To kamar yadda kuka sanni ni benaxir yar yawo ce ina kwaso labari da darussan yau da gobe na rayuwanmu. Na kawo na afrah. Dana indo dakuma na aliya. Harda ina tunanin gunwa zani sai aliya taban satan amsa inxo gun Bilkisu mai gadon zinare. Hakan kuwa akayi domin takanas daga bauchi nazo har garin gombe domin na tuntube bilkisu labarinta tun daga farko. Amma fa ba karamin wahala nasha ba kafin ta amince tabani. Don dai nace mata nida yan makaranta na zamu dau darasin rayuwana saboda kowa rayuwarsa akwai darasi. Gani ga balkisu .zata fara bamu labari yanuwa kubiyoni muzuba na zomaye Hmnnn sunana Bilkisu saad. Baba na maigarin kauyenmu ne. Natashi cikin wahala da talauci. Mu 36 ne a gun mahaifina matarsa guda hudu. Akwai rahama .siddiqa.suwaiba sai kuma mahaifiyata aisha.. Mu takwas ne agun mahaifiyata. Sai uwargidansu rahama tana da yara 10cif dukkansu mata. Siddiqa tanada 9 sai. Suwaiba tana da 8 . Gidanmu babban gidane. Haka zalika matsaloli da matsifar cikinta. Idan kana da baki ka kwace kanka. Sharri da makirci kuwa sai tubarkallah.mahaifiyata macece mai hakuri da shariya hakan yasa duk matan gidan ita take cutuwa. Mu biyu ne mata sauran shidan duk mazane. Mahaifina manomi ne sosai. Don haka kowani yaro inyataso gona yanufa. Bai yadda da karatun boko ba. Matan kuwa kinagama islamiyya kikai shekara 15 zai aurar dake . Auren dangi akeyi tunda natashi banga anyi auren bare a gydanmu ba. Da dadi daba dadi kowa aka samu acikin yayan bappanmu zaa hadaki. Shima yayansa sunkai 46. Ahaka nataso yanxu shekarana sha hudu. Iba islamiyya. Aladace kullum dare dare a gydanmu sai munfito yara munyi hira dayake yayan kishiyan umma na akwai saannina. Da khadija da aisha dakuma maryam. Duk dakinsu daban amma kanmu daya . Duk cikinsu nafisu nutsuwa fasali kyau dakuma ilmi. Khadija da maryam akwai rawan kan tsiya da surutu gasu da buri. Basuson zuwa islamiya sai suyita cin kudin samari. Ganin duk garinmu ana daraja gidanmu.nikuwa da wannan abun dasuke zan dauki littafina naje gun ummata tamin karin littatafai. Ta ban labarin dazasu amfaneni. Ummata irin mutannenan masu lura da kuma hangen yaransu hakan yasa bata wasa da lamrukanmu. Kanwata fatyma wacce muke kira hajja teema. Don tanada sunan kakarmu mamar mai gari.nikuma saboda kirar hutun da Allah yayimin kuma ya kasance kakana tafi sona duk jikokinta. Take cemin yar gata hakan kuwa akayi baa kira na da bilkisu saidai yargata. Kamar kullum nadauko littafin fiqhu na bayan sallar isha antaru a tsakar gida sai hira ake. Khadija ce ta ke tadin saurayin dasuka hadu a dandali wai yabata kyautan dari. Daya bata sai tamaka masa a fuska wai yamata kadan hakan yasa yabata dari biyu. Shine suka sayo doya da kwai sukeci. Ina kallonsu sai dariya suke ban ina karatu. Nagama hajja wato kakarmu tace yargata zomana. Naje kusa da ita tace anata labarin ke kinja gefe. Nayi murmushi nace inna kema kinsan ban kware a surutu kaman khadija ba. Tayi murmushi tace hakane. Yau mekike karantawa nace rukunnan sallah. Anan nazauna na biya mata. Aka zubo mana tuwon daren mu tuwon dawa miyan kuka. Namike naje mukaci sunaci suna tadinsu dama sunsanni sarai ba magana nake ba. Bayan mun idda namike nacewa hajja teema kixo muje mu kwanta tace toh. Muka shiga muka samu inna akan sallaya wanda aladarta ne sai tafi awa biyu akan sallaya bayan sallar isha. Muka kwanta muna hiranmu na ya da kanwa. Umma tace ina su abdul tana nufin yayanmu na fari nace mata yau baishigo gida ba. Dama ina nemansa yaban 35 zan siya littafin fiqh. Tace kekam kullum bakida abunyi sai tara littafi? nace uhm bazaki ganebane umma su suke sawa mu saya. Batace komaiba har mukayi bacci. Dasafe da asuva bayan idar da sallah sauga yaya abdul yashigo bayan sungana magana da umma zaifita nace yaya kasayamin littafi yajuyo yace nawane nace 35 yamikomin hamsin yace kibawa hajja teema sauran canjin nakarba ina godiya . Dayamma nashirya tsaf zantafi islamiya nida hajja teema. Munshirya cikin manyan hijabai nikam harda liqab. Muka wuce.akwai wani kofar shago inda samarin anguwan suje taruwa sunsan fuskokin yan gydanmu kaf. Ni ce natare musu hanya. Basu taba ganin fuskat ba. Akwai wani ahmed ya yanke shawaran sai yabude wataran kowa yagani. Danasan da wannan