⭐ABBANA⭐ 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚* Daga Marubuciyar👇🏻 *Meenalyn Daddy *Oga Habib *Fadeela *Abdurrahim *In da rai *Daga Allah ko dora ma Kai *So ne sila *Rayuwar Haidar *Bakin kishi. By FADILA SANI Bakori GARGADI Ban yadda ba, ban kuma laminta ba, wani ko wata ya canza min labari, ko ya yi min amfani da shi ba tare da amince wata ba. Yin hakan kuskure ne babba dan haka a kiyaye. P 1-2 Bismillahir rahmanir rahim. Garin Kaduna, safiya ce, 8:00AM wanda ya yi daidai da 9/7/2025. Amma sakamakon tsananin hadarin da yake garin ya sa garin ya yi hudu. Gudu take Wanda babu waiwaye acikinsa bare kuma alamar gajiyawa, sai uban haki da take yi. A yanayin yadda take gudin kadai zaka kalla ka san ba cikin hayyacinta take gudin ba. Ga garin ya yi duhun hadari Wanda har an fara sakin ruwa kadan-kadan. Bisa ga alama, hakan ya sa mutane su ka yi Karan ciki a hanyar, duk an yi gudun ruwa. Zan iya cewa ita kadaice a hanyar wadda baka jin komai sai shashshekar hakin da take yi. Ja ta yi ta tsaya dan tsananin ruwan da ake yi ya sa har ba ta ganin hanya. layi ta fara kamar wadda ta sha ta bugu. Daga karshe dai jirine ya dibeta ta yanke jiki ta fadi a wajan. Ya zamana ruwan saman nan gaba daya kanta yake sauka. Bisa ga alama Kuma kamar ba a suma ta yi taba, dan tana jijjuya hannunta wanda da alama ta bugu da shi ne. "Yaya kalli can ka gani kamar mutum?" Cewar wata matashiyar budurwa da suke cikin mota wanda da alama tsananin ruwan da ake yi ne ya sa suka yi parking. Da kallo ya bi in da Amina ta nuna mai. Shiru ya yi yana kallan matashiyar budurwar da ke kwance a wajan, ga ruwa na sauka kanta babu alamar za ta tashi. Motarsa ya fara ƙoƙarin ja ya bar wajan, Amina da suke tare ta ce "Yayana, mutum fa na ce maka a kwance, Kuma kana ƙoƙarin jan mota." "Amina, me za mu yi mata ana ruwan nan? Wana irin taimako za mu iya yi mata mu da ba yan garin nan ba?." "Ko Asibitin garin nan Yaya sai mu biya mu mikata Mana, daga can sai mu wuce." Kallan baki da hankali ya yi Mata ya ce "Amina kin san Allah babu inda zani, zai yi wahala ma ba mahaukaciya ba ce, in da dai babu yadda za ai mai hankali ya kwanta a kasa a titi ruwa na bugunsa." Yana gama fadar haka ya ja motarsa ya bar wajan sakamakon ruwan saman ya fara tsagaitawa. "Laaa, Yaya kalli tana daga hannunta, Wallahi daga gani taimako take naima dan Allah mu tsaya mu yi magana da ita ko damuwarta mu ji Mana."Cewar Amina. Tsaida motar Abba ya yi, yana kallan Amina, ya ce "Ki je ki dubata ki yi maganar da za ki yi da ita babu inda zani." Amina sauka ta yi tana tafiya dari-dari kamar mai jin tsoran za a kamata, a haka har ta karasa in da matashiyar budurwan nan take kwance. Amina cikin tsoro ta ce "Baiwar Allah Lafiya kika zo nan kika kwanta?." Da sauri matashiyar nan ta tashi kamar zautatta ta rirrike Amina tana cewa "Ki taimaka min dan Allah, ki taimaka min." Amina tsayawa ta yi tana kare Mata kallo, a iya fahimtarta kamar ba babu alamun hauka a tare da ita, tsabar razana ne da tashin hankali ta hanga tare da ita. Ajiyar zuciya Amina ta sauke, ta ce na ji zan taimaka Miki, fada min da me kike so in taimaka Miki?." Matashiyar budurwan nan, babu abin da take cewa ma Amina sai "ki taimaka min." abin da take ce Mata kenan. Amina hannunta taja suka nufi motar yayanta da ita. Tun kafin su karasa ta fisge hannunta daga na Amina ta ruga ta shige cikin motar da yake a bude Amina ta barta ta dauke umbrella da za ta fita sakamakon ruwan da ake yi. Daga Amina har yayanta da mamaki su ka bi matashiyar budurwan nan da kallo, wadda kallo daya za ka yi Mata ka fahimci ba cikin hayyacinta take ba. Abba kallan matashiyar budurwan nan ya yi ya ce, "Lafiya wacece ke?" Maimakon taba Abba amsar tambayarsa, kallansa ta fara yi, can Kuma ta Fashe da kuka tana huna masu hannunta tana cewa "Na kasheshi! Na kasheshi!! Na kasheshi!!! Kun ga hannuna." Ta idasa maganar tana nuna masu fararan hannunta. Abba kallan Amina ya yi yana cewa "Amina, kin ga abin da kika jawo Mana ko?." Yanzu sai ki san yadda zaki yi ki fitar min da ita daga mota." Ajiyar zuciya Amina ta sauke tana mai Kuma kallan matashiyar budurwan nan da har yanzu abin da take furta wa kenan na kashe shi, Kunga hannuna. Amina handbag dinta ta bude ta ciro kudi tana mika ma matashiyar budurwan nan ta ce "Kawata amshi wannan ki je ki sai wani abu ki ci kin ji ko." Maimakon ta amshi kudin da Amina ke miko Mata, Kai ta fara girgiza ma Amina tana Kara tsananta kukanta tana cewa "Na kasheshi." Tana mai Kuma nuna masu hannunta da basu fahimci kamai ba a hannun da take nuna masu. Amina cikin karfin hali ta ce "Wa kika kashe?." Kuka ta Kuma fashewa da shi Maimakon taba Amina amsa, ta Kuma maimaita mata "Na kasheshi." Amina Kai ta girgiza tana kallan Yayanta ta ce "Yaya Abba, ya za mu yi da ita? bisa ga alama ma kamar ba cikin hayyacinta take ba." "Babu yadda za mu yi da ita, Kuma kinsan dai ba zai yuwu mu tafi Katsina da ita ba, kin ji dai furucin da ke fita a bakinta." "A'a, Yayana Ina ganin kamar furgici ne ya sa ta fadin haka, wannan daga ganinta ko kiyashi ba za ta iya kashewa ba, ka ga har yanzu ruwan bai tsaya ba, Ina ganin mu yi hakuri mu tafi da ita kafin ta dawo hayyacinta, na san ko mama ba za ta yi fada ba, inda ita ke horarmu da yin taimakon." Shiru Abba ya yi bisa ga alama nazarin maganarta yake yi. Amina hannun yayanta ta kama ta ce "Dan Allah yayana." Motar Abba ya ja suka tafi ba tare da ya ce komai ba. Suna tafiya matashiyar budurwan nan ta kwanta ta kama barci. Amina da yayanta da kallo suka bi ta. Ba ita ta farka ba sai suna gaf da shiga garin Katsina, ta tashi a gigice tana ƙoƙarin balle murfin motar ta fita. Amina ganin abin da take ƙoƙarin yi ya sa ta ce "Yaya Abba, tsaidar da motar nan tana ƙoƙarin budewa ta fita." Gefan titi Abbab ya koma ya yi parkin. Matashiyar budurwan nan Kuma bugun glass din motar ta take tun karfinta. Bisa ga alama dai kamar a gigice take. Wata uwar tsawa Abba ya yi Mata Yana Mai bude mata murfin motar ya ce "Fita! Idan tafiya kike son yi fita na ce." Cikin gigi ta fita tana mai rike Amina da itama ta fito daga cikin motar. "Wayyo Allah na kashe shi! Na kashe shi!!." Ta fada da karfi tana mai Kuma rirrike Amina tana nuna mata hannunta." Amina kafin ta yi magana sai ganinta su ka yi ta yanke jiki ta fadi sumammiya. Abba kuma cikin takaicin wahalar da suka dakko ma kansu da kansu ya kalli Amina ya ce "Kin ga wahalar da kika sa muka dakko ma kanmu ko?, Kiri-kiri Kinga tana naiman tara Mana mutane, yanzu sai ki fada min yadda za mu yi da ita?." Amina cikin sanyi ta ce "Yaya dan Allah ka kamata mu kaita asibitinku Mana a dubata." Abba cikin takaici ya ce "Kina da kudin da za a dubata a asibitin mu din ko?."Yaya Abba Ina da su, ka kamamin ita mu maidata mota dan Allah." Abba kafafunta ya kama a kyamace kamar ya taba kashi suka shimfidar da ita cikin motar. Sannan ya ja motar suka tafi. Tafiya kadan su ka yi ya danna hancin motarshi cikin wata private Asibiti da ke bakin hanya. Amina cikin sanyi ta ce "Yaya dan Allah mu kaita asibitinku Mana, ka ga can komai zai zo da sauki, nan fa asibitin kudi ce ni dai dan Allah ka kaita asibitinku." Abba ko saurarar Amina be yi ba ya danna hancin motarsa cikin Asibitin. Suna zuwa ya kalli Amina ya ce "Na gama iya nawa, saura na ki, fitar min da ita daga motata." Yadda Abba ya yi magana bai ba Amina damar sake neman wata alfarmarsa ba. Hakan ya sa itama bata Kuma cewa komai ba ta fita daga cikin motar ta nufi cikin asibitin, babu jimawa suka taho da gadon da aka tana da dan taukar marasa lafiya. Da taimakon malaman Asibitin aka sa baiwar Alllah nan gadon da suka ta nada dan daukar marasa lafiya. Amina kallan Yayanta ta yi ta ce "Yaya daga an dubata zan taho nima." Shi dai ko tankama Amina bai yi ba ya ja motarsa ya tafi. Tafiya kadan ta Kai Abba gida, kasancewar babu nisa sosai tsakaninsu da Asibitin da ya Kai 'yar tsuntuwar tasu. Ana ta sallar la'asar hakan ya sa Abba bai shiga gida ba sai da ya yi Sallah sannan. Yaran kanwar Abba na jin parking din motarshi suka ruga da gudu suna mai oyoyooo. Take Kuma suka fara waige-waigen Amina ganinsa shi kadai. Amira ta ce "Yaya Abba Ina mommy Amina fa?." Abba murmushi ya yi masu ya shafa kan Sadik ya wuce ba tare da ya basu amsa ba. Mahaifiyarsu Amina da kallo ta bi Abba ganin ransa kamar a bace yake Kuma ba ta ga Amina ba, bacin ko lokacin da za suka taho sun yi waya da Aminar. Bayan ya zauna ta kallai ta ce "Abbana, ya na ganka Kai ka dai, Ina Aminar fa?." "Mama, ina tsoran Kar tausayin Amina ya jefata a wani halin." Nan Abba ya kwashe duk abin da ya faru ya sanar da mahaifiyar tasu. "Ikon Allah, ni ban san kalar zuciyar Amina ba, Kuma Abbana har da laifinka, taya zaka biye mata ku dakko yarinya tun daga garin Kaduna har nan Katsina, haba Abbana, sai ka ce baka san wacece Amina ba. Ni Kam na yarda da hausar nan da ake cewa wai d'an gado ya fi magaji. Haka mahaifinku yake da tsantsar tausayin nan amma Amina har ta fisa. Yanzu Abbana hakuri za ka yi in ka ci abinci ka koma kar yarinyar nan ta jawo Mana wata masifar. Abba ya San idan ya ce ba za shi ba mahaifiyarsa za ta yi ta yi masa magiya, har sai ya yadda ya tafi, hakan ya sa ya barta a zai je. Yana gama cin abincinsa ya kama hanya ya fita. Har dare mahaifiyar Amina ta ji shiru-shiru basu dawo ba, ba Abba ba Amina, Kuma ta Kira wayar Abba bai dauka ba, Amina ma haka ta Kira wayarta bata shiga. Mahaifiyar Amina tana zaune tana zagaye madaidaicin falonsu ganin har 8:30 babu ko mutum daya a cikinsu. Tana a haka Allah ya shigo da Abba. Tun kafin ya karaso ta ce mai, "Ina Amina?." Gaban Abba faɗuwa ya yi dan bai dauka ba har lokacin Amina bata dawo ba. " Ka je ka zo min da ita yanz..." Shiru mahaifiyarsu Amina ta yi sakamakon sallamar Amina da ta ji. Amina da sallamarta ta shigo falon tare da matashiyar budurwar da suka tsinto ita da yayanta. Mahaifiyar Amina da kallo ta bi Amina da matashiyar da suke tafe da Amina. Wadda sai zare ido take tana kallan mahaifiyar Amina. Amina cikin sanyi ta ce "Mama, kin jini shiru, ki yi hakuri tafe muke da bakuwa matsala ta fada Kuma sai da muka biya asibiti aka dubata." Mahaifiyar Amina dai bata ce komai ba, kallan yarinyar da ke tafe da Amina ta yi, tana mamakin yadda take kallanta ba tare da ta gaidata ba. Mahaifiyar Amina cire mamakinta ta yi ta kalli matashiyar nan ta ce " 'Yan Mata ya sunanki?." Shiru babu amsa, Kuma babu wata alamar da ta nuna bata ji ba, dan kallan Mahaifiyarsu Amina take yi. Amina ganin haka tashi ta yi ta dafa kafadarta ta ce "Kawata bi ki ji ba, Mamana na tambayarki sunanki ba? Ya sunanki?." Ido ta daga tana kallan Amina, sannan a hankali ta ce "Mansura." Amina kallan mahaifiyarta ta yi ta ce "Mama, kin ji wai sunanta Mansura." Mahaifiyar Amina shiru ta yi, sannan ta ce "Amina ku shiga ciki ta yi wanka ta ci abinci sai mu ji daga Ina take." Amina hannun Mansura ta kamo ta ce "Kawata, zo mu je ki watsa ruwa ki ci abinci ki Sha magungunanki." Amina ta fadi maganar tana kamo hannun Mansura, Mansura Kai ta girgiza ma Amina alamun ba za ta ba. Babu yadda Amina bata yi da ita ba, Amma taki yadda ta tashi ta bi Amina, daga karshe ma sai ta yi kwanciyarta kan caution din da take. Daga Amina har Mahaifiyarta da Abba da ke tsaye duk mamaki ya cika su. Mahaifiyar Amina kallan Mansura ta yi, ta ce a'a, ki tashi ki je ki ci abinci ki Sha maganinki tukun sai ki kwanta din." Mansura shiru ta yi kanta sama daga gani ma ta yi nisa a duniyar tunani ba jin abin da Mahaifiyar Amina ta ce ta yi ba. Abba da ransa ya fara baci ganin yarinyar kamar tana naiman raina masu wayau, ya ce "Ke! ba da ke ake magana bane, ba zaki tashi ba ana miki magana dan samun waje kin yi banza da mutane." Ya yi maganar cikin tsawa sosai wanda ba Mansura ba har Amina sai da ta firgita. Mansura ko da ba jin abin da ya ce ta yi, ita dai ta ji ya yi Mata tsawa, hakan ya sa ta tashi ta rirrike Amina jikinta na rawa. Yadda take rawar jiki kawai zai nuna maka ba Karamar furgita ta yi ba. Tana Kuma zare manyan idanunta. Amina ganin haka janta tayi suka nufi bedroom dinta da ita. Suna zuwa Amina da kanta ta hada Mata ruwan wanka, Amma babu dabarar da wayan da ba ta yi Mata ba taki yi, dole ta rabu da ita, ta kawo Mata abinci shima ko kallansa ba ta yi ba bare Amina ta sa ran zata ci. Amina ganin taki cin Abincin, Kuma taki shan maganin hakan ya sa ta kalleta ta ce " Ki dauki maganin ki Sha ko in je kin Kira miki yayana in ce kin ki shan magani." Mansura Kai ta girgiza ma Amina tana daukar maganinta ta Sha. Abincin ko babu wayan da Amina ba ta yi Mata ba Amma taki ci, har cewa ta Kuma yi zata Kira Mata yayanta, sannan ta samu dakyar ta yi 1 spoon. Tana gamawa ta kwanta a wajan Amina dai kasa ce Mata komai ta yi ganin ko Sallah ba ta yi ba. Tana kwanciya Kuma kamar an tsakureta ta tashi ta shiga bathroom din dakin bata jima ba ta fito, ta koma inda ta tashi ta kwanta. Amina na nuna Mata bed dinta amma ko kallanshi ba ta yi ba ta kwanta kasa. Amina Kuma wanka ta fara yi, kafin ta ci abinci dama kuma Sallah take yi ba. Amina na gamawa ta fita falon sakamakon kiranta da Mahaifiyarta ta yi. Amina zaune ta iske Mahaifiyarta da yayanta da alama dai suna tattaunawa ne game da bakuwar da su ka yi. Mahaifiyar Amina kallan Amina ta yi ta ce "Amina me kika fahimta game da yarinyar nan ?." Ajiyar zuciya Amina ta sauke ta ce "Mama, Wallahi har yanzu ban yi magana da ita ba, ban da sunanta da ta fada mana har yanzu ban San komai game da ita ba. Amma gaskiya kamar yadda likitan da ya dubaya ya yi min bayani har yanzu bata cikin hayyacinta, dan ina da karancin kudi ne ma amma sansamu tana da bukatar kulawar likita a halin da kwakwalwarta take ciki yanzu, kamar yadda likitan ya ce, Amma likitan ya ce mu ci gaba da janta a jiki har a samu ta warware ta dawo Normal Sense dinta." "A Wana gidan za a ci gaba da lallabata har ta dawo normal sense din nata?." Cewar Abba. Amina shiru ta yi, kafin ta ce "Yaya Abba dan Allah ka yi hakuri ko kwana uku mu bata mu gani. "Hmmmm, Amina kenan, kina Sara baki duba bakin gatari, yanzu dunuyar ce ta canza mutun mugu ne, Amma koma meye inda kin jajibota ya za mu yi dole mu yi hakuri mu bata nan da kwana biyu mu gani." Shi dai Abba bai ce kamai ba, inda yasan mahaifiyarsa ma halinta daya da Aminar, ba iya korarta za ta yi ba. Sai yanzu ma yake ganin laifinsa da ya biye ma Aminar suka dakkota. Amina ma sanadiyar gajiya da ta yi hakan ya sa tafiya ta yi ta je ta kwanta. Cancikin dare ihun da Mansura ke yi ya tada ilahirin mutanan gidan daga dogon barcin da suke yi. Ihu take tana Kiran "Abbana!, wayyo Abbana!!." Amina da sauri ta rirriketa tana tambayarta lafiya. Ita ko tun karfinta ta dage ta ture Amina tana Mai Kuma Kiran Abbanta da karfinta. Wanda mahaifiyar Mansura shigowarta kenan ta ci karo da ingizar da Mansura ta kaima Amina da ke ƙoƙarin riketa, ana cikin haka ne Abba m ya shigo dakin a rude yana tambayar lafiya. Amma ganin wadda ke ihun take ransa ya bace. Bai San sanda ya kamo Mansura ba yana girgizata ya ce "Ke! wacece ke da za ki zo cikin daran nan ki hana mutane barci kina Mana ihu cikin dare haka! Ko so kike ki tara Mana mutane ne?." Mansura ko bata fasa kukan Kiran Abbanta da take yi ba, sai dai yanzu ta rage sautin Kiran bakamar dazun ba. Abba hannu ya daga zai mareta, mahaifiyarsa ta yi sauri ta rike hannunsa ta ce "Kul, karka mareta, baka ga ba cikin hayyacinta take ba, ina jin ma kamar mafarki ta yi." Abba zafin mahaifiyarsa ta hanasa Marin Mansura ya sauke hannunsa akan fuskar Amina dake tsaye ba zato ta ji mari. Ya ce "Duk ke kika jawo Mana, Kuma Wallahi kin ji na rantse gobe karki yadda in dawo aiki in iske yarinyar nan a gidan nan, idan ba haka ba Wallahi! Wallahi!! Wallahi!!!, Kin ji na rantse Wallahi sai ranki ya yi munmunan ba ci na dawo na isketa a cikin gidan nan ✍🏻 Fadila Sani Bakori ce 🤗 Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LGosWoHsPkj3rhf9EbKjrK ⭐ ABBANA⭐ 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚* Daga Marubuciyar 👇🏻 *Meenalyn Daddy *Oga Habib *Fadeela *In da rai *Abdurrahim *Daga Allah ko d'ora ma Kai *So ne sila *Rayuwar Haidar *Bakin kishi Follow the ABBANA channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaYZGsNEFeXsr1CKQl3r P 3-4 Amina kwana ta yi tunanin yadda za ta kuri Mansura. Washegari, Amina bayan ta idar da sallar asuba kallan Mansura ta yi dake kwance babu alamar zata tashi. Amina bubbuga kafar Mansura ta yi ta ce "Kawata, ki tashi ki yi Sallah mana, ko kina hutu ne?." Mansura shiru ta yi bata tanka ma Amina ba, karshe dai Amina gajiya ta yi ta rabu da ita ta nufi bedroom din mahaifiyarta. Zaune ta isketa kan abin Sallaya tana lazimi, Amina zama ta yi har mahaifiyarta ta kammala laziminta. Amina cikin sanyi ta ce "Ina kwana mama." Lafiya lau Amina, ya bakuwarki ta tashi kuwa?." Cewar mahaifiyar Amina. Amina cikin damuwa da lamarin bakuwar tata ta ce, "Wallahi mama, nama rasa yadda zan yi bata tashi ba, jiya ma fa ko Sallah ba ta yi ba ta kwanta, yau ma na ga ba ta yi Sallah ba." Murmushi mahaifiyar Amina ta yi ta ce "A'a rashin sallarta ba damuwa ba ce kila tana hutu ne, ni dai yanzu Amina ya kike ganin za a yi da yarinyar nan? Kin ji dai abin da yayanki ya ce Kuma kin san halinsa." Amina shiru ta yi dan sosai ta rude da gargadin yayan nata tasan halinsa sosai. Kallan mahaifiyarta ta yi ta ce "Wallahi mama gaba daya tun jiya barci ya kaurace min, Ina tunanin yadda zan yi da ita, dama ban rabota da garinsu ba dada sauki." "Amina, ni yarinyarce sai inga kamar bata da hankali, anya ba ciwan hauka take ba? Yanayin yarinyar ni dai ya fi min kama da ciwan hauka." Cewar Mahaifiyar Amina. "Tom kila, Amma dai a asibitin da Yaya Abba ya kaimu sun fi danganta abin da razana, da tsananin damuwa, Kuma nima nafi yadda da haka kamar damuwa ce ta yi Mata yawa. Ni dai mama duk ba wannan ba, ya zan yi da ita kin ji dai abin da Yaya Abba ya ce min?." Mahaifiyar Amina Kai ta jinjina kafin ta ce, "Amina kin San dai halin yayanki, ba ƙaramin aikin shi bane ya kamaki ya buga akan yarinyar nan, dan haka idan za ki ji tawa ga kudi ina da su ki amsa daga gari ya Kara haske ki je ki sata a motar Kaduna ki dawo." Amina kamar za ta yi kuka ta ce "Wallahi Mama likitan da ya dubata ya tabbatar min ba cikin hankalinta take ba, ya ce mu bata nan da kwana biyu mu gani kila ta dawo cikin hankalinta. Dan Allah Mama ki yi ma Yaya Abba magana, Allah bashi daga ta dawo hankalinta sai ta tafi garinsu, dan Allah Mama mu tausaya Mata ba mu San halin da take ciki ba, daga ka ganta ka ga wadda razani da tashin hankali ya bayyanar Mata,Wanda daga gani shi ne silar damuwar nan tata." Mahaifiyar Amina shiru ta yi, sannan ta ce "Amina ba Wai naki bane, rayuwarce me wuya, kina ganin abin da ya faru da gwaggonki kwanakin baya daga taimako yarinyar nan ta yashesu, ga abubuwa nan dai da yawa wa inda muke jin labari sanadin taimako." "Mama ba fa duka aka taru aka zama daya ba, Kuma shi kenan saboda haka sai ka ga mutum cikin ƙunci kaki taimaka masa? Wannan dai daga ganinta Mama munsan tana bukatar taimako, Amma ni ba nace dole sai mun taimaka Mata bane, ina naiman alfarmatar mu bata nan da kwana biyu ta dawo natsuwarta koda za mu koreta, dan yanzu ko mun koreta ba lalle ne ma ta san inda zata ba, inda ba cikin hayyacinta take ba." Amina ta isa maganar tana kallan mahaifiyarta. Ajiyar zuciya mahaifiyar Amina ta yi ta ce "Shi kenan, amma ya za mu yi da yayanki? Kin ji dai rantsuwar da ya yi in ya dawo ya isketa a gidan nan." "Mama sai mu hanata fita falo inda dai Yaya Abba ba shigowa bangaremu yake ba." Amina ta idasa maganar tana langwabe kai, alamun mahaifiyarta ta tausaya Mata. "Shi kenan Amina, idan za ki iya tsareta ba zata fita falo ba, amma fa ki sani babu ruwana idan yayanki ya Kuma ganinta gidan nan?." "In Allah ya yadda ma ba zai ganta ba." Amina ta fadi maganar tana tashi ta fita. kitchen ta shiga ta soya doya ta dafa ruwan Lipton ta kaima mahaifiyata, ta zauna suka karya tare kafin ta hada na bakuwarta ta Kai Mata nata. Da mamaki Amina ta bi Mansura da kallo ganin har yanzu bata tashi ba tana nan a yadda ta barta. Amina hannu tasa tana bubbuga Mansura ta ce "Mansura, ki tashi Mana haka nan." Ido Mansura ta daga tana kallan Amina alamun ba barci take ba. Amina murmushi ta sakar Mata ta ce, "Ki tashi Mana ki watsa ruwa ko za ki ji dadin jikinki, ga abin breakfast na kawo Miki." "Na koshi." Mansura ta ce a hankali. Amina da mamaki ta kalleta ta ce "Kin koshi? Jiya ma fa biki ci komai ba kika kwanta, a'a dan Allah, ki tashi ki ci ko babu yawa." Amina hannun Mansura ta kamo ta ce "Mu je ki yi wanka za ki ji dadin jikinki, sai ki yi breakfast." Mansura bin Amina ta yi har bathroom din ba tare da ta so ba, Amina hada Mata ruwan wankan ta yi , sannan ta fito ta barta. Shiru-shiru Mansura bata fito ba, Amina jin shirun ya yi yawa ya sa ta matsa kusa da bathroom din ta ce"Mansura, kin gama wankan ne?." Mansura da tunda ta shiga tsugunne take tana kuka sai lokacin da ta ji Amina ta kirata kafin ta tashi da sauri ta yi wankan ta fito. Amina cikin kayan sawarta ta dakko wata goguwar riga ta ba Mansura. Amina da kyar ta samu Mansura ta sha tea din kadan, soyayyar doyar ko ko kallanta ba ta yi ba. Amina sosai take ƙoƙarin jan Mansura a jiki dan ta ji damuwarta, amma duk abin da za ta ce sai dai Mansura da kalleta da ido. Dole ta hakura ta rabu da ita. A haka Mansura har ta yi kwana uku har yanzu ba su san ko wacece ba, dan jiya mahaifiyar Amina da ta matsata mata da tambaya kuka tasa Mata, hakan ya sa dole suka rabu da ita. Yau kwanan Mansura uku kenan agidan, Kuma har yau Abba bai san tana gidan ba. Yanzu haka Abba zaune suke shi da mahaifiyarsa suna fira. Abba kallan mahaifiyarsa ya yi ya ce "Mommy nifa kamar kuka nake ji?" Mahaifiyar Abba da tun dazun take jin kukan, tana sane sharewa kawai take dan kar Abba ya fahimci har yanzu Mansura na gidan, shi ya sa ta yi shiru, dan tasan Mansura ce ke kuka. Abba jin mahaifiyarsa bata ce komai ba, ya ce "Kai mama, wannan kuka ne." Kallan Amira ya yi ya ce " Amira je ki gani Ina Amina." "Uncle Abba, ba fa Mommy Amina ba ce ke kuka, bakuwar nan ce wadda mommy Amina ta zo da ita ke kuka, haka take yi kullum sai na ganta tana kuka, mommy Amina da Mama su yi ta bata hakuri amma taki yin shiru.". Abba da mamaki ya kalli mahaifiyarsa ya ce "Mama, dama yarinyar nan har yanzu tana gidan nan?." Abba Mai da kallanshi ya yi ga Amira ya ce "Amira Kira min Amina." Amira da gudinta ta je ta kira Amina. Amina ko dama baki daya a tsorace take, jin yadda Mansura ke kuka da karfi ta San yayanta na gida zai iya ji. Yanzu haka hakuri take ba Mansura tana cewa, "Mansura dan Allah ki rufa min asiri ki yi shiru, Yaya Abba ya dawo yanzu kar ya jiki." Suna cikin haka ne Amira ta shigo ta ce, "Mommy Amina, Uncle Abba yana kiranki." Amina zaro ido ta yi tana kallan Amira, sannan ta ce "Amira Yaya Abba na falo ko?" Eh, Yana falo, shi ne ya tambaya wake kuka, na ce mai bakuwarki ce ke kuka, shi ne ya ce in kiraki." Tun kafin Amira ta gama Kai bayani Amina ta fara goge zufa, dan tasan yau mai kwatarta hannun yayan nata sai Allah. Amina har zata fita ta kalli Amira ta ce "Amira mama na falo?." Kai Amira ta daga Mata. Amina da addu'a ta idasa falon. Can falon ko, mahaifiyar Amina ta dage sai ba Abba baki take tana cewa "Abba, ni na ce Amina ta bar yarinyar nan ta wastsake tukun, Kuma ta wastsake, dan tun ranar da ka ce ta koreta ta yi niyyar zuwa ta sata a mota ta tafi, ganin halin da yarinyar take ciki na ce ta barta ta warware." Abba dai baice komai ba, dan yasan mahaifiyarsa ta fadi haka ne dan Kar ya bugu Amina. Suna a haka ne Amina ta shigo falon a tsorace. Kafin Abba ya yi magana, Amina ta ce "Yaya Abba, dan Allah ka yi hakuri." Abba be cema Amina komai ba, sai zuwa can ya ce, "Amina kinsan dai baki taba nuna kina son abu ba naki ko?." Kai Amina ta daga Mai. Ya ci gaba da cewa. " Tun da yarinyar nan ta zo gidan nan bayan sunanta kun Kara sanin wani abu akanta?." Nan ma Amina Kai ta girgiza ma Abba, alamun ba su sani ba. "Amma Kuma shine ke gaki shugabar masu tausayi duk da haka kina tausaya Mata, ba zaki iya barinta ba ko?" Ya ci gaba da cewa "Yanzu Zamani ya lalace Amina fiye da yadda kike tunanin, wama ya Sani kila wani takashe ta gudu, dan da bakinta ta furta Mana haka, Kuma kin ga in ta tabbata haka ne mun boye mai laifi kenan. In dai baki so mu samu sabani Ina so gobe ki sallami yarinyar nan ta bar gidan nan, ni baki daya hankalina bai kwanta da lamarinta ba." Abba 10k ya dakko ya ba Amina ya ce "Gashi, ki kaita tasha gobe ki sata a motar Kaduna." Amina cikin jin dadin ganin yayan nata bai mata komai ba ta ce "Na gode yayana Allah ya Kara arziki." Tana fadar haka ta tashi ta tafi. Abba Kuma kallan mahaifiyarsa ya yi ya ce "Mama, dan Allah ki yi hakuri idan na saba miki na korar yarinyar nan da na yi."A'a Abbana, baka saba min ba, ni kaina zaman yarinyar ma na naiman samin damuwa, in da dai ita har yanzu taki fada Mana ita wacece, daga sunanta bamu san komai ba game da ita, garama ta tafi, ita wannan uwar masu tausayin na samu in samu kanta." Haka dai Abba suka kare fira da mahaifiyarsa da sunan washegari za a kuri Mansura. Washegari Amina da wuri ta tashi ta yi masu abin breakfast, ta kawo ma bakuwarta nata. Mansura tea din tasha kadan, bread din ko ko kallansa ba ta yi ba. Amina na gamawa ta sa Mansura ta yi wanka bayan ta bata kaya ta sa, Amina ta kalleta ta ce, "Mansura, yanzu zan kaiki tasha ki shiga motar Kaduna ki tafi garinku, za ki gane in da zaki ko?." Mansura mai makon taba Amina amsa sai ta fashe ma Amina da kuka. Sosai ta ba Amina tausayi. Amina dafa ta yi ta ce "Baki son tafiya gidan ne?." Kai Mansura ta daga ma Amina. "Me ya sa biki son tafiya?." Amina ta tambayeta tana mai kureta da ido. Nan Kuma Mansura shiru ta yi bata tanka ma Amina ba. Amina hannun Mansura ta kama tana ja alamar ta zo ta rakata tasha ta sa ta a mota, Amma Mansura taki ta cije tana kuka. Amina babu yadda ba ta yi da Mansura ba ta tashi su tafi amma taki tashi karshe daga zata kama hanunta ita Kuma ta make hannunta taki yadda ta kama. Amina ganin haka wajan mahaifiyarta ta je, cikin damuwa ta labarta Mata abin da ke faruwa. Mahaifiyar Amina da mamaki ta ce "Ka ji min yarinyar, to mu ya za mu yi da ita, yanda Abba ya nuna damuwarsa da zamanta gidan nan ai ba zai yuwu ba, dole za ta yi hakuri ta tafi. Mu je in yi magana da ita." Mahaifiyar Amina ta dade tana kallan Mansura da ke uban kuka har da majina. Cikin sanyin murya mahaifiyar Amina ta ce "Yata, ki yi hakuri kin ji, Amina ta je ta saki a mota ki tafi gidanku." Mansura dai babu abin da take sai kuka sosai take kuka har da Majinarta. Amina da babu wuyar kuka ganin haka itama sai ta fashe da kuka. Mahaifiyar Amina Kuma duk sai ta shiga damuwa yadda ta ga Mansura na kuka, hakan ya nuna mata bata son tafiya ne. Mahaifiyar Amina cikin sanyi ta kalli Mansura tana mai dafata ta ce "Shi kenan, ya isa, ki yi shiru, fada min me ya sa biki son tafiyar?." Nan na Maimakon Mansura ta bata amsa sai kuka. Mahaifiyar Amina ta ce "Ai kin ji abinda ke hada ni da ke, ki yi shiru ki fada min me ya sa baki son tafiyar?." Babu yadda mahaifiyar Amina ba su yi da Mansura ba amma taki Magana sai kuka. Mahaifiyar Amina hannun Mansura ta kama ita kanta sai ta ji duk ba dadi ta mika ma Amina ta ce "Amina maza ku je ki sata a mota ta tafi." Amina kama hanun Mansura ta yi suka fita. Suna fita gidan, Mansura ta tsugunna kusa da get din gidan ta tusa kanta a tsakankanin kafafunta tana kuka. Babu yadda Amina ba ta yi da ita ba ta tashi su tafi amma taki, dole Amina ta gaji ta rabu da ita ta koma gida, ta sanar da mahaifiyarta abin da ke faruwa. Ajiyar zuciya mahaifiyar Amina ta sauke ta ce "Amina kin ga dai in da mun samu ta fita daga gidan nan shi kenan, duk da Wallahi duk na ji babu dadi kukan nata, ta bani tausayi sosai, to Amina rayuwarce sai a hankali Kai kanka ba ka gama maganin kukanka ba bare ka yi ma wani." Amina dai bata ce komai ba ta nufi bedroom dinta ta kwanta, saboda kanta dake Mata ciwo, dan tun jiya ba wani barci tayi ba, kwana ta yi tunanin Mansura. Kasan cewar Amina jiya ba wani barcin kirki ta yi ba, hakan ya sa tana kwanciya barci ya dauketa. Amina ba ita ta farka ba sai 1:50Pm, ana ta kiraye-kiran Sallah. Tashi ta yi ta fara gabatar da Sallah, sannan ta nufi hanyar fita gidan. Mahaifiyar Amina da ke kitchen Kiran Amina ta yi ta ce "Ina zaki kike sauri haka?." Mama, lekawa zan yi in ga Mansura na nan ko ta tafi." Shiru mahaifiyar Amina ta yi tana kallan Amina, ta san indai ta je ta Kuma ganin Mansura ba ta tafi ba za ta zo ne ta sa kanta cikin wata damuwar, hakan ya sa ta ce "Bana son shirme me za ta tsayayi tun dazu, ga abincinki can ki je ki ci." Amina cikin sanyi ta juya ta koma, in da ko tana nan ma babu wani abu da za ta iya Mata, tasan ita ta jawo ma kanta, kila da ta fada masu ita ko wacece ba ta jin yayanta ma zai koreta. Misalin 80:00PM Abba ya dawo wajan aiki, kamar yadda ya saba dawowa kusan kullum. Da mamaki ya ke kallan Mansura da bai gane kowacece ba, ya ga dai mutum a zaune ta tusa kanta a tsakankanin cinyoyinta. Abba fita ya yi daga motar daboda da kansa ya ke bude ma kansa get ya shiga da motarsa. Da mamaki ya ce "Ke! Lafiya? Me kike yi a nan?." Ya fadi maganar da karfi. Mansura ko da tun maganar farko ta gane muryarsa cikin tsoro ta tashi ta matsa da sauri ta bar wajan get din nasu. Abba da mamaki ya bita da kallo dan ya ganeta. Kallo daya ya yi Mata ya fahimci tsoran da ta shiga na ganinshi din da ta yi. Abba Matsawa ya yi har inda Mansura take, tsugunnawa ya yi ya na kallanta, Wanda ita Kuma Bata san yana yi ba, saboda ta tusa kanta a tsakankanin cinyoyinta. Cikin mamaki ko dare bata tsoro Abba ya ce "Me kike yi anan? Biki ji saukona bane ba, na ce Amina ta kaiki tasha ki shiga mota ki tafi garinku ba?." Mansura cikin tsoro ta ce "Zan tafi." Tana fadin haka ta tashi ta tafi✍🏻 Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LGosWoHsPkj3rhf9EbKjrK ⭐ABBANA⭐ 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚* Daga Marubuciyar 👇🏻 *Meenalyn Daddy *Oga Habib *Fadeela *In da rai *Abdurrahim *Daga Allah ko d'ora ma Kai *So ne sila *Rayuwar Haidar *Bakin kishi Follow the ABBANA channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaYZGsNEFeXsr1CKQl3r P 5-6 Abba tsugunnawa ya yi kusa da Mansura ,ya ce "Me kike yi a nan, baki ji saukona bane ba, na ce Amina ta kaiki tasha ki shiga mota ki tafi garinku ba?." Mansura cikin tsoro ta tashi ta ce "Zan tafi." Tana fadin haka ta tafi.. Abba tsayawa ya yi yana kallanta, so yake ya juya ya tafi amma Kuma ya kasa, ganin dare ne, gashi ba garinsu ba ina zata yanzu, hakan ya sa Abba ya bi Mansurar, wadda daga gani tafiya kawai take amma ba ta san inda zata ba. Abba shan gabanta ya yi ya ce, "Muje." Mansura juyawa ta yi ta bi bayan Abba. Abba da sallama ya shiga falon mahaifiyarshi, inda ya iske mahaifiyarshi da Amina zaune. Amina da Mahaifiyar Amina da mamaki suka bi Mansura da kallo. Abba zama ya yi ya nuna ma Mansura kuda da Amina ya ce "Zauna." Zama Mansura ta yi gefan Amina tana zare ido. Abba kallan Amina ya yi ya ce ,"Amina me ya sa baki kaita tasha ba kamar yadda nace?." Amina cikin raurau da fuska ta ce "Yaya Abba, Wallahi ka tambayi mama shirya zan rakata muna fita ta takure a bakin get taki tafiya." Abba mai da kallanshi ga Mansura ya yi ya ce "Wacece ke? Kuma me ya baro da ke daga gidan iyayanki?." Mansura kuka ta fara har tana shashsheka. mahaifiyar Amina dafa Mansura ta yi ta ce "Ki yi shiru Yata, ki fada Mana wacece ke?" Mansura dai ba ta ce komai ba, ta ci gaba da kukanta. Abba ransa fara baci ya yi, ganin kamar tana so ta raina masu wayau, daga tambayeta wacece ita sai kuka, hakan ya sa ya daka mata tsawa ya ce "Wacece ke nace? Ba kuka aka tambayeki ba." Ba Mansura ba hatta Amina sai da ta tsorata da tsawar da Abba ya yi ma Mansura. Mansura take jikinta ya fara rawa ta kasa magana, Wanda ita kanta tsoran shirun nata take ji. Amina a hankali ta ce "Mansura dan Allah ki natsu ki yi magana, Kinga ke Yaya Abba ke saurare. Shirun naki zai jawo ya yi miki wani zargin wajan Yaya Abba, ki yi magana dan Allah." Mansura cikin sarkewar harshe ta ce"Sunana Mansura, mamana da babana sun yi accident ne suka mutu." Mansura ta idasa maganar tana Kuma rushewa da kuka. Amina sarkin tausayi itama kukan ta fara. Abba shiru ya yi, kafin zuwa can ya ce "A'ina dangin baban naki suke." "Ba nida su, babana gudin hijira ya yi, a hanyarmu ta zuwa Kaduna ne muka yi accident din." Abba kwatakwata zuciyarsa ba ta gamsu da maganar Mansura ba. Amma ganin yadda mahaifiyarsa da Amina suka yadda ya sa bai ce komai ba. Mahaifiyar Amina cikin tausayin Mansura ta ce "Ki yi hakuri kin ji ba kuka za ki yi ba Addu'a za ki yi musu, Allah ya jikansu, Amina kamaya ku shiga ciki." Amina hannun Mansura ta kama suka shiga tafi. Abba kallan mahaifiyarsa ya yi ya ce "Mama ni fa ban yadda har yanzu da yarinyar nan ba, babu wani kamshin gaskiya a kalamanta." Mahaifiyar Abba zuba ma Abba ido ta yi tana mamakin furucinsa, ta ce "Abbana, babu abinda ka rage a halin mahaifinka, tabbas na yadda barewa Bata gudu danta ya yi rarrafe, haka mahaifinka yake shima bashi da yadda, Amma in ba haka ba meye na karyata, ko yana yin halin da yarinyar kadai take na furgici da razana ai ya ci ya sa ka yadda da maganarta. Ni yanzu abin da nake so da kai ka yi hakuri mu barta ta zauna tare damu har zuwa wani lokaci, alabashi idan ta aikata wani abu Wanda ba mu gamsu da shi ba sai mu koreta." "Tom ba damuwa mama, Allah ya sa mu dace." Abba ya fadi haka yana tashi ya nufi bangaransa. Haka rayuwar Mansura ta ci gaba da wakana a gidan. Sosai Amina ke bakin ƙoƙarin ta wajan ganin ta jawo Mansura a jikinta ganin ta kauda Mata damuwarta, Amma Ina abin ya ci tura. Amina ko fira ta kawo ma Mansura da ido kawai take binta har ta gama. Amina ganin haka ya sa ta watsar da Mansura. Mansura Kuma ganin Amina ta watsar da ita sai ta dawo tunaninta, duk Kuma sai ta damuwa, dan tasan sosai Amina ke bakin ƙoƙarinta ganin ta sata farin ciki. Mansura kallan Amina ta yi da ta yi banza da ita, yau tun da suka tashi bata tanka Mata ba, hakan ya sa Mansura ta ce "Amina yau tare za mu shiga kitchen kinsan ban iya girki ba Ina so ki koya min." Amina da murmushi ta amsa ma Mansura dan tun da ta zo gidan magana mai tsayi ba ta taba shiga tsakaninsu ba sai yau. Hakan ya sa Amina da murnarta ta ce "Tom zo mu je mu yi girkin, dama yanzu nake shirin shiga kitchen din." Koda suka shiga kitchen din, Mansura da kallo kawai take bin Amina inda ba iya girki ta yi ba, ko in zata dauki wani abun ta mika mata, a haka suka gama girkin. Tare suka ci duk da Mansura ba wani abun kirki ta ci ba. Da daddare suna zaune babu mai cema kowa koma. Amina datse shirun nasu ta yi ta ce "Mansura gobe zan koma makaranta, hutun mu ya kare, da yake Ina koyarwa. Yanzu idan na koma ya za ki yi Kinga mama Islamiya take zuwa, ke kadai za a rika bari a gida, ko in yi ma Yaya Abba magana ya sa ki a islamiyarsu mama zata debe miki kawar kadaici, ya fi mu tafi mu barki a nan ke kadai." A'a, ni dai bana so." Cewar Mansura. "A'a Mansura ba zai yuwu ba a barki ke kadai, kadaici damuwa zai Kara Miki. Ina kika tsaya a school?." Diploma certificate garan. "Yauwa, tom ko in ma Yaya Abba magana ke ma ko teaching ne ya Samar maki, inga kin huta zaman kekadai" Mansura turo baki ta yi ta ce "Ni dai bana so." Amina hakuri ta yi ta rabu da Mansura, haka Amina tai ta jan Mansura da hira, har ta ji Mansurar ta yi banza da ita alamun ta yi barci, dama Kuma daga, Eh, sai a'a, Mansura take yi a firar. Amina jin ta yi shiru alamun ta yi barci ya sa itama ta kwanta. Washegari, Amina da wuri ta tashi ta yi masu abin breakfast. Bayan ta shirya, tada Mansura ta yi ta mika mata wayar ta ce "Dear ga wayata nan ta debe miki kewa." Tana Bata ta tafi. Mansura ba ita ta tashi ba sai da ta ji yunwa na naiman takura mata kafin ta tashi ta yi breakfast, ta koma ta kwanta. Zaman kadaici sai ya je fa Mansura a duniyar tunani, inda gaba daya tunanin mahaifinta ya fado Mata rai. Mansura kuka ta fara, tun tana yi kadan-kadan har ta fara yi da karfi. tana cewa"Wayyo Abbana, Allah ka jikanka Abbana, Allah ya fe maka. Allah ba dan halina ba ina rokanka Allah ka samin nazuwa a rayuwata. Allah ka cire min damuwa da furgicin da ke damuna. Allah ka dandana min farin ciki koya yake kafin ruhina jikina ya yi ban kwana da gangar jikina nima. Wayyo Abbana." Mansura kuka take sosai da majina tana turje-turje tana Kiran Abbanta. Abba da shigowarshi gidan kenan, tun kafin ya karaso yake Kiran layin Amina. Amma Mansura da yake kukanta take sha ko ringing wayar ma bata ji ba. Abba jin yadda Mansura ke kuka tana Kiran Abbana, da sauri ya yi bedroom din Amina, dan shi ya za ci ma Amina ce ke kuka. Abba cikin gigita ha hau kan bed din da Mansura take tana bubbuga kadon tun karfin tana Kuma Kiran Abbanta. Gashi Kuma ta kudindi ne kanta cikin blanket din. Abba da gaba daya ya manta da wata Mansura dan tun ranar da ya dawo da ita bai sake ganinta ba, hakan ya sa gaba daya ya dauka Amina ce. Abba da sauri ya kamo Mansura yana cikin tashin hankalin halin da ya ganta ci, ya ce "Amina, lafiya? Me ya same ki? Wa ya taba ki kike kuka haka?." Mansura da gaba daya ta cukuykuye kanta da blanket , hakan ya Kuma