa su Abi kaya. Haba Anty kema kin san sai umma tayi miki faɗa, yaran da ba ganinsu kika yi ba balle kice zaki siya musu, kuma kin san ubansu yana da kuɗin siya musu kaya, idan ma kin saya waye zai kai musu har Abuja. Ikram yanzu tsakanina da yarana ba zan yi musu ihisani ba dan bana tare da ubansu, kawai kayan sunyi mini kyau ne shiyasa nace zan siya ko Yaya Kamalu zan aika masa ya aikawa Aminu. Tunda na kira na kira yaki ɗauka ƙiri ƙiri ya rabani dasu sai kace rabuwar kiyayya muka yi. To wlh gwara ki fasa saya tun kafin ki zo umma ta rufeki da fada, keda kike niman kuɗin da zaki bunƙasa kanki zaki ɓarnatar dasu a iska ga yaran da suka yi miki nisa. Dan na siyawa su Amrah kaya Wlh ba ɓarna bane, Ikram 'ya'yana ne fa, kawai dai zan fasa siyan tunda kin saka wannan bakin naki, na tabbatar kan na dawo kin haɗa mini bomb a gurin umma. Ai gaskiya na faɗa kuma ko umma da yaya Zaidu abinda zasu ce kenan. To naji Sameeha tace tana kashe wayar matar da suke cikini tana danna waya akan ta gama ta bada kuɗi, Saneeha da duk jikinta yayi sanyi, da kunyar tace mata ta fasa siya, haka dai ta daure ta cije tana cewa. Hajiya kiyi haƙuri na fasa sayan kayan gudun faɗar ummata amma In Sha Allah naga waje da zarar na samu dama zan zo na yiwa yarana siyayya. Ai daga jin wayar da kika yi na fahimci maganarki ba komai, amma ko ke ya kamata ki sayawa kanki abu muna da leshi atamfa da jakuna da takalma harma da gyale da kuma material, akwai wani da zai yi miki kyau bari na kawo miki. A'a hajiya da dai kin barshi kawai sai dai wani zuwan In Sha Allah. Matar ta miƙe taje ta ɗauko material ɗin ta miƙa mata lokacin Saneeha ta miƙe tana shirin tafiya, ita kanta material ɗin yayi mata kyau amma tace. Idan rabona ne inna dawo wani lokacin zan saya kiyi hakuri banyi miki ciniki ba zan tafi. Babu komai, kuma duba tara ne ɗinsa ba tsada, amma ina zuwa. Sai shiga office ɗinta ta ɗauko jaka da key mota tare da ɗauko leda ta saka material ɗin a ciki, ta ƙaraso gurin Sameeha tana cewa. Nima tafiya zanyi in ba damuwa na rafe mini hanya. Wani kallo Sameeha ta yiwa matashiyar matar, wacce ba zasu wuce sa'anni ba ko ta girmeta da kaɗan ne, sai Khairy ta sakar mata murmushi. Kiyi haƙuri naga kamar baki yarda dani ba, domin Allah zan rage miki hanya duk da ban san unguwarki ba hakanan naji kin yi mini. Sunana Ummulkairi Aliyu Turaki ina aure a sabon kawo yarana huɗu, Faisal, Hydar, Khadija da Humaira, sunan mijina Ahmad. A kaice kenan. Mamaki ƙarara ya nuna a fuskarta wanda yasa ta saki baki ta kasa magana, Khairy tace cikin sanyin jikin. Idan baki Aminta dani ba zaki iya tafiya amma har ga Allah da alkhairi a gare babu sharri, kuma banyi mamaki ba dan kin ƙi yarda dani saboda duniyar cike take da mutane ɓata gari marasa gaskiya, mutum abin tsoro ne. Sameeha ta sauke ajiyar zuciya tana jin ba daɗi kar matar taga ko bata yarda da ita ba ne, kuma har ga Allah tsoron mutane take saboda abinda ya faru da ita a gidan Aminu, sai tace. Babu damuwa ai hanyar muma ɗaya danni rafin guza nake, amma naga kamar baki ji daɗi ba, kiyi haƙuri kin san mutane ba gaskiya ina tsoron abinda zai je ya dawo mini. Khairan In Sha Allah, saboda Allah naji ina buƙatar zumunci dake duba da kema ba yarinya bace, sannan ni ban da ƙawayen sai 'yan uwana shiyasa kawai nace in rage miki hanya. Sameeha ta ce ba damuwa in ta shirya su wuce amma a zuciyarta cike take da zullumi da fargaba dan gaskiya tana tsoron mutane, musamman 'yan matan nan da suka yi mata sharrin lesbian, Khairy ta yiwa yaran shagonta sai da safe su kula idan wata matsala ta taso su kirata, sai suka fito suka wuce ta buɗe motarta data yi parking a gefen shagonta, ta shiga ta buɗewa Sameeha ƙofar gefenta ta shiga da bisimillah tare da addu'ar kariya a zuciyarta, ta kunna mota suka kama hanya, ba wani hira suke yi ba saboda Khairy ta kunna waƙar 'yan Sudan suna saurare, wani ma tana bi tamkar dai labaraci suke a wakar, Sameeha dai kallon hanya take tana tunani barkatai a zuciyarta. ***** Aminu. Tun da suka koma Abuja yake fama da rashin lafiya a tsastsaye, yayi ta zarya asibiti aka ce ya kamu da hawan jini ga kuma ulcer wanda dalilin damuwa da rashin cin abinci ya ja masa wannan ciwo, haka ya rame duk wannan ƙibar babu hatta tumbin da yake dashi ya tafi, ya dawo asalin bafulatanin Meyere sai karan hanci ake gani da kwala kwalan ido, saboda jinya har hutu ya ɗauka a gun aiki, ga rigimar su Abi da suka matsa masa akan dole sai ya mayar da su gun mamansu, musamman Amrah da ta fi Abi kawazucin uwa, lallashinsu yake yi da basu baki sai sun samu hutu zai kai su, dan tuni ya sama musu makaranta suka fara zuwa, sannan ya sama musu mai dafa abinci namiji dan shi ya buƙaci haka, wani abokinsa ya samo shi shima ɗin sai da aka yi masa gwaje gwajen ciwo aka tabbatar free yake ba cutar da ke damunsa kafin ya fara yi musu girki kuma ba laifi ya iya. Sannan drivernsu dake nan Kaduna shine ya je can ya cigaba da kai su makaranta, damuwarsa ɗaya ne yana buƙatar mace da zata riƙa zama dasu a gida in baya nan musamman in sun dawo daga makaranta. Hakan yasa ya kira wata gaggonsu ƙanwar Abba dake Meyere ita Allah bai bata haihuwa ba kuma mijinta na farko rasuwa yayi na biyun fara aura rabuwa suka yi saboda zaman nata yaki daɗi da kishiyarta, shiyasa ta aje auren tunda girma ya fara kamara ta cigaba da sana'ar cikin gida, lokaci zuwa lokaci tana zuwa Kaduna gurin su Alhasan, ita kawai Aminu yaji ya kira ta dawo gunsa da zama dan tana buƙatar taimako tunda ita ba ɗa gareta ba, koda ya sanar sa ita buƙatarsa tace ba damuwa zata zo, lokacin bikin Salma da bata ga yazo ba tana ta magana, sannan taji labarin ya saki matarsa abin bai yi mata daɗi ba, taso kiransa amma Allah bai nufa ba, yace ai bakomai jarabawarsa kenan, idan ta tashi zuwa zai aiko da driver ya ɗauketa, tace ya bata kwana biyu zata kira shi in ta sallami bashin da ake binta itama ta karɓi nata da ta ke bi, a haka suka yi sallama. Sati guda a tsakani Baba Saude ta zo Abuja Su Amrah sun ji daɗin ganinta wanda hakan yasa suka rage damun Aminu maganar mamansu, ko shi Aminu yaji daɗin zuwan Baba Saude domin ta rage masa damuwa sosai da yawan tunani, dan sai su raba dare suna hira tana bashi labarin garinsu da mutanen daya sani, da yake ta iya bada labari kuma shima yana son irin labaran, hakan yasa ɗan nutsuwarsa ta fara dawowa ya koma walwalarsa sai dai ba kamar na da ba. Ko lokacin da Sameeha take ta kiransa yasan tana so ya haɗa ta da yaranta ne, amma yayi biris yaƙi ɗagawa dan baya so tayi magana dasu su zo su riƙa damunsa akan ya kaisu gunta, shiyasa ma daga baya yayi blocking layinta ya cigaba da lallaɓa rayuwarsa da yake ji tamkar ma mutuwa zai yi. Haka aka shafe wata uku da kwanaki wanda yayi daidai da lissafinta Sameeha ta fita idda, duk da saki uku yayi mata amma kafin tayi wani aure dole sai tayi jini uku, kuma a lokacin yaran sun samu hutun makaranta, suka dame shi akan ya kai su kaduna tunda yayi musu alƙawari, amma yace suyi hakuri zasu je Ilori wani samina zai je kuma tare dasu zai je su raka shi. A lokacin ne Hauwa ta kirashi akan batun zuwansa Kaduna daya ce sai yara sunyi hutu, yace mata wani aiki ya taso masa zasu je Ilori sai dai in sun kuma samun wani hutu na gaba, cikin faɗa Hauwa tace. Kenan ni ka mayar dani mutumiyar banza, na dage akan maganar aurenka har na saka wa ɗiyar mutane rai amma kana son bani kunya sai wasa kake mini da hankali. Haba taya zan miki wasa da hankali, ai ni nace na amince. To yanzu ya kake so nayi? Kuma nace a wannan watan zaka zo ayi maganar aure amma abu yaci tura, ko yaranyar ma baka sani ba balle kuyi waya ku fahimci juna. To yanzu ya kike so ayi? ni dai bazan fasa tafiyata ba tunda abu ne daya shafi aiki na. Idan ka amince zan je na samu su yaya suje gidan su yarinyar su nima maka aurenta, sannan zan tura maka number ɗinta ka kirata ku fara zance. Murmushin gefen baki yayi yana mamakin ƙarfin halin Hauwa. To shikenan ki same su kuyi magana zan tura musu da kuɗin sadaki ayi komai ba sai ina nan ba, amma ko sunan Yarinyar ma ban sani ba yaya. Najwa sunanta, kuma wlh kyakkyawa da ita har tafi Sameeha kyau ga kuruciya. Hauwa ta faɗa cike da farin ciki a fuskarta dan rabon data yi farinciki haka tun lokacin da ya saki Sameeha, bata ɗauka zai yarda da maganar a yanzu ba, Hmmm yace ya kashe wayar yana maimaita sunan Najwa a zuciyarsa, tamkar ya taɓa sanin wata mai irin sunan amma ya manta ssboda sabgogi sunyi masa yawa, kuma rabuwarsa da Sameeha ya goge masa memory ɗinsa da yawa. Baba Saude ce ta fito daga ɗaki tana cewa. Sai naji kamar waya kayi da Hauwa. Yace mata eh kana ya kwashe yadda suka yi ya faɗa mata Baba tayi murmushi tana cewa. Hauwa rigima, ai gwara daka amince ayi ɗin, tunda zama haka ba mata da sauran ƙuruciyarka bai dace ba, itama Sameeha ba zama zata yi ba aurenta zata yi, gwara duk ku karɓi ƙaddararku hannu biyu. Aminu murmushi yayi shi kaɗai yasan yadda yake ji a zuciyarsa, kamar zai faɗa mata lalurar da yake fama da ita sai yayi tunanin in taji zata hana auren da Hauwa ta haɗo masa, shi kuma yana so yayi auren dan yayi maganinta. Yace. Baaba ina so ku shirya gobe In Allah ya kaimu da safe wajen goma zamu tafi Ilori, za muyi kusan mako biyu a can. Ilori wannan yaro, ashe zamu sha zaman mota. A'a jirgin sama zamu hau dan har nayi mana buking ticket. Ikon Allah Saude a jirgi taf! Allah yasa zan iya, dan naji ance akwai ɗaga hankali tashin jirki sama, har 'yan hanjin mutum sai ya kaɗa. Baaba da nake yi miki shirin Hajji bana dake za ayi, kice ba zaki iya zuwa ba. Zuwa kai ɗan nan, garin Manzo s.a.w fa, ai ko kasaye hanjin cikina zanyi wlh sai na je. Aminu ya kwashe da dariya su Abi suna tayashi, itama dariyar tayi tana cewa. Yo makka fa! wanda ban taɓa zata ba ko a mafarki, wlh ko da jan giuwa ne sai na je. Haka suka cigaba da hira gwanin sha'awa, haƙiƙa zaman baba Saude a gidan Aminu ya sauya rayuwarsa daga damuwa sosai, ya samar masa da farin ciki shida yaransa. ***** Hauwa da Najwa. Da yamma Hauwa ta garzaya babban gida tayi sa'a Alhasan ya dawo, nan ta zauna ta rattafa masa yadda suka yi da Aminu, yace shi bai yarda ba sai da ya kira shi ya tabbatar kafin yace zasu suje nima masa auren Najwa, sannan ta sanar da iyayen yarinyar su faɗi ran da zasu je, nan take Hauwa ta kira Najwa a waya, Najwa da take haɗa gawayin girki taji wayarta tana kara a ɗaki, tayi sauri ta miƙe zata je ta ɗauki wayar, sai inna ta dakatar da ita. Wlh koma ki haɗa wutar nan dan in kika ɗauki wayar nan yau bamu ba cin abinci dare da wuri, dan kin zama aljanar waya hatta haddar naki ya zama shiriri kin daina zuwa makaranta saboda kin sakawa kanki shirme. To inna wlh Haddar ce ya daina shiya, sai in dage inyi karatu sai naje badawa na kasa, shiyasa na hakura. Hmmm to kin sakawa kanki jarabar son aure kuma saurayin da kike ta faɗa zai turo shuru muke ji ɗan sanda yaci shirwa. Zai zo ne In Sha Allah, ba zama yake ba sai a waya muka hira shiyasa. Allah yasa ba irin mayaudaran nan bane, ya jirgaki a banza kina zaman jiransa. Ni dai ki bari na duba wanda ya kirani, kinga har sau biyu ana kira, wata ƙila ma shine ya kira. Inna bata ce komai ba ta cigaba da gyara kayan miya da zata jajjaga na dafadukan shinkafa da za suyi na manja, ganin bata ce komai ba yasa ta wuce ɗaki ta zauna gefen gado tana dubawa taga Hauwa ce, cikin zaƙuwa ta danna mata kira ringing ɗaya Hauwa ta ɗauka bayan sun gaisa Najwa ta bata hakuri akan bata kusa da wayar ne. Diyar Albarka babu damuwa dama maganar aurenku ne ya taso, ina so ki tambayi iyayenki yaushe za a zo nimawa Aminu aurenki. Wani irin miƙewa Najwa tayi cike da tsananin farin ciki dan ta daɗe tana jiran zuwan wannan ranar, tace zata sanar da inna in sun yanke ranar zata faɗa mata, haka suka yi sallama ta kashe wayar, Najwa ta daka wani uban tsalle tana ihun wayyo Allah daɗi. Da sauri inna tabar abinda take yi, ta leƙo ɗakin ta duba me ya sameta, dan har ga Allah tayi zaton ko wani abin tashin hankali ne aka faɗa mata a wayar. [7/7, 13:04] Buhainat😁: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shaidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.* 26. Najwa ganin Inna ta leƙo ta isa garena tana dariya. Inna albishirinki? Wani kallo Inna tayi mata mai ɗauke da harara sai Najwa taja da baya tana cewa. Kuɗin aurena fa za a kawo nake so na faɗa miki, yanzun nan aka sanar dani na faɗa muku ku saka ranar da iyayen Muhammad zasu zo. Kina da hankali kuwa Najwa? Yaron da bamu sanshi ba shi ne zai turo. Haba inna ke da zaki tayani murna shine zaki fara korafi, tun yaushe kike so kiga na fito da miji na yi aure, amma kike niman ki sakar mini da guiwa. Ni bawai bana murna bane kawai dai naga yaron nan bai taɓa zuwa wajen babanku ya nima izini ba ko ya turo a niman masa, sai kawai maganar aure, dama shi zancen ne kike yiwa ihu? na ɗauka ma ko mummunar labari aka baki. Zencen kenan inna. To Allah ya kyauta ni ki fito ki ɗaura sanwa biyar ta wuce, in babanku ya dawo zan sanar da shi muji ranar da zasu zo. To Najwa tace jiki na rawa ta aje wayarta ta fito ta cigaba da haɗa wutar , alla alla take ta gama ta koma ɗaki ta bawa Nafeesa labarin abinda ke faruwa, da duk ta sare ganin an shafe watanni ba wata magana har cewa Nafeesa take yi kamar dai auren ba zai yuwu ba, da alama ita ba tada sa'a ga Sameeha ta fita amma kuma shigarta gidan yana niman ya zama wahala, Binafa tace ko zasu gwada shiga malamai ne a karkato da hankalin Aminu, Najwa tace shagalarta bai kai nan ba dan haka zata cigaba da gwada sa'arta idan kuma lamarin ya ci tura sai su kauce hanya duk da ba hakan take so ba. Sai bayan sallar Isha'i Najwa ta samu kanta wanda a lokacin ta kira Nafeesa ta faɗa mata, ba ƙaramin murna tayi ba tace washe gari zata zo tare da Binafa dan su tayata murna, tace ba damuwa sai sun zo, nan dai ta hau online ta fara sakin status da wasu maganganu mai harshen damo, wanda yake nuna tana cikin farin ciki, wanɗanda suka gani suka kasa shuru sai da suka tanka tace ba komai tare da gindawo ƙarya, Ikram ma tana cikin waɗanda suka yi mata magana akan. Allah yasa ba wani kika cuta ba kike murna, dan nasan halinki uwar yaudara. Bana son tashin kanhali karki farraka mini farin cikin da nake ciki, kuma Zaidu ne nace bana so akai kasuwa idan ma dan shi kike wannan surutun. Kanki ake ji, kuma wlh a juri zuwa rafi watarana dole tulu sai ya fashe. Cewar Ikram Najwa ta rubuta mata tsaki tare da imoji na gwalo, Ikram bata ƙara bi takanta ba ta cigaba da chart da mutanenta. Inna a daren ta faɗawa baba yace su zo jibi Juma'a bayan sallar magariba ko isha'i. Inna tazo ta faɗa mata nan take ta kira Hauwa ta sanar da ita, ranar Najwa da Hauwa sunyi kwanan farin cikin da suka jima basu yi shi ba. ****** Ranar Juma'a. Kamar yadda suka tsara hakan ta kasance Yaya Alhassan Kamalu da Kawu Lawal da wani abokin Abba Alhaji Datti sune suka je nimawa Aminu auren Najwa, ba wani ja baba yace ya basu dan yarinya tace tana so kuma ba zai yi mata auren dole ba, ganin Baba yasan Alhaji datti ya kuma ce ɗan Amininsa ne daya rasu yasa shi saurin amincewa, sam Baba bai gane daga dangin mijin Sameeha bane tunda shekaru kusan goma sha ɗaya da yawa, sannan ma lokacin bikin Sameeha ɗaurin aure kawai yaje bai wayesu ba. Suka yanke sadaki dubu dari na gaisuwa dubu Hamsin sai kayan saka rana dubu Hamsin, nan suka basu musu dubu ɗari biyu cash 'yan dubu ɗai-ɗai, baba yayi matuƙar jin dadin tare da ɗan uwansa Malam Isyaku da kuma Junaid yayan Najwa, suka tsaida rana nan da wata shida mai zuwa lokacin azumi bai wuce wata guda ba, dan a lokacin ne Aminu ya buƙaci a saka rana a cewarsa lokacin ne ya kammala shiryawa, suka ce ba damuwa Allah ya kaimu, nan dai suka rabu cikin tsananin farin ciki suka tafi ko wanne yana sambarka, da baba ya sallami ɗan uwansa ya shiga gida ya kwalawa Inna kira a tsakar gida ta fito daga ɗaki tana amsawa, baba ya miƙa mata kuɗi dumus yana cewa. Ɗiyarki dai tayi goshi dubu ɗari biyu aka amsa na aurenta, an tsaida rana nan da wata shida a ƙarshen watan, ranar ne kaɗai ba a faɗa ba ko Juma'a ko Asabar. Malam daga zuwa ba wani bincike sai maganar aure gadan gadan har da saka rana. Ke dalla abu ne ma na gida, nasan ɗaya daga cikin manema auren kuma nan kusa suke unguwar dosa, kiyi fatan Allah yasa hakan alkhairi ne, yanzu kije ki adana kuɗin nan mu samu sayan mata kayan katako na MG furnitures, naji faɗi da aka saka bikin da nisa. To Allah ya nuna mana yasa ayi damu ya kuma sanya alkhairi kaga muma saimu shirya a hankali ba gaggawa. Cewar Inna baba yace hakane kam kana ya shiga ɗakinsa, inna ta tafi ɗakinta ta adana kudin ta fito ta shiga dakin Najwa da duk taji abinda suka tattauna, tayi murna cewar an kawo kuɗin aurenta na Aminu mijin Anty Sameeha da nan da kwanaki zata maye gurbinta, sai dai murnan ta bai kai zuciya ba ganin an saka bikin da nisa taso ace baifi wata biyu aka saka ba. Inna tace. To hankalinki sai ya kwanta an kawo kuɗin aurenki kuma an saka rana wata shida. Wlh inna na so wata biyu kawai aka saka ayi a huta. Daƙuwa inna tayi mata. Kin ci gidanku Najwa gabaɗaya kin zama fitsararriya na rasa meya sauya min ke duk ki canza hali. Inna zamani ne fa mu ba irin mutanen da bane komai yanzu an waye. Da rashin kunya ba. Allah dai ya kawo lokaci ki bar mini gida na huta da fitsaranki. Amin Najwa tace a hankali Inna tace. Au amsawa kika yi. Uu um inna bance komai ba. Najwa ta faɗa tana gumtse bakinta. Inna girgiza kai tayi ta wuce ɗakinta, Najwa kam ta hau WhatsApp tana rubuta status. _Ranar muke jira yau gashi ta zo, wato rana bata ƙarya sai dai uwar ɗiya taji kunya._ Nan mutane suka yi mata ca da tambaya, sai duk tsuit banza dasu ta cigaba da hira da Nafeesa da take bata labari, ba zata so aurenta ya bayyana ba sai ya zo gab saboda akwai samarinta da take so ta cigaba da wankesu son ranta, dan tayi alƙawari a jikinsu zata samu kuɗin sayan wasu kayan kitchen. ... Washe gari Asabar Inna ta tafi can gidansu ta sanar da 'yan uwanta, sannan tace in an kawo sweet da goro na saka rana zata aiko a rabawa dangi, daga nan ta wuce gidan su Sameeha dan ta faɗawa su Umma, koda taje ta samu Sameeha bata nan Umma tace mata taje kasuwa Ikram kuma lokacin ne ta dawo akan zata bi Sameeha Kasuwa su dawo tare, sai suka yi waya Sameeha tace a lokacin take shirin dawowa harma da zanen kayan da ta ce zata siyawa yaranta Ikram ta hanata. **** Sameeha. Da suka shigo kan titin Sabon kawo sun zo kan wani layi Khairy ta tsaida motarta a titi ta rage volume ɗin wakar da suke saurare, ta na cewa Sameeha. Wannan layin shine layin gidana idan kika shiga zaki ga wata makarantar boko private an rubuta Khairy nursery and primary academy. Ko makarantar kika shiga kice a kaiki gidan Ummulkairi maman Faisal za a nuna miki gidana. Allah sarki aiko wata rana zaki ganni bari na samu abin hawa na ƙarasa, nagode Allah ya saka da alkhairi. Sameeha tace tana tunanin makarantar ma nata ne a yadda ta faɗi kwatancen gidanta, to ko meye nawa a zuwa gidanta oho, tace a ranta sai ta juya tana ƙoƙarin buɗe motar Khairy tayi saurin saka shii a luck, da sauri ta waigo ƙirjinta na dukan uku uku, Khairy ta sakar mata murmushi. Har gida zan kai ki domin na ƙarasa samun ladanki. Wlh da kin barshi ai na kusa gida ko a kafa zan ƙarasa ma. Hmmm Khairy tace cike da ƙarfin hali ta kunna mota suka ci-gaba da tafiya, Sameeha ta kasa cewa komai sai mamakin ƙarfin halinta kawai take yi, ta cigaba da kallon gefen hanya ba wanda ya cewa kowa komai har suka fara shiga rafin guza, sai Sameeha ta tsinkayi maganar Khairy. Ina ne unguwarku. Layi na biyu ne idan kin je sai ki sauke ni bakin hanya na kasara. Murmushi Khairy tayi ta cigaba da tuƙi har suka kai kan layin Sameeha tana jiran ta tsaya sai taga ta shiga layin Khairy ko a jikinta, har tana jiman wuce gidansu sai ta dakatar da ita. Ai mun kawo wannan gidan ne mai baƙin gate. Masha Allah, na kawoki lafiya ba tare da na cutar da ke ba sai hankalinki ya kwanta dan naga a tsorace kike dani, ni kuma wlh zuciyata fes. Murmushin yaƙe Sameeha tayi. Haba karki ɗauka haka kawai dai kin san yadda rayuwar take yanzu mutum ba abin yarda bane, amma yau ke kin cire mini shakka, Nagode sosai bari na shiga gida Ba komai ga wayata ki saka mini number ɗinki mu riƙa gaisawa ko ta WhatsApp ne in kina yi. Sannan baki sanar dani sunan ba. Sameeha ba wani ja ba ta amsa wayar tana murmushi ta saka mata number ɗinta sai ta miƙa mata, ta buɗe motar da yake ta yi unluck ɗin motar, tana fita Anwar yana fitowa daga gida yana ganin Sameeha ya taraso da sauri yana. Anty Sameeha inna Rakiya tazo tare da Anty Kuluwa kuma innar Najwa tazo duk suna ciki. To kai ina zaka suda mai bakin magana. Pure water zan sayo na gida ya ƙare. Ya bata amsa yana wucewa, Sameeha ta rufewa Khairy motar tana cewa. Kiyi hakuri na tsaida ki, sunana Sameeha Ahmad maman Abi da Amrah. Murmushi Khairy ta yi tana gyaɗa mata kai kana suka yi sallama ta ja motar baya tayi ribas duk akan idon Sameeha kana ta juya motar ta wuce tana danna mata hon Sameeha tana ɗaga mata hannu kana ta shiga gida. Tana isa falon umma ta tadda baƙi wato Ƙanwar umma inna Rakiya da 'yarta Kuluwa da suka zo daga Zaria, sai inna Zulai mahaifiyar Najwa,nan ta zauna suka gaisa kana suka shiga hira inna Rakiya na cewa. Ai tun safe muka zo muna gidan baba nace nan zan kwana shiyasa na tawo da wuri muyi hira kuma zuwan ma kusan naki ne takanas. Sameeha ta saki murmushi. Naji daɗi Inna yau zamu faba dare muna hira. Gogganmu ina Najwa? ta kwana biyu bata leƙomu ba. Ta ƙare maganarta ga inna Zulai, sai tace mata. Ai Najwa an kusa girma dan an saka ranar bikinta nan da wata shida in Allah ga kaimu shiyasa nazo na sanar daku. Wani mai rabo ne zai yi wuf da ita haka, to Allah ya sanya alkhairi yasa ayi damu. Ameen ya rabbi, sunan yaron Muhammad yana aiki a Abuja. Lallai Najwa ta samo mana mai zafi ashe Abuja zamu kaita. Masha Allah nayi murna kwarai. To bamu san inda zata zauna ba tukuna tunda ance ɗan nan ne kowa nasa yana nan. Allah sarki to Allah ya sa albarka. Ni bari nayi sallar Azahar. Cewar Sameeha sai ta miƙe ta fito tsakar gida su kuma suka cigaba da hira dan duk sunyi nasu sallan. Sai wajen ƙarfe uku Inna tabar gidan a lokacin ne inna Rakiya ta samu damar faɗawa umma zacen dake cinta a zuciyata. Nifa yaya maganar Sameeha ya kawo ni, Idrisa ƙanin mijina dake aiki a Kano tunda yaji labarin mutuwar aurenta ya dage akan yanq ciki in ta fita idda zai zo ayi magana. Shine fa tunda yaji nace zan zo ya matsa mini numba, shiyasa nace zan sanar daku inna zo. Umma tayi shuru can ta kalli Sameeha da take gyara wake tana cewa. Ga ki ga Sameehan ai tana jinki, dan yanzu magana nata ne ba a yiwa Bazawara zaɓen miji sai wanda ta kawo. Ai nasan ɗiyata ba zata bani kunya ba, Sameeha ina so ki bawa Idrisa dama ku daidaita yaron yana da mutunci ga sanin ya kamata, yana aiki a kano a wani company amma matarsa tana nan cikin zaria kusa damu, yaransa biyu duk maza. Inna banƙi ta taki ba amma gaskiya a yanzu babu tsarin yin aure a zuciyata ko in ce nan kusa, ban sani ba ko nan gaba in abubuwa sun daidaita a zuciyata, dan in har na amince kamar na takurawa kaina ne. Haba Sameeha ƙanin mijina ne fa kuma nasan halinshi ba wata matsala wlh ko matarsa ba tada damuwa dan tasan yana sonki. Inna a bani lokaci. Sameeha ta faɗa tana miƙewa ta fita tsakar gida da ido suka rakata, Inna tana cewa. Ni wlh banda ya takura bazan yi maganar ba tunda yaushe ma ta fita idda, sannan ma ai da ciwo har yanzu a zuciyarta na abubuwan daya faru, zan sanar da shi ya hakura kawai dan ba zan so takurata ba Allah. A'a kar kiyi saurin yanke hukunci Rukayya, ki bari tunda tace a bata lokaci kuma nima zanyi magana da ita dan aure shine cikar mutuncinta ai. Haka suka dinga tattaunawa Sameeha tana jinsu duk zuciyarta a dagule, sarai ta gane wanda suke magana sam bai yi mata ba balle ta kawo wa zuciyarta sha'awar aurensa, haka ta ƙarasa yininta sukuku dan har gobe son Aminu yana manne a zuciyarta, dangana ne kawai tayi a ba yadda zata yi. ***** Khairy. Tana isa gida ta shiga kitchen dan dafawa kanta abinci saboda gabaɗaya yaran sun je gidansu suyi hutu saboda anyi hutun makaranta, ita kaɗai ce a gidan sai 'yar aikinta Naja sannan mijinta baya nan kuma ma ba itace da girki ba yana gidan amaryansa, wayarta data ji tana ƙara a falo yasa ta fito ta isa center table ta ɗauka, ganin anty Amina ce babbar yayarsu da take aure a Abuja yasa ta ɗaga da sauri. Ina yini Anty. Amina ta amsa suka shiga gaisawa da hirarsu ta zumunci, can sai Khairy tace mata. Anty yau na haɗu da mai kama da marigayiya Mubeena hatta wushiryarsu da dimple ɗinsu iri daya, sai dai ita wannan tanada manyan idanu. Nan ta kwashe yadda suka haɗu da Sameeha da komai da faɗa mata. Khairy sannu da ƙarfin hali, kawai sai ki shigewa mata baku ssn juna ba, kika sani ko tanada wani aure a kanta in kin yi zargin ma bata tare da uban yaranta. Anty Amina wannan ba tada aure dan a gidan iyayenta na sauketa. Alhamdulillah da alama Ibrahim ya samu mata, dan na tabbata in ya ganta tayi kama da Mubeena zai sota, sai dai kafin nan ki shiga jikinta sosai kisan abubuwa game da ita da bugan ruwan cikinta akan me ya rabata da mijinta. Idan kin samu bayani mai kyau ki riƙa sanar dani. Anty ai wannan dai ina ganin sakin ganganci mijin yayi mata dan wlh full option ce matar fita anguwa, yaya Khalil ya samu matar shiga taro tunda Labeeba tana ja masa aji. Aiko ajinta yana gab da tsinkewa dan gani take kamar ba zai iya ƙara aure ba tunda yaƙi karɓan tayi a cikin dangi da aketa yi masa na 'yan mata, Allah dai ya zaɓa abinda ya yake Alkhairi, karki faɗawa kowa wannan maganar har sai mun tabbatar da ta cancanta. To khairy ta faɗa tana murmushi kana suka shiga hirar walimar haddar da Ƙaninsu zai yi nan da wata guda, taro suke shiryawa na gani na faɗa dan shine autansu kuma mahaifinsu Allah yayi masa rasuwa sai Hajiyarsu ce data rage musu. Dan haka dole sune zasu tsaya su tsara komai yadda zasu fita kunyar mutanan da suka tara. Wani kira daya shigo wayarta yasa tayi sallama da anty Amina ta ɗauka tana cewa. Babban wa uba kuma mai share hawayen Khairy. Zaki fara ko? gani na shigo gari ki haɗa mini abinci na mutum biyar haka zuwa shida, meeting zanyi dasu da dare a guest house ɗina, kin san bana son abincin waje saboda tsaro, sannan Nabeela bata gari bana so naje gida nasa Ma'u girka Hajiya ta yi faɗa, kin san bata ƙaunar rashin zaman da Nabila bata yi a gari. Karka damu Honorable, kamar me zan dafa yanzu na fara shiri. Fried rice da tuwon shinkafa miyar agushi da kuma sauran abinda kika ga ya dace ki ƙara, karki damu da drink abincin kawai zaki girka na fita kunya. To In Sha Allah zuwa magrib komai ya kammala sai ka aiko a amsar maka. Ok ya faɗa kana ya kashe wayar ba jimawa taji alert ya shigo wayarta na dubu ɗari biyar, wani murmushi ta saki ta miƙe tana cewa a fili. Yaya kenan baya gajiya da kyauta, ɗan girkin nan shine ya bani wannan kuɗin haka. Ta ƙare maganar cike da tsantsar farin ciki da nishaɗi. [7/7, 13:04] Buhainat😁: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shaidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.* 27. Khairy sai gabda magrib ta kammala musu abincin wanda ta haɗa da farfesun naman rago da kuma soyayyar kaza haɗi da sakwara da ta tuƙa musu garinsa su ci da miyar aghushi, a cikin wasu jigaggun food wormers ta zuba abincin ta shiryasu akan dinning idan driver yazo ya kwashe, ta koma ɗaki ta bar Naja tana gyara kitchen ɗin, sai ta shiga wanka lokacin da ta fito ana kiran salla, dama da alwalarta ta fito ta saka hijab da zanin data ware na sallah ta gabatar da farilla, data idar ta miƙe ta shafa mai ta ɗauko wasu ƙananun kaya riga baka mai guntun hannu ta kamata sai legis baƙi shima ta ɗaure gashinta ta filo falo ta zauna a cushing tana mayar da numfashi, sosai ta gaji da girkin da tayi duk da ta saba da girki dan bata yarda mai aiki tana saka mata hannu a fannin abinci, shiyasa ta ciri tutu a gun mijinta dan yana matuƙar son abincinta saboda ta iya girki kala kala, musamman take da group a WhatsApp na girki tana faɗawa mata irin nata salon basirar kyauta. Sai kuma naƙasunta bata iya gyaran gida tana da shauni da son jiki bata son wahala hatta ɗakinta mai aiki take gyarawa ɗakin mijin ne take ƙoƙarin gyara masa dan bata yarda tana wasa da hidimarsa, sannan bata son raino shiyasa ta ce ita ta gama haihuwa hudun nan sun isheta. Wayarta ce ta katse mata kallon tv da take yi tana ringing, ko da ta duba Yaya Ibrahim ne ta ɗauka da sauri. Khairy abincin ya kammala kuwa? Tun ɗazu na gama driver zai iya zuwa ya ɗauka. A'a ki kira mijinki ki faɗa masa zaki kawo mini abinci, nafi so ki kawo da kanki dan bana yarda da kowa sama daku 'yan uwana sai matata a fannin abinda zan ci saboda tsaro, idan ba zaki iya tuƙi ba zan aiko driver ya zo ya ɗauke ki ya dawo dake. Zan iya ma bari na fito, amma guest house ɗin zan kawo maka dake NDC. A'a gidana dake unguwar sarki zaki kai mini. To tace masa ta kashe wayar tana miƙewa tare da komawa ɗaki ta ɗauki dogon hijab har ƙasa ta saka, sai ta ɗauki key motarta ta fito ta kwalawa Naja kira ta fito daga ɗakinta, sai ta yi mata umarni ta kwashe kulolin abincin zuwa mota. Ummulkairi kenan ɗiyar Alhaji Aliyu Turaki da Hajiya Aisha 'yar Saifullahi Wazirin Zazzau, su asalin 'yan zaria ne kuma Hausa Fulani aurensu haɗin zumunci ne su 'ya'yan abokai, wanda suma ɗin suna son juna dalilin da yasa iyayansu suka haɗasu. Aliyu ya samu karatun zamani sosai sannan yana da ilimin addini dan mahaifinsa malami ne wanda yake limamin gidan sarki, sannan shima Aliyu kafin ya bar zaria ya cigaba da limanci a masallacin bayan rasuwar mahaifinsa. Ya samu sunan Turaki ne kasantuwar ya gaji sunan kakansa, kasuwanci ne ya baro shi zaria ya yada zango a kaduna, a nan ne Allah ya nufa arzikinsa yake, domin ya shahara saboda company fulawa da yake da shi, semo, gishiri taliya dama kuma wani company daban na yin shinkafa. Yaransu biyar, Amina itabce farko tana aure a Abuja mijinta babban ɗan siyasa ne ya riƙe mukamai da dama daga bisani yayi retire ya cigaba da kasuwanci, yaranta bakwai ta aurar da huɗu saura uku, Sai Aisha ita tana aure a Yobe yaranta biyar ta aurar da biyu, sannan Ibrahim khalil shi yayi auren farko da 'yar ƙanwar Hajiyarsu mai suna Mubeena sai dai Allah ya yi mata rasuwa a gurin haihuwarta na farko, sai da ya shekara biyar kafin ya ƙara wani auren shima bisa matsawar da 'yan uwa suka yi masa da kuma takura shi da Nabeela ta yi saboda tana mutuwar sonsa, ita 'yar hanshaƙin mai kuɗi ne dan babanta ya riƙe mukamin Ministan kuɗi a wancen zamanin baya, sannan ya rasu ya bar musu dukiya wanda shine take juyawa take harkan business ba kama hannun yaro, matsalarta tafi martaba kasuwancinta fiye da aurenta duk da tana mugun sonsa amma harkan kuɗi ba tada sauƙi, plaza ɗinta biyu ɗaya a Abuja ɗaya a nan Kaduna. Lokacin Ummulkairi shekarar ta biyar da aure har ta yi haihuwa biyu dan lokaci guda aka yi aurenta da Ibrahim tana gama secondary ita da Mubeena aka yi musu aure sai dai Alkah ya rubuta Mubeena ba zata yi tsawon rai ba, khairy a ƙasar Sudan ta cigaba da karatunta har ta haɗa digree, saboda mijinta Ahmad a can ya yi karatu a matakin ƙarshe aka yi musu aure ya tafi da ita, yana gamawa ya samu aiki sai ya nima mata makaranta ta soma, basu dawo Nigeria ba sai a lokacin bikin Ibrahim da zai auri Nabeela wanda ta ƙare karatunta shine Ahmad ya aje aikinsa suka dawo gaba ɗaya. A lokacin Ibrahim yana ɗan majalisan jiha saboda shi tunda ya girma yake ƙaunar harkan siyasa shiyasa ya kama ƙafa da mijin anty Amina saboda yana da mutane sosai domin shima ya yi harkan, kuma ya samu goyon baya dan da farko Hajiya taso taƙi yarda amma data ga ya dage sai ta bishi da addu'a. Mahaifinsu ya rasu shekara uku daya wuce wanda mutuwarsa ya girgiza su dan ba wani ciwo ya yi ba daga ciwon kai ya kwanta sai dai suka same shi ya cika, sunyi kukan rashin sa daga bisani suka ɗauki dangana. An raba musu gado mai tarin yawa dan ko wannansu sai da ya samu kuɗi da gidaje. Anty Amina ta sayarsa kadarorinta ta gina gidajen mai ta buɗe wanda duk in aka ga AA Turaki petroleum and gas nata ne, Anty Aisha itama sayar da nata kadarorin tayi ta haɗe kuɗinta ta gina plaza, duk wani plaza da yake amsa AATuraki Plaza nata ne dan a plazanta ne Khairy take da shago a kasuwar gari, ita kuma Khairy wannan shagon boutique da kuma makarantar dara buɗe sune nata sai gidan goda da take harkan kiyon dabbobi, Ibrahim kuma company fulawa ne ya zama nashi da gida biyu da kuma kudi, ya mayar da hankalinsa akan company, Autansu kuma company shinkafa ne nashi da kuma kuɗi da gida, Hajiya kuma gidan marayu ta buɗe da kuma islamiyya domin ya zama sakatul jariya ga mijinta, sannan tana da gidan gona da kuma gidan da suke ciki nata neda kuma kudi masu nauyi. A lokacin da khairy ta ƙara samun yara biyu a sannan shima Ibrahim yaransa biyu duk maza, Haydar da ya 'ci sunan mahsifinsu sai Musa da yaci sunan mahaifin Nabeela suna ce masa Dady. Ibrahim bayan ɗan majalisan jaha ya ƙara tsayawa takarar ɗan majalisan tarayya na kasa sai dai bai samu ba, shiyasa ya haƙura ya cigaba da bunƙasa kasywancinsa dan har motoci yake sayarwa, shekarar data gabata ya tsaya takarar Senator ta Kaduna ta tsakiya wanda cikin hukuncin Alkah ya samu kujerar, watansa bakwai kenan akan kujerar Sanator, da yake shi mutum ne mai kyauta da son mutane wannan ne ya kaishi ga matakin cin nasara. Sai dai ya ƙara zama busy baya Abuja baya Kaduna, ko kuma ya fita waje dan wani aikin, yaso ya zauna a Abuja da iyalinsa amma Nabeela yaƙi saboda harkokin da ta ke gudanarwa a Kaduna, sannan bata fiye zama ba tana yawan fita kasar waje akan harkan kasuwancinta, ita fa muƙaminsa bai wani ɗaɗata da ƙasa ba dan burinta ta zama ta shahara an saka sunanta a cikin jerin matan da suka shahara da kuɗi, sai dai kullun nima take yi kuɗin sun ƙi haɗuwa yadda ya take so, dan ta raina wanda da take samu so take tafi haka dan da zata ganta a matsayin Ibrahim zata so, gashi ko Khairy da take zaune guri guda ta fita arziki da samun kuɗi saboda bata saka wa kanta son duniya ba kuma tana da godiyar Allah, balle a kaiga su Anty Amina da Aisha, wane ita ta kama ƙafarsu. Wannan buri na Nabeela yana damun Ibrahim ga dukiya da mulki duk ta samu amma ita hakan be mata ba a cewarta nashi nashi ne nata tana ne, shiyasa ya rabu da ita baya takurata saboda aure ne suke yinsa bisa tsarin boko da wayewa ba addini ba. Wannan rayuwar da Nabeela ta ɗaukarwa kanta yasa ta surewa 'yan uwan Ibrahim suka soma tsanarta saboda ba tarbiyyan gidansu bane duk da suna da dukiya da sarauta amma bai sa sun yada tarbiyyansu ba, domin sun fito daga tsatson malamai da kuma Hajiyarsu tayi matuƙar ƙoƙari wajen tarbiyyansu. Ko sha'aininsu bata zuwa sai ta ga dama muddun ya ci karo da nata hidimar kasuwancinta, bata zuwa gaishe da Hajiya sai tayi niyya kuma duk da gidansu manne yake dana juna har da ƙofa ma a tsakiya, hakan yasa suka dinga kawo 'yan mata daga cikin dangi akan ya ƙara aure yace shi ba zai ƙara ba, koma zai yi ba zai auri 'yar uwarsa ba yafi ƙaunar bare, sannan harkan siyasarsa ba zai bari ya samu lokacin mata biyu ba duk da akwai abubuwa da yawa daya rasa a gurin Nabeela dan hatta kwanciyar aure sukan ɗauki lokaci basu yi ba, to shi yana Abuja ita tana Kaduna sai abin ya matsoshi ne yake zuwa ya sauke nauyi, Allah yasa ma baya harkan matan banza duk da suna kawo kansu amma bai yarda ya kaune hanyar Allah shiyasa yake yawan yin azumin Litinin da Alhamis hakan har ya bi jikinsa. Yau ma ya shigo Kaduna ne domin tattaunawar sirri da zai yi da wasu mutane da suka zo daga Lagos, shiyasa yaso sauke su a guest house ɗinsa amma yana shiga gidansa na unguwar sarki mutane suka fara gewaye gidan shiyasa ya yanke yin meeting ɗin a gidan dan baya so ya fita da mota wasu su bishi suga guest house ɗinsa inda yake ɓuya ya huta, mutanen tun biyar na yamma suka zo dama yayi musu oder ɗin kayan ciye ciye, Abinci ne ya bawa Khairy tayi saboda baya cin na waje gudun matsala dan kuwa yana da maƙila fili dana ɓoye, dan yana da matuƙar farin jini saboda kyautatawarsa ga mutane, shiyasa Hajiya take yawan yi masa addu'a sannan tana cewa ya kula da abincinsa kar ya riƙa zuwa restaurant yana ci saboda rayuwar yanzu mutum ake kiwo ba dabba ba, shiyasa yake burin ya ƙara aure ya samu matar da zata kula da shi da kyau. Ko a Abuja gidan Anty Amina yake cin abinci ko ta aika masa yara har gidansa su kai masa, a nan Kaduna kuma ko yaci a gidansu ko kuma ya sa Khairy ta dafa masa duk abinda yake so, idan kuma matarsa tana gari ya saka tayi masa duk da ba son girkin take yi ba, nata ma tafi sakarwa masu aiki amma da yake tana son farin cikinsa ganin baya takura mata yasa take tsayawa ta girka masa. . .. Khairy tana kai masa abincin ta juyo gida, bata zauna ba ta gabatar da sallar isha'i, da ta idar ta ci abinci sai ta ɗan zauna a falo wajen goma saura ta kashe kayan kallo da wutan falon ta wuce ɗakinta ta kwanta, sai da tayi waya da mijinta dake Lagos dan baya gari da suka yi sallama sai ta kunna data ta soma chating, ta yiwa Sameeha sallama sai dai bata online ta cigaba da hira da 'yan uwanta. **** Sameeha. Tana kwance a uwar ɗakan umma taƙi zama a waje suyi hira dan sam taƙi samun sukuni tunda Inna Rakiya ta zo da zancen Idrisa, Ikram ta shigo ta zauna gefen gadon. Haba Anty ki fito ayi hira dake mana kin wani ƙunshe a ɗaki, ko dai dan maganar Idrisa ne yasa kika zama shuru shuru. Hmmm wlh sam abin bai kwanta bini ba shiyasa duk bana jin daɗin komai. Babu mai miki dole da in kince baki so. Kin san yanzu ma maganar Kuluwa suke yi, wai zasu yi musu haɗi ita da yaya Zaidu. Kai dan Allah. Sameeha tace tana tashi zaune dan maganar ya yi mata daɗi. Ikram ta mele baki tace a cikin ƙasa da murya dan kar aji. Anty kamar basu dace ba, yarinyar kwata kwata fa shekara sha takwas, yanzu take gama secondary, ni zan so ya auri babba mai ilimi wacce tafi Najwa. Abin ya zana ba dan Allah ba kenan, haba Ikram da imilinki zaki daɗi haka ai Kuluwa kuwa tana da kyau da ta samu hutu sosai zata yi fresh dan tana kama damu, ki ma bar wannan tunanin dan hali ake dubawa, ba ga Najwa ba tana da kyan ba hali sai son duniya ta sa a gaba, kinga imata aurenta zata yi dan haka in dai duk suna so ina goyon bayan haɗin. Hakane kuma to Allah yasa yaya Zaidu ya yarda dan naga yafi son classy beb. Sameeha tace Amin sai wayarta ta shiga ringing tana dubawa taga number ne kamar ba zata ɗaga ba sai ta ɗauka da sallama, jin muryan matar ɗazu yasa ta ɗan ɗaure fuska suka gaisa sai Khairy take cewa. Na yi miki magana online naga baki kai shine na ce bari na kira ki in kina free ki hau muyi hira. Allah sarki ya kika isa gida ɗazun? nafa gode. Yanzu kam barci nake ji dan har na kwanta kan gado. Nima na kwanta kafin barcin ya kamani ne nace ki hau muyi hira, yaran duk suna gidanmu na kai su suyi hutu, Abbansu kuma baya gari ko yana nan ma yana gun amaryansa. Allah sarki ashe kina da abokiyar zama. Eh shekara ɗaya da wata shida kenan da auren tana goyon yaronta Sadiq. To Allah ya haɗa kanku. Ameen. Kema Allah ya baki miji nagari. Ya aka yi kika san bani da aure? Sameeha ta faɗa tana waro ido waje, Ikram ko ta baza kunne tana jin hirarsu. Ɗazun naji kina magana da 'yar uwar ki a haka na fahimci kamar ba kida aure, ashe na cinka daidai. Hmmm aiko dai. To Allah ya zaɓa miki miji nagari ya baki wanda zai share miki hawaye ya Ƙaunaceki tsakani da Allah. Ameen, amma aure kam baya gabana dan gaskiya komai ya fice min a rai. Haba 'yar uwa da ƙuruciyarki fa, kuma duk macen data saba da namiji ai ba zata iya jure zama haka ba. Tun da na iya jure tsawon shekara shida aiko zan iya rayuwa ko ba aure. Sameeha ta faɗa cikin suɓucewar baki, Khairy kuwa gyara kwanciya tayi saboda an taɓo mata inda ke yi mata ƙaiƙayi. Ban fahimci me kika ce ba? Hmmm a bar maganar, kin ga yanzu ma mun cinye lokacin charting ɗin a waya nagode da zumunci. Ameen kina son dai kice kin gaji da hira da ni ne kawai. Murmushi Sameeha tayi tana cewa. Barci dai nake ji kuma na tabbata da oga na kusa ba zaki yi wayar nan dani haka ba. Taf ko zanyi, wlh banƙi na bawa amarya sati guda ba. Nifa na saka shi ka ƙara aure wlh. Ikon Allah ban taɓa jin macen da ta sa mijinta ya ƙara aure ba a zahiri sai ke. Ina da dalili, idan kin samu lokaci zan baki labari kota chart ne yanzu bari na barki sai da safe ki gaida du Umma. Zasu ji nagode. Tace mata sai suka aje wayar Sameeha tana mamakin sakewar da Khairy ta yi mata, Ikram da duk ta ji hirarsu tace. Anty wacece wannan naga kuna ta hira haka? Murmushi Sameeha tayi ta shiga bata labarin Khairy, sosai tayi mamakin yadda ta shigewa Sameeha. Anty ki dai bi a hankali nifa matan masu kuɗin nan da yawansu ba su da kamun kai, daga haɗuwarku ji yadda ta kiraki ta ɓata lokaci kuna magana, anya kuwa? In Sha Allah sai Alkhairi da Allah na dogara, kuma nima dole nayi taka tsantsan in naga abin nata yayi yawa blocking ɗinta zanyi wlh. Ki dai tsaya kiga gudun ruwanta, Allah yasa mu dace. Ta amsa da amin kana Ikram ta miƙe akan zata je bayi, Sameeha ta koma ta kwanta ta saka wayarta a silent ta yi addu'ar barci ta rufe idonta. Da safe ne Umma ke faɗa mata zancen su Zaidu kuma tayi magana dashi ya amince itama Kuluwa ta yarda, amma sai bayan azumi za a tada maganar aure, Sameeha tayi musu fatan alkhairi, umma ta amsa da amin kana tace. Kema da zaki bari ku daidaita da wannan yaron Idrisa da sai ayi bikin lokaci guda a huta, tunda kinga ansan shi ansan halinsa ba sai an yi wahalar bincike ba. Umma wlh sam abin bai kwanta mini ba, da zaki magana da inna ta bashi haƙuri kawai. Sameehaa bafa zaki zauna haka ba dole kiyi wani auren tunda ba halin komawa Aminu, ko da hali ma bai da lafiyar da zaki cigaba da zama dashi. Umma ki mini addu'a kawai amma Iddrisa bai kwanta mini ba gaskiya. Hmmm umma ta sauke ajiyar zuwa tana cewa. Shikenan zanyi magana da Rukayya a bashi haƙuri dan ba za mu yi miki dole ba. Anjima zan mu je babban gida a can zasu kwana gobe In Allah ya kwimu zasu wuce ki fito ki zo ki kama aikin gidan Ikram ta tafi makaranta. To Sameeha tace mata kana ta miƙe ta fito tsakar gida ta soma aiki. Data gama ta ɗaura abincin rana su Umma sai da suka ci kafin suka wuce gidan kakansu. Wajen ƙarfe biyu da rabi Sameeha tana zaune a tsakar gida tana katanta wani littafin Rahma Kabir Gashin Ƙuma a wayarta, sai taji sallamar Khairy ta shigo gidan da fara'arta. Da sauri ta ɗago tana kallonta cike da mamakin ganinta wanda ya bayyana ƙarara a fuskarta da kuma tunanin meya kawota gidansu. [7/7, 13:04] Buhainat😁: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shaidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.* 28. Sameeha tana kallonta har ta ƙaraso tabarmar da take zaune ta cire takalmi ta hau ta zauna tana cewa. Sannu da hutawa? Ke kaɗai ce a gidan? Yauwa sannu da zuwa. Lafiya kika zo? Sameeha ta bata amsa da tambaya fuskarta a dan ɗaure, Khairy sai da taji wani iri amma ta san dama dole za ayi haka tunda ba saninta tayi ba take shige mata, bata yi magana ba wayarta ta yi ƙara ko da ta duba Anty Amina ce dama sun haɗa plan idan ta zo zata yi mata text, to kafin ta shigo ta faɗa mata ta iso gidan shiyasa ta kira yadda zasu yi amfani da damar wajen Sameeha ta yarda da Khairy. Tana ɗaga kiran tace. Anty ina yini. Lafiya lau, kina gina kuwa. Aiko na je gurin mai kama da Mubeena dana ce miki jiya mun haɗu, wlh na kasa haƙuri na je gidansu, gata ma ku gaisa. Ta ƙare magana tana miƙawa Sameeha wayar tace. Yayata ce ku gaisa. Ba yadda taso dole ta amsa ta kara wayar a kunne ta gaisheta, Anty Amina ta amsa tana cewa. Kiyi hakuri da Khairy nasan ta takura mini haka take da shegen naci, kuma dalilin wai kina mata kama da wata ƙanwarmu ce da Allah yayi wa rasuwa, rana guda aka yi musu aure ita Khairy amma Allah yayi mata rasuwa gurin haihuwa, tun jiya ta kirani take cewa taga mai kama da Mubeena. Allah sarki Allah ya jikanta da Rahma yasa mu cika da imani. Ameen, ina ƙara baki hakurin takura miki da take niman yi. Bakomai ai, nagode. Cewar Sameeha kana tayi mata sallama ta miƙa wayar ga Khairy, tana amsa Amina ta rufe ta da faɗa kuma Sameeha tana ji saboda vulume ɗin wayarta ana ji sosai. Haba Khairy daga haɗuwa da mace zaki nima takurata me yasa kike haka, idan ke kin yarda da ita ita ta yarda dake ne da zaki nima shige mata, ba a haka gaskiya yadda rayuwar nan ta zama abin tsoro mutum ma abin tsiro ne, wai ma da kika fito kin faɗawa Ahmad ina zaki. Wlh da izininsa na fito, na faɗa masa zanje gun mai kama da Mubeenarmu. Wato shima kin faɗa masa kenan, kuma da yake shima sai a hankali ya biye miki ya barki kika fito, Allah ya kyauta amma bana so ki takurawa 'yar mutane ta ɗauka da wata manufa a ranki, tunda yanzu ɓata gari sunyi yawa, da mutuncinki da komai ki zubar da ƙimar gidanmu. Haba Anty ki daina yi mini wannan faɗar daga naje gunta, amma tunda hakane zan rabu da ita ni dai nasan wlh bazan taɓa cutar da ita ba balle nayi abinda zai ɓata sunan gidanmu. Tana kaiwa nan ta kashe wayar ta miƙe tsaye idonta cike da kwalla tana cewa. Dan Allah kiyi haƙuri ni ban zo gareki da nufin cutarwa ba, ban san da wani fuska ma kike mini kallo ba, amma ni tsakani da Allah nake nazo gareki kuma ganinki yana tuna mini 'yar uwata Mubeena ne. Sai anjima. Jikin Sameeha yayi sanyi sosai kuma ta fahimci lallai ba cutarwa a tare da ita musamman maganganun data ji yayarta tana faɗa, hakan sai ya saka ta samu natsuwa a ranta dan dama tana ta addu'a idan matar nan sharri ce a gareta Allah karya bata dama cutar da ita ya kuma rabata da ita. Da sauri ta dakatar da Khairy dan har ta kusa fita daga gidan. Dan Allah ki dawo Hajiya muyi magana. Tace cikin daga murya, Khairy data saki wani shu'umin murmushi sai ta gimtse fuska tayi na tausayi kana ta juya ta dawo ta zo ta zauna, kenan plan ɗinsu ya tafi kamar yadda Anty Amina ta tsara musu ɗazun da safe. Sai da ta zauna kafin Sameeha tace cikin kulawa. Meyasa zaki yanke mini hukunci ko kinji nace miki ina zarginki da wani abu ne? kawai dai ni tsoro kika saka mini dan gaskiya ina tsoron mutane musamman waɗanda nake ganin suna da damar cutar dani, da yawan matan masu kuɗi wasu ɓata gari ne kema kin sani, jiya muka haɗu sai gashi kin zo gidanmu yau kinga dole na cigaba da jin tsoronki, amma jin bayanin yayarki akan nayi miki kama da 'yar uwarku data rasu yasa na ɗan ji na rage shakka a kanki. Amma zan so ki nuna mini hotanta dan hakan ma zai ƙara kore mini shakku. Khairy bata ce mata komai ba sai duba wayarta data soma yi har sai da ta lalubo hotunan Mubeena wanda ciki har da na ɗaurin aurensu, ta miƙa mata Sameeha ta shiga duba hotunan tabbas suna yanayi da ita amma kuma Sameeha ta fita haske da shekaru, inda taga kamarsu sosai wani hoton Mubeena da tayi dariya wushiryarta ta fito da dimple, wanda yasa Sameeha yin murmushi ta ɗago tana kallon khairy dake kallonta. Na yarda da tayi maka dani musamman a wannan hoton, sai dai ita ta fini yarinya da kuma duhu. Shiyasa kika ga na nace miki saboda wlh ina ganinki a shagona na hango kamarki da ita, kinji dalilin daya saka naketa binki kenan, kuma wannan hotunan kusan shekara goma sha da suka wuce. Allah mai iko munyi kama a fusge, to Allah ya gafarta mata. Ameen, amma ina ƙanwarki ko itama ba ta nan? Ni kaɗai ce a gidan, sunje gidan kakanmu nan da bayan sallar la'asar zaki gansu. Allah sarki to Allah ya dawo dasu lafiya, kiyi hakuri na takuraki, wlh zaman gidan ba daɗi ni kaɗai shiyasa nazo dan na rage lokaci, ga babansu baya gari sai jibi zai dawo, yau kuma bama fita kasuwa, shiyasa nace bari kawai nazo gunki muyi hirar dana ce zan baki, sai kuma yaya Amina tazo ta rufeni da faɗa a waya. Ta ƙare maganar tana turmuke fuska, murmushi Sameeha tayi. Ai gaskiya ta faɗa kuma kema kin sani sai dai idonki ya rufe. Hmmm hakane, bari na baki labarin dalilin da yasa na saka mijina ƙara aure. Wlh tunda muka yi aure na fahimci shi mabuƙaci ne sosai haka na jure har muka baro ƙasar Sudan dana muka shafe shekara biyar a can, da yake ina gama secondary aka yi mini aure kuma muka tafi can, da muka dawo nan kowa yanata surutu na lalace, a haka har na haifi 'yata ta uku to ganin har lokacin ban dawo daidai ba yasa yayata Amina da kuma Aisha suka taso ni a gaba akan na sanar dasu damuwata dan sunga babu wata wahala a gidana sannan ma ga dukiyata ina juyawa, gaskiya ban so faɗa musu ba sai da suka matsa mini na faɗa musu halin da nake ciki, shine fa suka rufeni da faɗa akan zan kashe kaina akan sa tunda ba zan jure masa ba dole in bashi dama ya ƙara aure, in ba haka ba sai ya kasheni tun lokaci na bai yi ba kuma ya samu wata ya aura, maganar har gaban Hajiyarmu taje shine ta rarrashe ni dan taga su faɗa suke ta yi mini. Ni dai jinsu kawai nake amma ban jin zan yarda ya ƙara aure saboda mugun kishinsa da nake,'. To bayan shekara biyu na yaye Khadija sai na samu cikin Humaira kinsan maza suna masifar jin ɗanɗanon mai ciki, hakan yasa Ahmad ya matsa mini da takura, wanda ya jawo mini zubar jini ba ƙaƙƙautawa kamar zan sheƙa lahira, to wlh tunda na dawo hayyacina nace yaje ya nima aure bazan iya ba ko mu rabu. To kinji dalilin ƙara auren dana ce yayi duk da har gobe bawai ya daina matsa mini bane sai dai bana bashi fuska sosai dan gaskiya ina cutuwa, shiyasa kika ganni da ƙibata yanzu, amma da shekara uku baya ne wlh sai kin zata ciwo nake yi. Ta ƙare maganar cikin 'yar dariya, Sameeha ma dariya tayi tana cewa. Wannan shine kishiyar dole, wato ba dan wannan matsalar ba ba zaki yarda ta ƙara ba. To Allah ya baku hakurin zama. Ameen, ai kishiya Sameeha ba tada daɗi wlh sai dan dole in tana cikin ƙaddarar mace, amma da zafi fa kawai dai tawakkali na ɗauka yasa muke zaune lafiya, sannan karin samun kwanciyar hankalina ba gida ɗaya muke ba dan ban yarda ya hadamu ba. Amma ke ai ba kida kishiya ko a gidan baban yaranki. Ni kaɗai ce matar Aminu kuma ina ganin ni kaɗai ce zan kasance matarsa saboda wani dalili. Amma meyasa zaki ce haka? bayan kun rabu ai dole zai yi ƙoƙarin yin wani auren. Abin da ciwo shiyasa bana son tuna komai, amma ni nasan Aminu ba zai iya ƙara wani aure ba. Zan zo nasan labarinki amma bazan matsa miki ba dan naga har yanzu baki fita daga raɗaɗin rabuwarku ba. Bai wuce wata huɗu ba, ni yarana ma nake son gani ya ki kawo su. Ba'a garin nan suke ba? Nan ne ahalinsa suke, amma yana aiki a Abuja. Kiyi hakuri In Sha Allah watarana zaki gansu ki bashi lokaci wataƙila shima yana cikin damuwar da kike ciki ne. Allah ya baki juriya yasa kinci jarabawarsa dan wlh mutuwar aure ba ƙaramin ciwo gare shi ba sai a hankali zaki saba. Bari nazo na tafi wannan material ɗin ki ne na jiya dana ce zaki saya to na sayan miki, saura kice baki so tunda dai yanzu mun fahimci juna. A'a fa hajiya yanzu dai zamu fahinci junan, ba zan karɓa ba haka kurum na karya miki jali. Na dai yi niyya ba zaki saka naƙi samun ladanki ba wlh, dan narantse bazan tafi dashi ba in kin so ki bayar ko ki ƙona, Ki gaida su umma in sun dawo naso ma na gansu mu gaisa amma zan dawo wataran. Ta ƙare maganar tana miƙewa Sameeha itama ta miƙe riƙe da ledar kayan, tabi bayan Khairy zuwa bakin gate tana cewa. Ni dai wlh kin takurani da amsar kayan nan, haba wannan irin hidima, yo irin wannan kirkin naki ai sai mutum yaji tsoronki. Khairy ta kwashe da dariya. Ni dai ba mayya bace balle mai yankan kai, na dai gaya miki in baki so ki yar. Sai anjima Ta wuce ta buɗe motarta data yi parking a daidai ƙofar gate ɗin, Sameeha ta ware dan kwalinta ta yafe ta leƙo kai waje tana yi mata a sauka lafiya da godiya, sai da Khairy ta wuce kafin ta koma cikin gida tana jinjina wannan kirki na Khairy, ta zauna tana juya material ɗin tabbas yayi mata kyau sosai amma zata barwa Ikram ta ɗinki dan ita kam harga Allah ba zata yi amfani da shi tunda ma tana da kaya sosai. Sai bayan sallar la'asar su umma suka dawo sun tadda ta ɗaura tuwo a gawayi miyar kuka kuma a electric, ita da umma suna zaune a bisa wannan tabarmar da suke shan iska a kanta, Ikram ta fito daga ɗakin umna tana cewa. Anty wannan matrial ɗin fa na waye? na ganshi akan kayana. Na baki ne ki ɗinka. Kai amma anty nagode Allah ya saka da alkhairi. Ameen, matar jiya ce ta kawo mini, ɗazun tazo. Ba dai matar nan ta kasuwa ba da kuka haɗu? Ikram ta faɗa taba waro ido waje cike da mamaki, Sameeha tayi murmushi tana cewa. Ita fa, zauna dai kisha labari umma ma taji yadda ya wakata tsakani da ita. Nan fa Ikram ta zauna ta baza kunne umma ma da bata gane zancen su ba tana sauraren me Sameehan zata faɗa, sai ta shiga basu labari tiryan tiryen har da nuna musu hoton Mubeena da khairy ta tura mata, Umma itama taga kamarsu sosai tace haka Allah ke ikonsa, amma tayi mamakin yadda Khairy ta shige mata sosai, tace tabi a hankali duk da haka karta sake mata sosai dan bata son damuwa, Ikram dai tace wlh ɗinkawa zata yi taci bikin ƙawarta da bata samu yin anko ba, haka suna dinga hira gwanin sha'awa. ***** Aminu. Tunda suka tafi Ilori yake fama da busy dan in ya fita tun safe sai dare yake dawowa hotel ɗin da suka sauka, da yake Baba Saude tana tare da yaran shiyasa bayi da wata damuwa, ya kama musu falo da ɗaki biyu a ciki da bayi ko wane daki tamkar dai gida. Sai da aka ɗauki sati kafin ya samu kansa ya gama abinda ya kawo shi, sai ya shiga yawo dasu suna zaga wajen shaƙatawa suna ganin yadda tsarin garin yake, duk da dauriya yake yana danne zuciyarsa saboda kewar Sameeha daya dame shi, yaso ace suna tare a wannan tafiyar dan yasan Sameeha tana son tafiya haka musamnan garin da bata sani ba. Damuwarsa yadda yanzu Hauwa ta takura masa da kira akan batun Najwa da ta tura masa numbernta ya kirata, shi kuma sam baya ƙaunar kiranta dan in ya kira bai san me zai ce mata ba tunda ba sonta yake ba, sannan ma ga siraɗin daya ɗaura auren akai na zai yi ne domin ya hukunta Hauwa, sannan damuwarsa akan bai san ya Sameeha zata ji ba in aka ce zaiyi aure, dole zata yi zargin ƙila ya warke ya barta tana ta wahala ko kuma ya munafinceta. Kwana uku kenan da Hauwa tana kiransa yaƙi ɗagawa, dan yasan zencen nata baya wuce magamar auren wanda harta fara damunsa akan ya fara turo da kuɗin kayan siyan lefe, kwatsam sai gashi ta kirashi da wata number, yana ɗauka ta rufeshi da faɗa ta inda take shiga bata nan take fita ba, ya bata hakuri yace in ya dawo daga Ilori zai zo kaduna suyi magana, bata kuma magana ba ta kashe wayar alamar bata sauko ba tana fushi da shi, murmushi yayi yana ƙara mamakin ƙarfin halinta. Yana kwance a gado wajen goma na dare ga Abi yana kwance a gefensa yana barci, kira ya shigo wayarsa da number, ya duba da kyau bai san mai number ɗin ba sai ya ɗaga da sallama, Najwa da taji gabanta yana dukan uku uku yasa ta amsa a hankali cikin sanyin murya, ta gaishe shi ya amsa a daƙile da cewa. Wacece ke magana? Dam ƙirjinta ya buga dan ta gano yanayin muryansa fuskarsa a ɗaure yake, kuma kenan baiyi saving number ɗinta ba da Hauwa tace ta tura masa tun kwanaki. Idan ba ki da abin cewa zaki iya kashe wayar dan ba ni da lokacin ɓatawa. Ya faɗa a hasale, Najwa ta daure tace. Kayi hakuri na kiraka ne mu gaisa nice Najwa, Anty tace mini baka da lafiya shiyasa na kira nayi maka ya jiki. Murmushi yayi har hakoransa suka fito, wato Hauwa ta nan ta hudo kuma? tunda yaƙi kiran Najwan ya kuma daina ɗaukar wayarta shine zata saka ta kirashi. Ayya nagode, da yake data tura mini number ɗinki ban samu damar saving ba saboda busy, ya mutanen gidanku. Lafiya lau. To madallah, da akwai wata matsala ce? Babu amma dan Allah ina so ka riƙa kirana dan mu saba. Karki damu zan kira, ki tura mini account number ɗinki, sannan ki zauna kiyi lissafin abinda kike buƙata na shirye shiryenmu nan da kwana biyu sai ki faɗa mini in san abinda zan tura miki. To tace masa tana godiya, daga haka yace shi zai kwanta suka yi sallama ta kashe wayar tare da tura masa account number ɗinta, yana gani ya tura mata dubu talatin na kati, sai ya gyara kwanciya ya kashe wayar yana tunanin yadda zaman wannan auren zai kasance a tsakaninsu, shi baya sonta bayi da lafiya amma anya bazai cutar da yarinyar mutane ba? Wani ɓangare na zuciyarsa ya faɗi haka, yana gudun kar son ɗaukar fansa ga Hauwa ya jefa rayuwar yarinya ƙarama a gagari ya mayar da ita ƙaramar bazawara tunda yasan zaman ba zai ɗaure ba, sai yake ji kamar yace ya fasa kawai dan baya son ya cutar da kowa, amma in ya yuna matsalolin da Hauwa ta kunna masa Abin da ciwo kuma baya jin zai iya yafewa ba tare daya rama ba, kuma wannan auren ne kaɗai hanyar da zai ƙunsa mata baƙin ciki, da wannan tunanin barci ya ɗauke shi. Washe gari suka hau jirgi suka dawo Abuja, da yamma lis Aminu ya bar Baba Saude da yara ya kamo hanyar Kaduna dan yin magana da Hauwa. **** Najwa da Hauwa. Tun da Hauwa ta sanar da ita ta bashi number ɗinta zai kira take ta zuba ido har aka shafe sati ba labari, hakan ya fara damun Najwa take ganin wannan auren anya ba zai zame mata damuwa ba tunda alamu ya nuna Aminy baya sonta, sai yanzu take tunanin kila in ya ganta yace ma ya fasa tunda yasan ita 'yar uwar Sameeha ce, sai duk ta fara jin ta sare da alama rijiya ta bada ruwa amma gugu ya hana. Shiyasa ta shirya musamman taje gidan Hauwa tana yi mata ƙorafin Aminu bai kirata ba ta ɗaura da cewa. Yaya koda bai zo ba ya kamata ya riƙa kirana a waya dan mu saba, amma shuru fa har yau bai kiraba da sunan kuma ina matar da zai aura, anya zan iya kuwa? Haba Najwa sai da aski yazo gaban goshi zaki nima sarewa, ya sanar dani bayi da lafiya shiyasa bai kira ba, yanzu ga number ɗinsa ke ki kirashi kiyi masa ya jiki na tabbatar daga nan zaku cigaba da yin waya. Hauwa ta ƙare maganar tana miƙa mata wayarta akan ta ɗauki number ɗin Aminu, Najwa ta karɓa ta saka number ɗin a wayarta, nan dai Hauwa ta cigaba da rarrashinta a haka suka rabu ta bar gidan. Ita kuma Hauwa tunda Najwan ta zo tayi mata korafi taketa kiran Aminu yaƙi ɗagawa, hakan yasa ta yi fushi tare da kiransa da wayar yaronta koda ya ɗauka ta rufeshi da faɗa shine ya bata haƙuri akan da sun dawo daga Ilori zai zo Kaduna ya sameta. Najwa sai da ta kwana biyu tana taraddadin kiransa gudun kar ya wulaƙantata, Nafeesa ce ta ƙara mata ƙarfin guiwa akan ta ɗaure ta kira dan yanzu fa sun kusa zama ɗaya, ita ta sauke nata girman kan ta kira shi su daidaita, sai gashi ta kira shi kuma bai yi mata wulaƙanci ba sunyi magana, duk ba wa wani hira mai daɗi suka yi ba amma Najwa taji farin ciki, ƙarin murnanta yadda ya turo mata dubu talatin wai na kati, nan ta shiga hango ashe ba ƙaramin kuɗi yake sakarwa Sameeha ba, lallai in ta aureshi zata tara kuɗin da har sai ta siya gida dan ba zata kashe su a banza ba dole ne ta mayar da hankali ta kwashi rabonta, a ranar tayi barcin farin ciki. Da safe saida ta faɗawa inna kuɗin daya tura mata, dan koda yaushe cikin yi mata ƙaryan suna yin waya ne, wanda sai jiya ne ta samu damar yin magana da shi, sai da ta turawa Nafeesa duby biyu a cikun kuɗin dan ta shaida, nan suka dinga murna akan tayi miji wanda hannunsa a buɗe yake ba ikin na 'yan dembe ba. Aminu bayan sallar Isha'i ya sauka a Kaduna, da yake gidansa ya wuce sai da yayi wanka ya huta, wajen tare da rabi na dare ya bar gidansa ya wuce wani restaurant yaci abinci kana ya biya babban gida, ba karamin farin ciki suka yi ba da suka ganshi, sai dai ramar da yayi ya ɗaga musu hankali nan suka rufeshi da faɗa akan meyasa bai sanar dasu ba bayi da lafiya, ya basu hakuri akan ma ya samu lafiya yanzu sosai, nan suka cigaba da bashi shawara akan ya kula da kansa sannan suka ɗaura da maganar aurensa, yayi musu godiya akan ja gaba da suka yi kan maganar. Sai wajen sha ɗaya suka rabu ya wuce gida. Da safe wajen tara ya isa gidan Hauwa tana ganinsa ta saki fuska tana murna da ganinsa, dan tasan kuɗi yazo, dama tana cikin talaucinsu yadda rayuwa tayi tsada hannu baka hannu kwarya ake, ya zauna a falonta suka gaisa sai suka ɗaura da zancen bikin, yace ta yi lissafin kayan da za a siya sai ya tura mata kuɗin, har yake faɗa mata Najwa ta kirashi, ba ƙaramin daɗi taji ba, ba dan kar kwaɓarta tayi ruwa ba da tace taje gidansu Najwan suyi hira, amma tsoron abinda zai je ya dawo yasa ta yi shuru, ya jima suna hira daga bisani yace a ranar zai koma Abuja dan jirgin ƙarfe biyu zai bi, kuma bavdan yana cikin uzuri ba daya je yaga matar fata zaɓa masa, da sauri tace. Karka damu ko wayar dai in kunayi ya wadatar, in kazo nan gaba kwa gana dan kar a katse maka hanzari. Yaji daɗin yadda ta faɗa dan shima bawai dan yana so yaje ba ne yace mata haka, sai dan taga ya bada kulawarsa akan zaɓinta, daga bisani suka yi sallama ya tafi. Ƙarfe biyu yana yi da mintuna jirginsu ya tashi zuwa Abuja, driver ɗinsa shima ya tafi da motar zuwa Abujan. Sameeha.. [7/7, 13:04] Buhainat😁: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shai wanidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.