rana daban fitoba. Ina tafiya naji sallama ban amsaba hajja teema ce ta amsa . Yace da yarki zanyi magana batace komaiba haka zalika nima bance komaiba mukaxo daidai ahagon yanata binmu. Muna xuwa gun samarin yasha gabana kawai yatube min liqab da karfi hakan yasa hijabi nama tafadi. Gashina dake kwance har gadon baya suka zubomin a fuska cikin azama da bacin rai nadauki hannu na kwashe shi da mari. Zamu karasa gobe. Gud nyt Rike fuskarsa yayi bashi kadaiba dukka samarin gun kowa na mamaki biyu. Kyaun fuska na dakuma marinsa danayi. Shikuwa marin baidameshi ba salati naji yayi yana hamdala. Hakan yasa namayar da hijabi na nace hajja teema mutafi da Allah. Muka isa islamiyya . Muna dawowa ne naganshi da abokanshi suna zaune kokesuke fada sai Allah. Dayake mu biyar muke tafiyan dasu khadija maryam da aisha sai hajja teema. Cikin nutsuwa muka wuce. Har lokacin jikina bari yake don bantaba taba jikin namijiba bacin yayuna sai akanshi. Hakan yasa umma na ta tambaya nakuwa gayamata komai . Tamin fada sosai akan illan marinshi da nayi a cewarta wai namiji baa masa haka .zai iyacewa sai yarama kuma ba yadda na iya. Zai rama ta mumnunan hanya Allah kare. Nayi shiru amma jikina yayi sanyi. Da magriba muna zaune mukaji inna rahama na ihu tsakar gyda tana matsifa . Ummata bata leka ba sanin mexai biyo baya. Ni da hajja teema muka leka. Aikuwa saida mukayi dana sani. Inna rahama ta jawomu wai mu muka dauke mata daddawan data shanya a rana. Nida hajja muka zaro ido nace inna wlh munji kina matsifane muka leko. Karya kuke munafukai uwarku takoya muku sata ko? hajja teema cikin bacin rai tace kinga inna. Ki kare akanmu wlh karki karasamin uwa cikin zancenki. Aikuwa data jawo hajja tarinka kirba. Umma naji bata leko ba. Inna sadiqa ta fito tace kara mata. Nima yar nakeson daka. Dasu maryam take cemin wai tsabar wulakanci ance yargata ta mare mata saurayi. Na zaro ido nace inna banganeba. Tace zaki gane don uwarki. Yara saikace kune masu gida komai ku? suka kamamu suka jimda su yaya abduo basunan balle su kwace mu. Ummanmu kuwa badama tashiga yanxu sai su mata taron dangi mukaci kukanmu. Umma ranta yabaci sosai ta yanke shawaran gayawa maigari. Bayan yadawo tasanar dashi ya aika akiramu dukka harda su maryam. Yace tunda ni bazaku barni na hutaba kullum acikin dukkan yara kuke yau ku daki na wannan gobe na wancan to ya isa haka. Kowa taje tashirya nanda sati biyu zan aurar da maryam.khadija.aisha.dakuma bilkisu. Tundanake a rayuwata bantaba shiga tashin hankali irin wannan ba. Wannan ai matsiface baba zai dauken yabadani ina gani akan yayuna. Kuka nafarayi yace ku bacemin anan. Su maryam kuwa basuce komaiba. Asali murna suke don suna da tsayayyu a dangi nice dai daban da kowa. A daki umma tayi tagumi tace kiyi hkr danasan haka maganar zata dawo dabanjeba. Nayi shiru. Hajja ma ta tsorata sosai ita gani take zaa hada da ita. Gydanmu aka fara shirye shiryen biki mu hudu. Haka gydan bappanmu ma zasu fitar da maza hudu. Baba yakiramu ko muna da tsayayyu a dangi kowa tafada nata . Nikuwa nace banidashi. Haka kuwa akayi kamar yadda akeyiwa duk wacce bata fitarba zaa hadata da kowaye. Aka daura aurenmu. Dangin umma na sun hallata sosai naga gata kasancewa ni ce mace tafari da zaa kai a dakinmu duk yayuna mazane. Aka daura aure . Baba yace kowa tawuce dakinta da yamma. Ba ko ina bane sai gidan baffanmu. An yanka mana gefe guda. Kowa ciki da falo da bandaki. Kicin kuwa haduwa zaayi kowa ta girka abunta. Bansan mijina ba amma gyra kam nasha .umma tarinka min waaxi karki biyewa mutane kizauna da zuciya daya dakowa baruwanki da sa ido wa rayuwan wani. Tamin waazi sosai sanin datayiwa gidan. Dare dare aka kai kowacce dakinta. Aka barmu daga mu sai halinmu.. Ina zaune a yafe gashi ni ba kawayeba. Yayi sallama yashigo akasan makoshi na amsa masa. Yaxo gefena yazauna tare dacewa tashi muyi sallah. Natashi nadauro alwala mukayi sallah. Yamin addua sannan yace hau ki kwanta. Jikina nabari don tunda nake bantaba kebewa danamiji ba. Yahau gadon rumfan shima amma tagefe guda mukayi bacci. Tun ina dar dar har na sake jiki. Duk abinnan banga fuskansa ba. Balle nagane waya mijin.. Da asuba yatashen shima yayi masallaci. Bayan na idar nadan jinginu da bangon