batar da Abba itace, gashi dama kusan kirarsu daya da Amina. Abba cikin jin haushi ya fara fada Yana cewa"Amina kashe kanki kike son yi ne da za ki cukuykuye kanki haka." Yana maganar yana ƙoƙarin fito Mata da kanta. Mansura take natsuwa ta shigeta ta hadiye kukanta, ta yi tsit kamar an kashe inji. Abba da mamaki da yake bin Mansura da kallo wadda idonta ya yi jajir tsabar kukan da ta yi. Abba cikin tausasa murya ya ce "Me akai miki?." Mansura shiru ta yi tana yin kasa da kanta. Abba dago kan Mansura ya yi ya, ya Kuma maimai ta Mata tambayar, "Me aka yi miki?." Mansura goge hawayanta ta yi ta ce kamar za ta yi kuka, bakinta na rawa saboda tsoran Abba take. Cikin shashekar kuka ta ce "Abbana." Shiru Abba ya yi yana kallanta, kafin ya ce " Ina Abban naki yake?." "Ya mutu ya barni." Mansura ta fada tana Kuma fashewa da kuka. Abba cikin son kwantar mata da hankali dan ya san yadda mutuwar mahaifi take ya ce, "Ki yi hakuri kin ji, ba kuka ya kamata ki zauna kina yi masa ba. Abbanki bai yi gaggawa ba lokacinsa ne ya yi, addu'a ya kamata ki rika yi masa. Daga yau Kar in Kara ganinki kina Mai kuka, Kin ji ko?." Kai Mansura ta daga tana goge hawayanta. "Yauwa, good girl." Abba sauka gadon ya yi ya na cewa "ki shiga kitchen ko taliya inda tafi sauri ki dafa min, zan yi bako, dama Amina na yi niyyar sawa tom na zo Kuma ashe ta yi resume school yau, ki yi sauri dan Allah." Abba ya fadi maganar yana fita. Ba tare da ya bata damar cewa komai ba. Mansura turi baki ta yi ta ce "Ni ai ban iya girki ba." Mansura ta ce tana sakkowa daga kan bed din. Kitchen ta nufa, tana zuwa ta samu tukunya ta kusa cikata da ruwa, sannan ta zuba mai ya kusa kwalba, ba soyawa ba komai, ta daddaka tarugu da albasa suma ta wasa. Ruwan ko zafin kirki bai yi ba ta zuba taliyar. Magi ko duk magin da ke kitchen din babu Wanda ba ta sa ba, stone fishi din da ta gani shima ta dauka ta maka a ciki. Ta zauna zaman jiran ruwan taliya ya kone ta sauke taliyar. Taliya sai da ta zama kamar fate kafin Mansura ta sauketa. Ta dakko Plate ta zuba. Bangaran Abba, abokinsa har ya iso, Abba kayan sanyi ya fara kawo ma abokin nasa, kafin ya nufi bangaransu Amina zuwa dakko girkin Hajiya Mansura. Abba kitchen din ya je inda suka ci karo da Mansura da ke ta ƙoƙarin fitowa. Abba da kallo ya bita ya ce "Ina abincin fa?." Mansura plete din taliyar ta dakko ta mika ma Abba tana addu'ar Allah ya sa ya yi masu dadi. Abba amsa ya yi ya ce "Thanks." Yana zuwa ya aje ma Ahmad ya ce"Bismillah." Masoyiyarka ce, Taliya. Ahmad murmushi, kafin ya ce , "Na Kira number Amina Bata daga ba ko za ka Kira min ita." Ahmad ya fadi maganar cikin damuwa. "Kasan ta fara koyarwa, ba a dade ba na naiman manta koyarwa a wata primary nan kusa damu. Tom yau a gida ta bar wayar nima na kirata bata daga ba sai da na shiga naga wayar tata." Ahmad shiru ya yi bai ce komai ba. Abba Kuma Abincin ya Kara mika ma Ahmad ya ce "Ka ci abinci mana." Ahmad langabar da Kai ya yi ya ce "Zanci, Amma kafin sai na amayar maka da abin da ke cikina, inda Kai dan iska ne ka kasa fahimtata. Usman, ina son Amina ba tun yau ba, dan na jima da gabatar da kaina a wajanta, yanzu haka nai man aure na zo." Abba da mamaki ya kalli Ahmad ya ce "Wai da gaske?Kana yawan min maganar Amina Amma Wallahi ban taba kawo haka ba, sai na ga kamar ta yi Karama." Ahmad hararsa ya yi ya ce "Tsohuwa kake so in aura kenan." "Yanzu dai ba haka ba, ka ci abinci sai mu je makarantarsu Aminar." Ahmad bude taliyar ya yi, ba tare da tunanin komai ba ya diba tare da yin Bismillah ya afka a bakinsa cike da saukin maganar Amina da ya zo da ita, sai dai Ahmad duk yadda ya so ya daure ya hadiye abincin kasawa ya yi, ga uban yaji ga Magi bau. take ya furzar da abincin. Abba Kuma bai kawo komai ba a tunaninsa Ahmad kwarewa ya yi, hakan ya sa ya diba shima ya Kai bakinsa, ai har gara Ahmad ma Abba da gudu ya ruga toilet dinsa ya zubar da abinci ga uban shakewa da ya yi tsabar tsananin yajin da ke cikin taliyar. Abba da kyar ya samu kansa bayan ya kwankwali ruwa. Ahmad kallan Abba ya yi ya ce "Usman wa ya yi wannan girkin haka?." Hmmm, Wallahi wata sangartattar yarinya ce, mu je restaurant mu ci abinci." Restaurant mai tsada Abba ya kaisu suka ci abinci. Kafin suka nufi makarantar da Amina ke koyarwa. Amina da mamaki ta bi Ahmad da kallo dan ko jiya sun yi waya da shi Amma bai fada Mata zai zo ba. Amina ba sarwa ta yi ta ce "laa, Yaya Ahmad, yaushe ka zo?." Ahmad maimakon ya Amina amsa motar Abba ya nuna Mata ya je mu je." "Ina zuwa bari in zo." Amina cikin makarantar ta koma ta sanar da headmastern makarantar kafin ta fito suka tafi. "My Meena , ya hayaniyar yara." Alhamdullh ya Ahmad ya hanya." Lafiya lau." Amina Koda suka shiga gida, hannu kawai ta daga ma Mansura ta shige bathroom ta watsa ruwa da sauri ta fito. A gaggauce Amina ta Sha fa lotion dinta, ta jira doguwar rigar lass dinta. Mansura kallan Amina ta yi ta ce "Dear, unguwa za ki kika sha gayu haka." Amina zama ta yi kusa da Mansura ta ce "Dear Ina Wanda kike ji muna waya da shi kullum, shi ne ya zo abokin Yaya Abba ne." "Okay, dazu ko Yaya Abba ya sani na yi masa girki Allah ya sa ya yi masa dadi ma." Ameen, tashi mu je ku gaisa." Mansura shiru ta yi Amma har ga ranta ba ta ji dadin zuwan ba. Amma ba ta iya musa ma Amina hakan ya sa ta tashi suka fita tare suka nufi bangaran Abba, tana sanye da brown abaya a jikinta. Da sallama suka shiga in da suka iske Abba da Ahmad zaune suna hira. Mansura cikin girmamawa ta gaida Ahmad, sannan ta juya da sauri za ta tafi. Amina rike mata hannu ta yi ya sa ta dakata. Abba Kuma tashi ya yi ya basu waje. Amina kallan Ahmad ta yi ta ce "Ga sabuwar sisterna da nake baka labari." Ahmad cikin fara'arsa suka gaisa da Mansura. Mansura Kuma da ta jita duk a takure tashi ta yi zata tafi ta ce "Dear bari in shiga ciki." Amina plate din taliyar da Mansura ta dafa ta gani, Wanda tana gani ta fahimci girkin da Mansura ta fada Mata Yaya Abba ya sa ta yi ne. Amina kallan Mansura ta yi ta ce "Dear ki tafi da kayan nan." Mansura dawowa ta yi ta dauki plate din abincin. Abba Kuma falon mahaifiyarshi ya dawo ya zauna wanda da itama shigowarta kenan. Kallan Abba da ta yi ta ce "Abbana, ya na ganka Kai kadai bayan na ga mota a gidan." Murmushi Abba ya yi ya ce "Yarki ce ta yi bak'o." Kai mahaifiyar Amina ta jinjina, ta ce "Aminar ta yi bak'o bani da labari, hala Kai ta fada maka ne?." Abba gurin zama ya nuna ma mahaifiyarsa ya ce Mama zauna ki ji." Mama na zama Mansura ta yi sallama ta shigo rike da plate din taliyar da ta dakko. Mansura kallan Mama ta yi ta ce"Sannu da dawowa Mama." Tana fadin haka ta juya za ta tafi. Mama kiranta ta yi ta ce "Mansura a binci ne a plate din nan?."Eh Mama taliya ce." Mansura ta bata amsa. "Yauwa bani in ci." Mansura mika ma mahaifiyar Amina taliyar za ta yi Abba ya kalli Mansura ya ce "Ke kin ci ne?." Kai Mansura ta girgiza. Abba waje ya nuna ma Mansura ya ce "Zauna ki ci."A'a na koshi." Mansura ta idasa maganar tana mika ma Mahaifiyarsu Abba plate din taliyar. "Diba ki ci." Abba ya umarci Mansura. Mansura ba tare da gaddama ba ta yi 1 spoon. Tun shigar taliyar bakinta tasan an samu matsala, duk yadda ta so ta daure ta hadiye ta bakinta kasawa ta yi, hakan ya sa ta furzar da taliyar a hannunta, tana ya mutsa fuska, ga uban ya ji da har kwakwalwarta sai da ta amsa. Mansura tagowa ta yi ta kalli Abba Wanda shima ita yake kallo✍🏻 Fadila Sani Bakori ce. Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LGosWoHsPkj3rhf9EbKjrK ⭐ABBANA⭐ 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚* Daga Marubuciyar 👇🏻 *Oga Habin *Fadeela *Meenalyn Daddy *In da rai *Abdurrahim *So ne sila *Bakin kishi P 7-8 Abba a natse ya ce ma Mansura "Ke da kika dafa kinkasa ci Ina ga mu." Sannan ya maida kallanshi ga mahaifiyarshi ya ce, "Mama, dazufa na dawo gida dan sa Amina ta yi man girki, na iske bata nan, shi ne fa na sa yarinyar nan, shi ne ta dafa taliyar nan" Abba kallan Mansura ya yi ya ce "Shi kenan, za ki iya tafiya, dama na sa ki ci ne dan ki ji kalar abin da kika dafa ma mutane" Mansura da sauri ta tafi tana turo baki. Bayan ta tafi, Mahaifiyar Abba, kallan Abba ta yi ta ce, "Haba, Abbana haka ai gwalisa ne, ina laifin Wanda kaba aiki ya tashi ya yi maka." Abba dai bace kala ba, ya canza firar da cewa" Mama, Ahmad fa naiman aure ya zo, wai Amina yake so, so na aure." Murmushi mahaifiyar Abba ta yi ta ce "Abba akwai son da ba na aure bane, ni dama ba tun yau ba na fahimci yaron nan yana son Amina. Amma gaskiya na ji dadin jin labarin nan, dan Ahmad yana da hankali sosai. Don haka, babu abin da zance sai dai fatan alkairi in da itama Aminar na fahimci tana sonsa, dan na dade da fahimtar suna waya." Abba Kam mamaki ya yi dan bai taba dauka haka ba. Abba sun dade suna fira da mahaifiyarsa kafin Kiran Ahmad ya shigo wayarsa. Abba na dagawa Ahmad ya ce "Mama nake so ka zo ka yi min iso in ingaida, ka ga yanzu ta zama sirikata kunga nake ji." Malam, bana son kinibibi, Ina ita Aminar take ? Ta rakoka Mana." Abba na fadin haka ya kashe wayarsa. Amina ita ta yi ma Ahmad iso ya zo ya gaida mahaifiyrata har falonta. Ahmad dai ya kasa sakin jikinsa kamar yadda ya saba da. Mahaifiyar Abba kallan Amina ta yi ta ca"Tom lokacin Sallah ya yi maza ki je ki yi." Bayan Amina ta bar falon ne, mahaifiyar Amina, ta kalli Ahmad ta ce "Ahmad, na ji wani sako wajan Abba, Kuma ya yi min dadi sosai, Ina muku fatan alkairi." Ahmad cikin jin kunya ya amsa da "Ameen." Kafin ya yi ma Mata sallama dan yau zai koma. 10k ya ciro a ajjihunsa ya aje ma mahaifiyar Amina. Bayan sun fita Abba ya kallai Ahmad ya ce "Yanzu sai k.d, kenan?." Bari kawai, kasan na dade ban je gida ba wannan Karan......." Su Abba sun jima suna tattaunawa kafin Ahmad ya Kira Amina suka yi sallama. 10k itama ya faba ya tafi. Haka rayuwar Mansura ta ci gaba da wakana a gidan har ta fara sakin jikinta, amma duk da haka dai da wuya ka yi doguwar hira da ita. Yau ya kama weekend, mutanan gidan duk suna gida. Amina kallan Mansura ta yi ta ce "Dear ki shirya ki rakani Mama zata aike mu Mani wajan Aunty Zainab, za mu Kai Mata magani, da yake tun da kika zo ba ta zo ba, ita ke bima Yaya Abba, da yake tsohon ciki gareta Kuma tana shan wahala shi ya sa mama ta hanata zuwa sai ta haihu. Mansura shiryawa ta yi cikin daya daga cikin kayan Amina suka fito za su tafi. Inda suka iske Abba zaune a falon. Mahaifiyar Amina kallan Amina ta yi ta ce "Har Kun shirya?." Maganin ta dauka ta mika ma Amina ta ce "ku bata ,na yi Mata bayanin yadda za ta yi amfani da shi a waya." Amina har sun juya za su tafi, Abba ya ce "Karku Kai dare." Misalin karfe 10 su Amina suka shiga gidan Aunty Zainab. Amira murna ta yi sosai ganin Amina. Kallan Aunty Zainab ta yi tana nuna Mansura ta ce "Mommy kinga Mommy mai kuka da nake baki labari." Aunty Zainab da ke zaune da katoton cikinta, kallan Mansura ta yi ta na murmushi ta ce "Sanninku da zuwa Mansura, sai yau Allah ya yi za mu hadu." Mansura murmushi ta yi ta ce"Yauwa Aunty Zainab ya karfin jikin." Alhamdulillahi." Amina kallan Aunty Zainab ta yi tana turo baki ta ce "shi kenan, in da ni baki ganni ba." Dariya Aunty Zainab ta yi ta ce"Na isa ince ban ga autar mama ba. Haushi kika ban, Amina tun ranar fa da za ku Kaduna rabona da gida sati na 7 muke kenan. Amma shine ko kilekoni, yanzu ma nasan da mama ba ta Aiko ki ba da ba ganinki zan yi ba. "Aunty Zainab, sai ka ce kin manta waye Yaya Abba." "Ba wani Yaya Abba, ki ce dai kin samu k'awa kin rabu dani, idan kina son zuwa bani kike sawa ba in yi ma Abban magana ba." Tom Auntyna Afuwa, ba zan sake ba." Yanzu dai bani da wani abu na ci, ke Kuma Amina na San ba son abinci mai aiki kike ba, ni Kuma lallura tasa na Bilki nake ci, idan ba za ku ci nata ba ku shiga kitchen ku girka Mana baki daya." Su Amina sun jima suna fira da Aunty Zainab da yake mai firace, kafin Amina ta tashi ta shiga kitchen ta yi masu jallop din cous-cous. Amina ba suka fito gidan Aunty Zainab ba sai da aka yi sallar la'asar. Suna fitowa suka ga garin ya yi bakikkirin na hadari, tsananin hadarin da Aunty Zainab ta gani ya sa ta hanasu Amina tafiya. Ruwa aka yi sosai, sai 5 ruwan ya tsaya. Aunty Zainab babu yadda ba ta yi da su Amina su tsaya su kwana ba Amma Amina taki. Kasancewar ruwan da aka yi hakan ya sa suka samu tsaikon abin haka. Har Magriba ba suna tsaye babu mota. Da yake gidan Aunty Zainab ya na a bakin titi ne, Amina kallan get din gidan Aunty Zainab ta yi ta ce " Anya ko dear ba gidan Aunty Zainab za mu koma mu kwana b..." Amina bata rufe baki ba wata tsaleliyar mota ta saya kusa da su. Matashin saurayin tambayarsu ya yi Ina za su. "Cikin gari zamu shiga." Ku shigo mu tafi nima can na yi." Shiga suka yi ya ja suka tafi. Koda suka shiga cikin garin Katsina tambayar sunan layin su Amina ya yi, nesa da gidan su Amina ya yi parking ya saukesu, inda Amina ta bukata. Suna sauka yana son yi masu magana amma Amina bata bashi damar yi masu magana ba ta ja hannun Mansura da sauri suka wuce. A baya ya bisu ya ga gidan da suka shiga kafin ya dawo. Abba a kan idonsa aka sauke su Amina a mota zai shiga sallar isha'i kenan. Amina Kuma bayan sun shiga gida, kallan Mansura ta yi ta ce "Dear Yaya Abba zai tambaye mu dalilin da ya sa muka Kai dare, idan muka ce mai mun fito za mu tafi kenan, aka fara ruwa zai yi fadan me ya sa muka Kai la'asar, dan haka ce mai za mu yi tun da mu je ake ruwa." Da "to". Mansura ta amsa ma Amina suka shiga gidan. Koda suka shiga kan dadduma suka iske Mahaifiyar Amina, bisa ga alama sallar issha'i ta idar. Mahaifiyar Amina dago kanta ta yi ta kalli Amina ba ta ce mata komai ba ta maida kanta kasa. Amina zama ta yi tana fuskantar mahaifiyarta, cikin sanyi kamar za ta yi kuka ta ce "Mama Wallahi ki Kira Aunty Zainab ki ji muna fitowa aka tsuge da ruwa, kin ji dalilin da ya sa muka Kai dare." "Amina, ba tun yau ba kinsani bana son kai dare, nikam babu ruwana tsakaninki da yayanki, ko kafin ku fita sai da ya jaddada miki karku Kai dar..." Sallamar Abba ya sa Mahaifiyar Amina yin shiru. Mansura ko da ke tsoran Abba, hakan ya sa ta tashi zata shige bangaransu, jin sallamarshi. Har ta tafi Abba ya dakatar da ita ya ce "Ke." Mahaifiyar Abba kallan Abba ta yi ta ce "A'a Abbana, laifin Amina ne ita bata da laifi in da ba ta san dokar gidan nan ba. Mansura tafi abinki." Mansura saida ta sauke ajiyar zuciya tsabar jin dadi. Abba cikin fushi irin Wanda Amina ta sanshi da shi ya ce "Amina waya kawoku a mota?." Amina kallan mahaifiyarta ta yi tana langabar da kai ta ce "Mama Wallahi tun da muke je ake ruwa, shi ya sa muka rasa mota, shine dalilin da ya sa ma Koda ya yi Mana ta yi ma muka shiga motarsa ganin dare ya yi." Marin da Abba ya kaima Amina ne ya sa ta yi shiru ba tare da tasan ta yi shiru ba. Hannu Abba ya daga da sunan Kuma Kai Mata wani Marin mahaifiyar Amina ta rike hannunsa ta ce "Abbana inda ta ce ruwa akayi akwai uziri." Abba Kai ya girgiza ya ce "Wallahi mama karya take acan na yi sallar ajahar sai 3::00PM Na bar garin, Kuma lokacin haɗarin ba wani sosai bane bama. Kin ga sai yamma kila ma aka fara ruwan." Abba shako wuyan Amina ya yi ya ce"Su waye suka saukeku a mota?." Amina ihu take tana ba Abba hakuri. Wanda ko jinya baya yi, dan shi babu abin da ya tsana Kamar yaga yarinya na yawo a motar saurayi, atunaninsa haka yana taka mahimmiyar rawa wajan lalacewar tarbiya. Hakan ya sa Abba ya shake Amina Yana cewa "Ba zaki fada min ba su uban waye suka daukeku a mota?." Amina ko zare ido kawai take ta kasa magana yadda ya shaketa. Allah sarki uwa, mahaifiyar Amina kasa jurewa ta yi,ta kamo hannun Abba dake wuyan Amina ta yi ta ce, "Abbana, aika shaketa ba zata iya magana ba, ka saketa sai mu ji Wanda ya daukesu a motar." Abba sakin Amina ya yi wadda yana sakinta ta samu damar fashewa da kuka. Mahaifiyar Amina Kuma, tsawa ta yi ma Amina ta ce "Dan ubanki ba za ki fada Mana uban waye ya daukeku a motar ba?." Cikin kuka Amina ta yi masu bayani ta hada da cewa "Wallahi yana kawo mu yana tambayarmu Number waya, Amma ko sauraransa ba mu yi ba muka tafi." Abba Kai ya jinjina ya ce "Daga nan har ki bar gidan nan Allah ya sa wani dan isa ya Kara kawoki a mota, Wallahi tallahi ranar ba za a gane kamanninki ba." Yana fadin haka ya fita ya bar falon baki daya. Mahaifiyar Amina Kuma fada ta Kara yi ma Amina. Amina da kuka sosai ta shiga bangaransu, inda ta iske Mansura sai zare ido take, kallo daya za ka yi Mata kafahimci a tsorace take. Amina fadawa ta yi kan gadon tana kuka. Mansura dai bubbuga bayan Amina taita yi tana Kuma bata hakuri. Amina ta dade tana kuka kafin ta tashi tana nuna ma Mansura wuyanta ta ce "Dear duba min wuyana ki ga bai ji min ciwo ba?." Mansura duba mata ta yi, cikin tausaya Mata ganin yanda wajan ya yi ja na rikewar da ya yi Mata ta ce "Sorry dear." Ranar nan dai haka suka yi barci babu wata hirar kirki, uwa uba Kuma ga sanyi damuna, ga Kuma bacin ran dukan Amina hakan ya sa da wuri suka yi barci. Washegari, misalin karfe 7:00AM, mahaifiyar Amina ta samu Amina har dakinsu, bayan sun Kuma gaidata ta kalli Amina ta ce "Amina, Ina fatan Ahmad ya sanar da ke yau danginsa za su je wayan 'yan uwan mahaifinki naiman auranki?." Amina zaro ido ta yi tana mamaki dan ko yau shi ya tadata sallar asuba Amma bai fada Mata ba. Mahaifiyar Amina Kuma jin Amina bata ce komai ba, ta ce "Amina, ba da ke nake magana ba?." Amina cikin sanyi ta ce "A'a Mama bai sanar min ba." Shiru mahaifiyar Amina ta yi kafin ta ce "Tom Ina fatan babu wata matsala?." Eh, mama Babu." Cewar Amina. Ajiyar zuciya mahaifiyar Amina ta sauke ta ce "Tom ma Sha Allah." Sannan ta tashi ta fita. Mansura gaba daya jikinta sai ta ji yayi sanyi, tana tunanin yadda zata ci gaba da zama gidan idan Amina ta yi aure. Amina lura da tunanin da Mansura ta fada ne ya sa ta dafa Mansurar. Mansura kallan Amina ta yi, ta yi murmushi ta ce "Amarya, Allah ya kaimu lokacin." Ameen, dear kema Allah ya fito miki da naki ayi tare, bana son in tafi in barki a gidan nan ke kadai, Ina nan ma kullum cikin ƙoƙarin sama kanki damuwa kike Ina ga bana nan." Mansura sosai jin maganar Amina za ta yi aure ta daga Mata hakankali, dan tana tunanin yadda za ta rayu gidan babu Amina, Ina bata jin ma zata iya ci gaba da zama babu Amina. Take Mansura ta fara waye wani kan wani. Amina jin kamar shashshekar kuka da sauri ta dago tana kallan Mansura. Bata fuska Amina ta yi ta ce, "Haba, Mansura yanzu Kuma anan meye abin kuka, auran da ko sashi ma ba a yi ba, yau ne za a sashi, Kuma ke baki fatan Allah ya kawo mik naki kafin mawa a hada a yi." Ai Amina kamar ta ziga Mansura fashe Mata da kuka ta yi. Amina baki ta saki tana kallan Mansura, ganin abin da gaske take ya sa Amina ta fara lallashinta ta ce "Ki yi hakuri dear, nima bana son in tafi in barki ke kadai ne, in sha Allah ni Kuma na yi miki alkawari har sai kin samu miji ko zan yi aure, zanma Yaya Ahmad magana a sa lokacin da tsayi har lokacin da Allah zai fito miki da naki kema." Amina ta dade tana baansura baki kafin ta yi shiru. Misalin 5:00PM kanin mahaifinsu Amina ya yi sallama ya shigo falon mahaifiyar Amina. Bayan sun yi gaisuwa mai tsayi cikin mutuntawa da mahaifiyar Amina, ya dora da cewa "Tom Alhamdulillahi, baki sun iso kamar yadda suka ce. Duk wani Abu da ake bukata na sa ranar aure kudi suka bata gasu a hannuna. Mun sa ranar aure wata uku cif-cif, ya kika gani?." "Haba baban yara, ai duk yadda kuka yi Wallahi ya yi, sai dai mu yi fatan Allah ya kaimu lokacin. Kayan aure Kuma kar kice tsaki takura ma kanki, ki bar Komai a hannuna da Abba za mu yi." Godiya sosai mahaifiyar su Abba ta yi mashi, kafin suka yi sallama ya tafi. Bangaran Amina da daddare suna waya Ahmad ya ke sanar da ita lokacin bikinsu da aka sa musu. Amina zaro ido ta yi jin ya ce Mata wata uku. Tom Amma Kuma tana tsoran ta yi wata magana Mansura ta ji hakan ya sa ta yi shiru ta bari ta yi ma mahaifiyarta magana, inda akwai fahimta sosai tsakaninta da mahaifiyarta. Washegari, Amina ta samu mahaifiyarta da maganar. Amina kanta a kafadar mahaifiyar tata kamar za ta yi kuka ta ce "Mama ni dai lokacin auran nan da aka sa gaskiya ya yi kadan, dan Allah mama ki yi ma Yaya Abba magana ya yi ma Baban yara magana a Kara." Mahaifiyar Amina dago da kan Amina ta yi tana kallanta, dan ta gasgata abin da Amina ta ce. Shiru mahaifiyar Amina ta yi, kafin ta ce "Kamar ya wata uku ya yi kadan?." Amina kamar za ta yi kuka, ita dai duk dan mahaifiyarta ta sausaya Mata ta yadda da kudirinta ta ce "Mama kin ga idan na tafi na bar Mansura ba za ta ji dadi ba, da ni kadai ta saba a gidan nan. Amma kin ga yanzu idan aka Mai da shekara kafin itama Allah ya bata nata sai a hada a yi." Mahaifiyar Amina kallan baki da hankali ta yi ma Amina kafin ta ce"Amina ke ma lokacin da ta zo gidan ai ba sabawa ta yi da ke ba, sai a hankali-a hankali kuka saba, muma a hankali-a hankali za ta saba da mu daga taga baki." Ni dai gaskiya mama bana son in tafi in barta." Amina ta fada tana share hawayanta, ita dai duk dan mahaifiyarta ta tausaya Mata ta barta ganin bata son kukanta. Mahaifiyar Amina ido ta tsura ma Amina ganin tana share waye. Hannu tasa ta goge hawayanta ta ce "A'a abun ai Bai Kai haka ba Amina, kin ga Abba shi ne abokin Ahmad, Kuma lokacin da aka sa auran ba daga kowa ba ne daga Ahmad ne, shi ya bukaci haka, dan haka ki je ki samu Abba ki yi masa magana ya yi ma Ahmad magana a d'aga lokacin auran har zuwa lokacin da Mansura ta samu muji itama✍🏻 Fadila Sani Bakori ce. https://chat.whatsapp.com/LGosWoHsPkj3rhf9EbKjrK ⭐ABBANA⭐ 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚* Daga Marubuciyar 👇🏻 *Fadeela *Oga Habib *Meenalyn Daddy *In da rai *Abdurrahim *Daga Allah ko d'ora ma Kai *So ne sila *Rayuwar Haidar *So ne sila Domin samun littafin ABBANA daga farko 👇🏻Follow the ABBANA channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaYZGsNEFeXsr1CKQl3r P 9-10 Amina da zummarta ta tashi ta nufi bangaran Abba, zata shiga Abba Kuma zai fito ya yi shirin aiki. Amina cikin girmama yayan nata ta gaidashi ba Kuma kamar yau ba da take naiman alfarma agunsa. Abba amsawa ya yi yana kallan Amina, wadda yanayinta ya nuna tafe take da magana. Amina kallan Abba ta yi da shima ita yake kallo ta ce"Yaya Abba, dan Allah ka koma ciki za mu yi magana." Abba agogon hannunsa ya kalla ya ce "Amina, lokaci ya ja zan makara aiki, ki bari in nadawo sai mu yi maganar."Tom yayana Allah ya dawo da kai lafiya." Amina na fadin haka ta juya, da Sauri-sauri itama ta yi breakfast ta tafi aiki. Ya zamana gidan zai Mansura kadai, wadda duk lokacin da aka barta ita kadai kadaici sosai yake bankado mata rayuwartar. Ba kamar yau ba da gaba daya ta hana kanta sukuni tun da ta ji maganar auran Amina, gani take ba zata iya zama babu Amina ba, dan a iya tunaninta darajar Amina ma ya sa aka barta ta zauna gidan, tom ta ya Kuma za ta cigaba da zama babu Amina. "Wayyoo Allah na, ya zan yi? Ina zan koma da zama. Ya Allah ka kawo min daukin wannan tsillatsillar rayuwar da nake shirin fadawa. Allah ka iyakamce min haka nan, ba dan halina ba ko abin da na aikata, Allah ka dubeni da idon rahama." Mansura kuka take sosai na rayuwarta. Mansura tun da ta zo gidan ba ta yi kukan da ta yi yau ba, uwa uba ga damuwar da ta sa ma ranta na auran Amina. Hakan sai ya taru ya yi Mata yawa, Wanda take ya saukar mata da zazzabi. Kwance take duk ilahirin jikinta rawa yake tsabar zazzabin da take ji, ga gidan babu kowa sai ita kadai. Amina ma da ke banmata wayarta ta bar banmata, saboda ko ta bar Mata ba amfani take da ita ba, hakan ya sa ta bar barmata. Inda dama tana banmata ne dan ta debe mata kewa. Mahaifiyar Amina Koda ta dawo daga Islamiyar da take zuwa ba ta yi tunanin zuwa duba Mansura ba, in da dama ita ba ma'abociyar zaman falon bace. Hakan ya sa zazzabin ya ci gaba da rukurkusar Mansura, ga amai da take ta famar yi, Wanda hakan ya hadu ya Kara galabartar da ita. Amina ba ita ta dawo gidan ba sai 1:30PM kamar yadda ta saba dawowa kusan kullum. Amina Koda ta dawo da yake hankalinta na kan ta watsa ruwa ta yi Sallah, shi ya sa hankalinta bai kai kan Mansura ba dake kwance tana rawar sanyi. Amina ba ita ta lura da halin da Mansura take ciki ba har sai da taga Mansurar ta tashi ta ruga bathroom dinsu tana kwara amai. Amina da idar da sallar ta kenan, tashi ta yi tana kallan Mansura, Wanda Amina sosai ta rude ganin yadda Mansura ta fita hayyacinta. Amina cikin tsoro da yadda ta ga Mansura ta koma ta matsa da sauri tana kamo hannunta ta ce "Mansura, baki da lafiya ne dama ban Sani ba? Kin ga ko yadda kika rame lokaci daya haka." Mansura dai zame hannunta ta yi daga na Amina ta kwanta ta lillibe saboda sanyi da take ji. Sosai Mansura ke rawar sanyi. Amina mahaifiyarta ta je ta samu dake zaune tana tulawar karatun da suka yi, ba yan idar da sallar azahar da ta yi. Amina cikin damuwa da halin da ta ga Mansura ta ce Kamar za ta fasa kuka, "Mama, Mansura ba ta da lafiya sosai, bi ki ga yadda ta koma ba." Mahaifiyar Amina rufe littafin hannunta ta yi tana kallan Amina ta ce "Subahallah, da yake na saba ba fitowa take ba shi ya sa Koda ban ganta ba ban yi tunanin komai ba. Mu je in ganta." Amina da mahaifiyarta tsaye suka yi kan Mansura da ke tsananin rawar sanyi. Mahaifiyar Amina Koda ta taba jikin Mansura zafi ta ji sosai, hakan ya sa ta Kalli Amina ta ce "Amina, Kira yayanki a waya ki sanar da shi ya zo ya duba jikin nata." Amina Kiran Abba ta yi, Amma har ta katse bai dauka ba. Amina sai da ta yi ma Abba Kira uku bai dauka ba. Kallan mahaifiyarta ta yi ta ce "Mama bai dauka b..." Amina bata rufe baki ba Abba ya Kira, yana tambayar Amina lafiya. Amina cikin damuwa da halin da ta ga Mansura ciki ta ce "Yaya Abba, Mansura ce bata da lafiya tun safe take amai yanzu haka cikin zazzabi take sosai." Shiru Abba ya yi sannan ya ce "Me ya sa baki fada min ba kafin in fita." Yaya Abba kasan ita Bata magana, tom nima sai yanzu da na dawo na gani, mama, ta ce ka zo ka dubata yanzu." "Okay." Abba ya ce ya kashe wayarsa. Mahaifiyar Amina jin shiru-shiru Abba bai zo ba ya sa ta sa Amina ta Kuma Kira Mata Abba. Mahaifiyar Amina da kanta ta yi ma Abba magana akan jikin Mansurar. Shiru Abba ya yi, kafin ya ce "Mama Wallahi Ina cikin busy, Amma na kusa kammalawa yanzun." Atakaice Abba, bashi ya zo gidan ba sai 4:00.PM lokacin daga ka ga Mansura kasan ta gama galabaita. Abba ganin mahaifiyarshi ta daure fuska,alamun ta yi fushi, ya ce "Afuwa Mama, Wallahi ba laifina bane, Ina yarinyar take?" Amina ita ta yi ma Abba jagora har zuwa bedroom dinsu, dama Abba ya dakko duk abin da ya kamata, ya hado alluransa da drip din da zai sa Mata. Abba kallan Amina ya yi Wanda duk da bai yi magana ba ta fahimci abin da yake nufi. Hakan ya sa Amina ta hau kan bed din tana bubbuga Mansura ta ce "Dear, ki daure ki tashi ga Yaya Abba nan zai duba ki." Amina ta yi maganar tana yaye rufar da Mansura ta yi. Jikin Mansura rawa yake tsabar zazzabin dake cinta. Abba zama ya yi bakin gadon yana kallanta ya ce"Bayan zazzabin da kike ji sai me ke miki ciwo?." "Kaina da cikina." Mansura ta ce a hankali cikin rawar sanyin zazzabi. "Kina da ulcer ne?." Abba ya tambayeta har yanzu idanshi na a kanta. Kai Mansura ta daga mai. alamun Eh. Ruwan Allura Abba ya hada ya mika ma Mansura hannu almaun ta miko mai hannunta, Mansura Kai ta girgiza kamar za ta yi kuka tana kallan Amina, kamar ita ce za ta yi mata allurar, ta ce "Ni dai a ban magani, bana son Allura." Mansura ta idasa maganar kamar zata fasa kuka. Dan Babu abin da ke daga Mata hankali a ciwo kamar allura, duk da shima maganin ba shanshi take ba. Amma gara Mata magani tana daurewa ta sha. Amina kallan Abba ta yi cikin sanyi kamar za ta taya kawarta kuka ta ce "Yaya Abba, dan Allah ka bata magani mana ba sai ka yi Mata allurar ba." Da yake Amina itama bata son Allura shi ya sa ta fahimci halin da kawarta take ciki. Abba hanyar fita ya nuna ma Amina da hannunshi alamun ta fita. Hakan ya sa Amina ba tare da ta Kuma cewa uffan ba ta fita. Abba kuma , mika ma Mansura hannu ya yi alamun ta miko mai hannunta babu alamar wasa. Mansura yarfe hannunta ta fara kamar za ta yi kuka ta ce "Ni dai dan Allah ka ban magani n..." Abba jawo hannun Mansura ya yi batare da ya Kara magana ba, da kansa ya nannade hannun rigarta zuwa gwiwar hannunta yana naiman jijiya. Mansura hannunta gaba daya rawa ya kama gashi tana tsoran musa mai ganin yadda ya daure fuska. Mansura tsabar tsoro hannun rawa ya kama yi sosai, yadda babu yadda za a yi a yi allurar. Abba kallanta ya yi ya ce, "ki natsu ki bar rawa da hannunki, idan ba haka ba aka samu matsala babu ruwana." Mansura rufe ido ta yi jikinta gaba daya yana rawa, dan wannance ranar farko da wayanta da aka taba yi mata allura, ko za a yi Mata kuka take, mahaifinta Kuma da ya ga haka sai ya ce a rabu da ita a bata magani. Hakan ya sa gaba daya tunanin Mahaifin Mansura sai ya dirar Mata a rai, da ace shi ne da ba zai bari a yi Mata allurar nan ba. Mansura rufe ido ta yi lokacin da ta ji shigar allurar a jijiyarta. Abba Kuma ganin yadda take rawa da hannunta ya ce "Wallahi idan kika bari ta kauce sai na sake miki wata garama ki tsaya ruwan ya gama shiga jikinki." Kusan dai yadda allurar jiji take ruwan na fara shiga zaka ji wani zafi sosai. Mansura na jin zafin nan ta fuske hannunta tana mai fashewa da kuka. Dan gaba daya tunanin mahaifinta sai ya dawo mata a rai ga Kuma zafin allura. Abba da mamaki yake kallanta, ga ruwan allurar ko rabi bai shiga ba. Tashi ya yi ya barta zaune ya iske mahaifiyarshi da Amina. Amina ya watsa ma magungunan ya ce "Gashi nan ki bata yanzu ta sha dan ba tsayawa ta yi akayi allurar ba. Abba na fadin haka ya juya ya koma wajan aikinsa. Amina Kuma wajan Mansura ta koma, inda ta iske Mansura ta koma ta kwanta ta Kuma lillibe duka jikinta saboda sanyin da take ji. Amina zama ta yi bakin gadon ta ce "Mansura, ki tashi ki sha magani dan Allah, kin ga Yaya Abba ya ce baki tsaya ya yi miki allurar ba." Mansura cikin rawar sanyi ta ce "A'a ni dai ba zan sha ba." Babu yadda Amina ba ta yi da Mansura ba Amma taki shan maganin, daga ƙarshe ma da ta dameta kuka tasa mata. Amina wajan mahaifiyarta ta je ta sanar da ita abin da ke faruwa. Mahaifiyar Amina cikin takaici ta ce, "Ka ji min shirman banza, ki ce itama shashasha ce kamarki, ba ta son Allura Kuma ba ta son magani.mu je in sameta." Mahaifiyar Amina na zuwa da kanta ta tada Mansura, ta bare magunguna ta mika Mata tare da ruwa ta ce "Maza ki amsa ki shanyesu." Mansura amsa ta yi tana raurau da ido. Rufe idonta ta yi ta watsasu duka a bakinta. Amma Ina ko ciki basu kai ba ta dawo dasu. Mansura sai da ta amaye kaf abinda ke cikinta. Mahaifiyar Amina da takaici take kallan Mansura na amaye magungunan da ta yi. Cikin takaici ta ce "Mansura, yanzu kin fi son a barki da ciwan kenan? Haba Mansura ana ciwo ba a shan magani ne?." Mahaifiyar Amina haka tai ta yi ma Mansura fada-fada nasiha akan kin shan maganinta. Amina yaye bargon ta yi ta Kai bathroom dinsu ta wanke tas. Sannan ta je ta hado Mata ruwan tea. Amma Babu yadda Amina ba ta yi ba Mansura taki tashi bale ta sha tea din dole ta rabu da ita. Mansura na nan kwance har dare gashi har yanzu zazzabin bai sauka ba, hakan ya sa jikin nata ya yi taushi sosai. Abba kamar yadda ya sa ba dawowa aiki, haka yauma ya dawo. Mahaifiyar Abba kallan Abba ta yi ta ce "Abbana, ya aikin. "Alhamdulillah mama, aiki babu dadi Kuma ba a fatar a bari." Murmushi mahaifiyar Abba ta yi ta ce"Gaskiya ne Abbana. Dan Allah ka je ka duba jikin yarinyar nan, magungunan dakabada a bata tana sha ta amayar dasu, yanzu haka ba ka ji jikin nata ba kamar wuta, na ce ko ruwa zaka sa Mata ne, inda na ga dazu ka zo da shi." "Mama, ku shirya ku kaita asibiti kawai, ni ba zan iya dubata Yarinyar nan ba. Mutum ace baya son Allura Kuma baya shan magani to ya take so a yi Mata. "Abba ya fadi maganar yana tashi. Mahaifiyar Abba Kai ta girgiza ta ce "Abba idan Amina ce ya za mu yi haka nan za mu lallabata ta sha, dan haka wannan dinma daurewa za ka yi ka sake dubata." Abba juyawa ya yi zai fita ya kalli mahaifiyarsa ya ce "Mama bari in watsa ruwa sai in zo in dubata." "A'a Abbana, dazu da na taba jikinta ya yi taushi sosai, ka dubata kafin" Abba ba tare da ya musa ma mahaifiyarshi ba ya juya ya nifi bangaran su Mansura. Amina na zaune ta yi ta gumi ta tasa Mansura gaba tana kallo. Abba gefan bed din ya zauna, hannu ya sa ya yaye bargon da Mansura ta rufa, wanda har yanzu jikinta zafi rau. Abba tashi ya yi ya fita. Mahaifiyar Abba kallan Abba ta yi ganin zai fita ta ce "Abbana, ba dai har ka dubata?." "A'a mama, sai an sa Mata ruwa Ina zuwa bari in je chamist layin nan in siyo. Abba bai dade da fita ba ya dawo. Kwance ya samu Mansura kamar yadda ya barta. Allurai ya hadama drip din, kafin ya kamo hannun Mansura yana naiman jijiyar da zai jona mata ruwan. Mansura naiman janye hannunta take ganin allurar da Abba yake ƙoƙarin sa Mata ta Karin ruwan da zai Mata. Abba bai Sanda ya buga Mata wata uwar tsawa ba ya ce "Wallahi kika kauce jijiyan nan da na samo, ta kubuce za ki ga abin da zan miki." Mansura tsabar tsoro ga tsawar da Abba ya yi mata kasa tsayar da hannunta ta yi ya yi ta rawa. Abba hannu ya daga zai wanke ta da mari, Amina ta yi saurin rike hannun Abba ba tare da ta san ta yi ba. Da wani mugun kallo Abba ya bi Amina, kafin ya nuna Mata hanyar fita da hannunsa. Amina har tana tuntube garin sauri ta fita. Kallan Mansura ya yi ya ce "Kina son in tsira miki ita a cikin ido?." Mansura Kai ta girgiza kamar za ta yi kuka." "Yauwa tom, idan har baki so tom ki natsu ki bar rawa da hannunki, idan ba haka ba zan mareki Wallahi, Kuma akwai Allurar ta jijiya da zan miki idan na sa miki ruwan, gara ma ki natsu. Mansura kamar za ta yi kuka ta ce "Tom ai ba da gangan nake rawa da hannun ba, shi ne yake rawa." "Ki rufe idonki, har sai na ce ki bude ki bar gani." Mansura rufe idonta ta yi kamar yadda Abba ya umarceta ta mika mai hannun. Abba cikin lallabawa ya kama hannunta ya tsira mata allurar drip din." Mansura tsabar tsoro ko zafin allurar ba ta ji ba. Abba da sauri ya hada ta jijiyar zai tsira Mata ta bude ido jin shiru-shiru har yanzu ba a yi ba, ba ta san har ya sa mata ta Karin ruwan ba, wata zai Kuma yi mata. Mansura da sauri ta janye hannunta, Abba na gaf tsira Mata ta jijiyar. Abba kallanta ya yi ya ce "Me ye haka kuma ba na ce sai na ce ki bude idonki ba za ki bude ba?." Mansura kamar za ta yi kuka ta ce "Tom har yanzu ba ka yi min ba." Abba nuna Mata hannunta ya yi Wanda ya jona mata Karin ruwan ya yi. Mansura da mamaki ta zaro ido, jin ba ta ji shigar allurar ba. Abba umartar ta ya yi da ta sake rufe idanta. Mansura kamar dazu cikin tsoro ta sake rufe idon. Kasan cewar allurar jiji na da zafi, Kuma ita kadan-kadan ake sa ruwanta har ya gama shiga jiji, hakan ya sa ruwan na fara shiga jikin Mansura da sauri ta bude idanta tana naiman fuske hannunta. Abba da karfi ya rike hannun Mansurar ya ce "Wallahi idan baki tsaya ba allurar ta goce sai na sake miki wata." Hakan ya sa Mansura tsawa ba ta shirya ba. Abba na gama mata ya fita ba tare da ya Kuma tanka Mata ba, dan duk ta bashi haushi yadda ta ci mai alokaci abin da ya kamata ace tuni an angama ✍🏻 Fadila Sani Bakori ce Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LGosWoHsPkj3rhf9EbKjrK ⭐ABBANA⭐ 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚* P 11-12 Zaune ya iske mahaifiyarshi da Amina da a falon. Mahaifiyar Abba kallan Abba ta yi ta ce"Ta tsaya ka yi mata alluran ko?." Eh, na sa Mata wasu a drip din, daya ce aka yi mata ta jijiya, yanzu sai wadda za a rika mata kullum sau biyu kwana uku." Ma Sha Allah, tom Allah ya sawake."Ameen." Abba ya ce ya fita zuwa bangaransa. Amina Kuma bangaransu ta koma in da ta iske Mansura na ƙoƙarin yaye bargon da ta rufe da shi. Amina da sauri ta yaye mata bargon tana cewa "Alhamdulillah, da alama zazzabin ya sauka." Amina zama ta yi tana jiran ruwan da aka sama Mansura ya kare ta cire mata, barci ya dauketa. Mansura ko dama tana nan ta tasa ta tsare tana jiran ruwan ya kare ta zare abinta, yana karewa ta zare tana mai ciccije baki. Mansura kasa kwanciya ta yi saboda wata uwar yunwa da take ji. Tashi ta yi ta shiga kitchen din ta sa ruwan tea, ta hada tea ta sha kafin ta kwanta. Washegari, Abba kasan cewar 8:00AM yake fita aiki, hakan ya sa yana tashi, bayan ya zo sun gaisa da mahaifiyarsa ya ce "Mama, allurar yarinyar nan guda biyu ce a rana, idan ta tashi zan yi mata kafin in wuce" Abba suna cikin maganar Amina ta fito da shirinta na fita aiki itama. Amina da fara'arta ta gaida Abba, dan ta ji dadin haduwarsu dan ko ba komai zai rage mata hanya. Bayan Abba ya amsa gaisuwar Amina ya ce "Yarinyar nan ta tashi in yi mata allurarta" ."Kai, Aiko ba ta tashi ba, bari in tadata. "A'a, ki rabu da ita kawai" Abba ya fadi maganar yana tashi. Mahaifiyar Abba Kai ta girgiza ta ce "A'a Abbana, bari in tadata, ai tsallaken bashi da amfani, Kuma ka ga zazzabin ya bugeta sosai karya dawo mata gara a yi." Mahaifiyarsu Amina na fadin haka ta tashi ta nufi bangaransu Amina. Tana zuwa ta ji motsin ruwa a toilet. Zama ta yi tana jiran Mansura ta fito, dan ta San in ta koma ta sanar da Abba ta shiga wanka tafiyarshi zai yi. Mahaifiyar Amina na nan zaune Mansura ta fito. Mansura cikin fara sakin jiki a gidan ta gaida mahaifiyar