* 29. Sameeha. A hankali Khairy ta cigaba da shiga jikinta wanda a cikin wata guda da haɗuwarsu ta zo gidan ya kai sau biyar, tun su umma suna ɗari-ɗari da ita har suka sake suna ganin so gamon jini ne dalilin 'yar uwarta data rasu take yiwa Sameeha ƙauna, zuwanta na ƙarshe data yi shi ne tazo tare da yaranta sun dawo hutu dan har sun koma makaranta, tun rana suka zo tare da kayan ciye ciye data yi musu samosa da cake da kuma kunun zaki wannan musamman ne na umma, sai da suka kai dare wato suka ci tuwon dare a gidan bayan sallar isha'i suka tafi, wanda a lokacin saura sati guda walimar ƙaninsu da take ta mitan Sameeha taje mata, ita dai da to ta bita dan ta san ba zata wani je ba tunda ita taji zata iya jela zuwa nan gidansu ita ko ba zata wani shige mata ba dan wutsiyar raƙumi yayi nesa da ƙasa wato rayuwa ake na kwarya tabi kwaya, tana tunanin zuwa ayi mata wulaƙanci tunda da yawan masu kuɗi basa so ana rabar su, sannan ba dukansu bane masu sauƙin hali da sauƙin kai irin Khairy, shiyasa tace ba zata ba kowa ya zauna a mazauninsa ta dai amsa mata kawai zata ne. Duk da a 'yan kwanakin nan data zo ta haɗata da Hajiyarsu sun gaisa sannan ta haɗata da yayarta Aisha da take Yobe, da kuma mijinta shima ta haɗasu sun gaisa wanda har wautar ta ta gani da tace zata gaisa da mijinta, tana mamakin yadda Khairy ta ɗauketa a zuciyarta yadda ta saki kanta da kuɗinta ta nuna sun zama ɗaya, sam bata kyamarsu komai ta samu a gidan ci take yi, tun suna ɗari ɗari har sun sake mata, umma ta ɗauketa 'ya kamar yadda take kiranta da umma. Sameeha ta fito daga ɗaki riƙe da plate ɗin shinkafa da wake da ta yi musu mai da yaji, ta aje akan tabarma tana cewa. Umma gashi bari na dauko latas dana yanka mana Allah yasa baiyi sanyi ba a fridge. To Allah yasa, kin san dai ina fama da haƙori in yayi sanyi ba zai taunu mini ba. To umma bari na watsa masa ruwan ɗumi na san zai rage zanyi. Ta faɗa tana koma ciki ba jimawa ta fito da shi ta isa kichen ta zuba masa ruwan ɗumi ta juye a matsami ta kawo ta ajiye, ta zauna ta fara juya gefenta da hannu dan tare da umman zasu ci. Hannu kuma zaki saka? Yau so nake nayi mata cin ƙet umma, kin san ina son mai da yaji. Kice kawai kin mini wayo zaki fini ci. Umma ta faɗa tana dariya itama dariya tayi suka yi bisimillah suka soma ci, sallamar Ikram suka ji ta shigo gidan ta dawo daga makaranta, da sauri ta ƙaraso ta cire hijab ta aje a tabarma tana yi musu sannu da gida sai ta wuce kitchen ta ɗauko cokali ta zo da sauri ta zauna tana cewa. Wlh jikina har rawa yake yi dan yunwa, bari na taya ku ci in mun cinye ma ƙara. Laifin ki ne baki tsayawa ki karya da kyau, ki dai yi a hankali kar ulcer ta kamaki. Cewar umma, Ikram dai tattara hankalinta tayi tana ci dan ba tada lokacin mayar da magana. Bayan sun kammala sai Ikram ta kwashe kayan ta mayar kitchen ta shiga ɗaki ta cire uniform ta saka riga da siket na atamfa ta fito tana ɗaura ɗankwali. Anty bari na baki labarin iskanci da Najwa tayi min jiya a online da dare, lokacin kinyi barci, nake tambayarta ta fito mana da anko, wai idan ma ta fito da shi meye nawa a ciki, ai sai dai nayi na iyaye dan bana cikin ƙawayenta. Wallahi ko bikin ma in yazo bazan je ba dan tayi kaɗan ta wulaƙanta ni. Kema banda abinki Ikram idan tana so muyi ai har gida zata zo ta kawo mana, dan haka sai ta sha kuruminta ankonmu daban za muyi yan nan gidan. A'a ba zai yuwu ba idan kuka yi haka kun biye mata kenan, har yanzu Najwa da ƙuruciya akanta sannan ma kin san bakwa shiri tun rabuwarsu da yayanki amma kika takalo ta, gani zata yi kamar gatse kika yi mata da tambayar. Ni bana son ku saka a ranku dan zumuncinku mai karfi ne, kuma ita kaɗai ce mace a gidansu na tabbatar daku zata yi jiki sosai in hankalin aure ya shiga jikinta. Hmmm Allah ya kyauta amma Allah Umma bazan yi ankonta ba zan saka wanda Allah ya bani. Yauwa Anty zaki samu zuwa walimar ƙanin Khairy kuwa? dan kamar gobe Lahadi ne ko? in zaki sai ki jirani na dawo daga makaranta mu tafi tare. Keni ba inda zani wannan sha'ani ne na masu hannu da shuni bazan je ayita yi mini gani gani ba. Haba Anty wlh kema kin san ba kalar wacce za a kalla bace ayi miki wulaƙanci. Ba inda zani, bayan an gama taron zan shirya naje gidanta na bata haƙuri nasan zata sauko tunda ban taɓa ma zuwa gidanta ba. A'a Sameeha yarinyar nan da zuciya ɗaya take tare dake dan sosai take nuna miki so, ina ganin ya dace kije mata koda ba zaki daɗe ba tunda ma kin yi waya da 'yan gidansu ba lallai ayi miki wulaƙanci ba balle kina kama da 'yar uwarsu. Hmmmm umma tunda kinsa baki zani amma gaskiya bazan daɗe ba kinsan ni ban cika son shiga inda ba a sanni ba. Allah ya kaimu goben lafiya sai ki tafi da motarki in ma rainin ne baki so. Cewar Umma, Sameeha ta ce cikin murmushi. Wlh umma sam motar ta fice mini a rai baki ga ko fita zanyi sai dai Yaya ya kaimu tunda shike hawanta. Wlh Anty da ita zaki kuma ke zaki tuƙa ai ajinki ne wannan ba arowa kika yi ba taki ce, yadda yaya Zaidu ya saka aka yi mata sabon fenti ta ƙara kyau aiko kin goge raini. Murmushi tayi tana kallon Ikram da take jajjada magana, ta cigaba da cewa. Anwar da safe in Allah ya kaimu ya wanke miki ita, sai ki sanar da yaya Zaidu anjima in ya dawo yasan zaki fita da ita. To mama Ikram zanyi abinda kika ce uwar iya tsara zance. Sameeha ta faɗa tana dariya, wayarta data yi ƙara yasa ta duba sai taga Number ɗin Aminu ne ke kiranta, dam ƙirjinta ya buga sosai dan tasan ya yi blocking ɗinta, sai da wayar ta katse bata ɗaga ba Umma tana cewa. Waye ya kira naga duk kin sauya kamar an watsawa kaza gishiri. Umma Aminu ne ya kirani kuma... Bata ƙarasa maganar ba wani kira ya ƙara shigowa, da sauri ta ɗauka tana karawa a kunne tare da yin shuru, muryar Amrah daya doki kunenta yasa ta miƙe zumbur tana ambaton sunanta. Amrah! Amrata muryanki ne haka ina Abi kuna lafiya ya makaranta. Sameeha ta faɗa cikin tsantsar murna da farin ciki tana jera mata tambaya, Amrah ta ce cikin murna. Mamanmu muna lafiya Abba yaƙi bari muzo gunki wai sai mun ƙara yin hutun makaranta, yanzu ma saida nayi masa kuka kafin ya yarda ya kiraki, dan Allah mama ki dawo gidanmu Abba yace wai hutu kike yi a gida, dan Allah ki gama hutun ki zo. Dalla malama bani nima inyi magana da ita. Cewar Abi daya fizge wayar a hannunta ya ƙara a kunne, nan shima ya shiga magiyar akan ta dawo gidansu, Sameeha kasa daurewa ta yi sai ta fashe da kuka mara sauti tama kasa yiwa yaran magana sai tsiyayar hawaye, sai ta koma ta zauna tana toshe bakinta dan kar suji kukanta, Abi da Amrah sau kiran mama suke yi dan sun koma sun saka wayar a hands free, da kyar ta rarrashi kanta tace. Kuyi haƙuri kun ji watarana zan zo na ganku, kuma koda ban zo ba Abbanku zai kawo ku tunda ya yi muku alƙawari ku daina damuwa koda bama tare zuciyata tana tare daku, sannan ku mayar da hankali a karatunku domin shine gatanku a duniya, banda ƙawaye da abokai marasa tarbiyya ku riƙa tuno duk abubuwan dana ke faɗa muku akan aboki nagari da kuma mayar da hankali a karatu, ina sonku kuma duk runci zuciyata tana tare daku. Ta ƙare cikin kuka, Abi ya jefa mata tambaya. Mama kuka kike yi Abba ya rabamu ko.? A'a Abi ba kuka nake ba kuma abbanku bai rabamu ba tunda kuna tunani a zuciyarku nima ina tunaku ko ba kwa yi.? Taf kullun sai na tunaki mama. Nima ina tunaki mama kusan kullun sai na yiwa Abba kuka ma. Cewar Amrah cike da yarinta, haka suka ɓata lokaci tana hira dasu, wani lokacin ta yi hawaye wani lokaci tayi dariya abin kallo ta zamewa su umma suna kallon ikon Allah, sunyi kusan minti arba'in suna magana daga bisani taji muryan babansu yana cewa. Wayar ya isa haka ku bani ita nan. Mama sai mun sake kiranki kuma muna hutu zamu zo, ki cewa kaka umma ta tanadar mana waina dan shi zamu ci da mun zo mu cika cikinmu. To to take ce musu tana gyaɗa kai kamar suna ganinta, tana ji ya kashe wayar ta sauke wani numfashi tana mai jingina da bango ta fashe da sabon kuka, wai tsakaninta da 'ya'yanta ne ya zama sunyi nisan da sai da suka shafe watanni bata gansu ba kuma da ranta da labari, haƙiƙa duk wanda da saka hannunsa a mutuwar aurenta ba zata yafe masa ba dan sun farraka mata farin cikinta, a yadda Aminu bayi da lafiya ta ɗauki alƙawarin zama da shi a haka kodan saboda yaranta, tunda Allah ma bai ɗaura mata mugun sha'awa ba kuma ance sa rai da ci shike kawo jin yunwa. Umma ta matso ta dafata. Duk wanda ya dogara ga Allah ya isar masa Sameeha, Allah yana sane da halin da kika tsinci kanki, kuma zai kawo miki mafita ta alkhairi alfarman Manzon Allah s.a.w ba zaki taɓa taɓewaba In Sha Allah rayuwar sai tayi albarka, ki ƙara haƙuri akwai lokacin da zaki yi dariya duk sai kin manta da wannan ƙuncin. Maganganun umma su suka ƙara sanyaya mata rai ta goge hawayenta tana cewa. Amin Umma Allah ya amsa addu'arki. Ikram ta amsa da amin tare da cewa. Ku taso mu shiga ɗaki kun san yau asabar lokacin maimaicin Azrah yayi saboda jiya bamu kalla ba yanzu ƙarfe uku. Tana gama faɗa ta shige ɗaki suma suka bi bayanta dan suna son shirin sosai, kallon da suka fara yasa Sameeha ta ware sai dai tunanin yaranta yana maƙale a zuciyarta sai dai kawai dangana tayi ba yadda zata yi. . .. Washe gar, wajen ƙarfe biyun rana Sameeha ta shirya cikin doguwar rigar lashe wanda sabon ɗinki ne da Aminu yayi mata wanda zata saka a bikin Salma sai dai Allah bai nufa zata saka a lokacin ba, kusan dubu sittin da uku yake, bata taɓa saka shi ba sai yau shima dan Umma tace dole ta saka shi tunda sha'anin manya ne zasu, ta saka farin gyale da kuma farin takalmi da jaka, dan leshin orange da fari ne a jiki mai manyan zane, Ikram kuwa atamfa ta saka riga da siket sai ta ɗaura after dressing shara shara a sama mai hula, bata saka gyale ba ganin ta saka wanan kuma a mota zasu gashi ta caɓa uban ado kuma tayi kyau, Sameeha kuwa daga powder sai kwalli sai man baki data saka, Ikram ta kalleta. Anty dan Allah kiyi kwalliya mana. Ikram wa zan burge a can? ai kawai mu tafi haka dan kinsan ni kwalliya bata dame ni ba. Umma mu zamu wuce in kin ga mun dawo da wuri bamu samu fuska ba amma in mun jima to fa mun samu tarba mai kyau. To Allah ya tsare yasa ayi taro lafiya ki gaida Khairy, ina taya su murna. Zata ji In Sha Allah. Cewar Sameeha suka fito daga gidan suka shiga mota sai da tayi Bisimillah da addu'a kafin ta kunna motar tana jinta kamar sabon hawa dan ta jima bata yi tuƙi ba, sannan a wani ɓangare tunanin yaranta ya dameta dannewa kawai take yi. Haka suka kama hanyar unguwar rimi Ikram sai hira take yi mata ta amsa mata wani wani kuma tayi shuru har suka isa tangameman gidan su Khairy dan sosai ta gane kwatancen da ta yi musu kuma sun tsaya a hanya sunyi tambayar gidan Alh. Ali Turaki nan aka nuna musu hanyar da zai sadasu da gidan sai gasu a ƙofar gate, ta buga hon aka buɗe mata gate ta cilla motarta cikin gidan, yadda taga baban gida ne har da titi a ciki yasa ta ruɗe ta rasa ina zata yi parking sai da wani security yazo ya nuna mata gefen hagu yace ta shiga titi tayi parking gurin wasu fulalowi dan duk ko ina motoci ne kamar ana gasarsu, ga kuma kanofi da aka kafe daga can ɓangaren dama duk maza ne a gurin, bata ma san ta ƙofar da zasu bi ba su shiga sashin gidan, nan ta kira Khairy ta faɗa mata sun iso ta fito ta shiga dasu, sai tace ta yi hannun dama ta wuce wannan kanofi ɗin gata nan zuwa. Haka ta kashe mota ta fito riƙe da jakarta ta gyara zaman gyalen a kafaɗa, suka fara tafiya har suka kawo gurin mazan nan sai duk Sameeha taji ta tsargu kamar ita kaɗai ake kallo sai ta ƙara sauri dan su wuce gurin gashi ta ɗaure fuska hanya kawai take kallo, Ikram tana biye da ita a baya dan ta kasa kamota saboda saurin data ƙara, can ta hango Khairy tana tahowa bata san sadda ta saki murmushi ba dimple ɗinta ya lotsa wushiryar ta fito har ta ƙarasa gurinta, khairy ta rungumeta tana cewa. Oyoyi ƙawata sannu da zuwa. Ikram ya hanya ya kuka baro umma. Lafiya lau tace a gaishe ki tana muku murna Allah ya yiwa karatunsa albarka. Cewar Ikram, Amin ta amsa ta kama hannun Sameeha suka wuce wani madaidaicin gate, suka shiga wani gida a ciki, har babban falonsu daya sha kayan alatu ta kaisu ga mata cike a falon wasu sai hotuna suke wasu suna cin abinci wasu kuma suna zaune a kujeru da carpet suna kallo, Khairy har gaban wata dattijuwa ta kai Sameeha ta zauna a ƙasa kusa da karar ta, matar tana kan kujera ko ba a faɗa ba itace mahaifiyar su Khairy dan ta hango kamarsu, Sameeha cikin girmamawa ta gaisa da umma tare da juyawa ta gaida sauran mata tana yi musu Allah ya sanya alkhairi, Ikram ma bata yi ƙasa a guiwa ba ta shiga gaishesu suna amsawa, Hajiya ta kalli Khairy da sai dariya take tace. Wannan ita ce Sameeha ko.? Ta faɗa tana nuna Sameeha wacce nauyinta yasa ta ƙara sunne kai tana murmushi, cikin sauri khairy tace. Hajiyarmu ita ce dan Allah baki ga kamanninta da Mubeenarmu ba, wannan kuma ƙanwarta ce. Aiko dai suna yanayi da ita, Hajiya Fatima gafa mai kama da ɗiyarmu. Ta faɗa tana magana da ƙanwarta Fatima, Da sauri ta juyo dan tana magana da wasu mata tana cewa. Wallahi tunda suka shigo naketa kallonta sai dai tafi Mubeena haske, Allah dai ya jikanta. Duk suka amsa da amin, nan fa Khairy ta wage murna tana cewa. Jama'ar gidan nan ku zo ga Sameehata ta zo ku fito ku ganta ku kwashi gaisuwa. Nan fa duk hankalin mutane ya dawo gunta suka fara dan dazo a falon, waɗanda suke ɗakuna suka soma fitowa sai faɗi suke ina take ina take?. Lamarin yayi matuƙar bawa Sameeha mamaki yadda kowa keson ganinta, Ikram kuwa sakin baki tayi tana kallon ikon Allah, ta rasa ma me zata yi tunani akai, falon ya ƙara cika sosai Sameeha ko kunya ce ta hanata ɗago kai tare da mamakin wannan tururuwa da ake yi dan aganta, ta rasa me Khairy ta sanar dasu ko kuma kila suna son ganin me kama da Mubeenansu ce. Anty Aisha ce ta tsallako ta zo gabansu ta zauna itama ta ɗago kan Sameeha tana dariya. Ke ɗago mu ganki sai sunne kai kike kamar wata amarya. Aisha ku barta ta huta haka kun sa ta kasa sakewa, ke Ƙanwata taso mu shiga ciki dan ba zasu barki ba. Cewar Anty Amina data kama hannunta ta shiga janta, Ikram ma ta miƙe ta bi bayansu, Hajiya tana cewa. Ki sauke su falon Abbanku tunda ba kowa a can dan Allah kar a takura mata. To anty Amina tace sai Aisha itama ta bisu. A wani katon falo aka sauke su ga lafiyayyun kujeru na alfarma sai kace mai ɗakin yana raye, ga katon hotansa a jingine a bango ga kuma sauran hotunan da yake tare da iyalinsa gana Hajiyarsu, na yaran ma ga nasu, sai wani tashin kamshi ke tashi a falon. Bayan sun zauna Amins tace. Ni ce Amina wacce kika taɓa yin waya da ita. Muna farin ciki da zuwanki domin kin kore mana kewar Mubeena. Shigowa Khairy tare da wata mata yasa suka yii shuru har suka ƙaraso riƙe da tire biyu duk da kuloli da kuma drinks da plate, Aisha tace. Yauwa gwara da kuka kawo in taci ta ƙoshi sai ta fito muyi hotuna. Ni bari na je naji da baƙina. Ta miƙe ta fita, Anty Amina ma fita tayi tare da matar da ta taya khairy kawo musu abinci, nan fa ta shiga zuba musu waina da miya yaji ƙashin rago, ga kuma fried rice mai kyau ga pepper cikin da kuma samosa da meat pie da aka saka a foil paper, ga drink na kanti da kuma kunun aya da zoɓo, Sameeha ta kallesta tana cewa. Duk wannan abincin ina zamu kai shi? Sannan me kika faɗawa 'yan uwanki suke ta son gani na ne?. Ku zaku cinye abincin mana, sannan sun ga mai kama da Mubeena. Anya zan yarda dake kuwa.? Sameeha ta faɗa tana 'yar dariya, Khairy ma dariya tayi tana cewa. Ni dai ku ci abinci ku ƙoshi gani nan zuwa. Ta faɗa ta wuce, koda ta fita tambayar inda yayansu Ibrahim yake tayi amma aka sanar da ita kamar baya nan tun ɗazu, dan mutane suna ta zuwa suna tambayarsa ba ya nan. Sai ta wuce ɗakin Hajiya da niyyar ta ɗauki waya ta kira shi. [7/7, 13:04] Buhainat😁: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shai wanidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.* 30. Ikram saukowa tayi kan carpet inda aka jera musu abincin ta soma ci tana cewa. Wlh yau sai nayi halin Najwa na kwaɗayi, sai na cika cikina sosai na kwashi gara. Ki dai ci a hankali karki sa muji kunya. Cewar Sameeha data sauko itama ta wanke hannu a ruwan da suka kawo musu, sai ta fara cin wainar ta kai lomar farko sai taga wani ƙashi ya biya mata ta ɗauka ta kai baki tana yagar naman jikin ƙashin, sai ga Ibrahim ya fito daga cikin wani ɗaki kuma dai dai setinta, yana buɗe kofar suka yi ido biyu da Sameeha, bata san sadda ta saki ƙashin ba ya faɗi ƙasa ta sunne kai tana yiwa kanta dariya dan wlh dama a ɗarare take ci saboda kar wani ya ganta, tana mugun jin kunyar cin abinci a baƙon guri, Ibrahim ya zauna a cushing yana danna waya yayi kamar bai gansu ba, Ikram ce ta gaishe shi cike da ɗan tsoro dan ta gane shi shine Senator ɗinsu, dama data ga hotonsa a falon tana ta tunanin kamar ta taɓa ganinsa sai da ya fito ne ta gasgata shine Senator da akayi saɓensa watannin baya kuma shine yaci dan shi ma suka jefawa ƙuri'arsu. Kenan shima yayan Khairy ne, tace a zuciyarta cike da tsantsar mamaki da tunanin khairy ba ta ɗauki duniya da zafi ba har ta iya mu'amala dasu ta jawo su jikinta. Ibrahim ya amsa mata a daƙile fuska a ɗaure, saboda barci ya tashi kuma ga yunwa yana ji, Ikram ta cigaba da cin abincinta. ganin da alama an karramasu ne yasan abinci lafiyayye ne a kular daya gani, sai ya buɗe baki yana cewa. Ke ɗauki plate ki saka mini abincin dake kular. Sai da Ikram ta yi waige waige dan a zatonta da wata yake yi sai kuma taga ba kowa sai su ne a falon, shi kuma bai sake maimaitawa ba ya cigaba da latsa waya. Ikram ta haɗa ido da Sameeha sai ta ƙifta mara ido akan ta zuba masa, Ikram ta buɗe baki tace. Akwai waina da shinkafa wanne zan saka? Fried rice ce? Eh. Oka saka kaɗan sai ki kawo mini coke kuga ɗaya da ruwa. To tace masa sai ta ɗauki plate mai kyau ta zuba masa ta saka masa naman kazan da yawa a gefe, sai ta saka cokali ta miƙe tare da bottle water da kuma coke drink ta kai masa ya amsa ya ajiye akan cushing ya miƙe ya saka wayarsa a aljihu ya ɗauki abincin da ruwan ya koma ɗakin data fito ya turo ƙofa, yana rufewa Ikram ta waro ido waje. Anty kin san wanene shi? Sanator ɗinmu ne fa na nan cikin Kaduna, ashe yayan Khairy ce bata taɓa faɗa mana ba, wlh shine dan na shaida hotonsa sosai shi muka sakawa ƙuri'armu lokacin kina Lagos aka yi zaɓe. Ashe shiyasa ya fito yana jin kansa sai wani ɗaure fuska yake yi. Hmm mulki kenan anty, gaskiya su Khairy ba ƙaramin arziki garesu ba, nayi mamaki data ke zuwa gidanmu har taci abincinmu. Wannan shi ake kira da gadon arziki ba wanda suka yi haye ba, kuma in da dukiya akwai tarbiyya to dole za kiga haka. Ni saka mini shinkafar na fasa cin wainar. Ta faɗa tana gyara zama, nan Ikram ta zuba mata ta soma ci tana yi tana yagan nama tare da kurɓan zoɓo dan bata yarda ma ta ɗauki kunun aya ba dan tasan yana tayar mata da sha'awa, tana cikin ci ta cika cokali tana kai loma kamar ance ta kalli ƙofar da Ibrahim ya shiga sai taga ya kafeta da ido da sauri ta aje cokali tana tari dan ta kware, shi kuma murmushi ya saki ya koma ciki, dama bai rufe ƙofar ba tura ta yayi ɗazu shiyasa bata ji ƙarar buɗe ƙofar ba, shi kuma hakanan yaji ya leƙo ta yaga zata cigaba da cin abincin data daina ci ɗazun data ganshi, sai da ta sha rufa kafin tarin ya lafa Ikram da bata ga abinda ya faru ba ta shiga jera mata sannu. Garin ya kika kware. Ni ina ganin na haƙura da cin abincin nan tashi mu fita mu... Bata rufe baki ba Khairy ta dawo ɗakin tana cewa. Da fatan kun cinye abincin nan tas. Idan muka cinye aiko sai kin ce ba mu da lafiya, ni yanzu ma na kware naji na kwoshi ma. Cewar Sameeha tana zama a cushing dan ta miƙe daga gun abincin, Ikram da ke haɗa kayan ta na cewa. Anty Khairy ashe yayanku shine Sanator ɗinmu, ɗazun ya fito daga wancen ɗakin yace na zuba masa abinci sai ya koma ciki. Laaa ashe yaya nan yazo ya ɓoye kansa ba wanda yasan inda yake ana ra nimansa. Ina zuwa. Ta faɗa tana wucewa ɗakin ta tura ƙofa ta shiga ta same shi yana shirin yin wanka. Yaya dama nan kazo ka boye kanka bamu sani ba anata nimanka. Khairy ina buƙatar hutu kuma wannan damar kaɗai nake da shi shiyasa na ɓoye a nan, nasan ba wanda zai san ina nan. Wasu baƙi ne a falo? Ba na gargaɗeku kar wanda ya shigo nan ba. Yaya wannan special baƙi ne, ƙawata ce babbar, ƙaramar kuma ƙanwarta ce. Yauwa baka ga suna yanayi da Mubeenarka ba. Wacce daga ciki? Sameeha babbar. Haba banga wata kama ba, Mubeena baƙa ce wannan kuma fara ce. Haba yaya baka dai ƙare mata kallo bane amma hatta wushiryar su iri guda da dimple. Khairy kenan sai kawai na ƙurawa matar aure ido ina kallonta danna tantance kamarta da Mubeena, ko ance miki banda abin yi ne. Laaa ai ba tada aure, aurenta ya mutu watanni baya daya wuce yaranta biyu Wlh abin tausayi ya hanata yaran ma, ai mijinta yayi asarar mace ta gari. To ni da kika tasa ni a gaba da zancen na tambayeki ne? ki kwashe plate ɗin nan ki fita dashi ina so nayi wanka na shirya zan fito yanzu. Yauwa ka fito muyi hotuna. Saboda ni tsararki ne ko? Au na manta da Sanator mai tsada nake magana. Harararta yayi sai ya shiga toilet abinsa, ta bishi da dariya ta ɗauki plate da gorunan ta fito falon ta zauna kusa da Sameeha. Ku tashi mu je ayi mana hotuna. Sai ta miƙe ta matsar da abincin gefe suma suka miƙe suka fito tare zuwa farfajiyar gidan, suka tsaya ana ta hotuna kala kala banda me hoto yana ɗaukar nashi suma masu waya sai ɗauka suke, a haka har lokaci ya kure a fara kiraye kirayen sallar magrib. Kiran daya shigo wayar Ikram yasa ta matsa gefe ta ɗaga dan umma ce ta a kira. Ikram na jiku shuru baku dawo ba to Wlh ko mun dare ku zaku zo ku ɗaura abincin dare dan ban dafa komai ba. In Sha Allah yanzu zamu dawo shagalin ne yayi daɗi umma, zaki sha labari da yawa dan mun ga karamci iya mutunci. To Masha Allah haka ake so ki faɗawa Sameeha ku dawo yanzu fa, nayi ta kiran wayarta bata ɗaga ba. Ina zata ji kowa sai son ɗaukar hoto yake da ita abu dai kamar a film Sameehan umma ta sama tauraruwa, da alama addu'arki ya fara tasiri umma. To suda mai bakin magana faɗi ba a tambayeki ba. Umma ta faɗa tana murmushi, Ikram dariya ta saka sai ta kashe wayar dan wlh ta ƙosa su koma gida ta fesa musu labari jikinta har tsuma yake dan ta guntso labari mai daɗi. Sai ta koma inda au Sameeha suke ta faɗa mata saƙon umma nan tace dama sallah kawai zasu yi su wuce. Ibrahm yana gama shiryawa cikin wani tsadadden shadda sky blue riga da wando ɗinkin jamfa ya ɗaura hula da takalmi baƙi, ya fito a asalin Honorable ɗinsa, sai ya fita ta ƙofar baya dan dama ta nan ya shiga baibi ta falo ba, yana isa farfajiyar main house ɗin inda maza suke nan fa suka miƙe aka shiga taro shi maroƙa suka fara nasu aikin ana yi ana masa busa sai kace wani sarki, nan fa aka rufeshi kowa yana kawo gaisuwa yana amsawa fuska cike da amnuri, haka ya soma rabon kuɗi dan buɗe motarsa yayi ya dauko wata jaka ya bawa wani abokinsa yace a rabawa mutane sai ya wuce can ginin dake ɓangaren hagu wanda a da mahaifinsu ne ke ganawa da baƙinsa a gidan, ya zauna a baranda dan akwai kujerun hutu ga kuma sauran abokai da 'yan uwa da suka raka shi nan aka soma chapter, da aka kira sallamar magrib ne sai suka tafi Masallacin dake ƙofar gidansu wanda yake musamman na gidan ne Abbansu ya gina. Har Tafsirin Al-Qur'ani yana yi da watan azumi Usman yana ja masa baƙi lokacin da yake a raye. Kusan duk mazan nan a masallaci suka gabatar da Sallah liman ya jasu, bayan sun idar suka dawo cikin gida cikin tamfol suka zauna ana cigaba da hira. Sameeha sun fito bayan tayi sallama da mutanen gidan, hajiya tana ta saka musu albarka har suka fito, rakiya har da 'yan uwansu Khairy sannan ta haɗosu da wannan sauran abinci a kuloli tace wlh dasu zasu tafi sannan ta ƙara haɗa musu drinks da snack ga soveniers ko wanne saida ta bashi nashi har da na umma da yaya Zaidu da Anwar, har farfajiyar gidan suka rakosu inda maza suke sai Khairy ta kwalawa Shamsu kira ya taso da sauri ya zo ya risina yana cewa. Da girman kujerar Anty K, gani. Kaga bana son shiririta ga ƙawata ka kaisu gida a motarka. Sameeha nagode Allah ya saka da alkhairi ya bar zumunci wlh yau kin shayar dani farin ciki sosai. Shamsu fito sa motar ka kawo shi nan su shiga. To Anty Shamsu yace sai Sameeha tayi saurin katse shi. Barshi kawai malam Shamsu muna da abin hawa. Kamar ya fa? a daren nan? To bazan bari ku shiga napep ba. Cewar Khairy, Ikram ta fara dariya tana cewa. Anty Khairy da motar anty Sameeha muka zo, motar da Yaya Zaidu ke hawa nata ne fa, bata hawa shiyasa baki sani ba. Wani kallo Khairy ta yi mata na mamaki. Ikon Allah kawata abin duniya be dameki ba, ai ban taɓa sanin kina da mota ba shine ko ki faɗa mini. Labarin hakan ne bai zo ba kuma bana fita da ita ne shiyasa. Cewar Sameeha tana murmushi, nan ta faɗa musu inda tayi parking sai suka wuce har gurin, Shamsu yana tafiya tare da Ikram tana tambayarta sunanta da unguwarsu, Ikram taƙi yin magana saboda tasan tana da wanda zata aura, amma ganin ya na niman damunta yasa ta bashi number ɗinta akan za suyi magana, Shamsu bai yarda Number dai dai ta bashi ba dan haka ya juya da sauri ya dauko motarsa ya shiga ya jira har Sameeha ta tuko nasu Su khairy suna ɗaga mata hannu har ta bar gidan shima shamsu ya rufe musu baya, sai yanzu yake tunanin kamar ya san Ikram a wani guri wanda a hankali ya tuna Najwa dan suna ɗan kama da Ikram sai dai fari ne tafi Ikram ɗin. In har hakane to wataƙila 'yan uwane kuma yadda Najwa ta yi masa wulaƙanci tayi blocking ɗinsa to ko sai yayi yadda zai yi ya samu Ikram domin ya nuna mata shi ɗin ba matsiyaci bane kamar yadda tayi zato. Ba zai mance rabuwarsu da ita ba tun lokacin data tambaye shi kuɗi dubu goma sai ya tura mata dubu Ashirin, to tun ranar ya daina samunta a layi daga baya ma ya je gidansu hira tace ace bata nan, ya ƙara aikawa ta fito cikin masifa ta yi masa wulaƙanci son ranta akan yayi haƙuri ita ba zata iya aurensa ba bisa dalilin matsiyaci ne shi bai da kuɗin da zai iya kulawa da ita, sannan ma ko motar hawa bai da shi, kuma ba zata auri miji baƙi ba sai fari ɗan kwaliza dan ta kula ko wanka bai iya ba kullum cikin manyan kaya. haka ya tafi guiwa sake da alƙawarin ko ita ce autar mata ya haƙura. Dama tuntuni yaga take takenta shiyasa ya ɓoye mata asalinsa domin ya gwadata yaga ko zata so shi domin Allah sai kuma ta faɗi. Shamsuddeen. Shi yaro ne a gun babban yayan Hajiyar su Khairy, kuma shi ne yake matakin Wazirin Zazzau bayan rasuwa mahaifinsu, Shamsu yana da yayyi maza da mata dan akwai waɗanda suke 'yan uba amma a ɗakinsu shine auta, ya samu ilimin boko da addini sosai dan a yanzu haka shike riƙe da companyn Ibrahim na fulawa shine manager kuma mai kula da duk wasu harkan kasuwancin Ibrahim, saboda riƙo da addininsa da kuma ƙoƙarin riƙe Amana, a gidansu Khairy yake zaune dan ya zama ɗan gidan. Iyayensa sunata so yayi aure domin yadda yake kama manyan kuɗi, anata bashi 'yan mata a dangi ya zaɓa amma yace shi bare zai aura. Basu takura shi ba hakan yasa ya dage wajen niman ta gari wacce ba zata zama lashe money ba. Watarana yana tare da Usman sun je gidan Khairy to sai suka biyu ta badarawa ranar kasuwar sati hanya ta tushe yayi gosilo, sai ga Najwa ta zo ta wuce sanye da uniform ɗin iskamiyya ta shiga layinsu, da sauri ya cewa Usman ya fito ya amsa motar ya wuce zai zo ya sameshi s gida sai ya bi bayanta, Usman ya zagayo ya shiga ya zauna, har gida yabi Najwa wanda data zo shiga ya yi mata sallama ta juyo tana kallonsa sai ta haɗe fuska tana malam lafiya? Yace lafiya kalau kana ya koro masa bayaninsa ciki har da sunansa, Najwa ta taɓe baki dan daga sunan nasa har shi ba suyi mata ba, sai dai kawai ta amsa masa ne ta samu na kati dan bata hango ma yana da kuɗin da take burin samu a jikinsa ba. Ta bashi number ya amsa suka yi sallama, tun daga lokaci Najwa ke garashi bata tashi nimansa sai tana buƙatar abu shi kuwa cikin rawar jiki yake yi mata, bata taɓa tambayarsa abu yaƙi yi mata ba, ganin yadda ta mayar dashi saniyar tatsa yasa ya fara shakku akanta a yadda naga shigarta da kuma ƙoƙarinta na niman ilimin addini sunyi hannunvriga da halayyarta dan sosai ya gane ba sonsa take ba sai abun hannunsa, daga karshe ma ta sallamashi, da ace shi mutum ne mara yafiya da sai ya yi amfani da ƙarfin dukiya ya rama duk abinda tayi masa sai yayi haƙuri ya kyaleta, sannan ya kikayi niman wata budurwa dan ya ce zai fara nima a cikin dangi ko zai dace. Cikin ikon Allah sai ga shi yana ganin Ikram yaji ta kwanta masa a rai harma yake hango yanayin kamarta da Najwa haske kawai Najwan ta fita amma tabbas akwai kama ta jini. Haka ya cigaba da binsu, Ikram tana hankalce da shi data ga abin nasa da gaske ne yasa tace. Anty wancen motar ta bayanmu mu take bi fa. Kamar ya fa.? Sameeha tace tana kallonta tare da mayar da kallonta gurin mota. Allah kuwa mu yake bi wannan saurayin ne da Anty Khairy tace ya kaimu, da alama so yake ya ga gidanmu kuma ni wlh ina son Aliyu bazan yarda na bashi fuska ba. Aliyun da yake ta yi miki yawo da hankali, kinga Ikram ki shiga natsuwar ki kisan me kike ciki wlh, shekarunki fa ashirin da shida ina kamarki na shekara kusan takwas da aure, dan yanzu shekara ta ashirin da tara ina shekara sha takwas aka yi mini aure, dan haka ki buɗe idonki ki bashi dama ba kisan inda ƙaddara zata kai ki ba. Hmmm Ikram tace tana turo baki dan ita sam bata wani gamsu ba saboda Aliyun dai take so, Sameeha ta cigaba da cewa. Na dai gaya miki ki bashi dama kuma wlh zan faɗawa umma da yaya Zaidu wannan jiran da kike yi masa yayi yawa, tun yana makaranta fa daya gama yayi service yanzu kuma wai yana short service NDA, ai yaci ace ya turo manyansa an fara magana kafin ya fito a saka rana. Karki mamakin yana fitowa ya sauya miki ko yace anyi masa mata a danginsu, dan wlh da yawan mutane haka suke yi saboda kar aci arziki da bare sai dai masu su ci. Jikin Ikram yayi sanyi dan wlh ta fara sarewa itama da Aliyu sabods ko waya yi sai time ɗin da aka basu saboda gidan soja doka garesu, kuma tana ta yi masa maganar ya turo yace sai in ya fito, maganar dai tuntuni suke yinta amma ba sauyi, ta sauke ajiyar zuciya. To shikenan zan bashi dama amma saiku taya ni da addu'a Allah yasa na soshi dan wlh Aliyu ne a zuciyata. Allah ya zaɓa miki na gari. Sameeha ta faɗa Ikram tace Amin sai suka sauya hira zuwa irin tarban da suka samu a gidansu Khairy, har suka ƙarasa gida Sameeha tayi hon Anwar yazo ya buɗe musu gate Ikram ta fito Sameeha ta shiga da mota gida. Ikram motar Shamsu ta nufa yana ganinta ya sauko ya rufe motar har ta ƙaraso ta rungume hannunta tana cewa. Sannu da ƙoƙari, lafiya kake ta binmu.? Saboda inga gidan ku ba sai na sha wahalar sani ba. Ki shiga gida In Sha Allah gobe zan dawo muyi magana Allah ya huta gajiyarku. Ta amsa da amin kana tayi masa saida safe ta wuce cikin gida shi kuma ya shiga mota ya juya ya hau titi ya wuce. Tun ɗazu Ibrahim ke kiransa bai ɗaga ba dan kar su Ikram su ɓace masa sai yanzu ne ya samu damar kira yana riƙe da waya hannu daya yana tuki, da Ibrahim ya ɗaga yace cikin faɗa. Ina ka aje waya ina ta kira, duk inda kake ka dawo yanzu ka sameni a Part ɗin baƙi ina jiranka. To yace masa cike da girmamawa kana ya kashe wayar ya mayar da hankalinsa kan tuƙi. [7/7, 13:04] Buhainat😁: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shai wanidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.* 31. Shamsu yana isa gidan ya wuce part ɗin da Ibrahim yake ya same shi zaune shi kaɗai a falo, ga security a waje suna aikinsu na tsaro, ya zauna a can carpet dan su tarbiyyarsu indai babba yana kujera to su a ƙasa zasu zauna, ya ce cikin natsuwa. Yaya gani. Yauwa, ya labarin company da fatan ba wata matsala. Alhamdulillah komai yana tafiya yadda ya kamata. To madalla, akwai wani kwangila da zan baka wanda in kayi mini aikin daya dace zan baka motar daka ce kana so in siya maka. Cikin zumuɗi Shamsu ya gyara zama yana cewa. In Sha Allah zan yi maka aiki mai kyau ka faɗa kawai yanzu na fara shi ba ɓata lokaci. Good ina wannan ƙawar Khairy wacce ta zo tare da ƙanwarta suka tafi ash color mota. Eh na ganeta dan har gidansu na sani. Ya aka yi kasan gidansh? Ɗazu na bisu a baya saboda ina son daidaitawa da ƙanwarta. Ya ƙare maganar yana sosa kai, murmushi Ibrahim yayi ganin sunyi haɗaka akan abu guda, ya yi gyaran murya yace. Ina so ka yi mini bincike akan me ya kashewa yayar aure da duk wani bayani akansu, wato bincike mai kyau nake so da gamsasshiyar amsa. Ina so ya zama sirri a tsakaninmu ban yarda ka faɗawa kowa ba, nan da sati ɗaya zuwa biyu nake buƙatar sakamako. Idan kayi aiki me kyau to zaka je gurin Isyaku ka zaɓi matar data yi maka kuma idan aurenka ya tabbata zan yi maka lefe da komai. Cikin tsantsar farin ciki ya ce zai yi masa duk abinda yace, kana Ibrahim ya cigaba da cewa. Aikinka ya fara daga yau kar ka sake kaje gurin Khairy niman satar amsa dan bana so kowa ya sani. To In Sha Allah zanyi yadda kake so, ka fito lafiya. Ya faɗa kana ya miƙe ya fito yana mamakin Ibrahim, mutumin da yaƙi yarda ya ƙara aure shine zai ɓige a bazawara, abin ya ɗaure masa kai duk da yasan so ba ruwansa a duk inda ya ga dama sauka yake. Ya wuce part ɗin Hajiya ya samawa kansa abinci yana jin wani farin ciki a zuciyarta tare da tunanin fatansa ya tabbata shi ya auri Ikram Ibrahim ya auri Sameeha, ranar ba ƙaramin shagali za a yi a kaduna ba kuwa. ***** Aminu. Tun dawowarsa daga Kaduna yaran suka dameshi akan ya mamansu me saya bai zo tare da ita ba? sai yace bata nan tayi tafiya, haka suka dinga yi masa naci kullun sai sunyi zancen mamansu, wanda daga karshe Amrah saida tayi rashin lafiya duk na ƙawazucin uwa, baba Saude sai da ta saka baki akan ya yi hakuri ya haɗasu da mamansu ko a waya ne hakan zai rage musu damuwar da suke ciki. Shawararta yabi shine ya cire Number ɗin Sameeha daga blocking jiya ya kirata suka yi magana da yaran, hatta shi yana cikin tsantsar kewarta da son jin muryanta har da son ya ganta, duk da a yanzu ba aure a tsakaninsu, shi ya saka musu a handsfree yana jin muryanta yadda take rawa da kuka duk sai yaji ya karaya yaji kamar ya zaluncesu daya rabata da yaranta tunda ita tace zata iya zama da shi a haka, kuma zaman da yayi da ita ya kula bata ma yarda sha'awarta tana motawa, ko 'yan dabaru da yake yi mata bata wani damu ba wani lokacin sai ya ce zai yi ne take bashi dama amma bata wani damu da yayi ba, yanzu ne yake ƙara jin Sameeha ba zata aikata abinda yake zargi ba duk da akan idonta yaga komai amma zuciyarsa taƙi bashi damar yarda da hakan. Da ita ya kwana harya wayi gari wanda koda yaje aiki da tunanin a zuciyarsa, da ya bar gun aiki ya tsaya ya siya wa yaran ƙaramar waya ya saka musu sim akan su riƙa yin waya da mamansu, dan ya ɗauki alhakinsu daya nima shiga tsaninsu yanzu ne ya gane baya akan daidai. Yana cikin tuƙi kira ya shigo wayarsa sai da yayi parking a gefen hanya kafin ya duba dan yanzu yayi hankali baya ɗaukar waya in yana tuƙi saboda hatsarin daya yi a baya harvya jawo masa silar rabuwa da matarsa abar sonsa. Yana duba wayar yaga Najwa ce dan ko saving number ɗinta bai yi ba ya dai riƙe number ɗin musamman haruffan farko da ƙarshe, yaja guntun tsaki yana shirin kira sai ga shi ta sake kira ya ɗauka suka gaisa sai yayi shuru yaji uzurinta. Dama na kira na gaisheka ne. Ok na gode ya makaranta ko bakya zuwa. Ina zuwa makarantar Hadda amma munyi hutu ina gida. Masha Allah boko a ina kika tsaya? Secondary na tsaya amma ina burin inna yi aure zan cigaba. A wani gidan? Ba dai a gidana ba ko, dan ko matata da muka rabu bata cigaba da karatu ba saboda bana buƙatar haka. Wani dum Najwa taji ya turnuƙota daya kawo zancen Sameeha, sai da ta haɗiye miyau kafin ta cigaba da cewa. Kila ita bata da ra'ayin cigaba ne shiyasa amma ni burina kenan na cigaba da karatu dan Allah karka hanani. Aiko babu cigaba da karatu a gidana kamar yadda na hana Sameeha itama taso cigaba amma saboda na nuna bana so ta hakura, dan haka idan kina so ki cigaba da karatu sai a jinkirta auren koma a fasa ki yi karatunki karna daƙile ki. Dam dam ƙirjinta ya buga lallai akwai jan aiki a gabanta, ta nisa a hankali. To ba damuwa na haƙura. Ya dai fi miki dan ki sani yadda na tafiyar da gidana a baya haka ma zan ɗaura a yanzu babu abinda zai sauya mini ra'ayi. Ni ina kan hanya sai anjima ki gaida mutanen gida. Yana kaiwa nan a maganarsa ya kashe wayar, ya kunna motarsa ya wuce abinsa. Najwa kuwa bin wayar tayi da kallo wani ƙululun baƙin ciki ya tokare mara wuya, ta kalli Nafeesa da suke tare da duk taji hirar da suka yi tace. Anya Nafeesa mutumin nan zai juyu mini yadda nake so, kin ga yadda yake magana cike da gadara har yana sako mini zancen Sameeha. Najwa ina ga sai munyi yadda Binafa tace akan mu ɗan kauce hanya, Wlh mazan yanzu sai da mallaka balle kinga ke ga a yadda zaki yi auren, ina ma jin tsoro kar ya gane ke ce yace ya fasa ko kuma bayan auren yace zai sake ki. Nafeesa ki bani mafita wlh kaina yayi murfi ina cikin tsaka mai wuya, ga biyan buƙata amma ba kwanciyar hankali. Ai samun natsuwarki sai kin kama shi a hannunki Najwa dan wlh ina jiye miki zaman doya da manja da zaku yi da shi. Kawai hakanan zaki ɗaure mu nimo Binafa ta rakamu inda za a yi miki aiki ki samu kansa tun kafin ki shiga, in dai kina son zamanki dashi ya ɗaure. Najwa shiru tayi tana tunani dan tunda aka saka ranarta da Aminu bata wani cikin sukuni kullun cikin fargaba da zullumi ga shi kuma yadda yake nuna mata ko in kula ita ke kiransa kullun bai taɓa ɗaga waya ya kirata ba, koda ta yiwa Hauwa ƙorafi tace ta kwantar da hankalinta zai daina ne ta bashi lokaci, ita kam bata ɗaura niyyar yin aurensa ta fito ba, tana so ta aureshi sai mutuwa dan shine cikar zaɓinta wanda kullun take mafarkin samu, ga kyau ga kuɗi ga kuma nasaba sosai take ƙara jinsa a zuciyarta wanda take jin duk wanda ya nima rabata da shi to zata iya yin komai dan ganin bayansa, ta nisa cikin sanyin jiki. Dole na nima mallaka dan ina son zamana dashi ya ɗaure har abada. Ke ko Hauwa ce ta nima shiga gonata bazan raga mata ba akan Aminu dan yadda na iya rabashi da matarsa yar uwata to da kowa ma zan iya rabashi wlh, kira mana Binafa muji a ina zamu haɗu dan da zafi zafi ake dukan ƙarfe, tunda da kuɗin da ya tura mini kwanaki ban kashe ba to ga ranar amfaninsu. Da kyau 'yar gari gwara ayi komai a wuce gurin. Cewar Nafeesa tana danna number ɗin Binafa ta kira ta tambayeta ina take, Binafa tace tayi nisa sai dai gobe In Sha Allah su haɗu wajen tara na safe a gidansu sai suyi magana, a haka suka kashe wayar ta faɗawa Najwa yadda suka yi, sai suka cigaba da hira gabda magrib Najwa ta bar gidansu Nafeesa daya zame mata jiki kusan kullun sai ta je, dan a nan suke ƙullu duk wata munafurcinsu, a cewarta a gidansu inna tana kusa bata so taji komai. Washe gari da wuri Najwa tabar gidansu ta isa gidansu Nafeesa, sai wajen goma suka tafi gidansu Binafa, suna zuwa ta shirya dan tun jiya a chart Nafeesa ta sanar da ita inda suke so ta rakasu, sai kawai suka fita a motarta zuwa gidan wani malami dake can Mando, koda suka shiga ba kowa dan haka Binafa ta koro masa bayanin abinda ya kawo su, nan ya yi surkulensa a ƙasa tare da yin zane, yayi surutai marasa kan gado wanda yake muna wannan boka ne ba malam ba, sai da ya gama kafin ya dubesu yana cewa. Ba zaki taɓa mallakeshi ba sai in an raba zuciyarsa da matar da ya saka dan yana sonta sosai fiye da lissafi, saboda haka ki kawo mana kyallen zanin matar daya saka za muyi aiki da shi. Najwa taji kanta ya sara mata dan bata san inda zata je ta samu kyallen kayan Sameeha, sai ba tace cikin rauni. Babu wata hanya dole sai anyi haka.? Hanga ɗaya ce idan baki samu kyallen zaninta ba to ki kawo warin takalminta guda ɗaya, idan duk baki samo ba to ki saka a ranki bake ba mallake mijinki dan tabbas zaki aure shi amma akwai tarin matsaloli da zasu biyi baya. Zaku iya tafiya idan kin samo abinda muke buƙata sai ki kawo a fara aiki. Da wannan zancen nasa suka fito suka zauna a cikin mota Binafa tana cewa. Najwa kina ruwa dan akwai kura, yanzu ya za a yi mu samu abinda boka ya buƙata. Gidan zanje in samo warin rakalminta dan shi zaifi sauƙin samu, Binafa muje ki sauke mu a kawo ni da Nafeesa mu tafi gidansu. Kina ganin zaki samu fuska dan kince kin daina shiri dasu. Zan samu mana dan Umma tana da saukin hali Sameeha ma haka, Ikram ce dai 'yar rainin hankali. To sai kun dawo mu ji in zai yiwu mu koma gun Bokan a yau. Cewar Binafa sai ta saka key a mota suka wuce. Tana zuwa kawo ta samu guri tayi parking suka sauka sai ta wuce su kuma suka tsallako suka samu napep suka wuce gidansu Sameeha. ***** Sameeha. Sai da suka idar da sallar isha'i kafin suka zauna a falon umma suka shiga firar walima, wanda a lokacin ma suka baje kulolin abinci da kayan ciye ciye suna ci suna hira, a haka Zaidu ya shigo ya same su shima aka cigaba da cafta dashi, sosai suka yaba kirki da karamcinsu umma ta ɗaura da cewa. Gaskiya mutanen kirki ne Allah dai ya saka musu da alkhairi, ni wlh Allah yasa wannan yaro da gaske yake ya turo ayi magana kawai dan na gaji da zancen jiran Aliyu. Wlh umma nima abinda na faɗawa Ikram kenan, zan bincika Khairy naji ya suke dashi, na san ba zata ɓoye mana komai na shi ba, Allah dai ya tabbar mana da alkhairinsa. Cewar Sameeha umma ta amsa da amin kana suka cigaba da hira Zaidu yana cewa Ikram ta shiga hankalinta dan ba a yada irin wannan dangi masu mutunci ba irin su Hauwa ba, ai baya fata wata 'yar uwarsa ta faɗa ga dangin miji irinsu. Ba dan ma Aminu lokacin a tsaye yake ba da tuni sun kashewa Sameeha aure, nan dai suka dinga mayar da zance har lokacin barci yayi kowa ya kama hanyar gun kwanciyarsa. Da safe. Suna gama karyawa sai suka koma barci sai wajen sha biyun rana Ikram ta haɗa wanke wanke tana cewa Sameeha da ke haɗa wutar gawayi. Waye zau mayar da kulolin nan Anty Sameeha.? Idan saurayinki yazo anjima sai mu bashi ya mayar musu. Kai Anty ya zaki ce haka mutumin da bai samu matsuguni ba. Zaima samu ne Ikram kuma... Sallamar da Su Najwa suka yi yasa Sameeha yin shuru har suka ƙaraso cikin gidan fuskarsu ɗauke da murmushi, Ikram kuwa ta haɗe rai ta cigaba da aikinta. *Afwan yau aiki nasha kunsan ana ta shirin tarban Ramadan Allah yasa muga farko da ƙarshensa lafiya. Yasa mu kasance cikin 'yantattun bayi* _Mun kusa tafiya hutu sai bayan sallar In Allah ya kaimu zamu cigaba. Naso na gama kafin azumi amma bazai yiwu na guntule labarin ba, dan akwai abubuwan daya kamata a bisu daki daki._ [7/7, 13:04] Buhainat😁: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shai wanidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.* 34. Ƙaurin da inna taji na abincin dake wuta yasa tayi saurin fitowa daga ɗaki tana sababi, ta isa da sauri ta sauke ta mayar da tukunyar holoƙo ta saka ruwan wanka kana ta nufo ɗakin Najwa dan tayi mata faɗa akan ƙin sauke abincin da bata yi ba, Najwa tana jin motsin zuwan Inna yasa ta danne kukanta ta bawa ƙofa baya, Inna ta ce cikin faɗa. Wani irin shirme ne Najwa kike yi, nace ki sauke abinci amma kin samu guri kin kwanta, kin ma yi sallar magriba kuwa? Kaina ke min ciwo tun ɗazu da rana, da yamman nan kuma zazzaɓi nake ji da kyar ma na ɗaura girki, ɗazun mantawa nayi ban faɗa miki ba. Assha yanzu haka maleria ce, Allah ya sauke, bari Junaidu ko Sadiq su shigo sai a samo miki magani kisha, amma ki tashi kiyi sallah in baki yi ba. To Najwa tace mata, inna kuma ta juya zuwa ɗakinta sam bata gane halin da Najwan ke ciki ba, har zuciyarta ta yarda da ba tada lafiya ne tunda gashi ya nuna ma a muryarta da yayi sanyi. Najwa miƙewa tayi ta zauna tana jin wani tuƙuƙin baƙin bakin ciki yana ratsa illahirin zuciyarta da gabbai, sai ta miƙa hannunta gefen gado data aje wayarta ta dubo number ɗinki Hauwa ta danna mata kira, bugu ɗaya ta ɗauka Hauwa tana cewa. Amarya kinƙi ambato muna zancen ki sai ga shi kin kira, muna nan muna ta hada hadan haɗa akwatinki, kin san ke twmu ce komai muna su muyi shi waja wajaba laranta. Hauwa ta kai aya a maganarta tana saurare me Najwa zata ce mata, Najwa sai da ta lumshe ido kafin ta ja fasali tace cikin sanyin murya. Anty Hauwa kin samu labarin auren Sameeha da ƙanwarta Ikram da za ayi, ta samu miji ɗazun nan aka kawo kuɗin aurensu, sadakin Sameeha dubu ɗari biyu Ikram kuma dubu ɗari uku, abu kamar a film. Kutumelesi au Sameehan har ta samu miji? Ashe duk son da takewa Aminu ƙarya ce tunda gashi ko shekara bata yi da fita ba zata yi aure, to su waye zasu auresu haka? naji kin ambaci kuɗi masu yawa na sadaki. Ikram dai ɗan wazirin Zazzau zata aura Sameeha ce dai bamu sani ba amma ance mai kuɗi ne kuma ɗan uwan mijin Ikram ne, abu dai wlh kamar almara, nima nayi mamakin wannan daraja da suka yi musamman Ikram da take baƙa ba ta da fasali. Hmmm ayi dai mu gani in tusa zata hura wuta, yanzu haka asiri suka nima har suka samo su, tunda kin san Sameeha ta saba da gidan kuɗi ba zata yarda ta faɗawa talaka ba, kuma ta saba damin malamai kin ga kuwa ba abin mamaki bane in ta samo mai ƙumbar susa, In sha Allah muma za muyi miki kaya na gani na faɗa tunda kema ba talala zaki aura ba, saboda Aminu yanzu ma yake tashen kuɗi, ina saka ran kina shiga gidansa zaki samu motarki ta hawa. Allah Anty? Ni dai ina fargaba in ya gano nice matarsa, kamar bazai karɓeni ba ina jin fargaba sosai akan haka. Ke rabu dashi, an gaya miki haka zan barshi, dole zan nima miki taimako yadda zaki samo kansa sosai, ke dai ki cigaba da shiri kawai ki kwantar da hankalinki kamar kinyi bako ya mutu. Har naji daɗi Anty Hauwa dan wlh tunda naji batun bikin su Sameeha naji hankalina ya tashi, naso ma ace an riga ɗaura nawa kan nasu, dan su wata biyu aka saka. Karki damu kanki gaggawa aikin shaidan, ki rabu dasu yanzu haka ba su shuka alkhairi ba shiyasa suka saka da wuri, mu za muyi namu a tsanake kuma In Sha Allah bikinki sai ya fi nasu armashi. Najwa sai da ta saki murmushi jin maganar Hauwa dan sosai zuciyarta ta yarda da maganarta, duk da ƙasan zuciyarta ta san Sameeha bata bin malamai, sannan ga Ikram da zara auri ɗan gidan sarauta hakan yafi tsaya mata, haka suka ɗan taɓa hira daga bisani suka yi sallama, sai ta aje wayar ta wuce tsakar gida dan tayi alwala, duk da har yanzu bata dawo dai dai ba amma maganganun Hauwa sun ƙara mata kwarin guiwa. * Hauwa. Suna aje wayar take kallon Laure da suke zencen akwatin Najwa da Aminu ya fara turo mata da kuɗi, dan musamman taje babban gida dan su tattauna maganar, Hauwa ta labartawa Laure yadda tayi da Najwa duk da ta gane inda hirar ta dosa da suna waya, Hauwa ta kare da mele baki. Kinji dai tsautsayi ta faɗawa wani zai kwashi Sameeha alaƙaƙai, Allah dai ya sa su kwashe lafiya. Hmmmm ko kuma auren kashe wuta zata yi ba ta dawowa Aminu, dan kinsan irin son da take masa na tabbatar zata iya aikata haka. Allah ya kyauta kima daina yi mana wannan fatan domin mun riga da mun yada kwallon mangoro mun huta da ƙuda, Aminu ba zai taɓa sake dawo mana da ita ba wlh, ke duk inda zan shi to zan fita in tabbatar da haka bai faru ba. Ita da shi haihata haihata. In Sha Allah kuwa, domin bazan taɓa mance sakin data jawo mini ba, annoba ce Sameeha bana fatan ta dawo, suje can su karata sai dai tayi wa wasu fi'ili. Yanzu sai ki kira Aminu ki faɗa masa imma zai saki jiki yayi aurensa da zaifi masa, dan Sameeha ma ta mance da shi. Kuma fa hakane, bari na kirashi kinga yanzu ya zage yayi aurensa in ma yana tunanin Sameeha ne sai ya daina. Cewar Hauwa data ɗago wayarta ta shiga wajen kira ta danna number ɗin Aminu. Har ya kusa tsinkewa kafin ya ɗaga ta ƙara a kunne suka gaisa kana Hauwa ta shiga koro masa bayanin auren Sameeha har da karin gishiri a miya, Aminu sosai yaji maganar ta daki zuciyarsa dan bai ɓata zaton Sameeha zata yi aure nan kusa ba, sai sabon sonta ya taso mata tare da kishinta sosai, duk da lamarin ya taɓashi cikin dakiya yace. Amma yaya Hauwa a ina kika ji wannan labarin? anya ba karyar mutane bane? Haba Aminu ai da ban tabbatar da maganar ba bazan kira na faɗa maka ba, kuma daga majiya mai ƙarfi na ji, kasan zancen aure baya ɓoyo, ka sani ma ko taji labarin naka auren. Da taji zata yi mini maganar ko ta tambayi yara tunda suna waya. Amma ke waye ya faɗa miki an kawo kuɗin aurenta. Au baka yarda ba kenan? To sai ka kirata ka tambayeta tunda kana da numbern ta nasan ba zata ɓoye maka ba tunda ba igiyar aurenka akanta, waya sani ko auren huce takaici zata yi ko na kashin wuta danta dawo maka. Sameeha ba zata taɓa yin haka ba, na santa nasan halinta, domin tana da sani na addini ba zata yi auren kisan wuta ba. Hmmm ashe har yanzu dai da sauran ƙimarta da kake gani, to ai sai ka kirata kaji daga bakinta tunda ni baka yarda da maganata ba, koma dai miye yanzu ba aure a tsakaninku taje taita auren Allah yasa ta zauna. Hmmmm shikenan na yarda Allah yasa alkhairi, ya batun akwati kun fara siyan kayan ne? Yaushe ka turo kuɗin da zamu fara? Muna dai shirye shirye ne. To Allah ya taimaka sai anjima. Cewar Aminu yana kashe wayarsa bai jira amsarta ba, Hauwa ta aje waya a ƙasa tana 'yar dariya. Kin ga ko bai wani damu da maganar aurenta ba, ina ga dai Aminu ya daina son yarinyar nan asirin da suka yi masa ya rabu dashi maganar ma kayan akwati yayi fa yanzu. To ba dole yabar jikinsa ba saki uku fa yayi mata, Allah kaɗai yasan tsawon lokacin daya ɗauka yana cin ƙamu ƙamu, dan irinsu Sameeha har tsafi zasu yi dan su mallake namiji, balle Aminu yanavda abin hannunsa da dole ma ta bi malamai dan kar wata ta shigo mata gida. Mun dai rabu da alaƙaƙai aje cen a yiwa wasu. Cewar Hauwa, haka suka cigaba da hira wanda rabi zagin Sameeha suka dinga yi suna rage mata zunubi, tare da mugun fata akan Allah yasa auren ma kar yaje ko ina kowa ya gane ba 'yar kirki bace ita. * Aminu. Miƙewa yayi ya soma kai komo dan sosai abin ya taɓashi, bai taɓa zaton zai damu ba in yaji Sameeha zata yi aure, amma sai gashi ya samu kansa cikin mawuyacin hali har yake jin da zai ganta a gabanshi sai ya rufeta da mari saboda kishinta daya ji yana fusgarsa har wani hucin zafi yake fitarwa, ya kasa haɗa tunaninsa guri guda dan gani yake kamar Hauwa ƙarya take yi, saboda a ganinsa yayi wuri ace Sameeha tayi aure dan bata jima da fita idda ba, amma kuma ƙila ko auren huce takaici zata yi domin ta bashi haushi, haka ya dinga haɗa tunani ya rasa matsaya sai kawai ya yanke shawarar kiranta, ya isa centre table ya ɗauki wayarsa ya duba agogo takwas saura, ganin dare bai yi sosai ba yasan idonta biyu, sai ya danna number ɗinta nan take kuwa ta shiga ya kara a kunne. * Sameeha. Cikin farin ciki suke zaune a tsakar gida suna mayar da zancen abinda ya faru ɗazu na kuɗin aurensu da aka kawo, ko wanne fuskarsa cike da annashuwa,wanda Zaidu yake faɗar zai je MGfurnitures domin yin magana da shugaban company kan kayan katako da zai yi musu oder, Ikram tace cikin zaƙuwa. Aiko kayansu nake so, dan wlh sun iya aiki kayansu tamkar daga ƙasar waje kuma suke haɗawa da kansu a nan Kaduna, naji ance ba inda ma basa tura kaya a faɗin Nigeria har Niger ana fitar da kayansu. Yaya Zaidu nifa komai nasu na funitures nake so. To azagwaigwai kazar birni, Ikram ba kunya, ashe dai kina son Shamsu har haka yadda naga kina murna. Cewar Sameeha tana 'yar dariya umma tace. Rabu da sakarya ai da ta yiwa kanta illa ta rasa nagartaccen miji, ga Aliyun data damu dashi har yanzu ba labarinsa ma. Zaidu zai yi magana wayar Sameeha ta katse shi wacce take kusa dashi, Sameeha ta dauko wayar data aza a cinya ganin sunan Aminu data yi saving ta sauya masa da sunan da da ta aje numbernsa, yasa taji gabanta ya faɗi dan tasan yaranta yanzu suna da wayarsu daya siya musu, kuma dashi suke magana, har kiran ya kusa tsinkewa Umma tace. Ki ɗauka mana, waye ma ya kira naga kin yi sororo ne. Wai Aminu ke kirana wataƙila yaran nan ne suka ɗauka dan su kira ni. Ta bata amsa lokacin wayar ma ta tshinke har wani ya sake shigowa, sai ta ɗaga ta ƙara a kunne tana sallama. Jin anyi mata shuru sai saukar hucin numfashi da ta ji yasa ta gane Aminu ne, cikin karfin hali ta ce. Ina yini ya aiki? Sameeha! Ya faɗa cikin ɗaga murya ya ƙare da sauke numfashi, gabanta ne ya faɗi tama kasa amsa masa ta tsaya tana saurarensa, ya cigaba da cewa. Ance mini aure zaki yi dagaske ne? Sameeha sai da ta cire wayar a kunnenta ta ƙara duba number ɗinsa dan ta tabbatar da shi ne, kafin ta mayar ta ki cewa komai dan bama san amsar da zata bashi ba. Kinyi shuru ko amsar ki kenan? ya tabbata kenan aure za kiyi, hakan ya nuna dama tuntuni kina son rabuwa dani kije kiyi aure, sai kika ƙi nuna mini sai da abin nan ya faru kafin kika samu damar saki, ina ganin dama kin shiryawa hakan ne domin ki samu damar rabuwa dani, na jima ina mamakin ganin wannan 'yan matan a gidanmu bayan kinsan nace miki washe gari zan dawo da sassafe mu tafi kano, dama kinyi haka dan na gansu ne na sake ki tunda na tabbatar in sun kwana a gidan dole zan haɗu dasu, sai dai in kin ɓoye su a wani wajen. Haba Aminu ya zaka ce haka, ka sani yanzu ba igiyar aurenka a kaina dan zanyi aure ba haramci a ciki, kuma batun 'yan mata, to nace na aikata ɗin, hukunci kuma ka gama yanke mini tunda ka sakeni, babu sauran mayar da hannu agogo baya. Hmmm dole ki naɗe tabarman kunya da hauka Sameeha, domin yanzu ne na tabbatar da wacece ke tunda daga fita idda sai aure, kamar kina jira na sake ki, kin bani mamaki ban zaci haka daga gareki ba, nagode wa Allah daya bayyana mini ke wacece kuma In Sha Allah ki zuba ido zan nima lafiya duk inda yake koda nan da birnin sin ne zanje domin nima na yi aure, dama dakon sonki ne yasa nake ganin zan iya komawa ga Allah a yadda nake, amma yanzu kin shayar dani gubar mamaki daya zaburar dani akan na nima lafiyata, kin nuna mini ke ɗin 'yar Adam ce Sameeha wato butulu. Me nayi maka dana zama butulu Aminu? kawai dan zan yi aure kake faɗa min baƙaƙen magana saboda son zuciya, kar ka manta ƙaddara ita ta haɗamu kuma itace ta rabamu. Kaddara ko kuma cin amanata da kika yi Sameeha, ai da ban kamaki da yaran nan ba da yanzu muna zaman aurenmu. Zaidu ne ya fizge wayar daga hannun Sameeha ya kara a kunnensa, da yake duk suna jin maganar Aminu saboda sunyi shuru kuma volume ɗinta ana ji sosai koda bata saka handsfree ba, Zaidu yace cikin ɓacin rai. Dan Allah karka sake kiranta ka nima ɗaga mata hankali tana cikin farin ciki, tunda kai ka saketa kace baka yi da ita duk halaccin data yi maka ta zauna da kai tsawon shekara shida ba ka da lafiya amma ka saketa akan abinda ba kada tabbas, dan haka ta samu wanda yake sonta kuma yake ganin mutuncinta gidan mutunci ba irin 'yan uwanka ba marasa mutunci, yara kuma kar Allah yasa ka kawo su ka riƙe su In Sha Allah zata haifa mana wasu a sabon gidanta. Bai jira ya yi magana ya kashe wayar yana huci, Umma ta riƙe haɓa. Ashe shima baida mutunci ina yi masa kallon salihi, koda yake ai nono guba Hauwa ta sha ta sake masa, ina ganin abin nasu ya samo asali. Nifa ina ganin kishi ne yasa shi fusata haka, ko uban waye yace ya sake ta oho. Cewar Zaidu, Umma tace. To kishi sai ya saka idonsa ya rufe ya rika faɗin magana sai kace wanda cutar ɗan kanoma ya kama, haba abin ya yi yawa, ni nayi mamakin ma yadda ya samu labarin auren abinda akayi magana yau yau amma har magana ta isa gareshi shi da yake Abuja. Ai kiwon mutum ake yi Umma, da alama ƙila ya saka masu yi masa bincike akanta ne suna faɗa masa halin da take ci, in ba haka ba taya daga magana yau har ya samu labari. Cewar Ikram cikin faɗa, nan dai suka dinga juya maganar Sameeha dai ta kasa cewa komai sai maganganun Aminu ne suke yi mata yawo a zuciya, dan sosai lamarin ya taɓa ta ba yi zaton jin waɗannan kalamai a bakinsa ba, kira daya ƙara shigowa wayarta yasa ta duba taga number ce da tun ɗazu da take magana da Aminu ake kiranta, har ya katse bata ɗaga ba sai ma miƙewa tayi ta wuce ta ɗauki buta ta wuce bayi dan tayi fitsari, tana shiga ta saki kukun da take dannewa, sai dai bata bari tayi mai sauti ba dan kar su ji ta, gabaɗaya duk farin cikin da take ciki ya yaye sai baƙin cikin abinda Aminu ya yi mata yanzu daya maye gurbin zuciyarta, ko a mafarki bata taɓa tunanin zai yi mata haka ba, babban baƙin cikinta yadda ya gasgata ta aikata masha'a da 'yan matan nan, har gobe ba zata iya yafe musu ba dan duk sallah tana kai kukanta gurin Allah akan ya saka mata tare da jera musu Allah ya isa, babban farin cikinta yadda su Hauwa basu san dalilin mutuwar aurenta ba, da sun sani ta tabbatar ba zasu taɓa barinta ba dan sun riƙa zuwa kenan suna niman rikici da ita, haka tasha kukanta ta gama ta wanke fuska ta fito ta wuce ɗaki suf-suf bata bi ta kansu Ikram ba, su dai kallo suka bita dashi dan sun san in tana cikin damuwa to shuru take yi bata magana da kowa, sai ta kaɗaita kanta ita kaɗai tana sharɓan kuka, Ikram data bi bayanta da kallo har ta shige sai ta juyo tana cewa. Umma kuka fa tayi a bayi, baku ga yanayinta ya sauya ba. Na gani tunda nasan halinta, ku rabu da ita da kanta zata saki ranta, kuka da damuwa dole tayi domin duk inna tuna da wannan sharri da 'yan matan nan suka yi mata sai na tsine musu tare da addu'ar Allah ya tona musu asiri. Ameen nima wlh ina yin addu'ar Allah ya hana musu kwanciyar hankali. Cewar Zaidu, haka suka cigaba da hira wanda duk rabi akan zancen Sameeha ne. Aminu kam wayar yabi da kallo lokacin da Zaidu ya kashe kiran, ya tsugun kan guiwarsa yana jin wani ɗaci a makoshinsa, jikonsa har wani kalkarwa yake tsabar damuwar daya samu kansa, dana sanin sakin Sameeha ya rufe shi sai yaji dama saki ɗaya yayi mata ko biyu yadda zai samu damar gyara aurensu ta dawo masa, tabbas yadda yake ji a zuciyarsa hakan yana nuna shine ya zalunci Sameeha, domin kuwa dama a tsakanin ma'aurata duk wanda yayi zalunci to tabbas yana gamuwa da dana sani a gaba kuma wanda aka zalunta yana riga yin aure, bai san hawaye yake yi ba sai da ya taɓa kuncinsa ya shafa kafin ya gane haka, shima yasan duk maganganun daya faɗa mata ɓacin rai ne dan har gobe zai shaidi kyawawan halayyarta, sai ya miƙe cikin sanyin jiki yana ambaton sunan Allah dan hakan ne kaɗai zaisa ya samu sassaucin halin da yake ciki. *Barkanmu da Sallah fatan munyi sallah lafiya Allah ya maimaita mana yasa muna cikin yantattun bayi. Ameen.* [7/7, 13:04] Buhainat😁: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shai wanidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.