ina tunani shikenanfa nadawo matar auren dole. Hmnn. Sallama yayi na tsugunna na gaysheshi ya amsa. Batare da yakara cewa komai ba ya dale kan gado. Nikuwa namike da xummar namana abun karyawa. Kirana yayi KE kixo ki kwanta kawai zaa kawo anjima. Nace to jikina a sanyaye a zuciyana nace tabbas baisan wa aka aura masa ba shima. Nakoma kan sallayata har gari yawaye agun bacci ya kwashen. Bayan nafarka naga bai nan amma ga abincinnnan an ajiye. Benaxir intakaita miki watana hudu cif bansan mijin danake aureba. Inyafita da asuba sai dare yadawo kuma fitila bayi barina naga fuskarshi. Shima bai taba ganinaba. Muryarshi kuwa kamar na mawaki zaki ga dadin sauraro amma bai fiye maganaba.wataran ni nake kwana nikadai dare dare yakan sanar dani zaiyi tafiya . Wataran yayi sati wataran kuma sati biyu. Su maryam da khadija kuwa harda ciki. Kasancewar mu tubali daya yasa bamu cika hayaniya dasuba. Asalima kanmu a hadene saidai bani shiga cikinsu kamar yadda nake a gyda. Ganin zaman banzan yayi yawa yasa na yanke shawarar sayarda awara anan nasanar masa wata rana dare dare ya amince harda bani jari. Nafara sanaata ba kama. hannun yaro.watarana naje ganin gyda muna hira da ummata sai take tambayana game da rayuwan aurena ina bata amsa. Anan ta fahimci bansan komai akan aureba balle namata bayani in akwai matsala. Anan tafahimtar dani komai nace mata umma fa ko fuskanshi ban saniba. Tayi mamaki kwarai namata bayanin komai. Tace to ke zaki gyra rayuwar aurenki. Tamin nasiha sosai nace to . Namike nadawo gyda. Haka mukaci gaba da rayuwan. Maryam da khadija suka haifi namiji. Aisha kuma ta mace .A lokacin na fara fuskantar gori anfara cemin juya. Abun naidamenba. Umma ma tafara damuwa wai anya badaga nibane? yanuwana duk sun haihu nace umma haihuwa na Allah ne karki damu.tace karki sako Allah anan inada yakinin daga kene. Ai Allah yace tashi in taimakeka. Kuka nafarayi sosai inacewa umma ni umma wlh banya zanyiba. Itama tarasa yazatayi . Tace to kisan yadda zakiyi yadawo da rana. Ko fuskanshi kigani. Haba ace kin shekara da mijinki ku kwana tare baki masa farin saniba? yoo ahmed din nawa yake. Namiki kwatancen shi kingagara ganewa. Basai inbarki ba?nayi shiru. Ahaka har nakoma gyda. Kwanana biyu banjin daidai hakan yasa na kwanta yau akan bazanyi awara ba. Cikina ne yafara ciwo nafara juyi ina salati tun inayi a hankali har nafarayi da karfi. A haka aisha tajini tashigo atake ta aika akira ahmed daga kasuwa. Tafita hadomin ruwan kanwa. Sai gashi yayi sallama yashigo . Hmnn inacikin ciwo hakan bai hanani ganin kyakyawan fuskar mijina ba. Shikam ganina akwance yace ina bilkisun na kalleshi cikin mamaki. Ban bashi amsaba aisha tashigo tace yaya ahmed kaga jikintan ko? wlh taban tausayi shiyasa na aika akiraka. Kallona yake tayi hakan yasa naji kunya itakuwa ta karaso ta ajoyemin riwan kanwan tajuya ta fita. Ashe dama wannan ce matarshi? ko da wasa baitaba tsammanin haka take ba. Yasha ganinta a gefen dishashen fitila amma baitaba lura haka take ba. Kuma dayake kullum hijabi take sawa tarufe fuskanta yaukam gata da dan karamin riga daidai hannu. Ga gashi ya xubo har gadon baya.taguna kuwa. Duk gidan baffanmu banga kyakywa irinshiba xubinshi baiyi kama dana kauyenmu ba Kumin uzurri nadan huta Cikin tashin hankali ya karaso guna yarike hannuna zafin dayaji.ba shiri yasaken. hakan yasa dasauri yafice jim kadan yadawo hannunsa rike da kwarya. yadagoni na kurba dakyar ina yamutsa fuska. haka muka wuni dashi yana gefena sallah ke dagashi. . motsi kadan nayi idonsa na kaina. hakan yamin dadi a karo na farko tun zamana a gydan naga murmushinshi. muna haka sai ga yabi.matar baffa nane tashigo tana cewa ahmadu lafiya kuwa? yace kalao yabi zazzabine ke damunta. tace dafatan kabata magani yace ae. tace to bari mu aiko suwaiba taxo ta tayata zama. nidai abun yaban mamaki zazzabin kwana biyu nayi amma suwaiba batq tafiba. suwaiba yar kanin baffanmu ne maana muna yayan wa da kanne nida ita dakuma ahmed. tayi aure a zaria mijin yarasu .suwaiba irin matan nanne batada kyau amma kwaliyya na gyrata tayi mummunan wayewa. ta tare a dakinmu. dare ne kawai yake rabami da ita. mun shaku sosai. shikuwa ahmed suna mutunci ba laifi. watarana nafito daga dakin aisha