Amina. Mahaifiyar Amina Kuma tashi ta yi ta ce "Ki yi sauri ki shirya Abba na falo yana jiranki zai miki allurarki ta safe." Mansura da ba ta son allura bata fuska ta yi ta ce"Mama, na fa warke." Mahaifiyar Amina ko kanta ba ta koma ba ta ce "Bana son sakarci shi baisan kin warke bane, ki sa ko hijab ne gashi nan zuwa." Mahaifiyar Amina na kaiwa haka ta fita. Mansura Kuma kamar za ta yi kuka ta dakko hijab din sallarta ta zura, tana zama Abba na shigowa. Mansura Kara bata fuskarta ta yi, zabar razanar allura ko gaida Abba ba ta yi ba. Abba Kuma kallanta ya yi ya ce"Ina ledar magungunan take Alluran na ciki?." Mansura Kauda da fuska ta yi tana turo baki ta nuna ma Abba ledar da hannu. Abba kallanta ya yi da mamaki, amma sai baice mata komai ba ya je ya dakko ledar magungunan. Zama ya yi ya hada allurar, kafin ya umarceta da ta miko hannunta. Mansura goge hawayan ta yi da ya zibo Mata ta na tunawa da Abbanta da ta yi, duk ciwan da za ta yi baya bari ayi mata allura saboda ya san bata son Allura. Abba da mamaki ya kalli Mansura yana zaro ido ganin tana kuka akan Allura. Da katawa ya yi da kamo hannunta ya ce "Lafiya? Me akai miki?." "Ni dai bana son allurar." Mansura ta fada tana goge hawayanta. Abba kallanta ya yi ya ce "Idan kina da kudin da za ki biya na alluran shi kenan, sai in fasa miki kin ga ban yi asarar kudina ba." Tom, ka bari Amina idan ta dawo zan amsa in baka." Abba hannun Mansura ya jawo ya ce "Ki bari idan ta dawo kika amshi kudin kika ban na zubar da sauran." Mansura kuka ta fasa ilahirin jikinta na rawa. Abba tsayawa ya yi yana kallanta, dan ya ci karo da masu tsoran Allura da dama Amma nata azimin ne. Abba ganin za ta bata mai lokaci ya ce "Kin San Allah ko ki bar rawa da hannun ko Kuma in yi miki ita a cikin ido." Mansura jin Abin da ya ce yarfe hannu ta yi tana cewa "Wayyo Allah na ba fa nike rawa da hannun ba shike rawa da kansa." Abba hannun ya Kara kamowa, Mansura ta Kuma fusgewa tana cewa "Tom ka tsaya in shirya." Ta fadi maganar tana mai kara gyara zamanta, Wanda daga gani dai duk cikin razanar allura ne. Abba shi dariya ma taso ta bashi, ganin sai ciku-ciku take wai tana shiryawa. Abba ganin ciku-cikun yaki karewa kallanta ya yi ya ce "Kin gama shiryawa?." Kai Mansura ta girgiza kamar za ta yi kuka ta ce "Bari in daura dankwalina." Abba da mamaki ya kalleta ita dake sanye da hijab. Amma sai ya tsaya ya ga ikon Allah. Mansura tashi ta yi ta je ta dakko wata doguwar riga ta d'aga hijab dinta ta zira, sannan ta kama naiman hular da za ta sa. Abba ganin abin bana kare bane ya ce "Madam ke fa nake jira." Mansura kallan Abba ta yi kamar za ta yi kuka ta ce "Hulata nake nema in sa." Abba wurga mata wata hula ya yi da ya gani a kan bed din nasu, ya ce"Ga wata ki sa." Wannan fa ta yi datti." Abba ganin in dai ya biye ma Mansura bata da ranar shiryawa, inda ya fahimci allurar take so ta zukemawa , hakan ya sa ya tashi ya karasa inda take din ya kamo hannunta ya ce "Malama na makara zo in miki kin ga sai ki ji dadin naiman hularma a natse." Mansura kamar za ta fada ihu ta ce "Wallahi Allah yunwa nake ji." Abba Kai ya girgiza ya ce "Minti goma ya yi yawa ai, yanzu zan Miki, idan kuma kika aata min lokaci kin ji na ce Allah biyu zan Miki, Amma idan kika tsaya yanzu zan miki shi kenan." Mansura jin Abin da Abba ya ce mika mai hannun ta yi tana rufe idonta dake zubar da hawaye. Abba cikin dabara ya tsira mata allurar, Wanda tsananin tashin hankalin ya sa ko zafin allurar ba ta ji ba, sai ji ta yi ya saki hannunta yana cewa "Ki liliya wajan." Abba na fadin haka ya fita. Mansura Kuma dagewa ta yi tana liliya hannun. Abba Koda ya zo falon ba kowa, Amina ta yi tafiyarta, mahaifiyar Amina Kuma tana kitchen. Abba har kitchen din ya bita ya yi Mata sallamar ya tafi aiki. Amina kamar yadda ta saba dawowa aiki yauma haka ta dawo. Tana zuwa ta iske Amina zaune a falon tana cin Abinci. Amina ido ta zaro ta ce "Da alama dai Yaya Abba har da maganin cin Abinci ya hada miki." Mansura turo baki ta yi tana kallan Amina ta ce "Wallhi dear nima na fara tunanin haka, tom Amma Kuma ban sha maganin ba ko daya ba, kodai allurar da ya yi min tana sa cin Abinci ne?." Amina ido ta zaro ta ce "Wai kina nufin ba kisha maganin ba?." Ni Wallahi bana shan magani ni fa ko allura ba a taba yi min ba sai a nan, Abbana ma ko ban da lafiya idan akasa da Allura cirewa yake." Amina da yake itama ba gwanar shan maganin ba ce hakan ya sa ta ce "Ke kinsan Allah ban ga laifinki ba, nima fa haka nake, akwai ranar da ban da lafiya Mama ba ta nan ta je Kaduna biki, daga ni sai Yaya Abba, naki shan magani ya yi min duka ya Kuma ban maganin na sha, tun daga ranar idan ya ban magani na bar yi mai musu." Mansura ido ta zaro ta ce "Ki ce Allah ya taimakan, dazu da kila ma nima duka zai min?." Kai Amina ta girgiza ta ce "Ai Mama na nan, ba zai bigeki ba." Amina tashi ya yi ta ce "Bari in watsa ruwa." Amina gaf la'asar ta shiga kitchen ta dora masu tuwan dare, sai dai ta yi mamaki ko da ta fito kitchen din ba Mansura. Amina na cikin aikin ne mahaifiyarta ta yi sallama ta shigo. "Sannu da dawowa mama, ya jikin Aunty Zainab din?." Mahaifiyar Amina da murmushinta ta ce "Ta haihu, ta tafi da namiji." Ma Sha Allah, Wallahi mama bacin yamma ta yi da yau na je naga jariri." A'a, ki bari nasan kila gobe Abba zai je sai kuje tare." Amina ido ta zaro ta ce"A'a, gaskiya ba zan bi Yaya Abba ba, daga anje ya ce a tafi." Shi kenan, kin tafi ke kadai ai." Amina na nan falon suna hira da mahaifiyarta, ta na yi tana duba girkinta, a haka har ta gama. Amina ba ita ta koma bangaransu ba sai da za ta Sallah Magriba. Koda ta shiga kwance ta iske Mansura ta lillibe da bargo. Amina ganin yadda Mansura ke rawar sanyi cikin damuwa ta ce "Mansura, zazzabin ne ya dawo?." Mansura kai ta daga ma Amina. Amina shiru ta yi, kafin ta ce "Ki tashi ki daure ki sha maganin Mana." Mansura Kai ta kuma girgiza ma Amina ba tare da ta yi magana ba." Amina alwalla ta yi ta ta gabatar da sallar Magriba, kafin ta nufi site din mahaifiyarta, in da ta isketa zaune kan Sallaya ta idara da Sallah itama. Amina zama ta yi kamar za ta yi kuka ta ce "Mama, zazzabin mansura ya dawo, ashe tun dazu tana kwance." Mahaifiyar Amina bayan ta shafa addu'arta kallan Amina ta yi cikin fara damuwa da lamarin Mansurar ta ce "Amina, Wallahi na fara damuwa da matsalolin yarinyar nan, ace baka da lafiya ka ce Kuma ba za ka sha magani ba Kuma ba za a yi maka Allura ba, to ya take so a yi da ita. Daga ganinta ma dai irin shagwababbun yaran nan ce." Mansura turo baki ta yi jin mahaifiyarta kamar tana naiman kushe kawartata ta ce "Mama, magani fa ba shi da dadi." Tom ai shi kenan, sai ta zauna ta warke a haka." Amina ta san halin mahaifiyarta ko itace ta ce ba zata sha magani ba babin takanta za ta yi ba, hakan ya sa ta tashi bata Kara cewa komai ba ta fita." Bangaran Abba yau da wuri ya dawo gidan, dan yana gidan ma aka yi sallar magariba, bayan ya dawo daka masallaci ya shiga bangaran mahaifiyarsa, ganin bata a falon hakan ya sa ya nufi bedroom dinta. Zaune ya isketa tana duba majama'ul baharaini. Mahaifiyar Abba na ganin Abba ta rufe littafin, tana murmushi ta ce "Abbana yau 'yar wuri ce kenan?." Eh mama Ina nan ma aka yi Magriba, fatan Kuna lafiya, ya masu jegon."Suna lafiya Lau, ta fada maka kenan." Eh mama mun yi waya." Abba kallan wayarshi ya yi dake ringing, dagawa ya yi yana kanga wayar a kunne, ban ji mai aka ce ba na ji ya ce "okay gani a gidan ma." Yana fadin haka ya kashe wayarsa. Mahaifiyar Abba kallan Abba ta yi ta ce"Lafiya?." Amina ce ta kirani wai zazzabin yarinyar nan ya dawo." Mahaifiyar Amina cikin takaicin rashin son maganin Mansura ta ce "Ba dole zazzabi ya dawo ba, maganin da ka bata fa in Banda Wanda na bata ta amayar dashi, daga shi ko daya ba ta kara sha ba, to taya zazzabi ba zai dawo ba." Abba Kai ya jinjina ya ce "Mama ko daya kika ce bata sha maganin ba?." Wallahi Abba, ga zazzabin nan ma ya dawo." Abba baice komai ba tashi ya yi ya nufi bedroom din su Amina. Amina na nan zaune ta yi tagumi ta sa Mansura gaba tana kallo, cikin tsananin tausayi, Abba ya yi sallama ya shiga. Kallan Amina ya yi ya ce "Ina laidar magungunan?." Amina dakko ledar ta yi ta mika ma Abba. Abba sosai ya yi mamakin ganin magungunan suna nan yadda suke. Kallan Amina ya yi ya ce "Me ya sa ba ta sha ba?." Amina yadda Abba yake mata magana ya sa ta fahimci tuhumarta yake na rashin shan maganin Mansura, bi ma'ana dai tana da laifi. Abba jin ta yi shiru ya Kuma cewa, "Ba da ke nake magana ba, na ce me ya sa ba ta sha ba?." Yaya Abba, ita ce bata sha ba." Abba zama ya yi gefan gadon da Mansurar take ya ce ma Amina kawo min ruwa." Amina da sauri ta je ta kawo ma Abba ruwan. Abba bare magungunan ya yi sannan ya umarci Mansura da ta tashi. Mansura ta shi ta yi ta zauna tana mai kara kudindine jikinta da bargon, saboda sanyin da take ji. Abba mika mata maganin hannunshi ya yi da ruwan ya ce "Amsa ki sha." Mansura kallan Abba ta yi, irin kallan ka tausaya min. Abba babu alamar wasa tare dashi ya Kuma maimata "Amsa ki sha na ce." Mansura amsa ta yi tana goge hawayanta. Abba ruwan ya mika Mata ya ce "Watsa duka maganin a bakinki." Mansura watsa duka maganin ta yi, take ta fara kararin amai zata dawo da maganin. Abba tashi ya yi ya daga kanta ya kalli sama, sannan ya amshi ruwan ya tsiyaya mata a baki. Ya ce "Hadiye shi." Ya fadi maganar yana girgiza kanta. Mansura hadiyewa ta yi ba ta shirya ba. Abba sai da ya tabbatar ta hadiye kafin ya saki kanta. Mansura nishi ta fara irin na yaran da akai ma dure. Abba ruwan Allurar ya hada ya kamo hannun Mansura, take hannun Mansura ya kama rawa. Abba Amina ya sa ta rike mai hannun Mansura ya yi Mata allurar, take Mansura ta kama kuka. Amina murza mata hannun ta kama tana cewa "Sannu dear, yi hakuri." Abba maganin ya mika ma Amina ya ce "Gashi Allah ya sa lokacin shan maganin ya kara yi bata Sha ba, dukkanku ku biyun za ku yi min bayanin dalilin da ba ta sha ba." Abba na fahin haka ya fita. Wajan mahaifiyarshi ya koma suna fira. Mahaifiyar Abba cikin hirar tasu neka ta ce "Abba Kai kadai ne dana Namiji da nake kalla in ji dadi, kana min duk abin da na ce, sai dai har yanzu ka kasa cika muradina daya tal aduniya. Ba ni da burin da ya wuce Abba kamar in ga ka yi aure, sai yaushe ne za ka yi aure Abba? Yaushe za ka cika burina da na mahaifinka da har ya bar duniya bashi da buri kamar ya ga auranka, tom Allah bai nufa ba, baka yi ba, gashi har yana gaf da cika shekara biyar, har yanzu shiru babu ma wata alamar da kake nuna wa za ka yi aure." Shiru Abba ya yi kafin ya ce "Ki yi hakuri mama har yanzu ban samu wadda ta kwanta min bane." Shiru mahaifiyar Abba ta yi tana nazarin maganar da za ta fada ma Abba. Ta jima kafin ta ce "Abbana na yi maka matar aure wadda nake fatan in sha Allah ba za ka yi danasanin zama da yarinyar ba a yadda na fahimceta." Abba kallan mahaifiyarshi ya yi cikin rauni, dan duk ba ya jin zabin mahaifiyar tashi zai mai Amma Kuma duk da haka baya jin zai iya bijire ma umarninta. Hakan ya sa ya ce "Mama tun kafin in ganta na aminta da zabin naki." Ma Sha Allah , Allah ya yi maka albarka Abbana, da Alama dai ka gaji mai sunan naka, ba kowa bace na zaba, yarinyar ..... ✍🏻 Fadila Sani Bakori ce. ⭐ABBANA⭐ 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚* Damin samun littafin ABBANA daga faro Follow the ABBANA channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaYZGsNEFeXsr1CKQl3r P 13-14 Malamarmu Aisha na zaba, yanzu haka maganar da nake yi maka har na yi ma mahaifiyarta magana ma, kuma ta amsa min ta ce ka je ka ganta. Sanin ba za ka yi min musu ba ya sa sai da na fara sanar da mahaifiyarta kafin Kai." Abba Kai ya daga yana kallan mahaifiyarsa ya ce "Mama, in dai ta yi miki Allah ko ban ganta ba ya wadatar, amma duk da haka ki ban address din gidan nasu zan je har gidan." Mahaifiyar Abba sosai ta ji dadin yadda dan nata ya aminta da zabin ta cikin sauki. Cikin jin dadi mahaifiyar Abba taita zindimo masa albarka tana cewa "Abbana, in sha Allah za ka yi alfahari da wannan zabin nawa. Allah ya yi maka albarka, Allah ya baka duk abin da kake nema duniya da kuma lahira, Allah ya jikan mahaifinka, ya saka masa da alkairi bisa kyakkywar turbar da ya dora min Kai." Abba sosai ya ji dadin addu'ar mahaifiyar tasa, hakan ya sa cikin jin dadi ya ce "Ameen mamana." Abba sun jima suna hira da mahaifiyarsa kafin ya yi mata sallama ya koma sight dinsa. Washegari, Amina da wuri ta tashi ta yi duk abin da za ta yi kafin ta fita. Kallan Mansura ta yi dake ta tsattsakar indomie dake gabanta. Amina dakko maganin Mansura ta yi ta mika mata ta ce "Dear ga maganinki kisha." Mansura baki ta turo ta ce "Allah bakina fa har ya fara dacin magungunan nan, ni dai gaskiya ba zan sha ba." Amina ido ta zaro ta ce "Ba za ki shaba, baki ji abin da Yaya Abba ya ce ba ne jiya, ni dai dan Allah ki rufa min asiri ki Sha, Wallahi ya zo ya ga baki sha ba har nima ba gyaleni zai yi ba, kina ji dai a gabanki ya ce in mun isa karki Sha, ni dai ki rufa min asiri ki dauka ki sha." Mansura hannun Amina ta kamo, kamar za ta yi kuka ta ce,"Amina, zan fa babbare sai in zubar kin ga ai ba zai gane ban Sha ba" Uhmmm, Wallahi babu ruwana, idan fa zazzabin ya dawo miki? Yaya Abba da shegan bin diddigi in je ya gano ya ci ubana kila gara ma ke yana ganin bakuwace ya rabu da ke." Amina kamar za ta yi kuka ta ce "Yanzu ba zaki tausaya min ba?." Amina ma cikin son fahimtar da Mansura ta ce "Mansura ke ba ki san halin yaya Abba bane, ni dai kawai ki sha dan Allah." Mansura Kuma kallan Amina ta yi kwalla na taruwar mata ta ce "Amai fa nake ji." Mansura ki sha in Allah ya yadda ba zaki yi ba." Mansura rufe idonta ta yi ta watsa maganin bakinta ta bi da ruwa da sauri." Yunkurin amai ta fara, Amina da sauri ta fara bubbuga bayanta. Suna a haka Abba ya shigo yi mata allurarta. Amina gaida Abba ta yi tana mai ci gaba da bubbuga bayan Mansura da har yanzu dafe take da kirji ba ta daina yunkurin amai ba. Abba kallan Amina ya yi ya ce "Lafiya me ya sa ta yunkurin amana." Yaya Abba daga shan magani." Abba wata farar kwaya ya ciro a ajjihunsa ya mika ma Amina ya ca bata ta tsotsa." Amina mika ma Mansura ta yi, Mansura ganin magani ne yi ta yi kamar ta je fashi a bakinta taki sha, ta rufeshi a hannunta. Abba ledar magungunan Abba ya dakko ya hada allurar, Mansura take ta fara yarfe hannu. Abba kallan Amina ya yi ya ce "Reke min hannun yadda ba zai yi rawa ba." Amina rike hannun Mansura ta yi sosai, Abba daidai zai tsira ma Mansura allurar ta fuske hannunta, by mistake Abba ya caka ma Amina a hannu. Wani uban ihu Amina ta fasa, dan sosai allurar ta shigeta. Abba cikin bacin rai ya daga hannu ya wanke Mansura da mari. Mansura gigicewa ta yi, dan tun da take ba a taba marinta ba sai yau. Rike wajan ta yi tana murzawa tana kuka. Mahaifiyar Mansura da tun ihun Amina ta shigo dakin da saurinta har tana tuntube, jin kukan mutum biyu lokaci guda. Abba kuma daidai ya juya zai fita, suka ci karo da mahaifiyarsa. Mahaifiyar Abba kallan tuhuma take ma Abba, ganin Mansura dafe da kunci tana kuka, ga Kuma Amina rike da hannu itama tana kuka. Mahaifiyar Abba cikin tausasa murya ta ce "Abbana, ya haka Kuma?." Nan Abba ya kwashe duk abin da ya faru ya labarta mata. "Allah dai ya kyauta, ni ban ga abin tsoro a Allura ba, duk da ta jijiyar nan na da zafi, amma ya za a yi inda duk zafinta ba takai ciwan ba." Abba kallan Amina ya yi da har yanzu take dafe da hannun tana kuka, ya daka Mata wata uwar tsawa ya ce"Ba za ki yi ma mutane shiru ba." Abba ya fadi maganar yana kamo hannunta yana ganin inda ya caka mata allurar, sosai ya caketa. Abba murza mata wajan ya yi ya ce "Ki je motana akwai maganin zugi ki sha." Mansura ko Abba na daka ma Amina tsawa ta yi shiru, tana zare ido. Abba kallan Amina ya yi ya maka mata wata uwar harara kafin ya ce "Anjima idan na dawo ki zo in miki allurar, dan na gama biyoki nan." Yana fadin haka ya juya ya tafi. Mahaifiyar Amina hannun Mansura ta kamo tana liliyawa, kafin ta mai da kallanta ga Mansura ta ce "Shi ya sa masu iya magana suka ce idan ka ga zama ya yi karko wai hali ne ya zo daya. Yanzu me ya acikin Allura Mansura, to Wallahi ki natsu da kyau ki ji Abba ba sauki garesa ba, a haka ma dan har yanzu yana miki kallan bakuwa ne, dan da Amina ce da Kinga yadda zai yi da ita yau a gidan nan. Allura Kuma daga gobe dama an gama inda ya ce min ta kwana uku ce, Kuma kin ji abin da ya ce baya Kara zuwa nan yi miki, daga ya dawo kin ji muryarsa a falo sai ki samesa ya yi Miki, ko Kuma Amina ta rika rakaki bangaransa ya yi miki acan, idan kin natsu har ya gama miki tom,. Idan Kuma baki natsu ba tom babu ruwana, kin ga dai tun yana raga miki sai da kika kuresa." Mansura dai bata ce komai ba, mahaifiyar Amina ta gama fadanta ta fita. Amina na fita ta tafi wajan aikinta, mahaifiyar Amina ma ta tafi Islamaiya, ya rage gidan Amina ita kadai, abin da ya faru take ya tuna mata da mahaifinta mai ji da ita, Wanda baya Mata gyara akan duk abin da za ta yi, duk abin da ta yi daidai ne, amma yau ita ake Mata har ana mata faɗa, akan abin da ita bata ga laifi bane. Mansura kuka ta yi sosai, tana Kiran "Abbana! Wayyo Abbana!!." Kuka take sosai, wanda har sai da ta ji kanta ya fara ciwo kafin ta yi shiru. Abin da Abba ya yi mata Kuma ta barshi dan baya son zamanta gidan ne ya sa ya yi Mata hakan amma aganinta me ta yi mai da zai mareta ,dan ita bata ga abin duka ba, har ana mata tsawa haka. Allah sarki gata kenan, haka dan gata Wanda ba a kwabamawa yake, idan ya je gidan masu kwaba, sai ya ga kamar ba a sonsa ne a gidan ya sa ake kwabame. Mansura na nan kwance, Sallah kadai ke tada ta, har mahaifiyar Amina ta dawo daga Islamiya. Koda ta dawo ba ta bi ta Mansura ba. Kitchen ta shiga ta Samar masu abin da za su ci. Mansura na nan kwance har yanzu ba ta bar zubar da hawaye ba Amina har ta dawo. Amina ko da ta shigo bedroom din nasu, kallan Mansura ta yi jin ba ta tanka Mata ba, Amina ta ce "My dear, na yi laifi ne kin ganni kin kauda Kai." Abin mamaki Mansura kawai sai ta fashe da kuka. Amina cikin tashin hankali tahau kan bed din tana kamo Mansura ta ce "Mansura, jikin ne, ki yi shiru dan Allah ki fada min?." Amina ta idasa maganar kamar za ta yi kuka. Mansura cikin kuka ta ce "Ba Yaya Abbanku bane ya maran, Kuma mama ba ta yi masa fada ba, ni ta yi ma fada ma. Ni tafiya Zan yi in bar muku gidanku." Amina cikin tashin hankali, jin Mansura za ta tafi, ta rasa dalili tana matukar kaunar Mansura a ranta, hakan ya sa cikin tashin hankali ta ce "Wayyo dear dan Allah karki tafi, Wallahi Yaya Abba haka yake, ko nima baki ji ba yadda yake min fada, dan Allah ki yi hakuri Yaya Abba ba zai Kara dukanki ba." Mansura da har yanzu kuka take, dan har idanta ya canza kamanni ta ce "Tom ki ce ya ban hakuri, in ba haka ba Wallahi ni gara in tafi." Amina da kuka itama ba wuya yake Mata ba, fita ta yi daga bedroom din ta nufi falo fa gudu tana kuka. Tana zuwa ta fada kan mahaifiyarta dake zaune tana kuka. Mahaifiyar Amina kamo Amina ta yi tana cewa "Subahanallahi, Amina me ya faru Kuma?." Mama, Mansura ta ce tafiya za ta yi ba zata zauna ba, dan Allah mu je ki bata hakuri, ni dai Wallahi ina sonta bana so ta tafi." Amina ta idasa maganar cikin kuka. Mahaifiyar Amina ganin yadda Amina ke kuka buga Mata bayanta ta fara tana cewa "Shi kenan, Amina ki natsu ki fada min Mana, me ya sa za ta tafi?." Amina goge hawayanta ta yi ta ce "Yaya Abba ne dazu ya kama marinta, dan zai yi mata allura ta goce, Kuma kema mama kika yi ta Mata fada, ni dai Mama ki yi ma Yaya Abba magana dan Allah ya bata hakuri karta tafi." Mahaifiyar Amina al'ajabi ya sa ta kasa cewa komai. Bata taba tunanin sangartar Mansura takai haka ba, sai yau. Mamakin kalar shagwabawar da aka yi ma Mansura take, wadda ba ta san daidai ba kamar ta haka,. A iya shekarun yarinyar yanzu ai ya kamata ace ta san daidai ta san ba daidai ba. Amina Kuma jin mahaifiyarta ta yi shiru ya sa ta ce "Mama, dan Allah, kin ga marainiya ce, mu tausaya mata." Mahaifiyar Abba kallan Amina ta yi ta ce "Shi kenan, Zan ma Abban magana in ya dawo." Mahaifiyar Amina fadi haka ne dan Amina ta rabu da ita. Yau ma kamar jiya Abba ya dawo. Yana zaune suna fira da mahaifiyarsa, Amina ta shigo falon. Bayan ta yi ma Abba barka da dawowa zama ta yi ta yi shiru, tana sauraran ta ji Abba ya ce ta Kira Mansura ya bata hakuri ta ji shiru. Amina, kallan mahaifiyarta ta yi ta ce "Mama, kin fada masa." Ke baki da baki ne da ba zaki fada masa da kanki ba?." Amina baki ta turo. Abba Kuma aje wayar hannunsa ya yi yana kallan Amina ya ce "Me kike son fada min, da ba za ki iya ba sai mama ce zata fada mi? Fada min ina jinki?." Abba ya ce yana kallan Amina. Amina wasa da yatsun hannunta ta fara, da alama dai kamar maganar na naiman yi mata nauyin fada. Abba dai bai kuma tambayarta ba, amma ya mai da kallansa ga Amina, irin kallan ke nake saurare. Amina cikin kame-kame ta ce "Yaya Abba Marin da ka yi ma Mansura dazu ne take ta kuka har yanzu, ta ce tafiya za ta yi indai baka bata hakuri ba. Kuma Wallahi Yaya Abba baka ga fuskarta ba." Amina har ta Kai maganarta, daga Abba har mahaifiyarsa Amina kawai suke. Abba dan ya kauda mamakinsa, kallan Amina ya yi ya ce "Ita tace ni sai na bata hakurin marin da na yi Mata?." "Wallahi Yaya Abba baka ga fuskarta ba." Abba hararar Amina ya yi ya ce "Tambayar da na yi miki kenan? Na ce ita ta ce sai na bata hakuri.?." Eh, Yaya Abba dan Allah ka bata." Abba shiru ya yi yama rasa abin da zaice, kila shi ya sa ya kauda maganar ya ce "Ya jikin nata? Zazzabin ya dawo?." A'a, baidawowa ba. Amma ta ce min tunda ka mareta kanta ke ciwo." Shiru Abba ya yi, kafin ya ce "Kira min ita, ta zo da ledar maganin." Mansura tashi ta yi ta nufi sight dinsu, Kwance ta iske Mansura kamar yadda ta barta. Amina dafa Mansura ta yi da har yanzu hawaye bai bar fita a idonta ba ta ce "Dear ki yi hakuri haka nan dan Allah, na yi ma Yaya Abba magana yana falo ya ce ki zo." Amina hannu ta mika ma Mansura ta tashi, da yake tun safe taki cin komai hakan ya sa bata da karfin jiki sosai. Mansura na bin Amina suka isa har falon. Mansura zama ta yi kusa da Amina. Amina kallan Abba ta yi dake dannawa waya da alama kamar bai san sun shigo ba, Amina ta ce "Yaya Abba ga Mansurar." Abba Kai ya dago ya saukesu akan Mansurar. Abba ko ba a fada mai ba yasan ta ci kuka dan ga idanunta nan sun yi ja. Abba cikin kasa da murya kamar dole akai mai ya yi maganar ya ce "Lafiya me akai miki kike kuka?." Mansura goge hawayan da ya zibomata ta yi ta ce "Ba Kai bane dazu ban yi maka komai ba kamaran, Kuma har yanzu kunnena ciwo yake." Abba Kai ya dago sosai ya kalleta, ya rasa abin dama zai ce mata, ya dade yana kallanta kafin ya ce a hankali kamar ance dole sai ya bata hakurin ya ce "Sorry." Mansura dai kanta kasa bata ce komai ba, Kuma Bata fasa zubar da hawaynta ba, dan ta raina yadda ya bata hakurin. Mahaifiyar Abba kallan Mansura ta yi ganin har yanzu tana zubar da hawaye ta ce , "Tom ki yi hakuri ya isa sai ki bar kukan haka nan ko?." Abba hannu ya mika ma Amina alamun ta bashi magungunan Mansurar. Mansura Mika masa ta yi. Amina ta Mika masa magungunan ta yi. Abba lura da Mansura iya gaskiyarta take tsoran allurar ya sa bai bi takan Kuma yi mata allurar ba, ya hada allurar da maganin ya tusa a ajjihunsa. Mansura ko murmushin farin ciki ta yi, ganin Abba ya tusa ledar magungunan cikin aljihunsa, haka ya nuna ba zai Kuma yi Mata ba kenan, hakan ya sa Mansura cikin jin dadin yau ba za a yi mata allura ba ta tashi za ta tafi. Amina kallanta ta yi, ta ce "Mansura, Abinci fa?." Nakoshi." Mansura ta ce ta juya ta tafi. Amina tashi ta yi ta bi bayan Mansura, ta ji dalilin da ya sa ba zata ci abinci ba bayan tun safe rabonta da abinci. Mahaifiyar Abba kallan Abba ta yi, ta ce "Abbana, nikam sai inga yarinyar nan kamar tana da wata boyayyar damuwa da ta aje a ranta. Lokuta da dama zaka ga idonta ya yi jajir alamun ta ci kuka, Koda yaushe ina tambayar Amina kodai ta fada mata wani abu, amma sai ta ce min bata fada mata komai ba." Shiru Abba ya yi kafin ya ce "Mama, tun farko ba na fada miki yarinyar nan ba gaskiya ta fada mana labarinta ba." Kai mahaifiyar Abba ta jinjina alamun hakane ta ce "Gaskiya yanzu na fara yadda, saboda idan mutuwar iyayanta ce ya kamata ce ta dangana haka nan, hakika mutuwa na da radadi da Kuma magagi, tom Amma Allah na sa ma mutum juriya aransa, musamman idan aka arba'an, sannan in dai bawa ya yi imanun kowa zai mutu radadin mutuwa da magaginta na watannaine, Allah na sama bawa salama a rai, sai dai ranar da ya tuna ya yi kuka, amma ba irin Wanda nake ganin yarinyar nan na yi ba, kukanta baya kama da na rashi, ya fi yanayi da furgici da gigita. Tom, amma dai inda har yanzu bata nuna mana wani aibunta ba sai mu yi hakuri murungumi kaddarar kasancewa data." Abba kallan mahaifiyarshi ya yi kafin ya ce "Shagwaba ta yi ma yarinyar yawa da sangarta, bare a fahimceta da kyau, shi ya sa nake ganin ko tsabar shagwaba ne ya sa take hakan?." Tom, kila, zai iya yuwuwa shagwabarce. Yauwa Abba mu bar wannan maganar ma, na ce yau she zaka je ganin jaririn Zainab? Ka ga dai yau kwana biyu da haihuwar." Abba ido ya zaro da sai yanzu ya tuna da maganar haihuwar, ya ce "Gobe in sha Allah zani." Mahaifiyar Abba, hararar Abba ta yi ta ce "Kamanta goban mu ka yi da Kai za ka je ganin Aisha, yarinyar da muka yi magana." Abba shafa kan shi ya yi bisa ga alama ya manta, ya ce "Wallahi na shafa'a, in sha Allah goban sai inje, amma Mama ita ta san da zuwan nawa?." Ta sani Mana, mahaifiyarta ta sanar Mata, ka ga idan kuka daidaita ba sai a hada a yi da na Amina ba." Murmushi Abba ya yi ya ce "Allah ya kaimu goban sai in je in ganta✍🏻 Fadila Sani Bakori ce ⭐ ABBANA ⭐ 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚* Daga Marubuciyar *Fadeela *Meenalyn Daddy *Oga Habib *Abdurrahim *In da rai *So ne sila *Daga Allah ko dora ma Kai *Rayuwar Haidar *Bakin kishi Domin samun littafin ABBANA daga farko 👇🏻Follow the ABBANA channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaYZGsNEFeXsr1CKQl3r Litafin Abbana na kudi 400 my number 08063830828 P 15-16 Washegari ya kama juma'a, Abba 4 ya dawo aiki, Yana dawowa ya yi shirin zuwa wajan Aisha kamar yadda suka yi da mahaifiyarsa. Abba bayan ya fito da shirin zuwa gidansu Aisha, Kallan mahaifiyarsa ya yi ya ce "Mama, zan tafi gidansu Aishar." Mahaifiyar Abba zaro idanunta ta yi ta ce "Abbana, a haka zaka gidan surikan naka? Haba Abbana wayace maka ana zuwa gidan surikai da k'ananan kaya, ka sa manyan kaya mana." Abba bata rai ya yi ya ce "Haba mama, kayan nan me suka yi." Ni dai dan Allah ka je ka canza." Abba ba tare ya kara cewa komai ba ya tafi ya canza kayan daga can ya wuce gidansu Aisha, da yake yasan gidan yana kai mahaifiyarsa in abin Allah ya sa alkairi ya samu ko alakyauta. Kasan cewar ansan da zuwan Abban ya sa duk wani abu na tarbar bako an tanadar masa shi. Yana zuwa gidan ya Kira Aisha a waya. Aisha na zaune cikin jillimin bakon da mahaifiyarta ta sanar da ita zai zo wajanta yanzu, ta ji ringing din wayarta. Aisha cikin siririyar muryarta ta daga wayar tare da yin sallama. "Gani a kofar gidanku." Abba ya ce yana mai kashe wayarsa. Aisha tashi ta yi tana sanye da hijab dinkin bare kyada. Abba na nan tsaye hankalinsa gaba daya ya tafi a wayar hannunsa, Aisha ta yi masa sallama ta yi. Abba dago kansa ya yi yana mai zuba mata idanunsa. Aisha kanta kasa ta gaida Abba. Abba amsa mata ya yi babu yabo babu fallasa. Aisha kallan Abba ta yi ta ce "Mu shiga falon Daddyna kamar zai fi safe." Kai Abba ya girgiza ya ce "A'a nanma ya isa." Shiru ya yi kafin ya dora da cewa "Nasan gida an gabatar miki da koni waye tun kafin in zo." Aisha Kai ta jinjina ma Abba, ta ce "Eh, haka ne,Malama ta fada min komai." Abba shiru ya yi, kafin ya ce "Ma Sha Allah na ganki mai sunan mommyna, kamar yadda mahaifiyata ta umarce ni. Ya kiba ganni na yi Miki?." Abba ya tambayi Aisha. Aisha jin tambayar ta yi wani iri, kasa cewa komai ta yi kanta kasa. Abba, Kiran sunanta ya yi ya ce "Malama baki ban amsa ba kin sidda Kai kasa, dalilin da ya sa na yi miki tambayarne bansan ko kina da Wanda zaki aura ba ake son hadaki dani, kamar ni Kinga ban shirya aure ba, zan ne bisa umarnin mahaifiyata ba bisa son raina ba." Aisha shiru ta yi tana jin maganganun nasa wasu iri, hakan ya sa ta ce "Ayyah, yayana nima hakane a bangarena, zan yi biyayya da umarnin mahaifiyata ne." Murmushi Abba ya yi ya ce " Ni a ganina bai kamata mu yi abin da zamu cutar da kanmu ba ki yi tunani, na barki lafiya." Abba na fadin haka ya ja motarsa ya tafi ya abar Aisha da tunani, dan idan zata fada makanta gaskiya Abba ya yi Mata, dan haka ba ta jin zata iya mujirema bukatar zuciyarta, sanan uwa uba mahaifiyarsa na sonta. Abba ba shi ya koma gidan ba sai bayan sallar issha'i. Mahaifiyar Abba da fara'arta ta tarbi Abba tana cewa "Babana fira ta yi dadi, da alama dai tare da na Amina za a hada nan da wata uku musha biki." Abba zama ya yi yana murmushi. Amina ko da ta kaku ta ji sauran labarin ido ta zaro ta ce "Laa, Yaya Abba aure zai yi mama?." Amina ta ida maganar cikin jin dadi sosai. tana taba Mansura da yake duk suna falon. Mahaifiyar Abba murmushi ta yi ta ce "Aiko ki fara shirye-shiryan tarbar Auntynki. Oh namanta she bakya gidan kema lokacin za mu mika ki gidan Ahmad." Amina turo baki ta yi. Mahaifiyar Abba maida kallanta ga Abba ta yi ta ce "Abbana, ya Aishar?." Abba kallan mahaifiyarsa ya yi ganin yadda take ta doki da lamarin, cikin danne abin da ke damunsa ya ce "Na ganta Mama, ita ba kyakkyawa ba ita ba mummuna ba." Mahaifiyar Abba bata fuska ta yi ta ce "Abbana, babu mummuni a musulmi, Kuma kyawun zuciya ya fi na fuska, ni dai yanzu fadamin ya kuka yi da ita?." Abba ji ya yi bakinsa ya kasa furta kalmar a'a, hakan ya sa ya ce "Mama itama fa yarinyar ta sanar dani tana da Wanda take so." Mahaifiyar Abba bata fuska ta yi ta ce "Idan tana da Wanda take so kenan shi kenan Kai ma kana da wadda kake so baka sonta, Yes or no?." Abba kallan mahaifiyarshi ya yi wanda daga gani kiris take jira ta ji ya furta abin da ke ransa ta ci ubansa. Abba cikin jarumta ya ce "Mama, dan Allah ki canza min wata, yarinyar ta cika shiru-shiru, tana magana tana tsugunnar da Kai kamar munafuka." Mahaifiyar Abba ta dade tana kallan Abba kafin ta sauke ajiyar zuciya ta ce " Kamanta abin da ka ce min jiya ko, ka ce ko baka ganta ba in dai ta yi min to zaka aureta, kenan dadin baki ka yi min, dan haka in dai ka ga baka auri Aisha ba to ban da raine, amma Wallahi tun da bakinka ya furta sai ka aureta, inda har sai da na ji ta bakinka kafin in sanar da mahaifiyarta, dan haka baka isa ba kasa in yi karamar magana ba Wallahi, idan kana da shirin da za ka yima ka shirya dan in sha Allah tare za a hada auran da na Aisha, zan samu baban yara mu yi magana gobe." Mahaifiyar Abba na kaiwa haka ta tashi tabar ma Abba falon, dan bai taba bata mata rai irin yau ba, tun da ta fara ganin Aisha yarinyar ke burgeta, dan da dama itake masu karin karatu idan mahaifiyarta ba zata zo ba. Sai da Allah zai amsa mata rokanta da ta yi ya naimi kawo Mata matsala. Abba shiru ya yi ganin mahaifiyarsa ta tafi, dafe kai ya yi yama rasa abin cewa. Mansura da gaba daya itama ba cikin hayyacinta take ba tun da ta ji maganar auran Amina. Tashi ta yi da sauri ta bar falon jin kuka zai kubuce Mata. Amina Kuma zuwa ta yi ta zauna kusa da yayanta ta ce "Yaya Abba Wai meka faruwa ne tsakaninka da mama?." Abba kallan Amina ya yi cikin damuwa ya ce "Wata yarinya Mama ta lakaba min in aura, Wallahi Amina kafin in ga yarinyar sai na ji na aminta da zabin mama, Amma Kuma da na ganta sai na ji gaba daya bata yi min ba, shine nake sanar da mama akan ta canza min wata, kin ji dalilin fadan." Amina cikin damuwa itama ta ce "Amma Yaya Abba meye aibunta, gata da ilimin addini sosai, da dama ma fa ita ke koyar da su Mama."Amina Wallahi na rasa dalili, Amma actual abin da na sani bana so in ga mace ta cika sanyi irin nata haka." Amina kallan Abba ta yi ta ce "Tom Yaya Abba kana da wadda kake so ne?." A yanzu babu." Shiru Amina ta yi kafin ta ce "Yaya Abba indai haka ne ka yi hakuri da zabin mama, idan ba haka ba da alama zaku iya samun saba ni." Ajiyar zuciya Abba ya soke ya ce "Zan yi ƙoƙarin ganin na koya ma kaina sonta." Yauwa yayana shi ya sa nake yinka da yawa kana da saurin fahimta." Abba dungure Amina ya yi Yana murmushi ya tashi ya nufi bangaransa. Amina kwance ta iske Mansura tana kuka, ta tusa kanta tsakankanin cinyoyinta tana kuka. Amina cikin damuwa ta ce "Mansura wai ke yaushe zaki daina kuka ne? Baki gajiya da kuka ? Shi kenan ba damar ki kasance ke kadai sai kuka. Yanzu yi hakuri dan Allah ki fada min meye?." Mansura dagowa ta yi tana kallan Amina, ta ce "Idan kika yi aure dawa zan zauna, Kuma bansan Ina zani ba, nan da wata uku za ki yi aure ki barni. Wallahi ba zan iya jure abin da ke raina ba babu ke, kashe kaina zan yi in huta, da azabar kuncin da furgicin da nake sha a raye." Amina da idonta da ya cika da kwalla take kallan Mansura jin kalamanta. Amina ta dade tana kallan Mansura kafin ta ce "Mansura ki huta da kuncin da furgicin da kike sha a raye kika ce, kuma kika furta kalmar za ki kashe kanki, duk da na yi alƙawarin ba zan sake tambayarki akan abin da baki son asani ba, hakan ba zai sa in janye daga gareki ba, dan Allah Mansura ki bar irin kalaman nan, kin manta na yi miki alkawari zan yi ma Yaya Abba magana a d'aga har sai sanda kika samu muji kafin a hada a yi gabadaya?." Kai Mansura ta girgiza ta ce "A'a ni dai karki fada ma kowa Kar a hada auran, ni Babu wani miji da Allah zai fito min da shi, ni bazan taba yin aure ba.." Amina rasa abin da zata ce ma Mansura ta yi hakan ya sa ta yi shiru tana lallashin Mansurar, a haka dai har barci ya kwace Amina. Bangaran gidan su Aisha, mahaifiyar Aisha Koda ta tambayi Aisha yadda suka yi da bakonta, Aisha ba ta gayama mata gaskiyar yadda suka yi da Abba ba, ce ma mahaifiyarta ta yi sun aminta da junansu. Aisha duk da ba taga alamar Abba zai kirata a waya ba, amma tuk da haka daga wayarta ta yi ringing sai ta dauka ko shine, sai ta duba taka daga akasin hakan. Aisha wayata ta dakko ta tura ma Abba da sako kamar haka. "Ina fatan ka kaje gida lafiya." Bangaran Abba ko Koda ya ga sakon tsaki ya yi. Aisha irin matannan ce masu shishshige, hakan ya sa tana jin mahaifiyarta ta ce mahaifiyar Abba ta sanar ba za ta zo Islamiya ba kwana biyu saboda kanwar Abba ta haihu. Aisha kallan mahaifiyarta ta yi ta ce "Mama ni ko Ina son zuwa sunan." Aisha ta fada tana kallan mahaifiyarta ta ji abin da za ta ce. Mahaifiyar Aisha shiru ta yi, kafin ta ce "Shi kenan bari in sanar da Aishar." Da yake Aisha sunan mahaifiyar Abba gareta. Mahaifiyar Aisha Kiran mahaifiyar Abba ta yi ta sanar da ita ta Aisha za ta je masu suna. Mahaifiyar Abba ko da murnarta ta ce "Shi kenan, Zan ba Amina number Aishar sai su tafi tare." Mahaifiyar Abba bangaransu Amina ta shiga bayan ta gama wayar, zama ta yi tana cewa" Amina, gobe da yaushe ne za ku gidan sunan? Aisha wadda yayanku zai aura tana so za ta je na ce sai ku je tare." Amina ta shi ta yi da murnarta ta ce "Wayyo Mama ban numberta." Amina ta idasa maganar tana dakko wayarta. Mahaifiyar Amina number Aisha ta sama Amina ta mika mata ta fita. Amina da yake mai son mutane ce take ta doka ma Aisha Kira, sun jima suna waya kafin Amina ta yi mata sallama da sunan sai sun hadu gobe. Bangaran Aisha Kuma duk wata fargaba dake damunta game da Abba duk sai ta ji babu ita, dan kiran Amina sai ya Kuma tabbatar mata da auranta da Abba kamar yadda take fata. Hakan ya sa take ta dakko wayarta ta fara rubuta ma Abba text message kamar haka. "Assalamu alaikum mosoyin zuciyata, Ina fatan kana cikin koshin lafiya da nishadi." Abba Koda ya ga sakon Aishar tsaki ya yi ya maida wayarsa ya aje. Washegari, Amina da wuri ta tashi suka yi shirin tafiya gidan suna. Jin Aisha shiru kiranta ta yi ta sanar Mata sun shirya ita suke jira. Aisha ta ki Kiran Amina ne dama dan ta ga ko sun damu da ita, ana haka ko kiran Amina ya shigo wayarta ta sanar Mata ita suke jira. Aisha simple makeup ta yi, ta zura hijb dinta doge har kasa tare da nikabi ta rufe fuskarta. Sallama ta yi ma mahaifiyarta dan ta bata address din gidan surukan nata. Amina suna nan zaune Aisha ta yi sallama ta shigo gidan. Amina da kallo ta bita dan bata gane itace Aishar ba, mahaifiyar Amina da yake tana falon kallan Aisha ta yi tana murmushi ta ce "Amina ga Aishar nan ta karaso. Amina da gudu ta ruga ta rungume Aisha, a haka suka karaso har falon. Aisha cikin girmamawa ta gaida surukarta. Amina kallan Mansura ta yi tana mamakin halinta ganin ko inda Aisha take bata kalla ba, Amina dafa Mansura ta ce "Dear mu je ko?." Mansura tashi ta yi suka tafi. Bayan sun fita gidan Aisha ta kalli Mansura ta ce "Ina kwana sister." Lafiya." Mansura ta ce mata ta dauke kai. Amina da mamaki ta kalli Mansura amma Kuma sai ba ta ce mata komai ba. Napep suka hau har gidan sunan, Aisha da Amina sai firarsu suke Mansura dai ba ta sa masu baki ba. Amina cikin hirarne ta ce "Aunty amaryar yayanmu Abba, ni fa na gaji da kawaici ki bude mana fuska mu ganki." Murmushi Aisha ta yi ta ce "Ki bari sai mun je gidan sunanko ba a nan a titi ba." Amina bude baki ta yi ta ce "Tom mu da muka sa gyale sai Yaya kenan?." Dariya Aisha ta yi ta ce "Ku kunsaba fita haka, nima na saba fita a haka." Haka dai suka ci gaba da hirarsu har suka Kai gidansunan, ban da Mansura da bata tanka masu ba, dama Kuma ita ba ma'abociyar magana ba ce. Ko a gidan sunan Mansura fita waje ta yi dan duk sai taji ta takura kasan cewar yawan jama'a da hayaniya, hakan ya sa ta fita waje ta zauna. A cikin gidan kuma Amina sai naiman Mansura ta ke, Aisha ce ta kalleta ta ce "Anya kuwa ba fita ta yi ba." Wajan suka duba inda suka iske Mansura zaune ta yi tagumi, daga ganinta ta yi nisa sosai a duniyar tunani. Amina dafa Mansura ta yi ta ce "Mansura lafiya kika fito waje kika zauna anata hutuna?." Mansura dako jajayan idanunta ta yi ta ce "Ni gida Zan tafi." Amina da mamaki ta ce "Gida Kuma Mansura, baki ga na zo Mana da kayan canzawa ba ? A nan fa zamu kwana." Ni dai gida zan tafi." Mansura ta sake maimaitawa Kamar za ta yi kuka. Aisha tsugunnawa ta yi ta dafa Mansura ta ce "Sister, dan Allah idan wani abun akai miki ki yi hakuri ya za ayi kun zo suna daniyar kwana Kuma ku tafi gida, ko mama ma in taga Kun koma gida suna baiwatse ba ai ba zata ji dadi ba." Mansura ture hannun Aisha ta yi dake kan kafadarta ta ce "Da allacan malama ki sakan za ki zo ki kama dafa ni da katsamin hannunki." Amina da Mansura ta gama kaita bango cikin fushi ta ce "Haba Mansura wai meye kike yi haka ne? Matar da Yaya Abba zai aura kike in gijewa dan ta fada miki gaskiya." Mansura da babu abin da tasani ban da ririta, yana daya daga cikin abin da ya sa ta saki jiki da Amina har itama take mata kallan masoyiyartace, amma ganin yanzu ta dake tana mata faɗa akan Aisha sai ta ji ranta ya bace har ta fara daukar ko Amina ta gaji da ita ne. Mansura cikin goge hawayan da ya fara zubar Mata ta ce "Na ingijeta din." Amina kama hannun Aisha ta yi suka tafi suka bar Mansura nan tsaye. Mansura fashewa ta yi da kuka. Mansura ta dade tana kuka kafin ta samu napep ta tafi gidansu Amina. Mansura kallan mai napep din ta yi bayan ya sauketa ta ce "Dan Allah ka yi hakuri ban da kudi." Wani mugun ashar ya mulmulo ya danna ma Mansura ya ce "Wallahi ko ubawan waye ya tsaya miki sai kin ban kudina zaki bar wajan nan." Mansura da kwatakwata ba ta da wuyar kuka fashewa da kuka ta yi ganin wai yau itace za a rike akan k'ananan kudi. Gashi lokacin duhu ya fara yi ana ta sallar magariba, ana cikin haka sai ga Abba ya dawo Sallah zai shiga gidan. Abba damamaki ya tsaya jin kuka mace shi Kuma Mai napep din ya dage sai cewa yake "Wallahi ko kukan jini za ki yi sai kin biyani kudina, ubanwa ya ce ki hau min keke baki da kudi." Abba karasawa ya yi wajan ba dan ya san dawa ake fadan ba. Da mamaki Abba ya bi Mansura da kallo, ta dage sai uban kuka take ci. Abba tsawa ya yi ma mai napep din ya ce "Ba kada da ankali ne da zaka riketa akan k'ananan kudi, sakarta." Da yake mai napep din irin yan tashar nan ne ya ce " Yo rankashidade aban kudina mana aga in ban saketa ba." Sakarta. "Nawa ne kudin naka?." Dubu biyu ce." Abba kudin ya ba ma mai napep din, sannan ya kalli Mansura ya ce "Ina Aminar fa?." Tana can." Mansura ta ce tana goge hawayanta. Abba juyawa ya yi ya yi cikin gidan Mansura ta bi shi a baya. A falon Mahaifiyar Abba Abba ya zauna, kafin ya ce ma Mansura "Me ya sa ke kika dawo?." Mansura zata yi magana sai kuka, babu irin tambayar da Abba bai yima Mansura ba amma taki Magana sai kuka take. Abba Kiran Amina ya yi a waya tana dagawa ya ce "Amina me aka yi ma yarinyar nan?." Amina na jin haka ta san Mansura yake nufi, cikin jin haushin Mansurar ta ce "Yaya Abba babu fa abinda aka yi mata, ita kawai komai kuka take Mai, matar da za ka aurace fa daga ta yi...." Tsawar da Abba ya yi ma Amina ce ya sa ta yi shiru. Dan yasan wa take nufi an fada mishi tare da Aisha suka tafi. Abba cikin bacin rai ya ce "Wallahi Koda wasa kika kara hadani da yarinyar nan zaki ga abin da zan mik.." ai ko hadaka da ita yanzu ma ta fara, dan gobe iyayanka za su je naimamaka auranta✍🏻 Fadila Sani Bakori ce ⭐ ABBANA ⭐ 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚* Domin samun littafin ABBANA daga farko 👇🏻Follow the ABBANA channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaYZGsNEFeXsr1CKQl3r Litafin Abbana na kudi 400 my number 08063830828 P 17-18 Abba cikin bacin rai ya ce "Wallahi Koda wasa kika kara hadani da yarinyar nan zaki ga abinda zan Miki.." ai ko hadaka da ita yanzu ma ta fara, dan gobe iyayanka za suje naimamaka auranta." Abba shiru ya yi bai tanka, ba daga ƙarshe ya tashi ya koma sight dinsa. Washegari kamar yadda mahaifiyar Abba ta ce iyayan Abba suka je naiman auran Aisha. Kasan cewar iyayan Aisha manya mutane ne, mahaifinta babban malami ne kusan ansa shi kaf cikin garin Katsina, hakan ya sa aka yi komai kamar yadda addinin musulunci ya tsara.Inda aka sa ranar auran daidai dana Amina sati 11 kenan. Bayan an kammala komai baba karami ya taho da cingam da biscuit da sweet ya nufi gidansu Abba. Kasan cewar weekend ne ya sa Abba yana gida, yana falon mahaifiyarsa zaune baba karami ya yi sallama ya shigo rike da kwalayan biscuits a hannunsa, diresu ya yi kafin ya dora da cewa "Aisha ga abin sa ranar nan, munje anyi komai an gama an tsaida lokacin aure daya da na Amina. Amma gaskiya duk mun yi murna ganin inda Abba yaje ya naimi aure, dan gidan shaikh Sani babban gudane, juri'ar gidan duk malamai ne, fatan dai Allah ya nuna Mana ranar lafiya." Mahaifiyar Abba sun dade suna tataunawa da Baba karami akan auran kafin ya yi mata sallama, ya kalli Abba da bacin gaisawa da suka yi uffan baice ba. Baba karami ya ce "Abba muje sauran kayan na motata ka dakko." Abba tashi ya yi ya bi Baba karami, suna fita Abba ya kalli baba karami cikin alamun damuwa ya ce "Baba karami, Wallahi ko kadan bana son yarinyar nan da mama ke shirin hadani da ita, tom amma inda aikin gama ya riga ya gama ya zanyi, inda har kun riga kunje, Amma baba dan Allah Ina naiman alfarmar a daga auran nan da wata 5 lokacin na kammala duk wani shiri da zanyi, ka ga shi kanshi wanda zai auri Amina bashi da amini sama dani, dukanmu ba za mu ji dadin hudimarmu ta kasance rana daya ba." Shiru Baba karami ya yi kafin ya dafa Abba ya ce "Abba ka kwantar da hankalinki ka ji, hakika mahaifiyarka ta zabar maka aure gidan ya ya dace, gidan mutunci, in sha Allah za ka yi alfaharin zama da ita nan gaba, maganar aure Kuma da kake so adaga inda kaine me yi ba za a shiga hakinka ba za a d'aga kamar yadda kanaima, gobe zan je in samu iyayan yarinyar mu yi magana." Godiya sosai Abba ya yi ma baba karami kafin ya dauki kwalayan ya shiga da su falon mahaifiyar tashi. Aisha ko lokacin da mahaifiyarta tasanadarmata da sa ranarta da Abba tayi murnar amma fargaba tafi yawa atare da ita, dan tun ranar da Abba ya zo wajanta har yau bai sake dawowa ba, bare Kuma ya kirata. Amina wayarta ta dakko ta tura ma Abba da Sako kamar haka "Assalamu alaikum, amincin Allah ya tabbata ga zabin zuciyata. jiya na zo gidanku cike da dokin ganin kyakkyawar fuskarka, sai dai kash lokaci ya rike min Kai baibani damar ganawa da Kai ba, amma banyi fushi ba inda na ga fuskar da ta yi sanadin zuwan taka fuskar duniya. cikim hikimar Allah Kuma a yanzun nan na ji wani daddadan albishir din rayuwa tare da kai na har abadan abidina in sha Allah. Abba Koda ya gama karanta sakon Aisha tsaki ya yi ya goge text message din. Mahaifiyar Abba ko sosai ta yi mamaki lokacin da sakon daga ranar auran Abba ya isa gareta, ta nan zaune Abba ya shigo da shirinsa na tafiya aiki. Abba ganin yadda mahaifiyarsa ta daure fuska kamar ba ta taba dariya ba hakan ya sa ya sha jinin jikinsa, dan Koda ya gaidata ba ta amsa gaisuwarsa ba ta ce "Meye nufinka na daga auran nan da kasa aka yi?." Abba cikin son mahaifiyar tasa ta fahimce shi ya ce "Mama nifa kadai ne maiyin hidimar nan, duk da baba karami ya ce zai yi ma Aisha kayan daki ba barmai zan yi ba inda hidima yanzu shima ta yi mai yawa, Ina ganin kamar in aka daga din zan fi jin dadin yin tawa hidimar cikin kwanciyar hankali idan ba a hada ba." Murmushi mahaifiyar Abba ta yi ta ce "Hmmmm, Idan ma da wata manufar ka yi ya rage naka, dan ko bayan raina ka fasa auran Aisha ban yafe maka ba." Abba da mamaki ya dago kansa ya kalli mahaifiyarsa jin murucinta, amma baice komai ba ya yi mata sallama ya tafi. Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya babu ranar da Aisha ba za ta tura ma Abba sakon gaisuwa ba, daga ya ga itace ko karantawa ba ya yi yake gogewa. Mahaifiyar Amina ganin biki sai gabatowa yake har yanzu ba ta ji sun yi maganar anko ba ya sa ta samisu Aminar ta ce "Mansura Wai ba za ku fidda anko bane? Wata daya biki ya rage amma har yanzu ban ji Kuna maganar anko ba? Ko ba za ku yi bane, ga kudin gyaran jiki har na biya mai gyan jikin zata fara zuwa duk abin da za ku yi ku yi kafin a fara gyaran jiki dan daga an fara babu fita." Mansura duk da take ba ma'abociyar zuwa biki ba tasan ana anko, hakan ya sa ta kalli mahaifiyar Amina ta ce "Mama gobe sai mu je musiyo." Amina dai ba ta ce komai ba,dan tuni take so ta yi ma Mansura maganar ankon amma Kuma tana tsoran Mansura ta shiga damuwa dan daga anyi maganar bikin take shiga damuwa tunanin zata fara rayuwa babu Amina. Amina Kuma wayarta ta dakko ta Kira Aisha ta shaida Mata ta zo gobe za su je siyo anko." Aisha sosai ta yi murnar hakan, dan tana jin dadi duk lokacin da ta ga sun nuna kalawarsu akanta, hakan na rage mata fargabar zama da Abba inda Allah ya bata soyayyar danginsa. Washegari su Amina suka shirya suka je suka siyo ankon, inda suka zabi lass dinsu me kyau da atamfa. Suna hanyar dawowa ne Aisha ta kalli Amina ta ce "Amina za ku yi walima ne?." Tom Wallahi ban sani ba amma kila mama ta yi." Cewar Amina. Haka suka ci gaba da hirarsu har aka zo kofar gidansu Aisha ta sauka aka wuce da su Mansura gida. Tun daga wannan ranar walwalar Mansura ta rage ya zamana kullum cikin damuwa take. Haka nan take jin kamar ba za ta iya rayuwa a gidan babu Amina. Hakan sai ya Kara c maida Mansura shiru-shiru a gidan. Yau mahaifiyar Abba suna zaune kallan Abba ta yi ta ce "Wata daya kenan da kwanakai da sa ranar auranka da Aisha, tun da aka sa ranar ka je wajanta?." Abba Kai ya fara sosawa alamun rashin gaskiya. Mahaifiyar Abba kallan Abba ta yi kafin ta ce "Ka shirya ka je yau, idan ka je ka tambayeta nawa ne kudin ankon Amina kabata, Kuma ka kirata ka sanar Mata zuwanka." Abba shiru ya yi baice komai ba ya tashi ya fita. Amina ya Kira ya ce ta zo ta rakashi gidansu Aisha. Amina da dokinta ta bishi suka tafi bayan ta sanar da Mansura zata raka Abba. Abba suna tafiya ya kalli Amina ya ce nawa ne lass din da kuka fidda da atamfa?." Duka 45 thousands." Kai Abba ya jinjina. Suna zuwa kofar gidansu Aisha Abba ya tura ma Amina text message kamar haka "ki fito ga ni a kofar gidanku." Kasan cewar wayar Aisha ba ta kusa da ita hakan ya sa bataga sakon Abba ba. Abba jin shiru-shiru Aisha bata fito ba key ya sa ma motarsa ya juya zai tafi. Amina rike hannun Abba ta yi tana marairaicewa ta ce "Yaya Abba baka kirata Mana." Abba daure fuska ya yi ya ce na tura Mata text tun dazu wayau zata raina ma mutane." Amina Kai ta girgiza tana tunin in ita ce Aisha gara ta fasa auran nan, dan kadan daga cikin rashin son namiji kenan ba zai yi maka uziri ba ko daya, gashi nan ita tun kafin a yi auran ya kasa jurewa akan abin da baikai ya kawo ba. Amina wayarta ta dakko ta Kira Aisha, ba ta daga ba sai da ta sake Kira kafin ta dauka. Amina cikin tausaya ma Aisha ta ce "Mommyna gamu a kofar ginku ni da Yaya Abba." Aisha sai yanzu ta lura da sakon da Abba ya tura Mata. Hijab dinta ta zura har kasa ta fito. Amina kallan Abba ta yi ta ce "Yaya Abba dan Allah ka so Mommyna Mana kodan sunan mama da take da shi, Kuma Wallahi tana sonka sosai." Abba daure fuska ya yi, hakan ya sa Amina ta ja bakinta ta yi shiru. Suna a haka Aisha ta fito. Amina rungume Aisha ta yi tana cewa "Mommyna." Dan Amina sosai take jin son Aisha a ranta. Abba Kuma 30k ya ciro ya mika ma Aisha ya ce gashi ki yi manage na ankon Amina." A'a Yaya Abba hidima ta yi yawa dan Allah ka barshi Aisha ta fada cikin jin dadin Abba ya fara sonta. Abba Amina ya mikamawa ya ce "Amina amsa ki Bata." Aisha ganin haka ta dauka ya yi fushi ne dan taki amsa, hakan ya sa ta amsa daga hannun Abban. Abba kallan Amina ya yi ya ce "Shigo mu tafi." Amina shiga ta yi tana jin rashin jin dadin yadda Abba ya yi ma Aisha wanda ita Kuma jin dadi take ganin kamar ya fara sonta. Amina bayan sun taho tana so ta yi ma Abba magana akan abin da ya yi ma Aisha amma Kuma ba ta ga fuska ba, hakan ya sa ta ja bakinta ta yi shiru dole, amma sai ya ban halin Aisha take, wanda har ta gama Abba bai tanka mata ba. Bangaran Aisha ko tana rungume da kudin ta je ta nuna ma mahaifiyarta. Mahaifiyar Abba Kai ta jinjina ta ce "Amma kamar yanzu na ga kin fita, Kuma Aisha ina lura yaron nan ko waya bakwayi anya ko mahaifiyarsa ba tursasa mai auranki ta yi ba?." Aisha Kai ta girgiza ta ce "A'a mama muna chat sosai a WhatsApp, yanayin aikinsa ne ya sa kika ga baizuwa." Mahaifiyar Aisha shiru ta yi kafin ta ce "Oh ai ban san kuna chat ba."Mahaifiyar Aisha na fadin haka ta juya ta tafi. Aisha Kuma wayarta ta dakko ta fara rubuta ma Abba sako kamar haka "Habibatina na gode sosai ta kulawarka agareni, zan dade ban manta ba." Abba Koda ya ga sakon tsaki ya yi ya goge text din. Yau mahaifiyar Amina ta dakko Mai gyaran jikin da zata fara yi ma Amina gyaran jiki da Mansura kawar Amarya. Mansura kallan Amina ta yi bayan mahaifiyar Amina ta tafi jin ance har da ita ta ce "Amina dan Allah bana so kima Mama magana." Mai gyaran jikin da keta kallan Mansura ta ce ma Amina "Ni ko kamar na San wannan?." Ta fada tana nuna Mansura. Mansura Kai ta dako a gigice tana kallan mai gyaran jiki, jikinta har ya fara rawa. Amina Kuma da fata lura da halin da Mansura ta shiga ba ta ce "Eh ai haka ne kila maikama da ita kika Sani." Mai gyaran jikin kallan Mansura ta yi ta ce "Ke ko za a yi biki gidanku ki ce ba kyason gyaran jiki, Koda yake kila dan Kinga kina da kyau ne, amma da za ki yi kyanki zai Kara fita sosai. Mansura dai mai gyaran jikin gaba daya ta rudata furta kalmar kamar ta Santa da ta yi, hakan ya sa ba tare da ta ce mata komai ba ta tashi ta fita. Can cikin gidan Mansura ta fi je tana ta kuka, kuka take kamar wadda aka aikoma sakon mutuwar iyayanta. Kuka take tana mai cewa "Allah ka takaita min wannan razanannan rayuwar da nake yi, Allah ka kawo min dauki acikinta, Allah idan har rayuwata ba ta da alkairi cikin jama'a Allah ka dauki rayuwata. Kuka Mansura take yi sosai tana bubbuga kafarta. Abba da cikin barci yake jiyo kukan mace, Wanda har ya yi nasarar tadashi daga dogon barcin da yake yi. Abba dafe Kai ya yi kafin ya tashi ya zauna yana mamakin wake kuka haka. Abba tashi ya yi ya saka jallabiyarsa ya ya zo wajan window sa, da mamaki ya bi Mansura da kallo ganin yadda take kuka, daga gani tana cikin tsananin damuwa da tashin hankali. ga uwar rama da ta yi dama tun da bikin Amina ya gabato kulum cikin damuwar yadda za ta ci gaba da zama gidan ita kadai take yi babu Amina. Abba ya dade yana kallan Mansura da babu alamun zata yi shiru daga kukan da take yi, fita ya yi ya je ya sameta. Abba tsaye ya yi kan Mansura da ko'alamar tsayuwarsa bata ji ba balle ta ji tafiyarsa. Abba tsugunnawa ya yi kusa Mansura yana dago kanta da ta tusa tsakankanin cinyoyinta✍🏻 Fadila Sani Bakori ce. ⭐ ABBANA ⭐ 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚* Daga Marubuciyar *Fadeela *Meenalyn Daddy *Oga Habib *Abdurrahim *In da rai *Daga Allah ko d'ora ma Kai *So ne sila *Rayuwar Haidar *Bakin kishi Domin samun littafin ABBANA daga farko 👇🏻Follow the ABBANA channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaYZGsNEFeXsr1CKQl3r Page 19-20 Mansura dago jajayan idanunta ta yi ta saukesu kan Abba, Abba ya dade yana kallan Mansura kafin ya kamo hannunta, Mansura da kallo ta bi Abba, Abba na rike da hannun Mansura har zuwa madaidaicin falonsa ya yi ma Mansura masauki. Kallan Mansura ya yi da har yanzu ba ta fasa share hawayanta ba. Abba kan lover chair din falonta ya nuna ma Mansura da hannu ya ce "Zauna." Mansura zama ta yi tana mai goge hawayanta. Abba zama ya yi gefan Mansura kamo hannuwan Mansura ya yi guda biyu duka ya rike yana kallanta, Wanda Mansura ta sidda kanta kasa tana mai ci gaba da zubba hawayanta. Abba cikin sanyi ya ce "Idan har kina min kallan da Amina take min kin daukeni dan'uwanki tom ki fada min damuwarki?." Mansura kasa ta yi da kanta har yanzu hawayan dake zuba idanunta basu tsaya ba. Abba hannu ya sa ya dako kan Mansura ya ce "Ina jinki fada min me kike yi ma kuka?." Mansura goge hawayanta ta yi ta ce "Ina kukan rabuwa da Amina ne, inatunanin yadda zan yi rayuwa ni kadai a gidannan babu ita." Kai Abba ya girgiza ya ce "Karki yi min karya, kukanki bashi da alaka da auran Amina, amma zan iya yadda idan kikace auran Amina ya fama miki raunin dake zuciyarki, dan kukanki ya fi kama da na wanda aka fama ma wani rauni, zuwa yanzu ya kamata ace kin bar mana boye-boye, kin fada Mana gaskiyar abin da ke damunki, ni Kuma na yi miki alkawarin taimakonki akan duk halin da kikeci." Mansura shuru ta yi bata ce komai ba, Kuma ta tsaya da kukan da take yi. Abba jin ta yi shiru tana kallansa, ya ce "Ina jinki, meye damuwarki? Meke yawan saki kukan nan da kike yi?." Mansura goge hawayanta ta yi ta ce "Yaya Abba da Ina da wata damuwa da nasar da Amina tuni, saboda bacin Fatima kawata ban taba shaguwa da wani ba adduniya kamar Amina, Yaya Abba da ina da wata damuwa da na sanar da ita." Abba shiru ya yi yana nazarin kalaman Mansura da babu kamshi gaskiya kodaya a cikinsu, amma sai ya shareta ya ce "Ina ita Fatimar take?." Bakaramin tashin hankali Mansura ta shiga ba dalilin wannan tambaya da Abba ya yi Mata, hatta Abba ya fahimci halin da Mansura ta shiga sanadiyar wannan tambaya tashi. Abba ganin ta yi shiru sai hawaye dake ta gudana a fuskarta kamar an bude famfo. Abba cikin sanyi ya Kuma cewa "Ko itama Fatimar ta mutu n..." Abba bai karasa sanadiyar kukan da Mansura ta fashe dashi tana cewa "Wayyo Abbana Fatima, Wayyoo Fatima, ina kike Ina jin kunyarki bana iya hada ido dake wayyo Abbana me ya sa? Me ya sa..?." Abba dai ya zira mata ido yana kallanta yana Kuma jin furucin dake fita daga bakinta. Mansura Kuma zumbur ta yi ta tashi kamar wata zautatta har yanzu tana kiran sunan Fatima. Abba hannun Mansura ya kamo ganin kamar bama cikin hayyacinta take ba, ga uban kuka da take famar rushawa tana Kiran Fatima. Abba hannun Mansura ya rika murzawa yana cewa "Shi kenan ki yi hakuri ya isa haka." Handkerchief dinsa ya ciro ya mika ma Mansura, wadda ta ci kuka harda majina. Mansura kallan handkerchief din ta yi taki amsa. Abba cikin sanyi ya ce "Ki amsa ki goge hawayanki." Mansura amsa ta yi ta gode hawayanta tana jan ajiyar zuciya na irin wanda ya sha kuka sosai. Ana cikin haka ne wayar Abba ta hau ringing. Abba dagawa ya yi yana kanga wayar a kunnansa. Cancikin gidansu Amina, Amina hankalinta tashi ya yi sosai ganin ta duba ko Ina babu Mansura babu alamarta, hakan ya sa Amina ta fara kuka gashi ita kadaice a gidan sai mai yi mata gyaran jiki, Amina ganin kukan ba zai yi mata bane ya sa ta kira Abba ta fada mai bata ga Mansura ba cikin kuka. Abba kallan Mansura ya yi da har yanzu bata bar share hawayanta ba ya ce "Gata a bangarena ki zo ku tafi tare." Abba na fadin haka ya kashe wayar. Amina Kuma sosai mamaki ya kamata me ya Kai Mansura bangaran Yaya Abba. Abba Kuma bayan ya kashe wayar kallan Mansura ya yi ya ce "Mansura." Mansura da mamaki ta dako tana kallan Abba, dan ganin ba shiga safgarta yake ba ta yi tunanin ma yasan sunanta ba. Mansura cikin sanyi irin muryar Wanda ya gaji da kuka ta ce "Na'am." Kina son Amina?." Abba ya tambayi Mansura yana kallanta. Mansura turo baki ta yi ba ta ba Abba amsa ba. Abba murmushi ya yi kafin ya ce "Yau saura sati daya auran Amina, me za ki bata gudunmuwa?." Mansura kuma turo bakinta ta yi, can ciki ta ce "Ni ai banda kudi." Kai Abba ya jinjina dama amsar da yake so kenan daga bakinta ya ce "Inda baki da kudi yanzu abin da ya kamata ki bata wanda ba zata manta dake ba shine farinciki, farincikin nan ko zaki ba Amina shine ta hanyar kauda duk wata damuwa da ta dameki ki ajeta gefa har ayi baki a gama, saboda Amina tana dariya ne da dariyarki, idan kikace zaki ci gaba da kunci ko kuka Amina ba zata yi hidimar auranta cikin walwala ba, amma idan ta ga kin saki ranki kina mu'amularki kamar yadda kowa yake yi, itama zata gudanar da hidimar auranta ranta sake. Ina fatan zaki min haka? Daga nan har a daura auran Amina ba zaki Kara kuka ba ko wani damuwa d...." Daidai nan Amina ta yi sallama ta shigo cike da mamakin yaushe Yaya Abba da Amina suka Saba haka. Mansura tashi ta yi kafin ta mai da kallanta ga Yaya Abba ta ce "Ba zan sake ba." Mansura na fadin haka ta kama hannun Amina suka tafi, Amina dai da mamaki take kallan Mansura. Cikin sanyi Amina ta ce "Mansura kamar kuka kika yi ko naga idanki da muryarki sun nuna?." Mansura baki ta murguda ma Amina ta ce "Ai na daina." "Allah ya sa da na fi kowa murna." Mansura dai ba ta kula Amina ba. Amina kalan Mansura ta yi ta ce "Wai yaushe kuka fara magana da Yaya Abba ban Sani ba?." Mansura kwashe abin da ya faru ta yi kaf ta fada ma Amina. Mansura zuwa ta yi itama aka shafa mata ragowar hadin dilkar Amarya da ya rage. Tun daga ranar ya zamana Mansura ta fara sakin ranta a gidan, sosai take ƙoƙarin ganin ta kauta duk wata damuwa dake damunta, dan tana so Amina ta yi hidimar bikinta cikin kwanciyar hankali. Hatta mahaifiyar Amina sai da ta lura da sauyin Mansura. Yanzu haka zaune suke an gama yi ma Amina dilka, Amina ta ce "Mansura, na yi shiru na zira miki ido Ina jira in ji kinyi maganar kudin sitin Amma Kuma na ji kin yi shiru." Mansura kallan Amina ta yi ta ce "Me ye kudin sitin?." Amina da mamaki ta ce "Wai da gaske baki San meye kudin sitin ba?." Wallahi ban Sani ba." Shiru Amina ta yi kafin ta ce "Kila hausarce ta banbanta, ku ya kuke Kiran kudin da ake ba kawayan Amarya na girki ranar daurin aure?." Murmushi Mansura ta yi ta ce "Tun da nake sau daya na taba zuwa bikin aure, ke nifa duk wani abu da kika san za a yi kawai ki min magana ban San komai ba , ya kamata ki fahimta ma." Kai Amina ta jinjina ta ce "Gaskiya na ga alama ai, jiya na yi ma Yaya Ahmad maganar kudin sitin ya ce in yi ma Yaya Abba magana, wai duk abin da muke so mutambayi Yaya Abba, sai da na yi mai maganar ma na tuna ashe muna tare da babban abokin anko. Amma Mansura kinsan ni da kunya in ma Yaya Abba maganar kudin sitin, dan haka yau ko gobe ki yi mai, kin ga yau saura kwana hudu gobe uku ya kamata ce mun amsa musan abin da za mu yi." Mansura ido ta zaro ta ce "Wai ke bakya ganewa ne, Wallahi ban san yadda ake kowata hidima ba ni." Amina hararar Mansura ta yi ta ce "Haka fa kawai zakice mai Yaya Abba kudin sitin Kai muka sani abokin anko, idan kika amshi kadan Kuma kin cika sauran." Mansura ido ta zaro ta ce "Ni dai ki Kira wadda Yaya Abba zai aura mu yi mai magana tare gaskiya, ni Allah ban iya ba." Amina dungure Mansura ta yi ta ce "Kada Allah ya sa ki iyar babu wata mommy da zan yi ma magana wallahi, wai baki iya ba sai ka ce wani abu ake yi, cemaifa kawai za ki yi kudin sitin shi ai ya san maganar." Mansura ganin ran Amina kamar ya fara baci ya sa ta yi shiru, ta amsa za ta yi mai magana. Amina zaune suna hira da Mansura, duk da yawanci hirar Amina take yi, Mansura takan yi ƙoƙarin biye Mata suyi, amma bata taba kawo labari ba ko hira akaran kata, sai dai in an kawo ta yi t comment akai. Yanzu haka zaune suke suna fira Amina ta ce "Mansura kinsan Allah yanda hidimar nan ta gabato Yaya Abba a busy yake, bari in kirasa mu ji yana ina." Amina Kiran Abba ta yi a waya, ta ce "Yaya Abba muna ta tsimayinka shiru?." Amina shiru ta yi da alama dai Abba take saurare, kafin ta ce "A'a, Yaya Abba Mansura ke son magana da Kai." Mansura sai da ta dafe kirji jin Abin da Amina ta ce. Amina katse Kiran ta yi tana kallan Mansura ta ce "Kin ji ko gara da na kirasa, ya ce ki samai a bangaransa." Mansura dafe kirji ta yi ta ce "Ni dai Wallahi kin dora min aiki." Amina hararar Mansura ta yi kafin ta ce "Mansura dan Allah karki amsar Mana kudi kadan." Mansura turo baki ta yi ta ce ma Amina "Nawa to zance?." 200k zaki ce mai haka aka bamu a auran Maryam." Mansura shuru ta yi tana zaune sai aikin turo baki take ita kadai. Amina ganin Mansura ba ta da niyyar tashi ta ce "Mansura dan Allah ki je mana Kar ya fita, Kinga kyau gobe a je ayi cefanan komai." Mansura tashi ta yi tana yafa dankwakin doguwar rigar jikinta ta fita. Mansura bakinta dauke da sallama ta shiga falon Abba, wanda da ke waya da ango. Abba jin sallama katse Kiran ya yi bacin ya sanar dashi zai kirasa. Mansura zama ta yi tana mai gaida Abba, kafin ta dora da cewa "Yaya Abba kudin sitin na zo amsa." Nawa ?." Abba ya tambayeta. "Two hundred thousands." Abba aje wayarshi ya yi yana kallan Mansura ya ce "Dubu dari biyu ku yi me da su?." Mansura turi baki ta yi ta ce "Girkin abincin biki Mana." Kai Abba ya jinjina kafin ya ce "Ban account number zan muku transfer One hundred thousand." Yaya Abba Wallahi ya yi kadan, Amina ta ce bikin kawarta da aka yi ba a dade ba 200 aka basu." Shi kenan zan baku 150." Mansura turo baki ta yi ta ce"Tom Yaya Abba ka cike Mana, Wallahi Amina ta ce Idan bakabada da yawa ba ni zan cika." Abba Kallan Mansura ya yi ya ce "Idan basu isheku ba zan Kara muku, bani account numberki sai in miki transfer din kudin." Ka yi Mana a na Amina bani da account." Okay." Abba ya ce. Mansura Kuma tashi ta yi ta fita, cikin sanyin jiki ta koma wajan Amina saboda Abba bai cika masu kudin ba sunkai 200 kamar yadda Amina ta so. Amina shanjinin jikinta ta yi ganin yadda Mansura ta dawo. Amina kamo hannun Mansura ta yi cikin damuwa ta ce "Kadan ya bamu ko?." Kai Mansura ta daga ta ce "Wallahi na yi na yi ya cika ya Kai 200 ya ki, wai idan basu ishemu ba mu yi mai magana zai Kara Mana." Amina cikin kosawa ta ce "Wai nawa ya bamu." 150, ya ce zai tura a account dinki." Amina rungume Amina ta yi ta ce "Ni Wallahi na sadakar ma, ban sha zai bamu haka ba, yanzu gobe zan Kira Mommy da Hassana ku je ku yi cefanan tare." Mansura baki ta turo ta ce "Kinsan nifa bana son hayaniya, su je su kadai." Amina hararar Mansura ta yi ta ce "Kar ki so hayaniyar Mana Wallahi da ke za a. Kinga nama manta ince miki ki fada ma Yaya Abba gobe shi zai kaiku siyayar, inda mudai shi muka Sani amatsayin abokin anko shi Yaya Ahmad ya nada ya ce duk abinda muke so mu tambayeshi. Kobai nadashi bama dole ya kaimu inda Yaya Ahmad bashi da aboki sama da shi. Nasan halin Yaya Abba idan muka bari sai gobe zai iya cewa ba za shi ba baisan da maganar ba, dan haka bari in kirasa a waya ki fada Mai." Mansura turo baki ta yi ta ce "Ke ki fada mai Mana." Amina hararar Mansura ta yi ta ce "Ai kawaye ke yin irin haka ba Amarya ba, Kuma ma ai da kunya kamar banda kawaye ace ni zan Kira, Wallahi ke zaki Kira, tsabar mama ma tasan ke ce gaba da komai ya sa ta hada gyaran jiki harda ke a matsayinki na babbar kawar Amarya, Kinga ko komai kawa za ta yi kece nan za ki yi sa." Mansura hararar Amina ta yi ta ce "Anji din." Amina Mika ma Mansura wayarta ta yi ta ce "Amsa na kira." Mansura amsa ta yi tana tura baki. Ringing daya Abba ya daga." Yana cewa dama yanzu zan kiraki in ce ki samin account detail naki." Mansura tura baki ta yi ta ce"Ba fa ita bace." Abba shiru ya yi dan ya gane mai maganar. Mansura ma shirun ta yi, Abba jin shiru-shiru ba ta yi magana ba ya kashe wayarsa. Mansura Mika ma Amina wayar ta ta yi ta ce "Ga shi ya kashe wayar." Amina cikin jin haushi ta ce "Haba Mansura ba dole ya kashe ba, kin yi shiru ki sake kira." Mansura sake Kira ta yi sai da ta kusa katswa Abba ya daga. Mansura kamar yadda Amina ta tsara Mata ta ce "Yaya Abba dama zaka kaimu siyayyane gobe." Abba shiru ya yi, dan sun yi maganar da Ahmad tuni akan shi zai yi jigila dasu akan duk abin da ya kama, sannan Abba ya ce "Ke da wa zaku?." Da mommy da Kuma wata friend din Amina." Ya sunanta?." Abba ya tambaya dan idan har da Aisha ba zai kaisu ba wani zaisa ya kaisu, da yake Abba bai San mommy suke cema Aisha ba. Mansura Kuma ta ba shi amsa da "Hassana." Ajiyar zuciya Abba ya sauke jin ba su ambaci Aisha ba. Ya ce "Da misalin karfe nawa zaku tafi." Da yake wayar a speaker take Amina duk tana jin abin da suke cewa, da hannu ta nunama Mansura. Mansura ta ce" 10:00 AM." Okay Allah ya kaimu bana son shiririta ku shirya da wuri." Abba na fadin haka ya kashe wayarsa. Amina Kuma take ta tura ma Aisha da Hassana massage akan gobe su zo da wuri 10 za su tafi shiyayya, Yaya Abba ne zai kaisu baya son jira." lokacin Aisha da ta ci karo da sakon Amina sosai ta yi murna jin Abba zai kaisu, take Aisha ta fara shirya kalar kwalliyar da za ta yi tare da tanadan kalmomin masu hikima da basira da za ta yi amfani da su ko Allah zai sa ta ci zuciyar Abba da ya ki. Washegari Aisha da wuri ta tashi, ta samu kankana ta goge fuskarta dashi, sannan ta debo kurkur sokali daya da fulawa itama cokayi daya da Madarar gari itama cokali daya ta fasa danyan kwai tasa kwaiduwar ta hada ta motse kafin ta shafe fuskarta da hannuwanta da hadin. Bayan 30 minute Aisha ta wanke fuskarta da ruwan dimi, kafin ta shiga wanka. Da yake mahaifin Aisha komai yana koya masu hadin gargajiya ne saboda baya so su yi amfani da kwaya ko man bleaching, hakan ya sa yake koya masu hadin islami wajan gyaran jikinsu. Aisha bayan ta fito wanka man kwakwa ta shafe jikinta da fuskarta da shi. Kafin ta dakko wata bakar Abaya ta sa ta tanannane kanta da farin jesi. Wayyo Allah ku zo kuka Aisha yadda ta yi kyau, mahaifiyars Aisha kallan Yar tata taita yi ganin yadda take sheki. Aisha za ta fita mahaifiyarta ta kirata ta ce "Ki kula Wallahi idan mahaifinki ya ganki da gyale babu ruwana. Aisha turo baki ta yi ta ce "Mommy duk inda zamu a mota fa zamu ba a kafa ba." Shi kenan Allah ya tsare." 9:45AM Aisha ta shiga gidansu Abba.,...✍🏻 Abbana sai Monday za ku jini in sha Allah bana yin update ranar weekend, wancan week dinma na yi ne saboda a week din na fara littafin. Fadila Sani Bakori ce ⭐ ABBANA ⭐ 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚* Domin samun littafin ABBANA daga farko 👇🏻Follow the ABBANA channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaYZGsNEFeXsr1CKQl3r P 21-22, Aisha koda ta yi sallama falonsu Amina babu kowa, hakan ya sa ta nufi bedroom dinsu Amina kai tsaye. Amina da tashi ta yi tana murmushin ta rungume Aisha ta ce "Oyoyoo Mommyna." Aisha zama ta yi tana kallan Hassana ta ce "Hassana yahaya dama wai kina garinnan." Wadda Aisha ta Kira da Hassana murmushi ta yi ta ce "Ke dai zan ce kina gari." Take hira ta barke tsakaninsu dan sun dau dogan lokaci basu ga juna ba. Hassana kallan Aisha ta yi da yake Hassana irin masu shegen tambayar nan ne ta ce "Aisha a ina kika san Amina?." Amina amshe zancan ta yi ta ce "Yaya Abba ya hadamu, Yaya Abba zata aura yanzu haka wata hudu masu zuwa auransu." Hassana Kai ta jinjina ta ce "Ki ce daga yau mu dawo cewa Aunty Aisha mu bar cewa Aisha kaitsaye." Amina kallan Mansura ta yi da har yanzu take kwance bata tashi ba ta ce "Mansura 10:10AM fa dan Allah ki tashi ko wanka fa baki yi ba, yanzu za ki ga Kiran Yaya Abba Wallahi." Mansura tashi ta yi da sauri ta fada bathroom dinsu. Hassana kallan Amina ta yi ta ce "Amina wannan fa wacece?." Amina hararar Hassana ta yi ta ce "Wai ke dan Allah yaushe za ki bar wannan halin naki na tambaye-tambaye ne?." Hassana hararar Amina ta yi itama ta ce "Na ji ance tambaya rabin ilimi ce, meye laifin da na yi tambaya akan abin da ban Sani ba." Cikin jin haushi Amina ta ce ma Hassana "'yar kanwar mama ce." Amina Kai dubanta ta yi ga wayarta dake ringin tana addu'ar Allah ya sa ba Yaya Abba bane. Amina ido ta zaro ganin Abba ne, gashi tasan babu abin da ya tsana Kamar jira, hakan ya sa Amina na dagawa ta sanar dashi gasu nan fitowa. Amina kallan Aisha ta yi ta ce "Momnyna ku je dan Allah kafin Mansura ta fito idan ba haka ba tafiya zai yi Wallahi." Aisha kallan Hassana ta yi ta ce "Muje." Abba na cikin motarsa yana jiran fitowarsu Mansura, su Aisha suka karasa inda ya yi parking. Aisha gefan Abba ta matsa ta ce "Yaya Abba ina kwana." Abba da farko bai gane Aisha ba sai da ta yi magana dan ta yi mai kyau cikin shigar da ta yi. Abba babu yabo ba fallasa ya amsa gaisuwar Aisha da ta Hassana baki daya, yana tsaki tare da dayasanin amsa ma Ahmad da ya yi zai yi jigilar kaisu Mansura duk inda zasu. Abba kallan Aisha ya yi ya ce "Ku shiga Muje." Aisha zagayawa ta yi ta zauna a front seat. Abba jan motar ya yi zai tafi Aisha ta ce "Yaya Abba akwai sauran mutun daya." Abba dakatawa ya yi dan dama ya yi mamakin ganin baiga Mansura ba. Shiru-shiru babu Mansura babu alamarta, bunubunu Abba na duba agogon hannunsa, Abba wayarsa ya dauka ya Kira Amina ransa bace tana dauka ya ce "Uban waye drivernku da zaku shanyani ina jiranku?." Amina hakuri taita ba Abba, Abba ya kashe wayarsa. Amina Kuma can kallan Mansura ta yi da tasa wata green abaya. Amina cikin jin haushi ta ce "Mansura kina ji fa Yaya Abba ya Kira sai fada yake, amma killi yadda kike shiryawa kamar ba jiranki aike ba." Mansura kallan Amina ta yi da ta dage sai fada take mata, Mansura turo baki ta yi ta ce "Tom ban ATM cart din naki da pin din." Mansura da sauri ta fita. Mansura na zuwa Abba ya ja motar gaba daya ransa a bace yake, shi kansa baisan me ya bata mai raiba kawai haka nan ya tsinci kansa cikin bacin rai. Bayan sun yi dan yi nisa da tafiya kadan, Aisha ta katse shirun da cewa "Hassana Kun ko gaisa da Yaya Abba?." Eh mun gaisa." Aisha cikin son yin magana da Abba ta ce "Ban yadda ba, Yaya Abba wai kun gaisa da Hassana?." Biki ji abin da ta ce bane, ko karya za ta yi miki." Cewar Abba. Hassana Kuma carab ta amshe ta ce rabu da ita Yaya Abba dan ta tsokaneni ne." Na ga alama." Abba ya ce. Aisha Kuma turo baki ta yi ta ce "Babu maganar tsokana sanin halinki da na yi ne." Kut, Yaya Abba ka ji wai sanin halina da ta yi ne dan Allah idan a gaban bare ta fadi maganar nan Yaya Abba ba sai a dauka mugun hali garan ba." Abba murmushi ya yi ya ce "A'a babu wanda zai dauke ki haka, ai tunaninka kamanninka." Hassana cikin jin dadi ta ce ma Aisha "Muguwa kinji dai ko." Aisha murmushi ta yi ta ce "Yaya Abba meye Kuma tunaninka kamanninka, wata irin Hausa ce wannan." Ki tambayi kawarki." Aisha juyawa ta yi tana kalan Hassana ta ce "Fassara min Hausar Yaya Abba." Hassana harar Aisha ta yi ta ce sai kin biya." Aisha kallan Abba ta yi ta ce "Yaya Abba agabanka ake min wulakanci, kana jinta fa wai sai na biya, tom ki rike kalamanki nasan kema ba sani ki kaiba, Yaya Abba zai sanar da ni daga ni sai shi ba za ki ji bama." Daidai nan Abba ya yi parking ya ce "Mun zo sai ku yi sauri ku sayi abun da za ku siya ko ba a nan zaku yi siyayyar ba?." A'a Yaya Abba a nan ne." Cewar Aisha. Bude motar suka yi duk suka sauka, Mansura Kuma Mika ma Hassana ATM card din Amina ta yi tare da fata Mata pin din. Hassana da mamaki ta kalli Mansura ta ce "Sister bangane ba kin mikamin ATM card kinki fitowa?." Mansura ya mutsa fuska ta yi ta ce "Sister bana jin dadi kuje dan Allah." Hassana Kai ta girgiza ta ce "Haba sister kinsan mu mata da kishi Aisha ai ba zata ji dadi ba ta tafi ta barki da wanda zata aura tare." Abba juyowa ya yi yana kallan Hassana ya ce "Inda ta kawo muku uzirinta ku yi hakuri ku tafi Mana." Shuru duk suka yi sannan Aisha ta kamo hannun Hassana tana murmushi ta ce "Mu je kawata dole mu yi mata uziri inda bata da lafiya." Suna tafiya Hassana ta kalli Aisha ta ce "Caf dijam, Aisha ki ce kina nan da halin sakarcinki, wannance ta yi kama da mara lafiya, tana sone kawai ta tusa kanta a wajan Yaya Abba ta kwace miki shi, ke baki san yanzu yadda ake tashan kwacan saurayi bane. Baki ji yadda ta yi maganar ba ita aladole ga shagwababba, wai bana jin dadi ne ku je dan Allah. Ke daga jin yadda take magana kinsan makirci ne cike da cikinta." Aisha shiru ta yi kafin ta ce "A'a inaganin ita fa kamar haka take, yadda na lura da ita kamar bata son shiga hayaniya ne, saboda ranar da muka je gidan suna ma haka tayi, ƙarshe ta tafi ta barmu."Hmmm, ni dai hankalina bai kwanta da yarinyar nan ba." Cewar Hassana. Hassana duk yadda ta so su yi sauri a cefa nan abun gagara ya yi. Can bangaran Mansura Kuma suna tafiya ta tusa kanta atsakankanin cinyoyinta. Abba na lura da ita, hakan ya sa ya tashi ya koma inda take, Abba zama ya yi yana dago kan Mansura da ta tusa tsakankanin cinyoyinta. Kallan-kallo suka tsaya yima juna kafin Abba ya sa hannu ya goge ma Mansura hawayan da ke fita a idanunta, Abba cikin nuna damuwarsa ya ce "Ba za ki bar kukanba kenan, ya mu ka yi da ke?." Mansura fashewa da kuka ta yi tana cewa "Yaya Abba ba fa kuka nake yi ba, nima bansan hawayan na zubarmin ba. Abba bubbuga bayan Mansura yake yi kamar ana lallashin karamin yaro ya ce "Shi kenan na ji ba yadda ba kuka kike ba, ya Isa yanzu ki bar kukan." Mansura kasa tsaida kukanta ta yi, bisa ga alama ita kadai tasan zafi da kuncin da ke damunta. Abba ganin ya ba Mansura baki ta ki yin shiru hakan ya sa ya ya bude motar zai koma front seat ya rabu da ita. Mansura rike hannun