* 35. Aminu bai taɓa zaton Abin da ciwo ka saki mata wani ya aura ba sai yanzu, bai kawo zai damu ba in yaji Sameeha zata yi aure ba, sai gashi abu yana niman zama masa ƙaya a maƙoshi, zazzaɓi mai zafi yaji ya kamashi kuma a haka ya kwana, wanda da kyar barci ya ɗauke shi. Washegari da wuri ya shirya ta tafi asibiti, dan ya ɗauki alwashin nimawa kansa lafiya ko nawa zai kashe, sannan ma dole ne ya amsa auren da Hauwa ta samo masa domin ya huce takaicin Sameeha, zai yi fatan ya samu lafiya kafin bikinsa duk da ba yi da tabbacin zai samu lafiyar, amma ya ɗaura niyya sai inda ƙarfinsa ya ƙare. * Ibrahim. Tunda aka sanar dashi an gama komai na aurensu an saka rana sai yaji hankalinsa ya kwanta, dan sosai ya kamu da son Sameeha da ko magana basu taɓa yiba a tsakaninsu, hakan yasa shi kiran Khairy yace ta tura masa Number ɗin Sameeha, domin yana so su ɗan saba kafin bikinsu. Data turo masa Number ne sai ya soma kiranta a lokacin, sai yaji call waiting, ya kira sau biyu duk tana waya hakan sai ya bashi mamaki da tunanin da waye take magana da shi haka, duk da yana da tabbacin ba tada zawarawa amma jikinsa yana bashi kamar da wani take magana, nan take ya ji kishi ya ɗarsu a zuciyarsa wanda bai taɓa tsammani ba saboda shi mutum ne da ba ruwansa da wani kishi shiyasa matarsa Nabila take yin yadda taso, bata zama a gida kuma hakan ba ya wani dame shi bane, amma kam yadda yake jin Sameeha a zuciyarsa komai ma zai iya faruwa. Bayan ya bada wasu mintuna sai ya kuma kira, a wannan lokacin ne yaji bata yin waya sai dai bata ɗaga ba, hakan yasa ya miƙe da sauri ya shiga bedroom ɗinsa ya sauya kaya ya fito falo ya samu Nabila tana cin abinci. Sai ina kuma? Naji kace zaka yi barci da wuri saboda da safe zaka wuce Abuja. Taɗi zani wajen ƙanwarki. Kallonsa tayi sheƙeƙe tana 'yar dariya. Wasa kake yi, dan nasan ba kada wata mata sama da ni Nabila. Kama daina wannan zencen dan nasan ba mai yuwuwa bane. Allah ko Hajiya Nabila, to ki zuba ido kiyi kallo domin wannan karan da gaske nake ba wasa a ciki, idan naje zan kira ki ki gaisa da ita domin ki tabbar. Kuma ki fara lissafin abubuwan da kike buƙata na faɗar kishiya, sai na baki kuɗin ki haɗowa kanki. Baki sake Nabila ta bishi da kallo har ya fice daga falon ta kasa yin magana, da farko ta ɗauka wasan daya saba yi mata ne yayi, amma kuma yadda taga yana maganar fuskarsa washar ta soma gasgata haka, nan take taji abincin ya fice mata a rai ta tura plate ɗin ta soma kiran wayar wata ƙawarta Shema'u, tana ɗauka ta koro mata bayani tana ƙarawa da cewa. Allah zuciyata ta karaya ina ga da gaske yake duk da shi ya tabbatar mini da baya sha'awar mata biyu. Hmmm kin zauna ya gama jirgaki kin hau kin zauna, an faɗa miki namiji ba ɗan kunama bane, sai kin saki jiki kin daidaita zama ya gantsara miki cizo, kina tunanin yadda kike yawo ƙasa ƙasa ba kya zama hakan ba zai dame shi ba ko, to ko wannan dalilin zai sa ya ƙara aure kuma dama 'yan uwansa tuntuni suka so ya ƙara, kinga kuwa dole watarana zasu ci galaba akansa ya amince, idan zaki tashi tsaye gwara ki miƙe dan wlh in kika bari wata ta shigo zata amshe komai na uwargida tunda ke baki ɗauki auren a bakin komai ba sai niman kuɗi. Idan akan niman kuɗina ne to wlh yaje yayi ta auren ai ba kaina zata zauna ba, kuma nasan dai har abada bata isa ta kamo ƙafata ba tunda ni ina da kuɗi, kuma ba daga gidan talauci ya aureni ba. Haka zaki faɗa ko? Wai ke kuɗi zai iya sayan darajarki da komai ko, ana maganar kishiya kina niman nuna baki damu ba akan kuɗi. To Allah ya tsayar akan ki, idan kin so zaki iya zuwa gidana muje gidan wani malami domin ayi aikin da zai hana auren, idan kin manta bari na tuna miki itama amayar zata zo ta haihu kuma duk dukiyar da Ibrahim ya tara da ita za aci, kuma yana faɗi ya mutu gado ya zana keda ita da yara kinga kin samu naƙasu a kasonki. Ɗan jim Nabila tayi dan sosai maganar Shema'u ya zauna a zuciyarta, sai ta nisa tana cewa. Zan zo muyi maganar da safe In Sha Allah dan ban yarda kowa ya rabi dukiyar Ibrahim ba wlh. Da dai ki zauna ki ga zama. Sai kin zo ɗin. Cewar Shema'u, nan suka yi sallama suka kashe wayar Nabila ta miƙe tana kwalawa mai aikinta kira ta fito daga ɗaki da sauri, sai tayi mata umarnin ta kwashe plate ɗin data ci abinci ta kai kitchen ta gyara gurin, sai ta wuce ɗakinta tayi shirin barci sai dai tunanin maganar auren Ibrahim ya tsaya mata a rai, gani take kamar wasa yake yi mata, sai dai maganar Shema'u na zancen ta miƙe taye akan kar wata tazo gidan ta rage mata samun wasu kaso na dukiyarsa, yayi matuƙar tasiri wanda take jin zata iya aikata komai ma dan kar hakan ta faru. Ibrahim wajen tara da kwata na dare ya isa ƙofar gidansu Sameeha wanda ya samu motar Shamsu a Kofar gidan, hakan ya tabbatar masa da yana cikin gidan, ya kirashi yana ɗauka yace. Sarkin zumuɗi ashe har ka iso, to ka yiwa Ikram magana ta sanar da yayarta ina ƙofar gida ta fito ina cikin mota. Shamsu yana 'yar dariya yace to kana ya kashe wayar ya duba Ikram ya sanar da ita sakon Ibrahim, da sauri ta miƙe ta wuce cikin gida ta samu Umma a falo ta sanar mata, Umma tace. Ki shiga ki faɗa mata tana ciki nasan dai bata yi barci ba. Ikram ta wuce ciki ta samu tana kwance tare da danna waya kamar chart take yi. Anty Yaya Ibrahim yazo yana waje a cikin mota. Kije kice nayi barci bana cikin yanayin da zan fita masa. Haba anty ba zai ji daɗi ba fa, kin san yau ne farkon zuwansa ki daure ki saurare shi tunda anriga an gama magana yana da damar da zai ganki, sannan ki aje batun Aminu dan wlh yayi hakane dan ya farraka farin cikinki. Hmmm sarkin tsara zance, to jeki ce ina zuwa. Sameeha ta faɗa tana zuro ƙafarta ƙasa, Ikram murmushi tayi ta fice. Sameeha babban Hijab ta zura ta saka wani plat shoe ta fito Umma tana cewa. Ki dai saki fuskarki karki yarda ya gane kina cikin damuwa, kuma lokaci yayi da zaki yakice matsalar Aminu da 'yan uwansa ki fuskanci farin cikin daya tunkaro ki. Humm tace bata iya magana ta fice, har jikin motar ta isa ta tsaya a waje, ya sauke gilass ɗin mota yana cewa. Ranki yadaɗe ayi mini alfarma a shigo mota saboda bana so mutane su gane nine a nan dan Allah, naso na shiga gida to Shamsu ya riga ni. Bata ce komai ba ta je back seat ta kama zata buɗe sai ya cire motar a key ta buɗe ta shiga baya ta zauna ƙafarta suna waje, shima ya ɗaga glass ɗin motar ya ƙara AC ya juya yana dubanta, a hankali ta buɗe baki ta gaishe shi ya amsa fuska sake yana cewa. Gimbiya ɗazun nine na kira na samu call waiting sai kuma na ƙara kira baki ɗaga ba, Allah yasa ba da x mijinki kike waya da shi ba, dan jikina ya ba ni da namiji kike magana. Da sauri ta ɗago tana kallonsa dan taji mamakin fururucinsa, Ibrahim ya ɗage mata gira yana murmushin gefen baki sai ta sunne kai ƙasa ya cigaba da cewa. Idan ina son abu na saka shi a raina ina iya hasashe akansa koda ba haka bane abinda na faɗa za a iya jiyo ƙamshin gaskiya. Dalilin daya saka na zo kenan dan ƙin ɗaukar wayata da kika yi, koda yake ƙila bakya ɗaukar number saboda tsaro. Da fatan kina cikin koshin lafiya. Lafiya lau. Ta bashi amsa a takaice, Ibrahim ya kira sunanta ta ɗago kai tana kallonsa ba tare da ta amsa ba. Ina sonki har cikin zuciyata tun ranar dana yi tozali dake, ban taɓa kawo zan ƙara aure ba domin ni bani da ra'ayin haka, amma yanda kika samu gurbi a zuciyata naji bazan bari damar hakan ya kuɓuce mini ba tun sa'ilin dana samu labarin ba ki da aure, na tabbatar mijinki yana cikin cizon yatsa da kaicon rabuwa da ke domin kuwa ke Zara ce a cikin taurari, a ɗan binciken dana yi na tabbatar kina da tarbiya da kuma kyakkyawan hali, dan haka nake muradin zamowarki mata a gareni domin ki zame mini sanyin idaniyata, da fatan zaki zamo mini cikon addini na. Tun sadda ya soma magana ta sunne kai ƙasa take saurarensa har saida ya kai aya kafin ya yi shuru, amma ta kasa magana, saboda tunaninta yafi karkata akan Aminu da maganganun da ya gaya mata ɗazun, sai tsinkayo maganar Ibrahim tayi yana cewa. Nasan ban isa na samu gurbi lokaci guda ba a zuciyarki, saboda bansan irin ginin da Mijinki na baya ya gina ba a zuciyarki, hakan yasa nake jin rauni da sarewa musamman a yadda naga kin fito fuskarki ba walwala, hakan ya sa mini tunanin ko na takuraki ne da aurena, dan na san nayi miki katsalandan ban fara jin ra'ayinki ba na turo magabata na, dan haka har yanzu kina da zaɓi ina son duk abinda kike so, ni zan iya janyewa na haƙura muddun hakan zai saka ki cikin farin ciki Sameeha, nasan zan jima ina jinyar zuciyata amma dole zan haƙura na jure. Nan ma Sameeha bata yi magana ba sai hawaye data ji yana ciko idanunta, ba zata ce Ibrahim yana da makusa ba dan tabbas taji zata iya zama da shi, amma tasan ba zata sake son wani sama da Aminu ba, tabbas ƙaddara tayi mata kutse a rayuwarta dan tunaninta da komai ya koma gun Aminu, gani take so da kishi yasa shi kasa danne damuwarsa har ya kirata ɗazun, mamakinta taya aka yi ya samu labarin aurenta. Ibrahim shuru yayi shima dan ya kula ba zata yi magana ba sai da suka ƙara minti goma a haka kafin ya kuma cewa cikin sanyin murya wanda yake nuna damuwa a tare da shi. Sameeha zan baki lokaci ki zauna kiyi tunani da addu'a, idan har ban kwanta miki ba zan janye daga maganar aurenki domin farin cikinki shi nake so, amma ki sani ina ƙaunarki ina jinki har cikin jini na da ruhina, bana jin na taɓa jin irin ɗanɗanon sonki akan wata mace, ko Mubeena dana sota a baya banji irin haka akanta ba, ki je gida ni zan wuce sai da Safe ki gaida su Umma. Ya ƙare maganar cikin rawar murya dan sosai yake jin ya fashe da kuka ko zai samu sauƙin yanayin daya samu kansa a ciki, sai a lokacin Sameeha ta ɗago kai sai caraf suka haɗa ido dan akwai hasken wutar mota ɗaya kunna na ciki, wani irin abu ne nan take ya kai sako a idanunsa tamkar walkiya, kuma hakan yayi tasiri a illahirin jikinsu, dan wani shokin ne ya tafi da sauri cikin jijiyoyin jikinsu, wanda hakan yasa Sameeha ta sunne kai tana sauke ɓoyayyan ajiyar zuciya siririn hawaye ya sauka a kuncinta, Ibrahim ya hura iska mai dumi daga bakinsa yana jin wani yanayi na sanyin AC yana ratsa shi tamkar zazzaɓi yake ji, sai ya juya ya gyara zamansa yana jiran ta fita daga motar ya ja, amma sai ya tsinkayi muryanta tana cewa. Ba sai ka bani lokaci ba domin na amince da aurenka, fatanmu Allah yasa hakan ya zama alkhairi a garemu. Kayi haƙuri da yanayi na yau bana jin dadi ne, idan kaje gida ka gaida mini da Hajiya da kowa sai da safe. Ta ƙare maganar tana yunƙurawa zata fito daga motar, da Sauri Ibrahim ya buɗe ya riga fitowa ya isa inda take zaune ya tsaya a jikin ƙofa yana dubanta, itama miƙewa tayi ta tsaya suna kallon juna, Ibrahim ya saki miskilin murmushi. Kina son aurena kika yi da fuska kamar kinga mutuwa, bai kamata matar Ibrahim ta kasance a haka ba. Kaifa kace baka son mutane susan kaine a nan, ya kamata ka bani hanya na wuce ka koma cikin mota, Sameeha kowa ma ya ganni in dai dake nake a tare bani da damuwar komai, yanzu dai ki saki fuskarki kuma ki gaya mini me yasa ki fidda kwalla. Hmmm ka bani hanya na wuce. Ibrahim sai ya matso gabda ita kamar zaiyi kisin ɗinta, sai tayi baya da sauri ta zauna daɓar a seat, sai ya koma ya risina yana cewa. Hawayen zan goge miki dan akwai sauran damshinsa a fuskarki, kar ki shiga gida ace na bigeki daga zuwa hira kija mini Yaya Zaidu yace ya fasa bani ke. Wannan karan murmushi tayi tana cewa. Tunda nace naji na gani ba wanda zai hana maka ni. Allah da gaske kike yi? In dai haka ne zo ki shiga gida. Amma dai duk in kina cikin tunanin wani abu ki tuna ni Ibrahim Khalil ina sonki ina kaunar kasancewa dake. Yana gama faɗar haka ya matsa ya buɗe mota ya shiga ya kunna, Sameeha ta fito ta rufe masa ƙofar ta tsaya jikin tagarsa tana dan murmushi. Allah ya tsare hanya ya huta gajiya. Amin matar Khalil ki ɗaure ki aje number na a wayarki, kuma inna kira a ɗauka kinji ranki yadade. Ya ƙare maganar yana yi mata jinjina da babban yatsarsa na hannu, sai da ta saki murmushi kana ta juya ta soma tafiya, har ta kusa shiga gida taji ya kira sunanta ta juyo sai ya lumshe mata ido ya buɗe yana sakin kayataccen murmushi, bata san sadda ta mayar masa da murmushin ba kana ya ja mota ya wuce ita kuma ta shiga gida. Sosai Ibrahim ya soma tasiri a zuciyarta, bata taɓa zaton zai kasance mai sauƙi har haka ba, lokaci guda ya yaye mata damuwar Aminu wanda hakan yasa ta shiga gida fuska sake, ko da su Umma suka ganta haka ba wanda ya tambayeta domin sun san dalili, haka ta kwana tana tuna Ibrahim da magnganunsa wanda In ta tuna Aminu sai ta ji ba wani ɓacin rai sosai da take ji kamar ɗazun, Ibrahim ya maye mata gurbin damuwarta, a karo na biyu tana jin sata sake bawa soyayya dama domin ta ƙara kwankwaɗar zaƙinta, dan ga dukkan alamu Ibrahim wayayye ne kuma ɗan zamani, wataƙila ma yafi Aminu iya wasu abubuwan, musamman fannin nuna soyayya a zahiri. ***** Tum daga wannan ranar Ibrahim ya cigaba da kafa gwamnatinsa a zuciyar Sameeha, tun tana noƙewa har ta soma sakin jiki dashi suna hira, sai dai sunfi yin waya saboda baya zama, a hankali Sameeha ta yakice damuwar Aminu ta fuskanci gaskiya, kuma tun ranar daya kira bai kuma kiranta ba sai dai waya da take yi da yaranta, sannan ta zage sunata shirye shirye duk da ba wani shagali zasu yi ba saboda ita bata ƙaunar bidi'a Umma ma tace ba zasu yi komai dan albarkan aure take buƙata. Shamsu kuwa ya gama samun zuciyar Ikram, sosai yake samun damar zuwa hira kuma bata taɓa jin ta gaji da ganinsa ba dan ta kamu da sonsa na bazata, gabaɗaya ko wani ɓangare shiri suke na biki. Itama Nabila tanata nata shirin saboda tunda taje gurin malamin da Shema'u ta rakata ya yanko mata maƙudan kuɗi tace ba zata iya ba, dan bata yarda tayi asarar kuɗi ba tunda ta samu labarin an gama maganar aure biki ya rage, a kan haka saida suka yi faɗa da Shema'u kan ta bata kunya a gun malam, daga baya ne suka shirya ta cigaba da sabgoginta, domin Ibrahim miliyan biyar ya tura mata akan ta ƙara jali sannan ya ce ta faɗi kuɗin da zata haɗawa kanta a kwati, tace miliyan shida shima bai musa ba ya bata dan a zauna lafiya tunda bata nima ɗaga masa hankali ba, hakan yasa taji aurensa ma bai wani dameta ba tunda ya bata wannan kuɗin, ita kuɗi sune rayuwarta bata yarda tana wasa da su ba, shiyasa sam bata bin malamai a ganinta asara zata yi, tunda gashi bata je gunsu niman sa'a ba amma tana samu kasuwanta yana bunƙasa. Najwa kuwa danne duk baƙin cikinta tayi ta shiga jikinsu Sameeha dan ayi biki da ita taga duk abinda suke shiryawa, tun Ikram bata sake mata ba har ta mance komai suka cigaba da hidimarsu, duk da a gun Najwa na ciki na ciki. ***** Biki saura kwana biyar. A ranar ne aka kawo akwatin su Sameeha wanda set bibbiyu ne, set na farko guda biyar da kit, na biyu kuma uku da kit, babu bambanci a kayan da aka zuba sai zinarin Sameeha da yafi na Ikram tsada, da kuma key motarta da aka saka yafi na Ikram ɗin, gida ya cika da 'yan uwa ana kallon kayan arziki bayan dan ginsu ango sun tafi, Khairy dai tana nan maƙale da Sameeha dan kusan tafi zuwa gidan akan can gidansu. Najwa kamar zata haɗiye rai dan baƙin ciki, jikinta har wani ɗumi ya ɗauka ta kasa tsayuwa sai ta zauna tana kallo yadda ake ɗaga kayan arziki, Inna Rakiya kanwar Umma tace. Ni wlh nama kasa magana da ganin waɗannan kaya, ina ganin mijin Sameeha yafi na Ikram kuɗi dan wlh sarƙar zinarinta tafi tsada nesa ba kusa ba, ga motar ma sun faɗa. Wai yaya wani miji ne Sameeha ta samu haka? Kunga fa manyan leshi da atamfa da iya ganinka baka san ya zaka daɗi kuɗinsu ba, jama'a ban taɓa ganin akwati haka ba wlh tunda nazo duniya, ko aurenta na farko wane da wannan kaya. Nan fa kowa ya shiga faɗar albarkacin bakinsa ana ta yaba kaya, umma dai dariya take ta yi ta kasa rufe baki, innar Najwa tace. Wannan yara ai sunyi goshi suna da ƙashin arziki Allah ya basu, ita Sameeha ta bar gidan kuɗi ta ƙara faɗawa gidan daya fi na baya ma, dan ganin kayan nan ya nuna babban mai arziki ta samu, Ita kuma Ikram ta faɗa gidan sarauta wanda ko a mafarki bamu taɓa zaton haɗa jibi da mulki ba. Kai Alhamdulillahi haihuwa tayi mana rana, ina ma ace yaya yana raye yaga wannan ranar farin ciki haka, Allah ya jikanka yaya Amadu, bayanka tayi kyau wlh. Ta ƙare maganar tana matsar kukan farin ciki, haka dai kowa yake faɗar albarkacin bakinsa, Najwa kuma tana ƙara shiga tashin hankali na baƙin ciki kamar ta haɗiye rai ta mutu, bata iya jurewa ba ta miƙe ta fice ba tare da an kula da ita ba, ta tari napep ya wuce da ita tana matsar kwalla dan sosai taji baƙin ciki da ƙunci ganin akwatinan su Ikram, bata taɓa zaton zasu kai haka ba, yanzu ne take ƙara raina kanta dan tabbas darajar raƙumi yayi nesa da ƙasa, sun yi mata fincinkau a komai, dan tasan wlh Aminu bai da kuɗin da zai yi mata irin wannan kayan, saboda a cikin arzikinsa da zuciyarta take hasashe bai kama ƙafar mazajen su Sameeha ba, ji take kamar tsiya da talauci a kanta a ka ƙare, sam bata taɓa samun saurayi mai mugun kuɗi ba sai dai 'yan kuci ku bani, ita dai tana ganin kyanta bai amfaneta da komai dan da kyau zai jawo mata arziki da sai ta auri mijin daya taka na su Ikram, amma sai gashi ta ɓige da auren mijin da Sameeha ta bari bisa cin amana, wanda ma bata da yaƙinin zaman auren zai yi mata daɗi, haka ta dinga share hawaye tamkar wacce aka yiwa mutuwa. *Duk wacce ta karanta mini littafi bata biya ba, ta sani ta karanta da hakkina kuma In Sha Allah sai Allah ya saka mini.* [7/7, 13:04] Buhainat😁: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shai wanidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.* 36. Najwa gidansu Nafeesa ta wuce, ko da ta isa ta samu suna shirin zuwa dinner ɗin wata 'yar kanwar Hajiyarsu, amma a yadda Nafeesan ta ganta yasa ta jata ɗakinta suka zauna gefen gado tana dafa kafadar Najwa. Meke faruwa ƙawata? Na ganki a hargitse ne kamar kin gamu da abin furgici. Su Sameeha sun fini komai Nafeesa banda abinda zan yi gogayya dasu domin duk mazajansu sunfi Amunu da komai, akwatinansu abin kallo ne wanda ya gigita lissafina da tunanina nasan ni ban zo duniya a sa'a ba, komai nice ƙarshen baya ina ganin har na mutu bazan taka matsayin da nake buri ba a rayuwata ba. Nan ta kwashe labarin akwati ta faɗa mata komai da idonta suka gani, tana faɗi tana kuka hawaye shaɓe shaɓe. Sai da takai aya kafin Nafeesa ta ja numfashi ta sauke a hankali tana cewa. To sai me dan anyi musu kaya haka? Dama dole ki saka a ranki zasu samu haka domin kuɗin sadakinsu kawai ya nuna akwatinsu zai zo da kaya irin wannan, bana so kina saka damuwar su fiki kowa fa da arzikinsa, ina ce kema kin samu cikar burinki na auren Aminu, wanda shima ba talaka bane yana da kuɗi sosai, na tabbatar hatta motar hawa zaki samu a gidansa, kuma dama babu yadda za ayi kice komai daidai zaki samu dasu Sameeha domin yatsun nannunmu ma ba ɗaya bane, dan haka ki cire komai a ranki tunda kema ba talakan zaki aura ba. Amma Nafeesa duk yadda naso ba haka nake samu ba, bana so ko kaɗan su fini jin daɗi a gidan miji, burina kafin aga wani abu mai kyau da tsada a hannun 'yan danginmu an fara gani a hannuna, a kullun burina na kasance sama da kowa, sai dai burina ba zai cika ba tunda su Sameeha sun zama zakaran gwajin dafi, akomai suke fara tare mini hanya su rigani isa kafin na kai. Ni bikin ma bazan sake zuwa ba suyi kayansu dan kar baƙin ciki ya kashe ni a banza. . Aiko baki isa kice ba zaki je ba, in ba haka ba da wuri zasu gano kina musu hassada, gwara ki shiga a dama dake ta yadda zaki yi ƙoƙarin ganin abubuwa kema ki tsara aurenki da yadda zaki zauna a gidanki yafi nasu, idan fa kina so ki fisu to dole sai kin riƙa binsu kina shige musu tare da sanin duk halin da suke ciki, ta hakane zaki gina naki rayuwar yadda kike muradi, dan haka nima zan shiga bikin a dama dani dan na riƙa ƙara miki karfin guiwa, bana so ki sare akan cikar burinki. Allah ko Nafeesa? kina ganin hakan za mu yi? Sosai ma kuwa, yanzu ma tashi zaki yi ki wanke fuska na ara miki kayana ki raka ni dinner ɗin 'yar uwarmu kiga yadda ake shagalin masu kuɗi, shima wani darasin zaki ɗauka. Da sauri Najwa ta miƙe tana murmuahin jin daɗi, nan da nan ta sake ta watsar da damuwar su Ikram ta shiga shirin zuwa dinner dan duk abinda zai sa ta samu ilimi akan harkan kuɗi ba zata yi ƙasa a guiwa ba. Nafeesa tana ganin Najwa tana shiga bayi ta ɗauki wayarta dan ta san code ɗin buɗewa, ta ɗauki Number ɗin Aminu tayi saving a wayarta da suna Amina. Tun sanda Najwa take bata labarin Aminu yana kulata sosai yanzu har waya suke yi suna hira ya sake mata fuska, sai dai haɗuwa ce basu yi ba kuma yana tura mata kuɗi akai akai, Najwan tana nuna mata farin cikinta da samuwar kwanciyar hankalinta, har take cewa ko dan yaji Sameeha zata yi aure be shiyasa ya sake mata yanzu ya haƙura, to ita kuma Nafeesa ta samu matsala da wanda zai aureta gashi ba tada wani tsayayye, sai ta soma jin damuwa akan auren da Najwa zata yi ta rigata, ga kuma yanzu Aminu yana sake mata suna hira a waya ga kuɗi da yake yawan tura mata, shi kuma yayi hakane domin ya saba da ita dan sosai ya ɗauki kudurin gyara alaƙarsu yayi zaman aure da gaskiya da ita, saɓanin da daya ɗauki alwashin kin amsarta domin ya muzgunawa Hauwa, amma dalilin auren Sameeha yasa zai karɓeta domin ya huce takaici. Nafeesa ta yi tunani kala kala domin taga hanyar da zata lalata auren Najwa a fasa kamar yadda ta rasa saurayinta, sai ta fara hangen ko ta tonawa Najwa asiri Aminu yasan wacece, sai kuma daga baya taga ko ta tona ba lallai yayi tasiri ba tunda Hauwa tana bala'in son aurensu kuma ta san Hauwa zata iya komai ganin anyi auren, hakan yasa ta sake tunani akan ta ɗauki Number ɗinsa ta ja ra'ayinsa su fara soyayya, in yaƙi bada ƙofa ta shiga malamai ta samo kansa itama ya aureta, idan Najwa ta samu labari ta nima kawo mata wargi tayi mata barazanar tona mata asiri akan sharrin lesbian da ta ƙullawa Sameeha wanda tasan in Aminu yasan da haka dole ya rabu da ita, dan haka tasan ba zata yarda asirinta ya tonu ba zata yarda su zauna suci arziki tare, tunawa da wannan plan ɗin nata yasa ta saki wani shu'umin murmushi dan kuwa har hotonsa ta tura kwanaki a wayarta, dan itama ta kamu da sonsa na farad ɗaya tunda Aminu yana da kyau ga kuɗi baida makusa, dama namiji mai kyau haka mata suke rububi akansa sai wanda Allah ya tsallake ne baya faɗawa zina. Najwa koda ta fito shiryawa tayi sauri sauri a lokacin ana kiran sallar magrib amma saboda azalzala mata da Nafeesa tayi basu tsaya yin sallar ba suka tafi, a hanyarsu ne Inna ta kirata akan tana ta jira ta dawo daga inda taje su koma gida, nan Najwa take faɗa mata taje bikin wata 'yar ajinsu da ake dinner amma ba jimawa zata dawo, haka inna ta baro gidansu Sameeha tanata faɗan jiranta data tsaya yi ashe tayi gaban kanta, zuwa yanzu ta soma damuwa da sauyawar halayyar Najwa, ada tana jin magana da gudun ɓacin ranta amma yanzu komai yin gaban kanta take yi bata tsayawa niman izininta ko shawararta, sai take ganin ko dan auren da zata yi ne ya fara sauyata da tunanin haka ta isa gida. Najwa ko da suka isa gurin dinner Nafeesa sai ƙara kwantar mata da hankali take yi akan karta saka damuwar su Sameeha, dalilin daya saka Najwa ta ƙara samun natsuwa na sakin jiki suka sha hidimar dinner, wanda sai sai wajen goma na dare ta dawo gida. Ba ƙaramin fada Inna tayi mata ba, dan ma ta rufa mata asiri tace tana gidansu Sameeha ne, da ƙila Baba sai ya kusa dukanta, a ɗaki ta sameta tayi mata faɗa sosai, Najwa ta ɓata rai tana turo baki. Haba inna tare nake da Nafeesa fa kuma kin san duk inda zanje bazan taɓa yarda na ci amanarku ba, kuma nasan da maganar auren wani a kaina. Ni dai inna na kula kin gaji da ganina a gidan nan to  In Sha Allah nan da wata biyu zan bar miki gidan sai kin dawo kina kewata. Ni kike faɗawa haka ko? kin kyauta Najwa. Inna ta faɗa rai ɓace sai ta wuce ta fita, Najwa ta bita da cewa. Nifa gaskiya na faɗa miki, amma kiyi haƙuri naga ranki ya ɓaci. Inna bata tanka mata ba ta wuce zuciyarta tana yi mata suya, damuwarta yadda lamarin Najwa ke ƙara yin gaba, tsoronta kar taje gidan miji tana yi masa rashin ɗa'a ya gaji ya korota, dan yadda take fitar da magana bata taunata to ba ko wani namiji ne zai ɗauka ba, Addu'ar shiriya tayi mata ta shiga ɗaki ta kwanta. *** Kamar yadda Nafeesa ta tsara musu hakan ya faru dan washe gari da rana ta zo gidanau Najwa suka je gidansu Sameeha dan a cigaba da shagali tare dasu, koda Najwa ta gabatar musu da Nafeesa sun karɓeta dan dama ba wasu ƙawaye garesu ba har gwara Ikram, Najwa ta saka aka buɗe musu akwati suka gani, ita kanta Nafeesa sai da ta gigice bata ga laifin Najwa ba jiya da ta rikice tana fidda kuka, ashe gani ya kori ji, duk da ta fito gidan kuɗi kuma tana ganin manyan akwati na 'yan uwansu bata taɓa cin karo da wannan ba, ba a zuba kayan rashin hankali ba amma fa an zuba masu tsada sosai, ji tayi inama ace zata samu ɗaya daga cikin angwayen su so ta koda a ta biyu ko ta uku ta shiga, sai dai so ba samu bane, haka aka rufe akwati sunata santi tare da zuzuta shi, Ikram dai ko a jikinta dan ba su kaɗai bane suka yi wannan santin, Ita Sameeha tana ɗaki ana yi mata gyaran jiki da Khairy takawo musu har gida ake yi musu, kayan kuma suna ɗakin yaya Zaidu an rufe su. A hankali aka cigaba da shiri Najwa tana ƙara shige musu dan ana saura wana biyu biki ta tattaro kayanta ta dawo gidan tana kwana, ita kuma Nafeesa kullun sai tazo sai yamma lis take komawa gida dan ta sawa kanta sai taga ƙarshen wannan hidima, duk yadda Najwa taso ta san su waye zasu aura bata samu dama ba dan Shamsu tunda aka kawo akwati bai sake zuwa hira ba sai waya, ita dama Sameeha sun fi yin waya saboda baya zama, sunayensu kawai ta sani da Ikram ta faɗa mata, har tana cewa ta taɓa saurayi mai suna Shamsu ta koreshi saboda baƙi ne mummuna, Ikram tace ai dama ta santa da ruwan ido Allah yasa wanda zai aureta mai kyau ne, nan ta shiga zuzuta Aminu tana cewa fari yake tas ɗan fillo son kowa ƙin wanda ya rasa, haka dai suka dinga hira wanda itama har gyaran fuska anyi mata tare da wanke kai da kunshin lalle baƙi da ja, ta fito tayi fes itama kamar amarya. ****** Ranar ɗaurin aure. Faɗar kyawun da su Sameeha suka yi ɓata lokaci ne, domin wani tsadadden leshi suka saka su uku anko, umma da Sameeha ɗinkin doguwar riga buba, Ikram aka yi mata riga da siket saboda tace tafi son shi, musamman Khairy ta kawo mai makeup aka yi musu, sai zuba ƙamshi suke gwanin ban sha'awa, su Najwa ma sun saka anko tare da yin kwanliya sunyi kyau, Nafeesa kuma da bata samu anko ba ta saka atamfarta me kyau tasha kwalliya itama. Wajen ƙarfe goma sai ga su Hauwa, Laure, Sa'a da kuma ƙanwarsu Salma, sai 'yar Hauwa Adama data ce zata zo ta bawa ido abinci, dan har gida Zaidu ya kai musu katin gayyata da Umma tace akai musu saboda 'ya'yan Sameeha da suka haɗasu zumunci, koda suka shigo suna yatsine fuska Hauwa da Laure, ba wanda ya kula da su, su inna suka basu masauki a cikin tampol aka karramasu da abinci da nama zuƙu zuƙu a ciki dan kula guda aka basu da plate ɗin da zasu zuba, sai abin sha ruwan gora da kuma drinks, babu kunya suka buɗe ciki suka ci suka koshi, Hauwa har da cewa zata juye saura a leda ta tafi dashi gida dan dama ta yi alkawarin ɗibar abinci in ta samu da damar haka tunda ba kunya ce da ita ba, lokacin da su Sameeha suka fito har gunsu taje ta gaidasu suka amsa faran faran tare da taya ta murna, Adama da biyu tazo domin ta samu damar gayawa Sameeha baƙaƙen magana, amma yadda suka ganta tayi mugun haɗuwa ta sauya a Sameehar da suka sani yasa tayi musu kwarjini sosai, dan ta cika musu ido wanda a zahiri sun san tafi ƙarfin lissafinsu a yanzu, sai suka koma suna borin kunya tare da amsa maganarta cikin sauri kamar mai yi musu umarni, data gama dasu ta wuce ta koma inda take zaune dan ance zasu zauna guri ɗaya har sai an ɗaura aure, suna hango Ikram amma bata zo gunsu ba dan ba tasu take ba, Najwa kuwa tazo ta kwashi gaisuwa kamar dai irin sanin da ne data yi musu bata wani sake ba dan kar a gano wani abu, suna gaisawa ta wuce cikin gida. Da yake ɗaurin auren safe ne tunda ya kama ranar asabar, ƙarfe sha ɗaya da minti goma aka ɗaura auren anan ƙofar gidansu wanda aka zuba tempol da kujeru waje da cikin gida, mutane sun zo wannan biki dan unguwar Rafin Guza a ranar sai da suka tabbatar da ana biki, saboda tarin mutane da manyan 'yan siyasa dama manyan motoci da Sarakuna, dan hatta Sarkin Zazzau ya halarci ɗaurin aure da gomna Kaduna mai ci a yanzu, faɗan yawan security ba a magana domin unguwar gabaɗaya aka zuba su tun daga farkon shigowa Rafin Guza har can ciki, kuma masu shigowa sai an duba motarsu dama mutanen da suke ciki, lamarin yayi matuƙar gigita tunanin al'umma dan babu wanda yayi zaton irin wannan ɗaurin aure. Bayan an ɗaura auren Sameeha da Ibrahim aka ɗaura na Ikram da Shamsu, a hankali mutane suka fara tafiya masaukinsu domin yin walimar da Ibrahim ya shirya musu a gidansa dake unguwar rimi, hatta sarki ya tafi can dan Ibrahim ya hana su tafi da sauran abokansa na 'yan siyasa, Gomna ne dai ya tafi saboda babban uzuri dake gabansa, bayan mutane sun ragu sai ga Zaidu ya shigo yana cewa Angwaye zasu shigo gaisuwar iyaye yanzu a gyara, hakan yasa mata duk suka kame gefe guda aka bar musu babbar tabarma dake shinfiɗe a tsakar gida, saura kuma suna rumfa a zaune a kujeru. Maroƙa ne da masu busa sarewa sune suka fara shigowa gidan suna busa sarewa wanda yake nuni da sarauta, sai maroƙa da suke nasu fadancin, Shamsu shine farkon shigowa fadawa suna zagaye dashi maroƙa suna yi masa kirari. Taka Lafiya Shamsuddeen jikan wazarin Zazzau ɗan Wazarin Zazzauna, mulki a jininka take miji a gurin Ikram diyan Amadu da Halimatu Allah ya jikan Amadu domin kayi farar Haihuwa 'yarka ta dangwalo muku arziki wanda zai riƙa binku har 'ya'ya da jikoki. Takawarka lafiya mai girma Senator Ibrahim Ali Turaki jikan Limamin Zazzau, ga ilimi ga nasaba, Allah ya ja kwananka ya ƙara lafiya ya kuma saka albarka a cikin wannan auren naku. Wani daga cikin maroƙa yake jero nasa wannan kirari lokacin da Ibrahim shigo tare da securty ɗinta, nan fa kallo ya koma sama mata suka rikice kowa yana mamakin ganin Senator Ibrahim a cikin gidan, su Hauwa sai miƙewa suka yi suka zo suka tsaya dan tabbatar da abinda kunnensu yaji. Su Shamsu zama suka yi a tabarma Umma ta fito sanye dq hijab da sauran 'yan uwa da ƙawaye suka gaisa kana fa suka koma ciki, sai su Shamsi suka miƙe zasu wuce maroƙa suna ta kirari tare da ambato matsayin angwaye, a lokacin ne Khairy ta riƙo hamnun Sameeha suka fito daga dakin umma, Ikram tana a bayansu tare da Najwa da sauran ƙawayensu, Khairy ta ƙarasa da su gurin angwaye tana cewa. Yaya ku tsaya ayi muku hotunan tarihi. Sai ta kara Sameeha gefensa tana cewa mai hoto ya ɗauka, nan fa gida ta ƙara hargitsewa ganin Sanator Ibrahim shine angon Sameeha, su Hauwa suman tsaye suka yi suna rarraba ido, sosai suka tsorata da razanar ganin wannan lamari, Najwa kuwa gigicewa tayi ta tsaya tana kallonsu ana yi musu hoto jikinta har rawa yake saboda mamaki da tsoro, bata ƙara kurɓan gubar mamaki ba sai da taga an kara Ikram jikin Shamsu da har ta mutu ba zata mance fuskarsa ba yadda ta tsane shi saboda baƙinsa, wasu taurari suka soma gilmawa ganinta numfashim ya soma fita da kyar jikinta ya shiga kakkarwa, ga wani tururin zafi daya gewaye illahirin jikinta, dan sosai taji numfashi mai zafi take shaƙa ta fitar, sunan tsaye tayi dan kwakwalwarta lokaci guda ya daina aiki, har aka gama hotunan suka wuce ta nan a tsaye bata san wainar da ake toyawa ba, mutane kowa sai sambarka suke yi suna yaba wannan daraja da su Sameeha suka samu kamsu a ciki lokaci guda, su Hauwa kuwa giuwa sake suka koma mazauninsu suna mayar da numfashi, dan sosai suka yi mugun kaɗuwa da mazajen su Sameeha, hakan ya tabbatar da Sameeha ta take darajarsu ta shanye, yanzu sai dai su zama almajiranta ko 'yan koronta amma tafi ƙarfinsu, tayi musu nisa da tazarar da babu dawowa wanda dole ne a cewa mijin iya baba, dole su kwashi tsummar kunyarsu su ƙara gaba dan ko kallon banza basu isa su yiwa Sameeha ba in ba haka ba suna yin wata wargi zasu kwashi kashinsu a hannu. Najwa kuwa bata dawo hayyacinta ba sai da Nafeesa ta kamo hannunta ta kiran sunanta da cewa. Najwa Najwa! Jin bata motsaba yasa ta jijjigata sai taga ta biyota luuuu ta faɗa jikinta wanda ya tabbatar mata da a sume take. *Duk wacce ta karanta mini littafi bata biya ba, ta sani ta karanta da hakkina kuma In Sha Allah sai Allah ya saka mini.* [7/7, 13:04] Buhainat😁: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shai wanidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.* 37. Nafeesa cikin dabara ta kamata ta jata zuwa wajen bayi da yake kamar lungu, ta shiga jijjigata tana kiran sumanta a firgice, da kyar Najwa tayi yaƙi da numfashinta ta fizgoshi da ƙarfi ya dawo jikinta, sai ta sauke anjiyar zuciya mai nauyi, nan take kuma jini ya soma fitowa daga hancinta yana gangarowa, jikinta ya mutu sosai yana rawa ta kasa tsayawa, sai ta kama hannun Nafeeda ta tsuguna tana fidda numfashi da ƙarfi dan a riƙe yake, Nafeesa itama tsuguwa tayi tana cewa. Najwa kashe kanki za kiyi ne akansu? wlh ki dawo hayyacinki dan kema baki wuce ki ganki a matsayinsu ba, kar ki bari a gane halin da kike ciki ki jawa kanki magana dan Allah. Nafeesa! Nafessaaa ba ba mijin Sameeha bane kaɗai ya girgizani, saurayina Shamsu shine angon Ikram, ban zata yana da arziki ba, ban ɗauka daga gidan sarauta yake ba, ya ɓoye mini komai saboda in zai zo hira gidanmu wlh bada mota yake zuwa ba, baƙin fatarsa yasa nake ganin muninsa har yasa na koreshi, na zalunci kaina na yiwa kaina illa yanzu dani ne a matsayin Ikram, shikenan ni banda sa'a, ashe arziki yana tare dani na guje masa. Ta ƙare maganar cikin gunjin kuka mai tsanani wanda yasa Nafeesa ta toshe mata baki, dan itama maganar Najwa ya taɓa ta, yanzu take tuna Shamsu da take bata labarinsa, ashe shine mijim Ikram, lallai dara taci gida ba aje ko ina ba Najwa ta fara karɓan sakamako, ta raba Sameeha da mijinta gashi saurayin data wulaƙanta akan talaka ne Ikram ta aureshi kuma ɗan masu kuɗi gidan sarauta, sannan ga Sameeha tana auren Senator, wato dai hassada ga mai rabo taki, ta raba ta da mijinta akan ita ta shiga ta kwashi arziki sai ga Sameeha ta samu wanda ya fishi komai, har abada bata jin Najwa zata kama ƙafar Ikram balle ma Sameeha, ta sauke guntun numfashi daga zancen zuci da ta yi ta kalli Najwa tana cewa. Yanzu tashi za kiyi mu fita daga gidan nan, amma karki yarda a gane halin da kike ciki kuma ki ɓoye zancen Shamsu saurayinki dan karki tada wani ƙura, muje gidanku muyi magana cikin natsuwa. Gyaɗa kai Najwa tayi saboda zafin da zuciyarta ke yi mata ba zata iya magana ba, Nafeesa ta ɗauko mata buta dake bakin famfo ta kawo ta wanke fuskarta kana ta goge da gefen mayafin data yafa, dan musamman ta saya mayafin da zata ci biki duk da ba sakawa take yi ba, amma ganin bikin nasu ne kuma na masu kuɗi dole ta koyi shigarsu kamar yadda Nafeesa ta bata shawara, sai ta miƙe tana dafe bango Nafeesa ta gyara mazaunin gyalenta tana cewa zata ɗauko jakukunansu ta dawo, to Najwa tace kana ta cigaba da tsayuwa har Nafisa ta dawo ta kama hannunta suka fita, da yake gidan ya cika da mutane babu wanda ya kula da su har suka fita. Abin hawa Nafeesa ta samar musu suka wuce gidansu Najwa. Koda suka isa sun samu ba kowa a gidan dan ɗakunan a rufe suke ƙofar gidan ne yake a buɗe an jawo shi, Nafeesa ta ɗauki keyn ɗakin Najwa a jakarta ta buɗe ɗakinta suka shiga, Najwa ta faɗa gado dan sosai take jin jikinta ba ƙarfi tama buƙatar hutawa, ga tarin baƙin ciki goma da ashirin saboda tasan ta yiwa kanta mugunta, duk da Shamsu shi ya ɓoye mata asalinsa, amma da bata sanya son zuciya ba a lamarinta da yanzu shine mijinta, ko banza zata yi gogayya da Sameeha, Nafeesa ta fita can waje ta sayo musu ruwan sanyi a wani shago ta dawo ta bawa Najwa ta amsa ba musu ta tashi ta zauna tasha, sai dai ta aje leda dan duka ta shanye ta kalli Nafeesa tana cewa cikin rauni. Yanzu miye abinyi Nafeesa, Abun da ciwo inna tuna nice na yiwa kaina, na ɓata goma biyar bata gyaru ba, ina jin ƙunci a zuciyata kamar na hada Sameeha da Ikram na cinna musu wuta su mutu kowa ya huta, gabaɗaya sune suka tare mini hanyar cigaba na. Najwa sunyi miki fincinkau kima aje batunsu a gefe ki fuskanci gaba, dan yanzu ba ki da yadda zaki ki ja dasu, Aminun dai da kika samu ki kama shi hannu biyu dan shima ma ba baya ba da arzikinsa, kuma gabaɗaya yafi mazajen su Ikram kyau kuɗi kawai zasu nuna masa, kinga kina da miji na shiga taro wanda zaki kece raini, zan iya cewa duk ƙawayenmu babu wacce take da saurayi kamar naki, ko ba komai kina da tudun dafawa, kin fini ni da ba ni da kowa yanzu tunda na rabu da Hamis. Nafeesa ta kai aya a maganarta tana kallon Najwa wacce ta zuba uban tagumi, sauke numfashi tayi domin duk maganar Nafeesa gaskiya ce kuma ta gamsu sosai wanda yasa tace. Shikenan zan haƙura da komai na kama Aminu hannu biyu, amma bazan iya ƙarasa wannan bikin ba dan kar zuciyata ta buga. Bayan biki zanje naga ɗakunansu daga nan kuma munyi hannu riga. Ina wlh baki isa ba ai dole ki ɗaure a ƙarasa dake kiga yadda aka tsara gidajensu kema kisa a tsara naki haka. Bazan iya cigaba da bin lamarinsu ba dan ban'bu abinda zai haifar mini illa ciwon zuciya, ki rabu dani kawai Nafeesa na fuskanci gaskiya, na yarda sun fini kuma ba zan ƙara ja da haka ba zan yi daidai rayuwar da Allah ya zaɓar mini, damuwata duk randa Aminu ya san ni ya aura bansan ya zamu kwashe ba. Najwa ko zamu koma gurin malamin nan da Binafa ta kaimu sai ayi miki aiki akansa koda ya ganki ya kasa rabuwa dake. Bazan je ba domin wancen aikin dana bashi bana tunanin yayi, har takalmin Sameeha na kai masa sai gashi ta auri mijin daya fi na baya. To ai ba akan haka kika saka yayi miki aiki ba, akan Aminu kika ce ayi aikin kuma baga shi kin samu nasara ba tunda yana kulaki kuna hira har kyautuka yake yi miki, ki zauna kiyi tunani dan wlh ina jiye miki ɓacin rana, duk da kince Hauwa zata yi miki aiki akai kema ya kamata ki yiwa kanki tanadi. Kin san tunanin daya faɗo mini yanzu? Najwa ta faɗa tana ɗan murmushi, Nafeesa tace. Sai kin faɗa. Nafeesa babu abinda zanyi, idan ma yana ganina ya sake ni bazan damu ba domin yanzu Shamsu ne a tunanina, na ɗana arzikin gidan Aminu to ina da buƙatar ɗana gidan Sarauta, Shamsu ni ya fara so a rashina ne ya auri Ikram, na tabbatar in ya ƙara samun dama ta biyu a guna zai saurare ni. Wani irin kallo Nafeesa takewa Najwa wanda yake ƙunshe da tarin magana, Najwa ta muskuta tana cewa. Yadda na samu galaba akan raba Sameeha da Amunu ba tare da tayi mini komai ba, to tabbas sai na shaga tsakanin Shamsu sa Ikram tunda ta yi kokarin shiga gonata, domin ni ya fara so ta zo ta aureshi. Taya zaki hukuntata da abinda bata sani ba? na tabbatar bata san saurayinki bane shi, Najwa ki tsaida tunanin ki guri ɗaya ki tsaya a auren Aminu kawai. Nafeesa ko bazan auri Shamsu ba wlh sai na saka Ikram ta shiga ƙunci, idan banyi haka ba bazan samu sassauci a zuciyata ba. Kallonta kawai Nafeesa take yi dan ta kasa cewa komai saboda tsantsar mamakin Najwa, ta kula ba hassada kaɗai ke damunta dasu Sameeha ba har da mugunta da keta, ganin wanda yayi nisa baya jin kira yasa ta miƙe tana cewa. Ni zan koma gidanmu tunda kin ce ba zakin koma gidan bikin ba, sai bayan kwana biyu. Allah ya kaimu sai ta kwanta dan bata jin zata iya yi mata rakiya, Nafeesa ta fice tana mamakin Najwa da irin mugun tunaninta, ta rasa me su Sameeha suka yi mata da suka cancanci wannan ƙiyayya, gashi basu san tana yi ba kuma su sai nasara suke samu, a wannan karan ji tayi bata fata Najwa ta samu nasara akan abinda tace zata yiwa Ikram, tace a cikin ranta. Nima zan bi sahunki ya saka takalmi irin naki na yi miki cindunduniya kamar yadda kika yiwa wasu, nima na rama musu, dan Ins' Sha Allah nima sai na auri Aminu. Tayi maganar tana murmushi ta wuce zuwa bakin titi ta samu napep ta wuce gida. ****** Can gidan biki an cigaba da shagali kowa yanata hada hada ga ɗaukar hotuna da ake ta yi, amare suna shiga suna sauyawa gwanin sha'awa har zuwa bayan sallar la'asar, lokacin ne su Salma suka yiwa Sameeha sallama akan zasu wuce amma Hauwa da Laure sunce zasu je kai amarya ba dan komai ba sai dan su samu damar tariwo gulma yadda zasu ji daɗin bada labari, suga kuma irin daular da Sameeha ta samu, Sa'a dai tabi Salma da Adama dan tasan halin mijinta Kamalu bayi da sauki. Sameeha har cikin zuciyarta taji daɗin yadda su Hauwa suka muna mata kara duk da tasan da biyu zasu je kaita amma tasan sai dai su ga abinda zai damesu dan na gaba yayi gaba. Ikram tana zaune da ƙawayenta a ɗakin kusa dana Zaidu ta idar da salla suna hira, sai taji saƙo ya shigo wayarta, tana dubawa taga baƙuwar Number ta shiga wajen massage ta soma karanta saƙon kamar haka. Amarya bakya laifi, ina taya ki murnan Auren Shamsu sai dai ba nan gizo ke saƙa ba domin kuwa ina ɗauke da cikinsa na wata biyar daya ƙunsa mini ya gudu ya barni, a gunku mutumin kirki ne shi amma tantirin mazinaci ne na nunawa sa'a, idan kuma baki yarda ba ni ina da hujja, kisha amarci lafiya tare da baban ɗan shege ko shegiya. Wani irin gumi ne ya shiga karyowa Ikram innalillahi kawai take ambata a zuciyarta, da kyar tayi yaƙi da zuciyarta ta aro jarumta ta miƙe da sauri, wata ƙawarta tana cewa. Lafiya Ikram waye yayi miki saƙo? ko Aliyu ne ya tono miki da tsohuwar soyayya. Yaƙe tayi mata kawai tace eh, sai ta fice daga ɗakin saye da hijab ɗin data idar da sallah sai jakarta a hannu, ɗakin umma ta wuce ta shiga can uwar ɗakan da Sameeha ke zaune da Khairy da wata ƙawarta sai ɗiyan Inna Rukayya, Tana zuwa ta kama hannun Sameeha ta ce. Anty zo mu je ki gani. Ikram ki barni na huta ina fama da gajiya. Dan Allah ki zo mu je. Yadda Ikram tayi maganar kamar zata yi kuka yasa Sameeha miƙewa tabi bayanta, har tsakar gida suka fice zuwa ɗakin yaya Zaidu, Ikram ta ciro key a cikin ƙaramar jakarta ta buɗe bakin kana suka shiga ta rufo ƙofa, ta miƙawa Sameeha wayarta tana cewa. Kinga saƙon da aka turo mini yanzu da wata number. Sameeha ta amsa ta shiga karantawa ko ɗar bata ji ba a ranta dan wlh tasan sharri ne, a yadda Khairy take faɗar Shamsu ba zai taɓa aikata haka ba, ta duba Ikram tana cewa. Ki kwantar da hankalinki wannan ba komai bane face sharrin maƙiya, zan bincika komai In Sha Allah gaskiya zata yi halinta. Yanzu ki saki ranki kar a gane kina cikin damuwa kisa a ranki dukkan nasara yana tare da ƙalubale. Humm tace kana suka fita daga ɗakin Sameeha tana riƙe da wayar Ikram bata mayar mata ba, ta koma ɗakin umma Ikram kuma ta koma ɗakin da take tare da ƙawayenta. Sameeha bata sanar da kowa ba ta adana wayar Ikram a hannunta sai ta cigaba da hidimar ta. Bayan sallar magrib aka kawo motoci da zasu ɗauki amare, Ikram aka fara kaiwa wanda Sameeha sai da tayi mata rakiya zuwa gidanta dake umguwar sarki, babban filat mai kyau iya ganin mai kallo, yaji kaya na zamani da komai ga sabuwar motarta a tsakar gidan an parker, sai da suka yi sallar Isha'i kafin aka ɗauki Sameeha daga gidan Ikram aka wuce da ita gidan mijinta dake unguwar rimi, wato gidansu Khairy a babban part wato gidan sama dake tsakiya, nan Ibrahim ya gyara mata aka zuba komai akan in an gama biki zai wuce da ita Abuja gidansa dake can dan a Abuja zasu zauna, sai dai ya riƙa zuwa yana duba Hajiya da uwargidansa, can gidansa na Abuja a gyare yake an ƙara zuba masa kaya na buƙata sosai, Abujan da Sameeha ta guda da farko gashi Allah ya nufa dole sai ta zauna a can. Bayan sun isa sai da aka fara kaita sashin Hajiya ta gaishe su kafin aka kawota nata sashin, faɗar haduwarsa ma bata lokaci ne dan falon ƙasa komai nata ne da Yaya Zaidu yayi musu oder, falon sama ne Ibrahim yayi nashi hidimar, su Hauwa dai anga abinda ya kusa sasu suma dan kuwa sun gama santin gidan Ikram da gidan Aminu ko rabin kyansa bai kai ba, sai gashi na Sameeha ya ninka na Ikram kuma gidan sama ne, gida ne da yake da gate kusan uku, gate ɗin farko za a wuce a shiga na biyu wanda za a ga titi gabas kudu yamma, to a titin dake ɓangaren kudu za a miƙe a isa gate ɗin gidan Sameeha, dama sashin Hajiya daga ɓangaren gabas yake a cikin gate na biyu, haka mutune suka dinga yiwa su Sameeha murna domin sun taka gadar nasarar rayuwa, daga bisani aka mayar da kowa gida aka bar amare a gidansu. Wajen ƙarfe goma sai ga Ibrahim ya shigo sashinsu ba kowa a falo sai ya wuce ɗakin da yake matsayin na Sameeha a nan falon ƙasa, ya tura ƙofa da sallama ya sameta saman gado ta kwanta a gefe, shigowarsa yasa ta miƙe ta zauna tana amsa sallamarsa, ya zauna a gefen gadon ta shiga gaishe shi ya amsa fuska sake yana cewa. Barka da baƙunta amayar Iro, kiyi haƙuri an barki ke kaɗai a hankali zaki saba. Bari na watsa ruwa ina zuwa. Ya faɗa yana miƙewa, sai Sameeha ta tareshi da cewa. Dan Allah ina so ka bani lokaci kaɗan zamu yi wata magana. Ibrahim sai ya koma ya zauna yana sauraren ta, jakarta dake gefe ta ɗauko ta ciro wayar Ikram ta buɗe wajen massage ta miƙa masa tana cewa. Ɗazun da yamma aka turowa Ikram wannan saƙon shine nace bari na fara tattaunawa da kai dan bamu faɗawa kowa ba. Ya amsa wayar ya karanta ya ƙara karantawa cike da mamaki, bai ce komai ba sai wayarsa daya ciro a aljihun gabar rigarsa ya danna number ɗin Shamsu ya kirashi, yana ɗauka yace. Ka isa gida ne? Eh na iso amma Ikram tana ta kuka tunda na shigo, sai maganganu take faɗa mini na rasa ina zancenta ya dosa. Oka gamu nan zuwa. Abin da Ibrahim ya faɗa kenan, ya kalli Sameeha yana cewa. Tashi mu je gidan. Hmmm ai shiyasa na amsa wayar dan nasan halin Ikram ba tada haƙuri wlh, kuma sai da nace mata tabar komai a hannuna shiyasa ban tun kari kowa da maganar ba sai kai yanzu. Tashi dai muje In Sha Allah zamu gano wacce ta turo da wannan saƙon. Ya miƙe yana gyara mazaunin babbar rigarsa, Sameeha ma miƙewa tayi dan da mayafi a jikinta suka fito tsakar gidansu ga motar daya sauka yanzu, ya buɗe mata mazaunin kusa dashi ta shiga ya rufe kana ya zagaya ya shiga mazaunin driver ya kunna mota tare da hon mai gadin sashin ya buɗe masa gate kana ya fice da motar. **** Najwa. Tunda ta koma gida ta ƙasa komai sai saƙa da warwara, gani take in tabar Ikram da Shamsu sun ci bilis, shiyasa ta kashe wayarta gabaɗaya dan kar a dameta da kira, tana buƙatar zurfafa tunaninta akan hukuncin da zata ɗauka akansu, har wajen sallar azahar tana a kwance, da kyar ta miƙe ta gabatar da salla tana zaune bisa dadduma, dabarar turawa Ikram text ya faɗo mata, sai ta miƙe da sauri ɗan har wani kuzari ta samu saboda a yau tana so Ikram da Shamsu kar suyi kwanan farin ciki, dadduma ta naɗe ta zari jakarta ta fice zuwa bakin titin layinsu shagon mai sayar da layin waya, ta sayi layin MTN sabo mai register kana ta dawo gida ta saka layin a ƙaramar wayarta sai ta soma rubuta tex ɗin, data gama tayi saving ta aje har sai da aka yi sallar La'asar kafin ta turawa Ikram tana dariyar mugunta. Yau za a ci amarci da tashin hankali dan nasan Ikram ba tada sauƙi sai ta ɗaga masa hankali, Ni kuma haka nake so, kuma zan cigaba da tura mata saƙo yadda rikici zai cigaba da wanzuwa har sai Shamsu ya nima wacce ke tura sako, idan ya nima mu haɗu na bashi dama daga nan na shigar da nawa buƙatar, Wlh zan iya fasa auren Aminu In dai ya amince da aurena. Cewar Najwa a zahiri kamar mai taɓin hankali, ɗan sosai shaiɗan ya ƙara samun gurbi a zuciyarta yana haska mata Shamsu yafi Aminu shine ya dace da ita a yanzu. Haka ta dinga saƙa da warwara har aka yi sallar magrib, tayi zaton Ikram zata kira layin amma shuru hakan yasa ta kashe wayar da layin ke ciki ta kunna asalin babbar wayarta data kashe ɗazun, ita kaɗai a gida kamar mayya, dan inna can zata kwana kamar yadda itama take kwana akan, tasan mazan gidansu sai dare yayi zasu shigo tunda ba abinci zasu samu ba a gidan, har aka yi isha'i tana a haka, data idar ne ta fita zuwa waje ta siyo biredi da ruwan bunu ta dawo ta haɗa tea mai kyauri ta sha ta kwanta, a haka har barci ya ɗauketa da tunani barkatai. Shamsu da Ikram. *Duk wacce ta karanta mini littafi bata biya ba, ta sani ta karanta da hakkina kuma In Sha Allah sai Allah ya saka mini.* [7/7, 13:04] Buhainat😁: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shai wanidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.* 38. Ikram da Shamsu. Ya shigo da abokansa su uku falon yace su jirashi, sai ya isa bedroom ɗin Ikram akan ya kirata su gaisa amma sai ya samu ɗakin a rufe, ya buga bata buɗe ba sai ya shiga kiranta a waya yana ringing amma ba a ɗauka ba, ya shiga yi mata magana akan tayi haƙuri ta buɗe amma ta nuna tamkar bata cikin ɗakin, cikin sanyin jiki ya dawo gurin abokansa yana basu hakuri akan amarya ta ɓoye kanta, basu wani damu ba sun san ko wace amarya da kalan na ta salon dan haka suka yi masa sallama suka wuce, har mota yayi musu rakiya da suka wuce ya dawo ciki ya isa ɗakinsa ya watsa ruwa ya saka jallabiya kana ya ɗauki extra key a drower ya fito ya isa ɗakin Ikram yayi sa'a ta cire key a jikin ƙofa, yana sakawa ya buɗe ya shiga, Ikram tana ganinsa ta zabura ta miƙe tana cewa. Karka kuskura ka matso kusa dani in ba haka ba zanyi maka abinda baka taɓa tsammani ba, Shamsu nayi dana sanin aurenka kuma kasa a ranka ba zaka taɓa samun abinda kake so a gareni ba, ka fita bana son ganinka. Ta ƙare maganar a tsawace tana kuka ganin yana matsowa kusa da ita, tsananin mamaki yasa Shamsu kasa magana dan ya rasa ina maganarta ya dosa balle ya iya hasko inda matsalar take, cikin dakiya da danne damuwa ya soma cewa. Haba amaryata ki kwantar da hankalinki ni babu abinda zan yi miki, yanzu ki zauna muyi magana. Babu maganar da zan ɓata lokaci nayi maka domin ka gama ɓata rawanka da tsalle, na dai gaya maka baka isa ka samu abinda kake nima a guna ba, da zaka fita dana fi jin daɗi dan bana ƙaunar ganinka. Shamsu yana shirin yin magana sai wayarsa da ya saka a haljihun gaba ta soma ƙara, sai ya ciro yaga Ibrahim ne ya ɗauka da sauri har suka yi magana kana ya kashe wayar yana duban Ikram. Yaya Ibrahim da Anty Sameeha suna hanyar zuwa nan, duk da ban san dalilin zuwansu ba amma hakan yana da yanada alaƙa da wannan rikicin da kike yi mini, dan haka ki daina kuka koma miye gaskiya zata yi halinta In Sha Allah. Yana gama faɗar haka ya fito daga ɗakin ya zauna a falo tare da dafe kansa da duk hannunsa biyu, damuwa sosai ya shiga kan yadda ranarsu ta farko a gidan aurensu ya kasance, yadda yasan Ikram tana sonsa ya tabbatar ba ƙaramin abu bane yasa ta yi masa haka, kuma yasan tana da tarbiyya musu bai taɓa shiga tsakaninsu ba, haka ya zauna zaman jiran isowar su Ibrahim. Itama Ikram zama tayi a bakin gado tana matsar kwalla dan ta rasa yadda zata danne halin da take ciki ta ɓoyewa Shamsu, shiyasa ta kasa controlling kanta kamar yadda Sameeha tace karta nuna masa komai ta bar komai a hannunta, haka kowannensu ya zauna cikin damuwa har zuwa sadda suka ji hon ɗin motar Ibrahim a gate, hakan yasa Shamsu yayi saurin fita lokacin mai gadi ya buɗe musu sun shigo, Ibrahim yayi parking suka fito Shamsu ya ƙaraso yana yi musu sannu da zuwa cikin ladabi, suka amsa kana suka shiga cikin falo suka samu wajen zama Sameeha da Ibrahim a kujera mai zaman mutum uku suka zauna, sai Ikram da fitowar ta kenan ta samawa kanta guri a kujera mai zaman mutum ɗaya, Shamsu shi kuma ya zauna a kujera mai zaman mutum biyu, nan Ibrahim ya soma magana yana cewa. Shamsu ba ɓata lokaci za muyi ba saboda dare, ina so ka duba wannan saƙon kayi nazari akan waye ko wacece zata yi maka irin haka. Yayi maganar yana miƙa masa wayar Ikram daya amsa a hannun Sameeha, Shamsu ya taso ya amsa ya koma ya zauna ya soma karanta saƙon cike da tsantsar mamaki a fuskarsa, ya ɗago ya kallesu bayan ya gama karantawa ya ɗaura da cewa. Yaya ni ba ni da wani maƙiyi dana sani a zahiri da zai yi mini irin haka, ashe shine dalilin da ya sa Ikram ta rikice mini, Innalillahi wa inna ilaihir raji'un. Ya ambata yana mai dafe kansa da hannu bibbiyu domin saƙon ya kaɗa shi sosai kuma bai ga laifin Ikram ba domin saƙone da yake da tashin hankali a ciki, musamman ita da take a matsayin matarsa da aka ɗaura aure yau yau, Ibrahim yace. Shamsu kadai zurfafa tunaninka akai ƙila ka taɓa samun sabani da wani ko wata yace bari ya biyo ta wannan hanyar domin ya rama, abokin aiki ko budurwa, duk da ni ban yarda ka aikata ba saboda nasan tarbiyyarmu wlh ba zaka taɓa ɓata sunan ahalinmu ba wannan shirri ne dai. A zabure Shamsu ya muskuta ya ɗago kai yana cewa. Tabbas mace ɗaya ce nasan ƙila ta iya aikata haka saboda zafin da taji na auren Ikram da nayi, saboda budurwa ɗaya nayi a nan Kaduna sai Ikram dana aura yanzu, sannan ita wancen da kanta ta koreni tace ba zata iya aurena ba saboda banda kuɗi. Nan ya kwashe yadda suka rabu da Najwa ya basu labari tas kana ya cigaba da cewa. A zahiri na ɓoye mata asalina ne domin nasan zata soni saboda Allah sai kuma ta faɗi jarabawar ta nuna kuɗi take so, ta kuma sallameni da kanta akan karna sake zuwa gidansu. Dalilin da zai saka tayi mini wannan sharri saboda Ikram na aura, zata ga kamar nayi hakan ne domin na ƙuntata mata, kuma na soma soyayya da Ikram bansan alaƙarsu ba daga baya ne na fahimci kuna da alaka a Najwa. Najwa! Cewar Ikram da ƙarfi, Sameeha ma tace. Najwa kuma! Najwa Tamu dana sani ko wata daban. Ita dai cousin ɗinku wacce take a badarawa, na tabbatar bata san nine na Auri Ikram ba sai yau shiyasa ta biyo ta wannan hanyar dan ta ƙuntata mini, ƙila a ganinta na auri Ikram da gangan ne dan na bata haushi, wannan hasashena ne kuma bincike shine zai tabbatar da gaskiya, ita kaɗai nake zargi a yanzu. Ikram yau tunyaushe ne baki ƙara ganin Najwa a gidanmu ba, saboda na tuna ban ganta ba tun yamma dan bada ita aka kawo mu gidajenmu ba. Ai ni rabona da ita tun lokacin da aka fito ɗaukar hoto dasu Shamsu suka shigo gaisuwar iyaye bayan ɗaura aure. Cewar Ikram tana yawo da idanunta kamar mai tunani, Ibrahim yayi murmushi domin shima zarginsa ya faɗa akan Najwa sai yace. Da alama ita ce dan na tabbatar a wannan lokacin da muka shiga gida ta ga kaine mijin Ikram yasa ta bar gidan, kuma ta yi amfani da wannan damar dan ta lalata tsakaninka da Ikram, dan haka yanzu ta ina zamu tabbatar mu gano da ita ɗin ce ta aikata haka. Murmushi Shamsu yayi yana cewa. Ku bani number ɗinta yanzu na kirata da dayan layina da ba tada shi, yanzu gaskiga zata yi halinta. Cewar Shamsu, nan take Sameeha ta buɗe wayarta ta karanto masa number ɗin Najwa ya saka a wayarsa ya soma kira, Najwa a cikin barci taji karar waya hakan yasa ta farka ta duba wayar taga number ne har ya katse bata iya ɗauka ba ta mayar da wayar ta aje, sai ga wani kiran ya sake shigowa cikin gajiyawa da ƙarar tayi saurin ɗaukar wayar ta kara a kunne ba tare da tayi magana ba. Hajiya Najwa halan kina barci na tashe ki, kiyi haƙuri kamawa tayi da fatan kin gane me magana. Shamsu yace bayan ya saka kiran a handsfree yadda zasu ji komai, Najwa ta tashi zaune dan ta gane Shamsu ne amma saboda tayi masa wasa da hankali tace. Ban gane me magana ba. To Shamsu ne mijin Ikram, na kira ki ne na baki haƙuri akan hukuncin da kika shirya ɗauka a kaina, saboda kin turawa Ikram saƙo gashi ta rufe mini ɗaki tana ta cin mutumci na akan haka, a takaice gani zan kwana a mota dan ta fusata sosai ina tsoron kar dare yayi tayi mini wani illa in barci ya ɗauke ni. Hmmm ni ban fahimci inda ka dosa ba. Najwa ki nasan fa kin san komai ba sai mun tsaya muna wasa da hankulan juna ba, na tabbatar sai yau ne kika san nine mijin da Ikram ta aura, domin ɗazun na ganki a gidansu kuma tsakani da Allah bansan Ikram 'yar uwarku bace sai da aka gama zancen aurenmu da ita, lokacin take faɗa mini kema an saka bikinki to a cikin hira take faɗa mini inda kike har na gano ke ce, kuma in zaki yi mini adalci kece kika koreni dan haka bai dace ki hukunta ni ba. Hmmmm amma ka rasa wacce zaka aura sai 'yar uwata saboda kaci mini fuska ko, meyasa daka gano nice Najwa 'yar uwarsu baka fasa auren ba. Amma kin san an saka ranar aurenki hakan ya ƙara mini ƙarfin guiwan dana cigaba da niman Ikram, Najwa kinsan ina sonki kuma bazan taɓa son wata mace sama da ke ba amma kika koreni, na rasa me ye makusa a jikina kika yi mini haka. Meyasa zaka ɓoye mini asalinka? Meyasa ka ɓoye mini komai naka ka muna mini kai talaka ne. Saboda na gwadaki ne na gane zaki so ni domin Allah, sai kuma baki kaiga cin jarabawata ba kika ma koreni, ni dai yanzu ki faɗa mini me kike so a gareni domin ki wanke ni a gun Ikram, dan sosai kika haddasa husuma a tsakaninmu. Yanzu kana mufin Ikram ta kulle maka ɗaki a mota zaka kwana? Allah kuwa, yanzu ina tunanin kona je na kama hotel ne, ni ina so ki faɗa mini me kike buƙata da zai wanke laifina a gunki ki wankeni a gurin Ikram dan Allah. Ko meye nace ina so zaka yi mini shi? Najwa ta faɗa cikin jin daɗin hakkarta ta cimma ruwa, Shamsu yace cikin sanyin murya dan ya ƙara karya mata zuciya. Eh in dai baifi ƙarfina ba. To ina so nima ka aureni. What? Ya faɗa da ƙarfi su Sameeha ma mamaki yasa suka zazzaro ido waje domin tun sadda suka fara magana zuke mamakin Najwa, Najwa ta ce cikin 'yar dariya. Eh ko ba zaka iya aure na ba ne? to hakan shine zai wanke laifinka a guna kuma shine zai sa na numa ma Ikram cewar bakin rijiya ba wajen wasan yaro bane. Taya hakan zai yuwu? Keda ake shirin yin aurenki, sannan me Ikram tayi miki da ta cancanci haka a gunki. Hmmmm saboda ta aureka shine laifinta, sannan kuma idan ka yarda da aurena ni nasan yadda zan saka a fasa aurena da wancen. To shikenan zanyi tunani akai amma kinsan dole zancen aurenmu zai ɗauki lokaci saboda yanzu ne nayi aure. In dai ka amince to ko nan da shekara ɗaya ne zan jiraka, sannan ka aje batun zaka yi tunani idan ba haka ba wlh sai na cigaba da kunna maka abubuwan da sai kayi dana sanin auren Ikram. Sannan ko kaje ka faɗa mata nice nayi mata sako ba zata yarda ba saboda sun yarda dani kuma ina da hanyar wanke kaina. To hajiya Najwa nagode Allah ya saka da alkhairi da kika warware mana zare da abawa, ga yaya Ibrahim da Anty Sameeha dama Ikram duk suna jinki kuma suna gaisheki da jan aiki. Shamsu ya ƙare maganar yana 'yar dariya, a zabure Najwa ta tashi ta zauna tana jin wani gumi yana damunta, bata taɓa zaton gadar zare ya saka mata ba, tace cikin ƙara ji. Me kake nufi da zancenka Shamsu? Hanyar da kika bi nima shi nabi na gano gaskiyar abinda kika haɗa, Ikram ga 'yar uwarki kuyi magana. Ya kare maganar yana miƙawa Ikram wayar, Ikram tace cikin sanyin murya. Ni babu abinda zan iya ce mata taje ita da Allah. Najwa kin kyauta Allah ya shiryeki. Muryan Sameeha kenan data yi magana cikin damuwa, Najwa kashe wayarta tayi ta aje ta a kan gado tana jin wani baƙin ciki yana ruruwa a zuciyarta, wannan shine karo na farko data haɗa plan ya rushe bata kawo Shamsu daɗin baki yayi mata ba, aiko yaci bashi dan ta ɗauki alwakarin yin maganinsa sai ya san wacce yaci amana, haka ta miƙe ta manna bayanta a bango tana huci zuciyarta tana tafarfasa, dakar ta tausa kanta ta koma ta kwanta tana sauke ajiyar zuciya, yanzu kenan yasa taji kunya a idon su Sameeha, da wani ido ma zata kallesu? tana ganin ba zata sake taka ƙafarta ba zuwa inda suke dan abin da kunya, ba zata yarda ma inna ta san da wannan abin da tayi ba saboda tasan zasu kwashi rikici, addu'a take Allah yasa su rufa mata asiri su bar maganar a haka. Su Sameeha kam Ibrahim sosai ya yi musu nasiha yace kuma su bar zancen a tsakaninsu dan kar wasu suji suyi dariya tunda naka naka ne komin lalacewa Najwa jininsu ce, dan haka su barta da halinta kuma su rufe maganar kar ma su nuna mata ko a fuska, daga bisani suka yi sallama da juna wajen ƙarfe sha ɗaya da minti sha shida suka fito Ikram da Shamsu har mota suka rakasu kana suka wuce, sai suka dawo ciki Ikram sai ɓoye fuska take yi cike da jin kunyar abinda tayi wa Shamsu, da taji maganar Sameeha da bata riski kanta a haka ba, shiko Shamsu nuna wa yayi ko kaɗan bai damu ba kuma komai ya wuce. Duk da wannan abin ya faru bai hana gidaje biyu amare da angwaye sun more amarcinsu ba, dan kuwa ko wanne ya baza komar soyayyar sa ya kwashi roman so da ƙauna. Washe gari ne da yamma aka shirya kayataccen walima a cikin farfajiyar gidan Hajiya nan second gate, 'yan gidansu Ikram ma sun zo dan dama wasu sai a ranar ne suka samu damar zuwa ganin ɗakin amare, Ikram ma Shamsu ya kawota ta sauka a sashin Sameeha sai da lokacin walima yayi kafin suka tattara zuwa sashin hajiya, kota wani ɓangare soyayya ake nuna musu Masha Allah abun dai sai wanda ya gani, sun san sunyi dace da dangin miji saura musu kyautatawa da kuma kama mazajensu hannu bibbiyu. Duk waɗanda suka zo wannan walimar sai da suka tafi da kyautar zanin atamfa da kuma kayan ciye ciye, ga wa'azin da aka gabatar ya kayatar wanda mutane sun tafi da malama Haajara a baki saboda iya sarrafa harshe da kuma ilimin zaman aure da ta baje musu suka kwashi garaɓasa. Bayan sallar magrib kowa ya watse gida ya rage sai dangi na jiki, Ikram a sashin Sameeha ta zauna, sosai Sameeha ta kuma yi mata faɗa akan abinda ta yiwa Shamsu jiya, ta kuma nusar da ita yadda ake zaman rayuwa sosai, domin ita tana da wayewa da sani akan zaman aure dan jiya ba yau ba ne, Ikram ta yi mata godiya ta ɗaura da cewa. Nayi mamakin abinda Najwa ta aika jiya hakan yana nuna tana bakin ciki da aurena, kin ga kenan ashe bada zuciya ɗaya ta shigo jikinmu ba aketa hidimar biki da ita tunda kinga yauma bata zo ba sai Inna, wai harda cewa inna ta faɗa mana ba tada lafiya ne, banda kunce a rufe maganar da sai na faɗawa Inna abinda ta mini. Ikram ki bar komai ya wuce kin fita har a gurin Allah, sannan ki cire damuwarki akanka ki fuskanci aurenki, idan ta zo ta nima sulhu shikenan mu cigaba da zumuncinmu tunda son zuciya ya sa tayi haka, kuma ma da kunya tace zata ƙara aikata aikin rashin gaskiya a garemu. Anty wlh yadda na karanci Najwa sam baki gane halinta ba, na tabbatar ba zata sake zuwa inda muke ba tana da riƙo sannan kuma baƙin cikin nasarar da muka samu bazai barta ta cigaba da zumunci damu ba, ni kam ko ta dawo bazan sakar mata fuska ba dan nasan ta da mugun son zuciya. Ni dai nace ki bar wannan maganar kuma ga sakonki nan Khairy ta ce na baki tsumi ne da kuma gumba da kayan ciye ciye dai na mata, ki riƙa amfani dasu a hankali, in kuma baki gane ba ki kirani nayi miki bayani. Hmmm Anty khairy bata gajiya, ni dai wlh bazan sha wani abu yanzu ba dan hmmm. Sai tayi shuru tana sunne kai, Sameeha ta yi murmushi tana cewa. Yarinya da haka zaki saba Allah dai ya kawo 'yan dugui dugui masu albarka dan ke yanzu zaki fara aje garke nikam ba yanzu ba. Allah anty ina fatan ki haifa mana twins, nasan yaya Ibrahim sai yayi yayyafin kuɗi ga mutane dan murna. Ki fara faɗa a akanki kafin ni dan ina da Abi da Amrah. Sameeha ta faɗa tana miƙewa zata ɗauko wayarta a chrgy, Ikram tayi murmushi. Su can gidansu daban nan gidan kuma suma nasu zaki haifo musu. Ikram yaushe muka fara irin wannan maganar dake, wato aure daɗi ko. Laaa anty ni kin ma koreni, bari naje falo na jira yazo mu tafi. Kima kirashi yazo ya ɗauke ki kawai kin ji. Cewar Sameeha tana dariya Ikram ma dariyar tayi ta fice zuwa falo. Sai wajen tara da rabi Shamsu yazo ya ɗauketa suka wuce gida cike da farin ciki. ***" Aminu. Tunda ya tabbatar da an ɗaura auren Sameeha da wani ya kulle kansa a ɗaki da yake weekend ne ba aiki, yaci kukansa ya gode Allah daga bisani yayi mata addu'ar fatan alkhairi yasan ya rasata har abada dan abune mai matuƙar wahala ta fito daga gidan mijinta, saboda yadda yasan ta da iya kula da miji, haka ya yini yata tunanin rayuwarsu ta baya, ko yaransa a ranar sun san babansu yana cikin damuwa shiyasa basu takura shi ba da yake basu san mamansu tayi wani aure ba, baaba ce kawai ta sani itace ma ta dinga kwantarwa Aminu da hankali. Wajen misalin ƙarfe tara na dare yana zaune yana kallon tv, rabin tunaninsa yana ga Najwa da duk ranar basu yi waya ba wanda in bai kirata ba zata kirashi, sai ya bayar ko kila wani uzurin ne ya riƙe ta, yana cikin tunanin ya kirata sai wayarsa ta soma kuka ya duba yaga baƙuwar number ne, kamar ba zai ɗaga ba sai ya ɗauka ya kara a kunnensa yana sallama, ɗaya ɓangaren kuma Nafeesa ta amsa cike da natsuwa ta gaishe shi ya amsa yana tambayar wacece, sai da ta gyara kwanciyarta ta daidaita natsuwarta kafin ta amsa da cewa. Sunana Nafeesa Sabo Mai kanti, na siya waya ce second hand a hannun wani mai sayar da waya sai na tsinci number ɗinka a cikin wayar, dalilin daya saka na kiraka saboda sunanka ya kasance sunan fiyayyen Halitta ni kuma duk abinda ya danganci Manzon Allah s.a.w yana matuƙar burgeni. Allah yasa ban takuraka ba. Ta ƙare maganar tana jan fasali, Aminu kuwa yadda ta jero masa bayani ta kuma sako fiyayyen Halitta s.a.w sai hakan yayi matuƙar kayatar dashi, ya ƙara riƙe wayar yana cewa. Masha Allah kuma baki takurani ba sai dai nayi mamakin ƙarfin halinki na kiran wanda baki sani ba. Hakane amma na tabbatar Aminullah ba mai cutarwa bane domin suna linzami ne. Gaskiya ne ina godiya na yaba halina duk da baki waye ni ba. Nagode. Nice da godiya daka saurareni amma in ba damuwa zan iya cigaba da kiranka muna gaisawa saboda soyayyar Manzon Allah s.a.w . Tunda kika ce Manzon Allah s.a.w ai kin gama magana, kuma masoyina ne da babu tamkarsa a duk duniya, ina kuma son mu'amala da duk wanda yake ƙaunar Rasulillahi. Nagode sosai a gaida iyalin, zan barka haka karna cikaka da surutu. Idan kana yin WhatsApp chart zamu riƙa gaisawa ta can dan ba kowa ne ke son amsa waya ba. Ayya? ni chart bai dameni ba amma gaisawan ma ba damuwa nagode. Nima na gode sai da Safe yaya Aminullah. Bata jira amsar sa ba ta kashe wayar tana sakin murmushin farin ciki, shima Aminu tsintar kansa yayi yana yin murmushi dan sosai yaji ta rage masa damuwar da yake ciki saboda tsara zancenta, tunatar dashi da tayi akan soyayyar Manzon Allah s.a.w, sai nan take ya soma yi masa salati saboda yasan yin salati ga Annabi s.a.w waraka ce daga damuwa, mafita ce daga ruɗani, sannan kuma kuma samar da farin ciki da natsuwar ruhi. Muje zuwa.... [7/7, 13:04] Buhainat😁: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shai wanidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.