zankarbi quranina data karba dayamma . sai naga takalmin suwaiba adakina. nayi mamaki domin munyi sallama da ita shiga nayi natarar suna tadi da ahmed .nima zama nayi mukacigaba. batun ahmed kuwa munshirya sosai yadena zama agun aiki yana fita bayan awa biyu zakuga yadawo tarairaya kala kala. kayan dadi idan yasayo sai yakawomin wani abu baitaba shiga tsakaninmu ba. ahaka wata rana yabi tashigo nida suwaiba muna surfe tace ke balki ki saka kunnenki ki sauraren bamu dauko ki zauna kici ki koshi ba. mundauko kine ki hayyayafa mana. yanuwanki sun haihu ke inbanda ci mekikeyi? kullum sai ya kunso leda yakawomiki ni danake uwarsa bayamin abunda yakemiki. hawayene ke zuba a idona tace rufamin baki munafuka . nayi shiru ina hadiyan yawu. tadauki muciyan gefenta ta rinka gwabzamin abinda yaban mamaki shine suwaiba ko uhm batace ba balle uhm uhm. ko insa ran zata bada hkr. tundaga ranar nadawo abun tausayi . ahmed dani dukkanmi shi yana sona kuma yanada niyyan taimakona amma uwarsa tasani a gaba. ko kunshin leda tagani a hannunsa saita karba karshenta ma inzaixo saiyabi ta dakinta tagani ko akwai wani abun . tsangwama kuwa nafara gani tunda wankinta da wanke wanke yadawo kaina. kannensa kuwa duk abinda sukeso shi zaa girka. benaxir in takaita miki wlh kamar ba jinina ba sunmayar dani bare. Tashin hankali na yafara ne watarana naje gyda umma ta tsareni ko lafiya nace mata ae. naki sanar da ita halin danake ciki. munyida ahmed zan kwana. sai umma tace nadawo kawai. nadawo takalmin suwaiba nagani a dakin banyi mamaki ba kasancewar nasan suna tadi. nashiga falo bangansu ba hakan yasa nashiga daki kwance naga suwaiva da ahmed� duk da ban fahimci mesukeyiba don bansaniba. haibuwar uwarsu dana gansu yasa nayi auxubillah na fita. musha ruwa lafiya cike da azama nafice nabarsu tsakar gydanmu naje nazauna bande san mesukeyiba amma tabbas nasan cewa haramunne domin kuwa tsirara fa nagansu. Nakai minti ashirin ban ji motsinsuba hakan yasa na buga musu kofar tare dacewa.suwaiba kungama ne nashigo? batacemin komaiba hakan yasa nakoma nazauna. ni na kagu.su fito don sanyi nakeji sukuma ashe wai kunyata ne yahanasu fitowa.sunrasa yaya zasuyi.can dai suwaiba tafito jikinta a sanyaye nayi murmushi nace kekuma inata jiranki. mamike nasamu.ahmed yayi tagumi. nasharesa naci gaba da lamarin gabana. kwana biyu duk sunkasa sake jiki da niko yau ma ina wankin yabi taahigo tagama zage zagenta. tafita saiga suwaiba. tashigo tana murmushi nima shinamata tatayani muka gama girki. ahmed yadawo suna hiransu nima ina gefe inadan saka musu baki. ahmed yace balki shekaranki nawa? nace watan gobe zancika 16 ya gyada kai yace shiyasa. nace meyasa? ya ce babu. nayi murmushu nashare.ina duba tauheed na. sai yakara jefo wata tambayan yace innakara aure yazakiyu. ? nayi murmushi nace yazanyi kuwa? babana matansa hudu ai. kaga kuwa bazai damenba.yace hakane. suwaiba kuwa dariya tayi tayi nace kekuma meye kamar marar lafiya . tace babu. yanxu bakya kishin mijinki? nace chap. kishinne ai da iyayenmu sunyi.naa dariyan suka karayi.nadai ga abun rainin hankaline namike naje na kwanta. ina kwanciya.yabi tayi sallama. tare dacewa ina wannan tsinanniyar yarinyan? nayi tsit shikuwa ahmed cikin sanyin jiki yace tana ciki. bankado labulen tayi taredacewa yau zaki gayin ko uwarkice tasayamiki takalmina. na zaro ido. nace wanne takalmi? tace gashi a kofan dakinki. kafin nace wani abu tin lukwus saidata gama dakani sannan suwaiba ta leko wai laa.yabi kiyi hkr nina sako miki. tajuya tace ainazata wannan tsinanniyar ce. tafice. ina kuka saiga.ahmed da suwaiba sunshigo wai infice inbasu waje su huta . na fita falo na kwanta misalin karfe hudu na asuba naji gidan na kurwa. na leka kai naga.aisha na hanyyan xuwa guna idonta yayi ja. nace lafiya ? kafin nace wani abu tace ummanki ba lafiya. cikin salati na zurma dakinmu namanta ahmed da suwaiva naciki. yadda nagansu rannan haka nagansu yau . baidamenba nadauki hijabina nafice ummana nasamu a kwance kumfa nafita daga bakinta tana salati. antaru sosai. akanta. ckkin kuka nakarasa ina cewa unma na sannu Allah yakareki. hajja teema ne tajani take bani lbr wai ashe kwanan umma shida ba lafiya kullum su inna sadiqa da inna rahama dukanta