Abba ta yi ta ce "Na yi shiru Yaya Abba." Ta fada tana jan ajiyar zuciya tana goge hawayanta. Abba gaba daya yama rasa tunanin da zai yi akan Mansura, sun dade shiru kafin Abba ya ce "Daga nan har a yi bikin Aisha idan har kika Kuma yadda na ganki kina kuka tom zan bata da ke bazan sake shiga lamarinki ba inda bakya jin magana." Mansura tana ƙoƙarin tsaida hawayanta ta ce "Ba zan Kuma ba Yaya Abba." Yauwa yar Albarka." Cewar Abba yana Kuma share ma Mansura hawayanta. Ganin ta bar kukan ya ce "Kina so in Samar miki teaching a school din da Amina ke yi? Kin ga bayan bikin Amina kin huta zama gida ke kadai inda Mama kullum tana Islamiya." Mansura turo baki ta yi ta ce "Ni dai Yaya Abba bana so, ni ba zan iya hayaniyar yara ba." Abba shiru ya yi yana kallan Mansura kafin ya ce "Tom in mai da ke school sai ki ci gaba da karatunki?." Nan ma dai Mansura Kai ta girgiza ma Abba alamun bata so. Abba kallan Mansura ya yi kafin ya ce "Tom fada min me kike so? Ina son in Samar miki wani abin ne wanda zai hanaki zaman gida baki daya." Mansura turo baki ta yi ta ce "Ni dai Yaya Abba bana son komai, ni gara in ta zaman gidan ma." Abba da mamaki ya kalli Mansura ya ce "A'a, idan baki son komai sai mu yi Miki aure shi kenan." Mansura rufe idanunta ta yi kafin ta dago tana kallan Abba ta ce "Tom wa za ku aura min ni da bani da saurayi?." Ni da nake da abokai da yawa, baki ga Mansura bama cikin abokaina zata auri wani, ciki zan samo in aura miki kema." Mansura bata fuska ta yi kamar za ta yi kuka ta ce "Ni dai Yaya Abba bana son kowa, ni ba zan yi aure ba." Ai ko sai kin yi aure, akwai wani abokina ma ina jin zanma Mama magana bayan bikin Amina kema a yi naki." Take Mansura ta fashe ma Abba da kuka dan ta yi tunanin da gaske yake. Abba ido ya zaro yana cewa "Ke ni wasa nake miki aike ba za ki yi aure ba ai na sani duk wanda ya zo ya ce ma yana sonki sai na mishi kus'a." Abba ya fada Yana nushin Mansura a hankali a fuska yana gwada mata yadda zai yi ma duk wanda ya ce yana sonta. Abin mamaki sai ga Mansura tana dariya... Daidai nan su Aisha suka dawo, da mai baro da ya dakko masu kayan siyayyar da suka yi. Hassana nocking ta yi ma Abba ganin bai kula dasu ba hankalinsa na kan Mansura dake dariyar kus'a din da zai ma wa inda suka ce suna sonta. Abba fita ya yi yana kallan Hassana ya ce "Sanninku da dawowa." Hassana kallan Aisha ta yi irin kallan gingani ko ai abin da nake ce miki kenan. Aisha dai ba ta ce komai ba, amma bisa alama ranta ya bace yana yin fuskarta ya sauya. Abba bude boot din motarsa ya yi mai baron ya loda siyayyar da suka yi a ciki. Aisha jikinta gaba daya yayi sanyi a haka ta zagaya ta koma wajanta ta zauna. Abba har ya isa gida babu wanda ya yi magana a motar. Abba bayan ya yi parking umartarsu ya yi da su shiga da duk abin da suka siyo cikin gida. Gaba daya dauka suka yi inda duk suka dauki manya ledoji ban da Mansura da ta dauki 'yar Karama, har ta juya za ta bi su Aisha Abba ya kirata ya ce "Wannan Yar ledar zaki dauka? Zo ga wata in dora miki." Abba amsar ledar da Mansura ta dauka ya yi ya dora mata wata babbar leda akai. Yana dora mata Mansura ta durkushe har kasa tana turo baki ta ce "Yaya Abba ya fa yi min nauyi Wallahi ban iya tashi." Abba Kai ya girgiza ya ce "Wa'inna yan kayan ne za su yi miki nauyi, maza ki tashi Wallahi bana son ragonta." Mansura Kuma turo baki ta yi tana durkushe da ledar akanta ta ce "Allah Yaya Abba sun min nauyi." Allah karya ne ba su yi miki nauyi ba." Abba ya fada yana Mika Mata hannunsa ya ce "Kama ki Mike." Mansura kama hannun Abba ta yi ta miki daga durkusan da take. Bangaransu Aisha ko, suna tafiya Hassana ta ce "Kinga ni ai abinda nake fadamiki, dazu daga gani dama ni nasan lafiyarta Lau, amma ke kika naimi ki kareta wai bata son hayaniya. yanzu gata can tsaye ai suna fira a gabanki ko kunyarki ma bata ji ba." Fadin gata can din da Hassana ta yi ya sa Aisha juyawa, Hassana ma ganin waigawar ta yi daidai nan Mansura ta rike hannun Abba ta tashi daga durkusan da take, ta yi taga-taga zata fadi Abba ya riketa ya na mata dariya. Da sauri Aisha ta juyo, take taji wani irin bakin ciki da tsanar Mansura aranta. Hassana Kuma ta ci gaba da cewa "Wallahi tun kafin lokaci ya kure miki ki sanadar da Amina abin da ke faruwa na kwacan da yarinyar nan ke shirin miki ta take Mata burki. Aisha dai bata ce komai ba hassalima Kara saurinta ta yi. Suna shiga da gudu Aisha ta yi sight din Amina jin kukan dake ƙoƙarin kufce Mata. Mahaifiyarsu Amina dake falon da mamaki ta bi Aisha da kallo tana kallan Hassana ta ce "Hassana lafiya me ya samu Aisha haka ta shigo tana kuka." Mahaifiyar Amina ta yi tambayar cikin damuwa." Hassana cikin tsantsar nuna damuwa ga lamarin ta ce "Gaskiya mama akwai damuwa." Hassana ta fada tana shigewa bedroom din Amina ta bar Mahaifiyar Amina sake da baki. Can Kuma Aisha na shiga ta fada bed din da Amina take zaune tana chatting ta fashe da kuka. Amina cikin tashin hankali ta wurgar da wayar hannunta tana kamo Aisha ta ce "Mommyna lafiya ya aka yi ke da wa?." Aisha shiru ba amsa sai kuka da take yi. Amina kallan Hassana ta yi dake tsaye tana kallan Aisha. Amina cikin damuwa ta maida kallanta ga Hassana ta ce "Hassana wai lafiya? Ya aka yi ne ?." Hmmmm." Hassana ta ce ta zauna. Ana haka ne mahaifiyar Amina ma tashi dakin da saurinta jin sautin kukan Aisha. Mahaifiyar Amina ganin ba ta ga Mansura ba ya sa ta ce "Ina Mansurar, ko wani abun ne ya s..." Mahaifiyar Amina shiru ta yi jin sallamar Mansura. Mansura da mamaki ta bi Aisha dake kuka da kallo. Mahaifiyar Amina Kuma cikin damuwa ta maida kallanta ga Mansura da ta shigo yanzu ta ce "Mansura wai lafiya ya aka yi ne? Me ya samu Aisha take kuka ne?." Mansura cikin mamaki ta ce "Wallahi mama ban Sani ba, nima tambayar da zan yi kenan." Mahaifiyar Amina da mamaki ta ce "Batare kuke bane?." Tare muke." Cewar Mansura. Hassana Kuma dagowa ta yi tana hararar Mansura ta ce "Eh gaskiya fa dole kice baki Sani ba bacin kin manta snatching din saurayi." Mahaifiyar Amina damamaki ta kalli Hassana ta ce "Kamar ya bangane ba Hassana?." Mama Mansura soyayya suke da Yaya Abba." Mahaifiyar Abba da tsananin mamaki ta ke "Wana Yaya Abban?." Mama yaya Abban na gidan nan mana..✍🏻 Fadila Sani Bakori ce ⭐ ABBANA ⭐ 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚* Domin samun littafin ABBANA daga farko 👇🏻Follow the ABBANA channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaYZGsNEFeXsr1CKQl3r P 23-24 Mahaifiyar Abba cikin tsananin mamaki ta ce "Wana Yaya Abban?." Mama yaya Abba na gidan nan mana." Cewar Hassana. Mansura ko tsabar al'ajabi shiru ta yi tarasa bakin magana, tana mamakin shairin da suka kulla Mata. Mahaifiyar Abba rasa abin da zata ce ta yi dan ita ko magana banda ranar da Mansura ta zo gidan ba ta taba ganin ta hada Mansura da Abba ba, hasalima in ba yanzu ba Abba ba son zaman Mansura a gidan yake ba. Mahaifiyar Amina mai da kallanta ga Hassana ta yi ta ce "Tom waiku me kuka gani da za ku ce haka? Sannan yanzu meye dalikin kukan nata?." Hassana da ta rasa abin da zatace dan duk surutun Hassana bata da fiye karya ba hakan ya sa ta ce "Mama ki dai tambayi Aishar da bakinta ta fada miki." Mahaifiyar Amina hannun Aisha ta gama ta ce "Tashi mu je ki fada min in ji." Mahaifiyar Amina na rike da hannun Aisha har bedroom dinta, zaunar da ita ta yi kan one hand char din dake bedroom dinta, itama ta zauna, goge ma Aisha hawayanta ta fara yi kafin cikin taushin murya ta ce "Shi kenan kukan ya Isa haka nan, fada min shi Abban ne ya ce miki yana son Mansura?." Kai Aisha ta girgiza. Shiru mahaifiyar Amina ta yi kafin ta ce " Aisha ki natsu ki sanar dani kin ji zan yi maganin koma meye, Abba bai isa ba ko bayan raina ya wulakantaki ba bare Kuma da raina, fada min ya aka yi?." Aisha rasa abin da zata ce ma mahaifiyar Abba ta yi, hakan ya sa ta ce "Mama dan Allah ki tambayi Hassana tasan komai Kuma agabanta komai ya faru." Mahaifiyar Amina wayar Amina ta Kira ta ce ta turo mata Hassana. Hassana koda ta fito falon ba ta ga Mahaifiyar Amina ba, bedroom din mahaifiyar Amina ta shiga da sallamarta. Mahaifiyar Amina waje ta nuna ma Hassana ta ce "Zauna." Bayan ta zauna mahaifiyar Amina ta ce "Hassana na tambayi Aisha ta ce in tambayeki agabanki komai ya faru, Ina jinki fadamin meya faru bayan tafiyarku? Hassana Kara gyara zama ta yi kafin ta ce "Mama Kinga Koda muka tafi muka je zamu kasuwa siyayya Mansura kin fita daga motar Yaya Abba ta yi wai bata jin dadi, amma da muka dawo muka iskesu waje daya da Yaya Abba sai fira suke har tana dariya. Yanzu Kuma bayan mun dawo Yaya Abba ya ce mu shigo da kayan da muka dawo dasu, duk maka dako muka taho ita Kuma har ta taho Yaya Abba ya kirata wai ta dawo ta dauki Abba, Wallahi mama Koda muka juyo abinda Aisha ta gani shi ya sata kuka." Mahaifiyar Amina cikin sanyi ta ce "Me kuka gani da kuka jiyo din." Gani muka yi Yaya Abba yana rike da hannunta suna magana suna dariya." Ajiyar azuciya mahaifiyar Amina ta sauke. Shiru ta yi dan ta rasa abinda zata ce, sai zuwa can ta ce "Ki kwantar da hankalinki kin ji yayata, Abba bashi da Mata saike, Mansura Kuma duk abin da kika gani ya faru tsakaninta da Abba ki dauka kamar da Amina kika gani, dan Abba kallan kanwa yake Mata, Kar ki kuma sakanki damuwa indai akan haka ne Abba ba soyayya suke da Mansura ba kamar yadda kuka zarga." Aisha sosai ta gamsu da kalaman surukartata, hakan ya sa ce "Tom Mommy nagode Kuma in sha Allah ba zan sake sa kaina damuwa akan hakan ba." Yauwa 'yar Albarka Allah ya yi Miki albarka." Ameen Aisha ta ce kafin suka fita suka bar Mahaifiyar Abba dariyarsu, suna fita Abba yana shigowa dan har saida suka matsa mai ma. Abba kallan mahaifiyarsa ya yi ya ce "Mama Wana albishir din akai miki ne naga kina dariya." Hmmm Abba dole in yi dariya, Aisha ta zo ta dagamin hankali tana kuka wai soyaya kake da Mansura, Koda na tambayi ba asin maganar tasu duk kame-kame ce, daga ji dai kishi take na magana da Mansura da ka yi." Abba daure fuska ya yi ya ce "Lallai Kam aiki ya sameta." Mahaifiyar Abba gimtse dariyarta ta yi ta ce "Bana son shirme kamar ya aiki ya sameta? Kenan yanzu ka fara magana da Yan Mata a gabanta? Ko me kake nufi?." Abba kai ya girgiza ya ce "Kodaya ba haka nake nufi ba, Amma mama indai dan taga Ina magana da yarinyar can ne ai abin yaban mamaki, tom wata magana muka yi da har zai sa ta ce Haka." Kai rabu dasu shirmansu ne kawai. Dama Abba ina ta so in maka wata magana sai in mata, ka ga dai anci wata kusan biyu kenan da sa ranarka da Aisha, Kuma ni har yanzu banji wata magana da ka yi ba ta shirin biki da kake yi, ko maganar gininka ma ban ji kana maganar karasashi ba." Abba Kai ya sosa ya ce "Ko jiya mun yi magana da masu aikin, Ina so sai mun gama hidimar bikin nan ne kafin in dora aikin ba tsayawa." Tom Allah ya taimaka." Ameen." Abba ya ce. Sun dade suna tattaunawa da mahaifiyarsa kafin ya fita. Can bangaran su Amina ko bayan Mahaifiyar Amina ta Kira Hassana, ya rake daga Amina sai Mansura a dakin. Amina kallan Mansura ta yi cikin sanyi ta ce "Mansura wai meke faruwa ne?." Mansura fara goge hawayan da ya zibo Mata ta yi ta ce "Wallahi nima ban Sani ba, da na shigo ne na iske Mommy tana kuka, har zan tambayi lafiya na ji friend dinki na cewa wai na yi ma Mommy snatching din saurayi, wai Ina soyayya da Yaya Abba." Amina shiru ta yi ta rasa abin cewa, kafin ta ce "Tom yanzu Kuma meye abin kuka anan, ni abinda nake so in Sani me ya faru a tafiyar takune." Mansura kwashe duk abin da ya faru ta yi ta fada ma Amina. Amina shiru ta yi ta ce "Ki yi hakuri Mansura dan Allah karki dauki aka a matsayin wani abu nasan watarana zaki fahimci halin da Aisha ta shiga dazu, son Yaya Abba take sosai tattare da tsananin kishi akansa, shi yasa ta ji haushin barinku tare gani take Kun yi wata maganar ne, kinsan masoyi yana da zargi." Amina dai har ta gama maganarta Mansura bata ce komai ba. Suna ana haka Hassana da Aisha suka shigo. Shiru babu Wanda ya ce ma kowa komai, Amina ce ta katse shirun da cewa "Hassana Kun gama shigo da kayan ne?." Kai Hassana ta girgiza "Shi kenan ku bari na samu wani yaran ya shigo dasu." Aisha tashi ta yi tana kallan Amina ta ce "Amina zan tafi sai Kuma ranar daurin aure." Amina marairaice fuska ta yi ta ce "Na zaci kullum zaku rika zuwa nan mu wuni tare dan Allah." Aisha dai bata ce komai ba murmushi ta yi ta tafi. Hassana ma tashi ta yi ta ce "Nima ai tafiya zan yi jirani." Hassana tashi ta yi suka tafi tare da Aisha. Amina tashi ta yi ta rakasu har wajan get dinsu, bayan sun fitone Amina ta kalli Aisha ta ce "Mommy dan Allah ki yi hakuri abinda ya faru, amma a ainihin sanina Yaya Abba ko magana ba hadasu da Mansura, dan Allah ki yi hakuri zan mata magana." Aisha murmushi ta yi ma Mansura ta ce "Ayyah babu komai ya wuce ai." Bayan sun Hassana sun tafi Hassana kallan Aisha ta yi ta ce "Aisha kinsan Allah ki ci gaba da sa ido akan yarinyar nan, dan ni ban yadda basa soyayya da Yaya Abba, na fi tunanin dai ko su ne Basu son suna soyayyar ba." Aisha dai ba ta ce komai, ta yi ma Hassana sallama ta tari Napep ta hau. Aisha ta tafi babu jimawa mahaifiyarta ta zo gidansu Amina. Mahaifiyar Amina da fara'arta ta tari malamarta, bayan sun gaggaisa Mahaifiyar Amina take sanar da mahaifiyar Aisha, Aisha ma yanzu suka tafi babu jimawa. Malama kallan mahaifiyar Amina ta yi ta ce "Tun jiya nake cewa zanzo Allah bai yi ba, dama na zo in sanar dake ne na shirya Walima da za mu yi ta bikin Amina a gidan nan, shi ne na ce yaushe za a yi gobe ko sai ana gobe darin aure?." Mahaifiyar Amina da murnarta ta ce "Kai Malama, wannan babar hidima haka, tom angode Allah ya saka da alkairi, a bari a yi jibi ana gobe biki kenan." Shi kenan Allah ya kaimu. Malama sun dade suna fira da mahaifiyar Amina kafin ta yi mata sallama ta tafi. Mansura ranar gaba daya haka ta wuni babu dadi dan tashiga damuwar abin da su Aisha suka yi Mata, ta dauki hakan kamar cikin mutunci ne. Washagari Abokan Ahmad suka kawo lefan Amina. 'Yan'uwansu Amina da dama duk sun zo, hakan ya sa gidan yanzu ya fara cika, dole ya sa Abba ya bar masu bangaransa ya koma dakin abokinsa da kwana. Bangaran mahaifiyar Aisha Kuma tana ta shirin shirya masu walimar da za ta yi ta a bikin Amina a matsayin gudummuwarta. Mansura sosai take cikin damuwar rabuwa da Amina Amma ta daure dan karta rusa farincikin da Amina take ciki. Koda mai lalle ta zo yi masu Mansura kamar ta ce bata so amma tana tsoran maganar mutane hakan ya sa ta zauna aka ranga da Mata kunshinta. Ana yin kunshin Amina ta ce ma maikunshin "Ki yi Mata mai kyau fa kamar nawa itace babbar kawar Amarya." Hakan ya sa mai kunshin da zana ma Mansura filawa mai kyau. Da yake duk sun sha dilka hakan ya sa kyan kunshin ya Kara fita sosai. Washagari aka kafa manyan rumfuna a harabar gidansu Amina. Mahaifiyar Amina da Amina duk sunyi gayyatar walimar, haka mahaifiyar Aisha ma ta gayyaci duk dalibanta walimar, hakan ya sa walimar ta samu halartar mutane da yawa. Amarya Amina wanka ta yi ta cakare cikin wata farar lifaya, sosai ta yi kyau daga kaganta babu tambaya ka ga Amarya, duk wanda ya zo gidan sai ya yaba kyan da Amina ta yi. Mansura bayan ta tafito wanka ta dauki daya daga cikin kayan Amina za ta sa inda dama kayan Aminar take sawa. Amina dake zaune kusa da Mansura hararta ta yi kafin ta wurga Mata wata farar lifaya wadda adonsu ne kawai ya banbanta da tata, ta ce "Ga wadda za ki sa nan." Mansura da mamaki ta kalli Amina tana son yin magana Amina ta yi Mata nunu da mutane cikin dakin, hakan ya sa ta ja bakinta ta yi shiru. Wadda ta yi ma Amina kwalliya ita ta yi ma Mansura ta nada Mata lifayar. Wayyo mutane rasa Wanda ya fi kyau suka yi tsakanin Mansura da Amina, idan ka gansu zaka dauka su duka amaran ne. Amina ko da bata taba ganin Mansura da kwalliya ba sosai ta rude ganin yadda Mansura ta yi Mata kyau kamar ka saceta ka gudu. Wasu da dama kance Mansura ta fi masu kyau, wasu Kuma suce Ina ma za a hada Amarya ai dabance. Nan fa aka yi ta yi masu hotuna. Aisha ta tasha adonta cikin wani green hijab, duk sai ta sha jinin jikinta ganin yadda Mansura ta sha kyau kamar ita ce amaryar. Hutuna akaita daukarsu Amina, Wanda duk abin da ake Mansura na yake ne kawai, amma bi ainihi jitake kamar ta fasa ihu, amma ta daure ta cije dan karta sama kawarta damuwa. Hassana da itama tasha adonta da Hajiya babba sosai ta yi kyau, jawo hannun Aisha ta yi suka bar falon Abba da yake acan suke shirin nasu. Hassana kallan Aisha ta yi ta ce "Aisha in fada miki gaskiya kin yi kyau, amma shegiyar yarinyar nan ta fiki, ke bakya kishin Yaya Abba ya ganta haka, wai ke ko kunshin ma kinkasa yi." Aisha kallan hannuwanta ta yi ta ce "Ki bari kinsan Mommy ta dauki nauyin walimar nan tom aiki ya yi yawa, saidai gobe zan je a yi min da wuri, inda na ji ance sai lahadi za a kai Amarya ba ranar da aka daura aure ba." Hassana shiru ta yi ta ce "Shi kenan, Amma dai ki kula kema gobe ki yi wankan kece raini." In sha Allah ." Aisha ta ce tana kama hannun Hassana ta ce zo muje mu yi hoto da Amarya." Hassana da yake duk kawayansu daya da Amina kusan, hakan ya sa duk sai da ta bisu ta rada masu su yi hankali da Mansura maciyiya Amanace tana naiman kwace ma kawarta Aisha saurayin da zata aura, hakan ya sa duk sai suka rika yi ma Mansura kallan munafuka, sukaita sakar mata habaici. Amina tana so ta yi masu magana amma Kuma bata son Mansura ta ji tana musu magana inda ta ga kamar bata barga da ita suke ba. Mansura ko tasan ta ita suke saidai damuwar da take ciki ya sa bata maida hankali akan habaicin nasu ba, dan bisa ga alama ma ba ta su take ba. Aunty Zainab ta shigo bangaran Yaya Abba inda kawayan Amarya da Amarya suke. Aunty Zainab kallan Mansura ta yi cikin fada-fada ta ce "Mansura me kuke yi ne tun dazu gashi can har an fara gabatar da Malamai bakwanan." Mansura cikin sanyi ta ce "Afuwa Aunty Zainab, bamu san amfara ba." Mansura kama hannun Amina ta yi kawayan duk suka rufa masu baya suka fita. Suna zuwa aka gwada masu inda zasu zauna. Take Malama Safiya ta fara wa'azi akan falalar dake tattare da aure, menene aure, waya ce ai yi shi, da Kuma darajar da yake tattare da ita. Bayan ta gama dogan bayani, ta kuma koma magana akan hakin dake rataye akan mace akan mijinta. Take jikin mutane ya yi sanyi. Bayan ta gama taba Malama Farisatu wadda ta fara bada kisa akan yadda Nana Khadija ta zauna da ma'aiki S.A.W. jikin Amina sanyi ya yi da yake babu wuyar kuka take ta fara kuka wadda ita kanta bata san me ya sa ta kukan ba. Mansura da dama kiris take jira, take itama ta ji kukan na niyyar kwace Mata, hakan ya sa da wayau Mansura ta bar gun kamar tana sosa ido kamar wani abu ya fada mata a ido. Mansura can bayan window Abba ta je inda tasan babu wanda zai ganta ta duka a wajan ta fashewa da kuka. Mansura kuka take sosai har tana jan ajiyar zuciya irin na wanda ya gaji kuka ya yi yinsa. Mansura sai ji ta yi an dago kanta. Dago fuskarta ta yi wadda ta dame gaba daya saboda kuka. Abba bai cema Mansura komai ba handkerchief dinsa ya ciro yana goggo ma Mansura hawayanta. Sai dai ya gama kafin ya kama hannunta ta tashi daga duken da take. Abba kallan Mansura ya yi ya ce "Kalli yadda kika bata kwalliyarki, Haba Mansura ba za ki iya hakuri ki adana duk damuwarki ba har Amina ta bar gidan nan ba kamar yadda na ce maki ko? Kuma ahaka ne kike cewa ke bakya son komai kin fi so a barki ki ci gaba da zama gida, ai dole ma in sama maki abin yi idan aka gama hidimar bikin nan." Abba shiru ya yi yana kallan Mansura dake sauke ajiyar zuciya akai-akai, kafin zuwa can ya ce "Kin ga kin bata kwalliyarki, zo muje ki wanke fuskarki ki koma wajan walimar Kinga Amina yanzu zata kasa natsuwa idan ta fahimci baka wajan. Abba shigowarsa kenan ya shiga bangaransa ya dakko kayansa da zaisa gobe ya ci karo da kukan Mansura bayan window shi. Can bangaran Hassana ko ganin Abba ya shigo Mansura Kuma ta tashi ta yi bangaran nasa, Wanda basu san ita bata san shigowarsa ba, inda ita a saninta kamar yadda mama ta ce sai taro ya watse zai dawo da kwana gidan, hakan ya sa ita ba ta yi tunanin yana gidan bama. Hassana ganin haka radama Aisha ta yi, yarinyar can ina jin wajan Yaya Abba zata, Kinga ta yi bangaran da muka shiga dazu, ba ance nan ne sight dinsa ba, zo muje mugani idan ya tabbata hakane Wallahi mu taru mu taka Mata burki." Hassana dakyar ta samu Aisha ta yadda ta bita, dan ita Aisha bata son ganin abinda zai bata mata rai, Amma kamar yadda Hassana ta ce mata wai zata kafa hujja ne. Lokacin da Aisha suka iso wajan su Abba sun shiga falonsa kenan shida Mansura yana rike da hannun Mansurar. Hassana kallan Aisha ta yi ta ce "Kinga abinda nake fada miki ko? Yanzu Kinga ya kama hannunta sun shiga dakinsa, lallai Allah ya sa wannan ma ba wani mugun abin suke aikatawa ba." Aisha tsabar kishi kasa magana tayi sai hawaye dake zuba daga idanta. Suna nan tsaye sai ji suka yi an daba su. Hassana da sauri ta waigo tana kallan Khadija ta ce "Khadija lafiya?." Nazo wucewa ne na hangoku da fatan dai lafiya na ga Aisha na kuka?." Hmmm Ina fa lafiya ana shirin kwace mata Wanda zata aura." Nan Hassana ta kwashe komai ta fada ma Khadija. Khadija wani uban ashar ta yi ta ce "Yanzu kunsan yadda za yi ke Aisha ki tsaya acan yadda ba zai ganki ba, Hassana mu Kuma zo muje da sunan mun zo daukar Abu inda dai yasan nan muka zauna muka shirya, mu shiga mu gani." Aisha inda suka ce Mata ta tsaya tana jira, inda Hassana da Khadija suka tusa kansu cikin falon Abba ba tare da sun yi sallama ba. Abba Kuma daidai ya kama ✍🏻 Fadila Sani Bakori ⭐ ABBANA ⭐ 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚* Domin samun littafin ABBANA daga farko 👇🏻Follow the ABBANA channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaYZGsNEFeXsr1CKQl3r P 25-26 Abba daidai yana taimaka ma Mansura wajan gaya nadin Lifayarta su Hassana suka shiga. Ganin Abba da Hassana sai suka yi kamar marasa gaskiya, Abba Kuma kota kansu bai bi ba haka Mansura ma ci gaba da tayata ta gyara nadin Lifayarta ya yi. Kallan Hassana da Khadija ya yi da suka ja suka tsaya sukai kai kuri ya ce "Lafiya?." Khadija cikin wayancewa ta ce "Mansura dan Allah ba ki ga handbag dita ba kamar anan na barta." Ku shigo ku duba Mana. Abba ya ce yana kamo hannun Mansura suka fita. Khadija da Hassana rike baki sukai suna kallan juna. Khadija ta ce "Lallai maganarki gaskiya, wannan ma ai ya wuce soyayya sai dai abarshi layin iskanci, in ba iskanci ba lifaya fa yake tayata nadawa." Hassana dai tsabar al'ajabi ta kasa magana sai zuwa can ta ce "Tab dijam, inko hake ne akwai aiki a gaban Aisha babba ." Khadija Kai ta jinjina ta ce "Wani Anya ko Yana ma wani son Aishar kuwa?." Ke bisa ga alama fa Yana sonta, munafukar yarinyar nan ce ke son yi mai kutse cikin rayuwa, ni yanzu tunani na daya yadda za mu yi mu taimaka ma kawarmu dan idan har muka ce ta bar mata shi ai ta shadamu gara mu nuna Mata ita karamar Yar iska ce." Hassana koma hannun Khadija ta yi ta ce "Muje Aisha na can tana jiranmu." Har suka koma Aisha na kuka dan taga fitowar Abba rike da hannun Mansura yana mata magana mai kama da lallashi. Hassana dafa Aisha ta yi ta ce "Tabbas abin da zafi Wanda kake so ka bashi Amana ka ganshi yana cin amanarka, amma ki yi hakuri sai yarinyar nan ta yi fiye da kukan da kika yi. Yanzu muje ki wanke fuskarki Kar a ganema kin yi kuka." Aisha zuwa ta yi ta wanke fuskarta kafin suka koma wajan walimar inda suka iske Mansurama zaune kusa da Amarya. Kasan cewar an gayyato malamai mata da yawa hakan ya sa anjima ana walimar kafin aka rarraba abun rabon da mahaifiyar Aisha ta yi kafin aka watse daga walimar. Amina kalllan Aisha ta yi ta ce "Mommyna ya dai na ganki so silent." Aisha fashe ma Amina da kuka ta yi cikin kukan Aisha ke fada ma Amina ita ta hakura da Abba inda ta ga gaba daya hankalinsa ba akanta yake ba." Amina gudin Kar hankalin mutane ya dawo kansu ya sa ta jawo hannun Aisha da sauri suka nufi bangaran Abba, ganin sauran kawayansu a falon Abba ya sa Amina ta bude bedroom din Abba suka suka shiga. Amina zaunar da Aisha ta yi gefan katifar Abba, sannan ta zauna kusa da ita. Amina cikin damuwa da lamarin ta ce "Mommyna duk abin da zan fada maki ba lalle ki yadda ba, amma a iya sanina fara hidimar bikin nan nawa ne Yaya Abba suke magana da Mansura." Aisha Kai ta girgiza ma Amina ta ce "Amina Allah na hakura da Yaya Abba saboda dama nike sonshi shi baya Sona, sannan maganar ace wai yaya Abba baya soyayya da yarinyar nan ba haka bane, kila dai ke ce baki Sani ba." Amina shiru ta yi dan ta rasa yadda zata fahimtar da Aisha ta gane, Amina ta ce "Aisha Koda ma ace Yaya Abba na son Mansura kamar yadda kika ce kinsan dai sai ya aureki Koda zai aureta." Aisha Kai ta girgiza ta ce "Amina ba zan iya zama da wanda hankalinsa baya kaina ba Yana kan watane, da ace daga ni sai shi ne ina da tabbacin babu wata a ransa da zan iya hakura in auresa, amma yanzu Kam na hakura ina mai tabbatar miki yanzu haka daga na je gida zan sanar da Malama." Amina hankalinta tashe ta kamo hannuwan Aisha ta ce "Mommyna Wallahi Allah kin ji na rantse miki Yaya Abba baya sa soyayya da Mansura idan baki yadda ba Bari in Kira Mansurar ki ji daga bakinta." Amina na fadin haka ba ta saurari ta fita. Babu jimawa Amina ta dawo tare da Mansura. Bayan Mansura ta zauna Amina cikin sanyi ta ce "Mansura Aisha wai ta fasa auran Yaya Abba saboda ita a zarginta Kuna soyayya da Yaya Abba ne, na yi ƙoƙarin in fahimtar da ita taki ganewa shi ne na kiraki ki fada mata da kanki ko zata fi yadda." Mansura tabe baki ta yi kafin ta ce "Ni bansan meye ma wata soyayya da take magana akai ba, Yaya Abba ma ni sanadiyar bikin nan muka fara magana dashi, idan kin ce za ki fasa auranki da Yaya Abba ni babu ruwa." Amina kallan Aisha ta yi ta ce "Kin ji ko mommy, Idan da tana soyayya da Yaya Abba ai da nafi kowa Sani, abinda kike tunanin Wallahi ba haka bane." Aisha sai yanzu ta ji ta gamsu. Cikin sanyin muryarta ta ce "Shi kenan na fahimta." Amina ajiyar zuciya ta sauke ta ce "Wai lallai sannu hajiyar kishi, ki gode ma Allah ma Yaya Abba bamai kula-kulan yan Mata bane, ki ce da munsha kallo." Aisha murmushi ta yi Bata ce komai ba. Da daddare kawayan Amina duk sun watse ya rage daga Amina sai Mansura, Wayar Amina ringing ta yi, bayan ta dauka, ta ce "Okay gani nan zuwa." Aisha kallan Mansura ta yi ta ce "Ina zuwa Yaya Abba ke kirana, Allah dai ya sa ni ba aiki zai Sani ba." Amina zaune ta samu Abba cikin motarsa, Abba umartar Amina ya yi da ta shiga, Amina bayan ta zauna ta kallli Abba ta ce "Yaya Abba ka kirani Kuma ka yi shiru. Murmushi Abba ya yi ma Amina ya ce "Ba wani abu bane Amina tambayarki zanyi, tun da yarinyar nan ta zo gidan nan bata taba baki labarin wani na gidansu ba ko labarin mamanta ko babanta ba?." Amina shiru ta yi tana kallan Abba, azuciyarta ta ce "Me Yaya Abba zai yi da bincikar labarin Mansura, ko dai da gaske ne suna soyayyar kamar yadda Aisha ta ce ." Abba ganin Amina ta fada duniyar tunani muntsilarta ya yi ya ce "Idan kin gama tunanin ina jinki." Amina murmushi ta yi tana kallan Abba ta ce "Yaya Abba kasan Mansura bata magana ko labari ka kawo Mata daga eh, sai uhm, idan abun dariya ne ta yi murmushi shi kenan, kwanannan ne ma idan ina magana har take samun baki, Amma bata wata doguwar magana bare har ka ji sirrinta. Abba shiru ya yi kafin ya ce "Amma ke me kika fahimta game da yarinyar?." Shiru Amina ta yi kafin ta ce "Wallahi Yaya Abba na kasa fahimtar komai akanta, amma dai koma meye iyayanta da alama attajirai ne." Kai Abba ya jinjina ya ce "Nima naga alamar haka. Amina gobe za a daura miki aure ina so yau din nan, ki zungureta da maganar ahalinta da kin ji me zata ce, Ina so ki min recording hirar taku, abin da nake so ki ce Mata, Mansura niko inata so in tambayeki wai wacece Fatima da kike yawan Kira a mafarkinki." Daga nan Kar ki ce mata komai." Amina Kai ta jinjina ma Abba alamun za ta yi, kafin Amina ta ce tana wasa a hannunta alamun maganar kamar ta yi mata nauyin fada ta ce "Yaya Abba kana son Mansura ne?." Abba hararar Amina ya yi ya ce "Dan na yi miki wannan maganar akanta shi kenan ina sonta, Kinga ke aure zaki yi mama Kuma kullum tana Islamiya, shine nake so mu ji wacece ita in ta kama mu maidata gidan iyayanta sai mu maidata kamar zaifi." Amina turo baki ta yi ta ce "Allah sarki Yaya Abba tashin hankalin Mansura kenan akan auran nan nawa zaku ce ba za ku iya zama da ita ba, gashi nan tun kafin in yi auran Kun bayyana min hakan, inda gashi kana maganar maidata gidansu." Abba da mamaki ya kalli Amina dake goge hawaye ya ce "A'a Amina ya zamu koreta bayan kin riga kin maidata Yar gida, kawai dai Yana da kyau mu San wacece ita din." Shi kenan Yaya Abba zan tambayeta yanzu daga na shiga ciki, duk yadda muka yi da ita zan tura maka ta WhatsApp." Amina fita ta yi daga motar ta koma bangaran Abban da yake can zasu kwana. Amina kwance ta samu Mansura kamar yadda ta barta. Zama ta yi gefan Mansura tana kallanta ta ce "Na zaci zan dawo in iske Kun yi barci, in fara jin labarin Fatima, kinsan har so nake ki rigani yin barci dan in ji labarin Fatima, wai wacece Fatimar nan ne da kika dameni da kiranta a barcinki?." Tun da Amina ta fara magana Mansura ke aikin zazzare ido tashi Mansura ta yi daga kwancan da take ta ce "Dan Allah me nake cewa?." Amina hararar Mansura ta yi ta ce "Ina tambayarki wacece Fatimar da kike Kira a barcinki kina tambayata me kike cewa." Mansura tari ta kama ta dafe karjinta da take jin kamar zai fito, take idanunta suka kada suka yi jajir, har yanzu Kuma ba ta fasa tarin da take ba, take hankalin Amina ya tashi ganin yadda Mansura ke tari gata rike da kirji. Amina dafa Mansura ta yi tana mata aikin sannu. Mansura dago idanunta ta yi da duk haskansu sai da suka kada suka yi ja ta ce "Amina dan Allah ki yi shiru koda ace kin ji bakina ya furta wata kalma akan Fatima dan Allah karki tambayan akanta, zuciyata ta yi raunin da bana iya bayani akan komai." Amina Kai ta daga ma Mansura tana danasanin tambayar da ta yi mata ganin yadda take ta birkice Mata. Amina ruwa mai sanyi ta kawo ma Mansura ta ce "Dear ki sha ruwan sanyi." Kai Mansura ta girgiza ma Amina hakan ya sa ta aje ruwan cikin sanyi. Amina tsabar yadda jikinta ya yi sanyi da halin da taga Mansura ya sa ko takan Abba ba ta biba da yake jiran ta tura mai recording din da ta yi mai na firarta da Mansurar. Abba da ya ji shiru text ya tura ma Amina na ya ji shiru, Amina sending recording din ta yi ma Abba ta WhatsApp. Abba koda ya gama sauraran daukar bai fahimci komai ba game da Mansura, sai rudin da ya fahimci tambayar ta je fa Mansura, dan ko yananin yadda Amina ke magana ya nuna hankalinta atashe take ma Mansura magana. Abba bai gama jin ƙarshen daukar ba ya kashe ya Kira wayar Amina. Amina na dagawa Abba ya ce "Ba Mansura Wayar." Amina tashi ta yi ta kanga ma Mansura wayar a kunnanta. "Hello, Mansura kina jina." Mansura goge hawayanta ta yi ta ce "Eh Yaya Abba ina ji." Abba shiru ya yi kafin ya ce "Ya na ji muryarki kamar kina kuka?." Mansura sanin ta yi ma Abba alƙawarin ba zata Kara kuka ba ya sa ta ce "A'a ba kuka nake ba." Kin tabbata." Eh Allah Yaya Abba ba kuka nake yi ba." Okay gani a wajan get fito in gani." Abba na fadin haka ya kashe wayarsa. Mansura tashi ta yi tana Kuma goge hawayanta ta kalli Amina ranta alamun bace ta ce "Ke kika ce ma Yaya Abba ina kuka?." Amina kallan Mansura ta yi ta ce "kin ji na yi waya dashi ne?." Mansura kamar za ta yi kuka ta ce "Tom ni ya zanyi hawayena ya tsaya?." Amina tashi ta yi ta zauna tana kallan Mansura ta ce "Bari in Kuna miki kira'a ki saurara ranki zai yi sanyi." Mansura turo ma Amina baki ta yi ta ce "Yaya Abba fa ya ce inje in ya gani in ba kuka nake ba, Kuma na yi mai alƙawarin ba zan Kara kuka ba." Okay, ki dauraye fuskarki ki shafa powder ba zai gane ba." Mansura fuskarta ta dauraye ta zo Amina ta shafa Mata powder kafin ta fita. Abba na zaune ckin motarsa ya hango Mansura hakan ya sa ya fito daga cikin motar ya jingina da motar. Mansura na wasa da hannuwanta ta karaso inda Abba yake. Abba hararar Mansura ya yi ya ce "Baki iya sallama ba ko ?." Mansura shiru ta yi batace komai ba, Abba ya ce "Shi kenan inda ba zaki yi min sallama ba wace ki tafi." Mansura turo baki ta yi kafin ta ce "Assalamu alaikum." Ameen Wa'alaikumussalam. Yauwa ko kefa, bari inga da gaske ne baki yi kukan ba." Abba na fadin haka ya kunna flashlight din wayarsa ya haske Mansura. Mansura hannu ta sa tana kare fuskarta saboda haskan na kashe mata ido. Abba kashe hasken ya yi ya ce "Da gaske dai baki yi kuka ba, tom daga yau har a tashi taron baki idan har baki sake yin kuka ba ki fadi duk abin da kike so ni Kuma zan miki shi." Mansura dai murmushi ta yi ma Abba ba batace komai ba. Abba Kuma kallanta ya yi ya ce "Muje in rakaki." Abba sai da ya ga shigar Mansura kafin ya juya ya tafi. lokacin da Mansura ta koma Amina ta gama waya da Ahmad kenan. Amina kallan Mansura ta yi ta ce "Ina mamaki waiku salon soyayyartaku ta sirrce ce, yanzu na gama waya da Yaya Ahmad na tambayeshi dan nasan Yaya Abba na fada masa komai nasa, amma ya ce min bai sanar da shi soyayyarku ba. Mansura me ya sa kike boyemin soyayyarku da Yaya Abba? Ko shi ya ce ku boye ne?." Mansura hararar Amina ta yi ta ce "Wai ku anan Katsina haka ake yi ne babu damar a ga mace da Namiji suna magana sai ace soyayya suke, har yaya Ahmad dinma kenan baki yadda da abin da ya ce ba, Allah raina sosai yake baci idan Kuna irin wannan maganar sai inga kamar Kuna banbanta tsakanina dake ne dan da kin daukeni kamar yadda kike fada ba zaki rika hadani da Yaya Abba ba dan kinganmu kawai Muna magana." Amina shiru ta yi dan abinda Mansura ta fada hakane, ya za ai daga sun yi magana ace soyayya suke. Amina ganin ran Mansura ya bace hannunta ta kama ta ce "Yi hakuri Mansura, na yadda Allah tunda Yaya Ahmad ya fada min, nasan da ace Yaya Abba na sonki da ke kanki kafin ya fada miki zai fadama Yaya Ahmad ne, na gamsu Allah." Mansura da Amina sun yi fira kadan kafin duk barci ya kwacesu. Washagari da wuri mai dilkar Amarya ta zo ta yi ma Amarya da kawar Amarya, wadda ta ragu kawayan Amarya da dama suka shafa a fuskokinsu. Bayan Amarya da kawar Amarya sun wanke jikinsu daga nan suka dunguma suka tafi gidan Aunty Zainab da yake acan zasu yi sitin. Suna zuwa wasu daga cikin kawayan suka fara daura girki. Kawayan Amina kusan kaf sun hade ma Mansura Kai duk inda ta yi habaci kusan suke sakar mata. Mansura bata wani fahimci da ita suke ba, hakan ya sa hidimarta take ba ruwanta da kowa sai wata kawar Amina da ta nuna tana sonta. Hakan ya sa Mansura itama ita kadai take kulawa. Ana cikin hakane Amina ta shira cikin wani blue din lass, inda me makeup din ta yi Mata simple makeup. Amina sosai ta yi kyau, haka Yan matan Amaryar suka fara shiryawa daya bayan daya mai makeup na aikinta na gyara duk wadda ta shirya. A haka duk suka shirya, inda Mansura ma ta shirya cikin wata green atamfar anko da suka yi, sosai ta haskata ta yi kyau. Haka kawan Amarya ma duk suka gama shiryawa cikin wannan a tamfa ta anko. 2:30PM dubban jama'a suka shida daurin auran Amina da Ahmad....