* 39. Aminu a daren saida ya rayashi da sallolin nafila ya mayar da lamarinsa ga Allah, kafin daga bisani ya samu barci mai daɗi sosai, haka ya wayi gari wasai ba tare da sauran damuwa ba, hakika ya ƙara tabbatar da duk wanda ya bar Allah to shima sai ya barshi, da tun farko ya mayar da lamarinsa ga Allah to ba zai tsinci kansa a damuwa da auren Sameeha ba. Bayan ya kammala karyawa sai ya tuna da Najwa hakan yasa shi kiranta, wayar harta tsinke bata ɗauka ba a kira na biyu ne ta dauka bayan sun gaisa yake tambayarta lafiyarta tace tana fama da ciwon kai shine yasa ma jiya bata kira ba, yayi mata fatan samun lafiya kana suka ɗan taba hira daga bisani suka yi sallama akan zai kara kira anjima yaji jikinta, yana ƙoƙarin miƙewa saƙo ya shigo wayarsa ya duba yaga number jiya ce da ko saving bai yi ba, ya duba saƙon tana cewa. Barka da safiya mai babban suna fatan ka tashi lafiya ya kwanan iyali? Na duba ka a WhatsApp sai naga baka hau ba shiyasa na gaisheka ta nan, ka yini lafiya. Guntun murmushi yayi yana cewa a fili. Allah mai mutane kowa da irin halinsa da tunaninsa, ita Najwa da zan aura bata damu da saƙo haka ba amma ga wata ta damu dani. Ya kuma sakin murmushi kana ya miƙe ya wuce zuwa bedroom dan yayi wanka ya fita zuwa gurin wani likita da aka haɗashi dashi domin tattauna matsalarsa. **** Nafeesa. Tunda ta bar gidansu Najwa take tunanin yadda zata kira Aminu, harta isa gida tana tunani, da yake ba wani aiki zata yi ba sai ta kwanta a gado ta hau facebook tana duba abubuwan da mutane suka ɗaura, a nan taci karo da wani video na wani malami da yake magana akan Monzon Allah s.a.w, yayi bayani sosai akai, wannan ne ya bata damar yin tunanin hanyar da zata ɓullowa Aminu kuma cikin ikon Allah tayi nasara har ya ɗauki wayarta kuma ya saurareta, wato taci arzikin Manzon Allah s.a.w kuma ga dukkan alamu zata cimma nasara tunda ta kula Aminu yana da sauƙin kai, koda gari ya waye ta duba shi a WhatsApp bai hau ba sai ta yi masa saƙo duk da bata saka a ranta zai mata Reply, ta ɗan tsaya kaɗan bayan ta tura taji shuru sai kawai ta kunna data ta cigaba da sabgoginta, ba jimawa Najwa ta kirata take sanar da ita abinda Shamsu yayi mata jiya, Nafeesa kamar zata kwashe da dariya dan ba karamin daɗi taji ba dama sai da tayi addu'a akan kar Allah ya bata nasara dan ta fara gajiya da son zuciyar Najwa, sai tace cikin kulawa. Gaskiya banji miki daɗin haka ba, yanzu yasa kin ji kunya, amma ni shawarar da zan baki ki ɗaure kije har gidan Sameeha ki bata haƙuri na san zata yiwa Ikram magana ta yafe miki, kin ga saiku koma zumuncinku ba tare da wani tangarɗa ba. Allah ya kyauta naje na sauke kaina gaban Sameeha, ai ni dasu mun raba jaha kowa tashi ta fissheshi, dama an gaya miki inna auri Aminu zan yarda muyi hurɗa dasu ne, hmmm nifa wlh bani ba su, kuma Shamsu yaci bashi saina yi masa mummunar tabo da ba zai manta ni ba, dani yake wasa. Daɗi na dake Najwa riƙo baki da yafiya, kuma fa ke ce mai laifin amma sai kiyi kicin kicin ki azawa mutum, kawai ki bar komai ya wuce ki fuskanci aurenki tunda ya kusa. Hmmm Nafeesa naga kin fara saduda kina bin bayan su Sameeha, kodai da wata a ƙasa ban sani ba. Haba Najwa duk abinda nake faɗa miki domin cigabanki ne kuma kin san ke tawace bazan taɓa juya miki baya ba, kiyi tunani da kyau, ba kida kuɗi ko ƙarfin da zaki tunkari Shamsu ki rama abinda ya yi miki, dan wlh idan kika dage sai kin rama to kwaɓarki zata yi ruwa kuma ina mai tabbatar miki da zaki saka kanki a matsala, suna da mulki da kuɗi ke kuma ba ki da komai tunda baki auri Aminu ba balle kiyi tutiya dashi. Hmmmm Najwa ta sauke ajiyar zuwa domin duk maganar Nafeesa gaskiya ce, hakan yasa ta karaya tace cikin sanyin jiki. Shikenan na bar komai ya wuce, amma yaushe zamu haɗu mu fara shirin bikina tunda lokacin ya fara matsowa zan mayar da hankali akan haka. Yauwa ko kefa, kibari next week mu huta sosai lokacin sai mu haɗu mu yi maganar, sannan ya batun zuwa gurin malamin dana baki shawara. Sai kin zo muyi maganar. Cewar Najwa, da haka suka yi sallama. Haka Najwa ta kama ƙumbiya ƙumbiyarta bata bari Inna ta gane komai ba, dan dagewa tayi ba tada lafiya shiyasa bata je gidajen Amare ba, saboda Inna ta matsa lallai sai taje amma ganin ba lafiya ce da ita ba yasa ta rabu da ita kuma yadda ma taga bata fita ko ina yasa ta yarda da rashin lafiyar nata har tana saka Sadiq yana siyo mata magani. ***** Sameeha. Satinsu ɗaya da amarci Ibrahim ya koma Abuja a cewarsa sati na sama zai zo ya tafi da ita, to tunda ya tafi ta tare a sashin Hajiya barci ne kaɗai ke mayar da ita ɓangaren ta, ba karamin daɗi Hajiya taji ba saboda yadda Sameeha ta mayar da ita mahaifiyarta, in dai tana sashin bata bari ta kauda ko tsinke ita ke komai hatta abinci ita ke dafa musu bata bari masu aiki su girka, cikin ƙanƙanin lokaci ta shaƙu sosai da Hajiya tun tana kunyarta har ta ware suke shan hirarsu. Ikram ma tazo a kwanakin ya kai sau uku Shamsu ke kawota ya tafi aiki sai dare yake zuwa ya ɗauketa, Khairy itama tana jin labarin yadda Sameeha ke yini a gidan Hajiya hakan yasa itama koda yaushe tana hanya da ita ake komai, yanzu ne suka san sun samu surukai, saɓanin Nabila da take nuna musu ko in kula bata damu dasu ba balle su saba suyi jiki da juna. Lokacin da Ibrahim zai tafi ne ya ɗauki Sameeha ya kaita gidan Nabila, baa ta wani sake fuska ba sai wani fuska take a dole ga uwargida, sai dai duk yadda tayi zaton ganin amarya tafi ƙarfin tunaninta domin ta ganta babu raini matar fita anguwa ga kyau ga diri dan har ta fita cikar halitta, ganin bata amshe su yadda ya kamata ba basu jima ba suka bar gidan, shi dama Ibrahim ya haɗasu ne dan su saba koda baya nan Sameeha zata iya zuwa mata suyi zumunci, amma ga yadda ta nuna bata yi marhabun da hakan ba shiyasa Sameeha bata ƙara bi ta kanta ba, ta tsaya iya gidan Hajiya. * Ranar Juma'a ya kama kwana sha uku da aurensu ranar ne suka shirya zuwa gidan Umma suyi mata yini, dan washe gari Ibrahim zai zo lahadi kuma su wuce Abuja. Atamfa Sameeha ta saka green mai kyau ɗinkin riga da siket, sai ta saka hijab bata ɗaura ɗankwali ba ta ninke ta saka a jaka, a ranar ta fara fita da sabuwar motarta, kafin ta wuce sai da ta biya sashin Hajiya tayi mata sallama kana ta fito ta wuce gidan Ikram ta ɗauketa a mota dan dama haka suka shirya, kuma Ikram bata iya tuƙi ba tukunna sai an koya mata, itama Ikram atamfa tasha pink tayi kyau masha Allah duk kansu sunyi kumari ga hasken hutu daya fara ratsasu, duk da Ikram baƙa ce amma tayi haske kaɗan kuma ta murje sosai, haka suka wuce gidan umma suna hira a tsakaninsu wanda duk rabi na kewar gida ne da suka yi. Dama umma tasan da zuwansu dan haka ta rangaɗa musu waina da miya da kuma lafiyyyen farfesun naman rago wanda yaji kayan haɗi, koda suka isa sun samu ta gama komai su take jira, Zaidu da Anwar sun tafi Masallacin juma'a ita kaɗai suka samu. Suma saida suka gabatar da sallah kafin suka zauna a falo suka kara gaisheta sannan suka shiga hirar yaushe rabo, umma taji daɗi matuƙa da ganin yaranta cikin kyakkyawar kamala, hakan yasa ta ƙara samun natsuwar ruhi da kuma godiya ga Allah daya nuna mata wannan lokacin da kuma ni'imomin daya yi musu, su Zaidu da suka dawo nan chapter ta ƙaru suka shiga hira sosai cike da farin ciki da annashuwa, bayan sun gama ciye ciyensu suka fito tsakar gida kan babban tabarma da suka saba zama suka ci-gaba da hira, a cikin hirar ne Zaidu ya sako zancen yaran Sameeha yana cewa. Yanzu Sameeha gashi zaki koma Abuja kinga kin ƙara kusa dasu Amrah, da Aminu shi mai mutunci ne da ya baki su su zauna a gunki in sunyi hutun makaranta suje masa. Taf kaima kasan ba mai yuwuwa ba ne yadda Aminu ya ɗauka da zafi, tun rabuwarsu ƙiri ƙiri ya ki kawo su balle ya iya bar mata su, kawai dai dole zata nima inda suke tana zuwa ganinsu ko ya kawo su suna yi mata yini. Cewar Ikram, Umma ta ce. Gaskiya ba zai bada yaran nan ba, nima nafi yarda da su riƙa zuwa gaisheta su tafi dan kar a takurawa Ibrahima ko. Sameeha ta yi guntun murmushi tana cewa. Ni Allah ya saka mini dangana akan yaran, in yaso ya kawo su in ma yace bazai bada ba ya riƙe abinsa dole in su girma zasu nima in da nake. Haka suka ci gaba da hirar, nan umma ta sako zancen bikin Najwa tana cewa. Bikin Najwa saura wata ɗaya da sati guda yau, Sameeha zaki samu damar zuwa kuwa? Haba Umma dole na zo saboda Inna ba abin yadawa bace, anko ne ma ba muyi ba, zan barwa yaya Zaidu kuɗi ya saya mana Anwar ya kai mana wajen telenmu zan yi waya dashi, In an ɗinka sai a kawo umma ki aje mana, biki saura kwana biyu zan zo In Sha Allah har sai an gama komai. Aiko kin kyauta, ke Ikram tunda kina gari duk abinda ya taso in ya kama ki zo zan kiraki ayi komai dake, ina so ku shiga cikin dangi sosai a dama zumunci daku. Ni umma wlh banda Najwa taci darajar Inna da babu abinda zai kawo ni bikinta. Me kuma Najwan tayi miki dan nasan da walakin goro a miya, sam bakwa shiri kamar annabi da kafiri. Cewar Zaidu, Ikram zata yi magana Sameeha ta kwaɓeta. Amma nace bana son zancen nan Ikram, magana ta wuce miye amfanin taso da ita. Ikram faɗa mana me tayi? dan na kula sam Sameeha bata so ana faɗar laifin Najwa. Cewar Zaidu, Ikram tsalam ta miƙe daga gefen Sameeha ta tsallaka gefen Umma da yaya Zaidu ta zauna tsakiya dan kar Sameeha ta kai mata hannu, nan ta shiga basu labarin duk abinda ya faru lokacin biki, Umma salati ta riƙa yi tana tafa hannu sosai suka yi mamakin Najwa, Zaidu yayi 'yar dariya yana cewa. Ahaf sai dai ba Najwa ba, wlh zata aikata fiye da haka ma, na karanci yarinyar nan kamar yunwar cikina tana mugun son abin duniya da hangen na sama da ita, kunga kuwa daga haka sai Hasssada da kyashi ya samu gurbi a zuciyarta, Allah ya kyauta sai yanzu na ƙara godewa Allah daya rabani da ita, dan wlh ba zan jure wannan halin nata na son rai ba, taje can ta yiwa wani. Wlh yaya ta bani mamaki ai kaga da kunya tazo inda muke, har yau bata san kalar ɗakunanmu ba dan bata zo ba. Cewar Ikram, Zaidu yace cikin taɓe baki. Taya zata zo ta tafka abin kunya, ai wlh Najwa sai dai taci darajar Inna aje mata biki amma da dan halinta ne kare ba zata gani ba. Allah ya kyauta ya shiryeta ni wlh lamarin ta ya fara bani tsoro. Cewar Umma, Sameeha tace. Ai sai dai addu'a dan kuwa in da tayi nadamar abinda ta yi to da ta tako ƙafarta tazo gidajenmu ta bamu hakuri, ke kuma Ikram kin kyauta da kika fasa maganar, sai dai dan Allah mu barshi a tsakaninmu kar wanda ya nuna mata. Dama wa yake da lokacinta, darajar inna dai zata ci Allah yasa ta zauna a auren, dan wannan bakin hali gareta. Zaidu bana son haka dan fata na gari lamiri, duk lalacewarta jininmu ce fatan shiriya za muyi mata. Cewar umma, haka suka cigaba da hira har aka kira sallar La'asar suka tashi kowa yaje ya gabatar da nashi. Sai gabda Magrib su Sameeha suka bar gida, umma ce ma ta korasu da so suka yi sai bayan sallar isha'i su tafi tace bata amince ba su tafi ido na ganin ido, cikin farin ciki suka rabu da juna bayan sunyi guzurin sauran waina da farfesu, sannan Sameeha ta turawa Zaidu kuɗi masu kauri akan ya ƙara musu kayan abinci sannan Ikram ta bada dubu hamsin akan akaiwa Inna gudunmawarsu su duka, Zaidu kuma ya bawa umma dubu ashirin ta bada nata gudunmawar, wannan ahali suna cikin rufin asirin Allah da kuma kwanciyar hankali. Samedha sai da ta sauke Ikram a gida kafin ta wuce gidanta itama, a sashin Hakiya ta yada zango da tsarabar data soya a cewarta Umma ce ta ce a kawo musu tare da waina da farfesu, wanda Hajiya shi taci a abincin daranta, dan tana son waina sosai kuma taji dadin wannan, sai wajen ƙarfe goma saura Sameeha ta bar sashin Hajiya ta wuce ɓangaren ta. Washe gari Ibrahim yazo tunda ya dawo bai zauna ba dan haka a gurin uwargida ya sauka ya kwana, washe gari ma ya ƙara kwana sai ranar monday suka bar Kaduna da Sameeha. Koda suka isa Abuja gida ne mai matukar girma da kyau shima gidan sama ne har yafi gidanta na Kaduna kyau da tsaruwa, haka ta fara sabuwar rayuwa a gidan, Allah yasa akwai maikata har da me aiki wata dattijuwa mai suna iya, cikin kwana biyu ta saba da ita har suke ɗan taɓa hira in ta sauko ƙasa, saboda Ibrahim In ya fita tun safe sai dare yake dawowa, Sameeha bata yarda ta zauna ba dan ita ke girma musu abinci, sai dai Iya ta girka nasu da masu aikin gidan. A rana na uku ne Ibrahim ya kaita gidan Anty Amina can ta wuni sai dare ya biya ya ɗauketa suka koma gida. *** Ranar asabar. Da yamma Ibrahim ya ɗauketa zuwa wani super market dan tayi siyayyan kayan abinci data duba babu wasu a cikin cefanen da aka yi mata, Ibrahim yasha ƙananun kaya yayi kyau ita kuma ta saka ash ɗin jallabiya tasha aiki ta yane kanta da gyalen abayar, suna isa suka yi parking Security suka fito suka buɗe musu motar dan dama suna biye da motarsu a baya, sannan suka take musu baya suka shiga ciki, wani sucurity ya kamawa Sameeha keke ita kuma tana zabar abinda take so tana sakawa a ciki. Aminu tun shigowarsu ya angeta sai yayi sauri ya tare yaran kar su ganta saboda tare dasu ya zo siyayyar kayan ciye ciye na makarantarsu, tunda ya ganta zuciyarsa ta shiga bugawa da sauri da sauri yaga ta sauya komai nata ya nuna hutu da jin daɗi, yadda yaga Ibrahim yana take mata baya yasan mijinta ne kuma dama ya waye shi tunda Senator Ibrahim dole mutane sun waye shi, ko ba a fili ba a hoto ko a tv, Allah Allah ya riƙa yi su fita dan kar yaran su ganta shiyasa yayi sauri ya jasu suka isa wajen biyan Kuɗi duk da basu gama sayayyar ba, ya biya kuɗi aka zuba musu a leda ma'aikata gurin suka kai musu mota, ya buɗe mota da sauri yaran suka shiga shima ya shiga mazaunin driver yana shirin tada mota, Sameeha ce ta fito da sauri zata ɗauki wayarta data bari mota akan zata kira iya mai aikinta ta tambayeta wasu abubuwan da babu a kitchen ɗinsu na abinci su saya musu, Abi shine ya fara ganinta yayi wani zullo yana cewa da ƙarfi. Laaaa Abba ga Mamanmu wlh ita ce mamanmu ce, Amrah ga Mama. Amrah ta shiga raba ido tana kallon inda Abi yake nuna mata, aiko tana tozali da Sameeha ta buɗe mota ta fita da gudun ta bi ta isa gurin Sameeha data buɗe mota ta miƙa hannu dan ɗaukar wayarta sai taji an faɗa mata ta baya an riƙe ta da ƙarfi ana haki ba tare da anyi magana ba, da sauri ta juyo dan taga waye sai kawai tayi tozali da Abi yanata yi mata dariya ga hawaye kwance aidonsa, Amrah kuwa taƙi sakinta dan ta ruƙunƙumeta tana kuka, dan ji take kamar zata ɓacewa ganinta, Sameeha cikin rawar murya tace. Abi Amrah kune, in abbanku? Yana mota har zamu tafi mun gama sayayya naga kin fito daga ciki ashe Mama kina cikin garin nan baki zo ba. Mama wlh saina biki gida bazan koma gurin Abba ba. Cewar Amrah data ɗago tana kallonta ido shaɓe shaɓe da hawaye, kallonsu kawai take yi yaran sun sauya mata dan sosai suka ƙara yi mata girma ga fresh da suka yi na hutu, ta tabbatar suna samun kulawa mai kyau a gurin mahaifinsu. Ibrahim ne ya fito ya dubata dan yaji shurun yayi yawa sai ya hangeta tare da yara suna magana, ya ƙaraso security na biye dashi su biyu, yana ganin yaran ya tabbatar da yaranta ne saboda Amrah tayi kama da ita sosai, cikin fara'a yace. Ko ban faɗa ba yaranki ne ko? Big boy ya sunanka.? Ya miƙawa Abi hannu sai dai mai miƙa mata ba ya tsaya yana kallonsa dan bai waye shi ba, Sameeha ta dan yi murmushin yaƙe tana cewa. Abi shima babanku ne ka amsa masa magana mana. Abi yace sunana Adam, wannan kuma Ƙanwata ce Amratu. Masha Allah Allah ya muku albarka Amin. Hajiyata ya aka yi kika haɗu da yaran nan. Suma siyayya suka zo yi sun gama zasu wuce shine suka hango fitowata. Ayya to bari na jiraki ki gama da su kin san nan ɗin ba tsaro sosai. Cewar Ibrahim kana ya buɗe mota back seat ya zauna ya rufe ya shiga amsa waya, Aminu yana hango su amma yaƙi zuwa ganin yaran zasu bata masa lokaci ya fito yana kwala musu kira. Kai Abi Amrah kuzo mu wuce. Ni dai Mama ke zan bi. Cewar Amrah tana maƙewa babansu kafaɗa, Abi da yake yaron yana da wayo ya fahimci wani abu dan haka ya isa gurin Amrah yace. Kizo muje Abba zai kaimu gurinta kinji. Ni dai ba zan je ba. Haba Amrata Abban kike cewa ba zaki bi shi ba, kije zan zo har gida na ɗaukeku, karki ɓatawa Abba rai yayi fushi, ko kina so Allah ya saka ki a wuta ne kin ɓata masa rai. Cewar Sameeha, Amra ta girgizata mata kai alamar bata so Allah ya sata a wuta sai Sameeha ta kama hannunta ta jata tana cewa. Yauwa yarinyar kirki kije gurin Abba da kaina zan zo na ɗauke ku. Amrah bata ce komai ba sai ɓata fuska data yi a haka har suka isa gurin motarsu Sameeha ta buɗe back seat ta tura Amrah ciki kana ta rufe motar ta juya ta kalli Aminu tana cewa. Nagode da ganin yarana cikin kyakkyawar kamala, amma ina so ka gane ka daina ɗaukar alhakinmu domin ni dasu muna buƙatar juna. Tana gama faɗar haka ta juya ta wuto gurin mijinta ko waige bata yi ba, duk da zuciyarta a karye yake abu kaɗan zai iya saka ta fashe da kuka, dan sosai kewar yaranta suka taso masa har take jin wani damuwa a zuciyarta, Aminu kam bai ce mata komai ba ya buɗe mota ya shiga ya kunna ya rufe ta ciki dan kar Amra ta yi yunƙurin buɗewa, ya jasu suka wuce Amrah tana kwalawa Sameeha kira tana kuka. Maama, maaamaaa mun tafi dan Allah ki zo ki ɗauke mu. Sameeha buɗe mota tayi ta shiga ta zauna gefen Ibrahim ta shiga matsalar kwalla, bai ce mata komai ba ya cigaba da hidimarsa domin kishi ya motsa, dan gani yake ganin Aminu ne ya sata kuka ba yaran ba. Tofa... [7/7, 13:04] Buhainat😁: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shai wanidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.* 39. Aminu a daren saida ya rayashi da sallolin nafila ya mayar da lamarinsa ga Allah, kafin daga bisani ya samu barci mai daɗi sosai, haka ya wayi gari wasai ba tare da sauran damuwa ba, hakika ya ƙara tabbatar da duk wanda ya bar Allah to shima sai ya barshi, da tun farko ya mayar da lamarinsa ga Allah to ba zai tsinci kansa a damuwa da auren Sameeha ba. Bayan ya kammala karyawa sai ya tuna da Najwa hakan yasa shi kiranta, wayar harta tsinke bata ɗauka ba a kira na biyu ne ta dauka bayan sun gaisa yake tambayarta lafiyarta tace tana fama da ciwon kai shine yasa ma jiya bata kira ba, yayi mata fatan samun lafiya kana suka ɗan taba hira daga bisani suka yi sallama akan zai kara kira anjima yaji jikinta, yana ƙoƙarin miƙewa saƙo ya shigo wayarsa ya duba yaga number jiya ce da ko saving bai yi ba, ya duba saƙon tana cewa. Barka da safiya mai babban suna fatan ka tashi lafiya ya kwanan iyali? Na duba ka a WhatsApp sai naga baka hau ba shiyasa na gaisheka ta nan, ka yini lafiya. Guntun murmushi yayi yana cewa a fili. Allah mai mutane kowa da irin halinsa da tunaninsa, ita Najwa da zan aura bata damu da saƙo haka ba amma ga wata ta damu dani. Ya kuma sakin murmushi kana ya miƙe ya wuce zuwa bedroom dan yayi wanka ya fita zuwa gurin wani likita da aka haɗashi dashi domin tattauna matsalarsa. **** Nafeesa. Tunda ta bar gidansu Najwa take tunanin yadda zata kira Aminu, harta isa gida tana tunani, da yake ba wani aiki zata yi ba sai ta kwanta a gado ta hau facebook tana duba abubuwan da mutane suka ɗaura, a nan taci karo da wani video na wani malami da yake magana akan Monzon Allah s.a.w, yayi bayani sosai akai, wannan ne ya bata damar yin tunanin hanyar da zata ɓullowa Aminu kuma cikin ikon Allah tayi nasara har ya ɗauki wayarta kuma ya saurareta, wato taci arzikin Manzon Allah s.a.w kuma ga dukkan alamu zata cimma nasara tunda ta kula Aminu yana da sauƙin kai, koda gari ya waye ta duba shi a WhatsApp bai hau ba sai ta yi masa saƙo duk da bata saka a ranta zai mata Reply, ta ɗan tsaya kaɗan bayan ta tura taji shuru sai kawai ta kunna data ta cigaba da sabgoginta, ba jimawa Najwa ta kirata take sanar da ita abinda Shamsu yayi mata jiya, Nafeesa kamar zata kwashe da dariya dan ba karamin daɗi taji ba dama sai da tayi addu'a akan kar Allah ya bata nasara dan ta fara gajiya da son zuciyar Najwa, sai tace cikin kulawa. Gaskiya banji miki daɗin haka ba, yanzu yasa kin ji kunya, amma ni shawarar da zan baki ki ɗaure kije har gidan Sameeha ki bata haƙuri na san zata yiwa Ikram magana ta yafe miki, kin ga saiku koma zumuncinku ba tare da wani tangarɗa ba. Allah ya kyauta naje na sauke kaina gaban Sameeha, ai ni dasu mun raba jaha kowa tashi ta fissheshi, dama an gaya miki inna auri Aminu zan yarda muyi hurɗa dasu ne, hmmm nifa wlh bani ba su, kuma Shamsu yaci bashi saina yi masa mummunar tabo da ba zai manta ni ba, dani yake wasa. Daɗi na dake Najwa riƙo baki da yafiya, kuma fa ke ce mai laifin amma sai kiyi kicin kicin ki azawa mutum, kawai ki bar komai ya wuce ki fuskanci aurenki tunda ya kusa. Hmmm Nafeesa naga kin fara saduda kina bin bayan su Sameeha, kodai da wata a ƙasa ban sani ba. Haba Najwa duk abinda nake faɗa miki domin cigabanki ne kuma kin san ke tawace bazan taɓa juya miki baya ba, kiyi tunani da kyau, ba kida kuɗi ko ƙarfin da zaki tunkari Shamsu ki rama abinda ya yi miki, dan wlh idan kika dage sai kin rama to kwaɓarki zata yi ruwa kuma ina mai tabbatar miki da zaki saka kanki a matsala, suna da mulki da kuɗi ke kuma ba ki da komai tunda baki auri Aminu ba balle kiyi tutiya dashi. Hmmmm Najwa ta sauke ajiyar zuwa domin duk maganar Nafeesa gaskiya ce, hakan yasa ta karaya tace cikin sanyin jiki. Shikenan na bar komai ya wuce, amma yaushe zamu haɗu mu fara shirin bikina tunda lokacin ya fara matsowa zan mayar da hankali akan haka. Yauwa ko kefa, kibari next week mu huta sosai lokacin sai mu haɗu mu yi maganar, sannan ya batun zuwa gurin malamin dana baki shawara. Sai kin zo muyi maganar. Cewar Najwa, da haka suka yi sallama. Haka Najwa ta kama ƙumbiya ƙumbiyarta bata bari Inna ta gane komai ba, dan dagewa tayi ba tada lafiya shiyasa bata je gidajen Amare ba, saboda Inna ta matsa lallai sai taje amma ganin ba lafiya ce da ita ba yasa ta rabu da ita kuma yadda ma taga bata fita ko ina yasa ta yarda da rashin lafiyar nata har tana saka Sadiq yana siyo mata magani. ***** Sameeha. Satinsu ɗaya da amarci Ibrahim ya koma Abuja a cewarsa sati na sama zai zo ya tafi da ita, to tunda ya tafi ta tare a sashin Hajiya barci ne kaɗai ke mayar da ita ɓangaren ta, ba karamin daɗi Hajiya taji ba saboda yadda Sameeha ta mayar da ita mahaifiyarta, in dai tana sashin bata bari ta kauda ko tsinke ita ke komai hatta abinci ita ke dafa musu bata bari masu aiki su girka, cikin ƙanƙanin lokaci ta shaƙu sosai da Hajiya tun tana kunyarta har ta ware suke shan hirarsu. Ikram ma tazo a kwanakin ya kai sau uku Shamsu ke kawota ya tafi aiki sai dare yake zuwa ya ɗauketa, Khairy itama tana jin labarin yadda Sameeha ke yini a gidan Hajiya hakan yasa itama koda yaushe tana hanya da ita ake komai, yanzu ne suka san sun samu surukai, saɓanin Nabila da take nuna musu ko in kula bata damu dasu ba balle su saba suyi jiki da juna. Lokacin da Ibrahim zai tafi ne ya ɗauki Sameeha ya kaita gidan Nabila, baa ta wani sake fuska ba sai wani fuska take a dole ga uwargida, sai dai duk yadda tayi zaton ganin amarya tafi ƙarfin tunaninta domin ta ganta babu raini matar fita anguwa ga kyau ga diri dan har ta fita cikar halitta, ganin bata amshe su yadda ya kamata ba basu jima ba suka bar gidan, shi dama Ibrahim ya haɗasu ne dan su saba koda baya nan Sameeha zata iya zuwa mata suyi zumunci, amma ga yadda ta nuna bata yi marhabun da hakan ba shiyasa Sameeha bata ƙara bi ta kanta ba, ta tsaya iya gidan Hajiya. * Ranar Juma'a ya kama kwana sha uku da aurensu ranar ne suka shirya zuwa gidan Umma suyi mata yini, dan washe gari Ibrahim zai zo lahadi kuma su wuce Abuja. Atamfa Sameeha ta saka green mai kyau ɗinkin riga da siket, sai ta saka hijab bata ɗaura ɗankwali ba ta ninke ta saka a jaka, a ranar ta fara fita da sabuwar motarta, kafin ta wuce sai da ta biya sashin Hajiya tayi mata sallama kana ta fito ta wuce gidan Ikram ta ɗauketa a mota dan dama haka suka shirya, kuma Ikram bata iya tuƙi ba tukunna sai an koya mata, itama Ikram atamfa tasha pink tayi kyau masha Allah duk kansu sunyi kumari ga hasken hutu daya fara ratsasu, duk da Ikram baƙa ce amma tayi haske kaɗan kuma ta murje sosai, haka suka wuce gidan umma suna hira a tsakaninsu wanda duk rabi na kewar gida ne da suka yi. Dama umma tasan da zuwansu dan haka ta rangaɗa musu waina da miya da kuma lafiyyyen farfesun naman rago wanda yaji kayan haɗi, koda suka isa sun samu ta gama komai su take jira, Zaidu da Anwar sun tafi Masallacin juma'a ita kaɗai suka samu. Suma saida suka gabatar da sallah kafin suka zauna a falo suka kara gaisheta sannan suka shiga hirar yaushe rabo, umma taji daɗi matuƙa da ganin yaranta cikin kyakkyawar kamala, hakan yasa ta ƙara samun natsuwar ruhi da kuma godiya ga Allah daya nuna mata wannan lokacin da kuma ni'imomin daya yi musu, su Zaidu da suka dawo nan chapter ta ƙaru suka shiga hira sosai cike da farin ciki da annashuwa, bayan sun gama ciye ciyensu suka fito tsakar gida kan babban tabarma da suka saba zama suka ci-gaba da hira, a cikin hirar ne Zaidu ya sako zancen yaran Sameeha yana cewa. Yanzu Sameeha gashi zaki koma Abuja kinga kin ƙara kusa dasu Amrah, da Aminu shi mai mutunci ne da ya baki su su zauna a gunki in sunyi hutun makaranta suje masa. Taf kaima kasan ba mai yuwuwa ba ne yadda Aminu ya ɗauka da zafi, tun rabuwarsu ƙiri ƙiri ya ki kawo su balle ya iya bar mata su, kawai dai dole zata nima inda suke tana zuwa ganinsu ko ya kawo su suna yi mata yini. Cewar Ikram, Umma ta ce. Gaskiya ba zai bada yaran nan ba, nima nafi yarda da su riƙa zuwa gaisheta su tafi dan kar a takurawa Ibrahima ko. Sameeha ta yi guntun murmushi tana cewa. Ni Allah ya saka mini dangana akan yaran, in yaso ya kawo su in ma yace bazai bada ba ya riƙe abinsa dole in su girma zasu nima in da nake. Haka suka ci gaba da hirar, nan umma ta sako zancen bikin Najwa tana cewa. Bikin Najwa saura wata ɗaya da sati guda yau, Sameeha zaki samu damar zuwa kuwa? Haba Umma dole na zo saboda Inna ba abin yadawa bace, anko ne ma ba muyi ba, zan barwa yaya Zaidu kuɗi ya saya mana Anwar ya kai mana wajen telenmu zan yi waya dashi, In an ɗinka sai a kawo umma ki aje mana, biki saura kwana biyu zan zo In Sha Allah har sai an gama komai. Aiko kin kyauta, ke Ikram tunda kina gari duk abinda ya taso in ya kama ki zo zan kiraki ayi komai dake, ina so ku shiga cikin dangi sosai a dama zumunci daku. Ni umma wlh banda Najwa taci darajar Inna da babu abinda zai kawo ni bikinta. Me kuma Najwan tayi miki dan nasan da walakin goro a miya, sam bakwa shiri kamar annabi da kafiri. Cewar Zaidu, Ikram zata yi magana Sameeha ta kwaɓeta. Amma nace bana son zancen nan Ikram, magana ta wuce miye amfanin taso da ita. Ikram faɗa mana me tayi? dan na kula sam Sameeha bata so ana faɗar laifin Najwa. Cewar Zaidu, Ikram tsalam ta miƙe daga gefen Sameeha ta tsallaka gefen Umma da yaya Zaidu ta zauna tsakiya dan kar Sameeha ta kai mata hannu, nan ta shiga basu labarin duk abinda ya faru lokacin biki, Umma salati ta riƙa yi tana tafa hannu sosai suka yi mamakin Najwa, Zaidu yayi 'yar dariya yana cewa. Ahaf sai dai ba Najwa ba, wlh zata aikata fiye da haka ma, na karanci yarinyar nan kamar yunwar cikina tana mugun son abin duniya da hangen na sama da ita, kunga kuwa daga haka sai Hasssada da kyashi ya samu gurbi a zuciyarta, Allah ya kyauta sai yanzu na ƙara godewa Allah daya rabani da ita, dan wlh ba zan jure wannan halin nata na son rai ba, taje can ta yiwa wani. Wlh yaya ta bani mamaki ai kaga da kunya tazo inda muke, har yau bata san kalar ɗakunanmu ba dan bata zo ba. Cewar Ikram, Zaidu yace cikin taɓe baki. Taya zata zo ta tafka abin kunya, ai wlh Najwa sai dai taci darajar Inna aje mata biki amma da dan halinta ne kare ba zata gani ba. Allah ya kyauta ya shiryeta ni wlh lamarin ta ya fara bani tsoro. Cewar Umma, Sameeha tace. Ai sai dai addu'a dan kuwa in da tayi nadamar abinda ta yi to da ta tako ƙafarta tazo gidajenmu ta bamu hakuri, ke kuma Ikram kin kyauta da kika fasa maganar, sai dai dan Allah mu barshi a tsakaninmu kar wanda ya nuna mata. Dama wa yake da lokacinta, darajar inna dai zata ci Allah yasa ta zauna a auren, dan wannan bakin hali gareta. Zaidu bana son haka dan fata na gari lamiri, duk lalacewarta jininmu ce fatan shiriya za muyi mata. Cewar umma, haka suka cigaba da hira har aka kira sallar La'asar suka tashi kowa yaje ya gabatar da nashi. Sai gabda Magrib su Sameeha suka bar gida, umma ce ma ta korasu da so suka yi sai bayan sallar isha'i su tafi tace bata amince ba su tafi ido na ganin ido, cikin farin ciki suka rabu da juna bayan sunyi guzurin sauran waina da farfesu, sannan Sameeha ta turawa Zaidu kuɗi masu kauri akan ya ƙara musu kayan abinci sannan Ikram ta bada dubu hamsin akan akaiwa Inna gudunmawarsu su duka, Zaidu kuma ya bawa umma dubu ashirin ta bada nata gudunmawar, wannan ahali suna cikin rufin asirin Allah da kuma kwanciyar hankali. Samedha sai da ta sauke Ikram a gida kafin ta wuce gidanta itama, a sashin Hakiya ta yada zango da tsarabar data soya a cewarta Umma ce ta ce a kawo musu tare da waina da farfesu, wanda Hajiya shi taci a abincin daranta, dan tana son waina sosai kuma taji dadin wannan, sai wajen ƙarfe goma saura Sameeha ta bar sashin Hajiya ta wuce ɓangaren ta. Washe gari Ibrahim yazo tunda ya dawo bai zauna ba dan haka a gurin uwargida ya sauka ya kwana, washe gari ma ya ƙara kwana sai ranar monday suka bar Kaduna da Sameeha. Koda suka isa Abuja gida ne mai matukar girma da kyau shima gidan sama ne har yafi gidanta na Kaduna kyau da tsaruwa, haka ta fara sabuwar rayuwa a gidan, Allah yasa akwai maikata har da me aiki wata dattijuwa mai suna iya, cikin kwana biyu ta saba da ita har suke ɗan taɓa hira in ta sauko ƙasa, saboda Ibrahim In ya fita tun safe sai dare yake dawowa, Sameeha bata yarda ta zauna ba dan ita ke girma musu abinci, sai dai Iya ta girka nasu da masu aikin gidan. A rana na uku ne Ibrahim ya kaita gidan Anty Amina can ta wuni sai dare ya biya ya ɗauketa suka koma gida. *** Ranar asabar. Da yamma Ibrahim ya ɗauketa zuwa wani super market dan tayi siyayyan kayan abinci data duba babu wasu a cikin cefanen da aka yi mata, Ibrahim yasha ƙananun kaya yayi kyau ita kuma ta saka ash ɗin jallabiya tasha aiki ta yane kanta da gyalen abayar, suna isa suka yi parking Security suka fito suka buɗe musu motar dan dama suna biye da motarsu a baya, sannan suka take musu baya suka shiga ciki, wani sucurity ya kamawa Sameeha keke ita kuma tana zabar abinda take so tana sakawa a ciki. Aminu tun shigowarsu ya angeta sai yayi sauri ya tare yaran kar su ganta saboda tare dasu ya zo siyayyar kayan ciye ciye na makarantarsu, tunda ya ganta zuciyarsa ta shiga bugawa da sauri da sauri yaga ta sauya komai nata ya nuna hutu da jin daɗi, yadda yaga Ibrahim yana take mata baya yasan mijinta ne kuma dama ya waye shi tunda Senator Ibrahim dole mutane sun waye shi, ko ba a fili ba a hoto ko a tv, Allah Allah ya riƙa yi su fita dan kar yaran su ganta shiyasa yayi sauri ya jasu suka isa wajen biyan Kuɗi duk da basu gama sayayyar ba, ya biya kuɗi aka zuba musu a leda ma'aikata gurin suka kai musu mota, ya buɗe mota da sauri yaran suka shiga shima ya shiga mazaunin driver yana shirin tada mota, Sameeha ce ta fito da sauri zata ɗauki wayarta data bari mota akan zata kira iya mai aikinta ta tambayeta wasu abubuwan da babu a kitchen ɗinsu na abinci su saya musu, Abi shine ya fara ganinta yayi wani zullo yana cewa da ƙarfi. Laaaa Abba ga Mamanmu wlh ita ce mamanmu ce, Amrah ga Mama. Amrah ta shiga raba ido tana kallon inda Abi yake nuna mata, aiko tana tozali da Sameeha ta buɗe mota ta fita da gudun ta bi ta isa gurin Sameeha data buɗe mota ta miƙa hannu dan ɗaukar wayarta sai taji an faɗa mata ta baya an riƙe ta da ƙarfi ana haki ba tare da anyi magana ba, da sauri ta juyo dan taga waye sai kawai tayi tozali da Abi yanata yi mata dariya ga hawaye kwance aidonsa, Amrah kuwa taƙi sakinta dan ta ruƙunƙumeta tana kuka, dan ji take kamar zata ɓacewa ganinta, Sameeha cikin rawar murya tace. Abi Amrah kune, in abbanku? Yana mota har zamu tafi mun gama sayayya naga kin fito daga ciki ashe Mama kina cikin garin nan baki zo ba. Mama wlh saina biki gida bazan koma gurin Abba ba. Cewar Amrah data ɗago tana kallonta ido shaɓe shaɓe da hawaye, kallonsu kawai take yi yaran sun sauya mata dan sosai suka ƙara yi mata girma ga fresh da suka yi na hutu, ta tabbatar suna samun kulawa mai kyau a gurin mahaifinsu. Ibrahim ne ya fito ya dubata dan yaji shurun yayi yawa sai ya hangeta tare da yara suna magana, ya ƙaraso security na biye dashi su biyu, yana ganin yaran ya tabbatar da yaranta ne saboda Amrah tayi kama da ita sosai, cikin fara'a yace. Ko ban faɗa ba yaranki ne ko? Big boy ya sunanka.? Ya miƙawa Abi hannu sai dai mai miƙa mata ba ya tsaya yana kallonsa dan bai waye shi ba, Sameeha ta dan yi murmushin yaƙe tana cewa. Abi shima babanku ne ka amsa masa magana mana. Abi yace sunana Adam, wannan kuma Ƙanwata ce Amratu. Masha Allah Allah ya muku albarka Amin. Hajiyata ya aka yi kika haɗu da yaran nan. Suma siyayya suka zo yi sun gama zasu wuce shine suka hango fitowata. Ayya to bari na jiraki ki gama da su kin san nan ɗin ba tsaro sosai. Cewar Ibrahim kana ya buɗe mota back seat ya zauna ya rufe ya shiga amsa waya, Aminu yana hango su amma yaƙi zuwa ganin yaran zasu bata masa lokaci ya fito yana kwala musu kira. Kai Abi Amrah kuzo mu wuce. Ni dai Mama ke zan bi. Cewar Amrah tana maƙewa babansu kafaɗa, Abi da yake yaron yana da wayo ya fahimci wani abu dan haka ya isa gurin Amrah yace. Kizo muje Abba zai kaimu gurinta kinji. Ni dai ba zan je ba. Haba Amrata Abban kike cewa ba zaki bi shi ba, kije zan zo har gida na ɗaukeku, karki ɓatawa Abba rai yayi fushi, ko kina so Allah ya saka ki a wuta ne kin ɓata masa rai. Cewar Sameeha, Amra ta girgizata mata kai alamar bata so Allah ya sata a wuta sai Sameeha ta kama hannunta ta jata tana cewa. Yauwa yarinyar kirki kije gurin Abba da kaina zan zo na ɗauke ku. Amrah bata ce komai ba sai ɓata fuska data yi a haka har suka isa gurin motarsu Sameeha ta buɗe back seat ta tura Amrah ciki kana ta rufe motar ta juya ta kalli Aminu tana cewa. Nagode da ganin yarana cikin kyakkyawar kamala, amma ina so ka gane ka daina ɗaukar alhakinmu domin ni dasu muna buƙatar juna. Tana gama faɗar haka ta juya ta wuto gurin mijinta ko waige bata yi ba, duk da zuciyarta a karye yake abu kaɗan zai iya saka ta fashe da kuka, dan sosai kewar yaranta suka taso masa har take jin wani damuwa a zuciyarta, Aminu kam bai ce mata komai ba ya buɗe mota ya shiga ya kunna ya rufe ta ciki dan kar Amra ta yi yunƙurin buɗewa, ya jasu suka wuce Amrah tana kwalawa Sameeha kira tana kuka. Maama, maaamaaa mun tafi dan Allah ki zo ki ɗauke mu. Sameeha buɗe mota tayi ta shiga ta zauna gefen Ibrahim ta shiga matsalar kwalla, bai ce mata komai ba ya cigaba da hidimarsa domin kishi ya motsa, dan gani yake ganin Aminu ne ya sata kuka ba yaran ba. Tofa... [7/7, 13:04] Buhainat😁: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shai wanidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.* 40. Sameeha tana kuka tana sharewa Ibrahim ya muskuta alamar zai fita daga motar yana cewa. Da alama siyayyar nan ba zai yuwu yau ba tunda ganin tsohon mijinki ya tada miki hankali, ban zaci har yanzu kina son sa ba ai. Da sauri Sameeha ta ɗago kai tana mamakin maganarsa sai a lokacin ne ma ta fahimci fuskarsa ta sauya bata wani ɓata lokaci ba ta matsa ta rungumeshi ta gefe tana share hawayenta. Ni ba saboda shi nake kuka ba domin koda na ganshi babu abinda naji a raina saboda ka gama maye gurbin zuciyata, ni 'ya'yana ne suka bani tausayi saboda ya rabani da su, ƙiri ƙiri tun da muka rabu ban sake saka su a ido ba sai yau, haka suma yaƙi bari suzo inda nake, Amrah ce ta saka ni kuma da zasu wuce take maganar in zo in ɗauke su. Sauke ajiyar zuciya yayi yana cireta daga jikinsa ya juyo da kyau suna kallon juna yana cewa. Nafahimta amma me zaisa shi yin haka bayan ba rabuwar tashin hankali kuka yi ba, ai ba a raba uwa da 'ya'yanta dan sai mutum yaji kunya, idan kinsan inda suke gobe In Allah ya kaimu sai driver ya kaiki ki gansu, in ya baki yaran sai su zo su zauna damu ni ba ni da damuwar haka. Nagode nagode Mahboob ɗina kuma ni ba zan je ba domin in ya kula ina son ganin yaran zai nima muzguna mini, idan sun dame shi da kanshi zai kawo su. Hakane, yanzu ina gani ki zauna bari na saka security su ƙarasa siyayyan'r dan bazan so ki fito haka ba. Ina ganin ma a haɗa kayan da muka siya in yaso sai a aiko a ƙarasa siyayyar zuwa gobe in Allah ya kaimu. Cewar Sameeha, nan take Ibrahim ya kira ɗaya daga cikin security ɗinsa ya bashi umarnin ya amso kayan da suka ɗiba ya haɗa masa da ATM ɗinsa, ba jimawa ya dawo suka saka kayan a bayan boot kana ya saka wani security ya jasu shi kuma yana maƙale da Sameeha a baya ya rungumeta suna duba wani abu a yawarsa, suna yi suna hira ƙasa ƙasa tare ɗan murmushi kan fuskarsu a haka suka isa gida. Sameeha sam ganin Aminu bai wani dameta ba saboda tana da Ibrahim daya maye mata gurbinsa, sannan ma a wasu abubuwa na rayuwar aure Ibrahim yafi Aminu gogewa da wayewa sosai, shiyasa komai in yana yi mata take ganinsa a sabo dan bata saba da hakan ba, yanzu ne dai take kokarin sabarwa kanta, yaranta sune damuwarta kuma sune burin da ya rage mata ta gansu kusa da ita amma ta kula Aminu ya ɗauki lamarin da zafi, amma dole zata zuba masa ido taga iya gudun ruwansa dan dole wata rana zai nimeta akan yaran. **** Aminu. Koda suka isa gida rigimar da Amrah ta saka masa yayi matuƙar bashi haushi har sai da ya kai hannu ya bige ta abinda bai taɓa yi ba, wanda in za a bincika zuciyarsa cike yake da haushin ganin Sameeha da wani ya haifar da fushinsa, ganin yadda ya daki Amrah yasa Abi ya natsu suf-suf ya shige falo ya barsu a farfajiya, ya samu baaba a ɗakinta ya sanar da ita komai, sai ta fito falon ta samu Aminu a zaune ga Amrah can gefe tana kuka, wajenta ta isa ta fara rarrashinta kafin ta ce su wuce ɗakinsu su rage kayan jikin su tana zuwa, sai da ta tabbatar sun wuce kafin ta duba Aminu rai ɓace tana cewa. Kasan kana son mamansu ka saketa, ai da sai ka zauna da ita duk laifin da tayi maka, taya zata kuhunta yara da laifin da basu aikata ba, Aminu kada da son zuciya ya rufe maka ido ka riƙa aikata ba daidai ba, taya zata raba yara da uwarsu alhalin tana raye, duk da kun rabu wlh baku rabu ba domin yaran nan sun riga sun haɗa ku, idan kai ba zai yuwu kayi zumunci da ita ba to su bai dace ka shiga tsakaninsu ba, naga ma ƙoƙarin Sameeha data zuba maka ido har tsawon wannan lokacin bata buƙaci ka dawo mata da yara ba, in wata ce wlh kotu zata kaika tunda in Abi Musulunci ya baka ka riƙe shi ai Amrah musulunci ya bawa Sameeha damar ta riƙe ta har sai ta kai munzalin balaga, kayi tunani da kyau idan ƙanwarka aka yiwa haka ko ɗiyarka zaka ji daɗi ne, yau ko baram baram kuka rabu bai dace ka rabasu da uwarsu ba dan ba a sauyawa tuwo suna, uwa uwa ce ba a shiga tsakanin ɗa da uwa. To Baaba In Sha Allah zan gyara. Ya dai fi maka tunda kaga aurenka yana ƙaratowa sai ka kaisu can wajen mahaifiyarsu, mu mu tafi Kaduna ayi biki damu na yi zumunci da 'yan uwa, in yaso kaima sai ka samu damar ganawa da Amaryarka ba tare da takuran yaran ba, ni in an kammala biki zan komon nan Abujan na samesu, in ka dawo shikenan. To baaba za a yi yadda kika ce, Allah ya kaimu lokacin. Ta amsa da Amin kana ta miƙe tabi bayan yaran, shi kuma Aminu ya shiga mazarin maganarta, kuma tabbas yasan gaskiya ta faɗa amma a zuciyarsa bai so yaran su zauna hannun Sameeha ba, amma tunda Baba ta saka baki zaiyi haka ya huta tunda zai zamu damar yin bikinsa kuma shima zai zo Sameeha tasan aure zaiyi, hakan zai bashi damar ta gane ya samu lafiya taji haushi, wanda kuma lafiyar har yanzu bai samu ba yanata lallaɓawa ne da shan magunguna da aka ɗaura shi, wanda dai har yanzu ba wani sauyi. A ranar da dare ya kira yaran yayi musu alƙawarin zai tura su gurin mamansu su zauna a gurinta saboda zai yi tafiya shi da baaba, a can zasu cigaba da zuwa makaranta, amma sai nan da karshen wata, sunji dadi sosai duk da ba a daɗe da shiga sabon wata ba dole suyi hakuri har lokacin tunda yayi musu alƙawarin haka. **** Najwa. Shirye shirye take yi sosai dan ta mayar da hankali kan bikinta, gashi an bugo kati tana ta yawon rabo ita da Nafeesa, wanda a cikin hakane suka koma gurin malamin nan ta bashi kuɗi akan yayi mata aikin da ko Aminu ya ga itace matarsa bazai yi mata wulaƙanci ba balle ya rabu da ita, malam ya tabbatar da aiki kamar yankan wuka haka zai yi mata, daga bisani suka wuce Nafeesa tana ƙara mata ƙarfin guiwa, wanda ita kuma a bayan fage tana ta tusa kanta ga Aminu, a yanzu har ta fara jan ra'ayinsa yana charting da ita duk da ba wani hira suke yi ba amma sukan ɗan taɓa hirar duniya, sannan ma yayi mata alƙawarin duk in ya shigo Kaduna zai zo su gaisa, kuma ya sanar da ita aurensa tayi masa fatan alkhairi da addu'a, ganin bata nuna masa komai ba kan batun aurensa yasa shi ƙara sakin jiki da ita, dan a tunaninsa ƙila sonsa take yi da take yawan matsa masa da waya ko text sai kuma yaga saɓanin haka. Biki saura kwana biyu. Aka kawo akwatin Najwa guda Huɗu da kit yaji kaya ba laifi su Hauwa sunyi kokari sosai sun gwangwaje Najwa, maza suka kawo akwatin hakan yasa babu wanda ya gane daga dangin Aminu ne aka kawo dan sai da suka kawo a daren jiya inna ta kira 'yan uwa yau suka zo ganin kaya ciki har da Umma, ta kira Ikram yazo tace ba zata samu zuwa ba saboda ta tafi gidan Khairy kuma ƙarya ne ba inda taje zuwan ne ba zata yi ba dan tace sai ranar ɗaurin aure zaje ita da Sameeha. A ɓangaren Najwa sam kaya baiyi mata ba yadda take so, amma ya zata yi tasan dai bata isa ta haɗa kanta dasu Sameeha ba, tunda ko ƙaramin zinari basu saka ba sannan babu key mota a ciki, kadaran kadahan ta nuna farin cikinta. A lokacin da Nafeesa ta zo ta gani sai da Najwa tayi mata ƙorafin akwati bai mata ba Nafeesa tayi dariya tace cewa. Niko banga aibun akwatinki ba Najwa domin sunyi ƙoƙarin saka miki kaya masu tsada, ni da zan samu irin haka zan so wlh, Allah ya saka ni a damshin ki. Haba haba wlh kiyi fatan naki yafi nawa, ai ni Hauwa ta bani mamaki duk cika bakinta bata saka kaya na gani na faɗa ba, yanzu haka Aminu ya bata kuɗi masu yawa ta coge wasu dan nasan halinta da mugun son banza. Hmmm yau keda Hauwa za a ji kanku kenan, aiko sunyi ƙoƙari Najwa ki godewa Allah a haka. Hmmm kina zaton yadda suka yiwa Sameeha haka zan zuba ido suyi mini, ai wlh mace tayi katdan duk ubansu zanci ki dai zuba ido kiyi kallo duk zan yi maganinsu, ba dai buƙatata ta biya ba to an gama magana. Ohhh Najwa Duniya, wato kice shigo shigo ba zurfi kika yi musu dan ki cimma muradinki. Hahaha Nice fa ake faɗa miki, kina zaton Hauwa ta yarda da aurena ne hakanan, hmmm to itama taga zata juyani ne yadda take so ne shiyasa ta dage da ayi auren domin cikar muradinta, saboda Sameeha ma turje musu data yi yasa suka tsaneta. Lallai kice kowannenku yana da manufa a auren nan, to Allah ya baki sapa a kansu, dan wlh in kika yi musu bore ba ƙaramin rikici da tashin hankali zaki jawowa kanki ba. Ki dai bari ki kama Aminu a hannu yadda zaki ji daɗin yi musu abinda kika yi niyya. Murmushi Najwa tayi dan ita kaɗai tasan yadda zata yi maganin su Hauwa, sai sun ce Sameeha nafila ce dan ba zata ɗauki iskamcin da suka yi mata ba. ***** Abuja. Sameeha ta gama shiri a ranar juma'a zata tafi Kaduna domin bikin Najwa, wanda Jirgin kasa zata bi tare da securety saboda shi Ibashim ba zai samu zuwa ba dalilin aiki, ranar Alhamis tana zaune a falon ƙasa tana magana da Ikram a chart sai ga kiran Aminu ya shigo wayarta, bata yi mamaki ba dan tasan dole watarana zai nimeta dan tasan yaran zasu matsa masa akan ya kawo su gurinta, ya kusa katsewa kafin ta ɗauka suka gaisa kana ya sanar da ita zai kawo mata yara saboda aurensa ya matso, tayi mamaki sosai wanda yasa ta kasa haƙuri tace. Ashe ka samu lafiya kenan? Wacece zaka aura? Allah yasa wacce zata kula mini da tarbiyyan yarana ne. Inna samu lafiya inma ban samu ba wannan bai shafeki ba, ki tura mini adireshin gidanki driver zai kawo su yanzu. Tace ok tare da yi masa fatan alkhairi bata jira amsarsa ba ta kashe waya, nan take ta tura masa adreshinta ta massage, sai ta miƙe da sauri ta hau sama dan ta duba ɗakin da zata sauke su, sosai ta samu kanta a farin ciki wanda har a fuskarta ya nuna, ta kira Ibrahim ta sanar dashi shima murya ya tayata yace ta gyara musu masauki kana yace zai tawo musu da kayan ciye ciye na tarba dan sosai yake so ya saba da yaran, suka yi sallama ta cigaba da shirya ɗakin kusa da nata akan Abi ya zauna a nan Amrah ta sauka a ɗakinta, ita kuma ta riƙa kwana ɗakin Ibrahim dan dama nan ne makwancinta basu taɓa raba ɗaki ba in yana gari sai dai in baya gari ne take kwana ɗakinta, tayi kamar ta kira Umma ta faɗa mata sai kawai ta fasa dan dasu zata je Kaduna suga su Umma in yaso lahadi ko monday sa dawo saboda makarantarsu duk da taso sai tayi sati biyu kan ta koma amma saboda yaran zata dawo da wuri. Wajen karfe biyar da rabi sai gasu Driver ya kawo su ya sauke su da kayansu ya juya, Sameeha ta fito da saurinta suma suna ganinta suka ruga suka rungumeta sai farin ciki suke, ko ba komai zasu ɗebe mata kewarsu kwana biyu, tunda aure yayi tasan zai kwana biyu a Kaduna bai dawo ba in ya dawo ma da amaryansa yana buƙatar kaɗaicewa da ita, haka suka wuce cikin falo ta wuce dasu sama, sai da ta sada Abi ɗakinsa ya aje kaya sannan suka wuce ɗakinta suka zauna bakin gado suka shiga hirar yaushe rabo, Sameeha sai tambayarsu karatu take yi suna faɗa mata, a haka har aka kira sallar magrib kafin suka yi alwala suka yi sallah a tare kamar yadda suka saba a da. Ibrahim sai bayan sallar Isha'i ya dawo ya samesu a falo sun gam acin abinci, da fara'arsa ya shiga ya same su Abi ya gaishe shi ya amsa fuska sake, Amrah kuwa gum tayi sai da Sameeha tace ta gaishe shi kafin ta faɗa, Ibrahim ya kirata ta maƙe kafaɗa sai ya shiga ciro kayan ciye ciye daga leda, Amrah tana gani ta miƙe tsalam ta isa gurinsa, sai ya lakaci hancinta yana cewa. Ba zaki zo ba sai da kika ganni da kayan kwaɗayi ko, ya sunanki?. Amrah kuma zaka baki chocolate ɗinka? Ta faɗa tana marairaicewa. Zan baki tunda kin zo guna amma daga yanzu nima Abba ne ki daina jin tsorona. Ta gyaɗa masa kai alamar to kana ya miƙa mata kayan yace ta ɗiba abinda take so, shima Abi ganin an bata dama yasa shi miƙewa yazo ya kwashi nashi, Sameeha ta miƙe tana cewa. Muje kayi wanka ka huta tunda ka samar musu abin hira nasan ba zasu damu ba. Ibrahim ya miƙe yana murmushi ya wuce ɗakinsa tana biye dashi. Sai da ta kammala yi masa komai da ta saba kafin suka fito falon suka sabu Amrah har tayi barci, Ibrahim da kanshi ya ɗauketa ya kaita dakin Sameeha kana ya fito, Abi shima yace zai kwanta Sameeha ta rakashi ɗakinsa ta dawo, tana zama Ibrahim yana cewa. Da babansu zai yi haƙuri daya bar mana yaran nan zasu riƙa ɗebe mana kewa dan ina son yara sosai. Hmmm Aminu bazai barsu ba, yanzu ma dan yanada dalili shiyasa ya kawo su, wai aure zaiyi. Aure kuma? Ya samu lafiya ne? Yace yana dubanta dan Sameeha ta faɗa masa dalilin baida lafiya ne suka rabu. Tayi murmushi tana cewa. Ya samu kenan tunda gashi zai yi aure. Ko kuma zai yi na huce takaici ba tunda ya ganki da wani mijin, ke ki barmu mu maza fa, har yanzu yana jin haushin auren da kika yi duk da shi yayi sakin, to Allah ya basu zaman lafiya, ya zaki da yaran nan kema zaki Kaduna bikin Najwa. Dasu zan tafi suje su ga su Umma, kaga sa sada zumunci da 'yan uwa. Hakan yayi amma ki sanar da babansu kar yazo kuma yaji sunje Kaduna yayi faɗa yace bazai ƙara kawo su ba. Wlh bazan faɗa masa ba in yaji ma yace bazai kawo su ba shi ya sani, yanzu ma bani nace ya kawo su ba. Allah tawan, ashe kin iya faɗa kema? Ya faɗa yana 'yar dariya itama murmushi ta mayar masa ta miƙe tana cewa suje yaci abinci ita yau taci nata da yara bata jira shi ba. Su Hajiya Meeha har an fara wareni saboda ganin yara ko, ina ganin tare ma zamu Kadunan nan. Wayyo ba haka bane Mijin so na ɗan tuna baya ne da nake ci tare da su. Amma zaka bari na sauka a gidan umma ko. Naƙi wayon a gidana zaki sauka, ko da yake gidan yayarki zan sauka har mu dawo dan haka kije gidan umma wasa nake miki. Ina godiya babban mutum Allah ya tsare mini kai ya ƙara sutura ya kare ka daga idon maƙiya. Ameen matar so Allah yayi miki Albarka ya bamu aljanna maɗaukakiya. Sameeha ta amsa da amin ta matsa kusa dashi ta manna mata kiss a gefen kuncinsa domin nuna masa jin daɗin addu'arsa, shi kuma kamota yayi ta mannata jikinsa ya shiga kissing ɗinta kamar sai haɗiye ta, da kyar ta kwace daga riƙon da yayi mata ta wuce dinning da gudu yabi bayanta yana dariya. Hmmm su soyayya daɗi amma in kayi dace da masoyi. Washe gari. Ƙarfe goma da kwana a Kaduna tayi musu, su Abi sai murna suke yi da farin cikin son ganinsu Umma, da driver ya ƙarasa dasu ƙofa suka fita da sauri suka shiga gidan da gudu, Sameeha tana dariya tace. Yau zamu sha karamniya. Ai gwara kusha, yaushe rabonsu da haka. Cewar Ibrahim, haka suka fito suka jera zuwa cikin gidan. Umma tana ɗaki taji ihunsu Abi da sauri ta fito dan ta tabbatar saboda abin da mamaki, suna ganinta suka isa suka rungumeta ƙam suna murna, bata dawo daga mamakinta ba sai taga shigowar su Sameeha wanda a zatonta Aminun ne ya kawo yaran, har suka ƙaraso Ibrahim ya rusuna har ƙasa ga gaisheta ta amsa fuska sake tana cewa ya shiga ciki mana ya zai tsaya a waje, yace yana sunne kai ƙasa. Umma zan dawo anjima yanzu ana jirana ne, na dai shigo ne mu fara gaisawa. Allah Sarki to ba damuwa Nagode Allah yayi albarka. Ibrahim ya amsa da amin kana yayi musu sallama ya wuce, su kuma suka shiga ɗakin umma suka zauna, umma ta kasa haƙuri tana cewa. Sai gaki tare da yara ya aka yi haka? Hmmm bari dai mu huta Umma zan baki labari, ina Yaya Zaidu da Anwar. Sunje kasuwa yin cefane, Ikram ma tana hanya tace zata zo tunda taji a gida zaki sauka wai itama zata zo ta kwana biyu. Mayyata kenan, duk abinda nayi sai ta kwaikwaya, tazo din masha hirar da muka jima bamu yi ba. Tana rufe baki suka ji an buɗe gate an shigo, ganin sabon takalimi ƙofar ɗakin umma yasa Ikram ta buɗe murya tana oyayo Anty Sameeha, su Abi suka fita da sauri suka isa suka rungumeta, Ikram ta riƙe su tana tambayar yaushe suka zo.? Tare da Mamanmu muka zo. Abi ya bata amsa, da mamaki ta ƙaraso cikin falon tana riƙe da haɓa tace. Anty ya aka yi su Amrah suka je gunki? Kedai zauna mu gaisa kafin a kaiga yin labarin. Cewar Sameeha, Ikram ta ƙarasa ciki ta zauna tana gaida umma, daga bisani ta gaisa da Sameeha, a lokacin su Zaidu suka dawo suma suka shigo falo suka zauna suna murnan ganin juna. [7/7, 13:04] Buhainat😁: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shai wanidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.* 41. Matsuwar da Ikram tayi akan ta faɗa musu yadda akayi yara suka zo gunta yasa Sameeha basu labarin komai, sosai suka yi mamakin wai aure zaiyi Zaidu yace cikin ɗan murmushi. Auren dai huce takaici zaiyi amma yasan zai samu lafiya ya sake ki.? Ka sani ko ya dage da niman magani ya dace shiyasa zai yi auren. Cewar Ikram, Zaidu yaja tsaki. Ashe dagangan ya saki Sameeha ko da yake wataƙila dalilin zargin da yake yi mata yasa ya saketa, Allah dai ya tsinewa waɗanda suka aikata miki haka, nifa nafi zargin su Hauwa ne suka shirya miki haka dan ya sakeki tunda ba ƙaunarki suke yi ba. Ba abin mamaki bane yaya Zaidu Allah ya saka mini ya tona asirinsu. Cewar Sameeha fuskarta a dagule dan baƙin ciki take ji duk lokacin da aka tuna mata abinda waɗannan 'yan matan da suka ja mata saki uku. Umma tace cikin kulawa. Allah ya sanya alkhairi ya basu zaman lafiya yasa zata riƙe yaran nan amana. Duk suka amsa da amin kana Umma ta ɗaura da cewa. Anjima da yamma bayan sallar la'asar sai muje gidansu Najwa mu tayasu aiki zuwa dare Zaidu sai yazo ya ɗaukeku ni acan zan kwana da safe zan dawo nayi wanka na sauya kaya na koma. Nifa umma bazan je yau ba ki barmu kawai muyi hirarmu in yaso gobe in Allah ya kaimu maje. Cewar Ikram, Sameeha ta ce. Ni gida naso zuwa na gaishe da Hajiya kafin magrib sai na dawo. Yauwa muje can na rakaki Anty dan wlh badan Inna ba bazamu je bikin Najwa ba mara mutunci uwar cin Amana. Ke Ikram bana son shirme fa wai ke abu baya wucewa a gurinki ne, ni wlh bansan ina kika samo riƙo ba, sam bakya barin abu ya wuce kinta mita da naci, karna sake jin haka in ba haka ba ranki zai ɓaci. Cewar umma cikin faɗa, Ikram bata kuma yin magana ba dan Wlh sosai take jin Haushin Najwa akan abinda tayi mata, nan umma tace ta tashi ta sauya kaya ta shiga kitchen ta ɗaura musu abinci, haka ta miƙe ta shiga uwar ɗakan umma ta sauya kayan jikinta ta fito zuwa tsakar gida dan ɗaura girki, su Umma suka cigaba da hira Anwar ya fito dan ya yiwa Ikram jajjage. Da yamma umma ta tafi gidansu Inna su Sameeha kuma suka wuce gidanta ita da Ikram da yaran gabaɗaya a motar zaidu daya kaisu, daga nan Sameeha zata ɗauki tata motar dan suyi amfani da ita gurin biki. **** Hauwa. Suna can babban gida ana ta aikin biki ba kama hannun yaro, dan sosai suka yi gayyatar 'yan uwa da abokan arziki saboda su nunawa duniya wannan karan biki nasu ne sai abinda suke so yake faruwa, shiyasa tun biki saura kwana biyar ta koma babban gida da kwana uzuri mai ƙarfi ke kaita gida ta yi ta dawo, tun jiya take zuba ido taga 'yarta Adama tazo dan haka suka yi da ita in biki saura kwana biyu zata zo ta kwana har sai an kammala biki washe gari ta koma, ta kuma kiranta a waya bata ɗagawa hakan yasa ta ce in yamma tayi bata zo ba zata aika ɗanta yaje yaji ko lafiya. Ɓangaren Adama kuwa tun shekaran jiya laraba take yiwa mijinta mitar ya barta Alhamis taje gida bikin kawunta yace shi bai amince saboda ya gaji da yawan fitanta, ta bari ranar bikin Asabar sai taje washegari kuma ta dawo wato kwana ɗaya ya bata, tace ita fa hakan bai yi mata ba nan ya fice ya barta tana surutai. Washe gari haka ta kuma yi masa magana zata tafi yace bai amince ba saboda baƙin ciki har da kuka tayi masa amma ko a jikinsa ya ficewarsa. Yau Juma'a tana ganin ƙila ya barta taje tayi kwana biyu amma sai yace sai fa ranar biki zata je, nan ne Adama ta zage tayi masa rashin mutunci ta inda take shiga bata nan take fita ba, haushi ya rufe mijin nata bai san sadda ya rufeta da duka ba ita kuma ta shiga auna masa zagi tana yi masa Allah ya isa, takaici yasa mijin yace cikin fushi. Tunda baki san darajata ki je gida na sake ki saki uku, na gaji da halinki kullun cikin ƙunsa mini baƙin ciki kike yi, sannan nasan kina yi mini asiri amma na jure saboda nasan baya tasiri akaina domin duk abinda kike yi kin fallasa shi a kunne na ji, darajar yaranmu naketa dubawa amma tunda lamarinki ya zama haka na gama datse igiyar auren, yara kuma mahaifiyata zata riƙe mini su sai ki tattara ki tafi gidan ubanki kisha shagalin biki da hujja, ko ki yiwa Kawun naki zaman ɗaki tunda kin zama sakakkiya. Na shiga uku Basiru ni ka saka, dan Allah na tuba ka janye sakin nan wlh ko bikin ba zani ba, wayyo Allah na tono mini asiri dan Allah ka rufa mini. Hmmm daga baya kenan, kuma saki uku nayi miki ko ke mahaukaciya ce baki tantance saki. Innalillahi wa inna ilaihir raji'un, a cikin fushi kayi dan son Manzon Allah da darajar Umma ka mayar dani ɗakina, saki uku cikin fushi saki ɗaya ne, Basiru nice fa Adamarka karka mance soyayya da ƙauna. Ina cikin hankali nayi wlh sarai nasan me nake yi, saki uku nayi kuma babu zancen gyara ki tattara ki bar mini gidana tun kafin inyi miki watsi dasu, 'yar iska mara tarbiyya sai yanzu nasan na yiwa kaina zaɓen tumin dare nabi hasken fata. Yana gama faɗar haka ya fice fuuu kamar guguwa, Adama ihun kuka ta fashe dashi tana ambaton ta shiga uku ta lalace, ga wajen idonta daya kumbura mata da duka har idon ya tara jini, ta miƙe ta zauna gefen gadonta ta shiga tuna rayuwarsu ta baya tasan Basiru yayi haƙuri da ita saboda ta jima tana bashi matsala, duk kuwa da tutiyarta asirin mallaka da tayi masa shiyasa take samun galaba akansa baya yi mata wani hukunci, yau kam tasan kadarinta ya karye ta kashe aurenta da kanta a dalilin auren kawunta Aminu, bata san ya zata yi da wannan ƙunshin baƙin ciki data haɗawa kanta ba, tana kallon wayarta tana ringing amma ta kasa zuwa ta ɗauka wanda tasan bai wuce maman ta ne ke kira, haka ta cigaba da kuka tana tunanin yadda makomar rayuwar zai ƙare in ta koma gidansu zawarci, ta ina zata fara? Yadda tasan halin mamanta sai a hankali tasan dole zasu riƙa kai ruwa rana musamman a gurin abinci, yaranta guda uku ta duba kiri kiri yanzu ba zasu tashi a gabanta ba, na goyen ne ya rarrafo yazo ya dafata ya miƙe yana gwalan gwalan biyun sun tafi makaranta, ɗaukanshi tayi ta goya a baya dan dama ta gama shirya shi kenan suka fara rikici da mijinta, kaico da dana sani ne ya cikata tana cizon yatsa, musamman in ta tuna irin kulawar da mijin ke bata, bata rasa ci da sha ba balle sutura dai dai gwargwado yana sauke hakkinsa na miji akanta, tana kuka ta saka hijab ta ɗauki jakar kayanta data haɗa na cin biki da kuma ƙaramar jakar gayu da takalmi da ta saya sabo na biki ta rataya ta fito ta rufe ɗakin ta ratsa matan gidansu da suke jiran fitowarta suna gulma, suna ganinta suka yi gum sai kallonta suke kamar sun samu madubi, to me ya rage mata da zata ɓoye, sakinta dai aka yi kuma ba kome, hawayen dake zuba bai fasa fita ba haka ta ratsa ta wuce, tana saka ƙafarta a waje yaji yo shewarsu dan dama gidan an haɗa makirai, shiyasa bata shiri dasu sosai saboda saka ido da gulmarsu, baƙin ciki goma da ashirin ga abin faɗa amma ba halin tayar da kwanji, dole ta wuce jiki a sanyaye ta isa titi ta samu abin hawa ya wuce da ita gidansu. Data isa gida kayanta ta aje ta fito zuwa babban gida lokacin anata ƙoƙarin tafiya masallacin juma'a, tana shiga ta tadda mata da yawa a tsakar gida ana ta hada faten tsaki a ƙatuwar tukunya, ganin basu ganta ba sunata hira yasa ta ratsesu ta nufi can ɓangaren Laure tasan Mamanta tana can, tana isa kuwa ta same su sun baje a tabarma sunata shan rake ana hira, Adama ganin Hauwa yasa ta saki kuka dan sosai kukan yazo ta kasa danne shi, Hauwa ta miƙe da sauri tana faɗin lafiya ina sauran yaran? Mutanen da suke gurin suma tambayar lafiyar suka yi kowa ya baza kunne, Hauwa ta isa gurin adana ta tsaya sai Adamar ta faɗa jikinta tana. Mama Basiru ya sakeni. Da sauri Hauwa ta toshe mata baki tana wato ido waje dan tayi matuƙar kaɗuwa da sakin, kuma bai dace mutanen da ke gurin kowa ya ji ba, qi kamar ta tona musu asiri ne maƙiya suyi dariya, sai ta jayeta daga jikinta ta kama hannunta suka wuce ɗakin Laure, matan dake gurin wannan da kallon wannan ana gulma da ido, sunƙi magana saboda tsoron rashin mutuncin Hauwa. Da suka gisha ciki har sai da suka dangana da bedroom ɗin Laure wacce suka samu ta gama shiri zata fito dan wanka tayi, ganin Adama tana kuka ta tsaya turus tana kallonsu har suka ƙaraso ciki, Hauwa cike da tashin hankali tace. Me kika yi masa ya sakeki, Adama kin tona mini asiri ina cikin tsaka da farin cikin bikin Aminu zaki zo mini da labarin daya hautsina mini hanjin cikina, Allah yasa saki ɗaya yayi miki akau kome, dan wlh bazan jure ganinki a bazawara ba a gidana, ai ABIN DA CIWO. Adama ta ƙara rushewa da sabon kuka ta shiga cewa. Akan zanzo biki tun jiya ya hana ni, yau nace masa zanzo ya tubure dole sai gobe na koma jibi, shine rikici ya ɓarke a tsakaninmu daga bisani ya rufeni da duka yana zagina nima ina ramawa, shine daga ƙarshe yace ya sakeni saki uku. Innalillahi wa inna ilaihir raji'un, na shiga uku ni Hauwa ina zan saka kaina da wannan ƙunshin baƙin cikin Adama, meyasa zaki biyeshi ki jawo ya sake ki har uku? da kin kirani ko kin ɗauki wayata da naketa kira da zance ki haƙura goben kya zo, yanzu dan ubanki ina kike so zan tsoma zuciyata tayi mini sanyi. Ashe haka saki yake da zafi? ashe ABIN DA CIWO har haka, Laure kinji tashin hankalin da yarinyar nan ta jawo mini ina tsaka da farin ciki. Sai muryan Hauwa sirƙe tayi baya zata faɗi dan sosai jikinta yayi sanyi taji kamar an cire mata lakka, Laure tayi saurin riƙeta ta zaunar a gefen gado tana cewa. Dan Allah kibi komai a hankali Hauwa In Sha Allah komai zaiyi dai dai, karki jawowa kanki wani ciwon yanzu maƙiya suyi mana dariya. Ke kuma Adama baki kyauta mana ba meyasa zaki biye shi? ai in Namiji ya kafe akan abu haƙura ake abarshi dan in kika matsa sai naki ran ya ɓaci, gashi nan kin jawo mana abin magana, Allah ya kyauta. Ta ƙare maganar tana jan dogon tsaki, Hauwa ta fashe da kuka dan shine kawai zata yi taji sauƙin baƙin cikin daya turniƙeta, Adama ma kukan ta cigaba da yi Laure kuma tana tausarsu. Duk yadda Hauwa take burin in an kammala fate zata sha sai gashi ta kasa ko da loma ɗaya ne, Adama ma ta kasa cin komai Laure ce ta ɗan tsakura dan ta gusar da yunwa, itama abin ya dameta dan duk abinda ya samu Hauwa tamkar ita ya sama saboda shaƙuwarsu, haka suka yini a ɗakin Laure sun kasa fita har aka kira sallar magrib, zuwa lokacin labarin sakin Adama ya shiga cikin gidan sai gulma ake yi, su Sa'a da salma har ɗaki suka samesu suka jimanta, dan abin bai yi musu daɗi ba ko kaɗan, haka su yaya Alhasan da Kamalu sam basu ji daɗin lamarin ba, Aminu ma daya samu labari lokacin daya zo sosai abin bai yi masa daɗi ba, haka suka taru suka dinga lallashin Hauwa akan tayi haƙuri ta sake ayi biki bayan komai ya lafa zasu bi zancen, in da yuwuwar gyara sai a gyara auren, dole yasa ta saki ɗin duk da na ciki yana ciki. **** Gidansu Najwa. Ya cika da mutane ana ta gyaran kayan abincin gobe ɗaurin aure in Allah ya kaimu, itama tanata nata hidimar dan sosai take shirin zuwa gidan miji, Nafisa kuwa ita ce amara ƙirjin biki dan komai ita ta tsara sai sauran ƙawayensu na biki, Binafa sun so zuwa amman saboda kar Sameeha ta gansu yasa suka bari sai bayan biki suje suga ɗaki ita da ƙawarta Hanan. Kowa ka gani yana cikin farin cikin bikin, umma ce takewa Inna maganar kai kayan amarya tace. Zulai ya batun kayan ɗakin Najwa ko an kaine? naga baki yi maganar ba. Wlh in gaya miki 'yan uwan ango suka sama mana sauƙi, tun saura kwana biyar suka turo da mota akan a kwashe kaya su zasu gyara mata ɗaki, mantawa nayi ban faɗa miki amma tuni aka yi gyaran ɗakinta, kaita ne ya rage. Amma kuwa sun sama mana sauƙi sun kyauta, da haka ake dangin miji aiko da ko wace mace ta dace, lallai Najwa tayi dace da dangin miji sai dai fatan zaman lafiya ya kauda sharrin shaiɗan a ciki. Inna ta amsa da amin tare da sauran matan da suke gurin, haka suka cigaba da hirar suna yabon dangin da Najwa zata shiga. Washe gari. Da wuri su Sameeha suka shirya suka tafi gidansu Najwa dan basu tsaya jiran umma ta dawo ba balle su zo tare, duk da ba haka Ikram taso ba Sameeha ce ta matsa su tafi da wuri, a motarta suka wuce tare da yara da Anwar. Suna isa ɗakin Inna suka fara shiga suka gaisheta tare da Allah ya sanya alkhairi, kafin daga bisani suka fito suka samu su Umma a tsakar gida suka gaishesu sannan suka saka musu hannu wajen gyaran alayyahun miyar tuwon shinkafa, yara kuma suka haɗu da sauran yara suka soma wasansu, Anwar kuma ya fita waje saboda shi da girmansa. Najwa koda tagansu ɗauke kai tayi zata wuce Sameeha ta ce cikin zolaye. Najwa Amarya ba magana ne ya shirye shirye, gaskiya me kwalliyar nan ta fito dake da kyau, bari nazo na ɗaukeki hotuna kuma muyi tare kafin mu ɓata namu kwalliyar. Au Sameeha ashe kun zo ya gida. Ai sai Ikram da Sameeha suka kalli juna yadda ta iya kiran sunanta ba anty gatsar cike da rashin kunya, Sameeha jiki a sanyaye ta amsa da lafiya kafin ma ta kuma magana Najwa tayi gaba, Ikram cike da takaici tace ƙasa ƙasa. Ai gashi ta nuna miki ita din mara mutunci ne, meyasa ma kika kula ta, wlh Anty Sameeha na rasa wani irin zuciya ce dake. Ki rufe mini baki bana son maganar. Sameeha ta faɗa cikin ɗaure fuska, sai Ikram taja bakinta tayi shuru zuciyarta tana tafarfasa dan burinta ta samu damar da zata nakaɗawa Najwa duka ta yadda nan gaba zata shiga shakkarsu. Wajen ƙarfe sha ɗaya da kwata aka ɗaura auren Najwa a masallacin bakin titi na unguwarsu, wanda ɗumbin mutane suka shaida kuma Aminu da 'yan uwansa sun je dan Alhasan ne ya karɓan masa auren, Zaidu yana daga can gefe yana kallon ikon Allah dan sosai lamarin ya bashi mamaki tare da girgiza lissafinsa, wai Aminu ne ya Auri Najwa, ya rasa yadda zai lissafa lamarin yayi daidai da kwakwalwarsa, haka jikinsa yayi sanyi kalau ya kasa miƙewa ya fito daga masallacin har sai da mutane suka watse kafin ya iya yunƙurawa ya fito, a daidai lokacin su Aminu suna tsaye da wasu abokansa mutum biyu, ido cikin ido suka kalli juna da Zaidu amma ya kasa ce masa komai ya saka takalminsa ya wuce zuwa gidansu Najwa, koda ya ƙaraso ƙofar gidan yaga Anwar sai yace masa yayi sauri ya kira masa Ikram da Sameeha su zo, yace to kana ya shiga gidan ya samu ganin Ikram ya faɗa mata Sameeha kuwa tana can gurin saka tuwo a leda ana kullewa, Ikram bata kirata ba dan tasan halinta ko tace tazo ba zata zo ba, sai ta fito waje ta hango Zaidu fuska a mugun ɗaure, ta ƙarasa tana cewa. Yaya lafiya naga fuskarka a ɗaure, ko ba a faura auren bane? Ikram ina Sameeha? Tana cikin gida tana aiki kasanta ko na kirata ba lallai tazo ba. Ki shiga ki kirata tazo mu tafi gida. Saboda me? Meya faru yaya? Hmmm Zaidu yayi ajiyar zuciya yana girgiza kai saboda ɓacin rai, yace cikin takaici. Kinsan wai Aminu mijin Sameeha shine ya auri Najwa, ko baku ji sanarwa bane. Mun ji mana ance Muhammad Al'amin, amma ai bamu gane shi bane, kutumelesi Najwa ta iya cin amana ta rasa wanda zata aura sai Aminu. Ta faɗa cike da ɓacin rai ta juya a fusace tayi cikin gida a guje, tana faɗawa tayi sa'a Najwa tana tsakar gida da kawayenta suna hotuna, Ikram bata yi wata wata ba ta isa gabanta ta sharara mata mari tare shaƙo wuyanta ta maƙureta ta kaita ƙasa ta shiga dukanta kamar Allah ya aikota, ƙarfinsu bazai zo ɗaya ba saboda Ikram Aljanunta ne suka tashi suke hukunci, nan fa gida ya hautsine aka shiga ƙoƙarin kwatar Najwa amma ina Ikram ta hau ruwan cikinta tana dukanta iya ƙarfinta, nan fa aka fita aka kira maza wanda Zaidu yana ganin haka ya nufo gidan da gudu ya shigo, ga Sameeha ta yi kokarin kama hannun Ikram amma ina ƙarfinsu ba ɗaya ba, Ihu kawai Najwa take saki tana aceceta zata kasheta, da kyar Zaidu ya kama Ikram ta baya ya matse hannyenta da jikinta iya ƙarfinsa ya shiga tofa mata addu'a, yayan Najwa Junaid shima ya saka ƙarfi ya taimakawa Zaidu suka ɗaga Ikram daga cikin Najwa, Najwa kuwa marayan kuka ta saki ga bakinta ya fashe yana jini fuska tayi jajir dan wahala, a haka su Zaidu suka fitar da Ikram da kyar suka saka a motarsa ya rufe ta ta waje, ya koma cikin gidan ya samu ana gogewa Najwa fuska ya kalleta cikin jajayen idonsa ya koma da kallonsa gurin Sameeha yace cikin fusata. Ina umma, je ki kirata mubar gidan nan yanzu. Yaya meye haka? Dan Allah ka tafi sannan umma. Bata rufe baki ba ya daga hannu zai kwasa mata mari saboda haushin musun data tsaya yi masa, sai ya riƙe hannunsa tunawa da wani abu da yayi ya kalleta rai ɓace a mugun fusace. Dan ubanki ki tattaro yaranki kizo mu wuce, Umma Umma kina ina. Gani nan Zaidu wai lafiya kake abu kamar wanda ya sha kwaya, Ikram ta gama nata kaima zaka ɗaura. Haba Zaidu in rai ya ɓaci bai kamata hankali ya gushe ba, kayi haƙuri ka faɗa mana me ya faru, ina kuma ka kai Ikram. Cewar Innar Najwa, Zaidu ya danƙara mata wani mummunar kallo yace cikin ɓacin rai. Dole zaki faɗi haka mana tunda burunku ya cika kin aurawa Najwa Aminu mijin Sameeha daya saka, sai yanzu ma kwakwalwata suke haɗo mini abubuwa akan 'yarki Najwa mara godiyar Allah rashin kunya da tarbiyya. Ya faɗa yana zuba guntun murmushi, Umma ce ta matso ta wanke shi da mari akan rashin kunyar da yayi wa Inna, duk da taji maganar Najwa ta auri Aminu ya daki zuciyarta amma haka ta danne, Sameeha kuwa tun sa'ilin daya faɗa ta wuce suf suf ta fice daga gidan, Zaidu ya kalli umma yana son yin magana ta daka masa tsawa akan ya fita tare da nuna masa hanyar fita, bai ce komai ba ya fice ransa a matuƙar ɓace, Inna kuwa mutuwar tsaye tayi tana jin abinda yafi ƙarfin kunnen ta, Umma kuwa ɗakin Inna ta shiga ta ɗauko hijab ta saka bata cewa kowa komai ba ta fito daga gidan, ta samesu a wajen motar Zaidu, tace. Buɗe motar mu wuce anjima zai kazo ka ɗauki motar Sameeha. Ba musu ya buɗe motar umma da Sameeha suka zauna gidan baya suka saka Ikram a tsakiya da taketa kukan baƙin ciki, Anwar dasu Abi suka shiga gaban mota sai Zaidu ya zauna mazaunin driver ya tada mota suka nufi gida. _Hmmm an zo gurin..._ [7/7, 13:04] Buhainat😁: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shai wanidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.