suke sosai . sunhanata abincin gidan don baba ya bata jari. hawaye neke zuba a idona cikin kuka nace to baduka sunada abunyiba? ummace kawai baabu. hajja teema tace hakanefa. nace to yanxu meya sameta? tace wai yau yabi takawo mata abinci .hannu na daura akai nace haba hajja. lokacin dasuke muku azaban yunwa meya hana kizo kigayamin? sannan inasu yaya abdul? tacemin wlh bayanda batayiba tace innaje na gayawa wani bata yafeba. su abdul kuwa bata taba nuna musuba saidai sunacewa ta rame Hawayene sosai yake xuva. anan umma tayi salati tacika. nayi kukan dabantaba yiba a rayuwana. to ke umma taci musu? meye damuwansu da ita? Allah kasaka mana da gaggawa. bayan sadaqan bakwai baba ya umurceni da nakoma gidana. hajja kuma yaya umar yaxo yatafi da ita gidansa. yanxu gaba daya nayi sanyi. gashi wulakanci gaba yakarayi tunda yanxu harda yan cikin gydanmu.aisha ce kawai mai ragarmun juya suke cemin. nikywa.baidamenba don bawai nafahimce mesuke cewa bane Hajja sunkoma birni tare dasu yaya sukeiman. Yamin waaxi sosai na hakuri da rayuwan duniya akan zasuna lekoni . Sannan yaban kyautan kudi yana tafiya yabi ta kwace. Naci kuka sosai saboda nayi niyyan tabuka abun arziki da kudin gashi. Ta kwace. Abinci yaxo yafara gagarana aisha ce intayi sai ta kirani dakinta naci. Suwaiba kuwa da ahmed rayiwan mata da miji suke. Abun baitaba damunaba. Don bana kawo tsammanin komai. Wata rana ina daki na idar da sallan isha saiga ahmed yashigo rai murtuke kaman wanda yayi fada da karnuka . Na tsorata sosai ya damko wuyana don ubanki bana cemiki maggi. Hudu zakisaba. Meyasa naga kinsa shida hawaye nazuba nace masa baiji bane. Anan ya mammakeni yatafi. Haka yake daga baya abincinma yafara kirgawa sai yadibamin iya maggin dazansa har gishiri. Yawaremin kuma itace duk randa na tsallake ranan zanci duka. Kuma bazan samu abinciba.haka rayuwata ta kasance ga tsangwaman miji gana kishiya. Gana yayan uba gana dangin miji. Ramewa kuwa a tsaye kika tura hannunki ba abinda zai hanani fadi. Nadawo fatalwan dole idona xuru xuru. Nadawo kaman wata aljanna. Don akwai randa dan aisha nazaune dannan nadaukeshi kawai yafara tsala ihu. Yarinka kuka tana karbanshi yayi shiru. Duk randa nadaukeshi haka yake dole na nahakura. Kullum inbanda kuka dakai kara gun Allah ba abunda nakeyi. Nazama tamkar wata zautacciys Ina kwance akan sallaya rungume da quranina ahmed yashigo yace zan gyra dakinnan akwai jinkar akuyoyinnan zansa kayanki agun don aure zan kara. Bance komai ba nace to. Abin ashe dagaske yake? washegari yasa na kwashe kashin awakinnan na gyra gun namayar dakayana. Wai aure zaiyi . Nasamu suwaiba inagayamata tarinka bani hkr wai meruwanki da kiahiya? meye take dashi da baki dashi? ki kwantar da hankalinki ni nasancewa kece yar gaban goshi . Duk daban yadda da maganan ba amma hankalina yadan kwanta . Haka kuwa akayi akashirya tsaf akayi biki aka kawo amarya koda wasa banshiga harkansuba. Asalima kulle kaina nayi. A lokacin nayi nadaman fitowa daga babban gida irin namu. Marar tasiri. Benaxir karki dauka amaryan watace a a. Suwaiba ce aka kawomin abun ya matukar ban mamaki. A lokacin ne bappanmu yasa akirani dashida maigari bakaramin tsorata sukayiba dasuka ganni. Habawa anan hankalin bappanmu yatashi yace mamana auren ne yamayar dake haka? kamar nace ae nagayamusu komai. Sainatuna da kalman mahaifiyata a karshen hadiwanmu inkoyi hkr indena fadin sirrin aurena. Hawaye nazuba na girgiza kai tare dacewa a a. Abba. Bakomai nikam lafiyana kalao. Yace Allah yamiki albarka anan sukaban kayan fadan kishiya aisha ce tace abba to ai sunkoreta adakin anannefa akayita rikici ahmed yasha fada kam gashi yabi nagun tabbas nasan nashiga uku sai inda Allah yayi dani kuma domin sai sun koya min darasi. Anan akaje aka kara ware mana gu gefe daya nawa daya na suwaiba ammata fada akan ta nutsu ita babbace takuma kama girmanta.tace to. Su abba natafiya da suwaiba da ahmed suka fara dukana ranan dakyar na iya motsi. Satina biyu ina jinyan jikina amma babu abinda yaragu. Daga azaba saima karuwa. Duk abinda akeyi kuwa cikin gida bappanmu baisaniba balle mahaifina maigari. Hajja kuwa datakesona ta tsufa bata fita balle taxo taganni. Watan suwaiba uku. Rannan tafara nakuda . Nikuwa adole