✍🏻 Littafin ABBANA na kudi ne, free pages ya kusa karewa idan kin shirya 400 ne daga zarar na gama zai koma 500 my number 08063830828 Fadila Sani Bakori ce. ⭐ ABBANA ⭐ 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚* Domin samun littafin ABBANA daga farko 👇🏻Follow the ABBANA channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaYZGsNEFeXsr1CKQl3r P 27-28 Amina na zaune kawayanta sun sata tsakiya sai guda suke mata tare da shaigantaka irin ta kwayan Amarya, Allah ya kaimu shekara mai zuwa kamar haka mu sha suna. Amina dai ta yi banza dasu bata tanka ba, sai Aisha ce ke tare Mata. Mansura Mika ma Amina wayarta ta yi da aka Kira ta ce "Gashi, Yaya Ahmad ke Kira." Khadija rangada guda ta yi jin Wanda akace yana Kiran wayan, Amina Koda ta daga hayaniyarsu hanawa ta yi ta ji, hakan ya sa ya Ahmad tura Mata text kamar haka "Assalamu akaimu, zuwa ga zabin zuciyata a maryata, Ina fatan tana cikin farin ciki irin Wanda nima nake ci, na gode ma Allah da ya kaini wannan lokaci ya nuna min auran gimbiyata Amina, Ina rokan Allah ya bani tsawan randa zan rayu tare da ita, ya Kuma bani zuciyar kautata Mata Koda ace ta yi min badai ba, in sha Allah babu ranar da zanga abinda gimbiyata Amina ta yi min a matsayin laifi. Na kirane in jin muryar Mata, in kuma sanar da ita ta sanar da kawayanta 5:00PM zamu zo mu daukeku keda kawayanki zuwa wajan party da Abba ya hada Mana." Amina dora wayar ta yi a kirjinta bayan ta gama karanta sakon Ahmad tana rintse ido, da alama sakon Ahmad sun yi tasiri sosai a cikin zuciyarta. Khadija dafa Amina ta yi ta ce "Amarya an shiga sauki ne." Tana dariya ta idasa maganar. Amina bude ido ta yi tana hararar Khadija ta ce "Yar sa ido, yaya Ahmad ya ce ku shirya 5 za a zo daukarmu za a yi party wai." Khadija kallan Amina ta yi ta ce "Wato ma wai baki san da maganar bane?." Kai Amina ta jinjina ta ce "Allah ban Sani ba sai yanzu da yake fada min da alama shima bai Sani ba." Amarya da kawayanta haka suka ci gaba da hidimarsu, inda sukaita daukar hotuna, da videos tare da Amarya. Mansura ko kamar yadda ta yi ma Abba alƙawarin haka ta kasance ta aje duk wata damuwatata gefe hidimarta kawai take sha, daga ka ganta ka ga kirjin biki. Bangaran su Hassana ko tun suna habaicinsu har sun gaji sun yi shiru, dan sunga alamar Mansura batatasu take ba. Ana cikin hakane aka sanar dasu ga abokan ango nan zuwa, masu gyara daurin dankwaki na yi masu fesa turare da masu kara powder a fuska duka. Ahmad tare da abokansa a harabar gidan Aunty Zainab suka tsaya, sukasa aka Kira masu Amarya da kawayan Amarya a yi hoto. Wasu daga cikin kawayan amaryar ne suka fara fitowa da Amarya. Abba babban abokin ango ansha babbar riga wadda ta Kara fito da baiwar kyawunsa da Allah ya yi masa, sun yi shiga iri daya da ango ko mai nasu hatta agogonsu iri daya. A hankali-ahankali kawayan amaryar duk suka fito, Abba da wayau ya gama kallace kawayan amaryar kaf bai ga Mansura ba. Yana cikin naimanta da idanusansa Aisha ta zo da iyayinta ta ce "Assalamu alaikum, abokin ango mai kama da ango." Abba juyowa ya yi yana kallan Aisha, kafin ta kakaro, murmushi Abba ya yi mata ya ce "Mommyna, ya kuke ya hidima." Aisha cikin jin dadin yadda Abba ya amsheta ta ce "Alhamdullah, Yaya Abba ya taku." Alhamdullah." Abba da wayau ya Kara dubawa ganin bai ga Mansura ba ya ce "Kice mu kama karamin hole naga kamar baku da yawa." Aisha murmushi ta yi ta ce "Kuma ka ganmu Ina jin mutum uku ne basu anan suke je su dawo." Abba cikin son sanin su waye saboda yana saran ko akwai Mansura a ciki ya ce "Dawa-dawa ye basa nan?." Aisha da dadin soyayyar Abba ya kasa ankarar da ita Abba Mansura yake nema ta ce "Da Khadija da Rukayya da Jamila." Kai Abba ya jinjina. Zai yi magana Ahmad ango ya yafatoshi da hannu alamun ya zo su yi hoto." Abba kallan Aisha ya yi ya ce "Kin ga Ango na kirana ina zuwa." Aisha bin Abba ta yi ta ce "Yaya Abba muje a yi hoton dani." Abba zuwa ya yi kafin a dauki hoton ya matsa kusa da Amina saitin kunnanta yadda babu wanda zai ji ya ce "Amina, Wai Ina yarinyar nan ne?." Amina sai yanzu ta farga ba Mansura, waige-waige ta fara yi, ganin ba ta ganta ba ta ce ma Abba "Yaya Abba, tana cikin gidan ka Kira wayata tana hannunta." Abba kallan Aisha ya yi ya ce "Minti daya ina zuwa zan yi waya." Abba Matsawa ya yi ya Kira Mansura a waya. Mansura dake kwance tana danna wayar Amina tashi ta yi ganin Yaya Abba is calling. Amina picking call din ta yi tana sa wayar a kunnanta. "Kina nan kina aikin kukan naki ko?." Abba ya ce ma Mansura. Mansura turo baki ta yi kamar Abba Yana kallanta ta ce "Kai Yaya Abba, Allah duk yau ban yi kuka ba." Okay ki fito waje yanzu Ina jiranki." Mansura jimbur ta tashi ta fita, ita kanta Mansurar tana fita ta fara naiman Abba da idanunta. Can ta hangesa shi gefan ango da Amaya ga Aisha kusa da Abba ta nanike Mai ana hoto, ita ala dole bata son wata macan ta tsaya kusa da Abba. Mansura karasawa ta yi tana murmushi ta gaida Ahmad, Ahmad da fara'arsa ya amsa ya ce "Babbar kawar Amarya ya hidima." Mansura murmushi ta yi ta ce "Alhamdullah." Ahmad nuna ma Mansura ya yi kusa da Amina ya ce "Zo mu yi hoto." Mansura tsayawa ta yi kusa da Amina akadaukesu hoto su duka, da ita da Mansura da ango da Kuma abokin ango da Aisha. Abba ya yi mamaki yadda Mansura ta dauke kanta daga shi da ta fito. Da yake Amina ta rada ma Ahmad cewar ga wadda Abba zai aura wato Aisha ta nuna mai ita, dayake Ahmad ya san komai game da Aisha ita dince kawai baisani ba. Ahmad kallan Aisha ya yi Yana murmushi ya ce "Aisha zo mu yi hoto." Haka suka yi hoton su hudu da Aisha da ango da Amina da Kuma Abba." Bayan sun gama Ahmad ya ce ma Mansura itama ta zo su yi. Babbar kawar Amarya da baban abokin ango da ango da Kuma Amarya su hudu kenan." Mansura tsayawa ta yi gefan Abba, kamar yadda Amina take can gefan Ahmad. Abba take ma Mansura kafa ya yi da dan karfi, Mansura Kai ta dago ta kalli Abba tana turo baki. Daidai nan maihoton ya dauka. Abba Kuma kanne ma Mansura ido ya yi. Mansura ganin Abba da gangan ya takata hakan ya sa ta fara buga kafa tana Kara turo baki Wanda daga mai daukar hoton da Amina da angon da Aisha duk suna kule dasu ba kamar Aisha ba. Abba cikin kunnan Mansura ya rada Mata ya ce "Maganin wanda bai iya gaisuwa ba kenan." Ahmad tabo Abba ya yi, Abba waigowa ya yi yana kallan Ahmad, Ahmad Kuma a hankali Aminace kadai ta ji abinda ya ce ya ce "Amaryarka na kallanka dan haka ka kula malam." Abba harar Ahmad ya yi baitanka masa ba. Haka aka ci gaba da hotunan Wanda Abba shi dai gaba daya hankalinsa na kan Mansura, ya kasa iya rike kansa akan Mansurar, ta yi mai kyau sosai gashi ta saki ranta. Abba ya yi masu hotuna masu yawa shi da Mansura. Mutane da dama sun dauka budurwarsa ce, wa inda suka ji labarin saranarsa Kuma sun dauka ita zai aura. Aisha daga ka kalleta Kamar ta fasa kuka Amma ta daure tana yake ne kawai. Amina lura da hakan da ta yi ta sanar da Ahmad ta ce "Yaya Ahmad dan Allah ka yi ma Yaya Abba magana mana Allah haka cin fuska ne fa, ya za ai ya yi ta hotuna da Mansura a gaban Aisha haka ai ba zata ji dadi ba." Abba zuwa ya yi ya jawo Abba gefa ya ce "Abba meye haka ne za fa ka hada yaran nan fada ne abin da kake yi, Taya za ka zo kana hotuna da wata macan a gaban matar da zaka aura, gaskiya haka bai kamata ba cin fuska ne Wallahi." Abba bata fuska ya yi ya ce "Duk Mai gulma ya je ya yi ni kallan da nake ma Amina shi nake ma Mansura. Hoto Kuma kafin in yi da Mansura ai da ita na fara yi." Ahmad duk yadda ya so Abba ya fahince shi yaki hakan ya sa dole ya rabu da shi. Bayan an gama hotuna Abba kallan Mansura ya yi ya ce "Ku shirya nan da 1hour zamu zo mu dauke ku." Kai Mansura ta jinjina ma Abba, Abba har ya juya zai tafi ya kalli Mansura ya ce "Ki rike wayar Amina a hannunki zan kiraki." Mansura Kai ta daga ma Abba ya ja motarsa suka tafi. Hassana ce ta sanar da sauran kawayansu akan kowa ya sa lass din ankosa 5 za a zo daukarsu zuwa party. Bangaran Aisha waje ta samu ta zauna ta yi tagumi. Khadija da dawowarsu kenan kallan Aisha ta yi dake zaune ita kadai ta yi tagumi. Khadija karasawa inda Aisha take ta yi ta cire mata hannun da ta yi tagumi dashi ta ce "Aisha, lafiya kika zo nan kika yi tagumi kekadai?." Aisha dago manyan idanunta ta yi tana kallan Khadija kafin ta ce "Baba komai." Shi kenan." Khadija tace suka tafi. Khadija bayan ta shiga falon Aunty Zainab, Hassana ta naima dan ta fita kusa da Aisha tana tunanin in itace kila za ta iya fada mata damuwarta. Kasancewar wajan da mutane ya sa Khadija hannun Hassana ta kamo har zuwa inda Aisha take. Zama suka yi gefan Aisha, kafin Khadija ta ce "Hassana kawarki na gani cikin damuwa na tambayeta ta ce min ba komai shine na kiraki kila ke ta fada miki." Hassana dafa Aisha ta yi ta ce "Nasan tatsuniyar gizo bata wuce ta koki, Aisha akan Ina komai ya faru gaskiya harda laifinki, lokacin da kika je kina ma Yaya Abba magana baikwalasheki ba, hasali ma har hoto naga kunyi tare amma yarinyar nan na zuwa Ina lura da ke kika janye jikinki kika koma gefa, ma'ana kin bar mata shi kenan. Aisha idan har kina son Yaya Abba da gaske kamata ya yi ki tsaya ki yi yaki ki kauci soyayyarki." Hassana ta dade tana ba Aisha shawarwari kafin suka tashi suka shiga ciki domin canza kayansu zuwa lass Wanda za suje wajan partyn dashi. 5:00PM motocinsu Abba suka cika kofar gidan Aunty Zainab zuwa daukar kawayan Amarya zuwa wajan party. Kawayan Amarya kowace ta cakare fatar kowacce ace babu kamarta. Ga lass din peach color da dige-digen fari-fari, sai kalar ta haska kowa, hakan ya sa duk sai suka yi kyau. Mansura da Aisha suka rike Amina har zuwa wajan motar da Ahmad yake ciki. Wanda babban abokin anko wato Abba shi zai ja motar. Abba kallan Aisha da Mansura ya yi ya ce "Babbar kawar Amarya ta shiga gaba mu tafi." Abba Kiran wani abokinsa ya yi ya ce "Habibu, ga Mommyna nafi yadda da tukinka ka taho min da ita." Haka din da Abba ya yi sai ya rage ma Aisha zafin da take ji, inda ko mahaifiyar Amarya tana jin tana Kiran Mansura da babbar kawar Amarya har dilka ma tare aka yi masu. A cikin motar Amarya ko Abba ya kure volume din motar da wakar Hanta da jini. Tafiya suke Abba na karkada kafa da Kai. Mansura dai mamaki ya isheta ganin yadda Abba kebin wakar. Green g hotel anan Abba ya kama wajan gudar da partyn bikin kanwarsa da babban abokinsa. Mutane duk sun gama halartar a hall din, har iyayan Amarya duk an kawosu ya zamana Amarya da anko kawai ake jira. Bayan Amarya da anko sun iso MC ya fara announcing na isowar Amarya da anko. Kawayan Amarya da abokan ango suka je suka taro a Amarya da anko inda aka sasu tsakiya. Wasu daga cikin abokan manni kawai suke ma Amarya da angon a haka har suka karasa wajan zaman da aka tanada domin amarya da ango. MC ya dade yana bayanansa kafin aka tada daya daga cikin akoban anko ya bude wajan da addu'a. Bayan haka MC ya Kira Mansura babbar kawar Amarya yana son ganinta. Mansura kin tashi ta yi sai da wasu daga cikin kawayan Amarya suka kama hannunta suka rakata har wajan MC din kafin suka juyo. MC ya dade yana wasa Mansura, kafin ya Kira babban abokin Ango Abba. MC inda Mansura take tsaye ya nuna ma Abba ya tsaya kusa da Mansura, kafin ya ce "Jama'a dan Allah ku kallesu, ya kuka gansu dan Allah, a tafa ma babbar kawar amarya da babban abokin angonnan ." Rap-rap, haka hall din ya dauka. MC kallan DJ ya yi ya ce "DJ sa masu wakar da tadace tasu su bude Mana filinnan." Eye-eye eh-eh, a'a. Nasan so dashakuwa, jininmu ne yake ta haduwa, matso ki zo nasamu natsuwa, dannn kinhanaminni damuwa.oo'ooo oo'oo, laaaaaa oo-oo ." Take hall din ya dau ihu ganin yadda Abba ya fara bin wakar. "Wadda na damka amanata akanta na jaddada kalmanata, na fada zan nanata azuci nasata na riritata .... kamar wasa" wata kallar rawa Abba ya fara irinta Mayan guy , breaking dance, daidai lokacin da aka fara " kullum inata fada miki sai ke." Abba ya fada yana nuna Mansura, ya ci gaba da cewa yana nunata "Kaunarkice ke yimin tsinke, tattarani ta sani a shinke, sai da ta sani a tsinke, Bata barni da yunwa ba, ba ta ki bani ruwan sha ba, baza nace Mata uffan ba domin agaran haka ribace." Wani taku Abba ya yi yana dansewa har ya karaso wajan Mansura yana cewa "Mitazamanamu ba wa'adi, komai mukayo so ne sanadi, sa'in da ba kiciran wa'adi, rabo dake sai dai in na ji naga kaza ta yi kaho, mai kishina Ina sonki me zan baki na aureki, sonki yana ta ginan layi, mizamanmu atare acan ciki, acikin ciki can ciki." Hall din gaba daya ya dau ihu anata taba masu Abba dan sosai abin ya kayatar ya tada ma wasu tsimin soyayyarsu. Mansura dai tsaye take tana kallan Abba tana murmushi, wani wajan Kuma ta rufe ido. Abokan Abba ko ku zo kuga yadda suke yi ma Abba liki. Mansura ma wasu daga cikin iyayan Amarya sunyi Mata liki Amma kawaye ko daya babu wadda ta yi Mata liki. Mc yabama abokan ango ya yi sosai ya ce "Ya haka ne? abokanka Abba sun yi Kara munsan kana da Abokai Amma kawar Amarya har yanzu bamu shaida tana da kawaye ba, dan duk su mamane suka yi Mata liki, Dj sa masu wata wakar da alama waccan Bata burge kawayan Amarya ba ne." Dj waka nake so wadda ba zamu bar nan wajan ba sai abokin angonnan ya yi wuf da zuciyar kyakkyawar kawar amaryar nan." Hall din gaba daya ihu ya dauka jin wakar da dj ya sa. Abba take ya fara bin wakar tare da rawa irin wadda ta dace da wakar. " Dubaaa akanki ana kallona majanuni." Abba ya nuna Mansura ya ci gaba da bin wakar" Babban burina ki kasance daf dani, in zaaki irga masoya naki kisanyo dani, duba akanki ana kallona majanuni, ni Kuma nacee indai kainaki ne ban fadi ba, Sako ya bayyanane tun daga zuciya, sannan kaunarki tana kaman zuciya, kin kaaamani kurwata tun jiya, har yaake matsayin bana samun lafiya." Abba gab Mansura ya matsa ya kureta da ido kamar irin wajan bakowa sai su kadai haka yake ji ya manta da kowa, kallan Mansura yake Yana cewa "Kin shiga Raina kin zauna dan kinsamu guri inata kiranki na amsa kuma nazo da wuri, ki ce farko Kuma ki ce karshe bishiyar nan maigirma wadda kikai minni dashe, bana ji bana gani bana son mai kushe burina in rayu dake har numfashin ƙarshe." Abba nuna ma Mansura ya yi Yana cewa " kinkirkita dukka tunanina." Abba Hannu ya hada alamun roka lokacin da aka zo baitin "Taimakaki bani gurin kwana, sanki ya hanamini barcina, Ina ganki har a mafarkina, sonkiii yanaiii min dadi ban son mu rabu, kijaddada jaarumta taki karmu rabu, bani da kowa sai ke inatafe ba wani..." Abba dakatawa ya yi da bin wakar ganin Mansura ta yi kasa da kanta tana kuka, gaba daya sai ya ji rauni shima, hakan ya sa ya kama hannun Mansura yana rungumota suka bar cikin hall din da sauri...✍🏻 Littafin Abbana na kudi ne, wa inda suka biya kafin ingama free pages 400, daga na gama 500 zai koma, my number 08063830828. Fadila Sani Bakori ce. ⭐ ABBANA ⭐ 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚* Domin samun littafin ABBANA daga farko 👇🏻Follow the ABBANA channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaYZGsNEFeXsr1CKQl3r P 29-30 Abba dakatawa ya yi da abin da wakar ganin Mansura ta yi kasa da kanta tana kuka, gabadaya sai Abba ya ji rauni shima, hakan ya sa yakama hannun Mansura yana rungumarta suka bar cikin hall din da sauri. Abba inda ya yi parking din motarsa ya nufa da Mansura, cikin motarsa suka shiga, Abba kallan Mansura ya yi da har yanzu hawaye ke zuba a idanunta. Handkerchief dinsa ya ciro ya dago kan Mansura dake kafadarsa ya fara goge ma Mansura hawayanta, ya ce "Kinmanta alkawarin da kika yi min kenan." Abba ya ce yana kallan Mansura da har yanzu hawayanta bai tsayaba. Mansura hannu tasa tana goge hawayanta. Shiru Abba ya yi yana kallan Mansura da ta sadda kanta kasa. Abba cikin sanyi ya ce "Mansura, har yanzu baki shirya fadamin damuwari ba,. Meye sa ko cikin farin ciki kike kuka?." Mansura shiru kanta kasa batace ma Abba komai ba. Hannun Mansura ya kamo ya ce "Fada min yanzu me kike so?." Gida zani." Abba kallan Mansura ya yi kafin ya ce "Kinga yanzu idan kika tafi gida jama'a zasu dauka ko wani abune, ki yi hauri ki zo mu koma har a tashi." Abba ya fadi maganar yana fita daga motar, Mansura ma fita ta yi tana jingina da motar. Abba ruwa ya ba ma Mansura ta wanke fuskarta kafin suka jera suka koma hall din. Cancikin hall din ko lokacin da Mutane suka Ankara Mansura kuka take, bayan Abba ya fita da ita ihu aka kama, wasu nacewa shaukin so ne ya dibeta take kuka. Aisha ko daurewa kawai take, gudin karta fasa kuka cikin Jama'a, hakan ya sa ta lallaba mutane na can suna ma Amarya da ango liki bayan an fitar dasu fili Aisha ta fita daga hall din, daidai zata fito su Mansura kuma zasu shiga ita da Abba. Abba kallan Aisha ya yi da hanzari ganin yadda ta fito hall din, Abba juyawa ya yi yana kiran sunan Aisha ya ce "Mommyna ina zaki?." Aisha bata tanka ma Abba ba ta tafi da sauri. Abba juyawa ya yi ya bi Aisha, shan gaban Aisha ya yi ya ce "Mommyna lafiya ina zaki." Aisha da dama kiris kawai take jira ta fashe da kuka. Abba da mamaki ya bi Aisha da kallo ganin yadda take kuka, Abba cikin sanyi ya ce "Mommyna me ya faru?." Aisha banza ta yi da Abba, ta Kuma juyawa zata tafi, Abba hannun Aisha ya kamo ya ce "idan gida zaki ki tsaya in samu wani ya kaiki a mota." Abba ya fadi maganar yana Kira a wayarsa, sunanan tsaye saiga Wanda ya Kira ya karaso, Abba nuna mai Aisha ya yi ya ce "Bilya ka Kai Mommyna gida." Yana fadin haka ya juya ya tafi. Mansura Kuma tana nan inda Abba ya barta tsaye, Abba na karasowa inda take ya kalleta ya ce "Muje." Da yake hankalin mutane duk suna kan Amarya da ango dake tsakiyar hall din hakan ya sa mutane basu lura da shigowar Mansura da Abba ba, Abba bindir din dari biyu ya diba ya ba ma Mansura ya ce "Kima Amarya da ango liki." Yana fadin haka ya saki hannun Mansura ya yi wajan Amarya da ango Yana masu liki. Mansura ma tashi ta yi ta je ta lika masu kudin da Abba ya bata. An dade ana gudanar da hidimar bikin sai 11 kafin aka tashi suka dibi kawayan Amarya da sauran iyaye da basu tafi ba aka maida kowa gidansu Amarya. Aisha ko misalin karfe 8 ta koma gida tana zuwa ta nufi dakinta tana kuka. Mahaifiyar Aisha tsaye ta yi kan Aisha tana kallanta, Wanda ita Aishar ma bata lura da mahaifiyarta dake tsaye kanta ba. Mahaifiyar Aisha cikin daga murya ta ce "Ke Aisha lafiya meke damunki kike kuka haka?." Aisha dago kanta ta yi tana kallan mahaifiyarta ta ce "Malama, dan Allah ku janye maganar aurena da Yaya Abba." Aisha ta idasa maganar tana goge hawayanta. Malama zama ta yi gefan katifar kusa da Aisha, ta dade tana kallan Aisha kafin ta ce "Saboda me za a janye maganar auranku? Laifin me ya yi Miki?." Aisha gyara zamanta ta yi ta ce "Malama Yaya Abba zai aureni ne bisa umarnin mahaifiyarsa bawai dan Yana Sona ba, yana da wadda yake so, ki yi hakuri Malama rannan karya na yi Miki da nace miki Yana kirana muna chart na fadi haka ne kawai tunanin ko zai canza, Amma yanzu na gama tantance baya sona ba tani ma yake ba, ko na auresa bakin ciki kawai zan kwasa." Shiru Malama ta yi dan tuni ta fahimci haka, sannan tunda Aisha ta fito ta furta haka tasan tana da babban dalilinta. Malama kallan Aisha ta yi ta ce "Aisha, kin riga kin makaro da kika boyemin gaskiya tun farko, kina ganin yanzu zan iya tunkarar mahaifinki da maganar nan ne in ce mai bakya son Abba, ba zaima sauraran ba, dan haka ki yi hakuri kawai kita addu'a." Malama na gama fadin haka ta tashi ta fita ta ba Aisha waje. Ita ko Aisha abin da ya Kuma ta fasata ta tabbatar Abba baya sonta ganin ta tafi tana kuka Kuma baidamu yasan damuwarta ba, sannan ko ya kirata, abin da ya kamata yadda ya barta tana kuka ace ya kirata. Amina ko taron mutane da yawa hayaniya ta yi yawa shi ya sa bata lura Aisha ta tafi gida ba. Bayan su Aisha sun dawo gida daga wajan partyn, Amina kallan Mansura ta yi ta ce "Mansura kinsan Allah dazu a wajan partyn nan da aka ce keda Yaya Abba za ku bude fili har kosawa na yi inga Dj ya sa maku waka, inga yadda za ku yi, abin mamaki wai sai ga yaya Abba yana rawa, abin nikam na rasa yadda za ai ya bar ban mamaki." Mansura tashi ta yi ta zauna ta ce "Ni Wallahi kunya ma na ji da farko, ke kece fa baki lura ba tun a cikin mota lokacin da za mu tafi wajan fatin yake rawa baya sa wata waka ba, tun a nan ya fara rawarsa." Amina rike baki ta yi ta ce "Shi ya sa Yaya Abba akwai zuwa biki ai, Amma nikam na sha mamaki, Kuma Allah baki ga abin ba Kun bada kala fa, sai kuka yi kamar wasu Masoya." Mansura hararar Amina ta yi bata ce komai ba. Amina dai gudin karsu yi fada da Mansura cikin daran nan ya sa ta ja bakinta ta yi shiru ba ta Fadi abin da ke ranta ba. A haka barshi ya kwashesu. Washagari da wuri aka fara Shirin tafiya da amarya, dan abokan angon dama duk suna nan basu tafi ba. Da wuri mai yima Amarya makeup ta zo ta ta yi mata, aka nada Mata jar lifiya da ta ji adon stone daga wajan kan, sosai Amarya ta fito ta yi kyau. Mansura ko tun dazu jikinta ya yi sanyin rabuwa da Aminiyarta, hakan ya sa ko wankan ta kasa yi. Aunty Zainab da shigowarta kenan, kallan Mansura ta yi ta ce "Haba Mansura kina jin ance 10 za a tafi da Amarya Amma kallarki ko wanka ba ki yi ba." Mansura kanta kasa bata dago ba, Aunty Zainab hannun Mansura ta kamo ta rakata har bakin bathroom din kafin ta juyo. Mansura bayan ta fito babu yadda mai makeup din ba ta yi da ita ba ta yi Mata amma Mansura taki, dole ta rabu da ita ta. Amina 9:30 aka shiga da ita bangaran da iyayanta maza suke, wato kannan babanta su yi Mata nasiha. Sun dade suna Mata nasiha akan zaman aure da ankarar da ita akan mahimmanci dake tattare da hakuri, tun a nan Amina ta fara kuka. Aunty Zainab hannunta ta kama ta shiga da ita bangaran mahaifiyarsu, mahaifiyar Amina ma kukan take, Amina ganin haka sai ta kara azzaza kukanta. Sun dade kowa ya kasa cewa komai iyayan Amina Mata, su Abba ko suna waje kawayan Amarya da wasu daga cikin iyayan Amarya duk sun shiga mota Amarya kawai ake jira a tafi. Abba cikin jin haushi ya shigo gidan har falon mahaifiyar Rashi ya karasa inda sun tasa Amina sun taru kusan sai kuka suke, masu yin maganar kadan ne. Abba kallan Aunty Zainab ya yi yayar Amina wadda Amina ke bimawa ya ce " Zainab wai meye haka ne." Agogon hannunsa ya kalla ya ce "Kalli dan Allah 11:15AM, muda muka so tafiya tun 10. Aunty Zainab iyayanta ta yi ma magana akan su tashi su tafi ana jiransu. Amina suka dakko wadda ke aikin kuka tana rirrike mahaifiyarta, shi kanshi Abba sai ya ji jikinsa ya yi sanyi, Amina Kuma ganin Abba da sauri ta rungumesa tana kuka. Abba hannun Amina ya kama tare da sauran iyayanta da zasu tafi suka fita, da yake a motarsa zai dauki Amarya. Kasan cewar ya bar gidan gaba ne da a matsayin wajan da Mansura zata zauna, gashi Bata, Kuma Yana lure babu ita gaba daya motocin. Abba shiru ya yi dan baisan wa ma zai tambaya ba Ina take. Wayar Amina ya Kira ya ji ringing dinta a jakarta. Abba kallan Aunty Zainab ya yi dake kusa da Amarya ya ce "Zainab Ina Mansura ne, ta fito mu tafi Mana gashi har an fara tafiya." Sai yanzu Aunty Zainab tatuna da Mansura tashi ta yi ta ce "Laa ka ka ga namanta da antafi an barta." Zainab bangaran Abba ta nufa, kwance ta iske Mansura sai kuka take. Auny Zainab tsaye ta yi kan Mansura tama rasa abin da zata ce Mata. Hannun Mansurar ta kama ta ce "Shi kenan ki yi hakuri ya isa haka, tashi mu tafi ke ake jira." Mansura tashi ta yi ta rufe kanta da mayafinta kamar wata Amarya a haka suka karasa wajan motar da Aunty Zainab, Aunty Zainab da kanta ta bude ma Mansura motar ta shiga, kafin itama ta zagaya ta shiga. Suna shiga Abba ya ja motar suka tafi. Abba kallan Mansura ya yi da har yanzu ba ta yi shiru ba, ya ce "Ki yi shiru Mana, kanki fa zai iya ciwo." Aunty Zainab kallan Mansura ta yi ta ce "Mansura ba za ki yi shirun ba sai kanki ya yi ciwo kenan." Mansura da kyar ta lallaba kanta ta yi shiru daga nan barci ya dauketa. 3:00PM Abba suka shiga cikin gidan Ahmad dake cikin garin Kaduna. Yan'uwan Ahmad tarba mai kyau suka yi ma kawayan Amarya da yan'uwanta. Bayan an ci ansha sun huta, dangin Amarya suka shirya lafiyayyar walima a gidan Amarya. Sosai Walimar ta kayatar saboda ta hada da Amarya da ango kamar yadda ta zo a musulinci, an fadi hakin Mata akan miji, an Fadi hakin miji akan Mata, sai gaf magariba aka tashi daga walimar. Amina ba ta tashi lura Aisha bata zo ba sai dare, duk suna zaune suna hira ta lura Aisha ba ta zo ba. Amina sosai fargaba ta kamata dan tasan Aisha ta yi fushi ne. Amina suna zaune suna hira Abba ya Kira wayarta lokacin 8:30PM, banji mai Abba ya ce ba sai ji na yi ta ce "Bari in fada Mata." Amina kallan Mansura ta yi ta ce "Saurayinki na Kira." Mansura da yake tasan Abba Amina ke nufi hakan ya sa ta ce "Wallahi ban fita tun da kikace haka." Amina ido ta zaro ta ce "Ki rufa min asiri karyace ban fadamiki ba, dan Allah ki je." Da kyar Amina ta samu Mansura ta fita. Mansura can harabar gidan ta hango Abba tsaye a jikin motarsa yana danna wayarsa. Mansura da sallama ta karasa inda Abba yake. Abba dagowa ya yi Yana kallan Mansura yana murmushi ya ce .... ✍🏻 Karku manta bana update weekend, sai mun hadu Monday in sha Allah. Littafin ABBANA na kudi ne 400 kafin a gama free pages my number 08063830828 ⭐ ABBANA ⭐ 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚* Domin samun littafin ABBANA daga farko 👇🏻Follow the ABBANA channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaYZGsNEFeXsr1CKQl3r P 31-32 Abba dagowa ya yi yana kallan Mansura Yana murmushi ya ce "Ke ce farko, Kuma ki ce karshe, bishirnan mai girma wadda da kikai minni dashe, bana ji bana gani bana son mai kushe, burina in rayu da ke har numfashin ƙarshe...." Mansura rufe ido ta yi tana murmushi ta ce "Yaya Abba da alama kana son wakar nan?." Kai Abba ya girgiza ma Mansura ya ce "Ni ba waka na yi ba, sirrin dake cikin zuciyata na fada." Mansura da bata gane abin da Abba yake nufi ba ta ce "Yaya Abba wakace sirrin zuciyarka." Kai Abba ya girgiza ma Mansura. Mansura shiru ta yi dan bata gane abin da yake nufi ba, hakan ya sa ta wuce maganar ta ce "Yaya Abba Amina ta ce kana kirana gani." Abba kallan Mansura ya yi ya ce "Gaki, irin in baki abin da zan baki ki wuce ko?." Mansura Kai ta daga ta ce "Dare fa ya yi Kuma na gaji, sannan barci nake ji." Shiru Abba ya yi baice komai ba ya zuba ma Mansura idanu. Ya jima Yana kallanta kamar hoto, Mansura baki ta turo ta ce "Ni dai Yaya Abba Allah zan tafi." Ki tafi ai na baki sakon." Abba ya fada yana kallan Mansura. Mansura ido ta zaro ta ce "Kaban sakon Kuma? Yaya Abba Wana sako?." Shiru Abba ya yi kafin ya ce "Da farkon zuwanki wajan nan me na ce?." Shiru Mansura ta yi da alama tana son ta tuna Abin da Abba ya ce, sai zuwa can ta ce "Yaya Abba baka ce komai ba, waka ka yi fa." A wakar me na ce?." Mansura bata fuska ta yi alamun ta gaji da tambayoyin kafin ta ce "Tom ai ni ban iya wakar ba." Shi kenan zan tura ma Amina wakar ta WhatsApp ki ce mata ta baki ki ji sakona ne zuwa gareki." Mansura murmushi ta yi ta ce "Yaya Abba sakon waka?." Eh, ki je ki ji gobe ma yi magana akai, sai da safe." Abba yana tsaye sai da ya ga shigewar Mansura kafin ya koma part din Ahmad inda zasu kwana tare da Ahmad. Mansura lokacin da ta shiga Amina na waya da ango, ta shiga ba jimawa suka yi sallama inda shima bangaran angon abokin hirarshi wato Abba ya shigo. Amina kallan Mansura ta yi ta ce "Aunty Mansura kin dawo." Eh, na dawo Aunty Amina ya aka yi?." Cewar Mansura. Amina baki ta rike ta ce "Wallahi Aunty Mansura bakinki ya fara budewa fa." Mansura hararar Amina ta yi. Kiran da akai ma Amina a waya ya sa ta fasa fadar abin da zata fada, Amina daga Kiran ta yi tana saurar abin da yayan nata ke cewa, da "Okay bari in duba." Amina WhatsApp ta hau tana bude data sakon Abba yana shigowa. Amina kallan Mansura ta yi tana murmushi ta ce "Aunty Mansura Yaya Abba ya turo miki sako ya ce abaki." Amina playing wakar ta yi, tare da Mansura suka saurari wakar har ta kare. Amina kallan Mansura ta yi ta ce "Wani abun sai Masoya, Allah sarki sai na tuna soyayata da Yaya Ahmad, ranar da zai fara furta min kalmar so wata waka ya tura min ta Auta MG boy, labari a zuciya ke ce soyayyace taki ta yi tasiri 'yan mata. Kinsan Allah lokacin sai da ya zamana babu wakar da nake so kamarta, da ita Yaya Ahmad ya bayyana min kalmar so ba da bakinsa ba." Mansura shiru ta yi jin kalaman Amina, hakan ya sa ta dago idanunta ta suka fara tara kwalla ta ce "Amina idan na fahimci abin da kike nufi kina nufin nima Yaya Abba ya sanar min da sakon soyayyarsa ne dawakar nan?." Shiru Amina ta yi, kafin ta ce "Mansura bahaushe ya ce wai ido ba mudu ba amma yasan kima, yanzu ki a shekarunki ba za ki iya fahintar in Namiji na sonki ba? Tom zan sanar miki da abin da yaya Abba ke ƙoƙarin fada Miki ta waka ni zan fassara miki abin da yake nufi. Mansura Yaya Abba ya kamu da soyayyarki mai tsanani Wanda Ina jin shi kanshi bai san yaushe ya fara ba, amma Yana miki so mai girma wanda ya kasa boyuwa a cikin kwayar idanunsa..." Shashshekar kukan Mansura ya sa Amina ta dakata, ta tsaya tana kalan Mansura, Amina kallan Mansura ta yi damamaki ta ce "Me ye abin kuka aciki." Mansura kallan Amina ta yi ta ce "Nima ban Sani ba, ji na yi kawai Ina kukan." Kai Amina ta girgiza ta ce "Ki rika addu'a kin ji Mansura, Allah zai miki maganin koma meye, yanzu idan Yaya Abba ya tambayeki kin amshi ta yin soyayyarsa wata amsa zaki bashi?." Mansura cikin sanyi ta ce "Ni ba zan yi aure ba." Kai Amina ta girgiza ta ce "Ba wannan na tambayeki ba, shima ba maganar aure ya yi ba maganar soyayya wadda take kaiwa matakin aure ya yi, me za ki ce mai?." Amina ta fada tana kafe Mansura da idanunta. Mansura kasa ta yi da Kai kafin ta ce "Bansan me zancemai ba Amina." Shiru Amina ta yi kafin ta ce "Mansura kina son Yaya Abba?." Mansura Kai ta dago tana kallan Amina wadda itama ita take kallo, Mansura cikin sanyi ta ce "Ban Sani ba." Murmushi Amina ta yi ta ce "Mansura ni macece matashiya kamarki, zan iya yadda da furucinki wata soyayyar takan dade a zuciyarka kafin ka fahimci irinta, kai Karan kanka bare Kuma Wanda yake sonka, shi ya sa wata soyayyar sai ki ji cikin masoyan wani na cewa nakasa gane kan wance, alhalin ita kanta ma har yanzu ta kasa gane kan ainihin zuciyarta, idan na Fadi haka a wani wajan ana karyatani ace wai kana sanin sirrin zuciyarka, ni Kuma nasan zuciya ba ko yaushe take ba mai ita damar sanin sirrinta ba, dan haka na fahimceki na taba riskar zuciyata a matakin nan. Yanzu idan Yaya Abba ya ce ki fadi Mai amsar tambayarshi ki yi amfani da kalar salonsa ki bashi amsa, Ina da wata waka zan baki ki bashi amsa da ita kema." Mansura kallan Amina ta yi ta ce "Da wata wayar?." Amina murmushi ta yi ma Mansura ta ce "Kin manta Yaya Ahmad ya sa min waya a lefe, da ita zan fara amfani zan baki wayata ki tafi da ita ta rika tayaki hira inda kin zabi zaman gida."Na gode." Mansura ta ce. Amina sun jima suna fira da Mansura kafin suka kwanta. Washagari Abba ya Kira wayar Aunty Zainab ya sanar da ita su shirya da wuri, hakan ya sa Aunty Zainab da wuri suka tashi suka Kara gyagygyara dakin Amarya, suna cikin gyaran ne Abba ya da sauran abokan Ahmad da zasu maidasu gida suka zo, Abba fada ya yi ganin duk basu gama shiryawa ba, haka dai suka shirya da sauri-da sauri suka tafi. Lokacin da suka gama shiryawa za su rafi Amina rungume Mansura ta yi tana kuka taki sakinta, haka suka rungume juna suna kuka, Aunty Zainab da Hassana kawar Amarya babu yadda ba su yi ba amma sunki sakin juna. Abba jin shiru bayan sunce gasu nan fitowa number Aunty Zainab ya Kira Yana fada, Aunty Zainab cikin sanyi ta ce "Yaya Abba ya zanyi dasu gasu sun rungume juna mun yi munyi sunki sakin juna." Abba tsaki ya yi ya kashe wayar ya shigo har falon Aminar, Abba da kyar ya samu ya banbare Mansura jikin Amina, Mansura kuka take har da Majinarta tana "Wayyo Yaya Abba niba zan tafi ba ku barni." Sosai Mansura da Amina suka ba mutane tausayi, dan da yawansu sun san babu dadi irin rabuwar nan. Abba cikin lallashin Mansura ya ce "Ki yi hakuri ba za a jima ba zan kawo ki wajanta.". Abba na rike da Mansura dake rusa kuka a haka har suka karasa wajan motasa ya bude Mata ta shiga kafin ya zagaya ya shiga suka tafi. Sun yi nisa da tafiya har lokacin Mansura bata bar kuka ba. Su Aunty Zainab ne sukaita bata baki a haka suka samu ta hakura ta yi shiru. Da yake Basu fito garin da wuri ba hakan ya sa gaf La'asar suka shiga garin Katsina. Suna zuwa Mansura da tun a hanya kantake Mata ciwo na kukan da ta yi suna shiga ta ruga bangaransu da sauri tana kuka, mahaifiyar Mansura Kai ta girgiza ta ce "Dama ni nasan ai za a yi haka." Uhmm, mama danma baki ga yadda aka rabasu da Amina ba, Kinga yadda suka rike juna da kyar aka rabasu, Aminar ma can muka barota tana aikin kukan." Cewar Aunty Zainab. Kai Mahaifiyar Amina ta jinjina ta ce "Ni dama nasan za a yi haka." Haka dai Aunty Zainab taita ba mahaifiyar Amina labarin tarbar arziki da dangin Ahmad din suka yi masu, Aunty Zainab ta ce "Gaskiya mama Amina ta yi sa'ar dangi miji idan har zasu dore da abinda muka gani, sai dai mu yi mata fatan zaman lafiya Kuma." Mahaifiyar Amina sosai ta ji dadin maganar da Aunty Zainab ta yi hakan ya sa ta ce "Tom Allah ya daurar da kauna a tsakaninta da su da Kuma Ahmad din baki daya. Allah dai ya sa kun Kara jamata kunne da zaku taho duk da Amina bata da matsala." Ai mama Amina ko fada suka yi da Ahmad ni zan iya cewa laifinsa ne, yarinyar da batasan fushi ba, ba ta dauki rayuwar duniya komai ba ai Kar ki ji komai mama indai akan Amina ne." Lumshe ido Mahaifiyar Amina ta yi, tsabar jin dadin yabar Aminarta da Aunty Zainab ta yi ta ce "Tom Zainab ina rokan Allah Allah ya sa Amina ta ci gaba da tafiya kamar yadda muka Santa karta canza". Ameen mama." Aunty Zainab sun dade suna hira da mahaifiyarta. Bangaran Mansura ko Aunty Zainab ganin har an yi magariba Mansura bata fito ba hakan ya sa Aunty Zainab ta shiga wajan Mansurar da tea a hannunta,. Zaune ta iske Mansurar kan abin Sallah da alama bata jima da idar da Sallah ba, ta yi shiru ta yi ta gumi daga ganinta ta yi nisa a duniyar tunani. Aunty Zainab zama ta yi tasa hannunta daya ta cire tagumin da Mansura ta yi. Sai yanzu Mansura ta dago tana kallan Aunty Zainab. Aunty Zainab kallan Mansura ta yi ta ce "Dauki tea din kisha ga biscuits naga alama kema Amina ta koya miki shan tea da biscuit." Mansura yake ta yi ma Aunty Zainab kafin ta dauki tea din tana sha kadan-kadan a haka ta shanye. Aunty Zainab kallanta ta yi ta ce "In kawo miki tuwo Kinga tun safe rabonki da abinci." Mansura Kai ta girgiza ta ce "Na koshi." Jinjina Kai Aunty Zainab ta yi ta yi shiru tana kallan Mansura kafin ta ce "Mansura dan Allah karki sama ranki damuwar rashin Amina, haka dama ita rayuwar 'yamace ta gada, kema watarana haka zamu kaiki mu baroki Kuma dole zamu yi hakuri, daga kin yi hakuri a hankali za ki Saba, zan yima Yaya Abba magana kema ya Samar maki ko teaching dinne ya rage miki zaman kadaici." Aunty Zainab ta dade tana ma Mansura nasiha kafin ta fita ta barta. Aunty Zainab na fita Kiran Amina Amarya ya shigo wayar da tabar ma Mansura. Mansura bin wayar ta yi da kallo ganin sunan dake jikin layin my bea, Mansura daga Kiran ta yi ta ce "Lafiya Lau muka iso, ya muka barki?." Shiru Mansura ta yi da alamar Amina take saurare kafin ta ce "Tom ma Sha Allah ki gaida min Yaya Ahmad din." Bayan Amina ta kashe wayar Mansura tashi ta yi ta tada sallar issha'i, tana idarwa ta kwanta, tana kwantawa ko barci ya kwasheta. Bangaran Abba kasan cewar yasan wayar Amina na hannun Mansura ta bar Mata, hakan ya sa bayan ya yi shirin kwanciya ya Kira layin Amina dan yasan in ba sa'a ba Mansura nacan na kuka, saidai ya yi Kira harta katse ba a daga ba, sake Kira ya yi nanma haka, sai da ya yi ma Mansura Kira 5 Bata daga ba, kafin ya hakura ya kwanta yana tunanin kila ta yi barci ne. Washagari da wuri yan biki aka fara watsewa, zuwa a zahar ya zamana gidan babu kowa duk sungama tafiya sai Aunty Zainab kadai, itama mijinta anayin magariba ya zo ya dauketa suka tafi ya zamana sai Mama da Mansura kadai a gidan. Mansura ko washagari kota kan wayarta bata biba dan ta farka da ciwan Kai dan har sai da Aunty Zainab ta sa aka siyo Mata Panadol. Hakan ya sa kusan kwance ta wuni. Abba Kuma da yake yana wajan aiki hakan ya sa ya shiga busy sai dare ya dawo gidan, kallan mahaifiyarsa ya yi ya ce "Mama taro ya tashi kenan." Bari Abbana, taro ya tashi lafiya ma sha Allah." Abba sun jima suna hira da mahaifiyarsa har ya ci abinci Amma baiga fitowar Mansura ba, hakan ya sa ya ce "Mama na ganki ke ka dai Ina yarinyar nan fa?." Mansura, tana can kila kwance, ni banta ba ganin Wanda baya gajiya da kwanciya ba kamar yarinyar nan." Shiru Abba ya yi kafin ya ce "Wai mama kina nufin duk yau kwance ta wuni ko falon nan bata fito ba?." A'a, ta fito lokacin da Zainab zata tafi." Abba shiru ya yi baice komai ba, kafin ya tashi ya fita, yana fita ya Kira number Mansura, harta katse bata daga ba, sake Kira ya yi nan ma shiru ba a ta yi picking ba. Abba tafiya ya yi yana tunanin dalilin kin daga Kiransa da Mansura ta yi. Abin da ko baisani ba Mansura bata kusa ta shiga wanka. Bangaran Aisha sosai take cikin damuwar rashin ganin Kiran Abba a wayarta, hakan ya Kara tabbatar mata Abba ba ta ita yake ba, dan a ganinta ko yadda ta bar wajan party ya kamata ace ya kirata ya tambayi lafiyarta, haka Kuma Bata je Kai Amarya ba nanma a ganinta ya kamata ya Kira ya ji dalilin rashin zuwan nata, Amma shiru, hakan ya sa ta yanke ma kanta shawarar hakura da Abba, Amma Kuma ta sanar da mahaifiyarta ta ce bata isa ba, hakan ya sa Aisha ta kudiri aniyar sanar da mahaifiyar Abba, dan bata jin zata iya auran Wanda baya sonta. Aisha text ta tura ma mahaifiyar Abba kamar haka. "Assalamu alaikum, mama Ina wuni, ta fatan an tashi taro lafiya. Mama dan Allah kisa baki nasan Malama zata ji maganarki, na fasa auran Yaya Abba, na fada ma Malama taki yadda." Mahaifiyar Amina ba ita taga sakon Aisha ba sai da ta idata idar da sallar asuba. Sosai sakon furucin Aisha ya data Mata hankali, hakan ya sa ta kira Aisha a waya, mahaifiyar Amina cikin sanyi ta ce "Aisha yanzu naga sakonki, ko zaki fadamin dalilinki?." Aisha cikin sanyi ta ce "Mama Wallahi Yaya Abba baya Sona zai aureni ne kawai bisa umarninki." Shiru mahaifiyar Amina ta yi dan tarasa abin da zatace, hakan ya sa ta yi shiru ta ce "Shi kenan Aisha zan kiraki." Bangaran Abba ko duk ya kasa sukuni na rashin samun Mansura a waya da ya yi. Kamar yadda ya saba idan ya yi shirin tafiya aiki yana zuwa su gaisa da mahaifiyarsa. Yau Abba Koda ya shigo ya gaida mahaifiyarsa bata kallesa ba bare ta amsa mai. Abba shiru ya yi yana kallan mahaifiyarsa. Mahaifiyar Abba wayarta dake kusa da ita ta mikama Abba. Abba amsa ya yi ya karanta sakon Aisha, bayan ya gama karanta text din dagowa ya yi yana kallan mahaifiyarsa ...