* 42. Inna kuwa bayan mutuwar tsaye da ta yi numfashinta ne ya soma barazanar barin jikinta wanda nan take ta nima yanke jiki ta faɗi amma mutane suka tarota, suka kaita zuwa ɗakinta suka kwantar a gado tana mayar da numfashi da ƙarfi tare da zufa daya rufeta, sai sannu 'yan uwa suke jera mata idonta a rufe. Ɓangaren Najwa kuwa Nafeesa ce ta taimaka mata ta tashi tare da wata ƙawarsu, sai suka shiga kakkaɓe mata jiki kuka kawai take yi tana alwashin sai ta rama abinda Ikram tayi mata, ko kaɗan bata yi dana sanin dan sun san Aminu ta aura ba, ita taso ma ba a lokacin suka sani ba sai in an kaita suga gidan Sameeha ne ya zama mallakinta, duk da tana jin mutanen cikin gidan suna surutunta amma bai dame ta ba dan tasan watan maganar ne ya tsaya, da ɗingishi ta shiga ɗakinta ta zauna bakin gado tana shafa gashinta daya yi kura, dan tuni ɗankwalin da aka ɗaura mata yayi nashi wajen, a lokacin ne ta buƙaci wayarta domin ta kira 'yan daban da suka taɓa yiwa Jamila duka ta sakasu su je su rama mata abinda Ikram tayi mata, sai ta kalli Nafeesa tana cewa. Ina wayata.? Kin manta wayar tana hannunki da kuka soma kokawa, tuni kuka bi ta kanta taci screen, ko haske bata yi duk ta fashe tayi baƙi. Wlh Ikram taci bashi yadda ta dukeni sai jikinta ya gaya mata, kuma wlh sai na saka tayi asara kamar yadda nima nayi asarar wayata. Ta faɗa tana girgiza kai, Nafeesa ta isa gefenta ta zauna ta dafa kafaɗarta. Najwa an riga an ɗaura aurenki ya kamata ki gane yanzu rigima ba naki bane, ki barta da Allah ki fuskanci ƙalubalen dake gabanki tunda su inna sun san mijin Sameeha kika aure, sai ki tanadi maganar da zaki kare kanki. Nafeesa dan sun sani sai me, an dai riga an ɗaura ni banda damuwa da su domin dai nayi nasara da aurensa, ni yanzu in har ban rama abinda Ikram tayi mini ba ban cika sunana ba wlh. To shikenan Nafeesa tace ta koma gefe tana zuba abinci dan dama zasu ci ne suka fita waje yin hoto in sun gama su dawo su ci, Najwa sai kumbure kumbure take tana girgiza kai, ta cire sim ɗinta ta ce Nafeesa ta saka mata a wayarta saboda kar a kirata aji ba'a samu tunda akwai ƙawayenta da basu san gidansu ba, ba musu ta cire ɗayan layinta da bata cika amfani dashi ba ta saka ajaka kana ta sakawa Najwa nata sim ɗin. Baba ne da yayyin Najwa su uku suka shigo gidan, basu zame ko ina ba sai ɗakin inna, sun samu ta dawo hayyacinta tana zaune gefen gado sai dai har lokacin gumi take yi da alama in aka gwada jininta a lokacin to ya hau, ganin sun shigo yasa mutanen ɗakin suka fita baba ya samu gefe ya tsaya yana dubanta yaran kuma duk zama suka yi a ƙasa, baba yace cikin kulawa. Sannu Zulai ya jikin? Da sauki Alhamdulillahi, kaina ne ke sara mini kamar zai rabe. Allah ya sauke ya baki lafiya. Wai abinda naji da gaske ne akan Najwa mijin Sameeha ta aura, yanzu Junaid ya sameni da maganar wai har aljanun Ikram sun tashi sun yi faɗa da Najwa. Wlh malam nima a bakin Zaidu muka ji maganar tunda kasan shi yasan mijin 'yar uwarsa, sannan da shi aka daura aure, abinda ya bani mamaki da tsoro taya duk aka amsa musu bamu gane komai dan gane da haka ba, Najwa dai nasan ta san komai da haɗin bakinta da shi mijin Sameeha suka shirya komai, kuma 'yan uwansa sun san ita ce shiyasa suka ki bari aje kai kaya ashe da walakin goro a miya, hatta kayan lefe maza suka kawo dan kar mata su kawo a gane 'yan uwansa ne dan duk mun sansu. Amma wannan yarinya ta haɗa gurmi, da wani ido zamu kalli Halima, ai ana barin halal dan kunya, banji daɗin wannan lamari ba, dama ba a ɗaura ba sai a fasa amma aikin gama ya riga da ya gama. Cewar baba cike da ɓacin rai, Yaya Junaid ya miƙe a fusace ya fita zuwa ɗakin Najwa, yadda ta ganshi a fusace tasan dalili sai ta miƙe tana kallonsa yace cikin tsawa. Muje ɗakin inna za muyi magana. Yana faɗar haka ya juya, itama tabi bayansa tana ware ɗankwali ta ɗaura akai ta fice. Suna shiga ta samu gefe ta zauna nesa da 'yan uwanta, baba ya kalleta rai ɓace. Ya aka yi kika haɗu da Aminu har kuka yanke shawarar auren juna, domin an saka bikinki lokacin bai daɗe sosai da sakin Sameeha ba. Ni fa yayarsa Hauwa ta roƙeni Allah da Annabi in yarda da auren ɗan uwansu saboda ta yaba da hankalina, har aka ɗaura bamu haɗu da Aminu ba dan bai san nice matar da Hauwa ta zaɓar masa ba, saboda ita ce ta buƙaci kar ya sani, amma muna waya da juna sai dai bai ɗauki muryata ba. Yanzu dama Najwa duk wannan shirin Hauwa ce munafuka, duk yadda suke da Sameeha basa ƙaunarta amma suka jawoki a jiki domin su ƙara muzguna mata duk da ya rabu da ita, idan ita ta saka son rai a ciki ke meyasa ba zaki duba alaƙarki da Sameeha ba ki ƙi yarda da buƙatar ta, yanzu kin kyauta mana kenan? kina son ki zama silar lalawar zumuncinmu da iyalen yaya Amadu. Cewar inna cike da tsantsar damuwa, yaya Junaid ya ce cikin faɗa. Ni wlh ban yarda da maganar yarinyar nan ba karya take yi, ita tasan yadda ta tusa kanta garesu har suka yarda ya aureta, na tabbatar mugun son duniyarta yasa ta zaɓi auren mijin Sameeha. Zan yarda da bayaninka domin lokacin da su Sameeha suka bar lagos suka dawo nan Kaduna, yarinyar nan da ta je gidan ta haɗu da mijin Sameeha, ta dawo gida tana yi nuni surutu akan mijin Sameeha shine daidai irin mijin da take so ta aure, a lokacin na kwaɓeta tace mijin ta bar maganar, ashe abin yana ranta saida ta san yadda tayi ta samu ta aureshi, Allah ya wadaran halinki Najwa, basan a ina kika samo irin wannan son zuciyar ba, idan kin shuka alkhairi zaki gani haka ma in sharrin kika shuka In Sha Allah za ki gani. Inna kiyi haƙuri kar ki yi mata mugun baki, tunda an riga an ɗaura mu bita da fatan alkhairi Allah kuma ya shiryeki. Inji Sadiq da yake shi ustaz ne, nan dai suka cigaba da yi mata faɗa, suka yi mata kaca kaca Najwa dai sunne kai tayi tana ta ƙunƙune sam babu abinda ya shiga jikinta na faɗar da suke yi mata, cewa ma take a zuciya. Na kusa bar muku gidan gabaɗaya na huta, kuma wlh sai kun nimeni zan zo ma gidan. Tana faɗe tana kwafa, su kuma suna cigaba da yi mata faɗa, daga bisani suka yi mata nasiha sai suka sallameta ta fito su kuma suka cigaba da tattaunawa. Najwa tana shiga ɗakinta ta samu Nafeesa ta fita taro wasu 'yan ajinsu na islamiya sun zo basu gane gidan ba, sai ta bar waya a chargy ita kuma Najwa ta ɗauki wayar akan tayi waya da Aminu tace masa ya turo mota da wuri na ɗaukar amarya, ta zauna a bakin gado ta duba contact ɗinta bai hau kan wayar Nafeesa ba saboda a email take saving, Allah yasa ta haddace number ɗin Aminu akanta, sai tayi dialing number, abinda ya ɗaure mata kai ganin sunan Amina ya fito daga number, wato akwai number ɗin a wayar anyi saving, da sauri ta cire Number ɗin ta duba wajen kira, tana kuwa dubawa taga ko jiya sunyi waya, nan take ta shiga WhatsApp ɗinta ta duba number ɗin taga chart ɗin su suna magana a online, jikin Najwa ya soma rawa sai dai bata yarda ta bayyana hakan a fili ba saboda kar sauran ƙawayenta su gane, ta shiga chart ɗinsu taga hira sosai suka yi sai dai kafin ta karanta taji muryar Nafeesa sun shigo gidan sai kawai tayi saurin fita ta goge duk abinda ta san ta duba ta miƙe da sauri ta isa ta mayar da wayar a chargy, ta juyo kenan sai gasu sun shigo da fara'a ta isa ta rungume 'yan matan da suka zo su biyu, sai gumi take yi kamar wacce ta haɗiye ƙarfe dan ta kaɗu sosai dacin dunduniyar da Nafeesa take yi mata, hakan yana nufin ta fara hulɗa da Aminu ne domin ya aureta ne ko kuma ta tona mata asiri itama ta rasa mijinta kamar yadda ta rasa saurayinta, ta kaɗu sosai dan tasan babu sirrinta wanda Nafeesa bata sani ba, haka dai take ta saƙa a zuciya tana yiwa mutane yake suna hira dan ta kasa saka musu baki, bata sake marmarin ɗaukar wayar ba sai in an kirata ne Nafeesa ta ɗaga ta yiwa mutane kwatance dan ba zata yarsa wayar ta shiga hannun Najwa ba saboda tsaro, sai a lokacin ne taji dama bata saka mata sim ba dan kar ta gane suna magana da Aminu. Haka suka yi yinin bikinsu cike da armashi duk da bakin amarya a fashe yake, kuma ta cigaba da sauya kaya ana gyara mata kwalliya, a ranar salla dai tace haɗawa zata yi in an kaita gidanta sai ta rama dan bata son abinda zai ɓata kwalliyarta, sai dai abinda Nafeesa tayi mata ya tsaya mata a rai, tana saƙa da warwara akan irin hukuncin da zata ɗauka a kanta. Bayan sallar magrib ne aka zo da motar ɗaukar amarya, Hauwa da Laure da sauran dangi dasu aka zo ɗaukar amarya, dan a lokacin ne suka ga ya dace su bayyana kansu yadda su Sameeha zasu kurɓi gumar mamaki, sai dai abinda basu sani ba sun riga da sun san Aminu ne mijin Najwa, shiyasa suka yita baza ido su gansu amma ba ko ɗaya hatta ummansu ma basu ganta ba, hakan yasa suka yi zargin ƙila sun sani, sai bayan sallar isha'i aka basu amarya, koda ƙanwar baban Najwa Salima wacce take aure a Kano ta kama Najwa ta kaita ɗakin Inna akan ko zata ƙara yi mata faɗa, cewa tayi. Allah ya kaita gidanta lafiya ya sadata da alkhairin gidan ya rabata da sharrinsa. Zaku iya tafiya. Daga haka taja baki tayi shuru Najwa kam ko irin kukan nan ta rungumo inna bata yi ba, sai ta miƙe ta fice dan hankalinta yayi gidanta a kaita kawai saboda ta gaji da takurar innar, inna kuwa siriri hawaye ne ya sauko mata tana tunanin makomar auren 'yarta wanda har yanzu zuciyarta ta kasa kwanciya da shi, haka aka saka Najwa a mota suka wuce da ita gidanta tare da 'yan rakiyar 'yan uwa da ƙawayenta, sai dai dangin Inna da yawa babu wanda yaje dan sosai lamarin ya bata musu rai, wasu ma yamma nayi suka bar gidan, dangin Baba ne da su basu ga aibun auren ba sune suka yi shagalin biki cikin farin ciki da rakiyar amarya. ***** Sameeha. Suna isa gida Zaidu ya saka Anwar ya ɗauko katuwar tamarba ya shimfiɗa musu a tsakar gida, nan suka zauna kowa yana mayar da numfashi mai cike da damuwa, umma ce ta katse shurunsu da cewa. Zaidu da kai da Ikram banji daɗin abinda kuka aikata ba, koma meye ai aure suka yi ba haramci ba, sannan ma Aminu baya tare da Sameeha. Amma umma ai wannan cin amana ne wlh koda ya rabu da ita, ya rasa wacce sai aura ba sai Najwa hakan bai dace ba, itama munafuka in ba ta saka son zuciyata ba ai tasan ana barin halak dan kunya. Cewar Ikram tana share kwallarta, Umma ta dubeta tana cewa. Ai ni kun gama zubar mini da mutunci tunda kuka yi abin kunya a gidan biki, ko ba komai Najwa 'yar uwarku ce bai dace in rai ya ɓaci hankali ya gushe ba, to ma da Aminu ya je ya ɗauko wacce bamu sani ba ai gwara ya aura wacce muka sani kodan tarbiyyar yaran nan su Abi. Kefa umma gabaɗaya bansan meyasa kika kasa hango laifin Najwa ba, to bari kuji a ɗan nazarin dana yi na gano komai daya faru a tsakanin mutuwar auren Sameeha. Idan nace muku Najwa tana da saka hannu dumu dumu wajen yiwa Sameeha sharrin lesbian wlh babu musu ko kaffara, domin an saka bikin Najwa wata shida bayan mutuwar auren Sameeha, kuma wlh Najwa tana da masaniyar Aminu ne mijin da zata aura, zan iya ce muku Najwa bakinta ɗaya dasu Hauwa dan in har Hauwa bata yarda ya auri Najwa ba hakan bazai taba yuwuwa ba, bikinta saura wata hutdu aka saka nasu Ikram wanda akayi da wata biyu kafin aka zo aka yi na Najwa yau, kenan akwai wata a ƙasa, ko Aminu bai san Najwa ce matarsa ba ko kuma ya sani da biyu ya yarda dan ya ƙuntata miki Sameeha. Amma 'yan uwan Aminu da Najwa da saka hannunsu a cikin sharrin da aka yi miki aurenki ya mutu. Wlh na yarda da kai yaya domin biri yayi kama da mutum, domin lokacin da aka yi walimar dawowar su Anty Sameeha naga yadda Najwa take shige musu suke magana banga wata alamar hantara ko rashin mutunci a tsakaninta dasu ba kamar yadda suke nuna mini. Ina kyautata zaton Najwa tana son Aninu tun lokacin data fara zuwa gidan ta ganshi, wataƙila son duniyarta yasa ta ke ganin zata iya aurensa, amma gaskiya zata yi halinta In Sha Allah. Cewar Ikram, Sameeha kam zuwa yanzu hawaye take yi dan har lokacin bata fita da mamakin Aminu ba da Najwa, kuma ta hango ƙamshin gaskiya a manganun su Zaidu, umma ta nisa tace. Ina fatan duk kan abinda yake a rufe Allah ya bayyana shi, mu daina maimaita maganar dan ƙara ɓatawa mutane rai zai yi, Ikram in da ƙarfi a jikinki tashi ki dafa mana ko taliya ce tunda bamu ma ci abincin gidan bikin ba muka baro, kuma rana tayi hantsi ya duba ludayi. Umma bari na dafa ni zan iya. Cewar Sameeha tana miƙewa, Zaidu ma ya miƙe ya wuce ɗakinsa cike da tunani, umma sam bata son ana maganar amma daya fita ya bincika gaskiya, sai dai yadda tace abar maganar shima ya barta, Ikram kam wayarta ta ɗauka ta shiga charting da mijinta tana faɗa masa abinda ya faru, Umma kuma ɗaki ta shiga ta kwanta doguwar kujera tana huta gajiyar data kwasa a gidan biki, sosai lamarin auren Aminu da Najwa ya dameta amma ta danne hakan ne dan kar yaran su shiga damuwa, saboda abin baiyi mata daɗi ba ko ba komai Najwa ta nuna ba tada mutunci da kara, yadda suka ɗauketa ita ba haka ta ɗauke su ba. Haka suka yini jugum jugum har yamma, a lokacin ne yayan babansu yazo gidan ya bawa Umma Haƙuri akan abinda ya faru, ta nuna ita ba damuwa Allah ya ƙaddara Najwa matar Aminu ne kuma In Sha Allah ba zata yarda zumunci ya lalace ba a kan haka zata yi magana da yaranta, sai yayi mata godiya ya kuma bawa Sameeha Haƙuri itama tace babu komai ya wuce, haka ya tsaya suka sha hira sai gabda magrib ya bar gidan. Gidan Aminu. [7/7, 13:04] Buhainat😁: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shai wanidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.* 44. Aminu barci barawo ne ya ɗauke shi anan doguwar kujera sai kiran sallar asubahi ne ya tashe shi, ya miƙe ya fara yin wanka kafin ya saka jallabiya ya tafi masallaci bai dawo ba sai da gari yayi haske wajen shida da rabi, ya shiga falonsa ya zauna ya ɗauki wayarsa ya kira Junaid yayan Najwa, har kiran ya kusa tsinkewa kafin ya ɗauka cikin muryar barci, suka gaisa kana Aminu ya ce. Dan Allah ina so zan baka saƙo gurin su Inna, ka sanar dasu su shirya ƙarfe takawas zuwa da rabi suje gidansu Sameeha zamu haɗu a can akwai muhimmiyar maganar da za muyi. Ok ba damuwa In Sha Allah zan sanar dasu. Yauwa nagode. Aminu ya faɗi haka kana ya aje wayar, Junaid cike da mamaki ya tashi ya zauna yana tunanin me zaisa Aminu yace su inna suje gidansu Sameeha, da alama wani babban al'amari ne duk yadda aka yi, lamarin ya ɗaure masa kai wanda yasa ya kasa komawa barci sai ya cigaba da danne danne a waya da nufin zuwa anjima kaɗan sai ya sanar dasu inna tunda akwai sauran lokaci, kuma shima zai bisu dan ayi komai akan idonsa. Aminu kuwa miƙewa yayi ya shiga bedroom ɗinsa ya sauya kaya zuwa shadda ɗinkin tazarce, ya saka hula ya feshe jiki da turare sai ya ɗauki waya ya kira driver ɗinsa akan ya kawo masa mota, driver yace yana hanya ya kusa ƙarasowa, sai ya kashe wayar ya dawo babban falo ya zauna yana ɗan duba abu a waya. Najwa. Da kyar ta iya jan jiki ta hau gado ta kwanta daga haka barcin wahala yayi awon gaba da ita, ko kaya ta kasa sakawa sai bargo ta rufe jikinta dashi, ba ita ta farka ba sai ƙarfe shidan safe da minti biyar, ta buɗe ido sosai tana kallon silin wanda ya tabbatar mata da ba a gidansu ta kwana ba, abubuwan da suka faru a yinin bikinta suka dawo mata sabo, a hankali ta sauke numfashi tana jin wani tuƙuƙin baƙin ciki yana turniƙe ta, bata jin a tarihi akwai amarya kamarta akan irin abunda ya faru da ita a safiyar aurenta na dukan da Ikram tayi mata da kuma daren amarci da ango ya zaneta, komai ya lalace mata ta tadda bata yi tsammani ba, ta samu nasara akan auren Aminu amma kuma yazo a gaɓar da take jin dama bata same shi ba, bata so asirinta ya tonu ba da wuri duk Nafeesa ne ta ɓata mata komai, dana sani ne ya rufeta amma ba na nadama ba na tunkarar Nafeesa da maganar Aminu, tsabar wauta kuma har falonsa ta shiga suka yi magana yaji komai, tsananin haushin kanta ya rufe da kuma na Nafeesa tare da alwashin itama sai ta tona mata asiri, babbar damuwarta bata san ya makomar aurenta zai zama ba, zata so Aminu duk wulaƙancin da zai yi mata kar ya saketa dan taza jure duk wata uƙuba da wahala akan ya saketa ta zama ƙaramar bazarawa sakin wawa, dan in har ya saketa ya gama tona mata asiri ta san zaman kaduna sai ya nima ya gagareta, saboda maganar mutane sai yasa kamar tayi hauka, ta runtse ido hawaye yana kwaranta a kuncinta, ashe ma Aminu ba lafiya ce da shi ba da take ɗokinsa, sai duk taji wani sonsa ya fice mata a rai sai tsanarsa da yake maye zuciyarta, ko bai faɗa ba itama ba zata so ta zauna dashi ba har ƙarshen rayuwarta ba, domin zata so ta san ya namiji yake sannan ma ta haihu, kawai dai babbar damuwarta kar ya saketa yanzu ya ja mata gutsiri tsoma na mutane, zata jure zama dashi na shekara guda ko fiye zuwa lokacin ta tara kuɗin da zai isheta rayuwar zawarci kan tayi wani auren, ashe duk kyansa a fuska ne hoto ne shi Namiji ba abin, ina lafiya kuwa tunda babu ginshiƙin auren, data san da haka ba zata kwallafawa ranta son aurenshi ba da ta barshi da Sameeha su cigaba da zamansu tunda bama jin daɗin auren take yi ba zaman yara take yi, kuɗin ne a fili amma a baɗini cutuwa take yi, sai ta cije yatsa tana jin takaici yana rufeta da dana sanin da bata shiga lamarinsu ba tunda suna rayuwa da giɓi ne ba jin daɗinsa suke yi ba wannan kadai ya ishe su, sai gashi Sameeha ta samu wanda ya fishi lafiya kuɗi da komai ta samu duk wani abu na more rayuwa, Ikram ma ta biyo baya, ita ce dai bata zo duniya a sa'a ba. Babban maƙiyanta a yanzu da take jin in bata ɗauki fansa ba akansu ba zata rayu cikin salama ba, Nafeesa dole sai ta tona mata asiri, Ikram da Sameeha tana fatan ta samu damar da zata haifar musu da matsalar da ba zasu ji daɗin rayuwarsu ba, Aminu kuma da zata samu dama tabbas mutuwa ya dace dashi, domin ta samu babban kaso a dukiyarsa kafin yace zai saketa, dole ne ta zauna ta sake tsari yadda zata sauya daga wancan Najwa zuwa wata sabuwar Najwa, don ta kula a rayuwar nan in kana so ka zama wani abu to lallai sai mutum ya aje tausayi da imani kafin yake samun cikar burinsa, tun farko data bi shawarar Nafeesa akan ta asirce Aminu ta dage ta niman magani a waje mabambanta da ta samu kansa tuntuni, da bai isa ya yi mata abinda ya aikata jiya ba, kuma da alama malamin nan baiyi mata aiki mai kyau ba tunda ga sakamakon davta samu. Motsin shigowar Aminu data ji ya dawo daga masallaci yasa ta duba agogon dake manne a jikin bangon ɗakinta sai taga shida da rabi har da minti biyu, taja guntun tsaki dan ko sallar Asubahi bata yi ba ga kuma sallolin jiya data tara bata yi su ba, tunawa da hakan yasa ta miƙe da kyar ta sauko daga gadon duk jikinta yayi mata mugun tsami, a haka ta shiga bayin ta haɗawa kanta ruwa mai zafi tayi wanka da alwala ta fito, kayan jiya da Aminu ya cire mata su ta mayar ta yane gyalenta akai ta shimfiɗa dadduma ta shiga ramakon sallah a zaune dan jikinta babu ƙarfin da zata yi shi a tsaye, ta ɗauki lokaci mai tsaho tana abu guda, daga bisani ta idar kana tayi gajeriyar addu'a ta miƙe da kyar dan ƙafarta har tsami yayi ta isa jikin madubinta tana kallon irin yadda fuskarta tayi shedan bulala yayi ja, har wata 'yar rama tayi na wahala dan rabonta da abinci tun jiya da rana, sai yanzu ne ma ta fara jin yunwar tana taso mata amma halin da take ciki ko ta ga abinci ba zata iya wani ci ba dan sosai take fargaban Aminu ya saketa a yanzu, haka ta koma bakin gado ta zauna tana jiran shigowarsa dan ya rufeta ta baya balle ta iya fita ta haɗawa kanta ko ruwan tea ne ta jiƙa 'yan hanji. Driver ya kawowa Aminu mota sai ya sallame shi akan zuwansu Zaria ba zai yuwu yau ba sai gobe In Sha Allah, kana yasa mai gadi ya buɗe masa gate ya fita zuwa wani rastaurant, oder ɗin waina da miya yayi musu sai ya saya ruwan gora da kuma coka drink ita kuma ya saya mata fanta, wajen bakwai da rabi ya dawo ya aje nashi a falo ya isa ɗakin Najwa ya buɗe ta tana ganinsa ta miƙe zubbur tana kallonsa a firgice dan gani take kamar dukanta zai kuma yi, baice mata komai ba ya aje mata leda ya juya ya rufeta ya koma falon ya zauna ya buɗe takeway ya soma cin wainarsa yana yi yana kurɓan coke, Najwa kuwa ƙamshin daya ratsa hancinta shine ya bata tabbacin abinci ya kawo mata, sai hakan yasa ta dan samu natsuwa da tunanin ƙila ba zai saketa ba, da sauri ta isa ledan ta zauna a gurin daya aje ta ciro takeaway ɗin ta soma cin wainar, duk yadda tayi tunanin ba zata iya cin abinci sosai ba ta kasa dan kusan waina biyar ne sai da taci huɗu kafin ta kora da ruwan fanta, taji ta ƙoshi sai ta mike taje bayi ta wanke hannu ta dawo ta saka takeaway ɗin a leda ta mayar da komai ta zauna a gefen gado tana jiransa. **** Gidansu Najwa. Wajen takwas da wani abu Junaid ya samu Baba a ɗakinsa suna magana da inna, Baban ma kunu yake sha da kosai yana karyawa, Junaid ya zauna yana gaishesu kana baba ya kalleshi yana cewa. Junaidu ya aka yi ne, ka karya kuwa? Ai baba bani a cikin abincin bikin nan waje zan je na karya. Dama nazo na sanar daku mijin Najwa yace in faɗa muku kuje gidansu Sameeha akwai maganar da yake so zaku tattauna a can. Gidansa yake nufi ko? In kuma yana son magana damu ai nan ya kamata yazo in dai yana kallonmu da daraja. Cewar Baba yana rufe kwanan kununsa, Junaid yace. Nifa gidansu Zaidu yace kuje, wataƙila magana ce daya shafesu da yaransa, shiyasa nima nace zanje dan ayi komai a gabana. To faɗuwa tazo daidai da zama dama na bari mutane su watse naje na samu Halima na bata haƙurin Najwa na auran Aminu, nayi mata bayanin muma ba mu san shi bane mijin ba sai jiya. Hakane ta cancanta a bata haƙuri gaskiya dan zasu ga kamar mun munafurcesu, amma bari muje ɗin muji me shi Aminu zai ce, Junaid sai ka fita ka samo mana napep ko, ai kema Zulai a shirye kike. Eh nayi wanka tun ɗazu bari na ɗauko mayafi a ɗakina. Cewar inna sai ta miƙe ta fito Junaid ma ya fita samo musu abin hawa. Tunda suka kama hanya ko wanne da irin tunanin da yake yi a zuciyarsa, Junaid kuma a hanya ya kira Aminu akan sun tafi gidansu Sameeha yace to kana ya kashe wayar. Aminu da sauri ya miƙe ya zo ɗakin Najwa ya buɗe ya ce mata ta fito zasu fita ba musu ta biyo bayansa suka fito farfajiyar gidan, ya buɗe mota ya shiga mazaunin driver ita kuma ta tsaya tana jiran ya sanar da ita inda zata zauna, ya buɗe mata gefensa yace ta shiga, ba musu ta shiga ta zauna zuciyarta cike da fargaban ina zai kaita duk gani take wataƙila gidansu zai mayar da ita yace ya saketa, addu'a ta shiga jerawa a zuciya akan Allah ya ɗaurata akansa karya saketa, shi kuma yadda fuskarsa take a sake ba zaka taɓa cewa da damuwa ba, falalar ambaton sunan Allah shiya sanya masa natsuwa da takawakki akkan ƙaddarar data faɗa masa, ya rufe motar ya kunna suka kama hanya, Najwa kanta a sunkuye yake cike da damuwa, zaune take a takure ko hanya bata iya kallo dan fargaba take taga gida ya nufa da ita, a haka har suka shiga unguwar su Sameeha sai a lokacin ne ta ɗago kai, a razane ta kalle shi dan sosai ta firgita da inda zai kaina, cike da tsantsar tsoro tace. Ina zamu je? Gidansu tsohuwar matata domin in wanke mata zargi da damuwar ƙuncin da kuka sakata na sharrin da kuka yi mata. Dan Allah da son Annabi s.a.w karka yi mini haka wlh na tuba bazan ƙara ba, karka tona mini asiri Allah da kansa yace duk wanda ya rufawa ɗan uwansa musulmi asiri shima Allah zai rufa masa. Hmmm ga sani ga shagali ko, kuma Hadisi ne sahihi sannan ingantacce, amma ai ke baki yi aiki da Hadisin ba domin ke kika fara tona mana asirin da muka jima da birneshi ni da sameeha, yanzu dalilinki kowa sai ya san bani da lafiya. Dan haka dole ki je ki amsa laifinki ki kuma warware musu yadda kika haɗa makircinki. Innalillahi wa inna ilaihir raji'un dan Allah Aminu ka yafe mini kayi mini rai bazan iya dubansu da wannan maganar ba, wlh duk abinda kake so zanyi maka amma banda wannan. Hmmmm kina ɓata bakinki ne, kamar yadda baki yi tunanin zuwan irin wannan ranar ba kika aikata abinda kike so, dan haka banga abinda zai sa na fasa abinda nayi niyya ba nima. Najwa ta fashe da matsanancin kuka dan sosai ta shiga tashin hankalin daya fi na jiya muni, Aminu so yake ya kaita ƙasa ya wulaƙantata ya tozarta ta a idon maƙiyanta, dan ta tabbatar suma sun ƙullaceta zasu so suga ta wulaƙanta, ita kuma ba zata yi fatan hakan ya faru ba dan kar suyi mata dariya, wanda tasan Ikram sai ta zuba ruwa a ƙasa ta sha dan farin ciki, da yayi mata wannan hukuncin gwara yace ya saketa ta tafi gidansu, ganin sun kusa isa gidan yasa ta kama wajen buɗewa ta danna dan gwara ace ta mutu da ta muzanta a idonsu Sameeha, tasan idan yaga ta mutu bazai ma ɓata lokacin tona mata asiri ba, in ma ya tona bata duniyar balle taga sunyi mata dariya, sai ta soma kokawa da ƙofar motar amma taƙi buɗewa, ganin fa saura ƙiris su isa yasa ta faɗawa Aminu ta kama sitiyarin mota akan duk su mutu, Aminu ya saka ƙarfi dan ya tureta amma ina itama ta saka nata ƙarfin, gashi a daidai lokacin wata motar tifa data ɗauko yashi ta doso su, salati kawai Aminu yake yi yana cewa. Shikenan Najwa zaki kashe mu, innalillahi wa inna ilaihir raji'un. Mu tara a pegi na gaba... [7/7, 13:04] Buhainat😁: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shai wanidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.* 45. Aminu ganin da gaske fa Najwa kashesu zata yi, sai ya tattaro ƙarfinsa ya bisgeta daga gabansa ya wasar da ita a gefe ya kifa mata mari mai kyau, sai ya kama sitiyarin motar yayi gefe da motarsa da mugun sauri dan saura ƙiris suyi karo da wannan tifar har saida jikin motarsa ya gogi jikin tifar, mutane sai ihu suke suna salati dan sosai kowa ya sadakar da wannan mummunar hatsari daya kusa aukuwa, Ganin sun tsira yasa kowa yana musu sambarka Aminu ya isa gefen titi yayi parking yana mai sauke numfashi ga wani zufa da yake karyo masa saboda tsananin tashin hankali daya gani mararan, Najwa kuwa kuka kawai take dan itama ganin tifar tayo kansu ba ƙaramin firgita tayi ba, saida taga sun kauce masa yasa ta dawo hayyacinta tana sauke ajiyar zuciya, ashe dai tana tsoron mutuwa ganinta ne kawai da bata yi ba take lissafin gwara ta mutu amma data ga da gaske ne sun kusa mutuwar ta shiga hankalinta, mutane suka dinga tsallakowa suna yiwa Aminu barka shikam hannu yake ɗaga masu yana ya gode, saida ya daidaita natsuwarsa kafin ya kuma tada motar suka wuce. Ɓangaren su Inna kuwa har sun insa gidan, ita ta fara shiga kafin ta sanar da su umma tare take dasu ba kana ta fito tayi musu iso shi da Junaid, a nan tsakar gida suka zauna kan babbar tabarma da aka shimfida musu, Umma ta sako hijab ta fito suka gaisa kana su baba suka bata haƙuri akan abinda ya faru jiya da kuma nuna mata suma basu san da lamarin ba sai a jiyan, umma tace ba komai haka Allah ya ƙaddara, sai suka yi ɗan jim kafin Junaid ya isar mata da saƙon da Aminu ya sanar musu wanda yasa suka zo, umma tayi shuru tana mamaki tare da tunanin mai zai kawo Aminu gidansu bayan tun da ya saki Sameeha bai sake waiwayarsu ba, sai ta nisa tace Allah ya kawo shi kana ta miƙe ta shiga cikin ɗaki, ba jimawa su Sameeha suma suka fito suka gaishe su harda Zaidu dan duk suna a tare ne a ɗakin Umma sun gama karyawa, nan umma ta saka Zaidu ya bawa inna haƙuri akan abinda yayi mata jiya tace ba komai ai ya wuce, sai ya matsa kusa da Junaid suka shiga yin hira su Umma ma suna nasu. Aminu suna isa ƙofar gidansu Sameeha yayi parking ya kashe motar ya fito, Najwa ma fitowa tayi ya rufe motar ya tasa ƙeyarta suka shiga gidan, Najwa sai sunne kai take yi jiki a mace domin ruwa ya karewa ɗan kada, sun tadda har su inna sun iso suna zaune a tsakar gida bisa babban tabarma da alama zuwansa ake jira, ganin yana tare da Najwa yasa suka fahimci maganar ta shafesu duka ƙila kan batun aurensa. Su Abi suna jin muryan baban da yayi sallama suka fito daga ɗakin umma suka rungume shi ya kama su yana cewa. Yaushe kuka zo kaduna.? Shekaran jiya tare da mamanmu. Abi ya bashi amsa, Aminu yayi guntun murmushi. To yayi kyau ku koma ɗaki in mun gama magana sai na kiraku mu yi magana kan na wuce. To suka ce masa sai suka koma cikin ɗaki, shi kuma ya samu guri ya zauna kusa da inda Najwa take zaune, ta rufe fuskarta da mayafi bata buɗe ba balle tasan su waye zaune a tabarmar, zuciyarta ta gama tsinkewa sai bubawa take yi kamar zata faɗo ƙasa, Aminu daya zauna suka gaisa da su uma gabaɗaya sai a lokacin ne Najwa ta gane dasu innarta a gurin, take taji fitsari ya kamata jikinta ya ɗauki rawa, jin Baba ya soma magana yasa ta natsu tama rasa me zata yi. Yauwa Aminu gamu mun zo sai ka faɗa mana dalilin taruwarmu a nan. To baba maganace Nazo da shi akan abinda ya shafeni da kuma Sameeha sai kuma Najwa data shigo ciki, in ba damuwa a kira Sameeha tazo ayi maganar da ita. Nan take Umma ta kwalawa Sameeha kira sai gata ta fito sanye da hijab ta ƙaraso ta zauna daga gefen tabarma, sai ga Ikram ma ta fito ta zauna daga bakin ƙofa dan so take taji meya kawo su. Aminu ya cigaba da magana ya fara basu labarin dalilin sakin Sameeha da yayi dama yadda ya kamata da waɗannan 'yan matan, su inna da basu san zancen ba suka shiga mamaki sosai, Sameeha kuwa kuka ta fara mara sauti dan ya tuno mata da mugun giɓi da kuma ƙoƙarin tona maganar da yayi gaban su inna, Aminu ya cigaba da cewa. Sameeha kiyi haƙuri ba na dawo da maganar nan bane domin na tona miki asiri kona tozartaki ba, saboda ina so na ɗaura maganar akan yadda kowa zai fahimta. Ina son Sameeha amma haka na haƙura da ita badan na kamata da waɗannan 'yan matan ba sai dan na kuɓutar da ita daga faɗawa halaka, akan ta samu damar auren mai lafiya wanda zata tsira da mutuncinta dana yaranmu, wanda daga ni sai ita sai kuma in ta faɗawa su umma sune suka san da wannan maganar, dan ko 'yan uwana babu wanda yasan da maganar dan ban faɗa musu dalilin rabuwarmu ba sannan basu san bani da lafiya ba. A bayan rabuwarmu ne Hauwa ta matsa mini da zancen sai nayi aure, hakan yasa nace ta samo mini mata domin na samu hanyar da zan ƙuntata mata na rama duk wani abu da suka yiwa Sameeha nima suka yi mini, ita kuma bata san da wannan kuɗurin na amsa mata da auren ba, sai tace ta samo mini mata Najwa, wallahi Tallahi ban san wannan Najwan bace dan ban taɓa kawota a raina ba domin ban ma wayeta sosai ba dan haɗuwarmu da ita baifi sau biyu ba a gidanmu lokacin Samewha tana nan, haka ta haɗamu a waya muka cigaba da magana bamu taɓa haɗuwa ba sai jiya da aka ɗaura aurenmu har nasan wacece Hauwa ta aura mini, sai a lokacin ne na tuna irin kallon da Zaidu kayi mini ashe na tuhuma ce wanda ni ban fahimci haka ba. Najwa da Hauwa bansan a ina suka haɗu ba har suka haɗa kai wajen ganin sun cutar da Sameeha sun ƙuntata mata, ko da yake wannan ba shine abin mamakin ba dan nasan halin Hauwa zata iya aikata komai wajen ganin ta jawo Najwa a jikinta, sai dai kuma ita Hauwa tana nata Najwa ma tana nata haɗa tuggun. Kamar ya fa? ka warware mana maganar nan kai tsaye yadda zamu fahimta. Cewar Zaidu da duk ya ƙosa yaji ƙarshen maganar, Aminu ya yi guntun murmushin takaici ya girgiza kai yana cewa. Sameeha wannan lesbian dana kamaki da 'yan mata, ashe ba kowa ya haɗa wannan makircin ba sai Najwa da ƙawarta Nafeesa. Innalillahi wa inna ilaihir raji'un Duk suka haɗa baki wajen faɗa, Sameeha kuwa har da dafe ƙirji tana kallon Najwa dake rufe da gyale jikinta yana mugun rawa, Ikram tace da ƙarfi. Anzo wajen, yau dai Allah ya bayyana gaskiya kowa yasan wacece ke Najwa, Allah ya tsine miki albarka ya wadaranki. Karna sake jin maganarki Ikram. Cewar Umma data waigo tana gargaɗinta da nuna mata yatsa, Baba kuwa cire hular kansa yayi yana jin wani zafi yana hura shi, inna ma sosai ta soma gumi dan gashi nan akan fuskarta tayi matuƙar girgiza da wannan labari, Junaid ko girgiza kai kawai yake cike da ta'ajibi, Yaya Zaidu kam murmushin takaici yake saki yana cije gefen leɓensa zuciyarsa tana harbawa da sauri. Aminu ya cigaba da basu labarin bayan kawo Najwa da aka yi jiya da kuma hirarsu daya ji na faɗa ita da Nafeesa, babu abinda ya ɓoye duk wanda bai manta ba ya faɗa, ya ɗaura da cewa. Ga najwa nan a gabanku ku ji tabbaci idan sharri nayi mata, sannan ma akwai CCTV ɗin falona daya yi recoding komai, kuma akwai ƙawarta Nafeesa da zan iya kiranta yanzu tazo domin ta ƙara gasgata wannan labari. Sannan a hanyarmu ta zuwa saura kaɗan motar Tifa tabi ta kanmu Najwa data kama sitiyarin mota akan gwara ta kashemu dana tona mata asiri, idan muka fita zaku ga layin da motar tifar ya gogi gefen motata. Wannan dalilin yasa na buƙaci mu haɗu anan domin na bayyana komai na kuma wanke Sameeha akan sharrin da suka yi mata, yadda na godewa Allah maganar babu wanda yasanta sai mu nan kawai a yanzu. Amma Najwa ita ce ta aikata komai sannan ita tasan yadda ta haɗu da Hauwa har ta zaɓa mini ita a matsayin mata. Salati kawai suke yi Inna kuwa ta kasa daurewa sai kuka take yi, Baba kam girgiza kai yake yi Yaya Junaid ya kalleta cike da takaici. Kinyi asara Najwa ki rasa wacce zaki cuta sai Sameeha 'yar uwarki ta jini saboda son zuciyarki, babu mai mugun halinki a gidanmu bansan a ina kika samo shi ba, gaki da Ilimi amma sam baki yi aiki da shi ba Allah ya shiryeki. Najwa kuka mai sauri ta fashe dashi dan tuni ma ta saki fitsarin daya matseta a gurin, ga gumi data ke fitarta na rashin gaskiya, tunda take bata taɓa jin ta muzanta ba a duniya irin yau, Sameeha ce ta jefa mata magana wanda yasa ta ɗago da sauri da take cewa. Najwa me na tare miki a rayuwa dana cancanci irin wannan hukuncin a gareki? meye ribarki idan kin yi mini sharri an sakeni, ashe dama duk zuwan da kike yi kina gane mini sirrin gidana ne kina son ki auri mijina, nayi zaton Jamila 'yar aikina itace abin tsoro da nake takatsantsan da ita ashe kece abin tsoro ban sani ba. Itama Jamila ai wu Hauwa suka turota domin ta riƙa faɗa musu duk halin da kike ciki, sannan Jamila da ita aka haɗa duk wani makirci, kuma Hauwa itace shugaban haɗa komai. Najwa ta faɗa cikin kuka, Junaid ne ya wanka mata mari yana nunata da yatsa. Saboda baki da kunya har kin samu damar yin magana ko, 'yar iskan yarinya mai mugun hali, wlh Najwa saina karyaki kinyi jinya, sheɗaniya mara imani da tausayi. Najwa miƙewa tayi jikinta yana yararin fitsari tana kuka da ƙarfi dafe da kuncinta. Yaya karka barni da rai ka kashe ni ku huta dama nasan ba ƙaunata kuke yi ba, da wanne zanji kowa ya tsaneni ya ɗaura mini laifi bayan ba ni kaɗai na aikata komai ba. Laifi ne dan naso mijinta? laifine dan na aureshi? ai ko a musulunci banyi haramci ba tunda ba da iskanci na yi ba, laifine dan na zaɓawa kaina auren mijin dana san zan huta a gidansa fiye da gidanmu, shikenan komai na ɗaukaka sai dai a ganshi a gunsu nice a baya. Ai dolw ki ganki a baya tunda kin saka hassada da mugunta a zuciyarki, wlh Najwa kin bamu mamaki babu wanda zaiyi tunanin zaki aikata mana haka, to Alhamdulillahi kin rabata da gidan Aminu gashi ta samu kanta a gidan daya fi nashi ɗaukaka da komai, idan kina yi musu hassada to taki kike ƙara musu na daukaka, kuma ba dasu kike faɗar ba da Allah kike yi shiyasa ya nuna miki ikonsa, kaɗan ma kika gani. Cewar Zaidu yana nunata da tsaya, Najwa taja guntun tsaki tana yatsine fuska. Kai dai kaji haushi ne saboda nace bana sonka, kuma bana sonka ɗin domin ba kada komai da zaka bani, dan a jikin Sameeha kake samun na kashewa, Allah ya kyauta. Ke banason shashanci kinyi laifi amma kina da bakin da zaki yi magana, kaji min 'yar banza mara mutunci, zaki zauna ko sai na saka junaid yayi miki mugun duka da sai kinyi jinya dan mu huce takaicinmu. Cewar baba cike da ɗaure fuska, Najwa ta koma ta zauna tana gunguni, itafa har yanzu ta ƙi karɓan laifinta shiyasa take zuba borin kunya, ta kuma nuna musu ba tada kunyar. Sameeha kam shuru tayi dasu umma dan abin nata yafi ƙarfin lissafinsu, Baba yace sai Najwa ta bawa Sameeha Haƙuri akan abinda tayi mata, Najwa tayi shiru taƙi magana, baba zai fara faɗa Umma ta dakatar dashi akan. Malam ka rabu da ita har yanzu babu alamar nadama a tare da ita, dan haka ita Sameeha ko ta yafe ko bata yafe ba ta ga kyakkyawar sakamako kuma bata ma gama ganin Nasara ba In Sha Allah, Addu'a za mu taru mu yiwa Najwa akan Allah ya shirye ta, dan tuntuni na fahimci ta sauka daga tarbiyyar da kuka bata, sai kun saka ido sosai akan abokan da take hulɗa dasu. Baba girgiza kai kawai yake yi yana cewa. Dan Allah Halima kuyi haƙuri an cutar daku Allah ya saka muku, Aminu in ka gama magana mu zamu tafi. Aminu ya gyara zama yana ciro farar takarda a haljiunsa ya aje a gaban Najwa yana cewa. Ni Aminu na saki Najwa saki biyu ban ɗaura mata idda ba in ta samu muji tayi aure, sannan kuma na bada damar aje a kwashe kayanta a cikin makon nan dan zan rufe gidan na koma bakin aikina. Baba kuyi haƙuri akan hukuncin dana yanke domin koda Najwa bata yiwa Sameeha sharri ba bazan iya zaman aure da ita ba tana a matsayin 'yar uwarta, sannan ma ni bani da lafiyar da zan zauna da wata mace a yanzu. Sameeha ki yafe mini nasan na shiga hakkinki keda yara dana rabaku, dan haka a yanzu na yanke hukuncin yara sun dawo hannunki idan mijinki ya amince zai zauna dasu to ba damuwa, in kuma bai yarda ba ki barsu a gurin Umma nasan zasu samu tarbiyya mai kyau da kulawa, sannan zan riƙa biya musu kuɗin makaranta da duk wani hakkinsu dake kaina ban yarda kowa yayi ba, ina tunanin a cikin wata mai kamawa zan bar ƙasar nan zanje London yin wani aiki na shekara biyu In Sha Allah zan riƙa kira ina waya dasu Abi, umma ni zan tafi na barku lafiya ku yafe mini. Allah ya yafe mana gabaɗaya kuma Baka mana komai ba Aminu, Allah yasa albarka a cikin tafiyarka ya baka nasara da lafiya mai inganci. Aminu ya amsa da amin yana jin hawaye yana cika masa ido sai kewar mahaifiyarsa ya taso masa, ya mike yana yiwa su baba sallama suma fatan alkhairi suka yi masa sai ya wuce, Ikram ce ta kwalawa su Abi kira, da suka fito tace suje gurin babansu ya fita, Sameeha kam tausayin Aminu ne ya kamata sai ta miƙe ta shiga ɗaki tana matsar kwalla, Ikram ma tabi bayanta duk jikinta a sanyaye sosai itama taji tausayinsa, Najwa kuwa suman zaune tayi tana hawaye mara sauti sai yanzu ne jikinta yayi sanyi jin wai Aminu ya saketa bayan ya tona mata asiri sannan kuma ya rabu da ita ta zama bazawara, Abun da ciwo aure da kwana ɗaya an saketa, wannan wane irin mummunar ƙaddara ce yake binta, ita kam ta shiga uku ta lalace ta samu biyan buƙata a lokaci guda kuma a lokaci ɗaya ta rasa komai, sai kawai ta ruse da kuka mai sauti. Shikenan na sara komai a lokacin da nake farin cikin na samu, ni kenan banda sa'a a rayuwata, jiya jiya aka ɗaura yau ya sakeni ina zan saka kaina naji saukin wannan baƙin ciki, inna dama sai da kika yi mini baki gashinan ya bini, kun tsaneni saboda na zaɓawa kaina abinda nake so. Ta cigaba da muka baba ya miƙe yana cewa. Najwa ai shi mugun abu ɗan aike ne muddun ka aikashi wlh sai ya dawo maka, kaɗan ma kika gani Allah ya tsayar a kanki ya kuma shiryeki, ke Zulai tashi mu tafi gida, Halima mun gode Allah ya jikan Ahmadu ya yafe masa. Baba ya ƙare maganarsa yayi gaba, Inna ma godiya ta yiwa Umma akan in an kwana biyu zata dawo sai tabi bayan baba Umma tayi mata rakiya har gate, Junaid ne ya tasa ƙeyar Najwa suka wuce tana kuka wiwi, Zaidu kam miƙewa yayi ya ɗauko buta ya zuba ruwa a inda Najwa ta zauna tayi musu fitsari, ya bi bayan umma data shiga ɗaki suka zauna jugum jugum Ikram ta katse shurunsu da cewa. Ashe Najwa ta jima tana aikata mana mugun abu wlh ta bani mamaki, ashe makashinka yana tare da kai, gashi ba aje ko ina ba ta wulaƙanta ya saketa a gabanmu kuma jiya aka ɗaura aure yau an saketa, Allah ya kyauta ta gyara mana imaninmu. Ameen, amma ina so mubar maganar haka dan ba tada daɗi, Sameeha sai komai ya wuce a ranki tunda gaskiya tayi halinta ki kama mijinki da kyau, sannan batun yara ki barsu a nan kawai in kin zo hutu kya gansu, bana so a takurawa Ibrahim. Laaa umma ai baida matsala shima yace da Aminu zai bar mana su, yana da son yara. Duk da haka ki barsu anan hankali na zai fi kwanciya. Amma umma bakya ganin su Hauwa zasu nima takura miki in suna nan. Cewar Sameeha, Zaidu yayi murmushi yana cewa. Ai da ba yanzu bane Sameeha sun san munfi karfinsu, ai basu isa su kawo mana iskanci ba wlh dan sun san wanda kike aure. Nan Ikram tasa dariya tana cewa. Wlh kuwa ai ba zasu yi mana hauka ba, kunsan ni mai ya bani dariya Najwa harda fitsarin Zaune tsabar borin kunya, duk fa wannan maganganun tabarman kunya ta naɗe da hauka, Allah dai ya shieyeta amma tasan munyi gaba hassada kuma ta cigaba da yi muna samun ɗaukaka, zan saka Shamsu ya saka mana kare a gidanmu yadda duk randa ta tako ƙafarta tazo gidana nasa suyi mata rakiya shegiya. Amma ba kida kirki Ikram nasan ma ba zata zo ba, ai abin da kunya. Cewar Sameeha tana murmushi, shigowar su Abi da ledar biscuit da chocolate yasa su sauya hira, Zaidu kam sai sam barka yakewa kansa da Allah ya raba shi da Najwa, ɗan ko a ƙafa aka ɗaura masa ita baya jin zai jata. [7/7, 13:04] Buhainat😁: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shai wanidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.* 46. Aminu. Bayan ya sayowa yara kayan ciye ciye sai ya shiga mota ya wuce zuwa babban gida dan so yake yau Hauwa ta gane kuranta, yana tafiya yana duban a gogo wanda ya nuna kusan goma da mintuna yasan sun ɓata lokaci sosai a gidan umma, sai ya ji zuciyarsa fes kamar ya sauke wani mai nauyi, na farko ya wanke Sameeha ya kuma bata yaransu sannan kuma ya rabu da Najwa da yake jinsa kamar an ɗaura masa ƙarfe a wiya, yanzu ya zama free sai kuma ya mayar da hankalinta kan batun aikinsa, da farko da aka yi masa tayin aikin yaƙi amsa saboda yaransa da suke hannunsa, yaji ba zai iya barin mahaifarsa ba gwara a ɗaura wani akan tafiya London ɗin, su kuma sun fi so shi ya yi tafiyar domin sun san ba zai basu kunya ba, yafi ƙarfin wata da suke ta binsa da wannan maganar dan har bashi lokaci suka yi akan wataƙila ya sauta ra'ayinsa,sai gashi kuma cikin yardan Allah ya amsa musu da zai yi tafiyar ɗazun da safe ya kiransu, dan yana so yayi nesa da kowa ya yi rayuwa a inda ba wanda ya sanshi, kuma yana so ya mayar da hankalinsa wajen niman lafiya a can ƙila ya dace ya samu lafiyar, da tunani barkatai ya isa babban gida yayi parking a ƙofar gate ya fito ya shiga gidan, ya samu mata da yara ana ta hayaniya da alama basu daɗe da gama karyawa dan yaga kofuna da robobin na suka ci ƙosar birjik a tsakar gida, matan da suka fara ganinsa suka fara sakin guda suna ga Ango ga Ango, Aminu kam murmushin takaici yake yi yana gaishe su, a tsakar gidan ya tsaya ya tambayi Salma data fito daga ɗakin Sa'a ina Hauwa ta kira masa ita, tace masa to kana ta isa shashin Laure ta faɗa mata saƙon Aminu sai cewa tayi ta dawo tace masa ya zo sashin Laure, Aminu ya yi guntun murmushi ya ce. Ki ce mata ta fito tsakar gidan sauri nake yi. Salma ta koma ta faɗa mata sai gata tazo buguzum buguzum ta ƙaraso tana cewa. Haba Ango saurin me kake yi ko amarya tayi ce kira. To gani ya kwanan amarya fatan ka yaba da zaɓina. Ta ƙare maganar tana tsayawa a gabansa. Aminu ya kalleta ido cikin ido yana cewa. Gaskiya kam na yaba da zaɓinki wanda kika saka son zuciya a ciki da son kai, ban ɗauka tsanar da kika yiwa Sameeha har ya kai haka ba, ki rasa wacce zaki aura mini sai 'yar uwarta saboda kawai ki muzguna mata. Haba Aminu meye laifina dan na zaɓa maka matar da zata share maka hawaye ta kula da kai, yarinya mahaddaciya mai tarbiyya kuma. Bata rufe baki ba ya daga hannu ya wanka mata lafiyayyen mari kafin ta dawo dai dai ya ƙara marinta a ɗayan kuncin, a gigice Hauwa ta dafe duka kuncinta tana kallonsa a razane idonta a warwaje cike da tsantsar mamaki da tsoro tace. Ni ka mara Aminu daga abun arziki, in yi maka fari ni kayi mini baƙi, ko dai su Sameeha sun bi boka da malamai sun sauya maka tunani. Bata rufe baki ba ya dunƙula hannu ya nausa mata a baki wanda nan take bakin ya fashe ya soma jini, Hauwa ta tsandara ihu ta baje a ƙasa tana cewa. Shikenan sun rabani da ɗan uwana innalillahi wa inna ilaihir raji'un, Aminu ni kake duka ina matsayin yayarka. Aminu ya daka mata uwar tsawa wanda yasa mutane duk suka taru akansu, waɗanda suke nesa ma da basu san ana yi ba suka matso. Yayar banza yayar wofi muguwa azzaluma shaiɗaiya, idan sunan Sameeha bai fita daga bakinki ba wlh sai ba kasheki in yaso nima a kasheni. Kin tarwatsa mini farin ciki na da ni da iyalina, Hauwa kin zame mini matsala a rayuwata. Kece kika saka na rasa lafiyata wanda ya jawo dalilin dana rabu da mata ta, tun lokacin da kika kirani kika fana mini rasuwar Umma nayi accident a lokacin na rasa mazantakata na rasa lafiyar da zan kusanci matata, tsawon shekara shida Sameeha tayi dani tana haƙuri ba tare dana sauke hakkin aurenta ba, bayan mun dawo Kaduna kika matsa mata kika dinga yi mata bita da ƙulli duk saboda son zuciyarki bayan Sameeha ni take rufawa asiri take zaune dani nakassashe, ban faɗa muku ba ta hana ma na sanar da kowa, bayan na saketa kika nuna kinfi kowa murna kika je kika ci musu mutunci kika kwaso yara, kika dage akan sai nayi aure na amsa miki domin na nuna miki kinyi kuskure dan nasan ni ba mai lafiya bace, babu macen da zata zauna dani a haka, amma saboda ki muzgunawa Sameeha kika haɗa baki da 'yar uwarta Najwa kika fitar da Sameeha a gidanta sannan kika aura mini Najwa dan kwai ki kai Sameeha ƙasa saboda kin tsaneta, to ni kika tsana ba ita ba, nine baki so nine kikewa hassada da baƙin ciki Hauwa, to Albishirinki zan bar miki duniyar kici abinda zaki ci a ciki, kuma na saki Najwa domin bazan yarda na zauna da ita a matsayin auren cin amana ba, babban farin cikin da nake ji inna tuna an saki Adama 'yarki saki uku lokaci ɗaya kamar yadda na saki Sameeha, Allah ya nuna miki cewar shi ba azzalumin bawansa bane sai dai bawa ya zalunci kansa, kuma alhaki kuikuiyo ne gashi ya biki, ita kuwa Sameeha ta samu mijin daya fini, 'yan uwan da suka fiku inda ake yi musu so domin Allah, tana cikin farin ciki da ahalinta Allah bai bari sun wulaƙanta ba ya ɗagasu ya ɗaukaka daraja su wanda sai dai gani sai hange, wannan izina ce a gareki dama duk mai irin halinki kuma ki saka a ranki ɗan uwanki Aminu ya mutu wannan da yake a gabanki wani ne sabo bai sanki ba, ban san daga ina kike ba, Allah ya isa tsakanina dake. Ya ƙare maganar yana nuna ta da tsaya duk ya haɗa guimi saboda masifar da yayi, Hauwa kuka kawai take yi cike da tsantsar bakin cikin abinda Aminu yayi mata, ya wulaƙantata a gaban dangi, ya tona mata asirin mutuwar auren 'yarta da suke ta rufa rufa yanzu kowa yasan saki uku aka yi mata wanda a dalilin aurensa ne aka sakeleta. Mutane kam jugum jugum suka yi suna jin abin mamaki, musamman da Aminu ya faɗi rashin lafiyarsa, sunyi matuƙar tausaya masa, waɗanda basu san halin Hauwa ba yau sun sani sai um um da baki suke yi kowa yana tsoron furta nashi sanin halinta ta balbalesu da faɗa, duk da Aminu ma yayi mata hukunci harda fasa baki. Yaya Kamalu da Alhasan sun fito suma sunji komai da kunnensu, ba ƙaramin mamaki kalaman Aminu ya basu ba musamman na rashin lafiyarsa da kuma Najwa 'yar uwar Sameeha ce, basu ga laifin dukan Hauwa da yayi ba dan ita taja ta kuma zubar da girmanta, Aminu ya juya a fusace zai fita Alhasan ya kira sunansa sai ya juya, Aminu ya fashe da kuka ya isa gurinsa ya ɗaura kansa a kafaɗar Alhasan shi kuma yana dukan bayansa akan yayi hakuri, Aminu ya ɗago yana nuna musu Hauwa. Kunganta ita ce gabaɗaya ta rusa mini rayuwata, duk da na yarda da ƙaddara amma itace sila. Yana gama faɗar haka ya juya ya fice daga gidan yana share hawayensa, su Alhasan basu hanashi ba domin yana buƙatar kaɗaici, kallon Hauwa suke yi zaune a ƙasa sai suka danƙara mata mugun kallo kana Alhasan yayi waje Kamalu ma yabi bayansa, koda suka fita sai dai suka tadda kurar motar Aminu dan tuni yayi gaba abinsa, nan suka zauna ƙofar gida suna mayar da magana dan sosai suma suka ji kamar su rufe Hauwa da duka, suma banda a tsaye suke da haka zata tasa rayuwarsu a gaba dan Hauwa tana da mugun sa ido da shiga harkan da ba nata ba. Hauwa kuwa miƙewa tayi jiki a sanyaye ta wuce sashin Laure duk abin duniya ya dameta, domin wulaƙantata da Aminu yayi a bainan nasi ya tsaya mata a rai matuƙa, ga kuma tona sakin da aka yiwa 'yarta, ji tayi idan bata rama abinda yayi mata ba bata haifu ba, sai ta saka rayuwarsa a uku masifa ta yadda sai yazo akan guiwarta yana bata haƙurin abinda ya aikata mata, dan wlh idan zata ja duwawu ne sai ta lalata dukiyarsa dama duk wani abu daya ke taƙamata dashi, girgiza kai kawai take yi tana cizon leɓenta da ƙan8ance idanunta, tana jin su Laure suna bata haƙuri amma bata su take ba dan alwashin sai Aminu ya wulaƙanta take a zuciyarta. ****** Najwa. Suna shiga gida ta wuce ɗakinta tana kuka, Junaid ya shiga ɗakinsa shima ya ciro belt ɗinsa ya sameta a ɗakin ya shiga dukanta yana cewa. Wlh idan ban dukeki ba bazan huce takaicin baƙin ciki da kika ƙunsa mana ba, kinci mutuncin gidanmu kin ɓata manq sunanmu, shegiya mai mugun hali Allah ya wadaranki Najwa. Yaya ka kashe! nima na huta na tsani komai bana son wannan rayuwar ka kashe! Najwa tana faɗa cikin gunjin kuka tana kuma sosa jikinta da dukan da yake yi mata, sauran 'yan biki ne suka shigo ɗakin suka ceci Najwa, Salima ta wanke Junaid da mari tana zaginsa. Dan ubanka kasheta zaka yi, ka bari muji da abu ɗaya mana, ace jiya jiya aka ɗaura aure an sakota kazo kuma zana dukanta da wannan zata ji. Junaid ƙofa yayi ya fice abinsa ransa a matuƙar ɓace, Salima tabiyo bayansa ta tsaya a tsakar gida. Wlh babu wanda ya isa ya ƙara dukanta idan baku sonta ni ina sonta, haka kawai da wanne zata ji? Ai kowa ma yana kuskure sai ayi mata uzuri, dan haka yau ɗin nan zan tafi da ita kano ta cigaba da zama a guna ba zaku ƙara ganinta ba sai kun nimeta. Da kin kyauta kuwa Salima, kinga kin sauƙaƙa mana baƙin cikin da ta ƙunsa mana bamu ganta ba balle mu riƙa tuna abinda ta aikata, sannan ma kin rage mana zagin mutanen unguwa, in dai Najwa ce na yafe miki ita ba kano ba ki wuce kano da, ita ai dama ba a ɗaya a dangi, na tabbatar idan Najwa tayi gadon mugun hali to kuwa a gunki ta gado shi, dan kema babu irin surutun da baki saka iyayenmu ba har suka bar duniya da tabonki. Dama ai da abu ya taso saika goranta mini kuma su Mama basu bar duniya ba saida suka yafe mini komai, aure ne dai naƙi zamansa kuma yanzu Allah ya shieyeni ina zaune a gidan aure har da yara, abu ya wuce amma kullun sai ka dawo da magana baya, ni ba cikin shege nayi ba ko wani mugun abu, aure ne dai naƙi zamansa nayi har guda Huɗu, a na biyar ne na zauna kuma bazan zauna namiji yana cuta mini ba, ko yanzu baban su Lukuman ya yi mini iskanci zan cikawa wandona iska bazan zauna ba wlh. Allah ya kyauta. Dan haka ni na sallami kowa biki ta watse kowa ya zo ya kama gabansa tunda me auren ma an sakota saboda mugun halinta. Baba ya kuma faɗa ya fice daga gidan, nan fa sauran 'yan uwa kowa ya fara haɗa kaya, inna kuwa tunda ta kwanta a gado ta rufe ido bata motsa ba kuma bata son yin magana, tana jin abinda ya wakata da baba da Saleema saida tayi murmushin takaici dan kuwa baba Gaskiya ya faɗa Najwa halinta ta ɗauko dama ba a ɗaya a dangi, ga shegen son duniya da rayuwar ƙarya, haka ta gama zaga gidajen aure huɗu wanda kowa yasan arzikinsu take bi in taga bata samu yadda take so tasa miji ya saketa dole, wannan ne kawai ta zauna dan shima malami ne wataƙila wajen niman asiri ya ganta ya kuma maƙale mata saida ya aureta, daga bisani ma ya kafeta ya mallaketa shiyasa ta kasa kwakkwaran motsi a gidan dan mugun tsoronsa ma take ji, inna taji daɗin ma ta tafi da Najwa wataƙila malamin zai koya mata hankali ita ma ta dawo hayyacinta, dan zata saka baba ya kirashi ya faɗa masa komai ta yadda Najwa sai ta so dawowa nan kuma ba halin haka, sannan ya aurata mata duk wanda ya gadama zata so hakan ya faru. [7/7, 13:04] Buhainat😁: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shai wanidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.