murna nake zamuyi da. Aisha ce tace ke yargata? baki da hankaline? ancemiki mace na haihuwa wata uku ne? abin ya balain dauremin kai. Taja tsaki tace ni wlh bantaba ganin tsokuwa irinki ba. Kina girma hankalinki nakara dawowa kasa. Anan mukaji ihu. Suwaiba ce tahaifi danta cikakken da a wata uku. Zamu karasa gobe insha Allah. Wlh nagaji .kunsan anyi azumi yau BILKISU Ahmed nashigowa yafara zage zage wannan wacce irin rayuwace antaba haihuwa wata uku da aure? kinje kinyi karuwancin ki dai. Dayake subiyu ne a dakin nikuma ina zaure. Sai budan bakinta tace dadin abun kai kamin cikin inba kai kayiba dawa nake zama? kafini sani. Zare ido yayi yace wlh karya kike. Karma kifara wannan maganan yabi ne tashigo gidan ko sallama babu. Na tsorata sosai bata ko kalleniba tabankade labulen taredacewa kaje ka auro karuwa. Inba karuwa ba wacce macece zata haihu wata uku? to wlh kasani wannan ba matar zama bace. Cikin sanyi jiki yace umma kefa kikace na aureta don mu kuntatawa balki. Tace rufamin baki. Ai gwanda balki yar albarka ba irin wannan ba.tajuya tana harararn suwaiba ita kuwa ta murkuda baki tajuya kai itama. Yabi cikin haushi tace nikikewa tsaki? takai hannu zata daketa suwaiba kuwa ta cafe hannun. Abun yabata mamaki cikin harxuwa tace ina ganin mutuncinki yabi wlh zanmiki rashin mutunci idan kika tabani. Cikin mamaki yabi tace kanajin mai matarka take cewa ko?shikam tagumi yayi agefe baima san meke faruwa agunba cikin bacin rai yabi tafito tana cewa gun maigari zaaje dole yaraba aurennan domin ke mazinaciyace.a daren ranan ina cin tuwo nah. Saiga ahmed yashigo yana ban hkr. Kallonsa kawai nake. Yagama karyamin xuciya a dan shekaruna wahalan danasha akan aure dakyar akwai wata datasha tahakura. Nadai nuna masa bakomai yana cikin min bayanin kasuwa kawai labule mukaga anbuge ana shigowa daga idon dazanyi ruwan zafi naji ajikina. Aikuwa nasala ihu. Atake na sume. Duk jikina ya kauye . Cikin tashin hankali ahmed ya tsala ihu hakan yajawo hankalin mutane dayake darene ita kuwa suwaiba tuni tafice tadauki danta. Asibitin cikin gombe aka kawoni. A lokacin maigari yasanar da yaya sule cikin tashin hankali dashida hajja teema sukaxo. Ananfa ya sule. Yaroki alfarmar yakaini asibitin abuja don samun kulawa mai kyau haka kuwa akayi. Akwai na gargajiya dakuma na bature nafara warkewa saana daya bai samu fuskana ba. Hakan yasa a hankali nafara warkewa sosai. Cikin wata uku na murmure nayi kiba. Daga madara sai kayan kwalama. Matan yaya sule jamsy tanada kirki sosai. Yan gidanmu kuwa maigari yasa a kabada mota aka kawosu. Anan nakejin labari agun aisha shima ahmed ya kwanta ciwo yarame yayi kashi sosai . Ciwon yabawa kowa mamaki. A zuciyana nace kadan kenanma.sunkawo min tara na arxiki a lokacin ahmed yake cewa yaya sule kozan koma. Yaya sule ya girgiza kai. Yace kayi hkr amma azabar ta isa haka nan. Bazan taba barinta takoma gydanka ba. Bayan sati biyu ne naje gida ganinsu a daren ranan muke tadi da aisha take cemin suwaiba tun ranar har yau bawanda yaganta annemeta anrasata. Kulawa kuwa yan garinmu sunnunamin. Anan yabi naga tana kaffa kaffa dani. A zuciyata kuwa nagano metake nufi. Maigari yace nida ahmed washegari muje musameshi nasan maganan aurenmi zaayi. A daren ahmed yafara ciwon ciki da amai. Aka kaishi asibiti washe gari aka ce yana da ciwon kanjamo.. Ni abunda yaban mamaki shine yadda mutane suketa min kallon tausayi har akemin jaje. Wai inta hakuri haka Allah ya kaddara. Nasamu aisha namata maganan. Tace aishi kanjamo idan kikaji ance miji dashi to saiwani ikon Allahn matan bata samuva. Na tsorata sosai har nacemata to tayaya ake daukan cutan! Tace ta saduwa mana. Nayi shiruuu. Nace meye saduwan. Tsaki taja tare dacewa abindake shiga tsakaninki da mijinki dare dare. Nayi dariya nace to ai ni babu.. Taja tsaki tace yar rainin hankali wacce macece batasan wannan ba gwara kisake ranki kigayan donnima inayi.. Nace Allah wlh nikam nabu don baccina nakeyi. Ta tsorata sosai jin nayi rantsuwa kuma ta shaideni bana rantsuwa akan karya. Tace kina nufin shekaranki uku a gydan miji babu abinda yataba hadaku? nace to ko dai abunda sukeyi da suwaiba ne? tace meye? namata bayanin yadda nake ganinsu anan tayi salati. Tace kina nufin baku