✍🏻 Littafin ABBANA na kudi ne, 400 kafin in gama free pages daga na gammala zai koma 500 my number 08063830828 Fadila Sani Bakori ce. ⭐ ABBANA ⭐ 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚* Domin samun littafin ABBANA daga farko 👇🏻Follow the ABBANA channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaYZGsNEFeXsr1CKQl3r P 33-34 Abba amsa ya yi ya karanta sakon Aisha, bayan ya gama karanta text din dagowa ya yi yana kallan mahaifiyarsa. Mahaifiyar Abba cikin damuwa ta ce "Abba abinda zaka sakamin dashi kenan? Dawana ido kakeso in kalli Malama? Na baka nan da kwana biyu ka yi gaggawar daidaita tsakaninka da Aisha ta yanje kudirinta. Abba shiru ya yi kafin ya ce "In Sha Allah mama." Yana fadin haka ya tashi ya fita, Yana fita ya Kira number Mansura nanma bata daga ba, abin tsoro ya ba Abba gashi ya kasa tambayar mahaifiyarsa Mansura ganin yadda suke. Abba kallan bedroom din da Mansura da take ciki ya yi, tafiya ya yi ya tura kofar dakin Mansurar, Allah ya taimakesa kofar babu key a jiki ya tura ya shiga. Abba kallan Mansura ya yi da ta lillibe ilahirin jikinta da bargo, Abba tsaye ya yi yana kallanta, kafin ya sauke ajiyar zuciya ya matsa wajan gadon, bubbuga kafar Mansura ya yi, Mansura cikin barci ta ji ana taba mata kafa, Mansura bude ido ta yi tana kallan Abba dake tsaye akanta. Mansura tashi ta yi tana mutsika ido, tana kallan Abba. Abba cikin sanyi ya ce "Kin yi sallah?." Kai Mansura ta girgiza alamun A'a. "Tashi ki je ki yi Sallah." Mansura sauka ta yi kan gadon ta shige bathroom da sauri, babu jimawa ta yi alwal ta fito ta zo ta tada Sallah. Abba zama ya yi bakin bed din yana jiran ta idar da sallar. Mansura bayan ta idar da sallar, juyowa ta yi tana kallan Abba, kafin cikin sanyi kanta kasa tana wasa da hannunta ta ce "Ina kwana yaya Abba." Abba kallan Mansura ya yi ba tare da ya amsa gaisuwarta ba ya ce "Me ya sa kika ki daga kirana?." Mansura waige-waige ta fara nanaiman wayarta ta ce "Namanta da wayarne ban gants bama." Tashi ki duba wayar." Abba ya fadi maganar babu annuri a fuskarsa. Mansura tashi ta yi tanaimi wayar, Mika ma Abba wayar ta yi, Kai Abba ya girgiza ya ce "Duba ki gani Kira nawa na yi miki." Mansura dubawa ta yi kafin ta juyo da kallanta ga Abba ta ce "Yi hakuri Yaya Abba Banga Kiran bane." Abba tashi ya yi ya ce "Okay, ki ajeta kusa." Yana fadin haka ya tashi ya fita. Mansura da kallo ta bi Abba har ya fita, ganin yau yadawo mata ainihin Abban da ta sani. Abba ko yau Koda ya je aiki ya kasa komai saboda damuwar nauyin da mahaifiyarsa ta daura mai. Abba zaune yake a office dinsa ya kasa komai, so yake ya Kira Number Aisha amma ya kasa, dan gaba daya sai ya ji ta Kara fita ransa, Abba number Mansura ya Kira Kira daya ta daga. Abba cikin muryarsa mai bayyana yanayin damuwa ya ce "Assalamu alaikum, amincin Allah ya tabbata ga zuciyar da ta hana zuciyar Abba sukuni." Ya fadi maganar cikin rashin walwala. Mansura shiru ta yi, kafin ta ce "Tare da Kai Yaya Abba." Abba kuma ya ci gaba da cewa "Man's Ina cikin damuwa." Abba ya fada cikin damuwa. Mansura cikin alamun tausaya masa ta ce "Ayyah Yaya Abba me ya saka a damuwa?." Mama ce ta sani a damuwa Mansura." Mansura da alamun mamaki ta ce "Mama Kuma? Yaya Abba yadda mama ke ji dakai nasan ba za ta sa ka a damuwa ba, saidai in baka fahimci mama bane." Shiru Abba ya yi jin Abin da Mansura ta ce, ya ji ma baice komai ba, kafin ya ce "Man's kinsan ansamin ranar aure da mommy? To ta tura ma mama text cewa ta fasa aurena, amma mahaifiyarta taki yadda tana so mama ta je ta sa Mata baki mahaifiyarta ta amince tasan maganarta kadai zata ji, tom shine mama take ganin laifinane ya sa tace ta fasa auran, taban nan da kwana biyu in daidaita tsakanina da ita, na rasa yadda zan yi man's" Mansura shiru ta yi dan bata san me za ta ce ma Abba ba. Abba jin ta yi shiru ya ce "Man's ke fa nake saurare." Mansura cikin rashin sanin abinda zata ce ta ce "Yaya Abba ka yi abinda mama tace Mana." Tom ni ai bana sonta, akwai wadda nake so." Daga can bangaran Mansura ta ce "Yaya Abba, ita wadda kake son tana sonka?." Abba shiru ya yi, kafin ya ce "Ban Sani ba, amma dai na yi ma kaina alƙawarin dolanta ma ta soni." Ido Mansura tazaro ta ce "Yaya Abba ana soyayya dole ne? Idan takika fa?." Sai in makata kudi kawai." Mansura dariya ta yi bata ce komai ba. Abba jin Mansura ta yi shiru ya ce "Ya wakar nan da na tura Miki kin jita kuwa?." Mansura tana so ta cema ma Abba a'a amma Kuma ba ta iya garya ba, hakan ya sa ta ce "Na ji." Ido Abba ya lumshe kafin ya ce "Ina so ki Kara jinta, anjima idan na dawo za mu yi magana akan wakar." Kai Mansura ta daga kamar Abba na kusa da ita. Abba bayan ya gama waya da Mansura ji ya yi kamar anwanke mai duk wata damuwa dake damunsa, hakan sai ya bashi kwarin gwiwar Kiran Aisha. Aisha ba ta daga ba sai da ya sake Kira, kafin ta daga tare da sallama cikin sanyinta. Abba cikin salon yaudara dan Aisha ta janye kudirinta kamar yadda mahaifiyarsa ta umarcesa da ya sasanta tsakaninta da ita nan da kwana biyu ya sa Abba ya ce "Mommyna, laifin me na yi kika fasa aurena?." Aisha shiru ta yi kafin ta ce "Yaya Abba naga kamar baka sona ne shi ya sa." Kamar bana sonki, Mommyna da bana sonki da ba zan aminta da auranki ba, wayace miki anayima Namiji auran dole Mommyna haba, Yama za ai in ki son mommyna sai ka ce danbanza." Aisha dariya ta yi da yake zuciyar da ta kamu da so bata da wuyar yafiya ga masoyinta hakan ya sa Aisha gaba daya ta manta da furucinta da ta yi ta fara ganin gangancinta da wautarta ta ce "Shi kenan Yaya Abba, Ina tuba na janye kalamaina masu cike da tarin wauta." Abba cikin jin dadin furucin Aisha batare da yasha wuya ba ya ce "Yauwa Mommyna, yanzu yaushe za ki zo yi ma mama bangajiyar biki danni da ita mu shaida da kin janye maganarki?." Aisha murmushi ta yi ta ce "Umarninka kawai nake jira, ko yanzu ka ce min in je ashirye nake." Abba tabe baki ya yi ya ce "Ki bari sai weekend Kinga Ina gida lokacin." Abba sun jima suna waya da Aisha kafin ya yi Mata sallama da karyar in ya tashi aiki da wuri zai zo ya ganta. Abba bayan ya koma gida, falon mahaifiyarsa ya yi direct, sai dai yana magana tana dauke Kai, sallamarsa ma ciki-ciki ta amsa mai. Abba murmushi ya yi ya ce "Mama akan wata kike fushi da Abbanki, mai sunan mahaifinki." Mahaifiyar Abba hararar Abba ta yi ta ce "Akan Aisha ai Wallahi har falon nan ka kusa bar shigowa, nifa bawai na ce dole ka auri Aisha bane, alokacin da na yi maka maganarta sai ce min ka yi koma baka ganta ba inda ta yi min shikenan, Amma duk da haka ban yadda na yanke hukunci ba sai da ka je ka ganta ka amsa ta yi maka sannan na tura iyayanka, sai yanzu Kuma ka zo ka sani a kunya, tom Wallahi baka isa ba." Abba dariya ya yi ya ce "Mama inda mommy ce tuni muka shirya, dan ta sanar dani ma zata zo yi miki bangajiyar biki." Mahaifiyar Abba shiru ta yi tana kallan Abba, kafin ta ce "Abba dan Allah Annabi ka taimakeni ka fiddani a kunyar uwar yarinyar nan, kana ganin hidimar da ta yi abikin Amina, kasan ba dan itaba ba zamu ga malamai da damaba a wajan walimar nan." Abba kansa ya shafa yana sauke ajiyar zuciya ya ce "In Sha Allah mama zan auri mommy." Abba, bawai ka aureta kadai bane damuwar, ka sota, ka bata kulawa wadda duk wata 'ya mace take bukata, idan ka yi min haka ka gama min komai Wallahi." Abba hannun mahaifiyarsa ya kama ya ce "In sha Allah zan yi ƙoƙarin haka mama." Abba wayarsa ya dauka ya tura ma Mansura text kamar haka "Gani a falon Mama ki fito." Mansura bayan ta gama karanta sakon murmushi ta yi ta maida mai kamar haka. "Yaya Abba yanzu na bar falon, Kuma na yi ma mama saida safe." Abba bayan ya gama karanta sakon Mansura wani ya tura Mata kamar haka "Bana son musu idan kika dawo yanzu korarki za ta yi ki ce kin je kin kasa barci." Mansura bayan ta gama karantawa tashi ta yi ta fito. Abba kamar ba yanzu suka gama chart da Mansura ba dauke Kai ya yi. Mansura zama ta yi tana gaida Abba. Abba kallan mahaifiyarsa ya yi ya ce "Mama kullum idan na shigo bana samun Mansura a falon nan, na ce tana tayaki girki ma kuwa?." Mahaifiyar Abba murmushi ta yi ta ce "A'a ai har yanzu kewar kawarta bata saketa ba." A'a, Mama daga yau ta rika fitowa tana tayaki aiki itama ta huta zaman shirun da takeyi , Ina so ma in Samar Mata teaching a school din da Amina ta yi ta huta zama shirun." Mansura turo baki ta yi jin abinda Abba ya ce ta ce "Yaya Abba ni dai banaso." Abba da mamaki ya kalli Mansura ya ce "Shi kenan, akwai computer training in kina so?." A'a, Ni dai bana son komai." Mahaifiyar Abba dariya ta yi ta ce "Shi kenan Abba inda bata so karka takura mata." Abba daga nan baikuma cewa komai ba ya tashi ya fita. Bangaran Aisha da safe tana zaune ta turama Abba Sako na barka da safiya. Abba na wajan aiki ya ci karo da sakon Aisha kamar haka "Barka da Safiya Habibina da'ima. Na farka cikin wallawa, saboda kasancewarka a rayuwata. Ina addu'a Allah ya sa ka soni Koda rabin Wanda nake yi maka ne. Daga Masiyarka mai kaunarka har abadan abidina." Abba copy din text din Aisha ya yi bayan ya gama karantawa ya gyara ya tura ma Mansura. Abba replying a yi ma Aisha kamar haka "Na gode da kulawarki amaryata." Bangaran Mansura ko Koda ta ga sakon Abba maida wayarta ta yi ta aje. Bangaran Abba Kuma jira yake ya ga replying dinta ga ji shiru, hakan ya sa ya Kira Mansura, Kira daya ko ta daga. Abba cikin sanyi ya ce "Baki ga sakona bane?." Yaya Abba naka sakonka Amma.." shiru Abba ya yi kafin ya ce "Amma me?." Mansura cikin sanyi ta ce "Yaya Abba mommy." Shiru Abba ya yi, sannan ya ce "Mansura nasan da mommy ai nace Ina sonki, mommy zabin mahaifiyatace, ke Kuma zabina ce, dan haka daga yau Kar in Kara jin kin min maganar mommy." Mansura shiru ta yi batace komai ba, Abba jin haka ya ce "Mansura, ina sonki, na so ace mu yi maganar gani gaki, Amma naga kamar kina tsoran mama tasan muna soyayya, bana jin mama zata kiki Mansura, idan har mama kike gudu dan Allah ki saki jikinki dani, yau idan na dawo akwai maganar da nake so mu yi." Mansura shiru ta yi kafin ta ce "Yaya Abba mu yi ta a waya Mana." A'a zaki fi saurin amincewa idan muka yita a fili." Abba na fadar haka ya kashe wayarsa. Mansura bin wayarta ta yi da kallo. Abba bayan ya dawo aiki falon mahaifiyarsa yayo kasan cewar bata falon ya sa Abba ya shiga bedroom din Mansura. Mansura na kwance kamar yadda ta Saba, Abba kallan Mansura ya yi ya ce "Tashi ki zauna mu yi magana." Abba ya fadi maganar yana zama bakin gadon Mansura. Mansura tashi ta yi ta zauna tana kallan Abba batace komai ba ta maida kanta kasa. "Man's, ya zaman gida." Abba ya ce yana kallan Mansura. "Alhamdulillah." Mansura ta ce. Shiru Abba ya yi kafin ya ce "Mansura Ina so ki amince min a yi auranmu tare dana mommy." Mansura dago manyamanyan idonta ta yi cikin razana da jin Abin da Abba ya ce. Kai Mansura ta girgiza ta ce "A'a, Yaya Abba ba zai yuwu ba." Mansura ta idasa maganar tana kuka. Abba kallan Mansura ya yi dake kuka sosai kamar wadda aka yi mata wani abun ya ce "Shi kenan, ya Isa ki bar kukan, ki yi tunani tukun." Abba na fadin haka ya fita da sauri, dai-dai mahaifiyar Abba ta fito itama suka haɗe da Abba da yake fitowa daga bangaran Mansura. Mahaifiyar Abba da mamaki tabi Abba da kallo, dan asaninta ko lokacin da Amina na gidan baya shiga bedroom din Amina in ba ciwo take ba ya shiga ya yi mata allura. Abba kallon da mahaifiyarsa takemai sai ya naimi ya maidashi mara gaskiya, Abba kai ya sosa ya ce "Mama, shigowata kenan na duba Mansura inga lafiyarta na Kira wayarta bata daga ba." Mahaifiyar Abba bata tanka ma Abba ba, cikin falon ta karasa ta zauna kan 2seater kafin,ta kalli Abba da shima ya zauna har yanzu idanshi akan mahaifiyarshi ganin kallan tuhuwar da take mai. Mahaifiyar Abba cikin damuwa ta ce "Abba me ya kaika bedroom din Mansura?." Abba ajiyar zuciya ya sauke ya ce "Babu komai mama, na Kira wayarta ne bata daga ba shine na shiga in dubata." Kai mahaifiyar Abba ta jinjina alamun mamaki ta ce "Abba meye tsakaninka da Mansura? Kar dai kace maganar da Aisha ta taba fada min ina ganinta kamar a shirme ne gaskiya ce?." Abba shiru ya yi kansa kasa baice komai. Mahaifiyar Abba Kuma ta ci gaba da cewa "Ko shi ya sa kake wulakanta Aisha har ta ce ta fasa auranka?." Nan ma dai Abba shiru ya yi ya kasa magana. Mahaifiyar Abba cikin daga murya yadda Abba bai saba jin tana magana ba ta ce "Abba ba da Kai nake magana ba, me ye tsakaninka da yarinyar can nace." Abba dago idanunsa ya yi yana kallan mahaifiyarsa kafin ya ce "Mama dama ina son zan hada mommy da Mansura in aura rana daya idan kin amince." Mahaifiyar Abba tashi ta yi tsaye tana yi ma Abba kallan banza kafin ta ce " Baka isa ba Wallhi, ban amince ba bazan taba amince waba." Abba shiru ya yi kansa kasa, kafin ya dago yana kallan mahaifiyarsa da yake ma kallan mai saukin Kai ya ce "Mama, auran Mansura ne baki yadda in yi ba, koka in aureta da mommy rana dayane baki yadda ba?." Duka Abba ban yadda ba, ban aminta ka auri yarinyar da har yanzu taki fada Mana ainihin asalinta ba, idan har Mansura ta sanar da Kai ko ita wacece na yadda ka aureta amma idan har zata ci gaba da boyemana asalinta to ni Kuma ban yadda ba ka aureta." Abba shiru ya yi, ya dade bai Kara cewa komai ba kafin ya tashi ya fita. Abba ranar babu dadi a ransa ya yi barci. Washagari ya kama weekend Abba ba za shi aiki ba, Kuma ranar sukayi Aisha zata zo. Aisha da safe ta tura ma Abba sakon text message kamar haka " Assalamu alaikum, na kasa boye farin cikin dake cikin Raina, yau zan ga kyakkyawar fuskar yaya Abbana da nake muradin son gani kullum." Abba sai da ya ga text din Amina ya tuna da yau suka yi zata zo. Aisha da yake gandoki muje biki ce, gashi ta kosa dama taga masoyin nata hakan ya sa karfe goma ta yi shirin zuwa gidan su Abba. Abba ko dama yasan mahaifiyarsa na Islamiya, tana fita shi Kuma ya shiga bangaran nasu, Kiran Mansura ya yi. Mansura gaida Abba ta yi, Abba ko gaisuwar Mansura bai tsaya amsawa ba, da yake a matsaye yake da abin da yake son tambayar Mansurar, hakan ya sa Abba cikin sanyi ya ce "Mansura dan Allah ki fada min labarinki Mana ko kadanne, narantse miki babu wani abu da zaisa in gujeki, Mansura so kawai nake maki ba kaunace, kauna Mai zurfin gaske wadda babu abin da zaki aikata Koda duniya duka zata kiki ne ni ba zan iya kinki ba Mansura, karki ma furucina kallan kalaman baki kawai ko na fada don Ina son sanin wacece ke, da gaske nake har ckin raina nake fada miki haka. Ina jinki me ye ainihin abin da ya sa kika bar gidan iyayanki..✍🏻 Littafin ABBANA na kudi ne, 400 wa inda suka biya kafin in gama free pages daga zarar na kammala zai koma 500 ainihin kudinsa my number 08063830828 Fadila Sani Bakori ce ⭐ ABBANA ⭐ 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚* Masu tambayar Abbana daga farko ga Link nan 👇🏻Follow the ABBANA channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaYZGsNEFeXsr1CKQl3r P 35-36 Mansura dagowa ta yi tana kallan Abba da jajan idanunta, baki ta bude zata yi magana ta fashe da kuka. Abba shiru ya yi baice komai ba, yana kallan Mansura da ke aikin kuka, ganin bata da alamar yin shiru ya sa Abba ya ce "Shi kenan, baki son maganar?." Kai Mansura ta dagama Abba tana mai ci gaba da kukanta. Abba cikin damuwa ya ce "Mansura mama ba zata bari in aureki ba idan har baki fada min ainihin wacece ke ba." Mansura tashi ta yi da sauri zata bar falon tana kuka. Abba ma da sauri ya tashi ya rike mayafin Mansura. Mansura jan mayafinta ta yi zata fizge tana cewa "Yaya Abba ka sakan." Abba na rike da mayafin Mansura yana kallanta ya ce "Mansura, akaran kaina Wallahi bana bukatar sanin komai akanki, amma Ina da iyaye su ba za su yadda in aureki a haka ba. Mansura idan har kina sona ki yadda dan Allah ko ahalinki in sani." Mansura kuka take sosai wanda ya sa dole Abba ya yi shiru. Abba na rike da hannun Mansura suka zauna, bayan sun zauna Abba handkerchief dinsa ya ciro yana share ma Mansura hawayanta ya ce "Inda dai baka son maganar bazan sake yi maki itaba." Abba ya dade yanata lallashin Mansura kafin ya samu ta yi shiru, duk da taki cemai komai,shashshekar kuka kawai take. Suna a haka ne Aisha ta yi sallama ta shigo falon, Aisha daskarewa ta yi a tsaye a inda take ganin Abba da Mansura zaune gaf da juna. Abba kallan Aisha ya yi yana kakaro murmushi ya ce "Mommyna, ki shigo Mana." Aisha shigowa ta yi tana yake, duk annurin dake tare da ita take ya gushe ganin Abba da Mansura da ta yi tare. Abba wajan zanma ya nuna ma Aisha. Aisha cikin sanyi ta gaida Abba, dan gaba daya farin cikinta ya gushe. Abba cikin sakin fuska ya amsa gaisuwar Aisha ya ce "Mommyna, ya mutanan gidan, shi ne baki kirani ba kika sanar dani zuwanki ba ko?." Aisha murmushi ta yi ta ce "Ka manta Yaya Abba, yau na sanar da Kai Mana a text din da na tura maka." Abba sosa Kai ya yi ya ce "Ni Kiran waya nake magana ba text ba." Aisha kallan Abba ta yi tana murmushi ganin alamun canji da yayi, ada idan yana tare da Mansura ko kallo bata isheshi ba, hakan ya sa Aisha cikin sakin fuska ta ce "Afuwa Yaya Abba, hakan ba zai sake faruwa." Abba kallan Mansura ya yi da kanta yake a kasa ya ce "Mansura kawo Mata ruwa." Aisha kamar tace a'a, Amma saboda wadda ya sa ta kawo mata ruwan ya sa bata ce ba. Mansura tashi ta yi ta je ta dakko ma Aisha ruwa mai sanyi ta kawo mata. Aisha bude baki ta yi ta ce "Sister ana wannan sanyin damunar, idan akwai mara sanyi kiban in Sha." Mansura Kai ta girgiza ta ce "Babu duk sun yi sanyi." Ta fadi maganar ahankali kamar an yi mata dole. Abba kallan Mansura ya yi ya ce "Ki je falona akwai ruwa ki kawo Mata babu sanyi." Mansura juyawa ta yi ta fita ta nufi bangaran Abba. Aisha kallan Abba ta yi bayan Mansura ta fita ta ce "Yaya Abba, dan Allah meye tsakaninka da Mansura?." Shiru Abba ya yi, sai kuma ya ga ya yakamata ya fadamata gaskiya kamar yadda tanaima inda yana fadan auransu duk a hada a yi tare dana Mansura, hakan ya sa Abba ya ce "Mommyna, Mansura matar da zan aurece, rana daya nake so ayi tare da naki." Aisha dago idanta ta yi tana kallan Abba cikin gigita da jin Abinda ya ce, Aisha da hawaye har ya fara taruwar mata Kai ta girgiza ta ce "Yaya Abba indai hakane na hakura da kai Wallahi, na hakura ba zan iya kishi da Mansura ba, na hakura na bar Mata kai." Aisha ta idasa maganar tana tashi zata fita tana kuka. Abba hannun Aisha ya kamo cikin tashin hankali, dan yasan idandai ta furta ta hakura dashi ya bani wajan mahaifiyarsa. Hakan ya sa Abba cikin damuwa ya ce "Mommyna, dan Allah karki yi min haka Mana, ki zauna mu yi magana." Abba ya fada Yana nuna ma Aisha caution ta zauna. Aisha Kai ta girgiza ma Abba ta ce "Yaya Abba Ina sonka Amma Wallahi idan har da yarinyar nan zaka hada ka auremu na hakura dakai, ka sakar min hannuna tafiya zan yi." Abba goge zufarsa ya yi ya ce "Aisha na ji tom ki zauna mu yi magana." Daidai lokacin Mansura ta shigo rike da faro a hannunta, tsayawa ta yi tana mamakin abinda ya sa Aisha kuka. Abba kallan Mansura ya yi dake kallansu, Abba hannun Aisha ya kama ya ce "Muje in kaiki gida." Abba ya fadi maganar yana tafiya. Kallan Mansura ya yi da itama shi take kallo ya ce "Bari in Kai mommy gida." Mansura Kai ta daga ma Abba bata ce komai ba. Abba tare da Aisha suka jera suka bar falon, Aisha har yanzu tana goge hawaye. Abba bayan sun fita motarsa ya bude ma Aisha front seat ya ce "Shiga muje babu musu Aisha ta shiga. Bayan Aisha ta shiga Abba kallanta ya yi ya ce "Mommyna meye damuwarki da auran Mansura da zanyi? Idan ma baki so ku zauna gida daya sai ki zabi inda kikeso in ajeki ko nan gidan ko Kuma gidan da na gina." Aisha kallan Abba ta yi da idanunta dake zubba da hawaye ta ce "Yaya Abba dan Allah ka fahimceni ba zan iya kishi da Mansura bane, saboda nasan kana sonta fiye Dani, impart ita kake so bani ba, taya zan hada kishi da ita, bannaima ma kaina kwanciyar hankali bama idanna yi haka. Tursasani Kuma da kake so ka yi in amince maka kana yi ne Yaya Abba kawai dan ka guje ma fadan mama bawai dan kana Sona ba, Yaya Abba dan Allah mu fahimci juna Wallahi da gaske nake na kura dakai zan yi ma Mama bayani nice bana sonka Ina da Wanda nake so." Abba ajiyar zuciya ya sauke, dan yasan indai haka ta faru baya tunanin zai Kara ganin hakorin mahaifiyarsa, hakan ya sa Abba ya kalli Aisha ya ce "Idan na fasa auran Mansura shi kenan kin hakura zaki auran?." Aisha da mamaki ta kalli Abba jin abinda ya ce. Abba Kai ya daga ma Aisha ya ce "Da gaske nake zan fasa auran Mansura idan har zaki janye kudirinki." Aisha runtse ido ta yi jin abinda Abba ya ce, ko a mafarki Aisha bata taba tunanin Abba zai iya haka ba akanta, tunani ta fara anya ko ba gudin bacin ran mahaifiyarsa ya sa shi in yi haka ba, wata zuciyar ta ce Mata in ma yakasance haka ne zai kula dake kenan ko bayan aure saboda gudin bacin ran mahaifiyar tasa kenan. Aisha kallan Abba ta yi ta ce "Yaya Abba nasan baka sona karka yaudari zuciyata dan Allah, ka fadamin me ya sa ka zabeni akan Mansura? Bacin nasan Mansurace zabinka?." Abba shiru ya yi yana kallan Aisha, azuciyarsa ya ce tabbasa Mansura ce zabina. Afili Kuma ya ce "Mommyna, auran Mansura ni kadai nake maganarsa Amma mama taki aminta in aureta, Kinga idan na bari kika sukubuce min na yi biyu babukenan." Aisha sosai ta gamsu da hujjar Abba, hakan ya sa ta ce "Shi kenan Yaya Abba na fasa dama zan tursasa zuciyatane rabuwa da Kai ba wai danna daina sonka ba." Abba murmushin jin dadin nasara ya yi ya ce "Yauwa my love har hankalina ya kwanta." Abba na fadin haka ya tada motar suka tafi, suna tafiya suna hira har suka kai gidansu Aisha. Abba hira suka yi yau sosai da Aisha wadda basu taba irinta ba, Aisha bata taba jin ta gamsu da auran Abba ba sai yau, ji take kamar an cire mata wani nauyi a kanta. Abba bayan sun zo kofar gidansu Aisha kallan Aisha ya yi ya ce "Gamu a kofar gidanku, shi kenan in wuce?." Aisha kai ta girgiza ma Abba ta ce "Ka shiga ka gaida Malama kafin." Aisha ta fadi maganar dan ta ji abinda Abba zaice inda tasan Malama bata gida tana makaranta. Abba kayan jikansa ya duba ya ce "Kalli fa kayan dake jikina, gaskiya ba zan iya zuwa da k'ananan kaya ba." Aisha bata rai ta yi ta ce shi ya sa Wallahi na ce zan fasa auran baka sona gashi nan ko mamana baka taba gaidawa ba." Abba da a halin yanzu babu abinda ke tata mai hankali kamar Aisha ta ce zata fasa auransu, dan yasan mahaifiyarsa ko bata tsinenemai ba tom kadanne, inda ta ce ko bayan ranta in bai auri Aisha ba bata yafe ba. Abba cikin sanyi da son nuna ma Aisha ba haka bane ya ce "Mommyna so nawa Ina fada maki bani da lokaci in ba rana irinta yau ba, yanzu ki bari da daddre Zan zo sai in gaidata ya yi Miki?" Aisha damamaki ta ce "Da gaske zaka zo da daddre ka gaidata?." In sha Allah, ki kirani ki tuna min." Aisha yau cikin farin ciki suka rabu da Abba, soyayar Abba ko ta Kara nunkuwa a zuciyarta. Abba lokacin da ya shiga gida ya iske mahaifiyarsa harta dawo, saidai ita kadaice a falon babu Mansura. Abba fita ya yi ya Kira wayar Mansura, har ta katse bata daga ba saida ya sake Kira. Mansura daga wayar ta yi tana kangata a kunnanta. Abba cikin sanyi ya ce "Man's, gani na dawo ki fito falon Mama plz." Mansura kamar zata fasa kuka ta ce "Yaya Abba dan Allah ka rabu dani ka kyaleni." Abba shiru ya yi jin Abinda Mansura ta ce, Abba cikin damuwa ya ce "Man's ki yi hakuri nasan akan Aisha ne, idan ban yi haka ba Mama zata yi fushi dani kito fito dan Allah yanzu kin ji." Abba na fadin haka ya kashe wayarsa ya koma falon mahaifiyarsa, amma har ya gama zamansa Mansura bata fito ba, dole ya hakura ya fita gidan baki daya. Gaf magariba Aisha ta Kira Abba ta tuna mai zuwa gidansu, Abba kamar ya ce ba za shi ba, amma Kuma Yana tsoran ya yi ma Aisha laifi hakan ya sa bayan ya dawo sallar magariba ya shirya cikin wata brown din shadda ya yi kyau sosai ya shigo falon mahaifiyarsa. Zaune Abba ya iske mahaifiyarsa da Mansura suna hirar Amina da suka gama waya da ita yanzu. Abba cikin sanyi dan yanzu gaba daya mahaifiyar tasa ta canza mai ya ce "Mama zani gidansu mommy zan gaida iyayanta." Tom ka dawo lafiya." Mahaifiyar Abba ta ce. Abba fita ya yi yana kallan mansura da ta sadda kanta kasa. Abba fita ya yi ya Kai Koda ya juyo suka yi ido hudu da Mansura, murmushi Abba ya sakar mata ya tafi. Abba na gaf kaiwa gidansu Aisha ya kirata a waya ya sanar da ita zuwansa. Aisha daketa rawar Kan Abba na ji da ita yanzu, mahaifiyarta ta samu ta shaida Mata Abba na nan zuwa gaidata. Mahaifiyar Aisha da alamun mamaki a fuskarta ta ce "Abban ne zaizo gaidani?." Kai Aisha ta daga ma mahaifiyarta tana murmushi. Mahaifiyar Aisha kallan Aisha ta yi ta ce "Kin janye maganarki kenan ta fasa auran." Aisha dariya ta yi ta ce "Malama ai yanzu mun fahimci juna." Aisha suna cikin magana da mahaifiyarta Abba ya kirata ya sanar da ita ya karaso. Aisha kallan mahaifiyarta ta yi ta ce "Malama, bari in je in taho da shi." Aisha na fadin haka ta fita. Abba da ya shigo bayan ya gaida mahaifiyar Aisha har falon mahaifin Aisha aka kaisa ya gaidata kafin ya yi masu sallama ya tafi, bai biyema Aisha sun yi fira ba, Yana fitowa ya kalli agogon hannunsa ya ce "Mommyna dare ya yi bari in tafi." Tom Yaya Abba Allah ya tsaremin Kai cikin tsarewarsa." Abba bayan ya koma gida da ya shigo mahaifiyarsa bata falo hakan ya sa ya nufi badroom dinta. Abba sallama ya yi, yadda mahaifiyarsa ta amsa mai ya sanar dashi ta fara sakkowa. Abba zama ya yi Yana Bata labarin karamcin iyayan Aisha da tattakonsu. Mahaifiyar Abba cikin jin dadin hirar ta ce "Haba ai baka ga komai bama sai in Allah ya yi auranka da Aisha, zaka san ka yi aure gidan mutunci." Abba dai murmushi ya yi. Kafin Abba ya ce "Mama dama akan Mansura ne, baki ganin indan mun yi aure da ita zata sanar da ni ahalinta, saboda mama idan zaki kalli Mansura bata da wata wani mugun hali ko rashin da'a ko dabi'a, daga ganinta duk inda ta fito ta samu tarbiya daidai ta addini musulinci, Kuma Wallahi mama inaji ajikina akwai alkairi sosai a aurena da ita." Mahaifiyar Abba kallan banza ta yi ma Abba ta ce "Nima bance babu alkairi ba, Amma Abba indai ka ga ka auri Mansura ba tare da ahalinta ba saidai in bana raye, idan tana da gaskiya meye abin tsoro a sanin a halinta, tom Wallahi Koda wasa ka karamin maganar nan sai na bata maka rai, idan yau ka je ka ga a halinta na amince ko a ranar ka aureta." Abba shiru ya yi baice komai ba ya ja bakinsa ya yi shiru, ƙarshe ya tashi ya fita. Abba na fita bedroom din mahaifiyarsa ya yi wuf ya tura badroom din Mansura ya shiga. Lokacin da ya shiga bata dakin, Abba na zama ita Kuma ta fito daga toilet. Mansura karasawo inda Abba yake ta yi ta zauna kan abin sallayar da ta yi Sallah. Abba bakin bed din Mansura ya nuna Mata ya ce "Zo ki zauna magana za mu yi." Mansura tashi ta yi ta je ta zauna kusa da Abba, Abba kallan Mansura ya yi ya ce "Mansura, saura wata biyu bikina da Aisha, ina so in aureki kafin Aisha idan kin amince, amma Kuma auran sirri nake so mu yi bana son kowa ya sani har Amina bana so ta sani." Mansura Kai take girgiza ma Abba ta kasa magana, da yake bata da wuyar kuka goge hawayan da ya fara zubar Mata ta yi ta ce "Aure Kuma Yaya Abba, auran ma na sirri? A'a gaskiya ni ba zan iya haka ba, ba zan taba amincewa ba Yaya Abba." Abba shiru ya yi Yana kallan Mansura dake furta kalmar haka ba zai taba yuwu bama Ina. Abba cikin sanyi ya ce "Mansura ke kanki zakifi samun natsuwa, na tabbata auran zai rage miki wannan damuwar da kike cikinta, ki yi tunanin magata akwai alkairi sosai a cikinta." Mansura Kai ta girgiza ta ce "Yaya Abba dan Allah mu b.." Abba rufe ma Mansura baki ya yi jin Mahaifiyarsa na Kiran Mansurar tana cewa "Mansura badai kin yi barci ba zo ki bude min.. ... ✍🏻 Littafin Abba na kudine, 400 kacal kafin in gama free pages daga na kammala zai koma 500 my number 08063830828. Fadila Sani Bakori ce ⭐ ABBANA ⭐ 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚* Domin samun littafin ABBANA daga farko 👇🏻Follow the ABBANA channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaYZGsNEFeXsr1CKQl3r P 37-38 Mansura ido ta fara zarewa jin Kiran da mahaifiyar Abba take Mata. Abba cire hannunsa ya yi daga bakin Mansura ya je ya dauke takalminsa ya yi ma Mansura nuni da ta je ta bude ma mahaifiyarsa kofa da har yanzu take Kiran sunan Mansura tana buga kofar, shi kuma ya shiga bathroom din Mansura ya boye. Mansura tashi ta yi ta je ta bude kofar tana mutsika idanu alamun daga barci ta tashi. Mahaifiyar Abba kallan Mansura ta yi ta ce "Mansura me ya sa kike kwanciya baki ci abinci ba? Yanzu na shiga kitchen na ga jollop din da na yi biki ci ba, maza ki je ki dibo ki ci." Mansura Kai ta girgiza ta ce "Mama na koshi ne fa." Mahaifiyar Amina kofar ta ja ma Mansura ta ce "Shi kenan sai da safe." Mansura ajiyar zuciya ta sauke kafin ta koma inda take ta zauna. Abba na jin tafiyar mahaifiyarsa ya fito. Mansura kallan Abba ta yi ta yi dariya ganin yadda yake zare ido kamar wanda ya yi karya asirinsa ya tonu. Abba hararar Mansura ya yi bauce komai ba ya juya ya fita da sauri yana sauke ajiyar zuciya. Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya tsakanin Mansura da Abba, Abba bai sake mata maganar auran da ya naimi su yi ba, haka Kuma bai Kara tambayarta ba akan ahalinta kamar yadda ya yi mata alkawari. Bangaran Aisha Abba ya yi ƙoƙarin shirya tsakaninsu gudin karta Kuma cewa ta hakura dashi. Mansura ko kullum cikin waya suke, dan yanzu sai su raba dare suna waya ko chart. Yanzu haka saura wata daya auran Aisha da Abba, inda soyayyarsa da Mansura yanzu ta yi karfi sosai, dan ita kanta Mansura duk yadda take shashshare Abba yanzu ta daina, idan bai kirata bama har rasa nazuwarta take, sannan abinda Abba ya lura dashi yanzu shigowarsa rayuwar Mansura kamar ya rage mata kunci, ya rabu da ganinta tana kuka kamar yadda take yi da, duk da har yanzu lokuta da dama tana yin kuka amma ba kamar da ba. Yanzu Haka Abba zaune yake suna fira da Mansura a falon mahaifiyarsa da yake tana islamiya, Abba kallan Mansura ya yi ya ce "Man's kin yi shiru gashi lokaci sai gabatowa yake, na ce ki yi min list na abubuwan da kike bukata wanda zaki yi hidimar bikin Aisha dashi." Mansura dagowa ta yi tana kallan Abba da idanunta da suka cika da hawaye. Abba kai ya girgiza ma Mansura ya ce "Bana so, me ye Kuma abin kuka anan." Mansura goge hawayanta ta yi kafin ta ce "Yaya Abba narasa dalili bana son auranka da Aisha, baka ji ba yadda nake ji duk lokacin da ka yi min maganar." Abba ya dade yana kallan Mansura kafin ya ce "Kina so in fasa auranta ne?." Kai Mansura ta daga ma Abba. Abba murmushi ya yi ya ce "Shi kenan, gobe idan Mama ta tafi Islamiya zaki rakani wani waje kafin ta dawo." Mansura dai batace komai, Abba gudin Kar mahaifiyarsa ta dawo ta iskesu tare da Mansura tashi ya yi ya koma wajan aiki. Da yake yanzu Haka yake yi su samu su yi hira da Mansura idan mahaifiyarsa ta tafi Islamiya shi Kuma sai ya zo susha hirarsu. Washagari kamar yadda Abba yake yi bayan mahaifiyarsa ta tafi Islamiya Abba ya Kira Mansura a waya ya shaida mata ta samesa a waje. Bayan Mansura ta fito Abba fita ya yi ya daga cikin motasa ya rufe get din gidansu kafin ya ja motar suka tafi. Mansura kallan Abba ta yi ta ce "Yaya Abba Ina zamu." Abba bai tankama Mansura ba saida ya yi parking daidai kofar wani gidan almajirai, ya kalli Mansura ya ce "Mansura na yi iya bakin ƙoƙarina ganin na samomana hanyar da zamu cimma burinmu amma na kasa, hakan ya sa naga wannan hanyar ita kadaice mafitarmu." Mansura kallan Abba ta yi cikin sanyi ta ce "Yaya Abba ban gane me kake cewa ba, wata hanyar ce mafitarmu?." Abba fita ya yi daga motar yana kallan Mansura ya ce "Muje zaki fahimta yanzu." Mansura na biye da Abba har wajan wannan almajiran, Abba tambayar daya daga cikin almajiran ya yi ya ce "Kai Malam na nan?." Eh yanzu ya shiga gida." Kai Abba ya jinjina ya ce "Yauwa yi min sallama dashi." Abba nanan tsaye shida Mansura Malam ya fito. Da fara'arsa ya ce "Usman Kai ne, ku karaso ciki." Malam har cikin falonsa ya kaisu Abba, bayan sun Kara gaisawa ne Malam ya kalli Mansura ya ce "Usman wannan ce Yarinyar?." Abba Kai ya jinjina ya ce "Eh itace Malam." Malam maida kallansa ga Mansura ya yi ya ce "Yarinya ya sunanki?." Mansura kanta kasa ta ce "Mansura." Kai malamin ya jinjina ya ce "Ma sha Allah, Mansura ya sunan mahaifinki?." Take idanun Mansura ya juya jin tambayar da malam ya yi Mata, malam lura da halin da Mansura ta shiga ya ce "A'a yan Mata daure kinji sunan mahaifinki kawai zaki fadamin daganan shi kenan." Mansura cikin rawar murya ta ce "Kabiru." Ta fadi sunan kamar an fusgoshi daga bakinta. "Ma Sha Allah, Mansura da fatan kina son Usman Kuma kin aminta in miki jagoranci anjima za'a daura auranki dashi kamar yadda ya bukata." Mansura da tsananin mamaki take kallan Abba Wanda shima ita yake kallo. Mansura kuka ta fashe dashi tana tashi da sauri zata fita. Abba da sauri ya kamo hijab din Mansura yana girgiza Mata Kai. Malam kallan Mansura ya yi ya ce "Koma ki zauna kinji." Mansura komawa ta yi ta zauna. Malam cikin hikima ya fara yima Mansura bayani kamar haka "Mansura, Usman ya sanar dani duk abin dake faruwa, abinda zaiyi miki gatane sosai a rayuwarki a matsayin da kike yanzu babu abinda yafi da cewa dake kamar aure, Mansura wannan wata ni'imace Allah ya yi miki karki bujire ma ni'imar Allah Mansura, ki dauki haka a matsayin zanan kaddararki, ko wana dan adama zaki ga da yadda aure yake zuwa masa, dan haka ki amshi ta yin Usman kin ji." Mansura dai kanta kasa bata ce komai ba har yanzu kuka take, dan bata ganin aure ya dace da ita a rayuwarta. Malam jin Mansura ba ta ce komai ba ya ce "Mansura, kin amince in zama waliyinki a daura auranki da Usman?." Mansura kasa magana ta yi hakan ya sa ta daga ma Malam kai, ta tashi da sauri ta fita. Malam kallan Abba ya yi ya ce "Usman, ka yi jahadi Allah ya saka maka da alkairi, amma da alama akwai wani boyayan al''amari game da yarinyar nan, ka yi hakuri watarana zaka San komai game da ita. Abba godiya ya yi ma Malam sosai kafin ya ce "Malam yanzu maganar sadaki ita zanba?." Eh Mana Usman ita zaka ba." Abba godiya sosai ya yi ma Malam kafin ya tafi ya sanar da shi zai dawo anjima. Abba a mota ya samu Mansura ta tusa kanta tsakankanin kafafunta tana kuka. Abba cikin sanyi ya ce "Mansura bakya son auran ne ki sanar dani ba zan miki dole ba." Mansura kai ta dago tana kallan Abba, kafin cikin kuka ta ce "Yaya Abba me ya sa ka zabi mu yi auran sirri?." Ajiyar zuciya Abba ya sauke ya ce "Mansura, na yi ma mama maganar Ina so in aureki taki amince min, ta ce dole sai in naga ahalinki kafin idan ba haka ba bazata yadda da auranmu ba, kin ji dalilin da ya sa na naimi mu yi auran sirri." Mansura kallan Abba ta yi ta ce "Ranar da mama ta sani fa?." Bama zata taba Sani ba, sannan idanma ta sani zata yi hakuri dole." Mansura shiru ta yi bata Kara cewa komai ba, Abba ya tada motar suka tafi da sauri gudin Kar mama ta dawo. Bayan sun shiga gida Abba kallan Mansura ya yi ya ce "Nawa zan baki sadaki?." Mansura rufe idanunta ta yi bata yi magana ba. Abba murmushi ya yi kafin ya ciro kudi ya Mika ma Mansura ya ce "Gashi two hundred thousands ne, amma tsadarki ta ninninka haka, dan ke kin wuce a biya sadakinki da naira saidai saifa, Ina fatan za ki min alfarma ki amshi nairata." Mansura dai kanta kasa batace komai ba. Abba agogon hannunsa ya kalla ganin mahaifiyarsa na gaf da dawowa ya sa ya kalli Mansura ya ce "Zan tafi mama ta kusa dawowa, nan da 1 hour zan zama angon man's." Abba ya fadi maganar yana tafiya dan mahaifiyarsa zata iya dawowa a kowana lokaci. Mansura zama ta yi bayan tafiyar Abba tana tunanin rayuwarta, ta rasa halin da take ciki farin ciki ko akasin haka ta rasa, amma tana jinta kamar wadda bata da laka a jiki, gaba daya jikinta ya yi sanyi. Mansura na nan zaune cikin wannan yanayin mahaifiyar Abba ta yi sallama ta shigo gidan. Mahaifiyar Abba kallan Mansura ta yi damamaki ganin hijab a jikinta ga Kuma ta kalminta da ta gani kofar falon. Mahaifiyar Abba da mamaki ta ce "Mansura unguwa kika jene na ganki da hijab ga takalmi kofar falo da na gani?." Mansura ido ta fara rabawa ta ce "A'a mama sanyi nake ji na sanya hijab na fita Ina zazzagayawa harabar gida dan kar in kwanta." Mahaifiyar Abba murmushi ta yi ta ce "Da'alama dai 'yata ta fara zama jaruma." Mahaifiyar Abba ta fadi maganar tana zama. Bayan ta zauna kallan Mansura ta yi tana dubawa wayarta ta ce "Mansura zo ki gani, ankon bikin Abba da yan iskamiyarmu suka fidda, ni sai na ga kamar wanna tafi kyau?." Mansura da kallo tabi mahaifiyar Abba. Mahaifiyar Abba damamaki ta kalli Mansura ganin bata taso ba, hankalinta ma gaba daya ba akanta yake ba ta ce "Mansura lafiyarki kuwa?." Firgigi Mansura ta juyo tana kallan mahaifiyar Abba. Mahaifiyar Abba shiru ta yi tana kallan Mansura da mamaki ta ce "Mansura lafiyarki kuwa? Tunanin me kike haka?." Mansura kasa ta yi da kanta batace komai ba. Mahaifiyar Abba bata sake bin takan Mansura ba ta tafi ta barta nan zaune tana cewa "Allah yaye miki wannan tunane-tunanan Mansura, kina yarinyarki karama zaki maida kanki shohowa tsabar sama rai damuwa da kika yi." Mahaifiyar Abba har ta shiga bedroom dinta tana mita akan halin mansura na tunane-tunane da tasa ma ranta. Mansura tarasa dalilin rikicewarta akan maganar ankon bikin Abba da mahaifiyar Abba ta yi. Gaba daya wunin yau haka Mansura ta yi sa wani iri, ga damuwar auran da Abba daya dora Mata ga Kuma maganar auransa dake gabatowa. Abba bayan magariba ya dawo gidan ya nufi bangaran mahaifiyarsa, yau Abba ya dage sai ziba yake ma mahaifiyarsa, mahaifiyar Abba kallan Abba ta yi tana murmushi ta ce "Abba wannan fara'a haka, fada min wana albishir din akai ma?." Abba dariya ya yi yana kallan mahaifiyarsa ya ce "Mama Wallahi haka na tsinci kaina nima cikin farin ciki." Tom Allah ya daurar da shi, ya maganar lefan Aisha." Kai Abba ya sosa dan yama manta da maganar laife ya ce "Mama akwai wata Mata a asibitinmu sanarta kenan hada lefi, ita ta hadama