* 47. Najwa tunda taji Anty Saleema tace zata je da ita kano sai taji ɗan sanyi a ranta, dan yanzu abinda tafi so shine tayi nesa da inda take da kowa ma ƙila hakan zai saka ta samu sassauci daga halin da take ciki, sai kawai ta miƙe cikin zafin nama duk da tsamin da jikinta yayi na dukan jiya da yau, amma haka ta soma haɗa kayanta dan ko kayan akwatinta a yanzu bata buƙatarsu, kuma kayanta na gida ba a riga an kai mata ba dan haka cikin ƙanƙanin lokaci ta gama komai ta zura babban hijab ɗinta ta saka safa da niƙaf dan so take tayi ɓadda kama yadda babu wanda zai ganeta saboda tana kunyar mutane su ganta kar suyi mata dariya, a dalilin aurenta ta wulaƙanta mutane da yawa ta rabu da ƙawayenta na kan layinsu da yawa a ganinta ta wuce hulɗa da ƙananun mutane, ta jawo trolley ɗin kayanta tsakar gida ta tsaya tare da ɗaga niƙaf ɗinta ta rungume hannu tana jiran fitowar Saleema dan tasan ba zata ƙara kwana a gidan ba saboda itama akwai zuciya, ilai fitowarta da minti goma sai gata ta fito da jakar kayanta tana kwalawa inna kira akan ita zata wuce, ganin Najwa a tsaye da shirin tafiya yasa ta saki murmushi. Kunga 'yar halak harta kimtsa, aiko dama yanzu nake shirin yi miki magana ki shirya ashe harma kin fini zaƙuwar mu tafi, to In Sha Allah alkhairinki yana Kano sai mutane sunga irin wanda zaki aura, yadda kike da kyau da hasken fata mazan Kano ba ƙaramar ƙaunar farar mace suke yi ba. Hmmm ayi dai mu gani in tusa zata hura wuta, ni sai dai nayi muku fatan ku sauka lafiya amma in har Najwa bata sauya halinta ba to wlh kema sai ta gundureki. Najwa ina miki faran shiriya kuma In Sha Allah addu'ata kenan kullun dan hannu bai taɓa ruɓewa ka yanke ka yar, Saleema ki gaida maigidanki da abokan zamanki. Cewar inna data fito daga ɗaki cike da ƙarfin guiwa dan ba ƙaramar farin cikin tafiya da Najwa tayi ba, Saleema ta taɓe baki tana cewa. Ai dama nasan bakinki ɗaya da yaya, ko min abinku Najwa dai In Sha Allah sai ta zama zakaran gwajin dafi. To saleema ai banyi miki musu ba Allah ya sauke ku lafiya. Inna ta faɗa tana wucewa gurin kitchen dan ta ɗauki kofin Baba da aka wanke. Saleema bata ce komai ba ta gyara mazaunin gyalenta ta yi gaba Najwa ta sauke niƙaf ɗinta ta bi bayanta da trolley suka fice daga gidan, suna fita sauran 'yan uwa suka shiga zancen tafiyarsu Inna tana ji bata saka baki ba dan fatanta ma kowa ya watse ya bar mata gida ko zata shaƙi iska mai daɗi saboda abinda ya faru har yanzu baisa ta samu natsuwa mai kyau ba. Najwa suna fita suka samu napep ya wuce dasu tasha ba ɓata lokaci suka samu motar Kano suka shiga, Saleema ta biya kuɗin, mota tana cika suka kama hanya, sai a lokacin ne Najwa ta soma fidda zafafan hawaye taji duniyar ta yi mata kamun kazar kuku, tana gani ta rasa komai duk wani burinta ya ƙare a lokaci guda, dana sanin yadda ta kamu da son Aminu ta soma yi, ba wai dan tayi nadama ba sai dan dana sanin akan baida lafiyar da zai iya ɗauke nauyin duk Sha'awarta data jima tana yi akansa, ashe duk wani tanadi data yi masa aikin banza tayi, ji take duk abinda ya sameta Sameeha ce sila da bata dawo taje gidanta ba da duk haka bai faru ba, shiyasa take jin itace babbar maƙiyiyarta sai Ikram sannan Aminu da kuma Nafeesa data faɗo mata a rai, nan take ma ta tuna da tona mata asirin da tace zata yi domin tana so yadda ta rasa komai ta muzanta to itama Nafeesa ta shiga halin ƙunci, domin itama ta taka muhimmiyar rawa wajen sata yin wasu abubuwan, sai kuma su Binafa da suma ta yi alwashin tona musu asiri kowa kwaɓarsa sai tayi ruwa, a sannan ne ta saki murmushi wanda yake cike da tarin mugunta, ta ciro wayarta dake jaka sai ta tuna da ta ci screen, sai ta kalli Saleema tana cewa. Anty dan Allah ara mini wayarki akwai abinda nake son tura wa yanzu. Ba musu ta ciro wayar a jaka ta bata, Najwa ta saka sabon sim ɗin data yiwa Ikram text lokacin bikinta a wayar Saleema, sai ta kunna data ta sauya WhatsApp ɗin Saleema ta mayar da nata Number ɗin, dama duk numbers ɗin da take so tayi savimg a nan, dan haka cikin kankanin lokaci ta rubuta saƙo kamar haka ta turawa number ɗin yayan Nafeesa da take cewa. Ɗan uwa ina son in sanar da kai wani lamari wanda nake fatan mu samu masalaha a cikinta, nine Saurayin Nafeesa wanda muka samu matsala da ita muka rabu, dalilin akwai wani sirri da muka rufe wanda ya dameni sosai shiyasa na buƙaci na sanar da kai ko hakan zai sa mu samu maslaha. A lokacin da take zuwa Poly wani tsautsayi ya faɗa a tsakaninmu har na kusanceta sai kuma ciki ya samu, to gaskiya na shiga damuwa sosai wanda yasa nace dole sai an zubar saboda mu rufawa kanmu asiri, to shine ta samu cousin ɗinku Binafa suka san yadda suka yi aka zubar da ciki sai asirinmu ya rufu, daga nan kuma muka cigaba da mu'amalarmu amma tana yin planning yadda ciki bai sake samuwa ba. Ita Binafa ta rufa mana asiri muma mun rufa mata saboda munyi ban gishiri ne in baka manda, domin itama cikakkiyar 'yar lesbian ce wacce har aure tayi da wata ƙawarta Hanan a ɓoye, abubuwa dai da yawa sun faru kuma suna kan faruwa, to gaskiya wannan dalilin yasa naji bazan iya auren Nafeesa ba saboda zargi da ya shiga tsakanimu, amma bayan 'yan kwana biyu naji sam banyi mata adalci ba dana rabu da ita sai dai bazan iya cigaba da ɓoye wannan sirrin ba dole sai na fito na faɗa, wataƙila zamu samu maslaha ku yafe mini. Ta tura masa dan dama a ranar da aka kaita kafin ta yiwa Nafeesa magana lokacin da zata cire sim ɗinta ta ɗauki number ɗinsa a wayar Nafeesa tayi saving a ƙaramar wayarta. Najwa nan take taga yayi marking sai ta kashe data ta shiga hotunan Saleema tana kallo tana jin farin ciki a zuciyarta na tona musu asiri. Bayan awa guda ta ƙara kunna data sai ga sakon yayan Nafeesa kamar haka. Innalillahi wa inna ilaihir raji'un. Amma Hamisu kaci amana bamu zaci haka daga gareka ba, ai ko tunda abinda ya faru kenan dole ma ka aureta dan baka isa ka ɓatatq ba kace zaka rabu da ita, yanzu ina hanyar zuwa gida za ayi duk wacce za a yi ma. Najwa tana gama karanta haka ta saki shu'umin murmushi kana ta kuma kashe data ta kwantar da bayanta a jikin mota ta lumshe ido tare da jin wani farin ciki yana ratsata akan abinda ta aikata, tace a ranta. Yadda na muzanta na rasa farin ciki kuma sai kun rasa shi wlh, saboda tare daku muka aikata komai, dole ko wanne ya amsa nashi rabon baƙin cikin. A haka ta dinga tunani har barci ya ɗauketa, sai da Saleema ta tasheta tana cewa. Yadda kika samu barcin nan ya nuna alamar zaki samu natsuwa a garinmu, na tashe ki ne saboda mun kusa sauka tun ɗazu muka shigo Kano. Wlh da yake banyi barci mai daɗi ba shiyasa ga gajiyar biki dana duka. Ta faɗa cikin sanyin murya. Allah sai ya saka miki In Sha Allah. Saleema ta faɗa tare da yin shuru tana duba agogon hannunta. A takaice sun isa gida gurin ƙarfe uku na rana suna shiga yaran Saleema suka rugo suna yi musu oyoyo da uniform ɗin makaranta a jikinsu, suka amsa trolley Najwa suka wuce part ɗinsu, sai da suka sha ruwa suka zauna a cushing tana tambayar babbar 'yarta Ikilima me suka dafa? tace taliya ce dafadukan manja kuma ya ƙare, sai tace ta shiga kitchen ta dafa musu indimie guda Huɗu dan da yunwa suka shigo, tace to kana ta wuce kitchen, a lokacin ne ɗan kishiyarta ya shigo yana ce mata babansu yana kiranta a ɓangarensa, tace to kana ta miƙe ta mayar da mayafinta tabi bayan yaron. Babban gida ne da yake da part huɗu nata ɗaya sai na kishiyarta uwar gidan malam sai kuma na amaryarsa da bai jima da aurenta ba sannan nashi ɓangaren da yake ganawa da mutanensa, sannan kuma turakarsa ne duk me girki can take samunsa. Saleema tana shiga ta sameshi zaune a dadduma ya jingina da jikin cushing da fara'arta ta ƙarasa ta zauna a carpet tana gaishe shi ya amsa fuska a haɗe tare da cewa. An sanar dani kin dawo tare da baƙuwa shine na kira naji dalilin zuwa da ita ba tare da kin sanar dani ba. Wlh zuwan bana shiri bane shiyasa na tawo da ita, dama nace in muka ƙaraso sai na sanar da kai. Ke bana son shashanci taya zaki yi gaban kanki saboda baki ɗaukeni a bakin komai ba, Saleema na fa gaji da halinki duk cikin matana ke ce mai taurin kai kike bani matsala, banda ina duba darajar yaranmu da tuni na rabu dake wlh, to ina so ki tattarata ta bar mini gidana tun kafin dare yayi, dan kinsan bana karɓan baƙon da ba a sanar dani ba. Subhanallahi haba malam, meyasa zaka yanke mini hukunci irin wannan ba tare da kaji uzuri na ba kuma... Ki tashi ki bar mini falo tun kan ki harzuƙani, na kula ke zuma ce dole sai da wuta, in ba raini ba taya zaki yanke hukunci baki sanar dani ba, to na baki umarni ta bar mini gidana yanzu yanzu. Yayi maganar a tsawace jikin Saleema yana rawa ta miƙe saboda tana mugun jin tsoronsa dan ba haka ya barta ba, da tashin hankali ta baro sashinsa da tunanin ina zata kai Najwa ta zauna kafin ta shawo kan malam ya haƙura. ***** Nafeesa. Tun ranar data bar gidan Najwa take jin ranta babu daɗi dan bata taɓa zaton Najwa zata yi mata haka ba, duk da tasan itace ta ci amanar ta amma amintarsu da kuma taimakon data yi mata na samun cikar burinta bata cancanci irin wannan wulaƙancin ba, yanzu babban tashin hankalinta data san sirrinta data jima tana ɓoyewa, tasan kuma halin Najwa muddun ta matsa mata to zata iya tona mata asiri, dole ne ta nima hanyar sulhu su ahirya ta kuma rabu da Aminu shine kaɗai mafita a garera dan ba zata so abinda tabirne ya tonu ba. Har zuwa washe gari da tunanin ta tashi ta yanke zuwa gidan Najwa dan suyi sulhu. Wajen ƙarfe sha biyun rana ta je gidan sai dai maigadi ya tabbatar mata da babu kowa a gidan tun safe da suka fita da Aminu basu dawo gidan ba, sannan koda ta kira wayarta a kashe cikin sanyin guiwa ta koma gida da tunanin gobe in Allah ya kaimu zata koma ta sameta, kamar zata wuce gidansu Binafa sai kuma ta fasa ta koma gida ta kwanta dakinsu ba jimawa barci ya ɗauke ta saboda jiya bata samu barcin kirki ba. Yayanta Taju daya shigo gidan a hargitse ya wuce sashin mahaifinsu, nan ya same shi a falo ya zauna ya zayyana masa komai na saƙon da Najwa ta tura masa, ba ƙaramin tashin hankali babansu ya shiga ba dan haka cikin ɓacin rai suka baro part ɗinsa suka shiga sashinsu, a falo suka tadda mamanta nan itama suka sanar da ita salati take ta yi dan itama ta girgiza, Yaya Taju ya tambayi Nafeesan tana ina? Hajiyarsu tace tana ɗakinta a sama, cikin azama ya wuce zuwa ɗakin yadda ya bankaɗa ƙofar ta buɗe yasa Nafessa ta farka a firgice, sai dai kafin ta wastsake daga barci Taju ya rufeta da duka da belt ɗin wandonsa daya cire, ta shiga kwalla ihu tana kiran a ceceta sai dai babu wanda ya zo har sai da yayi mata lilis ya farfasa mata jiki kafin ya tsaya da dukan dan kansa yana mayar da numfashi, cikin huci yace. Tashi muje falon ƙasa. Bata yi watawata ba ta miƙe duk da ya tsamama mata jiki, haka ya tasa ƙeyarta suka sauko ƙasa, yadda taga fuskar mahaifinsu da Hajiyarsu shine ya ƙara mata tashin hankali dan nan take kwakwalwarta ta harbo mata da asirinta ya tonu Najwa ta tona mata asiri. Nafeesa ta gurfana a gabansu a ƙasa, Taju ya zauna a cushing ya ɗauko wayarsa ya soma karanta mata saƙon da aka turo masa, jikinta babu inda baya rawa dan sosai ta kaɗu da jin kamar Hamisu ne ya tona mata asiri ba Najwa ba, ana zaton wuta a makareta sai ga shi a masaka, Najwa ta bayar zata tona mata asiri sai gashi Hamisu ne yaci amanarta bayan ya ɓata mata rayuwa, sai ta rushe da kuka mai tsanani duk jijiyoyin kanta sun tashi tasan asirinta ya gama tonuwa, ƙarin takaici har da asirin Binafa ya tona, Taju ne ya daka mata tsawa akan ta faɗa musu gaskiyar abinda ya faru in kuma tayi masa ƙarya saiya karyata in yaso ayi jinyarta, to ya zata ɓoye ma bayan ranar wanka ba a ɓoyon cibi, dole ne ta amsa ƙaddararta tunda kuwa Alhaki kuikuyo ne ta tabbatar da hakkin Sameeha ne ƙila ya soma bibiyarta, tunda tasan da ita aka haɗa komai kusan itace ke ɗaura Nahwa akan yin wasu abubuwa, cikin kuka ta basu labari ta tabbatar musu da hakan ya faru harma da rayuwar da Binafa keyi na lesbian bata ɓoye ba, salati kawai iyayen suke yi Taju kuwa miƙewa yayi jikinsa babu inda bata rawa saboda masifa, ya shiga ya ɗauki Number ɗin da aka turo masa saƙon ya soma kira, sai dai baya shiga kwata kwata, ya dubeta a tsawace. Ki bani number ɗin Hamisu yanzu na kirashi. Duk da ba waya a hannunta ta haddace number ɗinsa, nan take ta karanto masa ya saka a wayarsa ya kira, da aka ɗaga wayar sai dai macece suka ji, Yaya Taju yace. Ina me wayar ki bashi. Sai suka ji ta buɗe murya tana cewa. Baby baby kazo ana kiranka a waya. Taju sansarai yayi yana jin kayan takaici, har Hamisu ya amsa wayar yana cewa. Hello waye ne ke magana naga number ne. Taju ya haɗiye miyau kwad na talaici yace cikin faɗa. Da yayan Nafeesa kake magana, wato irin cin amanar da kayi mana kenan ka rabata da mutuncinta sannan ka sa ƙafa ka rabu da ita saboda mugunta, to dan haka ina so mu haɗu ka zo gidamu domin a yi sulhu a gyara lamarin tunda kai ka ɓata ta kai ne zaka aureta.. Kut wlh ni yanzu babu Nafeesa a rayuwata domin kuwa makon daya gabata nayi aure, dama inata son kusan abinda ya faru domin na nima tafiyar ku, don Allah kuyi haƙuri tsautsayi ne amma ina yi mata fatan alkhairi allah ya bata miji nagari, saboda wlh inna ce zan aureta zamanmu bazai yi daɗi ba saboda zargi ne zai shiga tsakaninmu. Kutumar kaza kazanka ne, ka lalata mana yarinya sannan kana cewa ba zaka aureta ba, to ko yau kayi aure saika auri Nafisa in ba haka ba kuwa ka saurare sammaci daga kotu. Hmmm yaya kenan, in kuka yi haka ai 'yarku kuka ciwa mutunci domin duk wanɗanda basu san me takaikata zasu sani, kunga kun ɓata sunan gidanku da zubewar mutuncinku, ni kuma duk abinda nayi ado ne wlh babu abinda zai ɓata mutunci na tunda nasan yadda zan kare kaina. Nafisa ko kyautarta kuka bani wlh bazan iya aurenta ba domin na ci moriyar ganga, kuma zuri'arku babu tarbiyya daga 'yan lesbian sai mai bin maza, idan kuma kace zaka ja maganar ina shirye daku. Sai kit ya kashe wayarsa, tsabar jikin Taju daya yi sanyi komawa yayi ya zauna yama kasa magana, Iyayensu ma kasa maganar suka yi dan a handsfree ya saka wayar sunji duk maganarsa, Nafeesa kuwa kukan baƙin ciki take yi wanda yake cike da dana sani, ƙarin haushinta wai yayi aure ita ya gama da ita, mahaifiyarsu ce ta katse shurun da cewa. Ya riga ya gama cutar damu kuma kema kin cucemu Nafeesa, yadda nake kula da tarbiyyarku ban taɓa zaton haka ba, dan haka ni zai fi kyau a bar maganar dan mu tsire da mutuncinmu shi kuma mu bar shi da Allah, sai mu tari matsalar mu samu wani mu haɗashi aure da ita, dan wlh aurenta shine namu rufin asirin. Hmmmm Allah ya kyauta, kuma dole mu bar maganar, sannan Taju ina so Ka yiwa malam Sadi mai yiwa yara karatun islamiyar nan gidan magana ko zai iya aurenta, bana so ka rufe masa matsalarta ka sanar da shi in ya amince sati mai zuwa za a ɗaura aurensu, zan bashi gida kyauta da zasu zauna da ita ke kuma daga yau karna sake ganin ƙafarki koda a tsakar gida ne, sannan Hajiya ki amsa wayarta ki kawo mini. Batun Binafa kuma Taju kaje ka sanar da iyayenta. Alhaji yana gama faɗar haka ya miƙe ya bar sashin, Nafeesa ta ƙara rushewa da kuka akan haɗin da za ayi mata da Sadi, duk da ba mummuna bane amma bayi da komai talaka ne futuk, kuma babban ci baya ne a auransa ita da take da wayewa da ilimin zamani. Tsawan da Taju ya daka mata yasa tayi shiru ya cigaba da dura mata zagi yana cewa. Hukuncin Abbansu shine dai dai, haka ya fice daga falon rai a ɓace, Hajiyarsu ta miƙe ta kamota ta zaunar a cushing ta shiga rarrashinta tana cewa. Dama ki daina wannan kukan kiyi fatan Sadi ya amince da aurenki domin kuwa auren nan shine kaɗai rufin asirinmu, jin daɗi da gata yasa kika saka mana da mummunar tabo amma dai dai gwargwado ina kula da tarbiyyarku, kiyi haƙuri ki barwa Allah zaɓinsa yasa hakan ya zama miki alkhairi, kuma In Sha Allah za ayi miki biki na gata kamar yadda akewa kowa kinji. Nafeesa ta ɗaura kanta a kan cinyar momynsu tana yin marayan kuka jikinta har ciccira yake yi, dana sani sosai ya wanke zuciyarta wanda take jin dama ana mayar da hannun agogo baya tabbas da ta gyara kuskuran data aikata, tana jin dole ne ta nima yafiyar Sameeha wata ƙila ta samu sassauci daga halin ta taje ciki, dole ne ta saduda ta amsa ƙaddarar data kira da hannunta wanda tarin son zuciya ya kaita ya baro, fatanta Allah yasa Sadi ya yarda da aurenta, a yanzu ba tada zaɓi face zaɓin iyayenta da kuma karɓan ƙaddararta, wataƙila ta samu dacewa ta rabauta, sannan dama ba tada mashinshini ko wanda tasan zai aureta a yanzu, sai ta kara sakin kuka mai tsuna zuciya, ta tuna da Aminu da kuma Najwa tasan itama ko bajima ko ba daɗe dole asiri zai tonu, zata bar Aminu bari na har abada dan ta kama dahir, sannan zata yi ƙoƙarin sanar da Najwa gaskiya ko ƙila zata hankalta ta kama aurenta da kyau, Momyn ta cigaba da buga bayanta ita kuma kukan nadama take fiyarta gwanin tausayi. [7/7, 13:04] Buhainat😁: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shai wanidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.* 48. Nafeesa sai da zazzaɓi mai zafi ya rufeta saboda kukan data yi, da kyar momynsu ta lallaɓata ta kaita ɗaki ta samu barci, sai ta fito ta cigaba da ayyukanta. Taju daya fita yayan Binafa ya kira a waya ya tambaye shi ko yana gida, sai yace yana nan a haka suka aje wayar ya ɗauki motarsa zuwa gidan. Daya isa part ɗin mazan gidan ya wuce ya same shi a ɗakinsa wato falo, yana ganinsa ya miƙe cikin fara'a ya miƙa masa hannu suka gaisa kana suka zauna a cushing, Taju yace cikin zolaya. Maza ya kamata a barwa su Auwal gidan nan ka koma naka gidan, ayi mutum yaƙi aure yana niman tsufa a gida. Haba dame kwaɗo yafi gaya ai kaima ba jimawa kayi da auren ba, wato ka ji daɗinsa zaka fara yi mini gori, to bama wannan ba nasan duk in ka nimeni da akwai magana, meye labari?. Hmmm Nafeesa da Binafa ne suka nima chager mini kai yaran nan ƙiri ƙiri suna niman ɓata sunan zuri'armu. Me suka yi? Amma nayi mamaki daka ce har da Nafeesa dan ita tana da natsuwa da hankali ba irin Binafa da kullun cikin saka mu magana take yi ba. Nan Taju ya gyara zama ya ciro wayarsa ya buɗe WhatsApp ya bashi saƙon da aka tura masa, Hassan ya amsa ya karanta, koda ya gama mamaki ne ya maye fuskarsa Taju ya ƙara da bashi labarin abinda Hamisu yayi masa daya kirashi, sosai ran Hassan ya ɓaci ya miƙe cikin zafin nama yana cewa. Haba dama biri yayi kama da mutum, shegiyar yarinya kullun sai ta fita ko ta jawo mana ƙawaye su zo gidan nan, ashe iskancinta take yi son ranta wlh idan na gamu da Binafa rai kaɗan zan bar mata. Yana gama faɗar haka ya isa gurin daya saka chargy wayarsa ya ɗauka sai ya dawo ya zauna ya shiga kiran layin Binafa, har sai da ya tsinke ba a ɗauka ba ya kuma kira sai aka dauka yadda yaji murnar namiji ne sai ya dannw zagin daya yi niyyar dura mata, yace a dakile. Malam ina me wayar? Kana magana da Sagent Lawal mai wayar kuma mun kama tana nan police station bisa laifin Fyaɗe da suka yiwa wata yarinya suka lalatata, to dama mun so ta faɗa mana wanda zamu kira a 'yan uwanta amma tace bata da kowa tana so mu bada belinta amma hakan ba zai yuwu ba. Ok wane police station ne? Nan ɗan sandan ya sanar da shi, Hassan yace gashi nan zuwa sai ya kashe wayar yana duban Taju tare da bashi labarin a taƙaice, Taju ya miƙe yana cewa. Zama bai ganmu ba wato dai maganar da Hamisu ya faɗa ta tabbata, Allah ya shirya. Hassan bai iya cewa komai ba saboda takaici sai ya miƙe suka fita tare, a motar Taju suka je police station ɗin wanda sagent ɗin da ya ɗauki wayar shine ya turasu gurin DPO ya gabatar dasu, bayan sun gaisa DPO yace. Wlh munyi munyi su faɗa mana wani nasu amma sunƙi, iyayen yarinyar da suka yiwa Fyaɗe sun ce ba zasu haƙura ba sai anje kotu, a takaice tun wata guda daya wuce suka yaudari yarinyar suna kaita gidan Hanan a nan suka ɓata ta, yarinya 'yar shekara sha shida kuma ba sau ɗaya suka yi mata ba yafi sau biyar, mahaifiyar yarinyar ne ta kamata a ɗaki tana saka brush a gabanta shine data duketa matsa mata take faɗa mata yadda aka yi ta zama haka, to a nan gidan Hanan muka kamo su yanzu haka muna son ranar monday zamu miƙa maganar kotu tunda basu yi gardamar laifinsu ba, sai dai sun nima su bamu cin hanci dan mu rufe maganar hakan kuma ya ƙara laifinsu. Ni sunana Hassan wannan kuma Taju mu yayyin Binafa ne dan haka ina so ku cigaba da riƙe su har sai an shiga kotu an yanke musu hukunci, kamar yadda taƙi faɗar kowa nata ina so koda danginmu sun zo nimansu ku nuna basa nan, dan Allah ina son wannan ya zama sirri karku nuna mata mun zo ma, zan tafi da wayarta ta yadda ko ta bukaci yin magana da wani ba zata samu ba ku nuna mata babu dama. Haba Hassan ya zaka ce haka bai kamata in ta aikata laifi mu rufe maganar ga iyayenmu ba. Cewar Taju, Hassan ya saki guntun murmushin takaici yace. Ina so wannan ya zama babban darasi a garesu, kasan halin Binafa ba tada natsuwa ga taurin kai, ta jima tana aikata ɓarna ina son wannan ya zama hanyar shiriya a garesu, Allah yasa a kaisu gidan yari ma. DPO dan Allah kayi abinda nace maka dan wlh wannan shine kadai hanyar da zaisa Binafa ta shiga hankalinta. Karka damu zamu yi aikin daya kamata dan ba zamu taɓa yarda a danne zalunci akan gaskiya ba. Nan suka yi masa sallama ya basu wayar Binafa suka wuce. A mota Taju take cewa. Anya hakan bazai sa sunan zuri'armu ya ɓaci ba? bana so maganar nan taje kotu. Wlh sai taje fa, Taju kai dai ka saka ido kawai, ai su Dady sune suka ɗaure mata gindin yin komai dan haka bana tsoron duk abinda zai faru ta yadda kowa zai gane kuransa, kuma babu sunanmu da zai ɓaci nata ne dai zai ɓaci wlh. Haka suka dinga tattauna maganar Hassan ya roƙi Taju akan karya sanar da kowa maganar har sai anje kotu kafin maganar ta fita, ta hakane za a samu daidaiton tarbiyya dan abin yayi muni da yawa. Haka Taju ya sauke shi a gida sai ya wuce abinsa, ko shi yaji daɗin abinda Hassan yayi kawai baya son ya nuna rashin damuwarsa akai ne yasa yake ta bashi magana, amma hukuncin daya yanke shine daidai yana so Binafa ta gane kurenta ta yadda ba zata sake sha'awar wata mace ba a rayuwarta. ****** Hauwa. Ta kasa fitowa waje saboda kunyar abinda Aminu yayi mata sai da aka yi sallar magriba kafin ta tattara yanata yanata ta koma gidanta tare da yaranta duka. Dama tun rana baƙi kowa ya kama kansa sai 'yan kauye da suka rage akan washe gari zasu wuce suma. Saboda naushin da Aminu ya yi mata sai da ya saka hakoranta na gaba yin girgiɗi alamar zasu faɗi, gashi ya sakar mata zazzaɓi sai da tasha maganin rage zugi kafin ta samu barci a ranar. Adama kuwa baƙin ciki goma da ashirin ga saki ga kuma wulaƙancin da Aminu ya yiwa mamanta ga kuma lalacewar aurensa da Najwa wanda a dalilin auren itama ta rasa nata auren, tun tana yin kukan fili har sai da ta koma yin na zuci, dan hakanan take jera ajiyar zuciya wanda ya saukar mata da ciwon kai mai tsanani da alama jininta ya hau, da kyar ta samu barci. Washe gari Hauwa ta tashi saman dashishinta ya kumbura daga sama, sun tabbata fita zasu yi dan sosai suke yi mata ciwo, da kyar ma ta iya karyawa, bini bini take jan tsaki ta ƙumdumawa Aminu ashar, a haka Laure ta shigo gidan domin ta ƙara dubata da kuma jaje. Bayan sun gaisa Hauwa take cewa. Wallahi Tallahi bazan yafe wannan cin kashin da Aminu yayi mini ba, sai yayi nadamarsa dan sai na saka shi yayi kukan jini. Ni kam Hauwa da za kiji shawara da kin saki komai kin barwa Allah dan wlh ni na sare da komai saboda babu nasarar da muka samu komai lalacewa yake yi ba biyan buƙata, jiya fa Alhasan kamar zai rufeni da duka saboda masifar da yake ta yi mini wai ai duk bakina ɗaya dake, dana nima kare kaina ya ce inna kuma magana abakin aure na wai ya gaji da halina kuma aure dai zai ƙara ya huta da baƙin cikin dana ke ƙunsa masa, yanzu ma ƙarya nayi masa akan zanje dubiya na shigo nan, ƙila daya san nan zan zo ba zai bari ba, dan sosai ya goyi bayan abinda Aminu yayi miki cewa yayi da zai samu dama shima da sai ya nakaɗa miki duka, saboda duk cikinku ke ce kika fita zakka ya rasa ina kika samo mugun hali. To yanzu kin zo kina faɗa mini ne ki ƙara mini baƙin ciki ko jajenta abin da ya same ni, idan kin saduda ni ban sadudu ba kuma ki bar mini faɗar dama ban gayyace ki ba, zaki iya barin mini gida bana son damuwa. Haba Hauwa abokin kuka shi ake faɗawa mutuwa, ni na baki labari ne domin abin bai yi mini daɗi ba muyi wa juna jaje, kema kinsan muna tare, sai dai kawai na fita daga sabgar Aminu da Sameeha dama duk abinda ya shafesu dan in zauna lafiya, bana son na rasa aurena a karo na biyu kema shawarar da zan baki ki yi hakuri ki saki komai ki ɗauki haka a matsayin rubutaccen ƙaddara, ki kama 'yan uwanki ki zubar da makamanki. Kutumar kaza kaza 'yan uwan, mutanen da suke son ganin bayana, to ganin bayana mana dan babu wanda yake goyon bayana balle a tsawatarwa Aminu wulaƙancin daya yi mini, sam basa ƙaunata saboda Aminu yana da kuɗi ni kuma fuƙara'u ce, dan haka na san duk yadda zan zauna da ko wani tsinanne ne wlh, banda nasan uwa ɗaya uba ɗaya muke da sai nace ƙila ni tsintoni aka yi aka saka ni a cikinsu. Da wanne zanji da sakin Adama da aka yi akan wannan tsinannen auren ko da wulaƙancin Aminu. Haƙuri dai za kiyi Hauwa mu karɓi wannan ƙaddarar In Sha Allah Adama zata samu wanda yafi mijinta, muyi kokarin gyara kuskurenmu dan Allah, saboda in ɓera na da sata daddawa na da wari, Alhakin Sameeha ne yake binmu. Laure tashi ki bar mini gidana tun kafin raina ya ƙara ɓaci na zageki. Allah ya baki haƙuri yasa ki gane amma wlh ni dai na cire hannu na daga lamarin Aminu babu ruwana. Tana kaiwa nan ta miƙe ta gyara hijab ta fice daga dakin, Hauwa ta bita da mugun harara, wanda tana fita ta fashe da kukan baƙin ciki, ji tayi duniyar tayi mata zafi ga mari ga tsinka jaka da wanne zata ji. Aminu tunda ya bar gidan ya wuce gidansa sai da ya ɗauki kusan awa biyu a kwance a ɗakinsa, kiran sallar ya tashe shi ya gabar kana ya koma ya kwanta ko yunwa baya ji. A ranar dai baiyi barcin kirki ba domin kuwa ga yunwa ga kuma damuwa. Da safe da wuri ya shirya ya fita ta siyowa kansa abin kari yaci ya ƙoshi yana shirin sake fita sai gasu yaya Alhasan sun zo shi da Kamalu, da suka zauna suka gaisa kana suka jajanta masa abinda ya faru tare da bashi haƙuri akan ya yafewa Hauwa, Aminu ya nuna musu babu komai kuma komai ya wuce nan ya sanar dasu tafiyarsa London da zaiyi na shekara biyu, ya kuma faɗa musu yana so Baba Hansatu zata dawo nan babban gida ta zauna suna kula da ita kafin Allah yayi masa dawowa, suka yi masa murna da fatan alkhairi tare da tabbatar masa da zasu riƙe Baba a hannunsu, nan ya bar musu amanar gidansa su kula masa da shi har da yawo, ya kuma basu maƙudan kuɗi su raba da kuma kuɗin da zasu yi wa Salma gara in ta haihu, ya kuma sanar dasu hukuncin daya yanke akan yaransa na ya barsu a hannun Sameeha, sun ji daɗin haka kuma sun goyi da bayan duk hukuncin daya yanke, daga bisani suka yi hira sosai kana suka tafi ya rakasu har zuwa babban gida daga can ya wuce Zaria. A ranar su Junaid suka zo da mota suka kwashe kayan Najwa, dama Aminu ya bar key ɗin gidan a hannun me gadi, tas suka gama kwashe komai suka rufe gidan tare da mayar da key ɗin a hannun me gadi suka wuce. A ɗakin Najwa suka zuba kayan tunda bata nan sai suka rufe ɗakin gabaɗaya, a lokacin ne kiran Saleema ya shigo wayar Baba yaƙi ɗauka. ****** Kano. Tunda Saleema ta dawo sashinta sai ta shiga ɗakinta ta zauna bakin gado tana cike da damuwa kamar zata fasa kuka dan baƙin ciki, tunawa da tayi da Baban Najwa yasa ta fito ta amsa wayarta a hannun Najwa ta koma ɗaki ta kirashi, koda ya ɗauka ta zayyano masa duk abinda Mijinta ya ce da Najwa ba zata zauna masa a gida ba sai ta ɗaura da cewa. Dan Allah yaya ka kirashi kayi masa bayanin abinda ya faru nasan in ka saka baki zai bari ta zauna da mu. Hmmm Saleema kenan, kin ga tun kafin aje ko ina kin fara ganin sakamakon ɗaukar Najwa, yarinyar nan amanar zumunci taci shiyasa ba zata ga dai dai tunda har yanzu bata yi nadama ba, dan haka babu abinda zan ce masa bazan hana shi yanke hukunci a gidansa ba, ke da kika ji zaki iya da ita ki san inda zaki kaita. Haba yaya ya zaka ce haka... Bata gama magana ba ya kashe wayarsa, Saleema takaici ya cikata da tunanin mafita, tana zaune a wannan yanayin ga yunwa daya dameta sai ga Malam ya shigo sashinta Allah yasa baiga Najwa a falonta ba ya wuce bedroom ɗinta ya sameta ta rafka tagumi, tana ganinsa ta miƙe tsaye a tsorace fuskarsa kamar zata fashe da kuka. Me kike jira da baki sallameta ba? Saleema samun kanta tayi da tsuguna masa akan guiwarta ta fashe da kuka tana cewa. Don Allah kayi haƙuri malam ka duba zumunci ka barta ta zauna, yarinyar Yayanmu ne na Kaduna wacce aka yi bikinta jiya mijinta ya saketa a yau saboda baida lafiyar da zai kusanceta, ya ɓoye mana haka sai da aka yi biki muka sani yau daya sakota dan cewa tayi ba zata zauna da shi, yanzu ma na gama waya da yaya akan ya kiraka ya baka haƙuri yace bazai kira ba ba zai hanaka yanke hukuncin gidanka ba. Saleema ta samu kanta da shimfiɗa ƙarya akan labarin Najwa, Malam ya sauke ajiyar zuciya yace ta tashi ta zauna gefen gado, Saleema ta miƙe da sauri ta zauna, shima zama yayi kusa da ita yana cewa. Ni bawai na nuna ba zata zauna bane saboda na muzguna miki ba, kawai ina so na nuna miki ina da muhimmanci a gareki domin ki riƙa sanar dani duk abinda ya zama wajibi na sani, kinga da kin sanar dani komai a waya da babu yadda za ayi nace ba zata zauna ba, dan haka babu damuwa ta zauna damu Allah yasa hakan ya zama mata alkhairi ya zaɓa mata miji nagari, sai dai kinsan ina da sharuɗɗa, ki sanar da ita bana son yawo sannan ta zauna a nan ɓangaren karna ganta a farfajiya, idan ta samu natsuwa zan duba me ya dace da ita ko makaranta ko kuma auren. Nagode Malam Allah ya saka da alkhairi amma ni nafi son tayi wani auren dan mu bawa maƙiya kunya masu yi mana dariya. Ba dan Allah kike so tayi auren ba kenan, karma ki saka hakan a ranki ki taya ta da addu'ar mafi alkhairi a gareta. Duk abinda take so ta sanar dake ki faɗa mini Allah ya taya mu riƙo. Saleema ta amsa da amin kana ta yi masa godiya sai ya tashi ya fita itama ta bi bayansa har sai da yabar sashinta kafin ta dawo cikin falon tana kwalawa Najwa kira, data fito daga ɗakin yaranta ta zauna sai Saleema ta sanar da ita amincewar da malam yayi ta zauna a gidan, Najwa taji daɗi sosai domin ga dukkan alamu zata shimfiɗa duk abinda take so a gidan tunda suma masu kuɗi ne ba laifi gida ne me kyau, sai dai data sanar da ita baya son yawo tace ba damuwa amma a ranta tana cewa bata ga wanda zai hanata yin abinda take so ba. A ranar Najwa ta samu barcin da ta jima bata yi ba domin tuni ta watsar da damuwa ta fara tunanin yadda zata kafa sabuwar rayuwa, duk da haushin Aminu dasu Sameeha yana manne a zuciyarta. Washe gari ne bayan sun karya sai Saleema ta tasa ƙeyar Najwa zuwa ɓangaren malam domin ta gaishe shi, koda suka shiga sun same shi da baƙi maza biyu nan suka gaisa Saleema ta gabatar masa da Najwa yace. Baƙuwa da fatan zaki zauna damu da zuciya ɗaya, bana son yawo bana son na riƙa ganinki a farfajiya in ba kwakkwaran dalili ba, sannan ban yarda da bin shashin matana ba saboda bana son rikici. Najwa tace to amma a zuciyarta tana mamakin rashin karan da Malam ya nuna mata ƙarara, haka suka bar falon Saleema jikinta a sanyaye dan taji kunyar maganganun malam ga Najwa, suna fita Saleema ta kira Yaya domin ta sanar dashi malam ya yarda da zaman Najwa sai dai harya ringing bai ɗauka ba, da suka isa sashinsu ne ta kuma kira shine ya ɗauka take sanar dashi komai yace ba damuwa kana ya sanar da ita an kwaso kayan Najwa ɗazun. [7/7, 13:04] Buhainat😁: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shai wanidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.* 49. Su Saleema suna fita daga falon malam, sai ɗaya daga cikin mutanen dake falon yace cikin sosa kai. Malam in ba damuwa ina da magana akan wancen yarinyar da suka fita yanzu, amma Allah yasa ba matar aure bace. Malam sai da yayi 'yar dariya kafin yace. Ina jinka Atiku faɗi maganarka kai tsaye. Yauwa dama ina kamun iri ne idan ba matar wani bace, zan ƙara ta biyu da ita. Atiku manya daga ganinta sai kaji kana son ƙara aure anya kuwa?. Dama ina son na ƙara to har yanzu ban samu bane shiyasa, to yanzu ne na ga wacce ta dace dani dan sosai ta kwanta mini a zuciyata. To madallah kuma kayi rasa akan gaɓa domin kuwa ba tada aure sakin wawane ko nace auren rana guda ne da yini aka sauta, saboda mijin baida lafiya ya ɓoye musu gaskiya, ko idda bai ɗaura mata ba. Alhamdulillah gaskiya nayi farin ciki, ni dama nasan zuwa na nan alkhairi ne, ga cigaba na kasuwanci da nake samu bisa tallafin addu'o'inka gashi kuma zan samu mata. Allah yasa na samu karɓuwa a gunta. In dai wannan ne zata soka dan bata isa in kawo miji ta ce bata so ba, tuni zan yi maganinta, in dai da gaske kake to ka bar mini komai a hannuna. Nan Atiku ya shiga jero masa godiya kamar zai kwansa masa, malam ya gama aikin da zai yi musu ya sallame su akan zasu yi magana a waya. Suna fita malam ya yi duba akan Atiku da Najwa, nan ya hango aure zai tabbata kuma shima hanyar samunsa a jikin Atiku zai ƙara buɗewa dan ba ƙaramin morarsa yake yi ba, duk abinda ya gindaya masa na kuɗi baya taɓa kaucewa sai ya bayar, hakan yasa yaji dole ma Najwa ta aureshi dan ba zai yarda ya rasa wannan gwaggwaɓar samun ba. **** Bayan kwana. A Kaduna. Sameeha mijinta ya kirata akan ta shirya zasu koma Abuja a ranar saboda akwai wani taro da za ayi ranar Alhamis wato gobe In Allah ya kaimu, kuma tarone na manyan mutane da matansu, to yana so Sameeha ta kasance tare da shi a wannan guri dan yasan ita ɗin matar fita taro ce, hakan yasa dole ta shirya dan dama taso ta yi sati guda ne sai ta koma, tumi Ikram ta koma gida sai dai suyi waya, hakan yasa Sameeha ta kira Aminu kan batun yara, koda ya daga wayar suka gaisa sai ta ɗaura da ce masa. Abban Amrah dama na kira ka ne kan batun su Abi, Umma tace a gunta zasu zauna, shine nace bari na sanar da kai ko za a yi musu transfer ɗin makarantarsu zuwa nan Kaduna, tunda turkish school ne kuma nan ma akwai, ko yaya Zaidu zai riƙa kaisu makarantar. Masha Allah naji daɗin umma da zata riƙe su, nasan sai ta fiki kulawa da su tunda ke kina fama da mijinki ga harkar siyasa da kuke yi, sannan batun kaisu makaranta akwai driver da zai dawo nan da motarsu in yaso zai cigaba da kaisu ina biyansa, dama ɗan nan Kaduna ne kinga ya riƙa barin mota a nan gidan da safe ya riƙa zuwa, sannan duk inda Umma zata da Anwar sai ya kaisu kinga ya zama drivern gidan gabaɗaya. In Sha Allah cikin kwanakin nan zanyi komai na makarantar nazo na kaisu nan turkish ɗin, sannan zan haɗo kayansu gaba ɗaya ma, tare da sauran abubuwan da suka dace. Yayi maganar cikin fara'a fuska sake, murmushi Sameeha tayi jin zolayar da yayi mata a maganarsa ta farko, tace masa shikenan duk abinda ya yanke yayi dama ita yau zata koma Abuja, yayi mata fatan alkhairi sai suka yi sallama. Ba jimawa ya kira umma a wayarta bayan sun gaisa yake ce mata zai riƙa kiranta a waya suna gaisawa da kuma duk abinda ya shafi yaran ta riƙa faɗa masa yanzu ba yida mahaifiyar data fita, umma taji daɗin haka ta saka masa albarka tare da yi masa fatan gamawa lafiya, nan ta bawa su Abi wayar suka fita suna waya da babansu, Umma ta kalli Sameeha tana cewa. Wlh Aminu mutum ne, banda ƙaddara ta rabaku da zanso ya cigaba da zama sirikina, yana da kirki dan tausayi ma yake bani yanzu,Allah dai ya bashi lafiya ya warke ya samu mata tagari ya aura. Ameen umma ni ma kaina fatan lafiya nake yi masa kenan, domin a yanzu ina yi masa kallo tamkar ɗan uwana na jini. Allah ya rabamu da mummunar ƙaddara, da ace Najwa ta kirki ce da in ya samu lafiya sai ya mayar da aurensu. Haba umma wlh bana masa fatan Najwa, dan a yanzu haka ina masa kwaɗayin auren ƙanwar Shamsu wanda suke uba ɗaya, in har Aminu ya samu lafiya kuma bata yi aure ba wlh ita zan nima masa ya aura, yarinyar ga hankali ilimin addini da sanin ya kamata, ta kammala jami'a yanzu tana koyarwa a nan Nuhu Bamalli poly dake zaria, itama ƙaddara ya rabata da mijinta sanadin auren da ya ƙara yaranta biyu. Allah sarki kinji kowa dai da irin ƙaddararsa, zan so hakan ya faru kuwa, amma karki faɗawa kowa tukuna sai mun tabbatar da ya samu lafiyar ni da kaina zan shiga gaba wajen nima masa aurenta nasan Aminu zai yi mini biyayya. Murmushi Sameeha tayi tana gasgata maganar umma dan sosai taji daɗin yadda ta amsa maganar, haka suka cigaba da hira har zuwa lokacin da Ibrahim yazo ɗaukarta ya shigo har gida ya gaisa da umma kana ya bar musu maƙudan kuɗi kamar yadda ya saba, shima yaso umma ta bar musu yaran dan sunyi maganar da Sameeha amma tunda umma ta hana dole ya bar maganar, haka suka tafi su Abi suna yi musu bye bye. * Abuja. Bayan sun isa Sameeha ta ɗaura musu girki, Ibrahim yazo ya tsaya a bayanta yana cewa. Gaskiya yau matata ba zata girka komai ba, shiryawa za kiyi muje muci abincin waje, saboda akwai aiki na musamman da za kiyi anjima kinga in kin gajiyar da kanki yanzu aikin anjima bazai samu yadda naje so ba. Sameeha ta juyo tana fuskantarsa ɗauke da murmushi. Mahboob ɗina yau da kanka zaka ci abincin waje, ni dai ka barni na samu lada biyu na yanzu da kuma anjima. Naƙi wayon muje ki shirya mu fita dan gaskiya ina son more soyayya ne yau, nayi kewarki kwana biyu so badly. Ya ƙare maganar yana jan dogon hancinta ita kuma matsowa tayi tayi masa kiss a kuncinsa kana tayi masa a wuyansa, wanda ya saka shi sakin wani ƙara sai ta zame ta ruga a guje yabi bayanta yana cewa. Ai tunda kika fara kunna ni tun yanzu zan bankaɗa asirin soyayyarmu. Haka suka dinga zagaye falon suna dariya da junansu, saida Sameeha ta gaji kana ta zube a cushing tana mayar da numfashi, shima ya dawo gefenta ya zauna tare da cewa. Wa na kama. Ni, amma dan Allah karka mini komai muje muyi wanka mu fita nima ina muradin shaƙar iskar waje tare da gaurayyen numfashin mijina a kusa dani. Ta ƙare tana kanne masa ido, murmushi yayi wanda ya bayya kyawun fuskarsa. Allah yayi miki albarka Haskena ina alfahari da samunki, ban taɓa zaton aure yanada farin ciki da natsuwa ba a duniyarmu ta Hausawa ba sai dana sameki nasan haka, Sameeha na tabbatar samun irinki a duniyar nan sai an tona, duk da ina busy ina harkar siyasata amma wlh inna tuna dake sai naji babu gajiya ina samun kwarin guiwar gunadar da komai cikin salama. Wannan shine fatana a kullun ka kasance cikin farin ciki, ni baiwarka ce, masoyiyarka ce, sai yadda kayi dani domin zuciyata da gangan jikina mallakinka ne, ina sonka Ibrahim. Tana gama faɗar haka ta miƙe ta wuce tana rausaya cike ta jan hankalinsa, nan take ƙaunata da yake yi mata yaji ya nunku har wani hucin numfashi yake fitarwa, banda ya ɗaukarwa kansa alƙawari babu saki a rayuwar aurensa da Nabila amma da ya saketa ya kasance da Sameeha ita kaɗai, dan sai yayi ma da gaske zai iya yin adalci a tsakaninsu, to zuciya tana son mai kyautata mata haka kuma tana ƙaunar mai ƙaunarta domin Allah, ji yake kamar shi kaɗai ne namijin daya yi sa'an samun matar kwarai, Sameeha ta zame masa bangon jingina farin cikin rayuwarsa a nan duniya da kuma a aljanna da yake fata, haka ya miƙe yabi bayanta wanda koda ya shiga ya sameta cikin wani irin rigar barci da bai santa da shi b,a dan kuwa alƙawari ta yiwa kanta na faranta masa a duk lokacin data gane yana muradinta, Ibrahim bai tsaya ɓata lokaci ba ya bi lafiyar gado tare da ƙanƙameta yana shakar kamshin dake fita daga wuyanta, daga nan sai suka lula duniyar masoya sai da suka samarwa kansu natauwa kafin suka yi wanka tare suka shirya cikin ƙananun kaya, Ibrahim t-shirt blue ya sanya ya saka jins baƙi ya feshe jiki da turare, Sameeha kuwa top ta sanya pink da rashin blue a jiki, sai ta saka siket fari mai buɗewa kana ta ɗauki after dressing mai shara shara blue ta ɗaura akan kayanta ta yane kanta da gyalensa, yadda tayi masifar kyau sai da Ibrahim ya ɓata lokaci wajen yi mata hotuna sannan shima suka ɗauka tare itama tayi masa kafin ya saƙala hannunsa a nata suka fice daga gidan cike da tsantsar soyayya, shine da kansa yaja motar security kuma suna binsu a baya, a haka suka fita tare da buɗe saman mota iskar gari yana kaɗasu gidauniyar soyayya tana fizgarsu. (Ko wani aure akwai farin ciki a cikinsa muddun akwai kyakkyawar fahimta da kauna). **** Aminu. A cikin sati guda yaje Abuja ya koma Kaduna ya kai su Abi makarantar daya amso transfer ɗinsu, tare da driver suka zo ya gabatar dashi ga su Umma, sannan yaje kasuwa yayi wa yaran siyayya mai yawa da kayan abinci daya siyawasu Umma da yawa, kana ya turawa Zaidu kuɗi masu yawa akan cefanen gida mai ɗin mota da sauransu, ya yiwa su Umma sallama ya wuce babban gida nan ma ya sallami 'yan uwansa. A washe gari ya koma Abuja wanda bayan mako guda jirginsu ya ɗaga ya bar ƙasar zuwa London. ***** Nafeesa. Tunda aka amshe wayarta ta zama kamar mararniya saboda ta yi mugun sabo da waya, ba ƙaramin hukuntata akayi da shi ba dan ji tayi gwara kullum a bigeta akan a rabata da wayar, tana son yin magana da Najwa sannan ta amsa number Sameeha amma ina ba a barinta ta fita balle ta samu damar yin magana da su. Kuma a satin Taju ya samu Sadi yayi masa zancen Nafeesa sai dai ya sanar da shi Fyaɗe aka yi mata idan zai aureta to, yace ya amince domin kuwa ya yarda da ƙaddara tunda ba yin kanta bane Fyaɗe aka yi mata, sannan ma babu namiji kamarsa da za a bashi auren Nafeesa yace baya so domin daidai gargwado tana da kyau ga hasken fata kuma akwai diri, abu ne da bai taɓa zato ba ko ya kawowa kansa samun matar aure irinta dan haka ya amince. A satin iyayensu suka zo nima masa aurenta da sadaki dubu Hamsin wanda SaDi ya basu, Alhaji ya ce ya basu sannan da zasu tafi ya basu key ɗin gidan daya mallakawa Sadi, yace ya yafe masa akwati nan gaba in ya samu hali sai ya ɗinka mata suturar daya dace, ba ƙaramin daɗi suka ji ba tare da yin godiya. A ranar Juma'a aka ɗaura aurensu a Masallacin jikin gidan, ba wani taro aka yi ba sai dai 'yan uwa na kusa sun zo kuma kowa yayi mamakin wannan aure na gaggawa, sun dai bayar ƙila Nafeesan taƙi fito da mijine Alhajinsu ya yanke mata wannan hukuncin, ita dai a ɗaki ta yini dan ko fita ta kasa yi nan duk 'yan uwanta suka sameta suna bata haƙuri. Zuwa bayan magrib tayi wanka ta saka wani leshi da abbansu ya siya aka ɗinka mata, kana 'yan biko suka zo aka kaita gidan mijinta. Kowa yayi mamakin gidan da aka kai Nafisa dan gidane filat mai kyau da ɗakuna a katon falo guda huɗu ko wanne da bayi kuma an zuba kayan zamani masu kyau da tsada, hatta kitchen ɗin ya tsaru, sannan ɗakin da aka kai Nafeesa sun tadda setin akwatuna guda biyu da me set huɗu da kuma me set uku, koda suka buɗe sun same ahi cike da kaya masu tsada da kyau, Nafeesa ganin wannan ba zata ya sa ta samu ɗan natauwa a zuciyarta har take jin zata zauna da Sadi tunda bata muzanta ba ta samu gida mai kyau da kayan lefe, 'yan uwa sai sam barka domin malam Sadi ya basu mamaki kuma yayi bajinta, kuma dagasken shine ya yi mata wannan kayan dan ya jima yana tara kaya a gurin yarsa akan koda ya tashi aure bazai sha wuyan haɗa akwati ba, to ganin karamcin dasu Abba suka yi masa yasa shima yace zai gwangwaje Nafeesa da kayan lefe domin ya saka alkhairin da suka yi masa. Bayan kowa ya watse abokansa suka rakoshi yazo ya kirata ta fito cikin babban mayafi ta zauna a cushing nan suka rattafo musu nasiha akan zamantakewar aure dama koyi da sunnar Ma'aiki s.a.w da kuma matansa, wanda yasa jikin Nafeesa ya kuma yin sanyi ta ƙara saduda da karɓan ƙaddararta, bayan abokansa sun gama suka yi musu sallama suka tafi. A wannan dare Sadi ya angonce wanda ko kaɗan Nafeesa bata yi masa musu ba ta bada kai bori ya hau, da Safe bayan sun natsa ya bata sabuwar waya iPhone 13 a cikin kwalinta kyauta wanda yaya Taju ne ya bashi yace ya bata domin dai ta ƙara sakin jiki dashi tayi zaman auren, Nafeesa sai da tayi kukan murna dan sosai taji daɗin wayar sai dai ya sauta mata layi, nan ta yi masa godiya Sadi ya katseta da cewa. Nine ya dace na gode miki da kika amince da ni a matsayin mijinki baki yi mini jayayya ba ganin ni ba kowa nace almajirin gidanku. Haba kafi ƙarfin haka a guna domin bazan taɓa gujewa zaɓin iyayena ba, kuma yanzu na tabbata ba suyi mini zaɓin banza ba. Sai dai zan nima alfarma a gunka ka bani tsohon layina dan na cire numbobin daya dace. Layinki baya hannuna Nafeee, amma bada gmail kike saving ba.? Wasu suna cikin wayar amma akwai wasu a gmail. To kiyi amfani da gmail ɗinki In Sha Allah zaki samu duk number din da kike so a ciki. To tace masa kana ya miƙe yayi mata sallama ya fita, Nafeesa ta miƙe cike da farin ciki ta shiga zaga gidanta sai taga komai yayi mata yadda take so babu abinda ta rasa, nan ta shiga jero godiyarta ga Allah dan sosai ta yaba da Sadi saboda' jiya ya shayar da ita wani ruwa mai mugun zaƙi. Ashe Ustazai sun iya soyayya haka? Ta faɗa a zuciyarta. A hankali ƙin auren ya riƙa barin zuciyarta har ta fara samar masa gurbi a ciki. Nan ta koma ɗakinta ta kunna wayar dan dama ya sanar da ita anyi chargynta, ta duba ko akwai kuɗi a ciki taga kusan dubu biyar ga kuma data kusan 2gb ta saki murmushin farin ciki sai ta kunna data ta fara setting komai na wayar ta ɗaura gmail ɗinta, duk contact ɗinta suka dawo, nan take ta kira Najwa domin ita ce wacce take son fara kira ta sanar da ita damuwarta dama komai daya faru. Najwa tana kwance a ɗakin yara wanda yanzu ya zama nata, game take yi a wayar Siyama ɗiyar Saleema wanda a yanzu ya zama nata dan ta saka sim ɗinta a ciki, kiran daya shigo wayarta yasa ta duba taga number ne bata san me layin ba, kamar ba zata ɗaga ba sai kuma ta yanke ɗauka ta kara a kunne, muryar Nafeesa data ji yasa ta tashi ta zauna tana faɗin sunanta. Nafeesa ta amsa tana cewa. Ƙawata abubuwa da yawa sun faru dani ina son yin magana dake ban samu hali ba, sai yau da aka bani waya a hannuna. Ina jinki amma kafin nan da fatan kin bar mini Aminu ko, dan kin san har yau ban huce ba. Dalla waketa Aminu yanzu, ni da aka ɗaura aurena jiya da Sadi malamin yaran gidanmu. Kai dan Allah, garin ya haka ta faru.? Najwa ta faɗa tana dafe ƙirji da zaro ido waje dan taji lamarin yazo mata a bazata, Nafeesa ta nisa ta soma bata labari tun sadda Taju yaje gida ya sanar da saƙp da aka tura masa wanda Hamisu ne ya tura, tiryan tiryan take bata labari babu abinda ta ɓoye mata, har zuwa auren da aka mata gidan da aka kawota da kuma akwatina ga kuma kyautar waya da Sadi ya bata yau, nan take Najwa taji wani abu ya ɗarsu a zuciyarta wanda sam bata so ƙarshen Nafeesa yazo a haka ba, taso ace ta fita wulaƙanta sai gashi tona mata asirin da tayi yaja mata wani nasara har ta fita mutunci yanzu, Nafeesa jin Najwa tayi shuru bata ce komai ba yasa tace. Ƙawata kinyi shuru baki ce komai, wlh ke ce na fara kira domin mu shirya kiji kuma abinda ya sameni ki taya ni jaje da murna, sannan kinga yanzu bani ba Aminu sai mu cigaba da ƙawancen mu, ki bani labarin ya kika ƙare da Aminu daya ga ke ce Amaryarsa. Najwa wasu zafafan hawaye ne suka shiga zarya a kuncita ji take yi komai daya faru ya dawo mata sabo, ga baƙin cikin Nafeesa ta yi nasara akanta ita kam kamar tsiya akanta ya ƙare, cikin sanyin murya tace. Ai Nafeesa faɗan da muka yi dake a falon Amuni ya lalata komai domin yana ciki yaji komai hakan ya jawo mini duka a gunsa da safe kuma ya ɗaukeni har gidansu Sameeha ya tona mini asiri ya kuma sakeni saki biyu a gabansu, yanzu haka ina kano gurin ƙanwar babana Saleema, kowa ya juya mini baya. Innalillahi wa inna ilaihir raji'un, amma banji daɗin faruwar haka ba kiyi haƙuri ki yafe min domin nice naja komai. Ai dole ki bani haƙuri bayan kin cutar dani, to bari in faɗa mini ni ce nan na turawa yayanki saƙon nan a matsayin Hamisu ne domin tunda na rasa Aminu kema in tona miki asiri da Binafa. Najwa dama kece kika tona mini asiri? Yanzu na cancanci kiyi mini haka duk iya halaccin dana yi miki. Wlh Nafeesa fiye da haka zanyi miki domin kin rabani da farin ciki na. Hmmmm to ai ni gwara ma da kika tona mini asiri domin kuwa gaba takaini yadda kike fatan na wulaƙanta ban yi ba domin Allah ya rufa mini asiri kuma na karɓi ƙaddarata, wannan maganar da kika sanar dani yasa na ƙara fahimtar ke butulu ce kuma dole in raba hanya dake saboda ke ba mutumiyar arziki ba ce, ni na karɓi ƙaddarata kuma ina niman Allah ya yafe mini sannan har gidansu Sameeha zanje in nima yafiyarsu dan ina so nayi rayuwa da mijina cikin salama, daga yau bani ba ke Najwa domin zuciyarki ba tada kyau. Tana gama faɗar haka ta kashe wayar, na take tayi blocking number ɗin Najwa dan sosai take jin ba zata ƙara barin wata alaƙa ta shiga tsakaninsu ba saboda Najwa ba abokiyar arziki bace. Najwa kuwa kukan baƙin ciki ta fashe dashi da jin takaicin yadda Nafeesa ta samu rufin asiri cikin ƙanƙanin lokaci, taso ta wulaƙanta fiye da ita sai kuma hakan ya zama silar rufuwar nata asirin, dole itama ta yi aure cikin ƙanƙanin lokaci ko zata samu sassauci daga halin da take ciki. Binafa... [7/7, 13:04] Buhainat😁: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shai wanidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.* 50 Binafa. Saida suka ɗauki sati biyu a cel ba tare da an turasu kotu ba saboda tsaikon da aka samu daga gurin 'yan sanda na haɗa bayanai, sosai Binafa da Hanan suka shiga cikin tashin hankali ganin yadda aka mayar dasu kamar bayi an tsaresu ba duka ba zagi amma kuma su sauro suna ta sukuwa a jikinsu ga yunwa da ƙishir ruwa, abincin da ake basu sai kace 'yan bursina, da farko ƙin ci suka yi amma ganin yunwa zata yi musu lahani yasa suka fara ci, wannan wahalar da suke ciki yasa Binafa sarewa akan gwara ta sanar da iyayenta a kawo mata ɗauki duk da ta san zata fuskanci matsala dasu amma gwara a rabata da wannan wajen in yaso ko me zasu yi mata to suyi, ita dai ta bar cikin cel ɗin a rufe maganar ko dan kare mutuncin gidansu Iyayenta ma zasu so haka, lokacin da wani ɗan sanda ya kawo musu abincin dare a sannan ne take yi masa bayanin a bata wayarta zata kira 'yan uwanta susan da maganar, ɗan sanda yace su da suka ce ba su da kowa ai kawai su cigaba da zama har lokacin da za aje kotu, Binafa ta nima bashi cin hanci akan in sun fita zata biyashi da tsoka, yace shi ba irin waɗannan 'yan sandan bane da suke ɓarna a cikin aikinsu, dan haka ta kama kanta tun kafin ta ƙarawa kanta laifi kuma wayarta ma bata hannunsu bai san a inda take ba, yana gama faɗar haka ya wuce, jikinsu ne ya ƙara yin sanyi da labarin dan duk yadda suka ɗauka yafi ƙarfin lissafinsu, sosai hankalinsu ya ƙara tashi da damuwar makomar halin da suke ciki dan ba zasu jure zaman gurinba in ba haka ba wani ciwo sai ya shige su. Mako guda da auren Nafeesa a ranar monday aka tafi dasu babban offishin alkali dake nan high court, an gabatar da su tare da waɗanda suke yi ƙara zuwa office ɗin Alkali domin ko za a samu maslaha a daidaita lamarin, amma ana karanto wa Alkali laifinsu yace dole sai an je kotu saboda laifinsu ba ƙarama bace domin ayi musu hukuncin da zai zama izina ga masu irin halinsu dan haka ya tsaida ranar Alhamis zaman kotu, sai ya sallame su aka mayar dasu cel aka cigaba da tsaresu, a wannan lokacin kuka suka fara da dana sanin taɓa yarinyar mutane domin tabbas sune suka jawota jikinsu da kashe mata kuɗi har ta basu haɗin kai suka ɗaurata a hanyar, dana sani ne ya fara rufe su Binafa ta kalli Hanan cikin zubda hawaye. Ina tsoron duniya tasan me muke aikatawa ban san ya 'yan uwana zasu ɗauka ba, ni gwara tun yanzu na sanar dasu komai kafin a kaimu kotu. Hmmmm ai aikin gama ya gama dan ɓacin suna kam mun gama kirawa kanmu, bawai tsoron dan an kaimu kotu nake ba, Allah yasa kar a kaimu gidan yari dan wlh bazan jurewa wahalar ba. To sunƙi bamu ma haɗin kai balle na kira gida a kawo mana ɗauki, nasan dadyna zaiyi komai dan a rufe maganar, sai ma yanzu ma nake ganin wautata da na nima ɓoye maganar duk da a da ina hangen zan iya magance matsalar da kaina, ashe kuɗi basu isa su kwacemu ba, muna cikin babbar matsala fa Hanan. Binafa ta ƙarasa maganar tana matso hawaye cike da tsantsar damuwa, haka suka dinga mayar da magana wanda tarin dana sanin da suke ciki suke fitarwa. Kotu. Kamar yadda Alkali ya sanar ranar Alhamis aka shiga kotu, wanda su Binafa sunyi matuƙar mamakin ganin mutanen da suka taru, ciki har yayanta Hassan da Yaya Taju dama sauran yayyinta da kuma wasu a family ɗinsu maza, wanda take tunanin ya aka yi suka san tana gurin, kuma komai da yake faruwa Hassan yana da masaniya domin DPO yana sanar dashi saboda sun amsa bumber ɗin juna, tashin hankali gobarar gemu! Domin kuwa Binafa samun kanta tayi da jin tsoro da fargaban tonuwar asirinsu a bainan Nasi, hawaye ya soma zarya a kuncinta ta sunne kai jikinta ya ɗauki ɗumi tare da kaɗawa tamkar zazzaɓi take ji, Hanan kuwa da yake babu nata a gurin bata damu ba sai damuwar hukuncin da za a yanke musu take yi dan bata fatan a yanke musu zaman gidan kaso bata shiryawa hakan ba, kowanne dai da abinda ya dameta. Sai da aka fara gabatar da wani ƙara na masu bashi daga bisani aka gabatar da ƙaran su Binafa, haka aka tisa keyarsu aka sanya a cikin wajen amsa tambaya, nan Hassan ya fara ɗauka a wayarsa a ɓoye dan yayi alƙawarin nunawa iyayensu wannan abu tunda bai sanar dasu ba sai iya 'yan uwansa maza da wasu maza cousin ɗinsu, nan aka gabatar da Baristan masu ƙara ya miƙe yayi bayani tare da gabatar da kansa, Alkali ya buƙaci ganin baristan su Binafa, aka sanar da ba su da shi nan take ya wakilta wani daga cikin lauyoyin gomnati akan ya tsaya musu, cikin ƙanƙanin lokaci aka fara gudanar da komai. Aka ce ranar wanka ba a ɓoyon cibi su Binafa basu wahalar da Shari'a ba sun amsa laifinsu, hakan yasa alkhairi ya yanke musu hukunci kamar haka. An yanke musu tarar kuɗi million huɗu da rabi sannan da zaman gidan yarin na shekara biyu tare da aiki mai tsanani, idan kuma basu bayar da kuɗin tara ba da za a bawa yarinyar da suka cutar, to zasu yi zaman kaso shekara shida shida. (Wannan hukuncin daga alƙalamin marubuciya ce Rahma, ban tsaya na yi bincike kan case irin nasu ba na yanke hukunci ne domin gajarce ɓata lokaci, da kuma sauƙaƙa ƙarshen labarin.) Kuka suka fashe dashi domin ba suyi zaton wannan hukuncin ba, su bayar da taran kuɗin bai dame su sai zaman gidan yari ne ya ɗaga musu hankali sosai, nan Alkali ya ce za a iya ɗaukaka ƙara tare da sallamar case ɗin, haka aka tasa ƙeyar su Binafa aka fito dasu farfajiyar kotu, duk da Hassan yayi ƙoƙari sosai dan kar a bawa 'yan gidan tv da radio damar shigowa, sai dai duk da haka ansamu wasu sun ɗauki hotunan su Binafa a wayarsu, Binafa ta tsaya gaban 'yan uwanta ta tsuguna tana rusa kuka da cewar su ceceta su ɗaukaka ƙara a samar musu lauyan da zai karesu su fita daga wannan case ɗin, tasan suna da kuɗin da zasu yi mata haka, kuma in dady ya sani zaiyi wani abu su taimaka su sanar dashi, Hassan ne yace cikin ɓacin rai. Wlh ko dady ya sani to ni da kaina zan hana ya taimake ki Binafa, domin ina so jikinki ya gaya miki ki gane Allah ɗaya ne, wataƙila zaki dawo cikin hankalinki ki daina yin ƙazantacciyar rayuwar da kika zaɓarwa kanki, ina mai tabbatar miki da nasan kina gurin 'yan sanda da komai da ke faruwa, ban sanar da su Dady ba saboda azo wannan gaɓar da zaki muzanta asirinki ya tonu kowa yasan wacece ke, dan haka kisa a ranki zaman gidan yari wajibi ne a gareki babu taimakon da zaki samu a gunmu sama da abinci da ɗan abin buƙata a gidan, pyan sanda ku wuce da ita. Dan Allah yaya dan son Manzon Allah s.a.w kayi mini rai ka fitar dani a wannan kuncin, wlh tallahi nayi maka alƙawarin ba zan sake aikata komai ba na tuba na tuba na tuba. Ta ƙare cikin wani irin gunjin kuka dan ko miƙewa da kyau ta kasa. Hassan ya ce cikin dakiya. Binafa baki tuba ba tukuna sai kin ganki a gidan yari kina bin layin abinci a nan ne zaki tabbatar da yadda ake tuba. Abokai mu wuce kar mu ɓata lokacinmu a nan. Ya ƙare maganar yana duban 'yan uwansa, Taju da duk jikinsa yayi sanyi saboda tausayinta yace. Wlh ta bani taussayi sosai ƙila da gaske ta tuba ko za muyi wani abu ne akai Hassan. Wani irin harara Hassan yayi masa yana cewa. Babu abinda za muyi mata wannan shine kaɗai gatan da zamu nuna mata gwara ta ɗanɗana zaman gidan kaso taga yadda mutane ke cikin wahalar rayuwa, jin daɗi da gata da sangarci yasa take ganin zata aikara komai, ciki kuwa harda saɓon Allah mafi muni, ita ta haka ne zata nuna godiyarta a gareshi, to kaga gwara taga ikon Allah ya nuna mata da gatanta da komai amma ta rasa wa zai taimaketa, wataƙila hakan zai sa tasan ya rayuwa take ba munzo duniya dan mu shagalta da jin daɗi ba ne mu sabawa Allah son ranmu, Allah ya haliccemu ne domin mu bauta masa mu kaɗaitashi sannan mu yi koyi da halayyar Manzon Allah s.a.w domin mu gina lahirarmu da ayyuka na kwarai don mu samu Aljanna. Bawai dan banji tausayinta bane, ba kuma dan bana sonta bane, ina so ta gyara rayuwarta ne domin gatan da ya rage muyi mata ganen mu nusar da ita yadda rayuwa take da kuma yadda zata bi da lafiyarta da jin daɗinta gurin bautawa Allah. Maganganunsa sunyi matuƙar tasiri a zuƙansu wanda yasa suka ƙarfafa masa guiwa akan hukuncin da aka yanke musu shine dai dai, sannan ma ba zuba ido zasu yi ba su barta sakaka a can dole zasu na kai mata ziyara dan ganin wace rayuwar take gudanarwa a can fatan su dai Allah yasa hakan ya zama silar shiryuwarta. Da suka isa gida ne Hassan ya zayyano wa iyayensu duk abinda ke faru tare da bayanin Taju, Dady cike da tsantsar mamaki ya dubi momynsu yace. Me yasa tsawon kwanakin nan kika ɓoye mini Binafa bata nan, kullun na tambayeki sai ki ce kin aiketa ko tana gidan su Taju taje hutu. Wlh Alhaji text ta tura mini da wayarta akan tayi tafiya zuwa kano to bana son na sanar da kai kayi faɗa shiyasa naketa ɓoye maganar. Cewar mony cike da damuwa, Hassan yace. Ai nine na tura miki saƙon lokacin dana amso wayar a gurin 'yan sanda, nasan ba zaki so a san tayi tafiya ba shiyasa na tura miki dan ke zaki kareta tunda dama haka kika saba yi mata, wlh kuna da saka hannu a lalacewar Binafa dan haka yanzu gatan da zaku nuna mata ɗaya ne shine ku bari doka tayi aikinta yadda zata gyara ruyuwarta ta gane abinda take aikatawa a matsayin wayewa karyace, rayuwar da za abi dokokin Allah da bin sunnar Manzon Allah shine gaskiya. Babana shekara biyu fa a gidan yari baka ganin shekaru yayi yawa ina laifin wata shida, ko dai mu ɗaukaka ƙara ne a sake nima musu sassauci. Cewar Dady, momy ma nan ta goyi bayansa, Hassan yace. Bazan hana ku ɗaukaka ƙara ba, amma duk abinda yaje ya dawo babu ruwana ni kuma wlh idan Binafa ta cigaba da aiwatar da abinda take yi to da kaina zan kaita kotun musulunci su hukuntata. Jin maganar daya faɗa yasa Dady yace to ba damuwa a bar maganar a haka, sai dai zasu riƙa kai mata ziyara shi gani yake har da kuruciya ke damunta, amma yana ganin tana dawowa gida aure zai yi mata ya huta, haka dai sukaita tattaunawa daga bisani taron ya watse. Binafa an saukesu a babban gidan yari dake nan jihar Kaduna ɓangaren mata, ji take kamar ba ita ba tamkar wata aka sauya dan ko a mafarki bata taɓa kawowa kanta yin rayuwa a irin wannan ƙasƙantaccen gurin ba, Hanan kam kuka tun tana na zahiri har ta koma na zucci idanu sun koɗe kamar tsohon zani, nan aka gabatar dasu ga hukumomin gidan aka basu kayan da zasu saka na gidan yari riga da wando da kuma hijab, aka shigar dasu wani ɗaki suka sauya kayansu kana wanda suka cire aka adana musu,vnan aka shigar da sunayensu a lis aka tisa ƙeyarsu zuwa cikin gidan, faɗar tashin hankalin da suke ciki ɓata lokaci ne dan sosai suka karaya suka kuma tsunduma cikin gogin dana sani. ******* Najwa. Bayan sati biyu wanda ya kama wata guda kenan da zuwan Binafa gidan. Da dare lokacin sallar Isha'i ta idar da sallah kenan sai ga Siyama ta shigo tana ce mata mamansu tana kiran ta, Najwa ta miƙe ta cire hijab ta naɗe sallayar sai ta fito falo ta sameta a cushing sai ta zauna tana cewa. Anty gani. Yauwa dama baƙo ne Malam ya turoshi gurinki, sai ki fita ku gaisa, ina fatan ku daidaita kinga In Sha Allah ba zaki ɗauki lokaci ba zaki yi aurenki, kuma mutumin yana da abin hannu dan babban ɗan kasuwa ne matansa biyu. Haba Anty mata biyu fa kika ce, ina zan kai shi? tafɗi! wlh ba zan iya auren me mata ba saurayi ma sai na darje. Haba Najwa karki saka naji kumya mana malam da kamshi fa ya turo shi, kiyi mini kara ki bani haɗin kai na tabbatar in kika ce gidanki ke kaɗai kike so Alhaji Atiku zai gina miki dan yana da kuɗi sosai. Hmmm bari dai naje naga kalarsa tukuna kan nasan abin da ya dace nayi. Ta faɗa tana miƙewa tare da komawa ɗaki ta ɗauko hijab ta saka kana ta fita zuwa fargfajiyar gidan da bai wuce fitanta sau uku ba tun zuwanta gidan, daga can nesa ta hango shi tsaye jikin wata farar mota, hakan yasa ta nufi can ɗin dan tasan shine ma tunda ba wani da ta gani a farfajiyar gidan, sai mai gadi dake can wajen gate yana sauraren radio. Najwa tunda ta tunkaroshi yake washe mata baki kamar wanda ya ga wawan zama, takaici da baƙin ciki ya turniƙe Najwa domin mutumin baƙinƙirin yake hasken haƙoransa kawai take gani da farin idanu, yadda ta rainawa Shamsu wannan ma ya dama shi a baƙi ya tsanye, ga wani tumbi daya aje sai kace mai ciki, da ɗaure fuska ta ƙarasa ta tsaya tana gaishe shi a daƙile, Atiku ya washe baki yana amsa mata ya ɗaura da tambayar ta ya gida tace lafiya, sai suka ɗan yi shuru daga bisani ya cigaba da cewa. To Najwa mai daɗin Suna, ni sunana Alh. Atiku, tun ganin farko dana yi miki ranar kin shigo falo tare da matar malam a nan naji na kamu da sonki, kuma ni ba da wasa nazo ba aurenki yake son yi wanda kafin na zo sai da malamvya bani damar haka wato na nima izini a gunsa, dan haka ina so ki bani dama mu fahimci juna kafin daga bisani manya sai su shiga maganar dan bana so a ɗauki lokaci kan azumin nan ayi bikin a gama saboda a shirye nake. Malam dakata mini dan Allah, wani irin ganɗoki ne haka daga ganin ɗan fawa sai miya tayi zaƙi, to baka yi mini ba kaje can ka nima wata amma ba Najwan Inna ba, ko baka kalleni da kyau bane, nayi maka kala da matar da zaka aura? To nace a kai kasuwa. Ta ƙare maganar a cikin tsiwa tana murguɗa masa baki ta juya fuuu ta wuce ranta a mugum ɓace, Atiku kuwa tsayawa yayi kamar gunki yana kallonta shi yadda ma take yi masa tsiwan burgeshi tayi dan sai yaji ya ƙara sonta da son mallakanta dan ya nuna mata shiɗin ya isa ya aureta, yayi guntun dariya yana cewa. Yarinya kenan, hmmm da Atiku kike magana. Ya ƙare maganar yana girgiza kai sai ya wuce sashin malam dan so yake a yi ta ta ƙare, dole malam yayi wani abu dan ba zai taɓa yarda Najwa ta kuɓuce masa ba. Najwa kuwa tana zuwa falo ta fashe da kuka tana cewa. Haba Anty kinga mutumin ne kuwa? Baƙinƙirin da shi sai hasken ido da haƙora da yake washe mini su na gani, ga tumbi kamar mai cikin wata biyar wlh ko a ƙafa aka ɗaura mini shi bazan ja ba wannan ba irin kala ta bane balle ajina, wlh bai min ba bana sonsa haka kawai ban gama da wani baƙin cikin ba zaku zo ku kawo mini wani damuwar, dana auri wannan gwara na mutu ba miji Allah. Ta ƙare maganar tana jan tsaki tare da share hawayenta, sororo Anty Saleema ta yi tana kallonta har sai da takai aya, tayi murmushin takaici tana cewa. Allah yasa baki masa wulaƙanci ba dan wlh baki isa ki watsa mini ƙasa a ido ba, kuma malam bazai taɓa yarda da haka ba domin ba a yi masa musu a gidan nan, duk abinda ya yanke wa yaro bai isa ya ce a'a ba, hatta muma haka ne. Faɗa mata da kyau Saleema tasan waye Malam Umar, har ke wacece da zan kawo miki miji kice baki so, to wlh baki isa kina zaune a gidana ba kice ba zaki bi dokata ba ƙarya kike yi yarinya, dole ki aje duk wata tashen balaga kibi zaɓina in ba haka ba hukuncin da zan ɗauka a kanki ba zai taɓa yi miki daɗi ba, aure da ke da Atiku babu fashi kamar anyi angama. Cewar Malam daya shigo falon ransa a ɓace yaji Saleema tana yiwa Najwa magana har ya tari numfashimnta shima yayi nasa faɗar, dan babu abinda Atiku ya ɓoye masa, ya kuma ce yayi masa aiki akanta yadda zata so shi ta aureshi ko nawa ne zai biya, a haka suka rabu yazo nan domin nuna mata asalin ikon da yake dashi a gidansa. Najwa kuwa wucewa tayi zuwa ɗakinsu tama kasa magana dan takaici, amma duk wannan surutun na malam bai ratsa mata zuciyarta ba, kuma bata ji tsoronsa ba domin ta gama yanke sai dai sukai gawanta gidan Atiku amma ba dai da ranta ba. [7/7, 13:04] Buhainat😁: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shai wanidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.* 51. Najwa tana jin malam yana faɗa a falon haka tayi biris da shi ta kwana tana ƙananun surutai, daga ƙarshe youtube ta shiga ta soma kallo, can anjima taji shuru alamar malam ya fita ba jimawa sai ga Saleema ta shigo ta zauna a gefen godon da Najwa take kwance. Tashi mu yi magana. Saleema ta faɗa tana kallonta, Najwa ta tashi ta zauna ba tare da tace komai ba. A gaskiya Najwa kin watsa mini ƙasa a ido kin bani kunya sosai, saboda lokacin da malam ya sanar dani ga wani zai zo gunki ba ƙaramin koɗa tarbiyyarki nayi ba nace zaki amince da zaɓinsa, sai gashi ba aje ko ina ba kin nuna ban isa dake ba. Haba Anty da kinyi shawara da ni kafin ki yanke mini hukunci, dan ni dai wlh ba zan auri wannan ba, haka kurum ina kallonsa ina jin takaici da baƙin ciki. Ba halittarsa zaki duba ba kuɗinsa zaki kalla, kuma maza irin Alhaji Atiku suna mugun son farar mace irin ki, wlh in kika yarda da aurensa ke zaki yi mulkin da kike so a gidansa kuma malam ba zai barki haka ba sai ya baki maganin mallakarsa yadda zaki samu abubuwa a jikinsa. Ni dai wlh ko kaɗan ba abinda ya burgeni a gareshi ya riƙe kuɗinsa, ni ina son auren namiji kyakkyawa kuma mai kuɗi, dan haka ki faɗa wa mijinki ya aura masa Siyama amma ba dai ni ba dan ba haifata yayi ba da zai yi wani iko a kaina. Amma Najwa ba kida mutunci Malam ɗin kike faɗar magana haka akansa, yanzu na tabbatar da maganar yaya kuwa da yace zaki gundureni gashi ba aje ko ina ba kin nuna mini iyakata, kowa ya ƙi ki ni na nuna miki so na 'yanta ki amma da abinda zaki saka mini kenan. Ba sai kin mini gori ba Anty in ba zaki iya cigaba da riƙeni ba sai na san inda dare yayi mini. Haka ma zaki ce ko? Lallai Najwa ashe haka kike ba kida mutunci. Na wuce haka ma in dai akan kaina ne, bazan yarda idona biyu ku cutar dani ba wlh. In kin san wata ai baki san wata ba zan nuna miki iyakarki kuwa. Saleema ta miƙe afusace ta bar ɗakin, Najwa ta ja guntun tsaki tana mele baki. Kafin kiga iyakata ni zan ga naki ', wlh ko inna bata isa ta sa na auri wannan baƙar halittar ba balle ke. Sai ta miƙe ta sakawa ɗakin key ta sauko da trolleyn kayanta ta saka waɗanda suke a wadrob a ciki ta mayar ta rufe ta kimtsa komai kana ta buɗe ɗakin ta samu Siyama suna kallo ta wuce kitchen ta saka abinci ta fito falon ta zauna tana cin abinci, Siyama ta kalleta tana cewa. Anty Najwa Mama tace ta tafi sashin baba, in kinyi sallar asuba tace mu fere doya mu dafa sannan ki yiwa su Auwal wanka ki shiryasu kafin tazo nima sai nayi nawa shirin makaranta. To Allah ya kaimu Najwa ta faɗa kana ta cigaba da cin abincinta a zucitarta tana ganin daidai lokacin da zata yi abinda take ganin shine daidai yayi, tunda Amty Saleema tana gurin malam yau ita ce da girki, data gama ci ta wuce ɗakin Saleema ta fara yi mata bincike a nan ta samu kuɗi a ƙaramar pos ɗinta cikin kaya ta ƙirga dubu talatin da uku ta saki murmushi ta kwaahe su duka, ta fito ta shiga ɗakinsu ta saka kuɗin cikin trolley ɗinta ta mayar yadda yake, sai ta bi lafiyar gado tana jin wani daɗi yana rufeta da guduwan data shirya yi, nan take ta seta alarm a wayar ƙarfe huɗu, sai ta koma ta cigaba da kallon data fara a youtube, a haka har Siyama ta shigo kwanciya Najwa tace. Su Auwal sun kwanta ko? Eh tun ɗazu. Kin rufe ƙofa ne. Eh na rufe. Ok sai da safe. Najwa tace mata Siyama ta amsa tare da kwanciya kusa da ita ba jimawa barci ya ɗauketa, itama Najwa aje wayar tayi a ƙarƙashin filo ta rufe ido dan tayi barci saboda ta samu ƙarfin tashi. Ƙarfe huɗu na dare alarm ya tashe ta ta tashi ta zauna sai ta cigaba da zama har kusan ƙarfe huɗu da rabi lokacin ne barcin ya saketa, ta sauko daga gadon a hankali ta zura babban hijab ɗinta ta sauke trolley ta buɗe ɗakin ta fito falo ta jawowa Siyama ɗakin, sai ta isa ƙofar fita ta murɗa key ta buɗe ta fita da addu'ar kariya daga shaiɗanun dare, ta kuma rufe ƙofar sai ta ɗaura trolley a kanta ta bi bayan gidan ta wuce part ɗin Amaryar malam cikin sanɗa, har ta dangana da katangar baya sai ta ganta tana da tsaho amma da yake ta sakawa ranta sai ta fita, a gefe ta aje trolley kayan ta juya ta hango wani dogon benci na masu aikin fenti ne suka barshi a gurin, cikin dabara ta ɗauko shi ta ƙara a bangon sai ta ɗaura trolley ɗin akai itama ta hau, da dubara ta ɗaura trolley ɗinta a katangar itama ta hau daga gefen kayanta, sai ta tura trolley ɗinta ya faɗa waje itama ta diro akan trolley ɗinta, nan ta miƙe da sauri ta ɗauke shi akai ta soma tafiya sauri sauri tabar lungun ta fita titi ba kowa sai kiran sallar farko da wasu mallatai ke yi, a haka tabar nan unguwar ta faɗa wani layi shima sai da taga ƙarshensa kafin ta isa titi, nan ta hango junction ɗin 'yan napep gasu nan burjuk sun parker, da sauri ta isa gurin ta samu wani ba kowa a ciki ta shige ta yi pilow da kayanta ta soma mayar da numfashin wahala. Wajen ƙarfe biyar da kwata tana nan a cikin Napep ɗin dan sai da ta huta sosai har an shiga masallaci salla, a lokacin ne masu abin hawa suka fara gilmawa a hanyar, hakan yasa ta fito daga napep ɗin data ɓuya ta isa titi, ba jimawa ta samu napep ta tare ta sanar dashi Na'ibawa zai kaita can kan hanyar da zata samu motar Kaduna dan ba zata tasha ba sauri take yi, yace kuɗinta dubu uku ba musu ta shiga suka wuce. Sai wajen ƙarfe shida suka isa saboda nisan gurin gari yayi haske mutane sun fara hada hada, ta sauka ta biyashi ya wuce ita kuma ta cigaba fa tsayuwa tana duban hanya, duk motar data gani kamar ta haya ce saita saka mata hannu har kusan shida da rabi bata samu mota ba sai ta fara tunanin ko ta dawo baya ta tsaya a tashar dake wajen na'ibawan ta samu mota, tana wannan tunanin sai ga wata mota jeep ta wuceta can kuma aka yi ribas aka dawo aka tsaya, ƙirjinta ne ya shiga bugawa dan sosai ta razana, a tunaninta ko malam yasa anbi bayanta, shiyasa yltaƙi yarda taje tasha dan kar ma su binciketa a can su ganta, da yake motar tinted ce ita bata ganin na ciki sai da aka sauke gilas kafin ta sauke a jiyar zuciya ganin bata san mamallakin motar ba. 