taba ba? nace ae. Taja numfashi tace godiya ya tabbata ga Allah. Baki da hakkinsu ne shiyasa. Bayan kwana uku yaya sule yaxo da bayanin saki. Aka taramu nida ahmed da yaya sule. Hardasu aisha.da yabi. Anan maigari yace yakamata aisha kema kije a gwadaki don abun kunya kam ahmed kajawo mana. Narasa ina kayi wannan wayewan dahar zaka fuskanci zina. Anan yayita mana waazi da ya tuba ga Allah yakuma nemi yafiyana. Sannan aje a gwadani.aisha tace ai abba ba abunda yataba shiga tsakaninsu. Ba abba ba gaba daya falon sun girgiza dajin wannan labarin. Abba cikin bacin rai yamike yafara naushinshi ko ta ina. Maigarine yarikoshi. Yace kabarni nakashe danbanzan yaro. Ya ajiye mata sama da shekara uku? sannan yaje nema a waje? inbanda dabba wake wannan halin! inaso ka sauwake mata aurenta yanxunnan. Ananfa ahmed yafara kuka don in akwai abinda ya tsana to bai wice wannan kalmanba. Shiyanxu ko namansa zaana yanka kullum.ya yadda indai zaina ganina. Amma ina a take yasha naushi saidaya sallama min. Yaya sule yatusa keyana mukayo garon abuja. BILKISU Sati na biyu a abuja hajja teema ta koyamin abubuwa da dama. Anan yaya sule yasani a makaranta ss1. Ana mana lesson a gyda anan ne naji ashe yaya sule dakyar sai da akayi rikici yaroka akabar teema na karatu. Nima gashi yaxo yasani. Na mayar da hankalina kan karatu nakuma dawo bulbul. Don yaya da matarsa jamsy suna lura damu. Yaya nada rufin asirinsa daidai gwargwado kuma baida hangen nesa. Yana da lura sosai musamman mu. Ahaka nakammala secondry. Yaya yanema min admsn a gwagwalada. Munje gombe nida hajja hutun sati biyu. Anan ne nasamu naga yadda ahmed yadawo. Hmn yazama abun tausayi . Yana kwance kashi ajikinsa yake kuda saibinsa suke. Ba mai damuwa da lamarinsa. Suwaiba kuwa annan nasamu lbrn ta haukace takashe yarta da kanta. Nikam nadan tausaya musu yabi kuwa rannan takiran saiban hkr take nace mata bakomai. Muna gama sati biyun mu. Muka dawo muka fara xuwa lectures. Sannu ahankali sai gani ina aji uku. Nawaye na yi clean nadawo abin kwatance ashe inada kyau. Samari kuwa tun part one dina suke bina. Bana kula kowa haka hajja ma. Yaya sule kam arxiki sai tubarkallah. Da umma na raye data huta. Kullum muna mata addua.yaya yanada ubangida. Sunansa alhaji baba shiyasa yaya hanyan kasuwanci. Yakai anty jamsy da yaua sule makkah. Yanxu haka bana yace zamuje muma . Alhaji baba dansa daya amir yana karatu a turai. Hakan yasa yadaukemu tamkar yayansa. Yaya yasamu a cathering skul kullum muna zuwa mudawo idan mundawo daga lectures. Anan munje sahad muna fitowa wani yataremu daga ganinshi ya manyanta kadan. Muka shareshi. Ya tsaya gabana. Inzan wuce sai yatare hakan yasa naja nima na tsaya. Munkai minti sha biyar ahaka. Sannan ya girgiza kai yace wato kice in matsa miki ne bazaki iyaba. Na kauda kai gefe. Nace kaima kasan yakamaceka basai nafada makaba. Yayi murmishi sannan yace kina cuna baki bakiga kyan dakikayiba. Na juyo da niyyan maganan muna hado ido ya kanne yace dama zakice namiki sharri ko. Kawai sai nafashe da daruya . Amma nayi mamakin kaina dana saurareshi. Mukaje mukashiga mota zamu tafi sai ya leko kansa. Dan bani wayanki nakira wayan namanta inda najefar cikin hanzari namika masa tareda cewa kiranan gun Allah yasa wani bai daukaba. Yana murmushi yakarba. Yadanna abin mamaki shine naji wayan na ringing a aljihunsa yayi.murmushi tare dacewa nagode da no. Kallonsa nayi tare da mamakin yadda komai yakemin dawayo. Muka tafi gyda. Kamshin turarensa ne a jikin wayan. Kowani.morsi kamshin nakeji . Inacikin tunani aka kirani. Da mamakina naga aminu nidai a tunanina nasan bantaba savn wani aminu ba narasa waye. Donhaka sai nadauka. Sallama nayi ya amsa tareda cewa. Kunkoma kokuma kin tsaya jirane? anan naganeshine. Nayi murmushi. Mukayi tadi sosai. Acikin wata biyu muka shaku da aminu sosai. Har yayi gaysuwa. Kowa a danginsa ansanni nima haka. Yanada hankali sosai baruwansa. Duk da saidayasha wahala kafin nasake jiki dashi nagayamishi ni bazawarace amma haryau bai yarda ba. Munfito daga cathering skul ina rike da cake dinda mukayi yau a matsayin test hankalina na kasa bansaniba na bangaje wani. Tsaf ajikinsa ta fashe gashi fararen kaya. Cikin rudu da gigicewa nadago ina bashi hakuri