Aminu abokina, zan mata magana gobe."Bana son shiririta kaga saura kwana 33 yau bikin, ya kamata ace ka gama hada komai." Abba sun jima suna fira da mahaifiyarsa kafin ya fita ya nufi bangaransa, wanka Abba ya shiga, bayan ya fito ya shirya cikin wasu k'ananan kaya masu kyau ya dauki key din motarsa ya fita, baidade sosai ba ya dawo. Abba rufe motarsa ya yi ya fita rike da leda ahanunsa ya nufi bangaran mahaifiyarsa yana addu'ar Allah ya sa bata falon. Abba na zuwa ya tura kofar falon rufe ya jita alamun ansa Mata key, Abba Mansura ya Kira a waya da tundazu take tsimayinsa, ta ji an daura auran nasu ko a'a. Hakan ya sa Mansura na ganin kiran Abba ta daga. Abba cikin kasa da murya ya ce "Zo ki bude min kofar falo, amma fa ki yi a hankali Kar mama ta ji." Abba na fadin haka ya kashe wayarsa. Mansura lallabawa ta yi a hankali ta bude kofar falon kamar yadda Abba ya naima. Tana budewa Abba ya maida kofar ya rufe, Mansura magana za ta yi ganin Abba ya rufe kofar amma sai ya yi Mata nuna da hannu akan su shiga ciki." Mansura na biye da Abba har bedroom dinta. Abba zama ya yi gefan bed din Mansura. Mansura Kuma kanta a kasa daga gani dai tana jira ne daga Abban. Abba gyaran murya ya yi kafin ya ce "Mansura Kinga yadda kaddarar auranmu mukuma ta kasance ko? Dazu bayan na dawo dake gida na koma malam ya yi jagoranci aka Daura Mana aure bayan fitowa daga massalaci bayan sallar azahar. Ga sadakinki." Abba ya ciro kudi masu yawa daga cikin ajjihunsa ya aje a cinyar Mansura ya ce "Dubu dari da biyu ne kamar yadda na biya na Aisha, ina fatan za ki ci gaba da rufa asirin auranmu har ranar da Allah zai da mama ta amince da auranmu?." Mansura dago idanunta ta yi da suka cika da hawaye ta kalli Abba, amma bata ce komai ba, ta maida kanta kasa. Abba cikin sanyi ya ce "Mansura kuka baya maganin komai, duk da soyayyarki ita ta fara zama silar kulla wannan auran namu, amma abu na biyu har da fatan waraka daga zubar hawayanki na kulla Mana wannan auran Mansura." Mansura fashewa ta yi da kuka jin abinda Abba ya ce ta ce tana kuka "Yaya Abba, hawaye ba za su taba gushewa daga fuskataba har ranar da zan yi bankwana da rayuwa, na aikata kuskure mafi muni a rayuwata, na aikata kuskure Yaya Abba." Mansura ta yi maganar cikin tsantsar kuka. Abba kallan Mansura ya yi da ya kasa hanata daina kukanta cikin sanyi da rauni ya ce "Wana kuskure ki aikata Mansura? Fada min me kika aikata?." Mansura kuka take sosai wanda Abba bai taba ganin ta yi irinsa ba, Abba bai hanata ba sai da ya ji tana yi da karfi gudin Kar mahaifiyarsa ta jiyo ya sa Abba ya matso kusa da Mansura ya kwantar da kanta kan kafadarsa yana shafa bayanta, shi kansa ya kasa magana. Sun dauki shawan lokaci a haka. Sauke ajiyar zuciyar Mansura ya ji wanda ya tabbatar mai da ta yi barci, Abba dago kan Mansura ya yi da mamaki yaga barci take, hakan ya sa Abba ya matsar da Mansurar tsakiyar gadon ya kwantar da ita a hankali yana tsoran ta tashi. Abba bin ledar da ya shigo da ita ya yi da kallo ta kaza da Yoghurt ya mamanta da ita gashi wadda ya siyo mawa din ta yi barci. Abba tashi ya yi ya shiga toilet din Mansura kafin ya zo ya kwanta gefan Mansurar Yana tofe su da addu'a. 4:00AM Abba ya farka rike da kansa saboda wani mummunin mafarkin da ya yi, Abba sauka ya yi daga kan gadon ya je ya doro Alwallah ya yi nafila da naiman tsari akan mafarkin da ya yi, Abba nanan zaune kan abin sallah yana lazimi Mansura ma ta farka a firgice tana ihu tana Kiran "Abbana." Abba da sauri ya je ya rirrike Mansura Yana tofa mata addu'a ganin yadda ta firgice har yanzu Kuma Bata bar Kiran "Abbana." ba din da take yi. Abba rungume Mansura ya yi ajikinsa yana shafa kanta Yana Kuma tofa Mata addu'a. Mansura jinta jikin mutum da ta yi ya sa ta dawo natsuwarta, dago Kai ta yi suka hada ido da Abba. Mansura zaro ido ta yi tana ƙoƙarin tashi daga jikin Abba . Abba a hankali ya ce yana Kuma shafa kan Mnasura "Ki natsu Mana, Wana mafarki kikai wanda ya firgitaki haka?." Mansura goge hawayan da ya fara zubar Mata ta yi ta ce. "Yaya Abba na yi mafarkin Ina sanye da kayan prisoner hannuna an samin min handcuff." Abba shiru ya yi yana bin Mansura da kallo dan shima irin mafarkin ya yi. Mansura ko ta dage sai kuka take, Abba hannun Mansura ya kama ya kaita har toilet kafin ya dawo ya ce "Ki yi Alwallah yanzu za a Kira Sallah ki samu raka'atanal fijir." Bayan Mansura ta fito ta yi raka' a tanal fijiri, Abba ya jamusu limanci suka taka sallar subihi.... ✍🏻 Littafin ABBANA na kudi ne, 400 ne kafin in gama free pages daga zarar na kammala 500 my number 08063830828 Free pages ya kusa karewa. Fadila Sani Bakori ce ⭐ ABBANA ⭐ 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚* Domin samun littafin ABBANA daga farko 👇🏻Follow the ABBANA channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaYZGsNEFeXsr1CKQl3r P 39-40 Bayan sun idar da sallar Abba kallan Mansura ya yi da ta yi tagumi, Abba cire ma Mansura tagumin ya yi ya ce "Mansura dole za ki shiga Islamiyar da mama take zuwa, bazai yuwu a rika barinki ke kadai ba, yanzu bacin mun kwana tare da haka zaki Kari ihunki har ki farka, sannan ki rika salati ba ihu ba kar in kara jin kin farka barci kina ihu haka kamar ba musulma ba." Mansura dai Kai kawai take tada ma Abba amma gabadaya damuwar mafarkin nan ba karamin tashin hankali ya sata ba. Abba hannun Mansura ya kama ya ce "Mu je mu koma barci kafin 7." Abba na rike da hannun Mansura suka hau kan bed din Mansurar, Wanda ita gabadaya tsantsar damuwa tasa bin Abba kawai take ta zama kamar butun butumi. Abba bayan sun kunta da Mansura da tashin hankalin da damuwar halin da take ciki ya sa gaba daya kusan a rabin jikin Abba take amma damuwa da furgicin da take ciki bai bata damar ankarar da ita ba. Wanda yana yin kwanciyar da Mansura ta yi ajikin Abba sai ya taka muhimmiyar rawa ga Abba, Wanda ya ja hankalin Abba zuwa ga Mansura. A cikin sanyayyar Safiyar nan Abba ya kusancin Mansura, bayan mai faruwa ta faru barci ya kwashesu baki dayansu Wanda bugun da mahaifiyar Abba take ma su ne ya tadasu daga barcin da suke yi. Abba furgigi ya tashi da alamar bayyanar tsoro a tare da shi, dan yasan mahaifiyarsa tana buga ma Mansura kofa ne jin shiru Bata tashi ba. Abba wayarsa ya jawo Koda ya duba 8:30 AM, Abba kallan Mansura ya yi da itama daga gani a tsorace take da yanayin. Mahaifiyar Abba Kara bugawa ta yi tana cewa "Mansura, lafiyarki kuwa yau dinnan." Abba nuni ya yi ma Mansura da ta je ta bude ma mahaifiyarsa kofa. Mansura tashi ta yi tana ciccije baki, tana rike kanta dake ciwo sosai har bata gani ta nufi kofar. Abba Kuma ledar da ya shigo da ita ya dauka da wayarsa da takalminsa da sauri ya yi bathroom din Mansura dasu. Mansura na rike da kanta taje ta bude ma mahaifiyar Abba kofa. Mahaifiyar Abba bin Mansura ta yi da kallo ganin yadda Mansura ke rike da kanta. Mahaifiyar Abba dakin tashigo da sauri tana kamo Mansura ganin kamar tana layi zata fadi. Mahaifiyar Abba na rike da Mansura har suka karasa kan bed din Mansura. Kwantar da Mansura mahaifiyar Abba ta yi ta ce "Haba ni dama tun da na ga har 8 baki fito ba nasan kullum kina shigowa da asuba nasan yau ba lafiya, ga Abba ma yau sammakon fita ya yi ko shigowa wajena baiyi ba, amma bari in dakko wayata in kirasa ya zo ya duba ki, yau zuwa Islamiya ma ai bai ganni ba bari in je in Kira wayarsa in fada mai." Mansura dai bata ce komai ba mahaifiyar Abba ta juya ta fita, bedroom dinta ta je ta Kira wayar Abba, yana dagawa ta sanar da shi ya zo yanzu Mansura babu lafiya. Abba da baisan yadda zai yi ya fita bedroom din Mansura ba, gashi yana ji tana cewa yau babu zuwa Islamiya ma'ana zata yi jinyar Mansura kenan, Abba dabara ta fado mai ya ce "Mama, gani kusa da gida babu mota ma na fita ki je chamist din Auwal ki bashi wayar zan fada masa abin da zai baki daga na zo sai an mita allura kawai." Mahaifiyar Abba na kashe wayar ta zura hijab dinta ta ta fita daga gidan, Abba na jin fitarta ya fito da sauri ya nufi bangaransa. Da yake chamist din babu nisa sosai bayan layinsu ne, tana zuwa ta Kira Abba ta ba Auwal wayar, Abba magungunan da Mansura take bukata ya fadi ma Auwal ya ba mahaifiyarsa kafin ya kashe wayarsa. Abba bayan ya koma bangaransa wanka ya yi ya sa jallabiyarsa kafin ya Kira wajan aiki ya kawo uzirinsa. Mahaifiyar Abba bayan ta dawo gidan Kiran Abba ta yi ta sanar mai ta dawo, Abba ma cikin karyar da ya koyo yau dinnan ya ce "Mama gani nima yanzu zan shigo gidan." Abba bayan ya gama kimtsawa ya nufo falon mahaifiyarsa inda ya isketa zaune da ledar magungunan. Abba zama ya yi ya gaida mahaifiyarsa tare da cewa "Yau Asibiti aka kirani da wuri na yi fitar safe shi ya sa ban samu shigowa ba." Haba, ni dama yau na jika shiru baka shigoba ina jimamin ko lafiya, sai na tuna Mansura ma ban ji duriyarta ba duk yau, shi ne fa na je dakinta ashe kwance take ba lafiya ban sani ba." Kai Abba ya sosai ya ce "Ayyah, meke damunta?." Muje ka gani." Cewar mahaifiyar Abba tana tashi suka nufi bedroom din Mansurar tare da Abba. Har yanzu Mansura tana kwance ta rufe baki daya jikinta. Abba dake tsaye kan Mansurar hannu yasa zai yaye bargon Mansurar, mahaifiyarsa ta rike hannunsa ta ce "Ni fa dadina daku likitoci kamar ba kusan addini ba wasinku, sai ku bage da ai lallurace, yanzu da kake ƙoƙarin yaye mata bargo in fa ba komai jikinta." Abba Kai ya sosa baice komai ba, kafin ya ce "Tom mama ya zan dubata?." Mahaifiyar Abba da wayau ta fara duba Mansura ganin akwai kaya complete a jikinta ya sa ta ja bargon Mansurar ta ce "Tom Bismillah." Abba hannu ya Kai ya taba jikin Mansura, jin babu zafi sosai ya sa ya ce yana kallan Mansura da idanta yake a rufe ya ce "Har yanzu kan na yi miki ciwo?." Mahaifiyar Abba kallan Abba ta yi tana murmushi ta ce "Ka ce Kasan ma bata da lafiya?." Abba lura da subutar bakin da ya yi kai ya girgiza ya ce "A'a yanayin temperature din ajikinta ne ya nuna ta yi ciwan Kai." Owo, ai fa dadina daku kamar mayu kuke." Cewar mahaifiyar Abba. Abba dai baice komai ba. Allura ya ciro ya hada yana kallan Mansura ya ce "Ki juyo zan miki allura." Abin mamaki duk rakin Mansura a allura juyowa ta yi bata yi musu ba Abba ya yi mata allurar. Kallan mahaifiyarsa ya yi ya ce "Allurar ma kyau ace ta karya aka yi, Mama ko tea a kawo mata tasha sai tasha maganin." Mahaifiyar Abba juyawa ta yi ta fita ta je hado ma Mansura tea din. Bayan ta fita ne Abba ya ce "Am sorry Mansura, ya jikin naki, da fatan dai bayan kan babu abin da yake miki ciwo?." Mansura kai ta daga ma Abba bata ce komai ba. Abba kuma cikin marairecewa ya ce "Idan Mama ta shigo ki ce Mata ta yi tafiyarta islamiyarya kin ji sauki, sai in yi jinyarki da kaina." Kai Mansura ta daga ma Abba. Mahaifiyar Abba babu jimawa ta hado ma Mansura tea tare da soyayyar doya ta kawo Mata, tea dinma da kyar Abba ya samu tasha ya bata magungunan duk ta sha babu musu. Abba jin Mansura ba ta yi ma mahaifiyarsa maganar tafiya Islamiya ba da ya ce ta yi ya sa shi ya ce "Mama karfa ki ce ba zaki je Islamiya ba saboda ciwan, inda anyi mata allura Kuma ta sha magani yanzu zaki ga ta ji sauki." Kai mahaifiyar Abba ta girgiza ta ce "A'a gaskiya koma na tafi hankalina ba zai kwanta ba, gara dai in naga tabbacin saukin nata zuwa gobe sai in je." Abba baice komai ba ya kalli mahaifiyarsa ya ce "Allah ya bata lafiya na tafi aiki." Yana fadin haka ya tafi baiso ba yaso ace shi ya yi jinyar Mansurar. Abba yana gaf dawowa gida ya Kira Mansura ya ji ya jikinta da yake lokacin suna tare da mahaifiyar Abba ya sa bata daga Kiran ba. Abba 6:00PM ya shigo gidan rike da ledoji biyu a hannunta, zaune ya iske mahaifiyarsa tana yanka alayyahu. Abba zama ya yi yana mata sannu da aiki, kafin ya ce "Ya mai jikin mama?." Ta ji sauki, amma dai duk yau bata shigo falon nan ba." Abba ledar hannunsa ya mika ma mahaifiyarsa daya ya ce yana tashi "Bari in duba jikin nata mu gani ko tana da bukatar wani maganin." Abba na fadin haka bai saurari cewar mahaifiyarsa ba ya shige bedroom din Mansurar. Kwance Abba ya dadda Mansura ta rufe duka jikinta da bargo. Abba zama gefan bed din ya yi yana kai hannunsa akan Mansurar ya ji jikin nata. "Alhamdulillah, na ji jikin naki babu zafi, ko sanyin damuna ne?." Mansura dai bata ce komai ba. Abba ya Kuma cewa "Ya jikin naki ? Meke miki ciwo yanzu?." Kai Mansura ta girgiza ma Abba ta ce "Babu komai, sanyi nake ji na rufe jikina." Ajiyar zuciya Abba ya sauke, ya kama hannun Mansurar ya ce "Ki tashi ki zauna to." Mansura tashi ta yi ta zauna. Abba Kuma ledar ya shigo da ita ya dakko ya ciro yoghurt dinda ya siyo ma Mansura ya zuba Mata a cup ya mika Mata, da yake Mansura yunwa take ji duk ta kasa cin shinkafar da mahaifiyar Abba ta kawo mata da rana, hakan ya sa ta shanye yoghurt din. Abba ganin ta shanye wanda ya zuba Mata Kuma cika Mata cup din ya yi shima ta shanye, Kara Mata Abba zai yi ta girgiza kai ta ce "Ya isan." Abba ledar ya nuna mata ya ce "Akwai farfesu ciki sai ki ci anjima." Ya fadi maganar yana dakko biscuit ya fasa ya kai daya bakin Mansurar, Kai Mansura ta girgiza ta ce "Na fa koshi." A'a, ki ci biscuit din ki ji yana da dadi." Mansura bude bakinta ta yi tana cin biscuit din. Daidai Abba ya Kai biscuit din bakin Mansura yana Bata gashi sun zauna gaf-da gaf rabin jikin Mansurar kusan duk a jikin Abba take, dan duk ya manmatseta. Abba ganin mahaifiyarsa da ya yi ya sa ya rika Matsawa a hankali da wayau. Ita kanta Mansura batasan lokacin da ta amshi biscuit din daga hannun Abba, gashi dukansu sai su ka yi kamar marasa gaskiya. Mahaifiyar Abba kallan Abba ta yi ta ce "Ta sha maganin ko?." Kai Abba ya sosa ya ce "Eh da yake maganin na da karfi yana dakyau ta ci abinci kafin shine ya sa namatsa mata ta ci abincin." Mahaifiyar Abba bata ce komai ba, hannu ta mika ma Abba ta ce "Ban maganin in Bata?." Abba kai ya sosa dan babu magani ma tare da shi, take da bara ta fado mai ya ce "Mama baki ji ba, na ce da yake maganin na da karfi shi ne natsaya ina bata abinci in ba haka ba zai wahalar da ita maganin." Abba ya fadi maganar yana tashi ya ce "Akwai alllurar da zan mata anjima." Abba na fadin haka ya fita. Mahaifiyar Abba bin Abba ta yi yana ta sauri zai fita, mahaifiyar Abba Kiran Abba ta yi, karasawa cikin falon ya yi ya zauna yana cewa "Mama gani." Mahaifiyar Abba daure fuska ta yi ta ce "Abba anya ko kana aiki da ilimin islamiyarka?." Abba dago kai ya yi ya ce "Mama me ya faru?." Mahaifiyar Abba hararar Abba ta yi ta ce "Kai kanka ai kasan abinda ka yi baikamata ba inda kana ganina ka fara Matsawa, da da iliminka Abba zaka zauna kana nanike ma mace wadda ba murramarka ba, to daga yau ban amince ba ban yadda ba karka Kara shiga dakin Mansurar Kai kadai dan Wallahi ka fara bani tsoro." Abba dai baice komai ba kansa kasa, mahaifiyarsa ta gama fadanta ta tafi ta barsa a wajan. Abba tashi ya yi ya fita yana dariyar fadan mahaifiyar tasa dake cemai "Duk inda kake Wallahi ka tuna Allah na kallanka." Abba wanka ya yi da sauri kafin ya nufi masallaci, bai dawo gidan ba sai da ya yi sallar issha'i. Abba ya san ko ya yi ma mahaifiyarsa karyar zai yi ma Mansura allura tare za su shiga bedroom din Mansurar hakan ya sa ya share maganar. Koda ya zo ya ci tuwa ya zauna suka yi fira da ya tashi zai tafi Mahaifiyar Abba kallan Abba ta yi ta ce "Hala ka manta da allurar da ka ce za ka yi ma Mansura?." Ban manta ba na bari sai da safe ne, ganin bata dade da shan maganin ba." Shi kenan sai da safen." Mahaifiyar Abba ta ce, fita suka yi tare da Abba yana fita ita Kuma ta sama kofar falon key ta rufe ta koma bedroomta ta kwanta. Misalin karfe goma Abba ya tabbatar yanzu mahaifiyarsa ta yi barci ya Kira Mansura a waya akan ta zo ta bude masa kofar falon, Amma Mansura Bata daga ba, Abba sai da ya yi ma Mansura Kira 5 bata daga ba dole ya rabu da ita. Ya koma bangaransa yana jin zafin kin daga wayarsa da Mansura ta yi . Mansura ko tana ganin Kiran Abba haka nan taki dagawa. Washagari da safe Abba da ya shigo gaida mahaifiyarsa, bayan sun gaisa ya ce "Mama bari in duba jikin Mnasura in ga jikin nata zan tafi aiki Kar sai na je a kirani irin na jiya." Mahaifiyar Abba tashi ta yi ta rufe alQur'anin hannunta ta ce "Muje nima inga jikin nata." Mahaifiyar Abba ta sa Abba ta yi har bedroom din Mansura, zaune suka iske Mansura daga ita sai towel ta fito wanka. Mansura hijab dinta ta dakko tasa tana rufe jikinta, cikin ladabi ta gaida mahaifiyar Abba da Abba. Mahaifiyar Abba ta amsa Amma Abba da kallo ya bita yana tsaye, mahaifiyar Abba kallan Abba ta yi da yaja ya tsaya baice komai ba ta ce "Abba ka duba jikin nata Mana." Abba Matsawa ya yi inda Mansurar take ya juyo yana kallan mahaifiyarsa ya ce "Mama tasa hijab ta rufe jiki taya zan ji yanayin dumin jikin nata, inda dai ba zan gane da ido ba." Mahaifiyar Abba wajan Mansurar ta matsu itama ta ce "Bari inji jikin nata?." Mahaifiyar Abba hannu sata cikin hijab din Mansura ta taba gefan wuyan Mansura, sanyi ta ji babu wata alamar zazzabi, hakan ya sa ta kalli Abba ta ce "Jikinta babu wata alamar zazzabi." Ya yanayin sanyi yake?." Abba ya tambaya Yana kallan mahaifiyarsa, mahaifiyar Abba daure fuska ta yi ta ce '"Kamar ya Kuma ya yanayin sanyi yake? Shi sanyin har wani yanayi garai, jikinta dai babu zafi sanyi ne a jikin." Abba dafe kai ya yi ya ce "Mama ke ba likita bace ba zaki fahimci abin da nake nufi ba, akwai sanyin da idan ya yi yawa yake saukar da zazzabi." Mahaifiyar Abba rigar da Mansura ta ciro zata sa ta dauka ta bata ta ce "Je kisa kayanki ki fito ya ji yanayin jikin naki." Mansura dauka ta yi ta Koma bathroom din ta sa kayan kafin ta fito. Abba zuwa ya yi ya sa hannu a wuyan Mansurar. Waigowa ya yi yana kallan mahaifiyarsa ya ga idanta gaba daya akansa yake, Abba wayan cewa ya yi ya ce."Alhamdulillah, ta ji sauki babu zazzabin." Mahaifiyar Abba hararar Abba ta yi ta ce "Ba nace maka ba zaka nuna min iyawa." Abba dai baice komai ba ya juya ya tafi. Bayan ya je aiki ya Kira Mansura a waya, Kira daya ko ta daga. Bayan sun gaisa Abba ya ce "Man's me ya sa jiya baki daga wayata ba?." Yaya Abba na yi barci da wuri ne fa." Shiru Abba ya yi kafin ya ce "Shi kenan, yau karki yi barci daga mama ta rufe ta tafi ki zo ki bude min." Tom." Mansura ta ce. Bayan Abba ya dawo aiki ya zo sun gama fira da mahaifiyarsa kamar yadda ta saba bayan ya fita tasa ma kofar key. Mahaifiyar Abba na rufe kofa Abba ya Kira wayar Mansura ta je ta bude masa, Abba ya lallaba ya shigo yana shiga ya rufe bedroom din Mansura da sauri. Mansura kallan Abba ta yi tana dariya ta ce "Yaya Abba ka cika tsoro." Abba ido ya zaro ya ce "Hmmm." Abba zama ya yi yana ringumo Mansura suka karasa cikin dakin tare, Yana Zama Aisha na Kiran wayarsa, Abba bai daga ba jin tanace da Kira dama jiya ma ta Kira bai daga ba yau ma ya ga miss call dinta ya manta baibi ba, hakan ya sa Abba ya daga Kiran. Abba na dagawa Aisha ta fashe da kuka. Abba cikin sassauta murya yana satar kallan Mansura ya ce "Ya sallam, Momnyna meye na kuka tun da kika Kira wayata kika ji ban daga ba kinsan dai haka nan ba zanki daga kiranki ba, hankalina gaba daya yana akanki, yanzu yi hakuri ki fada min damuwarki ina jinki amaryata ya akai?." Mansura a hankali ta kwace jikinta daga rikon da Abba ya yi Mata ta matsa can gefe tana fashewa da kuka." Abba cikin sauri ya ce ma Aisha "Mommyna ina zuwa zan kiraki yanzu." Abba ya kashe wayar yana dawowa wajan Mansura. Abba na taba Mansura ta bige mai hannu ta ce "Karka Kara tabani ka tafi wajan Amaryarka wadda hankalinka gabadaya yake akanta ni ka rabu dani." Mansura ta fadi maganar tana Matsawa can karshen bed din tana fashewa da kuka, dan tasan bata ga komai bama sai Abba ya auro Aisha, inda ita ba wanda yasan da auranta. Abba jin yadda Mansura ke kuka da karfi rufe Mata baki ya yi ya ce "Mansura dan Allah ki rufamin asiri cikin darannan Kar mama ta jiyo kukanki, kinsan zata ce zata shigo, Aisha Kuma da kike magana akanta sanin kanki ne idan Kuma baki Sani ba ki tambayi Amina bisa umarnin mama zan auri Aisha, kwanakin baya ta yi yunkurin fasa aurena saboda rashin kulawata akanta, idan haka ta Kara faruwa zata fasa Wanda haka daidai yake da tsinuwar mama akaina, ki yi hakuri kin ji." Kai Mansura ta dagama Abb. Can bangaran Aisha Kuma ji ta yi kamar kukan Mace kusa da Abba, hakan ya sa ta Kara Kiran wayar. Har wayar ta katse Abba bai daga ba, hakan ya sa Aisha ta tabbatar yana kusa da Mansura sukai waya. Aisha tura ma Abba text ta yi kamar haka "Yaya Abba dole zaka ki daga wayata inda kana tare da Mansura." Abba ganin text din Aisha rudewa ya yi yasan in dai bai Kira Aisha ba zata dauka hakan ne Kuma yasan yadda take kishi da Mansura inda akanta ma ta ce zata fasa auransa, hakan ya sa Abba ya kalli Mansura ya ce "Man's kin amince in kira mommy, wayar minti goma za mu yi dan Allah?." Mansura kai ta dagama Abba. Abba Kiran Aisha ya yi yana kanga wayar a kunnansa.✍🏻 Kamar yadda kuka Sani bana update weekend, sai Monday in sha Allah za ku jini. Littafin ABBANA na kudi ne week din za zamu shiga zan kammala free pages idan kin shirya my number 08063830828 Fadila Sani Bakori ce. ⭐ ABBANA ⭐ 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚* Domin samun littafin ABBANA daga farko 👇🏻Follow the ABBANA channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaYZGsNEFeXsr1CKQl3r P 41-42 Abba Kiran Aisha ya yi yana kanga wayar a kunnansa. Daga bankaran Aisha cikin raunanniyar murya wadda ke nuna almar saura kadan ta fashe da kuka ta ce "Yaya Abba ka ce min ka fasa auran Mansura amma bisa ga alama har yanzu kuna tare da ita, nifa Yaya Abba ka fahimceni zuciyata na da rauni bana jure abu ko yaya yake musamman akan abinda nake so, shi ya sa na ce maka na hakura dakai saboda bana son damuwa." Abba kallan Mansura ya yi wadda itama shi take kallo duk da bata ji abin da Aisha ke cewa. Abba ajiyar zuciya ya sauke ya ce "Mommyna tuntuni na fada maki na fasa Kuma saboda ke na fasa, ki bar dawo min da magana baya dan Allah, yanzu fada min meye damuwarki?." Mansura itace damuwata idan har kana tare da ita ba zan iya auranka ba, Kuma ko yanzu da na Kira na ji kukanta shi ne ka kashe wayarka." Abba da ransa ya fara bacewa cikin daga murya ya ce "Idan kina ganin sai kin fi samun kwanciyar anhali in kika fasa auran nawa shi kenan ni ba zan miki dole ba." Abba na fadin haka ya kashe wayarsa. Abba tashi ya yi zai nufi inda Mansura take, Mansura ta yi sauri ta kwanta tana juya ma Abba baya. Abba hannu ya sa ya dago Mansura dake kwance ya ce "Afuwa meye Kuma na fushi bacin da amincewarki na yi waya da ita." Mansura dai bata ce komai ba. Abba jin ta yi shiru ya ce "Tom ya aka yi?." Ba komai." Mansura ta ce, amma a cikin ranta so take ta tambayi Abba akan Aisha amma ta kasa hakan ya sa ta ja bakinta ta yi shiru ƙarshe ma juyawa ta yi ta kwanta ta bar Abba nan zaune yana cike da fargabar maganar da ya fada ma Aisha, tsoran Kar Aisha ta aikata abinda ta ce ya sa ya tashi ya shiga bathroom din Mansura ya Kira Aisha. Kira daya ta daga, Abba tashin kukan Aisha ya ji. Shiru Abba ya yi yana sauraran kukan nata gaba daya ransa abace yake da ita, amma tsoran abinda zata aikata ya sa ya ce "Mommyna, tun yaushe nace miki na fasa auran Mansura, tun da kika fadamin ra'ayinki na sanar dake na fasa auran me ya sa Kuma yanzu zaki dawo da maganar baya, indai akan Mansura ne ki bar bata ranki kin ji?." Kai Aisha ta daga ta ce "Shi kenan na fahimta." Yauw Mommyna, Kinga dare ya yi ki kwanta ki yi barci sai da safe." Abba na fadin haka ya kashe wayarsa. Abbana na gama wayar ya Kuma badroom din inda ya bar Mansura kwance ya sameta tana kuka. Abba da mamaki ya matsa wajan Mansurar da bai san Abin da take ma kuka ba. Abbba hannu ya sa zai kamo Mansura Mansura ta daga ma Abba hannu ta ce cikin kuka "Ka fada Mata ka fasa aurena me ya sa ka aureni? Yaya Abba ka fada min me ya sa ka auran bacin ka yi ma wadda kake so alƙawarin ba zaka auran ba?." Abba ido ya fara zarewa yana mamakin ya akai Mansura ta ji wayarsa, sai dai yana daga kai ya ga akwai window a wajan Kuma window bude yake zata iya jin duk abin da yake cewa. Abba rasa abin da zaicema Mansura ya yi. Mansura Kuma cikin kuka ta ce "Sai yanzu na gane abinda kake nufi da ka ce mu yi auran sirri, dan Kar Aisha ta san ka aurene saboda ka yi mata alƙawarin ba zaka auran ba." Abba magana zai yi Mansura ta nuna mai hanyar waje ta ce "Yaya Abba ka fita kawai nagama fahimtar abinda kake nufi dani." Abba da mamaki ya kalli Mansura yadda take nunamai hanya ya fira alamun ba zama ta saurareshi ba, bacin aganinsa sanin kanta ne ita yake so ba Aisha ba, hakan ya sa Abba cikin bacin rai ya ce "Haba Mansura ki saurareni Mana nifa ba Aisha bace zabina ke ce zabina." Mansura kunne ta toshe, ta ce "Yaya Abba ka fita dan Allah." Mansura ta fadi maganar tana kuka. Abba kallan Mansura ya yi ya ce "Ba zan fita ba sai kin saurareni." Mansura da ranta ya gama baci, cikin fushi ta ce "Ki fita Wallahi ko in Kira Mama." Abba da zama ya yi bakin bed din Yana ma Mansura kallan mamaki. Mansura ganin haka daga murya ta yi tana Kiran mahaifiyar Abba tana cewa "Mama! Mama!! Maa.." Abba cikin tsoro ya tashi ya rufe ma Mansura baki yana zare ido cike da tsoro. Mahaifiyar Abba da barci bai dade daukarta ba ta jiyo Kiran Mansura, mahaifiyar Abba bakin kofar Mansura ta zo tana Kiran sunan Mansura ta ce "Mansura, lafiya ya aka yi?." Mansura to take ta yi magana amma Abba ya rufe mata baki yadda babu yadda za a yi ta iya magana. Mahaifiyar Abba Kiran sunan Mansura ta Kuma yi, jin shiru bata amsa ba ya sa ta dauka ko mafarki ta yi ta Koma ta kwanta. Abba da tsoran yin magana yake ji gudin Kar mahaifiyarsa ta ji hakan ya sa baiba Mansura damar Kara yin magana ba hannunsa na rufe da bakin Mansura ya kwantar da ita ya kwanta bayanta yana Mata magana a hankali a cikin kunne dan duk ya firgita da Kiran mahaifiyarsa da ta yi. Abba cikin sanyi da lallashi ya ce "Haba Mansura so kike ki tona min asiri kome? Meye na Kiran Mama cikin darannan? Yanzu dai inda duk bayanin da zan Miki kinki saurarata Kuma kin ki yadda da abinda nace zan Kira maki Amina ki ji, Wallahi har yanzu bana jin soyayyar mommy cikin raina zan aureta ne kawai dan in faranta ma Mama rai, maganar da kika ji ina yi awaya mommy ta fahimci ke nake so Kuma na fada Mata zan aureki shine ta ce ta hakura idan har zan aureki ba zata iya kishi dake ba saboda nafi sonki, tom idan har mommy ta furta ma Mama haka zan fuskanci fushin mama, Kuma kinsan fushin iyaye akan yayansu bashi da kyau, kin ji dalilin da ya sa na amsa ma Aisha na fasa auranki dan a wuce maganar." Abba har ya kari maganarsa ya gama Mansura batace mai komai, ranar dai haka suka yi barci kowa zuciyarsa ba dadi. Kiran sallar farko Abba ya tada Mansura ya bude kofar falon ya fita ita Kuma ta rufe ta koma ta kwanta. Mahaifiyar Abba bayan ta idar da sallar Asuba tana zaune Mansura ta shigo gaidata, suna cikin gaisawa Abba ya shigo. Mahaifiyar Abba kallan Mansura ta yi ta ce "Mansura hala jiya mafarki kika yi, kina ta Kiran sunana da karfi abin har ya naimi ya ban tsoro, na je Kuma inata bugun kofarki na ji shiru." Abba katse maganar ya yi ya ce "Ina kwana mama, kin tashi lafiya, hala mafarki ta yi." Lafiya lau Abba, ina jin Kam mafarkin ta yi baka ji ba Wallahi yadda take kwalamin Kira da na yi Mata magana Kuma shiru." Mansura tashi ta yi kanta kasa ta gaida Abba, ta tashi ta fita da sauri ta nufi kitchen tana so ta sha tea ta tashi da yunwa. Bayan Mansura ta fita ta jimawa Abba ya tashi ya fita, ya nufi kitchen din inda ya ga Mansura ta yi. Abba na zuwa ya yi hugging din Mansura ta baya ya ce "Da fatan kin tashi lafiya, ya fushi dani." Lafiya Lau, inanan Ina yi." Murmushi Abba ya yi ya ce "Shi kenan, yanzu za ki bar yinsa." Abba na fadin haka ya Kira Amina a waya. Amina da mamaki ta bi wayarta da kallo ganin kamar Kiran ya yi wuri. Dagawa Amina ta yi tana gaida Abba. Bayan sun gaisa da yake wayar a speaker ya sa Mansura na ji Abba ya ce "Amina Ina naiman taimakonki kisa baki Mana ko Mama zata janye aurena da Mommy." Daga bangaran Amina ido ta zaro ta ce "Yaya Abba har yanzu dai ka kasa hakura da Mommy, ko jiya Wallahi ta kirani tana kuka ta kawo min kararka ta ce baka kiranta sai in ita ta kiraka Kuma in ta kiraka dinma ba lallai ka daga ba. Haba Yaya Abba yau fa saura kwana 28 bikinku kake wannan maganar, Kuma kasan zaka fuskanci fushin mommy indai ka ce zaka fasa auran nan,Koda yake Yaya Ahmad ya ce wai Mansura kake so, tom Yaya Abba in ma Mansurarce zabinka ka hadasu su duka ka aura Mana." Shiru Abba ya yi yana kallan Mansura alamun kinji ko. Har yanzu hannunsa daya Yana rike Mansura. Daidai lokacin mahaifiyar Abba ta shigo kitchen din. Abba da sauri ya saki Mansura ya ce ma Amina "Shi kenan zan kirakk." Abba na fadin haka ya kashe wayar yana kallan Mahaifiyarsa ya ce "Ruwan zafi na zo samu yau a gida nake son yin breakfast." Mahaifiyar Abba bata tanka ma Abba, Abba Kuma ruwan zafin hannun Mansura ya amsa ya fita da sauri. Mahaifiyar Abba Mansura ta bi da kallo, kafin ta ce "Mansura kina so ki bata tarbiyar da nasanki da ita ko? Tom shi kenan babu ruwana idan kin biye ma Abba auransa zai yi kina gani, Kuma kisa a ranki duk yarinyar dake bari Namiji na taba bata wallahi ba auranki zai yi ba, inma Allah ya sa ya aureki ba zai ganki da daraja ba, idan ma tsoro kike dan karya rabu dake kike sake mai jikinki nanma daga ya samu abinda yake so rabuwar zai yi dake." Mansura dai shiru ta yi kanta kasa bata ce komai ba, mahaifiyar Abba Kuma ta dage sai fada take mata. Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya, inda yanzu shakuwar Mansura da Abba ta wuce duk yadda kuke tunani, soyayyarsu suke sha sosai abinsu, kullum mahaifiyar Abba daga ta rufe kofa Mansura zata je ta bude ma Abba ya shigo sai asuba zata bude mai ya fita ita Kuma ta rufe kofar falon ta koma ta kwanta. Sai dai yanzu Mansura cike take da fargaba da tunanin auran Abba da Aisha dan saura sati daya bikin. Yau Mansura suna kwance da Abba suna babarci ta tashi cikin gigita tana dafe Kai, saboda mafarkin da ta yi. Abba kallan Mansura ya yi yadda ta yi zufa kamar wadda ta yi gudu, Mansura Kuma fashewa da kuka ta yi tana cewa cikin kuka "Yaya Abba na sake maimai mafarkin rannan, na yi mafarkin ansa min handcuff a hannu gani a gidan yari Kuma Wai ga jariri a hannuna sai kuka yake." Mansura ta idasa maganar cikin kuka tana cewa "Na fara tsoran mafarkin nan na fara razana da abinda nake gani ina tsoro." Mansura ta idasa maganar cikin kuka sosai. Abba bubbuga bayan Mansura ya yi ya ce "In sha Allah babu abinda zai sameki sai alkairi, ki yi ta addu'a, yaron da kika gani Kuma yaron za ki haifa Mana ne in sha Allah." Kai Mansura ta girgiza ta ce "Ina yawan faduwar gaba Yaya Abba yan kwanan nan a firgice nake, Ina ji kamar wani mugun abu zaisam.." Abba rufe ma Mansura baki ya yi ya ce "Babu abin da zai sameki in sha Allah." Mansura bata Kuma cewa komai ba, kanta ta dukar tana kuka kadan-kadan. Abba cikin damuwa ya kalli Mansura ya ce "Mafarki fa ba gaskiya bane." Mansura goge hawayanta ta yi ta ce "Ko ba haka ba Yaya Abba mun kusa rabuwa za ka yi min nisa zaka koma gidan matarka da kwana, bacin kasa ba min barci tare da kai." Abba kan Mansura ya shafa ya ce "Shi ya sa na tsaida aikin gidana, ba ayi komai ba, yau dinnan nake shirin sanar da Mama Mommy anan gidan Aisha zata zauna a bangarena kafin na gara gidana, kin ga sai in raba maku kwana, duk ranar kwananki zaki bude min kofar in shigo nan in kwanta haka ya yi miki ai?." Mansura kamar za ta yi kuka ta ce "Ita Aishar ya za ka ce Mata duk ranar da ba zaka kwana dakinta ba?." Murmushi Abba ya yi ya ce "Zan fada mata a Asibiti aka maidani haka idan na yi kwana biyu gida kwana biyu a Asibiti." Mansura dai batace komai ba, Abba Kuma ganin an fara kiraye-kirayan Sallah ya kalli Mansura ya ce "Mu je ki bude min." Mansura bude ma Abba kofar falon ta yi ya fita ita Kuma ta rufe ta koma ta kwanta. Yau Abba bayan sun gaisa da mahaifiyarsa ya kalleta ya ce "Mama gobe zansa an yi fenti sabo a bangarena, saboda a nan Mommy zata fara zama, har yanzu aikin gidana ya kasa karasuwa, Wanda na ba kudin aikin gidan ya cinye kudin baiyi koma ba sai jiya da naje na gani." Shiru mahaifiyar Abba ta yi kafin ta ce "Shi kenan, sai ka yi kokari ka gyara karta jima a nan din." Abba sun jima suna magana akan bikin da mahaifiyarsa kafin ya tafi wajan aiki. Yau saura kwana uku bikin Abba da Aisha, yau Kuma Amina ta iso garin, zoka ga murna wajan Mansura da Amina kamar za su cinye juna tsabar murna. Mansura na rike da Amina ta saketa ta ruga da gudu zuwa bathroom tana amai. Amina bin bayan Mansura ta yi tana mata sannu, Mansura daga ma Amina hannu ta yi ta ce "Karki karaso kusa Dani, bana son kamshin turaran da kika sa shi ya sa ni amai." Amina da ido ta zaro ta ce "Ka ji wani ciwo mai kama da na masu ciki." Mansura hararar Amina ta yi batace komai ta dauraye bakinta ta fita. Abba ko bayan ya dawo aiki ya iske Amina ta zo bai yi wani dokin zuwan Amina ba saboda ta toshe duk hanyar zai samu su kebe da Mansurar, Abba akwatin da ya shigo da shi ya Mika ma Mansura ya ce "Gashi kayan da zaki sa na biki akwai angon da su mommy suka yi duka aciki." Mansura magana take son yi ma Abba amma ganin Amina ya sa ta waske ta ce "Na goge Yaya Abba Allah ya Kara budi." Ameen Abba ya ce ya tashi ya fita. Bayan Abba ya fita Amina ta bude akwatin amfofi ne da lass a ciki sai bra da panties. Amina ido ta zaro ta ce "Ki ce soyayyarku da Yaya Abba ta yi nisa haka ban Sani ba, Amma soyayar taku Kamar ta yan bariki har da bra da panties, kin San Allah ki dauke bra din nan da panties dinnan ki boye Kar mama ta gansu." Mansura daukewa ta yi ta bar kayan sawar kawai da handbag da kayan makeup ciki. Koda mahaifiyar Abba ta zo ta gani dadi ta ji sosai ganin yadda Abba ya gwangwaje Mansurar bata kawo komai a ranta ba. Haka aka ci gaba da shirye-shiryan bikin Aisha da Abba, gidan su Abba ko ya cika da baki, ana gobe bakin da baki Yan nesa duk sun iso. Ana gobe biki gidansu Aisha suka shirya Walima inda babu yadda Amina bata yi da Mansura dan suje walimar ba Amma taki zuwa, Amina ma lura da kamar Mansurar bata jin dadi ya sa ta rabu da ita. Washagari aka Daura auran Abba da Aisha, daga ka ga Abba zaka lura da rashin kuzarin da yake ciki. Bangaran Mansura ko duk hidimar bikin nan da ake Mansura tana yake ne kawai saboda bata jin dadin jikinta kusan kullum da zazzabi take kwana. Da magariba aka kawo Amarya gidan, inda gidan ya cika da mutane, Wanda duk budirin da ake yi Mansura na kwance ta lillibe kanta hidimar biki ya sa ba Wanda ya lura da halin da Mansura take ciki. Abba Kuma ya Kira wayarta ya fi a kirga ba ta daga ba dole ya sa ya rabu da ita. Washagarin kawo Amarya yan uwansu Abba duk suka watse ya zamana daga Amina sai Aunty Zainab, itama ana yin magariba mijinta ya zo ya dauketa ta tafi. Tun da aka fira hidimar bikin Abba baisa Mansura ba a idansa, gashi ko ya Kira wayarta bata dagawa. Abba shigowarsa gidan kenan ya iske mahaifiyarsa da Amina sun rako Aunty Zainab. Abba da sauri ya nufi bangaran mahaifiyar tasa har bedroom din Mansura, Kwance ya samu Mansura can karshen gadon bedroom dinta ta gudindine da bargo, Abba cikin damuwa da yadda ya ga Mansurar dan bisa ga alama bata da lafiya ya ce "Mansura." Ya Kira sunanta a hankali yana janye bargonta. Mansura cikin muryar irinta ciwo ta ce "Ni ka rabu dani ka tafi wajan Amaryarka, tun da aka fara bikin nan ka manta dani baka ma san halin da nake ciki ba." Abba cikin damuwa da yadda ya ji jikin Mansura rau da zazzabi ya ce "Haba baby kulllum sai na kiraki a waya baki dagawa ga gidan cike yake da mutane na rasa yadda zan yi in shigo, dama baki da lafiya baki fada min ba." Abba ya dago Mansura yana kallanta ta yi mai rama sosai kamar wadda ta dade tana ciwo. Abba cikin mamaki da ganin yadda Mansura ta rame mai ya ce "Subhannallahi, meke damunki kika rame haka?." Mansura fashe ma Abba da kuka ta yi. Abba kwantar kan Mansura ya yi kan kafadar yana bata hakuri ya ce "Ki yi hakuri bari in kawo miki magani ki sha." mahaifiyar Abba da Amina jin kukan Mansura suka shigo bedroom din. Daga mahaifiyar Abba har Amina da kallo suka bi Mansura da Abba, ganin yadda Mansura kusan gaba daya take kwance ajikin Abba tana kuka. Abba rudewar halin da ya ga Mansura tasa ya bai lura da yadda suke da Mansurar ba ya ce "Amina dama tun da aka fara hidimar bikin nan yarinyar nan bata da lafiya Amma dan iskan ciki baki fadamin ba kika ci gaba da hidimarki bacin ke ke tare da ita, kalli yadda ta rame kwana biyu kawai." Mansura ko har yanzu tana jikin Abba tana kukanta. Daga mahaifiyar Abba har Amina sun kasa cewa komai tsabar mamakin yadda suka ga Mansura jikin Abba kwance dukansu ko ajikinsu.....✍🏻 Littafin Abbbana na kudi ne na gama free pages daga yau na gama posting dinsa Mai bukata my number 08063830828 Littafin ABBANA cike yake da cakwakiya, karku manta Abba auran sirri ya yi da Mansura koya zamansu zai kaya.....? Wacece Mansura.... ? Shin bakwa ganin mafarkin Mansura zai iya zama gaskiya kuwa ? Koya zaman Mansura da Aisha zai kaya acikin gidansu Abba a matsayin kishiya da Kishaya..... Ko waye Wanda Mansura take yawan Kiran Abbana da shi a mafarkinta..... Duk mai bukatar cikigaban littafin Abbana my number 08063830828 Idan ba siya zaki ba karmu bata ma juna lokaci dan Allah 08063830828