'Yan mata ina zaki ne da wannan farar safiya? Kaduna zani mota nake nima, in hanyar kayi dan Allah ka rage mini ko a zaria ne ka sauke ni. Ok ya ce sai ya sauko ya buɗe mata boot ta saka kayanta kana ya koma ya shiga itama ta shiga gefensa ya tada mota suka wuce, saurayin ya kuma cewa. Amma bakay tsoron faɗawa motar mugayen mutane da kika zo hanya ki hau mota, ana yawan faɗa a riƙa daurewa a shiga tasha saboda halin rayuwa. Wlh nima dole ce ta saka amma ban taɓa hawa motar hanya ba sauri nake yi. Duk saurinki lafiya ai tafi komai, in ma kuɗin mota ce ba kida shi wadatacce saiki haƙura har ki samu. Wlh ina da ma kuɗi ina da dalilin daya saka banje tasha ba, kuma In Sha Allah daga yau bazan sake wannan gangancin ba. Allah yasa. Ni sunana Mujaheed ina zaune a Kaduna da kowa nawa, bikin wani abokina nazo jiya aka ɗaura sai kuma aka yi mini kiran gaggawa a gida shiyasa na fito da sassafe zan koma, kinga yanzu na samu abokiyar hira dama da niyyar haka na fito akan na rage wa wani hanya dan kar nayi tafiya ni kaɗai. Allah sarki naji daɗin haɗuwa da kai domin nima ka taimakeni a lokacin da nake buƙatar hakan, ni sunana Najwa kuma nima asalin 'yar kaduna ce iyayena da kowa na can yanzu ma gidan ƙanwar babana na baro dalilin auren dole da suke son yi mini. Mujaheed ya juyo ya kalle ta ya kuma mayar da fuskarsa kan hanya, yace cikin murmushi. Kyakkyawa da ke ayi miki auren dole ai an wuce zamanin. To dole suke son yi mini sun kawo min mutum akan mu fahimci juna nace bai yi mini ba, sun dage akan ban isa ba dole sai na yarda shiyasa na nuna musu iyakarsu na bar gidan tun asubar fari don na koma gidan iyayena wanda nasan ba zasu bari hakan ya faru ba. Gaskiya suma sun zaƙe da yawa ina ake yiwa mace kamar ki dole kuma ba su suka haifeki ba, gwara da kika gudu tunda gashi Allah ya haɗamu wataƙila ke rabona ce. Najwa ta kalleshi a takaice ta kawar da kai gefe tana ɗan murmushi ganin yana niman tusa kanshi gareta. Ba wani fari bane yana da hanci da idanu sannan kuma yana da ƙaramin jiki sai dai akwai shekaru a tare dashi daga gani, bafulatani ne amma na Hausawa tunda Hausarsa raɗau ne. Kinyi shuru baki ce komai ba ko banyi miki bane? Hmmm me zance bayan ban gama kashe wata wutar ba kai kuma kana ƙoƙarin kafa gomnatinka. Hmmmm Ni dai ina sonki saka ni a cikin list ɗin samarinki dan nasan kina su da yawa, saboda samari irinmu suna ƙaunar mace kyakkyawa haka kuma... Bai ƙarasa maganar ba kira ya shigo wayarsa ya duba yaga ogansa ke kira sai ya mayar yana jan tsaki. Duk kun dameni da kira sai kace dole ne sai kunyi tafiyar dani, in na ga dama Allah ko na zo gida bazan biku ba. Lafiya kake faɗa haka. Wai wani sabon company Abbanmu ya gina mini a Abuja to gobe ne suke son a yi lunching ɗinsa shine suka dameni akan dole sai na dawo yau mun tafi Abujan a yau, kuma na sanar dasu ni bana son company su barni na cigaba da harkan kasuwancinmu na Dubai amma sunƙi. Nan fa Najwa taji wani farin ciki ya cika mata zuciya jin yadda yake koro mata bayani, nan take taji wannan shine daidai da ita ga dukkan alamu in ta aureshi zata yi gogayya dasu Sameeha, shi kuma Mujaheed ganin kamar zurata da yayi ya samu gurbi sai ya cigaba da cewa. Kinga in kin amince sai muyi aurenmu mu wuce Dubai dan ba zan yarda na zauna a Abuja ba. Ya ƙare maganar yana ƙara sanyin AC motar, Najwa ta saki murmushi ta gyara zama tana cewa. Ka dai bari nayi tunani sannan in gama kashe wancen wutar tukuna. Haba Najwa wlh da gaske nake yi karki ɗauka wannan batun a matsayin wasa, amma ba damuwa zan baki lokaci. Najwa bata ce komai ba jin wayarta tana vibration ta ciro daga Aljuhun wando ta duba taga number ɗin Anty Saleema ce ta saki murmushi ta ɗaga wayar ba tare da tace komai ba. Najwa ina kika je? nazo ban ganki ba Siyama tace tun asuba data tashi sallah itama bata ganki ba. Na tafi gidan iyayena da ba zasu yi mini auren dole ba, ina hanyar Kaduna kuma kar kiga baki ga kuɗinki ba dubu talatin da uku nice na ɗauka nayi kuɗin mota. Tana kaiwa nan ta kashe wayar Saleema kuwa wani ashar ta saki jin ta kashe wayar ta fito da sauri ta nufi ɓangaren Malam. [7/7, 13:04] Buhainat😁: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shai wanidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.* 52 Saleema tana isa falon malam ta sane shi ya fito daga bedroom alamar fita zai yi, yadda ya ganta a hargitse yasa ya tambayeta ko lafiya? Cikin damuwa ta sanar da shi koma yasha mamakin rashin jin Najwa yace. Wato wannan yarinyar shaiɗaniya ce, ina shirin yin aiki akanta yau sai ta rigani ƙaddamar da nata shirin, amma duk da haka zanyi maganinta jeki ni zan mayar miki da kuɗin data ɗauke miki Allah ya shirya ta. Amin malam dan Allah ayi aikin da zaisa ta dawo dan ni ta yiwa baƙin cikin samun alkhairi saboda na san Alh. Atiku ba baya ba. Hmmm ni tafi yiwa baƙin ciki dan alkhairin da nake hangen zan samu a dalilinta da yawa, amma karki damu zata dawo da ƙafarta. Saleema ta saki murmushi saboda bayanin malam yasa taji ɗan natsuwa, musamman ma daya ce zai dawo mata da kuɗinta sai kawai ta fita ta koma sashinta, bata yi yunkurin kiran baban Najwa ba ta san zasu nimeta da kansu. *** Najwa. Da wuri suka isa kd wanda Mujaheed har gida ya sauke Najwa bayan sun amsa Number juna, yace in ya samu natsuwa zai kirata sai ta yi masa godiya ta shiga cikin gida tana jan trolley, ta samu gabaɗaya 'yan gidan suna tsakar gida Inna tana suyar kosai daga gefe, su kuma suna kan babban tabarma da baba suna karyawa, sallamarta ya katse musu hirar da suke yi cikin nishaɗi wato barinta gidan bai sa sun fasa yin walwalarsu ba, sororo suka bita da kallo itama ta tsaya tana ƙare musu kallo, yaya Junaid ne ya daka mata tsawa. Dalla malama ki ƙaraso ciki kin tsaya kina kallonmu sai kace wacce ta warke cutar makanta. To nayi sallama ai banji kun amsa ba Ta bashi amsa tana turo baki tare da jan trolley ɗin zuwa ciki ta jingine shi a gefe, ta samu ƙaramar kujera ta zauna daga gefensu. Baba ina kwana. Lafiya lau baba ya amsa a takaice kana ta gaisa da Inna ta amsa sai tabi sauran yayyinta ta gaishesu ɗaya bayan ɗaya, Sadiq ne ya amsa mata nashi daga ƙarshe yana cewa. Lafiya kika bugo sammako zuwa Kaduna sai ka ce an koro ki me ya faru ne? dan na san ba lafiya ba. Wai kawai auren dole zasu yi mini, sun turo mini mutum akan mu daidaita da juna ni kuma dana ganshi baiyi mini ba, shine wai ban isa ba dole sai na aureshi, shine na dawo nan dan sanan babu me yi mini dole a nan gida. Ba shakka Najwa itama Saleemar kin manna mata tsiyar ko, to ai shikenan sai ki cigaba da zama a nan tunda haka kika zaɓa, Allah ya shiryeki yasa ki gane gaskiya kan lokaci ya ƙure miki. Cewar baba, nan su Junaid suka rufeta da faɗa Najwa dai bata ce komai ba sai ƙunƙune take yi musu, Inna kam suyarta take yi bata saka baki ba dan takaici, daga bisani ne baba ya kira Saleema a wayarsa bayan sun gaisa yace mata sunga Najwa ta dawo, Nan saleema ta sanar dashi komai daya faru yayi murmushi yana cewa. Tunda ta gwada miki halinta yanzu ai shikenan Allah ya kyauta sai kiyi haƙuri. To yanzu yaya haka za a zura mata ido ba aure, sannan ni dan Allah zan turo mutumin yazo nan ku ganshi sai a bashi damar ya turo. Saleema kenan, kina tunanin in mun tursasa Najwa zata yarda da auren ne, aurenta na farko ita ta kawo shi bayan ɗumbin cin amanar data aikata, dan haka yanzu ma bazan taɓa yi mata dole ba dan nasan zata iya bani kunya, duk wanda ta kawo mini shi zan aura mata, ki bawa mijinki haƙuri ku bar maganar wancen mutumin kawai, domin ni nasan halin Najwa ku barta kawai. To shikenan yaya Allah ya shiryeta. Yace amin kana suka yi sallama suka aje kan wayar. Najwa ta miƙe ta isa ɗakinta taga a rufe sai a lokacin inna tayi mata magana. Ki wuce ɗakina ki aje kayanki dan ɗakinki an zuba kayan aurenki a ciki. Bata amsa mata ba ta wuce ɗakin inna ta cire hijab ta aje kayan kana ta fito ta ɗauki kofi ta ɗiba kunu, Inna ta zuba mata kosai sai ta koma kujerar data tashi ta zauna ta soma karyawa tama manta ko brush bata yi ba. Mazan gidan gabaɗaya suka fita suka yiwa inna sallama, baba ma wanka yayi ya wuce kasuwa aka bar inna da Najwa, inna ta kalleta tana cewa. Tunda kin dawo sai ki tashi ki naɗe tabarma ki share gidan ga kuma wanke wanke yana jiranki nima wanka zanyi zan fita dubiya. Haba Inna daga dawowata sai aiki sai kace baiwa ga gajiyar tafiya, waye ma ba lafiya da zaki fita da sassafen nan naga kamar ma da kunu zaki tafi. Najwa me yasa yanzu sam baki tauna magana kike fitar da ita, ke har yanzu baki shiga hankalinki akan abinda kika aikata bako, hmmmm ba baki nayi miki amma duniya zata koya miki hankali. Kai inna irin wannan maganar fa kika faɗa mini ranar aurena sai gashi washe gari an sakoni, ki yi mini Addu'a da fatan alkhairi mana. Hmmm ki dai tashi kiyi abinda nace miki dan ba zan daɗe ba yanzu zan dawo. Ikram ce ba lafiya an kwantar da ita a asibiti kwananta biyu kenan, ita ta saka nayi mata kunu da kosai dan jiya naje na duba ta. Inna waike sam bakya kishin abinda ya faru dani ne da ba zaki kyale su Sameeha ba, bayan duk sune sanadin halin da nake ciki, kina nuna sun fini daraja a gunki bayan ni ce taki su kara ne. Sun fi mini ke Najwa domin zuciyarsu tana da kyau ba irin taki bace kuma sun san nasu. Abin farin ciki ma ciki ta samu shine yake ɗan bata wahala. Sadda inna tace ciki ta samu sai da Najwa taji wani abu ya tsirga mata a zuciya nan take taji haushi, a zuciyarta tace. Allah yasa cikin ya zube ko ya kasheta muga idon ɗan iskan nan Shamsu. Sai ta ƙare da jan guntun tsaki tana miƙewa, Inna tana kallon yanayinta ta girgiza kai ta miƙe ta shiga ɗaki dan tasan in dai Najwa ce ba zata yiwa Ikram fatan samun lafiya ba saboda mugum halinta. Cikin sauri ta shirya ta ɗauki ƙaramin basket data saka jug ɗin kunu da kular ƙosai ta fice abinta. Najwa badan ranta ya so ba ta soma gyaran gidan, sai taji dama bata dawo ba saboda tasan ta dawo kenan aikin gidan yana kanta. **** Ikram. Tun bayan bikin Najwa ta soma laulayi kaɗan kaɗan sai dai kwaɗayi yafi yawa a ciki, da suka je asibiti likita ya tabbatar tana da shigan ciki wata ɗaya har da sati biyu, farin ciki wajen Shamsu ba a magana haka ma su Khairy sunji daɗin labarin dan Shamsu ita ya fara faɗawa ta sanar dasu Hajiya, nan suka yi musu fatan alkhairi da sauka lafiya. Musamman Hajiya ta aika cousin ɗin su khairy Zainab wacce take gabanta domin ta riƙa taya Ikram ayyukan gidan tunda har lokacin ba a samar mata mai aiki ba, kuma itama bata so domin tace tana tsoron masu aiki saboda abinda ya samu Sameeha. Umma ma taji daɗi labarin cikin, nan ta soma ɗawainiya da ita dangin kayan kwaɗayi tana aika Zaidu yana kai mata. Sameeha kuwa taso zuwa Kaduna dan ta ganta amna Ibrahim ya hana dan baya so tayi nesa dashi ko kaɗan, a waya dai suke magana tana jin lafiyarta. Kwana biyu daya wuce ne taci wani alale data saka Shamsu ya siyo mata a wani rastaurant taci shine ya sakata gudawa da amai duk ta galabaita, dalilin zuwanta asibiti kenan aka bata gado, Hajiya data samu labari ba ƙaramin faɗa tayi wa Shamsu ba akan me yasa bai faɗa ba tasa anyi mata a gida bata son suna cin abincin wajen nan saboda basu san yadda aka haɗa shi ba, nan ya bara haƙuri akan bazai kuma ba, shima a tsorace yake saboda kar cikin ya zube dalilin haka, sosai yaji haushin kansa daya sayo mata abinda ya illatata. Umma kam Ikram ɗin ta yiwa faɗa akan in ita ba zata iya dafawa ba me yasa bara kirata ta girka mata ba, taso ta zauna jinyarta amma su Hajiya suka ce ta barshi wata dattijuwa mai girka abincin gidan Hajiyar itace ta zauna da ita tare da Zainab, kuma tana samun kulawa sosai dan har ta fara dawo da jikinta data rame a lokaci guda. Inna tana isa ta wuce dakin da aka kwantar da ita nan asibitin garkuwa, wanda yake ita kaɗai ce a ciki ba wasu marasa lafiyan. Ta samu umma ma tazo tana zaune tana matsa mata akan tasha tea ɗin da aka haɗa mata amma taƙi sha, tana ganin inna da Kwanko ta haɗiye miyau dan dama tasan Inna zata kawo mata abu bata faɗa musu bane, inna suka gaisa da umma da Zainab dan baba Jimmai ta koma gida ta dawo, nan Ikram ta gaisa da inna tace cikin zaƙuwa. Allah yasa kunu da ƙosan ne Inna kika kawo mini. Aiko shine, da wuri na tashi na haɗa komai saboda ke, muma dashi muka karya babanku yace a yi miki ya jiki yana nan zuwa su Junaid ma suna ƙara yi miki ya jiki. Ina amsawa Inna, ai basu daɗe da fita ba ma yaya Junaid ɗin kika zo. Dama sunce zasu biyo su duba ki. Ga kunun ki fara sha saiki aje tea ɗin da naga baki son sha. Aiko gashinan ina ta godo da ita taƙi sha ashe tasan da zaki kawo mata abu. Ni wainar fulawa ma nayo mata taci kaɗan wai sai anjima, kuma ita ta saka nayi mata Cewar Umma, Inna tayi dariya tana cewa. Kin san ko wani juna biyu da nashi laulayin ita kuma a haka yazo. Allah ya rabasu lafiya. Amin suka amsa Ikram dai tuni ta fara shan kunu da Zainab ta zuba mata a kofi tana yagar ƙosai cike da farin ciki. Inna kuma ta samu wajen zama tana bawa umma labarin dawowar Najwa dama abinda ya faru, umma tace cikin jin daɗi. Ai wlh Zulai gwara data dawo gurinki domin tarbiyyar yanzu dole sai uwa, balle Saleema itama yaushe tayi hankalin, nasan ba ƙaramar taɓara zata bari Najwan tayi ba, kuma kema karki takurata ki riƙa janta sosai a jiki kina nusar da ita rayuwa In Sha Allah zata gyara halinta. To zanyi Haleema ai ya zama dole na rungumi ƙaddara tunda Allah ya jarabceni da Najwa, nima wlh tun sanda ta tafi da aka kwana biyu sai naji gidan yayi mini faɗi, naji son ta dawo amma ban furta ba na cigaba da addu'a. To Allah ya shirya mana ita, in banda Abin Saleema ai ba a nuna wa yaro dole, taya zasu tilasta mata auren wani basu suka haifeta ba da kuma ranku, sun so kansu da yawa. Umma ai maganinta kenan dama wlh an ɗaura auren muga ta tsiya. Cewar Ikram, umma ta danƙara mata harara sai ta sunne kai tana ɗan murmushi ta cigaba da karyawa, inna tace. Daina hararanta halin Najwan ne sai kaji kamar ka nakaɗa mata dukan tsiya. Yanzu ta dawo zan sha surutu da fama, Allah ya bani ikon cin wannan jarabawar. Ameen amma ki daure ki jata a jiki sosai kuma banda yawan faɗa irin su Najwa lallaɓasu ake yi Zulai. In Sha Allah zanyi haka. Nan suka cigaba da tattaunawa daga bisani kuma Innar tayi musu sallama ta tafi. **** Binafa. Hotunansu da wasu suka ɗauka shine suka yi sharing a facebook tare da labarin abubuwan da suka aikata har aka yanke musu zaman gidan kaso, a wannan lokacin duk wanda basu san da labarin ba a danginsu sun sani, wanda Nafeesa ma a facebook ɗin ta gani tayi matuƙar girgiza da lamarin wanda hakan ya ƙara mata shiga hankalinta ta kuma kama aurenta, musamman momynsu ta kirata a waya ta kuma ja mata kunne akan ta kama mijinta da aurenta da kyau dan ga abinda ya samu Binafa nan gwanin tausayi, Nafeesa ta tabbatar mata da zata kama kanta da aurenta gabaɗaya dan yanzu duniya ta koya mata hankali sosai. Hakan yasa ta cigaba da kyautatawa mijinta suka buɗe sabon shafin soyayya, da yake Sadi shima ba baya ba gurin tsafta dan sosai yake gyara kanshi saboda suji daɗin mu'amala, kuma yasan Nafeesa tana son namiji ɗan gayu yadda yake ganin samarinta a da suna zuwa fes dasu, shima ya ɗauki damarar yin duk abinda zai riƙa burgeta dan ya samu Zuciyarta. Sameeha itama ta samu labarin abinda ya faru saboda Zaidu ne ya gani a facebook yayi mata copying ya tura mata a WhatsApp dan bata yin facebook, nan tace sakayya ce daga Allah ko haka Allah ya barsu ya gama wanke mata zuciya ta kuma ƙare da fatan shiriya. Umma ma ta gani dan Zaidu sai da ya nuna mata tace sakkayya ce kuma dama wani hisabin tun a duniya Allah yake yinsa, Ikram ma ta gani ita Allah ya kara tayi musu tare da fatan Allah ya cigaba da tona asirin masu hali irin nasu. Najwa ma data gani dariyar mugunta ta riƙa yi tana Allah ya ƙara, ashe gwara ita tunda a iya saki nata ya tsaya suko gashi nan har da zaman gidan yari, cewa ma tayi hakan shine ya cancanta dasu dan sun kaune hanya da yawa, gwara ita zunubinta kaɗan ne, nayi ƙoƙarin kiran Nafeesa dan suyi maganar su Binafa, amma sai yaƙi shiga kwata kwata bata gane tayi blocking ɗinta ba. Su Binafa tunda suka shiga gidan yari suka gane shayi ruwa ne, saboda a cikin sati biyu jikinsu ma sai da ya tabbatar da sun shigo wani ƙaulin siraɗin rayuwa, sunyi duhu da rama ga wasu ƙuraje da suka fara fito musu a jiki da kwarin da suke cizonsu na rashin sabawa, Hanan dai wahalar tafi nunawa a jikinta dan ita fara ce kuma tana fama da nimoniya, ciwon ya fara damunta tana shan maganin da ake bata a nan gidan, duk da haka 'yan gidansu Binafa suna yo musu aiken abubuwan buƙata amma baya wadatar dasu, fatan su a fitar dasu ne daga gidan, sai dai sunga babu wannan halin. *** Najwa. Da yamma ta ɗaura girkin dare harta tuƙa tuwo ta ɗaura miya, tana zaune a tsakar gida tana danne danne a waya, sai ga kira ya shigo tana dubawa taga Mujaheed ne da ta yi masa saving, ta ɗaga kafin tayi magana ya rigata.. Gimbiyata shine ko ki kira ni kiji ya na ƙarasa gida. Kayi haƙuri nima ban samu zama ba tunda na iso gidan ina fama da aiki, inna ta sakar mini komai. Ayya karki damu soon zan rabaki da gidan ki zo ki huta a gidana. Hmmmm ya batun tafiyarka? Ina ban je ba ai, na tabbatar musu bana son companyn, dad ɗinmu yace abinda nake so shi za a yi mini. Ikon Allah, kace zaman ƙasar Dubai dai ya tabbata. Sosai ma kuwa sai ki shirya domin dake zani, anjima ina nan zuwa hira in ba zan takura ki ba. Ba matsala sai ka zo. Ta faɗa tana wani fari da ido na jin daɗi, nan yayi mata sallama suka aje wayar Inna tana fitowa daga daki tace. Waye kuma kike waya da shi.? Najwa tayi 'yar dariya kana tace. Kwanan nan In Sha Allah inna zan kuma yin wani auren, kuma ga dukkan alamu na dace dan yace ba a ƙasar nan zan zauna ba, kinga kuwa In Sha Allah mijina sai yafi na Sameeha balle Ikram da take wani nuna mini isa. Hmmm Najwa ke dai su Sameehan nan ba zasu fita a bakinki ba ko, ba dan Allah za ki auren ba sai dan ki fisu, wai ke yaushe zaki yi hankali ne Najwa, hassadarki tana nimar ta saka ki hauka ko, Allah yasa ki gane. Haba inna ke da zaki tayi mi murna kike yi mini faɗa kuma. To Najwa Allah yasa mutumin kirki ne shi, yasa kuma ba ƙarya yake yi miki ba. Wannan yafi ƙarfin yayi mini ƙarya ki dai yi mini fatan Alkhairi. To Najwan Inna Allah yasa alkhairi a tsakaninku, nima wlh zan so ki yi auren nan hankalin kowa ya kwanta in ga 'yan jikokina kin haifa mini kyawawa masu irin fuskarki. Kai inna har kin sa naji kunya. Najwa ta faɗa tana rufe ido cike da jin daɗin maganar innar, Inna girgiza kai tayi tama rasa a wani shafi zata aje Najwa, wauta ce da ita ko yarinya ko kuma rashin hankali ko kuma son zuciyarta ya rufe mata ido bata gane komai, addu'a tayi mata a zuciyarta tana cewa Allah yasa mutumin arziki ne yake nimanta. *****" Mujaheed. Lokacin daya aje wayarsa mai gadin da yake zaune kusa dashi yace cikin zolaya. Wacece wannan ta faɗa komar ka dan Alhaji? kuma ga dukkan alama tarko ya kama kurciya. Hahahah kai dai bari Tijjani, wata me zafi na samu wlh ganin farko nayi mata naji bazan taɓa bari ta kuɓuce mini ba, kasan 'yan matan yanzu sai ana yi musu ƙarya kafin kake samun kansu, wannan ta aure ce bata yaudara ba. Kace dai Allah yayi aure yazo mu huta da surutu, wataƙila inka aurenta ka rufe ƙofa 'yan mata ma zasu huta da yaudararka. Gaskiya inna auri wannan zan daina komai na kama aikina dan na auri matar data kere sa'a. Allah sarki Maman Jamila watan yi mata kishiya ya kama. To ya zata yi wlh sai na auri Najwa ko zata mutu, ba dan Mamanmu tana kwaɓata akanta ba ai da tuni na saketa na huta saboda shege ƙazantarta, gata bata ita girki ba balle iya rayuwar aure, kai auren mace 'yar sha bakwai zuwa ashirin matsalata ce basu iya komai ba sai shirme. To Allah ya sa ka dace da wannan ɗin mai tsafta ce. Kai hmmmm wannan fa matar manya ce, nima da karyata zan samo kanta ta aureni dan wlh tafi ƙarfina fa. Shege driver ɗan Alhaji, ai yau saura ƙiris ka rasa aikinka yadda alhaji yayi fushi da bai ga motarsa ba jiya. Kai dai bari ɗazun nasan ina ruwa kawai Allah ne ya fiddani saboda ina mugun shiri da Hajiya har ta goyi bayana, dalilin yadda nake koɗata, kasan fa bakin nan nawa yasha ceto na. Ai kai hmmmm, Allah yayi maka zarafin daɗin baki duk macen data faɗa komar ka sai Allah. Kamar yadda nake tunanin Najwa ta faɗa ciki tsundum In Sha Allah aurenmu ba fashi. Ya fada yana 'yar dariya, Tijjani ma dariyar yayi suka cigaba da hirar. Asalin Mujaheed su 'yan jihar Gombe ne... [7/7, 13:04] Buhainat😁: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shai wanidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.* 54. Najwa tana fita ta ganshi a daidai setin gidansu a jikin mota ya tsaya yana kaɗa key, shigar ɗazun ce ta gani a jikinsa amma kuma da rantsastsiyar mota, ta saki wani murmushi dan ga dukkan alamu yanzu ne ta samu miji wanda take ganin yafi Aminu komai, kuɗi kyau da ƙuruciya gwanin birgewa, ta isa gareshi suka gaisa kana yayi mata tayin su shiga mota suyi hira, ba musu suka shiga ta zauna a gefensa, ƙamshin dake tashi a motar ma ba a magana wanda yasa Najwa lumshe ido ta buɗe, da alama wannan ɗan gaye ne tace a ranta, nan suka soma hira yana zabga mata ƙarya ita kuma tana gyaɗa kai tamkar mai haddar maganarsa. A lokacin ne baba ya dawo ya shiga gida yana mamakin ganin mota a ƙofar gidansa, ya zata baƙi suka yi dan motar tinted ce ga kuma duhun dare ba wutan nepa ba za'a gane da mutum a ciki ba, ya shiga yana cewa inna. Motar waye na gani a ƙofar gida.? Ɗazun nan Najwa ta fita ƙila kona baƙonta ne. Amma ban ganta a wajen ba. Ba mamaki ko suna cikin motar. Ashsha! subhanallahi yaushe ta fara hira a mota? kinga Saleema ta ɓata tarbiyyar yarinyar nan ko. Yace cike da faɗa ya fice waje, yana isa jikin motar ya kwankwasa sai Mujaheed ya sauke glass Najwa tayi saurin cewa. Baba na ne. Ke dan gidanku hira kike yi a mota maza ki fito nan Shashasha. Najwa jiki na rawa ta fito baba ya nuna mata hanyar gida suf suf ta wuce, Mujaheed ya sunne kai yana bawa baba haƙuri baba yace. Yaro ban yarda da hirar mota ba, domin in dai kai ɗan mutunci ne ba zaka so a yi hira da ƙanwarka a mota haka ba, dan haka daga yau karna ƙara ganin haka, kuma in da gaske kake yi ka fito bana son ka ɓata mata lokaci. In Sha Allah baba zan gyara kuma da gaske nake da zarar mun fahimci juna zan yi mata magana na turo manyana. To hakan yayi sai ka gaida gida. Baba ya faɗa yana juyawa, Mujaheed har cikin ranta yaji daɗin yadda baba yayi masa, hakan ya bashi tabbacin gidan akwai tarbiyya, sai ya ƙara samun kwarin guiwa tare da ganin ya samu mata sai inda ƙarfinsa ya ƙare, sai ya ja mota cike da tsantsar farin ciki ya nufi gida. Najwa kuwa tana shiga gida ta shige ɗakin inna tana cewa. Inna kinga Baba ya koro ni dan kawai ina hira a mota. Yayi mini dai dai wlh ai kema kin san ya hana ki hira a motar saurayi. To amma ai ba wani abin zanyi ba kuma wlh mutumin kirki ne shi. Mutumin kirkin gidanku, kaga 'yar banza ana nima miki mutunci kina turewa, to daga yau inna ƙara ganin kin yi hira a mota zan baki mamaki, naga ma iskancinki gaba gaba yake yi, to zan saka ƙafar wando ɗaya dake. Cewar baba da ya shigo ya tsinkayi maganar Najwa, sai tayi mukus ta ƙi cewa komai dan tasan halin baba ba wasa, inna ma ta ɗaura da nata faɗar baba ya wuce yana cewa. Gwara dai ki mata faɗa taji, in ba haka ba ta saka tsiya na bada ita sadaka. Dan lamarin ta ya fara isata. Sai ya shige ɗaki Najwa dai ƙunƙuni take yi a dole bata son faɗar, inna ma sai da ta gaji da faɗar dan kanta tayi shuru. Tun daga wannan ranar kusan kullun sai Mujaheed yazo hira amma yafi zuwa da yamma saboda a lokacin ne yake da damar fita da motar gidan da yake driver, Najwa kuwa ganinsa da mabanbanta motoci yasa ta ƙara dulmiyar da zuciyarta akan ƙaunar aurensa. *** Bayan wata guda da sati biyu da haɗuwarsu Mujaheed ya turo manyansa aka yi maganar aure, wanda aka saka wata biyu mai zuwa. Musamman baba ya saka Junaid akan ya je ya bincika wanene Mujaheed domin kar a kuma yin aure irin na Aminu duk da shi wannan ya bayyana kansa, Junaid ya tambayi Mujaheed ranar daya zo hira sunan unguwarmu, bai musa ba ya faɗi sunan unguwar gidan da yake aiki bai kawo ko bincikensa zasu yi ba, a nan ne Junaid yaje unguwar ya yi bincike har ya gano asalin Mujaheed ɗan abakwa ne, da gidansu da komai sai da ya binciko nan ya gane duk zancen daya ji Najwa tana faɗawa inna cewar mai kuɗi ne ƙarya ne amma sai yayi muƙus bai faɗawa baba asalin bincikensa ba ya ce masa ya bincika mutumin kirki ne kuma yana da sana'a mai kyau, domin yana so Najwa ta aureshi ta hakane zata gane kurenta ta ragewa kanta dogon buri ƙila hakan zai sa ta gyara zuciyarta. Suka cigaba da shirin biki musamman Mujaheed daya ɗauko gyaran gida, dan so yake ko ya ya ne ya burge Najwa duk da yasan ba irin gidan yake cewa zai kaita ba, amma kuma yasan da ƙaryar ne kaɗai zai samu zuciyarta kamar yadda yake hasashe, kuma faɗuwa tazo dai dai da zama dan irin haka Najwa take so, dan da ace yazo mata a yadda yake baida komai to kallo ma bai ishe ta ba. Wannan lokacin Mujaheed ya rage zuwa zance saboda yana so yayi komai cikin lokaci, haka yaje ya zauna gaban Hajiya ya zayyano mata auren da zai ƙara da dalilinsa na ƙarawan, itama ta goyi bayan ya ƙara dan zama da mace ƙazamiya sai haƙuri nan ta ce zata sanar da Alhaji duk abinda ya bayar zata bashi. Haka kuwa aka yi ta sanar da Alhaji ya bashi gudun mawar dubu ɗari biyu, Hajiya ta bashi dubu hamsin, yaran gidan kuma daga mai dubu goma, ashirin, talatin ya haɗa kuɗi ya kai dubu ɗari huɗu da wani abu hakan yasa ya ƙara samun kuɗin haɗa akwati, dama yaje Gombe ya sayar da gonar babansu wanda ya kawo aka cirewa ƙannensa dana mamansu nashi ne ya soma gyaran gida, Mama ma ta ƙara masa da nata akan ya ƙara ga kuma tallafi daya samu gurin 'yan uwan baba da mama duk ya haɗa Allah ya rufa masa asiri ya rufu. Da kyar ya haɗa akwati biyu da kit ya cika su da kaya dai dai ƙarfinsa ya adana a ɗakin mama, yace amarya tace su danginsu ba a kai akwati sai dai yarinya ta gani a ɗakinta, mama ta yaba da aladarsu tace hakan ma shine dai dai. Ita kuma Najwa ce mata yayi su family ɗinsu ba a kai akwati sai an kai amarya ta gani a ɗakinta bayan kwana biyu, saboda kar a yi ɓarna a cikin akwatin dan kaya ne masu yawa sosai. Najwa ta yarda ta kuma ji daɗi dan har take tuna labarin da Nafeesa ta bata na ganin akwati a ranar da aka kaita kuma kaya sosai ya zuba, hakan yasa tace kaya ne ma da yawa ƙila bazai ɗauki gidansu ba tunda tasan Mujaheed masu mugun kuɗi ne. Haka dai akaita shirin biki inna duk ta sanar da dangi, wannan karan ma umma da ita ake yin komai, hatta lokacin da za a kai kayan ɗakin Najwa ango yace a badasu kawai suna da masu yin gyara kamar na farko dai, umma tace wa inna gwara dai aje a gani dan kar a ƙara yin irin na farko, Najwa fa ta dage akan kar aje, gwara ayi yadda ango yace bata son a samu matsala, to tunda uwar gayya tace ga yadda take so hakan aka yi mata aka bar zuwa, ita kuma a ganinta kar aje ayi mata sata ne dan yadda yake faɗar gidanta wane nasu Sameeha, tafi son kowa yaje a ranar da za a kaita dan asha mamaki da ganin suturar da Allah yayi mata, ƙannen Mujaheed sune suka yi gyaran ɗakin Najwa suka jera komai a muhallinsa, kayan ma sunyi yawa dan ɗakin ya cike, dole wasu sai da suka zuba su a extra ɗakin dake kusa da nata. Ana gobe biki umma ta matsawa su Sameeha akan lallai sai ta zo dan tana so su nuna komai ya wuce tunda Najwa wani zata aura ba Aminu ba, Ikram dai lafewa tayi akan ba tada lafiya, Sameeha kuwa Ibrahim ne ya tasota a gaba saboda cika umarnin umma, a ranar suka zo garin ya barta a gida. Washe gari da wuri suka tafi gidan inna ita da umma, nan fa kowa yayi mamakin ganin Sameeha ita da aka yiwa cin amana amma ta dage ta zo, umma ta nuna zumunci ya fi ƙarfin komai sannan su komai ya wuce. A tsakanin Najwa da Sameeha sai dai suka yi kallon kallo amma ba wanda ya yiwa ɗan uwansa magana dan Sameeha tace in dai Najwa tayi mata magana zata kulata amma in taba yi ba zata saka mata ido, albarkacin inna kawai taci tazo bikin bisa matsawar umma, dan Abin da ciwo in ta tuna abinda tayi musu kawai dai taci darajar iyaye ne. Najwa dai sai rawar kai da take zubawa domin duk kayan akwatinta na Aminu su ta dinga sakawa tunda babu abinda aka cire mata a ciki komai yana nan a sabo, hakan yasa ta samu damar ɗaga kai domin tasan kayan da zata samu sunfi waɗan nan, shiyasa ma bata damu a kawo na akwatinta ba tunda tana da waɗannan. Bayan an idar da sallar azahar aka ɗaura auren Najwa da Mujaheed bisa sadaki dubu ɗari biyu, wanda ɗumbin mutane sun shaida, Najwa an kuma ɗaura aurenta a karo na biyu. Yaran 'yan uwa sune ƙawayenta bata gayyaci kowa ba dan tai ta niman Nafeesa a waya baya shiga daga ƙarshe ta gane ko ta sauya layi ko kuma tayi blocking ɗinta, hakan bai wani dameta ba domin tasan ta samu mijin nunawa sa'a, a hankali zata samu sabbin ƙawaye masu aji da kuɗi ba irin Nafeesa ba, haka suka dinga ɗaukar hotuna ba laifi biki yayi armashi ba irin wancen na farko ba. ** Bayan sallar magrib aka zo da motocin ɗaukar amarya masu yawa, ciki har da Hajiya dan ita Mujaheed ya wakilta a ɗauko masa amarya tsabar yana girmamata, kuma yayi hakan ne dan kankarowa kansa mutunci mutane su gane shi ɗin wani ne, Hajiya da farko kamar ba zata je ba Alhaji ne ya ƙarfafa mata guiwa akan yadda Mujaheed ɗin ya ɗaukesu da muhimmanci, shiyasa tazo a motarta cikin shiga ta alfarma tare da ɗiyarta wacce take zawarci a gida, itace sawun gaba wajen karɓan amarya dan 'yan uwansa sai dai suka koma gefe, a motar Hajiya aka saka Najwa sai 'yan uwa mata biyu suka shiga baya suka sanya Najwa a tsakiya Hajiya da 'yarta suna gaba. Mujaheed ba ƙaramin gayyar abokai yayi ba kuma sunyi masa kara a gurin ɗaukar amarya, nan fa aka kwashi amarya da tawagarta zuwa gidan Mujaheed. Sameeha bata so zuwa ba amma umma tace dole sai sun je daga can sai su wuce gida dan a motarta suka je bikin saboda driver ya ɗauko motar a gidanta ya kawo mata, hakan yasa ta dauki umma da wasu 'yan uwansu a motarta sai tabi bayan 'yan ɗaukar amarya suka nufi gidan Najwa dake unguwar Abakwa. [7/7, 13:04] Buhainat😁: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shai wanidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.* 55. Motocin ɗaukar amarya ne suka yi jerin gwano akan babban titi, da yake dare ne ababan hawa sunyi ƙaranci aka hanya, tafiya suke a tsane ba hayaniya ko hargowar 'yan ɗaukar amarya, a haka har suka isa hanyar da zasu yi ratse su shiga Abakwa, Hajiya dake tuƙi ta kalli 'yarta kana ta mayar da kallonta hanya tana cewa. Daɗina da unguwannin nan ba su da kyawun hanya, ga babu wadataccen titi a cushe yake, in ba dalili ba babu abin da zaisa na shigo hanyar nan in gwaggwaɓe motata. Sai haƙuri kam kuma Mujaheed namu ne dole muyi masa kara, ina ganin ma in mun shiga unguwar dole sai dai mu fito ta ribas dan babu wadataccen wajen da za a juya mota. Sai dai in kin fito ki wuce mu bi ta junction ɗin unguwar shanu mu fita babbar titi ba dole sai mun koma ta nan ba. Dole haka zanyi dan kwanaki dana zo barkan matarsa ta haka ya mayar dani gida. Cewar Hajiya, Najwa dake cikin mayafi ta riƙa maimaita sunan unguwar da suka zo wai abakwa, ita da Mujaheed ya ce mata can cikin unguwar rimi ne wajen masallacin Almannar ne gidan yake, taya kuma zata ji suna maganar Abakwa, amma sai ta danne tambayarta dan ba halin tayi magana, har motarsu ta shiga cikin layi dan haka Hajiya parking tayi a gefen hanya har sauran motocin suka yi gaba suka shiga layin ita ce ƙarshen shiga, dan so take su wuce da wuri suna shiga su fito sai gida. Motoci duk sun tsaya ba batun a buga hon mai gadi ya buɗe, haka duk mutane suka fito 'yan uwan ango suka yi jagora zuwa cikin gida, Hajiya ma ta juya tana cewa su Najwa. To amarya gamu mun zo gidanki sai mu fita mu shiga ciki. Ƙirjin Najwa dai bugawa yake yi domin tunani ne ya cika mata zuciya dan hayaniyar mutanen layi ma ya tsaida mata geto area aka kawota, dan motaci suna dira maƙota yara da manya suka firfito tuna kallon motocin 'yan ɗaukar amarya, 'yan uwan baba suka fito ɗayar ta kama hannun Najwa ta fito sai suka wuce zuwa gidan Hajiya suna take musu baya, sun zo daidai ƙofar gidan Gaggo yar baban Najwa tace. Hankali dai karki faɗa kwata dan gata nan sai mun tsallaka kafin mu shiga gidan, ki buɗe ido kiga hanya kar amarya tayi wanka da kwata ki kafa tarihi. Dam dam ƙirjin Najwa ya buga tunani ta shiga yi ko ƙila gidan kakanninsa aka fara kawota kafin a kaita gidanta, dan dama duk kuɗin mai kuɗi yana da 'yan uwa talaka da 'yan kauye, wannan lissafin da ta yi yasa ta ɗan samawa kanta natsuwa kaɗan duk da wani ɓangare yana gaya mata ɗazun taji matar data tuƙosu tace an zo gidanta, haka ta ruɗa kanta da tunani daban daban har suka shiga cikin gidan ta rasa wanne ne matsaya a zuciyarta dan a rikice take. Har aka shigar da ita ɗakinta wanda yake cike da ƙamshin fentin da aka yi, waɗanda suka riga shiga ciki sai guɗa suke yi, ga ɗakin ya cika da mutane saboda kujerunta sun cike ɗakin babu fili sosai, dole sai dai wasu su shiga su fito wasu ma su samu damar shiga, Najwa dai sai da suka danganata da gadonta kafin suka ajeta ta zauna a gefe su kuma suka shiga ganin ɗaki, goggo tana cewa. Gida kam Tubarakallah sai dai ba kamar wancen na farko ba, Najwa Allah yasa nan ɗin gidan zamanki ne yasa nan ɗin arzikinki yake. Nan mata suka amsa da Amin. Sameeha kam tun sadda aka shiga da Najwa ta fito ta tsaya a ƙofar ɗaki tana jiran umma ta fito su wuce, umma kuma tana ciki tana cewa a fito da Najwa a kaita ɗakin maman mijinta sannan a haɗata da kishiyarta duk suna a cikin gidan yanzu 'yar uwar ango ke faɗa, A wannan lokacin ne Najwa ta yaye mayafinta ta miƙe kamar wacce aka tsikara tana daga kai sama tare sa juyawa tana ƙarewa dakin kallo, gaggo tace. Ke miye haka? ki bari in mun tafi sai ki ƙarewa ɗakin kallo yadda kike so, mayar da yafi muje gurin maman mijinki. Gaggo gaskiya bana tunanin nan ne gidan da Mujaheed zai aje ni, ko dai anyi musayar ɗaukar amarya ne bamu sani ba, ƙila nan za a kawo wata ba ni ba. Dalla rufe mana baki ki saka gyale ki zo muje, sai ki adana maganarki in angon yazo sai ki tambaye shi. Najwa kam a wannan lokacin ji tayi kamar ana zare mata lakka a jikinta dan gabaɗaya ji taji ba tada ƙarfi, gaggo ta ja gyalen ta yafa mata ta kama hannunta tamkar gunki ta jata, ita kuma tana binta kamar rakumi da akala, ganin komai take yi kamar mafarki har yanzu zuciyarta ta gasa gane zahirin da idanunta suke gane mata, haka suka isa ɗakin mama da ita suka zauna a kan tabarma da aka shimfida a falo, ɗaki kam sai tashin daddawa da kayan miya da mama ke sayarwa, nan fa suka gaggaisa, umma tace. To mama ga amanar 'ya mun kawo muku fatan zaku riƙe mana ita da kyau, in tayi kuskure a riƙa tsawatar mata ana nusar da ita. In Sha Allah mun karɓi wannan amanar Allah ya kaɗe fitina ya haɗa kanta da abokiyar zamanta. 'yata in kinga an yi miki ba daidai ki riƙa faɗa domin a gyara, rayuwar duniya zomu zauna zo nu saɓa ne, ga kishiyarki nan Safara'u tsawon shekara bakwai kenan ina tare da ita babu wata matsala tana yi mini biyayya da mijinta dai dai gwargwado, sannan kiyi ƙoƙari ki riƙe 'ya'yanta tamkar naki gasu nan Baba da kuma Jamila, Allah ya kauda shaiɗan a cikin zamanmu. Duk matan dake ɗakin suka amsa da Amin, Safara'u ta yashe baki tana cewa. Sannu da zuwa amaryarmu Ƙanwata, fatan kin zo lafiya da kuma shirin ayyukan gidan nan dan samun lada, ni wlh ina ta murna da zuwanki saboda nima zan huta da wasu ayyukan, Allah ya bamu haƙurin zama. Ta faɗa, wanda mama ce dake gefenta ta riƙa zunkuɗarta akan ta yi shuru ta san ba hankali ne da ita ba ta riƙa sakin magana tamkar saukar injin markaɗa, matan dake ciki suka ce amin amma suna cike da mamakin maganarta, kowa dai da yadda ya fahimci maganarta. Najwa kam zufa ne ya rufeta duk ta jiƙa kayan jikinta tana jin wani hajijiya akanta tamkar saukan aradu, har yanzu gani take bata farka daga mummunar mafarkin da take yi ba, fatan ta ta buɗe ido ta ganta a gadon inna, haka suka basu abubuwan da ake bawa uwar ango kamar yadda al'ada ta tanadar, suka miƙe tare da yi wa Mama sallama suka mayar da amarya ɗakinta umma tana cewa. Najwa mu zamu tafi ayi ta haƙuri da rayuwa kinga dai ba ke kaɗai bace a gunsa, ki kama kanki dan na kula wannan uwargidan taki ba tada seti, ki nuna tarbiyya da iliminki a cikin zamanku, ki kama mahaifiyarsa tamkar naki, sai kiga komai yana zuwa miki cikin sauƙi. Umma tana kaiwa nan a maganarta sai ta juya ta yiwa matan da ke ɗakin sallama ta fito, sauran ma suka fara fita sai ya rage mata kaɗan ne a ɗakin, koda suka fito sun tadda babu motoci dan kawo su kawai suka yi ko wacce ta koma da kanta, Umma dai da Sameeha tuni suka shige mota tare da matan da suka zo suka wuce, Hajiya ma tun ɗazu suka wuce dan Amarya tana shiga ɗakinta suka fito ko ɗakin mama basu je ba saboda haniyar tayi musu yawa. Matan da suka fito da niyyar a mayar dasu haka suka koma cikin gida zuwa ɗakin amarya suna masifar motoci sun gudu, wasu suka fara faɗar ko sisi basu ruƙo ba duk sun zata za a dawo dasu tunda ai ance mai kuɗi ne, dama dai abin duk karya ce nan magana sai ta zama abin gulma, haka suka haɗu su duka suka fito akan su taka a ƙafa in kuma sun samu motar bus a bakin titi sai su hau in sun isa gida baba ko inna sa biya, ƙarshe hatta ƙawayen da suka yiwa Najwa ƙawance basu zauna ba sunbi ayari aka bar Najwa ita kaɗai a ɗaki, sai a falo da 'yan uwan ango suka samu damar shigowa bayan tafiyar 'yan uwanta, a wannan lokacin zazzaɓi mai zafi ne ya rufe Najwa dan har wani nauyi kanta yayi mata saboda sara mata da yake yi, har zuwa lokacin ta kasa gasgata tsakanin mafarki take yi ko zahiri ne, haka ta kwanta daga gefe tana fitar da numfashi mai zafi sannan bugun da zuciyarta ke yi yasa sam jikinta ba ƙarfi ya ƙara narkewa, da kyar ta iya jawo jakarta dake gefe ta ciro wayarta ta cireta a key ta shiga wajen kira ta dannawa Mujaheed kira. Mujaheed tun ɗazu yana a can saman layinsu tare da wasu abokansa suna hira wanda rabi cikin zullumi yake da fargaban yadda Najwa zata ɗauki lamarinsa, shima bai san ya yi wauta ba sai yanzu da ƙarya ta kare masa ruwa ya ƙarewa ɗan kada, addu'a kawai yake yi Allah yasa ya shawo kanta ta haƙura duk da a ɗan fahimtarta da ya yi Najwa tana son rayuwar hutu da jin daɗi, kullun lissafinta gidan da zata zauna da irin rayuwar da zasu gudanar, yana cikin wannan fargaba ne yaji kira ya shigo wayarsa sai ya dubwa yaga ita ce, nan take yaji zuciyarsa ta tsinke yana niman rasa natsuwarsa, har ta kusa tsinkewa kan ya ɗaga tare da kara wayar a kunne ya miƙe ya bar inda abokansa suke hira ya maƙale jikin wani gida yana saurarenta ba tare da yace komai ba, Najwa cikin dakiya tace masa. Mujaheed ya naga haka? ina ji kamar mafarki nake yi an kawo ni wani gida ba wanda kavce mini ba, wai da mamanka zan zauna har da kishiya, dan Allah idan barci nake ka farkad da ni, dan lissafina ya kubce na gaza gane tsananin mafarki da zahiri. Najwa my love gidanki ne nan a zahiri ba mafarki ba, ki bari anjima inna shigo zan yi miki bayanin komai. Najwa dake kwance sai taji wani ƙarfi ya taso mata ta tashi zaune ta kuma ware idonta tana waigen ɗakin da kyau, sai ta miƙe ta shiga kallon ko ina har zuwa ƙofar data gani wanda ɗazun taji ana cewa bayi ne, taje ta buɗe ƙofar ta leƙa ta dawo ta zauna tana cewa. Kana nufin duk abin da na gani gaske ne ba mafarki ba, kana nufin zahiri nake gani, kana nufin nan ne gidan da zan zauna da mamanka da kishiya, ashe ma kana da mata baka faɗa mini ba, kana nufin duk zantukanka ƙarya ce ba gaskiya ba, Mujaheed kai wanene? waye ya aiko ka gareni domin ka ƙuntata mini ka tozarta ni a idon maƙiyana, shikenan yau maƙiyana sun ga ƙasƙantaccen gidan da zan zauna bayan na gama yin bayanin gidana babbane filat ne da kayan more rayuwa, kutumar uban can kayyasa to wallahi da sake! Ta ƙare maganar da ƙarfi sai ta kashe wayarta ta mayar jaka ta aje mayafi ta fito falo, wanda 'yan uwan Ango sun yi shuru suna saurarem maganar da take yi, fitowarta yasa suka bita da kallo itama tana binsu da kallo tare da ƙanƙance idonta, ta kama ƙugu ta soma kallon falon, ga kujeru fa sun cike ɗakin dan dama ba kalar irin ɗakin bane shiyasa suka cike guri, sai ta wuce kitchen shima kallo tayi masa na shaf duk da yana da ɗan girma amma ba sosai ba, kuma ya ɗauki kaya domin har da kitchen cabinet aka yi mata mai kyau, sai ta juyo ta rungume hannyenta a ƙirji tana duban matan dake ciki. Ku fice mini da gani tun kafin in muku ƙaramar hauka, kun zo kun jaɓe mini a kujera kuna tumurmusa sai ka ce daga gidan ubanku aka kawo. Haba amarya me yayi zafi daga cin arziki, dama mun zauna ne mu rage miki kewa kar a barki ke kaɗai. Dalla yaya Jimmai ki fito mu tafi kin tsaya yi mata bayani, ba kiga 'yar rainin hankali bace mara mutunci. Cewar wata figigiya data fice tana surutai, wacce aka kira da j'Jimmai ta bi bayansu suka fita Najwa ta koma ta zauna a gefen gado ta dafe kanta da hannu bibbiyu ta jijjigashi saboda nauyin da yayi mata, ga ƙirjinta da taji kamar an tokare da abu mai nauyi, ta kasa gasgata abinda idanunta suke gani, jin zuciyarta take kamar zata face dan raɗaɗi da zafin da yake yi mata, sai ta buɗe baki iya ƙarfinta ta saki wani irin ihu sai kace mai tashin jinnu, gani take hakan shine kaɗai zai sama mata sauƙin yanayin da take ciki, sai ta kuma ƙara sakin wani ihun ta fashe da gigitaccen kuka babu hawaye, haka ta miƙa ta zare ɗankwalin kanta ta barbaza gashin kanta tana kai koma jikinta rawa kawai yake yi, ga wani gumi da take ji ya rufeta. Wannan ihun da ta yi yasa 'yan uwan ango ruɗewa da tunanin ko mahaukaciya Mujaheed ya auro, nan take ƙanwarsa Jimmai ta kirashi a waya, yana ɗagawa ta sanar dashi yazo amaryansa ba lafiya, cikin tashin hankali ya nufo gida dan dama ya sallami abokansa yace baya buƙatar rakiyarsu, saboda bai san wani tarba zasu samu ba a gurin Najwa, yana shiga gidan ya taddasu sun yi cirko cirko a tsakar gida, ya tambaye su tana ina? mama tace. Tana ɗakinta, yarinya sai tsala ihu take yi kamar hauka sabon kamu. Mujaheed bai tsaya jin maganar mama ba ya wuce ciki, direct ya shiga uwar ɗaka, yadda ya ganta shima ya ji tsoro, Najwa kuwa tana ganinsa ta tsayar da kallonta gareshi sai a sannan ne taji hawaye ya soma kwaranya daga idonta yana sauka a kuncinta, ssi ta nuna shi da yatsa. Mujaheed kai waye? waya turoka ka kazo ka yaudareni da zantukanka na ƙarya, nan ina ka kawo n?i ba haka muka yi da kai ba, meyasa ka zamo wanda zai rushe mini duk wani farin cikin rayuwata. To wlh bazan zauna da kai ba ka sakeni kawai domin ni ba ayi ni dan zama a irin wannan gidan ba, ni ba matar da zata zauna da kishiya bace, Allah ya isa tsakanina da kai kacuceni ka rusa mini rayuwata, a karo na biyu zan ƙara zama bazawara. Sai ta tsuguna tana rushewa da kuka, Mujaheed ya risina dan ya kamata ya bata haƙuri, Najwa data ɗago kai iya ƙarfinta ta wanka masa mari. Karka kuskura ka taɓani wlh. Mujaheed ya dafe kuncinsa yana kallonta dan sosai ya tsorata da ita, bai taɓa zata zai fuskanci irin wannan ƙalubalen ba, yana ganin ai soyayyarsa tayi nisa a zuciyarta ko dan saboda nasarar yayi akan haka zata haƙura ta zauna dashi, sai kuma ya gane maganganunsa na ƙarya sune take so ba shi ba, ya miƙe ya tsaya yama kasa magana banda kallonta da yake yi, Najwa ta miƙe ta raɓe shi ta wuce zuwa falo Mujaheed yabi bayanta, kitchen yaga ta shiga ba jimawa ta fito riƙe da wuka a hannunta, Mujaheed da mugun sauri yayi baya yana cewa. Najwa meye haka? Me zaki da wuƙa? Kashe ka zanyi muddun kaba ce ka sake ni ba dan bazan taɓa zama da kai ba. A'a Najwa dan Allah ki mayar da wuƙar nan. Mujaheed ka sake ni tun kafin na illataka wlh bazan zauna da kai ba. Shikenan ki aje wuƙar muyi magana. Ya faɗa a kiɗime yadda yaga ta nufo shi gadan gadan dan babu alamar wasa a maganarta, Mujaheed yayi tsalle ya haye kujera ya shiga kwalawa mama kira. Mama! Mama! ki zo Najwa zata kashe ni Mama. Bai rufe baki ba Mama ta shigo ɗakin, ganin wuƙa ƙiri ƙiri za a kashe mata ɗa sai ta saki salati tana cewa. Innalillahi wa inna ilaihir raji'un, Mujaheed ka auro mahaukaciya zoka fita ta nan kafin ta yi maka illa. Mama ta nuna masa hanyar da zai bi, Najwa ta isa gurin ta tare, Mama tayi baya tana salati, Mujaheed haka yayi ta maza ya diro ƙasa ya tsaya Najwa tana kai masa wuƙa yana gocewa, a haka ya samu damar cafke hannunta ya kama gam ya kwace wuƙar kana ya juya ya fice da gudu da wuƙar a hannunsa, dama tuni mama ta fita tana bada saƙon a fita a kira maza su kawo musu ɗauki, sai ga Mujaheed ya fito a lokacin, Najwa ta durƙushe a ƙasa ta saki marayan kuka wanda yake tattare da tsantsar baƙin ciki, sai da tayi mai isarta kafin ta miƙe ta koma uwar ɗaka ta yafa gyalenta ta ɗauki ƙaramar jakarta kana ta ɗauki ɗankwali ta riƙe a hannu ta saka takalminta, sai ta fito ta tadda su a tsakar gida suna mayar da magana, suna ganinta duk suka yi shuru ta tsaya tana cewa. Idan baka aiko mini da takardar saki ba to ka saurari sammaci daga kotu. Tana gama faɗar haka ta juya ta fice daga gidan, Mujaheed ya yi yunƙurin bin bayanta mama ta dakatar da shi. Kasan Allah ba zaka bita ba bar ta tafi gwara ma ka saketa dan kar ta kashe mana kai abanza, saboda wannan da gani mahaukaciya ce. Mama wlh da hankalinta kuma duk laifina ne dana yi mata ƙarya amma In Sha Allah komai zai yi daidai dan ina ƙaunar matata ba zan iya sakin ta ba wlh. Au haka kace ko, to idan tayi ajalinka shikenan Allah ya jiƙanka. Tana gama faɗar haka ta wuce ɗaki cike da takaici, haka sauran suka dinga mayar da magana, Mujaheed komawa ɗakin yayi ya zauna ya rungume hannunsa yana tunanin abin yi. Najwa kuwa tana fita ta samu mashin ya ɗauketa akan ɗari biyar ta hau ta nufi gida. [7/7, 13:04] Buhainat😁: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shai wanidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.* 56. Najwa. Tana isa gida ta shiga kai tsaye babu fargaba ko shakkar ba zasu karɓeta ba, kamar wacce aka koro idanunta nan a koɗe ta shiga, sauran matan da basu samu damar kaita ba sune suka yi tozali da ita, suna ganinta suka saki salati da tambayar lafiya? ina sauran matan da suka yi mata rakiya zuwa gidanta?, dan har lokacin basu ƙaraso ba, inna data ɗan miƙe haƙarƙarinta a gado dan ta huta kafin 'yan kai amarya su dawo, jin an ambaci Najwa da salati yasa ta sauko ta fito tana salati, tana ganinta kuwa gabanta yayi mummunar faɗuwa, ta tsaya ta kasa yin magana ita kuma Najwa jikin bango ta raɓe tana matsa yatsunta ga gyalenta ya rufe fuskarta balle a san wani matsayi idanunta yake ciki, shigowar 'yan kai amarya yasa gidan ya hautsine suna ta zambaɗawa abokan ango zagi akan rashin dawowa dasu da suka yi ba, a lokacin ne goggo ta ke cewa inna. Wlh mun ci uban tafiya kafin muka kai babban titi muka samu mota bus ta ɗebomu, ga su can mun barsu da Junaid zai biya kuɗin motar, dana san ba zasu dawo damu ba ai da da shirina na fita yadda zan yiwa kaina taimakon gaggawa, ga ƙafafuna har zugi suke yi mini dan wahala. To ai amaryar da kuka gama wahala akanta gata ta rigaku dawowa, mun ɗauka ma ko kun san da dawowarta ko faɗa aka yi a gidanta ba a rabu ta daɗi ba. Cewar wata tsohuwa dangin inna, ai da tsananin mamaki duk suka bi inda aka nuna Najwa, sai suka saki salati suna mamakin ganinta, nan suka shiga mayar da zancen a can gidan suka barta ya akayi harta rigasu dawowa? kuma lafiya lau ba abinda ya faru na rikici a gidan, a lokacin baba ya shigo Junaid na biye dashi a baya suna maganar rashin mutuncin mai bus akan dole dubu biyar aka biya shi, ganin kowa a tsaye sunyi cirko cirko yasa su tambayar meke faruwa. Inna data kasa tsayuwa ta ja ƙaramar kujera ta zauna tana nuna musu inda Najwa take tsaye. Gata nan ta kuma dawowa har ta riga waɗanda suka kaita saurin shigowa gidan, ban san me ta aikata ba, ban san me Najwa take son zama ba, ita kaɗai mace a cikin yaran nan amma tana son ɗaura mini mummunar hawan jini wanda ƙila sai tayi ajalina hankalinta zai kwanta. Inna ta ƙare maganar tana matsar kwallar baƙin ciki, baba salati ya saki yana ambaton sunan Najwa, Junaid kuwa wani uwar tsawa ya daka mata yana nuna ta da tsaya. Me ya dawo dake? Meya faru kuma zaki dawo mana gida bayan mun sallameki. Wlh Allah ni ba zan koma gidan Mujaheed ba, bazan iya zama da shi ba saboda makaryaci ne yaci amanata ya yaudareni ya aureni da ƙarya, duk kuɗin da yake faɗa karya ne gidan da aka kaini wlh ba shi bane wanda ya faɗa zan zauna, bai sanar dani yana da mata ba, komai nashi shiri ne kamar an haɗa baki dashi ne domin a cutar dani. Najwa ai baki gama ganin komai ba domin kuwa irin Mujaheed ne ya dace dake, sam ba kida godiya Allah komai naki baki sanya tsoron Allah a ciki sannan kin ƙi yarda kin yi kuskure, aurenki na baya baisa kin gane kurenki ba balle ki shiga hankalinki, to hassadarki itace ta kawo ki wannan matakin kuma wlh dole ki koma ki karɓi ƙaddarar da kika zanata da hannunki, baki isa ki mayar damu mutanen banza ba, maza juya mu tafi tun kan raina ya ƙara ɓaci dan kin san zan iya karya ki wlh. Haba yaya miye laifina dan na zaɓawa kaina inda zan huta, taya na bar gida irin wannan in yi fatan samun irinsa, ni ba zan koma ba, ba zan zauna da makaryaci ba kuma... Bata kai aya ba Junaid ya nufe ta gadan-gadan zai rufeta da duka sai ta zabura ta ɓoye a bayan wata mata ta soma kuka, Baba da baƙin ciki yasa ya kasa magana tun ɗazun ya dakatar da Junaid yana cewa. Dakata Junaidu ba sai ka wahalar da kanka ba, Najwa zo nan. Ya ƙare maganar yana haɗe rai ya juya ta tafi ɗakinsa, Najwa ta bi bayansa suka shiga ciki Inna ma ta shiga ɗakin, Junaid ya tsaya a bakin ƙofar ɗakin, Najwa ta tsuguna a gaban baba daya zauna gefen gado. Baba Ya ya nuna mata kansa yana cewa. Ni wanene a gurin ki. Kai babanmu ne. To ina so in har kina so na cigaba da amsa sunnan mahaifinki ki tashi ki koma gidanki, idan kuma kin zaɓi duniya ce to zan barki da ita, sannan ba zaki ƙara amsa sunan 'yata ba dan zan tsameki daga cikinsu har abada bani ba ke, idan kin kaso aurenki to sai ki nima wani uban, dan kar ki kuskura naga ƙafarki a gidan nan na sallawa duniya ke, ko mutuwa nayi bance ki zo ba. Zaɓi ya rage naki. Yana gama faɗar haka yaja pillow ya kishingiɗa ransa a matuƙar ɓace dan har wani ɗaci ɗaci yake ji a makoshinsa, lamarinta a yanzu ya daina bashi mamaki face tsoro dan gani yake tamkar ba asalin Najwan su bace yarinya mai kunya da kawaici ga biyayya, shi dai kam data kaso aurenta a karo na biyu gwara ya sallamawa duniya ita dan baya jin zata kuma cin abincin gidansa balle ta samu wajen kwana. Bakwa ko jikinta yayi mugun la'asar da zantukan baba ta girgiza matuƙa akan furicinsa, wanda bata yi tsammani ba sam a zaton ta da ƙaramin lisaafinsa zasu goya mata bayane akan sakin tunda Mujaheed ya yaudaresu ne, Inna tace. Haka nima kazalika idan kika kaso wannan auren wlh bani ba ke Najwa, duk tarin soyayyar da kika ganin muna yi miki bazai sa idonmu ya rufe ba mu cigaba da zuba miki ido kina iskancin da kika ga dama ba, ya kamata ace kina da iyaka bazai yuwu ba, dan haka ki miƙe ki koma in da kika fito dan wlh yadda kika dawo ke kaɗai haka zaki mayar da kanki idan kin so ki yi zaman aure idan kin so ki kashe auren ki shiga duniya amma ba gidan nan ba, ai ba ke ce kaɗai pya ba sauran sun ishemu zaman duniya. Nan jikin Najwa ya ɗauki rawa zuciyarta kamar zata faɗo kasa, bata zaci haka ba tayi tunanin zasu goyi bayanta, yanzu da kunya ta koma gidanta ita kaɗai ba tare da an rakata ba sannan ma in ta koma tace me ita data nima saki, daka mata tsawan da Junaid yayi yasa ta miƙe zumbur tana matsar kwalla cikin kuka ta soma cewa. Yaya dan Allah ku saurari uzurina wlh ba a son raina ba na dawo, Mujaheed ya yaudareni yayi mini ƙaryar da bai dace nayi zaman aure da shi ba, yanzu ina kuke so na tsoma zuciyata, rana zafi inuwa kuna. Najwa duk abinda ya faru fa ke ce kika jawa kanki kuma Allah ya duba zuciyarki ne shiyasa ya zaɓa miki Mujaheed a matsayin miji, idan kin gyara zuciyarki tabbas Allah zai jiƙanki. Ki ɗauki wannan auren matsayin ƙaddara dan haka wuce muje. Ya ƙare maganar yana nuna mata hanyar fita, jikinta a sanyaye ta wuce yabi bayanta hawaye kawai take yi ta rasa meke mata daɗi, sai ta ja mayafinta ya rufe mata fuska ta wuce har titi ya samu napep ta shiga shima ya shiga gefenta suka wuce abakwa lokacin wajen goma saura, har ƙofar gidan suka isa, Junaid ya ciro wayarsa ya kira Mujaheed akan ya fito ƙofar gidansu, Najwa tayi mamakin yadda Junaid ya san gidan tunda ba tambayarta unguwar yayi ba, hakan ya na nufin yasan komai kenan, a haka Mujaheed ya fito shida Mamansu suka tsaya Junaid ya sauko daga Napep ya tasa ƙeyar Najwa suka isa ƙofar gida, mama da faɗanta tace. Allah yasa ba dawo da ita kayi ba, dan dama jira nake garin Allah ya waye mu aiko da takardan sakin da ta buƙata, dan bazan yarda ta kashe min shi ba a banza. Dan Allah mama kuyi haƙuri In Sha Allah ba zata sake aiwatar da komai ba, anyi mata faɗa sosai. Yaro batun kisa fa ake magana, yarinyar nan wuƙa ta ɗauko akan lallai zata kashe shi in bai saketa ba, Allah ne ya tsare shi ya amsa wuƙar fa, dan haka wlh ka mayar da ita gida sai anyi sabon zama bazai yuwu ta yi irin wannan abu ba in ɗauke shi da sauƙi. Mamaa tunda sun dawo na tabbatar ba zata yi komai ba wlh gidansu akwai kula da tarbiyya, kuma na faɗa miki laifina ne da har yasa tayi haka ni na ja komai. Cewar Mujaheed da duk ya ƙosa a bashi matarsa dan sosai yaji farin cikin dawo masa da ita, amma fir mama tace. Ai dama kai shashasha ne so ya rufe maka ido har baka gane kanka, yarinyar data nima kasheka kake rawar ƙafa akanta. Kai yaro ka mayar da ita gida sai munyi shawara tukuna dan wannan maganar sai mun zauna mu iyaye mun tattaunata. Shikenan mama Allah ya kyauta na gaba ya kuma ƙara muku haƙuri, ke kuma muje gida kin kyauta abinda kika yi. Ya faɗa yana juyawa Najwa kuka kawai take wanda hakan ya haifar mata da ciwon kai mai tsanani, akan wannan ƙasƙantaccen gidan mama tayi musu haka, wanda ita In son ranta ne ba zata zauna a ciki ba, ba ƙaramin muzanta tayi yau ba komai ya lalace mata a lokaci guda, haka ta juya suka shiga napep ya mayar dasu gida, Mujaheed kuwa kamar zai ɗaura hannu aka ya fasa ihu dan sosai ya ji ba daɗin abinda mama tayi, haka suka juya suka shiga gida kowanne ransa a jagule. Junaid suna isa gida yace ta wuce ɗakin inna shi kuma ya yi sallama ɗakin baba da suka yi masa izini ya shiga ciki ya zauna, nan ya basu labarin duk yadda suka yi da mahaifiyar Mujaheed, inna tace. Banga laifinta ba wlh dan tana da gaskiya, maganar kisa ba wasa bace, wlh Najwa sai ta san ta aikata waɗannan abubuwan, na rasa yadda aka yi ta sauya halinta gabaɗaya. Laifinki ne da baki saka mata ido, ga irin ta nan ai ita kaɗai ta hanamu saƙat. Haba malam kaima kasan ina iya ƙoƙarina, yadda ka shagoɓa Najwa ai ni bana yi mata da wasa, kawai dai halin ɗan yau ne ka haifa baka haifi halinka ba, fatanmu Allah ya sa wannan ya zama shine abu na ƙarshe yasa hanyar shiryuwarta ce. Suka amsa da amin, kana Junaid ya fito ya wuce ɗakinsa ransa ba daɗi, ya rasa wani irin rayuwa Najwa ta zaɓarwa kanta sam bata lissafi, duk abin da yazo mata a rai shi take aikatawa ko da hakan zai cutar da ita, ba zai ce yarinta ke damunta ba kawai tsabar son rai ne yayi mata yawa, haka ya kwanta da tumani barkatai, farin cikinsa ɗaya da Mujaheed ɗin yana sonta dan yaga haka ƙarara a idanunsa. Washe gari. Duk yadda suke tsammanin lamarin ya wuce tunaninsu, domin tun safen suke zuba idon ganin dangin Mujaheed har zuwa dare ba amo ba labari, da yake baƙi duk sun watse a ranar gida ya rage sai su kaɗai, Najwa kam daga kwanciya ba abinda take yi ga damuwa yayi mata yawa dan ƙiri ƙiri duk pyan gidan sun ɗauki gaba da ita ba mai yi mata magana, kota gaishesu babu mai amsawa haka ta yini a ɗaki, abinci ma sai dai inna ta shigo mata da shi ba um ba um um. Wasa wasa aka shafe kwana biyu ba labarin 'yan uwan Mujaheed kuma shima bai zo ba domin mama tace in yaje bata yafe masa ba, dan dole sai ta nunawa Najwa kuskurenta yadda in ta dawo gidan zata natsu tayi abinda ya dace, Najwa wani rama tayi na ban tausayi saboda yawan zazzaɓin da take fama dashi, ka kaɗaici dan har lokacin ba mai shiga shirginta, wayarta ma Junaid ya amshe ba abinda zata yi da zai ɗebe mata kewa, ko kallon tv ma ba daɗi yake mata ba kuma har lokacin bawai tana son auren Mujaheed bane, kawai dai biyayya ta ɗauki ɗamarar yi domin ta rabu da su Inna lafiya, amma tasan zaman gidan Mujaheed tamkar zaman kurkuku ne wanda babu farin ciki a ciki, bata tunanin zata so shi balle ta iya yi masa biyayya, tunanin mafitar yadda auren ba zai jima ba kawai take yi dan hankalinta ya koma Kano, gwara ta koma ta auri Atiku duk da yana da muni amma yanada kuɗin da zata ji daɗin rayuwa, ta yarda da su Sameeha sun fita kuma ƙaddararsu ba zata zama ɗaya ba amma tana buƙatar ace itama ta auri wani taji daɗin aure kamar yadda suma suke ji, haka take yini tunani da kuka babu abinda inna take sata tayi mata, ba mai hira da ita ba wayar da zata yi magana da mutane chart balle ta samu wacce zata fallasa sirrin dake ranta, tasan Anty Saleema ce kaɗai zata saurareta harta bata taimako da shawara, fushin da take da ita yasa ma bata zo bikin ba, tasan kuma In ta kirata ta bata haƙuri har ta sako zancen Atiku ƙila ta saurareta tunda itama tanada burin daya sa take so ta aureshi. Ganin fa in bata miƙe ta nimawa kanta mafita ba haka zata ƙare a kwance, hakan yasa ta miƙe ta fito daga ɗaki ta shiga ɗakin baba ta ɗauko wayar Inna data aje a nan, sai ta dawo ɗaki ta kwanta, dama innar ta shiga wanka ne, sai ta fara tunanin wanda zata kira a lokacin, Umma ce ta faɗo mata a rai dan tasan ita ce kaɗai zata iya taimakonta, dan tana da tabbacin bata san tana gida ba. **** Sameeha. Tun sadda suka bar gidan Najwa suka sauke matan da suka ɗauka a bakin titin gidansu Najwan sai suka wuce, Sameeha ta kalli umma tana cewa. Umma kinga inda Allah ya kai Najwa, kuma ba laifi gidanta yayi kyau kawai dai bata samu yadda take so ba, dan ina ganin Allah yasa ta zauna dan kamar ba haka taso ganin gidanta ba. In Sha Allah zata zauna ai so ba samu bane, mu bita da fatan alkhairi. Haka suka cigaba da tattauna maganar har suka isa gida, a daren Sameeha ta bawa Ikram labarin abinda ya faru na gidan Najwa, sosai Ikram tasha dariya tana cewa zata zo su je taga ɗaki dan wlh sai ta yiwa Najwa wulaƙanci, Sameeha tace ita ba ruwanta ba zata rakata ba haka suka sha hira. Washe gari ne Sameeha ta tashi da ciwon kai daga nan sai zazzaɓi da amai a takaice laulayin ciki ta soma, wannan yasa Umma bata samu komawa gidan inna ba balle susan meke faruwa, haka Sameeha tayi jinyar kwana biyu harta samu sauƙi sosai bayan sunyi zaryan asibiti. Ranar Laraba Ikram taje gida suka sha hira a nan ne take cewa washe gari tunda Sameeha ta samu sauki sai suje gidan Najwa, umma tace ba inda zasu je tunda itama Najwa bata je ɗakunansu ba bata son damuwa, suna cikin wannan maganar ne sai Najwa ta kira umma da wayar inna. Umma ta ɗauka da sallama sai dai muryan Najwa taji tana gaisheta ta amsa cike da mamaki tana cewa. Amarya ce da kanta ba dai har kin fara fita ba. Ina innar take? Umma ai ina gida tun ranar da aka kaini ashe inna bata faɗa miki ba. Subhanallahi me ya faru? Aiko Zulai bata faɗa mini ba, da yake nima ban samu dawowa ba saboda Sameeha ba lafiya. Allah ya ƙara sauƙi, dama ina so ki je gidan da kuka kaiki ki bawa mamansa haƙuri ta yarda na koma ɗakina, wlh abubuwa dai da yawa sun faru yanzu haka babu mai kulani a gidan nan kona gaishe su basa amsawa. Ta ƙare maganar tana matsalar kwalla, salati kawai umma ke yi zata yi magana taji inna ta amshe wayar tana faɗar waye Najwa ta kira, nan ta dinga surfa masifa ta inda take shiga bata nan take fita ba, Umma dai kashe wayar tayi tana mamakin me ya faru kuma. Umma menene ya faru? Cewar Sameeha, Umma ta sauke ajiyar zuciya tana cewa. Najwa ce wai take gida tun ranar da aka kaita ta dawo, na kasa gane kan lamarin yanzu haka innar ta amsa wayar bata bari mun gama magana ba sai faɗa take yi mata, wannan yarinyar kuma me ta kuma ɗaukowa? sam bata jin magana. Wlh umma alhakin anty Sameeha ke binta ai duk wanda yace tukanyar wani ba zata tausa ba to nashi ko zafi bazai yi ba. Dan ba tada kunya shine zaya kiraki kije kiyi mata me? Cewar Ikram. Umma ta danƙara mata harara. Wai ke abu baya wucewa ne a gunki ita wacce aka yiwa ta yafe komai ya wuce amma kita dawo da magana baya, Sameeha bari naje naji meke faruwa zama bai ganni ba idan su Khairy sun zo kwa gaidasu ƙila har su tafi ban dawo ba. Ta kare maganar tana miƙewa, Sameeha tace sai ta dawo umma ta shiga ɗaki ta sauya kaya ta saka doguwar rigar atamta ta sa babban hijab ta fito tana kwalawa Zaidu kira, dan yana ɗakinsa yana barci, cikin yanayin barci ya fito tace yaje ya shirya zai kaita anguwa yanzu, ba musu ya koma ɗaki ya zura riga ya ɗauki hula da key mota ya fito suka wuce. [7/7, 13:04] Buhainat😁: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shai wanidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.