amma ga mamakina kallona yake tayi baya ko motsi hakan yasa na tsorata kar yace zaimin wani abu nida teema munkai minti sha biyar muna bashi hkr ganin baice komaiba baikuma dena kallona ba yasa naja teema muka wuce. Dasauri yashigo falon mahaifiyarahi tana zaune yashigo tamike amir lafiya? yace umma naganta. Umma naganta. Cikin rudu tace wadin ? yace naga habbi. Abun yabata tsoro to kodai yafara haukane? Yau akalla shekara shida kenan kullum yace yayi mafarkinta. Kasancewar baisan sunataba yasamata habbi. Duk yadda akayi yayi aure yakiyi sai yace yana jiran habbinsa. To yau yace yaganta a zahiri ada tadau aljana ce ta auri dan nata tunda har tafara neman magani amma yau yace mata yaganta. To kuwa ko yar waye insha Allah zatayi kokari tasan yadda zatayi ta aira wa danta. Shekaransa shida yana kiwon wannan yar.rarrashinahi tare da cemata yamata kwatancen gydansu yace mata shi baisaniba. Nanfa abun yakara bata tsoro. Alhaji baba yabiyamin da hajja aikin hajj. Zamu tafi jibi donhaka damu da anty jamsy da yaya mukaje kauye muka musu sallama. Sannan mukaxo gydan alhaji baba shima don masa sallama. Anty jamsy sungaysa kenan da hajiya sai take cewa amir yadawo shekaranjiya ai. Sai take cewa ayya gashi baixo mungaysa ba. Tace kibari kawai daga dawowansa jiya wai yahadu da habbi.anty jamsy tayi murmushi tace Allah yanuna mana habbin nan tarufa mana asiri kar danmu ya wahala. Suna haka hajiya tace hajj jeki kira shi yana daki . Tamike tafice nikuwa na sunkuyar dakaina. Ina danna wayana. Sallama yayi yashigo tare da gaushesi suka amsa. Nima nadago kai na gayaheshi juyowan dazaiyi ya amsa kawai naga yamike tare da cewa momy gatanan. Dukkanmi muka tsaya kallonshi yace ga habbin man ita nagani. Mony wlh itace nikam tashi na fita. Ina tafiya kaina na sarawa. To meyake nufi . Yana nufin ni ce wacce yakeso? tunda anty jamsy taban labarinsa akan yarinyan dayake kiwon sonta. BILIKSU. Salati naji hakan yasa nakoma dasauri suma yayi dasauri aka daukeshi akayi asibiti dashi. Nikam nagama rudewa koda aminu yakirani nagagara dauka. Hankakinshi tashe yaxo gyda akace masa bamunan. Anan alhaji baba da yaya sule suka dawo aka sanar dasu. Yaya sule yakira anty jamsy suna magana. Shi ko ta hannun alhaji kabiyo don neman auren wani nashi zai bayar balke kuma kanwarahi uwa daya uba daya wacce take zaune gunsa. Anan abun yadaure musu kai .gashi akwai mai nemana.. yaya ya yanke shawaran gayawa alhaji baba. dayagayamishi kuwa har durkusawa sai da alhaji baba yayi kataimaken suleiman. wallahi kai. shaida ne yaron nan shekara shida yana mafarkinta baitaba ganintaba. kataimaken. yaya yayi sairin durkusawa shima don Aplah alhaji kayi hkr katashi wlh bai daceba. nikuwa hajja teema ne take ban lbr irin fadan da akayi da amir a kaina. tunkan yasanni. har wani zane takawomin tabbas nine. amma hajja tace bamu taba kawowa ke bane. saidaya nunaki nadauki zanen nagane kece. don Allah sis kiyarda jiki a sanyaye nace a a aminu kuma fa. inyi yaya dashi?. tace duk sonda aminu kemiki wlh baikai na amir ba shiru nayi saboda tabbas bakowani namiji bane zai iya abinda amir yayiba. sallama akayi mai aiki tasanar dani aminu na nemana .nafita ranshi a bace yace meyasa baki daukan wayana? nace babu. kawai wani broda na ba lafiyane. yace ko so kike saikun tafi makkan bamu haduba anan nayi dariya. muka shirya. mukayi sallama dashi. washe gari muka tafi . muka sauka a jidda kafin mukaje makkah. munyi aikin hajj alhmdlh anan nazabi mafi alheri daga cikin manemana da gaggawa . muna dawowa bayan komai ya nutsa. aminu yadawo da maganan aurenmu. amir har gyda yaje yasameshi amma ina yayi kunnen shegu karshe kanma dawo da auren mu akayi sati biyu. nikam nadai san cewa amir yafi kwantamin arai amma bayanda na iya hala zabin Allah ne. ran daurin aure abun yaban mamaki danaga andaura nawa dana amir . hajja teema da aminu. ba karamin tsorata tayiba. kuka takesosai. tace shiya aketa gyaramin jiki? yaya suke yashigo yabata banbaki bansan meyace mataba naga ta hakura. nikuwa dadi naji sosai. bawanda yakai amir jin dadi a takaice dai. aka kawoni nn gydan dakikaxo domin amir na aikin companin petir anan cikin garin gombe yayana biyu. muna morewa. to yanxu nabaki labarina. hankalinki ya kwanta?