* 57. Umma abakwa ta wuce Zaid har ƙofar gidan ya kaita yayi parking yana duban umma. Wai ina ne muka zo umma? Gidan sirikan Najwa ne bari na shiga na fito yanzu, ka jira ni. To yace mata sai tafi ta shiga gidan da sallama, su mama suka amsa da suke zaune a tsakar gida bisa tabarma, umma da fara'a ta ƙarasa ciki suka yi mata masauki akan tabarman da mama ke kai nan suka gaisa fuska sake mama ce tace. Kamar naso na wayi fuskarki kuwa. Eh mune muka kawo muku amarya Najwa har muka danƙa amanarta hannunki yanzu ma dalilin zuwana kenan, bawai dan naji me ta aikata ba sai dan na bayar da haƙuri ku yafe mata kin san halin ɗan yau basa abu da lissafi ko tunani, iya gwargwado Najwa mun bata tarbiyya dan har haddar Al-qur'ani ta fara Allah bai nufa zata haɗa ba, taci arzikin mu iyayenta ki amince ta dawo ɗakinta zuwa yanzu na tabbatar ta gane kurenta. Banƙi ta taki ba Hajiya, wlh lamarin ne ya bani tsoro tunda ta ambashi zata kashe Jaheedi, amma tunda kin zo ba zaki tafi haka ba dole na amince da buƙatarki dan haka na yarda ta dawo ɗakinta Allah ya kyauta na gaba. Mun gode Allah ya saka da alkhairi ya bar zumunci, ina ganin anjima sai mijinta yaje ya ɗauketa da kansa hakan ya nuna mutuntawa kuma iyayenta zasu ji daɗi. Eh gaskiya ne hakan za a yi kuwa In Sha Allah zan turashi yaje ya ɗauketa Allah ya haɗa kansu ya kauda shaiɗan. Ameen ya rabbi nagode sosai da karamci, ni sunana Halima matar yayan maman Najwa ce ina zaune a rafin guda In Sha Allah a hankali zamu yi zumunci tunda 'ya'ya sun haɗa. Aiko sun haɗamu kuma In Sha Allah za muyi shi, dan zumunci abu ne mai kyau. Cewar mama cike da jin daɗin sauƙin kan umma, sosai tayi mata kwarjinin da ba zata iya amsar roƙonta ba, haka suka dan taɓa hira umma tace zata wuce, mama tace ta tsaya Safara'u ta kawo mata ruwa tasha, umma tace ta gode daga haka ta miƙe tana ƙara yi mata godiya, mama har ƙofar gida ta rakota, abinda ya ƙara burgeta ganin da mota aka kawota hakan yasa mama ta dakatar da umma tana cewa. Hajiya da kin bani number ɗinki mu riƙa gaisuwar zumumci, sannan in yarinya ta yi ba dai-dai ba na samu hanyar da zan sanar miki domin arzikinki taci wlh. Umma tayi murmushi tana ƙara bata haƙuri, ta buɗe ƙaramar fos ɗinta ta ciro waya touch da Zaidu ya siya mata tace mama ta saka number ɗinta. Riƙe abarki wannan waya saiku manya ban san kanta ba, ga dai tawa ki saka naki number ɗin ki kira akwai 'yan canji a ciki. Mama ta faɗa tana ɗauko wayar a cikin lalitarta dake manne a jikinta, ta miƙawa umma ta amsa ta kaiwa Zaidu ya saka number ɗinta sai ta dawo ta kira ta miƙawa mama wayar tana ƙara yi mata godiya, a haka suka rabu ta koma ta shiga mota suka wuce, Mama sai da ta ga wucewarsu kafin ta koma gida tana jinjina umma yadda take da sauƙin kai ta wuce cikin gida tana. Aiko na samu ƙawa dan wlh zan je na dangwali arziki, da gani suna da kuɗi gashi ba tada wulaƙanci. A haka ta ƙarasa ciki tana kwalawa Safara'u kira akan tazo ta yi mata saving number umma da Hajiya Halima. Umma sai da suka hau hanya Zaidu ke tambayar meya sa tazo gidan, umma a taƙaice ta bashi labari Zaidu yayi murmushi yana cewa. Kina nufin a wannan gidan Najwa zata yi rayuwa, lallai ruwa ya daki ɗan zakara, dole tayi bori tace ba zata zauna ba, yanzu haka ƙarya yayi mata hali yazo ɗaya, Allah yasa ta zauna. Amin, fatan alkhairi zamu yi mata kuma in tayi haƙuri komai zai wuce, dan Maman mijin tana da kirki ba tada damuwa. Ta dai riga ta yiwa kanta, Abin da ciwo daga ɗari ta dawo sifili, dan kam ni data gujewa na fi ƙarfin abinda take kwaɗayi, nifa umma ina so ayi maganar aurenmu zuwa bayan sallah. Ya ƙare maganar yana shafa kai, umma tayi murmushi tana cewa. Maganar bikin Najwa ya ɗauke mini hankali amma mun fara maganar da Sameeha, Sannan ma ita kanta Rukayya ta kirani kan batun, In Sha Allah da anyi azumi da wata nake so ayi komai a wuce gun. Tp Allah ya tabbatar mana da alkhairi. Ameen, sai ka fara cigita gidan da zaka zauna kafin maganar tayi kwari ya zama akwai muhalli a ƙasa. Umma ai ni ina da gida dan Ibrahim mijin Sameeha shekaran jiya daya zo yayi mini maganar aure nake ce masa ina sa ran nan kusa nayi, shine yace gidana yana wuyansa karna damu da an sa key zai miƙa mini, amma kar na sanar da kowa tukuna, shiyasa ban faɗa miki ba. Ikon Allah to Allah ya saka da alkhairi sai ka cigaba da haɗa akwati. Wannan ma umma banda damuwa dan kuɗi zan baku ku ƙarasa haɗawa, kin san na samu wannan kwangilar na jakunan 'yan siyasa da zan haɗa Shamsu mijin Ikram ya samo mini, kuma ga dukkan alamu In Sha Allah umma bana zaki aikin Hajji dan da kuɗina zan biya miki. Kabbara umma tayi tsabar farin ciki tana sanya masa albarka, Zaidu yana amsawa da amin kana ya cigaba da cewa. Da gida nayi niyya in saya amma dana ji Ibrahim zai bani nasan kuma ba zai bani mara kyai ba, shiyasa kawai nace gwara na biya miki Hajji tunda kinga ga motar hawa ma ina da ita, sauran kuɗi zan faɗaɗa sana'ata kafin aiki ya fito, dan kinsan na bawa Ibrahim takarduna ina sa ran zan samu. Alhamdulillah i rayuwarku tayi kyau Allah yasa kyawunta har a aljanna, Allah ya ƙara shirya mini ku ya albarkace ku. Umma ta faɗa cike da jin hawayen farin ciki, Zaidu yayi murmushi. Ameen umma, kuma Duk yadda muka zama ke ce sila domin ke ce kika jajirce a kanmu kika bamu tarbiyya da muka san kanmu a yanzu, baba ma yayi nashi ƙoƙarin, Allah dai ya saka muku da gidan Aljanna. Yanzu ina zamu nufa.? Mu wuce gida kawai ba sai naje gidan Zulai ba na riga nayi abinda ya dace saji labari a can. Umma ta faɗa, haka suka cigaba da hira gwanin ban sha'awa har zuwa gida. **** Bayan sallar magrib. Mujaheed daya dawo daga gurin aiki mama ta sanar dashi zuwan umma har take bashi labari da yabon ƙirkinta, tace ya shirya yaje ya ɗauko matarsa. Cikin tsananin farin ciki ya wuce ɗaki ya watsa ruwa kana ya sanya manyan kaya ya fito yana baza ƙamshin turate, Safara'u sai washe baki take tana ambaton ango, Mujaheed ya dalla mata harara yana cewa. Shashasha wai ke ko irin kishin nan ba ruwanki. Ni dai Jaheedi karka riƙa gwasaleta gaban matarka ta rainata bana son haka. Cewar mama, Mujaheed baice komai ba ya fice dan a kullun Safara'u bata laifi a gurinta, haka ya tari napep ya nufi badarawa a asalin Mujaheed, yau ne rana ta farko daya je gidan bada motarsa ba, koda ya isa sallama ya yi a ƙofar gida Junaid ya amsa ya fito dan shike tsakar gida suna hira da iyayensu, koda yaga Mujaheed ne ya miƙa masa hannu suka gaisa kana ya yi masa jagora zuwa cikin gida, a nan tsakar gida aka shimfiɗa masa dadduma ya zauna ya gaishesu cikin mutuntawa da bayar da haƙurin jinsu shuru, a takaice bai ɓoye zafin da mama ta ɗauka ba dama zuwan umma gidan ɗazun wanda dalilin zuwanta yasa mama ta sauko, baba ya shiga girgiza kai. Halima! Halima kai Allah ya shiwa matar nan da albarka ta iya mu'amala, tasan ta rama alkhairi akan sharri, duk irin abubuwan da suka faru ta mance komai ta yi mana wannan halacci, Najwa! Najwa! maza zo nan. Baba ya ƙare maganar yana kwalawa Najwa kira cikin zafin rai, data fito ta tsuguna a gefe Baba ya nunata da yatsa. Kin ga duk irin abinda kika aikawata Sameeha bai hana Halima ta shiga gaba wajen gyara aurenki ba Najwa, wlh kibi duniya a sannu babu komai a cikinsa sai ruɗani, ki zauna a ɗakinki kiyi bautan Allah, ki mance komai ki gyara zuciyarki da halinki dan wlh idan kika aikata mummunar abu bani kika wulaƙanta ba Halima kika yiwa wacce ta yi miki halacci kuma bai dace ki ƙara saka mata da sharri ba, kin ga dai gamu nan mu iyayenki ba muda komai bamu bayar ajiya ba haka muke cikin rufin asirin Allah, ki saka a ranki arziki na Allah ne kuma yana goshin ko wani bawa ki taƙaita dogon buri domin ki wanye da duniya lafiya. Kai kuma don son ma'aikin Allah s.a.w ka cire ƙarya da yaudara a cikin lamarinka duk abinda zaka yi mata ka yi iya ƙarfin ka, ka gyara alaƙarka da ita in har kana so zamanku ya ɗaure, gata nan amana ce muka baka in kaci to wlh Allah bazai barka ba, Zulai in kina da abin cewa ki faɗa sai su wuce. Baba ya ƙare maganar ga Inna, itama faɗan ta kuma yiwa Najwa da nasiha ta haɗa da Mujaheed ɗin, daga bisani suka sallame su Najwa ta faɗa jikin inna tana ta kuka, hakanan taji zuciyarta ta tsinke wanda sai a wannan lokacin ne ta ji bata kyautawa Sameeha ba da kuma tunanin duk tarin abubuwan data yi bai hana umma ta shiga gaba ba wajen daidaita aurenta, ta kuma san har abada su Sameeha sun fita ba zata taɓa haɗa kanta dasu ba, tunda zama gidan Mujaheed ya zame mata ƙaya a maƙoshi bata san ranar fitanta ba, sai ta ƙara fashewa da sabon kuka. Baba da Inna ku yafe mini, In Sha Allah bazan taɓa baku kunya ba. Mun yafe miki Najwa dama mu fatanmu ki gane kinyi kuskure. Cewar Inna tana bubbuga bayanta, baba ko kwalla yaji ya cika masa ido dan yana matuƙar ƙaunar Najwa saboda ita kenan musu ɗiya mace, dole yake danne son saboda ya nuna mata kuskurenta. Haka Mujaheed yayi musu godiya da sallama ya fita shima duk jikinsa yayi sanyi da dana sanin ƙaryar daya yi mata, Najwa kuwa sai da inna ta ɗagata ta kamata suka miƙe kana ta kaita ɗaki ta kuma shiryawa sai ta rakota har ƙofar gida, Junaid ya yi musu rakiya har zuwa bakin hanya, ya tare musu napep suka shiga yayi musu fatan alkhairi suka wuce. Suna isa gida Mujaheed yayi musu jagora sai da suka fara shiga ɗakin mama Najwa ta gaisheta ta amsa fuska sake kamar ba wani abu daya faru, hakan ya faranta ran Mujaheed daga bisani suka wuce ɗakinsu ya buɗe suka shiga sai ya ce mata zai je ya dawo ya fito ya wuce, Najwa kuwa kwanciya tayi a gado bata cire komai a jikinta ba sai duniyar tunani data shiga da lissafin yadda zata fara rayuwa a gidan da ko a mafarki bata taɓa kawowa kanta ba. Kusan minti arba'in Mujaheed ya ɗauka kafin ya shigo gidan, sai da ya fara kaiwa su Mama nasu kazar yace ta ɗibarwa Safara'u sai yayi mata sai da safe ya dawo ɗaki ya samu Najwa a kwance, ya fita ya rife ɗakin ya ɗauko plate da kofi ya dawo ya zauna gefen gado ya ciro gasasshiyar kaza ya aje a plate ya buɗe kwalin holandiya ya tsiyaya a kofi ya ce. Najwa tashi kici abinci. Ba musu ta tashi ta zauna ganin kayan kwaɗayi yasa ta dan sake fuska, haka ta amsa kofin tasha ta sauko ƙasa kusa dashi suka fara cin kaza daga haka ya dinga janta da hira har ta saki fuska. A wannan daren dole Najwa ta bada kai bori ya hau dan kuwa Mujaheed ba baya ba wajen iya zuba lafazi, sai dai wannan karan ya yi ƙoƙarin gyara harshensa gudun yin ƙarya, ya samu Najwa a cikakkiyar budurwa hakan ya ƙara dulmiyar da zuciyarsa wajen soyayyarta dan son ta ya ninku. Najwa dai tasan ƙaddara ta riga fata so bai taɓa zama samu, Mujaheed shine babban ƙaddarar Jarabawanta a duniya. *Hoooohoho ya kamata ace littafin nan ya ƙare a nan fa, ko da yake akwai saura pages ɗaya ko biyu In Sha Allah* [7/7, 13:04] Buhainat😁: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shai wanidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.* 58 Da gari ya waye. Najwa ta shiga kitchen domin ɗaura musu ruwan wanka sai dai me babu gas domin haka aka kawo mata tukunyar, sai ta dawo uwar ɗaka ta zauna a gefen gado tana cewa Mujaheed dake kwance. Ya za muyi babu gas, kuma nepa sun ɗauke wuta. Subhanallahi yanzu ya zamu yi wanka, ko da yake bari na amso mana ruwa gurin mama dan tun asuba take tashi haɗa abin kari. In yaso anjima sai a siwo miki gawayi ki fara amfani da shi kan na siyo gas ɗin. Mujaheed gawayi fa kace? taya ina amarya nayi amfani da gawayi haba dai ɗan abincinmu kwata kwata kwaya nawa ne da sai na hura wuta, gas ɗin dai zaka siyo mini. Gaskiya Najwa bani da kuɗi dan abinda ya rage mini kenan na siyo kaji biyu da sauran abubuwan, dubu guda da ɗari biyu ya rage mini yanzu, in zan je aiki zan bawa mama ɗari biyar na cefane sauran nayi kuɗin mota. Haƙuri za kiyi ki amfani da gawayi dan yanzu so nake muyi zama da gaskiya ba zan yi miki abinda nasan bani da ƙarfinsa ba, in ma ba kida murhu akwai na mama dana Safara'u ki ara ɗaya ki amfani da shi sannan girki mama zata riƙa yi damu har na kwana biyu. Wlh bazan bar gawayi a gidanmu ba na zo nan inyi amfani da shi ba, ai gas ba ƙarya kayi ba dan ka siyan mini shi. Najwa sai fa kiyi amma banda kuɗin gas a yanzu. Yana gama fatdar haka ya sauko daga kan gado ya zura riga ya fice, Najwa wani baƙin ciki taji ya tsaya mata a maƙoshi wai gawayi, abinda take tunanin har gaban abada tafi ƙarfinsa a yanzu amma kuma yana niman laƙa mata amfani dashi na dole, bata jin zata yi amfani da shi domin tun a gidansu tayi hannun riga da shi, wayarta ta ɗauko taga ƙarfe bakwai saura still da sauran gari ya waye, amma ya zata yi dole ta kira gida dan a kawo mata ɗauki tunda suna son zamanta a gidan dole suyi mata abinda take so. Yaya Junaid ta kira cikin barci ya ɗauka yana tambayar lafiya ta kira shi da sassafe. Yaya gas ne babu ba a saka mini ba a tukunyar shine na yiwa Mujaheed magana wai sai dai inyi amfani da gawayi baida kuɗin sayan gas. To Najwa miye aibun gawayin naga anan gida ma da shi muke amfani. Haba haba yaya amarya ce ni fa taya daga zuwana sai gawayi, ya kamata kona shekara nayi amfani da gas. To shikenan bari anjima zan aiko yaron aikina ya amsa gas ɗin, zan bashi number ɗinki in yazo zai kira ki masa kwatance ya amsa ya ciko miki ya dawo da shi, dama inna tayi amfani dashi wancen auren naki da aka dawo dashi dan a cike yake, nace kar a aje ayi amfani dashi. To nagode yaya. Shikenan ko akwai bata damuwa.? Babu. To Najwa kita haƙuri ko ba komai ne rai yake samu ba. To tace masa sai suka yi sallama a lokacin har Mujaheed ya shigo da ruwan zafin a bokiti ya zauna ta gama wayar, tana ajewa kuwa ya kalleta rai a ɓace. Bazan lamunci kina tona asirin gidana ba, ai bance bazan siya ba kawai ki fara amfani da gawayi kafin na samu, shine har zaki kira gida domin aga gazawata dake. Kai kaso hakan ya faru amma banga dalilin daga zuwana gidanka na fara da gawayi ba sai kace amaryar tushe, wai ma ina akwatina daka ce sai nazo zaka nuna mini ko shima duk yana cikin ƙaryar daka yi mini. Yaushe kika zo gidan da kika ga kin jima ba a baki akwatin ba. Shuru tayi tana faɓe baki, Mujaheed yaja guntun tsaki ya miƙe ya shiga bayi yayi wanka da alwala kana ya fito itama ta shiga tayi nata. Wajen ƙarfe takwas da kwata aka aiko yara suka kawo musu abin kari kunun Tsamiya a katon jug sai kosai a ƙaramar kula, Najwa ta amsa ta aje har Mujaheed ya fito daga uwar ɗaka cikin shirin fita yana gyara zaman hular kansa ya zauna a cushing. Har an kawo abin kari kenan? Samo mana kofi ki zo mu karya. Najwa ta miƙe ta ɗauko kofi biyu ta aje tana zuba kunun taji wani baƙin ciki ya rufeta, sai da ta miƙa masa ya amsa kana ya buɗe ƙosan yana hamdala. Yauko zan yi kari mai nauyi zanji daɗin kunun nan. Aiko kai ne zaka sha dan banga dalilin da ina amarya za a tarbeni da kunu da ƙosai ba a abin kari, duk talauci da lalacewa ai na cancacni biredi da kayan tea ko ba kwai. Haba Najwa ki zama mai godiyar Allah wani ruwan koko ma nima yake bai samu ba, amma ke kin samu har da ƙosai da zafinsa kina kushewa, na kula kema kina da hangen nesa kuma ya kamata ki dawo da tunaninki daidai tunda tsakanin ni da ke mun san juna ba sauran ƙarya, haka muke rayuwa a gidan nan dai dai ƙarfina ba zaki zo ki sauya mini tsari ba. Dole kace haka mana tunda ka riga kaci moriyar ganga dama, ka gama yi mini ƙarya ka aureni, ai wlh banda darajar iyaye baka isa nayi zaman aure da kai ba domin nafi ƙarfinka. Murmushi Mujaheed yayi wannan karan bai tanka mata ba ya cigaba da karinsa ita kuma bini bini tana jan guntun tsaki, daya gama zai fita ta tareshi da. Ka bani kuɗi zan samawa kaina abinda zan ci. Idan ba zaki ci wannan ba ki zauna da yunwa cikinki ne. Ni dai bazan yi miki abinda banda halinsa ba. Ki saka hijab muje mu gaishe da mama idan kin gadama. Yauwa gwara daka ce inna ga dama dan maman ba ta kowa bace. Girgiza kai Mujaheed yayi tare da kwafa ya fice, ya kula Najwa tanada rashin kunya kuma dole ya seta mata hanya dan bazai ɗauki raini ba tunda Safara'u ba haka take masa ba, ya tsaya a ƙofar ɗaki har fito sanye da hijab yayi gaba ta bishi a baya, a nan falon mama suka tadda su gabaɗaya suka karya dan Safara'u komai take yi a dakin mama barci ke mayar da ita ɗakinta, suka zauna a tabarma da Mujaheed ya shimfiɗa daga gefe suka gaisa da mama ta amsa cikin fara'a tana tambayar Najwa kwanan baƙunta, tace lafiya lau kai a sunkuye kamar wata salaha, a nan ne Mujaheed yake cewa. Mama dama nace yau da safe sai muyi maganar rabon kwana tunda ga Safara'u ga ki, ina ganin in Najwa ta gama sati ɗayanta sai a fara rabon kwana biyu biyu ko wacce mai girki sai ta girka duk abincin gida. Baban Jamila ai tun yanzu amarya take fara girki tunda kwananta ne, ko ya kika ce mama. Cewar Safara'u cikin zaƙuwa, Mujaheed ya danƙara mata harara. Uban waye ya yace ki saka baki ina magana, bana son sakarci. Haba Jaheedi meye kuma haka ai gaskiya ta faɗa, amarya gobe In Sha zata amsa girki har sai ta cike kwanakinta kan Safara'u ta amsa. Dan Allah ina da magana. Najwa ta faɗa tana ɗago kai, Mujaheed da shima bai gamsu da maganar mama ba yace tayi maganarta. A gaskiya tun farko Mujaheed baka sanar dani kana da mata ba sai da aka kawo ni ne nasan da haka, kaga kuwa yanke mini hukuncin yin girki bai taso ba in dai za ayi mini adalci, tun farko ban zo gidan nan da tunanin yin girki da yawa ba balle rabon kwana amma tunda hakan yazo mini a ƙaddarata dole ne ya fita duk kan hakkinmu matsayinsa miji, dan haka rabon kwana bibbiyu yayi sai dai gaskiya bazan iya girki haka ba ko wacce ta girka abinda zata ci duk mai miji ta girka da miji in ba miji mace ta girka ita kaɗai. Yarinya baki isa ki tsara mana tsarinki ba, batun bakisan kina da kishiya ba wannan tsakaninki da Jaheedi ne ki sauke akansa, amma haɗa girki ba fashi dole ne duk mai girki ta girka duka gida sannan wacce ba tada girki itace keda alhakin sharan gida da wanke bayi da wanke wanke, mai girki girki kaɗai zata yi a ranarta sai in ta fita tayi sauran ayyuka kinji na gaya miki, wannan dokata ce dole a bi. Dokarki ce wannan ba dokar Allah ba kuma ni dokar mijina itace ya zama wajibi nabi domin shine ya aje ni ba zaman wani zanyi ba. Mujaheed kayi magana da mahaifiyarka duk dokarta ta tsaya akanka amma ni bazan bi dokarta ba domin ba haka musulunci ya tanadar ba hakkina a wuyarka yake. Lallai yarinyar nan ba kida kunya ni kike faɗawa haka. Mama ta faɗa tana nuna kanta, Safara'u kuwa tafɗi ta ce tana girgiza kai, Mujaheed ya sauke ajiyar zuciya. Mama kiyi hakuri zan fahimtar da ita Najwa muje ɗaki muyi magana. Wlh Mujaheed bazan iya duk abinda ta faɗa ba ina da bayi da kitchen a ɗaki z me zai haɗani da shara wanke bayi da wanke wanke, wannan ai zalunci da son rai ne. Ke Najwa ya isheki haka! mahaifiyata ba tsararki bace da zaki riƙa faɗar duk abinda yazo bakinki. Barta tayi mini rashin kunya, dama ba tada tarbiyya, kuma ki sani na amince da aurenki ne kawai domin ki zo ki riƙa gyaran gida kina wanke bayi da shara dan aikin Safara'u ba iya shi tayi ba domin ke kin fita waye da sanin duniya, idan kuma kin saka iskanci zaki wa aurenki domin wannan auren bazai je ko ina ba dan ba zamu iya ba. Wannan ya tabbatar da ni baki ɗauke ni a matsayin 'yarki ba kuma wlh ba zaki taɓa juyani ba domin ba ke nake aure ba, ashe ba don Allah kike son zama da shi ba saboda naki cikar burin ne ga 'yar aiki ya auro ko, to ban ga uban da ya isa ya tilasta ni akan haka ba, mama kin so kanki kin ji. Tasss Mujaheed ya kwaɗa mata mari Najwa ta dafe tana murmushin takaici. Ai dama tunda na tabbatar da kai matsiyaci ne to tabbas zan ga fiye da haka a gunka, kuma Allah ya isana. Tana gama faɗar haka ta miƙe fuuuuu ta bar ɗakin cike da tsananin takaici, babu abinda yafi ɓata mata rai sama da wai ya aureta ne domin ta zama musu 'yar aiki, yanzu ne ta gane tsagwaron rainin wayon da suke da shi, lallai bata jin wannan auren zai je ko ina, a fusace ta ɗauki wayarta ta kira Anty Saleema domin ita ce kaɗai zata iya seta mata hanya a yanzu, wayar ta kusa tsinkewa ta ɗaga Anty saleema ta ce. Mara mutunci to miye kike kirana kin gama watsa mini ƙasa a ido, gashi kin ƙi Alh. Atiku to Malam ya bashi 'yarsa zai aura 'yar uwargidanmu, kinga kinyi asara domin na samu labarin wanda kika aura matsiyaci ne yayi miki karya, halan har yanzu kina gida baki koma ɗakinki ba? Najwa fashewa da kuka tayi tana magana cikin kuka a haka ta bata labarin duk abinda ya faru yanzu da maganganun mamanshi, murmuahin takaici Saleema tayi. Yanzu wa gari ya waya, wanda ya buga sammako, ni me zan miki bayan kin ɓata komai da hannunki, na tabbatar da Alh. Atiku kika aura wlh sai ya mayar dake sarauniya amma ba kida rabo, dan ko kin fito babu abinda Alh. Atiku zai yi dake domin kuwa malam ya gama yin aiki akan 'yarsa kuma Atiku ya ruɗe akanta sai ɓarin kuɗi yake musu. Ni baƙin ciki kika yi mini amma baki mini ni kaɗai ba har da ke. Na shiga uku Anty ya zanyi dan Allah in kashe auren nan in dawo gunki, wlh zanyi miki biyayya nasan zaki samo mini miji mai kuɗi. Wa? wlh Najwa badai gidana ba malam ko mai kalarki ya gani sai ya hanata shiga gidanmu, dan haka ki zauna a inda ƙaddararki take dan kuwa baki zo duniya a sa'a ba. Najwa ta rushe da kuka tun ba aje ko ina ba taji ba zata jure zaman auren ba. Ba kuka zaki ba ki tashi ki nimawa kanki 'yanci dan yanzu an daina zama haka, ki tura mini kuɗi in kina da shi nasa ayi miki aikin mallaka yadda zaki juya mijin da uwarsa. To to anty kamar nawa zan turo? Dubu ɗari yayi dan aiki zan saka ayi miki mai kyau. Wlh banda su duka sai dai ƙila ki samu hamsin da wani abu. Ki turo su na cika miki badan halinki ba, yar banza ana nuna miki abu kina runtse ido, gashi ba aje ko ina ba kin gane kuranki. Nagode nagode anty sai kin jini. To zan tura miki account number ɗina in kin saka ki sanar dani. Da haka suka rabu, Saleema ta saki shewa tana dariya. Shegiya kuɗina da kika ɗauka sun dawo cikin ruwan sanyi har da riba, babu abinda zan yi miki halinki ya amshe ki a gidan, in kin kaso auren kya nima gidan zama ba dai nan ba. Tayi maganar a fili tana 'yar dariya sai ta fice ta cigaba da harkanta. Najwa kam bata san fitan Mujaheed ba dan shuru shuru har daga bisani taji hirarsu mama a tsakar gida hakan ya tabbatar mata da ya tafi aiki, dole dai wannan kunu da ƙosan ta karya da shi dan ba tada wani mafita. ***** Jamila. Tunda ta koma ƙauyensu rayuwa ta juya mata baya, ɗan daɗin da take samu a gidan aiki babu shi a nan, a hankali ta cinye duk kuɗin data koma da shi gida a ci banza ci wofi ya ƙare tas, daga bisani sai ta fara sace na mutane da zarar mutum yayi sakaci sai ta wafce, tun ba asan tana satar ba har abu yazo aka sani da an ganta ake kafa kafa dan karta yi barna, wannan dalilin yasa aka sanya mata suna Jamila asulluru, ganin an ganota yasa ta soma niman wacce take samar mata aiki a birni bata nan, data dawo matar tace ba zata tura ta ba taje ta riƙa yiwa mutane sata, a haka dai rayuwar Jamila ya zama sai addu'a ganin ba tada mashinshini dan wannan satan da take yi ya zame mata baƙin fenti, babanta ya bawa wani mahauci aurenta bisa dalilin biyan bashi daya yi da ita, dan mahaucin yana binsa bashi ya rasa yadda zai biya sai ya bashi auren Jamila. Tunda aka yi auren ta shiga cikin tashin hankali dan matansa biyu ita ce ta uku ga uban 'ya'ya, wahalar gidan ya gama nukurkusa ƙuruciyarta, kullun in ta zauna tana tuna baya sai ta yi kuka tare da tarin nadamar abinda ta aikatawa Sameeha, tana kuma tsinewa Najwa, wanda a kullun tana fatan su haɗu da Sameeha ta nima yafiyarta sai dai ba hanya, in ta zo Kaduna ma bata san a ina zata ganta ba tunda bata san gidan iyayenta ba, haka ta cigaba da rayuwa cikin ƙunci da rashin galihu, ta tabbatar alhakin mutane data zalunta kaɗai ba zai barta ta samu sauƙi ba, sai dai fatanta ta samu sauƙi a gurin Allah. Hauwa... *Afwan Samha ce ba lafiya shiyasa bana samun lokaci. Amma jikin da sauki Alhamdulillah* [7/7, 13:04] Buhainat😁: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shai wanidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.* 59. Hauwa. Tun lokacin bikin Aminu da Najwa ta tattara kuɗinta ta zuba a cikin sha'ani, tun daga suturar data ɗinki na fitar biki zuwa siyan kayan abinci wanda zata girkawa baƙinta, hakan yasa bayan biki ya zama ba ko sisi a hannunta Allah yasa suna da abimci a gida, to da 'yan kame kame suke samu suke dafa abinda zasu ci, duk da a lokacin bata bar alwashin lalata rayuwar Aminu ba kamar yadda ya wulaƙantata kuɗi kawai take jira ta samu, sai dai sunƙi samuwa tunda suna ta abinda zasu saka a bakin salati ne, ga Adama ta dawo gidan itama ba kuɗin take da shi ba, tunda dama a jikin mijinta take samu to yanzu ba auren har sun kwaso kaya, a hankali duniya tayi musu ɗaurin kazar kuku dan har bashi Hauwa ta soma ci ganin abincinsu ma ya tasarwa ƙarewa, ga su yaya Alhasan sosai suka ɗauki fushi da ita daga gaisuwarta basa sake yi mata magana, har kokenta takai gurin Sa'a akan ta yiwa Kamalu magana ya taimaka mata da wani abu tana so tafara sana'a, koda Sa'a ta sanar da shi shashantar da maganar yayi dan so yake sai ta gane kurenta akan duk irin tuggun da take aikatawa yana so ta gane Aminu yana da rana a gunta, jin shuru shuru ba aike yasa tazo Sa'a ta ce ta faɗa masa amma yace ta bashi lokaci, koda taje gun Laure cewa tayi ta rufa mata asiri ba zata jewa Alhasan da wannan maganar ba dan ko sunan Hauwa ta ambata hakan zai zame mata matsala, taimako ɗaya tayi mata ta bata dubu biya kyauta, kuɗin data bata yasa Hauwa farin ciki ta yi mata godiya ta dawo gida. To da wannan dubu biyun da kuɗin wayar kanin Adama data matsa dole ya sayar dubu goma sha biyu, shine suka ɗan saya kayan abinci sauran kuɗi dubu shida Hauwa ta yi cefanen waina ta soma sayarwa a ƙofar gida da safe. A hankali mutane suka fara ganewa da yake kan layi ne da kuma mutane sosai a anguwar, nan da nan sai Allah ya saka mata albarka har ta samu ta biya bashi sannan ta saka wani yaro kafinta ya buga mata runfar kwano a jikin gidanta da bancinan zaman mutane, daga gefe ta kafa tandar wainarta tana suya Adama tana rabawa mutane tana amsar kuɗi, cikin kwanaki Hauwa ta zama mai waina har daga nesan guri ake zuwa siya, ta soma tara 'yan kuɗinta suna cin mai kyau dan har kumari suka yi, sai dai wahalar aikin waina yanada yawa tun basu saba ba har abin ya soma bin jikinsu, daga waina loka ɗaya aka dawo yin biyu har zuwa biyar yanzu ma sun ƙara hannu suna yin loka bakwai kuma daga ƙarfe bakwan safe zuwa sha ɗayan rana ya ƙare. A wannan yanayin ne Mijinta ya dawo daga Lagos dan dama can yake ciraninsa yana sayar da kayan gwari, daga nan kuma mata su tattara 'yan kuɗin dan mazinaci ne na bugawa a jarida, shiyasa yake ɗaukar lokaci bai waiwayo gida ba, a wannan dawowar nasa da rashin lafiya ya sauka dan a can ciwon ya kama shi sosai duk kuɗinsa daya tara a magani ya ƙare, ganin in bai dawo gida ba zai iya yin mushe a can yasa shi roƙan abokansa suka saka shi a mota tare da biya masa kuɗin motan ya dawo Kaduna, Hauwa ta shiga tashin hankali sosai ganin mijinta a wannan yanayin dan tana matuƙar sonsa, dole 'yan kuɗin data tara dasu suka fara jinyarsa dan har kwanciya yayi a asibiti, wanda bincike ya tabbatar ciwon sida ya kwaso wato kanjamau, Allah ya taimako Hauwa ba tada shi dan bai goga mata, tunda ta gane cutar daya ke dashi kenan sai ta bara ja baya da lamarinsa ta nuna ta gaji dan ba zai yuwu tayi ta asarar kuɗi akansa ba, albarkacin yaransu kawai take dubawa yasa har take shiga lamarinsa, duk da haka dole tace a sallame su su nima na gida, da suka dawo ƙanin Adama shi ya cigaba da kula da shi ita kuma tana aikin waina, dan sai da suka yi kusan sati ba suyi ba, har an samu wata ta fara a unguwar, amma da yake kowa rabonsa yake samu bai hana Hauwa ta cigaba da yi ba, sai dai ya zama basa cinikin da saboda mutane sun fara tsegumin mijinta ya ɗauko misu ciwon sida, tun suna yi da yawa har suka koma yi loka biyu da kyar yake ƙarewa, wani lokacin ma sai dai su su cinye kayansu a abincin gida, Hauwa a wannan lokacin lamura sun fara haɗe mata sai ta zauna ɗaki taci kukanta ta gode wa Allah ba mai taimakonta dan duk 'yan uwansu sun zuba mata ido ne. Mijinta ya dawo da wata biyu Allah yayi masa rasuwa, bayan anyi zaman makoki aka watse sai Adama ta cigaba da suyar waina amma ba wani kasuwa, dalilin daya saka kenan suka daina wainar ta koma tana dafa shinkafa da wake dasu doya da miya tana kaiwa can bakin hanya gefen wani mai shago, a nan kuma ita Adama ta buɗe sabon nata rayuwar ta zama sakakkiya ba kamun kai, kowa nata ne duk wanda yace yana sonta koda ƙaramin yaro ne tana amince masa matuƙar zai riƙa sakar mata kuɗi, hakan yasa nan da nan rayuwarta ta soma sauyawa ta feƙe da rashin kunya, tana sayar da abinci tana haɗawa da rons da maza, nan da nan kuɗi suka zauna mata, Hauwa dai ta kasa yadda zata ɓullo mata domin ta nuna bata isa ta hanata rayuwar da take so ba, tunda ita ce ke ƙoƙarin ciyar da gidan, Hauwa sai dai ta zuba mata ido tana ta zaman takaba. Kwatsam wani mai napep ya fito yana son auren Adama, da farko taƙi amincewa amma daga bisani dole ta yarda dan ya sakar mata kuɗi, Hauwa ta ce bata amince ba ta bari ta fita takaba sai tayi auren, kuma itama tana son tayi auren dan karta jawo mata abin magana saboda duk abinda take aikatawa tana samun labari gurin yaranta maza, amma a yanzu dole ta haƙura da auren domin sana'ar da take yi shike riƙesu, Adama tace ita aurenta zata yi domin ta samu miji kuma kayan ɗakinta suna nan basu yi komai ba 'yan siyayya kaɗan zata ƙara, Hauwa ta ki amincewa duk da haka saboda ganin in tayi aure zasu shiga damuwa tunda bashi ke gareta ba, Adama ganin zata kawo mata cikas taje har babban gida ta haɗa Hauwa dasu yaya Alhasan, su ka zo suka samu Hauwa suka yi mata tas akan lallai dole ta barta tayi aure tunda ta fita idda, da kuma ta ɗauko musu magana dan sarai suna da labarin rayuwar da take yi gurin sayar da abincin gwara tayi auren, ba da son ran Hauwa ba Adama tayi aure ba, wanda sati biyu kenan da aurenta ta tare juma'ar data gabata, sai dai itama Adama zuwa yau tana dana sanin auren tunda abinda Isyaku ya nuna mata a waje to ba haka bane acikin gidan, babban family House ya kaita sannan yana da mata da yara shida, ga sauran matan ƙannensa duk a gidan da kuma uwarsa, ɗaki ciki ɗaya ya sauketa wanda gado ne kaɗai ya ɗauka da tarkacen kayan kitchen, kujerunta sai dai aka mayar dasu gida, kwananta ɗaya a gidan ta fara shiga damuwa dan hayaniyar gidan kaɗai bazai barta ta samu barcin rana ba da take tunanin in tayi aure zata huta, dan bata saba da wahala ba a gidan mijinta na farko, a hankali ta gane ta tsoma ƙafarta a gidan rikici dan tunda tazo gidan kullun sai an yi rikici a tsakanin kishin saurinta, idan kuma a ka fara sai a ɓata lokaci mai yawa ana abu ɗaya. Jiya da dare ma hakan ta faru akan shiga bayi suka kafa dambe basu suka samu yin barci ba sai kusan ɗayan dare, Adama ta sanar da Isyaku ya sauya mata gida ita ba zata iya da wannan hayaniyar ba, kallonta yayi yana 'yar dariya. Haba Adama ai ya kamata ki saba da hayaniya, tunda kin yi zaman bakin titi hayaniyar mota mashin da mutane duk kin sanshi, kinga kuma hayaniyar gidan nan da bambanci da wancan tunda ba kullun ake rikicin ba kuma naɗan wani lokaci ne. Wlh ban taso a gida irin wannan ba ba zan iya ba gaskiya. A hankali zaki saba, dan bani da halin kama miki haya nan ne iya ƙarfina. Hmmmm wlh da sake. Ta faɗa tana girgiza kai dan ga dukkan alamu wannan auren nata bazai je ko ina ba, shiyasa kamar ta sani ta tsiri yin planning dan bata yarda ta samu ciki da wuri ba sai ta ga kamun ludayin auren, bata yarda tayi ta raba yara ba hakan yasa ta ɗan samu natsuwa da tunanin fara shirin fita daga gidan. Yau juma'a kamar yadda ta roƙi mijinta zata gida, bai hanata ba dan ba ita ke da girki ba, da wuri ta shirya ta bar gidan dan gabaɗaya ji tayi ta gundura da komai na gidan, wajen sha ɗaya ta nufi gida sai dai ko da ta isa ta tadda Hauwa bata nan ta fita niman musu abinci dan zama bai ganta ba tunda Adama tayi aure, kuma musulunci ya yarda mace ta fita ta nima abinci matsawar ba tada mai taimaka mata in tana takaba, hakan yasa Adama ta zauna zaman jiran dawowarta dan tazo ne suyi shawara akan maganar kashe aurenta da take son yi. Hauwa kuwa rafin guza ta nufa taje wani gidan mai kuɗi da yake bayar da taimako, labarinsa ta samu shine tayi takanas taje dan ta samu rabonta, sai dai ta taki sa'a baya gari, dole ta kuma hawa napep da nufin dawowa gida, har sun wuce layin su Sameeha ta tuna wani abu sai ta sa mai napep ya sauketa ta biyashi ta wuce zuwa gidan, tana isa ta kutsa ciki tana sallama sai dai daga ciki aka amsa mata sai ta shiga falon ta tadda umma tana kishingiɗa a doguwar kujera, umma tana ganinta ta tashi ta zauna tana yi mata maraba fuska cike da fara'a, Hauwa ta zauna ta gaisheta kana ta ɗaura da cewa. Na zo wani dubiya ne can sama shine nace bari ba biyo mu gaisa sannan naga yarana na wajen Aminu dan ance suna nan. Aiko suna nan amma suna makaranta driver taje ɗaukosu. Ya kwana biya da yaran. Lafiya lau Alhamdulillahi, nasan baku san mijina ya rasu ba ko, yanzu haka ina cikin takaba dole ce tasa na fito. Allah sarki wlh bamu sani ba Allah ya jikansa da Rahma ya bada haƙurin rashi, na tausaya miki dan rashin miji ba daɗi saboda nima na san shi. Hakane gashi ya tafi ya barmu cikin yanayin rayuwa abubuwa sun sauya komai ya tsaya mana, dan Adama ce ke nima mana ta yi aure sati ɗaya kenan da tarewarta. Allah sarki sai haƙuri da rayuwarki kam, Allah ya sanya alkhairi ya rufa mana asiri duniya da lahira. Ameen ya rabbi, dama nace a faɗawa Sameeha in lokacin Zakka yayi a sakamu a cikin list dan nima yanzu na shiga jerin masu marayu, kuma dama Aminu ne mai taimakon to shima yayi fushi dani dan rabona da shi tun washe garin bikinsa ko gaisuwar mijina bai kira ko yazo ya mini ba. Kai Amma lamarin bai yi daɗi ba, ai ba a fushi da ɗan uwa, In Sha Allah zan yi masa magana dan yana kira yayi magana da yaransa, kiyi haƙuri In Sha Allah komai zai wuce. Bari a kawo miki abinci. A'a wlh ki barshi tafiya zanyi dan na baro yara a gida har ɗan Adama data bar mini yana hannu na. To yanzu abinda za ayi ki fita ki samo me napep ku zo tare zai ki tafi da wasu abinci, kiyi haƙuri yaran duk basa gida balle su taro shi. Haba wlh ba komai bari nayi sauri na samo. Hauwa ta faɗa cikin sauri da farin ciki, ta fita umma ta bita da kallon tausayi gabaɗaya Hauwa tayi laushi ta sauya, ga wani baƙin wahala da rama data yi, wato idan mutum yace shi mara mutunci ne to duniya kaɗai sai ta koya masa hankali. Hauwa bata jima ba ta dawo ta samu umma tana fito da kayan abincin data bata, da yake ɗakin kusa da kitchen shine suka mayar store sannan an gyara mata kitchen ɗin anyi cabinet da komai na zamani dan hatta falon umma Sameeha sun sauya mata shi da kayan zamani, kuma bata amfani da gawayi yanzu sai gas cooker, umma ta bata rabin buhun shinkafa, katom ɗin taliya sai makaroni guda takwas, da sugar loka biyu, indimie guda goma, madara rabin loka, maggi jaka da gishiri, har da garin tuwo umma ta ɗibar mata, haka ta haɗa mata kaya sha tara na arziki sannan ta ƙirga dubu ashirin ta bata na nefane, Hauwa har tsugunawa ta yiwa umma a ƙasa tana zuba mata godiya har da kukanta, umma ta kamata ta ɗaga tana cewa. Haba Hauwa ai zumunci yafi ƙarfin komai, duk da Sameeha bata gidan ɗan uwanku amma yara sun haɗa mu, dan duk abu na taimako in dai muna da hali za muyi muku Allah dai ya jikansa da Rahma, In Sha Allah kafin azumi zaki ga aike ko Zaidu yazo ko kuma Anwar zasu zo har gida. Nagode Nagode dan Allah ku yafe mini abubuwan dana aikata muku a baya, wlh sai yanzu nake jin kunyar komai ashe kune waɗanda zasu ji ƙaina tun ba aje ko ina ba, 'yan uwana ido suka zuba mini amma gashi ke kin yi mini taimakon da ban taɓa zato ba. Mu ai tuni muka yafe komai ya wuce, dan haka ki saki ranka damu wlh babu wani abu, ki yi maza ki tafi kin bar yara. Hauwa tace to tana ƙara cigaba da godiya ta share hawaye da gefen hijab ɗinta, sai ta fita ta yiwa mai napep magana ya shigo ya tayata kwashe kayan suka saka a napep ɗin, data gama ta kuma yiwa umma sallama kana ta fito suka wuce, haka Hauwa ta nufi gida da wannan kaya da ko a mafarki bata yi zaton samunsu ba, lokaci zuwa lokaci take share hawayenta wanda yake ƙunshe da tarin dana sani, Hauwa bata taɓa karaya da abinda ta aikatawa Sameeha ba irin yau, sai dai kuma takara kullatan Aminu a ranta dan in da ya yafe mata ya taimaketa ba zata zo ta yi abin kunya ba a gidan su Sameeha, dan Abin da Ciwo ace naka shi ke bada kai, haka ta isa gida mai napep ya sauke mata kaya ta sallameshi da dubu ɗaya ya wuce, sai ta leƙa gida ta kwalawa yaronta kira ya fito, yana ganin kaya jiki yana rawa ya kinkimi shinkafa yayi cikin gidan, Adama ganin haka yasa ta fito itama ta tayasu kwashe kayan suka shiga gida, Hauwa ta zauna a barandar ɗakinta ko shimfiɗa babu ta cire hijab tana fiffita da shi, Adama ta kalleta tana cewa. Mamaa ina kika samo waɗannan kaya goma ta arziki. Yau dai cire kunya nayi na yi roko kuma ya yi mini amfani, tunda ga kayan abinci na samo har da kuɗi dubu ashirin. Ikon Allah ina kika je aka baki mama a irin wannan marra da muke ciki yadda rayuwa tayi tsada, amma ko ba ƙaramin masu arziki bane kuwa. Gidan su Sameeha naje Ummansu ta haɗoni da alkhairi, kuma na dinga samu kenan dan tace zata yi mini aike. Kai mama yanzu can kika je kika zubar mana da ƙimarmu, haba haba wani irin gidansu Sameeha, haka kurum kisa suyi mana dariya, gaskiya banji daɗi ba wlh ko kaɗan. Dan ubanki idan banje can ɗin ba ƙasa kike so mu fara ci, ina ce nan na roƙeki Allah ki haƙura da auren nan na fita takaba sai kiyi saboda abincin da kike sayarwa shike riƙe mu amma kika ce atafau ke sai kinyi, dan haka tunda ke kin kasa taimakona naje inda suke da imani da taimako domin Allah ba dan halin mutum ba, kuma sannan Sameeha ɗan siyasa take aure ko ba komai munci rabonmu na gomnati, kuma bamu gama ci bama dan wlh naga gurin zuwa tunda kowa ya juya mini baya babu mai tausayina a dangi. Amma mama ni banji daɗi ba da kika je gurin maƙiyanmu niman taimako, ai dariya sun riga da sunyi mana, dan Allah karki ƙara zuwa. Ni ba maƙiyana bane in ma su ɗin ne na mayar dasu masoya dan babu wanda zai iya maka irin wannan ɗawainiyar ka ƙi shi, dan haka wlh sun fi mini Aminu da nake ciki guda da shi yayi mini cin mutunci ya wulaƙantani a bainan nasi, shine mai ƙumbar susan cikinmu amma yanzu kuɗinsa ba mai ci, dan haka ta ƙarfi dole su Sameeha su zama masoyana, domin in ci rabona a jikinsu wanda Allah ya tsaga zan samu. Hmmmm ke dai mama abin duniya nan da nan yake sauya mini tunani, amma wlh Abin da kunya ba kaɗan ba, ni ai bazan iya wannan sauke kan ba a gunsu duk kuwa da matsatsin da zan shiga. Ke kika ni kuma nice Hauwa akan kuɗi zan iya sauke kaina na same su. Kuma maganar ki ta ishe ni zoki kama hanya ki bar mini gida. Mamaa kenan, ni da nake shirin dawowa gidan gabaɗaya ma, dan wlh ba zan iya da auren Isyaku ba, ashe duk facakan kuɗin da yake mini ƙarya ne, bama wannan ke damuna ba gidan nan sai kace gidan bariki kullun faɗa kamar gidan 'yan dambe, hayaniyarsu sai ta haifar mini da hawan jini wlh bazan iya ba. Aiko baki isa ba Adama kinyi kaɗan ki kaso aurenki ki zo mini nan, yadda baki ji tausayina ba akan karki yi auren nan nima bazan raga miki akan ki dawo min gida ba, tunda kika zaɓi Isyaku a kaina na riga na sallamaki, dan haka ki sake tunani ba dai gidan nan ba. Mamaa ya kike so inyi? kin san banda inda yafi nan, ni dai na zo ne dama na faɗa miki dan kar kiga kwatsam na dawo. Adama tashi ki bar gidan nan tun kan inci uwarki da ubanki, kuma wlh yanzu zan kira Alhasan yazo na faɗa masa, kin san halinsu dai ki kuskura ki kaso aurenki wlh sai kin gwamace baki fito ba. Allah sai dai ayi mini duk abinda za a min, amma banga gidan zama ba nan ne zan dawo. Adama ta faɗa cikin ƙunƙuni ta gyara zaman mayafinta. Ni na tafi babban gida kafin ku ɗaura sanwa na dawo naci. Da ashar Hauwa ta bita Adama ta fice tana 'yar dariya dan tasan halin Hauwa dama dole su kwashi 'yan kallo, amma a hankali zata shawo kanta sai dai in bata nuna mata kuɗi ba. Hauwa kuwa miƙewa tayi tana gyara zani. Zaki dawo ki sameni 'yar banza, ka haifi ɗa ya riƙa juyaka, to baki isa ba kuwa, yara ba tausayi ba jin ƙan iyaye kamar waɗanda aka tsine mawa. Ta ƙare maganar tana ƙofa ta shige ɗaki. Da dare. Umma tasa Zaidu ya riƙa Aminu suka yi magana har ta kawo masa maganar Hauwa tana cewa. Ashe mijinta ya rasu baka sanar damu ba Aminu? yanzu haka Allah yace a kula da zumunci, ya kamata ka zama mai yafiya kaima sai Allah ya jiƙanka, bai dace in abu ya faru ba a riƙe shi a rai dole ana mance baya a fuskanci gaba domin gaba tafi baya yawa, kuma hannunka baya riɓewa ka yanke ka yar, naka naka ne duk lalacewarsa, domin jini ba wasa bane dan yafi ruwa kauri, ka daure ka kirata a waya kayi mata ta'aziyar mijinta dan ɗazun nan nasa Sameeha ta kiratq tayi mata gaisuwa dan ta tabbatar mini da zata kira, dan haka komai ya wuce domin nan gaba baka san inda rayuwa zai kai ka ba. In Sha Allah umma zan gyara kuma zan kirata na yi mata gaisuwa. Yauwa, kuma ɗan taimakon daka saba yi ka yi mata dan tana cikin buƙata sosai. To In s'Sha Allah umma. Yauwa Allah yayi albarka. Ya amsa da amin kana suka yi sallama, Zaidu ya amsa suka cigaba da magana daga bisani suka aje wayar Zaidu yana duban umma da cewa. Umma da alama Aminu da zai samu lafiya dan yanzu haka yabar London yana ƙasar Germany an haɗashi da wani sabon likita, kuma yace Alhamdulillahi ya fara jin sauyi a jikinsa. Shine yace in faɗa miki mu saka shi a addu'a. Kai Alhamdulillahi Masha Allah, Allah ya tabbatar da lafiyarsa, naji daɗin wannan labari. Wlh nima Umma naji masa daɗi sosai, ace mutum har mutum ba lafiya irin wannan ai ba rayuwa, dan matacce ne shi a raye. Hmmm ga dai shi nan rabo ya rabasu da Sameeha, amma banda haka ko shekara gashi ba ai da rabuwarsu ba amma kaga lafiyarsa tana niman samuwa. Ƙaddara ce mai zafi ya rabasu umma nima abinda nake faɗa kenan kullun in na tuna gwagwar mayar da aka sha, gadai Sameeha da Ibrahim tamkar ma shine ta fara aure yadda suke mugun ƙaunar junansu, abinda wasu basa ganewa kenan sai suga in aurensu ya mutum kamar shine ƙarshen rayuwarsu, kuma wata daga nan ne rayuwar ke buɗe mata sabuwa, sai tayi rayuwar farin ciki a gidan mijinta na biyu wanda bata samu kamarsa ba a gidan mijin ta farko ba, kamar dai yadda Sameeharmu ta samu. Wlh fa rayuwar kenan duk mai haƙuri shike fa riba, Allah kuma ya rabamu da mummunar ƙaddara ya bamu ikon cin jarabawar rayuwa. Zaidu ya amsa da amin sai suka cigaba da tattauna maganar bikinsa wanda ake ƙoƙarin tsaida rana. [7/7, 13:04] Buhainat😁: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shai wanidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.* 60. Aminu tunda ya gama waya da umma ya zauna ya ƙara zurfafa tunaninsa nan ya tabbatar da bai kyauta ba tunda duk abinda Hauwa tayi masa mutuwa ta wuce wasa, kuma koda su yaya Alhasan suka sanar masa a cikinsu baba wanda yace masa ya yiwa Hauwa gaisuwa, saboda suma sun san ta yi masa laifi shiyasa basu takurashi ba sun san komin daɗewa zai sauko. Da tunanin abin ya yi barci wanda daya farka lokacin mu nan garinmu ya waye shi kuma can lokacin ake yamma dan haka ya kira Hauwa, koda taga kiran kamar a mafarki ta ɗauka data ga da gaske ne sai ta ɗaga kiran da sallama, sai da Aminu yayi jim kafin ya amsa sallamar suka gaisa kana yayi mata gaisuwa mijinta, ta amsa tana tambayarsa aiki yace Alhamdulillahi kana suka yi sallama ya kace wayar, nan take ya tura mata dubu hamsin Hauwa saboda murna har da dan shewa tana cewa. Ikon Allah wato dai Umma ta yi masa magana kenan, sun dai rabamu da shi sun janyeshi, duk da sun rabu da Sameeha amma dai ba zasu bar shi ba, Allah ya wadaran naka ya lalace. Ta faɗa tana taɓe baki, sai ta yi ƙoƙarin kiransa tayi masa godiya amma bai shiga ba saboda ya saka number ɗinta a in da ko ta kira ba zai shiga ba sai shine yake da damar kira. Ta dangwarar da wayar ta soma tunanin wani hanya zata bi domin fa ba zata fasa abinda nayi niyya ba, tunda ga kuɗi sun samu dole ne ta zagara gurin malam ta bashi yayi mata aiki akan Aminu ya lalace dukiyarsa ma ta ƙare ya dawo baida komai, ta tabbatar in ya talauce to baida wani izza ko ƙarfin sake yiwa wani ɗan Adam rashin mutunci bama ita ba, dan haka miƙewa tayi ta saka hijab ta ɗauki kuɗinta dubu sha biyar da ATM ɗinta dan ta tsaya a hanya ta cire kuɗin ta kaiwa malam dubu hamain ɗin dan da kuɗinsa ma zata yi masa maganin, inya so kudin da umma ta bata zata biya kasuwar gari ta saro kayan moya ta fara sayarwa a ƙofar gida, haka ta fice ta samu napep ta hau ya wuce da ita unguwar kanawa dan fara isa gurin malam, tama mance takaba take yi saboda mugun abu ya tsaya a ranta, mai napep ya zo daidai Junction ɗin NDA zai hau kan babban hanya bai kula da wata motar Bus ba sai ya faɗa hanya motar kuwa ta angajesu suka daɗi, wanda wani ƙarfe ya danne ƙafar Hauwa, ihu ta saki a gigice nan take kuma ta suma, Hauwa bata san a inda kanta yake ba sai farkawa tayi ta ganta a gadon asibitin yara dake nan kusa da NDA, koda ta farka taga ƙafarta ta dama suntum sai wani uban zafi da yake ratsata har kwakwalwa, hawaye wani yana bin wani wata nurse ta zo tana cewa. Sannu ko Allah ya ƙara sauƙi, yanzu zaki bada number a kira 'yan uwanki domin su zo su ɗauke ki saboda kin samu karaya wata ƙila ɗaurin gida za a yi miki. Hauwa ta gyaɗa kai tana cewa a hankali. Fos ɗina tana ina? wayata tana ciki. Gaskiya koda aka kawo ki babu fos da aka bamu, domin mai napep mun sallameshi da yake ƙujewa kawai yayi, mai motar daya bigeku kuma ya bada kuɗi an duba ku ko kafin mu an kara ya sulale ya gudu. Na shiga uku na lalace wlh wayata da kuɗi dubu sha biyar suna cikin jakar ga ATM ɗina. Allah ya kyauta na gaba amma mutane yanzu ba gaskiya, yanzu dai ki tuna ko kin haddace number da za a kira wani naki. Sai dai na bada adireshin da za a je a kira su. Anan unguwar dosa nake layin jatau babban gida, duk wanda aka tambaya babban gida zai kaiku, sai ya sanar da duk wanda ya samu a gidan yace Hauwa ce tayi accident. Nurse ɗin tace to kana ta wuce suka aika wani mai sharar gurin da kufin mota ya tafi, kuma anyi sa'a duk su Alhasan suna gida dan a ƙofar gidan mutumin ya same su nan ya isar da sakon Hauwa, cike da damuwa suka shirya tafiya sai Kamalu ya fito da motarsa suka ɗauki mutumin zuwa asibiti. A takaice sune suka ɗauko Hauwa zuwa gidanta suka kira mai ɗauri yayi mata ɗaurin gida sannan suka biya kuɗin komai, Hauwa banda kukan azaba da baƙin ciki ba abinda take yi wato rijiya da bada ruwa amma guga ta hana, ƙiri ƙiri damar da ta samu kenan da zata nuna wa Aminu kurensa amma gashi ta nakasa wanda ta tabbatar da sai tayi zaman jinyar kusan watanni a zaune, hawaye ya cigaba da bin kuncinta tana jin baƙin ciki mai tsanani. Koda ta aika yaronta banki kan kuɗinta sun tadda an yashe dubu hamain ɗin, Hauwa ba ƙaramin takaici ta shiga ba haka dole ta cigaba da jinya Allah yasa suna da Abinci, Baba Saude ita su Alhasan suka yiwa magana ta zauna jinyar Hauwa, Adama kuwa kusan sai dai tazo ta dubu ta ta koma, dan sosai Isyaku ya nuna yanzu ne ya samu jin daɗin aure, kuma ba zai saketa ba aurensu tamkar na zobe ne, Alhasan sune suka cigaba da taimaka musu da kuɗin cefane, da suka sanar da Aminu ya tura musu kuɗi mai coka akan su kula da Hauwa sosai musamman cin nama domin a samu ƙafar ta warke da wuri, duk da sun sanar da Hauwa ba wani farin ciki tayi ba dan a sanadinsa ne ta samu kanta a haka, dan gabaɗaya shi ta ɗaurawa alhakin hakan. ***** NAJWA. Tunda ranar da ta yiwa mama rashin kunya Mujaheed ya fita sabgarta dan sati gudan nan sai da yayi mata na amarci, amma fa ko magana basa yi, ita Najwa ta dau zafi shi kuma yana son ya nuna mata bata isa ba, batun abinci kuwa sai dai ta riƙa dafawa kanta a ɗaki dan Junaid ya siya mata gas ɗin, cefane kuma sai dai ta yiwa kanta da kuɗinta, sai ta sa hijab ta fita ta siya duk abinda take so ba tare data tambaye shi izini ba mama da Safara'u kuwa nasu ido dan gabaɗaya ba mai shiga harkarta, a hakane ta samu ta turawa Anty Saleema kuɗi dubu arba'in da biyar dan bata samu tura hamsin ɗin ba saboda kashe kuɗin da ta yi a satin, dan abincin mai kyau fa take ci har da kifi da nama duk ta saya, data sanar da Saleema ta aika mata kuɗi tace ta gansu amma fa kuɗinta data kwashe mata ta gudu dasu to sune ta tura mata harda riba kuma babu taimakon da zata iya mata taa san yadda zata kwaci kanta a gidan mijin dan ba ruwanta, Najwa zata yi magana ta kashe wayarta sosai lamarin ya daki zuciyarta dan bata taɓa kayo zata yaudareta haka ba, har kukan baƙin cikin abin sai da tayi ga kuma damuwar Mujaheed ya daina kwana a ɗakinta, dan tunda Safara'u ta amsa girki bai sake waiwayenta ba, wani sa'ilin sai dai taji muryarsa a tsakar gida dan ko leƙowa ya dubata baya yi, duk da shima dauriya yake yi amma dole ya nuna mata shi na mijine, kuma umarnin mama yake bi dan ita ce ta tsara masa haka. A hankali Najwa ta kwashi wata a gudan da sati kuma a wannan ƙuncin kaɗaici, duk yadda ta ɗauka lamarin zai yi sauƙi amma ƙara gaba yake yi, ga kuɗin hannunta sun ƙare ya zamana sai dai ta dafa farar shinkafa taci da mai da yaji, data kira yaya Junaid ta sanar masa cewa yayi tayi haƙuri da abinda mijinta ke da shi, dan ba kai tsaye ta fito ta faɗa masa zaman doya da manjan da suke yi ba, sai ya ce zai tura mata katin ɗari biyar ta saka data, daga haka ya kashe wayar Najwa taji hawaye ya cika mata ido, jin kuɗin ya shigo yasa ta kira Inna koda ta ɗauka suka gaisa sai ta fashe da kuka. Inna ba zan iya zaman gidan nan ba dan Allah koda Mujaheed ya sake ni ki sa baki baba ya barni na zauna a gida. Wlh Najwa karki fara dan hatta ni ba zaki samu sauƙi a guri na ba, haƙuri za kiyi da duk yadda kika samu kanki. Wai ma meya faru da kike niman ɗaga mini hankali. Inna baya mini magana ya daina kwana a ɗakina tun sati ɗaya dana yi a gidan, rabon dana saka shi a ido har na manta, sun mayar dani saniyar ware hatta mahaifiyarsa ba mai shiga hurumina. Haba Najwa da abinda kika aika, na tabbatar ba zasu yi miki haka kurum ba, idan ma laifi kika yi musu ki basu haƙuri ki zauna a ɗakinki Najwa, yanzu fisabilillah ke kullun burinki ki baƙanta mana rai, tunda muka aured dake bamu samu kwanciyar hankali ba kullun maganar mu da fatanmu ki zauna a gidanki. Inna girki suka ce dole sai mun haɗa na gidan, sannan har da shara da wanke bayin waje bayan ni ina da komai a ɗaki, dan nace ban yarda ba shine suka yi mini haka. Hmmmm Najwa kenan, meye aibun ayyukan bayan duk kin saba yinsu a gida, in dai wannan ne hakanan zaki yi haƙuri kiyi yadda suke so a zauna lafiya, na tabbatar idan kinyi haƙuri watarana zai zama tarihi. Najwa kasa magana tayi sai kuka mai sauti, Inna data kasa jure kukanta saita kashe wayar cike da tsantsar damuwa, itama sam bata ji daɗin hukuncin da suka yanke mata ba ganin ita akwai komai a ɗakinta, amma tasan in dai da Mahaifiyarsa suke zaune dole ne ta bijiro da abinda yafi haka ma, dan iyayen miji wasu akwai iko da nuna isa wanda in da akan 'ya'yansu ne mata ba zasu zo uwar mijinsu ta takura su haka ba, ƙiri ƙiri suke nuna bambanci da nasu 'ya'yan, tamkar su matan da aka auro musu kamar ba 'ya'yan wasu bane, taja guntun tsaki tana cewa. Allah ya kyauta ya rabamu da son zuciya irin na wasu iyayen mijin. Sai ta miƙe ta cigaba da aikinta amma damuwar Najwa yana maƙale a zuciyarta. Najwa kuwa kwanciya tayi a doguwar kujera tana matsar kwalla daha haka kuma sai zazzaɓi ya rufeta dama tun safe data tashi tq ji jikinta ba daɗi, sauran shinkafar jiya ta ɗumama ta karya dashi wanda taji kamar zuciyarta tana tashi bata iya cinyewa ba tasha ruwan lipton ta aje sauran. Tana nan kwance har zuwa la'asar wanda barci ne ma ya ɗauketa, kamar a mafarki taji wani abu ya tokare mata numfashi da sauri ta tashi sai kuma ta fara kakarin amai ta zura hannunta a baki sai aman ya biyo baya, nan ta dinga yinsa kamar zata amayar da hanjin cikinta. Mama dake zaune a tsakar gida tunda taji aman ta miƙe ta leƙa ɗakin Safara'u. Ke zoki duba yarinyar nan kamar amai fa take yi. Wa? wai Najwa? Ina jin ta, wlh bazan duba ba Mama tunda ba tada mutunci. Amma ai rashin lafiya ya kori komai. Ni fa bazan dubata ba kar ma naje ta zageni kinsan ta ba mutunci ne da ita ba. Mama bata ce komai ba ta juya ta koma mazauninta sai ta ɗauki wayarta ta duba numbern Mujaheed ta kira shi, koda ya ɗauka ta sanar da shi aman da Najwa take yi, tace in yana kusa yazo ya dubata dan bata so ta shiga tayi mata rashin kunya, Mujaheed ji yayi kamar ta saka shi a aljanna dan dama dauriya kawai yake yi daya share Najwa, dan sosai yake jin sonta, ga kuma zumanta daya lasa sau ɗaya bai kuma ɗanɗana wa ba, kuma a yadda yaji Najwa tafi Safara'u sosai dan ɗanɗanonta daban ne, dan haka cikin sauri ya kashe wayar mama ya shiga cikin gida ya sanarwa Hajiya matarsa ba lafiya sai ta sallame shi ya wuce. Mujaheed yana shigowa gidan ɗakin ya nufa dan ko tsayawa yayi magana da mama bai yi ba, ya samu tana kwashe aman da tsumman ɗankwalinta, Najwa duk da ta san da shigowarsa amma ta basar ta cigaba da abinda take yi har ta gama ta shiga bayi ta wanke hannu ta fito suka haɗa ido, sai kawai ta ɗaure fuska ta samu guri ta zauna, yadda ta ɗan rame tayi haske yasa Mujaheed yaji tausayinta ya taso ya zauna a inda take ya kamo hannunta. Najwa meke damunki gabaɗaya kin sauya? Ban sani ba, dan Allah ka fita daga ɗakin nan bana son ganinka tunda na zama abin wulaƙanci daga ina nimawa kaina 'yanci. Kiyi haƙuri amma kema kin san baki kyauta ba mahaifiyata fa kika yi wa rashin kunya, ke in aka yiwa taki haka zaki ji daɗi. Yanzu tashi za ki muje asibiti dan na kula ba kida lafiya. Babu ruwan ka da rashin lafiyata, dama jikina kake so tunda ka samu biyan buƙata na zama abin wulaƙanci. Najwaa ki daina faɗar haka dan kaza tana tsakurar 'ya'yanta badan bata son su bane, nayi miki hakane domin ki gane baki kyauta ba. Kiyi haƙuri . Hawaye ne ya soma bin kuncinta, ganin haka shi kuma ya jawota ya rungume, daga haka ya cigaba da lallashinta dama kamar tana niman inda zata yi kuka, sai ta fashe da kuka mai sauti, kuma hakan ya taɓa zuciyarsa sosai da kyar ya samu tayi shuru ya lallaɓata suka tafi asibiti. Koda suka je gwajin farko ya tabbatar Najwa tana da shigar ciki, duk da Mujaheed baya son haihuwa amma kuma yayi farin ciki jin Najwa tana da juna biyunsa, wanda ya tabbatar hakan ƙila yasa ta sauko daga fushinta, kuma hakane dan itama ta yi murna jin nan da wata tara zata ganta da 'ya ko ɗa, haka suka dawo gida bayan ya siya mata magunguna da kayan ciye ciye. Mama koda ta samu labari itama tayi murna dan tana mugun son ganin jikokinta sun cika gida, wannan dalilin na samun cikin Najwa yasa ya kawo shiri a tsakanin Najwa da mama da kuma Mujaheed, duk da mama tace girka fa dole su haɗa amma batun wanke bayi da sharar tsakar gida ta ɗaga mata ƙafa har ta haihu, Najwa hakan bawai yayi mata bane amma dole ta haƙura dan taga in ta cigaba da ja dasu itace zata shiga ƙunci, sannan bata ga alamar zata bar gidan nan kusa ba sannan yanzu kodan abin da ke cikinta zara haƙura har ta haihu, ƙila zuwa lokacin su baba ko auren ya mutu ba zasu koreta ba. ***"* Bayan wata bakwai. Ikram ta haihu ɗa namiji yaci sunan baban Shamsu suna kiransa da Waziri ko suce baba ƙarami, ansha shagalin suna ba a magana dan a gidan Hajiya tayi jego ta hana ta koma gida. Bata yi arba'in ba Sameeha itama ta haihu 'ya mace nan Kaduna ta dawo aka yi komai yarinya taci sunan Hajiyarsu Ibrahim, faɗar shagali da irin kuɗin da aka kashe ba'a magana. A lokacin kuma matar Zaidu tana da ciki wata uku, dan wata biyar baya aka yi bikinsa gidan da Ibrahim ya bashi yana unguwar rimi katon gida da mota ya bashi, zuwa wannan watannin Zaidu ya zama alhajin kansa dan Ibrahim ya samar masa aiki a bankin CBN branch ɗinsu dake nan Abuja, duk weekend yake dawowa gurin matarsa. Najwa ta kasa zuwa bikin balle taga kayan baƙin ciki, dan har kuka sai da tayi jin zai yi aure ga kuma tarin arzikin da ya samu tayi dana sani da kaicon rabuwa da shi, sunan Ikram be bata je ba sai a sunan Sameeha ce inna ta matsa mata wanda har sai da ta nuna ranta ya ɓaci yasa ta shirya ta tafi da cikinta daya tsufa dan yana wata bakwai a lokacin, koda taje haka ta dinga raɓe raɓe su kuma sam basu nuna mata komai ba, anan taga yadda ake shagalin masu arziki da yadda arziki yake, haka ta dinga ɗari ɗari ta kasa sakin jiki Ikram kuwa sai janta take tana sakata cikin hidimar, dan walima aka yi kayatacce an raba abubuwa da yawa ciki harda kujerar umara ga wasu daga cikin dangi, inna ma ta samu da inna Rukayya ƙanwar umma da kuma wan babansu Sameeha, da sauran dangi daga cikin na su Ibrahim, sannan an raba atamfofi jakuna da kayan arziki, Najwa sai da ta kwana dan Sameeha ta hana ta tafi, ita dai ido take binsu da shi dan gani take ya kamar da gayya suke yin wasu abubuwan kuma har ga Allah su suna yin komai ne da tsarkin zuciya, kuma su sun mance duk abinda Najwa tayi musu suna son su cigaba da zumuncinsu kamar da, ita ko Najwa kamar ƙara ƙunsa mata baƙin ciki suke dan gabaɗaya mafarkinta tamkar su ta yiwa, haka ta tafi da sha tara na arziki zuwa gida duk da hakan ba wani burgeta yayi ba sai tarin damuwa data samu kanta a ciki, musamman yadda taga matar Zaidu tayi clean ta sauya kamanninta da Sameeha ya fito ga jikinta 'yar duma duma sai ta raina kanta dan ita cikin ta muni ya saka mata ga pimples a fuska da wani haske mara kyau, kuma ta rame saboda wahalar aikin gidansu dan hatta wankinta ita ke yi, ga ba abinci mai kyau, sannan ma wai matar Zaidu tana da motar da take jan kanta yanzu fa da itace a cikin wannan daular, kaico da cizon yatsa kawai ta ke yi dan tasan har abada ta saki damarta. Sameeha tayi arba'in da wata guda Najwa ta Haihu Namiji yaro yaci sunan Abubakar Sadiq, ranar suna Mujaheed cewa yayi ba taro dan lokacin yazo tsakiyar wata bai da kuɗi da kyar ma ya samu ya saya ragon suna, Najwa har kuka tayi dan in har ba ai taro ba ya gama zubar mata da ƙima, dan taci buri a sunanta itama tayi abin arziki koda bai kai na su Sameeha ba, taso ayi shinkafa alale da waina da miya sai drinks, amma ganin hakan ba zai samu ba itama ta amince da ba zata yi suna ba, mama kuwa tace ba zai yuwu ba haihuwar fari dole ayi taro ba dole bane sai anyi ƙarya, zasu yi abinda Allah ya hore musu sannan bata so suyi karanta ga dangin Najwa ashe haihuwarta basu taɓuka komai ba, hakan yasa ta ciro tsohon ajiyarta ta je kasuwar Laraba ta auno masara ta bayar surfe da ɓarjin fate tayi cefane dana zoɓo ta dawo gida, ana gobe suna suka yi aita da yaranta da sauran 'yan uwa na kusa, washe gari suka girka katon tukunya suka sharɓa faten tsaki na alayyahu, Najwa kamar ta ɗaura hannu aka ta tsandara ihu, nan ta kira gida akan ba taro inna tace koda ba taro zata aiko mutane da gararta, dan haka zata aiko su goggo da shinkafa loka goma da kuma cefane zasu zo su girka anan wanda zata sallami baƙinta, to kawai Najwa tace mata dan tasan ƙaryanta ta ƙare. Bangaren su Sameeha kuwa sun ci burin zuwa sunan Najwa musamman Ikram da bata san ɗakinta ba, hakan yasa da wuri suka haɗu a gidan umma da matar Zaidu suka haɗu suka tafi a motar Ikram dan itace ta jasu har da umma su huɗu, suka fara isa gidan inna suka sauke umma su kuma suka wuce gidan mai jego wajen ƙarfe sha biyun rana, sun shiga lokacin gida ya cika da 'yan uwan su Mujaheed sai sharɓan fate suke yi, ganin mata 'yan gayu yasa sai zuba musu gaisuwa suke su Sameeha suna amsawa suka wuce ɗakin Najwa da suka tadda 'yan uwansu a ciki waɗanda suka yi girkin shinkafa, bayan sun gaisa sai suka yiwa kansu mazauni a uwar ɗakan me jego wanda fuska muzu muzu ko kwallita bata yi ba saboda damuwa, Ikram da bata iya gani tayi shuru tace. Ke meye haka? yau ranar murna amma kin zauna da fuska sai kace wacce aka yiwa mutuwa, dalla zo in miki kwalliya da ɗauri ki fito a amaryar ƙarni da kyau. Gaskiya dai Ikram fito mana da mai jego tayi fes. Cewar Sameeha kuma har zuciyarsu bada cin fuska ko zaulaya suka yi ba, Najwa kuwa sai taga kamar da biyu suka yi mata haka, hawaye ya kawo idonta amma sai ta shanye tana gaishe su suka amsa da fara'a a lokacin ne aka shigo musu da abinci, Sameeha tace. Nikam ba zanci shinkafa ba ku kawo mini fate na sha na daɗe ban sha shi ba shi ɗan sha'awa ne. Ikram tace itama shi zata sha matar Zaidu ma haka, sai da Ikram ta yiwa Najwa kwalliya da ɗauri ta fito fes ita kanta data kalli kanta a madubi taga tayi kyau, nan suka saka ta ɗauki jariri suka dinga ɗaukar su har sai da suka gaji kafin Sameeha ta fita da kanta ta ɗebo musu fate suka zauna suna sha, Najwa dai sai kallonsu take taƙi sake jiki dasu balle suyi hira, sai ta zama kurma tana jin hirar da suke yi na business da Sameeha ta fara na sari kaya daga Dubai, Ikram tana cewa ita kiwo zata yi na kaji da kifi a bayan gidanta wanda Shamsu ya ware mata million biyu so take ta yi magana da Yaya Zaidu ya samo mata wanda zai kula mata dasu, Matar Zaidu kam cewa tayi ita shagon Saloon Zaidu yace zai buɗe mata a jikin gidansu dan har an fara gida shagon ma, haka suka dinga hira a tsakaninsu gwanin burgewa, Najwa ko wani irin hawaye taji yana cika mata ido amma dole take shanyewa dan kar su gane halin da take ciki, fuskar yaronta kawai take ta kallo tana shafa gefensa wanda sosai kamanninsa ya fito na Mujaheed, sosai ta kamu da soyayyar yaron wanda take jin zata iya cigaba da zama da Mujaheed dalilin yaron dan itama in tace yanzu bata son Mujaheed tayi ƙarya, kawai dai bayi da wadatar da take so ne, musamman ma yadda taji su Sameeha suna hirarsu ji take dama ita ce amma ƙaddararta a talauci ya zo, duk da itace da kanta ta nesanta kanta da arziki, su Sameeha suka cigaba da hirar bikin Aminu wanda zai auri yar uwar Shamsu, ɗan tuni ya warke sarai ba sauran ciwo, auren ma ba zai samu zuwa ba yana London in an ɗaura ne Sameeha da Ibrahim, Ikram da Shamsu sune zasu yiwa Amarya rakiya zuwa London daga can kuma zasu wuce Saudiya suyi Umara kafin su dawo, Najwa baƙin ciki goma da ashirin yanzu fa da ita ce tare da Aminu a London, ko dan wannan ɗaukakar da ta samu ai dole tayi gogayya dasu Sameeha amma kuma Allah ya ƙaddara aurensu ba zai je ko ina ba. Su Sameeha leshi mai tsada da atamfa biyu suka bata tare da kayan yaro kala biyar da takalmi ɗaya masu tsada, Najwa tayi musu godiya. Bayan La'asar aka kawo mata gararta buhun shinkafa da su mai da dai kayan da ya dace da tamfofi da kayan yaro, ba ƙaramin gara suka yi mata ba kuma hakan ya ƙara fito da ita sosai a gurin dangin miji. Da su Sameeha suka tashi tafiya ta ce Najwa ta bata account number ɗinta,ta karanto mata nan take ta tura mata dubu ɗari biyu tace. Nasan ba zaki taɓa tambayarmu abu ba duba da abubuwan da suka faru a baya tunda har yanzu kin kasa sake jiki damu mu dawo kamar da, amma ina roƙonki dan Allah Najwa in kina buƙatar abu ki sanar da ɗaya daga cikinmu, hatta yaya Zaidu wanki ne kuma zai miki duk abinda ya dace, sannan wannan kuɗin dana tura miki ki yi tunani ki fara business dashi In Sha Allah lokaci zuwa lokaci zaki riƙa ganin alert daga gunmu, ki maida komai ya wuce muyi zumuncinmu. Hawaye kawai Najwa take yi wanda tsantsar damuwa ce da tarin kunyarsu da ke damunta, ta ce ta gode sosai kuma itama komai ya wuce, haka suka yi mata sallama su barta a tsaye tana juya wayarta da mamakin kuɗin da ta tura mata, wannan shine mafarkinta ace ita ce take taimakonsu amma yanzu itace a kasansu kuma tasan har gaban abada sunyi mata nisan da ba zata taɓa kamo su ba sai dai wani ikon Allah, tabbas Abin da ciwo domin yana yi mata ciwo a zuciya wanda ba tada yadda zata yi haka ƙaddararta tazo, da wannan cutar Hassadar zata koma ga Allah dan ya riga ya nuƙurƙusa zuciyarta wanda sai wani ikon Allah ne zata daina jin haka a ranta. Ƙarshe. Alhamdulillah! Allah ya yafe mana kurarren ciki, alkhairin ciki Allah yasa muyi tarayya a cikin ladan. Ameen. Taku ce Rahma Kabir Sai mun haɗu a sabon littafina nan ba da jimawa ba In Sha Allah.